*MUHIBBA* *001* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM Daga yanda take zaune cikin mota tana iya hango dogon ginin gidan, gidan da ko ba’ace ba Kai tsaye zaka kirasa da gidan sarauta sabida yanda aka tsara ginin ga kyau ga girma had’ida tsawon gini.... A iyaka shekarun da tai bataga gidan ba tabbas ba wani abu muhimmi da ya canzu da tsarin ginin gidan saiko fenti da abinda ba’a rasa ba... Idan bata b’ata lissafi ba yau shekaru ak’alla goma sha biyar kenan rabonta da wann masarauta mai bak’in tarihi a gareta... Shin ta yaya ma zata mance shekarun, bacin dik wani iftila’in rayuwa da gwawarmaya data fuskanta wannan Masarauta shine sila... Masarautar dake tafe da K’ADDARAR rayuwarta a cikinta, Masarautar da ta canza labarin rayuwarta, Masarautar da take tamkar Kurkuku a idanunta, Masarautar da aka ginata kan mulkin zalinci a zahiri kuma ana rud’in mutane da yaudararsu da kyawawan d’abi’u na k’arya... Masarautar da babu tausayi balle jin k’ai cikinta.... Lokaci guda Ta saka bayan hannunta Ta goge hawayen da suka d’igo mata.... Matashin saurayi dake zaune gefenta wanda a k’alla bazai gaza shekaru 30 a duniya ba, girgiza kansa yai kad’an had’ida fuzar da huci a hankali.... Lokaci guda yake furta “HIBBAH da zaki bi shawarina Ki janye wannan k’udiri naki, Ki mance komai ki fawallawa Allah lamuranki da sannu zai saka miki, na tabbata bayan abinda suka miki Keda iyayenki Allah bazai barsu ba, Wllhi sai ya saka maku... So please Ki janye wannan k’udiri naki...Mulkin duniya bamai dawwama bane suma wataran zasu tafi yanda mahaifanki suka tafi... So please ki janye wannan k’udiri naki....!”Ya k’arashe cikeda kulawa..... Murmushi mai ciwo budurwar mai kimani shekaru 29 tai kana tace “Ansar wllhi wllhi bazan janye k’udirina ba... Wllhi sai na tozarta su a idon duniya... Sai na ruguza mulkin zalunci da sukeyi... Sai na nunawa duniya su wasu irin mutane ne... Wllhi bazan barsu haka nan ba, yanzu ne daidai lokacin da ya kamata na dawo, daidai lokacin da suka rasa mahaifinsu, na tabbata yanzu ne zasu soma yak’in neman mulki ni kuma zanyi amfani da wannan daman...!” Cikin tsananin karaji tai maganar tana mai duban Ansar kana ta maida dubantaga ginin masarautar, lokaci guda ta kuma sakin murmushi mai ciwo kana ta soma fad’in “Iyalan Sarki AbdulJabbar na dawo gareku, saidai wann karon ban dawo a matsayin Saudatu ba, bak’ar yarinya mummuna abin wulak’antawa...MUHIBBAH, a matsayin Muhibbah na dawo, abar soyuwa a gareku... Ku yi shirin tarban rugujewarku, k’uncinku da kuma tashin hankalinku... Zan zame maku musiba da annoba, zan zamto yunwarku na kuma zamto abincinku, kaman yanda zan zamto k’ishin ruwanku na zame maku ruwan shanku.... I’ll take you down to the ground, all of you... D’aya bayan d’aya... Wllhi sai na jefaku cikin tashin hankali had’ida k’uncin rayuwa fiyeda yanda kuka jefa nawa da na iyayena ciki... Wllhi sai na tarwatsaku da duk wani mulki da sarauta da kuke tak’ama dashi.... Alk’awari ne..!!!” Ta k’arashe tana mai kuma yarfe wasu hawayen da suka zubo mata.... Suna nan zaune cikin mota daga cen gefen kwalta yanda Ansar yai parking suka soma jiyo sautin siren... Gaba d’aya Unguwar ya d’auka da k’uwa sai kaucewa ake ana bada hanya, kana iya hango motoci na alfarma sun doso babban gate d’in Fadar, ko wata mota d’auke take da lambar Jos Emirate Council.... Ga wani zabgegen mutumi da jajayen kaya irinta dogarai ya zarkwad’o tuk’ek’iyar dorina daga waje yana korin mutane yana fad’in Ku gafara ‘ya’yan talakawa... Yarima MAI JIRAN GADO ya iso mahaifarsa.....” Duban Ansar tai kana ta maimaita abinda bafajen nan yake fad’i... “YARIMA MAI JIRAN GADO...?” Tai maganar d’aukeda alaman tambaya... Jinjina mata kai Ansar yai kana yace “From what I heard, yau ake saka ran isowar Babban d’an Sarki AbdulJabbar mai rasuwa, Wato Yarima MAHMOOD AbdulJabbar Mahmood... Shine babba cikin yaran Sarkin, da alama ya iso kenan daman yau ake saka ran dawowarsa daga K’asar Spain cen Madrid....” Katsesa tai da fad’in “Na riga nasan shine Babba cikin asararrun yaran Sarki AbdulJabbar, saidai tambayar da zan maka Wai dama dik tsawon shekarun nan baya k’asar nan...?” Fuzar da iska kad’an Ansar yai kana yace “K’warai baya k’asar nan, kuma na tabbata rikicin karb’an Mulkin gidansu ya sanyashi dawowa don ba don haka ba, Yarima Mahmood bazai tab’a dawowa Nigeria ba, shekarunsa kusan goma sha biyar kenan a turai...” Gabanta ya yanke ya fad’i lokaci guda.... D’agowa tai tana kuma duban Ansar dake ci gaba da kwararo mata bayani kana ta dakatar dashi da fad’in “Wait, kace shekara sha biyar baya Nigeria...?” Jinjina mata kai yai kana yace “K’warai shekaru goma sha biyar baya Nigeria, yana cen k’asar Spain tareda marigayiyar matarsa da d’iyarsa mai kimanin shekaru goma sha hud’u..” Muhibbah Ta kuma katsesa da fad’in “Marigayiyar Matarsa...?” Amsar ya jinjina kai yace “Shekara guda kenan da rashin matarsa da yayi, ‘Yar k’asar nan ne saidai daga yanda naji labari ita matar tasa d’iyar talakawa ce ba d’iyar masu mulki ko sarauta ba, hasalima tsangwamar matar tasa da iyayensa sukai ya sanyashi yanke shawarin barin k’asar da iyalinsa gaba d’aya, a nan Nigeria ya aureta suka tafi Spain tare, Allah ya albarkacesu da yarinya k’wara d’aya mace, and last year sunzo Nigeria sai tsintar gawarta akai a cikin d’aki har yau ba’a San cause na mutuwarta ba, ba’a San mai ya kasheta ba, kawai dai gawarta aka tsinta a d’aki .... Bayan watanni kad’an ya kuma rasa mahaifinsa Sarki AbdulJabbar the same shekaran da ya rasa matarsa Gimbiya Aliya, shekaran ta zamto shekarar k’unci ga Yarima Mahmood, toh tin daga nan ya d’auki d’iyarsa suka koma k’asar Spain bai kuma lek’o Nigeria ba sai yanzu da batun mik’a Mulki ya taso... Kaman yanda kika sani Sarki AbdulJabbar yanada k’anne ‘yan Uba wanda suma harin wannan kujera ta sarauta suke... And na tabbata Hajiya Turai Giwar Sarki AbdulJabbar bazata tab’a bari sarautan nan ya subce daga hannun yaranta ba....” Ambato Hajiya Turai da yai ya kuma sanyata jin wani irin tuya a k’irjinta tamkar ana barbad’a garwashin wuta.... A hankali ta furta “Ya isa haka banson jin labarinsu, balle sunayensu....” Ansar ya d’an dubeta a kaikaice kana ya girgiza kai yace “Kuma a hakan kike cewa kin shirya rayuwa cikin masarautarsu... Tell me Hibbah, Ta yaya zaki fuskanci mutanen da ko sunayensu baki sonji balle har kiyi rayuwa taredasu under same roof, Hibbah na rok’i arzikin ki Dan Allah Ki janye k’udirinki, let’s focus on our relationship please...” Ya k’arashe cikin marairaice mata murya.... Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Doc, please not now... Dan Allah kamin wnn alfarmar, ka barni na cika burina, na tarwatsa ahalin Sarki AbdulJabbar kaman yanda suka tarwatsa nawa ahalin, nai maka alk’awari da zaran na cika wannan buri nawa, zan sanar da Mummy da kaina a saka mana rana.... Nidai kawai babban taimako da zaka min shine ka shigar dani wannan masarauta na sami gurbin zama cikinta....!” Yanda tai maganar ya sanyashi d’an dubanta kad’an kana yace “Naji, zan shigar dake Masarautar nan, zaki sami gurbin zama cikinta, amma da sharad’i....” D’agowa Ta d’anyi had’ida dubansa kad’an kana tace “Mecece sharad’in...?” Ansar ya d’an daidaita zamansa kad’an kana yace “Nurse, sharad’ina shine randa na kawoki Masarautar nan zaki sanar dani abinda Iyalan Marigayi Sarki AbdulJabbar suka miki da har kike yunk’urin tarwatsa tsakaninsu....” Gabanta ya yanke ya fad’i, ta sani tina wannan bak’in labari na nufin tashin hankalinta ne, amma batada zab’i idan har hakan zaisa Ansar ya shigar da ita wannan masarauta toh zata tuno baya, za kuma ta waiwayi bak’in shafin rayuwarta da a kullum idan Ta bud’esa sai ta shiga matsanan cin tashin hankali domin kaw duk wani k’uncinta daga nan ya soma.... Ansar ya katse mata tinaninta da fad’in “Do we have a deal...?” K’ak’aro murmushi tai kana Ta jinjina masa kai a hankali kana tace “Zan sanar daki My Dr....!” Murmushi yai a hankali kana yayi key wa motar yana fad’in “Ya kamata mu d’auki hanyar Bauchi kafin Mummy Ta soma kiranmu....” Muhibbah Ta d’an murmusa a hankali itama kana tace “I’m sure inada missed calls d’inta ma Dan wayata throughout kashe take...” Jinjina kai yai idanunsa naga kwalta yake fad’in “Kunfi kusa ai, though idan anyi dare fad’an wa ni za’ai dukda cewa Kece na kawo Ki rubuta jarabawa...” D’an b’ata fuska tai kad’an kana tace “Naji dai, Babu mai shiga tsakaninmu da Mummy ta...” Murmushi yai wnn karon kana suka d’auki hanyar Bauchi.... *** JOS(FADA) Zaratan mazaje ne guda Uku tsartsaye a bakin Kamfacecen parlor na alfarma, ko wannensu sanye cikin shiga irinta mulki da sarauta, rigar Kufta da wandonta harmada da hula da takalmi, Dik yanda mazaje masu kyau suke wad’annan mazaje zasu amsa sunan... Hannayensu hard’e suna duban Mutumin dake k’arasowa garesu mai tsananin kamanni dasu saidai shi ya d’ara masu a shekaru, hannunsa na dama rik’e da hannun matashiyar budurwa mai kimanin shekaru 14 da suke tafe tare... Fadawa kuwa sai ci gaba da kod’asa suke suna wasashi.... _Allah ya yika Sarki... Mahamuda jikan Mahamuda, Dan na gada kafi Dan na koya... Allah ya baka gidanku, Mahamuda yayi sarauta Mahamuda zai kuma yi... Gaba salamun baya salamun, Allah yaja zamanin Sarki Mai jiran gado..._ Ire iren kirarin da suke masa kenan... Biyu daga cikin samarukan nan masu jiran k’arasowarsa murmushi ne fal fuskokinsu yayinda guda d’aya ya had’e Rai tamkar yaga ajalinsa, dan kirarin nan da Fadawa keyi jinsa yake tamkar ana yaryafa masa narkarkiyar dalma cikin k’irjinsa.... _Tafiya mai cikeda sark’ak’iya, rud’ani, tausayi, Fansa, sadaukarwa had’ida soyayya_ SameenaAleeyou📚 [5/20, 10:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *002* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin taku irinta wanda jinin mulki da k’asaita ke Yawo a jini da b’argon jikinsa yake k’arasowaga ‘yan uwan nasa, lokaci guda ya saki hannun budurwar dake rik’eda ita, duban masarautar nasu yake da wane irin idanu, Masarautar da ya rasa matarsa farin cikinsa a acikinta, Masarautar da yai alk’awarin k’aurece mata tsawon rayuwarsa... Toh amma yau ganin ‘yan uwansa haka ya sanya zuciyarsa karaya, shakka babu yayi kewar gida, d’aya daga cikin samarukan ne ya tako har gabansa, su duka biyu suna duban juna cikeda shauk’in sake ganin junansu, matashin bai iya furta komai ba sai rungumesa da yayi siririyar hawaye na d’igo masa murmushi bai bar saman fuskarsa ba, sosai suka rungume juna, kana matashin ya soma furta “Yaya... Yaya Barka da dawowa gida....Nayi murnan ganinka, na gode da ka amsa kiran Maami Welcome home...!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa, mutumin da ya kirada Yaya ya d’an buga kafad’arsa kad’an kana ya furta “Na gode _(Príncipe Fu’ad, Estoy feliz de verte_,)naji dad’in ganinka...” Daidai lokacin d’aya saurayin ma ya k’araso had’ida kai masa runguma, suka rungume juna cikeda Farin ciki kana matashin ya furta “Sannu da zuwa Yaya... Barka da sauk’a...!” Murmushi ya kumayi da gefen bakinsa kana yace “An gaida Veterinarian... Na gode k’warai Prince Jamal... Gracias...!” Saurayin da ya kirada Jamal ya murmusa kad’an kana ya matsa gefe daidai lokacin da Yarima Mahmood ya d’ago yana duban d’aya d’an uwan nasu wanda da gani ya girmema wad’ancen samari biyun, su duka biyu Sun kafe juna da idanu kaman babu mai motsawa Daga matsayarsu, lokaci guda d’aya matashin ya d’an saki murmushi wanda da gani kasan cike take da ma’anoni kana ya soma takowa cikin tsananin mulki, tak’ama, sarauta da kuma isa... Hannayensa duka biyu a hard’e yake takowa, ko ba’a ce kasan wann bawan Allah mulki da sarauta Sun gama ratsasa Sun kuma jik’asa... Har ya k’araso gaban Yayan nasu bai furta koda kalma ba sai wannan shu’umin murmushin dake bisa fuskarsa... “Yazeed...!” Yarima Mahmood ya furta cikeda kulawa.... Yazeed ya kuma sakin murmushi mai bayyana hak’wara wannan karon kana ya k’araso ya rungume d’an uwan masa yana mai furta (“Bienvenido a casa hermano) Barka da dawowa gida Yaya....!” Yai masa gaisuwar cikin harshen Spanish... Murmushi ya saki a hankali saidai kafin ya sami zarafin amsasa ya sinkayo muryar Yazeed cikin sigan rad’a daidai lokacin da suke rugumeda juna, saitin kunnensa yake rad’a masa “Karka rud’i kanka da kalaman da wad’ann dogarai Ke maka kirari dasu... Till now ba’a tantance wanene Magajin Kujerar masarautar nan ba... Sannan Jarumi masanin al’adun cikin gida shi ya cancanci rik’on kujerar ba wanda ya shafe shekaru a k’asar turai ba....!” Yai maganar fuskarsa fal murmushi... Yana k’ok’arin janye jikinsa, Mahmood ya damk’o damtsensa kad’an, saitin kunnensa shima yake rad’a masa “Hausawa na cewa Ba’a sanin maci tuwo sai miya ya k’are... You might be right, I might not be familiar with all you’ve listed, but let me remind you this,(Hermanito) K’aramin k’anina... As they say D’an na gada yafi D’an na koya, so as long as jinin sarauta yana yawo a jijiyoyin jikina, Mulkin Masarautar nan ka iya fad’owa hannuna... Saidai duk bama wannan ba... Ka sani bashi ya dawo dani ba... Inada babban dalilin da yasa na dawo wannan masarauta wanda yafi yak’in neman mulki da sarauta...Mantén esto en mente (Ka aje hakan a zuciyarka) k’aramin k’anina....!” Ya k’arashe yana mai gyarawa Yazeed rigar kuftarsa had’ida d’an buga kafad’arsa guda.... Yarima Mahmood ya d’aurada “Na gode da tarban da ka min... Prince Yazeed...!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarsa.... K’uri Yazeed yai masa har saida yasa kai ya shige yayinda sauran ‘yan uwan masa suka rufa masa baya... Suna dosowa mashigar parlorn kuwa bayi suka soma zubewa suna gaidasu.... Parlor ne da ya amsa sunansa wajen tsari da had’uwa, dik yanda royal parlor yakai to wannan parlor yakai, iyaka tsayewa ya gama tsaruwa, parlor ne da za’a iya kiransa da Aljannan duniya... Daga cen center kana iya hango wata kyakkyawar mace fara tas mai d’an jiki da tsawo zaune saman Hamshak’iyar kujerar, k’afarta d’aure suke saman babban pillow da akai mata kwalliya da asalin fatar damisa, kayan dake jikin matar kad’ai zai tabbatar maka dik yanda mulki da sarauta ta duniya take wannan mata ka iya taka wajen.... A haka bazakai zaton takai shekarun da take ba sabida jin dad’i da kuma kwalliya da gayu, sai ka k’araso sosai ka fahimci girma ya sauk’o mata, Dattijuwa ce ‘yar kimanin shekaru 65 a duniya.... Saida wata mata da ko ba’a fad’i ba zaka fahimci Jakadiya ce ta shigo cikeda risinawa ta sanar da isowar Yarima Mahmood kana tai masu izinin shigowa.... Fu’ad ne gaba sai Jamal Ke biyedashi sannan Mahmood Ke take masu baya... Matar Ta fad’ad’a murmushinta idanunta tab k’walla... Babban D’anta mafi soyuwa a gareta take hangowa tsakiyar ‘yan uwansa, ji tai tamkar Ta mik’e Ta rungumesa, Ta kasa b’oye tsananin Farin cikint dikda cewa a b’angaren Mahmood d’in ba hakan ne Ta kasance ba, sam babu d’igon annuri a fuskarsa saima kallon k’urilla da yake wa mahaifiyar tasa.... Wasu irin hawaye masu tsananin d’umi ne yaji suna zuwa cikin idanunsa, yayi saurin sadda idanunsa k’asa A hankali matar ta mik’e tana k’ok’arin kamo hannayensa, hannayenta duka biyu tasa had’ida tallafo fuskarsa, yai saurin kauda fuskarsa gefe saidai tuni matar ta rungumesa tana matsan k’walla... Take akai dismissing dik wani wanda ba ahalinsu ba cikin parlorn... Cikin tsananin rawar murya take furta “Sadauki, ashe zaka dawo... Barka da dawowa Magajin Babanshi... Naji dad’i da baka watsa min k’asa a idanuna ba, ka amsa kiran da nai maka, ka dawo mahaifar ka...!” Kaman wanda ya tina wani abu, ya saki murmushi wa mahaifiyar tasa for the first time tin bayan shigowarsa parlorn... Hannayenta cikin nasa yake furta “Maami kin wuce haka a wajena, kiyi hak’uri da na sab’awa umarninki a baya... Por favor perdoname Maami na...!” (Ki yafe min Maami na) Ta saki murmushi cikeda jin dad’i had’ida mamakin canzawar da Sadauki yai, kodashike tinda ya amince zai dawo Masarautar tasan tabbas tasan ya canza, lokaci guda ta janyo hannunsa suka zauna saman kujerar alfarmar dake parlorn, wani irin shauk’i da k’aunar d’an nata ke ratsa dik wata k’ofa Ta zuciyarta, murmushi mai gauraye da Hawaye a fuskarta take furta “Har kullum albarka ta ce a tattaredaku gaba d’ayanku....” Ta d’ago tana duban Jamal da Fu’ad kana tace “Ina Yazeed...?” Duban juna sukai kaman bazasu ce komai ba sai Mahmood ya tari zancen da fad’in “Ya tarbeni Maami... Duka ‘yan uwana sunmin tarba mai kyau da naji dad’insa... Madallah da ahalin marigayi Babana Sarki AbdulJabbar... Madallah da ahalinki Giwar Sarki....!!” Ya k’arashe yana mai kod’a mahaifiyar tasa... Ta kuma sakin murmushi cikeda shauk’i, Mahmood yai mata k’uri yana jira yaji Ta tambayi d’iyarsa Zahra, saidai sam Maami bata tambaya ba, ko dashike yasan hakan ka iya faruwa Dan haka baiyi mamaki ba.... Tuni Maami Ta mik’e taci gaba da bada order na shagalin da ake shirin had’aka da dare a fadar dan sanar da dawowar Babban d’anta... Shiko Mahmood Fu’ad ya tambaya ko Ina Zahra take... Nan Fu’ad ke sanar dashi tana cen sashen Yazeed... Jinjina kansa kurum yai kana ‘yan uwan Jamal da Fu’ad sukai directing nasa zuwa nasa b’angaren yanda aka gyara masa, babban abinda ya dad’a baiwa Yazeed takaici shine cikin sashen Marigayi Mahaifinsu aka baiwa Mahmood masauk’i, da gaske da k’arfi so ake a mallaka masa sarautar gidan, bayan dik tsawon shekarun da ya d’iba yana jiran wannan mulki ta fad’o hannunsa, dik wani taron sarakuna na mahaifinsu idan bazai sami halarta ba shi yake wakiltawa, komai na mahaifinsu shine akai, sai yau rana tsaka Mahmood da bai sha wahalan komai ma masarautar ba ace shi zai gaji mahaifinsu, idan akai haka tabbas ba’ai masa adalci ba, da yawan mutane suna masa lak’abi da Wakilin Sarki wasu kaw Magajin Sarki suke kiransa, yau rana tsaka ace D’an uwansa ne zai gaji sarautar da ya jima yana buri bashi ba, tabbas hakan ba mai yuwa bane, bazai tab’a barin hakan Ta kasance ba... Da wannan tunanin ya k’arasa sashensa cikin huci tamkar zai kifa k’asa... *** Zuhrah matar Yazeed ne da yaranta guda biyu Najimi mai kimanin shekaru 6 saiko mace mai kimanin shekaru 4 zaune a hamshak’in Parlorn nasu sai zuba surutu suke had’ida murnan ganin ‘yar uwarsu Zahra wacce sauk’arta a k’asar kenan... A haka Yazid ya shigo tamkar zai kifa k’asa, D’iyarsa Noor Ta tafi a guje tana k’ok’arin d’alewa jikinsa take fad’in “Daddy guess who’s here....” Saidai Yazeed bai ko bari ta k’arashe ba ya tureta daga jikinsa cikeda tsawa... A matuk’ar razane yarinyar ta kauce kaman zata kurma ihu... Ta juyo a guje zuwaga mahaifiyarta.... Kuyangin dake kaikomo tsakanin sashen tuni suka soma k’amewa suna kuma zubewa k’asa sanin k’asaita da mulki da Ubangidan nasu kedashi, hanyar da Yazeed yabi bawa bai isa takawa ba.... Daidaida matar tasa da yaran nasa basu ishesa kallo ba ya nufi sama kaman zai kifa da k’asa sabida tsananin huci da yake... Noor ta dubi mahaifiyar tace “Mummy what’s wrong with Daddy....?” Kafin Zuhra Ta bata amsa namijin mai suna AbdulJabbar suna kiransa Sultan yace “Maiyasa yake fad’a...?” Dafa yaran kad’an Zuhrah tai kana tace “Ku zauna da Addarku Zahra, I’ll go check on your Dad...” Gaba d’aya yaran suka jinjina mata kai harda namijin.... A parlorn sama Ta samesa ya kwab’e rigar sarautar dake jikinsa sai singlet, goran ruwan sanyi hannunsa sai faman kwankwad’a yake lokaci guda yana fidda wane irin fuci....Ta jima tsaye wajen tana karantar mijin nata kafin ta nufi gefensa ta d’an zauna a d’arare... Cikin kwantar da murya Ta soma fad’in “My Prince Wai meke faruwa ne....Why are you like this...? You scared the kids...!” Ta k’arashe cikeda kulawa.... Kwankwad’an ruwan ya kumayi yana fuzar da fuci a hankali kana ya soma fad’in “This is not possible, bazan tab’a k’yalesa ya d’auki abinda na jima Ina gina rayuwata akai ba... How dare he rana tsaka zai dawo yace zai amshi sarauta, Uban mi ma ya dawo dashi Masarautar nan, mai ya sani gameda mulki da sarauta.... Wllhi idan za’a kashe rai a masarautar nan bazan k’yalesa ya karb’e what’s rightfully mine ba, what I worked hard for.... Babu wanda ya cancanci mulkin Masarautar nan face ni Yazeed..!!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci yana buga k’afarsa daga zaune alamun k’unan zuciya had’ida matse gorar ruwan dake hannunsa lokaci guda yai jifa da gorar wanda har saida yasa Zuhrah d’an firgita... Ta d’ago tana dubansa a hankali kaman mai tsoron kallon nasa, Sauk’e ajiyan zuciya Zuhrah tai dan tasan halin zuciyar mijin nata, hannunsa ta janyo cikin nata dikda rawar tsoro da hannun nata keyi, ganin bai gwaleta ba ya sanyata d’an d’aura kanta gefen kafad’arsa a d’arare, lokaci guda take furta “My Prince, Nifa wannan sarauta bai dameni ba as long as our family is happy, ban damu sai kayi sarauta ba... Kuma Ya Mahmood shine gaba da kai, a ganina shi ya kamata ya gaji Baba....” Bata Kai aya ba ya dakatar da ita da fad’in “Ya isheki haka, ke wacece da zaki fad’a min ra’ayinki... Yaushe kika fara fad’in ra’ayin kanki a gidan nan, tashi Ki fita kafin raina ya b’aci, banson jin komai.... Tashi Ki fita.... I want to be alone...!” Dubansa ta kumayi kaman zatai magana saidai irin kallon da yake mata tasan babu k’ofan kuma magana... A hankali Ta mik’e Ta nufi k’ofa tana mai kuma waigowa cikeda firgici da tsoron mijin nata.... *** BAUCHI Cikeda tsananin tashin hankali Ansar ya taso daga mazauninsa ya komo gabanta, durk’usawa yayi nan gabanta yanda take shesshek’ar kuka bayan Ta gama karanto masa abinda ya faru da ita shekarun baya, shekaru goma sha biyar da ya shud’e.... Cikin tsananin k’unan rai yake furta “Dama abinda suka miki kenan.... Hibbah now more than ever bazan iya barinki Ki koma cikin Animals d’un nan ba.... Hibbah no..... No, bazan barki ba...!” Cikin kuka itama Ta mik’e tana furta “Ansar ban sanar dakai ba saida ka amince mun da buk’ata ta... Ka fad’a ta yaya zan cika alwashin da na d’auka na fanasar rayukan iyayena har biyu.... Ta yaya zan sami justice d’in da nake nemawa kaina da iyayena...? Ansar those people are powerful, sunada dukiya da mulki, bazan iya shari’a dasu ba amma zan iya rama abinda suka min, Ansar ko a addini banyi kuskure ba dan na rama abinda suka min... The only way to get the justice that I deserve shine na shiga rayuwarsu and ruin them all... Kuma Wllhi alwashi na d’auka sai na tarwatsasu... Ansar you can’t stop me now....!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka mai tab’a zuciya.... A hankali ya fuzar da huci yana dubanta kana ya jinjina kai a hankali.... Shafa fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kana ya zauna saman sofa gijif..... “You’re so stubborn..!” Ya furta a hankali Muhibbah ta tako gabansa a hankali ta duk’a k’asa nan gabansa.... “please do this for me... And my parents...!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya... Da gefen idanu yake dubanta, saida ya d’an d’ibi lokaci a haka kana yace “Hibbah I’m sorry, how can I allow you to endanger your life just like that, Hibbah mai na zama...? I wouldn’t be there to protect you....And... what should I tell Mum.... Naci gaba da mata k’arya cewa makaranta kike a jos... What if tace zata Kai maki ziyara...? What if something went wrong...? What if your plan fails...? Hibbah what if... Na rasaki...? Do you think I can bear that...!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya ga idanunsa da suka kad’a sukai jazir.... Mik’ewa tsaye tai tana goge ragowar hawayen idanunta kana tace “Shekara d’aya tak kawai zanyi cikin Fadar, da zaran an gama rikicin mulki, da zaran na gama tarwatsasu zan San yanda zanyi na fice daga wannan waje... And we would finally be together.... Please Dr... Kamin wannan alfarmar idan har da gaske kana k’aunata...” K’uri yai mata kana ya kuma mik’ewa tsaye yana mai zagaya parlorn yake fitar da fuci a hankali, a hankali yake furta “This is a tough decision Hibbah...!!!” “Ansar...!” Ta kirawo sunansa a hankali... Sauk’e ajiyan zuciya yai kana yace “Shikenan, I don’t want you to think that I don’t love you... Zanyi komai as far as zaki kasance cikin Farin ciki.... Akwai Umaima d’iyar k’anwar Hajiya Turai Giwar Sarki AbdulJabbar mai rasuwa, a gaban Hajiya Turai take zama, zan kirata na sanar da ita akwai ‘yar uwata zatazo karatu na tsawon shekara guda a nan asibitin koyarwa na jos, kuma ta rasa accommodation gashi batasan kowa ba, zan rok’i alfarmar Ta baki masauk’i a nan Fadarsu, karki damu Umaima mutuniyar arziki ce, Sabon social media mukai, tana following page d’ina da nake bada shawarwari kan irin abincin da mutum zaikeci ya rage tumbi k’iba da sauransu, da yanayin motsa jiki da ya kamata ya dingayi... Daga nan muka saba dan idan naje Jos har gayyata Ta Fada tanayi tamin tarba mai kyau.... So na tabbata bazamu sami matsala daga wajenta ba in sha Allah....” Tsananin Farin ciki yasa taji tamkar tai tsalle ta rungumesa.... Godiya taita jero masa cikeda Farin ciki... Ansar kaw dubanta kurum yake cikeda tausayawa musamman idan ya tuna labarin data gama bashi.... A ‘yan kwanakin Muhibbah ta soma shirin tafiya Fadar Jos, dan tuni Ansar sun gama magana da Umaima wacce tace dashi ya wuce neman alfarma wajenta, Fada gidansu ne shima, Masauk’i ko mutum nawa ne ya kawo zai samu balle k’anwarsa... A b’angaren Mum d’in Ansar kuwa sanar da ita yayi Muhibbah makaranta zata tafi Jos kaman yanda suka tsara shida Muhibbar, Sam Mum batada labarin wannan al’amari nasu.... Koda tace zatai rakiyawa Muhibbah sai cewa Ansar Yai tai zamanta kawai tinda ba lafiya bane ya isheta shi zai kaita, hakan kuwa akai... Muhibbah ta gama shirinta sukai sallama da Mum kana suka nufo Jos Babban gida..... SameenaAleeyou📚 [5/20, 10:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *003* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kishingid’e yake saman darduma shatin kwabo ta zallar fata, yana sanye da riga ‘yar shara irinta shan iskar masu sarauta... Gaba d’aya sai shekarunsa suka bayyana ba kaman lokacin da yake turai yake saka k’anan kaya dake b’oye yawan shekarunsa ba, sam bazaka bashi shekaru 46 ba a lokacinda yake k’asar Spain, yau kam sai Zahra taga girman Baban nata ya d’an bayyan dikda cewa Allah yayisa mai kyaun k’ira, da sallama saman bakinta Ta shigo farfajiyar harabar benen yanda Yarima Mahmood Ke kishingid’e.... Ya aje jaridar hannunsa yana mai amsa mata had’ida mik’ewa sosai ya zauna, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.... Lokaci guda yai alama da hannu ma dogarai guda biyu dake tsaye wajen tamkar an dasasu... Babu musu suka sa kai suka fice cikeda risinawa... Kaman kullum yauma fuskarta a murtuk’e yake alamun har yanzu batai Na’am da hukuncin da mahaifinta ya yanke na dawowa k’asarsu ta gado da sukai ba.... Gyara zamansa yad’an kumayi murmushi saman fuskarsa yake dubanta, lokaci guda yake furta “Esa ropa te queda bien mi princesa..” (Kayan nan sun maki kyau my Princess) K’ok’arin k’ak’aro murmushi tai kana tace “Buenos dias Paa..” (Barka da da hutawa Paa) Ta fad’i a tak’aice... Hannunta guda ya kamo kana yace “Zahra d’ago ki kalleni....” Ta d’anyi rau rau da idanu tana dubansa, shid’inma ita yake duba.... “Zahra Spain ba k’asarmu bane dole dik daren dad’ewa mu dawo nan wata rana... Ina fata ki fahimci haka...” Share hawayen da suka gangaro mata tai kana ta soma fad’in “Paa ba Wai dawowa Nigeria bane bana so... Dejè mi vida allá en españa Paa... Mis amigas, mi escuela, and everything..” (Na baro rayuwata a Spain Paa, abokaina, makaranta na and everything) Ta d’an ware idanunta kana taci gaba da fad’in “And you know what is worst...? Maami yanzu zata saka kayi aure, and Paa I hate Aunty Raheema... Bana so ka aureta Paa....!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Bata Kai aya ba kuwa babban bawan Yarima Mahmood mai kula da al’amransa mai suna Uban Doma ya shigo had’ida zubewa k’asa cikeda ladabi irinta babban gida yake fad’in “Allah ya taimakeka Jakadiya ta sanar dani isowar bak’uwarka....” Yai maganar kansa a k’asa... Duban Zahra Yarima Mahmood yanda annurin fuskarta ya kuma d’aukewa chak dan ta tabbata Aunty Rahima ce ta iso kaman yanda taji Kakarta d’azu na maganan tareda Jakadiya.... Ba don yayi niyyan maraba da bak’uwar tasa ba sai don baiso mahaifiyarsa ta kawo wani zargi ko kokonto gameda shirinsa, hakan ya sanyashi yin d’an gyaran murya kad’an kana ya jinjina kai a hankali, Uban Doma yasan mai hakan Ke nufi dan haka tuni ya kuma risinar da kansa yana mai furta “Godiya take Yariman Yarimomi Magajin Masarautar Jos.. Allah ya baka gidanku...Jaaa zamanin ka...!!!” Ya k’arashe yana mai baza jan babban gyaren dake jikinsa had’ida mik’ewa ya fice yana mai k’an k’an da kai alamun girmamawa..... Zahra kaw tana jin haka mik’ewa tai tana mai furta “Paa zanje k’ofan Aunty Zuhrah.... Na Barka lafia Paa...” Yarima Mahmood ya dakatar da ita da fad’in “Ki tsaya ku gaisa da Rahima....” Kanta a k’asa kaman zatai kuka take fad’in “Pero Paa....” (Amma Paa) Kasa k’arashewa tai ganin yanda mahaifin nata ya kafeta da dara daran idanunsa masu firgita duk wani mai laifi.... A hankali ta shiga jinjina masa kai kana tace “Estaré abajo Paa...” (I’ll be downstairs Paa) Ya jinjina mata kai a hankali kana ta mik’e cikeda risinawa ta sauk’o k’asa.... **** Tafe yake bisa k’osasshen dokinsa da shi kansa dokin tafiyar k’asaita da mulki yake, ko ba’ace ba zaka fahimci kilisa ya fito, bayan tattaunawa da su Galadima su Hakimi su Waziri da sauransu suka gudanar a yammacin jiya kan batun bada sarautar Masarautar dole ne ma ya fita kilisa ko zai rage wasu damuwar da sukai masa karan tsaye a k’ahon zuciyarsa...Dogarai guda biyu Ke take gabansa biyu Ke take bayansa, suna tafe suna kod’a Yazeed abinda yafi so a rayuwarsa... Kaman daga sama ya hangota tafe sun nufi sashen Mai Martaba itada Jakadiya, ‘yan mata bayi guda biyu suna take masu baya d’aukeda parantai na alfarma..... Shu’umin Murmushi Yazeed yai kana yai gyaran murya daga nan yanda yake saman dokin, cikeda ladabi dogaran suka tsaida dokin dan sunsan mai gyaran muryar Uban gidan nasu Ke nufi.... Lokaci guda bawa guda ya k’araso had’ida duk’awa Yazeed ya taka bayansa ya sauk’o daga saman dokin, kan kace mai guda d’aya ya bud’e lema ya rufawa Yazeed wanda tuni ya doshi su Rahima da Jakadiya cikin tafiyarsa irinta masu ji da mulki da kuma isa.... Suna k’arasowa gaban Rahima ya yanke ya fad’i dan k’amshin turarensa kurum taji Ta fahimci shine ya k’araso wajen, janye hular alkyabban dake d’an rufeda fuskarta tai tana mai kuma tabbatarwa idanunta.... Tuni Jakadiya da bayin nan sun soma zubewa suna gaida Yazeed.... Duban Jakadiya yai had’ida yin gyaran murya kana ya furta “Jakadiya ina san yin magana da Rahima...!” Jakadiya ta d’an d’ago a hankali kana tace “Allah ya taimaki Yarima Yazeed, Gimbiya Rahima tana kan hanyarta ne na ganawa da Yarima mai jiran gad.....” Bai bari takai aya ba ya dakatar da fad’in “Jakadiya kin kaw San da wa kike jayayya...!!!!” Cikin tsananin fushi yai maganar, yayinda dogaransa Ke ci gaba da fad’in “Hattara Jakadiya, Hattara dai Jakadiya.. Allah huci ran Wakilin Sarki Marigayi....!!” Cikeda tashin hankali Jakadiya Ta zube gwiwoyinta a k’asa tana mai furta “Tuba nake Yarima... Tuba nake Wakilin Mai Martaba...! Allah ya huci zuciyar Yarima..Tuba nake..!!!” Baice komai ba sai gyaran murya da yai dan tuni Jakadiya ta umarci bayin nan su baiwa Yarima Yazeed da Rahima fili suyi magana... Shima Yazeed d’in alama yayi da hannu wa dogaran nasa cewa su basu waje harda shi mai rik’e masa lemar.... Cikeda ladabi suka basu waje ya rage daga Rahima saiko Yazeed.... Shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa yake dubanta, banda lugude babu abinda k’irjin Rahima keyi.... Ta soma ‘yan waige waige tana mai furta “Yazeed not here please.... Mai kake tunanin kanayi ne... What if your brother sees us here, mai kake tunanin zai zaton muna tattaunawa... Na fad’a maka daga yanzu babu komai tsakaninmu ya riga da ya k’are tin lokacin da Mahmood ya amince zai dawo Masarautar nan... So please stay away from me, as far far away as you can....” Ta k’arashe cikin huci... Murmushin bai bar saman fuskarsa ba idanunsa a kannare yake dubanta, lokaci guda ya tsime had’ida furta “You Shut up..!! Babu wanda yake d’aga min murya bari kiji na fad’a miki...!!” Ya kuma kannare idanu yana k’are mata kallo daga sama har k’asa wannan shu’umin murmushin nasa saman fuskarsa yake furta “Does my brother knows... Yaya na yasan saurana zai kwasa....?” Ya k’arashe yana mai shafa hab’arsa... Waige waige Rahima taci gaba da yi kana ta rage murya sosai tace “Yazeed na rok’i arzikinka karka rusa min Farin cikin da na jima ina mafarkin samu tareda Mahmood, dan Allah ka barni na cika wannan buri nawa na mallakarsa.....” Murmushi mai d’an sauti wannan karon yayi kana yace “Bazan hanaki auren Mahmood ba, amma da sharad’i guda...” D’agowa tai tana dubansa cikeda k’osawa kana tace “Mecece sharad’in...?” Hannayensa ya hard’e ya maidasu baya kana yayi gyaran murya kad’an “Sharad’in shine ko bayan kin auri Yayana zamu ci gaba da mu’amala da juna... Idan yayi miki banida matsala idan kuma bai maki ba, ina mai tabbatar maki ni da kaina zan tunk’ari Mahmood na sanar dashi komai sannan zan sanar da matata Zuhra kalan cin amanar da kike mata claiming to be her best friend.... Kinsan ni Yazeed zan iya dik abinda na jero...!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa... Lokaci guda ya kuma gyara tsayuwarsa bai daina murmushin ba yake ci gaba da fad’in “Kije ku ganada Yariman naki, idan kun gama nima akwai ganarwamu da dare a yanda muka saba had’uwa...” Ya k’arashe yana mai fad’ad’a murmushinsa... Lokaci guda yayi alamawa dogaransa suka k’araso kana ya dubi Jakadiya da itama k’arasowarsu kenan yai gyaran murya yace “Jakadiya na bar Gimbiya Rahima lafiya a hannunki, da fatan Gimbiya zata kular min da Yayana fiyeda yanda Marigayiya Ta kula dashi...!” Ya k’arashe murmushin nan nasa mai tsorata wanda ake jifansa dashi saman fuskarsa, anayin murmushi ne aji sanyi amma na Yarima Yazeed sam ba haka bane, tsoratarwa yake, yanda ya bambambanta da sauran mutane kenan.... Zahra daketa lek’ensu Ta window haka kurum taji tattaunawar da Uncle Yazeed suka gamayi da Aunty Rahima sam bai kwanta mata ba, ita dai Allah ya gani bata k’aunar matar nan sam, bata sonta da Paa d’inta, sam tarayyarsu bai kwanta mata ba... A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida komawa cikin parlorn ta zauna saman kujera tana jiran k’arasowarsu.... Shigowarsu yayi daidai da sauk’owar Yarima Mahmood cikin shiga ta mulki da kamala ....Yayi kyau har ya gaji... Ba Rahima data daskare tana dubansa yanda yake sauk’owa daga bene tamkar wani d’awisu harta Zahra saida ta yaba kyaun da mahaifin nata yayi... Ta saki murmushi a hankali kana ta maidoda da dubantaga Rahima wacce Ta kafe mata Paa d’inta da idanu tamkar zata lashesa, take annurin fuskar Zahra ya d’auke.... Jakadiya da sauran bayin tuni suka zube suna gaidasa.... Rahima kam gaba d’aya Ta shagala da kallon Yariman nata, har saida Jakadiya ta d’an tab’ata kad’an alamun ta sadda idanunta kana Rahima tai k’ok’arin saita kanta had’ida sadda idanunta k’asa, ta d’an janyo hular Alkyabban nata zuwa goshi kad’an.... Cikin tafiya irinta wanda jinin Mulki da sarauta Ke Yawo a jinin jikinsa Yarima Mahmood ya k’araso parlorn, gaba d’ayansu risinawa suka kuma yi suna masu gaidashi cikeda girmamawa kana bayin nan guda biyu suka k’arasa saman tampatseten carpet d’in suka aje trays d’in dake hannayensu wanda Ke rufe da k’yallaye masu ruwan zinari saman darduma mai taushin gaske dake a saman carpet d’in, tuni suka kuma risinawa suna masu komawa cen k’arshen parlorn kansu a k’asa... Jakadiya ce ta bud’e murya kana ta soma fad’in “Allah ya taimaki Dan Sarki jikan Sarki, Allah ya taimaki babban Yariman Yarimomi a fad’in Masarautar nan, Madallah da samuwarka a wannan masarauta, hasken annurinka ya haskakaka illahirin wannan masarauta, D’awisu kake Sarkin Ado, Farin wata kake sha kallo... Jakadiya tana maraba da sauk’arka Yariman Yarimomi...!!” K’asaitaccen murmushi saman kyakkyawar fuskarsa ya d’anyi gyaran murya kad’an kana ya furta “Madallah da wannan yabo naki Jakadiya....” Jakadiya Kai a k’asa take furta “Godiya nake Yariman Yarimomi.... Idan kamin izini zan gabatar maka da isowar Gimbiya Raheema,Zinariya k’wara d’aya tak a masarautar k’asar Akwanga...!” Ta k’arashe tana nunida Raheema wacce kanta ke kife k’asa sai faman murmusawa take.... Jinjina mata kai yai ba tareda ya kuma furta koda kalma ba kana Jakadiya ta soma matsawa da baya.... Kanta a k’asa take furta “Na barku lafiya Allah shi taimakeka...!” Ta k’arashe tana mai ficewa daga parlorn Lokaci guda Mahmood Ke takowa zuwa gaban Raheema da Farin cikinta Ke ninkuwa.... Tana jin sanda ya iso dab gabanta ta kuma sadda kanta k’asa tana furta “Barka da sauk’a your royal highness...!” Murmushi yai da gefen bakinsa had’ida jinjina kansa alamun amsa gaisuwar nata, lokaci guda yake nuna mata kujera kana yace “Bismillah..!” Babu musu ta isa zuwa kujerar da yai mata nuni dashi ta zauna... Zahra Ta d’an dubesa tana son ta soma zuba masa shagwab’a saidai sam bataga wannan fuskar ba dan gaba d’aya mahaifin nata ya juye mata babban mutum ne yau d’in tamkar wani babban basarake, saikace ba Paa d’inta data saba tsalle jikinsa ba, ita wannan na d’aya daga cikin abinda yasa bataso suka dawo Nigeria ba dan tasan dole wannan sarautar ya zama shamak’i tsakaninta da Paa d’inta, bazasu tab’a zama kaman yanda suke a baya ba... Nuni yai mata itama da kujerar dake gefen Raheema yace ta zauna... Babu musu ta isa ta zauna dikda cin magani da take.... Raheema ta d’ago tana dubanta fuska d’aukeda murmushi, Zahra dai batako tankata ba saima dad’a d’aure fuska da tai, duban da mahaifinta yai mata ya sanyata sakin fuskarta kad’an kana ta gaida Raheema... Raheema ta amsada sakin fuska tana k’ok’arin creating guntun conversation tsakaninsu.... A taka’ice kawai Zahra Ke amsata, shid’inma sabida mahaifinta ne dikda rabin hankalinsa naga wayar salulansa ne.... Suna nan a haka Uban Doma ya shigo cikeda risinawa had’ida zubewa yana mai furta “Allah shi taimaki Babban Yarima... Gimbiya Umaima tana neman izinin shigowa...” Jinjina kai kad’an Mahmood yai alamun bada izini... Godiya Uban Doma yai kana ya fice ya sanar da Umaima cewa anyi mata izini.... Cikeda risinawa Umaima Ta shigo ta gaidasu kana tace “Yaya inaso na kamin izini na d’auki Zahra dan ta tayani tantance kalolin abincin da zan sauk’i bak’uwata dashi... K’awata zata iso Masarautar nan a yammacin yau da yardar Allah...” Ta k’arashe fuska d’aukeda murmushi... Zahra da kaman akan k’aya take zumbur Ta mik’e had’ida shagwab’e fuska tana fad’in “Paa please...!” Murmushi ya d’anyi kad’an kana ya jinjina masu kai alamun suna iya tafiya... Umaima Ta risina had’ida masa godiya, itama Zahran godiyar tai masa cikeda risinawa kana Umaima ta janyo hannunta suka fice... A b’angaren Raheema kaw ma iya cewa hakan yafi mata dan dama bawai San zaman yarinyar take a wajen ba kawai dai dan babu yanda ta iya ne... Tuni ta soma zak’ewa tana sanar dashi kalolin abincin data girka masa, tai alamu da hannuwa bayin cewa suzo su bud’e farantan da suka shigo dashi... Shi dai gogan daki daki kurum yake dubanta yana karantar wasu halayya da d’abi’u nata dikda hirar tasu ma iya cewa Raheema ce keyin akasari *** Isowarsu Fadar kenan suka tadda wata mata sai gudu take wasu mutane na biye da ita, gashin matar yayi duguzun alamun hauka, yanayin yanda take gudu kad’ai zai tabbatar maka babu hankali jikin matar..... Dikda bata iya ganin fuskar matar gaba d’aya ba, tsikar jikinta sosai ya tashi da ganin wannan mahaukaciyar matar, suna a haka wani Bafaje ya k’araso dan yi masu iso zuwa cikin Fada.... SameenaAleeyou📚 [5/21, 10:47 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBA✨👑* *004* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Muhibba bata ida firgita da lamarin matar nan ba saida matar ta k’araso ta tsaya cak gabanta tana binta da wani irin duba da idanunta masu matuk’ar firgitarwa, suffar matar kad’ai abin firgitarwa ne.... Tamkar irin bayin da aka ciwosu a zamanin farko...Gashi bata furta koda kalma ba sai duba irinta k’urilla da take binta dashi... K’irjin Muhibba yaci gaba da bugu a daidai lokacinda wasu dogarai k’arfafa har guda uku suka k’araso a guje suka capke matar nan daketa zillewa tana waigowa tana kuma duban Muhibbah.... Itama Muhibbar duban matar take har suka b’acewa ganinta Ansar ne ya d’an sunkuyo kad’an kana yace “Are you okay...?” Ta jinjina masa kai a hankali a daidai sanda aka bud’e masu wani tapkeken gate mai d’aukeda kuyangi sahu sahu, dik yanda suka Zo wucewa sai kuyangi Sun risina Sun gaidasu.... Tafiya mai d’an tsawo sukai kafin suka soma hango asalin cikin Masarautar.... Dogarin da yai masu rakiya ya sadda kansa cikeda risinawa kana yace a nan zai barsu akwai wad’anda zasu Zo su k’arasa dasu ciki.... Ansar ya jinjina masa kai murmushi saman fuskarsa had’ida masa godiya... Maidoda dubansaga Muhibba yai wacce har yanzu tamkar bata a cikin hayyacinta kana ya d’anyi gyaran murya yace “Hibbah, are you sure about this...? Hibbah kodai mu koma gida... I don’t know... But I’ve a bad feeling about this....!” Ya k’arashe cikeda kulawa... K’ak’aro murmushi tai kana tace “There’s no going back, I’ve already started... Dole na k’arasashi...” Ta d’anyi still kana taci gaba da fad’in “Ganin matar nan ya firgitani... Sam batai kamanni da bil’adama ba...” D’an dubanta kad’an Ansar yai kana yace “Da gani bamai hankali bace, mahaukaciya ce... Kiga yanda tazo ta tasamu a gaba da kallo tamkar mai san yi mana magana, musamman ke.... “ Muhibbah ta jinjina kai a hankali “Allah kad’ai yasan silan haukar matar nan...” Tai maganar a hankali... Sauk’e ajiyan zuciya Ansar ya d’anyi kana yace “Muhibbah Fada gida ne mai k’unshe da halittu iri daban daban, wanda ido ka iya gani dama wanda idanuwanmu bazasu iya gani ba, Muhibbah Fada babban gida ne wanda komai ka iya faruwa cikinta, dik yanda aka ce miki akwai mulki da sarauta Toh zai matuk’ar wahala ace babu zalunci sai wad’anda Allah ya kiyayesu.... Akan neman mulki da sarauta ta duniya wasu mutanen babu abinda bazasu iya ba... Shisa sam banso Ki dage da k’udirin nan naki ba... Dan dai kawai babu yanda na iya ne....!” Fuzar da fuci tai a hankali kana tace “Ansar mecece makomar rayuwata... Shin da wata fuska kake duban rayuwata a halin yanzu...?” Matsowa kusanta kad’an yai kana yai mata K’uri na wasu dak’ik’ai.... “Gwarzuwar mace, Jaruma a filin daga, Mace k’wara d’aya tak data tari gungun mayak’a Majiya k’arfi masu d’aukeda manyan makamai.... TAKWABI d’aya tak da zatai zarra Ta kwantar da dubban takwabban da suka zagayeta sukai mata kawayanta...SARAUNIYA k’wara d’aya tak a illahirin Masarautar nan....!” Ido cikin ido yake dubanta sanda yake furta mata kalaman.... Tabbas sai taji tsoron da ya lullub’eta ya yaye, ji tai ya bata wani irin k’arfin gwiwa wanda ko a baya bata sami hakan ba, tabbas sanda Ta saka k’afarta cikin Masarautar nan abubuwan da suka faru shekarun baya sun shiga dawo mata daki daki, sannan tsoro da firgici sun mamaye zuciyarta, koda yanzu Ansar yai mata wad’annan kalamai saiji tai zuciyarta Ta kuma samun k’warin gwiwa.... A hankali ta jinjina masa kai kana tace “Na gode daka d’aukeni matsayin Jaruma, kuma in sha Allah bazan baka kunya ba... Zakai alfahari dani a lokacinda na kawar da mulkin Zalunci da wad’ann azzaluman bayi na Allah suka gina a doron k’asa.... Labarin Masarautar da kalan zalunci da sukai bazai shafe a tarihi ba... Zan zamto sanadin bank’ado wasu bak’ak’en sirrikansu da suka jima da bisnewa... Labarinsu zai zamto izna ga wata Al’umma da zatazo a gaba....!!” Ta k’arashe tana goge hawayen zafin Rai da ya gangaro mata.... Ansar ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali, dan ko babu komai yanzu hankalinsa ya d’an kwanta, ya cirewa Muhibbah dik wani sauran burbud’in tsoro dake kwance cikin zuciyarta, yak’i ta tara wanda shi kansa bai isa yace ga yanda zata kaya ba, dan haka dole ya k’arfafa mata gwiwa domin kaw Muhibbah tana tsananin buk’atar hakan daga garesa.... “Yanzu ne naga asalin Muhibbar da na sani, wacce bata failing dik abinda Ta saka gabanta da izinin Allah... Always remember we are in this together, dik sanda kikaji wani abu ya canza, don’t forget I’ll always be here... Muhibbah ina sonki... With all my heart, bayan labarin gaba d’aya da naji yau, kin kuma zama tauraruwa d’aya tak a birnin zuciyata... I’ll wait for you till the end of this...!” Ya k’arashe cikin tsananin sanyin murya wanda ya sanya wani b’angare na zuciyar Muhibbah tsananin tausayin Ansar d’in... Ansar da mahaifiyarsa sune komai na rayuwarta... Mutanen da suka bud’e mata k’ofofin Alkhairai a lokacinda Duniya tai mata d’aurin goro... Mutanen da suka zamto shimfid’a mai taushi a gareta a lokacinda dik yanda ta saka hak’ark’arinta kaya ne mai tsananin suka... Shin ta yaya zata mance halarcin wad’ann bayin Allah a gareta... Da izinin Allah bazata tab’a watsa masu k’asa a idanu ba... Zasu sameta mai rik’oda Alk’awari.... Suna nan a haka muryar wasu kuyangi ‘yanmata guda biyu ya katse masu nisar da sukai a duniyar tunani su duka biyun.... Cikin ladabi irinta babban gida Kuyangin suka gaidasu kana guda d’aya Ta d’auki luggage d’in Muhibbah dake gefen k’afar Ansar yayinda guda d’aya tai masu jagoranci zuwa sashen Gimbiya Turai Giwar Sarki kuma uwar Taurari Hud’u dake a wannan masarauta.... *** Daga yanda yake tsaye saman bene hannayensa hard’e yana kuma nazarin mahaukaciyar matar da ya hango dogarai na kokawan kamata, shin wacece ita...? Tambayar da yai masa karan tsaye a zuciyarsa.... Yana nan a haka Ubandoma ya shigo cikeda risinawa had’ida fad’uwa k’asa yana kwasan gaisuwa.... Yarima Mahmood ya jinjina masa kai ba tareda ya amsa gaisuwar tasa ba, lokaci guda ya soma takowa gaban Ubandoma had’ida yin gyaran murya kad’an “Ubandoma...!” Yarima Mahmood ya ambato sunansa cikin muryarsa mai cikeda k’warjini.... Ubandoma ya amsa a lada ce yana mai furta “Allah shi taimakeka...” Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Wacece mahaukaciyar cen da d’azu naga dogarai suna kokawan kamata....?” Tambayar da ya haifarwa Ubandoma fad’uwar gaba.... Gumi ya shiga karyo masa ya rasa mai zai furta domin kaw Giwa tai masa kashedi mai tsananin kan irin sirrukan da zai bayyanawa d’anta Mahmood wanda a bayan tafiyarsa abubuwa da dama sun faru cikin Masarautar.... Gyaran murya da Yarima Mahmood yai ne ya dawo da Ubandoma daga duniyar tinaninda ya tafi, ya shiga furta “Tuba nike Allah shi baka yawan rai.... Ai wannan mahaukaciya da kake gani, yau shekaru goma sha biyar kenan tana fama da jinyar tab’in kwanya.....” “Shekaru goma sha biyar.....?” Yarima Mahmood ya maimaita da sigar tambaya... Kan Ubandoma a k’asa yake jinjinawa alamun tabbatarwa kana yaci gaba da fad’in “K’warai kuwa Allah shi taimakeka....” Shiru na d’an lokaci ya gifta kana Yarima Mahmood ya kuma d’an takawa kad’an har lokacin hannayensa hard’e Ta baya kana ya d’an dakata a daidai jikin gini yana mai k’arewa kampacecen masarautar nasu kallo iya ganinsa sabida tsananin girma da fad’i da Masarautar kedashi..... Yanada tarin tambayoyi da suke buk’atar amsa.... Kaikaitowa yai yana duban Ubandoma wanda Ke zube k’asa kana yace “Wacece wannan matar...? ‘Yantacciya ce kokuwa baiwace...?” SameenaAleeyou 📚 [5/22, 9:35 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑* *005* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar kana ya kuma risina yana mai furta “Allah shi taimaki Babban Yariman wannan masarauta, ita wannan mata ina tsammanin ba cikin Masarautar nan take ba... Randa dik ta b’alle ne sai ta shigo cikin Masarautar nan....” Ya k’arashe cikin sark’ewar harshe... Da wasu irin idanu Mahmood Ke dubansa, ba don ya aminta da kalaman dake fita daga bakin Ubandoma ba.... Lokaci guda ya juyo sosai yana duban Ubandoma, saida ya d’ibi wasu dak’ik’ai a haka kana yace “Ya akai har ta tsallake manyan k’ofofi dake a cikin Masarautar nan ta shigo...?” Ubandoma ya kuma had’iyan wani miyau d’in da k’yar kana yai k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa.... “Allah shi baka yawan rai.... Kasan idan akace mutum nada tab’in hankali komai zai iyayi... Ba yau ce rana ta farko da mahaukaciyar nan ta k’wace ta shigo Fadar nan ba... Dik randa ta k’wace daga turun ta takan fantasmo cikin Masarautar nan aita kokawan fitar da ita.....!” Ya k’arashe yana mai kuma d’aga hannu alamun jinjina yana mai furta “Allah shi baka yawan rai.....!” Shiru ya kuma biyowa kana Yarima Mahmood ya kumayin gyaran murya, wannan karon sunan Ubandoma ya kirawo cikin wane irin siga mai firgitarwa kana yaci gaba da fad’in “Idan na samu cikin zancenka akwai abinda ba gaskiya ba, zanyi maka horo mai tsanani....!” Daga haka yasa kai ya nufo k’asa cikin sassarfa da zafin nama... *** Sashen bak’i Umaima ta sauk’esu, kafin ta iso tuni an cika gabansu da kayan motsa baki, sai bayan shud’ewar wani lokaci Umaima ta k’araso fuskarta d’aukeda murmushin nan nata mai kyau, gefe da ita Zahra ce suna tafe tare dukansu cikin shiga irinta mulki da sarauta.... Tin daga nesa gaban Muhibbah ke fad’uwa, su Umaima da Zahara suna ci gaba da k’arasowa cikin parlorn k’irjinta na tsananta bugu..... Lokaci guda taji k’afafunta sun rinjayeta Ta mik’e tsaye tana dubansu yanda suke k’arowa garesu.... Ansar d’in ma mik’ewa tsaye yai murmushi kwance saman fuskarsa... Maraba da juna Umaima da Ansar suka somayi kana Umaima ta gabatar masa da Zahra d’iyar d’an uwanta.... Ansar ya d’an risinar da kansa fuska fal murmushi yana mai furta “Barkanki ranki shi dad’e, da fatan mun sameku lafiya...” Murmushi kad’an Zahra tai a tak’aice tana mai jinjina masa kai ba tareda ta amsa ba.... Idanunta suka sauk’a kan Muhibbah dake binta da kallo irinta k’urilla... D’an rausayar da idanu Zahra tai had’ida furtawa a hankali “¿Por qué ella me está mirando?” (Mai yasa take min kallon k’urilla) Gashi dik ita a tak’ure take da wad’ann kayan sarautar... Ita harga Allah ta gaji da k’asar da mutanenda ke cikinta, tana gani Ansar na introducing Muhibbah wa Umaima, had’ida dank’a mata amanar ‘yaruwarsa... Umaima tace “Bakada matsala Dr, in sha Allah ‘yaruwarka tana hannu mai kyau... Nai maka alk’awari....” Ansar ya jinjina kai a hankali kana ya mik’e daga zaune yana mai furta “Toh ni zan koma kar nai dare.....” Umaima tace “Da wuri haka kaman ana korarka....” Murmushi yai a fili a cikin zuciyarsa kaw tsantsan fargaban kewar Muhibbah ne da zaiyi Ke azalzalansa.... Suka dubi juna idanunsu suka had’e waje guda..... Umaima ta dubi Muhibbah wacce itama Ansar d’in take duba cikeda kulawa kana tace “Hibbah bari mu barku kuyi sallama da yayan naki....Ki saki jikinki tamkar a gida kike.... Ki d’aukeni tamkar k’awa ko nace ‘yar uwa a gareki...” Muhibbah ta jinjina mata kai fuska fal murmushi take furta “Godiya nake Rankishi dad’e....!” Umaima ta kuma murmusawa kana tace “You don’t need to be too formal, kar Ki biye na wannan Yayan naki... Just call me Umaima....” Jinjina kai Muhibbah ta kuma yi kana tace “Na gode Umaima...!” Umaima ta kuma sakin murmushi kana ta janyo hannun Zahra suka d’an basu waje danyin sallama.... *** Ita kad’ai cikin katafaren d’akin nata, sai faman safa da marwa take, Takai mari takai bango.... Tana jiran bak’in labarin da yau d’in zai risketa dan dik randa mahaukaciyar nan ta bayyana toh ko shakka babu sai tayi gamo da labari mafi muni... Sai wani babban al’amari ya faru cikin Masarautar.... Tana a cikin wannan yanayi Jakadiya Ta turo k’ofa ta shigo cikeda risinawa ta zube k’asa..... Gimbiya Turai, ko muce Giwa, ko muce Maibabban d’aki dan dika wad’annan sunayenta ne a cikin Masarautar.... Ta juyo tana watsawa Jakadiya wani irin duba, lokaci guda take takowa yanda Jakadiya ke zubewa tana kuma kwasan gaisuwa.... “Jakadiya Wani bak’in labari kikazo min dashi.....?” Giwa ta tambaya cikin kakkausar murya Jakadiya ta kuma risinawa tana mai furta “Allah shi huci zuciyar Giwar Sarki.... Na bincika gabas da yamma kudu da arewa babu bak’in labari da ya bayyana a cikin Masarautar nan.... Da alama wannan karon bata fito da wani mummunan labari ba... Allah shi baki yawan rai amma saidai....” Tai burkiwa kalamanta sabida k’irjinta dake tsananin bugu.... Cikeda son jin mai Jakadiya keson fad’i Gimbiya Turai tace “Amma mai... Mai kuma ya faru Jakadiya...?” Jakadiya ta had’iyi miyau kana tace “Allah shi baki yawan Rai, Ubandoma ya sanar dani Yarima Mahmood ya soma tambayar ko wacece wannan mahaukaciyar... Kuma daga yanda Ubandoma ya sanar dani Yarima bazai gajiya ba har sai ya gano ko wacece ita...” Dakatar da ita Giwa tai da fad’in “Jakadiya akwai k’ofofin da D’ah na bai isa bud’esu ba a cikin Masarautar nan... Wannan kad’ai yayi kad’an ace Mahaukaciyar nan ta bayyana a Fada... Karki mance dik randa ta bayyana wani babban al’amari ne Ke faruwa wanda za’a iya dangantashi da rasa rai.... Tabbas akwai wani abinda ya faru a cikin Masarautar nan wanda bamuda masaniya...!!” Ta k’arashe tana duban Jakadiya wacce itama ita take duba cikeda damuwa mai gauraye da tsoro.... Tabbas zama bata gansu ba... *** Yana fitowa bai zarce ko Ina ba sai bargan dawakin mahaifinsa.... A hankali yake takawa abubuwa da dama suna zuwa masa daki daki.... Wacece wannan matar...? Maiyasa yakeji kaman ya santa....? Dik yanda ya shige bayi sai sun risina Sun kwashi gaisuwa, Shiko Yarima Mahmood saidai ya jinjina masu kai alamun amsawa... Daga cen ya hango k’aramin k’aninsu Fu’ad yana k’arasowa.... Yarima Mahmood ya d’an fad’ad’a murmushinsa sanda Fu’ad ya k’araso gareshi, jerawa sukai su duka biyun suna ci gaba da takawa cikin bargan dawakin irin yanda masu mulki keyi.... “Barka da yammaci Yaya...” Fu’ad yace yana mai d’an sadda kai... “Baka Yarima Fu’ad...!” Yarima Mahmood ya amsa cikeda kulawa.... Hira suka somayi irinta ‘yan uwa wanda suka jima basu tareda juna.... Daidai jikin wata farar doki Mahmood ya tsaya yana mai k’are mata kallo tamkar mai tunanin wani abu, hannu yasa yana shafa fuskar dokin a hankali... Fu’ad ya d’anyi gyaran murya had’ida furta “Dik ranan sallah ita yake hawa yaje masallacin idi bisa....Ana mata ado da kwalliya irinta amaren dawakai.... Yana tsananin k’aunar dokin nan....” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai shafa gadon bayan dokin... Mahmood ya tari zancen da fad’in “Jafar ne kad’ai yake mata kwalliya irin wanda Maimartaba Ke so... Bai hawanta idan ba Jafar bane ya shiryata...!” Shiru na d’an lokaci tamkar wanda ya tina wani abu kana yace “JA’AFAR....! Ina Ja’afar Fu’ad...? Tinda na dawo Masarautar nan ban sakashi a idanuna ba....?” Fu’ad bai iya basa amsa ba saima sadda idanunsa k’asa da yai cikin wane irin sanyin jiki.... Kaman daga sama ya soma jiyo muryar Yazeed yana fad’in “Ta yaya kake tambayar mutumin da shi kansa bai jima da dawowa Masarautar nan ba... Idan zaka tambayi wani abu gameda Masarautar nan toh kada ka tambayi wannan k’anin naka...!” Ya k’arashe yana mai aikawa Fu’ad da kansa Ke k’asa muguwar kallo irinta k’ask’anci.... Yarima Mahmood ya kaikaito sosai yana duban Yazeed kana ya kuma duban Fu’ad.... Cruel smile d’in nan nasa saman fuskarsa yake d’aga gira alamun jaddadawa.... Dafa kafad’an Fu’ad Mahmood ya d’anyi kana yace “Fu’ad tell me, meke faruwa... Mai Yazeed yake nufi da yace baka jima da dawowa Masarautar nan ba... Ina ka tafi... Ko akwai course d’in da baka gama bane a Cyprus...?” Fu’ad bai iya amsashi ba sai kuma sadda fuskansa k’asa da yayi... Yazeed dake ci gaba da shu’umin murmushin nan nasa yai karaf ya soma fad’in “Tell him Fu’ad... Tell your big brother how you wasted time and resources a k’asar Cyprus ba tareda ka dawo da koda kwalin tsire ba... Koda shike ka dawo da ciwon shaye shaye na kayan maye... Hodar iblis Ta kusan illata maka kwanya gaba d’aya....!” Baikai aya ba Mahmood ya katsesa da fad’in “Enough Yazeed..!! Wasu irin kalamai kake jifan d’an uwanka dasu haka...” Murmushi da gefen baki Yazeed Ke ci gaba da yi kana yace “Gashi nan... Ask him... Ka tambayeshi idan k’arya na mishi.... Shekarunsa 28 amma baisan ina rayuwarsa Ta dosa ba... Ka tambayeshi kalan abin kunya da ya janyowa wannan masarauta... Ka tambayeshi gashi nan... Akanshi k’iris ya rage mulki Masarautar nan bata kufce daga gidan nan ba... Fu’ad you’re nothing but a great disappointment...” Fu’ad da tuni idanunsa sun kad’a sunyi jazir yana fidda wane irin huci na tsananin k’unan zuciya... Lokaci guda ya d’ago rinannun idanunsa masu zuban ruwa yana duban Yazeed yake furta “Yes..! Yes Yazeed... Ban dawo da ko wanne takarda ba sai na shan kayan maye kaman yanda ka fad’i.... Amma kar ka mance kaine sila... Kaine sanadi... Kaine Kai jagoranci wajen ruguza rayuwar innocent boy.....” Ganin Fu’ad ya soma sakin layi ya sanya Yazeed yowa kansa yana mai furta “Shut up... Shut the hell up...!! Don’t you dare put the blame on me...!!” Ganin bayi sun soma dubansu suna yaface had’ida nunasu wa junansu da baki ya sanya Mahmood daka masu tsawa da fad’in “Enough!! Ya isheku haka... Kusan a yanda kuke kun kuma San mai kuke fad’iwa junanku....?” Gaba d’aya sukai shiru suna maida huci tamkar wasu zakuna.... Yarima Mahmood ya dubi Fu’ad yace “Lets go Fu’ad.....!!!” Yai maganar cikin tsananin dakewa.....Babu musu Fu’ad ya take masa baya suna masu b’allawa juna harara shida Yazeed.... Suna shigewa Yazeed ya dakawa kuyangin dake zube a wajen muguwar tsawa da fad’in “Ku kuma mai kukeyi a nan... Ku b’ace min da gani kafin duk rasa rayukanku....!” Tuni suka mik’e suna k’ok’arin barin wajen cikin sauri har kaman zasu kifa... Hauni amintaccen bawan Yazeed yai kansu da k’atotuwar dorina yana zabga masu had’ida kwashe masu albarka.... Yazeed sai faman cika yake yana huruwa shi kad’ansa... Lokaci guda ya kuma sakin wata murmushi da shi kad’ai yasan ma’anarta.... Ya wani d’an gyara zaman rigar sarautarsa dake sanye jikinsa cikeda Izza wanda yin hakan d’abi’arasa ce ** Cikin sassarfa suke tafe, Mahmood na gaba yayinda Fu’ad Ke biye dashi, kaida ka gansu kasan babu lafiya, a haka suka nufi sashen mahaifiyar tasu... A daidai lokacinda Umaima, Zahra da kuma Muhibbah suka doson mashigar parlorn, cak suka tsaya suna duban Mahmood da Fu’ad dake tafe tamkar zasu kifa k’asa.... Tin Daga k’ololuwar kanta taji wani abu har izuwa tafin k’afarta.... Dikda fuskar Fu’ad ya canza sabida girma da yai ba kaman lokacinda Ta sanshi yana k’aramin yaro mai k’anan shekaru ba, kaman yanda nata fuskar ma ya canza hakan bai hana ta gane kamanninsa domin kaw kamaninsa da Mahmood ya kuma bayyana wanda shi Mahmood d’in babu abinda ya canza a kamanninsa da shike sanin matashi tai masa, saiko alamun girma da ya sauk’o masa..... Take idanunta suka kad’a sukai jazir tana duban Mahmood tana tina shine mutumin da ya d’auketa da hannunsa ya azata saman doki kyakkyawan fuskarsa d’aukeda murmushi a lokacin, fuskar da take gani a idanunta tamkar bak’ar k’umurcin macijiya mai mummunar guba....Lokaci guda Ta rintse idanunta da k’arfin gaske tana jin zuciyarta na wani irin fizga tamkar zai fice daga cikin k’irjinta.... SameenaAleeyou📚 [5/23, 6:41 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑* *006* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Suna k’arasowa kaga yanda Kuyangi ke k’amewa suna zubewa k’asa alamun girmamawa..... Zahra ta dubi Umaima fuska fal damuwa take fad’in “Aunty Umaima meke faruwa... Mai ya sami Paa da Uncle Best....?” Girgiza mata kai Umaima tai alamun itama bata sani ba... Lokaci guda Zahra tasa kai da zummar bin bayan iyayen nata ba tareda ta jira amsar Umaima ba... Saidai tuni Muhibbah ta rik’o hannunta alamun dakatarwa.... Zahra ta dubi hannunta da tsananin mamaki ganin wacece ta rik’eta... Ta kuma d’agowa sosai tana duban Muhibbah dake rik’eda hannunta guda alamun dakatar da ita..... Daidai da Umaima duban mamaki take bin Muhibbah dashi had’ida jinjina k’arfin hali irinta Muhibbah wacce zuwanta Masarautar kenan amma har tanada k’arfin halin dakatar da jinin sarauta daga gudanar da wani abu... Har saida su Yarima Mahmood da Fu’ad suka shige babban gwanin Giwa (Parlorn Giwa) kana Muhibbah ta d’an saki hannun Zahra had’ida sadda idanunta kad’an murmushin k’arfin hali saman fuskarta take furta “A.... Ki gafarceni ranki shi dad’e.... A ganina bai kamata Ki tunk’ari mahaifinki a halinda yake ciki ba... Kaman ransa ya b’ace yake... Allah shi taimakeki.... Ki gafarceni...!” Ta k’arashe tana mai sadda idanunta k’asa..: Gyara tsayuwa sosai Zahra tai tana dubanta kana tace “Wait... And who do think you’re... Wacece Ke da har kike fad’in ra’ayinki akan abinda ya dace nayi da kuma wanda bai dace nayi ba... Quién crees que eres..” (Kina tunanin Ke wacece) Ta k’arashe tana mai tsare Muhibbah da idanunta..... Umaima ce ta d’anyi gyaran murya kana ta kamo hannun Zahra tace “Zahra I think Muhibbah is right... Bakinsan mai ya b’ata ran Paa d’inki ba, kuma kinga bashi kad’ai bane... Besides nan gidan sarauta ne Zahra bazakiyi komai kai tsaye a bainar jama’a ba kaman yanda kikeyi a Spain... Abu k’ank’ani a nan sai ya zama scandal... Kuma nasan bazakiso Ki baiwa mahaifinki kunya ba... Muhibbah taimakonki tai Zahra... Godiya ya kamata Ki mata a ganina....” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta tana mai dubansu duka biyu daga Zahran har Muhibbar.... Shiru Zahra tai ba tareda ta furta komai ba sai d’an sadda idanunta k’asa da tai tana mai jinjina maganar... Lokaci guda ta d’ago ta d’an dubi Muhibbah kaman zatai magana sai kuma ta dubi Umaima tace “Aunty Umaima ni na shige ciki...” Tana kaiwa nan tasa kai tai shigewarta zuciyarta a b’ace.... Suka bitada kallo har ta b’acewa ganinsu kana Umaima ta maidoda dubantaga Muhibbah... Lokaci guda suka sakarwa juna murmushi kana Umaima tace “Ina fata kiyi hak’uri da d’abi’un Zahra... She’s going through a lot, bata jima da rasa mahaifiyarta ba, sannan bata son dawowa k’asar nan... Akan dole take zaune a k’asar nan shisa take wasu abubuwan da take, shisa take jin haushin kowa da kuma komai a k’asar., You know a teenagers are, a gab’ar take....Amma Zahra yarinyar kirkice ina mai tabbatar miki... Zaki k’aunaceta sannu a hankali....” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta... Murmusawa kad’an Muhibba ma tai kana tace “Karki damu, na fahimceta... Kallo d’aya nai mata na fahimci ita d’in yarinya ce mai saurin shiga rai... Kuma inaji a jikina we would get along someday...!” Umaima ta kuma murmusawa kana tace “Muje koh...!” Muhibbah ta jinjina kai murmushi saman fuskarta kana suka nufi dogon ginin.... *** Daga yanayin tafiyar da suke zaka fahimci ba lafiya ba, hakan yasa suna shigowa Babban gwanin Giwa Kaga yanda kuyangi Ke darewa suna basu waje... Kaf suka fice waje suna masu kwasan gaisuwa, tuni Mahmood da Fu’ad sun nufi upstairs yanda suka tadda Giwa da Jakadiya suna tattaunawa.... Tuni Jakadiya ta risina tana kwasan gaisuwa, Giwa ta jinjina mata kai alamun ta fice ta basu waje.... Take Jakadiya ta nufi k’ofa kai a k’asa tana mai kuma kirariwa yaran Sarkin.... Yanayinsu kad’ai ya tabbatarwa Giwa wani abu na faruwa, kan Fu’ad a k’asa har lokacin bai daina sakin huci a hankali ba.... Giwa tai gyaran murya tana mai furta “Lafiya Sadauki meke faruwa... Ya na ganku haka..? Wani abin ne ya faru...?!” Da idanunsa masu firgitarwa ya tsare Fu’ad, hannayensa hard’e Ta baya, lokaci guda yake furta “Maami what’s wrong with your son...? Wasu irin labari nakeji cewa zaman da yayi a Cyprus babu abinda ya tsinana... Shin da gaske ne baida wani sana’a sai shan kayan maye..?!!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya.... Daidai lokacin Yarima Jamal ya shigo yana mai dubansu d’aya bayan d’aya yanda sukai tsaye carko carko.... Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Maami Wai meke faruwa ne a Masarautar nan.... Meke faruwa cikin gidan nan....? I need answers...!!” Ya k’arashe wannan karon yana duban mahaifiyar tasu.... Jamal dake tsaye yana rarraba idanu cikin wane irin yanayi k’arasowa yai a hankali had’ida d’an dafa hannun Mahmood.. Lokaci guda yake furta “Calm down Yaya... Babu wani abin tashin hankali dake wakana a Masarautar nan, I promise you....” Yana maganar yana duban mahaifiyar tasu data tsare Mahmood da idanu.... Duban mahaifiyar tasu Mahmood ya kumayi kaman zai magana, saidai tuni ta mik’e tsaye ta iso garesa, lokaci guda ta sakar masa murmushi hannayensa rik’e cikin nata take furta “Haka ne D’ah na, ka yarda da batun d’an uwanka babu wani abindake wakana wanda ya canza a Masarautar nan.... Kada ka soma d’iban jita jitan babban gida kaji d’ah na... Kaine Magajin mahaifinku, a zaman gida irin wannan na sarauta da d’inbin al’umma dole kak’i gani kak’i ji....” Girgiza kai Mahmood yai kana yace “Maami ba wannan ba... Mai Fu’ad yake nufi da yace Yazeed Keda alhakin kasancewarsa haka...? Menene suka faru da bana nan...??!” Wannan karon harta Fu’ad saida ya d’ago yana duban Mahmood tsoro da firgici k’arara saman fuskarsa, Wani irin bugu Giwa taji a k’irjinta tamkar an aza mata guduma....Ta ware idanunta sosai tana aikawa Fu’ad wani irin duba na tuhuma.... Jamal ne ya katse shirun da yin gyaran murya kana yace “Yaya kasan halin Yazeed, kasan among us all babu wanda yake shiri dashi face ni da nake tolerating d’insa da halayyarsa... Yaya kasan Fu’ad nada zuciya matuk’a.... So ya fad’i haka ne kawai to get back at Yazeed, sabida yasan idan yace haka bazaka k’yale Yazeed ba, Bawai da wani nufi ya fad’i hakan ba... And one more thing Yaya... Yes, Fu’ad ya had’uda iftila’ai da jarabawa na shan kayan maye, but that was tin yana Cyprus, yeah koda ya dawo he was depressed sabida gani yake ya k’arar da rayuwarsa a iska ba tareda yayi abinda ya kaisa Cyprus din ba, wannan ya kuma Sa Fu’ad ya koma ruwa tsundum shaye shayen miyagun k’wayoyi to get rid of his problems... Anyi ta k’ok’arin ya rabu da abin gaba d’aya don har Rehab a Abuja an kaishi... Allah ya taimaka a cen Rehabilitation center d’in ya rabu da abin completely...ya dawo bai shan komai, ina mai tabbatar maka Fu’ad bai shan komai a halin yanzu Yaya....!” Ya k’arashe cikin tsananin sanyin murya... A hankali Giwa ta sauk’e wani irin ajiyan zuciya cikeda jin dad’i, dama ta sani idan ba Jamal ba babu mai iya gyarota, shi d’in d’an albarka ne mai tsananin sanyin zuciya a tsakanin yaranta.... K’uri Mahmood yai masa, dan gaba d’aya cikin ‘yan uwan nasa ya sani Jamal is different, tun tasowarsu mutum ne da ko mai zai fad’a maka iyakacin gaskiyarsa kenan dan haka take yaji sanyi can k’asar zuciyarsa... Tausayin Fu’ad ya kamasa.... A hankali ya soma takowa ya k’araso gaban Fu’ad d’in, ya d’an saka hannu saman kafad’arsa ya dafasa.... Fu’ad ya d’ago idanunsa masu zuban hawaye yana duban Mahmood... K’uri Mahmood yai masa cikeda tausayawa kana yace “Is okay Fu’ad... Mu ‘yan Adam ne masu kuskure... We ain’t perfect, dukkanmu muna kuskure... Mafi alkhairi a cikinmu Sune wad’anda idan suka fahimci laifinsu sai su komaga Allah su tuba.... Ko wane irin abin kunya ka jawowa Masarautar nan ya riga ya wuce Fu’ad... Its all in the past now, ba’a amfani da abinda ya riga ya shud’e..!” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yazeed yana fad’in “Correction brother!!” Gaba d’aya suka juyo suna duban Yazeed dake takowa cikin d’akin cikeda isa da k’asaita, lokaci guda Yazeed yaci gaba da fad’in “Unfortunately a rayuwa irinta babban gida kaman Fada, dik abinda kayi a baya zai cimmaka a gaba... Baya tab’a shud’ewa haka nan kawai ya b’ace a tarihi bai bar wani sign ba....Am I right...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa.... Giwa dai K’uri tai masa tana jin kalaman d’an nata tamkar da ita yakeyi.... Yayinda Fu’ad ya mik’e cikin hawaye yana duban Mahmood, lokaci guda yake furta “Im sorry Yaya..!!” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai ya fice Daga parlorn cikin sauri.... Mahmood ya dubi Yazeed da wasu irin idanu saidai a b’angaren Yazeed d’in ko a jikinsa saima shu’umin murmushin nasa dake bisa fuskarsa, lokaci guda yama k’arasa saman d’aya daga cikin hanshak’an kujerun da sukaima parlorn k’awanya ya hakince kan guda d’aya had’ida bud’e hannayensa ya bazasu cikin kujerar kana ya d’auki k’afarsa guda ya aza bisa d’ayan... Ya daiyi zama irinta masu jin mulki da kuma isa... Ya tasasu gaba yana binsu da kallo murmushin bai bar saman fuskarsa ba, saima juya zoben azirfa dake yatsarsa guda da yakeyi a hankali.... Tamkar tv haka Jamal da Giwa Ke dubansa, shid’inma suke yake duba yana mai ci gaba da kad’a k’afarsa da ya azata saman guda.. Girgiza kai kurum Mahmood yai kana yasa kai yai ficewarsa shima, yayinda Jamal ya janyo hannun Mahaifiyarsu ya nufi bedroom da ita yana fad’in “Muje ki huta Maami....!” Babu musu tabi umarnin d’an nata, zuciyarta na wane irin yankewa, dan tinda taji labarin bayyanar mahaukaciyar nan a fada tasan wannan sharan fage ne, dole akwai wani babban al’amari da ya faru cikin Masarautar, fatanta Jakadiya Ta dawo mata da batu mai dad’i... *** Muhibbah na zaune tana rarraba idanu tana duban kyau da tsarin d’akinda aka sauk’eta cikinsa Umaima ta turo k’ofa ta shigo... Cikin sauri Muhibbah ta mik’e tsaye su duka biyu suna sakin murmushiwa junansu... Umaima taci gaba da fad’in “Kiyi hak’uri na barki Ke kad’ai... Gashi ban samu ganin Maami ba, ta riga ta haura sama, Ina tunanin wani abin ne ya faru, zai wuya Ta sauk’o k’asa a yau d’un saidai ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu....” Girgiza kai Muhibbah tai a hankali kana tace “Babu komai Ranki shi dad’e, har dai Ina cikin gidan zamu gaisa ai, kinsan masu mulki basa son tak’ura inaga zaifi kyau ki k’yaleta har zuwa wani lokacin....!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi kwance saman black beauty face d’inta da yake tas dashi babu alamun koda k’warzani... Umaima ta murmusa kana tace “Muhibbah Ina mamakin ya akai kika San abubuwa da dama gameda masu mulki da kuma babban gida... Saikace a gidan sarauta kika girma... Kodai a babban gida kika girma ne...?” Murmusawa kad’an Muhibbar ma tai kana tace “Ni kuwa Ta ina zan girma cikin gidan sarauta Ranki shi dad’e, bayan gidanmu mu uku tak muke rayuwa cikinta, daga ni sai Mummy saiko Yayana Ansar...” Umaima Ta jinjina kai kana tace “Da alama ke d’in ‘yar baiwa ce.... Inaji a jikina zan k’aru dake sosai ko ince Masarautar nan zata k’aru dake sosai....” Ta k’arashe cikin sigar wasa... A tare sukai murmushi mai d’an sauti kana Umaima tace “Bara naje na turo miki aike, nima zan shigo anjima kad’an.... Feel at home dan Allah kinji...” Jinjina mata kai kurum Muhibbah tai had’ida kuma mik’a godiyarta a gareta... Umaima na ficewa Muhibbah ta mik’e ta yaye tapkeken labulen tagar tana lek’en yanda k’wan wuta suka kuma k’arawa Masarautar kyau da tsari da shike almuru ya doso... Nan Ta hangi Fu’ad na fitowa Daga b’angaren Mahaifiyarsa kaman zai kifa da k’asa, yanayin data gansa ciki har yafi na ganinsa d’azu da tai... Tai saurin janyo alkyabbar Umaima wanda d’azu Ta barta a nan d’akin... Cikin sauri ta rufa alkyabbar akanta ta janyo hular ya sauk’o kusan idanunta kana ta d’an waiga gefe da gefenta, a hankali ta fito ta nufi hanyar da taga Fu’ad yabi cikin sand’a..... SameenaAleeyou📚 [5/24, 9:28 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑* *007* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Lokaci ne na almuru hakan yasa ko bayi ma jifa jifa kake gani, kowa yana k’ok’arin komawa mahutarsa ne.... Hakan yasa sam babu wanda ya lura da Muhibbah da tuni ta takewa Yarima Fu’ad baya..... Sashe ne madaidaici ya shigo mai kyaun gaske, gini a jere masu kama da juna wanda ko ba’a fad’i maka domin yaran Sarkin akai, nan Muhibbah Ta hango Fu’ad ya shige d’aya daga cikin dogayen ginin... Tana nan tsaye taji motsin mutum na dosowa cikin sashen... Gabanta ya yanke ya fad’i tai saurin matsewa jikin gini k’irjinta bai daina bugu ba, jin tafiyar take Tamkar mab’oyar da take aka nufa.... Jim kad’an sai hango mutum tai ya shige parlorn da taga Fu’ad d’in ya shige... Ta fito daga mab’oyarta cikin sand’a kana ta nufi saitin window d’in parlorn ta lab’e jiki tana lek’e... Sosai ta hango Fu’ad na kuka tamkar k’aramin yaronda ya kasa jin lallashi... Yana tsugune gaban drawer dake jikin center table da akima parlorn ado dashi sai faman bincika drawer d’in yake yana kuka sosai, duk wasu tarkacen dake cikin drawer d’in jifa Fu’ad keyi dashi, gaba d’aya ya hargitsa wajen ya wargaza... Can ya ciro wasu magunguna cikin sachet yana k’ok’arin b’are ledar maganin... K’wayoyin sun kusan guda goma jikinsa na matuk’ar rawa musamman hannayensa da ya rik’e k’wayoyin dasu... Take ya d’aga kansa sama had’ida lumshe idanunsa masu zuban ruwa ya toshe hancinsa da hannu guda yana k’ok’arin watsa drugs d’in a bakinsa saiji yai an bigesu sun zube k’asa.... Ba Fu’ad dake k’ok’arin bud’e lumsassun idanunsa a hankali ba harta Muhibbah saida ta d’ago idanunta tana duban wanene ya hana Fu’ad aika ma cikinsa da k’wak’walwarsa wannan gubar.... Jamal ne tsaye ya hard’e rai sosai tamkar bai tab’a dariya ba, lokaci guda ya durk’usa suna fuskantar juna shida Fu’ad d’in.... Fu’ad ya matsa can jikin k’afar kujera yana tak’urewa waje guda yake fad’in “No...No no Jamal, I don’t want to live... I’m tired of living like this Jamal.. na gaji.....Na gaji Jamal....!” Ya k’arashe yana mai bin drugs d’in yana tattarosu tamkar dai mai tab’in hankali... Cikin zafin nama Jamal ya kamo fuskar Fu’ad yana fad’in “Look up Fu’ad, kalle ni nan....!” Ya k’arashe yana mai kuma matse fuskar Fu’ad da tuni har ya koma ja sabida tsananin damk’a da yasha.... Dole Fu’ad yai shiru sai duban Jamal da yake da idanunsa masu zuban ruwa, lokaci guda Jamal Keci gaba da fad’in “Now you’d do exactly as I say...!” Girgiza kai Fu’ad yake da k’yar yana mai furta “No no Jamal... No...!!” Ganin bazai shiru ba ya sanya Jamal zaro wata sirinji na allura cikin aljihun wandonsa, lokaci guda yai injecting Fu’ad da allurar.... Kankace mai Fu’ad ya fad’o jikin Jamal tamkar sumamme.... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Jamal yai kana ya rungume d’an uwan nasa sosai kaman mai tsoron kada a raba tsakaninsu.... Cikin rawar murya Jamal Ke furta “I’m sorry brother, I’m so sorry... I really don’t have a choice.... Ka yafe min Fu’ad....!” Ya k’arashe yana mai kuma k’ank’ame Fu’ad da har lokacin tamkar bai numfashi.... Lokaci guda Jamal ya mik’e ya aza Fu’ad a kafad’arsa kana ya nufi upstairs dashi, d’akinsa ya shigar dashi ya kwanyarsa saman gado, ya gyara masa kwanciyarsa sosai ya lullub’esa kana ya sauk’o k’asa ya tattare drugs d’in dake zube wajen... Saida ya tabbata ya tattare kaf drugs d’in kana ya saita kansa ya fice daga b’angaren Fu’ad.... Muhibbah dake lab’e bayan window a hankali Ta koma Ta jingina jikin bango tana maida numfashi a hankali... Meke faruwa...?” Fu’ad is living a miserable life... Meke faruwa dashi...?” Take taji b’angare na zuciyarta tana ayyana mata cewa ya cancanci fin haka, ya cancanci ya shiga k’uncin rayuwa fiyeda wanda yake ciki yanzu....Ta k’arashe tinanin tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Lokaci guda ta saita kanta kana ta fito daga b’angaren nasa.... Tana isowa sashen da aka sauk’eta kenan ta tadda Umaima tafe wasu kuyangi guda biyu na biye da ita d’aukeda manya manyan trays an rufe da k’yalle.... Muhibbah ta d’an sha jinin jikinta amma sai ta sami k’warin gwiwar dakewa kad’an... Umaima dake bintada kallon mamaki ta bud’e murya tace “Hibba ina kika fito da magrib d’in nan...? Hope all is well...?” Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Gida na mulki da sarauta yanada gizo da kuma cika idanu, amma saidai dikda wannan gizo da cika idanu nasa idan wanda bai tab’a zama cikinta ba ya halarceta tabbas zaija yana matuk’ar k’aunar ya zaga cikin gidan ya baiwa idanunsa abinci.... Tsananin son naga yanda yanayin Fadar take ya sanyani fitowa, amma saidai koda na fito na lura dare ya sako Kai babu abinda zan iya gani... Sannan naji tsoron nai gamo da abubuwa na babban gida wanda da yawan mutane suka aminta cewa a cikin Masarauta ko wacce iri ne akwai d’inbin abubuwa da idanunmu bazasu iya gani ba... Allah yasa banyi wani laifi ba ranki shi dad’e...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman kyakkyawan fuskarta... Cikeda jin dad’in baiwan kalamai da Muhibbah kedashi saman harshenta Umaima ta girgiza mata kai kana tace “Bakiyi laifin komai ba sai guda d’aya...” Muhibbah ta d’an d’ago tana dubanta tana jiran taji laifin nata, nan ta tina cewa Alkyabban Umaima ne jikinta, ta d’ago da zummar bata hak’uri saidai tuni Umaima ta katseta da fad’in “Laifinki shine kink’i ki daina kirana Ranki shi dad’e... Sunana Umaima, Ki kirani da Umaima kawai....” Murmusawa kad’an Muhibbah tai tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tace “Tuba nike bazan sake ba... Umaima....!” Umaima ta jinjina kai kana tace “Shigar sarauta ta amsheki, kiso kiga yanda Alkyabba tai kyau sosai a jikinki....” Tai maganar fuska fal fari’a.... Cikeda jin nauyi Muhibba tace “I’m sorry na saka babu izini.....” Umaima ta kuma murmusawa kana tace “Babu matsala dik lokacin da kike so zaki saka, hasalima hardai kina rayuwa cikin gidan nan zaki koyi saka kayan sarauta... Mu k’arasa ciki gobe idan Allah ya kaimu zan zagaya dake da kyau cikin Masarautar nan....” Muhibbah ta d’an ware manyan idanunta kana tace “Da gaske...?” Jinjina mata kai Umaima tai kana tace “K’warai kuwa zan zaga dake kiga ko ina... Allah yasa dai bakida makaranta goben....?” Sai yanzu Muhibbah ta tina ashe Wai makaranta ne ya kawota garin... K’ak’aro murmushi tai kana tace “Satin nan akai resuming so babu wani karatu mai tsauri da za’ai...” Umaima ta jinjina kai kana tace “Hakan na nufi kin amince kenan...” Muhibbah Ta jinjina mata kai murmushi bai bar saman fuskarta ba... Lokaci guda suka sa kai suka k’arasa cikin madaidaicin parlorn kana bayin suka take masu baya... *** Dare ya ratsa, k’afafuwa sun d’auke a cikin fada, bakajin komai sai kukan k’anan halittu wanda wasu idanu na basu iya hangosu cikin duhun dare... Dikda cewa Masarautar gauraye take da hasken fitilu da ya k’ara mata kyau.... Jakadiya ce ke gaba da ita, bak’ar Alkyabbace mai nauyin gaske tai mayafi dashi, baka iya hango komai sai alamun bak’in abu... A haka suka isa k’ofar, hannu tasa cikin wata k’aramar aljihu dake jikin bak’ar alkyabbar nan ta zaro wata ‘yar k’aramar mabud’i... Gini ne a zahiri domin kaw sam bazakai zaton wannan waje akwai k’ofa ba balle kai zaton har akwai mabud’i da zai bud’e ta har biladama ya ratsa Ta cikinta...Take ta soma fad’in wasu abubuwa tamkar yare lokaci guda ginin ke sauya launi alamun k’ofa na bayyana... Kafin ta k’arashe karanto surkullen nan k’ofa Ta bayyana... Mik’awa Jakadiya ‘yar makullin tai kana Jakadiya ta amsa ta bud’e... Abinda zai baka mamaki shine wannan waje da sam bazakai zaton akwai k’ofa wajen ba saigashi ya bud’e, sannan ba wannan kawai ba mataye ne cike a wajen, ‘yan mata daga kimanin shekaru goma sha hud’u zuwa ashirin da d’oriya, babu alamun namiji a wannan waje sai mata.... Da alama wata Al’umma Ke rayuwa cikin wajen...Suna shigewa matayen nan dake sanye cikin shiga iri guda suka risina gaba d’ayansu... Jakadiya da Giwa basu zarce ko ina ba sai wani k’aramin d’aki dake daga cen center.... Daga k’ofa Jakadiya ta tsaya dan bata shige cikin d’akin ba, yayinda Giwa ita kad’ai ta shige cikin wannan d’aki mai cikeda duhuwa... Wani jan darduma mai d’aukeda Tambarin Masarautar Giwa ta d’ale ta zauna... Zamanta babu jimawa saiga wani Dattijo ya bayyana gabanta, bak’ik’irin dashi gashi yai masa duguzun a jikinsa, idanunsa jajazir haka nan sumarsa gabaki d’aya fari ne sol... Murmushi maras kyaun gani saman fuskarsa yake dubanta.... Risinar da kanta tayi alamun gaisuwa kana tsohon ya yaryafa mata wani ruwa dake a hannunsa,bai daina mummunar murmushin nan ba yake fad’in “Nasan zakizo nan sabida ta bayyana kuma babu wani abu da ya faru a Fada face cecekuce tsakanin Yaranki...!” Jinjina masa kai Giwa tai kana tace “Tal’udu...! Mun duba gabas da yamma kudu da Arewa babu wani abu bak’o da ya faru, sannan babu wani rai da aka rasa, Tal’udu kar kace min Cikin Yarana guda babu wanda zai gaji Karagar mulkin Masarautar nan...!” Ta k’arashe tana mai tsaresa da kyawawan idanunta wanda suke cike dam da butulciwa mak’aginta..... Murmushi mai sauti wannan karon Tal’udu yai maras dad’in sauraro kana ya janyo wata jaka ta fata ya baje jakar a k’asa... Take jakar ta koma tamkar tray ta fata ga yashi mai tsananin taushi akanta... Da yatsunsa guda biyu yasa ya zana alama kusan guda hud’u kewaye da juna kan ya zana wani abu tamkar karagar mulkin Masarautar a tsakiya...Ya d’ago yana duban Giwa da kyau kana ya kuma Sa yatsunsa biyu ya zana wani alama daga cen gefe... Saida ya gyara zamansa sosai kana ya soma mata bayani... “Kinga wad’annan alamu hud’u dana zana yaranki ne guda hud’u.... Wannan da yake tsakiya Karagar Mulki ne... Tabbas a cikin yaranki akwai wanda zai gaji mahaifinsa, sannan sarautar Masarautar nan bazata fice daga cikin jinin ahalin Sarki AbdulJabbar ba.... Toh amma....!” Shiru yai yana dubanta... Giwa ta katsesa da fad’in “Amma mai Tal’udu..? Sannan shi wancan alaman da ka zana na menene.....?” Murmusawa yai kad’an kana yace “Wancan alama ta k’arshe dana zana fitilar tsafi bata hasko min komai ba, tsantsan duhuwa ne mai gauraye da bak’in k’ura a wajen wanda yake nunida cewa dik d’anki da ya d’ale wannan Karagar Mulki toh fah mulkinsa bazai k’argo ba sannan duk wasu sirrika da kika bisne a Masarautar nan zasu bayyana... Zaki rasa mulkin Masarautar nan dake da ahalinki zaku zamto tamkar ba’a tab’a yinku ba... Abubuwa da dama zasu canza....!” Katsesa Giwa tai da fad’in “K’arya ne wllhi.. Babu wani mahaluk’in da ya isa ya rabani da wannan gadon mulkin... Nida zuri’ata zamu ci gaba da mulkar Masarautar nan... Kawai ka sanar dani mai ka gani gameda bayyanar mahaukaciyar nan....!!” Kai tsaye ya soma fad’in “Naga guguwa mai k’arfin gaske gauraye da bak’in k’ura a cikin gungun mayaka... Naga TAKWABI mai kaifin gaske sannan naga mashi da kibiya mai tsananin tsinin... Kinyi kuskure da kika bar wannan k’ofa d’aya tak a bud’e...!!!” Giwa ta katsesa da fad’in “Wannan k’ofa kana nufin Ja’afar ne...?” Murmusawa yai kad’an kana yace “Ba Jafaru bane amma ita wannan k’ofar da kika barta da gib’i ka iya zamtowa sanadin ‘Yanta Jafaru....!!!” Daga haka dariya ya kwashe dashi mai mummunar sauti... Kan kace mai ya b’ace b’at kaman bashi a wajen..... Giwa ta mik’e da k’yar gumi na karyo mata... K’ofofi guda goma shabiyar ne rus a jere a gefen d’akin Tal’udu, ko wata k’ofa a k’ulle take sai guda d’aya da take hangota a bud’e wanda duk randa ta shigo wannan gida haka nan take a bud’e.... A hankali ta furta “Muje Jakadiya...” Babu musu Jakadiya tace “An gama Allah shi baki yawan rai....!” ‘Yan matan suka sadda kawunansu k’asa har saida su Giwa suka fice daga wannan gida da yafi kama da sansani.... Koda Giwa ta komo sashenta haka abubuwan saukaita mata yawo, batai mamakin ganin Jamal zaune hard’eda k’afofi alamun yana jiran dawowarta ba.... Domin kaw bazai tab’a bacci ba ba tareda ya nemi albarka mahaifiyarsa ba koda kuwa zai jira dawowarta har asubahi ne... Yanayin da yaga mahaifiyar tasa ciki na tashin hankali ya sanyashi k’arasawa gareta ya tarota... “Mamy...Mamy na meke faruwa....? Ina kika fito cikin daren nan...?” Idanu ta zuba masa tana dubansa, lokaci guda ta shafi gefen fuskarsa kana tace “Babu komai masoyina... Ya ka baro d’an uwanka Fu’ad...?” Fuzar da fuci Jamal yai a hankali kana yace “Karki damu Mamy zan kula da Fu’ad...” Ta jinjina masa kai a hankali ba tareda ta kuma cewa komai ba, Jamal ya d’an dubeta cikeda kulawa kana yace “Maami akwai wani abu ne..?” K’uri tai masa kana ta muskuta kad’an tace “Jamal ka tabbata gaskiya ka fad’in gameda batun Ja’afar...?” Wannan karon da gefen bakinsa ya murmusa kana ya tako zuwa gabanta a hankali... Durk’usawa yai nan gabanta kana yace “Ban tab’a miki k’arya ba Maami na dik abinda na sanar dake da gaske hakance Ta faru....!” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Giwa tai kana ta shafi gefen fuskarsa tace “Kaje ka kwanta D’ah na Allah shi maka Albarka...!” Ta k’arashe tana shafa sumarsa cikeda so da k’auna... Jamal ya amsada “Ameen Maami na kana ya kuma mata sallama ya fice... Giwa taci gaba da tinanin abububuwan da suka faru cikin Masarautar.. *** Ko kallo bata ishesa ba saima cire zobban hannayensa da agogo da yakeyi, ya zuba su saman bedside kana ya kwab’e rigar mulkin dake jikinsa kyakkyawar suffarsa Ta bayyana, Rahima tai saurin rintse idanunta tana tina yanda alak’arsu da Yazeed ya samo asali... Gimbiya Raheema k’anwacega Gimbiya Zeenatu amaryar Sarki AbdulJabbar mai rasuwa... Su d’in ‘Ya’yaye ne ga Sarkin Akwanga wanda ke k’ark’ashin mulkin Sarki AbdulJabbar gaba d’aya dashike garin a k’ark’ashin k’asarsa take,...A lokacin da Rahima tazo Masarautar Jos bikin ‘yaruwarta Zeenat a nan tai gamo da mutumin da zuciyarta Ke muradin mallaka, wannan mutumi kuwa ba kowa bane face Yarima Mahmood AbdulJabbar, saidai kash abinda yai mata cikas shine Yarima Mahmood baida lokacin wata Mace face na iyalinsa Aliya.... Hasalima Auren mahaifin nasa ya kawosa k’asar bayan matsa masa lamba da mahaifin nasa yai da cewa lallai lallai sai ya halarci d’aurin aurensa da zai sake... A lokacin daga shi sai matarsa Aliya suka zosu Nigeria d’aurin auren Mai Martaba basu taho da Zahra ba a cewarsu tana makaranta, sannan bayan sunyi Abinda ya kawosu da kad’an suka kuma tattarawa suka koma Spain dikda cewa Giwa bataso d’an nata ya kuma tafiya ba amma babu yanda zatayi wannan tsinanniyar matar tasa d’iyar matsiyata tasan dan ita yake gudun gidansu dan yasan muddin yana Nigeria idan batasa ya rabu da wannan matsiyaciyar ba toh kuwa ko shakka babu aure zasu sake masa a Fada ‘yar asali ‘yar babban gida kaman yanda yake d’an manyan mutane.... Rahima bata sami hakan ba taci kuka har ta gode Allah dan Shi Yarima Mahmood baima San akwai wata halitta mai suna Raheema dake k’aunarsa ba... Tun bayan auren Maimartaba Sarki AbdulJabbar da ‘yaruwarta Zeenat tai sai tai zamanta a wannan masarauta da burin wata rana Mahmood zai dawo gida ya aureta dan bata cire rai ba, a wannan zaman da tai a masarautar suka k’ulla abota da Zuhra matar Yarima Yazeed domin zasuzo tsara da Zuhra, tasu tazo d’aya sosai hakan yasa daga abokai har suka koma tamkar aminai, so tari Yazeed yakan tsinci hirar matarsa Zuhra da Rahima yanda Rahima Ke sanar da ita irin k’aunar da takewa d’an uwansa Mahmood... Shak’uwar Raheema da Zuhra dai tai nisa sosai tamkar wasu ‘yanuwan juna, ko Akwanga Rahima ta tafi Zuhra taita damunta da waya kenan tana tambayarta yaushe zata dawo tsaban shak’uwa da aminci dake tsakaninsu musamman dashike Zuhra mutum ce mai Saurin yarda da d’anadam ga sanyin hali da kyakkyawar zuciya.... Wata ranan jumma’a Rahima Ta shigo b’angaren Zuhra da niyyan surprising d’inta dan ranan ta dawo daga tasu Masarautar.... Bata tadda Zuhra da yaran a k’asa ba sannan babu motsin mutane cikin sashen, sai tai zaton Ta sallami kuyangin ne dan wataran idan zatai baccin rana takan sallamesu idan da mai yin wani abu nasa na k’ashin kansa ma ya samu yajesa yai, sannan watak’ila yaran na makaranta basu dawo ba, hakan yasa kai tsaye ta haye d’akin Zuhra ta bankad’e k’ofar da k’arfin gaske tana mai furta “Surprise...!!!” Birki tai da kalaman nata ganin abinda idanunta suka gano mata... Yana tsaye gaban gado jikinsa babu riga sai k’aramar towel dake rik’e hannunsa wanda da alama jik’akk’en sumarsa dake d’igan ruwa yake gogewa.... Rahima tai saurin rintse idanunta jiki na rawa take furta “I’m so...I’m sorry...I’m sorry please..!!” K’afarta har na hard’ewa take k’ok’arin juyawa saidai tuni taji an fizgota an dawo da ita cikin d’akin ta fad’o saman k’irjin mutum... Ta bud’e idanunta masu cikeda tsoro tana dubansa, saidai ga tsananin mamakinta shu’umin murmushin nan ne nasa saman fuskarsa... Lokaci guda kuma sai gani tai ya mugun had’e rai yana mai k’arewa fuskarta kallo idanunta zuwa bakinta... Jikin Rahima bai daina rawa ba mak’ale jikin Yazeed... Lokaci guda kuma sai gani tai ya d’an murmusa kad’an kana yace “Malama idan zaki saki jikinki ki saki jikinki, ce miki akai bansan ke d’in ‘yar hannu bace... Sai wani k’ifi k’ifi da idanu kike min, sarai target d’inki kenan tinda kinsa every Fridays Zuhra na tafiya sashen Giwa da yara suyi mata yini shine kika kasa rik’e kwad’ayinki kika lab’ab’o kika hauro har sama kika kawo kanki yanzu zaki wani matse fuska tamkar tsoron gaske kike, ko ce miki akai bana lura da irin kallon maitan da kike bina dashi ne...” Ya kuma murmusawa da gefen bakinsa kana yace “You don’t play such games with Prince Yazeed sweetheart.... Abinda kikazo nema zaki samu, batai aune ba sai jin fuskokinsu tai sun had’e waje guda.... Rahima ta raina kanta ta kuma raina duk wasu mazaje da tai huld’a dasu a baya, ta yarda Yazeed k’arshe ne yanda yake a zahiri haka yake a shimfid’a, idan kuwa har bazata sami Mahmood ba tinda batada tabbacin zai dawo Masarautar dan haka ta zab’i taita maida kwad’ayinta da d’an uwansa Yazeed wanda takeji tamkar da Mahmood d’in take tare.... Saidai bayan komai ya lafa tsakaninsu ko takanta bai kuma bi ba saima ficewa da yai kaman babu abinda ya faru tsakaninsu, haka dai Rahima ta mik’e ta kintsawa Zuhra d’akinta can k’asar zuciyarta tana jin sam bata kyautawa Aminiyar tata ba... Tin Daga wannan lokaci haramtacciyar alak’a ta k’ullu tsakanin Yazeed da Rahima... Tayi nisa cikin tinanin nan ta sinkayo muryarsa Cikin dakewa yana furta “ “Kinsan ba’a min yanga, so take that thing off....” Ya k’arashe yana mai kuma relaxing cikin gadon.... Jiki a matuk’ar sanyaye Rahima tasa hannu tana zame doguwar rigar dake jikinta hawaye basu daina gangaro mata ba.... Da gefen idanu yake dubanta har ta k’araso gabansa a d’arare tamkar mai tsoron taka k’asa, yau d’in ko idanunsa ta k’asa duba.... Saida ya kwashi dak’ik’ai yana k’are mata kallo daga nan yanda take tsaye kana ya bata izinin zama dan bata isa ta zauna saman gadon ba ba tareda yace tai hakan ba....Ta narka masa harara tana mai kuma ci gaba da share hawaye... A hankali ya mirgino gareta, Rahima na jin hannayensa cikin jikinta Ta fashe masa da kuka... Da tsananin mamaki Yazeed ke duban sabon salon nata... “Ke..!!” Ya daka mata uban tsawa, ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa, lokaci guda take furta “This is not good Yarima... Wllhi ni dama nayi zaton Yarima Mahmood bazai dawo bane nai zaton bazan tab’a samunsa ba shisa na biye maka... But wllhi na tuba daga wannan mummunar sab’on ni da aure nake son Mahmood, family nake so nidashi muyi building a sabon kingdom d’inmu...Pl....!” Sauk’an marin da taji ne babu zato ya sanyata had’iye sauran kalaman nata... Ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana duban Yazeed dake tsananin huci lokaci guda yake furta “Prince Yazeed AbdulJabbar can never be second option!!!... Ke kinyi kad’an kice a rashin wani kike taredani... And let me remind you this princess, idan kina tunanin jin kunyan idon duniya ne Toh ki sani a wannan duniyar babu wani abin jin kunya... Cos life itself is full of disappointment... Get out of my sight..!” Ya k’arashe yana nuna mata k’ofa... Da tsananin tsoro take dubansa kana tace “Yazeed a daren nan zan fita, ka kuwaga time...?” “I’ll be saying it twice if I said it again... Kuma kinsan bana maimaita magana....!” Jiki a matuk’ar sanyaye ta fice dan tasan kad’an da aikinsa yasa ai waje da ita.... Haka ta fice cikin daren nan k’afa dik ya d’auke, domin a nan d’aya daga cikin guest house d’in marigayi Mahaifinsa suke akasarin had’uwarsu... Tana fitowa ta shige cikin motarta k’irar Mercedes Ta nufi Fada, batabi ta babban gate d’in Fada ba dan tasan komai ka iya faruwa dan haka ta k’ofar bayi tabi ta shigo cikin Masarautar.. Motarta ma a nan sashen bayin Ta barota, Haka nan take tafe tana waige waige tamkar mai tsoron kar wani ganta... Muhibbah da ta kasa bacci dan idan ta tafi bak’on waje hakan ne Ke faruwa da ita a ranakun farko dan haka harabar masauk’inta ta fito tai zamanta tana bin taurari da suka haska sararin samaniya da kallo, lokaci guda tana tinanin Fu’ad da halinda ta gansa ciki.. Nan ta hango giftawar mutum, ta d’an mik’e kad’an tana kuma lek’awa tabbas mace ce kuma cikin shiga irinta alfarma nan ta hangeta ta shige hanyar da zai sadaka da wani sashen.... Jim kad’an sai hango hamshak’iyar jeep k’irar Ford tai ta shigo cikin Masarautar, ta nufi wani sashen gefen sashen dakeda tabbacin na Fu’ad ne.... Toh su waye wad’annan masu dawowa Fada cikin dare....? Tambayar da ya tsaya mata a rai.... SameenaAleeyou📚 [5/27, 10:42 AM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑* *008* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tinda ya kwanta yake wasu irin mafarkai marassa kyau, da fari mafarkin matarsa Aliya da mahaifinsa yai, bayan yayi addu’a ya sake komawa wani mafarkin ya kuma tadashi... Wannan karon akan K’annensa guda Uku ne, abinda ya gani cikin mafarkin sosai ya tada masa hankali... Tsaye ya hangi Yazeed da Fu’ad rik’e da takubba a hannayensu ko wanne takwabin dake hannunsa na d’igar da jini wanda yake jajazir.... Sunayensu ya ambata cikeda tashin hankali ganin abindake rik’e hannayensu, cikin kid’ima ya nufi yanda suke a tsaye suna maida huci suna nunasa da takubban dake hannayensu lokaci guda suka fashe da dariya basu daina nunasa da takubban ba... Mamakin dariyarsu yake bayan abinda ya gani rik’e hannayensu, k’arasowar da zai kusansu sai hango wani d’aki yai a bud’e cikin jerin wasu d’akuna... Basu daina dariyar da suke ba har Mahmood ya nufi cikin d’akin mai tsananin duhuwa.... Saidai yana shiga d’akin ya hango mahaifiyarsu zaune saman gadon sarautar masarautarsu... K’irjinsa yaci gaba da bugawa sanda ya hango d’an uwansa da yakeda tabbacin ya fita zakka cikin sauran ‘yan uwan nasa durk’ushe kan wata yarinya sai darza mata wuk’ar yake... Ga jini na kwarara amma da alama bata mutu ba.... Cikin zafin nama ya ambato sunan Jamal da k’arfin gaske, saidai ko gizau Jamal bai ba saima ci gaba da darza mata takwabin da yake... Tsalle Mahmood yai ya finciko Jamal don ceton yarinyar amma mai..? Yana d’agosa saiji yayi an luma masa takwabi a cikin cikinsa... Mahmood ya rik’e cikinsa yanda jini ke malala a k’asa.. Ya d’ago yana duban ‘yan uwansa guda Uku rikeda takubban saidai bazaice ga wanda ya caka masa ba cikinsu, maida dubansaga mahaifiyarsu dake zaune saman Karagar mulkin yai saidai wannan karon matarsa Aliya ya gani ba mahaifiyarsu ba...Hannu yake mik’a mata alamun neman taimako amma inaa batai ko gizau ba tana nan zaune saman Karagar mulkin saima sakin dariyar da take mai firgitarwa... A hankali yake ji numfashinsa na d’aukewa jikinsa na zamewa har saida ya fad’o kan yarinyar da Jamal ya gama yankata da takwabi, su duka biyu jini na malala daga jikkunansu.... A daidai wannan lokaci ne ya farka daga baccin cikeda tsananin tashin hankali... Addu’o’in da sukazo bakinsa kawai yake iya karantawa had’ida jero hasbunallah wa ni’imal wakil... A hankali yake jin natsuwa na sauk’o masa cikin zuciyarsa... Hannu ya mik’a ya kunna side lamp kana ya dubi k’aramar agogo dake gefen bedside ya nuna k’arfe 4:30am, anata kiraye kirayen assalatu... Shafe fuskars yai da duka hannayensa biyu kana ya mik’e ya nufi bathroom ya d’auro alwala, shimfid’a abin sallah yai amma ko tsayuwar sallar saiji yai ya kasa... Ya zauna nan bakin gado abubuwan na kuma zuwa masa... Wannan wane irin mafarki ne mai cikeda rud’ani da kuma tashin hankali.... Mai wannan mafarki yake nufi...? Take yaji wani b’angare na zuciyarsa na raya masa _Akasarin munanan mafarkai Daga shed’an ne ka nemi tsari da kariya daga shedan.._ Ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yana mai kuma shafe fuskarsa, tabbas ‘yan uwansa bazasu iya kashe ran wani ba koda bawa ne balle nashi.... Ya fuzar da fuci a hankali yana neman tsari daga shaid’an da kuma munanan abubuwan da ya gani a cikin baccinsa... Ya jima zaune wajen har saida ya soma jiyo kiran sallar asubahi... Ya mik’e ya d’auki cazbaha da k’aramar littafin azkar d’insa na hisnul Muslim kana kana ya nufi masallacinsu dake nan cikin Masarautar.... Nan cikin masallacin ya tadda Jamal zaune yana wurdi da alama sallar nafila ya ida yana jiran k’arsowar imam a tada sallar asuba... Yarima Mahmood ya saki murmushi a hankali natsuwa na sauk’o masa, tabbas wannan mafarki nashi daga shed’an ne... Of all people bazai yuwu ma ace Jamal ne zai caka masa wuk’a ba... Nan ya k’arasa had’ida zama gefen Jamal d’in... Suka sakar ma juna murmushi kana Jamal ya mik’a masa hannu alamun masabaha... Zamansa da kad’an kaw Imaam ya shigo suka tada sallah.... Bayan an ida sallah ne suka jera suna fitowa a tare suka nufi b’angaren mahaifiyarsu... Suna tafe Yarima Mahmood ya d’anyi gyaran murya kad’an kana ya dubi Jamal yace “Nikam har yanzu Yazeed na nan da halinsa na k’in zuwa sallah...? Naga tinda na dawo bana ganinsa a jam’i and Fu’ad ya akai yau bai fito sallah ba...?” Murmusawa kad’an Jamal yai wanda murmushin d’abi’arsa ce kana yace “Babu abinda ya canza da Yazeed Yaya... Fu’ad kuma baijin dad’i ne shisa baka gansa ba...” Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali suna tafe cikin kamfacecen masarautar nasu da duk yanda suka gifta sai bayi sun risina Sun gaidasu.... A haka suka iso sashen mahaifiyar tasu... Jakadiya ce Tai masu iso kana suka shiga suka taddata zaune saman abin sallarta da alama itama sallar Ta ida tana gabatar da wurdi... A jere sukai zama irinta rak’umi saman Darduma dake a saitin mahaifiyar tasu wanda dama dominsu darduman yake aje wajen, dik sanda suka shigo gaisheta a nan suke zama... Ta ida addu’o’inta suka shafa a tareda yaran nata, murmushi fal fuskarta take dubansu....Tsananin k’aunarsu na ratsa dik wani kafa na jikinta, Mahmood ne ya soma gaidata sannan Jamal... Ta amsa masu cikeda so da k’auna had’ida shi masu albarka... Daga nan ne take sanar dasu jiya Galadima ya sanar da ita cewa Yau d’in da yammaci zasuyi zama kan maganar wanda zai gaji mahaifinsu Sarki AbdulJabbar mai rasuwa... Sosai suka natsu suna sauraren Mahaifiyar tasu sanda taci gaba da fad’in “Sadauki..!” Yarima Mahmood ya d’ago yana dubanta, Giwa taci gaba da fad’in “Na riga na zab’eke matsayin wanda ni nakeso ya gaji mahaifinku, toh amma Galadima ya tabbatar min cewa cikin masu neman sarautar nan harda Majidad’i d’an d’an uwan mahaifinku Wambai da kuma biyu daga cikin yaran Marigayi Talba mai rasuwa, sannan da shi kanshi Chiroman gari yana neman Karagar Masarautar garin nan... Dan haka ni a nawa b’angaren na tsaida kai, kuma na tabbata king makers bazasu bani kunya ba, domin kaw daga Galadima har Waziri a b’angaren mu suke, kuma sunyi Na’am cikin masu neman sarautar Masarautar nan babu wanda ya dace ya maye gurbin mahaifinku sai kai Sadauki....” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta, yayinda Jamal yaci gaba da jinjina kai yana furta “Tabbas Maami, Yaya shi kad’ai ya dace ya gaji Abbah... Cikin duka wad’anda kika lissafo, sannan dama ance kyaun d’a ya gaji mahaifinsa... Kuma idan har sarauta ya fice daga gidan nan haka munaji muna gani za’a sallamemu mu bar Fada mu koma cen wani k’auye a nad’amu hakiman k’awye... Yaya you’re the rightful heir to the throne... Kai ka cancanta ka d’ale wannan karaga...!” Ya k’arashe yana duban d’an uwan nasa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.... K’uri Mahmood yai masu yana dubansu kana ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana mai shafe fsuksrsa da tafukan hannunsa, ta yaya zai sanar dasu ba abinda ya dawo dashi Masarautar nan ba kenan.. Ta yaya zai sanar dasu ba neman mulki bane gabansa, ta yaya zai sanar dasu abinda ya dawo dashi yasha bambam da abinda suke tinanin shi ya dawo dashi.... Muryar Giwa ya sinkayo tana ci gaba da fad’in “Kai nake sauraro d’ah na nasan bazaka bani kunya ba...!” K’ak’aro gajeren murmushi yai irinta masu mulki kana ya soma fad’in “Allah shi taimaki Giwar Sarki AbdulJabbar, Allah shi taimaki Mai babban d’aki... Allah shi taimaki Gimbiya Turai d’iyaga Sarki Jamaludden na k’asar Benin, La princesa de benin (the Princess of Benin), La reina de jos (the Queen of Jos)... Mi hermosa madre (Kyakkyawan mahaifiyata) Allah yaja zamaninki...!!” Tinda ya soma mata kirari take dubansa da murmushi saman fuskarta, hannu tasa ta shafi fuskarsa kad’an k’walla tab idanunta... Tana matuk’ar k’aunar Mahmood, akwai wani abinda ya banbanta dashi cikin ‘yan uwansa... Yarima Mahmood ya d’an kamo hannunta ya sumbata su duka biyu d’in suna sakarwa juna murmushi kana ya soma fad’in “Maami, bawai na banbanta da ra’ayinki bane... Bawai bana son amsar tayinki bane... Ke duk kin wuce haka a wajena... Umarni kawai zaki bani nabi.... But Maami, sarauta ba layina bane... Almost 14 years bana Masarautar nan saidai nazo lokaci zuwa lokaci, da yawan wasu abubuwan ban saba dasu ba, ban San ya ake gudanar dasu ba... Maami idan nace zan amshi sarautar Masarautar nan hakan na nufin tamkar sabon karatu zan fara, dole na koyi abubuwa da dama.... Inaga zaifi kyau Idan aka nad’a wanda yafini cancanta da dacewa da rik’on Masarautar...” Cikin saurin Yarima Jamal Ke girgiza kai yana fad’in “No, no Yaya... Babu wanda ya dace ya kuma cancanta face kai, Yaya kana so mun fice daga Masarautar nan ne cikin k’ask’anci da tozarci...? Yaya kana sona fidda matan mahaifinmu a d’akunansu akaisu wani k’auye ne..? Yaya so kake mu fice daga cikin gidan da aka haifemu aka renemu cikinsa...? Yaya so kake mu bar asalinmu da abinda muka gada... Nasan duk bazaka so abubuwanda lissafo su faru ba....!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Giwa kam k’uri taiwa Mahmuda tana kallon sarautar Allah... Yarima Mahmood ya kamo hannayen Yarima Jamal su duka biyu d’in suna duban juna sanda Mahmood Ke fad’in “Dik ba wannan nake nufi ba Jamal, kuma bana fatan d’aya daga cikin abubuwanda ka lissafo su faru, sannan Allah ya albarkaci mahaifinmu da yara maza d’ai d’ai d’ai har guda hud’u and we are all entitled to the throne.... Ga Yazeed gaka nan, even Fu’ad zai iya zama sarki ba wani abu bane.. Ba lallai sai Babba ba k’aramin cikinmu ka iya zama kan Karagar mulkin nan hardai yanada damar data mallaka masa hakan... So Maami why not a tsaida d’aya daga cikin ‘yan uwana....” Wata kakkausar murya ce da ko shakka babu sun San mai ita ta katsesu da fad’in “Babu wanda ya isa, babu mahaluk’in da ya isa ya fitar da mulkin Masarautar nan daga hannun ahalinmu... Babu wanda ya isa ya fitar dani daga gidan mahaifina, Mu kad’ai ne jinin sarauta, mu kad’aine muka gaji sarautar... And yes Yaya, you’re absolutely right... Naji dad’i daka d’auki shawarina... For the first time we’re on the same page, kai kanka ka amince babu wanda ya cancanta ya zama sarki face ni Yazeed..!!!D’add’aya yake maganar yana takowa cikin katafaren d’akin hannayensa guda biyu hard’e ta baya, cikin taku mai cikeda k’asaita yake tafiyar nasa tamkar wani Amale... saida ya iso dadai tsakiyar d’akin kana ya karkato yana fuskantar Mahmood, lokaci guda yake furta “And now that we are on the same page, inaso ka jaddadawa wad’annan masu sarautun Gargajiyan kar wani daga cikinsu yayi gigin shiga gonata, ina rantsuwa da mahallicina idan d’ayansu yayi kuskuren jayayya dani da sarauta ta, ba rawaninsa kawai da muk’aminsa zai rasa ba, zai iya rasa abinda yafi wad’ann mahimmanci a wajensa... Ina nufin zai iya rasa ransa..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Girgiza kai kad’an Mahmood yai kana yace “And kana tunanin kaine wanda ya dace da kujerar..?” Saida ya kuma takowa kad’an murmushin bai bar saman fuskarsa ba kana yace “I’m far better than right... I am perfect... Yeah Perfect..!” Ya k’arashe cikeda pride K’uri Mahmood yai masa yana dubansa , lokaci guda ya mik’e tsaye suna fuskantar juna shida Yazeed, idanu cikin idanu suke duban juna kana Mahmood ya soma fad’i cikin dakewar murya “Wanda duk yace shine toh ba shi bane, sannan ba’a shugaba mai zafin zuciya wanda baida jarumtar kwantar da zuciyarsa idan rai ya b’aci, ba’a shugaba maras d’a’a da ganin girman na gaba, ba’a shugaba maras tsaida dokokin Ubangijinsa... Shi shugaba ya kamata ya kasance mai taushin zuciya sannan Jarumi, taushin zuciya domin ya tausasawa al’ummansa yaji k’ansu sannan ya kwantata adalci a tsakaninsu, Jarumi domin ya zamto sulke wajen kare al’ummansa da tsaresu daga abokan gaba... Mai bin dokokin Ubangijinsa domin ya zamto abin koyi ga Al’ummarsa... Mai girmama na gaba domin wad’anda suke k’asa dashi su girmama shi.... Ta yaya nake tunanin zaka iya zamtowa shugaba bayan baka aikata d’aya daga cikin abinda na lissafo... Nayi kuskure da nai zaton zaka iya maye gurbin mahaifinmu.... Yanzu na tabbata baka cancanta ba Yarima Yazeed....!!” Ya k’arashe yana mai kuma matso da fuskarsa dab na Yazeed cikin muryarsa mai cikeda amo.... Shu’umin murmushin ne nasa saman fuskarsa, lokaci guda ya lank’wasa Kai kad’an yana mai k’arewa Mahmood d’in kallo kana yace “Toh waye ya cancanta..? Kai...?!” Yai murmushi mai sauti irinta masu mulki kana yaci ya a da fad’in “Idan duk kanada qualities d’in daka k’irgosu abu guda d’aya tak da ka aikata ya rushesu... Yarima Mahmood... Mak’aryaci yafi dacewa da shugabanci irinta siyasa amma ba shugabanci irinta Babban Gida ba..!!!” Cikin zafin nama Mahmood dake tsananin huci yake furta “Don’t Yazeed... Don’t you dare cross the line...!!!” Yazeed da ko a jikinsa Murmusawa ya kumayi kana yace “Oh really now... Your Royal highness..! Baka so a fad’i naka aibun, bayan Kai ka iya fad’in na wasu cikeda k’warin gwiwa... Ai ba’a sarki matsoraci mai tsoron Ta kife... K’aryar Jarumta kake...Yarima Mahmood..!!!” “Yazeeeedddd!!!!” Ya daka masa uban tsawa had’ida d’aga hannunsa da niya watsa masa mari... Saidai tuni Jamal ya shige tsakaninsu yana tausan Mahmood “Yaya please don’t... Kar ka mareshi... Kayi hak’uri dan Allah....Allah ya huci zuciyarka..!” Idanuwansa da suka kad’a sukai jazir yake duban Yazeed dasu, abinda da wanda bai iya b’acin rai ba sai abin ya zama abin ban tsoro... Kana iya hango yanda k’irjin Mahmood Ke hawa yana sauk’a alamun tsananin bugun zuciya da b’acin rai.... Lokaci guda yake nuna Yazeed da d’an yatsa kana yaci gaba da fad’in “I’ll warn you for the last time Yazeed.... Do...not..try..me!!! Do..not..cross..the line..!!!” Daga haka sa kai yai ya fice cikin sassarfa da tsananin b’acin rai... Yazeed ya rakasa da muguwar kallo kana ya kuma sakin shu’umin murmushinsa, gyara zaman rigarsa yai had’ida kuma hard’e hannayensa ta baya d’abi’ar masu mulki, ya maido da dubansanga mahaifiyarsu data cika tai fam, ta tsaresa da idanu cikin tsananin b’acin rai.... Dukda ya hango tsananin b’acin rai a idon mahaifiyarsu hakan bai hanasa sakin murmushi da gefen bakinsa ba, kana ya isa kusan k’afafunta ya zauna yana mai gaidata, ya k’arashe yana fad’in “A saka min albarka Maami na...!” Daga Giwa da Yazeed ya d’auko hannunta guda ya d’aura saman kansa alamun saka albarka har Jamal dake tsaye tamkar statue kallon mamaki suke bin Yazeed dashi... Shifa ko a jikinsa da alama, baima san yayi laifi ba... Yazeed bazai tab’a canzawa ba, Ta zaci aure zai canza Yazeed gashi yayi yara har biyu amma halinsa na nan babu abinda ya ragu saima wandake k’aruwa... Har kullum addu’an shiriya takewa Yazeed amma kaman dad’a tab’arb’arewa yake... Tana ji ya gama fad’in iyaka abinda zai fad’i tamkar wani mai bata sak’o kana ya mik’e yai ficewarsa cikeda k’asaita wanda Ke matuk’ar masa kyau... Jamal ya bisa da kallo har ya b’acewa ganinsa kana ya maidoda dubansaga mahaifiyarsu da ko shakka babu k’walla yake hangowa cikin idanunta, dukda k’ok’arin dannesu da takeyi, shid’in yafi kowa sanin mahaifiyarsu yasani idan abu na matuk’ar damunta... Bai wata wata ba ya isa yanda magungunata Ke aje ya d’auko da kansa yana b’alla mata dan bazai iya jiran wata kuyanga tazo bata magani ba... Sai faman sannu yake mata yana tausanta... Jinjina masa kai kurum take abubuwa da dama k’unshe cikin zuciyarta... Idanma aka ce an bar karagan mulkin nan tsakanin yaranta kad’ai tasan wani yak’i ne mai zaman kansa... Sai yanzu maganan Tal’udu ke kuma dawo mata da yace yaga k’ura mai duhuwan gaske da dandatson mayak’a... Amma koda za’a tashi wannan masarauta bazata tab’a bari dai sarautar ya kufce masu ba... “Wambai” sunan da zuciyarta ta ambata... Take ta sanar da Jakadiya Tai mata kiran Ubandoma... *** Tsaf ta shirya cikin jan leshi d’inkin doguwar riga da yai matuk’ar amsarta, ta d’aura alkyabba fara k’al wanda Umaima ta Aiko mata da safen nan... Tsaye tai gaban full length mirror tana duban Wai ita SAUDATU ke sanye da kaya ta mulki da sarauta yau d’in... Ta tina sanda ta fice daga Masarautar cikin k’ask’anci da tozarci yau sai gashi ta dawo cikin karamci da girmamawa... Tabbas Saudatu ta mutu Muhibbah ce a raye yanzu...Ta saki murmushi mai ciwo a hankali kumatunta suka lotsa... A fili take furta “You better be ready, cos my revenge is action...!!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji tana mai duban fuskarta cikin madubi..... (Anya bakiyi kuskure ba Muhibbah...? Muje zuwa..) SameenaAleeyou📚 [5/29, 9:41 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑* *009* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zama yai gefen bedside yana jiran fitowarta dan yaji alamunta a closet, ya sani bazai wuce shirin school take ba... Idanunsa suka sauk’a kan picture dake aje gefen bedside d’inta, ya jima yana duban picture d’in... Lokaci guda ya saki murmushi a hankali dan bazai tab’a mance ranan da sukai hoton ba a cen k’asar Spain, lokacin family d’insa na cikeda Farin ciki, inama abubuwa zaku koma kaman yanda suke before.... Yasa hannu ya d’auki hoton yana shafawa a hankali... Zahra da fitowarta kenan daga closet sanye cikin shiga irinta ‘yanmakaranta tsaye tayi tana duban mahaifin nata yanda yai k’urima picture d’insu, lokaci guda tausayinsu gaba d’aya na kuma kamata.... Ta d’an tako kad’an kana ta zauna gefensa... “Good morning Paa...” Ta fad’i sanda take zama... Gyara zamansa ya d’anyi yana mai aje picture d’in kana yace “Good morning my love... Da fatan kin tashi lafia..?” Jinjina masa kai tai kana tace “Lafia Paa... How about you Paa..? You seemed worried... Is something bordering you..?” K’ak’aro murmushi yai had’ida shafa kanta kad’an “Babu komai Princess, do you want me to take you to school by myself...?” D’an dubansa tai da mamaki kana ta murmusa “C’mon Paa, kai da kanka kake ce min nan ba Spain bane, things are different here...Well, I’m starting to get used to it... Nasan bazamu tab’a komawa kaman yanda muke a baya ba... It hurts tho..!” Ta k’arashe tana mai zura safar k’afanta.... Dubanta yake da wasu irin idanu, shi kad’ai yasan mai yakeji cikin zuciyarsa, yanada good relationship da d’iyarsa, bazaiso wani ko wani abu ya b’ata wannan alak’a mai kyau da yakedashi shida d’iyarsa ba, Amsar socks d’in da take k’ok’arin sakawa yai lokaci guda ya sauk’o daga saman gado yana zira mata safar a k’afarta... Zahra tai masa K’uri tana dubansa had’ida tunanin anya ba wani abin Ke damun Paa d’inta ba... K’ok’arin amsar safan take tana furta “Paa you don’t need to do this... Zan iya sakawa da kaina, I’m not a little girl anymore Paa...” Tana maganan murmushi kwance saman fuskarta... Bai saurareta ba har saida ya ida saka mata, kana ya d’ago yana dubanta shima murmushin ne saman fuskarsa, lokaci guda yake furta “Well, to me you’d always be the same that little baby I used to carry on my arms... Bazaki tab’a girma a idanuna ba.. And you know why is that my Princess..?” Ta girgiza kai tana mai dubansa itama murmushin ne saman fuskarta, lokaci guda yaci gaba da furta “It’s because you’re my daughter, my little baby...And I love you, so much..!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... K’arasowa tai ta rungumesa tana k’ok’arin maida k’wallan da suka ciko idanunta.... Lokaci guda Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Never doubt that my Princess...!” A hankali itama take furta “I love you too Paa...So much...!” Suka kuma duban juna su duka biyu kana Yarima Mahmood yace “Zahra, I want you to know that whatever happens, I mean ko menene always remember that your Paa loves you... Never doubt that kinji koh...!” Ta jinjina masa kai a hankali tana duban yanayinsa, dikda da yarinta a tattareda ita zata iya karanto damuwa cikin idanunsa, koda shike tin bayan rasuwar mahaifiyarta haka nan yake wasu lokutan.... “Do you want us to have breakfast together by the pool side..?” Yai maganar yana rik’eda hannayenta.. Jinjina masa kai tai kana tace “Sure Paa..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye had’ida zura k’aramar hijab d’inta na makaranta... Hannunta ya kamo suka fito tare... Kallo d’aya zakaiwa yarinyar ka fahimci tana cikin Farin ciki... Take ya sanar da Ubandoma ya fad’awa Jakadiya a shirya masu karin kumallo a gefen swimming pool shida d’iyarsa a nan cikin b’angaren mahaifiyar tasa.... Fu’ad da fitowarsa kenan bayan ya gaida Giwa ya hangi Zahra da YarimaMahmood suna cin abinci cikeda Farin ciki, hasken ranan hantsi ya haske fuskokinsu... Murmushi ya saki a hankali kana ya nufo yanda suke.... Kuyangin dake tsartsaye gefe suka rusuna suna gaidashi... Fu’ad ya k’araso k’asaitaccen murmushi saman fuskarsa, Zahra ce ta soma hangosa ta fad’ad’a murmushinta tana fad’in “ Buenos dias Uncle Best, join us for breakfast...” Dafa kanta Fu’ad yai yana mai furta “Princesa de la mañana..” (Morning Princess) Yai maganan murmushi saman fuskarsa.. Daga ita har Mahmood murmushi sukai Mahmood na furta “Da alama k’aramin k’anina ya kusa komawa spain....” Suka kuma murmusawa gaba d’ayansu kana Fu’ad ya zauna saman kujera guda yana mai gaida Yayansa Mahmood... Nan da nan d’aya daga cikin Kuyangin dake tsaye gefe guda ta k’araso tana serving Fu’ad.... *** Jerawa sukai itada Umaima suna tafe Umaima na bata gajerun tarihin cikin Masarautar, Muhibbah kaw sai kuma tambayarta take dik yanda suka shige, sosai ta ware idanu tana k’arewa Masarautar kallo tamkar bata tab’a kasancewa cikinta ba... Sashen Gimbiya Zeenat sukazo wucewa Umaima tace “Wannan shine sashen Gimbiya Zeenat amaryar Marigayi Maimartaba, bata jimada shigowa gidan nan ba Allah yaiwa Maimartaba rasuwa, da fari akasarin jama’an dake gidan sun zargeta da alhakin mutuwar Maimartaba tinda zuwanta bada jimawa ba ya rasu, toh amma dashike Giwa mutuniyar arziki ce itace tayi tsayin daka wajen ganin an daina jifan Gimbiya Zeenat da alhakin mutuwar Maimartaba, Giwa ita ta wanke Gimbiya Zeenat daga dik wani zargin da ake mata....Giwa wata irin mace ce mai son mulki lokaci guda kuma mai tsananin sauk’in kai ga Al’umman ta wannan yasa ta saye zukatan d’inbin jama’a dake Masarautar nan, ta d’auki Gimbiya Zeenat tamkar k’aramar k’anwa, bazaki tab’a cewa su d’in kishiyoyi bane, yanzu haka maganar da nake miki ana shirin had’a auren k’anwarta Rahima tareda Ya Mahmood, yanda zaki fahimci Giwa ‘yar uwa ta d’auki Gimbiya Zeenat..” Tak’aitaccen murmushi saman fuskar Muhibbah tana mai kuma k’arewa sashen kallo idan bata mance ba wannan sashen ne jiya taga wata mace ta shige cikin dare, Ta d’an kaikaito tana duban Umaima kana tace “Ita matar da za’a aurawa Yarima Mahmood d’in a nan cikin Masarautar nan take...?” Umaima ta jinjina kai fuska d’aukeda murmushi kana tace “Takan zo Masarautar nan wajen ‘yar uwarta ta jima sosai wasu lokutan, zan iya cewa akasarin rayuwarta ma ya dawo Masarautar nan ne...” Jinjina kai Muhibbah tai a hankali tana mai linke bayanan cikin k’wak’walwanta.... Umaima tace “Muje mu fara zuwa mu gaisa da Giwa kafin na dawo dake sashen Aunty Zeenat...” Jinjina mata kai tai a hankali kana suka nufi sashen Giwa.... Zahra Ta mik’e tana mai goge bakinta da tissue paper take fad’in “Paa, I’ll be going now nasan su Noor da Sultan na jirana... Uncle best idan na dawo zaka fitar dani kilisa as you promised...” Ta k’arashe tana duban Fu’ad baki a ture... Abincinsa yake ci yana jinjina mata kai lokaci guda yake furta “But first we need to ask for your Paa’s permission... Idan ya amince sai mu fita amma saidai a d’auraki saman rak’umi...” Gaba d’aya suka murmusa cikeda jin kana Zahra tai masu sallama ta wuce mahaifinta na saka mata albarka... Gudu gudu Zahra ta fito dan tuni lokacin tafiya makarantar ta ya gauta... Saurin da take yazo da tsautsayi takalminta ya karkaci tai loosing balance tim kakeji ta fad’i k’asa cikin wasu duwatsu da aka k’awata wajen dasu... K’ara ta saki tana kame goshinta da k’afarta dake mata zafi.... Faruwan hakan yai daidai da shigowarsu Umaima da Muhibbah... A tare suka ambaci sunanta had’ida nufowa gareta... Yayinda kuyanga guda Ta nufi sanar dasu Yarima Mahmood cikin sauri... Umaima na kiran sunanta tainai mata sannu saidai tuni Muhibbah ta d’agota ta azata saman cinyarta, tai saurin zame hijabin makarantar Zahra had’ida toshe goshinta yanda jini ke zuba ta umarci Umaima ta danne wajenda jinin ke zuba...Daidai kokacindasu Mahmood da Fu’ad suka k’araso cikin sassarfa Mahmood na ambato sunan Zahran.... Fad’i yake “Zahra, sweetheart..What happened to you Darling...!” Muryarsa data sinkayo daf da ita ya haifar mata da fad’uwan gaba mai tsanani, abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata.... Take taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, kasa d’agowa tai ta dubesa sabida tsananin zogi da zuciyarta Ke mata saima k’ok’arin d’aure k’afar Zahra take da d’ankwalinta da tuni ta zamesa tana baiwa yarinyar agaji na gaggawa... Jin muryar mahaifinta ya sanyata saurin d’agowa tana ambato sunansa cikin kuka “Paa..It hurts... My leg hurts Paa..!” Tuni Muhibbah ta janye jikinta daga wajen yayinda Umaima ke sanar dashi fad’uwa tai, tuni ya d’auketa cak ya nufi ciki da ita yana sanar da Fu’ad ya kirawo family Dr d’insu yanzun nan... Jikinta sai rawa yake zuciyarta naci gaba da bugawa ta koma sashen da akai mata masauk’i, ganin Mahmood da Fu’ad da tai kusa da ita ya jefata cikin tsananin tashin hankali, anya zata iya k’arasa abinda ta fara...? Tai saurin rintse idanunta had’ida zama bisa sofa, shigowarta da kad’an kuwa ta sinkayo ringing d’in wayarta cikin sauri ta isa domin d’aga kiran dan tasan mai kiran nata bazai wuce Ansar ba.... *** Prescribing magani likitan yai bayan ya gama dubata, Yarima Mahmood yace “Dr kana ganin basai anyi hoton k’afarba...?” Likitan ya d’an girgiza kai kad’an kana yace “Babu abinda ya sameta, da zaran tayi amfani da wannan magungunan dana rubuta shikenan, babu wani fracture, and it’s a good thing ta samu taimako na gaggawa... Wanda dik ya d’aure mata k’afar yayi k’ok’ari wajen bata agaji irin wanda ake so...” Sai yanzu abin ke zuwa kansa, ya d’an dubi Umaima dake zaune gefen Zahra tanai mata sannu kana ya maidoda dubansa ga likitan yana mai furta “I’ll walk you out Doc..” Dr ya jinjina kai yana mai furta “Godiya nake your highness..” Ya k’arashe yana mai sallamawa Zahra had’ida fatan samun sauk’i... A iyaka tinanin Mahmood Umaima batada wani ilimin abinda ya shafi asibiti, toh ya akai har ta baiwa Zahra irin taimakon da ake so cikin gaggawa.... Da wannan tunanin ya shigo d’akin bayan yayi rakiyawa Dr... A daidai bakin k’ofa ya tsaya yana jin tattaunawar Zahra da Umaima... Zahra taci gaba da fad’in “I feel bad Aunty Umaima, I treated her badly... Gashi ita ta taimaka min... Kinada gaskiya she’s a nice person... Please tell me Aunty Umaima, am I really a bad person...?” Ta k’arashe kaman zatai kuka... Hannunta guda Umaima ta kamo murmushi saman fuskarta kana tace “You’re not a bad person Zahra, and I’m sure Muhibbah ma bata d’aukeki haka ba... Ita da kanta ta fad’a watarana zakuyi shiri, and naji dad’i da tun ba’aje ko ina ba kin fahimci hakan... D’an Adam ko wane iri ne babu kyau wulak’antasa kinji sweetheart...” Jinjina mata kai tai kana tace “Yeah I know Aunty Umaima, my Paa taught me to always be nice toward others... Please kice wa Muhibbah na gode...!” “Muhibbah...!” Suka sinkayo muryar Mahaifin Zahra... A tare suka juyo suna duban k’ofa kana Umaima ta d’an risina, murmushi saman fuskarta take fad’in “Eh Yaya, Muhibbah itace wacce Ta baiwa Zahra agaji na gaggawa, ita d’in karatun zama malamar jinya take....” Shiru yai tamkar mai nazari yana sauraren Umaima kana yace “Wacece MUHIBBAH...?” *** “Jakadiya na kasa aminta Mahmood zai b’oye min babban al’amari irin wannan... Da ace wani na umarta ya gudanar min da aikin tabbas da zan amince aikin bai yuwu bane... Tabbas da zan amince Aliya bataci saiwar nan ba... Amma da hannuna na bata ta kuma ci dan bana fatan had’a iri da dangin bayi wanda basu gaji komai ba face bauta... Na kuma tabbata nayi aikin yanda Tal’udu ya umarta.... Toh ya akai bayan tafiyar Mahmood da Aliya k’asar Spaniya zasu dawo da d’iya... Kuma tabbas Tal’udu ya tabbatar min cewa yarinyar jinin AbdulJabbar ce...Shin ya akai aka haifeta bayan na tabbata da kaina Aliya bazata tab’a haihuwa da d’ahna Mahmood ba... Jakadiya wannan dalili yasa sam banajin k’aunan yarinyar cikin raina... Akwai wani rufeffen sirri gameda al’amarin yarinyar....Idan har ba Aliya bace ta haifeta toh hakan na nufin Mahmood ya haifeta da wata mace kenan...? Shin wannan dalili yasa yake gudun mulki...?” Ta k’arashe tana duban Jakadiya daga nan yanda take tsaye hannayenta hard’e ta baya... Jakadiya dake risine gabanta k’asa, girgiza kai tai a hankali kana tace “Allah shi taimakeki kina ganin Yarima mai jiran gado zai aikata babban laifi irin wannan...? Bana tunanin zai aikata babban abun kunyaga Masarautar nan irin haka... Idan har akace yarinyar nan ‘yar gaba da Fatiha ce toh fah kinsan wannan bak’in fenti sai ya shafi ahalin Marigayi Mai Martaba gaba d’aya... Wannan dalili ka iya janyowa Sarauta ta fice cikin gidan nan Allah shi baki yawan rai....!” A matuk’ar harzuk’e Giwa ta waigo tana watsawa Jakadiya firgitaccen kallo “K’arya ne... Wannan k’Arya ne Jakadiya... Shiyasa sam bazan tab’a bari magana mai kama da haka ya bayyana a Masarautar nan ba... Na gommaci ace wannan yarinyar jinin ‘yantacciyar baiwa ce akan ace sakamakon abin kunya ce... Bazan tab’a bari sunan zuri’ata ya b’aci ba Jakadiya....!!” Jakadiya ta shiga jinjina kai cikin sauri tana mai furta “Wannan haka yake Allah shi taimakeki... Allah huci zuciyar Giwar Amale... Allah shi baki yawan rai shugabata.. Ki jima kinayi zuri’arki su jima sunayi... Mulkin k’asar nan taki ce ya Shugabata...!!!” Ta k’arashe tana d’aga babbar yatsawa Giwa daga nan yanda take duk’e alamun jinjina... Giwa ta kuma sakin huci tana mai ci gaba da zagaya d’akin take ci gaba da fad’in “Na zab’i maganan ta zauna a haka, hardai bayyanarsa na nufin tarwatsa kan ahalina ne da mulki na...!” Jakadiya ta kuma jinjina kai tana mai furta “Allah shi baki yawan rai har abada wannan magana bazai fito ba...!” Giwa tai K’uri ma waje guda tana tinanin tabbas Yazeed ka iya sanin wani abu gameda al’amarin amma for now ta zab’i ya zauna a haka, akwai lokacinda ya dace maganar ta bayyana idan ma haka d’in ne... Ta k’arashe tinanin nata tana mai ci gaba da zagaye tapkeken d’akin nata... ** “Yaya Muhibbah K’awatce, karatu take a nan asibitin koyarwa, batada wajen sauk’a shine nai mata masauk’i a Masarautar nan...” Jinjina kai yai a hankali yana mai kuma takowa kad’an kana yai gyaran murya yace “Yayi kyau... Ina take yanzu...?”Ya k’arashe yana mai zama gefen Zahra Umaima ta d’anyi gyaran murya kana tace “Tana cen b’angaren bak’i dake bayan sashen Maami..” Jinjina kai ya kuma yi kana yace a tak’aice “Ina son ganinta...” Umaima murmushi fal fuskarta tace “Alright Yaya zanje na sanar da ita...” Jinjina mata kai kurum yai ba tareda ya amsata ba kana ta fice tana mai fatan samun lafiyawa Zahra... Murmushi kad’an Zahra tai kana tace “Tanada kirki sosai Paa...” Ya murmusa kad’an yana mai shafa sumarta lokaci guda yake furta “Akwai yanda Ke maki ciwo...?” Ta girgiza kai alamun a’a... Sai kuma taci gaba da fad’in “Please stay here with me Paa...” Dafa kanta ya kumayi kana yace “I’m here baby, I’m not going anywhere.. Okay...” Jinjina masa kai Ta kuma yi murmushi bai bar saman kyakkyawan fuskarta ba... Ya sumbaci goshinta a hankali yana mai furta “I love you...” Cikeda k’aunar mahaifin nata take furta “I love you too Papa...” Taita tina lokaci da dama da suke k’asar Spain... Saidai dikda jarumtarsa da k’warewa wajen b’oye dik wani abindake damunsa, zata iya karanto damuwa cikin idanunsa... Tin bayan rasuwar mahaifiyarta ya canza sosai amma wannan karon zata iya cewa akwai wani babban abin kuma dake damunsa, zatai iyaka k’ok’arinta wajen gano ko mai ke damun mahaifinta sannan dikda k’arancin shekarunta zatai k’ok’arin kawar masa da damuwar tinda baida wacce ta fita bayan mahaifiyarsa a halin yanzu.. Babu Maama d’inta dan haka bazataso taga mahaifinta cikin damuwa da tashin hankali ba... Suna nan a haka Rahima ta shigo cikeda d’imauta tana tambayar mai ya sami Zahra... Zahra kaw tamkar wacce akai mata albishir da ajalinta, Rahima na shigowa ta kauda kanta gefe had’ida rausayar da idanunta tana fad’in kalamai cikin harshen spanish a hankali... *** Ida wayarta da Ansar bada jimawa ba Umaima ta turo k’ofa ta shigo... Lokaci guda ta rungume Muhibbah tana fad’in “Kin cancanci yabo da godiya Hibbah, harta likitan da ya duba Zahra ya fad’i hakan... Zahra taji dad’I sosai da agajin gaggawa da kika bata... Ba don Ke ba ciwonta could’ve been worse... Thank you Hibbah...” Gajeren murmushi Muhibbah tai kana tace “You don’t need to thank me Umaima, I only did what’s right... After all, haka aikin mu ya gada... And haka ya kamata dik d’an Adama ya kasance, ka taimaka a lokacinda kakeda halin yin hakan... Besides this is nothing compared to taimakon da kuka min, kuka bani wajen zama kukai welcoming d’ina cikin masarautarku...I’ll be forever be grateful..” Murmusawa Umaima ta kumayi kana tace “Aff Kinga kafin na manta Ya Mahmood yace yana son ganinki...” Ambato sunansa da tai ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba, lokaci guda tai k’ok’arin dakewa had’ida zaro idanu waje kad’an kana tace “Allah yasa ba wani laifi naiwa Yarima ba....!” Umaima ta d’an dungureta kad’an kana tace “Kinjiki da wani batu kuma... Kinga idan babu abinda kike tashi muje, nasan by now Giwa ma ta sauk’o k’Asa....” Muhibbah ta mik’e tana mai gyara zaman alkyabban dake jikinta kana tace “Amma kafin nan sai mun k’arasa kin ida zagawa dani dik yanda ya kamata...” Umaima ta zaro idanu waje kana tace “Aw sai mu k’yale Yaya na jira... Babban Yarima guda...?!” Rausayar da idanu Muhibbah tai a hankali kana tace “Yarima shike son ganina bani Ke son ganinsa ba, a duk lokacinda yamin zan amsa kiransa... Dan haka nace sai mun k’arasa zagaye Fada, saidai kuma idan Yarima zai min mulkin kama karya ne... Dan na tabbata ko wani d’an adam yanada right d’insa koda kuwa k’ask’antaccen bawa ne...” Girgiza kai kurum Umaima tai tana murmusawa kana tace “Kuma kinada gaskiya ta wani b’angaren... Amma nan goyi bayanki ba wannan karon sai don hakan kika zab’a....” Suka murmusa a tare Muhibbah na fad’in “Naji na amince... Tinda jikin Zahra da sauk’I abinda ake so kenan... Komai zai biyo bayan wannan...!” “Zancenki haka ne ..” Umaima tace sanda suke fita.... SameenaAleeyou📚 [5/31, 11:08 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *010* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Da mamaki Umaima Ke duban Muhibbah “Ke kaw mai zaki gani a sashen bayi...?” Murmusawa kad’an Muhibbah tai kana tace “Ranki shi dad’e bayi na taka muhimmiyar rawa a kowace masarauta, sannan dik Masarautar da babu b’angaren bayi bai kai a ambacesa da sunan masarauta ba... Bayi suke gina masarauta, sune k’ashin bayan ko wani masarauta sannan ko wacce masarauta na alfahari da tulin bayin da take dashi, idan babu bayi babu masarauta... Bayi sune cikar Fada....” K’uri Umaima tai mata har takai aya kana ta jinjina kai a hankali “Kedai ko da yaushe baki rabo da hujja mai k’wari.. Tinda kince haka muje na kaiki....” Muhibbah ta jinjina mata kai murmushi saman fuskarta... Suna tafe sukazo shige Bargan dawakan Sarki.... Su duka biyun yanayinsu ya sauya sanda suka doso wannan waje... Umaima taja Ta tsaya tana duban wani spot a nan cikin Bargan dawakan Maimartaba yayinda Muhibbah tai saurin d’auke idanunta tana mai k’ok’arin saita kanta sabida wasu irin hawaye masu d’umi da suka ciko idanunta lokaci guda.... Saida ta tabbata ta saita kanta kana ta d’an dubi Umaima da har lokacin duban wannan b’angaren take “Wannan fah... Ina ne nan...? Ga dawakai masu kyau da d’aukan idanu gwanin ban sha’awa...!” Hannu Umaima ta saka tana goge hawayen da suka gangaro mata cikin sauri dan bataso Muhibbah ta fahimci wani abu, lokaci guda take furta “Nan Bargan Maimartaba kenan, yanda ake aje dawakansa...” Tai maganar a tak’aice... Dafata kad’an Muhibbah tai kana tace “Are you alright..? Akwai wani abu ne... Ki sanar dani dan Allah...” Ta k’arashe cikeda kulawa... Umaima ta k’ak’aro murmushi kana tace “Babu komai Hibbah mu k’arasa...” Hannunta Muhibbah ta rik’o had’ida girgiza kai har lokacin damuwa ne k’arara saman fuskarta kana tace “No Umaima, ban yarda babu komai ba, tinda mukazo wajen nan yanayinki ya canza, dan Allah ki sanar dani idan akwai wani abu ne... Hardai kin amince ‘yaruwa kika d’aukeni...!” Ta k’arashe cikin tsananin kulawa dan san jin taji ko menene... K’ak’aro murmushi Umaima tai kana tace “Wannan waje yana tina min shi... Yana tuna min irin zallan soyayyar da na nuna masa dikda cewa yasha jadadda min bai tab’a sona ba... Zuciyarsa mallakin wata yarinya ce k’arama wacce suka rabu ba tareda su duka biyu sunsan ma’anan soyayya ba a wancan lokacin... Ta tafi da zuciyarsa ta bar gangan jikinsa cikin Masarautar nan... Yasha jaddada min kar nayi gangancin fad’awa soyayyarsa dan bazan samu ba... Dikda sanin cewa shi d’in bawa ne hakan bai hana zuciyata afka ma soyayarsa ba domin kaw ita soyayya batasan bawa ba bata San Y’antacce ba, faruwa take a wani lokaci da sam baka shiryawa aukuwarta ba...!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Muhibbah da k’irjinta Ke ci gaba da tsananin bugu, dafa Umaima tai kad’an kana tace “Kiyi hak’uri ba nufi na bane na sakaki kuka....!” Umaima ta girgiza kai kad’an tana mai sakin murmushi “Babu komai Hibbah, Ja’afar ya riga ya zama tarihi a gareni domin kaw yau shekara guda kenan da barinsa Masarautar nan... An wayi gari aka nemesa aka rasa dan yasha jadadda min dama lokuta da dama dik daren dad’ewa zai fice ya nemo SAUDATU koda kuwa hakan na nufin bijire ma iyayen gidansa ne... “ Numfashinta ne ya sark’e lokaci guda... Take taji jiri na neman Kaita k’asa, duniyar taci gaba da juya mata... D’an uwa ta d’auki Ja’afar bata tab’a zaton shak’uwarsu yakai munzanin soyayya mai k’arfi haka ba... Maiyasa Ja’afar zai tafi ya bar Masarautar nan a lokacinda ta dawo kuma lokacin da tafi buk’atar kasancewarsa cikin Masarautar... Shin kodai yanada masaniyar abinda azzaluman cikin Masarautar nan sukai masu ne itada iyayenta...? Idan har kuwa yanada masaniya tabbas zai iya sanin mai akai da mahaifinta da har yau bata san wane hali yake ciki ba... Shin kashesa akai..? Ko kuwa dai Yana nan cikin wannan masarauta... Tabbas Ja’afar zata iya samun wasu amsoshi daga wajen Ja’afar idan har yanada masaniyar abinda akai masu... Toh amma Ina Jafar...? Ta ina zata soma nemansa bayan babu shi cikin Masarautar... D’an dungurinta da Umaima tai ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi... Ta saki murmushi a hankali kana tace “Kinga kallon dawakan nan ya d’auke hankali na...” Umaima ta murmusa kana tace “Ai naga alama... Mu k’arasa ko...” Muhibbah ta jinjina mata kai kana suka nufi b’angaren bayi... Suna tafe Umaima naci gaba da mata bayani... Sun kusan nufa gate d’in bayin kenan Umaima ta hango Rahima sai buga sauri take ta nufi wani b’angare nan cikin sashen bayin yanda tai parking motarta daren jiya... Mamaki ya d’an kamata ita kaw mai ya kawo motarta k’ofan bayi....? Muhibbah ta sauk’e idanunta a yanda Umaima ke duba... Lokaci guda take furta “Wacece wancan... Batai kama da bayi ba, mai ya kawota b’angarensu...?” Umaima ta d’an girgiza kai kana tace “Rahima ce k’anwar Aunty Zeenat..” Muhibbah tace “Matar da Yarima Mahmood zai aura...?” Umaima ta jinjina mata kai alamun eh kana taci gaba da fad’in “Toh amma mai ya kawo motarta nan...? Kinga mu k’arasa wajenta sai nai introducing naku...” Babu musu Muhibbah tabi Umaima suka nufi Rahima dake k’ok’arin shigewa mota, sai waige waige take tamkar maras gaskiya.... “Rahima..!” Muryar Umaima ya daki dodon kunnuwanta, abinka da maras gaskiya sai ta firgita, ta juyo cikin sauri tana dubansu... Lokaci guda kuma ta d’an saki murmushi kana tace “Haba Umcy wllhi kin razanani....” Tai maganar tana d’an dungurin Umaima da car keys d’inta... Umaima ta murmusa kad’an saidai kafin Takaiga bata amsa suka sinkayo muryar Muhibbah tana fad’in “Yo miye abin tsoro Keda kike kusa da Dakurun sarki idan ma hari aka kawo Masarautar...?” Tai maganar cikin sigar wasa tamkar itada Rahimar sunsan juna.... I zuwa wannan lokaci Umaima kam Ta soma Sabo da halin Muhibbah, ita kaw Rahima da tsananin mamaki take duban budurwar da tai maganan wacce sam kallo guda tai mata taji ko kad’an bata kwanta mata ba.... Murmushin yak’e ta saki kana tace “Toh wa ya sani ko harin ta cikin k’asa aka kawo wanda Dakaru bazasu ankara ba...!” Tai maganar tana juya idanu... Daga Muhibbah har Umaima murmusawa sukai kana Umaima tace “Rahima ga k’awata Muhibbah ku gaisa.. Muhibbah wannan itace Rahima ko nace our big Aunty, matar Yaya Yarima Babba...” Wannan kirari da Umaima tai mata ya sanyata sakin murmushi tana kuma jijjiga had’ida gyara tsayuwarta tana jin tabbas ta isa.... Muhibbah ta murmusa kad’an tana yaba kyaun halitta da Allah yayiwa Rahima, tabbas tayi kama da matan masu mulki.... Wayar Rahima ne yai ringing, ta d’an d’aga yatsarta guda alamun excuse kana ta matsa gefe ta d’auki wayar ganin ba kowa Ke kiranta ba face aminiyarta Zuhra.. Aiko tana d’agawa ta sinkayo muryar Zuhra cikin kuka... Gaban Rahima ya yanke ya fad’i, lokaci guda take furta “Zuzu meke faruwa... Please talk to me... Yazeed ya miki wani abu ne....?!” Cikin muryar kuka Zuhra Ke fad’in “Rahima na gaji, na gaji da wulak’ancin Yazeed, dan Allah kizo I really need you...!” Ta k’rashe cikin shesshek’an kuka... Fuzar da fuci Rahima tai a hankali kana tace “Alright ya isa haka Ki daina kukan nan, gani nan zuwa...!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin saita kanta yayinda kacaukam hankalin Muhibbah ke gareta tinda ta soma wayar, gaba d’aya hankalinta baiga Umaima daketa faman karanto mata bayani yawa malamar makaranta gaban d’alibai... Rahima ce ta K’araso yanda suke tsaye kana tace bara taje sashen Zuhra, gaba d’aya yanayinta ya sauya ko takan motar ma batabiba ta shige cikin sauri... Muhibbah tabi bayanta da kallo har ta b’ace mata kana ta maido da hankalintaga Umaima, ta riga da ta samu information d’in da take buk’atan sani gameda Ja’afar dan dama hakan ne yasa tace suzo sashen bayi...ta d’an langab’e kai tana fad’in “Gaskiya mu juya haka nan your highness, na gaji sai wani lokaci kuma....” Umaima ta murmusa kana tace “Da wuri haka...Dik San sanin Masarautar naki....?” Murmusawa itama Muhibbar tai kana tace “Fada da fad’i take your highness bazan iya zagayawa ba...!” Umaima ta kuma murmusawa kana tace “Toh mu k’ara gaba kad’an na nuna miki Rumbur sarki....” Muhibbah ta jinjina kai tana mai murmusawa kana tace “Idan kince haka...” ** Sauri sauri Rahima ta nufi b’angaren Zuhra tamkar zata tashi sama, dik kuyangin da zata gifta sai sun risina Sun gaidata, alla alla take ta isa taji wata uwar yau kuma d’an maras mutuncin nan yaiwa k’awarta... Aiko tana isowa ta hangesa tsaye k’ofar sashen cikin shiga irinta alfarma, yai tsayuwa irinta wanda keji da tsananin mulki da izza hasken rana ya haske kyakkyawar fuskarsa, kaman kullum babu alamun rahama ko fari’a a fuskar tasa... Ta sauk’e fuci a hankali tana girgiza kai kana taci gaba da dosowa sashen.... Tana hango dogaransa suna jinjina kai suna darewa a wajen alamun sallamansu yai, ta K’araso had’ida risinawa alamun gaisuwa... Har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya ya k’urama waje guda idanu... A zahiri zakai zaton gaisar dashi Rahima keyi... Bai amsa gaisuwar nata ba sai cewa da yai “What brought you here...?” Yai maganar idanunsa na duban wani b’angaren... Ta d’an saci dubansa kada’an kana tace “Prince what happened to Zuzu, is she well...?” Tai tambayar cikeda damuwa Shu’umin murmushin nasa ya saki a hankali kana ya d’an kaikaito yana k’are mata kallo daga sama zuwa k’asa.... “Maiyasa bazaki shiga ba and find out yourself... After all, abinda ya kawoki kenan... !” Tana gani yai alamawa Hauni cewa ya k’araso, lokaci guda tasa kai ta shige tasan koda taci gaba da tsayuwa wajen ba samun amsa zatai ba.... Tana fad’awa cikin gidan ta haye d’akin Zuhra... Kwance ta taddata saman gado sai kuka take hannunta dunk’ule da wani abu... Rahima na shiga Zuhra ta taso a guje ta rungumeta tana kuka sosai mai ban tausayi... Jikin Rahima a matuk’ar sanyaye ta rik’e Zuhra suka zauna saman sofa, lokaci guda take furta “Zuzu Kukan nan ya isa haka... Mai kuma ya faru....?” D’aga mata wuyarta tai taga alamun shati yayi jajazir, bata iya magana ba sai wani kukan da ta kuma fashewa dashi... Rahima ta zaro idanu waje... “Zuzu kina nufin kice min Yazeed ne yai maki wannan tabon..? Zuzu mai ya faru....?” Zuhra tai k’arfin halin share hawayen dake idanunta kana ta soma fad’in “Yazeed baida imani Rahima...Yazeed mugu ne, azzalumi ne.... Yazeed ya maidani tamkar shara cikin gidan nan, wllhi ko kuyanga ta fini ‘yanci cikin gidan nan... A duk lokacin da yaga dama zai d’ebo dik wani wulak’ancinsa ya zuba akaina... Rahima mai nai masa da tsanani...? Laifi ne don Allah ya jarabceni da soyayyarsa... Rahima na baro masarautarmu da Gata na da komai na, na zabi na zauna dashi... Amma kiga irin wulak’anci da cin kashin da yake min wanda ko kuyanga bazata d’auka ba... Daren jiya bai dawo gidan nan ba sai tsakiyar dare kuma na tabbata bai samu yanda yake so bane wajen ‘yanmatan nasa shiyasa ya dawo gareni ya sauk’e gajiyarsa da dik wani takaicinsa akaina... na tabbata da ya sami yanda yake so bazan ganshi ba sai Washe gari...wannan wace irin rayuwa ce...?” Ta k’arashe tana mai kuma share hawayenta... Cikeda kulawa Rahima ta dafa hannayenta kana tace “Shine yai maki wannan tabon don Kinyi magana...?” Zuhra na hawaye take jinjina mata kai, lokaci guda taci gaba da fad’in “Dama zai k’ara auren da yafi min sauk’i... Ni ba fita aiki nake ba balle hakan ya d’ibe min kewa, bana zuwa ko ina, kullum ina kulle cikin gidan nan ina cazagan bak’in cikin mijina... Shin haka auren masu sarauta yake...? Ba haka na tashi naga mahaifina nayiwa iyayena ba... Maiyasa ni zan tadda haka cikin gidan aurena...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Sauk’e ajiyan zuciya Rahima tai kana tace “But kin tabbata biye biyen wasu matan yakeyi, kodai Kawai zarginsa kike...?” Dubanta Ta d’anyi had’ida yin murmushi mai ciwo “Rahima kenan... Yazeed ne fah ba wani ba, wanda idan na hanasa kaina yakance yanada dubun wanda suka fini... Wllhi badon yana matuk’ar son mulkin Masarautar nan ba, nayi imani da a cikin gidana zai dinga aikata fasik’anci da matan banza, kawai yasan yin hakan ka iya shafa martabansa ne shisa...!” Ta k’arashe wasu hawayen na kuma gangaro mata.... Rahima ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “K’awata zan baki shawari, kici gaba da hak’uri wataran komai zai wuce ya zamto tarihi... Wataran macen da ya raina, Ke d’in da ya raina sai Allah ya jarabcesa akanki... Ki kwantar da hankalinki k’awata kima daina saka ma ranki damuwarsa kiji da yaranki kawai kinji koh... Kuma koda wasa kada Ki bari wannan batu ya isa Masarautar ku don kimanki ne zai zube...” Zuhra ta jinjina kai a hankali kana tace “Na gode K’awata... Allah ya bar min Ke, zanyi dik yanda kikace in sha Allah...!” Rahima ta murmusa kana tace “Yauwa yanzu naji batu K’awata, share hawayen ki ki kuma cancad’a kwalliya, ki nuna masa kaman ma ba’ai komai ba kinji koh...” Zuhra ta jinjina mata kai kana ta mik’e ta fad’a bathroom dan wanke fuskarta.... Tana shigewa Rahima ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida kishingid’a cikin kujeran... *** Kishingid’e suke k’asar wata ‘yar bukka dake wani b’angar a haraban Masarautar, anyi ado da kwalliya ma wajen da dardumai da kuma manyan pillows na alfarma, ko wannensu sanye cikin shiga irinta alfarma, kallo guda zakai masu su birgeka... Yazeed, Jamal saiko Fu’ad, an K’awata gabansu da kayan marmari... Jamal ya dubi Fu’ad da ya b’ata shiru tamkar bashi a wajen kana yaci gaba da fad’in “You can’t go on like this Fu’ad, you need to put an end to this... idan hakan yaci gaba da faruwa Ina mai tabbatar maka zamu maidaka yanda ka fito ne....!” Yai maganar Cikin zafin rai... Sai lokacin Fu’ad ya d’ago yana dubansa kana ya soma girgiza kai yana fad’in “No, no Jamal... You know I can’t go back to that place..” Baikai aya ba Yazeed dake kishingid’e daga tsakiya irin yanda masu sarauta keyi, cikeda izza yake jefa gyad’ar kwalba a bakinsa, ya katsesa da fad’in “Of course zaka koma, dear brother... So kake ka dinga jifanmu da abin kunya kana dawowa cikin Fada high, kana amai kana hauka gaban kowa bayi da sauransu...If you can’t control yourself, wllhi kaji na rantse ni da kaina zan mayar dakai....!” Fu’ad ya waigo yana d’an dubansa kana yasa tafukan hannayensa biyu ya shafe fuskarsa, lokaci guda ya d’an murmusa kana yace “Wait..? What are you two afraid of... You don’t want Yaya to find out.. Right..?” “Shut the hell up Fu’ad...!!” Jamal ya katse sa da fad’in haka kana yaci gaba da fad’in “Idan maganan nan ya fito fili, we are not going to lose only our Family and our power...Harta gidan nan sai mun rasa, So you better shut your mouth, and stop living in the past..!” Yazeed dake ci gaba da jefa gyad’arsa a baki kaman bashi a wajen K’uri yaima waje guda yanda suke k’arasowa... Tin daga k’afafunta yake dubanta har zuwa fuskarta.... Dik maganan da Jamal keyi baima saurarensa har saida Jamal d’in ya kaikaito yana duban abinda ya d’auke hankalin Yazeed, Fu’ad dake dubansu su duka biyun waigowa shima yai yana duban abinda suke kallo..... SameenaAleeyou📚 [6/1, 7:13 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *011* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zuciyarta taci gaba da bugawa da sauri da sauri tamkar zata b’alle daga cikin k’irjinta ta fito waje... Koda bata d’ago ta dubesu ba tayi imani ita suke kallo, ji tai k’afafunta na k’ok’arin sark’ewa, Ta soma ganin hanya duru duru, ita dai kawai jefa k’afafunta take... Shin ta yaya ma bazata tsinci kanta cikin wannan yanayi ba bayan yau d’in tayi arangama da mutanen da suka zama jigo wajen tarwasta rayuwarta, ahalinta da dik wani Farin cikin data baro a baya.... Tana jin yanda Umaima Ke karanto mata cewa wancan wajen hutu da yaran sarki Ke ciki nasu ne su kad’ai babu wani wanda Ke shiga cikin ‘yar bukkan nan kaf Fada face ahalin Sarki AbdulJabbar... Umaima taci gaba da fad’in “K’warjininsu ya cika wajen...Tabbas Ubangiji ya lullub’e Sarki AbdulJabbar da rahama da ya azirtasa da zaratan yara maza masu kyau irin wad’annan wanda zasu zama magadan wannan Masarautar... Mahmood shine babba cikinsu mai kimanin shekaru 46, lokacin da Giwa ta haifesa a yanda naji tarihi ansha bikukuna da shagali a wannan Masarautar kasancewarsa babban d’ah ga Sarki AbdulJabbar... Bayan ta haifesa ta jima bata kuma haihuwa ba dan saida tai shekaru a k’alla goma kana ta haifo Yazeed, d’ah na biyu a Masarautar nan mai kimanin shekaru 36, daga shi sai Jamaluddeen d’ah na uku mai kimanin shekaru 32 sannan d’an autan Yarimomin Fu’ad mai kimanin shekaru 28... Wad’annan sune ‘Ya’yan Sarki AbdulJabbar mai rasuwa...” Ta k’arashe murmushi kwance saman fuskarta... Batasan ya akai ba saiji tai bakinta ya bud’e yana furta “Tabbas Giwa ta haifo yara, cikinsu akwai Maciji, akwai Rak’umin dawa, akwai Kunama, Sannan akwai bushiya mai lullub’e da k’aya...Saidai kashhh, bata haifo Sarkin Dawa ba...!!” Tai maganar cikin wane irin yanayi da dik wandake dubanta zai iya firgita... Da mamaki Umaima Ke dubanta kana tace “Mai kikace..?!” Muhibbah tai k’ok’arin saita kanta kana ta d’an rausayar da idanu “Aw nace wani abu ne...?! Sorry that was nothing... Wani tunanin na daban nake...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta... Umaima ta d’an murmusa kana tace “I’m used to it by now, Allah yai maki baiwa da tsara kalamai saman harshe... zakiyi kyau da zama matar Saraki....” Ta murmusa kad’an kana tace “Mai mulki sai mulki, Talaka sai talaka, Mai arziki sai mai arziki...Haka rayuwar Ta koma k’awarya tabi k’warya... Ko ba haka bane...?” Ta k’arashe da alaman tambaya.. A hankali Umaima ta jinjina kai kana tace “Tabbas ga babban misali akaina, kaman yanda kikai magana haka Jafar Ke fad’a min... Alak’armu dashi sam bazai d’ore ba, kuma hakance ta kasance...!” Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Nan kuma Ina mukazo...?” Umaima ta saita kanta “Nan shine sashen Ya Yazeed da matarsa Gimbiya Zuhra, zamu shiga ku gaisa...!” Ta jinjina mata kai sanda suke shiga gate d’in sashen.... Tangamemen sashe ne mai ji da kyau da kuma tsari... A hankali take k’arewa sashen kallo har idanunta suka sauk’a zuwa parking lots, yanda hanshak’an motoci na alfarma Ke jere cikinsu ko wacce mota d’auk take da plate number mai sunan *Prince Zeed* hankalinta yafi karkata kan wata Jeep k’irar Ford, take hotunan abubuwan da Ta gani daren jiya suka shiga dawo mata, tabbas wannan motar ta gani ya shigo cikin Masarautar a daren jiya, nan kuma tunanin Rahima yazo zuciyarta... Kai tsaye bazatace itace ta gani ta shige sashen da Umaima ta ambata da sunan na Aunty Zeenat ba, toh amma mai yakai motarta k’ofar Bayi..? Sannan Maiyasa Ta razana sanda ta gansu...? Could it be Yazeed da Rahima ne jiya suka dawo Masarautar cikin dare..? Idan kuwa har haka d’in ne da gaske zatafi kowa Farin ciki... ! Ta saki murmushi mai cikeda ma’anoni tana ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarta, zatai k’ok’ari Ta gano bakin zaran komai cikin gaggawa... Allah sa hasashenta ya tabbata haka d’in domin kaw wannan ba k’aramin gudumawa zai baiwa mission d’inta ba... A haka suka nufi cikin gidan ** A b’angarensu Yazeed kaw K’uri sukai masu har saida yaga yanda suka shige Wato sashensa, saida ya tabbata sashensa yaga sun shige kana ya jefa gyad’a k’wara d’aya a bakinsa had’ida furta “Bingo..!!” Yai maganar yana mai sakin shu’umin murmushin nan nasa... Jamal ya furta “Wacece ita...?” Fu’ad da ya kasa janye idanunsa ya furta “She’s... Beautiful...!” Juyowa Jamal yai yana duban Yazeed dake ci gaba da jefa gyad’arsa a baki yanai masu wane irin tauna mai cikeda kasala da izza ya had’e rai kaman bashi bane ya gama murmushi yana furta Bingo... D’an girgiza kansa yai dan yasan wanene Yazeed ya kuma San mai yake nufi da ya furta Bingo.. Wato tama fad’a sashensa da kanta...Lokaci guda Jamal ya d’anyi gyaran murya kana yace “Probably ‘yar uwar Maami ce tinda gata tareda Umaima...” Fu’ad yace “But how comes bamu tab’a saninta ba...?” Jamal yace “Must you know everyone.. .” “No, naga dai tanada kyau ne... Ya kamata ace mun santa...” Ya k’arashe yan gutsiran apple da yaketa faman juyawa a hannunsa... Jamal ya d’an murmusa da gefen baki kana yace “But fuskarta ya min kaman na tab’a sanin mai irinta wani waje...” Katsesu Yazeed yai da fad’in “Cut it out you two, dik wannan yaba kyaunta da maganan da kuke none of you, babu d’aya daga cikin ku da yakeda courage d’in fad’i a gabanta... Let’s start with you vet Dr Jamal... Kai yaushe ma ka fara son mata..? Koda wasa ban tab’a jin kayi zancen mace ba, saidai ka k’are da duba lafiyar dabbobi...And you Fu’ad...” Yai murmushi mai cikeda k’asaita kana yace “Babu macen gaske wacce ta amsa sunanta mace da zata kula mahaukaci irinka dikda kuwa sanin cewa kai d’in jinin sarauta ne, kai inaga saidai a k’are a cikin kuyangin gidan nan a aura maka guda d’aya... Tarihi ya maimaita kansa kaman yanda Yayanka ya auri ‘Yantacciyar baiwa....So ku dena b’ata lokacinku ku already...!” Murmushi da gefen baki Jamal keyi kana yace “Well, kar kayi gaggawa dear brother... Duk duniyar nan mutum d’aya ne tak yasan Ko ni wane irin mutum ne... But idan haka ka d’auka then be it...After all, banida lokacin mata kaman yanda kace...!” Ya k’arashe murmushin saman fuskarsa.... Fu’ad da kalaman Yazeed sukai matuk’ar masa zafi, jinjina kai yai kana yace “Kana tinanin kai kad’aine Yariman da mata Ke rububi Prince Yazeed, well let me remind idan ka mance...Babu abu guda da kake tak’ama dashi wanda ni Fu’ad banida shi a fuskar halitta... Kwalin karatu da kake tak’ama dashi zan iya komawa makaranta a yanzu don bai k’ure min ba, I’m still young.. I can still make it...!” Ya k’arashe yana sakin fuci a hankali... Gira d’aya a sama Yazeed ke dubansa kana ya murmusa da gefen baki yana mai jefa gyad’arsa a baki lokaci guda yaci gaba da furta “Well, yanda muka banbanta ni bani bane zanbi matan su suke bina su suke kawo kansu gareni... Just like yarinyar da yanzu kuka gama sunbatu akanta, kuna gani dai akan idanunku ta shige b’angarena.. Kuma kaman yanda ta shige haka sauran matan suka kawo kansu... Yarima Yazeed baiga macen da takai shi ya nemeta ba saidai Ta kawo kanta har yanda yake...!” Ya k’arashe yana karkad’a k’afa daga kishingid’e cikeda izza... Fu’ad ya kuma fuzar da fuci a hankali yana k’ok’arin mik’ewa Daga wajen Yazeed ya katsesa da fad’in “But still, zan baka chance idan har kana sonta... I challenge you to win her heart first... Zaka iya...?!” Ya k’arashe yana mai d’aga gira guda sama had’ida tsare Fu’ad da idanu... Fu’ad yai tsaye yana dubansa tamkar bazai ce komai ba yayinda Jamal ma ya zuba masu idanu.... Yazeed yaci gaba da murmusawa yana mai furta “Jeka abinka and keep on doing drugs, that’s what suits you after all....!” Fu’ad bai iya furta komai ba sai zuciyarsa dake ci gaba da bugu, har yaushe Yazeed zai daina d’aukansa useless mutum maras amfani, har yaushe zai daina jifansa da muggan kalamai.... Yai tsaye yana sakin huci yana duban Yazeed... Jamal ya d’anyi gyaran murya kana yace “Fu’ad jeka abinka... Jeka ka soma shirin taron da za’ai anjima... Gani nan biyeda Kai...” Fu’ad ya girgiza kai alamun a’a... Kana ya mik’awa Yazeed hannu alamun masabaha yace “Challenge accepted... Prince Yazeed AbdulJabbar...!” Yazeed ya d’ago da mamaki yana duban Fu’ad, kana ya saki cruel smile d’in nan nasa... Bai mik’a masa hannun ba saima kwalbar gyad’a da ya dank’a masa kana yace “Kayi replacing drugs da wannan...!” Fu’ad da k’walla Ke neman ciko idanunsa cikin sauri ya bar wajen tamkar zai kifa k’asa... Jamal ya dubi Yazeed dake ci gaba da sakin murmushinsa kana ya girgiza kai “Yazeed ina tsoron ranan da zaka Kai Fu’ad bango ya bud’i baki ya fad’iwa Mahmood komai, dik abinda muka aikata... Dan Allah ka k’yale yaron nan haka he’s suffering already....!” Da gefen idanu Yazeed ke dubansa, saida dak’ik’ai suka shud’a kana yace “And what makes you think ina shakkan Mahmood yasan wani abu gameda rayuwata... I got nothing to be ashamed of... Idan da akwai wanda zaiji kunyar bayyanar abinda ya aikata a baya that person should be Mahmood.... Sabida ni dik barikancina ban yarda na bar tabo wa Zuri’ata ba...Cikin yarana guda biyu babu shege....!”Ya fad’i cikeda isa.... Jamal ya dubesa da mamaki kana yace “Ban fahimceka ba... Maiyasa kace haka...?” Yazeed ya kuma murmusawa kana yace “Kune Mahmood ke cika maku ido da salonsa na yaudara, amma bani ba... Babu wanda ya tab’a shafawa Masarautar nan irin abin kunyar da ya shafa mana...!” Jamal ya kuma girgiza kai kana yace “Yazeed Wai mai kake cewa ne...? Mai kake nufi... Please explain it to me...!” Duban Jamal yai yana mai gyara kishingid’arsa kana yace “Ask him about his daughter... Da aure ya haifeta kokuwa ciki yayima d’aya daga cikin ‘yanmatansa... Ask him idan Aliya matarsa ce ta haifa masa yarinyar...!” Ya k’arashe yana girgiza had’ida tsare Jamal da idanu... K’irjin Jamal bai daina bugu ba yake girgiza kai alamun a’a... Lokaci guda yake furta “No...no Yazeed... This is not possible...!” “Of course it is..!” Yazeed ya katsesa da fad’in haka kana yaci gaba da fad’in “So tell me Jamal, among us all wankeda bak’in tabo a tattaredashi....? Wa yafi cancanta yai sarautar k’asar nan...?” Share gumin da ya tsartsafo masa Jamal yai yana mai furta “Maami Ta sani...?” Yazeed ya tab’e baki kad’an kana yace “Duk duniyar nan babu wanda ya sani, daga ni sai Abokinsa Turaki... And now that I told you everything, ina son full support d’inka wajen neman Karagar mulkin nan, idan ba haka ba kuma zan fasa kowa yaji a Masarautar nan...!” Jamal ya shiga girgiza kai yana furta “No, no Yazeed hakan na nufin downfall d’inmu ne gaba d’aya, it will affect us all, including our mother...!” Yazeed ya jefa gyad’a bakinsa yana mai d’aga kafad’a guda alamun ko a jikinsa yayinda Jamal yaci gaba da jinjina lamarin cikin zuciyarsa... Tsananin mamaki kwance saman fuskarsa... Ya kasa aminta da abinda ya gama sauraro daga d’an uwan nasa... *** Shigowan su Muhibbah da kad’an Rahima tai ficewarta dan Allah ya gani tak’i jinin wannan Muhibbar, gashi dai yau suka fara had’uwa amma sam taji bata kwanta mata ba ko kad’an... Dan haka tuni tai sallama da k’awarta tana fad’in zata shigo da dare... Zuhra da san mutane nan ta rik’esu da fira, ta kuwa ji dad’in shigowar su Umaima da Muhibbah dan ko babu komai sun d’ebe mata kewar k’uncin da mijinta ya jefata ciki, dikda k’ok’arin b’oyewa da take saida Muhibbah taso fahimtar wani abu... Ta saki jikinta sosai da Zuhra kaman sunsan juna tuntuni... Dad’ida k’ari Umaima da Zuhra suna shiri sosai, dan koda suka Zo tafiya sai cewa Zuhra tai su tsaya suyi lunch a nan zuwa yamma sai su tafi... Hakan sosai yaima Muhibbah dad’i don ko babu komai zatai k’ok’arin k’ulla Sabo tsakaninta da Zuhra dan sanin meke wakana cikin gidan Yazeed... Harta da yaran Zuhra da suka dawo daga school sun sake sosai da Muhibbah dama Umaima kam ‘yar gidansu ce.... Gaba d’aya yinin ranan a sashen Yazeed sukayita saidai sam basuji d’uriyarsa ba dashike yana cen shirye shiryen ganawarsu da king makers... Koda suka dawo sashen Giwa ma basu taddata ba, Ta fice zagayen ran gadi kaman yanda take yi ko wani yammacin Alhamis tana bin fad’in Masarautar tana duba buk’atan kowa da lafiyarsa... Wannan na d’aya daga cikin dalilin da yasa suke kuma son Giwa had’ida bata girma.... *** D’aki ne mai tsananin duhuwa suka shige, Jakadiya na tafe gaba yayinda Giwa Ke take mata baya.... Mahaukaciyar matar ce kwance cikin d’akin an d’add’aureta da k’atoton sark’a.... Ubandoma ya risina kana ya kwashi gaisuwa wajen Giwa..... Ta jinjina masa kai tana mai kuma duban matar.... Lokaci guda Giwa ta K’araso gabanta cikin taku mai cikeda izza.... Giwa ta duk’a gaban mahaukaciyar nan tana k’are mata kallo, lokaci guda ta damk’o Fuskar mahaukaciyar tana tsananin huci take furta “Mai yasa rayuwarki Keda matuk’ar mahimmanci ga cikar burina..? Tabbas nafi kowa son naga kin mutu Izzatu... Ganinki ba komai yake tuna min ba face tozarci da na fuskanta daga wajen mijina... Guntile harshenki kad’ai yayi kad’an a irin uk’ubar dana tanadar miki da zaran burina ya cika... Da zaran na tabbatar sarautar Masarautar nan ahalina sun gajeta...!” Ta k’arashe tana mai jifa da fuskr nata had’ida sakin huci akai akai.... K’uri mahaukaciyar taiwa Giwa tamkar mai tinani sai kuma ta fashe da dariya mai kamada kuka, lokaci guda ta d’aga kanta sama tamkar mai duban wani abin... Cikin muryarta da bai fita sosai sabida harshenta da aka yanke mata take fad’in “Ranan ta matso kusa... Gaskiya zatai halinta... Bayyanar Hasken ya fitar dani a jiya...Zata zamto sanadiyar warwarewar wasu al’amra...!” Ta k’arashe tana dariya irinta masu tab’in hankali... Ba lallai ka gane ma mai take Fad’i ba don harshenta rabi ne cikin bakinta.. Maganan nata yafi kama da sunbatu a zahiri, saidai ga wanda zai iya fahimta maganace mai harshen damo.... Sam Giwa bata fahimci mai take fad’i ba sai aika mata mugun kallo da take, lokaci guda ta jifa mata ledar bread kaman jira take ta capke ta shiga mamuk’an biredin.... Giwa ta waigo tana duban Jakadiya, lokaci guda tai mata alama da idanu... Jakadiya ta jinjina kai kana suka nufo k’ofa Ubandoma ya kuma gark’ameta suka fice yanda Giwa taci gaba da zagayen rangadinta tamkar babu abinda Ke faruwa... A yayinda Giwa ke zagayen rangadinta yaran nata gaba d’aya suna cen babban gwanin Maimartaba kaman yanda yake yau d’in ne zasu gudanar da zama tin bayan dawowar Mahmood k’asar a karo na farko.... Hakimai, Galadima Waziri Talba da dai sauransu duk sun hallara a babban gwanin mai marigayi mai Martaba.... Mahmood da sauran ‘yanuwansa guda Uku duk sunyi shiga irinta mulki, ga algaita daketa faman tashi a d’aukacin Masarautar... Tinda Yazeed ya shigo cikin babban gwanin ya tsaya daga nesa yana k’arewa Karagar mulkin kallo, hannayensa hard’e yake duban Karagar mulkin wanda rawani had’ida takwabi, alkyabba da kuma sandar sarakuna Ke aje bisansa, dik wanda yayi nasaran zamtowa Sarki shi zai gaji wannan rawani Alkyabban da kuma takwabin... Ya saki murmushi da gefen bakinsa Dan ba kowa yake hangowa saman Karagar ba face shi Yazeed... A hankali yake takowa har ya k’araso cikin katafaren parlorn, ya zauna a mazauninsa nan yanda aka tanadar domin zaman yaran Sarkin... Ya kaikaito kad’an yana duban Mahmood dake zaune gefensa shu’umar murmushi saman fuskarsa... SameenaAleeyou 📚 [6/2, 6:08 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *012* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin sand’a ta fice ta nufi b’angaren babban gwani, sauk’inta guda hadari ne sosai a garin wanda yasa akasarin dogarai suka nemi mafaka, can bayan wani bene ta samu ta mak’ale saidai sam kunnuwanta basa sauraron abinda ake tattaunawa cikin tangamemen d’akin sarautar, abinka da gini mai aminci wanda ya kwashe d’inbin shekaru, tabbas ba hakan taso ba amma babu yanda ta iya, tinani ta soma ta tafi ne ko ta tsaya, saidai bata ida tinaninba ruwa ya kece tamkar da bakin k’warya...Ta rintse idanunta a hankali tana kuma duban yanda ruwa Ke zubowa da k’arfin gaske, ga gida na sarauta ko wani angle magudanan zuban ruwa ne...Ta kwashi kusan mintuna a k’alla goma sha biyar kana ta hango masu sarauta na aza babban riga na ficewa d’aya bayan d’aya... Yanayin fuskokinsu ya tabbatar mata basu samu yanda suke so ba.... Can ta hango Yazeed sai Washe baki yake yana taku cikeda izza ga bafaje guda ya rik’e masa lema sai kod’asa yake... Gabanta ya yanke ya fad’i, kardai Yazeed shine zai zamto Sarki na gaba, bazataso d’aya daga cikin iyalan Sarki AbdulJabbar su kuma d’alewa Karagar mulkin ba, burinta shine su rasa sarautar, su tozarta su kuma fice daga cikin Masarautar cikin k’ask’anci.... Zuciyarta taci gaba da mata zafi, ta kasa katab’us Dan batasan Ta yanda zata b’ullowa al’amarin ba... Yanzu mai zatai next...? Tana tsaka da tinanin ta hango wani Dattijo biyedashi Mahmood ne, sun nufo Ta yanda take b’oye... Ta kuma k’ara mak’alewa jikin gini dan kar su ganta.... Mahmood ya risina yana sauraren Dattijon “Yarima ba Wai ina neman haddasa gaba bane tsakaninka da sauran ‘yanuwanka, amma sanin kanka ne Mahmood babu wanda ya cancanci d’alewa wannan karaga face kai...Burin mahaifinku kenan tin kafin ya rasu, ka zamto magajinsa.... Mahmood Ta yaya zakace kai ka janye neman mulkin Masarautar nan... Ko akwai wani abinda ban sani bane...?!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Gyara tsayuwarsa ya d’anyi kana ya soma fad’in “Baba Wambai Maiyasa kake goyon bayan nayi sarauta bayan D’anka Majidad’i yana d’aya daga cikin masu neman mulkin nan....?” Mutumin da ya ambata da Baba Wambai murmusawa yai kana yace “Muhammadu kenan... Wato a sha’ani na mulki cancanta ake dubawa ba dangantaka ba... Maiyasa zan goyi bayan Majidad’i ko Yazeedu bayan nasan cikinsu dik kafisu cancanta.... Mahamuda, idan baka amshi sarautar k’asar nan ba don ra’ayin kanka zaka amsa ko dan wasiya da mahaifinka ya bari...!” Mahmood yai shiru tamkar mai nazari yana duban wani b’angaren hannayensa hard’e Ta baya, lokaci guda ya d’an kaikaito yana duban Wambai.... “Baba kana wajen mahaifina ya rasu...? Kuma Maiyasa bai zab’eka matsayin wanda zai gajesa ba sai ni... Kai yafi cancanta ka gaji sarautar Masarautar nan sabida Kai Uba ne a garemu, sannan kai Yayan mahaifina ne kafisa a haife, tun a fari kai ya kamata kayi sarauta bashi ba, yanzu da babu shi inaga lokaci yayi da zama amshi ragamar sarautar...!” Baba Wambai ya kamo hannun Mahmood suka zauna saman wata itaciya... Saida yai gyaran murya kana ya soma fad’in “K’warai kuwa ni ne gaba da mahaifinka a haife, amma a b’angaren cancancanta ya fini, shi yayi karatu mai zurfi boko da islama ni kuwa banyi boko ba, kuma sanin kanka ne a halain da muke ciki yanzu karatu na zamani na taka muhimmiyar rawa cikin rayuwarmu gaba d’aya, k’anina ya had’a komai da ya cancanta ya rik’i Karagar Masarautar nan, yanzu kuma da babu shi kaine magajinsa... Sannan Ina wajen sanda Allah yaiwa mahaifinku kuma d’an uwana cikawa.... Mahmood idan baka amshi sarautar nan ba kana kallo sarautar zata fice daga k’ofarmu, kana gani dai Talba da ‘yanuwansa sun k’wallafi ransu kan wannan muk’ami... Kuma abinda baka sani ba shine, Ina mai tabbatar maka mahaifinka kashesa akai dik akan wannan Mulki... So kake burinsu ya cika su amshe mulki daga hannun ahalin AbdulJabbar... Na tabbata bazakaso haka ba....!” Ya k’arashe yana dafe da hannayen Mahmood idanunsa k’unshe da damuwa... Mahmood ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Wambai kana yace “Kashe mahaifina akayi akan neman mulki...? Su waye suka kashe shi...?!” Wambai ya gyara zamansa kana yaci gaba da fad’in “Mahmood akwai sirrika da dama da suke lullub’e cikin bak’in duhu a Masarautar nan... Ka jima baka Masarautar nan, akwai abubuwa da dama da suka faru...” Yarima Mahmood ya katsesa da fad’in “Shin mai ka sani gameda mutuwar mahaifina..? Shin mutuwar mahaifina nada alak’a da mutuwar matata..? Wad’annan amsoshin na dawo nema Masarautar nan amma ba mulki ba...” Baba Wambai Yai murmushin cin nasara kana yace “Alhamdulillahi yanzu ka dawo hanya... Idan har kana son samun amsoshinka sai kanada k’arfin mulki a hannunka, idan ya kasance kaine wanda Allah ya d’aura masa nauyin gudanar da al’amaran cikin Masarautar nan toh fah ina mai tabbatar maka zaka sami amsoshinka cikin sauk’i... Amma muddin kace bincike zakai a gida irinta mulki da sarauta ba tareda kanada wadataccen ilimi gameda al’amran dake aukuwa cikin gidan ba to zaka b’ata ne a hanya ko kuma a b’ataddakai, Mahmood a gida irinta sarauta an b’atar da mutane da dama wanda har yau babu d’uriyarsu....Mahamuda, Kai tinani akan abinda muka tattauna, Ina mai tabbatar maka hardai Ina d’aya daga cikin masu nad’a sarki a wannan masarauta bazan tab’a saka hannu a zab’i wani matsayin sarki ba kai ba..!” Sauk’e ajiyan zuciya Yarima Mahmood yai kana ya mik’e tsaye lokaci guda... Ya d’an kaikaito yana duban Baba Wambai kana ya jinjina kai a hankali yace “Shikenan Baba... Zanyi tunani, na gode K’warai....!” Wambai ya jinjina kai kana yace “Allah shi maka Albarka...!” Yana k’ok’arin mik’ewa abinka da jikin tsufa Mahmood yai saurin tallafa masa ya mik’ar dashi tsaye... Daga yanda Muhibbah ke lab’e ta gama sauraren tattaunawarsu tana kallon yanda Yarima Mahmood Ke rik’eda wannan Dattijo suna tafe, Mai yasa yake nunawa kaman wani shid’in mutumin arziki ne... Maiyasa yake nuna tausayi da jin k’ai cikin Al’umma bayan tasan ba haka yake ba.. Mugu ne azzalumi ne... Wanda sukai tarayya shida ‘yanuwansa wajen ruguza rayuwarta data ahalinta.... Take ta kuma jin tsanar Mahmood dana ‘yan uwansa da uwarsu kanta na kuma mamaye illahirin ruhinta, abubuwan da Ta gama ji bazaisa ta janye k’udirinta ba, tayi imani sune azzaluman cikin Masarautar ba wasu daban ba, they cannot be victims, Ta tabba sune azzaluman... Tasa baya hannu Ta goge hawayen da suka zubo mata kana ta fito cikin sand’a, lokacin a idda ruwa saiko d’an yayyafi kad’an kad’an... Tana isowa d’aki kwab’e jik’akk’en kayan jikinta tai kana Ta fad’a bathroom had’ida sakar ma kanta shower, ta rintse idanunta sanda take hango Mahmood cikin k’wayar idanunta yana taimakawa Dattijon nan yawa wani mutumin arziki... Kuma rintse idanunta tai da k’arfin gaske ganin wani b’angare na zuciyarta na neman amincewa tabbas Mahmood mutumin kirki ne... Sauri sauri ta gama wankan nata ta d’auro alwala dan already magrib ya gabato... Tana fitowa ta shirya tsaf cikin wani cotton material sea green d’inkin doguwar riga da yai matuk’ar amsar jikinta... Ida shirinta da kad’an wayar Mummy ya shigo mata ta d’aga cikeda kewan gida.... Bayan sun gaisa Mummy Ke tambayarta karatu... Jiki a sanyaye Muhibbah ta amsa mata dan gani take kaman bata kyautawa Mummy ba b’oye mata babban al’amari iri wannan da tai... Har suka ida wayar jikinta a matuk’ar sanyaye yake, bugu da k’ari tinda taji tattaunawar Mahmood da Baba Wambai ta kuma jin rauni sosai daga wani b’angare na zuciyarta wanda bata tab’a jin irin hakan ba tun sanda ta sanyawa ranta k’udirin d’aukan fansa daga wajen wad’anda suka zalunceta.... Tai lamo cikin kujera tana mai lumshe manyan idanunta a hankali... Kiraye kirayen sallan magrib da aka soma ya sanyata mik’ewa dan gudanar da nata sallan... Bayan ta ida ta d’auko alk’ur’ani tana karantawa, take ta kuma jin wani irin rauni na ratsa illahirin b’argo da tsokanta, taji wasu irin hawaye suna k’ok’arin ciko idanunta... Tabbas Alk’ur’ani maganin dik wani gyambo ko k’ulli ne dake a cikin zuciya, kuka sosai Muhibbah keyi ba tareda ta iya ci gaba da karatun ba... Wani irin rauni takeji can k’asar zuciyarta, tai lamo saman abin sallar had’ida lumshe idanunta hawaye masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata, Ta tina sanda ya tambayeta da muryarsa mai cikeda k’warjini had’ida dad’in saurare murmushi saman kyakkyawan fuskarsa _”Kina son kiga wasan dawakin ne...?”_ Ta jinjina masa kai a hankali kana yace _Ya sunanki_ _Saudatu_ Ta fad’i tana wage baki cikeda jin dad’i tana kuma gustiran apple d’in da ya bata... Ya murmusa a hankali kana yace _Zo na d’auraki saman dokin_ Ta tina sanda sauran ‘yan uwan nasa keta dariya suna nunata da yatsa... Wannan tunani da Muhibbah keyi ya sanyata saurin bud’e idanunta zuciyarta na mata tsananin zogi, a fili Ta furta “Mayaudari ne, yaudarar mutane yake da kyawawan d’abi’unsa, dashi yai amfani suka cimma burinsu kan k’aramar yarinyar da bataji ba bata gani ba... Take taji wani b’angare na zuciyarta na raya mata, karki janye k’udirinki, kar Ki d’agawa d’aya daga cikinsu k’afa.. Ruin them all, expose them and take them down.... Ta k’arashe tana mai goge ragowar hawayen da suka zubo mata, sallaman Umaima ya sanyata saurin mik’ewa had’ida saita kanta kaman babu abinda Ke wakana... “Ke Wai baki gajjiya da zaman d’aki...Kinga taso mu tafi b’angaren Giwa d’iyanin muci dinner a cen....” Umaima ta fad’i daga nan yanda take tsaye... Saida ta d’an rausayar da idanunta kana tace “Yo naga dai gidan sarauta ai zaman d’aki da kulle ya gada ko ba haka ba... Kinga dama ke nake jira muje na duba jikin Zahra, tana raina tin d’azu...” Umaima ta d’an girgiza kai kurum tana mai janyo hannunta tana fad’in “Iyanin Ki amsa kiran Ya Mahmood..!” Saida k’irjinta ya buga jin tace ta amsa kiran Mahmood, harga Allah ta mance Wai yana kiranta... Banda guntun gulma mai zai mata, yaji da abubuwan da suke gabansa, tabbas da ace yasan wacece ita da kuma k’udirin da ya kawota wannan masarauta ko mai irin sunananta bazaiso ji ba balle ya buk’aci ganinta... Wani tapkeken parlor suka soma shiga, babu kowa cikinsa sai manya manyan standing ac daketa faman aikinsu suna huro ni’imtaccen sanyi... Hotuna ne a jere a parlorn sahu sahu na ahalin Sarki AbdulJabbar mai rasuwa.... Muhibbah tai k’uriwa hoton da yake daga center... Yaran Sarkin ne su duka hud’u cikin hoton, dukansu cikin shiga irinta mulki da sarauta, k’asaitaccen murmushi irinta ‘ya’yan sarauta kwance saman fuskokinsu, idanunta suka waiga gefe kad’an nan ta hango wani hoton, su duka hud’u amma wannan suna yarane masu k’ananun shekaru wanda tsaf ta gane fuskokinsu domin kaw sanin da tai masu kenan....Tai K’uri tana duban hoton zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri....Ji take tamkar ta rarumi koma minene ta tarwatsa hoton dashi, so take ta finciko hoton daga ma’ajiyinsa ta zane fuskokinsu tai masu lamba mai muni wanda suma har abada bazai shafe daga tarihin rayuwarsu ba kaman yanda sukaima nata rayuwarta lamba...Take ta dunk’ule hannayenta duka biyu tana mai ci gaba da sakin huci a hankali.... Sam bata ko kula da Umaima da ta fice ta wani k’ofar tana amsa kira a waya ba... Waige waige ta soma sanda ta tabbata babu kowa cikin parlorn sai ita kad’ai saiko na’urorin nasara.... Nan ta hangi matakalan haurawa bene daga gefe, ta soma takawa a hankali ta nufi benen dikda tsananin bugu da k’irjinta keyi, ita kanta ta sani abinda takeyi abune mai matuk’ar had’arin gaske.... Abinka da gini irinta sarauta nan ta hangi dogon corridor da yake open, ga k’ofofi birjit iyaka ganinka.... Ta rasa ta wane k’ofar zata soma bi, lumshe idanunta tai tana ambato Allah da neman taimakonsa, Ta bud’e idanunta a hankali tana jin k’warin gwiwa na zuwa mata... Cen ta hangi wani k’ofa da yake daga center, zuciyarta tafi amintar da tabi wannan k’ofa... A hankali cikin sand’a had’ida d’an sauri ta nufi k’ofan, ta d’an tura a hankali tana lek’awa, shima d’in wani hamshak’in parlor ne maiji da tsari... Tabbas ana baza mulki a wannan gida, Ta fad’i haka cikin zuciyarta.... Cikin sand’a ta kutsa Kai cikin parlorn, saidai shigarta Keda wuya Ta soma sauraron wasu muryoyi.... Tai saurin k’arasawa yanda take sauraron maganan, tabbas muryar Giwa ce dan bazata tab’a mance wannan azzalumin murya a dodon kunnenta ba, tana iya sauraro muryan d’aya daga cikin yaranta suna tattaunawa saidai bazatace ga wanene suke maganan ba cikin yaran nata dan gaba d’aya yaran murya kala guda Ke garesu, na Mahmood ne kad’ai ta d’an banbanta dan dik ya fisu gwab’in murya mai cikeda k’warjini... Hakan ya tabbatar mata da d’aya daga Cikin k’annensa Giwa ke tattaunawa.... Bataji gaba d’aya abinda suke tattaunawa akai ba amma tabbas taji Giwa na basa umarnin aiwatar da wani abu.... Jin kaman ana k’ok’arin tab’a k’ofa ya sanyata saurin sad’ad’owa ta fito k’irjinta na tsananin bugu.... Sauri sauri ta nufo dogon open corridor d’in nan tana tafe tana waigawa baya bata ankara ba saiji tai ta bige mutum ta fad’o cikin jikinsa.... SameenaAleeyou 📚 [6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *013* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ido cikin ido suke duban juna itada Yazeed, ga tsananin bugu da k’irjinta keyi, tamkar ta tsatta ma wannan fuskar tasa miyau haka takeji... Shiko sosai ya had’e rai yanai mata wane irin duba.. K’aran tafiyar mutane da suka soma jiyowa ya sanya tsoro ya kuma bayyana a fuskar Muhibbah tai k’ok’arin sa kai zata rab’a ta gefen Yazeed saidai tuni ya fizgota sun shige tsakankanin gini hakan yai daidai da d’aukewar wutan lantarki...K’irjinta yaci gaba da bugawa, duhu ya soma shigowa dan haka kana iya ganin mutum amma duru duru, tana iya hango Farin fuskan Yazeed cikin duhun yanai mata alamu da tai shiru.... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa sanda taji tafiyar yana nufosu sosai, tai saurin rintse idanunta a hankali yayinda Yazeed yaci gaba da k’are mata kallo from head to toe dan tsaf yana iya ganinta cikin duhun nan dashike shi Allah yayisa mai idon kallon mata... Giwa ce da Jakadiya suka taho zasu shige wani k’ofar, saida suka d’an tsaya kusan yanda Yazeed da Muhibbah Ke lab’e suna tatauna wasu al’amararsu da suka shafi cikin gidan Muhibbah najin sanda suka ci gaba da tafiya suka shige wata k’ofar ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Suna shigewa Muhibbah tai saurin matsawa baya tana sakin huci a hankali, lokaci guda take k’ok’arin saka kai zata shige dan ko takan Yazeed bata kuma bi ba tamkar wani babu abinda ya faru...Yazeed da ya kafeta da mayun idanunsa yana k’are mata kallo saurin tare gabanta yai da hannunsa guda kana yace “And just where do you think you are going..? Fad’a min zakiyi mai kikazo yi nan... Wacece Ke....? mai ya kawoki wajen nan..?!” Banda bugu babu abinda k’irjinta keyi, tsananin tsanarsa ne kwance cikin idanunta, bata d’ago fuskarta ba har lokacin saima bugu da k’irjinta Ke ci gaba da yi.. Mamaki ya cika Yazeed ganin tai masa banza kaman bataji abinda yake fad’i ba.... Wacece ita...? Yai tambayar a zuciyarsa... Ga duhu da ya gauraye wajen saiko hasken walk’iya dake haskawa lokaci zuwa lokaci... A hankali yake k’ok’arin mik’a hannunsa da niyyan d’ago fuskarta... K’irjinta yaci gaba da bugawa, zuciyarta naci gaba da mata zafi.... K’iris ya rage hannunsa bai sauk’a samar fuskarta ba wayarsa dake aljihun wandonsa ya d’auki ruri... Yai saurin mik’a hannu ya ciro wayar hasken wayar ya haske fuskarsa tarau, tai saurin karkatar da fuskarta sabida tsananin k’yank’yaninsa da ya sauk’o mata dikda Uban gayun dake jikinsa.... A yayinda hankalinsa ya ya karkata kan wayar salulansa Muhibbah ta hangi fad’uwan abu mai kamada sark’a ta mata daga aljihun nasa... Tana ganin sanda ya d’aga wayar yana mai juya baya, hakan ya bata daman silalewa tai saurin d’aukar sarkar tana mai sakar masa muguwar kallo kana ta juya cikin sauri ta fice daga wajen k’irjinta sai bugu yake tamkar ana iza mata guduma.... Sauri sauri ta nufo k’asa zuciyarta bata daina tsinkewa ba, dik wani motsin da zatai sai taji tamkar yanzu ne suka bangaji juna ita da Yazeed, uwa uba hannunta da takeji tamkar ba a jikinta yake ba har yanzu... Ji take tamkar ta guntile hannun ta jefar idan ta tuna sanda ya fizgo hannun nata suka b’oye... Takai dubanta ga hannun nata, sai lokacin ta tina ashe akwai sark’a rik’e a hannun nata... Idan bata b’ata gani ba wannan design d’in jewelry d’in irinsa ta gani a kunnen Rahima yau da safe da suka had’u a k’ofar Bayi...Toh kodai nata ne..? Ya akai yazo hannun Yazeed..? Tambayar dataji na tasowa daga k’asar zuciyarta... Ta saki murmushi a hankali dan ko babu komai ta sami wani abin... Sanda ta sauk’o k’asa ta tadda kuyangi da dama wannan karon sai kai komo suke, dik wanda tazo giftawa cikin Kuyangin sai sun risina Sun gaidata, itama har ta koya daga wajensu Umaima saidai ta jinjina masu kai murmushi saman fuskarta alamun amsawa... Tana tafe cikin kantamemen parlorn mai tsawo da fad’in gaske ta hango Umaima tsaye daga waje ta cikin glass d’in sliding door.... Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali kana ta nufi k’ofar da take hango Umaima, saidai tana isa jikin k’ofar ta hango Fu’ad zaune saman wasu kujeru na shak’atawa yayi zama irinta masu mulki k’afafu d’aya bisa d’aya, da alama magana sukeda Umaimar... Fu’ad ya murmusa kad’an kana yace “Kawai tambayarki nake, a ina kika samota...?” Umaima ta murmusa kad’an itama kana tace “Prince F kenan, ai abin ne ya bani mamaki, naga friends d’ina da dama sukan Zo Masarautar nan, baka tab’a tambayar koda sunayensu ba dikda cewa su sukan damu da zancen Princes d’in Masarautar nan... Kaga kuwa bazakaga laifina ba dan na tambaya kodai kodai....?” Ta k’arashe da sigar zolaya tana kashe masa idanu... Ya murmusa a hankali kana yace “I can’t deny that she’s kind of.... Beautiful...!” Ya k’arashe yana alamu da hannayensa tamkar wani mai describing irin kyaun da ya hango tattareda ita.... Umaima tai murmushi mai d’an sauti wannan karon kana tace “Prince F kenan kaidai kawai ka nad’ani matsayin campaign director d’inka dan Muhibbah k’anwarmu ce tinda k’anwar Ansar ce...” “Muhibbah..!” Ya nanata sunan a hankali kana yace “Beloved..!” Yana maganan yana jinjina kai lokaci guda yaci gaba da fad’in “Ta dace da sunanta.....!” Sabon bugun zuciya ne ya sauk’arwa Muhibbah tai saurin jada baya tana maida numfashi a hankali had’ida lumshe idanunta, wayoyin kanta suna k’ok’arin kwancewa... Anya zata iya k’arasa abinda ta fara... Wata zuciya taceda ita “Ke Saudatu what have you gotten yourself into...?” Take kuma taji wani b’angare na zuciyar nata na fad’i mata “Toh mahaifinki fah... Ta yaya zaki San asalin abinda ya samesa idan baki dawo ba...? Sannan mahaifiyarki da kika rasa fah.... Dik uk’uba da masifa da kika shiga a baya fah...? Shikenan sunci banza suna rayuwarsu cikin jin dad’i da zaluntar wasu al’umman... Saudatu zaki iya... Zaki iya abinda kika riga kika fara... Tabbas zaki iya...!!” Da wannan shawari na zuciyarta taji natsuwa na zuwa mata a hankali... Ta waiga gefe ta hangi wata Kuyanga zata shige... K’arasawa tai gareta ta tareta tana tambayarta ko ina d’akin Zahra yake....? Kuyangar ta nuna mata wani b’angare nan cikin parlorn da shima benen za’a d’ale kana tace “Ta nan ne Rankishi dad’e...” Tai mata nuni da b’angaren benen dake kallon hagu, dashike irin babban matakalan nan ne mai kunne biyu d’aya na kallon b’angaren dama yanda ta sauk’o bada jimawa ba saman d’ayan na kallon b’angaren hagu... Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Muje ki nuna min....” Kuyangar ta d’an d’ago tana dubanta kana ta kuma sadda idanunta tana fad’in “Kiyi hak’uri Rankishi dad’e bana d’aya daga cikin amintattun dake haurawa d’akin Gimbiya Zahra’u... Amma idan kika haura d’akin nata a nan yake...” Jinjina mata kai Muhibbah tai kana tace “Kina iya tafiya..” Kuyangar ta jinjina kai alamun amsawa kana Muhibbah ta nufi benen kaman yanda Kuyangar ta sanar da ita... Matsakaicin wajene mai kyaun gaske Shima, Muhibbah ta tsaya daga parlorn tana k’arema wajen kallo, tabbas sai a b’adda mutum b’att ba’aji d’uriyarsa ba a gida irin wannan... D’akuna guda biyu ta hango nan ta nufi d’akin dake daga gefen dama.. Ta d’anyi knocking a hankali sallama saman bakinta... Jin ba’a amsata ba ya sanyata d’an tura k’ofar a hankali... Nan ta hangota kwance saman royal bed da akai ma d’akin ado dashi wanda yake d’an tsurut a tsakiyar d’akin sabida girma da d’akin kedashi... Tai K’uri tana duban yarinyar dake baccinta hankali kwance... Ta tsinci kanta tana mai sakin murmushi, lokaci guda ta shigo d’akin had’ida tura k’ofar a hankali kaman mai tsoron kada ta tasheta... Muhibbah ta k’araso gaban gadon tana k’arewa Zahra kallo k’aunar yarinyar na kuma shigarta, batasan dalili ba amma dik tsanar da taiwa mahaifin yarinyar bata hango tsanar tattareda yarinyar saima k’aunarta da takeji na shigarta a hankali musamman dataji cewa ta rasa mahaifiyarta, kaman yanda itama ta rasa mahaifiyarta sannan a kusan shekaru irinta Zahran Ta rasa nata mahaifiyar itama... Janyo bargo tai ta rufawa Zahra kasancewar anyi ruwa garin ya d’anyi sanyi kana ta d’auki remote control d’in AC ta rage mata... Lokaci guda ta zauna a gefenta tana dubanta... A hankali Zahra ke bud’e idanunta har ta bud’esu tarau tana duban Muhibbah dake sakar mata murmushi... Zahra Ta mik’e sosai ta zauna murmushi saman fuskarta...Kafin ta sami zarafin magana Muhibbah tace da ita “How are you feeling now...?” Yarinyar ta d’anyi mata K’uri murmushin bai bar fuskarta ba kana tace “Much better...” Muhibbah ta d’an jinjina kai alamun rashin sabo kana tace “Akwai yanda ke maki ciwo kuma...?” Kanta ta kuma girgizawa alamun a’a... “Kin sha maganinki na dare...?” Take annurin fuskar yarinyar ya d’an d’auke alamun basu shiri da magani... Muhibbah takai dubanta ga yanda magungunan Ke aje bisa ruwa a gefe, kana ta isa ta d’auko... Zahra tai raurau kana tace “Paa ke sakani nasha dole... Banson drugs...” Gefe da ita Muhibbah ta zauna kana tace “Let me teach you something...” Tai maganan tana mai b’alle maganin kana tace “Oya close your eyes now and open your mouth... Just think of your favorite candy, kiyi tunanin shi kike sha... There....!” Ta k’arashe tana mai saka maganin bakin Zahra... Dik yanda Muhibbah tace Zahra tai hakan takeyi, a haka har Ta ida bata magungunan.... Su duka biyun fuskokinsu ya cika da annuri... Tsaye yai nan jikin k’ofa yana dubansu... It’s been a while since he saw his daughter as happy as she’s right now, akwai wani murmushi da takeyi wanda tun bayan rasuwar mahaifiyarta bai kuma hangowa a fuskarta ba sai yau.... So yake budurwar da suke tareda Zahra ta juyo yaga fuskarta don bayanta kawai yake hangowa amma sai bugu k’irjinsa keyi a hankali lokaci guda yana hango tsananin Farin ciki dake tattareda d’iyar tasa... Yai k’asaitaccen murmushi a hankali, bazaiso wani abu ya gifta tsakanin wannan Farin ciki da Zahra Ke ciki ba... A hankali yasa kai kaman zai juya, saidai tuni Zahra ta hangosa... Ta d’an bud’e murya had’ida kiran sunansa... Dummm!!! Haka k’irjin Muhibbah ya buga... Zahra taci gaba da fad’in “Paa ka shigo ku gaisa da Aunty Muhibbah...!” A hakali yake takowa cikin d’akin, cikin takunsa mai cikeda charisma yayinda zuciyar Muhibbah yaci gaba da bugawa da sauri da sauri cikin sakanni... Sai murza sark’ar dake hannunta take ba tareda ta iya koda motsa wuyarta ba balle tai tinanin juyowa.... Tana jin sanda Zahra Ke furta “Aunty Hibbah meet my Paa...!” Zuciyarta taci gaba da tsinkewa, bugun zuciyarta ya k’aru.. Batasan ta yanda zata soma juyawa tai idanu hud’u da wannan azzalumi ba and act like nothing ever happened.... Tana tsaka da tinanin ne sallaman Umaima ya katsesu.... Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali... SameenaAleeyou📚 [6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *014* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Umaima ta shigo tana mai fad’ad’a murmushinta “Yaya barka da shigowa...” Ta fad’i cikeda risinawa... Jinjina mata kai yai daidai sanda wayar salulansa ta d’auki ruri, abokinsa Turaki ne mai kiran... Dan haka kai tsaye ya juya ya fice daga d’akin... Muhibbah ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida bud’e lumsassun idanunta... Umaima ta k’araso tana fad’in “Sorry na barki ke kad’ai a parlor Prince F ya rikeni da hira, ashe kin hauro nan...” Muhibbah ta rausayar da idanu kana tace “Eh mana, kin barni ni kad’ai salon naje na b’ata a wannan k’atoton gidan... Allah yasa ban shige wani wajen ba nai karo da d’akin patient d’ita...” Umaima da Zahra suka d’anyi tak’aitaccen dariya a tare cikeda jin dad’i kasancewa da juna Umaima na fad’in “Kar ki damu babu wanda zai saceki cikin Masarautar nan...” Suka kuma darawa a tare Rahima dake lab’e jikin k’ofa k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi ganin wannan mayyar k’awar Umaimar mai bak’in shishigin tsiya tareda Zahra... Allah ya gani bata k’aunar yarinyar nan.. Bata iya shiga ba sai juyawa da tai zuciyarta na mata zafi... A b’angaren Yarima Mahmood kaw tinda Turaki ya sanar dashi isowarsa bai kuma dawowa d’akin Zahra ba dan tini ya samu Ubandoma ma na jiransa daga waje, yasan isowar Turakin zai sanar dashi.. Hakan sai yafi wa Muhibbah dan harga Allah batajin tayi shirin fuskantar babba cikin azzulaman ‘ya’yan sarki AbdulJabbar a yau bayan karon da tai da Yazeed da kuma zancen Fu’ad da Umaima da ta sinkaya... Dik surutun da Umaima da Zahra keyi da alama hankalinta bai taredasu... Tafi bada mahimmanci ga duban k’ofa kaman mai jiran shigowar wani... Cikin zuciyarta take sak’awa, tinda ba Yazeed bane ba kuma Fu’ad bane Giwa Ke tattaunawa da, tabbas da Jamal kenan take tattaunawar, a shi take bada umarnin zartar da wani abu... Mai kenan..? Meye take umartan Jamal yai da wannan kakkausar murya irin haka...? Idan bata b’ata ji ba kaman taji Giwa na cewa kaje ka duba ka gani ko har yanzu na raye... Wannan statement shi take ta nanatawa cikin zuciyarta har lokacinda sukai karo da Yazeed.... Waye Giwa take bada umarnin aje a duba ko Yana nan a raye... Could it be mahaifinta ne...? Kardai Abbanta ne tsawon shekarun nan yana cikin Masarautar nan basu kashe shi ba...? Ya zama dole tabi bayan Jamal taga yanda Giwa ta aikesa...?! Bata ida tinanin ba taji Umaima na dungurinta tana fad’in “Hibbah Wai ina kika tafi munata tambayarki...?” K’ok’arin saita kanta Muhibbah tai kana tace “Kinsan na baro wayata cen sashen bak’i kuma munyi da Mummy zata kirani toh ko shakka babu nasan tana kan nemata yanzu haka....” Umaima ta d’an girgiza kai tace “A’a Gaskiya bai kamata ki k’yale Mummy taita kiranki no response ba, zatai tinanin ko wani abin ne ya sameki... Kinsan iyaye da nuna damuwarsu musamman idan sun tura yara makaranta... Ki tashi kije ki d’au wayarki gaskiya...” Murmusawa Muhibbah tai kana tace “Toh shikenan ga patient d’ina na barta hannunki amana...” Suka murmusa gaba d’aya kana Muhibbah ta mik’e ta fice Zahra na labartawa Umaima yanda Muhibbah ta bata magani cikin dad’in rai ba tareda taji d’acin maganin ba... ** Gimbiya Zeenat ce hankice a parlornta na alfarma, bayi guda biyu sai aikin tausan k’afafunta dake bisan manyan pillows na sarauta suke... Shigowar Raheema fuska a tamke yasa Gimbiya Zeenat umartan kuyangin nata da su fice su basu waje... Babu musu kuyangin suka mik’e sukai kaman yanda uwar gijiyar tasu ta umarta... Raheema ta zauna saman kujera sai cika take.... Aunty Zeenat ta d’ago tanai mata wani irin duba kana tace “Ke kuma fah.. Wannan kumbure kumburen na minene... Ince kina cen kina kula da d’iyar mijinki... Meye kuma zaki shigo kina kumbura fuska..?” Raheema ta d’an kuma tura baki gaba tana kuma tab’e fuska kana ta dubi ‘yar uwar tata tace “Aunty wata mayya ce ta shigo Masarautar nan take neman shige min hanci da k’udundune.... Wllhi bakiga yanda take rawar k’afa kan ahalin Masarautar nan ba musamman Zahra... Aunty tsoro nake kar wannan shegiyar yarinyar Zahra tasa mahaifinta ya auka wa soyayyar wannan mayyar tinda dama yarinyar bak’ar munafuka ce dan na lura tamkar bata k’aunar alak’ata data mahaifinta....!” Ta k’arashe tana kuma tura baki gaba... Tsegege Gimbiya Zeenatu ke dubanta kana ta murmusa kad’an cikeda k’asaita sannan taci gaba da fad’in “Dad’ina dake Raheema wauta, Ke yanzu har akwai macen da zata baki tsoro akan Mahmood... Mutumin da matan ma basa gabansa, mutumin da har yanzu mutuwar matarsa bai gama ficewa daga jikinsa ba... Ni wannan wauta naki da yawa take Raheema saikace ba d’iyar Saraki kike ba, sam Bakida jarumta... Har yaushe zaki tsaya wata banza can Ta baki tsoro Yo ni ba don inason cimma burina wajen ganin kin auri Mahmood ba yaushe zan tsaya ina biyayyawa Giwa...Toh wllhi ki bud’e kunnuwarki da kyau ki saurareni... Idanma baki son Mahmood wannan Ke ta shafa iayakacin abinda na sani shine idan za’a kashe rai a Masarautar nan sai kin aure Mahmood dan yanda na zamto ‘yar kallo cikin Masarautar nan auren Mahmood da zakiyi shine zai dawo min da Martaba ta ya kuma d’aga darajata, don na tabbata da zaran Mahmood ya zama Sarki Ke kuma kin zamto matar Sarki Toh fah mulki ta dawo hannunmu sai yanda mukai da Giwa cikin Masarautar nan, da Sarki da Uwarsa dik zasu dawo k’ark’ashin mulkin mu....Tunda ban haifa Sarki ba don haka dole na zamto Sirkar Sarki, dole ta ko wanne hanya nasan yanda zanyi mulkin Masarautar nan Ta dawo gareni... Kuma hanya d’aya kenan tak shine ki auri Mahmood...!” Ta k’arashe tana zaro idanu waje... Raheema tai shiru tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali, k’aunar Mahmood na kuma fizgarta, dik yanda za’ai bazata tab’a bari wata tazo Ta rusa mata Farin cikin data jima tana k’ok’arin ginawa ba koda kuwa wann shegiyar d’iyar tasa bataso.... Da wann tunanin ta mik’e ta nufi d’aki shiryawa dan zuwa ganin Yarima Mahmood... ** Turaki ya kuma gyara zama yana mai kurb’an drink d’in dake rik’e hannunsa kana ya nusa kad’an yace “Toh yanzu what are you suggesting your Highness...?” Yarima Mahmood ya fuzar da fuci a hankali kana yace “I don’t know Turaki... Is getting more complicated... Na rasa ta ina zan b’ullowa al’amarin... Waye zan fara tuhuma..? Ta ina zan fara bincikawa... Sannan waye zan yarda dashi cikin Masarautar nan...?” Shiru ya d’an gifta tsakani kana Turaki ya d’an gyara zamansa had’ida fitowa daga cikin kujera sosai “A gaskiya your Highness ko ni ban goyi bayan ka amince da kowa cikin Masarautar nan ba... I’m sorry to say not even your brothers...It might sound ridiculous but gaskiyar kenan... Kuma kaman yanda Baba Wambai yace, if you really want to get to the bottom of all this, Toh fa sai ka zamto shugaba a Masarautar nan... Idan har kana tunanin mutuwar Matarka nada nasaba da mutuwar mahaifinka bazaka tab’a ganowa ba har sai ka zamto kaikeda mulkin Masarautar nan....” Yarima Mahmood yai shiru yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida fuzar da fuci a hankali... Lokaci guda abubuwa da dama ke ziyartan kwanyarsa... Mafarkin da yai da ‘yan uwansa harma da mahaifiyarsa, Sannan Maiyasa Giwa take so ya auri k’anwar matar mahaifinsa... Maiyasa yake jin can k’asan zuciyarsa bai aminta da wannan had’i da suke k’ok’arin yi ba... Maiyasa yake jin abubuwa da dama basa tafiya daidai cikin Masarautar... Tabbas ya kamata ya saka zancen Baba Wambai a ma’auni, bai kamata ya k’yale Yazeed ya d’ale Karagar Mulkin ba har dai yanaso ya samo amsoshinsa.... Turaki yaci gaba da fad’in “Mai kake gudu cikin sarauta Mahmood... Kana tinanin sirrin da ka b’oyewa d’iyarka shekara da shekaru na iya bayyana ne... Is that what’s holding you back...?” Ya k’arashe cikeda kulawa... Kaikaitowa yai wannan karon yanaima Turaki wani irin duba kana ya soma fad’i cikin karaji “She’s never going to find out.... I won’t allow that to happen... I’ll protect that from happening, no matter the cost..!!” Shiru Turaki yai ba tareda ya kuma cewa komai ba dan yasan wanene abokin nasa idan ransa ya b’aci... Bai kuma kawo zancen ba sai ma shiru da yai yana karantar Mahmood d’in da ko ba’ace ba lissafi da sak’e sak’e yake cikin zuciyarsa... Turaki ya girgiza kai cikeda tausayin abokin nasa.... *** A nan yanda ta mak’ale take jiran fitowar Jamal, Ta kusan minti talatin mak’ale a nan wajen tana ganin masu kaiwa da komowa amma bataga koda k’yallin Yarima Jamal ba... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai kuma lek’awa... Har saida ta cire rai bazataga giftawansa ba ta hango wani mutum sanye cikin bak’in kaya mai tsananin duhuwa ya nufo ta yanda take, baka iya hango fuskarsa don ya rufe da bak’ar hula mai yanayi da hular sanyi... Baka hango komai sai alamun mutum... Sosai k’irjinta ke tsananin bugu zuciyarta na tambayarta wanene wannan... Tana gani mutumin ya nufi wata hanya ga walk’iya da har yanzu akeyi had’ida tsawa mai k’arfin gaske... Take taji zuciyarta tana son ganin yanda wannan mutumi zai jesa... Lokaci guda ta sad’ad’o ta fito daga mab’oyar nata ta nufi mutumin cikin sand’a dikda cewa tafiyar mutumin yafi kama da sassarfa tamkar mai tafiya cikin iska dan har b’acewa ganinta yake..... Dikda tsananin tsoro da ya ziyarci zuciyarta hakan bai hanata bin bayan wannan mutumin da bata iya hango komai nasa face bak’in tufafi.... Suna tafe ta hango mutumin ya tsaya cak tamkar wanda aka tsaida shi... Gabanta ya yanke ya fad’i tamkar an iza guduma, idanunta suka firfito waje... Juyowan da mutumin zai yayi daidai da shigewar Muhibbah cikin tsakankanin gini zuciyarta bata daina tsinkewa ba, lokaci guda ta rintse idanunta sanda taji tamkar takun mutumin ya nufota.... SameenaAleeyou📚 [6/8, 8:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *015* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sosai take jin tafiyar na nufowa yanda take, banda karanto addu’o’i cikin zuciyarta bata iya komai, ta rintse idanunta a hankali tana jiran mai aukuwa ya auku.... Cak kuma sai taji tafiyar ta tsaya, tai saurin bud’e idanunta dake rintse k’irjinta naci gaba da bugu... A hankali ta d’an fito da kanta tana lek’en hanyar, bataga kowa ba sai wasu mage guda biyu suna cin abinci daga gefe.... Allah ya gani tsikar jikinta yai matuk’ar tashi da ganin wad’anann Magen dikda gasu farare ne k’al gwanin ban sha’awa.... Ta kuma lumshe idanunta a hankali tana karanto addu’a na neman tsari, Allah yasa ita d’in ma’abociyar zikirin safiya da maraice ne wanda dik d’an adam idan yai rik’o dasu Allah yayi alk’awarin karesa daga dikkan wani abin cutarwa saidai kuma idan k’addararka ce toh sai ya cimmaka.... Tabbas wannan mutumi mai bak’in tufafi ya b’acewa ganinta, batasan Ta yanda ya nufa ba dan haka dole ta hak’ura da bin bayansa, gashi bataga Jamal ba mak’asudin b’uyarta a wajen... Babu yanda ta iya haka ta nufi masauk’i tana ci gaba da sak’e sak’e cikin zuciyarta lokaci guda tana juya sark’ar data d’auka daga wajen Yazeed.... Tana isa d’aki ta d’au wayarta, Aiko nan ta iske missed calls d’in Ansar kusan guda biyar... Ta d’an lumshe idanunta had’ida bud’esu, lokaci guda tana fuzar da huci a hankali... Kaman jiran isowarta yake nan wayar taci gaba da ruri.... Ta d’auka a hankali sallama saman bakinta... Cikeda tashin hankali Ansar ke fad’in “Hibbah where have you been, I’ve been trying to reach you since ... Tell me akwai wani abu ne..? Are you okay... How are things there...?!” A jere yaita jero mata tambayar cikin tsananin damuwa... Shafe fuskarta tai a hankali kana tace “Relax please Ansar..Just calm down... Babu abinda ya sameni, idan kajini shiru Ina aiwatar da abinda ya kawoni ne kafin lokaci ya k’ure min.... And please I want to ask you this favor... Dan Allah ka daina yawan kirana on and on, someone might get suspicious of me, especially Umaima ta yarda dani sosai banso na breaking trust d’inta da take dashi akaina... She really is a good person banso taga kaman na yaudareta ne ko wani abu mai kama da haka... Kuma kaima yin hakan ka iya shafar alak’arku...Please Doc ka rage yawan kirana...You don’t need to worry about me, I can take care of myself...!”Ta k’arashe Murya fal damuwa... Fuzar da fuci yai a hankali kana ya soma fad’in “Seriously Hibbah...! Cewa kike na rage yawan kiranki bayan nasan abinda kikeyi abu ne mai matuk’ar had’arin gaske... And you’re even telling me kar na damu dake zaki iya kula da kanki...? Kema kinsan bazan tab’a yin haka ba... Idan bakiso naci gaba da kiranki on and on, then always keep me updated... I need to know everything that’s going on with you there...!” D’an rausayar da idanu tai kana tace “Alright fine... Kana so ka sani..?” Lokaci guda Ta soma sanar dashi abubuwan da suka faru tiryan tiryan a d’an shigowarta gidan da tai....Saidai tin bata gama bashi labarin abubuwan data gani ba ya mik’e daga zaunen da yake yana mai furta “No Muhibbah, you’re not pushing through with your plans... You know what..? This is over... Park your things gobe gobe zanzo na d’aukeki mu dawo gida... Bazan iya barinki tsakankanin wad’annan Animals d’in kici gaba da rayuwa ba... Who knows, wa yasan abinda zasu miki...?!” Ya k’arashe cikin tsananin k’unan rai... A d’an tsawace itama ta soma fad’in “Do you really think I like it here... Kana tunanin Ina jin dad’in zama cikin wad’annan azzaluman ne...? Do you think it’s easy for me facing them bayan dik abinda sukai min...? This isn’t easy for me.... Each time idan naga fuskokinsu sai na tuna wancan lokacin... So please idan bazaka ci gaba da k’arfafa min gwiwa ba ka daina sarar min da gwiwa...!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka.... Cikin sanyin jiki Ansar ke furta “I’m sorry... Ba nufi na ba kenan Muhibbah.... Na damu dake ne Muhibbah, you know how much I love you right...? So please kar kiga laifina dan na nuna damuwata, Kawai gangan jikina ne a nan but gaba d’aya zuciyata da ruhina suna taredake Muhibbah.... I’m sorry I made you feel that way...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Tsaye ta mik’e had’ida dafe kanta kad’an tana mai furta “Ansar shiyasa banso sanar dakai ba, ya kamata ka gane da da yanzu ba d’aya bane... Babban kuskuren da sukai shine da suka barni da rai... Allah bazai kuma basu daman cutar dani ba... Kuma yanzu da na tabbata akwai abubuwa da dama da suke rufe cikin Masarautar bazan tafi ba Ansar har sai nakai mak’uran bincikena da yardar Allah... Kawai kaci gaba da min addu’a kaji...!” Shiru yai tamkar mai nazari kana ya fuzar da fuci a hankali “Shikenan... Amma ki sani ba wai dan inaso ba na k’yaleki cikin Masarautar nan sai don Babu yanda na iya ne.... I love you so much Muhibbah... And ina kewarki sosai..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Jiki a matuk’ar sanyaye tace dashi “Ka gaisar min da Mummy, nima ina kewarku sosai... Sai mun sake magana...!” Sukai sallama su duka biyun jikkunansu matuk’ar sanyaye... Mik’ewa tai ta soma zarya a d’akin tana tunani abinyi gaba... Ta d’auko sark’ar tana ci gaba da juyawa... Tabbas ya kamata Washe gari juma’a takai ziyara k’ofar Yarima Yazeed.... Da wannan tunanin ta bud’e drawer ta linke sark’ar cikin k’aramar farar k’yalle kana ta fad’a bathroom ta d’auro alwala... ** Yauma da salati saman bakinsa ya bud’e idanu daga baccin da yake mai cikeda mafarkai marassa dad’i... Tabbas abin ya soma damunsa sosai, hardai zai kwanta toh sai yayi marfkin wani abin k’i.... Yau mafarkin nasa gameda Ja’afar ne... Ja’afar bawa d’ah ga sarkin dawakai na cikin masarautarsu... Kaman yanda ya gani cikin baccin nasa, Shida Ja’afar suna tafe cikin Bargan dawakan mahaifinsa su duka biyu Sun saka kaya irinta mulki da sarauta iri guda babu abinda ya raba, kwatsam abokan gaba suka far masu... A tare suka zaro takubbansu domin yak’an abokan gaban nan.... Cikin abokan gaban d’aya yayo kan Mahmood da takwabi saidai tuni Ja’afar ya tare masa saran kana ya mik’a masa hannu ya d’agosa tsaye, su biyu d’in hannayensu rik’e cikin na juna.... Yak’i sosai suke da abokan gaban nan har saida Suka kashe abokan gaban gaba d’aya hardai sukai nasaran kama shugaban abokan gaban nasu wanda ya jagoranci yak’in ...Babban abinda ya firgita Yarima Mahmood shine wannan shugaban abokan gaban da sukai nasaran capkewa k’afafunsa kawai Mahmood ya kalla ya gane d’aya ne daga cikin ‘yan uwansa.... Cikin tsananin tashin hankali yake bin k’afafun da kallo hardai ya kusan k’arasowa zuwa fuska... Saidai kash kafin ya k’araso zuwa fuskar ya farka daga baccin bai hangi ko wanene cikin k’annen nasa ya kawo masu wannan hari ba.... Yarima Mahmood ya fuzar da fuci a hankali yana mai shafe sumar kansa... Wannan mafarki da d’aure Kai yake... Waye cikin ‘yanuwansa yayi mafarki dashi...? Tambayar da ya tsaya masa a mak’oshi... Sannan mai yasa Ja’afar ya saka kaya na alfarma ba kayan bayi ba...? Sannan Maiyasa D’an uwansa ke k’ok’arin kashesa Ja’afar ya tare masa...? Shin ina Ja’afar...? Mai yasa zai tafi yabar Masarautar nan...? Sannan idan har Jafar ya cika bawa ai bazai tab’a barin Masarautar nan ba..? Toh ya akai ya sami k’arfin gwiwan barin Masarautar yana a matsayin bawa..? Wad’annan tunani sun kasa barin kwanyar Yarima Mahmood... Baccin da bai iya komawa ba, ya mik’e ya zira jallabiyarsa fara k’al kana ya fito waje.... A b’angaren Muhibbah kaw ma iya cewa da alama baccin ya k’aurace mata itama... Mafarkin mahaifanta taitayi, musamman mahaifinta da takeji can k’asar zuciyarta tamkar Yana nan a cikin Masarautar nan... Mayafi ta d’auka ta rufa akanta kana ta fito haraban masauk’in nata... Tai jigum tana duban sararin samaniya tana hango taurari jefi jefi... Lokaci guda tunanin rayuwarta na baya na zuwa mata... Maiyasa takejin rauni cen k’asar zuciyarta...? Maiyasa takejin d’aukan fansa bai kamaceta ba...? Shin anya abu mai kyau takeyi...? Shin hak’uri da yawan afuwa baifi d’aukan fansa ba....? Toh amma ta yaya zata iya yafe masu Ta mance komai...? Wasu hawayen suka kuma gangaro mata wani b’angare na zuciyarta naci gaba da raya mata “You’re not a bad person Saudatu... Ke ba muguwa bace, burinki na d’aukan fansa na nufin kema kin zamto daidai dasu... Ask yourself, Ki tambayi kanki Maiyasa cen k’asar zuciyarki kikejin rauni da fad’uwan gaba..? A fili ta baiwa zuciyar tata amsa “Sabida ni mace ce wacce a halittana tun fil azal akwai rauni....!” Take taji zuciyar nata na kuma bata amsa da fad’in “Ba haka bane... Sabida Ke ba muguwa bace, bazaki iya cutar da d’an adam kaman yanda su suka cutar dake... Saudatu Ki aje makamanki Ki bi shawarin Ansar ki komaga sabon ahalinki wanda Allah ya maye maki gurbinsu da iyayenki da ya d’auka daga gareki...! Cikin kuka take girgiza kai tana mai furta “Toh mahaifina fah da nakeji a ajikina Yana nan raye cikin Masarautar nan... Bazan iya tafiya ba tareda na tabbatar da zargina ba...!” Zuciyar tata taci gaba da fad’i mata “Mahaifinki baya raye Saudatu... Kawai kinsa ma ranki haka d’in ne shiyasa kike zaton hakan ne....!” Kame kanta tai sosai had’ida tak’urewa jikin garu tana kuka sosai take furta “No no no... Ya isa....ya isa haka...!!” Kuka sosai ya kufce mata... Tana mai k’unshe bakinta da duka tafukan hannayenta biyu... Kaman sautin kukan mutum yake saurarowa daga nesa, ya d’an dakata da tafiyar nasa had’ida kasa kunnuwansa sosai, kasancewar dare ne komin k’ank’antan k’ara sai kaji dab kunnuwanka... A hankali yake bin hanyar da yake sauraron sautin kukan na fitowa daga nan.... Cen ya hangota tak’ure ta kifa kanta da gwiwa tana cazgan kuka.... Tsaye yai yana dubanta cikeda tausayawa.... A duniyarsa baison yaga mace na kuka irin haka koda kuwa baiwace ba d’iya ba, harga Allah yakanji babu dad’i cikin zuciyarsa... A hankali yaci gaba da takowa zuwa gareta, saida ya k’araso har yanda take kana yai sallama cikin muryarsa mai cikeda aminci.... D’if kukan nata ya d’auke tamkar anyi ruwa an d’auke, dikda k’irjinta dake bugawa a hankali hakan bai hanata k’ok’arin saita kanta ba.... Tai saurin gogewa hawayen fuskarta had’ida d’agowa... A karo na farko da sukai eye contact tin bayan dawowarta Masarautar.... Yau Yarima Mahmood ne tsaye a gabanta, tabbas abubuwan da suka faru wancan lokacin sun shiga dawo mata daki daki, saidai ya zama dole tai k’ok’arin saita kanta ta tattaro duka jarumtarta ta had’e waje guda... Ta k’ak’aro murmushi a hankali kana ta mik’e tsaye tana mai gyara mayafinta.. “Barka da dare Rankashi dad’e..!” Tai maganar tana mai duban k’Asa... Yarima Mahmood da har lokacin hannayensa Ke hard’e ta baya jinjina mata kai yai a hankali kana yace “Barkanki...! Ke kuwa mai kikeyi a nan cikin daren nan.....?” Ta d’an saci dubansa jin tambayar da ya jefo mata kana Ta kuma k’ak’aro murmushi tace “Babu komai rankashi dad’e ni bak’uwa ce a Masarautar... I guess rashin sabo da wajene yasa bacci ya k’aurace min shisa na fito nan na zauna....!” Ta k’arashe tana wasa da ‘yan yatsun hannunta.... Jinjina kansa yai a hankali kana yace “Shiyasa kike kuka...? Ko kinsan sautin kukanki ka iya hana wasu halittu samun nitsatsen bacci cikin Masarautar nan...?” Wannan karon d’agowa tai tana dubansa sosai kana ta d’an kauda fuskarta gefe.... Ganin tayi shiru babu amsa yasa Yarima Mahmood gyara tsayuwarsa had’ida d’aga kansa sama kad’an.... “Bakiyi kamanni da bayi ba... Shin wacece Ke...?!” Ya k’arashe yana mai sauk’e idanunsa akanta da alamun tuhuma... Ji tai wani abu ya tokare mata mak’oshi, tai k’ok’arin daidaita natsuwarta “Bak’uwar Umaima ce ni Rankashi dad’e....!” Tai maganar tana mai sadda kanta k’asa... Sosai ya kaikaito wannan karon yana dubanta tamkar wanda ya tina wani abu kana yace “Muhibbah..?!” Ta d’ago itama tana dubansa, lokaci guda ta sami kanta tana mai jinjina masa kai alamun eh.... Yarima Mahmood ya gyara tsayuwarsa kana yace “It was you then...Kece wacce kika taimaki d’iyata Zahra...” Taji murmushi na zuwa saman fuskarta kana tace “Nayi abinda ya kamata ne your highness...!” Tinda suka soma magana sai yanzu ya sinkayo wani zak’i cikin muryar nata bayan ya ambaci Zahra.... Yai murmushi for the first time tin bayan had’uwarsu a nan wajen... Lokaci guda kuma ya d’aure fuska kaman wanda ya tina wani abu... Ita kaw Muhibbah zuciyarta sai ci gaba da tabbatar mata take, tabbas weakness d’in Yarima Mahmood d’iyarsa Zahra ce, hanyar da zata sami yardarsa kenan shine ta shiga jikin d’iyarsa sosai... Muryarsa ne ya katse mata tinanin nata “Kin min laifi...!” Ta d’an d’ago da alamun firgici wannan karon kana tace “Laifi kuma Rankashi dad’e...?!” SameenaAleeyou 📚 [6/8, 8:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *016* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “K’warai kuwa... Kinmin laifi...” D’an sadda kanta ta kumayi kana tace “Dikda bansan laifin ba, tuba nake Rankashi dad’e...!” Cikeda risinawa tai maganar... Ya d’an gyara tsayuwarsa a karo na UKU had’ida yin gyaran murya kad’an “Baki San laifin ba....?” Ta d’ago kad’an tana duban fuskarsa da security light ya haske tarau... Lokaci guda ta kuma maida nata fuskar k’asa tana mai furta “Tuba nike Rankashi dad’e...!” Yanda tai maganar sai yai masa tamkar ya tab’a sanin mai irin wannan muryar shekaru da jimawa... Ya d’an d’auke idanunsa daga dubanta kana yace “Umaima bata sanar dake sak’o na ba...?!” Sai yanzu ta tina ashe fah Wai tin jiya Umaima ta sanar da ita Yarima Mahmood na kiranta... Ta d’an daburce kad’an kai kace har cikin zuciyarta hakan ne kana tace “Allah ya huci zuciyarka Rankashi dad’e...!” “Baki amsa min tambayata ba... Sannan cikinku waye zan hukunta Ke ko Umaima...?!” Ya k’arashe Murya a dake... Dubansa kad’an tai kana ta shiga girgiza kai a hankali “Ta sanar dani Rankashi dad’e... A gafarceni laifin nawa ne... And please kar a hukunta Umaima batada laifi... !” Bai amsata ba sai jefo mata tambaya da yai.. “Kinada alak’a da gidan sarauta ne...?” Taji tambayar a bazata... Gyara tsayuwarta ta d’anyi alamun gajiya da tsayuwa kana tace “A’a Rankashi dad’e wannan shine karona na farko a gidan Sarauta...!” Ya jinjina kai a hankali yana jinjina d’abi’u irinta babban gida da take dashi, lokaci guda yana karantar ta da alama ta soma gajiya da tsayuwar.. Shiru ya gifta tsakaninsu har kaman babu mai yin magana cikinsu kana Yarima Mahmood yace “Baki sanar dani ba.. Kukan mai kike a nan...?” Ta k’ak’aro murmushi kana tace “Kewar gida nake Rankashi dad’e... Kaifa mai ya fito dakai cikin daren nan....?!” Saida tai tambayar sai kuma taga rashin dacewar tambayar tata, musamman da ta hangi irin duban mamakin da yake mata... Lokaci guda ta kuma risinawa tana mai furta “Tuba nake Rankashi dad’e... A gafarceni....!” Yanda tai maganan ya sanayasa sakin k’asaitaccen murmushi a hankali kana yace “Na kasa bacci ne kaman yanda kema kika kasa....” Mamaki ya cikata ganin ya amsata Kai tsaye, Ta d’an jinjina kai a hankali kana tace “Kai hak’uri Rankashi dad’e, not being nosy, har kuma masu mulki kunada damuwar da take hanaku bacci....?” Dariya taso basa wannan karon jin kalamanta tamkar ta k’aramar yarinya, saikace Zahra ce tai maganar... Gyaran murya ya kumayi kad’an bayan ya murmusa a tak’aice kana ya isa gefen dakali ya d’an zauna... Ganin tai tsaye wajen ya sanyashi nuna mata d’aya dakalin dake gefe kana yace “Bismillah..!” Babu musu ta isa ta zauna... Mahmood yaci gaba da fad’in “Baki San masu mulki sukeda damuwa ba... Shin baki San duk wanda Allah ya jarabcesa da jagoranci wasu Al’umma ya d’aura masa babban nauyi bane...? Ta yaya shugaba zaiyi bacci hankalinsa kwance bayan baisan halinda d’aukacin al’ummarsa suka kwana ba..?” Tai shiru ba tareda ta iya amsa masa tambayar ba... Yarima Mahmood ya jinjina kansa kana yace “Dik yanda bawa yakai da samun wani d’an Kaso na mulki daga cikin mulkin duniya da Allah ke rabawa tsakanin bayinsa bazai tsallake matsaloli na rayuwa ba... In one way or the other dole yanada matsalarsa... Cikan d’an adam kenan...!” Tai shiru tana jinjina kalamansa lokaci guda tana jin natsuwa na sauk’ar mata cikin zuciyarta a hankali... Sai takejin kaman she’s safe around him.... Lokaci guda taga ya mik’e hannayensa hard’e Ta baya kana yace “Kije kwanta dare yaja sosai, kokuma Ki tausashi zuciyarki da ambaton mahaliccinki, zaki samu natsuwa a cikin yin hakan....!” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai ya soma takawa a hankali.... Muhibbah tabi bayansa da kallo tamkar mai tinanin wani abu.... Cikin sauri ta mik’e tabi bayansa kana tace “Rankashi dad’e.... Na gode....!” Bai juyo ya dubeta ba saima sa kai da yai yaci gaba da tafiya... Muhibbah tabi bayansa da muguwar kallo cikeda tsana da k’yama har ya b’acewa ganinta, lokaci guda hawaye na kuma gangaro mata... Tasa bayan hannunta tana goge hawayen da suka wanke mata fuska... Zuciyarta naci gaba da mata zogi.... Lokaci guda kuma ta tsinci kanta tana mai bin shawarin Yarima Mahmood, Ta nufi d’aki ta d’auro alwala kana ta fito ta tada sallah kaman yanda ya bata shawarin yin hakan.. ** Washe gari Ta kama juma’a babban rana, sannan a wannan ranan Muhibbah ta sami ganawa da Giwa tun bayan zuwanta Masarautar... Wani ikon Allah had’uwa ta farko da Giwa da Muhibbah sukai Allah ya jefa k’aunar Muhibbah cikin zuciyar Giwa... K’awayen Umaima sunsha zuwa Masarautar amma bata tab’a gamo da wacce jininsu yazo d’aya irin Muhibbah ba, har tambayarta take gameda rayuwarta musamman da taji makaranta ya kawota garin... Giwa ta kuma gyarawa daga kishingid’en da take tana duban Muhibbah dake risine gabanta a k’asa kana tace “Kikace ke ‘yar asalin garin Bauchi ne...?” Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Eh Allah shi taimakeki, ni ‘yar asalin garin Giad’e ne dake nan jihar Bauchi amma cikin Bauchi muke zama, mahaifina Alhaji Iro Datti ya kwana biyu da rasuwa....” Ta k’arashe cikeda girmamawa... Giwa ta jinina Kai tana mai furta “Allah sarki ashe ked’in Marainiya ce... Toh ki saki jikinki kinji koh domin kaw kinzo gidan goya marayu... Ki zauna a Masarautar nan har iyaka lokacinda zaki kammala karatunki kinji koh...!” Muhibbah Ta d’ago cikeda jin dad’i tana duban Giwa dake ci gaba da sakin murmushi a hankali kana tace “Godiya nake Rankishi dad’e... Na gode na gode K’warai Allah ya k’ara girma...!” Giwa ta girgiza kai a hankali murmushi bai bar saman fuskarta ba take ci gaba da fad’in “Babu komai Muhibbah ki saki jikinki tamkar Umaima nan gidanku ne kinji koh...!” Muhibbah Ta kuma risinawa tana godiya yayinda Umaima Ke tayata godiyan cikeda jin dad’i... Har Giwa tai masu izinin ficewa Jakadiya bata daina jifarsu da muguwar kallo ba... Suna fita Jakadiya Ta gyara zama tana duban Giwa “Allah shi taimakeki anya baki gaggawan maraba da wannan yarinyar ba, bansan dalili ba amma sam bata kwanta min ba....Allah shi baki yawan rai a duba lamarin...!” “Jakadiya yaushe kika fara samun ra’ayin kanki a gidan nan banida labari”Giwa tace tana mai aikata mata wulak’antaccen kallo... Jakadiya yada kai k’asa tana neman afuwa da tuba... K’asaitaccen murmushi saman fuskar Giwa kana taci gaba da fad’in “Jakadiya kenan... Kaman baki san ko ni wacece ba har yanzu... Duk abinda nayi Jakadiya yanada manufansa... Kin tab’a tambayata Maiyasa dik abinda Umaima zatayi ko zatazo dashi cikin Masarautar nan bana dakatar da ita...?!” Jakadiya ta girgiza kai a hankali alamun a’a... Giwa Ta jinjina kai cikeda k’asaita kana taci gaba da fad’in “Umaima zata min amfani nan gaba kad’an a shirina Jakadiya... A halin yanzu Umaima ta gama aminta ni d’in Sarauniyar K’warai ce mai kimanta adalci da k’aunan jama’a... Dik abinda zan bijiro mata dashi nan gaba kad’an bazata watsa min k’asa a idanu ba, dan Haka Jakadiya koda wasa kar na sake zartar da hukunci cikin Masarautar nan mu samu sab’anin ra’ayi, duk abinda nayi ko zanyi ki ya zama wajibi akanki ya zama dole Ki aminta dashi... Da ace wata ce cikin bayi tayi wannan magana ba ke ba Jakadiya da yanzu ta jima a barzahu...!” Jakadiya Jiki na matuk’ar rawa take fad’in “Tuba nake Allah ya taimakeki... Allah ya huci ran Giwar Amale... Jakadiya tana neman afuwanki Allah ya baki yawan rai...!” Ta k’arashe tana mai d’ago hannu daga nan durk’ushe alamun jinjina... Shigowar Jamal ya sanya Jakadiya mik’ewa Ta basu waje bayan ta gama kwasan gaisuwa wajen Yarima Jamal.... Cen saman kujera na alfarma dake gefe cikin d’akin ya zauna... Mahaifiyar tasa ta dubesa kana tace “Baba na ya haka... Ya na ganka haka, akwai matsala ne...?” Jamal ya fuzar da huci a hankali kana yace “Maami magana ce kan Ya Mahmood...!” Ta gyara zama sosai tana duban Jamal kana tace “Umhum Ina saurarenka, mai kuma ya faru da Mahmood d’in...?” Shafe fuskarsa Jamal yai da duka tafukan hannayensa kana yace “Maami Wai kinsan d’iyarsa Zahra ba Aliya bace ta haifeta... Yarinyar bada aure ya haifeta ba...!” Shiru Giwa tai tamkar mai nazari tana mai kuma tabbatar da zarginta kan lamarin yarinyar, Toh amma saidai abu ne mai kaman wuya ace Mahmood zai aikata wani abu makamancin wannan, idan za’a saka mata takwabi zata iya rantsuwa d’anta Mahmood bazai tab’a aikata mummunan sab’o irin wannan ba... Ance ba’a shaidan d’an adam amma ita tayi shaidan Mahmood... Toh yaya akai hakan ta kansance...? Muryar Jamal ya dawo da ita daga Duniyar tunani yanda yake fad’in “Maami abin ya matuk’ar bani tsoro da mamaki... Ya za’ace Yaya ya aikata babban abin kunya irin wannan, Maami bayyanar wannan magana barazanace garemu baki d’aya....!” Dubansa ta d’anyi kana tace “Babu wanda zai sani, kuma kaima banaso ka nuna masa kasan komai, maganan zai zauna a haka kaman ba’ayi ba....!” Su duka biyu sukai shiru kowa na sak’awa da warwarewa cikin zuciyarsa.... ** A b’angaren Mahmood kaw tinda aka fito daga masallacin Juma’a ya b’adda kama ya fice ya nufi gidan D’an uwan mahaifinsa Dattijo Baba Wambai, ko Ubandoma baisan ya fice ba, sannan ko motar Masarautar bai d’auka ba, hasalima motar haya ya shige ya nufi gidan Baba Wambai.... Tamkar wani buzu haka yasha rawani ya nad’e fuskarsa, a k’ofar gidan ya tsaya yanda ya tadda wani yaro ya taho zai shige k’ofar gidan.. Yarima Mahmood yai kiransa kana yace “Kai yaro shin kana shiga wannan gidan...?” Yaron ya jinjina kai alamun eh kana ya k’arada “Amma matar gidan masifaffiya ce tana koranmu idan mun shiga d’iban ruwa....” Yarima Mahmood da ya b’adda kama zuwa bak’on Buzu yace “Ka shiga ciki kace ana sallama da Baba Wambai.... Idan an tambayeka inji Wanene kace bak’on Buzu ne...” Yaron ya jinjina kai yana mai amsawa kana ya nufi cikin gidan... Jim kad’an saiga Baba Wambai ya fito a daddafe yana rik’eda yaron yake fad’in “Kai Muntaqa ka faye wasa gaban famfo shiyasa Innani Ke korinka, muje naga bak’on Buzun....!” Yaron yai masa nunida yanda Yarima Mahmood ke tsaye kana yace “Gashi nan ai Baba...!” Baba Wambai yakai dubansa ga mutumin saidai duba d’aya yai ma k’wayar idanunsa ya fahimci Mahmood ne... Ya saki murmushi a hankali kana yace “Mahmuda kaine tafe da tsakar ranan nan...?” Yarima Mahmood ya d’an murmusa kad’an yana mai jinjina kai yake furta “Ai nayi zaton bazaka ganeni ba Baba...” Murmushin Baba Wambai ma yayi kana yace “Yo banda abinka Mahmooda dik yanda zaka kai ga canza kamanni ai bazaka b’ace min ba... Wannan idanu nawa da kake gani tarau yake, gashi gidanmu munyi gadon ciwon ido amma ni nawa har yafi Naka mai cikeda k’uruciya.... K’araso daga ciki....!” Mahmood ya d’anyi still a wajen yana mai rik’o hannun Baba Wambai yake fad’in “A’a Baba Wai da nafiso mu zauna daga waje don banaso wani ma yasan nazo shiyasa na b’adda kamanni....” Baba Wambai ya jinjina kai kana yace “Kayi gaskiya Mahmuda, hakan da kayi kayi daidai, mu k’arasa k’arkashin bishiyar Gamjin cen....!” Mahmood ya jinjina kai yana mai taimakawa Baba Wambai har suka isa k’ark’ashin bishiyar, suka zauna saman manyan reshen bishiyar da suka sauk’o k’asa..... Bayan sun gaisa Baba Wambai yace “Ina saurarenka Mahamuda, meke tafe dakai...?” Mahmood ya d’an gyara zamansa had’ida kwance rawanin kad’an kana ya soma fad’in “Wato Baba kan mafarkan nan ne da suka addabeni wanda babu daren da zaiyi na kwanta bacci na tashi ba tareda nayisu ba... Abun ya fara damuna sosai Baba....!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Dattijo Wambai yai K’uri yana duban wani gefen kana yace “Mahamuda dik yanda akai wannan mafarkai naka da kake yawanyi sunada manufarsu... Banida ilimin fassarar mafarki amma koma minene Allah shi yasan maiyasa yake nuna maka abu makamancin haka cikin baccinka.... Wasilci na farko da zanyi maka shine kaci gaba da k’ok’arin kwatanta rik’o da addini... Sannan abu na gaba kaci gaba da taka tsan tsan cikin wannan gida D’ah na...! Gidan sarauta gida mai kafi da abubuwa na ban mamaki had’ida tarihi.... Kasa ma ranka babu wanda ya isa ya cutar dakai face da izinin mahaliccinka... Sannan ka tausaya ma wad’anda suke k’asa dakai domin ka samu sauk’in gudanar da al’amara daga wajen mahaliccinka....” Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “In sha Allah zan yi k’ok’arin kwatanta dik abinda ka umarta Baba...” Baba Wambai ya jinjina kansa alamun gamsuwa kana yace “Sannan abu na gaba shine tunda yanzu Allah yasa ka dawo, kaci gaba da abinda iyayenmu suka rik’e gidan dashi, don na tabbata tun bayan rasuwar mahaifinmu Sarki Kakanka mai rasuwa aka daina wannan kyakkyawar d’abi’a a cikin gidan....!” Ya d’an dubi Baba Wambai kana yace “Me kenan Baba...?” “Duk ranan Juma’a akanyi sauk’an alkur’ani mai girma cikin fada sannan mahaifinmu yakan fita masallacin juma’a ya raba sadaka ma yara da gajiyayyu sannan yakan sauya kama ya zaga ya duba marassa lafiya wasu lokutan harma da gidajen marayu...da kuma kasuwanni domin yaga mai yake wakana a k’asarsa. yakan kuma kai ziyara gidan yari yaga halinda fursunoninsa Ke ciki....Duk wad’annan d’abi’u ne masu kyau wanda shugaba idan ya suffanta dasu tabbas yayi koyi da shugabbannin K’warai.... Tin bayan rasuwar mahaifinmu aka daina gudanar da irin wad'annn al'amara a Fada... Daga nan abubuwa suka rikice, domin kaw duk gidan da ba'a ambaton Allah cikinsa wannan gida tamkar kufai ne....” Mahmood yai shiru yana mai jinjina kansa kana yace "Haka ne Baba, in sha Allah za’aci gaba da sauk’an alk’ur’ani mai Girma duk juma’a cikin gidan kaman yanda akeyi a baya....” Baba Wambai ya jinjina kai yana mai furta “Masha Allahu... Hakan yayi kyau Mahmuda, Ubangiji ya maka Albarka ya tsareka da tsarewarsa daga dikkan sharri da zai tunk’aroka...” Mahmood ya amsa da Ameen kana ya jefowa Baba Wambai tambayar da ya sanyashi d’agowa sosai yana dubansa... “Baba nikam nace ba, shin kasan lokacin da Ja’afar ya tafi ya bar Masarautar nan..? Shin dama Bawa na iya tsallake Masarautar su ne ya tafi wani wajen....? Shin Baba mai yasa Ja’afar ya tafi rana tsaka yabar Masarautar nan...? Kanada wata masaniya akai ne Baba....?” SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *017* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali Baba Wambai ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya kuma duban Yarima Mahmood a karo na biyu.... “Baba akwai wani abu ne...?” Mahmood d’in ya bid’a.. Baba Wambai ya girgiza kai a hankali alamun a’a kana yace “Banida masaniyar abinda ya fitar da Ja’afar daga Masarautar nan... Kaman yanda ka dawo ka tarar baya nan, nima kwatsam na fahimci baya nan, Mahmuda abubuwa da dama cikin Masarautar sai ayi ban sani ba... Inaga idan akwai wanda yafi cancanta ya amsa maka wannan tambaya taka toh ba kowa bace face mahaifiyarka, sai ko kuma Waziri....!” Ya k’arashe yana duban Mahmood d’in.... Shiru ya d’an gifta tsakani ba tareda ya kuma cewa komai ba, tabbas yana so ya nemo Ja’afar yanda ya shiga ya fita.... Ya kuma d’agowa ya dubi Baba Wambai kana yace “Na gode Baba, ni zan wuce...!” Yai maganar yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye... Baba Wambai ma k’ok’arin mik’ewan yake saidai tuni Mahmood ya taimaka masa ya mik’ar dashi tsaye had’ida rik’e hannunsa guda.... Lokaci guda suka nufi k’ofan gidan Baba Wambai a haka, yayinda Dattijo Wambai yaci gaba da fad’in “Sarkin gobe bazaka sha ko ruwa gidan Baban naka ba...?” Murmushi saman fuskarsa yake fad’in “A’a Baba na gode k’warai, Allah ya k’ara maka lafiya.....!” Baba Wambai ya amsada Ameen yana mai ci gaba da sakawa Mahmood Albarka, a daidai sanda suka iso Gate d’in gidan... Baibar k’ofar gidan ba har saida ya tabbata Baba Wambai ya shige ciki lafiya kana ya matsa daga wajen ya ciro wayarsa a aljihu yana neman layin Turaki... ** Giwa dake tsaye tana huci had’ida aikama Ubandoma dake duk’e gabanta jahilin kallo, lokaci guda Ta ambato sunan Ubandoman cikin wane irin kakkausar murya... Ubandoma ya risina yana mai amsawa had’ida kirariwa shugabar tasa... Giwa da kanta Ke sama tana duban wani gefen cikin tsananin k’unan rai taci gaba da fad’in “Zaka amshi horon mari daga hannun Jakadiya..!” Jakadiya da Ubandoma suka dubi juna a tare cikeda firgici.... “Jakadiya..!!!” Giwa Ta kuma ambato sunan Jakadiya cikin kakkausar murya... Babu shiri Jakadiya ta risinawa tana mai furta “Angama rankishi dad’e, Ubandoma godiya yake...!” yayinda Ubandoma ya baje babbar riga yana mai kuma neman gafara wajen Giwa, Jakadiya ta mik’e tana nad’e hannun rigarta su duka biyun duban juna suke itada Ubandoma... Yana k’yafata mata idanu had’ida had’e hannayensa biyu waje guda alamun neman afuwa... Gigirza masa kai kurum Jakadiya takeyi alamun batada zab’i... Ubandoma ya kuma risinawa yana fad’in “Rankishi dad’e a duba lamarin nan dai.. Ai mani aikin gafara bazan sake ba Allah shi taimakeki....!” Duban da Giwa tai masa ya sanyashi had’iye sauran kalaman nasa... Take Ubandoma ya soma karanto sunbatu cikin zuciyarsa yana mamakin Wai Jakadiya ce zata mare sa.... Aiko bai ida tinanin ba yaji sauk’ar wata jahilar mari a k’uncinsa wanda saida ya tafiyar masa da jinsa da ganinsa na wasu dak’ik’ai... . Ya dafe k’uncinsa a birkice yana kuma sadda kai k’asa yana fad’in “Tuba nake Allah shi taimakeki... Tuba nake sarauniyar Masarautarmu... Ki yafeni Giwar Amale...!” Giwa ta kuma takowa gabansa kad’an cikeda mulki da isa kana tace “Ka sanar dani Ubandoma shin kunje wani wajen ne...?!” Ya girgiza kai cikin sauri yana mai furta “Allah shi taimakeki tare muke a masallaci toh sai ya bani damin kud’i na rabawa mabuk’ata da musakai dake zama bakin masallaci... Daga nan na nemeshi na rasa Rankishi dad’e... Ko k’yallinsa ban kuma hangowa ba...!” Ya k’arashe yana mai kuma sadda kai k’asa har yanzu rik’e yake da k’uncinsa yanda Jakadiya Ta shata masa mari... Taci gaba da huci tana aika masa muguwar kallo, lokaci guda take ci gaba da fad’in “Sabida Mahmood d’in Aljani ne shiyasa zakace ya b’ace maka ko... Sau nawa zan sanar dakai koda wasa kada ka kuskura ka bari Mahmood ya b’acewa ganinka... Dik yanda Mahmood zai kasance ya zamana kaima kana wajen... Toh kan mai zaka Zo min da batu irin wannan...?!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci lokaci guda ta juya ta bada baya tana mai fad’in “Ubandoma..!!! Zaka karb’i horona mai tsanani idan har abu makamanciyar haka ta kuma faruwa...!!” Ubandoma ya kuma zubda kai k’asa yana mai ban hak’uri da neman gafarar Giwa, jikinsa har wane irin karkarwa yake... Alamu da ido taima Jakadiya kana Jakadiyar ta bud’e murya tace “An sallameka Ubandoma... A kiyaye ayi kuma hattara....!!” Ubandoma ya kuma risinawa yana mai mik’a godiyarsa tareda tabbatarwa Giwa hakan bazai kuma faruwa ba... Yana ficewa Giwa ta dubi Jakadiya dake zube k’asa a wajen kana tace “Jakadiya..!” Jakadiya ta kuma risinawa had’ida d’ago jannu guda alamun jinjina kana tace “Allah shi taimakeki...!” Giwa taci gaba da fad’in “Mai kike tunani kan Yarima Mahmood...?!” Jakadiya Ta kuma risinawa kana tace “Allah shi baki yawan rai Yarima Mahmood yaro ne mai biyayya tun tasowarsa...!” Giwa tai shiru tamkar mai nazari kana tace “Mai kike tunani idan ya tsananta bincike...?!” Wannan karon a firgice Jakadiya ta d’ago tana duban Uwar gijiyar tata kana ta kuma maida kanta k’asa, cikin daburcewar murya take furta “Bazai fahimci komai ba Rankishi dad’e... Amma saidai... Ina tsoron ranan da zai tono sirrikan da muka jima da aza masu k’as.....” Batakai aya ba Giwa ta dakatar da ita da fad’in “Jakadiyaaa.!!” Cikin sauri Jakadiya ta rik’e labb’an bakinta duka biyu tana mai furta “Tuba nake Allah shi taimakeki... Yarima Mahmood bazai tab’a tono komai ba... Amma Rankishi dad’e idan har ya tabbata Sarki na gaba komai ai ka iya faruwa....!” Wannan k’asaitaccen murmushi Giwa tai kana tace “Inada manufata da yasa nake so lallai lallai shine zai d’ale Karagar mulkin a daidai wannan lokaci.... Tal’udu bazai tab’a min K’arya ba Sarautar bazata fice daga cikin Ahalin Mijina ba....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin murmushi had’ida kishingid’a cikin gadon mulkinta.... *** Da tsananin mamaki Turaki ke dubansa hannu a kunkumi, lokaci guda yake furta “Unbelievable..! Wai dan Allah your Highness kaine haka...? Shikenan daga Spain ka koma Niger....!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa... Mahmood yace “Ina ka aje motar...?” Turaki yai masa nuni da motar dake pake tsallaken kwalta... Yarima Mahmood yace “Muje da Allah kafin wani yai noticing d’inka ma...” Bai ko jira amsar Turaki ba yasa kai ya nufi motar... Turaki yabi bayansa da kallo yana furta “Mahmood mai abin mamaki...” Lokaci guda ya girgiza kai yana mai sakin murmushi kana yabi bayan abokin nasa.... Daidai nan motar Majidad’i D’an wajen Baba Wambai mai neman sarautar Ta shigo kwanar... Bayan Turaki kawai ya hango ya gane abokin Yarima Mahmood ne... Toh mai ya kawo abokin Yaima Mahmood gidansu...? Kardai Mahmood ne ya turosa wajen Mahaifinsa dan su kuma saye zuciyar Mahaifin nasa su kuma karkatar da ra’ayinsa... Lallai Mahmood baisan ko Shi d’in wanene ba har yanzu... Bazai yuwu ya shiga tsakaninsa da mahaifinsa ba ya hanasa amshe gadon sarautar Kakansu da Uban Mahmood yai fin k’arfi wa mahaifinsu....Toh idan za’a tashi Masarautar wllhi sai ya amshe mulkin gidan daga hannun ‘ya’yan Abduljabbar..... Da wannan tunani ya isa Gida, ko parking mai kyau bai ida ba ya fito yana tafe yana sakin huci kaikaice tafashesshen Koko ne.... Ya iske ma’aikatan gidan tsakar gida suna gaidasa ko ci kanku baice dasu ba ya nufi b’angaren mahaifiyarsa tamkar zai kifa da k’asa, yana tafe yana k’walla mata kira... “Innani..! Innani..!! Innani...!!!” Budurwa mai kimanin shekaru 26 wacce ke kwance bisa kujera mai d’aukan mutum uku itace Ta amsa masa da fad’in “Kai Yaya irin wannan kira saikace Aunty Jamila ce ko kuma Yasir ko Nimra ne ka rasa d’aya cikinsu.. Ni wllhi ka razanen...!” Ta k’are ashe baki a ture.. Majidad’i yace “Ke Juwairyya ni ba sa’anki bane zakiyi ma sarki magana haka ne...?” Juwariyya ta zaro ido waje had’ida k’ame baki “Tabb Yaya ai wllhi dama hak’ura Kai dan...” Batakai aya ba ya bige bakinta yana fad’in “Sai na karyaki na sake jin kince banyi zubin sarakuna ba... Ina Innani take...?!” Juwariyya na k’unk’uni rik’eda bakinta ta nuna masa hanyar bene.... Daidai sanda Majidad’i yakai dubansaga b’angaren benen Dattijuwar mai k’aramin jiki irin masu suffan mafad’atan nan ta fito tana gyara d’aurin kwali take fad’in “Yaya Wai yaya akai ne...Sarkin gobe Kai kuma fah, lafiya daga Ina haka.. Waye ya b’ata maka rai inyi...?!” Juwariyya dai ficewa tai tana ci gaba da k’unk’uni... Lokaci guda kuma ta lab’e jikin k’ofa tana sauraran tattaunawan Yayanta da Mahaifiyarta.. Majidad’i na sakin huci yake fad’in “Innani uban mi ya kawo Mahmood gidan nan...?” Innani ta dafe k’irji tace “Mahmuda fah... A’a badai shi ka gani ba don baizo gidan nan ba...” Majidad’i bai daina tururi ba yake fad’in “Ba yanzu naci karo da abokinsa waje ba...!” Innani dafe da k’irji take girgiza kai kana tace “A’a bakadai duba da kyau ba... Yo Mahmuda yazo gidan nan yamin mai balle har abokinsa...!” “Ai dama ba wajenki zaizo ba wajen tsohon nan mai d’aure masa gindi da zigasa zai zo shi....!” Innani ta girgiza kai tace “Kai Majidad’i ka b’ata gani, yau bak’o guda Babanka yayi tun wayewar gari kuma bak’on Buzu ne... Ka kwantar da hankalinka Majidad’i ko Mahaifinka baya so sai kayi sarauta kaji koh... Haba ni da na tabbata Mahmood da ‘yan uwansa kashe juna zasuyi sabida fitinan son mulki.... Kaga cikin sauk’i zakayi sarauta.. Su Turai a fice a bamu waje, yanda nake ‘yar tsurut d’in nan haka zan fitar da Giwa daga gidan wayaga cinnaka ta kori Giwa...!!” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya... Yayinda d’an nata ya bita da kallo yana mai ci gaba da sakin huci a hankali... Juwariyya na gama nad’e komai ta koma gefe ta zaro wayarta take ta shiga neman layin Raheema...! *** Kasancewar duk daren Juma’an k’arshen wata Ahalin Giwa na hallara gaba d’aya a sashenta da daddare don cin abinci a farfajiyan b’angaren nata yanda ake k’awata wajen da manyan dardumai da kuma pillows na alfarma had’ida k’awata wajen da ado da kwalliya irinta alfarma yasa sai shirin fita taron suke.. Muhibbah ta dubi Umaima da mamaki kana tace “Kuma Wai Hakan a’adan gidan nan ne... Toh maiyasa ni zanje tinda Ahalin cikin gidan nan ne kawai Ke hallara...” Umaima tace “Ke bak’uwarmu ce dan haka har zuwa lokacinda zaki tafi ki bar gidan nan ki dinga lissafin kanki cikin Ahalin gidan nan, ai dai kinji mai Maami tace, bazataji dad’i ba idan bata ganki wajen ba....” Muhibbah tai shiru tamkar mai nazari, hakan na nufin zata had’u dasu kaf d’insu kenan a daren nan.... What if ta kasa jurema hakan har tai wani abinda zata fallasa kanta..? Take taji b’angare na zuciyarta na k’arfafa mata gwiwa da fad’in zaki iya Saudat.... D’agowa tai ta d’an dubi Umaima murmushi saman fuskarta kana tace “Shikenan na amince zanjeni...” Umaima ma Ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa ko kefa yanzu naji batu...” Take Umaima ta fito masu da kaya irinta mulki da sarauta tace shi zasu saka... Muhibbah ta dubeta ta dubi kayan... Kafin tai magana Umaima tai saurin katseta da fad’in “Don’t say anything Hibbah... Tashi kawai ki shirya bara nayi wanka Zahra ma na shiryawa already....” Ta k’arashe tana mai fad’awa bathroom yanda Ta bar Muhibbah tsaye nan cikin closet d’in rungume da lallausar Cotten lace kalar ja anyi masa ado da duwatsu masu d’aukan idanu anyi mata d’inkin doguwar riga irin mai bajewa daga k’asa... Ga wani mayafi mai k’yalk’yali da d’aukan idanu jikin kayan... Murmusawa Ta d’an kumayi kana ta saka rigar kaman yanda Umaima Ta buk’ata.... Ya Subhanallah! Sosai rigar ya zauna jikinta, ita kanta saida ta jita wane iri cikin kayan... Ita kanta saida ta yaba kyaun da kayan yai a jikinta sanda ta dubi kanta jikin marfin wardrobe d’in da yake zallan madubi ne... Tsaf Ta ida shirinta ta nufo parlor sai watsa k’amshi take, ita kanta tasan tayi kyau dukda babu kwalliya a fuskarta.... Tai tsaye a parlorn tana kallon wani hoton zane na ginin gidan sarauta dake lank’aye jikin garu nan cikin parlorn tsakanin D’akin Umaima da Zahra.... A haka Umaima ta gama shirinta itama ta fito.. Tai tsaye tana duban Muhibbah dake bin zanen ginin da kallo cikeda nastuwa tamkar mai nazarin wani abu.... Umaima ta k’araso tana fad’in “Wai dama Kina tsaye a parlor...? I thought kina tareda Zahra...” Ta murmusa kad’an had’ida juyowa tana duban Umaima da Ta fito cikin shiri kana tace “Ina tsamman Zahra bata gama shiri ba dan banga fitowar Kuyangarta ba...” Umaima Ta jinjina kai a hankali tana duban hoton zanen gidan Sarauta da Muhibbah ta tsaresa da idanu kana tace “Wannan hoton Yarima Jamaludden naji dashi sosai... Kyautarsa aka basa sanda yai rakiyawa mahaifinsa zuwa wata masarauta a cen k’asashen nahiyar Yamma...!” Jinjina kai Muhibbah tai tana mai kuma duban hoton da yake k’unshe da wasu sirrika kana tace “Duk wanda ya zana tabbas ya iya zane...” Umaima ta jinjina kai “Sosai kuwa, ai kyautace ta musamman akaiwa d’an Sarki...” Muhibbah Ta kuma jinjina kai kana tace “Amma Maiyasa Yarima Jamal ya lank’aya hoton a nan dik irin mahimmancin da hoton kedashi a gareshi... Ya kamata hoton ya kasance yana kusa dashi ne...” Ta k’ara tana mai tsare Umaima da idanunta da suke farare k’al wanda suka dace da cute round face d’inta... Umaima da tai shiru tamkar wacce tai nisa a wani duniyar na tunani a hankali ta soma takowa ta k’araso gaban hoton... Lokaci guda tasa hannu tana shafawa, hannunta nakan hoton take furta “Kasancewata masoyiyar zane ko wanne iri yasa ya aje hoton a nan, da fari naso ya bani kyauta amma ya sanar dani mahimmancin hoton a gareshi don haka ya aje a nan don na dinga gani....!” Muhibbah ta jinjina kai a hankali tana mai kuma nazartan wannan zanen gida mai dadd’en tarihi da aka yishi da wane irin fasaha mai rud’ar dakai... Dan kashi dai zanen gidan sarauta ne mai kyaun gaske amma baka isa kace ga k’ofar shiga ba dukda cewa ta wata fuskar idan ka dubi zanen zakaga kaman ga k’ofofi rututu amma idan ka matso sosai k’ofofin zasu b’acewa ganinka sai Kaga Tamkar kwalliya ne ba k’ofofi ba.... Tana nan tsaye tana kuma nazarin hoton taji muryar Umaima na fad’iwa Zahra “Yauwa kin fito, dama fitowarki muke jira... Muje Hibbah...” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Muhibbah da har lokacin bin wannan hoto takeda kallo... Zarah kaw sai yaba kyaun da Muhibbah tai take Umaima na tayata, ita kaw Muhibbar bama tasan sunayi ba dan har wanna lokaci nazarin zanen nan take.... Suna tafe bisa matakala suna sauk’owa Zahra Ke fad’in “Nifah Aunty Umaima wllhi banson Kuyangar nan da Maami tace lallai lallai ita zatake kula da al’amra na, nifa ban saba haka a Spain ba, nafi ganewa nayi komai da kaina daga ni sai Paa d’ina....!” Ta k’arashe baki a ture daidai sanda suka ida sauk’owa Kuyangar kaw na biye dasu kai a k’asa... A daidai sanda suka ida sauk’owa daga matakalan benen Umaima ta d’agawa Kuyangar hannu alamun ta daina binsu kana ta dubi Zahra tace “Aiko hak’uri zakiyi Gimbiya, dan nan da spain ba d’aya bane... Sannan a wannan stage d’in da kike dama dole a miki assigning Kuyangar da zatake kula dake da kuma al’amaranki musamman da shike babu mahaifiyarki a raye...!” Ta k’arashe cikeda tausayawa... Kalaman Umaima na k’arshe ya sanya Muhibbah juyowa kad’an tana duban Zahra cikeda tausayawa musamman da taga yanayin da fuskar yarinyar ya shiga.... Hannun Zahra ta kamo kad’an kana tace “But you’ve your Grandma, and your Paa, ga kuma Uncles d’inki sanan ga Auntynki Umaima... Kuma duka suna sonki kinji koh...!” Ta k’arashe tana k’ok’arin cheering yarinyar... Murmushi Zahra ta saki a hankali kana tace “Thanks Aunty Muhibbah... Amma saidai kin mance da mutum guda...!” Muhibbah ta d’an zaro ido kad’an kana tace “Wa kenan...?” Umaima tai karaf tace “Raheema matar Paa d’inta....” Take annurin fuskar Zahra ya d’auke lokaci guda take furta “No, bana sonta, kuma bana so Paa ya aureta.... Ni ke nake nufi Aunty Muhibbah, kin manta baki lissafo kanki ba cikin wad’anda nake dasu a yanzu...” Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Aw ai gani nayi ni ba jimawa zanyi a Masarautar ba shiyasa... But Kiyi hak’uri kar Ki d’auka da wani nufi kinji.... You’ve me as well..!” Ta k’arash murmushi fal fuskanta.... Cikeda jin dad’i Zahra ta rungume Muhibba tana fad’in “Gracias Tìa Hibbah....!” Ta murmusa itama kana tace “Wait mai kikace kinsan bana jin Spanish...” Zahra ta rausayar da idanu kana tace “Well, Assignment...!” Muhibba ta girgiza kai kana tace “No way... I hate assignments... Nadai San Gracias godiya ne but Tia... Ban sani ba....” Zahra ta d’an kuma darawa kad’an had’ida yin fari da idanu kana tace “Tia Sabon sunan da zanke kiranki dashi kenan.... Tia means Aunt in Spanish...” Suka d’an dara gaba d’aya a tak’aice harda Umaima daidai lokacinda Raheema ta shigo parlorn Kuyangarta na biyeda ita a baya.... Cak Ta tsaya tana dubansu yanda suka cika da Farin ciki gwanin ban sha’awa... Zuciyarta ta soma mata zogi, hannu ta d’agawa Kuyangar nata alamun dakatarwa kana ta soma takowa garesu cikeda k’asaita..... SameenaAleeyou 📚[6/14, 6:09 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *018* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Raheema na K’arasowa tai k’ok’arin d’aura fake smile saman fuskarta mai cikeda k’asaita, a daidai lokacinda Umaima tai noticing d’inta.... Umaima ta tareta da fad’in “Barkada isowa Gimbiya Raheema kuma matar Yayanmu....!” Tai maganar murmushi fal fuskarta... Dik sanda aka ambaceta da matar Mahmood ji take kanta na kuma fashewa, tana jin wani irin dad’i can k’asar zuciyarta... Ta d’an fad’ad’a murmushinta had’ida furta “Barkanki Gimbiya Umaima kuma k’anwar mijina....!” Suka kuma murmusawa a tare kana Raheema ta kaikaito tana duban Zahra da tai kaman bataji isowar mutum wajen ba... Ta d’an tako zuwa gaban Zahra kad’an kana tace “Daughter ya jikin naki.... I’m glad you’ve recovered....!” Ta k’arashe cikeda kulawa Rausayar da idanu Zahra tai kana tai wasu ‘yan maganganunta cikin harshen spanish sannan ta sakarwa Raheema murmushin yak’e tace “Oh really... Well thanks then.. If you’re really sincere...!”Ta k’arashe tana mai janyo hannun Muhibbah had’ida furta “Tia Hibbah muje, let’s sit together... There’s a lot more I need to know about you....” Ta k’arashe murmushi fal fuskanta yayinda Muhibbah ta saci kallon Raheema dake binsu da wane irin kallo kana Ta maidoda dubantaga Zahra tana mai ci gaba da amsata cikeda Farin ciki... Fuzar da huci kad’an Raheema tai daidai sanda wayar salularta ya soma ringing... Gimbiya Zeenat ce mai kiran nata.... Rai b’ace ta d’aga wayar... Daga d’aya b’angaren Gimbiya Zeenatu tace “Kina ina...? Maza kizo ina nemanki...!” Bata jira amsar Raheemar ba Ta katse kiran..... Rausayar da idanu Raheema ta kumayi tana hangen su Zahra da Muhibbah daga nan yanda take tsaye ta cikin k’ofar glass sai raha suke daga cen yanda suke zaune a farfajiyan haraban.... Ta kafe Muhubbah da wani irin duba na tsana kana Ta juya ta fice Kuyangarta na take mata baya... Tana isa ta tadda Gimbiya Zeenat a d’aki sai faman safa da Marwa take... “Aunty lafiya irin wannan kira haka....!” Muguwar kallo Gimbiya Zeenat ta watsa mata kana tace “Raheema Wai lafiyarki kuwa.... Kan wane dalili zaki k’i d’aga wayar Juwariyya bayan kinsan kalan information d’in da muke samu daga wajenta.... Sanin kanki ne wannan Majidad’in ba yarda da uwarsa mukai ba, na tabbata ko asiri sai tayi dan d’anta ya d’ale Karagar mulkin nan... Mu kuma babban burinmu shine Mahmood ya sami mulkin domin mu sami yanda muke so... Amma kan mai Juwariyya data juyawa ‘yanuwanta baya zakiyi banza da kiranta harda baiwa Kuyangarki wayar kice bakida lokacin d’agawa... K’ilan baki son mijin naki ya sami sarautar ne koh...?” Ta k’arashe tana kuma aika mata wani duban... Fuzar da fuci kad’an Raheema tai kana tace “Allah Aunty na zaci wani abinne... Yo kan wannan ne dama...?” Gimbiya Zeenat ta kuma watsa mata harara kana tace “Ban fahimceki ba, wannan d’in k’aramin abu ne... Muna magana ne kan sarautar mijinki Raheema...!” “Aunty nifa yanzu ba sarautar Mahmood bane gaba na... Wllhi ni yanzu na mallakesa gaba d’aya shine damuwata da sarauta ko babu sarauta... Ni shi d’in kawai nake so na mallaka, babu ruwana da wani sarauta ko rashinta as long as he’d remain mine, ni kad’aina and no body else’s...!” Ta k’arashe tana sakin huci... Shaye da tsananin mamaki Gimbiya Zeenat Ke dubanta kana tace “Eh lallai na yarda...! Toh barikiji na fad’a miki, wllhi wllhi bazan zauna na zuba miki idanu Ki rusa min plans d’ina ba... Dole Mahmood yai sarauta dan idan ya aureki bai a matsayin Sarki banga amfanin auren ba.... Dan haka dole kici gaba da baiwa Juwariyya had’in kai tana kawo mana rahoton dik abinda Ke wakana cikin gidansu...!” Daga haka Gimbiya Zeenat tasa kai zata shige... Raheema ta katseta da fad’in “Aunty duk bazaki fahimci Abinda nike nufi ba, amma idan kika fita kikai tozali da shegiyar yarinyar nan mai bak’in shishigin masifa da nake baki labari zaki yarda ba yak’in neman mulkin Mahmood bane gabanmu yak’in raba wannan tsinanniyar da Masarautar nan ne babba gabanmu....!” Ta k’arashe tana mai k’arasowa gaban ‘yar uwar tata.... Dubanta kurum Gimbiya Zeenat tai kana ta saka Kai Ta shige dan ita bama ta d’auki maganan Raheema da mahimmanci ba, yo har wata tsiyace zatazo ta tsone masu idanu bayan suna d’iyoyin sarki jinin sarauta gaba da baya... Ta tabbata shashanshanci ne kurum irin na Raheema ba wani abu ba.... ** Daga yanda suke zaune su Duka ukun Sun kafeta da idanu Fu’ad yai gyaran murya kad’an kana ya furta “She’s different...! Way too different, bansan a wani sahu zan ajeta ba... But her beautiful eyes sunada matuk’ar gizo ka dubi cikinsu and tell her how exactly you feel about her....!” K’asaitaccen murmushi Yazeed yai yana mai jefa grapes cikin bakinsa kana yace “While you’re here thinking of how to approach her... prince Yazeed already had body contact with her..!” Ya k’arashe yana mai kuma daidaita kishingid’arsa shu’umin murmushin saman fuskarsa, yanayi yana shafar hab’arsa Daga Fu’ad har Jamal dubansa sukai da tsananin mamaki... Jamal yace “Yazeed mai kake nufi... Wai kana nufi har ka mata magana...?” Murmushin bata bar saman fuskarsa ba, idanunsa kan Muhibbah da ko shakka babu a tsarge take a wajen dan tasan ‘ya’yan Sarkin ita suke duba probably ma magananta suke... Yazeed yaci gaba da fad’in “Prince Yazeed never fails...! Kuma babu macen da Ta tab’a rejecting d’insa duk fad’in duniyar nan.... And believe me, she and I have an unfinished business...!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushin nasa.... Girgiza kai Jamal yai kana yace “But you’ve your own wife Yazeed... Kar ka b’ata mata lokaci...” A kaikaice yake dubansa kana yace “Did you hear yourself Jamal... B’ata lokaci fah kace... Ka mance ni namiji ne, I’m entitled to 4 wives Jamal, Shari’a Ta yarje min nayi hud’u kuma idan na zama Sarki dik mace mai kyau dake cikin Masarautar nan Ta zama Kuyangata, sun zama nawa sai abinda naga dama nayi dasu... Kai duk mace mai kyau idan ta shigo Masarautar nan ta zama baiwata dokan da zan zartar kenan....!” Jamal ya murmusa kana yace “Dama k’ara auren kai ka dena b’ata lokacin ‘ya’yan mutane....” Yazeed ya tsaresa da fad’in “Correction! duk su suke kawo kansu babu wacce na tab’a bi....!” D’an girgiza kai Jamal ya kumayi kana yace “But still your Highness ya kamata a duba lamarin....” Fu’ad ya katsesu da fad’in “Leave Muhibbah out of this Prince Yazeed, don’t you dare try that with her...!”Yai maganan yana sakin huci.... Duban da mai kiwon kare keyiwa sabon kuikuyo da kariyarsa Ta haifo masa yai ma Fu’ad kana yace “Looks like those pills you’ve been taken ya maidaka mahaukaci na gaske... And here I thought kafin mu fito wajen nan, I made it clear to you boy, that you should be in your best behavior tonight..!! Don’t tell me kasha kayan haukan kafin ka fito nan...?!” Jamal ne yai saurin katse zancen da fad’in “Wai ina Yaya... He should be here by now...!” Daga Yazeed har Fu’ad babu wanda ya amsashi saima aikama juna muguwar kallo mai had’eda huci da suke faman yi.... Yazeed ya saki cruel smile d’insa kafin ya maida dubansaga Muhibbah wacce itama shi take duba wannan lokacin... Daidai sanda Gimbiya Zeenat da Raheema suka k’araso wajen... Idanunsu k’yam kan Muhibbah Raheema na sanar da ita cewa ta dubi abinda take sanar da ita da kyau.... Su duka biyun duban Muhibbah suke, itama d’in su take duba Kuyangi har kusan guda uku biye dasu.... Suna k’arasowa Rumfar da aka tanadar masu suka k’arasa, kaman yanda yake a al’adarsu ba’a gaishe gaishe har sai Giwa ta iso ta zauna kafin kowa ya mik’e ya kai mata gaisuwarsa saiko sauran jama’a a gaisada juna..... Jim kad’an kuwa mai gayya Ta samu hallara, tawagarta guda biyeda ita, kaga yanda ake karramata ake bata girma abinda tafi k’auna a rayuwarta... Fadawa kuwa sai kod’ata suke suna wasata tamkar wata bakin wuk’a.... Bayan ta zauna a nan mazauninta wanda yake gefen na Gimbiya Zeenat kowa ya soma tasowa yana kawo tasa gaisuwar.... Sukanyi irin wannan royal gathering d’in sau d’aya ko wacce wata, dik juma’a da take zuwa a k’arshen wata hakan sukeyi, so kowa ya saba da had’uwar... Hardai aka soma ciye ciyen abinci Muhibbah Ta kula bataga Zuhra matar Yazeed da yaransa ba, sannan ko k’yallin Yarima Mahmood ma bata gani ba.... Tana tsaka da tinanin taga Giwa tai alamawa Jakadiya... Babu b’ata lokaci Jakadiya ta isa rumfar su Yarima Yazeed tai masa iso da mahaifiyarsa.... Dikda Muhibbah bata iya sauraron abinda Giwa da Yazeed Ke magana akai ta tabbata bazai shige kan rashin ganin iyalinsa da batai wajen bane... Ba Muhibbah kad’ai ba harta Raheema ta kula da wani abu... Tasan kad’an ne daga cikin aikin Yazeed ya hana Zuhra da yaranta halarta wannan waje, tsaf tasan ko wanene Yazeed ba mutunci bane dashi... Yanzu haka wani abin Zuhra tai ya hanata fitowa.... Tana gani ya kirawo Hauni babban bawansa yai masa magana bayan mahaifiyarsa tai masa magana... Cikin sauri Hauni ya mik’e ya fice yana sab’a babban gyare.... Jim kad’an bayan ficewarsa saiko gashi nan ya shigo tafeda yaran Yazeed guda Sultan da Noor.... Su duka biyu cikin shiga Ta alfarma da sarauta... Suna k’arasowa suka tafi wajen Kakarsu a guje suka zauna cikin jikinta... Giwa ta rungume ‘yan jikokinta tana sumbatar kawunansu.... Daga yanda Muhibbah ke zaune ta gama karantar komai, Wato dai maganar da Giwa sukaida Yazeed bai shige kan rashin ganin matarsa da yaransa wajen bane kenan, har saida Giwa tai magana sannan ya bari aka kawo yaran... Toh matarsa Fah..? Shin mai yasa ya hanata..?? Tambayar da taita wa Muhibbah Yawo a kwanya, lokaci guda tana hankalta da irin duban da Yazeed da Raheema Ke aikawa juna tsakaninsu.... She really needs to figure something out... Idanunta suka sauk’a zuwa kunnen Raheema.... Tabbas earrings d’in wannan sark’a data tsinta ne daga aljihun Yazeed... Wato dai da gaske hasashenta ya tabbata, Yazeed da Raheema sunyi tarayya wajen cin amanar Zuhra... Tabbas b’atan basira ne ya sanya Raheema saka wad’annan ‘yankunnen.... Tana nan zaune tana tinanin taga Raheema tai alamawa Yazeed da idanu kana ta mik’e ta nufi wani k’ofan daidai sanda hankulan mutane ya karkarta zuwaga cin abinci... Jim kad’an taga Yazeed ya mik’e yabi bayanta... Ta waiga gefe da gefe tana tinanin abinyi... Tana jin Umaima na tambayarta mai zataci amma sai ta rik’e mararta kad’an tace “I’ll use the restroom first, Ina dawowa bada jimawa ba....” Umaima ta jinjina kai tana mai furta “wait kinsan hanya ko nai assigning wata cikin kuyangi tai miki rakiya....?” Muhibbah ta girgiza kai murmushi saman fuskarta “No karki damu ai dai yanzu Bazan b’ata cikin gidan nan ba na fara sabawa I guess...” Sukai murmushi su Duka biyu kana Muhibbah tai saurin bin hanyar da taga Yazeed da Raheema sunbi.... Tana tafiyar tana sand’a had’ida waige waige.... Cen ta soma jiyo muryoyinsu a hankali.... Tai saurin k’arasowa yanda take jin sautin muryoyin nasu na fitowa... Gabanta ne yai mummunan fad’uwa ganin irin yanayin data hangi Yazeed da Raheema ciki... Sun fice hayyacinsu gaba d’aya kaman zasu cinye bakunan junansu.... Tai saurin komawa da baya had’ida rintse idanu tana mai sakin ajiyan zuciya a hankali... Banda Innalillahi da tir da Allah wadai zuciyarta bata iya komai... Ta mak’ale nan wajen tana sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Dan harga Allah ta razana da abinda idanunta ya gano mata... Cen kuma sai ta soma jiyo muryar Raheema na fad’in “Enough Yazeed... Please ya isa haka ka mance ina muke ne...?” Yazeed da bai cikata ba yaci gaba da fad’in “And so what....! Tsoron wannan lusarin husband to be d’in naki kike ya ganmu ko kuwa k’awarki aminiyarki kike tsoro ta ganmu....?!” Turasa ta d’an kumayi tana fad’in “Duka ba laifi bane idan naji tsoron faruwan hakan... Yazeed please Zuhra doesn’t deserve any of this...Wllhi tausayi take bani... Tana matuk’ar k’aunarka bai kamata kake tsnanta mata horo don ta nuna damuwa akanka ba... Sanin kanka ne idan Ta rubuta wasik’a ta fad’i halinda take ciki a Masarautar nan Ta tura tasu Masarautar komai ka iya faruwa... You might lose your wife Yazeed... Watak’ila harda yaranka...!” Murmushi ya saki yana shafan gefen fuskarta kad’an kana yace “Babu wanda ya isa yaga downfall d’ina because I am Prince Yazeed AbdulJabbar... Sarki mai jiran gado.... Zuhra tawa ce, kuma bazata tab’a aikata abinda kike tunani ba... Idan na riga na shiga rayuwar mace bazata tab’a iya rabuwa dani ba kuma har abada... Kaman yanda kema bazaki iya rabuwa dani ba koda bayan kin aure Yaya na...!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa.... A hankali Muhibbah ta soma jada baya zuciyarta naci gaba da bugawa... Tana tafe da baya da baya bata ankara ba Ta bangaji flower vase ya fad’i k’asa.... Ta kame bakinta had’ida zaro idanu...Tai Saurin mak’alewa jikin gini tana jira mai aukuwa ya auku... Tana ganin sanda suka fito daga mab’oyar tasu suna lek’e lek’e kasancewar basuga kowa ba yasa suka kuma komawa yanda suka fito.... Tai saurin fitowa ta fice daga wajen gaba d’aya bata daina waige waige ba... A daidai hanyar da zai fiddaka haraban wajen suka kusan yin kar da mutum yana tafe waya manne kunnensa.... Ta juyo a firgice had’ida rintse idanu alamun tsoro sai kuma ta shiga basa hak’uri idanun nata a lumshe “Sorry sorry sorry... Dan Allah kai hak’uri wllhi banga isowarka ba...!” “Muhibbah..!” Ya ambato sunanta yana mai dubanta cikeda mamaki... Jin muryarsa ya sanyata had’iye sauran kalaman nata ta kuma kasa bud’e idanu sai kunyan kanta ma da ta soma ji ganin irin firgitan da tai lokaci guda.... Yarima Mahmood ya saki murmushi a hankali yana mai duban yanda ta kasa bud’e idanunta.... “Are you alright...!” Ya tambaya yana mai dubanta cikeda kulawa.... Sai lokacin ta d’an sami zarafin ware idanunta kana ta sadda kanta k’asa tace cikin sanyin murya “Lafiya nake your Highness... Am... I’m sorry Your Highness, ban San kana tafe bane....!” Tsareta da idanu yai kana ya d’an murmusa kad’an sai kuma yace “Yanayinki yafi kama da yanayi na tsoro...kaman wani abin gudu ne ya biyoki a guje...?!” Tai k’arfin halin d’ago idanunta had’ida waresu murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta take furta “No..no Your Highness babu komai...!” Baisan dalili ba amma harga Allah ganinta ya sanaya shi nishad’i musamman d’abi’unta da yanda fuskarta Ke komawa idan taji tsoro... Gashi dai sau biyu suka tab’a had’uwa kuma duka da dare ne amma zai iya cewa k’wayan idanunta daban suke a cikin nashi idanun... Yanayi na tsoro yana matuk’ar k’ara masu kyau.... Jin kaman bazai magana ba yasa Muhibbah fad’in “Tuba nake Rankashi dad’e...!” Ya d’anyi gyaran murya a hankali had’ida maida hannayensa duka baya kana yace “Ina kika nufa....?” Ta d’ago tana k’ok’arin yi masa alama da hannu saidai gaba d’aya ma gani tai kaman ta b’ata hanyar... Gaba da’aya sai ta daburce tama rasa inane hanyar... Ya kuma murmusawa a hankali yana mai jefa wayar salulansa cikin aljihun wandon kayan sarautarsa kana yai gyaran murya cikin dakewar murya “Looks like Princess ta b’ata cikin Fada trying to rescue her prince....!” Ta d’ago da tsananin mamaki tana dubansa tamkar bashi yai maganar ba, da alama babu yanayin wasa a fuskarsa sannan wani b’angaren ma yake duba...sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Muje na fitar dake... But next time Ki kiyaye kisan ina kike zuwa...!” Godiya ta kuma masa kana tabi bayansa sad’af sad’af kaman wata munafuka kanta a k’asa.... Giwa da gaba d’aya ta soma jin kaman wani abu na mintsilinta, gaba d’aya kasa sukuni tai a wajen... Take hannunta na hagu da ko yaushe rufe yake cikin wani bak’ar safa ya soma mata k’aik’ayi.... Takai dubantaga Jakadiya wacce tuni Ta fahimci halin da Uwargijiyar tata ke ciki.... Tai saurin k’arasowa gareta had’ida kwanto da kanta alamun jinjina da gaisuwa a zahiri... Saidai su biyu d’in saiko mahaliccinsu ne suka san abinda suke tattaunawa.... Cin abincin da ba’a ida taredasu ba suka bar wajen.... A b’angaren Gimbiya Zeenatu kaw K’uri tai masu sanda suke k’arasowa, tabbas gabanta ya fad’i sanda Ta hangi Yarima Mahmood tace da wannan budurwa, sai yanzu take ganin ashe ba laifin Raheema bane da ta tada hankali kan yarinyar... Tin yaushe ake jajen isowar Yarima Mahmood sai gashi ya k’araso tareda wannan yarinyar... Ita data tura Raheema taje ta nemo Mahmood yanda ya shiga ya fita su taho tare, gashi tana cen tana sakarci wannan shu’umar ta samosa... Waima ina Raheema ta tsaya...? Amsar data kasa samowa... Cen kuma ta hange mazaunin Yazeed babu kowa, fuci ta saki a hankali tana mai girgiza kai... Sarai ta sani wajen d’an iskan cen Yazeed ta makare... Tabbas sai ta koyawa Raheema hankali yau d’in nan basai gobe ba... Cikin tsananin k’unan rai ta mik’e tai tafiyarta itama Kuyanginta na biyeda ita.... Yayinda Zahra dasu Sultan su Noor yaran Yazeed suka kewaye Yarima Mahmood kowa yanaso ya sauraresa hakan ya baiwa Muhibbah daman silalewa ta isa gefen Umaima ta zauna tana hango tsananin k’aunan yaran gaba d’aya a fuskar Mahmood.... Maiyasa takeji cen k’asar zuciyarta shid’in yanada wani kyakkyawan hali cikin mutane gaba d’aya wanda ba kowa Keda irin wannan halin ba...? Maiyasa takejin tsira da kwanciyar hankali a duk sanda ta kasance tare dashi... Daren jiya bayan tattaunawarsu sosai ta sami natsuwa cikin zuciyarta, sannan yanzu datai zaton su Yazeed zasu kamata bayyanarsa sai ya jefata cikin nastuwa da kwanciyar hankali.... Bugu da k’ari alak’arsa da mutanen Masarautar gaba d’aya ko shakka babu yanada kyau....Toh maiyasa ya kasance azzalumi daga fari...? Kasa samun amsar tai sai wani b’angare na zuciyarta dake raya mata.. Ba’a canza wa tuwo suna... Watak’ila wannan nasa salon kenan na yaudara... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tanajin tsanarsa na kuma taso mata daga cen k’asar zuciyarta lokaci guda.... Saurin kawar da fuskarta tai Daga barin dubansa hakan yai dai dai da hango Raheema da tai tana k’ok’arin k’arasowa wajen sai waige waige take kana ganinta Kaga maras gaskiya.... Muhibbah ta kafe Raheema da idanu yanda take bin Yarima Mahmood da Mayen kallo, ko ba’ace ba so take taje wajensa saidai hakan ba mai yuwa bane kaman yanda yake a tsarin gidan... Idan d’an sarki na neman aurenki koda kina rayuwa cikin gidan kai tsaye bazaku keb’e ba har sai Jakadiya tai iso an shirya had’uwar ta musamman kafin ku gana... Lokaci guda Raheema Ta maidoda dubanta ga Umaima da Muhibbah dake cakalan fruits d’in gabanta tamkar wata mai tausayinsu.... Cikeda k’asaita Ta soma takowa garesu... Umaima ce ta tarbeta da fari’a yayinda Muhibbah ke binta da kallon k’yama bayan abinda Ta gani tsakaninta da Yazeed.... Murmushi saman fuskar Raheema take duban Muhibbah, nan taga hankalin Muhibbar naga Zahra da mahaifinta yanda take serving d’insa abinci ba tareda ta bari wata baiwa tai masa ba.... Bud’e murya Raheema tai kana tace “Sun burgeki koh...?” Da mamaki Muhibbah ta kaikaito tana duban Raheema dake ci gaba da sakin shu’umin murmushi.... Lokaci guda Muhibbar ma ta d’aura murmushi saman fuskarta kana tace “Duk wanda ya dubesu dole su burgesa sannan kuma yai masu fatan su tabbata a haka ba tareda wani ya shiga tsakaninsu ya zamto sanadiyan lalacewar wannan kyakkyawan alak’a dake tsakaninsu...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta tana duban Raheema da tuni kalaman Muhibban sun sanyaya mata jiki... Murmusawa Raheema ta kumayi kana tace “Muhibbah koh...? I hope you know your place... Ya kamata ki rage shigewa Zahra..!” Muhibbah ta kuma murmusawa tana duban Zahra dake cen wajen mahaifinta kana tace “I’m sorry your Highness, but I think that’s for her to decide... You can’t choose her friends... Am I right...?!” Raheema tai murmushi da yafi kama da yak’e kana tace “What Zahra needs is a mother, and not a friend..Kin fahimta..!!” Wannan karon daga sama zuwa k’asa Muhibbah ke duban Raheema, murmushin bai bar saman fuskarta ba take furta “And wa kike tinanin ta cancanta da zama mahaifiya ga Zahra... You..?!” Lokaci guda ta kuma sakin murmushi kana tace “Ki kwantar da hankalinki your Highness, Yarimanki bai gabana, bashi bane a gabana... Karatun da ya kawoni garin nan shine gabana... So Ki kwantar da hankalinki kinji, I’m not an enemy here Princess...Kema idan kinaso mu k’ulla k’awance zamu iya zama k’awaye kinji koh....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin wani murmushi kana ta furta “Na barki lafiya your Highness... Have a good evening...!!” Har ta juya zata wuce sai kuma ta juyo tana kuma duban Raheema kana Ta kuma sakin murmushi tace “Oh... Nice earrings tho...!” Tana ida fad’in haka tasa kai tai shigewarta ko sallama da Umaima ma bata sami zarafin yi ba aka bar Raheema baki sake tana bin bayanta da kallo... Shiko Yarima Mahmood lek’en ta yanda zai hangota yake kan faman yi amma bai hangota d’in ba... Ba dan yaso ba ya kuma maida hankalinsa ga yaransa.... *** Yamutsettsen tsoho mummuna abin tsoro da k’yama da Giwa Ke kirada Tal’udu shine ya kuma mik’ewa tsaye gaban Giwa cikin tsananin k’unan rai ga hayak’i da ya gauraye wajen gaba d’aya lokaci guda yake furta “Turai..!!! Kina Ina d’anki ya had’o kan Malamai suna cikin Masarautar nan suna k’ona min dakaruna dake ko wacce kusurwa ta cikin gidan nan....!! Idan har hakan yaci gaba da faruwa toh fah dole ya wargaza duk wani sauran shirinmu....!” Giwa ta soma girgiza kai tana furta “Bazan tab’a barin Mahmood ya wargaza min shirina ba...Kafin ya wargaza min ni zan gama dashi...!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci.. Tal’udu yai wani irin dariya mai mummunan sauti kana yace “Kina gab da makara Turai domin kaw wannan yaro naki da shirinsa ya dawo... Kuma ya dawo ne domin ya yak’eki ya bankad’o duk wasu sirrikanki...!!!” Giwa ta d’ago tana huci lokaci guda take furta “Bazai yuwu yaron dana rik’esa matsayin d’anda na haifa shekara da shekaru ya zama silan rugujewata ba... Dannewa da nai da rik’onsa da nai tsawon shekarun nan ya isheni uk’uba, ya isheni k’unci... Kai da bakinka ka fad’a min Mahmood bazai k’argo kan gadon Mulki ba... Da zaran ya mutu kuma d’ah na ne Yazeed zai d’ale Karagar....!!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci.... Tal’udu ya kuma fashewa da wata irin dariya kana yace..... SameenaAleeyou📚 [6/15, 7:17 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *019* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tal’udu yaci gaba da fad’in “Ai kin makara tinda kika sake wannan yarinyar ta kufce miki.... Fitilar tsafi ta nuna min gudan jinin na tattareda ita...!!” Wani irin mummunan fad’uwan gaba ne ya dirarwa Giwa lokaci guda... Ta d’ago idanu tana duban Tal’udu dake tsaye gabanta daga shi sai wata ‘yar bante kalan ja, yamutsattsen fatarsa babu kyaun gani...... Giwa Ta shiga girgiza kai tana furta “Wacce kenan... Wace yarinya ce wannan Tal’udu....?!!” Ya kuma fashewa da wata irin dariya kana yace “Yarinya Ta farko da ya kamata na tara da ita, ban tarada ita ba Allah ya bata sa’an tserewa.... Tabbas itace gudan jinin...!!” Gaban Giwa ya kuma bugawa... Batasan sanda Ta mik’e tsaye ba tana fad’in “Kana nufin kace ba’a sami gudan jini tsakanin duka wad’annan ‘yanmatan da suke wajen nan ba...?” Tal’udu ya kuma fashewa da dariya kana yace “Ai na fad’a miki gudan jinin ka iya tsayawa akanta ita d’ayanta... Kuma idan har ya tsaya akanta ita d’aya toh fah ko shakka babu K’addarar Masarautar nan na rataye ne a wuyanta....!!” Giwa na tsananin huci take furta “Amma yarana sun tabbatar min cewa wannan yarinyar Saudatu ta jima da mutuwa sun kasheta..!!” Tal’udu yai wata murmushi mai mummunan sauti kana yace “Tin a lokacin na fad’a miki yaranki k’arya suke maki Allah bai basu sa’an kashe wannan yarinyar ba kaman yanda suka sanar dake Sun kasheta...!!” Giwa Ta soma ganin jiri duniyar na juya mata, ta dafe kanta da ya shiga sara mata lokaci guda.... Meke shirin faruwa da ita, idan Saudatu tana raye toh tana ina... Kai ina ita bata yarda ba, bata yarda Saudatu na raye ba... Bata kuma yarda k’addarar Masarautar Ta na rataye a wuyarta ba... Lokaci guda ta d’ago tana duban Tal’udu cikin wane irin fuci take furta “Hakan ba mai yuwa bane Tal’udu... Babu yanda za’a ce k’addarar Masarautar nan na rataye a wuyar wannan k’ask’antacciyar yarinyar d’iyar k’ask’antattu... Idan duk baka sami gudan jinin cikin wad’annan ‘yanmatan goma sha hud’u da suke a matsayin mallakinka a yanzu dole a sake nemo wata budurwa a jarabba da ita... Ni bazan tab’a yarda da fad’uwa ba Tal’udu....Na riga dana bisne sirrinka da babu wani mahaluk’i da ya isa ya bincikosu.....!” Ta k’arashe tana tsananin huci Juya mata baya Tal’udu yai kana yace “Turai ina gargad’inki dik randa Mahmuda yai nasaran bud’e kurkuku dake k’ark’ashin k’asan Masarautar nan.... Ki tabbata daga wannan rana daga ni har Ke k’arshemu yazo....!!!” Yana ida fad’in haka hayak’in dake cikin d’akin ya kuma turnuk’ewa hannun Giwa dake lullub’e cikin bak’in safan shima ya soma hayak’i... Ta zaro ido tana duban hannun nata cikeda firgici... Cen kuma hayak’in ya soma gushewa, a haka itama hayak’in dake fitowa daga cikin hannun nata ke tafiya har dai hayak’in ya k’are gaba d’aya... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai kana Ta sauk’a daga saman jan darduman su ta tsafi mai d’aukeda Tambarin Masarautar tasu.... Tana fitowa ta tadda Jakadiya na jiranta, tai tsaye tana k’arema ‘yanmatan dake kai komo wajen kallo... Ta hangi wannan d’aki da kullum yake a bud’e... D’akin da ya kamata ace Saudatu ce a ciki amma an bar d’akin da gib’i... Wannan yarinya ba k’aramin cutarta tai ba, da ace bata gudu daga wajen Tal’udu ba da yanzu babu wani barazana gaba gareta... Ta yaya Tal’udu zaice k’addarar wannan Masarautar na rataye a wuyan tsinanniyan yarinyar nan wacce itada iyayenta suka tasamma kawowa mulkinta sanadi... Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tai alamawa Jakadiya suka soma Tafiya, ‘Yanmatan gaba d’aya masu sanye da tufafi iri guda su goma sha hud’u suka jera a layi sahu biyu kansu a k’asa har Giwa ta fice daga cikin wajen... Koda Giwa ta iso d’aki hankalinta bai kwanta ba, kaman ko yaushe Yarima Jamal ta tadda zaune a d’aki yana jiran k’arasowarta.... Yanayinta da ya gani ya tabbata akwai abu mai girma dake damun Mahaifiyar tasa.... “Maami lafiya na ganki haka...?” Ya bid’a fuskarsa d’aukeda damuwa... K’ak’aro murmushi Giwa tai dan har abada bata yarda ta nuna gazawarta ba kana tace “Lafia lou nake Ubana... Baka kwanta ba...?” Jamal ya murmusa kad’an kana yace “Maami kinsan bazan tab’a kwanciya ba tareda naga kin kwanta bacci cikin aminci ba....!” Tai murmushi cikeda jin dad’i kana tace “Allah shi maka Albarka Jamal, biyayyan da kake min kaima Allah shi baka yara masu yi maka irinta...!” Bata Kai aya ba tai saurin katse addu’ar tata kaman wacce ta tina wani abu... Jamal ya tsareta da idanu yana jiran yaji k’arshen addu’an nata... Kaman ko yaushe yaji tayi shiru batai masa fatan samun yara ba... Mik’ewa yai ya k’araso gabanta had’ida duk’awa, ya d’ago kai yana dubanta kana yace “Maami mai ya hanaki k’arasawa...Shin baki so nima nai aure na haifi nawa yaran ne....?” Tai masa K’uri tamkar mai tunani, kana ta shafi gefen fuskarsa kad’an, lokaci guda ta sakar masa murmushi kana tace “Tanadin da nai maka na musamman ne Jamal, K’warai Inaso naga ‘ya’yanka kuma wataran zasu gaji sarautar gidan nan... Toh amma Jamal idan Kai aure yanzu waye zaike kula dani yanda kake kula dani... Sanin kanka ne cikin ‘yanuwanka kaf ka fisu kula dani da kuma al’amra na... Kaine Gwarzo na Jamal, idan Kai aure hankalinka zai karkata zuwaga iyalinka.... Wa zai kula dani Jamal...?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Jikin Yarima Jamal yai sanyi... Yana matuk’ar k’aunar mahaifiyarsa fiye da komai a duniya... Ko wace irin biyayya ne yai alk’awarin yi mata wannan biyayyar matuk’ar zai sanyata cikin Farin ciki... A hankali ya mik’e daga durk’ushen da yake ba tareda ya kuma juyowa ya dubeta ba yai ficewarsa zuciyarsa na matuk’ar masa zogi... Ya rasa gane dalilin da yasa sam mahaifiyarsa bata k’aunan ya kawo maganan aure cikin rayuwarsa... Maiyasa take masa haka, ya kasance mai tsananin biyayya a gareta, Bai tab’a sab’a umarninta ba tsawon rayuwarsa... Toh Maiyasa shi bazata barshi ya cika burinsa na ganin ya aje iyali ba...? Idan dan tsoron kar biyayyan da yake mata ya daina ne yayi imani babu macen da zatazo Ta hanasa biyayyawa mahaifiyarsa... Da wannan tinanin ya nufo matakalan benen, idanunsa suka sauk’a zuwa b’angaren Umaima da Zahra... Yai K’uri yana duban k’ofan parlorn nasu... A hankali ya soma takawa har ya isa ya bud’e k’ofar parlorn cikin tsanaki.... Ya soma takowa cikin d’an madaidaicin parlorn yana mai k’arewa k’ofar d’akin Umaima kallo... Lokaci guda idanunsa suka sauk’a kan zanen gidan sarautar dake lank’aye wajen wanda shine ya baiwa Umaima ta lank’aya a wajen.... Ya tako har zuwa gaban zanen ginin gidan sarautar yana shafawa a hankali tamkar mai nazarin wani abu.... Lokaci guda ya maida dubansa zuwaga k’ofar d’akin Umaima, ya jima yana duban k’ofan d’akin kafin ya soma takawa a hankali cikin tsanaki ya isa jikin k’ofar ya tura a hankali, nan kuwa k’ofar ta bud’e.... Cikin sand’a yake takowa zuwa cikin d’akin har ya iso gaban gadon Umaima dake baccinta hankali kwance.... Yai mata K’uri yana dubanta, daidai lokacinda Umaima Ta d’anyi juyi cikin bacci bargon da ta rufa ya d’an janye ya yaye k’afafunta zuwa cinyoyinta suka bayyana... Zuciyar Jamal tai wani irin tsinkewa, yai saurin rintse idanunsa yana mai kauda Kai gefe... K’irjinsa bai daina bugu ya soma k’ok’arin Kai hannunsa da niyyan janyo mata bargon ya rufa mata, hannayensa sai rawa suke... Ba tareda ya kuma duban k’afafun nata ba ya janyo bargon ya gyara mata a hankali... Bayan ya rufa mata durk’usawa yai gaban gadon nata kana yai mata k’uri... Ya saki murmushi a hankali yana duban idanunta dake rufe ruf alamun bacci.... Cikin zuciyarsa yake fad’in “Ke tawa ce Umaima... Na rabaki da Ja’afar domin na mallakeki... Na kuma mallaki soyayyarki... Bazaki sake ganin Ja’afar ba har abada Umaima... Ja’afar bawa ne k’ask’antacce wanda bai cancanci soyayyarki ba... You’re mine Umaima... Kuma duk namijin da yai yunk’urin raba tsakaninmu zan b’atar dashi kaman yanda na b’atar da Ja’afar... Umaima, koda ace mahaifiyata bazata amince min da aurenki ba, toh kema bazan tab’a bari kiyi aure ba... Sabida ked’in tawa ce, na gwammaci nayita ganinki haka koda bazamu sami zarafin kasancewa da juna ba... Ina sonki Umaima.. Ina matuk’ar k’aunarki.. With all my heart..!” Ya k’arashe siririyar Hawaye na gangarowa Daga idanunsa guda... Ganin ta soma muskutawa alamun farkawa ya sanyashi saurin mik’ewa ya nufi k’ofa... Cikin sand’a ya fice kana ya janyo mata k’ofar a hankali ya nufi k’asa ya fice daga sashen gaba d’aya... *** Washe gari ta kama asabar ranan hutun aiki sannan d’alibai ma suna gida babu makaranta... Hakan yasa koda Zahra ta tashi tai wanka ta shirya sai ta nufi cen b’angaren bak’i yanda Muhibbah take.... Muhibbah batai mamakin ganin Zahra zaune a parlor tana jiran fitowarta ba... Suka sakar ma juna murmushi kana Zahra ta soma gaidata, Muhibbah ta amsa da sakin fuska ta k’arada “Yau mai nayi da na cancanci amsar bak’uncin kyakkyawar Gimbiya da sanyin safiyar nan... Gaskiya yau d’in ga dukkan alamu na tashi da sa’a...!” Ta k’arashe tana mai fari da idanu... Zahra Ta murmusa kana tace “Zuwa nai na gayyaceki karin kumallo a cen b’angaren mahaifina...!” Take annurin fuskar Muhibbah ya d’auke cak... Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i... Karin kumallo a b’angaren Yarima Mahmood... Wai kuma tareda ita Muhibbah...?! Ganin yanayinta ya canza ya sanya Zahra sakin murmushi kad’an kana tace “Bakiso ko...?” K’ak’aro murmushin yak’e Muhibbah tai kana tace “Ba haka bane Princess, kawai gani nai kaman bai dace ba... Maybe mahaifinki ma bazai so haka ba, or maybe hakan ya sab’a al’adu da d’abi’un Masarautar nan... Karki mance Zahra nan ba Spain bane yanda dik abinda kike ganinshi normal a can a nan ka iya zama akasin haka...” Ta k’arashe cikeda kulawa... Zahra Ta d’anyi rau rau da idanu kana tace “But ni banga komai ba cikin yin hakan... You’re my only friend here... Har yanzu ko sch banyi k’awaye ba.... Kuma shi yace min nazo muyi breakfast taredashi, na tambayeshi idan zan iya zuwa da friend d’ita.. Ya tambayeni wacece friend d’in tawa nace mishi ke ce.... Bai hana ba, kuma ai abinci kawai zamuci tare duka ni banga wani kuskure a cikin hakan ba... Ko shima sab’a dokan gidan nan ne...?!” D’an fuzar da iska kad’an Muhibbah tai kana ta k’araso ta rik’e hannayen Zahra cikin nata “Princess ba haka bane... But baki tunanin maybe Paa d’inki yanaso ku kasance ku biyu ne, to spend time together... Daughter and Dad bonding... Baki tinanin haka.?” Ta k’arashe tana kashe mata idanu guda.... D’an turo baki kad’an kana tace “Fine tinda kink’i zuwa... But promise me anjima zamu fita mu shak’ata a Lambun Masarautar nan sai muyi namu bonding time d’in...” Murmusawa kad’an Muhibbah tai kana tace “I promise you...!” Ta k’arashe tana mai d’aga tafin hannunta alamun alk’awari.... Zahra na ficewa da kad’an Umaima ta shigo ta d’auketa suka tafi b’angaren Giwa domin karya kumallo daga cen kuma sashen Zuhra matar Yazeed suka nufa.... ** Sanda Zahra ta k’araso sashen mahaifin nata, samansa ta haura don sanar dashi ta dawo ya sauk’o suyi breakfast saidai wayan da taji yana yi ne ya sanyata tsayuwa ba tareda Ta iya ci gaba da tafiya ba... Mahmood da sam baisan da isowar d’iyar tasa ba yaci gaba da fad’in “Must we talk about that Turaki... Sau nawa zance maka sanin gaskiyar babu wani amfanin da zaiwa Zahra... I cannot break my daughter’s heart, rashin mahaifiyarta da tai is enough... Zahra went through a lot already... Rasuwar Aliya, d’aukota daga Spain mu dawo Nigeria, rabata da rayuwar data saba, makarantar ta abokanta da sauransu don’t you think is enough for her... Bai kamata na kuma bijiro mata da wani tashin hankali ba... The only abinda na sani shine bazan tab’a bari tasan gaskiya ba muddin gaskiyan zai jefata cikin tashin hankali... I already lost my wife, I can’t lose my daughter Turaki...!” Dukda k’arancin shekarunta hakan bai hanata k’ok’arin saita natsuwarta ba... Taji jiri na neman kada ita... Mai Paa d’inta yake b’oye mata... Meye ne wannan abin da baiso ta sani...? Meye a k’unshe da rayuwarta da yake b’oye mata...? Ta yarda da Paa d’inta tsawon rayuwarta, bata tab’a kawo akwai abinda zai b’oye mata mai girma har haka ba.... Ita zata iya cewa ma tafi shak’uwa dashi sama da mahaifiyarta... Toh meye ne ake mata rufa rufa akai... Toh kodai Paa d’inta nada masaniya ne akan mutuwar mahaifiyarta tinda gashi taji yana cewa ya rasa matarsa bazai kuma rasa d’iyarsa ba... Idan bata mance ba zuwansu Nigeria ne aka tsinci gawar Maama a d’aki... Toh ko Paa yasan wani abu ne gameda mutuwar mahaifiyarta shine yake b’oye mata...?! Take taji wasu k’walla suna kuma zuwa idanunta.. No Paa d’inta bazai tab’a yin wani abu mai kama da wannan ba, bama zata bari zuciyarta ta raya mata hakan ba.... Tayi nisa cikin tinani ta jiyo muryarsa yana fad’in “I guess my princess’s starving already... Forgive your Paa ya barki kinata jiranshi... Do you want me to serve you...?” Ya k’arashe yana mai k’arasowa jikin dining table d’in.... K’ak’aro murmushi tai kana tace “No it’s alright Paa... Just sit down I’ll serve you...!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye cikin tsananin sanyin jiki... Yarima Mahmood yai mata K’uri yana duban yanda yanayinta ya sauya gaba d’aya... Ta k’araso tana k’ok’arin had’a masa shayi, har lokacin idanunsa akanta.. Hannunta ya d’an rik’e alamun dakatarwa kana yace “Are you sure you’re alright sweetheart..? Wait ina friend d’in taki... Why isn’t she here...?” K’ak’aro murmushi ta kumayi na k’arfin hali kana tace “I’m fine Paa... Tace ba yau ba maybe some other time...!” Ya jinjina kansa a hankali yana mai ci gaba da karantar yanayin d’iyar tasa... Har Ta gama had’a masa shayin ta koma mazauninta ta zauna Yarima Mahmood bai daina karantarta ba, yasan dole akwai abinda Ke damunta... Sai yai k’ok’arin danganta hakan da rashin amsar tayinta da Muhibbah batai ba.... Yana son d’iyarsa sosai, a Duniyarsa baison ganin b’acin ranta haka yaita k’ok’arin cheering d’inta, ita kaw Zahra har yanzu wayan dataji mahaifin nata nayi take tinani.... *** Tafe suke hanyar da zai sadaka da b’angaren Yazeed wata kuyanga Ta k’araso cikeda risinawa ta gaidasu kana ta dubi Umaima taceda ita Yarima Fu’ad ke son magana da ita... Umaima ta d’anyi still tana dubanta kana tace “Ina Yarima Fu’ad d’in yake...?” Kuyangar Ta kuma sadda kanta kana tace “Yana bayan lambun dake b’angaren sashen Giwa, yana jiranki a cen Rankishi dad’e..!” Jinjina kai Umaima tai kana tace “Ki sanar dashi Ina zuwa...” Kuyangar ta jinjina kai cikeda ladabi irinta babban gida had’ida amsawa kana tasa kai ta shige... Umaima ta dubi Muhibbah kafin tai magana Muhibbah tace “Just go your Highness, ni zan k’arasa sashen Gimbiya Zuhra idan yaso sai ki sameni a cen...!” Umaima ta jinjina kai murmushi saman fuskarta dan tasan kiran da Fu’ad Ke mata bazai shige akan Muhibbar ba kana tace “Da fatan dai bazaki b’ata a hanya ba...!” Murmusawa Muhibbah tai kana tace “Tinda ban b’ata cikin duhun dare ba ai ina tinanin banzan b’ace cikin hasken rana ba ranki shi dad’e..!” Suka kuma murmusawa a tare kana Umaima tace “Haka fah... Kinyi gaskiya, I’ll see you later...” Muhibbah Ta jinjina mata kai kana Ta nufi sashen Yarima Yazeed... Tana isowa sashen ta tadda Kuyangi daga waje sai risinawa suke suna gaidata, ita kaw taita jinjina masu kai alamun amsawa, a haka Ta nufi cikin gidan... Shiru ta tadda parlorn saidai tana shiga tai arba da k’atoton hoton Yazeed wanda akai masa daga sama har k’asa yai tsayuwa irinta masu mulki, yana sanye da kaya irinta mulki da sarauta, komai na jikinsa na sarauta ne har zuwa takalmin kufta dake k’afafunsa... Kansa nad’e cikin Farin rawani mai kunne biyu, idanunsa rufe da bak’ar tabarau wanda ya dad’a fito da hasken fusakarsa, yana sanye da alkyabba fara k’al haka nan hannunsa na dama rik’eda doguwar sanda irinta masu mulki... Kaman ka kirasa ya amsa....Sosai zuciyarta ke tafarfasa tana duban wannan hoto na Yazeed... Ji take kaman ta janyo hoton k’asa tai rugu rugu dashi wala’alla zataji sauk’in zoginda zuciyarta ke mata... Da k’yar Tai k’ok’arin saita kanta kana ta nufi cikin parlorn... Ganin babu kowa cikin parlorn ya sanyata d’an waige waige... Nan ta hangi hanyar upstairs... Take taji zuciyarta na raya mata ta haura saman... Ta kuma d’an waigawa kana ta nufi hanyar da zai sadaka da upstairs.... A hankali takejin kaman sautin kuka na tashi... Ta kuma kasa kunnuwanta had’ida mak’alewa jikin k’ofar kad’an... Tana iya sauraro muryar Zuhra cikin kuka tana fad’in “Wlhi Raheema na ga sark’ar buduwar tasa da idanuna kuma a nan cikin drawer na ajiye shine da nai masa yamin wulak’ancin da ko kare bazai ci ba...” Raheema da k’irjinta Ke tsananin bugu tace “Toh yanzu ina sark’ar...?” Zuhra ta kuma goge hawayen dake idanunta kana tace “Ya d’auka yana wajenshi.. Na d’aga sark’an ne da niyyan na nuna miki evidence cewa ba sharri nakewa Yazeed ba, wllhi yana cutar dani...!” Raheema data sauk’e ajiyan zuciya a hankali jin Yazeed ya d’aga sark’ar, kamo hannun Raheema tai kana tace “K’awata you don’t need to show anything for me to believe you K’awata,nasan zaman hak’uri kike da wannan azzalumin mijin naki.. But Zuhra dole haka zaki ci gaba da hak’uri don kare martabarki da na yaranki... Nasan maybe wataran zai kaiki bango da wannan d’abi’u nasa har kiyi tinanin komawa masarautarku, Toh ki sani yin hakan na nufin tonon asirinki ne Zuhra... Kici gaba da hak’uri akan wanda kikeyi... Kuma Ki d’auke idanunki kan abubuwan da mijinki keyi balle ya saka miki wani ciwon kinji koh....!” Zuhra ta jinjina kai tana mai godiya wa Raheema da kyawawan shawarin da take bata... A hankali Muhibbah ta nufo downstairs bayan Ta gama jin komai....Daidai tsakiyar stirs ta hangesa tsaye ya kafeta da mayun idanunsa.... SameenaAleeyou 📚 [6/19, 9:22 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *020* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallo yake binta dashi daga sama har k’asa, wannan karon sai yafi samun daman k’are mata kallo fiyeda wancan lokacin da yai arba da ita a cikin duhun dare... Ala dole tai k’ok’arin saita kanta dikda tsananin zogi da zuciyarta Ke mata musamman ganin irin duban da Yarima Yazeed yake mata.... Bazata bari ya zargi wani abu daga gareta ba... Dan haka lokaci guda tai k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta “Barkada safiya Your Highness...!” Ta fad’i daga nan yanda take tsaye kyakkyawan murmushi saman fuskarta... Bai amsata ba saima duba na k’urilla da yake mata... Ganin haka ya sanya Muhibbah soma takowa cikin salo na yaudara da d’aukan hankali.... Saida ta k’araso dab kusa da Yazeed kana ta d’an risinar da kanta tana mai furta “Idan Yarima yamin izini zan sauk’a k’asa....!” Ga tsananin mamakinta karkacewa taga Yazeed yayi yana k’ok’arin bata hanya... Ta k’araso zata rab’a ta gefensa ta shige dikda tsananin bugu da k’irjinta keyi... Dab saitin kunnenta dake b’angarensa Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Looks like destiny wants us together...!” Yai maganan yana mai aika mata wani irin duba shu’umin murmushinsa saman fuskarsa.... Batakaiga Koda motsa ‘yar yatsarta ba Ta kuma jiyo muryarsa yana fad’in “Be careful what you’re getting yourself into... You might get trapped in the middle..!” Tai saurin d’agowa tana dubansa, shid’inma ita yake duba babu ko alamun gizau a tattaredashi, lokaci guda ya sakar mata wannan murmushin nasa maras kyaun gani... Muhibbah tai saurin kauda fuskanta gefe tana mai ci gaba da tafiya har ta sauk’a k’asa... Sauk’anta Keda wuya Umaima suka shigo tareda yaran Yazeed da dawowarsu kenan daga islamiya.... Noor ta taho da gudu ta rungume Muhibbah tana k’ok’arin biya karatun da Ta koya a islamiya... Shikaw Sultan sakai yai ya shige abinsa ba tareda yabi takansu ba dan dama hakan nan yaron yake ga k’asaita ga miskilanci... Kana ganinsa Kaga jinin sarauta.... Muhibbah ta saci duban upstairs yanda ta bar Yazeed tsaye saidai sam bata hange koda k’yallinsa ba da alama ya shige wane wajen... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali dikda yawo da kalaman Yazeed Keyi a kwanyarta... What if Yazeed ya ganeta ne..? What if ya fahimceta ne... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un! Idan hakan ta kasance ya kenan zatai ita da bata fara komai cikin abinda ya kawota ba... Muryar Umaima ne ya dawo da ita daga duniyar tinaninda ta tafi yanda take sanarda kuyangar dake rik’eda Noor zasu haura sama data sanarwa Gimbiya Zuhra shigowarsu... Kuyangar ta jinjina mata kai cikeda risinawa kana Ta nufi benen rik’eda Noor... D’an duban Muhibbah Umaima tai Dan Ta lura kaman wani abu na damunta... “Hibbah lafia...? Akwai wani abu ne..?” K’ok’arin saita kanta Muhibbah tai had’ida girgiza kai kana tace “No babu komai, mai kika gani..?” Umaima ta d’an murmusa kad’an kana tace “Well, ni inada wani batu da nakeso muyi dake..” Muhibbah ta d’an zaro idanu waje kana tace “You seems serious... Hope all is well..!” Umaima ta kuma murmusawa kana tace “K’alau saima alkhairi...!” Muhibbah Ta d’an kuma yin fari da idanunta kana tace “Now you’re making me nervous... Rankishi dad’e wai meke faruwa ne..?!” Kashe mata idanu guda Umaima tai kana tace “Idan mun fice a nan zan sanar dake komai in details... Relax K’awata na fad’a maki babu komai sai alkhairi...” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta... Murmushin yak’e Muhibbar ma tai daidai sanda Zuhura da Raheema suka nufo parlorn... Raheema na hangosu ta rausayar da idanu had’ida fuzar da huci a hankali, Ta tsani wannan shegiyar Muhibbar, Ta tsani ganinta.. She can’t stand the sight of her... Dafa k’awarta tai a hankali tana mai furtawa cikin sigan rad’a “You take care K’awata... Da dare zan shigo mu k’arasa zancenmu... Ki kwantar da hankalin ki kinji... And think about dik abubuwan da na fad’a miki....!” Jinjina mata kai Zuhra tai a hankali kana Raheema ta d’agawa Umaima hannu alamun gaisuwa ko takan Muhibbah batabi ba tai ficewarta.... Zuhra ta k’araso garesu da fari’arta tanai masu sannu da zuwa, sai nan nan dasu take gwanin ban tausai, dubanta kurum Muhibbah keyi amma tausayinta ne fal k’asan zuciyarta, shin ya zataji idan taji aminiyarta wacce ta aminta da ita take kawo mata kokenta da dik wani sirri nata da ita mijinta yake cin amanarta... Kai wannan duniya da amana tai k’aranci shin ina zamu kai girman hakki... Sun jima sosai b’angaren Gimbiya Zuhra Muhibbah na karantarta tsaf, har sai bayan sallan azahar kana suka nufo b’angare Giwa.... Har wannan lokaci Muhibbah dai bata wani saki jikinta ba, sosai kalaman Yazeed ya d’aga mata hankali... Ta yaya ma zata kwantar da hankalinta bayan kalaman da taji suna fita daga bakin Yazeed... Bazata bari Yazeed ya rusa mata dik wani shirinta ba, dole tasan yanda zatai Ta tabbata hankalinsa baikaiga yanda take tinani ba.... Basu samu ganin Giwa ba Jakadiya ta sanar dasu Giwa na sama tana ganawa da yaranta, hakan yasa suka yada zango nan b’angarensu Umaima... Hango Fu’ad daga k’asan bene da Umaima tai ya sanyata fasa shigewa parlorn dole ta nufo k’asa tana fad’iwa Muhibbah ta jeta tana nan tafe.... Muhibbah ta jinjina kai kana tasa kai kaman zata nufi b’angaren benen da zai sadaka da sashen su Umaima.... K’uri taiwa b’angaren Giwa dan tinda taji ance Giwa na ganawa da yaranta taji tana son jin kan mai suke tattaunawa... Ta d’an waiga gefe da gefe bataga kowa ba, hakan ya bata daman kutsa kai ta nufi sashen matakalan Giwa.... Cikin sand’a take tafiyar nata har saida ta k’araso jikin k’ofar dataji maganganunsu kwanakin baya... Ta tura a hankali kana ta d’an kutsa kanta ta shige cikin sauri ta mak’ale jikin k’ofa... Shigarta keda wuya kuwa ta soma jiyo muryar Yazeed yana fad’i cikin gadara da isa... “Mamee babu wanda ya isa ya hanani neman sarautar nan... I’m sorry to say not even you... Wllhi wllhi na rantse da mahaliccina ko Abbah ne ya taso daga kabarinsa saidai muyi takara dashi muga waye zai kada wani...” “Yazeeeed!!!” Mahmood ya daka masa tsawa cikin karaji... Shima Yazeed d’in cikin tsananin karaji yake ci gaba da fad’in “What..!!! Zaka hanani ne... C’mon Yaya, among the two of us kafi kowa sanin ni nafi cancanta da wannan Mulki , a ijiye maganan cewa ka jima baka k’asar nan, a dawo maganan kamala da cancanta, I’m a family man bacin haka ni inada Magaji kaikuwa fah...? Bakadashi, d’iyarka d’aya ce tol kuma mace kaga bazata gaji Karagar Masarautar nan ba... Aje ma mace zata iya mulki shin taka d’iyar zatai mulki ne..? Ko ka mance cewa....!” Bai kai aya ba Mahmood dake tsananin huci ya d’ago yatsarsa dake rawa sabida b’acin rai yana mai furta “Kar ka bari na sake maka kashedi Yazeed... Leave my daughter out of this...!!!” Sai sannan Giwa ta katsesu da fad’in “Ya isa...! Ya isa haka nace..!! Shin wai ku bazaku tab’a zama inuwa guda ba... Haba Haba shin sai kunga bayana... Wannan wace irin masifa ne... Kai Yazeed na riga na gama magana idan bazakaga girman Yayanka ka bar masa wannan Karagar mulki ba ni dana haifeka Ina tsammanin zakaga girma na... Wllhi bazaka tab’a samun albarkana da goyon bayana ba idan dai akan mulkin nan ne..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji hawaye na k’ok’arin kawowa idanunta... Jamal da k’irjinsa Ke tsananin bugu hango hawaye da yai kwance cikin idanun Mahaifiyarsu, a tamanin ya tafi ya duk’a gabanta yana lallashinta yana bata baki cikin tsananin damuwa da nuna tashin hankali... Wani wulak’antaccen kallo Yazeed ya watsa mata, kana ya murmusa da gefen bakinsa... “I thought I made myself clear Maami... You can’t stop me... I won’t allow you to deny me what’s rightfully mine...!” Yana kaiwa nan yasa kai ya nufo k’ofa cikin sassarfa kaman zai kifa da k’asa... Jin takunsa ya sanya Muhibbah saurin mak’alewa bayan k’ofa... Tana ganin Yazeed ya fice cikin tsananin huci da b’acin rai... Yazeed na ficewa Mahmood ya k’araso gaban Giwa ya zuba gwiwoyinsa a k’asa... Lokaci guda ya d’aura hannunsa guda saman nata... Giwa ta d’ago idanunta masu rauni a yau d’in tamkar ba ita ba tana duban Mahmood dake duk’e gabanta... Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Maami Ki yafe min, Ki yafewa d’an uwana Yazeed... Ba nufinmu bane mu sakaki cikin k’unci da bak’in ciki, na sani a koda yaushe Uwa batada burin da ya shige Ta sanya yaranta cikin Farin ciki... Na sani dik wannan fad’i tashin da kikeyi sabida mu ne... Amma Maami abu guda da nakeso Ki sani shine, shifa Mulki Allah Ke badashi ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso a kuma lokacinda yaga dama... So Maami idan Allah ya k’addari Yazeed shine wanda zai d’ale Karagar Masarautar nan inaso ki bashi full support d’inki ki kuma bashi albarkanki da addu’o’inki domin hakan ne zai leading d’insa to what’s right...” Saurin d’agowa Giwa tai tana dubansa, kaman Ta shak’esa Ta huta haka takeji... Fad’i take cikin zuciyarta _”K’arya kake Mahmood, baka isa ka tsallake Karagar nan ba a yanzu... Dole ka d’ale sannan ka mutu kafin d’ah na Yazeed ya k’arb’a yai dogon zango har k’annensa da d’ansa ma suzo suyi... Mahmood kenan, ai nafi kowa son ganin Yazeed saman Karagar nan amma hakan ba mai yuwa bane a halin kana nan da rai.. Sai ka shid’a ka tafi ka tadda iyayenka a cen barzahu kafin Yazeed ya d’ale... Na riga nayi tanadima yarana Mahmood.. Ni ce nan na datse mahaifar matarka donma kar Ta haihu balle ka sami Magaji har ka saka ran wataran zai sarauta, Kaga da zaran ka mutu zuriyarka Ta k’are kenan a Masarautar nan Mahmood, saiko wannan shegiyar d’iyar taka wacce koda namiji ne shege bai gadon sarauta...!”_ Tana ida tinanin taji wani irin sanyi na sauk’a mata cikin zuciya, taji murmushi na zuwa saman fuskarta... Hannu tasa ta shafi fuskar Mahmood tana mai furtawa a fili “Mahmood d’ah na Allah dai shi maka Albarka... Ka cika d’ah mai biyayya da ko wacce uwa zatai mafarkin samu... Kalamanka gaskiya ne Mahmood, Allah shine mai bada mulki, shiyasa nake rok’onsa babu dare babu rana da ya mallaka maka wannan gadon mulki... Ni kaine zab’ina Mahmood, idan baka d’ale Karagar mulkin nan ba zanji kaman ban cika burin mahaifinku bane na ganin cewa kai ka zamto magajinsa... Kullum burin mahaifinku kenan ka gajesa Sadauki...!” Ta k’arashe cikin rau rau da murya... Daga Mahmood har Jamal saida mahaifiyar tasu Ta basu tausayi, sam rauni ba d’abi’arta bane, idan ta shiga yanayin sai ta baka tausai... Yarima Mahmood ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Kici gaba da mana addu’a Maami, addu’anki yafi komai... Allah yai mana zab’i na alkhairi...!” Ta jinjina masa kai a hankali tana mai kuma saka masa albarka kana ya mik’e yana furtawa Jamal zai duba Zahra ya kula da mahaifiyarsu... Jamal ya jinjina masa kai yana mai furta “Alright Yaya, kaje zan kulada Maami...” Jinjina masa kai Mahmood yai kana yai sallamada mahaifiyar tasu... Yana fitowa Muhibbah tabi bayansa da kallo, harga Allah bata San dalili ba amma cen k’asan zuciyarta sai ta sami kanta da jin tausayinsa, wani b’angare na zuciyar nata kuma na waswasi da kokonto kan batun da taji Yazeed nayi akan d’iyar Mahmood d’in... Kaman akwai wani ayan tambaya kan d’iyar tasa... Take taji tana son sanin menene Yazeed yake son fad’i kan Zahra.... Bayan Mahmood ya fice itama ta sad’ad’o ta fito daga mab’oyarta... Yarima Mahmood na fitowa bai zarce ko Ina ba sai d’akin Zahra....Kwance ya hangota saman gado tamkar mai bacci, ya saki murmushi a hankali kana ya soma takowa cikin d’akin... Ita kaw Zahra tanajin tafiyar mahaifin nata ta lumshe idanunta tamkar mai baccin da gaske, dan bayan maganganun da taji yanayi a waya bata tunanin zata kuma iya duban idonsa and act like babu wani abindake faruwa.... Tana jin sanda ya zauna a gefenta had’ida gyara mata mayafinda Ta rufa.... Murmushi saman fuskarsa yake dubanta, ya d’an d’auki lokaci yana dubanta kafin ya sumbaci goshinta ya mik’e ya fice daga d’akin gaba d’aya... Yana ficewa, hawayen da Zahra ke mak’alewa suka gangaro mata, lokaci guda Ta mik’e Ta zauna sosai kana ta d’auki family picture d’insu dake aje saman bedside d’inta.... A hankali take shafa hoton, hawaye na gangaro mata lokaci guda take furta “Paa why... What’s that you’re hiding from me... What’s that that you don’t want me to find out... Does it have to do with my Maama’s death... ¿Tienes algo que ver con la muerte de mi mamá? (Shin kanada sa hannu ne a mutuwar magaifiyata.) Paa I love you, I love you so much... And I don’t want our relationship to be ruined...Pero Paa, si me entero de que tienes algo que ver con la muerte de mi Maama ... no sé si alguna vez podré perdonarte Paa (Idan na fahimci da saka hannun ka a mutuwar mahaifiyata, Bana tinanin zan tab’a yafe maka Paa..)” Ta k’arashe tana mai rungume hoton cikin k’irjinta hawaye na kuma gangaro mata... Muhibbah dake lab’e tana duban yarinyar a hankali ta saka hannu ta d’anyi knocking... Zahra ta shiga goge hawayenta da sauri tana mai juyowaga k’ofan... Ganin Muhibbah ce ya sanyata sakin murmushi... Muhibbar ma murmushin take kana tace “May I...?” Jinjina mata kai Zahra tai tana mai furta “Please come in....” Fuskarta d’aukeda murmushi ta shigo kana ta zauna a gefen Zahra... Lokaci guda ta k’ura mata idanu tamkar mai karantarta.... Saida ta d’an muskuta kad’an kana tace “Are you alright mi Amiga...?” Jin Ta ambaceta da Amiga ya sanyata sakin murmushi kana tace “Did you just call me your friend..?” Jinjina mata kai Muhibbah tai kana tace “Of course I did... Ko mu ba k’awaye bane...?” Murmusawa Zahra ta kumayi kana tace “Yeah, haka ne... You’re my only friend here... After all..!” Muhibbah ta kuma murmusawa kana takai dubanta ga hoton da Zahra ke rik’eda... Ta d’an dubi Zahran wacce itama ita take duba Lokaci guda Muhibbah Ke furta “You really miss your mom, right...!” Jinjina mata kai Zahra tai tana mai kuma goge ragowar hawayen dake idanunta “So terrible... I miss my Maama... Ina kewarta sosai...!” Ta k’arashe wasu hawayen na gangaro mata... Tausayin yarinyar ya kuma kama Muhibbah, lokaci guda ta matso kusanta sosai had’ida bata warmed hug... Lokaci guda take lallashinta had’ida kwantar mata da hankali... “Ki kwantar da hankalinki Zahra, kuma kisa a ranki duk mai rai mamaci ne... Wataran muma duka babu mu, and be thankful you still have your Father who adores you very much... Ganinki haka cikin damuwa I’m sure it will break him.. So instead ki d’agawa mahaifinki hankali ki kwantar da hankalinki kici gaba da yiwa mahaifiyarki addu’a kinji koh...!” Ta k’arashe cikeda kulawa... D’agowa Zahra tai tana dubanta kana Ta shiga jinjina mata kai alamun amincewa, lokaci guda take furta “You still have your mother, right.?” K’uri Muhibbah tai mata, tana tina sanda mahaifinta da ‘yanuwansa sukai tarayya wajen kassara mata rayuwarta... Idanunta suka kad’a sukai ja lokaci guda.... Zahra ta d’an matsa daga jikin Muhibbah tana mai furta “Oh... I’m sorry, I’m sorry please...!” Girgiza mata kai Muhibbah keyi had’ida k’ak’aro murmushi ta d’aura saman fuskarta “No is okay dear... Yeah, I still have my mom... But I lost my father when I was your age....!” Zahra ta dubeta cikeda tausayawa kana tace “Kin rasa mahaifinki ni kuma na rasa mahaifiyata...!” Muhibbah ta jinjina mata kai tana mai k’ok’arin saita kanta, lokaci guda taci gaba da furta “It’s part of life... Samu da rashi, wasu lokutan mu rasa mutanen da muke matuk’ar so sukeda mahimmacin a rayuwarmu... But babu yanda muka iya da hukuncin Ubangiji.. Saidai mu karb’e k’addararmu a yanda yazo mana...!” Zahra ta jinjina kai kana tace “Yeah.. You’re right..!” Muhibbah tai mata K’uri ganin kaman tana son fad’in wani abu ne... Hannayen Zahra ta kamo kana tace “If you need someone to talk to... Don’t forget I’ll always be here kinji koh...!” Jinjina mata kai Zahra tai murmushi saman fuskarta take furta “You’ve no idea how much your presence means to me... Thank you Tia for being here with me...!” “Ki daina min godiya Zahra.. Haka nan Allah ya jefa k’aunarki cikin zuciyata....!” Yarinyar ta kuma murmusawa kana tace “Nima Ina k’aunarki...!” Suka kuma murmusawa a tare kana Muhibbah ta hangi textbook na mathematics a gefen Zahra da alama karatu zatai... Ta d’an gyara zamanta tana mai furta “Lissafi ne za’ai...” Tai maganan da sigan wasa to cheer her up.. Zahra takai dubantaga book d’in kana tace “Oh.. Exams zamu fara gashi I’m not good at mathematics shiyasa zan fara dashi... Ko zaki koya min ne.. Dama Paa ke koya min...” Ta zaro ido kad’an “Ni da lissafi.. Lissafi ba layina bane inama kice biology ne ko chemistry maybe wannn na iya karambani...” Zahra ta murmusa tace “Wannan ma zaki koya min... But I don’t believe baki iya lissafi ba....” Muhibbah ta d’an dubeta kana tace “Maiyasa Paa d’inki bazai koya miki ba tinda dama shi yake koya miki...?” Take mood d’in Zahra ya canza, Muhibbah kaw na hankalce da ita dan dama so take ta d’ago wani abu shisa ta ja zancen nasu yai tsawo... Zahra Ta d’an girgiza kai tace “I don’t want him to be my tutor anymore..!” Gyara zama Muhibbah Ta kumayi kana tace “But why...?” Dubanta Zahra tai kana tace “Paa d’in dana sani a Spain yasha banban da Paa d’in da nake gani a Nigeria.....” Sameena📚 [6/19, 9:22 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *021* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Gyara zama Muhibbah tai tana duban yarinyar sosai kana tace “I don’t get you Zahra... What exactly are you trying to say...?” Without any hesitation Zahra ta d’ago tana dubanta had’ida furta “Paa ya canza, I’ve a feeling he’s hiding something from me... Something very serious..!” Ta k’arashe damuwa k’arara saman fuskarta... Gyara zama Muhibbah Ta kumayi kana tace “Mai kike tinanin yana b’oye miki...?” Zahra ta d’an dubeta kaman zatai magana sai kuma ta mik’e tsaye tana mai fuzar da huci a hankali, lokaci guda take furta “I don’t know, but jikina na bani its something that has to do with my Maama’s mysterious death... What if Paa yasan wani abu gameda mutuwar mahaifiyata... Mutuwan da gawanta kawai aka tsinta cikin d’aki..” Mik’ewa tsaye Muhibbah ma tai had’ida dafa Zahra kad’an kana tace “But do you think your Paa can do something as evil as that...?” Saurin d’agowa Zahra tai tana dubanta kana Ta shiga girgiza kai, lokaci guda take furta “No, no I don’t want to believe that... Paa bazai tab’a kashe mutum ba and much less my Maama, ya sota da dika zuciyarshi... But what I don’t understand here shine Maiyasa bazai sanar dani ba idan yasan wani abu ne gameda mutuwar nata, who is he protecting...?!” Ta k’arashe damuwa kwance saman fuskarta... Muhibbah dake ci gaba da karantar yarinyar matsowa kusanta Ta kumayi kana tace “Then talk to your Father... Ask him... Ki tambayeshi meye yake b’oye miki...!” Zahra ta d’an dubeta kana tace “But how... Paa kallon yarinya yake min har yanzu, I’m quite certain bazai Fad’a min komai ba...” Janyo hannunta Muhibbah tai suka zauna saman kujera kana tace “In that case, maybe baiso Ki damu ne... Tinda kince har yanzu kallon yarinya yake miki wacce bakisan komai ba... But if I were you, zan bud’e idon mahaifina ya gane cewa ni fa yanzu ba yarinya bace... I can differentiate what’s right from wrong... You’re already a young lady now... So bai kamata Ki bari yaita treating d’inki kaman wata k’aramar yarinya ba musamman in some cases like this... We’re talking about your Mother here Zahra... Idan har da gaske kasheta akai cikin Masarautar nan and your Paa knows something about it, but baidata cewa coz he’s protecting someone kaman yanda kika ce... Ni a ganina Ke bai kamata kiyi shiru ba.... Mahaifiyarki Ta cancanci adalci koda kuwa nan d’in gidan sarauta ne da basu d’auki doka kan masu mulki a bakin komai ba..!” Yanda take maganan zaka fahimci tamkar tana fitar da wani abu ne da ya jima yana cin zuciyarta... Zahra tai shiru tamkar mai tinani yayinda Muhibbah taci gaba da karantarta.... Lokaci guda Zahra ta shiga jinjina kai tana mai furta “You’re right... I need to find out about everything..!” Jinjina kai Muhibbah tai cikeda jin dad’in yanda cikin sauk’i tai convincing yarinyar... Lokaci guda take ayyana yanda zata tarwatsa rayuwar Mahmood Ta hanyar amfani da gudan jinin da yafiso a rayuwarsa... Tabbas D’iyarsa itace weakness d’insa.... A haka Umaima ta shigo ta taddasu... ** A b’angaren Mahmood yana ficewa ya tadda Ubandoma yanda yake samar dashi zuwan Waziri... Jinjina kai Mahmood yai cikeda sarauta kana yaceda Ubandoma a shigar da Waziri d’akin ganawa na bak’i.... Ubandoma ya kuma aza babban riga yana d’agowa Yarima Mahmood hannu alamun jinjina, lokaci guda yake furta “An gama Rankashi dad’e... Allah shi baka gidanku... Waziri godiya yake...!” Lokaci guda Ubandoma ya kuma aza babban riga kana ya shige cikin sauri... Daidai nan Yazeed ya k’araso wajen shu’umin murmushin nan saman fuskarsa, hannunsa na dama rik’eda hannun d’ansa Sultan...”Taking a break your Highness...?” Ya fad’i murmushin bai bar saman fuskarsa ba... Murmusawa kad’an Mahmood yai kana ya shafi kan Sultan yace “Hello your Royal Highness..!” Yaron ya d’ago fuskarsa yana murmushi yake duban iyayen nasa kana ya dubi Mahmood yace “Do you also think one day I’ll become a King Uncle...?” Duban Yazeed dake ci gaba da sakin shu’umin murmushinsa Mahmood yai kana ya maido da dubansaga Sultan ya shafa gashinsa kad’an kana yace “Of course Champ, one day zaka zama Sarki mai mulkin Masarautar nan... But when that time comes inaso kasa a ranka cewa shi shugaba Bawan Al’ummansa ne mai masu hidima da tausayinsu kaji koh...!” Saurin katse tattaunawar Yazeed yai da fad’in “Sultan jeka Hauni ya d’auraka saman doki, I’ll catch up with you in a bit....!” Yaron ya jinjina kai cikeda jin dad’i kana ya wuce... Duban Mahmood Yazeed yai kana yace “Yaya I’m sorry, but you’ve no right to discipline my son... Idan akwai wanda yafi dacewa ya baiwa d’ah na horo that person should be me,just me and no one else...! Sabida Kai bakada Magaji shine bari ka cire masa son mulki da izza... Sultan jinin sarauta ne dan haka dole ya zamto namijin gaske maiji da mulki da izza...!” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “You’re right... He’s your Son, after all...” Yazeed ya kuma jinjina kai cikeda jin dad’i kana yace “K’warai kuwa d’ah na ne kuma Magajin Masarautar nan..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige shu’umin murmushinsa saman fuskarsa... Yarima Mahmood ya bisa da kallo har ya b’acewa ganinsa kana yasa kai yai shigewarsa... Yana shigowa parlorn ganawa da bak’in Waziri da Ubandoma suka risina suna kwasan gaisuwa... Mahmood ya k’arasa ya zauna a mazauninsa kana Ubandoma yai ficewarsa ya basu waje... Mahmood ya dubi Waziri kana yace “Naji dad’i daka amsa kirata ta gaggawa Waziri...” Waziri ya kuma risinawa kana yace “Allah shi baka yawan rai Farin cikin nawa ne, da sarki mai jiran gado zai nemeni... Ka fad’i dik abinda kake so Waziri yai maka shi a Masarautar nan Rankashi dad’e..!” Shiru ne ya d’an ratsa tsakani kana Mahmood ya d’anyi gyaran murya yace “Waziri..!” “Allah shi baka yawan rai...!” Waziri ya amsada haka... Mahmood yaci gaba da fad’in “Mai zakace gameda b’acewan Ja’afar a Masarautar nan...?!” Tambayar da ya sanya Waziri saurin d’agowa yana duban Mahmood saidai gizo da k’warjini had’ida cika idanun da Yarima Mahmood kedashi ya sanyashi saurin sadda kansa... Lokaci guda yake furta “Allah shi taimakeka Jafaru dai rana d’aya aka nemeshi aka rasa cikin Masarautar nan...!” Shiru ya kuma ratsa tsakani kana Mahmood yace “Yaushe ne aka fahimci cewa Jafar baya Masarautar nan...?” Waziri da gaba d’aya tamkar a birkice yake ‘yan kame kame ya soma da fad’in “Eh toh... Allah shi taimakeka Yau kusan shekara guda kenan idan ban b’ata lissafi ba...!” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Kenan hakan yana nufin, da mutuwar mahaifina, da mutuwar matata da b’acewan Jafar sun faru ne a jere, d’aya na bin d’aya right Waziri...?!” Shiru Waziri yai kaman mai tunani kana yace “Eh Toh hakan ne yake a bayyana Allah shi jada ranka...!” Shiru ya biyo baya kana Mahmood yace “Yanzu kai a naka shawarin Waziri ta ina za’a fara nemo Jafar sabida ina buk’atarsa a Masarautar nan...!” Waziri ya d’an d’ago yana duban Mahmood kana yace “Eh Toh Allah shi taimakeka ban isa ince ga nan ta yanda za’a soma neman yaron nan ba don kar a sami mishkila ko akasi....” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Haka ne Waziri... Toh amma ni inada aiki da zan baka....!” Waziri ya kuma gyara zamansa kana yace “Mecece wannan aiki Rankashi dad’e....?” Mik’ewa tsaye wannan karon Mahmood yai hanayensa hard’e ta baya, yana d’an takawa kad’an irin yanda masu mulki keyi kana yace “Inaso ka wakilta masu bincike... A bincika duk k’asashen da muke gab’a dasu dan na tabbata bawa kaman Jafar bazai nisan da zai tsallake wad’annan k’asashenba...” Sauk’e ajiyan zuciya a hankali Waziri yai kana yace “An gama Allah shi baka yawan rai... Za’a baza dakaru domin a zak’ulo Jafar yanda ya shiga ya fita...!” Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “Da kyau Waziri... Kana iya tafiya...!” Waziri ya kuma mik’a godiyarsa kana ya kwashi babban rigarsa a hannu ya fice.... Yana ficewa sukaima juna wane irin duba shida Ubandoma tamkar wasu mak’iya... Waziri yaci gaba da sab’a babban rigarsa takalma a hannu ya fito daga b’angaren Maimartaba yanda nan cikin b’angaren sashen Mahmood yake.... Waziri yana fitowa wata Kuyanga dake daga b’angaren Gimbiya Zeenat Ta k’araso tai masa gaisuwa kana ta mik’a masa takardan dake hannunta... Yasa hannu ya amsa yana karantawa.... Babu b’ata lokaci yaceda Kuyangar Ki sanar da ahugabanki Waziri Yana nan tafe.... Kuyangar ta jinjina kai kana tai shigewarta... A cen wane b’angare mai duhuwa suka had’u shida Giwa Jakadiya na take mata baya....Duba guda yai mata ya d’auke kansa sai faman sakin huci yake... Giwa taci gaba da takowa cikeda k’asaita.... “Yaya kukayi da d’ah na Mahmood Waziri...?!” Ta tambaya cikeda izza... Saida ya kuma fuzar da fuci kana yace “D’anki ji yake shi d’in kaman wani sarki ne...Doka da Umarni yake bani tin yanzu Ina a matsayin Wazirin mahaifinsa....!” Giwa ta murmusa cikeda k’asaita kana tace “Na d’an lokaci ne Waziri.....!” Dubanta Waziri yai a kaikaice kana yace “Kin tabbata na d’an lokaci ne.... Shin kinada masaniyan cewa Yarima Mahmood ya soma tono diddigin abubuwa... Mai zai faru sanda ya isa k’arshen k’urya...?!” Murmushi Giwa tai kana tace “Mai ya tambayeka...?” Waziri ya gyara tsayuwarsa yana mai furta “Matarsa, mahaifinsa da kuma Jafaru...!!” Nan ma murmushi Giwa Ta kumayi kana tace “Toh mai zai dameka Waziri bacin bamuda alhakin mutuwar matarsa dana mahaifinsa a wuyanmu.... Kaima kasan wakeda alhakin Mutuwar Maimartaba da Aliya...!” Ta k’arashe wani murmushin saman fuskarta... Waziri yai mata K’uri kana yace “Kin tabbata Jafar baya raye....?” Cikeda isa Giwa Ke kuma murmusawa kana tace “Jafar ya zama tarihi tinda jimawa...!” Waziri ya jinjina kai kana yace “Allah yasa gaskiya kike fad’i, domin kuwa Jafar shi kad’aine yasan hanya da kuma launin mabud’in kurkun dake k’ark’ashin Masarautar nan, wanda tonoshi na nufin k’arahenmu ne... Dan nayi imani Yarima Mahmood sawa zai a fille kawunanmu koda kuwa Ke d’in mahaifiyarsa ce...!!” Giwa Ta kuma murmusawa kana tace “Anyima kurkukun rufinda har abada bazai kuma bud’ewa ba....!” Waziri ya murmusa kad’an kana yace “Kar kiyi gaggawa Turai domin kaw mabud’an wannan kurkuku mijinki ya mallakama wani wanda har yau bamu San ma waye ya mallaka ba...” A harzuk’e Giwa ta d’ago tana dubansa kana tace “Inada tabbacin ma Jafar ya mallaka shiyasa na b’atar da Jafar.... Na kuma rufe bakin Jafar rufuwa ta har abada....!!!” Waziri ya kuma jinjina kai kana yace “Allah yasa bakiyi kuskure ba wannan karon... Zan wuce na duba Gimbiya Zeenatu...!!” Giwa Ta murmusa kana tace “Zeenatu Karen farautarmu... Kaje kaji da mai tazo wannan karon...!” Waziri ya d’an murmusa kad’an kana yace “Tana nan tana haukarta akan mulkin Mahmood.... Da ace tasan tarkon da kika d’ana mata na tabbata da tayi yanda tayi ta fitar da kanta da kuma ‘yar uwarta daga wannan masarauta...!!!” Ya k’arashe mummunan murmushi saman fuskarsa... Giwa Ta murmusa cikeda k’asaita kana tace “Gimbiya Turai bata yima kowa alkhairi face tanada nufinta akansa....Zeenatu da ‘yaruwarta tabbas sun fad’a Tarko na... Tabbas Alhakin mutuwar Mahmood zai rataya ne a wuyansu... Zasu fice daga cikin Masarautar nan suna k’ask’antattu... Kaga na kashe tsuntsu biyu ko nace uku da Dutse d’aya tak..!!” Ta k’arashe mummunan murmushi saman fuskarta... Waziri ya murmusa kad’an kana yace “Mahmood mai Uwa... Tabbas kin cika Uwa Ta gari...!!” Giwa Ta kuma murmusawa kana tace “Na masa d’aurinda sam babu mai warwaresa...!!” Ta k’arashe dikda cewa cen k’asan zuciyarta kalaman Tal’udu ne Ke mata Yawo cewa wannan gudan jinin bai shiga cikin tandun tsafi ba kuma dik a ta dalilin wannan tsinanniyar yarinyar Saudatu.... Take tinanin Mahaukaciya Izzatu ya fad’o mata, lokaci guda Ta dubi Jakadiya dake cen gefe kana tace “Jakadiya...!” Jakadiya ta k’araso cikin sauri had’ida zubewa k’asa tana mik’awa Giwa jinjina... Giwa taci gaba da fad’in “Yau da dare zamu kaiwa Izzatu ziyara...!” Jakadiya ta jinjina kai cikeda girmamawa tana mai amsawa shigaban nata... Waziri da Giwa sukaima juna wane irin duba kana Waziri yace “Na k’agu naga Yazeedu kan Karagar nan...!” Murmusawa Giwa ta kumayi kana tace “Na d’an lokaci ne kad’an... Masarautar zata zama mallakinmu gaba d’aya...!” Suka kuma murmusawa a tare kana Waziri yai masu sallama yayi shigewarsa.... *** Misalin k’arfe tara da rabi na dare ta shigo b’angaren nata, ta soma gudanar da shirye shiryenta na bacci, bayan tayi wanka da alwala ta tada sallah tai shafa’i da wutiri kaman yanda yake a al’adarta... Tana zaune saman abin sallah tana tinanin yanda al’amara Ta kaya yau tsakaninta da Fu’ad ga kuma fargaban abinda ka iya zuwa yazo tsakaninta da Yazeed, sannan ga rashin yarda da juna da take so Ta k’ulla tsakanin Mahmood da d’iyarsa, kaman daga sama taji ana knocking a k’ofar parlor... Bata kawo komai ba dan a zatonta Umaima ce ko wata Kuyanga ce ‘yar aike... Dan haka ba tareda wani damuwa ba ta isa ta bud’e k’ofar.... Saidai mutumin data gani ne tsaye k’ik’am a bakin k’ofar yai mugun bata shock..... Sameena📚 [6/22, 1:05 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *022* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallon kallo suke ma juna su duka biyun, idanun Yazeed ko k’yaftasu baiyi dikda cewa Allah yasa bata cire Hijab d’in data ida sallah dashi jikinta ba.... Take ta tuna kalaman da ya fad’i mata d’azu da safe, kardai yazo ya tona asirinta ne... Ga wani irin mayen kallon da yake binta dashi... Ganin idan tai wasa zata iya b’ata komai dan gaba d’aya ji take kaman wuta ne Ke cin illahin jikinta da wannan irin duban da Yazeed Ke mata, d’aya daga cikin mutane biyar d’in da tafi tsana a duniyar ta... Lokaci guda tai K’ok’arin tattaro nutsuwarta kana ta d’an saki murmushi “Your Highness... What brings you here...?!” Ta fad’i murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta... Har lokacin bai furta komai ba sai k’are mata kallo da yake ci gaba da yi.... Lokaci guda kuma yasa kai ya shigo cikin parlorn k’irjinta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri ganin Yazeed ya kutso Kai cikin parlorn kai tsaye... Tai saurin jada baya don tabbas idan bata matsa ba zai bangaji jikinta ne... Ta had’iyi abinda ya tsaya mata da k’yar a mak’oshi kana ta d’ago tana dubansa.... Ko gizau babu a tattredashi.... Baibi takanta ba saima k’arasawa da yai ya zauna saman kujera irin zaman da masu mulki suka fayeyi... Muhibbah tai saurin kauda fuskarta gefe tsan tsan tsanar wannan halitta naci gaba da wanzuwa cikin zuciyarta.... Har wannan lokaci Yazeed bai furta koda kalma ba saima ci gaba da murza zobban hannunsa da yake yi... Gaba d’aya sai ta d’an daburce don yanzu kam abin Yazeed tsoro ya soma bata amma dole tai jarumtar kauda tsoron kodan tsira da mutuncinta domin kaw sam bazata bari Yazeed ya kamata ba, bari Ta b’ullo masa a k’wararriya.... Ta sauk’e fuci a hankali kana ta saki murmushi mai kyau wannan karon... Jikin k’aramar fridge ta isa ta d’auko masa bottle water harda glass cup Ta kawo Ta ijiye gabansa, kujerar dake cen gefe ta k’arasa ta zauna, k’afafu d’aya bisa d’aya... Lokaci guda take furta “To what do I owe the honor your Highness...!” Tai maganar tana mai rausayar da idanu had’ida girgiza k’afafunta dake d’aya bisa d’aya.... Murmushi ya sakar mata wannan karon yana mai dubanta, kaman bazaice komai ba sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “I can see you’re well trained... Tabbas kin K’ware a fanninki...!” Ta kuma dubansa ba tareda ta fahimci Ina ya dosa ba.....Saida ya lank’wasa k’afarsa guda wannan karon kana yace “Tell me, a ina kika tsaya..? Mai da mai kikai discovering zuwa yanzu..?!” Gabanta yai wane irin fad’uwa... Ta d’ago dara daran idanunta da suka k’ara girma lokaci guda tana dubansa... Shikenan Yazeed ya gane ko ita wacece... Su duka biyun suna duban juna, k’irjinta sai fat fat yake... Kai no bazata bari ya kamata ba, she will play his game.... Lokaci guda kuma ta saki murmushi kana tace “Excuse me your Highness, but I don’t get you... What exactly do you mean...?!” Shu’umin murmushinsa ya saki kana yace “Kin fini sanin mai nake nufi...Aren’t you a spy....!?” Wane irin ajiyan zuciya ta sauk’e jin bai fahimci cewa itace Saudatu ba... Lokaci guda ta kuma sakin murmushi kana tace “A spy...? Where’s that coming from your Highness...?!” Mik’ewa tsaye yai had’ida maida hannayensa baya, lokaci guda itama Ta mik’e tsaye.... Saida Yazeed ya kuma daidaita tsayuwarsa kana ya soma fad’in “Daga Masarautar su matata kike... Sun turoki domin ki bincika irin zaman da Zuhra keyi a Masarautar nan....Am I right...!” Harga Allah dariya yaso bata jin yanda gaba d’aya tinaninsa ya karkata.... Murmushi mai bayyana hak’wara wannan karon tai tana mai d’an rufe bakinta da yastun hannunta, dariyar take d’anyi har wannan lokacin.... Yazeed yai tsaye yana dubanta, lokaci guda take d’an k’ok’arin saita kanta kana tace “Oh I’m sorry your Highness, but you’ve that got that wrong....Do I look like a detective to you Rankashi dad’e...? I’m here to study... Karatu nake a nan, you can have me investigated if you wish.... But wait..!” Ta k’arashe tana mai dubansa sosai wannan karon... Shid’inma ita yake duba musamman labb’anta da k’wayan idanunta... Lokaci guda Muhibbah taci gaba da fad’in “Mai yasa zakai tinanin ni ‘yar bincikece... Akwai wani abu ne da bakaso Masarautar su matarka su sani gameda kai..?!” Ta k’arashe tana mai rage girman idanunta.... K’uri yai mata kaman mai tinani, kana ya saki murmushi da gefen bakinsa had’ida daidaita tsayuwarsa “You expect me to believe that...? Well I don’t buy that... I’m not the kind of prince that can be easily fooled... But be grateful you’re beautiful... Idan kinaso ki fanshi kanki, kinada abinda zaki iya fansar kanki dashi ba tareda kin fuskanci horo da k’ask’anci daga Masarautar nan ba...!” Ya k’arashe yana mai k’arasowa dab kusanta had’ida mata kallon k’urilla.... Dikda bugu da k’irjinta keyi hakan bai hanata k’ok’arin tattaro natsuwarta ba... Tai k’ok’arin janye jikinta ta matsa daga kusansa lokaci guda take furta “I’ve got nothing to be afraid of your Highness... Like I told you, idan kana so zaka iya yin bincike akaina and clear all your doubts...!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.... Miyau ya had’iya da k’yar kana ya d’anyi gyaran murya yace “If you’re really telling the truth, idan har gaskiya kike fad’i, baki tinanin ya kamata Ki samawa kanki Yarima a Masarautar nan wanda zai zamto garkuwa a gareki kafin ki gama karatunki ki tafi...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa... Kauda fuskarta tai had’ida fuzar da fuci a hankali dan sarai Ta fahimci ina zancen nasa ya dosa kana ta kuma maidoda dubanta garesa ta saki murmushi a fili dikda cikin zuciyarta kuwa tsananin k’una ne, lokaci guda take furta “I’m sorry your Highness, but I really don’t need a Prince, coz I already have a King..!!” Ta k’arashe murmushin saman fuskarta... Tamkar an buga masa babban Dutse akai haka yaji, lallai wannan yarinyar babban ‘yar rainin hankali ce, yau shi mace Ke turning d’insa down... Shi Yazeed.... Kai no, babu macen data isa tai turning Prince Yazeed down, babu ita dik fad’in duniyar nan... Murmushin k’arfin hali Yazeed ya saki kana yace “Then name your price...!” Yai maganan yana mai kuma matsowa kusanta... Dikda k’una da zuciyarta ke tsananin yi hakan bai hanata sakin murmushin takaici ba kana ta k’arasa da sauri ta bud’e masa k’ofa... Lokaci guda take furta “You’ve got a reputation to protect Rankashi dad’e...? And na tabbata baka fatan abinda zai shafawa sarautarka bak’in fenti....Zaifi kyau idan ka fice daga nan... And never think of coming back...!!” Da tsananin mamaki Yazeed ke dubanta, da gaske ne abinda yakeji... Shine mace Ke fad’a masa haka yau d’in... Shi Yarima Yazeed...!!! Kasa motsa koda d’an yatsar k’afansa dake sanye cikin takalaminsa yai, sai duban mamaki da yake binta dashi... Muhibbah da tuni taji hawaye na neman ciko idanunta lokaci guda Ta d’an kauda kanta gefe har lokacin tana nan rik’eda k’ofa tana jira Yazeed ya fice... Tai k’ok’arin maida hawayenta dikda sakin huci da take ci gaba da yi a hankali... Cikeda k’asaita ya soma takowa bai daina bintada kallon mamaki ba, saida ya k’araso daidai k’ofan kana ya kuma karkatowa yana dubanta kaman zai magana sai kuma yasa kai ya nufi k’ofa yana sakin huci... Muhibbah ta bud’e murya tace “One more thing your Highness.... Remember this, not all women have a price... Some can’t just be bought... Have a good evening, Rankashi dad’e..!!” Daga haka Ta maida k’ofa ta rufe ta bar Yazeed nan tsaye tamkar an dasa sa.... Idanunsa jajir yake duban k’ofar parlorn, jijiyoyin jikinsa sukai rud’u rud’u... Idanunsa sukai jazir... Yau shine mace Ta yarfa... A Masarautar Sa....in his very own kingdom.... Shi Yazeed AbdulJabbar..!!! Yaci gaba da sakin wani irin huci maganganun suna masa Yawo a kunnuwansa... Cikin sassarfa yasa kai ya fice a wajen kaman zai kife k’asa... Muhibbah kaw tana maida k’ofar ta lumshe idanunta hawayen da taita k’ok’arin hanasu fitowa suka shiga gangaro mata d’aya na bin d’aya... Lokaci guda ta durk’usa a wajen tana mai sakin kuka mai tsuma zuciya.... *** Yazeed gaba d’aya ficewa yai a Masarautar.... Cen club d’in da suka saba had’ewa da abokansa ya tafi..... Kaman ko yaushe, kansa a sama ya nufi spot d’in da yake nasu ne su kad’ai babu mai zuwa wajen saidai idan su suka buk’ata.... Ta wani k’ofa da babu mai noticing d’insu suke shiga, yanda aka ware masu domin zamansu, a wajen kuwa K’atoton TV ne suna ganin dik abindake wakana cikin club d’in, idan sunga budurwar da tai masu saidai suce a shigo masu da ita su d’auketa su fita... Sam bazaka San suna zuwa club d’in ba.... Zayyad amininsa ya tadda a wajen, yana ganinsa ya mik’e yana zolayarsa had’ida masa gaisuwa irinta masu sarauta.... Ko takansa Yazeed baibi ba ya zauna cikin kujerar yana mai ci gaba da sauk’e fuci a hankali.... Zamansa Keda wuya ma’aikacin club d’in ya k’araso dan taking order d’insa.... As usual Zayyad ne yace da waiter d’in a had’owa Rankashi dad’e double whisky... Shidai Yazeed bai furta koda kalma ba har wannan lokacin k’afarsa d’aya bisa d’aya yana sauk’e huci lokaci guda kalaman Muhibbah naci gaba da buga kwanyarsa... Zayyad ya matso kusansa kad’an kana yace “Your Highness Wai meke faruwa ne...? I thought bazamu sake ganinka a club d’in nan ba tun bayan mutuwar mahaifinka.... I thought kace ka daina b’ata lokaci a nan tinda Kai d’in Sarki ne mai jiran gado..!!” Shak’o wuyarsa Yazeed yai yana mai ci gaba da sakin huci yake furta “Haven’t I informed you yet, that my despicable brother is back in the country..? yana k’ok’arin k’wace abinda na jima ina hari....!!!” Zayyad da yasha damk’a da k’yar yake k’ok’arin k’watan wuyarsa yana furta “Easy your Highness... Let me go please, bani na kar zomonba....!!” Yazeed yai jifa dashi yana mai ci gaba da sauk’e huci, lokaci guda haushin abinda Muhibbah tai masa had’ida tsanar d’an uwansa Mahmood naci gaba da fuzgarsa a zuciya.... He really needs to teach that girl a great lesson... Shine Prince Yazeed wanda yafi k’arfin wulak’ancin ko wacce irin mace....!! Ganin yanayin da yake ciki yasa Zayyad kiran sauran abokan nasu guda biyu a waya.... Sosai ya razana da yanayin da yaga Yazeed ciki... Gefensa ya komo ya zauna yana mai ci gaba da sosa wuyansa yanda Yazeed ya shak’esa “Zeed.... Wai meke faruwa ne, ni ban yarda kan brother d’inka kawai kayi haka ba.... Tell me akwai wani abu ne bayan wannan....?!” Yazeed dake ci gaba da sakin huci yana murza zobban hannunsa a hankali lokaci guda yakai dubansaga Zayyad kana yace “You wanna know the whole thing..? Then fine.... Tonight, I’ve just received the insult of my life.... My evening is completely ruined, all thanks to her...!!!” Da tsananin mamaki Zayyad ke dubansa kana ya furta “Unbelievable! Yau kaine kake maganan mace taci mutuncinka your Highness...? Wow.. Just wow.... this is unbelievable..!!!” Daidai sanda ma’aikacin club d’in ya kawowa Yazeed barasan sa... Ba tareda b’ata lokaci ba ya shiga kwankwad’a kaman mai shan ruwa... Wa’iyyazubillah... D’an dafasa Zayyad yai yana duban TV d’in yanda ashararrun mata Ke rawa suna bayyana jikinsu kana ya murmusa yace “I think you needs someone to take out a little bit of stress you’ve been going through your Highness..!” Ya k’arashe yana duban ‘yanmatan murmushi saman fuskarsa... Lokaci guda yana kuma fasa kan Yazeed da cewa ba’ayi macen data ci mutuncinsa ba ta nuna masa kasawansa *** A b’angaren Muhibbah kaw tun bayan ficewar Yazeed bacci ya k’aurace a idanunta, sai faman juyi take a gado ba tareda bacci ya d’auketa ba... Ta mik’e ta zauna had’ida kunna side lamp, Ta janyo wayar salulanta tana duba time... K’arfe shad’aya da kusan rabi na dare... Jan labule ta d’anyi tana lek’a waje sararin samaniya... Taji natsuwa na zuwa zuciyarta a hankali... Lokaci guda taji tana son fita waje tasha fresh air... Mik’ewa tai ta zira doguwar riga kana ta d’aura mayafi akanta ta nufo waje.... Tana tafe taga kaman giftawan mutum sanye cikin bak’in tufafi... Exactly irin wancan mutumin data gani kwanaki biyu da suka shige... Mutum sanye da bak’ak’en tufafi ba’a ganin komai nasa.... Ta jima tana duban hanyar da taga giftawar nasa... Take taji k’afafunta sun soma janta Ta nufi wannan hanyar.... Dik irin saurinda Muhibbah keyi bata cimma wannan mutumin ba, ba kuma taga lungun da ya shige ba... Komawa da baya tai tana sauk’e huci a hankali kana Ta furta a hankali... “Muje zuwa watarana zan fahimci ko kai d’in wanene da kuma yanda kake zuwa....!!” Ta kuma fuzar da iska a hankali kana Ta juyo da zummar soma tafiya saidai ganin wad’annan Kenwa guda biyu data kuma gani yau ma yaso firgitata... Ta shiga karanto addu’o’in da suka Zo bakinta tana mai barin wajen cikin sauri.... Jefa k’afafunta kawai take dik yanda suka sauk’a tana mai jero addu’o’in da dik suka Zo bakinta.... A daidai k’ofan shiga sashen masauk’in nata ta kusa yin karo mutum... Tai saurin matsawa da baya tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali.... D’ago fuskan da zatai sukai ido hud’u da juna, hannayensa hard’e ta baya yake dubanta... Bugun zuciyarta ya k’aru ganin shid’in ne gabanta... Tai k’ok’arin tattaro natsuwarta had’ida d’aura murmushi mai kyau saman fuskarta dan harga Allah ganin shine ba wani ba sosai hakan ya jefa zuciyarta cikin natsuwa... “You again..” ya fad’i yana mai dubanta fuska babu walwala..... Ta k’ak’aro murmushi had’ida risinawa kana tace “Barkada dare Rankashi dad’e..!” Ya jinjina mata kai a hankali kana yace “Mai ya fito dake cikin daren nan...?” Ta d’an daburce gaba d’aya tama rasa mai zatace... Gajeren murmushi tai mai cikeda k’asaita yai kana ya gyara tsayuwarsa wann karon.... “Da alama yauma kin b’ace a hanya...!” Dubansa ta d’anyi kana ta kuma sadda idanunta k’asa... Gyaran murya ya d’anyi kad’an kana yace “Roaming around the palace at this hour..?” Batakaiga samo amsa ba Ubandoma ya k’araso ya risina yana mai gaida Shugaban nasa yake fad’in “Allah shi baka yawan rai mun duba ko ina bamuga mutumin da kace ka gani ba.... Masu tsaron k’ofofi da dogarai duk suma sun tabbatar basuga kowa ba..!” Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “A baza dakaru da dogarai Ta ko Ina a zak’ulo mutmin nan kafin wayewan gari...!!” Ubandoma ya risina yana mai jinjina kai had’ida amsawa kana ya baza babban rigarsa ya nufi aiwatar da umarnin Ubangidansa... Muhibbah da zuciyarta Ke raya mata Anya ba mutumin da take gani bane Rankashi dad’e yake nema... Toh Wai waye wannan mutumin....? Batakai ga samo amsa ba ta sinkayo muryar Mahmood yana fad’in “Zaifi kyau idan koma d’aki a daidai wannan lokacin..!” Daga haka bai kuma cewa komai ba yasa kai ya shige... Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya b’acewa ganinta... Tana kallo Dogari suka soma firfitowa Ta ko wane sak’o cikin Masarautar... Cikin sauri itama ta koma masauk’inta ta natsu waje guda tana tinanin toh Wai waye mutumin nan da yake Yawo cikin dare a Masarautar.... *** Giwa sai kaiwa da kawowa take, takai mari takai bango.... Mahmood yana neman zamema rayuwarta barazana... Shin maike shirin faruwa da ita ne... Anya batayi gangancin barin Mahmood raye ba... Maiyasa bata kashesa ba tintini, Maiyasa ya rainesa da hannunta... Anya ba ajalin mulkinta Ta raina da hannuwanta ba... Lokaci Ta kuma fuzar da fuci daidai sanda Jakadiya ta shigo a firgice tana fad’in “Rankishi dad’e Ta bayyana...! Izzatu Ta bayyana..!!!” A d’ari Giwa Ta mik’e tsaye idanunta suka firfito waje cikeda tashin hankali....! Sameena📚 [6/24, 11:48 AM] +234 703 881 5154: *MUHIBBAH* *023* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Hankali tashe Giwa Ke fad’in “Ke Jakadiya Ki natsu Ki sanar dani abindake tafe dake cikin daren nan... Bana san shashanci da hauka...!” Jakadiya na sauk’e haki take fad’in “Allah shi baki yawan rai Ina tinanin Izzatu ce ta bayyana dan ga Yarima Mahmood ya cika Fada da dakarai, ga dukkan alamu Masarautar babu lafia...!” Giwa ta isa jikin window ta yaye labule nan ta hangi dogarai sai kaiwa da komowa suke... Juyowa tai tana duban Jakadiya kana tace “Kin tabbata Izzatu ce ta bayyana... Ko kuwa wani abinne daban...?!” “Allah shi taimakeki idan ba Izzatu ce ta bayyana ba maizaisa Dakarai su bazama cikin masarauta...?!” Giwa ta girgiza kai tana mai furta “Sam hakan bamai yuwa bane Jakadiya... Sanin kanki ne bayyanar matar nan na nufin tashin hankalinmu ne...Ina Ubandoma...?” Jakadiya batakaiga bata amsa ba Jamal ya shigo yana tambayan Jakadiya abinda Ke faruwa cikin Masarautar nasu dan yaga Dakarai ta ko wani angle.... Jakadiya ta basa amsa da fad’in “Allah shi taimaki Gwarzon Giwa, ai Ina tsammanin cikin Fada ne Babu lafia...!” Yarima Jamal ya jinjina kansa kad’an kana ya dubi mahaifiyarsa yace “Maami are you alright..?!” Ta jinjina masa kai alamun lafia take... Lokaci guda Jamal ya nufi k’ofa yana fad’in bari ya duba meke faruwa cikin Masarautar.... Jinjina masa kai kurum Giwa tai ba tareda ta iya basa amsa ba... Yana ficewa Ta kuma duban Jakadiya kana tace “Maza kije ki nemi Ubandoma yanda ya shiga ya fita kiji abindake wakana cikin Masarautar sannan ki tabbata Mahmood baiga Izzatu ba....!!” Jakadiya ta jinjina kai tana mai amsa mata kana Ta fice cikin sauri... Ta bar Giwa nan d’aki sai kaiwa da komowa take, ga hannunta dake rufe cikin safa sai mintsilinta yake a hankali, wannan alamace na cewa shirinta na iya backfiring d’inta kaman yanda Tal’udu yasha sanar da ita.... Sosai Ta matse hannun tana huci take furta “Turai nake, murucin kan Dutse ban fito ba saida na shirya, kayi kad’an Mahmood iyayenka ma sunyi kad’an... Na kassarasu balle kai... Na d’aid’aita ahalinka, kaid’in kayi kad’an kace zakajada Giwa.....!!” Tana ida fad’in haka ta d’an zame safar hannun nata... Gabanta ya yanke ya fad’i ganin Yana nan a halittansa na launin bak’i... Tai saurin maida safar ta rufe kana takai dubanta ga d’aya hannun nata dake sarari shi d’in fari ne tas gwanin ban sha’awa.... A hankali ta fuzar da fuci tana jiran taji da mai Jakadiya zatazo mata.... A kusan k’ofan bayi Jakadiya ta had’uda Ubandoma... Ta d’an murmusa kad’an kana tace “Wai fushi kake dani har yanzu, kaima kasan bayin kaina bane.. Ya na ita da umarnin Giwa...” Ubandoma ya kuma watsa mata harara kana yace “Wannan hannu naki da ya jeme ya sud’e dan bauta ba dole naji marin nan ba, har yanzu Jakadiya jinyar k’uncina nake...!” Dariya yaso kubcewa Jakadiya, Ta d’anyi kad’an kana tace “Yanzu dai ba wannan ba, Giwa ce ta aikoni dan sanin meke wakana cikin Masarauta... Ko Izzatu ce ta bayyana...?!” Ubandoma ya watsa mata muguwar kallo kana yace “Banda k’ask’anci da tozarci a rasa waye zai mareni sai Baiwa gajiyayya...!” Jakadiya ta kastesa da fad’in “Kai Ubandoma... Zaka amsa tambayar Uwargijiyarka ce kokuwa wani marin kake so ka sake amsa...?!” Ubandoma ya sab’a babban riga yana mai kad’a Kai cikeda takaici kana yace “Wannan karon kam saidai kece zaki amsa marin dan kin sanar da Giwa abinda ba haka ba... Take ya sanar da Jakadiya abindake wakana cikin Masarautar da kuma yanda Yarima Mahmood ya bada umarnin binciko wannan mutumin cikin gaggawa... Babu b’ata lokaci Jakadiya ta shige Kai sak’owa shugabanta... ** A babban haraban Masarautar Jamal ya tadda Mahmood, ya k’arasa gareshi suka gaisa yana tambayansa ko wani abu ne Ke wakana cikin Masarautar... Mahmood ya sanar dashi abindake faruwa... A tare Mahmood da Jamal suka ci gaba da gudanar da binciken mutumin da aka gani cikin Masarautar wanda ba’a ita identifying kamanninsa ba sabida shiga Ta bak’ak’en tufafi da yakeyi... Haka nan suka umarta Dakarai da aci gaba da searching cikin Fada har zuwa wayewan gari don Mahmood ya tabbatar mutumin cikin Masarautar yake, babu yanda za’ai ace shigowa yai bayan irin tsaron dake a cikin Masarautar... Haka sukaita bincike har kusan asubahi babu wannan mutumi babu dalilinsa... Yarima Mahmood ya d’an dafa kafad’ar Jamal kana yace “Kaje ka huta k’anina...!” Jamal ya girgiza kai cikeda kulawa kana yace “A’a Yaya, bazan tafi na Barka kai kad’ai a nan ba... Kar ka damu dani, lafia lou nake..!” Ya k’arashe cikeda kulawa... K’uri Mahmood yai masa kana ya jinjina kai a hankali alamun gamsuwa... Suna nan tsaye a wajen Sport car d’in Yazeed k’irar Lamborghini ta kutso Kai cikin masarautar... Suka bi motar da kallo har ya k’araso ya shige sashensa ... Girgiza kai kad’an Mahmood yai yana duba lokaci a wayar salulansa.... Jamal ya d’an kai dubansaga Mahmood d’in kana yai gyaran murya kad’an “Yaya ko zaka koma cikin gida ka huta, ka barni in charge zan kula da komai...!” Baice komai ba sai sa kai da yai ya nufi sashen Yazeed... Ya tadda Yazeed d’in ya fito daga mota... Kallo d’aya Yazeed yai masa ya watsar.... Ko a jikinsa ya nufi cikin gidan... Mahmood ya bud’e murya kad’an ya kirawo sunansa.... Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba... Yarima Mahmood yaci gaba da takowa har ya k’araso kusan Yazeed d’in.... “Yazeed kakuwa San yanzu k’arfe nawa ne..?!” Ya tambaya yana duban Yazeed d’in... Sai sannan Yazeed ya kaikaito yanaima d’an uwan masa wani irin duba... “Na sani... Why...Do you’ve problem with that...?!” Ya fad’i cikeda gadara ga tangad’i da yake alamun giyar bata sakeshiba dikda k’ok’ari da yake kar a gane a buge yake.... Mahmood ya girgiza kai a hankali kana yace “Yazeed mai ka d’auki rayuwar nan ne... Yazeed mata da giya duka biyu ka had’a...? Yazeed I thought ka canza, I thought ka aje duka wad’annan d’abi’un tuntuni.... Yazeed mai kake son maida rayuwarka data iyalanka...? A haka ne kake so ka zamto Shugaba a Masarautar nan...? Kana dawowa cikin Fada tsakar dare kuma a d’auke..? Wannan shine misalin dake so ka bayar a mulkin ka... Wannan shine misalin da kakeso ka baiwa yaranka...” Katsesa Yazeed yai da fad’in “Cut the lecture please Yaya... Will you..?” Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Why do you even care.. Rayuwatace nayi yanda nake so da ita... Kuma wannan bashi zai hanani zamtowa Sarki na gaba ba... Wllhi kaji na rantse maka da Sarkin dake busan numfashi akan sarautar nan zan iya aiwatar da komai... Ko mene shi, and just so you know, I won’t hesitate to run over who ever gets in my way...!!” Yana k’arasa fad’in haka yasa kai ya shige yana mai ci gaba da tangad’i... Fu’ad dake tsaye daga bayansu cikin sanyin jiki ya k’araso ga Mahmood... “Yaya good evening...!” Ya fad’i yana d’an shafa sumarsa.... Mahmood ya dubesa da mamaki kana yace “Bakai bacci ba Fu’ad.... Mai kakeyi a nan...?!” D’an shafa kansa Fu’ad ya kuma kana yace “Na farka ne Yaya sai nakeji kaman cikin Masarautar babu lafia... Can I be at any help..?” Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “Is ok karka damu, ba wani abun damuwa bane... Guards are already taking care of the situation..!” Fu’ad ya jinjina kai cikeda k’aunan d’an uwan nasa, Mahmood d’in ma murmushi ya saki masa kad’an yana mai d’an buga kafad’an Fu’ad yake tambayarsa ya yake Kwana biyun.... A haka suka jera gwanin ban sha’awa suka ratsa cikin Masarautar... A haka suka k’araso suka tadda Jamal yanda yake ci gaba da umartan dakarun tsaron cikin gidan.... Jamal na hangosu ya k’araso yana tambayarsu ko akwai abinda ya canza... Yarima Mahmood ya girgiza masa kai a hankali alamun babu... Gyaran murya kad’an Jamal yai kana yace “Yaya maybe idonka ne ya gane maka wannan mutumin, maybe wani ka gani cikin dakarun gidan nan kai tinanin ko wani daban ne ko wani mugu ne... Yaya I’m sure babu wanda zai iya haye manyan ginin Masarautar nan ya shigo kokuma ya tsallake dika Jami’an tsaron dake cikin gidan nan... I think babu kowa kaman yanda muke tinani....!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Fu’ad ya jinjina kai yana mai furta “I agree with Jamal Yaya... Maybe wani ka gani cikin dakaru...!” D’an jim Yarima Mahmood yai kana ya jinjina kai yana mai fuzar da fuci a hankali “You’ve a point... But I’m sure naga mutum cikin bak’ak’en tufafi, sannan zuciyata bai kwanta da ganin wannan mutumin ba.. Na soma binshi sai naga tafiyar tasa kaman gudu gudu ne...! But is okay, let’s not think of the worse...” Fu’ad ya jinjina kai alamun gamsuwa kana Jamal yace “I’ll check on Maami...” Jinjina masa kai sukai a tare kana ya shige Mahmood da Fu’ad ma sukai ma juna sallama kowa ya nufi b’angarensa... *** Sosai hankalin Giwa ya kwanta jin ba Izzatu bace Ta bayyana kaman yanda Jakadiya tazo mata da batun daga fari... Washe gari sassafe sukai shirin zuwa ganin Izzatu itada Jakadiya... Kasancewar Giwa takan fita rangadi a Masarautar yasa sam bazakai zaton wani mugun nufi ne da ita ba.... Dik yanda ta shige bayi sai Sun risina suna kwasan gaisuwa... Jakadiya Ke amsa masu... Muhibbah da tin fitowarsu take biyedasu ba tareda sunyi noticing d’inta ba tana ganin sun nufi wata k’ofa daga cen b’angaren hagu dake gabashin Masarautar taji gaba d’aya jikinta bai aminta da yanda suke zuwa ba.... Mak’alewa tai jikin dogon gini tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali, lokaci guda take k’arfafawa kanta gwiwa, zuciyarta na ayyana mata cewa zaki iya Saudatu... Zaki iya... Lokaci guda taji wane irin k’warin gwiwa na zuwa mata... Abinka da gida na sarauta Kuyangi dik sabgogin gabansu suke babu mai noticing d’inta musamman dashike itama d’in shiga irinta mulki tai dan haka babu wanda zai kawo wani zargi ko shakku da kokonto a gameda ita.... Tafiya mai d’an tsawo sukai cikin Masarautar kafin Ta hangi Giwa da Jakadiya sunja sun tsaya jikin wani gajeren garu wanda saika kula sosai ka fahimci akwai d’aki wajen... Muhibbah ta kuma mak’alewa jikin gini tana mamakin mai sukeyi tsaye wajen nan.... Cen bada jimawa ba ta hango wani mutumi ya k’araso ya nufi k’ofan gajeren ginin yana k’ok’arin bud’ewa... Sam bazakai zaton akwai gini wajen ba... Tsananin mamaki ya kamata... Wai dama d’aki ne a wannan wajen.... Take ta kuma jin tana san ganin menene cikin d’akin nan... Ta d’an sad’d’o had’ida fitowa daga mab’oyar nata sanda taga sun sunkuya Sun shige cikin ‘yar d’akin nan.... Cikin sand’a Muhibbah ta k’araso jikin d’akin k’irjinta na tsananta fad’uwa.... Hankalinta bai ida tashi ba saida ta lek’a cikin d’akin yanda ta hango Giwa tsaye gaban wata mata dake duk’e gabanta an d’add’aureta da manyan sark’a.... Tsoro da firgici sosai ya kama Muhibbah ganin wannan matar dake d’aure da manyan sark’ok’i ba kowa bace illa wannan Mahaikaciyar da suka fara arba da ita farkon shigowarsu Masarautar.... Jikin Muhibbah ya d’auki rawa, take taji k’afafuwanta na yunk’urin gaza d’aukarta, hawaye taji na k’ok’arin ciko idanunta... Tai saurin saka hannayenta biyu ta toshe bakinta dan ko shakka babu kuka ne sosai Ke k’ok’arin b’alle mata... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Kalaman da zuciyarta Ke iya nanatawa kenan... Tai saurin komawa da baya ta jingina jikin garu har lokacin hawaye basu daina zarya a fuskarta ba... Hannayenta kuwa sosai ta k’unshe bakinta dasu dan karma sautin kukan ya bayyana.... Cikin sauri Tai k’ok’arin barin waje dan take taji duniyar na juya mata, take taji tana kewan gida, tana son kasancewa da Ansar da kuma Mummy.... Da k’yar ma ta fahimci hanyar databi har Ta samu Ta k’araso masauk’i... Tana k’arasowa d’aki ta fad’a saman gado tana kuka mai tsuma zuciya.... Tana a haka taji k’aran shigowan sak’o... Tai k’ok’arin mik’ewa Ta janyo wayar nata tana mai goge hawayen fuskarta... Ansar ne ya turo mata sak’on barkada safiya kaman yanda yakeyi ko wace safiya, yakan turo mata sak’o dan jin ya Ta kwana Ta kuma tashi.... Ta kuma saka bayan hannunta tana share hawayen bayan Ta ida karantawa... Ta saki murmushi a hankali tana mai jin dad’in sak’on da Ansar ya turo mata wanda ko yaushe sai ya fad’i mata how much he loves and misses her... Sosai taji tana son tafiya gida bayan ganin mahaukaciyar nan da tai cikin tsananin ukuba... Lallai Giwa tayi nisa a mugunta, azzaluma ce wacce batasan ta yanda zata misalta kalan zaluncinta ba... She wasn’t mistaken, she was right all along... Wannan masarauta babu komai cikinsa face bak’in zalunci.... Take Ta turama Ansar sak’o cewa tana zuwa gida gobe.... Koda Ansar yai receiving sak’onta yayita kiranta amma bata d’agawa, k’arshe haka ya hak’ura ya zubawa sarautar Allah ido dan yasan halin kayansa idan batayi niyyan bazata d’aga ba.... Haka nan take da kafiya akan dik abinda Ta saka gaba... *** Washe gari kaw Ta kama monday tsaf tai shirinta da zummar tafiya makaranta, sassafe Ta shirya tin k’arfe bakwai ta nufo tasha ta d’auki hanyar Bauchi.... A hanya take ganin kiran Umaima, bata d’aga ba sai sak’o data tura mata cewa ta tafi makaranta tanada aji tin daga safiya har zuwa yamma, Umaima ta tura mata da sak’on nasara da fatan alkhairi... Murmushi Muhibbah tai tana ayyanawa cikin zuciyarta cewa tabbas Umaima ta banbanta da mutanen wannan masarauta... Haka Fu’ad da Zahra suka tasa Umaima gaba da tambayar ko Ina Muhibbah, nan Umaiman Ta sanar dasu kaman yanda Muhibbah ta sanar da ita.... Fu’ad ya d’an dubi Umaima kana yace “Perfect place kenan for us be meeting nida ita....” Umaima ta d’an murmusa kana tace “Prince F naga alama zuciyarka fah tai nisa bata jin kira...!” Ya murmusa kad’an cikeda k’asaita wanda Ke k’ara masa kyau ba tareda yace komai ba.... ** BAUCHI (Tambari Housing Estate) Misalin k’arfe 8:30am ya shigo cikin parlorn sanye da tracksuit d’insa da alama daga motsa jiki yake.... Mummy da fitowarta daga kitchen kenan tai tsaye sororo tana dubansa... “Kai kuma fah...? Wai ba ce min kai kamada appointment a asibiti 8:30am ba, ya na ganka a nan...?!” Rage kayan jikinsa yake yana fad’in “Nayi shifting d’insa zuwa yamma ne...!” Ya fad’i yana nufa dining table... Mahaifiyar tasa ta d’an kuma dubansa kana Ta tab’e baki kad’an tace “Wani wajen zaka jene...?” Ya d’an girgiza kai kad’an yana mai bud’e foodflask d’in dake bisa dining table d’in lokaci guda yake furta “Ina nan a gida Mommy....!” Ta d’anyi Jim tana dubansa kana Ta jinjina kai tana mai furta “Toh Allah shi taimaka....” Lokaci guda Ta nufi corridor ta barsa nan tsaye jikin dining table sai kuma shafa wayar salulansa yake... Wayarta yaketa k’ok’arin nema amma bai samunta, gajeren tsaki ya saki a hankali kana ya fice daga parlorn ya nufi d’akinsa danyin wanka.... Wajajen k’arfe 9:30am Mommy na tsaye parking lot tana k’ok’arin bud’e mota da zummar tafiya aiki sai hango Muhibbah tai tana shigowa... Baki sake Mommy Ke dubanta, motar da bata shige ba Ta karkata sosai tana kuma dubanta... Muhibbah na hango Mummy ta tafi da gudu ta rungumeta harda ‘yar tsallenta... Mommy ta d’ago sosai tana dubanta kana tace “Wai wa nake gani haka kaman Hibba... Daga tafiya sch ko sati bakiyi ba shine har kinzo...?” Muhibbah Ta d’an cuno baki gaba kana tace “Kai Mommy nifa kewarki nake sosai bazan iya sati ban ganki ba...” Mommy ta d’an harareta kana tace “Toh mai amfanin wayarki basai muyi vid call ba....” Kafad’a ta d’an mak’ake kana tace “Vid call daban zuwa daban Mommy...!” Dungurinta Ta d’anyi tana fad’in “Kyaji da gulmarki dai... Kinga ni Office na nufa ma...” Rik’eta Muhibbah tai tana fad’in “Chabb! Ai wllhi mommy tinda dai nazo ba wani tafiya Office nida yau yau zan juya Jos... Haba Mommy...!” Ta k’arashe tana kwantar da kai cikin jikinta had’ida janyota suka nufi cikin gida... Ansar dake tsaye daga cen k’ofar parlornsa hannaye sakale cikin aljihun wandonsa ya nufo yanda suke... Sukaima juna K’uri daga shi har Muhibbar.... Mommy Ta dubesu kana Ta jinjina kai tace “No wonder kak’i tafiya office ashe ta sanar dakai tana tafe... Kun k’ulla abunku dama tare..!” Itadai Muhibbah murmushi kawai take shi kuwa Ansar babu wani walwala saman fuskarsa, saima kallon tuhuma da yake bin Muhibbar dashi.... Dikda ganin irin duban da Ansar ke mata hakan baisa tabi takansa ba saima dad’a shigewa jikin Mommy da tai tana fad’in yanda tayi kewarta... Office d’in da Mommy bataje ba kenan suka b’ige da hira da d’iyarta har saida akai mata waya daga office d’in ana nemanta cikin gaggawa kafin ta kuma shirin fita... Har bakin haraban gidan Muhibbah ta rako Mommy tana fad’in da la’asar zata wuce Jos ba lallai ta dawo ta sameta ba... Mommy Ta d’an dafata kad’an kana tace “Banso kina tafiyan yamma yanzu lokaci ne na damuna Ki bari da safe Ansar ya maidake...” Muhibbah ta d’an sadda kai kana tace “Mommy zanso hakan but first thing tomorrow morning inada class mai mahimmanci ne shisa...” Mommy Ta d’anyi Jim kana tace “Oh is that so...? Toh ko na bar tafiya Office d’in na maidaki ne...” Gaban Muhibbah ya ya Ke ya fad’I tai k’ok’arin saita kanta kana tace “No Mommy you don’t need to worry ai zan iya komawa da kaina...” Girgiza mata kai Mommy tai kana tace “Ni drivers d’in nan ne ban wani aminta da tuk’insu ba musamman duba da yanda suke gudun fitan hankali saman kwalta ga kuma lokaci na damina....” Kafin Muhibbah takaiga bata amsa suka sinkayo muryar Ansar yana fad’in “Zan mayar da ita Mommy..!” Dubansa Mommy tai kana ta jinjina kai tace “Toh shikenan hakan yayi, amma kaima idan ka kaita sai kaika kwana cen Jos d’in gobe da safe idan Allah ya kaimu ido na ganin ido saika komo...” Ansar ya jinjina mata kai yana mai amsawa... Mommy suka kuma yin sallama da Muhibbah kana ta shige mota tana fad’iwa Muhibbar “Nacewa Larai yau Ta girka favorite d’inki for lunch...” Murmusawa Muhibbah ta kumayi cikedajin dad’i da k’aunar mommy kana suka kumayin sallama sannan Mommy ta fice tana mai mata fatan alkhairi... Motar mommy na ficewa ta juyo kad’an tana duban Ansar dake jingine jikin k’arfen parking lot har lokacin fuskarsa babu walwala... K’arasowa tai itama nata Fuskar babu walwala kana tace “Maiyasa ka cewa Mommy zaka maidani bayan ko gaisuwata baka amsa ba...?” Da wutsiyar ido yake dubanta kana yace “Kaman bakisan laifin da kikai ba....!” Ta kuma dubansa kad’an kana tace “Laifi kuma... wane irin laifi...?” Faran kujera dake gefe ya janyo ya ajiye mata kana yace “Zauna..!” Babu musu ta gyara kujeran ta zauna shima ya janyo wata kujerar ya zauna... Ansar yace “duba wayarki kiga sau nawa na kiraki...” Murmusawa Ta d’anyi kana tace “Wannan ne yasa ake fushi dani Likita...?” Ya d’an dubeta kana yace “Not only that... Maiyasa bazaki bari nazo na kawoki gida ba na maidake dakaina kaman yanda muka faro...Maiyasa zaki taso Ke d’ayanki Ki fito... What if wani abin yaje ya sameki Hibbah...?” Ya k’arashe cikeda damuwa... “Relax Doc, babu abinda ya sameni... Haba saikace wata k’aramar yarinya... I can take care of myself fah Yaya Dr, kuma kaima bai kamata na katse maka aikinka ba ai... Nifa zan iya komawa ma, kawai kayi saurin fad’iwa Mommy zaka maidani ne...!” Girgiza kansa yai kad’an kana yace “So tell me... Meke faruwa a cen Masarautar...?” Gyara zamanta ta d’anyi had’ida fuzar da huci kad’an kana tace “Let’s not talk about that...besides nazo nan ne na mance da abubuwan dake faruwa, na d’an sami fresh air naga gida da mutanen da nayi kewarsu..” Ansar ya d’an fito daga cikin kujeran fuska fal damuwa yake fad’in “Tell me did they do something to you..? Did they hot you...? Talk to me Hibbah... Mai suka miki...?!” Ya k’arashe cikeda tashin hankali... Ganin yanda hankalinsa gaba d’aya ya kad’u sai ya bata tausayi, sosai Ansar ya damu da ita fiyeda yanda ta damu da kanta... Girgiza masa kai kad’an tai kana tace “Basu mun komai ba.. But naga abinda ya d’aga min hankali ne... Ansar mutanen nan basuda imani...!” Ansar ya kuma gyara zamansa yana fad’in “Tell me, mai kika gani...?” Batakaiga basa amsa ba wayarta ya d’auki ruri... Bak’uwar lamba ce Babu suna... Ta d’anyi excusing kanta kana ta d’aga wayar da sallama... Kaman baza’a mata magana ba dan har saida ta kumayin sallama tana tambayar ko wanene sannan taji anyi gyaran murya cikeda k’asaita.... Jin muryar Yarima Fu’ad cikin wayar ya sanyata d’ago fuska tana duban Ansar da shi d’inma ita yake duba.... SameenaAleeyou📚 [6/27, 10:26 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *024* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Barkada safiya Rankashidad’e..!” Ta fad’i murmushin da yafi kamada yak’e saman fuskarta... Daga cen b’angaren Fu’ad ya murmusa kana yace “Ashe zaki d’auki muryata...” Ta kuma murmusawa kana tace “Murya mai kaman busan sarewa ba’a mancesa cikin gaggawa Rankashi dad’e...!” Tai maganar cikeda k’issa... Ansar dake zaune gabanta fuzar da fuci yai had’ida mik’ewa tsaye yana mai juya baya lokaci guda yana fuzar da fuci d’aya na bin d’aya... Yana jin sanda Muhibbah ta kuma murmusawa tana fad’in yau d’in batada hutun tsakankanin class gaba d’aya busy day ne da ita bazasu iya had’uwa ba saidai next time... Ji yake kaman barbad’a masa garwashin wuta take a kunne da wannan wayar da take wanda ya tabbata ko shakka babu da d’aya ne daga cikin ‘Ya’yan Sarki AbdulJabbar take... Kasa jurewa Ansar yai sai faman dunk’ule hannunsa yake yana sakin fuci, lokaci guda ya juyo had’ida fincike wayar daga hannunta ya kashe yana mai furta “Ok that’s enough.! Ya isa haka..!!” Da mamaki Muhibbah ke dubansa, lokaci guda ta mik’e tsaye cikin tsananin b’acin rai “Ansar miye haka...? Ka kuwa kasan mai ka aikata..!!?” Rai b’ace shima yake fad’in “A gabana kike waya da wani k’aton banza... You know what Hibbah.? I was such a jerk da na yarda miki Ki tafi kiyi rayuwa cikin Masarautar nan in the first place... I shouldn’t have allowed you to go back to that place..!!” Katsesa tai da fad’in “And you think you can actually stop me now...? Well no, bazaka iya hanani ba...Those people turned my life into a nightmare, thay took everything away from me, basu cancanci rayuwa cikin Farin ciki ba... Gaba d’ayansu basu cancanci rayuwa cikin kwanciyan hankali ba... I promised to take them down, even if it will cost me my life, wllhi sai na d’aid’aitasu...!” Ta k’arashe hawayen k’unan rai na gangaro mata... Lokaci guda Ta koma ta zauna cikin kujeran tana mai ci gaba da kuka maras sauti.... Ansar ya fuzar da fuci kad’an kana yan janyo kujeran ya zauna shima “Hibbah that too much resentment dake kwance cikin k’irjinki bazai haifar miki da komai ba face tarin dana sani... And do you know what’s worse..?, na tabbata gaba d’aya idanun Princes d’in akanki yake... Hibbah mai kike tinanin zanji...? Do you think this is fair for our relationship..? Please try to be a little bit considerate Hibbah...Zuciya batada k’ashi, kuma ita soyayya batasan sanda take shiga ba... What if you ended up falling in love with one of those princes..?” Da tsananin mamaki ta d’ago idanuwanta masu zuban hawaye tana dubansa, lokaci guda take girgiza cikin rashin yarda da abinda kunnuwanta Ke jiyo mata, murmushin takaici mai tsananin ciwo saman fuskarta take furta “Bayan dik abubuwan dana sanar dakai har kana tinanin ni Muhibbah zan afka soyayya da d’aya daga cikin mutanen dana fi tsana sama da komai a duniyar nan, mutanen da sukai jagoranci wajen ruguza rayuwata data ahalina... Ansar ban tsamman zanji haka daga gareka... Na zaci zakafi kowa fahimtata...” Batakai aya ba ya katseta da fad’in “Muhibbah abinda nake gani ne... Jiba fah kiga yanda kike waya da wannan d’an Sarkin kama wasu masoyan gaske..!” Wannan karon mik’ewa tai cikeda b’acin rai, ta dakatar dashi da fad’in “Cut the crap..! Ka kuwa San mai kake fad’i Ansar... Ni kake had’awa da wad’ann mutanen...?” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata.... D’an fuzar da fuci ya kumayi kana yace “I’m sorry Hibbah, please forgive me.... Hankalina bai kwance ne muddin kina taredasu...!” Hannu tasa Ta goge hawayen cikin zafin rai take fad’in “This should be the last time da zaka had’ani da wad’annan disgusting creatures din...!” Ansar ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Bazan sake ba Muhibbah... So tell me mai da mai kika fahimta zuwa yanzu... How far have you gone..?” Zama tai cikin kujera had’ida k’urama waje guda idanu lokaci guda ta saki murmushi a hankali kana Ta soma furta “Dukansu da kake gani na karanci weakness d’insu, kuma dashi zanyi ruining d’insu.... Fu’ad da kaji muna waya dashi, a nashi haukan ya fad’a soyayya dani, wannan mahaukacin his weakness is his insecurity... Zanyi amfani da wannan daman to toy with his emotion and watch him crumble... Shi kuma Yazeed..!” Tai murmushi a hankali kana tace “Na riga dana fara bashi... His pride, son mulki had’ida son mata shi zai kaishi k’asa warwas, I’ll use that to ruin his marriage and make him look like a loser...And Yarima Mahmood...!” Ta d’an murmusa kad’an kana taci gaba da fad’in “His daughter will be his own downfall... Zanyi amfani da ita to bring him down... Guda d’aya daga cikinsu shine har yau ban fahimci ko shi d’in wane irin mutum bane.. Yanada wahalan fasaltuwa, yafi kamanni da hawainiya mai canza kala, mutum ne da baka fahimtar gabansa ko bayansa balle ka gane ina ya dosa... Amma daga yanda tinana ke bani shid’in yafi kusanci da mahaifiyarsu.. Idan nayi nasaran d’aid’aita masa rayuwa ko shakka babu kaman na cakkawa Turai wuk’a ne a k’ahon zuciyarta... Sannan idan nai nasaran d’aid’aita rayuwar Turai kaman na cakkawa Jamal wuk’a ne a k’ok’on zuciyarsa... Su biyu d’in suna tafiya kafad’a da kafad’a ne... Kaga koda ace banyi nasaran karantar Jamal ba ruguza Mulkin Giwa da yaranta daidai yake da ruguza Giwa da d’anta Jamal...!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin murmushi... Fuzar da fuci a hankali Ansar yai yana mai murza tafukan hannunsa kana yace “Must you really have to involve Mahmood’s daughter.. I mean she’s an innocent kid, she had nothing to do with what her father did in the past....Laifin na mahaifinta ne ba nata ba, karkizo kiyi abinda later on you will regret doing it..!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Shiru tai tamkar mai tinani kana Ta fuzar da fuci a hankali lokaci guda taci gaba da fad’in “Ni kaina banso Zahra Ta shigo cikin shirin fansa na sabida yarinya ce mai hankali da kuma hangen nesa, Yanda kasan ba zuri’ar Sarki AbdulJabbar ba... But nasan abinda nakeyi, bazan bari Ta cutu ba... From what I learnt, her father’s been lying to her, he’s hiding something from her... Something very serious, Ina tsamman ya shafi mutuwar mahaifiyarta... Zan saka mata kokonto da shakkun mahaifinta cikin zuciyarta, after all dama shid’in mutumin banza ne, bai cancanci zama mahaifin Zahra ba...!” Ta k’arashe tana sakin huci... Ansar yai shiru kaman mai tinani kana yace “This is a very delicate matter Hibbah, we are talking about an innocent child here...Make sure she doesn’t get hurt..!” Fuzar da fuci tai a hankali tana mai dubansa damuwa k’arara saman fuskarta kana tace “Believe me sabon kwanaki kad’an da nai da ita I become very fond of her, bazan bari ta cutu ba da izinin Allah...!”Ta k’arashe damuwa kwance saman fuskarta... Mik’ewa tsaye Ansar yai yana mai furta “Bana fatan kiyi abinda zakizo kina dana sanine Muhibbah... Kodashike Na yarda dake... And I know you’re a good person, nasan dik abinda kikeyi saida kikayi tinani sosai ... And addu’ata da soyayyata na tareda Ke ko yaushe... I hope everything will soon come to an end, so that we can finally get the chance to be together... Forever..!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Murmushi ta sakar masa cikeda tausayinsa kana tace “In sha Allah My Dr...!” Ya murmusa kad’an shima kana ya duba agogon dake d’aure hannunsa na hagu yace “Zanje asibit kafin la’asar zan dawo sai na shirya... Is it okay with you..?” Murmusawa tai a hankali kana tace “Sure... Take your time Likita, nima zan shige Kitchen ne na taya Larai da wasu aikace aikacen...” Lokaci guda take d’an masa waving tana fad’in a dawo lafia.. Tsaye yai hannayensa sakale cikin aljihun wando yana dubanta har Ta shige kana ya fuzar da fuci a hankali ya nufi ma’ajiyar motarsa... *** Suna tafe a hanyar komawa Jos take labartawa Ansar abinda ta gani gameda mahaukaciyar da suka soma arangama da ita farkon zuwansu Masarautar... Shima sosai yaji mamakin wannan lamari had’ida kuma tabbatarwa lallai akwai abubuwan dake b’oye cikin wannan masarauta, kuma idan har Muhibbah zata zamto silan warwarewan wasu al’amara a Masarautar tabbas now more than ever bazai hanata ba dan wannan dangin jihadi ne saidaima yaci gaba da mata add’uan samun nasara.... Nan take kuma tabbatar masa hakan ya nuna k’ila tabbas mahaifinta na nan raye cikin Masarautar, k’ila Giwa bata kashesa ba, k’ila Yana nan raye tanai masa uk’uba kaman yanda takeyiwa mahaukaciyar nan... And now more than ever bazata janye k’udirnta ba har sai ta ceto mahaifinta da duk wani rai da ahalin AbdulJabbar ke zalinta.... Yamma lis goshin magrib suka iso Masarautar saidai Ansar bai shiga ba hasalima daga cen nesa da ginin masarautar ya ijiyeta kana ya shige masauk’i da zummar Washe gari da sassafe idan Allah yakai rai zai d’auki hanyar gida... ** MASARAUTA Zaune suke a hamshak’in parlorn na alfarma... Raheema an ci gayu cikin kaya na mulki da sarauta, kan nan a k’asa yawa mutuniyar arziki, sai faman sakin murmushin yak’e take, itafa wannan yarinyar tasa mugun shiga hakkinta take, tama kula tsaban Mahmood baison kasancewa da ita dik randa zasuyi zance dole Zahra na wajen.. Ta lura da biyu yake barin d’iyar tasa Ta kasance wajen tsaban baison keb’ewa da ita.... Kuma shi ba komai yake ce mata a hiran ba saidai tayita faman sakin murmushin k’arya a barta da ciwon kumatu tinda murmushin na dole take... Ta gaji ta gaji da wannan shegiyar d’iyar tasa da tai mata k’ebebe a mak’ogoro take neman Ta hanata rawar gaban hantsi.... Ga wani uban sakalta yarinyar da yakeyi saikace kansa aka fara haihuwa... Shi ko irin hallayan gidan sarautar nan ma baiyi yanda masu sarauta Ke son yara maza Dan su zamto magadansu amma shi kacaukam hankalinsa kan wannan yarinyar...Kodashike dan yaga baida wasu yaran ne sai ita, da zaran ta shiga gidansa ta haifa masa yara maza ‘yan tagwayen zai mance wannan tsinanniyar yarinyar ya watsar da tashanta, sannan ya koma yayinta itada yaranta da zata haifa masa...! Ta k’arashe tinanin nata tana sakin murmushin cin nasara.... Tana tsaka da murmushin ne taga Zahra ta mik’e ta nufi cen bayan parlorn tana k’ok’arin amsa waya.. Umaima ce mai kiran nata “Seriously Aunty Umaima... Tia ta dawo, please kice mata Ta k’araso sashen Paa d’ina Ina cen Ina jiranta.. Please please kar tace no...And tell her Zanyi fushi yanzu kam idan tak’i amsar gayyatana..!” Bata jira amsar Umaima ba ta katse kiran dan tasan Muhibbah na iya cewa bazata ba kaman yanda tai mata jiya da safe na maganan breakfast... Tana ida wayar ta juyo ta komo cikin parlorn,tana duban Babanta take fad’i cikin harshen Spanish “Paa este lugar es aburrido..Por eso le pedí a la tia que viniera... Espero que no te importe Paa (Wajen nan babu dad’i Paa, is kind of boring.. Shisa nace Tia tazo... I hope you don’t mind Paa) K’asaitaccen murmushi ya sakar mata kana shima ya amsa cikin harshen spanish “Cualquier cosa por mi princesa..” (Duk abinda Gimbiyata take so) Itadai Raheema sai dubansu take tana faman ci gaba da murmushin yak’e dan bama tasan mai suke fad’i ba.... Lokaci guda ta d’an gyara zamanta cikeda k’issa kana Ta dubi Zahra tace “Daughter nima dai za’a koya min Spanish d’in nan yanda nan gaba za’ake tattaunawar dani...!” Murmushin da yafi kama da yak’e Zahra tai kana tace “Sí Señora, I don’t have problem with that..!” Raheema ta kuma sakin murmushin yak’e kana tace “Toh yanzu dai a fassara min mai Daughter da Paa suka tattauna..” Murmusawan Zahra Ta kumayi dan already Mahmood ya tashi daga parlorn ya shige wani k’ofan yana amsa kiran Turaki Zahra Ta d’an gyara zamanta kana tace “Pronto lo verás con tus ojos” Raheema Ta kuma yin yak’e kana tace “Ai kin kuma shigar dani duhu daughter...!” Murmusawa Zahra tai kad’an kana tace “Cewa nai da sannu idanunki zasu gane miki...!” Raheema Ta kuma sakin murmushi kana tace “Oh I guess babban surprise za’a min...!” Zahra Ta murmusa da gefen baki kana tace “Créeme uno muy grande” (Ki yarda dani, Babba ma kuwa)... Raheema Ta kuma sakin murmushi cikeda jin dad’in babban surprise d’in da Zahra zatai mata, watak’ila Zahra ta fara sonta da mahaifinta ne... Ta kuma sakin murmushi tana mai gyara zamanta, lokaci guda tana mai kuma initiating fira tsakaninsu da Zahra... ** Muhibbah ta dubi Umaima tana mai girgiza kai “What..! No gaskiya ni bazanje sashen Yarima Mahmood ba, mai kike tinanin za’a d’auken a Masarautar nan... Zahra yarinya ce bazata fahimci komai ba... Ki k’yale zancenta kawai...” Ta k’arashe tana mai tufke sumarta data ida tajewa cikin ribbon... Umaima ta zauna saman stool kana tace “Babu wanda zai kawo komai, besides Raheema na cen... Kika sani ko da amincewarsu gaba d’aya suke so kije cen... It is not as if kin aikata wani abu maras kyau ne, ga Zahra ga kuma Raheema duka suna cen ba Ke kad’ai bace...” Muhibbah ta kaikaito tana dubanta kana tace “Raheema na cen..?” Jinjina mata kai Umaima tai kana tace “K’warai kuwa...!” Lokaci guda Muhibbah ta juyo tana kuma duban kanta a madubi, ta saki murmushi mai k’unshe da ma’anoni kana ta juyo taceda Umaima “Alright fine... Kunci gari Keda Zahra...!” Umaima ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa ko ke fah, maza tashi tashi ki shirya.. I’ll help you get ready....” Take Umaima ta tayata shiryawa cikin kaya na alfarma, dikda babu wani kwalliya saman fuskrta tayi kyau har ta gaji... Umaima tai mata K’uri kana tace “Inama ku had’uda Prince F a hanya sai ya kusan sumewa ina fad’i maki.... Hararan wasa Muhibbah Ta aika mata kana tace “Kedai kinji dashi.. Must I have to wear all this...? Ni fah ba d’iyar Saraki bace....” Umaima na kuma sakin murmushi take fad’in “Soon zaki zama matar Saraki, so better get used to it...” Muhibbah ta girgiza kai a hankali kana tace “Au har kin yanke...?” Umaima Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa d’an sarki ma Sarki ne...!” D’an murmusawa sukai gaba d’aya a tare kana suka nufo k’ofa.... Suna isowa k’ofar Yarima Mahmood Umaima ta juya tana fad’in “Ai Ke kad’ai zaki shige dan ni ba’a bani izinin shigowa ba...!” Muhibbah ta dubeta baki sake kana tace “Wai da gaske kike..?” Umaima ta d’aga mata gira tana fad’in “Sosai kuwa... A fito lafiya Rankishi dad’e..!” Tana ida fad’in haka ta juya tana murmushi Sauk’e fuci Muhibbah tai a hankali tana duban k’ofar sashen..... SameenaAleeyou 📚 [6/29, 4:49 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *025* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Daga yanda yake tsaye ya baiwa k’ofa baya yana fuskantar tanfatsetsen window dake gabansa tai tsaye tana dubansa... Wani irin muguwar fad’uwan gaba taji sanda ta hangi gadon bayan Mahmood, yanda kasan mai laifi yaga wanda yaima laifi hakan nan ta tsinci zuciyarta cikin wannan yanayi... Maiyasa dik sanda ta kasance taredashi takeji wane irin al’amari na daban, maiyasa dik irin tsanar da tai masa yafi k’ullatanta a bayan idanunsa, maiyasa da zaran tai arangama dashi sai ta nemi wannan tsanar ta rasa, sai ta rasa control ta kuma rasa wane irin yanayi ne take tsintar zuciyarta ciki.... Wayar da yakeyi ne ya tafi da hankalinta... Ta d’an lab’ab’e kad’an jikin k’ofar tana sauraron abinda yake fad’i cikin wayar “I can’t be mistaken Turaki, na tabbata naga wannan mutumin, kuma ka sanni I won’t rest har sai na isa k’arshen al’amarin nan.. Dole za’a k’ara tsaro cikin gidan sannan za’ai installing CCTV cameras all over the Palace koda hakan na nufin karya k’a’idan Masarautar ne, hakan ne kawai zai bamu daman warware wasu al’amara dake faruwa cikin gidan cikin sauk’i.... Gabanta ya yanke ya fad’i, cikin zuciyarta take kuma nanatawa CCTV cameras, hakan na nufin za’a ganta kenan... Kai no no way bata fara komai ba, maiyasa Mahmood ke shirin ruguza mata shirinta... Idan tai sake tabbas Mahmood zai lalata mata dik wasu shirinta tun kafinma Ta fara... Fuzar da fuci tai a hankali sanda muryarsa ya kuma dawo da ita daga duniyar tinanin da ta tafi... Da mamaki saman fusakarsa yake dubanta... Tai k’ok’arin dawowa cikin hayyacinta, murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta... “Your Highness, barka da dare...!” Ta fad’i murmushin saman fuskarta... Har lokacin dubanta yake fuskarsa babu alamun walwala, baice da ita komai ba saima had’e hannayensa da yai waje guda yana dubanta, wane irin duba yake mata tamkar duba na tuhuma ko na mai laifi, take taji jikinta yayi sanyi sosai, domin kaw sosai ya tsareta da wannan idanun nasa masu firgitar da dik wani mai laifi... Ta had’iyi miyau da k’yar tana kuma satan kallonsa... Tamkar ta juya ta koma a guje haka taji... Neman kalamai ta soma saman harshenta dake faman sark’ewa tana furta “Am...Am... I’m sorry your Highness, I... I was told that..!” Muryar Zahra ta sinkayo kaman daga sama ne ya katse mata bayanin da take da k’yar da baki da hannaye “Tia Hibbah...! I thought you wouldn’t come... Sannu da shigowa... k’araso, shigo...!” Ta k’arashe tana mai kamo hannun Muhibbar suka shige cikin parlorn... Ita dai Muhibbah gaba d’aya jikinta ba’a sake yake ba, sai faman waigowa take tana kuma duban Mahmood da yai tamkar baisan suna wajen ba.... Ga mamakinta sai kuma taga bai nan da alama k’ila saman bene ya haye ko ficewa yai gaba d’aya.... What if ya ganeta ne... What if ya fara saka shakku da kokonto akanta... Tabbas gaining trust d’in Zahra kawai yayi kad’an dole ta sami yardar Mahmood... Bazata bari ya saka shakku akanta ba, sannan wannan cameras da yake maganan installing ko ina cikin gidan babban barazana ne ga shririnta.... Raheema dake faman zuba had’edd’en soup cikin bowl tana fad’in “Ehen Daughter you need to taste this soup kafin Paa ya tasting, I cooked it myself... I really want to hear your opinion....!!” Burki taiwa kalaman nata sanda ta juyo rik’eda bowl d’in tana duban abin mamaki... Wai dama wannan shegiyar uwar shishigince surprise d’in da Zahra Ke fad’i... Baki sake take dubansu... Bata ankara ba saiji tai bowl d’in ya fad’i tauu saman k’afarta, soup mai zafi dake ciki ya k’ona mata k’afa ga tangaran d’in ya yanka mata fata... Ta saki k’aran azaba daidai lokacinda Muhibbah ta isa da sauri tana k’ok’arin taimaka mata... Raheema ta finciki k’afarta tana fad’in “Don’t you dare.... How dare you..!! Mai ya kawoki nan... You’ll pay for this munafuka algunguma mayya...!!” Daga Zahra har Muhibbah tsaye sukai suna mata duban mamaki... Zahra da tsoro ya nuna saman fuskarta tace “Aunty Raheema meke faruwa, Mai Tia taimaki... Taimakonki fah take son yi... Look you’re wounded, Deja que ella te trate la herida ... es su profesión” (Ki k’yaleta ta duba ciwonki fanninda ta k’ware ne...) A zuciye Raheema dake tsananin fuci ta juyo tana duban Zahra kana Ta soma fad’in “Shut your mouth you little brat, this is all your fault...How could you... Ta yaya zaki katse min hira da mijina ki kirawo mana wannan shu’umar wajen nan... Just who do you think you are..!? Na jima da sanin baki so na auri mahaifinki, but ban zaci munafuncinki yakai har haka ba, tell me so kike Ki lik’awa babanki ita ko mai da zaki gayyato mana ita...? Toh bari kiji na fad’a miki, Yarima Mahmood is mine, he’s mine... I don’t care if you’re his daughter... The next time da kika sake yunk’urin aikata wani abu mai kama da haka ni da kaina zan hukuntaki, maras kunya kawai...!” Zahra da tuni ta soma huci da hawaye, lokaci guda take furta “You’ve no right to talk to me that way..! You are not my mother, you can’t punish me... You’ve no right over me...I hate you, I hate you.... And yes I never liked you, I don’t want you for my father... To hell with you..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin daka tsawa hawaye na sauk’o mata.... A zuciye Raheem Ta mik’e zatakaiwa yarinyar mari Muhibbah tai saurin rik’e hannun Raheema tana mai sakin huci itama... “Don’t you dare lay a finger on her...!!” A guje Zahra ta nufi upstairs tana kuka sosai take kiran mahaifinta.... Raheema ta dube Muhibbah shaye da mamaki kana tace “Excuse me...! Wacece Ke... How dare you interfere..! Sakar min hannuna kafin na sakaki kiyi nadaman da baki tab’a irinsa ba tsawon rayuwarki.... Munafuka mai bin mazan mutane..!!” Wannan karon murmushi Muhibbah tai kana tace “Why...? Tsoro kikeji...? Baki yarda da kanki bane...? How many times do I have to tell you babu abinda zanyi da Yarimanki... Ni inada Sarki already... Bana buk’atan Yarima, amma ga shawari guda d’aya... If you’re scared of losing your prince... Then ki sami igiya mai k’arfi ki d’aure zuciyarki dana d’iyarsa waje guda... Aikin banza kike idan har yarinyar nan bata k’aunarki... Shawari ce..!!” Ta k’arashe tana mai sakin murmushi saitin fuskar Raheema... Tana ida fad’in haka tasa kai tai ficewarta daga sashen gaba d’aya, tana tinanin mai zatai gameda batun dasa cameras a cikin gidan da Mahmood Ke k’ok’arin yi, she really needs to come up with something, dole tasan yanda zatai tasa a datse batun saka cameras cikin gidan.... Haka Raheema tabi bayan Muhibbah da kallo har ta b’acewa ganinta, kumafa abinda Muhibbah ta fad’i mata gaskiya ne... Idan har tana son samun kan Mahmood da gaske toh fah dole tai hak’uri da wannan sangartacciyar yarinyar har ta samu ta mallakesa, idan yaso daga baya sai tasan yanda zatai da yarinyar.... Tana ida tinanin ta d’aga idanu tana duban benen, lokaci guda ta kuma sauk’e huci a hankali kana ta soma jan k’afarta mai ciwo ta nufi benen da d’ingishi... Tana haurawa ta hango Zahra zaune parlorn saman ta tak’ure waje guda ta kifa kanta cikin gwiwarta tana kuka mai tsuma zuciya.... Ta gallawa yarinyar harara tana mai yatsina fuska, lokaci guda tai k’ok’arin saita kanta kana ta nufi cikin parlorn cikeda k’issa, gefe da Zahra ta isa ta zauna had’ida kwantar da murya “Daughter I’m sorry... Believe me I didn’t mean to... Kiyi hak’uri dan Allah... Please don’t tell your Paa about this... Kiyi hak’uri rainane ya b’aci amma bana nufin dik abinda na fad’i kinji koh....!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin rungumo Zahra... Idanunta masu zuban hawaye ta d’ago tana duban Raheema dashi kana tace “Don’t touch me... Karkizo kusa dani... Bana sonki da Paa d’ina... Bana so ya aureki... Ke muguwa ce... Ni Ki k’yaleni... Just go away..!!” Ta k’arashe tana mai kuma kifa kanta cikin k’afafunta... Takaici ya kuma turnuk’e Raheema a mak’oshi, batasan Mahmood da matarsa wane irin goyo sukaiwa d’iyarsu ba, shakka babu goyon turai Mahmood yai mata shisa bata ganin mutane da gashin ido, an gama sakalta yarinyar sai abinda take so... Ji take kaman ta d’add’auketa da mari amma sai tai k’ok’arin saita kanta sanda ta tuna kalaman Muhibbah... A hankali ta mik’e tana kuma duban Zahran kana ta fice daga parlorn ta nufo k’asa... Gimbiya Zeenatu na kwance saman kujera mai lilo na sarauta, gefe da ita kuyangace ke rik’eda parantin kayan marmari tana d’auka d’aya bayan d’aya tana ci cikeda kmasaita da mulki... Tamkar wacce aka jefota haka suka hango Raheema na shigowa na sakin huci... Kuyangin suka shiga sadda kawunansu suna gaidata, sai faman sakin huci take tana jan k’afarta dake ciwo... Gimbiya Zeenat ta tashi daga kishingid’en da take ta zauna sosai tana duban Raheema... “Ke kuma fah... Miye haka...?” Raheema taja Ta zauna kujera mai duban ‘yar uwarta kana tai alamawa bayin kan cewa su fice... Babu musu suka risina suka fice gaba d’aya.... Gimbiya Zeenat tace “Ke nake saurare Raheemah, mai kuma ya faru... Ya na ganki kin dawo cikin fushi keda kika tafi zance da masoyinki.... Sannan mai ya sami k’afarki na ganki haka nan...?” Huci kawai Raheema ke sakewa tamkar tafashesshen kunu.... Gimbiya Zeenat tace “Ke Raheema ki bud’e baki kimin magana Bana san shashashancin banza...!!” Tai maganar cikin hasala.... Raheemar ma a hasale take fad’in “Aunty ni fah na gaji, na gaji da wannan shed’aniyar d’iyar Mahmood d’in... Wannan yarinyar da kike gani sam babu alkhairi a tattare da ita....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin huci... Mik’ewa tsaye wannan karon Gimbiya Zeenat tai kana tace “Bani labari mai ya faru...?!” Tas Raheema ta kwashe dik abinda ya faru ta sanar da ‘yar uwarta... Da mugun mamaki Gimbiya Zeenat ke dubanta kana ta d’an girgiza kai alamun rashin yarda tace “You mean to say Mahmood baisha miyar nan da muka gama masa had’i ba..?!!” Sai sannan Raheema ta tina ashe fah miyar da aka shirya musamman dan Mahmood an gama masa had’i da komai shine ta tuntsirar dalilin ganin Muhibbah... Ta dafe kanta cikin sauri tana mai furta “Na shiga uku Aunty wllhi baici ba...!” Saukan wane irin jahilin mari taji a k’uncinta, ta d’ago tana duban Auntyn tata dake sakin hucin b’acin rai... “Ashe ke shashasha ce ta bugawa a jarida ban sani ba... Ashe Ke doluwace Ta k’arshe.. Kinsan da yaya aka had’a maganin nan... Kinsan kwanakin maganin nan nawa a tsibirin iskokai... Shine dan dak’ik’anci da shashashanci zaki zubar kuma dik zaman nan baki San yanda duk kikai kika basa yaci ba..?? Dak’ik’iyar inace Ke Raheemah..!!?” Ta k’arashe tana mai jijjiga Raheema dake kuka dafe da k’uncinta.... Raheema na kuka take fad’in “Aunty wllhi ba laifina bane laifin shegiyar Muhibbar nan ne.... Aunty makirar nan ta shige dik tinaninki...!” Hankad’ata gefe Gimbiya Zeenat tai tana mai ci gaba da sakin tururi “Bazamu tab’a rasa Mahmood ba, dole ya zamto yana k’ark’ashin ikonmu.... Amma kafin nan sai mun b’atar da wannan yarinya Muhibbah dake k’ok’arin kutso Kai cikin rayuwarsa data d’iyarsa..!!” Raheema ta dubeta da mamaki kana tace “Aunty ya za’ai mu b’atar da ita, bayan ko idanunta tsoro suke bani...!” K’asaitaccen murmushi Gimbiya Zeenat tai kana tace “Na b’atadda wad’anda suka fita balle ita... Akan mulkin nan babu abinda bazanyi ba... Juwariyya..!!!” Raheema ta kuma dubanta da mamaki kana tace “Mai ya kawo Juwariyya cikin batun nan Aunty..?!” Murmusawa Gimbiya Zeenatu Ta kumayi kana tace “Itace solution d’inmu... Itace zamu umarta ta bincika mana komai gameda Muhibbah... Idan muka San ko wacece ita kaita k’asa bazai mana wuya ba, dan ni ban yarda da wannan Muhibbar ba...!” Raheema ta saki murmushi cikeda jin dad’i “Gaskiya Aunty Ke d’in ta dabance, badon Giwa ta rigaki shigowa gidan nan ba da anyi shu’umar Sarauniya.! Toh amma do you think we can trust Juwariyya..?!” Murmusawa Gimbiya Zeenat ta kumayi tana mai zama cikin kujerar lilonta, tana juyi bisa take fad’in “Ai a halin yanzu babu wacce zamu yarda da ita samada Juwariyya tinda har ta juyawa ahalinta baya dan cikar burinmu... Karki mance duk wani information kan Yayanta ita ke kawo mana, so na tabbata bazamu samu matsala da ita ba....!” Murmusawa Raheema tai kana tace “K’warai kuwa Aunty shawarinki yayi..!” Suka kuma duban juna a tare suna masu sakin murmushin cin nasara.... *** Zagaye d’akin take faman ci gaba da yi waya manne kunnenta tana mai ci gaba da fad’in “Ansar please pick up... Pick up please... Ina tsananin buk’atar shawarinka...!!” Har saida wayar ta kusan katsewa Ansar ya d’aga yana mai furta “I can see someone’s already missing me, Sorry wanka na shige ban jima da isa masauk’i ba na tsaya restaurant nayi takeaway... Do you want some... Na kawo miki...?!” Yai maganan teasingly... Katse wasan nasa tai da fad’in “Ansar akwai matsala....!” SameenaAleeyou 📚 [7/1, 10:39 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *026* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Gathering natsiwarsa yai waje guda yana mai furta “Ina saurarenki... Meke faruwa...?” Fuzar da fuci tai a hankali tana mai zama cikin gado “Ansar Mahmood yana so ya dasa cameras in every angle cikin Masarautar... I mean he can’t do that... Zai b’ata min shirina, bayan babu abinda na fara...” Ta k’arashe cikeda damuwa... Lokaci guda ya isa ya zauna bakin gado yana mai furta “What..! Hibbah you need to leave that place right away, muddin aka saka cameras you’d definitely get caught..!” Jinjina masa kai tai kaman yana kallonta kana tace “What do I do now Ansar... Mai zanyi na hana yuwar hakan...?!” Fuci ya fuzar a hankali kana tace “Muhibbah ki bar maganan mission d’in nan naki... Abubuwan da suke faruwa sign suke nuna miki cewa akwai matsala gaba... Before everything gets out of hands let’s leave, tun ban bar cikin garin nan ba... Zanzo ni na d’auki, mu koma gida...!” Katsesa tai da fad’in “Haba Ansar, kai saikace ba namiji ba, sai gashi kaman ka cire tsoro da shakku cikin sai kuma ka sake komawa ruwa..!” Shima ya katseta da fad’in “Dik abinda ya shafeki Muhibbah bazan masa tinani d’aya ba.. I’ll think through and think through and think it through... Karkiga laifina sabida banso ki shiga matsala ne....!” “Are you saying na ajiye makamaina na bika mu koma gida, what about the justice that I deserve..? So kake na tafi na mance komai..!?” Cikin kwantar da murya yake fad’in “Ba nufina ba kenan Muhibbah... Nafi kowa so Ki samu adalcin da kika cancanta duk duniyar nan...!” “Idan gaskiya kake fad’in then ka dena sare min gwiwa with your negative thoughts...!” Ansar ya fuzar da huci, cikin b’acin rai yake furta “Ni ban hanaki aiwatar da komai ba... From the very start, I’ve done nothing but supporting you, amma abinda nakeso ki gane a nan shine dik abinda zakiyi do it the right way...think it through first Muhibbah.. Idan Ke baki damu da kanki ba wasu sun damu dake..!!” Cikin tsananin b’acin rai take furta “You know what...! I should not have called you, you aren’t helping at all... Zanyi abuna yanda na tsara ba tareda neman shawarinka ba.. Goodnight.!!” Ta k’arashe tana mai katse kiran... Shiru yai had’ida k’urama waje guda idanu... A hankali ya fuzar da fuci mai tsananin d’umi had’ida shafe fuskarsa da duka tafukan hannayensa biyu.... A b’angaren Muhibbah kaw zama tai dirshan saman gado tana tinanin mafita... Ita yanzu bama saka cameras a fada ba, mai zai faru idan Mahmood nada shakku da kokonto akanta ne..? Zahra..! Itace Ta fad’o ranta... Lokaci guda ta mik’e ta soma shiri kana ta nufi sashen Giwa.... Saidai a bakin k’ofan parlornsu Zahra taja ta tsaya sakamakon sauraro muryar Zahra cikin kuka tana fad’in “Paa you actually take that woman’s side..? Paa banifa na k’onata ba, bani naji mata ciwo ba... Ita da kanta taji ciwo ma kanta... and Paa...” Cikin tsananin k’unan rai ya katseta da fad’in “Just shut up Zahra... Ban miki wannan goyon ba, rashin kunya ba d’abi’arki bane... First thing in the morning zakije ki baiwa Raheema hak’uri...sannan kiyi alk’awarin bazaki sake abinda kika aikata ba....!” “Really now Paa... You believe that woman over your own daughter...? Paa that woman is a liar.. She is a hypocrite...” “Zahraa..!!” Ya daka mata uban tsawa yana mai k’ok’arin d’auketa da mari... Muhibbah tai saurin shigowa ta shige tsakaninsu had’ida rungume Zahra lokaci guda take furta “I’m sorry your Highness, I didn’t mean to interfere...But please don’t hurt her she’s still a kid...!” Tsaye kurum yai yana mai ci gaba da sakin huci, jijiyonsa sunyi rud’u rud’u sabida tsananin b’acin rai... Gaba d’aya itakam Muhibbah ma tsoro ne ya rufeta ganin yanda Mahmood ya koma lokaci guda, babu yanda Ta iya ne dole tai hakan badon haka ba da koda wasa batai gigin shigowa har ta shige tsakaninsa da Zahra ba... Cikin tsananin huci yake nuna Zahra yatsa kaman zai magana sai kuma ya juya yasa kai ya fice daga d’akin gaba d’aya... Zahra ta kuma shigewa jikin Muhibbah tana mai ci gaba da sakin kuka.... Muhibbah kuwa sosai ta rungumeta tana kuma lallashinta, cikin zuciyarta take ayyana cewa ko shakka babu goyon turai akaima Zahra, wannan zai bata dama ta shawo kan yarinyar cikin sauk’i ta tarwatsa mahaifinta.... Ta saki murmushi a hankali tana mai ayyana yanda Mahmood zaisha kunya ya kuma fad’i k’asa warwas a bainan jama’an sa.... Lokaci guda ta kuma janyo Zahra suka zauna saman gado tana mai furta “Is ok Zahra... Kukan nan ya isa haka, maza share hawayenki kinji koh....!” Zahra ta d’ago tana dubanta da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda take furta “My Paa has changed, bai tab’a d’aga min murya ba sai gashi yau har zai maren all because of that witch...!” Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da wani kukan... Bubbuga bayanta Muhibbah keyi a hankali tana fad’in “Kukan nan ya isa haka Zahra, karkiyi saurin yanke hukunci kan mahaifinki... Abinda ya fad’i maki gaskiya ne, ya kamata kije ki baiwa Raheema hak’uri.... Ba’a San d’iya Ta gari ‘yar babban gida da raina mutane ba kinji koh...!” Da mamaki Zahra ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubanta kana tace “Kema kin zab’i kibi bayan wannan mayyar ne... Wllhi nayi imani ba tsakanida Allah take son Paa d’ina ba... I know she’s after something, sam bana son ya aureta...!” Ta k’arashe cikin rawar murya... Dafa hannunta kad’an Muhibbah tai kana tace “I understand where you’re coming from, it’s natural for girls like you to get jealous idan mahaifinsu zai k’ara aure, ko dan taya mahaifiyarsu kishi.....Kiyima Raheema kyakkyawan zato kinji koh... Sannan kiyi kaman yanda Paa d’inki yace... Apologies to her kinji koh...And also to your Paa..!” D’an kallon Muhibbah tai kana tace “Alright fine zanjeni amma sabida ke... Kuma tare nakeso muje...!” Jinjina mata kai Muhibbah tai tana mai kuma dafa kanta take fad’in “Sure... Zan rakaki in sha Allah kinji koh... So ki kwantar da hankalinki....!” Ta jinjina mata kai a hankali tana mai goge ragowar hawayenta... Mahmood dake tsaye daga k’ofa yana saurarensu take yaji wane irin sanyi cen k’asar zuciyarsa, ji yake Zahra na cikin aminci muddin tana tareda Muhibbah... Can k’asar zuciyarsa yakejin kwanciyar hankali da tarrayan Muhibbah da kuma Zahra, bugu da k’ari wannan kyawawan shawari da Muhibbah ke bata su suka cancanci yarinya mai shekaru irin nata... Take tinanin matarsa Aliya ya fad’o masa, tabbas ko wace uwa wannan shekarun take jiyewa d’iyarta, wannan dangerous stage ne a rayuwa da yake buk’atan taka tsantsan, shekarun teenage... Idan har Muhibbah zata kasance da d’iyarsa a haka baida haufin cewa zai sami kwanciyar hankali da yin hakan... Ya saki murmushi mai taushi a hankali kana yasa kai ya fice... Muhibbah dake satan kallon bakin k’ofan da wutsiyar idanunta murmushi Ta saki a hankali don ko babu komai tasan kwalliya ta biya kud’in sabulu, tarkonta ya d’anu.. Ta sami yardar Yarima Mahmood... Yanzu next move d’inta shine maganan dasa camera...! Taita faman sak’e sak’e cikin zuciyarta tana neman hanyar da zata b’ullowa Al’amarin... Mutum guda ne ya fad’o zuciyarta Yazeed...! Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta... Tabbas Yazeed ne kawai zai kawo cikas a wannan shiri na dasa na’urorin d’aukan hoto masu motsi cikin gidan....! Da wannan shiri ta Kwana cikin zuciyarta da niyyan Washe gari zatai k’ok’ari ta riga Mahmood making move... Sam Zahra bata bari Muhibbah ta koma cen masauk’inta ba, haka taita mata magiya saida suka kwana tare... Ko shakka babu SHAK’UWA CE mai tsafta ke shiga tsakaninsu a hankali.... Washe gari bayan Muhibbah ta nufi sashenta ta shirya dawowa tai ta jira har Zahra ta farka bayan ta sad’ad’a asibahin fari ta ajiye likankken takarda mai d’aukeda rubutu jikin k’ofar motar Yazeed yanda dole a gani... Koda ta ijiye takardan successfully murmushi ta saki a hankali tana mai furta “You’re the only person that can ruin his plan... After all kud’in baku jituwa.. Hakan dalili ne na kuma tarwatsa tsakaninku...Da sannu zaku rasa mulkin Masarautar nan gaba d’ayanku sannan ku fice a Masarautar cikin k’ask’anci da d’ibewa juna albarka....!” Tana ida fad’in haka tai saurin gyara alkyabbarta Ta rufe fuskarta kana ta fice daga wajen gaba d’aya... Koda ta shigo duba Zahra nan Ta makara wajen taya Zahra shiryawa, daidaida kayan da Zahra zata saka Muhibbah ce ta tayata zab’e.... Gaba d’aya yarinyar ta cika da farin ciki gwanin ban sha’awa... A haka Umaima ta shigo ta taddasu tana mamakin yanda Sabo mai k’arfi ya shige tsakanin Zahra da Muhibbah lokaci guda, hakan sosai yaiwa Umaima dad’i ko dan ganin Zahra cikin Farin ciki bayan rasa mahaifiyarta da yarinyar tai... Dik mai k’aunar Zahra dole yaji dad’in kasancewar Muhibbah cikin Masarautar domin kaw ta maidowa yarinyar wani b’angare na Farin ciki data rasa sakamakon rashin mahaifiyarta da tai... Su duka ukun sukai karin kumallo Umaima Zahra da kuma Muhibbah a nan parlorn su Umaimar.... Idan ka gansu yanda suke gudanar da al’amransu del su birgeka... Muhibbah sai saka masu chapter take suna darawa kaman ba gidan sarauta ba, sosai suka baje suna jin dad’in moment d’in.... Giwa da Jakadiya ne suka taho zasu shige nan suka sinkayo hayaniyar su Zahra... Giwa ta dubi Jakadiya da alaman tambaya saman fuskarta... Jakadiya tai gyaran murya tana mai furta “Allah shi baki yawan rai ai wannan yarinya bak’uwa da akai a masarauta mai suna Muhibbah itace ta dawowa Gimbiya Zahra’u da Farin cikin data rasa...!” Ta k’arashe tana mai kuma jinjinaga shugaban tata... Giwa tai shiru tamkar mai nazari kana ta jinjina kai tace “K’warai yarinyar tanada saurin shiga zuciya banga laifin Zahra’u ba... Hakan zai kyau idan har zata zamto mai d’ebewa yarinyar kewa...!” Ta k’arashe k’asaitaccen murmushi saman fuskarta lokaci guda ta nufi parlorn su Umaima Jakadiya na biyeda ita... Muhibbah ce ta soma hango Giwa tai saurin mik’ewa alamun girmamawa kana ta risina tana kwasan gaisuwa had’ida kambaba Giwa... Giwa ta saki murmushin jin dad’i sanda su Umaima da Zahra sukai kaman yanda Muhibbah tai, abin sai ya kuma birge Giwa, tana matuk’ar son girma.. Tana son mutumin da zai bata girma ya kuma aza mata k’asa sam bata lamuntan raini shisa ba ko yaushe tasu ke zuwa d’aya da Raheema ba.... Sosai taji dad’i har k’asan zuciyarta tana mamakin yanda Muhibbah ta k’ware wajen koyi da d’abi’u da al’adun babban gida... Daga Umaima har Zahra mamaki suke yau Giwa ce ta shigo har parlornsu, ita kaw Jakadiya sam zuciyarta bata aminta da wannan k’auna da Giwa ke nunawa Muhibbah ba yarinyar da sam basu wani San tushenta da asalinta ba, ita dai sam zuciyarta bai kwanta da yarinyar ba musamman ganin yanda zuciyar Giwa dana yarinyar suka had’e waje guda tun daga had’uwar fari... Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yarima Yazeed yana dokawa Jakadiya kira dik Kuyangin dake bisa hanya k’arewa suke suna kwasan gaisuwa wajen Yazeed...Jakadiya ta dubi Uwargijiyarta kana tai mata izini ta hanyar jinjina kai.... A hanyar matakala Jakadiya ta iske Yarima Yazeed, tai saurin zubewa tana kwasan gaisuwa... “Jakadiya ina Maibabban d’aki...?!” Yai tambayar a hasale... Jakadiya ta kuma risinawa zatai magana sai muryar Giwa suka sinkaya tana fad’in “Yazeed mai kake nema da safiyar nan....?!” A cen parlorn su Umaima kaw tinda Muhibbah taji Yazeed na neman Jakadiya tasan tarkonta ne ya d’anu dan haka murmushin jin dad’i kurum ta saki tana mai tiniwa Zahra cewa anjima kad’an zasuje sashen Gimbiya Zeenatu domin neman afuwan Raheema... ** Yazeed na matuk’ar huci yake furta “Your beloved Son, the perfect one among us all yana nema ya b’ata al’adun gidan nan tun kafin ya hau mulki...!” Dubansa Giwa tai ba tareda ta furta komai ba kana ta nufi wata k’ofar yanda zai fitar dakai sararin veranda dake a saman benen... Suna shigewa Giwa ta kuma dubansa kana tace “Ina saurarenka Yazeed mai kuma Mahmood yai wannan karon...?” Yazeed ya kuma fuzar da fuci kana yace “Kan mai zaice zai saka CCTV cameras cikin Masarautar nan..? Maami hakan karya dokan masarauta ne, cin amanan tsari da tarihin Masarautar nan ne... Sannan wulak’anta babban gida irin wannan ne... Yanzu inada tabbacin cewa kin yarda Mahmood bashi ya cancanci gadon sarautar nan ba, tin yanzu tin bai d’ale Karagar ba gashi nan yana nema ya kawo sauye sauye cikin Masarautar nan... Yana nema ya rusa ya lalata duk wasu al’adu na cikin gidan nan tin shekara da shekaru... Yana neman ya kawo mana d’ab’un Yahudu da Nasara cikin Gidan... Maami Masarautar nan bazata tab’a amincewa da wannan ba sam..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci... Giwa da taji wani irin gumi na neman keto mata, duban Yazeed Ta kumayi kana tace “Bakaji da kyau ba Yazeed... Ta ya Mahmood zaizo da batu irin wannan cikin Masarautar nan, tin iyaye da kakkani ba’a tab’a zuwa da batu mai kama da wannan ba... Hakan wulakanta ahalin gidan nan ne..!!” Ta k’arashe cikin tsananin tashin hankali... Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yarima Mahmood yana fad’in “A’a Maami hakan ba wulak’anta ahalin gidan nan bane... Hakan na nufin tsare ahalin gidan nan ne... Kuma babu gudu babu jada baya, kaman yanda ka fad’i Yazeed tabbas za’ai instilling cameras cikin Masarautar nan ta ko wane b’angare domin tabbatar da tsaro cikin Masarautar.... Abubuwa da dama Sun faru cikin Masarautar nan kuma suna kan faruwa, misalin mutuwar mahaifina da akace heart attack ne yai ajalinsa, mutuwar matata wacce gawarta kawai aka sinkaya cikin d’aki... Sannan b’acewar Ja’afar da har yau babu shi babu dalilinsa... Don’t you think duka abubuwan da na lissafa sunada connection...?!” Ya k’arashe d’aukeda alamun tambaya hannayensa hard’e Ta baya yayi tsaye gaban Yazeed su duka biyun suna fuskantar juna... Babu alamu ko gizau na shakku da tsoro a tattareda Mahmood...! Giwa kuwa tuni kanta ya soma juyawa, hankalinta yakai k’ololuwa wajen tashi, batai zaton Mahmood went far har haka ba... Lallai tayi gangancin raina capabilities d’in wannan d’an mijin nata... Mai zatai yanzu kafin Mahmood ya tono sirrikan gidan, shin anya batai ganganci uzzura masa ya dawo Nigeria ba..? Ya zata dawo dashi yazo yana yak’arta... Karfa maganan Tal’udu ya tabbata cewa Mahmood yak’i ya dawo yai da ita, dole tasan abinyi... Dole tasan yanda zatai ta takawa Mahmood birki da wannan shiri nasa da yakeyi... Muryar Yazeed ta sinkayo yana fad’in “And kana tinanin kashe maka matarka akai cikin Masarautar nan...? Ko kana tinanin kashe mahaifinmu akai...?!” Mahmood ya katsesa da fad’in “Everything is possible a gida irin wannan, d’ah zai iya kashe Uba dan ya gaji Kujeran mulkin mahaifinsa...!!” Cikin murya mai yanayi da kuka Giwa ta katsesa da fad’in “Haba Sadauki ya zakake magana haka..? So kake kace cikin ‘yanuwanka wani ne ya kashe mahaifinku dan ya gaji sarauta... Shin akan wannan mulkin ne rabuwar kai da zargi ke neman shiga tsakaninka da ‘yanuwanka, shin zargin ahalinka kake da alhakin mutuwar mahaifinku da matarka... Sadauki ban zaci haka daga gareka ba... Da zuciya d’aya nai muradin ka dawo ka amshi jagorancin Masarautar nan a matsayinka na babban Magajin mahaifinku... Da ace nasan abinda zai dawo dakai kenan rabuwar kawunanku da ahalinmu da banyi burin ka dawo ba... Bana nufinka da komai daga kai har ‘yanuwanka sai alkhairi amma bazan so naga kawunanku ya rabe ba... Mahmood kaine Babba cikinku kai ya kamata ace ka had’a kan ahalin nan sai gashi kana k’ok’arin rabawa tin ina raye balle ace Babu ni... Nayi zaton I can count on you koda bayan raina ashe nayi kuskure..!!” Ta k’arashe cikin kuka kana ta nufi saman d’aya daga cikin kujerun shak’atawa dake baje fsrfajiyan Ta zauna tana hawaye... Dafe kansa kad’an Mahmood kana ya nufi Giwa ya duk’a gabanta, cikin kwantar da murya yake fad’in “Maami baki fahimci ne... Please karki mun mummunan fahimta...” Katsesa tai da fad’in “Banaso na fahimceka Mahmood... Ka bani kunya, a koda yaushe nida mahaifinku mun zaci kaine zakabi yanda yake tafiyar da mulki da kyawawan d’abi’unsa da halayyarsa, kuma kaine zaka had’a kan ahalin gidan nan... Ashe munyi kuskure, na godewa Allah da mahaifinka baiga rana irin wannan ba tabbas da wannan maganan Naka shi zai kashesa fiyeda bugawan zuciya..!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin kuka daidai lokacinda Jamal ya shigo.... Jiki a matuk’ar sanyaye ganin mahaifiyarsu na hawaye dan ba k’aramin abu Ke sakata kuka ba, sannan ga Yayansu Mahmood duk’e gabanta ga kuma Yazeed nan tsaye gefe yana sakin shu’umin murmushin nan nasa, ya sakasu gaba yawa TV... Jamal ya dubi Yazeed yana tambayarsa meke faruwa “Yazeed what’s going on here... Why’s Maami crying..?!” Yai tambayar cikin tsananin tashin hankali... Yazeed bai daina murmushin ba saima gyara tsayuwarsa da ya kuma yi yana fad’in “Why not ask your beloved brother... The one you all think is a saint, I’m sure yanada ansar da zai baka don na tabbata shine dalilin zuban hawayen mahaifiyarmu...” Da mamaki Jamal ke duban Mahmood da tuni ya mik’e tsaye yana aikawa Yazeed wane irin firgitaccen duba... Jamal ya d’an tako kad’an yana duban Mahmood yake fad’in “Yaya mai Yazeed yake fad’i... Shin da gaske sabida kai Maami Ke kuka...?!” Kafin Mahmood yakaiga basa amsa suka sinkayo muryar mahaifiyar tasu tana fad’in “Jamal Yayanku zargin ahalin nan yake... Yana zargin ahalinsa da alhakin mutuwar mahaifinku da matarsa gashi har yana k’ok’arin dasa na’urorin cameras da zasuke hasko masa abinda ke wakana cikin gidan nan dikda ya sani cewa yin hakan wulak’anta Martaban Masarautar nan ne..!” Ta k’arashe tana mai kuma matsan k’walla... Lokaci guda Jamal ke duban Mahmood yana fad’in “No Yaya you can’t do that... Yin hakan tozarta al’adu da tarihin Masarautar nan ne... Yaya idan akan mutumin da kake tinanin ka gani jiya cikin Masarautar nan ne shisa kake yunk’urin aiwatar da wannan abu bana tinanin nima zaka sami goyon bayana... Ko wane masarauta Yaya sunada d’abi’a da kuma tasu al’adun... Abinda kake shirin yi kaman bud’e duk wasu sirrika na Masarautar nan ne da wasu kafi na tun iyaye da kakanni... Yaya I’m sorry but I don’t agree with you either..!” Ya k’arashe yana mai k’arasawa ga mahaifiyarsu ya rik’o hannunta yana fad’in “Maami muje ki huta, this isn’t good for your health..!” Mahmood yabi mahaifiyarsu da kallo har suka fice kana ya maidoda dubansa ga Yazeed wanda ke ci gaba da sakin shu’umin murmushi, lokaci guda Yazeed d’in ke furta “Slowly slowly Yaya...I’ll prove to everyone that I’m better than you, sannan ni ne nan na cancanci Karagar nan, na fara daga cikin gida zan isa har izuwaga wad’anda sukeda alhakin nad’a sarki a Masarautar nan...!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi kana yasa kai ya fice... Fu’ad dake tsaye daga k’ofa mugun kallo suka aikawa juna shida Yazeed har Yazeed d’in ya fice kana Fu’ad ya k’arasoga Yayansa Mahmood... Murmushi suka sakarma juna Fu’ad d’in na k’ok’arin gaidashi, ko ba’ace ba Kasan Mahmood k’arfin hali kurum yake... Kai a risine Fu’ad ke fad’in “Yaya dan Allah kayi hak’uri da Yazeed da halayyan da yake maka... Baka cancanci hakan ba...!” D’an dafasa Mahmood yai murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake fad’in “Is Ok Fuad, nasan Yazeed tun yarinta... So babu wani d’abi’a nashi da yake Sabo a idanuna... Kar ka damu kaji koh...!” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’anshi... Jinjina kai Fu’ad yai a hankali kana yace “Yaya dama akwai abinda nake so na fad’a maka...!” Wanann karon cikin tsananin nuna damuwa yai maganar, tsoro da tashin hankali kwance saman fuskar Fu’ad... Mahmood yai masa K’uri kana yace “Ina saurarenka Fu’ad mai kake son sanar dani...!” SameenaAleeyou 📚 [7/4, 7:09 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *027* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kasa magana Fu’ad yai sai duban Mahmood da yake da idanunsa wanda tuni sun sauya launi... A hankali Mahmood ya dafasa “Fu’ad... Brother are you alright...?!” A hankali Fu’ad ya jinjina kansa yana mai k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa... Daidai nan Jamal ya k’araso yana sakin murmushi had’ida aikawa Fu’ad wani irin duba... Yarima Mahmood yace “Fu’ad ina saurarenka menene zaka sanar dani..?!” Fu’ad ya soma k’ok’arin saita kansa sabida irin duban da Jamal Ke aika masa, tuni ya soma ‘yan kame kame... Mahmood ya dafa kafad’arsa kad’an “Fu’ad, ka natsu ka sanar dani abinda kake son sanar dani....” Jamal ne ya katse zancen da fad’in “Yaya our little brother here wanted to tell you that he’s going back to school, zai koma makaranta yai karatunda baiyi ba a baya... Right Fu’ad...?!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai tsare Fu’ad d’in da idanu... Fu’ad ya d’an shafa kansa kad’an yana duban Jamal, lokaci guda ya jinjina kai a hankali “Eh haka ne... Haka ne Yaya, na yanke shawari ina so na koma makaranta...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Mahmood ya d’an dafasa kad’an cikeda tausayinsa kana ya janyo dokin wuyarsa irin yanda babban wa keyiwa k’ani suka nufi wasu kijeru na shak’atawa dake nan farfajiyan suka zauna... “Fu’ad nayi matuk’ar farin ciki daka yanke shawarin komawa makaranta... Kuma zan baka goyon bayana d’ari bisa d’ari kaji koh... So tell me, wane makaranta ne ka yanke shawarin komawa...?” D’an fuzar da fuci kad’an Fu’ad yai kana yace “I haven’t decided yet Yaya, ban zab’i makaranta ba tukuna...” Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “Ka zab’i dik yanda kake so kuma a ko wacce k’asa... Saidai a shawarce nafi so kayi karatun naka a nan gida Nigeria, if possible ma a jami’ar garin nan ta yanda bazakai nesa da gida ba...!” D’an dubansa Fu’ad yai cikeda k’auna kana ya jinjina kai yace “In sha Allah Yaya, and this time around I won’t disappoint you...!” Mahmood ya kuma murmusawa yana mai buga kafad’an Fu’ad a hankali kana yace “Yayi kyau Fu’ad... May Allah always be with you...!” A tare Fu’ad da Jamal suka amsa da Ameen kana Jamal ya d’an bud’e murya yace “Yaya a nawa shawarin kamata yai a tura Fu’ad can wani wajen yaje yai karatunsa zaifi bada himma samada idan yana gida...!” Bai kai aya ba Fu’ad ya shiga girgiza kai tamkar mai k’aramin tab’in hankali yake furta “No... No I don’t want to leave.... Banso naje ko ina, no.. No... I wanna study here...!” Yana maganan yana girgiza kai yana rintse idanu had’ida kame kansa.... Saurin rik’osa Mahmood yai yana k’ok’arin calming nasa yake fad’in “Calm down Fu’ad... Babu wanda zai sakaka tafiya makarantar da bakaso kaji koh... Dik yanda ka zab’a nan zakiyi ka kwantar da hankalinka...!” Fu’ad yai masa K’uri k’walla tab idanunsa yake furta “Thank you Yaya... Na gode Yaya Mahmood...!” Ya k’arashe yana mai kai masa runguma had’ida k’ank’amesa sosai kaman mai tsoron kada a rabasu.... Mahmood ya jinjina masa kai a hankali yana mai amsawa kana ya maidoda hankalinsa kacaukam kan Fu’ad dan shi bai yarda Fu’ad iyakacin gaskiyar Abinda yake son sanar dashi ya fad’i mishi, he can feel akwai abinda yake b’oyewa, yanaji cen k’asan zuciyarsa kaman akwai abinda yake tsananin damun yaron kuma yanaso ya fitar saidai baisan yaya zai ya fitar da abin ba.... But tinda yanzu Yana nan zai k’ok’ari ya taimaki d’an uwansa da izinin Allah.... Murmusawa Jamal yai yana mai dafa kafad’ar Fu’ad yake furta “I wish you all the best my brother... Idan ka zab’i yin karatu a nan then fine... Allah Ubangiji ya dafa maka k’anina...!” A tare Mahmood da Fu’ad suka amsa kana Jamal yai masu sallama ya nufi Parlorn Giwa.... Hannun Fu’ad Mahmood ya dafa a hankali kana ya ambato sunansa... Fu’ad ya d’ago yana dubansa. Mahmood yaci gaba da fad’in “You know you can trust me right..?” Fu’ad ya jinjina kansa a hankali alamun tabbatarwa kana Mahmood ya d’orada “And you can always count on me...!” Nan ma jinjina kai Fu’ad yai... Mahmood ya gyara zamansa kad’an kana yace “Idan akwai abindake damunka kar kaji shakkun sanar dani kaji k’anina... Your big brother is here to listen..!” Ya k’arashe yana mai duban Fu’ad d’in cikeda tausayawa... K’ak’aro murmushi Fu’ad yai kaman zai magana sai kuma ya rungume Mahmood d’in yana fad’in “I’m glad you are here now Yaya... Please don’t leave us kaji.. Kar ka sake komawa Spain ka barmu a nan, ina matuk’ar son kasancewarka a nan...!” D’an bubbuga bayan Fu’ad yake yana mai furta “Bazan sake tafiya ba Fu’ad, zan zauna tareda ‘yanuwana a nan gaba d’aya kaji koh...!” Fu’ad ya murmusa cikeda jin dad’i su duka biyun suna duban juna cikeda k’auna... ** Jamal na ficewa bai zarce ko ina ba sai d’akin Giwa yanda suka k’ume su biyu d’in cikin d’aki.. Zuba masa idanu Giwa tai sanda yaci gaba da fad’in “Your little boy almost screwed up Maami... He almost ratted us out, if only ban isa akan lokaci ba... Nayi imani da Fu’ad ya bud’e bakinsa ya sanar da Yaya Mahmood komai, dik abinda muka aikata ranan hawan k’aramar sallah shekaru gomasha biyar da suka shud’e....!” Ya k’arashe yana sakin huci... Giwa ta mik’e tana murza hannunta dake rufe cikin safa... “Jamal k’aninku baida hankali da wayo har yanzu, idan Mahmood yasan batun nan bazai tab’a yafe mana ba dikda cewa sabida ku gaba d’aya dukanku hud’u muka aiwatar da wannan abin, da bamu aikata hakan ba ina mai tabbatar maka d’ah na da yanzu an jima da koran mu cikin Masarautar nan, kana tinanin ba dan ina tsaye akan k’afata ba da yanzu ba’a d’aid’aitani a kassarani a Masarautar nan bane yanda akega duka ‘ya’ayan Sarki AbdulJabbar ni ce nan na haifesu gaba d’aya ku duka hud’un... Dik abinda muka aiwatar shekarun baya sabida nasaranku ne... Malami na ya tabbatar min duka ‘ya’yana sai kunyi sarauta tin daga kan Yayanku Mahmood har zuwa kan d’an autanku Fu’ad...” Jamal ya d’ago yana dubanta cikin wane irin yanayi, lokaci guda ya furta “But Maami Yaya bai aikata laifin ba, shin ya za’ai shi d’in yai sarautar...?!” Murmushi ta sakar masa tana mai shafa fuskarsa take fad’in “Kud’in kun wadatar ko Yayanku bai aikata ba zai sarauta tinda ku d’in kun aikata....!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta lokaci guda taci gaba da furta “Na sadaukar da abubuwa da dama sabidaku ‘ya’yana ciki harda wani b’angare na jikina...!” Ta k’arashe tana mai duban hannunta guda dake rufe cikin bak’ar safar nan.... Zaunar da ita Jamal yai yana mai furta “Karki damu Maami na fahimceki, babu uwar da bazatai komai dan ceton yaranta da cikar burinsu ba, wanann gidan shine asalinmu kuma shine tushen mu, dik abinda kikai kinyi ne domin amfanin ‘ya’yanki domin Ki rufawa ‘ya’yanki asiri domin Mu dawwama cikin wannan masarauta har k’arshen rayuwarmu kuma ban tab’a dana sanin yin duk wasu abubuwa da kike umartata ba... Ya Mahmood nasan bazai tab’a fahimtar hakan ba, he’d judge you... Shi d’in baisan cewa zama cikin gida na sarauta dole sai kanada shiri ba...!” Murmushi Giwa ta saki a hankali tana mai duban Jamal, lokaci guda take furta “Kafi kowa fahimtata duk cikin ‘yanuwanka... Shisa nake matuk’ar k’aunarka nake ji dakai Gwarzo na.... Koda wasa kada ka bari Fu’ad ya sanar da Yayanku abinda muka aikatawa yarinyar nan SAUDATU da ahalinta....Munyi hakan ne domin KARE KARAGAR Masarautar nan, da bamu aikata hakan ba da yanzu mun jima da zama tarihi a Masarautar nan....!” Jamal ya jinjina kai “K’warai kuwa Maami bazan tab’a bari Fu’ad ya sanar da Yaya ba, hasalima lokaci yayi da zamu d’aga Fu’ad daga cikin Masarautar nan, mu turashi makaranta cen wata k’asa mai nisa yanda zai nesa da gida..!” Ya k’arashe yana duban mahaifiyar tasa... Mik’ewa tsaye tai tana dunk’ule hannunta dake rufe cikin bak’ar safar nan kana Ta shiga girgiza kai tana furta “A’a Jamal, banaso wani daga cikin ‘ya’ya na ya sake nesanta na, Fu’ad har yanzu yaro ne baida hankali k’wayoyin nan sun gama illata masa kwanya, ina tsoron mu turasa wata k’asa yaje ya aiwatar da suicide sanin kanka ne yasha attempting yin hakan a nan gida tin bayan abinda ya faru da wannan yarinya Saudatu da ahalinta...!” Jamal ya fuzar da fuci a hankali kana yace “K’warai kuwa Maami my brother couldn’t get over it, Fu’ad gawwaki biyu ya tsallake kuma unfortunately Shi ya cakkawa Mutumin takwabi har ya mutu, Saidai baiyi hakan Da nufi ba k’ok’arin kub’utar da mutumin yake daga dakarun da na tura... Maami a wancan lokacin Fu’ad yaro ne d’an shekaru goma sha uku kacal a duniya, it was really a traumatic experience for him... Ban tab’a zaton zai iya rayuwa da Abinda ya rayu ba... Fu’ad ya wahala cikin wannan rayuwar Maami...!” Jinjina masa kai tai a hankali abubuwan data aikata a Masarautar na kuma zuwa mata daki daki tin daga cin amanan da mijinta yai mata...Ta basa kyautar baiwarta a matsayin tukuici yaci amananta da Baiwar ya ‘yanta Baiwar Sannan ya auri Baiwar a bayan idonta a wani tafiya mai dogon zango da sukai shida Kyakkyawar Kuyanganta data mallaka masa....AbdulJabbar ya tozarta ta ya kuma ci mutuncinta ya wulak’antata sannan Bai cancanci yafiyarta ba even if in his death...! Gimbiya Turai tafi k’arfin tayi kishi da baiwa, baiwarma ta Masarautar ta...! Sannan kuma Wai ace Baiwar har ta riga haifawa mijinsu Magaji.... Inaa hakan sam bazai yuwu ba... Bazata tab’a bari jinin bauta ya k’wace mulki daga gareta ba koda kuwa cewa an ‘yanta mahaifiyarsa... Tabon bauta bazai tab’a shafewa a jininsu ba har abada...!! Ta k’arashe tinanin nata tana mai ci gaba da sakin huci... ** A daren wannan rana Giwa ta ziyarci Tal’udu... Tana zaune kan jan daddumarsu Ta tsafi take ci gaba da fad’in “Idan SAUDATU na raye ya zama dole ka zak’ulota Tal’udu yanda ta shiga ta fita.. Babu kasawa babu fad’i a lamarina, saidai nasara da ci gaba...!” Ta k’arashe tana sakin huci... Wani irin murmushi mai sauti Tal’udu yai yana mai buga turb’ayan dake gabansa... Wani irin jan k’ura ya tashi ya gauraye wajen gaba d’aya... Saida k’uran ya kwashe mintoci kana ya lafa.. Tal’udu ya dubi Giwa da firgitattun idanunsa “Babu wani haske gameda tak’aimemmen yanda yarinyar take a halin yanzu... Dama tun fari saida na miki kashedi muddin yarinyar nan ta kubce matsala ne Babba zai faru, kikai sake kika bari Ta kufce sannan yaranki suka miki k’arya cewa sun kasheta.... Idan har tana raye hakan nada tabbacin Mahmood zai zamto magajin Mahaifinsa... Sannan hakan zai kuma zamto dalili na rugujewarki..!!” Gumi ya shiga tsartsafowa Giwa lokaci guda take furta “Yanzu miye abinyi gameda Mahmood..?!” Murmusawa Tal’udu ya kumayi kana yace “WAMBAI.!!” Giwa tai saurin d’agowa tana dubansa cikeda firgici... Tal’udu yaci gaba da fad’in “Mabud’in fursunan sirri na wajen d’anuwan mijinki kuma idan har ya dank’awa Mahmood shikenan bazai tab’a dawowa hannunki ba JAFAR ka iya dawowa...!” Yanzu kam kan Giwa ne ya soma kwancewa... Tai wuf Ta mik’e tsaye tana fad’in “Bayaga Jafar shin akwai wanda ya isa ya bud’e k’ofar da ni kad’ai Ke iya bud’ewa...?!” “Kinyi kuskuren aminta da Wambai Turai... Keda Wambai tabbas kunyi tarayya wajen aikata wani laifi saidai kaman yanda na sanar dake zai iya zamewa yaci amanarki.... Kafin yaci amanarki kiyi maza ki aiwatar da wani abu kan Wambai, domin fitilar tsafi ta hasko min cewa akwai cin amana tsakaninku...!” Huci kurum Giwa Ke sauk’ewa a hankali... Ta yaya Wambai zaici amanarta, ya zama dole ta b’atar dashi kafin a isa wajen... Bayan sun fice daga wajen Tal’udu ta komo d’aki nan ta umarci Jakadiya da tai mata kiran Waziri a waya.... Waziri na d’agawa Giwa ta amshe wayar cikin sauri tana mai sanar dashi cewa yai saurin cimma Wambai kafin Mahmood ya rigasu... Waziri ya sanar da ita kada ta sami damuwa Mahmood bazai cimma Wambai ba, idanma ya cimmasa saidai ya cimma jana’izarsa.... Giwa ta saki murmushi cikeda jin dad’i Dan tasan Waziri bazai tab’a bata kunya ba har abada... *** Kaman ko yaushe yauma nad’in buzaye yai ya nufi gidan Baba Wambai... Bak’on Buzu abinda ya sanarda Innani kenan Dan kar ta zargi wani abu... Wannan karon a parlorn Baba Wambai suka keb’e... Baba Wambai ya tsaresa da idanu kana yace “Ina saurarenka d’ah meke tafe dakai wannan karon...?!” Mahmood ya d’anyi gyaran murya kad’an yana mai kuma gyara zamansa “Wato Baba abubuwa sun kuma rincab’ewa, dik yanda nake tinanin zasuzo da sauk’i amma abu yaci tura... Baba na rasa yardan mahaifiyata data ‘yanuwana, sun soma saka shakku da kokonto a gamedani...!” Murmusawa irinta manya Baba Wambai yai kana ya soma fad’i cikin muryarsa da girma ya kama sosai “Sadauki.... Ni na sani za’azo wanann matakin.. Sai ankai yanda kowa zai juya maka baya a cikin Masarautar muddin zaka taho da batu na gaskiya...!” Mahmood ya fuzar da fuci kad’an kana yace “Amma Baba banaso a sami wani conflict tsakanina da ahalina, banaso mu sami rashin jituwa... Baba ni ne Babba, yanzu da babu mahaifinmu kamata yai ace na had’a kan ahalin ba na wargazawa ba... Sannan mahaifiyarmu...” Katsesa Baba Wambai yai da fad’in “Mahmood yak’i kake ciki tsundum, yak’i mafi had’ari... Yak’inda baka San yaya kamannin abokin gabanka yake ba balle kai yunk’urin kare kanka idan ya kawo maka sara....!” Yarima Mahmood yai shiru yana sauraren Baba Wambai... Lokaci guda Baba Wambai ya mik’e yana mai furta “Ina zuwa....” Jinjina kai kurum Mahmood yai ba tareda ya iya amsawa ba... Baba Wambai ya shige wata ‘yar d’aki... Jim kad’an ya fito hannunsa rik’eda wata ‘yar k’aramar jaka ta fata mai kaman posa... Zama yai yana mai mik’awa Mahmood ‘yar jakan “Ungo nan amshi wannan...!” Mahmood yasa duka hannayensa guda biyu ya amsa a hankali yana mai juya ‘yar jakan.... Muryar Baba Wambai ya sinkayo yana mai furta “Mahmuda, inaji a jikina banida sauran lokaci mai tsawo a wannan rayuwar... Akwai abubuwa da dama da lokaci baida ikon ara mana kansa... Zanso ace ina numfashi a doron k’asa har zuwa wannan lokacin... Saidai bamukeda linzamin rayukanmu a hannayenmu ba...” Cikin d’an sanyin jiki Mahmood ya katsesa da fad’in “Baba ka daina fad’in haka, tsufa bashine mutuwa ba... Zan iya zamtowa gawan fari na rigaka tafiyaga magaliccinmu wanann duka iko ne na Allah...!” Baba Wambai yai murmushi irinta manya yana mai jinjina kai “K’warai kuwa Sadauki, maganarka gaskiya ne...Amma tsufa d’aya ne daga cikin alamominta kuma bazan maimaita yawan shekarunda nayi a baya ba sannan ni nasan abinda nake ji Mahmuda D’ah na... Wannan yak’i da keke tunk’ara ina mai rok’on Allah ya dafa maka cikinta... Sannan wannan k’undi dana baka akwai ranan da zaka buk’aci bud’esa... Inaso Kai masa ajiya mai kyau, irin yanda zaka ijiye abu mai matuk’ar mahimmanci a gareka....!” Mahmood ya jinjina kai a hankali yana mai furta “In sha Allah zan ajiye wannan k’undi da kyau da aminci kaman yanda ka umarta Baba...!” Baba Wambai ya jinjina kai yana mai sakin murmushi lokaci guda yake kuma sakawa Mahmood Albarka had’ida fatan samun nasara... Bayan sunyi sallama Mahmood ya tafi Baba Wambai ya isa ya d’aga k’asar katifarsa da k’yar ya ciro wani zanen ginin gidan sarauta mai yanayi da zanen dake lank’aye parlorn su Umaima... K’uri yaima zanen hawaye na gangaro masa... Lokaci guda yake furta “Wannan shine iyaka abinda zan iya yiwa Mahmuda bayan amanan iyayensa dana ci akan dalilin son mulki da son zuciya irin tawa...!”Ya k’ara she yana mai shafa zanen da hannunsa Hawaye naci gaba da gangaro masa... Yana nan tsaye ya sinkayo muryar Waziri daga waje.... Gabansa ya yanke ya fad’i...... SameenaAleeyou📚 [7/6, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *028* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Daga yanda Wambai ke tsaye yana iya sinkayo muryar maid’akinsa da Waziri suna gaisawa cikeda girmamawa, ya kuma sinkayo muryar Waziri yana tambayarta ko Wambai na Gida dikda cewa safiya ne sosai... Innani Ta jinjina kai tace “Aikuwa Yana nan yana tareda bak’o....!” Gaban Waziri ya yanke ya fad’i, lokaci guda yake furta “Bak’o kuma da safen nan...?!” Innani tace “Eh bak’on Buzu bai jima da shigowa ba, bara na lek’a sai na maka iso...” Ta k’arashe tana nufan sashen parlorn Wambai... Shidai Waziri sai faman safa da marwa yake a wajen yana sab’a babban riga yana murza hannayensa waje guda.. Waye kuma bak’on Buzu...? Bai ida tinanin ba ya sinkayo muryar Innani cikin wane irin k’aran gaske tana furta ta shiga uku ta lalace, tana kururuwa tana salati tana kiran sunan mijinta.... Babu shiri Waziri ya nufi parlorn da saurin gaske kaman zai kifa da k’asa, hakan ya kuma janyo hankulan sauran mutanen dake gidan ciki harda Juwariyya autar Baba Wambai... Waziri yai tsaye yana duban ikon Allah, Wambai kwance k’asa tamkar baya numfashi.... Innani sai kuka take tana kuma jijjiga mijinta Juwariyya ma na tayata... Cikin k’ok’arin kwantar da hankali Waziri ke basu baki yana k’ok’arin duba Wambai... Hindu mai aikace aikace na cikin gidan ita ta janye Innani da k’yar tana mai kuma tausanta had’ida bata baki, Waziri ya d’an tattab’a wasu jijiyoyin jikin Wambai lokaci guda ya fuzar da fuci a hankali yana mai sanar dasu su kwantar da hankulansu Wambai na numfashi... Lokaci guda ya umarci Hindu ta kawo masa ruwa ya zubawa Wambai... Innani kaw har lokacin bata daina kururuwa tana salati ba, Juwariyya kuma jin mahaifin nasu bai mutu ba ya sanyata neman layin Yayanta Majidad’i ta sanar dashi halinda ake ciki, ba zallan Majidad’i ba ma harta sauran yayyenta mata dake gidajen aurensu saida ta kirawosu ta sanar dasu, yayyenta maza dake karatu Jami’a saida ta kirawosu suma... Majidad’i na K’arasowa ya kirawo likita a fujajan, mintoci kad’an likitan ya iso.. Nan ya buk’aci dik su fice a parlorn su barsa ya duba jikin Wambai... Waziri yai amfani da wannan da wannan daman ya keb’e ya kirawo Giwa ya sanar da ita halinda ake ciki... Yana tsaka da wayar ne ya sinkayo muryar Innani tana tambayar likita maike damun mijinta... Cikin sauri Waziri ya katse kiran yana mai sanar da ita dik halinda ake ciki zai sanar da ita... Gaba d’aya suka nufo likitan suna sauraren abinda yake fad’i.... “Wato a gaskiya Majidad’i bazan b’oye maku ba, Wambai ya sami bugawan zuciya had’ida shanyewar b’arin jiki lokaci guda, wanda hakan yasa zaiyi matuk’ar wahala ya sake yin magana saiko wani ikon Allah duba da yanayi na tsufa da yake ciki..Paralyze d’in ya shafi idanunsa guda da kuma kunnensa guda had’ida b’angaren harshensa wanda hakan yasa a halin yanzu baiji da kunne d’aya sannan bazai iya magana ba sabida b’angaren harshensa da ya shanye sannan idanunsa guda bazai sake gani dashi ba....!” Ai likitan bai ida rufe baki ba Innani ta dafe k’irji tana kuka take fad’in “Lafiya lou fah na barsa da bak’onsa... Toh mai bak’on Buzu ya sanar dashi ni...?!” Gaba d’aya suka dubi juna “Bak’on Buzu...?!” Majidad’i ya nanata... Innani ta jinjina kai “K’warai kuwa bak’on Buzu, ai ya kwana biyu yana ziyartan mahaifinku...” Waziri ya cab’i zancen da fad’in “Shin waye bak’on Buzun kuma a ina yake kuma daga ina yake...?!” Innani tai jigum tamkar mai tinani kana tace “Wambai ne kawai zai iya baku wannan amsa don ni kaina ban tab’a ganin Fuskar bak’on Buzu ba kuma ban san daga wace duniya yake zuwa ba...!?” Gaban Waziri ya kuma yankewa ya fad’i sanda Majidad’i Ke fad’in “Ta yaya Baba zai iya amsa mana bayan ya zamto bebe kuma makaho... Innani ina san sanin wanene bak’on Buzu don jikina na bani yanada nasaba da ciwon mahaifina....!” Waziri yai saurin jinjina kai yana mai furta “K’warai kuwa Majidad’i kayi gaskiya, dik yanda bak’on Buzu ya shiga ya fita ya zama dole ka zak’ulosa ya amsa hukuncinsa...Bazanso ganin Yayan aminina Sarki mai rasuwa kwance haka ba..!” Majidad’i na sakin huci yake fad’in “I’ll make it my mission to catch whoever is responsible for my father’s illness and make him pay...! Bak’on Buzu...!! Ka shirya domin sai na zak’uloka ko a ina kake..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin fuci... Ya dubi Likita yace “Yaushe za’a tafi dashi asibiti....?!” Likita yace “Ko yanzu ma dan zamansa a gida komai ka iya faruwa...!” Babu b’ata lokaci suka d’unguma suka tafi asibiti... Tareda Waziri akai komai domin ko giftawa baiba... Babban tashin hankalinsa shine da akace Wambai bazai sake magana ba, shin ya za’ai yasan cewa ya bud’e sirrinsuwa Mahmood ko bai bud’e ba... Shin ya basa k’undi ko bai basa ba.... Ya zama dole ya bincika gidan Wambai ya samo wannan k’undin tin abubuwa basu ida rincab’e masu ba.... ** Giwa ta kuma fuzar da fuci tana duban Waziri lokaci guda ta marairaice fuska tana fad’in “Waziri dole kayi ko menene ganin cewa k’undin nan ya dawo hannunmu... Bazamu bari Wambai ya dank’awa Mahmood ba...!!” Matsowa Waziri yai cikeda tausayinta, ji yake tamkar ya rungumeta ya lallasheta Ta daina kukan nan... Lokaci guda yake furta “Karki damu Gimbiya, alk’awari nai miki muddin Waziri na numfashi bazakiyi kuka ba, sai yanda k’arfina ya k’are wajen ganin Duka burikanki sun cika... Wannan k’undi nayi maki alk’awari har abada bazai isaga Mahmood ba....!!” Ta saki murmushi a hankali tana mai kuma duban Waziri wanda shid’in ma ita yake duba yana sakin murmushi... Giwa ta nusa tace “Toh shi wannan bak’on Buzun fah, mai kake tinani gamedashi... Anya babu wani rufeffen al’amari gameda Shi,... Kasan fah gidan nan kowa ba abin yarda bane... Anya wani bai rigamu isaga Wambai ba koda ba Mahmood bane...?!” Murmusawa Waziri ya kumayi kana yace “Bakida damuwa da wannan, na riga na ziga Majidad’i cewa dik yanda Bak’on Buzun nan yake ya zak’ulosa domin kuwa shikeda alhakin ciwon mahaifinsa... Kinsan halin yaron da kafiyan bala’i na tabbata sai ya nemo koma wanene wannan bak’on Buzun... Muna nan dake zakiga yanda za’a zak’ulo Bak’on Buzu a yanke masa hukunci mafi tsauri... Yanzu abinda Ke gabanmu shine binciko wannan k’undi dake cikin gidan Wambai, zan tura yarana cikin dare suje su bincika gidan tinda yanzu hankulan mutanen gidan gaba d’aya ya karkarta zuwa asibiti... Zasu bincika gidan sannan su kawo min wannan k’undi... Babu wanda zai fahimci cewa mai akai saidai suyi tinanin cewa b’arayi ne suka shiga gidan cikin dare...!” Giwa ta girgiza kai kad’an kana tace “Waziri zama bai ganmu ba, ai bazamu bari Majidad’i ya rigamu capko Bak’on Buzu ba, ya kamata kafin Majidad’i ya gane ko wanene bak’on Buzu mu ya kamata mu soma cimmasa koma shid’in wanene Dan idan ya rigamu ko shakka babu bana haufin hakan ka iya tona asirinmu...!” Waziri ya jinjina kai yace “K’warai kinyi gaskiya amma bakida damuwa Ki barmin wannan zan kamo Bak’on Buzu yanda ya shiga ya fita.....!” Ubandoma dake lab’e jikin k’ofa ya gama jin komai, a hankali yasa kai ya fice yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa ya zama dole ya samo wannan k’undin kafin ya isa hannun Waziri, Dan idan ya samo k’undin nan zai sami Abinda ya jima yana buri Wato ‘Yanci... Yana matuk’ar san ya tashi daga bauta ya koma ‘yantacce, wannan itace kad’ai Damarsa don ya tabbata idan ya samo wannan k’undin dik abinda yace Giwa tai masa in exchange zatai masa domin ta mallaki wannan k’undi koda kuwa menene...!Ya kuma sakin murmushi a hankali kana yasa kai ya fice cikin sauri..... *** Koda labarin ciwon Wambai ya isa Fada sosai hankalin Yarima Mahmood ya tashi musamman da yaji irin abinda ya sami Wambai wanda idan ya had’uda tsufa da k’yar ake tashi saiko wani ikon Allah... Haka yaita tuna tattaunawarsu Ta k’arshe wanda tamkar bankwana Wambai d’in ke masa... Yana matuk’ar k’aunar Wambai baya k’aunar abinda zai cutarda Wambai... Tamkar mahaifi haka ya d’auki Baba Wambai dikda cewa shid’in d’anuwan mahaifinsa ne dama.... Shida Fu’ad suka garzayo zuwa asibitin babu b’ata lokaci Ubandoma na biye bayansu.... Suna doso kai d’akinda aka kwantar da Wambai Mahmood ya sinkayo muryar Majidad’i na fad’in ko Wanene bak’on Buzu sai ya zak’ulosa don shikeda alhakin ciwon mahaifinsa... Yasan shid’in ne shine bak’on Buzu amma baisan ya akai ciwon Wambai Keda alak’a da bak’on Buzu ba tinda yasan lafiya lou sukai sallama... Tabbas bazai bada wani clue ma Majidad’i da har zai fahamci cewa shine bak’on Buzu... On the other hand shima yanaso yasan komai in details, yanda akai bak’on Buzu Keda alhakin ciwon Wambai... Toh ko hakan nada alak’a da wannan k’undin da ya dank’a masa ne..?? Tabbas ya kamata Shima ya bincika don ko babu komai Baba Wambai ya masa abinda babu wanda ya masa shi tin dawowarsa cikin Masarautar... Da sallama suka shigo cikin d’akin... Majidad’i da Innani suna ganinsu suka had’e FUSKA gaba d’aya tamkar sunga ajalinsu... Mahmood bai k’asa a gwiwa ba ya soma gaida Innani dake faman cika, Ta amsa da k’yar kana Fu’ad ma ya gaidata sukai mata yaya mai jiki... Nan ma da k’yar ta amsa... K’warjinin Mahmood ya cika wajen gaba d’aya wanda hakan ya hana Majidad’i da mahaifiyarsa wulak’anta su Mahmood.... Amma kam tabbas Majidad’i ji yake tamkar ya fitarda Mahmood daga cikin d’akin, da ace yanada ikon yin hakan da yayi.... Bayan sun ida gaisawa ne Mahmood ke tambayarsu yanda al’amarin ya kasance....Innani ta karanto masa komai yayinda Majidad’i ya k’arada “Bak’on Buzu baici banza ba Innani wllhi sai na zak’ulosa na d’auki fansar mahaifina akansa...!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci lokaci guda ya janye jiki ya fice daga d’akin gaba d’aya.... Mahmood yaima Wambai dake kwance saman gadon marassa lafiya K’uri tausayinsa na d’awainiya dashi.... A hankali ya isa jikin gadon ya dafa hannun Baba Wambai maras cannula... Lokaci guda yake karanto masa addu’o’in samun lafiya, cikin zuciyarsa na ayyanawa cewa in sha Allahu sai yanda k’arfinsa ya k’are wajen ganin Baba Wambai ya sami lafiya.. Akwai abubuwa da dama da yake neman amsoshinsu daga wajen Baba Wambai bayan dank’a masa wannan k’undi da yayi... A hankali ya furta “Allah ya baka lafiya Baba ya tashi kafad’unka....!” Gaba d’aya mutanen dake cikin d’akin suka amsada Ameen... *** Fitowarsu daga cikin asibitin Mahmood yaga kiran Turaki na shigo masa, excusing kansa yai ya nufi ‘yar wata hanya nan cikin asibitin domin amsa kiran Turaki yayinda Fu’ad da Ubandoma suka nufi mota.... Yana tafe yana k’ok’arin amsa kiran ya hango Juwariyya d’iyar Baba Wambai... Tabbas tsaf ya ganeta don ga kamanninsu nan tanadashi dikda cewa rabon da yaga yarinyar zai iya cewa tun wani zuwansa Nigeria lokacin yana Spain... Abinda ya tafida hankalinsa ya mantar dashi wayar da zai amsa shine sinkayo muryar Juwariyya da yai cikin waya tana fad’in “Ni fah Raheema babu wani binciken k’wak’waf da zan maki gameda Muhibbah sabida ni yanzu abindake gabana yafi k’arfina... Ni dama ba ‘yar bincike bace kawai dai Ina baku information ne gameda Yaya na Dan nima banaso yai sarauta sabida na tsani matarsa nafi so Ya Mahmood yai shisa nake baku duk wani information akan abindake faruwa cikin gidanmu... Amma ni harga Allah ba ‘yar bincike bace bazan iya wani bincike kan wata Muhibbah ba... Naji da jinyar mahaifina ne ko naji da wani bincike...Mtsww..!” Taja dogon tsaki tana mai katse kiran take ci gaba da fad’in “Ko sun zata sabida abin duniya nake masu aiki oho... Allah ya sawak’e su sakani wani aikin da banyi niyya ba ina a matsayin jinjin sarauta... Yanda suke jin kansu d’oyiyin Sarki nima jikar Sarki ce nafi k’arfin......!” Burki taiwa kalamanta sakamakon hango Yarima Mahmood da tai fuskar nan nasa tamau ya tsareta da idanunsa masu firgita dik wani mai laifi.... Jikin Juwariyya ya d’auki rawa, tasan Yarima Mahmood ya gama sauraren wayarta yaji komai, ai ko irin duban da yake mata tasan ya riga da yaji wayar da take da Raheema... Juwariyya ta had’iyi miyau da k’yar tana murza wayar salulanta da duka hannayenta biyu... Lokaci guda kuka Ke k’ok’arin zuwa mata, tuni ta soma kuka tana k’ok’arin duk’awa gaban Mahmood dake tsaye hannayensa hard’e Ta baya tana fad’in “Yaya Dan Allah kayi hak’uri... Wllhi Anty Raheema so take kawai Kai sarauta shisa Ta sakani nake kawo mata rahoton dik abinda ke faruwa cikin gidanmu gameda neman mulkin da Ya Majidad’i yake... Yaya wllhi mu kai muke so kai sarauta shisa.. Amma babu wani abu mai muni da mukai sai yanzu da Anty Raheema Ke cewa nai mata bincike kan Muhibbah Wai Dan kar ta sace mata kai... Yaya Dan Allah....!” Kanta a k’asa tana duk’e take maganaganun saidai d’agowar da zatai ta hangi wajen wayam babu Mahmood babu dalilinsa, b’at ya b’ace a wajen ba tareda yace da ita k’ala ba.... Juwariyya ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida dafe k’irjinta... Idan bata mance Innani na basu labari a lokutan baya idan aka sameka da laifin cin amana a Masarautar hukuncin kisa ake yankewa mutum idan bawa ne, idan kuma d’ah ne hukuncin shekaru masu yawa ake yanke masa a kurkukun masarauta... Ta kuma Sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai ayyanawa har abada Ta dena aikiwa Raheema da Gimbiya Zeenat.. Yo ita koma sanin wanann Muhibbar da suke cewa tai masu bincike kanta batai ba....Toh wacece Muhibbah...? Sannan mai ya kawota Masarautar..?”Take taji tana son sanin ko wacece Muhibbah... Lokaci guda kuma ta shiga neman layin Raheema Dan sanar da ita abinda ke wakana.... Raheema dake kwance saman gado tana jiran Yazeed ya fito daga bathroom sai ganin kiran Juwariyya tai na kuma shigo mata... Tsuka tai had’ida tura wayar gefe tana furta “Banza kanki akeji har ni zaki nunawa Mulki da sarauta... Dama ki dawo kan hanya ne yarinya...!” Tana nan a haka Yazeed ya fito d’aure da towel yana goge sumarsa da k’arama guda d’aya... Cikeda salo Raheema ta mik’e ta isa gareshi had’ida shigewa cikin jikinsa tana fad’in “You look handsome my Prince..!” Yazeed ya tallafota suka nufo gadon a haka bakunansu cikin na juna.... Har wannan lokacin wayar Raheema bai daina ruri ba, k’arshe Yazeed ne ya danna wayar a silent saidai tuni Raheema ta hango shigowar sak’o tai k’ok’arin ture Yazeed kad’an Ta janyo wayar... Dik yanda Yazeed Ke k’ok’arin k’wace wayar Raheema tak’i saki har saida ta ida karance sak’on... Jikinta ya d’auki rawa... Innalillahi kawai take ambata, shikenan Mahmood yasan komai... Lallai wannan Juwariyyar anyi babban jaka gidahuma... K’ara Ta saki had’ida tura Yazeed daga kanta ta mik’e babu shiri tana k’ok’arin zira tufafinta.. Yazeed na tambayarta meke faruwa inaa ko amsasa batai ba ta suri handbag d’inta saida ta kusan k’ofa ta juyo tana fad’in “Zeed I can’t lose Mahmood... I just can’t, I need to go right now....!!” Bata ko jira cewar Yazeed ba Ta fice cikin sauri tamkar zata kifa k’Asa...... Yazeed ya fuzar da huci cikeda b’acin rai yana mai jifa da pillow guda, ya kuma dunk’ule hannunsa ya daki cikin katifa lokaci guda yake furta “Mahmood..! Komai Mahmood.. Kowa Mahmood...!! Mahmood Mahmood Mahmood..!! Zancen kenan, na gaji da jin wannan sunan... I hate you Mahmood... I hate you more than anything in this world...!!” Ya k’arashe yana mai kuma dukan garu da hannunsa kana ya mik’e ya soma shiryawa Shima... Ransa gaba d’aya a jagule...!! *** Har suka iso gida bai daina juya kalaman Juwariyya cikin kwanyarsa ba, if there’s one thing he hates shine ai abu akansa bayan idanunsa koda abin amfanin kansa ne.... For what Raheema zatai masa haka...! Ita wacece da zatai katsalandan haka cikin rayuwarsa... Waya bata wannan damar...?!! Yana tinanin yana mai ci gaba da murza zoben azirfa dake yatsarsa guda... Idanunsa kaw tinda ya shige motar na kallon window... Fu’ad dake gefensa ya kula da yanda yanayin Yayan nasa ya canza tin bayan shigowarsa motar... Yaso tambayarsa ko akwai abindake damunsa ne amma sai yai shiru zuciyarsa na mai raya masa cewa k’ila sabida ganin jikin Baba Wambai ne ya sanyasa cikin yanayin... A haka suka iso Fada... Suna isowa Ubandoma dake zaune gaban Jeep d’in ya fito ya bud’ewa Mahmood yanai masa Fadanci... Dogarai ma sai zuba masu fadanci suke daga Mahmood d’in har Fu’ad... Fu’ad yaso bin bayan d’anuwansa ganin yanda ya shige sashensa cikin sauri yana fad’iwa Ubandoma yai masa kiran Jakadiya.... K’arar da wayar Fu’ad d’in yai ya sanyasa baibi bayan Mahmood ba... Sahibarsa Muhibbah ce mai kira, Dan tinda ta hangi shigowar mota Fada jikinta ya bata su Fu’ad da Mahmood ne suka dawo... Fu’ad ya d’aga wayar cikeda jin dad’i yana mai zolayarta da fad’in har tayi kewarsa kenan tinda basu jima da yin waya ba.... Daga d’aya b’angaren Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Karka laifina Prince... Soyayya Ke d’awainiya dani...!” Fu’ad ya kuma murmusawa kana yace “Toh ai ked’in ce kin hanani ganin kyakkyawar fuskarki cikin Fada da yanzu na k’araso har yanda kike....!” Ta kuma murmusawa kad’an kana tace “Gida na sarauta Rankashi dad’e sai anayi ana taka tsantsan kasan abin magana baya kad’an a gida irin naku, ni kuma bazanso naga abinda zai b’ata maka suna da martabarka ba dukda cewa ba abu maras kyau mukeyi ba...but nasan da yawa bazasu fahimcemu ba only few can understand...!” Ta k’arashe cikeda k’issa... Fu’ad ya jinjina kai yana mai amintada kalamanta yake fad’in “K’warai kuwa kinyi gaskiya Gimbiyata... Abun magana baya kad’an a wannan gida namu... Ni d’in shaida ne, kuma bazanso na zamto silan da zaisa ki bar Masarautar nan ba...Zanyi hak’uri naci gaba da ganinki a makaranta har zuwa lokacinda zaki amince mu bayyana soyayarmu ga kowa a cikin Masarautar nan....!” Rausayar da idanu tai cikeda k’osawa Dan Allah na gani kan sole take waya da Fu’ad, jin muryarsa da kalamansa take tamkar garwashin wuta cikin kunnuwarta... Lokaci guda ta saki murmushin dole da k’yar kana tace “So Ya kuka sami mai jiki....?” Fu’ad yace “Toh gashi nan dai bazamuce babu sauk’iba.. An godewa Allah... But yanda mukaga jikin Baba Wambai da alama ya d’aga hankalin Yaya Dan koda muka dawo tuni ya nufi sashensa, dik yanda yake k’ok’arin b’oye tashin hankalinsa hakan taci tura saida fuskarsa ya nuna... Tinda naji yayi kiran Jakadiya nasan hankalinsa a matuk’ar tashe yake... Yayana ya fuskanci rashi da dama a rayuwarsa ga mahaifinmu ga kuma matarsa shisa yakega kaman zai kuma rasa Baba Wambai ne...!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Muhibbah Ta mik’e daga zaunen da take cikin sauri Dan tinda taji Fu’ad yace Mahmood yayi kiran Jakadiya jikinta ya bata wani abin Ke faruwa, ya zama dole tasan yanda zatai ta shiga sashen Mahmood danjin abinda zai tattauna da Jakadiya.... Suna ida waya da Fu’ad ta mik’e tai shirinta tsaf kana ta nufi sashen Mahmood a sace... Tana mak’ale jikin gini ta hango Jakadiya ta nufi sashen Yarima Mahmood Gimbiya Raheema na biye bayanta... Muhibbah ta murmusa a hankali tana mai ayyanawa dama jikinta ya bata sauyawan Mahmood da Fu’ad yace nada babban dalili... Suna shigewa ta sad’ad’o a hankali, daidai lokacinda Jakadiya ke magana da Dogarai masu tsaron k’ofa hakan ya bata daman shigewa cikin sand’a ba tareda sunyi noticing d’inta ba... SameenaAleeyou*MUHIBBAH* *029* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tsaye ta hangosa yana fuskantar window ya baiwa parlorn baya, k’irjin Raheema yaci gaba da dukan tara tara... Harga Allah batasan mai zatace ba, batasan da wata kalma zata soma kare kanta gaban Yarima Mahmood ba, ganin har Ta ida shigowa cikin parlorn tai tsaye bai juyo ba bai kuma tankata ba abin ya kuma tada mata hankali... Ta soma k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta da nufin gaidashi.. Har lokacin baice da ita komai ba bai kuma juyo ba... Itadai Muhibbah na rakub’e daga gefe tana kallon ikon Allah... Saida suka kwashe dak’ik’ai a haka kana Mahmood ya juyo har lokacin hannayensa hard’e ta baya... Ba Raheema dake tsaye cikin parlorn ba harta Muhibbah saida yanayin fuskar Mahmood ya bata tsoro... Zatace bata tab’a ganin tsananin b’acin rai kwance saman fuskarsa kaman yanda Ta gani yau ba.... Raheema kaw rawa jikinta ya d’auka gaba d’aya sai ta tsure gani take tamkar yasan alak’ar dake tsakaninta da d’an uwansa Yazeed ne... Ta had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’ogoro da k’yar... Kujera yai mata nuni murya a dake ya furta “Zauna...!” Jiki a matuk’ar sanyaye ta isa ta zauna kaman yanda yace.. Lokaci guda shima ya tako ya zauna a kujera guda... Dak’ik’ai suka kuma shud’ewa a haka kaman babu mai cewa komai cikinsu har saida Raheema Ta d’an d’ago ta saci kallonsa, tai saurin maida kanta k’asa zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Hardai Muhibbah ta sadakar Bawan Allahn nan bazaice komai ba sai kuma ta sinkayo muryarsa mai amo kama daga sama yana furta “Maiyasa kika aikat..Why..?!!” Yai tambayar yana mai tsare Raheema da idanu... Raheema taci gaba da k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta “Your Highness... Wllhi Allah ni dama kawai I wanted to help ne...Allah wllhi ni taimakonka nake son y.....!” Katseta yai da fad’in “Na tab’a neman taimakonki..?!” Tai saurin girgiza kai alamun a’a... “Na tambayeki ki taimaka min...?!” Nanma girgiza kai tai alamun a’a... “Namiki kamada mabuk’acin taimako daga wajenki..?!” Izuwa lokacin Hawaye sun soma wanke fuskar Raheema tai saurin girgiza masa kai tana mai furta “Dan Allah Your Highness kai hak’uri... Na sani na shiga hurumin da ba nawa ba but in sha Allah bazan sake ba... Dan Allah kai hak’uri ka yafe min...!” Mahmood yai mata K’uri yana karantarta kana ya kumayin gyaran murya kad’an yace “Kinsan hukuncin abinda kika aikata a dokan Masarautar nan...?!” Tai saurin d’agowa a zabure tana dubanta zuciyarta naci gaba da tsinkewa....Lokaci guda taci gaba da girgiza kai had’ida had’a hannayenta biyu waje guda “Rankaidad’e dan Allah kai hak’uri... Dan Allah kada ka sallameni daga Masarautar nan... Dan Allah kada ka bari a maidani Masarautar mu... Wllhi ina matuk’ar k’aunarka Yarima... Bazan rayuwa babu kai ba....!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin sabon kuka.... Yai mata k’uri yana dubanta cikin yanayin zamansa irinta masu mulki ba tareda ya furta mata komai ba... Har saida kukan ya tsagaita dan kansa kana yace “Banikeda alhakin sallamarki daga Masarautar nan ba dan har yanzu ni ba sarki bane... Ita kuma wacce kikasa ai bincike akanta fah...?” Gaban Muhibbah ya yanke ya fad’i, wacece Raheema tasa abincika mata...? Bata ida tinanin ba ta sinkayo muryar Raheemar tana fad’in “Your Highness wllhi sharrin Juwariyya ne ni ban umarceta tai wani binciken k’wak’waf kan Muhibbah ba... Yarima dan Allah ka yarda dani... Why would I have her investigated... What for..? Wllhi sharri ne kawai irin ta mutanen Fada...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya mai raunin gaske... Daidai nan Ubandoma ya shigo parlorn yana mai zubewa k’asa yake fad’in “Ina mai neman afuwan Babban Yariman Masarautar nan da shigowa da nai Kai tsaye...Tuba nake Allah shi baka yawan rai...!” Mahmood yace “Ina saurarenka Ubandoma meke tafeda kai....?!” Ubandoma yaci gaba da fad’in “Dama su Galadima Danmadami da Talba da kuma D’anisa harmada Madaki ne sukace ai masu iso wajenka... Gaba d’aya suna haraba suna jiranka Allah shi baka yawan rai...!” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Ubandoma..!” Ubandoma ya amsa cikeda ladabi kana Mahmood ya k’arada “A bud’e masu Galadima Babban gwani su shiga ciki Ina nan tafe..!” Ubandoma ya kuma rusinawa yana mai amsawa had’ida mik’a gaisuwarsa ga Raheema tareda mata kirari kana ya mik’e da azama dan isarda sak’on ubangidansa... Ubandoma na ficewa Raheema ta kuma kifa kanta tamkar wata mumina tana mai ci gaba da shesshek’an kuka dan kawai Mahmood yaji tausayinta... Tsaye ya mik’e yana mai fuskantar center hannayensa hard’e Ta baya irin tsayuwar da masu mulki suka faye yinta... Lokaci guda ya karkato da fiskarsa yana dubanta kaman zai magana sai kuma yasa kai yai shigewarsa cikin tafiya da tafi kama da sassarfa... Yana ficewa Raheema Ta d’ago kanta had’ida sakin makirin murmushi, a fili take furta “Sannu a hankali zaka shigo hannuna..!” Ta kuma sakin murmushi kana ta waiga gefe da gefe... Lokaci guda tai azamar mik’ewa tsaye yayinda Muhibbah ta kuma mak’alewa bayan staircase tana hangota sosai... Cikin azama Raheema ta shiga d’aga alkyabbarta, tai saurin zak’ulo wani garin magani dake d’aure cikin leda bak’a... Ta kwance d’aurin cikin sauri kana ta isa saman kujerar da Mahmood ya faye zama.. Nan ta saki murmushi sannan Ta soma barbad’a garin maganin, haka tabi sauran kujerunma duk ta barbad’a sannan ta yayyafa a bakin k’ofar fita... Tana ida barbad’e barbad’enta ta cusa ledar maganin cikin alkyabbarta kana ta bubbuge hannayenta ta gyara zaman alkyabbarta sosai sannan Ta fice daga sashen zuciyarta nai mata sanyi... Tasan yau dole Aunty Zeenat tai alfahari da ita... Yau dai kam ta cika aiki tasan babu yanda za’ai Mahmood tsallake tarkonsu yau tinda hardai zai shiga sashen dole ya bi ta saman shirinsu sannan hardai zai zauna a parlorn toh fa sai ya zauna akan shirinsu... Daga rana mai kaman ta yau Mahmood ya zamto sai yanda tai dashi a Masarautar.... Raheema na ficewa Muhibbah ta sad’ad’o ta fito tana mamakin abubuwan da taga Raheema ta barbad’a... Ta K’araso cikin parlorn sosai tana ware idanunta ko zataga alamun garin magani amma to her surprise babu ko alamun gari... Bazaka tab’a cewa an zuba wani abu mai kaman gari wajen ba... Tsaye tai tana tinanin abinyi kafin wani ya shigo ya ganta a sashen.. Amma kam tabbas sai tayi yanda tasan ta kawar da abinda idanunta sukaga Raheema ta barbad’a koda ace bata iya ganin abin a zahiri... Waige waige ta soma cikin parlorn nan ta hangi goran ruwa saman dining table, tai saurin k’arasawa Ta d’auko goran ruwan, cikin azama ta warware d’aurin d’ankwalinta ta zuba ruwan ta jik’a d’ankwalinta dashi kana tabi gaba d’aya kujerun Ta gogesu da d’ankwalinta mai damshin ruwa... Haka dik yanda taga Raheema tayi barbad’an a parlorn saida tabi Ta goge tsaf... Harta da bakin k’ofan parlorn saida shima ta goge shi tass... Tana idawa ta Sauk’e huci a hankali kana tai k’ok’arin sad’ad’awa Ta fice daga sashen.... Saida ta isa masauk’i kuma ta soma tuhumar kanta, maiyasa ma zata taimaki Mahmood... Maiyasa bazata K’yalesa ya fad’a tarkon Raheema ba..? Wata zuciya tace hakan da kikai shine daidai dan idan kika bari asirinsu Raheema yai tasiri akansa toh fah zaki rama abinda yai maki ne bashi a cikin hayyacinsa... Gwara yana cikin hankalinsa yanda zaifi jin zafin duk abubuwan da zaki masa... Abinda kikai kinyi daidai Muhibbah ba taimakon mak’iyinki kikai ba... Ta k’arshe tinanin tana mai zama cikin sofa lokaci guda tunanin abinda taji Raheema na fad’i ya dawo mata... Wato binciken k’wak’wafa Raheema zata saka ai akanta... Idan kuwa haka ne toh fah zama bai ganta ba... Ya zama dole ta toshe duk wani hanya da real identity d’inta zai bayyana... Bazata bari Raheema Ta kawo mata cikas a shirinta ba... Toh ya zatai mai zata farayi... Ta ina zata b’ullowa Al’amarin...? Tai zaune tana tinani... Idan har Raheema zatai bincike kanta Toh fah saidai Ta tafi makarantarsu ta soma binciken don ta nan ne kawai zata iya yin bincikenta cikin sauk’i tinda ita ba ‘yar gari bace...! “Ansar...!” Ta furta a hankali... Shine kawai mutumin da zai zamto mata cover... Tai saurin janyo wayar salulantar da zummar dialing layin Ansar sai kuma taji jikinta yai matuk’ar yin sanyi ganin rabuwarsu Ta k’arshe da Fad’a suka rabu... Ta kuma ce masa bazata sake tambayar komai daga garesa ba koda shawari ne...Ta lumshe idanunta a hankali tana mai ije wayar gefe guda... *** A can babban gwani kuwa masu sarautar sunyi zaune gaba d’aya... Su Waziri Galadima Hakimi da Talba da dai sauransu, Sun zagaye Karagar Mulki dake daga center... Mahmood na gefen Waziri Talba yaci gaba da fad’in “Bazai yuwu mu zauna haka nan babu sarki ba har yanzu... Kundai ga abinda ya sami Wambai, kai tsaye bazance wanine ke nufinsa da sharri ba amma mu munsan gida irin namu... Tinda cikinta aka haifemu muka kuma yi wayo cikinta har kawowa girmanmu... Idan muka zauna muka zuba idanu toh haka kaf sai anbi kanmu d’aya bayan d’aya an illatamu.... A ajiye maganan b’angaranci da son Mulki a gefe kowa yayi hak’uri a baiwa wanda ya cancanta mulkin nan... Kuma ni nan na janye neman mulkin nan da nake na mik’a wuyaga d’ah na Mahmooda dan shine ya cancanci wannan sarauta...!” Su Waziri gaba d’aya suka shiga jinjina kai suna furta “Wannan gaskiya ne Mai Girma Talba....!” Dogarai dake tsartsaye gefe suka soma wasa Mahmood suna fad’in Allah ya bashi dama gadon gidansu ne... Talba yaci gaba da fad’in “Alhamdulillahi tinda duk munyi na’am sai a tsayar da ranan da za’a nad’a Sarki Mahmooda na biyu... Idan kuma akwai wanda bai amince ba sai muji dalilinsa..!!” Kaman daga sama suka sinkayo murya cikeda iko da gadara yana fad’in “K’warai kuwa akwai wanda bai amince ba..!!!” Gaba d’aya suka kaikaito suna duban k’ofar had’ida da mamakin wanda yai maganar.... Waziri ya kifa kansa kurum yana girgizawa a hankali.... SameenaAleeyou 📚[7/8, 10:10 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *030* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Majidad’i...!!!” Hakimin gari ya furta cikeda mamaki sanda Majidad’i yaci gaba da kutso Kai cikin tampatstetsen parlorn... Shamak’i ya zube yana kwasan gaisuwa yake furta “Ku gafarceni Majidad’i yak’i sauraro na saima nuna min takwabi da yai a wuyana.!” Ya k’arashe yana muzurai alamun har lokacin tsoro ne dabaibaye dashi... Masu sarautun gargajiya suka soma mik’ewa tsaye babu shiri ganin zarkwad’ed’iyar takwabin dake rik’e hannun Majidad’i sai faman shek’i take tana k’yalli.... Waziri yai azama yana mai furta “Kai Majidad’i lafiyarka... Meye haka nake gani... Ka kuwa San mai kake aikatawa..? Ka kuwa San ko ina kake... Ko kuwa hankalinka ne ya gushe...?!!” Cikeda izza had’ida rashin tsoro Majidad’i yace “K’warai kuwa Waziri babu wanda ya isa ya d’ale Karagar nan muddin ba’a zak’ulo mutumin da ya illata min mahaifina ba... Sannan sanin kanku ne muddin Wambai na numfashi a doron k’asa sai da yardarsa da amincewarsa a nad’a Sabon sarki a Masarautar nan.... Oh Wato kunzo nan kun had’e kawunanku zaku nad’a sabon sarki mahaifina nacen kwance... Toh ina mai tabbatar maku babu wanda zai hau Karagar nan har sai an zak’ulo wad’anda Keda alhakin kasancewar mahaifina a haka... A shirye nake na fafata da dik wani wanda yace zai jayayya dani....!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci... Cikin tsananin b’acin rai Waziri Ke furta “Kayi kuskure Majidad’i.. Ka wulak’anta gidan nan kaci mutuncin ahalinta dan haka dole ka amshi horo... Sarkin Gidaaa...!!! Yai maganar cikin d’aga murya yana mai ci gaba da fad’in “A d’auke Majidad’i a tafi dashi Gidan Yarin Wutin gadi....!!!” Take Majidad’i ya bada balance ya d’aga takwabinsa yana fad’in dik wanda ya nufo yanda yake sai ya fille kansa... Mahmood ne ya tako gabansa ba tareda shakku ko tsoron makamin dake hannun Majidad’i ba... Gaba d’aya sukai K’uri suna duban ikon Allah... Majidad’i yana duban Mahmood take ci gaba da sakin huci yana kuma d’aga takwabin nasa sama.... Cikin tsananin huci yake k’ok’arin kaiwa Mahmood d’in sara ganin bai daina takowa yanda yake ba... Saidai ga tsananin mamakinsu tuni Mahmood yakaiwa takwabin damk’a ya rik’e sosai cikin tafin hannunsa dukda tsananin kaifi da takwabin kedashi.... Majidad’i yaci gaba da huci yana k’ok’arin cire takwabin daga cikin hannun Mahmood amma abu yaci tura... Su kansu saida sukai mamaki ga kuma jini dake gangarowa daga cikin tafin hannun Mahmood d’in alamun yanka... Su Galadima su Waziri sukai K’uri suna duban ikon Allah dan gaba d’aya sai Yarima Mahmood ya juye masu mahaifinsa Sarki AbdulJabbar.... Galadima da Waziri suka dubi juna a tare idanunsu na firfitowa waje sosai.... Sarkin Yak’i kuwa tuni ya daka tsalle ya zaro takwabin dake mak’ale gefen d’amaransa wanda dama dik sanda za’ai taro cikin Fada da d’amararsa ta yak’i yake halarta.... D’aga masa hannu guda Mahmood yai alamun dakatarwa kana ya maidoda dubansaga Majidad’i dake ci gaba da sakin huci har lokacin bai iya k’wace takwabin daga cikin hannun Mahmood ba.... Ga tsananin mamakinsu k’asaitaccen murmushi Mahmood ya sakarwa Majidad’i saikace baijin zafin yankar wuk’an na ratsa sa, lokaci guda yake furta “Ka kwantar da hankalinka D’anuwana, kaman yanda kace babu wanda zai hau Karagar nan har sai an binciko musabbabin ciwon Baba Wambai... Idan don ni Mahmood ne na amince da haka d’in... Ka sani Babu wani Sarki da zaiso a zubar da jini a mulkinsa, kuma babu wani sarkin da zaiso yaga an zubar da jinin Al’ummansa kafin ya d’ale Karagar mulki.... Zamanin yanzu yasha bambam da wancan zamanin, kasan ance Sarki goma Zamani goma..!” Ya k’arashe yana mai jifa da takwabin dake damk’e cikin hannunsa guda wanda ko motsata Majidad’i ya kasayi... Waziri ya had’iyi miyau da k’yar wanda tai masa k’ebebe a mak’ogoro... Lallai yau yaga jarumtar Mahmooda, sam bai tab’a kawowa shid’in zai jarumta irinta mahaifinsa ba sai gashi yana nema ya zarce AbdulJabbar... Anya bokan Turai bai shera mata k’arya ba kuwa... Anya idan suka sake Mulkin nan ya fad’o hannun Mahmooda zasu cimma burinsu cikin sauk’i kuwa...? Gaba d’aya Waziri ya zama lost, gaba d’aya yama rasa abinyi... Tsoro da tashin hankali sun cika zuciyarsa sosai... Mahmood nayin jifa da takwabin Dakaru suka K’araso a tamanin suka capke Majidad’i Waziri na fad’in a tafi dashi fursuna.... Mahmood ne ya dakatar dasu da fad’in “Ku sakeshi, ku k’yaleshi yai tafiyarsa... Amma wannan zai zamto gargad’i na k’arshe da zai kutso cikin Fada da takwabi tsirarta alhalin masarauta na cikin lumana.... Ubandoma..!!!” Ubandoma ya k’araso had’ida zubewa gaban Mahmood yana mai furta “Rabkaidad’e..!!!” Mahmood yaci gaba da fad’in “Ka raka Majidad’i har zuwa bakin k’ofar Masarauta, a tabbata Majidad’i ya fice daga cikin Masarauta cikin lumana da aminci....!!” Ubandoma ya kuma risinawa yana mai amsawa kana ya tasa k’eyar Majidad’i yana fad’in “Godiya Majidad’i yake Allah shi baka yawan rai...!!” D’anmaliki da Talba suka dubi Mahmood cikeda jin dad’in abinda yayi yanzu, hakan ya kuma tabbatar masu da cancantar Mahmood na zama Sarkinsu na gaba... Haka aka san Sarki da jib’antan lamuran Al’ummansa had’ida jarumta da kuma rangwame da sassauci ga wad’anda Allah ya hukunta masa zamtowa shugaba a garesu... Abinda Majidad’i yayi yaci a tafi dashi gidan Yari amma Mahmood yai masa afuwa ya kuma ce ai masa rakiya har k’ofar Fada a tabbata ya fita lafiya cikin aminci sannan ya janye sarautar da aka basa har sai an warware wasu al’amara a Masarautar kaman ciwon Baba Wambai dan shi bai yarda Bak’on Buzu nada alak’a da ciwon Wambai ba tinda dai yasan shid’in shine bak’on Buzu... Baisan dalili ba amma jikinsa na basa akwai wata k’ulleleliya a al’amarin.... ** Bayan an watse a Fada ne Waziri ya k’araso yana kuma ingiza Mahmood cewa lallai ya d’ale Karagar nan a yanzu, dan hakan ne kawai zai basa daman aiwatar da al’amara yanda suka kamata... Ya k’arada “Rankaidad’e Kaga dai yanda maras kunyar yaron nan d’an wajen Wambai ya shigo yai abin kunya da Allah wadai cikin Fada, na tabbata Mahaifiyarka bazataji dad’i ba muddin taji cewa Kingmakers sunyi ma’am gaba d’aya cewa ka zamto Sarki harma ana k’ok’arin tsaida ranan rantsar dakai matsayin Sarkin wanann nahiya tamu mai babban daraja amma kak’i kace a sarara zuwa wani lokaci... Rankaidad’e da dai an duba lamarin... Wanann sarauta dama gadonka ne Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe yana mai kuma k’ank’an dakai... Shiru tamkar mai nazari Mahmood yai hannunsa mai d’igan jini na dunk’ule yake furta “Waziri..!!” Waziri yai saurin mik’o masa jinjina yana mai amsawa... Mahmood yaci gaba da fad’in “Ina labarin neman Jafar da na wakiltaka.... Shin a ina aka tsaya...?!” Waziri ya had’iyi miyau da k’yar kana ya soma fad’in “Allah shi baka yawan rai, ai shi Bawa idan ya samu wata ‘yar k’ofar da zai tsere sam bazai tsaya gari kusa ba... Allah shi taimaki Saraki Babban Sarki a wannan daula tamu Jafar babu shi babu labarinsa... Babu hanyar da bamubi ba harta hanyoyin bincike na zamani dana gargajiya duk munbi amma shiru babu wani labari gameda Bawa Jafaru...!!” K’uri Mahmood yaima k’ofa yayinda Waziri yaci gaba da muzurai yana k’ok’arin had’iyi tuk’in goro da ya tsaya masa a mak’oshi... Bai kuma furta komai ba sai sa kai da yai ya fice daga parlorn hannayensa hard’e ta baya... Waziri yabi bayansa da kallo yana mai tofar da tuk’in goron dake bakinsa kaman ya bisa ya shak’esa... Lokaci guda yake sakin huci yana furta “Zamaninka mai k’aramin wa’adi ne Mahmooda... Zakabi zahun mahaifinka nan bada jimawa ba... Bazan tab’a bari jarumtarka na k’arya ya bani tsoro ba... Nayi Imani Sarki Yazeed sai yafika Jarumta dan ko a yanzu ma bazaka nuna masa komai ba...!!” Ya k’arshe yana mai sab’a babban garensa kana ya fice daga Masarautar cikin sauri dan a daren yau yakeso ya tura ‘yanta’adda zuwa gidan Wambai dan su zak’ulo masa k’undi koda kuwa a k’asan gini Wambai ya b’oye... *** A b’angaren Yarima Mahmood kuwa yana fitowa sashen Giwa ya nufa, kuyangi sai risinawa suke suna gaidasa had’ida basa hanya... Dik yanda ya shige kuwa jinin yankan hannunsa na nan na d’iga dukda cewa ya dunk’ule hannun sosai saidai abinka da yankan takobi ba k’aramin yanka bane.... B’angaren matakalan da zai sadaka da babban Parlorn Giwa ya nufa sai kuma yaja ya tsaya sakamakon sinkayo muryar d’iyarsa Zahra cikeda annashuwa... Haka kurum yaji yana so ya lek’a Zahra musamman da ya tuna tsawar da yai mata da kuma rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu for the first time dik akan Raheema da yau yaga true color d’inta... Gaba d’aya sai yaji kaman bai kyautawa d’iyar tasa ba dan shekaran jiya har kusan marinta yai dik sabida Raheema... Tsaye yai a bakin k’ofar d’akin Zahran yana hangosu d’aukeda littafi Muhibbah na fad’in “Wait Kinsan gwamnati Ta hana aikin banza dan haka idan na koya miki karatu nima zaki koya min yaren Spanish.. Do we have a deal..?!” Zahra ta jinjina mata kai cikeda raha harda d’aga mata babbar yatsa tana mai furta “Na yarda na amince bakida matsala... Kisa a ranki kin iya spanish an gama...!” Suka tafe hannaye a tare Muhibbah na fad’in “Wayaga Muhibbah na magana cikin harshen spanish... Aiko zanyi tsiyawasu Mummy idan na koma gida dan na daina masu magana da ko wane yare sai Spananci... Wait bari muga, mai zance idan inaso nace “Mummy I’m home..?” Kaman daga sama kafin Zahra ta bata amsa suka sinkayo muryarsa yana furta “Mami estoy en casa..!” Yana fad’in haka yasa kai zai juya saidai tuni sun hangosa, da alama maganar fito masa kurum yai baiyi niyya ba... Zahra ta mik’e da sauri ta rik’o hannunsa tana fad’in “Paa Tia mi Amiga tana koya min biology... Shigo ka gani, she’s very good in biology, so so amazing...!” Burki taiwa kalaman nata jin ta kamo danshin abu cikin hannunsa... Hankali tashe take duban hannun nasa tana mai furta “Paa you’re bleeding... Pa mai ya sameka... What happened to your hand..?!” Gaba d’aya ta rikice wanda hakan yasa Muhibbah ma saurin mik’ewa tsaye tana duban hannun nasa dake d’igan jini... Shafa kan Zahra yai da d’aya hannun yana furta “Is nothing serious princess... Just go and continue with your studies, I’ll be fine.. Okay....!” Girgiza kai take cikeda tashin hankali tana furta “No... No Paa, your wound needs to be treated... Please kashigo let’s clean it...!” Taci gaba da janyo Mahaifin nata cikin d’akin fuskarta fal damuwa take furta “Aunt Hibba please clean my father’s wound... Nasan fanninki ne dan Allah ki treating masa...You stay right here Paa let me go bring the first aid...!” Bata jira cewarsa ba ta barsa nan tsaye gaban Muhibbah suna fuskantar juna ta fice cikin sauri... Yanda sukai tsaye gaban juna ya haifar masu da shiga wane irin yanayi su duka biyun... A yayinda Mahmood ya tsareta da idanunsa ita kaw hannunsa mai ciwo kurum take duba yanda jini Ke zuba.. Batasan dalili ba amma ji tai Ta k’agu Zahra ta kawo first aid d’in ta rufe ciwon Mahmood ya daina zuban jini... Gani take tamkar jinin nasa k’arewa zai.... Jinin sai yanai ma idanunta gizo tamkar yana zuba ne gudu gudu d’aya na bin d’aya cikin sauri... Ji tai zuciyarta na furta “What’s taking you so long Zahra.. You need to hurry...!!” Bata ida tinaninba Ta hango Zahra ta shigo cikin sauri rungume da firstaid d’in... Cikin sauri ta isa ta amshe kit d’in saidai kuma koda ta amsa ji tai ta k’asa juyowa ta fuskancesa... Aima kamata yai Ta barsa jininsa ya k’are ya mutu.. Miye amfanin taimakawa mak’iyi....? Bata ida tinanin ba taji Zahra na janyo hannunta tana fad’in “Please Tia treat my Paa’s wound...!!” Tamkar Rak’umi da akala haka Muhibbah ke bin Zahra har ta duk’arta k’asa gaban Yarima Mahmood dake zaune saman gadon Zahra ya tsare Muhibbar da idanu tamkar mai karantar wani abu, ko k’yafta idanunsa baiyi sai duban fuskarta kurum yake wanda hakan ba k’aramin daburtar da Muhibbah yai ba... Batansan dalili ba amma duban da yake mata na matuk’ar tasiri cikin k’wakwalwarta harma da illahirin jikinta... Ta had’iyi zuciya da k’yar sanda Zahra tai alamawa mahaifinta ya mik’o hannunsa mai ciwon... Kaman bazai mik’a hannun ba har saida Muhibbah ta d’ago dara daran idanunta da rauni ya bayyana cikinsu lokaci guda tana mai dubansa... K’waya idanunsu suka had’e waje guda... Saurin sadda nata idanun tai yayinda Mahmood yai k’ok’arin mik’a hannunsa tamkar wanda ya tina wani abu.... Tabi hannun nasa da kallo Wai itace zata rufe masa ciwon lallai Zahra ta jefata a tsaka mai wuya... Ta yaya zata soma treating wound d’in babban mak’iyinta dan take dik abubuwan da suka faru da ita suka shiga dawo mata... Tsananin tsanarsa na buga zuciyarta da kwanyarta... Jin hannun Zahra tai a kafad’arta rana mai furta “Are you alright...?!” Muhibbah tai saurin daidaita kanta kana ta sakarwa Zahra murmushi tace “Yes let’s clean your father’s wound... Ungo karb’i wannan ki warware min a nitse...!” Ta k’arashe tana mai dank’a mata roll d’in bandage.... Babu musu Zahra ta amsa cikin sauri tana furta “Sure...!” Take ta somayi kaman yanda Muhibbah ta umarceta... Shi kaw Mahmood sai suka zame masa tamkar TV.. Sosai sukai masa kyau yanda suke gudanar da al’amaransu ya shagala sosai da kallonsu har saida yaji zogin shigan magani dake nad’e da cotton wool cikin ciwon... Ya d’an saki k’ara kad’an yana mai dunk’ule hannun nasa da zogi ya ratsa wanda tuni ashe ya had’e da hannunta.... Tamkar wacce aka zabura haka ta d’ago manyan idanunta tana dubansa k’irjinta naci gaba da bugu... Shid’inma ita yake duba fuska a matuk’ar d’aure da alama bai ma kulada abinda yai ba, duban da yake mata irin tamkar da gayya take zuba maganin cikin ciwon nasa... Itama d’in fuska a matuk’ar d’aure take dubansa tanajin yatsunta cikin hannunsa da yak’i saki..... SameenaAleeyou📚 [7/10, 9:16 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *031* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Koda Ubandoma yai rakiyawa Majidad’i zuwa bakin k’ofar Fada fincika Majidad’i yai ya shige motarsa yana ci gaba da fitar da huci.. Saidai ga tsananin mamakinsa yana shigewa cikin motar yai tozali da mutum zaune gefen mai zaman banza sai faman sakin murmushi yake... Shaye da tsananin mamaki Majidad’i yace “You..! Ya akai ka shige min mota...?!” Yazeed dake ci gaba da sakin murmushi yana shafa hab’arsa a hankali gyara zamansa yai yace “Ba wannan zaka tambayeni ba.. Kamata yai ka tambayeni mai ya shigo dani cikin motarka ba yanda akai na shigo ba.... But before that ci gaba da driving.. Let’s get out of here and talk somewhere else...Nida Kai munada abubuwa da dama da zamu tattauna akai...!!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa... Majidad’i da har lokacin mamaki bai sakesa ba dak’ik’ai ya kwashe yana duban Yazeed had’ida karantarsa kana ya finciki motar suka fice daga wajen gaba d’aya... *** Zahra Ke warware bandage d’in tana fad’in ashe dai zata iya aikin asibiti itama, sai faman zuba surutunta take da alama bama ta lura da abindake wakana tsakanin Babanta da Muhibbah ba... Tana gama warwarewa ta d’ago fuska tana mik’awa Muhibbah bandage d’in data warware “Here... Gashi nan na gama...!” Birki taiwa kalaman nata tana binsu da kallo, ta dubi wannan ta kuma duba wannan mamaki kwance saman fuskarta... Lokaci guda zuciyarta na ayyana mata wani abu, take taji murmushi na zuwa saman fuskarta... “Hello..!” Zahra ta furta tana dubansu su duka biyun... A d’an daburce Muhibbah tai saurin danna ragowar maganin dake rik’e hannunta cikin ciwon wanda ya sanya Mahmood saurin sakin hannunta yana mai yarfe hannun nasa cikin dakewa kaman bashine ya shagala da kallon nata ba... Muhibbah Ta wayance da fad’in “Oh sorry sorry Your Highness... Does it hurt..?!” Tai tambayar tana dubansa... Baice komai ba sai kauda fuskarsa da yai kad’an Zahra na fad’in ya mik’o hannun nasa a rufe masa ciwon... Saida ya dubi d’iyar tasa tamkar mai san yin magana sai kuma ya maidoda dubansaga Muhibbah dake k’ok’arin daidaita bandage d’in... Kana ganinta kasan ba daidai take ba, gaba d’aya ma hannunta rawa yake... Zahra ta tsare mahaifin nata da ido har lokacin sihirtaccen murmushi saman fuskarta, a hankali Ta furta “Paa.. Your hand...!” Ta k’arashe tanai masa nuni da cewa ya mik’o hannun... D’an sauk’e fuci yai a hankali kana ya mik’o hannun nasa a hankali tamkar mai tsoron mik’owa... Hannunta bai daina rawa ba sanda take k’ok’arin d’aura bandage d’in saman hannun Yarima Mahmood, ga k’irjinta dake ci gaba da bugu tamkar zai tsage... Addu’a kurum take Allah ya bata jarumta... Idanunsa k’yam akanta take rufe ciwon tana nannad’e hannun da bandage d’in cikin tsanaki dikda rawa da hannunta keyi... Saida ta gama lullub’e hannun da bandage tsaf kana ta d’ago idanunta masu alamun rauni tana dubansa, suka kuwa had’a ido... Tai saurin kaida fuskarta gefe tana fuzar da fuci a hankali... Zahra ta soma k’ok’arin tattara kit d’in saidai tuni Muhibbah ta amshe tana fad’in ta bari zatai, dan harga Allah ji tai tana Allah Allah ta tashi ta bar wajen... Batako jira amsar Zahra ba tuni ta soma tattare box d’in cikin tsananin sauri kana ta mik’e tana mai excusing kanta... A tare suka bitada kallo daga Mahmood d’in har Zahra kana Zahra Ta maido da dubantaga mahaifinta “She’s nice, isn’t she...?!” Ta fad’i tana duban mahaifinta... Jinjina mata kai yai a hankali har lokacin bazai iya cewa ga abinda yakeji cikin zuciyarsa ba... K’aran da wayar salularsa yai cikin aljihu ya dawo dashi daga duniyar tunaninda yai nisa... Yasa hannunsa maras ciwon ya ciro wayar cikin aljihu... Turaki ne mai kiran nasa... Cikin azama ya mik’e yana mai k’ok’arin k’ara wayar a kunnesa... Zahra tabi mahaifinta da kallo har ya fice, ita dai kam ta hango wani abu tsakanin Paa d’inta da Tia Hibbah, da ace hasashenta zai tabbata da sai tafi kowa Farin ciki... Amma tunawa da tai Paa ya canza akwai abinda yake b’oye mata sai taji jikinta gaba d’aya yai sanyi... Idan har zarginta akansa ya tabbata Toh kuwa Tia Hibbah bata cancanci miji irin mahaifinta ba, domin itad’in mutumiyar arziki ce ba kaman mahaifinta da takeda tarun shakku da kokonto akansa ba... Ta lumshe idanunta a hankali tana mai silalewa saman gado... ** A b’angaren Muhibbah tana ficewa bata zarce ko ina ba sai masauk’inta.... Tai zaune saman gado tana maida numfashi had’ida ajiyan zuciya d’aya na bin d’aya.... She shouldn’t have treated his wound... She should have let him bleed to death, it’s what he deserve after all.... Maiyasa bata k’yale shi jinin yaita kwaranya ba...?! Tai gajeren tsuka a hankali tana tina yau d’in taimako biyu taiwa Mahmood wanda duk bai cancanta ba... Na farko tsallake tuggun Raheema, sannan ga gyara masa hannunsa da tai... Tunanin abin sai yasa taji tamkar yanzu ne take rufe ciwon Mahmood, komai ya shiga zuwa mata daki daki tai saurin rintse idanunta da k’arfin gaske tana mai shafe fuskarta da duka tafukan hannayenta... Ware idanunta da zatai tai tozali da d’igon jinin Mahmood cikin tafin hannun nata... Tai K’uri tana duban drop na jinin da tuni ya bushe cikin tafin hannunta, k’irjinta bai daina bugu ba tai saurin fad’awa bathroom ta bud’ewa tafukan hannayenta ruwa tana mai gurje tafukan hannayen nata da k’arfin gaske tamkar zata cire fatarta... Saida ta d’ibi lokaci tana wanke hannun dikda jinin ya fice kana ta d’ibi ruwa cikin tafukan hannun nata ta wanke fuskarta har kusan sau uku, lokaci guda tai K’uri tana duban fuskarta cikin mirror... Ta janyo k’aramar towel Ta goge fuskar tata dashi kana ta nufo d’aki ta d’au wayarta lokaci guda tai dialing layin Ansar... Cikin sauri kuma ta katse kiran saidai tuni ya shiga, ta komo kan gado ta zauna tana tinanin toh ma mai zata soma ceda Ansar...? Ta kuma lumshe idanunta a hankali tana juya wayar cikin hannunta, kaman daga sama sai ganin kiran nasa tai.. Ta d’ago fuskar wayar tana duban sunan Ansar dake kira, kaman dai bazata d’aga ba sai kuma ta d’aga cikin kasaliyar murya.... Daga d’aya b’angaren Ansar ke amsa sallamarta yana mai tambayarta ko tana lafia, kaman dai Babu wani abinda ya faru haka nan yake amsa wayar... Cikeda borin kunya Muhibbah tace “Maiyasa ka kira..? The last time I checked fushi kake dani kuma kace bazaka sake kirana ba...!” Murmusawa yai kad’an kana yace “And last time I checked kece kika soma kirana... So tell me, what’s wrong this time...? Nasan haka kawai bazaki kirani ba, you must have a reason...Fad’a min What went wrong this time...?” Rausayar da idanu tai a hankali kana tace “Yanzu haka ka d’aukeni bazan kiraka ba saida dalili...? Ni ba kiranka nai ba... Idan kuma na kiraka bansan nayi ba..!” Ta k’arashe cikin fad’a... Ya kuma murmusawa a hankali kana yace “Alright fine... Naji baki kirani ba ni na kiraki sannan kuma ni na tambayeki Ki sanar dani abindake faruwa...Is there anything I can do to help..?!” Fuzar da huci tai a hankali kana tace “They wanted to do a background check on me...Ansar they were planning to have me investigated...!” A tak’aice Ta labarta masa tattaunawar Mahmood da Raheema dataji...Ta k’arashe tana mai dafe goshinta da hannu guda... Kaman wanda yake ganinta yace da ita “Just calm down and take a deep breath..! As long as ina taredake bazan bari susan ko ke wacece ba... Karki damu kinji, just leave that to me, I would take care of that...abinda kawai nakeso dake shine kici gaba da kula, karki basu wata k’ofa da zasu fahimci ko ke wacece kinji koh...” Ta jinjina masa kai a hankali “In sha Allah... Bazan basu ba... Thank you Dr, thank you for always having my back..!” Suna gama waya da Ansar tura file d’in gabansa yai yana d’an dukan kansa da pen, baida lokacin tsayuwa yin fad’a ko fushi da Muhibbah... Yafi kowa Allah Allah ta gama wannan mission d’in nata ta dawo ai maganar aurensu once and for all... Dole yai hak’uri da dik wani fushi da fad’a ya aje komai a gefe ya taimaka mata ta ida wannan so called mission d’in nata dan idan ba haka ba the more yana biyeta sunayin fad’a the more yawan lokacinda zatai zaune cikin Masarautar yana k’aruwa... Ya kuma fuzar da fuci a hankali yana mai bada izini ma patient na gaba da ya shigo... *** A b’angaren Muhibbah kaw zuciyarta ne yai wasai dan tasan Ansar zai toshe dik wani k’ofardasu Raheema zasubi a makaranta su gano asalinta, yanzu abinda ya rage mata shine tai monitoring duk wani move nasu Raheema idanma son samu ne ta shige jikinsu ta samu yardarsu dukda tasan hakan abu ne mai matuk’ar wuya tinda tin farkon had’uwarsu babu jituwa sam tsakaninsu musamman dashike Raheema gani take tamkar Ta shigo Masarautar ne dan Ta k’wace mata masoyinta Yarima Mahmood.. Dan haka shiga jikin Raheema zai matuk’ar mata wahala... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai kuma sak’e sak’e cikin zuciyarta had’ida neman mafita... ** A cen parlorn Mahmood kuwa tsaye yai yana duban Turaki hannayensa hard’e ta baya... Saida ya kuma takowa kad’an kana yaja ya tsaya “Turaki bana shakkan su fahimci cewa ni ne bak’on Buzu... Abu guda da zaisa bazan bayyana masu kaina a matsayin bak’on Buzu ba shine nima akwai abinda nake bincike cikin gidan sannan Ina akwai abinda nake son fahimta gameda ciwon Baba Wambai... Idan har da gaske akwai wani abinda Baba Wambai ya sani gameda abubuwan da suka jima suna faruwa a gidan nan Kaga babu makawa za’a nemi a b’addashi Ta ko wacce hanya ko kuma a hansa yin magana.. Everything is possible a gidan nan, zasu iyayin komai to silent him dan asirinsu ya rufu...So kaga dole na k’ara taka tsantsan hardai inaso na sami amsoshin da na jima Ina nema...!” Jinjina kai Turai yai a hankali yace “Wannan gaskiya ne Your Highness... Toh yanzu mai kake shiryawa...?” D’an dubansa da wutsiyar idanu Mahmood yai kana ya kauda fuskarsa kad’an “Lokaci zai sanar damu...!” Ya fad’i yana mai zama cikin kujera... Turaki yai ma abokin nasa k’uri kana yace “Toh shi Majidad’i fah... Ya zakai dashi... I’m sure he won’t stop tunda ya soma kutso Kai cikin Fada d’aukeda makami... Sannan na tabbata a shirye yake sosai...!” Ba tareda ya dubesa ba yake furta “Zan k’yalesa yaci gaba da bincikensa... In the process na bincikensa zai iya samomin wani abu da zai min amfani a binciken da nake, wannan na d’aya daga cikin dalilin da yasa nace a k’yalesa... Is possible someone has been monitoring my every move all this time... Ta yuwu akwai wanda yasan cewa nine bak’on Buzu saidai bazai iya fitowa ya fad’i ba dan shima mafita yake nema ma kansa...Ta yuwu ya fahimci ina gab da tono gaskiya shine bari ya rufe bakin Baba Wambai ta wannan hanya.... But koma menene I’d make sure to be one step ahead of them...!” Ya k’arashe yana mai duban Turakin.... Turaki ya murmusa kad’an cikeda jin dad’i yana mai jinjina kai lokaci guda yake ci gaba da yabawa zurfin tunanin abokin nasa... Tabbas ya yarda Mahmood zai zak’ulo duk wanda sukeda hannu cikin manak’isar wannan gida.... Yarima Mahmood ya d’auki glass cup dake aje gefensa na dama saman k’aramar table dake tsakankanin kujeru ya kurb’a, har lokacin k’uri yaima waje guda yana mai murza bandage d’in dake d’aure hannunsa... Soma murza bandage d’in Keda wuya tinaninta ya fad’o zuciyarsa... Take ya soma tina duk abubuwan da suka faru daki daki, sanda take goge masa ciwon da kuma sanda take rufe tafin hannun nasa da bandeji... For the first time da ya saki murmushi tun bayan abubuwan nan dake kan faruwa... Turaki yai masa K’uri ganin ya k’urama waje guda idanu yana sakin sihirtaccen murmushi mai taushi wanda saika kula ka fahimci hakan... Sallaman Ubandoma ya dawo dashi daga duniyar tinanin da yai nisa ciki... Ubandoma ya zube yana kwasan gaisuwa, nan yake sanarda Yarima Mahmood Giwa tayi Aiken Jakadiya cewa tana san ganin Yarima... Jinjina masa kai yai alamun amsawa... Turaki ne ya soma ya soma mik’ewa sukai sallama kana suka jera a tare suka fito... Suka tsaya nan cikin haraban sashen Mahmood d’in... Yarima Mahmoood yaci gaba da fad’in “Wani aiki nakeso kamin Turaki...!” Turaki ya jinjina kai “Duk abinda mai Martaba yace...!” Jinjina kai Mahmood d’inma yai had’ida yin gyaran murya kad’an “Ja’afar...!” Turaki ya dubesa da mamaki yana jiran yaji mai Mahmood d’in zai d’aura... “Turaki I want you to hire a private detective wanda zai mana bincike akan where about d’in Jafar, dik yanda Ja’afar ya shiga ya fita inaso a samoshi... Can you do that..?!” Turaki ya jinjina kai “Of course your Highness, leave it to me... I can handle that Rankaidad’e..!” Jinjina kai Mahmood ya kuma yi kana sukai masabaha had’ida sallama Turaki na fad’in sai yaji daga garesa... Kallo guda zakai mata ka fahimci tana cikin tsananin tashin hankali.. Aiko Mahmood na shigowa Giwa ta k’araso garesa tana mai janyo hannunsa mai ciwo take fad’in “Sadauki lafia kake... Shin ta yaya wannan mahaukacin yaron zai shigo har cikin gidan nan yai mana wannan wulak’ancin... Toh wannan masarauta bazata lamunta ba, ya zama dole a hukuntasa...!” Ta k’arashe cikin tsananin huci cikeda tashin hankali... Kafad’unta Mahmood ya kamo ya zauanrta saman cushion a hankali lokaci guda yake furta “Take it easy Maami, ki kwantar da hankalinki banaso kina saka irin wad’Annan abubuwan a zuciyarki...!” Giwa ta d’an marairaice fuska tace “Shikenan sai in zuba idanu su sakaka gaba... Kaima kasan bazan iya hakanba Sadauki...!” Ta k’arashe cikeda kulawa... Nusawa kad’an yai yace “Maami a gida irin namu dole mu saba da irin wad’ann abubuwan so ba wani abu bane In sha Allah...!” Ta mik’e daga zaunen da take tana mai karantarsa, a hankali take zagaya d’akin har ta k’araso gabansa ta tsaya “Sadauki... Maiyasa kak’i amsar Sarauta...?” “Maami inada manufata da shirina...!” Ya fad’i kansa tsaye... Giwa ta had’iyi miyau da k’yar zatai magana kenan Jamal ya shigo da sallama... Dubansu yake da alamun tambaya saman fuskarsa dan tuni ya karanci halinda mahaifiyarsu Ke ciki...Shid’in ya santa sosai wanda idan tana cikin tashin hankali zai iya fad’i haka idan tana cikin Farin ciki da annashuwa zai iya fad’i... Shid’in yasan ko wane motsi na Mahaifiyarsu... Jamal na shigowa Mahmood yai sallamada Giwa ya fice... Sukabi bayansa da kallo har ya b’ace masu daga ita har Jamal... Yarima Mahmood na ficewa Jamal ya k’araso da sauri yana tambayarta meke faruwa Giwa ta k’arasa ta zauna saman kujeranta na alfarma “Gwarzo..!” Ta ambato sunan Jamal cikin kakkausan Murya... Ya k’araso ya duk’a gabanta yana dubanta cikeda kulawa “Inaso kaja hankalin d’an Uwanka Mahmood ya amince ya amshi sarautar nan idan ba haka ba munaji muna gani sarautar nan zata kubce daga gidan nan duk abubuwan da muka jima munayi zai tashi a banza, zamu fice daga gidan nan cikin k’ask’anci da tozarci... Nasan bazakaso haka ba d’ah na...!” Ta k’arashe tana aika masa wani irin duba... A hankali ya shiga jinjina kansa “Maami Karki damu zanyi duk yanda zanyi Yaya ya amince ya amshi sarautar nan... Bayan abinda ya faru yau cikin Fada ya zama dole Yaya ya amshi sarautar nan ko dan ya kare Martaban Ahalinmu a kuma gidanmu...!” Giwa ta jinjina kai su duka biyun suna masu duban juna... *** Tafiya mai nisa Majidad’i yai tamkar masu barin gari, saida sukeje wajen gari yanda babu mutane sosai yaja yai parking... Ya kaikaito yana duban Yazeed dake zaune gefensa... “Ina saurarenka, mai kake nema wajena kana jinin AbdulJabbar...?!” Murmusawa kad’an Yazeed yai “Abinda kake nema shi nake nema... The THRONE...!!” Majidad’i ya dubesa da mamaki, lokaci guda ya saki murmushin rainin hankali “Toh mai kakeso nai maka..? Ai d’anuwanka Mahmood ya kamata kaje ka samu da wannan batu amma bani ba...!” Murmusawa Yazeed ya kumayi yana mai gyara zamansa cikin kujeran “Kana tunanin nida kai zamu samu sarautar ne muddin Mahmood na tsakani...?” D’an rage girman idanunsa Majidad’i yai yana mai girgiza kai “Ban fahimceka ba... Go straight to the point...!” Yazeed ya shafa hab’arsa kad’an “Abu guda nake nufi muyi tarayya akai dan cikar burinmu...Let’s take my brother down....!!” Yai maganar yana tsare Majidad’i da idanu shu’umin murmushin bai bar saman fuskarsa ba... SameenaAleeyou📚 [7/12, 4:21 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *032* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Bazawarin murmushi Majidad’i yai a karo na biyu, ya kuma gyara zamarsa sosai yana duban Yazeed da ya kafesa da idanu babu alamun wasa a tattaredashi... “Ni zaka rainawa hankali...? So kake kai amfani dani wajen cimma burinka...? Kai d’in kana tinanin ni zan barka kai amfani dani ne... Har abada bazan tab’a amincewa da wani cikin zuri’ar AbdulJabbar ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Shu’umin murmushi Yazeed ya kumayi a karo na babu adadi “A cikin wannan battle d’in you need me more than I need you, zan maka amfani fiyeda yanda zaka min... Kasan ance da d’an gari akanci gari.. Bazaka tab’a samun Karagar nan ba ba tareda taimakon d’aya daga cikin ahalin AbdulJabbar ba... Idan baka amince min ba haka Kanajina kana gani sarauta bazata tab’a komawa gidanku ba, Idan Yayana Mahmood ya gama zamaninsa ni ne nan zan amshi mulkin ba kaiba haka idan na gama Magaji na d’ah na ko d’aya daga cikin k’annena shi zai amshi mulkin... Kaman Yanda Baba Wambai ya tsufa bai gaji gidansu ba tarihin abinda ya faru dashi zai kuma maimaita kanshi akanka kaga har abada jininku bazasu kuma samun wannan sarauta ba... Amma idan ka amince min muka had’a k’arfi da k’arfe muka yak’i Mahmood yak’in neman sarautar zai tsaya ne tsakanin mu biyu... Ni da kuma Kai...!” Ya d’anyi fasali yana duban Majidad’i da tuni ya apka tarkonsa, ya kuma sakin murmushin nasa kana ya mik’a hannu ya d’auki takobin Majidad’i da hannu guda ya d’agata sama yana juyata a hankali yake k’are mata kallo lokaci guda yake ci gaba da sakin murmushi yana furta “Takobi zai maye gurbin Mahmood a tsakaninmu... Domin kuwa shi ne zai fitar da Jarumi cikin mu biyun...Takobi shi zai raba gardama a tsakaninmu sannan ya tantance Jarumi cikinmu...Shi zai tantance waye ya dace da rik’on Sarautar wannan Masarauta...!!!” Ya k’arashe yana mai d’ora bakin takwabin a saitin wuyar Majidad’i murmushin bai bar saman fuskarsa ba... Murmushi Majidad’in ma yai kana yace “Kana tinanin zaka iya karawa dani...?!” Hab’ar Majidad’i kad’an Yazeed ya kama daidai sanda yake Yawo da makamin a saitin wuyar Majidad’in, lokaci guda yake furta “Babu alamun ragwanci ga mutuminda ya nuna abokin karawansa da makami har yai nasaran saita makamin a mak’oshinsa... I can cut your throat right this instant amma bazanyi hakan ba dan nafi so mu kara a filin daga yanda babu Dakarun da zasu kawo mana d’auki... Takwabi ce kad’ai zatai magana a tsakaninmu...!” Ya k’arashe yana mai cire takobin daga wuyan Majidad’i... Wani murmushi renin hankali Majidad’i yai yana mai jinjina kai “Finally jinin AbdulJabbar mai tinani irin nawa... Jarumi shi ya cancanci sarautar wannan masarauta namu, kaman yanda kace Takobi zata raba gardama tsakaninmu a filin daga... Zamu dawo da tsohon Al’adun kakaninmu wanda Jarumi kad’ai Ke yin Sarauta.... Naji dad’in wannan shawari naka Yarima Yazeed... Toh amma wani hanzari ba gudu ba... Shin kana tunanin Masarauta zata amince ta dawo da Al’adar da aka jima da banning d’inta, Al’adar da aka jima da kasheta a wannan masarauta tamu...?!” Gajeren murmushi Yazeed yai “Kadai muyi k’ok’arin kawar da Mahmood a tsakani duk abinda zaizo daga baya mai sauk’i ne.... Partners..?!” Ya k’arashe yana mai mik’a masa hannu alamun musabaha.... Majidad’i ya mik’o masa hannu sukai masabaha yana mai jinjina kai yake furta “Partners..!!” Daga nan sallama sukai da Yazeed yanda Yazeed d’in ya kirawo abokinsa Zayyad yazo ya d’aukesa dan tuni Majidad’i yayi tafiyarsa bazasuso a gansu tare ba... Zayyad na k’arasowa da mamaki yake duban Yazeed sanda ya bud’e marfin mota ya shige “Rankaidad’e Wai mai ya faru ne... What really happened... Why are you here all alone... Ina motarka, Ina Hadiminka...?!” Ko tambaya guda Yazeed bai amsa ba sai ci gaba da sakin murmushi da yake lokaci guda yake furta “I’ll soon get rid of one of my major problems...!” Ya k’arashe yana sakin murmushin nan nasa.... Zayyad da tuni ya soma driving murmusawa yai kad’an yana furta “WOW! This calls for celebration Your Highness... Fad’a min ina zamuje muyi celebrating...?!” D’an dubansa da wutsiyar idanu Yazeed yai ba tareda yace komai ba... Zayyad yaci gaba da fad’in “I guess ka sami kan yarinyar nan ne dataci maka mutunci ko kuma ka samo hanyar da zakai ka fitar da Mahmood daga masarauta...!” Dubansa da wutsiyar idanu kana yace “Abokina na yarda ka sanni sosai yanzu kam... Idan na zama sarki komai mai yuwa ne sannan ne zan rama abinda tai min don bataci banza ba... No one messes with Prince Yazeed AbdulJabbar..!” Ya k’arashe yana sakin murmushi sanda yake tuna kalan wulak’ancin da zaiwa Muhibbah muddin ya zamto Sarki... Sai ta gwammaci dama batazo duniya ba da irin wulak’ancin da ya tanadar mata... Zayyad na tambayarsa destination ko answer sa bai ba sai sakin murmushin mugunta da yake ci gaba da yi a hankali.... Sanin Yazeed d’in bazai amsasa ba ya sanyashi yin shiru da bakinsa ya nufi shisha spot d’insu da suka saba zuwa... ** Waziri ya gama had’a kan ‘yandabansa cikin dare ya basu umarnin su shiga Gidan Wambai su nemo k’undin nan yanda ya shiga ya fita, idan ta kama su tone k’asan gidan ne su tone su ciro masa k’undin nan duk yanda za’ai.... Ya kwance bakin rawaninsa ya nunawa shugaban exactly kalan jakar fata da k’undin ke ciki Wanda zasu d’auko masa.... Shugaban ‘yandaban ya amsa ya juyata ya k’are mata kallo kana ya risina yace “An gama mai girma Waziri... Idan cikin tandu take sai an d’auko maka ita...!!” Waziri yace “Yauwa haka nake sonji... Kuyi dik yanda zakuyi ku d’auko min wannan jaka sannan Koda wasa kar ku bari a kamaku, kuma kada ku bar wata alama da zata nuna cewa Waziri ne ya turoku...!” Suka jinjina kai suna masu furta an gama Mai Girma Waziri..! Ubandoma dake lab’e bayansu murmushi yai dan yasan tinda wad’annan ‘yandaba ba ma’abota sarauta bane bazasu fahimci yanda Wambai zai aje wannan k’undi cikin sauk’i ba, dan haka zai k’yalesu su gama dube dubensu har su fice sannan ya shiga ya d’auko k’undin cikin tsanaki yakaiwa Giwa da sharad’in mallaka masa ‘yanci...! Ya saki murmushi yana mai gyara zaman layarsa da zai danna dan ya b’ace da zaran yaji alamun za’a kamasa... Hakan ce kuwa ta kasance tuni ‘yandaban Waziri sun isa gidan Wambai Ubandoma na biye dasu ba tareda saninsu ba.... Gidan babu kowa sai ma’aikata, ba tareda b’ata lokaci ba suka kame ma’aikatan gaba d’aya suka d’auresu suka kullesu a nan D’akin Maigadi... Tuni suka shiga suka soma bincikensu... Sun kwashe kusan awanni biyu suna wannan bincike babu k’undi babu alamunsa... Haka suka wargaza gidan gaba d’aya sukai d’add’aya da komai amma babu k’undi babu alamun k’undi... K’arshe haka suka hak’ura suka fice, ogansu ya kirawo Waziri yana mai sanar dashi Rashin sa’an da sukai... Suna ficewa shi kuwa Ubandoma ya shigo ya soma nasa binciken musamman da yaji basu dace ba... Waziri ya sanar da shugaban ‘yandaban nasa da suyi maza su fice daga gidan kafin azo a kamasu, daga nan Fada ya nufa wajen Giwa dan dole taji wannan batu cewa dik yanda akai Bak’on Buzu ya rigasu isa wajen Wambai, ya tabbata wannan mutumi bak’on Buzun shine ya amshe k’undin nan daga wajen Wambai.. Ya zama dole su zak’ulo waye Bak’on Buzu kafin Mahmood ya rigasu sanin ko wanene Bak’on Buzu....!! Majidad’i yasha mamaki sanda ya shigo gidan Mahaifinsa ya tadda mai gadi da ma’aikata rufe nan d’akin Maigadin sunsha d’auri... Take tunanin Bak’on Buzu ya fad’o masa... Babu shiri ko takan mai gadin da ma’aikatan baibi ba ya fad’a cikin gidan a guje, yasan duk wanda ya shigo gidan ba b’arawon gaske bane akwai abinda ake nema ne wajen mahaifinsa kuma ta haka ne kawai zai capke wanda keda alhakin ciwon mahaifinsa....! Ya zaro takobinsa ya nufi cikin gidan cikin sand’a... Ubandoma dake faman bincike kaman b’era sai k’wak’ule k’wak’ulen rami yake sam bai aune da shigowar mutum ba sai jin sauk’ar takobi yayi a wuyarsa ana furta “Mik’e ka nuna fuskarka..!!!” Muryar Majidad’i ya daki dodon kunnuwansa... Take jikin Ubandoma ya d’auki rawa, karkarwa kurum jikinsa keyi ga gumi dake keto masa... Ya kasa tashi ya kasa d’ago fuskarsa da tuni ya jik’e da gumi... Majidad’i ya capko wuyarsa da k’arfin gaske yana k’ok’arin d’agosa.. Daidai wannan lokaci Ubandoma ke kokawan danna layarsa saidai ga tsananin mamakinsa ko gizau layar tak’i dannuwa.... Majidad’i ya kwashe da muguwar dariya sanda layar ta fad’i k’asa... K’afa yasa ya shura layar yana fad’in “Kana tunanin laya tana tasiri a wannan gidan ne... Ai bari kaji ba Fada bane kawai takeda shiri ko wane gida nada nasa shirin... K’aramin munafuki tashi ka nuna kanka kuma ka fad’i waye Ubangidanka..!!” Ya k’arashe maganar yana mai fincike rawanin Ubandoma... Take fuskar Ubandoma ya bayyana gumi sai tsartsafo masa yake... Baki sake Majidad’i Ke dubansa “Kai..!!! Kaine kenan... Kaine Bak’on Buzu...!!!” Cikin rawar murya Ubandoma Ke fad’in “Allah shi taimakeka wllhi bani bane... Wllhi banida masaniya sahub b’arawo na taka kamin rai dan Allah..!” Baikai aya ba Majidad’i ya kwahesa da wata irin jahilar mari wanda ya sanya Ubandoma zubewa k’asa yana mai ci gaba da rantsuwa yana fad’in bashi bane Bak’on Buzu baida masaniya kan Bak’on Buzu.... Damk’o wuyarsa Majidad’i yai yana fad’in “Ka shiga hannu kuma kenan ai... Sai ka sanar dani Ubanda kakema aiki...!!” Ubandoma yaci gaba da magiya yana fad’in ai masa rai baisan komai ba... ** A cen Fada kuwa hankulan Giwa da Waziri ne yakai k’ololuwa wajen tashi... Giwa bataga Ta zama ba, tabbas akwai wanda Taguwarsa tafi tasu Gudu cikin Masarautar ya zama dole a yau d’in ta gana da Tal’udu duk yanda za’ai... Wannan mummunan labari da Waziri ya kawo mata ba k’aramin barazana bane a gareta... Waziri na tafiya Giwa da Jakadiya sukai shirin zuwa ganin Tal’udu... Giwa tai zaune saman jar dardumanta mai d’aukeda tambarin masarauta na tsafi... Jim kad’an guguwa ya kaure mai cikeda jan hayak’i, nan take Tal’udu ya bayyana cikin shigarsa maras kyaun gani.... Yana fitowa Giwa ta kifa kanta alamun gaisuwa, tinda taga jan guguwa tasan yau ba kanta, tashin hankali ne take fuskanta... “Turai kinyi kuskure..!” Tal’udu ya fad’i cikin tsananin huci... Giwa Ta shiga girgiza kai tana fad’in “Babu laifina ko guda Uban tsafi... Na tabbata wani ne da yasan da batun K’undin nan ya rigamu isaga Wambai... Amma yanzu so nake ka duba min mai fitilar tsafi ta hasko maka gameda wannan K’undi... Shin ina k’undin yake a halin yanzu...?” Cikin tsananin b’acin rai ya buga jan sandar dake hannunsa, lokaci guda yake furta “Har abada K’undin nan bazai tab’a dawowa hannunki ba Turai... Kin riga da kin tapka kuskure... Kuma iyaka abinda fitilar tsafi Ta hasko mana shine K’undin zaiyi nisan tafiya har ya isaga wannan yarinya SAUDATU... Ita kad’aice zata iya bud’e wannan k’undi domin idan baki mance ba K’ADDARAR MASARAUTAR nan yana ratayene a wuyarta... Da ace yaranki sunyi nasaran kasheta tun a wancan lokacin k’ila da K’addarar Ta iya sauyawa... Barinta a raye yafi muni fiyeda rashin tarewa da banyi da ita ba.... Turai kina cikin had’ari muddin baki nemo Saudatu yanda Ta shiga Ta fice ba...!!” Ya k’arashe yana mai kuma dukan k’asa da sandar hannunsa... Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana.... A ina Saudatu take... A wane duniya Ta b’uya da har Tal’udu ya kasa gano yanda take rayuwa... Tabbas ya zama dole duk nisan duniyar data tafi ta nemo ta... Har abada bazata bari wulak’antacciya irin wannan yarinyar tayi sanadin mulkinta da duk wani Farin ciki nata ba... Ta d’ago idanunta da sukai jazir tana duban Tal’udu “A ina zan samo Saudatu Uban tsafi...?!” Gashin girarsa guda d’aya ya tsinko ya aza saman tafin hannunsa yaceda Giwa matso nan ki gani... Babu musu ta matsa kusa tana Ware idanunta sosai... Ga tsananin mamakinta tsillin gashin taga ya kama da wuta yanaci sosai baka iya ganin komai sai bak’in hayak’i... Tal’udu yaci gaba da fad’in “Yanda wannan wuta Ke ruruwa baki iya ganin alamun tsillin gashin nan Toh haka Saudatu zata k’ona rayuwarki ba tareda kin iya ganin koda alamunta ba....!!” Giwa ta had’iyi miyau cikeda fargaba da kuma tashin hankali... Take ta kuma d’agowa tana duban Tal’udu.... Da tuni ya soma sakin murmushi... Lokaci guda yaci gaba da furta “Saidai akwai mutum d’aya wacce tasan yanda Saudatu take... Shiyasa na fad’a miki har abada bazaki iya kasheta ba domin itace kad’ai zata iya sanar dake yanda SAUDATU take... Ko ni ban sani ba amma ita d’in ta sani...!!” Giwa da tai masa K’uri tun bai kai aya ba Ta furta “IZZATU..!!” Tal’udu ya kuma murmusawa yace “K’warai kuwa Izzatu ce kad’ai tasan Duniyar da Saudatu Ke rayuwa a halin yanzu... Izzatu ce kad’ai makaminki na k’arahe akan wannan yarinya Saudatu... Wannan na d’aya daga cikin dalilin da yasa na hanaki kashe Izzatu, domin ita kad’aice fitilar tsafi ke hasko min a duk lokacin da na soma bincike kan Saudatu, hakan na nuni da cewa itace zatai maki jagoranci har ki isaga Saudatu...Lokacin da Izzatu zatai maki amfani yazo Turai..!!!” Yana ida fad’in haka guguwa ya kaure b’at ya b’ace daga cikin d’akin... Tashin hankali wanda baa saka masa rana, waige waige Giwa ta soma tana kiran sunan Tal’udu lokaci guda take furta “Ta yaya matar da bata cikin hankalinta zata sanar dani wani gameda Saudatu..? Ta ya zan sami wasu amsoshi daga wajen matar da babu hankali a tattareda ita...? Ta yaya matar da babu harshe cikin bakinta zata iyayin magana..?!! Tal’uduuu...?!!” Ta k’arashe tana mai k’walla masa kira amma saidai babu Tal’udu babu alamunsa.... Giwa ta sauk’e nannuyan ajiyan zuciya kana ta mik’e ta nufo waje... Tai k’uri ma wannan d’akin da kullum yake nan a bud’e... D’akin da ya kamata ace Saudatu ke rayuwa ciki tareda Tal’udu... Tana ficewa daga cikin gidan Tal’udu ta tadda Jakadiya na jiranta... Jakadiya tace da ita “Allah shi taimakeki ina muka nufa....?!” Giwa ta kuma gyara bak’ar Alkyabbarta Ta rufe fuskarta sosai kana taceda Jakadiya “Wajen Izzatu muka nufa... Kiyi min kiran Ubandoma...!!” Daga haka sa kai tai Ta wuce cikin sauri Jakadiya na fad’in “An gama Allah shi baki yawan rai...!!” Take Jakadiya ta soma neman layin Ubandoma... Muhibbah dake zaune haraban masauk’inta tana duba wani k’aramin littafi na addu’o’i lokaci guda tana karanta sak’onnin soyayya da Fu’ad ke Aiko mata tana sakin tsuka a hankali nan ta hangi alamun giftawan mutane cikin wane irin sauri tamkar zasu tashi sama... Ai take taji koma su wanene tana son ganin yanda suka nufa... Babu shiri ta mik’e ta gyara rufin kanta sannan ta fito cikin sand’a tabi hanyar da taga sunbi.... SameenaAleeyou 📚 [7/14, 7:36 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *033* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin tsananin rud’ani da tashin hankali Giwa Ke duban Jakadiya “Jakadiya ban fahimceki ba.... Mai kike cewa...?!” Jakadiya Ta kuma risinawa “Allah shi baki yawan rai kaman yanda kikaji na fad’i ba Ubandoma bane ya amsa kiran kuma ga dukkan alamu Uabdoma yana cikin had’arin gaske, dan wannan murya da naji cikin wayar salulan ba k’aramin tada min hankali yai ba Allah shi taimakeki...!” Ta k’arashe tana mai kuma sadda Kai... Giwa ta fuzar da fuci kana tace “Shige ki bud’e mamu k’ofar...!” Babu musu Jakadiya ta isa ta bud’e k’ofar da yake mai nauyin gaske, da k’yar take iya jan k’ofar... Koda gani wannan dadd’en gini ne mai matuk’ar k’argo da aminci... Muhibbah dake gefe a lab’e tai K’uri tana dubansu har suka shige cikin d’akin... A hankali ta sad’ad’o ta k’araso had’ida rakub’ewa tsakankanin tapkeken k’ofar da yake mai kunnuwa biyu, tana iya hango Giwa da Jakadiya Ta tsakankanin ramin k’ofar yanda sukai tsaye gaban mahaukaciyar matar nan dake d’aure da manyan sark’ok’i.... Matar tana ganin Giwa sai ta soma k’ok’arin fincika tana san sance d’aurinda aka mata... Ita kad’ai sai fincika take tamkar zatayo kansu... Dama Ubandoma ke bugunta idan tai yunk’urin kaiwa Giwa damk’a gashi yau babu Ubandoma... Jakadiya ce Tai ta maza ta janyo k’atoton dutsin dake gefe ta aza saman k’afafun mahaukaciyar wanda ya sanyata sakin k’aran azaba... sai kuma ta koma tai lak’was tana fidda numfashi a hankali sabida tsananin azaban nauyin dutsen da takeji saman k’afafunta... Giwa Ta sami zarafin k’arasowa cikeda k’asaita... Lokaci guda Ta umarci Jakadiya data baza mata mayafinta Ta zauna bisa... Jakadiya ta d’an dubeta da mamaki kana tace “Allah shi baki yawan rai zama a wannan k’ask’antaccen waje mai cikeda k’azanta da k’ask’asanci bai kamaceki ba...!” Batakai aya ba Giwa Ta katseta cikin tsananin daka tsawa “Jakadiya har yaushe kika fara sa’insa dani... Umarni nake baki ba shawarinki nake nema ba...!!” Babu shiri Jakadiya ta risina “Tuba nake ya Shugabata... Allah ya huci zuciyar Sarauniya tilo d’aya a Masarautar nan...!!” Ta k’arshe tana mai yaye mayafin kanta kana Ta baza ma Giwa a nan gaban mahaukaciya Izzatu... Giwa Ta tako Ta zauna irin zaman da masu mulki keyi kana tai k’urima Izzatu... Daga yanda Muhibbah ke tsaye bata iya sauraron abinda suke fad’i dan d’akin nada matuk’ar zurfin gaske abinka da gini irin na gidan sarauta da ya kwashe shekaru aru aru, gashi dai tana iya hangensu da duk wani motsin da suke amma bata iya sauraren abubuwan da suke fad’i duk kalan kasa kunnuwan da tai kaw... Ga kukan hadari dake k’aruwa wanda ya dad’a taimakawa wajen hanata auraron abinda suke fad’i... Giwa takai hannunta guda cikin tsananin b’acin rai ta damk’o wuyar Izzatu, kana iya ganin yanda jiniyoyin hannunta sukai rud’u rud’u sabida tsananin b’acin rai “Izzatu kinyi kad’an kiga baya mulki na... Ke k’ask’antacciya ki bud’e baki ki sanar dani wace duniya kika b’oye Saudatu..?!!” Giwa Ta k’arashe tana mai kuma matse wuyan Izzatu da tuni Ta soma k’ak’arin amai sabida tsananin rik’onda Giwa tai mata..!! Jakadiya gaba d’aya Ta razana ganin Giwa na shirin aika Izzatu lahira gashi Tal’udu ya sanar da ita cewa idan har tana k’aunar zaman lafiyarta toh bazata kashe Izzatu ba...! Tuni Jakadiya ta zube tana dannan zuciyar Giwa kafin da k’yar Giwa ta sararawa Izzatu... Giwa Ta kuma jefa mata tambayar Ina Saudatu...? Saidai abinka da mai tab’in hankali dariya Izzatu ta kuma fashe masu dashi tana mai furta wani magana da yafi kama da gwalamniya kasancewar babu harshe cikin bakinta... Giwa ta sauk’e nannuyan ajiyan zuciya, lallai akwai aiki ja a gabanta idan har za’ace mahaukaciya kuma bebiya ce zata sanar da ita duniyarda Saudatu ke rayuwa... Wannan wane irin al’amari ne...? Bata tab’a zaton Izzatu zata zamto mata k’adangaren bakin tulu ba... Ta yaya za’a ce sa’arta na tareda Izzatu... Ta sauk’e fuci a hankali sanda Jakadiya ke furta “Allah shi baki yawan rai inaga mu k’yaleta haka nan na yau kuma har sai zuwa wani lokaci... Inaga da kad’an da kad’an idan muna bijiro mata da zancen har Allah zaisa mu dace ta bud’i baki ta sanar damu...!” Ta k’arashe tana mai kuma k’ank’an da kai gaban Giwa... Badon Giwa taso ba Ta mik’e tana mai ci gaba da duban Izzatu dake sakin murmushi cikin yanayin fuskarta da ya cika da datti da kuma daud’a.... Duban Jakadiya Giwa tai ta mata alama da cewa su fice... Babu musu Jakadiya tabi umarnin uwar gijiyarta... Sam Muhibbah bata ankara dasu Giwa da tuni sun nufo k’ofa gadan gadan ba, hankalinta da tinaninta yayi nisa wajen tunanin shin wacece wannan mahaukaciyar, maiyasa Giwa ta ajeta a wannan sunk’urumin d’akin sannan mai take zuwa yi wajen wannan mahaukaciya... Ya kamata tasan wacece wannan mahaukaciyar.... Kaman daga sama taji alamun tab’a k’ofa babu shiri tai saurin komawa da baya k’irjinta naci gaba da bugu... Giwa ce ta d’anja ta tsaya sanda taji tamkar akwai alamun mutum a wajen... Jakadiya ta d’ago tana dubanta, lokaci guda Giwa ke furta “Jakadiya, kin tabatta mu biyu ne a wajen nan bamuda wani d’an rakiya...?” Jakadiya Ta waiga gefe da gefe kana tace “Rankishi dad’e mu biyu ne rak saiko Izzatu dake cikin d’aki...!” Giwa Ta d’anyi Jim tana mai kuma karantar wajen.... Lokaci guda ta kaikaito sosai tana mai k’arewa d’akin Izzatu kallo... Babu shiri Muhibbah ta zame daga jikin k’ofar ta shige cikin d’akin dan tabbas idan Giwa ta matso sosai zata iya ganinta jikin k’ofar... Giwa ta dubi Jakadiya tace “Jakadiya ban yarda babu kowa a nan ba mu koma da baya...!” Babu musu Jakadiya tabi umarnin uwar gijiyarta... Duk addu’an da yazo zuciyar Muhibba yinta kurum take.... Ta sadakar shikenan Giwa da Jakadiya Sun kamata, kaman daga sama taji an janyota Ta baya... Zuciyarta ta kuma tsinkewa sanda taga mahaukaciyar nan ne Ta rik’eta sosai ta b’oyeta k’asan gadon katakon da aka d’aureta bisa.... Tana jin sanda su Giwa suka dawo da baya suna masu k’arewa d’akin kallo na wasu dak’ik’ai... Giwa taceda Jakadiya ta bincika ko ina har k’asan gadon Izzatu... Zuciyar Muhibbah ta kuma tsinkewa shikenan Sun kamata an gama... Tai saurin rintse idanunta had’ida toshe bakinta da duka hannayenta biyu... Jakadiya na k’ok’arin duk’awa Izzatu tai tsalle Ta mak’uro Jakadiya tanai mata wani irin duka wanda da kaga mai yinta kasan babu hankali a tattaredashi... Giwa ta Wato ido waje don basusan Izzatu likamau tayi ba ashe dai ba d’aure take ba... Bugun Jakadiya take tamkar wacce aka aikota bataji bata gani...Jakadiya na sakin k’aran azaba... Giwa kanta saida ta firgita da irin bugunda Izzatu keyiwa Jakadiya tasan ko shakka babu idan ta gama da Jakadiya kanta zata hauro tunda ba hankali bane jikinta... Ai tuni Giwa ta soma jada baya Jakadiya na fad’in ta ceceta... Inaa Giwa ko takan Jakadiya batabi ba ta fice da baya da baya tana waige waige... Da k’yar da mak’yark’yata Jakadiya ta samu ta k’waci kanta hannun Izzatu ta fito a guje babu shiri amma kam ko shakka babu Ta daku irin bugun da akewa dawa idan an ciro daga gona... Haki kurum Jakadiya take d’ankwali a hannu haka ta nufo waje tana gumi da haki had’ida d’ingishi... Suna ficewa Izzatu ta duk’a ta yaye mayafin k’asan gadon nata yanda Muhibbah ke b’oye ciki.... Jikin Muhibbah ya d’auki rawa ganin irin bugunda taiwa Jakadiya kardai itama ta lallasa mata nata bugun... Saidai ga tsananin mamakinta murmushi ta sakar mata kana ta mik’a mata hannu alamun tana jira ta mik’o nata hannun ta fito da ita... Dukda rawa da jikin Muhibbah keyi hakan bai hanata jarumtar mik’awa mahaukaciyar nata hannun ba... A hankali take janyota har Ta fito da ita daga k’asan gadon... Sukaima juna K’uri su duka biyun... Sai yanzu ne Muhibbah ke iya tantance mahaukaciyar da ko shakka babu Dattijuwa ce sannan da alama ta jima a wannan yanayi sabida daud’a da jikinta yayi sosai, data k’urawa mahaukaciyar idanu sai ta fahimci farar fata ce ba bak’a bace dan ga alamun asalin kalarta Ta ramin idanunta da kuma k’ark’ashin kunnuwarta ashe bak’in datti ne ya rufe mata fata har ya zamto tamkar wani layer.... “AUDOTU” (SAUDATU) abinda mahaukaciyar kenan Ta fad’i cikin kalamanata da basa fita sosai... Gaban Muhibbah ya yanke ya fad’i jin wannan mahaukaciya tamkar sunanta taji Ta ambata... Muhibbah ta d’ago firgitattun idanunta tana duban mahaukaciyar wacce tuni ta kuma sakar mata murmushi.... Hannun Muhibbah taci gaba da janyowa har suka isa jikin shirgin kayanta, itada dai Muhibbah bata dawo daidai ba har wannan lokaci saima bugu da k’irjinta Ke ci gaba da yi... Tana gani mahaukaciyar ta soma bincike kayayyakinta... Can k’asan kayan ta ciro wani zane mai yanayi da zanen dake lank’aye parlon su Umaima... Gaban Muhibbah ya kuma yankewa ya fad’i... Mai wannan zane yake nufi....? Batakaiga samo amsa ba taji sauk’ar takardan a hannunta mahaukaciyar ta mallaka mata ta dunk’ula mata sosai cikin hannunta tana mai ci gaba da sakin murmushi... Lokaci guda kuma Ta koma mazauninta Ta zauna, Ta rarumo ledar bredin da jiya Jakadiya da Ubandoma suka kawo mata Ta barka ledar ta hau mamuk’ar bredin kaman mai tsoron kar wani ya k’wace... Muhibbah ta tsaya daga yanda take tai mata K’uri don ba kowa ta tina mata ba face Mahaifiyarta... Haka mahaifiyarta Ke tsananin k’aunar bread shine abincin da yafi soyuwa a gareta a lokacinda take raye.... Ta lumshe idanunta a hankali sanda take jin wasu hawaye daga can k’asan idanunta suna yunk’urin fitowa... Jin kaman alamun tafiyan mutane ya sanyata saurin saita kanta kana ta nufi k’ofa sauri sauri wannan zanen na damk’e cikin hannunta ta fice daga cikin d’akin tana mai kuma waigowa tana duban mahaukaciyar nan itama mahaukaciyar idanunta k’yam akan Muhibbar har Ta fice... A haka Muhibbah ta nufi d’aki, har lokacin bata dawo daidai ba, abubuwan da suka faru suna kuma dawo mata... Musamman da Ta tuna taji kaman matar nan Ta ambaci sunanta... Toh wacece mahaukaciyar nan...? Ya akai ta santa...? Shin wacece ita..? Ta k’arashe tunanin nata tana mai bud’e wannan taswira da mahaukaciyar ta damk’a mata... Tai k’urima zanen ginin tana mai kuma k’are masa kallo... Lallai ya zama dole tasan yanda za’ai tai comparing wannan zanen da wanda Ke lank’aye parlorn su Umaima, idan har sun zmato iri guda toh ko shakka babu akwai wani b’oyayyen sirri tattareda zanen...! Ta k’arashe tinaninta tana mai kwanciya rigingine saman gado... Ta janyo wayarta tana mai k’ok’arin neman layin Ansar... Saidai kira kusan sau uku tai bai d’aga ba... Sai sannan ta duba time taga dare ya d’anja sosai dan haka bata kuma kiran nasa ba barshi har sai zuwa safiya... ** Kafin Washe gari iyaka buguwa Ubandoma yayi laushi a hannun Majidad’i... Idan Kaga Ubandoma dole ya baka tausayi irin yanda bugu ya sauya masa halitta... Kankace mai labari ya bazama Fada cewa an kama Ubandoma a gidan Wamabai... Wannan labari ba k’aramin d’aga hankalin Giwa da Waziri yai ba... Mai yakai Ubandoma gidan Wambai... Shin kodai munafuntarsu yake... Shin kodai shid’in ya amintada Mahmood ne...? Bacin haka ma Uban wa yake aiki Tunda dai sunsan su basu aikesa gidan Wambai ba.. Shi kuwa Mahmood mamaki abin ya dinga basa... Shin mai yakai Ubandoma gidan Wambai..? Shin kodai yasan cewa shine bak’on Buzu...? Ya zaci Ubandoma aminatccen hadiminsa ne, kenan Ubandoma na munafuntarsa ne..? Yayi daidai da bai aminta dashi ya bud’e masa wasu sirrika nasa... Tabbas zarginsa ya tabbata wannan gida ba kowa ba abin yarda bane... Kenan zata iya yuwa wasu sunyi amfani da kusancin dake tsakaninsa da Ubandoma dan yai masu aiki.... Lallai ya zama dole ya k’ara taka tsantsan kuma Ubandoma zai fad’i abinda ya kaisa gidan Baba Wambai da kuma wanda ya turasa... Da wannan tunanin Bawa guda ya k’araso ya zube gabansa yai gaisuwa kana ya k’arada “Allah shija zamaninka an tafida Ubandoma Gidan Yarin wucen gadi dake nan cikin Masarauta Dan a tsaresa...!” Jinjina kai Yarima Mahmood yai a hankali alamun amsawa... Lokaci guda ya haura sama domin shiryawa dan ya zama dole ya gana da Ubandoma a yau d’in.... **** A daidai k’ofar shiga masarauta Yazeed da Majidad’i suka had’u... Yazeed ya fad’ad’a murmushinsa sanda yake k’ok’arin k’arasowa dab da Majidad’in... Bayan sun gaisa ne Yazeed yai gyaran murya cikeda k’asaita “Ashe an kama b’era... Bravo gaskiya kayi k’ok’ari Partner... I’m so proud of you..!” Ya k’arashe yana mai tafe hannu a hankali shu’umin murmushi kwance saman fuskarsa... Murmushin Majidad’i ma yai kana yace “Idan nasa abu a gaba bana fasawa har sai naci nasara domin ni d’in mai sa’a ne a koda yaushe...!” Ya k’arashe cikeda ziga kansa... Shu’umin murmushin bai bar saman fuskar Yazeed ba ya d’an kwanto da fuskarsa kad’an saitin kunnen Majidad’i “Kar kayi gaggawa Abokina domin tafiya ce mai tsawo a gabanka...!” Majidad’i ya murmusa kad’an yana mai duban Yazeed yake furta “At least yanzu na nuna maka what I’m capable of....Kai kuma fah shin ka nuna wani jarumta...?!” Murmusawa kad’an Yazeed ya kumayi kana yace “Ta yuwu a idanunka kaga kaman ka fini k’arfin jiki... Amma saidai ni inada k’arfin tunani wanda zan iya yak’an tawaga guda da wannan tunanin nawa...!!” “Ban gane mai kake nufi ba...!” Majidad’i yace yana duban Yazeed d’in... Kafad’arsa kad’an Yazeed ya buga kana ya kuma matso da fuskarsa dab kunnen Majidad’i “Waye kake tunanin ya umarci Ubandoma da ya shiga Gidan Wambai...?!” Majidad’i ya dubesa shaye da mamaki yana nazarin maganar.. Lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “Ta yuwu shi yakai kansa babu wanda ya turasa tunda wannan gida namu kowa ba abin yarda bane... kuma babu irin bugun da banyi masa ba dan ya fad’i Waye ya turo shi amma ya sanar dani babu wanda ya turo shi..!” Yazeed ya kuma sakin wata murmushi yace “And you believe him...?” Yai tambayar yana mai tsare Majidad’i da idanu.... Lokaci guda ya kuma sakin murmushi ganin ya jefa Majidad’i cikin shakku da kokonto, Yazeed yaci gaba da fad’in “Ubandoma Hadimin waye... Waye Ubangidansa...?!” Majidad’i na tsananin sakin huci ya d’ago yana duban Yazeed... Lokaci guda cikin karaji yake furta “Yarima....Mahmood..!!!” SameenaAleeyou 📚 [7/16, 5:34 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *034* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Yazeed ya kuma sakin murmushi yana mai jinjina kai “Tabbas Mahmood is behind all this, shine silan ciwon mahaifinka... Zai iya yin komai dan yaga ya mallaki sarautar nan Ta ko wacce hanya ce, gashi ya soma da mahaifinka... Wannan dama ce ta samemu muyi amfani da ita wajen kaisa k’asa...!” Ya k’arashe yana sakin huci a hankali... Majidad’i ya d’anyi shiru tamkar mai nazari sai kuma ya nusa yace “Toh amma kan wane dalili Mahmood zai cutar da mahaifina... Da ni da kai munsan cewa tun daga fari mahaifina is being very supportive to Mahmood, Toh kan mai zai nemi rayuwar mahaifina bayan shid’in ya zabi ya goyi bayansa yayi sarauta sama dani da nake d’ansa....?!” Yazeed ya daidaita tsayuwarsa hannayensa hard’e ta gaba ya d’an turo k’irjinsa gaba kad’an irin tsayuwar da masu mulki keyi... “Da alama har yanzu baka fahimci yanda al’amara Ke gudana cikin gidan nan ba... So tari a gida irin namu mafi kusanci dakai shine mak’iyinka, wanda ka aminta dashi can easily betray you... Correct me if I’m wrong..!” Jinjina kai Majidad’i yai yana mai kuma karantar Yazeed lokaci guda yace “Kana tunanin Mahmood could be behind my father’s illness..?!” Yazeed ya saki murmushin cin nasara yana mai ware hannayensa “Isn’t it obvious..? Ai a bayyane yake Mahmood shine sila, da umarninsa Ubandoma ya shiga gidan Wambai... And believe me idan bakai komai akai ba sai Sun kashe Wambai har lahira...!” Majidad’i yace “Toh yanzu miye abunyi Ta yaya zamu kama Mahmood da laifin idan har ba Ubandoma bane ya fad’i cewa da umarninsa ya kutsa gidan Wambai kuma shine bak’on Buzu...?!” Yazeed ya murmusa a hankali kana yace “We make him talk... We gonna make sure he rats Mahmood out... Dole mu tabbata ya fad’i cewa Mahmood shine yai masa umarni da ya shiga gidan Wambai... After all, haka zancen yake tunda Ubandoma Hadiminsa ne...!” Ya k’arashe babu alamun jin k’ai ko imani cikin k’wayan idanunsa... Jinjina kai kurum Majidad’i yake cikeda tsanani tsanar Mahmood “Zan d’auki fansar ciwon mahaifina zan tabbata Mahmood bai zama sarki ba sannan sai ya tafi gidan Yari har tsawon lokacinda mahaifina zai kwashe a kwance....!” Yazeed ya saki murmushi yana mai furta “Impressive..!! Yanzu abinda ya kamata muje muga Ubandoma musan ta yanda zamu b’ullo masa..!” Babu musu Majidad’i ya jinjina kai kana yabi bayan Yazeed suka shige cikin Fursuna... ** Dogari guda ne ya k’araso cikeda risinawa ya bud’ewa Mahmood gark’amemen k’ofar fursunan da aka rufe Ubandoma ciki wanda sai ka shige manyan k’ofofin k’arfe har kusan guda uku kafin ka cimma d’akinda Ubandoma Ke ciki..... Ubandoma na hango Yarima Mahmood ya shiga sanne kansa ya zube gwiwoyinsa ya had’e hannayensa waje guda yana fad’in “Rankaidad’e dan Allah ka ceceni kamin rai ka fitar dani daga wajen nan... Wllhi banida laifi sahun b’arawo na ta...!” Hango tsagwaron b’acin rai saman fuskar Mahmood wanda bai tab’a ganin irinsa ba tattaredashi tsawon zamansu tare ya sanyashi saurin had’iye zancensa gumi naci gaba da tsartsafo masa... Yazeed da Majidad’i da k’arasowarsu wajen kenan tin daga k’ofa Yazeed ya umarci dakarun dake tsare da fursunan da su bud’e masu suga Ubandoma... Dogarin ya risina yace “Allah shi taimakeka Mai Girma Yarima Mahmood yana ciki bazamu iya barinku ku shiga ba...!” Wani jahilin duba Yazeed ya watsa masu “Kun kuwa San ko ni wanene...? Kun kuwa San da waye kuke magana..?!” Dogaran suka kuma risinawa d’ayan na fad’in “Umarnin Yarima Mahmood ne kuma zab’ebb’en sarki na gaba Allah shi taimakeka... Wannan ba umarninmu bane...!” Yazeed da Majidad’i suka dubi juna... Yazeed dake tsananin huci yana k’ok’arin damk’o wuyan Dogarin Majidad’i yai saurin taresa kana ya d’aga bakin rigarsa kad’an zarkwad’ed’iyar wuk’a mai tsananin shek’i sabida kaifi Ta bayyan... Dodagarin ya had’iyi miyau da k’yar dan tsoro yana mai k’ifta idanu... Lokaci guda ya matsada baya yana mai basu hanya... Yazeed ya dubi Majidad’i yace “Zaifi kyau idan ka jirani a nan... Shiganmu a haka mu biyu zaisa Mahmood ya zargi wani abu....!” Majidad’i ya jinjina kai kana ya koma da baya ya bar Yazeed ya soma shigewa... ** Mahmood ya girgiza kai yana duban Ubandoma lokaci guda ya d’an gyara tsayuwarsa yana mai fad’in “Kai nake saurare, ka sanar dani gaskiyar Al’amari idan har kanaso na taimakeka..!!” Ubandoma ya kuma goge gumin dake ci gaba da karyo masa, Ta ya zai soma sanar da Mahmood ga abinda ya kaisa gidan Wambai, Ta yaya zai soma sanar dashi zancen Giwa da Waziri yaji har ya jefasa a ukun da ya tsinci kansa... Sanar da Mahmood gaskiya na nufin tono komai na Masarautar kenan... Idan har ya sanar dashi ga shirin Giwa da Waziri komai ya riga ya lalace kuma yayi imani hakan na iyayin sanadiyan rayuwarsa tinda yasan wacece Giwa ballantana Waziri... “Kai nake saurare Ubandoma..!!! Wai ma tsaya tukuna, who are you..? Wanene Kai..? Ka sanar dani idan akwai wanda kake munafunta dashi cikin Masarautar nan..!!” Ya k’arashe cikin tsananin zafin rai... Ubandoma ya shiga girgiza kai yana furta “Allah shi taimakeka BillahilAzim bani ha’intarka da kowa... Ka yarda dani Rankaidad’e, ka min rai ka cireni daga wajen nan..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai k’ank’an da kai... Girgiza kai kurum Mahmood yai kana yace “Had’in kanka shi kad’ai zai bani damar taimakonka Ubandoma... Amma a halin yanzu ni kaina ban yarda dakai ba, inada kokonto da tarin shakku akanka... Zan baka nan da kwanaki Uku Ubandoma, ka gama dik tinanin da zakai... Idan ka zab’i ka fad’i gaskiya watak’ila ka tsira da mutuncinka amma idan ka zab’i akasin haka... Kafi kowa sanin zaka dawwama cikin k’ask’anci a gidan Yari har lokacinda Allah zai baiwa Wambai lafiya ya bud’e bakinsa ya fad’i komai...!” Daga haka juyawa yai da niyya ficewa Yazeed dake mak’ale daga gefen gini ya gama sauraren duk abinda suka fad’i, shiru yai yana nazari... Kenan Ta tabbata ba Mahmood bane ya tura Ubandoma..? Kenan akwai wani wanda Ubandoma yafi aminta dashi a Masarautar sama da Mahmood... Idan ya fahimci wani abu tabbas akwai wanda yake son ganin bayan Mahmood cikin Masarautar fiyedashi... Toh wanene wannan wanda Ubandoma kema aiki... Waye mak’iyin Mahmood har haka..? Lallai ya zama dole yasan ko wanene wannan...?! Ya k’arashe tinanin yana mai juyawa da baya shiga wajen Ubandoma da baiyi ba kenan... Dole yai shiri ya kuma San takunsa da alama Kuraye sunyi yawa a Masarautar tasu... Mahaifiyarsu tana cen tana fatan Mahmood ya d’ale Karaga ashe akwai wani wanda Ke cin dunduniyarsu basu sani ba.. Yayi imani Giwa batasan Ubandoma na munafuntar d’anta da tafi so da sarauta ba...! Shafa hab’arsa yake a hankali yana nazarin waye ke son ganin bayan Mahmood sama dashi irin haka a cikin Masarautar..!? ** Mahmood yana fitowa yaceda Dakaru masu tsaron Fursunan kar su bari wani ya gana da Ubandoma har nan da tsawon kwanaki uku, dan yasan idan aka bari kowa yana shiga munafukin da Ubandoma ke masa aiki zai iya tsoratasa har ya canza niyyansa na fad’in gaskiya tinda ya kula kaman Ubandoman ya soma karaya da alama zai fad’I gaskiya bayan kwanakin da ya d’ibar masa cewa yai shawari da zuciyarsa.... ** Wayar mak’ale kunnenta na b’angaren hagu ta kuma sauk’e huci a karo na biyu, saida ta canza wajen zama kana taci gaba da fad’in “Ansar I’m quite certain matar nan sunana Ta kira... She knows me Ansar... Duk yanda akai ta sanni... Tambayar a nan shine wacece ita..?!” Daga d’aya b’angaren Ansar ya fuzar da fuci a hankali kana yaci gaba da fad’in “Hiba kiyi tinani maybe kin tab’a saninta a shekarun baya, watak’ila tun tana cikin hankalinta kafin lalurar hauka ya sameta... Kiyi tinanin mutanen da kikai rayuwa dasu a shekarun baya...!” Shiru tai tamkar mai nazari sai kuma tace “Ansar bazan iya tunawa ba, bazan iya tuna sanin wata mace mai yanayinta ba... The only thing da na sani shine inajin wani babban al’amari gameda matar sannan inaso na taimaketa bayan haka inason sanin asalin labarinta da kuma yanda akai Ta k’are rufe a cikin wannan masarauta..!” Ta k’arashe maganar cikin rawar murya.. Shiru na d’an dak’ik’ai suka gifta kana Ansar yace “I have faith in you Hibbah... Nasan duk wad’annan abubuwan da kika saka gabanki da izinin Allah zaki Kai k’arshensu... Addu’ata da soyayyata na taredake ko yaushe kinji koh, dan haka Koda wasa kada Ki karaya... Jinjina masa kai tai a hankali tamkar yana ganinta kana sukai sallama cikeda kewar juna... Takardan zanen da mahaukaciyar ta damk’a mata Ta d’auko Ta ware tana kuma k’are masa kallo.. Ya kamata taje sashen Giwa ta had’e zanen waje guda don ta tabbatar ko iri guda ne... Mik’ewa tai ta soma shirin nufa sashen Giwa... ** Cikeda ladabi Jamal ya k’araso gaban Giwa yana sauraren kiran gaggawa da tai masa... “Ina zanen yake..?!” Ta tambaya cikeda kulawa... “Maami wane zane kenan...?!” Fuzar da fuci tai a hankali kana tace “Jamal sanin kanka ne Masarautar nan babu lafiya akwai wanda Ke mana zagon k’asa.. Na tabbata yana nan yana neman zanen nan... A ina ka ijiye...?!” D’an jim yai kana yace “Maami na kyautar...!” “Ka me...?!” Giwa Ta tambaya tana dubansa “Na kyautar Maami...!” Take gumi ya shiga tsartsafowa Giwa... Wannan zane guda UKU ne rak a duniya, kuma ko wanne nada alak’a da juna... D’aya bazai tab’a warwaruwa ba saida d’aya, duk randa zanen nan guda uku suka shiga hannun mutumin da yake masu zagon k’asa a Masarautar tabbas mabud’an sirrikanta sun yaye... Guda d’aya yana wajen d’anta Jamal, d’aya yana wajen Wambai guda d’aya ne batasan yanda yake ba saidai tafi k’arfafa zaton yana wajen Jafar ne....Tabbas idan aka had’e wad’annan zane guda uku waje guda zai baka jimillan wasu hanyoyi da k’ofofi masu rikitarwa da wahalan fasaltuwa.... Tayi imani Bak’on Buzu wannan zanen yake nema wajen Wambai.... Ta juyo cikin tsananin fusata tana duban Jamal... “Ashe kai bakada hankali ban sani ba... Jamal ta yaya zan sanar dakai mahimmancin abin nan ka kama ka kyautar...Anya cikin hayyacinka kake...?! Jamal cewa nayi ka k’ona k’urumus tun a wancan lokacin bawai ka kyautar ba..!!!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin cakumo wuyansa.... Tsoro da mamakin mahaifiyarsa ya somaji ganin yanda ta fice a hayyacinta lokaci guda... Fincikar rigarsa yai yana mai ci gaba da sakin fuci, lokaci guda yake furta “Maami laifina kike gani..? Maami idan ban mance ba kece da kanki kika dank’a min zanen nan kikace Abbah ne ya bani, lokacin ina yaro sosai mukayai wani tafiya kikace a wancan Masarautar aka bashi kyauta shi kuma ya bani... Da bakinki kikace nayi nesa da hoton daga cikin Masarautar nan... Kuma nayi kaman yanda kikace...!” Ya k’arashe yana sakin huci.... K’ok’arin saita kanta Ta d’anyi had’ida dafasa “Gwarzona ka tabbata zanen baya cikin Masarautar nan...?!” Saida ya had’iyi miyau don tunda yake bai tab’a k’aryawa mahaifiyarsa ba sai yau sannan bai tab’a questioning duk wani umarni da zata basa ba....Lokaci guda ya shiga jinjina kai yana fad’in “I promised Maami... Wanann zanen yayi nisa da Masarautar nan..!” Ya k’arashe yana dubanta... Murmusawa tai kad’an tana mai shafa fuskarsa take fad’in “Kasan na aminta dakai sama da sauran yarana, nasan bazaka tab’a bani kunya ba..!” A hankali ya jinjina kansa yana mai k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarsa “Har abada bazan tab’a baki kunya ba Maami... Alk’awari ne..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice... Bai zarce ko ina ba sai parlornsu Umaima... Yai tsaye yana duban hoton... Tabbas mahaifiyarsa bata shigowa b’angarensu Umaima sabida mulki irin nata amma kam tabbas da tayi tozali da zanen nan... Yau ce rana ta farko da ya tab’a mata k’arya tsawon rayuwarsa, akan macen da yake so ya zab’i yayiwa Giwa K’arya for the first time... Bazai iya k’wace abinda ya baiwa Umaima da hannunsa ba... ya shirya daukan risk d’in ko menene nufin Giwa na cewa a fitar da zanen cikin Masarautar tun wancan lokacin.... Taku kad’an yai ya k’arasa jikin hoton ya k’ura idanunsa... Lokaci guda yasa hannu ya ciro hoton ya shiga juyashi yana k’are masa kallo.... Umaima ce ta fito daga d’aki cikin shirin sauk’a k’asa sai kuma tai karo da Jamal tsaye nan wajen rungume da Taswiran yana sakar mata murmushi... Harga Allah batasan dalili ba amma sosai taji tsoron ganinsa a wajen...Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ta sakar masa “Yaya... Barkada safiya ..!” Murmushi bai bar saman fuskarsa ba ya amsa mata kana ya dubi writs watch d’insa yace “Looks like wata yanzu tashinta a bacci shiyasa take mun gaisuwan safiya bayan yanzun agogo ya nuna k’arfe shabiyu ne da rabi na rana..!” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa Murmushin da yafi kama da yak’e tai kana tace “Kuma fah haka ne ashe rana tayi already...!” “Ina zaki sani your Highness tunda kina kwance cikin d’aki kina hutawa...!” Ta d’an murmusa kad’an “Kai Yaya hutu ai na wajenku...” Shid’inma murmushin yai “Ina wani hutu bayan ban jima da dawowa daga bargan dawaki ba na duba lafiyarsu....!” Murmusawa ta kumayi tana dubansa simplicity d’insa na burgeta harga Allah... Sam bai d’auki sarauta wani aba ba... Kasancewarsa d’an sarki bai saka masa girman kai ko jin shid’in daban ne ba, ba kaman d’an uwansa Yazeed da yakeda tsananin jida mulki da isa ba... Kai gaba d’aya ma cikin yaran sarki Jamal ya fita daban, sam baida wani aibu baida tashin hankali uwa uba ga sauk’in Kai wanda kaf harta Mahmood baida sauk’in kai irin nasa dan idan jin mulki ne ma da alama Mahmood d’in duk ya d’ara sauran sabida shi sarauta mai aji yake ba kaman Yazeed wanda zaka fahimci tsantsan hauka a lamransa ba...Sannan tana iya tuna sanda Jafar ya gudu ya bar Masarautar bayan zuciyarta tayi dumu dumu cikin kogin begensa Yarima Jamal ne yaita consoling d’inta har ta d’an mance da ciwon da Jafar ya tafi ya bar zuciyarta ciki... Har abada bazata tab’a mance halaccin Yarima Jamal a gareta ba... Idanunta suka sauk’a kan Hoton zanen dake rik’e hannunsa... D’ago zanen yai shima yana dubawa... Ta sakar masa murmushin da yafi kama da yak’e.... Dai dai lokacinda ya soma takowa gareta zuciyarta naci gaba da bugawa... Muhibbah da isowarta kenan tai tsaye tana dubansu, lokaci guda Ta d’an matsa kad’an Ta mak’ale jikin cottons tana mai kuma b’oye zanen dake hannunta cikin rigarta.... SameenaAleeyou📚 [7/23, 9:36 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *35* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Daidai gaban Umaima yaja ya tsaya yana mai jifanta da wani irin kallo dake ci gaba da haifar mata da fad’uwan gaba... Baice komai ba sai kallon k’urilla da yake mata da matsakaitan idanuwansa da basu faye girma ba, uwa uba sam bata hango annuri saman fuskar nasa ba wanda hakan sosai ya kuma haifar mata da matsanancin tsoro wanda sam batasan dalilin jin hakan ba... Ba Umaima dake tsaye k’ik’am gaban Jamal ba harta Muhibbah dake mak’ale jikin cottons ta razana da irin kallon da Jamal keyiwa Umaima.... Zuciyar Umaima bata daina yankewa ba take k’ok’arin matsawa baya tana neman kalamai saman harshenta saidai murmushin da Jamal ya sakar mata ya sanyata fasa janye k’afafunta.. Lokaci guda yake furta “Ina kuma zakije your Highness... Did something happen..?!” Ya tambaya yana d’an bud’e idanunsa... Murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar masa “A’a no... Nothing has happened, babu komai...I think I left my phone in the room....I need to go get it...!” Ta k’arashe tana mai saurin juyawa da niyyan komawa d’aki saidai tuni Jamal yasha gabanta yana mai ci gaba da aika mata mayen kallo wannan karon fuskarsa a marairaice... Ta d’ago tana dubansa k’irjinta naci gaba da bugawa, Jamal ya d’anyi k’o’arin saita kansa had’ida d’aura murmushi saman fuskarsa, lokaci guda yai stepping back yana mai furta “Did I scare you...?!” Ya tambaya yana dubanta, sihirtaccen murmushi kwance saman fuskarsa... Bata iya cewa komai ba sai girgiza masa kai da tai alamun a’a, Jiki a matuk’ar sanyaye... Murmusawa ya d’anyi sai kuma ya d’ago mata frame d’in yana mai furta “Zaki iya bani aron wannan..?!” Ta saki murmushi wanda yafi kama da yak’e “Ai..Ai dama naka ne Yaya... So zaka iya d’auka ko babu iznina...” Ya girgiza kai kad’an murmushin bai bar saman fuskarsa ba “No it’s yours Umaima... Na riga na baki ai, wannan kyauta da na miki tamkar zuciyata ne na mallaka miki idan Kinga na amsa toh ki tabbata zuciyata na amsa daga gareki...!” Ya k’arashe cikin wane irin siga yana k’ura mata idanu... Gaba d’aya sai ta rasa gane ina kalaman nasa suka dosa, sai ta zama lost and confused.... Jamal da tuni ya fahimci hakan ya d’an sakar mata murmushi da gefen baki “Sorry, I mean kawai zan ara ne zuwa wani d’an lokaci.. I promise zan dawo miki dashi... Amma idan baki min izina ba babu yanda na iya bazan d’auka ba...!” Sigan da yai magana dashi sai ya bata dariya, ta d’an murmusa kad’an tace “Aw haka ne..? Toh na baka aro har lokacinda kaji ka dawo min dashi dan rad’in kanka..!” Yai murmushi mai d’an bayyana hak’wara wannan karon “Gaskiya naji dad’i K’anwata... Thank you...!” Ya k’arashe yana mai kasheta da wani irin duba wanda Ke kuma haifar mata da wane irin yanayi... Shiru ya d’an ratsa tsakani kaman babu mai cewa komai... Jin shirun yai yawa ya sanya Umaima d’agowa da niyyan magana saidai shima Jamal d’in maganan tasoyi... Kowa yai shiru dan baiwa juna dama suyi magana... Jamal yace da ita “You go first...!” Ta girgiza kai alamun a’a sai kuma ta d’ora da “Dama Babu komai... Kawai zan shige ne...!” Ya jinjina kansa kad’an yana mai kuma karantar Ta, lokaci guda yai gyaran murya yana mai gyara tsayuwarsa “Umaima there’s something you need to know... Something I’ve been keeping for a long time now... Umaima I don’t know if you’ve ever noticed... But...!” Ya d’an fuzar da huci a hankali had’ida murza tafukan hannunsa “Wait, how do I put it...!” D’an dubansa tai k’irjinta naci gaba da bugawa lokaci ba tareda Ta iya furta komai ba... Jamal ya d’an kauda kai gefe yana mai sauk’e fuci a hankali.. Lokaci guda ya kuma juyowa yana dubanta “Bansan yaya zaki d’auki lamarin ba k’anwata, but I think lokaci yayi da zan sanar dake...!!” Ya k’arashe cikeda tsananin kulawa... K’ok’arin saita kanta tai kad’an “Yaya mai kake son sanar dani you making nervous already... Allah Sa ba wani abin nai maka ba..?!” Ta k’arashe tana rau rau da idanu... Ya sakar mata murmushi mai taushi kana yai mata nuni da kujera “Sit down..!” Babu musu Ta isa ta zauna... Shima ya k’arasa ya zauna yana mai aje Frame d’in zanen dake hannunsa gefen kujeran wanda tuni idanun Muhibbah sun sauk’a kai... Jamal ya d’anyi gyaran murya kad’an “Umaima I fell in love...!!!” Yai maganar kaman mai tsoron yinta.. Tamkar sauk’an aradu haka taji batun... Tai saurin d’agowa tana dubansa, fuskarta d’aukeda alamun tambaya... Jinjina mata kai yai kad’an alamun jaddadawa “Yes I fell in love with you... I don’t know when or how... But all I’m certain of shine na aukawa soyayyarki... It might sound weird or maybe ridiculous... But, believe me I’m deeply in love with you... I love you so much that I couldn’t hold myself back anymore... I love you...!!” Ya k’ara fad’i yana mai duban cikin idanunta wannan karon sosai had’ida zamowa kad’an daga cikin kujera... Har lokacin shock bai saketa ba... Ta kasa aminta da abinda takeji... If there’s one person da zatazo tai soyayya dashi cikin yaran Yayan mahaifiyarta, that person should be Mahmood... Shine mutumin da take so da duka zuciyarta tun tana k’aramar yarinya koda ta fahimci su d’in were never meant for each other sai ta hak’ura tai k’ok’arin yakice soyayyar Mahmood sannan bayyanar Jafar cikin rayuwarta ya kuma sa ta mance babin Mahmood ta kuma aminta yarinta ne yasa takejin bata da miji bayan Mahmood...But Jamal, yeah they get along and he has all the qualities da ko wace mace zataso ace ya zama mijinta amma batajin sonsa ko kad’an cikin zuciyarta, da zai tsaya matsayin Yayanta da yafi mata sauk’i... Muryarsa ne ya dawo da ita daga duniyar tinanin data tafi... “You don’t need to answer me right away... Ki samu lokaci kiyi tunani, at least yau zanyi bacci mai dad’i na sanar da masoyiyata abindake cikin zuciyata....!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye ya nufi k’ofa... Har ya kusan k’ofa ya juyo kaman wanda yai mantuwa daidai nan Zahra dake haurowa daga k’asa ta nufo parlorn nan idanunta suka sauk’a kan Muhibbah dake da fitowarta kenan daga cikin labule tana duban abinda Jamal zai d’auka tana addu’an Allah yasa kar ya d’auki zanen nan har sai ta comparing... Zahra ta dubeta da mamaki murmushi saman fuskarta ta kirawo sunanta... Ai a d’ari Muhibbah ta daka tsalle ta isa kusan Zahra ba tareda ta bari Jamal dake k’ok’arin waigowa ya ida waigowa ba... Da mamaki Zahra ke dubanta, saidai kafin Zahran tai magana Ta katseta da fad’in “I... I was looking for you dama... Thank Goodness I found you here..!” Zahra ta d’an dubeta “Is something wrong...?!” Tai saurin girgiza kai alamun a’a sai kuma tace “About our Spanish classes.. Yaushe zamu fara...!” Ta k’arashe tana mai fari da idanu... Murmusawa kad’an Zahra ta d’anyi kana tace “Wai dama wanann ne ai kin riga kin fara Tia coz already kin iya gaisuwa kuma kin fara tsintar wasu words...!” Muhibbah ta murmusa hannun Zahra cikin nata take furta “Yeah dukda haka dai nafi gane na shiga class, kinsan ance cikar d’alibi saida aji...!” Suka d’an dara kad’an a tare daidai sanda suke isowa cikin parlorn.... Kallo guda zakaiwa Umaima ka fahimci ba daidai take ba... Shiko Jamal murmushi saman fuskarsa yake dubansu, Zahra ce ta soma gaidashi... Ya amsa da sakin fuska yana mai dafa kanta da hannu guda yayinda Muhibbah ta sauk’e idanunta kan d’aya hannun nasa dake rik’e da zanen....Kauda kanta gefe kurum tai had’ida rintse idanunta a hankali... Shikenan Jamal ya b’ata mata shirinta, yanzu bazata ita comparing zanen ba... Mai zatai yanzu...? Bata kaiga nemo amsa ba ta sinkayo muryar Zahra na tambayar Umaima ko lafiya take Dan tuni Jamal kam yayi ficewarsa..... Zahra ta kuma dafa Umaima da Ta zauna gijif cikin kujera tana faman k’irga ‘yan yatsun hannunta... “Aunty Umaima.. Lafia, Wai meke faruwa....? Are you sure you’re okay...?!” Murmushin k’arfin hali Ta sakarwa sanin cewa bazata daina tambayar nata ba kana tace “Babu komai Zahra... I’m fine, kawai yau Uncle d’inki ya karb’e kyautar da ya bani ne...” Ta k’arashe tana mai duban ma’ajiyan frame d’in... Zahra ta d’anyi Jim sai kuma tace “Shiyasa kike fushi.. Amma maiyasa Uncle Jamal zai amshi frame d’in nan bayan ya jima da baki.. Kodai naje na amso miki ne..?” Ta murmusa kad’an sai kuma tace “No it’s okay, ni na bashi da kaina... I think kaina Ke ciwo, zan koma d’aki na kwanta...!” Muhibbah ta tako gabanta kad’an tana mai dubanta “Do you need a pain killer..?” Ta girgiza kai alamun a’a “Idan nayi bacci shikenan... Na gode da kulawarku..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye da k’yar ta nufi d’aki... Suka bita da kallo har ta shige kana Zahra ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai furta “She’s like a mother to me... Ina sonta sosai, Aunty Umaima nada zuciya mai kyau just like you Tia...!” Ta k’arashe tana duban Muhibbah dake tsaye.. Muhibbah ta murmusa kad’an had’ida zama gefen Zahra, Zahra taci gaba da fad’in “She lost both her parents when she was very young, Maami itace mahaifiyarta kuma itace mahaifinta... Kaman yanda naji labari tun tana jaririya Maami tazo da ita cikin Masarautar nan...” Muhibbah ta gyara zama sosai tana duban Zahra “Kina nufin tun tana tsumman goyo...!” Zahra ta jinjina kai “K’warai kuwa haka Uncle Fu’ad ya sanar dani kaman yanda ya sami labari Kinsan Iatda Uncle Fu’ad shekaru biyu ne tsakaninsu ya d’an girmeta kad’an so tare Maami ta rainesu... Amma saidai ita an barta hannun Kakata mahaifiyar Maa d’ita ita ta raineta har saida takai kusan shekaru goma kafin aka dawo da ita cikin Masarautar nan... Maybe shiyasa nake jinta sosai cikin zuciyata, itada Maa are practically sisters.... I love her..!” Ta k’arashe cikin sanyin murya murmushi saman fuskarta Muhibbah ta d’an girgiza kai kad’an tana duban Zahra “Ban fahimceki ba Zahra... Kina nufin kice Umaima ‘yar uwar mahaifiyarki ce..?!” Girgiza mata kai tai alamun a’a sai ta d’orada “Aunty Umaima d’iyar k’anwar Maami ce, wani tafiya Benin da Maami tayi shine ta dawo da Aunty Umaima rik’e a hannu cikin zanin goyo, a cewar Maami wuta ya cinye Iyayen Aunty Umaima...!” Ta d’anyi fasali sai taci gaba da fad’in “Kinsan Maman Mamata Baiwa ce toh shine Giwa ta bata rainon Aunty Umaima tun tana jaririya har zaita takai shekaru goma kafin ta dawo da ita hannun Giwa a lokacin ana shirye shiryen Bikin mahaifiyata da Paa d’ina...!” Shiru Muhibbah tai tamkar mai nazari had’ida k’urama waje guda idanu... Ta juyo tana duban Zahra ta d’anyi gyaran murya kad’an tace “Toh ina Kakarki mahaifiyar maman naki take..?!” Zahra ta bud’e hannayenta alamun bata sani ba, taci gaba da fad’in “You know that’s why banson gidan sarauta... Sirrika sunyi yawa, all I know gameda mahaifiyar Maama shine tun lokacinda Paa ya dage zai auri d’iyarta Maami ta umarceta da tai nesa da Masarautar nan a cewarta baza’a ringa nuna d’anta a gari ana cewa ya auri d’iyar bayi ba...!” Muhibbah ta katseta da fad’in “Toh baki tab’a tambayar Mamanki Ina mahaifiyarta ta tafi ba...?” Zahra ta d’anyi shiru kaman mai nazari sai kuma ta girgiza kai tace “Dik sanda na tambayi Maa sai tace nayi shiru kuma kar na sake tambayarta and I don’t think ko Paa ma ya sani... Ina tsamman babu wanda yasan yanda Maman Maama Ta tafi...!!” Ta k’arashe cikin sanyin murya... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Muhibbah tai tana mai bin maganganun Zahra’u daki daki nan ta sinkayo muryar Yazeed yana waya zai shige b’angaren Giwa, da alama wayan nasa ya shafi kama Ubandoma da akai... Duban Zahra ta d’anyi kana tace “Ki shiga ki duba Umaima, I’m sure akwai abindake damunta... Maybe ke zata sanar dake k’ila ganin ina wajen tai shiru bata sanar dake komai ba...” Jinjina mata kai Zahra tai tace “Ok zan dubata yanzu..” Ta k’arashe tana mai nufa d’akin Umaima... Muhibbah ta sauk’e wani ajiyan zuciya kana ta lek’o kanta kad’an yanda ta hangi Bayi guda biyu rik’eda kaya hannunsu, suka risina suka gaida Yazeed da har lokacin waya yake kana suka shige... Saida ta jira shigewan Bayin kana ta sad’ad’o ta fito... Taso bin bayan Yazeed dan taji tattaunawarsu da Giwa saidai hakan ba mai yuwuwa bane domin kaw da alama yau sashen Giwan cike take da bayi, kawai sai ta zab’i tabi bayan Yarima Jamal zuwa sashensa taga yanda zaiyi da zanen da ya d’auka daga wajen Umaima.... ** Giwa ta d’ago tana duban Yazeed idanu a kannare sanda yaci gaba da fad’in “Bansan Maiyasa kika dage sai Mahmood bane zai gaji sarautar nan... Amma ki sani Maami what so ever your reason might be bazan canza k’udirina ba... Sarautar nan tawace..!!” Ya k’arashe yana sakin huci... “Ka gama Yazeed...?Nace ka gama...?!!” Har lokacin hura hanci yake yayi zama irinta masu mulki sai karkad’a hannunsa guda yake... Giwa ta mik’e cikeda izza tana takowa zuwa gareshi.... “Yazeed kalleni nan..!” Ya d’ago rinannun idanunsa yana dubanta “Ka sanar dani shin kaine ka tura Ubandoma gidan Wambai...?!” Da tsananin mamaki yake dubanta kana ya gyara zamansa... “Maami what exactly are you implying here..? Mai kike nufi....?!” Ba tareda ko Gizau ba Giwa ta kuma furta “Nace ka sanar dani idan Kai ka tura Ubandoma Gidan Wambai dan ka k’ala sharri wa d’anuwanka a hanasa sarauta, tunda nasan akan sarautar nan you’re capable of anything Yazeed.. Kuma dani dakai sarai munsan Mahmood bazai aikata abu makamancin wannan ba, So gwara ka sanar dani komai tun muna mu biyu...!” Ta k’arashe cikin tsananin k’unan rai tana mai sauk’e fuci... Take idanun Yazeed suka kuma kad’awa sukai jazir, fatarsa Ta sauya zuwa ja... Tururin k’unan rai da fuci kurum yake har wani rawa jikinsa keyi... Lokaci guda ya mik’e tsaye yana duban cikin idanun mahaifiyar tasa ”Unbelievable!.. Are you seriously throwing that on me Maami...! Sabida d’anki mafi soyuwa a gareki yayi laifi and you can’t simply accept the fact that Mahmood isn’t what you think he is shine bari ki d’aura laifin akaina... Maami tell me Ubandoma Hadimin waye...? Da wa ake ganinshi..? Ma waye yake hidima..? Is it me or my brother..?!” Shiru ya d’an ratsa tsakani sai hucin da Yazeed ke sauk’ewa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “Bakida amsa Maami....! Bari kiji na fad’a miki Giwa, believe whatever you want to believe I do not give a damn! babu abinda zai sa na fasa k’udirina... Idanma kina tinanin nine bak’on Buzu, then be it.... Abu guda da zan sanar dake shine kiyi taka tsantsan domin kuwa rayuwar Mahmood is in great danger... Kuma bani bane abin tsoron akwai wani wanda yafini san ganin Mahmood bai d’ale Karagar nan ba...I’m sure bakisan da wannan ba, duk abinda ya sami Mahmood karkiyi tinanin nine domin kaw Kurayen sunada yawa..!!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice cikin tafiya da tafi kama da sassarfa... Yarfe gumin da ya keto mata tai sanda ta doka kiran Jakadiya..! Nan kuma ta tuna ashe Jakadiya bata warware daga bugun da Izzatu tai mata ba... Taja gajeren tsuka a hankali sanda hadimarta guda ta shigo tana mai risinawa... Giwa ta fatattaketa tace tajeta tai mata kiran Jakadiya bata damu ko ta warke ko bata warke ba, dik yanda za’ai tazo Ta tana nemanta... Babu shiri Baiwar ta mik’e cikeda girmamawa ta fice... Giwa sai faman safa da marwa take tana huci.... *** Sauri sauri ta fito da niyyan bin bayan Jamal amma saidai mai, tana fitowa suka kusan karo da Fu’ad zai shige sashen Giwa.... Fu’ad ya tsaya cak yana mai dubanta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... Dukda k’atutun bak’in ciki da ya tokare mata mak’oshi hakan bai hanata k’ak’aro murmushin yak’e ta sakar masa ba.... “Your Highness... Barka da rana...!” Ta fad’i murmushin bai bar saman fuskarta ba... Saida ya rage girman idanunsa kad’an sai kuma yace “Bazan amsa irin wannan gaisuwar ba Hibbah... Mu gaisa a cen..!” Ya k’arashe yana mai duban sliding door dake gefe yanda zai fitar dake madaidaicin wajen shak’atawa... Bayi masu kaikomo kaw idan suka Zo shigewa sai Sun risina Sun gaidasu... Muhibbah da gaba d’aya ranta ya gama jagulewa sabida plan d’inta da Fu’ad ya b’ata mata k’ok’arin saita kanta tai tace “But your Highness ka mance sharad’ina, banso kowa yasan alak’ar for now a Masarautar nan... Gudun k’anan maganganu irinta gidan sarauta... Nafiso mu fahimci junanmu sosai and... to be sure of what we feel for each other..!” Fu’ad ya d’an kuma takowa kusanta kad’an had’ida rage muryarsa “And you think zan iya jure wannan sharud’an Naki Hibbah... Is not as if we are doing anything wrong.... So banga abin damuwa ba... And one more thing...!” Ta d’ago tana dubansa jin yayi fasali Fu’ad yaci gaba da fad’in “My feelings for you are real Muhibbah... Bana buk’atan yin wani tunani gameda soyayyarmu... Unless kuma kece baki so na...!” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu... Tamkar takai masa naushi a fuska haka takeji jin yanda yake furta mata kalaman Soyayya wanda tayi imani da yasan ko wacece ita bazai soma hakan ba... Badon karta ruining plans d’inta ba data masa kaca kaca tun daga nan amma saidai hakan ba mai yuwa bane... Tai k’ok’arin d’aura fake smile saman fuskarta “Ba haka nake nufi ba your Highness..” Fu’ad ya katseta da fad’in “Idan har ba haka kike nufi ba, then prove it...!” Bai jira cewarta ba ya shige k’ofar... Ta fuzar da fuci a hankali badon taso ba tabi bayansa zuciyarta gaba d’aya a cunkushe.. Shiko Fu’ad ganin ta biyo bayansa sai zuciyarsa ta aminta tabbas Muhibbah k’aunarsa take... Toh wata mace ne ma zata k’isa, baijin akwaita... Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake dubanta cikeda jin dad’i, tuni ya sakankance yaci gaba da jero mata kalaman k’auna... Shigowarsa sashen kenan ya hangesu, kanta a k’asa tana faman sakin murmushi ga Fu’ad tsaye gabanta yana kasheta da wane irin kallo wanda ko ba’a fad’i maka ba kasan abinda irin kallon Ke nufi... Da gani suna matuk’ar jin dad’in zancen da suke.... Cikin sakanni zuciyarsa Ke harbawa.... SameenaAleeyou 📚[7/24, 6:11 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *36* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali yake murza hannunsa dake rufe cikin bandage wanda sam baisan yana yin hakan ba, ya kasa janye idanunsa daga barin duban nasu bai kuma daina murza hannun nasa ba wanda da alama ko zogin ciwon baiji... Ji yake tamkar zuciyarsa zata b’allo daga cikin k’irjinsa ta fito waje.. Kan kace mai jini ya soma d’iga a wajen... Sauk’owar Zahra kenan Ta hangi mahaifinta ya k’urama waje guda idanu ga jini na kuma d’iga daga cikin hannunsa... Cikin sauri Zahra ta k’araso tana duban hannun nasa take fad’in “Paa... Paa you’re bleeding again....!!” Muryar Zahra da Muhibbah ta sinkayo ya sanyata saurin waigowa tana duban wajen... Ido suka had’a da Mahmood saidai tuni yasa kai ya juya ya fice gaba d’aya daga sashen yana mai tamke hannunsa mai d’igan jini, lokaci guda yake ceda d’iyarsa it wasn’t serious she shouldn’t worry... Zahra tuni tabi bayansa yayinda Muhibbah kacaukam hankalinta ya koma garesu... Ta dubi Fu’ad daketa faman duba abu cikin waya da alama baisan wainar da ake tuyawa ba... D’an dafa kanta tai kad’an had’ida tamke idanunta... Fu’ad ya d’ago yana dubanta had’ida daina abinda yake “Are you alright..?!” Ya tambaya yana dubanta... K’ak’aro murmushi tai tace “Kar ka damu just a headache...!” Cikin nuna kulawa Fu’ad Ke fad’in “Headache.! Subhanallah, do you want to see a Doctor... Should I call one...!” D’an girgiza masa kai tai tace “No kar ka damu, idan nai bacci zai daina, na gode da kulawa...!” Ya sauk’e fuci a hankali sai kuma yace “Are you sure..?” Ta jinjina masa kai ba tareda tace komai ba... Daidaita tsayuwarsa ya kumayi sai kuma yace “Muje na rakaki..” Ta girgiza masa kai a hankali “Ka mance conditions d’ina... We shouldn’t be seen together..” Ya d’an ware idanunsa kad’an kaman zaice wani abu sai kuma yace “Alright fine... But promise me one thing..!” Ta d’ago tana dubansa.. Fu’ad yaci gaba da fad’in “You’d take good care of yourself for me..!” Ya k’arashe cikin kwantar da murya.. Dariya yaso bata amma sai ta gimtse tace “I’d in sha Allah... I promise..!” Fu’ad ya murmusa kad’an yana mai bata hanya alamun ta shige... Ta tako zata shige, Daidai k’ofa Ta sinkayo muryarsa yana fad’i tamkar mai rad’a “I love you..!” Murmushi kurum ta sakar masa ba tareda tace komai ba ta shige... ** A b’angaren Mahmood kuwa suna tafe shida Zahra Raheema ta hangosu, cikin sauri ta take masu baya tana tambayan Zahra meke faruwa... Shi kuwa Mahmood cikin sassarfa kurum yake tafiyar nasa ba tareda yabi takan Raheema dake tambayar Zahra abindake faruwa ba... Hannunsa a tamke sosai yake tafiyar zuciyarsa naci gaba da bugawa, suna shigowa parlorn ya shiga warware bandage d’in k’arfi k’arfi wanda har saida yaso baiwa Zahra tsoro... Raheema ta k’araso cikin rawar jiki take fad’in “Yarima mai ya sameka... Ina ka sami wannan k’aton yankan...?” Ta dubi Zahra dake tsaye gefe tana duban mahaifin nata cikin kid’ima tace “Zahra get the first aid let’s treat his wound...!” Muryarsa suka sinkayo yana furta “No..!” Raheema Ta dubesa tace “But you’re bleeding..” Katseta yai cikin tsananin d’aga murya “I said no... Ko bakiji bane..!!” Raheema ta koma gefe tana duban ikon Allah yayinda Zahra Ke furta “Paa should I call Aunty Muhibbah tunda itace tai maka treating, na kirata ta sake..” “Whattt..!!” Raheema ta furta cikin zuciyarta, ina take har akai wannan iskancin... Wannan shegiyar mayyar yarinyar ta wanke ciwon mijinta... Eh lallai Aunty Zeenatu tayi gaskiya da tace wannan yarinyar karuwanci kawai take sonyi da Princes d’in Masarautar nan.... Toh wllhi tayi k’arya ta fara da Mahmood d’inta.. Tayi nisa cikin tunani har batama San sanda Mahmood yai hayewarsa sama ba Zahra kuma ta fice tuni ta barta nan tsaye... Ta d’aga Kai tana duban matakalan bene zuciyarta naci gaba da harbawa... Toh maiyasa har yanzu maganin bai soma aiki ba, maiyasa gaba d’aya bata gabansa, tama kula tamkar yanzu yafi yin watsi da ita unlike before, dik tsiya da yakan aika ai kiranta koda ba wani zancen arziki zasuyi ba amma yanzu ko takanta baiyi, jibi har ciwo yaji duk bata sani ba tana can baki sake wata ‘yar banza na neman k’wace mata Mahmood d’inta... Toh wllhi da sakel hakan ba mai yuwa bane... Ta k’arashe tunanin nata tana mai ficewa fuuu tamkar zata tashi sama... ** Yana haurawa sama shirin fita yai kana ya fito waya manne kunnensa yana magana da Turaki... Turaki yace “You can’t drive like that your Highness ka bari nazo na kaika...!” Cikin kakkausar murya yake fad’in “Mai ka d’aukeni, kan wannan k’aramin ciwon kake cewa bazan iya driving ba... Banida lokacin jiranka Turaki, and I don’t trust anyone cikin Masarautar nan...!” Yana ida fad’in haka bai ko jira cewan Turaki ba ya katse kiran had’ida jefa wayar cikin aljihu... Turaki na kiran sunansa inaa ko amsa sa baiba ya isa ma’ajiyan mitocinsa ya shige guda d’aya yayi ficewarsa... Yana ficewa Waziri ya lek’o daga mab’oyarsa yana wani muzurai da idanu, take ya ciro waya cikin babban rigarsa ya k’ara a kunnensa “Ya fito, kabi bayansa... Kuma ka tabbata bai b’ace maka ba....!” Daga haka katse kiran Waziri yai kana ya nufi sashen Giwa... Duba d’aya Giwa tai masa ta kauda kanta gefe... Waziri ya saki murmushi mai taushi yana mai duban yanda Giwa Ke sakin huci... Da kirari ya soma mata, ya wasata sosai yai mata kirari da yabo sosai kana ya k’arada “Muddin Waziri na numfashi bakida damuwa, idan akan Mahmuda ne kisaka ma ranki Mahmood a tafin hannunki yake domin koda Ubandoma ya munafuncemu ya had’e kai da wani cikin Masarautar nan na aje mutum guda wanda zai dinga bibiyan al’amaran Mahmood da kuma duk yanda yake zuwa zai sanar damu...!” Giwa Ta d’an dubesa kad’an har lokacin fuskarta babu walwala.. “Allah yasa gaskiya kake fad’i...!” Ya kuma murmusawa yana mai takowa gabanta kad’an “Burinki k’iris yake da cika, Ina mai tabbatar miki..!!” Sai wannan karon ta murmusa kad’an kana Ta mik’e cikeda k’asaita, fuskarta na duban wani b’angare take furta “Waziri akwai sauran rina a kaba... D’azu Yazeed yazo min da wani zance kuma na duba maganganunsa sosai na aunasu, tabbas akwai kuraye da dama cikin Masarautar nan... Idan har Ubandoma nada k’arfin halinda zai iya cin amanamu toh ko shakka babu zai iya tona mana asiri.. Ubandoma yasan sirrikanmu da dama bazai yuwu mu k’yalesa haka nan ba..!” Waziri ya tako kad’an yace “Mai kike so Ayi....?” Giwa ta waigo tana dubanasa lokaci guda take d’an buga hannunta dake rufe cikin bak’ar safa... “A sakashi yayi shiru na har abada... A b’atar dashi kaman yanda aka b’atar da sauran..!!” Waziri ya kuma takowa kad’an, shiru na d’an dak’ik’ai suka gifta “Ba abu bane mai sauk’i duba da cewa Mahmood yana nan cikin Masarautar nan a halin yanzu, amma bakida damuwa Allah shi taimakeki... Zan kula da wannan..!!” Giwa ta juyo tana dubansa murmushi saman fuskarta, lokaci guda ta tako daidai gabansa su duka biyun suna duban juna cikin idanu murmushi kwance saman guskokinsu.... K’wank’wansa k’ofan da suka sinkayo ne ya sanya Waziri komawa da baya kad’an ya wani risina kaman mutumin arziki yayinda Giwa ta k’arasa saman kujera tai zamanta... Jakadiya ce ta shigo cikin d’ingishi ga fuskarta gaba d’aya a kumbure sai tururin man zafi ne Ke tashi a jikinta... Waziri yaima Giwa sallama yayinda Jakadiya ta k’araso tana mai gaida Waziri... Kallo guda Giwa tai mata ta ayyana cikin zuciyarta lallai Jakadiya ta daku wajen mahaukaciyar nan, amma ya suka iya haka dole zasu sake komawa har Izzatu ta bud’i baki ta sanar dasu yanda zasu sami Saudatu kafin tayi ajalin mulkinta... Jakadiya ta zube da k’yar tana nishi take gaida Giwa... Giwa ta amsa a dake ko sannu da jiki Jakadiya bata sami darajan wannan ba wajen Giwa... Murya a dake Giwa Ke fad’in “Jakadiya wajen Izzatu muka nufa..!” Gaban Jakadiya ya yanke ya fad’i, ta d’ago kumburarren idanunta tana duban Giwa tsoro dabaibaye saman fuskarta “Allah shi baki yawan rai matar nan fah zata iya kisa... Anya bazamu k’yaleta..” Batakai aya ba Giwa ta aika mata wani irin muguwar kallo, lokaci guda take furta “Yaushe kika fara sanar dani abinda ya kamata nayi Jakadiya...?!” “Tuba nake Allah shi taimakeki... Ayimun aikin gafara..!!” Ta k’arashe tana mai sadda kai... Giwa Ta kauda fuskarta gefe tana mai furta “Zamuje muga Izzatu daren yau dan haka Ki shirya...!” ‘Yan hanjin Jakadiya suka kuma kad’awa, cikinta ya bada wani sautin k’ara, Allah ya gani ko sunan Izzatu taji an ambata yanzu sai gabanta ya fad’i... Tamkar ta kurma ihu haka ta daure tana amasawa Giwa murya cikin inda inda.... Kana ganin Jakadiya kasan ba har cikin zuciyarta take maganar ba akan dole takeyi... ** Tafe yake cikin mota hannunsa duka biyu saman steering wheel, har lokacin itada Fu’ad yake hangowa cikin idanunsa, maiyasa tunanin ya kasa barin zuciyarsa, maiyasa suka kasa b’ace masa daga k’wayan idanunsa... Maiyasa ma abin Ke damunsa in a any case...! Ya d’an fuzar da fuci kad’an yana mai dukan steering wheel da hannunsa maras ciwon.... Yana k’ok’arin saka trafficato kenan ya d’ago idanunsa yana duban mirror nan ya hangi wata mota tamkar tana biye dashi... Idan bai b’ata gani ba wannan motar tun fitowarsa daga masarauta take biye dashi... Speed ya rage kad’an kana ya canza hanya... Yana ganin mai motar ma yai slow kad’an yana k’ok’arin juyawa... Mahmood ya murmusa kad’an yana mai ci gaba da driving d’insa... Kai tsaye gidan Turaki ya nufa ya kirawo Turakin yace dashi gashi nan tafe ya fito haraban gidan kawai ya jirasa dan ba shiga zai ba... Turaki ya fito waje yana jiran isowar Mahmood.. Jim kad’an Mahmood ya k’araso, Turaki ya isa da kansa ya bud’e masa gate... Mahmood ya shigo cikin gidan yai parking motarsa a parking lot... Turaki ya nufo garesa yana tambayarsa meke faruwa... Dubansa Mahmood yai yace “Bani car keys d’inka...” Turaki ya dubesa da mamaki saidai baice komai ba ya nufi cikin gidan, Jim kad’an ya fito da key ya damk’a masa... Mahmood ya amsa cikin sauri kana ya nufi ma’ajiyan motar Turaki.. Turaki ya d’an k’araso yana tambayarsa meke faruwa Kaikaitowa Mahmood yai yace “Kaikam zamuyi magana idan na dawo, just make sure mota ta bata fice daga cikin gidan nan ba..!” Jinjina masa kai kurum Turaki yai yana mai furta “Do you want me to come with you..?” Girgiza masa kai kurum Mahmood yai yace “Kar ka damu kaidai kawai kayi yanda nace...” Turaki ya jinjina masa kai yana mai masa fatan sauk’a lafiya... ** Mahmood yana fitowa daga gidan Turaki bai zarce ko ina ba sai asibiti wajen Baba Wambai kaman yanda likitan ya sanar dashi cewa Baba Wambai ya farka amma sunan Mahmood d’in kurum yake ambata tinda ya farfad’o shisa bai kirawo kowa ba sai shi... Mahmood ya k’araso cikin sassarfa yanda Likitan tuni ya tareshi... Tare suka nufi cikin d’akin Mahmood na tambayarsa ya jikin Baba Wambai... Suna shiga d’akin ya hango Wambai kwance idanunsa na kallon sama... Mahmood ya k’arasa cikin sauri yana ambaton sunansa... Lokaci guda yakai hannunsa ya dafa saman na Wambai yana mai furta “I’m here Baba...!” Baba Wambai da idanunsa Ke duban sama a hankali yake kuma ambato sunan Mahmood da k’yar cikin muryarsa da bai fita sosai tamkar ta ‘yan koyo, lokaci guda yake k’ok’arin ciro wani takarda k’asan matashinsa... Mahmood yai masa K’uri yana duban abinda Baba Wambai keyi... Lokaci guda ya d’ago hannunsa dake tsananin rawa rik’eda wata ‘yar takarda ya aza saman hannun Mahmood.... Mahmood ya rik’e takardan yana juyawa a hankali daidai sanda Majidad’i da mahaifiyarsa suka shigo d’akin a kid’ime.... Saidai shigowarsu Keda wuya Wambai ya soma wane irin numfashi tamkar ransa zai fice cikin jikinsa..... Dr ya k’araso da sauri yana mai umartansu da su fice su basu waje domin su duba jikin Wambai.... Majidad’i kuwa sai fuzga yake yana ambaton sunan mahaifinsa... Nurses sai turasa waje suke yana tarjewa... Mahmood ne ya kamo hannunsa yana k’ok’arin fitar dashi yayinda Majidad’in ya d’ago jajayen idanunsa yana duban Mahmood cikin wane irin huci.... SameenaAleeyou 📚 [7/28, 9:43 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *37* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Turaki yai turus yana duban Mahmood da ya koma tamkar babu laka jikinsa... Lokaci guda kuma yai saurin basa hanya yana fad’in “Shigo daga ciki Your Highness...!” Babu musu Mahmood yasa kai ya shigo cikin parlorn ya k’arasa ya zauna saman kujera, har lokacin bai iya ceda Turaki komai ba... Glass of water Turaki ya mik’awa Mahmood d’in yana fad’in “Have some water..” Nan ma babu musu ya amsa ya kurb’a kad’an... Turaki ya k’arasa ya zauna saman kujera mai kallon na Mahmood d’in.... “Talk to me Your Highness... Meke faruwa..? Ya jikin Baba Wambai..?” Sumarsa ya shafa da duka hannayensa biyu had’ida fuzar da fuci a hankali “Dole na bar cikin asibitin Turaki...That idiot almost creates a scene there regardless of his father’s condition....!” “Kana nufin Majidad’i...?” “Who else..!” Ya bashi amsa yana mai kuma kurb’an ruwan... Fuzar da fuci kad’an Turaki yai sai kuma yace “Allah dai ya baiwa Wambai lafiya ya tashi kafad’unsa, jikina na bani ta hanyarsa zaka sami wasu amsoshin da ka jima kana nema...” Bai rufe baki ba Mahmood yakai hannunsa cikin aljihu tamkar wanda ya tina wani abu, nan ya ciro takardan da Wambai ya damk’a masa ya shiga warwareta... Turaki yai masa K’uri yana duban yanda yake ware takardan... Tas ya warware yana duban hoton zanen gida tamkar na sarauta.... Ya jima yana duban hoton yana k’arema zanen kallo... “What’s that..?!” Turaki ya tambaya... Ba tareda ya amsa masa ba ya mik’a masa zanen... Turaki ya amsa yana juya zanen mai wahalan fasaltuwa... Ya d’ago ya dubi Mahmood “Ina ka sami wannan...?” “Wambai ya bani before na bar asibitin...!” Turaki yai shiru yana mai kuma duban zanen.. “Kaman ginin gidan sarauta..” ya fad’i yana mai kuma juyawa... Mahmood ya jinjina masa kai alamun tabbatarwa... “Bansan mai yake nufi da dank’a min wannan zanen ba, amma koma menene nufinsa nasan zanen nada matuk’ar mahimmanci..!” Turaki ya jinjina kai yace “K’warai kuwa,and probably it might link you to all the answers you’ve been looking for...” Mahmood ya dubesa kad’an kaman zaice wani abu sai kuma ya linke zanen ya tura cikin aljihu, ya d’ago ya dubi Turaki “Ya labarin neman Jafar... Have you found something yet...?” Ya girgiza masa kai a hankali “Dik yanda nake tunanin abin zaizo da sauk’i ya wuce haka... But kar ka damu ina nan ina bincike...” Mahmood ya kuma jinjina kai a hankali... Turaki ya d’an kuma muskutawa yace “Wai mai ya faru ka aje motarka a gidan nan ka fita da tawa..?” Dubansa da gefen idanu Mahmood yai yana mai kuma kurb’an ruwan dake hannunsa, saida ya kwashi wasu dak’ik’ai kana yace “I noticed Someone was following me... Dole nai branching a gidanka dan ya rasani... I’m sure ko wanene Ubangidansa yana can yana basa bad news..!” Turaki ya murmusa kad’an yana mai duban Mahmood da har lokacin juya cup d’in dake hannunsa yakeyi ya k’urama waje guda idanu... Ba komai yake hangowa ba face Fu’ad da Muhibbah... Ya d’an lumshe idanunsa a hankali had’ida fuzar da fuci lokaci guda yake kauda fuskarsa zuwa wani b’angaren... Sosai yake so ya yakice tinanin amma ya kasa... Gyaran murya kad’an Turaki yai yace “But your Highness are sure babu wani abu dake damunka kuma... You seemed preoccupied..” Mahmood ya dubesa kad’an ya kuma kauda kai gefe, bayan shud’ewan wasu dak’ik’ai ya mik’e yana furta “With everything that has been going on you still ask me that question..... I’ll go ahead Zamuyi magana anjima... Keep me posted idan akwai abinda ya canza regarding the search for Jafar...” Turaki ya jinjina masa kai a hankali yana mai furta “An gama Ranakashi dad’e...” Har saida yakai k’ofa ya juyo yana furta “Aff kaga na mance ban tambayi Madam da yara ba...” Turaki ya murmusa kad’an yace “Daga baya kenan Your Highness, bayan kayi nisa duniyar tunanin Gimbiya Raheema.. Toh Madam da yara duk suna lafiya, gobe suke cika sati guda a Jalingo, inaga cikin satin nan zanjeni na d’aukosu dan duk gidan ya min girma gwara su dawo hutun ya isa haka...” Sai wannan lokacin Mahmood ya murmusa kad’an yace “Ashe dai kaid’in gawro kake...!” Yai maganar yana k’ok’arin had’o kalaman wanda daji kasan bai saba ba... Turaki ya murmusa kad’an yana mai mik’ewa tsaye danyiwa abokin nasa rakiya, lokaci guda yake furta “Na shigo layinku Rankaidad’e for the time being muji yanda kukeji tunda kak’i kaba da himma kan batun Auren nan naka...!” Yai maganar yana sosa kai... Mahmood dai murmusawa kurum yai without saying a word... Turaki ya kasa gane cewa shid’in ba aure ne ko soyayya ne ya dawo dashi ba... Yanada babban dalilinsa, dalilin kuwa shine to find answers and get justice ga wad’anda aka zalunta cikin Masarautar.... ** Wani jahilin mari Waziri ya kuma sauk’ewa d’an Aiken nasa wanda Ke bibiyan Mahmood... “Ashe kai shashasha ne ban sani ba, ta yaya Mahmood d’in zai b’ace maka... A iska yake tafiya kokuwa....!” D’an Aiken Waziri ya dafe k’uncinsa yana sosawa sabida zafin marin lokaci guda yake fad’in “Allah shi taimakeka wllhi nemansa nayi na rasa nadai ga kaman wani gida ya shige daga nan ko k’yallin motarsa ban kuma gani ba...” Waziri yaci gaba da sakin fuci yana aika masa jahilin kallo... “Tashi ka b’ace min a nan kafin nai maka horonda ruhinka zai gaza d’auka...!!” A d’ari d’an Aiken ya mik’e a guje yana mai ci gaba da sosa fuskarsa... Waziri ya dafe kumkuminsa da duka hannayensa biyu, Ta yaya zai soma sanar da Giwa wannan batu... Inaa ko kusa bazai sanar da ita Sun sami mishkila ba gwara ya bada himma a k’ok’arin kawarda Ubandoma da suke k’ok’arin yi... Buge babbar garensa yai ya shige cikin sauri tamkar wani zai kifa k’asa... ** Yazeed yai K’uri yana duban Majidad’i dake tsaye gabansa yanaci gaba da sakin fuci “You mean my brother was here...?!” Ya tambaya yana duban Majidad’in... “Maimaita maka kake so na sakeyi... Wllhi idan mahaifina ya mutu alhakin mutuwansa nakan Mahmood ne... Shine ya kashe Wambai...!” Ya k’arashe cikin tsananin fuci... Yazeed ya jinjina kai cikeda jin dad’i yace “Zuwa yai to finish what he started... To kill Wambai... Kar ka damu kaji da mahaifinka ni zanji da wancan munafukin Hadimin Mahmood d’in ya k’arashe yana mai d’an bubbuga kafad’ar Majidad’i... Suna tsaka da zancen ne kaman daga sama suka sinkayo kururuwan Innani tana fad’in ta shiga uku ta mutu ta lalace Sun kashe mata miji..! Yazeed da Majidad’i suka dubi juna a tare... Babu shiri suka fad’a cikin d’akin Majidad’i kaman zai kifa k’asa yake ambato mahaifinsa.... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Dukkanin mai rai mamaci ne, yanda akazo haka wata rana dole a tafi duk daren dad’ewa, koda anaso koda ba’aso idan wa’adi yayi dole bawa ya komaga mahaliccinsa.. Allah ka bamu k’arshe mai kyau Ameen..! Koke koke sukaci gaba dayi cikin asibitin, yayinda Yazeed ya zame jikinsa ya fice daga cikin asibitin... ** A can Fada kuwa tun bayan dawowan Mahmood gida ya aika ai masa kiran Fu’ad... Yana zaune parlornsa yana duba mail d’insa da ya jima baibi takansa ba sabida abubuwa dake kan faruwa a Masarautar Fu’ad yai sallama ya shigo... Idanunsa naga computer dake bisa teburi gabansa ya amsa sallaman Fu’ad d’in had’ida masa izinin zama .... Fu’ad ya furta kalaman godiya kana ya isa ya zauna a d’arare dan harga Allah mugun nauyin Yayan nasa yake tamkar wani mahaifinsa... Shiru ya d’an ratsa tsakani Mahmood naci gaba da abinda yake bisa computer... Sai bayan kaman ahud’ewar wasu dak’ik’ai Mahmood ya kashe computer d’in had’ida zame farar tabarau dake mak’ale fuskarsa wanda ko ba’ace Kai tsaye zaka iya cewa na k’ara k’arfin gani ne... Hakan ya baiwa Fu’ad daman zamowa kad’an daga cikin kujera ya gaida Mahmood d’in... Babu yabo babu fallasa ya amsa masa kana ya soma masa tambaya gameda sabon karatunda bai jimada farawa ba “Ya karatun naka... Kanadai yi koh...?” Yai maganar yana mai daidaita zamansa cikin kujera Fu’ad ya jinjina masa kai alamun tattabatarwa kana ya k’arada “Alhamdulillah Yaya jiya na kammala registration..” Jinjina masa kai yai kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Yayi kyau...!” Shiru ya d’an ratsa tsakani kafin Mahmood d’in yai gyaran murya kad’an yace “Fu’ad I want you to concentrate on your studies for now... Banda maganan mata da abokai barkatai, ba komai zasu haifar maka ba face distraction....Priorities your studies first... Ka fahimta..?” Ya k’arashe yana mai tsare Fu’ad d’in da idanu... A hankali Fu’ad Ke jinjina masa kai “Na fahimta Yaya... And in sha Allah this time around I’d not disappoint you, zanyi iyaka k’ok’arina naga nayi graduating da yardar Allah... But Yaya wani hanzari ba gudu ba...!” Mahmood ya d’ago yana dubansa.. Kafin Fu’ad ya sami zarafin magana Sarkin Gida ya shigo a firgice had’ida zubewa k’Asa yana furta “Tuba nake Allah shi taimaki ‘ya’yan Sarki.. A gafarceni na shigo babu izini Babban Al’amari Ke tafe dani...!” Yarima Mahmood yace “Fad’i damuwarka Sarkin gida meke tafe dakai...?” Sarkin gida ya kuma risinawa yana mai yarfe gumin goshinsa yake fad’in “Allah shi taimakeka Wambai ne...!” Baikai aya ba Mahmood ya mik’e tsaye zunbur yana furta “Ya jikin Wambai...?” “Allah shi taimakeka Wambai dai Allah yayi masa cikawa....!!” Ya k’arashe yana mai karanto addu’o’i ga Wambai d’in... Hannayensa hard’e Ta baya ya lumshe gajiyayyun idanunsa yana mai furta Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un cikin zuciyarsa... Fu’ad ma ambaton Allah ya somayi yana mai jinjina lamarin... Take Yarima Mahmood ya d’au wayar salulansa saman center table ya nufi k’ofa babu shiri lokaci guda yake ceda Fu’ad “Call your brothers Yazeed and Jamal, and please ka shiga ka sanar da Maami calmly...” Fu’ad ya jinjina kai yana mai furta “Okay Yaya... Right away...!” Mahmood ya kuma duban Sarkin Fada yace maza a sanar da ahalin Fada shi ya wuce gidan Baba Wambai.... Sarkin Fada ya amsa yana mai masa addu’an sauk’a lafiya had’ida karanto addu’o’in neman rahama ya Wambai... Yana tafe ya kirawo Turaki ya sanar dashi, babu b’ata lokaci Turakin yace su had’u can gidan Wambai d’in.... Daga can Sarkin Mota ya hangoshi ya taso a guje ya nufosa yana masa fadanci yake fad’in “Allah shi baka yawan rai Ka baiwa Sarkin mota izini ya tuk’a ka rik’e sitayari(Steering) ba naka bane... Kokuma d’aya daga cikin drebobin gidan ya tuk’a Allah shi taimakeka... Balle ma kaid’in Sarkin Mota shi yafi cancanta ya jaka... Godiya nake Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe yana mai bud’ewa Mahmood d’in owners corner... Shidai kawai shigewa motar yai ba tareda ya tsaya sauraren Sarkin Mota ba... Bafaje guda d’aya ya shige gaban mota...Kankace mai Sarkin mota ya jata sun fice cikin Fada.... A can k’ofar gidan Wambai suka tadda su Waziri Hakimi Galadima Jarmai da dai sauransu.... Sanda Mahmood ya iso suka soma gaisawa suna masa ta’aziya had’ida sanar dashi Wambai na cikin ana masa sutura... Fitowar Majidad’i tareda Yazeed kenan sukai tozali da Mahmood.. Ganinsu su biyu a tare sosai ya baiwa Mahmood mamaki, ya akai har Yazeed ya sani ya rigasa k’arasowa kuma Sarkin Fada mashi ya soma sanarwa... Toh Wai ma ya akai yaga Yazeed da Majidad’i a tare... Wata zuciya tace rasuwa akai so ba komai bane dan ka gansu tare... Mutuwa na sa a aje duk wani gaba da k’iyayya a gefe... Majidad’i sai aika masa muguwar kallo yake yayinda Yazeed ya k’arasoga su Galadima yana sanar dadu an gama shirya Wambai... Mahmood kaw k’arasawa wajen Majidad’i yai ya masa gaisuwa dukda cewa ba wani amsa sa yai ba... Isowar Turaki dasu Fu’ad su Jamal dadai wasu tsiraru daga cikin tawagar Fada suka d’unguma zuwa cikin gidan gaba d’aya sukaima iyalan Wambai gaisuwa... ** Kasancewar hankulan mutanen gidan ya karkata zuwa rashin da akai ga d’aukacin Masarautar hakan sai ya baiwa Muhibbah dama domin ta binciko zanen da takeda tabbacin Jamal ya d’aika daga wajen Umaima.. Sashen Jamal a kulle yake gashi wannan shine damarta na k’arshe dan batasan sanda zata sake samun dama irin wannan ba... Mayafin kanta Ta cire Ta had’a da d’ankwalinta tai majajjawa ta jefa sama nan ta samu kuwa ya kama... Tuni Ta soma k’ok’arin haurawa sama da igiyar data k’ulla dikda cewa k’iris ya rage bata zulo k’asa ba... Cikin sa’a da ikon Allah ta samu ta dafe jikin gini ta k’arasa haurawa da k’yar tana mai tsananin haki... Ta koma gefe tana maida numfashi tana duba hannayenta yanda Ta kukkuje... Cikin sauri Tai azaman tashi had’ida kakkab’e jikinta Ta bud’e sliding door da zai sadaka da cikin d’akin Jamal daga nan sararin shak’atawa dake a saman nasa... Cikin sand’a take gudanar da al’amran nata... D’akin Ta soma k’arewa kallo kafin ta soma binciken drawers tana duba ta yanda zata sami wannan zanen... Drawers da dama ta bincika bata samu ba saidai tana janyo wani drawer dake a k’Asa gabanta ya yanke ya fad’i, hannunta na tsananin rawa take janyo abinda Ta gani cikin drawer d’in... Farin k’yalle Ta gani da shatin jini jiki... Jikinta bai ida mutuwa ba saida taga Fararen k’yallayen har guda goma sha biyar ne ko wanne da shatin jini a jiki.... Sosai jikinta Ke tsananin rawa tana mai ci gaba da k’arema k’yallayen kallo.. Gabanta ya kuma tsinkewa ya fad’i sanda taga ko wani k’yalle d’auke yake da suna daga k’asansa... SAUDATU shine sunan data hanga jikin k’yalle na k’arshe wanda shima d’auke yake da shatin busasshen jini.... Take ta rintse idanunta had’ida toshe bakinta da duka hannayenta biyu jin wane irin kuka mai k’arfin gaske na zuwa mata.... Ta koma gefe guda ta tak’ure sosai tana kuka mai tsuma zuciya.... Abubuwan da suka faru da ita shekarun baya sukaita dawo mata... Da k’yar ta iya saita kanta tai saurin tattare k’yallayen ta maidasu yanda ta samu... Har ta saduda bazata sami hoton zanen ba dan gara tai ta fice kafin a taddata cikin d’akin komai ya rushe mata... Kaman ance ta d’aga bakin katifa nan taji ta kamo alamun abu... Tana janyowa kuwa taga frame d’in ne... Sauk’e deep breath tai kana tai saurin ciro wayarta ta soma d’aukan hoton zanen... Sauri sauri take k’ok’arin maidawa... Tana shirin ficewa ne taji alamun ana haurowa saman babu shiri Ta koma da baya k’irjinta naci gaba da bugu... Ta rintse idanunta tana karanto addu’a cikin zuciyarta... Muryar Giwa ta sinkayo cikin fad’a fad’a tanaima Jamal d’in magana shi kuma yak’i tsayawa ya saurareta sai haurowa sama yake... D’aki ya shigo rai a matuk’ar b’ace kafin ya maida k’ofan Giwa ma ta bangaji k’ofan ta shigo tana furta “Ka saurareni nace Jamal.... Kana jina koma wacece budurwar taka ka aje maganar soyayya ba yanzu ba na fad’a maka sai babu adadi akwai shiri na musamman da nake maka...!” Cikin tsananin k’unan rai yake dubanta kana ya girgiza cikeda rashin yarda da kalaman dake fitowa daga bakinta “Har yaushe kenan Maami... Har yaushe zanyita zama a haka... Maami girma nake ba k’ank’ancewa nake ba... I want to start my own family, na rok’i arzikinki Ki k’yaleni haka nan... Ya isa haka please..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o... Giwa ta k’araso ta rik’o hannayensa cikin rawar murya itama take furta “Zakai naka family d’in d’ah nah believe me... Kawai so nake ka k’ara hak’uri kaji...!!” Ya d’ago rinannun idanunsa yana dubanta, lokaci guda yake sakin murmushin da za’a iya kira da na takaici “Oh really..! Na k’ara hak’uri... Wai mai kike tsoro Maami... Na fad’a miki ko nayi aure bazan daina miki biyayya ba ki k’yaleni nayi aurena kafin na sanar da Ya Mahmood cewa kin hanani aure...!” Saurin toshe bakinsa tai tana mai furta “Kul ahir d’inka, na haneka... Idan ka sanar da Mahmood shikenan asirinmu ya tonu kasan shi bazai fahimci komai ba... Toh naji kanaso kai aure wacece matar daka samu... D’iyar wace masarauta ce..? Ko kuwa d’iyar wani mai mulki ne...?” Jamal ya saki murmushi a hankali yana mai dubanta kan ya isa saman gado ya zauna “Maami kinfi kowa kusanci da ita...” Giwa ta gyara tsayuwarta tana mai dubansa “Ban fahimceka ba.. Wacece ita..?” Murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake furta “Your niece Umaima...!” K’iris ya rage Giwa batakai k’asa ba... Tashin hankali ana wata ga wata... Umaima dai... Umaima Jamal Ke so...Take annurin fuskar Giwa ya d’auke cak... Ta shiga nunasa da yatsa tana mai furtawa da k’yar “Koda wasa kada ka kawo min wannan rainin hankalin a gidan nan... Bazaka auri Umaima ba.... Na gama magana...!” Tana ida fad’in haka ta fice fuu tamkar zata tashi sama... Jamal yaci gaba da sakin fuci yana mai jifa da pillow... Lokaci guda ya mik’e ya nufi bathroom... Muhibbah dake mak’ale bayan cottons Ta fito a hankali tana goge gumin dake goshinta... Cikin sand’a tabi Ta hanyar data shigo.... Shakka babu ta bangaji tubalin flower Wanda hakan ya janyo hankalin Jamal... Babu shiri ya fito yana lek’en meke faruwa... A hankali yake bin alamun k’fafu har ya iso yanda ya jiyo sautin... Baiga kowa ba amma yaji alamun fad’uwan abu.... Yai saurin saurin isa jikin gini yana lek’a k’asa.... Ya k’urama waje guda idanu yanda ya tsinci k’aramin k’yalle kaman an fincika ne ya rage saura... D’aukan k’yallen yai a yatsun hannunsa yana juyawa a hankali.... Idanunsa suka kuma sauk’a kan alamun shatin jini yanda ta kuje gwiwar hannunta... Jamal yai saurin k’arasawa had’ida k’urama wajen idanu... Hannu yakai ya d’an shafi jini yana duba... Tabbas jini ne... Kenan hakan na nufin wani na bibiyarsa a Masarautar... He needs to find out koma wanene...! Ya murmusa kad’an yana mai furtawa a fili “You chose the wrong prince.. Ko wanene kai I’d hunt you down myself...!!” Ya k’arashe yana mai gimtse fuska had’ida sakin huci... ** Tareda yaran Sarki AbdulJabbar gaba d’aya akai komai idan ka cire Jamal wanda ya tafi amsa kiran mahaifiyarsa Daga bisani aka kai Wambai cikin Fada yanda ake bisne sarakuna da ‘ya’yayensu nan aka bisne Wambai... Kowa ya watse aka bar Mahmood da Majidad’i suna tsaye kan k’abarin suna addu’o’i ga Wambai... Majidad’i ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Mahmood... Murmushi ya saki da gefen bakinsa yana mai furta “Aikin banza kenan idan kana tunanin add’u’anka zai isaga mutumin da kai ajalinsa... Da zaka matsa daga kan mahaifina da ya fiye min komai domin tsayuwarka a nan ba amfanansa da komai yake ba... Kuma bari kaji na sanar dakai Billahillazeem sai na d’au fansar mutuwar mahaifina... Kuma sai na amshe mulki ya koma gidanmu koda hakan zai zamto abinda zan aikata na k’arshe kenan a rayuwata..!!” Daga haka sa kai yai ya shige cikin tsananin huci tamkar zai kifa k’asa... SameenaAleeyou 📚 [7/30, 7:10 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *38* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Da idanu Mahmood ya rakasa har ya b’acewa ganinsa kana ya maidoda dubansaga k’abarin Baba Wambai, abubuwa ne jibge cikin zuciyarsa da zaiso amo dasu amma saidai babu halin yin hakan... Ya kuma lumshe idanunsa a hankali kana yasa kai ya nufi k’abarin mahaifinsa wanda ratan dake tsakaninsa dana Wambai kad’an ne... Ya jima yana tsaye wajen yana karantowa mahaifinsa addu’a kana ya nufi na matarsa itama addu’an yai mata had’ida sauran mutattun dake kwance wajen cikin harda kakanninsa... Daga nan fitowa yai ya nufi sashen Giwa yanda ya tadda ta fito tana shirin tafiya Gidan Wambai Jakadiya na biyeda ita da kumburarren fuska sai muk’arabbanta na cikin Fada dake take masu baya, Mahmood na k’arasowa suka zube suna kwasan gaisuwa, Jakadiya sai faman b’oye kumbararren fuskarta take cikin mayafi... Mahmood ya kuma duban Jakadiya dake ci gaba da k’ok’arin janyo mayafi tana kare fuskarta... Sunanta ya ambato wanda ya sanya gabanta fad’uwa... Cikin ‘yar daburcewa Jakadiya Ke k’ok’arin amsawa tana mai kuma risinawa “Allah shi taimaki Yarima mai jiran Gado...!” Mahmood ya gyara tsayuwarsa kad’an “Jakadiya mai ya sameki... A ina kika samu rauni...?” Jakadiya ta d’an saci duban Giwa dake jifarta da muguwar kallo... K’ok’arin saita kanta tai had’ida furta “Allah shi baka yawan rai k’aramin had’ari na samu amma da sauk’i...!” Yai shiru tamkar mai nazari sai kuma yace “Likita ya dubaki....?” Wannan karon Giwa ce ta basa amsa da fad’in “Karka damu Sadauki lafiya lou take wannan raunin ba komai bane, na riga masa likita ya dubata...” Jakadiya ta had’iyi k’uncinta jin abinda Giwa ta gama fad’iwa Mahmood, lallai ta yarda Giwa tayi nisa a makirci tinda har ita da take ta hannun damarta bata k’yale ba... Jinjina kansa kad’an Mahmood yai had’ida mata fatan samun sauk’i Giwa na fad’i masa zasu wuce gidan Wambai gaisuwa... Jinjina kai yai cikeda girmamawa yace a sauk’a lafiya... Tawagar Giwa suka sa kai ana ci gaba da wasa Giwa duk wani taka k’afarta da zatai a k’asa.. ** Video call yau d’in yaji ya kirata sabida kewarta da yai sosai, yana zaune Office d’insa saman kujerarsa na duba marassa lafiya yai mata K’uri ta fuskar wayar nasa yanda take ci gaba da goge gwiwar hannunta data karje with cotton wool... Lokaci guda take ci gaba da fad’in “I couldn’t believe what I saw either, I mean... Mai ya kawo sunana rubuce jikin k’yalle, and what worries me the most shine k’yallen da sunana Ke rubuce bisa anyi crossing... Mai ahalin AbdulJabbar suka aiwatar da sunana...” Katseta Ansar yai da fad’in “Wait what’s that... Are you injured...?” D’an fuzar da fuci tai a hankali tana mai gyara zamanta take kuma duban hannun nata kana tace “Oh! Just a small scratch but I’m okay... Kar ka damu likita...” Fuzar da huci yai a hankali yana mai kauda kai gefe cikeda damuwa “Hibbah bamu yi haka ba... You promised me you won’t put yourself in harm ways.. You promised me you’d take good care of yourself... Toh mai nake gani yanzu...!” Ya k’arashe cikin d’an tsawatarwa... Fuzar da huci tai a hankali kana tace “I’m sorry..Okay, it won’t happen again...I’d be more careful next time...Yayi maka..!” Ta k’arashe cikin raunin murya... Shafa fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kana yace “Do I have a choice..!” Dariya yaso bata ta d’anyi kad’an yayinda Ansar ke fad’in “Aw Wato ma dariya na baki...!” Muhibbah tace “Gani nayi Likitana ya fini damuwa da lafiyata...!” “Of course you’re right... Na fiki damuwa da lafiyarki... My next patient zai shigo Hibbah.. Do you want me to attend to them...?!” Yai tambayar cikin kashe murya... Murmusawa tai kad’an tace “Likita bakada dama... We talk later.. Take care.. Bye..!” Katseta yai da fad’in “I love you...!” Murmushi kurum tai cikin tsananin sanyin jiki wanda ita kanta bata San dalilin jin hakan ba kana Ta katse kiran ta koma cikin kujera ta zauna sosai tana mai lumshe idnunta.. Abubuwa ne da dama cunk’ushe cikin zuciyarta... ** A can gidan Wambai kuwa yanda aketa karb’an gaisuwa Gimbiya Zeenatu ma da tata tawagar Sun halarta... Raheema sai faman aikawa Juwariyya muguwar kallo take, dik itace ta janyo Mahmood yanzu bai kulata, gashi ta kula sam maganinsu baiyi tasiri akan Mahmood d’in ba tinda gashi shiru shiru har yanzu babu wani canji tun ranan data barbad’a maganin a sashensa... Tai k’wafa tana mai kuma hararan Juwariyya... Ga mamakin Raheema Murmushi Juwariyya Ta sakar mata kana ta tura mata sak’o ta waya _Haba mutumiyar ko gaisuwa babu, ai ya kamata Kimin ta’aziya for old time sakes... How about idan muka keb’e Ta baya, I’ve something special for you..!_ Raheema ta karance sak’on ta kuma d’agowa tana duban Juwariyya dake ci gaba da sakar mata murmushi tana mai mik’ewa tsaye kana ta shige wata k’ofar.. Tana shigewa Raheema ma ta mik’e tana mai gyara mayafinta had’ida satan idanun mutane musamman Su Zuhra da Zahra da Umaima dake zaune daga can gefe... Ta d’an rank’wafo taceda Zuhra “Best bara na d’an amsa waya...” Zuhra ta jinjina mata kai tana mai ci gaba da jan cazbaha dake hannunta Raheema tasa kai tabi k’ofar da taga Juwariyya tabi... Raheema na shigewa Juwariyya ta maida k’ofar ta rufe... Raheema ta finciko wuyan Juwariyya tana fad’in “How dare you... Laifinki ne Mahmood bai kulani yanzu, you messed everything up...!” Fincikewa Juwariyya tai tana fad’in “Ki saurareni Raheema shisa na kiraki wajen nan to make it up to you.. Amma idan bazaki saurareni ba fine kina iya tafiya...!” Ta k’arashe cikin huci... Gyara tsayuwarta Raheema tai tana fad’in “Fine, tell me mai kike son sanar dani... Wani amfani abinda zaki sanar dani zai min...?!” Juwariyya ta murmusa kad’an kana tace “Zai muku amfani both you and Mahmood, it might help you win him back.... Shi kuma Ya Mahmood zai masa amfani yasan yanda zai ya kare kansa da mulkinsa...!” Raheema ta d’an gyara tsayuwarta tana fad’in “Mai kike nufi...?” Juwariyya ta fuzar da iska kad’an kana tace “You know nafi kowa san Ya Mahmood ya d’ale Karagar nan... Banson Yaya na ya d’ale...” Raheema ta katseta da fad’in “Ke naji naji... Just go straight to point da Allah bansan iyayi...!” Juwariyya tace “I saw my brother and Ya Yazeed together at the hospital before my father passed away...!” “So, sai mai dan kin gansu tare..Ta yaya hakan zai taimaka min win Mahmood back...?” Juwariyya ta fuzar da fuci a hankali... “Dad’ina dake baki cin Riban zance Anty Raheema.. Ahalin gidan nan da ahalin Sarki AbdulJabbar basa jituwa anyi masu wannan shaidan, so zai matuk’ar wahala for those two to get along, naji sun ambaci sunan Ya Mahmood, and one thing to be certain of shine ba abin arziki suke k’ullawa ba..They might be planning something against him... Ya kamata ki sanar da ya Mahmood yasan yanda zai fuskanci wad’annan biyun kin fahimta...” Shiru Raheema tai tamkar mai nazari sai kuma ta jinjina kanta tana mai sakin murmushi a hankali... Juwariyya Ta murmusa tace “Na gyara abinda na b’ata I guess...” Kafad’anta kad’an Raheema ta dafa kana tace “Baki tab’a birgeni irin na yau ba... I must say thank you...” Ta k’arashe tana mai nufan k’ofa... Saida ta fice da wasu dak’ik’ai kana Juwariyya ta fice.... Ko ba komai yau ta sami abinda zatai amfani dashi ta karkato hankalin Mahmood zuwa gareta, amma kafin nan ya kamata ta soma shan cikin Yazeed taji mai yake shiryawa kan Yarimanta... Tai k’wafa tana jinjina bak’in zuciya irinta Yazeed wanda har zai kaisa ga halak’a d’an uwansa... ** Yazeed ya kuma gyara zamansa yana duban Ubandoma daketa faman had’iyan abincin da Yazeed d’in ya kawo masa hannu baka hannu k’warya... Ya ida ci yana mai tand’e yatsu yake fad’in “Godiya nake rankashi dad’e shakka babu yau d’in Sun mance dani... Yunwa kaman zai karni sai gashi Allah ya kawoka, Ubangiji ya saka da Alkhairi Rankshidade...!” Yazeed ya katsesa da fad’in “Daina godiya tun yanzu kasan ance komai yanada lada...!” Yai maganar shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa... Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana k’walalo idanu yake duban Yazeed... Yazeed ya kuma gyara rigar kufta dake sanye jikinsa cikin yanayin salonsa da yafeyi idan yana shirya wani mugun abin... “Ubandoma na tabbata ka yarda dani tinda har na baka abinci ka ci without thinking twice... Ba tareda kayi wani tunani ba sabida yunwa dake azalzalanka ka amsa kaci...!” Ya d’anyi fasali yana mai rage girman idanunsa yake furta “Baka tunanin zan iya sanadin rayuwarka yanzu a wajen nan...?!” Gumi ne ya shiga karyowa Ubandoma, ya shiga zaro idanu waje jikinsa na rawa yake furta “Kamin rai Allah shi baka yawan rai... Wayyo na shiga uku ni jikan Tandu inada yara kada ka maidasu marayu Allah shi baka yawan rai...!” Ya k’arashe yana hawaye had’ida had’e hannayensu biyu waje guda alamun rok’o... Murmusawa kad’an Yazeed yai da gefen bakinsa kana yace “Kar ka damu ni ba mugu har haka bane... Abu guda yanzu nakeso kamin shine ka biya ladan abinda na maka yau...!” Ubandoma ya zaro idanu yana fad’in “Mai kenan Rankaidad’e...?” Yazeed ya kuma murmusawa kad’an yace “Da kyau Ubandoma, kai d’in kanada saurin fahimta... Nasan ba Yayana Mahmood bane ya baka umarnin shiga gidan Wambai... Kuma ban damu nasan ko wanene ya kake ma aiki ba, iyakacin abinda na sani shine kaid’in munafukin Mahmood ne... Toh inaso kai amfani da wannan shara taka ta iya makirci da munafunci ka d’aura alhakin dik abinda kai akan Mahmood... Ka sanar da Masarautar nan cewa Mahmood shine bak’on Buzu kuma ya turaka ne domin ka kashe Wambai... Ka fahimta...?” Da tsananin mamaki Ubandoma ke dubansa. Lokaci guda ya shiga girgiza kai yana duban Yazeed d’in yake fad’in “Ta yaya zan soma k’age irin wannan Rankaidad’e... Da dai ka nemi wani abin amma banda wannan...!” Huci kurum Yazeed yake yana dubansa rai b’ace... Lokaci guda ya shak’o wuyan Ubandoma yana fad’in “Kai k’ask’antaccen Bawa, kai kayi kad’an Yarima Yazeed ya nemi wata alfarma wajenka... Umarni kawai zan baka kabi .... Ka fahimta...?!!!” Ya k’arashe yana mai jifada Ubandoma gefe wanda tuni ya zube yana haki had’ida sosa wuyarsa dake masa zogi, sai tarin azaba yake... Yazeed ya d’an yarfe hannunsa kad’an had’ida gyara zaman zobensa da ya kusa ficewa kana ya kuma duban Ubandoma, murmushi ya sakar masa wannan karon kana yace “Idan ma baka goyi bayana kayi abinda na umarceka sanin kanka ne bazasu barka da rai ba... You know perfectly well how they do things here... Bazasu barka ka fita da rai dubu ya faru da haka... Kuma kar ka mance Wambai ya riga ya rasu fitarka a nan a halin yanzu zai matuk’ar wahala...!” Ubandoma ya kuma zaro idanu yana maimaita “Wambai ya rasu...?!” Yazeed ya murmusa yace “Karka damu idan ka bani had’in Kai zan fitar dakai muddin na zama Sarki... Sannan zan baka matsayi mai girma, zan fifitaka fiyeda yanda ba’a tab’a fifitaka cikin Masarautar nan ba... Kawai Kayi abinda na umarceka shikenan ka tsira...!” Ya k’arashe cruel smile d’in nan nasa saman fuskarsa... Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana duban Yazeed da tuni yakai k’ofa.... Ya kuma juyowa kaman zai magana wayarsa Ta d’auki ruri Raheema ce mai kiran nasa... Yana d’agawa daga d’aya b’angaren tace “You and I need to talk... Let’s meet up...!” Bata jira amsarsa ba Ta katse kiran.... ** Zama Muhibbah tai tana kuma warware zanen nan had’ida nazarinsa, nan Ta d’auko wayarta Ta kunna ta had’e zanen tana k’are masu kallo... Babban abinda ya bata mamaki shine duk yanda tai zaton zanen nan abu guda ne ashe ba abu guda bane, sunada salo da tsari iri guda amma Sun banbanta kad’an... Ita kanta bazatace ga difference d’in tai figuring out a halin yanzu ba hasalima sosai kanta ya kuma shiga duhu... Ga dai hikima iri guda anyi amfanida wajen tsara Taswiran amma sun banbanta da juna... Ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya a hankali, ya zatai yanzu... Lumshe idanunta tai a hankali ta tafi duniyar tunanin abinyi... Idan har tana so ta fahimci zanen nan Ta iya warwareta ya kamata ta zaga cikin gidan nan ta k’arewa ginin kallo tunda gida ne na sarauta sannan ta shiga museum na cikin Masarautar nan taga Taswirori na tarihi wala’alla Ta sami wani clue gameda wannan Taswira mai wahalan fasaltuwa da fahimta... Watak’ila Ta iya samun wani HASKE a can Zauren Ajiya na kayan tarihi dake cikin Masarautar... Sauri sauri ta mik’e ta shirya tsaf, tai shiga irinta masu mulki harda Alkyabba, sosai shigar ya amsheta, nan ta fito tana taku cikeda k’asaita irinta masu mulki... Tana tafe take tinanin toh wa zata soma tunk’ara tunda hankalin mutanen gidan gaba d’aya bai jikinsu sabida rashi da aka masu, Toh kodai ta kirawo Fu’ad ne.... Toh amma bataso ake ganinsu tare balle wani yai suspecting wani abu... Kawai ta yanke shawarin tambayan Sarkin Fada... A haraban Masarautar ta tadda wasu bayi ‘yanmata guda biyu yanda ta tanbayesu suyi mata jagoranci zuwaga Sarkin Fada, babu musu bayin sukace Ta biyosu... Muhibbah tasa kai tana tafe biyedasu Can Rumfar Sarkin Fada suka taddashi tareda wasu Fadawan, suna ganinta suka isa sukai mata gaisuwa... Muhibbah ta dubi Sarkin fada tace “Da Allah wani tambaya nake...!” Sarkin Fada yace “Rankidad’e kyakkyawa fad’i tambayarki..!” Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Shin yaushe ne ake bud’e d’akin ajiya na cikin Masarautar nan... So nake nasan wasu al’adu na cikin gidan nan kafin na tafi...!” Sarkin Fada da sauran Fadawan suka dubi juna jin tambayar da tai... Muhibbah ta bisu da kallo gaba d’ayansu yanda suke kallon kallo ma juna... Murmushin yak’e tai wannan karon kana tace “Ah shikenan, Ina tunanin ba ko yaushe ake bud’ewa ba kenan...!” Sarkin Fada yace “Ba haka bane Rankaidad’e Mai kyau, ai Wato idan ba ahalin gidan nan ba Sarkin Fada baida hurumin bud’e miki Ma’ajiyin Gidan nan... Yin hakan zaisa na shiga matsala...!” Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tace “Toh shikenan babu matsala, na gode sosai...!” Har tasa kai ta juya saiga wani bawa guda ya k’araso yayiwa Sarkin Fada magana a kunne... Tana tafe ta sinkayo muryar Sarkin Fada na fad’in “Rankidad’e Mai kyau... Dawo da baya... An umarce Sarkin Fada ya bud’e miki duk wata zaure da kika buk’ata cikin Masarautar nan.... Sarkin Fada yana neman afuwanki...!” Ya k’arashe yana mai baza babbar riga had’ida mik’ewa... Ita dai sai ‘yan waige waige take tana mamakin waye yai umarni da a bud’e mata Zauren Ajiya.... Tafiya mai d’an tazara kad’an sukai kana suka iso Zauren ajiyan kayan tarihi na Masarautar.... Sarkin Fada yasa mabud’i ya bud’e... Ta ware idanunta tana duban dogon ginin mai tsawon gaske da dadd’en tarihi... A hankali tasa k’afarta tana takawa cikin ginin tana duban manyan zanen hotunan bayi da masu sarauta da irin yak’i da akai a shekarun baya shekaru masu yawan gaske na wasu k’arnin.... Ji tai k’ofar mai nauyin gaske ya rufe da ita a ciki, dan bata ankara ba sai jin sautin rufuwarsa tai gashi abinka da tsohon gini mai girman gaske ko ina saida ya amsa... Ta waigo cikin sauri tana duban bayanta, gabanta ya yanke ya fad’i ganinsa da tai tsaye bayanta hannayensa a hard’e Ta baya shid’inma ita yake duba... Yana sanye cikin bak’ar rigar Kufta wanda ya fito da asalin Farin fatarsa, shigar kufta yai gaba d’aya dan harta takalman k’afafunsa bak’ak’en Kuftane da akai masu kwalliya da farin zare mai d’aukan idanu k’warjininsa sai ya cika wajen gaba d’aya....Tai saurin janye idanunta daga barin dubansa k’irjinta naci gaba da bugawa... ** Gimbiya Zeenatu na kishingid’e a parlornta na alfarma bayan sun dawo daga ta’aziyan gidan Wambai Hadimarta ta shigo ta sanar da ita shigowar Yarima Yazeed... Sosai tai mamakin jin Yazeed yazo gaisheta har sahsenta, kodashike ba abin mamaki bane tunda rashi akai gaisuwan ta’aziya ya shigo mata... Tuni Ta basa izinin ya shigo... Ya kuwa shigo cikeda k’asaita, sukai gaisuwa irinta masu mulki kana yai mata ta’aziya... Gimbiya Zeenat taji dad’in shigowarsa tuni aka cika gaban Yazeed da kayan mak’ulashe da tand’e tand’e, ya kuwa zauna sosai kaman wani mutmin arziki, Gimbiya Zeenat ta mik’e ta basa waje dan ya saki jikinsa yaci kayan motsa baki da aka kawo masa.... Haurawarta sama da kad’an Raheema ta fito cikin gayu da kwalliya... Yazeed dake kishingid’e irin zaman masu mulki murza zobban hannunsa kurum yake yana k’arema Raheema dake sauk’owa kallo from head to toe.... *Sak’on gaisuwa mai tarin yawa tareda fatan Alheri gareku msoyana... Sameena na kaunarku a dik yanda kuke..!* SameenaAleeyou📚 [8/1, 8:41 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *39* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tai k’ok’arin tarttaro natsuwarta gaba d’aya, murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskrta “Your Highness... Barka da yammaci.!” Tai maganar tana mai daidaita tsayuwarta... Kaman bazaice komai ba har wannan lokacin, sai dubanta da yake daga nan yanda yake tsaye hannayensa hard’e Ta baya... Gaba d’aya sai tajita ba daidai ba, zuciyarta yaci gaba da bugawa da sauri sauri... Maiyasa yake dubanta haka..? Kodai ya karanceta ne ya soma zarginta... Kai inaa hakan bamai yuwa bane, musamman yanzu data soma samun hanyar da matsalanta zai warware.. She can’t allow someone to get suspicious of her...Tai saurin d’ago idanunta aiki nan idanunsu ya sark’e waje guda.. Fuskar nan nasa tamau... Ta had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’oshi ya kasa shigewa.... Gyaran murya Tai kad’an tana k’ok’arin had’o kalamai saman bakinta “Tuba nake your Highness... Na zaci kowa zai iya ziyartan Zauren ajiya na.....” Burki tai ma kalaman nata ganin ya soma d’ago k’afafunsa yana takowa cikeda k’asaita... Zuciyarta taci gaba da bugawa ganin ita yake nufowa... Tai saurin lumshe idanunta tana k’ok’arin karanto duk addu’an da yazo bakinta... Dai dai gabanta Mahmood yaja ya tsaya har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya yai k’uri ma labb’anta yanda take motsasu a hankali alamun tana karanto addu’a, a hankali yake k’arewa fuskar nata kallo tin daga labb’anta zuwa karan hancinta har zuwa idanunta da suke a lumshe masu cikeda tsoro... Wani irin yarr yaji gaba d’aya illahirin jikinsa... Yanayin da ya jima baiji hakan ba a tsakanin lokacin... A hankali ya janye idanunsa daga barin duban nata, cikin takunsa mai cikeda k’asaita ya soma takawa har ya isa gaban wani k’aton hoto mai k’unshe da zanen mutane cikin shiga irinta mulki da sarauta... Ya kafe hoton da idanu hannayensa hard’e ta baya... “Halittanmu baisha bambam da mutanen da sukazo kafin mu ba, saidai halayya da d’abi’unmu sun banbanta...Wani zamani muke ciki wanda cin amana da yaudara, zalunci da k’eta su sukafi jagoranci sama da kyawawan d’abi’u masu nagarta...!” Ya k’arashe yana mai juyowa... Tinda ya soma magana take k’ok’arin bud’e idanunta a hankali har Ta ida waresu... Daga nan yanda yake tsaye yai gyaran murya kad’an yace “Having curiosity aroused..?!” K’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e tai ta d’ora saman labb’anta “K’warai your Highness... Masarauta mai cikeda d’inbin tarihi da kyawawan d’abi’u had’ida al’adu irin haka... Babu wanda zaiso ya shigo cikinta ya tafi ba tareda ya yi dubi da wad’ann kyawawan hikayoyi da suka aje Martaban Masarautar har Ta kawo tsawon wannan lokaci...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Baisan dalili ba amma tunda ta soma magana yakejin kumatunsa na motsawa kad’an sihirtaccen murmushi da ba lallai ka fahimci hakan ba shine sama fuskarsa tasa... Ya d’an gyara tsayuwarsa yana dubanta sosai, saida yai taku kaman guda uku, sai kuma yaja ya tsaya “You seemed so sure...?!” Ya fad’i yana dubanta.... Ta kuma murmusawa kad’an tana mai k’arasawa jikin wani k’atoton zane mai d’aukeda hoton wani basarake sanye da rawani da alkyabba wanda ko ba’a ce ba kasan dadd’en zane ne... Tasa hannu tana shafa wasu rubutun da akai k’asan zanen da haruffan ajami na Arabic... Lokaci guda taci gaba da furta “An samu Masarautar ne ta hanyar nagartattun mutane wanda jajircewarsu da k’wazonsu had’ida gaskiyarsu da son gaskiyarsu sune suka had’u suka kafa Daular... Kuma da sannu al’umman Masarautar zasuyi fatan magadansu suyi koyi da kyawawan d’abi’u masu nagarta irin nasu... Fata mai kyau a koda yaushe yana tafiya tareda Al’umma nagartacciya ce Rankaidad’e...!” Ta k’arashe tana mai juyowa gareshi... Kai tsaye bazaice ya fahimci duka abubuwan data fad’i ba, amma har k’asan zuciyarsa yake jin kalaman nata.... Ya isa jikin k’atoton hoton ya tsaya gefe da ita, su duka biyun suna duban hoton... Cikin kalmomi da basu shige uku zuwa biyar ba ya fad’i k’arnin da aka kafa Daular a tak’aice... Ta karkato kad’an tana dubansa murmushi saman fuskarta... Lokaci guda tace “Ka iya bada labari your Highness... Kodai History ka karanta...?” Duban da yai mata ya sanyata had’iye sauran zancen nata tana mai furta “Tuba nake Rankaidad’e...!” Baice komai ba sai soma takawa da yai zauren na amsa sautin duk wani aje k’afarsa da zai a k’asa mai cikeda charisma... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai furtawa cikin zuciyarta _Muhibbah nemi abinda ya kawoki kafin lokaci ya k’ure miki.._ Take ta hangi wani dogon shelf d’aukeda manyan takardu da littafai, ta waiga gefe da gefe bata hangi Mahmood ba hakan ya bata daman k’arasawa jikin shelf d’in cikin sauri tana dubawa a hankali... A yayinda shima Mahmood d’in tsaye yake ta bayan shelf d’in yana bincika takardu wanda zai iya kamanceceniya da zanen gidan sarauta da Wambai ya damk’a masa... A tare suka hango wani littafi mai tarihin gaske, ba tareda sun sani ba sai kai hannunsu sukai lokaci guda kowanne cikinsu na son ya d’auki littafin.... K’irajensu ne suka buga sakamakon jin hannayensu da sukai cikin na juna sun sark’afe waje guda... Muhibbah tai saurin zaro idanu waje zuciyarta naci gaba da bugawa.... Hannunsa guda yasa ya matsar da littafan da cikin shelf d’in dan tabbatarwa idanunsa cewa hannunta ya rik’e... Sukai tsaye suna duban juna ta cikin shelf d’in... Muhibbah ce ta soma yunk’urin janye hannunta cikin tsananin rawar jiki, saidai fuzge hannunta da zatai k’atoton ma’ajiyan takardun ya dawo kanta.... Suka d’aga idanu suna duban katakon yanda ya nufota... Tsayuwa kurum tai had’ida dafe kanta tana jiran mai aukuwa ya auku.. Lokaci guda ta saki wane irin k’ara... Bata ankara ba sai ji tai ya bangajeta gefe guda katakon ya fad’o kansa... Muhibbah dake zube gefe dafe bakinta tai da duka hannayenta biyu tana mai kuma firfito da idanunta waje ganin bata ko hango Yarima Mahmood sai k’uran shelf d’in nan da ya fad’o kansa.... Gaba d’aya k’ura ya turnuk’e wajen.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai zuciyarta Ke nanatawa... A d’ari ta mik’e ta nufo wajen tana ambato sunansa amma shiru bai amsa ba, zuciyarta ya kuma tsinkewa... Take taji hawaye na neman ciko idanunta... Ta shiga k’ok’arin janye shelf d’in daga kansa tana kiran sunansa amma inaa shiru babu amsa... Hawaye na gangaro mata take kuma k’ok’arin janye k’atoton katakon da ko motsa sa bata iya yi... A hankali k’uran Ke lafawa yanda Ta soma hango fuskarsa da k’ura ya lullub’e idanunsa a lumshe.... Cikin azama taci gaba da k’ok’arin janye katakon tana furta “Yarima..! Yarima please wake up... Dan Allah ka tashi..!!” ** Yazeed ya kuma relaxing cikin gadon yana mai rakata da idanu shu’umar murmushin nan nasa saman fuskarsa... Raheema ta margino cikin k’irjinsa tana shafa fuskarsa a hankali take furta “You seems to be in a good mood Your Highness... Fad’a min sirrin...” Ta k’arashe cikin salo tana mai fatan ya zayyano mata komai gameda shirinsu shida Majidad’i kan Mahmood cikin zuciyarta... Sumarta yake shafawa a hankali murmushin bai bar saman fuskarsa ba “Well, I’ve every reason to be in a good mood... Soon enough burina zai cika..!” Raheema Ta kuma gyara kwanciyarta sosai tana mai dubansa take furta “Wow... Da gaske.. Ba dai burinka na zama sarki ba..!” Yai murmushi da gefen bakinsa yana mai dubanta da wutsiyar ido wannan karon “Very soon komai a Masarautar nan zai zamto yana k’ark’ashin iko na... Kowa zai zama yana k’asa dani... Sai abinda nace kuma sai abinda naga dama za’ayi... Ciki harda Yaya na Mahmood..!” Ya k’arashe muguwar murmushin saman labb’ansa... Raheema Ta kuma zama sosai tana dubansa lokaci guda tana k’ok’arin karantarsa... “Tell me... Mai kake shiryawa...?!” Da wutsiyar idanu ya kuma dubanta wannan karon ma... “Sabida kije ki fad’awa Mahmood..?” Ta d’an sha jinin jikinta kana tace “Ban gane naje na fad’awa Mahmood ba... Mai kake nufi Zeed..?!” Murmusawa ya kumayi lokaci guda ya mik’e yana mai zura tufafinsa yake furta “Drop the act Princess... You can’t fool me... Na gane nufinki...And believe me bazakiji komai daga bakina ba... Kinyi kuskure da kikai underestimating d’ina... You might be a woman but Prince Yazeed AbdulJabbar ya shige duk makircin wata mace Sweetheart..!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi had’ida zira zobbansa yasa kai ya fice... Gimbiya Zeenat dake lab’e jikin staircase tana ganin shigewan Yazeed ta fuzar da fuci a hankali.. Ta rasa Raheema wace irin kariya ce mai take samu wajen wannan watsettsen Yazeed d’in da ta tabbata ko sarautar ce bazai tab’a yi ba... A fusace Ta nufi d’akin da Yazeed ya fito yanda Ta tadda Raheema na shirin fitowa... Fincikota tai Ta dawo da ita baya tana fad’in “Shige ki Fada’ min uwar mai kuka gamayi Keda watsettsen can...!!” ** Duk iyaka k’ok’arinta Ta kasa janye katakon, gaba d’aya itama ta jigata, tuni ta kwab’e alkyabban jikinta tana k’ok’arin had’o duka k’arfin da Allah ya huwace mata ganin Ta ceci rayuwar Mahmood... Ganin dai bazata iya janye katakon ba ya sanyata saurin nufa k’ofa neman agaji... Saidai wani tashin hankalin shine ta kasa koda motsa k’ofar ne abinka da ginin zamanin da mai aminci.... Ta shiga dukan k’ofan tana kiran taimako nan ma shiru dan yanda ginin Keda matuk’ar zurfi da tsawo zai wuya na waje ya iya saurarenka... Sabbin hawaye suka kuma ciko idanunta, yanzu idan ya mutu nan no one would believe cewa ba ita ta kashesa ba.... She can’t let him die here...! Lokaci guda ta koma da baya tana mai ci gaba da k’ok’arin janye k’kk’arfan katakon mai minci... Da k’yar da nishi ta samu ta d’an matsar da katakon.. Lokaci guda tana mai kuma ambato Yarima, daidai nan Mahmood ya soma tari da atishawa alamun yana fitar da k’uran da ya shak’a.... Muhibbah tai hamdala cikin zuciyarta tana mai ci gaba da k’ok’arin janye katakon take furta “Rankaidad’e ka tashi... Alhamdulillahi... Sannu Rankaidad’e...!” Hannu yasa da k’yar ya matsar da katakon daga kansa yana mai k’ok’arin mik’ewa da k’yar had’ida kakkab’e k’uran dake bisa jikinsa... Sai faman sannu take masa fuska fal damuwa, harda ‘yar murmushin da bata San ya subce mata ba... Ta kuma matsowa kusansa kad’an tanai masa sannu... Ido ya d’ago yana dubanta wanda ya sanyata stepping back kad’an... Lokaci guda yake furta “Are you hurt..? Did something happen to you..?” Saurin girgiza masa kai tai alamun a’a.. “I’m fine your Highness, babu abinda ya sameni... We need to get out of here...” Jinjina mata kai yai a hankali yana mai d’an dafe kansa dake masa zogi had’ida lumshe idanunsa a hankali... Lokaci guda yasa kai ya nufo k’ofa dukda d’an jan k’afafunsa da yakeyi... Tai tsaye tana binsa da kallo daga nan yanda take tsaye... Kaman wacce aka sinkaya tai saurin nufosa tana mai furta “Rankaidad’e..!” A hankali ya kaikaito kad’an yana dubanta, cikin tsananin sanyin murya take furta “Thank you for saving me..!” Baice da ita komai ba sai kallonta da yai na wasu ‘yan dak’ik’ai, lokaci guda ya isa jikin k’ofan ya danna wani b’angare ya tura baya nan k’ofan ya bud’e... Muhibbah taita mamakin yanda ita ta kasa bud’ewa... Sauri sauri ta biyo bayansa kafin k’ofan ya kuma rufewa da ita ta rasa na yi... Sai faman waige waige take, ita kanta batasan biye take dashi ba ta dai San tafiya kurum take... Saida suka nufo kusan sashen Mahmood d’in a haka tana biye dashi a baya Zahra ta habgosu... Ta k’araso da sauri saidai tuni tai turus ganin jikin Mahaifin nata duk k’ura... Ta dubesa ta dube Muhibbah... Zahra tace “Paa mai ya sameka... Daga ina kuke...?!” Sai lokacin Mahmood ya juya ya dubi Muhibbah dake biye bayansa... Jin babu amsa ya kuma sanya Zahra matsowa ta kamo hannun mahaifin nata “Paa are you alright...?!” Baice da ita komai ba sai k’ok’arin sa kai da yai ya nufi cikin sashen nasa... Zahra ta dubi Muhibbah da tai sororo wajen “Aunty Muhibbah meke faruwa... Mai ya sami Paa d’ina...?” “A minor accident, please Ki bashi pain relief... And take care of him...!” Tana ida fad’in haka ta juya cikin sauri ta nufi nata b’angaren har k’afafunta na hard’ewa waje guda... Ga zuciyarta da ya kasa daina bugawa... Zahra ta d’an bita da kallo kana Ta maido da dubanta ga Mahaifinta da tuni ya shige sashensa... Cikin sauri ta take masa baya... ** Raheema dafe da k’uncinta take duban ‘yar uwar tata da ta shafeta da mari mai kyau... Lokaci guda Gimbiya Zeenat Ke fad’in “Sabida Ke bakida hankali shashasha ce gidahuma ko..? Toh bari kiji ban d’auko na kawoki Masarautar nan dan ki shantak’e da ‘ya’yan Sarki ki jaza min abun kunya ba... Kawoki nayi domin ki maido min da Martabata da na rasa cikin Masarautar nan ki auri Mahmood wanda zai kasance Sarkin gobe kin fahimta..!” Ta k’arashe cikin tsananin huci... Raheema ma hucin take sosai “This is who I’m Aunty Zeenat... Ya rage naki ki accepting d’ina yanda nake ko kar kiyi... Baki fini son kasancewa Matar Mahmood ba amma Yazeed nada wani gurbi mai girma cikin zuciyata kuma barikiji na fad’a miki wannan ya zama na k’arshe da zaki kuma d’aura hannunki a fuskata da sunan mari... Wllhi kinji na rantse miki dik sanda kika sake gigin tab’a lafiyata sannan ne zan nuna miki hauka gaskiya ce... Kuma Wllhi sai na sanar da Giwa duk shirinki akan d’anta da kuma Masarautar nan... Dan haka idan kunne yaji jiki ya tsira...!!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice fuu kaman zata tashi sama... Gimbiya Zeenat tabita da kallo shaye da tsananin mamaki... ** Tunda ta iso d’aki ta rasa sukuni, tinanin abubuwan da suka faru sun kasa barin kanta... Bathroom ta fad’a tai wanka da ruwa mai d’umi sosai kana ta d’auro alwala dan magrib ya hararo already... Doguwar riga mai laushi Ta zira kana Ta nufo wayarta yanda yaketa faman ruri... Fu’ad ne mai kiran nata... Bata d’aga ba saima fuzar da fuci da tai a hankali ta zauna gefe tana duban wayar har ta k’arashi ringing d’inta, daidai nan Umaima tai sallama... Zama sukai suna fira har aka soma kiraye kirayen sallan Magrib, nan Umaimar Ke sanar da ita gobe Juma’ar k’arshen wata akwai Royal Gathering kaman yanda aka saba gudanawar duk juma’ar k’arshen wata amma saidai batasan ko rasuwar nan da akai yasa a d’aga ba... Ita kaw Muhibbah da za’a d’aga da hakan yafi mata dad’i dan harga Allah ji tai batason fuskantar yaran Sarkin a halin yanzu musamman bayan ceton rayuwarta da Mahmood yai a yau d’in gaba d’aya sai tana jin shakku can k’asar zuciyarta... Maiyasa take ji Mahmood d’in tamkar mutumin kirki ne... She needs to get her head straight... Ta lumshe idanunta a hankali had’ida tada ik’aman sallah.... ** Bayan an ida sallah a masallaci Galadima, Hakimi, Waziri da kuma Danmaliki suka had’e kansu waje guda suna kuma jajantawa juna rashin Wambai da sukai lokaci guda suna karanto masa addu’an samun rahamar Ubangijinsa... Waziri ya gyara zama had’ida yin gyaran murya “Toh kunga dai abinda ya faru da Wambai, kai tsaye bazamuce kashesa akai ba amma alamu sun nuna hakan...” Galadima ya jinjina kai yace “Wannan gaskiya ne.” Waziri yaci gaba da fad’in “Toh bazai yuwu mu zauna mu zuba idanu har a gama mana kisan d’auki d’ai d’ai a Masarautar nan bamu nad’a Sarki ba... Idan nan mance ba duk munyi ittifakin cewa Mahmooda shine zai gaji sarautar mahaifinsa....!” Danmaliki yai karaf yace “Bayan abunda ya faru na fara shakkun mik’awa Yarima Mahmood mulki... Duba da cewa Ubandoma da ake zargi da saka hannu cikin salwantan rana Wambai Hadiminsa ne... Inaga bai kamata muyi saurin yanke hukuncin mik’a masa mulki ba har sai an gama bincike kan Ubandoma...” Hakimi ya jinjina kai yace “K’warai na yarda da shawarin Mai Girma Danmaliki....” Waziri ya gyara zamansa sosai yana mai ci gaba da fad’in “Dani daku duka munsan Mahmooda bazai aikata haka ga Wambai ba... Cikin ‘yan uwansa yafi kowa cancanta ya gaji Karagar nan... Kuma shi Ubandoma har yau bai amsa cewa Mahmooda ne ya turasa gidan Wambai ba... Idan zamu adalciwa Yarima Mahmood bai kamata mu soma tunanin zarginsa da mummunan laifi irin wannan ba... Kundaiga halin dattakon da yai lokacin da Majidad’i ya kawo masa hari har cikin fada a gabanku... Mutumin da yai haka bazai yuwu ace zai cutar da wani ba... Musamman ma ace Wambai...!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Gaba d’aya masu sarautun suka shiga jinjina kansu da kalaman Waziri... Galadima yace “K’warai kuwa Waziri, Wannan gaskiya ne... Nidai a b’angare na har yanzu banida canditate bayan Yarima Mahmooda... Idan duk mun amince akan haka inaga gobe juma’a idan Allah ya kaimu mu sanar cewa rana iteyau Wato Juma’a mai zagyowa kenan za’a nad’a Mahmooda matsayin Sarki a wannan masarauta....!” Waziri ya shiga jinjina kai cikeda jin dad’in burinsu shida Giwa ya kusa cika... Nan suka soma masabaha had’ida sallama da juna kan cewa sai Sun had’u goben.... A daren Waziri ya shiga ya tadda Giwa da batun, Farin ciki kaman Ta zuba ruwa a k’asa tasha... Giwa tace “Amma wani hanzari ba gudu ba Waziri, ya kamata mu aika Ubandoma lahira dan ya riga yasan abubuwa da dama game damu...!” Waziri ya jinjina kai yace “Kar kiji komai ni zan kula da wannan ina mai tabbatar miki kafin safiya Ubandoma ya zama tarihi...!” Ya k’arashe muguwar murmushi saman yanutsattsen fuskarsa.... SameenaAleeyou📚 [8/5, 6:03 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *40* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zahra ce ta shigo sashen nasa rik’eda pain relief Ta isa jikin dispense ta tara masa ruwa a cup kana ta nufi upstairs tana kirawo sunansa a hankali... Ta d’an dakata bakin k’ofar d’akinsa tai knocking shiru babu amsa, tai kaman sau uku tana mai k’wank’wasawa take ambato Paa amma shiru babu motsinsa hakan ya bata daman d’an tura k’ofan kad’an, ta shigo da sallama amma shiru babu alamun mahaifinta a d’akin Sannan babu alamun yana bathroom..Fitowa tai ta kuma nufan d’aya d’akin nan ma shiru.... Tai tsaye rik’eda maganin had’ida fuzar da fuci a hankali “Where could he be..?!” Ta fad’i tana mai d’an k’ifta idanunta... Juyawan da zatai ta hango bayansa zaune daga can farfajiyan filin saman nasa hasken k’wan wutan lantarki ya haskaka ko ina tarau Tamkar rana, k’aramar allo gabansa saman ‘yar stand irin yanda ma’abota zane Keyi... Ta saki murmushi a hankali kana ta nufi k’ofar... A hankali take takowa tana kallon painting d’in da mahaifin nata keyi mai matuk’ar kyau cikeda k’warewa da fasaha... Kansa ya d’aga yana duban sararin samaniya yanda wata Ta baje sosai cikin gajimare lokaci guda yake kuma zana abubuwan da idanunsa ke iya gani.... Zahra ta k’araso a hankali kyakkyawan murmushi saman fuskarta, tana duban mahaifin nata yanda ke zanen cikeda k’warewa had’ida shauk’in abinda yakeyi..... Daga cen gefe ta zauna ta d’ora hab’arta saman hannunta guda tana mai duban mahaifin nata murmushi bai bar saman fuskarta ba.... Aje alk’alman dake hannunsa yai kana ya kaikaito yana dubanta shima d’in murmushin ne saman fuskarsa... “Such a beautiful evening.. Everything is so beautiful...!” Zahra ta fad’i fuskarta d’aukeda murmushi, lokaci guda ta isa ta mik’a masa pills d’in... Babu musu ya amsa ya sha yana mai mata godiya... Ta koma ta zauna daga gefe tana mai ci gaba da duban Art work d’insa... Sihirtaccen murmushi saman fuskar Yarima Mahmood yace “Do you like it...?” Ta fad’ad’a murmushinta “Of course I love it Paa...it’s so beautiful..!” Ya murmusa shima yana mai kallon zanen.. Ga wanda yai masa Farin sani zai iya fahimtar wani yanayi ne mai wahalan fasaltuwa Yarima Mahmood Ke ciki... Yayi nisa duniyar tunanin sanda ya sinkayo muryar Zahra na fad’in “Tunda muka dawo k’asar nan banga kayi painting ba Paa bayan kuma sanda muke Spain kana matuk’ar son Painting... Naji dad’i dana soma ganin Paa d’ina na Spain na dawowa gradually... I’ve missed the old you Paa...!” Ta k’arashe cikin tsananin raunin murya irinta mai kuka... Janyota yai ya rungumeta kad’an had’ida share mata hawayenta, tausayinsu su duka biyu na ratsa zuciyarsa, ya sani zai matuk’ar wahala ya koma Paa d’in da Zahra ta sani a baya musamman ranan da tasan sirrin da ya jima yana b’oye mata tsawon shekarun nan... Zama sukai saman kujera hannayensu cikin na juna, lokaci guda Mahmood yai gyaran murya kad’an “Zahra... Inaso ki saka a Ranki duk abinda zai faru ina k’aunarki kuma kar ki tab’a kokonton haka kinji koh...!” Ta d’an saka bayan hannunta Ta goge hawayen da ya gangaro mata kana tace “Paa, is there something you’re not telling me...?!” Hannu yasa ya d’an dafa kanta kad’an kana yace “I love you.... Is getting late, tashi kije Ki kwanta... You’ve school tomorrow..!” Ya k’arashe yana mai mik’arta tsaye... Tai masa K’uri tana mamakin har yanzu kallon k’ararramar yarinya yake mata, bata kuma cewa komai ba sai jinjina masa kai da tai... Murya can k’asan mak’oshi tace “Que pases una buena noche paa..!” (Na barka cikin dare mai aminci Paa) Ya jinjina mata kai a hankali alamun amsawa kana Zahra tasa kai ta shige jiki a matuk’ar sanyaye... Ya bita da kallo har Ta b’acewa ganinsa... A hankali ya lumshe gajyayyan idanunsa yana mai shak’an iskar Ubangiji... ** Yazeed ya kuma duban Ubandoma a karo na biyu kana ya gyara tsayuwarsa yana mai maida hannayensa duka biyu baya “Ka shirya kayi magana...?!” Ubandoma ya d’ago jigataccen fuskarsa yana duban Yazeed, ya had’iyi miyau da k’yar cikin rashin sanin abinyi.... Lokaci guda ya kuma kauda fuska gefe.... Yazeed ya tako gabansa cikeda k’asaita “Kar ka damu kanada daga nan zuwa wayewar gari, karka mance gobe kake cika kwanaki uku rufe a wannan fursunan da bakada ranan fita muddin baka yanke shawarin da zai ceceka ba... Idan kuma kaga ka fice daga Fursunan nan ka tabbata gawanka aka fitar, dani dakai munsan yanda al’amara ke gudana cikin Masarautar nan... So shawari ya rage naka Ubandoma..!” Ya k’arashe shu’umin murmushi saman fuskarsa.... Yazeed yana ficewa Ubandoma yaci gaba da matsan k’walla, shin da waye zai Yarda Mahmood ne kokuwa Yazeed ne..? Yasan babu mai ciresa a ukun da ya shiga face Allah... Toh waye zai sanadin fitarsa Mahmood kokuwa Yazeed... Sarai yasan shirin Giwa akan Mahmood ya kuma san idan yayi gigin sanar da Mahmood wani abu toh fah saidai wani bashi ba dan ko shakka babu Waziri da Giwa har lahira zasu aikasa... Toh amma Yazeed fah... Yace zai basa muk’ami a mulkinsa, ya masa alk’awra masu yawan gaske... Amma zai cikasu..? Amsar da baida tabbas akai... Wata zuciya tace tabbas idan har kai sanadin hawansa mulki zai baka duk wani muk’ami da kake so cikin Masarautar... Zai ‘yantaka k’ila ma har ka zamto Wazirinsa... Idan kuwa ka tsayaga Mahmood tabbas koda ka fice a gidan Yari zaka tabbata ne matsayin bawa k’ask’antacce ‘yanci da kake mafarkin samu har abada bazaka tab’a samu ba....! Ya k’arashe tinanin basa yana mai aza kafad’arsa saman katifa da aka sak’ata da buhu da ciyayi.... Can bayan ya kwanta da kad’an yaji ana kokawa jefa kansa cikin buhu.... Ubandoma ya mik’e firgit daga baccin da yake yana k’ok’arin k’watan kansa yana ihu neman d’auki.... Cikin azama yake kokawan k’watan kansa.... Kaman daga sama saiji yai b’at mutanen sun b’ace alamun sun danna layun zanansu... Bai ankara ba saiji yai an d’aukesa cak an fice dashi daga cikin furaunan gaba d’aya... ** Washe gari ta kama juma’a ranan da masu sarautun gargajiya na cikin Fada Ke shirin shirya zama ta musamman dan tabbatar da Yarima Mahmood matsayin sarki mai jiran Gado.... Waziri sai safa da marwa yake cikin zauren nasa, ya kasa ficewa Fada... Shi kad’ai yakai mari yakai gwauro... Can wasu maza guda biyu k’arfafa suka shigo kawunansu a k’asa.... A d’ari Waziri ya nufesu yana furta “Yaya yaya menene labari... Kada kuce min bakuyi nasaran kashe Ubandoma ba...!” Matansa sai duban juna da ido kurum suke wannan ya kalli wannan suna kifa kawuna a k’asa suna sosa k’eya.... Daga impressions d’insu kawai Waziri ya fahimci basu cika aikin da ya basu ba... Wasu jahilan mari ya dinga d’aukesu dashi, cikin tsananin k’unan rai yake furta “Ashe ku sakarkaru ne... Ta yaya za’a ce bawan nan shi kad’ai ya gagareku....?!” D’ayan yace “Tuba muke mai Girma Waziri, gaskiya bashi kad’ai bane cikin d’akin wani ne ya taimaka masa...!” Waziri ya danna masa harara yace “Ban gane bashi kad’ai ba... Duk kuyi nasaran sakawa masu tsaronsa maganin bacci amma ku kasa kashesa...? Wai mai kuke nufi ne ma...?” D’ayan yace “Duk munyi haka mai girma Waziri, Ina mai tabbatar maka masu tsaronsa mun barbad’a masu hodar gusar da hankali amma mun iske wani cikin d’akin wanda bamu iya tantance fuskarsa ba shi ya taimakawa Ubandoma...!” Gumi ya shiga ketowa Waziri, sai faman kama gefen babban garensa yake yana kece gumin... Cikeda b’acin rai ya furta “Ku b’ace min da gani Bana buk’atar sake ganinku... Sakarkaru marassa amfani...!!” Suna ficewa ya kuma iza babban garensa kana ya fice ya nufi Fada a fujajan.... ** Turaki yai tsaye gaban paint work d’inda Mahmood yai a daren jiya yana kalla yana sakin murmushi a hankali.... Daidai nan Mahmood d’in ya fito cikin shiri farar jampa k’al sai k’amshin Dolce & Gabbana ke tashi a jikinsa lokaci guda yana k’ok’arin saka cuff links yake fad’in “Muje mu samu ayi addu’ar nan damu, and banso na rasa hud’uban juma’a...!” Juyowa Turaki yai yana duban abokin nasa har lokacin murmushin ne saman fuskarsa.... Mahmood da gaba d’aya hankalinsa kega mak’ala links d’insa jin Turaki yai masa banza ya sanyashi d’agowa yana duban Turakin.... Ya k’arasa abinda yake kana ya furta “I hope dai lafiya kake tsaye wajen kanata faman sakin murmushi... Ko Hidaya na hanya ne yau d’in...?!” Ya k’arashe cikin sigan zolaya... Turaki yai taku kad’an ya k’arasoga Mahmood d’in, har lokacin murmushin bai bar saman fuskarsa ba... “Rankaidad’e akwai abinda ake b’oye mana ne ba’a so mu sani...?!” Yai maganar cikeda zolaya... Girgiza kai kad’an Mahmood yai kana yace “Kaga babu lokacin hayaniyar nan naka Turaki...!” Bai kuma cewa komai ba yasa kai ya nufi downstairs cikin sassarfa... Turaki ya fad’ad’a murmushinsa yana furta “Allah huci ran Sarki mai jiran Gado tuba nake... Inama sarki zaimin izini na fad’i wani abu da ya tsaya min a mak’oshi....!” Shidai Mahmood bai amsasa ba har suka nufo parlor, yanda Turaki Ke ci gaba da fad’in “Yarima I can see you’re in love..!” Cak Mahmood ya tsaya ya kasa ci gaba da tafiya... Lokaci guda ya kaikaito yana duban Turaki, girgiza kansa kad’an yai yana mai furta “Where is that coming from..?!” Turaki ya gyara tsayuwarsa yace “You paint in the middle of the night when you’re in love... And this is exactly what happened when you fell for Marigayiya, Allah yai mata rahama... Musamman kake neman waje maras hayaniya ka keb’e kaita zanen abubuwa masu ban sha’awa a tsakiyan dare, Sannan zanan can da kai yayi shige da wanda kayi lokacin Aliya...!” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da takowa a hankali “Mahmood tell me wacece Ta kuma sace zuciyarka haka dan dai na tabbata ba Raheema bace...?!” Gajeren tsaki yai kana yace “Stop talking nonsense, will you..! You talk too much...!” Yaci gaba da tafiya dukda heart d’insa dake beating very fast... Lokaci guda yake furta “Banida lokacin shiririta nan naka Tukraki...!” Yai maganar yana mai ficewa daga parlorn... Turaki ya rakasa da ido hannayensa sakale cikin aljihu kana ya d’an fuzar da fuci kad’an had’ida tab’e baki murmushi saman fuskarsa... Mahmood kenan, shid’in yasan abokinsa Farin sani kuma ya san abokin nasa needs him now more than ever...! Ya kuma murmusawa a hankali kana ya takewa Mahmood d’in baya... ** Giwa ta kuma kece gumin da ya sauk’o mata.. Cikin tsananin tashin hankali take furta “Waziri bamuyi haka dakai ba, kayi alk’awarin bazaka bani kunya ba toh mai kuma nakeji haka... Ubandoma na raye...? Kenan duk wanda Ubandoma Ke masa aiki yafimu saurin motsawa kuma ko shakka babu shine bak’on Buzu, ina tsoron kada wannan bak’on Buzun ya rigamu isaga Mahmood... Dani dakai duka mun sani idan har ya rigamu isaga Mahmood toh fah kashinmu ya bushe cikin Masarautar nan...!” Ta k’arashe cikin tsananin huci tana hura hanci... Lokaci guda ta tako zuwa gaban Waziri, bata daina huci ba take furta “Waziri tun wuri ka gyara wannan al’amari... Matsaloli sunmin yawa ko kasan Jamal ya auka soyayya da yarinyar nan Umaima...? Sannan har yau Izzatu tak’i sanar dani yanda Saudatu take... Kodashike ta yaya zan tsammaci samun amsoshi daga wajen matar da babu hankali tattareda ita cikin sauk’i... Na bijiro mata tako ina amma babu wani canji, na mata da k’arfi na mata da lallama na mata da hauka duka babu canji... Waziri kar ka k’ara wani abin kan matsalolin da suke kaina, ka ida abinda ka riga ka soma... A binciko Ubandoma da mai taimaka masa yanda suka shiga suka fita idan kuma ba haka ba kana iya mancewa nid’in TAKACE....!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji.... D’ago idanu yai yana dubanta, lokaci guda yake furta “Zan gyara abinda na b’ata na miki alk’awari... Sabida Ke Turai babu abinda bazanyi ba..!!” Ya k’arashe cikin tsumewa yana sakin huci.... Giwa ta murmusa a hankali kana tace “Inaso naga Mahmood saman karaga Sati mai zuwa...!” Waziri ya jinjina kai “An gama Allah shi taimakeki...!!” Daga nan ficewa yai waya manne kunnensa... ** Fitowarsu daga gidan Wambai suka nufi fursunan da Ubandoma ke rufe ciki dan yau ne wa’adin da Mahmood d’in ya d’ibar masa ya gama duk wani tunanin da zai kafin masarauta ta yanke masa duk hukuncin da zata yanke masa... Toh amma labarin da suka tadda wajen masu tsaron fursunan shine ya d’aure masu kai... Mahmood ya tsaresu da idanu yana karantarsu sai sosa Kai suke suna neman afuwansa.... Ya d’an taka kad’an zuwa cikin d’akin yana k’arema d’akin kallo... Ya kaikaito yana duban guard guda “Kace baku San yaya akai ya fice ba..?” Guard d’in ya jinjina kai cikeda risinawa “Allah shi baka yawan rai bacci ya d’aukemu daga nan bamu kuma sanin komai ba sai farkawa mukai muka tadda babu Ubandoma..!” Mahmood ya fuzar da fuci a hankali yana mai binsu da idanu.... Tsaban takaicin da suka sakasa ciki bai iya cewa komai ba saima fitowa daga cikin fursunan da yai Turaki na take masa ba.... Waya ya ciro ya kirawo Sankira yace a sanar dasu Galadima akwai zama yau d’in na gaggawa a nan cikin Fada... Kan kace mai masu sarautun gargajiya sun hallara... Waziri sai muzurai yake kaikace baisan meke wakana ba.... Gaba d’aya suka had’u a babban Zauren zama na musamman dake a cikin Masarautar... Waziri ne ya soma yin gyaran murya yace “Allah shi taimaki Yarima kuma Sarkin mu mai jiran Gado... Mun amshi sak’on kira na gaggawa daga bakin Sankira...Allah yasa dai lafiya...!” Ya k’arashe cikeda risinawa... Mahmood yai gyaran murya kad’an daga yanda yake zaune “Haka ne Waziri, na umarce Sankira ya kirawoku gaba d’aya dan na sanar daku abindake wakana cikin Masarautar...!” Wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan haka suka dingayi.... Suna iya hango tsagoron b’acin rai kwance saman fuskar Mahmood... Waziri ya kuma duk’awa yace “Allah shi huci zuciyan Sarki mai jiran gado...!” Mahmood yaci gaba da fad’in “Na sani ko baku fad’i ba wasu daga cikinku zasuyi kokonton cewa ba ni ne na tura Ubandoma gidan Wambai ba sabida Ubandoma Hadimina ne..!” Basu iya furta komai ba sai duba da ido da suke dan gizonsa bazai bari su katse zancen nasa ba... Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Magana Ta gaskiya bani na tura Ubandoma gidan Wambai ba... Hasalima ni Mahmood banida masaniyar yayi hakan har sai bayan da aka kamashi..!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya hannayensa hard’e ta baya yayi tsayuwa irinta masu mulki.. Gaba d’aya suka shiga jinjina kai Waziri na fad’in “Wannan gaskiya ne Yarima... Kuma muna masu tabbatar maka duk mun aminta bazaka aikata wani abu mai kamada wannan ba... Dole a hukunta Ubandoma na cin amanan da yaima Masarautar nan...!” Mahmood ya kuma yin gyaran murya cikin muryarsa mai amo wanda kana iya sauraron dirin sautin nasa na amsa babban Zauren yake ci gaba da fad’in “A daren jiya Ubandoma ya gudu daga fursunan da aka ajesa wutin gadi.... A sabida wannan zanso ku gama duk wani shawarin da zakuyi zuwa gobe a nad’a sarki a wannan masarauta namu dan bazai yuwu muyita zama haka babu shugaba ba kowa yayi abinda yakeso... Sannan dole a zak’ulo Ubandoma yanda ya shiga ya fita...!” Rufe bakinsa Keda wuya suka sinkayo murya na fad’in “Basai kunsha wahalan neman Ubandoma ba... Gashi nan zai bayyana gabanku ya kuma fad’i wanda yake ma aiki dan hallak’a rayuwar Wambai... Sannan da akai rashin sa’a aka kamashi sai wannan mutumi ya tura a kashe Ubandoma a daren jiya... Ni ne nan na ceci rayuwar Ubandoma, da yanzu ya zama tarihi kaman yanda saura suka zama...!” Ya k’arashe yana mai k’arasowa gaban Yarima Mahmood su duka biyu suna duban idanun juna... Yazeed ya sakar masa shu’umar murmushin nan nasa kana ya maidoda dubansaga masu sarautun gargajiya dake faman jifan juna da kallon mamaki, gyaran murya yai kad’an yana mai takowa gaba garesu cikeda k’asaita yake furta “Kuna mamaki ne...? Well, gaskiyar kenan mutumin da kuka d’auki yarda kuka d’aura masa shid’in ba mai gaskiyar bane kaman yanda duk kukai zato...” Waziri dake faman muzurai ne gumi na kuma keto masa yai azaman katse Yazeed da fad’in “Hattara Yarima Yazeed, kasan cewa Sarki ne gaba gareka...!” Yazeed ya watsawa Waziri jahilan kallo kana ya matso dab gaban Wazirin, ya tsaresa da idanu kaman zai magana sai kuma ya saki murmushin nan nasa... “Waziri kenan, ai a iyaka sanina ba’a nad’a Muk’amin Sarki a Masarautar nan ba tun bayan mutuwar mahaifina... Saidai kuma ban sani ba idan Kai ka nad’a... Kuma ma ka d’an dakata kad’an... Ai a iyaka sanina duk mutumin da aka kamasa da laifi mai girma irin na kisa da cin amanan masarauta bazai tab’a yin mulki ba haka nan jinjinsa bazasu tab’a gadan sarauta ba... Shin nayi gaskiya..?!” Ya k’arashe cikin sigan tambaya yana mai tsare Waziri da firgitattun idanunsa... Waziri bai iya furta komai ba sai muzurai da yake yana k’ok’arin had’iye ragowar tuk’in goro da ya tsaya masa a mak’oshi... Yazeed ya kaikaito cikeda iko kana yaci gaba da fad’in “Wai aka ce wak’a bakin mai ita tafi dad’in saurare... Hakimai masu daraja Zan bada izini a shigo da Ubandoma domin ya fayyace maku komai da bakinsa...!” Lokaci guda ya dokawa Hadiminsa Hauni kira yace a shigo da Ubandoma... Ga mamakinsu sai hango Ubandoma sukai na shigowa kai a k’asa hannayensa a d’aure waje guda.... Manyan masu muk’amin cikin Fada suka ci gaba da kallon kallo suna ‘yar k’usk’us tsakaninsu... Masu aza babban gare daga zaune nayi.... Ubandoma ya k’araso ya zube a k’asa ba tareda ya iya d’ago idanu ya dubi jama’an dake wajen ba.... Yazeed yai gyaran murya kad’an yace cikeda isa “Kai muke saurare Ubandoma..!” Zauren yai tsit gaba d’aya ana jira aji daga bakin Ubandoma wanda ko motsi k’wakk’wara bai iyayi sai had’iyan miyau da yake da k’yar.... Ganin yayi shiru ya kasa magana yasa Mahmood soma takowa gaba gareshi cikin salo irinta masu mulki... Saida ya d’ibi wasu dak’ik’ai yana duban Ubandoma dake duk’e wajen yana muzurai daga zaune kana yai gyaran murya kad’an... “Karkaji tsoron kowa kuma kada kaji shakkan kowa... Ka sanar damu abinda Yarima Yazeed Ke k’ok’arin fad’i...!” Zuciyar Ubandoma yaci gaba da bugawa musamman yanda ‘Yay’an Sarkin guda biyu suka sakashi gaba... A hankali ya d’ago ya saci kallon Yazeed dake ci gaba da aika masa mugun kallo lokaci guda na sakar masa wannan murmushin nasa da gefen bakinsa... SameenaAleeyou📚[8/7, 8:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *41* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallon ina binka bashin ceton rayuwarka da nayi Yazeed Ke aika masa... Gumi yaci gaba da tsartfsafowa Waziri, ya kasa koda duban b’angaren da Mahmood yake balle su had’a idanu, hasalima bazai iya duban cikin idanun nasa ba.... Gyaran muryar da Mahmood yai ne wanda saida ya amsa illahirin Zauren ya sanya Ubandoma k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa.... “K’warai... K’warai Wannan gaskiya ne Yarima Yazeed shi ya ceci rayuwana a daren jiya da aka kawo min farmak’i har cikin fursuna... Badon Yarima Yazeed ba da yanzu na zama tarihi nabi sahun Wambai....!” Ya k’arashe cikin rawar jiki.... Mahmood da tinda ya soma magana ya tsaresa da idanu cikin dakewar murya yace “Baka amsa tambayar da masarauta tai maka ba Ubandoma.... Shin wanene yake baka umarni... Wanene jagoranka a wannan laifi da kuka aikata...?!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya mai amo.... Ubandoma ya kasa magana sai k’ok’arin ware idanunsa da tin bugun da Majidad’i yai masa ya sauya masu kamanni... Ubandoma ya kasa cewa uffan sai muzurai da yake... Ya jima yana ha’intan Yarima Mahmood duk bai isheshi ba ace yanzu kuma ya k’ago babban k’arya ya lak’a masa.. Muryar Yazeed ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yai nisa ciki “Kai magana Ubandoma.. Ka fad’i waye yake baka umarni..?!” Ya k’arashe yana jifan Ubandoma da kallon Karka mance na ceci rayuwarka you owe me that one.. Ya kuma had’iyan miyau da k’yar kana ya d’ago hannayensa dake d’aure yana k’ok’arin pointing Mahmood cikin tsananin rawar jiki, hannayen nasa sai b’ari suke ya k’arashe nuna Mahmood yana mai furta “Gashi nan... Gashinan.... Shine wannan...Yarima Mahmood ne..!” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum Mahmood ke nanatawa cikin zuciyarsa... Yayinda sauran masu muk’amin Fada suka shiga tsananin shock, sai duban juna suke cikeda tsananin mamaki.... Mahmood ya lumshe idanunsa a hankali had’ida fuzar da fuci... Ya tako gaban Ubandoma ya tsaresa sosai da idanu, kan Ubandoma a k’asa ya kasa d’agowa sai matsan k’walla yake.... Waziri ya mik’e a birkice yana sab’a babban gare ya isaga Ubandoma dake duk’e wajen yana furta “K’arya kake la’ananne bawa... Ba’a haifi Bawan da zai tozarta jinin mulki a Masarautar nan... Tsinuwar Allah ya tabbata kanka Ubandoma... Allah ya kwashe maka k’ask’antaccen bawa..!!” D’aga hannu Mahmood yaiwa Waziri alamun dakatarwa cikin wane irin yanayi da basu tab’a ganinsa ciki ba.... Ya tako ya k’araso gaban Ubandoma... K’afafunsa dake rufe cikin bak’ak’en Lacoste cover shoe kurum Ubandoma ya gani yaji k’irjnsa yai wani irin bugawa kaman an sauk’e masa guduma...Jikinsa yaci gaba da karkarwa, ya soma yunk’urin d’ago idanu da zummar duban Mahmood saidai yana d’ago kai yai saurin maida idanunsa k’asa... Yazeed na jifansa da wane irin kallo... Take Ubandoma ya zube a wajen sunamme tun kafin Mahmood yakaiga masa magana.... Yazeed yai saurin duk’awa yana jijjiga Ubandoma lokaci guda yake cewa a kawo ruwa a yayyafa masa... Take d’akin taron ya hautsine... Waziri sai tokarinsa da k’afa yake yana fad’in suman k’arya yai ya tashi ya k’aryata abinda yace cewa Mahmood ne ya turasa gidan Wambai.... Waziri baiji bai gani sai tokarin Ubandoma yake, ta ko ina kai naushi yakewa Ubandoma dake zube wajen tamkar maras numfashi... A fusace Yazeed ya mik’e yana sakin wane irin huci yake nunida Waziri lokaci guda yake furta “Waziri..! Idan kayi sanadin mutuwar Ubandoma a wajen nan karkaji da Wai zan zaro takobi na fille wuyanka kaima take a wajen nan..!!” Yanda yake maganar k’irjinsa na sama na k’asa idanunsa a waje zai tabbatar maka cewa tsaf zai aika abinda ya furta... Waziri ya zaro idanu waje jin Yazeed na cewa har lahira zai kashesa muddin yayi sanadin rayuwar Ubandoma.... Take Waziri ya kifa kansa yana fad’in “Tuba nake Yarima..!” Yazeed ya kuma watsa masa wata muguwar kallo take ya doka kirawa Hauni, babu shiri Hauni ya k’araso tareda wasu dogarai guda biyu... Yazeed yace ya d’auki Ubandoma a wuce dashi asibitin cikin Masarauta a basa kulawa na musamman... Bayan ya gama bada wannan umarnin an kwashe Ubandoma an fice dashi ya maidoda dubansaga masu sarauta.... Gaba d’aya risinawa sukai gaba ga Yazeed saikace wani Sarki... Abin ba k’aramin dad’i yayiwa Yazeed ba ganin yanda masu muk’amin cikin Fada har sun soma basa girma tamkar an nad’asa Sarkin... Musamman da ya waiga yaga babu ko k’yallin Mahmood wajen... Murmushin nan nasa ya kuma sakewa, cikin zuciyarsa yake furta “Good... Bravo Prince Yazeed..! You actually did it... In no time zaka zama Sarkin wannan Masarauta... Burinka yana gab da cika... Kai d’in baka saka abu gaba Kaga kasawa...!!” Ya k’arashe tinanin nasa yana mai sakin muguwar murmushi lokaci guda kuma ya tsime sosai tamkar wanda ya tina wani abin.... Gyara tsayuwarsa yai had’ida yin gyaran murya ya dubi Waziri da gaba d’aya tamkar ba’a hayyacinsa yake ba kana ya kuma takowa dab gaban Waziri ya d’ibi wasu ‘yan dak’ik’ai yana duban Wazirin... Saida yai gyaran murya kad’an yace “Waziri... Na tabbata bakaso kai wasa da muk’aminka... Toh ina mai shawartanka da kai hattara kafin soyayyar da kake nunawa criminal irin Yarima Mahmood ya kaika ya baroka....!” K’asa k’asa yai maganar yanda Waziri ne kad’ai ka iya sauraro... Waziri ya had’iyi miyau da k’yar musamman da yaga yanda Takororinsa masu Sarauta tuni kaman sun soma goyawa Yazeed baya.... ** Tinda ya fito daga Zauren taron tafiyar kurum yake ba tareda yasan yanda yake jefa k’afafunsa ba... Kallo guda zakai masa ka fahimci yana cikin matsananin tashin hankali had’ida b’acin rai... Tafiyar kurum yake yana dukan k’asa da k’afafunsa yake ratsa cikin Fada, dik wanda ya gansa a haka sai yasha jinin jikinsa ya k’ame ya risina saidai shi Mahmood d’in baima kula da kowa, gani yake tamkar shi kad’ai ne tareda matsalolinsa cikin Masarautar... K’arfin halinsa yasa yake k’ok’arin danne abindake tasowa daga can k’asar zuciyarsa amma kam shi kansa yasan ana gab da kaisa mak’ura a Masarautar... Raheema da fitowarta kenan daga sashen Gimbiya Zeenat Ta hangi Yarima Mahmood tafe ya nufi sashensa, yanayinsu ya bala’in tada mata hankali... Ta dubi Hadimarta Mashkura da a yau d’in ita ke take mata baya... Jinjina mata kai tai alamun tana iya tafiya bata buk’atarta... Mashkura na shigewa Raheema tasa kai tabi bayan Mahmood... A daidai k’ofar sashensa Ta cimmasa, tai gyaran murya kad’an had’ida risinawa kaman yanda tarbiyan babban gida yake “Barkada yammaci Your Highness..!” Duba d’aya yai mata ya watsar Dan har yanzu ba Wai sun koma normal bane tun bayan tattaunarwarta da Juwariyya da ya sinkaya.... Raheema ta kuma gyaran murya kad’an tace “Rankaidad’e akwai abinda ke damunka ne... Kai hak’uri na tunk’aroka ba tareda iso ba... Yarima I just couldn’t help it... Ganinka haka ya d’aga min hankali.. Definitely nasan something is wrong... Zan iya taimakawa da wani abu....?!” Ta k’arashe tana k’ifk’if da idanu had’ida rau rau da fuska alamun nuna damuwa.... Dubanta yai na wasu ‘yan dak’ik’ai, ba tareda ya furta koda kalma guda ba yasa kai ya shige sashensa.... Raheema ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta, wannan damarta ne to win Mahmood back zatai duk yanda zatai ta tabbata shid’in ya kuma zama nata a yau d’in... Murmushi Ta saki kana tasa kai Ta shige cikin sashen nasa... Tsaye ta hangesa ya bada baya yana duban window, hannayensa hard’e Ta baya... Raheema ta k’arasa Kai a k’asa yawa mutumiyar arziki... Saida ta kuma yin gyaran murya kad’an kana tace “Yarima there’s something I need to tell you... Ka cancanci ka sani...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... A hankali ya kaikaito yana dubanta, kanta a k’asa taci gaba da fad’in “Nasan ba lallai ka kuma yarda dani ba Yarima... I did something behind your back... But believe me nayi komai ne don amfaninka kuma with pure intentions... Yarima I did all that for you, sabida Farin cikinka... I hope abinda zan fad’a maka yanzu zaka yarda dani... Kuma ba Dan na saye zuciyarka ko wani abu mai kamada hakan ba... Zan fad’a maka ne because I care about you... And I love you...!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata cikin yanayi mai ban tausayi.... Ganin yayi K’uri yana dubanta ya sanyata samun daman ci gaba da magana... “Yarima akwai wasu mutane da suke maka k’ulleliya a bayanka, mutanen da suke son ganin downfall d’inka... Ni da idanuna na gansu a asibiti sanda naje duba Baba Wambai, su biyu d’in basa jituwa sam amma da na gansu a tare nasha mamaki..!” Katseta yai cikin kakkausar murya da fad’in “Raheema...! Mai kike son cewa, just spell it out once and for all, su waye kike magana akai...!!” Jinjina kanta tai a hankali kana tace “It’s your brother Yazeed and Majidad’i... I saw the of them together, they were conspiring against you... Naji da kunnuwana suna cewa zasu kaika k’asa by every means...!” Ta k’arashe tana zaro idanu waje had’ida jinina kai alamun tattabatarwa.... Tinda ta soma magana yake dubanta ba tareda ya janye idanunsa ba, ga wani irin gumi dake tsartsafowa daga goshinsa, take idanunsa suka kad’a sukai jazir haka nan fatar jikinsa, kana iya hango yanda yake sakin huci cikin wane irin yanayi... Idanun Raheema suka sauk’a kan hannayensa da tuni ya damk’esu jijiyoyin sunyi rud’u rud’u... Baiso ya yarda da zancen Raheema Dan shi ba mutum ne mai d’aukan magana haka kurum ba tareda k’wakk’waran hujja ba... Amma bayan abinda ya faru yanzu a Zauren taro baijin akwai sauran hujja da yake nema... Bai kuma furta komai ba sai ficewa da yai kaman zai tashi sama... Jamal da Fu’ad dake tafe haraban Masarautar hango Yayan nasu a haka yasa suka dubi juna... Fu’ad yaceda Jamal meke faruwa..? Girgiza kai kurum Jamal yai alamun shima bai sani ba.... Fu’ad yace “Mu k’arasa muji...!” Babu musu Jamal ya jinjina masa kai sukabi bayan Mahmood...! ** Giwa na tsaye gaban Yazeed tana ci gaba da sakin huci take furta “Har abada muddin Yayanka na raye bazakai saurata shi ya rasa ba Yazeed... Yazeed mai kake so ka zama..? Shin maiyasa kake neman ka raba kan ahalinmu...! Yazeed ka d’ago idanu ka dubeni ka sanar dani dik abinda Ubandoma ya fad’i k’arya ne kai ka tsara masa Mahmood bazai aikata haka ba..!!” Giwa bata rufe baki ba Mahmood ya banko k’ofa ya shigo cikin yanayin da basu tab’a ganinsa ciki ba... Jajayen idanunsa masu cikeda b’acin rai ya sauk’e kan Yazeed kan kace mai yayi tsalle ya cakumo wuyan Yazeed ya masa wani irin damk’a da duka k’arfinda Allah ya huwace masa.... Cikin kakkausar murya mai firgitarwa yake furta “I have warned you time without numbers... Do not cross me Yazeed... Now tell me what’s your role in all this..! Talk to me Yazeed..! Talk...!!!” Ya k’arashe yana kuma jijiga Yazeed da iyaka k’arfinsa... Giwa da gaba d’aya duniyar ta juye mata ga wane irin rawa da illahirin jikinta keyi, gaba d’aya ta kasa furta komai sai wane irin karkarwa jikinta keyi... Daidai nan su Jamal da Fu’ad suka shigo... A d’ari Jamal ya isa garesu yana k’ok’arin janye Mahmood yake calming d’insa amma inaa tamkar baiji saida matse Yazeed yake yana wane irin huci... Tuni idanun Yazeed sun furfito waje tamkar an matse mage a buhu.... Giwa cikin rawar murya mai cikeda firgici had’ida tashin hankali take furta “Mahmood kar ka kashe d’an uwanka... Ka sakar masa wuya, ka bashi dama yayi bayani...!” Bai sakesa ba sai jijiyoyin jikinsa dake kuma fitowa rud’u rud’u... Dik iyaka k’ok’arin Jamal da Fu’ad wajen janye Mahmood sun kasa, koda wasa basu tab’a ganin wannan side d’in nasa ba basu tab’a sanin cewa yanada zuciya har haka ba... Har saida Giwa ta fashe da kuka tana janye Mahmood tana fad’in idan zai iya kashe d’anuwansa Yazeed Toh itama kawai ya shak’e mata wuya ya fara da ita.... A hankali yake sassauta rik’onda yayiwa Yazeed har ya cikasa gaba d’aya... Yazeed ya zube gefe yana haki sosai had’ida gumin azaba... SameenaAleeyou📚 [8/9, 11:27 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *42* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* D’agowa Yarima Mahmood yai ya dubi Giwa na d’an wani lokaci kana ya furta “Kiyi hak’uri Maami... I’m sorry...!” Daga haka waigowa ya kumayi yana aika muguwar kallo wa Yazeed da har yanzu bai iya mik’ewa ba... Bai kuma cewa komai ba ya fice daga sashen gaba d’aya.... Jamal yai saurin k’arasawaga mahaifiyarsa ya taimaka mata ta suka shige d’aki yana mai k’ok’arin calming d’inta... Parlorn ya rage saura Fu’ad da Yazeed.. Fu’ad kaw girgiza kai kurum yai yana duban Yazeed “Wannan shine abinda nake jiye maka Yazeed, raininka da wulak’ancinka ya soma yawa...!” Katsetsa Yazeed yai da fad’in “Don’t you dare lecture me you idiot... Kaje ka sami wancan mahaukacin Yayan naka shi yake buk’atan lecture sama dani tinda cikin mu biyun shine criminal, ya kashe Wambai tareda taimakon Hadiminsa sannan ya zago yana so ya kashe Hadimin nasa before he rats him out... Kuma Wllhi abinda yayi mun baici banza ba sai na koya masa hankali... No one messes with Prince Yazeed AbdulJabbar..!” Ya k’arashe yana sakin huci da haki had’ida sosa wuyarsa da tuni fatan tayi jazir... Sai yanzu Fu’ad ya fahimci meke faruwa... Gajeren murmushi yai yace “Kafi kowa sanin cewa zancen da kake babban k’arya ne Yazeed, ko ka mance cewa cikin dukanmu hud’u shine ba criminal ba... The three of us are criminals, we are the criminals Yazeed, You Jamal and I...Kuma cikinmu gaba d’aya shi kad’ai ya cancanci zama Sarki sabida ba’a Sarki criminal...!” Katsesa Yazeed yai da fad’in “Shut up! Just Shut the hell up Fu’ad... Kai mahaukaci ne k’waya ya gama illata maka kwanya... Baka da sauran amfani Fu’ad, dakai da babu a Masarautar nan duk d’aya ne... Kai gwara ace babu kaima at least bazaka dinga jawo mana abun kunya da wannan haukar Naka ba wanda bakada ranan warkewa...!” K’walla masu zafi suka ciko idanun Fu’ad lokaci guda... Ya shiga dunk’ule hannayensa sabida tsananin b’acin rai... Yazeed kuwa abinda yakeso kenan yai provoking d’insa, take ya saki shu’umin murmushin nan nasa da gefen baki... Ya mik’e tsaye da k’yar ya matso dab gaba Fu’ad saitin kunnensa yake rad’a masa... “You’re useless Fu’ad, bakada amfani... Babu wanda yake sonka sabida kai psychopath ne, ko budurwar da kake mutuwar so ka kasa samun amincewarta Fu’ad... You’re nothing but a failure Fu’ad...! Just accept the fact bazaka tab’a birge kowa ba Fu’ad... Not even your Criminal brother Mahmood..!!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi had’ida d’an buga kafad’an Fu’ad d’in... Bai kuma tsayawa sauraren kowa ba yasa kai zai fice yana mai ci gaba da sosa wuyarsa... Fu’ad dake tsananin huci hannu yasa ya damk’o hannun Yazeed ya dawo dashi baya... Su duka biyun sukai tsaye suna duban juna... Fu’ad ne ya soma sakar masa murmushi kana yace “You’re a loser Yazeed...! Sarautar da kake so bazaka tab’a samu ba, kanaji kana gani Yaya zai d’ale Karagar nan... Kuma kasan maiyasa na kiraka da loser...” Ya murmusa kad’an kana yaci gaba da fad’in “Sabida dik abinda ka sa gaba baka samun nasara... How about our bet... Nasan maybe ka mance sabida ta yab’a maka magana ta ajeka a yanda ya kamaceka... Kuma kasan menene zaifi maka ciwo Prince Yazeed... Ni da ita d’in masoya ne, she chose that psychopath over you...you lost to me Yazeed and too bad kana cikin Masarautar nan zakaga aurenmu... To cut it short, Na d’agaka na bugaka da k’asa a wannan wasan kaman yanda Yaya zai kuma bugaka da k’asa a wasanka dashi... So now tell me Yazeed AbdulJabbar... Among the two of us who’s a failure..?!” Ya k’arashe yana mai sakar masa murmushi da gefen baki... Yazeed yaci gaba da tururi yana aikawa Yazeed muguwar kallo... Hannu ya d’aga zai kai masa mari “How dare you Fu’ad!!” Fu’ad ya damk’e hannun nasa shima cikin huci yake furta “Kada ka kuskura ka sake kwatanta wannan kuskuren dani Yazeed... If not...!” Ya murmusa kad’an sai kuma ya saki hannun Yazeed d’in ya fice gaba d’aya daga parlorn.... Yana ficewa Yazeed yasa kai ya fice cikin sassarfa zuciyarsa naci gaba da k’una.... Zuhra na ganinsa haka tai saurin sallaman kuyanginta tana mai k’arasawa garesa cikin tsananin tashin hankali... “Prince lafiya... Mai ya faru dakai..?!” Ta k’arashe tana mai rik’e baki ganin wuyansa yayi shati kaman ya tara jini.. Bai amsata ba hasalima kota kanta baibi ba yayi hayewarsa sama, sai sakin fuci yake, gaba d’aya zuciyarsa a jagule take... Haushin komai da kowa yake, Zuhra ta turo k’ofa ta shigo cikin sand’a kaman mai tsoron kada ta tada jariri mai bacci... Ta saci dubansa kad’an ta d’an had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’oshi tana yunk’urin k’arasawa gareshi da zummar duba ciwonsa... Cikin k’arfin hali Ta d’an fuzar da fuci a hankali kana ta nufi yanda yake tana k’ok’arin massaging wuyarsa da towel... Cikin daka tsawa yace da ita “Get out..! Tashi ki fita nace bana buk’atar kulawarki...!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci.. Jiki a matuk’ar sanyaye Zuhra ta mik’e ta fice hawaye masu d’umi na gangaro mata.... Tsaki ya buga tana ficewa ya maida k’ofan ya rufe yana ci gaba da fuzar da huci mai tsananin tururi... Yana sosa wuyarsa yanda Mahmood ya shak’esa kalaman Fu’ad na dawowa kwanyarsa.. Wato Muhibbah take ko waye ta sanar da Fu’ad kalan wulak’ancinda ta masa, Yana nan yana faman famkam famkam Fu’ad na masa kallan k’ask’antacce wanda mace Ta yarfa... How dare she..! Wllhi sai ya koya mata hankali, this isn’t over, in fact is far from over... He must teach her a lesson, a very good one...! Babu macen data kai ta wulak’anta Prince Yazeed AbdulJabbar....! Ya k’arashe tinanin fuskan mutum biyu da yafi tsana na masa gizo cikin idanunsa, Mahmood da kuma Muhibbah.... A b’angaren Zuhra kuwa tana fita parlor ta tadda Raheema ta shigo, ganinta haka ya tabbatarwa Raheema cewa plan d’inta yayi aiki tasan Mahmood ya confronting Yazeed ko babu komai tasan yanzu Mahmood zai soma yarda da ita.... Tai saurin k’arasawa fuska fal damuwa ta kamo Zuhra tana tambayarta meke faruwa.... Zuhra bata iya cewa komai ba saima kukan da take k’ok’arin dannewa ne ya kufce mata.... Cikin nuna kulawa Raheema ta kamota suka zauna saman kujera tana k’ok’arin comforting d’inta... Lokaci guda san jin meke faruwa da Zuhran... ** A b’angaren Fu’ad gaba d’aya yinin ranan yinta yai yana tinanin abinda su kaiwa wa yarinyar shekarun baya... Yana so ya mance komai ya soma Sabon rayuwa musamman da yanzu Muhibbah ta shigo cikin rayuwarsa saidai baijin zai iya yin hakan sabida Shi kanshi baijin zai iya yafewa kansa balle ita yarinyar da suka zalunta da ahalinta... Fu’ad ya dafe kansa dake tsananin sara masa had’ida rintse idanunsa, lokaci guda yake furta “No no no I don’t want to Yazeed...! Just let me go... I don’t want to do it....!” K’ara ya kuma sakewa shi k’ad’ai yana mai watsi da k’wayoyin dake cikin tafin hannunsa yake furtawa da k’arfi “Just leave me alone... Please leave me alone, bana son yin abinda kuke umartana... Just leave me alone.. Leave me alone..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai tak’urewa can k’arshen gado... Yanda Fu’ad yaga rana haka yaga dare, gaba d’aya tashin hankalin ya dawo masa Sabo tamkar mai tab’in hankali haka ya dinga yin abubuwa.... Gaba d’aya Masarautar ma abubuwa sun kuma tab’arb’arewa, a b’angaren Waziri da Giwa basuyi k’asa a gwiwa ba dan koda wasa bazasu bari Yazeed ya soma d’alewa Karagar nan ba maganar Tal’udu ya tabbata kaman yanda ya sanar dasu cikin yaran Sarkin duk wanda ya soma zama Sarki shine gawan fari don fitilar tsafi ta hasko masa mutuwa a Masarautar... Tuni sun samo mafita yanda Waziri ya tafi asibiti cikin shiga na b’adda kamanni tufafi irinta bayin Masarautar mata ya saka sannan ya d’auki farantin abinci tamkar wanda zaikaiwa fursunan abinci yanda babu mai zarginsa.... Yana shigewa d’akinda Ubandoma Ke kwance ya maida k’ofa ya rufe... Ubandoma yai k’uri ganin ba likita bane ya shigo.... Yai Saurin mik’ewa ganin mutumin da yai shiga irinta mata na kuma nufosa... Kafin yai yunk’urin gudu Waziri ya damk’osa ya yaye mayafin daya rufe fuskarsa dashi... Zuciyar Ubandoma ya tsinke ganin Waziri ne... Waziri ya sakar masa murmushi yana mai furtawa cikin sigan rad’a “Kwantar da hankalinka Ubandoma bakada wajen gudu... Kuma idan har kanaso ka tsira da rayuwarka data iyalanka toh kayi yanda nace..!” Ya k’arashe yana sakarwa Ubandoma murmushi mai muni.... Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana mai furta “Waziri kamin rai dan Allah kada ka kasheni ko ‘ya’yana wllhi Yarima Yazeed ne ya tilasta min fad’in duk abubuwan dana fad’a a Masarauta... Amma ko kad’an babu hannun Mahmood cikin abinda nayi, hasalima na sinkayo tattaunawarku da Giwa ne cewa akwai abinda kuke nema gidan Wambai ni kuma naga abinda nada matuk’ar mahimmanci wajenku sannan idan na rigaka samo abin watak’ila Giwa ta ‘yantani na sami ‘yanci na bar bauta abinda na jima Ina burin mallaka tsawon rayuwata... Kaji dalilina Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe jiki na matuk’ar rawa... Waziri ya saki wata bazawar murmushi yace “Shege Ubandoma... Ni dama nasan za’a aika... Wato ki gaka mai wayo koh... Haba Ubandoma kana bawa yaushe har zakai tunanin kaid’in shirinka zai aiki akan namu... Toh kana jina...” Ubandoma yai saurin jinjina kai alamun eh.... Waziri yaci gaba da fad’in “Zan k’yale wannan ya shige Ubandoma amma da sharad’in zaka k’aryata abinda ka fad’i gaban Masarauta... Zaka sanar da Masarauta cewa Yazeed ne ya tilasta maka fad’in hakan Ka fahimta...!” Ubandoma yai saurin jinjina kai sai kuma ya d’anyi jim tamkar yana tuna wani abin... Waziri yace “Ya naga kayi shiru..?” Ubandoma ya muskuta kad’an yace “Toh Yarima Yazeed fah Rankashidad’e kasan halinsa idan na janye abinda na fad’i gameda Yarima Mahmood hakan ka iya janyo min matsala wajen Yarima Yazeed..!” Ya k’arashe fuska fal damuwa... Waziri yace “Bakada matsala Ubandoma Yazeed bazai maka komai ba ina mai tabbatar maka... Kaidai kawai kayi yanda na umarceka...!” Ubandoma ya jinjina kai cikeda girmamawa yana mai tabbatarwa Wazir cewa zai yanda yace.... ** Yazeed ya gama tunanin Ta yanda zai b’ullowa Mahmood ya d’auki Fansarsa, ya saki murmushin nan nasa a hankali had’ida furta “His daughter... Itace weakness d’in Mahmood kuma da ita zai amfani ya tarwatsa Mahmood... Lokaci guda ya mik’e ya fice daga sashen nasa... Zuhra na hango fitarsa ta window ta lumshe idanunta tanai masa addu’an shiriya cikin zuciyarta... ** Zahra Ta ida shirin baccinta kenan taji ana knocking a k’ofarta... D’an jim tai tana duba time kafin ta saki murmushi dan tasan bazai wuce Paa d’inta ba tinda yau d’in duka basu had’u ba ta dubashi a sashensa da duk yanda take tinani cikin Masarautar zata sameshi bata sameshi ba... Tasan bazai iya bacci bai ganta ba, cikin sauri ta isa k’ofa ta bud’e tana mai furta “I thought yau bazan ganka ba Paa...!” Birki tai ganin Uncle Yazeed tsaye bakin k’ofar cikin wane irin yanayi... “Uncle.. Lafiya...?!” Ta tambaya tana dubansa fuska d’aukeda damuwa... Yazeed ya sakar mata murmushi mai kyau yace “Princess... Aren’t you gonna let your Uncle in....?” Cikin sauri ta matsa gefe ta basa hanya tana mai furta “Sorry Uncle... Please come in...!” Yazeed ya kuma sakar mata murmushi kana yasa kai ya shigo... Yana tafe ne Zahra ta hango wuyansa yayi shati jajazir kaman ciwo.... Ta taresa da fad’in “Uncle wait... What happened to you... Mai ya sameka..?” Ta k’arashe cikeda kulawa.... Yazeed ya d’an shafi wuyansa yace “Oh this...” Yai maganar yana mai zama saman doguwar kujera dake cikin d’akin lokaci guda Zahra ta K’araso ta zauna gefensa duk ta damu da ciwon da ta gani wuyarsa... Yana mai sosa wuyan yake ci gaba da fad’in “Someone tried to kill me Zahra...!” Yai maganar yana mai duban cikin idanun yarinyar... Ta zaro idanu waje “Kasheka Uncle... Waye kenan... Maiyasa ba’a kamashi ba... Whoever did this to you needs to pay Uncle..!” Ya murmusa kad’an yace “You think so..?!” Zahra tace “Haka ne ya kamata Uncle...” Yazeed ya fuzar da fuci kad’an sai kuma yace “Zahra’u mai kike tunani a duniyar da babu adalci..? Mai kike tunani a Masarauta mai cikeda azzalumai wanda suka d’auki kashe rai ba komai ba...?!” Kalamanta sunyi mata nauyi, gaba d’aya kwanyarta sai yana neman juyawa, lokaci guda tunanin mutuwar mahaifiyarta yazo mata, k’walla suka ciko idanunta.... Cikin rawar murya take furta “Uncle bana son rayuwa a irin wannan Masarautar... What if... What if this kingdom is cursed... I lost my Maama here... Bana so na sake rasa wani cikin iyayena Uncle what’s wrong with this palace...?” Janyota yai ya rungumeta yana lallashinta lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Kar ki damu Princess, that won’t happen kinji koh... Amma inaso kisan waye yamin wannan abun Princess...” Ta d’ago tana dubansa had’ida share hawayen idanunta “Uncle who attempted to kill you..?” Yazeed ya tsareta da idanu lokaci guda ya furta “Your Father... My brother did this to me... Akan mulki komai za’a iyayi a Masarautar nan.... Mahaifinki kuma d’anuwana da muka fito ciki d’aya shi yayi min haka Zahra...!” Ya k’arashe babu alamun wasa a tattaredashi... Take Zahra ta mik’e cikeda tsoro tana girgiza kai take furta “No...no Uncle You must’ve got that wrong... My Paa can never do something like that... Please Uncle tell me it isn’t true... Dan Allah kace min ba gaskiya bane.. Not my Paa please...!” Ta k’arashe cikin shesshek’an kuka.. Yazeed ya mik’e tsaye ya kamo hannunta had’ida furta “Unfortunately Zahra... It’s the truth... Your Father is not what you think he is... He’s capable of the worse akan Mulki...!” Ya k’arashe yana mai kuma jaddada kalamansa.... K’ara Zahra ta saki had’ida zubewa wajen daidai lokacinda Mahmood ya banko k’ofa ya shigo... Hankali tashe yai kan Zahra yana ambato sunanta yana jijjigata...Lokaci guda ya mik’e ya cakumo Yazeed yana jijjigasa yake furta “What did you do to my daughter... Ka fad’a min Yazeed mai kaiwa d’iyata....Yazeeed!!” Ya k’arashe yana mai kuma jijjigasa... Yazeed bai daina sakin murmushi ba yake furta “I didn’t do anything to your precious princess Your Highness.. But you did.. Kai ka jefata a condition d’in da take ciki Rankaidad’e..!” Mahmood yana tsananin huci yake furta “Yazeed don’t involve my daughter...I’m warning you...!!” Yazeed ya murmusa yana mai furta “Zaka kasheni ne... Banji mamaki ba Your Highness tinda kayi attempting hakan....!!” Cikin tsananin huci Mahmood ya dunk’ule hannunsa yana k’ok’arin kaiwa Yazeed naushi Zahra ta mik’e ta tare Yazeed tana mai girgiza kai take furta “Why Paa... Why...? I’m disappointed Paa... Totally disappointed..!!” Tana ida fad’in haka ta fice a guje tana mai ci gaba da kuka... Mahmood yabi bayanta yana k’walla mata kira inaa ko juyawa batayi... Zahra bata zarce ko ina ba sai masauk’in Muhibbah.... SameenaAleeyou 📚 [8/11, 10:09 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *43* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Bacci ya soma d’aukanta sanda ta jiyo sautin kuka ana bubbuga mata k’ofa... Ta mik’e zumbur tana k’ok’arin danna side lamp, wayarta ta janyo ta duba time tana mamakin waye wannan mai buga mata k’ofa a daidai irin wannan lokacin gashi kuma kukan kaman k’aruwa yake... Jin muryar Zahra na ambato sunanta ya sanyata saurin mik’ewa ta janyo hijab ta zira kana ta nufo parlor... Tana bud’e k’ofar kuwa Zahra batai wata wata ba ta fad’o cikin jikinta tana kuka sosai... Mamaki had’ida tsoro suka kama Muhibbah.... Toh lafiya... Meke faruwa...? Tai tambayar cikin zuciyarta, tana nan tsaye tamkar statue ta hango Yarima Mahmood na K’arasowa cikin tafiya da yafi kama da sassarfa.... “Zahra please, sweetheart listen to me...!” Bai rufe baki ba Ta d’ago fuskarta dake jik’e sharkaf da hawaye tana girgiza kai alamun a’a take fad’in “Just go away Paa... I don’t want to see you..!” Ta k’arashe maganar tana mai fad’awa bedroom d’in Muhibbah a guje ta maida k’ofan ta kulle.... Yarima Mahmood ya lumshe gajiyayyun idanunsa a hankali had’ida fuzar da huci mai d’umin gaske.... Muhibbah dai kallon ikon Allah kurum take tana mamakin Toh mai ya had’a d’iya da mahaifin har haka.... Ta d’anyi gyaran murya ganin har wannan lokacin ya kasa bud’e idanunsa “Your Highness... Lafiya, meke faruwa...?!” Sai sannan Mahmood ya ware idanunsa ya sauk’esu saman fusarta, ya d’an kwashi dak’ik’ai yana dubanta kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Please take care of my daughter...!” Daga haka bai kuma cewa komai ba saima sa kai da yai ya fice daga sashen gaba d’aya... Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya b’acewa ganinta kana Ta nufi k’ofan d’aki tana k’wank’wasawa... Da fari Zahra k’in bud’ewa tai har saida tace mata itace kuma Paa d’in ya tafi sannan Zahra ta bud’e mata.... Tana bud’ewa ta kuma komawa ta zauna bakin gado tana mai ci gaba da matsan k’walla... Gefe da ita Muhibbah ta zauna ba tareda tace komai ba tana sauraron yanda yarinyar ke kuka a hankali, bayan shud’ewan mintoci k’alilan Muhibbah ta kaikaito tana dubanta, lokaci guda ta d’aura hannunta guda saman na Zahra... Zahra ta d’ago kod’add’un idanunta tana duban Muhibban... Murmushi ta sakar mata mai sanyin gaske “Kina buk’atan wani abu...?” Girgiza mata kai tai alamun a’a... Muhibbah Ta jinjina kai tace “Alright, ki kwanta ki huta haka nan is late already kinji koh...!” Bud’e bakin Zahra sai cewa tai “I’ll never forgive him... Ever, wllhi na tsaneshi, Wannan shine abinda yake b’oye min... Na tabbata da saka hannunsa a mutuwar mahaifiyata... If he can kill his own brother da suka fito ciki guda ko shakka babu zai kashe mahaifiyata dik akan banzan Mulkin duniya da bazaka tabbata kanayi ba...!” Kuka yaci k’arfinta.... Sauk’e ajiyan zuciya Muhibbah tai a hankali tace “A duniyar da adalci yayi k’aranci babu abinda ba za’ayi ba Zahra... A duniyar da son mulki da neman dukiya tako wane irin hanya yayi k’amari babu abinda baza’ayi ba... Ana kashe rayuwa domin a cimma wani buri na duniya... Shi d’an adam mai yawan zalinci ne kuma mai yawan bijire maI yawan bijire ma rahamar Ubangijinsa ne... Amma maiyasa kike danganta mahaifinki da munanan laifuka irin wannan...?!” Dubanta Zahra tai hawaye na gangaro mata “Sabida yau d’in ni ganauce ba jiyau ba... Mahaifina ya tasamma kashe Uncle Yazeed akan rikicin mulki... Idan baki manta ba na tab’a sanar dake inaji a jikina yana b’oye min wani abu gameda mahaifiyata wanda baya so na sani... Ko shakka banayi abu ne da ya shafi mutuwarta.. A ido mahaifina yafi kowa kyawawan d’abi’u cikin gidan nan ashe a zuciya yafi kowa munin halayya.... Ya cuceni ya zalunceni ya rabani da mahaifiyata...!” Ta k’arashe ciki shesshek’an kuka... Rungumeta Muhibbah tai cikeda tausayawa lokaci guda cikin kwantar da hankali take fad’in “Wasu lokutan mukanyi mummunan zato ga mutanen kirki kaman yanda wasu lokutan mukanyi kyakkyawan zato ga mutanen da ba na K’warai ba, amma a koda yaushe ana so mutum ya kasance mai kyautata zato tsakanin al’umma... Shi munana zato bazai kaika ga komai ba face tarin dana sani da kuma zunubi mai girma... Zahra shin kina zaton shi Uncle d’in naki mutumin k’warai ne...?!” Tai tambayar tana mai tsare yarinyar da idanu... Dubanta Zahra tai had’ida jinjina kai alamun eh... Muhibbah ta jinjina kai tace “Da kyau da kikai masa zato mai kyau... Toh inaso kiyi haka ga mahaifinki, ki kyautata masa zato... Kince rikicin mulki suke shiyasa kike ganin mahaifinki shine bad guy a nan koh... Tsawon shekarun da kikai da mahaifinki kin tab’a shakkun kyawawan d’abi’unsa a baya...?!” Zahra tai saurin girgiza kai alamun a’a... Muhibbah taci gaba da fad’in “Ya tab’a aibataki ko mahaifiyarki a gaban idonki kokuma kiji labari...?!” Nanma girgiza kai Zahra tai alamun a’a... “Kin tab’a jin labarin yaci zarafin wasu mutane tun kuna k’asar Spain har kawo dawowarku Nigeria...?!” Naman Ta girgiza kai alamun a’a cikin matuk’ar sanyin jiki... Muhibbah Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “SARAUTA...! Sai akan sarauta kike zaton zai aikata abubuwan da ya aikata koh...?!” Tai saurin jinjina kai alamun amincewa... Muhibbah ma Ta jinjina kai a hankali kana tace “Toh kisa a ranki cewa rikici na mulki ne tsakanin mahaifinki da d’an uwansa... Amma kar Ki tab’a kokonton k’irkin mahaifinki kinji koh...!” Tai k’uriwa Muhibbah tana dubanta, lokaci guda Ta jinjina mata kai a hankali sai kuma tace “Toh ta yaya zan cire kokonton abinda yake b’oye min gameda mahaifiyata Tia.... I really want to know what he’s hiding...!” Muhibbah tai mata K’uri na wasu ‘yan dak’ik’ai kana tai gajeren murmushi tace “It’s simple Zahra.... Kinaso mahaifinki ya sanar dake abinda yake b’oye miki ba tareda wani kwana kwana ba...!” Yarinyar tai saurin jinjina kai alamun eh... Muhibbah ta jinjina kai tace “You ask him in public... Ki tambayesa a bainar jama’a mutanen da yake jin nauyinsu yake kuma da kima a idanunsu...” Zahra ta dubeta cikin rashin fahimta tace “But I know Paa, bazai bani amsa direct ba... Ni nasan ko Shid’in wane irin mutum ne...!” Muhibbah Ta murmusa kad’an sai kuma tace “Kema ba direct zaki tambayesa ba... You accuse him of something very big... Abinda kike tunanin shi yake b’oye miki... Like mutuwar mahaifiyarki... Ina mai tabbatar miki muddin baida saka hannu ciki zakiji komai dan bazai juri jin kunyan idanun duniya ba... Take zai fayyace miki duk wani Abinda ya jima yana b’oye miki...!” Ta k’arashe cikin jaddada kalamanta... Murmushi Zahra Ta saki kana tace “Kai amma na gode Tia... Perfecto, wannan shine kawai hanyar da Paa zai sanar dani abinda yake b’oye min.. Thank you thank you Tia... Gracias..!” Ta k’arashe tana mai rungumarta... Murmushi Muhibbah keyi tana shafa kan yarinyar lokaci guda tana hango fuskar Mahmood yanda zai falling gaban d’inbin jama’an Masarautar nan... Zai sha kunya zai fad’i k’asa warwas kuma abinda zaifi masa ciwo shine d’iyarsa itace downfall d’insa... He’d definitely get what’s coming for him.... Finally zata gama da Mahmood da martabansa cikin Masarautar...! Ta k’arashe hawaye mai ciwo na gangaro mata, lokaci guda tinanin k’uncin rayuwa da uk’uban da ta shiga ansanadiyan yaran Sarkin na zuwa mata daki daki... Ta lumshe idanunta tana k’ok’arin saita kanta dan kar Zahra ta fahimci wani abu... A tare sukai bacci nan d’akin Muhibban tana mai kuma calming Zahra harda bedtime stories tai mata Zahra na dariya take fad’in Ta tuna mata lokutan baya haka Maa d’inta da Paa sukan sakata tsakiyan gado suyita bata tatsuniyoyi da labarai masu dad’i har bacci yayi gaba da ita kafin su tafi nasu d’akin.. Wasu lokutan ma haka gaba d’aya bacci yakan d’aukesu gaba d’aya.... Muhibbah saidai tai murmushi tana jin Zahra na labarin wasu kyawawan d’abi’u na mahaifinta.. Ba tareda tasan cewa cikin zuciyar Muhibbar babu komai sai tsanar Mahaifin nata da k’yamatarsa.... A haka bacci b’arawo ya sacesu... ** Washe gari Fada ta cika fam da masu sarautun gargajiya, yaran Sarkin kaf suna nan idan ka d’auke Mahmood wanda tun safe yai ficewarsa daga Masarautar... Yazeed sai famkam famkam yake za’a tabbatar dashi matsayin sarki mai jiran Gado sannan Juma’a mai zuwa a nad’asa... Sautin algaita da tambura sai tashi suke cikin masarauta... Yazeed yasha gayu cikin kayan sarauta tamkar wani d’awisu haka yake taka k’asa Hadiminsa na biye dashi yana masa kirari da yabo irina gidan sarauta.... Babban Zauren taro ya cika fam da masu sarauta... Yazeed ya k’araso gaban Fu’ad dake binsa da muguwar kallo tun shigowarsa, murmushin nan nasa ya saki da gefen baki, yayi tsayuwa irinta masu ji a Mulki gaban Fu’ad, hannayensa hard’e yake dubansa kana yai gyaran murya kad’an yace “Aren’t you gonna congratulate me little brother... Ko har yanzu kana shakkun ni ne nan zan zama Sarki...?!” Fu’ad ya d’an murmusa had’ida shafe fuskarsa da tafukan hannunsa biyu wanda yin hakan d’abi’arsa ce, ya k’arewa Yazeed kallo daga sama zuwa k’asa ya d’an kauda kai gefe yana kuma sakin murmushi yace “Ai banga Sarkin ba balle nai maka murna... B’ata lokacinka kawai kake don na tabbata kai d’in har abada bazaka tab’a zama Sarki ba muddin za’a bi cancanta da kuma dacewa...!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya... Yazeed ya kai k’ololuwar b’acin rai... Sai faman sakin huci yake yana tururi yake duban Fu’ad ji yake tamkar ya kai masa naushi sai faman dunk’ule hannunsa yake... Bazai iya jure kalaman Fu’ad ba... Ya yunk’ura zai kai mai naushi Jamal dake gefe yai saurin rik’esa a hankali yake furta “Don’t make a scene here please Yazeed..!” Fu’ad na murmushi yake fad’in “Barshi... Please do it... Go ahead, do it Yazeed... Ka nuna musu asalin kaid’in ba wanda kake faking ba... Just do it...!” Ya k’arashe cikin huci.... Jamal ya janye Fu’ad yana fad’in “Ya isa haka Fu’ad, karku bamu kunya dan Allah... Martaban gidanmu zaku tab’a...!” Fu’ad ya d’an dubi Jamal had’ida fincike hannunsa ya koma gefe ya zauna yana sakin huci dan dukansu biyu da Yazeed d’in har Jamal d’in haushi suke basa idan ya tuna tilasta masa da sukai ya aikata laifin da har yau yake danasanin aikatawa tsawon rayuwarsa.. Laifin da ya zama silan rugujewar rayuwarsa da Farin cikinsa.... Yazeed kaw k’arasawa yai yana ci gaba da taku cikin babban Zauren masu muk’amin cikin Fada na kawo masa caffa (Gaisuwa irinta masu mulki) kai kace an riga an nad’asa... Shi kad’ai sai wani cika yake yana ayyana hukunci mai tsauri da zai yanke wa Mahmood da zaran an nad’Asa Sarki.... Tabbas Mahmood zai zama abin kwatance cikin Masarautar, sai ya d’and’ani kud’ansa Ta yanda sunan Sarki Yazeed kawai yaji an ambata zai daburce hankalinsa ya gushe... Ya murmusa kad’an yanajin badon Shid’in yanzu sarki bane da tuni ya fashe da dariya tsaban tsananin munin horon da ya tanadarwa Mahmood d’in.... Yana tsaka da tinanin ne yaji cak sautin algaita da tambura sun tsaya kaman daga sama ya hango Majidad’i ya shigo cikin Zauren kai kace jeho sa akai... Doguwar takobinsa rik’e a hannunsa sai faman huci yake tamkar wani zaki.... A d’ari Yazeed ya mik’e tsaye yana ware idanu tabbas wannan mahaukacin ne rik’eda takobi.... Majidad’i na dariya yake fad’in “Wow wow wow..! King Yazeed AbdulJabbar ai ban zanci har munyi wasan Takobin har kaci har an nad’aka ba.... Ka mance ne na tuna maka...? Agreement d’in namu ba haka bane Dark Prince... Bayan mun kai Mahmood k’asa Wasa za’ai d’aya ya fille kan d’aya wanda yai nasara shine zai zama Sarki..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji yana mai zaro Takobin daga cikin gidanta... Gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen suka mik’e tsaye suna kallon kayan Al’ajabi wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan.... Ana tsaka da wannan yanayi kururuwa da hayaniya had’ida ihu ya gauraye cikin Fada ana fad’in bayyanar Mahaukaciya... Dogarai sai faman guje guje suke ana kokawan Kamata amma sun kasa.... Giwa Alkyabba a hannu ta nufo k’asa dan ita kanta kururuwan da hayaniyar har tsakan kanta takeji ga hannunta dake tsananin mata k’aik’ayi wanda bata tab’a jin irinsa ba.... Tafiya kurum Giwa take ba tareda sanin yanda take jefa k’afafunta ba... Bayi sai k’amewa suke suna bata hanya ... lokaci guda take doka kiran Jakadiya a hargitse... Masarauta babu lafiya... *Toh fah yau akeyinta ga Izzatu ta bayyana....Ga kuma Yazeed da Majidadi ko yaya wasan zata kaya.....??? SameenaAleeyou📚 [8/13, 7:34 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *44* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A daidai mashigar sashen nata suka had’uda Jakadiya jikinta sai karmami yake, illahirin jikinta rawa yake... Cikin tsananin tashin hankali Giwa taceda Jakadiya “Jakadiya mai nakeji... Shin da gaske Izzatuce ta bayyana...?!” Jakadiya tai saurin jinjina kai tana mai zubewa saman gwiwoyinta “Allah shi taimakeki gaskiya ne Izzatu...Izzatu itace Ta bayyana cikin Fada...!” Giwa ta zaro idanu waje tana dafe da k’irji take fad’in “Jakadiya hakan ba mai yuwa bane... Sanin kanki ne bayyanar matar nan tashin hankali ne tsantsa da musiba cikinta... Bayyanar Izzatu yana nufin za’ai babban rashi cikin Masarauta... Jakadiya ina Ubandoma... Shi kad’ai yake iyawa da Izzatu ta k’arashe cikin wane irin yanayi mai gauraye da d’imauta.... Jakadiya Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Allah shi taimakeki kin mance cewa Ubandoma yana tsare hannun Masarauta... Bamuda hurumin tunk’aransa a halinda ake ciki...!” “Jakadiyaa!!” Giwa ta darara mata wani irin gigitaccen tsawa wanda ya sanyata mik’ewa tsaye zumbur ba tareda tasan tayi hakan ba... Giwa taci gaba da fad’in “Mune Masarauta, mune Fada Jakadiya babu Uban da ya isa ya hanani aiwatar da dik abinda naga dama cikin Masarautar nan, ba’a haifa ba kuma baza’a haifesa ba... Badon mahimmanci da rayuwar Izzatu kedashi a gareni ba da yau d’in Ta bak’unci lahira kowa ya huta...!! Jakadiya inaso Ki nemomin Ubandoma yanda ya shiga ya fita..!!” Cikeda risinawa Jakadiya tace “An gama rankishidad’e..!!” Daga haka sa kai tai Ta famtsama cikin Masarauta tana tinanin Ta yanda zata soma neman Ubandoma gashi babu Waziri babu dalilinsa, duk tulin kiran da Giwa Ke masa sam bai d’aga ko guda d’aya ba... K’irjin Giwa yaci gaba da bugawa ba tareda tasan dalili ba... Hankalinta bazai kwanta ba muddin bataga Izzatu a hannunta ba... Ya zama tilas Ta canza ma Izzatu ma’ajiya idan ba haka ba tabbas duk wasu abubuwan da ta jima tana ginawa tsaf zasu rushe, sadaukarwar data jima tanayi zai tashi a aikin banza ita kuwa sam bazata tab’a barin hakan ya kasance ba...! Ta k’arashe tinanin nata tana mai fitowa daga sashen nata... Ganin Masarautar a cike mak’il yasata tina cewa ashe akwai taron cikin Masarautar sam sabgogin gabanta sun sa ta mance hakan... K’irjinta ya kuma bugawa tamkar an sauk’e mata guduma... Lallai kuwa Izzatu bata zab’i rana mai kyau ba... Bazai yuwu yau d’in tayi shawagi cikin Masarauta ba hakan barazana ne Babba gareta... Babu shiri ta koma sashenta yanda ta umarci Hadimanta guda biyu su fiddo mata sutura na mulki da k’asaita dole ta nufi babban Zauren taro zama a fadarta bai ganta ba yau d’in.... Muhibbah da fitowarta kenan daga b’angaren su Umaima tayi rakiyawa Zahra ta barota tareda Umaiman bayan taceda Umaiman ta kula da ita dan har lokacin Zahra bata wani dawo dai dai ba nan ta hangi wilk’awan Giwa tamkar giftawan walk’iya... Koda ganin irin tafiyar da Giwa take kasan babu lafiya... Tai d’an jim tana mamakin meke faruwa dan su sam basuji duk hayaniyar da ake cikin Masarautar ba... Wasu bayi dake kakkab’e babban parlorn Giwa na k’asa ta sinkayo suna fad’in tashin hankalin dake cikin Fada na bayyanar mahaukaciya... Gabanta ya yanke ya fad’i kenan mahaukaciyar nan ta kuma bayyana... Cikin d’an sassarfa Ta iso yanda bayin suke... Suna ganinta suka had’iye sauran maganganun nasu suka risina alamun girmamawa... Muhibbah ta bisu da kallo ba tareda tacedasu komai ba tasa kai tai shigewarta... Zama bai ganta ba, dik yanda za’ai ya zama dole tasan yanda zatai taga mahaukaciyar nan k’ila wani haske ya kuma yaye mata.... Dik yawon da tai cikin Fada babu mahaukaciya Izzatu babu alamunta... Hango Giwa da tai ta nufi wata hanyar cikin shigata alfarma Hadimanta guda biyu biyeda ita hakan yasa Muhibbah tai saurin take masu baya.... Shigewarsu Giwa da kad’an Jakadiya ta iske Waziri da Ubandoma had’ida wasu dogarai majiya k’arfi dake rik’eda Ubandoman... Yanayinda Waziri ya ganta ciki ya tabbatar mata babu lafiya... Jakadiya ta dakatar dasu ta buk’aci ganin Waziri a keb’ance... Nan take sanar dashi abindake faruwa... Babu shiri Waziri ya umarci dogaran su kwance Ubandoma... Sukai yanda yace, ba tareda b’ata lokaci ba Waziri ya sanarda Ubandoma abindake faruwa... Kan kace mai sun fantsama neman Izzatu cikin Fada Ta yanda sukeda tabbacin zasu sameta....! ** Matawalle ne ya mik’e a fusace yana fad’in “Kai Majidad’i haukar nan taka Ta ishemu kar ka kawo mana shashashanci nan...!” Majidad’i ya d’ago Takobin sama ya nuna Matawalle dashi yace kana k’arasowa nan zan farke cikinka har lahira.... Wllhi na rantse da Ubangijin dake busan numfashi bani barin wajen nan sai na kara da wannan d’an tayin marassa kunyan... Sai na nuna masa ba’a cin amanata a kwana lafiya... Fad’a ni sayenta ma nake balle nawa... Zamu kara... Ko ni...Ko kai.... Wanda ya riga fille wuyan d’an uwansa Sarautar tasa ce..!!” Ya k’arashe yana mai duban D’angundan da suka shigo tare dashi yace “Fara aikinka..!” Babu musu D’angundan ya soma busa irin nasu na ‘yan dauri yanayi yana wasa Majidad’i had’ida ihu irin nasu.... Daga Jamal har Fu’ad ganin abin suke tamkar mafarki... Meke faruwa ne haka... Wannan wane irin al’amari ne... Jamal yasan Majidad’i yasan ko wani kalan mahaukaci ne shid’in... Bayayiwa Majidad’i kallon cikakken mutum mai lafiya yasan sarai aka k’yalesa da d’an uwansa ko shakka babu zaiyi halin dabbobi ne ga d’an uwansa Yazeed tinda kaf abokan Majidad’i ‘yangunda ne da ‘yandauri hasalima Majidad’i yasha maganin k’arfe Takobi bata kamasa, trap shima ya had’awa Yazeed kan cewa su amince a gwada k’arfi da Takobi wanda duk yai nasaran kashe d’aya shi zai zama Sarki, yasan yasha na k’arfe dan haka a sauk’ak’e zai fille wuyan Yazeed mulki ya dawo gidansu.... Jamal yai tsalle ya raba tsakaninsu, yana mai duban Majidad’i yake fad’in “Babu wani wasan da za’ai... An jima da daina irin wannan jahilcin a Masarautar nan, addini ya wadata bazaku kawo mana abin fad’i a sauran masarautu dake kewayenmu ba...!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji.... Majidad’i da a yau d’in harda tozali ya shafa cikin idanunsa k’uri yaiwa Jamal kana ya tintsire da wata irin bahaguwar dariya, yana nuna Jamal da Takobin yake fad’in “Sai na fille wuyanka, na fara dakai kafin na isa kan d’anuwan naka Kaga sai ayi gawa biyu a take ku hutasar da mahaifiyarku da yin kuka biyu... Zatai kuka d’aya ma mutuwa biyu...!!” Ya k’arashe yana mai d’aga Takobin sama da niyyan sarawa Jamal... Daidai nan Giwa ta K’araso cikeda tashin hankali zuciyarta na zillo cikin k’irji... Hankalinta bai ida tashi ba saida ta hango Majidad’i na yunk’urin sauk’ewa d’anta mafi soyuwa a gareta Takobi a wuyansa... Giwa ta k’walla kiran sunan Jamaal da wane irin k’aran gaske daidai lokacinda Jamal d’in ya kauce Takobin ta samesa a kafad’a ya keta masa hannun riga had’ida kuskuran fatarsa kad’an, ji kake kyaaat.... Dukda zuciyarta dake tsananin bugu hakan bai hanata k’arasowa cikin parlorn ba tana fad’in waye ya baiwa wannan mahaukacin izinin shigowa cikin Fada...! Kallon k’ask’anci Majidadi ya rakata dashi a daidai kokacin da aketa zubewa ana faman gaisheta.... Dariya ya kuma fashewa dashi kana yace “Madallah da isowarki Rankidad’e... Idan kin mance na tuna miki nine nan wanda ba’a sakani ba’a hanani kuma ajalin mulkin ahalin Sarki AbdulJabbar... Yayi daidai da kikazo nan ki gani da idanunki yanda basai ankai miki labari cikin Fada ba... Kiga yanda zan murk’ushe wuyan ‘ya’yanki musamman wannan babban maci amanan...!!” Ya k’arashe yana mai nuni da Yazeed da har lokacin bai daina binsa da ido yana sakin huci ba.... Dikda tsananin shakkarsa da Dogarai keji hakan bai hanasu yunk’urin dakatarda Majidad’i ba ganin yana k’ok’arin wuce gona da iri har Giwa ce zai dinga fad’i mata kalamai haka....! Takubba biyu ya rik’e a duka hannayensa yana mai nunasu da Takobin yake fad’in dik wanda ya fasa tunk’arosa bai haifu ba... Ko step d’aya bazai k’ara ba amma duk wanda yai wauwautan k’arasowa gabansa ko shakka babu saidai uwarsa ta haifi wani amma bashi ba dan har lahira zai cire wuyan mutum... Ya k’arashe zancen nasa yana mai kuma d’ago Takubban.... Yazeed da ya kula ya maida hankalinsa ga dogarai tsalle yai ya tokari Majidad’i saida ya kaisa k’asa kana finciko Takobi guda dake hannun Majidad’in... Majidad’i ya rakasa da kallon mamaki dan bai zaton Yazeed zai iya koda motsa Takobi hannunsa ba balle har ya k’wace..... Lokaci guda Yazeed ya sakar masa murmushin nan nasa had’ida d’aga gira guda... Ya k’arasa gaban Majidad’i dake zube wajen yana juya Takobin dake hannunsa yasa k’afarsa guda ya take k’irjin Majidad’i lokaci guda yake nuna k’wayar idanunsa da tsinin Takobin, murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake furta “Ina Jarumtar naka..? Kodai dama a baki ne ba’a fagen daga ba...?!” Shiru ya d’an ratsa tsakani kana Yazeed yaci gaba da fad’in “Zan iya fille kanka a nan idan naso, idan kuma naga dama muka kara naci k’arfinka sai na maidaka bawa har k’arahen rayuwarka... Ka rayu cikin yimani bauta... Na tabbata bazakaso hakan ba... Partner..!” Ya k’arashe muguwar murmushi saman fuskarsa... Lokaci guda ya kuma d’agowa yana bin illahirin mutanen dake wajen da ido ciki harda mahaifiyarsa da tsananin tashin hankali ya nuna saman fuskarta... Fuskar nan nasa a matuk’ar d’aure ya bud’e murya yana fad’in “Inaso kowa ya bud’e idanunsa da kyau yaga yanda zan gama da wannan d’anta’addan kuma sannan hakan ya zamto izna da ishara ga duk wani mai yunk’urin ta’addanci irin nasa... Masarautar nan bazata lamunci ta’addanci ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji Majidad’i dake kwance k’asa gaban Yazeed da ya take masa k’irji da k’afa guda murmusawa shima yai ba tareda ko gizau ba yace “Tsari mai kyau Your Highness, dad’ina dakai akwai kwanya da kaifin basira... Kai da kanka kake kawo shawarin abinda za’ayi kuma shawarin Naka yayi daidai da tunanin duk wani mai san mulki... Naji dad’in shawarinka a karo na biyu... Mu kara a fafata wanda dik yaci galba kan d’an uwansa sai ya k’arashi rayuwarsa cikin Bauta... Zanso jinin AbdulJabbar ya zamto Bawa mafi k’ask’anci a gareni...Amma saidai kashh banjin zan yafewa duk wani wanda yaci amanata har na bashi daman sake rayuwa... Abu guda nake ma duk wanda yaci amanata shine KISA... Dama guda kake dashi yanzu da nake kwance gabanka ka gama dani tin ina kwance k’asa k’ark’ashin k’afanka dan nayi imani ni kuma idan har ka bari na tashi sai na kasheka...!!” Yazeed da baisan dawan garin ba dan sam baisan Majidad’i yasha maganin k’arfe ba cikin tsananin huci yake kuma danna k’afarsa saman k’irjin Majidad’i ya shiga k’ok’arin darza masa Takobin da iyaka k’arfinsa, sai faman haki yake yana kuma darza Takobin amma saidai abin mamaki ko kad’an tak’i ratsa fatar Majidad’i balle ta shiga cikin jikinsa... Majidad’i yai masa K’uri saima sakin murmushi da ya soma lokaci guda murmushin nasa na rikid’ewa dariya had’ida shewa... Jikin Yazeed yai bala’in sanyi... Ya darza ya darza Takobi ta kasa shigewa... Idanunsa suka firfito waje... Cikin tsananin tashin hankali Giwa Ke girgiza kai tana k’ok’arin fincika daga rik’onda Jamal yai mata take fad’in “Jamal ka k’yaleni na ceci d’an uwanka mahaukacin nan kashesa zai...!” Illahirin jama’an dake wajen wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan... Harta Muhibbah dake lab’e daga gefe abin itama tsoro da mamaki ya bata... Ta kuma duban Majidad’i tana mamakin wanene wannan da tsana mai k’arfi yai k’amari tsakaninsa da ahalin sarki AbdulJabbar... Kuma ga dukkan alamu baida tsoro ko gizau a tattaredashi.... Tinaninta ya katse sana Majidadi ya tsagaita da dariyarsa yana duban Yazeed da tuni ya gaji da darza Takobi sai faman haki yake gumi na gangaro masa... Murmusawa yai kana yace “Ka d’auka zanzo wajen nan ne unprepared your Highness.... Ka tapka babban kuskure daka zaci you can outsmart someone like me.... Yanzu ni kuma zan baka abinda kake nema... Zan kashe na cire wuyanka ayi min roman k’wak’walwanka sannan nayi sark’a da k’wayan idanunka na ratayeta a wuyana...!!” Ya k’arashe yana mai daka tsalle daga kwance sai gashi ya mik’e tsaye Yazeed ya zube k’asa... Lokaci guda ya soma nufo Yazeed yana sakin muguwar murmushi Yazeed d’in na faman jada baya daga zaune zuciyarsa naci gaba da tsinkewa yaga mutuwa muraran.... Giwa na kuma fincika take fad’i ma Dogarai su kama wannan d’anta’addan amma ko gizau babu wanda ya matsa sabida tsananin tsoron Majidad’i dan yanda yace d’in tabbas zai kashe rai.. Ta koma gasu Galadima su Hakimi dansauransu tana fad’in haka sunaji suna gani zasu bar wannan mahaukacin ya kashe mata d’a... Suma babu wanda ya motsa saima muzurai da suke, yanda Takobin Majidad’i Ke tsananin k’yalli tabbas tsaf zai fille wuyan mutum.... Fu’ad da tuni kansa ya soma juyawa waya ya ciro ya kirawo Yayansa Mahmood amma bai d’agawa... Kansa taci gaba da sara masa... Sosai ya kame kansa dake tsananin sara masa ya fice daga cikin wajen gaba d’aya cikin wane irin sauri kaman zai kifa k’asa... Muhibbah tana ganin ficewarsa tai saurin bin bayansa dan babu sauran abinda zata tsaya kallo ko shakka babu wannan D’angundan zai kashe Yazeed kisan wulak’anci a sauk’ake sakayyanta data ahalinta na bibiyan wannan ahali... Koda wannan tashin hankalin aka k’yale Giwa tasan ta sami nata ajalin kenan... Gwara tabi wancan mahaukacin Fu’ad taga shi kuma mai yake shiryawa.... ** Kafin kace wani abu cikin Masarauta gaba d’aya ya yamutse, hargitse ne ta ko ina, Isowar Ubandoma da Waziri ya hana Majidad’i sarawa Yazeed Takobin wanda tuni ya sadakar Majidad’i ya fille wuyansa.... Ubandoma yace “Ku dakata zan fad’i gaskiya..!!” Kallo ya dawo kan Ubandoma da Waziri.. Waziri ya jinjina masa kai alamun yayi magana.... Ubandoma ya soma fad’in “Yarima Mahmood baida laifi... Kawai na fad’i hakan ne dan ceton rayuwata da Yarima Yazeed yayi kuma shima Yarima Yazeed baida laifi duk abinda na fad’i ni ne nan na k’ago na fad’a babu laifin ahalin Marigayi Sarki AbdulJabbar ko d’aya..!!” Ya k’arashe yana mai duban Majidad’i.. Dariyar rainin hankali Majidad’i ya fashe dashi yace “Ni ne nan zaku rainama hankali ku maisheni dolo wanda baisan mai yakeyi ba... Kunje kun kitsa yanda zakuyi... Nayi imani ku kuka kashe min mahaifina dan ku d’in ba’a aminta daku nayi kuskure da na yarda dakai Yazeed bayan kaid’in kaci amanan d’anuwanka... Gashi nima kaci amanata... Kaid’in ba d’an halas bane dan haka yanzu zan gama dakai bayan na sanar da d’inbin al’umman dake wajen nan irin cin amanar dakaiwa d’an uwanka Mahmood kaso d’aura masa gagarunin sharri...!!” Daidai lokacin Mahmood da Turaki suka shigo... Muryar Mahmood suka sinkayo yana fad’in “Mai kake cewa Majidad’i... Meye kuka k’ulla min kaida Yazeed..?!” Giwa ta k’ara so ga Mahmood tana fad’in “Sadauki kada ka yarda da zancen wannan mahaukacin so yake ya raba tsakaninku.. So yake ya tarwatsa ahalinmu shid’in D’anta’adda ne... Kar ka yarda da kalma guda da zai fito daga bakinka....!” Dariyan da Majidad’i ya fashe dashi ne ya sanyata dakatawa tana mai rakasa da wani irin duba... Mahmood ya d’an dafata kad’an yana mai furta “Maami Kiyi hak’uri, Ina son jin abinda Majidad’i Ke son fad’i...!” Majidad’i ya kuma fashewa dariya kana yace “Da kyau Rankaidad’e, ni kuma yanzu zan sanar dakai abinda wannan k’Aramin maras kunyan yaso shirya maka..!” Babu b’ara lokaci Majidad’i ya fad’I duk wani shirinsu da Yazeed a bainar jama’a... Yana ida fad’i ya kuma d’aga takobin zai dab’a masa Jamal ya isa a guje da zummar taimakawa d’anuwansa Yazeed ya janyesa daga wajen dan har lokacin Yazeed zube yake wajen gaban Majidad’i ya kasa koda motsa ‘yar yatsansa sabida hanjin cikinsa da suka gama kad’awa.... Saidai akayi rashin sa’a duk’awan da Jamal zai da niyyar taimakawa d’anuwansa Yazeed Takobin mai d’aukeda guba mai muni ta sauk’a kan k’afar Jamal... Ta yanki Jamal a k’afarsa na dama... Wane irin k’ara ya saki had’ida zubewa wajen yana mai kama k’afarsa... Sara Takobin da Majidad’i zai Dogarai suka sami chance d’in rufe kansa cikin buhu sukai masa caa suka cafkesa, D’angundansa zai arce shima aka capkosa... Tuni aka fice da Jamal neman agaji na gaggawa dan tuni ya had’a gumi sabida tsananin guba da Takobin Ke d’aukedashi, da ace a ciki ko wuya yankan ya samesa tabbas da tuni ya shek’a lahira... Babu shiri Giwa da Hadimanta harmada Jakadiya suka take masu baya, saiga Giwa na kuka sharhsar da hawaye... Cikin zuciyarta take furta Jamal d’inta bazai mutu ba dan muddin ya mutu ko shakka babu itama binsa zatai... Tabbas wannan shine ma’anar bayyanar Izzatu... Jamal d’inta ne ashe.... Wani sabon kuka ya kuma kufcewa Giwa sai had’e hanya take suka nufi asibitin cikin Masarauta, Jamal bai daina damk’e k’afarsa dake tsananin masa zogi ba yana fad’in Giwa ta yafe masa mutuwa zai... A b’angaren Mahmood kaw tinda Majidad’i ya ida fad’in abinda d’an uwansa na jini Yazeed yai masa bai kuma sanin meke wakana wajen ba... Yanajin hayaniyar mutane daga can nesa nesa.. He couldn’t believe his own brother can do this... Turaki ne ya taimaka masa ya zaunarsa saman kujera... Turaki cikin Washe baki yake fad’in “Allah ya wanke ka abokina... Allah ya wankeka a idon duniya.... Mahmood d’ago kaji gashi nan ana sanarwa kaine Sarki, ka zama Sarkin Masarautar nan your Highness...!” Siririyar hawaye ne ta gangaro masa sanda yaji Tambura da algaita na tashi ga zigazigi yana wasashi yana ambato sunansa anai masa kirari irin na Saraki “D’an Toron Giwa... Gaba salamun baya salamun... Allah ya baka... Allah yaja zamanin Sarki Mahmooda d’an AbdulJabbar jikan Mahmooda...!!” Siririyar murya ce ya katse shagalin tana fad’in “Ku dakata shid’in bai cancanta ya zama Sarki ba...!” Da tsananin mamaki illahirin jama’an cikin Zauren suka juyo suna dubanta da tsananin mamaki.... Mahmood ya furta “Zahra!!!” A hankali... Lokaci guda Zahra taci gaba da takowa cikin tapkeken parlorn hawaye na gangaro mata... A haka ta isa gaban mahaifin nata.... ** Haka Muhibbah ta dinga bin bayan Fu’ad har suka shige sashensa yanda ya fad’a bedroom ya janyo wata drawer ya jawo k’wayoyi cikin hannunsa yana k’ok’arin afasu cikin bakinsa yake fad’in “No no no please... Please forgive me... I was forced to do it.... Please just leave alone..!!” Ya k’arashe yana mai kuma tak’urewa jikin gini daidai lokacin Muhibbah ta shigo jiki a matuk’ar sanyaye take dubansa.... Yana k’ok’arin afa k’wayoyin tai saurin bige hannunsa suka watse k’asa.... Fu’ad ya d’ago yana dubanta lokaci guda yaci gaba da matsawa jikin gini yana furta “Please forgive me...Please please please.. I don’t want to.. Please...!!” Tamkar mai tab’in hankali haka yake sunbatu yana kuma matsawa jikin gini.... Muhibbah tai zaman rak’umi gabansa tace “Fu’ad meke faruwa... Please tell me wane laifi ka aikata kake neman afuwa...?!” Ta k’arashe cikin d’an d’aga Murya.... Dubanta yai da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda yake furta “Please forgive me Muhibbah... Baki cancanceni ba... I’m a monster a killer... A ra....!!” Ya kasa ci gaba da magana sai hawaye dake kuma ambiya a fuskarsa.... Lokaci guda yanayinta ya sauya, idanunta sukai jazir, cikin dakewa take ci gaba da fad’in “If you truly love me, you tell me what exactly you’re hiding Fu’ad... Idan ba haka ba ka mance dani dan bazan tab’a kasancewa da mutum irinka ba... Now go ahead and tell me what really happened...!!” Cikin wane irin yanayi yake furta “I cant Muhibbah... Mahaifiyata da ‘yanuwana zasu disowning d’ina muddin maganan ya isaga Ya Mahmood...!!” Cikin wane irin sanyin jiki had’ida bugawan zuciya tace “I don’t get you Fu’ad... Meye kake b’oyewa Yarima Mahmood..!?” Fu’ad na kuka sosai yake furta “Wani babban laifi da muka aikata nida ‘yan uwana guda biyu... Yazeed Jamal da kuma ni Fu’ad... Wani laifi ne da muka aikataga wata ‘yar talikan yarinya shekaru goma sha hud’u baya... Mun aikata laifin ne a bisa umarnin mahaifiyarmu... A cewarta idan har bamu hakan ba bazamu tab’a tabbata akan Karagar mulkin Masarautar nan ba... Na aikata laifin ne dan sadaukarwa ga ahalina Muhibbah... Amma tun bayan wancan lokacin ban kasance cikin kwanciyar hankali ba har yau...!!” Ya k’arashe hawaye na kuma ambaliya a fuskarsa... Muhibbah da tuni duniyar ya soma juya mata, cikin tsananin sanyin jiki had’ida rawar murya take furta “Mai kuka aikatawa yarinyar da ahalinta..?!” Ta k’arashe siririyar hawaye na gangaro mata.. Fu’ad yace “Zalunci mafi muni... Mun mata fyad’e dukanmu uku... Muka kashe mahaifinta sannan muka cinna wuta cikin gidan ta k’one da ita da mahaifiyarta suna cikin gidan... Wuta ya cinyesu a gaban idanuna... I couldn’t do anything to stop the fire... Yazeed da Jamal sun janyeni sun hanani taimakon yarinyar da mahaifiyarta... Haka muka k’yalesu suka k’one k’urumus cikin gidan... Bazan tab’a yafewa kaina ba Muhibbah...!!” Ya k’arashe cikin tsananin kuka... Muhibbah da hawaye Ke ambaliya a fuskrta cikin tsananin rawar murya tace “Kana nufin ku kuka aikata laifin banda Mahmood...?!” Fu’ad ya jinjina kai yace “Idan Yaya ya sani tabbas zamu rasashi bazai tab’a yarda ya rayu cikin ahali azzalumai ba... Mahaifiyarmu zata rasashi amma a cewarta duk abinda mukai sadaukarwa ce gareshi dan tasan shi bazai tab’a aikatawa ba shiyasa mu Ta umarce mu muyi... Ranan bukin wata sallah ce... Mun fita mu dukanmu hud’u akan dawakanmu dan zaga gari, saiko bawanmu Ja’afar dake rik’eda linzami na sabida a lokacin ni k’arami ne sosai ban wuce sha uku ba shisa Jafar ke rik’e min linzami ko fita kilisa zamuyi... A can wajen gari muka tsinci yarinyar tanata kuka da alama tabi ‘yan kallon dawakai da wasan sallah masu zaga gari shine ta b’ace... A lokacin almuru ya k’arato... Yaya shine ya soma hango yarinyar ya umarci Ja’afar ya k’arasa ya duba dan yaji kaman kukan mutum... Jafar yai kaman yanda Ya Mahmood yace....!” Ya d’anyi fasali hawaye naci gaba da gangaro masa... Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Akai sa’a Jafar yasan yarinyar a bayan masarauta gidansu yake kaman yanda Jafar ya sanar da Yaya... Yazeed yace mu tafi mu barta bai kamata a ganmu da k’ask’antattun mutane irin wad’Annan ba... Yaya yace koda wasa baza’ai haka ba... Yaya da kanshi ya d’auketa ya azata saman dokinsa da yake bisa tana gaba yana baya ya bata apple d’in da yake ci, kallo guda zakai masa ka fahimci tsantsan tausayin yarinyar da ya kamasa...” Muhibbah Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka gangaro mata tana mai tuna tabbas anyi haka, wannan kyakkyawan murmushin nasa shine saman kyakkyawan fuskarsa... Ta sinkayo muryar Fu’ad naci gaba da fad’in “Ga dukkan alamu yarinyar da Jafar sunsan juna sosai dan na kula da irin duban da sukewa juna tana daga saman doki Jafar na janye da linzamin doki na.. Hasalima sanin Jafar da tai yasa Ta amince damu...” “A Haka muka iso har masarauta, dan lokacin da muka iso har yarinyar tayi bacci jikin Yaya sabida tafiya ne saman doki dole akwai gajiya musamman ga yarinya mace irinta... A lokacin da muka iso masarauta d’an aike ya taremu ya sanar damu mahaifinmu Wato Mai Martaba Amale yana kiran Ja’afar kirata gaggawa... Yaya Mahmood yace maza Ja’afar yaje ya amsa kiran Amale shi zai kula da yarinyar zai kaita Gida sannan zai sauk’o ya rik’e linzamin dokina dan kar na fad’i...Ja’afar yai masa kwatancen gidansu yarinyar kana ya tafi Fada amsa kiran Mai Martaba... A daidai lokacinda Ja’afar ya tafi amsa kiran Amale ita yarinyar ta farka daga baccinta... Tabi bayan Ja’far da kallo tsoro sosai saman fuskarta, da alama Ta razana sosai damu tinda dama sabida Ja’afar ta yarda ta bimu gashi shi kuma ya tafi....” “Mun kula tunda Ja’afar ya tafi hankalin yarinyar bai kwanta damu ba... Sosai tsoronmu ya bayyana a tattareda ita musamman dataji Yazeed yanata mitan maiyasa zamu taimaka ma k’ask’antacciya irin wannan yarinyar...! Ya Mahmood shi ya sakar mata murmushi ya tambayeta zata gane gidansu daga nan bayan Masarauta, tai saurin girgiza kai cikeda tsoro tace dashi ita bazata gane ba dan basu jima da dawowa garin ba kuma a lokacin akwai duhun dare..! Mukaita dariyarta muna daga saman doki Yaya ya tsawatar mana yace mu daina mata dariya, ya kwantar mata da hankali da fad’in cewa zamu kaita har gida....!Ana haka muna tafe Yaya ya rik’e linzamin dokina da kuma dokin da ita yarinyar ke bisa d’an aike ya kuma zuwa yayi kiran Yaya inji mai Martaba... Yaya ya bar mana amanan Yarinyar ya janyo Yazeed gefe yaja masa kunne kan cewa mu tabbata mun kai yarinyar har gidansu, shi zai jeshi ya amsa kiran Mai Martaba.... Muhibbah ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen suka zubo mata... Tabbas bata kula da tafiyar Mahmood ba sabida duhun dare kuma muryar yaran Sarkin kusan duka iri guda ne ashe Mahmood ya tafi bata sani ba... Ashe amanarta ya damk’a hannun ‘yanuwansa da ya aminta dasu.... Wasu hawayen masu d’umi suka kuma gangaro mata sanda Fu’ad Ke ci gaba da fad’in “Ga mamakinmu Yazeed ya amsa masa bai masa gardama ba, yace ya jeshi babu matsala shi zai kula damu gaba d’aya... Bayan tafiyan Yaya Jakadiya Ta cimma Yazeed da sak’on Giwa kan cewa a daren ranan zamu yarinya muyi mata fyad’e mu dukanmu uku idan har munaso mu tsira da mutuncin gidanmu... Yazeed ya sanar da ita cewa anyi an gama... Dan koda Jakadiya Ta tambayesa ina za’a sami yarinya cikin daren nan sai ce mata yai akwai yarinyar da suke tafe da ita.... Jakadiya tace hakan yayi su tabbata sunyi yanda aka umarcesu... Ta bada garin magani ma Yazeed kan cewa duk wanda yazo amfani da ita cikinmu sai ya Shafa a al’aurarsa kaman yanda malamin Giwa yace... Muna jin sautin murya ana k’walla kiran suna SAUDATU alamun ahalinta na nemanta, kafin tayi yunk’urin amsawa Yazeed yai saurin rufa mata alkyabbansa akanta ya toshe bakinta ya janyota muka shige wani lungu nan bayan masarauta.... Jamal wanda shima da alama yasan abinda Ke wakana shi ya d’aure idanun yarinyar da k’yalle duk ihu da birgima da take.... Abinda ban tab’a gani ba shi ya faru gaban idanuna... A gabana Yazeed ya lalata rayuwar yarinyar cikin wulak’anci da cin zarafi.... Bayan ya gama Jamal ma yayi... Ina kuka ina sanar dasu ni k’aramin yaro ne haka suka tirsasa min shafa wanann garin maganin a al’aura na abin mamaki kuwa sai ji nayi ina matuk’ar son kasancewa da mace... Nima nabi sahunsu... Muka wulak’anta k’aramar yarinyar da Yaya ya bamu amanan cewa mu kaita ga iyayenta.... Koda muka gama sai k’arasowa Jakadiya Tai ta d’auki yarinyar wacce ko numfashi batayi tace kar mu damu bata mutu ba ita zata kula da ita, a cewarta ita zata Kai yarinyar ga iyayenta Ta sanar dasu an tsinceta an mata fyad’e.... Nidai tindaga wanann lokacin kuka kawai nake bansan meke faruwa ba, umarni kawai suke bani sai ganin dogari guda biyu nayi Yazeed da Jamal suka janyoni muka bi bayan dogaran... Ina tambayarsu Ina Yarinyar... Jakadiya ta Kaita gida..? Sai ce min sukai eh Jakadiya takaita ga iyayenta... Kuma yanzu zamuje ne mu tabbatar da hakan... Hakan yasa nabi bayansu muka k’arasa wani gidan wanda gidansu Yarinyar ne.... Dogaran su suka sanar da mutumin cewa anyiwa d’iyarsa fyad’e tana can asibitin bayan Fada yazo ai masa rakiya yaje ya ganta... Mutumin ya kame k’irjinsa yana salati... Ashe Jakadiya na biye damu amma babu yarinyar a tattareda ita... Tanayi tozali da mutumin mukaji Ta ambato sunansa... Tace Saudatu d’iyarka ce....??! Mutumin ya zaro idanu waje bai iya bata amsa ba... sai gani nayi ta juya cikin sauri ta janyo Dogari guda sunyi magana... Dogarin yana dawowa baiyi wata wata ba ya zaro Takobi da niyyan cire kan mutumin ni kuma nai k’ok’arin kare mutumin Jamal da Yazeed suna k’ok’arin janye ni... Ina fad’i masu bazai yuwu munaji muna gani mu bari a kashe bawan Allahn nan ba bayan cin zarafin da akayiwa d’iyarsa wacce bamusan yanayin da muka barta ciki ba... Yazeed yana janye ni yana yunk’urin hanani saiga wani mutumi ya fito daga cikin gidan Dogari guda ya cakka masa Takobi a ciki... Nayi k’ara na finciko Takobin dake d’amaran d’aya Dogarin nayi k’ok’arin kare Mahaifin yarinyar saidai tuni k’addara ta riga fata ainka da k’aramin yaro Takobin yamin nauyi sosai ban ankare ba sai ji nayi na sare k’irjin mahaifin yarinyar da takobi b’angaren da yake rik’eda tin sanda Labarin fyad’en ya isa masa.... Na saki wane irin k’ara a wajen na kama kaina dake tsananin bugawa, take na zube wajen ban farka ba saida naji d’umin zafin wuta da sautin k’onewar abubuwa, turirin hayak’i shi ya tadani... Naga gidan su yarinyar nata faman ci da wuta... Na yunk’ura zan fad’a cikin gidan Ina mai sanar dasu Yarinyar da mahaifiyar na cikin gidan mu taimaka masu... Yazeed ya janyoni baya ya kikkifa min mari masu zafin gaske yace yarinyar da mahaifiyarta sun mace cikin gidan wuta ya cinyesu, nima idan na shiga saidai nabi sawunsu.... Haka Ina kuka suka janyeni muka nufo Fada Giwa da Jamal suka kafa min warning kan cewa babu abinda ya faru idan kuma nayi gigin sanar da wani fa abinda ya faru zan mance cewa ni ahalin gidan ne musamman Yaya Mahmood wanda ake shirye shiryen bikinsa a lokacin....!! Shin Ta yaya zan iya yafe wa kaina wannan babban laifi wanda muka aikata... Ki fad’a min Muhibbah..!!” Ya k’arashe cikin tsananin kuka... Itama d’in kuka take sosai... Tabbas farkawa kawai tai ta ganta a wani d’aki a kulle ga wani tsohon mutumi kaman maye yanata zagaye kanta da jan k’yalle yana maganganu marassa dad’in sauraro... Ganin haka yasa tai likimau dukda azaban da takeji wanda bata tab’a jin irinsa ba... Hankalinta bai gama tashi ba saida taga wannan tsinannen halittan ya duk’a ya bud’e k’afafunta yana katsan wani abu a al’auarta ga tsananin zafi da zogi mai d’imautarwa da takeji har k’wak’walwan kanta.... Ta kuma rintse idanunta dan hawayen ma sun daina fitowa... Tana jin sanda tsohon mai k’irar abin tsoro ya mik’e ya fice rik’eda k’ok’on da ya gama katse jinin dake fita daga al’aurantar a hannunsa... Ta hango sararin waje daga yanda take kwance cikin d’akin mai tsananin duhuwa... Dukda azaban da takeji hakan bai hanata furta Basmala ba ta karanto ayatul kursiy ta karanto falak’i da nasi... Cikin wane ikon Allah yunk’urin da zatai sai ji tai Ta mik’e zunbur... _Laa ilaha illa Anta subhanaka inni kuntu minazzalumin_ Shine addua’an da harshenta keta nanatawa... Tafiya kawai take ba tareda tana ganin hanya ba take kuma nanata addu’an... Tabbas taji ana kirawo sunan ya da wani irin sauti amma wannan addu’a bai bar saman harshenta ba, duk razanata da ake da abubuwa na ban tsoro bakinta bai daina karanto wannan addu’a ba har saida Ta bud’e idanu Ta ganta a wajen Masarautar... Sai lokacin zafin ciwowwukan dake jikinta suka kuma dawowa ga busasshen jini dake bin k’afarta... Wato ashe Jakadiya ita ce ta kaita ga wannan matsafin mutumin data farka ta ganta gabanshi.... Ashe Mahmood baida laifi hasalima baisan komai ba... Ta zalunci bawan Allah ta had’asa fad’a da d’iyarsa... She needs to stop Zahra tun kafin lokaci ya k’ure... Muryar Fu’ad ne ya dawo da ita daga duniyar tunaninda ta tafi yanda yake fad’in “Baya duk abubuwan da kikaji gamedani nasan bazaki tab’a sona ba Muhibbah... Will you still accept me...?!” Wani irin duba take masa da idanunta masu zuban hawaye, tsanarsa na kuma ratsa zuciyarta lokaci guda take furta “Ka cuceni Fu’ad... Kasa na fara soyayya dakai... You’re a Criminal, I’d never love someone like you... Never, ka mance ka tab’a soyayya da wata mai suna Muhibbah... I hate you.. Na tsaneka Fu’ad, bazan tab’a soyayya da criminal irinka ba... Kuma kasan meye.. Hauka shi ya cancanceka bayan abinda kukayiwa yarinyar can da ahalinta... Ina fata ka tabbata cikin hauka Fu’ad, kada Allah ya kawo rananda zaka warke..!!!” Tana kaiwa nan ta mike ta fice a guje tana kuka sosai, kukanda batasan na tausayin kanta bane ko na tausayin Mahmood ne wanda baida laifi ko k’ank’ani cikin duk abinda ya faru da ita... Cikin wane irin k’ara Fu’ad ya k’walla mata kira yana mai kuma tamke kansa dake ci gaba da sara masa... Lokaci guda ya shiga tattaran pills d’in da baisan adadinsu ba yana turawa cikin bakinsa.....Take ya zube a wajen rik’eda kansa tamkar maras numfashi... Gudu kawai take cikin Masarautar tana addu’an cimma Zahra Ta tareta kafin Ta isa babban Zauren Taro Ta tozarta Mahmood... Saidai tana isowa ta hango Zahra ta fito daga Zauren a guje tana kuka sosai... Tana hango Muhibbah ta fad’a jikinta tana mai kuma fashewa da kuka... Take Muhibbah ta rungumeta hawaye masu tsananin zafi na gangaro mata... Tabbas d alama ta makara Zahra ta riga ta yarfa Mahaifinta cikin d’imbin jama’an Masarauta... D’ago idanun da Muhibbah zatai suka had’a ido da Mahmood wanda fitowarsa kenan daga parlorn ya biyo bayan Zahra... wasu irin kwantattun hawaye Muhibbah ta hango cikin idanunsa wanda ko ba’ace ba jarumta ne da tsananin k’arfin hali suka hanasu zubowa..... SameenaAleeyou 📚 [8/14, 10:58 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *45* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Hawaye ne suka ci gaba da gangaro mata su biyun suna duban cikin idanun juna, Ta kasa janye idanunta daga barin dubansa ta kuma kasa sakin Zahra dake shesshek’ar kuka saima dad’a matse Zahra da tai cikin jikinta hawaye masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata.... Tana ganin sanda Mahmood yasa kai ya fice daga wajen baki d’aya Turaki na biyedashi... A hankali ta lumshe idanunta wasu hawayen na kuma gangaro mata tsananin tausayin Yarima Mahmood da d’iyarsa cikin zuciyarta... Zahra ta d’ago tana dubanta, cikin kuka take fad’in “Dan Allah ki fitar dani daga Masarautar nan wllhi banson zama a nan... Na gaji na gaji da rayuwa cikin gidan nan... Dan Allah ki fitar dani daga gidan nan..!” Kuka yaci k’arfinta.. Muhibbah tai saurin rungumo kanta cikin k’irjinta cikeda tausayawa, cikin tsananin rawar murya take furta “Everything will be ok Zahra.. Ki kwantar da hankalinki kinji komai zai shige ya zama tarihi... Zo muje you need to rest..!!” Bata jira amsar Zahra ba ta janyeta suka nufi Fadar Giwa... Har lokacin jikin Muhibbah a matuk’ar sanyaye yake... Suna tafe suka hange Zuhra da Raheema harmada Umaima hankali tashe sun fantsama cikin Masarauta dan da alama labarin abindake faruwa ya gama karad’e cikin Fada... Muhibbah tana hangosu Ta kuma janyo hannun Zahra had’ida canza masu hanya cikin sauri dan bata fata ta had’uda kowa cikin Masarautar a halinda Masarautar Ke ciki.... Gaba d’aya ranan Masarautar a yamutse take abubuwa ne da dama suka faru gashi uwa uba an nemi Mahaukaciya Izzatu cikin Masarautar an rasa... Neman duniyar nan anyi an rasa yanda Ta shige... Ga Jamal kwance rai hannun Allah kan kace mai dafin jikin Takobin da Majidad’i ya sara masa a k’afa tasa k’afar tayi bak’ik’irin tamkar ba’a jikinsa yake ba, shi kad’ai yasan azaban da yakeji... Cikin gaggawa aka nufi asibitin koyarwa dashi koda wani abinda za’a iya dan da alama cikin sakanni dafin Ke haurawa jikinsa kaman wani Saran bak’in kumurcin maciji, gaba d’aya k’afar ta sauya halitta ta koma tamkar bak’in gawayi Dukda kuwa hasken fata da Jamal kedashi..... Duk wannan hali da ake ciki babu wanda yasan Fu’ad yana kwance cikin d’aki yana aman farin kumfa sakamakon drug overdose da yai... Tashin hankali ne dai wanda ba’a saka masa rana kowa cikin Masarautar hankalinsa a tashe yake.... Dole Mahmood da Turaki ma suka nufi asibitin koyarwa dan sanin halinda Jamal Ke ciki Dukda kuwa tashin hankali da shi kansa Mahmood d’in yake ciki bayan abinda d’iyarsa Zahra tai masa a bainar jama’an Masarauta.... Shi kuwa Yazeed tinda ya samu ya kub’uta daga hannun Majidad’i babu wanda ya kuma sakasa a ido dan tin lokacin yai ficewarsa gaba d’aya daga cikin Masarautar, bai zarce ko ina ba sai club d’in da suka saba had’ewa da watsattsun abokansa... Tinda ya isa wajen kuwa banda kwankwad’an Barasa baya aikin komai, harta abokan nasa saida suka razana da irin giyar da Yazeed Ke zubawa cikinsa... Bai masu magana ba bai ce masu komai ba tinda ya isa wajen shan barasa kawai yake ko zai mance tashin hankalin da ya baro cikin Masarautar su... ** A b’angaren Muhibbah kuwa bata k’yale Zahra ba daidai da dak’ik’a guda, har saida bacci ya d’auki yarinyar, tai zaune a gefenta tana duban fuskarta cikeda tausayawa, taita tuna abubuwa da dama gameda yarinyar da mahaifinta tin farkon zuwanta Masarautar... Hoton Zahra rungume da Mahaifinta dake gefen bedside Muhibbah ta d’auko tana kallo hawaye tab idanunta, tasa hannu a hankali tana Shafa hoton hawayen na zirarowa daga idanunta... Ta lumshe idanunta a hankali sanda taji kuka mai k’arfin gaske na zuwa mata, a hankali Ta maida hoton yanda ta d’auko kana Ta fice daga d’akin cikin sauri... Masauk’inta ta tafi ta shige k’uryar d’aki ta fad’a saman gado tana shesshe’k’ar kuka mai tsuma zuciya... Tana ganin kiran Ansar na shigo mata amma sam bata iya d’agawa ba sai kuka dake kuma kufce mata mai ban tausayi.... Kaman wacce aka sinkaya ta mik’e ta soma shiri... Kayanta ta shirya cikin akwati da zimmar Washe gari idan Allah yakai rai asubahin fari zata d’auki hanyar Bauchi... ** Babu yanda Mahmood baiyi ba Giwa ta koma masarauta amma fir tak’i tace bata barin cikin asibitin har sai likitocin da suka shiga aiki ma Jamal sun fito sun sanar da ita d’anta is stable, daga ita har Jakadiya sai faman kai komo suke, tana tafe Jakadiya na take mata baya sauran Hadiman nata na risine daga gefe... Mahmood da Turaki harmada Waziri suma duk suna gefe suna jiran fitowar likita... Jim kad’an likitan ya fito ya nufosu, sukai masa chaa suna jiran ta bakinsa.... Da hak’uri likitan ya soma masu, Giwa ta shiga girgiza kai tana fad’in “Likita bana son jin irin wad’annan kalaman, ka bud’e baki ka sanar dani halinda d’ah na Ke ciki...!!” Dogari guda ya bud’e murya yace “Hattara Bokan Turai, Giwar Amale bata jiran amsa daga bakin Talakawanta....!!” Likita yai gyaran murya yace “Prince is stable now....But there’s something in his life that would remain irreversible... I’m sorry to say we did everything we could ganin gubar batai tasiri cikin jikinsa ba, a dalilin haka... we had to amputate his leg... Da ace bamuyi gaggawan cire k’afar ba tabbas da gubar ta haura zuwa zuciyarsa wanda hakan ka iya kawo sanadiyar mutuwarsa....!!” Kuka ya kufcewa Giwa yayinda Mahmood ya lumshe idanunsa a hankali, yai saurin k’arasawa ga Giwa yana bata baki... Ya dubi likitan yace suna iya ganin Jamal... Likita ya jinjina kai yace “We’re moving him to the resting room in a bit... Zaku iya shiga can ku gansa Your Highness... Excuse me...!” Ya k’arashe yana mai shigewa... Yarima Mahmood ya janyo hannun Giwa da har lokacin bata koma daidai ba ta k’asa yarda Wai Jamal d’inta ya zama mai k’afa guda, haka suka nufi d’akin da aka kwantar da Jama cikin matuk’ar sanyin jiki.... Giwa tana hango Jamal kwance da yankakken k’afa Ta rintse idanunta tana k’ok’arin danne kukan dake zuwa mata, Ta k’arasa jikin gadon tana shafa k’afar nasa take fad’in “Jamal d’ah na..!!” Tsananin rawa da muryarta keyi ya hanata ci gaba da magana... Mahmood ya tsaya daga d’aya gefen yana duban d’an uwan nasa cikeda tausayawa... A hankali Jamal ya bud’e idanunsa yana dubansu, lokaci guda ya yunk’ura zai tashi yaji tamkar babu k’afarsa guda a jikinsa... Yai saurin kai hannunsa maras cannula dan tabbatarwa ai kuwa babu k’afar an cire... Cikin tsananin tashin hankali yake furta “No no no no... This can’t be happening... Maami what’s going on... Where’s my leg... I want my leg back... Tell them to bring me back my leg...!!” Mahmood ne yai saurin dafasa cikin k’ok’arin bashi baki “Calm down please Jamal, everything will soon be alright kaji, just calm down kaji d’an uwana... Bayan takobi mai guda da Majidad’i ya sara maka is a miracle you survived... Ka gode ma Allah kaji da ya k’addari cewa akwai sauran rayuwa gaba gareka...!” Cikin zuban hawaye Jamal Ke fad’in “Yaya shikenan na zama nakashashhe... Yaya ka dubeni fah ka gani... Ka dubi halinda nake ciki you could you except me to calm down...! I shouldn’t be in this position, maiyasa na karb’i fad’an Yazeed wanda shi bazai min haka ba... He should be the one here not me...!” Mahmood yai saurin dafasa yana mai girgiza kai yake furta “Kar kayi magana haka Jamal kai musulmi ne kuma nasan ka yarda da K’addara mai kyau ko akasinta... Wannan itace k’addararka Jamal, koda ace Yazeed bai zama sanadi ba kasa a ranka hakan zai sameka... Bawa baya wuce k’addararsa kaji koh... Kayi fatan Allah ya baka ikon cinye wannan jarabawa taka...!” Jamal da hawaye Ke gangaro masa k’uri yayima Mahmood yana dubansa lokaci guda yake furta “Yaya... Yaya I’m sorry... Please forgive me...!!” Mahmood ya dubesa da mamaki yace “Jamal mai kai kake neman afuwa... Ni baka mun komai ba...!” Wani irin duban da Giwa ta aikawa Jamal ya sanyashi lumshe idanunsa a hankali daidai lokacinda wayar Mahmood d’in ta soma ruri... Excusing kansa yai ya fice amsa kiran dan da alama daga masarauta ake masa kiran... Mahmood na ficewa Giwa ta dubi Jamal tace “Koda wasa kada kayi gigin sanarda Yayanka wani abu... Koda wasa Jamal...!” Jamal na hawaye yake aika mata wani irin muguwar kallo da rinannun idanunsa, lokaci guda yake furta “Maami zunubaina ne suke bibiyata, shiyasa na tsinci kaina a halinda nake yau, na tabbata hakkin wannan yarinyar da duka ‘yanmatan da na lalatawa rayuwa suke bibiyata.... Wanda Duka ke kika umarceni kan son mulkin banza wanda ba tabbata zai ba....Yau ga halinda na tsinci kaina ciki...!!” Saurin toshe bakinsa Giwa tayi tana fad’in “Rufe bakinka Jamal, duk abinda kayi sadaukarwa ne ma gidanku da ahalinka... Kuma abinda ya sameka ba laifin d’an uwanka Yazeed bane kaima ba laifinka bane laifin wancan tsinannen mahaukacin ne kuma nayi imani sai ya biya abinda ya aikata... Dan haka koda wasa kada na sake jin maganganu irin haka daga gareka...!” Banda aika mata mugun kallo Jamal baya komai, lumshe idanunsa yai wasu hawayen suka kuma gangaro masa Mahmood ne ya turo k’ofa ya shigo, yanayin da suka gansa ciki sosai ya kuma firgitasu.... Giwa ta tsaresa da ido tsoro bayyana saman fuskarta, duk a nata zaton yaji tattaunawarsu da Jamal ne.... Ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Sadauki lafiya na ganka haka...?!” D’an satan kallon Jamal yai yaga idanunsa a lumshe suke kana ya matso kusan Giwa yai mata rad’a a kunne... K’unshe bakinta tai ba tareda ta iya furta koda kalma ba duniyar na neman juye mata... Mahmood ya isa ga Jamal dan baiso hankalinsa ya kuma tashi a condition d’in da yake ciki... D’an dafasa yai kad’an yace “We’d be around idan kana nemanmu, for now Likita yace ka sami hutu kaji...Akwai dogari guda da zaizo ya kula dakai, Allah ya baka lafiya kaji k’anina...!” Jamal ya jinjina masa kai yana mai dubansa cikeda so da k’auna, ya rik’o hannunsa kad’an yace “Thank you Yaya..!” Murmushi Mahmood ya sakar masa had’ida shafa sumar kansa kad’an kana yasa kai ya fice Giwa na biye dashi tamkar tayita kurma ihu haka take ji ko zata sami sanyin rad’ad’in da zuciyarta Ke mata... Suna tafe take ceda Mahmood “Ina Fu’ad d’in... Oh ni Turai naga ta kaina wannan wane irin al’amari ne Ke faruwa da ahalina...?!” Mahmood ya rik’ota kad’an yace “Maami ki kwantar da hankalinki, Fu’ad yana ER and he’s out of danger now... Turaki yana can wajensa taking care of everything...!” Giwa na hawaye take duban Mahmood tace “Shi kuma mai ya sameshi...?!” “Drug overdose...!” Ta kuma rintse idanunta tana wasu hawayen na zubo mata tashin hankali daga wannan sai wancan... Mahmood yaima Jakadiya alama da hannu tazo... Ta k’araso cikeda risinawa.. Nan yace Ta kula da Giwa zai k’arasa ya sami Likita... Babu musu Jakadiya Ta k’arasa wajen Uwargijiyar tata wacce ta koma tamkar wata abin misali cikin k’ank’anin lokaci... Tabbas Mulkin duniya ba komai bane, take Allah yake sauya al’amaransa ya maida bawa ba koman komai ba ya nuna masa kasawarsa da kasawar duk wani mulki da dukiya nasa... Bawa yabi Allah shine tsiransa, kada Allah ya jarabceka da d’an wani k’ank’ani mulki na duniya ko k’ank’anin arziki da zai gushe ka zata ka samu duk wani power da kake nema a duniya kuma zaka iya takawa kowa yanzu sai ya karb’e komai ya kuma maidaka ba kowa ba dan shid’in shi kad’aine mai dawammamen mulki da baida farko baida k’arshe... Ya Allah kada ka jarabcemu da bijire ma rahamarka garemu..Ameen! A d’an tsakanin wannan lokaci idan Kaga Giwa dole ta baka tausayi, gaba d’aya Ta fice a hayyacinta Ta koma tamkar ba ita ba, yaranta har guda biyu kwance asibiti, duk San mulki irin na Giwa wanda k’asa ma da k’yar take takawa sabida Izza sai Gata nan tana taka k’asar asibiti cikin sanyin jiki da karb’an umarni daga wajen likitoci... Idan da ace Tanada sauran rabo tabbas zata fahimci darasi cikin abubuwan dake faruwa da ita... Har kawo zuwa dare Fu’ad yana kwance unconscious bai farfad’o ba baisan yanda kansa yake ba, koda ace ya farfad’o su kansu likitocin basusan da mai zai farka ba, hauka ne kokuwa akasinta... Hakan yasa suka sanar da family d’in Fu’ad they should be ready for anything dan komai ka iya faruwa... ** MASARAUTA Sassafe ta ida shirinta tsaf da zummar barin gari, saidai ji tai bazata iya tafiya bata duba halinda Zahran Ke ciki ba, Ta mik’e ta nufi b’angaren Giwa yanda ta tadda Zahran da Umaima na shirin fita zuwa asibiti duba Jamal da kuma Fu’ad... A nan ne suke sanar da ita abinda ya sami yaran Sarkin... Harga Allah bayan abubuwan da sukai mata itada ahalinta zata iya cewa ko gizau bataji tausayinsu ba hasalima ma abinda ya cancancesu suka samu... Umaima ta dafata kad’an tace “Ni kad’ai nasan labarin soyayyarku da Fu’ad, are you sure bazakije ki ganshi ba...?!” Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali kana tace “Zanso hakan Umaima amma saidai nima kiran gaggawa na samu daga gida Mummy na asibiti ba lafiya tin daren jiya... Idan kinje ki gaisar min da Fu’ad... Harmada Jamal d’in...!” Shiru Umaima ta d’anyi tana karantar yanayinta kana ta jinjina kai tace “Tace shikenan, zan fad’i sak’onki, kuma nima ki gaisar min da Mummy da kyau, kice ina mata fatan samun lafiya...!” Ta jinjina kai a hankali tana murmusawa... Zahra ta k’araso sukai K’uri suna duban juna... Lokaci guda ta isa ta rungumeta tace “Tia ki gaishe da Mummynki, kuma idan kinje please ki had’amu a wayar na gaisheta...!” Muhibbah ta jinjina mata kai a hankali kana ta Shafa kan yarinyar kad’an tace “Kiyi kaman yanda Nace miki jiya, apologize to your Paa kinji... Kinga dai abubuwan dake faruwa cikin Masarautar nan, your Paa is going through a lot Zahra... Please don’t add to his problems kinji... Try to be more understanding with him... Baya buk’atan tashin hankali daga gareki a halinda yake ciki yanzu...!” K’uri Zahra tai mata sai kuma ta girgiza kai alamun k’in amincewa tace “That has nothing to do da amsoshin da nake nema daga wajen Paa.. I won’t stop har sai ya sanar dani...!” Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa, tabbas tasan tank’waro Zahra ba abu bane mai sauk’i... Murmuahin da yafi kama da yak’e ta sakar mata kana ta kuma masu sallama... Umaima tace ta bari su fita tare ko ma a kaita gida a motar masarauta.. Fir Muhibbah tak’i hakan hasalima sauri sauri ta fice daga Masarautar... Tana tafe tana neman abin hawa ya hangeta, tinda ya fice daga Masarautar jiya bai dawo ba, hasalima watsewarsa ya gama a club sai yanzu ya nufo gida dan jin yanda al’amra suka kwana... Yana hangota ya saki murmushin nasa yana mai shafa hab’a... Lokacin da yake jira, dama itama shak’e yake da ita... Kaf takaicinsa zai sauk’esu ne akanta Ta yanda gobe ko mai irin sunansa taji zata basa Girma...! Ya k’arashe tinanin nasa yana karya kan Mota... Tana tsaye bakin kwaltar da babu mutane sosai babu ababen hawa saman kwalta saiko jifa jifa abinka da hanyar da ba’a faye bi ba.... Kaman daga sama taga bak’ar G-wagon taja ta tsaya gabanta, haka kurum taji bata aminta da motar ba dan tasan ba motar k’anan mutane bane, idanunta suka sauk’a kan plate number na motar aiko nan Ta hango Prince Zeed rubuce jiki... Innalillahi kawai take karantowa Ta soma janye luggage d’inta cikin sauri tana San barin wajen... Saidai tuni motar taci gaba da nufota, daidai gabanta ya kuma jan birki ya zube glass yana k’arema Fuskarta dake cikeda tsoro wane irin duba... Ya sakar mata murmushin nan nasa kana yai gyaran murya kad’an “Look who’s here...! Tafiya cikin rana bai kamace Tough girl irinki ba Rankidad’e... Shigo mana let me give you a ride..!” Take taji k’arfin hali na zuwa mata, Ta murmusa kad’an dukda tsananin tsanar wannan fuska tasa da takeji... “Karka damu Your Highness.. Ai mu talakawa mun saba da wahala... Yanzu ba da jimawa ba zan sami abin hawa irin namu na talakawa...!” Yazeed ya kuma murmusawa yace “Ba’a rejecting offer d’ina... So dole ki shigo...!” Jada baya ta soma tana fad’in “Ni kuma nace bazan shiga ba Rankaidad’e.... Why can’t you just go ahead....!” Fitowa yai daga cikin motar zuciyarta naci gaba da tsinkewa, taci gaba da janye jakarta cikin sauri saidai tuni ya cimmata.... Dosowarsu hanyar kenan zasu nufi masarauta ya hangi Yazeed na kokawan tura mace cikin mota... Yai saurin duban Turaki dake driving yace “Wait... Mai nake gani haka...!?” Sai sannan Turaki ya kula da abinda ya gani.... Mahmood ya furta “Wacece yarinyar can da Yazeed yai forcing d’inta cikin motarsa... Lets follow them Turaki... Muyi saurin bin bayansu, jikina na bani wani abu maras kyau Yazeed zai....!” Turaki ya karya kan Mota yana fad’in “Got it your Highness...!” Take motarsu tabi bayan motar Yazeed... Suna ganin yanda motar Yazeed ke sharara gudu saman kwalta tamkar mai shirin barin gari... Mahmood K’uri kawai yai wa motar yana ganin yanda Yazeed Ke wasa da k’arfen nasara saman kwalta... Shikadai sai murza ‘yan yatsunsa yake yana ganin tamkar Turaki ba gudu yake ba, traffic light ya raba tsakaninsu... Cikin tsananin huci yake fad’iwa Turaki “Speed it up Turaki we can’t lose them.!!” Turaki jinjina kai kurum yake yana mai ci gaba da falfala gudu had’ida k’ok’arin ganin Yazeed bai kufce masa ba saidai duk iyaka k’ok’arinsa suna karyo kwana suka nemi motar Yazeed suka rasa, mashigar hanyoyi ne har guda hud’u suka rasa wannene d’aya Yazeed yabi.... ** Suna isowa gidan Yazeed ya zakayo Ta yanda take zaune ya bud’e motar ya shiga fincikota da iyaka k’arfinda Allah ya hore masa, sosai jikinta ke rawa tana tarjewa tana fad’in kada yazo kusanta... Take abubuwan da suka faru da ita shekarun baya suka shiga dawo mata... Sosai ta shiga matsanancin tashin hankali tana mai furta “Please don’t... Don’t please..!!” Tarjewa yakushi cizo da dik wani abinda take tunanin zai ceceta hannun wannan azzalumin bawa tayi amma a banza... Haka Yazeed ya dinga janyota har suka shige cikin gidan... ** Suna nan suna tunanin hanyar da zasu bi Mahmood yai shiru tamkar mai nazari sai kuma ya d’ago ya dubi Turaki yace “Ina tinanin nasan yanda Yazeed ya tafi... Around this place idan ban mance ba akwai guest house d’in mahaifinmu... Inada tabbacin can Yazeed yakai yarinyar nan... Lets go before he does something to her...!” Cikin sauri sukabi hanyar da Mahmood yakeda tabbacin nan ne gidan yake... Aiko suna zuwa suka hango motar Yazeed.. Suka dubi juna a tare... Babu shiri suka nufi cikin gidan.... A daidai sanda suka shigo parlorn daidai lokacinda Allah ya baiwa Muhibbah daman roza ma Yazeed flower verse a kansa... Ta taso a guje tana kuka sosai... Da tsananin mamaki Mahmood ke dubanta “Muhibbah..!!” Ya fad’i zuciyarsa na bugawa... Bata iya cewa komai ba sai kuka... Tsananin tsoro bayyane saman fuskarta... Zuciyar Mahmood taci gaba da bugawa da sauri da sauri, shi kad’ai sai sakin huci yake suna sauraro muryar Yazeed alamun yana neman Muhibbah.. Cikin zafin nama Mahmood ya nufi yanda yake sinkayo muryar Yazeed d’in... Turaki na kiransa inaa ko waigawa baiba... Yana hango Yazeed ya tafi ya dunk’ule hannu yakai masa naushi a hanci, take Yazeed ya zube bakinsa da hancinsa na fidda jini... Cikin wane irin karaji Mahmood yasa hannayensa biyu ya kuma d’ago Yazeed sama ya k’ara masa wata naushin, dukan sa’a yakewa Yazeed wanda Ke kwance waje yana haki da k’yar... Mahmood na nunasa da yatsa yake fad’in “Kaci amanan iyalanka, ka wulak’anta Martaban gidanmu... Ka zakunci ‘ya’yanka... You should be ashamed of yourself Yazeed...!!” Ya k’arashe yana kuma kai masa tokari da k’afa... Yazeed bai iya komai sai haki da k’yar jini da yai masa faca faca a fuska ga yanda Muhibbah ta fasa masa da verse ga kuma uban bugun da yaci hannun Mahmood... Fitowa yai yana huci, Turaki ya taresa yace “Ina Yazeed..?!” Wane irin duba yaiwa Turaki ba tareda ya amsasa ba saima tambayarsa yarinyar da yayi... Turaki yai masa nuni da yanda Muhibbah ta tak’ure ta kifa kanta tana cazgan kuka... A hankali ya isa gabanta ya durk’usa, yana mai k’ura mata idanu cikeda tausayawa... Tai saurin d’agowa da zummar jada baya.. Mahmood ya d’an bud’e murya kad’an yace “Karki damu we won’t hurt you, you’re safe now... Did he do something to you..?!” Tai saurin girgiza masa kai alamun a’a hawaye naci gaba da ziraro mata... Mahmood ya jinjina kai had’ida kauda kai gefe yana mai fuzar da huci a hankali.... Gyaran murya ya kumayi yace “Mai ya fito dake daga masarauta kuma Ina zakije da kaya...?!” Tasa hannunta share hawayen fuskarta, cikin rawar murya tace “Gida Zanje...!” Mahmood yace “Kina nufin garinku..?!” Tai saurin jinjina masa kai alamun eh... “Ina ne garin naku..?!” “Bauchi..!” Ta basa amsa a tak’aice... Juyawa yai ya dubi Turaki dake binsu da kallon mamaki, lokaci guda ya mik’e had’ida furta “Saka luggage d’inta a mota, zamu tafi Bauchi yanzu..!” Turaki ya dubesa da mamaki “Bauchi fah kace your Highness..!” “Bazaka iya zuwa bane..?!” Ya tambaya yana duban wani b’angaren.. Turaki yace “A’a ni ban isa nace haka ba Rankaidad’e, Ina Jos ina Bauchi ai ko Borno kace zamu tafi yanzu babu b’ata lokaci balle nan Bauchi..!” Ya k’arashe yana mai janyo jakan kayan Muhibbah... Ta d’ago tana duban Mahmood kaman zatai magana, kafin tai maganar sai cewa yai cikin dakewar murya “Tashi muje...!” Babu musu ta mik’e tabi bayansa jiki a sanyaye... SameenaAleeyou📚 [8/15, 9:48 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *46* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Har suka shige Mota Turaki bai daina mamakin Wai da gaske Mahmood yake barin gari zasuyi tsakar safiyar nan, Wai ma Toh wacece wannan yarinyar, ga dukkan alamu sunsan juna itada Prince, kuma ko a wasa bai tab’a kawo masa labarinta... Turaki ya murmusa a hankali yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa saidai ba Mahmood d’in ba, abinda zai baiwa mutane mamaki shi ba komai bane wajensa... Back seat Ta shige Turaki na driving Mahmood na mazaunin mai zaman banza, yanda ta tak’ure cikin motar zai tabbatar maka har lokacin tsoron abinda ya faru da ita bai fice daga jikinta ba... Ta side mirror yake dubanta zuciyarsa naci gaba da k’una, ya k’udiri niyyan bazai k’yale Yazeed ba da abinda yayi mata, tabbas sai ya koya masa darasi ta yanda nan gaba idan yaga mace ko wata irice zai koyi girmamata, a duniyarsa yak’i jinin yaga ana wulak’anta mace a cewarsa duk namijin da zaici zarafin mace shi d’in ba namiji bane, hasalima bai cancanci a kirasa namiji ba.. Kuma Wai a haka Yazeed yake ikirarin zama Sarki da wannan disgusting halin nasa...! Ya k’arashe tinanin yana mai ci gaba da murza zobban dake hannunsa har lokacin fuskarsa a matak’ar murtuk’e... Lokaci zuwa lokaci Turaki Ke satan duban b’angaren Mahmood d’in amma Ko gizau fuskar nan nasa babu alamun walwala sam.. Sanin halin abokin nasa za’a iya tafiya duk nisan duniyar da za’a tafi baice uffan ba yasa Turaki danna radio d’in motar, ya kamo tashan labarun wasanni dan yafi zaman hakan.... ** Tinda Jamal yaji cewa Umaima na asibitin hankalinsa ya gaza kwanciya, baya fatan ta gansa a halinda yake ciki dama da yakeda cikakkiyar lafiyarsa bata so shi balle yanzu da ya riga ya zama nakasasshe... Ya rintse idanunsa a hankali hawaye na kwaranyo masa... Zahra jiki a mace ta matsa jikin gadon nasa tace “Uncle please ka k’yale Anty Umaima ta shigo ta ganka wllhi ta damu dakai sosai...!” Jamal ya dubi Zahra da idanunsa masu zuban hawaye, lokaci guda yake girgiza mata kai alamun a’a “No Zahra... Umaima can’t see me like this, dan Allah kice mata ta tafi kawai na gode da gaisuwa...!” Ya k’arashe wasu hawayen na kuma zubo masa... Zahra ta fuzar da fuci a hankali kana ta kaikaito tana duban Zuhra wacce itama juyin duniyar tayi kan Jamal ya k’yale Umaima ta shigo ta gaishesa amma yak’i amincewa... A hankali Zuhra ta tako gaban gadon nasa, sukai shiru gaba d’aya suna sauraren yanda Jamal Ke kuka mai tsuma zuciya, lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Labarin soyayya na ya k’are tun kafin ya fara... Bayan abinda na zama yanzu na tabbata Umaima bazata tab’a sona ba, shikenan burina bazai tab’a cika ba... Mace d’aya k’wal da nake so bazan tab’a kasancewa tareda ita ba... Bazata tab’a yarda ta auri mai nakasa irina ba Zuhra...Shikenan na rasa farin cikina har abada..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Zuhra tasa ‘yar yatsanta ta goge hawayen da ya mak’ale mata cikin ido, ta girgiza kai a hankali tace “Jamal don’t talk like that... Nakasa ba kasawa bace, kuma dukkanmu nan da kake gani babu wanda ya isa yace hakittarsa ya kammala har sai ranan da Allah ya kiramu zuwa gareshi... Jamal, a kowace rana na rayuwarmu sabon shafin rayuwace take bud’ewa kuma Ko wacce tana zuwa ne tareda k’alubalenta da jarabawar data k’unsa... Kowa da kake gani a nan yanada nasa damuwar babu wanda zaice maka rayuwarsa gaba d’aya jin dad’i ne duk dukiyarsa duk lafiyarsa duk mulkinsa... In one way or the other yanada nasa matsalan da yake dealing... Jamal this is the reality now, you just have to accept it, and stop making things harder on you... Ina fata Allah ya baka lafiya ya kuma baka ikon cinye wannan jarabawa da ya jarabceka dashi..!” Daga Jamal har Zahra shiru sukai suna saurarenta, dagajin yanda take magana zaka fahimci wani damuwa dake kwance cikin zuciyarta take son amowa.... Basu ankare ba sai hango Umaima sukai tana shigowa hawaye na gangarowa saman k’uncinta.... Jamal yana hangota yai saurin kauda fuskarsa hawaye naci gaba da siraro masa lokaci guda yake k’ok’arin janyo bedcover yana kuma rufe gundulumin k’afarsa.... Zuhra na ganin haka ta janyo hannun Zahra suka fice suka basu waje... D’akin ya rage saura su biyu... Fuskarsa naga wani b’angare yake furta “What are you doing here...Maiyasa kika shigo...? Dan Allah ki fice bana san ganinki, just get out please..!” Ya k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka... Bata fice d’inba saima kuma matsowa kusansa da tai...Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka ziraro mata, lokaci guda take furta “You can’t avoid me forever Yaya... Maiyasa zaka gujeni bayan kaid’in masoyina ne... Maiyasa bazaka karb’i k’addarar ka ba bayan ansan musulmi mai imani da yarda da k’addara kyakkyawa koko akasinta... Ya Jamal dan Allah kada canjin dake jikinka a halin yanzu yasa ka gujeni kaji... Promise me bazaka gujeni ba..!” Tai maganar cikin rawar murya su duka biyun hawaye na gangaro masu... Girgiza mata kai take a hankali yana mai furta “You deserve someone better than me Umaima... Tambayar da na miki kwanakin baya bata buk’atan amsa, halinda na tsinci kaina ciki yanzu itace amsar..!” Ta girgiza kanta da sauri tana mai kuma share hawayen fuskarta take fad’in “Don’t talk like that please... Muyi fatan Allah ya baka lafiya ni kuma na maka alk’awarin bazan tab’a guje maka ba...!” Yai mata K’uri tsananin soyayyarta na kuma ratsa duk wata k’ofa na zuciyarsa... Shigowar Dr ne ya sanyasu k’ok’arin saita kansu, Umaima ta fice ta barsu da Dr Jamal sai binta da kallo yake har ta b’acewa ganinsa... Likitan ma saida ya fahimci haka d’in ya kuwa samu abin zolayar Prince Jamal.. ** Tafiyar awanni biyu jal sukai suka shigo garin Bauchi, idanunta naga window abubuwa da dama cikin zuciyarta harma batasan sun kusa shige unguwarsu dake daga farkon shigowa gari ba... Turaki ya d’an waigo kad’an ya dubeta yace “Destination..?” Tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Tambari housing estates..!” Sai lokacin Mahmood ya kaikaito yana dubanta, Shiko Turaki idanunsa naga kwalta yake fad’in “Aiko mun shige Tambari dan gashi har mun iso Zaranda...!” Cikin ‘yar daburcewa tace “Laa dan Allah kuyi hak’uri, ban kula bane...!” Turaki ya murmusa yace “A’a Rankidad’e karki damu ba wani abu bane ai sai muyi U turn, Keda kike tafe da rakiyar Mai Martaba da kansa...!” Kallon da Mahmood ya jefa masa ya hanasa k’arasa zancen nasa... Ya d’anyi gyaran murya kad’an ya dubi Mahmood d’in yace “Rankaidad’e sannu da hanya..!” Yanda yai maganar dole ya baka dariya amma Mahmood Ko gizau bai dariyar ba, idan da Sabo ya saba da halin Turaki, abokinsa ne amininsa ne kusan tare suka taso,Kakansa Tukari shine Turakin Jos mai rasuwa.. Asalin sunansa kuwa Yusuf ne Yusuf Turaki, tun daga makaranta Turaki yabi bakin mutane dashike family name d’insu ne hakan yasa gaba d’aya sunan nasa ya koma Turaki.. Itada Turaki ne suketa maganarsu yanda take masa kwatancen street d’in nasu har suka iso, shiko mai sarautar tamkar kurma haka ya koma cikin motar, baya um baya umum... Suna isowa Turaki ya bud’e motar, ya fito ya bud’e booth ya ciro jakan kayanta... Fuska d’aukeda murmushi ta gyara zaman mayafinta, ta risina tanaima Turaki godiya... Turaki ya murmusa yace “A’a Rankidad’e ai ba wani zakiyi godiya ba... Wa Rankaidad’e zakiyi godiya...” Ta d’ago idanu tana duban Mahmood dake zaune gaban mota shid’inma ita yake duba... Haka kurum taji gabanta yayi mugun fad’uwa, Ji take kaman ya fahimceta ita d’in itace silar tashin hankalin dake tsakaninsa da d’iyarsa.. Gaba d’aya sai taji kaman duk Duniyar kallon mai laifi ake mata... Kanta a k’asa tace “Na gode Rankaidad’e... Na gode sosai da taimakonku gareni...!” Ta d’an kuma duban Turaki tace “Bazaku shigo ku sha ruwa ba..!” Turaki yace “Wai ai sai abinda Rankaidad’e yace, idan yace mu shiga musha ruwa bazamuk’i tayin Sarauniya ba...!” Mahmood ya jefo masa wata kallo da tabbas yasan ma’anar kallon... Girgiza mata kai Turaki yai yace “Mun gode da tayi Rankidad’e, amma yanzu zamu d’auki hanyar Jos, Kinsan yanayin da muka baro Masarautar ciki..!” Ta jinjina kanta a hankali tace “Haka ne... Allah Ubangiji ya tsare maku hanya ya kaiku lafiya.. Na gode sosai...!” Turaki ya amsa mata da Ameen sai kuma yace “Rankidad’e na shigar miki da jakan ciki mana..” Yanda yai maganar yaso bata dariya,ta d’an murmusa kad’an tace “A’a karka damu zan iya na gode sosai ..!” Turaki ma ya murmusa yace “Tunda kince haka shikenan Kinsan ba’a jayayya da mutanen Fada..” ya k’arashe yana mai bud’e mota ya shige... Turaki na k’ok’arin jan mota Mahmood ya dakatar dashi, kallo yabi bayanta dashi har saida yaga gidan data shige... Tana shigewa kuwa yace suje... Turaki yaja mota yana shirya kalolin tambayoyin da yai zaiwa abokin nasa kan wannan yarinyar da Ko shakka babu yana jin akwai wani alak’a mai girma tsakaninta da Mahmood d’in dukda kuwa yasan bazai samu amsoshinsa yanda yake so ba sanin ko wanene abokin nasa... Tindaga nesa da ya hango mota k’irar BMW new brand Ta fito daga ciki yaketa alla alla ya iso dan idanunsa ya gane masa kaman itace ta fito daga motar... Aiko tana k’ok’arin tura gate motarsa ya k’araso, duba d’aya yai mata yaji gabansa yayi mugun tsinkewa musamman da ya ganta da kaya ga kuma yanayin da take ciki wanda zaice bai tab’a ganinta ciki ba... Ta kaikaito a hankali tana dubansa, murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar masa... Yana k’ok’arin fitowa tace “Yi zamanka Dr bara na bud’e maka gate d’in...!” Shidai bai tankata ba saima duban mamakin da yake binta dashi... Ansar ya ida shigowa da motarsa ya k’arasa parking lot yai parking yana mai hangota daga can bakin gate d’in yanda take k’ok’arin rufe gate d’in cikeda kasala tamkar babu laka jikinta... Baba Larai ce ta fito daga kitchen tana fad’in “Likita ka dawo baka jira nazo na bud’e maka Gate d’in ba...!” Tai Burki sakamakon hango Muhibbah da tai da kaya nik’i nik’i... “A’ah kace bak’i mukai gidan namu, Hibbatu sauk’an yaushe...?” Ta k’arashe tana amsar jakan kayan... Muhibbah ta murmusa ta gaisheta kana tace “Yanzu shigowata Iya Larai, mun sameku lafiya..?” “Lafiya lou Hibbatu ya karatun..?!” Saida ta saci kallon Ansar da yai kaman bashi a wajen saima k’ok’arin rufe motarsa da yake kana ta maidoda subantaga Iya Larai... “Alhamdulillahi Iya Larai, Mummy bata dawo daga office ba koh...?” Iya Larai ta jinjina mata kai alamun eh “Kinsan Mamar taku kaman agogo take wajen aiki ko Likita nan ya ganta ya barta wajen san aiki...” Muhibbah ta murmusa dan tayi kewarsu gaba d’aya, daidai lokacinda Ansar ya k’araso Iya larai na masa sannu da zuwa ta shige ciki abinta tana fad’in yau d’in mutuminsu Ta dafa... Muhibbah da Ansar suka jero suna takowa, kaman babu mai magana ma d’an uwansa.. Ta d’an bud’e murya kad’an ta gaishesa.. Ya amsa yana mai rataye lab cot d’insa a kafad’a.. Yai mata sannu a hanya itama ta amsa har suka k’araso cikin parlorn... Juyowa Ta d’anyi Ta dubesa kana tace “Ni zan shige ciki na gaji sosai...!” Ansar ya tsareta da idanu har Ta soma tafiya ya kirawo sunanta.. Ta d’anyi still a wajen kana ta juyo gareshi... “Haka zaki shige ki barni without any explanation..?” Yai maganar yana dubanta.. Ta d’an dafa kujeran da take tsaye gefensa tace “Gani nai yanzu ne dawowarka kaima Dr... Ya kamata ka k’arasa ka huta kafin lunch ya kammala..!” Katseta yai da fad’in “Kema Kinsan akanki bazan huta ba sai naji komai, you come first before anything else..!” Ya k’arashe cikin dakewar murya.. Rausayar da idanunta tai kad’an had’ida fuzar da iska tace “Ansar please not now... Can’t you see I just got here., Please ka k’yaleni ba yanzu ba... Ni na shige we talk later..!” “Muhibbah I’m serious... Whose car was that, su waye suka ajiyeki... Maiyasa zaki shiga motar wasu, wannan shine agreement d’inmu, kinje kina shiga motar maza maza suna dawowa dake har gida... How could you Muhibbah, wannan shine rayuwar da Kika zab’arwa kanki cikin Masarautar... Who knows mai kikeyi a can, just answer me Muhibbah..!!” Katsesa tai da fad’in “Ya isheka haka.. Don’t you dare judge me, you have no idea what I’ve been through... So you better hold it right there..!!” Ta k’arashe cikin wane irin karaji hawaye na ambaliya a fuskarta.. Lokaci guda tasa kai zata shige... Ansar yai saurin shan gabanta yana furtawa cikin sanyin jiki “Hibbah please.. Kiyi hak’uri..!” Yai maganar cikin sanyin murya.. D’ago idanunta masu zuban hawaye tai had’ida girgiza kai “Why is it so easy for you to judge others bayan watak’ila bazaka Iya d’aukan rabin iftila’in da suka tsinci kansu ciki ba... Ansar ba ma wannan ba shin haka ka d’aukeni... Ballagaza mai bin maza..!” Kuka yaci k’arfinta, cikin sautin kuka take ci gaba da fad’in “Do you think I went there just catch some fun... Not a day goes by banji zafin rayuwa k’asan rufi guda da nake taredasu ba... Ansar na tafi Masarautar nan ne badon kawai na d’auki fansar abinda suka min ba saidan Nayi tunanin mahaifina might still be alive sannan zan iya samunsa cikin Masarautar watak’ila sun maidasa bawa ko wani abu dan bamuga gawarsa ba.. Only to find out he was killed by those monsters, sannan sun k’ona gawarsa cikin gidan... Ansar mahaifina bai samu an masa wanka da sutura kaman yanda musulunci ya tanadar ba... An k’onasa a wulak’ance cikin k’ask’anci wanda ko tokarsa ba’a samu ba baida kabarin da zance eh yana makwancinsa a kwance... Shin idan kaine hakan ya faru da kai yaya zakaji...!” Hawaye suka gangaro masa, Muhibbah taci gaba da fad’in “Bayan na fahimci wannan na kuma fahimtar wani sabon abu cewa mutumin da nafi k’ullata da gaba baida Sa hannu ko kad’a cikin abinda ya faru dani, na cutar dashi na had’asa da d’iyarsa.. Na kunyatasa a idanun al’ummarsa... Shin wannan wane irin zalunci nayi Ansar..? Da wane ido zan dube mutumin da ya taimakeni a lokacinda mak’iyina yaso cimma mummunan burinsa akaina... Ya k’ub’utar dani daga sharrinsa cikin ikon Allah ya kawoni gida safe and sound, bai bar k’ofar gidan nan ba har saida yaga shigewata gida cikin aminci...Wannan mutumin ne a baya nai masa mummunan zato, na dangantasa da laifin da ko a mafarki shid’in bazai aikata ba... Ansar na cutar da mutumin kirki wanda baida buri da ya wuce ya taimaki bayin Allah... Shin kana tunanin Allah zai barni haka...!” D’agowa sosai wannan karon Ansar yayi da idanunsa masu zuban ruwa yace “I don’t get you Hibbah... Wane mak’iyinki ne yaso cimma burinsa akanki....!” Tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka kuma ziraro mata tace “Fad’a maka baida wani amfani, tuno abin tashin hankali ne da k’unci ma zuciya... Sannan komai ya riga da yazo k’arshe bazan koma wancan Masarautar ba... It’s over..!” Ta k’arashe cikin rawar murya.. Ansar dake sakin huci da ya fahimci tabbas d’aya daga cikin yaran Sarkin ne ya kuma attempting raping d’inta for the second time... Dunk’ule hannunsa yai ya daki garu yana mai fuzar da huci yake furta “Wllhi idan nayi ido biyu dashi sai na kasheshi ko ba jima ko ba dad’e..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci... Sanin tsananin suya da zuciyarsa keyi yasa ya fice daga parlorn gaba d’aya kaman zai kifa da k’asa... Iya larai ta hangosa, tana kiransa tana fad’in abinci ya kammala inaa ko waigowa baiba balle ya amsata saima huci da yakeyi kaman wani zaki... Iya Larai ta bisa da kallo cikeda mamakin meke faruwa... Parlor ta lek’o yanda taga Muhibbah jingine jikin garu idanunta a lumshe ga hawaye na gangaro mata.. Ta koma da baya a hankali tana k’ok’arin lalumar wayarta dake k’ulle bakin zani dan ya kamata Ta kira Hajiya ta sanar da ita abinda ke faruwa... ** Turaki yaja Burki gefen kwalta yana duban Mahmood da har lokacin tamkar gunki yake, banda sakin huci da murza zobban yatsunsa baya komai... “Haba your Highness, Wai dan Allah shikenan bazaka cire wannan abu a ranka ba, Allah ya kiyaye we arrived there on time babu abinda yayi mata, ita da kanta tace babu abinda ya faru.. Kayi hak’uri ka cire abin nan haka a ranka please your Highness..!” “Shut the hell up Turaki...! What if ya sakeyi.. I need to teach him a lesson a very good one ta yanda bazai sake marmarin that disgust act ba..!!” Turaki ya fuzar da huci a hankali kana ya tashi Mota suka ci gaba da tafiya.... ** Giwa da dawowarta kenan daga asibiti wajen ‘ya’yanta Jakadiya Jakadiya ta tareta da mummunan labarin har yau babu Izzatu babu dalilinta... Dafe da kai Giwa ta zauna gijif cikin kujerarta na alfarma tana kame b’angaren k’irjinta da takeji kaman caccaka mata manyan k’ayoyi... Fad’I take “Jakadiya idan kika sake zuwa min da labari maras dad’I hakan ka iya sanadin rayuwarki...!!” Jakadiya ta kuma risinawa cikeda tsantsan damuwa had’ida tashin hankali dan tasan itama idan har asirin Giwa ya tonu to nata k’arshen ne yazo.. “Tuba nake Rankidad’e... Allah ya huci zuciyar Giwar Amale... Allah ya baiwa ‘ya’yan Sarki lafiya...Jaa zamaninki Giwa guda d’aya tilo cikin Masarautar nan..!” Ta k’arashe tana mai d’ago babban yatsarta alamun jinjina... Daidai lokacin Yazeed ya shigo da kumburarren FUSKA tamkar wanda aka jefosa... Ba Jakadiya kawai ba harta Giwa saida ta razana da ganin yanda halittar fuskan Yazeed ya koma sabida kumbura da alamun ciwo.... SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH* *47* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin tsananin huci Yazeed yake furtama Giwa “Ina d’anki wllhi sai na kashesa, sai na masa illan da gobe ko cewa akai ya d’aga hannu ya d’aura jikina bazai ba... Ina yake ki fito mun dashi..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji... Giwa Ta baiwa Jakadiya izinin fita kana ta maida hankalinta kacaukam kan Yazeed dake ci gaba da huci “Yazeed.. Meye haka nakeji, Wai dama ba had’arin mota kayi ba.. Waye ya maka irin wannan bugun...?!” Yazeed dake aika mata wulak’antaccen kallo matsowa kusanta ya kumayi yana furta “Wllhi sai na kashesa, sai nayi ajalinsa koda hakan zaisa ki had’iyi zuciya tunda shi kika fifita akaina... Wllhi sai nayi ajalin Mahmood muddin Ina numfashi a doron k’asa...!” Kaman daga sama ya sinkayo muryar Mahmood d’in yana fad’in “Idan bakayi ba Yazeed baka cika ba... Yau ka tabbatar min da cewa kaid’in maras mutunci ne kuma maras imani, so duk abinda zakayi yanzu bazai bani mamaki ba..!!” Yayi maganar cikin tsananin huci k’irjinsa na kuma bud’ewa kaikace wani bugun zai sake yiwa Yazeed... Giwa da zuciyarta Ke ci gaba da tsinkewa ta tari Mahmood da fad’in “Sadauki Wai meke faruwa ne... Kan wane dalili zakaiwa d’anuwanka na jini irin wannan bugun kawo wuk’an bayan iftila’i da tashin tashin hankula da muke fuskanta cikin Masarautar nan...?!” Bai janye idanunsa daga duban k’yama da yake aikawa Yazeed ba yace “Maami ask your Son mai ya aikata... Ask him wane irin k’azamin laifi yau d’in ya tasamma aikatawa...!!” Giwa ta dubi Yazeed wanda shima hucin yake sakewa yana duban Mahmood, Ta kuma juyowa ta dubi Mahmood d’in da shima Ke ci gaba a sakin huci idanunsa kan Yazeed... “Mahmood mai kake nufi, wane irin kaifi Yazeed ya tasamma aikatawa..?!” Cikin karaji Yazeed yace “Maami don’t listen to any of his lies... K’age yakeso yamin dan nima nayi kamanceceniya da hali irin nasa sabida yasan cewa d’iyarsa ta hanyar banza ya sameta..!” Baikai aya ba Mahmood ya toshe bakin nasa da naushi, Yazeed ya zube k’asa yana kame bakinsa... Da yatsa Mahmood ke nunasa “Baka San komai akan d’iyata ba..! Dan haka kada ka sake ambatan sunanata a wannan k’azamin bakin naka...!” Cikin d’imauta Giwa Ke fad’in “Wai meke faruwa daku ne... Shin sai d’ayanku ya kasheni ne... Wai menene haka kukeyi...!” Yarima Mahmood ne ya katseta da fad’in “Maami kinada masaniyar cewa d’anki is a criminal... He almost raped someone’s daughter... Tir da hali irin naka Yazeed, kuma kada kaji da Wai baka sha ba ni nan zan damk’aka wa hukuma a k’watar ma wacce kaso zalinta hakkinta... Maras mutunci kawai...!!” Giwa da duniyar Ke juye mata gaban Mahmood Ta k’araso ta rik’e hannunsa tana fad’in “So kake ka tozartamu ka b’ata Martaban gidanmu... Shin ka kuwa San abinda kake k’ok’arin yi Sadauki... Ka tab’a ganin an kira hukumar ‘yansanda cikin Fada...!” Cikin k’unan rai yana mai girgiza kai ya katseta da fad’in “Sabida Fada ba’a gayyato hukuma shine ya baiwa mutanen cikinta dama su ci zarafin sauran Al’umma... Shin Maami ki fad’a min wata dokace ta baiwa ‘ya’yan Masarautar nan daman su ci zarafin sauran bayin Allah... Shin wannan shine mulkin adalci..? Idan har baza’a baiwa kowa dama da ‘yanci irinta mutanen cikin masarauta ba bana tunanin wannan sarauta an gina sa ne kan adalci...!” Giwa da takaicinsa ya gama k’ulle mata mak’oshi ji take kaman ta fincikosa ta shak’esa ya mutu har lahira ko zata huta, saurin katsesa tai a hasale da fad’in “Wane adalci kake magana...? Adalcin da zai tab’a Martaban gidanku... Adalcin da zai sakaku jin kunyar duniya... Adalcin da zai zamto tozarci a gareku.. Shine kake magana Mahmood..? Ince da bakinka kace attempting yayi bai aikata ba... Toh kan wane dalili zaka Sa Jami’an tsaro su shigo har cikin Fada su kama d’an uwanka... Shin wannan shine irin sarautar da zaka gudanar Mahmood... Ka rusa Martaban Gidan nan ka wulak’anta mutuncin rawani...?! Idan har kuwa kayi hakan Ina mai tabbatar maka saidai ka nemi wata mahaifiyar amma bani ba..!!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Shaye da tsananin mamaki Mahmood Ke duban mahaifiyar tasu ganin yanda b’aro b’aro ga gaskiya gabanta amma Ta zab’i ta rufe idanunta... A hankali yake girgiza kai kana ya soma fad’in “Ban tab’a tsammanin zanji haka daga bakinki ba Maami a matsayinki na shugaba ga Al’umma sannan kema mace ce Maami, na zaci ciwon d’iya mace na d’iya mace ne... Maami sanin kanki ne babu abu mafi muni da zai auku ga d’iya mace tamkar wani yaci zarafinta Ta hanyar fyad’e... Tashin hankali ne da zai rayu da ita tsawon rayuwar da zatayi a duniya...Maami fyad’e k’azamin laifi ne mafi muni wanda duk wanda zai aikata irin wannan laifi bai cancanci a kirasa d’an Adam ba don babu mutum mai hankali da yake cikin hayyacinsa da zai aikata k’azamin laifi irin fyad’e... Maami koda ace duka yaranki maza ne ya kamata ki tuna ita wacce yaso zalunta d’iyar watace... Maami kiyi tunani da ace Yazeed ya aikata laifin nan wane irin k’unci da tashin hankali Mahaifiyar yarinyar zata tsinci kanta ciki...Fyad’e k’azamin laifi ne, mummunan aiki ne wanda duk mutum mai hankali zai k’yamace shi..!” A hasale Yazeed dake rik’eda bakinsa da jini ya b’ata ya mik’e yana fad’in “Really Your Highness... Shin laifin ka k’yamata kokuwa dai kanada wani abu ne a zuciyarka... Why can’t you just admit it already, son yarinyar kake shiyasa duk hankalinka ya tashi kake ganin kaman na rigaka saninta saurana zaka samu..!!” Ya k’arashe shu’umar murmushin nan nasa saman fuskarsa... Mahmood dake tsananin sakin huci da yatsa ya nunasa yace “Idan ka sake magana cikin d’akin nan zan tako har wajen na kikkifa maka mari... Mutumin banza kawai, Allah ya wadaran hali irin naka...!” Ya k’arashe yana mai ficewa daga sashen gaba d’aya... Yana ficewa Giwa ta k’arasoga Yazeed tana aika masa muguwar kallo, shid’inma muguwar kallon yake aika mata.. Tsuka yai ya mik’e sosai yana furta “What..? Ai na zaci zaki bari Mahmood ya mik’ani ga hukuma ne tinda duk kin fifitasa akanmu and especially me... Da kuwa kinyi gigin barin hakan ya kasance wllhi da na tono baya na sanar dashi wacece ta koya mana aikata laifin fyad’e tun bamu Kai haka ba...!” Yai muguwar murmushin nan nasa Giwa tai saurin Kai hannu ta toshe bakinsa tace “So kake ahalinmu ya tarwatse...?!” Yazeed ya fincika hannunta ya bud’e bakinsa yace “Tarwatsewa na yaushe, ga can halinda kika baro ‘ya’yanki ciki and you’re losing Mahmood too dan na tabbata bayan juya baya da kikaiwa gaskiya a yau zai wuya yaci gaba da miki irin biyayyar da yake miki a baya Gimbiya Turai... Kuma barikiji na fad’a miki muddin kikaci ba da goyon bayan Mahmood yai sarauta wllhi kinji na rantse miki sai na tono baya... Sai na sanar dashi mummunan aikin da kika sa muka aikata..!!” Ya k’arashe yana mai jifarta da muguwar kallo kana yasa kai ya fice... Saiga Giwa tayi zaune dirshan saman gwiwoyinta hawaye na gangaro mata... Bataci ta zama ba da irin babubuwan dake faruwa da ita, dole ta ziyarci Tal’udu taji a ina ya makara tulin abubuwan nan suke faruwa da ita wanda ko ta ina babu wani sauk’i... Jakadiya ce ta shigo tana mata Fadanci dan ranta yayi sanyi amma tsawan da Ta dakama Jakadiyan ya sanyata komawa da baya babu shiri har tana karo da k’ofa... Giwa ta zube wajen sosai tana kuka da gaske ko zata samu taji sanyi cikin zuciyarta... ** Duk yanda Yazeed zai wuce kowa idan ya dubesa saidai ya kauda fuska sabida yanda halittar fuskar tasa ta sauya, gashi babu rawani balle ya rufe fuskar tasa da ita, banda harara baya aika wa mutanen cikin Masarautar komai, wasu bayi guda biyu da suka kasa janye idanunsu daga barin dubansa ya daka masu tsawa da fad’in “What are you looking at..! Ku b’ace daga nan kafin ku rasa rayuwarku.. K’ask’antattu kawai.!!!” Ya k’arashe yana mai shigewa sashensa... A parlor ya tadda Zuhra da Raheema suna fira irinta k’awaye...Aiko suna hangosa haka suka mik’e babu shiri... Bai tanka kowa a cikinsu ba saima kallon banza da ya rakasu dashi kana yayi hayewarsa sama.... Zuhra da Raheema suka dubi juna, Raheema tace “Zama bai ganki ba Zuhra, tashi tashi maza kije kiji abinda ya sami mijinki Ina tunanin had’arin mota ya samu...!” Zuhra ta jinjina kai kana ta mik’e a sauri Ta haye sama d’akin Yazeed... Tana haurawa Raheema ta mik’e cikin sand’a ta waiga gefe da gefe kana ta lallab’a ta haura saman itama, daidai jikin k’ofar d’akin Yazeed ta lab’e tana sauraren tattaunawarsu... Cikeda tsoro Zuhra ta k’arasa zata amshi ice block d’in dake nad’e cikin towel hannunsa da niyyan taimaka masa, kallon wulak’anci ya aika mata kana yace “Kika k’araso nan sai na fasa miki k’ank’aran nan akai...!” Tai tsaye daga yanda take tana mai shanye k’uncinta, jinjina kanta tai a hankali kana tace “Naji bakaso na taimaka maka but please ka sanar dani Ina ka sami raunin nan, a matsayina na Matarka ya kamata na sani Prince, kodai had’arin mota ka samu...?!” Murmusawa yai da gefen bakinsa kana ya shiga k’are mata kallo daga sama zuwa k’asa a gadarance, duba irinta k’ask’anci “Su matata manya..! Dan Ke matata ce sai akace sai dole kisan komai gamedani...? Kin zata dan kina matata kinada wani k’ima ko daraja a idanuna ne... Kin San mai na d’auki mata...! Abun holewa ne kawai da shak’atawa, nothing more nothing less...! So dan kina a matsayin matata hakan bai baki wani kima ko daraja a idanuna ba..Now get out of my sight..! Fita nace kafin Ranki ya b’aci...!!” Ya k’arashe cikin karaji... Babu shiri Zuhra da tuni hawaye sun wanke mata fuska ta fice a guje tana toshe kukan da yazo bakinta gadan gadan kana Ta fad’a d’akinta tai ma k’ofar key ta haye gado tana canzan kuka... Raheema dake mak’ale bayan k’ofa Zuhra na ficewa daga d’akin Yazeed tai wuf ta shige ta maidoda k’ofar ta rufe.... Kallo guda yai mata ya watsar yana mai ci gaba da abinda yake cikin ko in kula... Gabansa ta k’araso ta tsaya tana huci take fad’in “You’re not a man Yazeed... How could you say those horrible things to your wife.... You disgust me..!!” Da idanu guda yake dubanta daga sama zuwa k’asa kana yace “Did you say I disgust you..? What if I take my anger out on you..!!” Ya k’arashe yana mai zabura kaman zaiyo kanta.. Raheema tajada baya cikeda tsoro lokaci guda Yazeed ya koma ya zauna yaci gaba da abinda yake, murmushi saman fuskarsa yake furta “And the loyal best friend come to the rescue..! Ke har kinada bakin da zakiyi magana dan an wulak’anta Zuhra...Tell me duk fad’in duniyar nan akwai wanda ya wulak’anta Zuhra sama da wulak’ancin da Ke kika mata ne...?!” Raheema ta katsesa da fad’in “Yes nasan naci amananta in the most painful way but bana goyon bayan ka wulak’anta ta ka aibata Ta, ka k’yaleta taji da cin amanarta da kake da matan banza a waje... Wait speaking of matan banza, don’t tell me garin biye biyen matan Naka ne akaji maka wannan raunin...?!” Ya kafeta da idanu murmushi saman fuskarsa, lokaci guda ya mik’e yana takowa gabanta sosai har saida suka isa jikin gini, fuskarsu dab kusan na juna yake fad’in “Why... Why do you care..? Tell me are you jealous...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa... Raheema dake sakin huci a hankali k’ak’aro murmushi tai tace “Me.. Jealous of you..? Allah ya sawak’e min Kaima kasan zuciyata na Mahmood ne shi kad’ai...!” Wannan karon murmushi mai bayyana hak’wara Yazeed yai kana ya saita idanunsa cikin na Raheema ya kuma gyara tsayuwarsa yana mai furta “What if na sanar dake cewa Yarima Mahmood shine yaji min wannan raunin kuma ba akan kowa ba sai akan mace kaman yanda kikai zato...!” Ta d’ago firgitattun idanunta tana dubansa a razane “Yazeed mai kake son cewa ban fahimceka ba...?!” Yazeed ya kuma murmusawa yace “Zama ki fahimceni... Your beloved Prince is in love with another girl... Ke barin fad’a miki Mahmood bai k’aunarki coz I can see it in his eyes wannan yarinyar yake so kuma akanta ne yamin jina jina dan yana tsoron na rigashi saninta... Now that you know get out of my room kafin nima na sauk’e takaicina akanki na miki jina jina a wajen nan..!!” Huci kurum Raheema take tana mai furta “K’arya kake Mahmood bazai tab’a min haka ba, ni yake so... Hasalima shi ba mai kula mata bane baida wannan lokaci.....!” Batakai aya ba taji Yazeed ya damk’o wuyarta da k’arfinda Allah ya hore masa, cikin huci yake furta “Ni kike kira mak’aryaci... Sai na karya wuya ki a wajen nan naga gatanki...!!” Raheema sai firfito da idanu waje take tana k’ok’arin janye hannun Yazeed daga wuyarta, tana rok’onsa Allah Annabi ya sakar mata wuya kada ya kasheta cikin muryarta da bai fita sosai... Saida tai Laushi yayi jifa da ita gefe.. Ta fad’i k’asa tana tari da k’yar a hankali dan kar a jiyota, tanayi tana sosa wuyarta... Tsuka ya buga kana ya k’araso yanda take ya shiga janyota kaman kayan wanki yayi jifa da ita daga cikin d’akin kana ya maida k’ofa ya rufe... A d’ari Raheema ta mik’e ta nufi downstairs cikin sauri dan kar Zuhra ta fito ta ganta.. Tana tafe tana sosa wuyarta da har lokacin zogi yake mata.... ** BAUCHI Suna zaune itada Mummy a parlor, tv na aiki lokaci guda Mummy na sorting wasu takardu dake gabanta yai sallama ya shigo da alama daga asibiti yake.... Mummy tace “Likita an dawo..?” Tai maganar tana aje wasu takardun gefe had’ida zare Farin gilashi na k’arin k’arfin gani daga idanunta.... Ansar ya jinjina kai yace “Eh Mummy mun sameku lafiya...?” Ta amsa masa kana ya gaisar da mahaifiyar tasa yana mai satan duban b’angaren da Muhibbah take ko zatai masa magana amma shiru batace komai ba, Mummy na hankalce dasu dan tinda rana da Iya Larai ta kirata ta sanar da ita dawowar Muhibbah da kuma abinda ta gani babu yanda batai ba Muhibbar ta sanar da ita abinda ke faruwa amma sai ce mata tai babu komai lecture free week suke shisa tazo gida.. Muhibbah ta mik’e tana furta “Mummy zan duba Iya Larai a kitchen...” Dakatar da ita Mommy tai da fad’in “Dawo nan Muhibbah, Zo ki zauna...!” Babu musu da ta dawo mazauninta ta zauna fuskarta babu walwala, har lokacin Ansar bai daina satan kallanta ba... SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH* *48* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Dubansu duka biyu Mommy tai kana tai gyaran murya kad’an tace “Ina saurarenku.. Can anyone explain what’s going on here..? And don’t even think of lying to me Dan Larai ta kirani ta sanar dani komai..!” Muhibbah tai saurin d’ago idanunta masu rauni tana duban Mommy da sam babu walwala tattareda ita... Jin sunyi shiru su duka biyun yasa Mommy kuma fad’in “What’s wrong with the both of you... Kai Ansar kaine Babba Wai meke faruwa ne..? Meke faruwa tsakaninku..?!” Ansar ya fuzar da fuci kad’an yace “Mommy is nothing serious, Kinsan Iya Larai da exaggerating abu...!” Galala take dubansa kana tace “I see, ni zaka rainawa hankali... Tunda nake daku ban tab’a ganin ka dawo aiki Muhibbah batai maka sannu da zuwa ba duk fad’a da fushin da zakuyi da juna, nasan ba abu ne mai sauk’i zaisa shigowarka ya sanyata ficewa daga parlorn nan ba... Amma idan kunce haka, tsakaninku ne, kuyi sulhu da kanku banso tun yanzu na dinga shiga fad’arku..” Ta dubi Muhibbah da har lokacin jikinta a sanyaye yake tace “Tashi kije abinki kinji d’iyata..” Muhibbah ta jinjina kai a hankali tace “Toh Mommy, kana Ta mik’e Ta wuce jiki a sanyaye Ansar na satan kallanta... Tana shigewa Mommy ta maidoda hankalinta sosaiga Ansar tai gyaran murya ta kirawo sunansa... Ya amsa cikin risinawa, Mommy taci gaba da fad’in “Ni ba ma wannan ba d’azu Baffanka Yawale yaje har office ya sameni da batun saka maku rana, nace masa sai nayi shawari da duka yarana biyu naji yaushe suke so a saka bikinsu...!” Tai maganar tana mai maida glasses d’inta had’ida janyo wasu takardun... Cikin wane irin bugawan zuciya Muhibbah dake k’ok’arin shigewa corridor taja ta tsaya d’agowa tana duban Mommy daga can yanda take zaune cikin parlor, ta kuma dubi Ansar da annuri tuni ya cika fuskarsa, lokaci guda yake furta “Mommy Baffah Yawale da kansa yake fad’in a saka mana da Muhibbah, kenan yanzu ya amince na aureta..?!” Sauk’e ajiyan zuciya tai kad’an tace “Ya amince amma Yana nan akan bakansa na aura maka d’iyarsa Hameeda, idan ka amince da sharad’insa sai a aura maka su biyun rana guda...!” Cikin k’unan rai Ansar ke furta “Wai Mommy Baffah Yawale wane irin mutum ne shi, Wai ana aure dole ne... Nace bana son wannan yarinyar, bana sonta ko ana so dole ne... Mommy ni fah Muhibbah kawai nake so, kuma ita kad’ai ta isheni... In fact banida ra’ayin Auren mata biyu sabida nasan duk macen dana had’ata da Hibbah bazan tab’a mata adalci ba... Haka kawai bazan kai kaina wuta ba Mommy... Nidai ki fad’a masa bana son d’iyarsa...!” “Kai rufe min baki, bansan rashin kunya... Da kake gaya min sak’o kake bani naje na fad’a masa... Kana gani tun daga tasowarka kawo girmanka irin gwagwarmayar da nayi da mutanen nan akanka... Babu yanda basuyi ba sai Sun karb’eka daga hannuna tun bayan rasuwar mahaifinka amma na jajirce na hanasu nace babu mai rabani da d’ah na dan na tabbata cikinsu babu wanda zai baka future mai kyau... Ansar babu irin wulak’anci da ban gani ba daga wajen dangin mahaifinka ganin sun karb’eka daga hannuna amma na shanye komai, naita gwagwarmayar rainonka ganin ka sami ingantacciyar rayuwa... Babu irin sunayen da basu dangantaka dashi ba sunce ka zama D’an mace, sunce na maisheka had’e, sunce K’abila ta sace d’an Ard’o...Har cewa sukai zan maidaka Arne cikin ‘yan uwana Arna, wanene wanene amma duk na shanye nace naji na gani ni ce nan zan raineka da dad’i da babu dad’i... Toh amma yau dashike ka girma ka zama mutum gashi suna son had’a iri da had’e... Toh amma shi mutum ka tura masa aniyarsa... Hamida da mahaifiyarta basuda matsala, yarinyar tanada hankali da hali irin na mahaifiyarta... Dan ka aureta ni inaga ba wani matsala bane kuma inada tabbacin baza’a sami matsala daga Muhibbah ba...” Ansar dake k’ok’arin danne b’acin ransa yace “Mommy a gaban idonki mutumin nan yace bazai barni na auri Muhibbah ba sabida batada asali... Shine yanzu zaice ya amince na aureta dan kawai na auri d’iyarsa... Toh gaskiya Mommy ni bazan iya auren d’iyarsa ba... Maganan gaskiya kenan, kawai ni za’a tak’urani ne... I’m sorry Mommy but gaskiya I can’t...!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye zuciyarsa naci gaba da tafarfasa... Kallo mahaifiyar tasa Ta bisa dashi har ya b’acewa ganinta, ta girgiza kanta a hankali tana mai ci gaba da abinda take... Muhibbah kuwa d’aki ta shige ta fad’a saman gado tana kukan da ita kanta bata San dalili ba... Kodashike dalili da yawa zai iya zama sanadin kukan nata... Bayan gwagwarmayar da suka sha da dangin mahaifin Ansar na ganin sun koreta ma daga gidan gaba d’aya wanda badon Allah yasa Mommy mace ce jajirtacciya wacce ke tsaye kan k’afafunta da sun jima da yin sanadin barinta gidan musamman da suka fahimci soyayya da shak’uwar dake tsakaninta da Ansar... Bayan duka wannan yanzu at last wanda yafi kowa k’ullatanta da kyaranta ya amince Ansar ya aureta amma kuma wai da sharad’in zai auri d’iyarsa, rana guda za’a d’aura masu aure...Bayan wannan kuma gacan halinda ta baro Zahra ciki a masarauta wanda duk abinda yaje yazo tsakanin Yarima Mahmood da d’iyarsa itace sila... Har abada bazata tab’a samun kwanciyar hankali ba sanin cewa ta b’ata tsakanin d’iya da mahaifi... Ita duk bama wannan ba yau da taji da kunnuwarta ana maganan saka masu rana da Ansar ji tai kwata kwata bata muradin auren, tana ki can k’asan zuciyarta bazata iya rayuwa dashi matsayin miji ba...Shin yaya zatayi... Menene abinyi..?! Ta lumshe idanunta wasu hawayen suka kuma gangaro mata, hijabi Ta janyo ta zira ta fice ta k’ofan baya ana kiraye kirayen sallan Isha ta nufi layin bayansu gidansu k’awarta Meenatu... A parlor ta tadda Meenatu da k’annenta suna kallon shirin film a zeeworld yayyensu maza na shirin fita sallah suna masu fad’an suma su tashi su shige suyi sallah su bar kallon nan... Muhibbah ta gaisa dasu Yaya Huzaifa kana Ta nufo cikin parlorn... Meenatu na ganinta ta tafi da gudu tanai mata oyoyo had’ida tambayarta sauk’an yaushe... Tai aya tana duban idanun Muhibbar dake d’aukeda alamun kuka... Janyo hannunta tai suka nufi d’aki tana tambayarta lafiya meke faruwa... Muhibbah ta kuma saka hannu ta goge hawayen da suka ziraro mata “Meenah komai ma ya faru...!” Meenah Ta gyara zama tace “Ban gane ba, Kina nufin a sch d’in..A can Jos d’in... Kinga kin ma tuna min jiya a Islamiya Malam Ayuba Ke tambaya kwana biyu baya ganinki nace masa ai kin tafi makaranta Jos zaki k’ara karatu zakiyi Bsc Nursing... Toh.. Wai meke faruwa ne Hibbah..? Ni kinsa duk jikina yayi sanyi..!” Ta k’arashe cikeda kulawa... Ta Sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Meenah ba makaranta na tafi Jos ba...!” Meenatu ta dubeta da tsananin mamaki “Ba makaranta kika tafi ba... Toh ina kika tafi....?!” Cikin muryar kuka take furta “I went there for a mission Meenah... And everything now is a complete messed up...!” Jiki a sanyaye Meenatu ta zauna gefenta “Hibbah you’re scaring me...Wane irin mission kuma Ni Saamina....?!” Cikin zuban hawaye take furta “Zan fad’a miki komai k’awata... Zan fad’a miki harda labarin da baki sani ba game dani... But for now dan Allah so nake ki sanar dani ya kake gane kana son mutum...?!” Meenatu Ta rausayar da idanu kad’an tace “Toh yau kuma Keda kanki kike tambayar haka ta Yaya Dr... Bayan ked’in tuni kin tsaida gwani...?!” Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali had’ida fuzar da fuci tace “Haka nayi zato a baya... Bayan abubuwan da suka faru dani a yau, inajin shakkun abubuwan da naji a baya... Please tell me Wai ma mecece ita soyayyar nan..?” Meenatu an tab’o chapter da take so... Ta murmusa kad’an had’ida rausayar da idanu, harda su sauk’e ajiyan zuciya tace “Toh ita dai soyayya wata aba ce da Allah ya kana halitta a zukatan ‘yan adam... Idan kina son mutum zakiji kin damu dashi sosai kuma kin damu da al’amransa gaba d’aya, sannan kina son kasancewa dashi...Idan ya shiga damuwa zakiji kema kin shiga damuwa... Haka idan yana cikin Farin ciki kema zaki tsinci kanki cikin Farin ciki...Kina gudun duk abinda zai b’ata masa sannan kina muradin duk abinda zai faranta masa... Na tak’aice maki soyayya is all about CARE...Kalman Kula da ita soyayya ke farawa kafin komai ya biyo baya.... Kin gamsu...?!” Ta k’arashe tana Ware idanunta gaba d’aya hab’arta saman hannayenta... Muhibbah dake kallonta tamkar wata d’aliba gaban malama ta jinjina kanta a hankali had’ida sauk’e ajiyan zuciya tace “Na gode k’awata... Bara na tashi naje kafin dare yayi..!” Meenatu tace “Kai k’awata da wuri haka... Ki tsaya kici cake gaya can Ummati na baking mana...” Muhibbah na daidaita mayafinta akanta take fad’in “Aiko ga k’amshin duk ya cika min hanci amma dai bazan iya jira ba, ku ajiye min nawa share d’in da safe ku kawo min.. Ina Mama ban gaisheta ba, kodashike barta kawai dare ma yayi na shigo gobe mu gaisa tinda yanzu na dawo...!” Meenatu tace “Toh bara na taka miki...!” Tai maganar tana janyo mayafinta suka jera suka fito a tare... Suna tafe suna hira har saida suka hango ‘yan masallaci na fitowa kana Muhibbah taceda Meenatu ta koma kawai gaya can ‘yan masallaci sun fito ma... Meenatu tace Ok sai goben, sukai sallama kowa ta nufi gidansu... A daidai gate ta had’u dashi ya fito masallaci... Da sauri tayi niyyan shigewa ya tare k’ofan “Ina kika fito a daren nan..?” Ya tambaya yana dubanta.. Fuskarta naga wane b’angaren tace “Ina ruwanka da yanda na fito, ko har yanzu zargin nawa kake baka yarda dani ba...?!” Dafe kansa yai kad’an yace “Wai har yanzu maganan zargin nan bazai fita daga bakinki ba... Hibbah why are you acting like this.. This isn’t you, gaba d’aya kaman an canzaki, yaushe kika soma maida min magana anyhow...!” Wannan karon galala ta dubeta kana ta kuma kauda kai gefe tace “Dan Allah ka matsa min na shige bazan iya jure tsayuwar nan ba...!” Ansar yai shiru yana dubanta, lokaci guda yace “Alright, naji zan matsa ki shige amma sai kin tabbatar min kinyi hak’uri kuma bazaki sake maganan zargin nan ba... Only then zan baki hanya ki shige... Ta d’an cizi leb’en bakinta kad’an tana mai duban wani gefe tace “Naji shikenan ya wuce... Ka matsa min na shige...” Ya d’anyi mata K’uri na dak’ik’ai kana ya matsa mata tasa kai ta shige... Bayanta ya biyo yana mai fad’in idan Mommy bata parlor ta jirasa a nan zai d’auko wayarsa a d’aki ya k’araso... Ko amsasa bata iya yi ba saima shigewa da tai cikin sauri... ** MASARAUTA Shi kad’ai a d’aki yana neman mafitar hanyar da zai b’ullowa Mahmood, bazai yuwu ya k’yalesa yaita cin kashinsa a ransa yanda yake so ba, har shi ne Mahmood zaice zai dank’asa ga Hukuma.. Toh ma su waye hukumar..? Ai Fada itace hukuma mai zaman kanta... He needs to take Mahmood outta his way completely... Toh amma ta yaya zai hakan...?! K’aran da wayar salulansa tai ne ya katse masa tunanin nasa... Zayyad ne mai kiran.. Ya d’aga kaman baison d’agawa.. Daga d’aya b’angaren Zayyad yace “Allah shi taimaki Sarki mai jiran Gado...!!” Gajeren tsaki Yazeed yai yace “Zayyad this place is a complete chaos...But trust me I’d never give up... The word losing is not even in my vocabulary... I was born to become a King..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji... Daga d’aya b’angaren Zayyad ya murmusa yace “Gaskiya ne Your Highness, nasan bazaka tab’a giving up ba my King... The throne is surely yours... Allah shi ja zamaninka... Ai yanzu ma nake jin rad’e rad’i cikin gari kan abin kunyar da d’iyar Yarima Mahmood tai masa cikin d’inbin jama’an masarauta...!” Yazeed da baisan da wannan zancen ba, mik’ewa tsaye yai sosai yana furta “Ban fahimceka ba Zayyad.. Yimin bayani yanda zan fahimta, mai ya faru..?!” Zayyad yace “She creates a scene there... Apparently tana kokonton mahaifinta na b’oye mata wani abu, something very big da ta danganta da mutuwar Mahaifiyarta... Na tak’aice maka zance your Highness bayan abinda d’iyar Mahmood tayi bana zaton za’ai nad’in sarautarsa a matsayin Sarki..!” Baisan sanda ya bushe da dariya ba wanda ya jima baiyi irinta ba “At last labari mai dad’i... Zayyad kaci kyauta, Madalla da wannan labari naka...!” Bai kuma jiran cewar Zayyad ba ya katse kiran yana mai ci gaba da darawa shi kad’ai cikin d’akin... Ya akai Hauni Hadiminsa bai labarta masa wannan batu ba mai dad’i haka ba, kodashike gaba d’aya yau d’in shi ya hana Hauni kusantar yanda yake sabida tsananin b’acin rai da bak’in ciki da yake ciki... Zuciysrsa tayi wasai yanzun... Zahra itace greatest weakness d’in Mahmood... What if yaje ya k’yank’yasa wa Zahra wani abu gameda ko wacece ita...? Yai murmushi a fili yana mai jinjina kai lokaci guda yake d’an buga kafad’arsa kad’an yana mai ziga kansa da fad’in “You’re genius Prince Yazeed... Great..! Good..! Kaid’in na daban ne...!!” Ya kuma sakin murmushi yana mai furta “Sarautar taka ce Yazeed.!” Ya k’arasa jikin k’aramar fridge ya ciro kwalban barasarsa ya d’aga sama had’ida furta “Cheers to you victory..!” Lokaci guda ya kuma fashewa da wata irin dariya kana ya shiga kwankwad’a... ** Giwa zaune gaban Tal’udu ga wani bak’in tulu akanta mai tsananin nauyin gaske sai haki take gumi na tsartsafowa daga ko wane sak’o na jikinta... Tal’udu yaci gaba da sumbatu cikin wane irin yare maras dad’in ji... Take cikin bak’in tulun dake bisa kan Giwa ya kama da wuta bal bal... Tal’udu ya daka tsalle ya jada baya yana duban cikin tulun... Giwa kuwa k’ara Ta saki sabida azaban zafi da takeji daga tsakar kanta har zuwa k’asanta... Fad’i take “Ka cire min wannan azaban kai Tal’udu... Kar ka barni na halak’a..!!” Sai ihu take tana jin kaman ana dafa naman jikinta har zuwa b’argonta cikin wuta mai k’unan gaske... Take wutar ta kuma ruruwa sosai Giwa na kuma sakin k’ara har saida tulun ta tsage wutan ya soma k’ona sumar Giwa... Birgima ta shigayi a wajen tana ambaton Tal’udu ya taimaketa ya cire mata wutan dake k’onata... Da k’yar wutar ta daina ci amma kam ya k’one rabin sumarta... Ta koma gefe tana haki bak’in hayak’i ya b’ata mata fuska kaman wata dodanniya... Tal’udu ya tako gabanta ya kirawo sunanta cikin wata irin kakkausar murya “TURAI..!!” Giwa ta d’ago da k’yar tana kallonsa... Tal’udu yaci gaba da fad’in “Garin yaya kikayi sake Izzatu ta kufce daga hannunki..?!!” Giwa na haki take furta “Banida masaniya... Kayi duk abinda zakayi ka zak’ulo matar nan... Wannan shine aikinka dama...!!” Sandar hannunsa ya buga k’asa kana ya d’aga Kai sama yana girgiza kai yake fad’in “Na fad’a miki, duk randa mahaukaciyar nan ta bayyana tashin hankali ne gareki, sannan idan har kika sake ta kufce miki gaba d’aya hakan ka iya zamtowa bayyanar sirrikanki gaba d’aya... Kar ki mance na fad’a miki ita kad’aice zata iya sanar dake yanda yarinyar nan Saudatu take...!! Sannan abu na gaba d’anki Jamalu zai karya lak’anin da muka d’aura kansa cewa bazai tab’a yin aure ba... Kin mance kin sadaukar dashi ga Aljana Tamuna wacce duk ‘yanmatan da yake masu fyad’e k’wark’warori ne gareta... Duk macen da zai tara da ita dole ta na kusanceta kuma dole ta zamto k’wark’wara ga Sarauniya Tamuna... Kinga hakan na nufin Matar da zai aura dole ta zamto tamu... Sarauniya kuma bata tarayya da wata mace wani yaci gaba da tarayya da ita hakan na nufi D’anki Jamal zai iya mutuwa kenan idan har hakan ta kasance..!! Tun a fari ke kika janyo muka rasa wannan yarinyar Saudatu... Da ace Sarauniya Tamuna ta sameta da shikenan d’anki bazai shiga halinda yake ciki yanzu ba... Idan har kina son dawamammiyar Mulki irinta Sarauniya Tamuna dole d’anki yaci gaba da kawo mata k’wark’warori ta hanyar fyad’e wa k’anan ‘yan mata... Babu aure a tsarin mu Turai... D’anki Jamalu bazai tab’a aure ba... Wannan itace dokar..!!” Cikin rawar jiki Giwa Ke fad’in “A’a a’a Jamal Bazai tab’a aure ba... Alk’awari na maka... Shid’in bazai aure ba... Bazan rasa d’ah na ba...!!” Tal’udu ya kuma buga sandarsa yace “Turai fitilan tsafi ya hasko tashin hankali gaba gareki... Idan har baki nemo Izzatu cikin kwanaki UKU ba... Zaki iya rasa komai na rayuwarki, Mulkinki da kuma ‘ya’yayenki..!!” Ya k’arashe yana mai buga sandar tasa guguwa ya kaure b’att ya b’ace cikin d’akin.... Giwa ta shiga doka masa kira tana fad’in duka wanann iftila’in da take ciki yana nufin akwai wani gaba gareta...! Gefe ta koma tana shafa gefen kaita yanda wuta ya kwashe sumar... Da farko ta rasa hannunta guda da ya k’one k’urumus yanzu gashi ta rasa wani b’angare na sumarta... Shi haka wuta zaita cinye b’angarori na jikinta har ta k’one gaba d’aya kafin burinta na kafa ‘ya’yanta kan mulki ya tabbata..! Inaa bazata bari hakan ya kasance ba... Dole Waziri yasan yanda za’ai ya zak’ulo Izzatu duk yanda ta shige a fad’in k’asar kuwa... Da wanann tunani ta mik’e ta rufa alkyabbarta ta fito ta tadda Jakadiya.. _Sak’on ta’aziya ga d’aukacin members na Sameena Aleeyou novels sakamon rashin member guda d’aya da ya riskemu... Umm Jafar Muna addu’an Allah ya karb’i shahadarki... Allah ya baki Aljannah mad’aukakiya ya kuma d’ayyaba bayanki... Ameen thumma Ameen..! Dan Allah muna rok’onku da bakunanku masu albarka duk wanda yaga wannan yai mata add’ua.._ *MUHIBBAH* *49* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Jakadiya na ganinta tai saurin zabura kaman taga wani abin tsoro sai kuma ta zube tana kwasan gaisuwa cikeda tsoro, dan harga Allah uwargijiyar tata ta bata tsoro a yanayin data ganta ciki... Giwa ta watsa mata muguwar kallo tace “Dodanniya kika gani ko mai...?!” Jakadiya tai saurin girgiza kai tana mai kuma risinawa “Allah shi baki yawan rai kinfi gaban dodanniya annurinki da k’warjininki ya cika wajen nan gaba d’aya..!” Ta k’arashe tana d’ago babbar yatsarta alamun jinjina... Cikin zuciyarta kuwa cewa take ai kinfi gaban dodanniya a munin halitta yau d’in... Ta kuma risinawa tabi bayan Giwa dake kuma rufe fuskarta cikin bak’ar alkyabbarta... Mahmood dake tsaye sararin farfajiyan sashensa nan ya hangi mutane suna tafiya cikin bak’ak’en kaya... Kafin ya ankare sai wulk’awansu ya gani bai kumaga yanda suka nufa ba... Toh su wanene wad’annan..? Take tinanin abinda ya gani kwanakin baya ya dawo masa... Mutumin da ya tab’a gani cikin Masarautar da bak’ak’en kaya... Toh su kuma wad’annan su wanene... Shin su waye suke shawagi cikin dare a Masarautar..? He needs to find out..! Ya k’arashe tinanin nasa yana mai kuma k’arema fad’in Masarautar kallo daga can sama yanda yake tsaye... Zanen ginin gidan Sarauta da Wambai ya basa ya d’auko ya k’urama taswiran idanu sosai yana son fahimtar wani abu abinka da mai ilimin sanin sirrikan zane iri da kala... A hankali ya saka yatsar hannunsa guda yana bin wani layi dake jikin zanen, yaita bin dik wani hanya da layin ya ratsa har saida ya iso mahad’an layin yanda dogon layin ya tsaya... Da alama layin ba’a nan zai k’are ba, duk yanda akai akwai ci gaban wannan zanen dake rik’e hannunsa... Toh ina zai samu...?! Yai shiru tamkar mai nazari... A hankali ya ninke taswiran ya maidata ma’ajiyarta ya aje.... ** Juyi taketa faman yi saman gado amma babu bacci babu alamunsa, tayi salloli tayi addu’o’i amma duk dai baccin bai Zo mata ba... Idan ta rintse idanunta shi take hangowa sanda ya fito daga babban Zauren taro kwantattun k’walla cikin idanunsa, Ta mik’e ta zauna sosai tana tina tun Farin had’uwarsu sanda ya d’aurata saman dokinsa tun tana k’aramar yarinya, ta tuna had’uwarsu ta farko bayan komawarta da nufin tarwatsa ahalinsu, ta tuna sanda ya saving rayuwarta a cikin museum sanda ya tureta katako ya fad’i kansa...Ta tina kub’utar ta da yai yau d’in a hannun Yazeed.. Ta tuna yanda ya kawota har gida ya tabbata she’s safe...! A hankali ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen suka gangaro mata... Shin Maiyasa rayuwa haka..? Maiyasa mutanen kirki suke shan wahala... Yanzu shikenan ta janyo mutumin da yafi kowa cancanta da mulkin Masarautar zai rasa sarauta kuma ya rasa d’iyarsa... Maiyasa ta mishi mummunar zato...? mutumin da tun farkon had’uwarsu bai mata komai ba sai d’inbin alkhairi..? Anya zata iya yafewa kanta abinda ta aikata garesa..? Tabbas zata rayu da guiltiness ne tsawon rayuwarta..! Ta koma jikin gado ta kwanta wasu hawayen masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata... Ta mik’e a hankali ta isa jikin jakan kayanta ta ciro zanen ginin gidan sarautar nan da mahaukaciyar nan ta bata, tai K’uri ma zanen tana kallo... Toh wacece mahaukaciyar nan da har sunanta ta kira alamun ta santa, sannan Maiyasa ta bata wannan Taswiran...? Tabbas tanada unfinished job a wannan masarauta, duk yanda akai mahaukaciyar nan tanada dalilinta na mallaka mata wannan Taswiran... Toh amma meye dalilin nata...? Babban tambayar ma a nan shin wacece wannan mahaukaciyar..? Ta kuma lumshe idanunta a hankali had’ida fuzar da fuci mai d’umin gaske... So many reasons for her to go back to that Kingdom... K’uri taima zanen tana kuma karamtarsa Dukda cewa ba fahimtar wani abu tai gameda zanen ba.... ** MASARAUTA Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Yazeed dake ci gaba da jinjina mata Kai alamun tabbatarwa “Uncle what exactly do you mean...? Uncle ban fahimceka ba..! Mai kake nufi...?!” Yazeed ya kamo kafad’un Zahra ya zaunarta saman kujera ya tsaya sosai gabanta yace “Zahra gaskiyar kenan... Mahaifiyarki ba itace ta haifeki ba... Ni nan da kike gani naji tattaunawarsu da Yaya na Mahmood before they left for Spain....!” _Flash Back_ Yazeed yaci gaba da fad’in “Cikin dare naga shigowar motarsa cikin Masarautar nan, nabi bayansa a hankali dan na kula da yanayinsa kaman akwai abinda yake b’oyewa... Aikuwa to my surprise sai gani nai ya fito da jaririya lullub’e cikin zani ya shige cikin sauri alamun baiso wani ya gansa... Nabi bayansa har zuwa sashensa ba tareda yayi noticing d’ina ba... Aliya dake zaune parlor tana jira dawowarsa, tana jin an tab’a k’ofa ta dubi time k’arfe biyu da rabi na tsakar dare... Share hawayen da suka gangaro mata tai ta mik’e tana jiran shigowarsa... Yana shigowa ta daskare tana duban abin mamakin da Yarima Mahmood ya shigo mata dashi... “Yarima... Mai nake gani hannunka..? Ina ka fito da jariri cikin daren nan....?!” Aliya tace cikin rashin fahimta... K’arasowa yai ya mik’a mata yana furta “Karb’eta ki ganta, ba jariri bane, jaririya ce... And I named her after my grandmother, Maman mai Martaba.. Na sanya mata sunan Fatima Zahra...!” Yai maganar yana mai duban jaririyar kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... Kukan da Aliya ke dannewa yaci k’arfinta “Yarima... A ina ka samu jaririya, wacece mahaifiyarta..?!” Ya d’ago yana duban Aliya “She’s my daughter... And you’re her mother... D’iyarki ce Aliya, inaso ki rik’eta matsayin d’iyarki kuma har abada kada ki tab’a ce mata ba kece kika haifeta ba...!” “Yarima dan Allah ka sanar dani ina ka samo yarinyar nan...!!” Cikin d’aga murya yaceda Aliya “I told you she’s my daughter... ‘Yata ce ita d’in ‘yata ce, banida lokacin maki duk wani bayani... We’re leaving to Spain in a couple of days... Bana so kowa yasan da jaririyar nan cikin gidan nan... Not even Jakadiya... Bazasu San da labarinta ba har sai mun kuma dawowa k’asar nan wani lokaci... A lokacin zamuyi introducing d’inta matsayin d’iyarmu da muka haifa can Spain... Kin fahimta..?!” Aliya na hawaye Ta amshi jaririyar tana kallo, wane ikon Allah kallo d’aya taima jaririyar taji shauk’i na k’aunarta, kaman sunada connection haka taji koda shike Mahmood yace d’iyarsa ce k’ila sabida soyayyar da take masa yasa taji take itama son yarinyar ya shigeta... Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Yarima Mahmood lokaci guda take furta “Nai maka alk’awari zan rik’eta tamkar ni ce na haifeta, bazata tab’a sanin ba nice mahaifiyarta ba... Ta zamto tawa kaman yanda kake nawa, Zahra d’iyarmu ce ni da kai Yarima...!!” Ta k’arashe tana mai rungumar jaririyar hawaye na gangaro mata... Yarima Mahmood ya k’arasa ya rungumesu gaba d’aya yana mai furta “Kud’in ahalina ne... Ahalin da zamu rayu a Spain, cikin rayuwa mai ‘yanci ba tareda an tak’uramu da maganar bin dokoki na gidan sarauta ba.. Zamu rayu kaman yanda sauran mutane suke rayuwa babu tak’uri da nauyin bin dokoki irin na gidan sarauta... I promise to make you both happy... In sha Allah.. You two are my world..!” Ya k’arashe yana mai kuma matsesu cikin k’irjinsa....” Yazeed yana kaiwa aya ya kuma juyowa yana duban Zahra da tuni hawaye sun wanke mata fuska.... Ya k’araso gabanta ya duk’a yace “Zahra d’ago ki kalleni... Na aje wannan abu cikin zuciyata tsawon shekarun nan... But I know ko ba dad’e ko ba jima watarana zaki sani... As they say no secret remains hidden forever.... Mahmood ya b’oye miki haka ne dan watak’ila watarana zaki iya zama magajiyarsa... Amma kuma kinsan ko a shari’a d’an da aka haifa bata hanyar aure ba baida gadon Mahaifinsa... Mahmood yaji tsoron rasa Magaji a Masarautar nan shiyasa ya b’oye miki sabida Ke kad’ai ce k’wall magajiyarsa.... Zahra yau kinsan abinda mahaifinki ya jima yana b’oye miki tsawon rayuwarsa... Yanzu abinda ya rage miki shine kije ki tambayesa wacece mahaifiyarki... Da wacece yaci amanar Aliya har ya haifeki ta k’azamar hanya..!!” Ya k’arashe cikin karaji.... Mik’ewa Zahra tai tana kuka sosai take furta “So wannan shine dalilin.... Wannan shine abinda ya jima yana b’oye min... Paa ka cuceni, kazalunceni... Ka lalata min rayuwa... Na tsaneka na tsaneka...!!” Ta k’arashe cikin fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya... Yazeed yai K’uri yana duban yanda Yarinyar Ke kuka tana furta Ta tsani Mahmood... Muguwar murmushin nan nasa saman fuskarsa yake ayyanawa cikin zuciyarsa “That’s it Mahmood... K’arahenka yazo... Na tabbata zaman Masarautar nan zai gagareka... I’m getting rid of you at last.. Yarima Mahmood..!!” Ya k’arashe yana mai kuma gyara tsayuwarsa zuciyarsa nai masa wani irin sanyi.... ** Tafiya kurum take tana had’a hanya bataji bataji bata gani... Raheema dake tafe zata nufi sashen Yazeed wajen k’awarta Zuhra nan ta hangi Zahra ta nufi sashen mahaifinta tana kuka sosai... Lokaci guda Raheema ta fasa shigewa b’angaren Zuhra tabi bayan Zhara cikin sauri.... Yana tsaye tareda sabon Hadiminsa Barde yana basa umarni kan wasu abubuwa Zahra ta shigo kaman wacce aka jefota... Duban Barde yai ya basa umarnin tafiya kana ya maidoda hankalinsa ga Zahra wacce Ke tsananin huci... “Princess meke faruwa... Ya na ganki haka..?!” “Paa tell me the truth... Who’s my real mother..?!!” Tai maganar cikin tsananin dakewar murya... Zuciyarsa ta yanke lokaci guda, ya kuma duban Zhara da mamaki kana yace “Zahra lafiyarki... Where did you get that idea from... Tell me ina kika samo wannan gurb’attacciyar tunani...?!” Yai maganar cikin tsawa Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tace “Paa please na rok’eka, babu wani nok’e nok’e it’s over, na riga nasan komai, nasan Maa ba ita ta haifeni ba... I’m your daughter with another woman right..? So tell me wacece mahaifiyata...!!” “Get out Zahra... Fita nace kafin ranmu gaba d’aya ya b’aci...!!” Da tsananin mamaki take dubansa “Paa ka zaci bazan tab’a sani bane... Paa I’m not a kid anymore... For once in your life tell me the truth please..!!” Sauk’ar marin da taji a fuskrta ne ya sanyata had’iye sauran maganganun nata... Dafe da k’uncinta take dubansa da jajayen idanunta masu cik’eda k’unci hawaye naci gaba da gangaro mata.... “I hate you... I hate you Paa..!!” Tana kaiwa nan ta fice a guje... Raheema na k’ok’arin tareta Ina ko tsayawa batai ba... Juyowa Raheema tai ta dubi Mahmood dake ci gaba da sakin huci, lokaci guda ta isa ta kawo masa ruwa tace dashi ya zauna yasha ruwa... Bai mata musu ba ya zauna ya amshi ruwan yana kwankwad’a zuciyarsa naci gaba da masa d’aci.... Bai tab’a zaton zaiga negative impact a irin tarbiyan tashin cikin turawa da d’iyarsa tai ba sai gashi yanzu yana gani...Muryar Raheema ya katse masa tinaninsa “Your Highness, Kai hak’uri har yanzu ita d’in yarinya ce... But...!” Shiru tai ta kasa ci gaba da magana sabida tsananin shakkunsa da take ji... Wani duba Mahmood yai mata yace “Continue, ci gaba... Go ahead and ask me... Nasan kema shakku kike gamedani bayan abubuwan da kikaji Zahra ta fad’i mun... Right..!” Saurin girgiza kai Raheema tai tace “Your Highness bazan tab’a saka kokonto ko shakku gameda kai ba, I know you’re a good person, kuma nasan ko meye kake b’oye mata is for her own good... Na sani bazaka tab’a yin abinda zai cuceta ba... Your Highness na yarda dakai d’ari bisa d’ari... Idan da zakabi shawarina, kai gaggawan d’auke d’iyarka daga Masarautar nan... Send her to boarding school, idan hakan bazai yuwu ba kafin ka rasa Martabarka da kimarka cikin Masarautar nan ka d’auke d’iyarka ku koma yanda kuka fito... Babu komai cikin Masarautar nan sai cin amana da tashin hankali, kai tunani Tunda ka dawo babu wani abu mai kyau da ya faru dakai sai akasin haka... Ka d’auki ku koma can Spain ki ci gaba da rayuwarku mai tsafta babu hayaniyar cikin Masarautar nan... But before then make sure ka sama wa d’iyarka uwa... Kar ka mance Zahra tana delicate stage ne yanzu... Gaba mai had’ari take, tanajin kanta itad’in yanzu young lady ce... A wannan shekaru na teenage da take ciki tana buk’atar uwa a tattareda ita your Highness... Ka sama mata uwa wacce zata kula da ita da shawarwari masu kyau ku tafi ku koma Spain... Shawarina kenan your Highness..!” Ta k’arashe cikeda kulawa... Mahmood da yaima b’angare guda k’uri sai faman juya cup d’in dake hannunsa yake yana kuma jinjina maganan Raheema... Raheema tai masa K’uri zuciyarta na mata dad’i, Tunda ta kula asirinsu ba kamasa zai ba gwara tai amfani da wannan damar ta saye zuciyarsa da kalaman kwantar da hankali, ta gwammaci suyi aurensu su tafi can Spain d’in dan dama ita wannan sarautar ba wai ya dameta bane muddin zata sami Mahmood ita shikenan koda sarauta ko babu sarauta ba damuwarta bane.... A hankali ta mik’e ta risina tace “Na Barka lafiya your Highness...!” Lokaci guda tasa kai zata shige sai sinkayo muryar Mahmood d’in tai ya ambato sunanta... Taja ta tsaya kana ta juyo a hankali ta risina had’ida amsa masa... A hankali ya furta “Thank you..!” Raheema ta murmusa zuciyarta na mata wasai ta jinjina masa kai a hankali kana tasa kai Ta fice... Tana ficewa ya d’auki wayarsa saman center table ya shiga dialing layin Turaki.... ** Raheema na fitowa ta hangi Yazeed tsaye hannayensa hard’e yana dubanta muguwar murmushin nan saman fuskarsa, murmushin itama ta sakar masa kana tabi wani hanya, saida ya waiga gefe da gefe kana yasa kai shima yabi bayanta.... Yazeed ya dubeta yace “So tell me plan d’in yayi working...?!” Murmusawa tai tace “Kaid’in na daban ne... Na tabbata bayan abinda ya faru Mahmood zai aureni ya d’auke d’iyarsa mu bar k’asar nan...!” Ta kuma takowa zuwa gaban Yazeed lokaci guda tasa hannu ta dafe fuskrsa, cikin kissa take furta “Yanzu ka hak’ura kenan ka bar wa Yayanka ni..?!” Murmushin nan nasa saman fuskarsa yake furta “Akan SARAUTAR nan babu abinda bazanyi ba, babu abinda bazan sadaukar ba... That throne is mine.... So na zab’i na rabu dake muddin zan gaji sarautar mahaifina...!!” Ya k’arashe yana mai d’an bubbuga fuskarta yanda akewa yara... Yazeed yaci gaba da fad’in “Mahmood is all yours ke kad’anki sai yanda kikaso kiyi dashi...!” Suka murmusa a tare kana Yazeed yace “Yaushe zaa bani na k’ashe tinda na sallamawa Mahmood..?” Ta murmusa tace “Karka damu Prince akwai farewell da zamuyi... Just make sure you didn’t ruin our plans...!” Yazeed ya murmusa yace “An wuce wannan ai tinda har aka sako Zahra ciki... She’s his greatest weakness... Ina mai tabbatar miki nan bada jimawa ba zakiji ya tafi masarautar ku neman aurenki..!” Raheema ta kuma murmusawa cikeda jin dad’i tace “At last burina zai cika... Na Barka lafiya Your royal Highness...!” Yazeed ya jinjina mata kai alamun amsawa murmushin nan nasa saman fuskarsa... ** Cikin rashin fahimta Turaki ya mik’e tsaye yana furta “You can’t be serious your Highness... Please think your decision through, Your Highness you can’t leave... Musamman yanzu da family d’inka suka fi buk’atarka... Ka duba kaga halinda Jamal da Fu’ad ke ciki, haka zaka tafi ka barsu... And and ina labarin neman justice da kakewa mahaifinka da matarka... Ina maganan search for Ja’afar da kake...? Shin duk ka mance wanann zaka aje komai ka tafi.... Your Highness ina alk’awarin da kayiwa Wambai... Are you going to leave all this behind.... Sannan bayan duka wannan ka zab’i ka auri macen da baka so ka tafi kai rayuwa cikin k’unci... C’mon your Highness, think about all this... This is not the right time for you to leave...!” Katsesa Mahmood yai da fad’in “Yes Turaki na zab’i na bar komai behind for my daughter.. Can’t you see I’m loosing my daughter here... It’s over I’ve made up my mind zan auri Raheema na d’auki d’iyata mu koma Spain... She’s better off this way Turaki banso mukai peak d’in da zan rasata gaba d’aya... Zahra ita kad’ai nake gani na tuna Aliya.... Nothing can stop me now Turaki... Ka shirya within the week zamu tafi Masarautar su Raheema neman aurenta..!” Turaki dake dubansa cikeda mamaki girgiza kai kurum yake hannayensa dafe da kunkumi, ya kasa yarda da abinda yakeji daga abokin nasa.... ** D’aki ne mai tsananin duhuwa wanda baka iya ganin komai koda kuwa tafin hannunka ne sabida tsananin duhuwansa, Ubandoma ya sa hannu ya daki k’ofar take haske ya bayyana... Cikin sauri tasa tafukan hannayenta biyu tana kare fuskarta.... Ubandoma ya isa ya aje mata kwanon abincin dake hannunsa... Matsawa da baya take tsoro bayyane saman fuskarta Lokaci guda Ubandoma yace “Ki kwantar da hankalinki Kin kub’uta daga hannun azzalumai bazan miki komai ba....!” *MUHIBBAH* *50* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ubandoma ya koma gefe ya zauna yai mata k’uri yana duban yanda take jefa abincin cikin bakinta hannu baka hannu k’warya alamun ta galabaita da yunwa.. Shikadai saiko mahaliccinsa yasan abinda yake k’ullawa cikin zuciyarsa.... Ya sani duk duniyar nan yanzu Giwa batada burin da ya wuce ta sami Izzatu... Bazai bari hakan ya kasance ba dan shima nada nasa shirin akanta... Watak’ila Izzatu ta zamto mabud’in samun ‘yancinsa.... Ya saki murmushi a hankali kana ya matso kusanta yace “Ki kwantar da hankalinki bazan sake d’aureki da sark’ok’i kaman yanda nakeyi a baya ba... Kin fahimceni...?!” Bata amsasa ba saima ci gaba da tura abincin da take cikin bakinta... Mik’ewa Ubandoma yai ya fice daga cikin d’akin ya kuma kulleta nan cikin d’akin kana yai tafiyarsa.... Ubandoma na ficewa mahaukaciya Izzatu ta mik’e tana shafa ginin da Ubandoma ya ijeta ciki a hankali hawaye na gangaro mata... Cokalin da Ubandoma ya kawo mata abinci dashi ta soma karjan ginin tana saka hannunta tana gogewa... Cikin ikon Allah ginin sai ya soma b’anb’arewa yana zubewa duk yanda ta karje da cokalin... Ta zauna sosai tana ci gaba da karje ginin da iyaka k’arfinta bataji bata gani sai aikin abu guda take karje garu.. Ginin sai zuba yake a hankali tana kuma samun hanya... ** A can asibiti kuwa yau ake saka rana sallaman Jamal shi kuwa Fu’ad har yanzu babu yanda yake, ya farfad’o amma da alama muggan k’wayoyi sun kuma juya masa kwanyarsa dole akai transferring nasa to psychiatric ward... Shi kad’ai yake buga kansa jikin garu yana jin ciwo ma kansa tinda ya farka, aikin abu guda yake babu magana babu komai sai dukan kansa jikin garu ala dole aka dadd’aure Fu’ad da manyan sark’ok’i a fannin mahaukata dake nan cikin teaching hospital d’in, Giwa bata iya komawa ta gansa ba dan bazata juri ganin d’anta a d’aure da sark’ok’i ba cikin hauka tuburan... Shi kuwa Jamal alla alla yake ya dawo gida sabida duk dare akwai yanda yake zuwa cikin Masarautar, idan baije ba komai ka iya faruwa... Saidai yana tinanin ta yanda zai soma shiga Masarautar a matsayin gurgu makasashe saman wheelchair... Hawaye masu tsananin d’umi suka ciko idanunsa, Umaima dake gefe murmushi Ta sakar masa tace “Yaya Dr yace yanzu zai sallameka mu koma gida... I’ll park your belongings..!” Ta k’arashe tana mai isa yanda kayayyakin nasa suke... Cikin rawar murya yake furta “I can’t Umaima, bazan iya komawa Masarauta a haka ba... Dan Allah ki ce masu su dawo min da k’afata....!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa... Gaban wheelchair d’in nasa ta k’araso ta d’an duk’a kad’an tace “Ya Jamal I thought we’ve already talked about that.... Yaya please ka karb’i k’addararka babu wanda Yafi k’arfin hakan... Tsautsayi tana kan kowa... Shin kanaso ka zamto cikin mutane wanda basa yarda da k’addara ne...? Yaya kada ka zamto mai butulci wa mahalaccinka... Kaji please..!” Ta k’arashe kaman zatai kuka... Dubanta yake da idanunsa masu rauni kana yace “Nasan kina fad’a min haka ne kawai dan naji dad’i amma babu wanda zai kuma accepting d’ina the way I’m, even you Umaima bazakiso ki auri nakasashe irina ba...!” Hawaye na gangaro mata take dubansa lokaci guda take furta “Ya Jamal ina sonka... Ina sonka a duk yanayin daka tsinci kanka ciki, ka daina doubting soyayyar da nake maka... Wasu lokutan ba appearance na mutum ake dubawa ba, kyawawan d’abi’u da halayya ake dubi da... Mutum mai kyawawan d’abi’u irin naka ba’a sakaci da soyayyarsa... I love you Ya Jamal..!” Jamal yai mata K’uri yana dubanta zuciyarsa na masa wane irin sanyi“Zaki aureni a yanda nake.. Kin amince da zaran mun koma masarauta a saka bikinmu...?!” Murmushi saman fuskarta take jinjina masa kai “Yes Yaya... Na amince zan aureka... Na amince a saka mana ranan aure..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta hawaye na gangaro mata... Murmushin Shima ya sakar mata yace “Thank you so much my love... I love you...!” Daidai nan Dr ya shigo da takardun discharging Jamal sai zolayan Umaima yake yana fad’in daga yau ta daina yinin asibiti.. A ‘yan kwanaki biyun da Jamal yai kullum can wajensa take yini wanda hakan sosai yake d’ebe masa kewa... ** A b’angaren Giwa abubuwa sun kuma rikice mata, babu labari mai dad’i daga Ubandoma ko Waziri gameda neman Izzatu gashi gobe wa’adin da Tal’udu ya bata yake cika... Gaba d’aya ta rasa yana zata saka kanta sabida tashin hankali, har wani rama da bak’i Giwa tayi.. Ko Fadarta bata iya fitowa kullum cikin neman mafita take... Babu abinda yake gabanta yanzu tamkar taga Ta sami Izzatu yanda ta shiga ta fita, idan kaga Giwa zakai zaton ciwo take... Kowa a Masarautar sabgan gabansa da abinda ya damesa yake... Yazeed na k’ok’arin yanda zai ya kawar da Mahmood daga Masarautar shima Mahmood d’in na k’ok’arin yaga ya shawo kan d’iyarsa daga iftila’in da suka tsinci kansu ciki... Tuni ya sanar da Giwa k’udirinsa na auren Raheema saidai bai sanar da ita shirinsa na barin k’asar tareda Raheema da d’iyarsa Zahra ba, Giwa tayi na’am musamman dataji za’a had’a Bikin aurensa da Bikin nad’asa sarauta ne hakan sosai yayi masu dad’i itada Waziri, a k’arshe zasu rabu da Mahmood su huta su kuma d’aura alhakin mutuwarsa kan matarsa Raheema da kuma yayarta Gimbiya Zeenatu, shikenan sun kashe tsuntsu biyu da dutse guda... Shi kuwa Yazeed bai nuna damuwarsa da batun nad’in sarautar da za’aiwa Mahmood ranan bikin aurensa ba tinda yasan shirin Mahmood d’in barin k’asar zai da zaran ya auri Raheema bazai jira su nad’asa sarauta ba, a k’arshe idan babu Mahmood dole a nad’asa shi Yazeed a matsayin Sarki.... Ita kuwa Raheema tuni ta koma Masarautar su tinda aka soma batun aurensu da Mahmood.. Gimbiya Zeenatu bata sama bata k’asa burinta na mallakan masarauta ya kusa tabbata... ** Jamal ne a d’akinsa shi kad’ai sai kai komo yake dafe da sandarsa ta crotchets yana zullumin abinda ka iya zuwa yazo bayan kwanaki biyu da ya shafe bai je yanda yake zuwa cikin Masarautar ba... Waht if ya mutu...? Wata zuciya tace idan ya mutu ai hutunka tinda dama kace da Giwa ka riga ka kashesa tun wancan lokacin sannan Umaima zata zamto taka kai kad’ai har abada... Mutuwar nasa zai fi maka... Toh amma idan bai mutu ba fah... Idan ya sami wani hanya yayi escaping fah..? Kai ai Babu hanyar da zai samu ya gudu bayan alluran gusar da hankali da kake jibga masa had’ida k’wayoyin da kake narka masa a ruwan shansa.... Bazai tab’a iya escaping ba... Lokaci guda kaman wanda aka sinkaya ya isa jikin drawer ya janyo ya ciro doguwar syringe d’in ya zuk’i ruwan magani ya d’agata sama yana kallo kana ya saki murmushi a hankali yana kad’a syringe d’in daidai lokacinda Umaima tai knocking hannunta d’aukeda tray na fruits... A d’ari Jamal yai saurin maida syringe d’in cikin drawer ya juyo yana tambayar ko wanene... Umaima tace itace daga nan yanda take tsaye bakin k’ofa... Sauri sauri ya maida duk abubuwan da ya d’auko kana ya isa k’ofar dafe da crutches d’insa ya bud’e mata murmushi saman fuskarsa.. Murmushin ta sakar masa itama wanda yafi kama yak’e kana tace “Naga baka parlor nace barin hauro maka dashi tinda ka hana duk Kuyangin gidan nan shigowa sashenka kuma time d’in shan maganinka yayi...!” K’uri yai mata yana jin dad’in yanda take nuna damuwarta akansa... Lokaci guda ya kauce ya bata hanya yace “Please come in...!” Umaima ta jinjina kai ta rab’a ta shige a hankali kana ta isa ta aje masa tray d’in saman rug... Jin k’aran rufe k’ofa ya sanyata saurin juyowa alamun tsoro fal fuskarta... Murmushi ya sakar mata yana mai dogarowa yanda take yace “Ya naga yanayinki ya canza... Ko tsorona kike...?” Ta kuma sakar masa murmushi wanda yafi kama da yak’e tace “A’a Yaya... Ka sha maganinka kafin lokaci ya k’ure..!” Ya jinjina mata kai alamun toh zaisha... Suna a haka Giwa ta shigo sashen nasa... Kallo taiwa Umaima ta watsar, Umaima ta sinne kai ta gaisheta dan tun bayan da suka soma soyayya da Jamal nauyin Giwa ya k’aru cikin idanunta... Tai excusing kanta ta fice Jamal na biyeda ita da ido.... Umaima na ficewa Giwa tace “Kai mai yarinyar nan take d’akinka...?!” Ya kuwa watsa mata harara dan yanzu kallon arziki bai shiga tsakaninsa da mahaifiyar tasa... “Is non of your business...!” Ya fad’i yana mai juya mata baya.... Giwa ta k’araso sosai cikin d’akin had’ida furta “Tun wuri ka janye wannan shiririta da kake... Babu kai babu auren Umaima...!” Kaikaitowa yai yana dubanta kana ya murmusa kad’an yace “Da gaske Maami..?!” Ya murmusa kad’an yace “Kin makara, na riga na gama miki biyayya muddin kikai gangancin yunk’urin dakatar da aurena da Umaima... Yau d’in nan basai gobe ba zan sanar dasu Galadima batun aurena da Umaima, in fact tareda na Yaya Mahmood nake so a had’a..!” Giwa da fuzar da huci kad’an tace “Gwarzona kalleni nan kaji... Ni fah bance kada kayi aure ba amma da ka d’an sarara ka sake dubawa ko zaka sami wata, ni tabbata ba wata soyayya bace tsakaninku da Umaima SHAKUWA CE kawai....!” Wane irin duba ya watsa mata kana ya saki murmushi da gefen bakinsa yace “A yanayin da nake ciki har cewa kike na tsaya na sake dubawa bayan nasan babu mai k’aunata tsakanida Allah a yanda nake... Maami koma akwai ni bani son kowa sai Umaima kuma dole a saka aurenmu lokaci guda dana Yaya Mahmood tinda nida ita mun sasanta da juna kuma duka abin d’aya ne Maami, nida Umaima duka ‘ya’yanki ne... Idan har zaki amince Yaya Mahmood ya auri k’anwar kishiyarki na tabbata zaki amince na auri d’iyar d’an uwanki... Saidai kuma idan akwai abinda kike b’oyewa wanda ni kaina ban sani ba Maami.....?!” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu... Ganin ta kasa magana ya sanyashi sakin murmushi yace “Nasan baki fata dark secrets d’inki su soma bayyana...! Dan wllhi if you try something funny zan baki mamaki irin wanda baki tab’a zato daga gareni ba...!” Ya k’arashe yana sakin huci... Idanu waje Giwa ke dubansa zuciyarta na wane irin bugawa, Yazeed threatens her yanzu ga Jamal ma nayi, wannan wace irin rayuwa ce ace ‘ya’yanka na cikinka na maka barazana bayan duk sadaukarwa da take sabida su ne da samun ingantacciyar rayuwarsu... Ta had’iyi miyau da k’yar kana ta murmusa tace “Yanda kake so Gwarzona...!” Tana kaiwa nan ta juya ta fice cikin sassarfa.. Jamal yabita da idanu har ta b’acewa ganinsa kana ya d’auko syringe d’insa da zummar ficewa.... Yana rik’eda syringe ga kuma crutches hakan yasa yai losing balance Allurar ta karkace ta sokesa a cinya.... K’ara ya saki ya zube a wajen yana rik’eda cinyarsa yanda allurar ta cakkesa... Kan kace mai idanunsa sun soma lumshewa ya zube wajen.... ** Cikin sa’a taci gaba da kankare ginin har ta soma jin wane irin yanayi gaba d’aya illahirin jikinta... Bata fasa abinda take ba taci gaba da karjan ginin ko Allah zai bata dama ta gudu.... Ginin yai dogon rami da kana iya hango d’aya b’angaren dukda ba wani sosai ba... Idanunta ta lik’a jikin ramin ga mamakinta d’aki ta hango iyaka ganinka... Dukda akwai duhuwa saidai kaman tana iya jiyo sautin numfashin mutum yana fita da k’yar... Zuciyarta ya kuma yankewa Ta k’ara manna k’wayar idanunta jikin ramin.... Kaman daga sama taji an tab’a k’ofarta, tai saurin komawa ta zauna a mazauninta had’ida toshe ramin da take karjewa... Ubandoma ne ya kuma shigowa ya aje mata abinci maiji da lafiya harda ruwan sha kana ya kuma ficewa.... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali ta koma jikin ramin tana ci gaba da karje ginin sannu a hankali.... ** BAUCHI Fitowa yai cikin shirinsa na tafiya office, ya lek’a kitchen ko zai ganta dan wasu lokutan nan yake taddata tareda Iya Larai sabida akasarin lokutan tare suke ayyukan... Bai taddata ba sai Iya Larai dake sauraron shirye shiryen safiya a radio... Gaisawa sukai kana ya tambayeta Mommy, Iya larai tace ai tuntuni ta fice Office... Ansar ya jinjin Kai ba tareda ya kuma cewa komai ba, Iya Larai ta fahimcesa sarai Muhibbah yake son tambaya, Ta d’an bud’e murya tace “A kawo maka shayin naka ne...?!” Ya girgiza kai idanunsa naga wayar salulansa yake fad’in “A’a Iya Larai na gode azumi nake..!” Iya Larai tace “Aff ashe yau alhamis ai na mance azumin alhamis da litinin basa shigeka... Ka gaisa da mutumiyar taka ce... Tana ciki yau duka bata fito ba..?!” Janye idanunsa yai daga saman screen d’in wayar tasa yace “Amma lafiya bata fito ba..?” “Eh Toh kasan tinda ta dawo daga makarantar nan gaba d’aya mun rasa gane kanta amma dai naji jiya da dare tanaceda Hajiya yau d’in Zata koma makaranta sabida jarabawa dake gabato masu...” Bai ida sauraren Iya Larai ba yasa kai ya shige cikin sauri,.. Iya Larai tabisa da kallo had’ida girgiza kai a hankali... K’ofar d’akin nata ya tsaya yana knocking... A zatonta Iya Larai ne ta d’an bud’e murya tace “Iya shigo abinki had’a kaya nake..” Aya taima kalaman nata ganin wanda ya turo k’ofar... Ta d’an kauda fuska kad’an had’ida fuzar da iska... Murya can k’asa ta gaishesa... Ya amsa yana mai bin jakan kayan nata da kallo “Why are you parking... Ina zakije..?” Yai mata tambayoyin a tare... Idanunta naga wane b’angaren take furta “Zan koma Masarauta ne..!” Dafe da handle d’in k’ofa yake dubanta “What.!! Masarauta kuma... What for..? I thought we’ve already talked about that, bazaki koma wannan Masarautar ba...!” Katsesa tai da fad’in “I’ve changed my mind... Zan koma..!” Murmushin da yafi kama da yak’e Ansar yai kana yace “But abinda van gane ba shine mai zaki koma yi cen..?!” “Zan koma ne to fix what I ruined... Bazan iya zama a nan ba alhali ina saneda cewa na b’ata tsakanin d’iya da mahaifi... I need to go back na gyara abinda na b’ata...!” Fuzar da huci yai a karo na biyu yana mai girgiza kai yake furta “Kinyi haka ne a bisa rashin sani Muhibbah, You don’t need to go back... Ya kamata mu bada hankalinmu kan batun aurenmu dake k’aratowa... Akwai maganar da nake so muyi dake dama..!” Ta katsesa da fad’in “Kan Hameedah...? Kar ka damu bakada matsala dani, taimakona kukayi and duk wani condition d’in da zaku gindaya min zan d’auka... Nasani Baffah Yawale ya amince da aurenmu ne da sharad’in shima zaka auri d’iyarsa Hameedah right..?!” Ansar ya shafe fuskarsa da tafukan hannunsa had’ida gyara tsayuwarsa yace “Ba haka bane Muhibbah..!” “Then yaya ne..? Make me understand..! Shikenan dan an taimakeka sai ace rayuwarka ma sai yanda akeso za’a tsara..? I’m not saying kada ka auri ‘yar uwarka..!” Katseta yai da fad’in “Hibbah please listen to me first... Wannan ba yin na bane kuma ba yin Mommy bane... Hibbah idan dan tani ne bazan auri d’iyarsu ba amma saidai Mommy bata buk’atan wani tashin hankali a halin yanzu shisa tace na amince da auren Hamidar..” Murmushin da take ya katsesa, tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata “Karka damu bakada matsala daga b’angare na... All I’m asking now shine ka barni naje na gyara abinda na b’ata kafin ai maganar aurenmu... Besides babu wani zab’i ga wanda yai losing hope..!” Yanda tai maganar tamkar sak’o take basa a dunk’ule... Yai mata K’uri na ‘yan dak’ik’ai kana ya girgiza kai yace “Ban fahimceki ba... Wanda tai losing hope kaman yaya...?!” Ta k’ak’aro murmushi had’ida girgiza kai tace “Rayuwar da kake mafarkin samu wanda bazaka tab’a samu ba... Toh duk rayuwar daka tsinci kanka ciki sai kai fatan Allah yasa hakan ya zame maka alkhairi..!” Girgiza kai Ansar yai yace “Rayuwa dani ne k’addara..? Kokuwa dai rayuwa da kishiya ne k’addarar...? Kodai kinada wani wanda kike mafarkin rayuwa dashi ne matsayin ma’aurata K’addara take yunk’urin hana yuwar hakan... Muhibbah wannene ciki...? Talk to me answer me... Do you love someone else..?!” Tambayar da yai mata ya haifar mata da wane irin fad’uwan gaba Ta d’ago dara daran idanunta tana dubansa zuciyarta naci gaba da bugawa... Murmusawa tai kad’an “Ya kake magana haka... Ni kuma soyayya da wani...? Sanin kanka ne bayan iftila’in da ya auka dani na d’auki lokaci mai tsawo kafin na amince akwai wata aba Wai ita soyayya tsakanin mace da namiji.... Bansan soyayyan kowa ba sai naka Ya Ansar... Maiyasa kake tinanin inada ‘yanci da soyayya da wani bayan kai...?!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Cikin sanyin jiki Ansar ya duk’a gabanta yace “Muhibbah you’ve all the right kiyi soyayya da wanda kike s koda ba ni bane.... Muhibbah ina sonki, ina k’aunarki... And I’m not asking you to love me back... Kuma ki daina d’aukan kanki a matsayin wacce aka taimaka dole tayi duk abinda muke so... No kin wuce haka a wajenmu, kin cancanci Farin ciki kema... Idan kikace baki sona I can understand you...!” Ya k’arashe cikin rawar murya... K’uri tai masa hawaye na kuma gangaro mata... Ansar yai k’ok’arin saita kansa yace “Idan kin gama parking d’in muje na maidake, I’ll cancel my appointments for today...!” Tai saurin mik’ewa tana mai girgiza kai take furta “No, kar ka damu zan tafi bakin hanya yanzun nan nasan bazan rasa motan Jos ba... Bai kamata ka dakatar da aikinka sabida ni ba...!” Girgiza kai yai yana mai shafa wayar salulansa yake furta “I insist, you first before anything else, and is not safe nowadays ka shiga mota daga kan hanya, idan har shiga motan hayan ya kama dole toh yafi dacewa kaje tasha ka shiga motar da zai tashi daga gari zuwa gari direct..” (Matafiya a dinga hattara duba da yanzu yanda hanyoyinmu suka koma... Allah yaci gaba da karemu ya kawo mana lafiya da zaman lafiya a k’asarmu..Ameen!) Jiki a matuk’ar sanyaye take ida shirin nata sanda ya janyo jakan kayan nata waya manne kunnensa yake furta “Doc eh wllhi, tafiya ce ta gaggawa ta taso min.. Ok toh shikenan babu matsala... Zamuyi magana later... Yauwa thank you..” Ya k’arashe maganar yana mai ficewa... Tausayinsa ya lullub’eta gaba d’aya... Ansar ya cancanci Farin ciki... Shida mahaifiyarsa mutanen kirki ne... Koda ace bata sonsa tabbas zata iya sadaukar da soyayyarta ta amince ta aureshi domin shid’in yayi mata dukkan wani hallaci... So tari zaka so abu babu alkhairi cikinsa, sannan so tari zaka k’i abu shine maka alkhairi... Zataci gaba da addu’a Allah ya sanya aurenta da Ansar ya zamto Alkhairi ya kuma zamto silan mance duk wani k’unci na rayuwa data tsinci kanta ciki a baya... A haka suka d’auki hanyar Jos duka su biyu d’in babu walwala a tattaredasu... Sanda suka isa yai parking a yanda ya saba parking... Ya juyo ya d’an dubeta kana ya sakar mata murmushi “Idan har dawowarki don ki gyara abinda kika b’ata shine kwanciyar hankalinki na amince miki da hakan... Allah ya baki nasaran cimma burinki cikin sauk’i....!” Ta murmusa kad’an tace “Na gode Yaya Ansar... Na gode da fahimta da kake min a koda yaushe, sannan ina mai sanar dakai da zaran ka koma Bauchi kuyi shawari da Mommy ku yanke ranan aurenmu, duk lokacinda ya kwanta maka... Ni kuma nayi na’am da hakan... I’m ready to be all yours..!” Ta k’arashe murmushin k’arfin hali saman fuskarta... Jin abin yai kaman wasa, ya kuma gyara zama yana dubanta “Are you serious Hibbah..?!” Murmushi saman fuskarta Ta jinjina masa kai alamun tabbatarwa... Murmushin shima yayi kana yace “Bazan iya ce miki komai a yanzu ba, dan bansan ta yanda zan soma had’o kalaman Farin cikin da na tsinci kaina ciki ba... The only abu da zan fad’a miki yanzu shine na miki alk’awarin bazakiyi danasanin aurena ba in sha Allah...!” Ta murmusa tana mai sadda kai k’asa tace “Ya kamata ka d’auki hanya kada rana yai maka...!” Ya jinjina kai had’ida d’aga mata hannu alamun salute yace an gama your Highness yanzun nan ma kuwa...!” Muhibbah ta murmusa tai masa fatan sauk’a lafiya kana sukai sallama ta d’auki hanyar masarauta gabanta na tsananta fad’uwa... Hanshak’an motoci na Alfarma data gani ne barbaje cikin Masarautar ya sanyata ci gaba da tafiya cikin sanyin jiki tana kuma bin motocin da ido... Ga dogarai da Fadawa Ta ko ina suna gyara kimtsi... “Tooh yau kuma meke faruwa cikin Masarautar...?!” Ta furta a hankali... Can ta hangosa cikin shiga ta manyan kaya, farar shadda k’al ‘yar ciki da babban gare ga kuma farar rawani mai kunne biyu akansa, sosai k’warjininsa ya kuma fitowa... Wani taku yake irinta asalin jinin sarauta wanda babu sirki ko gauraye da jinin bauta...Tai tsaye tana dubansa zuciyarta naci gaba da bugawa... Sai fadanci ake masa masu sarauta na take masa baya... Tana gani aka bud’e masa rantstiyar SUV fara k’al ya shige ciki Turaki ya shige ta d’aya b’angaren shima yayi shiga irinta masu mulki... Hadiminsa ya shige gaban motar bayan ya gama bud’ewa Ubangidan nasa... Sauran masu sarauta su Waziri da su Galadima suka shige sauran motocin yayinda motar security Ta soma ficewa daga cikin Masarautar ana baza hidiman iko... Tabisu da kallo har suka fice kana ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali ta nufo cikin Fada... Tana tafe ne ta hangi Ubandoma sai waige waige yake a yayinda hankulan jam’an masarauta ya karkataga fatan sauk’a lafiya ga Yarima Mahmood ko muce Sarki Mahmood mai jiran nad’i.... Haka kurum taji tabi bayan Ubandoma taga mai yake shiryawa... SameenaAleeyou 📚 SameenaAleeyou 📚 SameenaAleeyou📚[8/23, 10:35 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *51* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Jikin tsakankanin gini ta mak’ale tana duban Ubandoma da ya shige wani d’aki... Mamaki ya cikata dan koda wasa batai zaton akwai d’akuna a wannan waje ba a ciki Masarautar... Ikon Allah watau shidai wannan masarauta wani irin gine gine yakeda masu rikitarwa wanda idan bakasan kansa ba tabbas zaka auka ramin da bazaka iya ficewa ba har a mance dakai... Ta kuma lallab’awa ta isa jikin k’ofar d’akin da taga ya shige tana lek’e a hankali... Duhuwan dake cikin d’akin ya hanata ganin abinda Ke aukuwa cikin d’akin amma kam jikinta ya bata wani abin yake k’ullawa a wannan waje mai surk’ullen gaske... Tana jin alamun zai fito tai saurin komawa mab’oyarta Ta b’oye... Ubandoma ya fito yana ‘yan waige waigensa kana yasa kai ya shige cikin sauri.... Abin mamakin data gani wannan karon sai yafi d’aure mata kai... Gashi dai gini ne Babu alamun k’ofa amma sai gashi ginin ya bud’e Ubandoma ya fice... Tinanin Taswira mai wahalan fasaltuwan nan ya fad’o mata... Tabbas yayi kamanceceniya da ire iren wannan gini.. Amma ko dan Ta kuma fahimtar Taswiran nan zata isa jikin ginin taga ko Allah zaisa ta iya bud’e wannan k’ofa da baida wani alamu... Yana shigewa da wasu ‘yan dak’ik’ai Muhibbah ta fito ta nufi jikin ginin tana shafawa a hankali.... Sosai ta k’urawa ginin idanu nan ta hangi wani dogon layi jikin ginin yasha kwalliya da fenti irinta gidan sarautar wanda sam bazakai zaton ba ado ne kawai na gine ginen gidajen sarauta ba... Dukda gabanta dake tsananin fad’uwa hakan bai hanata saka ‘yar tsarta tsakankanin wannan ginin ba... Ga tsananin mamakinta saiji tayi kaman ginin na motsi... Ta kuma yin basmalah ta tura yatsarta taji tabbas motsi yake.... Allah mai iko Wato ashe k’ofa ce aka yita cikin gini wanda sam ga wanda bai sani na bazai fahimci hakan ba... K’irjinta yaci gaba da fad’uwa tana tunanin mai zata gani bayan wannan gini idan ta bud’e... Lumshe idanunta tai tana k’arfafawa kanta gwiwa da fad’in zata iya da yardar Allah... Ta kuma ambato sunan Allah kana ta d’an bugi ginin da hannunta.. Ga tsananin mamakinta sai gani tai ginin ya soma bud’ewa d’aki mai tsananin duhuwa ya bayyana... Mamaki ya kuma cikata, tabbas d’aki ne a wannan waje.... Toh miye a ciki..? Bata kaiga samo amsa ba ta hango mutum daga can k’uryar d’akin tana ci gaba da karjan gini alamun bataji shigowarta ba.... Dukda bayanta kawai take iya hanga bataga fuskarta ba dashike Ta bada baya ne ma k’ofar, hakan bai hana Muhibbah ci gaba da takowa cikin d’akin k’irjinta naci gaba da bugawa ba, addu’o’i kuwa duk wanda yazo saman harshenta shi takeyi.... A hankali take takawa har ta isa taga abinda matar take.... Cak Izzatu Ta dakata da abinda take dan taji kaman mutum ne a bayanta... Aiko take ta juyo da zummar capko mutumin dake bayanta, Muhibbah ta rintse ido tana jiran mai auka ya auku tinda ta gane matar mahaukaciyar nan ce da Ta kirawo sunanta.... Bata auka mata ba saima tsayawa da tai tana binta da kallo... Muhibbah ta bud’e idanunta a hankali tana duban matar da tai mata K’uri, cikin d’an tsoro tsoro take takowaga matar wacce tuni Ta soma sakar mata murmushi... Muhibbah taji k’warin gwiwa na zuwa mata.... Murmushi itama ta sakar mata kana tace “Mai kikeyi a nan... Wa ya canza miki d’aki...?!” Bata bata amsa ba sai nuna mata ramin da take tono datai jikin gini wanda tuni yayi zurfi.... Muhibbah ta dubi ramin da mamaki Ta kuma duban matar... Jinjina mata kai matar tai k’walla tab idanunta... Lokaci guda take kuma janyo hannun Muhibbah ta zaunarta jikin ramin tana mata alamu da hannu kan ta tayata suci gaba da tonon ginin.... Ita dai Muhibbah duk bata kawo komai ba, duk a nata zaton cikin haukar wannan matar take ceda ita su karje gini... Ta k’ak’aro murmushi ta sakar mata kana Ta mik’e ta shiga janyo hannunta tana fad’in “Zo mu tafi... Zan fitar dake daga Masarautar nan, bazan bari su kuma zaluntarki ba... Zo muje..!” Ta k’arashe tana mai kuma janyo hannun mahaukaciyar wacce tak’i koda motsa k’afarta ne... Muhibbah ta juyo ta dubeta da mamaki kana tace “Bakiso ki kub’uta daga hannun wad’annan azzaluman ne...?” Matar ta girgiza mata kai alamun a’a kana ta kuma mata nuni da ginin da take karja.... Muhibbah ta dubi ginin ta d’an murmusa kad’an dan tasan duk cikin gushewar hankali ne kana ta matso kusanta tace “Kar ki damu ni nasan k’ofar da zamubi mu fice ba sai kin karje gini ba... Idan kika tsaya yin wannan har zasu cimma Ki su kuma kamaki... Zo muje kafin ya dawo...!” Ta k’arashe tana mai kuma janyo matar wanda wannan karon sosai ta b’ata fuska tana duban Muhibbar... Lokaci guda ta finciki hannunta daga rik’onda Muhibbar tai mata ta koma jikin ginin taci gaba da karjewa ba tareda Ta kuma bin takan Muhibbah ba... Muhibbah ta bita da idanu cikeda mamakin yanda ta koma ta duk’a gaban garun tana ci gaba da k’walk’walewa... Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali wata zuciya na cewa bazaki Iya da matar nan ba Ke kad’ai, Ki fice Ki karya Giwa kafin ki dawo ki ceci matar nan idan ba haka ba kema in suka kamaki haka zasu maisheki, kinga baki taimaki matar nan ba gashi kema an kamaki.... Da wannan tunanin Muhibbah tasa kai zata shige ta k’yale Mahaukaciya Izzatu... Har takai k’ofa sai kuma ta tsaya cak tana tunanin anya lafiya mahaukaciyar nan Ke karjan gini haka kurum... Anya bazata duba abinda mahaukaciyar nan keyi ba...? Take taji tana son ganin abinda mahaukaciyar keta k’ok’arin nuna mata tai zaton cikin haukarta ne... Dawowa da baya Muhibbah tai ba tareda taceda mahaukaciyar komai ba ta duk’a a hankali tana duban abinda take... A hankali Muhibbah ta saka idanunta tana duban cikin ramin wani irin yanayi da bazatace gashi ba yana fuzgarta, zuciyarta na bugawa cikin nastuwa... Tai k’ok’arin janye hannayen Izzatu daga jikin ginin kana ta saka k’wayar idanunta tana lek’awa.... Duhu ne iyaka ganinka amma taji wani irin yanayi kam... Toh nan d’in kuma inane... Wata zuciyar tace k’ila mahaukaciyar tayi zaton ta nan d’in zata sami hanya...! Hakan yasa Muhibbah waigowa da niyyan k’ok’arin shawo kan mahaukaciyar nan Ta amince Ta bita su fice... A yunk’urin da zatai da zummar waigowa kunnenta guda ya tsaya daf jikin ramin da Izzatu ta karje yayi zururu... Kaman wanda iska ya koro sautin haka ta jiyo sauk’an numfashin mutum cikin kunnenta... Zuciyarta ta kuma tsinkewa.. Tabbas akwai bil’adam bayan wannan gini... D’agowa tai Ta dubi Izzatu da tai mata K’uri kana tace “Akwai mutum a bayan ginin nan..!” Izzatu Ta jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa... Cikin sauri Muhibbah ta mik’e tana duban Izzatu take furta “Wannan gini bazamu iya turasa ba, koda zamuyi kwanaki muna tono... Amma da izinin Allah zamu kub’utar da mutumin nan dake rufe a wannan fursuna mai tsananin duhuwa...” Ta kamo hannayen Izzatu duka biyu tace “Kin tuna Taswiran da kika bani..?” Izzatu ta jinjina mata kai alamun eh.. Muhibbah taci gabada fad’in “Zanen dake cikin Taswiran yayi yanayi da ire iren wad’annan gine gine na sarauta, yau d’in na tabbatar da haka... Idan muka fice a nan zamu zaga ta baya ko Allah zaisa mu sami k’ofar da zata cimmamu da d’akin da aka rufesa... Muje bamuda sauran lokaci...!” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Izzatu suka fice cikin sauri.... Saidai koda suka fito babu wata alamu da zasu iya gane akwai hanya da zai sadasu da wata d’aki a wajen... Muhibbah tai K’uri tana kallon dogayen gine ginen... Waigowa tai Ta dubi Izzatu da itama gine ginen take duba... Fuzar da fuci kad’an Muhibbah tai kana ta nufi wata hanyar dake nan b’angaren hagu da ginin... Nan ma shiru babu alamun hanya... Magana Izzatu take mata saidai maganar bata fita baka fahimtar komai sai gwalamniya... Muhibbah tai mata K’uri cikeda tausayawa, lokaci guda ta matsoga Izzatu ta kuma dafe hannayenta tace “Banjin zamu samu hanyar da zamu kub’utar da mutumin dake wancan d’akin amma mu koma cikin wancan d’akin muga idan zamu iya karje ginin cikin gaggawa...!” Ta fad’i hakan ne Dan baiwa mahaukaciyar da a yanzu take tantaman haukarta k’warin gwiwa.... Muhibbah ta kamo hannunta suka saka kai zasu koma cikin d’akin... Kaman daga sama suka sinkayo murya yana furta “Ina kuke tunanin zakuje..!!!” Cak suka tsaya yayinda Izzatu ta finciki hannunta ta soma jada baya tana nok’ewa had’ida yin wasu abubuwa na marassa hankali.... Muhibbah kaw rintse idanunta tai a hankali Dan ta tabbata yau kam shikenan an kamata.... Mutumin yaci gaba da takowa yanda suke har lokacin idanun Muhibbah a rintse suke, ya bud’e murya yace “Juyo Ki kuma nuna kanki..!” Bata juyo ba sai addu’o’i da take jerowa cikin zuciyarta.... The more tana add’ua the more tana jin k’warin gwiwa na zuwa mata tsoro na yaye mata... Ji tayi zata iya fuskantar koma wanene idan ta kama su kara ne ma sai su kara d’in... Fuska a matuk’ar murtuk’e Ta waigo cikin dakewa... Ubandoma yai mata K’uri yana son gane ina ya santa... Ya saki murmushi yana nunata da yatsa yace “Kece.!! Haba ai biri yayi kama da mutum, Jakadiya tayi gaskiya da tace bata yarda dake ba... Ashe ked’in kin jima kina k’ulla abubuwa cikin Masarautar nan.. Akwai babban dalili da ya shigo dake... Zaki gane kurenki yarinya... Zaki d’and’ani kud’arki, zaki gane cewa ba’a diran mik’iya ma Masarauta irin wannan... Kin tapka babban kuskure yarinya.. Kin hak’i kabarinki da kanki... Yanzu ba tareda b’ata lokaci ba zan d’aukeki ga Giwar Amale... Na tabbata zan samu babban rabo...!!” Ya k’arashe yana mai fashewa da dariya... Yayinda Muhibbah tai masa K’uri tana duban yanda yake dariya... ita kaw Izzatu gefe ta koma ta mak’ale jikin gini tana girgiza kai... Ubandoma na k’ok’arin takowa yanda Muhibbah take Izzatu ta k’arso a guje ta rungume Muhibbah tana hawaye take Girgiza wa Ubandoma kai alamun a’a... Ko gizau Muhibbah batai ba saima ci gaba da duban Ubandoma da take da idanunta wanda babu alamun tsoro ko sarewa cikinsu... Cikin dakakkiyar murya Ta soma furta “Shin wace riba da ka samu daga wajen Uwargijiyarka idan ka bari aka cutar da rayukan da basuda alhakin kowa..? Shin wace riba zaka samu a wannan ta duniya wacce ita d’in ba matabbatace face GIDAN ARO... Shin wace riba ka samu a iyaka shekarun da kai kana ha’intar mutane da basuda hakki... Ka dubi tsawon shekarun da kai a baya, ka d’auki tsawon rayuwarka kana bauta ne ma wacce bata ganin darajarka balle kimarka saima d’inbin wulak’anci da tozarci da kake fuskanta daga gareta... Shin mai zai ragu jikinka idan ka zab’i ka aiwatar da abinda ya dace... Na tabbata tsawon rayuwarka ka yisu ne a matsayin bawa maras ‘yanci wanda sai abinda aka umarcesa...!” Katseta yayi da fad’in “Ke yarinya hattara, kar Ki bada shaida akan abinda bakida masaniya... Wannan abu da kikaga nakeyi nima ba son raina bane... Kaman yanda kika ce tsawon rayuwana na shafesa ne wajen bauta tabbas haka ne.. Kuma wannan abu da nake yanzu inada tabbacin shi zai bani ‘yanci da na jima ina nema sabida duniyar nan yanzu babu abinda za’a baiwa Giwa Ta shiga nishad’i tamkar wannan matar..!” Ya k’arashe yana nuni da Izzatu, lokaci guda yaci gaba da fad’in “Wannan mahaukaciya da kike gani itace tikitin samun ‘yanci na da zuri’ata..!” Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Kanada tabbacin zata cika maka burinka..? Kokuwa a iyaka tsawon lokacinda ka kwashe kana mata bauta Ta tab’a cika maka alk’awari...?!” Ubandoma yai shiru yana juya kalamanta cikin sanyin jiki...! Ganin yanayinsa ya kuma baiwa Muhibbah k’warin gwiwar ci gaba da magana... “Babu cika alk’awari a duniyar da babu komai cikinta face zalunci... Shi azzalumi a koda yaushe hanyar da zai rud’eka ya cutar dakai ya kuma yaudareka yake nema.. Babu Aminci a duniyar da yarda da rik’on amana yai k’aranci cikinta..!” Ta kuma sassauta murya tana duban Dattijo Ubandoma tace “Baba lokaci bai k’ure maka ba, you can still do the right thing... Zaka iya zab’an tafarki mai kyau... Alk’awarin Allah gaskiya ne Baba... Shid’in yana tareda masu gaskiya ne..! Kai abinda ya dace ka juya bayawa azzalumai.. Kaji tausayin wannan Baiwar Allah da halinda Ta tsinci kanta ciki wanda idan son ranta ne bazataso ta ganta a yanayin da take ba..!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka.... Allah sarki saiga Hawaye suna gangarowa daga idanun Ubandoma... Ya k’arasa jikin dakali dake wajen ya zauna yana mai ci gaba da matsan k’walla... Lokaci guda yana tuna abubuwan da Giwa ta umarcesa yayi marassa kyau, ya tuna babu alk’awarin da ta tab’a cika masa, ya tuna kalan wulak’acin da tai masa wanda bazasu lissafu ba ciki harda marin da Jakadiya tai masa, wanda tayi hakan ne bisa umarnin Giwa... Muhibbah ta dubesa ta kuma duban Izzatu hawaye na gangaro masu gaba d’aya... Lokaci guda Ubandoma yaci gaba da fad’in “Kaico na! Kaicon son zuciya irin nawa..! Tinda nake ban tab’a jin kalaman da suka sanyar min da gwiwa suka sakani nadama ba irinta yau... Hak’ik’a na tafiyar da rayuwata ga bautawa zalunci da juyawa gaskiya baya... Ban tab’a danasanin abubuwan da nayi irinta yau ba.. Yarinya kinyi gaskiya da Kikace azzalumi bazai tab’a cika alk’awarinsa ba, hanyar da zai amfana dakai kurum yake nema... Babu lokacinda zan miki bayanin abubuwan da nayi marassa kyau bisag umarnin Gimbiya Turai amma da na baki labarin komai a yanzu basai anjima ba... Ina fata wad’anda na zalunta ta dalilinta zasu yafeni... Musamman Mahmood... Shid’in mutumin kirki ne... Kuma ina tsoron kasancewarsa cikin Masarautar nan da azzalumai sukai yawa dan rayuwarsa na cikin had’ari..!” Kiran sunan Mahmood da yai ya sanya wasu hawaye kuma gangarowa Muhibbah tana mai tuna mummunar zato da tai masa a baya.... Tai saurin saka hannu Ta share hawayen da suka gangaro mata tace “Baba tinda ka fahimci haka Alhamdulillah, Ina mai tabbatar maka in sha Allahu bazan bari wani ya cutar da Mahmood ba... Yanzu ka taimaka mu fitar da wani rai da yake bayan ginin nan, mu kub’utar dasu daga wannan azzaluman masarauta..!” Ubandoma ya dubeta yace “A ina kenan...?!” Muhibbah tai saurin masa nuni da cikin d’akin kana ta basa labarin abinda ta tadda Izzatu nayi... Yai shiru kaman nazari kana ya murmusa yace “Hak’ik’a gidan nan yanada surkulle da k’ofofi wanda wasu ma iyayenmu basu San dasu ba... Abinda yasa nima nasan da wannan waje an tab’a rufe mahaifina a ciki ne lokacin sarki Baban AbdulJabbar, mahaifina sunyi wani laifi sunci amanan masarauta aka kawosu wanann waje shiyasa nasan da wajen, ba kowa ya sani ba cikin Masarautar nan... Kuma akwai ire iren wanann da dama cikin Masarautar nan... Kinga can..!” Yai mata nuni da wani ginin... Yace inada tabbacin a nan k’ofar d’akin yake, Zo muje...!” Ya k’arashe yana mai sab’a babban gare yayi gaba... Muhibbah tabi bayansa cikeda mamakin yanda zasu samu k’ofa a wannan waje.... Aiko suna zuwa taga Ubandoma yasa hannu ya tab’a zanen Tanbarin Masarautar da akaima ginin kwalliya da ita... Aiko nan garun ya soma gaucewa... Ga tsananin mamakinta saiga k’ofa.... Suka dubi juna itada Ubandoma, lokaci guda yace da ita su shiga... Itadai da bismillah ta shige cikin d’akin Mahaukaciya Izzatu na biye dasu... Suna shigewa kuwa Ubandoma ya zaro tocilan dake aljihunsa wanda yake haska waje idan zai kawo wa Izzatu abinci ya shiga haska cikin d’akin... Ga tsananin mamakinsu k’aton k’arfe suka hango had’e da manyan sark’ok’i an dadd’aure mutum dashi ga kwanukan abinci ga syringe na allurai a warwatse a wajen... Mamaki ya cikasu, kallo guda zakai ka fahimci mutum ke rayuwa cikin buwayar Ubangiji a wajen... Tsoro da mamakin zalunci dake cikin wannan masarauta suka kuma kama Muhibbah... Cikin sauri Ubandoma ya k’arasa ga mutumin dake fidda numfashi da k’yar alamun ya gama galabaita sabida tsananin yunwa da k’ishin ruwa.. Kai a d’auke wannan ma mutum ya rayu wannan waje saidai buwayar Ubangiji wanda babu abinda ya gagaresa, bazaka mutu ba sai ranan da yace zaka mutu, duk tsanani kuwa idan lokaci baiyi ba shi zai raya abinsa.... Ubandoma jiki na rawa dan shima ya razana sosai... Yasa hannu ya d’an mirgino da mutumin wanda babu komai jikinsa sai ‘yar bante irinta bayin zamanin da turawa Ke d’iban bayi a k’asashen bak’ak’en fata.... Cikin yankewar zuciya ya furta “JA’AFARU...!!” Sunan Ja’afar da ya ambata ya Sanaya Muhibbah dake bin syringe d’in kallo tana karantawa abinka da wacce Ta karanci wani fanni na kula da majinyata... Tuni ta daskare zuciyarta naci gaba da tsinkewa..... SameenaAleeyou 📚 [8/24, 10:02 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *52* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sunan Ja’afar dataji Ubandoma ya ambata ya sanyata mik’ewa jikinta na matuk’ar rawa ta nufo yanda yake a kwance tamkar marass numfashi... Tuni Ubandoma ya warware rawanin kansa ya suturta ma Jafar jikinsa... Muhibbah tai tsaye tana duban fuskar mutumin da Ubandoma ya ambata da Jafar, yau ahekaru goma sha hud’u da kwanaki kenan rabonta dashi... Tabbas ya canza koda kuwa bai cikin yanayin wahala da suka tsincesa ciki, girma ya k’ara canzasa saidai duba guda tai masa ta fahimci shine... Wasu irin hawaye suka gangaro mata, wannan masarauta cike yake da abubuwan mamaki... Tana nan tsaye tamkar statue ta sauraro muryan Ubandoma naci gaba da fad’in “Ja’afaru bawa ne a Masarautar nan wanda ya b’ace tsawon shekara guda yau... Ni nasan ba b’acewa yayi ba Dan a zatona Giwa ce ta gama dashi, ashe a wannan waje aka ajesa ba tareda sanin kowa... Lallai na yarda Giwa zata iya yin komai sabida Ta dawwama kan Karagar mulki... Mulkin duniya da batada tabbas wanda duk soyayyarka da ita dole ka barta..!” Muhibbah ta duk’a a hankali hawaye naci gaba da gangaro mata... Ta dubi Ubandoma tace “Anya yanada rai...?!” Ubandoma ya jinjina mata kai bayan ya tab’a wasu jijiyo a wuyansa “Yanada rai, zuciyarsa na bugawa... Bai mutu ba... Abinyi shine muyi gaggawan kub’utar dashi da kuma Izzatu daga cikin Masarautar nan kafin Giwa ta cimmamu Dan nasan duk yanda take yanzu hankalinta a tashe yake...!” Muhibbah tai saurin jinjina kai tana mai mik’ewa tsaye tace “Haka ne wannan gaskiya ne... Kuma kaima idan tasan ga abinda kayi bazata k’yaleka ba.. Toh amma yanzu meye abinyi..? Ina zamu kaisu..?!” Ubandoma yai shiru tamkar mai nazari sai kuma ya dubi Muhibbah yace “Akwai wani k’auye can gabas da Masarautar nan mai suna Galambi, k’auyen iyayen matata ne, yanzu haka na tura yarana can tun lokacin da Waziri da Yazeed suka soma min barazana da yarana kasancewar matata Ta rasu banida kowa sai yarana guda biyu... Shisa nake neman ‘yanci na bar bauta ya ko wace irin hanya domin na inganta rayuwar yarana guda biyu kada suma su taso cikin bauta.. Alk’awari na d’aukarwa mai d’akina shisa kikiga idanuna sun rufe bani gane daidai da abinda ba daidai ba burina na samu ‘yanci na cika mata burinta na fidda yaranmu daga k’angin bauta...!” Muhibbah ta jinjina kai tace “Na fahimceka Baba... Toh yanzu ya za’ai mu kaisu garin matar taka...?!” Ubandoma yace “Idan muka tafi gaba d’aya Ke za’a iya zarginki a Masarautar nan... Zaifi kyau ni na tafi dasu tinda nasan dole a nemeni kuma dole ayi tunanin ni ne na taimaka masu, sannan babu abunda zasu min barazana dashi a Masarautar nan tinda na tura yarana can da nisa yanda bazasu samesu ba... Ni zan tafi taredasu ayi masu duk wani jinya da ya kamata Dan iyayen matata sunada sani sosai akan abinda ya shafi cututtuka da kuma magani, Allah ya huwace masu wannan baiwar..!” Muhibbah ta jinjina kai tace “Alhamdulillahi! Amma wani hanzari ba gudu ba Baba... Shin ya za’ai mu fice da Jafar yanda yake a kwancen nan ba tareda an ganmu ba...?!” Ubandoma ya murmusa kad’an yace “Karki damu d’iyata wannan ai ba matsala bace, muda muka taso cikin bauta... Bari kiga yanda akeyi...!” Ga mamakin Muhibbah dik girman jiki da tsawo da Allah ya huwace wa Jafar sai gani tai Ubandoma ya ciccib’esa ya azasa bisa kafad’arsa... Ya dubi Muhibbah yace ta fito da Izzatu su bi bayansa... Jinjina masa kai kurum tai kana ta janyo hannun Izzatu suka bi bayan Ubandoma sauri sauri gudun kada suyi artabo da wani... Ga mamakin Muhibbah wani hanya taga sun nufa can yamma da Masarautar, itadai sai waige waige tsoron kada a gansu... Ubandoma ya d’an dubeta yace “Ki kwantar da hankalinki babu wanda zai ganmu, wannan k’ofa da kike gani ba kowa ya san da ita cikin Masarautar nan ba... K’oface da dakarunmu suke kwanton b’auna ga abokan gaba musamman a lokutan da suke kokonton samun nasara... Tsohuwar k’oface mai tsohon tarihi wanda a mutanen wannan zamani dake rayuwa cikin Masarautar ba kowa yasan da ita ba...!” Muhibbah ta jinjina kai suna ci gaba da tafiya tace “Baba da alama kanada ilimi sosai gameda wannan masarauta, kasan abubuwa da yawa k’unshe cikinta...” Ubandoma ya jinjina kai yace “Shiyasa Giwa Ta janyo ni jiki take amfani dani... Kinsan ance da d’an gari akanci gari... Mahaifina shine Hadimi mafi kusanci ga mahaifin Sarki AbdulJabbar Wato Sarki Mahmuda, Mahaifina yasan tarihin Masarautar nan sosai wanda shima wasu daga nasa Mahaifin ya gada ya sani, nima nawa mahaifin ya sanar dani wasu abubuwa gameda Masarautar har kawo lokacinda aka had’a baki dasu tsautsayi ya auka masa yaci amanar masarauta aka kawosu wannan fursunan da kikaga na San da ita... Giwa Tasan inada masaniya sosai gameda Masarautar nan shiyasa batai wasa da tarayyarmu ba... Babu wanda ya kaini sanin cikin Masarautar nan wannan dalili yasa idan Mahaukaciya Izzatu ta b’ace cikin Masarauta ta shiga wani sak’on babu mai iya zak’ulota sai ni...!” Ubandoma yaci gaba da fad’in “Kar na shiga miki wani labari daban kinji dalilin...!” Muhibbah ta kuma jinjina kai a daidai sanda suka shige wata k’ofa wanda itama ba lallai ka fahimci k’ofa bace idan ba kanada masaniya ba.... Haka sukaita ture gidan gizo gizo suna kutsawa alamun an jima ba’a non wannan hanyar.... Tafiya mai d’an tsawo sukai kana suka fita daga cikin Masarautar... Ubandoma yace “Alhamdulillah mun fita daga cikin Masarauta... Shin zaki iya gane hanyar komawa..?!” Muhibbah tai shiru tamkar mai nazari sai kuma tace “Idan ban gane ba sai na bi ta Sabon titi na shiga ta babban k’ofa wanda kowa ya San da ita...!” Ya jinjina kai yace “Hakan yayi dan kar wani ma ya zargeki, nasan watak’ila Giwa ta soma nemanmu cikin Masarautar....!” “Toh yanzu Baba wa zai kaiku tashar mota...?!” Ta tambaya tana dubansa... Ubandoma yai shiru yana dubanta cikeda kulawa, wasu abubuwa suna zuwa kwanyarsa... “Amma yarinya kafin mu d’auki hanya ina son sanin wacece Ke...?!” Tambayar da yai mata kenan yana mai tsareta da idanu... Ta d’ago idanunta masu cikeda rauni wannan karon jin irin tambayar da yai mata... Kafin ta kaikaga basa amsa ya d’ago ‘yar yatsarsa guda yana nunata... Lokaci guda yake furta “Tabbas kece... Kece SAUDATU... Yarinyar da matsafan Giwa suka bata tabbacin cewa K’addarar wannan masarauta na tafe da tata k’addarar... Tabbas kece yarinyar da Gimbiya Turai take nema... Kece silan aje Mahaukaciya Izzatu da Turai tayi... Bansan labarinki ba yarinya amma Rayuwarki na cikin had’ari Babba a wannan masarauta, mai ya dawo dake yarinya..?!” Muhibbah ta share hawayen da suka gangaro mata kana tace “Kaman yanda kace Baba, da izinin Allah ni ce nan zan kawo k’arshen mulkin zalunci da Turai ta d’aura Masarautar nan bisa wannan kad’ai ya isa dalilin da zaisa na dawo... Karka damu Baba, Allah bazai bata nasara ba wannan karon... In sha Allahu bazata kuma cutar da wani wanda baiji ba bai gani ba...!” Ubandoma ya jinjina kai yace “Tinda kikace Allah kin gama magana... Wanda duk yakeda Allah shi yake da babban makami da kariya a tattare da shi... Allah Ubangiji ya tsareki ya kareki ya kuma dafa miki...!” Ta amsa da “Ameen Baba, kuma kuyi sauri ku d’auki hanya kafin wani abin ya faru...!” Ta maidoda dubantaga Izzatu wacce ta kasa janye idanunta daga barin dubanta, ta tako har gabanta a hankali kana Ta kamo hannayenta ta rik’e cikin nata, saida ta sakar mata murmushi mai kyau kana tace “Kin tsira da izinin Allah... Babu wanda zai kuma azabtar dake...Ku tafi cikin aminci da kariyar Ubangiji..!” Mahaukaciyar ta sakar mata murmushi itama kana tasa hannu ta shafi Fuskar Muhibbah, tai wani magana da bazaka iya fahimta ba sabida rashin wadataccen harshe cikin bakinta.... Ubandoma ya dubi Izzatu yai mata alama da hannu kan cewa su tafi kada a cimmasu.... Ta kuma duban Muhibbah kana ta k’araso ta rungumeta sosai cikin jikinta... Hawaye suka gangaro wa Muhibbah da k’yar suka raba jikinsu itada Izzatu ko damunta daud’an jikin matar baiyi ba... Bata bar wajensa saida ta tabbata sunyi nesa da Masarautar kana Ta juyo tana k’arewa Masarautar kallo daga nan yanda take tsaye.... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tasa kai ta soma tafiya ta bayan Fada dan bazata iya komawa Ta hanyar da Ubandoma yabi dasu ba... Ta k’ofar bayi ta b’ulla hakan yasa kawai tabi wannan k’ofar ta shige cikin Masarautar Allah yasa dama tun shigowarta Kuyanga guda ta amshi jakan kayanta ta kai mata masauk’i... Kai tsaye sashen Giwa ta nufa b’angaren su Umaima da Zahra... Nan ta tadda Zahra na sharb’an kuka Umaima na bata baki..Tsaye tayi tana sauraren abinda Zharan Ke fad’i “Wllhi Anty Umaima na tsane matar nan na tsaneta Ta ya Paa zaice zai aureta... Of all mata ya rasa wacce zai d’auko sai wannan matar... Wllhi ban sonta kuma bazan tab’a sonta ba....!” Umaima ta dafata tace “Zahra Raheema batada matsala kece dai baki sonta, Aminiyar Aunty Zuhra ce fah kuma kiga yanda kowa yake yabon kirkin Aunty Zuhra cikin Masarauta nan... Ki kwantar da hankalinki kiyi addu’an Allah yasa haka shine mana alkhairi gaba d’aya..!” Galala Zahra Ke dubanta kana ta kuma goge hawayenta tace “Ni nasan yanzu Paa bai sona bai damu da abinda nake so da wanda bana so ba, yanayin haka ne kawai dan ya k’untata min sabida ya daina sona, He’s changed now, and he’s becoming more violent har marina yayi abinda bai tab’ayi ba a baya, he really is hiding something from me...But if not for that maiyasa zaice zai auri matar nan all of the sudden..!” Umaima ta nusa tace “Zahra neman izinin auren suka tafi ba auren ba, watak’ila ya sauya ra’ayi idan har baki sonsa da ita...!” Ji tai bakinta ya bud’e tana furta “Rankaidad’e ne ya tafi neman izinin aure..?!” A tare suka juyo suna dubanta, Zahra ta tafi da gudu ta rungumeta “Tiaaa..! I’m glad you’re finally back, you’ve no idea how badly I need you right now... You’re the only one who understands me after all..!” Tai maganan tana mai tab’e baki har lokacin bata saki Muhibbah ba... Muhibbah ta k’ak’aro murmushi tace “I’m here now... Tell me meke faruwa... Naji kuna maganan saka Rana....!” Tai maganar cikin yanayi na yak’e... Zhara baki ture tace “Can you believe my Pa, ya tafi neman auren wannan witch d’in... Wai aurenta zai very soon..!” Umaima ta katseta da fad’in “Ba da wannan zamu fara ba, da gaisuwa ya kamata mu fara kafin komai ya biyo baya...” Ta dubi Muhibbah tace”Sorry Zahra ta tareki da zance babu ko gaisuwa balle sannu da zuwa..” Murmushin da yafi kama yak’e ta kumayi kana tace “No is alright, after all ni na tambaya...Ya kuke...? How are things here...?!” Tai maganar tana mai janyo hannun Zahra suka zauna saman couch... Zahra tace “Um ba wani abu mai dad’i da ya auku a nan tinda kika tafi... Koda yake akwai abu mai dad’i guda d’aya... An sallami Uncle Jamal daga asibiti... And guess what..!” Ta k’arashe tana duban Umaima cikeda zolaya taci gaba da fad’in “Anty Umaima said yes to him... They’re getting married anytime soon... At least auren da mukeso ba irin na Paa da wancan witch d’in ba..!” Ta k’arashe tana kashewa Umaima idanu, itakaw Umaimar sai k’ok’arin toshe bakin Zhara take su duka biyun suna dariya... Gaban Muhibbah ya kuma yankewa dan tasan sam Umaima bata dace da Jamal ba, ita d’in mutumiyar kirkice shi kuwa akasin haka, kaman yanda Mahmood bai dace da Raheema ba, shid’in mutumin kirki ne itakaw akasin haka.... Zahra taci gaba da zolayan Umaima, Umaimar na kuma janyota tana toshe bakinta tana fad’in zata had’ata da Uncle d’inta... Sai dariya suke cikeda nishadi yayinda Muhibbah tai nisa duniyar tunani... Ta yaya zata hana yuwar wad’annan auratayya...? Kaman daga sama ta sinkayo Umaima na fad’in “Hibbah sorry bamu tambayi jikin Mommy ba, kuma tinda kika tafi baki had’amu a waya ba, shi Dr kam ma ban samun layinsa...” Jiki a sanyaye Muhibbah ta murmusa tace “Jikinta da sauk’i sosai shisa na dawo....!” Sukai mata addu’a gaba d’aya Muhibbar tana amsawa da Ameen cikin tsananin sanyin jiki... Gajeren hira sukai Muhibbah tace zata masauk’i ta d’an huta gajjiya... Zahra tace zata shigo anjima kafin la’asar... Da kai kurum ta amsa mata amma ta kasa aminta da abinda taji...Wai Rankaidad’e zai auri wannan Trap d’in wacce Ta gama watsewarta da wancan watsattsen k’anin nasa... Inaa no she can’t allow him to fall into her trap, but ta ya zatayi haka... Ta yaya zata bud’e idon Rankaidad’e ya gane wanan matar ba k’aunarsa take ba..? In fact su biyu d’’in duniyarsu Ta banbanta....! Amsar data kasa nemowa... Alolan sallan la’asar tai kana Ta d’an kishingid’a saman gado idanunta na kallon sama, sai faman sak’e sak’e take cikin zuciyarta... Allah ya gani ta k’agu taga ya dawo Masarautar yace ya fasa auran Raheemah ko hankalinta zai kwanta... Tana nan a haka bacci yayi gaba da ita.... ** Wane irin k’aik’ayi ne na bala’i ya addabeta lokaci guda, ga b’arin kanta yanda sumar suka k’one sunayi ga kuma hannunta k’onanne da shima ya addabeta da k’aik’ayin.... K’aik’ayi ne mai fidda hayak’i wanda ba kowa Ke iya ganin hayak’in ba face ita da abin Ke jikinta.... Tun tana Susa a cikin kallabi hardai Ta cire kallabin tayi wurgi dashi.... A baya susa ba girmanta bane a matsayinta na mai jida mulki da izza sai gashi yanzu Susa na nema ya zama babban d’abi’arta.... Ko dan sabida yawan k’aik’ayi dake addabanta bata fita fadarta cikin mutane.... Yau d’inma a d’aki suke itada Jakadiya taketa faman soshe soshen, k’arshe ta umarci Jakadiya ta sosa mata kanta ita taji da hannunta.... Abin yayiwa Jakadiya banbarak’wai Giwa da susa babuji babu gani.... Jakadiya tace “Allah shi taimakeki Susa ba girmanki bane.... Anya wannan k’aik’ayi naki ba ture bane... Kodai asibiti za’a tafi....!” Giwa ta katseta da fad’in “Ni Turai nafi k’arfin wani yayo min ture.... Nasha gaban kowa a tsafi, ni nakeda Tal’udu mai Fitilar tsafi...Ni nake turawa badai a turomun ba, kaman yanda na sace Sarautar Izzatu, da rayuwarta data cancanta na kuma guntule harshenta yanda bazatayi magana ba balle wani ya d’auki muryarta sannan na manna mata ciwon hauka daga k’arshe....Na kuma rabata da yaranta da duk wani dangi nata.... Kinga dai yanda nayi da Yarima Alfah da yaransa guda biyu da matansa guda biyu da ya taso har k’asar nan ya biyo sawun ‘yaruwarsa a lokacinda labari ya cimmasa cewa na maida Gimbiya Izzatu baiwa na maye Gurbinta da kaina...!” Jakadiya Ta had’iyi miyau da k’yar tana jinjina ta’addanci irin na Giwa... A iyaka zatonta Izzatu Hadimarta ce aminattciya dataci amanarta ta aure Sarki AbdulJabbar bayan Giwa ta mallaka masa ita a matsayin tukuici ashe abin ba haka bane... Ashe Giwa Itace Hadimar Izzatu wacce Ta aminta da ita taci amanarta ta sace sunanta da rayuwarta harma da mijinta... Jiki na matuk’ar rawa Jakadiya ta soma jada baya tana duban Giwa cikeda tsoro... “Rankidad’e Ki gafarceni amma ta yaya akayi haka....?!” Giwa ta murmusa tace “Kar kiji tsoro Jakadiya nidake mun zama d’aya... Kinsan sirrikana da yawa... Yau zan sanar dake Sirrin da dagani sai Tal’udu saiko Marigayi Wambai ne muka sani... Sirrin da Wambai ya rufeta cikin K’undi...!” Jakadiya dake rakub’e gefe har lokacin jikinta bai daina rawa ba take duban Giwa.... _WAIWAYE_ Gimbiya Turai d’iyace ga Sarki Jamaludeen na k’asar Benin, su biyu rak Allah ya baiwa Sarki Jamal... Daga ita sai k’aramin k’aninta mai suna Alfah... Sarki Jamal ya d’auki soyayyar duniya ya d’aura akan yaransa guda biyu Gimbiya Turai da kuma Yarima Alfah... Mahaifiyarsu ta rasu a lokacinda ta haifi Yarima Alfah, daga nan Sarki bai kuma haihuwa ba... Hakan sosai yayi dad’i ga Al’umman masarauta dake harin kujeran Sarki Jamal....Gimbiya Turai tanada wata Hadimarta wacce suke kusan s’anni saidai idan ma Hadimar tata zata d’ara mata bai wuce ta d’arata da Shekara d’aya zuwa biyu ba... Gimbiya Turai Allah yayita mace mai sauk’in kai da son Al’ummarta hakan yasa itada Hadimar tata mai suna Izzatu suka zamto aminai daga amintaka suka koma tamkar ‘yanuwa wanda suka fito ciki guda... Gimbiya Turai bata b’oyema Izzatu komai nata... A lokacinda d’an Sarki Mahmood Wato Sarki AbdulJabbar yaji labarin Gimbiya Turai na k’asar Benin... Al’adar k’asar ce a wancan lokacin Gimbiya bazata fita zance wajen manemin aurenta ba sabida mulki saidai Hadimarta ta fita suyi hira da mijin ita Hadimar sai ta kawo sak’on duk abinda aka fad’i a hiran ta gayawa Gimbiya... Kuma Hadimar idan ta fita itama bazata bud’e fuskarta ba har a gama hiran... A tak’aice miji bazai San fuskar matarsa ba sai randa aka kai masa ita gidansa...!” Giwa Ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Tun daga wannan lokacin da nayi shiga irinta masu mulki na rufa kaina na fita wajen Sarki AbdulJabbar a matsayin wacce ta fito ganawa da mijin da zata aura sai na d’and’ani zak’in mulki naji duniyar nan babu abinda ya kaita dad’i ashe... Ina can ina bauta... Uwa uba da na k’yallara idanu kan kyakkyawan Sarkin maiji da k’uruciya da Mulki naji duniyar nan bazan iya rayuwa ba taredashi ba... A lokacin mahaifin AbdulJabbar ya rasu za’a nad’asa sarauta akace sai yayi aure ai masa nad’i gaba d’aya... Hakan yasa yayi tattaki har Benin dan lokacin Sarki Jamal yayi sanarwa k’asashe daban daban cewa d’iyarsa zata zab’i miji, aka saka wa masu Mulki rana kowa yazo ya nuna bajintarsa... Toh koda yaran sarakuna da masu mulki suka Zo wannan gasa na zab’en gwani da Gimbiya Turai zatai Sarki AbdulJabbar bai sami halarta ba baida lafiya... D’anuwansa Wambai shi ya halarta a matsayin wakilin k’aninsa... Anyi gasar gwani Wambai yaci gasa yace ma Sarkin k’asarsu yaci wannan gasa kuma d’an uwansa... Wambai shi kad’ai yasan fuskar Gimbiya Turai ya dawo gida da labari mai dad’iga d’anuwansa Sarki AbdulJabbar... “ “Koda aka d’aura auren Sarki AbdulJabbar da Gimbiya Turai bata buk’aci a kawota wannan Masarautar da tarin Hadimai ba, a cewarta ni kad’ai na isheta.... Al’ada ce a wancan lokacin Matar Sarki bazata iso masarauta ba sai ta yada zango a wata k’aramar gari kafin Ta iso masarauta.. Hakan Ta faru damu... Nida Uwargijiyata Gimbiya Turai matar AbdulJabbar, Wambai wanda shine tsaye akan komai na auren d’an uwan nasa tin a lokacin na hango hassada da k’yashin d’aukaka da Allah ya baiwa d’an uwan nasa sama dashi, nayi amfani da wannan damar na rinjaye Wambai tinda shi yaje gasa shikadai yasan fuskar Gimbiya Turai Sarki AbdulJabbar bai sani ba... Muka had’e kai dashi cewa ni ce zan zamto matar AbdulJabbar da sharad’in zan taimaka masa mu kawar da AbdulJabbar ya d’ale Karagan mulkin mahaifinsu wanda shi ya kamata ya gada amma aka baiwa AbdulJabbar, naita gurb’ata masa zuciyarsa da tunani marassa kyau har na samu nasaran shawo kansa....A wannan garin na fantsama wata daji neman maganin da zan rufe bakin Gimbiya Turai, a nan na had’u da Tal’udu ya sanar dani banida matsala... Tal’udu ya zamto gatana, ya tura bak’in Aljani ya kashe Sarki Jamal na k’asar Benin Wato mahaifin Gimbiya Turai... Daga nan Gimbiya ta zamto batada kowa sai k’aramin k’aninta Alfah wanda shi a lokacin k’aramin yaro ne baida ko masaniyar Sarkin wata k’asa ce ya auri ‘yaruwarsa sabida k’ank’ancin shekaru nasa, yadai an gasa akai wani Sarki ta k’asashen gabas yaci gasar amma bai San wace k’asa bace....Tuni masu wawoson mulki sukai ma k’aragar mulkin caaa, aka mance da Alfah da ‘yaruwarsa Turai... Saidai tin kafin na tareda Sarki AbdulJabbar Gimbiya Turai ta riga ta basa ni a matsayin kyauta, Wanda dama al’ada ne kyauta tsakanin sabbin ma’aurata, ka d’aga abu mai daraja ka baiwa partner d’inka... Toh ita sai ta basa baiwarta Izzatu a matsayin tukwici, labari ya isa masa daga wajen Wambai... Randa za’a kawoni masarauta ranan muka gana dashi dan tuni Tal’udu ya rufe bakin Gimbiya Turai duk abinda na bata umarni shi takeyi, haka nan mace da ita daga wancan lokacin itace Izzatu Hadimata ni kuma nice Uwargijiyarta Gimbiya Turai... Sadai ta sami kanta da amsa min da min biyayya dan bazata iya ce min a’a ba... Kallon farko ashe Sarki ya auka wa soyayyar Baiwa Izzatu....Sarki AbdulJabbar yabada umarnin a k’arasa dani Masarauta ita kuma Baiwar a bar masa ita a nan wannan garin zasu k’araso tare... Haushi da takaici ya cikani ta yaya gani nan sabuwar amaryarsa ya zab’i ya taho tareda Kuyanga... Na dad’a k’ullatan Turai wacce itace Izzatu a halin yanzu, na tsaneta da duka zuciyata dukda na sace identity nata da komai amma da alama Sarki yana son k’ulla alak’a da ita... Naji takaicin basa kyautar baiwa da tayi... Ashe bayan tafiyar mu Fada Sarki ya umarci Wambai a d’aura masu aure shida Baiwa Izzatu ya kuma riga tarewa da ita yayinda ni kuma muka taho Fada na ije Tal’udu nan cikin Masarauta tareda taimakon Waziri wanda tuni mun k’ulla alak’a dashi ba tareda sanin Mai Martaba ba musamman da mai Martaban ya sanar dani cewa ya tare da Baiwa Izzatu kuma ya aureta Ta zama matarsa kaman ni.. Nace atafau Baiwa bazata tab’a zamtowa kaman ni ba, dan haka dole ya barta a wancan garin Ta zauna a can idan yana neman zaman lafiya... Ban hanasa ya auro ko wata mace ya kawota cikin Fada ba amma banda baiwata Izzatu, nafi k’arfin nayi kishi da ita... Sarki ya amince da sharad’ina musamman da ya lura da irin halarcin da nai masa na basa kyautar Baiwa wacce ya aukawa soyayyarta har takaisu ga aure...!” K’aik’ayi ya hana Giwa ci gaba da magana... Zumbur ta mik’e taceda Jakadiya su tafi wajen Tal’udu... Jakadiya ta zaro idanu waje tace “Allah shi taimakeki yau kuma wajen Tal’udu rana tsage tsage....?!” Tsawa Giwa ta dirara mata tana ci gaba da susa... Babu shiri Jakadiya Ta mik’e zumbur tana furta “Tuba nake Allah shi taimakeki..!!!” SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *53* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Dariya Tal’udu yake amma wani irin hayak’i ne Ke fitowa daga cikin bakin nasa... Yai alamawa Giwa data masto kusa sosai.... Babu shiri Giwa ta matsa kusansa tana lek’a cikin k’aton tulun tsafi da yake aza mata akanta duk randa za’ai mata wani aiki... Sannan duk randa tulun yaci wuta tabbas babu nasara a aikin da za’ayi.... Giwa ta shiga girgiza kai tana furta “Tal’udu kayi wani abin amma babu ta yanda za’ayi na yarda a kuma azamin wannan tukunyar azabar.. Kaga dik yanda sassan jikina Ke k’onewa, ga azaban k’ai....!” Batakai aya ba ya katseta da fad’in “Ke Izzatu ba’a mana gardama a nan..!!!” A zabure ta d’ago tana dubansa jin ya kirata da sunanta na yanka... Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Maiyasa yau ka kirani da sunana na yanka...? Tsawon shekarun da mukai tare baka tab’a yin hakan ba..?!” Ta k’arashe tashin hankali bayyane saman fuskarta... Wata dariyar mai wani irin sauti maras dad’in sauraro ya kumayi kana ya d’auko wata fitila mai launin ja ya haska cikin tulun dashi yace “Lek’a nan..!” Babu musu Giwa ta lek’a cikin tulun da tuni jan fitilar ya haske ciki da wane irin jan haske maras kyaun gani... Ga mamakinta Gimbiya Turai na k’asar Benin ta gani cikin shiga irinta mulki da sarauta babu yanayin hauka a tattereda ita... Gefe da ita zaratan mazaje ne guda biyu duk sunyi shiga irinta masu mulki saidai bata tantance fuskokin mazajen ba sabida hasken fitilar dake kawowa yana d’aukewa kaman walk’iya.... Zuciyar Giwa yaci gaba da bugawa, jikinta ya d’auki karkarwa... Ta d’ago a zabure tana duban Tal’udu dake rik’eda fitilar... Baki na rawa Giwa Ke furta “Mai nake gani haka badai Izzatu ta sami lafiya ba..? Kuma a ina take...?!!” Ya kuma darawa a karo na biyu yace “Ai saida naja miki kunne, saida na miki kashedi kan cewar kar Ki bari Ta kufce miki...!” A fusace Giwa Ta katsesa da fad’in “Wannan kuma laifinka ne tinda aikinka kenan ka cika min duk wasu burika na wannan dalilin yasa na d’auko ka na aje cikin Masarautar nan... Idan dukuwa bazaka cika min burikana ba zamanka cikin Masarautar nan baida amfani... Tsohon kawai..!!” K’uri yayi mata da kannararren idanunsa kana ya murmusa yace “Bakida hurumin fitar damu daga cikin wannan gini da muka riga muka gina alk’aryarmu cikinta... Kuma tinda kikace haka daga yau na barki da iyawarki har sai ranan da kika shiga taitayinki da kyau... Abubuwa suka kuma kwab’e maki... A lokacin Ke da kanki zaki nemi hanyar alk’aryarmu Ki rasa..!” Ya k’arashe yana mai buga mata sandar tsafin akanta... Giwa ta saki wani irin k’aran azaba had’ida rik’e kanta lokaci guda tana mai rintse idanunta sakamakon ji da tai tamkar wuta aka watsa mata cikin illahirin jikinta sabida tsananin azaba... Bud’e idon da zatai ta ganta a gefen Jakadiya Tal’udu ya cillosu waje... Jakadiya ta k’arasa da sauri tana taimakawa Sarauniyar tata, ta d’agota sosai tana tambayarta “Rankidad’e ya akai...?! Mai ya faru...?!!” Cikin tsananin tashin hankali Giwa Ke furta “Jakadiya.. Jakadiya Ina cikin tsaka mai wuya, Tal’udu yana neman ya juya min baya...!” Jakadiya ta nusa tace “Nifa inaga k’arfin tsafinsa ne ya soma k’arewa Rankidad’e.. Kinsan fah duk abinda yakeda rai dole yana tsufa, ilimin tsafin Tal’udu ne ya soma gushewa sabida tsufa... Rankidad’e Allah ne kad’ai mai dawamammen iko kan komai da kuma kowa, shi kad’ai ne rayayye wanda buwayarsa baya gushewa... Anya Rankidad’e lokaci baiyi ba da zamu tuba, mu nemi yafiyar wad’anda muka zalunta..!!!” Batakai aya ba Giwa Ta katseta da fad’in “Har abada Giwa bata fad’uwa k’asa...Ke Jakadiya kin tab’a jin ance miki Giwa ta fad’i k’asa idan ba mutuwa tayi ba..!! Toh Babu gudu babu jada baya.. Babu abinda zan fasa... Da sannu zuciyar Tal’udu zata huce... Shige muje...!!” Jakadiya da tin labarin Izzatu da taji jikinta yai matuk’ar yin sanyi a hankali ta soma takawa tabi bayan Giwa tamkar Kazan da ruwa ya shanye... Harga Allah a firgice take da Al’amarin Giwa.. Giwa ta shige duk tinaninta a baya... Suna tafe ne suka hango Jamal na dogarawa da sandar crutches d’insa, sai ‘yan waige waige alamun baiso ai noticing d’insa.... Giwa ta dakata kad’an had’ida dakatar da Jakadiya ma... Suka mak’ale gefe suna duban Jamal da hanyar da yabi... Giwa taceda Jakadiya su bi bayansa... Sannu a hankali suka dinga bin bayan Jamal har suka shigo wani sunk’urumin waje da su kansu basusan da wajen ba cikin Masarautar... Yana shigewa cikin d’akin suka take masa baya... Hankali tashe Jamal ya k’arasa jikin k’arfen da ya d’aure Jafar da sark’ok’i, babu Jafar babu alamunsa sai sark’ok’insa zube wajen... Hankali tashe Jamal ya duk’a yana d’aga sark’ok’in dan tabbatarwa idanunsa... Tabbas babu Jafar babu alamunsa saiko magensa da yake zuwa taredasu guda biyu a wajen suna kalatan sauran abincin da ya rub’e a wajen... Jamal ya shiga girgiza kai yana mai furta “No no this isn’t happening..!” Juyowar da zai sukai ido hud’u da mahaifiyarsa, ga Jakadiya tsaye bayanta kanta a k’asa....Ya mik’e zumbur yana dubanta... “Maami mai kikeyi a nan... Ta yaya har kika iya biyoni...?!” “Ba wannan zaka tambayeni ba Jamal... Bayani zakamin meke faruwa a nan... Wanene ka ije cikin wannan waje...? Don’t tell me Izzatu ka aje tsawon lokacin nan da muke nemanta...?!” Jamal dake asibiti a ‘yan kwanaki baimada masaniyar b’acewar Mahaukaciya Izzatu ya d’an tab’e fuska yace “Maami I don’t know what you’re talking about...!” Giwa dake sakin huci Ta matso kusansa sosai ta kama kafad’unsa da k’arfin gaske tana furta “Jamal tell me the truth, idan ba Izzatu ka aje cikin wajen nan ba waye ka aje... Kamin magana talk to me...!!” Ta k’arashe tana mai jijjigasa... Shaye da mamaki yake dubanta yanda tai masa wane irin damk’a tana jijjigasa da iyaka k’arfinta tashin hankali maras misaltuwa bayyane saman fuskarta...Fincika yai yana furta “Enough Maami, let me go... I don’t know what you’re talking about... For crying out loud I just got out of the hospital ta yaya zansan abinda kike fad’i...!!” Cikin kid’ima da d’imauta Giwa Ke fad’in “Toh idan ba Izzatu ba waje ka aje cikin wajen nan..? Waye ka aje a wajen nan Jamal.. Ka bud’e bakinka kamin maganaa..!!!” Ta k’arashe cikin wane irin tsawa tana mai kuma jijjigasa... Da k’arfin gaske ya fincike jikinsa yana mai sakin huci yake furta “It’s Jafar..!!! I kept Ja’afar here... And and I’m afraid he’s escaped...!!!” Jiki a matuk’ar sanyaye Giwa ta sakesa tana dubansa da tsananin mamaki... Wai Jafar ya aje cikin wajen nan tsawon shekara guda harma da watanni da yayi bai cikin Masarautar ashe Yana nan Jamal d’anta ya b’oyesa... Cikin rawar muryar Giwa Ke furta “Jafaru fah... Jafaru fah kace Jamal..? Shin ba ka sanar dani ka kashesa ba..? Mai kuma kake sanar dani yanzu..?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... “I couldn’t kill him... As much as I wanted to kill him, I just couldn’t, bansan dalili ba but na kasa kashesa... Na ajesa a wajen nan tsawon shekara guda ina azabtar dashi Ta hanyar injecting d’insa da kuma drugging nasa da miyagun k’wayoyi...!” Giwa dake tsaye tana duban d’an nata tamkar wacce ruwa ya shanye Ta nanata abinda ya fad’i kana ta d’aurada “Kan mai zaka ajesa a nan idan ba gamawa dashi zakai ba..?!” A hasale yace da ita “Na tsanesa, na tsane wannan k’ask’antaccen Bawan... Especially idan na gansa tareda Umaima... Maami duk abinda nai masa it’s because of her... Zan Iya yin komai akanta... That’s how much I love her..!!” Ya k’arashe yana sakin huci... Cikeda tsoro Giwa take dubansa, lallai ta yarda shid’in d’anta ne, zai komai kan abinda yake so kaman yanda zatai komai kan abinda take so... Jamal bai rage mata komai ba hardai zai iya aje mutum yana azabtar dashi tsawon shekara guda, can k’asan zuciyarta kuma sai taji dad’i da ya d’auko wannan hali nata ko Babu komai zai iya tsayuwa yaga ya sami abinda yake so koda bata raye ne... Saidai a halin yanzu tashin hankali ne take fuskanta tinda da alama Jafar ya gudu.... Bata ankara ba sai sinkayo muryar Jamal tai yana fad’in “Someone helped him escaped Maami, kinga hujin da akaima garun nan....!!” Daga Giwa har Jakadiya suka k’arasa suna kallon ramin da aka huda... Jamal ya murmusa kad’an yace “Tabbas a d’akin dake gefe da wannan aka b’oye Mahaukaciyar da kike fad’i Maami... Kuma sun taimaka ma junane itada Jafar suka gudu...!” Giwa da kanta gaba d’aya ya kwance, girgiza kai ta soma tana furta “Izzatu babu hankali jikinta bazata iya taimakama wani har su gudu ba..!” Jamal yai shiru tamkar mai nazari sai kuma yace “Jafar must be very weak, sabida azaban da yasha a nan... Bazai iya taimakama wani ba shima... Toh Who helped them escape...?!” Baikai aya ba Giwa Ta basa amsa da fad’in “Wanda ya rufe Izzatu a wancan d’akin shi ya taimaka masu suka gudu..!” Jamal yace “Waye shi Maami... Ki fad’a min sunansa yanzu na gama dashi..!” Giwa tace “Wanda yafi kowa sanin lungu da sak’o dake cikin Masarautar nan.. UBANDOMA..!!” Lokaci guda Ta ambato sunan Jakadiya... Jakadiya da tinda suka soma magana hankalinta bai jikinta sakamakon ji da tai Jafaru da Izzatu sun kub’uta tasan ko shakka babu k’arshensu yazo kenan... Dan idan asiri ya bayyana tayi imani itakam tsire wuyarta tsaf da ayi a matsayinta na baiwa da taci amanan Iyayen Gidanta... Jin bata amasata ba ya sanyata kuma doka mata kira... A firgice Jakadiya ta amsa da “Allah shi taimakeki..!!” Ta zube a wajen zuciyarta naci gaba da tsinkewa.... Giwa tace “Maza kije kizo min da Ubandoma yanda duk ya shiga ya fita... Ki sanar da Sarkin Dogarai yau kada ya shigo cikin Fada face yana tareda Ubandoma... Idan ba’a samesa ba azo da ‘ya’yansa... Kinji abinda na fad’i..!!?” Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar, kanta a k’asa take furta “An gama ya Shugabata...! Allah ya huce zuciyar Giwar Amale...!!” Daga nan mik’ewa tai cikin sauri tabi ta hanyar da suka shigo.... Giwa da Jamal suka jera suma suka fito su duka biyun, kowa da abunda yake sak’awa cikin zuciyarsa.... Suna isowa sashen Giwa Jamal ya dubeta yace “Maami idan an kamo Ubandoma I’ll be the one to punish him... Zai d’and’ani kud’arsa...!” Giwa ta fuzar da fuci tana dunk’ule hannu take zaga cikin d’aki lokaci guda tace “Ni kaina bansan irin horon da zan masa..!” Jamal ya murmusa yace “Ki barni dashi, ni ne Gwarzonki Maami kuma na tanadi muggan horo da zanyima wannan k’ask’antaccen Bawan....!!” Giwa ta jinjina kai tace “Nasan bazaka bani kunya ba Gwarzona... Zan baka Ubandoma kayi duk abinda kaso dashi, idan kaga dama kada ka ragar masa ruhi...!!” Jamal yai wata murmushi da gefen bakinsa yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa cewa muddin ya damk’o Ubandoma zaiji jiki, zai masa horo fiyeda wanda yayima Ja’afar, tabbas ba’a shiga gonarsa a wanye lafiya... Dik manyan syringe na zira ma dabbobi da yaita huda jikin Jafar dashi mai sauk’i ne akan irin horon da ya tanadarwa Ubandoma muddin yayi ganganci shiga hannunsa.... ** Firgita ta farka daga baccin nata salati saman harshenta, Wai ashe daga kishingid’a har bacci b’arawo yayi gaba da ita... Baccin da zata iya cewa sam bataji dad’insa ba domin kuwa haka taita mafarkai sarara marassa dad’i ciki harda na auren Yarima Mahmood da Gimbiya Raheemah... Wai anyi aurensu sun taho masarauta tare... Gabanta ya kuma tsinkewa tana add’uan Allah ya hana wannan mafarki nata yuwa... Wayarta ta lalub’a taga time yaja sosai dan da alama magrib ma yana shirin karatowa... Sauri sauri ta mik’e ta kuma d’auro alwawa tazo ta tada Sallan la’asar wanda daga yin alwala tana jira a kira sallan baccin ya saceta... Bayan ta gabatarda Sallan La’asar d’in ne ta koma gefe tai lamo tana tinanin mafarkin da tai... Abu biyu ne a mafarkin nata... Na farko bayan auren Raheema da Mahmood yayi Raheema ta dab’awa Zahra makami ta kasheta, sai kuma auren Jamal da Umaima wanda Jamal da Giwa suka taru suka jefa Umaimar cikin wata irin kasko mai girman gaske suka busneta ciki.... Duk iyaka k’ok’arinta ganin ta taimaki Zahra da Umaima bata iya taimakon su ba cikin baccin.... Ta lumshe idanunta a hankali tana karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Wad’annan aurattaya dake shirin wakana cikin Masarautar da alama sam babu alkhairi a tattaredasu... Shin ta yaya zata iya hana yuwar wad’annan auratayya...? Amasar data kasa samowa... Saida Ta jira akayi sallan Magrib kafin Ta mik’e ta nufi b’angaren Giwa ko Allah zaisa ta sami wani chance da zata iya karkato ra’ayin Umaima gameda Jamal.... A parlor ta tadda Umaimar harma da Jamal d’in alamun zance suke... Takaici ya turnuk’e mata mak’oshi, tai k’ok’arin sa kai da zummar juyawa dan ji tai bazata iya shigewa ba kuma... Saidai tuni Umaimar ta ganta, taceda ita ta shigo mana ai Zahra na ciki... Badon taso ba Ta ida shigowa... Ta gaida Jamal babu yabo babu fallasa... Saidai ganin k’afarsa a guntule ba k’aramin mamaki ya bata ba... Ashe dai an guntule k’afar nasa..? Tai zancen cikin zuciyarta... Allah ya gani ko tausayi bai bata ba.. It is what he deserved after all.. Ta shige ta nufi wajen Zahra tana sinkayo muryarsa yana kuma kashe Umaima da salon k’aryarsa... A zuciyarta take Addu’an Allah ya fitar da Umaima daga sharrin wannan bawa nasa... ** Giwa ta kuma karkatowa tana duban Jakadiya data kawo mata labari maras dad’i... Babu Ubandoma babu ahalinsa... Gasu Waziri har yanzu basu samu dawowa daga tambayo auren Yarima Mahmood ba... Giwa ta tsare Jakadiya da idanu kana tace “Jakadiya dole a samo Ubandoma bazai yuwu Jafar ya kuma dawowa cikin Masarautar nan ba daga shi har Izzatu... A halin yanzu Bana buk’atar Izzatu koda kuwa itace zata sanar dani Duniyar da Saudatu take... Akan asirina ya tonu gwara na rasa Saudatu har abada... Zan iya sadaukar da komai akan na rasa mulki na...!” Jakadiya Ta jinjina kai tace “Allah ya kareki ya kare Karagarki, a yanda nasan Ubandoma bazai tsaya nan kusa ba.. Zai wuya a samesa... Rankidad’e Anya kuwa abubuwan nan lafiya suke faruwa yanda suke faruwa a yanzu... Karfah ki mance ga auren Yarima Jamal da yarinyar nan Umaima da ya kafe akai babu jada baya..!” Giwa ta murmusa cikeda izza da k’asaita tace “Har abada bazan tab’a barin hakan ya kasance ba... Sanin kanki ne mai auren Yarima Jamal yake nufi, inaji Ina gani bazan rasa d’ah na ba...!!” Jakadiya ta d’an gyara zama tace “Allah shi taimakeki ga wani shawari... Tinda dai yarinyar nan da k’udurin sadaukarwa na k’arshe kike aje da ita... Mai zai hana Ki amince Yarima Jamal ya aureta, tinda a k’a’idan Sarauniya Tamuna sau d’aya zai tara da mace ta zama tata... Duk matayen Sarauniya sai yayi mu’amala dasu sau d’aya kafin su zama nata... Toh mai zai hana ki amince da auren... Daren da suka tare muka tabbatar mu’amala na auratayya ya shiga tsakaninsu sai mu d’auke ita Umaimar mu damk’ata ma Tal’udu kinga hakan ka iya sanyaya ran Tal’udu da fushin da yake dake... Anyowa Sarauniya sabuwar Amarya...! Rankidad’e inaga wannan shawari ce kawai ta kamata tinda mun sani Yarima na matuk’ar k’aunar yarinyar nan bazai tab’a janye k’udirinsa na aurenta ba..!!” Giwa taiwa Jakadiya K’uri tana mai jin dad’in shawarin Jakadiya... Lokaci guda Ta saki murmushi tace “Madallah da wannan shawari naki Jakadiya... Dama Sadaukarwa ta Farko Jinin Sarki Jamaluddeen ne mahaifin Turai... Sannan na aje wannan yarinya Umaima ce jininta ya zamto Sadaukarwa na k’arshe.... Wannana shawari naki yayi Jakadiya, hakan za’ayi.... Zan amince ayi auren nan, sauran aiki naki ne Jakadiya... Dole kiyita zarya a sashen Yarima Jamal daren da aka kai masa Umaima... Idan har kika tabbata mu’amala ya shiga tsakaninsu mu kuma sai mu saceta akaitaga Tal’udu ya cika aiki ya baiwa Sarauniya Tamuna amaryarta Kinga jinin d’ah na ya kub’uta..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta... Jakadiya ta jinjina kai tace “Wannan haka ne Ya Shugabata... Allah ya k’ara miki lafiya.. Jaaa zamaninki... Ki jima kiyi kargo zuri’arki suyi Kargo..!!” Ta k’arashe tana d’aga mata babban yatsa alamun jinjina.... Suna a haka sukaji k’aran shigowar motoci cikin Masarautar alamun su Yarima Mahmood Sun dawo.... Muhibbah da Zahra dake zaune d’akin Zahran a tare suka mik’e suka nufi jikin window... Zahra tai saurin yaye masu labulen suna hangen sararin waje ga wutace sun haske ko ina cikin Masarautar.... Zuciyarta ne yai wani irin bugawa sakamakon hangosa da tai yana fitowa daga cikin mota hasken wutan lantarki ya haske kyakkyawar fuskarsa mai cikeda k’warjini sai kirari ake masa “Takwarka lafiya Hadari malfar duniya..! D’an na gada Kafi d’an na koya... Lafiya baya goya marayu..! Lafiya limamin sarakuna..! Lafiya Azurfa babu gauraye..! Lafiya linzamin sarakuna..!Laaafiya mai ado da tagulla..! Lafiya mai sulken yak’i.. Lafiya mai tambura goma sha biyu..! Lafiya Uban gabasawa..!! Lafiya zauna gari k’i tashi..! Lafiya Bango majinginan Al’umma..! Lafiya tada kufayi..! Lafiya cika sarari..!! Laaaafiya D’an mai kiran gabas Arewa ta amsa..!! Allah ya Jaaa zamaninka Uban Fadimatu Zahra’u...!!” Muhibbah tai masa K’uri tana kallon yanda ake masa kirari yana takawa gwanin ban sha’awa... Sosai sarautar ta amshesa, batansan sanda take sakin murmushi zuciyarta na mata wane irin sanyi... Yazeed dake hangowa daga can saman benensa anaima Mahmood d’in kirari yanaji kaman garwashin wuta ake watsa masa illahirin jikinsa... Giwa da Jakadiya dake hangosa daga nasu b’angaren, yanda ake masa k’irarin yana takowa ba k’aramin tada masu hankali hakan yayi ba... Ga Waziri a gefensa yana rarraba idanu wanda shima ko ba’ace a firgice yake....Ko shakka babu sunga jinin mulki a tattareda Mahmood d’in wanda k’warjininsa yai bala’in firgita duk wani mai k’ullin a zuciyarsa.... SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH* *54* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kaman ance ya d’aga kansa sama b’angaren d’akin Zahra, nan ya hangosu su duka biyun suna dubansa, idanunsa ya sauk’a kan Muhibbah wacce baisan ta dawo Masarautar ba...Cak ya tsaya ba tareda ya ci gaba da tafiya ba... Harga Allah ganinta tareda Zahra ba k’aramin sanyaya zuciyarsa yayi ba dukda cewa yau d’in gaba d’aya zuciyarsa a cubkunshe take bayan decision da ya yanke na auren Raheemah... Turaki dake gefensa ya d’aga Kai yana duban abinda yake kallo... Take Turaki ya saki wata irin sassanyar murmushi dan yaga abinda Mahmood ya gani... D’an matso da bakinsa kusan Mahmood d’in yai yace “Rankaidad’e jama’an Fada na kallonka, ya kamata ka sauk’e idanunka bamu fatan Mai Martaba Amale yai tuntub’e gaban Talakawansa..!!” Sai sannan ya janye idanunsa ya aikawa Turaki wata irin duba cikeda k’asaita ba tareda yace komai ba.. Shi kaw Turaki sai k’ok’arin tsime dariyarsa yake a matsayinsa na hannun daman Mai Martaba... A haka akaiwa Yarima Mahmood rakiya zuwa b’angaren mahaifiyarsa Giwa... Kafin su shigo Giwa da Jakadiya sunyi k’ok’arin kintsawa... Yarima Mahmood na shigowa Giwa ta isa garesa da fari’arta wanda da gani kasan da k’yar take nuna hakan... Waziri na bayansa kai a k’asa sai faman muzurai yake yana kuma kod’a Sarki Mahmooda...! Giwa kanta yau d’in kirari tai masa irinta Saraki...Ta rik’o hannayensa bayan tawagarsa sun fice, sannan Ta sallami duk Hadiman dake cikin parlorn ya rage saura su kad’ai...Fuska a marairaice Giwa Ke fad’in “Alhamdulillah..! Allah zai cika min burina na ganinka saman Karaga Sadauki...! Yau ina ma mahaifinka nada rai ya ganka saman Karagar nan.. Babban burinsa kenan ka gajesa ka gaji gidanku...! Nafi kowa Farin ciki da wannan Al’amari... Na godewa Allah da ya karkato da hankalinka daga can k’asashen Yamma ya dawo dakai gida, mahaifarka ka kuma amince zaka gaji Gidanku... Sadauki ka gama min komai...!!” Ta k’arashe tana matsan k’walla... Harga Allah yaji babu dad’i ganin yanda Giwa Ke farin ciki zai zamto Sarki... Anya hukuncin da ya yanke bai tsauri ba... Maiyasa zai zab’i ya watsawa mahaifiyarsa k’asa a idanu... Amma idan hakan shine zaman lafiyar d’iyarsa fah..! Mahaifiyarsa tanada sauran yara a nan, idan ta rasashi akwai sauran ‘yanuwansa, hasalima this is not the first time da ya tafi Turai ya zauna da family d’insa, dan ya kuma yi bazai zama bak’on Al’amari ba.. Sannan Zhara ita kad’ai yakeda... Bazaiso ya rasata ba, he’s doing all this for her.... But still mahaifiya mahaifiya ce ko yayane... Kuma ko ‘ya’ya nawa takeda tana son ‘ya’yanta equally, bazataso taga babu guda d’aya ba...Take yaji duk babu dad’i, ya d’ago hannu ya shafi fuskar Giwa yace “Maami Ki daina yawan shiga damuwa, everything will be alright in sha Allah...!” Jamal dake tsaye daga bayan Giwa ya k’araso cikin dogarawa da sandar crutches d’insa yana sakarwa Mahmood d’in Murmushi yake furta “Congrats Yaya..! I’m so happy for you, zaka angwance kuma za’a nad’aka matsayin Sarki...!” Mahmood ya sakar masa murmushi kana ya bud’e masa hannayensa yace “Come here, give your big brother a hug..!” Jamal na murmushi had’ida sinne kai yake furta “Yaya kaifa yanzu Sarki ne..!” Ya k’arashe yana shafa kai alamun jin nauyi... Murmushi mai kyau Mahmood yai yace “Koda ace ni sarki I’ll always be your big brother kaji koh..!” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’an Jamal d’in kana ya k’arada “Ya jikin naka..?” “Da sauk’i Yaya Alhamdulillah..!” Mahmood yace “Masha Allah.. Allah ya k’ara maka lafiya...! Ka shirya gobe da safe in sha Allah zamuje asibiti mu duba Fu’ad...!” Jamal ya jinjina kai yace “In sha Allah Yaya, dama nima goben inada zuwa ganin Dr na...” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da fad’in “ Yaya akwai maganar da nakeso muyi... Idan bazaka damu ba...Allah shi taimakeka...! Allah shi ja zamaninka..!!” Ya k’arashe yana kirariwa Yayan nasa... Giwa ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Jamal ka k’yale Yayanka yaje ya huta yayi tafiya ya gaji...!” Mahmood ya girgiza kai yace “A’a no... Family first, Ka tafi sashe na ka jirani a can, I’ll check on Zahra idan na fito sai muyi maganan koh...!” Ya k’arashe cikeda tausayin Jamal d’in duba da lalurar da yake fama dashi a yanzu... Jamal ya jinjina kai cikeda jin dad’i yana mai masa godiya had’ida kwad’a masa kirari har ya haye sama... Ya maidoda dubansaga Giwa wacce Ke muzurai ya danna mata wata muguwar harara kana yasa kai yai shigewarsa, tana kiran sunansa ko tsayawa baiba balle ya amsata... Muguwar haushi take basa sabida bata goyon bayan aurensa da Umaima..! Giwa tai saurin bin bayansa ta kamo sandar crutches d’insa hakan yasa ya dakata ba tareda yaci gaba da tafiya ba... Fuska babu walwala yace “Let go... Ki k’yaleni na tafi Maami, I’m not in the mood for your lectures..!” Giwa ta kuma had’iyan miyau da k’yar tace “Jamal ka saurareni please... Ba abinda kake tinani bane, ba maganan hanaka auren Umaima zanyi ba..!” A hasale yace idan ba haka ba mai zakiyi... Mai zaki cemin...?!” Giwa ta kuma marairaice fuska tana mai k’ak’aro murmushi yawa mutumiyar arziki tace “Ce maka zanyi na amince ka auri ‘yaruwarka Umaima.. Na amince ka fad’awa Yayanka a saka maku rana tare..!” Da mamaki yake dubanta murmushi saman fuskarsa “Da gaske Maami...! Kin amince na auri Umaima..?!” Giwa ta jinjina masa kai murmushi saman fuskarta... Baisan sanda ya rungumeta yana furta “Thank you..! Thank you Maami.. Kin gama min komai...Na miki alk’awari zan rik’e Umaima da amana, zan d’aura daga yanda kika tsaya.. Tin tana k’arama rik’onta a hannunki yake dan haka ni zanci gaba da rik’eta bisa gaskiya da amana..!” Giwa Ta kuma murmusawa ta shafi gefen fuskarsa kad’an “Nasan zaka iya Gwarzo... Na gama iyaka tunanina idan ba kaiba babu wanda zai rik’e min Umaima bisa gaskiya da rik’on amana... I trust you Gwarzona..!” Shima murmushin ya sakarwa mahaifiyar tasa su duka biyun suna duban juna... ** Mik’ewa Muhibbah tai ta dubi Zahra tace “Princess zan wuce, zan koma masauk’i, Ina fata zakiyi duk abubuwan dana fad’a miki...” Zahra ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida jinjina mata kai baki a ture kad’an...Muhibbah Ta sakar mata murmushi kana ta d’an dafata kaman zatace wani abu sai kuma tasa kai ta shige cikin tsananin kariyar zuciya, ta sani Raheema bata dace da Rankaidad’e ba amma yaya zatayi idan zab’insa kenan, bayan abubuwan da suka faru dashi bata fata ta kuma ganinsa broken, kuma tayi imani duk randa yasan abinda mahaifiyarsa da ‘yanuwansa sukai zai zama broken, bazataso Ta k’ara masa akai da matsalar Raheema ba...Zatai masa addu’an Allah yasa alkhairi a cikin aurensa da Raheema ya kuma shiryeta ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ahalin da yake k’ok’arin ginawa tareda ita...Tana fatan aurensa da Raheema zatai ya zamto silan shiriyarta domin shid’in mutumin kirki ne ya cancanci mace Ta k’warai....A hankali Ta saka hannunta ta murd’a handle d’in k’ofar.... Idanunta dake duban k’asa suka soma hango had’add’iyar takalmin kufta da k’afafunsa Ke rufe ciki, gabanta ya yanke ya fad’i.. Ga wani musulmin k’amshi da yai sallama ma k’ofofin hancinta, k’amshin nan dai da ya cika motar abokinsa sanda suka maidata gida...Cikin d’ak’ik’a zuciyarta Ke harbawa da sauri da sauri... A hankali take k’ok’arin d’ago k’wayar idanun nata zuciyarta bai daina harbawa ba har ta d’ago sosai suka dubi juna... Gani tai idanunsa k’yam akanta hannayensa hard’e waje guda fuskarsa d’aukeda alaman tambayar ya akai kika dawo..?! Ta had’iyi miyau da k’yar ganin babu wani walwala saman fuskrsa, tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi wanda kai tsaye zaka kirasada yak’e. “Your Highness..! Barkada sauk’a..!!” Tai maganar cikin rabewar kalmomi... Zaida ya kuma d’iban wasu dak’ik’ai kaman bazaice komai ba sai kuma yai mata alama da kai alamun amsawa ba tareda ya furta komai ba sai duban tuhuma da yake mata wanda sosai hakan ya haifar mata da tsarguwa... Ta d’an sadda kanta tana k’ok’arin matsawa alamun basa hanya... Bai janye idanunsa ba har saida yaga tana k’ok’arin d’ago fuskarta.... Yai saurin kauda fuskarsa sabida zuciyarsa data gaza natsuwa... Muhibbah tasa kai Ta shige zuciyarta naci gaba da bugawa... Kaman daga sama ta sinkayo muryarsa na fad’in “Maiyasa kika dawo..?!” Taji tambayar tamkar sauk’ar aradu..! Ta d’ago da sauri tana dubansa, sosai ya had’e gira... Rasa mai zatace tai sai murza ‘yan yatsunta da take... Da wutsiyar idanu yake dubanta alamun yana jiran amsa...! Saida Ta had’iyi miyau da k’yar, kana Ta soma k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta dikda cewa lokaci guda taji bata k’aunar tai masa k’arya amma babu yanda Ta iya ne... “Amm... Dama lecture free week nake shisa na koma gida... And and Mommy was sick, so sai naje duba jikinta... But she’s ok now shisa na dawo sabida exams..!” Ta k’arashe da k’yar kaman mai laifin da aka titsiye gaban Kuliya... Ya tsareta da idanu sosai kana yace “Dole sai cikin Masarautar nan zaki zauna..?!” Maganarsa ya haifar mata da sanyin jiki, dan sam bata fahimci cewa ya fad’i haka ne gudun kada Yazeed ya kuma attempting cutar da ita har dai zasu zauna gida guda... Itakam ji tai maganar nasa kaman hannunka mai sanda yake mata... Batakaiga basa amsa ba ta kuma sinkayo muryarsa yana fad’in “At least you’ve someone to protect you here... It’s not safe out there...!!” Tai saurin d’agowa tana dubansa dan sai yanzu ta fahimci mai yake nufi, saidai tuni yasa kai ya nufi cikin d’akin ba tareda ya tsaya jiran amsa daga gareta ba...Tabi bayansa da kallo had’ida sakin murmushi kad’an.. Daga nan yanda take tsaye tana iya hango alamu daga yanayin Zahra ko shakka babu Ta d’auki hud’ubar da tai mata cewa Ta nemi yafiyar mahaifinta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali zuciyarta na mata wane irin sanyi Mahmood da d’iyarsa zasu sasanta... A haka ta nufi masauk’i tai kwance tana tinanin abubuwa da dama... Saidai duk juyi da zatai sai Rankaidad’e ya fad’o mata... Maiyasa tinaninsa ya addabeta..? Toh Kodai dan a baya tanajin guiltiness ne, toh amma yanzu fah..? Ai ya kamata ta yakishesa a zuciyarta tinda ta tabbata Zahra zata d’auki hud’ubarta ta baiwa mahaifinta hak’uri su sasanta tsakaninsu... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana tuna had’uwarsu da sukai d’azu... Kalamansa na k’arshe zuciyarta keta nanatawa _You’ve someone to protect you here.._ Ta kuma sakin murmushi a hankali had’ida lumshe idanunta... ** Washe gari Zahra Ke sanar da ita yanda sukai da mahaifinta, sosai taji dad’in hakan, saidai a cewar Zahran duk sabida Muhibbar tai haka... Aje dai a hakan taji dad’i sosai da suka sasanta tsakaninsu... Zataso komawa gida tinda tayi Major abinda ya dawo da ita saidai alk’awarin da ta d’aukarwa Ubandoma da mahaukaciyar matar nan harmada Jafar shine kawai zai iya zaunarta a Masarautar bacin haka bataga kuma mai zata zauna tai ba tinda tayi abinda ya dawo ita...A bakin Zahran take jin cewa mahaifinta ya sanar da ita an saka bikinsu da Raheema nan da sati biyu kuma ta basa goyon bayanta dikda cewa bata k’aunar alak’arsu da Raheemar amma tinda yana so zatai hak’uri ta accepting d’inta muddin hakan zai faranta masa rai.... Take jikin Muhibbah yai sanyi tamkar an tsoma a k’ank’ara... Ta d’ago idanunta masu rauni tana duban Zahra dasu “Kikace an saka auren Paa d’inki..?!” Zahra ta jinjina mata kai tace “Haka Paa yace min an tsaida aurensu nan da sati biyu dan masu mulki basa jira... Amma na gaya masa dan dai kawai yana sone idan ta ni ne bana son ya aureta... But I guess I don’t have a choice then..!” Ta k’arashe cikin sanyin murya tana mai zama saman koren ciyawan da yaima lambun shak’atawan k’awanya... Muhibbah ta zauna a sanyaye tana mai jinjina lamarin, in the next two weeks Rankaidad’e zai auri matar nan... Ta had’iyi miyau da k’yar tana mai ayyanawa cikin zuciyarta, tabbas bazata jira sati biyu yai mata a wannan masarauta ba gwara kawai ta tafi dan Allah ya gani bazata juri ganin auren Rankaidad’e da matar nan ba... Zataji kaman taci amanarsa ne tinda ita tasan mai zai aura shi kuma bai san mai zai aura ba... Duk surutun da Zahra ke mata bata d’aukan komai tuni tai nisa cikin duniyar tunani... Yarima Mahmood da Turaki kaw daga can saman bene suke hangan Zahra da Muhibbah, hannayensa hard’e ta baya yake dubansu zuciyarsa naci gaba da raya masa wasu abubuwa... Turaki dake tsaye gefensa sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an kana yace “Your Highness har yanzu kana nan akan bakan ka na barin k’asar... Dan Allah think your decision through, wacce kake shirin yin wannan abu domin ita gashi ta kwantar da hankalinta, a tunanina Rankaidad’e you don’t need to leave anymore...!” Ba tareda ya dubesa ba har lokacin idanunsa naga Muhibbah yake furta “I’m sure this is all her doing... Inada tabbacin cewa ita ta shawo kan Zahra, she’s a good influence to my daughter... Saidai ita d’in ba mai zama cikin Masarautar nan bane, akwai randa zata gama abinda ya kawota Ta tafi... I’m afraid idan ta tafi Zahra zata iya komawa ruwa, musamman akwai ire irensu Yazeed cikin Masarautar nan masu poisoning zuciyarta da gurb’atattun tinani... Zaifi kyau idan na d’auketa daga cikin Masarautar nan...!” Turaki yayi shiru yana dubansa, lokaci guda ya girgiza kai yace “I’m sorry Rankaidad’e but ya zama dole na fad’a maka gaskiya hardai kana nan a matsayinka na Abokina.... Mahmood bari na maka magana da siga ta abokantaka mu aje mulki da matsayinka a gefe.. Ina maka magana ne a matsayina na abokinka ba a matsayinka na Sarki ba...Wannan hukunci da kake k’ok’arin yankewa akwai ranan da zakai nadamar yinsa... Your life is right here, cikin Masarautar nan... Bakada sauran rayuwa a Spain...!” Cikin karaji yaceda Turaki “I don’t remember asking for your opinion...!” Turaki ya nusa kad’an kana ya furta “Fine naji baka nemi shawarina ba... But ya zama dole na fad’a maka ko bazaka saurareni ba Your Royal Highness...!! Haka zaka tafi kana mai sab’a alk’awari..Haka zaka tafi ka bar mutuwar mahaifinka da matarka unpunished..? Haka zaka tafi ka k’yale mahaifiyarka da jin kunya bayan Ta aminta da kai..? Haka zaka tafi ka bar Al’ummanka masu k’aunarka broken..?!” Ya d’an sassauta muryarsa yana mai ci gaba da fad’in “Haka zaka tafi ka k’yaleta da k’aninka mai kwad’ayin jikinta cikin Masarautar bayan ka mata alk’awarin kareta..?! Haka zaka tafi ka hana zuciyarka kasancewa da zab’inta... You can’t leave all these behind your Highness...!!Ya k’arashe yana mai duban abokin nasa cikin wane irin yanayi.... A hankali ya karkato yana duban Turaki zuciyarsa na kuma bugawa, lokaci guda yake furta “What exactly do you mean..? Wacece kake nufi..?!” Turaki bai basa amsa ba saima maida dubansaga b’angaren dasu Muhibbah Ke zaune da yayi... Lokaci guda yake ci gaba da furta “You can’t deny it your Highness, You love her... So much...!!” Ya k’arashe yana duban Mahmood d’in cikin idanu... Bai iya furta komai ba sai duban Turaki da yake babu k’yafta idanu, fuskar nan tasa kaman bai tab’a dariya ba... Turaki na ci gaba da sakin huci yake furta “Your Highness abinda kake k’ok’arin yi cin amanan Masarauta ne..! Cin amanan Al’ummanka ne...! Cin amana Ahalinka ne..!! Ba’asan Sarki da sab’a Alk’awari ba Rankaidad’e... Sunnan Sarakuna ne cika alk’awari da yin magana k’wara d’aya tak..! Kada ka zamto Sarki na farko da zai bar abin fad’i a tarihi..!!” Da tsananin mamaki Mahmood ke dubansa, shine Turaki Ke fad’a masa magana haka....Lokaci guda yai gyaran murya Parlorn ya amsa... Take Hadiminsa ya k’araso yana mai zubewa had’ida kwasan gaisuwa... Har lokacin idanunsa naga Turaki hannayensa hard’e ta baya, fuskar nan tasa tamau, saida ya kwashe dak’ik’ai kaman bazai magana ba Hadimin nasa na nan risine wajen sai kuma ya bud’e murya yace “Kai masa rakiya zuwa k’ofan Fada...! Kuma kar a sake barinsa ya shigo har sai na bada umarnin hakan..!!” Turaki ya sadda idanunsa k’asa dan yasan hakan ka iya faruwa... Lokaci guda yake furta “I’m sorry Your Highness... But I know my way out..!!” Yana ida fad’in haka ya risina yace “Na Barka Lafiya Rankaidad’e..!!” Lokaci guda yasa kai ya nufi k’ofa... Barde ya mik’e yana an gama Rankaidad’e..! Allah shi ja zamaninka..!!” Lokaci guda yabi bayan Turaki yana furta “Fada bata Marhaban da kai...!!” Mahmood dake nan tsaye wajen fuzar da huci mai tsananin d’umi yayi zuciyarsa na masa k’una... Yana mai tuhumar kansa da abubuwan da Turaki ya zayyano masa, ciki babu wanda ya tsaya masa a rai kaman cewa da yai son yarinyar nan yake... Hannayensa biyu yasa ya shafi fuskarsa yana mai kuma fuzar da fuci yake taka cikin tampatsetsen parlorn nasa cikin taku d’ai d’ai irinta masu mulki... SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH* *55* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Yau kusan sati kenan babu su Ubandoma babu labarinsu, fad’in tashin hankalin da Giwa Ta tsinci kanta ciki b’ata baki ne... Ga duk wanda yai mata Farin sani kallo guda zai mata ya fahimci bata a hayyacinta, tabbas duniya tai mata atishawan tsaki, abubuwa sunci gaba da tafiya ba yanda taso ba... A halin yanzu nad’in sarautar Mahmood da auren Jamal da Umaima ne kawai take tinanin Sune sa’arta na k’arshe, amma kam b’acewar Izzatu da Jafar harmada Ubandoma ba k’aramin d’aga hankalinta hakan yayi ba... Daga ita har Waziri an rasa mai dannan wani... Shima a nasa tinanin lokaci ya kusa da zai juya mata baya dan a nasa tsarin da zaran sun kauda Mahmood Karagar tasa ce ko kusa bazai bari Yazeed ya d’ale Karagar ba... Wannan k’udiri nasa ya jima cikin zuciyarsa tun ba yanzu ba... ** A b’angaren Yarima Mahmood kaw tinanin abubuwan da Turaki ya fad’i masa sun kasa b’acewa daga kwanyarsa... Kullum cikin tunani yake, kalaman Turaki na k’arshe su suka tsaya masa a zuciya _”Abinda kake k’ok’arin yi cin amanan masarauta ce, cin amanan Ahalinka ne.. Cin amana Al’ummanka ne..! Cin amana Zuciyarka ne..”_ Ya kuma lumshe idanunsa a hankali yana mai aje pencil d’in da yake sketching dashi... Ya mik’e yana zaga farfajiyan benen nasa lokaci guda yana tunanin abinyi... Wata zuciya tace ka sami d’iyarka da batun kar rana tsaka taga zaku koma Spain Ta kuma zarginka da wani abin...! Ya kuma sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana yayi kiran Hadiminsa yace a kirawo masa d’iyarsa Zahra... Babu jimawa Zahra ta shigo kanta a k’asa ta duk’a ta gaida mahaifin nata... Ya amsa mata da sakin fuska kana ya nuna mata gefensa yace tazo Ta zauna... Ta d’an d’ago idanu ta dubesa daga nan k’asa yanda take zaune kana tace “Paa kaifa Maimartaba ne yanzu...!” Ya murmusa kad’an yace “Kema Maimartaba ce, Zo ki zauna...!” Ta mik’e cikeda jin nauyi ta isa ta zauna a d’arare ba kaman yanda ta saba a baya ba domin kaw tabbas mulki ba k’arya bane akwaita da gizo... Mahmood ya karkato kad’an yana dubanta kana yai gyaran murya ya soma fad’in “Zahra Ina son Ki sani duk abinda nakeyi sabida Ke nakeyi, bazanyi abinda zan cutar dake ba... Kuma bazan yanke shawarinda bazai miki amfani ba..!” Yanda yake maganan gaba d’aya sai yasa jikinta yin sanyi, Ta d’an d’ago idanunta masu rauni tace “Paa you’re starting to scare me now, just tell me ko menene nasan bazaka cutar dani ba.. Aunty Muhibbah tace a koda yaushe na kasance mai kyautata zato wa mutane and especially to you Paa, coz you’re my Father and you love me unconditionally...But with the way you’re talking Paa, sai ina jin tsoron abinda zai fito daga bakinka.. You become totally irrational tinda muka dawo k’asar nan... Paa what exactly are you afraid of telling me..?!” Ta k’arashe cikin raunin murya.. Sirhitaccen murmushi saman fuskarsa yake dubanta, cikin zuciyarsa yana kuma nanata sunan Muhibbah... Lokaci guda ya jinjina kai yace “Your Tia was right... Ina k’aunarki sosai kuma bazanyi abinda zai cutar dake ba..! Zahra, Decidí que volveremos a España tan pronto como me case con Raheema..” (Zahra na yanke shawarin zamu koma Spain da zaran na auri Raheema) “We’d have a new life there the three of us..!” Da tsananin mamaki Zahra ke dubansa... Ta d’an girgiza kai tace “Is that really necessary Paa..?, Wai zamu sake komawa Spain, kuma da matar nan...But Paa...” Katseta yai da fad’in “It’s for the best Zahra.. I promise..!” Kaman zatai magana sai kuma tai shiru cikin tsananin sanyin jiki take furta “Alright..!Shikenan ..! Si tú lo dices Paa” (Idan kace haka Paa) Lokaci guda ta mik’e ta d’an sadda kanta tace “Na Barka lafiya Papa..!” Ya jinjina mata kai a hankali yana mai binta da kallo har ta b’acema ganinsa... A hanya Muhibbah Ta hangeta tana tafe tana matsan hawaye, babu shiri tabi bayanta tana tinanin mai ya faru da ita kuma... Can k’asar wata bishiya Zahra Ta k’arasa Ta zauna tana ci gaba da kuka a hankali... Muhibbah ta k’araso ta d’an dafata kad’an “Are you alright..?!” Ta tambaya tana duban Zahran... Mik’awa Zahra tai Ta rungumeta sosai tana mai ci gaba da kuka... Muhibbah dake tsaye tamkar statue tana sauraron kukan da yarinyar keyi har cikin zuciyarta, a hankali Ta soma lallashinta tana tambayarta meke faruwa..? Zahra tasa hannu ta goge hawayen da suka jik’a mata fuska “My Paa have decided we’re leaving back to Spain bayan ya auri wannan witch d’in...!!” Ta k’arashe tana sakin huci wasu hawayen na kuma gangaro mata... Kaman sauk’an aradu haka Muhibbah taji batun “Zaku koma Spain... Wait he can’t do that... I mean your life is right here...!” Zahra Ta jinjina kai tace “I don’t want to leave with that woman.. I don’t want her in our lives... Dik iyaka k’ok’arina naga na sota ko kad’an ne wllhi banjin sonta, kullum k’ara tsanarta nake... And and what’s worse is that.. I don’t want us to be separated.. Idan muka koma Spain shikenan bazan sake ganinki ba Tia..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka... Janyota Muhibbah tai ta rungumeta kad’an tana lallashinta “Everything will be alright in sha Allah... kinji Ki kwantar da hankalinki....!” Zahra tai shiru cikin k’irjinta tana ci gaba da ajiyan zuciya Muhibban na shafa kanta a hankali, su duka biyun zukatansu na bugawa... So wannan shine dalilin da yasa Rankaidad’e ya dage da batun auren matar nan lokaci guda... Turai zasu tafi tare, ashe kenan bazai tsaya a nad’asa Sarauta ba... Hakan na nufin idan ya tafi wani zai maye gurbin Sa ya zamto Sarki... Toh waye zai maye gurbin nasa..? “YAZEED” sunan da zuciyarta ya raya mata kenan... Take Ta shiga girgiza kai tana ayyanawa cikin zuciyarta bazata tab’a bari hakan ya kasance ba... Yazeed bazai zama Sarki ba koda na rana guda ne... She needs to come up with something as soon as possible...! Ta k’arshe tana tunanin Menene abinyi... ** A can Masarautar su Raheema kuwa Amarya gyara ake da shirin biki babuji babu gani dikda cewa Yazeed ya tak’ura mata da waya akan sai ta dawo masarauta sunyi final goodbye da juna... Yau d’inma wayace mak’ale kunnenta anai mata gyaran jiki tai excusing kanta tana mai ci gaba da amsa kiran nasa “Wai mai kake nema a wajena ne prince... Na zaci munyi sallama ai..!” Yazeed ya murmusa kad’an yana shafan hab’arsa yace “Rankidad’e Amarya hak’uri zakiyi ki dawo masarauta muyi proper goodbye, I’m not even sure idan zan iya barinki wa Mahmood gaba d’aya..!” Fuzar da huci tai tana mai rausayar da idanu tace “Kaga Yazeed I’m not in the mood to play such game with you, it’s over between us.. Dan Allah ka k’yaleni najida..!” Katseta yayi da fad’in “And who’s playing games with you...!! It’s not over, until I say so..! Ki dawo Masarauta muyi sallaman k’arshe idan har kinaso Mahmood ya zama naki..!” Ta fuzar da fuci kad’an tana mai dafe kanta tace “But mai zance... Ta yaya za’ayi na d’auki k’afafu na tafi Masarautar su mijina tun ba’a d’aura aure an kawoni ba... Kasan yanda abubuwan sarauta suke yanzu yin hakan sai ya zama wani babban scandal..!” Ya katseta da fad’in “Come up with something.. Ba Yayarki tana Masarautar ba, kuma akasarin zamanki tinda yayarki tai aure ya dawo wannan Masarautar ne..Sai kisan k’aryar da zakiyi kizo idan kuma ba haka ba..?!” Yai wata murmushi ba tareda yace komai ba... Cikeda k’osawa tace “Fine naji... Zanga mai zan iyayi...!” Yazeed yace “Bawai zakiga mai zaki iyayi bane... Dole Ki Zo, ko dan samun zaman lafiyarki da kwanciyar hankalinki.. Mu had’u gobe a yanda muka saba had’uwa..!!”Daga haka katse kiran yai ba tareda ya kuma sauraronta ba... Muhibbah dake mak’ale jikin staircase tsaf taji tattaunawar Yazeed da Raheema, cikin sand’a tai k’ok’arin ficewa daga sashen ta fasa shigewa... D’aki Ta komo tana tinanin mafita, ta tina Yazeed yaceda Raheema su had’u gobe a yanda suka saba had’uwa basai ta shigo Masarautar ba dan gudun maganganun mutane... Hakan zaisa babu wanda zai gane ma tazo Masarautar koda kuwa Yayartace Gimbiya Zeenat... Muhibbah ta k’ume a d’aki tana tinanin abinyi, wata dabarace Ta fad’o mata... Kai tsaye D’akin Zahra ta tafi yanda ta tadda Zahran na baiwa wasu bayi guda biyu umarnin su sorting wasu stuff d’inta alamun ta saduda ta soma shirya kayayyakinta dan tafiya k’asar Spain dake gabansu... Tana ganin Muhibbah ta sakar mata murmushi ta isa gareta... Muhibbah ta dubeta ta dubi Kuyangin guda biyu dake shirya kayayyakin Zahra.. Ta d’an waro idanu waje tace “Kin fara parking already..?!” Zahra ta d’an tab’e baki tace “Kind of... Since I don’t have a choice...!” Muhibbah Ta sakar mata murmushi wanda yafi kama da yak’e... Zahra tai alama wa Kuyangin suka fice... Lokaci guda Muhibbah Ta janyo hannunta suka zauna saman sofa.... Muhibbah tai gyaran murya kad’an tana mai tsare Zahran da idanu tace “Do you really want to leave...?!” Zahra ta fuzar da iska kad’an tace “Only because I don’t have a choice..I’m doing this for my Paa... Idan tani ce baniso ya auri matar nan balle har mu bar k’asar nan tareda ita...!” Muhibbah Ta jinjina kai tace “Ki kwantar da hankalinki Zahra... You’re not leaving, and your Paa is not getting married to that woman... I promise you..!” Zahra Ta dubeta da mamaki tace “But how...?!” Muhibbah Ta kuma gyara zama tace “I’ve a plan... matso kusa kiji..!” Babu musu Zahra ta matso kusanta sosai... Take Ta sanar da Zahran abinda ta shirya a zuciyarta... Cikin Rashin fahimtar abinda Muhibbar Ke nufi Zahra tace “But idan yak’i zuwa fah ...?!” Muhibbah ta murmusa tace “Ke kad’aice wani abu zai sameki ya bar dik abinda yake ya fito.. So bazaiki’i zuwa ba...!” Zahra ta d’anyi jim tace “Toh Wai mai zaije gani... I’m lost..!” Muhibbah Ta kuma murmusawa tace “Abinda zai hanasa auren matar da baki so ya aura shi zai gani... All you need to do is to trust me and stick to our plan... Kin fahimta...?!” Zahra ta jinjina kai a hankali tace “I trust you... Na yarda dake Tia...!” Muhibbah Ta murmusa tace “Tomorrow in the evening..!” Jinjina mata kai Zahra tai tace ta fahimta... Da wannan shawari Muhibbah harmada Zahran suka sami bacci mai kyau... *** Washe gari Zahra ta sami mahaifinta da batun tana so taje ta duba Uncle d’inta Fu’ad a asibiti kafin su bar k’asar... Mahmood ya amince mata amma da sharad’in Umaima ko Jakadiya d’aya zatai mata rakiya.... Zahra Ta marairaice fuska tace “Paa fah harda gidajen k’awayena zan zaga nai masu sallama, ni banson rakiyar kowa...!” Da wutsiyar idanu ya dubeta, dak’ik’a guda Ta gifta kana ya girgiza kai yace “Bana son gardama...!!” Ta sadda kanta k’asa kad’an tace “Alright zan fad’iwa Jakadiya..!!” Bai tankata ba saima kiran Hadiminsa da yai... Hadimin ya k’araso ya zube yana kwasan gaisuwa... Mahmood dake tsaye hannayensa hard’e ta baya ya bud’e murya kad’an yace “Barde aimin ison Jakadiya..!!” Barde ya d’ago hannu alamun jinjina “Allah shi taimakeka..! An gama Rankaidad’e..!!” Ya mik’e da sauri a durk’ushe ya fice isar da sak’on shugabansa... Zahra ta saki baki kurum tana duban mahaifin nata wanda ga dukkan alamu mulkin ya soma ratsa jikinsa, tayi imani da a baya ne iyaka abinda take so shi za’ai amma yanzu abubuwa yake irinta masu ji da Mulki... Ta had’iyi miyau da k’yar dan idan dai da Jakadiya za’ai tafiyar shirinsu da Muhibbah zai b’aci... Yanzu mai zatai..? Batakaiga samo amsa ba Jakadiya Ta shigo a duk’e tana gaida Sarki... Mahmood yai gyaran murya kad’an ya ambato sunan Jakadiya “Allah shi baka yawan rai...!!” Jakadiya ta fad’i tana mai kuma risinawa alamun amsawa... “A tafi da ita duk yanda take so, karki rabu da ita daidai da dak’ik’a guda...!!” Jakadiya ta kuma risinawa bayan ta dubi Zahra dake tsaye gefen Babanta kana tace “An gama Rankaidad’e.. In sha Allahu ko k’uda bazai tab’a ta ba...!!” Zahra ta narkama Jakadiya harara dan yanda bata k’aunar Kakarta Giwa haka bata k’aunar Jakadiya.... Ya jinjina masu kai had’ida basu izinin fita.... Tana fitowa ta turawa Muhibbah sak’o cewa Paa d’inta ya k’yaleta taje asibiti duba Fu’ad amma harda rakiyar Jakadiya... Muhibbah ta ida karance sak’on had’ida rintse idanunta dan babu Jakadiya a tsarin nasu, kasancewarta ka iya b’ata komai... Sak’o Zahra ta kuma turo mata _What do I do..?_ Dafe kanta tai tana tinanin abinyi... Kaman ance ta kalli can gefe da yanda take tsaye Ta hango Jamal kishingid’e cikin rumfar shak’atawa ta alfarma yana juya wani guntun k’yalle a hannunsa, Ta tsare k’yallen da idanunta daga nan yanda take lab’e... Ko shakka babu ta fahimci k’yallen mayafinta ne da ya gutsire sanda ta haye saman ginin benen b’angaren Jamal d’in lokacinda take binciken Zanen ginin gidan sarauta dake wajen Jamal d’in....Wato ya d’auki k’yallen kenan yana neman mai tufafin... Tabbas idan yasan wanene mai Tufafin zai fahimci tana masa binciken k’wak’waf ne... Bazata bari ya kamata ba... Amma mai zatai... Take tinanin Jakadiya ya fad’o mata... Ta tina cikin labarin da Fu’ad ya bata Jakadiya itace ta d’auketa ta kaitama wancan tsinannen bokan wanda yaso k’ara aikata alfasha da ita akan wanda ‘ya’yan Sarkin suka mata.... Take taji wani irin tsanar Jakadiya na kuma taso mata... Tabbas Jakadiya yau zata karb’i nata itama wajen Jamal... Ba tareda d’aukan doka a hannunta ba Jamal zai zartar mata da nata hukuncin, dan yanda taga fuskar nan nasa babu alamun rahama tasan idan ya kama mai tufafin nan bazai masa da dad’i ba.... Sak’o ta turama Zahra cewa tazo sashen bak’i ta sameta kafin su fice amma kada ta sanar da Jakadiya ga yanda zataje... Zahra tai yanda Muhibbar tace... Ta dubi Jakadiya tace ta jirata nan tana zuwa... Jakadiya Ta jinjina kai tace an gama Rankaidad’e.... Zahra ta iso jikin k’ofar Muhibbah tai knocking a hankali... Muhibbah Ta lek’o kana Ta janyo hannunta zuwa cikin parlorn... Ga mamakin Zahra wani mayafi Muhibbah Ta mik’a mata... Zahra ta juya mayafin tace “Mai zanyi da wannan...?!” Muhibbah tace “A tsarinmu Babu Jakadiya ciki... Wannan mayafin shi zai hana Jakadiya daga ficewa cikin Masarautar nan... Ki bata kice ta yafashi ke bazaki fice da ita tagajan magajan ba ana kallonku haka.... Idan ta yafa kubi ta k’ofar Shataletale (Yanda Jamal Ke zaune)..” Zahra dai bata fahimci komai ba amma Ta sami kanta da yin yanda Muhibbar Ta umarta... Sai juya mayafin take hannunta har ta iso yanda ta bar Jakadiya na jiranta... Tana k’arasowa Jakadiya tai mata jinjina da gaisuwa.... Zahra Ta sakar mata murmushi kana Ta mik’a mata mayafin dake hannunta tace ta yafa shi... Jakadiya Ta shiga juya mayafin tana mai furta “Allah shi taimakeki wannan ai naku ne masu mulki, Ina na isa yafa wannan Ina talakarku...!” Zahra ta murmusa tace “Karki damu Jakadiya, dukkanmu da kike gani d’aya muke a wajen Allah, idan ma kinfini tsoron Allah sai ki fini matsayi wajensa... Dukkanninmu bayin Allah ne.. Ke ‘yaradam ce kaman ni... So ki karb’a kawai ki yafa babu wani abu...!” Jakadiya tai mata K’uri tana dubanta cikin tsananin sanyin jiki, tinda take a Masarautar ba’a tab’a karramata irinta yau ba... Bata tab’a jin tanada daraja a matsayinta Ta ‘yaradam kaman yau ba... Allah sarki sai ta tuna jik’onda Giwa tasa taita d’irkawa matar Yarima Mahmood Aliya wanda ya lalata mahaifarta kuma sukeda tabbacin bazata tab’a haihuwa ba... Sunada tabbacin Zahra ba d’iyar Aliya bace dan Tal’udu ya tabbatarwa Giwa Aliyar bazata tab’a haihuwa ba duk asibitin duniya da zasuje shisa koda suka dawo da Zahra k’asar a matsayin d’iyarsu sukeda shakku da alamun tambaya akan yarinyar.. Amma dai abinda yarinyar nan tai mata yau tayi imani d’iyar halak ce koda kuwa ta wata hanyar aka sameta... Zahra ce ta katse mata tinanin da fad’in subi ta k’ofar Shataletale... Suna tafe tana jan Jakadiya da hira.... Jakadiya sai Washe baki take tana jin kanta tamkar ‘yantacciya musamman data rufa mayafi irinta masu Mulki... Daga can yanda take kishingid’e a Rumfar hutawarsu Ta ‘ya’yan sarakuna yana mai ci gaba da juya k’yallen ya hango Jakadiya da Zahra na tahowa... Ya k’urama Jakadiya idanu da mayafin dake kanta, ya kuma juya k’yallen dake hannunsa... Lokaci guda ya shiga jinjina kai... Wato Jakadiya ce mai masa bincike a d’akinsa... Alk’awari ya d’auka idan ya kama mai masa binciken k’wak’waf d’in nan sai ya hukuntasa hukunci mai tsauri dan shi a nasa tsarin babu yafiya, duk wanda ya shiga gonarsa sai ya hukunta sa, hakan yasa ya hukunta Ja’afar sannan Majidad’i ma bai mance dashi ba h’d definitely get what’s coming for him... Yanzu ma dole ya hukunta Jakadiya... Ya k’arashe yana sakin huci... Bawa guda dake tsaye gefensa yai masa alama yazo.... Take ya basa umarnin yai masa kiran Jakadiya... Bawan ya tafi yayi yanda Jamal yace.. A tare Zahra da Jakadiya suka k’araso... Jakadiya ta zube tana kwasan gaisuwa... Zahra ma Ta gaida Uncle d’in nata da sakin fuska.... Jamal ya tambayeta Ina suka nufa..? Yana tambayar yana k’arema mayafin Jakadiya kallo dan tabbatarda zarginsa har dai idanunsa suka sauk’a kan yanda gutsirin k’yallen ya fice... Ta tabbata Jakadiya ce mai masa binciken sirri watak’ila ma bakinsu d’aya da Ubandoma ita ta had’a baki da Ubandoma suka kub’utar da Ja’afar.... Ya dubi Zahra yace “Princess, gashi kuwa inaso Jakadiya tai min wani aiki... Ko na had’aki da wata Hadimace Ta rakaki...?!” Zahra cikin jin dad’in Ta sami hanyar rabuwa da Jakadiya a sauk’ak’e tace dashi “Karka damu Uncle na bar maka Jakadiya, zan samu d’aya cikin Hadimaina tai min rakiya...!” Jakadiya na son cewa umarnin mahaifin Zahra ne babu hali haka tanaji tana gani Zahra tasa kai abinta Ta shige bayan tayiwa Jamal sallama.... Tana shigewa ta kirawo Muhibbah ta sanar da ita Uncle Jamal ya rik’e Jakadiya zatai masa wani aikin.... Muhibbah ta murmusa, a fili ta furta “Perfect..!!” Cikin zuciyarta kuwa fad’i take Jakadiya kema tak’i Ta sameki.... SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH* *56* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ba tareda rakiyar ko wacce Hadima ba Zahra tai ficewarta kaman dai yanda suka tsara da Muhibbah... A farfajiyan asibitin Ta umarci driver ya ijeta, tana fitowa daga motar ta soma dialing layin Muhibbah... Juyowar da zatai ta ganta tsaye gefenta, Zahra ta d’an zaro idanu tace “Yaushe kika iso..?” Hannunta Muhibbah ta kamo tana mai sanar da ita bata jima da isowa ba dan tin fitarsu itama ta fice ta shiga motar haya hasalima biyedasu Zahran suke a baya... Zahra tace “Toh what next.. Mai zamuyi yanzu..?!” Muhibbah tace “Zamu shiga ki duba Uncle Fu’ad d’in kaman yanda kikaceda Paa d’inki..” Zahra ta jinjina kai a hankali kana suka nufi psychiatric ward... Suka zauna a wajen da visitors Ke zama, d’aya daga cikin mai kulada marassa lafiyan ya k’araso yana tambayarsu wajen wanda sukazo.. Babu b’ata lokaci sukace dashi ga wajen wanda sukazo, Zahra tace ita niece d’insa ce... Nurse d’in ya jinjina kai yace amma saidai Fu’ad bai cikin majinyatan da ake fitowa dasu sabida hauka tuburan da yake, duk mai son ganinsa saidai ya shiga ya gansa a d’aure da sark’ok’i jikin gadonsa... Koda suka shiga wajen Fu’ad ba Zahra kawai ba harta Muhibbah saida ta tausayawa Fu’ad... Irin d’aurin mahaukata da mahaifiyarsa taima mahaukaciya Izzatu irinsa akaima Fu’ad cikin sark’ok’i sannan yanda mahaifiyarsa Ta yanke harshen Izzatu babu magana haka nan shima gadai harshe cikin bakinsa amma kaman an d’aureta Bai iya cewa komai saidai yana iya sauraron magana...Bai cewa um bai cewa a’a sai kallon mutane da ido... Zahra na hawaye daga nan yanda take tsaye Ta kasa ci gaba da kallonsa... Cikin kuka Ta k’unshe bakinta Ta fice ta bar d’akin dan bazata juri ganinsa a haka ba... Fu’ad yana ganin Muhibbah ya bar dik wani bige bige da yake yana binta da kallo, Muhibbah tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata... A hankali take takowa har Ta iso kusan jikin gadon, Fu’ad bai daina dubanta ba.... Saida tai k’ok’arin saita kanta kana ta soma fad’in “Wasu lokuta a rayuwa mukanji cewa inama mukeda ikon tsara k’addararmu yanda muke so... Saidai Allah bai hukunta hakan ba a tsakaninmu, shikeda cikakken ikon tsara mana rayuwa yanda duk tazo mana... Wasu k’addaran sukan faru damu ne domin su zamto iznah a garemu, wasu kuma sukan faru ne domin su zamto jarabawa a garemu... Rayuwar gaba d’ayarta jarabawa ce, da dad’i ko Babu dad’i...Mai hak’uri da d’aukan k’addara shi yakeda riba... Ina fata wannan ciwo da kake ciki ya zamto iznah ga ire iren mutane masu tunani irin naka wanda basa d’aukan k’addara su maida la’amaransu ga mahaliccinsu, saidai su jefa kawunansu cikin shaye shayen miyagun k’wayoyi don a nasu k’aramin tinanin wad’annan miyagun k’wayoyin sune zasu zamto makawar damuwarsu da suka tsinci kansu ciki... Watak’ila kuma hakan ya zamto hukuncinka ne bayan abinda kuka aikata ma wancan yarinyar shekarun baya... Fu’ad I’m quite certain you’re not like your two brothers, kaso yin abinda ya kamata tuntuni amma bakada courage... Sabida ‘yanuwanka da mahaifiyarku da suke maka barazana... Ko dan dalilin wannan zan yafe maka dikda cewa akwai jinin mahaifina a hannunka... Jinin mahaifina yayi staining hannunka Fu’ad... Kai ka kashe Abbah na, amma na yarda bada son ranka bane ka aikata hakan....! Na yafe maka Fu’ad kuma ina rok’on Allah ya sassauta maka... Ya baka lafiya, ya kuma inganta rayuwarka..!!” Ta k’arashe idanunta na kuma kad’awa... So yake yayi magana amma babu hali sai hawaye dake gangaro masa fuskarsa d’aukeda alamun tambaya...Muhibbah dake zuban hawaye ta jinjina masa kai alamun tabbatarwa, lokaci guda take furta “Yes... Yes Fu’ad... I’m that girl that you and your brothers abused... Ni ce Saudatu...!!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata... Fu’ad yaci gaba da tsareta da idanu hawaye naci gaba da gangaro masa... Muhibbah taci gaba da fad’in “Na dawo cikin rayuwarku ne domin na tarwatsa ahalinku, saidai tun kafin nakaiga tarwatsaku da alama zunubanku suna hunting d’inku d’aya bayan d’aya...I’ve never loved you Fu’ad... Kawai nayi amfani da damar ne to ruin you, saidai kaida kanka tuni ka tarwatsa kanka Ta hanyar d’irka ma kwanyarka miyagun k’wayoyi...Ina fata Allah ya kawo maka sassauci Fu’ad... Sannan Ina maka bankwana na k’arshe watak’ila bazamu kuma had’uwa ba... Allah Ubangiji ya sassauta maka....!” Ta k’arashe tana mai ficewa daga cikin d’akin.... Fu’ad yabi bayanta da kallo har Ta b’acewa ganinsa wasu irin hawaye na kuma gangaro masa... A hankali ya lumshe idanunsa wasu hawayen suka kuma gangaro masa... A nan kujerun da visitors ke zama ta tadda Zahra tai zaune damuwa fal zuciyarta... Daga gefenta Muhibbah ta zauna ta d’an dafata kad’an, Zahra Ta d’ago idanunta masu rauni tana dubanta lokaci guda take furta “He’s my favorite you know... it breaks me seeing him like this... Uncle Fu’ad yanada kirki, he might have his own faults a matsayinsa na d’anadam but I can assure you he’s a good person...!” Jinjina mata kai Muhibbah tai tace “Na yarda, yanada zuciya mai kyau... Kiyi mishi addu’a Zahra Allah ya bashi lafiya...!” Zahra Ta jinjina kanta hankali had’ida fatan samun sauk’iga Fu’ad... Saida suka d’an b’ata lokaci a asibitin kafin suka saci wata hanya suka fice yanda driver d’in bazai gansu ba... Shiru shiru yana jiran fitowar Zahra hardai ya yanke shawarin sauk’a ya duba ta ina Zahran take... Tin yana d’aukan abin wasa hardai ta tabbata babu Zahra babu dalilinta.... K’ololuwar tashin hankali ya shiga... Haka ya dinga karad’e ward d’in yana furta Rankidad’e amma babu ita babu alamunta... Koda ya tambayi nurses d’in dake wajen sai ce masa sukai eh wata ‘yar matashiyar budurwa ta shigo ta duba Yarima Fu’ad amma Ta fice tuntuni... Kuma Bafajen dake gadin k’ofan d’akin Fu’ad akai rashin sa’a ya fice Sayen goro har Muhibbah da Zahra suka shigo suka fice... Cikin tsananin kid’ima driver ya kirawo layin Hadimin Yarima Mahmood.... ** Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar tana duban sunk’urun d’akin da suka shigo itada Yarima Jamal wanda babu komai cikinta sai wata kujerar katako k’wara d’aya tak...Ta risina kad’an tace “Allah shi taimakeka ko wani abin zanyi maka cikin d’akin nan..?!” Yanda ta hango fuskar Jamal d’in ya sanyata had’iye sauran kalaman nata... Sai kuma taga ya sakar mata murmushi lokaci guda... Yai mata nuni da wata ‘yar akwati mai kaman briefcase yace Ta d’auko ta kawo gabansa... Babu musu Jakadiya ta isa ta d’auko Jakan ta aje gaban Jamal cikeda risinawa... Jamal ya kuma sakin murmushi yace “Dad’ina dake Jakadiya akwai bin umarnin iyayen gidanki... Shiyasa zanji mamaki matuk’a idan akace kinci amanar iyayen gidanki...!” Jakadiya ta Washe baki had’ida risinawa tace “Ai Rankaidad’e bana fata wannan rana tazo... Ranan da zan juya ma ahalin gidan nan baya... Duk abinda kuka umarceni sami’ina wa’ad’ana ne a matsayina na baiwa mai biyyaya.. Allah shi taimakeka..!!” Ta k’arashe tana mai kuma d’ago masa hannu alamun jinjina... Kansa a karkace yake dubanta, lokaci guda ya kuma sakin murmushi kana yai mata nuni da wannan kujerar k’wara d’aya tak dake cikin d’akin yace ta k’arasa ta zauna a samansa... Jakadiya ta soma shan jinin jikinta, ta d’an d’ago tana dubansa kad’an “Rankaidad’e ina baiwa ina zama kan kujera a gaban Ubangidanta...?!” Jamal ya kuma murmusawa yace “So nake yau ki zamto Sarauniya cikin d’akin nan... Sabida ke kikeda mulkin wannan d’akin a yau.. Na tabbata zakiso kiji yanda Iyayen gidanki sukeji koda na rana guda ne..!” Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar tana washe baki wanda yafi kama da yak’e “Toh Rankidad’e idan kace haka.. Ni umarninka nake bi...!” Jakadiya ta isa saman kujerar ta zauna tana mai daidaita saman kujerar a hankali lokaci guda tana mai ci gaba da wage baki yawa an mata alk’awarin kujerar Makkah... Sai bud’e kafad’a take saman kujerar tana jinta tamkar Sarauniya... Yai tsaye jikin sandar crutches d’insa daga nan yanda yake tsaye yana dubanta, murmushi bai bar saman fuskarsa ba... “Ya kikaji Jakadiya..? Ya kikaji zak’in ‘yanci da Mulki..?!” Jakadiya tace “Ba’a magana Rankaidad’e... Duk yanda zanso fasaltawa bazan iya ba..!” Ya jinjina kai a hankali kana ya isa gefe ya d’auko wata igiya... Itadai Jakadiya duk bata ankare ba sai juyi take saman kujera tana jinta yawa Sarauniya.... Bata ankara ba sai ganin Jamal tai duk’e gabanta... Cikin kid’ima take furta “Allah shi taimakeka kai min rai ka tashi a gabana kar wani ya shigo ya ganmu haka tsire kaina za’ai... Kai min rai ka tashi Rankaidad’e...!!” Duk surutun da take Jamal Bai tankata ba har saida ya ida abinda yake tsaf kana ya dafa sandarsa ya mik’e yana sakin murmushi... Jakadiya ta yunk’ura zata tashi amma mai..? Saiji tai k’afunfunta gaba d’aya an d’aure jikin kujerar... Ta d’ago a firgice tana duban Jamal da ya koma tamkar bai tab’a dariya ba... Murya na rawa take furta “Rankaidad’e... D’aureni Kai.. Rankaidad’e idan wani laifi nayi ka yafeni, tuba nake..!!” “Karki damu yau Sarauniya kike... Mulki zaki baza amma a saman kujerar nan...” Ya ida maganar yana mai d’aure hannayenta biyu jikin kujerar... Izuwa lokacin hanjin cikin Jakadiya sun soma kad’awa... Taga irin azaban da wannan mahaukacin yayiwa Jafar har suka zaci Jafar mutuwa yayi tsawon shekara guda wannan mugun ya kullesa yana azabtar dashi...bata fata ya kwatanta hakan da ita... Jiki na matuk’ar rawa take furta “Rankaidad’e... Wayyo ni Talle... Wayyo Allah na... Rankaidad’e kamin rai na tuba...!!” Yanda Ta rikice gaba d’aya sai ta zamto Tamkar mai laifi abinka da wacce bata k’ulla gaskiya da alkhairi tsawon rayuwarta... Gabanta ya k’araso bai daina sakin murmushin ba yace “Relax Jakadiya, ke ai yau Sarauniya ce... Har yanzu sai wasan kwaikwayon muke...!!” Jin haka yasa Jakadiya Ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an kana ta saki murmushi tace “Rankaidad’e ai ka bani tsoro ne...!!” Jamal ya tsareta da idanu yana mai ci gaba da karantarta, lokaci guda ya gyara tsayuwarsa jikin crutches d’insa kana yace “Jakadiya a matsayinki na Sarauniya saman karagarki wani hukunci zaki yanke wa bawan da yaci amanarki...?!” Jakadiya Ta jinjina kai tace “Hukunci mai tsauri, hukuncin da nan gaba bazai sake tunanin cin amanan bawa d’an uwansa ba balle Ubangidansa...!!” Jamal ya murmusa yace “Da kyau Jakadiya... Naji dad’in wannan shawari naki...!” Ya isa jikin ‘yar k’aramar jakan ya bud’e... Equipments d’in da ake operation ma dabba sune a jejjere cikin jakan.... Jakadiya ta ware idanu tana kallan k’araffan dake shirye cikin wannan ‘yar jaka.... Wata k’usa ya d’auko mai kamada noti ya k’araso kusan Jakadiya yana mai sakin murmushi yake furta “Nasan zaki tuna a zamanin da can baya kakanninku an masu huji a labb’an bakunansu yanda ake gark’ame bakunan nasu da kwad’o koh...?!” Jikin Jakadiya ya d’auki rawa, Ta shiga rawar d’ari tana mai furta “Rankaidad’e Yarima amin rai... Tuba nake...! Wllhi bani k’aunar zama Sarauniya... K’arya nake Rankaidad’e... Kaji k’aina kada ka azabtar dani... Wayyo ni Talle k’arshena yazo....!!” Ta k’arashe cikin murya irinta mai kuka... Tsawa ya daka mata yace tai masa shiru...! Jakadiya ta had’iyi kukanta tana mai rintse idanunta had’ida jinjina kai alamun tayi shiru.... ** A wane irin hautsine ya shigo ya tadda Ubangidan nasa... Mahmood ya mik’e daga kishingid’en da yake yana mamakin yanda Barde ya fad’o kansa haka... Har k’asa ya risina yana fidda haki yake fad’in “Tuba nake Allah shi baka yawan rai... A gafarceni...!!” Mahmood yace “Lafiya ka shigo haka nan...?!” “A gafarceni Rankaidad’e kira na samu daga matuk’i....!!” Sosai wannan karon ya kuma gyara zamansa yanda Barde yaci gaba da fad’in “Matuk’i ya nemi Gimbiya Zahrau ya rasata...!!” Baikai aya ba sak’o ya shigo cikin wayar Salulan Mahmood d’in wanda ba kowa Keda layin ba sai amintattun mutane... Bai kuma tsayawa sauraren Barde ba sai duba Sak’on da yake _We’ve your daughter your Highness, and if you want to see her alive you need to do exactly as we say.._ Cikin sauri ya shiga k’ok’arin dialing layin amma bata shiga... Wani sak’on ya kuma shigo masa _Don’t try anything foolish your Highness... Don’t involve cops, Kai even watchmen na cikin Fada do not involve them.... Kai d’aya mukeso kazo.._ Take aka rubuto masa address d’in location d’in da ake so yajesa.... Barde na gani Ubangidan nasa ya mik’e ya fice ba tareda yacedashi komai ba... Mota ya shige yana k’ok’arin dialing layin Zahra amma bai shiga... Cikin tsananin k’unan zuciya yake tuk’a motar yana falfala gudu saman kwalta... Bai zarce ko ina ba sai k’ofan gidan Turaki... Turaki na ganin wayar aminin nasa ya saki murmushi a hankali dan yasan dole Mahmood d’in ya nemesa, d’aya bazai Iya babu d’aya ba haka abotansu yake... Kaman bazai d’aga ba sai kuma ya d’aga shima babu wani walwala taredashi ya gaida Rankaidad’e... Daga d’aya b’angaren Mahmood yace “Ka fito Ina jiranka waje..!” Daga haka bai kuma cewa komai ba saima katse kiran da yai... Turaki ya tsaya juya wayar cikeda mamaki, yana nanata abinda Mahmood d’in ya fad’i masa... Bai ida tinanin ba ya soma jiyo sautin horn alamun dai da gaske yana k’ofar gidansa... Girgiza kai kurum Turaki yai ya mik’e ya nufo waje... Yana K’arasowa Mahmood da tuni ya hangosa Ta mirror ya zuge glass d’in “Get in the car..!” Turaki yai masa k’uri cikeda mamaki lokaci guda ya girgiza kai, lokaci guda kuma ya d’an saki murmushi yace “Rankaidad’e nasan gaba d’aya fad’in garin nan talakawan ka ne amma bazakazo har k’ofan gidana ka nuna min iko ba..!” Mahmood ya kaikaito yanai masa wane irin duba lokaci guda ya bud’e security lock yana mai furta “We don’t have much time... Please get in..!” Yanayin da yai maganan yasa jikin Turaki d’anyin sanyi, sai kuma ya gyara tsayuwarsa yace “I’m sorry your Highness but I’m not going anywhere har sai kamin bayanin ina zamuje...!” Izuwa lokacin Mahmood ya soma k’osawa da taurin kan Turaki.... Bai amsasa ba sai mik’a masa wayar da yayi daidai kan sak’on da aka turo masa... Turaki ya karance, lokaci guda ya d’ago yana duban Mahmood d’in a d’an firgice... Babu shiri ya finciki marfin motar ya shige, cikin ‘yar daburcewa yake furta “Your Highness bazamu biye tasu ba... We need to inform the authority right away..!” Katsesa Mahmood yai da fad’in “No Turaki hukuma bazata sani ba... can’t you see my daughter’s life is at stake here...! What if they did something to her... No bazamu kira kowa ba... We do exactly as they say..!!” Turaki ya jinjina kai a hankali yace “Toh mai suke buk’ata... Did they ask for Ransom..?!” Girgiza masa kai yai alamun a’a sai kuma yace “Ina zaton ba kud’i suke buk’ata ba nid’in suke buk’ata... Kuma duk bazai wuce akan wannan banzan sarautar ba... Mai yuwa rayuwata suke nema domin su cimma burinsu na d’akewa Karagar nan... Turaki son duniya da Mulki ba abinda ba zaisa mutane suyi ba...!” Turaki ya jinjina kai yace “Tabbas it might be a trap... Rayuwarka suke buk’ata ba kud’in Fansa ba... Rankaidad’e shisa nace muyi abin in the right way... Let’s call the cops right away...!” Saurin dakatar dashi Mahmood yai da fad’in “Have you ever lost your loved one...? Turaki rayuwar d’iyata muke magana a nan... No one must know about this... I’ll submit myself to them idan hakan zaisa su sakar min d’iyata..!!” Ya k’arashe yana mai sakin huci... Turaki ya jinjina kai cikeda tausayin abokin nasa yace “I’m sorry your Highness, I understand where you’re coming from... Amma abinda nakeso yanzu muyi before mu confronting kidnappers d’in let’s check the hospital first... Maybe sunga wani abu... Ko ma su nuna mana CCTV footage d’insu watak’ila mu samu wani clue gameda kidnappers d’in kuma shima driver d’in da ya kaita dole Mu bincikesa tinda kace tareda Jakadiya ka had’asu suka fita..!” Mahmood ya jinjina kai ba tareda yace komai ba... Ganin irin driving d’in da yake yasa Turaki karb’an motar yaci gaba da tuk’asu... Koda sukaje asibiti suka tadda driver d’in duk a rikice nan yake sanar dasu Zahra ita kad’ai ta fito ba tareda rakiyar Jakadiya ba, sannan masu kula da majinyata na cikin asibitin sun tabbatar masu Zahra ta shiga wajen Fu’ad tareda wata mace... Saidai babu wanda yasan macen da Zahra Ta shigo da ita amma kam tabbas ba Jakadiya bace... Koda suka shiga wajen Fu’ad suka tambayesa ko zai iya tuna matar da Zahra Ta shigo tareda ita Fu’ad d’in bai iya cewa komai ba sabida halinda yake ciki dukda cewa gashi kaman so yake ya masu magana... Mahmood ya matso jikin gadon Fu’ad ya d’an rank’wafo kad’an yana kuma tambayarsa cikin tsanaki “Fu’ad try to remember something... Who’s that woman..? Please Fu’ad your niece’s life is in danger... Please try to remember something..!!” Kallonsa kurum Fu’ad yake hawaye na gangaro masa yana son yin magana babu hali.. Lokaci guda ya shiga buge buge yana tak’urewa waje guda... Babu shiri nurses d’in suka k’araso suna rok’on Mahmood ya fice sabida jikin Fu’ad d’in da ya kuma rikicewa... Turaki yai k’ok’arin janyo Mahmood d’in suka fice waje, shi kansa Turaki tsananin tausayin ahalin Mahmood ke d’awainiya dashi.... Suna fitowa daga wajen Fu’ad Mahmood ya buk’aci a nuna masu CCTV footage na asibtin saidai akai rashin sa’a Cameras d’insu gaba d’aya basa aiki... Huci kurum yake sakarwa yana fad’ida Turaki “You see... K’asarmun kenan, komai babu maintenance babu management mai kyau... Ba dole ta’addanci yayi yawa ba..!!” Turaki ya jinjina kai yace “Hakane Rankaidad’e saidai muyi addu’an Allah ya kawo mana sauk’i... Shisa muke so mu samu shuwagabanni ire irenku wanda zasu kawo mana sauyi... Ka bar batun komawa Spain d’in nan ka karb’i ragamar mulkin Masarautarmu..!” Bai tsaya sauraren Turaki ba ya nufi mota.. Tuni Turakin ya take masa baya, daidai sanda sak’o ya kuma shigowa Mahmood cewa idan yana son sake ganin d’iyarsa da rai yazo address d’in da aka turo masa nan da mintoci da basu gaza arb’ain ba idan kuma ba haka ba ya shirya d’aukan gawar d’iyarsa... Time ya soma reading tik tok..!! Jifa da wayar yai ya finciki d’an makullin hannun Turaki ya shige Mota ba tareda ya kuma bi takan Turakin ba... Turaki na k’ok’arin tsaidashi inaa tuni ya kwali motar ya fice daga cikin asibitin... Haka Turaki yai tsaye yana duban motar har ya fice... Yana ficewa Turaki yai saurin ficewa daga asibitin ya tari motar haya dukda baida tabbacin location d’in da Mahmood ya nufa.... SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *57* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Mamaki ne ya cikasa ganin motar Yazeed pake farfajiyan gidan da aka tura masa adireshin... Toh meke faruwa..? Badai tsanar da Yazeed yai masa har ya kawo wannan munzanin ya nemi cutar da d’iyarsa ba... Kai Yazeed bazai haka ba, dikda cewa yasan baida hali akasarin lokuta amma zai wuya ace zai aikata abu makamancin wannan... Jiki babu laka Mahmood yaci gaba da takowa yana k’arema gidan kallo har ya iso jikin k’ofar da zai sadaka da asalin cikin gidan... Shewan mutane mace da namiji da ya soma saurare ne ya sanyasa d’an dakatawa kad’an daga jikin k’atoton window na parlorn... “Gaskiya zanyi kewarki... Wai haka kika k’ara sugar, tab lallai da bakizo ba dana tapka babban asara dan wannan garan tsaf Mahmood ne zai kwashe... Amma ko yanzu saidai ya sami saurana..!” Ya k’arashe shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa... Raheema ta rausayar da idanu tace “Ai kama kasan nid’in bata wasa bace na d’ara matarka sau babu iyaka, kuma duk cikin matan da kake Mu’amala dasu babu wacce takaini... Aini bari kaji Yazeed duk d’ah namijin da ya riga ya shiga hannuna toh fah zai wuya ya iya manceni... Haka nan nake da tsayuwa a zuciya, ko shi Mahmood d’in da yake wani jin kansa yana ganin ba auren soyayya zai dani ba auren jeka nayika ne kawai to save his daughter da zaran ya shigo hannuna Ina mai tabbatar maka zai sauk’e wannan jin kan nasa ya susuce akaina... Daga nan sai yanda nayi dashi nayi da d’iyarsa, kai k’arewa wannan shegiyar d’iyar tasa da ya samota Ta gurb’ataccen hanya sai na rabasa da ita dan bana buk’atan bastard child d’insa a gidana... ‘Ya’yan sunnah zan haifa masa...!!” Yazeed bai daina shafa hab’arsa ba idanu a kannare yake dubanta, lokaci guda yaci gaba da furta “Allah Sa Ki jure rashina kusanki dan Yaya na bazai iya dake kaman yanda ni na iya dake ba...!” Raheema Ta kuma murmusawa tace “Haka kake tunani.. Ai ba’a sanin maci tuwo sai miya ya k’are... Kai ko a ido kasan Yarimana Gwarzo ne ba rago ba... Wani abin ma sai mun d’aga zuwa k’asar Spain na kashesa da kissa da makirci tinda na kula asiri bai tasiri akansa... Da kissa zalla zan rabasa da wannan shegiyar d’iyar tasa muci soyayyarmu a k’asar Spain...!” Yazeed ya kuma murmusawa yace “Toh Nidai kar a cikani da zancen Mahmood, tinda yau d’in gaba d’aya nawa ne..!” Ya k’arashe yana mai kuma janyota kusansa... Raheema na murmushi take furta “Karka damu ai yau d’in gaba d’aya takace dan ko masarauta babu wanda zai San nazo... Till down za...!!” Bai juri k’arasa sauraren maganganun nasu ba yai saurin juyowa idanunsa na kuma kad’awa... Saidai d’aga idanun da zai yaga Zuhra tsaye tana hawaye... Mahmood ya dubeta da mamaki sai kuma ya juyo yana duban k’ofan parlorn, bazaiso ta shiga taga wannan mummunan cin amana da k’awarta da mijinta sukai mata ba... Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali dan baisan da mai zai soma ma Zuhra ba... Zuhra na hawaye take girgiza bata tsaya sauraren Mahmood dake k’ok’arin dakatar da ita ba ta finciki k’ofar parlorn.... A wane irin firgice Raheema ta mik’e zuciyarta na kuma tsinkewa... Hawaye na gangaro mata take dubansu... Take Raheema tai saurin kame bakinta had’ida d’aura hannu aka... Lokaci guda ta silale saman gwiwoyinta tana duban Zuhra dake zuban hawaye... “Zuzu wllhi ba yin kaina bane... Zuzu dan Allah Ki yafe min...!!” Yazeed ne ya katseta da fad’in “Ke dallah shut up... Kar Ki ishe mutane... Uban mai akai mata...?!” Ya dubi Zuhra dake tsaye wajen idanunta sun kad’a sunyi jazir yace “Ke Uban mai ya kawoki wajen nan..? How did you get here..? Da izinin wama kika fito...?! Zaki bud’e baki kiyi magana ne Ko sai na K’araso wajen na faffalla miki mari..!!” Cikin tsananin huci Zuhra Ke furta “Try it please...! Ka kwatanta marina Yazeed, yau ni kuma zan nuna maka jinin mulki da sarauta na nan na Yawo jikina... Azzalumi macuci maci amana... Ka cuceni ka zalunci yaranmu tirr ace kaine mahaifin ‘ya’yana... Nayi nadaman had’a zuri’a dakai, amma ka saka a ranka daga yau ni Zuhra na gama zaman aure dakai... Kuma ka jira hukuncin da zan yanke..!!!” Tana ida fad’in haka tasa kai zata juya... Raheema tai saurin rarrafawa ta kamo bakin zaninta... “Aminiyata dan Allah Ki yafe min, wllhi sharrin shaid’an ne kuma tilasta min Yazeed yayi... Wllhi ba halina bane... Dan Allah karki bari Yarima Mahmood yaji wannan batu nayi imani fasa aurena zai... Dan Allah Zuhra kimin rai kimin wannan alfarmar kinji k’awata...!” “K’awa...?!” Zuhra Ta nanata tana dubanta, lokaci guda tai murmushi wanda da gani kasan na takaici ne “Amma lallai na yarda Raheema bakida kunya, kuma baki gaji kunya ba... Anya Ke jinin babban Gida ce... Babu Gimbiya ko Sarauniya da zata watsar da kanta taci mutuncin kanta kaman yanda kikayi... Wllhi ko a haka kin shafawa Masarautarku b’ak’in fenti wanda zai wuya ya shafe.. Bani kika cuta ba Raheema..! Kanki kika cuta.. Kin cuci rayuwarki, kin kwab’ar da duk wani daraja da k’ima da Allah yayi miki a matsayinki na d’iya mace... Kin yaye Hijabin mutunci da Allah ya halicceki da ita... Kin..!” Yazeed ya katseta da fad’in “Idan kin gama wa’azin naki ki fice kuma kije ki jirani a gida... Ina nan zuwa dan wllhi kinji na rantse sai na hukuntaki..!!” Zuhra ta d’ago tana watsa masa duban k’yama... Lokaci guda Ta murmusa tace “Zakasha mamaki irin wanda baka tab’a sha ba Yazeed..!!” Daga haka fincikan mayafinta tai daga hannun Raheema had’ida shureta da k’afarta tasa kai Ta fice abinta... Zuciyarta na tsananin mata zogi... Tana fitowa ta tadda babu Mahmood alamun ya tafi... Mota ta shige ta kifa kanta tana kuka sosai... Driver d’in da Hadimarta dake jiranta daga nan waje cikin mota abin sai ya masu wane iri ganin shugabar tasu tana kuka.. Hadimar tata ta umarci driver d’in ya fice daga cikin motan ya d’an basu waje taji damuwar Uwargijiyar tata... Driver yayi yanda tace Hadimar ta d’an risina tace “Rankidad’e kuka bai kamaci kyakkyawar Gimbiya irinki ba... Ko akwai abinda zan iyayi na tsaida hawayen shugabata masu tsada su daina zuba..?!” Zuhra ta d’ago Tai k’ok’arin saita kanta “Babu komai Hindu kiyi magana ma driver ya shigo mu koma masarauta...!” Baiwar data kira da Hindu ta dan jinjina kai sai kuma tace “Ki gafarceni ya Shugabata, Kodai wani abin tashin hankalin kika gani cikin gidan nan..?!” D’an daka mata tsawa tai da fad’in “Nace miki babu komai Hindu, Ki kirawo Driver mu tafi... Bana son gardama..!!” Hindu Ta risina tace “Tuba nake Rankidad’e... Kimin aikin gafara..!!” Ta k’arashe tana mai bin umarnin shugabar tata... Har suka isa masarauta Zuhra bata daina matsan k’walla ba tana tina kalan cin amanar da K’awarta aminiyarta da mijinta sukai mata... ** A b’angaren Mahmood kaw tinda ya bar wajen yake falfala gudu saman kwalta, clash Turaki yayi da motar tasa yai saurin takewa Mahmood d’in baya... Ganin irin tuk’in da yake kaman wani mai shirin barin gari yasa Turaki umartan mai tasi d’in yasha gaban motar Mahmood... Haka mai tasi d’in ya k’ure malejin motar saida suka cimma Mahmood d’in... Turaki ya sallami mai tasi kana ya nufo yanda Mahmood d’in ya paka motarsa.... “Rankaidad’e Wai mai ya faru...? Ina Zahran...? Ya na ganka kai kad’ai, badai wani abin sukai mata ba koh...?!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Mahmood ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Turaki dasu... Sosai Turaki ya razana da yanayin abokin nasa... Murya na rawa yake furta “Rankaidad’e... Kamin magana dan Allah...!!” Bud’e masa lock yai ba tareda yace komai ba, Turaki ya shige cikin motar Jiki a matuk’ar sanyaye dan shi dik a zatonsa wani abin ne ya sami Zahra... Suna tafe a motar babu mai cewa uffan, sai falfala gudu da Mahmood keyi dasu bisa kwalta... Idan ya danna birki saidai Turaki ya dubesa, Turaki ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali har suka iso wani waje mai yawan ciyayi da duwatsu... Shidai Turaki duban Mahmood d’in kurum yake a matuk’ar tsorace da yanayin nasa... Murya can k’asa yace “Kenan a wannan dajin suka b’oyeta...?!” Sai lokacin Mahmood yace “Ita wa..?!” Turaki da mamaki yace “Rankaidad’e Zahra’u nake nufi...!” Nusawa Mahmood yai kad’an kana ya juyo yana duban Turaki idanunsa na kuma kad’awa, ya fuzar da fuci mai d’umi yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa... Lokaci guda ya zauna saman Dutse guda d’aya had’ida kalmashe k’afarsa guda... Turaki ma ya k’arasa ya zauna jikina sanyaye “Rankaidad’e...” Bai bari ya ida fad’in abinda zai fad’i ba yace “Zahra bazatai wannan tunanin ita kad’ai ba... Ta yaya ma zata San cewa akwai wata alak’a mai muni tsakanin Yazeed da Raheemah... Dole akwai wanda ya shirya mata hakan..!” Ya k’arashe yana mai duban Turaki... Turaki da gaba d’aya ya zama confused yace “Your Highness... Ban fahimceka ba.. Wai meke faruwa ne..?!” Cikin kalmomi k’alilan Mahmood ya sanar dashi abinda ya faru a gidan da sukai zaton an aje Zahra... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Turaki Ke nanatawa yana jinjina lamarin “Turk’ashi..!” Ya d’an nusa kad’an sai kuma yace “Abokina Allah ne ya soka da alkhairi ya nuna maka hakan tun kafin akaiga aure... Amma kuma maganarka akwai k’amshin gaskiya cikinta Rankaidad’e, Zahra bazata iya tsara wannan abin ba, dole akwai wanda ya tsara mata hakan... Toh amma wa kenan..?!” Mahmood ya d’an dubesa yace “Na tadda Zuhra matar Yazeed a wajen wanda bansan ya akai taje wajen ba... It might be possible Zuhra tasan komai tuntuni ko tana zarginsu sai ta had’a wannan plan d’in domin ta kamasu red handed..” Turaki ya jinjina kai yace “Kaji tunani na manya.. Tabbas haka ne Rankaidad’e, kuma ko acan asibiti ma an tabbatar mana Zhara tajeta tareda wata mace... Ko shakka babu hakan ne..!” Mahmood yai shiru tamkar mai nazari har lokacin ransa a matuk’ar b’ace yake.. Turaki ya d’an sadda kai yace “Hak’uri zakai Rankaidad’e, ita rayuwa...” Duban da Mahmood d’in ya aika masa ya hana Turaki k’arasa magana.. Lokaci guda Mahmood d’in Ke fad’in “Maiyasa kake bani hak’uri bayan nan tab’a sonta ba... Abinda ya dameni shine involving Zahra da akai... Bai kamata tasan ire iren wad’annan abubuwan ba... Why must she involve my daughter, da ni ta samu da batun yafi Ta samu d’iyata da irin wannan batu...!” Ya k’arashe cikin tsananin nuna b’acin rai... Turaki ya d’an shafi kansa yace “Haka ne Rankaidad’e amma kasan ba kowa zai iya samunka da wannan batu ba... Watik’ila shiyasa Ta biyo Ta wajen Zahra...!” Mahmood ya katsesa da fad’in “That doesn’t justify what she did....she shouldn’t have involved my daughter... !!” Turaki ya risina yace “Allah ya huce zuciyar Sarki... Tuba take Allah shi taimakeka, itama na tabbata tana cikin tashin hankali tinda Yazeed mijinta ne... A gafarceta Rankaidad’e..!!” Ya k’arashe yana risinawa gaban Mahmood d’in... D’an girgiza kai kurum Mahmood yai yace “Tashi mu tafi...!” Babu musu Turaki ya mik’e yana fad’in ya kamata suje masarauta suga halinda Zahra ke ciki... Yai maganar yana mai amsar car keys d’in Mahmood d’in.... ** Koda suka iso masarauta Mahmood ya tadda Zahra bacci ma take hankali kwancewa a d’akinta... Yai mata k’uri kaman mai tinanin wani abu, lokaci guda ya janyo mata k’ofan d’akin ya rufe... Yana ficewa Zahra ta bud’e idanunta a hankali tana sauk’e ajiyan zuciya lokaci guda tana addu’an Allah yasa Plan d’in Aunty Muhibbah yayi aiki akan Paa d’inta zai fasa Auren wannan mai suffar mayun.... Ta k’arashe tinanin nata tana mai darawa harda ‘yar tsallanta saman gado.... Mahmood na ficewa sashensa ya komo yanda ya tadda Zuhra zaune saman darduma alamun isowarsa take jira, har lokacin bata daina matsan hawaye ba.... Tana jin sallamansa tai k’ok’arin saita kanta had’ida risinawa Ta gaidashi... Mahmood ya amsa cikeda tausayinta yasan tayi hak’urin zama da d’anuwansa... Can kujerarsa ya isa ya zauna kana ya soma fad’in “Zuhra, Yazeed mijinki ne kuma nasan kinyi hak’urin zama dashi tsawon shekarun da kukayi tare... Bazan hanaki yanke duk hukuncin da kikaso gameda ci gaba da zama dashi ba... Idan kin yanke hukuncin tura sak’o Masarautarku bazan hanaki ba sabida Ke aka zalunta, sannan idan kin yanke hukuncin komawa Masarautarku shima duk bazan hanaki ba... Kinada duk wani zab’i gameda ci gaba da zamanki cikin Masarautar nan... Idan har ni ne Sarki zan baki goyon baya d’ari bisa d’ari akan duk hukuncin da zaki yanke... Amma saidai inaso na miki wata tambaya Zuhra.! Shin ya akai kikasan abinda Ke wakana har kika tafi wancan gidan..?!” Ta risina kad’an tana goge hawayen da suka kuma gangaro mata “Rankaidad’e sak’o na samu an turo min cikin wayata cewa Yazeed yana cikin wane yanayi naje na cecesa... Shine najeni nai wannan mugun ganin...!” Mahmood yai shiru yana mamakin jin cewa itama batada masaniya gameda alak’ar Yazeed d’in da Raheemah..! Jinjina kansa yai a hankali sai kuma ya d’an nusa yace “Kikace sak’o aka turo miki da bak’uwar lamba..?!” Zuhra ta jinjina kanta a hankali “K’warai Rankaidad’e, sak’o aka turo min gashi ma ka gani..!” Ta k’arashe tana mik’a masa wayar.... Ya duba sak’on sosai kana ya ciro wayarsa yai comparing sak’wannin... Lambobi daban daban ne suka tura masu sak’on... Koda yayi dialing wannan lambar ma bata shiga... Watak’ila ma mai turo sak’on ya karya SIM cards d’in... Fuzar da fuci yai a hankali ya mik’a mata wayar... Ta tabbata Zuhra kanta batada masaniyan cin amanan da mijinta da k’awarta suke mata sai yau... Mutum gudace zata amsa masa tambayoyinsa itace d’iyarsa Zahra.... Ya d’anyi gyaran murya Murya kad’an yace “Sanda kika tadda Yazeed da Raheema sunada masaniyar naje wajen..?!” Ta girgiza masa kai a hankali alamun a’a ta k’arada”Basu sani ba Rankaidad’e dan Raheemah har rok’ona take kada na sanar dakai don kar ka fasa aurenta..!” Ya jinjina kai a hankali yace “Yayi kyau..!” Ya numfasa kad’an yace “Zan nemi wani alfarma a wajenki..!” Zuhra tai saurin d’agowa tana saurarensa cikeda jin nauyin Kalmar alfarma da ya bid’a daga gareta yana Sarki, Allah yasa ba cewa zai ta yafewa Yazeed ba..! Tana tsaka da tunanin ta sinkayo muryar Mahmood d’in naci gaba da fad’in “Banaso Raheemah ko Yazeed susan cewa nasan wannan batu ko kad’an... Zaki Iya min wannan..?!” Zuhra Ta jinjina kai tace “Bakada matsala Rankaidad’e... In sha Allah bazan tab’a sanar dasu cewa kasan komai ba...!” Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Kina iya tafiya..!” Ta risina tai masa sallama kana Ta fice jiki babu laka.... A hankali ya mik’e yana zaga parlorn nasa cikin taku d’aid’ai irinta masu Mulki.... ** Sauri sauri ta ida had’a kayanta kaf dan Allah ya gani bazata kuma kwana ko guda cikin Masarautar ba tinda Ta gama abinda ya kawota... Ta tabbata yanzu Mahmood bazai yarda da auren Raheema ba sannan Zuhra bazata ci gaba da zama da Yazeed a wannan masarauta ba... Auren Yazeed zai lalace Zuhra zata koma Masarautarsu tareda yaranta Yazeed zai zama baida kowa dan bayan abinda Mahmood ya gani bazai tab’a barinsa yayi sarauta ba... Kuma tayi imani idan maganan ya isa Masarautar su Zuhra babu Masarautar da zasu kuma yarda su baiwa Yazeed mata, shikenan martabansa ya zube... Zai rasa ahalinsa ya kuma rasa Sarautar, sannan Jamal ko yanayin da yake ciki ya ishesa Ta tabbata idan yayima Jakadiya horon da hankali bazai d’auka ba Umaima zatak’i amincewa da aurensa... Giwa kuwa halinda yaranta da MasarautarTa Ke ciki kad’ai ya isheta kuma tasan ko ba jima ko ba dad’e Ja’afar da Mahaukaciya Izzatu harmada Ubandoma zasu dawo sannan ne Giwa zata girbi duk abinda ta shuka...! Ta saki murmushi a hankali kana Ta janyo jakan kayanta, sauri sauri ta fice daga cikin Masarautar... Tsaye tayi daga can nesa tana k’arewa Masarautar kallo, a hankali ta furta “Alhamdulillah..! A yau ni Saudatu na kammala abinda ya dawo dani wannan Masarauta mai bak’in tarihi a gareni... Zan koma ga mutaneda suka amsheni suka maidani mutum bayan an wulak’antani anci mutuncina an tozartani...! Ni Saudatu Sabon shafin rayuwa zai kuma bud’e min tareda masoyina na gaskiya Dr Ansar..!!” Ta saki murmushi a hankali kana tasa kai rik’eda jakan kayanta... Sanda ta isa tashan mota ta samu babu motar da zata kuma tashi saidai Washe gari... Wata mata mai saida abinci bakin tasha ne Ta taimaka mata da wajen kwana zuwa Washe gari, Akai sa’a matar mai mutunci taceda ita budurwa kamanta haka bai tsari ta fito tashan motoci cikin dare ba sabida yanda duniyar Ta lalace, mugaye sunyi yawa wani dama kad’an zai samu sai ya cutarki... Muhibbah tai mata godiya sosai tace ta riga ta fito daga cikin makaranta ne kuma idan Ta koma baza’a bud’e mata shiyasa amma in sha Allah nan gaba zata kiyaye... Taita mata godiya kan taimakon da tai mata... Washe gari kuwa motar sassafe tabi zuwa garin Bauchi... ** Dandatson mutanen da ta ganine a unguwar tasu yasa gabanta mugun fad’uwa... Ko ba’ace ba taron d’aurin aure ne.. Toh auren wa ake d’aurawa..?! Tambayar da taiwa kanta zuciyarta naci gaba da tsinkewa... SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *58* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Bata iya bi Ta gaban masallacin unguwar tasu ba wanda yake babu nisa da gidansu hakan yasa mutane har k’ofar gidan nasu, ga kuma ababen hawan mutane a pappake Kota ina... Cikin sauri ta canza hanya tabi ta k’ofar baya k’irjinta naci gaba da bugawa musamman data hango Ansar tsakiyan abokansu sunata d’aukan hotuna, yasha farar shadda k’al kaman wani Ango... Jiki babu laka ta nufi cikin gidan ta nan k’ofar bayan yanda ta tadda Iya Larai na shanya... Ganin babu mutane cikin gidan nasu ya d’an sauk’ar mata da natsuwa k’ila auren d’aya daga cikin abokansa ake a unguwar... Suka gaisa da Iya Larai tai mata sannu da zuwa sai zolayanta take da fad’in “Amarya ta dawo Amarya Ta dawo...!” Wad’annan kalaman Iya Larai d’in ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba “Amarya kuma..?!” Ta nanata a hankali... Kardai hasashenta ya zamto gaskiya..?! Bata iya kuma tsayawa sauraren Iya Larai ba sai sa kai da Tai cikin gidan tana ganin hanya na had’e mata... Babban abinda ya kuma sanyar mata da jiki shine hango akwatuna da kayyaki barbaje tsakiyar parlorn da tai, Mommy da wasu k’awayenta guda biyu Anty Gudidi da Aunty Salamatu sai shirya kayayyakin suke wanda komai set biyu ne... Aunty Salamatu fad’i take “Oh Ansar mai tagwayen mata... Kaga yaro d’an baiwa... Mommy dai sai murmushi take tana Allah san barka yayinda Anty Gudidi ke faman tab’e tab’en baki tana fad’in “Ni wllhi bansan dalilin da yasa kika aje tsintacciyar mage gidanki ba Murjah... Kuma Wai har k’i k’are kice zaki had’ata aure da d’anki... Tabd’im haka kawai babu wanda yasan asalinta, yarinya ta zauna ta tsara maku k’arya kun yarda.. Waima a wace duniyar kika tsintota ne..?!” Mommy Ta katseta da fad’in “A’a Gudidi, Muhibbah ba tsintacciyar mage bace, d’iya ce kaman kowa... Sau nawa zance miki a hanyarmu Ta dawowa daga Lafia muka tsinceta can wajajen dajin garin Jos, wllhi abin tausayi b’arayin daji sun kashe Iyayenta makiyaya suka k’ona rigarsu da dabbobinsu itama suka biyota zasu kasheta Allah yasa muka tsinceta, lokacin Ansar na ajin k’arshe a Secondary sch hasalima d’aukosa mukaje can makarantarsa dake Nasarawa Lafia toh a hanya muka tsinceta, Ansar da Sabo driver na suka dage kan cewa mu taimaka mata... Muka d’aukota muka kawota gida mukai mata duk abinda ya dace har makaranta ta koma... Kuma ban tab’a danasanin rik’e Muhibbah ba musamman da yanzu zata zamto matar d’ah nah..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta... Aunty Salamatu tace “Oh Allah sarki gaskiya Hajiya Murjah kinada zuciya mai kyau, Keda kika amshi musulunci daga baya har kin fimu da muka taso cikin musulcincin zuciyar imani... Allah k’ara ire irenku masu taimako babu dalili...!” Aunty Gudidi Ta katseta da fad’in “Ba maganan imani ake a nan ba, maganar makomar d’anta muke... Wayasani koma B’arayin dajin sune iyayen yarinyar nan, haka kurum d’anki ya auri dangin ‘yanfashi azo ana haifa maki jikoki ‘yantadda babu gaira babu dalili... Shifa aure d’an asali ne... Asali ake jiye miki Murjah da abinda ka iya zuwa yazo in the future...!” Daidai lokacin Muhibbah tai sallama jiki a sanyaye, Mommy Ta fad’ad’a murmushinta “A’a Hibbatu... Lale lale barkada sauk’a...!” Ta k’arashe cikeda fari’a... Muhibbah na murmushi ta k’araso ta duk’a gabansu kanta a k’asa Ta gaidasu.... Mommy da Aunty Salamatu ne kawai suka amsa mata da sakin fuska ita kaw Gudidi a dak’ile Ta amsa mata tana aika mata muguwar kallo... Mommy tace “An gama jarabawar lafiya inji..?” Muhibbah ta jinjina kai a hankali “Eh Mommy..!” “Toh Masha Allah... Ubangiji ya baku sa’a... Kinga kin dawo a daidai ga kayyakin Ki nan da na ‘yar uwarki Hameedah...!” Muhibbah dai bata iya cewa komai ba sai sadda kanta da Ta kumayi tana k’ak’aro murmushi da k’yar... Aunty Salamatu tace “Oh Murjah bakya bari ko d’an surkunta ya soma shiga tsakaninku ba... Duk kinsa tana jin kunya... Tashi Ki shige abinki..!” Mommy Fad’i take “A’a babu wani surkunta tsakanina da d’iyata...!” Gudidi Ta katse zancen da fad’in “Ke tashi kije kin wani zauna kin tsare mutane yaran yanzu babu kunya...!” Muhibbah bata kuma cewa komai ba ta mik’e ta nufi ciki Mommy na fad’in maza tai wanka ta fito taci abinci.... Shigewan Muhibbah da kad’an Ansar ya shigo gidan ya taddasu Mommy nan a parlorn suna ci gaba da sorting kayayyakin... Aunty Salamatu Ke zolayarsa da fad’in angon wani sati ita kaw Aunty Gudidi sai yatsina baki kurum take dan Allah ya gani bata fata ayi wannan aure, ita da zata samu sarari ma zata kuma ziga Yawale koda wasa kada ya biyewa Murjanatu na aurawa d’an d’an uwansa tsinatcciyar mage... Aunty Salame ke sanar dashi Muhibbah ta dawo tana ciki... Ai tuni ya mik’e yana sosa kai tana ci gaba da zolayarsa mai tagwayen mata... Silalewa yai ya nufi corridor, yana k’ok’arin knocking kenan Ta bud’e k’ofar alamun zata fito... Sukai tsaye suna duban juna, sosai shigar manyan kayan ya amshesa dashike ba gwanin saka manyan kayan bane.... Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi kana Ta matsa Ta basa hanya ya shigo... Daga can gefe ta zauna Shiko na tsaye jikin k’ofa, Muhibbah ta gaishesa babu wani walwala tattareda ita... Harga Allah kalaman Aunty Gudidi ya tsaya mata a rai, sai tana jin tabbas Ansar bai cancanceta ba... Gyara tsayuwarsa yai yana mai tsareta da idanu “Mun d’aura auren k’awarku Azeema yau wata sati kuma a d’aura naki...!” D’an Murmusawa tai tace “Aw Wai dama auren Azeema ake..?!” Ansar ya jinjina kai yace “Eh Musbahu ya zama Ango...” Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Allah sarki, Allah yasa albarka... Ai Azeema da Musbahu sun dace da juna..!” (Azeema da Musbahu dukansu ‘yan Estate d’in ne kuma Musbahu aminin Ansar ne Azeema kuma islamiyansu guda dasu Muhibbah.. Taron aurensu Muhibbah ta tadda..) Ganin yanayinta yasa Ansar d’an nusawa yace “Kema Rana itiyau an d’aureki...!” Ta d’an dubesa da mamaki tace “Next week fah kake magana..?!” Ansar ya jinjina kai yace “Bakiga su Mommy a parlorn suna had’a lefe ba..” Ta jinjina kai a hankali tace “Na gani... Amma sai inaga next week kaman yayi kusa...!” Ansar ya d’an tako kad’an ya jinginu jikin dressing mirror yana mai karantar ta “Mai yasa zakice yayi kusa bayan cikan burinmu kenan mu kasance tare...” Gyara zamanta tai tana mai duban wani b’angaren, lokaci guda Ta fuzar da fuci a hankali tace “Ba haka nake nufi ba, ai inaga aure yana buk’atan shiri balle ma Amarya wacce aka santa da wasu ‘yan kintse kintse...!” Yana murmushi ya furta “Relax Amarya Ta to be, Baffah Yawale ne ya matsa a d’aura auren gaba d’aya next week tarewa Mommy tace ba yanzu ba sai ta gama shirin bukinta, kinga auren kawai za’a d’aura ba wai tarewa zakiyi yanzu ba... Nima gidan nawa akwai fittings da ba’a gama ba, Ki kwantar da hankalinki kina nan tareda Mommy har nan da wata guda... Ku gama duk wani shirye shiryenku da zakuyi Keda Mommy, wata guda ai ya isheku..!” Ta murmusa kad’an har lokacin babu walwala tattareda ita... Gyaran murya yai kad’an yace “Hibbah kalleni nan..!” Ta d’ago idanunta masu rauni tana dubansa “Maiyasa nake ganinki haka..? Ko baki Farin ciki ne..?!” Hawayen da ya gangaro mata tasa hannu Ta share, lokaci guda take furta “Ba haka bane Yaya Dr, gani nake kaman baka cancanceni ba... Kar ka mance Mommy batada masaniyan gaskiyar abinda ya sameni, idan nayi shiru na aureka a haka Anya na kyautawa Mommy..? Kai d’aya ne d’anta.. Mommy Ta cancanci sanin komai kafin aurenmu..!” K’arasowa yai ya d’an duk’a gabanta yana kallon yanda hawaye ke gangaro mata... Lokaci guda yake girgiza kai “Hibbah no... Ba lallai sai Mommy tasan abinda ya sameki ba, ni ne zan zama mijinki kuma naji na gani nayi accepting d’inki yanda kike... I don’t care if you’re a rape victim... Ba son ranki bane hakan ya faru dake, Maiyasa zan k’yamaceki bayan nasan k’addara na kan kowa... Su wad’anda suka aikata laifin sune ya kamata suji kunya... Hibbah I...!” Cikin kuka Ta katsesa da fad’in “Kana fad’a min haka ne dan naji sanyi a zuciyata... Amma bazan tab’a zama kaman ko wacce mace ba... Sun cuceni Sun zalunceni Sun d’auke min abinda yafi komai mahimmanci da daraja a gareni... Ansar ko baka fad’a min ba nasan dole can k’asan zuciyarka kana jin zafin abin... Maza har Uku sun lalata rayuwar macen da zaka aura lokaci guda..!!” Daidai nan Anty Gudidi Ta shigo tana tafe hannaye had’ida salallami “Na shiga uku ni Gudidi mai nake ji... Maza har uku, d’aya biyu uku... Sauransu zaka aura Ansar... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Yau na shiga uku ni Gudidi ka kaita ina... Wllhi Allah ya tsari gatari da saran shuka..!!” Ansar ya tareta da fad’in “Aunty ki dakata, ki saurareni..!” Bata dakata d’in ba sai ci gaba da tafe hannaye take tana salallami tana doka kira wa Mommy “Murjah..! Murjah!! Na shiga uku ni Gudidi Toh kizo kiji abinda nakeji a nan..!!” Daidai sanda Mommy da Aunty Salame suka k’araso a firgice suna tambayan Gudidi meke faruwa... Nuni tai masu da Muhibbah dake zaune saman stool kanta kife tana hawaye Ansar tsaye gefe idanunsa sunyi jazir yana aikama Gudidi muguwar kallo.. Mommy tace “Gudidi meke faruwa kike salati haka kaman anyi rashi..!” “Yo ba gwara mutuwa ba da abinda naji... Gata nan Munafuka ta bud’e baki ta fad’i maki... Ta wane sinne kai zatai rufa rufa Ta aure miki d’ah..!” Ansar ne ya katseta da fad’in “Ya isa haka Aunty... Bai kamata Ki saka Muhibbah gaba kina aibatata ba... Babu abinda ta miki na aibu..!” “Kai rufe min baki shashasha.. Wannan ai aurenta da kake k’ok’arin yi shine babban aibu... Ace namiji ba d’aya ba ba biyu ba har uku sun gama watsewarsu da ita kai kuma da yake hidahumi ne shashasha zaka yarda ka aureta a haka har kana wani cewa ba son ranta bane..!” Cikin tsananin k’unan rai Ansar ke fad’in “Eh Aunty I don’t care idan duka mazan duniyar nan ne suka lalata mata rayuwa sabida ba laifinta bane, itama bata tab’a fatan hakan ya faru da ita ba... Akan mai za’a dinga nuna k’yama da tsangwama ga wad’anda tsautsayi da k’addarar fyad’e ya auka masu.. Shin son ransu ne..? Shin suma bazasuyi fatan su kasance kaman ko wacce mace bane..? Aunty rape victims sunada ‘yanci da zasu rayu kaman ko wata mace a fad’in duniyar nan.. Tunanin k’yama da tsangwama da zasu fuskanta tsakanin Al’umma shi yake jefa da yawa cikinsu cikin hali na ha’ula’i wasu a garin haka har kashe kansu suke sabida tsoron tsangwama daga sauran mutane... Maiyasa baza’a jasu jiki ba a nuna masu cewa rayuwa bata k’are masu ba... Zasu iya samun Farin ciki kaman ko wata mace.. Instead ki tsaya a nan kina aibata Ta a matsayinki na matar cikakken Alk’ali da taimakawa kikayi aka capke wad’anda suka aikata laifin, dan rashin hukuntasu shi zaisa gobe su kuma..!” Mommy Ta katsesa da fad’in “Ansar Wai maganan da nakeji gaskiya ne..?! Kenan Muhibbah tai mana k’arya da tace b’arayin daji Sun halak’a ahalinta...?!” Ansar ya d’an fuzar da huci yana shafa kansa yace “Mommy Ki tsaya kiji I’ll explain everything..!” Girgiza kai Mommy tai tace “Shikenan kuma ai... Kasan ni bana son mak’aryaci ko yaya ne... Balle yanda naji kana maganan fyad’e kenan Allah kad’ai yasan B’arayin daji nawa ne sukai mu’amala da ita..!” Anty Gudidi tace “Alhamdulillah abinda nake nufi kenan... Ta yaya zaki bari d’anki k’waya d’aya tol a duniyar nan ya auri wannan abar.... Wayasan mai wad’ancan kmazaman b’arayin dajin suka gama yi da ita kawai d’anki yazo ya kwashi ragowarsu... Wllhi Allah ya sawwak’e wannan ai sai ki zama abin nunawa tsakanin k’awaye...!” Mommy na tsananin huci take duban Muhibbah dake duk’e a wajen tana sharb’an kuka mai tsuma zuciya.... “Ke.. D’ago ki kalleni dan daga yanzu bazan kuma kiranki da sunan Muhibbah ba... Allah kad’ai yasan menene asalin sunanki da abubuwan da kike b’oyewa... Na rik’eki da zuciya d’aya ashe Ke ba haka kika d’aukemu ba.. Kin b’oye mana wannan babban al’amari... Toh kiji da Wai d’ah na bazai auri mace irinki ba...!!” Muhibbah ta d’ago a firgice tana duban Momy da idanunta masu zuban ruwa... Ko saurarenta Mommy bata tsayayi ba tasa kai Ta fice daga d’akin a tsananin fusace yayinda k’awayenta suka take mata baya... Ansar yai saurin bin bayanta yana ambato sunanta inaa ko tsayawa batai ba.... Muhibbah kaw tana ganin sun fice Ta maida k’ofan d’akin Ta silale a wajen tana cazgan kuka mai tsuma zuciya... Ansar ya dawo yana bubbuga k’ofar inaa bata bud’e ba sai ma shesshek’an kuka da take... ** A can Masarauta kuwa daren jiya kusan gaba d’aya mafarkai ya dingayi sarara marassa kan gado... Mafarkinsa na k’arshe ne ya tsaya masa a rai yanda suke tsaye shida ita cikin Babban Zauren ajiya na masarauta... Su duka biyu Suna rik’e da wannan Taswiran ya rik’e b’angare guda itama ta rik’e b’angare guda, kowa a cikinsu yana so ya amshe Taswiran daga hannun d’an uwansa ga Wambai daga gefe yana sakin murmushi yana kallon kokawan k’wace wannan Taswiran da Mahmood keyi hannun Muhibbah... Dik k’ok’arin Mahmood ganin ya amshe wannan Taswiran daga hannunta bai iya amshewa ba dukda cewa ya dage k’arfinsa gaba d’aya... Yana juyawa yana kallon Wambai yana cewa ya taimakesa kada ta gudu da Taswiran, Wambai sai murmushi yake masa lokaci guda yana cewa ya bita duk nisan duniyar da zatai itace zata zamto fitilar haska masa duhun dake gaba garesa... Haka ya dinga binta a guje har ta shige wani k’ofar... K’ofar tana gab da rufewa ya isa ya saka hannayensa duka biyu yana k’ok’arin janyota yana son k’wace wannan Taswiran amma bata sakar masa ba... K’iris ya rage k’ofar bai rufe ba ya farka daga baccin...! Shafe Fuskarsa yai da duka hannayensa biyu daidai lokacin da sallaman Zahra ya daki dodon kunnuwarsa... Zahra ta bisa da kallon mamaki dan bakinta na uku kenan tana sallama mahaifin nata baiji ba.... Ta k’arasa ta zauna daga can kusan k’afafunsa, Ta risina tana gaidashi... Saida ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ya amsa mata... Zahra Ta d’an muskuta tace “Paa are you alright..? You seem deep in thoughts...!!” K’uri yai mata sai kuma ya nusa kad’an ya kirawo sunanta da siga mai firgitarwa... Zahra ta d’ago a d’an tsorace tana dubansa “Paa..!” Mahmood yaci gaba da fad’in “Tell me what really happened, kuma kada kimin k’arya...!!” Zahra Ta shiga murza hannunta cikeda tsoron abinda ka iya zuwa yazo, dan yanda taga mahaifin nata sosai tasha jinin jikinta “Paa... Paa Wllhi bansan mai ya faru ba nima kawai cewa tayi idan kaje zakaga abinda zai hanaka auren Anty Raheema shisa na yarda da plan d’in nata... Amma wllhi wllhi Paa I’ve no idea what her plan was... Kawai tace I should trust her the plan would definitely work... Amma bansan menene ba... Mun shigo motar haya muka dawo masarauta tace na kashe wayata she can handle the renaming parts of the plan... Paa I’m sorry kawai banso ka auri matar nan ne..!” Tinda Ta soma magana yai mata K’uri, ya gyara zama kad’an yace “Wacece ita..?!” Zahra na muzurai tace “Aunty Muhibbah..! But Paa please kar ka mata fad’a laifina ne..!” “Muhibbah!” Ya nanata cikin zuciyarsa, yarinyar da yai mafarki da ita jiya... Toh Wai wacece ita.. Mai take nema cikin Masarautar..? Ya kamata yasan komai gameda ita... Ya jinjina kai kad’an yace “Karki damu bazan mata komai ba... Kije Ki kirawo min ita...” Zahra tace “Ai bamu ganta ba, Ta bar note wa Aunty Umaima cewa Ta gama jarabawa Ta koma gida...!” Ya jinjina kai a hankali yace “Ki kirawo min Umaima..!” Ta amsa had’ida risinawa kana ta fice kiran Umaima.... Koda Umaima ta iso parlorn Mahmood tambayarta komai gameda Muhibbah yayi... Umaima ya sanar dashi duk abinda ta sani gameda ita.... Ya jinjina kai a hankali kana ya baiwa Umaima izinin tafiya... Umaima na ficewa ya kirawo Turaki yace yanaso yaje Jami’ar garin ya bincika masa komai gameda abinda take karantawa dan ko shakka babu ya soma tantaman idan da gaske makaranta ne ya kawota Masarautar.... ** Gimbiya Zeenat Ta kuma kaiwa Raheema rank’washi a matuk’ar fusace tace “Na rasa ke wata irin shashasha ce Raheema, wane jarabar ne zai dawo dake Masarautar nan bayan Muna gab da mallakar Mahmood... Wannan gantalellen Yazeed d’in ban San kalar asirin da ya miki ba...!” Raheema na hawaye take fad’in “Aunty wllhi Yazeed tilasta min yayi nazo... Bansan Zuhra zata kamamu ba... Nidai fata na Aunty Allah Sa kada ta sanar da Mahmood dan wllhi idan ya sani bazai yarda ya aureni ba..!” Gimbiya Zeenatu Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa uwarsu ta sani ma koran wulak’anci zatai mana a Masarautar nan mu k’asa mallakan abinda muka jima Muna hari...! Yanzu ke bazaki bari kowa yasan kinzo Masarautar nan ba... Salin alin kiyi ficewarki Ki koma kuci gaba da shirin biki ni zanji da ita Zuhrar..!” Raheema ta murmusa tace “Yauwa Aunty na shisa nake k’ara sonki... Dan Allah kar ki bari Zuhra ta fasa maganan nan cikin Masarauta..!” Gimbiya Zeenat ya murmusa tace “Yo mud’in na wasa ne..! Ke yanda na k’wallafa rai billahillazim sai kin auri Mahmood sarauta ta tashi daga hannun Giwa ta dawo hannunmu... Maza tashi kije kafin munafukan kuyangin Masarautar nan su soma tururwa...!” SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *59* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Hankali kwance Raheema ta koma masarautarsu akaci gaba da shirin biki, a nan Masarautar su Mahmood ma ba’a fasa komai ba anci gaba da shirin biki tareda nad’in sarautar Sarki Mahmood, sam bai nunawa Yazeed yasan wani abu gameda alak’arsa da Raheema ba haka nan Zuhra ma bata nuna komai ba kaman yanda Mahmood d’in ya buk’ata daga gareta... Koda Gimbiya Zeenat ta kirawota har d’aki ta tareta da zancen murmushi mai ciwo Zuhra tai tace “Aunty Zeenat kenan ai abinda ya riga ya faru ya faru, bazamu iya canza komai ba saidai muyi fatan hakan ya zamto na k’arshe domin kuwa Sarki Mahmood mutumin arziki ne bazanso matarsa ta kasance macuciya azzaluma irin Raheema ba...!” Gimbiya Zeenat Ta tareta da fad’in “Naji dad’i da kika fahimci hakan Zuhra, kuma babu wani riba a b’ata sunna ma’aiki da ake k’ok’arin k’ullawa kuma kema Ina fata Keda Yazeed ku daidaita kanku dan ba wani abu bane sharrin shaid’an ne... Koda wasa kada ma Ki bari wannan labari ya fita daga cikin Masarautar nan balle har ya tsallaka Masarautarku..!” Murmushi mai ciwo Zuhra tai tace “Aunty kenan.. Inaga ci gaba da zama gidan Yazeed ko rashin ci gaba da zama dashi wannan wani abu ne da ya dace ni na zab’a ba Ke ba... Inaga bakida hurumin da zaki dubi tsaban idanuna kice min naci gaba da hak’urin zama tareda Yazeed Dan haka kar mu sake wannan zancen... Maganan Raheema kuma tuntuni ni na rufe babinta a rayuwana, na barta da wanda ya halicceni ya kuma halicceta shi zai min sakayyan abinda suka jima suna min itada Yazeed... Hasalima bani Ta sab’a ba mahaliccinta Ta sab’a shi zata nemi yafiyarsa.. Idan babu wani abinda zakice ni zan tafi Aunty...!” Gimbiya Zeenat tabita da kallo jiki a mace ta k’ak’aro murmushi wanda yafi kamada yak’e “Toh..Toh shikenan... Ai Babu matsala kina iya tafiya Zuhra...Allah ya shiga lamuranki..!” Zuhra ta amsada “Ameen Aunty..!” Kana ta mik’e tai ficewarta Hadimarta na tsaye daga k’ofan shiga parlorn tana jiranta... Tana fitowa ta take mata baya suka nufi sashen Zuhran... Saidai suna shiga sashen nata suka tadda Yazeed zaune parlorn tareda yaransa sai wasa yake masu suna tsalle jikinsa abinda bai saba ba... Da gani kasan wani abin kawai yake shiryawa... Zuhra ta sallami Hadimarta kana tasa kai zata haura sama... Yaran suka tafi da gudu suna rik’o hannunta tazo Daddy yai masu doki gaba d’aya.. Wasa suke Sultan ne sarki Daddy ne dokinsa.. Zuhra ta dafa kan yaran tace suje suyi wasansu bacci takeji... Dik yanda yaran suka so tazo suyi wasan tareda ita tak’i amincewa idanun Yazeed k’yam kanta, sam bai tab’a zaton Zuhra nada zuciya har haka ba, shi sam baiyi zaton zata iya fushi irin wannan ba Ta daina shiga sabgarsa gaba d’aya... Kallon arziki ma bai isheta ba... Yana matuk’ar k’aunar Zuhra da bazai iya jure shariyarta garesa ba amma harga Allah shi bai ma San ya ake baiwa mace hak’uri ba balle ya bata... Ya fuzar da fuci kad’an yana mai shafa sumarsa... Tana hayewa ya faki idanun yaran nasa dake ci gaba da wasansu da pillows yabi bayan Zuhra... Aiko tana ganinsa cikin d’akin Ta shiga nuna masa k’ofa “Get out..!” Yazeed ya dubeta da mamaki Wai shine Zuhra ke nuna masa k’ofa tana koransa... Ya shanye b’acin ransa had’ida fuzar da fuci... “I said get out of my room..!!” Ta fad’i a karo na biyu tana mai kuma nuna masa k’ofa... Ko gizau bai ba saima tsareta da idanuwa da yake ci gaba da yi... “The last time I checked this is my kingdom, so duk yanda naga daman shiga zan shiga... Idan kin mance na tuna miki..!” Ya k’arashe cikeda gadara... Murmushi mai ciwo tayi wanda da gani kasan na takaici ne... Lokaci guda Ta d’auki wayarta da counter da take mak’alawa a ‘yar yatsarta tace “Basai ka tuna min ba... Amma tunda kace haka ni zan fice na baka waje Dan na tsani ganin wannan fuskar taka... You disgust me your Highness..!!” Ta k’arashe cikin karaji had’ida sa kai zata fice... Yazeed yai saurin fuzgota ta fad’o jikinsa, su duka biyu suna sakin huci mai zafi yake fad’in “Da alama kin mance da wa kike magana... Zuhra ni ne nan Yazeed wanda mace bata min gardama, let me remind you Idan kin mance..!!” Fincika tai daga rik’on da yai mata tana mai ci gaba da sakin huci take fad’in “Kash..!! Wannan ba Zuhrar da ka sani bane wacce take matuk’ar tsoronka da shakkanka... Idan baka sani ba ka sani, kan mage ya riga ya waye... Zaman d’an wani lokaci nake a gidanka... Da zaran wa’adin dana d’ibar wa kaina da ‘ya’yana zaka nememu a Masarautar nan ka rasa... Bana shayin duk abinda zaka min Yazeed... Ka rigada ka gama dab’awa zuciyata wuk’a mai bak’in guba wanda zai wahala ya warke... So duk abinda zaka min yanzu bana shakku... Go ahead Your Royal Highness... Kai duk abinda zakayi...!!” Ta k’ararashe cikin huci... Shima hucin kurum yake saki yana dubanta da tsananin mamaki, ko a mafarki ne akace masa Zuhra zata dawo haka zai fark’a yace k’arya ne sai gashi a zahiri yana sa’insa da Zuhra wacce a baya babu irin cin kashin da bai mata ba... Ya had’iyi miyau mai d’aci na bak’in ciki... Yana mai nunata da yatsa saidai ya kasa furta koda kalma sai idanunsa dake kuma kad’awa... Cikin huci yasa kai ya fice jin yaransu na haurowa saman benen a guje... Yana ficewa ta lalumi saman gado ta zauna tana mai dafe kanta dake tsananin sara mata, lumshe idanunta tai had’ida kishingid’a cikin gadon Dan gaba d’aya bata gane kanta kwana biyun... ** Turaki ya shigo da sallama yanda ya sami abokin nasa na zaman jiran k’arasowarsa, yanda yaga fuskar Turakin ya tabbatar masa da zarginsa kan yarinyar ka iya zama gaskiya.... “Barkada hutawa your Highness..!” Turaki ya fad’i yana mai zama daga can gefe, lokaci guda ya mik’awa Mahmood d’in wasu takardu... Mahmood yasa hannu ya amsa yana mai ware takardun... Saida ya karance tsaf kana ya d’ago yana duban Turaki da mamaki saman fuskarsa.. “Does this means she’s a fraud...?!” Turaki ya nusa kad’an yace “Lets not judge her right away Rankaidad’e... Maybe tanada dalilinta na yin k’aryar...!” Girgiza kai Mahmood yai yace “What could be her motive Turaki..? Kan mai zatazo Masarautar nan tayi k’aryar ita d’aliba ce a jami’ar garin nan alhali ba haka bane, sannan har tayi k’aryar batada masauk’i...Ko mai irin fuskarta basu tab’a gani cikin makarantar ba... Turaki yarinyar nan mak’aryaciya ce kuma tanada babban dalilinta na zuwa Masarautar nan... Kar ka mance tun farkon zuwanta Masarautar nan nakeda alaman tambaya akanta, what if da biyu ta shiga jikin Zahra...? Wayasani ma ko itace taita feeding Zahra da k’arerayi har Zahra ta koma yanda take a yanzu..?!” Turaki ya katsesa da fad’in “Ka gafarceni Your Highness, ni a tunanina kaida kanka kace zamanta da Zahra alkhairi ne Dan ita ta shawo kan Zahra lokacin da Yazeed ya tasamma gurb’ata zuciyarta da k’arerayi...” Mahmood ya kuma katsesa da fad’in “And what makes you so sure itada Yazeed basu san juna ba....?? Maybe she’s helping him in some ways.....! Waht if itada Yazeed are lovers,maybe d’aya ce daga cikin ‘yan matansa da yake cin amanar matarsa dasu.... wayasani ma ko ya d’aukota ya aje cikin Masarautar nan ne just to ruin me, and they used my own daughter to bring me down....! And after she learns yana cin amanarta da Raheema shine ta fallasa Raheema kuma kar ka mance mun tab’a kub’utarta hannun Yazeed,maybe Yazeed gaskiya yake fad’i ba raping d’inta yaso yi ba... Maybe dama sunsan juna tuntuni... Is her way of getting back at him shiyasa ta tona asirinsu shida Raheema...!! I was such a stupid for believing in her..!!” Ya k’arashe yana sakin huci mai wane irin zafi yanaji zuciyarsa kaman tana rarrabewa gunduwa gunduwa, lokaci guda yasa hannu ya daki jikin gini zuciyarsa na kuma masa d’aci... Turaki yai shiru Dan bayan tabbatarwa da sukai Muhibbah ba d’aliba bace a makarantar kaman yanda tace Mahmood yanada duka damar da zai zargeta da komai, wacce har tai k’arya irin haka baida lasisin da zai kareta dukda cewa shi sam zuciyarta bata aminta da cewa Muhibbah mutumiyar banza bace musamman da ya fahimci abokinsa ya aukawa soyayyarta wanda bai tab’a ganinsa cikin irin wannan soyayyar ba koda kuwa zaita denying... Turaki ya d’an shafi fuskarsa da duka hannayensa biyu yana mai tsare abokin nasa da idanu wanda sosai yake iya hango tsagwaron b’acin rai kwance saman fuskarsa... Shi zai iya cewa ma bai tab’a ganin hakan daga garesa ba... Ya d’an nusa kad’an yace “What are you suggesting your Highness..?!” Wane irin duba kurum Mahmood yai masa ba tareda ya kuma cewa komai ba yai hayewarsa sama... Turaki yabi bayansa da kallo tausayinsa na kuma lullub’esa Dan yayi imani sosai ya kamu da san yarinyar sai gashi tayi breaking zuciyarsa tun ba’aje ko ina ba.... Bai ida tunanin ba ya hango Mahmood ya sauk’o cikin shiri irinta Buzaye... Turaki ya mik’e babu shiri yana dubansa baki sake.... “Bak’on Buzu kuma Rankaidad’e..?!” Turaki ya fad’i yana duban Mahmood d’in dake k’arasowa cikin parlorn.... Lokaci guda yaci gaba da furta “Ai na zaci an rufe shafin Bak’on Buzu tuntuni Rankaidad’e...?!” Har lokacin bai tankasa ba saima k’arasawa jikin babban mirror na alfarma dake gefe daga nan cikin parlorn yana gyara nad’in buzayensa.... Lokaci guda ya soma furta “Jikina yana bani Baba Wambai bazaice na nemeta itada zata linking d’ina to all the answers I’ve been looking for a banza ba, watak’ila itada Yazeed sun jima suna shirya abubuwa akaina... Idan ban samu amsoshin a wajen Yazeed na ita zan iya samu a wajenta...!” Turaki ya jinjina kai yace “Toh yanzu ina muka nufa Rankaidad’e..?!” Ba tareda ya dubesa ba yace “Bauchi..!!” Saida gaban Turaki ya fad’i, ya d’ago taintsiyar hannunsa yana duba time... “Rankaidad’e da dai mun bar tafiyar zuwa gobe, Idan muka tafi yau zamuyi dare sosai a hanyar dawowarmu...!” Mahmood ya katsesa da fad’in “Are you coming or not..?!” “A’a yanda kace hakan za’ai Your Highness..!” Turaki ya fad’i yana mai take masa baya... Babu wanda yaga ficewarsu ko hadimin Mahmood d’in baisan Sun fice ba hasalima da motar Turaki sukai amfani suka fice. ** A b’angaren Jakadiya kuwa neman duniya anyi ba’a sameta ba cikin Masarautar, hankalin Giwa yakai k’oluluwa wajen tashi... Wai meke faruwa da ita ne..? Daga wannan sai wancan.... Yau kwana biyu kenan babu Jakadiya babu dalilinta kuma babu wanda yasan yanda take... Gashi Giwa ta hana a yad’a Labarin b’acewar Jakadiyar Dan bata so ya isa ga Mahmood balle har aje ga tono ina Ubandoma ya shige tinda shima ba’a gansa ba... Gashi Tal’udu ya mata iyaka da sashensa balle Takai masa kokenta na abubuwan dake faruwa da ita... Tashin hankali daga wannan sai wancan... Ita duk tsoron ta kar dai Ubandoma ne ya zago ya sace Jakadiya tinda tayi imani yana tareda Ja’afar da kuma Izzatu mutanen da suke barazana ga rayuwarta... Tayi imani randa duk suka bayyana cikin Fada Toh fah kashinta ya bushe... Taci gaba da zaga cikin d’akin nata yanda Jamal ya shigo ya taddata... Daga can gefe ya zauna yana k’are mata kallo dan da alama bataji shigowar tasa ba... Ya d’anyi gyaran murya kad’an yana mai daidaita zamansa had’ida aje sandarsa Ta crutches... “Maami Wai meke damunki ne..?!” Ya tambaya cikeda kulawa... Giwa Ta juyo tana dubansa da mamakin yaushe ya shigo ko k’aran sandarsa bataji ba.... “Gwarzona na yaushe ka shigo..?!” Ta tambaya cikeda kulawa... “Maami tun d’azu fah na shigo, inata miki magana amma kinyi nisa duniyar tunani... Maami meke damunki duk kika fice a hayyacinki haka... Tell me is there something I can do to help..?!” K’ak’aro murmushi Giwa tai Ta k’araso kusan d’an nata Ta zauna, hannunsa ta dafa kad’an tace “Meyasa abubuwa suke faruwa yanda bana so Jamal... Meyasa komai yake nema ya sukuruce min...? Nayi zaton inada k’arfin zuciya da k’arfin hali, Maiyasa nakeji kaman na zamto mai rauni.... Jamal babu Ubandoma, yaci amanata ya gudu da mahaukaciyar nan da kuma Jafaru... Yanzu kuma an wayi gari Jakadiya ta b’ace itama... Jamal idan na rasa Jakadiya tamkar rayuwata na rasa..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Jamal yai shiru yana duban mahaifiyar tasa sai kuma yace “Maami har haka Jakadiya Keda mahimmanci wajenki..?!” Giwa ta nusa tace “Bazaka gane bane Jamaluddeen, Jakadiya tasan sirrika na da yawa wanda b’acewarta tashin hankali ne a gareni...!” Jamal ya tsareta da idanu sai kuma ya d’an gyara zama yace “Maami akwai wasu sirrikan da kike b’oyewa ne wanda Jakadiya ta sani ni ban sani ba...?!” Tambayar da ya haifarwa Giwa da fad’uwan gaba tinda tasan yaran nata basu san cewa ta salwantar da shigabanta bane ta maye gurbinta, yaranta basu san cewa ita d’in baiwa bace k’ask’antacciya maras ‘yanci... Shiyasa duk yanda zatayi dole tayi komai Dan ganin itada ahalinta sun tabbata cikin wannan masarauta tunda basuda yanda yafi masu nan...! Ta girgiza masa kai a hankali alamun a’a tace “Iyakacin abinda ka sani sune Jakadiya ta sani amma duk randa ya isa kunnen Yayanku Mahmood zai tsaneni a matsayina na mahaifiyarsa dole duk yanda zamuyi mu aje Jakadiya a k’ark’ashin ikon mu Jamal..!” Yai shiru had’ida tsurama waje guda idanu tamkar mai tunanin wani abu... Giwa ta tsaresa da idanu tana karantarsa, Ta d’an muskuta kad’an tace “Jamal... Anya kuwa babu abinda kake b’oye min..? Kodai kasan wani abu gameda b’acewar Jakadiya..?!” Jamal yai shiru ba tareda ya amsata ba... Giwa Ta mik’e tana fad’in “Jamal ina Jakadiya..? Mai kai mata..?!” D’agowa yayi yana dubanta sai kuma ya kauda fuskarsa zuwa d’aya b’angaren “Maami Jakadiya macuciya ce cin amanarki take a bayan idanunki shisa nake hukunta ta..!” Giwa ta shiga tafe hannaye tana salati babu shiri tace dashi maza ya kaita taga Jakadiya.... ** BAUCHI Mommy tai jigum tana sauraren Baffah Yawale yanda yaci gaba da fad’in “Haba ni nasan za’a rina, wannan yarinya da kika d’auko kika aje gidanki tsintacciyar mage ce, a tunaninki irin na mata taimako kikayi gashi nan da idanunki kin gani, Allah ya bud’i bakinta da kanta Ta sanar dake k’arya ta miki a baya... Allah kad’ai yasan yawan sauran abinda take b’oye miki.... Ki gode ma Allah da ya fargar dake kafin ki kaiga aikata babban kuskure na aura ma d’anki wannan yarinya maras asali balle tushe...!” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Ansar yana fad’in “Dukda rashin asalinta naji na gani na amince Ina sonta a haka... Ni ne nan zanyi zaman aure da ita ba d’aya daga cikinku ba, so ni nakeda alhakin zab’awa kaina macen da ta dace Tai zama matata kuma uwar yaran da zan haifa gaba.!” “Ansaar.!!!!” Mommy ta daka matsa tsawa tana mai mik’ewa tsaye... Ansar bai daina huci ba yake furta “Mommy Ki k’yaleni na fad’I gaskiya, wannan mutumin yazo yana poisoning zuciyarki da kalamansa na son zuciya..!” Momy ta katsesa da fad’in “Nace kamin shiru... K’anin mahaifin Naka kake wa magana haka...? Ansar I didn’t raise you to become like this... Rashin kunya ba halinka bane kada ka fara kan wannan mak’aryaciyar yarinyar..!!” Ansar na tsananin huci yake girgiza kai yana duban mahaifiyarsa, lokaci guda yake furta “Mommy shin zaki bari son zuciya ya rufe miki ido..? Mommy Muhibbah bata miki komai ba, Mommy don’t judge her akan abinda bakida masaniya akai... Mommy ki bari nai miki bayani na tabbata zaki fahimci komai..!” “Shut up.!! Kamin shiru nace... Bana buk’atan naji komai, kuma bana so na fahimci komai... The only abinda na sani shine bazaka auri yarinyar nan ba period.!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci.. Shima Ansar d’in huci yake idanunsa na kuma kad’awa, lokaci guda yake furta “Fine..! Haka kikace Mommy..? Kin mance same mutanen da suka k’yamaci aurenki da Daddy sabida ke tibabbiya ce same mutanen suke tunzuraki ki aikata abinda zakizo kina danasani daga baya... Mommy why can’t you open your eyes and see the truth...! Toh wllhi kinji na rantse miki.... ina mai tabbatar maku idan har baku d’aura aurena da Muhibbah ba wllhi bazan zauna da yarinyar da kukeso ba, zaku aura mata wofi ne Dan wllhi tafiyata zanyi ku nemi ni ku rasa..!!” Marin da Mommy Ta wankesa dashi ne ya sanyashi dakatawa da magana, ya d’ago dafe da k’uncinsa yana dubanta, Baffah Yawale ya mik’e ya tsaya a tsakiya yana duban Mommy yake fad’in “Kiyi hak’uri Murja... Har yanzu dai Yakubu(Ansar) yaro ne... Baisan menene daidai da abinda ba daidai ba... Kiyi hak’uri abi abun a sannu....!” Mommy na hawaye take nunawa Ansar k’ofa “Get out... Get out before I lost it all on you... Fita nace..!!!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata.... Ansar ya aikawa Baffah Yawale wani duba kana yasa kai ya fice kaman zai kifa da k’asa... Ansar na ficewa Baffah Yawale ya taro ruwa a dispense ya kawowa Mommy... Babu musu Ta amsa ta kurb’a... Bafah Yawale ya koma mazauninsa ya zauna, saida dak’ik’ai suka d’an shura kana yai gyaran murya yace “Murja ni inaga bata nan zamu b’ullowa yaron nan ba, idan har yana ganin yarinyar bazai tab’a cireta a zuciyarsa ya mance da ita ba... Idan bata gidan nan shine zai manceta gaba d’aya... Amma muddin yana ganinta Toh fah bazai mance ba....!” Mommy ta dubesa jiki a sanyaye tace “Yawale mai kake nufi...? Kasan dai bazan iya koran Muhibbah ba, dikda abinda taimin I still love her like my own daughter... Bazan iya korinta ba..!” Baffah Yawale ya murmusa yace “Murja kenan.. Ai nima ba abinda nake nufi ba kenan, ba korinta zakiyi ba... Aurarta zakiyi ga wani daban, kinga idan kika aurarta Ansar yasan ta haramta garesa shikenan dole ya cireta daga zuciyarsa gaba d’aya ya rungumi k’addara ya zauna da matarda Allah ya had’asa zaman aure da ita Wato ‘yar uwarsa k’anwarsa Hameeda... Kinga shikenan hankalinki kema ya kwanta..!” Mommy tai shiru kaman mai nazari sai kuma tace “Toh amma waye mijin da za’a aura mata..? Ina zan samo mata miji da zai dace da ita wanda bazai mata gori daga baya ba..?!” Baffah Yawale ya murmusa yace “Murja kenan... Ai samun miji ga kyakkyawar yarinya kaman Muhibbah bazai wahala ba... Ni zan tafi da hotonta wajen manyan mutane masu mutunci a haka zamu sama mata miji... Amma ita yarinyar karki sanar da ita an fasa aurenta da Yakubu shima Yakubun ki barsa akan za’a aura masa Muhibbah saidai yaji daga baya ba shi aka aura mata ba... Ina mai tabbatar miki rana guda za’a d’aura aurenta da Yakubu amma ba dashi ba da waninsa...Kinga dole yayi hak’uri ya rungumi k’addara... Ki share zancen Yakubu ki daina damun kanki ki bar min wuk’a da nama... Ni nasan duk yanda zanyi...!” Mommy ta jinjina kai tace “Nidai idan har bazata auri Ansar ba toh shikenan, amma Yawale ka tabbata gidan mutunci ka kai Muhibbah..!” Baffah Yawale ya Washe baki cikeda jin dad’i yace “An gama Hajjaju... Wannan ai mai sauk’i ne... Ina mai tabbatar miki yanda Yakubu ya makance da soyayyar yarinyar nan har yana sa’insa dake kika sake kika amince ya aureta Toh fah saidai Ki zuba mishi idanu Don kin haifo mata shine...!” Ya k’arashe yana mai kuma tunzura Mommy.... Mommy tace yaje yayi duk abinda ya dace... Baffah Yawale ya fice yana Washe baki... Daga nan yanda suke tsaye suka hango ficewar mutumin daga gidan... Turaki ya k’arasa ya tadda mutumi mai teburin kayan miya, yai masa sallama da musabaha suka gaisa... Idanunsa naga k’ofar gidan su Muhibbah da Baffah Yawale Ke k’ok’arin burka babur d’insa.... Mai Teburin kayan miya ya dubi Turaki yace “Bawan Allah na nawa za’a baka...?” Turaki ya d’anyi gyaran murya yace “Tambaya nake dama...!” Mai kayan lambu yace “Allah yasa na sani...!” Turaki yai nunida gidansu Muhibbah yace “Da Allah wata yarinya nake nema a can gidan sunanta Muhibbah.. Ko ka santa...?” Mai kayan lambu ya Washe baki yace “Aw Muhibbah... K’warai na santa... Ai d’iyar rik’o ce a gidan... Yaron gidan likita shine zai aureta...Idan ban b’ataji ba ma sati mai zagayowa za’ai bikinsu... Kaga wancan wanda yake k’ok’arin burka babur shine K’anin mai gidan, kuma a yanda naji basa so yaron gidan aure ita yarinyar... D’iyar wancan k’anin Baban nasa sukeso ya aura...!” Mai kayan lambu yaci gaba da zuba bayani kai kace tanbayrsa akai... Turaki ya jinjina kai yace “Na gode...!” Sukai sallama mai kayan lambu yaci gaba da ‘yar wak’e wak’ensa abinka da mutane wanda bakinsu bai iya yin shiru... Turaki na k’arasowaga Mahmood ya sanar dashi yanda duk sukaida mai kayan lambu.... Mahmood yace “What..! No Turaki dole musan abinyi... She can’t get married... Idan tayi aure komai ya lalace Turaki... Wannan yarinyar must answer to me first...Idan ta kama na janyota da kaina Ta koma cikin Masarautar nan zanyi Turaki...!!” Ya k’arashe cikeda tsanar hallaya irin nata.... Turaki yace “Alright your Highness... Bamuda time muyi sauri mubi bayan mutumin kafin ya b’ace mana...!” Cikin sauri suka nufi mota Turaki ya tada sukabi bayan Babur d’in Baffah Yawale.... SameenaAleeyou *MUHIBBAH* *60* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Daga cen nesa da k’ofar gidan da Yawale ya shige sukai parking, suka k’araso k’ofar gidan Turaki ya bud’e murya yai sallama, saidai basuji an amsa masu daga ciki ba... Sun kusan minti biyu tsaye wajen babu wanda ya lek’o daga cikin gidan har kaman zasu juya saiga wani yaro ya fito rik’eda allon karantu Ta ‘yan makarantar zaure... Turaki yai saurin taresa da fad’in “Kai Yaro gidan nan kake...?!” Yaron ya jinjina kai yace Eh... Turaki yace “Shiga ciki kace ana sallama da mai gidan...” Yaron ya dubesu da mamaki sai kuma yace “Ai masu gidan sunada yawa, k’ofofi kashi kashi ne cikin gidan... Wanne zan kirawo maku...?!” Turaki ya d’an shafi kansa yace “Toh..! Bakaga wani mutumi da ya shige yanzu ba da Babur..?” Yaron yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Kodai Baffah Yawale kuke nufi shine naji k’aran babur d’insa yanzu...” Turaki yaji sunan kaman wanda mai kayan lambun can na k’ofar gidansu Muhibbah ya fad’a masa, saurin jinjina kai yai yace “Yauwa shi dai... Shiga kace ana sallama dashi..!” Yaron ya jinjina ya koma cikin gidan... Jim kad’an ya fito yace dasu Wai yana zuwa.... Bayan shigewar yaron da wasu mintoci Yawale ya fito yana mamakin Ina ya samu bakin buzaye shida babu kowa nasa k’asashen hamada.. Iso yai masu cikin Zauren yanda tabarma ke shimfid’e, yai masu sannu da zuwa suka gaisa gaba d’aya, Yawale ya bud’e murya yace “Saidai kuma ban gane daga ina bane..?” Turaki ya d’an murmusa yace “Eh Toh daga k’asashen can arewacin hamada muke, dama tambaya mukazo gameda d’iyarku mai suna Muhibbah...!” Ai Tun kafin Turaki ya rufe baki Yawale ya soma fad’in “Fad’uwa tazo daidai da zama, dama mun rasa mijin da zamu aura mata, Allah yasa idan kun aureta kuyi nesa da ita da garin nan... Ku tafi can k’asarku da ita yanda bazata kuma dawo mana ba, bazamu kuma cin karo da mai irin fuskarta ba..!” Turaki da Mahmood suka dubi juna da mamaki, Baffah Yawale yaci gaba da fad’in “Kar Kuji komai ba’a mata miji ba, dama uwar goyon nata tace duk wanda ma samu na aura mata, ko kuturu ko makaho kai ko wane irin mutum ne... Toh Alhamdulillah tinda ta samu mutumin da zai ketara da ita wata Nahiyar ai abin ai godiya ne... Dama mu kasancewarta kusa damu ne bamu fata... Wata sati ake bukin d’aura mata aure... Bayin Allah sadaki kawai zaku kawo ni ko yanzu zan kirawo shaidu a d’aura auren...!” Turaki yai murmushi wanda yafi kamada yak’e yace “Oh haka ne Baba..! Toh ai inaga zamu koma dai muyi shawari da magabata...” Turaki bai rufe baki ba suka sinkayo muryar Mahmood daga cikin nad’insa ta buzaye yana fad’in “Babu shawari Baba... Mune nan magabatan wanda mukazo nemawa auren... D’an uwana k’anina zan nemawa aurenta... Yanzu basai anjima ba zan damk’a maka sadaki...!” Ya k’arashe yana mai zira hannu cikin aljihun babban rigarsa Ta buzaye, ya ciro wata ‘yar jaka ta fata ya mik’awa Baffah Yawale... Yawale hannu na rawa ya amshi ‘yar jakar Ta fata, ya shiga warwareta yana ganin abin mamaki.. Silallala ne zallan zinari wanda darajarsu zai iya kaiwa dubu d’arurruka.... Yawale ya kuma murtsuka idanu yana ganin wannan ikon Allah, a ina mutane irin wad’annan suka sami wannan dukiya shidai bai gansu da wata babbar Mota ba hasalima bai gansu da abin hawa ba, daga su sai suturan jikinsu ya gansu... Kaman Mahmood yasan tunanin da yake ya soma fad’in “Kar kaji mamaki Baba sabida mu haka al’adarmu take, mace Tanada matuk’ar daraja, duk mutum yakaiga talauci sai ya nemo silalla na zinari kafin a basa mata, iyayenmu sukan bar mana gadon Rak’uman da muke kiwo Dan muyi kud’in aure dasu....” Yawale ya jinjina kai har lokacin jikinsa rawa yake yana juya coins na zallan gold a hannunsa... Lokaci guda yace “Ai..Toh... Toh ai shikenan, kasan kowa da al’adarsu... Babu komai sati mai zuwa kuzo ku amshi auren d’an uwanku...!” Mahmood ya jinjina masa kai ba tareda yace komai ba saima k’ok’arin mik’ewa da yake da zimmar tafiya... Yawale ya tsare fararen k’afafunsa da kallo wanda da gani kasan hutu da jin dad’i ya zauna a wajen babu wani alamun tafiya cikin hamada a k’afafun balle har ace makiyayi ne mai kiwon Rak’uma cikin Hamada...Anya wannan ba manyan mutane bane suke son b’adda kama... Wad’annan basuyi kamanceceniya da gajiyayyu ba... Shifa baya fata yarinyar nan ta samu wajen maik’o yafi so ta tagayyara, kardai ya kaita yanda zata huta... Toh amma ai shi dama so yake ta fice daga rayuwarsu dan idan har tana tareda Murja da kuma Ansar sam bazata tab’a bari ya cimma burinsa akan dukiyar D’an uwansa da ya mutu ya barwa Ansar da Murja gado, kuma dukiyar Murja ma harinta yake tinda batada magaji bayan Ansar d’in... Idan kuma Ansar ya mutu baida Magajiya face d’iyarsa Hameedah wacce zata zamto matarsa , komai ya dawo hannunsa a sauk’ak’e.... Sallaman Matarsace rik’eda ruwa a faranti ya dawo da Yawale daga duniyar tunanin da ya tafi, da alama baima San bak’in nasa sun fice ba har sun tafi.... Matarsa ta tambayesa Ina bak’in...? Yace Ai har sun tafi Ta koma da ruwan... Ya k’arashe yana mai b’oye silallan zinarin cikin aljihunsa.... Bai isa kowa yaga wannan dukiya ba, ko Murjah bazata gani ba... Kasuwa zai tafi ya saida guda d’aya tak ya kaiwa Murja a matsayin kud’in auren Muhibbah... Sauran kuma ya dafe Allah ya kashe ya basa, shikenan ya samu kud’ad’en da zai kayan d’aki wa Hameedah a sauk’ak’e... ** Har suka shige Mota Turaki bai daina mamakin abinda Mahmood yai ba, shi tsananin mamaki ma ya hanasa furta koda kalma.... Da alama shi kuwa Mahmood d’in ko a jikinsa... Turaki ya nusa kad’an yace “Your Highness, ka tabbata da abinda kayi..? Shin waima cikin k’annenka waye ka nema masa auren Muhibbah, Yazeed ne ko Jamal ne kokuwa Fu’ad ne..?!” Ba tareda ya dubesa ba yace “Maiyasa ka faye gaggawa Turaki..?!” Turaki ya girgiza kai yace “Your Highness zarginta kawai kake baka tabbatar ba, bakada k’wakk’waran shaida da zai tabbatar maka da hakan...!” Idanunsa da suka kad’a sukai jazir naga kwalta yake furta “Bayan k’aryar da tayi mana, Iyayenta ma neman kai sukeda ita... Ai kai shaida ne tinda gabanka akayi komai... Wannan kawai ya isa na kuma aminta da cewa ita d’in ba mutumiyar K’warai bace..!” Turaki ya girgiza kai yace “Mugaye sunyi yawa a duniyar nan, wasu idan har basu suka haifi yaro ba toh basu damu da duk halin k’uncin da zasu jefasa ciki ba, your Highness ya kamata kayi tunani akan hukuncin da kake k’ok’arin zartarwa... Nasan kana son yarinyar nan, kar kayi abinda daga baya zaizo ya dameka ...!” Katsesa yai da fad’in “Bana sonta ban tab’a sonta ba kuma bazan sota ba..!!” Turaki ya murmusa kad’an yace “Idan da baka sonta bazaka tab’a damuwa da al’amranta ba... Your Highness case d’in Muhibbah da Raheema ya banbanta, Raheema ka kamata dumu dumu ita kuwa Muhibbah zarginta kake wanda ni nayi imani can k’asan zuciyarka baka yarda zatayi duka wad’annan abubuwan ba... Nasan baka yarda ba Mahmood..!” Turaki ya k’arshe cikin sanyin murya.. Window kurum Mahmood yake duba Dan baiso ya yarda da kalaman Turaki... Shi hukuncin da ya yanke shine daidai... Idan har yana so Muhibbah Ta dawo cikin masarauta toh hanyar kenan ya aura mata wani cikin Masarautar kafin iyayenta su aurarta ga wani tinda idan tayi aure babu hali ta dawo cikin Masarautar, dole duk yanda zai ya nemama wani cikin Masarautar aurenta...! Ya k’arashe tinanin yana mai dunk’ule hannunsa sabida tsananin b’acin rai... Muryar Turaki ya sinkayo yana fad’in “Toh idan ka aura mata d’aya cikin ‘yan uwanka ita kuma Raheemar fah... Wa zaka aura mata..?!” Ba tareda ya dubesa ba yace “Idan Allah ya kaimu lokacin zakaji ko wanene mijin nata...!” Turaki yai shiru yana duban abokin nasa ba tareda ya kuma cewa komai ba saima maida hankalinsa ga tuk’i da yayi.... ** MASARUTA Giwa da mamaki take duban yanda halitta Jakadiya ya jirkid’e lokaci guda... Ko iya d’ago kanta batayi, Gata nan dai d’aure saman kujera iyaka jin jiki tayisa kam... Ko Iya d’aga kanta Jakadiya batayi, Giwa kanta saida ta firgita da ganin yanda halittan Jakadiya ya sauya lokaci guda, bata tab’a tsammanin muguntan Jamal yakai wannan mataki ba... Jiki na rawa Giwa ta isaga Jakadiya tana k’ok’arin dungurinta take fad’in “Anya tanada rai..?!” Jamal ya jinjina kai yace “Tanada rai Maami kawai alluran hutu tasha, nanda wasu sa’o’i zata farka...!” Giwa tai mata K’uri tana duban yanda fuskar Jakadiya ya kumbura ga wata akwati d’aukeda tools a gefe... Dank’ari mak’ari, wannan wane irin azaba Jamal ya baiwa matar nan... Giwa Ta dubesa tace “Jamal mai Jakadiya tai maka..?!” “Amanata taci... Kuma kema taci amanarki don na tabbata ita ta taimakawa Ja’afar ya gudu...!” Ya k’arashe cikin huci... Giwa Ta lumshe idanunta a hankali dan tasan tsanar Jafar ne ya shafi Jakadiya, Jamal zai iya yin komai akan yarinyar nan Umaima... “Toh amma ya akai ka Sani....?!” Giwa ta tambaya tana mai tsaresa da idanu... Mayafin Jakadiya dake aje gefe ya nuna mata yace “Kin gani wannan ne shaida...!” Take ya labartawa Giwa duk yanda abin yake... Giwa Ta d’aga mayafin tana juyawa... Ko shakka babu bai kamada mayafin bayi ba, duk yanda akai wannan ba na Jakadiya bane... Akwai wata k’ulleliya, amma bazatace komai ba har sai Jakadiya ta farka.... Da k’yar ta shawo kan Jamal ya sassautawa Jakadiya da irin uk’ubar da yake mata, Kwanceta yayi ya ajeta a nan d’akin had’ida treating duk wasu wounds dake jikinta... Giwa kanta saida ta tausayawa Jakadiya Dan ko motsi bata iya yi... Haka suka fice suka barta rufe nan cikin d’akin kafin alluran su saketa ta farfad’o.... ** Sharkaf da zufa tamkar babu AC cikin d’akin haka ya farka daga baccin nasa, mafarki yayi wata Murya da baisan daga ina bane tana fad’i masa Maiyasa zai zamto mai munana zato da mummunan zargi ga mutanen kirki... Da yawa daga cikin zato zunubi ne, kuma sashenta ba gaskiya bane..! Ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa mafarkin na dawo masa daki daki... Wasu mutanen kirki ne ya munana masu zato..? Tambayar da zuciyarsa tai masa... Toh kodai Yazeed ne..? Ko Raheema ce..! Toh amma ya kamasu red handed ba zato yake masu ba.... Take yaji zuciyarsa Ta ambato masa MUHIBBAH... Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai kuma shafe fuskarsa, Toh idan sashen zaton nasa ya zamto gaskiya fah...? Wata b’angare na zuciyarsa ta basa amsa da fad’in Kai da kanka ka kasa aminta cewa zatai abinda kake zaton ta aikata...! Ya fuzar da fuci mai tsananin d’umi tunanin na kuma damunsa, duk yanda yaso ya yakishe tinaninta cikin zuciyarsa ya kasa... Dik yanda yaso ya amince cewa ita d’in mutuniyar kirkice ji yake bazai iya hakan ba musamman da Zahra ta sanar dashi duk wasu shawarwari da Muhibbah taita bata tin daga fari, har cewa da tai ta tambayesa a cikin mutanen da yake jin nauyinsu... Kenan Muhibbah itace Ta tunzuro Zahra tai masa abinda tai... Gaba d’aya sai yana jin bazai iya aminta da ita ba bayan all that he learned about her... Da k’yar ya iya mik’ewa ya nufi bayi Don d’auro alwala.... ** Giwa sai faman safa da Marwa take a k’uryar d’aki Jamal na gefe yana juya mayafin, kenan Zahra itace Ta baiwa Jakadiya...! Jamal ya dubi Giwa yace “Maami amma Zahra bazata iya lek’en asiri cikin d’akina ba... Maiyasa ma zatayi haka...? What could be her reason..?!” Giwa tai shiru tana nazari sai kuma tace “K’warai Zahra bazatayi duk abinda ka zayyano mai wannan mayafin tayi ba, duk yanda akai akwaita a k’asa... Kodai akwai wata ‘yar lek’en asiri cikin Masarautar nan ko kuma bata cikin Masarautar amma tana amfani da Zahra...!” Jamal yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Maami karki damu, I’ll talk to my niece a nitse nasan zata sanar dani komai... Kinsan na k’ware a iya shan cikin mutane Dan naji labari...!” Giwa ta murmusa tace “Hakan yayi Gwarzo na... K’warai na yarda dakai.... Idan muka sami wacece wannan ‘yar lek’en asirin...” Jamal ya katseta da fad’in “Horon da nayima Jakadiya sai ya zamto horo mafi rahama a gareta... Sai ta zab’i mutuwa da rayuwa...! Sai ta tsuguna kan gwiwoyinta tana rok’on na kasheta don hakan sai Yafi mata sauk’i kan irin azaban dana tanadar mata..!!” Ya k’arashe yana tsananin huci jijiyoyin jikinsa na kuma fitowa... Giwa tai masa K’uri tana sakin wane irin murmushi na jin dad’i... ** BAUCHI Iatakam tasha mamakin ganin Mommy Ta sauk’o daga dokin fushinda ta d’ale, har idan ta shiga gaisheta bata korinta, ganin yanzun ma bata koreta ba ya sanyata zama daga can gefe wajen k’afafun Mommyn... Dak’ik’ai suka d’an shud’a kana Muhibbah ta soma fad’in “Mommy zuwa nai na miki bayanin komai dalla dalla ba tareda na b’oye miki wane abu ba...!” Mommy ta katseta da fad’in “A’a Hibbah ni bana son naji komai balle ma bak’in labari, kedai kije kuci gaba da shirin biki Keda k’awayenki kinga babu wani sauran time kwanaki ne kawai suka rage, duk abinda kuke buk’ata ku sameni, idan bazaki iya samuna ba Meenatu Ta sameni... Bana son na kuma jin kin tono zancen nan... Allah ya baku zaman lafiya a gidajen aurenku...!” Jiki a sanyaye Muhibbah Ta amsa da “Ameen Mommy..!” Allah ya gani tana son Mommy ta bata chance ta sanar da ita labarinta daga farko har had’uwarsu har kawo yau, tayi imani Mommy zata fahimceta amma tak’i bata wannan daman ko menene dalilinta... Wata zuciya tace k’ila bataso taji yanda akaci zarafinki ne... That’s how much she loves you.... Bata ida tunanin ba Aunty Gudidi tai sallama tana rangad’a gud’a tafe da wasu ‘yan Office d’in su Mommy guda biyu wanda duka k’awayensu ne... Muhibbah ta gaishesu Aunty Gudidi harda rungumarta tana nunawa K’awayen nasu ga d’aya amaryar dashike Mommy Ta sanar da ita yanda sukai da Yawale akan Muhibbar... Itadai Muhibbah sai mamaki take yanda Mommy da k’awayenta suka canza lokaci guda... A b’angaren Ansar ma yaji dad’in hakan don tuni sukaci gaba da shirye shiryen biki, har can gidan Baffah Yawalen ma yaje da yaga sun saduda sun amince ya auri zab’insa hakan yasa yai alk’awarin bazai watsa masu k’asa a idanu ba suma zaibi umarninsu a matsayinsa na iyayensa koda hakan bazai faranta masa ba... ** A can masarauta ma shirye shirye ta kankama, Mahmood ya sanar da Giwa harda auren Jamal da Umaima duk za’a had’a a d’aura, Giwa bata damu ba tinda tasan sunada shirinsu na musamman akan Umaimar, hasalima tuni tasa aka killace Umaima Kuyangi na kula da ita na musamman, wannan dalili yasa sam itada Jamal basu sami damar yin magana da Zahra ba Dan tsananin Farin ciki da Jamal Ke ciki ma yasa ya mance da batun tambayar Zahra, Giwa kaw Ta bada Himma ne sosai wajen ganin Jakadiya ta warke dan tunk’aran Tal’udu dole saida Jakadiya batasan wannan zuwan wane sassan jikinta ne zaici wuta ba musamman sanin yanda sukai baram baram da Tal’udun a had’uwarsu ta k’arshe.... ** Yau d’in Ta kama Alhamis kwanaki biyu tak suka rage a d’aura aurarrakin... Turaki na gefensa yana ci gaba da karantarsa, koda ganinsa kasan babban al’amari ke damunsa... D’an gyaran murya Turaki yai yace “Your Highness, da an k’ara duba lamarin nan daga gobe ne fah ake saka ran d’aurin auren nan.....!” Ba tareda ya dubesa ba ya jinjina masa kai a hankali “Na riga na gama magana Turaki, my decision is final... Dani dakai zamu tafi mu karb’o auren yarinyar Dan ina buk’atarta a cikin Masarautar nan... Sannan zan wakilta Galadima da Sardauna harma da Hakimai kaman guda uku su tafi Masarautar su Raheema su karb’o aurenta itama...Waziri dasu Matawalle da Liman zasu tsaya a nan su d’aura auren Jamal.... Haka na tsara tafiyar....!” Ya k’arashe yana murza zobban hannunsa a hankali... Turaki ya had’iyi miyau da k’yar yana mai jinjina kai Dan yasan wannan hukunci da abokin nasa ya yanke dole nadama ya biyo baya.... Fatansa bai wuce Allah ya shiga lamarin ba ya tabbatar da ikonsa akan komai.... ** RANAR ASABAR 29 GA WATAN AFIRILU... Kaman yanda Sarki Mahmood ya tsara hakan ce ta kasance, shiga irinta Buzaye sukai daga shi har abokinsa Turaki harmada amintaccen Hadiminsa Barde, baka hango komai cikin nad’in fuskokinsu face karan hancinsu da k’wayan idanunsu... Suna zaune cikin Mota suna hango dandatson mutane a k’ofar gidan Yawale sai kai komo suke, Mahmood yai k’uri wa mutanen da suke kaiwa da kawowa, Turaki ya d’an kaikaito ya dubi Mahmood dake zaune bayan Mota yace “Rankaidad’e mun iso..!” Jinjina masa kai Mahmood yai ba tareda yace komai ba, saima sak’on da yake k’ok’arin turawa cikin waya... Yana ida tura sak’on yasa k’afafunsa ya fito daga cikin motar Barde dake zaune gaban Mota ya fito da sauri ya bud’ewa Ubangidan nasa... Mahmood ya dubesa yace “Barde a nan dani dakai d’aya muke har sai mun koma masarauta...!” Barde kai a k’asa yace “Allah shi taimakeka bawa bazai tab’a zama kaman kai ba... Tuba nake ka gafarceni Rankaidad’e bazan iya abinda kake fad’i ba...!” Mahmood yai gyaran murya kad’an yace “Umarni nake baka Barde, ba shawarinka nake nema ba..!” Barde ya jinjina kai a hankali yace “Tuba nake Allah shi taimakeka, yanda duk kace haka za’ayi...!!” Mahmood ya jinjina kai yace dasu su k’arasa cikin Zauren taron... Turaki da k’irjinsa ke ci gaba da bugu yasa kai suka soma tafiya... A can gidan Mommy kuwa Gudidi da Mommy sun baiwa Ango Ansar da Amarya Muhibbah maganin bacci, K’awayen Muhibbah na nan cike d’akinta amma basuga idanun Amarya ba sun kulleta can d’akin Mommy tana shek’an bacci Tamkar macecciya.... Shima Ansar a nan d’akin dake gefe da na Mommy suka kullesa abokansa dake jiransa a sashensa Mommy ta isa ta taddasu sai trying layin Ansar suke bai shiga... Suna ganin Mommy suka soma gaidata suna sanar da ita abindake faruwa.. Damuwa k’arara saman fuskar Mommy take fad’in “A’a Wai dama bai sanar daku ba..? Ai jiya ya bar gidan nan zai kama d’aki a hotel sabida cunk’oson taron mata na biki... Kunsan akwai Amarya d’aya gidan nan bai kamata ango yana tsakani ba... Kai Musbahu ai na zaci tare kukaje kai ka masa rakiya ya kama otel d’in...?!” Musbahu ya girgiza kai yace “Mommy wllhi ni bamuyi wannan zancen dashi ba... Kuma ga wayoyinsa duka basu shiga, mun fara damuwa da halinda ka iya kasancewa ciki...!” Mommy ta d’an murmusa tace “Kayya Babu wani abu zumud’i ne kawai irinta sabon ango, kasan tagwayen mata garesa... Kaima satin baya akayi Naka bukin ai ya kamata ka fahimci haka...! Kudai yanzu kuyi maza ku tafi ku sami d’aurin auren k’ila yama tafi tuntuni ya mance wayoyin nasa a d’aki....!” Abokan suka jinjina kai sukace Eh kuma hakan ka iya kasancewa, sauri sauri suka fice dan kar su rasa d’ahtoh aure... K’awayen Muhibbah ma dake zaman jiranta a d’aki Gudidi ce ta shiga ta samesu tace Amarya tana can ana kintsata bazasu sami ganinta yanzu ba.. Hakan yasa K’awayen sukaci gaba da sabgoginsu, masu ciye ciye nayi masu tad’i nayi... Gudidi ta rakasu da harara da gefen idanu tana mai ayyanawa cikin zuciyarta “K’awarku kam kun rabu da ita kenan har abada dan mu kanmu bamusan duniyar da za’a kaita ba..!!” Ta fice tana sakin murmushin jin dad’i.... ** A can Masarautar su Raheema kuwa wata Kuyanga ce ta shigo a fujajan ta zube gaban Raheema tana fad’in “Ki gafarceni ya Shugabata wani labari na kawo...!” Raheema ta watsa mata harara, d’aya daga cikin Hadiman dake shiryata ta dubi Baiwar tace “Ke kuwa wani labari ne zai sa ki fad’o kan Gimbiya haka, bayan Kinsan yau d’in rananta ne ranan Farin ciki ne a gareta...!” Baiwar naci gaba da haki take fad’in “Ki gafarceni ya Shugabata wani labari nakeji na Yawo cikin Fada..!” Raheema da ta kai matuk’a wajen tunzura da wannan baiwa, fincika tai Ta mik’e tsaye tana fad’in “Ke k’ask’antacciyar Baiwa wane labari ne zaisa ki fice hayyacinki haka.. Labari guda d’aya ke yawo cikin Fada, labarin Farin ciki... Labarin auren Gimbiya Raheema da Sarki Mahmood... Shi kad’aine labarin dake yawo cikin Fada..!!” Baiwar na haki take girgiza kai.... Raheema da k’irjinta ke bugu batasan sanda ta damk’o wuyar Baiwar tana fad’in Ta sanar da ita labarin dake tafe da ita... Batakaiga rufe baki ba suka sinkayo sautin algaita na tashi ana ambato sunan Gimbiya Raheemah da angonta matsayin ma’arauta..... *MUHIBBAH* *61* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Raheemah bata daina jijjiga Baiwar nan tana mulke mata fuska da k’unshin dake hannunta ga algaita na kuma tashi duk ya karad’e cikin Masarautar.... Daidai nan Gimbiya Zeenat Ta shigo a fusace hankali tashe tana fad’in “Raheemah mai nake ji, Wai Yazeed aka aura miki ba Mahmood ba... Ta yaya wannan abu ya kasance...?!!” Raheemah na kuka tamkar mai tab’in hankali duk ta shafe jikinta da k’unshin da ake zana mata tace “Aunty wllhi k’arya ne... Wanda suka Zo d’aura auren su sukayi munafunci, Aunty Mahmood na sona nayi imani yana sona bazai tab’a barina ma k’aninsa ba... Aunty dan Allah tun kafin su tafi ki taresu su warware wannan auren wasan da sukayi su maida aurena kan mijina Mahmood... Aunty I can’t lose Mahmood... Wayyo na shiga uku.... Dan Allah Ki fita ki taresu wllhi dariya za’a mana cikin Masarautar nan... Sanin kanki kishiyoyin Ummah bazasu barmu musha iska da habaici ba..!!” Gimbiya Zeenat naci gaba da huci take furta “Ai duk laifinki ne... Ga irinta nan..! Ga irin ranar da nake jiye miki, kin maida kanki tamkar wata kariya... Na tabbata Mahmood yasan Keda d’anuwansa kunada alak’a a b’oye shiyasa ya juya akalar auren ya koma kan d’anuwansa... Ai abin kiyi Farin ciki ne yanzu sai kuyi mai dalili.!!!” Raheemah ta katseta da fad’in “Aunty dan Allah kije ki tari Hakiman nan kar su fice a Masarautar nan... Mishkila aka samu Mahmood ne mijin ba Yazeed ba..!!” Ta k’arashe tana mai nufan k’ofa kai babu ko rufi tsaban ta shiga tashin hankali maras misaltuwa... Gimbiya Zeenat tabi bayanta a fujajan tana k’ok’arin dakatar da ita inaa Raheema bataji bata gani tuni Ta tsallake bene ta nufi dandatson jama’an dake haraban Masarautar.... Abinka da babban gida sai aka samu abinyi, bayi na k’usk’us ‘yan gida kaw masu jimami nayi masu dariya na yi... Haka Raheema ta fice tana fad’iwa masu algaita su dakata... Ta kutsa sosai har gaban su Galadima tana fad’in wannan auren bai d’auru ba... Sarki Mahmood ne mijinta ba Yarima Yazeed ba..! Galadima ya girgiza kai yace “Rankidad’e kaman yanda Sarki Mahmood ya umarta hakan mukayi... Yarima Yazeed shine mijinki ba Sarki Mahmood ba...!” Raheema ta shiga fatali da kayan kid’e kid’e dake wajen tana fad’in k’arya ne wannan auren bai d’auru ba...! Ala dole wasu bayi ‘yanmata guda hud’u suka kamata aka shige da ita cikin gida sai hauka take wanda hakan sosai ya zubda Martaban masarautarsu... ‘Yanuba kuwa suka sami abin goriwa Zeenat dan sun tabbata wannan abin kunya da Raheema tayi tsaf sai ya koma Masarautar da Gimbiya Zeenat ke aure... Haka Gimbiya Zeenat ta aje shagalin buki a gefe ta shiga rara kuka tana kaico, shikenan Sarautar da take hari ta hanyar auren Mahmood da k’anwarta zatayi ya tashi a aiki... Har abada bazata tab’a samun hakan ba, wannan abin kunya ma da Raheemah tayi bai k’aresu da komai ba face fad’a zubda mata jima da tayi... Yanzu ko nan cikin masarautarsu mahaifarta batada wani kima balle aje can masarautarsu mijinta... Sosai Gimbiya Zeenat Ke kuka tana nadaman abubuwan da tayi a baya... Kaicon son zuciya, yau ga yanda son zuciya ya kaita... Dama komai zakayi ka saka tsoron Allah a ciki idan kuwa ba haka ba sai Kaga ba daidai ba...! ** Bakin Turaki ya gaza rufuwa, Mahmood ya shammacesa... Wato dama kansa ya nemawa auren Muhibbah... Gashi kuma ya karb’awa kansa auren nata ba tareda wakilcin kowa ba... Kai sai a gaisheda Mahmood inji Turaki.. Fataken Buzaye sun amshi auren Muhibbah yanda suka buk’aci a basu amaryarsu su tafi can k’asarsu da ita... Yawale yace kar suji komai su taho da motar da sukayo haya su biyosa suje har yanda zasu d’auke amaryarsu... Ba tareda b’ata lokaci ba kuwa sukabi bayan Yawale dake bisa babur d’insa, nan take suka nufo gidansu Muhibbah... Aka bar mutane da jimamin abunda ya faru da jinjina lamarin, wasu daga cikin Baffanin Ansar da suke Uba d’aya da mahaifinsa suka titsiye Yawale suna fad’in rashin kyautawar da yayi ace baka San mutane ba baka San daga yanda suke ba ka d’auki mutum sukutum ka basu...! Yawale yace Babu ruwansu tunda ba ‘yarsu bace kuma Ansar shine kad’ai dolensa basu ba...! Haka dai Yawale yai masu d’add’aya ya barsu nan suna jimamin wannan abinda ya faru wanda saikace wani wasan kwaikwayo... Abinda suke ganina wasannin kwaikwayo da littafai sai gashi zahiri a gabansu.... Shidai Mahmood sai karantar Yawale kurum yake da idanu.... Suna isa unguwar Yawale yace suyi Parking daga can nesa za’a fito da ita... Turaki yai parking daga nesa kaman yanda Yawale ya buk’ata... Nan take Baffah Yawale ya ciro wayarsa a aljihu ya kirawo Gudidi yace da ita masu d’aukan Amarya sun iso Ta fito da Amarya... Gudidi tace an gama gasu nan fitowa.... Cikin sand’a don ko Mommy bataso ta ganta ta kirawo k’awarsu Salame tace ta taimaka mata su fito da Muhibbah tinda dama bacci take.... Salame dai tsoro saman fuskarta tabi bayan Gudidi suka shiga d’akin yanda Muhibbah Ke yashe tana bacci, tausayin Muhibbah ya kama Salame... Idanunta sukai rau rau tana dubanta.... Gudidi kaw ko a jikinta saima d’auko mayafi da tai Ta rufawa Muhibbar tana k’ok’arin mik’ar da ita tsaye.... Ta dubi Salame dake tsaye tana duban Muhibbah cikeda tausayawa kana taja tsuka a hankali tace “Toh Sarkin tausayi da imani, dramar ya k’are taimaka min zakiyi mu fitar da ita daga cikin gidan nan....!” Salame Tai k’ok’arin maida k’wallan da suka ciko idanunta tace “Gudidi babu wanda yasan duniyar da za’a kai yarinyar nan... Babu wanda yasan su waye suka auri yarinyar nan..? Wasu irin mutane ne... Na gari ne ko na banza... ‘Yan shan jini ne koma matsafa ne... Gudidi baki tausayin yarinyar nan..? Baki tsoron hakki..!!” Gudidi ta katseta da fad’in “Kinfi Murja sonta ne..? Dashike ba d’anki aka so lik’awa ba dole Ki wani marairaice kice ke tausayi kike... Itama yarinyar inace iyayenta b’arayin daji ne yo koma su waye ta aura ai ‘yan ta’adda ne ‘yan uwanta... Kinga idan har kina k’aunar Murja a matsayin k’awa zaki taimaka min mu fitar da wannan annobar yarinyar daga cikin rayuwarta....!!” Ta k’arashe cikin huci.. Jiki a sanyaye Salame ta k’arasa ta tallafi b’angare guda na Muhibbah Gudidi na rik’eda b’angare guda suka fito da ita suna janyota kanta rufe da mayafi....A haka suka fakaice idanun mutane da hankalinsu ya tafi ga masu busa dan tuni an soma dawowa daga wajen d’aurin aure ga labaru daban daban na tashi na irin d’aurin auren da akai.... Sai sannan ne Mommy take jin Wai ma wasu fataken Buzaye Yawale ya bada auren Muhibbah... Hankali tashe Mommy Ke kuma tambayar mutanen dake wajen yanda al’amarin auren ya kasance... Tuni su Gudidi Sun fita Ta can bayan layin suna jan Muhibbah da k’yar da k’yar har dai suka hango Yawale tsaye jikin wata mota.... Yawale ya d’ago masu hannu yace su k’araso... Tuni suka k’arasa yanda motar take... Take Barde ya fito ya bud’e masu d’aya b’angaren da babu kowa suka ajeta ciki gefeda Mahmood... Itadai Salame tsoron mutanen ne ma ya rufeta, jikinta har rawa yake tana alla alla su bar wajen... Suna ajeta Barde ya maida k’ofar mota ya rufe yai sallama da Yawale.... Suka koma gefe suna kallo aka tafi da Muhibbah Yawale na Washe baki yana fad’in “An yarda k’wallan mangoro an huta da k’uda...!” Harda d’aga hannu yana waving motar... Guididi ma Ta tintsire da dariya tana tayasa da fad’in “A k’are can a duniyar matsafa dan wannan daga gani ‘yan shan jini ne suka sayi yarinyar nan...!” Yawale yai shiru kaman mai nazari sai ya jinjina kai yana mai tabbatarda maganan Gudidi da tace ‘yan shan jini ne suka sayi Muhibbah dan ya tuna mak’udan zinarin da suka bada matsayin sadakinta, sai yanzu yake ciza yatsa dama ya saida masu ita da tsada da yanzu yayi dukiya, amma dukda haka ya samu ai, sannan ga Hameedarsa zata auri Ansar d’an Hajiya Murjah... Mommy a fujajan ta nufi d’aki yanda aka kulle Muhibbah saidai babu Muhibbah babu dalilinta... Take taji wasu irin hawaye na zuwa mata, Ta shiga bud’e k’ofofi tana ambato sunan Muhibbah mutane na kallon ikon Allah... Shigowarsu Salame da Gudidi yasa Mommy ta nufesu tana tambayarsu ko sunga Muhibbah... Salame na k’ok’arin danne kukanta take girgiza kai, lokaci guda take furta “Murjah Muhibbah ta tafi... Ta tafi kuma bazaki sake ganinta ba..!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Tamkar mutum mutumi haka Mommy ke dubansu hawaye basu daina ambaliya a fuskarta ba... Cikin wane irin zabura tasa kai Ta nufi waje tana fad’in “Ina suke... Na fasa na fasa aura masu Muhibbah... Ku dawo min da d’iyata wllhi na fasa..!!” Gudidi tai ta maza ta kamo Mommy ta dawo da ita cikin gida... Gidan biki dai ya kacame da maganganu da hargitsi... Wannan kenan..! ** Tunda suka d’au hanya ya kasa janye idanunsa daga kanta, tsananin tausayinta yakeji na taso masa daga can k’asar zuciyarsa.... Idan da ace bai aureta ba tabbas wad’annan mugayen mutane da Sun bayar da ita ma ko wane irin mutum, tabbas zasu iya salwantar da rayuwarta sabida son zuciya... A hankali harshensa ya furta “You’re safe now..!” Dai dai lokacin da aka d’ale speed bump abinka da mai bacci sai ta fad’o cikin jikinsa tai matashi da k’irjinsa... Dukda bacci take yana Iya jin bugun zuciyarta cikin nasa k’irjin, tamkar zukatan nasu lokaci guda suke bugawa... Yanayin da ya jima bai tsinci kansa ciki ba ya ziyarcesa.... A hankali yake k’ok’arin kai hannu jikinta yana son gyara mata kwanciyar zuciyarsa naci gaba da harbawa... Wai fah ita d’in matarsa ce yanzu, ji yake kaman idan ya tab’ata zata farka.... Ya maida hannunsa ya ajesu ba tareda ya gyara mata kwanciyar ba, tana nan kwance cikin k’irjinsa.... Burki da Turaki ya d’an ja ne ya sanyata zamowa daga kan k’irjinsa zuwa cinyarsa.... Yai mata K’uri yana dubanta, wane irin duba yake mata wanda ko iya janye idanunsa baiyi, a hankali ya kai hannunsa yana k’ok’arin yaye rufin dake fuskarta.... Sannu a hankali yake janye mayafin hardai fuskarta ya bayyana... Zuciyarsa ta kuma bugawa lokaci guda, fuskar nata fayu babu ko kwalliya tamkar ba Amarya ba, hasalima a kod’e fuskar tata take irin na wanda yaci kuka harda sauran busassun hawaye a fuskar nata... Dogayen bak’ak’en gashin idanunta da sukayi marfi wa manyan idanun nata duk sun shige cikin juna alamu kuka taci sosai, idanunsa suka sauk’o kan labb’anta masu d’an duhu kad’an wanda kaman an zane k’arshensu da liner... A hankali ya lumshe idanunsa yana mai k’ok’arin janye fuskarsa daga barin dubanta, nan idanunsa suka sauk’a kan hannunta da yasha zanen flowers na lalle dunk’ule da wata ‘yar takarda... Yai K’uri yana duban hannun nata... Duk wannan bacci da take takardan na nan mak’ale cikin hannunta bai fad’i ba... Daga gani ba rik’on wasa taiwa takardan ba... Mahmood yakai hannunsa yana k’ok’arin bud’e hannun nata dake dunk’ule da takardar... A hankali ya warware hannun nata har ya ciro takardan... Gabansa ya buga kikaci guda sanda ya warware takardan... Zanen ginin gidan sarautar nan ya gani... Take mafarkin da yayi da ita tana guduwa da zanen ya shiga dawo masa... Ikon Allah..! Wato dai mafarkinsa ta tabbata gaskiya... Yarinyar nan tanada wani agenda d’inta cikin gidan...! Toh ya akai irin zanen da Wambai ya basa ya fad’o hannunta... Mai takeyi da zanen..? Kuma a ina Ta samu..?! Tambayoyin da suka tsaya masa a rai har suka isa masarauta... Lokacinda suka hankulan d’aukacin jama’an Masarautar naga hidindimun bikukuna da ake sannan wata labari da d’umi d’umi ta iso Masarautar cewa auren Raheemah dai ba da Mahmood aka d’aura ba da K’aninsa Yazeed aka d’aura... Wannan hargitsi yasa har Mahmood ya ciccib’i amaryarsa ya shige da ita sashen da ya tanada na musamman Don ajeta ciki... Yana fitowa ya tadda Barde da Turaki har sun sauya shiga suma, take ya kuma jaddada masu cewa babu wanda zaisan batun aurensa da Muhibbah..! Barde ya jinjina kai cikeda risinawa yana mai tabbatar masa amincinsa garesa...! Mahmood ya jinjina kai yace “Ina Kuyangin dana ce ka ware mun su...?!” Barde ya kuma risinawa yace “Allah shi baka yawan rai suna nan waje suna jiran umarninka...!” Nan ma jinjina kai yayi yace “Kasan sashen da na ajeta ai..?!” Barde ya jinjina kai yace “K’warai Rankaidad’e...!” Mahmood ya kuma daidaita tsayuwarsa yace “Akai Kuyangin wajen, aikinsu kenan su dinga kula da ita, kama daga abinda zataci zuwa komai na buk’atarta... Koda wasa kada a bari ta lek’o koda k’ofa ne har sai idan ni ne na umarta..!” Barde ya kuma risinawa yace “An gama Allah shi taimakeka...! Jaaa zamaninka dogon Sarki mai dogon zamani..!” Ya gama kirariwa Ubangidan nasa kana ya mik’e ya fice... Barde na ficewa Turaki da har lokacin bai daina sakin murmushi a hankali ba yace “Rankaidad’e ango yanzu haka za’ai hidimar nan bazaai shelan auren mai Martaba cikin Fada ba..! Ko Haka zaka tare ne bazaka bari ahalin Fada su shaida ba..!” Ya k’arashe cikin sigan zolaya yana sosa kai... Wani irin duba kurum Mahmood d’in ya aika masa, Turaki yai murmushi da tafi kama da yak’e yace “Tuba nake Allah shi taimakeka...!!” Girgiza kai kurum Mahmood d’in yayi yace “Kanada gaggawa Turaki... Sau nawa zan ce maka Ina buk’atarta cikin Masarautar nan shiyasa na aurota kafin su aurarta ga wani... Idan amfaninta ya k’are a cikin Masarautar nan zan sawwak’e mata taje ta auri wanda take so.. Babu wani abu da zai shiga taakanina da ita.. Hakan yasa na killaceta b’angare guda..! Ka fahimta..?!” Turaki ya jinjina kai yana mai k’ok’arin matse dariyarsa dan ko babu komai gaban Sarki yake... Shidai yanzu hankalinsa ya kwanta tinda bai aurarta ga wani cikin Masarautar ba ya aurawa kansa, yasan daga baya zai yarda da batunsa cewa sonta yake... Sallama Turaki yai masa dan shi kam ba baisan auren Raheema da Yazeed Mahmood ya umarta a d’aura ba... Hakan yasa baibi takan ahalin masaeautar ba yai tafiyarsa gida dan huta gajjiya daga baya yazo yayiwa Jamal murnan aure... ** Yazeed dake zaune spot d’insu shida abokansa su Zayyad suna kuma kid’asa dan ya sanar dasu daga yau ya zama Sarki, sabida ana d’aura auren Mahmood zai d’auki matarsa su koma Spain... Abokan sai kuma haukatasa suke suna duk’awa gabansa suna fad’in Allah shi taimakeka Rankaidad’e Mai Martaba Sarki Mai talakawa...! Zayyad ne ya koma gefe yana amsa waya da alama labarin ta iso masa da d’umi d’uminta... Dama a ido ne suke nuawa Yazeed suna sonsa cikin zuciyarsu kuwa har kullum downfall d’insa suke son gani shiyasa duk abotan da ba’a gina cikin tsoron Allah ba ka guji irin wannan abota da wad’annan miyagun abokai wanda zasu kaika su baroka... Babu shiri Zayyad ya k’araso yana labarta masu labarin da yaji... Tamkar sauk’an aradu haka Yazeed yaji abun, ya mik’e ya cakumo Zayyad yana fad’in “K’arya kake... K’arya kake Zayyad Mahmood ne ya auri Raheema kuma d’aukanta zai su tafi Spain ni ne nan zan zama Sarki..!!” Zayyad ya finciki wuyarsa daga hannun Yazeed yana furta “Ka zaci zan maka k’arya ne haka kawai, ai taimakonku yayi daga kai har Raheemar ya aura maku juna yanzu sai kuyi wanda babu zunubi sai Lada Your Highness ko ya kukace guys..?!” Ya k’arashe yana duban sauran abokan... Gaba d’aya suka tuntsure da dariya suna jinjina k’arfin hali irin na Mahmood, kuma abinda Mahmood d’in yayi sosai ya burgesu... Sai dariya sukewa Yazeed suna fad’in karfa ya zama loser da gaske... Mahmood ya d’arasa a ko ina... Da alama sarautar nan bazai tab’a gadanta ba... Huci kurum Yazeed yake yana ayyanawa cikin zuciyarsa Wai Yayansa Mahmood ya aura masa Raheema... Kenan shi bai aureta ba ya aura masa, kenan shirinsu ya b’aci, Mahmood bazai koma can k’asar Spain ba... Waima sabida tsaban wulak’anci da bai aureta ba shine bari ya aura masa... Who does he think he is da zai dinga yin abu gaba gad’i ba tareda neman izinin kowa ba... Lallai ma Mahmood ya wuce iyakarsa.. Waye ya basa daman deciding ma rayuwarsa... Wllhi ya taro fad’an da bazai iya, yau sai ya shayar dashi mamaki ya nuna masa bai isa dashi ba...! Fuuu ya mik’e yai ficewarsa... Zayyad yasha gabansa yace “Your Highness the bill waye zai settling bills...?!” Rai b’ace Yazeed ya ciro card d’insa ya mik’awa Zayyad zai fice Zayyad yace “No Your Highness, na sani ko empty account ka bani, ai jira zakai a duba a gani...!” Shi dai Yazeed bai iya cewa komai ba sai tururi da yake... Aiko ana zuwa wajen biyan Kud’i kati yak’iyi saima nuna declined da yakeyi... Yazeed da mamaki yake dubansa kenan an rufe katinsa bazai samu access to family account d’insu na cikin Fada ba... Gashi d’aya account d’insa babu kud’i ciki kwanakin baya abokan sunyi duping d’insa ba tareda saninsa ba suka kwashe miliyoyin dake ciki... Zuciyar Yazeed kaman zata tsage ta fito waje... Lallai Mahmood ya gama raina masa wayo... Toh wllhi yau sai anyita ta k’are koda zasu raba zumunta ne na har abada...! Yana ficewa abokan suka bisa da kallo suka fashe da dariya Zayyad na fad’in “Idan talauci Ta cinyesa ya kawo min SUV d’in nan na saya a wulak’ance dan nasan za’a kai wannan stage d’in dama ni ita nake hari..!” Sauran abokan suka kuma kwashewa da dariya d’ayan na fad’in shi kuma Ford d’in Yazeed d’in zai saya idan an karya mata farashi..! Haka suka dinga aibata Yazeed suna fad’in yanda suke tsananin son ganin k’arahensa a tsiyance... ** Da tsananin mamaki Giwa take duban Waziri da alama da matarsa ya gama waya yana sanar da ita amfani kawai yakeda Giwa tinda ta gama aminta dashi idan suka kawar da Mahmood shi kuma bazai bari Yazeed ya d’ale karaga ba kaman yanda Giwa taci buri... Zaisan yanda zai ya kawar da Yazeed sarauta ya zamto nasu...! Yau saiga hawaye na fitowa daga idanun Giwa jin irin bak’in cin amana da Waziri ya tasamma yi mata.... Giwa na hawaye take furta “Ni zaka cuta Shayibu... Ka rasa wa zaka cuta saini... Kana ikirarin kashe d’ah na dan ka d’ale karaga.. Bayan duk fad’i tashin da mukayi tare ashe cin dunduniyata kake ban sani ba... Shayibu ka bani mamaki.. Ni Turai zaka cuta..!” Waziri na muzurai yake furta “Baki fahimceni bane Rankidad’e, kinsan halinku mata saida dabara... Ta tab’a kamani ina waya dakene shine nai mata wayo nace da ita munafuntarki nake don na sami yardarki... Idan ba ya haka ba bazan tab’a shawo kanta ba da yanzu tuntuni ta jima da fallasamu.. Amma kema Kinsan bazan tab’a cin amanarki ba Giwata..!” Giwa ta katsesa da fad’in “Rufe mun baki munafukin banza munafukin wofi, bayan d’an da kake k’ok’arin ganin k’arahen nasa ma D’anka ne..! Yazeed d’anka ne ba d’an AbdulJabbar ba.. Idan ka kasheshi ka kashe d’anka da hannunka ne..!!” Muryar Yazeed suka sinkayo yana fad’in “Maami...!! Mai nakeji.... Mai nake jin kina cewa..?! Wannan mutumin... Shine mahaifina..!!!?” Ya k’arashe hannunsa na tsananin rawa yana nuna Waziri... Giwa da batasan da shigowar Yazeed ba dafeda k’irji take dubansa yanda yake wani irin tururi da huci jikinsa sai karkarwa yake yana nuna Waziri... Shi kansa Waziri da yaji batun a bazata idanu waje yake duban Giwa yana duban Yazeed.... Yazeed da jijiyoyinsa suka firfito waje tsalle yayi ya shak’o wuyan Giwa yana fad’in “Answer me..!! Tell me the truth... Waye mahaifina... Kuma karkice min wannan k’ask’antaccen mutumin shine mahaifina... Dan nayi imani sai na hak’a rami na banka maku wuta dukanku biyu kun mutu..!! Ki amsa min Maami... Kice min Abbah na mai Martaba shine mahaifina ba wanann wulak’antaccen mutumin ba..! Ki amsa min Turai..!!!” *MUHIBBAH* *62* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Giwa taji damk’a irin wanda bata tab’aji ba sai muzurai take idanunta na kuma firfitowa waje, Ji take kaman ranta zai fice daga cikin jikinta sabida tsaban azaba don wane irin damk’a Yazeed yai mata irinta wanda ransa Ke tsananin k’una... Ganin Yazeed dai kashe Giwa yake k’ok’arin yi yasa Waziri Saurin k’arasawa yana k’ok’arin ceton Giwa daga hannun Yazeed... Wawan naushin da ya kaiwa Waziri saida ya zaunar dashi har k’asa Waziri ya rik’e cikinsa yana murk’usoson azaba a wajen abinka da wanda shekaru ya ja tsufa ya sauk’o masa, zai wahala idan naushin da Yazeed yai masa bai targard’a masa wani k’ashi ba.... Yazeed bai saki Giwa ba yana hawaye yake dubanta yanda take k’ifk’if da ido tana neman tsira daga azaban da take ciki... Hawaye na zubo masa yayi wurgi da Giwa Ta koma gefe, bai daina huci ba yake nunata da yatsa yana fad’in “Kin cuceni kin zalunceni, Allah da kikayi sanadin zuwana duniya, da na zamto d’an wannan mutumin gwara ba’a haifeni ba..!! Ki tashi ki sanar dani komai da bakinki..! Ki tashi nace..!!” Ya k’arashe yana kuma finciko Giwa da har lokacin bata daina haki tana sosa wuyanta yanda Yazeed ya shak’eta ba... Shar shar da hawaye Yazeed Ke kuka yana kuma jijjiga Giwa yake fad’in “Talk to me..! Tell me everything..! Ki fad’a min ya akai wannan k’ask’antaccen mutumin ya zamto mahaifina..!!!” Ya k’arashe hawayen k’unan rai na tsartowa daga idanunsa da ya koma jazir... Giwa na hawaye take furta “Yazeed ka yafe min, wllhi bada son raina bane... Duk abinda nayi dominku nayi kaida ‘yanuwanka... Yazeed ka yarda dani, wllhi sabida ku nayi komai...!” Cikin daka tsawa hawaye basu daina zuba masa ba ya kuma fad’in “Ki gaya min ta ina kika taimakeni bayan kin sameni Ta haramtacciyar hanya... Hanyar da ko sarautar da nake da buri tsawon rayuwata banida gadonta... How could you do this to me Giwa..! How could you..?!!” Ya k’arashe yana mai kuma jijjigata hawaye naci gaba da zuba masa.... Cikin kuka Yazeed yaci gaba da fad’in “Now I get it... Shiyasa kika fifita Mahmood sama dani sabida Mahmood shine d’an AbdulJabbar ni kuma d’an wannan k’ask’antaccen mutumin... That’s why kika dage sai Mahmood ne zai sarauta... Yanzu na fahimci komai..!” Katsesa Giwa tai da fad’in “No Yazeed ka saurareni ba haka bane..!” Cikin huci ya katseta “Then how..! Yaya ne...? Bakida wani dalili da ya wuce wannan..!” Giwa ta katsesa da fad’in “Mahmood shine babban mak’iyina a duniyar nan... Mahmood shine ya hanani rawar gaban hantsi... Mahmood shine ya zame min ciwon ido... Banida buri da ya wuce na kawar dashi a doron k’asa..!!!” Ta k’arashe tana sakin huci tamkar wata zakanya... Izuwa lokacin da tsananin mamaki Yazeed ke dubanta cikin tsananin sanyin jiki.. Ya shiga girgiza kai alamun ya kasa aminta da abinda yakeji Wai mahaifiya zata tsani d’anta haka..! “Maami shin Mahmood ba shine d’ah mafi soyuwa a gareki ba..?!” Muryar Waziri ya sinkayo yana fad’in “Yazeed Mahmood ba d’an mahaifiyarka bane..!” Cikin tsananin shock Yazeed ke k’ok’arin juyowa yana duban Waziri da yayi maganar.... Waziri ya jinjina masa kai alamun tabbatarwa kana yaci gaba da fad’in “Mahmood d’an Baiwa ce, Baiwar da sukaci amanar mahaifiyarka itada AbdulJabbar bayan mahaifiyarka Ta basa kyautanta a matsayin tukwici...!!” Girgiza kai Yazeed keyi kana ya kuma karkatowa yana duban Giwa cikin rashin fahimtar abindake wakana... “Mai...Mai yake cewa Maami...? Ki min bayani.. Shin abinda mutumin nan yake fad’i gaskiya ne..? Ba kece kika haifi Mahmood ba...?!” Giwa ta jinjina masa kai hawaye na zubo mata “K’warai Yazeed kaman yanda kaji Waziri yace Mahmood shine product na cin amanata da Baiwata Izzatu da kuma mijina AbdulJabbar sukayi... Shiyasa naci alk’awarin maidashi nawa dan na d’au fansata akansa... Duk yanda Kaga na k’agu ya d’ale karaga ba sabida komai bane sai don malami na ya sanar dani wanda duk ya fara sarauta cikinku bazai k’argo ba zai mutu.. Kaga idan Mahmood ya d’ale yayi guntun zamaninsa sai kai ka d’ale ka jima kana mulkin ka wannan shine tanadin da nayi maka... Wannan shine dalilin da yasa kaga na dage Mahmood ya soma d’ale karaga dan ya tafi ya bamu waje mu kafa mulkinmu da zuri’armu..!!” Yazeed ya zauna dirshan a k’asa yana nanata kalaman mahaifiyar tasa cikin kwanyarsa... Ganin yayi shiru yana nazari yasa Giwa kamo hannayensa tana fad’in “Yazeed ina matuk’ar k’aunarka duk wannan fad’i tashi da nuna ina son Mahmood a fili dukda kasheni da hakan yake can k’asar zuciyata wa kai nake da ‘yanuwanka mu samu mu kawar da Bare d’an Baiwa cikinmu..!” Jajayen idanunsa ya d’ago yana dubanta kana yace “Koda ace shi d’an Baiwa ce but at least he carries my father’s blood, yana d’aukeda jinin AbdulJabbar na Yawo a b’argonsa... But what about me... Bana d’aukeda jininsa sai na wannan k’ask’antaccen mutumin kwarto mai bin matan mutane... Now I get it... Ashe ga yanda nayi gado..!!” Ya k’arashe yana sakin muguwar murmushinsa yana aikawa Waziri jahilar kallo... Lokaci guda ya maidoda dubansaga Giwa ya tsime sosai yana mai ci gaba da fad’in “Su kuma ‘yan uwana waye mahaifinsu tinda naga alama k’aryace zalla cikin rayuwar ahalinki... Baki haifi Mahmood ba kikac kin haifa.. AbdulJabbar bai haifeni ba kikace ya haifa.. Toh su kuma Jamal da Yazeed fah...? Naki ne ko suma satansu kikayi... Ko kuwa dai suma wannan mutumin shine mahaifin nasu.. Kodai ma akwai wani wanda bamu sani ba..?! Talk kimin magana Giwa..! Ki bud’e baki ki amsa min tambayoyi na..!!” Ya k’arashe yana mai firfito da idanunsa waje tamkar zai kuma shak’ota.... Kaman daga sama suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “Fad’a mana Turai... Jamal da Fu’ad suma ‘ya’yana ne...?!” Giwa Ta d’ago tana dubansu, ta kalli wannan ta kalli wancan, ta had’iyi miyau da k’yar sai kuma ta soma fad’in “Banida tabbas akan Jamal, Don a lokacin na shiga rud’ani... Amma Fu’ad d’an AbdulJabbar ne... Shi kad’ai ne jininsa cikin yarana guda uku...!!” Yazeed na sakin huci yake aika mata wulak’antaccen kallo, lokaci guda yake jinjina kai yana fad’in “No wonder mahaifinmu yafi son Mahmood da Fu’ad ashe yanaji a jikinsa sune jininsa na asali, no wonder sukafi kamanceceniya Ta fuskar halitta ashe sud’in sune ‘yan uwan juna...!” Ya mik’e sosai yana ci gaba da fitar da huci yake fad’in “Now that I learned banida wata alak’a ta jini da d’an Baiwa Mahmood I won’t have mercy on him... I’ll not spare him...! Now more than ever I’ve every right to the throne sabida D’an Baiwa bai gaji sarauta ba...!” Giwa tai saurin katsesa da fad’in “Karka d’auki mataki yanzu Don idan Mahmood ya san cewa banice na haifesa ba shirinmu zai lalace akansa...!!” Cikin k’unan rai Yazeed yace “To hell with your plans Giwa..!! Do you think I care...?! My life is ruined...! Kin lalata rayuwana da kika bari wanann mutumin ya zamto mahaifina..! Kin cuceni da baki bari na fito a tsatson Abbah ba... I don’t give a damn idan Mahmood yasan cewa shi d’an Baiwa ce..!!” Giwa na girgiza kai take fad’in “Idan ka sanar dashi yanzu shikenan bazai d’ale karaga ya mutu ba.. Kaga idan ka d’ale kaine zaka mutu ni kuma bazan juri rasaka ba d’ah na..!!” Ta k’arashe tana rau rau da idanu.. Shiru yayi yana dubanta tamkar mai nazari har lokacin bai daina sakin huci ba... Suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “K’warai d’ah na sarauta takace amma ka bari har mu kawar maka da Mahmood..!” A fusace Yazeed ya katsesa da fad’in “Don’t you dare call me your son ever again..! I’m not your Son.. I’m my Father’s Son..! I’m Yazeed AbdulJabbar Mahmood...! You’re not my father and you’ll never be..Get that through your this empty skull of yours..!” Ya k’arashe yana mai bubbuga rawanin Waziri Giwa Ta had’iyi miyau da k’yar sai kuma tace “Yazeed ka basa girma ko d’an kad’an ne tunda yanzu kasan komai...!” Shu’umar murmushinsa yayi yana watsa masu wulak’antaccen kallo dukansu biyu sai kuma yace “Ai kun zubar da girmanku tun lokacin da kuka zab’i ku haifoni Ta wannan hanya... Thai man is not my father, zan fad’a kuma zan nanata... I might carry his blood but har abada bazai tab’a zama mahaifina ba... My Father is dead.. Mai Martaba AbdulJabbar shine mahaifina, and Ni ya fi dacewa na gajesa ba Mahmood d’an Baiwa ba k’ask’antacciya ba...! I’d never allow d’an Baiwa jinin Bauta ya mulki Masarautar nan ba..!!” Ya k’arashe yana mai watsa masu muguwar kallo lokaci guda yasa kai ya fice daga d’akin kaman zai tashi sama zuciyarsa naci gaba da suya... ** K’AUYEN GALAMBI Ubandoma yai jigum yana duban Baba Nomau yanda yake had’a wani ruwan magani cikin sabon goran da suka ciro daga daji suka fafeta.... Ubandoma ya d’an gyara zama yace “Yanzu Baba Wai kana nufin dama ba yanke harshenta matar nan akayi ba..?!” Baba Nomau ya murmusa yace “Ubandoma kenan, matsafa babu abinda bazasu iya yi ba kai dai muyi addu’an Allah ya shiga tsakaninmu da mugu.... Ba yanke harshenta sukayi ba saidai sun d’aure harshen nata ne da muggan bak’ak’en zare da allurai na tsafi... Kaga wannan ruwan magani ne da Allah ya sammana wani d’an b’angare na ilimin saninsa, mukan tsinko ganyen cikin daji shine zatake kuskure bakinta dashi har na tsawon kwanaki uku... sai kuma ruwan addu’o’i da ayoyin Alk’ur’ani mai girma wanda babu shirka ciki da zata Ke sha na tsawon wannan kwanaki ukun..... Cikin ikon Allah da buwayarsa muna fata wannan sihiri ya karye harshen nata ya warware ya dawo dai dai cikin bakinta..!” Ubandoma ya jinjina kai yace “Masha Allah..! Allah Ubangiji yasa a dace ya kuma bamu nasara..!” Dattijo Baba Nomau ya amsada Ameen..! Suna a haka suka sinkayo muryar mai d’akinsa tana fad’in su taho Jafaru ya farka..! A tare Baba Nomau da Ubandoma suka mik’e Ubandoma na taimakawa Baba Nomau sabida girma sosai da ya sauk’o masa.... A haka suka isa wajen Jafar wanda idanunsa Ke bud’e tarau yana duban sama... Ubandoma ya zuru yana duban ikon Ubangiji Wai yau Jafar ne ya bud’e idanunsa wanda tun zuwansu wannan gari kusan sati biyu kenan yana kwance a haka ko motsawa baiyi yau sai gashi ya bud’e idanunsa.... Allahu Akbar ashe dai Allah zai tashi Jafaru...! Baba Nomau yaceda maid’akinsa Ta kawo masa ruwan maganin Jafar da ake yayyafa masa... Babu musu ta mik’e ta kawo, Baba Nomau yai bismillah ya soma yayyafawa Jafar ruwan maganin daga kansa zuwa k’afafunsa.... Wane irin mik’a Jafar yayi numfashinsa na fita a hankali a hankali.... Baba Nomau ya bud’e murya yace “Sannu yaro sannu kaji... Allah ya k’ara maka lafiya..!” Ubandoma da mai matar Baba Nomau mai suna Tabawa suka amsada Ameen a tare... Bana Nomau yace “Tabawa kawo masa ruwan addu’an da nace Ki aje shi zai soma sha idan ya farfad’o..!” Tabawa ta amsa da toh Malam kana ta mik’e ta nufi can wata Rumfar zana ta d’auko ruwan addu’an rufe cikin kwano... Ta kawowa Baba Nomau Baba Nomau ya dubi Ubandoma yace ya d’ago masa Jafar kad’an... Ubandoma yayi kaman yanda Baba Nomau yace... Baba Nomau yace “Yi bismillah kasha ruwan nan yaro..!” Lumshe idanunsa Jafar yai da alama yayi bismillah kaman yanda Dattijon ya fad’i masa amma saidai maganan nasa bai fitowa sosai... Ya kafa kansa ya shanye ruwan tas... Sauran Baba Nomau ya shafe masa fuskarsa dasu... “Sannu yaro... Ya sunanka..?!” Ya tambaya yana dubansa da alama so yake ya gane ko Jafar d’in ya dawo hayyacinsa... “Sunana Ja’afar...!” Sukaji Jafar d’in ya baiwa Baba Nomau amsa da fad’in haka... Ubandoma dake gefe bakinsa ya gaza rufuwa sabida tsananin farin ciki baisan sanda ya rungumi Jafar yana fad’in “Alhamdulillah..! Alhamdulillah Jafaru..! Jafaru Allah yayi ikonsa akanka...!!” Jafar ya d’ago idanu yana duban Ubandoma lokaci guda ya furta “Ubandoma..!!” Ubandoma ya kuma Washe baki cikeda Farin ciki yace “Jafaru ka ganeni...! Jafaru ya gane ni..!” Ya kuma fad’i yana duban Baba Nomau da tuni ya umarci matarsa ta kawowa Jafar damin fura mai kauri yasha... Jafar ya d’aga kai yana duban duniyar da yake da kuma mutanen dake wajen, lokaci guda ya maidoda dubansanga Ubandoma yace “Ina ne nan... A ina nake...? Su waye wad’annan mutanen..?!” Ubandoma yace “Ka kwantarda hankalinka Jafaru kana hannu mai kyau... Labari ne mai tsawo.. Amma kana Iya tuna mai ya sameka..?!” Take Jafar ya shiga jinjina kai idanunsa na kuma kad’awa... Lokaci guda yake furta “Na tuna..! Na tuna komai..!! Take ya soma basu labari da fad’in _Falsh back_ “Wata rana ina gyaran harawan da zan baiwa dawakin mai Martaba, ya aika a kirawoni... Kasan akwai shak’uwa da kusanci sosai tsakanina da Mai Martaba wanda sam babu shamak’i a tsakaninmu, na jima da sanin cewa matarsa Giwa bata son wannan alak’a dake tsananina da Mai Martaba Sarki...!Koda aka kirawoni ban samesa a Fadarsa ba, hakan yasa na zauna a mazaunin da na saba zama Ina jiran fitowarsa... Jim kad’an Mai Martaba ya fito da kaya irinta masu mulki a hannunsa... Bansan dalili ba amma naga daga fitowarsa ya k’araso ya rungumeni... Ya sumbaci goshina kuma naga hawaye kwance cikin idanunsa... Jikina yayi sanyi matuk’a da ganin wannan yanayi daga MaiMartaba Sarki... Yanayi ne da ban saba ganin Sarki ciki ba... Lokaci guda naga ya kamo hannayena yana duban yanda suka koma sabida ciro ciyawan abincin dawakai da aikin wahala... Take ya tambayane cikin rawar murya “Ja’afar Ina ka samu wad’annan raunin..?!” Cikin sanyin jiki nace dashi “Allah shi baka yawan rai wannan ai ba komai bane...!” Take naga Mai Martaba yasa bayan hannunsa ya share hawayen da suka zubo masa... Ban kawo komai ba dan duk a zatona cikin irin shak’uwa da Sabo ne da mukayi da juna... Jiki na ya soma matuk’ar yin sanyi, na d’an risina nace “Rankaidad’e zaka fita kilisa ne kana so a shirya maka Doki..?!” Sai gani nayi ya saki murmushi mai bayyana hak’wara, lokaci guda ya shiga bubbuga kafad’ata guda kana ya damk’a min tufafin dake hannunsa yace “Ka shiga wancan d’akin ka saka wad’annan suturan..!” Na dubi tufafin da ya bani masu daraja na kuma dubesa... Lokaci guda na kuma risinawa nace “Allah shi baka yawan rai Bawa kaman ni ban kamaci saka wad’annan kayan ba...!” Gani nayi ya saka hannu ya rufe mun baki yace “Kada ka sake ambata kanka da Bawa... Akwai maganan da nakeso muyi amma sai ka saka wad’annan suturan....!” Na jinjina masa kai a hankali dan bazan iya musu da Mai Martaba... Nayi kaman yanda yace na nufi d’akin da ya nuna min... Koda na shige d’akin tsayuwa nayi Ina kallon kayan alatu da aka k’awata wannan d’aki dashi... Nan dai na makare wajen kallon kayyayakin da idaniyata basu tab’a gani ba abinka da wanda ya taso cikin Bauta....! Bayan kaman shud’ewar wasu muryoyi sai na soma jiyo sautin Mai Martaba da Mai D’akinsa yana mata magana cikin tsananin fad’a da fushi amma bana iya fahimtar abubuwan da yake fad’i nayi saurin matsowa jikin k’ofa Ina lek’en abindake faruwa... Gani nayi Giwa ta duk’a saman gwiwoyinta ta d’aga hannayenta guda biyu sama tana rok’on Mai Martaba tana kamo k’afafunsa yana bugeta... Bai tsaya saurarenta ba ya shige wata k’ofa... Nan naga Waziri ya fito daga wata k’ofar yana dariya... Itama Giwar Dariya tayi Ta mik’e tana fad’in “Yana isa d’akin Zeenatu kafin yayi wani katab’us ya mutu dan ya riga ya shak’i iskar guban dana busa masa hannuna bazan tab’a bari ya tona min asiri ba...!” Waziri yace “Toh wani hanzari ba gudu ba, inada tabbacin ya sanar da Jafaru komai... Duk yanda Jafaru ya shiga ya fita cikin Masarautar nan mu kamasa mu gama dashi mu b’atar dashi kaman yanda muka b’atar da saura...!” Giwa tace “Aiko ya zama dole mu kashe Jafaru...!” Ni kuma jin haka yasa nayi tunanin ya zama dole nasan yanda zanyi na tsira da rayuwata daga cikin wannan masarauta da ake farautar rayuwata...! Sosai na hango tashin hankali kwance saman fuskar Giwa tana fad’in “Waziri na tabbata idan har Mai Martaba ya gana da Jafar Toh ya sanar dashi komai... Ya zama dole mu kashe Jafar... Idan har kana son alak’armu ta d’ore toh a kawar da Jafar a kashesa har lahira abinda ya kamata muyi tuntuni bamuyi ba...!” Daga nan ban kuma tsayawa saurarensu ba na nemi hanyar tsira... Na k’ulle ‘yan kayyakina da niyan barin gari koda kuwa zan sami k’alubale... Cikin daren na nemi Umaima dan nayi mata sallama a yanda muka saba had’uwa saidai wannan had’uwar cikin dare mukayi dan bazan bari gari ya waye min cikin Masarautar ba... Dan nayi imani kafin wayewar gari mugayen mutanen nan zasu iya zartar mugun nufinsu akaina...! Ban samu damar mata bayani ba saidai nace tai k’ok’ari Ta cireni cikin zuciyarta Ta mance dani... Taci kuka sosai kaman bazata k’yaleni na tafi ba... Haka dai na bata hak’uri nace Ta mance dani zanyi nesa da Masarautar nan...! A haka mukayi sallama da Umaima na tafi na barta tana kuka... Saidai Ina k’ok’arin guduwa daga cikin Masarautar naji an rad’eni da sanda an buga min sanda akai na fad’i sumamme... Ban kuma farkawa ba sai a cikin wani d’aki mai duhuwan gaske yanda naga D’an Sarki Yarima Jamal ashe shine ya dakeni da sanda ya kawo ya d’aure da sark’ok’i yana azabtar dani saidai kullum dare sai ya kawo min abinci a tsawon shekara guda da nayi rufe wajen har kawo ranan da kuka kub’utar dani cikin ikon Allah..!” Ya k’arashe yana mai sauk’e ajiyan zuciya...! Jafar yaci gaba da fad’in “Sun kashe Mai Martaba..! Kuma basu bari ya sanar dani abinda yake son sanar dani ba..! Sunyi zalunci mafi muni cikin Masarautar..!!” Baba Nomau yana mai girgiza kai yake jinjina zalunci irin na Giwa... Ubandoma yai shiru kaman mai nazari... Ya sani shi da hannunsa ya canza Jariri Ja’afar da d’an Bawa Sarkin Dawakan cikin Fada... Kardai Jafar d’an Sarki AbdulJabbar ne Giwa Ta damk’a masa ta umarcesa ya canza da gawan jaririn Sarkin Dawakai... Tabbas Giwa ta basa jariri a tsumma wanda baisan daga inda ta samo ba kuma ta umarcesa ya canza wannan jaririn da Jaririn Sarkin Dawakai wanda daga jaririn har uwar jaririn Ta kashesu... Ta kuma sanyashi ya kawo mata gawan jaririn amma banda na uwar yaron...! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Yasan yayi mugayen ayyuka ma Giwa amma wannan yana d’aya daga cikin aikin da bazai tab’a mancewa ba sabida ya shafi jariri wanda baida hakkin kowa, hakan yasa tun tasowar Jafaru cikin Masarautar yake k’aunarsa dan yasan shi ya canzasa da d’an sarkin Dawaki bayan Giwa ta kawosa cikin Masarautar... Toh ina Giwa takai wancan gawan Jaririn da ya kai mata wanda ta saka shi ya canza da Jafar... Kenan Ta aje Jafar ya rayu da Sarkin Dawakai kan cewa uwar Jafar matar Sarkin Dawakai Ta mutu Ta bar jinjiri a raye kenan.. Bayan kuma ya sani Matsafan Giwa su suka kashe Matar Sarkin Dawakai da jaririnta, Giwa ta karb’i gawan jaririn ta canzasa ma uwar Jafaru... Toh Wai ma wacece Uwar Jafaru da Giwa tayi wannan badak’ala da d’anta... Maiyasa ta canza mata d’anta da macacce..?!” *MUHIBBAH* *63* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali take jin idanunta da suka matuk’ar mata nauyi suna bud’ewa... Ta saka hannayenta tana murtsuka idanun nata... Tin daga kan gadon da take kwance bisa ta soma bi da kallo har izuwa d’akin da take ciki... Ta d’aga kanta sama sosai tana duban d’akin wanda yafi mata yanayi royal bedroom, komai na cikin d’akin gwanin ban sha’awa ne da burgewa... Ta kuma mik’ewa zaune sosai tana mai kuma k’are ma tangamemen d’akin kallo, ga kayan ado na alfarma da aka k’awata d’akin dasu... Toh inane nan...? Yama aka tazo nan, ita abinda zata iya tunawa shine tana zaune rik’eda Taswiran da mahaukaciyar nan ta damk’a mata tana kallo tana hawaye tana ayyanawa cikin zuciyarta shikenan Allah ya nufa bazata San dalilin da yasa matar nan ta bata taswiran ba kwatsam Aunty Gudidi ta shigo da wani had’i cikin cup tace da ita maza ta kafa kai ta shanye yanada kyau wa amare..! Koda taji shigowar Aunty Gudidi sai tayi saurin dunk’ule takardan cikin hannunta.. Ta amshi cup d’in da d’aya hannun Ta kafa kai ta shanye abinda Aunty Gudidi Ta umarceta da Ta shanye, tin daga nan bata kuma sanin ina take ba tasan dai kaman bacci ne yayi awon gaba da ita...! Toh mai ya faru tinda tayi baccin..?! Kenan ta jefar da zanen garin bacci ba tareda ta sani ba..! Toh Wai ma ina sauran mutanen suke, ina k’awayenta ina Ansar.. Ina Mommy..? An d’aura auren ko ba’a d’aura ba..? Waima a wace duniyar take ne..??! Tambayoyin da Ta dinga jerowa kanta kenan... Ta mik’e k’afafunta a hankali ta sauk’o saga saman gadon tana mai taka cikin d’akin kaman mai tsoron tafiya... Allah ya gani kanta ya d’aure Ta rasa meke wakana a rayuwarta... Ta isa jikin window a hankali tasa hannunta kaman mai tsoron kada a ganta ta d’an janye labulen... Nan ne gabanta yayi wane irin yankewa ya fad’i, ta sake shafe idanunta domin tabbatarwa.. Cikin masarauta Ta dawo..? Waye ya dawo da ita..? Shin kodai Giwa tabi sawunta ne ta dawo da ita bayan ta fahimci itace Saudatu..? Kodai Fu’ad ne ya sanar dasu itace Saudatu kuma tana raye shine suka bita har gida suka saceta ranan aurenta suka dawo da ita cikin Masarautar..! Tinani barkatai taketa faman yi tana sak’awa tana warwarewa... Da alama daga ita sai suturan dake jikinta tazo... Gashi babu wayarta a tareda ita balle tayi k’ok’arin kiran Ansar taji meke faruwa.. Ita kam gaba d’aya kanta ya k’ulle.... Tana nan tsaye wasu bayi ‘yanmata guda uku suka turo k’ofa suka shigo... Gaba d’aya suka zube har k’asa suna kwasan gaisuwa wajenta... Muhibbah tabisu da kallo cikeda mamaki tana ganin abin banbarak’wai... Bayin cikin Masarautar sun saba duk’awa suna gaisheta amma yanda wad’annan suka zube gaba d’aya gabanta lokaci guda sai taga abin yayi mata wane iri... Ta kasa furta komai sai binsu da kallo da take... ‘Yar babbar matar daga cikin Kuyangin ta bud’e Murya tace “Sunana Kande sunan wancan Julde, ita kuma wannnan sunanta Hasiya.. Mune masu kula da al’amaranki da duk abinda kike so Ya Shugabata..! Ga ruwan zafi mai k’amshin furanni an shirya miki a ban d’aki Ki shiga kiyi wanka..! Idan kika fito sai ki sanar damu kalan abincin da kike so a kawo miki..!” Izuwa lokaci Muhibbah ta soma k’osawa da wannan karatun da Baiwar ke karanto mata wanda bama fahimta take ba, hakan yasa ta katseta da fad’in “Wa ya baku umarnin kuyimin wannan hidima..? Kuma Maiyasa aka kawoni nan aka ajeni..?” “Ki gafarceni ya Shugabata.! Umarni muke bi muma, idan kinyi mana izini zamu baki waje domin Ki kimtsa..!” Ta k’arashe kanta a k’asa... Muhibbah tai shiru yana dubansu ba tareda Ta kuma cewa komai ba... Can kaman bazatayi magana ba sai kuma tace “Ina son sanin umarnin wanda kuke bi...!” Kuyangar Ta murmusa kad’an tace “Zan sake neman gafara a gareki.. Ki gafarceni Rankaidad’e amma sanar dake umarnin wanda muke bi ba huruminmu bane... Aikinmu kad’ai shine kula dake... Allah shi taimakeki..!!” Takaicin Kuyangar ya kama Muhibbah sanin cewa ita Amarya ce ta tabbata mijinta da Mommy suna can suna neman duniyar take wannan matar ta zauna tana mata wani fadanci maras dalili... Ta dubi sauran bayin ‘yanmata guda biyun tace “Ku kuna iya tafiya amma Ke ki tsaya..!” Ta k’arashe tana nuni da Babbar wacce ta gama mata magana... Suka dubi shugabar kuyangar tasu ta jinjina masu kai alamun suje.. Take suka kuma duk’awa alamun girmamawa ga Muhibbah kana suka fice... Suna ficewa Muhibbah ta k’araso gaban Matar tana dubanta, lokaci guda kuma Ta zauna dirshan a gabanta itama, cikin yanayi kaman Ta mai son yin kuka Ta soma fad’in “Dan Allah Ki taimakeni..! Kada Ki bari azzaluman Masarautar nan su cimma burinsu akaina.. Wllhi nasan kasheni sukeda niyya... Kinga ni Amarya ce yau ake d’aura aurena suka sato ni.. Kin gani kinga k’unshi na kin gani dan Allah Ki taimakeni kema mace ce ki tai..!” Gaba d’aya tamkar wacce bata a hayyacinta haka yake maganganun tana nunawa Kuyangar lallen hannuwanta tana kwaye zaninta tana nuna mata na k’afafunta alamun tana tabbatar mata da cewa ita d’in Amarya ce.. Saurin rik’o hannunta Kuyangar tai ta dakatar da ita da fad’in “Kiyi hak’uri Rankidad’e, ni kaina banida bayanin da zan miki a halin yanzu.. Abu guda da na sani shine zaki rayu a nan na d’an wani tsawon lokaci... Watak’ila Ki samu amsoshin da kike nema..!!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye, Ta risina alamun girmamawa tace “Zan jiraki daga waje har ki gama kimtsawa..!” Ta k’arashe kanta a k’asa... Muhibbah tana gani Kuyangar nan ta fice ta barta nan zaune dirshan a k’asa wani irin kuka had’ida tausayin kanta na zuwa mata... Meke faruwa da ita..? Shin kodai nan ba Masarautar data sani bane.. Ko wasu mutane ne daban..! Innalillahi wa Innalillahi raji’un..! Shi take nanatawa cikin zuciyarta... Ta mik’e da sauri ta isa jikin window ko zata hango wasu mutane tayi ihun taimako... Toh amma idan tayi ihun taimako tasan babu mai taimakon nata tinda mutanen da suka ajeta a nan dole sun bata tsoron da bazata iya guduwa ba... Allah ne kad’ai zai ceceta daga wannan uku d’in data tsinci kanta ciki... Ta koma kan gadon ta zauna ta tak’ure waje guda tana kuka sosai... Daga nan cikin d’akinsa yana zaune saman sofa k’afarsa d’aya bisa d’aya yake kallon duk wani movement nata a makeken na’uran nasara dake gabansa wanda k’ank’anuwar camera dake cikin d’akin nata yana nad’o masa komai ya nuna masa... Yai mata K’uri yana duban yanda take cazgan kuka... Ta kuma mik’ewa ta nufi window harda ‘yar k’ok’arin tsallanta alamun tana son ta bud’e tagar tai escape... Yanda take tsallen yaso basa dariya amma bai dariyar ba sai ma saita remote da yayi ya kashe na’uran... Zobban dake hannunsa yake murzawa a hankali yana mai furtawa a fili “Whatever you’re hiding nasan dole zai fito... Sannu a hankali zan fahimci wacece Ke da kuma abinda kike b’oyewa...!!” Yai shiru yana nanata kalamanta ga Baiwar _Ni Amarya ce ki taimaka ki fitar dani, mijina na can yana nemana... kasheni zasuyi.._ Kalmar zasu kasheni data fad’i yaketa nanatawa, kenan tabbas akwai wani k’ulli da take dashi cikin Masarautar.. Ko menene wannan k’ullin... Sannu a hankali zai fahimci haka.. Ya k’arashe tunanin nasa yana mai warware zanen ginin gidan sarauta da ya samu a hannunta... Lokaci guda yake kuma karantar zanen... A hankali ya mik’e ya fito sararin waje daga nan saman benen nasa yana k’arewa fad’in Masarautar kallo... Can ya hangi motoci ‘yan kawo Amarya Raheema suna tururuwar shigowa... Ya saki murmushi da gefen bakinsa a hankali kana ya nad’e hannayensa ta baya yana mai kallon yanda motocin Ke shigowa sahu sahu... Yana ganin aka fito da Raheema rufe cikin Alkyabba aka nufi b’angaren Giwa da ita.. Bai kuma bi takansu ba sai ma sauk’owa parlornsa na k’asa da yayi ya kunna labaru... ** A can Fadar Giwa kaw ana tsaka da bukin al’ada Amarya Umaima na tsakiya an rufa mata alkyabba ana raye raye da kid’i kid’i kaman yanda yake a al’adarsu ranan d’aurin aure akanyi irin wannan bukiga amarya kwatsam sukaji isowar su Raheema da masu kawota...dama tuni labari ya iso masu cewa auren Yazeed da Raheema aka d’aura... Hankalin Giwa da Waziri idan yayi dubu ya tashi dukda k’ok’arin danne hakan da Giwa take dan a halin yanzu abubuwan dake kanta sun sha k’arfinta k’iris ya rage su tarwatsa mata kwanya, ga takaicin shikenan shirinsu na d’aura alhakin mutuwar Mahmood kan Raheema da Zeenatu ya tashi a aiki tinda ba’ayi auren da Mahmood d’in ba, Gashi tinda abin ya faru ko idanun Mahmood basu gani ba dan su duk a nasu zaton shima can wajen Auren Raheemar ya tafi hakan yasa Giwa bata ko yi tunanin nemansa ba... Har sai yanzu da aka shigo mata da Raheema matsayin matar Yazeed..! Yanzu ne suke kuma tabbatarwa Yazeed aka aurawa Raheemah ba Mahmood ba.. Tirk’ashi..! Kuka sosai Raheemah take cikin dandatson taron ‘yan biki tana fad’in itafah sai an canza wannan aure an maida kan Sarki Mahmood... Ita ba Yarima Yazeed bane mijinta...Gimbiya Zeenat na gefenta tana lallashinta... Abinka da gidan biki cike gidan yake da ‘yanuwa da abokan arziki dikda cewa sabida tsaban mugun hali irin na Giwa bata cika tara mutane ba amma an cika kam abinda da gida na sarauta... Matayen masu madafan ikon cikin Masarautar duk suna nan, kama daga matan Waziri Galadima Matawalle Liman Sardauna da dai sauransu duk Sun hallara a Fadar Giwan dashike yau d’in ranan shagalin buki ne Giwa ta dubi tawagan ‘yan tawagan kawo Amarya tace “Ku kwantar da hankalinku za’ai komai a tsanake irinta babban Gida...!” Muryar Zuhra ne kaman daga sama suka sinkayo tana fad’in “Ina girma a gidan da babu wani Girma..!” Gaba d’aya kallo ya dawo kan Zuhra harta Giwa saida ta kaikaito tana duban Zuhra dake K’arasowa cikin Fadar...! Zuhra ta K’araso tsakiyan taron ta isa har gaban Raheemah... Gimbiya Zeenat na k’iftawa Zuhra idanu kan tayi shiru amma inaa ko kallo bata ishi Zuhra ba... Zuhra ta tsaya sosai gaban Raheemah.. Ta saka hannu ta d’aga alkyabbar da aka rufa mata, fuskarta ya bayyana.... Murmushi Zuhra ta saki kana tace “K’awata ko ince kishiyata...Haba Amarya miye na d’aga jijiyar wuya kan cewa sai an canza aure ya koma kan Mai Martaba Sarki Mahmood..? Karfa ki mance kowa da daidanshi Allah yake had’asa kuma shi Sarki taimakonku kawai yayi ya rufa maku asiri gashi Ke kina neman tonawa kanku asiri..!” Gimbiya Zeenat ta katseta da fad’in “Ke Zuhra ya kike abu kaman ba d’iyar manyan mutane ba... Kaman ba jinin sarauta ba...!” Zuhra ta murmusa tace “Tuba nake Rankidad’e..! A gafarceni amma gaskiya nake fad’i... kuma Ita wacce aka d’aurama auren ta fini sanin gaskiya nake fad’i..!” Ta juyo tana duban Raheema da Hawaye Ke kuma gangaro mata tace “Da bakiyi bore kin tonawa kanku asiri ba kika bar abin a rufe kaman yanda Sarki mai adalci da halin Dattako yayi maku abin a sutirce da ya fi miki... Amma kika zab’i Ki tona kanku.. Toh nidai babu abinda zance saidai nace Allah ya bada zaman hak’uri dan idan a baya anyi zaman sharholiya da shagala yanzu kam saidai Ayi hak’uri... Ayita hak’uri da juna ana kai zuciya nesa dan shi maci mana baya fasa hali.. Sai ki gani ki kauda kai kiji kiyi kaman bakiji ba shawarita kenan...” Katseta Gimbiya Zeenat tayi da fad’in “Amma dai ke bakida kunya, dik yanda akai ke ba ‘yar babban gida bace... Kishi ne kawai yasa kike fad’in haka dan Raheema ta aure mijinki..!” Zuhra ta katseta da fad’in “Wazai b’ata lokacinsa ya tsaya kishi kan wanda baisan k’imar d’iya mace ba balle har yasan sadakar Aure.?! Rashin kunya yasan yanda ya samo asali... Auren Sarki Mahmood da kike k’ok’arin k’ullawa tsakaninsa da k’anwarki ba sabida komai bane sai don kinaso ku shanye Sarki Mahmood ya koma sai yanda kukayi dashi, dan bakida burin da ya wuce ki mallaki matsayin Giwa cikin Masarautar nan.. Shin gaskiya na fad’i..!” Ta k’arashe tana dubanta... Gimbiya Zeenat Ta soma muzurai tana tattare tabarmar kunya da bori... Ita kaw Giwa batai mamakin jin haka ba tinda har Waziri ma ya tasamma cin amanarta,kowa ba abin yarda bane a wannan Masarauta... Ita Giwa tana k’ok’arin k’ulla tugguwa Raheema da Zeenatu bayan Raheemar Ta aure Mahmood ashe suma su Raheemar da nasu k’ullin akan Giwan... Tirk’ashi Mahmood dai da baida hakkinsu gaba d’aya Allah ya tsallakar dashi, shiyasa duk abunda mugu ke k’ulla maka idan baka da hakkinsa sai Allah ya maida masa sharrinsa kansa... Gashi dai Allah ya tsallakar da Mahmood tsakanin k’ullin wad’annan mugayen mutanen... Taro ya hargitse mata aka soma ‘yar k’usk’us ana kame baki... Kayan kunya dai bazasu daina faruwa cikin wannan masarauta ba... Matar Wambai kaw da nata tawagar suka sami abinyi... Iyakacin kunya dai Giwa ta gama shansa a bainar jama’a... Haka aka dinga silalewa ana ficewa daga Fadar Giwa... Umaima kaw kuka Ta dinga yi ganin wannan kayan tashin hankali dake faruwa ranar aurenta... Haka Zahra da Hadimanta suka janyota d’aki suna lallashi... Giwa ma dai da taimakon Hadimanta ta bar cikin Fadar dan har yanzu Jakadiya jinya take bata warware ba da itace zatai jagorawa Giwa... Aka bar Raheema da tawagarsu nan wajen, sai kuma jinjina lamarin suke, masu k’usk’us daga gefe nayi.. Lallai sun sami labarin komawa masarautarsu dashi... ** Hankali kwance yake kallon tashan labaru na Aljazeera, hayaniyar Yazeed ya somaji da alama dogarai masu tsaron k’ofarsa sun hana Yazeed d’in shigowa... Can kuma saiga Yazeed d’in ya kutso yana fad’iwa Hadimin Mahmood koda wasa kada ya k’araso kusa dashi... Hannu Mahmood ya d’agawa Hadimin alamun ya fice ya k’yalesu... Barde ya risina alamun girmamawa kana ya fice... Yazeed na huci yake duban Mahmood lokaci guda yake furta “Yaushe Bayi k’ask’antattu suka samu ‘yanci cikin gidan nan da har zasu hanani shiga yanda duk nakeso a fad’in Masarautar nan... Waye ya baiwa Bawa k’ask’antacce ikon dakatarda ‘yantacce...!?” Daga yanda yake kishingide ya lank’wasa k’afarsa guda had’ida d’aura hannunsa guda saman k’afar yana murza zobensa a hankali, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa ya baiwa Yazeed amsa da fad’in “Ba ma kowa na saka shamak’i cikin ahalin gidan nan ba... Wa mutum d’aya na saka kuma kaine... So umarnina suke bi da sukayi yunk’urin hanaka..!” Yazeed na sakin huci yake furta “Ka daina yin wani abu kaman kaid’in ka zama Sarki... Karka mance har yau ba’ai bikin nad’aka matsayin Sarki ba, ba’ai maka wankan sarauta ba, ba’a mallaka maka sandar Mulki ba, ba’a d’aura maka rawanin Sarki ba, ba’a d’aura maka d’amaran Sarki ba, ba’a rufa maka alkyabbar sarauta ba, ba’a kuma buga maka Tambarin Saraki ba... Har yau baka d’ale Karagar ba suna suke baka a baki...So komai ka iya faruwa...! You never know mai zai faru anjima ko gobe... Everything is possible... Ta yuyu wannan karaga da kake ganin k’iris ya rage ka d’ale ba Naka bane..!!” Ya k’arashe yana sakin muguwar murmushi.... Murmushin Mahmood ya mayar masa kana yace “Allah shike bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso a kuma lokacin da yaga Dama...! Zuciya da ta aminta da tayi imani da hakan bazata tab’a damuwa don ta samu ko ta rasa ba... Komai a rubuce yake tuntuni..!!” Yazeed yaci gaba da sakin huci yana duban Mahmood d’in yana ayyanawa cikin zuciyarsa ranan da Mahmood d’in zai San cewa ba Giwa ce ta haifesa ba k’ask’antacciyar Baiwa ce ta haifesa... Har ya sa kai zai fice sai kuma ya dawo da baya yace “Kayi gaggawan warware auren wasan yaran daka d’aura min dan ban amince da wannan auren ba kuma bazan amince ba...!” K’asaitaccen Murmushi kwance saman fuskar Mahmood yake fad’in “ Wuk’a da nama a hannunka suke dear brother..! Kayi yanda Kaso da Matarka taka ce..! She is all yours... Igiyar aurenta a hannunka yake ba’a hannuna ba sai yanda kaso kayi..!” Daga haka maida hankalinsa kacaukam ga talabijin yayi ba tareda ya kuma bi takan Yazeed dake tsaye nan waje takaici na neman kashesa ba... Ji yake kaman ya k’arasa ya lumawa Mahmood d’in wuk’a a ciki kowa ma ya huta... Ya tsani Mahmood ya tsanesa, baida babban mak’iyi a duniya sama dashi..! Fuuu yasa kai ya fice kaman zai kifa k’asa, duk ya fice hayyacinsa ko buttons d’in wuyar rigarsa bai iya had’awa duk ya koma kaman wani zaucecce lokaci guda.... ** Safa da Marwa kurum Giwa take nan k’uryar d’aki, takai mari Takai gauro... Ya zama dole taga Tal’udu dan yanda take tunanin al’amaran sun kai har sun zarce nan... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *64* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Koda Zuhra ta koma sashenta rungume yaranta tayi tana kuka sosai, sai kuma taji sam bata kyauta ba... Komin yaya ne halin Yazeed he’s still her children’s Father, Ji take kaman Ta muzanta yaranta ne a idon duniya... Gaba d’aya sai tausayin yaran nata ya rufe ta... Tana kuka ta rungumesu sosai tana furta su yafe mata dukda cewa yaran bama su fahimci nufinta ba sudai kawai sunga mahaifiyarsu na kuka sosai... Ta macen tasa hannu tana sharewa mamarta hawaye suna masu ci gaba da bata hak’uri.... Hadimarta Ta K’araso ta risina tace “Rankidad’e an gama shirya kayyakin gaba d’aya...!” Zuhra ta jinjina kai tana mai k’ok’arin saita kanta tace “Ki sauk’o da kayan k’asa gobe idan Allah ya kaimu fitan sassafe zamuyi...!” Hadimar ta jinjina kai had’ida risinawa tana mai amsawa... Sultan ya dubi nahaifiyarsa yace “Momy tafiya zamuyi..? Ina zamuje..? Ba’ayi hutun sch ba..!” Ta k’ak’aro murmushin k’arfin hali ta shafi kan yaron tace “Masarautar su Deedah zamuje baka so..?!” Jin an ambaci Deedah kakarsa sai ya soma murna yana cewa eh yana son zuwa...! Suna a haka Yazeed ya shigo tagajan magajan tamkar wanda aka jefosa... Sultan ya tafi ga mahaifinsa da gudu yana fad’in “Daddy zamu tafi Masarautar su Deedah kaima zaka bimu...?” Baki sake Yazeed Ke duban yaron cikin rashin yarda da abinda yakeji daga bakin yaron, ya dubi Zuhra wacce tai kaman bata San yana wajen... Bai ida mamaki ba saida ya hango Kuyangar taba sauk’owa da suitcases nik’i nik’i... Ya kuma maida dubansaga Zuhra wacce Ke k’ok’arin mik’ewa... Tamkar zautacce ya isa gareta yana fad’in “Can you tell me what’s the meaning of this..?!” Zuhra ta bud’e murya ta kirawo Hadimar tace ta haura da yaran upstairs.. Babu musu Hadimar ta k’araso ta risina ta gaida Yazeed Wanda ko kallo bata ishesa ba kana Ta janye yaran suka haura sama... Zuhra tasa kai kaman zata shige Yazeed yai saurin rik’ota da k’arfin gaske yana sakin huci yake fad’in “I think I asked you a question..?!” Murmushi tai wanda kai tsaye za’a iya cewa na takaici ne kana tace “Abinda idanunka ya gane maka Toh haka ne..!” “I’m still your husband Zuhra..! You’re not going anywhere.. Dan haka ki cire ranki... Kina nan a Masarautar nan tareda ni da yaranmu... Bazan tab’a barinki ki tarwatsa ahalinmu ba... Sultan zai gaji sarautar wannan masarauta dan haka bazan barki ki b’ata min shirina ba kin fahimta..!” Ya k’arashe yana sakin huci... Wulak’antaccen kallo take aika masa kana tace “Wane ahali kake magana..?! Ahalin da ka riga ka gama tarwatsawa.. Tausayin yarana nake ace sunada Uba irinka.. Shiyasa sam bazan barsu su girma cikin wannan Masarautar ba wanda koba jima ko ba dad’e sai an goranta masu halin mahaifinsu da abun kunyar da ya jawo masu..! Yazeed ka mance da batun aurenmu dan ka sami wacce zata maye gurbina a yanzu, yarana kuma bazan barsu hannun azzalumar matarka ba dan bansan wane irin tarbiya Zata basu ba, idan sun girma sun mallaki hankalin kansu zasu iya dawowa Masarautar mahaifinsu amma ba yanzu ba... A halin yanzu yarana ni sukeda buk’ata bakai ba...!” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige... Yazeed yai saurin shan gabanta yana mai ci gaba da huci... Sallaman mutane ne da suka sinkaya daga k’ofar Parlorn ya karkata hankalinsu.... Tawagan ‘yan rakiyar Amarya Raheema ne suka rakota sashen angonta.... Zuhra tana ganinsu Ta saki murmushi mai kyau kana Ta maidoda dubantaga Yazeed tace “Looks like your bride is here already, Allah bada zaman Lafiya ya kad’e fitina..!” Ta kuma sakar masa murmushi tayi hayewarta sama ya barsu... Shi kuwa Yazeed dafe da kunkuminsa yake dubansu... Baiko bi takansu ba yayi ficewarsa... Can spot d’insu ya tafi dan gaba d’aya ji yake duniyar na juya masa, da ace zai sami sararin yin kuka da yayi ko zai d’an ji sanyi cikin zuciyarsa... Haka ya dinga d’irkawa cikin barasa babuji babu gani a tinaninsa hakan ne kawai zaisa ya sami sauk’in abinda yakeji cikin zuciyarsa.... Tin ma’aikatan club d’in na d’aukan abin kaman wasa hardai sukaga abin ya zarce tunaninsu gashi yau d’in babu abokan Yazeed ko guda da suka je, haka dole guda d’aya daga cikin ma’aikatan ya d’aga waya ya kirawo Zayyad ya sanar dashi halinda Yazeed ke ciki... Babu shiri Zayyad ya k’araso ya tadda Yazeed sai layi yake yana sunbatu ma’aikatan club d’in sun hanasa fita bai biyasu kud’i ba... Yazeed ya cakumo guy d’in yana fad’i cikin murya irinta ‘yan maye “Kasan ko ni wanene...! Kasan ko ni wanene da har zaka hana ni fita...? I’m Prince Yazeed AbdulJabbar..! I can buy the whole club including you yourself..!” Ya k’arashe yana mai kuma shak’e masa wuya... Da k’yar Zayyad ya b’anb’are mutumin hannun Yazeed ya ciro kud’i ya biya bashin da ake bin Yazeed d’in kana ya shiga janyosa yana fad’in su tafi, Yazeed d’in sai tarjewa yake yana sunbatu yana amo da bak’in cikinsa... Har cikin Masarauta Zayyad ya kawosa a haka, yana shiga sashensa yaci karo da Raheemah cikin d’akinsa saman gadonsa ta baje tana shek’a bacci... Da tangad’i ya isa gareta ya k’ura mata idanu, baice komai ba ya nufi closet ya zaro belt ya nannad’e cikin hannunsa, Raheema da san bataji shigowar mutum ba sai sauk’ar bulala taji cikin jikinta, ta kwand’ara ihu ta mik’e tana fad’in kwarankwatsa ya fad’o mata... Yazeed yace “Bai fad’o maki ba tukuna somin tab’i ne wannan.... Uban wa ya baki izinin d’ale min kan gado..?!” Raheemah na hawaye take furta “Yazeed Ina zanje fisabilillahi, Aunty Zeenat ta koroni daga sashenta tace tinda Bazan zama matar Sarki Mahmood ba zamana wajenta baida amfani tace dole na tafi d’akin mijina na bar mata sashenta..!” Yazeed ya tintsire da dariya yana nunata da belt belt d’in yake fad’in “Itama tasan bakida amfani kenan tinda baki auri Mahmood ba... Toh haka nima babu amfanin da zaki min tinda kika kasa cika min burina na auren Mahmood... Da yanzu kin auri Mahmood da na zama Sarki amma sabida dolanci irin Naki kika bari Zuhra tabi bayanki har Ta gano ina kike zuwa...!” Cikin kuka Raheema ke girgiza kai alamun a’a tana fad’in “Wllhi Allah ban San Zuhra zataje wajen nan ba, kaima kasan nafi kowa yin taka tsan tsan... The whole thing affects me more, na rasa Aminiyata na rasa masoyina Mahmood, wllhi ji nake rayuwar gaba d’aya ta fice raina..!” Yazeed yace “Munafuka rufe mun baki... Duk kece kika janyo halinda na tsinci kaina ciki, kuma yanzu basai anjima ba zaki fara nadaman aurena da kikayi..!” Yana kaiwa nan ya shiga janyota tana tarjewa tana fad’in mai zai mata.... Ko amsata baiba saida ya d’auko sellotape d’in da yake manne bakin Zuhra dashi idan zai jibgeta danma kar tayi ihu aji... Haka Raheema tana ji tana gani tana zaro idanu waje cikeda mamakin abinda Yazeed ke k’ok’arin yi... “Yazeed no...What are you doing..? Please no..!” Inaa ko saurarenta baiba ya manne bakinta da sellotape d’in ya kuma janyota ya d’aure jikin gado ya shiga jibganta tamkar wanda aka turosa, baiji bai gani dukan Raheemah yake tana runtse idanunta masu zuban hawaye babu hali tayi ihu dan bakinta a rufe yake... Duk wani takaici da bak’in cikin da Yazeed ke ciki akan Raheema ya sauk’esu tass da bugu... Saida yaga kaman numfashinta na neman d’aukewa kana ya sarara mata da bugu .. Yana nunata da bulalar yake fad’in “A nan zaki kwana a d’aure kuma babu mai shigowa balle ya ceceki... ** A b’angaren Muhibbah kuwa sosai taci kuka har Ta gode Allah, tayi tunanin tashi ta gabatar da salloli ko zata sami sauk’in halinda ta tsinci kanta ciki amma sai taci karo da al’adarta tazo mata... Tai saurin mik’ewa tana duba bayan skirt d’inta yanda yayi stain... Ga dare gashi bama tasan ya za’ai ta sami sanitary pads ba, gashi Kuyangin duk basa nan... Ta isa k’ofa tana bubbugawa ko za’ajita amma shiru alamun babu kowa gajeren tsaki tayi Ta komo cikin d’akin tana tinanin abinyi... Closet ta bud’e yanda taga kayyaki ne na alfarma jere cikin closet d’in na kwalliyan mata amma saidai babu alamun sanitary pad a wajen... Ta d’an tab’e baki kad’an ta nufi bathroom d’in dan dole tayo wanka a halinda ta tsinci kanta ciki.... Komai na band’akin abin burgewa ne, ga wani ni’imtaccen k’amshi da yake tashi... Harda Sabon toothbrush da toothpaste aje saman sink Wato dai duk an aje mata kenan, ko wane salo Giwa tazo dashi kuma yanzu oho... Can sama da jacuzzi ta hango k’aton tambarin heart mai furanni ciki an rubuta M&A... Taita nanatawa cikin zuciyarta M&A ko mai hakan yake nufi oho... Batayi using ruwan k’amshin da aka had’a mata ba Sabida yanayin da take ciki, koma bata a wannan yanayin bazata shiga ruwan da bata San wane tsidsabaru bane Giwa ta saka mata ciki... Wa ya sani ma ko ta haka zatai mata nata kisan gillan, ta nufi cubicle dake gefe nan cikin bathroom d’in abinta ta sakar ma kanta shower.... Tana jin ruwa mai d’umin na ratsa cikin kanta da jikinta hawaye na kuma gangaro mata... Ansar kurum take hangowa tasan duk yanda yake yanzu hankalinsa yakai k’ololuwa wajen tashi... A daidai lokacin da take wannan tunani tana hawaye Ansar yana can gadon asibiti yasha drip guda an d’aura masa na biyu yana kuma sha... Mommy da Hameedah zaune gefensa an rasa mai lallashin wani cikinsu.... ** Da mamaki Turaki yake bin wayar nasa da kallo, k’arfe shabiyun dare har ta gauta... Allah yasa yana parlor yana kallo bai shige d’aki ba tukuna... Ya d’aga wayar Rankaidad’e suna gaisawa , daga d’aya b’angaren Mahmood yace “Sanitary pads nake so...!” Turaki ya gyara zama yana nanatawa “Cikin daren nan Rankaidad’e...?!” Mahmood ya jinjina masa kai yace “Eh cikin daren nan...!” Turaki yace “Amma Rankaidad’e baza’a bari zuwa safiya ba...?!” Cikeda k’osawa Mahmood yace “It can’t wait till morning... Yanzu nake so..!” Turaki ya murmusa kad’an yace “Toh an gama Rankaidad’e..!” Mik’ewa yayi ya zari car keys d’insa ya tsaya a manyan store’s da yasan zai samesu a bud’e komin daren, ya saya ya nufi Fada dashi.... A parlor ya tadda Mahmood d’in alamun isowarsa yake jira... Kasancewar dare ne yana damk’a masa bai wani zauna ba ya juya abinsa... Mahmood kaw da kansa ya nufi b’angaren dan Dama sashensa da yayi zaman aure da Aliya nan ya aje Muhibbah ciki, yanada mabud’an ko wani k’ofa a sashen... Abinka da dare k’afa ya d’auke babu wanda ya kula da fitowarsa har ya isa shashen... Da mabud’an hannunsa yayi amfani ya bud’e ko wacce k’ofa har ya isa d’akin da Muhibbah take... Yayi tsaye yana jin yanda ruwa Ke zuba daga bathroom alamun har yanzu dai bata fito daga wankan ba... Can gefe ya hangi abincin da aka kawo mata ko tab’awa batai ba, babu abinda taci ko ruwa bata sha... Yasan bazai wuce tsoro takeji ba, hannu yasa cikin aljihun jallabiyarsa ya ciro ‘yar k’aramar pen ya isa jikin paper bag d’in yayi rubutu... Ita kaw Muhibbah har lokacin tunanin Ansar da Mommy take hawaye na ci gaba da zuba mata tasan dukansu biyu hankalinsu ba’a kwance yake ba da tashinta duk yanda suke... Duk azzalumin da ya d’aukota ya aje a nan ya cuceta ya kuma cuci ahalinta, har abada bazata tab’a yafe masa koma wanene.. Balle ma tasan Bazai wuce aikin Giwa azzaluma ba, tasan wani tanadin mugunta take mata, kafin Ta cimma burinta akanta zata San yanda zatayi ta guje daga wannan kurkukun da izinin Allah... Tana wannan tunani Ansar yana can ya kuma bud’e idanunsa ya dubi Mommy ya dubi Hameedah... Mommy Ta taso da sauri ta dafasa tana fad’in “Ansar a kira Dr ne... Ansar d’ah na talk to me..!” Lumshe idanunsa ya kumayi sai yace “Mommy Muhibbah... Take me to her... I want see her... Please take me to her...!” Tin daga haka bai kuma cewa komai ba sai kuma rufe idanunsa da yayi... Kukan da Mommy Ke k’unshewa ya kuma kece mata... Kuka take tana fad’in “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Oh ni Murjah yau naga takaina... Na halak’a d’ah nah da kaina...! Ansar duk abinda ya sameka Bazan tab’a yafewa kaina ba... Domin kuwa ni ce sila..!” Ta k’arashe cikin kuka sosai... Hameedar ma kuka take sosai Ta isa Ta dafe hannun Mommy tace “Mommy Kiyi hak’uri in sha Allah Ya Ansar zai sami lafiya, ki daina fad’in maganganu haka... Bawa baya wuce k’addrarsa a rayuwa..! Allah ya k’addari hakan sai ya faru.. Kiyi hak’uri kiyi masa addu’a kinji mommy... Addu’arki shi Yafi buk’ata a yanzu..!” Jinjina kai kurum Mommy take bata ko iya amsa mata, Yarinyar ta kamo hannun Mommy ta k’araso da ita saman sofa dake daga can gefe cikin d’akin tace “Mommy ki kwanta a nan, kinga Kema d’azu Dr yace jininki ya hau, ya kamata ki huta Ya Ansar baziji dad’i ya tashi yaga kema kin kwanta rashin lafiya ba.. Ki huta Kinji mommy..!” Ta k’arashe tana taimakawa Mommyn ta kwantarta... Hameedar bata bar gefen Mommy ba har saida taga Ta lumshe idanunta irinta mai bacci.. Ta mik’e ta komo kusan Ansar Tai masa K’uri hawaye na ambaliya a fuskarta... Lokaci guda take masa fatan samun lafiya had’ida sauk’in al’amarin da suka tsinci kansu ciki gaba d’aya... ** Koda Muhibbah ta fito mamaki ne ya cikata ganin shopping bag aje saman gado, kaman mai jin tsoro haka ta isa jikin ‘yar jakan... Gabanta sai fad’uwa yake dan a iya saninta Kuyangin sun tafi bacci Toh waye ya shigo ya aje wannan jakan... Tsoro ya kuma kamata, Ta shiga ‘yan waige waige bataga kowa ba... Toh kodai kuyangin basu tafi bane..? Ta lek’a cikin jakan a hankali nan taga sanitary pads ne cike cikin ‘yar jakan... Gabanta ya kuma tsinkewa... Ya akai Kuyangin suka San tanada buk’atan wannan... Saikace masu aiki da iskokai... Kodai matsafan Giwa ne suka sanar da ita..? Toh amma Maiyasa Giwa bata fara mata azaba ba har yanzu saima treating d’inta nicely da takeyi... Zuciyarta ta raya mata babban ukuba take tanadar miki shiyasa take binki a sannu..! Ta d’ago jakan tana binsa da kallo nan gefe taga wani rubutu mai d’an karan kyau gashi dai da biro akayi rubutun balle tace bugun company ne masu k’era jakan ne suka rubuta... Sam bai yi kama da ace hannu ne ya rubuta ba, abinda aka rubuta shine yafi tafiya da hankalinta.. _Kina tareda kariya a nan fiyeda yanda kike zaton zaki fi samun kariya.. Rashin cin abincin ka iya janyo miki rashin lafiya_ Ta karance sak’on yafi sau abinda yafi... Tinda ta tab’a jakan hannunta ya kamata k’amshin dake jikin jakan... Ta rasa a ina tasan irin k’amshin kuma wannan k’amshin shine taji duk ya dabaibaye jikinta sanda ta farka a bacci... Tasan irin k’amshi but she couldn’t figure out ina tasan k’amshin... Wani ikon Allah bayan karance sak’on nan da tai sai taji natsuwa ya d’an sauk’o mata kad’an, Ta d’auki bag d’in ta bathroom dan kintsa kanta... Lallausar doguwar riga ta zira ta bar kanta a bud’e dan ya ida bushewa, k’anan kitson aurenta da aka mata ya bi wuyanta ya kwanta luf... Tinda Ta fito a haka daga closet d’in ya kasa janye idanunsa daga dubanta, hab’arsa d’aure saman hannunsa yake kallon duk wani motsinta yacce kasan mai kallon shirin film da yayi matuk’ar tafiya da hankalinsa da tunaninsa baiso yayi missing koda scene guda ne... Yanda take tafiyar kaman wata mai tsoron taka k’asa haka ta k’araso saman darduman ta zauna a hankali tana mai bin kayan abincin da kallo... Ta hard’e k’afafunta ta zauna tana bud’e dishes d’in... Allah ya gani batada appetite bazata iya cin komai ba... Maida murafen tai ta rufe kana Ta rapka uban tagumi tana duban jerin abincikan dake gabanta... Ji yake bazai iya bacci ba har sai ta tabbata ta saka wani abu a cikinta, duk abinda ya sameta Ta dalilin yunwa zai zamto laifinsa tinda shi ya d’aukota ya ajeta... Ya lumshe idanunsa a hankali yana tunanin kodai yaje ya turasasa mata cin abinci ne... Amma yin hakan na nufin ya tona kansa kuma bazata bari ya fahimci ainihin motive d’inta gameda Masarautar ba harma da rayuwarsa da na d’iyarsa da taso tarwatsawa... Idanunsa a lumshe yake tinanin kaman ance ya bud’e ya dubeta nan yaga Ta janyo farantin fruits Ta lumshe idanunta had’ida furta bismillah a hankali... Nan Ta soma cakalan fruits d’in dan rabonta da abinci tun had’inda gudidi ta bata tace ta shanye kuma idan har tana so ta cimma burinta na gudu daga wannan kurkuku she needs to maintain her strength idan ba haka ba bazata iya guduwa ba dan haka cin abinci ya zamto mata dole koda bata so... Haka Ta rintse idanunta taita tura abincin tana b’ata fuska tamkar mai cin magani... Yanda take da fuskarta sosai yaso basa dariya... Can k’asan zuciyarsa yana jin sanyin ta saka wani abu a cikinta at least, yanzu zai iya kwanciya... Da wannan tinanin ya mik’e ya nufi band’aki ya d’auro alwalais yazo ya tada sallah nafilfili wanda d’abi’arsa ce duk dare before going to bed...! A b’angaren Muhibbah kuwa tunda ta d’an saka wani abu a cikinta bacci ya kuma yin gaba da ita... Nan cikin baccin nata take mafarki da Mahaifinta... Tana kuka tana sanar dashi azzaluman Masarautar Sun kuma kamata zata nemi hanyar guduwa Ta ko wani hali ta gudu... Mahaifinta ya girgiza mata kai yace “Nan shine gidanki Saudatu..! Bazaki bar gidan nan ba... Akwai mutane da suke buk’atar kasancewarki a nan ciki harda k’annenki guda biyu...!” Daga haka Mahaifinta ya b’ace bata kuma ganinsa ba... Da salati saman bakinta ta farka zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Wannan wane irin mafarki tayi da Abbanta... Mai yasa yace nan shine gidanta..? Su waye k’annenta guda biyu... A iyaka saninta batada k’anne... Kuma k’anwarta d’aya ce mai suna MUHIBBAH kuma ta rasu tana jaririya a lokacinda wuta ya cinyesu itada Mahaifiyarsu a sansanin ‘yan gudun Hijira da suka fake a Sansanin dake Yalawan Shandam..! Hasalima sunan k’anwar tata Muhibbah ta maida wa kanta...Toh su waye k’annenta da Babanta yace suna nan cikin wannan masarauta..?!! SameenaAleeyou 📚 SameenaAleeyou📚 *MUHIBBAH* *65* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED! Ta lumshe idanunta a hankali mafarkin bai b’ace mata a kwanyarta ba, Toh kodai Taswiran nan abinda yake nufi kenan... K’ila akwai wasu mutane b’oye cikin ginin azzaluman cikin Masarautar nan sun b’oyesu Babanta yanaso ta taimaka masu amma baya ga haka bata tunanin akwai wani jininta cikin wannan masarauta... Toh mi zatai menene abinyi gashi ta baro zanen a gida, hasalima batasan yanda ta jefar ba...! Ta dafe kanta a hankali zuciyarta na ambaton Allah ya warware mata wannan al’amari cikin sauk’i... ** Safiyat Washe gari a d’aki Jamal ya tadda Giwa sai faman kaiwa da kawowa take tana sak’awa tana warwarewa... Yau kam jikin Jakadiya da d’an sauk’i dan tare suka shigo da Jamal d’in Dama isowarsu Giwa take jira... Suna shigowa Giwa ta dubi Jakadiya tace “Kin tabbata Zahra’u ce ta baki mayafin nan..?!” Jakadiya ta jinjina kai tace “Allah shi taimakeki wllhi Allah nayi imani Gimbiya Zara’u itace Ta bani mayafin nan..!” Jamal da Giwa suka dubi juna, Jamal zai magana Giwa ta k’araso gabansa tace “Kada ka damu d’ah na kaje kaji da Amaryarka, so nake ka tareda kyakkyawar Amaryarka a yau... Kaga kai sabon ango ne bai kamata wani hidimar ko wani damuwa yasha gabanka ba, I can handle Zahra I promise..!” Jamal yai shiru ya tsareta da idanu sai kuma yace “Maami gobe nakeda ganin Dr a asibiti yace k’afar roba da aka min ya zama ready... Ni a nawa tsarin nafi so idan aka zaka min sabuwar k’afata na tareda Amaryarta dan banaso ta ga k’afata a haka..!” Giwa Ta k’ak’aro murmushi tace “Toh banda abinka Jamal ai a haka da yankakken k’afar taka ta ganka tace tana sonka, Umaima sam bazata damu dan taga k’afar angonta guda d’aya ba dama tasan abinda ta aura ai... So wannan ba abin damuwa bane... Tuni nasa an gyara maku sashen da zaku zauna, an zuba komai na buk’ata ciki... Gida ya tsaru masu shi kawai yake jira...Ni nafi so ka bada himma ga batun tariyarku dan Farin cikinka shine gaba da komai a wajena..!” Ta k’arashe tana shafa b’angaren fuskarsa guda cikeda kulawa wanda zaka rantse har cikin ranta Farin cikin d’an nata ne ya dameta... Murmushi Jamal yayi yana kuma jin son mahaifiyarsa cikin zuciyarsa... Yasa hannu ya damk’e hannun mahaifiyar tasa cikin nashi, ya sumbaci hannun nata kad’an yace “I love you Maami nah.. Ina matuk’ar k’aunarki Rankidad’e..!” Tai murmushi tace “Nima ina matuk’ar k’aunarka masoyinah Farin cikinka shine nawa... I can’t wait naga ‘yan jikokina ‘ya’yanka da Umaima suna guje guje cikin fad’in Masarautar nan...!” Annashuwa da annuri ya kuma cika Jamal, wani irin sanyi yakeji can k’asar zuciyarsa... Bai kuma bin takan batun Zahra ba kaman yanda Giwa ta buk’ata hankalinsa yafi karkata kan cewa daren yau za’a shigo masa da Amaryarsa...! Yana ficewa Giwa ta dubi Jakadiya ta nuna can gefe k’asan file tace ta zauna nan wajen... Babu musu Jakadiya tayi yanda Giwa tace D’aya daga cikin Hadimanta Giwa tasa tai mata kiran Zahra... Jim kad’an Hadimar suka shigo tareda Zahra, Zahran na mamakin dalilin kiranda Giwa tai mata da tsakar safiyan sanin cewa ba sonta Kakar nata take ba... Zahra ta risina ta gaida Giwa... Gani tai Giwar ta amsa mata da sakin fuska, Ta nuna mata gefenta tace tazo ta zauna... Babu musu Zahra Ta isa ta zauna har lokacin da bata gama aminta da yanayin Kakar nata ba... Giwa ta sakar mata murmushi tace “Zahra wata magana nake so muyi..!” Zahra ta k’ak’aro murmushi tana mai jinjina kai ba tareda Ta amsawa Giwar ba... Giwa taci gaba da fad’in “Zahra nace ba... Shin ina kika sami mayafin nan da kika baiwa Jakadiya..?” Zahra ta d’anyi jim sai kuma tace “Mayafi kuma Maami..? Wanne mayafi kenan..?!” Giwa ta murmusa tace “Karki damu Zahra mayafin ne bai cancanta Bayin cikin Masarautar nan su saka ba shiyasa na tambayeki... Kinsan akwai d’abi’u da al’adu na cikin Masarautar nan da har yanzu you’re not familiar with them... Sai a hankali zaki gama fahimtar komai... Zahra Maiyasa kika baiwa Jakadiya wannan mayafin..? Ko Kinsan cewa kin kusan saka Jakadiya cikin had’ari.. Ki dubi yanda ‘yan uwanta bayi sukai mata jina jina duk a dalilin sun ganta da babban mayafi irin wanda bata kamaceta ba... A nasu zaton sata tayiwa iyayen Gidanta..!” Giwa ta k’arashe cikeda kulawa Cikeda tsoro Zahra Ke duban b’angaren da Jakadiya Ke risine, harga Allah sosai Jakadiya ta bata tausayi, bata so kowa ya cutu sabida ita koda kuwa bawa ne k’ask’antacce, ta maidoda dubantaga Giwa tace “But akan mayafi sai su mata irin wannan bugun Maami... Rhis isn’t good Maami, this has stop, bai kamata a barsu suna irin haka ba...Aunty Muhibbah ce ta bani wannan mayafin tace na baiwa Jakadiya kuma itama nasan batasan tsarin Masarautar nan bane da bata bata ba... Lo siento, esto es todo mi culpa..” ( I’m sorry this is all my fault..) Ta fad’i cikin harshen Spanish tana duban Jakadiya da har lokacin kanta a k’asa yake tana haki da k’yar dan Giwa ce ta umarceta tayi hakan.. Giwa ta nanata “Muhibbah..?!” Ji tayi ma batasan waye mai irin sunan ba... Zahra ta kuma Jinjina mata kai alamun tabbatarwa... Jakadiya ta d’ago a zabure jin an ambaci Muhibbah yarinyar da tun zuwanta Masarautar taceda Giwa ita sam bata aminta da ita ba...! Duban Jakadiya Giwa tai Jakadiyar na isar mata da wani da idanu... Giwa ta maidoda dubanta ga Zahra ta murmusa tace “Kina iya tafiya abinki jikata...!” Zahra ta jinjina kai had’ida risinawa kana Ta mik’e Ta fice... Tana ficewa Giwa ta k’araso gaban Jakadiya tana sakin tsananin huci “Jakadiya wacece Muhibbah..?!” Jakadiya ta risina tace “Allah shi taimakeki Muhibbah itace wannan yarinyar da nace miki inada shakku akanta tun farkon zuwanta Masarautar nan... Muhibbah itace bak’uwar Gimbiya Umaima data shigo da ita cikin Masarautar nan..!” Giwa tai shiru tana nazari lokaci guda tana mai ci gaba da sakin huci... Sai yanzu hoton yarinyar ke kuma dawowa kwanyarta... Ta waigo tana duban Jakadiya bata daina sakin huci ba tace “Jakadiya ya zama dole duk yanda za’ayi musan wacece wannan yarinyar Muhibbah da dalilinta na shigowa Masarautar nan...!” Tana ida fad’in haka ta d’auki wayar salulanta ta shiga dialing layin Jamal... ** A b’angaren Zahra kuwa tana ficewa b’angaren mahaifinta ta nufa tana tinanin Maiyasa a ‘yan kwanakin kowa ke son sanin abu gameda Aunty Muhibbah.. Itakam koda kowa zai tunanin Aunty Muhibbah ba mutumiyar kirki bace bazata tab’a yi mata wannan tunanin ba... Ta tabbata she’s a good person... Da wannan tunanin ta isa b’angaren mahaifinta... Tinda ya tashi a bacci yake jiranta Ta Tashi, ko sauk’a k’asa yayi breakfast ya kasa, yafi so sai ya tabbata da Ta tashi taci abinci kafin shima ya sauk’a k’asa yaci abinci... Duk abubuwan da takeyi akan idanunsa, tin daga tashinta daga bacci har shigewarta bathroom dan yin wanka... Sanda Ta shiga wanka shima ya tashi ya fad’a bathroom d’insa dan yin wankan... A tare sukai wanka kowa a nasa band’akin lokaci guda... Koda Mahmood ya fito daga wanka idanunsa akan na’uran yana duban ko yarinyar nan ta fito daga bathroom... Bai mamakin ganin bata fito ba tinda yasan yanayin da take ciki na rashin tsarki.... Yana rik’e da k’aramar towel yana goge sumarsa kaman ance ya dubi na’uran ya hangota ya fito d’aure da towel daidai cinyarta, yau d’in batai amfani da bathrobe kaman yanda tayi jiya ba... Mutuwar tsaye yayi yana k’arewa santala santalan cinyoyinta kallo... Zuciyarsa taci gaba da bugawa... Ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta ya kuma kasa ci gaba da abinda yake...! Zahra na nan zaune parlor tana kuma duba agogo tana mamakin rashin sauk’owan mahaifin nata yau har wannan lokacin... Kodai makara ne yayi... Tasan Paa d’inta baya shige irin wannan lokacin bai breakfast ba, Toh kodai hakan nada alak’a da abubuwan dake kan faruwa cikin Masarautar ne, k’ila fushi yake shiyasa har yanzu bai fito ba.. Itakam idan dai akan rashin auren Aunty Raheema ne da baiyi ba tafi kowa Farin ciki da faruwan hakan, koda mahaifinta baiso hakan ba... Ta isa dining area tana duban breakfast d’in nasa shirye saman dining table ko tab’awa ba’ai ba... Ta d’an kuma komawa ta zauna tana mai ci gaba da duba time.. Gaba d’aya sai tana jin she’s responsible for everything that’s been happening..! ** Yana gani ta nufi closet ta zab’o wasu kaya marassa nauyi Ta dawo cikin d’akin da zummar shiryawa, sosai bugun zuciyarsa ya k’aru ganin da gaske zame towel d’in takeda niyyan yi... Daidai nan yaji knocking daga k’ofarsa d’if ya kashe na’uran zuciyarsa bata daina bugawa ba.. Jallabiya kawai ya zira yana mai sinkayo muryar Zahra daga k’ofa tana fad’in “Paa are you there...? Paa..!” Tana maganan tana k’wank’wasawa a hankali kaman mai tsoron kada Ta d’agasa a bacci... K’arasowa yayi ya bud’e had’ida sakar mata murmushi mai kyau... “Buenos dias paa..!” (Barkada safiya Paa) “Buenos días princesa..” (Barkada safiya Princess) Ya fad’i kyakkyawan murmushin bai bar saman fuskarsa ba... “Paa yau ka makara.. Lafiya kuwa.. Espero que todo esté bien con usted..!” (Ina fatan lafiya kake) Fitowa yayi ya nufi downstairs yana fad’in “Todo esta bien cariño..!” (Komai lafiya sweetheart) “Vamos a desayunar ... Sé que aún no has comido” (Muje Mu Karya kumallo dan nasan bakiyi ba tukuna) Tana murmushi biye dashi take fad’in “Por supuesto que todavía no he desayunado..( K’warai banci karin kumallo ba)..” Ta d’an murmusa a hankali sai kuma tace “Ta ya zanci abinci bayan ban tabbatar da cewa Paa d’ina ya tashi cikin k’oshin lafiya yaci abinci ba after all that has happened..!” Ta k’arashe tana mai zama a kujeran dake daga gefe lokaci guda tana mai ci gaba a karantar yanayinsa, batayi zaton zata gansa cikin annashuwa ba bayan duk abinda ya faru na aurensa da Aunty Raheema da bai yuwu ba... Ta d’an muskuta tace “Paa you seems to be in a good mood... I thought zakayi fushi dani na b’ata tsakaninku da Aunty Raheema da nayi...? Paa I’m sorry.. I truly am...!” Katseta yayi da fad’in “Is okay Zahra... Everything is fine.. I promise..!” Zahra Ta d’an d’ago ta dubesa tace cikin sanyin murya “You’re not mad at me..?!” Murmushi ya sakar mata yace “Of course I’m not...! Oya eat your food before it gets cold..!” Ta jinjina kai a hankali tace “Alright Your Highness..!” Suka sakar ma juna murmushi a tare tana mai cakalan abincin kaman tana tsoro... Mahmood na hankalce da ita... Ya zari tissue paper ya goge bakinsa kad’an, har lokacin bai daina karantar Zahra ba.. Saida yai gyaran murya kad’an yace “Princess, is something bordering you... You look a little bit disturbed.. Tell me akwai abinda Ke damunki ne..?!” Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali tace “Paa it’s about Aunty Muhibbah.. Do you remember her..?!” Gyara zamansa sosai yai jin ta ambaci Muhibbah yace “What about her.?!” Zahra ta d’an kuma muskutawa tace “Paa why’s everyone so curious about her this days.. First it was you, and now...Grandma ta kirani asking questions about her.. Paa I believe she’s a good person... But Maiyasa zata bani mayafi tace na bawa Jakadiya ta yafa..!” Zuciyarsa Ta kuma tsinkewa, ya aje spoon d’in da yake juyawa cikin mug yana mai kuma tsareta da idanu... Sosai ya gyara zamansa yace “Tell me everything Zahra... Ta bawa Jakadiya mayafi, kuma ma Ke ta bayar tace ki baiwa Jakadiya..?!” Zahra Ta jinjina kai tace “You remember that day..? Ranan da nace maka ita ta had’a gaba d’aya plans d’inta tace min I should trust her..!” Mahmood ya jinjina kai yace “I remember..!” Zahra taci gaba da fad’in “Paa the truth is that ta bani wannan mayafin tace na baiwa Jakadiya ta saka, idan har Jakadiya ta yafa toh Babu halin ta bini Mu fita tare kaman yanda ka umarta kace Jakadiya tamin rakiya...! Toh na bata wanann mayafin Ta yafa muka had’uda Uncle Jamal yace zai assigning wata Hadima Ta min rakiya sabida Jakadiya zatai masa wani aikin...! Toh sai nace masa he shouldn’t bordered zan sami wata cikin Hadimaina tamin rakiya... Paa believe me I didn’t know an hana Hadiman cikin Masarautar nan yafa mayafi mai kyau... It was never my intention na cutar da Jakadiya... A dalilin wannan mayafin nayiwa Jakadiya Duka an ji mata ciwo Paa... All because of me..!” Ta k’arashe cikin rawar murya.... Sosai ya fad’a duniyar tunani, kenan Ta kuma tabbata Muhibbah tanada agenda d’inta cikin Masarautar nan... Why’s she connected to almost everything that’s been happening...? Farko rayuwarsa da Zahra, Raheema da Yazeed.. Taswiran da Baba Wambai ya basa wanda ya tsinci makamancinsa hannunta...Yanzu kuma harda Jakadiya da Jamal..? And if Jakadiya is somehow involved Toh Giwa ma might also be involved tinda yasan matsayin Jakadiya wajen Giwa... Kuma idan hakan Ta kasance zai iya yuwa tasan wani abu gameda ciwon Fu’ad tinda zuwansu asibiti shida Turaki nurse guda ya tabbatar masu cewa matar data shigo da Zahra Ta jima sosai cikin d’akin Fu’ad tana dubasa...Who are you Muhibbah...?! Mai kika shigo yi cikin Masarautar nan..?! Maiyasa kike neman ki tarwatsa ahalinmu..Duk abubuwan da suka faru, everything is pointing directly to you ne... What exactly do want from our family..?! Har Zahra Ta fice bai fahimci Ta fice ba, sosai yai nisa a duniyar tunani... Idan Muhibbah tanada alak’a da duk abubuwan dake faruwa cikin Masarautar Toh ya zama dole yayi taka tsan tsan dan da alama bata shigo Masarautar ba saida Ta shirya... Babu wanda zai iya tunk’aran masarauta mai girma irin nasu yanda tayi ba tareda shiri ba... Shi mamaki ma abin ya soma basa... Sauri sauri ya haura sama ya kunna na’uran computer d’in yana duban abinda take a daidai lokacin... Kuangin ne suka shigo nata da abin kari... Ta d’auki fork bayan sun fice tana k’ok’arin bud’e lock d’in k’ofa dashi... Yayi K’uri yana dubanta yanda take dage k’arfinta gaba d’aya wajen ganin Ta bud’e k’ofar... Cikin zuciyarta take furta “I really need to escape kafin Giwa ko d’aya daga cikin azzaluman yaranta su cimmani... Nasan mutanen da Abbah yace na taimaka masu suna b’oye cikin Masarautar nan... I need to escape kafin su cimmani..!” Ta k’arashe tana mai kuma dage k’arfinta, saidai abinka da k’ofa mai aminci ko gizau bai ba... Saima karyewa da cokalin yayi... Cikeda takaici tayi jifa da cokalin ta koma cikin d’akin ta zauna dirshan tana kuka mai tsuma zuciya... ** Huci kurum Jamal yake fitarwa yana mai furta “I knew it.. Since from the beginning ban yarda da yarinyar nan ba Maami... But tinda ita d’in k’awar Umama ce komai yazo cikin sauk’i... Kamota bazai mana wahala ba... Umaima zata sanar damu yanda take rayuwa and believe Maami zan kawo miki ita har nan kiyi yanda kike so da ita... Kiyi gunduwa gunduwa da ita idan kina so... I promise I’d bring her here..!” Ya k’arashe yana mai kuma fitar da huci... Giwa Ta jinjina kai tace “Na tabbata yarinyar nan koma su waye suka turota ta riga ta gama mana b’arna cikin Masarautar nan... Kuma da alama bata Zo ba saida Ta shirya... Amma zatayi nadama da danasanin sanin wannan masarauta da tayi balle har tayi gangancin shigowa cikinta... Mun gama da wanda suka fita balle ita k’aramar alhaki... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *66* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zuwa safiya an samu Ansar ya d’an zama stable saidai har lokacin hawaye basu daina zubowa daga k’uncinsa ba... Cikin zuban hawaye ya kuma duban Mommy yace “Alfarma d’aya zaki min Mommy....! Ki sanar dani su waye suka nemi auren Muhibbah..? Ma waye aka aurar da ita..?!” Cikin kwantar da kai hawaye na gangaro mata tace “Ansar I’ve no idea they are..! Kuma bana tsammanin shi kansa Yawale yasan daga wata duniya suke...!” Ansar ya kuma dubanta da tsananin mamaki yana girgiza kansa, ya kasa yarda k’iyayyan da Yawale yakewa Muhibbah har yakai wannan matakin, abinda ko wa mak’iyinka bazakayi ba..! Kan mai zai aurartaga mutanen da babu wanda yasan daga inda suke... Ya sauk’e wane irin nannauyan ajiyan zuciya yace “Mommy this cant be possible... Dole a nemo Muhibbah kuma dole a warware wannan auren muguntar da akai mata... Yau d’in nan basai gobe ba zan shigar da Yawale k’ara... Wllhi sai na d’auresa kodai ya fito min da Muhibbah..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Mommy kanta dubansa kurum take dan bata tab’a ganin d’an nata cikin yanayi makamancin wannan ba..! Muryar Hameedah dake gefe tana hawaye suka sinkayo tana fad’in “Baffah ya aurar da Muhibbah ne ga wasu Buzaye... Wanda shi kansa baisan daga Duniyar da suke ba..! Nasan Baffah bai kyauta ba amma dan Allah kayi hak’uri Yaya Ansar kar ka shigar dashi k’ara zai zame min abin gori ne daga cikin gidanmu har izuwa mutanen unguwa... Hamma Ansar nasan baka sona ka aureni... Dole akayi maka, dan Allah naci darajan ‘yan uwantaka... Kada ka tozartani a idon duniya....!!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata.... Tausayin yarinyar dasu kansu gaba d’aya duk sai ya kuma rufe Mommy, tasan yarinyar batada laifi mahaifinta ya jawo mata halinda Ta tsinci kanta ciki... Mommy batakaiga magana ba suka sinkayo muryar Ansar yana furta “Bak’in Buzaye..!” Sai yayi Burki ya kuma furta BAK’ON BUZU..!!” Idan bai mance ba Muhibbah ta basa labarin yanda akaita binciken wanene Bak’on Buzu a masarauta...! Duk yanda akayi Wani ne daga Masarautar yazo ya aureta cikin yanayin shiga na b’adda kamanni...! Zasu halak’ata a wannan Masarautar muddin suka fahimci wacece ita... No no bazai bari hakan Ta kasance ba...! He needs to save her..! Su Mommy gani kawai sukai ya hau fincike igiyar drip yana shirin dirowa daga saman gado... Mommy ta isa ta rik’esa gam tana fad’in “Ansar lafiya kake...! Ina zaka a haka..?!” Bai daina fincika ba yake fad’in “Mommy I need to go..! Muhibbah needs me Mommy... Mommy I need to save her... Her life is in great danger...! Mommy rayuwar Muhibbah na cikin had’ari mai munin gaske..!” Ya k’arashe yana mai zira takalmansa... Mommy da Hameedar duk sun rikice, a rikice Mommy dake rik’eda Ansar ta dubi Hameedah tace maza ta fice ta kirawo likita... Taci gaba da fad’in “No Ansar bazan Barka ka fice a haka ba...! Ka natsu ayi komai a sannu, bakada lafiya, Maiyasa zaka fincike drip...!” B’anb’anre hannunsa daga rik’onda Mommy tai masa yana mai furta “Mommy Wai kin mance ne.. This is my profession..! I’m also a medical Dr... Mommy I know what I’m doing... Please let me go...!” Mommy na hawaye take girgiza masa kai tana furta “No Ansar I can’t let you go... I just can’t...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana... Girgiza kai shima yake yana hawaye yake furta “Mommy I’m sorry... But I’m going... Ki min fatan nasara kawai... Na tafi ko na mutu ko nayi rai... But I must go..!” Yana ida fad’in haka yasa kai cikin sauri... Mommy na kuka sosai tana k’walla masa kira... Cak ya tsaya ya juyo yana duban mahaifiyarsa... Lokaci guda ya dawo da baya ya rungumeta sosai yace “I love you Mommy.. Please forgive me...!” Daga haka Ansar bai kuma tsayawa wata wata ba yasa kai ya fice cikin sauri... Mommy na kuka tana kiran sunansa inaa ko juyowa baiba ya fice a d’ari...! ** MASARAUTA Koda Zuhra ta fito zata tafi sai taji ta lek’a Raheema taga ya ta kwana dan bataji alamun d’uriyarta ba, wata zuciya tace ina ruwanki sabuwar amaryace k’ila baccin huce gajiyan biki take... Hakan yasa bata kuma bi takan Raheemah ba ta janyo ‘ya’yanta suka nufo downstairs... Saidai tana k’ok’arin sauk’a taji kaman k’aran fashewan abu daga d’akin Yazeed... Ta d’aga idanu tana duban d’akin... Sai kuma ta dubi Hadimarta tace “Hindu fita da yaran ina nan tafe..!” Babu musu Hadimar tayi yanda tace... Sauri sauri Zuhra ta koma upstairs ta d’an ja ta tsaya jikin k’ofan d’akin Yazeed zuciyarta na bugawa... Wata zuciya tace idan kikaga abinda zai dameki fah..? Take b’angare na zuciyarta Ta bata amsa da fad’in “Mijin K’warai akema kishi... Toh idan kikaga abinda bai dace ba fah..?! Tai shiru tana tinanin abinyi... Tasan halin Yazeed tsaf zai iya kulle Raheema yayi tafiyarsa ba tareda taci koda abinci bane... Maiyuwa ya kulleta ne ma yayi tafiyarsa tinda ba da jimawa ba taji ficewar motarsa... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali zuciyarta na kuka nanata mata “Ina ruwanki, Ke naki a wanne idanma wani abin yayi mata... Ai sunfi kusa a halin yanzu...!” Dikda irin wannan batu da zuciyarta Ke mata hakan bai hanata d’an bubbuga k’ofan ba.. Kaman sautin mutum takeji amma muryar bai fita... Hakan yasata saurin murd’a handle amma da alama an kulle k’ofar... Sauri sauri ta isa ma’ajiyan spare keys na gidan Ta d’auko key d’in d’akin ta bud’e... Can jikin gado ta hango Raheema d’aure ta gama jigata ta galabaita.... Raheema na hango Zuhra ta kuma fashewa da kuka hawaye na ci gaba da gangaro mata... Shaye da tsananin mamaki Zuhra Ke dubanta irin d’aurinda yayiwa Raheema wanda ko ita bai mata irin wannan... Ta isa da sauri ta b’alle sellotape d’in da ya manne bakin Raheemah dashi... Tai wani irin jan numfashi had’ida shak’an iska... Sauri sauri Zuhra ke kwance hawaye basu daina zubowa daga idanun Raheema ba... Bayan ta gama kwanceta ne ta mik’e da zummar tafiya dan da alama ko idanu Raheemar ta kasa d’agowa su had’a... Ji tayi Raheema ta rik’o hannunta guda tana kuka sosai, cikin muryar kuka take furta “Zuhra na gode... Na gode..! Dukda ban cancanci taimako a gareki ba amma kika zab’i ki taimakeni... Hak’ik’a ke d’in kinada zuciya mai kyau... Nasan nan cancanci yafiya daga gareki ba kuma banaso nati taking advantage d’in kyakkyawan zuciyarki na nemi tafiyarki dan nasan babu wacce zan mata abinda na miki ta yafe min... Amma hakan bazai hana na rok’i gafararki ba k’awata... Zuhra dan Allah Ki yafe min..! Kiji taisayina karki tafi ki barni da hakkinki... Ki yafe min dan Allah..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya ga rawan d’ari na zazzab’i da jikinta keyi... A hankali Zuhra Ta juyo tana duban Raheemah hawaye kwance saman fuskarta itama... Lokaci guda take furta “Shi taimako ana yinsa ne a lokacinda ka Keda halin taimakawa... Kar kayi la’akari da ma wa zaka taimaka... Ka tuna cewa waye yayi umarni da ayi taimako... Idan zakayi taimako kayi Dan Allah domin ladanka na wajensa..So kar kiji mamaki dan na taimaka miki...!” Ta d’anyi fasali kana taci gaba da fad’in “Raheemah kin min zalunci mafi muni... Na aminta dake kinci amanata! Kinyi amfani da kusancin dake tsakaninmu kin yaudareni... Amma tun kafin aje ko ina ga sakayya kin fara gani, Allah yasa hakan ya zamto wa’azi gareki da masu halayya irin naki... Ina kuma miki fatan Allah ya kawo miki sauk’i cikin rayuwar da kike fuskanta... Ni na yafe miki Raheemah, bazan tafi da k’ulli cikin zuciyata ba... Na yafeki duniya da lahira.. Ina kuma fatan Allah ya yafe miki..!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka... Rungumeta Raheemah tayi tana kuka sosai, su duka biyun suna kuka sosai mai tab’a zuciya... Cikin kuka Raheemah Ke fad’in “Na gode..! Na gode k’awata..! Na gode miki..! Allah Ubangiji ya canza miki rayuwarki da abinda yafi zama alkhairi a gareki...! Thank you my friend..!” Murmushi Zuhra Ta sakar mata kana tace “Allah sada mu da alkhairi Raheemah... Goodbye..!” Raheemah tai tsaye tana duban Zuhrar kaman wanda bazasu sake gamuwa ba, kodashike ta tafi kenan bazata kuma dawowa Masarautar ba a cewar Zuhra, idan Yazeed bai aika mata takardan sakinta ba Alk’ali ne zai rabasu...! Zuhra na fitowa ta tadda Motar da aka turo daga masarautarsu domin ya kwashesu ya iso... Hakan yasa tuni dogari ya fito ya fara loda kayansu a k’aruwar motar ta alfarma... Haka Hadimanta na cikin Masarautar sukaita kukan tafiyarta domin kaw zasuyi kewarta, Hadimarta d’aya tak da tazo da ita daga Masarautarsu mai suna Hindu kawai ta d’auka.. Amma duk Hadiman Masarautarsu Yazeed bata d’auki ko guda ba... Motarsu na shirin tashi Yazeed ya iso yana faman cika, cikin huci ya nufo Zuhra zai damk’ota Dogarin ya tare gabansa yana fad’in “Hattara Yarima..! Umarnin mai Martaba ne yace a dawo da Gimbiya Zuhriyya Gida..!” Yazeed bai daina huci ba yake fad’in “Toh sai mai idan Mai Martaba ne yace a maidata gida..! Shi yake aurenta ko ni nake aurenta..?!” Ya maidoda dubansaga Zuhra wacce ta cika tai fam yace “Kisa aniya ki fito min da yarana daga motar nan dan babu yanda zaki kaimin yara..!” Zuhra ta murmusa tace “Na gaba ya riga yayi gaba Yazeed.. Na baya kuwa sai labari..! Ai na fad’a maka k’afata k’afan yarana.. Ka gaya min ma waye zan damk’a amanan tarbiyan yarana cikin Masarautar nan...? Dan haka I’m leaving with my kids..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin shigewa mota... Yazeed yayi saurin rik’ota yana sakin huci yake furta “No.. Wllhi bazan barki ki tafi min da yara ba..! They’re my children, ‘ya’yana ne they belong here and no where else.. Nan shine mahaifansu..!” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “K’warai babu yanda zaki tafi dasu Rankidad’e..! Idan zaki tafi Ke kina iya tafiya amma yara zasu tsaya a gidan mahaifinsu...!” A fusace Yazeed ya juyo yana watsama Waziri mugun kallo lokaci guda yake furta “And who gave you the right to interfere..?!” Yayi maganan cikeda takaicin Waziri dan ya gane nufin Waziri tinda yasan yanzu yaran jikokinsa ne shiyasa bazaiso a fita dasu daga cikin Masarautar ba... Abu kaman wasa labari ya soma karad’e Fada Gimbiya Zeenat zata tafi da yaranta Yarima Yazeed ya doge ya hana... Babu shiri Giwa ta lek’o ta Samanta tana kallon wannan drama.. Zuhra bata kuma bi takan Yazeed ko Waziri ba Ta bud’e mota ta shige abinta taceda Driver su tafi..! Ai Yazeed bai bari Driver d’in ya soma tafiya ba ya finciki k’ofar driver d’in ya saka duka hannayensa biyu ya cakumo driver d’in yayi jifa dashi waje ya shige cikin motar... Kaman mai tab’in hankali yake furta “So kike ki tafi fine..! Zamu tafi gaba d’aya..! Zamu mutu gaba d’aya kinga shikenan jin huta... Sanin rashin hankalin Yazeed yasa Zuhra soma girgiza kai tana duban yaranta dake daga bayan jeep d’in Hadimar Ta rungumesu sai kuka suke... Cikin rawar murya Zuhra Ke furta “Yazeed no please...! Yazeed akwai yaranmu cikin motar nan..! Don’t please Yazeed..!!” Inaaa ko Sauraronta bai ba ya finciki motar kaman mahaukaci suka fice daga cikin Masarautar... A d’ari Giwa ta sauk’o k’asa tana fad’ida Waziri maza yabi bayan Yazeed dan tasan haukansa komai ka iya faruwa... Zuhra na kuka tana fad’in yayi hak’uri ko dan yaransu ya tsaya, Ta amince bazata tafi ba.. Amma inaa Yazeed balbala gudu kurum yake saman kwalata yana mai ci gaba da sakin huci wanda da ganin kasan ta ko wane b’angare na rayuwarsa bai masa dad’i... Cikin huci yake furta “No Zuhra I cannot be a loser..! I can’t be a loser.. I’m Prince Yazeed AbdulJabbar... Idan bazan zama Champion ba bazan zama loser ba... We’ll die together... No one is leaving me.. Not you nor our children..!!” Kuka take tana furta “Yazeed please..!” Cikin daka tsawa ya juyo yace da ita “Shut up..! Shut the hell up..!!!” Daidai sanda k’aruwa motar trailer ta dososu daga d’aya length d’in wanda sam Yazeed baima kula da zuwanta ba... Ji kake gau motocin sun had’a, motar da suke ciki ta fettu gefe ta had’uda jikin bishiya... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un...! ** Duk wannan buduri da ake cikin Masarautar Mahmood baida labari yana nan gaban na’uransa yana ci gaba da hasko masa ita, hannayensa rik’eda Taswiran yana kuma gathering duk abubuwan da ya sani gameda ita cikin kwanyarsa, zuciyarsa naci gaba da bugawa yake furtawa a fili “I need to confront her to end all this..!” Yana tsaka da wannan tinanin ita kaw Muhibbah dake daga can nata b’angaren itama sak’e sak’en yanda zatai ta fice daga kurkukun da aka ajeta take, tinda b’alla k’ofa bazai working ba she needs to come up with something as soon as possible..! Take tinanin ciwo yazo mata, idan tayi ciwon K’arya tasan dole Kuyangin su bud’e k’ofa, idan kuma suka bud’e zasuyi tinanin taimaka mata harm su tafi kiran iyayen gidansu ita kuma sai tayi amfani da daman ta gudu kafin su cimmata...! Da wannan tinanin ta soma tamke cikinta ta isa jikin k’ofa da k’yar tana bubbugawa tana fad’in taimako..! Taimaki..! A taimaketa..!! Kasancewar babu Kuyangin wajen yasa babu wanda ya jita... Bata fasa kame cikinta tana sakin k’ara had’ida ambaton a taimaka mata ba... Daga nan yanda yake kallonta hankali tashe ya mik’e yana kuma duban yanda take murk’usoso alamun batada lafiya... Bai wata wata ba ya fice ya nufi b’angaren nata hannayensa rik’eda Zanen guda biyu.... Cikin sauri ya bud’e k’ofar ya hangota nan kwance Ta rik’e cikinta sosai.... Cak ya tsaya yana sauk’e haki a hankali yayinda itama ta tsaya cak da rik’e cikin nata tana dubansa idanu waje... Su duka biyun duban juna suke, jiri ne taji yana neman d’ibanta da gaske bada wasa ba... Tana gab da silalewa k’asa Mahmood ya k’araso a d’ari yayi jifa da takardun dake hannun nasa ya isa gareta ya tallafota ta fad’o cikin jikinsa... Tsananin mamaki ya hanata katab’us saima juya mata da duniyar yake, da gaske Rankaidad’e take gani kuma yasa hannaye ya rik’eta...MEKE FARUWA..?! Ido cikin idanu suke duban juna har lokacin na tallafe da ita, k’irajensu basu daina bugawa ba... Babu wanda ya iya furta koda kalma sai duban juna da suke... K’aran da wayar salulansa yayi ne ya dawo da hankalinsa... Ya saketa a hankali yana mai zura hannu a aljihun jallabiyarsa, daga can asibiti wajen Fu’ad ake kiran.... Lokaci guda Mahmood ya bata baya yana amsa kiran bataji mai akace ba tadaiga ya nufi k’ofa da sauri yana furta “Are you serous Dr..?! Fu’ad can talk again...! I’ll be there in a bit...!!” Sauri sauri ya fice ya barta nan durk’ushe zuciyarta naci gaba da tsinkewa... What’s the meaning of all this..? Mai ya kawo Rankaidad’e cikin image d’in... What is his role...? Mai hakan yake nufi...? Badai shima sunyi tarayya dasu Giwa bane wajen yunk’urin cutar da ita..? Tinanin da ya tsaya mata a rai kenan, a wani b’angare wayan da Mahmood ya fita yana yi shima ya tsaya mata a rai... Wai Fu’ad ya soma magana..! Wannan shine Ana wata ga wata.. sam bazata tsaya su cimmata ba, yanzu da Ta samu Rankaidad’e ya mance k’ofa a bud’e zatayi maza ta fice ne kafin su cimmata... Sauri sauri take k k’ok’arin ficewa daga d’akin kaman ance ta kalli gefe nan taga Taswirorin nan guda biyu wanda ko shakka babu Rankaidad’e ne ya shigo dasu... Ta duk’a da sauri ta d’auka tana dubawa... K’irjinta ya bada sautin Dammm! Ko shakka babu wannan guda d’ayan nata ne wanda mahaukaciyar nan Ta mallaka mata... Wannan kuma batasan dashi ba sai yau... Ya akai na hannunta ya isa wajen Rankaidad’e..?! Kardai shine yaje har gidan Mommy ya satota... Kuma ko shakka babu wannan Taswira guda d’ayan shine wanda take nema kwanakin baya da ace zata had’a dana cikin wayarta wanda ta gani d’akin Jamal tabbas da zanen ya bayyana mata ya fito fili... Abinda Ta jima tana nema zai bayyana...! Toh amma yanzu wayarta baya tareda ita... Shin yaya zatayi..? Bazatayi wasa da wannan daman na k’arshe ba... Allah yasan dalilin da yasa zanen ya kuma dawowa hannunta... zatayi duk yanda zatayi Ta shiga d’akin Jamal ta nemo wancan na cikin d’akin nasa ta had’e zanen waje guda, watak’ila mutanen da Abbanta yake so ta taimaka cikin Masarautar suna k’ark’ashin wannan zanen ne...! Da wannan tunanin ta janyo mayafi guda ta nad’e fuskarta dashi yanda baza’a ganeta ba, cikin sauri ta fice daga d’akin.... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *67* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Muhibbah na k’ok’arin ficewa daga sashen kenan taci karo da d’aya daga cikin Kuyangin dake tsaronta... Tai birki taja ta tsaya... Kuyangar ta zaro idanu waje tana furta “Rankidad’e ba’a baki izinin fita ba, Kiyi hak’uri ki koma kada ki jefamu cikin masifa... Ki cecemu ki koma cikin d’akin...!” Muhibbah na girgiza kai take furta “Hasiya taimako na zakiyi, Ki tuna idan kin taimaki wani Allah zai taimakeki.. Rayuwata data wasu mutane yana cikin had’ari mai munin gaske a Masarautar nan... Ki taimakeni Hasiya bamuda sauran lokaci, na baro ahalina cikin tashin hankali, mutanen nan satoni sukai suka rabani da mijina wanda aka d’aura min aure dashi suka kawo nan suka aje domin cimma burinsu... Hasiya kema mace ce kuma wataran zakiyi aure zaki fahimci abinda nake nufi... Dan Allah Ki taimakeni kada ki tona min asiri..!!” Jikin Kuyangar ya d’anyi sanyi, ta risina tace “Toh yanzu Rankidad’e ya kike so nayi, mai kike so na miki...?!” Muhibbah ta murmusa tace “Kayan jikinki nake so ki bani ke ki amshi na jikina Ki saka, idan na fita da wad’annan tufafin zasu iya gane ko ni wacece tunda su suka ajeni a wajen nan...!” Kuyangar ta d’anyi Jim kaman mai tunani sai kuma tace “Amma ni zaki sakani cikin masifa Rankidad’e...!” Muhibbah ta girgiza kai tace “In sha Allah Babu abinda zai sameki, Allah yaga nufinki, da niyyan taimako kikayi babu abinda zai sameki... Allah zai kiyayeki...!” Kuyangar ta jinjina kai tace “Tinda Kikace Allah kin gama magana Rankidad’e... Kuma nima bazanso su cutar dake ba idan har da niyyan cutarwa suka rufeki cikin gidan nan... Zanso nayi taimako koda so d’aya ne a rayuwata a lokacinda nakeda halin yin taimakon... Rankidad’e mu shiga daga ciki na baki tufafi na..!” Muhibbah Ta murmusa cikeda Farin ciki tai saurin janyo hannun Kuyangar suka shige daga ciki tanai mata godiya.... Haka suka canza Tufafi ta saka kalan tufafin Bayin cikin Masarautar yanda babu mai cewa ba Kuyangar cikin Masarautar bane... Ta kuma rufe fuskarta yanda baz’ai saurin ganeta ba.... Kuyangar Hasiya ta shige cikin d’akin ta zauna a matsayin Muhibbah... Tana fitowa ta soma bin bango tana tinanin ta ina zata b’ullowa al’amarin, idan ta nufi d’akin Jamal kai tsaye ko shakka babu zata iya taddasa nan cikin sashen nasa zai iya kamata kuma idan ya kamata komai ya b’aci..! Meye abinyi wanne zatayi...?! B’angare na zuciyarta yace ki fara duba sashen Giwa, da alama hankalin Masarautar ba’a kwance yake ba dan taci karo da wasu bayi a hanyar ta na fitowa sai gudu suke kaman dai cikin Masarautar babu lafiya...! Zuciyarta ya raya mata Ta fara duba sashen Giwa ta tabbata Jamal yana can kafin ta tunk’ari d’akinsa... Haka cikin sand’a da dabara wanda zakayi zaton kuyanga ce ta nufi b’angaren Giwa harda d’aukan paranti daga parlor yanda Kuyangi Ke kaiwa suna komowa Ta nufi upstairs dashi, tsaf zakayi tunanin Kuyanga ce take gudanar da ayyukanta.... A daidai mashigar parlorn Giwa na sama ta soma jiyo muryar Giwa da Jakadiya, Jakadiya na fad’in “Allah shi taimakeki ai Rankaidad’e Yarima Jamal ya kasa hak’ura har dare yayi akai masa amaryarsa, da alama burinki zai cika kafin dare...!” Giwa tace “Ban fahimceki ba Jakadiya..! Kinaso kice Umaima tana b’angaren Yarima Jamal yanzu haka..?!” Jakadiya Ta jinjina kai tace “K’warai Rankidad’e..! Gimbiya Umaima tana can b’angaren Yarima Jamal, ni ya umarta yace nai masa kiranta duk yanda za’ai akwai magana mai Muhimmanci da yake so su tattauna.... Kuma nasan bazai wuce kan wannan yarinyar ‘yar lek’en asiri Muhibbah ba... Toh kinga kuwa Rankidad’e idan suka keb’e su biyu ai zai wahala ya barta Ta fito ba tareda wani Al’amari ya gifta tsakaninsu ba... Ke shaida ce yanda yake matuk’ar k’aunar yarinyar da son kasancewa da ita...!” Take Giwa taji wane irin Farin ciki na zuwa mata finally zata cikawa Boka Tal’udu burinsa... Ta Kece da wani irin dadiyar k’eta tamkar ba basarakiya ba tana furta “Da kyau..! Yayi kyau Jakadiya..! Kin kwana biyu bakizo min da labari mai dad’i irin wannan ba... Daga rana mai kaman ta yau Umaima Ta zama tarihi... Na ajiyeta ne Ta zamto sadaukarwa ta k’arshe daga tsatson Sarki Jamaluddeen.... A yau idan har d’ah na Jamaludden ya kusanceta shikenan ta zama tarihi a wannan duniya tamu..! Nasan wanann babban kyauta zai kuma d’aga darajata a wajen Sarauniya Tamuna..!!” Ta kuma kecewa da dariya kaman wata mai tab’in hankali... Zuciyar Muhibbah yayi wani irin tsinkewa, k’iris ya rage batayi fatali da farantin dake hannunta ba jin irin k’ullin da Giwa Ke shiryawa Umaima... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai take iya nanatawa cikin zuciyarta... Lallai Giwa tayi nisa a kafurci da son mulkin Duniya... Batasan a sahun da zata aje wanann azzalumar matar ba... Tsayuwa a nan bai ganta ba, she needs to save Umaima duk yanda za’ayi...! Cikin sauri tasa kai ta juya zuciyarta bai daina bugawa ba... Da dabara ta isa sashen Jamal, dukda tsananin had’arin dake tunk’aranta ji take bazata iya barin Umaima Ta halak’a ba, ko babu komai Umaima ta mata hallaci... Yanzu ceton rayuwar Umaima shine top priority d’inta... Bazata bari Giwa ta kuma salwantar da wata rai sabida son zuciya irin nata ba... Zuciyarta sai bugawa yake tana mai hango tsananin had’arin dake gaba gareta, a hankali ta mak’ale jikin window d’in parlorn tana sauraren tattaunawar Jamal da Umaima... Jamal ya kuma duban Umaima hannayenta rik’e cikin nasa yace “Sweetheart, she deceived you... She tricked you, she used you... That girl is nothing but a fraud..! Nasa anmin bincike ita d’in ba student bace... Kawai Masarautar nan tazo da wani agenda d’inta wanda bai wuce taga bayan ahalinmu ba...!” Cikin rashin yarda Umaima Ke girgiza kai tana furta “But... How is this possible, Muhibbah tanada zuciya mai kyau na kasa yarda zatayi abu makamancin haka..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Janyota cikin jikinsa yayi yana mai furta “Is okay my love, kanta Ta cuta, kanta tayima... Yanzu ni abinda nake so dake, ki fad’a min where we can find her... Kinga an sace wa Maami wani abunta mai matuk’ar mahimmanci kuma munada tabbacin yarinyar nan ita ta sace... So tell me a ina take..?!” Ya k’arashe cikin lallama da kwantar da hankali... D’ago idanunta masu zuban hawaye tai tace “K’anwar friend d’ina ne a yanar Gizo...!” Da tsananin mamaki Jamal Ke dubanta yace “Baby Wai kina nufin Ta yanar Gizo kawai kuka tab’a had’uwa shine har kika aminta da ita kika kawota cikin Masarautar nan aka bata masauk’i... Baby how can you be so naive..? People nowadays ba abun yarda bane.. I mean you can’t just meet someone on social media and trust them like that... What if Ta cutar dake.. What if tayi miki wani abun..!!” Ya k’arashe cikin d’aga murya.... Umaima na kuka take fad’in “Yaya believe me wllhi bansan duk haka zata kasance ba, ni da zuciya d’aya nayi... Kuma Dr Ansar mutumin kirki ne..!” Katseta yayi da fad’in “Dr Ansar...!” Ta jinjina kanta a hankali, murmusawa yayi kad’an dan yasan tracking d’insa down bazai wahala ba, ko ta accounts d’insa na yanar Gizo zai sami informations akansa yanzu rayuwa tayi sauk’i ta yanar gizo tsaf zaka sami duk bayanan da kake nema akan mutum... Bai kuma cewa komai ba dan baiso ta fahimci shirinsa na zak’ulo wannan likitan yanda ya shiga ya fita... But idan har yanada wani motive d’insa na shiga rayuwar Umaima zai iya amfani da fake accounts dan ya cimma burinsa hakan na nufin kafafen sadarwarsa zai iya zama na bogi... Tunda gashi ita yarinyar itama bogi ce, da alama saida suka shirya sosai kafin sukayi amfani da Umaima suka shiga jikinta dan su cimma burinsu na shigowa cikin Masarautar., wanda duk suka aikata abu makamancin haka zai matuk’ar wahala a kamasu cikin sauk’i, komai nasu na social media zai iya zama bogi... Kwalin likitancin nasa ma zai iya zama na k’arya ne, Ta yuwu yayi haka ne kawai to get to Umaima...Toh meye abinyi...? Yana tsaka da tinanin abinyi ne ya sinkayo sautin kukan Umaima tana fad’in “This is all my fault... Duk laifina ne, I feel responsible... Maami bata cancanci haka ba, ta min komai na gata a rayuwar nan... Maiyasa wata zata cutar da ita ta dalilina... I need to go see Maami, this isn’t fair..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye... Saurin rik’o hannunta Jamal yayi, ya dafa crutches d’insa ya mik’e tsaye, har lokacin Umaima bata daina kuka ba... Ya d’an rungumeta ta B’angaren k’afarsa mai lafiya, cikin kwantar da hankali yake lallashinta “Baby stop blaming yourself, you’re also a victim here... Ta miki wayo ne kawai irin nasu na frauds, but I assure you daga kan wannan Masarautar bazata kuma cutar da wasu ba... Ki kwantar da hankalinki Kinji...!” Ya k’arashe yana mai zame d’aurin kanta lokaci guda yana shafa sabon kitsonta a hankali, murya can k’asan mak’oshi yake furta “Lets talk about ourselves Baby.. Tunda akayi aurenmu bamu samu mun zauna ba abubuwa sai faruwa suke daga wancan sai wannan, idan muka biye na mutanen cikin Masarautar nan bazamu tab’a samun lokacin kanmu ba..!” Ya d’anyi fasali yana mai tsareta da mayen kallo... Lokaci guda yaci gaba da furta “Kitson nan yayi kyau Sosai..!” Yai maganar yana mai wasa da yatsun hannunsa saman sumar nata... Gabanta taji yayi wane irin fad’uwa, haka kurum taji tana jin wani irin muguwar tsoronsa dukda kwantar mata da hankali da yake k’ok’arin yi... Take taji jikinta ya d’auki rawa... Zame jikinta tayi kad’an ta janyo headtie d’inta ta rufa kanta jikinta sai rawa yake... Cikin ‘yar daburcewa tace “I need to talk to Maami, I want to make sure she’s fine...!” Jamal ya kauda kansa gefe cikeda takaici, ya d’anyi k’ok’arin dannewa yace “Princess Maami is fine, you don’t need to worry... Ita d’in tanada zuciya mai kyau, duk wanda ya cutar da ita tura masa aniyarsa take... Zo nan ki zauna abinki...!” Ya k’arashe yana mai kuma janyota kusansa... Zuciyar Umaima bai daina tsinkewa ba take furta “Dukda haka... Nidai kawai ka k’yaleni naje na ganta... Kuma ma batasan nazo nan ba... Maybe ma tana nemata..!” Ta k’arashe duk a daburce... Jamal ya d’an lumshe idanunsa kad’an yace “Baby ko tasan kinzo nan ko bata sani ba babu abinda zatace, I’m your husband and you’re my wife..! Babu wanda zai tuhumeki dan kinje d’akin mijinki so ki kwantar da hankalinki kinji koh... We ain’t doing anything wrong...!” A d’an daburce ta jinjina masa kai tace “I know... But dukda haka nidai nafi so ka k’yaleni naje naga Maami please...!” Ta k’arashe idanunta suna rau rau kaman mai shirin kuka... Ganin ta rikice gaba d’aya yasa Jamal dafe crutches d’insa ya mik’e yana furta “Alright fine... Ni zanje na gane miki Maamin na kuma tabbatar miki she’s fine... Amma sai kinmin alk’awarin zaki jirani a nan dan bamu gama tattaunawa ba, zaki bani full name d’in likitan nan da garin da yake zama da duk wani information da kika sani akansa... So Kimin alk’awarin zaki jirani naje na dawo..!” Tai saurin jinjina kai tace “I promise zan jiraka...!” Daga ganin yanda tai maganar zaka fahimci alla alla take ya bar kusa da ita.... Jamal yana ficewa Muhibbah Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Saida Ta Ta bata ya fice kana tasa kai Ta shige cikin parlorn... Umaima na ganinta ta mik’e tsaye cikin tsananin tsoro tana nunata da ‘yar yatsa take fad’in “You..!!” ** A can asibiti wajen Fu’ad kuwa Mahmood na isowa likitan ya taresa da batun, damuwa kwance saman fuskarsa yake furta “Dr are you sure Fu’ad yayi magana kuma sunana yake Ta ambato..?!” Dr ya jinjina kai yace “I’m his psychiatrist, kuma dani dashi mukai magana, I can assure you jikin Fu’ad da sauk’i sosai... Yayi magana yace a kirawo masa kai kai kad’ai yake son maganada shiyasa bamu kirawo kowa a family d’in ba kaman yanda ya buk’ata muka kiraka...! Za’a shigo dashi in a bit...!” Mahmood ya jinjina kai a hankali tausayin d’an uwan nasa na kuma lullub’esa... Daidai nan kuwa aka shigo da Fu’ad sanye cikin Farin tufafi kaman yanda majinyatan Ke sakawa, nurse d’in da ya shigo dashi na rik’edashi... Mahmood na ganinsa ya mik’e da sauri yana duban yanda Fu’ad d’in ya koma, kodashike yanzu jikin nasa da kyaun gani akan kwanakin baya... Babu tsananin rama irin na kwanakin baya, sai duhu kawai da yayi, harta labb’ansa da tafukan hannayensa duk sunyi duhu wanda bazai wuce side effect na strong magunguna da allurai da yake sha ba..! Da murmushi saman fuskar Mahmood d’in ya k’araso garesa ya rik’o hannayensa... Fu’ad na d’ago idanu ya dubi Mahmood sai ya fashe da kuka... Lokaci guda ya rungume d’an uwan nasa yana kuka sosai.... Jikin Mahmood yai matuk’ar yin sanyi, rungume Fu’ad d’in shima yayi yana furta “Is okay Fu’ad..! I’m here now..! Kayi shiru kaji...!” Cikin kuka Fu’ad ke furta “Yaya..! Yaya...!! I’m sorry Yaya...! I’m sorry please firgive me...! I’m sorry I’m sorry I’m sorry...!” Gaba d’aya sai kuma kaman ya dad’a rikicewa dan abinda yake iya fad’i kad’ai kenan.... Mahmood yaci gaba da bubbuga bayansa yana furta “Ya isa haka Fu’ad... Kayi shiru haka nan kaji..!” Fu’ad yaci gaba da kuka yana girgiza kai yake furta “No..No Yaya..! I’m a criminal..! I’m a criminal... I need to turn myself in...! I don’t belong here Yaya.. Tell them I belong to prison, I need to pay for my crimes..! Yaya naji sauk’i I can turn myself in now.. Mu gudu Yaya, kar mu tsaya a nan, muje ka kaini police station, I need to give my statement... Muyi sauri mu gudu daga wajen nan kar su kuma kulleni...!” Yanda yake maganar yana zaro idanu yasa jikin Mahmood yin sanyi, da alama dai lafiya bata samu ba... Mahmood ya rik’esa sosai yana furta “Ya isa haka Fu’ad... You’re not well, magunguna suke baka a nan ba cutar dakai suke ba...!” Fu’ad yaja hawaye yake girgiza kai yana furta “No Yaya... Kar ka yarda dasu, wllhi ni d’an ta’addane... Dukanmu UKU ‘yan ta’adda ne... Ni Yazeed da kuma Jamal... Even our Mother itama ‘yar ta’addace... We’re all bunch of criminals..!” Izuwa lokacin Mahmood ya kuma tabbatarwa haukan Fu’ad yakai wani mataki tunda har zai ambaci mahaifiyarsa da sunan ‘yart’adda... ** A nan parlorn Jamal kuwa girgiza kai Umaima taci gaba da yi tana mai furta “Wllhi idan baki fice ba zan miki ihu macuciya azzaluma kawai.. Kin cuceni kin yaudareni, kinyi amfani dani ki cutar da ahalina..! How could you do this to me...! Tsakanina dake babu komai face alkhairi amma kika zab’i ki cutar dani... Why..? Maiyasa.??!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka... Muhibbah na girgiza kai yake furta “Duk abinda kika fad’i gaskiya ne... I tricked you, I deceived you... I used you... But idan kikaji dalilaina zaki fahimceni Umaima... Please hear me out first... Kinsaurareni dan Allah..!” Umaima Ta katseta da fad’in “You’ve got some nerve..! You really have no shame..! Bayan duk abinda kikayi har kinada k’warin gwiwan had’a idanu dani kice zakimin bayani... Mutanen nan da kika zalunta they’re my family.. They’re my everything... I owe them my life... How could you use me to destroy them... How could someone be so ungrateful...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana... Hawaye na zubowa daga idanun Muhibbah take furta “Kafin na rok’eki ki bani dama nayi miki bayani... Inaso ki bani dama na kub’utar dake daga mutanen da kike zaton ahalinki ne... Inaso ki bani dama na kub’utar dake daga mijin da kike zaton you’re safe around him...! Ki bani dama na kub’utar dake daga auren da kike tunanin an ginasa ne kan Soyayya..! Umaima your life is in great danger.. these people are planning to have you killed... Burinsu shine idan Jamal ya kusanceki Su halak’aki, suyi tsafi dake... Domin su d’in bak’ak’en matsafa ne..! Dik yanda za’ayi kiyi gaggawan ficewa daga gidan nan kafin su cimma burinsu akanki... Umaima babu lokaci, kiyi gaggawan b’arin Masarautar nan...!” Da tsananin mamaki Umaima Ke dubanta sai kuma tace “Oh ta nan kika b’ullo... Shin ke wace irin azzaluma ce mai sak’a alkhairi da sharri... Shin ke...!” Batakai aya ba Muhibbah Ta katseta da fad’in “Ki kirani da duk sunan da ya kwanta miki... Amma ki sani ba k’arya nake miki ba... Wad’annan mutanen ba mutanen k’warai bane kaman yanda kike zato... Wad’annan mutanen ruined my life, they destroyed my family... They abused me... Your husband is one of them... Umaima your husband is a rapist, a heartless being...! A criminal who deserve to rot in jail..!” Cikin wane irin kuka Umaima ta toshe kunnuwanta tana mai furta “Just shut up..! You’re lying... You’re a liar... How could you expect me to believe someone like you... After all the lies you told me... After how you tricked and used me..! How could you expect me to believe a fraud like you..!!” Cikin tsananin huci Muhibbah ta k’araso ta damk’e arms d’in Umaima dake tsananin kuka tana mai jijjigata take furtawa cikin tsananin karaji itama hawayen ne Ke zubo mata “I’m telling you the truth..! You need to believe me..! This is nothing but the truth..! Mijinki shi ya b’oye Masoyinki na asali Ja’afar k’ark’ashin bak’in kurkuku a ciki masarautar nan...! Jafar didn’t leave you, Jafar bai gujeki ba Umaima Jamal shine ya b’oyesa tsawon shekara guda dan ya raba tsakaninku..!” Izuwa lokacin sosai jikin Umaima ya d’auki rawa... Tana girgiza kai take furta “No Ja’afar yamin sallama da kansa cewa ya tafi ya bar Masarautar nan... Maiyasa zaki k’alawa Jamal alhakin tafiyar Ja’afar..! What have I ever done to you to make you destroy my life like this..! Mai na miki da tsanani Muhibbah...?!” Huci Muhibbah take tana dubanta, lokaci guda take furta “Kinaso ki gani da idanunki....! Kinaso kisan mijinki wane irin mutum ne... Zan nuna miki ko shid’in Wanene.... Watak’ila ki yarda..!!” Daga haka bata kuma tsayawa sauraren kukan Umaima ba Ta finciko hannunta suka nufi matakalan benen da zai kaisu d’akin Jamal d’in... ** Jamal da ya sinkayi tattaunawar Giwa da Jakadiya ba tareda saninsu ba, a hargitse ya shigo cikin d’akin hawaye na zubo masa... Daidai gaban Giwa ya isa ya tsaya yana wane irin huci yake furta “Kar kiyi tunanin min k’arya dan na riga naji komai..!! Is it true kashe Umaima zakiyi...? Dalilinki na aura min ita shine dan ki kasheta...! How could you Maami... How could you do this to me...! I love Umaima..! I love her with all my heart and soul... Like I’ve never loved someone before... She’s my life Maami... How could you think of taking her away from me...! Just how..!!” Ya k’arashe cikin tsananin d’aga murya yana mai jijjiga Giwa dake tsaye gabansa tana hawaye.... Lokaci guda Jamal yaci gaba da fad’in “I’ve done everything for you... I’ve become a Criminal duk saboda Ke da k’ok’arin miki biyayya dan cikon burinki... Nayi fyad’ewa k’anan ‘yan mata sunfi a k’irga duk sabida ke... Wad’annan duk basu isheki ba sai kin d’auke mi mace d’aya tak da nake so...! Maami how could you do this to me.. Answer me Giwa...!!” Ya k’arashe jijiyoyin jikinsa na kuma mimmik’ewa... Cikin kuka Giwa Ke furta “Komai sabida ku nakeyi Jamal, ka yarda dani I’m doing all this for you... Wllhi sabida kai da ‘yan uwanka nake komai...!” “Shut up..! Just shut up, I’m tired of listening to all this...! You know, I should never have obeyed you from the very beginning... Duk abubuwan da kike shiryawa no one ever works... Maiyasa hakan bai isheki ishara ba... You’re the reason why our family is going through all this... You tormented Fu’ad, Kin haukatasa, kin raba Yazeed da family d’insa... Kin hana Ya Mahmood samun farin cikinsa... I know you’re behind all that I listed.... And now the only person da ta rage a rayuwata kina nema ki d’auke min ita...! Wllhi kinji na rantse bazan barki ki aikata hakan ba... I’m leaving this place together with my wife.! Bazan tsaya cikin Masarautar nan ba and go down with you... Zan d’auki matata muyi nesa da Masarautar nan and start a fresh...!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice... Giwa na kiransa inaaa ko tsayawa baiba balle ya saurareta... ** Drawer mai k’yallaye d’aukeda jini Muhibbah Ta soma janyowa idanun Umaima suka sauk’a kan fararen k’yallayen... Jikinta na matuk’ar rawa ta shiga warwaresu tana ganin jini had’ida sunayen mata rubuce jikin k’yallen... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa... Ita kaw Muhibbah data tabbata Umaima taga abinda zai sa ta aminta da duk abubuwan da take fad’I mata tuni ta soma neman muhimmin abinda ya shigo da ita... Aiko tana d’aga bakin katifa taci karo da Taswiran...! Ta saki murmushi a hankali tana mai furta “Alhamdulillah..!” Bayan duk tsawon lokacin nan Taswiran guda uku sun fad’a hannunta.... Ita kaw Umaima tsaye tayi da k’yallayen tana duban abin mamaki, jiri na neman kada ita... Daidai lokacin sukaji an banko k’ofa an shigo... Karaf suka d’ago idanunsu suna kallon wanda ya shigo..... *MUHIBBAH* *68* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Koda Babba cikin kuyangi masu kula da b’angaren Muhibbah ta shigo mamaki ne ya cikata ganin Hasiya sanye da Kayan Muhibbah... Ta k’araso cikin tsananin tashin hankali tana furta “Ke Hasiya lafiya na ganki da kayan Gimbiya...! Mai hakan yake nufi..? Ina ita Gimbiyar...?!” Hasiya tai rau rau da idanu tace “Bata nan ta amshi tufafina ta saka kuma ta gudu...!” Kuyangar ta dafe kanta tana furta “Shikenan Hasiya kin kashemu.! Ta yaya kika amince da hakan.. Hasiya kin kuwa San tashin hankalin da kika jefamu ciki.. Yanzu mai zamu sanar da Rankaidad’e..?! Wata k’arya kike so muyi dan kare kanmu...?!” Hasiya tace “Ni taimakonta nayi dan tana buk’atar taimako amma ai ga tufafinta jikina ki barni na zauna nan cikin d’akin nata a matsayin ita Gimbiyar idan Rankaidad’e yazo sai na rufe fuskata... Amma idan ba haka ba bana tunanin munada wani mafita dan na tabbata Gimbiya tayi nisan da bazamu cimmata ba..!” Sauk’e ajiyan zuciya Kuyangar tayi tace “Idan hakan baiyi aiki ba Hasiya kin sakamu a uku dan alhakin b’acewar Gimbiya zai rataya ne a wuyarmu..!” Ta k’arashe damuwa k’arara saman fuskarta... ** Jikin Umaima ya d’auki rawa, yanda taga fuskar Jamal ba k’aramin firgitata yayi ba, gaba d’aya ta rasa gane wacce duniya take sai rawa da jikinta keyi... Ko motsa ‘yar yatsar k’afarta ta kasa sai tsananin tsoro da ya lullub’eta, ga wani irin b’ari da illahirin jikinta keyi... Muhibbah kaw rabin idanunta naga kwalban turare dake bisa dressing mirror rabi na kan Jamal dan bataso tayi losing sight d’insa tasan yana iya masu komai yanda Ta hango fuskarsa a matuk’ar dame..! Murmushi Jamal ya sakarwa Umaima yana k’ok’arin nufota yake furta “Baby don’t believe a single word da wannan mayaudariyar zata sanar dake... She’s a fraud Baby kin mance ne.. She tricked you..!” Girgiza kai Umaima take tana kuma k’ok’arin jada baya cikin tsananin tsoro da firgici, muryarta na rawa yake furta “No... No don’t come near me..! No no please...!” Jamal bai daina yunk’urin nufota yana furta “Baby ni ne fah... Ni ne Yarima Jamal d’inki, your husband...!” Muhibbah dake hararan kwalban turaren tana takawa a hankali tana matsawa kusan dressing mirror d’in take fad’ida Umaima “Run Umaima, don’t listen to this criminal... Run, ask for help... Don’t just stand there..! Ki gudu Umaima karki sauraresa...!!” Umaima kaw ta kasa katab’us shock d’in abunda tai discovering a yau d’in ya kasa sakinta... Ko motsi mai kyau ta kasa sai rawa da jikinta yake sabida tsananin tashin hankali.... Daidai nan Muhibbah tayi nasan rabza masa kwalban turaren akai... Ya fad’i k’asa had’ida rik’e kansa yana mai sak’in k’ara... Umaima ma k’aran ta saki Ta mak’ale b’angare guda had’ida kame kanta da duka hannayenta biyu, jikinta bai daina rawa ba.. Kana gani kasan ba’a hayyacinta take ba... Muhibbah tai saurin tura Taswiran cikin rigarta, ta shiga janyo hannun Umaima tana fad’in “We need to get out of here Umaima.. Bamuda lokaci, bani hannunki..!!” Bata kai aya ba taji sauk’an wani irin abu a goshinta wanda ya sanyata zubewa a wajen duniyar na juya mata bata iya fahimtar komai ba saima lumshewa da idanunta sukai jini na kwarara daga goshinta... Sandar crutches d’insa ya rabza mata akai da iyaka k’arfin da Allah ya hore masa... Cikin rawar jiki Umaima ta mik’e tana ambato sunan Muhibbah inaaa bata iya komai sai k’ok’arin bud’e lumsassun idanunta take cikin tsananin azaba...! Da k’yar tana ganinsu nesa nesa take iya furta “Run Umaima..! Run.! Ask for help..! Ki gudu, ki tsira da rayuwarki...!!” Cikin kuka Umaima ke fad’in “Bazan iya barinki a haka ba...! Ki tashi mu gudu dan Allah..!!” Inaa tana maganan ma cak ji tayi kaman numfashin Muhibban ya d’auke.... Umaima ta juyo ta hangi Jamal dake k’ok’arin zuba wani ruwan magani cikin handkerchief, a daburce Ta mik’e tana furta “Help..! Someone help us..!!” Ta nufi k’ofa a guje... Saidai tuni Jamal ya cimmata, Ta shiga bige buge tana k’ok’arin k’wace kanta saidai k’arfin namiji da mace ba d’aya ba balle ma ita da take cikin yanayi na matuk’ar tsoro...Tuni ya matseta sosai cikin hannunsa sai hura hanci yake yana haki, lokaci guda ya danna mata handkerchief d’in a hancinta... Aiko tana Shak’an ruwan maganin idanunta suka lumshe jikinta ya sake gaba d’aya, cak Ta daina duk buge bugen da take... Jamal na murmushi yake furta “Where do you think you’re going Sweetheart..? You’re mine, Ke tawa ce Umaima... Idan kinga kin fice daga gidan nan ni ne kawai zan fitar dake...!” Ya k’arashe zancen nasa yana mai d’aurata saman gado... Haka yana cangwala sandarsa ya isa jikin wani drawer ya zaro igiya doguwa ya shiga d’aure Umaima jikin gado, tsaf ya gama d’aureta yana mai sakin murmushi... Maidoda dubansaga Muhibbah tai wacce take yashe a wajen lifeless kana ya furta “You’re now under my custody Muhibbah..! Zaki d’and’ani azaba zakiyi danasanin shigowa cikin Masarautar nan balle har kiyi gangancin zab’oni a matsayin abokin gaba...!!” Take ya isa gareta da igiyoyin nasa ya shiga d’aureta tin daga hannayenta har zuwa k’afafunta, wane irin d’auri yayi mata ya had’e hannayen da k’afafun ya d’aure waje guda... Sai gumi yake yana haki yana ciza labb’ansa sabida tsananin bak’in zuciya... Gefe ya koma yana sauk’e haki yake dubansu su duka biyu, itadai Umaima a nan zai barta yayita kula da ita har ya samu ya shawo kanta su gudu tunda babu mai tuhuma Ina take, matarsa ce babu wanda zai zargesa akanta...ita kuwa Muhibbah tunanin abinyi yakeyi da ita... Take tunanin tattaunawar Giwa da Jakadiya da ya sinkaya ya fad’o masa cewa zasu baiwa Aljanah Sarauniya Tamuna matarsa Umaima matsayin sadaukarwa, Toh mai zai hana ya canzawa Giwa Umaima da wannan ‘yar lek’en asirin, sai Giwa ta bada ita ga Bokanta a matsayin fansar matarsa Umaima, idan yaso shi sai ya d’auki matarsa su gudu daga Masarautar, bayada buk’atan komai cikin Masarautar, ya zab’i ya tsira da rayuwar matarsa...! Take ya saki wata irin muguwar murmushi yana duban Muhibbah da har lokacin idanunta a lumshe suke saiko Jinin dake kwance goshinta, d’aure da manyan igiyoyi... Yasa hannu ya d’an shafi k’eyarsa yanda Ta kwad’a masa kwalban turare yaga d’an jini kad’an... Murmusawa ya kumayi yana mai furtawa a fili... “Ba’a zubar da jinin ahali Sarki AbdulJabbar a banza yarinya..! Kinyi babban ganganci.. Wannan Jinin da kikayi sanadiyar d’igansa zaki biyasa da rayuwarki..!!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin wata murmushi lokaci guda ya kullo k’ofa ya fito ya nufi b’angaren Giwa... ** Cikin rashin gane inda kalaman nasa suka dosa Mahmood d’in ya kamo hannunsa suka zauna saman doguwar kujera dake cikin d’akin ganawa da marassa lafiyan.... “Fu’ad ka natsu ka sanar dani... Mai kake son cewa..?!” Fu’ad na hawaye ya d’ago yana dubansa sai kuma ya sadda kansa k’asa yace “It was that night... Daren Washe garin sallah k’arama..! Yaya ka tuna, shekaru goma sha hud’u da suka shud’e...!” Mahmood ya kuma gyara zamansa yace “Fu’ad ban fahimci mai kake nufi ba, anyi bikukunan sallah da yawa wanne kake nufi..? Kuma mai ya faru lokacin..?!” Fu’ad yasa tafukan hannayensa duka biyu ya shafi fuskarsa sai kuma yaci gaba da fad’in “Bikin k’aramar sallah wanda bayanshi da kad’an akayi bikin aurenka...!” Yai shiru yana duban Fu’ad sai kuma ya soma tuno abinda ya faru “We were all together, ni da kai da kuma Yazeed da Jamal, it was such a nice evening..! Tun bayan wannan shekaran bamu sake wata fita saman Dawakai tare ba the four of us, koda kuwa kilisa ne.. How can I forget that Eid.. Yana d’aya daga cikin best Eid na rayuwana gaba d’aya sabida kiran da Mai Martaba ya min a lokacin ya sanar dani an saka aurena da Aliya bayan duk gwagwarmayar da muka sha da Maami na k’in amincewa da auren da tayi... But at the end wannan daren Mai Martaba ya kirani ya sanar dani ya saka mana ranan aure, Kaga kuwa bazan tab’a mance wannan daren ba..!”Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa sai kuma yaci gaba da fad’in “It was such a memorable Evening..! Munyi wasan Dawakai sosai Ni da kai da Yazeed da kuma Jamal harmada Ja’afar... Mukayi dare a hanyarmu Ta dawowa, bamu dawo Fada da wuri ba..!” Fu’ad ya jinjina kai yace “That same night... Komai ya fara ne daga wannan daren, halinda na tsinci kaina ciki ya soma ne daga wannan daren Yaya...!” Mahmood ya tsaida murmushin da yake lokaci guda yana mai duban Fu’ad d’in, sai kuma yaci gaba da fad’in “Something happened that night, kaman mun tsinci mutum a hanyar mu ta komawa gida.... I think it was... A girl... Yeah a girl, we even helped her...! But wait, na tafi na barku tareda Yarinyar..! Mai Martaba ya aiko sak’on yana nemana...! What happened that night Fu’ad..! Mai ya faru sanda na barku da yarinyar..? Tell me Fu’ad..! Tell me everything..!!” Ya k’arashe tashin hankali k’arara kwance saman fuskarsa... Fu’ad yaja wane irin dogon numfashi yana mai lumshe idanunsa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “After you left, Jafar left as well...! Ya rage saura mu uku da yarinyar.. Ni Yazeed da kuma Jamal...! Yaya we did something terrible to the girl...!!” Kuka ya hana Fu’ad ci gaba da magana... Izuwa lokacin hankalin Mahmood ya tashi sosai, zuciyarsa bata daina tsinkewa ba, fatar jikinsa ta soma komawa ja...With a straight face yake furta “Fu’ad you tell me what you three did...! What did you do to that girl...! What Fu’ad..?!!” Ya k’arashe yana jijjiga Fu’ad kad’an idanunsa duk sun firfito waje zuciyarsa naci gaba da bugawa.. Fu’ad na hawaye yana girgiza kai yake furta “We abused her Yaya..! The three of us raped her..! Yazeed started it, then Jamal..! Then me...! Ka yarda dani Yaya, Wllhi banso aikatawa ba...But they forced me...! Yazeed da Jamal sun tilasta min sunce umarnin Maami ne dole na aikata hakan....!” Mahmood da yakejin maganar tamkar sauk’ar takobi cikin zuciyarsa... Dakatar da Fu’ad yayi da fad’in “I don’t get you Fu’ad... What are you trying to say...?! Kana so kace min my brothers... My three brothers Kun lalata rayuwar wannan yarinyar kuma Maami ita tai maku umarni ku lalata rayuwar yarinyar...! Fu’ad talk to me..! Kamin magana da yaren da zan fahimta..!!” Ya k’arashe fuskarsa na kuma rikid’ewa gaba d’aya.... Cikin kuka Fu’ad Ke jinjina kai yana mai furta “Yaya gaskiya nake fad’a maka..! Duk abinda na fad’i mun aikata kuma bisa umarnin Maami muka aikata..!!” Izuwa wannan lokaci Mahmood ya kasa fahimtar wacce duniya yake..! Ya kasa yarda ‘yanuwansa da suka fito ciki guda zasu aikata mummunan laifi irin wannan, waima bai tsaya a nan ba harda mahaifiyarsu..! Kai inaa Fu’ad baida lafiya bai kamata ya yarda dashi ba in the first place... No ahalinsa bazasu tab’a zama azzalumai irin haka ba.. They might have their own differences amma bazasu tab’a zama azzalumai abin k’yamata irin haka ba...! Muryar Fu’ad ya sinkayo yana ci gaba da sanar dashi yanda duk abun ya kasance tin daga farko...! Wane irin gumi na tsartsafowa Mahmood d’in, jikinsa ya d’auki rawa... Lokaci guda ya d’ago yana duba Fu’ad d’in, cikin wane irin kakkausar murya yace “Fu’ad you’re talking about our mother here..! My mother Fu’ad...!! Maami can never do something like that..! You are sick in the head Fu’ad..! And this place is where you belong..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Lokaci guda ya mik’e yana kiran nurses d’in suzo su shige da Fu’ad su maidasa d’akinsa na majinyata babu alamun lafiya a tattaredashi ko abubuwan da yake sanar dashi.... Take nurses d’in suka k’araso suna k’ok’arin janye Fu’ad yana tarjewa, yana juyowa yana duban Mahmood d’in yake kuma fad’in “Yaya I’m not sick anymore..! I’m telling the truth..! Why can’t you believe me..! Wllhi gaskiya nake fad’i maka..!! Yaya please ka saurareni..! Take me to jail please, I need to pay for my crimes..! Yaya dan Allah ka saurareni..!!” Inaa tuni an shige da Fu’ad, Mahmood kaw tsaye kurum yayi yana duban yanda aka janye Fu’ad, zuciyarsa na tsananin bugawa kaman zai tarwatse ya fito waje..! Take yaji tsakiyar kansa ma na sarawa kaman kan nasa zai rabe k’wak’walwarsa ta tarwaste...!Ya kasa yarda ‘yanuwansa harda mahaifiyarsa zasu aikata irin wannan mugun abin, mummunan laifi abin k’yamata ga duk wani d’an adam mai hankali...!Ta yaya za’ace ahalinsa sun aikata irin wannan laifi...! Shin wannan wane irin al’amari ne...! Barde ya k’araso cikeda risinawa yana fad’in “Rankaidad’e a k’araso da motar nan ne..? Allah shi baka yawan rai nace a k’araso da motar nan ne...?!” Barde yaji Mahmood d’in bai basa amsa ba bai kuma dakata ba saima ci gaba da tafiya da yake...! Barde ya d’ago kai yana duban Ubangidan nasa, sosai ya razana da ganin yanayin Mahmood d’in wanda Tafiya kurum yake ba tareda yasan yanda yake jefa k’afafunsa ba... Cikin sauri Barde ya ciro waya ya shiga kiran layin Turaki.... Turaki na d’agawa Barde ya sanar dashi halinda ake ciki, babu b’ata lokaci Turaki yace yana nan tafe...! Mahmood kaw hotunan abinda suka faru can shekarun baya ne Ke dawowa idanunsa, dukda bazaice ga kamannin yarinyar ba yana hangota a idon zuci.. Maiyasa ya tafi ya k’yale ’yan uwansa da yarinyar..? Maiyasa bai tsaya ya kaita gida da kansa ba..? Maiyasa ya aminta da cewa ‘yanuwansa bazasu cutar da ita ba..?! Fyad’e fyad’e., mummunan laifin da yafi k’ymata a rayuwarsa, yau sai ga ahalinsa Sun aikata hakan kuma Wai bisa jagorancin mahaifiyarsu..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!! Yanaji shid’in kaman ba d’aya bane daga cikin ahalin, ta yaya ahalinsa zasu zamto irin wad’annan mutanen.. Koda shike mutum ba shi yake zab’an ahalinsa ba amma kam tabbas da ace zab’a ake da bazai zab’i ya fito cikin irin wannan ahalin ba...! Yana tsaka da tinanin idanunsa suka sauk’a b’angaren emergency.. Ashe har ya k’araso emergency tin daga psychiatric ward da k’afafunsa ba tareda ya sani ba.. Barde na nan biye dashi duk yanda ya saka k’afafunsa.... Yana kallon yanda ake guje gujen d’auko gado mai tayu na d’aukan majinyata ana turawa zuwaga k’atuwar ambulance dake pake tana bada sautin taimakon gaggawa...! Ganin mutanen yake kaman daga can nesa nesa suke, haka nan sautin mutane da sautin motar yana jinsu kaman daga can wani nisan duniya suke...! Shid’in yana jinsa ne kaman wata duniya ta daban yake... Gaba d’aya baisan mai yakeji ba..! Can ya hango ana wucewa da mutanen ana koran jama’an dake cike wajen.... A gefe guda ya hango Waziri da wasu dogarai kusan guda hud’u, dogaran suka k’araso garesa cikeda risinawa suna kwasan gaisuwa wajen Mahmood d’in da har lokacin ya kasa katab’us Waziri ne ya k’araso yana kuka shar shar da hawaye yake furta “Rankaidad’e Yarima Yazeed ne..! Yarima Yazeed da ahalinsa sun gamu da mummunan had’arin mota gaba d’ayansu suna cikin mawuyacin hali....!” Mahmood baikaiga magana ba Dr guda ya k’araso garesu cikeda risinawa ya dubi ahalin Babban Gida yace “Munada buk’atan jini ga Yarima wanda za’ayi gaggawan masa aiki dan tsaida jinin dake zuba jikinsa kafin a iya rasashi...!” Waziri yayi saurin cewa “Su kuma ahalin nasa wane hali suke ciki Likita..?!” Dr yace “Bazamu iya cewa komai a halin yanzu ba har sai lokacin da sakamakon gwaje gwaje ya fito, amma a halin yanzu duk suna ciki ana basu agaji na gaggawa.. Abinda kawai zamu iya sanar daku shine ku shirya ma faruwan koma menene...!” Waziri yaci gaba da salati yana kwarfe gumin dake kuma keto masa.... Nan cikin emergency d’in suka shige suna jiran bayani daga likitocin... Bayan an auna jininsu koda wanda zai dace dana Yazeed, Jinin Waziri shine ya dace da Jinin Yazeed, Jinin yayansa Mahmood bai matching nasa ba... Take aka shige da Waziri aka zuk’i jininsa, Mahmood bai kawo komai a ransa ba hasalima tashin hankalin da yake ciki ya wuce gaban ya tsaya tunanin ya akayi jininsa bai matching na d’an uwansa da suka fito ciki guda ba sai na Waziri... A haka Turaki ya k’araso ya taddasu cikin tsananin damuwa shima Tinda Turaki yaga yanayin Mahmood dukda kuwa k’arfin hali irin nasa yasan ba k’aramin al’amari bane Ke damunsa, kodashike yanayin da Yazeed da ahalinsa kad’ai Ke ciki sun isa su jefa Mahmood d’in cikin irin wannan yanayi... K’urama waje guda idanu kurum yayi kalaman Fu’ad na kuma Yawo a kansa, mahaifiyarsa tayi umarni ma ‘yan uwansa suci zarafin k’aramar yarinya su lalata mata rayuwa kawai sabida son duniya da Mulki... Mulkin Duniya da babu wanda zai tabbata akansa..! Wannan tashin hankali da mai yayi kama.. Koda yake Spain yana d’aya daga cikin founders na wani foundation wanda suka gina dan k’wato hakki da kuma taimakawa mata da k’anan yara maza da mata da akaci zarafinsu Ta hanyar fyad’e... Yau sai gashi nan laifin da ya jima yana yak’a a k’asar Spain cikin gidansu, cikin ahalinsa.. K’annensa ‘yan uwansa da suka fito ciki guda sun aikata irin wannan laifin da ya k’yamata tsawon rayuwarsa bisa son zuciya da umarnin mahaifiyarsu..! Ya lumshe idanunsa a hankali zuciyarsa na kuma masa zafi...Yana tsaka da tinanin ya sinkayo muryar Turaki yana fad’in suje suyi sallah su dawo, dan lokacin kiraye Kirayen sallan la’asar ake... Babu musu ya mik’e yabi bayan Turaki dake masa jagora...! Koda sukayi sallah nan cikin masallacin dake emergency d’in sun dawo sun tadda har lokacin ba’a fito daga aikin da akewa Yazeed ba... Yaransa guda biyu ma duk aiki ake masu na gaggawa domin ceton rayuwarsu.... Can kusan magrib dan har an soma kiraye kirayen sallah wasu likitoci guda biyu suka fito suna zane hand gloves d’insu nurse mask...! Waziri har yana tuntub’e ya nufesu yana tambayan jikin Yazeed ko na yaransa... Dr ya k’araso har gaban Mahmood wanda shima ya mik’e tsaye yana jiran abinda likitocin zasu ce.... Likitan ya d’an risina yace “We did everything we could your Highness... But we couldn’t save any of his children...! They’re both gone...!” Rintse idanunsa yayi a hankali d’aukacin mutanen dake wajen suna masu furta Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Mahmood ya fitar da huci a hankali kana yace “And Yazeed... How’s he Dr...?!” Dr ya d’an dubesa sai kuma yace “Kana iya biyoni domin kaga halinda yake ciki Rankaidad’e...!” Babu musu Mahmood yabi bayan likitan, kwance ya hango Yazeed saman gado na’ura ko ta ina a jikinsa.... Mahmood yayi tsaye yana duban yanda halittan d’an uwansa Yazeed ya koma cikin sa’o’I k’ank’ani, ya tuna rabuwarsu a daren jiya lafiya lou yake da cikan halittarsa ba kaman yanzu da halittarsa ta sauya ba kuma bazata tab’a dawowa kaman da ba... Hak’ik’a ba’a gama halittan bawa ba har sai randa ya komaga mahaliccinsa, kar ka zamto mai d’agawa da nuna kai wani ne dan kaid’in ba kowa bane, cikin k’ank’anin lokaci labarin rayuwarka zai iya canzawa...! Muryar Dr ya sinkayo yana furta “Yanda ya rik’e steering wheel haka hannayensa suka dagargaje tareda steering wheel d’in, we had to amputate both his hands...!” Mahmood yai K’uri yana duban gundulumin hannayen Yazeed dage d’aure da bandage duka biyu tun daga elbows d’insa.. A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai kuma jinjina lamarin... ** Can d’akin da ya ganawa Jakadiya azaba suka aje Muhibbah.. Saman kujeran da ya d’aure Jakadiya saman Kujeran ya d’aureta itama, saidai ita d’aurin da ya bada igiya bane kaman yanda yayiwa Jakadiya da handcuffs ya d’aureta yanda ko motsi mai kyau bata iyawa...! Giwa ta Washe idanu tana duban yarinyar zuciyarta naci gaba da tafarfasa..! Duk itace silan komai, Ta tabbata itace Ta janyo duk halinda suka tsinci kansu cikin Masarautar.... Ta dubi Jakadiya dake tsaye rik’eda ruwa cikin bucket tace “Jakadiya..!” Jakadiya ta risina tana mai furta “Allah shi taimakeki..!” Giwa taci gaba da fad’in “shek’a mata ruwan nan ta bud’e idanunta..!!” Babu musu Jakadiya tayi yanda Giwa tace, ta watsawa Muhibbah ruwan mai matuk’ar sanyi tun daga tsakar kanta har zuwa k’afafunta tana mai furta “Tashi Munafuka..!” Aiko nan tayi wani irin jan dogon numfashi ta bud’e idanunta da suka mata matuk’ar nauyi da k’yar tana jinta gaba d’aya a tamke...! A hankali Ta ida ware idanun nata yanda taga Giwa, Jamal da kuma Jakadiya tsartsaye gabanta dukansu Uku sun zuba mata idanu.... SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH* *69* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin tsananin huci Giwa Ke furta “Da kyau..! Da kyau d’ahnah..! Kai d’in ka cika jinina, ka cika min alk’awari ka kawo min wannan ‘yar lek’en asirin har tafin hannuna...!!” Jamal dake dafe da sandarsa idanunsa naga Muhibbar shima yake furta “Maami I told you so.. Na fad’a miki zan kawo miki ita har yanda kike, ban tab’a disappointing d’inki ba Maami...!” Giwa ta jinjina kai tace “Ina matuk’ar alfahari dakai...!” Ta kuma duban Muhibbah wacce Ke sakin huci tana dubansu da idanunta wanda tuni sun rikid’e sun koma jazir ga ruwan da Jakadiya ta watsa mata sai faman d’iga yake a fuskarta... Take Giwa ta soma takowa gabanta cikin tsananin huci, saida ta k’araso har gaban kujerar da Muhibbah ke d’aure bisa kana ta bud’e murya tace “Ke k’aramar alhaki, ki sanar damu waye ya turoki Masarautar nan..! Ma waye kike lek’en asiri cikin Masarautar..?! Wacece Ke..?! Su waye shuwagabanninki..?! Daga wace masarautar kike..?!”Ta k’arashe tana mai kamo hab’ar Muhibbah ta d’ago fuskarta da k’arfin gaske... Muhibbah bata daina huci ba tana aika ma Giwa kallon k’yama take furta “Maiyasa kike tunanin zan sanar da azzaluma irinki ko wacece ni..?!” Take Giwa ta d’auketada wani irin jahilin mari wanda saida ya tsaga mata leb’en bakinta jini ya fito... Muhibbah ta rintse idanunta sabida azaba, Giwa zata kuma kai mata wani marin Jamal ya dakarta da ita da fad’in “Haba Maami just mari won’t make her talk, har yanzu ita d’in ji take wata babbar k’waro ce tinda har ta Iya shigowa cikin Masarautar nan ta tashi duk wani bomb data dasa ba tareda wani ya fahimceta ba, har Ta iya Sa k’afa Ta tsallake ta gudu, hakan bai isheta ba ta zabi ta kuma dawowa...! Zaifi kyau idan kika mik’a min ragamar hukuntata, Ina mai tabbatar miki nan bada jimawa ba zata bud’e baki tai magana harda abinda ba’a tambayeta..!” Giwa na sakin huci take furta “Na baka wuk’a da nama Jamal, kayi mata duk wani nau’i na azaba da kakeda tabbacin zaisa ta bud’e baki ta fad’i ko wacece ita da kuma abinda ya kawota cikin Masarautar nan...!!” Jamal ya murmusa kana yace “Godiya nake Rankidad’e Giwa, hukuntata zai bani pleasure sabida ta shiga gonata..!” Ya kuma kai dubansaga Jakadiya yace “Jakadiya..!” Jakadiya ta yada kai tana mai amsawa da “Rankaidad’e..!” Jamal yaci gaba da fad’in “Ki mik’o min jakan kayan aiki na..!” Babu musu Jakadiya ta jinjina kai tana mai furta “An gama Rankaidad’e..!” Jakadiya ta tafi mik’o kit d’in Jamal tana mai furta “Yarinya yau ranar ki ce, bayan bani mayafi da kikayi kika k’ala min sharri banci miki ba ban sha miki ba gashi nan zaki girbi irin ukuban da kika sakani ciki..!!” Ta k’arashe tana mai aje kit d’in gaban Jamal wanda har lokacin bai janye idanunsa daga kan Muhibbah ba..! Tsoro da firgici suka cika Muhibbah ganin irin takarcen mugunta da zalunci dake cikin jakan da Jamal yai umarni ta mik’o masa... Tana gani ya soma ciro allurai da wasu k’arrafa saikace wanda zaiyi aikin kanikanci...! A idonta ya soma had’a wasu ruwan allurai yana zira su cikin doguwar syringe irin wanda ake amfani wa dabbobi dashi.. Ta tina ire iren syringe d’in da suka gani a d’akin da ya rufe Jafar, badai itama tura mata wad’annan ruwan bala’in zai ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Abinda zuciyarta Ke iya nanatawa kenan dukda k’irjinta dake tsananin bugu, gashi ko motsi mai kyau bata iya yi dan d’aurin handcuffs Jamal yayi mata, harta k’afafunta suma ya d’aure cikin k’araffa yanda ko kusa bazata iya tunanin guduwa ba... Allah kawai take ambato ya ceceta daga hannun wad’annan azzaluman bayi nasa dan tasan shi kad’ai ne zai ceceta..! Jamal ya nufota da alluran muguwar murmushi saman fuskarsa..! Girgiza kai Muhibbah take tana hawaye bakinta bai daina ambaton Allah ba..! Giwa kuwa fad’i take “Danna mata alluran Jamal, nace kada ka ragar mata ka danna mata ya shiga tin daga kwanyarta har izuwa k’afafunta..!” Jamal yai wata murmushi na mugunta yana tsaye gaban Muhibbar yake fad’in “Kinga wannan alluran, Ina miki ita shikenan gab’ob’inki Sun tashi a aiki...! Ban tab’a yiwa kowa irin wannan alluran ba a kanki zanyi lunching d’inta..! Allura ce wacce idan na miki ita shikenan kin koma saidai kallo da idanu, babu wani joint na jikinki da zai kuma motsawa, komai saidai ai miki.. Idan har kika sake allurar nan ta huda jikinki shikenan you’ll be paralyzed for the rest of your life...! So I’ll still ask you nicely... Who are you..?! Wacece Ke...?! Wane ganganci ne ya shigo dake cikin Masarautar nan..?!” Dukda tsananin tsoron abinda ka iya zuwa yazo gameda ita hakan bai hanata murmusawa ba tana mai furta “I’d definitely tell you who I’m Dark Prince..! Mai kake ci na baka na zuba..!? But before then, kafin na sanar dakai ko ni wacece sai na tabbata rayukan da suke cikin had’ari a Masarautar nan sun kub’uta... Ka fahimta..!” Jamal bai daina huci ba yake dubanta da tsananin mamaki, rashin tsoronta sosai ya basa mamaki tana a matsayin mace, kodashike abinda tayi ko mazan ma ba kowa ne zai iya kasadan da tayi ba, ta tsallaka ta shigo Masarautar ta kuma shiga jikin ahalin Masarautar ba tareda sun fahimci motive d’inta ba... Hannu ya d’aga zai kwad’a mata mari sai kuma ya dakata yana murmushi, lokaci guda yace “Kafin ki zuk’i ruwan allurar nan ya kamata a soma cire wasu parts na jikinki dan idan kinyi paralyze abin bazai maki wani ciwo ba, gwara kinaji kina gani da lafiyarki a soma rabaki da wasu sassa na jikinki, zan kuma fara da bakin ki, I’ll cut off your tongue sai muga da bakin da zakiyi tsaurin ido...!” Ya k’arashe yana ciro wasu k’araffa cikin akwatin nasa... Giwa ta katsesa da fad’in “Ai idan ka yanke harshenta bazamuji mai ya kawota ba, ka dai soma da wasu sassa na jikinta kaman yatsun hannayenta zuwa k’afafunta, na tabbata idan taji zogi da azaba zata yi magana..!” Jamal ya jinjina kai yace “Zan iya farawa da murafen kunnuwanta Ta yanda zataji abinda zamu sanar da ita da kyau...!” Ya k’arashe yana ciro wasu k’araffan... Zuciyar Muhibbah bata daina tsinkewa ba ganin da gaske wannan mugun yanka sassan jikinta yakeda niyya... Allah kawai take ambato had’ida kauda fuskarta gefe, ta tamke idanunta sosai zuciyarta naci gaba da tsananin bugu tana jira taji ya kama marfin kunnenta guda kaman yanda yace.... Kaman daga sama wayar salulansa ta soma ringing.. Aje k’araffan yayi ya soma k’ok’arin lalumo wayarsa cikin aljihun wandonsa, number ce mai kiran nasa, yana d’agawa aka sanar dashi halinda Yazeed da kuma ahalinsa Ke ciki a asibiti...! Zuciyar Jamal ya tsinke, ya d’ago yana duban Giwa... Ganin irin duban da yake mata ya sanyata maida hankalinta kacaukam garesa tana tambayarsa meke faruwa... Hankali tashe Jamal Ke sanar da ita abinda aka sanar dashi a wayar... Take jikin Giwa ya d’auki rawa, cikin yanayi na tashin hankali take furta “Yazeed..! Yazeed.. Yazeed d’ah nah, zanje na gansa yanzun nan... Ina son ganinsa...!” Bata kuma tsayawa bi takan kowa ba Ta nufi k’ofa hankali tashe... Tuni Jakadiya ta take mata baya, Shiko Jamal duban Muhibbah yayi yace “Allah ya ceceki for now, amma ki sani ina nan dawowa, sai kin d’and’ani azabata..! No one messes with me...!!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice yana cangwala sandarsa... Muhibbah da hawaye Ke zubo mata sauk’e ajiyan zuciya tayi wasu hawayen na muma kwaranyo mata, ta soma jijjiga kujeran ko Allah zaisa cuffs d’in su b’alle.. Inaa ko gizau batayi, wasu hawaye masu d’umi suka kuma zubo mata... Toh kenan basu ne suka ajeta wancan d’akin ba... Kenan babu saka hannunsu a dawowarta Masarautar..! Toh waye ya dawo da ita idan har ba Giwa bace ba kuma d’aya daga cikin azzaluman yaranta bane..?! Tambayar da zuciyarta tai mata... Toh amma taga Yarima Mahmood a wannan d’akin da aka ajeta..! Toh mai ya kaisa d’akin..? Kodai shine ya satota..? Toh amma mai zaisa ya sato ta ya dawo da ita cikin Masarautar ranan aurenta idan dai har baiyi tarayya dasu Giwa wajen yunk’urin cutar da ita ba... Shin waye zai iya warware mata k’ullin dake cikin kwanyarta..?! Ta kuma lumshe idanunta a hankali wasu hawayen suka gangaro mata, tasan duk yanda akayi Mommy da Ansar suna can suna nemanta, ta sani hankulansu ba’a kwance yake ba kaman yanda nata ma bai kwance... Allah taci gaba da ambato domin ya kawo mata d’aukin halinda Ta tsinci kanta ciki.... ** D’aki Jamal ya dawo domin shiryawa dan shima dole ya nufi asibiti yaga halinda Yazeed Ke ciki...! Sauri sauri ya kwab’e k’anan kayan dake jikinsa ya zira jampa, Umaima da tun shigowarsa idanunta biyu kikimau ta kumayi tamkar har lokacin bata farfad’o ba.... Tana jin sanda ya ida shirinsa ya k’araso gareta ya manna mata peck a goshi yana mai furta “I’ll be right back my love...! Zan dawo na d’aukeki muyi nesa da wannan Masarautar... Na tanadar mana rayuwa mai kyau sweetheart... You just need to trust me Umaima, zan baki rayuwar data dace dake..! I Wait for me kinji love..!” Ya k’arashe yana mai gyara mata kwanciyarta dukda cewa d’aure take da jikin gado...! Jamal na ficewa wasu irin hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata, Ta bud’e idanunta da sukai matuk’ar mata nauyi tana k’arema d’akin kallo... Wani irin d’auri yayi mata hannu da k’afafu yanda zai matuk’ar wahala tai escape...! Take ta kuma fashewa da wani irin kuka wanda bata San na menene ba, na kasancewar wannan azzalumin mutumin a matsayin mijinta ne ko kuwa na tausayin halinda ta tsinci kanta ciki ne..! Maiyasa bata saurari Muhibbah ba tin daga farko k’ila da yanzu daga ita har Muhibbar Sun kub’uta, gashi bata San duniyar da yakai Muhibbah ba, koma tana raye ko ya kasheta sai Allah..! Ta kuma rintse idanunta wasu hawayen masu matuk’ar zafi suka gangaro mata... Tana tsaka da kukan ta hangi wani abu Can k’asa saman rug, kaman waya kaman kwali.. Saidai bazama Ta iya mik’ewa ba balle ta isa ga abun... Ta shiga k’ok’arin janye jikinta tana yunk’urin d’aga kanta, nan Ta hangi tabbas waya ce.. K’ila k’aramar wayar Jamal d’in ce ta fad’i garin sauri da yake don shiryawa...! Ta shiga k’ok’arin jijjiga hannayenta da k’afafunta ko Allah zai bata sa’an kwance d’aurin... Inaa ko motsawa batayi, gadai waya tana hangowa nan k’asa kusan k’afarta amma bazata iya janyowa ba sabida d’aurin da aka mata.. Ta kuma rintse idanunta hawaye naci gaba da gangaro mata... ** Tashin hankali maras misaltuwa Giwa ta tsinci kanta ciki sanda taga halinda Yazeed yake ciki, da gaske dai Yazeed d’in dataci masa burin zama Sarki shine kwance saman gado babu hannaye... Yazeed ya rasa hannayensa ya kuma rasa ‘ya’yensa duk a sabida bak’in zuciya irin nasa... Wannan rayuwa da mai yayi kama, abin bazai kuma masa ciwo ba har sai randa ya bud’e idanu ya gansa a halinda yake ciki kuma shine yayi silan faruwan komai, shine yayi silan rasa hannayensa da mutuwar yaransa gaba d’aya... Lallai tashin hankali na gaba gareshi... Jamal ma sosai hankalinsa ya tashi da ganin halinda Yazeed ya tsinci kansa ciki, dukda ya rasa k’afarsa gani yake nasa mai sauk’i ne tinda gashi har za’ai masa wata k’afar, shi kuwa Yazeed babu hali ayi masa hannaye haka zai k’arashe rayuwarsa babu hannaye bazai iya yiwa kansa komai ba saidai ayi masa dukda kuwa pride da jin kai da isa irin nasa... Cikin tashin hankali Giwa ta isaga Mahmood da tin shigowarsu asibitin kallon kirki bai shiga takaninsu ba saima kai komo da yake da likitoci suna updating nasa halinda Matar Yazeed da Handimarta Ke ciki... Ga dukkan alamu Hadimar nata itama Allah ya amshi rayuwarta amma matar Yazeed ta rayu, anyi gwaje gwaje akanta kuma babu wani internal injury data samu saidai wad’anda idanu ka iya gani, babu wani fracture data samu saiko buguwar k’ashi, a halin da ake ciki Zuhra tana d’akin hutu tana ci gaba da samun kulawa dan har kawo zuwa lokacin bata farfad’o ba bayan gwaje gwaje da akai mata... Likita da Mahmood suka gama tattaunawa, Mahmood ya saka hannu a takardan amsan gawawwakin ya kuma yin sallama da likita...! Tinda Giwa taga Mahmood bai ko bi takanta ba tasha jinin jikinta tasan duk yanda akayi wani babban al’amarin ya faru... Dakatar da Jakadiya tai kana tabi bayan Mahmood d’in kafin ya b’acewa ganinta, can daidai wani lobby yanda babu mutane Giwa ta cimmasa, sunansa ta kira amma bai tsaya ba saima ci gaba da tafiya da yake... Ta d’an kuma d’aga k’afa tana mai furta “Sadauki ka saurareni..!” Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba zuciyarsa naci gaba da tsananin zogi, Allah ya gani dukda ta kasance mahaifiyarsa ko fuskrta bai k’aunar gani... Giwa ta k’araso tana furta “Haba Sadauki..! Ya ina maka magana kana kuma tafiya.. Sadauki ba kai kad’ai bane halinda Yazeed da ahalinsa suka tsinci kansu ciki ya d’aga ma hankali, dukkanmu nan hankalinmu a tashe yake.. Kai d’aukacin masarauta hankali a tashe yake...! Ni fah mahaifiyarsa ce har kana tunanin zaka fini shiga damuwa Mahmood..?! Mahmood anya babu wani abinda ke damunka d’ah na.. Ka sanar dani.. Haba Mai Martaba Sarki mai jiran gado..!” Ta k’arashe cikin kwantar da murya... Juyowar da zai, yanda Giwa taga k’wayar idanunsa da yanayin fuskarsa ba k’aramin firgitata yayi ba, yau d’in sai ya koma mata tamkar AbdulJabbar ranan da asirinta ya tonu a idanunsa, domin kuwa wani kamanni ne na musamman ya kuma fitowa tsakaninsa da Mahaifin nasa... Cikin kakkausar murya Mahmood ke furta “Sarki..! Sarki..! Mai za’ayi da Sarautar da aka gina kan zalunci...? Mai za’ayi da sarautar da akaci zarafin wad’anda basuda hakki dan a tabbatar da samuwar wannan sarautar..! Ki fad’a min Maami mai za’ayi da irin wannan sarautar..?!” Ba Giwa dake rarraba idanu gabansa ba harta Jamal dake daga can bayan Giwan saida yasha jinin jikinsa ya tsaya cak ya kasa ci gaba da dogara sandarsa..! Zuciyar Giwa na bugu take furta “Sadauki ban fahimceka ba... Mai kake nufi...?!” Sosai ya kaikaito wannan karon yana dubanta, jijiyoyin jikinsa na kuma mik’ewa yake furta “Ina nufin babu abinda zanyi da sarautar da kika nemawa ahalinki ta hanyar Malamai ‘yan tsubbu mushurikai masu kaikuga halak’a...! Maami how could you..! How could you do something like this..? How could you turn your children into criminals..!!” Cikin rawar murya Giwa Ke furta “Mahmood ban fahimce ka ba... Mai kake nufi..?!” Girgiza kansa kurum yake cikeda tsananin takaici, lokaci guda yake ci gaba da furta “Fu’ad told me everything... Abubwan da suka faru fourteen years back, Fu’ad ya sanar dani how you ruined our family and destroyed the life of an innocent child....! Shin Maami ina zaki kai girman zunubin da kika d’auka, kin saka yaranki sun lalata rayuwar k’aramar yarinya akan son zuciya... Kin maida yaranki ‘yan ta’adda..! Fyad’e fyad’e Maami..! Shin wace uwa ce zatai jagoranci ma yaranta su aikata mummunan laifi irin wannan... Wace irin uwace zata aikata haka Maami, Fu’ad was only a kid then amma da k’arfi saida kukasa ya aikata laifin... Ki fad’a min ina zaki kai girman zunubin nan..?!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irin na wanda ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci... Giwa na girgiza kai take furta “Mahmood Fu’ad mahaukaci ne mai yasa zaka yarda dashi...! Ko a kotu ne mahaukaci baya bada shaida..! K’wayarsa ce ta sanar dashi hakan shiyasa ya sanar dakai duk wannan k’arerayi marassa asali balle tushe..! Yanzu kai a naka tunanin zan aikata laifi makamancin wannan..? Haba Mahmood ya kake abu kaman ba Babba ba..!” Katseta yayi da fad’in “I tried not to believe him amma zuciyata ta k’i aminta da hakan...! Na yarda Fu’ad ya fad’i gaskiya sabida bayan duka wannan shekarun bai mance komai ba..!” Sai sannan Jamal ya k’araso yana fad’in “Yaya Fu’ad was lying to you... How can you believe a psychopath like him..!” Cikin tsananin huci Mahmood ya katsesa da fad’in “Shut up..! Rufe min baki...!! That’s because kun tilasta masa yin hauka.. You and our mother tormented Fu’ad.. Ya sanar dani yanda kayita drugging d’insa kana injecting d’insa dan kawai ku mantar dashi komai ku hanasa magana.. You’re the real psychopath here Jamal... Na zaci gaba d’aya cikinku ka fisu hankali, kullum ina maka zato mai kyau dan kafi Yazeed hankali a fuska Ta d’abi’a ashe ba haka bane, you’re the worse..! Ta yaya zaka halak’a kwanyar d’an uwanka da strong drugs, Kai kayi introducing k’wayoyi masu gusar da tunani ma Fu’ad tun yana k’arami baisan illan abunba... kawai dan ku hanasa fad’in laifin da kukayi tarayya wajen aikatawa... How could you do this to your own brother...! I can’t believe this, I can’t believe my on family can be this heartless..!!” Kan Jamal na k’asa yawa mutumin arziki yake furta “Yaya wllhi Fu’ad cikin haukarsa ya sanar dakai haka, duk abubuwan da ya sanar dakai none of them is true..!” “Nace kamin shiru kafin na k’araso wajen na k’arasa karya d’aya k’afar taka mutumin banza kawai...!” Giwa na k’wak’ulo kukan k’arya take kuma k’aryata zancen... Girgiza kai kurum Mahmood yake kana yai saurin sa kai ya fice daga asibitin dan idan yaci gaba da tsayuwa wajen zai iya mance ita d’in mahaifiyarsa ce wanda baya fata a isa peak d’in.... ** K’AUYEN GALAMBI Jafar da Ubandoma zaune daga can wani b’angare na tsakar gidan sun kunna k’irare suna shan d’umi dashike tsakar gidan akwai yalwan fili... Ko wannen su rik’eda gasasshiyar masara suna ci suna shan d’umin wutan dan anyi ruwa garin ya d’auki sanyi sosai, Ubandoma na kuma labartawa Ja’afar abubuwan da sukaita faruwa cikin Masarautar a lokacinda yake rufe...! Jafar sai faman murza masaran dake hannunsa yake yana hango k’uran da zai tashi idan ya saka k’afarsa cikin Masarautar... Dan yayi imani koda ace shi bawa ne duk wanda suka cuzgunawa rayuwarsa cikin Masarautar sai sun biya abinda suka masa... Ko zafin k’una hannunsa da masarar keyi bayaji sai kuma mutsuk’ata yake cikin tafin hannunsa.. Hasken Farin wata ya haske kyakkyawar fuskarsa wanda a ‘yan kwanakin da sukayi wannan K’AUYEN har ya sauya kamaninnsa na asali ya kuma bayyana... Gaban Ubandoma ya yanke ya fad’i domin kuwa harta zaman da Ja’afar yayi irinta masu mulki ne... Kardai jinin Saraki ne Giwa ta basa ya canza da d’an Bawa...! Idan kuwa hakan ne baijin Jafar zai yafe masa musamman da yaga irin tanadin da Jafarun yayiwa wad’anda suka zaluncesa randa duk ya saka k’afarsa cikin Masarautar... Bai ida tunanin ba suka sinkayo muryar Tabawa matar Baba Nomau ta fito tana furta “Malam..! Malam kazo kaga abin mamaki...!” Jafar da Ubandoma suka dubi juna, cikin sauri suka mik’e suka nufi yanda Mama Tabawa ke kira... A tare suka saka kai k’asan rumfar yanda Mama Tabawa Ke haske Mahaukaciya Izzatu sai aman bak’ak’en zaren masu kama da saiwar itaciya take... Ga wasu dogayen bak’ak’en allurai masu kamanni da k’ayar beguwa tana amo dasu... Baba Nomau da k’arasowarsa kenan hamdala ya soma yana furta “Allah ya amshi addu’armu gashi nan ta fitar da mugun k’ullin tun kafin kwanaki uku su cika... Alhamdulillahi Allah abin godiya..!” Yana ida fad’in haka ya zauna daga can gefe saman tabarmarsa ta azara.. Ya dubi Ubandoma da Jafaru yace suma su zauna...! Babu musu sukayi yanda Baba Nomau yace.... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *70* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tambayoyi Baba Nomau yake jero mata daki daki tana amsawa “Zaki iya tuna wacece ke, daga wace nahiyar kike..? Kuma yaya akayi kika k’are a halinda kika tsinci kanki ciki...?!” Ta d’ago ta dubesu d’aya bayan d’aya kana ta jinjina kai a hankali, cikin tsananin sanyin murya Ta furta “Sunana Turai, ni d’iya ce ga Sarkin Benin Jamaluddeen...!” Ta d’anyi fasali sai kuma taci gaba da fad’in “Allah shi ya k’addari kasancewata a yanayin da na tsinci kaina ciki domin kuwa Bawa bai shige k’addararsa...!” Baba Nomau ya murmusa a hankali yana mai jinjina kai yake furta “Wannan haka ne..!” Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Amma Amintattar Hadimata wacce na aminta da ita ta zamto tamkar ‘yar uwa a gareni itace tayi sanadiyan halinda na tsinci kaina ciki..! Sabida tsananin amintaka dake tsakaninmu a wancan lokacin wasu har cewa suke muna da kamanni, kasancewar ban zab’i Hadimata ba saida na darje na zab’o mai kyau cikin Hadimaina wacce muke kusan tsara a shekare, dan tun ina yarinya ‘yar kimanin shekaru takwas na zab’o Izzatu matsayina wacce zata zamto amintattar Hadimata, harta abinci da wasanni tare mukeyi da ita koda kuwa sauran ‘yan uwanta Bayi basa k’aunar suga hakan... Saidai ni sam bai dameni ba dan tuni Allah ya jefa k’aunar junanmu cikin zukatanmu, wasu lokutan haka zan tashi daga bacci naga Izzatu rik’eda mahuci tana min fififta, sai nace mata Ta hawo gadon itama ta kwanta, tun tana tsoro har Ta daina tsoro, dai dai da ‘yar tsanata tare muke wasa da... Tayita d’aukan ‘yar tsanar tana mata kitso, wasu lokutan har tambayata take ta saka tufafi na, ni kuwa nakan ce mata duk wani abuna nata ne, kada ta damu...! Da murnanta takan saka tufafin tayita kallon kanta jikin madubi... Wata rana ne data saka tufafun ta fito dasu jikinta bayi ‘yan uwanta sukayi mata chaa har horo saida akayi mata... Tayita kuka har ta d’an ja jiki dani... Abinka da yarinta sai nace da ita ta kwantar da hankalinta itama wata ran zata zamto mai mulki idan ma tana so ni zan bata nawa mulkin mu raba...Wannan kalman da na Fad’i ashe Izzatu tana rik’edashi har zuwa girma cewa itama zata zamto mai Mulki zamu raba nawa sarautar mu biyu....Tai shiru hawaye na gangaro mata... Baba Nomau ya nusa yace “Zaki iya tuna ko mai tayi miki...?!” Ta d’ago ta d’an kuma dubansu kana Ta jinjina kai tace “K’warai zan iya tunawa..!” Take ta shiga jero masu bayanin yanda Giwa ta amshe mata mijinta da kuma sarautar Ta ta maida ita Baiwa a gidan aurenta...! Ja’afar ya kasa motsawa sai duban matar yake da tsananin mamaki, ya kasa aminta abubuwan da yaji gaskiya ne Wai Giwa Baiwa ce ba Basarakiya ba, ya kasa aminta da abubuwan da yake ji na fitowa daga bakin matar nan...! Gimbiya Turai taci gaba da basu labari “Tin daga lokacin da Izzatu ta jefeni da muguwar asirinta na zamto banida ta cewa sai abinda tace... Bokanta ya sanar asirinta zai tasiri akaina na d’an wane lokaci, bayan wanann lokacin asirin zai karye sabida tun lokacin da aka haifeni an dafani da magunguna na bada kariya, kunsan gidajen Sarauta sun yarda da neman tsari kuma ko wanne gidan Sarauta da nasu al’adar, musamman zamanin da da ilimi bai yawaita ba, hakan yasa sam hankalin Izzatu bai kwanta ba dukda cewa banida Ta cewa a wajen kowa sai abinda ta min umarni, daidai da sunanan na asali banida iko akansa dan tuni Ta mana musayen sunaye, na kuma yi na’am da abinda tace, na soma amsa sunan Izzatu tin daga wannan lokacin, ita kuwa ta koma amsa sunan Gimbiya Turai ta k’asar Benin....” “Kaman yanda Izzatu ta buk’ata kan cewa mijinmu bayan ya ‘yantani daga bauta ya aureni ya maidani matarsa bayan ta kyautar dani garesa matsayin tukuici, Toh sai aka barni a wancan garin yanda muka soma zama nidashi, sam Izzatu bata bari an kaini cikin Masarauta ba koda da rana guda ne...! Ina zaune a wannan gari matsayin Matar sarki kuyangarsa wacce ya ‘yanta ya kuma aura... Tunda Sarki yasa k’afa ya koma masarauta ban kuma saka shi a idanu na ba, Ina zaune a wannan garin ina zaman jiran tsammani daga ni sai Hadimata mai suna Fattu saiko mijinta mai suna Giro, suna zaune ne a wani b’angare na cikin gidan dan kula dani kaman yanda Mai Martaba yai masu umarni ya kuma ajesu a kusana..Toh muna zaune a wannan k’aramar k’auye ga laulayi da ya addabeni, dan tinda Sarki ya tafi ban kuma yin lafiya ba...! Kwatsam wata rana ina tsaka da amai saiga Izzatu tazo ta wannan gidan ba tareda rakiyar kowa ba, dan ko Hadimanta bata taho dasu ba, ta razana sosai da ganin halinda nake ciki... Tin daga nesa ta tsaya ta zuba min idanu tana duban yanda nake durk’ushe tsakar gidan shek’a amai.. Ta k’araso Ta dafa kafad’ata tace “Ke Izzatu mai zan gani, amai..! Ciki..!” Ta shiga zaro idanunta waje tana dubana.. Duk’awa tayi gefena tace “toh kina jina koda wasa kada ki tura sak’o wa mai Martaba cewa kina d’aukeda juna biyu, kinji abinda na fad’a miki...!!” Cikin sauri na shiga jinjina kai dan idan baku mance ba na sanar daku cewa Asirin da Izzatu tamin shine duk abinda ta bani umarni na amsa mata nai mata biyayya irin yanda bawa yakema Ubangidansa, ko kusa bana mata musu... Ta murmusa tace dani na mik’e tsaye..! Babu musu nayi yanda tace..! Ta d’aga tufafina tana duban shafeffen cikina wanda babu wani alamu, sai gani nayi tana murmushi... Wani bak’in Dutse ta manna min a saman cikin... Naji wane irin zogi ya ratsa cikin jikina tinda ta manna min wannan bak’in dutsin..! Koda ta manna min tsugunawa nayi wajen Ina rik’e marana dake tsananin min zogi... Take naga ta juya ta bani baya wani mummunan halitta ya bayyana gefenta sanye da bak’ak’en tufafi, dariya ya kece dashi yace “Wannan juna biyu bazai fice ba sai an haifosa duniya... Kuma shine zai zamto d’ah na farko ga Sarki AbdulJabbar...!” Giwa ta shiga girgiza kai tana fad’in “Bazai yuwu ba..! Wanann k’ask’antacciyar baiwar bazata rigani baiwa mijina Magaji ba domin kuwa ni ce nan zan kafa Mulki na a wannan Masarautar, kowa sai ya zamto yana k’ark’ashin iko na...Menene abinyi..?!” Daga nan ban kuma jin tattaunawarsu da matsafin mutumin data shigo tareda shi ba nidai na kwanta nan wajen ina rik’e marata dake tsananin murd’a min Ina neman agaji... Can da jimawa Fattu tazo ta taddani, cikin rawar jiki take fad’in “Rankidad’e..! Lafiya kike..?! Rankidad’e ko na kira Giro ne ya nemo amalanke mu fitar dake gari mu kaiki asibiti...?!” Girgiza mata kai nayi nace “Fattu ba sai kun fitar dani ba ki bani ruwa nasha k’ishin ruwa nakeji..!” Cikin sauri Fattu ta kawo min ruwa nasha..! Na lumshe idanuna ta taimaka min na kwanta bisa tabarmar sak’a dake gefe.. Fattu tayi jigum tana dubana cikeda tausayawa, lokaci guda ta kuma fad’in “Rankidad’e kodai Giro yayi tattaki ya tafi Masarauta ne ya sanar da Amale halinda kike ciki..?!” Cikin sauri na d’ago sabida tsananin tsoron abinda ka iya zuwa yazo tinda Izzatu ta haneni nace da Fattu koda wasa, ko ita ko mijinta kar sukai wannan batu wa Amale..! Fattu dai ba dan taso ba sai dan babu yanda ta iya ta amince da batu na..! Muna nan a haka wasu lokutan haka zanyita ganin abubuwa na ban tsoro suna kawo min ziyara, a haka cikina yaketa girma har zuwa ranan da zan haihu... Wani ikon Allah ranan haihuwata Fattu bata gidan, ko ita ko Giro Babu kowa amma saiga Izzatu tafe da zungureren ciki tareda wannan mutumi matsafin, Izzatu ita ta amshi hauhuwata dukda zungureren cikin dake jikinta... Inajin kukan jariri sanda ya fito daga jikina.. Amma daga haka ban kuma sanin mai ya faru ba ban kuma farkawa ba sai a gadon asibiti a nan cikin k’auyen dan dajin da gidan yake yana da d’an nisa da gari... Na tashi ina tambayar Ina jariri na Malam asibiti sukace haka aka kawo masu ni rai hannun Allah, Allah ne ma yayi taimako an iso dani asibiti da wuri da tuni jinin jikina ya k’are.. Fattu ta tusani gaba cikeda tausayawa tana tambayar Rankidad’e ina jaririn ya akayi hakan ta kasance mai ya faru..?!” Kuka kurum nake ban Iya ceda Fattu komai ba dan na tuna duk abinda ya faru, na tuna cewa Izzatu Itace ta amshi haihuwata...! Fattu tace Giro zai tafi Masarauta yaje ya sanar da mai Martaba..! Kuka sosai na dingayi Ina rok’on Fattu idan tana ma Allah ko Giro kada ta sanar dashi wannan al’amari..! Na tambayi Fattu ya akayi Ta kawoni asibiti..? Fattu ta sanar dani tana can gona itada Giro ta dawo gida kai masa abinci nan Ta taddani a halinda nake ciki, tayi gaggawan fitowa gari ta sami masu amalanke suka taimaka suka kawoni asibiti...!” Gimbiya Turai ta lumshe idanunta wasu hawayen suka kuma zubo mata... Daidai da Jafar da Ubandoma suma hawayen ne suka zubo masu, harta Mama Tabawa itama hawayen take da jin irin wannan al’amari.... Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Muka rufe wannan batu nida Fattu babu wanda yaji tinda dama Sarki baisan da labarin juna biyun ba, bayan wani lokaci mai tsawo Mai Martaba ya waiwayeni, baida labarin ya barni da ciki har na haihu kuma har na rasa abinda na haifa...Ashe a wannan lokacin juna biyun da Izzatu kedashi shine ya janye hankalinsa har ya mance da ni ya bada hankalinsa kacaukam akan Izzatu da cikinta...Bansan ya akayi ya kuma waiwayoni ba, nadaiga yana zuwa wajena akai akai, dukda babu wani Sabo a tsakaninmu yakan bani labarin d’ansa mai suna Mahmood wanda matarsa Basarakiya ta haifa masa... Saidai nayi murmushi amma bana iya cewa komai... Bayan wasu shekarun yaci gaba da ziyartata, amma ban sake koda b’atan wata bane sannan da alama Izzatu ma bata kuma haihuwa ba tin d’anta mai suna Mahmood da yace ta haifa masa, ya kasance Mahmood shine kad’ai dan Sarki AbdulJabbar wanda ya d’auki son duniya ya d’aura masa, a nan a haka kwatsam ya sanar dani matarsa ta haihuwa ta kuma haifa masa wani d’ah ya saka masa suna Yazeed, Yazeed ya taso ya fara wayo shima, saidai har lokacin magana Mai Martaba bai wuce Mahmood, da matuk’ar wahala kaji ya ambato k’aramin d’ansa mai suna Yazeed, nikam har na mance da haihuwa domin kuwa shekarun da d’an yawa tun bayan dana rasa abinda na haifa daga farko, a tsakanin wannan lokacin nima kwatsam sai na soma laulayi... A lokacin da yazo min da labarin Gimbiya ta haifa masa d’ah namiji ya kuma saka masa sunan mahaifinta Sarki Jamal a lokacin ashe nima inada ciki k’arami ba tareda na sani ba... Naci kuka sosai jin Izzatu ta kuma haihuwa an sakawa yaron sunan mahaifina Sarki Jamaluddeen saidai banida ikon fad’iwa Sarki AbdulJabbar komai... A ‘yan kwanakin da Mai Martaba yayi wajena nan ya fahimci nima ina d’aukeda juna... Toh sai yayi dogon zango wajena bai koma masarauta ba, ashe hankalin Izzatu ya tashi matuk’a ganin Sarki bai waiwayeta ba dukda sabon jariri da take dashi, koda Mai Martaba ya koma sai ya sanar da ita juna biyu gareni da alama Allah ya amshi addu’arsa gashi bayan duk tsawon shekarun nan Izzatu ma zata haifo masa Magaji Wato Izzatu ni kenan kaman yanda ya sanni... Giwa Ta shiga damuwa ashe ciki ne dani kuma har ya fito sam bata kawo zan kuma haihuwa da Sarki ba dan rata ne sosai tsakani tinda da ace jaririn dana rasa yana raye da ya kusa isa munzanin k’aramin matashi, lokacin jaririnta yayi k’wari sosai dan yakai watanni kusan takwas, ta barsa wajen masu kula dashi tazo ta ga halinda nake ciki, saidai wanann zuwan da zatayi batazo da rakiya matsafinta ba, ga dai ciki jikina har ya fito babu halin ta salwantar da cikin tinda Mai Martaba ya sani... Sosai na hango tashin hankali tattareda ita, ta tanbayeni komai gameda cikin, babu abinda na b’oye mata harta asibiti da Mai Martaba ya kaini da kansa saida na sanar da ita, ta dinga sakin huci jin irin kulawa na musamman da Sarki Ke bani sabida cikin... Ta tambayeni yaushe akace zan haihu a asibiti..? Babu musu nan ma na sanar da ita...! Duk wannnan abinda ake Hadimata na tsaye bayan k’ofa rik’eda yarinyarta mai suna Aliya ‘yar shekaru uku a duniya, dan lokacin Hadimata Fattu Allah ya azurtasu d samun yarinya d’iya mace kuma har Ta shekaru hud’u a duniya...!” Ubandoma da gumi Ke ci gaba da tsartsafo masa yace “Fattu da d’iyarta, Dama Fattu Hadimarki ce..?!” Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “Fattu Hadimata ce wacce Mai Martaba ya ijeta da mjinta matsayin masu kula dani...!” Gimbiya Turai ta nusa taci gaba da fad’in “Fattu taga duk abinda ya faru kan idanunta yanda Izzatu ta tasani gaba da tambayoyi kuma ban b’oye mata komai ba na sanar da ita... Hankalin Fattu sosai ya tashi daga nan yanda take lab’e... Kukan yarinyarta shine ya janyo hankalin Izzatu ta dubeni tace wacece wannan..? Nace da ita Hadimata ce mai Martaba ya bani...! Giwa ko ince Izzatu ta tsare Fattu da d’iyarta Aliya da idanu... Bata masu dai komai a wannan lokacin ba saidai Ta gargad’eni cewa kada Mai Martaba yasan ta kawo min ziyara..! Na jinjina mata kai nace bazai sani ba... Toh ko bayan data tafi Fattu taso mu sanar da Mai Martaba cewa matarsa ta kawo min ziyara amma na gargad’i Fattu nace da ita kada ta sanar da mai Martaba ko mijinta ma kada ta sanar dashi.. Abin sosai ya dami Fattu dan haka nan kawai bata aminta da ziyaran da Giwar Amale ta kawo min ba na bazata... Toh a haka Mai Martaba yakan kawo min ziyara har dai lokacin haihuwata yazo, a lokacin haihuwata banga Mai Martaba ba, baizo ba saidai kwatsam naga Izzatu tace min Mai Martaba ya turota ta amshi haihuwata... Ta bani wani ruwan magani tace nasha shine zai d’aga min nak’uda..! Babu musu na amsa ruwan maganin na shanye kaman yanda Ta umarceni, ai kuwa Ina shan ruwan nan nak’uda ya tashi gadan gadan, na haihu ban haihu ba ban sani ba, tin daga wannan lokacin ban kuma sanin wacce duniya nake ba sabida tsananin azaba, bani a cikin hayyaci na, farkawa kawai nayi na ganni gefen Fattu dake kuka rungume da jariri... Cikin d’imauta naceda Fattu ina jaririna..! Fattu na hawaye ta mik’o min shi tace dani jaririna baizo da rai ba...! Naci kuka sosai, na rungume gawan jaririna ina hawaye.... Giro da wasu mutanen gari su sukaima jaririna sutura aka rufesa... Bayan faruwan wannan al’amari da kad’an Mai Martaba yazo ya tadda na haihu yaro baizo da rai ba... Sosai shima ya shiga damuwan rasa jaririn da mukai... Ashe abinda ya hanasa zuwa ya kwanta jinya ne na d’an wani lokaci wanda har bai fita koda Fadarsa ne, yana warkewa kuwa ya taho gareni dan duba halinda nida Jaririna muke ciki...! Tin daga bayan wannan lokaci ban kuma samun haihuwa ba, tun bayan rasa jaririna da nayi...!” Muryar Ubandoma suka sinkaya yana fad’in “Ki yafeni Rankidad’e..! Kimin aikin gafara Ranki dad’e..!!” Cikin kuka yana mai zubewa saman gwiwoyinsa yake furta wad’annan kalamai... Gaba d’aya kallonsu ya koma kan Ubandoma dake duk’e gaban Gimbiya Turai yana kuka yana neman gafara....! Baba Nomau ne ya dafa Ubandoma yace “Kar ka katseta ka dakata ta ida sanar damu dukkan abinda ya faru gudun kada mu fad’a wani labarin..!” Ubandoma ya jinjina kai har lokacin yana duk’e yana hawaye... Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Bayan kaman shekaru biyar da faruwan wannan al’amari wasu fatake suka tsaya a garinmu suka nemi a taimaka masu da ruwan sha a nan gidan da aka ajeni...! Sun razana sosai sanda sukayi tozali dani a cikin gidan... D’aya daga cikin rundunar fataken ta saki Kwanun shan da aka kawo mata ruwa ciki ya zube sabida tsananin tsorata da tai da ganina... Cikin rawar murya ta ambato sunana “Gimbiya Turai..!” A razana nake sanar dasu bani bace...! Nayi saurin guduwa d’aki ina kuka... Fattu Ta bisu da kallon mamaki tana kuma mamakin jin sun ambaceni da Gimbiya Turai... Fattu ta k’arasa garesu tace “Bayin Allah ko akwai wani abu ne..?!” Matar data ambaceni da Gimbiya Turai tace “Mu Fatake ne daga can Nahiyar Benin, wannan matar data gudu d’aki d’iyar Sarkin k’asarmu ne wanda bayan aurenta da kad’an mahaifinta Sarki ya mutu, dangin dangau sukai qaqa gida suka haye gadon mulkin mahaifinta sabida d’an uwa d’aya tak gareta, kuma a lokacin da Sarki mahaifinta ya rasu d’anuwanta yana k’arami bazai iya yak’in neman mulki ma kansa ba, dangin mahaifiyarsa suka d’aukesa sukai nesa dashi, kwanakin baya ya dawo k’asar Benin yana tambayar Sarkin wane nahiya ne ya auri ‘yar uwarsa dan a halin yanzu ya girma har ya zamto Magidanci.. Ashe ‘yaruwasa tana nan a wannan Nahiya, tabbas zamu koma masa da labari..!” Fattu dai saurarensu kawai tayi har suka gama shan ruwan da zasu sha suka d’auki hanya.... Bayan sun tafi Fattu ta shiga k’wank’wasa min k’ofa tana sanar dani Sun tafi... Na fito illahirin jikina rawa yake... Na mance inada d’an uwa sunansa Alfah...! A lokacin da wad’Annan Fataken suka ambaci Alfah sai na tuna shi, take naji ina son sanar da Mai Martaba duk abinda ya sameni, take naji kaman an sauk’e min wani dutse mai nauyi a k’irjina, tsoron sanar da Mai Martaba halinda Izzatu ta jefani ciki duk sai naji kaman an yaye min lokaci guda... Na sanar da Fattu komai duk abinda ya faru..! Fattu ta dinga aljabi tana mamakin yanda Izzatu ta canza kanta dani.. Nan naga kukan Fattu ya kasa tsagaitawa..! Na dafa Fattu nace “Fattu akwai wani abu ne..?!” Fattu na kuka take cedani “Rankidad’e tabbas na yarda matar nan zatayi duk abinda kikace domin kuwa Jaririn da kika tashi kika gani matsayin d’anki ba naki bane... Ina lab’e akan idanuna Ta canza jaririnki da gawa.. Naji tsoron yin magana ne a matsayi na na baiwa tinda banida shaidu babban magana ne da ya shafi matar Sarki wanda ban isa nayi jayayya da ita ba... Shiyasa kika tashi kika ganni rungume da hajaririn ina kuka... Rankidad’e duk yanda akayi jaririnki yana nan a raye.. Watak’ila Giwa ta b’oyesa a wani wajen... Kuma zai iya yuwuwa cikinki na fari kin haifa.. Zai iya yuwa itace ta salwantar da jaririnki na farko..!” Ubandoma dake hawaye jinjina kai yake yana furta “Tabbas inada masaniyan kan jaririnki na biyu kuma yana nan a raye..!” Yayi maganar cikin rawar murya... Gimbiya Turai ta share hawayen da suka zubo mata kana taci gaba da fad’in “Nida Fattu muka yanke shawarin idan d’iyar Fattu ta dawo daga makarantar Allo Giro ma ya dawo daga Kasuwa zamu tattara mu d’unguma mu tafi Masarauta dan mu sanar da Mai Martaba halinda ake ciki tunda yanzu Allah yayi na dawo hayyacina..! Da wannan shawari muka nufo tsakar gida dan soma shiryawa....Wani ikon Allah muna fitowa tsakar gidan muka tadda Izzatu cikin bak’ak’en tufafi Alkyabba da rufin kai, hannunta rik’eda fitila jan wuta naci a cikin fitilar, Ta kafe mu da idanu cikin yanayi na ban tsoro ga wani k’aton bak’in tulu gabanta bak’in hayak’i na fitowa daga cikin tulun....!” Jikinmu ya d’auki rawa sabida tsananin firgici da tsoron yanayin da mukaga Izzatu ciki wacce bamusan da zuwanta ba sai bayyanarta.... Murmushi ta sakar min tace “Gimbiya Turai k’araso mana, ki k’araso ga Hadimarki Izzatu kuma Aminiya a gareki...!” Tana maganar tana duban bak’in tulun dake ajiye gabanta yana fidda bak’in hayak’i... Fattu jiki na rawa yake furta “Rankidad’e kada ki k’arasa...!” Fattu batakai aya ba Ta had’iyi kalamanta sakamakon wani garin magani da Izzatu ta busa mata.. Jikina na rawa na isaga Izzatu dake tsaye gaban tulun... Ta kuma murmusawa tace “Turai lek’a cikin tukunyar nan ki gani..!” Jikina bai daina rawa ba sabida tsananin tsoro na lek’a tukunyar mai fitarda hayak’i.... Wani ikon Allah Magidancin mutumi na gani mai kamanni irinta mahaifinmu saidai baikai Mahaifina a shekare ba..!” Na d’ago a tsorace ina dubanta, murmusawa ta kumayi tace “Wannan shine d’anuwanki Alfah da ya shiga duniya nemanki...! Lek’a ki gani ya girma... Yayi aure aure har yanada iyali wanda ya aura a yawonsa Ta duniya da sunan yana nemanki...! Kar ki damu basai kin sha wahala ba ni nasan yanda yake... Fitilar tsafi ya hasko min hakan... Ta kuma tura fitilar cikin Tulun tana dariya take furta “Kinga gashi har matar tasa ta haihu, matar da ya aura a yawon nemanki... Kin gani lek’o ki gani Turai..!” Ta k’arashe tana mai kuma tura kaina cikin tukunyar yanda naga mutumin rik’eda jaririya sabuwar haihuwa..! Hawaye na zubo min nake k’ok’arin kai hannuna Ina furta “Alfah..! Alfah d’an uwana..!” Maidodani baya Izzatu tayi tana mai ci gaba da sakin wane irin dariya lokaci guda take ci gaba da furta “Wannan basu kad’ai bane ahalinsa, wad’annan a yawon nemanki ya samesu, akwai ahalinsa da ya baro ya fito yawon nemanki wanda fitilar tsafi bai hasko mana duniyar da suke ba...! Amma zamu fara da wannan ahalin nasa kafin sauran su bayyana mana...!” Tana ida fad’in haka ta danna hannunta cikin tulun wanda tuni jan wuta ya soma fitowa daga ciki... K’ara ta saki wanda take mukaga gidan da muke ciki ya soma cida wuta... Tana kuma danna hannunta wutan na kuma kama ko wani kafa na cikin gidan... Dukda azaba da take sha hakan bai hanata tura hannunta cikin tukunyar ba... Muna a haka Giro ya shigo ya tadda wanann tashin hankalin... Take muka hango wannan matsafin ya bugawa Giro wata Sanda akansa... Tinda ya buga masa sandar bai kuma koda shurawa ba, Giro ya fad’I macecce a wajen... Fattu ta yunk’ura zatayo kan mijinta matsafin mutumin ya nunata da sandar hannunsa tuni Fattu ta komada baya jikinta na wane irin rawa... Ni kuwa inaji Ina gani Izzatu ta janyoni waje ta turani cikin wani mota irin wanda ake zuba awakai, ta koma cikin gidan tana kallon yanda wutan Ke ci, Mutumi mai tuk’a motar ba kowa bane illa Wambai, Ina kuka Ina dubansa dan na ganesa shine Yayan AbdulJabbar da ya soma zuwa neman aurena a Masarautar mu kafin isowar AbdulJabbar... Ina hawaye na hango hawaye kwance shima cikin idanunsa,cikin rawar murya yake furta “Kiyi hak’uri babu yanda na iya ne, sun d’aureni ta ko ta ina... Amma ga wannan Taswiran zan baki ki adana duk daren dad’ewa shine zai toni asirin wad’annan azzalumai.... Ki b’oye wannan Taswiran cikin jikinki duk yanda za’ayi kada ki bari su gani...!” Jikina na rawa na amsa Taswiran da Wambai ya bani na tura jikin k’ullin gashina... Daga nan isowar Izzatu naji yanda Ta busa min wani garin magani.....Tin daga haka farkawa nayi na ganni a wane irin sunkurumin d’aki, da ita da matsafin mutumin nan suna tsaye gabana... Izzatu tana kan wani jan Darduma mai d’aukeda tambarin masarauta... Nan ta soma sanar dani abubuwan da suka faru “Turai ko Ince Baiwa Izzatu mai k’wacen miji daga rana mai kaman ta yau kin fita daga rayuwar AbdulJabbar, kin fita daga rayuwar mijina kuma uban ‘ya’ya na, wannan waje da kike gani shine zai zamto ma’ajiyanki, Sarki AbdulJabbar ya zaci kin mutu a cikin gobaran da ya tashi a gidanki, Wuta ya cinyeku keda Mijin Hadimarki...! Amma kar Ki damu nayi mutunci tunda Hadimarki da d’iyarta sun rayu, suna cikin Masarautar nan a nan b’angaren bayi, tinanin Hadimarki ya shafe bazata iya tuna komai ba balle ta sanar da AbdulJabbar... Sannan d’an uwanki Alfah a lokacin da na isa gareshi ya tafi ya koma ga asalin iyalansa na farko, matarsa da babbar d’iyarsa mai shekaru biyu a duniya hakan yasa ban cimmasa a wannan gidan ba, zai koma ya samu wuta ya cinye iyalansa, koda shike nayi mutunci shima, na taho da gudan jininsa ciki Masarautar nan, jaririyar da amaryarsa Ta haifa wacce ya aurota a yawon nemanki na taho da ita cikin Masarautar nan, zan goyata a matsayin d’iyar d’an uwana daga k’arshe itama zanyi sadaukarwa na k’arahe da ita daga tsatson mahaifinki Sarki Jamaluddeen wanda ni ce nan nayi sanadiyar mutuwarsa...! Ko ba dad’e ko ba jima sauran ahalin Alfah zasu bayyana mun kuma sai nayi ajalinsu suma dan babu wani dangin Jamaludden da zasu rage a doron k’asa balle wataran suyi sanadin Mulkina..!!” Ta kuma kecewa da dariya kana ta d’auko wata doguwar wuk’a tana fad’in zata cire harshena yanda bazan kuma yin magana ba... Wani ikon Allah wuk’an bai yanka harshena ba, gani nayi Ta ambato Jakadiya dake tsaye daga waje, Jakadiya ta shigo ta baiwa Jakadiya umarnin ta bud’e bakina da k’arfin gaske...! Haka sukayi tarayya itada Jakadiya suka bud’e bakina matsafin mutumin nan ya zuma min wani abinda bazan iya cewa gashi nan ba... Tin daga wannan lokacin naji harshena ya d’aure ban iya cewa komai, sannan ina fama da gushewan hankali na wasu lokuta wasu lokutan kuma nakan jini cikin hankalina, da alama asirin gushewan hankali da sukai min baiyi wani tasiri akaina ba... Na zauna cikin ukuba hannun wad’annan matsafa na tsawon shekaru dan har girma ya soma sauk’a min... Wata rana Izzatu ta shigo...!” Taja Burki ta d’aga kai tana duban Ubandoma wanda Ke duk’e gabanta yana hawaye... Hannu tasa ta share hawayen da suka zubo mata, lokaci guda taci gaba da fad’in “Izzatu ta shigo tana fad’in d’an uwana Alfah yana wanann gari kuma kusada Masarautar nan, da alama bai jadadda da batun nemana ba... A lokacin ina cikin yanayi na hankali amma sanin halin wannan muguwar mata zata iya yin komai idan Ta fahimci a hayyacina nake hakan yasa na nuna mata a lokacin ma cikin hauka nake tuburan... Tinda naji tace Alfah na garin nake neman hanyar guduwa na sami yanda zan gana da d’an uwana domin na kub’utar dashi daga sharrin wanann azzalumar mata... Wata rana na samu na gudu, wannan mutumin ya mance bai d’aureni ba dan dama shine da Jakadiya masu lura da yanda nake... Shi yake d’aureni da sark’ok’i Jakadiya tana bani abinci, sun cutar dani sun d’aureni tsawon shekaru babu ibada ga mahiccina yanda ya kamata, saidai idan Ina cikin hankali nayi ishara a zuciyara tinda haukan nawa zuwa zuwa ne...Rayuwata haka taci gaba da tafiya cikin halin ha’ula’i a wannan kurkuku... Ranan dana samu na gudu domin na nemi d’an uwana Alfah a ranan bukin wata k’aramar sallah ne...!” *MUHIBBAH* *71* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Ranan bukin hawan doki na, Washe garin sallah kenan... kasancewar hankula sun karkata zuwaga shagulgulan bukin sallah ni kuma nayi amfani da wannan damar na gudu na fice cikin Masarauta da zummar neman d’an uwana Alfah dukda sanin cewa bansan ta yanda zan soma nemansa ba balle nayi tunanin samunsa, wani ikon Allah sai na hangi Jakadiya rungume da mutum saman kafad’arta sai faman waige waige take da alama wani hidiman yasha gabanta sunma mance Sun barni a kwance kuma a bud’e... Sannan akwai duhun dare a lokacin zai wahala a ganeni...Na dinga lallab’awa ina bin bayan Jakadiya a nawa tunanin itace zata kainiga d’anuwana Alfah... Aiko cikin wane ikon Allah sai na hangeta ta isaga Izzatu ta duk’a gabanta kana ta’aje wata ‘yar matashiyar yarinyar data aza a kafad’arta, cikin yanayi na firgici take furta “Rankidad’e munje har yanda Yarinyar take rayuwa da iyayenta saidai naga abin al’ajabi...!” Cikin huci Izzatu taceda Jakadiya “Mai kika gani Jakadiya..?!” Jiki na rawa Jakadiya take nuna yarinyar dake kwance tamkar gawa kana tace “Wannan yarinyar da za’ayi asirin gadon Mulkin su Yarima da ita d’iya ce ga wannan mutumi da kika nuna mana hotonsa a tukunyar tsafi kikace duk wanda ya gansa cikin garin nan ya sanar dake..!” Izzatu ta zaro idanu waje tace “Kina nufin d’iyar Alfah ce..?!” Jakadiya ta jinjina kai tace “K’warai Rankidad’e da idanuna naga mutumin...!!” Cikin wane irin daka tsawa taceda Jakadiya “Maza ki koma ki tabbata Alfah ya mutu wannan karon daga shi har matar tasa ku k’onesu da wuta, kada ki bari ya kufce..!! Ita kuma wannan yarinyar zan mik’ata ga boka Tal’udu domin ya sanar dani duk yarinyar da ‘ya’yana suka lalata ma rayuwa itace gudan jinin da K’addarar Masarautar nan zai rayu a wuyatan, itace zai tsafi da ita domin ya tabbatar da dawamammiyar mulki na data ‘ya’yana cikin Masarautar nan...! Wannan yarinya SAUDATU itace makullin mulki na data ‘ya’yana...!!!” Ta k’arashe tana sakin wane irin shewa, ni kuma a lokacin naji jikina na wane irin karkarwa, naga wannan yarinyar d’iyar d’anuwana kaman yanda Izzatu tace tana buk’atar taimako daga gareni dan idan na barta Izzatu zata halak’ata, koda ba d’iyar d’anuwana bace rai ne mai buk’atan taimako daga hannun wannan azzalumar Baiwa da babu Allah cikin zuciyarta... Na isaga yarinya SAUDATU na tallafota na k’urama fuskarta idanu sai na hango kamannin d’anuwana a tattareda ita, naji wasu irin hawaye suna zuwa min, jikina ya d’auki rawa... Duk wannan abinda nake Izzatu bata lura dani ba sai sakin wane irin muguwar dariya take tana furta a yau burinta zai cika za’a kulle k’ofar sarautun Masarautar nan akanta da ahalinta da jinin wannan yarinyar... Cikin rawar jiki na soma k’ok’arin gudu rungume da yarinyar saidai ashe bokan Izzatu tuni ya hangoni sai ganinsa nayi gaba gareni cikin wane irin yanayi maras kyan gani.... Kafin nayi wani aune ya nunani da sandar tsafinsa sai gani nayi kaman an finciki yarinyar daga hannuna ta fad’a hannunsa, naji mummunar muryarsa yana furta “Wannan tamu ce, ita d’in an d’aura mata aure da Sarauniya, Amaryarmu ce wacce sarauniya zata zuk’i jininta..!” Take naji kaman an kifar dani k’asa tin daga lokacin ban kuma sake sanin komai gameda Alfah da ahalinsa ba domin kaw farkawa kawai nayi na ganni a d’akina wannan mutumin ya d’aureni da sark’ok’i... Hakan yasa nasan Fuskar d’iyar Alfah... Kuma ko bayan shekaru da na sake ganinta sai na fahimci itace, kenan Allah bai ida nufin Izzatu da Bokanta akan d’iyar Alfah ba, ya kub’utar da ita da buwayarsa daga hannun wad’annan azzaluman bayi nasa... Shiyasa na k’udiri niyyan mallaka mata wannan Taswira da Wambai ya bani shekara da shekaru Ina ajiye dashi, domin kuwa jikina ya bani itace zata zamto silan tonon asirin Izzatu...!!”Tana hawaye taci gaba da basu labari har kawo zuwa yanda Muhibbah ta taimakesu itada Ja’afar da taimakon da Ubandoma yayi masu bayan duk abubuwan da yayi mata a baya wanda Muhibbah itace Ta matso masa da tsoron mahaliccinsa kusa har ya karyar masa da zuciya yayi abinda ya dace..!! Gaba d’aya baka jin sautin komai sai ajiyan zuciya da zuban hawaye... Sosai Ja’afar yake kuka ya matso kusan Gimbiya Turai ya duk’a yace “Rankidad’e kikace budurwar data taimaka mana sunanata Muhibbah Kuma Ta ambaci sunana tace ta sanni..?!” Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “K’warai ta ambato sunanka J’afar, kuma ta sanka, kuma wanann budurwar itace SAUDATU d’iyar d’anuwana Alfah wanda Izzatu ta halak’asa...!!” Hawaye suka kasa daina zubowa daga idanun Ja’afar, lokaci guda yake furta “Saudah ta dawo, ta dawo cikin Masarautar nan...!!” Gimbiya Turai ta jinjina masa kai tace “K’warai Jafar ta dawo kuma nasan duk yanda take cikin Masarautar nan tana buk’atar taimakonmu domin kuwa idan har Izzatu ta fahimci wacece ita toh rayuwarta ka iya kasancewa cikin had’ari mafi muni fiyema da wanda ta shiga a baya...! Amma ya akayi kasan SAUDATU..?!” Ja’afar da idanunsa suka kad’a sukai jazir bayan hannunsa yasa ya share hawayen da suka zubo masa lokaci guda ya soma furta “SAUDATU wata yarinya ce da muke had’uwa da ita a k’aramar Kasuwar dake gabashin Masarautarmu, nakan shiga kasuwa duk ranan asabar domin nayi cinikin harawan dawakan Sarki na musamman, kaman yanda kuka sani ni d’in dah ne d’aya tol ga Sarkin Bargan Dawakan Sarki mai rasuwa mai suna Almu, mahaifiyata kuwa mai suna Kumbo tun lokacin data haifeni Allah yayi mata cikawa kaman yanda mahaifina ya bani labari, tun tasowata bansan komai ba face kulada dawakan Sarki kaman yanda mahaifina ya d’aurani akai, hakan yasa har bayan rasuwar mahaifina Mai Martaba bai yarda da kowa yaci gaba da kula masa da dawakansa ba sai ni dukda kuwa k’arancin shekaruna a wancan lokacin, tun ina k’arami na iya zuwa kasuwa nayi cinikayyan abincin Dawakan Sarki da kaina sabida nid’in nasan kan kalolin ciyayi abinci Dawakai wanda yafi kyau ma Dawakai... Wannan dalili na d’aya daga cikin abinda ya kuma jefa shak’uwa da Sabo tsakanina da Sarki AbdulJabbar... Toh Kasuwar da nake zuwa nakan had’u da yarinya Saudatu wasu lokutan da ‘yar jakanta Ta kayan data saye a kasuwa... Na lura yarinyar kaman tanada tsoron mutane dan ko kallo idan ka faye mata zakaga ta soma jada baya kaman zata gudu, da shike kasuwa ne k’arami hakan yasa yawancin mutanen da suke halartan kasuwan akai akai sukan iya sanin juna... Wata rana ta gama sayyayan kayan lambu dangin su tumatur ni kuma na d’auko harawata ta Dawakai na yunk’ura zan mik’e d’aukeda harawa a gadon bayana kwatsam mik’ewar da zanyi naji nayi fatali da abu ashe kayan miyanta na watsar mata... Ta durk’usa a wajen tana duban kayan miyan tana kuka...! Akaita bata hak’uri tak’i tayi shiru, nima da naji haushi nayi zuciya nace kar Allah Sa kiyi hak’uri Ke wannan yarinyar dama haka kike ko yaushe kina yawan zuwa kasuwa amma kaman akwai abinda kike b’oyewa, wasu irin iyaye ne gareki ma da bazasu Zo kasuwa da kansu ba sai su turo k’aramar yarinya kaman ke...!! Haka nayita mata masifa a wajen har ta tsagaita da kukan da take ta tsaya tana dubana... Ashe itama taji haushi matuk’a ai kuwa tuni naga ta daka tsalle ta finciko harawana ya tsinke gaba d’aya k’ullun dakai masa ya watse a wajen... Sai faman sakin huci take tana hararata... K’arshe jama’an dake wajen suka shiga bamu hak’uri da ni ita, aka tattara mata kayan miyanta nima aka tattara min nawa harawan..! Sosai rashin tsoronta ya bani mamaki... Ni kuwa nace wannan yarinyar batada tsoro kuma ban santa a fad’in yankin ba, bansan su waye iyayenta ba, amma wannan rashin tsoro nata yayi min kamada d’iyar manyan mutane ko masu mulki, nace sai nabi yarinyar naga inane gidansu... Tana tafe ina biye da ita har ta fahimci Ina biye da ita... Taja ta tsaya ta rik’e kunkumi tanaci gaba da sakin huci, lokaci guda kuma naga Ta auna a guje tana k’ok’arin canza hanya.. Nayi saurin shan gabanta nace “Ki tafi a hankali kada ki kuma zubar da kayan miyanki, ni babu abinda zan miki...!” Sai naga taja Ta tsaya amma dai tsoro bai rabu da ita ba... Na aje harawana gefe nace “Ke kuwa yarinya menene sunanki kuma daga ina kike dan ni ban tab’a ganinki a yankin nan ba sai tsakanin kwanakin nan..!” Ta kauda kanta gefe kaman bazata min magana ba sai kuma tace “Abbah na ya hanani magana da kowa a garin nan..!” Mamaki ya kamani nace “Ya hanaki magana da kowa kuma shine yake turoki Kasuwa kiyi sayayya..?!” Ta jinjina kai tace “Eh ya hanani magana da kowa yace akwai dalilin da ya kawo mu garin nan da zaran mun sami dalilin zamu tafi mu bar garin nan, Abbah na baya fitowa daga gida sai dare sabida yace akwai wasu mugaye a garin nan da zasu iya cutar dashi shiyasa baya iya zuwa kasuwa saidai ya turani...!” “Sosai mamaki ya kamani jin irin kalaman da take fad’i, na jinjina kai nace “Toh Ummanki fah.. Maiyasa bazata miki rakiya zuwa Kasuwar ba..?!” Ta d’an dubeni kad’an sai kuma tace “Ummah ta batada lafiya, ta kusa haifa min k’aramin k’ani bazata jure fitowa kasuwa ba..!” “Na jinjina kai nace toh inane gidanku..?! Daga yanda muke tsaye tamin nuni da wani gida can da yake arewa da yanda muke tsaye, gidan shi kad’ai ne a wajen tol ko mak’ota basu dashi..! Na jinjina kai nace ni kuma cikin Masarauta ne gidanmu kuma sunana Ja’afar...! Ni ba mugu bane kaman yanda kikayi zato, kiyi hak’uri da zubar miki kayan miya da nayi..! Wani ikon Allah sai gani nayi ta murmusa tace “Shikenan Babu komai nima kayi hak’uri da zubar maka harawarka da nayi..!” “Na kuma murmusawa Ina dubanta sai kuma nace “Basai kin bani hak’uri ba ni na hak’ura... Ki tafi gida kar a soma nemanki..! Ki wuce har ki shige gida ina kallonki bazan bari wani ya cutar dake ba..! Ta murmusa tace min na gode, zan iya kiranka Yaya Ja’afar tunda banida kowa a garin nan kuma ba’a barina na fita ko ina sai kasuwa kasuwan ma sai ranakun sati..!” “Na kuma murmusawa nace “Toh ai ban wani girmeki sosai ba ni kar ki tsufar dani ki kirani Yaya..! Ta kuma murmusawa tace “Amma ai ka girmeni, kuma nasan k’anwarka ce tsarata kaga ni banida wani Yaya banida kowa sai Ummah na da Abbah na saiko k’aramin k’anin da zata haifo min..!” “Tayi maganan cikeda yarinta, na murmusa nace “Toh shikenan tinda bakida Yaya Ki kirani Yaya nima tinda banida k’anwa kin zamto k’anwata...Hakan yayi miki..!?” “Ta jinjina kai tana kuma murmusawa tace yayi min.. Yaya Ja’afar..! Daga haka d’aga min hannu tayi ta shige tana waigowa har ta kusan isa gida Ina nan tsaye Ina dubanta, sai kuma na dakatar da ita nace “Gashi kuma Yaya baisan sunan k’awarsa ba har zata shige..!” Ta murmusa kad’an tace “Sunana SAUDATU..!” “Na jinina kai nace “K’anwata Saudatu..! Tai gajeren murmushi Ta kuma d’ago min hannu tace sai anjima...! Har saida naga shigarta gida kafin nasa kai nima na d’auki ciyawata na shige...! Toh tin daga wanann lokacin Sabo ya shiga tsakaninmu da Saudatu, nakan mata rakiya har zuwa gida, a haka bukin sallah ya k’arato na kula tana son zuwa taga hawan Dawakai amma baza’a barta ba a gida tinda ba’a barinta taje ko ina... Nayita bata labarin yanda hawan bukin sallah yake kasancewa, sosai yake sakata nishad’i yanda kasan ta had’a jini da sarauta... Kullum bata da labari da ya wuce na Dawakai da gidan sarauta... Tace min tana son ta shigo Masarautar nan wata ran taga yanda ginin gidan sarauta yake.. sabida idan tanama Abbanta labarin sarauta da abinda ya shafi gidan sarauta sai yayita mata fad’a yace koda wasa babu abinda ya had’ata da sarauta, babu komai cikin gidan sarauta sai zalunci... Dukda kuwa tsananin son kasancewa gidan sarauta da Saudatu keyi... Wata Rana Nace ta biyoni na shiga da ita taga yanda gidan sarauta yake ko sau d’aya ne a rayuwarta...haka kuwa akayi wani rana ta biyoni a tsorace na nuna mata cikin Masarauta, tayita mamakin girman gidan sarauta da yanda ake gudanar da al’amaran cikin Masarauta.. Naga yanda take matuk’ar son gidan sarauta da abinda ya shafi sarauta... Nace tinda ga k’aramar Sallah ta gabato ta fita taga yanda ake wasan Dawakai masu mulki suna hawa dawaki kuma suyi wasan saman dawaki su nuna bajintarsu.. Tace dani Aiko duk yanda za’ayi zata nemi hanya ta fito dukda ba sanin gari tayi ba, amma tana matuk’ar son ganin wasan doki... Nace zanso nayi mata rakiya tinda batasan kan gari ba amma saidai nid’in Bawa ne banida iko sai abinda Iyayen gidana sukace.. Na bata hak’uri nace bazan samu mata rakiya ba domin kuwa ni ne nake jan linzamin dokin D’an Sarki k’arami Wato Yarima Fu’ad sabida bai iya rik’e linzami..! A haka dai tace toh shikenan amma tabbas zata fita taga yanda wasan Doki yake kasancewa...!” J’afar ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya hawaye naci gaba da gangaro masa yake furta “A ranan bukin wannan sallan tabbas wani al’amari ya faru... A hanyarmu ta komawa dani da yaran Sarki gaba d’aya wanda mune mukai dare sabida wasan doki da yaran sarki suka tsaya yi... A hanyarmu muka tsinci Saudatu ta b’ata sabida batasan kan gari ba... Yarima Mahmood wanda duk cikin yaran Sarki yafisu jin k’an mutane shi yayi umarni mu d’auketa mu maidota gida dan na sanar dashi na santa kuma har gidansu na sani.. Hakan yasa muka d’aukota muka nufo Masarauta... Na tafi na barta tareda yaran Sarki..!!” Muryarsa ya carke hawaye naci gaba da zubo masa...! Lokaci guda ya kuma d’agowa yana duban Gimbiya Turai wacce itama hawayen take... Cikin rawar murya yake furta “Kenan sun lalata rayuwar Saudatu..! Sunci zarfinta.. Sun tarwatsa ahalinta..!!! Tabbas daga baya na daina ganinta a kasuwa na kuma tadda gidansu su Saudatu ya k’one babu kowa cikinsa ya zama kango... Kuma babu wanda ya sansu balle naji labarun ina suka koma.! Ashe abinda Giwa da ‘ya’yanta suka aikata ma Saudatu kenan..!!” Ya k’arashe cikin wane irin huci lokaci guda ya mik’e yana furta “Wllhi sai na d’au fansa akan abinda suka mata..! Sai nayi ajalinsu d’aya bayan d’aya koda nima za’a d’auki nawa a matsayina na k’ask’antaccen Bawa..!!” Ya k’arashe cikin wane irin karaji... Muryar Ubandoma suka sinkaya cikin zuban hawaye yana furta “Kai ba k’ask’antacce bane Ranakaidad’e..! Kai d’in Mai Martaba ne jinin mai Martaba..! Kai d’in D’ah ne ga Sarki AbdulJabbar mai rasuwa kuma mahaifiyarka tana nan a wajen nan tareda Kai...!!!” K’irajai suka shiga bugawa..!! Gaba d’aya idanu suka koma kan Ubandoma.... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *72* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ubandoma ya d’an tsagaita da kukan da yake ya d’ago ya dubi Gimbiya Turai ya kuma duban Ja’afar wanda su duka biyun hawaye ne Ke gangarowa daga idanunsu ya kuma saita dubansaga Gimbiya Turai ya duk’a gabanta had’ida risinar da kansa “Rankidad’e Jaririn da Giwa ko ince Izzatu ta canza da naki shine jaririn Malam Almu Sarkin Barga... Izzatu itace Ta kashe matar Malam Almu ta kuma kashe jaririn, tazo da da wani jariri rayayye ta canza da jaririn matar Almu, ni....!” Muryarsa ta soma rawa sosai sanda Ja’afar da tuni jikinsa ya soma rawa sosai ya duk’a gaban Ubandoma yana mai furta “Da wani jariri ka canza..! Kayi magana, ka sanar damu wanene jaririn..!!?” Ubandoma yaci gaba da hawaye yana mai furta “Gaba d’aya cikin laifukan da nayi a baya bisaga umarnin Izzatu babu wanda ya tsaya min a rai irin wannan sabida ya k’unshi jariri wanda baida hakkin kowa... Bansan daga yanda ta samo rayayyen jariri a wancan lokacin ba Ta bani nayi musayen jaririn da na matar Malam Almu wanda tuni tayi tsafi ta kashesu daga shi har uwarsa...!” Ya kuma d’agowa yana duban Ja’afar da Gimbiya Turai kana yaci gaba da fad’in “Rankidad’e wannan jaririn da aka kai miki matsayin naki tabbas ba naki bane kaman yanda Fattu Ta gani kuma ta fad’i maki... Jaririnki yana nan da raye..! Rankidad’e jaririnki ba kowa bane face JA’AFARU..!!!” Ya k’arashe cikin wani irin kuka yana mai zama dirshan a dandamalin k’asa...! Innalillahi wa inna’ilaihi ilaihi raji’un..! Kalaman da zukatansu Ke iya nanatawa kenan...! Ja’afar da yaji batun a wane irin ba zata d’ago gajiyyayun idanunsa yai yana kuma duban matar da Ubandoma ya gama sanar dasu cewa itace mahaifiyarsa kuma shid’in ba Bawa bane d’ah ne ga Sarki AbdulJabbar mai rasuwa... Giwa itace ta rabasa da mahaifiyarsa ta kuma maidasa Bawa k’ask’antacce a gidan Mahaifinsa... Ya rayu a matsayin Bawa a cikin Masarautarsa..! Shin wannan zalunci da mai yayi kama...!! Sosai jikinsa yake rawa gumi na kuma karyo masa dukda iskan damuna dake hurawa, ji yake kaman numfashinsa na neman d’aukewa ya bar jikinsa.... Bai kuma fahimtar meke faruwa ba saida yaji hannun matar nan tana shafa fuskarsa cikin rawar murya take furta “Kaid’in d’ahna ne..! Tabbas kai d’in d’ah na ne... Domin kuwa jikina ya bani akwai abuna mai mahimmanci a gefen d’akinda Ubandoma ya rufe ni.. Ban fasa kankare jikin ginin ba, ban kuma amince na tafi na barka hannun azzaluman nan ba har saida na tabbatar Allah ya kub’utar damu tare...! D’anah.! Jaririna..!!!” Wane irin kuka mai k’arfi ya kufce mata tana mai janyo Ja’afar d’in cikin jikinta da tuni ya koma tamkar wanda yayi sumar tsaye..! Jijiyoyin jikinsa sai mimmik’ewa yake ba komai yake tunawa ba face irin wulak’ancin da yaran Giwa sukai masa musamman Yazeed da Jamal, Yazeed akan tsananin son Mulki da izza shi kuwa Jamal akan Umaima ne... Ya tuna akwai wani rana da Yazeed ya take gadon bayansa ya d’ale doki, ya tuna akwai wata rana da Jamal ya sakasa ya sumbaci takalminsa dan ya gansu da Umaima kawai don ya nuna masa cewa shid’in k’ask’antacce ne bai dace da basarakiya jinin sarauta kaman Umaima ba....Dan ma shid’in Allah yayisa mai taurin kai da kafiya ne tun a baya lokacin yana matsayin Bawa, yakanyi abu tamkar ba Bawa ba musamman idan ka tasamma tab’a mutuncinsa sam bazai barka ka k’ask’antashi ba a matsayinsa na d’anAdam wanda Ubangijin talikai gaba d’aya ya d’aga darajan d’an adam kan sauran halittun duniya..! Shi mutum ko yaya ka gansa ba abun wulak’antawa bane, baka San kalan Baiwar da Ubangijinsa yai masa ba, kuma bakasan koma ya fika daraja a wajen mahaliccinku ba, idan yafika tsoron Allah sai ya fika daraja..! Sam Shari’a bata bama kowa daman kaci zarafin wani wanda yake k’arashinka ba koda kuwa bawanka ne...! Ya dinga tuna ire iren cin mutunci da wulak’anci da ya fuskanta daga wajen wannan ahali... Sai yanzu komai yake dawo masa daki daki, watak’ila Mai Martaba ya fahimci shine mahaifinsa na asali da Giwa ta fahimci hakan shine ta kashe mai Martaba shima kuma Ta nemesa zata kashesa.. Wannan mata takai mak’ura wajen zalunci... Shi ko a labarun hikayoyi da ake karanto masu da cikin Fada bai tab’a cin karo da labarin azzaluman Baiwa irin Izzatu ba...! Amma zuluncinta yazo k’arshe da izinin Allah, sai ta girbi duk abinda ta shuka daga ita har yaranta guda biyu...! Yana mamakin yanda Yarima Mahmood ya kasance daga cikin ahalin wannan azzalumar mata domin kuwa shid’in ya banbanta da muguwar ahali irin wannan.. Kodashike Allah yakan fidda rayayye daga cikin macecce sannan ya kan fidda macecce daga rayeyye... Domin kuwa babu abinda yafi k’arfin buwayarsa...! Ja’afar ya lumshe idanunsa a hankali sanda yaji hannun Gimbiya Turai tana shafe fuskarsa da ruwa dan su duk a zatonsu suma yayi...! Yaja wane irin dogon numfashi had’ida sauk’e idanunsa kan matar, yai mata K’uri bayanan kalan azabtarwa da muzgunawa had’ida mummunan cin amanan da Baiwar ta tai mata na kuma yawo a kwanyarsa...! Hawaye suka soma gangarowa daga idanunsa wanda tuni Sun kad’a sunyi jazir.... Ji yayi yakai hannunsa dake tsananin rawa saman fuskarta yana share mata hawayen dake kuma gangaro mata. Cikin rawar murya yake furta “Ta cutar dake..! Ta miki zalunci mafi muni Ummi tah... Ta maidaki Baiwa cikin gidan Mijinki sannan Ta maida d’anki Bawa cikin gidan mahaifinsa... Daga k’arshe ta haukataki ta kuma salwantar da sauran ahalinki..! Wannan matar bata cancanci yafiya ba domin idan na yafe mata ni kaina bazan iya yafewa kaina ba sabida abubuwan da tai miki Mahaifiyata..!!” Ya k’arashe cikin wane irin cazgan kuka..! Tuni Gimbiya ma kukan ya kufce mata suka had’e goshinsu itada d’anta Ja’afar waje guda suna yin mai isarsu...!! Tirk’ashi..! Rayuwa mai bud’e ma Bawa shafuka daban daban, ko wanne da yanda yake zuwa maka, wad’annan bayin Allah rayuwa ta kuma bud’e masu sabbin shafuka.. Bayan tsawon shekarun nan gashi Allah ya had’a fuskokinsu, tabbas tsanani yana tareda sauk’i mai hak’uri shikeda riba...! Bayan komai ya tsagaita Baba Nomau ya nusa had’ida furta “Alhamdulillahi..! Alhamdulillah...! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin da babu wani bayan shi, mai mulkin Sammai da k’assai da abinda ke cikinsu da abinda ke tsakaninsu, tsira da amincinsa su sake tabbata ga Annabinsa fiyayyen halitta wanda babu yashi, Manzon tsira (S.A.W)...!” Ya juyo kad’an ya dubi Ubandoma yace “Hak’ik’a ka tapka kurakurai a baya, wanda a ajizancinmu na ‘yan adam zai wahala wani ya yafe maka..! Ubangijinmu ne zamuyi masa laifi duk girmanta duk yawanta ya kuma gafarta mana mu maimaita mu kuma sake rok’onsa ya yafe mana matuk’a bazamu masa tarayya wajen bauta masa ba... Shirka itace mafi munin zalunci da Bawa zai aikataga Ubangijinsa a doron k’asa, Shirka itace mafi girman laifi da mutum zai mutu yanayi Ubangiji bazai gafarta masa ba.. Amma duk wani laifi bayan shirka Ubangiji mai iya gafartawa ne idan yaso domin shid’in shine Algaffar kuma Arraheem..! Ka tapka kurakurai a baya amma daga k’arshe ka gane kuskurenka kuma kayi abinda ya dace sannan ka rok’i Ubangijinka gafara, Muna fata ya gafarta mana baki d’aya... Sannan muna fata wad’anda kaima wannan aika aika su gafarta maka domin shi addu’an wanda aka zalunta babu hijabi tsakaninsa da Ubanginsa..! Sannan ko a Shari’a idan an maka laifi ka rama gwargwadon abinda aka maka bakayi laifi ba amma saidai da zaka zamto mai afuwa da yafiya sai ya fi maka alkhairi... Allah yana son masu afuwa kuma yana tareda masu hak’uri..!” Ya maidoda dubansa ga Ja’afar da mahaifiyarsa wanda kawunasu ke k’asa suna saurarensa, Baba Nomau yaci gaba da fad’in “An zalunceku kuma an cutar daku... Wannan mushirikar matar Ta maku zalunci mafi muni amma ku sani wani shari’ar sai a lahira..! Tinda Allah yasa duk mun fahimci haka kuma ya baki lafiya a halin yanzu ya kuma had’a fuskarki dana d’anki bayan kun d’ibe tsammanin sake had’uwa da juna.. Sai mu gode masa da wannan rahama nasa sannan gobe idan Allah yasa muna cikin masu nisan kwana mu d’unguma mu koma Masarauta a ida warware komai..!” Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “Haka ne Baba...!” Ja’afar ma jinjina kansa yayi saidai kafin yakaiga furta wani kalma Ubandoma ya katsesu da fad’in “Bazan iya komawa Masarautar nan ba har sai na tabbata kun yafe min... Dan Allah ku yafe min duk abubuwan da nai maku a baya...!!” Murmusawa Gimbiya Turai tai tace “Na yafeka tuntuni tun lokacin da ka zab’i kayi abinda ya dace bayan kanada damar da zaka kuma mik’ani hannun wannan azzalumar Baiwar, amma ka zab’i kayi abinda ya dace kayi sanadiyar kub’utarmu nida d’ah na ka kuma kawo mu yanda maganinmu yake cikin hukuncin Ubangiji da ikonsa..! Kaima abin mu maka godiya ne Ubandoma... Allah Ubangiji ya saka maka da mafificin alkhair bisa abinda kayi...!” Ubandoma ya duk’a yana hawaye yake furta “Na gode na gode Rankidad’e..! Ubangiji ya k’ara girma..!” Ya kaikaito kad’an yana duban Ja’afar... Kafin yayi magana Ja’afar yayi saurin d’agosa ya rungumesa, lokaci guda yake furta “Tun zamanin da nake na matsayin Bawa cikin Masarauta baka tab’a muzguna mun ba hasalima kai d’in kana d’aya daga cikin masu kwatanta alkhairi a gareni.. Sannan daga k’arshe kamin abinda bazan iya saka maka ba koda kuwa daga farko ka zamto silan shiga rayuwar da na girma na tsinci kaina ciki..! Na gode maka Baba..!” Ubandoma na hawaye yake furta “Rankaidad’e nifa Bawanka ne ka daina furta min kalman godiya.. Ka barni na duk’a gabanka..!” Ja’afar na murmushi yake furta “Ni dakai duk d’aya muke wajen Allah mu duka bayinsa ne kuma har kullum kai d’in tamkar Uba ne a gareni dan bazan mance yanda ka kula dani ba bayan babu iyayen da na girma na sansu matsayin iyayena.. Babu k’ask’antacce sai wanda ya k’ask’antar da kanshi kaji koh..!” Cikin sauri Ubandoma ya shiga jinjina kai cikeda jin dad’i yana kuma godiya... Fuskoki suka cika da annuri da Farin ciki... Ja’afar da mahaifiyarsa suka kasa sakin juna sabida Farin ciki.. Gani take kaman wani abu zai kuma giftawa ya raba tsakaninta da d’anta...! Baba Nomau ya kuma basu wasu add’u’o’i yace suyita nanatawa suna ambaton Allah domin kuwa duk yanda wad’anda suka cutar dasu suke suna cikin tashin hankali... ** Tinda suka baro asibitin wajen Yazeed yake shek’a gudu saman kwalta daga gani zaka fahimci neman hanyar fitar da b’acin ransa kurum yake, ya kasa yarda ‘yan uwansa da mahaifiyarsa zasu aikata irin mugun abinda yaji sun aikata, Allah ya gani ko k’aunar ganin fuskokinsu baya yi shiyasa ma koda suka iso asibitin yake alla alla ya fice daga cikin asibtin... Babu yanda Turaki bai ba ya basa motar ya tuk’a amma yak’i sai zuba gudu dasu yake saman kwalta... Bai cewa uffan sai shek’a gudu yake jijiyoyin jikinsa suna kuma fitowa duk sanda kalman fyad’e da k’annensa suka aikata ma k’aramar yarinyar nan zaizo zuciyarsa.. Idanunsa suna kuma kad’awa...! Turaki kansa ya rasa gane kan abokin nasa, tashin hankalin da yake hangowa tattareda Mahmood d’in yafi k’arfin ace dan sabida iftila’in da ya aukawa Yazeed da ahalinsa yake ciki tinda yasan abokin masa musulmi ne kuma yayi imani da K’addara mai kyau ko akasinta... Amma ya rasa gane ina tauhidin abokin nasa ya tafi yake neman yin wasa da rayuwarsu saman kwalta... Shi kansa Turaki bai iya cewa komai sai ambaton Allah kurum da yake cikin zuciyarsa.... ** A b’angare guda tun fitowar da yayi daga Bauchi sai yanzu Allah yayi isowarsa, mota ta b’aci masa a hanya sannan ya rasa mai gyara ya kuma rasa wanda zai tsaya ya taimaka masa, gashi dama ba isasshen lafiya bane dashi tinda daga asibiti ya cire ruwan drip ya fito sam babu wani k’arfi jikinsa, bashi ya samu isowa garin Jos ba sai wannan lokaci dan da kam ma ya yanke shawarin tsayawa a Toro ya kwana ne amma sai yaji inaa bazai Iya kwana baisan halinda Muhibbah ke ciki a wannan masarauta ba hakan yasa ya k’udiri niyyan komin dare sai ya shiga Jos da izinin Allah... Daidai yanda suka saba parking idan ya kawota a wajen yayi parking can tsallake da Masarautar... Yayi tsaye yana tinanin abinyi, ta yaya zai doshi Masarautar ba tareda an tambayesa wanene shi daga ina yake kuma wajen waye zai jesa, yasan by now Umaima zata iya fahimtar shid’in ya mata k’arya, Toh ta yaya zai shige Masarautar bata hanyar Umaima ba... Kodashike ita d’in tana da zuciya mai kyau watak’ila tansauraresa ta kuma basa uzuri... Take ya lalaumo wayarsa cikin mota ya soma dialing layin Umaima..! Saidai sam wayar tata bata shiga... Dafe kansa yayi a hankali had’ida jefa wayar cikin mota dan shima wayar tasa chaji gab take da k’arewa... Ya fuzar da fuci yana tunanin abinyi ya wane irin jiri dake neman kaisa k’asa dan tun bayan drip d’in babu wani abu da ya saka cikinsa..! Wata zuciya tace tsayuwa a nan bai ganka ba Ansar Muhibbah tana cikin Masarautar nan kuma tana tsananin buk’atarka ka shiga kawai ka fito da ita komai ta fanjama fanjam, komai zai faru kawai saidai ya faru but ya zama dole ka shiga ka ceto masoyiyarka...! Da wannan tunani Ansar ya nufi Masarautar yana tafe ko ganin gabansa baiyi.... A daidai lokacinda su Mahmood suka doso Masarautar suma.. Turaki ne kawai ya hango mutum yana tafe bisa kwalta tamkar mai tab’in hankali shikam Mahmood sam baiga mutum ba dukda cewa hasken wutan streetlights sun haske ko ina... Turaki fad’i yake “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Watch out your Highness..!!” Inaaa sam Mahmood baima saurari abinda Turaki Ke fad’i masa ba saiji yayi ya d’auke mutum da k’arfin gaske...! Ya taka burki babu shiri Allah yasa babu wata motar ma bayanshi da shike wannan close d’in babu gidan kowa wajen ba kuma hanyar wucewa zallan Masarauta ce kawai a wajen...! A tare suka fito suna duba mutumin da suka bige... Turaki ya d’an tab’asa yana furta “Kaman yana numfashi Your Highness.. Muyi gaggawan kaisa asibiti mafi kusa..!” Cikin sauri Mahmood d’in ya taimakawa Turaki suka ciccib’i mutumin suka saka bayan Mota... Babu shiri Turaki ya amshi makullin motar suka nufi wani privare hospital da baida nisa sosai da Masarautar... ** A can asibiti wajen Yazeed kuwa gaba d’aya Giwa ji take kaman an mintsileta, Ta kasa zaman asibitin Ta kuma kasa komawa Masarauta, batasan dalili ba amma zuciyarta sai yankewa yake yana bugawa yanda kasan ana sauk’e mata shirgegen guduma saman k’irjinta haka takeji... Ga wani irin muguwar k’aik’ayi da bata tab’a jin irinsa ba tsawon rayuwarta, hannunta nayi kanta nayi... Ta gaza zama ta gaza tsayuwa, gaba d’aya Giwa ba a hayyacinta take ba ta alak’anta hakan da asirinsu da Fu’ad ya tona wajen Mahmood..! Jamal ya da shima hankalinsa ba’a kwance yake ba ya k’araso ga mahaifiyar tasa cikin cangwala sandarsa, ya tsaya dab da ita yana muzurai yake furta “Maami meye abinyi yanzu da Yaya yasan laifin da muka aikata shekarun baya... Maami jikina na bani Yaya bazai dakata ba until he seek justice for what happened to that girl, koda kuwa mu d’in ahalinsa ne.. Maami kin sanshi kinfi kowa saninsa tinda Ke kika haifesa...!” Cikin tashin hankali Giwa dake faman soshe soshe Ta katse Jamal da fad’in “Bani na haifesa ba kar ka sake cewa ni na haifi wannan tsinannen yaron... D’anda na haifa bazai tab’a kiranada ‘yar ta’adda ba...!!!” Cikin rashin gane ina kalamanta suka dosa Jamal yace “Maami ban gane ba... Ban fahimta ba...! Yaya ne fah..! Yaya Mahmood nake nufi..!!” Cikin daka tsawa Giwa tace “Uban Yaya Mahmood ne ba Yaya Mahmood ba... Allah yasa Mahmooda Uban AbdulJabbar ne..! Kai nace maka bani na haifesa ba kar ka sake cewa d’ah na ne..!!” Ta k’arashe tana mai ci gaba da susa...! Jamal yasha jinin jikinsa yana dubanta cikeda tsoro saikace wata sabuwar kamu..! Koda shike k’ila fushi take da Mahmood d’in shisa take ambatonsa da cewa ba ita ta haifesa ba..! Ya d’anyi shiru sai kuma yace “Maami ya kamata mu koma masarauta Kinsan akwai aikin da bamu k’arasa ba can Masarautar..!” Nan ma katsesa Giwa tayi da fad’in “Kai nace maka bazamu bar asibtin nan ba sai Yazeed ya farka..! ko ni ko kai babu mai barin asibitin nan sai mun tabbata d’an uwanka ya farfad’o, ince da handcuffs ka d’aure yarinyar toh uban waye zai kwanceta...!!” Jamal ya kuma jinjina kai a hankali yana kallon bak’on lamari daga mahaifiyar tasa... Bai kuma cewa komai ba sai komawa gefe da yayi...! Can Giwa ta hango Waziri ashe Shima ya kasa tafiya yana nan yana jiran farfad’owar Yazeed... Giwa tana ganin giftawarsa tai saurin bin hanyar da yabi... Koda Jamal dake fakaice da ita yaga tabi bayan Waziri sai shima ya saci idon Jakadiya yabi bayan mahaifiyarsa a hankali... Tsaye yayi ya lab’e yana sauraren tattaunawar Giwa da Waziri... Cikin k’unan rai Giwa ke ci gaba da fad’in “Saida nace kabi bayansa ka dakatar dashi, Wannan duk laifinka ne... Ka kasa dakatar dashi... Da ace ka dakatar dashi da yanzu d’anmu yana nan da lafiyarsa, da yanzu bai rasa hannayensa ba balle ‘ya’yansa... Idan Yazeed ya farka bazai tab’a yafe maka ba kuma bazai tab’a amsarka a matsayin mahaifi ba...!” Cikin tashin hankali Waziri Ke fad’in “Ki dakata ki saurareni Turai, Yazeed ni na basa jini ni na taimaki d’anmu na basa jini akai masa aiki, da ace banyi gaggawan basa jinina ba k’ila da yanzu mun rasashi gaba d’aya.. Ki gode ma Allah ki gode min har yanzu Yazeed yana numfashi...!” Cikin karaji Giwa Ke fad’in “Meye abin godiya a nan bayan kasa d’anmu ya zama muskini shikenan haka zai tashi yaga ya rasa hannayensa.. Duk burin sarautar da naci masa yanzu bazai samu ba..! Ka cuceni Waziri... Ka cuci D’anka Yazeed..!!” Kaman daga sama suka sinkayo muryar Jamal cikin wane irin yanayi yana furta “Maami did I hear it right..! Naji da kyau cewa Yazeed d’an Waziri ne..?!!” Daga Giwa har Waziri aka rasa mai basa amsa...Jamal dake ci gaba da sakin huci ya k’araso gaban Giwa sosai yana furta “Answer me..! Ki amsa min...! Yazeed d’an Waziri ne..?!” Giwa bata iya furta komai ba sai muzurai.. Ya kuma d’aga murya yana jefo mata tambayar... Waziri ne ya basa amsa da fad’in “K’warai abinda kaji haka ne Jamal... Yazeed d’ah na ne da mahaifiyarka....!!” Cikin tsananin Shock yake duban Giwa zuciyarsa na kuma tsinkewa har wani irin rawa jikinsa keyi, kana iya hango hakan daga sandar crotchets d’insa yanda sandar ke rawa kaman zai dungurar da Jamal d’in k’asa..! Cikin wane irin yanayi yake girgiza kai yana duban Giwa “You tell me what really happened..! You tell me ta yaya wannan mutumin ya zamto mahaifin d’an uwana da muka fito ciki guda muka girma a matsayin ‘yan uwa da suka had’a duka iyaye biyu..! Maami ki bud’e baki ki sanar dani..!!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa cikin tsananin k’unan rai...! Giwa dake danne kukanta tace “Ya faru ne hakan..! Domin kuwa Waziri shi yake taimaka min da komai wajen ganin na kafa mulki na cikin gidan nan..!” Jamal ya katseta da fad’in “Shiyasa kikaci amanan mahaifina kika basa kanki...! Maami how could you do this..! Ke fah mai sarauta ce mai Martaba..! Ta yaya zaki aikata k’ask’antaccen laifi irin wannan..!” Giwa ta katsesa da fad’in “Kada ka yarda ka yanke hukunci akaina domin kuwa baka San kalan rayuwar dana fuskanta a baya ba dan na tabbatar da mulkin nan bai kufce min ba..!” Cikin huci Jamal d’inma ke furta “Wane mulki kike magana bayan d’an naki ba Magajin mahaifinmu bane... Ince Yazeed kike maganan d’aurawa saman Karagar..? Ashe dama duk son Yaya da kike na k’Arya ne..? Toh idan ba ke kika haifesa ba wacece Ta haifesa..?!” Giwa Ta basa amsa da fad’in “Wannan ba matsalarka bace a halin yanzu.. Kaidai tinda kasan kaid’in d’ah ne magana ya k’are..!” Waziri ya katseta da fad’in “Ina magana ya k’are tinda shi baisan waye nasa mahaifin ba..!!” Ya karkata ya dubi Waziri da tsananin mamaki hawaye naci gaba da gangaro masa lokaci guda ya maidoda dubansaga Giwa yace “Answer his question... Waye mahaifina Giwa...?!” Hararan Waziri kurum Giwa take kana tace “Mahaifinka Sarki AbdulJabbar ne..!!” Waziri ya bud’e murya yace “K’arya take maka ita kanta batasan waye mahaifinka ba domin kuwa Ta shiga rud’u a lokacin..!!” Jamal ya fiddo idanu waje yana duban Giwa lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “You’re unbelievable..! Shin abinda yake fad’i gaskiya ne Giwa..?! Do I need to take a DNA test for me to know who my father is..?!! Answer me Giwa..?! Ki amsa min nace..!!” Cikin zuban hawaye Giwa Ke jinjina kai tana furta “Gaskiya ne Jamal bansan waye mahaifinka ba...!” Dakatar da ita yayi ta hanyar d’aga mata hannu yana mai sakin huci yake furta “No..! My father is dead..! My father was King AbdulJabbar... Shine mahaifina... Bazan tab’a zama product na cin amanar da kika masa ba..! You’re a worthless mother..! Mujiyar uwace Ke mai kashe ‘ya’yanta..! Ko baki d’auki wuk’a kin dab’a mana ba kin kashe mu da abinda kika mana... Gaba d’aya rayuwana nayisa ne wajen miki biyayya..! Ashe duka rayuwan nawa k’Arya ne... Babu komai cikinta face k’arya...! Duk fad’i tashin da Kike wajen ganin kin kafa mulkin babu komai a cikin labarin face k’arya..! Kina neman ki d’aura ‘ya’yanki saman Karagar da basuda gado..! Maami kin cuceni kin zalunceni..! Nayi nadaman miki biyayya da nayi a baya dukda ire iren muggan abubuwan da kika sa na dingayi.. Allah ya isa tsakanina dake Giwa.. Kuma yanzu basai anjima ba zanje na kwance yarinyar nan bazan sake miki biyayya ba daidai da dak’ik’a guda..!” Ai bata bari ya fice ta shiga janyosa tana basa hak’uri yana fuzgewa.. Ya juyo yace “Kika kuma tab’ani wllhi zan rabza miki sandar nan kinji na rantse..!!” Giwa na kuka taceda Waziri ya dakatar dashi yana hanasa ficewa...! Da k’yar Waziri ya rik’o Jamal dake faman bige bige yana kuka yana fad’in ya tsani Giwa...! Saman wata kujera Waziri ya zaunar dashi ya rik’e sandar nasa wanda babu hali yayi tafiya babu ita.. Waziri ya duk’a gaban Jamal dake ci gaba da sakin huci yana murza tafukan hannayensa sabida tsananin b’acin rai... Lokaci guda Waziri Ke furta “Jamal basai kayi gwajin k’wayoyin halitta ba dan kasan wanene mahaifinka... Kasa a ranka cewa mahaifiyarka itace k’wal d’aya taka domin kuwa tayi sadaukarwa da dama a sabida ku ‘ya’yanta...Duk abubuwan da take, duk fad’i tashin nan sabida kai da ‘yan uwanka take..!” Cikin karaji Jamal ya katsesa da fad’in “Can’t you see she’s ruining us... Duk abubuwan da take babu wani alfanun da suka mana saima d’aid’aita rayuwarmu da sukayi... Ka gaya min cikin yaran nata wanene ya taka matakin nasara,,, Yazeed dake kwance babu hannuwa babu iyali ne..? Ko kuwa ni da nake dogarawa da wannan sandar ko Fu’ad dake kwance gadon asibiti wanda tasa muka maidasa mahaukaci da k’arfin gaske..! Ka gaya min wanene zai gaji kujeran dataci burin cikinmu..?!!” Ya k’arashe sabbin hawaye na gangaro masa..! Waziri yace “Dukda haka dai, yanzu idan ka juya mata baya zaku tafi k’aaa tare ne gaba d’aya ko ince dukanmu gaba d’aya..!” Giwa dake gefe tana hawaye Ta shiga jinjina a masa kai tana furta “Ni d’in mahaifiyarka ce Gwarzona, ko mai Nayi bazaka gujeni ba, domin kuwa ba’a sake mahaifiya, bamu San waye mahaifinka ba amma nid’in nice mahaifiyarka..! Jamal karka guje ni da bazan iya k’arasa yak’in nan ba tareda kai ba d’ah nah..!!” Ta k’arashe cikeda kissa tana kuka tana dafe k’afan d’an nata... Lokaci guda Jamal yasa hannuwansa ya d’agota zaune... A hankali yake furta “What’s done is done Maami...! Naji zan tsaya tareda Ke mu k’arabs abinda kika riga kika soma... Nima ina cikin yak’in nan already...! Now that I know sarautar na namu bane zanyi komai domin naga ahalinmu basu tagayyara ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci da zafin zuciya... Giwa Ta saki murmushi tana dubansa, lokaci guda take furta “Hak’ik’a kai d’in ka cika d’ah na kuma jinina..!!” ** Iyaka jigata Umaima Ta gama yi, da k’yar da tura k’afa da nishi da komai ta samu ta janyo wayar da babban yatsarta.... Ta had’e k’afafunta tana k’ok’arin d’ago wayar zuwa hannunta, nanma wani jan aiki... Sai ta kama kaman zata iya d’aukowa sai ya fad’I k’asa... Ga dare na kumayi, k’arshe haka ta hak’ura ta maida jikinta baya tana nishin wahala da k’yar... Firgit Ta farka Ta hango hasken hantsi alamun gari ya soma wayewa.... Taci gaba da k’ok’arin d’aukan wayar da k’afafunta har Allah ya bata sa’an d’aukan wayan... Saidai tana samun nasaran d’aukar wayar taji kaman shigowarsa, zuciyarta ta yanke... Cikin Sauri ta tura wayar ta zauna bisa... Tai saurin gyaran kwanciyarta ta lumshe idanu tamkar mai bacci zuciyarta bata daina tsinkewa ba...! K’arasowa gareta yayi ya zauna gefenta had’ida k’ura mata idanu... Yakai hannunsa a hankali yana shafa goshinta zuwa fuskarta, lokaci guda yake furta “I’m sorry my love..! Ba’a son raina na d’aureki na barki kika kwana d’aure daren da ya kamata mu rayasa cikin faranta ran juna... Please forgive me Umaima... I promise zan kula dake... Zan baki Farin ciki a gidan aurenki, zan zamto the most loving and caring husband da ko wace mace zatayi fatan samun irinsa....Dukda cewa a yau labarin rayuwana ya canza... Amma na miki alk’awari soyayyar da nake miki bazai tab’a canzawa ba..! I love you so much Umaima..!” Ya k’arashe yana mai sumbatar goshinta..! Hawayen da take mak’alewa suka shiga gangaro mata... Lokaci guda Jamal yai k’ok’arin saita kansa yana dubanta... “My love kin tashi..! Akwai abinda kike so..! Tell me ko menene zan kawo miki..!” Yananyin data gansa gaba d’aya kaman bashi ba harga Allah tun bayan abubuwan data gani mugun tsoronsa take.. Amma dole tasan yanda zatayi Ta kub’utar da kanta da kuma Muhibbah daga hannun wannan mahaukacin mutumin tinda har Allah ya bata Sa’an d’aukan wayar salulansa..! Dole tayi acting very smart idan tanaso Ta cimma burinta..! Cikin rawar murya take furta “Ya Jamal meke faruwa..?! Maiyasa ka d’aureni..! Na gaji, bathroom nake son shiga dan Allah ka kwanceni kaga ko sallah banyi ba..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..! Dubanta yayi duk a rikice sai yace “Are you sure..! Zafi kikeji da gaske.. where does it hurt.. Nuna min ina Ke miki ciwo.?!” Ya k’arashe yana kai hannunsa jikinta.. Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Ko inama ciwo yake min a jikina... I spent the whole night like this.. Maiyasa ka d’aureni.. Ina sonka bazan tab’a gudunka ba... Please untie me..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Kaman wanda yaji maganarta ya soma yunk’urin kwanceta, sai kuma ya dakata yana furta “No... Zaki gujeni, sabida munafukar nan Ta fad’a miki k’Arya akaina... No Umaima bazan kwanceki ba har sai na tabbata ked’in kin zama tawa gaba d’aya... Zanje na kashe wancan munafukar na dawo na d’aukeki mu bar Masarautar nan..!” Yana ida fad’in haka ya mik’e ya nufi k’ofa...! Aiko yana ficewa, cikin rawar jiki Umaima ta d’auko wayar ta soma k’ok’arin bud’eta Allah yasa k’aramar wayace ba’a kulle take ba... Babu lambar kowa a gidan saita Giwa cikinta, da alama Giwa kawai yake kirada layin... Ta soma tunanin bayan lambar Jamal d’in lambar waye Ta had dace a gidan..! Lambar Zahra kawai ta had dace hakan yasa ai Saurin latsa lambobin Zahra.... Zahra da tashinta kenan tana k’ok’arin shiryawa ta fito Fadar Giwa taji meke faruwa cikin Masarautar da yasa tin jiya da dare bataga kowa ba nan taga kira da bak’on lamba na shigo mata kaman bazata d’aga ba dan har Ta kusan matsewa tinda tsirarun mutane ta sani a gaba d’aya k’asar zai wahala ace wani bak’on lamba da ba na ahalin cikin gidansu ba na nemanta, sai kuma ta dai taji ta d’aga kiran... Aiko tana d’agawa ta sinkayo murya kaman ta Aunty Umaima tana fad’in “Zahra ki saurareni...!” Zahra cikin wane irin yanayi tace “Aunty Umaima is that you..! Meke faruwa...?!” Cikin sauti Umaima dake k’ok’arin saving chajin wayar dan ta kusan mutuwa gaba d’aya battery d’in... Nan taci gaba da fad’in “Follow your Uncle Jamal, and save Muhibbah..! Zahra don’t ask questions kawai kiyi yanda nace.. Ki bi bayansa kiga yanda ya b’oyeta and run straight to your Paa..! Ki sanar da Paa d’inki..!!” Bata ida maganar ba d’iff wayar ta katse chaji ya k’are... Cikin rawar jiki Zahra Ke juya wayar hannunta.... Sauri sauri ta fito daga d’akin kota kan Hadimatarta dake sanar da ita abincin karin ta ya kammala bata bi ba..! Zuciyarta sai tsinkewa yake... Tana ficewa taga Masarautar babu wani mutane sosai kaman anyi shara, kodashike safiya ne sosai garin bai ida wayewa ba.... Cikin sand’a Ta fito Ta soma tafiya, zuciyarta sai bugawa yake, can kusan sashen Jamal ta hangosa ya fito cikin shiga ta kayan sanyi bak’ar riga mai hood, yanayin data gansa ciki sosai ya bata tsoro tai saurin bin bayansa kaman yanda taji Umaima tace.... Abinda ya bata mamaki shine hanyar da taga yabi mutane basu faye bin wajen ba, hasalima tamkar abandoned waje ne a cikin Masarautar... Dukda zuciyarta dake matuk’ar tsinkewa bata fasa bin bayan Jamal ba.... Tafiya mai nisa sukayi tanayi tana lab’ewa jikin Gini har dai taga ya tura wani k’ofa ya shige... Ta sad’ad’o a hankali ta nufo k’ofar da taga ya shige...! Zuciyarta ne tayi wani irin tsinkewa sanda Ta hango Uncle d’inta Jamal tsaye gaban Muhibbah dake daure saman kujera kanta a kife a lamun takai mak’ura wajen jigata..! Akan idanunta Jamal ya d’auke Muhibbah da wata irin jahilar mari yana furta “Wake up..! Tashi munafuka it is morning already..!!” Muhibbah ta d’ago kanta da k’yar tana k’ok’arin bud’e idanunta sukai luhu luhu dan tsananin azaba, ga wane irin tsami da jikinta Ke mata, kwana a zarge saman wannan kujera da ko motsawa baka iyawa ba k’aramin azaba bane...! Jamal ya sakar mata murmushi yace “Good morning Beautiful..! How was your night..?! Na tabbata kinji dad’i...!” Wayar salulansa ne da tai ringing ta katsesa..! Ganin Giwa ce mai kiransa abin ya basa mamaki dan shida ita sunada wayan da su kad’ai suke kiran juna da... Toh ina ya bar wayan... Wata zuciya tace tsakanin asibiti zuwa d’aki.. Yana d’agawa ya soma fad’in “Maami nifa van samu naje jana’izan yaran Yazeed ba, na taho direct zuwa wajen yarinyar nan..! Kuma banaso na had’u da Ya Mahmood can wajen jana’izan..!” A hautsine Giwa tayi da fad’in “Kai Jamal ba wanne bane dalilin kiranka... Karka bar kusan yarinyar nan... Itace ta dawo..!!” Baiji mai tace ba network ya katse cikin sauri ya fice neman service... Hakan ya baiwa Zahra daman shigowa, a tsorace take duban Muhibbah dake zuban hawaye... Cikin rawar jiki ta isa da zummar kwance Muhibbah saidai babu hali domin kuwa da handcuffs Jamal ya d’aureta bada igiya ba babu key babu halin Ta kwanceta..! Ta d’ago a razane tana dubanta lokaci guda Muhibbah ke girgiza mata kai domin kuwa ta hango Jamal na dosowa... Take ta tuna sunyi Spanish classes da Zahra, Zahran ta koya mata wasu kalmomi daga cikin yaren... Sannan har Ta bata wani littafi na koyon yaren wanda ta tsinci wasu kalmomi ciki... A hankali take furtada Zahra cikin Spanish “Zahra, Pon tu mano dentro de mi camisa..!” (Zahra ki saka hannunki cikin rigana.) “Papel..!” (Takarda) Zahra ta gane kalman Papel takarda yake nufi da spanish.. Muhibbah taci gaba da fad’in “No tengas miedo..!” (Karkiji tsoro) “Solo haz lo que te digo..!” (Kiyi yanda nace) Zahra Ta jinjina mata kai a hankali kana tayi yanda Tace dukda tana Iya jin sautin sandar Jamal a bayanta alamun ya kusa cimmata..! Zahra ta ciro takardun Taswiran Muhibbah ta had’esu waje guda Allah yaso ruwan daka watsa mata bai jik’e cikin takardun ba sai gefe gefe... Muhibbah Tace “Esconderlo..!” (Ki b’oye).. Zahra Ta kuma jinjina mata kai a hankali kana tayi saurin turawa cikin rigarta...! Daidai nan Jamal ya k’araso ya finciko wacce yake gani tsaye gaban Muhibbah ta basa baya... Ga tsananin mamakinsa Zahra ya gani...! SameenaAleeyou📚 *MUHIBBAH* *73* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin wane irin sauti Jamal ya furta “Zahra..! Mai ya kawoki nan...? Ya ma akai kika shigo nan..?!” Zahra dake nan tsaye tana dubansa itama shaye da mamaki tace “Uncle I followed you here...! Wait what’s going on.. Why is she tied up..? Mai Ta maka Uncle..?!” Huci kurum Kamal keyi yana duban Zahra wacce itama idanu waje take dubansa... Lokaci guda ya kuma finciko hannun Zahra yana fad’in “You’re too young to understand Zahra.. Just come with your Uncle..!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin janyota.... Fincike hannunta tayi da k’arfin gaske tana fad’in “No Uncle I’m not leaving this place sai ka sanar dani mai ta maka ka d’aureta a nan..! Uncle you’re not a bad person right..!” Ta k’arashe cikin yanayin tsoro idanunta suna firfitowa waje... Jamal da ya gama k’osawa da yarinyar, k’ok’arin finciko hannunta yake yana fad’in “I said come with me Zahra, you talk too much...!!” Ya k’arashe yana mai damk’o hannunta da k’arfin gaske ya shiga janyota... Tarjewa take tana furta “Let go Uncle,You’re hurting me.. Let me go..!!” Inaa bai saketa ba saima kuma janyota da yake dad’a yi... Cikin yanayin gwari gwari dan yaren ba wai ya gama nuna a bakinta bane kalmomi take tunowa Ta samu Ta harhad’o su bada ma’ana, nan ta bud’e murya taceda Zahra “Morder su mano Zahra..!” (Ki ciza hannunsa Zahra).. “Y corre directo a tu Paa” (Ki gudu zuwa wajen Paa d’inki) Jamal bai daina janye Zahra ba yake waigowa yana duban Muhibba yana fad’in “You witch, what are you telling her..?!” A daidai wannan lokacin Zahra tayi amfani da damar tayi abinda Muhibbah ta fad’a mata, ta sunkuya ta had’e hak’waranta ta gantsarawa Jamal cizo.... Ya saki k’aran azaba lokaci guda ya saki sandarsa da hannun Zahra ya zube k’asa.. Zahra ta soma gudu tana fad’i da Muhibbah “No te preocupes, la tía mi papá vendrá a rescatarte, te lo prometo...!” (Kar ki damu Tia, Paa d’ina zaizo ya taimakeki... Nayi Alk’awari)... Ita dai Muhibbah idanunta naga Jamal dake k’ok’arin jan jiki yana rarrafawa ga sandarsa... Cikin tashin hankali take ceda Zahra “Ejecuta Zahra..!” (Ki gudu Zahra) “Y dale esos papeles a tu Paa..!” (Ki baiwa Paa d’inki takardun nan) Zahra da jikinta bai daina rawa ba lokaci guda take jinjina kai tana furta “Si segura le daré..!” (Eh K’warai zan bashi)... Cikin hawaye Muhibbah Ke furta “Te amo zahra..!” (Ina k’aunarki Zahra) Zahra da har ta kai k’ofa juyowa tayi cikin hawaye itama ta furta “Yo tambien te amo tia..!” (Nima ina k’aunarki Tia) Daga haka ficewa tayi a guje dai dai nan Jamal ya samu ya janyo sandarsa ya mik’e... Cikin wane irin bud’e murya yake dokawa Zahra kira... Saidai tinda Zahra ta fice take gudu hanya na had’e mata sam bata gane ta yanda suka shigo wannan wajen ba balle ta fice... Taja ta tsaya zuciyarta naci gaba da yankewa... Juyawa baya tayi ta kalli gabas ta kalli yamma kudu da arewa... Ko ta ina bata fahimci hanya ba.... Ga wasu irin jerin k’ofofi duka iri guda... Tana a haka ta soma jiyo sauti kaman na sandar Jamal alamun yana nufota... Zuciyarta ta kuma tsinkewa, nan Ta kuma daburcewa Ta rasa wane hanya zata bi... ** Tinda suka fito daga Janaza basu wuce Fada direct ba yanda aka bisne ‘ya’yan Yazeed a nan cikin Masarauta mak’abartan da ake busne ahalin gidan... Su sai basu k’arasa masarauta ba suka nufi wajen mutumin da suka bigesa a daren jiya, suna addua’n Allah yasa su samu ya farka... Turaki ne ya soma yin gaba Mahmood ya tsaya amsa kiran Likitan Yazeed dan tun daren jiya Yazeed d’in ya farka yake hauka, he couldn’t accept changes d’in da ya farka ya tarar tattaredashi...! Turaki kaw yana isa d’akin da aka kwantar da mutumin ya tadda sai sa’insa tsakanin likitan da mutunin ake... Mutumin yana fad’in “Look Dr, we have same profession.. You can’t detain me here, da hankalina nasan abinda nake...I’m leaving this place right this moment.. With or without your permission..!!” Ya k’arashe yana mai fincike drip d’in... Dr ya girgiza kai yace “Toh idan Kai likita ne bana tsammanin kasan aikinka... Maybe you’re a quack..!” A zuciye Ansar ya mik’e yana k’ok’arin shak’o wuyan likitan yake fad’in “What did you just call me..!” Daidai nan Turaki yai saurin k’arasowa yana k’ok’arin raba tsakaninsu... Likitan na huci yake furta “Yauwa yayi kyau da ka k’araso... Please ka d’auke mana wannan lunatic a nan, what he needs is a psychiatrist.. Wannan mutumin tinda ya tashi hauka kawai yake... Jiya an kawosa nan ruwa ruwa babu abinci a cikinsa babu komai yau yasha drip har ya samu k’arfin da zai bud’e baki yace yasan abinda yake shi likita ne... Ance maka zama likitan cin tuwo ne..! Take him away please..!!” Ansar ya kuma harzuk’a yana sakin huci zai kuma cakumo mutumin... Turaki yai saurin rik’esa yana basa hak’uri.. Shidai likitan tattara folder d’insa yai ya fice ya barsu nan cikin d’akin...! Turaki ya k’araso yana duban mutumin wanda goshinsa Ke mak’ale da bandage, ya mik’a masa hannu alamun musabaha yace “Yusuf Turaki..!” Da idanu kurum Ansar ke dubansa, kaman bazai mik’a masa hannu ba sai kuma ya mik’a sukai masabaha... Turaki yaci gaba da fad’in “Jiya mun bige ka a k’ofar masarauta sai mukai rushing d’inka to this hospital, bamu samu komai tareda kai ba, babu ID babu komai shisa bamuyi gaggawan kiran family d’inka ba... How are you feeling now...?!” K’ok’arin sa kai Ansar yake yana furta “Get out of my way... I need to save her..!!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin ficewa... Cikin sauri Turaki ya take masa baya dan ya soma yarda da batun Dr da yace wannan mutumin kwanyarsa ba’a saite yake ba, kuma sanda suka bigesa tafiya yake gaba gad’i saman kwalta ta yuwu da gaske ba mai lafiyar kwanya bane... Haka suka nufo dogon corridor na asibitin Turaki na biye dashi yana furta “Abokina tsaya ka saurareni, d’an tsaya ka saurareni.. Sanar dani inane gidan naku sai na kaika... Ko ka kawo lambar wani naka daga gida a kira...! Kanada mata ne..?!” A harzuk’e Ansar ya juyo yana furta “This is exactly why I’m here, to take my wife back...! Sun rabamu da k’arfi.. Muhibbah is mine..! Ita d’in tawa ce..! We were about to get married but they took her away from me...!!” Hawaye suka ci gaba da gangaro masa sanda yake furta “Sun cutar da ita..! Sun lalata mata rayuwa, hakan duk bai ishesu ba...! And now sun kuma zagayowa sunyi auren nunafunci da ita kawai dan su gama da ita, su kasheta... Na tabbata wannan dalili yasa suka zagayo suka bada dukiya suka sayeta dan kawai su kasheta... Nayi imani sun fahimci cewa Muhibbah itace SAUDATU yarinyar da ‘ya’yan Sarki suka lalata ma rayuwa 14yrs back..!!” Muryar Ansar yaci gaba da rawa yana duban Turaki dake tsaye tamkar statue a gabansa yake ci gaba da furta “Wannan Masarautar babu komai cikinta face zalunci..! Yes zalunci..!! They all deserve to die..! Ka fahimceni..!! Ka fahimceni yanzu.!!!” Ya k’arashe yana mai jijjiga Turaki dake tsaye tamkar gunki gabansa, cikin wane irin kuka Ansar ke jijjiga Turaki Wanda da gani kasan fitar da k’uncinsa da damuwarsa yake..! Ba Turaki da yayi mutuwar tsaye yana duban yanda Mutumin Ke kuka dirshan a k’Asa ba, harta Mahmood da tin isowarsa yake tsaye yana dubansu ji yayi jiri na neman kifar dashi k’asa..! Kalaman Fu’ad dana wannan mutumin suna buga k’wak’walwarsa dake barazanar tarwatsewa..! Da zaka d’aura hannunka kuwa a k’irjinsa zaka iya jin yanda zuciyarsa ke bugawa kaman zata b’alle ta fito daga cikin k’irjin nasa... A haka ya dinga jefa k’afafunsa har ya iso gaban Ansar, ya saka hannayensa biyu ya d’agosa, hawayen da baisan daga ina bane suna gangaro masa... Cikin wane irin rawar murya mai rarrabewa yake furta “What did you say..?! Tell me what you know about Muhibbah..! Tell me what you know about my wife..!!!” Ya k’arashe yana mai kuma dage k’arfinsa yana matse rigar Ansar wanda har ya soma b’arkewa sabida tsananin damk’a da Mahmood yai masa... Tashin hankali sosai ya bayyana a fuskan Turaki... Ansar ya gane Mahmood, ya gane shine Babban d’an Sarki AbdulJabbar wanda daga farko Muhibbah tai masa mummunan zato... Ashe shine kenan ya zago ya aure Muhibbah..! Shine Bak’on Buzu da yayita b’adda kama a cikin Masarautar, lokaci guda cikin tsananin huci Ansar ke furta “Yes your Highness..! You heard me loud and clear.. Your three Bastard Brothers raped Muhibbah when she was a Kid...! Ta girma da k’udirin dawowa wannan Masarautar to take her revenge.. Ko ince tayi zaton mahaifinta was somehow hidden cikin Masarautar... She thought harda Kai a cikin ‘yanuwanka da sukaci zarafinta suka d’aid’aita mata ahali... Suka tarwatsa rayuwarta, shiyasa taci alwashin kai wannan Masarautar k’asa by all means... She promised to take each and everyone of you down koda hakan zai zamto abinda zatayi na k’arshe a rayuwarta..! Taso tayi amfani da d’iyarka to ruin you sai ta fahimci kaid’in baka daga cikin wad’anda sukaci zarafinta suka d’aid’aita mata rayuwa...! Bayan ta had’aka fad’a da d’iyarka Ta zab’i Ta kuma dawowa Masarautar domin ta gyara abinda ta b’ata sabida kaid’in baka d’aya daga cikinsu... Dukda sanin had’arin dake tattareda ita na dawowa cikin Masarautar but still Ta zab’i Ta dawo tayi abinda ya dace, Ta zab’i ta dawo only for you and your daughter... To fix your relationship with your daughter...! That’s how much she loves your daughter..! Amma yanzu daka satota ka kawota cikin Masarautar ranan da ya kamata ya kasance ranan aurenmu nayi imani mugayen ahalinka bazasu k’yaleta ba har sai sunga bayan rayuwarta..!!!” Mahmood da jikinsa Ke tsananin rawa bai iya k’arasa sauraren Ansar ba yayi jifa dashi gefe guda ya fice a guje cikin wane irin tashin hankali... Turaki da shima har lokacin bai koma daidai ba ya kasa aminta da abubuwan da yaji, jin abin yayi tamkar wani a film... A guje yabi bayan abokinsa yana furta “Your Highness..!!! Mahmood..!!!” Inaaa tuni Mahmood ya fice... Ansar ma ya mik’e da k’yar ya biyo bayan Turaki...! ** Haka Zahra Ta mak’ale jikin wani gini ta k’unshe bakinta tana jin kuka na zuwa nata sosai, sai taji kaman sautin tafiyarsa ta wani wajen sai ta canza wajen b’uya a hankali tana mai kuma toshe bakinta da duka hannayeta biyu gudun kar kukan da take ya kufce ya fito, Ta rintse idanunta da k’arfin gaske wasu irin hawaye suka zubo nata sanda taji alamun gadan gadan ya nufo ta yanda take... Yana gab da cimmata dan har ya soma k’ok’arin tura k’ofar zanan da take mak’ale bayansa taji sautin murya kaman na Giwa tana fad’in “Jamal bamuda sauran lokaci Ina yarinyar take.. Ina Saudatu..!?” Jamal yace “Maami tana kulle a d’akinta... Yanzu zan k’arasa nai mata alluran..!!” Giwa Ta girgiza kai tace “Ka bar batun allura Jamal, dama itace gudan jinin da K’addarar Masarautar nan Ke wuyanta, itace wannan gudan jini tol da k’ofarta Ke bud’e a Fadan Sarauniya Tamuna, idan a yau d’in nan Tal’udu yayi abinda bai yi da ita a baya ba shikenan k’ofar zai rufe kaida ‘yan uwanka dole ku tabbata akan Mulkin gidan nan.. Mulki bazai tab’a kufce mana ba... Muje muyi sauri mu mik’ataga Tal’udu ya cika aiki Kaga matarka Umaima ta tsira..!!” Jamal na girgiza kai yake furta “But Maami Zahra tana nan a wajen nan, Ta b’ace min ban ganta ba, yanzu haka ita nake nema..!!” Giwa Ta zaro idanu waje tace “Jamal Zahra kuma..! Zahra fah kace..? Mai ya kawota nan.. Ya akai tazo nan..?!” Girgiza kai yake yana furta “I don’t know Maami..! She followed me..!” Giwa tace “K’yale batun Zahra ka shige muje kafin damarmu na k’arshe ya kufce mana..!” Jamal ya girgiza kai yace “Maami don’t underestimate that girl.. What if taje ta fad’awa Mahmood..?!” Giwa Ta buga Uban tsaki tace “Idanma ta fad’a masa bazai samemu ba dan muna Fadan Sarauniya tareda ita yarinyar, sannan abu ne mai matuk’ar sauk’i yanzu da muka samu k’ofar makullin Mulkinmu zai rufu ruff sai mu kashe Mahmooda harma da d’iyarsa kaga mun cire bare cikinmu tinda daga shi har d’iyar tasa ba jina bane.. Dama na gaji da pretending..! Shige muje.. Muyi sauri bamuda lokaci..!!” Ta k’arashe tana turasa Jakadiya na biye dasu... Hankalin Zahra yakai k’ololuwa wajen tashi...! Tana jin Sun wuce ta bud’e bakinta data toshe Ta fitar da kukan da ya kuma taso mata tin daga k’irji..! Kuka take tana mamakin badak’alan zalunci da aka jika anayi cikin Masarautar su... Babu abina yafi tsaya mata kaman jin muryar Giwa da tayi tana fad’in Mahmood da d’iyarsa ba jininta bane..! Ashe ba ita ta haifi Paa d’inta ba shisa tun can basa wani son juna irin yanda jika da Kaka Ke son juna... Wasu hawayen suka kuma gangaro mata tsananin tausayin Paa d’inta na kuma kama Ta....! Tunowa da halinda Muhibbah Ke ciki ya sanyata Saurin mik’ewa Ta nufo waje babu shiri tana kuma neman hanya... Allah kurum take ambato tana rok’onsa ya fitar da ita ta isa ga mahaifinta..!! ** K’iris ya rage bai had’ada masu tsaron k’ofar Masarautar ba, saida ya shige har tsakiyar farfajiyan Masarautar kana yaja wani irin burki... Zuciyarsa bata daina bugawa ba ya finciki marfin motar ya fito... A guje ya nufi b’angaren da ya ajeta, jama’an masarauta sai zubewa suke suna basa hanya cikeda mamakin yanayin da suka gansa ciki... Turaki da Barde harmada Ansar suka k’araso cikin Masarautar suma hankali tashe... D’aya daga cikin Kuyangi masu kulada b’angaren Muhibbah itace Ta soma hango Rankaidad’e cikin wane irin yanayi da bata tab’a ganinsa ciki ba...! Ta shige a guje tana fad’in “Hasiya..! Hasiya ki shirya ga Rankaidad’e..!!” Gaba d’aya Kuyangin sun rikice duk sun zuzzube a k’Asa zukatansu naci gaba da tsinkewa... Babu kaman Hasiya wacce Ke zaune saman gadon Muhibbah ta janyo alkyabba ta rufe fuskarta da ita, zuciyarta sai tsinkewa yake sanda taji Rankaidad’e ya turo k’ofar d’akin ya sako k’afafunsa ciki... Kai tsaye ya nufeta zuciyarsa bata daina tsinkewa ba, lokaci guda yakai hannunsa ya janye Alkyabban... Zuciyarsa tai wani irin tsinkewa sanda yaga ba Muhibbah bace..!! Fuskarsa Ta kuma rinewa zuwa ja haka nan idanunsa... Ga wane irin gumi da ya wanke masa fuska gaba d’aya sai d’iga yake... Ita kaw Kuyangar sai karkarwa jikinta keyi sabida tsananin tsoro tamkar zata had’iyi ranta... Mik’ewa yayi ya dafe kansa da duka hannayensa biyu dai dai lokacinda sauran kuyangin suka shigo kawunansu a k’asa... Shugabar tasu ce ta soma duk’awa tana furta “Rankaidad’e kai mana aikin Gafara...!” Cikin wane irin yanayi yake dubanta kana yace “Where’s my wife..?! Ina matata nace..?!!” Kuyangar jiki na rawa take furta “Allah shi taimakeka.. Munyi iyaka k’ok’arinmu ganin mun dakatar da ita amma tak’i tsayuwa..!” Bai daina huci ba yake dubanta lokaci guda yake furta “Wannan shine umarnin da aka baku..?! Nace wannan shine umarnin da aka baku..?! Wacece take nan sanda hakan ya faru..?!” Hannu na rawa d’aya ‘yar matashiyar ta nuna Hasiya da tuni ta silalo ta zube k’asa daga saman gadon..! Tana jin ya soma takowa zuwa gabanta Ta soma fad’i cikin tsananin rawar murya “Rankaidad’e kai min gafara wllhi babu yanda banyida Gimbiya ba amma ta had’ani da Allah tace rayuwarta na cikin had’ari a Masarautar nan ya zama dole ta gudu shiyasa mukayi musayen kaya ta saka nawa na Bayi gudun kar azzaluman da suke nemanta su kamata..! Rankaidad’e Gimbiya tayi nisa da Masarautar nan dan tun jiya bata nan..!” Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa, kenan da gaske su Giwa suna nemanta zasu halak’ata..! Ina Ta tafi..?! Bai tsaya nemo amsa ba ya nufo waje yanda ya tadda Ansar da Turaki.. Ansar na ganinsa ya k’arasa yana tambayarsa Ina Muhibbah.. Ko kallon arziki Ansar bai samu daga Mahmood d’in ba.. Saima duban Barde da yayi yace a rufe Kuyangin nan har sai an sami Muhibbah... Hakan yasa suka fahimci Muhibbah bata a cikin gidan...! Bai kuma bin takan kowa ba ya nufi b’angaren Giwa kaman zai kifa k’asa..! Saidai koda ya nufi b’angaren Giwa bata nan babu Jakadiya babu Zahra ma sai taron ‘yan karb’an gaisuwa irinsu matan Waziri Talba Madaki da dai sauran masu sarauta harda iyalan Wambai...! Cikin sauri ya fito ya nufi b’angaren Jamal tinda harda shi a case d’in..! Nan ma bai tadda kowa ba, yayi tunanin ko yana waje can wajen maza su Talba da su Liman da dai sauran masu sarauta dake cike a Fada dan karb’an gaisuwa da jajen abinda ya sami Yarima Yazeed... Yana k’ok’arin sa kai da niyyan ficewa ya sinkayo muryar mace daga upstairs alamun tana neman taimako... A hankali ya furta Muhibbah... Babu shiri ya nufi saman yana bud’e k’ofofi yake ambato sunanta...! Can saman gado ya hango Umaima ta gama jigata maganan ma da k’yar take..! Cikin tsananin sanyi jiki had’ida mamakin ahalinsa ya isaga Umaima ya hau kwanceta..! Yana kwanceta yake tambayar “Who did this to you.?!” Cikin kuka take sanar dashi duk abinda ya faru tin daga kan abubuwan da Muhibbah ta sanar da ita gameda Jamal har kamasu da Jamal d’in yayi ya d’aureta.. Bata kuma San ina yakai Umaima ba... Har kawo kiran Zahra da tai a waya duk saida Ta sanar dashi..! Cikin kuka daidai sanda ya ida kwanceta take fad’in “Yaya please you need to go after Zahra..! You need to save them both.. I’m sure idan Jamal ya ganta itama bazai barta ba..!!” Umaima bata ida magana ba Mahmood ya mik’e ya soma jada baya zuciyarsa na barazanar fitowa waje... Mutane biyu da sukeda matuk’ar mahimmanci a rayuwarsa suna hanun mahaukacin k’aninsa... Matarsa da kuma d’iyarsa suna hannun Jamal..! Lokaci guda yake girgiza kai yana kuma jada baya..! Take ya nufo downstairs yana ambaton sunan Jamal da k’arfin gaske..! Duk wanda yaci karo da Mahmood cikin Masarautar sai yasan babu lafiya.. Hanya kurum ake basa ana risinawa, duk wanda ya giftasa kuwa sai ya bisa da kallo.... Yana fitowa babban haraban Masarautar yayi wani irin k’ara cikin muryarsa mai amon gaske yana ambato sunan Jamal...! Can ya hangi Zahra ta nufosa a guje sai layi take alamun Ta jigata.. Fsukarta shar shar da hawaye take furta “Paaaa!!!” “Zahra..!” Ya furta zuciyarsa naci gaba da tsinkewa..! Zahra tana isowa ya tarota ta fad’o hannunsa dan k’iris ya rage bata zube k’Asa ba sabida tsananin tangad’i da take..! Mahmood ya shiga jijjigata yana kiran sunanta yana tambayarta Ina Jamal da Muhibbah..! Cikin kuka Zahra Ke. Furta “Paa you need to save her..! Her life is in great danger Paa..! Maami and Uncle Jamal zasu kasheta..! Paa I don’t want to lose her..!” Cikin tsananin rawar murya yake furta “No Zahra bazamu rasata ba kinji.. Tell me ta ina suke..! Talk to me Zahra... Fad’a min yanda suke..!!” Ya k’arashe yana jijjiga Zahra da har lokacin bata gama dawowa daidai ba.. “Paa bazan iya ganewa ba...! All I know kawai daga ta can ne yanda na fito..! Paa you need to hurry..!” Bai kuma tsayawa sauraren Zahra ba ya nufi yanda take nuna masa.. Turaki dasu Barde harma da Ansar da k’arasowarsu kenan sukabi bayansa... Turaki yaceda Barde yaje yazo da Dakaru a bazama nema cikin Fada...! Umaima da itama bata jima da k’arasowa ba suka rungume juna itada Zahra suna kuka sosai..! ** Bata kuma sanin meke faruwa ba tinda taga Giwa da Jamal a gabanta sai bud’e idanu tayi ta ganta cikin wani d’aki a wane irin waje... Ta ware idanunta da sukai matuk’ar mata nauyi tana k’arema d’akin kallo..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ta fahimci wannan d’aki, bayan shekaru goma sha hud’u da suka shud’e Ta fahimci d’akin.. Shine d’akin da ta farka ta tsinci kanta ciki bayan yaran Giwa sun lalata mata rayuwa.. Allah ya taimaketa Ta kub’uta daga hannun wani azzalumin mutumi mushiriki mummuna wanda sam baida kyaun gani...! Yau Gata nan Ta kuma tsintar kanta cikin d’akin bayan duka wad’annan shekaru..! Ta yuwu wannan shine K’addararta.. Koda ta gudu a baya yanzu gashi ta kuma dawowa bayan shekarun nan..! Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka gangaro mata..! Ta yunk’ura zata tashi taji inaa gaba d’aya a zarge take, irin d’aurin da akema abin yanka idan za’a yanka irin d’aurin akai mata..! Aka had’e hannuwanta da k’afafunta aka d’aure waje guda..! Bud’e idanun da zatai Ta hangi Giwa, Jamal harma da Jakadiya tsaye daga k’ofar d’akin suna dubanta..! Giwa ta kece da wani irin dariya yau d’in sanye take da bak’ar lkyabbarta na tsafi ga wani bak’in tulu gabanta harda wani jan fitila maici da jan wuta... SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *74* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin zuban hawaye take dubansu d’aya bayan d’aya zuciyarta na kuma karaya da tinanin watak’ila itakuma tata K’ADDARAR kenan ta mutu cikin wannan d’akin hannun wad’annan azzaluman... Ta lumshe idanunta hawaye suka kuma gangaro mata.. Cikin zuciyarta take furta “Ya Allah kada ka k’addara mutuwata hannun wad’annan azzaluman bayi naka..! Ya Allah ka kub’utar dani da buwayarka kar ka basu nasaran cutar dani..!” Bata ida ba taji Giwa tasa k’afa ta shureta... Tayi tsaye gaban Muhibbar had’ida k’ura mata idanu, lokaci guda ta shiga jinjina kai tana furta “Tabbas ke ce..! SAUDATU..!” Ta kuma sakin murmushi kana taci gaba da fad’in “Na tabbata kin gane d’akin nan..! D’akin da ya shekara goma sha hud’u a bud’e yana zaman jiranki, yau gashi kin dawo cikinsa kuma zaki dawwama cikinsa domin kuwa wannan d’aki Naki ne wanda aka ambacesa da sunanki Saudatu aka kuma rubuta saman Farin k’yalle, Ked’in kyauta ce ga Sarauniya, a yau Zata cika k’udirin ta ta kuma cika min Mulki na da gudan jininki..!!” Ta kuma kecewa da dariya..! Muhibbah da hawaye Ke gangaro mata take Ta soma furta “Allah bai baku nasara shekarun baya ba, Maiyasa kike tunanin zai baku nasara yanzu..? Maiyasa kike tunanin zaki tabbata kina zalunci..! Barin tuna miki idan kin mance.. Ni ce nan wacce na shigo rayuwarku na tarwastaku ba tareda kun ankare ba..! Kuma ni ce nan zan zamto silan tonuwar asirinki dake da muk’arabbanki... Zaki gani da sannu Ubangijina zai kawo min d’auki ya kawo wanda zai fiddani daga sharrinku..!!” Batakai aya ba Giwa ta d’auketa da muguwar mari.. Lokaci guda take furta “Babu wanda zai fitar dake daga wajen nan Saudatu, duk duniyar nan babu wanda yakeda mabud’in wannan gini... Mutum guda yake da mabud’in wannan gini kuma ya mutu.. Mabud’in wannan gini guda d’aya ne tak kuma an bisneta cikin K’undi da jimawa... Saudatu bazaki tab’a ficewa daga wajen nan ba... Nima kaina banida wannan mabud’in wanda ya adana wannan mabud’in har ya bar duniya bai mallaka min ba... An busnesa tareda k’undin cikin turb’aya....Tal’udu shi ya bani karatun tsafi da zanke biyawa ginin ya tsage min na shige.. Sannan ko Jakadiya da a kullum take min rakiya bata iya wannan karatun tsafin ba.. Gata nan ga Jamal ki tambayesu ya akai suka shigo wajen nan... Bud’e idanu kawai suma sukai suka gansu cikin wajen nan kaman yanda Kema bud’e idanu kurum kikayi kika ganki ciki..! Har abada babu wanda zai iya fitar dake Saudatu..!!” Ta kuma kecewa da wani irin dariya.. Muhibbah na murmushi take furta “Wanda ya fitar dani daga farko inada tabbacin shi zai kuma fitar dani..! Dashi nayi imani dashi na dogara, kuma na tabbata shine zai taimakeni..! Da sannu zai tona miki asiri, sannan ya k’asak’antar dake, zaki koma bakida wani daraja ko matsayi ta yanda k’ask’antaccen bawa sai ya fiki daraja cikin Masarautar nan..!” Bata kai aya ba Giwa ta kuma kwashe ta da wata mari.. Tana huci take nunata tana fad’in “Ke k’aramar maras kunya..! Na gama da iyayenki na gama da kaf zuri’arki balle ke..Tin daga Kan Kakanki Sarki Jamaluddeen na k’asar Benin wanda shine ya haifi mahaifinki Yarima Alfah d’an uwa ga Gimbiya Turai matar Sarki AbdulJabbar wacce na maidata Kuyanga a gidan Mijinta, mahaifiya ga ‘ya’yan Sarki guda biyu Yarima Mahmood wanda na maidashi nawa tin yana jariri domin na cika k’udirina akansa, da kuma Ja’afar wanda na maidashi d’an Bawa ya girma cikin k’ask’anci da bauta a gidan mahaifinsa a Masarautar Sa.. Dan haka ki sani gamawa dake abu ne mai matuk’ar sauk’i a gareni k’aramar Alhaki..!!” Ta k’arashe tana mai d’ago fuskar Muhibbah wacce ta shige rud’u sosai.. Bata fahimci mai wannan matar take fad’i ba gaba d’aya ta zama lost and confused..! Cikin wane irin yanayi take duban Giwa da idanunta da suka firfito waje tana jin kanta na juya mata... Giwa ta kuma kecewa da dariya tace “Nasan duk bakisan wad’annan labarun ba, bakida masaniya amma bazan bari ki tafi ba tareda kin sani ba... Zan baki labarin duk abubuwan da nayi ma zuri’arki tin daga tushe... Idan kika tafi a haka ba tareda kin sani ba kinci banza..! Gwara ki San komai, kisan duk abubuwan dana aikata kafin k’ofar d’akin nan ya rufe dake rufuwa ta har abada..!!” Ta kuma kecewa da muguwar dariya... Take Giwa Ta shiga labartawa Muhibbah duk abubuwan da suka faru tin daga farko, Dik wani k’ulli da makirci da tayi da lokutan da abubuwan suka faru da komai da komai..! ** A can asibiti wajen Yazeed kuwa bore da hauka yake ci gaba da yi, an masa alluran baccin ma kaman a banza don yana somawa allurar zata sakesa ya farka yaci gaba da ihu yana fad’in a dawo masa da hannayensa da yaransa... Ya dubi Waziri dake zaune gefensa dan tinda ya farka bai bar gefen Yazeed d’in ba...! Cikin wane irin huci yake ceda Waziri “Kai Old Geezer, Take me to the palace..! I want to see Mahmood, I want to rub it to his face... Ina so naga fuskarsa idan yaji cewa shid’in ba kowa bane d’an Baiwa ce k’ask’antacciya mai k’wacen mijin Uwargijiyarta..! Ka d’aukeni ka kaini Masarauta na sanar da Mahmood haka, ya daina jin kansa shid’in wani ne ko shi d’in yafi wani... Baifi kowa ba shid’in k’asaitacce ne d’an Baiwa... Baiwarma Ta wani Masarautar wacce aka sadakar da ita...! Ka d’aukeni Ka kaini nace... I can’t be the only loser..! Mahmood ma dole ya d’and’ani irin k’uncin dana d’and’ana... Na tabbata yana can yana murnan abubuwan da suka sameni..! Amma idan yaji asalinsa da tushensa zai fahimci cewa shid’in k’ask’antacce ne... Bawa bai dace da sarautar Masarautar mu ba... Gwara nakasasshe ya zamto Sarki akanka D’an Baiwa ya gaji sarauta..! Ashe abin a jini yake shiyasa ya k’are ya auri d’iyar bayi...! Toh yau d’in nan wllhi zaiji asalinsa koda zai had’iyi zuciya ya mutu ne..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da fidda huci..! Waziri dake faman muzurai zuciyarsa na tsinkewa ya soma fad’in “A’a Yazeed kai hak’uri dai har ka k’ara samun lafiya...!” Baikai aya ba Yazeed ya katsesa da fad’in “Kai Dattijo kayi abinda na umarceka idan kana son kanka da lafiya.. Har gobe nid’in sama dakai nake domin ni d’an Sarki AbdulJabbar ne... Ko a mafarki kada ka tab’a zaton zan kalleka matsayin mahaifi..! Tashi ka kaini masarauta idan baka so na k’arasa kashe kaina yanzu a asibitin nan..!!” Waziri ya had’iyi miyau da k’yar yana sab’a babbar riga cikeda daburcewa yake fad’in “Toh..Toh.. Toh ai Wato ai gani nayi ciwonka d’anye ne dukda cewa na rufe cikin bandeji..!” Yazeed ya katsesa da fad’in “Zakayi abinda na umarceka ne kokuwa...!!” Waziri ya kuma mik’ewa zunbur yana furta “A’a ba za’ayi haka ba Rankaidad’e..!!” Lokaci guda ya mik’e ya nufi k’ofa yana fad’in bari ya kirawo malaman asibiti su kwance ruwan da aka d’aura masa...! Bai kuma tsayawa sauraren Yazeed ba ya fice...! Yazeed ya shiga k’walla masa kira, inaa Waziri ko juyowa baiba dan ko kusa bazai biyema Yazeed su tapka wannan rashin hankalin ba... Domin kuwa ba asirin Mahmood zai tona ba asirin mahaifiyarsa zai tona...! Yazeed yaji zuciyarsa kaman zata buga Dan babu abinda zai iyayiwa kansa... Ya shiga shure shure da k’arfin gaske har dai ya samu ya finciki drip d’in dukda tsananin azaban hannayensa da yakeji... Amma dole ya daure koda jini zai b’alle a jikinsa ne sai yaje ya tunk’ari Mahmood ya tarwatsa zuciyarsa kaman yanda nasa rayuwar Ta tarwatse... Haka ya lallab’a ya sauk’o daga saman gado babu hannaye... Taimakonsa d’aya Waziri ya mance k’ofa a bud’e nan yabi ta k’ofar yana tafe yana ciza labb’a sabida tsananin azaban da hannayensa ke masa, zafin zuciya irin nasa da tsanar Mahmood bazai bari ya zauna a asibiti Mahmood yana can yana jubilating nakasan da yayi ba... A haka ya fito yana bin garu yana satan idon mutane har ya samu ya fito haraban waje... Nan ya iske Waziri na k’ok’arin shigewa Mota... Cikin sauri Yazeed ya nufi Waziri yana furta “Kai Oldtimer..! Kai Dattijo..!!” Waziri na k’ok’arin kutsa kai Mota dan baiyi zaton zaiga Yazeed ba, Yazeed ya k’araso yana hakin azaba lokaci guda yake furta “Kana jina wllhi ko ka d’aukeni ka kaini masarauta ko kaima na tona maka asiri kaci amanan amininka ka nemi matarsa har kun haihu... Kasan ni a halin yanzu I’ve got nothing to lose..! My whole life is already ruined... Abokin tafiya nake nema shiyasa zan fuskanci Mahmood na sanar dashi asalinsa..! Idan kana son kanka da lafiya, idan baka so ka tafi k’asa taredani da Mahmood, Toh ka d’aukeni ka kaini Masarautar nan,.. Kuma Kai banda abinka, idan naje Masarauta na tona asalin wanene Mahmood ai Kasuwarka ce Waziri, kaga watak’ila sarauta ta fice daga ahalin AbdulJabbar ta har abada Kaga shikenan ka samu tsuntsu a sama gasasshe... All thanks to your Bastard Son, at least ko ban maka noma ba na baka abinda yafi Gonakin ka da ‘ya’yanka suka jima suna noma maka..! Na baka sarautar k’asar baki d’aya...! Ko ya kace Old geezer.. Kaga watak’ila nayi recognizing d’inka as Uba..!!” Ya k’arashe muguwar murmushin nan nasa saman fuskarsa... Waziri ya shiga Washe baki yana furta “Allah koh Yarima..! Kuma fah kaima ka kawo wani shawari... Idan na zama Sarki shikenan batu yayi dad’i, duk Sadaukarwa da mahaifiyarka tayi bai tafi a banza ba..! Shige muje..!” Ya k’arashe yana mai bud’e ma Yazeed d’in marfin Mota.... ** Neman duniyar nan cikin Masarautar sunyi babu Giwa babu Muhibbah balle Jamal ko Jakadiya..! Babu su Babu alamunsu... Idan Kaga Mahmood dole ka tausaya masa, gaba d’aya ya fice hayyacinsa harta Ansar saidai yasha mamakin kalan tashin hankalin da Yarima Mahmood ya shiga na rashin ganin Muhibbah... Ko shi da yake ikirarin yana sonta sai yaga nasa ashe wasan yara ne..! Saima ya soma tuhumar kansa anya yana sonta kuwa..? Ji yayi kaman ba soyayya yake mata ba tinda yaga yanda Yarima Mahmood ya gama susucewa cikin Masarauta na rashin ganinta da tinanin halinda zata iya kasancewa ciki..! Allah ya gani Mahmood d’in sai ya basa tausayi sanin cewa ahalinsa ne suka cutar da matar da yake matuk’ar so irin haka... Anyi searching anyi anyi babu su babu alamun su, idan aka soma tunanin dakatawa da nema Mahmood d’in yakan ce babu mai hutawa koda gari zai rufe ya kuma wayewa ne sai an zak’ulo yanda suke cikin Masarautar..! Turaki ya dafe kansa kurum yana duban Mahmood d’in dake Ta k’ok’arin tokarin wani k’ofa da iyaka k’arfinsa wanda shida Turakin ne suka k’araso wajen..! Bai sarara ba saida yaga ya bud’e k’ofar..! Suka ja sukai turus shida Turaki ganin kujera ajiye daga center Babu kowa akai sai handcuffs da sauran busasshen jini... Cikin sanyin jiki zuciyarsa na bugawa ya isaga Kujerar take ya zube ya duk’a saman gwiwoyinsa ya d’aga handcuffs d’in yana juyawa yana kallo... Turaki ma ya k’araso yana kallon kayan mamaki.. Da gaske dai mutanen nan bak’ak’en azzalumai ne.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Can ya hango hawaye daga idanun Mahmood suna d’agowa... Baida daina juya handcuffs d’in ba yake furtawa cikin tsananin rawar murya “They tortured her..! Sun azabtar da ita Turaki...! They’re not humans..! Ta yaya d’an adam zai aikata haka..! Kodai akwai laifin da nake aikatawa ne Allah ya jarabceni da irin wad’annan ahali..! Tell me Turaki..! Please tell me..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Turaki ya dafasa yace “Mahmood kowa da irin jarabawarsa a rayuwar nan, wani a jarabcesa Ta iyalansa wani ta ahalinsa, wani ta wajen sana’arsa.. Wani ma da lafiyarsa za’a jarabcesa.. Duk dan a gwada k’arfin imaninmu..! Kada ka kauce hanya your Highness..! Ubangijinka yana gani kuma baya bacci da sannu zai kawo maka sauk’i iftila’in da ya Aiko maka..! Tashi muje.. Watak’ila sun fitar da ita daga cikin Masarautar nan muyi saurin cimmasu..!!” Yai k’ok’arin mik’ar da Mahmood d’in suka nufo waje dukda shi kansa Turakin baisan Ta inda zasu kuma nufa ba..! Rik’o hannun Turaki Mahmood yayi yace “Kana tunanin sun kashe Muhibbah..?!” Yayi maganar cikin tsananin rawar murya.. Turaki ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali, dan duk abinda zai fad’iwa abokin nasa a halin yanzu yasan k’arya ne, amma babu yanda ya Iya Mahmood yana buk’atar a kwantar masa da hankali a kuma nuna masa akwai hope..! Nan Turaki yaci gaba da basa k’warin gwiwa yana nuna masa kada ya karaya da izinin Allah Muhibbah tana nan da rai kuma zasuyi rayuwa mai tsawo nan gaba tare..! A tare suka nufo yanda suka baro su Ansar da sauransu, jikkunansu a matuk’a sanyaye daga Mahmood d’in har Turakin tun bayan da sukaga wajen dasu Giwa da Jamal suka aje Muhibbah... Izuwa wannan lokaci cikin Masarauta ta gama rikicewa gaba d’aya, kama daga b’angaren masu sarauta har zuwa b’angaren bayi.. Zancen kenan guda d’aya ake.. Masu mamaki nayi masu jimami nayi... Illahirin Masarautar tausayin halinda Mahmood ya tsinci kansa ciki suke..! Su matan Wambai kuwa sai jinjina lamarin suke masu k’ara gishiri da onga nayi.. Harda masu cewa Giwa ce ta cinye ‘ya’yan Yarima Yazeed Wai mayya ce, ita ta cinye matar Mahmood ta cinye mai Martaba harma da Wambai itace Ta cinyesa Ta kuma cinye k’afar Jamal guda Ta cinye hannayen Yazeed..! Juwariyya d’iyar Wambai da itace takaiwa su Raheema da Gimbiya Zeenatu labari gaba d’aya tsoron al’amarin ya gama cikasu.. Gimbiya Zeenatu jikinta yafi na kowa yin sanyi, zataso Ta sami Mahmood Ta sanar dashi yanda ta rufe asirin Giwa na kashe matarsa da tayi dan kawai k’anwarta Raheema Ta aure Mahmood d’in, akan idanunta Giwa Ta halak’a Matar Mahmood, Ta kuma ce ta halak’ata ne dan Mahmood ya auri k’anwar Zeenat d’in Raheemah... matuk’a Aliya nada rai tasan d’anta Mahmood bazai tab’a kallon wata mace ba balle ya aureta, Anya bazat sami Mahmood Ta sanar dashi gaskiyar batun ba..? Ta k’arashe tunanin nata tana mai mik’ewa tsaye cikin tsananin sanyin jiki.. Juwariyya dake ci gaba da labartawa Raheema yanda abubuwan suka kasance dakatawa tai suna duban Gimbiya Zeenat da Ta mik’e jiki babu k’wari..! Raheema tace “Aunty Ina kuma zakije.. Kinaji ance cikin Masarauta babu lafiya Dakaru ne ta ko ina.. Salon Ki fice wani tsautsayin ya ritsa dake, Allah ya gani Masarautar nan ya soma bani tsoro asubahin fari gobe zan tattara na koma Masarautar mu saidai duk abinda za’a fad’i a fad’i..!” Gimbiya Zeenat da har lokacin jikinta a matuk’ar sanyaye yake tace “Raheemah Mahmood nake son gani akwai abinda nake matuk’ar son sanar dashi.. Gwara na sanar dashi bazan iya ci gaba da rik’ewa a cikin zuciyata ba..!!” Ta k’arashe tana mai rufa alkyabbarta ta nufi k’ofa... Raheemah na kiranta inaa ko tsayawa batai ba.. Juwariyya Ta dubeta tace “Ahtoh dai ki tafi ki bar Masarautar nan kafin ta iso kanki..!” Raheemah Ta dubeta da mamaki tace “Ban gane ba..?! Wai mai Giwan tayi yanzu ake nemanta haka..?!” Juwariyya ta tab’e baki tace “Tabb! Yanzu ne duk labarin da nake baki ina hankalinki yake..! Ance miki ta sace matar d’anta zata cinye..!” Raheemah ta girgiza kai tace “Ban fahimceki ba..! Wai kina nufin Zuhra..! Zuhra kam ai tana asibiti inji..!” Juwariyya Ta dubeta shek’ek’e tace “Wata Zuhrar..! Ana miki maganan matar Yarima Mahmood..!” Mamaki ya kuma kama Raheemah..! “Matar Yarima Mahmood fah kikace..? Yaushe Mahmood d’in yayi auren..?!” Juwariyya Ta yab’e baki tace au ashe fah bakida labari kina nan kina jimamin rashin aurensa da bakiyi ba, gashi kin kasa zuwa asibiti kiga yanda mijinki Yazeed ya koma...!” Cikin tashin hankali Raheemah ta katseta da fad’in “Ke ni k’i k’yaleni da zancen Yazeed, duk halinda ya tsinci kansa ciki ba matsalata bace tinda shine ya jefa kansa ciki..! Tambayarki nake shin Yariman nawa shine yayi Auren...Mahmood ne yayi aure...? Yaushe kuma a ina..?!!” Ta k’arashe idanunta na firfitowa waje hannuwa dafe da k’irji...! Juwariyya da tai sakare rana dubanta jinjina mata kai tai tace “K’warai kuwa Rankaidad’e yayi aure, ranan da ya d’aura miki aure da Yazeed ranan yayo aurensa shima...! A yanda naji labari na Yawo cikin Masarauta babu wanda yasan yayi auren sai abokinsa Turaki da Hadiminsa, ke ko Giwa bata sani ba, naji ana cewa ya b’oye mata auren gudun kada Ta lashe masa matar tasa ne kaman yanda ta lashe matarsa ta farko, Aiko gashi data fahimci yayi auren Ta lashe sabuwar amaryar tinda babu wanda yasan k’anda suke yanzu.. Labari fah nata Yawo cikin Masarauta gashi ance Sosai Rankaidad’e ya rikice da neman matar tasa da alama yana matuk’ar k’aunarta..!!” Gaba d’aya Raheemah bama Ta gane mai Juwariyya Ke fad’I saima hawaye dake k’ok’arin ambaliya a fuskarta..! Babu shiri Ta mik’e ta nufi waje cikin kuka..! Juwariyya Ta mik’e tabi bayanta tana kiran sunanata...! Inaa Raheema bata tsaya ba burinta kawai ta isaga Mahmood ta tabbatar da gaske aure yayi ta kumaga matar da ya aura... ** Ana tsaka da wannan kwanacala Yazeed ya iso Masarauta.... Ganin yanda ake satan kallonsa ana k’usk’us cikin Masarautar sosai ya kuma tunzura Yazeed, Wato yanzu ya zama abin nunawa da baki.. Wasu bayi da suka kasa janye idanunsu daga barin duban nasa suka kuma kasa duk’awa gabansa wane irin tsawa ya darara masu yana fad’in Shine Yarima Yazeed wanda ya kuma cancanci gadon mulki ko ba’a sarki maras hannaye za’a soma a kansa..! Shidai Waziri gaba d’aya yasha jinin jkinsa da ganin yanda Masarautar take a hautsine.. Duk basu kawo komai ba dan duk sunyi zaton dalilin tsautsayin da ya afkawa Yazeed da iyalansa ne Masarautar Ke yamutse... Duk wanda yaga Yazeed sai ya kuma dubansa kafin ya risina... Sai sakin huci Yazeed yake yana ayyanawa cikin ransa duk Mahmood ne ya janyo, da ace ya auri Raheemah Sun tafi k’asar Spain duk da hakan bata faru dashi ba, da yanzu hannayensa da ahalinsa duk suna nan, wani irin tsanar Mahmood d’in ya kuma tokare masa k’irji... Inama yanada hannuwa biyu da ya shak’e Mahmood a yau ya mutuwa ya huce takaicin ganinsa a doron k’asa... A daidai mashiga babban k’ofar da zai sadaka da cikin Masarauta su Yazeed suka had’uda tawagar Mahmood.. Da alama ficewa neman su Giwa zasuyi... Gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen suka maida dubansu ga Yazeed wanda tuni ya isa gaban Mahmood yana mai sakin huci... Waziri yana k’ok’arin sallaman wad’anda ba ahalin gidan ba Yazeed ya bud’e murya yace kowa ya tsaya, ayi a gaban kowa susan wanene Mahmood..! Shi kuwa Mahmood kalaman Ansar ke ci gaba da buga zuciyarsa cewa ‘yanuwansa su suka lalata rayuwar Muhibbah, ya tuna Fu’ad ya sanar dashi Yazeed ne ya soma..! Zuciyarsa taci gaba da bugawa musamman da yaga Yazeed tsaye gabansa... Sai dunk’ule hannayensa yake yana murzasu wani irin gumi na tasowa tun daga tsakar kansa yana bin goshinsa har zuwa saman karan hancinsa yana gangarowa... Ji yake idan ya rik’e wuyan Yazeed tabbas zai iya kaisa lahira... Muryar Yazeed d’in suka sinkaya yana furta “Kaji dad’i..! Nace kaji dad’I Mahmood..!! Yanzu da kake ganin sarauta takace kai kad’ai dan ba’a Sarki muskini..! Idan ba’a Sarki muskini Toh ka sani ba’a sarki k’ask’antacce...! Yes na fad’a ba’a Sarki k’ask’sntacce, jinin Bauta wanda bai gaji komai ba face Bauta..!!” Mamaki ya cika fuskokin mutane da jin irin kalaman dake fitowa daga bakin Yazeed...! Lokaci guda Yazeed d’in ya juyo yana duban mutane kana yaci gaba da fad’in “Jama’an Masarautar nan a yau d’in nan inaso na sanar daku ko wanene Yarima Mahmood da wasunku suke masa lak’abi da Sarki mai jiran Gado...! Ina son kowa ya shaida cewa Shid’in ba kowa bane face k’ask’antaccen Bawa..! Mahaifiyarsa Baiwa ce ga matar Sarki Gimbiya Turai..! Mahaifiyarsa Hadima ce da Gimbiyar Turai tayi tukuici da ita ga mahaifina Sarki AbdulJabbar mai rasuwa..! A tarihin Masarautar nan d’an Baiwa bai tab’a mulki ba sai d’an Sarauniya..! Wannan dalilin ya tabbatar cewa Mahmood bazai tab’a gadon Karagar mulkin gidan nan ba..!!” Ya k’arashe yana mai sakin huci yana kuma duban Yarima Mahmood wanda jikinsa Ke sakewa a hankali, hannunsa dake faman dunk’ulesu yana waresu a hankali alamun ya shiga tsananin Shock da abinda yakeji na fitowa daga bakin Yazeed d’in... Ganin haka yasa Yazeed d’in ci gaba da fad’in “K’warai..! Ina so kowa ya shaida cewa ba mahaifiyata Gimbiya Turai bace ta haifi Mahmood Hadimarta ce k’ask’antacciya da taci amanan Uwargijiyarta ta haifo Mahmood.. Wannan magana da nake sanar daku Gimbiya Turai kuma Giwar Amale da bakinta Ta sanar dani sabida zuwan irin wannan rana..! Mahaifiyata bata haifi d’an Sarki Mahmood ba... Inada k’wak’warran shaidu da zasu tabbatar da hakan..!” Cikin tashin hankali Talba ya katsesa da fad’in “Kai Yarima, kana cikin hayyacinka kuwa kodai had’arin da kayi ya tab’a maka kaine.. Ka kuwa San abinda kake fad’i..?!” Yazeed ya karkato yana duban Talba kana yace “K’warai kuwa Talba..! Da hankalina tsaf nasan abinda nake fad’i..! Kuma idan kuna ganin k’Arya nake zan gabatar maku da shaidun da zasu tabbatar cewa Mahaifiyata Giwa ba itace Ta haifi Yarima Mahmood ba, shid’in d’an Baiwarta ce kuma k’ask’antacciya ..!!” Cikin sakin huci da jin zafin abinda Yarima Yazeed keyiwa d’an uwansa a bainar jama’a Talba ya bud’e murya yace “Su waye shaidun da kake magana akai Yarima Yazeed..! Su waye zasu tabbatar da k’arerayin da kake fad’i..?!” Kafin Yazeed yakai ga bada amsa suka sinkayo wata murya mai amon gaske tana fad’in “Ni ne nan zan bada shaida..!!” Gaba d’aya suka juya suna duban wanda yayi magana cikin tsananin Shock.. Harda Yazeed d’in wanda yake yunk’urin nuna Waziri a matsayin shaida..! Ga tsananin mamakinsu suka zuba wa mutumin da yayi magana, sanye yake cikin shiga irinta Mulki, yayi tsayuwa irin yanda masu Mulki keyi..! A hankali Mahmood ya furta “JAFAR..!!”Koda ace ya sanya tufafi irin na masu mulki tabbas kamanninsa bai b’ace ba..! Mamaki da aljabi ya cika illahirin jama’an dake wajen sanda Ja’afar ya soma takowa cikin haraban Masarautar..! Mutane sai darewa suke suna basa hanya, wasu na k’ok’arin guduwa ganin Tamkar Fatalwa ne a gabansu.. Babu kaman Waziri wanda tuni fitsari ya cika mararsa.. Kai tsaye gaban Mahmood Ja’afar ya isa ya tsaya su duka biyun suna duban juna cikin idanu... Wani irin duba Jafar keyiwa Mahmood d’in kalman Yazeed na Yawo a kwanyarsa cewa Giwa ba itace Ta haifi Mahmood ba, mahaifiyarsa Hadimarta ce..! Wato mahaifiyarsu d’aya kenan, ya shiga tuno abubuwan da mahaifiyarsa Ta sanar dashi wanda Giwa tai mata..! Kenan Yarima Mahmood shine Babban d’a ga Mai Martaba wanda Bokan Giwa yace sai an haifosa duniya..! Kenan sace Yarima Mahmood tayi Ta rabasa da mahaifiyarsa kaman yanda Ta sacesa shima..! Lokaci guda yaji hawaye na neman ciko idanunsa.. Gashi ga d’anuwansa wanda suka fito ciki guda...! Shima Mahmood d’in wane irin duba yake ma Ja’afar d’in, sai yana ganin kaman ya tab’a ganin Ja’afar d’in da irin shigar da ya gansa ciki yau... Cikin wane irin murya mai raunin gaske ya furta “Ja’afar..!!” Hawayen dake mak’ale cikin idanun Ja’afar suka gangaro..! Lokaci guda ya rungume Mahmood d’in hawaye naci gaba da gangaro masa..! Mamaki ya kasa sakin d’aukacin jama’an dake wajen... Tirk’ashi..!Wannan shine ana wata ga wata..! Waziri da ya tabbata Ja’afar yake gani raye a gabansa cikin dabara ya soma k’ok’arin silalewa yana neman hanyar da zai fice daga wajen..! Gudu gudu ya soma jada baya yana k’ok’arin tattare babbar rigarsa, kaman daga sama yaji ya bangaji mutum har rawaninsa na zubewa k’asa. D’aga kansa da zai yaga ba kowa bane face Ubandoma..!! SameenaAleeyou *MUHIBBAH* *75* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ubandoma ya sakarwa Waziri murmushi maiji da lafiya had’ida furta “Rankaidad’e..! Mai girma Wazirin Wazirai..!!” Waziri bai iya amsawa ba saima muzurai da yake ci gaba da yi...! Lokaci guda yaci gaba da ‘yan waige waige kana ya had’e hannayensa biyu waje guda yana duban Ubandoma yake furta “Dan Allah.! Dan darajan manzo salallahu alaihi wasallama... Kayi min sutura kaman yanda Allah yayi maka, ka rufa min asiri...!!” Ubandoma ya kuma murmusawa yana azawa Waziri rawaninsa akai yake furta “Haba Mai Girma Waziri..!!” Waziri ya katsesa da fad’in “Banida wani girma wllhi..! K’ila ma ka fini girma a halin yanzu..!!” Ubandoma ya girgiza kai yace “Yau nida nake duk’a maka kaine kake duk’a min Waziri..? Tabbas na yarda da hausan da ake cewa RUWA YA K’AREWA D’AN KADA..! Ruwa ya k’are maku Waziri bakuda wajen guduwa... Watan tonuwan asirinku da duk wani mummunan aiki da kuka jima kunayi cikin Masarautar nan ne ya tsaya...! Shige muje ai bazaka bar cikin Masarautar nan ba sai ka bada shaidar cewa ba Giwa bace Ta haifi Yarima Mahmooda kaman yanda Yarima Yazeed yace..!!” Ya k’arashe yana mai dank’wafo Waziri dake kuma duk’awa yana d’ago hannu yana rok’on Ubandoma ya rufa masa asiri..! Ubandoma ya shiga janyo Waziri yana furta “Da ka tuna haka tinda wuri ka rufa ma kanka asiri kayi abinda ya dace da bai kawomu ga wannan munzani ba..! Ka sani Waziri kaida kanka ka toni asirin kanka babu wanda ya tona maka asiri..! Shige muje..!!” Ya k’arashe yana mai kuma hankad’o Waziri... Rik’e gaskiya domin itace take fitar da tsirrai har tayi ‘ya’ya... K’arya fure take bazata Tab’a yin ‘ya’ya har a amfana da ita ba...! Ba’a tab’a cewa gaskiyarka Ta k’are saidai ace k’aryarka Ta k’are... Babu k’ask’antacce sai wanda ya k’ask’antar da kansa... Yau ga Waziri yana duk’awa gaban Bawan da a baya shi yake duk’a masa dan asirinsa ya rufu... Allah ka rabamu da jin kunya duniya da lahira Ameen..! Cikeda isa da gadara Yazeed ya dakatar da Ja’afar da fad’in “The drama is over kai k’ask’antacce Bawa..! Idan ma banda lalacewa Ta yaya za’a ce Basarake yana rungumar Bawa..! Wannan ya tabbatar da abinda nake fad’i cewa Mahaifiyata ba ita ta haifi Mahmooda ba, shid’in jinin Bauta ne gashi nan kuna gani Bawa d’an uwansa na rungumarsa... Watak’ila sud’in sun had’a jini.. Wannan shine kuke so ya zamto Sarkinku..! Ace Sarki yana rungume rungumen bayi..?! Wace masarauta ce kuka tab’a ganin anyi haka..! Lallai lalacewa yakai lalacewa..! Har abada jinin Bauta bazai tab’a mulkanmu ba..!” Ya k’arashe yana fidda huci... Daidai nan Ja’afar da idanunsa suka gama kad’awa ya juyo ya Yazeed yana takowa gaba garesa cikeda izza da isa shima wanda sam baisan yanada irinta ba, nan yake furta “Tabbas kayi gaskiya mud’in ‘yan uwan juna ne wanda suka fito ciki guda..! Tabbas kayi gaskiya shid’in bai fito daga tsatson mahaifiyarka ba ..! Tabbas kayi gaskiya jinin Bauta bazai tab’a mulkin Masarautar nan ba..! Wanda hakan ya tabbar da kaid’in har abada bazaka tab’a d’ale Karagar mulkin gidan nan ba a matsayinka na D’AN BAIWA..!!” Ya k’arashe yana mai matso da fuskarsa dab na Yazeed zuciyarsa naci gaba da wane irin tafarfasa...!! Yazeed d’inma da wasu irin idanu yake duban Ja’afar d’in yana jin inama yanada hannuwa ya shak’o wuyan wannan bawa ya saka sa a yanda ya kamacesa..!! Cikin tsananin huci Yazeed Ke furta “Kai k’ask’antacce Bawa..! Wa ya baka daman ka gaya min maganganu haka..! Kai har ka isa ka kira Mahaifiyata da Baiwa.. K’ask’antacce kaman Kai..!!!” Muryar Ubandoma Yazeed ya sinkaya yana fad’in “Waziri shi zai tabbatar da abinda Yarima Ja’afar yake fad’i..!!” Gaba d’aya mutanen dake wajen suka shiga juya sunan da Ubandoma ya kirawo Jafar dashi.. Yarima Ja’afar..! Yarima Ja’afar dai..! Shin yaushe Ja’afar ya zamto Yarima..? A Iya sanin kowa JA’AFARU D’an Bawa ne wanda bai gaji komai ba sai Bauta toh a ina ya samo title d’in ‘ya’yan Saraki..!! Da tsananin mamaki Yazeed yai k’ok’arin kaikaitowa yana duban Ubandoma dake tafe tareda Waziri wanda ko d’aga Kai baiyi..! Shikam Mahmood badon Allah ya taimaka yanada k’arfin zuciya ba tabbas da tuni ya silale k’asa sumamme da irin abubuwan da yake gani suna faruwa gaba gareshi wanda yafi kamanceceniya da ire iren mafarkan da yake..! Yazeed ya dubi Ubandoma ya dubi Waziri..! Ubandoma ya kuma duba yace “Kai k’ask’antacce Bawa..! Ka kuwa San abinda kake fad’i..?!!” Ubandoma ya risina gaban Yazeed yace “K’warai Rankaidad’e abinda nake fad’i gaskiya ne..! Mai girma Waziri shi ne zai bada shaida..!!!” Wane irin k’asaitaccen murmushi Yazeed yayi ya dubi Waziri yace “Waziri inaso ka k’aryata wad’annan mak’aryatan a bainal jama’a..! Ina so ka bud’e baki ka bada shaidar cewa Mahmood d’an Baiwa ce bai gaji sarauta ba..! Domin kuwa D’an Bawa baya sarauta..!! Ina so ka bud’e bakinka Waziri ka sanar da d’aukacin ahalin Masarauta yanda Hadimar Mahaifiyata Ta yaudari Mai Martaba ya fad’a tarkonta har Ta haifo masa d’ansa Mahmood..!!” Shidai Waziri banda rawa babu abinda jikinsa keyi, ga wane irin gumi dake tsartsafo masa babu k’akk’autawa..! Gaba d’aya saima silalewa saman gwiwoyinsa da yayi...! Al’ajabi ya kuma cika mutane, Yazeed ya tsaresa da idanu yana mamakin yanda ya zube k’asa yana mai farawa da neman gafara..! Lokaci guda Waziri yaci gaba da furta “Nidai amin aikin gafara..! Wllhi sharrin shaid’an ne da kuma sharrin zuciya had’ida rud’in duniya..!!” A wane irin zuciye Yazeed ya katsesa da fad’in “Kai Old man ba wannan aka tambayeka ba..! Babu wanda yace kayi ma kanka tonan asiri..! Ba asirinka nace ka tona ba..! Asirin Mahmood nace ka tona..! Ka tona asirin Mahmood kowa yasan shid’in d’an Baiwa ce k’ask’antacciya..!!!” Ya k’arashe yana mai shure Waziri da k’afafunsa..! Waziri da tuni ya ciro rawani ya nad’eta kan hannunsa, cikin rawar murya yake furta “Duk abinda Yarima Jafaru ya fad’i gaskiya ne babu k’arya ko d’aya cikinta..! Dashi da d’an uwansa Yarima Mahmooda Sune ‘ya’yan Sarauniya Turai kuma Giwar Amale ta asali..! Wacce kuka sani a matsayin Sarauniya Turai ba ta gaskiya bace... Hadimarta ce ta sace komai nata, ciki harda mijinta da kuma ‘ya’yanta guda biyu... Yarima Mahmood Ta maidasa nata don ta kashesa a gaba..! K’udirinta shine Bokanta ya sanar da ita cewa duk d’an Sarki da ya soma mulki zai mutu shiyasa Ta dage sai Yarima Mahmood ya soma hawa mulki..! Ta tilasta masa dawowa daga k’asar sifaniya Kawai domin Ta cika burinta akansa..! Shi kuma Ja’afaru Ta canzasa da d’an Bawa Almu, Ja’afaru d’an mai Martaba ne.. A lokacin da ta fahimci Ja’afaru ka iya sanin wani abu sai ta nemi rayuwar Jafaru wanda hakan ya sanyashi guduwa daga Masarautar..!” Muryar shi na rawa yaci gaba da furta “Mun fahimci Mai Martaba yasan gaskiya duk abubuwan da suka faru dashi sabida wasik’a da muka tsinta wanda matar Mahmood Aliya Ta bar masa, cikin wasik’ar ba komai bane face duk wasu abubuwa da Giwa tayi wanda mahaifiyarta Ta sanar da ita a lokacin da tazo barin duniya..!” Ya d’ago yana duban Mahmood wanda ya koma tamkar bashi a wajen kana yaci gaba da fad’in “Idan baka mance ba Rankaidad’e, ka kawo ziyara k’asar nan bada jimawa ba aka tura sak’on mutuwar mahaifinka..! A wannan kawo ziyarar da kayi a lokacin Aliya Ta rubuta wannan wasiya fa mai Martaba Wanda Mahaifiyarta da ta kasance Hadima ga mahaifiyarka Gimbiya Turai ta asali itace ta sanar da ita domin kuwa Mahaifiyar tata a gabata komai ya faru duk abubuwan da suka faru da Gimbiya da yanda aka salwantar da ‘ya’yanta...!” Zuciyar Mahmood taci gaba da bugawa yana tuna tun bayan da suka kawo ziyarar da Waziri yake fad’i bai kuma gane kan Aliya ba har kawo zuwansu sanda Mai Martaba ya rasu wanda a lokacin itama aka tsinci gawarta a d’aki..! Ashe Giwa ce ta kasheta sabida tasan wani dark secret nata..! Turaki dake jin abin kaman a shirin finafinai, saurin tsayawa a gefensa yayi dan yasan komai ka iya faruwa dudka k’arfin zuciya na abokin nasa..! Abu ne mai matuk’ar tayar da hankali komin k’arfin hali da mutum yakedashi..! Ta yaya za’ace matar da ka girma ka santa matsayin mahaifiya k’arya ta jima tana shera maka tsawon rayuwarka...! Babu komai cikin Rayuwar face k’Arya da zalunci..!! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!! Muryar Waziri ya sinkaya yana mai ci gaba da furta “A lokacin da kuka Zo k’asar sanda mahaifinka Sarki ya rasu a lokacin Giwa Ta fahimci cewa matarka Aliya ita ta sanar da Mai Martaba ta hanyar ajiye masa wasik’a.. Kuma kaima zata iya sanar dakai shiyasa ta kasheta..!!” Baikai aya ba yaji sauk’an naushi ta ko ta ina Yazeed dake tsananin kuka yana naushinsa da duka k’afafunsa yake furta “K’arya kake..! Mahaifiyata itace Gimbiya Turai..! K’arya kake Mahaifiyata Gimbiya ce kuma sarauniya ce..!!! Ka bud’e baki kace k’Arya kake Waziri..! Har abada bazan tab’a zama jinin Bauta ba..! K’arya kake Waziri..!!” Waziri na hawaye yake furta “Gaskiyar kenan Yazeed Mahaifiyarka Baiwa ce datayi k’wace da fin k’arfiwa Uwargijiyarta wacce ta aminta da ita bata kuma nufeta da komai ba face alkhairi..! Mahaifiyarka butulu ce mai saka alkhairi da sharri..!!” Yazeed dake cazgan kuka ya kuma kai masa naushi yana furta “K’arya kake mak’aryaci..! Babu wanda zai yarda da kalamanka sabida kaid’in maci amana ne kuma mayaudari..! Kaci amanan abokinka Sarki AbdulJabbar ka nemi Mahaifiyata da aurensa akanta.. Wazai yarda da kalamanka..!!” Cikin kuka Waziri ya katsesa da fad’in “Banci amanan Abokina ba..! Mahaifiyarka babu aurensa akanta, bai aureta ba makircinta kawai tayi Ta rabasa da matarsa da ‘ya’yansa Ta haukatar da ita.. Kai a Naka tunanin Yazeed matar Sarki zatabi wani namijin ne..! Mahaifiyarka ba matar Sarki bace Baiwa ce k’ask’antacciya wacce ni nai mata sutura cikin Masarautar nan har Ta haifoka gudan jinina Ta kuma dangantaka ga Sarki AbdulJabbar..! Badon ni ba da bata haifoka ma Sarki ba..!!” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Wad’annan bayin Allah haka sukayita kwance ma kansu zannuwa a kasuwa, sunzo wajen domin su kwancewa Mahmood zani a kasuwa su sanyashi yaji kunyar duniya sai gashi reshe ta juya da mujiya sai bankad’o asirai suke Wanda suka jima a bisne babu wanda yasan dasu saiko su sai mahaliccinsu... wannan rayuwa da mai yayi kama..! Shuka kirki domin ka girba gobenka..!! Haka aka dinga silalewa a wajen cikeda wane irin Al’ajabi, Yazeed bai daina naushin Waziri yana fad’in har abada bazai tab’a zama mahaifinsa ba shid’in d’an Sarki AbdulJabbar ne..! Raheemah da Gimbiya Zeenat sukaga tashin hankalin da yafi k’arfinsu, sosai Raheema Ke kuka tana fad’in Ta cuci kanta ta zalunci kanta, Tabbas Zina babban laifi ne wanda tin daga duniya zai kaika ga k’ask’anci, dukda kasancewarta d’iyar masu mulki gashi zina ya janyo mata Ta auri mutumin da aka haifesa ba Ta hanyar aure ba sannan kuma ba d’an sarauta ba d’an k’ask’antacciyar Baiwa maciya amana..! Laifin zina duk shine ya janyo mata wannan k’ask’anci da tozarci a rayuwa, yau ko da wanann tashin hankali aka barta tana cikin tsaka mai wuya, a duniya kenan balle ka isa masauk’i na har abada lahira..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Ya Allah kai mana katangar k’arfe da manyan alkaba’irai harma da k’ananan wanda bazasu kai mutum ga komai ba face halak’a..! Ja’afar ya isa gaban Yazeed da Waziri yanda suke zube a k’asa Yazeed na kuma tsinewa mahaifinsa Waziri albarka su duka biyun suna kuka suna nadamar rayuwa..! Ja’afar ya dubesu gaba d’aya sai kuma ya dubi Waziri yace “Dukda laifukan da ka aikata bazanso asirinka ya bankad’u haka a idon duniyaba amma saidai ka sani daga cikin sharrin zina da illolin Sa yana janyo jin kunya da zubar da mutunci tin daga duniya har izuwa lahira..! Da wannan kawai aka barka ya isheka hukuncin duniya Waziri.. Ya kuma maida dubansaga Yazeed yace “Toh Yarima Yazeed ko ince Bawa d’an Baiwa Yazeed..! K’arshen tikatiki tik Inji masu iya magana..! Yau gaka nan a k’asa dani kana duk’e gabana, babu hannuwa babu mulki babu sarauta babu asali balle Tushe..! Babu babunka sunyi yawa Yazeed..! Ka sani Allah shi yake bada mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso..! Bayan duk kalan abubuwan da mahaifiyarka ta aikata dan ta tarwatsa mahaifiyarmu da zuri’arta tayi iya k’ok’arinta wajen ganin Ta fitar dani da d’an uwana daga gidan mahaifinmu da sarautar da take gadonmu ne yau gashi nata ahalin sune suka tozarta..! Babu komai a cikin tsananin son mulki face halak’a..!” Ya d’an tsagaita sai ya kuma duk’awa saitin kunnen Yazeed yake furta “Kai k’ask’antacce Bawa, namu dakai bata k’are ba bari duk wata k’ura Ta lafa..! Yarima zai kuma waiwayanka..!!” Ya k’arashe yana mai sakin murmushi saman fuskar Yazeed dake zuban hawaye..! Ya dubi Waziri a hankali yace “Baba Kwarto ashe anko kukayi da d’an Naka shima d’in wani k’Aton Kwarto ne mai danne ‘ya’yan mutane aje gida a masa tarbiya akwai ‘ya’yan bayi cikin Masarautar nan, Masarautar bazata lamunci mummunan d’abi’a irin wannan daga d’aya cikin Bayinta ba..!” Ya k’arashe yana mai had’e girnsa had’ida tsimewa sosai wanda tuni yasa Waziri soma jinjina kai yana mai ci gaba da matsan k’walla..! Ya mik’e yana gyara rigarsa Ta sarauta had’ida daidaita tsayuwarsa... Har ya soma tafiya ya juyo ya dubi Dakarun dake gefe yace su kame Waziri su rufe a nan fursunan cikin Masarauta dan sai yazo ya sanar dashi yanda akai ya kashe mahaifinsa Sarki in details..! Dakaru suka risina suna furta “An gama Rankaidad’e Yarima..!!” Suka k’arashe suna masu tattaro Waziri dake faman magiya yana Baiwa Yarima Ja’afar hak’uri... Yazeed dake duk’e wajen bayan Ja’afar yabi da kallo Hawaye na kuma gangaro masa yana tuna babu irin cin kashin da baiyiwa Ja’afar d’in ba a matsayinsa na d’an Sarki wanda Ja’afar d’in Ke k’asansa, yau sai gashi Wai Ja’afar shine a sama dashi shine suka canza title shi ya koma Bawa wanda yake k’asa da J’afar yayinda Ja’afar d’in ya Koma jinin Saraki wanda yake sama dashi..! Da rarrafe Yazeed yake k’ok’arin mik’ewa yana huci yana dararawa bayin dake tsaye wajen suna kallonsa tsawa..! Bawa guda ya bud’e murya yace “Kai billahillazim idan ka kuma zaginmu zakaji a jikinka dan damu da kai babu banbanci, kai gwara mu ma da aure aka haifo mu..! Duk fad’in Masarautar nan babu wulak’antaccen Bawa irinka dan haka kana kuma cewa fit wllhi zamu tara maka na gajiyya mu k’arasa karya sauran k’afafunka..! Tashi ka b’ace mana a nan kafin mu k’arasa ka..!!” Yazeed ya soma jada baya ganin gungun bayin na yunk’urin nufosa..! Cikin wane irin tashin hankali ya nufi b’angarensa wanda bai tab’a tsintar kansa ciki ba tsawon rayuwarsa..! ** Zahra da har wannan lokaci bata dawo hayyacinta ba kwance take zazzabi na neman rufeta, Umaima wacce itama k’arfin hali kurum take itace a gefen Zahran tana kula da ita.. Bacci har ya soma d’aikam Zahra Ta farka a firgice tana ambaton sunan Muhibbah da k’arfin gaske, mafarki take Jamal na binsu itada Muhibbah, suna gudu ya kama Muhibbah dake ambata mata sunan takarda da yaren Spanish..! Take ta nanata sunan takardan a fili “Papel..!!” Ta shiga tuno kalaman Muhibbah a gareta cewa Ta baiwa Paa d’inta Takardun data d’auka cikin rigarta..! Babu shiri Zahra Ta zira hannu cikin rigarta Ta ciro takardun wanda har sun soma d’an diddigewa sabida damshin ruwa da ya tab’a su... Juya takardun ta shigayi tana duban Umaima take fad’in “Paa..! I need to give this to Paa..! I need to go Paa right now..!!” Bata kuma tsayawa sauraren Umaima ba Ta fice a guje tana neman Mahaifinta, Umaima na d’ingisawa take k’ok’arin bin bayanta saidai bazata iya ba sabida gurd’a mata k’afa da Jamal sabida d’aureta da yayi Ta jima a d’aure.. Haka Ta koma ta zauna da k’yar tana kame k’afarta... Zahra kaw tuni ta fantsama Masarauta a guje...! ** A hankali Mahmood Ke takowa yanda take zaune Ta bada baya tana duban fad’in Masarautar da irin rayuwar da tayi ciki... Al’amarin mahaifiya ya wuce wasa, tabbas shiyasa yaji wani al’amari mai girma a tattareda matar sanda suka soma had’uwa a lokacin tana cikin halin hauka wanda Giwa tai sanadiyar kasancewarta ciki..! Rauni sosai ya bayyana tattare dashi, dole ma yaji rauni domin kuwa mahaifiya ba abin wasa bace..! Tsawon rayuwarsa yayi ne yana yima wancan azzalumar matar biyayya.. Ashe ba itace Ta haifesa ba rabasa tayi da mahaifiyarsa..! Ko mai zai ma Giwa baijin zai huce domin kuwa Ta masa abubuwa da dama wanda duniyar nan tayi kad’an yace zai rama a cikinta saidai ya barwa wanda ya haliccesa ya kuma hicceta yayi hukunci tsakaninsu domin shi kad’ai ne zai iya hukunci ma wannan azzalumar matar wacce babu d’igon imani ko rahama cikin zuciyarta..! Ya duk’a a hankali gijif saitin k’afafunta yana jin wani irin kuka mai k’arfin gaske na zuwa masa..! A hankali ya saka yatsun hannunsa yana shafa yatsun k’afafunta dasu.. Hawayensa na d’iga saman k’afafun nata..! Baisan sanda ya kifa fuskarsa saman k’afafun nata yana kuka sosai..! Itama kukan take tana dafe dashi..!! Ta kasa aminta shid’in d’anta na fari ne data rasa tsawon shekaru... Su duka biyun babu mai iya cewa komai sai kukan rahama da suke, hak’ik’a Ubangijinsu ya cika rahamarsa a garesu, bayan d’ebe tsammani na tsawon shekaru yau sai gashi ya kuma had’e fuskokinsu matsayin d’ah da uwa..! Allahu Akbar komai yayi tsanani yana tare da sauk’i, duk tsananin da ka tsinci kanka ciki, kada ka karaya, ka yarda da Ubangijinka kayi imani cewa zai kawo maka sauk’i...! Hannayenta na rawa ta d’ago fuskarsa dake jik’e sharkaf da hawaye wanda ya rine zuwa ja sabida tsananin kuka..! Turaki da Ansar dake gefe guda suna kallon wannan kayan Farin ciki da Al’ajabi duban juna sukai had’ida sakar ma juna murmushi lokaci guda Turaki na labartawa Ansar d’in wanene Mahmood, d’abi’unsa tsakanin mutane kama daga ahalinsa har zuwa al’ummarsa..! Ansar na duban reunion d’in Mahmood da mahaifiyarsa yake furta “Ban tab’a cin karo da labari irin na wad’Annan bayin Allah ba..! Hak’ik’a an masu zalunci mafi muni a doron k’asa..! Daga k’arshe Allah ya kuma had’e fuskokinsu.. Sun cancanci farin ciki a sauran rayuwar da Ta rage garesu..!!” Turaki ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Wannan haka ne..!” Ubandoma ne ya k’araso yana kuma sanar dasu yanda al’Amara suka kasance..! Nan su Turaki ma Ke sanar dashi yanda al’amaran suke a Masarauta, sosai hankalin Ubandoma ya tashi jin Muhibbah na hannun Giwa, ya tuna sanda suka rabu tai masu sallama..! Tabbas idan Giwa ta gane itace Saudatu bazata barta da rai ba...! Hankali tashe yake tambayar su Turaki ina ake zaton Giwa takai Muhibbah..! Turaki yace ai babu irin neman da basuyi ba cikin Masarautar, har dai Sun soma tunanin ko ta fice da ita daga cikin Masarautar ne..! Ubandoma ya nusa kaman mai tunani sai kuma ya girgiza kai yace “Giwa bazata tab’a fitar da Saudatu daga cikin Masarautar nan ba, ita d’in ta jima da k’udirin tsafi akan yarinyar..!” Turaki da Ansar suka dubi juna suka kuma duban Ubandoma cikeda mamaki lokaci guda suka maida dubansu gaba d’aya ga su Mahmood.. Hannayen Mahmood ta shiga warwarewa kaman tana neman wani abu, nan tsakanin yatsun hannunsa na dama ta hango irin alaman dake nata hannu Wanda ashe shima yanada irinta, take ta ware hannunta itama Ta jera da nasa hannun, alaman tabon ya bayyana saman tafukan hannayensu, su duka biyu sukai K’uri suna duban irin alama guda da Allah ya halitta masu, ko shakka babu su d’in d’ah ne da mahaifiya..! Wani sabon kuka ya kufce mata.. Take Ta rungume d’anta tana kuka sosai..! J’afar da k’arasowar kenan shika cikin tsananin sanyin jiki ya isa ya rungumesu gaba d’aya..! Su duka ukun suka rungume junansu kaman masu tsoron kada a kuma raba tsakaninsu.. Sosai suke kuka mai ban tausayi da tab’a zuciyar duk wani mai imani... Dattijo Baba Nomau dake zaune daga gefe shima saida ya kamo bakin babbar rigarsa yana tsane k’wallan da suka gangaro masa..! Toh daga nan fah bayan wanann ya lafa aka sako batun neman Muhibbah..! Yasu yasu ne zaune k’asan Rumfar yanda suke tattauna ta inda zasu b’ullowa al’amarin tinda an bincika ko ina ba’a sami su Giwa ba..! Gimbiya Turai ta dubi Mahmood tace “Izzatu bazata tab’a fitar da Saudatu daga cikin Masarautar nan ba, domin kaman yanda na baku labari ita d’in ta jima da k’udirin yin tsafi da d’iyar d’an uwana..! Amma saidai akwai abinda nake tunani shine zai kaimu ga yanda Izzatu Takai Saudah..!” Mahmood ya d’ago a firgice yana dubanta duk ya jigata a d’an tsawon yini guda da wannan al’amari Ke faruwa..! Gimbiya taci gaba da fad’in “Wambai ya bani wani Taswira yace na adana shine zai toni asirin Izzatu duk daren dad’ewa..! Kuma na baiwa Saudah wannan Taswiran..!!” Zuciyar Mahmood bata daina bugawa ba yake tuno abubuwan da suka faru... Sai yanzu zanen ginin gidan sarauta da Wambai ya basa da kuma wanda ya tsinta hannun Muhibbah ya fad’o masa..! Ya mik’e babu shiri yana furta “Nasan yanda Taswiran suke nima Wambai ya bai guda d’aya kafin ya bar duniya..! Amma fallen zanen guda uku ne.. Bazamu iya gane inda zanen ya dosa ba da abinda yake nufi sai mun cika guda ukun... Ina zuwa..!!” Bai kuma tsayawa sauraren kowa ba ya shiga cikin sassarfa ya nufi d’akin da aka aje Muhibbah..! Saidai babu zanen babu dalilinsu..! Hankali tashe ya dawo ya sanar dasu babu zanen bai gansu ba...!! Kaman daga sama ya sinkayo muryar Zahra ta nufosa a guje tana ambatonsa.. Ya waigo yana dubanta, bata daina haki ba take mik’a masa Takardun dake hannunta, lokaci guda take furta “Paa Aunty Muhibbah tace na baka wannan..!!” Cikin sauri Mahmood ya amshi takardun, jikinsa har na rawa yake warwaresu..! Ga tsananin mamakinsa Map d’in nan ne mai d’aukeda wani irin rikitaccen zane..! Ya d’ago yana dubansu kana yace “Gashi nan..! Alhamdulillah ya zanen nan..!!” Gaba d’aya suka mik’e sanda Mahmood ya k’urawa zanen idanu yana karantarta..! Babu shiri ya nufi saman benensa a guje su Ubandoma dasu Jafar na biye dashi..! Can saman tsauni ya hau ya tsaya yana karantar fad’in Masarautar da kuma zanen..! Daga can b’angaren hagu daga Masarautar ya hango hanyar da yayi linking wannan Taswira..! Tabbas wani gini ne cikin Masarautar wanda hankalinka da tunaninka bazai baka akwai wani mihimmin abu wajen ba, anyi amfani da wad’anda sukeda ilimin sanin gini na zamanin da sai aka b’atar da ginin cikin ado da kwalliya wanda zakayi zaton ginin kwalliya ce kawai ga Masarautar..! Babu shiri ya nufo k’asa suka kuma biyo bayansa har saida ya tsaya gaban wannan ginin... Ya isa yana shafawa a hankali yana mai kuma bin diddigin zanen..! A daidai center ya hangi wani alamu kaman shatin kwbo wanda akai masa ado a tsakiyarsa da alamun tambarin masarauatr su..! Ya saka hannunsa yana shafe shatin kwabon..! Baba Nomau da yayi masa k’uri tamkar mai nazari ya bud’e muryarsa da girma ya kama yace “Akwai wani sirrin k’unshe da wannan alama..! Mutanen zamanin da sun yarda da alama musamman mai d’aukeda tambari irin wannan na sarauta..! Muryar Ubandoma da shima yayi nisa cikin zurfin tunani suka sinkaya yana fad’in “Mahaifina ya bani wani labari cewa akwai wani fursuna da aka ginata shekaru d’aruruka, tin zamanin wani Sarki can da jimawa..! Wannan fursunan ba’a tab’a rufe kowa cikinta ba ko shi Sarkin da ya ginata, ko wani sarki yakanyi zamaninsa ya shud’e ba tare da ya bud’e wannna fursunan ba, kuma ko wani Sarki kafin ya bar duniya yakan barwa Babban d’ansa mabud’in wannan bak’in fursunan... Kenan mahaifin Sarki AbdulJabbar bai barwa Sarki AbdulJabbar mabud’in wannan fursunan ba ya bar mabud’in hannun babban D’ansa Wambai tinda dama ko wani Sarki ma babban d’ansa yake barin mabud’in..! Kuma wannan fursunan Tanada mabud’i ne guda d’aya tak a duniya..!!” Ya d’anyi fasali kaman mai tunani sai kuma yaci gaba da fad’in “Lokacin da hankalin Giwa ya tashi na neman wanene Bak’on Buzu da yake ziyartan gidan Wambai Tabbas naji tana maganan neman wani k’undi daga hannun Wambai wanda shine dalilin da yasa na zaga na shiga gidan Wambai Dan na samo wannan k’undi ganin irin mahimmancin da yake dashi a wajen Giwa..! Na tabbata wannan k’undin yanada alak’a da wannan zanen..!!” Ai Ubandoma bai gama rufe baki ba Mahmood ya soma jada baya yana furta “Tabbas ni ne Bak’on Buzu, na b’atar da kama ne domin na samo amsoshin da na dawo k’Asar nan ina nemansu kuma Tabbas Wambai ya bada Bak’on Buzu wani k’undi wanda yace akwai lokacin da zan buk’aci bud’e wannan k’undin..! Tabbas mabud’in wannan Taswira yana cikin k’undin da Wambai ya bani..!!” Daga haka ya nufi d’ajinsu a guje Dan d’auko k’undin da Wambai ya damk’a masa... *MUHIBBAH* *76* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sharkaf Ta jik’e da gumi tana duban Giwa tana girgiza kai hawaye suna ci gaba da ambaliya a fuskarta sahu sahu, wani na bin wani... Ta kasa gasgata abubuwan da taji daga bakin wannan azzalumar mata wacce take tantama anya ‘yaradam ce..? Idan kuwa ‘yar adam ce Anya akwai zuciya cikin k’irjinta...? Hawaye had’eda zufan da ya wanke mata fuska take duban yanda Giwa Ke kuma sakin wane irin shewa akanta, ji tayi kaman maganan Ta ya d’auke cak sabida tsananin shiga tashin hankali da tayi domin kuwa ko kalma guda ta kasa furtawa, ga wani irin juyawa da kanta yake sai tanajin kaman a wani nisan duniya take sinkayo dariyar Giwa da shewarta... Bata kuma sanin meke wakana ba saidai kawai ganin Jamal tai tsaye kanta muguwar murmushinsa saman fuskarsa yake furta “Saudatu.!!! So you’re back..! Kin dawo dan Ki d’auki fansarki akanmu, kin dawo kin tarwatsa ahalinmu... Kin lalata komai, Na rasa k’afata guda d’aya, kin rabani da matata Umaimah..! Ban damu ba idan itad’in ‘yar uwarki ce, Umaima itace rayuwata, kuma har abada bazata tab’a sanin cewa ked’in ’yar uwarta bace, baza San cewa ga abinda na aikata ma ‘yar uwarta ba wanda suka had’a uba d’aya..! Ita d’in tawa ce bata da sauran ahali a halin yanzu da ya wuce ni Jamaluddeen..! Kece kika dad’a haukata Fu’ad sannan kika toni asirin Yazeed kika hana Mahmood Auren Raheemah..! Yazeed lost both his hands sabida Ke, he even lost his children duk a dalilin ki.. Ke harta aurensa ya rasa duk sabida Ke..! Ta yaya kike zaton zan goyi bayan a yafe miki..! Ai yanda Giwa ta fad’i Zata cika mana mulkin ahalinmu da gudan jininki babu ja babu komawa baya.. Sannan abu na k’arshe kafin Ki tafi daga wannan rayuwar zanso na sake d’and’ana zumarki dana d’and’ana a baya domin kuwa dukda shud’ewar shekarun nan, na lalata rayuwar ‘yan mata da dama banci karo da wacce naji dad’in kasancewa da ita sama dake ba..! Kafin na mik’a ki ma bokan Gimbiya ya gama abinda zai dake ya tura ma Sarauniya mai gadon Mulkin tsafi tarihin abinda muka aikata maki shekaru goma sha hud’u baya zai maimaita kansa...!” Ya kuma d’aga allurar dake hannunsa yace “Kinga wannan allurar ban mance da ita ba, musamman sabidake na zubata a syringe, sai na miki ita kafin na mik’aki ga bokan sarauniya, zan nuna miki k’arshen taurin kai yau, sai kinyi da kinsanin dawowa cikin wannan masarauta..! Zan miki wulak’ancin da ban miki irinsa a baya ba domin kuwa nid’in na k’ware wajen wulak’anta ‘ya’yan mutane ta hanyar lalata masu rayuwa wanda duk kece sila..! Duk yaran da na lalata ma rayuwa kece sanadi domin akanki na fara..! Da ace kin tsaya tun wancan lokacin an cika mulki da gudan jininki watak’ila da ban zamto abinda na zamto a halin yanzu ba... Dan ni da kike gani ban tab’a kusantar wata d’iya mace ba ba Ta hanyar fyad’e ba...!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin b’alle botiran rigarsa muguwar murmushin bata bar saman fuskarsa ba... Allah ya gani babu abinda take fahimta saima idanunta da suka kakkafe suna kallon sama, haka nan Ta koma tamkar wacce bata numfashi... Ga tsananin nauyi da k’irjinta harma da harshenta suka mata, addu’an ma bata iya furtawa da baki... Iyakacin abinda Ta sani shine shine zuciyarta bata daina ambaton mahaliccinta ba, zuciyarta bata daina tsarkake mahaliccinta tana mai k’ak’antar dakai garesa had’ida neman taimakonsa da agajinsa daga hannun wad’annan mugayan mushirikan mutanen data fad’a hannunsu..! Tayi imani Ubangijinta maiji ne kuma mai gani wanda ganinsa da jinsa suka sha bambam dana ko wani makhaluk’i..! ** Jikin Mahmood na tsananin rawa yake warware k’undin...! Ga tsananin mamakinsu wannan alamun shatin kwabo da suka gani daga tsakiyar ginin coin mai irin alamun ne cikin k’undin wanda yakeda matuk’ar nauyi a hannu sai faman shek’i yake kaman an tsoma cikin ruwan silver..! Baba Nomau dubi Mahmood da har lokacin jikinsa bata daina rawa ba bai kuma saki wannan shatin kwabon ba yace da Mahmood d’in “Ka natsu Mahmooda ka ambaci sunan Allah ka saka wanann shatin kwabo a jikin gini yanda yake d’aukeda alamun..!” Jinjina masa kai Mahmood yai, yayi kaman yanda Baba Nomau yace, da sunan Allah saman harshensa ya manna wannan shatin kwabo jikin garun..! Yana mannawa gaba d’aya Masarautar tayi wane irin girgiza wanda duk wani mahaluk’i da yake cikin Masarautar saida yaji wannan diri da d’aukacin Masarautar tayi.. Tsofaffin gini wasu saida suka b’anb’are wasu na zubewa k’asa..! Baba Nomau yace dasu kowa ya nastu suci gaba da ambaton sunayen Allah suna tsarkakesa..! Wannan dirin da d’aukacin Masarautar tayi sai gani sukayi wajen da Mahmood ya manna shatin kwabon gini yana bud’ewa kaman ana turasa...! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un zukata Ke ambato..! Cikin iko na Ubangiji ginin nan yake bud’ewa suna hango wani alk’arya guda a bayan wannan ginin, domin kuwa cikin wannan gini wani masarauta ne mai zaman kansa..! Mahmood ya yunk’ura zai danna kai ciki Baba Nomau yayi saurin rik’osa ya dawo dashi baya yace dashi, gini irin wannan da yayi shekaru da dama a rufe haka dole akwai wasu halittu dake rayuwa ciki wanda mu namu idanun bazasu iya gani ba..! Inaso cikinmu gaba d’aya wanda duk baiyi azkar na safiya na neman tsari ba Toh yayi yanzu..!” Sannan karanto masu addu’o’in neman tsari da zasu karanto kafin su shiga..! Ya kuma karanto matayassara daga littafin Allah mai tsarki..! Su Duka suna masu yak’in da kariyar Ubangijinsu wanda babu abinda yafi k’arfin jkinsa..! Kowa yayi kaman yana Baba Nomau yace, suka nufi cikin wannan gini da basa iya ganin komai sai jemagu da wasu irin k’wari marassa kyaun gani.. Ja’afar da Mahmood saiko Baba Nomau da Ubandoma sune suka shigo cikin wannnan kangon Masarauta mai tarin kayan al’ajabi .. Bakunansu basu daina ambaton Allah ba..! ** Tun sanda ginin yayi wani irin diri fatar jikin Tal’udu ke fitar da wani irin bak’in hayak’i mai mummunan d’oyi, Kan Giwa da hannunta da ya tab’a cin wuta suna fitar da irin wannan hayak’in da kuma d’oyin... Jakadiya Ta razana matuk’a sai faman muzurai take tana tambayar Giwa mai ke faruwa...Giwa Ta rufa bak’ar Alkyabbarta hannunta rik’eda rik’eda fitilar tsafi.. Ta zauna saman Darduman tana fad’ida Jakadiya “Wannan shine cikan Mulkina Jakadiya..! Wannan alamu ce da take nuna Sarauniya zata cika mulki na a yau d’in..!!” Ta k’arashe tana mai kuma tura fitilar cikin Bak’in tukunyar Tana ganin yanda bak’in hayak’i ya rufe Tal’udu gaba d’aya... Jakadiya tace “Amma Rankidad’e bamu ganin alamun Tal’udu bak’in hayak’i ya rufesa.!!” Giwa taci gaba da fad’in “Sharad’in kenan ranan da Mulkina ya cika ranan Tal’udu zai bar cikin gidan nan tareda duk wani abu da yake daga tsatsonsa inada tabbacin wannan bak’in hayak’i alamu ce ta nasara..!!!” Jakadiya tai K’uri tana kallon wannan tashin hankali tana mamakin ta ya za’a ce bak’in hayak’i had’ida mummunan d’oyi ya zamto nasara..!! A daidai wannan lokaci su Mahmood suka iso...! Su Giwa suka soma hangowa tana zaune saman Jan Dardumanta na tsafi ga tukunyar tsafi gabanta gacan wani bak’in hayak’i turnuk’e gabanta wanda Tal’udu ne cikin hayak’in, bak’in hayak’in ya rufesa baka iya hango komai nasa..! A take suka soma toshe hancinsu suna kuma k’arasowa wajen..! Jakadiya ce ta soma hangosu, ta saki wani irin k’ara tana mai sililalewa k’asa Giwa kam hankalinta naga bak’in Tulu tana kuma tura fitalar tsafi ciki tana furta “Ya Ke Sarauniya uwar tsafi yau na cika miki k’udirinki na kawo miki Amaryarki da Ta gudu daga gareki shekara goma sha hud’u baya..! A yau na mallaka miki gudan jininta ki cika min Mulkina dashi..!!” Mahmood dake tsnanin huci ne yai wani irin tsalle ya tokari bayan Giwa kwatsam fuskarta ya fad’a cikin bak’in tulu had’e da jan fitilar dake hannunta..! Aiko fuskar Giwa na fad’awa cikin tulun nan wuta bal bal ya kama a cikin tukunyar ya shiga cin naman fuskarta..! Ta saki wani irin k’aran azaba mai muni gashi fuskarta ya rik’e cikin tulun mai ci da wuta..! Juyin duniya ta ciro fuskarta ta kasa cirewa sai ihu take zallan fuskarta na cikin Tulu yana cida wutan azaba..! Jakadiya jiki na rawa tab’e furta “Kumin rai..! Kuji k’an baiwarku mai biyayya a gareku..!!” Ubandoma yace “Allah yaji k’an masu jin k’an bayinsa na K’warai amma banda Ke Talle..!!!” Batakai aya ba Mahmood dake ci gaba da sakin huci ya damk’o wuyarta da duka hannayensa biyu cikin wane irin yanayi da babu wanda ya tab’a ganinsa ciki yake furta “Ina Muhibbah..! Ina Muhibbah..! Ina matata nace..?!!” Jakadiya da taji damk’a hannu na tsananin rawa take nuni da d’akin da Muhibbah da Jamal ke ciki wanda yake daga center k’ofar a bud’e..! Jifa yayi da Jakadiya tana ida nuna masa ya nufi d’akin a guje..! Jakadiya bata fad’a ko ina ba sai hannun Giwa dake ci gaba da kururwa tana kalaumen iska tana neman agaji take fad’in a cire mata tulun azaban da ya kame fuskarta..!! Aiko Giwa tanajin ta capko mutum ta damk’e Jakadiya gam tana fad’in sai ta cire mata tulun azaban dake mak’ale a fuskarta..! Jakadiya na kokawar k’wace kanta daga hannun Giwa, inaa Giwa bata daina janta ba tana fad’in ta cire mata tulun har saida suka dangana da hayak’in Tal’udu..! Jakadiya na kururuwa tana fad’in su ceceta zata mutu, inaa tuni Giwa ta jefata cikin hayak’in Tal’udu..! Babu wanda ya iya kusantar wutan tsafin da yake tasowa daga jikin Tal’udu yana haurawa jikin Jakadiya ...Tun ana hango hannun Jakadiya da take d’agowa sama har dai aka daina hangowa..! Baba Nomau da Ja’afar da Ubandoma suka fantsama sauran d’akunan dake jere wajen Ja’afar yana tokarin ko wace k’ofa tana bud’ewa..! Wani kayan tashin hankali da al’ajabi shine ko wane d’aki sai Sun tsinci gawan mace budurwa..! (Idan baku mance ba wad’annan ‘yanmata sune wad’anda Jamal ya lalata masu rayuwa Tal’udu da Giwa suka ajesu a wad’annan d’akuna da sunan sud’in matayen Sarauniya ce wanda d’aya d’akin da a kullum yake bud’e shine Saudatu... Sun rigada sunyi tsafi da wad’annan ‘yan mata sun halak’asu...) Mahmood yana fad’awa d’akin ya hango Jamal haihuwar uwarsa yana k’ok’arin duk’awa ga Muhibbah..! Cikin wane irin daka tsalle ya isa ya kai masa wata jahilar naushi wanda saida ya watsar dashi da sandarsa gefe guda..! Ya kuma janyosa ya shiga kai masa naushi ta ko ina kaman wanda aka aikosa, yana tokarinsa hawaye na tsartowa daga idanunsa... Bai daina tokarinsa yana kai masa bugu ta ko ta ina ba a haka ya dinga naushinsa yana cillosa waje da tsananin bugu gashi babu k’afa balle ya tashi ya gudu..! Ja’afar ne ya k’araso ya dafa Mahmood yace “Yaya Kaji da matarka..! I’ll take it from here..!!” Duban Ja’afar kurum yake da rinannun idanunsa yanajin idan bai kauce masa ya kashe Jamal ba zai iya had’awa dashi... Ja’afar na k’ok’arin kuma tausan Mahmood da Ko kalma guda ya kasa furtawa har lokacin sai wani irin tsima da jikinsa keyi yana fidda gumi kaman wani rikitaccen zaki wanda ya birkice cikin garken Giwaye..! A d’an wannan tsakanin Jamal ya samu yake rarrafawa ya nufi wajen mahaifiyarsa.. Da lalume Giwa ke fad’in “Jamal..! Gwarzona ka cire min wannan tukunyar azabar..!” Inaa tsaban bugun da Jamal yaji hannun Mahmood bai iya furta koda kalma sai nishi.... Ana haka Giwa taji ana janye Jamal daga cikin hannunta..! Taci gaba da kuruwa tana fad’in kar Jamal ya tafi ya barta ya cire mata wannan tulun azaban da ya manne mata fuska..! Fad’I take “Gwarzona ka taimakeni..!” Saidai Gwarzo ma takansa yake..! Ashe Tal’udu ne Ke janye Jamal yana fad’in shid’in daga tsatsonsa yake bazai tafi ya barsa ba..!! Manna hannun da Tal’udu zai jikin Jamal wuta ta kama tin daga Kwankwason Jamal har zuwa cinyarsa... Haka wuta tai masa sutura ta zamto wandonsa domin kuwa wuta ce ta rufe al’auran Jamal gaba d’aya ta zamto sitira garesa..! Ihun azaba da ya saki ya maidoda hankulan su Ja’afar..! Giwa na ihun Fuska cikin Tulu Jamal yana ihun wuta na cin iyakacin al’aurarsa ta masa sutura bata bari al’aurarsa ta bayyana ba, mummunan jan wuta taita ci yana ihu yana neman agaji.. A d’ari Mahmood ya koma cikin d’akin yanda Muhibbah Ke kwance har lokacin idanunta kaman a kakkafe suke..!A hankali cikin wane irin murya mai rarrabewa ya furta sunanata, jikinsa har wani irin rawa yake ya janyota cikin jikinsa, ya shiga jijjigata yana ambato sunnanta... A hankali yaga idanunta suna dubansa kaman zatayi magana..! Yaci gaba da jijjigata yana ambato sunanta.. Saidai lokaci guda idanun nata suka kuma rufewa ruf jikinta ya kuma sakewa cikin jikinsa...! Yai saurin d’agota yai mata irin rik’on da akema jarirai ya fice da ita daga wajen hankalinsa a matuk’ar tashe..! Giwa na ihu Jamal na ihu, a haka Giwa take takawa tana lalumen wajen tsira har ta nufi d’akin da Muhibbah ta kub’uta daga ciki, tana shiga da shike ba gani take ba fuskarta na rufe cikin tulu nan taji k’afarta ya cakki wani abu kaman allura..Aiko nan ta fad’i k’asa ta tuma da k’arfin gaske domin kaw gaba d’aya ji tayi jikinta ya sake kaman babu wani jijiya da ya kuma rik’e gab’ob’inta.. Aiko tana fad’uwa tulun ya fashe fuskarta da ya gama melewa ya koma kaman jan gauta ya bayyana, tulun tsafin na fashewa wani d’oyi ya kuma gauraye wajen, ashe allurar paralyze da Jamal ya aje zaiywa Muhibbah bayan ya ida cin zarafinta a karo na biyu shine Giwa Ta taka tayi takalmi dashi ya cakketa a k’afarta..! Haka Giwa Ta zube a wajen tana fitar da wani irin turiri had’ada gurnani na azaba ga fuskarta baka hango komai sai alamun melewar fata..! Shi kaw Jamal saida wuta ta ci al’aurarsa sosai kafin Ja’afar ya samu ya k’araso ya rufa masa rigar kuftarsa da yake sanye da ita Dan sanda wutar ke gauk’in ci tsaban turirin da take da huci Babu mai iya kusantarsa balle ya basa agaji.... Shid’inma sakin hucin azaba kurum yake... Can bayan wutan ya lafa suka hango Jakadiya itama wuta sosai yaci b’angaren jikinta gefe da ita Mushirinki mutumin ne wanda da alama shikam ma kaman babu rai jikinsa, ya k’one sosai baka hango komai tattar dashi sai wannan jan banten da a kullum yake d’aurawa..! Wutan duniya kenan taci wad’annan bayin Allah cikin ‘yan mintoci da basu shige a k’irga ba amma suka k’one irin haka, inaga wutan lahira wanda baida misali... Tun daga duniya Fuskar Mushirika Giwa wanda bata sujada wa mahaliccinta dashi sai Bokanta da sarauniyar tsafinsu yaci wuta ya mele ya koma abin tsoro da k’yama, shi kuwa Jamal al’aurar da yake sab’on Allah dashi yake cin zarafin ‘ya’yan mutane dashi ana tsafi dasu yaci wuta ya mele ya k’one k’urumus..! Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu kayi mana mai kyau duniya da lahira Ameen..! A can b’angaren Mahmood kuwa yanda ya fito da Muhibbah saman hannunsa yana gudu cikin Masarautar duk yanda ya gifta sai Sun zabura Sun kuma dubansa... Can ya hango Turaki da Ansar suna tsayuwar jiran fitowarsu ne daga cikin ginin da alama..! Cikin wane irin murya yake sanar da Turaki ya kawo mota..! Gaba d’aya Turakin ma ya rikice, sai ya rasa wace hanyar zaibi saida Ansar yai directing nasa..! Mahmood bai daina jijjigata cikin hannunsa yana ambato sunanta ba.. Turaki na isowa da motar Yarima Mahmood ya bud’e baya ya shimfid’ata, take shima d’in ya shige ya aza kanta bisa cinyarsa har lokacin bai daina jijjiga fuskarta yana ambato sunanta ba..! Shi kuwa Ansar da yake likita ne sai ya k’araso yana k’ok’arin dubata..! Mahmood da bai daina sakin huci ba cikin wane irin darara tsawa yaceda Ansar “Don’t touch her..! Don’t you dare touch her..!!” Yanda yake maganan zai tabbatar maka bai k’aunan yaga hannun wani namiji kusanta..! Ansar da tsawar ta shigesa sosai, girgiza kai yake yana duban Mahmood d’in yake furta “Ni likita ne, zan duba na gani ne if she’s still breathing..!” Baikai aya ba saiji yayi Yarima Mahmood ya shak’o wuyarsa ya janyosa kusan fuskarsa yana furta “She’s breathing..! She’s alive..! Kada ka sake tunanin Ta mutu..! Idan na kuma jin irin wannan kalma daga bakinka zansa Dakarun Masarautar nan su fille wuyarka..!!” Yana ida fad’in haka yayi jifa da Ansar gefe guda..! Turaki yai masa K’uri sanda yake fad’i da Turakin ya tada mota su fice..! Turaki bai kunna motar ba sai duban Mahmood d’in kurum da yake da idanu..! Mahmood ya d’ago a zuciye yana tambayan Turaki mai yake jira..! Har lokacin Turaki bai amsasa ba bai kuma tada motar ba sai k’arasawa da yayi ya d’aga Ansar daga k’asa..! Cikin tsananin tafarfasan zuciya ya fito daga motar ya isa ya Turaki yana fad’in ya basa keys..! Turaki bai basa sai ma duban Ansar da yayi yace “Dr please check on her..!” Cikin huci Mahmood ya janyo Turaki da wuya ya maidasa gefe ya kuma tare gaban Ansar yana furta “Wannan mutumin bazai tab’a min mata ba..!!” Turaki ya dafe kansa yace “Your Highness please..! Ba maganar matarka ake a nan ba..! Maganan ceton rayuwar Muhibbah ake a nan..! What if tana buk’atan wani taimako na gaggawa before we make it to the hospital, what if akwai abinda ya kamata a mata kafin mu tafi asibitin wanda zai taimaka..! Mahmood idan Muhibbah ta mutu yanzu a nan zai zamana kai k’arasata, kishinka ne ya k’arasa kasheta..! Please let him check on her , ka bari ya dubata don ko asibtin kaje wani likitan ne zai dubata..!” A hankali Yarima Mahmood ya janye jikinsa ya baiwa Ansar hanya ba don yaso ba, yana mai aikawa Turaki muguwar kallo, idanunsa k’yam akan Ansar d’in yana duban yanda yake k’ok’arin kai hannunsa saman fuskar Muhibbah da zummar d’aga marfin idonta..! Cikin sauri Mahmood ya mik’a hannunsa ya d’aga masa marfin idon nata yana furta “Duk abinda zakayi ka fad’a min ni zan maka..!” Turaki dai girgiza kai kurum yayi yana kallon wannan drama na Rankaidad’e..! Ansar ya d’anyi gyaran murya yace “Rankaidad’e da ka kaita d’aki ka kwantarta saman gado, inaga ba wani abin tashin hankali bane, Shock d’in data tsinci kanta ciki had’ida girman abubuwan da suka faru da ita that’s the reason she passed out, you can take her to her room your Highness..! Idan yaso sai ka kirawo likitan daka yarda dashi ya dubata..!” Idanunsa na kan Ansar bai daina fitar da huci ba yake furta “You don’t tell me what to do..! Musamman Abinda ya shafi matata..!! Now get lost..!” Ya k’arashe yana mai kuma d’aukota saman hannunsa.. Har ya soma tafiya ya kaikaito ya dubi Turaki yace “I need a female Dr..!” Bai kuma furta komai ba ya nufi sashensa da ita.. Turaki ya sauk’e fuci a hankali, kafin yayi magana Ansar ya girgiza masa kai yace “Kar ka damu I understand where he’s coming from, yanzu da ya fahimci abinda ya faru da Muhibbah bazai aminta da ko wane namiji kusanta ba koda kuwa likita ne..!” Turaki ya jinjina kai a hankali yana fuzar da wani hucin, lokaci guda ya ciro wayarsa ya shiga kiran asibiti..! ** D’akin dake gefe da nasa ya kaita ya kwantarta saman gado, ya d’an rank’wafo da wuyarsa kad’an sanda yake k’ok’arin ajiye kanta saman pillow, daidai saitin wuyarsa yaji kaman hucin numfashinta, ya karkato da fuskarsa yana duban nata fuskar yanda idanunta ke lumshe... Ya jima sosai yana duban fuskar nata da yanda jini ya d’an bushe ciwon da Jamal yaji mata, sosai ya runtse idanunsa sanda ya tuna ganin Jamal da yayi yana k’ok’arin auka mata wanda ba don Allah ya kawosa akan lokaci ba da ya aikata mata abinda suka aikata gareta shekarun baya, wancan ma da suka aikata duk tunowa da zai sai yaji kaman mashi ake caka masa a k’ahon zuciyarsa balle yanzu da yaga Jamal akan idanunsa na k’ok’arin aikatawa..! Sai faman dunk’ule hannunsa yake idanunsa na duban wani b’angaren zuciyarsa na kuma masa zogi yana murza zoben dake hannunsa, har saida yaji k’aran fad’uwar zoben saman tile kafin ya maidoda dubansaga zoben nasa..! A hankali ya mik’e ya nufi bathroom ya d’ebo ruwan d’umi kad’an a roba had’eda k’aramar towel ya zauna gefenta ya shiga danna mata goshinta dashi..! Yana danna mata towl d’in yana tuno duk abubuwan da suka faru tin daga lokacin da ya d’aurata saman dokinsa tana k’arama ranan Washe garin sallah da suka tsinceta, ranan da Giwa da ‘ya’yanta suka b’ata mata rayuwa..! A hankali ya soma furta “I shouldn’t have left you alone with them..! I should have stayed..!” Muryarsa ya sark’e sabida tsananin rawa da muryar keyi, lokaci guda yake furta “Please Ki yafe min, Ki yafe min da ban tsaya na kaiki gida ba..!” Ya k’arashe yana mai k’ura ma fuskarta idanu fsukarsa dab kusan nata, hawayen dake mak’ale cikin idanunsa guda ya d’igo, ya d’iga a daidai saitin idonta, hawayen nasa ya ratsa ya shige cikin idonta wanda yasa idanun nata motsawa..! Idanunsa a lumshe hannunta guda rik’e cikin nasa ta soma k’ok’arin bud’e idonta..! A hankali take jin idanunta suna k’ok’arin bud’ewa, tana iya hango fuskarsa dururu, har sai da ida bud’e idon nata.. Cikin yanayin tsoro Ta soma k’ok’arin mik’ewa, Mahmood ya bud’e idanunsa Tar cikin nata idanun... Zuciyarta yaci gaba da bugawa abubuwan da suka faru suna kuma dawo mata, yanzu ga Rankaidad’e zaune kusanta hannunta cikin nasa..! Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa, tsoron abubuwan da suka faru da wanda taji suka kuma dawo mata..! Numfashinta ya soma fita da sauri sauri tana mai kuma k’ok’arin fuzge hannunta daga rik’onda Mahmood d’in yai mata..! Bai saki hannun nata ba saima dad’a matse hannun nata da yayi cikin nasa...! Tana gani yake k’ok’arin kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunta suka kuma firfitowa waje tana k’ok’arin k’walla ihu yai amfani da d’aya hannun nasa ya toshe bakinta, saitin kunnenta yakai bakinsa had’ida rad’a mata “You’re safe now, you’ll always be safe... around me..! Stay here in bed and get some rest..! Likitarki zata K’araso nan bada jimawa ba..!!” A hankali yake jin bugun zuciyar nata na raguwa alamun tsananin tsoron na d’an sakinta, idanunsu cikin na juna har lokacin hannun Mahmood na saman bakinta, har saida yaji natsuwa na sauk’o mata a hankali kana ya zame hannunsa daga saman bakinta..! Ta ja wani irin ajiyan zuciya tana mai dubansa har ya mik’e tsaye, tana gani ya ciro wayarsa a aljihu yana amsa kiran Turaki da alama maganar likitar suke..! Mahmood na ficewa ta mik’e zaune da k’yar tana mai kuma jan wani dogon numfashin had’ida dafe kanta idanunta a rintse..! Kusancinta da Rankaidad’e ya soma d’aure mata kai, a yau d’in tasan Shi baidaga cikin ahalin Giwa kuma shid’in d’ah ne ga yayar Mahaifinta amma kasancewarsa d’an uwanta bai halatta masa kusantuwa da ita har haka ba..! Tab’a k’ofar da akai ya sanyata saurin bud’e idonta da yai mata tsananin nauyi, wata mata ce ta gani wacce kaman tasan fuskarta a wani wajen, gefe da ita wata matar ce wacce ke sanye cikin shiga irinta likitoci... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *77* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Muhibbah tai K’uri tana duban matar wacce itama d’in ita take duba, tana mai takowa cikin d’akin a hankali..! Sai yanzu ta fahimci ko wacece wannan matar, mahaukaciyar nan ce data bata Taswira, wacce ta taimaka masu suka fice daga cikin Masarauta taredasu Ubandoma da Ja’afar, sannan itace Giwa ta sanar da ita cewa mahaifiyar Yarima Mahmood ne da kuma Ja’afar, ‘yar uwa ga Marigayi mahaifinta..! Take taji wasu irin hawaye suna zuwa idanunta, duk labarun zalunci da Giwa tayi ma wannan mata da ahalinta suka shiga dawo mata daki daki..! Tana gani matar dake zuban hawaye takai hannunta dake tsananin rawa tana shafa fuskarta, su duka biyun suna duban juna hawaye na gangaro masu... A hankali matar ta janyota cikin jikinta ta rungumeta sosai kuka mai k’arfi na kufce masu gaba d’aya, saida sukayi mai isansu kana ta kamo hannayen Muhibbah tana juyawa tana kuma kallon illahirin jikinta har zuwa fuskarta... Muhibbah dake sakin murmushi takai hannunta a hankali tana share hawayen matar, su duka biyu murmushi ne mai gauraye da hawaye saman fuskokinsu... Hannayenta rik’e cikin na matar take tambayarta “Sun kuma cutar dake..?!” Ta girgiza mata kai a hankali alamun a’a “Allah bai basu nasara ba..!” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya.. Lokaci guda taci gaba da fad’in “Ke ‘yaruwar.. Mahifina ne... Giwa ta fad’a min haka da bakinta, ta sanar dani abubuwa da dama, ciki harda yanda ta rabaki da ‘ya’yanki guda biyu... Rankaidad’e da Ja’afar ‘ya’yanki ne..! Haka tace..! Muje muje mu samesu mi sanar dasu..!!” Ta k’arashe a d’an rikice tana mai k’ok’arin sauk’owa daga saman gadon... Hannunta Gimbiya Turai ta kamo ta zaunarta kana tace “Sun riga Sun San komai, asirin Izzatu ya gama tonuwa a cikin Masarautar nan..! Illahirin jama’an K’asar nan a halin yanzu sunsan wacece Izzatu da ta’asan da ta jima tana aikatawa shekara da sharkaru..! Allah shine abin godiya wanda ya k’addari sake had’uwarmu ya kuma cire fargurbi cikinmu..!!” Muhibbah ta jinjina kai a hankali sai kuma tace “Inaso naje naga Umaima domin kuwa Giwa ta sanar dani cewa Umaima ‘yar uwatace wanda matar da mahaifina ya aura a lokacin da ya tafi nemanki ta haifa masa, Ta sanar dani yanda ta hallak’a mahaifiyar Umaima cikin wuta ta kuma tahoda Umaima cikin Masarautar nan..!!” D’ago kan da zatayi ta hango Umaima na shigowa cikin d’ingishi hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta..! Muhibbah tana ganinta ta mik’e zumbur wasu hawayen na kuma gangaro mata, lokaci guda Ta soma takowa dukda rashin k’arfin dake jikinta, saida ta k’araso har gaban Umaima kana taja ta tsaya hawaye basu daina ambaliya a fuskokinsu ba.. Lokaci guda suka rungume juna suna masu ci gaba da sakin kuka..! Gimbiya Turai tai masu K’uri tana dubansu cikeda shauk’i, Allah sarki d’an uwa mai dad’i, a yau ahalin d’an uwanta Alfah sun had’e waje guda... Allah ya kuma had’asu gaba d’aya shin mai yafi wannan d’ad’i... Inama Alfah yanada rai yaga d’iyoyinsa Allah ya had’esu, tabbas Allah ya cika abin godiya mai yawan rahama ga bayinsa.. Yau ko babu Alfah Allah ya bar zuri’arsa a doron k’asa bayan duk kalan makircin da Izzatu tayi domin ta k’arar da ahalinsa a bayan k’asa... Tabbas Sara da sassak’a baya hana Gamji toho, Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho toh fah sai yayi, Ko a yanzu Allah ya d’auki rayuwarta ya cika mata burinta, ya had’ata da ‘aya’yenta guda biyu bayan tsawon shekarun nan sannan ya had’ata da ‘ya’yan d’anuwanta wanda zataga d’anuwanta a tattare dasu..! Umaima da Muhibbah hannayensu rik’e cikin na juna suka zauna saman gado Umaima na fad’in “Nayi zaton bayan Giwa da ahalinta banida sauran dangi a duniyar nan kaman yanda Ta sanar dani, Ashe ba haka bane ita d’in hankaka ce mai maida d’an wani nata Domin ta cutar dashi, ita d’in ta k’ware wajen satan yaran mutane..! Taso tarwatsa ahalinmu sai Allah ya sake had’amu a cikin gidan nan, tin kallon farko da na miki Muhibbah naji ina k’aunarki ashe ked’in ‘yaruwata ce ta jini..! Alhamdulillah Allah ya nuna min ahalina na gaskiya, ba wannan azzalumar matar da d’anta da suka so cutar dani ba..!” Muhibbah ta murmusa ta kuma kamo hannun Umaima tace “Hakance ta kasance dani sanda na soma tozali dake Umaima, Alhamdulillah.. Mun godewa Allah da baiwa wad’annan azzaluman damar cutar damu ba..!” Umaima ta kuma murmusawa tana goge hawayen fuskarta take furta “Thank you Big Sis for saving me..!!” Muhibbah tai mata K’uri jin ta ambaceta da big Sis, Ashe akwai rana irin wannan da zatazo ta ga jininta tayi zaton tun bayan rasa k’anwarta da tai bazata kuma jin wani ko wata ya ambaceta da ‘yaruwa ba sai gashi yau d’in taji haka... Tai saurin janyo Umaima cikin jikinta ta rungume suna matsan k’wallan Farin ciki..! Likita ma saida ta matse k’walla ta dubi Muhibbah tace “Anya Rankidad’e ked’in patient ce kuwa, naga kaman da k’arfinki... Yanda aka d’ago min hankali na fito babu shiri ban zaci zan ganki haka ba..!” Murmusawa Muhibbah tai tace “Lafiyata lou Dr, kaina ne kawai Ke min ciwo...!” Dr ta jinjina kai tace “Naji dad’i da jin hakan, Allah ya k’ara lafiya..!” Ta ciro PCM cikin ‘yar jakan nata ta mik’a nata tace “Idan kinci abinci sai ki sha ki d’an samu bacci ki huta koh..!” Nan ma jinjina mata kai Muhibbah tai had’ida mata godiya..! Likita tai masu sallama sukai mata godiya gaba d’aya kana Ta fice.. wata Hadima ce ta shigo ta risina gaban Gimbiya Turai tai mata magana kaman mai bata sak’o... Yayinda Muhibbah da Umaima Ke ci gaba da tattaunawa Umaima na fad’in Ta bata labarin mahaifinsu da abubuwan da suka faru..! Gimbiya Turai ta katsesu da fad’in “Yarana ku tashi muje koh..!” Babu musu suka mik’e gaba d’aya Muhibbah na dafe da Umaima tana taimaka mata, a tare suka nufo downstairs, nan Muhibbah Ta fahimci b’angaren Rankaidad’e suke, bata dai ce komai ba har lokacin... Suka fito gaba d’aya yayinda wasu Hadimai guda uku suka risina masu alamun gaisuwa, lokaci guda sukai masu jagoranci zuwa masauk’in Muhibbah wanda Yarima Mahmood ya ajeta kafin su Giwa su kamata, Kaman bazata shiga ba taja Ta tsaya turus tana duban Umaima da Gimbiya Turai.. Gimbiya Turai ta kamo hannunta guda tace “Nasan kinada tambayoyi da Dama k’unshe cikin zuciyarki Saudah, wanda da zaki so a amsa miki su cikin gaggawa, amma inaso ki k’ara hak’uri har abubuwa su kuma daidaita cikin Masarautar zakiji komai daki daki kinji koh..! Yanzu ki shiga cikin d’akinki ki samu kiyi wanka ki sauya wannan tufafi domin wad’annan tufafi basu kamaceki ba ked’in Gimbiya ce kuma Sarauniya..!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. K’ok’aro murmushin Muhibbah ma tayi ba tareda Ta fahimci abinda take nufi da tace itad’in Gimbiya ce kuma Sarauniya, ta alak’anta maganar nata da kasancewarta d’iyaga d’anuwanta D’an Sarki jinin Sarauta..! A haka suka k’arasa cikin sashen, yanda suka tadda Kuyangin fin na da, saidai wannan karon wasu ne ba wad’ancan Kuyangin data tadda sanda ta farka ta tsinci kanta cikin d’akin ba.. Gaba d’aya suka zube masu suna kwasan gaisuwa.. Hadimar guda tace da Gimbiya Muhibbah an shirya mata ruwan wanka da komai da komai.. Sannan ko akwai wani abu da Gimbiya Ke buk’ata..? Umaima ce ta jinjina kai tace “Kuna iya tafiya, Gimbiya hutu take buk’ata..!!” Hadimar ta kuma duk’awa tayi godiya kana suka sa kai suka fice..! Muhibbah Ta d’an dubi Umaima ta rausayar da idanu tana mai furta “Nifah wllhi duk ban saba da wad’annan abubuwan ba, sai inajin gaba d’aya kaman wata duniya ta daban nake, nafi sabawa da yin komai ma kaina..!” Murmushi Umaima tai tace “Da sannu zaki saba da d’abi’u da al’adun Gidan nan..! Muje na zab’a miki tufafin da zaki saka..!” Ta janyo hannunta suka nufi closet tare..! Gimbiya Turai ta raka su da kallo murmushi saman fuskarta, mik’ewa tayi itama ta nufi closet d’in tana tayasu zab’an tufafin... Dashike almuru ya riga ya sako kai, dare ya riga ya soma shigowa hakan ya sanyasu zab’a mata tufafi mai sauk’i sanyawa irinta masu mulki da sarauta..! ** A can b’angaren su Mahmood kuwa ko takan Giwa da ayarinta bai kuma biba tinda ya tabbata an fice dasu daga cikin Masarautar an tafi dasu asibiti domin nema masu taimako Ta gaggawa, iyaka taimakon da zai iya masu kenan dama a fice dasu daga Masarautar a nema masu agajin halin da suke ciki dukda cewa sune silan jefa mawunansu cikin wannan yanayi da suka tsinci kawunansu ciki...! A parlor ya tadda Ja’afar da Turaki suna jiran sauk’owarsa bayan komai ya d’an lafa, Turaki ya mik’e yana fad’ida Ja’afar “Kaga ga Rankaidad’e d’in ya fito... Ni zanje na baiwa Ansar masauk’i dan yace min idan yaji k’arfin jikinsa gobe yake komawa Bauchi..!” Ja’afar yace “Bazai bari ya kwana biyu ba.. Kuma ai akwai masauk’i cikin Masarautar nan, inaga basai ya fice..!” Muryar Mahmood suka sinkaya yana fad’in “Mutumin nan baida masauk’i cikin Masarautar nan..!!” Ja’afar ya had’iyi sauran kalamansa, Turaki ya jinjina kai yace “Dama can gidana zamu tafi your Highness..! Allah ya huci zuciyar Sarki mai jiran nad’i, Baban Zahra’u, kuma Angon Gimbiya Saudah Muhibbah..!!” Ya k’arashe yana mai d’ago masa hannu alamun jinjina.. Yasan ‘yan tsiyar Turaki ne suka motsa hakan yasa sam baibi takan Turaki ba saima zama da yayi saman kujera ya d’aura k’afarsa d’aya bisa d’aya yana murza zobban hannunsa a hankali..! Turaki ya risina yace “Rankaidad’e ni zan wuce, Masarauta is all settle now..!” Ya d’ago idanu guda yana duban Turaki ya dubi Ja’afar dake gefe... D’an gyaran murya yayi ya ambato sunan Ja’afar..! J’afar ya amsa cikeda risinawa irin yanda k’aramin k’ani keyiwa babban wa.. Tambayarsa yayi Mahaifiyarsu.. Ja’afar yace “Tana can tareda..!” Yayi shiru ya kasa k’arasa sunan Muhibbah..! Mahmood ya tsaresa da idanu.. K’ok’arin saita kansa Ja’afar yayi yace “Tana can tareda Gimbiya Muhibbah, Tana sashenta..!” Ya jinina kai a hankali sai kuma ya mik’e yana mai furta “Ka jirani a nan ina dawowa..!” Ja’afar ya jinjina kai a hankali yana mai amsa masa, duban Turaki Mahmood d’in yayi lokaci guda ya soma takawa, Turaki na biye dashi yasan hakan na nufin rakiya zai masa..! Suna tafe yana furta “Kasan irin kalaman da zaka Ke furtawa gaban k’anina..!!” Turaki ya had’iyi dariyarsa yace “Tuba nake Rankaidad’e... Yanzu shi Ansar d’in Dawakai nawa za’a basa kyautarsu..!” Had’iye maganar nasa yayi ganin ya kaikaito a hankali yana dubansa..! “Turaki..!!” Turaki ya amsa da “Rankaidad’e.!!” Mahmood yaci gaba da fad’in “Kar ka sake ambaton sunan mutumin nan a nan, nasan mai ya kawo shi ba komai bane ya kawoshi illa tsananin soyayyar da yake mata..!” Turaki ya jinjina kai yace “Toh amma Rankaidad’e gani nayi baka gabatar da kanka gareta ba tukuna.. Bamuda tabbacin If she feels the same for you, a tunanina sabida binciken gaskiya da kake cikin Masarauta shiyasa ka aurota gudun kar Waliyyinta ya bada aurenta ga wani wanda hakan ka iya hana kasancewarta cikin Masarauta... Tunda yanzu komai ya fito fili inaga ya kamata ka sauwak’e mata tun kafin ka kaiga sanar da ita matsayinka a wajenta..!” Burki yayi had’ida k’urama Turaki idanu ganin cewa da gaske yake fad’in duk abubuwan da yake fad’i, lallai ya yarda notin kan Turaki sun kwance...! Saida yayi gyaran murya hannayensa hard’e Ta baya ya soma furta “Idan na sauwak’a mata sai shi kuma ya aureta ko yaya..?! Kai ka tab’a jin Sarki mace talakansa ya aura..?!” Ya k’arashe yana duban Turakin k’asa k’asa Turaki ya jinjina kai yace “Toh idan kuwa haka ne, ya zama dole Sarki ya Sauk’e kansa ya sanar da ita how he feels..!” Ya katse Turaki da fad’in “What if zuciyarta na k’aunar Likitan nan ne..?!!” Turaki ya jinina kai yace “Then sai ka sawwak’e mata, Ta cancanci Farin ciki, Dan bazai yuwu kaita ajiyeta a d’aki ba tareda sanin madafar rayuwarta ba..!” Muguwar kallo ya kuma aikawa Turaki ba tareda yace komai ba..! Lokaci guda yake furta “Have I ever told you neman shawarinka is useless sometimes...!!” Turaki ya jinjina kai yace “Kasha fad’in haka Rankaidad’e, Allah ya huci ran Amale tuba nake..! Na barka lafiya Rankaidad’e...!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai bud’e motarsa, yasan cewa k’arshe za’a nemosa ne...! Da kallo kurum ya raka Turaki har ya shige yana tsaye a wajen hannayensa hard’e Ta baya... Duk duniyar nan Turaki ne kawai mai yab’a masa magana yanda yaga Dama.! Ya kuma fuzar da wani hucin yana tunanin al’amarin... Ta yaya zai fara tunk’ararta da batun, Ta yaya zai soma sanar da ita cewa shid’in mijinta ita matarsa ce..! Mai zai faru idan tak’i amincewa da hakan..!? Girmansa fah ya fad’i kenan musamman yanzu da yasan cewa su d’in ‘yanuwan juna ne matsayin k’anwa take masa..! Ya fuzar da fuci mai d’umin gaske yana mai shafe fuskarsa da duka hannayensa biyu..! Kai tsaye sashensa ya koma yanda ya baro Ja’afar na jiransa..! Daga bakin k’ofa ya tsaya yana duban yanda Ja’afar Ke shafa wani k’atoton hoton Mahmood da ‘yanuwansa su Duka hud’un sunyi shiga irinta Mulki saman Dawakai akai masu hoton, sunyi bala’in yin kyau kana ganinsu kaga ‘ya’yan Sarauta..! Ja’afar yasa hannunsa yana share hawayen dake gangaro masa yake kuma shafan hoton, a hankali Mahmood ya k’araso ya tsaya bayansa hannayensa hard’e yake duban hoton shima, lokaci guda yake furta “Kai yafi cancanta ka kasance cikin hoton nan, amma bata baka daman hakan ba, she deprived you your right, komai a nan da kake gani naka ne..! Everything is yours, sarautar da komai Naka ne ba nasu bane..! Duk abinda Ke cikin hoton nan ba komai bane face k’arya..!!” Ja’afar ya kaikaito yana dubansa, lokaci guda yasa hannunsa yana kuma goge hawayensa, a hankali yake furta “Akwai abu guda d’aya da yake ba k’Arya ba cikin hoton Yaya..! And that’s you..! Koda ace ban mallaki damata cikin Masarautar nan ba, ina Farin cikinka girma cikin gata da k’aunar mahaifinmu Yaya..! At least akwai abu guda da yake gaskiya ne a cikin Masarautar... And that’s you Yaya..! Wannan kawai idan na tuna nakanji Farin ciki..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka..! A hankali Mahmood ya janyo kafad’arsa ya rungume a gefen damansa, lokaci guda yake d’an bubbuga kafad’arsa yana lallashinsa irin yanda yakeyiwa Fu’ad..! A hankali Mahmood d’in yakai dubansa kan Fu’ad a cikin picture d’in... Ya saki murmushi mai sanyin gaske... Saida ya d’anyi gyaran murya kana yace “Gobe in sha Allah ka shirya zamuje wani waje..!” Ja’afar ya jinjina masa kai a hankali yace “Toh Yaya..!” Mahmood ya jinina kai kana sukai sallama da d’anuwan nasa ya haye samansa..! Yana isa d’aki ya kunna computer d’insa dake hasko masa d’akinta tareda nad’o masa sautin abindake wakana...Zaune ya gansu itada Umaima da kuma mahaifiyarsa sun saka a tsakiya... Ya zauna saman kujera yana mai bada hankalinsa sosai garesu.. ** Muhibbah ta d’ago tana dubansu su duka biyun, saida tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka zubo mata kana ta soma fad’in “Kaman yanda kuka sani Sunana Saudatu, na taso ni kad’ai wajen mahaifana, mahaifi na da Mahaifiyata ‘yanuwan juna ne sabida kaman yanda suka bani labari cewa bayan mahaifina ya rasa iyayensa sai mahaifin Mahaifiyata ya d’aukesa suka baro can garin nasu domin su tsiratar da mahaifina daga wad’anda suke nemansa da sharri..!” Ta d’anyi fasali kana yaci gaba da fad’in “Nasha yiwa iyayen tambayoyi da Dama wanda basu bani amsarsu ba sai yanzu nake ganin amsoshin tambayata garesu, daga ciki harda tambayar da nayi masu ina ne asalin garinmu, ina sauran danginsu..? Mahaifina saidai yace min kar na sake tambaya makamancin wannan..! Duk wani abinda zai tuno masa bayansa baya k’auna, sannan na kasance ina son labarun tarihi irinta gidajen Mulki da sarauta amma sam mahaifina baya k’auna, duk abinda ya shafi sarauta mahaifina baya k’aunar wannan abin...! Mun kasance muna tafiye tafiye daga gari zuwa gari tun bayan da muka rasa mahaifin Mahaifiyata wanda shine d’an uwan mahaifina da ya rainesa ya girma gabansa ya kuma ya aura masa d’iyarsa wacce ta zamto amana a garesa Wato Mahaifiyata kenan, bani mancewa mun zauna a wani gari mai suna Katakore a can k’asashen yamma... A wannan garin ne har aka sanyani makarantar boko da na Islama, mun d’anyi dogon zango a wannan garin kafin daga bisani muka soma shirye shiryen dawowa k’asashen Arewa....!” Ta d’anyi birki kana ta d’ago tana duban Gimbiya Turai tace “Bansan ko Zaki iya sanin Kakan nawa ba dan shi d’in d’anuwana ga mahaifina..!” Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “Tabbas Baba Sadi ne wanda kaman k’ani yake wa mahaifiyarmu, munada dangantaka dashi na tabbata shine ya d’auke Alfah gudun kar masu wawason gadon Mulki su cutar dashi..! Allahu Akbar bansan Baba Sadi yanada d’iya ba.. koda shike watak’ila nayi aure kafin ya haifeta ko kuma ya haifi mahaifiyar taki amma tana k’arama lokacin shiyasa bazan santa ba..!” Muhibbah ta jinjina kai kana taci gaba da fad’in “Abbah ya tattaro Mu gaba d’aya ya taho damu neman abu mai mahimmanci a gareshi da kullum yake fad’i wanda Nidai ban San menene wannan abin ba mai yuwa Sabida k’arancin shekaruna a wancan lokacin amma ta yuwu Mahaifiyata ta sani..! Ashe a wannan lokacin Mahaifiyata tana d’aukeda juna biyu..! Kafin mu k’araso garin Jos mun tsaya a wani gari mai suna Tafisu a can kusan yankin Niger state..! Toh a wannan garin taita rainon Jaririn cikinta har dai labari ya iso ga mahaifina cewa abinda yake nema yana a nan garin Jos, dukda juna biyu da take dashi haka muka baro garin Tafisu muka nufo garin Jos.. A lokacin juna biyu da Mahaifiyata kedashi ya d’an soma girma...!!” Tai shiru hawaye naci gaba da gangaro mata..! Muryarta yaci gaba da rawa sanda taci gaba da basu labari tazo daidai yanda ‘Ya’yan Giwa sukaci zarafinta, da yanda Ta farka Ta tsinci kanta gaban wannan matsafin..! Mahmood dake kallonsu daga d’akinsa hawaye ne shima yaji suna gangarowa daga fuskarsa..! Yaci gaba da matse zobban hannunsa wanda har baisan yaji masa ciwo a d’an yatsa ba sabida yanda zuciyarsa Ke tsananin tafarfasa...! Muhibbah ta share k’wallan da suka zubo mata kana taci gaba da fad’in “Sun tarwatsa ahalin da suka rage min a wancan lokacin..! Sun cinnawa gidanmu wuta wanda hakan ya samu tserewa da rayuwarmu...! Zan iya ce maku bansan yaya akayi na had’u da Mahaifiyata ba, wane irin tashin hankula ne muka tsinci kawunanmu ciki a wancan lokacin wanda baki bazai iya fad’I ba, zuciya bazata iya kwatanta girman tashin hankalin ba... Iyakacin abinda na sani shine Mahaifiyata tace dole mu gudu mu bar wannan garin, dan a daren da abun ya faru a daji muka kwana, gashi cikinmu babu mai wani k’arfi, ita tana fama da juna biyu ni kuma ga iftila’i da tsautsayin da ya auka min wanda ko tafiya bana iya yi saidai Mahaifiyata da take fama da juna Ta Azani a bayanta..! Shin ku gaya min nayi laifi da nace zan dawo d’aukan Fansa..?!!” Hawaye ya kasa daina gangarowa daga fuskokinsu... Lokaci guda taci gaba da fad’in “Da taimakon wani mai motan kwaso dabbobi daga arewa akwaisu Kudu shi ya taimaka mana ya fitar damu zuwa garin Yalwan Shandam, koda mukaje garin tana cikin yanayi na tashin tashin hankula, a nan wannan garin dai muka samu mafaka a sansanin ‘yan gudun Hijira wanda har na d’an sami kulawa daga likitoci masu kawo agaji ma ‘yan gudun Hijira Mahaifiyata ma ta sami kula daga wajen likitocin duba da yanayin da take ciki...! Maikatan lafiya dake kula da ‘yan gudun Hijiran sunyi mamaki da jin zafin yanda akaci zarafina gashi dududu ba wani shekaru ne dani ba..! Na shiga tashin hankali Mahaifiyata ma ta shiga tashin hankali maras misaltuwa da abinda ya sameni, na zamto bana shiga cikin yaran dake wannan sansanin domin kuwa tinda mutanen dake cikin sansanin suka soma ‘yar gulmace gulmacen abinda ya sameni kowa sai yana janye ‘ya’yensa daga gareni, babu mai barina na kusanci ‘ya’yansa balle nayi wasa taredasu.. Na koma tamkar wata mujiya abin gudu ga kowa... Rayuwa Ta mun d’aci matuk’a, na fuskanci kyara da tsangwama, kowa ya ganni sai gudu tamkar anga dodanniya... Wannan rayuwar itace na fuskanta a Sansanin da muka tsinci kawunanmu ciki... Inada tabbacin tsananin da muka shiga tareda k’uncin abinda ya sameni shi ya sanya Mahaifiyata haihuwa yazo mata ba tareda lokacin haihuwar ya cika ba..! Mahaifiyata ta haifo d’iyarta mace kyakkyawa, saidai tinda Ta haihu batayi lafiya ba... Na buk’aci a sanyawa Yarinyar suna Muhibbah domin ta samu soyayyar mutane kaman yanda sunan nata yake..! A daidai wannan lokaci ‘yan tadda suka kawoma Sansanin Farmak’i... Suka cinna ma Sansanin wuta, aka soma gudu kan mai uwa dawabi ana tattara yaran dake Sansanin dan tseratar da rayuwarmu.. Banga Mahaifiyata ba banga jarriyarta ba.. Na dinga tsalle ina ihu ina k’ok’arin k’watan hannuna daga hannun ‘yan kwana kwanan da suka kawo mana d’auki Ina fad’in su k’yaleni Mahaifiyata da k’anwata suna cikin Tent d’inmu wanda Ke ci da wuta..! Haka suka hanani zuwa suna sanar dani saidai nayi hak’uri Mahaifiyata da ‘yaruwata sun mutu a wannan wutar sun zama toka go gawawwakinsu ba’a gani ba..!” Ta kuma goge wasu hawayen kana taci gaba da fad’in “Ya kuke tunanin yarinya mai k’aramin shekaru kaman nawa zataji a wancan lokacin.. Ta yaya bazan girma da k’udirin tarwatsa mutanen da suka tarwatsa min ahalina ba..!” Cikin muryarta dake tsananin rawa taci gaba da furta “Na k’wace hannuna na soma gudu banma San ina nake zuwa ba.. A iyaka sanina shine bazan kuma zama a wannan Sansanin babu Mahaifiyata babu k’anwata ba...!” “Sansanin dake Yalwan Shandam..!” Ya nanata a hankali...Take ya shiga tuna abubuwan da suka faru baya, abinda suka bisne shida abokinsa Turaki tsawon shekaru..!Shafe fuskarsa da gumi Ke tsartsafo masa ya kumayi yana jin yanda Muhibba taci gaba da bada labarin yanda ta kub’uta daga wannan sansanin har kawo zuwa yanda iyayen Ansar suka taimaka mata, suka zamto sutura da Gata a gareta, Ansar ya zamto tamkar wani fitila wanda ya haskaka mata rayuwa.. Shida mahaifiyarsa sunyi mata komai. Taji tsoron sanar dasu abinda ya faru da ita gudun kar suma su k’yamace ta kaman yanda aka gujeta a Sansanin Yalwan Shandam..! Haka taita basu labari har dawowarta Masarautar da k’udirinta da kuma yanda Ansar ya taimaka mata sukayi komai tare hardai zuwa k’alubalen da suka fuskanta daga wajen Yawale da Gudidi kan batun aurensu da yanda mahaifiyar Ansar tak’i amincewa bayan dataji abinda ya sami Muhibbar wanda bata baiwa Muhibbah ko Ansar daman yi mata bayanin abinda ya faru ba..! Hardai zuwa ranan aurenta data farka Ta tsinci kanta a wannan d’akin...! Gimbiya Turai ta dafe hannayensu su duka biyun tace “Duk wannan iftila’i da rarrabuwan ahali da muka tsinci kawunanmu ciki tuni Allah ya k’addari faruwan hakan saidai akwai sanadi, sanadi kuma Izzatu ce..! Dole mu godewa Allah mu kuma gode masa da a k’arashe ya had’e ahalinmu waje guda..! ‘Yanuwanmu da suka rigayemu gidan gaskiya Ubangiji ya gafarta masu mu kuma idan namu tazo ya d’auki ranmu muna masu imani, mutuwa dole ce hanyace guda d’aya wanda dole kowa sai yabi..! Banaso ku saka ma ranku cewa wani ne ya jawo kuka rasa masoyanku iyayenku da ‘yanuwanku, a’a wani baya rayawa kuma baya kashewa.. Allah shi kad’ai ne mai rayawa ya kuma kashe, duk wanda ya rasu lokacinsa ne yayi saidai wani ya zamto sanadi kun fahimta..!” Suka jinjina kansu a hankali suna masu share hawayensu..! Sun d’an jima kad’an har sukaci abinci tare gwanin dad’I da sha’awa kana sukaima Muhibbah sallama kowa ya nufi nasa b’angaren, Gimbiya Turai ma da nata Hadiman ta nufi nata b’angaren da aka Ware mata na musamman... Can ta tadda Gimbiya Zeenat na zaman jiran K’arasowarta..! Gabatar da kanta Gimbiya Zeenat tayi had’ida neman yafiya kan biyewa Giwa da tayi Ta kasa tona mata asiri na kisan matar Mahmood Aliya da tayi dan kawai ‘yaruwarta ta auri Mahmood d’in.. Gimbiya Turai tace ai Babu komai itama ta fad’a tarkon Izzatu ne, tana fata abubuwanda suka faru cikin Masarautar ya zamto wa’azi garesu gaba d’aya Dama wad’anda sukaso kwakwayon wannan muggan d’abi’u..! ** Zama yayi bisa couch yana duban duk wani motsinta tinanin labarinta bai daina Yawo akansa ba... Lokaci guda ya hangota ya fito daga closet, wannan karon doguwar rigar bacci ce mai laushin gaske Wanda ya kwanta luf jikinta..! Ya lumshe idanunsa a hankali yana tunanin idan yana son sanin cewa Muhibbah da Zarah ‘yan uwan junane Toh ya kamata ya d’auko sample d’in Muhibbar cikin daren nan Washe gari ya bada a running masa DNA test tsakanin samples d’in nasu guda biyu..! Toh amma ta ya zai sami sample d’in Muhibbah cikin daren..?! Ya kuma lumshe idanunsa yana tunanin abinyi, wata zuciya tace kaje ka samo da kanka..! Yana ganin sanda ta ida sallan shafa’i da wutiri Ta linke abin sallahn ta mik’e ta haye gado had’ida kashe wuta..! Mik’ewa shima yayi ya zira jallabiyarsa fara k’al sai k’amshi ke tashi ya nufi nata b’angaren..! Harga Allah bataji shigowar mutum ba dan bacci yayi gaba da ita... Ya jima sosai yana k’are mata kallo da d’an hasken dake hasko cikin d’akin daga waje... Ya zauna a gefenta a hankali yana mai ci gaba da k’arema halittar jikinta kallo... Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai jin yarrr gaba d’aya stikar jikinsa na tashi... Wata zuciyar tace kayi abinda ya kawo ka ka fice kafin Ta farka ta ganka...! Da wannan tunanin ya soma zame hular bacci dake kanta a hankali kaman mai tsoron kada ya tada ita ga wani irin bugu da zuciyarsa keyi..! Cak ya tsaya da abinda yake sanda ya soma sinkayo muryarta cikin tsananin tsoro tana fad’in kada su cutar da ita alamun mafarki take na abubuwan da suka faru da ita..! Tai wani irin k’ara tana mai k’ank’ame jikinta waje guda, juyin da zatai Ta jita cikin jikin mutum ya mata runfa had’ida matseta tsam cikin jikinsa, tanajin hucin numfashinsa alamun yana karanto mata add’u’o’in tsari yana tofa mata..! Zuciyarta yaci gaba da yankewa, tanajin yanda k’irjinsa yai mata rumfa.. Meke faruwa da ita.. Shin Rankaidad’e ne yake bibiyarta haka..? Toh mai hakan yake nufi..?! Take taji zuciyarta naci gaba da tsinkewa abinda ya faru da ita shekaru goma sha hud’u baya ya shiga dawo mata.. Tsoro da firgici suka cikata..! Ya fahimci yanayin da take ciki na tsananin tsoro da firgici, hakan yasa ya kuma rufeta sosai da k’irjinsa, saitin kunnenta yake rad’a mata “bani daga cikin shaid’anun mutane, bani daga cikin wad’anda suke keta haddi kan abinda damarsu bai mallaka ba..! I’m here now, kiyi bacci cikin aminci.. Bazan bari wani abu ya cutar dake ba... I’ll watch you sleep the whole night..!!” Ya k’arashe yana mai rufa masu bargo da d’aya hannun nasa har lokacin bai saketa ba yana rik’eda ita cikin jikinsa...! Cikin yanayin tsoro take furta “Rankaidad’e.. Shin kaine..? saida maka ni sukai..?!” Cikin tsananin rawar murya take ci gaba da furta “Kaji tsoron mahaliccinka wanda yake iya ganinka komin duhun daren nan... Kada ka cutar dani..!” Ta sinkayo muryarsa kaman mai rad’a yana furta “Do you have to keep on buzzing..? Stop asking questions..! Just close your eyes and go to sleep now...!” Samun kanta tayi tana mai bin umarninsa, Ta rintse idanunta da k’arfin gaske zuciyarta bata daina tsinkewa ba, wannan murya Ta Rankaidad’e ne..! Toh mai yake nufi da kalamansa da yace baya daga cikin shed’anun mutane wanda suke keta haddi kan abinda damarsu bai mallaka ba..? Toh kodai siyar masa ita Baffah Yawale yayi shiyasa ya kawota cikin Masarautar ya aje... Kardai a matsayin Kuyanga ya sayota, kardai ba’a d’aura mata aure da Ansar ba..! Shin Wai meke faruwa ne..?!! Toh kodai ma ba Rankaidad’e bane..!? Idan bashi bane Wanene...? Ta lumshe idanunta har lokacin tsoron bai saketa ba, tanajin yanda zukatansu Ke bugu cikin na juna, bata San ya akayi bacci ya saceta a yanayin da take ciki ba, farkawa tayi da asuba taga baya nan... Tai saurin kunna side lamp zuciyarta na kuma tsinkewa bataga kowa ba sai wannan musulmin k’amshin nasa dake tashi a hankali kama daga jikinta zuwa yanda ya kwanta..! Ta lumshe idanunta a hankali tana ambaton Allah.. Kalaman mutumin yana dawowa kanta wanda tafi bada k’arfin zaton Rankaidad’e ne..! Meke faruwa..? K’ila dai sayota yayi matsayin Kuyanga..! Wannan tunanin shine yafi tsaya mata a zuciya..! Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata... Sai tana ganin abin tamkar a mafarki ne ya kasance..! Sosai Ta shiga rud’u da damuwa... Ta shiga lalumen magungunan data sha daren jiyan tana tinanin anya batayi overdose ba..! ** A b’angaren Mahmood kuwa tinda ya dawo nasa b’angaren ko wane juyi zai sai ya tuna daren jiya, da yanda sukayi bacci cikin jikkunan juna, inama hakan ya kasance ko yaushe, yasan ya barta cikin tarin rud’u da tunanin abinda Ke faruwa tinda har wannan lokaci bai fito fili ya sanar da ita dalla dalla abinda ya faru ba..! Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai tuno k’amshin da ya shak’a cikin jikinta, shikad’ai sai sakin murmushi yake... Yana jan cazbahan dake rik’e hannunsa yana kuma sakin murmushi sanda ya tuna kalamanta a garesa wanda sosai sukaso basa dariya amma ya gimtse... A fili ya furta “So innocent..!!” Tunowa da yayi Muhibbah zata iya kasancewa ‘yaruwar Zahra ya sanyashi mik’ewa zaune sosai yana tuno abubuwan da suka faru... Ya jima yana zaune wajen yana tuna abubuwan da suka faru sai faman sak’awa da warwarewa yake, dole ya gwada k’wayar halittarsu cikin gaggawa domin tabbatarwa idan sud’in ‘yanuwan juna ne, saida gari ya d’an soma wayewa kana ya fito domin ya nufi k’abarin mahaifinsa.. A hanya ya had’uda Ja’afar da alama shima k’abarin MaiMartaba mahaifinsu ya nufa..! Ja’afar yana ganinsa ya k’araso suka gaisa, a tare suka jera suka nufi k’abarin mahaifinsu.. Suka jima sosai suna masa addu’a kafin daga bisani suka nufi b’angaren mahaifiyarsu... A parlor suka taddasu itada Baba Nomau yana karanto mata Alk’ur’ani tana biyawa..! Cikin jin dad’I suka k’araso suma suna sauraro, saida suka ida karatun kana Mahmood da Ja’afar suka risina suka gaisheda mahaifiyarsu... Suka isa can saman Darduman da Baba Nomau Ke zaune bisa sukai masa musabaha had’ida gaisuwa..! Baba Nomau ya kamo hannun Ja’afar yace suje Bargan Dawakai ya nuna masa Doki mai Fararen sawaye da yake basa labari kafin ya koma gida..! Ja’afar na murmushi ya amshi jakan fata ta Alk’ur’an d’in Baba Nomau suka nufo waje yana fad’in “Baba ashe dai baka mance ba..!” Baba Nomau yace “Yarima ina zan mance, bayan abinda nake son gani ne..!” Ja’afar ya kuma murmusawa yana mai furta “Aiko wajensu na nufa dan nayi kewan Dawakan gaba d’aya..” Suka jera suka nufi Bargan Dawaki, Hadiman Masarautar duk yanda suka gansu sai Sun risina Sun gaidasu, abinda Ja’afar yakema wasu a baya yau sai gashi ana Yi masa..! Allah kenan mai juya al’amaransa a lokacin da yaso..! A can parlorn Gimbiya Turai kuwa gyaran murya tai ta ambato Mahmood da fad’in “Saraki..!” Mahmood ya amsa mata cikeda girmamawa.. Gimbiya taci gaba da fad’in “Dama inaso nai maka magana kan Saudah...!” Ya d’ago a hankali yana duban mahaifiyar tasa sai kuma ya maida kansa k’asa... Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Tinda ga yanda auren naku ya kasance, kafin Ayi shelanka matsayin Sarki.. Kafin ai maka nad’i ina son sanin matsayin auren naku tunda kasan sharud’a da k’aidojin al’adu da dabi’u na cikin Masarautar nan..! Idan har Saudah bata k’aunarka a matsayin miji da zatai rayuwa dakai bazanso Ta kuma wani rayuwar k’unci nan gaba ba... Ta cancanci Farin ciki bayan tulin iftila’i na rayuwa data fuskanta..! Shiyasa nace kafin ayi maka nad’i a ambaceka a matsayin Sarki, Ina son sanin matsayin wannan auren naku..!!” Ta k’arashe cikeda kulawa.. Wai ance ba’a San Sarki da fad’uwan gaba ba sannan ba’a Sarki rago amma shikam tabbas wannan tambaya da mahaifiyarsa tai masa ya d’auresa gaba d’aya had’ida haifar masa da fad’uwan gaba wani na bin wani...! D’an gyaran murya yai yace “Ummi dama akwai wani alfarma da nake so..!” “Alfarma kuma Saraki..?!” Ta nanata a hankali tana mai dubansa... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *78* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kafin Mahmood yakaiga furta wani kalma amintacciyar Hadimar Gimbiya Turai ta nemi izinin shigowa, saida ta duk’a cikeda risinawa ta gaida Yarima da mahaifiyarsa kana tace “Allah shi baka yawan rai Barde yana k’ofa yace a sanar dakai isowan Turaki..” Mahmood ya jinjina kai a hankali alamun amsawa, Ta kuma risinawa ta nemi izinin fita... Maidoda dubansa ga mahaifiyarsa yai kaman zai magana sai ta katsesa da fad’in.. “Yanayin dana ganka ciki Allah yasa lafiya...? Ina saurarenka wane alfarma kake magana..?” Shiru ne ya d’an biyo baya kafin yai gyaran murya kad’an yace “Kan batun d’iyata Zahra ce... Inaso ki bani lokaci kad’an, nayi alk’awarin zanzo miki da bayanin komai a dunk’ule..” Maganan Muhibbah suke ba Zahra ba, amma da alama so yake ya kawar da zancen shiyasa ya kawo batun Zahra, shiru ne ya ratsa tsakani kana ta jinjina kai tace “Ba damuwa, Allah ya kaimu lokacin... Kaci karin kumallo ne..?” Ta tambaya tana dubansa cikeda kulawa.. Wani irin sanyi mai gauraye da rahama yakeji cikin zuciyarsa, tinda yake da Giwa bata tab’a tambayarsa lafiyarsa ba, yunwarsa ko k’ishin ruwansa damuwarta kawai ya cika mata burinta ya d’ale Karagar mulki... Yau ga mahaifiyarsa Ta asali tana kula dashi irin yanda akema k’aramin yaro Dukda yawan shekarunsa.. Ya jinjina kai a hankali yace “Naci Dibino da ruwan shayi kafin na shigo..” Kanta a k’asa irin kunyar nan da akewa yaran fari ta murmusa domin kuwa ba kowa ya tuno mata ba face Mahaifinsa, hakan yakeyi wasu lokuta.. “Ka zama Bak’on Buzu da gaske kenan..” Ta fad’i murmushin bai bar saman fuskarta ba... Shima d’in d’an Murmusawa yai kad’an yana mai k’ok’arin mik’ewa Ya risina kad’an yace “Na barki lafiya Rankidad’e..!” Harda ‘yar d’aga babban yatsa yai mata alamun jinjina... Sai yana tuno mata da lokutan baya lokacin tana can masarautarsu kafin tayi aure... Hak’ik’a lokaci yayi da zasu waiwayi gida... ** A parlornsa ya tadda Turaki yana jiran k’arasowarsa... Bayan sun gaisa Turaki yai gyaran murya yace “Wai lafiya ka d’add’agoni da sassafen nan... Kodai Gimbiya turned Rankaidad’e down ne..” Ya k’arashe cikin sigan wasa.. Mahmood yai masa wani duba da gefen idanu had’ida girgiza kai, shidai Turaki ba’a rabasa da jin baki, ba tareda ya furta komai ba ya nufi upstairs.. Jim kad’an ya dawo rik’eda sealed ledoji guda biyu a hannunsa, ya mik’awa Turaki yace “Gwajin k’wayar halittar samples d’in nan nake so... If possible kar ya shige cikin satin nan kafin ayi nad’in sarautar nan...” Turaki ya dubesa da mamaki yace “DNA test your Highness..? Samples d’in su Yazeed ne ko kuwa na su waye..?” Fuzar da huci yai kad’an ba tareda yace komai ba saima juya ledojin yake a hannunsa wanda d’aya toothbrush d’in Zahra ne ciki d’aya kuma sumar Muhibbah ne da ya tsinko jiya akanta a ciki... Murmusawa Turaki yai yace “Mahmoodu hadari sa gabanka yanda kake so.. Tambihi gagari fasahar yaro... Idan tayi tsami dai zata fito Fada Sank’ira ya mana shela..” Murmusawa yai kad’an wannan karon suna duban juna su duka biyun sanda Turaki yasa hannu ya amsa... A hankali ya furta “Thank you..” Murmusawa kurum Turaki yai had’ida furta “An gama Rankaidad’e.. Zanyi k’ok’ari na tabbata an samu within the week..” Mahmood ya jinjina masa kai, har zai fice ya dawo da baya yace “Aff kaga na mance Rankaidad’e.. Tare muke da Dr Ansar zai shigo yai maka sallama idan anyi masa izini, sannan a bashi dama yayi sallama da Gimbiya Muhibbah, yau yake son komawa garinsu...” Take ya had’e rai sosai yana duban Turaki k’asa k’asa, kaman wanda baison magana ya soma fad’in “How Many times do I have to tell you.. I don’t trust that Dr, especially around my wife..!” Turaki ya d’anyi jim kansa a k’asa yake furta “A dai duba lamarin Rankaidad’e.. A basa wannan damar duba da matsayin da ahalinsa kedashi wajen Muhibbah.” Ya tsare Turaki da idanu na wasu dak’ik’ai kana yakai dubansa gefe, a hankali ya jinjina kansa yana mai furtawa da k’yar “Send him in..” Turaki ya murmusa yana duban Mahmood d’in “Godiya yake Rankaidad’e..” Ya k’arashe yana mai d’ago masa babban yatsarsa guda alamun jinjina... Bai kuma bi takan Turaki ba ya k’arasa saman kujerarsa yai zama irinta masu mulki yana jiran shigowar Ansar... Kan Ansar a k’asa ya shigo Barde na biyedashi yana kod’a Sarki Mahmood mai jiran nad’i , Ansar ya k’arasa ya zauna saman Darduman dake gaban Mahmood had’ida masa gaisuwa irinta masu mulki... Da kai kurum Mahmood ke amsawa yana karantar Ansar d’in da idanu, sam shi bai yarda dashi ba... Barde ne Ke amsa gaisuwar da fad’in “Sarki ya amsa maka Likita Bokan Turai.. Jaaa zamanin Sarkin Sarakuna...” Ansar yaci gaba da furta “Godiya nake Rankaidad’e.. Akan hanya nake yau in sha Allah zan koma gida shine nace b’arin shigo nai maku sallama.. Allah shi taimakeka..!” Yai maganan yana dunk’ule hannunsa guda had’ida mik’a jinjina ga Mahmood d’in... Shiru ya ratsa tsakani sai sautin kirari kawai da Barde keyiwa Mahmood “D’awisu Sarkin kwalliya.. Kaga d’an jimina gagara d’aukan shaho..! Girgije sa gabanka yanda kake so.. Dogon Sarki mai dogon zamani.. Allah shi jaa zamaninka...” Ansar ya zaci Mahmood d’in bazai kuma fad’in wata kalma ba har saida ya d’an d’ago ya dubesa.. Ya soma k’ok’arin mik’ewa yana furta “Idan Sarki yamin izini ni zan wuce...Na barku lafiya your Highness..” Yai maganan yana mai risinawa... Ya kuma jinjina masa kai ba tareda ya furta koda kalma guda ba... Barde ya soma k’ok’arin rakiyawa Ansar yana furta “Sarki ya maka izini Likita..” Gyaran Muryar Mahmood da suka sinkayo ne yasasu dakatawa Barde na k’ok’arin k’arasowa cikin d’an gudu gudu ya zube gaban Sarkin... Murya can k’asa yake furtawa Barde a zab’awa Ansar doki mai kyau cikin Bargan Fada sannan ai masa rakiya wajen Gimbiya Muhibbah.. Barde ya jinjina masa yana mai furta “An gama Rankaidad’e.. Godiya yake..” Ansar Wanda a gabansa akai maganan amma tsaban mulki ba’ayi direct to shi ba sai ya dawo da baya ya risina yana fad’in “Godiya nake Rankaidad’e.. Amma da dai an bar dokin..” Baikai aya ba Barde ya katsesa da fad’in “Hattara Bokan Turai, Sarki baya kyauta a dawo masa..” Ansar ya had’iyi abinda ya tsaya masa a mak’oshi... “Godiya nake Rankaidad’e..!” Ya fad’i tareda jinjina.. Har sun soma tafiya suka sinkayo muryarsa mai amo ya amsa illahirin parlorn cikin yin gyaran murya, babu shiri Barde ya koma da baya ya zube.. Mahmood ya d’ago yatsarsa yayi alama guda d’aya biyu zuwa uku, kaman wanda baison magana ya furta “Minti uku kacal..” Barde ya jinjina kai yana mai furta “An gama Rankaidad’e...” Barde ne kawai ya fahimci Sarki na nufin minti uku kacal aka baiwa Ansar yayi sallama da Gimbiya... Shikam Ansar d’in bai fahimci komai ba dan ba wani gane yaren sarakunan yake ba... ** Tsaf Ta shirya cikin wani lallausan leshi da akai masa d’inkin riga da skirt, sosai ya amsheta, Ta jima tana duban kanta jikin full-length mirror abubuwa da dama suna zuwa zuciyarta, kaman anyi ruwa an d’auke Wai yau babu su Giwa cikin Masarautar.. Allah kenan Buwayi gagara misali... Ta tako a hankali tana mai tuna daren jiya da abinda suka faru, zama tai bakin gado tana mai kuma nanata lamarin cikin zuciyarta..Tana nan a haka Hadimarta ta nemi izinin shigowa kana ta shigo kanta a k’Asa bayan Muhibbar ta mata izini.. “Ki gafarceni Rankidad’e, Barde yace in sanar dake kinada bak’o a waje...” “Bak’o.!” Ta nanata a hankali tana tunanin waye ma Barden.. Ta dubi Hadimar kad’an tace “Wanene Barde..?” Hadimar ta kuma risinawa tace “Amintaccen Hadimin Sarki Mahmood mai jiran nad’i kenan Allah shi taimakeki..” Muhibbah tai shiru kaman mai tunani sai kuma ta jinjina kai a hankali tace “Kije ki tambayo ko wanene bak’on..” Hadimar ta kuma jinjina kai had’ida bin umarnin uwargijiyarta.. Jim kad’an ta dawo ta risina tace “Allah shi taimakeki kaman yanda Barde ya sanar dani, Maimartaba Sarki Mahmood ne ya turosa..” Tai still tana duban Hadimar, jinjin kai tai a hankali tace “Kije ki sanar dashi ina tafe..” Hadimar ta amsa cikeda girmamawa kana ta fice... lokaci guda Muhibbah Ta mik’e had’ida janyo alkyabbarta ta rufa bisa kanta, A parlor Ta tadda Hadimar tana jiran fitowarta lokaci guda tai mata jagoranci zuwa wani madaidaicin parlor a k’asa... Ga tsananin mamakinta Ansar ta gani, ta saki murmushi a hankali shid’inma murmushin ne saman fuskarsa... Yana hangota ya mik’e tsaye yana jin zuciyarsa na fuzga kaman zai fasa k’irjinsa ya fito waje... Tana K’arasowa ya silale k’asa hm had’ida d’ago babbar yatsarsa alamun jinjina gareta “Rankidad’e..!” Dariya yaso bata amma sai ta murmusa kawai ta k’araso ta zauna saman kujera tana mai furta “Ka tashi ka zauna idan ba so kake nima na duk’a gaba gareka ba..” Ya mik’e da sauri yana murmushi ya koma saman kujera ya zauna had’ida furta “Wane ni Gimbiya Ta zauna k’asa gabana.. Ai sai kisa na koma garinmu da k’afa guda..” Nan ma murmushi kawai tai wanda da gani na k’arfin hali ne.. Shiru ya ratsa tsakani zukatansu saiko bugun zukatansu, gaba d’aya sai tana jin wane irin nauyinsa.. Muryarsa Ta sinkayo yana furta “Cant I talk to my sister in private..?” Yai maganar yana duban Hadimar dake tsaye gefen kujerar da Muhibbah Ke zaune bisa kanta a k’asa... D’agowa Muhibbah tai Ta dubi Hadimar tai mata alama da hannu kan cewa Ta fice daga parlorn.. Hadimar ta risina tayi yanda Muhibbah ta umarta... Shiru ya d’an ratsa tsakani kana Ansar yai gyaran murya ya soma fad’in “I know by now kinada masaniyar cewa ba’a d’aura mana aure ba..” Ta d’an d’ago a d’an firgice tana dubansa, Ansar ya jinjina mata kai alamun Tabbatarwa yace “Muhibbah ba’a d’aura mana aure ba kaman yanda mukaci buri.. Sun mana fin k’arfi... Sun rabamu da k’arfin mulki da dukiya.. Ko Kinsan wanene ya aureki..?” Yai tambayar cikin rawar murya yana duban Muhibbah da tuni k’walls sun ciko idanunta... Ansar yaci gaba da furta “Muhibbah Yarima Mahmood shine ya aureki... Kuma ba don yana k’aunarki ba sai don yayi amfani dake ki zamto bakin zaren da zai warware masa duk wani k’ulli dake cikin Masarautar nan... Hibbah Mahmood sayenki yayi da mak’udan kud’ad’e daga wajen Yawale... Nasan shid’in d’an uwanki ne... Nasan bai kamata naita fad’in kalamai irin haka ba, but is the truth Muhibbah... Shid’in ba Auren soyayya yayi dake ba.. Satoki yayi daga wajen masoyinki na asali..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Muhibbah dake jin batun tamkar wani sauk’an aradu duban Ansar take hawaye na gangaro mata “Kace ya auroni ne domin na zamto bakin zare a garesa..?” Ansar ya jinjina kai yace “K’warai domin yayi amfani dake ki warware masa duk wani k’ullin dake cikin Masarautar nan, Don’t you find it strange yanda yazo ya ajeki ba tareda wani bayani ba, sannan saida aka drugging d’inki aka kawoki cikin Masarautar nan, nima kuma akai drugging d’ina aka hanani halartar aurenmu... Mahmood da Baffah Yawale planed everything Hibbah.. Harta Mommy batasan da wannan shirin nasu ba.. Tana can hankalinta tashe da tunanin wanene mijin da aka aura miki..Hibbah Mommy bata cancanci haka ba.. None of us deserve this..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Izuwa lokacin kukan da Muhibbah keyi ya k’aru, Wato wannan shine dalilin Rankaidad’e na bibiyanta, she was right sayota yayi tamkar wata baiwa ya ajiyeta babu wani bayani, shin ta ya ma za’ai mata irin wannan auren kawai dan yana basarake.. Har abada bazata aminta da wannan auren ba.. D’ago idanunta masu zuban ruwa tai tana mai jinjina kai take furta “Ina mai tabbatar maka wannan auren won’t last, ban amince ba kuma bazan tab’a amincewa ba...!” Har cikin ransa yaji dad’in kalamanta, shawo kanta bazai masa wahala ba... Bazai bar masarautar ba har sai ya tabbata ya d’auke abinda aka sace daga garesa.. Wannan dalili shiyasa ya sauk’ar da kansa ya saye zuciyar Turaki da d’abi’u masu kyau tinda ya fahimci duk duniya babu wanda Yarima Mahmood yake d’aukar maganansa irin Turaki shiyasa ya biyo ta jikin Turaki dan ya sami amincewa e Ammar Mahmood cewa shid’in mutumin k’warai ne kuma baizo dan ya lalata aurensa ba.. Ya saki murmushi a hankali yana mai duban Muhibbah yanda take cazgan kuka mai tab’a zuciya, Ya jinjina kai a hankali kana ya soma furta “Don’t ever agree to this marriage Muhibbah..! Baffah Yawale sold you, martabanki da kimarki ya wuce a aurar dake a wulak’ance just like that...You’ve been through a lot, you deserve happiness... Ke Sarauniya ce, Martabarki ya wuce a aurar dake a wulak’ance...!” Muryarsa ya soma rawa sanda yake ci gaba da furta “Mahmood doesn’t love you Muhibbah.. Kawai k’arfin mulki ya gwada akanki...Da ace yana sonki bazai auroki a wulak’ance ba, he kidnapped you, satoki yayi Hibbah... Na sani d’anuwanki ne but I’m sorry to say he’s just like them.. Shima d’in d’an ta’adda ne tin da sayenki yayi wajen Yawale ya kawoki nan sabida baki cikin hayyacinki.. Hibbah please don’t agree to this marriage, do it for me.. For the love we have for each other.. Muhibbah kar ki bari su k’wace min ke... I still love you, so much..!” Ya k’arashe yana mai silalowa daga saman kujera ya duk’a gwiwoyinsa gabanta had’ida had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o.. Hawayene kurum Ke ziraro mata d’aya na bin d’aya... Ansar ya mata hallaci a rayuwa, kuma sud’in masoyane basu cancanci haka daga Rankaidad’e ba.. Dama dangin sayenta yayi, tayi gaskiya da tace sayota yayi tamkar Baiwa.. Kenan yajesa ya saye Yawale da kud’i ya saida masa ita... Ta yaya zai aikata haka..?! Ta yaya zai sayota tamkar wata Baiwa, dole mana ya kulleta a d’aki ya hanata fita. Raheemah dake lab’e jikin window wani irin murmushi ne saman fuskarta, Wato abinda ya faru kenan, idan kuwa haka ne dole tayi amfani da wannan damar su had’a k’arfi da k’arfe itada wannan mutumin su raba Mahmood da Muhibbah, itama ta sami chance da zata rama abinda Mahmood d’in da Muhibbah sukai mata... Ansar ya mik’e jiki a sanyaye yana furta “Ni zan koma Hibbah, I hope zakiyi abinda ya dace ... Ki k’wace ‘yancinki daga hannun mutumin da ya sayoki tamkar Baiwa a kasuwa..!” Yana ida fad’in haka Barde ya lek’o yana furta “Lokacinda mai Martaba ya d’ibar maka ya cika Bokan Turai...” Ansar ya jinjina kai yana mai k’ok’arin saita kansa had’ida mik’ewa “Na barki lafiya Rankidad’e..!” Ya fad’i yana duban k’asa kana yasa kai ya fice yanda ya bar Muhibbah naci gaba da matsan hawaye zuciyarta na tsananin mata zafi... A hanya Raheemah Ta had’uda Ansar ya fito daga Bargan dawakai ya zab’i doki mai kyau kaman yanda Mahmood yai masa kyauta... Yai tsaye da mamaki yana duban matar data tsaya gaba garesa cikin tufafi irinta masu mulki ga Hadimarta guda tsaye bayanta... “Lafiya..?” Ya furta yana dubanta... Alama da hannu Raheemah taiwa Hadimar don ta basu waje... Raheemah ta murmusa tace “Lafiya sai alkhairi..” Shima murmusawan yai kad’an yace “Ban fahimceki ba.. Wacece ke..?” “Call me solution to your problems..!” Tai maganar murmushi bai bar saman fuskarta ba... Gajeren murmushi yai yace “I don’t get you..” “Da sannu zaka fahimta tinda na kula kaima k’arfin mulki da iko aka nuna maka aka rabaka da masoyiyarka kaman yanda nima aka rabani da nawa masoyin aka aura min wanda bana so..” Ansar ya dubeta da tsananin mamaki yace “Kina nufin yanda aka aura min wacce bana so kema haka aka miki..?” Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa and if you want Muhibbah back ni kad’aice zan taimakeka duk fad’in Masarautar nan..” Yai K’uri yana dubanta sai kuma yace “How is that possible..?” Raheemah ta murmusa kana ta mik’a masa wayar salulanta tace “Zuba digits d’inka a nan...” Babu musu ya amsa ya hau zuba mata lambar wayan salulansa... Ya amshi wayar bayan ya gama kana tace “Sai kaji daga gareni..” Daga haka sa kai tai Ta shige Hadimarta ta take mata baya.. Ansar yabi bayanta da kallo har ta b’ace masa cikeda mamakin makirce makirce dake cikin wannan masarauta.. Koda shike shi ina ruwansa idan dai zai samu Muhibbah ta dawo garesa, akan son da yakewa Muhibbah babu abinda bazai ba don kawai ta dawo garesa.. Bazai tab’a bari a rabasu haka kurum ba... Ya k’arashe yana mai jin zafin Wai Mahmood da gaske ya aure masa Muhibbarsa... Sabida tsaban an rainasa ma bacci akasashi yayi kafin akai masa wannan rainin wayon.. Yai k’wafa yana mai ayyanawa bazai tab’a hutawa ba har sai ya tabbata auren Muhibbah da Mahmood ya lalace.. ** A can b’angaren Ja’afar kuwa tun bayan da suka baro Bargan dawakai shida Baba Nomau ya nufo b’angaren Yazeed, tsaye yayi yana k’arema sashen kallo yana tuna abubuwa da na wulak’anci da tozarci da ya fuskanta daga wajen wad’annan ahali... A hankali ya soma takowa cikin sashen hannayensa hard’e ta baya yana mai kuma k’arema sashen kallo... Daga k’ofar Parlorn ya tsaya yana duban Yazeed dake zaune dirshan a k’asa hotonsa wanda da ka shigo parlorn zai maka marhaban cikin shiga irinta mulki aje gabansa ya tasa hoton gaba yana cazgan kuka kaman wani k’aramin yaro ga wasu Kuyangi tsartsaye gefensa suna bin umarnin da yake basu ba don sunso ba, harta abinci a baki suka basa da alama... Suna ganin shigowar Ja’afar suka rirrisina suna kwasan gaisuwa.. J’afar ya amsa masu yana mai jinjina kai... Alama yaima Kuyangin da hannu kan cewa Su fice, babu shiri suka fice kawunansu gaba d’aya a k’asa... Yai tsaye gaban Yazeed har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya... Daga k’afafu Yazeed ke duban Ja’afar har izuwa Fuskarsa take yaji kaman an luma masa mashi a k’ahon zuciya, yai saurin rintse idanunsa dan bazai iya jure ganin wannan kayan bugawar zuciyar ba.. Ubandoma dake biyeda Ja’afar ganin yayi shiru yana k’arewa Yazeed d’in kallo ya sanyashi fad’in “Rankaidad’e mai kake so ayi dashi, a fattatakesa daga cikin Masarauta ne ko kuwa a fatattakesa ya koma can yanda aka fito.. Ma’ana b’angaren Bauta..!” Hannu yasa ya d’an sosa kunnensa guda kana yace “Kasan idan mutum nada zuciyar musulunci duk yanda yaso rama mugunta bazai jura ba.. Kuma wad’annan ahali duk abinda zamu masu bazamu rama zalunci da sukaima Al’umma ba, ko a haka Sun amshi sakamakon duniya.. Right Yazeed..!” Ya k’arashe yana mai duban Yazeed dake zaune dirshan gabansa.. Yazeed bai iya amsawa ba saima dad’a kifa kansa da yayi... Ubandoma ya kai masa shura da k’afa yana mai furta “Hattara D’an Bayi..! Tashi ka duk’a da kyau ka amsa Yarima... Yarima baya jiran amsa daga wajen k’ask’antacce Bawa irinka...” Cikin tsananin huci Yazeed yake furta “I rather die akan na risina gaban wanda yake a matsayin Bawa na a baya...!” Ya k’arashe Wasu irin hawayen d’acin rai suna gangaro masa... Ubandoma ya nufosa zai kai masa damk’a Ja’afar ya dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu, murmushi saman fuskarsa ya kwanto da fuskar tasa dab kusan na Yazeed d’in “We shall see..! Bawa d’an Baiwa..!!” Ya kuma murmusawa kad’an lokaci guda ya shiga zagaye tampatsetsten parlorn Yazeed d’in na alfarma, yana k’arema kayan alatu da aka k’awata Parlorn dashi kallo... Ya iso gaban family Picture d’in su Yazeed wanda yake manne cikin parlorn gwanin ban sha’awa... Yai K’uri yana k’arema picture d’in kallo, lokaci guda yake furta “How Pity..! You’re all alone now, they all left you..” Ya d’an girgiza kansa kad’an yana mai yin wani salo irinta tausayawa, lokaci guda yaci gaba da furta “Babu izza..! Babu sarauta..! Babu asali..! Babu mata..! Babu ‘ya’ya..!” Daidai lokacin ya kaikaito sosai yana duban Yazeed kana yaci gaba da fad’in “And what is worse, kaga wannan luxury d’in da kake cikin zakai bankwana da ita a yau domin kuwa angulu zata koma gidanta na tsamiya.. Za’a koma yanda aka fito.. Yankin bayi da Bauta...!” Ya k’arashe idanunsa tar kan Yazeed d’in wanda ya kasa gaskgata abinda yakeji daga bakin wulak’antaccen Bawan da ya raina a baya irin Ja’afar wanda ko yanda ya taka bai isa ya taka k’asar wajen ba, cikin wane irin yanayi yace “Ja’afar..! B’angaren Bayi fah kace.. Ni Yazeed ne zan koma rayuwa cikin Bayi..?!” Ubandoma ya katsesa da fad’in “Hattara D’an Baiwa.. Ba’a jayayya da Yarima..!” Yazeed ya had’iyi miyau da k’yar yace “Yarima..!” Yai maganar da k’yar kaman mai koyon magana.. Ja’afar ya kaikaito yana dubansa yace “Eh b’angaren bayi zaka koma Yazeed domin kuwa nan ne ya kamaceka..! Da ace ka zamto d’ah ga Maimartab watak’ila da an ajiyeka a gidan tsoffin k’wark’warorin Sarakuna wanda suke rayuwa da ‘ya’yensu amma martabarka da darajarka batakai nasu ba, sabida kaid’in ba ahalin gidan nan bane... Jinin k’ask’antacciyar Baiwa ce wacce taci amanan Ubangidanta... A b’angaren bayin ma yankin da zaku zauna kaida sauran ‘yanuwanka idan sun fito daga asibiti bazai kai na sauran bayi daraja ba domin kuwa kud’in maciya amanan masarauta ne...!” Ya k’arashe yana mai maidoda dubansaga Ubandoma... Murya a dake yaceda Ubandoma aima Yazeed rakiya zuwa sabon sashensa.. Daga haka bai kuma tsayawa jiran komai ba yasa kai zai shige abinsa Ubandoma yana fad’in “An gama Rankaidad’e..! Yazeedu godiya yake Rankaidad’e...!” Da tsananin mamaki Yazeed ya koma tamkar an dasa a wajen yake duban Ja’afar har ya b’acewa ganinsa, ya nemi hawayen da suke zubo masa ya rasa, Ashe kuka ma rahama ne... Ji yayi inama zai iya ci gaba da kukan da yake da sai yafi masa sauk’i... Yanaji Ubandoma ya kamo hak’ark’arinsa ya mik’ar dashi tsaye yana fad’in “Maza a koma tushe, a koma yanda aka fito...” Wai yau shi Yazeed, shi Prince Zeed ne aka maidosa sashen Bayi na cikin Masarautarsu... Masarauatr da yaci burin Mulka kowa ya zamto yana k’asa dashi sai gashi kowa ya zamto sama dashi, harta bayin da yake ganinsu k’ask’antattun yau sun fisa daraja a cikin Masarautar sa... Giwa itace Ta jawo masa wannan k’ask’anci wanda gwara ya mutu da yaga irin wannan rana...Gwara ya kashe kansa da yaga irin wannan takaici.. ** Jiki a matuk’ar sanyaye ta nufi sashen Gimbiya Turai tana ganin hanya na had’e mata kalaman Ansar suna kuma buga kwanyarta _Ked’in sayoki yayi, satoki yayi, bakida wani daraja a idanunsa kuma bazaki tab’a yin daraja a idanunsa ba, k’arfin mulki ya nuna akanki, don yayi amfani dake kawai wajen cimma burinsa ya dawo dake cikin Masarautar.. Kuma burin nasa ya cika tinda kika taimaka masa ya fidda Giwa da ahalinta daga cikin Masarautar_ SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *79* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A parlor ta tadda Gimbiya Turai taredasu Umaima da Zahra, Hadimai sai sintiri suke tsakanin sashen ana kawo mata kyauttutuka daga matayen masu muk’amin gargajiya kaman yanda yake a al’adance... Yanayin da sukaga Muhibbah ciki sosai ya basu tsoro, Umaima ta mik’e da sauri ta isa ta kamo hannunta tana tambayarta meke faruwa.. Duban Umaima takeda idanunta masu zuban ruwa, lokaci guda Ta rungume Umaima kuka na kuma kufce mata... Zahra da Umaima suka dubi juna yayinda Gimbiya tai alamawa Hadiman da hannu cewa su fice su basu waje... Hannun Muhibbah Umaima ta kamo suka k’araso saman Darduman da suke zaune bisa itada Zahra kana ta zaunar da Muhibbar... Zahra ta matso had’ida mata k’uri murya a hankali take furta “Tia.. Is all well..? Lafiya kike kuka haka..? Kodai Giwa ce ta dawo cikin Masarautar..? Talk to us please..!”Ta k’arashe fuska fal damuwa... Umaima Ta kamo hannun Zahra tana mata alamu da ido kan tai shiru ta daina jerowa Muhibbah tambayoyi irin haka... Gaba d’aya sukai mata K’uri suna duban yanda take k’ok’arin daidaita kanta tana share hawayen dake mak’ale cikin idanunta... D’agowa tai ta dubi Gimbiya Turai, muryarta na tsananin rawa tace “Ummi da gaske Rankaidad’e ne ya aureni..? Da gaske shine mijina..?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Zahra da Umaima suka dubi juna suna masu shan jinin jikinsu... Gimbiya tai masu umarni su fice su basu waje itada Muhibbah.. Jiki a sanyaye Umaima ta janyo hannun Zahra suka nufi k’ofa, Zahra na fad’i k’asa k’asa “Kina tunanin bazata amince da auren Paa d’ina ba.. But I thought they loved each other.. And they’ll make a perfect couple together...!” Ta k’arashe cikeda kulawa.. Umaima ta girgiza kai kad’an tace “Just shut up Zahra, and stop meddling...” Zahra ta sauk’e huci a hankali tana mai kuma juyowa tana duban Muhibbah dake duk’a gaban Gimbiya Turai cikeda mamaki, ita gani take idan Muhibbah tak’i Paa d’inta sam bata kyauta ba.. Su Zahra suna ficewa Gimbiya Turai ta saka hannayenta biyu ta kamo Muhibbah ta d’agota had’ida zaunarta gefenta, saida Ta bari natsuwa ya d’an kuma sauk’a mata kana Ta soma fad’in “Mahmood shine ya aureki Muhibbah..! Amma ki sani akwai sharad’inmu dashi, sharad’in kuwa shine idan baki so zaa warware wannan aure kafin ai masa nad’i...” Muhibbah Ta saka hannunta ta goge ragowar hawayenta jiki a sanyaye take duban Gimbiya Turai wacce itama itad’in take duba... Janyota tai cikin jikinta tana shafa bayanta a hankali alamun lallashi... Suna a haka Hadimar Muhibbah Ta shigo Ta risina, ta mik’a gaisuwarta kana tace “Ki gafarceni Rankidad’e.. Mai Martaba yayo aike.. Kinada sak’on kira daga garesa..” Zuciyarta yai wani irin tsinkewa, Ta d’ago tana duban Gimbiya Turai.. Jinjina mata kai tai tace “Maza tashi kije, kuma kar kisa wani damuwa ma ranki... Bazan bari wani basarake ya miki dole ba, share hawayenki maza ki tafi ki amsa kiran nasa..!” Ta mik’e da k’yar tana mai gyara zaman alkyabbarta.. Lokaci guda tasa kai Hadimar tata na biyeda ita.. ** Tinda Ta shigo sashen nasa gabanta Ke tsnananta fad’uwa, tana k’arasowa Barde ya soma mata kirari da jinina yana mai sanar da ita Rankaidad’e yana farfajiyan samansa yana jiran isowarta.. Batareda ta amsashi ba ta haye sama jikinta a matuk’ar sanyaye ga zuciyarta dake ci gaba da bugu... Yana zaune saman Darduma ta alfarma wanda aka k’awatasa da manyan pillows na alfarma irinta gidajen masu Mulki... Kanta a k’asa take takowa tanajin bugun zuciyarta na k’aruwa lokaci guda tanajin kalaman Ansar suna kuma Yawo a cikin kanta da kunnuwanta suna neman tarwatsa mata kwanyarta... A haka take had’e hanya dan wani irin fuzga takejin zuciyarta na mata... Ji tai kaman wacce ake turata da k’arfin gaske, taji wani irin jiri na k’ok’arin kaita k’asa... K’iris ya rage bata zube k’asa ba sai tsintar kanta da tai cikin hannun Rankaidad’e.. Ta bud’e idanunta tana dubansa, shid’in ita yake duba fuskarsa dab nata kaman tsinin hancinsu zai had’e... Dukda kyaun halitta da k’warjini da fuskarsa nasa kedashi hakan bai hanata tuno abinda yayi mata ba, ya auorta zuwa Masarautar a wulak’ance domin cikar burinsa.. Hawaye suka gangaro mata lokaci guda tana mai kauda fuskarta gefe... Ya jima sosai yana dubanta cikin hannunsa kafin ya mik’arta tsaye yana tambaya a hankali “Are you hurt..?” Ba tareda ta dubesa ba ta girgiza kai alamun a’a... Hannunsa guda taji saman nata ya kamo hannun nata ya nufi saman shimfid’ar da ita... Ta dubi hannun nasa yanda ya rik’o nata hannun cikin nasa... Ta kasa janye idanunta har saida yai masu masauk’i saman Dardumar ta alfarma... Zamansu yai daidai da shigowar wayan Turaki, ya mik’e ya d’an taka kad’an zuwa jikin fence ya bata baya yana amsa wayar wanda bazai shige kan sak’on da ya bawa Turakin bane Sai lokaci ta sami zarfin d’agowa ta dubesa, sanye yake cikin tufafi irinta masu mulki, Riga da wando na kufta mai ruwan k’asa wanda suka sha kwalliya da surfani mai ruwan zinari, kansa babu hula sai kwantattun sumarsa bak’i wuluk Sai shek’i suke... Ta kauda fuskarta a hankali tana k’ok’arin nitsa zuciyarta, lokaci guda tana mai kuma aminta da batun Ansar ko kusa kar ta yarda da wannan wulak’antaccen auren,.. Tayi nisa duniyar tunani bama tasan ya k’araso ya zauna ba sai muryarsa ta sinkayo yana furta “I need all your attention here your Highness..” Ya fad’i daga nan yanda yake a kishingid’e yana murza zobban hannunsa... Ta d’ago ta d’an dubesa hawayen mak’ale cikin idanunta, ji tayi wani irin k’warin gwiwa na zuwa mata dukda wani irin abu da yake fuzgar zuciyarta wanda bazatace ga abin ba...Cikin murya mai rauni had’ida zafin nama take furta “Why your Highness..? Maiyasa..? Sabida kayi amfani dani ka toni asirin Giwa da ‘ya’yanta cikin Masarautar nan shiyasa ka sayoni daga wajen Yawale..? To fulfill your own mission...? Maiyasa ku masu mulki kukeda zalunci..? Maiyasa baku duba buk’atan kowa sai kanku..?! Maiyasa kanku kawai kuka sani..?! Mai yasa baku damu ba who’ll get hurt..? Maiyasa baku damu ba..!” Mahmood dake murza hannunsa kad’an yana jin kalamanta suna tsananin masa zogi cikin zuciyarsa, cikin wane irin daka tsawa ya katseta da fad’in “Enough..! Ya isheki haka..! You don’t know anything, so you better hold it right there..!” Ya k’arashe yana sakin huci... Kukan da take rik’ewa ya kufce mata, Ta shiga girgiza kai tana hawaye.. Lokaci guda take furta “This isn’t fair..! It isn’t fair..!” Ta yunk’ura zata mik’e Ta fice cikin sauri rik’eda bakinta wanda kuka ne kawai ciki...Bata ankara ba saiji tai ya fuzgota Ta fad’o cikin jikinsa... Sosai take kuka tana k’ok’arin cire jikinta daga nasa, bai saketa ba saima dad’a matseta da yayi har saida yai tunanin kar ya karya mata wani k’ashi... Saitin kunnenta yake maganar cikin fuci mai yanayi da rad’a “Ba’a tashi gaban Sarki sai yaba da izini.. You lack manners... Ki koyi yanda zakike magana dani idan har kina son samun amsoshinki... Kin fahimta..?!” Ya k’arashe yana mai sassauta rik’on da yai mata... Wani k’arfin hali ne taji yana zuwa mata, ta shiga b’anb’are hannun nasa daga cikin jikinta take furta “Ban amince da wannan auren fin k’arfin ba kuma bazan tab’a amincewa ba... Your Highness..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin cire jikinta... Tsam ya rik’e yatsun hannun nata, yai amfani da d’aya hannunsa ya janyota ta kuma fad’owa cikin jikinsa, hab’arsa ya aza kad’an saman kafad’arta, cikin sigan rad’a yake ci gaba da furta “Haven’t they informed you yet.. Sarki baya saki, idan kika shigo kin shigo kenan.. Prepárate para convertirte en mi reina (Kiyi shirin zama Sarauniyata) Y prepárate para realizar todos los deberes de una mujer casada.” (Sannan kiyi shirin sauk’e duk wani nauyi da ya rataya bisa matar aure) Bata fahimci kalamansa ba kasancewar cikin harshen spanish yayi, saidai ta tsinta kalmomi da baza’a rasa ba... Tana jin sanda ya sakar mata hannu ba tareda ya kuma bin takanta ba ya koma saman darduman yai zamansa lokaci guda yana mai saka apple cikin bakinsa... Tai tsaye tana mamakin k’arfin hali na wannan Basaraken... Kaman bashi bane ya ida magana ko kallon b’angaren da take bai kumayi ba kaman bashi a wajen... Kanta a k’asa ta juya ta fice daga wajen wasu hawayen na kuma gangaro mata.. Ba ma kanta take wannan yak’in ba wa Ansar take domin kuwa sam bai cancanci haka ba.. Rankaidad’e k’arfin Mulki kurum ya nuna masa ya samu Baffah Yawale mutum ne mai son duniya shiyasa yai sauk’in shawo kansa, sannan babu riba cikin auren da babu soyayya tinda ba sonta yake ya aurota ne kawai dan wani buk’ata ne nasa... Tana tafe taji ta bangi mutum, ta d’ago tana dubanta ba kowa bace face Raheemah... Raheemah tai mata K’uri murmushi saman fuskarta lokaci guda take furta “Muhibbah... Ko ince Rankidad’e.. Long time no see.. Kodashike ku matan sarakuna dama da kulle aka sanku..!” Muhibbah dake tsananin huci tana duban Raheemar bud’e baki tai da niyyan magana Raheema Ta dakatar da ita da fad’in “A’a’a no.. Don’t you dare..! Bakida wani excuse Muhibbah.. Kin tona mana asiri nida Yazeed dan kawai ki mallaki Mahmood ma karan kanki... Good burinki ya cika kin zama matar Yarima Mahmood kuma Sarki mai jiran Gado...!” Ta d’anyi fasali tana mai murmusawa, lokaci guda taci gaba da fad’in “Ashe dai ba ni kad’ai maci amana ba... Ni k’awata naci amana kekuwa amanar soyayya kikaci.. Amanar mutanen da suka zamto fitila ga rayuwarki... How shameful ba’a San jinin babban gida da cin amana ba..!” Ta k’arashe tana yatsina fuska... Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Koda wasa kar ki kwatanta kanki dani, balle abunda Kika aikata.. Ked’in kinci amanan mahaliccinki ne bayan ya baki amanan kanki, kinga kuwa cikin mu biyun kinfi dacewa da akiraki da maci amana..!” Dukda kalaman Muhibbah sun mata zafi hakan bai hanata furta “Admit son Mahmood kike.. Ai dama na fad’a tun farkon zuwanki idonki akansa suke...Kin yaudare mutumin da ya shafe shekaru yana dakon soyayyarki... Kin cika butulu Muhibbah..!” Cikin sauri Muhibbah tasa kai zata shige sabida zuciyarta dake tsananin tafarfasa, Raheemah tai saurin tare gabanta tana furta “Fuskarki ya nuna komai Muhibbah... Idan har bada biyu kika toni asirinmu da Yazeed ba, idan har ba don ki mallaki Mahmood kikayi haka ba, idan har ba don kici amanan masoyinki na gaskiya kikayi haka ba.. Toh kisa Mahmood ya sawwak’e maki kafin ai masa nad’i kafin ayi bukin tarewarku domin kuwa muddin akai masa nad’in sarauta bazai sakeki ba sannan ko da ace ya sakeki zaki k’are rayuwarki ne gidan tsaffin matayen sarakuna bazaki tab’a auren wanda ranki yake so ba. Bazaki tab’a auren masoyinki ba har abada domin kuwa haka k’a’idan sarautar yake..! Idan har kin cika jinin sarauta d’iyar masu mulki, idan har jinin yana Yawo a jijiyoyin jikinki bazaki tab’a zama mayaudariya maci amana ba, idan har kin cika duk abubuwan dana zayyano Yo kiyi proving... ki nuna min ba sabida amfanin kanki kika tozartamu nida Yazeed a idanun duniya ba.. Kiyi abinda ya kamata kafin wa’adi ya cika miki Muhibbah..!” Ta k’arashe tana mai gyara zaman alkyabbanta kana ta nufi b’angaren Yazeed zuciyarta na mata wani irin sanyi, don tasan ko shakka babu kalamanta zasuyi tasiri a zuciyar Muhibbah... Ga tsananin mamakin Raheema a gark’ame taga k’ofan sashen... Ta dubi wasu bayi dake zaune gefe tai alama wa guda d’aya ya k’araso cikeda risinawa “Yarima Yazeed fah..?!” Ta tambaya tana dubansa, Bawan yace “Allah taimakeki ai Yazeedu zakice, yanzu bashida maraba damu k’ila mun fisa..” Raheemah ta katsesa da fad’in “Ba wannan na tambayeka ba.. Shin ina yake..!” “Tuba nake Rankidad’e, Wato Yazeed dai ya koma b’angaren can..!” Yai mata alama da hannu Ta sashen Bayi.. K’irjinta yai wani bugawa, Ta dubi hannun nasa da mamaki tana mai girgiza kai cikeda shakku take furta “Ban fahimceka ba.. B’angaren Bayi fah kake nuna min..!” Hadimin ya kuma jinjina kai yace “Haka ne Allah shi taimakeki... Can ya koma b’angaren Bauta da bayi..” Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa, Wai Yazeed Yazeed dai Prince Yazeed a b’angaren bayi... Afujajan ta janyo alkyabbarta ta nufi b’angaren Bawan na kuma risina mata.. Tana isa sashen ta soma yatsine yatsine tana toshe hanci dan wari yake mata a cewarta... Taga wasu ‘yanmata guda biyu sunyi tsaye suna lek’en wani rub’ebb’en d’aki, da alama lek’en Yazeed d’in suke suna gulmarsa... D’ayan har tana cewa “Ashe da rabon a samu kyakkyawan Bawa irin Yarima Yazeed..!” Ta had’iye sauran maganan nata sanda Raheemah ta k’araso wajen.. Gaba d’aya suka duk’a suna gaidata...! Da tsawa tace dasu duk su b’ace daga wajen kana Ta nufi cikin d’akin tsoro da Al’ajabi na kuma kamata.. Zaune taga Yazeed dirshan tamkar mutum mutumi bai um bai um um... Jiki na rawa Raheemah ke dubansa daga nan yanda take tsaye “Zeed..! Zeed is that you...?” Tai saurin k’arasowa had’ida duk’awa gabansa cikin tsananin rawar jiki, murya na rawa take furta “C’mon talk to me Yazeed, Wai da gaske kaine a nan..? Yazeed why..? kan mai zaka k’ask’antar da kanka ka kawo kanka cikin wannan dottin.. Look dubi everywhere is liking.. My Goodness you might catch infection here..!” ta k’arashe tana d’aga kai sama tana duban gajiyayyen d’akin a yatsine... Lokaci guda Ta soma k’ok’arin mik’ar dashi tsaye tana furta “You don’t belong here Yazeed... Tashi mu tafi..” Tarjewa yayi yak’i tashi... Raheemah Ta juyo tanai masa duban mamaki, lokaci guda Yazeed Ke furta “Let me be.. this is where I belong after all..! My life is completely ruined... I have nothing left Raheemah... I don’t want live anymore.. I’m sick and tired of this miserable life I’m living now... Pls end my life Raheemah, just kill me please..!” Ya k’arashe wasu irin hawaye na zubo masa... Take Raheemah ma taji hawaye na zubo mata, lokaci guda take girgiza kai tana furta “No Zeed, this is not the end of it... Bazan barka a nan ba, You’re still that prince with so much pride and power..! Yazeed please ka tashi mu tafi..!” Dubanta yayi da kod’add’un idanunsa kana yace “I’m worthless now, bazan amfani kowa ba, kowa guduna yake even my friends left me.. Kema nasan you’re just faking it... You love Mahmood, kawai dan babu yanda kika iya ne... And you’re doing all this out of pity... Kuma kin sani duk duniyar nan babu abinda nafi tsana kaman naga wani yana jin tausayina.. The moment na koma abin tausayi shikenan rayuwata ta k’are.. And that’s exactly what I’m now..!!” Ya k’arashe wasu hawaye na gangaro masa.. Raheema ta dubi hannayensa guda biyu tana mai tabbatar da abinda yake fad’i lokaci guda yake furta “But you still have me Yazeed.. I’m your wife ka mance...!” Yai murmushi mai ciwo yace “Kar mu yaudari kanmu Raheemah.. Na tabbata daga yanzu jin kanki kike way too outside my world, we are not in the same league anymore... so please , just go and leave alone...!” Share hawayenta tai tace “You know what I don’t give a crap about Mahmood anymore.. Kuma Wllhi sai na tarwatsa Farin cikin da yake k’ok’arin ginawa, kar ka damu Zeed zan d’aukar mana fansa kan wad’anda suka wulak’anta mu... Kuma sai kayi alfahari dani..! Tashi muje to your favorite place..” Ta k’arashe tana mai kamosa ta d’agosa tsaye.... ** Ubandoma ya dubi Ja’afar sanda driver ya ida parking dalelliyar BMW X6 sai walk’iya take.. Yaci Uban gayu kana ganinsa Kaga d’an masu muk’ami... Ga wasu zuk’a zuk’an dogari har guda biyu biyedashi.. Ubandoma na daga b’angaren damarsa suka nufi ward d’in da aka ajesu Jamal bayan sunsha surgery an ceto rayuwarsu... Gadajensu ne guda uku a jere, na Giwa daga farko sai na Jakadiya.. Na Jamal kuwa na daga d’aya b’angaren labule ne ya raba tsakaninsu... SameenaAleeyou📚 SameenaAleeyou📚 *MUHIBBAH* *80* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ko duban b’angaren da Giwa take Ja’afar beyi ba a cewarsa ziyaran na Jamal ne... Muryar Giwa ce ya soma masu sallama a galabaice sanda suka shiga Sai fad’in muggan abubuwan da tayi take... Idan tayi tayi sai ta k’ara da ihu tana fad’in ta shiga uku... Likitan ya dubi su Ja’afar da Ubandoma yace haka nan ta Kwana tana wanann sunbatu tunda aka fito da ita daga surgery... Gaba d’aya ta damesu ta cika masu kunnuwa... Ja’afar ya girgiza kai a hankali ba tareda ya furta komai ba, Ubandoma ne yace “Ai Izzatu Ta tapka ta’asa a doron k’asa dan haka duk abinda kace tanayi likita bazanji mamaki ba... Allah Ubangiji yasa mufi k’arfin zukatanmu..” Likita ya amsada Ameen... Can yanda Jakadiya Ke kwance Ubandoma ya k’arasa, shi kuwa Ja’afar yana nan jikin gadon Jamal yayi tsaye yana k’arema Jamal d’in kallo yanda ya koma abin tausayi lokaci guda... Likitan ya k’araso gefen Ja’afar ya tsaya yana masa bayanin ciwon Jamal d’in dan sosai k’unan nasa ya shiga deep harma ya d’ara na Giwa da Jakadiya da k’yar akai masa aiki aka samu fitsari Ke fita kad’an kad’an daga mafitsaransa a haka ma saida taimakon katata kafin ciwon nasa ya warke aga abinda hali zai, gaba d’aya ya koma tamkar wani halitta ta daban... Ja’afar ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yace “Yanzu Dr kanaga zai iya kaiwa yaushe kafin ya farka..?” Dr yace “Ai ko d’azu ma ya farka, shi kuma duk farkawan da zai toh da tsinuwa da la’antar mahaifiyarsa yake tashi, kaji irin tashin hankali da wad’annan bayin Allah suke ciki..!” Nanma girgiza kai kad’an Ja’afar yai yana mai kuma duban Jamal da tsoron duniya... Dr na matsawa da kad’an Jamal ya bud’e idanunsa yana duban Ja’afar dake tsaye kansa... Yai ma Jafar K’uri idanunsa suna rinewa zuwa ja... Cikin wane irin yanayin murya mai tsananin rawa ya furta “What brings you here..?! Kazo ne kaga yanda na koma..? Kazo ne ka tabbatar da idanunka..? Well, gani nan ga yanda na koma.. K’ask’antacce muskini saika zuba ruwa a k’asa kasha.. And don’t you dare think of taking my wife away from me, dan bazan tab’a bari hakan ta kasance ba.. Umaima tawa ce, she’s my wife, she and I are married.. You better stay away from my wife..!!” Ya k’arashe kaman zai finciko Ja’afar d’in sabida yanda yake tsananin tururi... Tinda ya soma magana Ja’afar bai furta koda kalma ba har ya ida sunbatunsa cikin zuban hawaye, hannu Ja’afar ya zaro paper da pen cikin aljihunsa ya aje gefen Jamal fuskarsa a matuk’ar murtuk’e ya furta “Write..! Rubuta mata tun muna mu biyu nida kai..!” Jamal ya dubi takardan ya kuma dubi Ja’afar yace “Do you think I’m that stupid, well you’re mistaken your Highness idan kana tunanin zanyi abinda kake umarta na... Never bazan tab’a rubutawa she’s mine..!” Ciki wane irin huci Ja’afar ya kwanto da fuskarsa tamkar zai shak’o wuyan Jamal d’in yake furta “Don’t you test my patience..! Idan kana son kanka da lafiya ka rubuta tun muna mu biyu a nan wajen, don idan ba haka ba ni nan zan tabbatar maka ba kai kad’ai ne keda ilimin mugunta ba.. Bakaji azaba ba duk wannan rad’ad’in da kake ciki har sai ka bari ka shigo hannuna baka aikata abinda na umarceka ba.. Sannan ne zaka San the real meaning of the word pain..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Ga tsananin mamakin Ja’afar murmushi saman fuskar Jamal ya gani irin na ko ajikina, lokaci guda yake furta “Babu abu mafi zafi da d’aci a duniyar nan da na fuskanta kaman rabuwa da rayuwata ta baya... So duk abinda zaka min duk kalan horon da zaka min na shirya amsan sa idan dai akan abu guda d’aya tak da ya rage min a duniyar nan ne.. Umaima ita kad’aice ta rage min kuma kaji na rantse maka ko kotun duniya zaka kaini gaban Alk’alin duniya saidai ka kaini amma bazanyi abinda kake umartana ba... Ka fahimta..?!” Ya k’arashe yana sakin huci... Ja’afar d’inma huci kurum yake yana dubansa lokaci guda yake furta “You want battle..? Then I’ll give you war.. And don’t forget I’m the one with power now..!!” Daga haka mik’ewa yai ya nufi k’ofa cikin sassarfa kaman zai kifa k’asa yana iya sinkayo muryar Giwa tana fad’in “Ku kira min d’ah na Mahmood yazo ya kaini asibitin k’asar waje a sake mun fuska.. K’arya Izzatu tazo Ta shera masa, Mahmood d’ah na ne..!!” Ko takanta Ja’afar baibi ba yayi ficewarsa... Ubandoma ne ma ya biyeta da furta “Hattara k’ask’antacciyar Baiwa, Butulu la’antar Allah da tsinuwarsa su tabbata gareki kin cutar da Sarauniya Giwar Amale Gimbiya d’iyar masu mulki... Allah dai ya kwashe miki mushirika..!” Jakadiya tana kiran Ubandoma tana fad’in ya taimaketa ya canza mata d’aki kar zunuban Giwa da Jamal suci gaba da bibiyarta dan Ta tabbata yanda suke tsinema juna cikin d’akin bala’i na gaba nan tafe garesu.. Ya taimaka mata yasa likitocin su canza mata d’aki... Ubandoma ya dubeta yace “Ni... Tare na ganku, dama duk wanda yace tukunyar wani bazai tafasa ba toh fa nasa ma ko zafi bazai ba... Allah ya kawo sauk’i Talle kar Ki damu na yafe marin da kika min bazan rama ba.. Kiji da wannan kawai.. Ni kinga tafiyata..!” Yasa kai ya shige yana fad’ida Ja’afar “Yarima gani nan tafe..!” ** Koda sukaje club d’insu Yazeed k’in fitowa yai, Raheemah ta duk’a gabansa tana fad’in “Zeed ya kamata ka fahimci this is who you are now, if you accept yourself the way you’re that’s when people will accept you.. So just come out and stop hiding from your friends kaji koh..” Da idanu kurum Yazeed ke dubanta kana ya furta “Bazan basu satisfaction d’in ganin downfall d’ina ba.. You know what Raheemah you’re just wasting your time... Bazan shiga wajen nan ba, I was once the king here, bazan tab’a shiga ciki a matsayin k’ask’antacce ba..!” Raheemah Ta murmusa tace “But you’ve my company ba kai kad’ai zaka shige ba... Mu shiga kasha iska kad’an..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’arsa tsaye, ya d’anyi k’ara kad’an sabida ciwonsa da sukai masa tsami gashi yau d’in ba’ayi dressing ba... Raheemah na rik’e dashi ta b’angare guda ya fuzge yana fad’in he can walk by himself... Saidai to their surprise suna isa spot d’insu Yazeed aka hanasu shiga... Raheemah tace “Baku gane wanene bane.. Prince Zeed ne fah..” Guard d’in yace “We’re sorry miss.. He’s not allowed in... Kawai ku koma..” Yazeed dake tsananin tururi matsowa sosai yayi yana furta “Cut the crap you imbecile..! How dare you..!” Guard d’in ya kuma furta “We’re just following orders here... Bazaka shiga ba and that’s final..!” Hawaye sukaci gaba da gangarowa Yazeed, ya dubi Raheemah dake tsaye tamkar ruwa ya shanyeta, lokaci guda Ta dubi Guard d’in tace “How much did pay you..? I’ll double the amount... Just let him in...!” “Ma’am.. I think it will be better idan kuka tafi..” Yazeed har wani irin rawa jikinsa yake, yau shine ake wulak’antawa irin haka, baisan ya akai ya isa jikin motar ba, kawai gani yayi Raheemah na bud’e masa marfin Mota... Bai shige ba sai wani irin kuka da ya fashe dashi yana jin zuciyarsa na masa d’aci yana tuna abubuwan sharholiya da sukayi cikin wajen shida abokansa da yanda yayita d’aukan nauyinsu suna abinda sukaso a doron k’asa yau gashi sun juya masa baya sabida halinda ya tsinci kansa ciki... Yana kuka yake furta ya zama k’ask’antacce... Raheemah ta fuzar da huci kad’an tace “Waye yace kai k’ask’antacce ne... Kaifa mijin Gimbiya ce har yanzu, ko ka mance ba Zuhra bace kawai Gimbiya.. I’m also a Princess.. Har yanzu kai d’in mai sarauta ne... I can give you back your title..” Ta k’arashe cikeda kulawa... Cikin huci yake furta “If you can give me back my title, can you bring me back my reputation..? Can you bring me back Zuhra..?! Can you bring me back my two children wanda na kashesu Da hannayena guda biyu...?! Tell me Raheemah can you bring back all that I mentioned..!” Kuka yaci k’arfinsa sanda yaci gaba da fad’in “Of course you can’t Raheemah.. Bazaki iya ba.. look at me now.. D’ago ki kalleni na koma babu hannaye babu mulki babu sarauta babu family babu asali da nasaba..! Toh mai ya min saura a wannan rayuwar Raheemah.. Tell me mai ya min saura..?!” Kaman daga sama suka sinkayo muryan abokansa su Zayyad suna furta “Tabbas babu saura Yazeed... It’s all over, there’s no more Yazeed AbdulJabbar.. You’re completely ruined.. Shara ya fika daraja Yazeed dan na tabbata akwai masu bibiyan bola suna tsintar bola.. But you Babu wanda zai rab’eka sai wannan kwandon sharar ‘yaruwarka..!” Ya k’arashe yana nunida Raheemah a wulak’ance... Wani kukan k’ura Yazeed yai yayo kan Zayyad yana kai masa bugu da gundulumin hannayensa Ta ko ina yana wane irin cazgan kuka... Da k’yar Raheemah ta iya janyesa jini duk ya b’ata Farin bandage d’in da aka rufe hannun ciki.. Lokaci guda Yazeed Ke sakin k’ara yana fad’in hannunsa zafi.. Hankali tashe Raheemah ta nufi mota dashi tai rushing d’insa zuwa asibiti... ** A b’angaren Muhibbah kuwa tinanin abubuwan da Raheemah Ta sanar da ita su suka taru suka tsaya mata a zuciya, Ta k’ule a d’aki tana sak’awa tana warwarewa... Bazata bari Rankaidad’e yai mata wannan Mulkin malllakan ba, kafin ai masa nad’i kafin Ta tare dashi kaman yanda Raheemah tace ya kamata ta amshi takardanta daga gareshi.. Tinda idan Ta bari aka nad’asa sarauta shikenan babu hali Ta koma ga Ansar wanda sam bai cancanci hakan ba.. Life is all about sacrifice, she needs to do this for Ansar...! Ta k’arashe tinanin nata tana mai zama saman gado, toh amma idan tana so ya sawwak’a mata cikin sauk’i dole sai ta sauk’ar da kanta gabansa ta nemi abin cikin lallama babu tashin hankali... Tai shiru tana tunanin toh kodai ta kirawo Zahra ne..? Sai kuma ta girgiza kai. A hankali ta furta “No I don’t want to involve his daughter..” Ta fad’i tana mai kuma mik’ewa tsaye, lokaci guda ta kuma furta “Toh kodai Ummi zan samu da batun.?” “But she’s his mother, koda zatabi bayana cikin zuciyarta zataji zafin abun... I need to this alone by myself..” Ta k’arashe tana mai murza hannayenta had’ida tinanin Ta k’anda zata tunk’ari Rankaidad’e... Daga yanda yake dubanta ya kuma karkata k’afa d’aya bisa d’aya fuskar nan nasa a tamke kaman tana ganinshi, sai faman murza hannunsa guda yake... Cikin ransa yake furta “We shall see..” Lokaci guda ya d’auki wayarsa dake saman table ya shiga dialing layin Hadiminsa Barde Muhibbah na nan tana tunanin yanda zata tunk’ari Rankaidad’e taji ana k’wank’wasa k’ofarta, Hadimarta ce ta shigo ta risina tace “Allah shi taimakeki sabuwar Jakadiya ce take sallama..” Muhibbah ta jinjina mata kai tace “Bismillah shigo da ita..” Hadimar ta kuma risinawa had’ida amsawa, Jim kad’an suka shigo tareda wata Dattijuwar mace mai kamala, Ta risina tana gaida Muhibbah... “Kece sabuwar Jakadiya..?” Jakadiya Ta risina tace “K’warai nice Rankidad’e... Kuma sak’o ne tafe dani daga Mai Martaba, yace Lallai a sanar dake yanada buk’atar ganinki.. Allah shi taimakeki..” Ta k’arashe tana mai kuma risinawa gaban Muhibbar... Ta mik’e zumbur cikeda mamaki saikace yasan neman hanyar tunk’ararsa take, jinjina mata kai tai tace ”Shikenan Jakadiya Ki jirani a parlor ina nan fitowa..!” Jakadiya Ta risina tana mai amsawa kana Ta nemi izinin fita parlor.. Doguwar riga ce ta atampa jikinta anyi mata d’inkin fitted gown, sosai ya amshi suffar jikinta, Ta d’auko alkyyabrta ruwan madara ta zira alla alla take ta isa suyita da wajewa itada Rankaidad’e... A haka ta fito suka nufi sashen nasa itada Jakadiya... Tana tafe zuciyarta na tsananta bugawa domin kaw duk sanda zasu keb’e hakan takeji... Babu kowa a parlorn nasa hakan yasa suka nufi upstairs Jakadiya na gaba tana biyeda ita, A wani madaidaicin parlor ta hangesa yana zaune bisa kujera tv gaba gareshi ya baima kallan nasa mahimmanci sosai.. Ta d’an tab’e baki a ranta tace wayaga Sarki da kallon tv... Jakadiya ce ta soma neman izinin shiga, ta shiga ta zube tana kwasan gaisuwa kana Ta sanar dashi tafe suke da Gimbiya Muhibbah... Mahmood ya jinjina kai a hankali yace a shigo da ita.. Jakadiya ta amsa had’ida godiya da jinjina a garesa.. Nan ta k’araso ta sanar da Muhibbah sak’on Rankaidad’e.. Zuciyarta bata daina bugawa ba sanda ta kutso kai cikin d’an madaidaicin parlorn wanda yasha kwalliya da kayan sarauta irin na gargajiya da akai modernizing d’insu, gwanin ban sha’awa ko ina... Kasa d’ago kanta tai ta dubesa dukda tasan cewa nasa idanun akanta suke, tai tsaye sororo a wajen tamkar wata dogariya... “Meke tafe dake..?” Kalaman da taji sun fito daga bakinsa kenan saikace bashi ne ya aika a kirawota ba... Ta d’an d’ago idanu ta dubesa yayi zama irinta masu mulki k’warjininsa ya cika wajen gaba d’aya... A hankali Ta samu kanta da silalewa saman k’afarta, ta zauna nan gaba gareshi irin zaman rak’umi... Murya can k’asa take furta kalaman gaisuwa, ya amsa a tak’aice ba tareda ya kuma cewa komai ba... Kusan dak’ik’a biyar babu wanda ya kuma magana, da dai taga da gaske bazai kuma magana ba sai ta d’an gyara zamanta tace “Jakadiya tace kana kirana..” Shiru ya d’an gifta kaman bazai amsata ba “Baki amsa min tambayata ba.. Meke tafe dake..?” A ranta tace yau naga ikon Allah ni Muhibbah wannan wace irin tambaya ce, wata zuciya tace watak’ila damarki kenan na rabuwa da aurensa... Ta d’an kuma yin gyaran murya kad’an tace “Nima ban sani ba..!” “Baki sani ba..?” Ta jinjina masa kai a hankali dan bata San ta yanda zata fara ba da gaske... Mik’ewa tsaye yayi ba tareda ya kuma ceda ita komai ba ya nufi wata k’ofar tabi bayansa da kallo tana tab’e baki kad’an... Jim kad’an Ta gansa ya fito da shiga irinta Buzaye... Tabisa da kallon mamaki har ya dawo mazauninsa ya zauna... Saida ya daidaita zamansa saman kujerar kana yace “Kinga haka..! Toh a haka na auroki.. Kuma kaman yanda kika fad’i na auroki ne da dalili.. Toh hakan ne yake, dalili kuwa shine ki zamto min bakin zaren warware matsalolin da suka shige min duhu a cikin gidan nan.. Gaskiya ne..! ked’in kece Bakin zaren kuma kin warware... Akwai k’arin bayanin da kike nema..?!” Ya k’arashe yana mai warware nad’in fuskarsa... Zuciyarta bata daina bugawa ba Ta had’iyi abinda ya tsaya mata a mak’oshi da k’yar.. Lokaci guda ta furta “Tinda na warware maka k’ullin dake cikin Masarautar inaga lokaci yayi da zaka sawwak’e min Rankaidad’e... Tinda wannan shine dalili na auren..!” K’uri yai mata yana murza zobbansa a hankali kana yace “Baki da hurumin da zaki buk’aci wannan daga wajena, har sai lokacin da ni nayi ra’ayin kaina..!” Ta d’ago a razane tana dubansa... Lokaci guda ta mik’e zumbur tana girgiza kai take furta “Kar kayi min haka Rankaidad’e.. I’ve been through a lot.. Dan Allah kar ka zamto sanadiyan da k’addarar rayuwata zata kuma sauyawa..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata.. Mahmood yaci gaba da takowa gaba gareta tana k’ok’arin matsawa baya, har saida taji alamun Ta isa jikin gini kana ta tsaya ta daina motsa k’afafunta... Fuskarsu dab kusan na juna yake furta “Kinaso na sawwak’e miki..?” Ta jinina kanta a hankali hawaye na kuma gangaro mata, lokaci guda ya saka hannunsa ya dafe ginin yai mata rumfa gaba d’aya, zuciyarta sai tsinkewa take ko k’wakk’warar motsi ta kasa... Mahmood yaci gaba da furtawa a hankali “Zan sawwak’a miki amma nima inada sharad’una..!” Ta d’an d’ago fuskarta ta dubesa sai kuma ta maida k’Asa a hankali tana mai furta “Menene sharud’an naka...?” Stepping back yai kad’an had’ida juawaya ya bata baya hannayensa rik’e ya bayan, saida wasu dak’ik’a suka kuma shud’awa kana Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Kinada jarabawa na tsawon kwanaki uku, idan kinci zan sawwak’a miki kafin ayi mun nad’in sarauta...! Idan kuma kika fad’i shima zan sawwak’a miki amma sai bayan an nad’ani sarauta yanda ko na sawwak’a miki bazaki tab’a ficewa Ki auri wanda kike so ba.. Zaki k’arasa rayuwarki ne a gidan tsaffin matayen sarakuna da k’uruciyarki.. Kin amince da sharad’ina..?!” Ya k’arashe yana mai juyowa ga dubanta... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa da jin wanann batu nasa,tasan jarabawar zai zamto mai matuk’ar wahala amma batada wani zab’i... A hankali ta shiga jinjina kai tace cikin rawar murya “Na amince...!” Mahmood ya murmusa kad’an for the first time tun bayan shigowarta kana yace “Buena..!” (Da kyau) Ya d’an kumayin gyaran murya kad’an yace “Sharad’i na biyu Ummi must not know about this.. Kin amince..?!” Nan ma a hankali ta jinjina masa kai alamun amincewa... Shiru ya d’an ratsa tsakani yana mai ci gaba da karantar ta... Lokaci guda yake furta “Ki sami Jakadiya zata sanar dake tsarin jarabawar..!” Daga haka bai kuma bi takanta ba ya nufi wata k’ofar ya barta nan tsaye tana mai bin bayansa da kallo zuciyarta naci gaba da tsinkewa da fargaban amsar sharud’an Rankaidad’e da tayi... Cikin tsananin sanyin jiki Ta nufo downstairs yanda Jakadiya Ke jiran fitowarta... Jakadiya tana ganin isowarta ta k’araso murmushi saman fuskarta take furta “Rankidad’e an fito..?!” Muhibbah ta jinjina mata kai a hankali tace “Eh Jakadiya.. Yace min na sameki zaki min bayanin komai..” Murmusawa Jakadiya ta kumayi kana Ta nuna mata wata hanya tace “Rankidad’e mubi wannan hanyar..” Babu musu Muhibbah tasa kai Jakadiya na biye da ita... Wata k’ofa ce hanyar ta fitar dasu, can Ta hangi kuyangi ‘yanmata da manyan mata sai aiki suke da alama kitchen ne na musamman, wasu na yankan ganye wasu na girka abinci wasu na aikace aikace irin na kitchen... Muhibbah tabisu da kallo d’aya bayan d’aya sai aikace aikacensu suke... Jakadiya ta tafe hannayenta biyu alamun kira a garesu, nan da nan kowa ta bar abinda take ta nufo yanda suke tsaye, gaba d’aya suka risina suka kwasa gaisuwa... Jakadiya ta d’anyi gyaran murya tace “Kowa ta bar aikin da take ta fice..!” Idanu waje Muhibbah Ta kaikaito tana duban Jakadiya shaye da tsananin mamaki jin tace subar tulin aikin da suke su fice... SameenaAleeyou 📚[10/2, 12:37 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *81* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Mamaki bai saketa ba take duban manya manyan tukwanen dake bisa madafi, uwa uba tulun tsabar shinkafar data gani an ida wankewa za’a zuba... Bata ida mamaki tana ci gaba da waige waige ba Ta sinkayo muryar Jakadiya tana fad’in “Allah shi taimakeki ni zan koma zuwa lokacin da Mai Martaba ya d’ibar miki sai in dawo...” Tasa kai zata juya cikin risinawa... Baki sake Muhibbah Ke dubanta sam bata fahimci mai take nufi ba... Kafin takai k’ofa tai saurin kamo hannun Jakadiya tana fad’in “Dan Allah karki tafi ki barni a nan ni kad’ai... Bansan mai zanyi ba..” Jakadiya ta d’an dubeta sai kuma tace “Rankidad’e a al’ada irinta gidan nan ranan da Matar Sarki zata soma ziyartan Turakan Mai Martaba akan sakar mata ragamar girkin Fadah gaba d’aya na wannan ranan wanda harta Sarki wannan abincin zaici.. Domin a gwada jarumtar Giwar Amale a fagen Girki.... Za’a zuba saman farantai a shigar ko wani k’ofa kowa yaci ya fad’i ra’ayinsa akan girkin... Idan wanda suka yabi girkin sunfi Rinjayi Masarauta tayi dace, idan kuma wanda basu yaba ba sunfi rinjayi Masarauta Ta samu nak’asu a wannan fannin.... Tsarin kenan Allah shi taimakeki..” Ta k’arashe tana mai kuma risinawa... Zuciyar Muhibbah yaci gaba da tsinkewa, babu abinda zuciyarta Ke nanatawa kaman cewa da Jakadiya tai randa Matar Sarki zata fara ziyartan turakansa ranan ake wannan al’ada ta girkin.. Ta lumshe idanunta a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa, b’angare na zuciyarta na bata k’arfin gwiwa da fad’in zaki iya Muhibbah.. Zaki iya.. In exchange of your freedom zaki iya.. Ta k’arashe tunanin nata tana mai sauk’e huci a hankali.. Bud’e idanun da zatai taga babu Jakadiya.. Shafe fuskrta tai tana mai kuma k’are ma tampatstetsen madafin kallo... Take taji wani irin k’warin gwiwa na zuwa mata, Ta zame alkyabbarta ta aje a gefe kana ta nufi manya manyan tukwanen tana ganin abinda masu abincin Ke dafawa ciki... Saida ta kuma sauk’e wani ajiyan zuciyar tana mai ambaton Allah ya taimaka mata... Da alama tuwon farar shinkafa ne miyar taushe suke girkawa... Sa’arta guda shine sun rage k’arfin aikin k’arashi ne saiko abinda take fargaban bazata iya ba bazai wuce juya muciya cikin tuwon ba... Ta saka bayan hannunta ta share gumin da tuni Sun karyo mata... Tanayi tana fuzar da fuci.. Ga kayan k’amshi da na d’and’ano ko wanne jere saman faranti... Cikin k’warin gwiwa Ta soma k’ok’arin gudanar da aikin nata mai matuk’ar yawan gaske dukda cewa batada tabbacin idan zata iya wannan aiki wanda sam hankalinta bai kama ba.. ** A daidai k’ofar shiga sashen Gimbiya Turai suka kusan cin karo, zuciyarsa cunkushe take da b’acin rai sakamakon taurin kan da Jamal yai masa yau a asibiti.. Sam baiga zuwanta ba itama bataga nasa ba sai karo da juna da sukai.. Tai saurin komawa da baya tana rik’e goshinta had’ida ‘yar k’ara lokaci guda take Masifan “Wai ku Kuyangin gidan nan yaushe ne zaku koyi tafiya kuna kallan gabanku..!” Birki taima kamalan nata ganin namiji ne tsaye gabanta kuma cikin shiga irinta masu mulki... Ta d’ago tana dubansa har lokacin hannunta dafe da goshinta... “Tuba nake Your Highness..!” Ya fad’i yana mai d’an sadda kai k’asa... Murmushin da yafi kama da yak’e tai tace “Your Highness..!” Ja’afar ya katseta da fad’in “Nafi gane Ki kirani da Ja’afar d’ina Rankidad’e..” Nanma murmushin tai kad’an tana mai daidaita tsayuwarta take fad’in “Dole na kiraka your Highness, domin kuwa Kaid’in Mai Martaba ne a halin yanzu..! Idan Rankaidad’e ya min izini zan shige..!” Ta k’arashe kanta a k’asa.. A hankali ya d’an ja jikinsa gefe ya bata hanya, kaman wacce take bisa k’aya yana matsawa tasa kai zata shige... Saida tai taku kad’an Ja’afar ya ambato sunanta.. Bata juyo ba saidai cak Ta tsaya zuciyarta naci gaba da bugawa... Ya d’an tako kad’an ya tsaya daga gefenta, shiru kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Maiyasa tinda na dawo kike guduna...?” Shiru itama kaman bazata amsa ba sai zuciyarta dake ci gaba da tsinkewa.. Siririyar hawaye ya gangaro mata, cikin rawar murya take furta “Sabida haka ne ya kamata gudun kada mu fad’a ga fushin Ubangiji... Ja’afar nasan kanada masaniyar cewa akwai auren wani akaina..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka... Jiki a matuk’ar sanyaye yake dubanta kana ya jinjina kai a hankali yace “Haka ne..! You’re right.. I’m sorry, you can go ahead..!” Ya k’arashe yana mai sadda idanunsa k’asa.. Umaima dake k’ok’arin matse kukan da yazo mata gadan gadan, cikin sauri tasa kai ta shige tana mai toshe bakinta... K’ok’arin saita kansa Ja’afar yai yana mai furtawa a hankali bayan Ta shige... “Everything will soon be over... Soon enough.. I promise you..!” Ya k’arshe yana mai kutsa kai sashen mahaifiyarsa... ** Iyaka jigata ta gama jigata, aiki ne na tarumi aikin gayya aikin da mutane da yawa keyi sai gashi cikin ikon Allah taci k’arfin aikin, tunaninta d’aya yanda zata tuk’a wannan Uban tuwo wanda ko gardawan maza iyaka... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai furta “You need to do this Muhibbah..! For Ansar and Mommy, you need to be very strong..!” Ta k’arashe tana mai sauk’e huci had’ida gyara tsayuwarta gaban tukunyar, sosai ta bada wani irin balance kaikace wacce take shirin wasan dambe ce... Ta kamo muciyar wanda tuni ya d’auki zafi k’au Ta shiga juyasa da k’yar tana tamke idanu tana ciza labb’a... Ga wani uban gumin dake tsartsafowa daga ko wane mahudan gashi na cikin jikinta... Sai tayi kaman zata saki muciyar sai ta tuno sharud’an Rankaidad’e... A haka tanayi tana hutu hardai Ta samu tayi abinda zata iya dan ba’a ce tayi komai daidai ba aiki ne na gayya mutum guda Ke jagoranta.. Gefe ta koma tayi lak’was tana sauk’e huci tana duban yanda ta kammala aikin cikin ikon Allah, abinda ya rage kawai shine ta jira dahuwar abincin sai a zuzzuba kaman yanda Jakadiya tace... Ta shiga juya tafin hannunta tana ganin yanda cikin hannun yayi jajazir har kaman yanaso ya d’ura ruwa... Ta rintse idanunta a hankali domin kuwa gaba d’aya gab’ob’inta Ji take tamkar ana sassara mata su... Tana a haka Jakadiya ta k’araso tanai mata sannu... Muhibbah ta d’ago a galabaice tana duban Jakadiya... Saida Jakadiya ta isa jikin tukwanen ta lek’a ko wanne ta tabbata Muhibbah ta aikatu kana ta dawo gareta ta kuma risinawa tace “Sannu da k’ok’ari Rankidad’e.. Jibi yanda kika gudanar da komai cikin k’ank’anin lokacin nan kaman wacce aka saka miki hannu..?” Murmusawa Muhibbah ta kumayi kad’an tana mai yarfe gumin dake kuma gangarowa daga cikin kanta zuwa goshinta.. Daga can gefe Jakadiya taja ta tsaya suna jiran dahuwar abincin.. Bayan shud’ewan wani lokaci Jakadiya ta dubi Muhibbah dake kishingid’e gefe tana maida hucin gajiya, ta d’anyi gyaran murya tace “Ki gafarceni Rankidad’e ko zaki duba girkin naki..?” Muhibbah ta mik’e zumbur da k’yar ta isa jikin tukwanen tana k’ok’arin bud’esu, wanda girman murafen ma kawai abin kallo ne... Duk ta soye hannayenta jikin murafen tukunyar... Ta d’auko k’atoton ludayin tana juya miyar ta tabbata yayi... D’an duban Jakadiya tai tace “Jakadiya inaga abincin ya kamalla.. Ya kamata a zuzzuba na samu naje nayi wanka na gaji sosai..” Jakadiya ta jinjina kai tace “An gama Rankidad’e... Tafe hannayenta Jakadiya ta kumayi take Kuyangin suka soma shigowa sahu sahu suna mamakin abinci ya kammala... Suka risina suna gaida Muhibbah, Allah ya gani ko iya jinjina masu kanma batayi sabida tsaban gajiya... Wani hamshak’in paranti na alfarma mai ruwan zinari Jakadiya ta mik’o gaba gareta ta risina tace “Rankidad’e wannan parantin a ciki zaki zuba kason Mai Martaba, Kason Sarki ake soma zubawa kafin kason sauran ahalin Fadah ya biyo baya..” Muhibbah ta amsa tana mamakin fidda ficce da al’adu irinta gidajen Sarauta... Ta isa ta malmala tuwon ta d’ora kan parantin, Jakadiya ta kuma mik’o mata wani d’an madaidaicin bowl wanda da gani basai ance maka mahad’in parantin bane tace ta zuba miyan ciki.. Tayi gaba d’aya yanda Jakadiya ta umarceta kana ta kawo wani marfi wanda da gani kasan shima marfin wannan farantin ne... Aka rufa aka d’aura saman babban tray kana aka kawo wani k’yalle mai ruwan zinari shima aka rufa parantin dashi.. Bayan an gama duka wad’annan ta dubi Muhibbah tace “Toh Rankidad’e kin gama naki, saura ya rage kije kiyi wanka Ki kimtsa Ki tafi B’angaren Mai Martaba, za’a shigo da abincin da zaran kin isa sashen nasa..” Cikeda k’osawa Muhibbah tace “Yanzu Jakadiya abincin ma baza’a kai masa ba sai ina wajen..?” Jakadiya ta murmusa kad’an tace “Ki gafarceni Rankidad’e ai inaga ko ba al’adan gidan sarauta bane hakan ne ya kamata... Miji yaci abinci gaban matarsa domin ya samu daman yabonta... Hakan na k’ara dank’on k’auna tsakanin ma’aurata..” Ta k’arashe cikin hikima irinta wanda yakeda experience.. Ita dai Muhibbah tab’e baki kurum tayi kad’an dan dai Jakadiya bata San akan mai ake duka wad’annan abubuwan ba da bata tsaya b’ata bakinta tana wannan bayanin ba.. Auren da aka yosa babu soyayya wani dank’on k’auna za’a nema cikinsa.. Dan dai kai babu yanda ta iya ne tinda sharud’an da Rankaidad’e ya gindaya mata take bi.. K’in komawa sashen nasa ka iya janyowa yace ta fad’i jarawar... Ta dubi Jakadiya ta jinjina mata kai kad’an zatayi kaman yanda tace... Daga haka Jakadiya ce Tai mata Rakiya zuwa yanda suka baro Hadimarta na jiranta kana Muhibbah da hadimar suka nufi sashenta yayinda Jakadiya ta koma sashen madafi... Da k’yar ta isa d’aki sai sauk’e fucin gajiya take, tana isa ta kwab’e kayanta ta fad’a bathroom ta gasa jikinta da ruwa mai d’umin gaske had’ida kayan k’amshi na wanka... Ta jima sosai cikin bathroom d’in kana ta fito d’aure da towel tana goge sumarta data wanke da wani towel d’in... Cikin zuciyarta take tinanin inama Ta sami dryer da ta busar da wannan gashin nata... Aiko tana tsaye tana ci gaba da tsane sumar nata taji knocking.. Ta janyo hijabi ta zira kana ta bada izinin shigowa.. Hadimarta ce ta shigo rik’eda ‘yar jaka ta risina ta ajiye mata tana mai furta “Aike ne aka bata ta shigo dashi..” Muhibbah tasa hannu ta d’ago jakan tana juyawa, ga mamakinta k’aramar hand dryer ta gani mai kyau ciki..Toh waye yayo mata wannan aiken..? Ta dubi Kuyangar tace daga inane..? Kuyangar tace “Allah shi baki yawan rai d’aya daga cikin Hadiman cikin gida ne ta shigo dashi tace Wai a baki..” Jinjina kai tai tana kuma mamaki, watak’ila Umaima ne ko Zahra d’ayansu ta bata, toh amma ai basu san tana buk’ata ba..? Wata zuciya tace k’ila sunyi tunanin bakidashi kuma zaki iya buk’ata shisa suka baki.. Da wannan tunanin ta amsa kana ta sallami Hadimar.. Nan da nan ta jona ta shiga busar da sumarta... Tsaf ta shirya cikin wani dubai material mai kyaun gaske wanda akai masa kwalliya da sequence mai ruwan zinari sai d’aukan idanu yake.. Batayi niyyan shafa komai a fuskarta ba amma sai tayi tinanin hakan ka iya janyowa ta fad’i jarabawrta, Sannan tafi so ta nunawa Rankaidad’e cewa ita d’in ba raguwa bace zata iya lashe jarabawarsa, ya kamata taje da k’arfin gwiwarta, sam bazata basa wani k’ofa da zaice ta fad’i jarabawarta ba... Ta zauna gaban dressing mirror ta shafa iyaka abinda idanunta ka iya gani wanda tasan baza’a kalleta ace fuskarta tayi fayau ba sannan baza’a kalleta ace tayi kwalliya mai yawa ba.. Abinka da wacce ta jima batayi ba dan zata iya cewa tin tana Collage of nursing rabonta da ta zauna tace zatayi kwalliya na musamman, Yo ita da burin fansarta ke kanta wani make-up ma zata zauna tanayi batada wannan lokacin... Kallo d’aya zakai mata Kaso sake kallonta, babu shakka tayi kyau.. Ta tupke sumarta a k’eyarta kana tayi d’auri wanda ake turosa gaban goshi... Ya salam ita da kanta tasan tayi kyau Masha Allah.. Alkyabba mai ruwan zinari ta rufa kan sequence material d’in wanda shi kad’ai ma d’aukan idanu yake ga kuma alk’yabbarta... Ta feshe jikinta da turaruka masu natsettsen k’amshi kana ta fito.. Daidai da hadimarta saida ta shaga da kallonta.. Ta risina tace “Ki gafarceni Rankidad’e.. Kin k’ara kyau fiyeda kullum...!” Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Babu komai Hasiya, muje kimin rakiya zuwa k’ofa.” Hadimar ta kuma risinawa cikeda girmamawa tace “Toh Rankidad’e..!” Muhibbah tai gaba Hadimar na biyeda ita.. Har k’ofan sashensa tai mata rakiya kana ya bata umarnin komawa... Dikda zuciyarta dake tsananin bugawa hakan bai hanata daurewa ta nufo cikin parlorn kanta a k’asa sallama saman bakinta... Daga nan yanda yake zaune ko k’yafta idanunsa bai iyayi, saima tsarkake mahaliccin wannan kyakkyawar halitta dake nufosa da yake... Tin daga yatsun k’afafunta yake duba har izuwa fuskarta.. Ita kaw da k’yar take takowa dan tasan babu shakka idanunsa akanta yake, sai had’e hanya take sabida yanda zuciyarta ke tsananta bugu, hakan sai ya zamto mata tamkar wani salo ne na tafiya... Da k’yar ta iya k’arasowa cikin parlorn ta risina gaba garesa had’ida baza alkyabbarta a k’asa irin yanda masu mulki keyi... Dak’ik’ai suka shura kaman bazaice komai ba sai gani tayi ya mik’e tsaye, zuciyarta taci gaba da bugawa tana tinanin Toh mai kuma ya mik’arsa tsaye... Gabanta ya k’araso ya tsaya, zuciyarta naci gaba da tsinkewa, ga tsananin mamakinta hannayenta guda biyu taga ya mik’o mata... Ta d’ago idanunsa masu haske wanda kwalli ya k’ara masu haske tana dubansa dasu... Da gaske hannayensa yake mik’a mata... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa tana tinanin Ta mik’a masa nata hannayen ne kokuwa, k’in mik’awar ka iya janyowa ta fad’i jarabawarta tinda duk abubuwan nan da take cikin jarabawa ne.. Ta d’ago hannayenta a hankali ta mik’a saman nasa, ji tai ya rik’e hannayen nata cikin nasa, ya mik’ar da ita tsaye a hankali kana suka soma takowa a jere.. Zuciyarta bata daina tsinkewa ba har saida ya k’araso da ita gefen kujerar da yake zaune bisa ya zaunar da ita... “Yanzu zan amsa gaisuwarki..” ya fad’i yana mai dubanta... Ta murmusa kad’an tace “Na zaci ba’a gaisar da Sarki a saman kujera..!” Cikin sigan wasa tai maganan amma sam bata hango alamun raha saman fuskarsa ba.. Ta had’iyi sauran kalaman nata tana tinanin kardai tayi abinda zaisa ta fad’i jarabawarta.. Lokaci guda ta tsime ta sadda kanta k’asa tana gaishesa.. Ya amsa a tak’aice daidai sanda Jakadiya ta nemi izinin shigowa parlorn... Mahmood ya bata izini, ta shigo ta risina gaba garesu tace idan an bata izini zata gabatar da girkin Gimbiya... Mahmood ya kuma jinjina mata kai yace anyi mata izini... Ta mik’e ta fice tana godiya... Jim kad’an Ta shigo tareda wata Hadima rik’eda parantin.. Jakadiya tai mata nuni da yanda zata ajiye.. Hadimar Ta isa ta ajiye tana mai kwasan gaisuwa daga garesu... A tare Hadimar da Jakadiya suka nemi izinin fita... Mahmood ya zauna saman darduma irin zaman da ake na cin abinci, Muhibbah ta k’araso cikin tsanaki tana serving d’insa, duk wani motsi da zatayi idanunsa na kanta... A haka ta ida jera masa komai Ta koma gefe saman Darduman ta zauna... Saida wasu dak’ik’ai suka shura kafin ya d’auki spoon ya d’ebo abincin da Bismillah yakai bakinsa still idanunsa akanta, itama wannan karon idanu ta d’an d’ago tana dubansa dan taga kalan expression d’in da fuskarsa zai bada... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa ganin ya bar abincin cikin bakinsa shi bai tauna ba shi bai had’iye ba... Idanunta suka firfito tana fad’i cikin zuciyarta.. Shikenan k’ila abincin ya bada taste maras dad’i ne dan idan bata mance ba ko tasting abincin batai ba... Taga ya had’iyi first spoon da k’yar, jikinta a mugun sanyaye take ayyanawa cikin zuciyarta shikenan na fad’i.... Jakadiya ce ta nemi izinin shigowa.. Tana shigowa ta risina ta gaidasu... Lokaci guda taci gaba da fad’in “Allah shi taimakeka abincin Gimbiya ya zaga cikin Fadah kaman yanda yake a al’ada... Kuma..!” Ta d’anyi shiru kaman bazatace komai ba, Muhibbah na kuma zaro idanu tana dubanta... “Ina sauraronki Jakadiya.. Kuma mai..?” Jakadiya ta murmusa tace “Mafi rinjaye Sun yana hasalima ba’a sami wad’anda suka kushe wannan girki ba... Masarauta tayi dace Rankaidad’e hannun Gimbiya mai Albarka ne...” Muhibbah bata San sanda Murmushi mai kyau ya kufce mata ba, harda ‘yar sauk’e ajiyan zuciyarta... Shikaw yai mata K’uri yana kallon yanda farin ciki ya mamayeta... Duban Jakadiya ya jinjina kai a hankali kana ya Bawa Jakadiya izinin tafiya... Har lokacin Muhibbah bata daina sakin murmushi ba, Ta d’an tsuke fuska kad’an ta waigo tana dubansa had’ida d’aga masa gira guda alamun an wuce wannan... Spoon d’aya zuwa biyu yai ta nemi izinin tafiya... Ya jinjina mata kai alamun yayi mata izini, saidai tana isa k’ofa ta sinkayo muryarsa yana furta “And where do you think you’re going Your highness..?!” Ta tsaya cak had’ida lumshe idanunta zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Izuwa lokacin ya mik’e ya nufo yanda take tsaye hannayensa hard’e Ta baya ya d’an kwanto da hab’arsa saitin kafad’arta, cikin sigan rad’a yake furta “Find some clues that will lead you to the next part of the exam..!” Yana ida fad’in haka ya juya ya nufi upstairs cikin takun k’asaita... Muhibbah ta bi bayansa da kallo har ya shige had’ida fuzar da huci kad’an....clues dazasu leading d’inta... Tai tsaye tana k’arema parlorn kallo tana tianin wasu clues kenan... A hankali Ta shiga zagaye parlorn tana neman clues d’in... Harta pillows saida ta d’add’aga... Can idanunta suka sauk’a gefen yanda ya zauna, akwai remote control a wajen... Tai saurin k’arasawa ta d’aga remote d’in dan taga kaman akwai takarda k’asan remote d’in Aiko takarda ce a ninke, ta warware tana karantawa an rubuta, _Escalera.._ (Staircase) Ta rik’e takardan tana juyawa tana nanata kalman ya mata kama da yaren Spanish.. Toh mai Escalera yake nufi.. Ta d’an dafe kanta tana tunanin words d’in data sani a yaren bata fahimci menene ba... Amma kuma ya mata yanayi da escalator... Ta juya hagun da dama bataga alamun escalator ba amma akwai matakalan bene... Cikin sauri ta nufi matakalan benen tana dubawa... Nan jikin staicase taga anyi drawing arrow ya kalli sama an rubata a k’asan arrow d’in _Sigue moviéndose recta_ (Ci gaba da tafiya a mik’e) Taita nanata kalaman dan akwai words d’in data fahimta hakan yasa ya mik’e taci gaba da hawa benen... Tana cikin cikin tafiya taji kaman Ta taka wani paper, tai saurin duk’awa ta d’auki paper d’in ta warware an rubuta _Sigue tu izquierda_ (Ki bi b’angaren hagunki) Nan ma Kalmar izquierda ta fahimta yana nufin hagu, take ta soma bin wannan b’angaren tana k’arema ko ina kallo ga d’akuna a jere... Nan ta kuma cin tuntub’e da wani takardan.. Ta duk’a ta warware tana karantawa an rubata _Segunda a la última habitación_ (D’aki na kusa da k’arshe) Wannan yafi ko wanne bata wahalan fahimta dan bayan sunan d’aki data sani batasan wani kalma ba kuma dake cikin takardan sannan d’akuna da dama a wajen batasan wanne yake nufi ba... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana kuma nanatawa, zuciyarta tace kawai ta bud’e duk wanda ya kwanta mata... Ta shiga bin k’ofofin d’akin da kallo tana tinanin wanne zata bud’e tinda idan ta bud’e ba wanda yake nufi ba k’ila ta fad’i jarabawarta.. Kalmar k’arshe ne ya fad’o mata dan haka ta nufi k’ofa na k’arshe har bata tura taga d’akin dake gefe gefe da wannan key d’in jiki yana d’an kad’awa a hankali alamun ba’a jima da bud’ewa ba.. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai furta Allah yasa daidai tayi.. Da Bismillah ta tura k’ofar d’akin... Tai tsaye tana mai k’arewa d’akin kallo... A hankali Ta soma takowa cikin d’akin tamkar mai gudun kar aji motsinta, taita yaba kyaun d’akin da tsarinsa... Can saman gado ta hango wani kwali ajiye... Ta k’arasa a hankali tana duba kwalin... Jikin kwalin taga an rubuta open... Ta saka hannunta a hankali tana d’aga marfin k’aton kwalin... Cikin tsanaki take zaro abindake linke cikin kwalin wanda rigace ta bacci ‘yar yaloluwa mai siririyar hannu... Ta zaro idanunta waje tana kuma juya rigar mai kalar ja... Cikin girgiza kai tana mai kuma juya rigar take furta “No.. I’m not wearing this... I’m done playing your games Rankaidad’e..! bazanci gaba ba kuma.” Ta k’arashe tana mai jifa da rigar saman gado... But idan bata k’arasa jarabawarta ba shikenan Rankaidad’e zai ajeta gidan tsaffin matan sarakuna... She can’t afford to fail the exam..Bata da wani zab’i da ya wuce taci jarabawar nan komin wahalarta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta janyo rigar ta nufi wani hanya dake daga can gefe cikin d’akin wanda tayi zaton closet ne... Canza kayan jikin nata tai tana mai duban yanda rigar ta zauna jikinta wanda ita kanta kunyar kanta taji...A gefen mirror taga an rubuta da hausa wannan karon “D’aki na k’arshe...” Ta furta cikin rarrabewar kalma...Duban kanta Ta kumayi jikin dressing mirror kana ta janyo Alkyabba ta rufa ta tukukuye jikinta cikin Alkyabbar, Allah ya gani bazata iya tunk’arar Rankaidad’e da ‘yar wannan rigar ba, ta fito ta nufi d’akin k’arshe.. Zuciyarta sai tsinkewa yake... Tafi minti uku masu kyau tana tsaye bakin k’ofa tana zullumin shiga cikin d’akin.. Sai tazo kaman zata shige sai ta fasa... Daga k’arshe dai tai ta maza ta murd’a handle d’in sallama saman bakint kanta a k’asa... Ta ida shigowa tana mai ayyana kyau da tsari na d’akin.. Tai tsaye tana faman waige waige dan bataga kowa ba... Saitin kunnenta ta sinkayo muryarsa yana furta “I don’t remember asking you to wear this Alkyabba your Highness..” Yai maganar cikin wane irin salo Ta rintse idanunta a hankali tanajin tururin numfashinsa cikin kunnenta,.. Murya na rawa take furta “But Rankaidad’e..!” “Shiiiii” ya d’aura yatsarsa guda saman labb’anta, har lokacin tsaye yake Ta bayanta “No buts.. Remember the rules.... Take it off..!” Ya fad’i cikin tsarewa.. Ta Ware idanunta a d’an zabure... Kaman mai shirin kuka take furta “Rankaidad’e ni dai dan Allah wllhi kunyar nake..!” Taso basa dariya yanda tayi maganar amma ya gimtse yace “Do you want to fail the exam..?” Idanunta a rufe take girgiza kai alamun bataso ta fad’I jarabawar... “Then take it off..!” Ya kuma fad’i babu wani walwala... Rintse idanunta kurum tai tanajin sanda alkyabbar Ke k’ok’arin isa k’asa... Zuciyarta taci gaba da harbawa hawayen na k’ok’arin ciko idonta... Tai k’ok’arin kai hannunta zata rik’e alkyabbar taji ya kamo hannun nata cikin nasa...har lokacin idanunta a rintse suke ta kasa bud’esu... Tana jin hucin numfashinsa saitin kunnenta yana rad’a mata “You’re more beautiful like this..!” Ta ware idanunta da sauri tana jin abin wani irin bambarak’wai Wai Rankaidad’e Ke furta wad’Annan kalman... Ganin yana k’ok’arin kaikaito da jikinta su dubi juna ya kuma sanyata saurin rintse idanunta...Sosai taso basa dariya yanda ta tamke idanun nata da k’arfin gaske... Ya murmusa da gefen baki yana mai duban fuskar nata wanda har lokacin light make up d’inta na nan, d’an bakin nata shi yafi komai tafiya dashi kafin ya soma sauk’o da idanunsa yana duban yanda ‘yar rigar ta zauna cas a jikinta... “Open your eyes..!” Kasa bud’ewa tai saima dad’a tamke idanun da tai... Ya d’auki lokaci sosai yana k’are mata kallo kafin ya bud’e murya yace “Kinsan idan baki bud’e idanun nan ba zamu koma daga farko komai ya rushe..?” Zumbur ta bud’e idanunta had’ida waresu tar saman fuskarsa... Kallon kallo suke ma juna zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Tamkar wacce aka zabura cikin rawar murya take furta “I think I’m hungry your Highness.. Can I please go get something downstairs..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Saida dak’ik’ai suka gifta ya bud’e murya yace “So bakici that spicy food da kika bani ba...?!” Ta d’an dubesa a razane, shi d’inma ita yake duba fuska a tsare, lokaci guda yaci gaba da furta “Does the Queen know that har yanzu ina jin yajin a bakina.. I can’t get rid of the taste..” Ya k’arashe yana mai kuma tsareta da idanunsa masu matuk’ar firgitata.. Ta d’an kauda kanta gefe tana dariyar mugunta a hankali, ashedai abincin yaji yayi shiyasa Rankaidad’e ya kasa had’iyewa at first.. Yayi just one spoon ya ajiye.. Ahtoh mai yake expecting an tara mata girkin gayya... Ya gode Allah ma da ba gishiri bane.. Itakam saidai ma tace Allah k’ara alhakinta ne ya kamasa.. Ya tallafo fuskarta yana furta “Dariya kike...?” Ta girgiza kai kad’an had’ida sadda kan nata k’asa har lokacin bata daina murmushi ba sai kuma tace “Wai gani nayi Sarki bai kamata yaji zafin yaji ba..” Ya saka hannunsa guda a kunkuminta ya d’an janyota zuwa jikinsa da hannun nasa “Why..? Is he not human..?” Ya fad’i yana kasheta da wane irin duba wannan karon.. Dukda tsananin tak’ura da tai hakan bai hanata furta “Sabida shi Sarki ne.. Baijin zafin komai... Baka tab’a jin tarihin Sarkin da aka kulle yatsarsa a mota ba bai magana ba har saida suka isa yanda zasuje aka bud’e yatsar nasa.. Da kuma Sarkin da kunama ya cijesa ya take kunamar ba tareda yaji zafin cizon ba...” Tinda Ta soma magana yake duban yanda bakin nata Ke motsawa a hankali, baisan ta iya zuba surutu haka ba... Ta cika masa kunne da surutu bata ankara ba taji ya manne bakunansu waje guda... Tanzaro idanu waje tanajin bak’on Al’amarin da Rankaidad’e keyi... Saida suka jima cikin yanayin kafin ya cire bakinsa a hankali yana jin yanda ta kwantar da kanta cikin k’irjinsa sabida tsananin kunya da ya dabaibayeta... Cikin sigan rad’a yake furta “You talk too much...!” Lokaci guda tsakala yatsunsa cikin nata ya soma janyotaya suka nufi tapkeken gadon nasa ta alfarma... Binsa kurum Muhibbah take tamkar rak’umi da akala... Tana gani ya nufi wani d’an madaidaicin fridge ya d’auko farm fresh ya mik’a mata “Drink this..!” Ta mak’e kafad’a tace “I’m not hungry anymore... I just want to sleep, na gaji sosai, please ka k’yaleni na tafi..!” Ta k’arashe cikeda shagwab’a... Hab’arta ya tallafo yana mai k’ura mata idanu lokaci guda yake furta “Yau daren jarabawarki ne Rankidad’e, babu bacci...!” Idanunta da sukai rau rau take dubansa dasu, bata kuma fahimtar abinda Ke wakana tsakaninsu ba cikin wane irin salo da ya jefata shakkun anya da Rankaidad’e take tare kokuwa dai an canzasa ne... Illahirin jikinta ya d’auki rawa, yanayi ne da ya jefata cikin tunanin abinda ya faru da ita shekaru gomasha hud’u ba... Hawaye suka shiga gangaro mata, ta soma shid’an numfashi tana tuno sanda suka keta mata tufafi sukaci zarafinta... Wane irin k’ara ta saki tana mai janye jikinta had’ida tak’urewa waje guda hawaye na kuma ambaliya a fuskarta.. Cikin sauri Mahmood ya rungumota cikin jikinsa yana k’ok’arin calming d’inta “Is ok.. Kiyi shiru kinji... Ya isa bazan miki komai ba..!” Ya d’anyi fasali yana mai kuma shafa bayanta a hankali yanajin yanda take shan zuciya alamun tsoro da tashin hankali... Yaci gaba da lallashinta yana furta “Until you’re ready..!” Ya kwantar da ita a hankali had’ida rik’eta sosai cikin jikinsa bai daina lallashin nata ba.. Yanajin yanda tai lak’was a jikinsa zuciyarta naci gaba da bugawa, A haka ya janyo masu bargo ya rufa yanajin yanda zuciyarta Ke tsananin bugawa kusan tare tare na nasa bugun zuciyar...Idan yace zai tab’a yafe masu kan abinda suka aikata wa Muhibbah Tabbas yayi k’arya... Yana jin wane irin zogi da rad’ad’i cikin zuciyarsa wanda bazai iya misaltuwa ba... Gaba d’aya sun cancanci duk wani misfortunes da suke fuskanta... Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai shak’an k’amshin sumarta... A haka bacci b’arawo yayi gaba da su... ** Safiyar Washe gari koda Ta farka bata gansa a gefenta ba, saidai taga takarda aje gefe yanda ya kwanta da red rose saman takardan, Tai saurin janyo takardan tana warwarewa... _Buenos dias su alteza_ (Barkada safiya Rankidad’e) Ina tayaki murnan cin jarabawarki zagayi na farko... Murmushi saman fuskrta ta ida karantawa Wanda ita kanta batasan daga yanda murmushin ke zuwa ba, a hankali ta shafe fuskarta tana tuno abubuwan da suka faru daren jiyan... Kaman dai ba Rankaidad’e ba... Ta sauk’e fuci a hankali tana tuna sauranta kwanaki biyu... Tana nan zaune tana sakin murmushi a hankali Ta hango saitin kaya aje daga gefe.. Ta mik’e ta nufi yanda kayan yake tana duba, shima takarda ne aje saman kayan an rubuta _De rey a su reina_ (Daga Sarki zuwaga Sarauniyarsa) Tabbas Ta fahimci kalmar Sarki da Sarauniya a wajen.. Ta kuma sakin murmushi tana duban tufafin wanda Sarkin nata ya ajiye mata domin tai masa kwalliya cikinsa... A hankali take furta “Yau naga wane irin jarabawa ni Muhibbah wanda ake maka da yarenda baka iya ba..!” SameenaAleeyou📚 [10/2, 12:37 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *82* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Saida ta ida shiryawa tsaf kafin ta fito tana k’arema sashen kallo, wani k’ofar glass ta gani daga can center yana bud’e gaba d’aya, lokaci guda taji tabi wanann k’ofar taga sararin waje... Cikin taku mai cikeda natsuwa ta nufi wannan k’ofar... Tai tsaye tana kallon frames d’in dake aje wajen jeri jeri wanda Mahmood ya zana... Dangin zanen k’oramu bishiyoyi da dai abubuwa masu ban sha’awa had’ida jefa natsuwa cikin zuciya idan kana dubansu... Taci gaba da takowa a hankali tana mai kallon zanen, babu wanda yafi tafiya da tinaninta kaman wani zane da yakeda yanayi da gidan sarauta.. Ta isa jikin zanen tana tuna Taswiran da ya zamto mabud’in sirrin su Giwa a garesu... Ta jima sosai tana duban zanen kafin Ta sinkayo muryar Zahra ta shigo a guje Ta rungumeta tana fad’in “Tia, good morning, I’m glad I found you here..! I told Aunty Umaima you and Paa loves each other so much..!”Tai maganar suna rungume da juna Muhibbah ta murmusa kad’an kana ta janyo hannun Zahra suka zauna saman wasu k’anan kujeru da aka k’awata wajen dasu.. Zahra bata daina murmushi ba take duban Muhibbar lokaci guda take ci gaba da furta “Zanfi kowa jin dad’I idan kika zama matar Paa d’ina.. Coz I know he loves you.. So much..!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta... Ita kuwa Muhibbar har lokacin bata iya tanka Zahra ba saima k’urama beautiful art works d’in Mahmood idanu da tai... Zahra ta dubeta taga abinda idanunta Ke duba.. A hankali ta murmusa kana taci gaba da furta “You know, Paa loves to paint.. Especially when he’s in a good mood.. Ta haka nida Maama muke gane idan wani abu na damunsa back then in Spain.. And ever since Maama passed away ya daina painting.. Har sanda muka dawo k’asar nan... Sai bayan kin shigo rayuwarmu Paa yaci gaba da painting.. Tia inada tabbacin kece sanadi, you’re the one who inspired him again... Please don’t leave my Paa shid’in masoyinki ne da gaske..!” Ta k’arashe idanunta na rau rau... Cikin sanyin jiki Muhibbah ta kamo hannunta guda tace “Zahra don’t you think this is something your Paa and I should decide..” Cikin rawar murya Zahra ta katseta da fad’in “I know I shouldn’t interfere, but my Paa has been through a lot... Baki tunanin ya cancanci Farin ciki... Please don’t break his heart..!” Muhibbah ta kuma kamo hannayenta tace “Zahra kalleni..!” Zahra ta d’ago idanunta masu d’igan hawaye tana duban Muhibbah wacce itama tuni k’walla sun ciko idanunta, lokaci guda taci gaba da furta “ Your Paa doesn’t love me, bai tab’a fad’in haka ba.. Aurenmu K’addara ne..!” Cikin sanyin jiki Zahra tace “But I know he does, ta yuwu bai furta ba.. But as they say actions speak louder than words...” Murmusawa kad’an Muhibbah tai tana mai duban yarinyar kana ta rik’e hannunta cikin nata, saida ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali taci gaba da fad’in “There are some points in life da zaka zamto baka da zab’i... Sadaukarwa shine zai zamto zab’inka... You might be too young to understand all that I’m telling you now, but banida zab’in da ya wuce na fad’a miki.. Inada tabbacin akwai lokacinda zaki fahimci abinda nake nufi...!” Zahra na hawaye take girgiza kai alamun k’in amincewa lokaci guda take furta “No Tia... Maybe har yanzu bansan mecece soyayya da kamanninta ba.. but We both know that you and Paa loves each other.. You can’t deny you love him... Maiyasa zakiyi sadaukarwar da zai cutar dake...?” Muhibbah na hawaye take furta “Bazaki tab’a fahimta ba Zahra duk yanda zan so na fahimtar dake...!” Zahra ta girgiza kai tace “But you’re married to my Paa now... You’re his wife, you’re not going anywhere right..?!” Cikin tsananin sanyin jiki tai maganar Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Only for three days Zahra.. After three days shikenan your Paa and I will be separated... Nasan bai kamata na sanar dake wanann ba, but banida zab’i, bazaki k’yaleni da tambayoyi ba... Zahra nida mahaifinki munyi yarjejeniya.. Our marriage will only last for three days...!” Ta k’arashe cikin rawar murya.. Da tsananin mamaki Zahra ke dubanta.. Lokaci guda take girgiza kai cikin rashin yarda da abinda takeji... Muhibbah ta jinjina kai a hankali alamun tabbatarwa tace “Promise me bazaki sanar da kowa abinda na sanar dake ba.. Especially Ummi..!” Dubanta tayi da idanunta masu zuban ruwa ba tareda ta iya furta koda kalma ba.. Muhibbah Ta kuma kamo hannunta with a straight face tace “Promise me Zahra..!” Ta kuma fad’i tana d’an jijjiga Zahran A hankali Zahra ta shiga jinjina kai idanunta na kuma zuban ruwa take furta “As you wish your Highness..!” Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai k’ok’arin share hawayen da suka wanke fuskar Zahran... Saidai ga tsananin mamakinta ji tayi Zahra ta saka hannu ta janye hannun Muhibbar daga fuskarta.. Lokaci guda take furta “If you may excuse me Rankidad’e..!” Ta k’arashe da alamun risnawa, lokaci guda ta mik’e ta fice cikin sauri kaman zata kifa k’asa Muhibbah tabi bayanta da kallo har ta b’ace mata hawaye naci gaba da gangaro mata, kifa kanta tayi tana kuka da gaske lokaci guda tana tambayar kanta Maiyasa rayuwa yake zuwa haka, daga wannan k’alubalen sai wancan.. Shin ta yaya zata fahimtar da Zhara cewa dole ce ta sakata rabuwa da mahaifinta.. Ta yaya zata fahimtar da ita sadaukarwa take wa mutanen da suka sadaukar da abubuwa da dama sabida ita.. Shin meye laifinta a nan..? Ta kuma fashewa da sabon kuka... Haka yinin ranan tayisa jikinta babu K’warai, sannan bata sami kiran Rankaidad’e daga wajen Jakadiya ba dan da alama yau d’in shima ya zama busy ne da maganan nad’in sarautar sa.. Yini zubur yayi a cikin Fadarsa suna tattauna al’amaran da ya shafi cikin gidan da manyan masu sarauta na gargajiya.. Sallah ce kawai yake fitar dasu sai ko lokacin cin abinci... Tin Ja’afar yana ganin abin bak’on Al’amari a garesa har dai ya saki jiki... Neman duniya anyi ba’a san yanda Waziri yake ba, Ja’afar ya hani Ubandoma da fad’in yanda suka b’oye Waziri a cewar J’afar d’in Waziri bazaici banza ba... Ko kullesa a bak’in fursuna da sukayi suka tsoratar dashi duk dare ya ishesa horo.. Ta tabbata dai ba’a ga Waziri ba an nemesa sama da k’asa an rasa, can iyalansa ma nemansa suke.. Daga wanda suka damu da b’acewar nasa sai wanda damuwarsu kawai ya bayyana ya amsa masu laifukan da ake tuhumarsa da bakinsa ne musamman matansa da yaci amanarsu da Giwa harda d’ah tsakaninsu... A b’angaren Fu’ad ma duk wanann kwamacala da abubuwan ban mamaki da na al’ajabi harma da tausayi da suka faru cikin Masarauta baida labari da shike yana killace ne can a asibitin masu tab’in hankali... ** BAUCHI Tinda Ansar ya dawo gida baya kula kowa bai shiga hark’ar kowa, babu yanda Mommy batayi ba yayi hak’uri da al’amarin Ubangiji suci gaba da addu’a Allah ya bayyana masu Muhibbah shi kuma ya d’auki matarsa su tare can gidansu amma Ansar yak’i aiwatar da hakan... Sosai Mommy ta damu da yanayin da tilon d’an nata ke ciki, uwa Uba ga tausayin Hamida da takeji wacce sunan aure kawai tayi amma tinda tayi auren babu komai cikinsa sai tashin hankali.. Tabbas auren dole bashida wani alfanu, gashi ta gani akan d’anta... Kyakkyawar magana bai tab’a shiga tsakaninsa da Hamidar ba tinda ya dawo Sannan ko Asibiti ya daina zuwa saima tsananin fad’a fafa da ya soma, d’abi’arda sam ba nasa bane a baya yanzu kuwa ya ara ya yafa.. Daidai da iya Larai bai ragar mata ba, ‘yar wasan da suke a baya yanzu bai d’auka.. Gaba d’aya ya koma very violent kaman ba shi ba... Iya Larai kaw saidai taceda Mommy aita had’a masa da addu’a har Allah ya sassauta masa... Yana zaune cikin d’aki ya bada hankali ma wayarsa lokaci zuwa lokaci yana sakin tsuka yana fuzar da fuci.. Hamida dake mak’ale jikin k’ofa rik’eda jug da cup tana San shigowa amma batasan ya zasu kwashe da mijin nata ba.. Tai k’arfin halin yin sallama ta shigo.. Dukda sanin darajar sallama bai iya amsa mata ba sabida tsananin tururi da zuciyarsa keyi... Tasan bazai mata magana ba koda zata kwana tana tsaye wajen.. Ta duk’a a hankali ta shiga tsiyaya masa juice d’in dake cikin jug d’in a cup d’in a hankali.. Jiki a matuk’ar sanyaye ta mik’a masa tana fad’in “Yaya kasha wannan, na kula yinin yau d’in bakaci komai ba..!” Wani duban da ya watsa mata ya sanyata had’iye sauran kalaman nata.. Ta sadda kanta a k’asa zuciyarta na kuma harbawa.. “Ke ni sa’anki ne..? idan baki fice min a d’aki ba kinji na rantse saina b’abb’allaki Kinga sai akai ma Baffah k’asusuwanki ya had’a ya sayar ya k’ara jari kan wanda ya amsa da sunan kud’in auren Muhibbah.. Munafukar banza tashi ki fita min a nan.!” Hameedah ta tintsire da wane irin kuka mai k’arfi ta mik’e zata fice a guje.. Ya katseta da fad’in “Dawo Ki tattari tsiyarki dan ban San mai aka baki akace ki zuba min ba.. Tattara and get the hell outta my room..!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye had’ida nuna mata k’ofa... Cikin kuka Hameedah ta tattari jug da cup d’inta Ta fice... Tana ficewa yaja dogon tsaki had’ida furta “Munafuka kawai..!” ya mai maida hankalinsa kacaukam kan wayarsa... Tin safe dialing wayar Raheemah yake bata d’agawa.. Cikin sa’a yaji ta d’aga... Da masifa ta taresa da fad’in “Wai kai bakasan uzuri bane a rayuwarka.. Sau nawa zan ce maka mijina baida lafiya ina asibti taredashi kan mai zaka bi duk ka d’aga min hankali..?!” Ansar ya katseta da fad’in “And do you think I give a damn about that Bastard..?! Toh ya mutu ma mana for all I care..” Raheemah ta katsesa da fad’in “Bana son tashanci ka gane.. Na fad’a maka matarka will soon come back to you.. I’ve already poisoned her mind... Na tabbata bayan abubuwan dana sanar da ita bazata bari ayi nad’in sarautar Mahmood da aurensa akanta ba.. So just chill lover boy..!” Ansar dake tsananin huci ya katseta da fad’in “No bazai tab’a yuwa Sarkin nan ya tsare Muhibbah ya hanamu kasancewa ba.. She’s mine.. Ita d’in tawa ce... Da kika San zakije ki tare asibiti wajen d’an iskan mijin nan naki da baki bari na baro Masarautar tareda Muhibbah ba...!!” Mommy dake tsaye k’ofa bayan Hameedah taje mata tana kuka ta taho d’akin Ansar d’in rai b’ace danjin Ba’asan abinda yai mata take kuka sosai nan ya sinkayi wayar da yake da Raheemah... “Ansar..!” Mommy ta furta a hankali tana mai dubansa fuska a matuk’ar d’aure.. Gaban Ansar ya yanke ya fad’i babu shiri ya kaste wayar da yake da Raheemah... Mommy ta ida shigowa cikin d’akin tana tambayarsa cikin tsananin Shock.. “Ansar dama ka sami Muhibbah.. Ka San yanda take, ka sanar damu kwnanka guda kana nemanta baka sameta ba..! Ansar what is going on..? Ka sanar dani..!” Ta k’arashe tashin hankali kwance saman fuskarta... Ansar dake girgiza kai cikin wane irin yanayi yake furta “Mommy ki saurareni..!” Katsesa tayi da fad’in “Saurarenka nake Ansar... Tell me, where’s Muhibbah..? Where’s my daughter..?!” Ta k’arashe idanunta na firfitowa waje... Cikin sanyin jiki Ansar ya silale saman gwiwoyinsa hawaye na gangaro masa, lokaci guda yake furta “Mommy I’m sorry... I lied to you..!” Cikin tsananin sanyin jiki Mommy ta duk’a gabansa itama had’ida furta “Ansar... Mai kake cewa..?!” Cikin zuban hawaye yaci gaba da furta “I lied to you Mommy.. Na miki k’arya.. Nasan yanda Muhibbah take kuma nasan wanda ta aura...!” Cikin tsananin mamaki da sanyin jiki Mommy Ke fad’in “So tell me.. Where is she.. Ina take Ansar.. We need to go get her, tashi muje Ansar tashi muje ka kaini.. I need to see my daughter.. You shouldn’t have kept something like this Ansar..!” Jawo hannunta Ansar yai yana hawaye yake furta “ Mommy I’m afraid we can’t..! Muhibbah Sarki take aure... Abubuwa da dama Sun faru Mommy, na b’oye miki ban sanar dake komai ba.. But believe me I didn’t mean to.. I only want her back in our lives... Mommy I still love her.. So much...!” Ya k’arashe cikin tsananin rauni... Hannunsa Mommy ta kamo tace “Ansar tell me everything..! Ka sanar dani labarin Muhibbah gaba d’aya harda wanda ban bata daman sanar dani ba... Please tell me everything Ansar..!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata.. Cikin zuban hawaye Ansar ke jinjina kai yana furta “Zan sanar dake Mommy.. Everything..!” Lokaci guda Ansar ya soma zayyanowa Mommy labarin Muhibbah tin daga kan abinda su Yazeed sukai mata, har zamanta a sansanin Yalwan Shandam da yanda akai Ta rasa ‘yar uwarta da mahaifiyarta... Har kawo tsintarta da sukai suka taimaka mata... Har zuwa shirinta na komawa Masarauta, da yanda ya taimaka mata ta koma masarauta.. Had’uwarta da ahalin Masarauta harmada Yarima Mahmood, da yanda al’amarin aurenta ya kasance da ta’asan da Giwa tayi a Masarautar da kuma dangantakarda Muhibbah kedashi da ahalin cikin Masarautar... Mommy ta kasa daina zuban hawaye da jin cikakken labarin Muhibbah... Sosai take kuka gumi na tsartsafo mata.. Ansar ya share hawayen da suka kuma gangaro masa yace “Mommy ki daina kuka haka, Muhibbah is safe babu abinda zai kuma samunta da yardar Allah... Gida take cikin ahalinta...!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa dukda hawaye dake zubo masa... Mommy na kuka take furta “Ta yaya bazanyi kuka ba Ansar da jin irin wannan al’amari... Ta yaya bazanyi kuka ba... Ban baiwa Muhibbah dama tamin bayani ba nabi zugan Gudidi da Yawale.. Ta yaya bazanyi kuka ba Ansar...!!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da sabon kuka... Ansar ya jinjina kai yace “But Farin ciki zamuyi yanzu Mommy, Muhibbah ta samo asali, ita d’in ‘yar asali ce d’iyar masu mulki ce.. Duk wad’anda suke mata girin asali it turned out ita d’in ta fisu asali... Mommy baki ganin abin muyi mata murna ne..!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi.. Murmusawa Mommy ma tai tace “Haka ne... Dole nayi ma d’iyata Farin ciki dukda cewa bazamu kuma irin rayuwar da mukayi tareda ita a baya ba... Ta sami asalin ahalinta, Sannan tayi aure yanzu ta auri d’an uwanta na jini kuma mai mulki.. Ita d’in mai mulki ce da mai Mulki ta dace..!” Take annurin dake bisa fuskar Ansar ya d’auke cak... Ya dubi Mommy yace “No mommy, she’s coming back to us.. She’s not staying there.. She’s mine Mommy..!” Ya k’arashe yana sakin huci.. Da tsananin mamaki Mommy ke dubansa, lokaci guda take furta “Kar na sake jin kalma makamancin wannan daga bakinka... Ina karatun naka yake..? Ina hankalinka yake..? Matar wani kake cewa ita d’in taka ce..? Ansar kana cikin hankalinka..?!” “Mommy ina cikin hankalina.. He took her against her will dan haka dole ya sakar min ita... ita d’in tawa ce..!” Baikai aya ba yaji sauk’ar lafiyayyar mari a fuskarsa.. Ya d’ago dafe da k’uncinsa da tsananin mamaki yana duban Mommy dake ci gaba da sakin huci... SameenaAleeyou 📚 [10/3, 5:48 PM] Sameena Aliyou: *MUHIBBAH* *83* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Mommy kan na fad’i gaskiyar abinda Ke zuciyata..?” Ansar ya furta har lokacin dafe yake da k’uncinsa.. “K’warai kuwa, kuma idan ka sake furtawa zan k’ara maka wani marin.. Shashasha kawai maras hankali...!” “But Mommy ko ban fad’i ba auren nasu ba k’argo zai ba..!” Mommy ta katsesa da fad’in “Anya Ansar kana cikin hayyacinka.. Maiyasa zakace haka..?!” Silalewa yai ya zauna saman kujera yana mai furta “I did something terrible Mommy... Worse than wanda kikaji..!” Cikin bugawan zuciya Mommy Ke tambayarsa “What did you do Ansar..? Ka sanar dani..!” Ya d’ago idanunsa masu zuban ruwa yace”Mommy na fad’awa Muhibbah k’arya da gaskiya akan Mahmood gameda yanda aurensu ya kasance.. I badmouthed him, na Fad’i abubuwa da dama gameda Shi.. And what’s worse nayi teaming up da ex girlfriend d’in Mahmood kuma matar Yazeed dan mu raba auren Muhibbah da Mahmood..” Ya k’arashe cikin zuban hawaye.. Baki sake Mommy Ke dubansa lokaci guda take girgiza kai tana furta “Ansar.. You did all that.. Why Ansar..? Maiyasa zakayiwa Muhibbah haka..?!” Cikin zuban hawaye yake furta “Because I still love her Mommy.. I couldn’t get over her... Shiyasa na zab’i na bi ko wani hanya domin na rabata da Mahmood...!” Girgiza kai Mommy take cikin rashin yarda da abinda takeji daga bakin Ansar “Shiekenan ka zama shed’an mai datse igiyan sunnan ma’aiki...!” “Mommy shaid’an fah kikace min...?!” “Yo Ka zama Shaid’ani mana..A cikin shaid’anun ma Babba mai datse aure... Ta yaya zaka zab’i ka rabata da nata Farin cikin don samuwar Naka Farin cikin..? Haba Ansar..? Haba.. How could you do something terrible like this... Wanann ba tarbiyarka bane... Kai banda shashanci ma irin naka ina ka tab’a jin sarki ya saki mata wani ya aura.. Wanann ai raina Sarki ne da sarauta ma kake.. Wanann magana ya isa fa Sarki ka kuka da kanka, domin kuwa duk abinda yai maka kai da kanka ka saya da kud’inka.. Har zaka biye wata can ku k’ulla makirci irin wanann...Wannan shiririta da yawa take... Kuma idan har kana son Muhibbah kaman yanda kace ai zaka barta ta samu farin cikin da bata samu ba baya tsawon rayuwarta.. Kana wajen kaga komai kaga gwagwarmaya da fad’in tashin da shi Mahmood d’in yayi dan ya ceci rayuwarta amma duk kayi biris ka k’ek’ashe idanu ka sanar da ita k’arya da gaskiya.. Allah na tuba da ace ba shine ya aureta ba ince da yanzu bamuSan duniyar da Yawale ya aikata ba, amma da shike batada hakki sai Allah ya turo masoyinta kuma jininta ya aureta ya maidata gida cikin ‘yanuwanta, haka Allah yake al’amarinsa idan har mutum baida hakki toh sai ya kawo masa mafita ta yanda bai tsamman ba.. A duk labarin da ka fad’i Sarkin nan ya fika k’aunar Muhibbah Ansar... Ya soma k’aunarta ne tin had’uwarsu Ta farko... K’addarar rayuwa ta rabasu., idan ma wa ta soma sani ne ai shi ta soma sani kafin kai...Tashi muje..!” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye... Ansar ya dubeta a sanyaye yace “Ina zamuje Mommy..?” “Masarautar zamuje ka warware abinda ka k’ulla..” Ya shafe fuskarsa a hankali yace “Mommy Idan Sarkin nan yasa aka fille min wuya fah..?!” “Oho maka wanann kuma ai kai ka siya da kanka, wayace ka shiga hurumin da ba Naka ba, waye ka shigar masa gonansa, ai duk hukuncin da yanke maka kai ka siya da kud’inka... Kuma tafiya masarauta babu fashi..!” “Wai yanzu yanzu zamu tafi Mommy..?” Ya kuma tambaya jiki a sanyaye “Maimaita maka kake so nayi.. Ka tashi nace, ai sanda kaso tafiyarka baka tina yamma tayi ba, dan haka yanzu ma Jos zamu tafi babu b’ata lokaci... Zan shiga nayi sallama da Hameedah da Larai kafin nan ka shirya kaima ka fito..!” Jinjina mata kai kurum yai zuciyarsa na tsinkewa, Allah ya gani baisan da wasu idanu zai dubi Muhibbah ba bayan k’arerayin da ya Fad’a mata gameda Mahmood.. Sannan ya tabbata idan sukai idanu hud’u da Mahmood d’in ya kumaji abinda yayi toh fah kashinsa ya bushe...Da k’yar ya mik’e ya soma shiryawa... Har wajen Mota Hameedah taiwa Mommy rakiya.. Ansar yana ganin yarinyar yai kaman zai kauda kai Mommy na tsaresa da idanu... Ga mamakinsu yau d’in har sallama yai mata.. Nanda nan suka d’auki hanyar Masarauta.. ** MASARAUTA Kishingid’e Zahra Ta samesa a parlorn nasa alamun yana jiran k’arasowarta... Sallama saman bakinta ta shigo cikin parlorn cikin tsananin sanyin jiki, gaba d’aya tinda Muhibbah ta sanar da ita aurensu da Paa d’inta na kwanaki k’alilan ne sai ta koma wata sukuku da ita, gani take shikenan zasu rasa Muhibbah ma zata fice daga cikin rayuwarsu gaba d’aya... Ta risina a hankali ta gaishesa bayan ta duk’a nan gabansa... Mahmood yai mata K’uri yana karantar ta, ko bata furta ba yasan akwai abinda yake damun d’iyar tasa... Saida dak’ik’ai kad’an suka d’an shud’a kana ya bud’e murya ya kirawo sunanta.. Ta d’ago a hankali had’ida amsawa.. “Akwai abinda Ke damunki ne..?” Ya tambaya yana dubanta.. Jiki a sanyaye Ta girgiza kai tace “A’a Paa babu komai..!” “Are you sure..?!” Ya kuma tambaya cikeda kulawa... Ta kuma jinjina kai cikin tsananin sanyin jiki da tausayin Mahaifin nata, tasan dole ce tasa zai rabu da Muhibbah amma yana matuk’ar k’aunarta... Muryar Mahmood ya katse mata tianin nata sanda yake ci gaba da furta “Zahra, tarihin rayuwarmu zai iya canzawa gaba d’aya.. Inaso Ki sani a yau d’in zaki samu wasu amsoshi da kika jima kina nema tsawon rayuwarki..!” Ya k’arashe yana mai janyo wata doguwar envelope fara k’al... Gaba d’aya Sai Zahra tama rasa mai yake fad’i, tunda taga ya janyo doguwar takardan nan tasan bazai shige takardan sakin Muhibbah bane... Shiyasa yace labarin rayuwarsu zai kuma canzawa... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, Muhibbah gaskiya ta fad’i mata da tace aurensu da Paa d’inta bazai k’argo ba.. Gashi nan kuwa hakan ya tabbata... K’ok’arin saita kanta ta d’anyi dan bata so ya fahimci tasan wani abu, muryarsa ne yankatse mata tinaninta “Zahra..!” Ya ambato sunanta cikin dakewa... Lokaci guda ya mik’a mata doguwar takardan yace “Make sure kin damk’a mata a hannunta...!” Bata amsa ba Sai tsananta fad’uwa da gabanta yake, tana son tambayarsa takardan ta Mecece amma yin hakan ba huruminta bane, wace ita ma da zata bud’i baki taima Mahaifinta tambaya makamanciyar wannan.. Ta kuma sinkayo muryarsa cikin dakewa yana furta “Karb’a mana..!” Jiki a matuk’ar sanyaye, hannunta na tsananin rawa Ta amshi envelope d’in da duka hannayenta biyu... Mahmood yai gyaran murya ya furta “Tashi kije, ki bata hannu da hannu sak’o ne mai matuk’ar mahimmanci ciki wanda ban amince wani Ko wata cikin Hadiman gidan nan su bata ba face ke.. Dan haka kar kiyi wasa dashi Kin fahimta..?!” Ta jinjina masa kai a hankali tace “Na fahimta Paa...!” Lokaci guda ta kuma neman izinin tafiya yace tana iya tafiya kana ta mik’e jiki a matuk’ar sanyaye Ta nufi k’ofa.. ** Koda suka isa nan suka sanar sud’in bak’i ne zuwaga Gimbiya Muhibbah sannan wasu Dakaru daga cikin masu tsaron babban gate d’in Fada sun gane Ansar, hakan yasa ba’a wani tsaya tsananta bincike akansu ba.. Aka had’a Mommy da wasu Dogarai guda biyu sukai mata rakiya cikin Fada, a wani parlorn sauk’an bak’i aka sauk’i Mommy kafin aka tura wata Hadima taje ta sanar da sak’on bak’uwa da Gimbiya Muhibbah kedashi... Koda sak’on ya isa ga Muhibbah batai zaton Mommy bace, sanin cewa bata wani San mutanen garin sosai ba ya sanyata tinanin ko daga inane bak’in nata.. Da wannan tinani ta nufi parlorn bak’in.. Ga tsananin mamakinta Mommy ta gani.. Aiko sunan ganin juna Muhibbah ta taho a guje ta rungumeta... Suka rungume juna suna hawaye... Ai tuni Muhibbah tace ta k’araso daga ciki, sashenta suka nufa suka k’ule a d’aki suna kukan yaushe rabo... Nan Muhibbah ke sanar da Mommy watak’ila su koma tare idan har Mahmood ya sawwak’e mata... Aiko nan Mommy ta gyara zama ta ambato sunanta, Muhibbah ta amsa cikin sanyin jiki “Dama maganar ya kawo ni, dan ko ruwa bazan sha ba zan amo dashi... Sannan koda ace kina matsayin Gimbiya kuma Sarauniya ni zan miki fad’a a matsayinki na d’iyata..!” Gaban Muhibbah ya fad’i tana mai duban Mommy da Ta had’e rai sosai, cikin rawar murya tace “Mommy mai nayi.. Kema kina zaton zan maku butulci ne..?!” Kasteta Mommy tai da fad’in “Ashe bakida hankali ban sani ba..?” Ta d’ago idanunta da sukai rau rau tana duban Mommy... Mommy taci gaba da fad’in “Ansar ya sanar dani komai kuma banji dad’i wannan rashin hankali da yayi ba.. Yau idan mun taimakeki sai kin saka mana.. Idan akace haka za’ake taimako don a rama maka abinda akai maka mai sunan abin kenan.. Ashe ba wajen Allah kake neman ladanka ba kenan..! Muhibbah Ansar ya fad’a miki k’arairayi ne kawai dan ki dawo cikin rayuwarsa amma ba gaskiya bane.. Mahmood masoyinki ne Muhibbah domin kaw ina mai tabbatar miki badon Allah ya k’addari aurenku ba da yanzu bamu San waye Yawale ya aura miki ba..!” Muhibbah da gabanta yai wani irin tsinkewa ya fad’i d’agowa tai tana duban Mommy dake ci gaba da karanto mata duk yanda al’Amara suka kasance... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa wasu irin hawaye suna gangaro mata.. Abubuwan sai suna Zuwa kanta daki daki... Mommy ta k’arashe da fad’in “Koda wasa kar inji kin kashe aurenki akan shiriritar banza kinji koh...!” Girgiza kai Muhibbah take tana hawaye take furta “Mommy I’m afraid it’s too late...! Mommy any moment Rankaidad’e zai iya sauwak’a min..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Baki sake Mommy Ke dubanta “Ban fahimceka ba Muhibbah..!” Cikin rawar murya Muhibbah ta sanar da Mommy yanda sukaida Rankaidad’e... Mommy ta shiga tafe hannaye tana salallami... Yanzu duk yanda nake ganinki mai wayon nan Ashe ba haka bane.. Ina tunaninki ya tafi Muhibbah da har zakiyi irin wannan yarjejeniya da mijinki... Kin kuwa San girman zunubin mace Ta bud’i baki Ta nemi saki daga wajen mijinta..? Haba Muhibbah.. Ina karatunki ya tafi..?!” Cikin zuban hawaye take furta “Mommy banso na cutar da kowa, a tunanina Ansar bai cancanci abinda Rankaidad’e yai masa ba.. Dan duk abinda kika sanar dani is a total opposite da wanda ya sanar dani.. I was so confused Mommy, dan Allah kada kiga laifina..!” Ta k’arashe cikin zuban hawaye murya na rawa sosai.. Bata ida rufe baki ba Hadimarta ta nemi izinin shigowa ta risina ta sanar da ita shigowar sak’on Gimbiya Zahrau wacce Ke zaune parlor tana jira.. Muhibbah dake k’ok’arin saita kanta, share hawayen da suka wanke mata fuska tai kana taceda Hadimar tana nan tafe... Hadimar ta risina Tai godiya kana ta fice... Jim kad’an Muhibbah ta fito waiting room d’in yanda Zahra Ke zaune saman wasu kujeru na alfarma tana jiran fitowarta... Fuskar Zahran kad’ai Muhibbah ta gani ta fahimci babu lafia, domin kaw ta hango tsagwaran tashin hankali kwance saman fuskar nata.. Tasan bazai shige fushin da take da ita bane... Murmushin k’arfin hali saman fuskarta Ta k’arasoga Zahran... Saidai bata kaiga furta koda kalma guda ba Zahran ta mik’a mata envelope dake rik’e hannunta tana mai furta “Paa yace na baki wannan..!” Muhibbah ta dubi Zahra da mamaki Ta kuma dubi takardan da take mik’a mata zuciyarta na tsananta bugawa... Bata amsa ba saima duban Zahra data kumayi tana mai furta “Wannan kuma fah Zahra..?!” A hankali Zahra ta girgiza kai tace “I’ve no idea, he just asked me to give it to you..!” Lokaci guda Muhibbah ta shiga girgiza kai tana mai furta “Ni kuma..? Rankaidad’e..?” Zahra ta kamo hannunta guda ta damk’a mata takardan cikin tafin hannunta.. Lokaci guda take furta “Bansan mai takardan Ke k’unshe dashi ba, amma ga dukkan alamu k’unshe yake da abu mai mahimmanci tinda har ya tsallake Hadiman gidan nan ya bani umarnin na kawo... Watak’ila burinki ya cika miki cikin Takardan nan..! Ina miki fatan alkhairi.. Tia..!” Tana ida fad’in haka bata kuma tsayawa sauraren wata kalma daga Muhibbar ba tai saurin sa kai tana matsan k’walla... Muhibbah dake tsaye wajen tamkar wacce ruwa ya shanye duban Zahra kurum take har ta b’acewa ganinta tana rik’eda takardan dake rik’e cikin hannunta.. Cikin tsananin bugun zuciya ta sauk’oda idanunta masu zuban ruwa tana duban takardan tana kuma juyasa Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Takardan Saki Rankaidad’e ya bata,shikenan ya sauwak’a mata kaman yanda yace idan taci jarabawar zai sauwak’a mata... Batasan sanda sanda kuka ya kufce mata ba... Ta nufo cikin d’aki afufujajan tana kuka take fad’ida Mommy “Mommy Rankaidad’e ya sawwak’e min, shikenan ya rabu dani Mommy... Mommy dan Allah kice masa na fasa banso naci jarabawar kuma..!” Cikin tsananin kuka take maganar dunk’ule da takardan a hannunta... Mommy Ta taso da sauri ta rik’eta tana tambayarta ta nastu ta sanar da ita abinda ke faruwa.. Inaa kuka kurum Muhibbah take.. Lokaci guda Ta mik’e ta nufo waje da gudu alkyabbarta na biye da ita tana shek’ar kuka.. Babu shiri Mommy ta mik’e ta biyo bayanta.. Hadimanta suna tambayarta “Rankidad’e meke faruwa..?” Bata tsaya basu amsa ba suma ta shigesu tana mai ci gaba da kukanta ta nufi sashen Gimbiya Turai... Kan cinyarta ta fad’a tana kuka sosai dunk’ule da takardan a hannunta take fad’in “Ummi dan Allah kice masa na fasa, wllhi banson lashe jarabawar kuma..! Dan Allah Ummi kice masa yayi hak’uri ni na fasa yarjejeniyar..!” Gimbiya da bata fahimci yanda Muhibbah ta dosa ba, d’agota tai tana kuma tambayarta abinda Ke faruwa.. Tace “Ki natsu kimin bayani Saudah, Wai meke faruwa..? Ina Sarakin yake..? Mai kuma ya faru yanzu..?!” Cikin kuka Muhibbah Ke fad’in “Ummi cewa yayi ya sauwak’a min...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana... Gimbiya Turai ta shiga karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ta kuma duban Muhibbah dake matsan hawaye tace “Shi ya sauwak’a miki..?!” Cikin kuka ta kuma jinjina kai ba tareda ta iya furta komai ba sabida tsananin rawa da muryarta keyi... Gani kawai sukai Gimbiya ta mik’e ta fice cikin tsananin b’acin rai... Muhibbah ta rarrafa kusa da Mommy ta kwanta saman cinyarta tana ci gaba da shek’ar kukanta har lokacin takardan damk’e yake cikin hannunta... Mommy sai bata baki take tana calming d’inta amma kaman cewa take ta k’ara, tinanin ‘yan kwanaki biyun da sukai matsayin ma’aurata take.. Beautiful moments da suka tsinci kawunansu ciki a ‘yan kwanakin gashi yanzu shikenan ya zama tarihi Rankaidad’e ya kufce mata na har abada, domin kuwa a tsarin Sarki baya komen mace, idan ya sauwak’a mata kafin nad’in sarauta shikenan bayan nad’in sarauta bazai kuma dawo da ita ba.. Sabon kuka ya kuma kufce mata labarin yanda al’amarin aurensu ya kasance da Mommy Ta sanar da ita na kuma Yawo a kwanyarta, Rankaidad’e is her savior, tin daga fari shi ya soma tsintarta a lokacin data b’ace ranan bukin sallah kuma badon Allah ya k’addari su Yazeed sai Sun cutar da ita ba tabbas da Rankaidad’e bai Tafi ya k’yaleta taredasu ba.. Sannan ya kub’utar da ita a hannun Yazeed a lokacinda yaso lalata mata rayuwa a karo na biyu.. Bayan wanann ya kub’utar da ita a hannunsu Giwa da Jamal wanda shima Jamal d’in yaso kuma lalata mata rayuwa a karo na biyu... Gashi da taimakon Allah shi ya kub’utar da ita bai bari Yawale ya aurarta ga duk sharan da yaso ba... Shin tayaya zataso rabuwa da irin wannan miji wanda a kullum burinsa shine ya zamto mata katanga... Shid’in ya zamto tamkar garkuwa ga rayuwarta.. Maiyasa bazatayi kukan abinda tai masa ba.. Tana tsaka da kukan taji hannayen mutum saman arms d’inta.. Cak ta had’iye kukan nata sakamakon jiyo dadd’an k’amshinsa da tai wanda yayima k’ofofin hancinta sallama... Mahmood ya mik’ar da ita tsaye, har lokacin bata daina ajiyan zuciya ba, ta kuma kasa d’ago idanu ta dubesa.. Mommy ta mik’e sad’af sad’af ta fice ta basu waje, kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Hadimar Gimbiya Turai taceda Mommy ta biyo bayanta dan Tuni Gimbiya tace ai mata iso... Parlorn ya rage saura Mahmood da Muhibbah, kanta saman k’irjinsa ta kasa d’agowa sai ajiyan zuciya da take... Kaman mai rad’a yake furta “Maiyasa kike kuka, ba Abinda kike so na baki ba..?!” Kasa cewa komai tai dan har lokacin ajiyan zuciya take... Mahmood yaci gaba da fad’in “Na cika miki alk’awarinki na baki abinda kika jima kina so ..!” Sai Sannan ta d’ago pale eyes d’inta ta dubesa, shid’inma ita yake duba, lokaci guda yace “Oya open it.. Bud’e ki karanta dan nasan baki karanta ba...!” Yanda Yai maganar a tsare ya kuma sanyar mata da gwiwa, Ta mak’e masa kafad’a tace cikin rawar murya.. “Ni banaso naci jarabawar..!” Sosai ta basa dariya amma ya tsime yace “Don’t you want be brave again..?” Ta kuma mak’e masa kafad’a.. Ya murmusa kad’an har lokacin tana cikin k’irjinsa hab’arsa saman kanta da shike ya d’arata a tsawo, lokaci guda yaci gaba da furta “Bakisan cewa Sarki baya sab’a alk’awari ba..? Sunnan Sarakuna ne yin magana d’aya tak.. Dan idanma baki bud’e ba ni zan sanar dake da bakina..!” Hawaye suka kuma gangaro mata, sharad’in saki shine idan bata karanta da idanunta ba ko kuma idan bai fad’a mata da bakinsa taji ba Tabbas bata saku ba shiyasa ma tak’i karantawa.. Muryarsa ya kuma katse mata tunani “Hibbah open that envelope and read now..!” Cikin tsananin dakewar murya yayi maganar.. Tasa bayan hannunta ta share hawayen da suka kuma zubo mata, lokaci guda Ta shiga warware envelope d’in hannayenta na matuk’ar rawa... Zuciyarta naci gaba da tsananta bugawa... Cak Ta tsaya da abinda take sakamakon sinkayo muryarsa da tai yana fad’in “Idan kin gama karantawa Jakadiya tana jiranki a k’ofa..!” Daga haka bai kuma cewa komai ba ya fice cikin taku irinta masu mulki hannayensa hard’e Ta baya.. Muhibbah ta lumshe idanunta, wasu hawayen suka gangaro mata, Wato ma Jakadiya ce zatai mata rakiya zuwa k’ofar Fadah.. Aiko ya bari dai tayi sallama da ‘yaruwarta Umaima da kuma Ummi... Lokaci guda tasa d’aya hannunta tana share hawayenta take furta “Enough Muhibbah, ya isa haka... Ina amfanin zama da mutumin da bai k’aunarki.. Tinda ya zab’i ku rabu, fine, sai ku rabu d’in.. He’s not worth a single drop of your tears..!” Lokaci guda ta shiga warware takardan a hankali.. Cak Ta tsaya tana kuma nanata abinda ta gani saman takardan, a hankali Ta furta... “DNA test result..!” Idanunta suka sauk’a k’asa, sunanta take gani ga kuma sunan Zahra... Zuciyarta tai wani irin tsinkewa... A fili take furta “70% matched..!” Kenan itada Zahra are related... Kusanci mai tsanani wanda zasu iya kasancewa sun had’a both iyaye.. Kenan Zahra ‘yaruwarta ce da suka fito ciki guda, mahaifiyarta da mahaifinta aune suka haifi Zahra... Take taji duniyar na juya mata.. Ta dafe kujera a hankali ta zauna tana kuma juya takardan.. Nan wata takardan Ta fad’o tai saurin d’auka Ta warware da zummar karantawa.. Daidai lokacin Ummi, Mommy da Umaima suka shigo... SameenaAleeyou 📚 [10/5, 6:23 AM] +234 703 881 5154: *MUHIBBAH* *84* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Takarda ce mai k’unshe da bayanan komai gameda Zahra... Hawaye basu daina zubowa daga idanunta ba take ci gaba da juya takardan, ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansu d’aya bayan d’aya, sud’inma ita suke duba hawaye saman fuskokinsu... Umaima ta d’an dafe hannunta guda tace “Go ahead Sis, read it... Read..!” Ta k’arashe murmushi da hawaye saman fuskarta... A hankali Muhibbah ta jinjina mata kai kana Ta soma karantawa _”Yammacin wata Rana ce mai d’aukeda bak’ar hadari wanda ya sanya tsaban duhun hadarin da k’yar mutum Ke iya ganin gabansa.. A wannan yammaci d’iyata Zahra ta shigo rayuwata... Kan hanyarmu muke na dawowa daga garinsu matar abokina Turaki, nayima Turaki rakiya a lokacin yana zuwa neman auren Hidaya.. I was the one driving the car sanda wata mata from no where ta bayyana gabanmu, ban kula da ita ba kasancewar akwai duhun hadari sosai.. Ga sauri da muke dan mu samu mu iso Masarauta kafin wannan ruwan ya sauk’a...”_ Muhibbah ta d’anyi fasali kafin taci gaba da karantawa _”Sam ban kula da wannan matar ba wacce take rungume da jaririya sabuwar haihuwa, kafin na ankare na buge wannan matar da mota.. Cikin tsananin tashin hankali muka fito muka nufi wannan matar dake kwance gefe tamkar bata numfashi, sam bamu kula da jaririyar da take d’aukeda ita wacce tuni ta fettu gefe, muka nufo kan matar muna k’ok’arin bata agaji na gaggawa tareda tabbacin cewa tana numfashi... Cikin sauri muka d’auki wannan matar muka nufi Mota da ita dan muyi rushing d’inta zuwa asibiti dukda cewa wajen daji ne babu asibiti kusa... Sam bamu kula da jaririyar ba a zatonmu k’unshin tsummokaranta ne marassa amfani.. Bamu takan k’ullin kayan ba dan rayuwarta yafi mahimmanci, sam bamu San cewa ba k’ullin kaya bane d’iyarta ce lullub’e cikin zanin... Nan da nan muka nufi asibitin cikin garin Yalwan Shandam da ita dukda cewa a lokacin garin yana hautsine sabida rikicin ta’addanci da ake a garin a wancan lokacin... Mun samu da k’yar muka samu Likitan da yayi attending wannan matar.. Hankalina sosai ya tashi a wancan lokacin dan ban tab’a buge koda k’aramar dabba bane tinda na soma tuk’i sai gashi na buge mutum sukutum kuma Ta shiga cikin mawuyacin hali na kota ta mutu ko tayi rai dukda cewa a zahiri babu ko k’warzani alamun ciwo jikinta..Muka jira aka dubata ta ta d’an farfad’o kad’an, Likitan yace damu mu shiga mu ganta Ta farfad’o but her heart was very weak, Da alama batada k’oshin lafiya, komai ka iya faruwa.. Likita ya k’arada fad’in kaman akwai abinda take son fad’i.. Aiko muna shiga muka samu tana magana kaman sumbatu tana fad’in yaranta yaranta, Sansanin Yalwan Shandam, akwai jinjirarta a goyo bayanta.. ina jinjirarta..? Daga wad’annan kalaman bamu kuma sinkayo muryarta ba.. Na dubi Turaki cikin tsananin tashin hankali nace matar nan akwai jaririya a tareda ita dole mu koma wajen da muka bugeta.. Turaki yace anya kuwa Rankaidad’e kodai sumbatun zafin ciwo kawai take.. Na girgiza kai naceda Turaki hankalina bazai kwanta ba sai na koma wannan wajen na tabbatar da kalaman matar nan...Haka na fice a cikin sauri Turaki na k’ok’arin dakatar dani kasancewar garin ba’a kwance lafiya yake ba ga dare ya soma shiga.. Naceda Turaki koda zan had’uda ajalina Zanje na duba na tabbata bamu bar wata rai a wannan wajen ba wacce bazata iya yiwa kanta komai ba.. Haka na fice na nufi wannan wajen... Nayita dubawa banga k’ullin kayan ba.. Ga yayyafi da tuni aka soma ga kukan hadari, har na hak’ura zan tafi na sinkayo kukan jaririya... Nai saurin juyawa ina duban yanda nake sinkayo kukan.. Can k’asan wata bishiya na hango k’ullin kayan.. A hankali na duk’a na shiga warwarewa.. It was a baby girl.. A beautiful baby girl wacce kallo guda nai mata naji wane irin shauk’i had’ida tausayi.. Hannayena suna rawa nasa na d’auko jaririyar wacce taketa kuka sabida yunwa da jigata, Na soma jijjigata a hannuna amma batayi shiru ba, nai saurin shigewa da ita mota tsoron kar ruwa ya jik’ata ya k’ara mata fever, nan da nan muka bari wajen dukda cewa ana iya tareni a tuhumeni a ina na samu jaririya musamman sabida halin rashin tsaro da ake fama dashi.. Haka tana hannuna Ina jijjigata Ina driving har Allah ya taimakeni tayi bacci... Kasancewar motata lambar emirate council ne shiyasa van sami wani matsala da Jami’an tsaro ba... Haka na nufo asibtin rungume da jaririyar saidai a lokacinda na iso na tadda Turaki yayi jigum yana jiran k’arasowata.. Na k’arasa da fari’ata rungume da yarinyar ina fad’ida Turaki gashi na samo jaririyar ina mahaifiyarta take...? Jiki a sanyaye Turaki yake girgiza kai, na tsaya ina dubansa cikin tsananin sanyin jiki.. Lokaci guda na fad’a d’akin da matar take rungume da jaririyar a hannuna.. Saidai ga dukkan alamu lokaci yayi Allah ya amshi ran matar nan kafin na kawo mata jaririyarta... Na k’arasa cikin sanyin jiki na ajiye mata jaririyar a gefenta ina furta ga d’iyarki na kawo miki.. Ki tashi ki ganta... Ina maganan hawaye suna gangaro mun.. Likita ya shigo ya dafani yace Rankaidad’e Allah yayi mata cikawa, Ina ‘yanuwanta suke..? Daga ni har Turaki babu wanda yasan inda dangin wannan matar suke amma saidai munji ta ambaci Sansanin Yelwan Shandam.. Muka fito nida Turaki muna tunanin abinyi ga jaririya rungume hannuna.. Turaki yace Rankaidad’e yanzu meye abinyi..? Nace dashi sassafe idan Allah yasa muna cikin masu rai zamu tafi Sansanin Yelwan Shandam mu bincika ahalin matar nan, Turaki ya dubeni yace yarinyar fah..? Sai sannan na tuna da jaririyar dake rungume cikin hannuna..! Nai mata k’uri Ina dubanta ba tareda na iya furta koda kalma ba.. Bamusan a ina sansanin yake ba hakan yasa muka soma tambaya cikin daren.. Nan ake sanar damu ai ‘yan tadda Sun tashi wannan Sansanin Sun k’oneta babu wanda yasan yanda Refugees d’in suka koma... Wani sabon tashin hankali, kenan bazamu samu sauran ahalin matar nan ba, Turaki ya kuma dubana rik’eda yarinyar yace Rankaidad’e yaya zamuyi da yarinyar nan..? Na kuma dubanta k’walla Tab idanuna, lokaci guda naceda Turaki I won’t give her away.. She’s mine Turaki, Zan zama mahaifinta..! Batada kowa bayan ni.. She lost the only family she had left, which’s her mom.. na zamto sanadiyan rasata da tayi, zan zama gatanta in sha Allah... Zan bata duk wani kula da mahaifi yake baiwa d’iyarsa.. Har abada bazata tab’a sanin cewa bani na haifeta ba..! Turaki ya dubeni sosai yace Rankaidad’e are you sure about this.. This is a serious decision your Highness..! Naceda Turaki k’warai ni ne mahaifinta, kuma matata Aliya itace mahaifiyarta...Zamu binne hakan dani dakai yanzu a nan wajen.. Kamin alk’awari babu wanda zaiji wannan batu..? Turaki yai shiru yana nazarin girman alk’awarin da zai d’auka..! Na kuma dafa kafad’arsa nace ka min alk’awari brother..? A hankali Turaki ya jinjina kai yace nayi maka alk’awari amma ta yaya zaka b’oye hakan daga mutane..? Nace dashi yazo a daidai tinda dama shirye shiryen barin k’asar muke nida matata Aliya a lokacin sabida tak’urawa matata da Giwa tayi a cewarta Baiwa ce bata kamaceni ba.. Nace dashi zamu tafi da ita K’asar Spain zamu raineta a can, a lokacin da zamu dawo zamu Zo da ita matsayin d’iyarmu da muka haifa can k’asar Spain.. A wannan daren na kawowa matata Aliya d’iyata wacce na sanya mata suna Fatima Zahra... Yanda Aliya taimin alk’awarin cewa zata rufa wanann sirrin itama, Zahra ta zamto d’iyarta.. D’iyarmu nida ita... Washe gari muka koma wannan garin muka had’a jama’a akaiwa Mahaifiyar Zahra sutura da sallah kaman yanda yake a addini muka kaita makwancinta na gaskiya.. Na kuma d’aukan alk’awari saman k’abarinta cewa zan rik’e d’iyarta bisa gaskiya da amana...! Wannan shine Labarin d’iyata Zahra.. Zahra k’anwarki ce Muhibbah..! Zahra itace jaririyar k’anwarki wacce kuka rabu da ita da mahaifiyarku a Sansanin Yalwan Shandam..!”_ Tana ida karantawa ta saki takardan ya fad’i k’asa tana mai shessh’ek’ar kuka.. Zahra wacce itama tana durk’ushe wajen tinda Muhibbah ta soma karantawa tana fitar da wane irin kuka mai ban tausayi.. Da rarrafe Muhibbah ta K’araso yanda Zahra ke duk’a lokaci guda ta janyota cikin jikinta suka rungume juna cikin wane irin shauk’i, su duka biyun kuka suke mai tab’a zuciyar mai sauraro.. Illahirin mutane dake wajen hawaye suke da jin irin wannan al’amari... Cikin kuka Zahra Ke fad’in “My sister..! You’re my sister..!!” Tsananin kuka ya hanata ci gaba da magana.. K’ank’ameta Muhibbah ta kumayi tana mai kuma kwantar da kanta cikin k’irjinta take furta “Yes Zahra.. I’m your sister.. Your big sister... Allah ya kuma had’amu bayan mun rabu na tsawon shekaru..!” Zahra ma cikin muryar kuka take ci gaba da furta “Since the I first saw you... I felt something very special about you, like we’re connected somehow..!” Muryarta ya carke sai kuka... Muhibbah ta kuma rungumarta tana furta “Likewise Zahra... I felt the same, mu d’in ‘yan uwa ne..!” Ta kasa ci gaba da nagana itama sai kuka... Umaima ta k’araso ta duk’a gefensu tana kuka itama, lokaci guda ta dafa hannayenta saman kafad’unsu.. Suka d’ago suna duban juna su duka ukun... Lokaci guda suka rungume juna gaba d’aya su ukun suna wane irin kuka mai tab’a zuciyar mai sauraro.. Gimbiya Turai ta taso ta had’esu gaba d’aya ta rungume tana matsan hawaye itama.. Lokaci guda take furta “Alhamdulillah..! Alhamdulillah..!! Allah na gode maka daka had’e kan ahalinmu waje guda.. Bayan duk k’ok’arin da wasu sukayi suga Sun tarwatsa kan wannan ahali sai gashi ka had’emu waje guda cikin labaru da k’addarori na rayuwa daban daban.. Wa zaiyi tunanin wad’annan ‘yanmata guda uku tsatso guda ne.. Sai gashi cikin hikimarka da buwayarka ka had’esu waje guda.. Allah na gode maka daka had’e kan ahalin Alfah waje guda..!” Kuka yaci k’arfinta ga tsananin rawa da muryarta yake... Mommy dake gefe sai matsan k’walla take tana duban wannan al’amari mai cikeda al’ajabi ga kuma tab’a zuciya.. Allahu Akbar Allah mai iko... Ashe wannan masarauta k’unshe yake da ahalin Muhibbah shiyasa taji duk yanda zatayi sai tazo wannan Masarautar.. Ashe dai Allah ne ya dawo da ita cikin ahalinta.. Kai wanann kayan Farin ciki da yawa yake.. Ubangiji ya cika abin godiya...! Wannan rana ta kasance wani sabon rana ne na Farin ciki ga wannan ahali, Muhibbah ta had’e kan ‘yanuwanta ta shige tsakiya ta rungumesu tamkar mai tsoron kar wani abu ya kuma gifta tsakaninsu.. Mafarkinta da mahaifinsu ta tina, ashe dai ahalinsa gaba d’aya suna a cikin wannan masarauta, yau da za’a tashi mahaifinsu ya gansu gaba d’aya su duka uku tare Tabbas da ya cika da Farin ciki... Allah ya had’e masa kan ahalinsa waje guda, duk yanda Izzatu taso Ta k’arar da zuri’ararsa a doron k’asa Allah bai nufi hakan ba.. Shiyasa Bawa baya iyayiwa d’an uwansa Bawa abinda Allah bai k’addara masa ba.. Duk abinda ya sameka ka k’addara daga Allah ne, shi ya k’addari yuwar hakan.. Wani bai isa ya maka abinda Allah bai k’addaro maka ba... Suka kasa sakin juna sai wani sabon shauk’i da k’aunar juna suke.. Sai nan nan da juna suke musamman ‘yar autarsu Zahra wacce ita d’in shalele ce a wajensu... Zahra sai tambayar Muhibbah take ya kamannin mamansu da wa take kama, ya na babansu da waye yake kama cikinsu.. Umaima tace gaskiya zataso sanin kamannin Abbansu tinda tin tana k’arama Giwa ta rabasu bata sanshi ba.. Muhibbah ta murmusa tana dubansu gaba d’aya ukun wane irin Farin ciki maras misaltuwa yana ratsa duk wani k’ofa na zuciyarta, hannayensu ta rik’o cikin nata, ta dubi Umaima dake b’angarenta na dama tace “Well, Ke kin d’an d’auko kamannin Abbah kad’an dan kin d’auki hasken fatarsa dukda bansan ya kamannin mahaifiyarki yake ba...” Ta juyo b’angaren hagu ta dubi Zahra, ta kuma murmusawa tace “Kema kin d’an d’auko hasken fatarsa tinda kinfini haske ni Umma na biyo.. Saidai kin d’an d’auko manyan idanunmu nida Umma..!” Gaba d’aya suka murmusa cikeda jin dad’i Muhibbah ta rungumesu tana shak’an Ni’iman canjin rayuwa wanda bata samu ba a baya... Umaima tace “Giwa itace tayi sanadiyar rabuwarmu gaba d’aya..!” Zahra ta k’ara da “Zanso na sake ganin fusakar azzulaman matar nan naji dalilinta na wanann bak’in zalunci da tayima ahalinmu..!” Umaima tace “Ko kad’an banji tausayinta ba, She got what she deserved after all..!” Muhibbah ta kuma rungumosu tana fad’in “Kar mu tuna bak’in ciki, tuna wannan baiwa da rahama da Allah ya lullub’emu dashi.. Mu gode masa sai muyi Farin ciki...!” Gaba d’aya suka murmusa Zahra na fad’in “Y la parte más asombrosa de todo es que ahora estamos todos juntos, como siempre deberíamos estar..!” (Sannan abu mafi birgewa muna tare yanzu gaba d’aya, kaman yanda ya kamata mu kasance tun daga farko..) Hancinta Muhibbah ta d’an jawo tace “Mudai a daina mana Spanish a nan dan bamuji.. Right Umaima..?” Ta k’arashe tana mai d’agawa Umaima gira guda sama.. Umaima ta d’an kashe idanu guda tace “Ahh yaren masoyi ni na isa nace a dena yi..!” “Au kema haka zakice..?” Muhibbah ta fad’i tana duban Umaiman sanda suka shagala da dariya daga Zahran har Umaimar.. Suna a haka Jakadiya ta nemi izinin shigowa.. Ta risina ta gaidasu kana ta k’arada “Rankidad’e.. Mai Martaba Sarkin mu na gobe mai jiran nad’i yace a sanar Gimbiya yana son ganinta..!” Ta k’arashe kanta a k’asa.. Gaban Muhibbah ya fad’i jin Mahmood yana kiranta... D’an duban Sisters d’inta tayi tace “Gaskiya nidai yau d’in gaba d’aya taku ce banson matsawa daga kusa daku..!” Umaima Ta d’an rausayar da idanu tace “Mu mun isa mu hana Rankaidad’e ganin Queen d’insa, a’a Sistu gaskiya dai ki amsa kiran Mai Martaba.. Right Zahra..!” Ta k’arashe tana d’agawa Zahra gira guda.. Muhibbah ta tab’e baki kad’an tace “Then he wait, I’m not done catching up with my sisters..!” Umaima tace “A’a Sistu ai ba’asan sarki da jira ba mu dai zamu jira..” Zahra ta d’anyi gyaran murya cikin sigan zolaya tace “Kaman dai ba yanzu aka gama kuka akan Paa d’ina ba..!” Muhibbah ta janyo pillow ta jifa mata tana fad’in zaki sani ne yarinyar nan.. Zahra ta zille tana dariya ta fad’a jikin Umaima tana fad’in “Aidai gaskiya na fad’i ko Aunty Umaima, Paa d’ina is one in a million.. Kuma ma mu wajen Ummi zamuje ta bamu labarin Masarautarsu Abbah..!” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Umaima.. Umaima na jinjina kai take furta “K’warai muje muji labarin Masarautarsu Abbah..!” Daga haka suka fice rungume da juna cikeda jin dad’i.. Muhibbah tabi bayansu da kallo zuciyarta na mata wane irin sanyi.. Tunawa da tai Jakadiya na waiting room tana jiranta su tafi wajen Rankaidad’e hakan ya sanyata mik’ewa Ta soma kintsawa a nitse zuciyarta na wane irin fuzga mai gauraye da annashuwa... Koda suka iso sashen Mahmood ita kad’ai ta shige ba tareda rakiyar Jakadiya ba.. Cikin natsuwa take takunta a hankali har ta nufi saman benensa.. Bataji alamunsa ba hakan yasa ta nufi b’angaren paint works d’insa.. Haka ta dinga takawa tana ganin baiwar da Allah yaima Sarkin nata.. Kyakyawan murmushi saman fuskarta, tai tsaye jikin wani k’aton frame tana kallo.. Kaman daga sama taji hannayen mutum saman cikinta ya rungumota ta baya daga nan yanda take a tsaye... Zuciyarta ya tsinke ta d’an zabura kad’an Mahmood ya kuma matseta a hankali yake furta “Ina zaki gudu kije..!” Yai maganar cikin salo na d’aukan hankali... A d’an shagwab’e tace dashi “Ba kaine ka tsoratar dani ba..!” Ya juyo da ita suna fuskantar juna dukda cewa ita nata idanun k’asa suke duba, lokaci guda yaci gaba da fad’in “Kin cika tsoro, na kula komai tsoro yake baki.. Bansan yaya akayi kika iya lek’en asiri cikin Masarautar nan da wannan tsoron naki ba..” Murmushi mai sanyi tayi wannan karon har lokacin kanta a k’asa... Bai janye idanunsa daga dubanta ya kamo hannayenta ya sakale yatsun cikin nasa lokaci guda yake furta “Gashi kuma na saka Ki kuka, yanzu kuma na baki tsoro.. Duk ni kad’ai..?!”Ya k’arashe murya a hankali Ta kwantar da kanta cikin k’irjinsa cikeda kunyan abinda tayi... Ta d’an mak’e kafad’a tana nan kwance cikin k’irjin nasa, tamkar wacce zata kuma wani kukan tace “Nifa ba kuka nayi ba Rankaidad’e..!” Ya murmusa kad’an yana mai kuma shigar da ita cikin jikinsa “Oh na mance ashe sakamakon jarabawar ne bai miki ba.. Kodai a sake wani jarabawar ne..?” Ta d’ago a d’an zabure tana dubansa wannan karon sai kuma taji kunyar kanta da kanta Ta kuma bama kanta dariya.. Rufe fuskarta da tafukan hannayenta tai tana mai murmusawa a hankali.. Lokaci guda Mahmood wanda shima sihirtaccen murmushi ne saman fuskarsa ya kuma janyota cikin jikinsa yana mai furtawa a hankali “Karki damu ni da ke auren zobe mukayi.. Mutuwa ce kawai zata rabamu kinji koh..!” Ya k’arashe yana mai aika mata wasu salonsa masu sanyawa taji duniyar tamkar su biyu ne kad’ai suka rage a ciki... Hannunta ya kamo yana mai furta “Come let’s talk..!” Ya k’arashe yana mai masu masauk’i saman Yalwataccen Darduma ta alfarma mai d’aukeda manyan cushions irinta gidajen masu sarauta.. An k’awata saman darduman da kayan marmari sai wanda zuciya ta zab’a... Zaune suke suna fuskantar juna, idanunsa akanta yayinda ita kuma Muhibbah ta sadda nata idanun k’asa... Dak’ik’ai sukad’an gifta kafin yai gyaran murya ya soma fad’in “I believe by now keda Zahra kunsan cewa kud’in ‘yanuwan juna ne.. Harma da Umaima..!” Ta jinjina masa kai a hankali ba tareda Ta amsa ba.. Lokaci guda yaci gaba da furta “Abubuwa da dama Sun faru ko nace suna kan faruwa..! Ban tab’a tsammanin rana irin wannan zatazo ba, ranan da zan sanar da Zahra cewa bani na haifeta ba.. But as they say No secret remains hidden forever... Duk daren dad’ewa dole wata rana zata sani..!” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da fad’in “I don’t know, bansan ta yaya zan soma sanar da matata da kuma yarinyar da na raineta like my own cewa I was the one who ran over their Mom, ni ne nayi sanadiyan rasa mahaifiyarku da kukayi Hibbah.. Bansan yaya zaku d’auki al’amarin ba, it was hard for me to confess, but I had no choice ya zama dole na sanar daku koda bazaku Iya yafe min ba.. Muhibbah ni Mahmood ni na buge mahaifiyarku da Mota wanda yayi sanadiyar barinta duniya.. Zafin wannan abin yasa naji Eh gwara na swwak’a miki dan kar abin ya maku yawa nima kuma bazan iya rayuwa da hakan cikin zuciya na ba.. But then I realize I couldn’t... I can’t let you go... Because I love you...!” Cak ta d’ago idanunta masu zuban ruwa tana dubansa jin abinda yake fad’i, lokaci guda Mahmood da idanunsa tar suke kanta yaci gaba da fad’in “So much...!” Ya d’an had’iyi throat d’insa yanda kana iya hango motsawar wuyan nasa ta waje kana yaci gaba da fad’in “I’ve always loved you since the day I first saw you, when you were little...!” Ya d’anyi fasali yana daidaita numfashinsa, idanunsa wanda babu komai cikinsu face tsantsan gaskiya suna dubanta yaci gaba da furta “Bayan na sake had’uwa dake a cikin Masarautar nan a karo na biyu as a full grown woman, I can admit I feel something... Something very special... Te amo demasiado Muhibbah..!” (Ina matuk’ar k’aunarki Muhibbah) Tinda ya soma magana take duban cikin k’wayan idanunsa hawaye na gangaro mata... A hankali ta lumshe idanunta hawaye naci gaba da gangaro mata... Hannayensa taji saman nata ya rik’o nata hannayen.. Cikin rawar murya yake furta “Will you still accept me, after learning that I was the one who ran your mom over..! Hibbah will still accept me.. Talk to me please Hibbah...!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai kuma matse yatsun hannunta cikin nasa.. A hankali yaji tana janye hannayenta... Yayi tsam ya rik’e yatsun nata, lokaci guda yake furta “Bazaki tab’a yafe min ba koh...?” Bud’e idanunta tai masu zuban ruwa Ta ware su tsaf saman kyakkyawan fuskarsa wanda ya cika da rauni a yanzu saikace ba Sarkin nata ba.. A hankali Ta soma furta “Rankaidad’e Maiyasa zaka ce haka, bayan bada ganganci ka aikata hakan ba.. Maiyasa zakace haka bayan kaid’in Allah ne ya k’addari had’uwarku da ita don ka zamto garkuwa ma jaririyarta wanda azzalumai suke neman ganin bayan ahalinmu a wancan lokacin.. Allah ya maido da Zahra cikin ahalinta ne shiyasa ya k’addari rik’onta a hannunka..! You’re like an Angel Your Highness..Ka bayyana a rayuwar Zahra kuma ka haskaka rayuwarta, ka bata dukkan kulawa da ya dace.. Rankaidad’e ka mance cewa buge Umma da kayi ko k’warzani bata samu ba, kawai kaid’in ka bayyana ne domin ka kula da Zahra..! Sannan Bawa baya shige ajalinsa, kowa ajalinsa a rubuce yake Rankaidad’e.. Kuma Idan akwai wad’anda zamuce sunyi sanadin mutuwar Umma toh ba kowa bane face Giwa da ‘ya’yanta domin kuwa tun bayan abinda ya sameni da mahaifina, zuciyar Umma yayi rauni bata kuma lafiya ba ga juna biyu da take d’aukedashi.. Koda Ta haifi Zahra cikin jinya take batayi lafiya ba.. Idan baka manta ba kaman yanda kace Likita yace her heart was weak toh haka d’in ne zuciyarta tayi matuk’ar rauni tun bayan wad’ancan iftila’i da suka auku mana.. Baka kashe Umma ba Rankaidad’e.. Lokacinta ne yayi sannan Giwa da ‘ya’yanta sune sanadi..!” Cikin tsananin rawar murya take ci gaba da fad’in “You gave my sister a life Rankaidad’e..! Thank you, thank you for taking care of my sister..? Thank you your Highness..!” Muryarta ya sark’e sabida kuka...Lokaci guda Mahmood ya janyota cikin jikinta cikin jikinsa kaman jira take nan kuma ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro... Ya matseta cikin jikinsa sosai yana lallashinta.. Haka yayita riritata yana bata baki had’ida jero mata kalaman k’auna masu sanyaya zuciya wanda har saida tayi mamakin Wai Dama ya iya fad’in kalmomi haka... Kaman dai ba Rankaidad’e d’in data sani ba... Rayuwa ta kumayin dad’i abubuwa Sun kuma warwarewa, ahalin sun cika da Farin ciki maras misaltuwa... Tuni an soma gudanar da shirye shiryen bukin tarewar Muhibbah da Mahmood.. Shi Mahmood kam ma da anbi Ta nashi ne baza’a tsayawa wani biye wa al’ada ba zai tare da amaryarsa amma Ummi tak’i amincewa tace sai nan da sati guda bayan an ida yiwa Muhibbah duk wasu tanadi da ake na al’ada an kuma yi bukin yanda yake a al’adance.. Tuni ta killace Muhibbah yanda ko samun ganinta Mahmood baiyi, gaba d’aya ji yake wannan al’ada da sarautar ba k’aramin tak’urasa sukai ba... Mommy ma ta koma gida dan gudanar da ‘yan kintse kintse, a zaton Muhibbah mommy ta tafi kenan bazatazo Bikin ba, haka taita magiya tana cewa Mommy ta taya ayi da ita, Mommy tace bayan abubuwan da sukai musamman Yawale da Gudidi ita har kunyar Muhibbar take balle ahalinta, uwa uba kuma ga abinda Ansar yazo yayi daga baya... Da k’yar dai ta amince watak’ila ta dawo ayi da ita... Zahra da Umaima basu sama basu k’asa, hidimar tasu ce ta ko ina... Ranan alhamis ake saka ran Amarya Muhibbah zata tare yayinda juma’a ake bukin nad’in sarki Mahmood.. Fadah ta kacame gaba d’aya, matan masu mulki daga ta ko ina Zuwa suke, kama daga matan Su Talba Galadima Matawalle da dai sauran Hakimai, harta matar Baba Wambai tazo, Majidad’i kansa ya samu Mahmood ya risina gaba garesa ya basa hak’uri dan ya yarda idan Rana ta fito tafin hannu bata kareta, Zakaran da Allah ya nufa da cara ko Ana muzuru ko ana shaho toh fah sai yayi... Hassada taki ne ga mai rabo inji masu iya magana... Nan ya sanar da Mahmood d’in duk abubuwan da suka k’ulla masa shida Yazeed.. Ya kuma nemi gafara.. Mahmood yace bai tab’a rik’esa cikin zuciyarsa ba Allah yasa ya amfana da darasin rayuwa da ya d’auka bisa abubuwan da suka aikata.. Shi kuwa Ja’afar tsaresa da idanu yai yana fad’i a hankali daidai kunnen Majidad’in “Fadah bata marhaban da munafukai balle azzalumai, dan haka ka tabbata tuban gaske kayi ba tuban d’an muzuru ba dan idan na fahimci tuban d’an muzuru kayi.. Zaka amshi sakamako irin wanda ya dace dakai..!” Majidad’i ya d’an d’ago yana duban Ja’afar dake tsume da fuska yana dubansa shima.. Ubandoma ya dubguri k’eyar Majidad’i yace “Yarima yana magana amsa masa ake..! Hattara Majidad’i..!” Majidad’i ya jinjina kai a hankali yace “In sha Allah Masarauta zata sameni da cika alk’awari.. Tuban k’warai nayi Yarima Ja’afar..!” Ja’afar ya jinjina kai a hankali ba tareda ya furta komai ba... Manyan masu sarautun gargajiya sai sanyawa ‘ya’yan Sarkin Albarka suke.. Tun ana sauran sati Tambura da algaita suke guguwa a masarautar... Ga duk wanda yasan Masarautar shekaru k’alilan baya ya kuma ganta yanzu yasan abubuwa da dama Sun sauya.. Wani ni’iman kwanciyar hankali da annashuwa ne zalla cikin d’inbin Masarautar... A can b’angaren mata ma kowa ya hallara idan ka d’auke matan Waziri wanda abin kunyar da mijin su ya jaza masu ya hanasu shiga cikin mutane... Yau ta kama laraba Washe gari ake saka ran gudanar da bukin aurensu itada Rankaidad’e... Tana zaune ana shafe tafin k’afafunta da lalle kaman yanda yake a al’ada, Umaima da Zahra suka shigo murmushi saman fuskokinsu... Zahra ta Ware idanu tana duban yanda ‘yaruwar tata ta k’ara shek’i da kyau a ‘yan kwanaki biyun da tayi a killace, tace “Kai Tia Wai Dama haka kikeda fitanennen kyau ne.. Black is gold, Kinga fuskarki kuwa.. Gaskiya Paa dole ya k’ara sadaki..!” Umaima ta kai mata bugun wasa tana fad’in “Ja’irar yarinyar matar Baban naki ne abokiyar wasanki..” Zahra ta d’anyi k’ara kad’an tana furta “Ouchh Aunty Umaima daga wasa.. Kuma ma ai Paa Yaya na ne ta wane b’angaren.. Ni daga yanzu ma Yaya Rankaidad’e Paapa angon Tia zanke kiransa..!” Harta da dattab’an matan dake zaune wajen saida suka nurmusa Umaima na kuma janyo kunnen Zahra guda.. Ita kaw Muhibbah shiru ta b’ace wajen tana jin wani bak’on al’amari tattareda ita, Wai bukin aurensu ake da Rankaidad’e... A tare Umaima da Zahra suka k’arasa gabanta suka duk’a, tausayinta sai ya kamasu... Umaima ta sanya hannu a robar lallen ta d’an lakata ta shafa mata a hanci tana mai furta “Be happy sister.. Coz you deserve all the happiness in the world..!” Muhibbah ta murmusa kad’an tana duban ‘yar uwar tata cikeda shauk’i... Zahra ma ta lakata lallen kad’an a yatsarta ta shafa mata a goshi tana furta “ Sé feliz hermana...!” (Ki kasance cikin Farin ciki ‘yar uwata.) Murmushi take tana dubansu lokaci guda itama ta lakaci lallen tana k’ok’arin shafa masu suka mik’e suna zagaye kampacecen d’akin suna cewa su ba amare bane bazata shafa masu lalle ba.. Aiko nan taita binsu tana fad’in saita shafa masu suma.. Haka saida suka sa Muhibbah taita ‘yar dariya kafin suka k’yaleta.. Zahra da Umaima suka dubi juna suna ‘yar murmushi... Muhibbah ta dubesu tana Ware idanu “I know you two are up to something again..!” Suka murmusa a tare kana Umaima tace “Manyan bak’i muke tafe miki dasu..” Ta d’anyi Jim tace “Manyan bak’i..” Zahra ta jinjina kai tace “K’warai kuwa.. Wait..!” Ta isa tana mai yin iso ma bak’in.. Ga mamakin Muhibbah ba kowa bane face Meenatu aminiyarta ai ko Meenatu tana shigowa ta tafi ta rungume Muhibbah cikin murnan tsalle, lokaci guda take k’ok’arin saita kanta had’ida furta “Wayyo Rankidad’e tuba nake.. I just couldn’t hold myself..!” Muhibbah ta dungureta kad’an tana mai fad’in “Zaki sani ne... Kai k’awata naji dad’i da zuwanki zaki halarci bikina ashe..!” Meenatu tace “Of course I wouldn’t miss your wedding for any thing in the world k’awata...!” Muhibbah ta kuma rungumeta cikeda Farin ciki, nan kuma annurin fuskarta ya d’an ragu tana fad’in “Mommy fah, batazo ba..? She’s not coming koh..?!” Bata kai aya ba ta sinkayo sallaman Mommy k’awayenta guda biyu kuma aminanta na biyeda ita, Aunty Gudidi da Aunty Salma..! Su Gudidi sai rarraba idanu ake yawa mage ta fad’a talge.. Sai kwantar dakai take tana ganin abin kaman a mafarki Wai Muhibbah itace sarauniyar wannan Masarautar gaba d’aya... SameenaAleeyou 📚 [10/6, 2:34 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *85* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Suka rungume juna itada Mommy, Ta d’ago tana duban Mommy tace “Mommy ashe dai zaki zo..?” Murmusawa kad’an Mommy tai tace “Kin tab’a ji anyi biki babu uwar Amarya.. Kuma da irin wannan karramawa da Mai Martaba yayi min ai dole na amsa gayyatarsa koda kuwa Uwar Amarya bata zuwa Bikin d’iyarta... Sannan ni da kaina zan sakaki a lalle Hibbah am..” Kunya ya d’an kamata sai kuma tace “Mommy Rankaidad’e ne ya tura maku katin gayyata..?” Mommy ta murmusa tana kuma duban fuskarta tace “Komai ma ya tura Muhibbah, duk wasu abinda kika sani na al’ada na aure ya tura an raba kaf unguwa dangi na kusa dana nesa, inaga idan akwai wad’anda basu shaida ba bazai shige Yawale da iyalansa ba dan ni da kaina na hana a tura masa ko dan abinda yayi miki..” Muhibbah ta d’anyi shiru tana mai sadda idanunta k’asa sanda Mommy ta ambaci sunan Yawale.. Lokaci guda Mommyn taci gaba da fad’in “Yanda yaso ya tozartaki Sai Allah bai nufi hakan ba.. Ashe ma Sarki ya aurar dake ba tareda ya sani ba.. Yanzu kaf unguwa labarin irin kayan bajinta na gani a fad’i da aka aika daga Masarauta ake ni kaina darajata da kimata ya k’aru a idanun mutane sabida ke Muhibbah.. Ga karramawa da aka min Sarki ya d’aga tawaga tun daga Masarauta suka tafi har can Masarautar Bauchi suka kuma yin wani zugan kana suka nufo gidana.. Shin mai yafi wannan dad’i Muhibbah.. Karkiso kiga d’aukakan da Allah yamin duk a dalilinki.. Allah dai ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba..! Hak’ik’a kinyi dacen miji mai k’aunarki da ganin k’imanki d’iyata... Wanda har zai girmama Uwar rik’onki irin haka bama mahaifiyar data haifeki ba irin wannan miji abin alfahari ne,abin a rik’esa hannu bibbiyu ne Kinji koh.. Domin kuwa duk wanda zai daraja iyayenki shine mijin aure... Ki rik’i aurenki da kyau kinji d’iyata..!” Ta k’arashe cikin rawar murya yayinda Muhibbar ma hawaye ke ziraro mata... Kalaman Mommy duk Sai ya sanya jikinta yin sanyi... Suka kuma rungume juna suna hawaye Mommy na fad’in zatayi kewarta sosai Muryar Gudidi suka sinkaya tana duk’e wajen take furta “Rankidad’e nidai gafararki nazo nema.. amin aikin gafara.. Ki yafeni Gimbiya Muhibbah, wllhi duk abinda na miki sharrin shaid’an ne da kuma sharrin zuciya.. Hassada muguwar ciwo ce.. Hassada itace tamin jagoranci na aikata abinda na aikata... Nayi miki hassadan auren d’an k’awata wanda a baya naso ya auri d’iyata bai aureta ba har tayi aure.. Naji hassadan ya auri tsintacciyar mage irinki wacce batada asali balle tushe ashe ba haka abin yake ba.. Sai gashi hassadan da na miki na taya Yawale wajen ganin mun durk’usar da rayuwarki ashe d’aga darajarki mukayi ba tareda mun sani ba.. Na yarda da hausan nan da ake cewa Hassada ga mai rabo taki ne.. D’an hakin daka raina wataran shi zai tsone maka idanu.. zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho sai yayai... Idan rana ta fito tafin hannu bata tab’a kareta..! Tabbas mun miki hassada ya kaikiga alkhairi.. Munso nisantaki da Duniyar ahalinda kika girma taredasu suka maye gurbin ahalinda kika rasa daga farko ashe mun mik’aki ma ahalinki na jini ne bamu sani ba... Munso ki k’ask’anta da muka aura miki wannan mutumin ashe darajarki muka d’aga ba tareda mun sani ba.. Gimbiya ki yafe ni kimin rai ki yafe ni... Murja taso hanani zuwa amma na dage sai nazo na nemi afuwarki..! Ki yafeni Gimbiya Muhibbah..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin kamo k’afar Muhibbah wacce tuni ta duk’a ta kamo hannayen Aunty Gudidi, tana girgiza kai take fad’in “A’a Aunty ni ban tab’a rik’eki cikin zuciyata ba.. Ked’in tamkar uwace a gareni domin kuwa ked’in k’awar Mommy ce.. Allah ya yafemu gaba d’aya...” Cikin tsananin kuka Gudidi ta rungumo Muhibbah tana fad’in ta cika mai kyakkyawan zuciya.. Mommy da Aunty Salma suka share hawayen da ya gangaro masu suma.. Daga bisani Muhibbah ta samu ta gaisa da Aunty Salma itama ta nemi yafiyarta dukda cewa duk abinda sukayi ba yin kanta bane Gudidi ce ta tilasta mata.. Daga nan kuwa suka k’ume a d’aki itada k’awarta Meenatu tana labarta mata yanda abubuwa suka kasance bayan aurenta da Bak’on Buzu... Gashi yanzu tinda labari ya karad’e unguwa Sarki take aure kowa har son sake ganinta yake, harta ita kanta Meenatun a halin yanzu wani matsayi ta samu wajen K’awaye dashike itace aminiyarta.. Rayuwa kenan, duniya rawar ‘yanmata na gaba Sai ya koma baya, na baya ya dawo gaba... Yau ga Muhibbah da har cikin k’awaye ana k’yamatar sabida rashin cikakken asalinta sai gashi yanzu har ana tsere tseren rab’an makusanta ta bama ita kanta ba.. Shiyasa sam raina d’an adam baida alfanu bakasan mai Allah ya aje wajenba shi da ya halicci kayansa.. Allah kasa mu dace duniya da lahira.. Ameen! ** A can Bauchi kuwa tun bayan ficewarsu Mommy Ansar ya shirya tsaf ya nufi gidan surkinsa Yawale bayan gudanar da sallar la’asar, Sosai yaci gayu cikin shiga Ta kamala, jampa harda hula shida ba gwanin saka manyan kaya ba... Baffah Yawale ya fito yana Washe baki yake furta “A’a Yakubu dama kaine tafe..?” “Eh Baffah ni ne.. Mun sameku lafiya..?” Ya k’arashe yana duk’awa cikeda girmamawa yau d’in yake gaida Yawale.. Yawale yaci gaba da goga karan asuwakin dake bakinsa ya fuzar da tuk’an kana yace “shine baka shiga daga ciki ba ka tsaya daga nan saikace wani bak’o..” Ansar ya murmusa yace “A’a Baffah ai nan d’inma yayi.. Ai akan hanya ma nake..!” Baffah yace “Au toh toh..! Inji dai ba ja’irar yarinyar nan Hameedah ce tai maka wani abin ba..?” Yai maganar cikin fad’a.. Girgiza kai Ansar yai yace “A’a Baffah Hameedah batai min komai ba... Tafiyar dama takace..!” Yawale ya kuma Washe baki ganin yanda sirkin nasa yaci gayu gashi yace tafiyar tasa ce, toh kodai wani babban kyauta zai masa..? K’ila ma gida ya sai masa... Zai masa irin nasu na yaran zamani yayi masa surprise.. Yaci gaba da Washe baki yana furta “Toh toh toh Allah sarki.. Wato dai tafiyar tawa ce..?” Ansar ya jinjina kai a hankali yana mai bud’ewa Yawale marfin Mota yake furta “Muje Baffah babu lokaci..” Yawale ya shiga tofar da tuk’an aswakin da yake goge hak’waransa dasu yana furta “Toh Toh ai kuwa dai Babu lokaci.. Ku likitoci lokacinku ai a k’ayyade yake.. Toh Wai nace ko zan shiga naima Innar taku sallama..?” Ansar ya girgiza kai yace “za’a Baffah ai ba sai ka mata sallama ba, muje kawai...!” Ya k’arashe yana mai kuma hangame masa marfin motar.. Yawale ya rik’e mota ya shige yana furta “Kai kaji Mota mai taushi kaman a saman auduga nake..!” Yai maganar yana d’an tsalle daga zaune saman kujerar... Sanyin AC ya dake sa yace “Allahu Akbar! Kai kaji Ni’ima kaman a turai.. Yo irin Ni’ima ai bazakso a isa yanda za’aje ba Yakubu.. Kai Yakubu kana hutawa fah..” Ansar da idanunsa kega kwalta yace “Is the reward of my hard working Baffah..” Yawale yace “Na’am mai kace Yakubu..?” “A’a bance komai ba Baffah.. Nace tafiya mai d’an tsawo zamuyi..!” Yawale ya kuma wage baki yace “Ai babu komai ni dama yau d’in babu yanda zanje... Yau ina mahaifinka yana raye yaga yanda Ka zama.. Allah sarki d’anuwna ba rabon yaga gurmanka ba..” Gaba d’aya ya cika masa kunne lokaci guda ya murd’a radio yana fad’in “Baffah kaji radio kasan ba’a rabaku da ita..” Daga haka bai kuma bitakan Yawale ba saima maida hankalinsa ga yuk’i da yayi.. Yawale Sai maganarsa yake shi kad’ai k’arshe dai har bacci ya soma d’aukansa basu isa yanda zasuje ba.. ** Kaman sauk’an aradu haka Raheemah dake asibiti wajen Yazeed ta tsinci zancen, sai huci take tana zagaya d’akin, tanata k’ok’arin neman layin Ansar amma bai shiga.. Ta buga tsuka tana fad’i a fili dole ta tafi Masarauta taje ta tsayar da wannan auren koda za’a mutu ne... Muryar Yazeed Ta sinkayo cikin tsananin jinya yana fad’in “Please call me Mahmood and his wife... Dan Allah ki kira mun su...!” Raheemah ta dubesa da mamaki tace “Mai zaka masu... Ina ruwanka dasu.. Ko bakaji cewa bukin aurensu had’eda nad’in sarautar Mahmood ake ba..?” “Ki kira min su Raheemah..!” Ya kuma fad’in cikin rawar murya.. Raheemah ta girgiza kai cikin rashin yarda da abinda takeji “Yazeed mai zakaida mutanenda sune sanadin kasancewarka a asibitin nan.. Mai zaka ce masu..?” Idanunsa na duban sama hawaye na ziraro masa yake furta “Just call them, Ina matuk’ar son Nayi magana dasu..Please ki kira min su, kimin wannan alfarmar..” Raheemah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida jinjina kai.. “Fine zanyi yanda kace idan haka zai saka Farin ciki...” Yazeed dake hawaye ya furta “Na gode..!” Raheemah ta kuma dubansa cikin tsananin sanyin jiki Wai yau Yazeed ne ke godiya.. Ikon Allah kenan.. Tinda ta baro asibitin haka ta nufo Masarauta jikinta a matuk’ar sanyaye, saidai tinda ta iso Masarautar jikinta ya kuma yin sanyi ganin d’imbin Al’umman dake cikin Masarautar, ga algaita nata tashi ga Dogarai sai wasa Sarki da amaryar suke wacce itama amaryar sarkin d’iyar sarauta ce gaba da baya.. Gwiwoyin Raheemah suka kuma yin sanyi, sanda ta isa sashen Gimbiya Zeenat ta tadda ita kanta Gimbiya Zeenat d’in bata k’asa bata sama.. Sai kai komo Kuyangi suke a sashenta ana had’a kyautttuka na bajinta, na sarki daban na matarsa daban na mahaifiyarsa daban.. Baki sake Raheemah Ke dubanta yanda take bada umarnin inda za’a kai kyauttukan wanda aka rurrufesu saman manya manyan parantai masu ruwan zinari an rufesu da manyan k’yalle masu d’aukan idanu kaman yanda sukeyi a al’ada lokutan auratayyansu... “Aunty kema murna kike da auren..?!” Raheemah ta tambaya jiki a sanyaye.. Gimbiya Zeenat ta dubeta galala tace “Bak’in ciki kike so nayi.. Mutanen da suka mana halacci, yau da sunso bayan irin k’ulle k’ullen da mukai cikin Masarautar nan da sun koremu daga cikin Masarautar nan...Amma basuyi ba suka amshe mu hannu bibbiyu... Yau ko Masarautarmu kinaji kina ganin wulak’ancin da suka mana a lokaci aurenki sai gashi su Sun amshe mu Sun mance duk abubuwan da mukai a baya.. Ke nayi bak’in ciki na mai bayan wanda Allah ya riga ya d’agasa kai baka isa ka karyasa ba.. Ya kamata ki d’auki darasi cikin abubuwan da suka faru a Masarautar nan... Yau Ina Giwa da ahalinta..? Babu su kaman an shafesu a doron k’asa wasu ma sun fara mancewa dasu tun basu bar duniyar ba.. Toh ita rayuwa haka take, abinda ka shuka shi zaka girba.. Kiyi wa’azi ma kanki Raheemah, kiyima kanki karatun ta nastu tin kinada ikon yin hakan... Idan kuma rikici zakici gaba da janyo min cikin Masarautar nan toh gaskiya banida zab’in da ya shige na sallameki daga cikin Masarautar nan.. Ko ki tafi kibi mijinki can b’angaren Bayi kokuma ki koma can Masarautar mu wanda nasan bayan abubuwan da suka faru da k’yar idan zasu amsheki...” Baki sake Raheemah ke dubanta hawaye na gangaro mata “Aunty ni zaki kora cikin Masarautar nan..?” “K’warai kuwa idan dai fitina zaki jazamin... I won’t hesitate to throw you away.. Dan haka gwara tun wuri Ki zaba, ko ki natsu ki zama mutumiyar kirki ko ki kama gabanki..!” Tana ida fad’in haka tasa kai Ta nufi d’aki yanda k’awayenta Ke jiranta, sune su keta tayata shirya kyaututtukan... Raheemah ta zauna dirshan tana matsan k’walla, yau itace Aunty Zeenat take cewa zata koreta daga Masarauta kaman wata shara.. Lallai ta yarda rayuwa ta sauya... Da k’yar ta Iya mik’ewa ta fice ta nufi Sashen Gimbiya Turai... Tana isa ta tadda Hadimai masu kai komo a sahen Ta shiga tambayarsu ina zataga Muhibbah.. Hadima guda d’aya Ta dubeta sama da k’asa kana tace “Mai kikace..? Gimbiya Muhibbah ce kike zare Sunana ta babu wani girmamawa..?!” Raheemah dake sakin huci tace “A wajenku ne take Gimbiya.. Nida Muhibbah ‘yar lek’en asiri na santa kuma dashi zan kirata..!” Bata kai aya ba Hadima guda ta matso zata d’auketa da mari, wacce take gefe ta dakatar da ita... Hadimar tace da kin barni na wanketa da mari dan batada wani maraba damu matar Bawa ne a cikin Masarautar nan, matar Yazeed ce..!” Dukda hawaye da suka ciko idanun Raheemah sabida wulk’anci da wad’annan Hadiman suke mata, bai hanata hura hanci tana nunasu da yatsa tana fad’in “Zaku sani.. Duk sai kun yaba wa aya zak’inta zakusan kun shiga hurumin da ba naku ba k’ask’antattun bayi kawai..!” Hadiman basu daina bata amsa da fad’in batada wani maraba dasu d’in ba.. Umaima da Zahra ne suka taho zasu shige sunci uban gayu irinta yaran masu mulki wanda kallo guda zaka masu kaso sake kallonsu nan suka tadda Raheemah na rikici da wad’annan Hadiman... Umaima ta katsesu da tambayan ba’asin abinda Ke faruwa.. Hadima guda d’aya tace “Rankidad’e Wai wannan matar Bawan ne tazo nan zatai rashin kunyawa Gimbiya kuma Giwar Masarautar nan matar Amale ...Shine muke son koya mata tarbiyan Bauta tunda itama cikinmu zata shigo yanzu, ai Bawa take aure..” Harga Allah yanda Hadimar Ke magana taso baiwa Umaima dariya.. Amma tai k’ok’arin saita kanta sanda ta sinkayo muryar Raheema tana fad’in har abada bazata tab’a zama jinin Bauta ba... Umaima tai alamawa Hadiman cewa su tafi su basu waje su barsu da Raheemah.. Babu musu suka risina sukai yanda Umaima tace... Umaima ta dubi Raheemah tace “Kiyi hak’uri da abinda Hadiman nan sukai miki, Kinsan...” Katseta Raheemah tai da fad’in “Where’s Muhibbah.. I need to speak to her right this instant..” Umaima bata kaiga bata amsa ba Zahra Ta k’araso gabanta rik’eda kunkumi.. Tana duban Raheemar daga sama har k’Asa lokaci guda take furta “Ba ko wace shara bace take iya ganin Sarauniya kai tsaye.. Dan haka bazaki samu ganinta ba, Ki b’ace a nan kafin na saka wad’ancan Hadiman su b’atar dake da k’arfin gaske..!” Ta k’arashe tana ware manyan idanunta.. Zuciyar Raheemah taci gaba da tururi, ta yunk’ura zata cakumo Zahra take fad’in “Ke yarinyar nan wllhi yau sai na cire miki rashin kunyarki tsaf naga gatanki dan ko Ubanki bazai iya k’watanki ba...!” Umaima tai saurin shiga tsakiya, yayinda Zahra taci gaba da fad’in “Ya riga ya miki nisa nisanda sai gani daga nesa... Saidai Ki k’are da auren Bawa..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta... Umaima ta girgiza kai tace “Raheemah ki tafi kawai, bazaki samu ganin Muhibbah ba.. Just go please..” Zahra ta kuma katseta da fad’in “Har sai kin rok’eta Sis..? Ai kawai wad’ancan Hadiman zamu sa suyi mata bugun surfe a turmi...! Zaki b’ace ne ko sai na kirasu..?” Zahra ta kuma fad’i cikin daka tsawa wanda saida ‘yar muryar tata ta firgita Raheemah.. Babu shiri ta juya da baya tana jin zuciyarta na mata wane irin d’aci... Tana shigewa Umaima ta dubi Zahra tana girgiza kai, lokaci guda kuma suka tintsire da dariya a tare musamman da suka dubi yanda Raheemah Ke buga sauri tana waige waige tsoron kar hadiman nan su capkota... Zahra ta tab’e baki tace “Allah dai ya ceci Paa wannan matar a naira goma aka baka ita an cuceka wllhi.. Can ta k’arata wutsiyar rak’umi yayi nesa da k’asa Paa d’ina ya d’ara ajinta.. Saidai a k’are a fannin Bayi..!” Umaima Ta janyo hannun Zahran tana fad’in “Yarinyar nan bakida da Dama, ni ko shige muje Meenatu naga missed call din Meenatu nasan yanzu haka Sistu Ke nemata..” “An gama Rankidad’e..!” Zahra ta fad’i harda ‘yar risinawarta... Suka kuma murmusawa a tare kana suka shige... ** Yamma Lis suka iso bayan Yawale ya gama baccinsa, yaji Ac yasha bacci harda su miyaun bacci... Ansar na ida parking bai tashesa ba saida ya ciro wayarsa yai making call yana fad’in gasu nan sun iso... Yana zaune gefe yana duban Yawale dake ci gaba da baccinsa harda su gwarti yanda kasan wanda ya kwana bai bacci ba... Jim kad’an wata Mota bak’a k’irar corolla ta iso tai parking gefe.. Ansar ya d’an bibbigi kujerar da Yawale yake bisa wanda har kwantar masa da kujeran Ansar yai dan yaji dad’in yin baccin... Ya bibbigi kujerar yana furta “Mun iso Baffah..” Yawale ya mik’e zaune da k’yar yana mutsuka idanunsa wanda har lokacin da sauran bacci ciki.. Lokaci guda yake furta “Mun iso Yakubu...Oh Yakubu wannan wane irin gida zamuje da sai yanzu muka iso.. Kodai Habuja muka taho zaka yanka min tikin kujerar Makkah na sauk’e farali bana..” Ansar bai amsasa ba sai bud’e masa marfin Mota da yayi yace “Baffah gasu nan..!” Ai a d’ari Yawale ya kuma ware idanunsa yana sake murtsukasu ganin k’artai da yayi tsaye bisa kansa sun rurrufe fuskokinsu da bak’ak’en masks... Jiki na rawa Yawale ya soma furta “Kalu Innalillahi.. Yakubu mai zan gani..? Ina ka kawoni..? Su waye wad’annan..?!” Ansar yace “Baffah ba kud’i kake so ba shiyasa ka saida Muhibbah, Toh ai wad’annan da kake gani sunji labarinka kana saida yaranka da sunan aure shine suka taho suna nemanka, sud’in masu cinikayyan bil’adam ne.. Da suka sameni nace ‘ya’yan Naka sun k’are dan Ta k’arshen kenan ka aurar min shine suka bani kud’in kanka mukayi cinikin kanka dasu.. Yanzu haka zan kaima Innah kud’in kanka tinda da dai ace ka saida sauran yaranka mata k’anana gwara ace babu kaid’in.. Gwara a sayar dakai.. Yara kuma k’annen Hameedah zan rik’esu in sha Allahu.. Amma ka gama saida Bil’adama Baffah..” Ya k’arashe yana fad’in ku d’aukesa.. Cikin kuka had’ida tsananin tashin hankali Yawale yake fad’in “Kamin rai Yakubu.. Nifa k’anin mahaifinka ne..! Kuma ita wancan yarinyar ai ba jininmu bane, Kai kana tunanin zanyi haka ma ‘ya’yan ciki na ne..! Dan Allah ka rufa min asiri dama akanta kawai nayi haka kuma bazan sake ba..!” ya k’arashe yana kuma zillewa had’ida daka tsalle yana son k’wacewa daga hannun mutanen... Ansar ya dakatar dasu ya dubi Yawale yace “Auho sabida ba ‘yarka bace shine ka zab’i ka cutar da ita koh.. Ka bayarda ita ga mutanen da baka San daga duniyar da suke ba ka aura ma d’iyarka saurayinta koh..? Toh ai d’ah na kowa ne Baffah.. Muhibbah d’iyarka ce tinda kaine alwalinta.. Kawai kaje Allah yajik’anka Baffah.. Allah yasa k’arshen wahalan kenan.. kar ka damu zan kula da iyalanka in sha Allahu..! Ku tafi dashi..!” Ya k’arashe yana kuma masu umarni.. Yawale yaci gaba da tsalle yana kokawan k’wace kansa yake fad’in “Kamin rai Yakubu.. Kaji k’aina Yakubu.. Wllhi na tuba.. Na tuba bazan sake ba..!” Inaa tuni gardawan mazan sun jefa Yawale cikin mota mai lullub’e da tint.. SameenaAleeyou 📚 [10/9, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *86* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Gefe ya koma yanda Turaki Ke tsaye yana dariyar Baffah Yawale da Dogaran da suka b’adda kama suka sauya tufafi harda rufe fuskokinsu da masks... Turaki yace “Gaskiya Likita baka kyautama surkinka ba.. Ya zaka sake had’a idanu da d’iyarsa..?” Ansar ya murmusa kad’an yace “Mai Sarauta kenan, ai ni nasan halin Baffah tinda tin ina k’aramin yaro Babana ya rasu.. Babu irin karan tsaye da Baffah baiyiwa rayuwata data mahaifiyata ba duk akan abinda Babana ya bari, ba don Allah ya rufa asiri Mahaifiyata tsaye take kan k’afafunta ba wajen neman abinda zata rufa mana asiri da yanzu Allah kad’ai yasan yanda rayuwata zata kasance sabida Yawale ya handame duk wani abinda mahaifina ya bari da ka sani...” Turaki ya girgiza kai yace “Ai wasu dai basu san illan cin dukiyar maraya ba, kuma k’alubalen da yanzu muke fama dashi kenan.. Wani yana Allah Allah nasa ya mutu ya hau kan dukiyar yayi babakere kuma karkaji da Wai idan ya cinye dukiyar nan bazai taimakawa marayun ba, basusan cewa wuta suke ci ma cikinsu ba..” Ansar yace “Kaidai saidai kawai Allah ya kyauta duniyar Ta gama lalacewa da kwad’ayi da kuma rowa, mai kud’i baya tausayin talaka kansa da ‘ya’yansa kawai ya sani babu taimakekeniya tsakanin Al’umma, shima talakan baya tausayin kansa ga bak’ar hassada da k’eta da zai samu dama sai yayi zalunci... Hassda da k’eta had’ida bak’ar zalunci sun dabaibaye Al’umma ta yaya kuwa zamu zauna lafiya ba dole bala’u da musiba suyi yawa ba.. Kaidai kawai saidai muce Allah yayi mana maganin abun ya shiryar damu zuwaga tafarkin daidai.. Shi kuma Baffah idan Allah zaisa hakan ya zamto hanyar shiriyarsa ai abin mu godewa Mai Martaba ne daga ni har Hameedar domin kuwa duk kalan wa’azin duniyar nan da ka sani anyi wa Baffah akan kwad’iyin dukiya da jaraban son abin duniya.. Yanzu idan aka barsa haka nan gobe ma zai iya aikata abu makamancin hakan.. Ni naji dad’i da aka masa haka.. Allah yasa hanyar shiriyarsa kenan ..”Turaki ya amsa da Ameen kana ya k’arada “Mu k’arasa Masarautar koh..” Ansar ya amsada “An gama Mai Sarauta..” Tare suka nufi Masarauta motarsu gaba a baya.. ** Suna shiga da Yawale motar suka gyara maza zamansa suna masu risinawa had’ida gaidashi.. Mamaki ya cika Yawale.. Yana ‘yan koke kokensa yana fad’in “Bintu shikenan ashe ba da rabon na miki sallama ba.. Ni kuma haka Allah ya k’addaro min.. Oh ashe dai ajalina ne yazo..!” Cak Yawale ya dakata da koke kokensa yana duban mutanen, cikin rawar jiki da rawar murya yace “Yal.. Yallab’ai nace ba.. Dama wllhi inaso ince maku na tuba.. In sha Allahu ni bazan sake aikata abu mai kamada haka ba.. Kuma kud’in auren yarinyar yana nan idan kuna so sai in baku.. Shikenan ku rabu dani salin alin in komaga iyalina.. Yallab’ai Iayalai ne dani nid’in..!” Ya k’arashe yana d’ago masu hannu alamun rok’o.. Babu dai wanda ya amsasa cikin su har suka shigo cikin Masarautar... Tsaban tsoro da tsananin tashin hankali da Yawale ke ciki baima fahimci cewa Masarauta ce suka shigo ba.. Shidai damuwarsa kawai su k’yalesa ya tafi... Suka isa wani b’angare nan cikin Masarautar aka bud’e masa k’ofa bayan driver ya ida parking... Guda d’ayan ya dubi Yawale ya risina yace “Muje Baba..” Yawale yace “Na’am.. Toh toh.. Yallab’ai nace dai a duba lamarin kar a yanka ni wllhi Dattijo ne ni akwai iyalai.. Na baro iyalai gida..!” Guda d’aya yace “Baba mu shiga daga ciki za’a baka sutura ka shirya sannan ka gudanar da sallar mangariba kafin a kaika kaga shugabanmu...” Zuciyar Yawale Ta kuma tsinkewa, shikenan saima an shiryasa kafin akaisa ga shugaban mayankan.. Kaico son duniya irin nashi.. Bai tab’a nadaman kwad’ayi da son abinda duniya da yake irin na yau ba.. Wato ashe haka yarinyar nan Muhibbah taji.. Allah sarki ya cutar da ita.. Watak’ila ma har an yankata ansha jininta.. Yau gashi yanajin irin abinda taji.. Baisan ya akai ya isa cikin k’atoton parlorn na alfarma, dogari guda yai masa rakiya zuwa wani d’aki.. Yawale ya saki baki da hanci yana duban kayan alatu a wannan gida.. Nan fah ya mance da cewa mayanka aka kawosa sai jinjina mak’udan kud’ad’en da aka kashe a wannan tsararren gida yake wanda ya masa lak’abi da aljannar duniya.. A hankali yake furta “Wai dank’ari mak’ari Aradu wagga gini kinci kud’in kayukan bil’adama.. Allah kad’ai yasan Kayuka nawa akayi ginin nan dasu...!” Yai tsit kuma yana tuna Toh wato dai yanzu harda nasa kan za’a k’ara watak’ila sai gidan yafi haka tsaruwa idan aka k’ara da nasa kan... Ya cire hularsa ya shiga shafa kansa kaman mai auna size din kan nasa... Ga tsananin mamakin Yawale kaya irinta masu mulki aka basa, kaya masu matuk’ar tsada harda rawani.. Ya juya kayan yana kuma furta “Ikon Allah kenan.. Su kuma wad’annan tufafi fah.. Toh kodai kar yasa ne.. Amma idan bai saka ba rabjejen mutumin nan idan ya kuma shigowa ya taddashi fah..? Wata zuciyar tace ai gwara ka saka kayan kafin su yanka ka ko banza ka tab’a saka kayan masu mulki irin haka... Yawale am ka shiga tarihi.. Ya k’arashe tinanin nasa yana kwab’e nasa gajiyayyun tufafin... Koda Yawale ya fito zasu tafi fannin oga Sai rarraba idanu yake yana mamakin mutanen da suka kamosa sun sauya shiga sun saka jajayen tufafi masu ratsin koriya irin tufafin dogarai.. Mamaki ya cika Yawale musamman da suka fito yaga dogayen benen da suke ciki masu zubi da gidajen masu mulki.. Ikon Allah toh meke faruwa ne... Ya tambayi kansa cikin zuciyarsa... Yaga sunata shige mutane sahu sahu kama daga masu shiga irinta Bauta zuwaga masu shiga irinta muk’ami, yaga duk sanda zasu shige taron bayi sai an risina an gaidashi.. A’a Yawale naku fah Sai ya soma k’umewa yana wani jin kansa yana jinjina kai alamun amsawa.. Jin kansa yake yawa wani basarake... A haka suka iso babban Parlorn Mahmood wanda tsarinsa da kyaunsa yasha gaban wancan parlorn da aka soma sauk’an Yawale.. Ya saki baki da hanci yana kallon chandeliers ta ko ina sai wal wal suke kaman wani rana.. A fili yake furta kalman yabo ga wanann gida mai matuk’ar kyaun gaske... Sanda zasu shiga asalin Parlorn da Mahmood Ke ciki yaji muryar Dogarai masu tsaron wannan k’ofar suna furta Gyara kimtsi..! Gyara kimtsi da kyau..! Had’ida masa maraba da isowa... Yawale yaci gaba da Washe baki yana jinina kai... Suna shigowa parlorn ya hango wani kyakkyawan Basarake zaune saman kujera yasha kwalliya cikin tufafi irinta masu mulki, kallo guda zaka masa ka fahimci shid’in Basarake ne.. Gefe dashi saman darduma kuwa matsa ne guda biyu.. Bai ida tantance matasan ba saida ya k’araso sosai yaga ashe Ansar ne d’aya matashin d’ayan kuma kaman yaso ya gane fuskarsa.. Yawale ya k’arasa kusan Ansar yana furta “Yakubu..! Yakubu ina ne nan..? A ina muke..?” Muryar Mahmood ya sinkayo yana furta “Barkada k’arasowa Baba..! Fadah tayi Farin ciki da tarban bak’uncinka..!” Yawale ya kaikaito da k’yar yana so ya d’ago yanda yasan muryar.. lokaci guda yake duban Mahmood dukda tsananin gizo da k’wayar idanunsa ke masa.. Tabbas yaso ya gane wannan k’wayan idanu da karan hancin.. Ya shiga tuna a cikin nad’in Buzaye yaga wannan k’wayan idanun.. Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa sanda ya kuma waigawa da sauri yana duban Turaki dake gefe wanda a zuwansu na farko shi babu nad’in Buzayen a tattaredashi.. Barde ya bud’e murya bayan Mahmood ya ida magana yana furta “Godiya yake Sarkin Sarakuna..! Dattijo yana godiya da karramawa Sarki...!” Hannu na rawa Yawale ya shiga nuna Turaki yana furta “Yakubu gasu nan.. Wad’annan sune suka amshi auren Muhibbatu..! Alhamdulillah Allah ya nuna mana su.. Yanzu sai a warware aure kaga sai a fasa cinikin kaina...” Barde dake tsaye daga gefe ya furta “Hattara Dattijo kana gaban Mai Martaba Sarki ne..! Hattara da kalamanka Dattijo Sarki baya saki.. Gimbiya Ta shigo gidan Alkhairi.. D’iyar masu mulki ce kuma matar masu mulki.. Jaaa zamanin Dogon Sarki...Sarki Mahmooda ibn AbdulJabbar..!” Tinda Barde ya soma magana zuciyar Yawale ke ci gaba da tsinkewa... Meke faruwa..? Wannan mutumin Dama Sarki ne.. Gimbiya..? Wacece Gimbiya..? Muhibbar ce Gimbiya..? Yai saurin juyowa ga Ansar yana furta “Yakubu meke faruwa ne a nan.. Shin ina kasan mutanen nan..?” Ansar yace “Baffah wannan Sarki ne.. Kuma shine ka aurar masa da Muhibbah b’adda kamanni yayi dan ya ceci Muhibbah daga gadar zaren dakaso k’ulla mata.. Shid’in d’an uwanta Baffah.. Muhibbah asalinta d’iyar masu mulki ce kuma ma d’an uwanta ka aurar da ita.. Gida Ta koma Baffah.. Shine yace azo dakai domin Masarauta tayi maka karramawa na musamman...” Ansar ya k’arashe murmushi saman fuskarsa.. Innalillahi wa Inna’ilaihi raji’un..! Tinda Yawale yake bai tab’a jin kunyar duniya irin wanda yaji yau ba.. Wato ashe haka al’amarin yake.. Dukda sanyin Ac dake circulating cikin parlorn bai hana zufa tsartsafowa Yawale ba.. Allah mai iko.. Yanzu ashe Dama wa Sarki ya aurar da Muhibbah.. Kai jama’a Kaicon hassada da son zuciya.. Mai za’ayi da hassada da k’yashi.. Ubangiji Allah ka tsarkake mana zukatanmu ka nisantamu da wad’Annan munanan d’abi’u.. Ai tuni hawaye suka soma zarya saman kumatun Yawale.. Ya kasa kaikaitowa ya dubi yanda Mahmood Ke zaune saima juyawa da yayi gaba d’aya ya basu baya hawaye naci gaba da gangaro masa.. Ansar ya rarrafo kad’an ya kamo hannayen Yawale yana fad’in “Baffah, ka juyo kayi ma Sarki gaisuwa sannan kai masa godiya...” Girgiza kai kurum Yawale yake yana ci gaba da hawaye yake furta “Yakubu bazan iya ba.. Allah ya gani bazan iya juyo ba.. Kace ma Rankaidad’e ya yafeni.. Kace ma Gimbiya Muhibbah ta yafeni.. Wllhi sharrin zuciya ne da son abin duniya had’ida muguwar hassada da k’eta... Yakubu kace Rankaidad’e ya yafeni.. Na tuba wllhi..!” Kuka ya hana Yawale ci gaba da magana... Turaki ya k’araso gabansa ya duk’a yace “Baba bakaima Sarki laifi ba.. Hasalima dan yayi maka godiya ya gayuaceka Fadah tareda karramawa..!” Yawale da hawaye da gumi suka wanke masa fuska girgiza kai yake yana duban Ansar da Turaki yake furta “A’a.. Wllhi A’a ni ne nazo neman gafara da yafiya.. Kuyiwa Allah kuce Mai Martaba ya yafeni na tuba wllhi.. Itama Gimbiya ta yafeni...!” Yaci gaba da matsan k’walla.. Da k’yar Turaki da Ansar suka sa Yawale ya kaikato daga nan yanda yake duk’e yana fuskantar Mahmood.. Turaki ya d’anyi gyaran murya kad’an bayan shud’ewar wasu dak’ik’ai kana yace “Alhamdulillah..! Mun gode ma Allah da yasa ka fahimci kuskurenka Baba.. Ina kuma fata wannan ya zamto wa’azi gareka da masu hali irin naka... Ka aurawa Mai Martaba macen da yake matuk’ar k’auna a lokacinda kake da ikon aurartaga waninsa dan haka ka cancanci kyauta daga Masarauta dukda cewa da wani nufi kayi hakan cikin zuciyarka.. Allah yasa wanann ya zamto izna a gareka damu baki d’aya.. Kar dan ka samu dama akan mutum kace zaka cutar da rayuwarsa baka San mai gobe zata haifar ba..!” Cikin rawar murya had’ida rawar jiki Yawale Ke furta “Wannan gaskiya ne.. Wannan gaskiya ne Rankaidad’e.. Allah dai yayi mana tsari da sharrin zuciya..” ya saci duban Mahmood yana mai kuma duk’awa had’ida d’ago babbar yatsa yake furta “Godiya nake Allah shi taimakeka..! Tuba nake Allah shi baka yawan rai.. Ja zamaninka angon Gimbiya Hibbatu d’iyar albarka..!” Shi kansa Mahmood saida Yawale yaso basa dariya.. Ansar da Turaki suka murmusa a hankali kana Ansar ya dubi Mahmood wanda shima gajeriyar murmushi ne saman fuskarsa yace “Your Highness zan tafi dasu masauk’i idan kamin izini..” Mahmood ya jinjina kai yana mai alamawa Turaki da ya k’araso.. Turaki ya matso yana sauraron sak’on da yake basa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... Ko da gani kasan bazai shige kyautukan karramawa yake umarta a baiwasu Yawale... Sukai masa sallama had’ida godiya kana suka fice tareda rakiyar Turaki.. Yawale yana fad’in shidai so yake yaga Murjah yayi mata murnan wannan babban al’amari mai dad’in ji sannan idan da hali ma yaga Gimbiya Hibbatu ya nemi yafiyarta da gafararta ya kuma mata murnan wannan babban abin arziki da ya sameta... Sun sami ganin Mommy harma da Muhibbah kasancewar a daren za’a rufeta a lalle kaman yanda yake a al’adarsu sai kuma Washe gari akaita d’akinta kai tsaye bayan an rufa mata Alkyabba Ta amarci, nan Yawale yayita neman afuwa a wajenta, shima Ansar ya rok’eta Gafaran abinda yayi mata da Mahmood.. Fadah ta kuma cikada albarka.. Su gudidi ba’a sama ba’a k’asa an samu karamci Sune kan gaba wajen saka Amarya a lalle.. Sai pictures ake ana watsawa social media ko wanne picture da Gudidi zata maka status sai tayi caption maiji da lafiya tace gasu waje kaza Iyayen matan Sarki.. Mommy dai saidai ta kalleta ta murmusa tace oh su Gudidi budurwar zuciyar na nan dai ba’a girma ma hidiman social media.. Gudidi tace ah zamaninsu ne dole su shana ina ta tab’a zaton zata zamto k’awar Maman Matar Sarki da kansa.. Hidima yayi hidima ta ko wanne b’angare sai son barka.. Washe gari tun bayan ida sallan asubahi tambura da algaita Ke tashi cikin masarauta, lokutan sallah ne kurum yake sanyasasu tsagaitawa ana idar kuwa sautin algaita zaici gaba da tashi.. Matayen masu Mulki dasu Mommy harma da Gimbiya Zeenat su suka raka Amarya Muhibbah sashen mahaifiyar mijinta Gimbiya Turai.. Sai gud’a mata suke, nan aka rufa mata sabuwar Alkyabba k’ar mata naci gaba da gud’a .. Masu zuba turare nayi masu rawa nayi.. Masu fatan Allah sanya albarka nayi.. Zigazigai kuwa Sai kod’a Amarya da ango suke harma da uwar angon da Marigayi mahaifin Amarya Wato Yarima Alfah.. Duk wannan hidima Raheemah na k’ume a d’aki tana sharb’an kuka dan akan kunnuwanta komai ke faruwa saidai ko fitowa ta k’asa saidai kawai taga pictures a status din Umaima.. Ko asibti wajen Yazeed ta kasa komawa, tana nan k’ume a d’aki tana cazgan kuka.. Su Zahra dasu Umaima dasu Meenatu suma dai da alama ‘yan team d’in Aunty Gudidi ne ‘yan ayi pictures a tura status ne... Sai pictures suke Meenatu na turo ma K’awayensu da basu samu halarta ba.. Kai saidai ace Masha Allah komai ya tafi yanda ya kamata... Su Mommy sukai mata rakiya har sashenta dake nan cikin Masarautar yanda komai kama daga finiture zuwa duk wani abin buk’ata na cikin sahen a tsakanin satin Rankaidad’e yasa akayo order.. Allahu Akbar yau dai ga Muhibbah cikin d’akinta sosai suka rungume juna itada Mommy suna kuka su Gudidi da Aunty Salma Sai basu baki suke.. Mommy ta kuma mata nasiha kan rayuwa da abinda ya shafi zamantakewa na aure domin kuwa sabon babin rayuwa zata soma.. Daga bisani sukai mata sallama kowa ya koma masauk’insa... Tana nan zaune tana tinanin rayuwarta tin daga farkon abinda ya sameta a wannan masarauta har zuwa had’uwarsu da Rankaidad’e da yanda Allah ya k’addari faruwan abubuwa... Sam batasan lokaci yaja ba tana nan zaune taji k’amshin turarensa nayima hancinta sallama.. Ya zauna gefenta kad’an yana mai tsareta da idanu har lokacin fuskarta rufe take cikin alkyabbar.. Zuciyarta taci gaba da tsinkewa jin ya zauna gefenta.. Hannunta guda dake aje saman gadon ya kai nasa hannun ya d’aura saman nata.. Lokaci guda yai amfani da d’aya hannun ya yaye alkyabbar dake rufe fuskarta.. Yai mata K’uri yana duban yanda hawaye ke kuma gangarowa daga cikin idanunta... A hankali yake furta “I thought kuka ya k’are tunda baza’a sake jarabawar ba..Unless kuma kina so a sake..?” Ya k’arashe tamkar bashin yai maganar ba ‘yan yatsun hannunta cikin tafin hannunsa... Ta saki murmushi a hankali tana mai sanne kai had’ida mak’ale kafad’a, ya murmusa kad’an wannan karon yace “Have you eaten..?” Ta jinjina masa kai a hankali alamun eh.. Cikin kashe murya yace “You sure..?” Nan ma jinjina masa kai tai.. Goran fresh milk da ya shigo dashi ya shiga bud’ewa yana furta “But still you’ll drink this..!” Ta d’an marairaice fuska tace “Nifa na k’oshi your Highness..” Bai daina abinda yake ba, cikin tsarewa yake furta “Do I need to remind you your Highness, ko kin mance ba’a gardama a Fadah.. so just open your mouth and drink all this.. I need an empty bottle.” Ya k’arashe yana mai matso da goran saitin bakinta.. Yana furta “If you don’t drink this zamu sake sabon jarabawa yanzun nan.. So just drink it..!” Kaman zata kurma ihu haka ta lagnab’e kanta waje guda.. Yanda ya tsareta da rikitattun idanunsa ya sanyata bud’e bakinta a hankali tana mai shan madaran da k’yar.. Bata wani sha sosai ba tace ta k’oshi saidai Mahmood bai k’yaleta ba saida ya tabbata tasha sosai.. Ya gyara zamansa sosai yana dubanta kana yace Ta shiga bathroom tayo alwalwa tazo suyi sallaha.. Jikinta a matuk’ar sanyaye Ta mik’e Ta nufi closet, cire alkyabbar jikinta tai ta lank’aye kana ta nufi bathroom ta d’auro alwala kaman yanda ya umarceta.. A nan closet d’in ta tsaya duba hijab yanda ta samesu a shirye a anjesu a mazaunansu.. Ta d’auko wani dogo har k’asa mai ruwan k’asa ta zira kana ta komo cikin d’akin yanda Ta hangi bayansa yana shimfid’a masu abin sallah.. Jallabiyarsa fara k’al sai d’aukan idan take.. Tai tsaye a wajen tana dubansa.. A hankali ya kaikaito yana dubanta yanda tai tsaye nan wajen.. Ya sakar mata murmushi kana ya soma takowa gaba gareta.. Hannayenta ya kamo yana duban kyakkyawan fuskarta dake duban k’asa... A hankali ya matso da ita cikin jikinta had’ida manna mata kiss a goshi, Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali tanajin sauk’an labb’ansa had’ida hucin numfashinsa saman goshinta... Murya can k’asa ya furta “Lets pray mu kuma godewa Allah da wannan babban Ni’imah da ya lullub’emu dashi..!” Ta jinjina masa kai a hankali har lokacin k’asa take duba, ya shiga janyo hannunta tana binsa kaman rak’umi da akala har saida suka isa saman abin sallar tasu.. Mahmood yai masu limanci suka sallaci raka’a biyu na nuna godiya kaman yanda yazo a sunnah... Ya kuma kama forehead d’inta ya karanto addu’an neman alkhairi da tsari... Daga nan janyota cikin jikinsa yai yana mata tambayoyin da suka shafi addininta musamman b’angaren fiqhu tana basa amsa daidai gwargwado, dukda wani irin bugu da zuciyarta keyi.. Yanda yake mata tanbayoyin cikin sigan raha har sai ya sanya ta soma sakin jiki dashi.. Idan Ta basa amsa sai yai murmushi yace ashe dai zata lashe wannan jarabawar..! A haka dai salon jarabawar tasu Ta soma sauyawa.. Tun tana fahimtar tambayoyin Sarkin nata har dai ta kasa banbance yaren da yake mata jarabawar da ita... Tabbas wannan jarabawa yafi duk sauran jarabawar da yai mata a baya... Dare ne mai matuk’ar mahummanci a gareta kaman yanda yake a wajen ko wacce d’iya mace.. Saidai in her own case can k’asan zuciyarta tanajin kaman ba haka zai kasance a gareta ba bayan tuna tsautsayi da iftila’in da ya faru da ita da tai... Dukda kuwa cewa Angon nata zallan k’aunarta yake nuna mata... Sosai ta k’ank’ame bedcover tana kuka da duka zuciyarta harda shesshek’a.. Wanda hakan ba k’aramin karyar masa da zuciya yai ba... Tausayinta gauraye da k’aunarta na kuma ratsa duk wani k’ofa na zuciyarsa... A hankali ya matso kusanta ya janyota cikin jikinsa... Kaman zatai magana amma kuka ya hanata.. “Shiii!” Ya furta yana mai kwantar da kanta cikin k’irjinsa, lokaci guda hawayen zafin zuciya ya d’igo daga cikin idanunsa zuwa cikin sumarta...A hankali yake fad’in “Don’t say a word..! I love you.. I love you so much.. I love everything about you... Just stay right here..!” Ya k’arashe yana mai sumbatar cikin sumarta had’ida lumshe idanunsa... Wani hawayen ya kuma d’igo masa.. Allah ya gani baida tabbacin zai tab’a yafe wa su Yazeed... A wanann dare Mahmood ya tabbatar mata shid’in masoyinta na gaskiya ne.. Haka yaita tarairayanta yana nuna mata soyayyarsa mai tsuma zuciya.. Safiyar washe gari idan Ta tina abubuwan da suka faru saidai ta kulle fuskarta taita sakin murmushi a hankali.. Anya ma zata iya sake had’a idanu da Rankaidad’e..? Ta shiga girgiza kai ita kad’ai tana mai kuma sakin wani murmushin a hankali.. Gaba d’aya jiyan ya juye mata tamkar dai ba Rankaidad’e data sani ba, ko ina sarautar tasa suka tafi oho.. Ta kuma murmusawa a hankali tana tuno kalamansa a gareta... Murmushi bai bar saman fuskarta tayi k’uri ma hasken hantsi take furta “Allah ya tsare mun kai Rankaidad’e..!” Ta k’arashe tana mai kuma lumshe idanu tsan tsan k’aunar mijinta na fuzganta....Shige da ficen Hadimai da take saurarowa daga downstairs ya sanyata mik’ewa a hankali Ta nufo k’asan nan kuwa Ta tadda su Meenatu da Umaima shigowarsu kenan suma.. Meenatu ta shiga zolayarta da fad’in Amarya baki laifi ko kin koda kin k’ona Karagar Sarki..” Bata amsata ba Sai hararar da take jifanta dashi... “Tuba nake Rankidad’e kar kisa Dogarai suyi majajjawa dani...” Sai sannan Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Kedai bazaki bar hali ba... !” Meenatu tace “Ina kuwa zan bari Rankidad’e, ni yanzu haka ma zuwa nai na miki sallama anjima zamu tafi..” Muhibbah Ta zaro idanu waje tace “A’a Haba banson rashin M.. Ai dai zaki jira ayi nad’in sarauta...” “Anya kuwa Toh Bandai San mai Mommy zatace ba dan dama kwana biyu Mama ta bani..” Muhibbah Ta katseta da fad’in “Ba sai na kira Maman ba nace a barki kiyi sati..” Meenatu Ta zaro idanu tace “Sati.! Ai sai kisa Sarki ya koreni garinmu babu shiri..” Umaima ce ta k’araso waya mak’ale kunnenta tana fad’in “Eh Ummi ta tashi lafiya.. Muna can side d’in nata ma.. Okay I’d make sure she eat..” Daga sallama sukai Ta zauna daga gefe tana fad’in “Surkarki ta kira tana tambayan ko kinyi breakfast, nace mata kar ta damu muna nan a nan, we’d feed you if we had to tinda hidiman sarauta ya hana Angon zana balle ya kula da amaryar tasa..!” Ta k’arashe cikin sigan zolaya... Suka d’an dara gaba d’aya Muhibbah na fad’in “Zaki sani ne..” daidai lokacin Mommy dasu Aunty Gudidi sukai sallama ga Kuyangi biyedasu nik’i nik’i da kaya.. Gudidi na baiwa Hadiman umarnin yanda zasu aje kayan.. Su Gudidi abin nema ya samu sai bada doka da order ake.. ** A b’angaren Mahmood ma yanda take yau d’in babban rana ce a gareshi kaman yanda daren jiya ya zamto babban dare mai cikeda alkhairai a gareshi, yanajin kaman bazai iya amsar shugabancin nan ba domin kuwa ko shakka babu Sarautar ya shige hakkinsa.. Kamata yayi ace yanzu yana tareda amaryarsa yana tarairayarta amma gashi wannan hidimar sarautar ya hana faruwan hakan, shi gaba d’aya ya soma tantama idan zai amshi mulkin... Isowar Turaki ya katse masa tunanin nasa... Barde ya shigo ya zube yai gaisuwa kana ya sanar da zuwan Turaki... Mahmood ya basa izinin shigowa... Daga yanda Turaki ya gansa ya fahimci abokin nasa ango yake, dan kyakkyawan annashuwa na musamman kake hangowa saman fuskar tasa mai cikeda gizo... Tun kafin Turaki yakaiga mik’o gaisuwarsa Mahmood ya soma fad’in “Ba’a Turaki da yaro..!” Turaki ya duk’a yana masa jinjina yake furta “Rankaidad’e..!” Mahmood ya kuma fad’in “Ba’a Turaki da yaro..!” “Rankidad’e.. Godiya nake..!” Turaki ya kuma fad’i yana masa jinjina murmushi saman fuskarsa... Lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Galadima ya sanar dani komai ya kammala fitowar ka kawai ake jira Rankaidad’e.. Already an bud’e Babban Gwani (Fadan Mai Martaba Sarki) anyi all the necessary arrangements.. Sarakun yankinmu na kusa sun soma isowa.. Hakimai da manyan masu muk’amin cikin masarauta duk sun hallara kaid’in ake Jira Rankaidad’e..” Ya k’arashe yana mai kuma d’ago masa yatsa alamun jinjina... Mahmood yai shiru tamkar mai nazari wanda har saida yasa Turakin d’gowa yana dubansa... A hankali Mahmood Ke furta “Im not sure Turaki.. I think I’m having a second a thought...!” Turaki ya d’an dubesa da mamaki yace “Ban gane ba your Highness..!” Mahmood yaci gaba da fad’in “I just want to be with my wife.. That’s all Turaki... Babu hidimar sarauta babu damuwar komai..” Turaki ya d’an fuzar da huci yace “But your Highness..” Katsesa yai da fad’in “Can’t you see I’m stuck here... Turaki I can’t do this anymore.. I’m stepping down..!” Ya k’arashe yana murza zobban dake hannunsa.. Turaki ya d’an fuzar da iska kad’an yace “I understand where you’re coming from Your Highness... But ya kamata ka fahimci girma ne ya hau kanku both you and your wife, dole ku sadaukar wasu lokutan naku ga al’umma.. Your Highness you can’t back down now.. I mean ya zamuyi da d’imbin manyan mutanen da aka gayyata.. Mai zamu fita mu sanar dasu..?!” Mahmood ya shafe fuskarsa a hankali had’ida fuzar da huci “Just come up with something.. Whatever, ko kuma a nad’a wani ba dole sai ni ba..” Baikai aya ba Turaki ya katsesa da fad’in “But you’re their choice.. Kaine zab’in mutane.. People chose you.. I’m sure you don’t want to disappoint your People... Babu wanda yafi cancanta sama dakai your Highness.. Na tabbata ita kanta Muhibbah bazata so jin haka daga gareka ba balle Ja’afar da mahaifiyarka.. Please do this for them.. for your people.. And for me as well..!” Ya k’arashe cikin tsananin rauni... Mik’ewa Mahmood yai suna duban juna shida Turakin... Lokaci guda yake furta “Ko da yaushe kana tare dani, through good times and worse... Ka wuce aboki a wajena Turaki.. You’re my brother, kai d’in d’an uwa ne a wajena... Today I want to thank you from the bottom of my heart...For everything...” Katsesa Turaki yai da fad’in “That’s what brothers are for... Bani da buk’atan kamin godiya your Highness.. Fata ne shine Allah ya sanya maka albarka a aurenka ya kuma yi maka jagoranci a shugabancinka.. Allah ya shiga al’amaranka abokina..!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa harda ‘yar guntuwar hawaye cikin idanunsa... Su duka biyun murmushi suke suna duban juna suna sauraro yanda Sautin algaita da tambura ke kuma gauraye d’aukacin Masarautar ... A haka Ja’afar ya shigo ya taddasu ya sanar dasu komai ya kammalla su ake jira... A haka suka nufo babban Gwani Ja’afar da Turaki sun saka shi a tsakiya ... Dogarai suna biye dasu suna ci gaba da kod’a Mahmood d’in wanda gaba d’aya ji yake jikinsa na wane irin tsuma Wai yau shid’in zai taka k’afafunsa cikin Fadan mahaifinsa Babban Gwani, ya shiga tuno rana na k’arshe da yaga mahaifinsa saman Karagar wani zuwa Nigeria da yayi a lokacin yana can k’asar Spain.. Ya tuna mahaifinsa yace dashi duk daren dad’ewa akwai ranan da zaizo ya gaji wannan Karagar... A lokacin ya dai saurari mahaifin nasa ne amma yafi bada k’arfin Yazeed shine wanda zai gaji mahaifin nasu tinda ya fisa jib’antuwa da al’amaran sarauta... Ja’afar dake gefensa shima wani irin fuzga yakeji zuciyarsa na masa ya shiga tuno abubuwa da dama ciki harda rayuwa k’ark’ashin Inuwar Bayi da yayi cikin Masarautar.. Yau sai gashi nan zai taka cikin Babban Gwanin Mai Martaba kuma shid’in yana daga cikin ahalin gidan... A hankali ya lumshe idanunsa hawaye suka gangaro masa... Sanda suka isa cikin Babba Gwani gaba d’aya King makers suka mimmik’e tsaye suna bud’e manyan garensu suna furta “Lafiya D’an Toron Giwa... Gaba salamun baya salamun... Ka shigo cikin aminci.. Karagar taka ce..!” Saida ya isa daidai saman darduman nad’in sarautar mai tambarin masarautarsu yaja ya tsaya yana duban Ja’afar.. Hannun Ja’afar ya kamo suna fuskantar juna, lokaci guda Mahmood Ke furta “Shin zaka iya...? Zaka iya zama saman Karagar nan ka tsare Martabar gidanmu...?” Cikin tsananin sanyin jiki Ja’afar Ke girgiza kai yana furta “No Yaya.. Bazan iya ba, amma inada yak’inin kai zaka kwatanta da taimakon Allah... We’re all here for you Yaya kai ka cancanci ka d’ale Karagar.. Hawaye suka taru can cikin idanunsa ba tareda sun gangaro ba.. Mahmood ya dafa kafad’ar Ja’afar yace “You spent all your life serving this Palace.. An mai dakai Bawa a cikin Masarautarka.. Bata baka dama ka rayu matsayin d’ah a cikin gidan nan ba, Sabida haka ka cancanci rik’e ragamar jagorancin gidan nan... A yau inaso kai ka gaji mahaifinmu....!” Ya k’arashe hannayensa guda biyu dafe da kafad’un Ja’afar d’in. Girgiza kai Ja’afar yake yana furta “A’a Yaya kai ka fini cancanta da ka gaji mahaifinmu I’m sure da ace yana raye da abinda zaiso kenan... Sarautar taka ce Your Highness... Mu muka zab’eka ba kai ka zab’I kanka ba... Munbi cancancanta kuma duk munyi mubaya’a cewa kaine kafi kowa cancanta...!” Kaman daga sama suka sinkayo wata murya... SameenaAleeyou 📚 [10/9, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *87* *©️Sameena Ameeyou...✍🏽* A tare Mahmood da Ja’afar suka juyo suna duban Fu’ad dake takowa gaba garesu, hawaye Tab idanun Fu’ad d’in yake ci gaba da takowa cikin Babban Gwanin, cikin wata irin murya mai gauraye da rauni da k’warjini yake furta “Kai kafi kowa cancanta Yaya... Ja’afar yayi gaskiya, kaine ka cancanci ka gaji Abbah..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya a daidai lokacinda ya k’araso gabansu... Yai tsaye gaban Mahmood suna duban juna, lokaci guda Mahmood Ke furta “Fu’ad kai nake gani a gabana...?” Fuad ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Ni ne Yaya.. I’m out of the mental facility..!” Yana kaiwa aya Mahmood ya rungumesa sosai yana furta “Naji dad’i Fu’ad.. Naji dad’i da Allah ya baka lafiya... Alhamdulillahi..!” Fu’ad ya d’an murmusa kad’an yana duban Mahmood d’in wanda shine favorite d’insa gaba d’aya cikin ‘yan uwan nasa... Take kuma ya sadda kansa k’asa bayan yakai dubansaga Ja’afar yana tuno abubuwan da Jamal ya sanar dashi bayan ya kai masu ziyara a cikin asibitin kafin ya nufo Masarauta... Ja’afar ya d’an dafa Sa kad’an yana sakin murmushi.. “It shall all be well... Brother.. Im glad you’re finally home.. Allah ya k’ara maka lafiya...!” A tare Mahmood da Fu’ad suka amsada Ameen Mahmood d’in na duban k’annen nasa... Lokaci guda ya rungumosu gaba d’aya ya k’ank’amesu cikin jikinsa.. Su duka ukun suka rungume juna gaba d’aya hawaye na gangaro masu... Tausayinsu ya cika zukatan mutanen dake wajen.. Kaga yanda masu rawani Ke matsan k’walla.. Allahu Akbar dole ka koka ma wannan ahali wanda suka sha fama da gwagwarmayar rayuwa... Bayan lafawan komai Algaita yaci gaba da tashi.. Aka soma gudanar da cika ciken nad’in sarauta kaman yanda yake a al’adance... Mahmood yai zama irin zaman da ake idan za’a ci abinci nan saman darduman, Dogarai sukaci gaba da kod’asa sanda ake fesa masa turaren mulki.. Galadima da Talba suka d’auko Alkyabba fara k’al wanda akai mata kwalliya da zare mai kalar zinari suka rufa masa basmala saman harshensu... Shima Mahmood d’in bai daina tsarkake mahaliccinsa ba Sarkin da babu ya shi... Yanaji wani irin babban al’amari ne Ke aukuwa dashi... Gaba d’aya Sai yanajin zuciyarsa tana wane irin fuzga daga cikin k’irjinsa.. Sanda akazo za’a d’aura masa hular Kambin sarautar Galadima ya umarci Ja’afar da ya d’aurawa d’anuwansa Mahmood Kambin Mulkin a saman kansa... Jafar ya k’araso hawaye da murmushi gauraye saman fuskarsa ya amshi hular hannun Galadima.. Har ya soma k’ok’arin d’aurawa saman kan Mahmood sai kuka ya dakata, gaba d’aya suka tsaya suna dubansa, Sunan Fu’ad ya ambata wanda yasa Fu’ad d’in d’agowa cikin fad’uwar gaba, Ja’afar na sakin murmushi yace dashi a hankali “Come here Brother.!” Saida ya d’an d’ago yana duban mutanen dake wajen kaman mai tsoron motsawa, Mahmood ya sakar masa murmushi yana dubansa, a hankali Fu’ad ya mik’e ya k’arasa gaban Ja’afar d’in.. Lokaci guda Ja’afar ya kamo hannunsa ya aza saman Kambin yace “Lets do this together Brother..!” Cikin tsananin sanyin jiki Fu’ad ke dubansa, lokaci guda ya shiga girgiza kai yana furta “No Ja’afar, I can’t do this.. Banida matsayin da zan d’aura Kambi saman kan Sarki..!” Ja’afar ya dafa hannunsa yace “But you’re our brother Fu’ad, it doesn’t matter idan ba Matar Sarki bace Ta haifeka.. Kuyangar Sarki ce ta haifeka, kai d’in d’an mahaifinmu ne .. Ko ka mance Mahaifiyarmu ta bama mahaifinmu Mai Martaba kyautar Baiwarta mahaifiyarka, kai d’in d’ansa ne Fu’ad.. Kai d’in d’an K’wark’wararsa ce.. Ka amince da haka mu d’aurawa Yaya Kambin mulki akansa...!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa.. Fu’ad dake zuban hawaye lokaci guda ya shiga jinjina kai kana yakai hannunsa saman kambin....A tare suka mik’e suka rik’e hular hawaye na gangarowa daga idanunsu.. Shi kansa Mahmood d’in hawaye ne ya mak’ale cikin idanunsa ya kasa gangarowa sai wane irin tsuma da illahirin jikinsa keyi... Bayan sun d’aura masa Kambin Baba Talba da Galadima sune suka soma d’aura masa farar rawanin akansa wanda take fara k’al sai d’auke idanu take... Take aka nad’a masa rawani mai kunne biyu akansa, Wali ya k’araso da d’amaran Mulki sanda Mahmood zai mik’e Dogarai suka baza babban garensu suna furta gyara kimtsi da kyau.. Saida har ya mik’e tsaye kana Wali da Maga yak’i suka k’araso suna d’aura masa d’amarar... Bayan sun ida d’aura masa d’amaran Mulkin Shattima ya k’araso da Takobin hannunsa... Ya mik’awa Magayak’i.. Magayak’i ya amsa ya sakama Mahmood Takobin cikin damararsa... Had’ida mik’a masa Sandar Mulki ya rik’e yana duban d’imbin Al’umman masarautarsa...Allahu Akbar kallo guda zaka masa kace ga Sarki nan wanda zai amsa sunansa Sarki... Babban Gwani Ta kacame da kalaman yabo.. A hankali Mahmood ya soma takawa sanda ya nufi Karagar zai d’ale.. As he was walking towards the Throne Abubuwan da suka faru cikin gidan sai zuwa masa suke, kama daga canza identity d’in da Giwa tayi har zuwa duk wasu abubuwa da suka faru.. Ya jima sosai yana duban KARAGAR hawaye tab idanunsa.. Take ya nemi tsari daga mahallicinsa daga sharrin dake tattareda wannan Karagar ya kuma rok’i mahaliccinsa da ya tabbatar masa da dukkan Alkhairi dake tattareda Karagar sannan yayi masa jagoranci bisa jarabawar da ya jarabcesa dashi na shigabancin Al’umma... Sanda ya d’ale saman Karagar da basmala daidai nan hawaye guda d’aya ta d’igo daga cikin idanunsa.. Allahu Akbar nan kaji Babban Gwani ya kacame da ambaton Allah... Bakunansu sai furta alkhairi suke.. Algaita yaci gaba da tashi.. Take aka buga masa Tambura guda sha biyu na Masarautar.. Yana jin jikinsa na wani irin Karma alamun da gaske sai dai yau shi Mahmood ya d’ale Karagar.. Bayan tsawon shekara guda da watanni da akai babu Sarki a Masarautar sai iftila’i da k’alubale da sukaita faruwa sai gashi yau Allah ya tabbatar da ikonsa ya d’aura Sarki a wannan Masarautar saidai muce Ubangiji yayi masa jagoranci... Ko wanne Tambari guda Goma sha biyun nan da za’a buga sai an ambaci ma’anarta.. Haka saida aka buga masa shabiyu russ ana fad’in ma’anarsu... Daga bisani Masu sarauta suka soma k’arasowa suna zubewa suna kwasan gaisuwa... Galadima ya fara yin nasa Barde yana amsa masa da fad’in “An gaisheka Galadima..! Mai Martaba ya amsa..! Matawalle ma yayi nasa Barde ya kuma amsa masa da “An gaisheka Matawalle..! Mai Martaba ya amsa..!” Haka duk masu sarauta kowa saida ya kawo nasa caffan ga Sarki Mahmooda d’an AbdulJabbar... Turaki na hawaye ya k’araso ya mik’a gaisuwarsa da taya murna ga abokinsa yana mai furta “Long live the King..!” Ja’afar ma ya k’araso yai masa haka Fu’ad ma... Ko wannensu hawayen Farin ciki kwance cikin k’wayan idanunsu... Shagulgulan bukin nad’in sarauta sukaci gaba wakana... Zigazigai naci gaba da yin kirariwa Sarki “Allah shi jaaa zamaninka..! Lafiya Baya goya marayu... Lafiya cika sarari..! Lafiya mai sulken yak’i..! Lafiya mai Tambura goma sha biyu... A laaaaafiya azurfa babu gauraye...!” Ire iren kirarin da ake tayiwa Mahmood kenan ana fad’in Allah ya bashi gidansu... Yinin ranan Masarautar taci gaba da karb’an kyauttuka daga masarautu daban daban.. Yammacin ranan masu mulki suka hau Dawakai sukayita kawo caffa (gaisuwa) saman dawakai ma Sarki dan nuna Farin cikinsu... Ja’afar ya dubi Fu’ad da har lokacin Bai wani saki jikinsa ba, kana ya dafasa kad’an yace “Kana so mu hau Doki muyi wasan doki..?” Fu’ad ya dubesa hawaye kwance cikin idanunsa yake furta “You know, to be honest I still can’t believe my own Mother can do all those horrible things.. How can someone be so inhuman...!” Ja’afar ya dafasa kad’an yace “Fu’ad wasu lokutan mukanso abubuwa su kasance yanda muka tsarasu amma saidai ba muda ikon yin hakan sai abinda Allah yayi... Mutum baya wuce k’addararsa, na sani da ciwo amma kayi hak’uri sai kaci jarabawarka..!” Cikin rawar murya irinta mai kuka Fu’ad Ke furta “Inajin nid’in kaman ba d’aya bane daga cikin ahalin gidan nan.. Ina jin kaman ban cancanci zama ahalin gidan nan ba..!” Saurin kamo hannunsa Ja’afar yayi yace “Of course you’re one of us.. You are a part of this family.. You’re our brother Fu’ad we share the same Father.. So don’t say those things kaji.. Kai ahalin gidan nan ne..!” Kuka ya kufcewa Fu’ad, lokaci guda Ja’afar ya rungumosa shima hawayen na gangaro masa... Saida Fu’ad ya nastu kafin Ja’afar yace suje suyi wasan Doki Su gwada linzami... Suka d’ale saman Dawakan suna duban juna murmushi saman fuskokinsu... Ja’afar ya dubansa yace “Ready...?” D’an tsaresa da idanu Fu’ad yai yace “Ta yaya D’alibi zai gwada k’warewa da Malaminsa... Idan ban mance ba kai kake koya min Doki a baya...” Murmusawa Ja’afar yai yace “Watak’ila D’alibin har Sai yafi malamin.. Lets do this..!” Ya k’arashe yana jan linzamin had’ida zaburan dokin... Take Fu’ad ma ya zabure nasa dokin yabi bayan Ja’afar a guje zukatansu cikeda annashuwa... ** A b’angaren Muhibbah kuwa yau d’in su Mommy dasu Meenatu zasu tafi hakan yasa hankalinta ya karkarta zuwaga yin sallama dasu dukda cewa kuwa can k’asan zuciyarta tsananin kewar mijinta take.. Yinin ranan zubur basu had’u ba, batasan har haka take son mijinta ba.. Ta fara shakkun idan zata iya jure rashin ganinsa irin haka tinda yauma kenan akayi nad’in balle ace ya soma hidiman al’umma gadan gadan.. Ta lumshe idanunta a hankali tana tuna yanda a lokaci k’ank’ani Allah ya sauya mata k’addarar rayuwarta.. Wai yau itace Matar Sarkin wannan Masarautar.. Ta tuna sanda tazo Masarautar a k’ask’ance yau sai gashi Allah ya k’addari ta zamto matar Sarkin Masarautar gaba d’aya tabbas babu abinda ya gagari Allah... tana nan tana tinanin Ta sinkayo sallamansa... Zumbur ta mik’e tana duban k’ofa... Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake dubanta.. Itama d’in murmushin ta sakar masa tana jin zuciyarta na wane irin fuzga... Ganinsa da tai cikin shiga irinta Sarki sak sai taga k’warjininsa ya kuma bayyana... Ta sadda idanunta a hankali tana k’ok’arin duk’awa gabansa dan kwasan gaisuwa... Cikin sauri ya tallafota had’ida mik’ar da ita tsaye.. Suna fuskantar juna hawaye na zirarowa daga cikin idanunta, da gaske yau babu Giwa kuma Mahmood ya d’ale KARAGA... Cikin hawaye take furta “Kaine Sarki.. Ka cancanci zama Sarki mijina.. Ina maka fatan alkhairi tareda addu’an Ibangiji yayi maka jagoranci..!” Ta k’arashe murmushi da hawaye gauraye saman fuskarta... Tallafe da fuskarta yake furta “My love... My beautiful Queen.. I don’t need all this things... For me you’re all I want... And Wannan Kambin naki ne.. Idan akwai wanda ya cancanta ba kowa bane face ke..! Kece kika cancanci Karagar da Kambin domin kece kika yak’i Giwa da zaluncinta.. Kece kika shigo cikin Masarautar nan wanda yake gauraye da duhu kika haskaka shi da gaskiya.. Duhu ya yaye.. Haske ya bayyana... Ta sanadiyanki Allah ya kawo k’arshen Giwa da bak’in Mulkin zaluncin data gina cikin Masarautar nan..!” Ya d’anyi fasali hawaye na gangaro masa har lokacin yana tallafe da fuskarta.. A hankali yaci gaba da furta “Just like your name MUHIBBAH tabbas ked’in abar soyuwace ga duk wanda kika crossing path d’insa.. Ked’in kin zamto tamkar wata tsauni cikin Masarautar nan da rayuwarmu gaba d’aya.. Kin taka rawar gani cikin rayuwarmu gaba d’aya... Kinyi sadaukarwa da Dama dan ki tabbatar haske ya bayyana cikin Masarautar nan.. Thank you for coming into our lives..! Thank you for being mine..!” Ya k’arashe a hankali... Kukan da take k’ok’arin dannewa ya kufce mata.. Lokaci guda ta rungumesa tana kuka sosai... Saida tayi mai isanta Mahmood na lallashinta kafin ya kamo hannunta yace tazo suje.. Ta d’an dubesa sai kuma tace “Ina zamuje your Highness..?!” Bai tankata ba har saida suka k’araso farfajiyan benen... Ya kaikaito da ita suna fuskantar juna lokaci guda kamo hannunta ya shiga janyota yana furta “Come I wanna show you something my Queen.. Turn around and close your eyes..!” Ta d’an Ware idanunta tana tunanin mai zai nuna mata, lokaci guda tayi yanda yace d’in... Wani k’aton frame dake rufe da Farin k’yalle Mahmood ya bud’e kana yace ta juyo ta gani... A hankali take juyowa har ta sauk’e idanunta kan k’atoton frame d’in wanda zane ne na gidan Sarauta... Ta kame bankinta da hannayenta biyu tana duban yanda zanen ya tsaru... Ya tako a hankali ya tsaya daga bayanta had’ida d’aura hannayensa saman cikinta su duka biyun suna duban zanen yace da ita “Do you like it..?” Kyakkyawan murmushi saman fuskarta tace “Of course I love it... It is so Beautiful..!” Ya d’an kwanto da fuskarsa ya manna mata peck a gefen kumatunta kana yace “I’m glad you love it.. Kin gane ina ne..?” Murmushin bai bar saman fuskarta ba tace “Is this also part of the exams your Highness..?” D’an tab’e baki yai kad’an yana jinjina kai yace “Maybe..! Idan kin canka daidai na mallaka miki zanen kyauta idan kuma baki canka ba....!” Yai shiru bai k’arasa ba... Ta d’an kaikaito tana dubansa... Sai kuma ta saki murmushi a hankali Ta furta “Masarauatr su Abbah ne.. Masarautar k’asar Benin...!” Ya d’an yi K’uri yana duban waje guda har ta soma tunanin kodai bata canka daidai ba, Ta sinkayo muryarsa saitin kunnenta yana rad’a mata “Congratulations..!” Ta d’ago tana duban fuskarsa a hankali ta furta “Na gode..” Girgiza mata kai yai yace “Ba irin wannan godiyan nake so ba” Ta d’anyi rau rau da idanu tace “Wanne kake so Your Highness..?!” Kunkuminta ya kuma kamowa suna fuskantar juna lokaci guda ya turo mata labb’ansa alamun ta sumbacesa.. Ta rintse idanunta sabida kunya.. Mahmood yace “Your Highness yaufa babu yanda zakije sai kin bani tukuwici na..” ya k’arashe yana mai kuma tura mata labb’an nasa.. Tace “Fine amma sai ka rufe idanunka..!” “Well that won’t be a problem Rankidad’e..” Ya lumshe idanunsa yana jiran ta sunbacesa... Tai masa k’uri tana duban kyakkyawan fuskarsa, wani irin shauk’in k’aunarsa na fuzganta... Ido guda ya d’an bud’e kad’an jin Ta d’auki tsawon lokaci batai ba nan yaga fuskarta dab da nasa Sai faman rintse idanu take Zuciyarta na bugawa...Aiko a tare suka bud’e ido sanda fuskokinsu suka kusa had’ewa... Ta Ware idanunta tana k’ok’arin juyawa yai saurin rik’ota zatai magana yai ma bakinta marfi da nasa... Cak ya sureta ya nufi bedroom d’insa da ita yana nuna mata tsantsan k’aunarsa gareta... ** Wai akace bayan wuya Sai dad’i sannan tsanani na tareda sauk’i... Al’amara sun soma daidaita cikin Masarauta tuni anyi nad’e nad’en sarauta, a b’angaren su Mommy Tunda suka koma gida kusan kullum sai tayi waya da d’iyarta Gimbiya Muhibbah... Ansar ma tuni ya d’auki matarsa Hameedah sun tare a gidansu.. Hankalin Mommy ya kwanta faranta Allah ya azurta yaran nata da zuri’a masu albarka... A b’angaren Raheemah kuwa nadama yazo mata itama, musamman duba da yanda Yazeed ke mata wa’azi gameda duniya da rayuwar duniya.. Rayuwar da sukai kad’ai ya ishesu wa’azi a cewar Yazeed ya kuma rok’onta Ta taimaka Ta kirawo masa Mahmood ya gansa ya rok’esa gafara koda abinda zaiyi kenan na k’arshe a rayuwarsa domin kuwa Yazeed d’in ya zama weak sosai da ace zai iya tashi daga saman gadon jinyarsa da koda rarrafe ne zaije ya rok’i Mahmood da Muhibbah gafara... Raheemah na hawaye Ta dubesa tace “Banida tabbacin Sarki zai amsa gayyatarka amma Zanyi k’ok’ari na gwada koda Ta k’afar matarsa ce... Yazeed yai mata godiya kana ta fice hawaye.... Koda Ta iso masarauta Jakadiya ce tai mata iso wajen Gimbiya Muhibbah... Sosai Muhibbah taji tsoron yanayin da taga Raheemah ciki, duk ta kod’e ta jeme kaman ba Raheemar data sani ba... Jiki a matuk’ar sanyaye Muhibbah Ke dubanta yanda ta duk’a gabanta tana cazgan kuka, lokaci guda take ci gaba da rok’on Muhibbar gafara... Muhibbah ta mik’ar da ita tsaye suna fuskantar juna, a hankali take furta “Raheemah ki daina rok’onta gafara irin haka ni baki min komai ba... Dukkanmu ‘yan adam ne kuma masu kuskure... Idan muka rok’i Allah gafara matuk’ar tuban gaskiya mukayi tabbas zai yafe mana koda kaifukan namu yakai yawan kumfan teku domin kuwa shi Allah mai yawan afuwa ne... Allah ya yafemu gaba d’aya kinji koh...!” Cikin kuka Raheemah Ta rungumeta tana fad’in “Kinada zuciya mai kyau Muhibbah... Na gode na gode k’warai..!” Muhibbah ta rik’o hannayen Raheemah cikin nata tace “Babu komai Raheemah...!” Raheemah ta d’an jinjina kai tana duban Muhibbar sai kuma tace “Wani alfarma kuma nake so Kimin...” Dubanta tai da mamaki kana tace “Wane alfarma kenan..?” Raheemah taci gaba da fad’in “Akan Yazeed..!” Take fuskar Muhibbah ya sauya ta zame hannayenta daga cikin na Raheemah... Raheemah ta kuma share hawayenta tace “Nasan bai kamata na ambaci sunansa a gabanki ba amma babu yanda na iya ne Muhibbah.. Domin yana cikin tsananin jinya... Abinda yake buk’ata kawai shine yafiyarki... Muhibbah ki yafewa Yazeed dan Allah sannan ki rok’i Mai Martaba yaje yaga Yazeed domin banida tabbacin Yazeed zai iya fita daga asibiti... Please Muhibbah can you do this..?!” Ta k’arashe tana mai kuma kamo hannayen Muhibban cikin zuban hawaye... Muhibbah da tuni itama hawaye sun fara gangaro mata, a hankali takai hannunta Ta goge hawayen... Tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Fansa baida wani amfani Raheemah.. Tun lokacinda na watsar da k’uduri burin Fansar abinda suka aikata min na samu salama cikin zuciyata Raheemah... Na zab’i na bar komaiga mahaliccinmu yayi hukunci tsakaninmu... Raheemah I’m sorry I don’t know if I can still forgive him... I’m not really sure...! Amma na miki alk’awari zan rok’i Mai Martaba yaje yaga Yazeed kaman yanda kika buk’ata...!” Ta k’arashe hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta... Cikin tsananin sanyin jiki Raheemah Ke jinjina kai tana furta “Na fahimceki, kuma na gode sosai... Thank you so much Your Highness..!” Muhibbah ta rungumota su duka biyun suna hawaye... Koda Ta sami Mahmood da batun da fari k’in amincewa Yayi dan a cewarsa bayan abinda suka aikata mata baijin zai iya kuma had’a idanu Yazeed balle har ya yafe masa... Muhibbah tai rau rau da idanu tace “Please my King.. Kaje kaga d’anuwanka...!” A tsawa ce ya katseta da fad’in “He’s not my brother, we’re not even related... Not by blood not by anything.. So don’t you call him my brother again..!” Ya k’arashe yana sakin huci... Had’iye abinda ya tsaya mata a mak’oshi tai kana tace “You grew up together as brothers isn’t that enough...?!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Cikin tsananin huci yake ci gaba da dubanta, lokaci guda ya kamo arms d’inta ya shiga jijjigata, bai daina hucin ba yake furta “Are you serious Hibbah..? Do you really want me to go see that Criminal.. What for..? Tell me Muhibba kan mai Zanje na gansa..?!!” Yanda yake jijjigatan yana sakin huci kuka kurum take tana rintse idanunta, cikin zuban hawaye tai k’ok’arin bud’e muryarta tace “Because everyone deserve a second chance.. Yazeed ya tuba ya gane laifinsa.. Sannan idan zaka yafewa Fu’ad Maiyasa shi bazaka iya zuwa ka gansa ba koda bazaka yafe masa ba...!” Katseta yai cikin zafin nama da fad’in “You don’t know what you’re talking about, Fu’ad is also a victim here just like you, dan haka kar ki sake ambata mun sanan that imbecile a wajen nan..!” Cikin zuban hawaye take dubansa yanda yake sakin tsananin huci zuciyarsa naci gaba da tafarfasa, cikin murya irinta mai kuka take furta “Do you think this is easy for me..? Have you ever thought of how I must be feeling..?Kana tunanin ko sunayensu naji bana tuna ga abinda suka min ne..? Amma bazai yuwu muci gaba da rayuwa da grudges cikin zukatanmu ba.. I choose to let go and move on koda ace hakan zai matuk’ar wahala a gareni...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka... A hankali ya rungumota cikin jikinsa sai kuma ya soma lallashinta yanajin zuciyarsa na masa wani irin nauyi... Lokaci guda yake furta “It’s ok..! Don’t you ever think that way.. We are in this together kinji koh..!” Yaci gaba da shafa bayanta yana lallashinta Yanda ake ma babies idan suna kuka...Tai lamo cikin k’irjinsa tana kuka mai tsuma zuciya, haka ya k’ank’ameta yana jin zagin kukan nata har cikin k’ahon zuciyarsa ... Baida tabbacin idan zai Iya sake had’a idanu da d’aya cikin ukun Yazeed Giwa da Jamal.. Amma idan hakan zai kwantar da hankalin Muhibbah baida zab’i da ya wuce yaje asibti ya duba Yazeed... Washe gari Sarki Mahmood ya shirya tsaf ya nufi asibiti duba Yazeed tareda rakiyar k’annensa guda biyu Ja’afar da Fu’ad... Kwance Mahmood ya hango Yazeed saman gado cikin tsananin jinya wanda duk rashin imanin mutum dole ya tausaya masa... Daga nesa ya tsaya suna duban juna... Yazeed yai masa K’uri ganinsa da yayi cikin shiga irinta Mulki kambin rawanin masarautarsu bisa kansa, ga kuma Alkyabba da Sandar Mulkin Masarautar su... Abinda yaci burin mallaka kota halin k’ak’a sannan yayi duk yanda zaiyi yaga Mahmood bai samu ba yau Sai ga Mahmood d’in tsaye gabansa da Duka wad’annan abubuwan da yaci buri... Tabbas Mulki na Allah ne shi yake baima wanda yaso ya kuma hana wanda yaso a lokacinda yaga Dama... Cikin rawar murya Yazeed ke furta Yaya..!” Muryarsa ya sark’e .... Mahmood ya soma takowa cikin d’akin rik’eda sandarsa idanunsa akan Yazeed d’in yana mai tuno abubuwa da dama da suka faru.. Har saida ya iso gaban gadon Da Yazeed d’in ke kwance bisa.... * Wasu nurses ne suka shigo d’akinsu Giwa dan masu dressing.. Guda d’ayar sai toshe hanci take tana duban Giwa a yatsine take fad’in “Nifa wllhi bana son shigowa d’akin nan balle na tab’a mutanen nan, harga Allah wane irin d’oyi suke ga fuskar wannan matar tsoro yake ban kullum na ganta sai nayi mafarkin mummunan fuskarta.. Gaskiya bazan iya ba.. Ni zuwa ma zanyi naga Sarki.. Naji ance siren d’in nan da d’azu mukaji daga wajen asibiti Sarki ne yazo..!” D’ayar tace “No wonder ba’a shigo asibti da siren d’in ba aka kashe daga waje ai mun zaci ambulance ne.. Toh ina Sarkin yake..?” Guda d’ayar Ta basu amsa da fad’in “Yana ward 3 naji ance brother d’insa Yarima Yazeed yazo dubawa..!” Bata rufe baki ba Giwa dake kwance saman gado matashiyan Ta soma fad’in “Mahmood.! Mahmood yana asibtin nan..? Mahmood ni yazo dubawa.. Yazo d’aukana mu tafi..!” Daidai lokacin Fu’ad ya shigo d’akin idanunsa naga Giwa yanda takeda korirtoto tana ambaton sunan Mahmood... K’walla tab idanunsa ya soma takawa cikin d’akin... A haka har ya isa gaban gadon da Giwa Ke kwance bisa... Yai K’uri yana duban yanda fuskar nata ya sauya, halittarta gaba d’aya ta sauya... Fatar fuskar mele gaba d’aya, idanun baka ganin Farin Sai k’wayan bak’in kawai kake iya hangowa suma da k’yar aka bud’esu bayan anyi surgery d’aya yayi sama d’aya yayi k’asa.. Karan hancin babu sai alamun huji guda biyu wanda suma saida akayi surgery Allah ya taimaka aka bud’esu... Fatar bakinta kuwa gaba d’aya ya kwashe babu Sai hak’waran kawai kake hangowa a waje... Kanta ne kawai mai iya motsawa a jikinta... Sanda taji alamun tsayuwar mutum akanta Ta soma furta “Mahmood.. Sadauki nah.. Mahmood kaine...!” Ta k’arashe tana mai karkato a wuyanta wanda shi kad’ai take iya motsawa a gaba d’aya illahirin jikinta... Fu’ad Ta gani tsaye kanta hawaye na gangaro masa... Lokaci guda Giwa Ke furta “Kukan mai kake Fu’ad bayan burinka ya cika ka gayawa Mahmood gaskiya.. Duk kai ka soma jefa Mu a bala’in Da muka tsinci kanmu... D’aukeni ka kaini wajen Mahmood Ina son ganinsa.. Nasan munafukan Masarauta ne suka shiga tsakaninmu.. D’auken ka kaini Fu’ad..!” Ta k’arashe cikin daka tsawa hawaye basu daina zubowa daga cikin idanun Fu’ad ba... Jamal dake can basa b’angaren yana sauraron duk abinda ake fad’i Wai Mahmood cikin asibitin.. Mahmood shine yayi sanadiyan kasancewarsa kwance a nan cikin nakasa, tabbas idan har Mahmood na cikin asibitin duk yanda zai sai Sun had’u shima ya nakasa sa koma yayi ajalinsa gaba d’aya... Ya saki muguwar murmushin nan nasa da gefen bakinsa... ** Yazeed na kallon sama hawaye naci gaba da zubo masa yake fad’in “Na kasance d’ah maras ji a idon mahaifinmu dukda cewa ni ne nake kula da duk wasu al’amran sarauta na gidan... Abbah baya gani, ko da yaushe kaine a gabanshi, Kaida Fu’ad kune favorites d’insa dukda cewa kud’in baku kasance masu son gadon gidan ba... Baka hidiman da ni nake masa..But still ya zab’i ya fifitaka sama dani wanda banida buri da ya wuce na gajesa.. Maybe yanaji can k’asar zuciyarsa kaida Fu’ad ne kawai ‘ya’yansa shiyasa yafi baku duk wani kulawa da soyayyarsa, especially you...!” Ya kaikaito yana duban Mahmood d’in wanda shima shi yake duba... Lokaci guda Yazeed yaci gaba da fad’in “Banida burin da ya wuce na tozartaka a rayuwana, but Look at me now, babu sarautar babu asali babu dangantaka.. And what’s worse na kashe yarana da hannayena guda biyu..Kai kuma gaka nan da sarautar, yau Allah ya baka... Na yarda cewa Rayuwar nan gaba d’ayanta jarabawa ce.. Allah shike bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, fad’in rai da nuna d’agawa da isa ba ya kai mutum ga Komai face k’ask’anci.. Tabbas duk wanda yayi d’agawa ya nuna shi wani ne ya nuna yanada k’arfin Mulkin da zai taka kowa kafin ya bar duniya sai Allah ya nuna masa isharan cewa shid’in ba kowa bane kaman yanda ya k’ak’antar da Fir’auna ya nuna masa shi bai isa ba Allah shi kad’aine isasshe...!” Muryarsa ya soma rawa sosai sanda yake furta “ Your Highness a yau inaso na rok’eka gafara from the bottom of my heart Dan Allah ka yafe mun duk wasu abubuwa da nayi maka a baya... Sannan ka rok’ar min matarka itama Ta yafe mun... Dan Allah ku yafe mun ko naji sauk’in halinda nake ciki..!” Kuka ya hana Yazeed ci gaba da magana... Daidai lokacin Fu’ad dake tura Giwa saman wheelchair kanta a karkace gefe suka nufo d’akin Yazeed d’in.. Duk wanda yayi arba da Giwa sai yaji kaman ya ruga a guje sabida yanda fuskarta ta koma... Ja’afar da tawagan Dogaran Sarki Mahmood dake tsaye daga k’ofa tsaye sukai suna duban ikon Allah dan ko gane Giwa basuyi ba, sundaiga Fu’ad na turo dodanniya saman wheelchair... Saida ta soma korortoto kafin suka d’ago muryar Giwa.. Dogarai suka k’araso suna fad’in bazata shiga ciki ba Sarki na cikin d’akin.. Giwa taci gaba da ambato sunan Mahmood tana fad’in su barta ta shiga taga d’anta... Ja’afar ya tako gabanta yana k’are mata kallo.. Kafin yayi magana Fu’ad yace dashi “Please Ja’afar, nasan bata cancanta but please ka k’yaleta Ta ganshi just this once..!” Ya k’arashe cikin rawar murya... Tausayin Fu’ad d’in ya kama J’afar, duk shirin walak’ancin da yayi niyyan yi ma Giwa sai yaji bazai iya ba ko dan idon Fu’ad.. Duk abinda tayi she’s still his mother.. Sosai Fu’ad ya basa tausayi.. A hankali ya matsa gefe yai umarni ma dogaran su basu hanya su shige... Suna shigewa shika yabi bayansu ya shige cikin d’akin... Aiko Jamal dake biye dasu dafe da sandarsa sannan ya kuma dank’wafewa sabida k’unan wutan da yayi.. Aiko Dogaran nan suna bada hanya shima ya duk’a yana rarrafawa da hannayensa had’ida janyo sandarsa a hankali har ya samu ya shige cikin d’akin hannayensa rik’eda almak’ashi har guda uku wanda ake masa dressing dasu.. Dukda azaban zafin da yakeji amma sabida taurin zuciya bai fasa jan jiki har ya tsinta kansa cikin d’akin.. A yayinda hankulansu gaba d’aya yayi kan Giwa dake ambato sunan Sadauki kaman yanda take kiran Mahmood d’in, a daidai wannan lokaci Jamal yai k’ok’arin mik’ewa saman sandarsa Sai ciza labb’a yake sabida azaban da yakeji... Mahmood da idanunsa ke kan Giwa yana ganin halittar data koma Sam bai kula da Jamal ba wanda ya saita almak’ashin yana sakin huci zai cakkawa Mahmood a k’ahon zuciya... Daga nan yanda yake tsaye can bayansu dafe da sandarsa yake fad’i cikin zuciyarsa.. A yau zaka bak’unci lahira Mahmood.. Wannan karaga bazaka tabbata akai ba kaman yanda Ubana Tal’udu ya fad’i a yau zan gajesa zanyi ajalinka nayi ajalin Mulkinka.. Zan cikawa Mahaifiyata burinta sannan na tabbatar da kalaman mahaifina cewa Mulkinka Bazai k’argo ba....! Yana ida tunanin ya saita bakin almak’ashin masu tsananin tsini dai dai saitin k’ahon zuciyar Mahmood yai majajjawa ya jefasu a tare.... SameenaAleeyou 📚 [10/10, 7:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* _(MAY 2021)_ *88* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Yazeed da shi kad’ai ne yake iya hango Jamal da abinda yake k’ok’arin yi... Dan hankalin Mahmood gaba d’aya naga Giwa yayinda Fu’ad da Ja’afar suka bama Jamal d’in baya hakan yasa bazasu iya ganinsa ba...Wani irin k’arfi ne yazo ma Yazeed yai tsalle daga nan saman gadonsa ya isa ya hankad’a Mahmood gefe ya tare masa makamin da Jamal ya jefa masa ai kuwa take guda biyun suka cakki wuyansa suka huda, guda d’aya ya karjesa a k’irji amma babu Wai na wuyan sun huda masa wuya sun b’arka masa mak’ogoro, take ya zube a k’asa jini ya shiga fita daga bakinsa har hancinsa... Mahmood ya tallafosa ya fad’o saman hannunsa yana ambaton sunansa yayinda Giwa Ta k’walla wani irin k’ara tana ambaton sunan Yazeed itama... Ja’afar da Fu’ad a tare suka juya suna duban wanda yayi wannan aika aika wanda target d’insa Mahmood ne... Aiko Jamal yana ganin sun waigo ya shiga jada baya cikin sauri dafe da sandarsa..Mahmood ya shiga fad’I masu cikin tsananin tashin hankali su kira Dr, a d’ari Ja’afar yabi bayan Jamal da tuni ya fice bayan ya shime dogari guda da sandarsa sannan ya cakka ma guda d’aya scissors a wuya... Can Ja’afar ya hango Jamal yana k’ok’arin guduwa Ta k’ofar baya... Cikin wane irin doka kira yace dashi “Jamaaaal..!!” Aiko Jamal yana hango Ja’afar ya k’ara sauri, take Ja’afar ya nad’e hannun rigarsa yabi bayan Jamal a guje... Jakadiya wacce dama tana biye dasu a rakub’e saidai sanin batada ‘yancin shiga d’akin ya sanyata tsayawa daga waje tana ganin abindake faruwa Ta sami zarafin shigowa cikin d’akin itama... Aiko Giwa tana ganinta tace da ita maza ta fitar da ita taga Jamal d’inta kar su kamasa su kashesa... Jakadiya zatai magana Giwa ta katseta da fad’in ta fitar da ita taga Jamal d’inta kar wani abu ya samesa ba k’oshin lafiya bane dashi... Haka Jakadiya ta shiga turo Giwa suka nufo waje... Yazeed da jini ke zuba daga cikin jikinsa kwance yake saman cinyar Mahmood yana so yai magana amma babu hali... Cikin d’igan hawaye Mahmood Ke dubansa yana fad’in “Just hang in there Yazeed... Zaka samu lafiya in sha Allah, Fu’ad yaje kiran Likita yanzu zasu shigo su dubaka... Just stay with me kaji...!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin k’arfafawa Yazeed d’in gwiwa... Daidai lokacin Fu’ad da Dr suka shigo cikin tsananin sauri tare da wasu nurses biye dasu...Fu’ad ya isa ya dafa kan Yazeed yace “Brother zaka sami lafiya In sha Allah...!” Shidai Yazeed bai iya furta masu komai ba Sai dubansu da ido da yake... Sauri sauri Fu’ad ya fice dan ya cimmasu Jamal da Ja’afar.... Dr da nurses suka amshi Yazeed daga hannun Mahmood suna fad’in “We’d take it from here your Highness...!” A hankali Mahmood ya jinjina masu kai kana ya fito waje yana jiran su gama duba Yazeed d’in su fito masa da bayanai, Allah ya gani ko motsawa daga wajen bazai iya ba har Sai yaji a wani hali Yazeed yake... A can waje kuwa Jamal ya haye can k’ololuwar saman wani bene uncompleted building dake a nan cikin asibitin yana duban Ja’afar dake k’ok’arin cimmasa yana lek’a k’asa Dan babu wajen tsira wajen gudu ya k’are... Saidai yayi tsalle ya fad’o k’asa... Ja’afar ya d’anyi surrender hannayensa duka biyu a sama yake fad’in “Don’t Jamal.. Don’t jump, it’s over... Just turn yourself in...!!” Cikin huci Jamal ke fad’in “I rather die than na tsaya na tafi prison ko na zamto bawanka.. Gwara na kashe kaina da na zamto bawanka Ja’afar..!!!” Ja’afar ya jinjina kai a hankali yace “Please don’t Jamal, don’t kill yourself, just surrender now...!” Daidai lokacin Fu’ad ya k’araso saman benen, ya tsaya gefen Ja’afar shima yana duban Jamal dake yunk’urin fad’awa daga saman ginin... Fu’ad ya shiga girgiza kai yana k’ok’arin K’arasowa kusan Jamal d’in yake furta “Please Jamal, don’t, don’t think of doing that...!” Cikin zuban hawaye Jamal Ke dubansa yana fad’in “No Fu’ad... Babu sauran rayuwa a gareni, bazan tsaya na zamto Bawa a gidan dana girma cikinsa matsayin Yarima ba.. Bazan tsaya na kalli matar da nake matuk’ar son kasancewa da ita ta k’are da wancan Bawan ba..!” Ya k’arashe yana nuna Ja’afar lokaci guda yaci gaba da furta “Just take care of Maami please Fu’ad.. Duk abinda tayi tayisu ne sabida mu.. Nida kai da kuma Yazeed.. Bata da kowa sai kai Yanzu, dan Allah ka kula da ita kaji..!” Ya k’arashe cikin zuban hawaye... Fu’ad d’in ma cikin zuban hawaye yake furta “You can still choose to do what’s good Jamal, please don’t kaji..!” Ya k’arashe yana kuma matsowa a hankali yana so ya rik’o Jamal d’in ya hanasa fad’awa.. Sandarsa ya d’ago ya dafe gini kad’an yana nuna Fu’ad da sandar yake fad’in “Don’t come near me Fu’ad idan ba so kake mu fad’a tare ba.. Just stay right there.. Maami still needs you, take care of her kaji.. Tell her I love her, and I do everything for her...! Goodbye Fu’ad... Goodbye brother! Yana ida fad’i haka ya ci gaba da takawa da baya da baya har ya isa k’arshen ginin... Fu’ad ya nufosa a guje yana k’walla kiran sunansa inaaa tuni Jamal ya fad’a da baya... Suna jin sautin k’aran da ya saki alamun wani abu ya sokesa kafin ya k’arasa k’asa... Giwa da k’arasowarsu kenan Ta hangi wannan tashin hankali Jamal d’inta ne Rodin gini ya sokesa ya huda cikinsa... Ta saki wane irin k’ara mai tsananin gaske tana duban wannan tashin hankali... Fu’ad da Ja’far suka k’arasa cikin sauri yanda suka hango Jamal a k’asa k’arfen da ake ginin dashi ya hudasa... A tare sukai saurin rintse idanunsu had’ida dawowa da baya.. Ja’afar yai saurin rungume Fu’ad wanda tuni ya zama out of control sabida ganin wannan kayan tashin hankali da yayi... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Kowa farkonsa ya sani bai San k’arshensa ba.. Ya Allah ka bamu k’arshe mai kyau kasa muyi mutuwa mai kyau ..Ameen..! Yau ga bak’ar zuciya takai Jamal ga kashe kansa, hukuncin wanda ya kashe kansa kuwa babu shi babu rahamar Ubangiji domin ya mutu kafuri ne... A daidai gaban Giwa ya fad’o.. Babu abinda zata iya yi, ko motsawa ta isa garesa bazata iya ba sabida Jamal d’in ya riga ya nakasata da allurar da yaso nakasa Muhibbah dashi.. Haka Giwa tanaji tana gani taga d’anta mafi soyuwa a gareta wanda suke duk wani dirty works d’in tare kwance a k’asa cikin jini, yanda suka halak’a mutane da dama ba tareda wasu nasu sun Iya yin komai ba yau ga Jamal d’inta itama kwance gabanta kuma babu abinda zata iya akai... Rayuwa kenan ka shuka alkhairi domin ka girba mai kyau... A can cikin asibiti ma likitoci sunyi all they could amma da alama lokacin Yazeed ya riga yayi, Jamal yayi sanadiyan mutuwar Yazeed sannan shima ya kashe kansa... Mahmood ya buk’aci ya shiga yaga gawan Yazeed.. Yai tsaye saman kansa hawaye na gangaro masa.. Lokaci guda ya shiga tuno rayuwarsu na baya, sun kasance basa jituwa tsawon rayuwarsu yau sai gashi Yazeed d’in ya sadaukarda rayuwarsa gareshi, sai gashi ya zamto shine mutum na k’arshe da ya gana da Yazeed d’in kafin ya bar duniya.. Take wani irin kuka mai k’arfi yazowa Mahmood, ya kifa kansa gefen Yazeed d’in yana kuka sosai, lokaci guda yake furta “Allah ya yafe maka Yazeed.. Allah ya yafeka Brother..!” Ya k’arashe yana mai dafa tafin hannunsa saman goshin Yazeed... Hankula sun tashi sosai, kan kace mai labari ya isa masarauta.. Wannan kayan tashin hankali da yawa yake, yau babu Yazeed babu Jamal... Innalillahi wa Innalillahi raji’un.. Ya Allah ka bamu jarabawar da zamu iya ci... Idan Kaga Fu’ad dole ne ma ya baka tausayi saidai ko kusa Ja’afar bai bar side d’insa ba tun bayan da abun ya faru.. Kullum Ja’afar na taredashi yana kwantar masa da hankali... Yau kwanaki bakwai kenan da mutuwar Yazeed da kuma Jamal Fu’ad yai sallama ya shigo Babban Gwani... Ya risina ya gaida Mai Martaba... Mahmood yace dashi “Fu’ad an fito..?” Fu’ad ya jinjina masa kai a hankali yace “Eh Rankaidad’e na shirya, flight d’in k’arfe shabiyu na rana ne..” Sarki Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Da kyau..! Mun riga munyi magana da mutanenmu na can Spain d’in komai an gama shirya maka, da zaran ka isa zasu nemeka..” Fu’ad ya risina ya kuma yima Mai Martaba godiya kana ya k’arada “In sha Allah nayi maka alk’awari zan nastu na k’arasa karatuna... In sha Allah..” Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Masha Allah.. Ubangiji yayi jagora, I trust you Fu’ad..! Nasan zaka iya, and zamanka a can zaisa ka d’an mance wasu abubuwan.. I know there’s nothing we can tell you that will ease the pain you’re going through.. So the best solution shine kayi nesa da Masarautar nan na d’an wani lokaci...Just focuss on your studies kaji koh..!” Fu’ad ya jinjina kai a hankali yana amsawa lokaci guda ya k’arada “Dama inason alfarma Your Highness.. Inaso naje na duba Maami a asibiti kafin na wuce..!” Mahmood ya jinjina masa kai a hankali yace “Kafin driver ya wuce da kai airport sai ka tsaya kai mata sallama ko...” Ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Godiya nake Rankaidad’e..!” Ya nemi izinin tafiya.. Har ya mik’e ya soma tafiya Mahnood ya ambato sunansa, ya dawo da baya kad’an... “You take care and study hard..!” Mahmood ya fad’i yana duban Fu’ad d’in... A hankali Fu’ad ya saki murmushi had’ida jinjina kai... Lokaci guda yasa kai ya fice fadawa na masa fatan alkhairi.. Mahmood kaw yabi bayansa da kallo har ya b’ace masa zuciyarsa cikeda k’aunan d’anuwan nasa.. Iyakacin gatan da zai masa kenan ya fitar dashi daga wannan environment for the mean time... Fu’ad yana fita ya tadda Ja’afar na jiransa, suka sakar ma juna murmushi suka nufi Mota a tare, Zahra da Umaima dake tsaye daga can saman bene suna hangensu.. Zahra taci gaba da fad’in “He’s my favorite you know.. I feel sorry for him... Ace ga halinda mahaifiyarka ke ciki ‘yanuwanka babu ko guda d’aya.. Jamal ya kashe Yazeed ya kuma kashe kansa wannan tashin hankali da yawa take gwara yayi nesa da wajen nan hakan sai yafi masa sauk’i fiyeda zamansa a nan.. Koda kuwa muna son kasancewarsa a nan tareda mu..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Umaima Ta jinjina kai a hankali idanunta naga su Fu’ad d’in take furta “Yeah.. Zaifi kyau yayi nesa da wannan Masarautar na d’an wani lokaci..!” Daidai lokacin kaman ance Fu’ad ya d’aga kai sama... Ya hangosu tsaye suna dubansa hawaye saman fuskar Zahra... Ya murmusa kad’an had’ida Girgiza mata kai alamun banda kuka, lokaci guda ya d’aga mata babban yatsa cikin salon da suke ma juna.. Ta saki murmushi mai bayyana hak’wara itama tai masa irin yanda yai mata... Umaima da Ja’afar suka murmusa suma kafin Fu’ad yai masu waving suma sukai masa suna masu sakin murmushi had’ida masa fatan alkhairi har suka nufi yanda aka paka hamshak’iyar SUV d’in driver na jiran isowarsu... Dogarai suka bud’e masu motan Ja’afar da Fu’ad suka shige tare Dan har airport Ja’afar d’in yai masa rakiya... Kafin su k’arasa airport d’in saida suka biya yai sallama da Giwa dake asibti tana ci gaba da jinya... Abubuwa goma da ishirin sun taru sun mata yawa Ta wayi gari yau babu kowa nata a tareda ita.. Babu Yazeed babu ‘ya’yan Yazeed sannan babu Jamal ga Fu’ad ma ya tafi nisan duniya wanda bata San ko su sake had’uwa ko ba su sake had’uwa ba... Giwa Ta koma bata kowa bata da komai daga ita sai ko Jakadiya wacce itama a halin yanzu Ta kanta take ba Ta Giwa ba.. Koda aka sallamesu a asibti Basu San yanda zasuje ba Dan basu san yaya zasu kwashe da ahalin Masarauta ba... Ta yaya ma zasu soma shiga cikin Masarautar..? Da wasu idanu zasu dubi ahalin wannan gidan wad’anda suka masu bak’in zalunci a baya... Jakadiya taja Ta tsaya tana haki Dan harga Allah ta gaji da tura Giwa saman wheelchair.. Lokaci guda take furta “Ke Izzatu nifa ba baiwarki bace ki barni najida ciwon jiki dake damuna wanda kece kika jaza min.. Kowa ta kama gabansa cikinmu Dan Allah ya gani bazan iya d’awainiyar Ki ba ehe..!” Giwa na hawaye take furta “Jakadiya ni ce fah Giwa..!” A wulak’ance Jakadiya Ta dubeta kana Ta shek’e da wata irin muguwar dariya tace “Giwa a ina.. Giwa ko b’arauniya.. Kin dai sace sunan asalin Giwa kin rad’a ma kanki.. Nida Ke babu maraba.. Ke har gwara ni na rik’i matsayin Jakadiyar Sarki Ke kuwa Baiwa ce tukuf wacce a cikin bayin ma ina tsamman ke Bakida cikakken asali.. A nan zan barki kema kiyita kanki.. Ai na gama miki mai wuyan tunda na fito dake nan..!” Giwa na hawaye taci gaba da fad’in “Yanzu idan kika barni a nan naje Ina Jakadiya..? Kema babu yanda zakije Don bakida wajen zuwa, kina tunanin Idan kin koma masarauta zasu karb’eki ne.. Jakadiya bamuda Kowa sai mu biyun... Gwara mu taimaki juna..!” Jikin Jakadiya yayi sanyi Dan gaskiya Giwa Ta fad’i basuda kowa sai su biyun.. Lokci guda Jakadiya tace “Toh Ina kike so muje Izzatu.. Tinda dai masarauta yafi k’arfin shigarmu yanzu...” Giwa tace “Haka zamu sad’ad’a mu shiga ta k’ofar bayi mu samu wani waje mu fake tunda duk duniyar nan babu yanda zamuje da ya shige Fadah..” Jakadiya tai shiru sai kuma ta jinjina kai tace “Haka ne Izzatu bamuda wajen zuwa da ya wuce masarauta a yanda kike d’in nan idan na shiga gari dake gudu za’ai gashi ni kaina ba wai lafiya bane ya isheni Tabbas mafaka muke nema a halin yanzu..” Giwa tace “Naji dad’i da kika fahimci haka, yanzu mu San yanda zamuyi mu shige cikin Masarauta koda da dabara ne..” Jakadiya tace “Hakan bazai yuwu ba sai cikin dare lokacin k’afa ya d’auke tinda ta k’ofar Bayi zamu samu mu shige...” Suka tsaida shawari akan cikin dare zasu saci k’afa su shige Masarauta.. Hakan ce ta kasance... Suka saci k’afa suka bi Ta k’ofan Bayi abinka da wanda suka San kan gidan... A wani tsukin d’aki da ya gama rub’ewa ciki babu komai a nan suka samu suka yada zango.. Babu komai cikin d’akin sai wata mutacciyar tabarma.. Haka Jakadiya ta watsar da Giwa saman tabarman... Kafin safiya Giwa ta gama b’ata wajen da k’azanta.. Wanda hakan yasa Jakadiya tashi tana fad’in gaskiya bazata iya rayuwa Inuwa guda da Giwa ba Allah ya gani bazata iya mata jinya ba.. Saidai Ta rub’e a wajen... Giwa na kiran Jakadiya ko sauraronta Jakadiya batayi.. Saidai Jakadiyar na ficewa taga gungun Bayi suna fad’in saidai ta koma cikin d’akin ta fito da Giwa su shige su bar cikin Masarautar dan basu buk’atan annoba taredasu kokuma su had’asu gaba d’aya itada Giwan su cinna masu wuta su ida k’onewa.. Haka babu yanda Jakadiya ta iya ta shiga ta zuba Giwa saman wheelchair d’inta daga ita har k’azantarta, ga wani irin d’oyi da takeyi.. Jakadiya sai toshe hanci take ta fito da Giwa.. Aiko nan gungun Bayin nan suka shiga toshe hanci masu gudun gananin yanda halittar Giwa ya koma nayi... Take yaransu suka shiga jifanta suna kiranta dodanniya... Kan kace mai Bayi sun cika dam a wajen ana kallon abin Al’ajabi yanda Giwa Ta koma.. Muhibbah da Umaima harma da Zahra suna zaune gefen Gimbiya Turai a Fadarta tana basu labarin masarautarsu da d’an uwanta mahaifinsu Sabuwar Jakadiya tai sallama Ta risina ta kwashi gaisuwa.. Yanayinta kad’ai ya tabbatar masu babu lafiya.. Gimbiya Turai tace “Lafiya Jakadiya..? Meke tafe dake..?!” Gaba d’aya su Muhibbah suka zuba mata idanu suna duban yanda take a birkice gaba d’aya.. Lokaci guda Jakadiya Ke fad’in “Allah shi taimakeki cikin Masarauta ne babu lafia...!” Su Umaima suka dubi juna cikeda mamaki, rabonsu da ace cikin Masarauta babu lafiya tun bayan ficewarsu Giwa a Masarautar.. Gimbiya Turai tace “Ina saurarenki Jakadiya.. Meke faruwa cikin masarauta..?!” Jakadiya tace “Allah shi taimakeki Tsohuwar Jakadiya mai murabus tareda Baiwa Izzatu sune a cikin Masarautar nan, gashi can gungun bayi sai jifansu suke dasu da yaransu..!” A tare Su Umaima suka mik’e da jin wannan batu.. Giwa a cikin Masarauta..? Gimbiya Turai taceda Jakadiya ta tsaya su tafi tare.. Jakadiya ta jinjina kai har Gimbiya ta mik’e ta kintsa, su Muhibbah ma suka rufa Alkyabbarsu kana suka nufo bayan Gimbiya Jakadiya na masu jagoranci har suka iso yanda Giwa da tsohuwar Jakadiya suke a wulak’ance sai jifansu yaran Bayi suke suna fad’in basa son dodanniya su fice masu.. Gimbiya Turai tai tsaye tana duban Giwa yayinda Giwar ma ta zuba masu idanu gaba d’ayansu yanda suka jeru gaba gareta cikin shiga irinta masu Mulki.. Ga Gimbiya Turai ga kuma ‘ya’yan Yarima Alfah Muhibbah, Umaima da kuma Zahra..! Mutanen dataso ganinsu a k’ask’ance a wulak’ance, mutanen dataso d’aid’aita rayuwarsu da k’arfin gaske.. Mutane data sace komai daga garesu ta azurta kanta dashi yau gasu nan sun tsaya gabanta bayan duk k’ok’arin da tayi Dan Ta kawar dasu a doron k’asa Ta kafa mulkinta da nata zuri’ar Allah bai nufa ba... Yau ga Turai itace Allah ya nufi nata zuri’ar da samun duka wad’annan abun... Sabuwar Jakadiya tai tsawa ma yaran ta hanasu abinda suke.. Aiko illahirin bayin suna ganin su Gimbiya Turai da kuma matar mai Martaba Gimbiya Muhibbah take suka risina waje yai tsit saima k’ok’arin kwasan gaisuwa da suke.. Gimbiya Turai ta soma takowa gaba ga Giwa tana kallon yanda Allah ya maida Giwa cikin lokaci k’ank’ani.. Izzatu ta zama k’ask’antacciya abun wulak’antawa abun gudu, abin tsoro... Giwa na hawaye take duban Gimbiya Turai.. Lokaci guda ta lumshe idanunta tana furta “Ya Shugabata..! Kimin aikin Gafara, nasan na zalunceki kuma ban cancanci neman afuwa daga gareki ba... Na zalunci kaina kin sakani a inuwa na fitar dake rana.. Kin cireni daga cikin k’angin Bauta kika bani ‘yanci amma na miki butulci.. Kin bani komai naki sarautar Ki harmada abinda yafi soyuwa a gareki Wato mijinki amma na zab’i naci amanarki na rufe idanu sabida son zuciya na miki butulci mafi muni...!” Cikin rawar murya Giwa taci gaba da fad’in “Nasan ban canci yafiyarki ba.. Amma Rankidad’e dukda haka zan nemi yafiyarki ya Shugabata..!” Muryar Muhibbah ne ya katseta yanda take takowa gaba Gareta tana furta “Sabida kinsan tanada zuciya mai kyau zata yafe miki Ko ince ta riga ta yafeki tuntuni shiyasa kika sami k’warin gwiwar rok’onta gafara.. Shin idan ita ta yafeki ina Allahan mutanen da kika zalunta Giwa..? Shin mahaifinta Sarki Jamaluddeen da kika rabasa da raywuwarsa shi ya yafeki..? Kokuma ‘ya’yanta da kika rabasu da mahaifiyarsu sun yafeki..? Kika kashe matar Mahmood bayan kin datse mahaifarta Dan kar ya samu magaji sannan kika maida Ja’afar Bawa a gidan Mahaifinsa.... Kin mance da d’an uwanta Yarima Alfah wanda kika halak’asa kika kuma tarwatsa ahalinsa... Matar da kika maidata baiwa mahaukaciya a cikin gidan mijinta kika azurta kanki da Martabarta kika toshe duk wani hanya na kwanciyar hankali cikin rayuwarta, daga k’arshe kika kashe mijin nata kika hana ta masa takaba yanda ya kamata wannan matar kike neman yafiya da afuwa daga gareta..? Ki fad’a min Izzatu wannan matar ce kike rok’onta Ta tafe miki..!!” Muhibbah ta k’arashe cikin d’aga murya hawaye na gangaro mata, illahirin mutanen dake wajen hawaye na gangaro masu.. Lokaci guda Muhibbah taci gaba da girgiza kai tana furta “Saidai ita din tanada zuciya mai kyau na tabbata bazataso ganinki a yanayi Da kike ciki ba... Zataso Ki samu sassauci dukda tulin abubuwan nan da kika mata..!” Giwa na hawaye take furta Saudatu..!!” Muhibbah Ta jinjina kai tace “K’warai ni ce nan SAUDATU wacce kika k’udiri niyyan cika Mulkinki da ita kuma nice nan MUHIBBAH wacce Ta miki alk’awari zata kawo k’arshen Mulkin ki da zaluncinki da taimakon Allah.. Yau gashi na cika miki alk’awarinki GIWA...Na fad’a miki dama zaki koma sharan cikin Masarautar nan Sai ya fiki daraja, zaki kasance cikin k’ask’anci da tozarci yau gashi nan duk sun tabbata akanki... Ki sani Allah baya barin zalunci ya tabbata...!!!” Ta k’arashe hawaye na gangarowa daga idanunta... Daidai nan Gimbiya Turai Ta k’araso ta rungumeta su duka biyun suna hawaye kana Gimbiya ta bud’e murya tace “Duk abinda zan fad’i d’iyata ta riga ta fad’i maki Izzatu.. Bayan tulin abubuwan da kika mana zan barki ki k’arasa jinyarki cikin Masarautar nan dan iyakacin abinda zan iya miki kenan dan nasan bakida wani wajen zuwan da yafi nan..!” Ta kuma duban tsohuwar Jakadiya da kanta Ke kife k’asa tana matsan hawaye itama kana tace “Ke kuma Jakadiya bayan cin amanan Masarauta da kikayi hukuncin ki daga Masarauta shine kiyita kula da ita har k’arshen rayuwarta tinda tare kuka jima kuma sak’awa kuna k’ullawa... Ubangiji ya sassauta miki Izzatu...!!” Giwa ta shiga godiya tana hawaye Jakadiya ma na hawaye tana godiyan dole dan Allah ya gani kukan hukuncin kulada Giwa da aka yanke mata kawai take, kashi futsari cin abincin Giwa da komai ya dawo hannunta... Kafin su baro wajen Gimbiya Turai ta tsawatar ma Bayin da yaransu akan wulak’anta mutum, a cewarta duk cikin masarauatr babu wanda yake abun wulak’antawa daga masu Mulki har b’angaren Bayi.. Masarauta bazata lamunci mummunan d’abi’a ba.. Kowa yanada ‘yancin rayuwa mai kyau a matsayinsa na d’an adam cikin Masarautar... Wannan jawabi nata sosai ya kuma yin dad’i ma ahalin Masarautar gaba d’aya... Rayuwar masarautar ta kuma sauyawa kowa daraja kowa yake da mutuntawa babu wulak’anci babu tozarta kowa... Giwa da Jakadiya suna can b’angaren su suna jinya dukda cewa wasu lokutan Jakadiya bata iya jurewa.. Sosai Jakadiya tayi nadaman rayuwar data tsinci kanta ciki, da ace batabi son zuciya ba da yanzu tana nan cikin Masarauta a matsayinta na Jakadiya gashi yanzu ta dawo b’angaren k’anan bayi wanda ko matsayin shiga sashen masu mulki basu dashi... Bayan faruwan haka da kaman sati biyu Jakadiya ta farka daga bacci cikin dare taga wani irin k’atoton bak’in kumurcin maciji ya kanannad’e Giwa ga wasu irin kukiyoyi munanan sai yagan naman jikinta suke... Giwan tana sakin wane irin k’ara na azaba... Ai da rarrafe Giwa ta fice daga d’akin tana neman d’auki.. Saidai tana ficewa k’ofar ya rufe da Giwa... Akayi akayi a bud’e tun cikin daren k’ofa Ta kasa bud’uwa.. Tun ana sauraro gurnananin ihun Giwa har dai aka daina saurarowa, wajen yai tsit alamun ran Giwa yayi halinsa...! Allahu Akbar kabiran... Yau babu Giwa, Duk Mulkin data baza a doron k’asa yau Ta tafi a wulak’ance..... Rayuwa kenan, yau kaine gobe ba kai ba... Haka da k’yar aka b’alla k’ofar aka fitar gawan Giwa wanda banda d’oyi baya komai... Da k’yar daga cikin tsirarru suka fitar da ita daga cikin Masarautar ko ina suka nufa da ita sai Allah ko Sun mata sallah ko basu mata ba Allah kad’ai ya Sani dan labarin mutuwar Giwa bai isa cikin Fadah ba saida gari ya waye sosai... Dukda abubuwan da Giwa tayi wanda hankula suka gaza d’auka hakan bai hana ahalin Masarautar tausaya ma irin mutuwar da tayi ba.. Da k’yar aka sanar da Fu’ad dake can k’asar Spain.. Ya nuna damuwarsa da tausayin yanda mahaifiyarsa ta k’are dama yasan akwai rana irin wannan da zaizo tunda Giwa dai babu wani abu na alkhairi data shuka a rayuwarta sai akasin alkhairi.. Ta kashe rayuka da dama ta cutar da dama sannan uwa uba laifin Shirka da take wanda Allah na yafe ko wani irin laifi da rahamar sa idan yaso matuk’a baka mutu kana shirka ba... Mutuwar Giwa ya zamto wa’azi Babba ga d’aukacin Al’umman cikin wannan Masarauta harmada wad’anda labarinta ya cimmasu... Kaman anyi ruwa an d’auke yau babu Giwa da ahalinta da duk wani Mulkin zalunci datayi a Masarautar... Bayan wasu kwanaki da faruwan wannan al’amari Ja’afar da Ubandoma suka fito da Waziri, ya koma kaman bashi ba duk ya jeme ya zama abin tausayi, suka gurfanar dashi gaban Mai Martaba.. Mahmood yace yaci Albarkacin Yazeed, Masarauta tai masa rangwame yajesa an tub’esa daga sarautar Waziri sannan bazai sake tako k’afarsa cikin Masarauta ba har abada..Waziri yana kuka yana godiya haka ya fice daga Fadah babu rawani... ** Kwanaki sun tafi, satuttuka sun shud’e har an soma k’irga watanni... Tsaye take gaban k’atoton madubin d’akin nata tana d’aura d’ankwali.. Kallo guda zakai mata ka fahimci hutu da kwanciyan hankali sun Zauna a wajen.. Ta k’ara cika da kyau ga wani annuri na musamman daya cika fuskarta... Zahra ce ta shigo da sallama tana fad’in “Your Highness Mommy unborn Ke kad’ai ake jira a rufawa Amarya Alkyabbarta.. Ummi tace babbar Ya Uwa baza’a rufawa Aunty Umaima Alkyabba ba sai kina nan...!” Muhibbah Ta murmusa a hankali tace “Aiko Ummi tayi gaskiya dan ko an rufa alkybbbar nan sai an yaye na sake rufa ma ‘yaruwata...!” A tare suka murmusa kana Muhibbah takai dubanta ga cikinta mai kimanin watanni biyar wanda har ya fito waje kaman wani cikin wata bakwai... Zahra Ta d’anyi gyaran murya tace “You know I can’t wait Baby na ya fito duniya zanfi sonsa fiye da kowa.. Coz I’d be his or her Godmother..! Muhibbah ta d’an ja hancinta kad’an tace “Toh Sarkin ‘yan surutu zaki shige muje ne ko kuwa..!” Zahra na murmushi tace “Tia..!” Muhibbah Ta dubeta tace “Yes princess..” D’an kwantowa jikinta tai kad’an tace “I love you..” Murmushi saman fuskarsa Muhibbah ta rungume ‘yar uwar tata had’ida furta “I love you too Baby..!” Suka kuma sakar ma juna murmushi kafin suka nufo downstairs yanda Hadimansu Ke jiransu... Ansha Bikin Yarima Ja’afar da Gimbiya Umaima lafiya.. Amarya da ango sun tare a b’angaren su wanda Sarki ya k’awata masu shi da kayan alatu.. Saidai Fu’ad bai samu yazo ba dan jarabawa suke.. Zahra ce taita nuna masa Bikin Ta hanyar tura masa pictures wasu lokutan kuma Sai ya kirata suyi video call tana had’asa da mutane ‘yan biki su gaisa... A haka akaci biki lafia aka tashi.. Rayuwa tayi dad’i Ta ko wanne b’angare sai son Barka... Amarya Umaima da angonta Ja’afar sun bud’e Sabon shafin soyayya na rayuwarsu... Zahra ma ta maida hankalinta sosai ga karatunta... A haka Muhibbah Ta isa watan haihuwarta yanda Ta haifo d’anta namiji kyakkyawa mai kama sak da mahaifinsa.. Kaman Kakin Mahmood.. Allahu Akbar Zo kaga murna wajen Mahmood Dama d’aukacin mutanen cikin wannan masarauta.. Babu ya Gimbiya Turai wacce bayan tsawon shekarun nan yau Allah ya nuna mata gudan jinin Mahmood d’inta.. Allahu Akbar lallai mai rai kar ya zamto mai cire tsammani ga Rahamar Ubangijinsa...Bayan Giwa tayi duk yanda zatai ganin cewa Mahmood bai samu Magaji ba yau Sai gashi Allah ya azurtasa da Magaji.. Yai tsaye yana dubanta yanda take bacci hankali kwance ga Baby a gefenta. A hankali ya k’arasa ya duk’a gaban gadon.. Yai mata K’uri yana duban fuskarta da yai fayau dashi.. A hankali ya sumbaci goshinta yana mai duban fuskarta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.. A hankali take bud’e idanunta har ta sauk’esu saman kyakkyawan fuskarsa.. Suka sakar ma juna murmushi, lokaci guda yakai hannunsa guda yana shafa fuskarta, a hankali yake furta “How are you feeling my Queen..?!” Hannunsa Ta sakale cikin nata had’ida sumbatar hannun nasa tace “Good.. I’m feeling Good my King.!” Murmushi bai bar saman guskokinsu ba suke ci gaba da duban juna cikeda so da k’auna.. Mahmood ya zauna gefenta kad’an kana yasa hannu ya d’auki jaririn dake kwance gefenta Sai wutsil wutsil yake alamun ya tashi bacci.. Ya sumbaci yaron a goshi yana mai lumshe idanunsa.. Muhibbah tai masu K’uri tana godiya wa mahaliccinta da ya lullub’eta da wannan rahama bayan iftila’in rayuwa data fuskanta kala kala wanda bata tab’a tsammanin rayuwa zata sauya mata irin haka ba.. Ya shiga jijjiga yaron daketa k’ok’arin tsala kuka yana lallashinsa yake furta “C’mon Champ, Paapa is here.. Are you hungry..? Or do you wanna go horse riding my prince .. Shiii is okay, Maama is still weak ka barta Ta huta kaji koh..!” Ya k’arashe yana mai jijjiga yaron a kafad’arsa.. Sosai ya birge Muhibbah tai masu K’uri tana dubansu murmushi saman fuskarta.. A haka Mahmood yaita jijjiga yaron har ya koma bacci... Ya d’ago yana duban Muhibbah da tai masu K’uri ya d’an kashe mata idanu guda yace “You can go back to sleep now shima yayi bacci..!” Murmusawa tai kad’an tace “I never knew Sarki ya iya raino haka..” Kusan kunnenta ya matso kaman mai rad’a yace da ita “Ni kuma yanzu waye zai raine ni tunda sun rufeki a nan..Inaga dai k’arshe zan karb’i tayin da aketa min daga garuruwa daban daban ne..!” Ai bai kai aya ba tai kicin kicin da fuska kaman mai shirin kurma ihu tace “Your Highness Ummi fah zata iya shigowa yanzu kawai ka tashi kaje.. ai dama nasan ku sarakuna baku iya zama da mace guda.. So nasan wataran zakayi ai ko an maka tayi ko ba’a maka ba..” Ta k’arashe fuska a tamke kaman ba ita ba.. Ya d’an murmusa kad’an yace “Allah huci ran Gimbiya Giwar Amale...Duk suyi zamansu I don’t need to do what other Kings are doing, To me you’re more than enough my Queen..!” Ya k’arashe idanunsa cikin nata.. Ta murmusa kad’an cikeda kunya.. Shima murmushin yai yace “Wai dama haka kikeda kishi ne..?” Murmushin ta kuma yi tana mai sanne kanta... Ya ajiye Jaririn gefenta kad’an yana mai dubansu su duka biyu.. Lokaci guda Muhibbah tace “Wanne suna zaka saka masa have you thought of the name..?” K’uri yai mata ya kuma duban yaron kana yace “You choose the name.. Duk wanda kike so..!” Tai murmushi a hankali kana tace “Mahmood..! Mahmood (Hamdaan)..!” Yai mata k’uri yana dubanta kana yace “Yarima Mahmood Hamdaan ibn Mahmood..! Wow what a beautiful name.. Na gode da aka min Takwara..!” Ta matso kusansa a hankali ta saka hannunta cikin nasa lokaci guda take furta “Ka cancanci fiyeda haka my King.. Ka haskaka min rayuwata a lokacinda nayi zaton babu wani haske da zai kuma bayyana cikin rayuwata.. Ka dawo min da Farin cikin dana rasa a rayuwata ko ince Wanda banyi zaton zan samu ba bayan iftila’in da ya auka min.. You’re not just my king Your Highness..! You’re my world..!” Murmushi saman fuskarsa ya sumbaci goshinta zuwa labb’anta.. Lokaci guda yake furta “Manzon Allah S.A.W yana cewa _Aldunya mata’un.. Duniya jin dad’i ne.. Wa khairu mata’uddunya.. Mafi alkhairin jin dad’in duniya Almar’atussaliha.. Itace mace Ta k’warai.._ Ni nayi dace da samun mafi alkhairin jin dad’I na duniya wacce nake fatan har a aljannah ta zamto wannan jin dad’in nawa.. I love you so much My Queen..!” Ya k’arashe yana mai rungumeta had’ida lumshe idanu.. Su duka biyu suka jima cikin jikin juna kaman kar su rabu da juna har saida suka soma sinkayo kukan Yarima Hamdaan kafin Mahmood ya sassauta rik’on da yai mata.. Ya d’auki yaron ya mik’a mata, Ta shiga bama yaron abincinsa Mahmood na tayata cikeda nuna kulawa da k’auna.. Ranan juma’a akayi shagulgulan rad’in sunan Yarima Mahmood Hamdaan.. Akayi wasan Dawakai a Fadah aka buga Tambura aka busa algaita.. Kowa na son barka da Yarima da mahaifiyarsa yanda suka amshi kyauttuka kama daga kan Mai Martaba har izuwa sauran ahalin gidan.. Suna yayi albarka an cika sosai su Mommy dasu Gudidi duk sunzo harmada matar Ansar wacce itama nata cikin ya d’an soma fitowa dashike tafiyar ba wani mai tsawo bane kuma da lafiyarta shiyasa Mommy Ta amince suka taho gaba d’aya... Harta Raheemah ma tazo suna daga can masarautarsu... Kaman yanda yake a tsarin gidan daren Jumma’an aka had’a hamshak’in Royal Gathering, kowa yai shiga Ta alfarma harta da jariri Yarima Hamdaan shima ba’a barsa a baya ba.. Yana rungume hannun Kakarsa Gimbiya Turai.. Muhibbah tai tsaye daga can saman benen Mahmood tana hango yanda aka hallara gaba d’aya Masarautar.. Hasken wuta ya gauraye ko ina tamkar rana.. Ta lumshe idanunta tana godiya wa mahaliccinta da wannan baiwa da ya lullub’esu dashi.. A hankali taji alamun Rankaidad’e Ta bayanta yanda ya rungumota had’ida d’aura hab’arsa kad’an saman kafad’arta.. Su duka biyun sukai k’uri suna kallon yanda Ahalinsu ya cika da albarka.. Zahra tana video call da Fu’ad tana nuna masa Prince Hamdaan, Fu’ad sai wasa ma yaron yake ta cikin waya kaman yana ganinsa, Umaima da Ja’afar wasu love birds d’in suna daga gefe suna zuba nasu love d’in... Allah ya raya Yarima Hamdaan..! Mahmood ya kuma matseta cikin jikinsa yana shak’an k’amshinta mai sanyaya zuciya.. Murmushi kwance saman kyakkyawan fuskarta take ci gaba da duban illahirin fad’in Masarautar, a hankali Ta furta “Hamdaan katheeran Ya Rabb..!” Nima a nan na tayata da furta ALHAMDULILLAH..! *A nan na kawo k’arshen wannan littafi nawa mai taken MUHIBBAH.. Ina rok’on Allah ya yafe min kurakuren dake ciki, fad’akarwan dake ciki Ubangiji ya amfanemu dashi baki d’aya..Ameen..!* *Bazan iya ajiye alk’alamina ba tareda na mik’a godiyata da jinjinata a gareku ba d’imbin masoyana.. Hak’ik’a kun nuna min k’auna dani da wannan labari nawa mai taken Muhibbah.. Idan babu ku babu Muhibbah...A duk yanda kuke a fad’in Duniyar nan ina k’aunarku nima.. Ubangiji ya bar k’auna...* *Sameena Ke maku Fatan Alkhairi...* SameenaAleeyou📚