An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Mugun albishir . Page 1 Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . Na dade ina ganin kyawawan 'yan mata a duniya. Wadanda ke da kyawawan halittu da Kuma kyawawan fuskoki da kowa zai gani ya yaba ya yi sha'awarsu. Sau da yawa irin wadannan taurarin 'yan mata wasu da zarar mun rabu bana sake tuna su a xuciyata, sai ka ce tun fil'azal ban ta6a ganin su ba. Wadansu Kuma a cikinsu jefi-jefi su kan fado mani a rai, da zarar na tuno da kamanninsu sai in yi murmushi ni kadai in sake mancewa dasu. To amma Kuma duk da haka Akwai wata fitacciyar taurarruwa guda daya, wacce duk lkcn da na dubi xuciyata sai naci karo da hotonta dake maqale a ruhina shekara da shekaru. . Sunan ta zubaida! . Ba zan ta6a mance ranar da na fara ganin ta ba. A ranar wata litinin ne wacce ta xo dai-dai da goma sha hudu ga watan takwas alif dari tara da casa'in da tara miladiyya. Ita ce rana ta farko da na fara karatu a kwalejin ilimi ta tarayya dake a birnin zaria. . Ina zaune ni kadai a gefe guda akan doguwar barandar ajin da zamu dauki darasi, ina sanya da farin Wando da Kuma farar riqa mai ruwan qwai dake da jajayen rubutu sirara a gabanta. Sauran dalibai kowa yana ta harkar da ta dame shi. Ana ta kaiwa da komowa da kuma surutai da kuma if-iden matasa 'yan bana bakwai sabbin dalibai. . Kamar daga sama, sai na dago kai na hangeta, tana tahowa kai tsaye xuwa gare ni. Tana sanye da shudin leshi da Kuma baqin takalmi. Ta rungumo takardun karatunta a cikin fayil, sannan Kuma ta maqalo baqar jakarta kalar takalminta. . Zubaida kyakkyawace! . Kada ka zargeni don nayi mata wannan kirarin tun a karon farko. Don kuwa rude wa nayi tun a gani na farko da nayi mata. A rayuwata koda ace bani da qwarewa akan komai, to akwai wani abu daya da na tabbattar na qware akan sa. duk lkcn da na ga kyakkyawr mace ko daga nesa ne, na san a layin da zan ajiyeta, don kuwa na dade ina ganin su. Don haka Zubaida kyakkyawa ce fiye da duk yadda zan kwatanta maka ita a cikin wannan labarin. . Ku biyo ni. jimawa kadanmugun albishir . Page 2 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . Zubaida kyakkyawa ce fiye da yadda duk zan misalta maku ita a cikin wannan labari. . Akwai wani yanayi dake tattare da ita, Wanda ke sa mutane su kasa tantance doguwa ce ko Kuma gajeruwa ce? Sannan Kuma yanayin dake tattare da kyakkyawar fuskar mai annuri irin sa ne yanayin da duk lkcn da wani Sauran ya kalleta sai yaga kamar murmushi take yi masa, Wanda na tabbatar hakan ya sha tilastawa daruruwan samari fadawa a cikin kogin qaunarta kamar dai yadda nima na fada tun a karon farko. . Na ci gaba da kallon ta lkcn da take tahowa sannu a hankali kamar wata dawisu. Ba ni kadai ba hatta Sauran daliban dake a wajen kama daga 'yanmata har samari yawanci ynx duk hankalinsu a kanta yake, kowa yana so yaga a inda zata yada zango. To amma Kuma abin mamakin ga alama har ynx wurin nawa take tahowa. 'na shiga uku!' . Shin damar can ta ta6a gani na ne? Na ji gabana ya fadi. sannan Kuma tsoro ya kama ni. Ban yi mamaki ba don kuwa ta haka nake gane mace kyakkyawa a cikin mata masu al-alfahari da xunxurutun kyau. Da ace ban ji tsoro ba a lkcn da na fara ganin ta, da tun farko ban saka maka ita a cikin layin kyawawa ba, don kuwa ba don ta tafi da hankalina ba da wannan fuska tata mai annuri da duk abubuwan da zasu faru basu faru ba. . Ta qariso inda nake ina ta kallon ta ko qiftawa bani yi, ina ta mamakin wannan mace mai qyalqyali kamar tauraruwa sai ka ce ita ta qera kanta a duniya. . Ta zauna a kusa da ni muka hada ido, muka yiwa juna murmushi, tuni qamshin turaren dake fita a ji6anta da Kuma daddadan qamshin daya-sayen da ta shafa sun mamaye iskar safiyar da ake busawa. Ta sa hannu ta gyara dogon igiyar kitsonta da ya kusa rufe mata ido a cikin dogayen igiyar kitson da suka warwatsu a kafadarta, Suna ta sheqi da daukar ido. ta ce da ni a cikin sassanyar murya. . 'sannunka.' . Sannan ta kashe mani fararen idanunta dake motsawa tarwai dara-dara kamar gilashi. Na biyata murmushi sannan nima na ce da ita. . 'ke ma sannunki.' . Ta kai ganin ta inda Sauran dalibai ke zazzaune fululu a ko'ina, ta dawo da hankalinta kaina ta ce mani. . Qq "ga alama kai ma irina na ce, baka son yawan surutu shi yasa ka ke6e gefe guda ka xauna anan ko mallam?" . Na sake cewa da ita. . "gskyrki, Wlh ban cika son yawan surutu ba." . Muka yi dariya a lkc guda, sannan ta tambayeni. . "ya sunan ka?" . Na ce da ita cikin farin ciki. . "Suna na mansur. Ke Kuma Fa ya sunan ki?" . Ta ce da ni. . "ni Kuma Suna na Zubaida . Ga al'darmu ta qasar hausa, duk lkcn da irin wadannan hirarrakin suka faru a tsakanin saurayi da budurwa, to ana sa ran soyayya ta qullu. Don haka nima ban yi mamaki ba da naji cikin dan lkc qanqani nkamu da ciwon son wannan 'yar talika mai Suna Zubaida ba." muka dauki lkc zaune a wurin mu biyu muna ta hira gwanin ban sha'awa. A lkcn ne ta sanar da ni cewar ita ma sabuwar daliba ce irina. . Duk lkcn da zata sanar da ni wata magana sai in ji bana son tayi shiru, don kuwa daddadan muryarta tafi kama da sarewa, yana matuqar tasiri a dodon kunnena. Bana son in rabu da wannan sabuwar masoyiya tawa, to amma Kuma anyya kuwa ta san cewar na kamu da ciwon son ta? Ban yi tsammanin hakan ba." . . Lp=3Mugun albishir . Page 3 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . Tare da ni Abu ihsan bn ishak Madugun taska . "TASKAR GIDAN LITTAFI"bata amince da daukar shafin ba, yin hakan kuskure ne a kula . . Ban yi tsammani ba! . Bamu dade ba mallamin da zai yi mana darasi ya xo, nan da nan muka shiga tare da Sauran dalibaI aka soma karatu. Ba wuri daya muka zauna ba." a tsakanina da Zubaida Akwai mutum bakwai, sai dai duk da haka hankalina yana kanta. Wani lkcn kamar a jikinta ta san wani yana kallonta haka kawai sai ta waigo inda nake mu hada idanu. Duk lkcn da zata waigo sai ta same ni ita kawai nake kallo ba mallamin ba, Kuma duk lkcn da zamu hada idanu sai ta yi mani murmushi da tattausan le6enta dake sheqi. Nan da nan naji duk na qosa a tashi darasin, na qosa mu fita waje ni da masoyiyata Zubaida. addu'ar da nake yi a lkcn da muke cikin ajin ita ce. Allah ya sa Zubaida ta fahimci ina son ta, kuma allah yasa ita ma ta amince ta so ni. . To amma Kuma a lkcn da aka tashi karatu abin yaxo minn a bazata. Na dauka cewar Zubaida zata tsaya ta saurare ni, mu tafi tare muna hirarmu ta soyayy. . Maimakon haka sai ta ce da ni a lkcn da ta fahimci ina son tsare ta da surutu. . "to mansur, lkcn xuwa gida yayi, ni zan tafi sai gobe Kuma idan mun sake dawowa." . Nayi mata murmushi, kafin in sake cewa da ita wani abu har ta tafi ta bar ni. A haka na tsaya wurin ina ta wasi-wasi da tunane-tunane har daliban da suke a sashen mu suka watse suka bar ni ni kadai A tsa. . Me yasa ban sanar da ita ina sonta ba? Na zargi kaina, don kuwa abin da xuciyata ta gani tana so, bai kamata in yi shiru in 6oye a raina ba." bai kamata in yi kawaici in kasa sanar da ita ba." a ranar ban iya cin abinci ba, sannan Kuma barci ma qaurace min yayi kwata-kwata daga idanuna. Muryar Zubaida ta ci gaba da amsa kuwwa a xuciya. A lkcn da ta xo wurina ta zauna. Ba zan manta lkcn farko da ta fara yi mani magana ba." . "sannun...yaya sunan ka?" . . ** ** ** . . Tun ranar da wannan al"amarin ya faru na kasa samun sukuni a xuciyata. Don kuwa duk lkcn da naxo makaranta har qosawa nake yi in nemo ta in ganta don hankalina ya kwanta. to amma Kuma sbd tsananin fargabar da nake yi tun farko da Kuma razana, har aka dauki lkc mai tsawo ban sanarwaa kowa ba a cikin Abokina dake a makaranta. Ina matuqar jin tsoron in sanar da ita, daga Bayani Kuma ta nuna mani rashin goyon bayanta. Shi yasa na 6oye a xuciyata. To amma Kuma a haka zan ci gaba da son wacce bata san ma ina yi ba?" . kullum bani da wani aiki da ya wuce tunanin wannan kyakkyawar budurwa zubaida. Gashi kuma ko ho hotonta bani dashi, ballantana idan naje gida in riqa dubawa yana debe mani kewa. Don haka idan naje gida sai dai in kwanta ni kadai a daki in rufe qofa ina ta tunaninta, don Kada wani tunanin yaxo ya katse min hanzarina. Kullum idan ina tunanin Zubaida sai in riqa aiyanawa a xuciyata cewar waigo gashi nan har mun yi aure, muna zaune tare zaman soyayya da qauna a wani qayataccen gida na alfarma. to amma Kuma ni na san cewar Zubaida ba ta ni take yi ba, don kuwa ita a tsammaninta mutunci kawai muke yi irin na dalibai, bata yi tsammanin na kamu da matsanancin sonta ba tun ranar da na fara ganinta. . Sannu a hankali da ciwon sonta yayi qarfi a jikina wani lkcn haka kawai bana sanin sanda nake ambaton sunan ta. Sauran da yawa idan nayi shiru ina tunani sai in kira sunantta ba tare da na sani ba." abokaina da basu san me ke faruwar ba idan irin haka ta faru sai su tambayeni ni. . "mansur wacce ce zubaida? . Duk ranar da Zubaida bata xo makaranta ba, bana iya karatu bana iya magana da kowa, don kuwa duk ranar da na wayi gari ban ganta ba, wunin nake yi da zzazza6i mai zafi. Sai na ganta washe gari sannan nake warkewa. Gashi Kuma Kullum kamar qara kyau take yi. Kullum ta xo makaranta sai in ga tafi lokutan baya haske da Kuma annuri, da zarar na jiyo muryarta ko daga nesa ne, sai in ji gaba na ya fadi , xufa tana kwararo min, kai! Abin dai ya zame min kamar masifa. Wannan wacce irin soyayya ce ta same ni? . Kullum muka hadu a makaranta Bayan mun gaisa bana yarda Zubaida ta fahimci irin kallon da nake yi mata, don haka idan tana tare da qawayenta, sai in raku6e a jikin bishiya ina hangenta daga nesa, ko Kuma in 6oye a jikin tagar ajinmu. Ina matuqar sha'awar in hangeta tana dariya cike da farin ciki, sannan Kuma ina sha'awarsu in hangeta tana tafiyar tana rausaya cikin bunqasa da qima da kwarjini kamar wata sarauniya, ina sha'awar in saurari sassanyar muryarta, koda kuwa ace ba da ni take magana ba." duk lkcn da ta aback sunana da daddadan muryarta a ranar da farin ciki nake komowa gida. Shi yasa na haddace duk wata magana mai dadi da na san ta ta6a sanar da ni. . "....yaya sunan ka?" "...sannunka mallaam..." "...mansur kaxo lfy?" .jiya ban xo ba Wlh yaya schl din?" "....yaya schl din mansur....?" . To amma Kuma ni duk wadannan maganganun basu gamsar da xuciyata ba na samu kwanciyar hankali, don kuwa bani kadai bane dalibin da Zubaida take gaisa wa irin haka ba, kasancewar tana gaisa da samari da dama, don haka ba lallai bane don mun gaisa ni da ita in gani cewar ta fahimci ina son ta, Kuma ita ma tana sona ba. . Nayi son ta ce min. . "ina son ka mansur, kamar yadda im na tabbatar kana sona." . Ko Kuma ta ce min. . "allah yasa muyi aure in zama maTarka." . Sai yaushe Zubaida zata sanar da ni wannan kyakkyawan albishir na so da qauna a duniya? . . . ** ** . . Sannu a hankali sai na fahimci Zubaida tana da matsayin da aji da ko kusa ni ba Abokin rayuwarta bane, don kuwa da xuqa-xuqan motoci take xuwa na milyoyin kudade, sannan Kuma da wahala ta sanya kayan a jikinta ta sake maimaita su. . . Lp=4Mugun albishir Page 4 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak Madugun taska "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar wannan shafin ba." . . . Kullum kayan da take xuwa dasu kala daban ne na alfarma, wadanda yawancinsu lesuka ne na manyan mata da Kuma manyan atamfofi masu tsadar gaske. na san cewar ko sarqoqin da take yawa sun ishe ni hidimar karatu a rayuwata. don haka Zubaida ta fi qarfin, amma Kuma Kullum qara son ta nake yi, Kuma Kullum ina addu'ar ta zama matata, idan so samu ne. . Kwanaki suka yi ta xuwa Suna wucewa, watanni Suna biyo Bayan su, shekara daya Bayan daya har muka yi shekara uku a haka tare da Zubaida Kullum da sonta nake kwana nake tashi a xuciyata. Amma Kuma ita bata sani ba." wani abin takaici Kuma shi ne a cikin shekaru uku da muka yi tare da Zubaida an samu raguwar alaqar mutuncin da muke yi ni da ita. Sau da yawa sai mu hadu da ita a wani lkcn ma ko kallon inda nake ba zata yi ba, sai dai ni da nake binta ina yi mata magana, don kuwa na fadi maku duk ranar da ban ganta ba, Babu Sauran kwanciyar hankali a xuciyata . Sannan Kuma a cikin shekaru uku da muka yi ban san takamaimen gidansu ba, Kuma Babu Wanda nake tsammanin ya sani a cikin daliban ballantana in tambaye shi. Don kuwa Zubaida bata cika baiwa mutane fuska Suna doguwar magana ba." Babu Wanda zai ce ya san gidan su, ko Kuma ya ce ya san ko ita "yar wace ce a birnin zariya. . Rayuwata bata sake fadawa a cikin xullumi da tagayyara ba sai da lkcn jarrabawarmu ta qarshe ya xo. daga ranar Kuma shi kenan mun yi bankwana da juna, mun gama makaranta, ba zamu sake xuwa mu hadu da junanmu ba, sai dai Xiyara. Dalibai 'yan kwana Suna ta farin ciki da xuwan ranar qarshe, zamu gama jarrabawarmu amma Kuma ni baqin ciki nake yi, don kuwa lkcn rabuwa da masoyiya ta yayi. . Na san cewar idan muka rabu shi kenan, wata qila Kuma har abada ba zan sake ganin Zubaida ba." me yiwuwa ma ba zamu sake ganin juna ba." idan Zubaida tayi kwana daya bata xo makaranta ba, ranar rashin lfy nake yi sbd ban ganta ba, gashi Kuma ynx zamu rabu rabuwa ta har abada. Anyya kuwa zan iya rayuwa ba tare da wannan masoyiya tawa ba?" . Da ranar kammala jarrabawarmu ta zo ban yi barci ba, kwana nayi a zaune ina xullumi Wata xuciyar tana raya mani cewar ya kamata in cire fargaba in sanar da ita cewar ina sonta. Don kuwa idan muka rabu ban sanar da ita ba, ban san inda zamu sake haduwa ba." . Ka shaida mata kana sonta mansur, ko banza dai yafi ace ka bar abin a iya xucyarka ba tare da ta sani ba." koda kuwa ace ba zata amince ba, ta san cewar dai kana sonta, Kuma duk inda take a duniya ita ma zata riqa tunaninta a matsayin masoyinta. . Da wannan shawarar na tafi makaranta a raina, ina ta mamakin irin wannan soyayya da ta cafi xuciyata.tun a ranar farko da muka fara karatu na fara sonta, gashi Kuma ban sanar da ita ba sai ynx a ranar mu ta qarshe da zamu rabu. Shekaru uku cur ina tfama da ciwon son ta a raina, Babu Wanda ya sanin ballantana ya taimaka mani ya jefi-jefi ya sanarwa kyakkyawa Zubaida . Bayan mun fito jarrabawarmu dalibai Suna ta gaisawa da juna, kowa yana neman dan uwanshi don a yawa juna Tunda dai rabuwa ta zo, ni Kuma sai nayi sauri na garzaya na bi Zubaida a guje, da na hangeta ta kama hanya ta tafi inda motarta take zata tuqa ta tafi. Na sha gabanta ina numfashi da qyar kamar raina zai fita. Muka hada ido ta yi mani murmushi sannan ta ce da ni. . "mansur ban ganka ba sai ynx, yau Kuma ranar rabuwa ta zo, mu yawa juna sai wata rana." . Na tuno ranar da muka fara haduwa a makaranta, shekara uku da suka wuce, sannan na sake tuno magana da ta sanar da ni da ke 6oye a dodon kunnena tsawo lkc. . "sannunka. ga alama kaima irina ce baka son yawan surutu, shi yasa ka zo ka zauna...." . Na ji hawaye sun tarar mani a idanuna, qwalla ta cicciko mani, nayi sauri na share hawaye na ce da ita cikin qarfin hali. . Yawan comment dinku shi ne kuzarina wajen sanqamo Page 5mugun albishir Page 5 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . Naji hawaye sun taru a idanuna, qwalla ta cicciko min nayi sauri na share hawaye na. Na ce da ita cikin qarfin hali . . "haka ne Zubaida yau ce ranar mu ta qarshe a makarantar nan, daga yau Kuma sai yaushe kenan zamu sake haduwa, ko kina nufin mun rabu kenan har abada? . Zubaida tayi dariya, ga alama bata fahimci irin matsanancin halin da rayuwata ta shiga ba." tayi mani farin da fararen idanunta sannan ta ce da ni. . "gsky mansur bana tsammanin zamu sake haduwa har abada . Tayi shiru tana tunanin wani abu. A yayin da ni Kuma na qarawa kyakkyawar fuskarta idanu. Wata xuciyar ta fara yi mani kururuwa. . "ka fadi mata kana sonta mansur, kayi sauri ka sanar da ita, sbd daga yau ta ce ba zaku sake haduwa ba a duniya har abada!!! . Kafin in dawo hayyacina in ce da ita wani abu ne, sai ta ce da ni cikin farin ciki. . "Akwai wani albishir mai dadi da zan sanar da kai mansur, Wanda ba kowa ne ya sani ba a makarantar nan, na san cewar zaka yi farin ciki, ina nufin zaka taya ni farin ciki. . Naji farin ciki ya kama ni. . ...."wane irin albishir ne Zubaida fada min..." . Na ce da ita cikin zaquwa, don kuwa ni a shirme na tayi tsammanin ina matuqar sonta ne, shi yasa ita ma zata sanar da ni cewar tana sona. . Zubaida ta duba agogo sannan naga ta dan 6ata rai. ta ce da ni kai tsaye. . "kai kada in 6ata maka lkc mansur, nima sauri nake yi, dama ba wani albishir bane, so nake yi dama ka taya ni farin ciki, ina gayyatarka xuwa daurin aurena a wannan asabar din mai xuwa. Na sami miji zan yi aure." , Naji kamar ta watsa min garwashin wuta a fuska. . . . ~~~~~~~{ mugun albishir }~~~~~~~~ . . . Kowanne dan adam a duniya Akwai abubuwa da dama da suka fi bashi sha'awa a rayuwarsa. Alal misali wani shi a rayuwarsa yafi so yaga an yi ruwan an dauke, ni'ima ta wadaci ko ina a duniya, ana busa sassanyar iskar damina. . Wani kuma shi a nasa 6angeren yafi son ya ji ana zafi, don kuwa a irin wannan lkcn yafi walwala da nishadi tare da Sauran bani adamu. Wani kuma yafi son ya wuni yana yawo bashi a nan bashi a can. Wani kuma shi in har zai samu ya kwanta ya wuni yana barci, to duniya ta yi masa dadi koda kuwa bai samu abin da zai jefa a bakin salati ba." . Ni kaina ina da irin wannan buqata kamar Kowanne dan adam. To amma Kuma Babu mamaki ni a nawa 6angaren abin da nafi so ya banbanta da na Sauran mutane. Na san cewar mutane da dama zasu sha dariya idan na shaida masu cewa a rayuwata nafi so in zauna a daki ni kadai tun safe har dare ba tare da nayi magana da kowa ba." . A cikin irin wadannan ranakun da na samu wannan gara6asar ta zama ni kadai a yammacin wata lahadi ba zato ba tsammani sai naji sallamar wani yaro mai qirar wayayyu dan kimanin shekaru bakwai a dai dai qofar dakina. Tun kafin in amsa sallamar ya sa hannu ya yaye tsumman labulen dakina Wanda yayi fata-fata kamar kallabin mahaukaciya. . Muka hada ido ni da yaron, ina zaune ina gyaran wata tsohuwar rikoda tawa, wacce Kullum sai na dirka mata dundu Sau ba iyaka, sannan nake samu in ji labaran duniya. . : "wai an ce ka xo ana kiranka a waje." . Na dubi yaron cikin damuwa, ganin irin kallon da nayi mashi naga ya dan jawo baya a tsorace. To amma Kuma wata qila ba kallon da nayi mashi bane ya tsorata shi, Babu mamaki tsohuwar rikodar tawa ya gani ya furgita, don kuwa ko ina a taskar dakina kayan cikinta ne falle-falle kamar an fede akuya. Amma Kuma duk da haka sai faman 6urari take yi da tsuwa a natalie tsammanin waqar fina-finan hausa take yi. Na ce da yaron. . "wane ne ke kira?" . Ya ce da ni. . "maman bose ce. . Maman bose? Na tambayeni kaina. Lallai Babu lfy. Don kuwa na san abin da ya kawota. na xurawa yaron idanu. Na ce dashi. . "ka ce da ita bani nan...ka ce da ita baka ganni ba." . A dai-dai lkcn da nake yiwa yaron burga ne, kakata ta fita daga dakinta dake kusa da nawa, tana dauke da bata zata yi alwala. Ta ce da yaron. . "kai je ka ce gashi nan xuwa ka ji ko? . Yaron ya garzaya waje da gudu bayan ya ce. . "to." . Nan da nan ta fara yi min sababin da ta saba tana cewa. . "sakarai, mutumin banza, kai dai mansur ba zaka ta6a jinjinawa nasiha ba." ace Kullum aka zo gidan nan yin sallama da kaI sai ka ce ace baka nan...ka ynx mutane ashe ba rahama bane mansur....ina amfanin wannan shashancin da kake yi a gidan nan?" . Na riqa na saba da halinta, in Sau dari za ayi sallama da ni, in har tana gidan to ban isa in ce bani nan ba." to amma Kuma a zahiri irin wannan ziyara da Maman bose mai shago ta kawo man Babu alheri a cikinta, ba rahama ba ce, don kuwa na dade ina yi mata qarairayi ina amsar bashin kayanta dake a shagon layinmu. Babu shakka yau ta gaji ne shi yasa ta biyo sawu na. . . Ina jiran tarin comment dinku kafin in watso page -6 mugun albishir Page 6 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . . Wata qila yau ta gaji ne shi ya sa ta biyo sawuna har gida don ta tsare ni in biyata kudinta, gashi Kuma tsawon wunin yau ko qwandala ban gani ba ballantana in mallaketa a Aljihuna. Don haka ya rage nawa in san yadda zan da wannan mafadaciyar bayerabiyar dake a qofar gida tana jira na. Na ci sa'a ma da ba ta shigo har cikin gidan namu ba." don kuwa bana son kakata juma ta san halin da ake ciki. . Na tashi gabana yana haduwa na tsallake rikodar da nake gyarawa, na fita waje ina wasi-wasi ni kadai. Na wuce juma tana alwala tana surutai ita kadai. . "in ba lalata ba." a kira ka amma ka ce wai a ce baka nan. Baka san alherin da yasa aka xo neman ka ba, iirin wannan ke sa mutum ya 6arar da qoqon furar arziqinsa da kan shi bai sani ba." . Ni dai ban ce mata komai ba, don kuwa abin dake damuna a raina ya ishe ni. Wani lkcn na kan biye mata mu wuni muna jayayya ni da ita. To amma ban da irin wannan lkcn da Maman bose ta xo ta ritsa ni. . Da fita ta qofar gidan na same ta a tsaye tana ta kumbura tana sacewa, kamar anan qara mata iska da fanfon mota, kumatunta sun kumbura kamar kwallon kafa . 'yar gajera ce dunqulalliya wacce ba Kowanne qato zai iya kayar da ita ba idan za ayi kokuwa. Na tsaya baya na jingina da qofar zaurenmu, sannan na lalubi wani murmushi na musamman Wanda yawanci bana yin irin sa sai rana ta 6aci in an zo an tsare ni in biya bashi, ni Kuma bani dasu. To amma Kuma a wannan karon murushin nawa bai yi rana ba, don kuwa matar bata saki ranta ba." Maimakon haka ma sai ta sake hade fuska kadan ake iya ganin idanunta dake 6oye a cikin loko. Na ce da ita. . "Maman bose manyan gari ...ashe ana ganin Ku haka..." . Ta daka mani tsawa a fusace ta dakatar da ni ba tare da na shirya ba." . "kada ka raina min hankali mansur ni ba wannan ya kawo ni ba..na zo ne ka biya ni kudina, na gaji da qarairayi da kake man. Kwanaki da na ganka ka ce min shekaran jiya zaka bani. Shiru-shiru baka zo ba, jiya Kuma ina hangenka ka zagaye baka biyo ta qofar shago na ba don Kada in tamvayeka. To ynx na biyo ka gida Tunda baka da niyyar biyana, ko an ce maka ni a banza nake debo kayan a kasuwa? . . Ku yi haquri da iya wannan. Sai mun hadu a page 7Mugun albishir Page 7 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . Tare da ni Abu ihsan bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI"bata amince da daukar shafin ba. . Ko an ce maka a banza nima nake debo kayan a kasuwa?" . Nayi ajiyar xuciya da naji ta kai qarshe. Na san cewa Babu ta inda zan layancewa wannan mata. don kuwa ta ji hausa radau, kamar jakar Kano. Duk ta inda na biyo mata tana kallona. Na ce da ita cikin lallashi . "ina sane da kudinki Maman bose, ba cewa nayi zan cinye ba, ina sane dasu. Garin ne ya dan yi mana zafi, wallahi Jira nake yi komai ya warware zan xo in yi maki balas, ai ina sane, ba dari hadu da tamanin bane? Ina sane Wlh ban mance dasu ba." . Ta sake murtuke fuska, ta haye sama. . "baka yi niyyar biyana ba, da ace kana da niyyar biyana ai ba zaka riqa zagaye wa ba idan ka hange ni a shago. Ka biya ni kudina kawai yau Tunda na gaji na biyoka har gida, ka biya ni ko in tara maka mutane ehe!" . Na waiga kusa da mu, naga wasu almajirai riqe da robobi sun tsaya kallo, da suka ga yadda bayerabiyar take daga muryarta tana kwaratsi. Daga can nesa Kuma a kusa da shagon wani iyamuri wai shi obi wasu mutane ne a zazzaune sun quro mana idanu, shi Kuma iyamurin yana dariyar mugunta daga nesa, don kuwa shima na cinye masa wasu ragowar dari da ashirin. A dalilin haka muka 6ata baram-baram don kuwa cewa nayi idan ya sake tambayata sai na kwantar dashi, ku ji Fa sbd tsabar zalunci, sai dai Kuma gashi tun ba aje ko ina ba wata mace wacce ta fi ni hadama ta ritsa ni ina zaman-zama na. Ta sake daka min tsawa. "zan tara maka mutane mansur, Wlh ka biya ni kudina ko in tara maka mutane." . Na ce da ita cikin damuwa. . "mutane Kuma Sau nawa zaki tara min su Maman bose? Ai in dai mutane ne ko ynx ma kin tara min su." . Maman bose ta waiga taga mutanen dake kallon mu daga nesa, su Kuma almajiran dake kusa suka watse da gudu a tsorac, da suka ga ta wurgo masu wata harara. Ta dawo kaina ta sake cewa. . "mansur ka bani kudina in ba so kake yi mu kwashi bala'i da kai a wurin nan ba, ba Fa tsoronka nake ji ba." . Na jawo baya a tsorace da naga ta matso tana huci,ganin cewar tayi min barazana da mutane ban damu ba, shi yasa zata biyo min ta hanyar dambe da kokuwa. Ynx kam ta biyo min ta hanyar da zan biya ta, da ace ina dasu. To sai dai Kuma har ga allah bani da ko kwabo a aljihuna. Sannan Kuma idan na bari ta ci min kwala to sai ta yi min kayi dari a banza ban rama ko daya ba, don kuwa ruwa ba tsaran Wanda bane. . Na rasa inda zan sa kain, sbd masifa. Na ji hawayen baqin ciki Suna neman taruwa a idanuna, don kuwa tun lkcn da na gama makaranta shekara uku kenan ina fafutikar neman aiki ban samu ba." da na gaji shi ne na dawo na zauna a gida, na shiga sawun masu zaman tsammanin warabbuka, wai malam ya qirga noma don zakka. Shekara uku ba wasa ba ce, na sha wahala a baya, ko Kuma in ce ina kan shanta, don kuwa yau gani a gaban azababbiyar matar da ko mutuwa zan yi ba zata yafe min bashin da take bi na ba." ta sake cewa min..." . "idan lissafi zamu yi allah ne kadai ya san adadin kudin da nake bin ka mansur. Sauran biyu kana amsar taba (rothmans), ni na mance dasu ma sai ynx na tuno. Kuma kwanaki ma ka sha a bakin shagona ko ka mance ne....? . Gabana ya fadi, nayi saurin dakatar da ita. . "ina sane, haka mama bose, meyer Kuma na wani tone-tone?" . Nayi saurin katseta ne sbd a 6oye nake sha tabar, bana son kowa ya sani, ita ma don ya zama dole ta sani ne Tunda dai tana siyarwa. Nayi saurin kasa kunne ko zan ji tafiyar kakata juma, bata damu ba don ta ji anan rigima da ni akan kudi domin kuwa ta saba. To amma Kuma da zata ji maganar taba na san cewar sai ta fito ta ji ko waye yake sha. Idan kuwa ta fahimci cewar ni ne nake sha, to na shiga dari ba ma uku ba." don kuwa duk danginmu, na kusa da na nesa har ma Wanda ba a qasar yake zaune ba sai ta kai masa lbr. . Da mafadaciyar matar ta fahimci bana son ayi magana taba sai ta fahimci mahalarta. Sbd tsabar rashin mutunci sai ta sake daga murya. . "an fada, kana shanta tabar ko baka shafi'u ne iye! Sai ka biya ni kudin taba ta da ka xo ka amsa ka kunna ka sha..." . Na ji kamar in sa itace in buge ta sbd tsabar takaici, na leqa waje sosai inda mutanen unguwarmu ke zazzaune, na hango iyamuri yana dariya da qaton ciki. . Muna nan tsaye cirko-cirko ni da matar tana huci,ganin a Gabana kamar zata cinye ni danye. Kamar aikin budar idanu sai naga wata danqareriyar mota tana malalowa kusa da mu kamar ba zata qare ba, kafin mu tsayar da hankalinmu kan matar tuni har ta tsaya tana fitar da sauti kadan-kadan kamar iska. Bayan an kashe motar sai....... . Lp= 7mugun albishir Page 8 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . . Bayan an kashe motar an bude qofar sai kawuna alh. Badamasi dake a kaduna ya fito yana murmushi. Muka hada idanu, naji farin ciki ya kama ni don kuwa allah ya kawo min kudi a lkcn da nake neman su ruwa a jallo. Yana sanye da fararen kaya shadda riga da malum-malum. Dan matashin dattijo, mai kimanin shekaru hamsin a duniya, Wanda ko kusa a tarihin rayuwarsa bai shafi'u wata wahala ba." shi ya sa siffarsa babu alamun gajiya ko tsufa. . Da fitowarsa na tar6e shi cikin farin ciki . "sannu da xuwa alhaji." . Ya kama hannuna ya riqe yana dari. . "mansur manyan samari." . Muka kama hanyar zamu shiga cikin gida, Maman bose dake tsaye tana kumbure-kumbure ta ce a fusace. . "baka bani kudina ba, za Kuma ka shiga ciki." . Na juyo a fusace na harareta. . "amma ai sai ki bari sai naxo shagon, ko baki gani mun yi baqo ynx?" . Ta ce da ni. . "ni gsky ban yarda ba sai ka biya ni kudina." . Kawuna ya kallon, sannan ya kalli matar cikin damuwa. . "me yake faruwa ne?" . Ya tambayata. . "wane kudi zai baki?" . Maman bose tace dashi. . "bashi nake bin shi wata daya kenan ya hana ni. Shagona ya xo ya amshi tab..." . Jin zata tona min asiri yasa na hanzarta daka mata tsawa, na ce. . An tambayeki abin da naxo na amsa ne mara mutunci? Ki fadi kudinki mana a biya ki." . Kawuna ya ce da ita. . "ynx dai ke kudinki nawa ne malama?" . Maman bose ta ce dashi cikin ladabi. . Dari hudu ne da tamanin alhaj." . Kawuna ya zaro dari biyar a dunqule ya miqa mata. Tayi sauri ta miqo busassun yatsunta ta warce kudin. Ta ce dashi." . "na gode alhaji, gashi Kuma bani da canji, zan baka naira ashiri." . Alh. Badamasi ya ce da ita. . "jeki kawai abin ki, an bar maki." . Ta yi murmushi. Na sake hararta na ce. . "ba ki ci bulus ba, zan xo in amshi cannjina ke ma kin sani." . Kawuna ya janye ni muka shiga cikin gida, bamu zame ko ina ba sai dakin kakata, Kada ka tambayeni inda iyayena suke, don kuwa mahaifina qaramin ma"aikacin hukumar aikin gona ne a qaramar hukuma..yana can zaune a gidan ma"aikata tare da mahaifiyata da Kuma Sauran qanne na uku. Da yake kakata juma ta saba da ni, bata son rabuwa da ni, shi yasa bata amince in zauna a gidan mahaifina ba na ma"aikata. Duk kuwa da irin fafatawar da muke yi da ita, Fadan safe daban, na rana daban, haka na maraice, to amma ai duk laifinta ne, tunda dai ita ba zata iya gani ta yi shiru ba, sai dai Kuma da ace ta san ina shan tabar a 6oye aniya kuwa zata amince ta zauna tare da ni? . . . ** . . Minti goma bayan haka muna zaune a dakin kakata tare da Kawuna da ya kawo min ziyara yana yi min fada cikin fushi. . "ina amfanin irin wannan rayuwata takalmi mansur? Ace kai kenan Kullum naxo gidan nan sai na sameka a cikin masala. Ba ka da wata qwaqqwarar sana"a sai rigima da mutane akan kudi, kana jin wanna ita ce rayuwa mai kyau?" . Na sunkuyar da kai ban ce komai ba." . Kakata ta ce. . "Tunda ynx kaxo ka fada mashi, wata qila kai yaji maganarka. Amma ni da yake ya raina ni yaushe zai ji Fadan? Nayi juyin duniya da yaron nan ya samu sana'a, tunda dai aikin gwamnatin ya qirga samuwa, ya qi sbd girman kai. Wai shi tunda dai yayi karatun book bai ga dalilin da zai sa ya yi aikin qarfin ba." wai sai dai ya ci a huce." . Kawuna ya yi tsaki, ya ce. . "to ina maganarka hutu a qasar nan? Ai babu hutu mansur, haka nan zaka dake ka nemi na kanka ka hucewa kanka takaici da wulaqancin mutane." . Ya dan saurrara sannan ya ce da ni. . "Tunda abin ya xo a haka, ina ganin abin da zamu yi shi ne....! Ka shirya mu tafi kaduna tare.sai in samar maka aiki a can. . . Lp=9Mugun albishir page 9 . Daga alqalamin Shafi'u Dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak (Madugun taska) . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba. . . Ka shirya mu tafi kaduna tare, sai in samar maka aikin yi a can. Dama Akwai wani abokina da yake neman doreba, Kuma ni ya baiwa alhakin in nemo mashi yaro nutattse, don kuwa mutumin gurgu ne bashi da qafafuwa." . Na dago kai cikin damuwa na dubi Kawuna . "amma Kawuna sbd allah idan ma tuqin zan yi sai in rasa wanda zan riqa tuqawa sai musaki mara qafafu?" . Kawuna ya fashe da dariya, sannan ya ce da ni. . "ka cika gajen haquri mansur, in banda abin ka ai sai ka tsaya kuna in yi maka bayani. Kada ka raina wannan gurgun, duk da kasancewar sa musaki ina son ka san cewar duk fadin birnin kaduna babu hamshaqin mai kudi kamar sa. Idan har ka amince zaka bi ni ka riqa yi mishi tuqin to ka gama hayewa mansur....don kuwa a qalla duk wata zai riqa biyanka ladan duba talatin." . "dubu talatin?" . Na tambayi Kawuna cikin xumudi. . Ya ce da ni yana fara''a, . "qwarai kuwa. Bayan haka shi zai baka muhalli, shi zai dauki nauyin abincinka safe da rana ko da yaushe." . Nayi shiru ina tunani don kuwa arziqi ya soma qwanqwasa min qofa. Nayi saurin lissafa dubu talatin Sau goma sha biyu, naga cewar kudin sun kai har naira dubu dari uku da sittin. a shekara daya fa kenan kawai. To idan Kuma na kai shekara goma milyan nawa kenan? . Naji xufa ta fara kwararo min, Kawuna yana kallona yana murmushi. . Haqiqa arziqi ya samu!" . Abu na farko da na fara rayawa a xuciyata shi ne, aure Zubaida. abu na biyu Kuma shi ne yadda zan yada zango a qofar shagon Maman bose cikin isa da qasaita a duk lkcn da nazo garin. In fito daga cikin mota ta mai shegen tsaya in more. Kawuna ya ci gaba da cewa. . "ya kamata tun ynx ka fara tunanin abin da zaka yi da kudin da zaka samu mansur....bana son almubazzaranci, ya kamata ka yi aure nan ba da jimawa ba." don kuwa in kana da aure zaka fi zama mutum nutattse mai kamala a idon mutane." . Aure! naji Kawuna ya sake budo min wani babi mai cike da damuwa a xuciyata. Kullum in aka yi min tadin aure sai na tuno da abar begena Zubaida. har ynx ina son Ku san cewar tun lkcn da nayi bankwana da Zubaida a ranar mu ta qarshe a makaranta har ynxn qaunarta tana nan daram a xuciyata. Kamar aikin sihiri, Kuma tun daga lkcn ban sake jin labarin inda take ba a duniya. Ban san a inda tayi aure ba, to amma Kuma xuciyata ta kasa jurewa in haqura da son ta, har ynx ban sake jin ina son wata mace ba a duniya. Bani da tamkar Zubaida. Kuma ba zan sake samun tamkarta a duniya ba." don kuwa ita kadai ce mace da xuciyata take so da qauna. Kuma Kullum idan na kwanta barci sai na ganta a mafarki. Wani lkcn in ganta a cikin damuwa, wani lkcn Kuma in ganta cike da annashuwa. Amma Kuma duk sanda nayi mafarkinta bata tsyawa muyi hira, sai dai in qura mata ido tana tsaye. . A haka nake ta bin rayuwar wannan masoyiya tawa, na san cewar ita tana can tuntuni ta mance da ni a rayuwata. Amma Kuma ni gashi ta barni ina ta fama da ciwon sonta shekara da shekaru. "sai yaushe wannan ciwon mai tsanani zai rabu da xuciyata, don in samu sukuni a rayuwata?" . Nayi murmushin qarfin hali na cewa Kawuna. . "alhaji ai ni tuni na haqura da aure a duniya." . "sbd me mansur...a qanne dalili?" . Na kalle shi, sannan na waiga gefen da kakata juma take na ce dasu cikin damuwa. . "tun lkcn da na rasa wata masoyiya tawa a makaranta mai Suna Zubaida. Tun lkcn na haqura da batun aure a rayuwata. Don kuwa ita kadai ce macen da nake so Gashi kuma ta tafi ta barni." . . ** . Tun lkcn da na sauka daga tasin da ta daukoni daga gidan Kawuna na fara hango katafaren gidan Alh. Bashir Gurgu. farin sol dashi daga nesa kamar an daukoshi daga birnin sin. Na tsaya akan titi ina kallon gidan xuciyata cike da mamaki, don kuwa duk tagogin gidan da Kuma qofofin duk na gwalagwalaine. Sannan Kuma ga shuke-shuke nan burjik sun zagaye gidan cike da furanni jajaye da farare masu ban sha'awa. . Bayan na gama kallon ne sai na kama hanya na tunkari faffadar qofar shiga gidan. Daga nesa ina iya hango wani tsohon mai gadi a zaune riqe da bulala a bakin qofar. Kwana biyu kenan da xuwanka kaduna tare da kaduna tare da Kawuna. A cikin kwanaki biyun suka gama shirya komai da alhaji bashir gurgu, ynx xuwana kawai ake jira in xo in fara aiki, Kuma gashinazo. . Kafin in qarsa inda mai gadin yake sai da na sake tsayawa na dubi kayan dake jikina, kafin in baro gidan Kawuna na daukar cewar kayan da na sako na qure adaka zasu fitarku da ni kunya. To amma Kuma a halin ynx da naxo naga yanayin gidan, sai Kuma naji kwalliyar da nayi ba ta gamsar da ni ba." na dubi takalmina mai kan ,.kura, Wanda shi kadai ne abin arziqi a kayan jikina. Bana shekara takalmin shiga kenan a wajena, a wurin wani tsohon dan sanda mai ritaya na sayen shi. Kada ka so jin Sauran kayan dake jikina, don kuwa kodadden wando ne shudi Wanda ya sha faci manya-manya kamar tamfol din fyadin masara. Sai Kuma baqar riga mai kwala da Kuma shudiyar hula hana-sallah da na ta6a ciyota a wajen caca. . Na sake duban katafaren gidan naji tsoro da Kuma rashin qarin guiwa sun kamani. Don haka ina xullumin wataqila idan Alh. Bashir yaga shigar da nayi ya ji ban kwanta mashi a raina ba." wataqila ma ya ce ya fasa daukata aiki a gidansa. To amma kuma me zai sa in damu kaina? Shi Fa gurgu ne, ni Kuma ina da qafafuwana. . Don haka sai na tunkari gidan kai tsaye, na samu tsohon dake gadi a zaune kan bench, tun kafin in yi masa sallama ya dago kai ya duba ni sannan yayi min murmushi, kamar damar can ya ta6a ganina, sai dai Akwai alama ya san da xuwana. . Bayan nayi masa sallama ya amsa, tun kafin in yi masa Bayani ko ni wane ne, sai ya tambayeni. . "kai ne mansur da aka ce zaka xo?" . Nayi saurin gyada masa kaina. . "eh, ni ne." . Tsohon ya riqe ya tarbeni cikkin girmamawa. . . Lp=10Mugun albishir page 10 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak (Madugun taska) . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . . Tsohon ya tarbeni cikin girmamawa. Akwai alamar fadanci a tattare da shi, sannan Kuma idan mutum yayi la'akari da busassun idanunsa da ya ragadawa kwalli da Kuma yadda Ya karkace hularsa gefe daya, nan da nan mutum zai gane cewar a wani zamani can da ya gabata sanda yana Saurayi da wahala idan ba taqadarin yaro akayi ba." . Tsohon ya sake ce min..." . "sannu da xuwa mansur...ai tun daxu Alh ke tsammanin xuwanka. Ya ce da ni in ka xo in jagoranceka mu shiga tare. Zo mu je mansur." . Na bi Tsohon a baya muka shiga cikin gidan, ina zazzare idanu kama 6atacciyar tunkiya. A farfajiyar gidan, danqara-danqaran motoci ne guda biyar Suna ta qyalqyali kowacce launinta gaban. Tsohon ya bude wata qofa. Muka shiga wani dogon daki mai cike da gwala-gwalai. Sai qamshin ke tashi a ciki. An malale darduma mai taushi kamar zata hadiye qafar mutum idan yana tafiya kanta. Na ja na tsaya a wuri guda ina kallon ikon allah. Tsohon ya juyo cikin mamaki ya ce da ni. . "zo mu je mana mansur." . Na ce dashi. . "ina Kuma zamu je banda nan baba?" . Tsohon ya bushe da dariya sannan ya ce da ni. . "ai bamu kai falon alhaji ba." nan ai zaure ne kawai mansur....kai dai biyo ni kawai mu tafi." . Tsohon ya sake ja na muka fita daga tsararren dakin, muka fada wani tanqasheshen falo mai dauke da wani qaton gilashi a bango yana bayyanar da hotunan namun daji iri-iri, da Kuma kyawawan furanni, sai ka ce fuskar majigi. Shima wannan gwala-gwalai ne a jiki kamar kayan wasa. Na rabu6e a jikin bangon falon ina jiran Tsohon ya bani izini, don kuwa tsammanin da nake yi duk inda na tsaya a cikin falon laifi ne....! . Tsohon ya dube ni cikin murmushi . "naga ka sake tsayawa mansur. Me ya faru Kuma?" . Na ce dashi. . "ai na dauka nan ne falon alhaji din da kake magana." . Tsohon ya sake yin dariya ya ce da ni. . "haba mansur, me alhaji zai yi da wannan falon, kai dai baka rabo da abin dariya Wlh. Wannan ai dakin saukar baqin ne, masu neman ganawa da alhaji kafin ya buqaci ganin su." Kada ka damu mansur, zamu je kaga falon alhaji." . Tsohon ya sake shigewa gaba, na bishi a baya muka fice daga wannan falon ya sake tura wata qofar zinare dake kalle, duk jikin qofar qyalqyali yake yi. Nayi tsammanin zan hango ko me ke a cikin dakin ta gilashin qofar, Maimakon haka sai na hango hoton razananniyar fuskata a jikin gilashin qofar. Nan da nan sai na fara addu'arziqi allah ya sa babu qananun yara a gidan. Don Kada in tsorata su su da abin da na gani a jikin qofar a matsayin fuskata. Tura qofar keda Wuya sai ta bude ba tare da wani sauti ba, a lkcn ne to naga wani abin mamaki, Kuma na gamsu haqiqaTsohon nan bai yi qarya ba, Sauran dakunan da muka je a baya, idan aka saka su a cikin tsararren falon Alh.Bashir Gurgu to duk sai sun 6ace ma an rasa inda suke. Tsohon ya shige gaba na bishi a baya. na saka qafata a cikin tsararren falon mai dauke da lallausan kilishi. Na fara kalmar shahada a 6oye a xuciyata, don kuwa nayi tsammanin xuqeni kilishin zai yi. . A zagaye da falon kujeru ne na alfarma shiga-shiga sun yi kuri sun saka wani faffadan teburi a tsakiya, yana ta sheqi da daukar idanu. Tunda nake a duniya ban ta6a ganin kwatan-kwacin kayan alatun da na gani a wannan falon ba." gabaki daya gidan cunkushe yake da kayan alatu. Sai da naga tsohon ya xube a qasa cikin girmama, sannan na lura da abin dake zaune dan surutu akan kujeru kamar kashin tsoro. Wani motsattsen mutum ne dan tsurut a zaune' qafafuwan wandon shi biyu suna ta reto babu komai a cikin. Idanuwanshi jawur kamar garwashin wata. Dogon hancinshi da Kuma tsukakken baking shi hade da motsattsiyar fuskarshi su ne suka maishe shi xuwa siffar aku kuTuru sannan suka maida shi mai siffar 'yan bori . "rana ya dade ga mansur din da ka ce in ya xo a shigo dashi." . Tsohon ya fada a sanyaye sannan ya tashi cikin girmamawa ya fice daga falon kamar walqiya. Mutumin da na kasa tantance aljani ne ko bil adama , ya dube ni sannan yayi murmushi. Ina tsaye akan shi qerere ina dubanshi. Wani in ya zo ya same shi zaune a falon, yana iya daka mashi tsawa ya ce zai kore shi. Don kuwa sam muhallin baiwa yi kama dashi ba sam. Zai yi kimanin shekaru hamsin, kanshi cike yake da furfura, kamar an yi 6arin garin masara. . "ga wuri nan mansur, zauna mana." . . Lp"11 mugun albishir Page 11 . . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni. Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . "ga wuri nan mansur, zauna mana." . Ya ce da ni, sannan ya nuna min kujera da hannunshi. Nayi ajiyar xuciya sannan na za6i kujera daya na zauna. Duk da yake Akwai na"urar sanyaya daki a falon, hakan bai hana ni jin xufa na keto mani ba, don kuwa na tabbatar wannan firirinn da na iske a ynx shi ne attajirin da ya dauke ni aiki, Kuma shi ne ke da wannan tarin dukiya kamar qasa. . Ganin na qurawa qafafuwan wandonshi idanu, sai mutumin ya dubi datsattsun qafafuwanshi sannan ya dubenni ya ce da ni. . "kada kayi mamaki mansur, na san cewar kawunka ba zai rasa baka labarina ba, bani da qafafuwa, ni gurgu ne, yadda ka ganni zaune a haka nake kwana nake tashi babu inda nake xuwa." . Na girgiza kaina cikin damuwa. Don kuwa ban san abin da zan iya cewa ba, ya sake cewa da ni. . "to amma duk da wannan naqasar da nayi mansur, ina da milyoyin kudi masu yawa. Sannan Kuma duk abin da nake neman a duniya na samu." . Ya yi murmushi, shi kanshi ga alama abin da ya fada yayi mashi dadi. Nayi shiru ban ce dashi komai ba, xuwa can Kuma sai na ji yayi ajiyar xuciya, ya dawo maganar da ta kawoni gidanshi. . "mansur kamar yadda ka sani, ka xo gidan nan ne a matsayin direba to amma Kuma ba ni zaka riqa tuqawa ba, ni Babu inda nake xuwa, matata zaka riqa tuqawa a mota, duk inda zata je kai nake so ka riqa tuqata kana kai ta." . Ya tsayar da idanunshi akaina sannan ya rage fara"a. . "ka san abin da yasa nake son ka zama direban matata mansur?" . Na ce dashi. . "A 'a." . Alh Bashir ya ce da ni cikin damuwa, . "ban yarda da ita bane mansur, ina zarginta, don kuwa ta kan dauki mota ta fita ban san inda take xuwa ba." Babu mamaki don taga na zama gurgu na naqasa shi yasa take xuwa wajen wasu mazan a can wani wajen. Shi yasa na yanked shawarar in nemo mata direba. . Ya sake yi min murmushi, ina zaune ina kallon shi. . "ina matuqar son wannan mata tawa mansur." . Ya ce da ni. . A duniya kaf ban ta6a ganin abin da nake so ba irin ta, shi yasa nake masifar sonta, ko kallon ta naga wani namijin yayi, sai in ji duk na damu. Zan iya sa bindiga in harbe mutum idan na fahimci yana son wannan mata tawa. Shi yasa aka nemo min kai mansur, don kuwa na samu labarin kai yaro ne mai amana. Kuma nutsttsen mutum, na san cewar zaka riqe min amanar matata. Na barta a hannunka amana mansur, Kada ka bari mutane su riqa kallonta. Ko kallon ta ba na so a riqa yi. Ina fatan zaka riqe min amanar ta mansur?" . Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da shi. . "ba komai Alh. In allah ya yarda zan riqe maka amanarta kamar yadda kake so." . Alh.Bashir yayi murmushin jin dadi. To amma ina matar tashi take? Na qosa in ganta. . Muna nan zaune sai muka ji sautin shigowar mota cikin gidan, a can harabar gidan. Aka ba motar wuta xuwa can kuma aka kashe motar, sai muka ji an rufe ta da qarfi garam! Alh.Bashir ya ce da ni cikin damuwa, bayan ya dube ni. . "matata ce ta dawo mansur, haka take Kullum bata tuqa mota a hankali, duk ta lalatamotocin gidan nan." . Muna nan zaune sai muka ji sautin tafiyarta zata shigo falon. Qwas-qwas! Naji gabana ya fadi, don kuwa akwai wani zamani da ya wuce na ta6a jin irin sautin tafiyar. . Ta turo qofar falon ta shigo a fusace Babu ko sallama, na waiga cikin kidimewa na dubeta. Jikin jikina ya tsaya cak!! Sannan hantar cikina ta kada. Numfashina ya tsaya na wucin gadi sbd tsananinn kaduwar da nayi a dalilin ganiNta . Tana nan da xunxurutun kyanta kamar yadda na santa tun a shekarun baya da suka wuce fuskarta mai cike da annuri tana nan wasai, ta qara annuri da kwarjini. Na tuno ranar farko da muka fara haduwa a makaranta. . "yaya sun ka.." Na tuno daddadar muryarta mai kama da dorewa. . Kafin in dawo hayyacina ne Alh. Bashir ya yi min dariya sannan ya ce da ni. . "ita ce matata da nake baka labarin ta mansur, Kuma gaisa mana. 'yar garinku ce, a dariya na aurota, sunan ta Zubaida!! . . Lp=12mugun albishir Page 12 . . Daga alqalamiN Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . . "yar garinku ce, a zariya na auro. Sunan ta Zubaida!!" . . . ** ** ** . . Ganin kamar a fusace take sai Alh.Bashir ya ce mata. . "Kada kina damu Zubaida wannan yaro ne mai ladabi. Don baki san shi ba ne, amma Kuma kema zaki gani da idon ki, shi ne sabon direban da na samo miki. Duk inda zaki je kina iya fadi mashi, nafi son ya riqa tuqa ki, bana son kina fita ke kadai." . Zubaida ta yatsina fuskarta sannan ta wuce ba ta yi magana ba, ta bude wata qofa dake a cikin falon ta shiga ciki. . Alh.Bashir ya ce da ni. . "Kada ka damu mansur, haka take da saurin fushi, amma zata huce ne daga baya. Kayi haquri da halinta ni ma haka nake haquri." . Nayi ajiyar xuciya, sannan na share xufar dake a fuskata, don kuwa ji nake yi kamar fatalwa na gani ko aljana. Naji soyayyar Zubaida ta sake taso min a xuciyata. Na sake tuno ranar qarshe da zamu rabu a makaranta. . "yau Kuma ranar rabuwarmu ta zo mansur, mu yafewa juna, sai wata rana..." . Da Alh.Bashir ya ga ta dade a cikin daki bata fito ba, sai ya qwala mata kira da qarfi. Zubaida bata amsa ba, ta fito cikin damuwa,,ta sauya kayan dake jikinta, ta sako wata doguwar riga fara da Kuma dogon siket mai qyalqyali kamar jikin macijiya. Ta xubo da gashin jikin ta kan kafadunta kamar balarabiya. Hakan shi ya sake tuno min da ranar da ta xo wurina ta zauna tana yi min murmushin farin ciki. Da xuwanta ya ce da ita. . "ki tafi dashi ki kai shi dakin da zai riqa kwana, ki yi sauri ki dawo ina son ganin ki." . Zubaida ta wuce gaba, na yi sauri na tashi guiwa ta Babu qwari na bi bayanta tana tafiyar a cikin taqama, muka fita daga falon, naga ta bude wata qofar, muka nufi dakin da za a saukeni. Da shigarmu dakin naga ta juyo ta dube. Muka qurawa juna idanu a lkc guda. Ta ambaci sunana da zazzaqar muryarta. . "mansur!" . "na'am, Zubaida?" . Ta sake ce min..." . "baka samu aiki ba ne tun lkcn da muka gama makaranta me kake yi?" , Nayi ajiyar xuciya, don kuwa ban san abin da ya dake in ce da ita ba." to amma Kuma ai gashi ynx na samu, Kuma na samu masoyiyata da nake ta faman neman ruwa a jallo. Muna nan a tsaye ni da ita.mun yi cirko-cirko a cikin dakin muna kallon juna, sai muka ji mijinta ya fara daka tsawa a fusace. Da yake daga cikin dakin idan mutum ya tsaya a jikin taga zai iya hango komai na cikin falon alhaji ta hanyar wagegiyar tagar falon. Alh.Bashir ya sake daka mata tsawa. . "Zubaida me kake yi ne a dakin? Ba cewa nayi ki kai shi ki yi sauri ki dawo ba? Uban me kuke yi ne a dakin?" . Zubaida tayi sauri ta fice a tsorace. Nayi mamakin ganin yadda take jinjinawa Tsoron shi sai ka ce ba gurgu ba." to amma Kuma da nay la'akari da tarin mmilyoyin kudin da ke shaqare a gidan da kayan alatu burjik a ko ina, bai kamata in yi mamaki ba don ta ji Tsoron shi. . Lp=13Mugun albishir Page 13 . Daga alqalamin shafi'u dauda Giwa . Tare da ni Abu ihsan bn ishak (Madugun taska) . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Bai kamata in yi mamaki ba don ta ji Tsoron shi. . Tun lkcn ban sake jin motsin Zubaida a gidan ba." da lkcn cin abincin dare ya yi Alh.Bashir da kanshi ya qwalla min kira. Na same shi a falon ta jera mashi abinci, ta shiga dakinta ta kulle. Ya umarce ni mu ci abinci tare. Ga alama Alh.Bashir yana matuqar sona. Na sa hannu na muka ci lafiyayyar sakwara da naman shanu zuqa-zuqa a daddadan miyan taushen. To amma har lkcn da muke cin abincin hankali na yana kan dakin Zubaida. Na qosa ta fito don in sake ganinta, zan so ace na sake ganin masoyiyata ba don mijinta dake zaune a falo dare da rana ba." . "..bana son a riqa kallon ta...ina matuqar son matata... . na tuno gargadin shi. . . ** . . Wannan shi ne dan taqaitaccen abin da ya faru a rana ta ta farko a gidan Uban gidana da ya dauke ni aikin tuqa matarsa, ni Kuma tsohuwar masoyiyata Zubaida. Don haka da dare yayi sai naji na kasa barci, xuciyata ta cika da baqin kishi mai tsanani , da Kuma damuwa, da na tuna cewar Zubaida masoyiyata tana cikin daki tare daki tare da wannan lanqwasasshen mutum. To amma Kuma ni menace nawa a ciki? Shin ba mijinta ba ne?" na san cewar tunanin dake a xuciyata ba qaramin wauta ba ne da Kuma shirme. Don kuwa in ba tsabar sakarci ba me zai sa in riqa jin haushin mutumin dake tare da matarshi? . To amma Kuma ya kamata ni ma fa a tausaya min, don kuwa na riga shi fara son ta. Tun muna makaranta nake nuna mata soyayya. To sai dai Kuma soyayya ta banza ce, tunda dai ni ba ni da motoci da gidan alfarma. Ita Kuma Zubaida kyakkyawa ba matar riqaqqen talaka ba ce irina. Ina ma laifi da na samu aka daukeni aikin direbanta? . Ganin cewar barci ya qauracewa idanuna, sai na fito waje cikin tsakiyar dare na zauna ni kadai nayi shiru. . Dole ne in qwace Zubaida daga hannun wannan shashashan gurgun mijin nata. . Dole ne ya sake ta ya bar min ita in aura, ko yana so ko baya so. . Tsawon lkc ina nan zaune kamar a cikin mafarki, sai naji ihun Zubaida a cikin daren ta qwala kuka iya qarfinta. Na tashi xumbur a cikin sauri jikina yana tsima, na nufi inda wagegiyar tagar falon take na leqa. A lkcn ne naga abin takaicin da har abada ba zan ta6a mancewa da shi ba." . Alh.Bashir ne riqe da bulala yake dukan Zubaida. Tana durqushe cikin ladabi akan dardumar falon tana kuka, shi Kuma a zaune dan tsurut akan kujera yana ta tsala mata bulala tana kai hannu tana karewa, tana kuka. Ya zaro mata idanu a fusace ya ce..." . "don ubanki ko mutuwa zaki yi sai na cikashe bulala hamsin din da nayi niyyar yi maki, ina lissfawa ynx talatin da uku nayi." . Ya ci gaba da tsala mata bulala tana noqewa. Ta ja da baya tana sosawa cikin tsananin azaba. Ya ce da ita. . "ki matso in qarishe Sauran bulala shida, arba'in da hudu nayi, ina lissafe." . Naji tsananin takaici ya soki zuciyata. . "shiga ciki ka kashe shi mansur..! . Wata xuciyar ta fara yi min kururuwa. Amma ina kallo Alh.Bashir ya qarishe bulalarsa a jikin masoyiyata Zubaida, Babu wanda zai ceceta. Da ya kammala kanta sai ya wurga mata bulalar yayi murmushin mugunta, ya ce da ita. . "dauki bulalar gata nan ki 6oye min ita, sai Kuma gobe idan lkcn duka ya yi. Tashi ki bani wuri 'yar iska munufukar banza." . Zubaida ta tashi tana sauri da bulalar a hannunta, a haka har ta shige dakinta ta turo qofa ta kulle. Na ji kishi da damuwa sun cika xuciyata. Na san cewar bani da hujjar da zan shiga cikin falon in ce da mijinta wani abu. Don kuwa ko me yayi mata matarsa ce..." ko kasheta yayi ba ruwana. Maimakon haka sai na tsaya jikin tagar Tsawon lkc ina xubar da hawaye. Ina tausayawa masoyiyata Zubaida. . . ** . Washe gari da sassafe na nufi falon Alh.Bashir cikin damuwa. Na same shi a zaune kamar yadda nake tsammanin zan same shi. Na durqusa cikin ladabi na gaisheshi ina kumbure-kumbure,don kuwa da baqin ciki na kwana a raina. Ya amsa yana murmushi, sannan ya ce da ni, da yaga alamar zan tashi in tafi. . "dawo ka zauna mansur, ina son muyi wata 'yar magana ni da kai, zo ka zauna." . Na juyo na dube shi cikin mamaki da Kuma fargaba, don kuwa bana son ya fahimci Akwai wata sanayya a tsakanin da matarsa Zubaida. Na dawo na zauna akan daya daga cikin kujerun falon ina fuskantarshi. Ya kanannade kamar alkaki. Ya tattara hankalisa akaina, sannan ya ce da ni. . "mansur tun lkcn da kaxo gidan nan daga jiya xuwa yau, na san cewar dole ne ka riqa ganin wasu abubuwa Suna faruwa a tsakanina da matata Zubaida, wadanda zasu daure maka kai sosai. Shi ya san nake son muyi hira in baka wani labari, don ka san ko wacece Zubaida. Sannan Kuma ka san ko ni wanene." . Na bi shi da kallo Gabana yana faduwa, don kuwa nima na fara jinjinawa tsoron wannan lanqwasasshen Tsohon mai baqin ran tsiya. To amma Kuma ni ba bulalarsa nake jin tsoro ba, ni bindiga nake tsoro, don kuwa na san cewa a 6oye a jikinshi ba a rasa shi da bindiga. Tabbas ba haka nan yake zaune a falon ba. . "mansur." . Ya sake kirana, na amsa. Ya ce da ni. . "ka ta6a yin aure a garinku ku?" . Na girgiza kai cikin mamakin wannan tambaya. . "A 'a, bani da mata alhaji, daga ni sai halin." . Alh.Bashir ya yi murmushi ya shafi busassun yatsunshi. . "kayi sa"A mansur da baka da mata, don kuwa ynx ne zan baka shawarar irin macen da ya kamata ka aura duk lkcn da ka tashi yin aure." . Ya sake gyara zaman qafafunshi, qafafun wandon suka motsa suka hadu da juna, Babu komai a cikin su." . "Sau da yawa mu maza muna da wani irin halin mansur," . Ya ci gaba da cewa. . "wannan halin kuwa shine, duk lkcn da zamu yi aure muna son mu auri mata kyawawa a duniya wadanda duk inda a shiga zamu a riqa kallonsu anan yawa." . "haka ne alhaji." . na ce dashi. Don kuwa lalla6a shi nake yi don mu rabu lfy, bananas son ya ga kamar na raina shi. . Ya yi min murmushi, sannan ya ci gaba. . "nima ina da irin wannan halin mansur....na ina son in ga na auri mace mace mai kyau a duniya nan...ka . . Lp=14Mugun albishir Page 14 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . Tare da ni . Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . . Ni ma ina da irin wannan halin mansur, ina son in auri mace mai kyau a duniyar nan. Kai bari dai in taqaice maka labari, tun ina yaro kamar ka har tsufana, ni ban ta6a son wata mace ba sai kyakkyawa. Ban damu da kowanne irin halin mace take dashi ba, in dai kyakkyawa ce to ni kam ta gama biyana komai mansur." . Ya sake dubana har cikin idanuna, ya ci gaba. . "wannan shi ne abin da ya sa na kamu da son wannan mata tawa Zubaida. Lkcn da na fara ganin ta ban tsaya wahalar binciken halinta ba, haka kawai sai naji duk duniyar nan babu wacce nake so in mallaka kamarta. Ina son Zubaida sosai fiye da yadda zan fasalta maka. Ina sha'awar in ganni tare da ita a cikin mota ta ta haske ko'ina da kyakkyawar surarta. Ni Kuma ina tuqata muna yawon a cikin jin dadi da kwanciyar hankali." . Alh.Bashir yayi ajiyar xuciya. . "Zubaida kyakkyawa ce, sai dai Kuma halinta bai zamo kyakkyawa ba mansur. Zaka yi mamaki sosai idan na ce da kai Zubaida ce ta mayar da ni gurgu. Shekara uku da suka wuce lfy ta lau, ina da qafafuwa na kamar kowa, ina so ka sani, ba qafafuwa kadai ta so ta raba ni dasu ba, raina ta so ta raba ni dashi mansur. So ta yi ta kashe ni gaba daya!" . Kisa? Na tambayi kaina a tsorace. Kamar ya san abin da nake tunani sai yayi farat ya ce da ni. . "ba lallai ba ne ka amince da labarin da nake baka mansur. Don kuwa nima a wasu lokuta da suka wuce, sanda na fara son Zubaida da aka zo min da labarinta qin amincewa nayi, sbd na mace akan qaunarta. Sai daga baya da abin ya faru gare ni sannan na gano cewar gsky ake fada. Mansur ni ne mijin Zubaida na tara, Kuma duk cikin mazan da ta aura Babu talaka, duk mutane ne masu bilyoyin kudi irina. To amma Kuma ba wannan ne abin mamaki ba, ina son ka sani cewar mazaje takwas na baya da Zubaida ta aura tuni sun riga mu gidan gaskiya. Sun mutu!" . Na sake duban motsattsen mutumin a tsorce. Ya zaro min idanu ya ce. . "qwarai kuwa mansur, sun rasu baki daya. Don kuwa duk lkcn da Zubaida ta auri namiji ba ya wuce wata hudu a duniya, wasu Kuma su kan yi tsawon rai su kai har wata shiga ko bakwa, ba ciwon kai ba na qafa sai a wayi gari a ga mutum ya mutu . To amma Kuma ni duk na fi su tsawon kwana. Don kuwa ni shekararmu uku kenan ni da ita har ynxn ban mutu ba, qafafuwa na kawai na rasa." . Ya yi murmushi kamar abin da ya fada ya burgeshi. To amma Kuma ni ban yi murmushi ba . Ku yi haquri da iya wannan. Sai gobe in Allah ya kaimu a . Page 15mugun albishir Page 15 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . . To amma ni kuma ban yi murmushi ba, don kuwa tsoro ne cike da xuciyata. Dole ne in ji tsoron wannan labarin da na samu, don kuwa ni ina son in aureta . Gashi kuuma tun ba a je ko ina ba na samu wannan labarin wai mazan da take aura mutuwa suke yi. . Na sa hannu na share xufar dake a goshina. Alh.Bashir ya ci gaba da bani labarin . "wani lkcn mu maza muna da matsala mansur.ba mu san halin mata ba amma Kuma su sun san halin mu. Mu maza har Kullum mukan dauki kanmu ne a matsayin mutane wayayyu, don haka ba mu da tsayawa mu yi bincike ba akan mace idan zamu aureta. . Lkcn da na auri Zubaida na rainata mansur, don kuwa ni din nan da kake gani Dakta ne, ita Kuma yarinya ce qarama, ba wani karatun kirki tayi na azo a gani ba, don kuwa ko digiri ba ta yi ba." to amma Kuma sbd tsananinn wayau da makirci, duk da tarin ilimin nawa, wannan bai hana Zubaida ta shirga min maqarqashiya ba." . Ya yi saurin sauya akalar hirar . "bari in baka labarin abin da ya faru a tsakanina da matata Zubaida a lkcn da take so ta kashe ni. . "Alh. Ya kawar da idanunshi daga kaina ya qurawa wani qwan lantarki na gwal ido, sannan ya ce da ni. . "bana kusan shekara uku kenan da yin aurenmu ni da ita. Na fara haduwa da ita ne a wajen wani biki a zariya, duk cikin daruruwan 'yanmatan dake a otel din da aka yi shagalin bikin Babu wacce ta kai Zubaida kyau. Nan da nan na tuntu6eta muka fara hira. Abu kamar wasa tun a ranar farko ta yi min alqawarin zata aure ni, sbd ta san cewar ni ba qaramin attajiri bane. To amma Kuma kafin Zubaida ta yi alqawarin zata aure ni, sai da gindaya min sharudanta, cewar bata zama da kishiya, a lkcn ina da matata mai Suna fiddausi, dawowa ta gida keda wuya na sake ta, muka rabu. Bayan mun rabu sai na kwashe yaranmu biyu na kaisu legas wajen wata qanwata dake zaune a can. Don kuwa Zubaida ta ce min bata son hayaniyar yara a gidanta. Ni Kuma bana son in yi abin da zai 6ata mata rai a rayuwata. Ba a jima ba na aurota mansur, muka zauna kamar da gaske." . Ya ci gaba da kallon bango kafin ya ci gaba. . "bayan an yi wata uku da yin aurenmu, wata rana kwatsam sai Zubaida ta ce min wai zamu yi wata tafiya. Zamu je wani qauye can gariin kakanninta zamu gaishe su." muka shirya tun da sassafe muka shiga mota. A lkcn ne Zubaida ta ce min ita zata tuqa motar wai a cewarta bata so taga ina shan wahala. Ban yi mata musu ba mansur, na bata kan motar, ni Kuma na zauna a gefenta tana tuqa motar ina kallonta, muna hira a haka har barci ya kwashe ni ban sanI ba, don kuwa tafiya ce mai nisa, kuma gashi hanyar qauye ce akwai muka da kwazazzabai." . Alh.Bashir ya yi shiru na dan wani lkc sannan ya ci gaba. . "ina a cikin motar ina barci ban sanin ba mansur, sai Zubaida ta tsayar da motar akan wani tsauni mai bisa, Kuma a gefen tsaunin Akwai wasu manyan ramuka masu girma. Shi ne sai ta fito ta barni a a ciki. Motar ta fara gangarowa baya ita kadai, ba a jima ba ta saki hanya ta fada a cikin qaton ramin dake a gefen tsaunin. . Motar ta tarwatse a cikin ramin, ni dai ban farka ba sai akan gadon asibiti an yanked min qafafuwa. Ita Kuma Zubaida tana can a hannun 'yan sanda Suna tuhumarta a yadda aka yi ta bar wannan hadarin ya faru bata a cikin motar." . Lanqwasasshen mutumin ya dan saki ransa kadan ya dube ni. . "ka san abin da Zubaida ta fadiwa 'yan sanda da suka tambayeta mansur?" . Na girgiza kai a tsorace, xufa na wanke min fuska." . "cewa ta yi wai tana cikin tuqa motar ne sai ta ji fitsari ya kamata, shi ne a cewarta wai sbd tsabar matsuwa ta tsayar da motar ta fito bata kashe ta ba, Kuma bata sa waigi ba har motar ta fara gangarowa da baya. Ita Kuma wai sai sautin fadowarta kawai ta ji cikin rami. "yan sanda basu amince da wannan labarin da ta bayar ba, don kuw duk wanda ya ji wannan labarin ya san na qanzon kurege ne, ta shirya wata hanya ne kawai da zata kashe ni ta kaucewa zargi. To amma Kuma da yake ina matuqar qaunarta ni da kaina na dauki lauyoyi na tura su na ce su kareta, Bayan an gama shari"a an yafe mata, sai na dawo da mata ta Zubaida muka ci gaba da zama a matsayin mata da miji." . Na ji xuciyata tana harbawa fas! Fas! Don kuwa na gama tsorace. Da qyar nake shaqar numfashi. . "anya kuwa masoyiyata Zubaida ita ce take da irin wannan mummunan hali? Me yasa to take son ta kashe mijinta? . Kamar Alh.Bashir ya san tunanin da nake yi sai ya ci gaba. . "ba wani dalili ya sa Zubaida take son ta kashe ni ba mansur, sai don kawai tana so ta mallaki dukiyata ita kadai. Don kuwa ta san sirrin komai na dukiyata. Daga baya na sa an yi min bincike sosai akanta. Duk mazajen da ta aura a baya ita ce ta kashe su." tun tana yarinya matashiya take aure tana kashe mazajen ta. Wani abin takaici a game da munanan halayenta shi ne, Zubaida ta kan yi aure biyu ko uku a lkc daya. Don kuwa mazajen da take aure yawancinsu ba a zaune suke ba 'yan kasuwa ne dake yin kasuwanci tsakanin qasashen qetare. Sannan da na yi bincike akanta ya nuna cewar iyayenta na bogI ne ba na gsky ba ne....! Wasu "yan damfara ne kawai ta samu suke zama matsayinn iyayenta idan zata yi aure, wurin su ake xuwa a daura mata aure. . . Lp=16 Mugun albishir page 16 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak . . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Idan zata yi aure wurin su ake zuwa su daura mata aure." . Wannan labarin dole ne ya tayar min da hankali, don kuwa idan har wadannan halaye sune halayen masoyiya ta Zubaida to tabbas rayuwata tana cikin masifa. Don kuwa ni dai ina sonta ko da kuwa ni ma kashe ni zata yi a ranar da na aureta ba zan iya daina sonta ba." . Alh.Bashir ya ci gaba da cewa. . "mutanen duniya sai dai a barsu wajen neman abin duniya mansur. duk da wannan abu da ya faru wannan "yar talika bata daina qoqarin ganin ta kashe ni ba." Kullum ina lura da ita, so take yi ta kashe ni, Kuma na san cewar yau da gobe bata bar komai ba." wata rana zata kashe ni. Zata yi masara." . Ya sake fadada murmushi ya ce da ni . "shi ya sa ni Kuma na fahimci kudina take so, sbd haka ne nake yi mata dukan kudina Kullum. Don kuwa Tunda ta mayar da ni gurgu, babu wani abu da zan yi a rayuwata in ji dadi, shi yasa nayi alqawarin daga nan har xuwa ranar da zata kashe ni Kullum sai na yi mata bulala hamsin mansur....na kasancewar kome zan yi mata ba zata bar gidan nan ba sai ta cimma burinta. Ina matuqar jin dadin zamana da wannan mata tawa mansur. Kada ka ta6a zaton don so da qauna take zaune da ni alhalin ina gana mata wannan azabar, ni na san Akwai abin da take son ta mallaka a wurina." . Ya yi dariya...Akwai alamar shi kanshi yana matuqar jin dadin wannan labarin da yake bani. To amma Kuma ni dai ban ji wani dadi da wannan labarin yake dashi ba." . Nayi ajiyar xuciya na ce dashi. . "wannan matsalar ka ce kai da matarka alhaji. Bai kamata ka sanar da ni ba." wannan sirri ne da ya shafeka kai da ita. . Ya yi min murmushi sannan ya harare ni. . "kaima ya shafeka mansur." . Na ji Gabana ya fadi. Me ya shafe ni? Na shiga uku, anya kuwa bai fahimci Akwai wata alaqa tsakanina da matar shi ba? . "wannan magana ta shafeka mansur." . Ya sake tabbatar min yana kallona. . "don kuwa a jiya da daddare lkcn da nake dukan matata nayi mamaki da na hangeka a bakin tagar falo kana kuka. Me yasa to kake kuka don kawai kaga ina dukan mata ta, ko kana jin tausayinta ne mansur?" . . ** ** ** . . Wasu tsofaffin mata ne su shida a zaune kowacce ta tasa qatuwar qwarya a gabanta Suna ta amada ba ji ba gani. Ni Kuma ina tsaye a gabansu ina ta kallonsu, gashi dai ina son in taka rrawa, amma Kuma wata qatuwar malum-malum da na jibga a jikina ita ce take rinjayata, ko motsi bana iya yi. Wasu Suna zagaye da ni Suna kallona Suna yi min dariya, waigo ina son in taka rrawa amma Kuma na kasa motsawa. . Ina nan Kuma tare da tsofaffin dake kidan amadar, sai naji sun sake kaurewa da kidan kamar zasu fasa min dodon kunnena. Na ji sautin kidan ya kaure ga Kuma dararrakun da "yan kallo suke yi ya ta"azzara. A daidai lkcn ne na farka a gigice daga barcin da na ke yi. Na ganni kwance a dakin da aka sauke ni matsayin direban Hajiya zubaida. Sai a lkcn ne na fahimci mafarki nayi. . A daidai lkcn ne Kuma naji anan kwankwasa min qofar dakina da qarfi. Na yunqura daqyar na fara qoqarin tare mayafin dake nannade da ni kamar ankwa. Wannan shi ne ya ganar da ni cewa ashes sautin amadar da nake ji ba wasu mata ne ke kidan ba, qofar dakina ake bugawa. San Kuma da na saurara da kyau naji kukan tsuntsaye da tantabaru a cikin daren, sai na fahimci ko shakka babu sune suka zo min a matsayin dararrakun da mutane ke yi min a cikin mafarki. Sannan kuma qaton mayafin da ya taushenni shi ya shiga hana ni in iya motsawa in taka rawa a gaban tsofaffin matan dake buga min amada ba ji ba gani. . Na ji an ci gaba da buga min qofar . . Lp=17Mugun albishir Page 17 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Na ji an ci gaba da dukan qofar, nan da nan nayi sauri na ture mayafin dake lulli6e da ni na sauke daga kan gadon, na lalubi makunnin wutar lantarkin dakin dake jikin bango na kunna, haske ya gauraye dakin. Na duba agogon bango naga qarfe daya da minti bakwai na dare. Na ji tsoro ya sake kama ni. Wane ne yake tashi na a cikin wannan uban daren? Na tambayi kaina, a daidai lkcn ne na isa bakin qofar na sa hannu na dafa ta, aka sake bugawa da qarfi. . "wane ne?" . Na tambaya a tsorace. A daidai lkcn ne naji zazzaqar muryarta Zubaida ta keto daga cikin daren ta yada zango a kunnena. . "bude min mansur, ni ce...." . Shiru ban iya motsawa ba da na fahimci ko wace ce...." Me ya kawo Zubaida dakina cikin wannan talatainin daren? . Ta sake bubbuga qofar cikin qosawa ta ce...." . "ya sauri ka bude min mansur, ni ce Zubaida." . Na bushe a jikin qofar ina xullumin budeta. Don kuwa na san in har mijin ta ya san cewar ta xo dakina a cikin wannan uban daren, to babu abin da zai hana shi ya harbeni a washe gari. Dama daxun ya gama gargadina cewar kada ya sake ganin nayi kuka don naga yana dukan matarsa. . To a qalla dai bai gano cewar masoyiya ta ba ce, sai dai Kuma a halin ynx idan ya ji maganarta a dakina abin da zai yi min ya wuce gargadi. . "mansur ka bude min qofar mana, ni ce Zubaida, Kada ka ji tsoro." . Zubaida ta sake rero min muryarta daga can waje, nayi sauri jikina yana tsima sbd razana na bude mata qofar a rikice. A daidai lkcn da qofar ta bude ne, hasken wutar lantarkin dake a cikin dakina ya sauka akan kyakkawar fuskarta, Kuma a lkcn ne ta saki wani tattausan murmushi a lkcn da muka hada ido ta ganni a tsorace kamar an koro zamo daga rami. Tana sanye da doguwar riga mai ruwan ciyawa, ta lullu6a wani qaramin gyale mai shara-shara a saman wadataccen gashin kanta, Wanda ke motsawa kadan a sakamakon wata qaramar iska da ake yi a waje. . Ganin cewar na bushe a tsaye ina kallon ta, sai ta sawo kai ta shigo kai tsaye bata daina murmushi ba, ta ce min..." . "ba ni wuri in shigo, ina ta faman bubbuga maka qofar kana ji na ko mansur?" . Na kauce na bata wuri ban ce da ita komai ba, na bi ta da kallo a lkcn da naga ta za6i wurin zama a gefen gadon da na tashi Babu dadewa. Nayi qarfin halin tambayaRta. . "Zubaida lfy kika zo dakina a cikin wannan daren? Kuma ba kika jin Tsoron kada ya jiyo muryarki kike daga murya kina surutu?" . Ta ce da ni ba tare da ta sake kallon razananniyar fuska ta ba." . "Babu damuwa mansur." . Ban gane manufarta ba." ganin cewar ban saki jiki da ita ba, sai ta dago kai ta sake kallona ta yi min murmushi ta ce...." . "don allah ka saki ranka mansur, ka cika tsoro, sai ka ce ba namiji ba." tun da na ce maka ba matsala. Ya yi barci, ba zai farka ba sai gobe da safe." . Nayi ajiyar xuciya sannan na dan ji sanyi a raina, don kuwa na gama tsorata da wannan mijin nata. Ina kyautata zaton yafi ni son Zubaida dari bisa dari. Ta sake cewa da ni. . "yau tun da wuri ya buge ni mansur, shi yasa yayi barci tun daxun, Kullum sai ya zane ni da bulala. Haka rayuwata take kasancewa, Babu yadda zan yi sai dai haquri." . Na ji tausayinta ya kamani a lkcn da naji tayi wannan maganar, musamman ma da naga tayi shiru tana tunani. na bi ta da kallo tsawon wani lkc, ban san abin da take tunani ba." ni Kuma ban tambayeta ba." xuwa can Kuma sai ta yi ajiyar xuciya ta ce da ni. . "zauna mansur, Akwai maganar da nake son muyi ni da kai, shi yasa Kaga na zo wurinka a daidai wannan lkc. Kada ka zargeni, ba wani abu yasa ka ga naxo dakinka ba." . Na samu wuri a gefen katifar dake kan gadon na zauna, nesa kadan daga inda Zubaida take zaune. To amma Kuma tazarar dake a tsakaninmu bata hana ni shaqar qamshin dake a jikinta ba, Wanda na rasa gane ko qamshin mene ne a tsakanin turare da man shafawa. To amma Kuma ko ma dai mene ne, ni dai ya burgeni. Don kuwa duk ya cika dakin kamar qamshin dakin amarya a qasarmu ta hausa. Na tuno zamanin da ta zo wurina ta zauna. . "....ga alama kaima irina ce...." . Zubaida ta katse min tunanin da na fara ta juyo ta dube ni da fararen idanunta, hannunta daya na dafe da gyalen da ta yafa akanta. Ta ce da ni. . "naxo wajen ka ne akan wata magana da naji mijina ya sanar da kai daxun da safe. Ina raku6e ina jin ku, ina jin duk abubuwan da ya fada maka mansur....na san cewar ynx fahimci kai duk ka amince da wannan sharrin da yayi min ko mansur? ta ci gaba da kallona don jin abin da zan ce...." . Nayi saurin girgiza kaina, da naga bata dauke idanunta akaina ba." . "ko kusa ban amince da wannan labarin ba Zubaida. Don kuwa tun muna makaranta na san cewar ke macece mai kyawawan halaye da mutunci. Ba zai ta6a zama gsky ba ace ke ce ke da irin wannan halin, tun daxun da ya bani labarin ni tunic na mance da maganar, in dai wannan shi ne abin dake damunki kika kwantar da hankalinki, har abada Babu wani mahaluqi da zai tunkare ni da irin wannan mmaganar a game da ke in amince." . Zubaida ta dan saki ranta a lkcn da na kai qarshe. Ban sanin ba ko don ta ji dadi na yabeta shi ya san ta mance ta saki dan figigin mayafin dake lulli6e da kanta. Ta yi sauri ta sake jawo shi ta dora a saman gashinta, Wanda yake ta sheqi a cikin hasken dake dakin aduk lkcn da ta motsa. . "na gode sosai mansur." . Ta ce da ni. . "naji dadi da ban same ka a cikin mutanen da suke dora min zargi akan abin da ban aikata ba." Sau da yawa ina mamakin halin wannan mijin nawa mansur....ba ya kyautata min, baya gani na da mutunci, shi a tunanin sa waigo Kullum kashe shi nake so in yi. To akan me zan kashe mijina ina da hankali mansur? . . Lp=18mugun albishir Page 18 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . To akan me zan kashe mijina ina da hannkali mansur? Wannan hadarin da ya baka labari, ba laifina ba ne tsautsayi ne....! Amma Kuma ya qi ya gane . Akan haka ne yake min irin wannan cin mutuncin, Kullum sai ya buge ni kafin in kwanta barci. Wai shi ba zai barni in zauna haka ba, tunda dai na jawo mishi ya zama gurgu babu abin da zai iya yi, a Maimakon haka yake yi min bulala hamsin a kowacce rana kafin in yi barci, sbd tsabar zalunci." . Zubaida ta saurara tana qoqarin mayar da numfashi, don kuwa Akwai alamar bata son tuno da al"amarin. Na gane haka ne da naga tana fadin maganar cikin fushi da Kuma sauri. Nayi sauri na kwantar mata da xuciyarta na ce da ita. . "ku yi haquri Zubaida matsalar zaman aure kenan sai haquri. Kin san wasu maxan haka suke yiwa matansu irin wannan wulaqancin da Kuma cin zarafin. Gsky bai kyauta ba, amma Kuma idan baki da alhakinshi wata rana zaki ga sakayya, in allah ya so zaki rabu dashi ki samu wani dan arziqi da sanin ya kamata ki aura." . Na fada mata haka ne don tun ynx in gyara tawa gwamnatin. Ina son in nuna mata kuskurenta ne da ta auri wannan Tsohon mai kudin ta bar yaro dan zamani irina. (amma Kuma talauci kamar 6eran maSallaci). . A cikin sa"a Kuma sai Zubaida tayi tsaki ta ce da ni cikin damuwa. . "na gama tsorata da halin maza mansur.ni ynx Babu wani abu da namiji zai fada min in yardda dashi. Don kuwa na sha wahalar aure ba Sau daya ko sau biyu ba." duk maza haka kuke mansur, halinku daya." . Na ji tsoro ya kama ni na ce da ita . "ba haka ba ne Zubaida. Wlh ba halinmu daya ba." Akwai masu hankali. Ke dai kawai ba ki yi dace bane. Amma ki qara jarraba ko da mutum daya ne ki gani a nan gaba." . Na qura mata ido ina qoqarin karantar abin dake kan fuskarta. To amma Kuma da naga ta fara sakin ranta, sai naji dadi a raina. Don kuwa ina so ne in riqa kushe mijinta don ta yi qoqari su rabu, daga baya Kuma ni in zagaya in aureta. . Ta sake yin ajiyar xuciya, sannan ta yi tagumi tana kallon dardumar dake a malale a tsakar dakin, sannan ta ci gaba da cewa. . "wannan hadarin da ya faru kamar inda ya sanar da kai, ba a fi wata uku ba dayin aurenmu, sai naga cewar ya kamata mu je wani garin kakannina don na gaishesu Kuma su ga mijina. A ranar da zamu yi tafiyar tun da sassafe muka shirya muka shiga mota muka tafi. Ganin cewar ni na san garin, sai na amshi tuqin motar shi kuma mijina ya zauna a daya 6angered. Muna tafiya muna hira, har barci ya kwashe shi, na ci gaba da tuqin ni kadai ban tashe shi ba." . Zubaida ta jawo numfashi cikin damuwa sannan ta ci gaba . "ina cikin tuqa motar sai na ji fitsari ya kama ni mansur, nan da nan sai na rage gudu, nayi fakin na tsayar da motar a gefen wani qaton rami mai kama da rafi a gefen titi, sannan tsabar matsuwar da nayi sai na mance na fito ban bar motar a giya ba, Kuma ban sanya birkin yin fakin ba." gashi Kuma a saman tsauni ne, ban sani ba a lkcn da na juya baya na tsuguna ina fitsari ashe motar ta fara gangarowa tana komawa baya,sannan Kuma ba wani waigi da zai tare ta a gefen titin." . Muryar Zubaida ta fara rawa, sannan Kuma ta fara shassheqar kuka. Na qura mata ido ko qiftawa bana yi, a lkcn ne ta ci gaba da bani labarin. . "ban ankara ba mansur, sai na hangi motar ta tunkari qaton ramin dake a bakin titin, ta fada ciki. Ina kallon lkcn da motar tayi qundunbala Sau biyu ta fada qasa ta hadu da duwatsu ta tarwatse. Ba zan ta6a mancewa da irin mugun sautin da na ji ba a lkcn da motar ta tarwatse a cikin ramin. Mijina yana ciki yana barci. Na taso a tsorace ina kururuwa ni kadai a cikin naji mansur, Bayan motoci sun tsaya mutane sun taru, sai aka ciro motar aka bude aka fito da mijina jina-jina bai san inda yake ba, amma Kuma mun yi sa'a, bai mutu ba." da aka kai shi asibiti ne suka yanke masa qafafuwa don kuwa sun yirugu-rugu. Bayan ya yi watanni yana jinya sai muka dawo gida. Tun daga wannan lkcn bamu sake zaman lfy ba a gidan nan. Kullum sai ya ci min zarafi ya zazzage ni, Kullum sai ya dauki bulala ya dake ni akan abin da ba laifina ba ne....! A haka muke zaune tsawon shekaru biyu da suka wuce..." . Ta fashe da kukan baqin ciki, Wanda wannan shi ne ya tilasta mata dakatar da labarin da take bani. Ta sunkuyar da kai tayi tagumi, daga inda nake zaune ina iya hango hawayen dake cinye gudu a kumatunta. Na ji tausayinta ya kama ni fiye da Kowanne lkc a rayuwata. Sautin kukan ta ya ci gaba da fita Sannu a hankali a cikin daren ina zaune ina saurarenta. Takaici da baqin ciki ya sake kama ni, don kuwa na san cewa Zubaida masoyiya ta tana cikin wani qangin rayuwa, Wanda in har da gasske ina sonta to ynx ne lkcn da zan nuna mata irin wannan soyayya dake a xuciyata . Ya zama dole in raba ta da wannan azzalumin mijina nata Wanda yake yake azabtar da ita dare da rana. Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da ita . "Kada kina damu Zubaida kina yi haquri, komai na duniya yana da iyaka. Kamata ya yi kina kai shi qara a raba kina dashi, Kada ya halaka kina da irin wannan zaluncin da yake yi ciki Kullum." . Tsawon wani lkc Zubaida bata ce min komai ba, ta ci gaba da kusa kukanta kamar ba ta ji ni ba, xuwa can Kuma sai ta bani amsar maganata, ta ce da ni cikin kuka. . "Akwai lokuta da damar da nake yin shawarar in gudu in bar shi, sai dai Kuma idan nayi la'akari da halin da yake ciki sai in ga cewar bai kamata in gudu in gudu in Bashir ba." don kuwa ko ba komai ni ce silar matsalar da ta same shi har ya naqasa ya zama gurgu." . Na ce da ita cikin lallaShi . "kina daina damuwa Zubaida. Abin da ya faru ba laifinki ba ne....! . . Lp=19mugun albishir Page 19 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ba laifinki ba ne.tsautsayi ne, Wanda zai iya faruwa da kowa a duniya, ko kina a cikin motar, idan allah ya qaddara wannan abu zai faru dole sai ya faru." . Zubaida ta share hawayen dake a idanunta, a wannan lkcn gyalen da yake rufe da gashin kanta ya sa6ule ya gangaro kan kafadunta, amma Kuma bata damu ba, a lkcn da take share hawayen ne gashin kanta ya fara qyalqyali a cikin hasken dakin. Ta ce da ni. . "na san tsautsayi ne, to amma Kuma shi har abada ba zai gane hakan ba." duk lkcn da ya hadu da mutane sai ya basu wannan labarin da ya baka. Ba komai zan ci gaba da zama dashi, har xuwa lkcn da mutuwa zata raba mu. Ba zan iya guduwa in bar shi a cikin wannan halin ba." don kuwa ni ce nake daukar duk dawainiyarsa tunda baya iya tashi ya yi wani abu da kanshi, komai sai dai in yi mashi." . Na ji kishi mai tsanani da takaici ya sake kama xuciyata. Don kuwa duk wannan baqar wahala da Zubaida take sha a wurin mijinta, ba ta so ya rabu da ita. Tana son zama dashi a haka. Naji duniyar tayi min qunci, don kuwa na fahimci babbar matsalar da zata yi min cikas wajen mallakar Zubaida ta zama matata, bai wuce wannan shashashan gurgun mijin nata ba dake zaune a falo a kan keken guragu. Nayi qarfin halin tambayarta. . "to amma ke kina jin ya dace ki yi ta zama da mijin da baya sonki har qarshen rayuwa Zubaida?" ya kamata ki yi tunani sosai, ya kamata ki yi qoqari ki rabu dashi don ki samu wani mijin Wanda yake sonki Ku yi aurenku na soyayya ba irin wannan ba." . Zubaida tayi shiru tana kallon bangon dakin tana tunani, bayan wani lkc sai ta ce da ni. . "wannan shawara ce mai kyau mansur. Idan har mijina ya mutu ba zan sake auren wani mai kudi ba." na gwammace in samu wani Saurayi sabon jinni in aura, yaro matashi dan zamani Wanda zamu yi soyayya, ni ynx ba kudi suka fi damuna ba a rayuwata na fi so in samu nutsuwa da kwanciyar hankali tare da masoyina." . Na ji farin ciki da xumudi sun kamani, don kuwa Zubaida ta ta6o layina. Ta ta6o min 6angaren da ya fi qaiqayi a xuciyata. Idan har ta amince zata auri Saurayi dan gaye, dan zamani, to babu abin da zai hana in aureta. Wannan wata dama ce a garre ni. To amma Kuma ta ce wai sai mijin ta ya mutu, sannan zata sake yin wani auren, sai yaushe wannan mijin nata zai mutu? . Nayi saurin dakatar da tunanina, na tambayata. . "Zubaida kin san lkcn da zai mutu ne da zaki fadi haka? Me yiwuwa ya qara lkc mai tsawo ba ki sani ba..." . Ta yi murmushi a karo na farko tun sanda ta kammala bani labarin hadarinsu da mijinta. Sannan ta juyo ta dubeni muka hada ido. Duk dna uban kukan da ta ci idanunta Suna nan tarwai farare. . "Kada ka yi mamaki don na fadi haka mansur, mijina ya kusa mutuwa, don likitoci sun aunashi, Kuma sun fadi mani iyakar adadin kwanakin da zai iya qarawa a duniya." . Zubaida ta miqe sannan ta jawo gyalenta ta dora a saman lallausan gashin kanta, ta ce da ni. . "zan koma daki in kwanta mansur, na gode sosai da 6ata lkcn ka da kayi ka saurare ni, Kuma na gode da shawarwarin da ka bani, sai da safe." . Zubaida ta nufi qofar dakin cikin taqama, na miqe cikin sauri na bi bayanta na ce da ita. . "Zubaida baki fada min lkcn da likitoci suka ce zai qara a duniya ba." ki fada min don allah, kwanaki nawa likitoci suka ce zai qara a duniya?" . Zubaida ta dafa qofar dakin da hannunta sannan ta juyo da fuskarta ta dubeni, ina kidime cikin qosawa, ta yi min murmushin soyayya sannan ta ce da ni. . "Kada ka damu mansur, ba wani lkc mai tsawo suka ce zai qara ba, sun yi min albishir mai kyau. Sun ce mijina ba zai wuce shekara talatin ba a duniya . Zubaida ta fice ta barni a tsaye kamar an dasa ni, naji sautin tafiyarta a cikin sauri a lkcn da ta nufi dakinta.. Har xuwa lkcn da na daina jiyo tafiyarta qwaqwalwata a rikice take, kamar Wanda aka yi wa albishir da xuwanka barzahu. . . ** ** ** . . Akwai wani zamani da ya wuce kafin in fara ganin kyakkyawa Zubaida, an sha fada min cewar soyayya ta kan san mutum ya fita hayyacinsa, idan Kuma abin yayi nisa wasu an ce har haukacewa suke yi. An sha fada min cewar Sauran da yawa akwai mutanen dake fadawa tarkon soyayya har su aikata abin da ba a yi tsammanin mutum mai hankali zai aikata irin shi na. . A zamanin da naji zantukan ban amince da su ba." ni a tunanina haukar soyayya ba gsky bane. Ban ta6a yarda cewar mutum zai iya fita a hayyacinsa ba don kawai son wata mace. . To amma Kuma a halin ynx da son wannan kyakkyawar mace Zubaida ya kama ni, bani da wani aiki dare da rana sai tunaninta, sai na fara tunanin haqiqa nayi kuskure a shekarun baya, sannan Kuma na yi wa soyayya mummunar fahimta, a halin ynx kam na san yadda soyayya take burkita tunanin ma'abocin yin ta, kamar yadda ta burkita nawa tunanin, gashi ynx idanuna sun makance Zubaida kawai nake son in gani a duniya. . Duk wannan tunanin nayi shi ne a lkcn da nake tsaye a cikin dakina ina tunanin maganar da Zubaida ta sanar da ni, sannan Kuma ta fice ta barni a cikin xullumi da wasi-wasi . Wannan maganar da ta sanar da ni ba wani albishir ba ne mai dadi. Sai dai in kira maganar da Suna [Mugun Albishir] . Haqiqa wannan mugun albishir ne, don kuwa idan har a cewarta ba zata iya rabuwa da mijinta ba sai lkcn da ya mutu shi Kuma ba zai mutu ba sai ya qara shekaru talatin a duniya, shakka Babu rayuwata tana cikin hadari . Ba zan iya tsayawa ina kallonshi har nan da shekara talatin ba ina kallonshi . "ba wani lkc mai tsawo likitoci suka ce zai qara ba, sun ce ba zai wuce nan da shekara talatin a duniya ba...." . Na sake tuno maganar Zubaida. Ban san lkcn da hawayen baqin ciki ya fara sartu akan fuskata ba." . . Lp=20mugun albishir Page 20 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ban san lkcn da hawayen baqin ciki ya fara sartu akan fuskata ba. Na yi ajiyar xuciya sannan na motsa jikina dake a bushe tun tafiyar Zubaida. Na koma na nufi gado. Da zaunawata sai na kwanta cikin damuwa na qurawa sararin samaniyar dakin idanu, ina tunanin hanyar da ya kamata in dauka don mallakar Zubaida. To amma Kuma tsawon lkc ban gano wata sahihiyar hanya mafi sauqi da zan bi in auri Zubaida ba." sai shekaru talatin masu xuwa. . Shin mene ne jin dadin rayuwa idan har xuciyata bata cikin sukunni? na san cewa idan har ban auri wannan masoyiya tawa ba, har abada ba zan sake samun sukunni a xuciyata ba." gashi Kuma ba ni da wata hanya da zan bi in aureta. A halin ynx matar wani ce, Kuma ba zai iya sakinta ba har abada, ita ma ba zata iya bijire masa ba su rabu, sannan Kuma ana tsammanin ba zai mutu ba sai nan da shekaru talatin masu xuwa. Kuma zai iya kasancewar in zauna in jira shi har xuwa lkcn, daga baya Kuma ya xo bai mutu ba, wa ya sani ma ko wataqila ya qara shekara saba'in a duniya? Ko Kuma ya mutun, ta auri wani daban ba ni ba? Sai tsoro ya sake kamani sannan Kuma takaici mai tsanani ya sake mamaye xuciyata. . Dole ne in sake dabara! . Na tabbatar wa kaina. Ya zama dole in bi duk hanyar da zan bi don in samu nasara idan har ina son in auri wannan tauraruwar mace mai qyalqyali kamar daimon. . A lkcn ne mugun tunanin da ya zamo musabbabin ruguza tarihin rayuwata ya fado min a xuciyata. Wannan shi ne karo na farko da na fara tunanin kashe mutum. ' tabbas ya zamo mani dole in kashe Alh.Bashir!' . Na yi mamaki da na ji cikin qanqanin lkc xuciyata ta gamsu da wannan tunani mara kyau. Don kuwa a rayuwar da nayi a can baya ni mutum ne mai tausayi da Kuma tsoro. Ko kiyashi bana iya kashewa, to amma sai gashi ynx zamani ya xo, sbd wata mace guda daya har na fara tunanin kashe mutum ba ma kiyashi ko dan tsako ba." xuciyata ta ci gaba da ingiza ni tana yi min kururuwar shaidan . 'yi sauri ka je ka kashe shi mansur! Idan har ka barshi a raye to har abada ba zai ta6a rabuwa da Zubaida ba." Kuma ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya, ka yi sauri ka je ka kashe shi don ka mallaki kyakkyawar masoyiyarka wacce ka ke so shekara da shekaru. . Tunane-tunane barkatai mara san kyau suka cika min qwaqwalwa. Na tuno zazzaqar muryarta da Kuma kyakkyawar surar jikinta. Xuciyata ta wassafa min lkcn da za a ce gashi an daura aurenmu ta zama mata ta. . "idan har mijina ya mutu ba zan sake aurenmu wani mai kudi ba." na gwammace in sami wani saurayi sabon jini Kuma yaro dan zamani wanda zamu yi soyayya . Wannan shi ne albishir din da Zubaida ta yi min, Kuma na sannan cewar da ni take. Bata so ne ta fito fili ta sanar da ni, sbd tana jin kunyata. To amma Kuma Babu komai na gane hakan da kaina. In dai saurayi take so dan zamani, idan ba kudi da motoci take so ba....to ta samu abin da take so. Ynx kam ya rage nawa in yi sauri in je in kashe mijinta. Don wannan albishir da tayi min ya zama gsky. . Na tashi xumbur, kamar Wanda aka cakawa allura na sauko daga kan gadona, na bude qofar dakin na fice waje a fusace, xuciyata na tafarfasa na nufi falon da Alh.Bashir gurgu yake babu alamar tsoro ko fargaba a tare da ni, don kuwa na qosa in ga ya mutu. . . Lp=21 Mugun albishir Page 21 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Na nufi falon Alh.Bashir gurgu Babu alamar tsoro ko fargaba a tare da ni, don kuwa na qosa in ga ya mutu. Babu motsi ko sautin wani abu da ake iya ji a cikin gidan face kukan tsuntsaye da ke wasanninsu akan bishiyoyin dake a can wajen gidan da Kuma wadanda ke shigowa Suna guje-guje akan qananan shuke-shuke. . Na san cewar tuni Zubaida ta kwanta ta yi barci, da wahala ta ji motsina a lkcn da na shiga falon. Na rage saurin da nake yi na fara tafiya Sannu a hankali ina sanda a cikin daren, kamar 6arawon tantabaru. Na tura qofar gilashin falon a hankali ta bude ba tare da tayi wani motsi Wanda zai iya farkar dashi daga barci ba, na shiga cikin falon, duk an kashe qwayayen babu wani haske, hakan bai hana ni ganin inda alhaji ke kwance ba akan doguwar kujerar dake a falon inda yake kwana ya wuni a zaune. . Na san cewar barci yake yi, to amma Kuma duk da haka idan nayi motsi qwaqqwara me yiwuwa ya tashi a firgice, Kuma idan har na sake ya farka ya ritsa ni, a cikin dare irin wannan a falon shi, to kashina ya bushe, domin ina zargin ba za a ta6a rasa shi da bindiga a 6oye ba." Kuma kai tsaye zai harbeni, don kuwa ya san cewar in dai har ina da gsky to Babu abin da zai san in shigo falon ina sanda da qarfe kusan biyu na dare. . Da nayi wannan tunanin sai nayi sauri na qarisa inda yake kwance ya miqe ya bi tsawon kujerun kamar matacce, ko numfashi baya yi, to amma Kuma ni dai na san cewar barci yake yi. . Ban tsaya jiran komai ba sai nayi tsalle na cafi wuyansa da kanshi, cikin sauri na murde wuyansa ya karye, naji sautin karyewar qashi kamar an 6allah sillan kara. Nayi mamaki sosai da naga bai motsa ba, Kuma bai farka ba yana a kwance kamar mushen zakara. To amma Kuma wannan bai karya min guiwa ba, ya riga ya mutu. Da wahala a karya wuyan mutum Kuma ya qara shekara talatin a duniya . Na yi sauri na ja da baya na fara shirin ficewa daga falon, xufa na kwararo min ta ko ina a jikina. Don kuwa nayi abin da ban ta6a yi ba a duniya. Sannan Kuma abin da ban ta6a tsammanin aikatawa ba." . Na kashe mutum!! . Nayi saurin bude qofar na fice xuciyata tana rufdugu kamar ana daka lura a cikin ta. Na koma dakina na shiga na rufe qofa na zauna a bakin gadona ina mayar da numfashi. duka-duka abin ya faru ne a cikin dan lkc qanqani, xuwan Zubaida dakina da Kuma ficewarta, sai Kuma xuwana falon, kashe mijinta da Kuma dawowata. Abin kamar aikin bude idanu. Ko shakka babu abin da ya faru ya faru. Na kashe mijin Zubaida Alh.Bashir mutumin da ya daukeni aiki. Kuma yayi alqawarin zai kyautata min a rayuwata in har na riqe mashi amanar matarsa. Haqiqa ban yi amana ba, Kuma ban riqe alqawarin ba." wannan wani abu ne Wanda zai zauna min a xuciyata ya yi ta bi na a duniya yana damuna shekara da shekaru masu xuwa. . Da naji zafi ya dame ni sai na kashe wutar dakina na zauna a cikin duhu, nayi tagumi. Ni kaina na san cewar nayi abin da baiwa dace ba." nan da nan naji tsoro ya kamani, da na tuna cewar a halin ynx muna tare da gawa a cikin gidan. Duhun da nake ciki da Kuma talatainin daren da ake ciki su suka sake taruwa suka iza wutar fargabar da nake ciki. . Na san cewar Babu wani maganar barci, don haka sai na ci gaba da zama ni kadai a cikin daren ina wasi-wasin halin da abin da na aikata,sannan Kuma a lkc guda ina addu'ar allah ya mallaka min wannan masoyiya tawa da nake ta so shekara da shekaru wato Zubaida. Gara in roqi allah, don Kada in yi wannan mugun aikin a banza. . . ** ** . . Wani zakara mai zaqin murya ya kwantsama cara iya qarfin sa ta karade kusan ko ina a unguwar. A daidai lkcn ne Kuma na jiyo daddadar muryar Zubaida ta kwantsama tata carar ta 6urari ita ma iyakar qarfInta . "wayyo allah na shiga uku na lalace....alhaji...?" . Na ji gabana ya fadi ina zaune nayi tagumi, na san cewar asuba ta yi. Zubaida ta fito zata yi alwala kenan Kuma ta tsinci gawar mijinta a falon yayi kwanan Keso. . Na san cewar idan har ban tashi na je na ga abin da ya faru ba, me yiwuwa ta zargeni, sai nayi sauri na tashi na bude qofar dakina a cikin sauri na nufi falon, daidai lkcn ne na ci karo da mai gadi ya shigo cikin gidan a guje riqe da kwari da baka a hannunsa, kamar Wanda zai je farautar ragon maza. Muka fada cikin falon a lkc guda ni da shi. A lkc ne muka samu Zubaida ta durquusa a gaban gawar mijinta tana kuka kamar ranta zai fita. . "hajiya lfy? Me ya faru?" . Dan Tsohon dake gadi ya fara tambayarta a tsorace. Zubaida ta ce dashi tana 6urari. . "alhaji ne ya rasu, yi sauri ka yiwa 'yansanda waya su zo falalu." . Dan tsohon ya saki kwari da bakar hannunsa yana kyarma, yana qoqarin motsa baki . Wataqila Kuma yana qoqarin tuno wata addu'a ce da ya dade da mancewa, Zubaida ta sake ce mashi a fusace. . "ka yiwa 'yansanda waya su zo ko baka ji ba ne?" . Dan tsohon ya dan murmure yana inda-inda, yayi sauri ya fice daga falon yana mis-mis da baki. Nayi ajiyar xuciya sannan na durquusa kusa da Zubaida, ina kallon gawar Alh.Bashir yana kwance kamar yadda na barshi jiya da dare. Na ce da Zubaida . "ya kamata kina daina kukan haka nan, don kuwa kowanne mai rai mamaci ne, ki daina kukan, addu'a ya kamata ki yi masa.' . Zubaida ta sassauta kukan da take yi, sannan ta kawar da kai cikin damuwa, tana sanya da doguwar rigarta ta daren jiya, amma Kuma a wannan karon ba gyale ta yaro ba, dankwalin rigar ta daura Wanda aka qawata shi da adon wasu dinkakkun furanni a saman goshinta. Ban san me yasa take jin kunyar hada idanu da ni ba." Babu mamaki Kuma me yiwuwa tana zargin ni na zo na kashe shi cikin daren. To koma dai me zata yi tunani aikin gama ya riga ya gama. Shekaru talatin sun zo qarshe. . Ta ce min ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya, shi ya sa ni Kuma na dan rage yawansu suka qare a cikin dare daya. Don kuwa na qosa in aureta, na qosa ta zama mata ta. . Tsawon lkc muna a durqushe ni da Zubaida mun tana gawar gabanmu, ita Kuma tana shassheqar kuka. Xuwa can sai muka jiyo sautin jiniyar motar 'yansanda ta shigo cikin gidan. Nayi mamaki da naga har ynx Zubaida bata daina kuka ba, sai ka ce tana baqin ciki da mutuwarshi, sai ka ce ba shi ne yake jera mata bulala hamsin ba Kullum a gadon bayanta kafin ta kwanta barci. . 'Yansanda hudu suka shigo cikin falon sanya da baqaqen kaya, Babu alamar wata damuwa a fuskokinsu. Muka jiya muka dube su. A lkc ne na miqe tsaye na basu wuri, suka kalle ni a lkc guda sannan suka mayar da hankalinsu akan gawar Alh.B. Wani a cikinsu ya tambaya. . "muna Fatan dai Babu Wanda ya ta6a gawar a cikin Ku?" . . Lp=22mugun albishir Page 22 . daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . "muna Fatan dai babu Wanda ya ta6a gawar a cikin Ku?" . Zubaida ta girgiza kai tana shassheqar kuk, ni ne samu damar yi musu magana. . "Babu wanda ya ta6a gawar shi, a haka muka same . Wanda ya yi tambaya da farko ya sake cewa. . "shi kenan, kuna iya tafiya, amma kada Kuma yi nisa domin bayan mun gama binciken akwai tambayoyi da zamu yi maku." . Nayi sauri na fice daga falon, don kuwa xufa nake yi, duk iskar safiyar da ake busawa. Na san cewar idan har 'yan sanda suka yi la'akari da yadda na rude, me yiwuwa asirina ya tonu su gane ni na kashe mijin Zubaida . Na fita waje naga tuni gari ya waye. Na hango Falalu mai gadi raku6e a jikin falwayar da ta shigo katafaren gidan inda mai gadi yake zama. . Da gani na ya yi sauri ya tarbeni ni kamar Akwai wata magana da yake so ya sanar da ni. Muka hadu ni dashi har ynxn baiwa daina karma ba, Kuma Akwai alamar hawaye a cikin busassun idanunshi. . "Mansur." . Ya kira suna na. Ban yi tsammanin ya riqe suna na haka ba, don kuwa kwana na biyu kawai a gidan, Kuma tun xuwa na ban fito mun yi hira ba." Me zai sa in fito, tunda dai muna tare a ciki ni da masoyiya ta? . na amsa kiran da ya yi min, na ce dashi. . "Baba sai haquri ka daina kuka, shi dama rai baqon duniya ne, idan lkc ya yi sai tafiya. . Tsohon ya share hawaye ya ce da ni. . "wannan gsky ne mansur, to amma dole ne in yi jima da wannan rasuwa ta alhaji. A ce abu cikin dare daya ba ko ciwon kai ba na qafa.." . Ya sake rikicewa yana qoqarin gyara tsayuwa, don kuwa duk ya birkice, kamar Wanda aka dora shi akan bishiyar macizai. Na ce dashi. . "idan kwana ya qare ko babu ciwo sai an je baba. Sai dai a yi mashi addu'a" . Akwai alamar zargi a xuciyar Tsohon, na gane haka ne da naga ya yi saurin waigawa duk wani 6angare na gidan. Da ya tabbatar Babu Wanda yake saurarenmu sai ya yi qasa-qasa da muryarshi ya ce da ni. . "Mansur ina zargin hajiya. Da wahala idan ba ita ce ta kashe alhaji ba, don kuwa dama ana zarginta ta ta6a yunqurin kashe a lkcn baya. Domin kuwa ta ta6a jefa shi cikin rami a mota, a dalilin haka ne ma ya zama gurgu. Dama can tana son ta kashe shi." . Daqyar na kawar da fushin dake xuciyata, don kuwa Tsohon ya gama qule ni. Bai san irin son da nake yi wa Zubaida ba, shi ya sa yake gulmarta a gaba na, amma don Kada ya yi zargin wani abu sai na ce dashi. . "Babu mamaki Kuma ba ita din ba ce, don kuwa idan kwana ya qare ko ba a kashe mutum ba, shi da kan shi ma zai iya faduwa ko Babu ciwon kai ba na qafa." . Da dan Tsohon ya ji na kare Zubaida sai ya yi gum da bakin sa, yayi shiru yana girgiza kai, muka yi tsaye mu biyu kowa yana tunanin da ya dame shi. Na san shi tunanin mutuwar mai gidan sa yake yi, ni Kuma lissafin kwanakin da Zubaida zata yi kafin ta gama takaba nake yi. . Bayan wani lkc sai na hangi Zubaida ta fito daga cikin gidan ranta a 6ace, ga alama ni take nema. Don kuwa da fitowarta ta tsaya tana dube-dube, da ta hango ni tare da mai gadin a tsaye bakin qofa sai ta yafito nI da hannunta. Na bar dan Tsohon na nufi inda take cikin sauri. Da xuwa na ji ta ce da ni a sanyaye. . "ka shiga ciki. 'yansanda ne suke son ganin ka, ni na gama amsa nawa tambayoyin." . Na dubi Zubaida sosai, tana nan a cikin damuwa, Kuma da alama kamar tana fushi da ni, sai ka ce nayi mata laifi . Sai ka ce ba mijinta kawai na murde wa wuya ya mutu ba." . Na shiga cikin gidan kai tsaye na cire duk wata alama da zata san 'yan sanda su gane bani da gsky a fuskata. Na saki 'yan sanda su hudu a falon suna jira na kamar kuraye sun samu tunkiya. . Sun yi min tambayoyin da ban san iyaka ba." har da tambayar yadda aka yi aka haifeni? To Amma Kuma amsa daya na tsaya mawa. Ni baqo ne a gidan, ban san abin da ya faru ba." na kwanta barci da wuri, Kuma na farka da safe naji matar gidan tana 6uurari waigo mijinta ya mutu. Dole akan haka suka rabu da ni, tunda dai ko maqure ni zasu yi ba zan tonawa kaina asiri ba in ce ni na kashe shi. Na bar su a cikin falon suna gwaje-gwajen su na al'ada, a lkc da na fita waje ne naga wata doguwar farar motar asibiti ta daukar gawa ta shigo gidan. Ta yi fakin , wani likita ya fito dan sirri sanye da farar riga da Kuma farin tabarau, wasu qananan likitoci biyu Kuma suka biyo bayan shi suka fito da wata makarar asibiti ta qarfe. . . a lkcn da na wuce cikin faffadar farfajiyar gidan ne na hango Zubaida a cikin mota daya daga cikin motoci biyar din dake qyalqyali a cikin hasken safiyar. . Zubaida ta tayar da motar, sannan ta tuqo ta cikin sauri, ta zo daidai inda nake tsaye ina kallonta. Ta dube ni sannan ta ce. . "shigo mu tafi." , Na tsaya sororo ina kallonta... . . Lp=23Mugun albishir Page 23 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak Madugun taska . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Na tsaya sororo ina kallon ta, ganin bata son ta yi min dogon sharhi sai na fasa tambayarta inda zamu je a daidai wannan lkcn da ake tsaka da bincike a gidan. Na zagaya 6angaren damar na bude motar na shiga baya na zauna, ita Kuma ta tuqa ta nufi qofar shiga da fita ta gidan, wacce ke a bude fayau! Shi kansa mai gadin ya rude, ya mance bai rufe ba." . Zubaida ta fice da mu, muka bar gidan. Ta hau kan titin layin gidan, muka doshi yamma. Bayan mun yi nisa mun daina hangen gidan, sai tayi fakin da motar a bakin titi, a wani waje da ke da qarancin mutane. Har xuwa lkcn ban ce da ita komai ba, ban tambayeta dalilin da yasa ta daukoni muka fito ba, har xuwa lkcn da ta kashe motar ta juyo ta dube ni. To amma Kuma na san cewar wata magana ne mai muhimmanci take son mu yi, wacce take buqatar sirri. . "mansur" . Zubaida ta ambaci Suna na a cikin damuwa da Kuma shiga6a. . "na qura mata ido ban amsa ba, na ci gaba da sauraren abin da take son ta fada min..." . "ina so ne muyi wata magana mansur." . Ta ce da ni. . "ina so ne ka fada min gsky bana son ka yi min qarya. Me ka sani a game da rasuwar mijina?" . Ta qarishe maganar a cikin kuka, hawaye ya xubo mata cikin sauri. Ta share hawayen sannan ta tsayar da ganinta a kaina. . "ka yi min magana mansur." . Ta sake cewa da nni cikin damuwa. . "me ka sani game da wannan mutuwar?" . Na yi ajiyar xuciya sannan na ce da ita. . "ni na kashe shi." . Tsawon lkc muna kallon juna Babu wanda ya sake cewa wani abu. Na sake tabbatar mata. . "tabbas ni na kashe mijinki Zubaida. Na san cewar ke kanki kina zargin hakan, Kuma ke ce kika roqe ni da kada in yi maki qarya. Shi yasa na fadi maki gsky." . Zubaida ta lumshe idanunta cikin damuwa, sannan ta dafa sitiyarin motar xuwa can ta bude idanunta ta qurawa gilashin motar idanu. . "me ya sa ka kashe min mijina mansur? A wane dalilin zaka kashe shi?" . Zubaida ta tambayeni lkcn da wasu sababbin wahayen ke gangarowa daga cikin idanunta. . Na ce da ita. . "sbd ina sonki Zubaida." . Ta juyo a tsorace ta kalle ni, muka hada ido. . "so?" . Ta tambayeni . Na share xufar dake a goshina. Sannan na ce da ita. . "ranar wanka ba a 6oyon cibi Zubaida, ina son ki san cewar na dade ina son ki a rayuwata. Tun ranar da na fara ganinki a makaranta, tun ranar na ji ina sonki a duniya. A haka na dauki shekaru uku ina faman da radadin soyayyarki a xuciyata amma Kuma na kasa sanar dake, don kuwa na san cewar kin fi qarfin matsayina Zubaida." . Har xuwa lkcn da muka gama karatu ban daina sonki ba Zubaida. Ban san inda zamu sake haduwa ba, a haka na sanyawa xuciyata tabbacin haduwarmu wata rana, don in ganki in samu sUkuni a xuciyata. . Lkcn da na zo nan garin neman aiki, sai Kuma sai na ci sa'a, mijinki yana neman direba, shi ya daukeni aiki, a lkcn ne na sake ganinki, sannan Kuma na ji soyayar da nake yi maki tun shekarun baya ta sake taso min ta dawo sabuwa. Sauran abubwan da suka faru kuma kin sani Zubaida. Don kuwa a dalilin lbrn da kika bani a daren jiya cewar mijinki ba zai mutu ba sai ya qara shekaru talatin a duniya sai na ji kishi da Kuma damuwa sun cika min xuciyata. Don kuwa ba zan iya tsayawa ina jiran shi ba, shi yasa na kashe shi, don ina so ki aure ne.kamar yadda kika yi min alqawarin idan ya mutu ba zaki sake auren tsoho ba, yaro zaki samu irina wanda zaki yi soyayya dashi ki more quruciyarki." . Zubaida ta sunkuyar da kanta a kan sitiyarin motar ta na xubar da hawaye a lkcn da ta ji na kai qarshe. Ta ce da ni. . "ka yi kuskure mansur,don kuwa wannan abu da aka aikata ni zaka dorawa laifi, kasancewar na fading maka mutane da damar Suna zargina waigo ina so in kashe shi, ynx idan aka yi bincike dole ne a nemo wani abu da za a rataya min, don a ce na kashe shi. Babu wanda zai dora maka zargin kisan kai mansur....na tunda kana so na da gaske. Me zai san ka jawo min laifin da ban aikata ba? Wannan ita ce soyayyar da kake yi min?" . Nayi ajiyar xuciya sannan na ce da ita. . "Kada ki damu Zubaida, Babu wanda zai dora maki zargi. Ni nayi alqawarin in har sun gane kashe shi aka yi, to zana fito in fadi masu gsky cewar ni na kashe shi. Ba ke ce kika kashe shi ba." . Zubaida ta dago kanta a sanyaye daga kan sitiyarin motar ta yi min kallon soyayya, to amma Kuma Akwai hawaye a idonta. Ta ce da ni cikin sassanyar murya. . "ban ta6a tsammanin kana sonar kamar haka ba mansur.. Allah ya bar mu tare ni da kai masoyina, Kuma in allah ya yarda ba zasu gano cewar kashe shi aka yi ba.da zarar na gama takaba zamu yi aurenmu na soyayya." . Tunda na zo duniya ban ta6a jinjinawa wata magana mai dadi da sanyaya xuciya kwatankwacin wannan ba." na ji farin ciki da kuma annashuwa sun cika min xuciyata. Ta6! Waigo ni ne yau Zubaida take kallo tana kirana masoyina. Abin da nake ta mafarki shekara da shekaru gashi ynx ya zama gsky. . A daidai lkcn da muke zaune a cikin motar ne muka ji 6urarin motar asibiti ta dauko gawa. Ita ce motar da ta dauko gawar marigayi mijin Zubaida. Motar tazo ta wuce mu kamar iska ta juyo mana baya a guje, muka bi ta da kallo ni da Zubaida masoyiya ta. . Don kuwa mun san Kowanne ne a cikin motar, muka kalli juna cikin kunyar abin da muka aikat, sannan muka yi saurin kawar da kanmu. Kafin motar gawar ta 6ace ne mu daina ganinta na tuno Alh.Bashir da kuma lbrn da ya bani da zaman soyayyarshi da zubaida, na tuno lkcn da ya kira ni muka ci abinci tare a falo. Yana matuqar so na! . Na tuno gargadin da ya sha yi min tun xuwana gidan. . ..ka riqe min amanar matata Zubaida....."Don kuwa duk duniyar nan babu abin da nake so kamar ta...." . A karo na farko na dan ji tausayinsa ya yi zarya a xuciyata. . . ** ** ** . . Bamu samu sukuni ba har aka yi biyar da yin rasuwar, don kuwa 'yansanda tuni sun miqa maganar xuwa kotu. Kullum sai mun samu baqin dake kawo mana ziyara, baqin kuwa ba wasu bane, 'yansanda ne da lauyoyi wadanda ke xuwa su tsare mu da tambayoyi. Don kuwa mutane da damar Suna ta bayar da jita-jitar wai wwannan mutuwar da mijin Zubaida yayi wai ba ta allah da annabi ba ce. Kashe shi aka yi. Ni da zubaida masoyiyata muna shanta tsinuwa a wajen mutanen duniya kamar 'yan kashin kasuwa. Don kuwa ni da ita aka dorawa zargin kashe Alh.Bashir gurgu. . Tun anan saura kwana biyu a fara shari'a. Zubaida ta dauki lauya Wanda zai karen mu a kotu. Da ranar shari'ar ta zo tun da sassafe jami'an tsaro suka zo suka yi awon gaba da mu har da mai gadi muka dunguma. Aka fara shari'a. . Abin ya zo a bazata, don kuwa 'yansanda sanda sun yi dogon bincike, mai tsanani . Kuma sun gano abubuwa da dama fiye ma da yadda muka yi tsamni . . Lauya kotu shi ya fara miqewa yayi jawabin share fage a shari'a ar. Kuma miqewarsa ke da wuya ya fara jawabinsa kai tsaye. . "wannan shari'ar ba zata daukemu xuwa wani dogon lkc ba, don kuwa tuni mun gano yadda wannan ala'amari ya gudana. Zubaida ce ta kashe mijinta, Kuma ta kashe shi ne ta hanyar ba shi guba a cikin lemon gwangwani . Jikina ya auna gawarmarigayin kumaa zamu tsayar dashi a gaban kotu don ya ba.da shaida a bisa binciken da ya yi. Sannan Kuma shi kansa Wanda ya siyarwa da Zubaida wannan guba zamu gabatar da shi a gaban kotu don ya ba.da shaida..." . Abin ya bani mamaki, Kuma ya yi matuqar jikina ni. . . Lp=24mugun albishir Page 24 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Abin ya yi matuqar bani mamaki Kuma ya rikita ni, don kuwa ni dai na san cewar ni na kashe shi. Ni na karya mashi wuya, to amma Kuma gashi lauyoyi sun yi bincike sun gano cewar wai guba ya sha ya mutu. Wata qila Kuma biri yayi kama da mutum, don kuwa ni dama a lkcn da na je na kashe shi, ban ga yayi motsi ba." . Lauyan kotu ya gabatar da likitan da ya xo ya auna gawar Alh.Bashir yayi gamsasshen bayani. Kowa ya gamsu tabbas gubar marigayin ya sha ya mutu. Daga baya Kuma Lauyan ya gabatar da wani mutum, mutumin ya ce sana'arsa ne sayar da magungunan qwari shekara da shekaru. Zubaida ta zo wurin shi ta sayi magani mai qarfin wanda tace zata xubawa wasu qwari dake gina mata rami a lambun gidan ta...." a ranar da ta sayi maganin a ranar ne Kuma mijinta Alh.Bashir ya rasu ta hanyar shan guba a cikin lemonn gwangwani . Lauyan dake karemu ya tashi yayi nashi surutun, to amma Kuma bai samu wasu hujjoji ba da zai dogara dasu. Don kuwa lauyoyin dake a 6angaren kotu sun fi shi hujjoji da za a yarda dasu. . Na dubi Zubaida dake a tsaye naga tana hawaye a gaban kotu, naji tausayinta ya kama ni, don kuwa ni na jawo mata wannan masifar, dama ta ce da ni dole ne a nemo wani abu da za a dora mata zargin a ce ita ta kashe shi, tunda dai tayi qaurin Suna a wurin mutane. . Da na tuno alqawarin da na yi mata cewar ba zan ta6a bari a dora mata laifi ba, sai na ce da Lauyan dake a 6angarenmu ina da magana. Mutanen dake a kotu suka dube ni, alqalin da lauyoyi kowa ya dawo da hankalinshi wuri na. Na ce. . "ba Zubaida ta aikata wannan laifi ba, , ni na aikata laifin kashe mijinta. Ni na sayo guba na xuba mishi a cikin lemo ya sha. Amma ita Zubaida da ta sayo tata gubar qwari ta xubawa a cikin fulawoyi." . Mutane da dama sun yi mamakin abin da na fadi. Don kuwa ba a ta6a ganin wanda ya dorawa kanshi laifin kisan kai ba don kawai ya kare wata mace. To amma Kuma mecece soyayyar? Idan har da gaske kana son wata mace kamar yadda nake son Zubaida to dole ne mutum ya sadaukar da rayuwarsa. Dominn kuwa mace kamar Zubaida ta cancanci komai daga wurin masoyinta. . A qarshe alqalin kotun ya nuna damuwarshi akan yadda wannan shari'a ta zo a rikice. Don kuwa shaida qwaqqwara da hujjoji sun nuna cewar Zubaida ce ta kashe shi. Gashi Kuma na fansheta na ce ni na kashe shi, amma Kuma ni ba a ga wata hujja da za a bi ace ni na kashe shi ba." don haka sai alqali ya yanke min hukuncin daurin shekaru goma a gidan yari sbd babu qwaqqwara hujjar ni na kashe Alh.Bashir Kuma a yadda kowa ya fahimci shari'ar shi kanshi alqalin ya san Zubaida ce ta kashe shi, a 6angarena Kuma ina ganin tunic nayi alqawarin karemu masoyiya ta, bayan haka Kuma ni ma ai na murde wa gawar wuya a cikin dare. . A haka 'yansanda suka yi awon gaba dani. Muka hada ido ni da Zubaida masoyiya ta tana kukan baqin ciki. Nayi mata murmushin Kada ta damu, zan fito komai dadewa, ina fatan zata riqe min alqawarin ta jira .ni. Zubaida ta yi min murmushin Kada in damu. Zan jiraka masoyina, komai dadewa ina nan ina jiranka. Na gode sosai da soyayyar da ka nuna min, ka fansar da rayuwarka a kaina. . 'yansanda suka buga min ankwa a hannuna da qafafuwana, suka iya qeyata suka raba ni da masoyiya ta Zubaida da muke kallon juna, suka yi waje da ni suka bude mota suka ingiza ni ciki. Motar ta fara tafiya da ni xuwa wata duniya ta mutanen da basu da 'yanci a rayuwarsu. Har tayi nisa xuciyata cike take da farin ciki. Don kuwait a qalla ban tozarta masoyiya ta Zubaida ba." shekaru goma Kuma basu kai shekaru talatin yawa ba, na san cewa Zubaida tana so na Kuma zata jira ni in gama zaman gidan yarin in fito muyi aure. . Motar ta wuce da ni saitin wata makaranta inda wasu yara qanana ke wasan qwallo cikin farin ciki, Suna sanye da kayan makaranta iri daya. Yaran suka dagowa motar hannu kamar sun san ina ciki ina kallon ta ggilashi. Duk da yake basu ganni ba, sai da na daga masu hannu nima na ce dasu a xuciyata . "allah ya kare Ku da sharrin soyayya idan girma yara." . . *************************** . Bayan shekara goma. . Wata azababbiyar bulala dake kama da Fatan giwa ta ratsa gadon bayana. Na farka a gigice babu shiri, a lkc ne na ganshi a tsaye a kaina riqe da doguwar bulalarshi kamar Kullum. . Na dube shi a fusace bayan na wartsake daga barcin, yana tsaye yana murmushin mugunta da yamutsattsiyar fuskar mai kama da fasasshen tumaturi. . Da azzalumin gandiroban ya ga na tashi sai ya mayar da hankalinshi akan sauran abokan kwanana da muke cunkushe a daki daya mu shida kamar kifayen gwangwani. . Lp=25Mugun albishir Page 25 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." , Da azzalumin gandiroban yaga na tashi sai ya mayar da hankalinshi akan sauran abokan kwanana na da muke cunkushe a daki daya mu shida kamar kifayen gwangwani. Haka gandiroban ya bi su daya bayan daya yana tsala masu bulalar Suna farkawa a furgice, don kuwa idan ya fara dukan mutum in har ba farkawa yayi ya tashi ba, to ko bulala dari zai yi masa ba zai gaji ba, duka ne dashi tamkar Zazza6i. . Bayan mu duka mun farka daga barci, sai azzalumin gandiroban ya dube mu a lkc daya, sannan ya ce. . "na san cewar ynx kun gama wartsakewa." . Muka gyada kawunanmu cikin fushi kamar qadangaru. Don kuwa duk da yake xuciyarmu ta bushe sbd wahalar gidan, to hakan bai hanamu tsoron wannan gandiroban ba, Wanda a shekara goman da nayi a gidan yarinn, tun xuwa na shi yake bin dakunan fursinoni yana tashin su daga barci idan safiya tayi. . Wannan gandiroban da yake tashinmu daga barci ya fi duk Sauran ma'aikatan gidan yarin baqin jini a wurin mu. Don kuwa duk lkcn da muka kwanta barci bamu son wani abu ya tashe mu, sbd wuni muke yi muna shan wahala tun safe har dare. A haka muke kwantawa barci a gajiye da tsamin jiki, muna cikin barci Kuma babu zato babu tsammani sai mu ji saukar duka, da zarar mun ji haka mun san cewar gari ya waye kenan. . Gandiroban ya nannade doguwar bulalar ya sa6ata a kafadar shi kayan qato guda, ya ce da mu. . "ya kamata wanda zai yi sallah ya je ya yi, wanda Kuma ba zai yi ba ya je ya dauraye fuskar shi, yau tun da wuri zamu fita aikin fasa dutse." . Ya fice ya bamu wuri, mun yi shiru muna tunani, muna jin shi ya shiga wani daki Wanda yake kusa da mu. Muka ji qarar saukar bulalar shi a kan wasu irinmu da tsautsayi ya fado mawa suka xo gidan yarin, ko da yake wasu ba za a ce tsautsayi ya kawo su ba, wasu ganganci ya kawo su, da Kuma hadama da neman duniya. . Sauran abokan kwanana su biyar da muke kwana tare a cunkushe shekara da shekaru, sun bani labarin abubuwan da suka yi aka kawo su gidan yarin. Bangis da Gambo riqaqqun 'yan fashi ne da suka dade Suna daukar rayukan bil'adama. Sada dan damfara ne, Dumfama Kuma safarar miyagun qwayoyi yake yi. Jabiru shi ne mai dan dama-dama a cikin su, satar mitar wutar lantarki ya ce yana yi a gidajen mutane kafin dubun shi ya cika. . Ni kadai ne azal ta fado mawa, a lkcn da na basu lbrn cewar ni wata masoyiya tawa na fanshi laifinta don Kada a yanke mata hukuncin kisa, gabaki daya shu'man mutane biyar din da na taras a dakin sai da kowa ya yi min mari goma-goma. Bangis ne ya riqe ni da tsiya suka yi layi Suna wanke min fuska da busassun hannayensu dake kama da bayan Kada. Bayan sun gama kumbura min fuska sai Bangis ya ce da ni. . "ka san abin da ya san muka hora ka?" . Na girgiza kaina cikin tsoro, don kuwa a lkcn ni baqo ne ban saba dasu ba." Bangis ya ce. . "ka 6ata mana rai mansur,don kuwa mu biyar din nan da ka gani, mu duka jarumai ne....! kowa akwai gagarumin laifin da yayi aka kawo shi nan... Amma kai ka rasa abin da zaka yi na arziqi sai soyayya? Akan mace za ka zo gidan yarin?" . Na ce dasu. . "ina matuqar sonta ne shi yasa. Bana son wani abu ya same ta...." shi ya same na gwammace ni a yi min hukuncin da za a yi mata.." . Ragowar'yan fursunan suka kashe da dariya. Dumfama ya ce da ni. . "lallai kam baka da hankali mansur. Baka san halin mata ba." domin kuwa duk da wannan halaccin da ka yi, to zai yi wahala ta riqe maka alqawarin. Can zata je ta sami wani ta aura ta mance da kai, kana nan kana shanta wahala. Ka yi kuskure mansur." . Jabiru ya ce da ni. . "Sau daya na ta6a yin soyayya a duniya mansur....na wata bebi ce dake a layinmu, wacce muka yi alqawarin aure ni da ita. Na sha wahala ina nemo abin da zan aureta, har garinmu na bari. Amma lkcn da na dawo Bayan na samo abin da zan aureta, sai na sami labarin ta kaI wata biyu a dakin mijinta. Tun daga lkcn na daina soyayya a rayuwata." . Fursunonin sun bani labarai da dama na surqulle Wanda ya sa suka kauracewa soyayya, to amma Kuma ni duk wannan baiwa tsorata ni ba." ina nan da soyayyarki Zubaida a raina, Kuma ina fatan duk lkcn da na fito daga gidan yari zata zama mata ta...." . Sai dai kuma na fara shan jinin jikina. Don kuwa tun da na zo gidan yarin ko Sau daya Zubaida bata kawo min ziyara ba, sannan Kuma bata aiko min da wani saqo ba, Wanda zai sa in kwantar da hankalina, in san cewar tana nan tana jira na. Kwanci tashi gashi har an yi shekara goma. . Baqin cikin rashin ganin Zubaida masoyiyata, da Kuma tsananinn wahala da muke sha a gidan yarin, ya sa duk na kode na lalace. Nayi baqi wuluk, sannan Kuma gasusuwa sun firfito min a fuska duguzum, na zama abin tsoro a wurin yara qanana da ace zan fito duniyarsu su ganni. . Sau da yawa na kan rabat dare ina kukan baqin ciki idan na tuna cewar duk sbd soyayyar Zubaida na tsinci kaina a wannan wuri. Amma Kuma gashi ko sau daya ba ta zo ta ganni ba." . . Lp=26 Mugun albishir Page 26 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Sau da yawa na kan raba dare ina kukan baqin cikI idan na tuna cewar duk sbd soyayyar da nake yiwa Zubaida na tsinci kaina a wannan wuri. Amma Kuma gashi ko sau daya ba ta xo ta ganni ba." to amma babu mamaki Kuma wani abu ne ya faru da ita a lkcn da zan zo gidan yarin. Ban san ynx a wane halin take ba." . Don haka nan take sai naji tausayin Zubaida ya kama ni. Ina xullumin ko wani abu ne ya same ta, gashi Kuma bani a tare da ita ballantana in sake taimakonta. Kullum sai na tuno bankwanan da muka yi a lkcn da aka yanke min hukuncin a kotu. A lkcn da take kallona fuskarta sharkaf da hawaye. . Kafin mu tashi mu fita daga dan tsukukin dakin mai kama da akurkin tantabaru ni da Sauran abokaina biyar sai aka turo qofar dakin ta bude. Wani gandiroban ya shigo, to amma shi ba da bulalar ya shigo ba, ya shigo ne da wata doguwar takarda a hannunshi, da shigowarshi ya ce da mu. . "wane ne mansur a cikin Ku?" . Na ce dashi. . "ni ne....! . Gandiroban ya dube ni cikin farin ciki ya ce. . "to mansur sai ka yi bankwana da abokanka. Yau ne ranar da za a sallameka daga wannan gida. Yau ka cika shekara goma. Yi sauri ka zo mu je ofishin kwantirola." . Na ji farin ciki ya ishi xuciyata. Na dubi abokan kwanana su Bangis da Gambo, na ji tausayinsu ya kama ni, don kuwa su hukuncin daurin rai da rai aka yanke musu. Bangis ya ce da ni. . "mansur shi kenan Kuma zaka tafi ka barmu, Fatan nan gaba zaka kiyaye wajen yin soyayya . Sauran fursunan suka fashe da dariya. . Dumfama ya ce. . "muna Fatan wata rana zaka zo mana da Zubaida don mu ganta." . Nayi masu alqawarin zan zo da ita idan na aureta. Sannan na bi gandiroban muka fice muka bar dakin. Na ji iskar safiya mai sanyaya xuciya ta bugi fuskata sannan Kuma annashuwa da murna suka mamaye min xuciyata. Don kuwa rayuwata ta dawo sabuwa. Lkc ya yi da zan fita in ga Zubaida, na ce a xuciya ta...." gani nan xuwa, ina Fatan baki mance da ni ba." ni ne mansur Tsohon masoyinki, tun na shekaru goma da suka wuce." . . ** . . Lkcn da aka sallame ni na fito daga gidan yari, ban zame ko ina ba sai unguwarsu da nake tsammanin zan ganta. Gidan Alh.Bashir yana nan kamar yadda na bar shi tun shekara goma da suka wuce. Sa6anin wancan lkcn, ynx ba dan tsoho Falalu mai kwari da baka ke gadin qofar gidan ba, a wannan karon wani baqin soja ne a zaune rungume da doguwar bindigarshhi Wanda nake kyautata tsammanin rabonshi da ya yi fara'a, Babu mamaki wataqila tun yana yaro qarami, lkcn da ake Bashir kudin tara. . Na qarisa inda yake nayi mashi sallama, kafin ya amsa sai da ya kalle ni sama da qasa, da ganina ko mutum bai tambaya ba ya san ceewar daga gidan yari na fito. Don kuwa Bayan kodaddun kayana masu kama da ragowar kura, duk jikina tabon duka ne kamar dokin suga. Da yaga na tsaya a gabnshi ina nemo abin da yafi dacewa in tambaye shi. Sai shi ya dakatar min tsawa. . "wa ka zo nema?" . Na ce dashi . "na zo neman Zubaida ne.l" . Sojan ya ce da ni. . "Babu wata Zubaida a gidan. Ya ce da ni gidan na wani kanal din soja ne." . nayi mashi gdy, sannan na fice cikin rashin sanin inda zan je on ga Zubaida. A halin ynx na fahimci cewar sayar da gidan aka yi Bayan rasuwar mijinta. . Don haka kai tsaye sai na wuce gidan Kawuna Wanda ya fara yi min hanyar xuwana gidan marigayi mijin Zubaida. . . Lp=27Mugun albishir Page 27 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Don haka sai na wuce kai tsaye gidan Kawuna Wanda ya fara yi min hanyar xuwana gidan marigayi mijin Zubaida a matsayin direba. Daga shi har iyayena da Sauran 'yan uwana, na san cewar ynx tuni sun haqura da ni. Don kuwa har na je gidan yari nayi shekaru goma babu wanda ya waiwaye ni. Su a 6angarensu Suna tsammanin ni ke da laifi, tunda dai ni na kashe wa Zubaida miji. . Da na je gidan Kawuna nan din ma ban yi katarin samun shi ba, don kuwa gidan a kulle yake da kwado. Da na tambaya ne ake ce min ya tashi ya bar kaduna tun shekaru biyu da suka wuce babu kowa a gidan. . Na rasa inda zan sa kaina in ji dadi, don kuwa a halin ynx ban san kowa ba." nima Kuma Babu wanda ya sanni. Zubaida ce kadai zata ganni ta tuna ni, gashi Kuma ita ma na neme ta sama ko qasa na rasa inda ta shiga a duniya. Shin anya kuwa Zubaida tana a raye? Wannan ita ce tambayar da na riqa nanatawa a xuciyata har nayi kwana daya ina neman ta, amma Kuma ko labarin ta ban samu ba." . Wasa-wasa har aka yi mako guda ina ta cigiyar inda masoyiyata Zubaida ta ke. Haka nake wuni tun safe har dare ina shige da fice a cikin garin. Duk wani wuri da na san cewar ta ta6a bani labarin ta je, sai da na je nayi tambaya a wurin, amma Kuma ban samu sa'a, wani ya ce min ya san inda take ba." . Aka yi wata daya Babu labarin Zubaida Babu labarin Wanda ya san inda take. Da naga cewar an yi wata uku ban ganta ba, sai na cire rai da Kuma tsammanin ganinta. Don kuwa nayi duk wani qoqari da ya kamata ace masoyi ya yi wajen neman masoyiya amma Kuma ban gano Zubaida ba." . Ganin yadda rayuwata ta zama a dalilin son wata mace daya a duniya, ina ta faman wahala akanta gashi har girma ya zo min ban sani ba." na kusa shekara arba'in amma Kuma ban samu nasarar mallakar wacce nake so ba, Kuma ban san inda take ba, wataqila tana raye a can wani garin, Babu mamaki Kuma ta dade da rasuwa. . Ba a jima ba da naga cewar ba ni da wata qwaqqwarar sana'a, tun fitowata daga gidan yari, sai na nemi aikin leburanci a wani reshen hukumar ruwa. Aikin mu shi ne xuwa haqa ramukan fanfuna da Kuma sauran aikace-aikace na leburanci. Wanda mutum zai yi ya samu abin da zai ci kada ya mutum da yuNwa. . Wata rana muna zaune ni da Sauran leburori 'yan uwana a hukumar. Sai wani mutum ya silalo motarshi mai qyalqyali da ganinta an san an mori inuwar sili, mutumin ya fito wani dan gajere mai fadin fuska yana sanye da kayan alfarma wadanda suka taimaka wajen rage masa muni. Ya shiga xuwa ofishin shugaban hukumar. Xuwa can suka fito tare, suka xo inda muke a Zazzaune muna jiran aiki. Shugaban hukumar ya ce. . "mansur zata ka je gidan wannan mutumin, sunan shi Alh. Rufa'i. zaka haqa mashi sabon rami, yana so ne a canza mashi hanyar ruwa. Ya ce ya baiwa iyalinshi sallahun cewar zata a je, don haka an san da xuwanka." . Alh. Rufa'i ya miqo min wani qaramin kati mai dauke da adireshin gidan nashi da Kuma lambar wayarsa. Na amshi katin, sannan na dauki kayan aiki shebur da Kuma diga. Na hau dan acha6a nayi masa kwatancen adireshin gidan ya dauke ni a cikin mintI bakwai muka isa unguwar, sannan muka je har qofar gidan. . in ban da na tabbatar cewar shi ne gidan da yaxo daidai da adireshin dake a jikin katin ba, da babu abin da zai sa in amince in shiga gidan. Don kuwa a tsarin ginin da aka yiwa gidan da wasu irin furanni dogaye da aka qawata gidan dasu, ya sa ni tsammanin ko shugaban qasa yake zaune a ciki ya ca6a.m. . Na sallami dan acha6a ya tafi, na isa bakin tangamemiyar qofar gidan riqe da kayan ginin a hannu na, sai ka ce mai xuwa ginin kabari, duk kayana, sun yayyage. A qalla dai na ci sa'a Akwai masu gadi a qofar gidan, don ina jinjinawa Tsoron in shiga Babu izini mutanen gidan su yi min ihun mahaukaci. . Na qarisa wajen masu gadin su uku ne sanye da kayan buzaye, kowannensu yana riqe da zabgegiyar bulala sannan Kuma sun bar gashin baki a fuskokinsu zaro-zaro. . Nayi masu sallama sannan na nuna masu katin shaidar aikina na leburanci, suka gani. Nayi masu bayanin abin da na zo yi da Kuma katin adireshin da mai gidan ya bani. Daya daga cikin buzayen wani sangamemen qato mai qirar 'yan kokuwa ya ce da ni. . "baring in shiga in sanarwar hajiya, bata son a shiga a dame ta in tana barci. Bamu son ka shiga ka bata tsoro, bata san da xuwanka ba, Kada ka jawo mana laifi a banza." . Sauran qartin suka yi dariya daya a cikin su ya ce. . "gskyrka mamuda, ya fi kyau ka jefi-jefi ka fara sanar da ita. Don kuwa idan rana ya 6aci sai ta rufe mutum da zagi kamar ita ta haife shi." . Qaton farko da ya fara magana Wanda shi ne suke cewa mamuda ya tashi ya shiga cikin gidan....xuwa can Bayan wani lkc sai ya fito ya dube ni.ya ce. . "ta ce a shigo da kai ta san maganar." . Na bi shi a baya muka shiga cikin gidan....tare. 6ata lkc ne na zauna bayyana aljannar duniyar dake maqare a cikin gidan. Don kuwa duk inda mutum ya kai dubana a farfajiyar gidan dawisu ne manyan da qanana fululu suke yawo, sannan Kuma a wani sashi bene ne hawa uku an qawatashi da gilasai da Kuma matattakalar zamani. Na ci gaba da zare idanuwa ina kallon abin mamaki a lkc guda Kuma ina biyu da qaton Wanda ke tafiya daqyar sbd qarfi kamar toron agwagwa. . Mun xo bakin wata qofa daidai inda wata siriyar hanya ta ratsa cikin wasu shuke-shuke, sai qaton da ya rakoni ya juyo y ce da ni.ya . "ka tsaya nan ka jira zata fito." . Sannan ya komai can wajen abokan aikinshi, ina nan tsaye dauke da diga ina mamakin a inda mutane suke samun irin wannan dukiya mai yawa a wannan duniya. Xuwa can sai naji an bude qofar, sannan an yi motsi a kusa da ni.ya na dawo da hankali na inda na ji motsin. Tana a tsaye a jikin qofar gilashi sanye da qananan kayan na dogon wando da kuma guntuwar riga. Ta xubo dogayen gashin kanta sun watsu a kafadarta kamar yadda ta saba yi a shekarun baya. . Ban san lkcn da na xube kayan haqan ramin ba na baje a qasa. Ko a wanne zamani, Kuma ko a ina na ganta to dole ne sai na gane ta. na dubi fuskarta mai cike da annuri duk da irin tsawon shekaru goman da nayi ban ganta ba, ni dai ban ga wani canji ba." tana nan radau da kyanta sai kace wacce ake canzawa fata. Sai sheqi take yi. . Na tuno muryarta dake a 6oye a dodon kunnena tun zamanin da muna makaranta. Tun muna yara. . "...yaya sunan ka...?" . Haqiqa nazo a sa'a. Na gano masoyiyata Zubaida. . . . ** ** ** . . . Zubaida!!!" . Na ambaci sunan a tsorace ina kallonta cikin tsananin kidimewa kamar naga aljana ko fatalwa. Na qara taku daya na matsa daf da inda take tsaye tana kallona sheqeqe kamar wacce take kallon mahaukaci. Ganin na matsa kusa da ita cike da farin cikin ganinta, sai ta ja da baya a tsorace. . "a ina ka ta6a gani na ka san ni malam." . Ta tambayeni cikin mamaki. . "Kuma wa ya fading maka Suna na?" . Na ce da ita a kidime. . "ni ne mansur.... Na fito daga fursuna tun wata uku da suka wuce. Ina ta nemanki, Zubaida me kike yi a nan gidan?" . Zubaida ta dan yi jim tana kallona, ga alama tana tunno inda ta sanni ne....! Xuwa can ta ce da ni.ya . "don allah ka sake tuno min inda na sanka, a ina muka hadu?" . Na ji xuciyata ta harba kamar talge . Na ji mamaki da damuwa sun taru a xuciyata. Wai ace Zubaida bata gane ni ba, Bayan Kuma ni ne masoyinta dake riqe da qaunarta fiye da shekaru goma shafi'u shida, tun ina saurayi dan makaranta. . "zaune kina nufin ki ce kin mance da ni'? Ni nefa mansur masoyinki. Ni ne Wanda na ceto rayuwarki a kotu a lkcn da na bayyanawa kotu ce ni ne na kashe mijinki Alh.Bashir ba ke ce ba." . Zubaida ta dan yi murmushi kadan kafin ta ce. . "oh...(i could remember), sai ynx na gane ka. Ashe dama kana a raye mansur? NI na dauka cewar tuni ka dade da mutuwa kaima. " . Na ji Gabana ya fading ras, don kuwa a yadda Zubaida take kollona tana fada min maganganun Babu wata alamar soyayya, kamar ma ba ta ta6a ganina ba sai ynxn. Ta ce da ni cikin damuwa. . "me ya Kawoka gida na, Kuma wa ka zo nema?" . Na ce da ita cikin damuwa. . "baiwa kamata ace kin yi min irin wannan tambayar ba Zubaida. Da ace kin san yadda na qarar da gaba daya rayuwata kan soyayyarki, da ba ki yi saurin mancewa da ni ba." . Zubaida ta ce da nia fusace. . "baka da hankali."Kai ynxn har kana tsammanin akwai wanii lkc da zan ji ina son wani mutum irinka a duniya mansur? . . Lp=28Mugun albishir Page 29 . Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ba ka da hankali." . Ta ce da ni.ya . "kai ynx kana tsammanin akwai wanii lkc da zan ji ina son wani mutum irinka a duniya mansur? Kada in sake jin ka fadi irin wannan maganar a nan gidan, don kuwa ni matar aure ce, Kuma nan gidan mijina ne." . Zubaida tayi ajiyar xuciya, sannan ta ci gaba da cewa. . "bari in fadi maka wani abu wanda baka sani ba." tun lkcn da ka fara gani na a makaranta ni matar aure ce. Ban ta6a zama babu aure biyu ko uku akaina ba." na ta6a zama da maza hudu a lkc daya, Kuma babu wanda ya sani a cikin su, ba qananan milyoyin kudi na ke samu ba a dalilin wannan aurace-aurace da nake yi mansur. Ni ce nake kashe mazajena in kwashe dukiyarsu. Idan na qarar da wadannan mazajen sai in qara auren wasu. Abin ya zame min kamar sana'a." . Na ji tsoro da fargaba sun kama ni, na xubawa Zubaida ido ina mamaki jin cewar wai ita ce da bakinta take iya fadin wadannan kalamai. To amma Kuma dama marigayin mijinta ya bani wannan labarin a wani zamani da ya wuce. . Ta ci gaba. . "duk lkcn da naga wani miloniya, Kuma naji ina son ya aure ni in zama matarshi bana shan wahala mansur. Don kuwa ni kyakkyawa ce. Ba Kowanne namiji zai ganni ya ce baya sona ba!" . Zubaida ta fadada murmushinta tana kallon wani dawisu dake gudu a harabar gidan cike da jin dadin abin da take fadi. Har xuwa lkcn da dawisun ya 6ace a cikin 'yan uwanshi, bata dauke idanunta daga kansu ba." ni Kuma ban daina kallon ta ba." ta ce da ni tana tunani. . "na dade ina son in kashe Alh.Bashir don kuwa duk a cikin mazajen dana aura shi ya fi bani wahala fiye da kowa a cikin su." ya cika taurin ran tsiya, na bi hanyoyi da dama don in kashe shi, amma Kuma ban samu nasara ba." gsky ne, haqiqa ni ce na tura shi a rami da gangan, musamman na samu waje nayi fakin da motar don ta dawo baya ta fada cikin ramin yana barci bai sani ba." tun kafin mu fito na zuba mashi maganin barci a shayi. Nayi haka ne don in tuqa shi yadda nake so ba tare da ya farka ya fahimci abin da nake son aikatawa ba." to amma a wannan hanyar ma ban samu nasara ya mutu ba, sai dai kawai ya rasa qafa ya zama gurgu." . Zubaida ta dan yi siririyar dariya, sannan ta dawo ta hade ranta. Naji xufa na keto min ta ko ina. Ta dube ni cikin raini , sannan ta ce. . "ina ta neman hanyar da zan bi in kashe gurgun mijina kwatsam, sai ga ka mansur wai ka zo mijina zai daukeka aikin direba. Da ganin haka na san cewar na samu hanya da zan kashe mijina cikin sauqi Kuma in fitar da kaina daga zargi. Don kuwa na san cewar kana sona, kana qaunata tun muna makaranta. Ban ta6a fitowa na nuna maka na fahimci kana qaunata ba sbd baka kai matsayin da zan yi soyayya da kai a duniya ba mansur." . Don haka sai na yaudareka, nazo dakinka a cikin dare na baka labarin qarya don ka ji tausayina ka taimake ni. Kuma na baka tsoro na ce mijina ba zai mutu ba sai ya qara shekara talatin a duniya. Abin da baka sanin ba shi ne; Tun kafin in zo in baka wannan labarin dama tuni na zubawa mijina guba ya sha a lemu. Sai da na tabbatar ya mutu san naxo na same ka a dakinka. Nayi maka haka ne don ka tashi ka je ka kashe shi ka riqa tsammanin kai ka kashe shi ba ni ba." ina ganin lkcn da ka shiga falon kana sanda a cikin dubu ka mirdewa gawarshi wuya. Sannan ka koma daki. Nayi haka ne sbd kodak anzo shari'a ba zaka bari a dora min laifi ba Tunda kana qaunata, Kuma kayi alqawarin zaka yi wa kotu bayanin kaina ne ka kashe shi." . Bayan mun je kotu an yanke maka hukuncin daurin shekara goma, ni Kuma sai na sake samun wani attajiri, Wanda yake son yaga ya ajiye kyakkyawar mace yarinya. Kafin wata hudu ya bi Alh.Bashir shiga na kashe shi. A cikin shekaru goman da kayi a furzun ba zan iya fadin adadin mazan da na aura ba kai tsaye, sai dai Kuma a halin ynx sun zama tarihi." . Xuciyata ta ci gaba da bugawa kamar zata fasa qirjina ta fito waje. Don kuwa Zubaida ta gama rikita ni. Na bi ta da kallo cike da takaicin ganin na qarar da rayuwata a qaunarta, amma Kuma ita ba ma ta ni take yi ba." sannan Kuma na dorawa kaina laifin da ba ni na aikatashi ba, don in karen rayuwarta da mutuncinta naji nayi shekaru goma a gidan yari, duk a dalilin wannan kyakkyawar mace dake tsaye a gabana tana yi min kallon mahaukaci sha-sha-sha! . . Naji hawaye sun taru a cikin idanuna, sannan Kuma naji ni kaina na tsani kaina. Na ce da Zubaida ina kuka. . "Kada ki yi min haka Zubaida. Duk duniyar nan ban ta6a jin ina son wata mace ba sai ke kadai. Ki ji tausayina Zubaida Kada ki karya alqawari." . Hawayen baqin ciki suka fara kwaranya a idanuna, Zubaida ta dube ni a yatsine cikin izgilanci ta ce da ni.ya . "kayi kuskure mansur, Tunda nake ban ta6a jin ina sonka ba, Kada ka ta6a rayawa a xuciyarka na ta6a sonka a duniya, Kuma har abada ba zan ta6a sonka ba." . . Lp=30Mugun albishir Page 30 . daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . Ka yi kuskure mansur, tunda nake ban ta6a jin ina sonka ba, Kada ka ta6a rayawa a xuciyarka na ta6a sonka a duniya, Kuma har abada ba .zan ta6a sonka ba." . Muka hada idanu da ita tsawon lkc, xuwa can Kuma sai naga kamar zata fashe da dariya, sai nace da ita. . "ni dama na san cewar wasa kike yi min, kin cika son wasa Zubaida. Bai kamata ace kina yi min irin wannan wasan ba, ni na san kina sona, kina dai fadar wadannan maganganun ne don ki bani tsoro....bana son irin wannan wasan, in abin ya xo da tsautsayi sai ki ga mutum ya kamu da hawan jini." . Zubaida ta murtuke fuskarta a fusace ta ce da ni. . "wa ya fadi maka cewar wasa nake maka? To bari in tabbatar maka cewar ba na sonka Kuma ba wasa nake yi maka ba mansur." . Tana gama fadin haka sai ta daga zazzaqar muryarta ta kwadawa qartin da na baro a waje kira. . "kuna ina?" . Na ji qartin sun amsa baki daya kamar kwaduna. . "gamu nan xuwa hajiya." . Na ji sun rugo aguje kamar an koro raquma har qasa ke amsawa. Suka shigo harabar gidan suka shawo kwana kowannensu da qaton ciki kamar masaki. Da xuwansu tun kafin su huta, sai Zubaida ta nuna ni da dan yatsa sannan ta ce a fusace. . "Ku lallasa min wannan baqon har sai kun ga baya numfashi." . Tun kafin ta rufe baki babban cikin su ya daukeni yayi qoli-qoli da ni kamar ya dauki 6awon kara, ya kwada ni da qasa, kaina ya hadu da dutse, naji xogi da radadi sun soke ni, na fara ihu ina yi masu magiya. . Qato daya ya sake rarumata ya yi sama da ni shima ya sake ni na fado tim! Suka hau ni da duka kamar Suna buga ganga. Tun ina iya yin ihu har na kasa motsawa. Abu na qarshe da naji kafin in suma shi ne tattausar muryar Zubaida tana dakawa qartin tsawa a fusace tana cewa. . "ku dauke shi ku je can ku jefar dashi a bakin titi ya qarisa a can!!" . . ** . . Ban san adadin lkcn da na yi a some ba, na dai farka na samu kaina a kwana a cikin wasu ciyayi dake a cunkushe da bakin titi. Na dago kaina daqyar naji hucin wucewar motoci Suna wucewa ta Gabana a guje kamar kibiyoyi. Nayi qoqari na tashi daqyar. Idanuna sun yi min nauyi, daqyar nake iya ganin hasken sararin samaniya. Yamma tayi sosai Babu hasken rana, ga alama qarfe shida tayi na yamma. Wannan shi ya ganar da ni cewar na dauki fiye da awoyi biyar a cikin ciyayin ban san inda kaina yake ba." idan nayi la'akari da lkcn da masu gadin Zubaida suka lallasa ni a gidan ta, kafin su dauko ni su zo su watsar da ni a bakin titi kamar yadda ta basu umarni cikin fushi. . Na kama ciyayin da na tsinci kaina a ciki na fara yunqurin miqewa tsaye, hannu a hankali ina qara samun sauqi, don kuwa na fara ganin abubuwa dake kai komo a wurin da aka jefar da ni. Inda Babu kowa, ga alama Bayan gari ne....! Don kuwa Babu Wanda ya san ina kwance a wurin. Babu mutane sai jefi-jefi da gine-ginen qananuun masana'antu da aka rufe suka daina aiki a bakin titin. Wannan shi ya ganar da ni cewar babu mama a cikin mota suka xubo ni suka zo da ni suka watsar. . Na lalla6a na samu a hankali na fito daga cikin ciyayin kayana sun yi fata-fata, duk jikina a kumbure yake don kuwa na ci uban duka kamar kalangun noma. a haka na samu ina tafiya juwa na barazanar daukata ta kayar da ni a qasa, har dai na samu na kai kaina gida inda nake kwana a wani aljihun aure a gidan wani mutum da ya saba da ni Bayan na fito daga gidan yari. . Bayan na kwanta sai abubuwa masu yawa suka riqa dawo min cikin xuciyata . "ku lallasa min wannan baqon har sai kun ga baya numfashi..." . Na tuno muryar Zubaida sannan kuma na lkcn da take cewa qartin. . "Kuma dauke shi Kuma je can Kuma jefar dashi a bakin titi. Ya qarisa a can...." . Abin da ya faru ya riga ya faru! Ynx tunanin abin da ya wuce Bashi da amfani. Don kuwa tunanina bai wuce na Zubaida ba." gashi kuma ta butulce min ta yaudare ni ta cuci rayuwata. Kin zalunce ni Zubaida! Na ce a xuciyata ina kukan baqin ciki . To amma kuma nima na zalunci kaina, don kuwa tun farko da ace na haqura tun a lkcn da na fahimci Zubaida ta fi qarfina da duk wannan matsalar bata faru da ni ba." sannan kuma wannan lamarin da ya faru da ni, na san cewar alhakin marigayin mijinta ne Alh.Bashir gurgu. Don kuwa na ci amanarshi na goyawa Zubaida baya ta kashe shi. Alhakinshi ne ya fara kama ni, kuma zan ci gaba da fuskantarabubuwa da dama a gaba a dalilin wannan son xuciya da nayi na kasa mashi amanar da ya bani. . Ba zan ta6a mance lkcn da motar asibiti ta dauko gawarshi ta wuce ta gaban mu muna a cikin mota muna kallo ni da matarshi Zubaida ba." lkcn ban ta6a tsammanin zata yaudareni ba, haqiqa nayi kuskure. Kuma nayi abin da xuciyata take so na 6ata tarihin rayuwata . na san cewar ba zan ta6a daina son Zubaida ba a rayuwata. Har ynxn kuwa da ta san aka yi min wannan rubdugun dukan, ina nan ina sonta a cikin xuciyata. To amma Kuma ya zame min dole in haqura in qaurace mata. Don kuwa ruwan ba tsaran kwando bane. Babu matsala! Na ce a xuciyata. Ba ni kadai bane namiji na farko da ya ta6a samun matsalar soyayya. Akwai mutane da dama a duniya wadanda suka dade Suna neman soyayyar wasu matan, kuma basu samu goyon baya ba." . Zubaida bata qaunata! Don haka na haqura da ita!! . Na rufe babinta a cikin xuciyata. Amma Kuma duk da haka idan nayi sa'a, wata rana zata canza ra'ayinta ta xo wurina ta ce ta dawo tana sona. Zan amshi soyayyarta Kuma cikin gaggawa sannan Kuma zan yi farin ciki mai yawa a duniya. To amma kuma anya Zubaida zata so ni? . Bayan nayi kwana ina jinya kamar Wanda yayi hadarin mota, sai qarfina ya dawo na ci gaba da harkokina. A safiyar rana ta uku ne, ina zaune nayi tagumi ina sauraren qaramin rediyona ina jin labaran duniya, sai naji muryar matar dake gabatar da labaran tana cewa; . "A yammacin jiya ne jami'an tsaro suka cafke Hajiya Zubaida wacce aka kama dumu-dumu da laifin kashe mijinta alh.rufa'i, ta hanyar tuno shi daga bene mai hawa uku. Wata majiyar ta ce Zubaida ta auri mazaje barkatai sun mutu. Kuma anan zargin duk ita ce take kashe su." a halin ynx dai tana nan a babban ofishin 'yansanda na jiya. To allah ya kyauta, Kuma ya jiqan marigayi Alh. Rufa'i...." . Tun kafin in gama jin labarin nayi sauri na miqe tsaye Xumbur! A tsorace kamar Wanda aka tsirawwa allura. Wacce Zubaida Kuma 'yansanda suka cafke? Na tambayi kaina. Zubaida masoyiyata? ko shakka Babu ita ce, don kuwa sunann mijinta alh. Rufa'i! Shi ne mutumin da ya aikeni gidanshi aikin gida ramin fanfo har matarshi Zubaida ta sa aka lallasa ni.ya kwana uku fa kacal kenan da ganin mutumin, amma Kuma gashi ynx anan bayar da sanarwar mutuwarshi a rediyo. . lp=31 Mugun albishir Page 31 . (kammalawa} Daga alqalamin Shafi'u dauda Giwa . . Tare da ni Abu ihsan Bn ishak (Madugun taska) . "TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba." . kwana uku kacal fa kenan da ganin mutumin amma Kuma ynxn gashi anan bayar da sanarwar mutuwarshi a rediyo. . Duk da haka sai naji tausayin ta ya kamani, don kuwa ina yi mata so ne irin wanda ko me zata yi min a duniya ba zan ta6a ganin laifinta ba." bana so in amince da wannan zargi da naji an fadi a rediyo, Wanda aka dora shi a wuyan kyakkyawa Zubaida. Bana son in ji mutane Suna cewa ita ce ta kashe mazajenta. To amma Kuma dole ne in amince tunda dai ni da bakinta ta sanar min..." . Haqiqa masoyiya ta 'yansanda suka kama!! Naji hankali na ya tashi sannan Kuma tsoro ya kama ni. Wa zai taimaka mata a wannan karon don kada a yanke mata hukuncin kisa? Nan da nan naji tuni na mance da dukan da ta sa aka yi min, naji ina muradin sake xuwa in taimake ta ko da kuwa wannan shi ne abu na qarshe da zan yi a rayuwata. . Na san cewar wasu zasu ga laifinta akan wannan aikin keto da zan sake yi wa masoyiyata. To amma Kuma me zai sa mutane su ga laifina don na ceto rayuwar wacce xuciyata ke bege dare da rana? Duk lkcn da dan adam ya fada tarkon soyayya, to shi kenan rayuwarsa ta fada cikin hadurra masu yawa, don kuwa babu mamaki don ma'aboci soyayya ya sadaukar da rayuwarsa ga macen da yake so. Ko da kuwa ace ita bata qaunarshi, kamar dai yadda nima na fada cikin tarkon son Zubaida Kuma nayi rashin sa'a, ita bata so na a rayuwarta. . Nan da nan cikin sauri na fice daga dakin, na bazama xuwa babban ofishin jami'an tsaro don in ga masoyiyata, Kuma na dauki alqawarin sai na ceto rayuwar ta kamar yadda na ta6a ceto rayuwarta a wani zamani can da ya wuce. Mai yiwuwar a sake yanke min hukuncin daurin shekaru goma, idan ban ci sa'a ba kuma a yanke min hukuncin daurin rai da rai, ko Kuma hukuncin kisa. . To a qalla dai ko ma dai me za a yi min, na san cewar ba a kashe min wannan kyakkyawar mace da nake so ba shekara da shekaru. Wani dadin gushi Kuma na san cewar ko bani a raye zata riqa tuna ni tana baiwa mutane labarin soyayyar da nayi mata a duniya, Kuma ta haka ne zata gane cewar ni ne masoyinta na gsky, Wanda ba zata sake samun kwatankwacina ba a rayuwarta. . . ** . . Lkcn da na isabella ofishin 'yansanda na roqi ganin Zubaida na dan sha wahala kafin a amince a bani wannan damar. Daga baya ne aka hada ni da wasu kwalawa biyu suka raka ni xuwa wani daki inda aka kume ta da wani murgujejen kwado kamar Damisa. da yake Akwai dogayen qarafunna da suka tare qofar dakin, ta nan na hangota a zaune ta kifa kanta akan guiwoyin qafufunta tayi shiru ga alama kuka take yi. . 'yansanda suka ce sun bani minti biyar agurguje, sannan Kuma suka dan matsa daga nesa suka bani wuri. A lkcn ne na kira sunanta a cikin tausayawa. Zubaida ta dago kanta a cikin kaduwa da mamaki a lkcn da tajikistan muryata. Idanunta sun kode sbd tsabar kukan da ta ci. sannan Kuma duk gashin kanta ya hargitse da gani ka san ta ci uban wahala a wajen tuhumar. Ta taso cikin sauri ta matso jikin qarafunan, sanye da doguwar riga baqar mai kwalliya a qirjinta. Ta tsaya a jikin qarafunan muka qurawa juna idanu. Ta fashe da kukan nadama ta ce. . "ba zan iya hada ido da kai ba mansur....na cuci rayuwarka na zalunceka a duniya ka yafe min..." . Na ce da ita cikin tausayawa . "....kada ki damu Zubaida na yafe maki duniya da lahira, ba koma..." . Zubaida ta sake dubana hawaye Suna tsere akan kyakkyawar fuskarta ta ce da ni.ya . "tun lkcn da jami'an tsaro suka kamani suka kawo ni wannan wurin, Babu wani mutum da ya xo ya kawo min ziyara yaga halin da nake ciki mansur....amma gashi kaine mutum na farko da yaxo ya kawo min ziyara, duk da butulcin da nayi maka baka mance da ni ba mansur?" . Ta sake fashewa da wani kukan. Na ce da ita. . "ba komai Zubaida, wannan ya wuce, ki daina wannan maganar, na san cewar abin da ya faru sharrin shaidan ne. Kuma ynx ma na sake xuwa ne don in ceto rayuwarki, ba zan ta6a bari wani abu ya sameki ba muddin ina numfashi a duniya. Na zo ne in sanar dake cewar zan fadawa 'yansanda cewar nine na turo mijinki Alh. Rufa'i daga saman bene ya mutu. In yaso ke ma ki basu wannan labarin, na amince ko me zasu yi miki ni suyi min a madadinki Zubaida." . Zubaida ta girgiza kai cikin rashin amincewa. Ta zzaro hannunta ta dora su akan yatsun hannuna dake riqe da qarafunan. Wannan shine karo na farko a rayuwata da ta ta6a yi min haka. Ta ce da ni. . "ba zai yiwu ba mansur,don kuwa ka dade kana shanta wahala a dalilin qaunar da kake yi min.ko me ya faru da kai ni ce na jawo maka. Lkc ya yi da ya kamata nima in fuskanci na wa hukuncin, don kuwa na aikata laifuka masu yawa a duniyar nan. Ba zan sake bari laifina ya shafeka ba." ynxn kam na amince kai masoyina ne mansur,don ka san martabar soyayya, Kuma ka san haqqin masoyrka, amma Kuma baka yi dace da wacce kake so ba." ban dace da irin rayuwarka ba mansur....kai mutumin kirk ne, ni Kuma mai laifi ce. Ina fatan zaka samu wata masoyiyar wacce ta fi ni a duniya, don kuwa ni tawa tazo qarshe. A wannan satin za a yanked min hukuncin kisa!!!" . Naji takaici ya lulli6e min xuciyata, sannan Kuma hawaye suka fara xubo min..." Zubaida ta sake qanqame yatsun hannuna ta ce da ni.ya . "Kada ka damu mansur, mutuwata ita ce samun sauqi a gareka, idan ina raye zan ci gaba da jawo maka wahalhalu a rayuwarka, don kuwa kana matuqar sona, ba zaka iya bari wani abu ya faru da ni ba." kayi haquri kabarin su yanke min wannan hukuncin a halin ynxn na amince da soyayyarka, to amma kuma hakan Bashi da wani amfani. Bakin alqalamin ya riga ya bushe."l . Muka kalli juna muna kukan soyayya da baqin ciki. Zubaida ta yi min murmushi kamar Babu wani abu da yake damunta. Ta ce da ni a sanyaye. . "na da dade ina yi maka (MuGun ALBISHIR) mansur. To amma kuma yau a karon farko zan yi maka albishir mai kyau. Wannan shine sakayyar da zan yi maka a bisa wahalhalun da kasha da ni baya. . "wane irin albishir zaki yi min Zubaida?" . Ta rage muryarta kamar zata yi min rada sannan ta ce . "mansur ina dare yayi ka je Bayan gidan mijina da na turo shi daga saman bene, marigayin Alh. Rufa'i idan ka je zaka isle shuke-shuke a cikin lambun dake a bayan gidan. A cikin wadannan shuke-shuke zaka iske watgajeruwar bibiyar gwanda, ka tonal gindin bishiyar, zaka iske wani qaton akwatu na 6oye, kudi ne a ciki naira milyan hamsin ka dauka duk rabonka ne, damar na 6oye su ne don Kada azo bincike a gansu. Ka daukesu na bar maka su kyauta. Na gode Kuma da soyayyar da ka nuna min, Kada ka mance da ni masoyina, na gode, ina yi maka bankwan...." Wasu hawayen suka sake zuba mata. To amma Kuma ni a halin ynx ba kudi suka fi damuna ba, baqin cikin rayuwar da ita shi yafi damuna. Kafin in sake cd ita wani abu ne naji hannayen 'yansanda da suka rakoni sun ta6a ni a baya. Na waiga a tsorace na gansu su biyu sun qariso. Lkc ya cika kenan. Suka janyeni da tsiya daga qarafunan da suka ga bani da alamar tafiya. Suka 6an6are hannuwanmu dake manner da juna ni da Zubaida. . Ta dago min hannu tana yo min bankwana, wannan shi ne hoton da ta ajiye min a cikin xuciyata. Wanda ba zan ta6a mancewa dashi ba." shi yasa tun a farkon wannan labari na fading maku na dade ina ganin 'yanmata a duniya ina mancewa dasu. To amma Kuma ba zan ta6a mancewa da masoyiyata Zubaida ba." . Na daga Zubaida hannu ina tafiya ina waigowa muna kallon juna har na fice daga gidan tuhumar. Na fara tafiya ni kadai a kan titi ina baqin cikin rabuwa da Zubaida. Sai na fara kokwanton anya kuwa ba sharrin ake yi mata ba? Na tuno yadda muryarta musamman a ranar da muka fara haduwa, tun lkcn da ta zo wurin ta zauna, tana yi min kallon soyayya. . "....ya sunanta...? . Anya kuwa Zubaida ce take kashe mazajenta? Ba zan ta6a amincewa ba." na ce a xuciyata. Sharrin ake yi mata. Ta amma Kuma ita ma ai ta fading min da bakinta. Ba gsky bane. To dukan da ta sa aka yi min fa? Shima wannan ba laifinta bane, don kuwa tayi ne don ta karen martabar aurenta. Don Kada in sake binta gidan miji in murderers masara wuya. . Zubaida bata da wani laifi, tabbas sharrin ake yi mata. Wataqila Kuma ita ce ta aikata laifukan. To amma Kuma ni dai banana....." zarginta. Yaya kuwa zan dorawa wacce nake so a xuciyata laifin kisan kai? Bayan Kuma ita ce mace ta farko da na fara so a rayuwata? sannan Kuma zan ci gaba da son Zubaida har nan da qarshen rayuwata. . . Alhamdulillah!! Na sadaukar ga kafatanin ahalin "TASKAR GIDAN LITTAFI" . Jinjinawa ga mai mai gida shafi'u D Giwa . Kina na a xuciyata khadija musa shehu. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels