MIJIN TACE 4 NA HAJ. HAFSAT C. SODANGI (Mrs. Yunus Abdullahi Dabai) 1 GODIYA Godiyar ga Allah take, Subhanahu wata'ala, Masanin yau da gobe, Gwani Mai Hikima, wanda yayi halitta tasa duka bibiyu, mace da namiji, ya kuma halicci mutum da aljan don su bauta mishi. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga cikamakin Annabawa Shugaban Manzanni, Annabin tsira, Annabin karshe Muhammad (S.A.W), da Alayensaa da Sahabbansa, da wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar karshe AIkiyama. Bayan haka, ina mika godiyata ga Makaranta littattafaina, wadanda kullum sakonninsu basu yankewa a gare ni, suke ma kara min hima wajen ganin na fiddo musu da sabbin takardu. Na gode da hakurinku a kaina, na kuma gode da kulawarku kan rubutuna. Ubangiji ya saka muku da mafificin sakamako. Na gode. Hafsat Chindo Sodangi 17/1/2013 2 SADAUKARWA Sadaukarwar kullum ta Iyayena ne saboda kulawarsu da tarbiyarsu a gare ni. Alhaji Chindo Muhammad Sodangi, da Hajiya Fatima C. Sodangi, Allah ya saka muku da mafificin sakamakonsą, amin. TUKUICI Tukuicin littafin na dangin miji ne, Jama'ar Dabai. Na gode. JINJINA Jinjinar taka ce Muhammad Kabir Sodangi (A.T.B.U Bauchi) FATAN ALHERI GA Sha'awa Kabiru Mamman Namani Tsafe Da Halima Ibrahim Dogarai (Dauravwa S.P.S Primary School) Da Asiya Sani Yashe (Mrs Mustafa Marafa, Gusauu Zamfa State) Da Hajara A.S Mai Salati Niger Badi'atu Dr. Yusuf Dan Sadau 3 Amina Ibrahi Farouk (Mrs Magaji Abdussalami Majia) Dukkan ku na gode da kulawarku. KUNA RAINA Ubaidah Ladan Sokoto Wasila Mahmud Kano Mariya Aliyu Halima Adam Kwayakusur Karimatu Gamawa Aisha Muhammad Jikamshi Amina Ahmad Baballe Umahmah Abdullahi Gusau, Zamfara Abidah Kabir Usman Bauchi Maryam Abdussalai Kabara Dukkanku ina yi muku fatan alheri tare da iyalanku baki daya, na gode. GAISUWAR SADA ZUMUNCI GA Ga Sister Baturiya Yar'adua Psychiatric Hospital Katsina. Na gode YABO Yabon naki ne Hajiya Iyatu Abba (B.R.C) Bauchi 4 GODIYA Ga Dr. Zayyanatu Ahmad GAISUWAR BAN GIRMA Ga dan uwana , Mallam Jibrin Adam Sodangi Da iyalanshi, Ubangiji ya saka maka da alherinsa kan zumuncika, amin. FADAKARWA Litattafan Sodangi basa mufin habaici ko yi da wani, an rubuta su ne kawai don fadakarwa, nishadanmtarwa da taya hira, ana neman afuwa ga duk wanda yaga wani abu. a ciki yayi daidai ko shigen kama da abin da ya, shafe shi, bs da shi din ake ba dace ne kawai. Na gode. Fatan alheri gare ku dukkamku Hajiya Hafsat C. Sodangi 2/4/2013 22/5/1433 Hijrah Littattafan SODANGH 1- Uwar Miji -Naga Ta Kaina - Wayyo Duniya - Rabon Kwado... ikar Alkawari 1 -Tabbataccen Alamari -Yi wa Wani.." -Abu Naka. Nufin Allah -Garin Banza.. -Gani Gare Ka - Me Za Mu Ce Da Maza? - Biyan Bukatar Rai - Kif Na Ganinka.. -Da Kamar Wuya... - Daga Kin Gasciya... - Shamaki - Mai Uwa.. - Hattara Mata Da Kicin Dinsu - Mata Masu Duniya - Duk Daya Kyautata - Ayi Dai Mu Gani,.. Wacece Ni? -Wata Fuskar... - Mijin-Tace 6 MIJIN-TACE 4 Gari ya gama wayewa ne kawai a cikin gida ni da Ado muka ga gaba daya cewar jiya da daddare Ado da Goggo Ayalle sunyi kaca-kaca akan kawai ta gaya wa Humairah gaskiya. In ban da ma ita Goggó ta nuna halin girma, bata tanka wa maganganun nashi ba watakila da dukan tsiya ya nada mata. Baba Tanimu da kanshi a wannan lokacin salati yake yi, yana karawa, tare da kanbama al'amarin, sai fadi yake yi "Lalle al'amarin Adamu akar wannan yarinyar ya wuce yanda duk ake zato." Sai yada wannan maganar ake yi, Goggo Ayalle tana ji ta ki yarda ta dubi girman sheckarunta ta gyara al'amarin, ni na yarda ta fadi gaskiyar abinda ya faru kar ta rufe komai, yafi min sauki kan ace wai Ado ya zage ta a kaina, wai har mą in ban da tayi shira da dukd ya nada mata. Cikin zuciyata ha ce, watakila ma dai dama itama Goggon dan kiris take jira da ni. Tuni matan gida suka mike tsaye suna ta aikéwa 'ya' yan gidän mata da suke aure a wastu gidaje da labarin abin da suka ce wai ya faru. Ita kuwa Goggo tayi kwanciyarta a daki ko kosan ranar bata fito tayi ba, wai ba za ta iya ba sai Ruwaila ce tazo ta dauki kullin ta soya, wai don kar 7 abar shi ya lalace. Ni kam ina kwance 1amo akan gado, in ban da kuka babu abinda nake yi, ana cikin haka naga Ado ya shigo dakin, ko kallon inda Goggon take bai yi ba, ya ce min tashi Humairah tashi ki koma dakinki" Ban motsa daga yanayin kwanciyar tawa ba, ban ma so ya shigo in da nake ba, balle yazo yana yi min wata magana ba tare da ya kula da Goggo Ayalle me dakin ba, tashi mana. Hanmu biyu ya saka ya đauko ni ya saukar dani, alamar zai iya daukana ya fidda ni . in ma ban yi hakan ba. Na kalli in da Goggo ke kwance, na gaishcta idonta a rufe bata amsa ba, wai ita a dole bacci take yi. Tasa ni a gaba yayi ya kai ni wurinmu, sa bamu ki share hawayenki, kerin sake-ganin zubarsu, in ba so ki ke gaba daya ratimu ya baci ba, ka sani da baka yi mata magana ba. ' Shhhhhhh! Ya dora dan yatshinšhi a lebenshi ya fitar da sautin alanar kashedi na' kar in sake furta mishi wannan maganar. Sa kai yayi ya ita ya bar ni bayan yasan nayi wanka ya tasa ni a gaba sai da yaga nayi shafa na gyara jikina na sanya atamfata mai kyau na kuma shiga dakin dahuwarmu wanda na same shi a gyare tas, na kama aikin girka mana abincin da zamu ci. Amma dai ni kam yi kawai nake yi, amma ni 8 kadai nasan yanda zuciyata take ciki gace da tsoron abin da zai faru, duk da dai Adon yayi tayi min kashedin wai kar in tsorata, yana kallon duk abin da ake yi babu kuma abin da zai same ni. Kan ka ce meye wannan? Matan gida suka hadu akan sai an kama ni an dana min duka ne zai sa in natsu in shiga hankalina, in daina kwasar maganar mutane ina gayawa mijina, ina bata tsakaninshi da 'yan uwanshi. Na shiga tsakaninshi da Hajiya Majadan ta hakura dashi ta bar min shi, to su ba zan shiga tsakaninsu da shi su hakura dashi su bar min shi ba, maganina kawai zasu yi. A wannan lokacin na kai matuka wajen tsorata, ba wai dukan da zasu yi min din ne yafi tsorata ni ba, a'a! abin da zai faru tsakanin Ado da masu zuwa dukan nawa ne yafi zamo min abin tsoro, gashi kuma ya tattara komai ya dora laifinshi akan Ruwailah, duk da har zuwa yanzunnan babu wanda ya ji bakinta a ciki. Baba Tanimu ne ya hana yunkurin dukan nawa da aka yi bisa dalilin da ya basu na ccwar shia matsayinshi na babba, yana gida bai kamata ya bari ayi abu na rashin hankali irin wannan ba. Adau dai dan shi ne da dan uwanshi ya baifa ya bar mishi, don haka ba zai yarda a raba shi da shi ba, tunda kuwa abin yazo kan iyalinsti, to ai gab yake da 9 isowa kan shi, ko ma ya ce ya iso. Don haka abar mishi lamarin kawai a hannunshi a ga abin da zai yi, gaba daya suka amsa haka ne Baba, haka ne. Adamu ka ai bai taba sabawa da kowa ba, gaba daya dangi da 'yan uwa kowa nashi ne, sai a wannan lokacin a sanadin matarshi yanzu tsakaninshi da Jafaru basa wata mu'amallah. Shi da matar Jafaru kuwa Ruwaila basa ko ga maciji, da ya ba, 'ya'yan Jafaru wani abu su anfana dashi gara ya baiwa na waje da bai hada komai da su ba, ai kuwa da magana suka ce kwarai Baba. Duk wannan karin bayanin da na ji na Baban yana yi musu ne, a zuciyata na ce uh'uh hun! Baba ashe kaima "MIJIN-TACE' ne, wannan lokacin ne na kara yarda da maganar Ado. Tun kafin yamma tayi kuwa sai naji Babà yana yi wa Ado magana, kan yaje ya duba wasu yanmata da suke wasu gidaje da ya gaya mishi su. Ina jin Adon yana ce mishi ni da ba ni da daki Baba in naje naga yarinya aka ce an bani ita ina zaan sa ta? A dai yi min hakuri kadan in samu in gina 'yan dakuna koda biyu ne. Da daddare muna tare da shi nayi wanka nayi kwalliya da sabbin rigunan baccin da na tarar ya tara a dakin don in sa shi ya ji dadi, duk da nasan cikin 6acin rai na wuni, amma nasan bai kai nashi ba, 10 tunda sau biyu ina jin shi yana tarmbayata. Anya ca namiji yana da ranar da yake fita daga maraicin wa kuwa Humaira? Na kalle shi cikin natsuwa aa ce mishi, "Yana fita niana." Ya sake kallona ya ce anya? Sanin yana cikin wani hali da kua jin maganar Baba Tanimu da na yi ya kara sa ni fahimtar Goggo Ayalle ta niyyar taimakon surukarta a kaina ne, yasa tusawa mijinta wasu maganganu. Musamnan da yake rashir shirin Ado da Ruwailah ya haifar da koma bayan mu'mamallah tsakaninshi da Yaya Jafaru, tunda shi ma wata kila tana gaya mishi wani abuu yana dauka. Gyara yarinyar nayi tsaf, hayan nayi mata wanka na gasa mata jiki don taji dumi tayi bacci mai nauyi tun akan 'ya'yan da Innata take haifa na koyi wannan. Na kaita can gefen katifa ta karshe na kwantar da ita, na lullube ta na daw0 na samu Ado a inda yake zaune, ya mike kafarshi guda daya ya kuma tsayar da guda daya ya tsaida gwiwan hannunshi akai don ya ji dadin dafe goshinshi da tafin hannun nashi. Na matsa jikinshi na jingina kaina da kirjinshi nasa hannu ina cire mishi botin din da ke jikin T-shirt din shi. Zubo idanuwanshi akan fuskata cikin murya mai sanyi ya ce min a bacin ran abin da 'van wauna suka yi mi a gidan nan yau Humaira har za ki iya 11 kulawa dani ki bani lokacinki? Na kalle shi cikin natsuwa, sannu a hankali na sakar mishi lallausan murmushi, don in samu damar isar da sakon da nake son isarwa zuciyarshi, don kuwa na nga na yi niyyar rike mijina a hannuna. Na sani babu abin da zai farantawa Mama rai irin ta ganni a gida babu auren Ado a kaina, ace mata yan uwanshi ma'ana dangin ubanshi nc suka yi nasarar raba ni da shi. Yan uwanmu ne dukanmu kawu, ba 'yan uwanka ba ne kai kadai, don sunyi mana wani abin da bai yi daidai ba ba zai hana ka samun lokacina ba, kai mijina ne. Kai ne kuma mafi darajar mutancn yanzu a wurina, ina kuma sonka. Ban taba furtawa Ado irin wadannan kalaman ba, ban taba kallon idonshi na furta mishi wata kala ta nuna kauna ko mihimmancin a wurina haka ba. Don haka maganar ta shige shi da kyau, abin da kuma dama nake son gani kenan. Humaira! ya fadi sunan cikin wani yanayi, yaja bakinshi yayi shiru, wata kila saboda ya rasa kalmar da zai gaya min, ina sonka kawu, na sake furta mishi kalmar. Jikin Ado ya dauki rawa, tanfar dai wani irin tsimi aka bashi, nayi amfani da damar da na samu wajen yi mishi abinda ya dace in yi saboda in kara 12 mallake abinda yake dama nawa ne. Lokaci mai tsawo muka dauka ni dashi cikin wani irin yanayin da ba zai yiwu in kwatanta shi ba, sannu a hankali ya yi gyaran murya bayan ya samu natsuwar da ta dace da shi, a hankali ya soma yi min magana. Zan sallame ki gobe in muna raye kije gida kiyi bakuntarki, duk da ba a haka naso kiyi tafiyar ba, ba kuma a goben na shirya ki tafin ba. To amma kuma ba zan iya barinki a gidan a yanzu ba don ina bukatar kwanciyar hankali da zan yi wasu abubuwa kan abubuwan da suke 2aruwa. Wani irin sanyi ya sauka cikin raina, ina fata za ki je ki dawo ba tare da kin gayawa inna wannan damuwar ba? Nayi maza na ce mishi ko, kadan, to gaya min in ji ke da kanki don in ji irin adalcin da za ki yi min, kwana nawa zaki yi? Cikin zuciyata naji tanfar in ce mmshi to in yi wata biyu? Sai naji tsoro kar ya ce ya tasa, na ce mishi da dai kai da kanka ne ka gaya nin da yai. Yana makale dani a jikinshi yayin da kurma nake bai wa yarinya nono, ya ce a'a ai ni nace ki fada sai dai a duk wani hukunci da za ki zartar a tsakanina da ke, na roke ki kar ki so kanki a kaina, komai za ki yi kiyi adalci a tsakaninmu. Ki sani ba a yau ki ka fara ji na ina furta kaimar ina sonki ba, nayi hakan yafi a kirga. A yau kua ina 13 so in kara jaddada miki ina sonki fiye da duk yanda ki ke tunani, gaba daya fatana da burina kuma bai wuce in samu wata dama da zan nuna miki halaccina ba, in dai nuna miki cewar ni din namiji ne. Na ce to in yi...ban san yanda aka yi ba, sai naji bakina ya ce mishi, kwana goma? Yayi murmushi alamar ya ji dadin hakan da na fada, za ki iya yin har sati biyu babu damuwa. Na ce mishi to na gode. Gari na wayewa na soma shirye-shiryen yin tafiyar da Adon ya ce zan yi a ranar yayin da shi kuma ya ce min zai je wani wuri ya dawo, na ce mishi to. Yana fita kuma ya toro min Bala, wai yazo in ba shi ayyukan da zai taimake ni da su, na kuma san har da tsaro yasa ya turo shi. Yana taya ni aikin yana ta murna, Mallam ya ce zai yi min rakiya zuwa gidanmu, kai Innarku da kirki take Anti Humaira, na ce ko? Yayi ta rantsuwa, na ce ai na yarda Bala huta da rantsuwar taka haka. Tunda Ado ya bar gida wajen shidan safe bai dawo ba, sai wajen sha biyun rana. Kan nan kuwa babu abinda ban yi ba har miyar da na saba yi mishi wacce yake tafiya da ita Danja tun bayan rikicin da muka yi kan zamanshi a can na soma yi ishi. Ki gama dai ko? Na ce mishi eh, ya ce ina Umahmah? Na ce tana wurin Goggo Ayalle. Ya zuba min ido, nayi mishi bayani na gyarata naje na kai 14 mata ita. Ba zai yiwu ace zan dauki mataki akanta ba, suma mutanen gidan duk naje na gaishe su, amma ban yi musu maganar tafiyar ba, tunda baka gaya min ba. To kin kyauta, bari in je in gaya musu, na ce to. Ya fita bai dade ba ya dawo, kai Bala jeka kayi shiri kazo ka fitar da kayan nan ga motar da zaku yi tafiyar da ita can a waje, yayi maza ya fita sai washe baki yake yi. Na zubo abinci naje na kai mishi na zauna yana ci shi kuma yana yi min bayani, na dan yi miki sayayyar tsaraba, sai dai bata da yawa tana bayan mota nayi godiya tare da yi mishi addu'a bayan naa tabbatar mishi da cewar ta ishen. Ya turo min wani dan kunshi wanda ya nadc cikin leda, ya kuma yi rafin din soletep ya nadu sosai, nasa hannu na dauki kunshin ina dan jinjina shi a hannuna, bai kalle ni ba ya ce min kudi ne a ciki, ki kaiwa Baba ki ce mishi na roke shi ya biyawa Inna kujera taje ta sauke faralinta. Ban san san'da nayi jifa da sunkin kudin nan ba na kankame Ado don farin ciki, in kin je gida ki ce ina gaishe su na ce mishi to. Sallama nayi da kowa a gidan cikin wani yanayi da bazan iya kwatanta farin cikina ba, ina fitowa daga wurin Ruwailah ina jin ta tana cewa yar hirarta ai 15 una nan da ita sai ya nuna mata cewar shi din da namiji ne. Na shiga wurin Goggo Ayalle nayi mata sallama nasa hannu na dauki Umahmah na rungume a kafada maimakon in bari a biyo ni da ita saboda gaskiyar magana ita ce girma da kunyarta da nake ji sun yi matukar raguwa don ta riga ta bar ni na gane in da ta dosa. A cikin motar ni da Ado ne a baya saboda wai zai sauka ne a mararrabar Danja ya tafi Danjan mnu kuma sai mu nufi Kudan zuwa Makarfi, daga nan mu isa Kano mu dauki hanayr Bauchi, shi kuma Bala da direba suna gaba. Kwalliya sosai Ado yayi yana rungume da yarinyar a cinyarshi, na kalle shi naji dadi mijina ai cikar halitta ne mai kuma tsabta ga kwarjini ga zati kalaman Baba Tanimu suka fado cikin raina na yaje ya duba wasu 'yanmata. A hankali cikin natsuwa na tambaye shi, amma ai ba za ka fara zuwa tadi a bayana ba ko? Bai juyo ya kaile ni ba murmushi yayi ba tare da ya daga shi daga kallon 'yan yatsun hannun Umahnah ba a hankali ya ce min kina tsoro ne? Na dan matsa kusa dashi na kwantar da kaina a gefen kafadarshi nayi mishi magana a hankali ba tsoro nake ji ba ina dai son mijina ne kawai, shiru yayi bai ce min komai ba. 16 A mararrabar Danja ya miko min yarinya na karbe ta ina shirin sallama dashi yasa hannu a kui6in wandonshi ya ciro kudin da ban san adadinşu ba, ya jawo jakata ya sanya a ciki ya zuge zib din ya fita, bayan yasa bannu ya dauki food flaks din miyarshi Suka yi sallama da direba da kuma Bala ya tsallaka in da zai hau mota mu ma muka mika muka kama tafiya. Tafiyace ta fara mikawa sosai kewar mijina taci gaba da karuwa a gare ni ina kara nesa dashi kewa da kaunarshi suna karuwa cikin zuciyata. Ban san yanda aka yi ba sai kawai naji zuciyar tawa ta kama yin nazari da tunani cikin al'amarin aurena da Ado wanda aka faro shi watanni ashirin da daya da suka wUce, watanni ukun farko muka yi su a gidan Babana, kusa da yan uwana da iyayena da dangina watanni goma sha takwas din bayan nan kuma tare da na shi dangin. Tunani na sosai nayi har kafin zuciyar tawa ta kawo ga tunanin bali da kuma irin sallamar da nayi da kowane bangare, na rabu da Ado ne bayan ya tabbatar min da cewar fatan shi da burinshi bai wuce nuna min halaccinshi ba, ta hanyar tabbatar min da cewar shi din da namiji ne. Yayin da ita kuma Ruwaila da nata mukarraban suma suke yi min fata da barin muna nan tare daşu shi Adon ya nuna min cewar shi din da namijin ne. 17 To wai wancne da namiji? Ko kuma me kalar da na miji ke nufi? Wannan ita ce tambayar da ta zo min cikin zuciyata. Namiji ni a sanina shi ne suna mafi daraja da Ado ke yi wa kanshi lakabi ko kuma in ce kirari dashi. Sannan duk da ban taba yi mishi tambaya yayi min bayanin abinda yake nufi da kiran kanshi da wannan sunan ba, ni, a fahitata kalmar Namiji' a wurin Ado yana nufin suna na cikakken mutum jarumi mai iya fuskantar kowane irin al'amari da zärfin zuciyarshi. Mai tsayawa kan abinda ya sanya a gabanshi, mai iya tsayawa ya fuskanci kowane irin wahala da jaruntakar shi don ya zamo kariya ga na kasa dashi, mai sanin ya kamata wanda yake iya saka alheri da alheri. To amma a wurin mutane kamar su Ruwailah da masu fahita irin nata, ina ganin shi 'namiji' ba kowa ba ne a tasu fahimtar face jarumin da ke iya danne na ƙasa dashi. Jarumin da bai kamata mace ta bashí amana ba saboda bai da alkibla guda daya, yana iya canzawa a kowane lokaci, ya manta da farko ya saka aheri da mummuna tunda shi din kanshi kadai ya sani. Bai kuma damu da rayuwar kowa ba sai tashi, tunda a bakunansu dai kusan kullum sai ka ji su suna 18 fadin in dai 'Namiji' ne ai gashi nan ga ta nan yanzu-yanzun nan ne kuma zaka ji su suna cewa wa shi 'namijin ba dan goyo ba ne. Da dai na tsunduma sosai cikin wannan tunanin musamman da na tuna tun kafin in ji irin wannan kalmar a bakin su Ruwaila, na taba jin ta a bakin Babana, shima ya taba ce min in dai Ado namiji ne to gani nan gashi nan. A bakin Mama kuwa ta gaya min yafi sau shurin masaki, sai na kasa ganewa na kasa gane wanne zai dauka cikin biyun? Namiji zan dauka a fahimtar da na yi wa Ado ko 1amiji zan dauka a fahitar su Ruwailah? Mama har da Babana? Da na kara nazari cikin tunanin hankali sai naga to ai ba zai yiwu in karyata fahintar su Ruwailah ba tunda har da Babana a cikinta. Haka nan ba zan Karyata mijina kai tsaye ba, saboda girma da darajar shi a wurina. Don haka sai naga to me zai hana in bar komai na bar wa zamani lokaci mu kara tafiya cikin al'amaring rayuwa a sannu don in kara yin ilimi da fahitar da zan gane wane ne cikin biyun'? Zan gamsuda nasu ra'ayin? Tunda ai kwata kwatana ma yanzu ne nake cika shekaru ashirin da daya a duniya, don haka bai kamata in fara yankewa al 'amura hukunci ba kallo kawai ya kamata in yi tayi 19 ana kara ilimi da fahinta, musamman ma da yake masu ra'ayoyin nan duka biyu ba sa'o'ina ba ne. Watakila kowane bangare a cikinsu yana da madogarar da ya dogara da ita, wacce shi din ganau ne a kanta ba jiyau ba. ** Mun isa gidanmu lafiya, Inna tsaya cewa an karbe ni? To na tsaya bata bakina ne, sai dai abinda yafi komai bani mamaki shi ne wanda yafi kowa karban nawa da nuna farin cikin ganina wai Babana ne. Duk da cikin dare uka isa, daren ma har ya fara nisa dakin Mama na fara shiga saboda umarnin da Adon ya bani kenan amma wai a wannan tsohon daren ina gaida Mama, 1donta yana kan zanina tana kokarin tantancewa super ta asali ce ko ta kwaikwayo? Ni kuwa na gyara mata sosai don taga abin da take son, cikin zuciyata kuwa cewa nake yi uh uhun, ba a dai bar hali ba. Na fito daga dakin Mama jikina a sanyaye kwarai saboda tsananin ranmar da na gani a tare da ita, gashi tayi duhu ga wasu wunduna guda biyu a tsakanin hakoran gabanta guda biyu. Nayi tunanin abinda ya baddasa mata hakan, sai da kyar na iya tunawa da cewar jajayen hakoran da ta 20 sanya ne sanda ta tafi aikin Hajji suka tafi suka bar mata bakin nata, a zuciyata nayi dariya na ce kai wadannan hakora sunyi tsiya. Maimakon su tafi su bar mata natan sai ga hadfa har dasu? Na ce to ko da yake dai ai tayi ado dasu, na sake tunawa da irin adon da Mama tayi da hakoranta na ce to sun mori juna. Na shiga dakin Innata wacce ko lekowa mu hada ido bata yi ba tun zuwana gidan, jikina a sanyaye kar dai duk mutanen gidan haka suka zama tunda Baban nawa ma ya zube ba kamar da ba, amma kam nashi wasa ne akan na Mama Inna tana nan kalau dinta, sai ma kara murjewa da tayi, ta yi shar gwanin sha'awa da ita, kuruciyarta sai karuwa take yi, tayi kwalliyarta daidai da ita, gashi komai da kuma ko'ina dinta sai kamshi yake yi a cikin kuma tsabtar da ta dace da shi. Zama a gaban kujerar da take zaune nayi a kasa na kwantar da kaina a jikinta ina shakar kamshinta, waiyyo Inna! Na fadi hakan cikin murya mai rauni kwarai. Ashe kuna tafe? Ai bai fadi kuna hanya ba, sai dazu dazun nan da ya tabbatar kun kusa shigowa gari wai don kar in yi ta damuwa. Na kara makalewa na kara kwantar da kaina a cinyar Inna sosai, cikin shagwaba na soma ce mata naji mararinki Inna, naji marmarinki na ii mararinki 21 har na rasa yanda zan yi ke kuma ki ka ki zuwa." Ta ce, to ba muna gaisawa a waya ba? AAi abubuwan rayuwa ma sunyi sauki, ko baka ga mutun ba zaka ji muryarshi ku debewa juna kewa, mu da iyayen mu suka bada mu ai gamu gasu amma basu ganmu ba basu kuma ji muryoyin namu ba sai da aka dauki lokaci mai tsawo. Sa'adatu tazota wuce tana goye da Umahmah a bayanta, Babana ne yake kwala nata kira, a zuciyata na ce kai lalle wani sabon abu yana faruwa a gidanmu, ko ma in ce ya faru. Babana yana mu'amallah da kowa daidai da cewar mu'amallar a gaban Mama tana kallo lalle an samu yancin rayuwa. Sa'a ta sake dawowa tana kallona cikin murmushi, "Kai Anti, wane irin tsarata kika yi haka? Na kalle ta cikin natsuwa na ce mata, ban ma ganta ba Sa'a, sayayyar yayanki ne. Tayi murmushi, to wai in ji Baba a ina za a sa miki kayan gasu nan ana shigowa da su, na kalli Inna naga sha'aninta take yi. Na maida kallona wajen Sa'adatu na ce mata kin ga ni Sa'a akwatin kayana kawai za ki dauko, tsaraba asa a dakin Baba ko falonshi, ta ce haka ne ta juya ta fita. Rannan ni da Inna muna kan gadonta yayin da Umahmah take wurin Sa'a a dakinsu, na kalli Inna 22 bayan mun gama magana da Ado a wayar Inna nayi murmushi na ce, inna ina ta tunanin yanda zan gan ki gabana yana ta faduwa sai kuma na gan ki fa da ke. Komai din ki kalau, sai ma abinda ya faru ga su Baba karani da...ban san yanda aka yi ba kasa fadin sunan Adam nayi kamar yanda na saba, ban taba sanin sunan yana yi min nauyi haka ba sai yau. Don haka na bar fadin sunan na ce duk sun girmna Inna, komai na ki a cikin rufin asiri yake. Inna ta saki wani irin lallausan mnurmushi ta ce, ai haka al'amarin Ubangiji yake, wani lokaci sai ya yi maka wani abu, kayi ta bakin ciki saboda wauta da ajizanci na rashin sanin abinda yake boye. Sai daga baya a hankali sai ka gane ai wanan abin da ya baka shi ne alherin da kullum da kullum ka ke rokon shi ya ban, ba tare na fahimci in da zancen Innan ya dosa ba na ce mata haka ne Inna sai naga ta zuba min ido cikin tsananin natsuwa ta ce min ki kadai nasan irin bakin cikin da nayi akan aurenki. Ni kadai nasan irin kukan da nayi a bayan ido kowa, ni kadai nasan tunda aka furta auren ban sake rufe ido cikin dare nayi bacci ba, gayawa Ubangiji ina rokonshi ya kawo wani dalili da auren zai fasu. Ba tare da wata fitina ta auku ba, in kuma kaddara ce sai an yi, to ya hana su cutar min da ke ya kuma tsare min ke daga duk wata fitina, ya kuma 23 nuna mnana alheri mai yawa bayan hakan. To gashi nan a yau ba a je ko'ina ba auren naki ya zama shine aure mafi 'yanci da duk yaran gidannan suke yi, gabana ya fadi jin abinda Innan ta fada, na kuma san da iyakacin gaskiyarta take yi. Don haka nayi shiru kawai ina sauraronta, ta ci gaba da cewa, auren naki shi ne aure mafi zaman lafiya da kwanciyar hankali, cikin raina na sake cewa uhun, Inna kenan, ko dai don ban tona miki abinda nake ciki bą? Shi nekuma auren da yafi kowanne zamo min sanadi na rufin asiri mai yawa, shagon nan da yaron nan ya bar min ai ba karamin alheri ya bar min ba Ga wannan yaron da aka sanyawa suna kina ta kuka ina baki hakuri don bai kamata komai in biye miki muyi tayin abu ba, ashe shima alherin ne, na samu A.C saboda shi. Na samu albashin wata sabo da shi, nayi maza na kalli Inna na ce, albashi? Ta ce, eh, bai gaya miki ba ne? nayi maza na ce, a'a Inna. Ta ce, ai tunda mijinki ya soma aiki bai taba fashin aiko mishi da kudin madararshi ba, a zuciyata na ce uh uhun, Inna tana ta famann murna kan wadannan abubuwan don ma bata san wani alherin da Adon ya sake aiko mata ba. Sai na ji ta ce min, shi yasa dukanku a yanzu nake gaya muku dama duk wani wanda zan gayawa 24 ya ji, kullum ka tsaya akan yin addu'a, kar kuma ka cuci kowa, a kan saninka. Abinda duk ya same ka kuma ka dogara ga Ubangiji kar ka yarda zuciyarka ta raya maka cewar wani ne yayi maka ko da kuwa a zahiri shi ne sanadin abin. In ka nemi abu baka samu ba kuma ko wanda ba ka zato yazo maka to ka roki Ubangiji ya zama shi ne mafi alheri a gare ka, tunda duk al'amarin nashi ne. Cikin natsuwa na ce mata haka ne Inna. Rannan haka muka kwana muna hira ni da Inna akan gadonta muna kwance yayin da itama Sa'a ta kwana hidima da Umahmah, wacce ta ki yin bacci tana 'yan koke-kokenta a nasu dakin. Ko kawota kuma bata yi sai in Inna ta ce to tunda ba ki da nonon da za ki baiwa yar taki ai gara ki kawo ta a bata ko ta kara jin dadin rikicin nata, a duk lokacin da na karbi Umahmah ina bata nono Inna ta rinka kallonta kenan tana bin gabobinta tana dubawa. A duk sanda ta gama dubawan kuma sai ta ce to yaushe wa ya taba sanin wannan shi ne abin da zai faru? Ni kam ban mike na gyara kwanciya da nufin yin bacci ba, sai da aka yi kiran sallar farko, Inna tayi maza ta kallen ta ce, wannan ai shi ne karya, ki kwana kina magana Asuba tayi ki ce za ki yi bacci Ai mikewa za ki yi kivi alwala kivi nafila kafin 25 lokacin sallar tayi. Ina idar da sallah su Atika da sauran yan uwa suka soa kiran wayar Inna suna yi min sannu da zuwa tare da fadin ga sunan zuwa, don haka na mike naje nayi wanka da ruwa mai dui na watsake, nazo na zauna ina shafa. Sa'adatu ma tana sanyawa Umahmah kayanta, suma wankan suka yi. Kai Anti, kin iya sayen rigunan yara, na ce bani ba ce Sa'a kai ji wannan ma, wanne zan sa mata? Ji wata ma, kai ga wata. Inna ta ce, da dai kin hakura kin sa mata guda daya yau da gobe sai ki ga kin sanya mata sauran ma, kin gansu a jikinta. Kwalliya sosai nayi, wata super na sake daukowa gara ta jiya da nazo da ita ma na taba daurata, wannan sabuwa ce dal, Sa'a ta kalle ni tayi dariya ta ce "Anti ai ke har kin fi ma matan masu kudin daura zannuwa. Nayi murmushi na ce, "Wannan shi ne iya shege matar me kudi bata daura zani ta daura gwal ta hau mota me numfashi ba me tayi? Inna tayi murmushi ta kalli Sa'adatu ta ce mata, kawo yarinyar ki kawo mata ajiyarta, ta kawo mata ita ta wuce cikin dakin Inma, wata 'yar leda ta kawo min wacce da gani na sani daga Saudi take, ga kuma alamarta, ga yan akwatina a ciki har guda uku. Daga ina wannan Inna? Ina bude su ina tambaya, sarkokinki ne da ki ka tafi ki ka bari na baiwa Mama 26 sanda za su tafi aikin hajji da Aliya, na ce ayi ciko a canzo miki sarkoki ne guda biyu babba da karama, ga kuma warawarai guda hudu da zobuna biyu, wanda ni su suka fi daukan hankalina ma. Don nan take na zuba su a hannayena ta kuma sa zobunan, in ban da Inna ta ce in sanya karamar sarkar ma ni ka da hakan ma ya ishe ni. Godiya mai yawa nayi mata. Na tashi na fito tsakar gida saboda jin da nayi Babana yana tambayar wai ni Aisha bata tashi ba ne? nayi maza na ce ai ban ma kwanta ba Baba, wanka nayi. Akan katuwar shifidaddiyar tabarma na same shi a tsakar gida yana zaune wanda wannan-ba wani abin mamaki ba ne, dabi'ar gidan ne yin hakan, abin maakin dai shi ne, yau shi kadai na ganshi zaune akai, ban ga Miama ba, ban ma ji motsin fitowarta wajen ba tunda gari ya waye ban ma ji wo muryarta ba ko da daga cikin dakin ne, shiru. Sai Zubaida da ke ta faman kai-kawo tsakanin kicin da tabarmar Babanmu. Kai Antin Sa'adatu kin yi kwalliya kin kuma yi kyau ba an ce min garin naku kauye ne ba? Na kalli Zubaida nayi murmushi na ce, Anti kenan. Karo na farko da bakina ya yarda ya kirata Anti, ba akan an tilasta mishi ba. Babana yayi tsaki ya ce, ka ji wani zance wurin 27 yarinyar nan, to harkar yau aljihunka ba shi ne birninka ba? Kana zaune a birni ba ka da ko kwabo ai ka zama dan Rauye, sai dan kauye ya ci duniya in yana da kudinshi kai baka ci ba. Tayi maza ta ce, haka ne kam, itama bin atanfar tawa take yi da ido, a zuciyata na ce itama ta koya wurin Mama, zuwa can kuma sai naji ta ce mu ma fa atamfofin da ya aiko mnana super ne, ban tanka mata ba Na kalli Babana wanda shia dadin ganina ya kama shi, ga kwalliya mai kyau mai kuma tsada, na ce mishi Baba bari in je in gaida Mama, ya ce to kar ki dade, don yanzu zamu karya. Me ki ke so ki karya da shi? Na ce duk abin da Anti Zubaida tayi dashi zan karya. Yana murmushin jin dadin ganin mu'amallata da Amaryar tashi, Sa'adatu ta kawo mishi Umaimah daidai zan shiga dakin Mama. Sau biyu nayi sallama katin ta amsa, bayan tana ganina ina ganinta, na ce mata sannu Mama, ta ce yauwa sannu kadai, muka sake gaisawa ba tare da ta tambayeni Ado ba, balle 'yarshi. Ni kuwa na bararraje na zauna mata a daki sosai, cikin zuciyata ina fadin abinda ka shuka shi ka ke girba, komai na dakin yayi dikin-dikin alamar datti ya kama shi saboda ba ta shi ake ba, ba a da lokacin shi balle a samu zarafin gyara shi. 28 Wai Mama da Babana suna hade a gida amma babu mai kula wani, kowa harkar gabanshi kawai yake yi, in da wani abin da ban taba zaton zai faru ina raye ba ai shi ne wannan. Ni 'yanjakar ubannan sun ma zo sun gaishe ki kuwa? Daga waje Babana ya daga murya yayi min wannan tambayar, nayi kamar ban gane su waye ba, tunda ina jin motsin mutane a dakın Mama, na kuma san su Suwaiba ne sun ki fitowa ne kawai don kar muyi ido hudu da su. Watakila suna tunanin kwana daya ko biyu zan yi, su waye kenan Baba? Cikin natsuwa da murmushi mai yawa don dai ma Mama ta kara sanin mun shirya da Baban nawa, nayi mishi tambayar. "Wadannan 'yanjakar uban mana." Ya sake yin zagin, mamaki ya kama ni ban san Babana da yawan zagi ba, watakila itama Mama abin ya dame ta, don wani mummunan tsaki naji taja kafin naji ta ce. "Kai Allah kenan, rayuwa dai bata yi ba tunda an kare da zage-zage. Da sauri na kalli Mama saboda jin maganar tata dan kirin ya rage in kyalkyale da dariya, saboda yanda ta tsuke fuska ga ta kuma dama ta zama 'yar karama. Wadannan yan jakar uban Mama su Habiba masu gadon mugun abu ai suna nan a ciki." Gabana ya yanke ya fadi, cikin tsoro da kunyar masu gadon mugun abin da yake fada nayi maza na 29 ce, a'a Baba, ai ma ba laifinsu ba ne nawa ne, da na yi wa gidan shigowar dare. Da sauri na mike na nufi can cikin dakin na Mama na barta tana tsaki tare da fadin wannan yaron ai wahala ta same shi, tunda ya gamu da mutane marasa Imani, balle tausayi." Ko a jikina. Ashe kuna ciki? Nayi tambayar daidai na daga labulen kofar wanda ya zama tanfar ba na Mama ba don datti. Abinda na ganin yayi matukar kadani, tukunyar alala akan risho a bayan kofar Mama yana tafasa, ga Anti Sha'awa da Habiba suna kwance kan katifar da ke yashe a kasa sun tasa 'ya'yansu a gaba suna basu non. Suwaiba ce a gaban tukunyar tana rantsuwar ita da kanta zata raba don ba za ta yarda ta bar musu ba su kwashe su baiwa 'ya'yansu, su bar mutane da yunwa. Na kalli 'ya'yan sun kai biyar ban da masu shan nonon, sun takura waje daya gaba dayansu ya'yan Anti Sha'awa ne. na ce, kai su Buhari ne haka? Suka zubo min ido alamar a cikin doka suke. Muka gaisa da Sha'awa da Habiba har na karasa shiga na yi wa 'ya'yan da suke shayarwa wasa, Suwaiba ta sunkuyar da kai kasa tayi kamar bata ganni ba, nima na wuce na fito ban tanka mata ba. Na kama hanya zan fita saboda jin muryar Salisusu da nayi, na kalli Mama nayi murmushi na ce 30 Kawu fa ya ce a gaishe kir da kyau-da-kyau, ta ce madailah. A tsakar gida Salisusu yana tsugune suna gaisawa da Babana, ga katuwar kula a gefenshi alamar shi yazo da ita, sannu da zuwa Yaya, ya dago ya kalle ni cikin murmushi, Anti ashe kun iso? Na ce eh. Ina Baban ba ka zo min da shi ba? Yayi murmushi, suna nan zuwa. Muka gaisa sosai, cikin yanayin suruka kafin ya mike ya shiga wurin Inna. Babana ya kalle ni ya ce min, ga abin karyawa nan daga wajen Atika. Nayi murmushi na ce, an gaishe su, amma sai naci na gida na Anti kafin in ci na wani, dadi ya sake kama Babana. Muna cikin haka sai ga su Buhari a guje Suwaiba ta biyo su tana duka, wai ta ce kar suyi warwaso sun yi, Baba ya daka musu tsawa kai ku min shiru ku koma dakinku ku zauna kar kuzo nan ku cika min kunne da ihu, 'yan jakar uba kawai marasa da'a masuu abin tsiya. To an koya musu. Cikin zuciyata na ce, oh oh, Baba kuma sarar da ya samu kenan? Ko da yake dai ba laifin shi ba ne, Maman ce ta koya ishi komai yaro yayi, ta ce mishi wai uwarshi ta koya mishi. To gashi abin yazo kanta, a wancan lokacin da take sha'aninta kuwa bata taba tsammanin abin zai 31 koma mata ba. Salisusu ya yi wa Babana sallama ya tafi, sai kuma ga dan aika daga gidan Hajiya Aliya, da manyan kuloli itama abin karyawan ta aiko dashi, ga kuma na Zubaida shima ya kammala. Na kalli Babana a hankali cikin natsuwa na ce mishi, bari in kira su Habiba mu karya tare Baba. Ya yi maza ya yautsa fuska, kar. ki kira in wadannan yan jakar uban yaran. Na sake bashi hakuri kafin na dauko wata katuwar tabarmar na shifida na leka falon Mama na ce "Habibah ku fito nan mu karya. Buhai ku ma kuzo dukkanku. Na koma sabuwar tabarmar don mu zauna dasu, tunda sun kasa zuwa kusa da Baba, na ce 'rai dai' wai in ji kuda, Mowowin Baba wadanda suke komai suka yi daidai ne, sune yau suka zama babu wata mu'amalla a tsakani sai na zare ido da mmuzurai. Na kira Zubaida na nuna mata abin da Atika da Aliya suka aiko dashi, na ce mata samo wuri ki diban wa Baba nashi da na Mama da Inna da naki ta ce to, nayi zaton Mama zata ce ba ta so sai naga tasa hannu ta karba. Mu ma na Zuzzuba mana har yaran nasa musu nasa kuci a natse in baku koshi ba sai a kara muku, suka ce to ita ma Suwaiba na aike mata na kira Sa'a na ce mata ta kawo mana kunun gyadan da inna tayi. 32 Gaba daya mun suke muna hira har Habiba tana tambayata mace fa kema ki ka haifa ko? Nayi murmushi ban yi magana ba, sai kawai naji Babana yana cewa uh'uh hun, rabin da suka iya kenan, su sami abin dadi su rufan mishi su rinka ci suna zare ido suna gwalo. Amma su su zauna ana su' dakunan auren sun kasa mugun halin da aka koya musu ya hana su, gaba daya zaman aure ya gagaresu, sun dawo min gida sun z0 Sun zama min da:wasu munanan ya'yansu masu kama da "ya'yan tanda. Duk ku watse a nan ku bani wuri, yan jakar uba. Gaba daya su da ya'yan nasu suka watse da gudu, yuu suka shige dakin Mamna. Ni kam duk da na sani da wuya kwarai in ga Mama cikin wani hali da zai bani tausayi cikin sauri, halin da ya'yanta ke ciki na kasa zaman 'aure da yanda suka lalace suka zama tanfar ba su ne wadannan yan gatan ba-da suke sha'aninsu irin yanda suka ga dama. Su daura zani irin wanda suke so komai suka yi shi ne daidai, ra'ayinsu kua shi ne abin dauka, a bar nà kowa ya bani tausayi bana kuma jin dadin irin tsana da tsangwàmar da Babanmu ke nuna musu a zahir nafi sha'awar da sai ya bar abin tsakaninshi da uwarsu, tunda ita ce tayi sanadin komai. Wanda duk yasan Mama, ya santa yasan halinta, 33 yagar hain da ita da 'ya'yanta suke ciki a yau, kalma guda daya da zai iya furtawa cikir sauri ita ce, laifin uwarsu ne. Watsewar da aka yi aka bar mu dagani sai Baba atsakar gida, yasa shi kallons cikii tnuroushi ya ce min ba za ki sa a kwashe kayan da ki ka zo da su a kaiwa innarku ta raba ba? Nayi murmushi na ce ai sai ta.raberwa danginta Babe namu dangin basu samu bą. Babana yayi dariyar jin dądi a dalilin jin da yayi na tsame kaina daga cikin dangin Innata. Na ce, ai kai ne za ka raba sai kowa ya samu tunda kowa naka ne. Wani dadin ya sake kama shi, na ce amma kar ka manta da mutanen giyade, yayi dariya mai karfi. To in yi rabo kuma in manta da mutanen giyade Humaira? Rabo na gaskiya Babana ya yi yanayi ina tuna mishi wadanda ya manta da śsu. Makwabta yan uwa, abokan tare ta kowane bangare ya bayar, don ko ta bangaren Zubaida ya bata turmi biyu ya ce na mahaifiyarta da kanwarta, sabulai da omo na mutanen gidansu. Mama kuwa kaya masu yawa ita da duk wanda tasa zata ba har ma nata kason yafi na lnnarta yawa, yana kallona ya ce bamu yi wa Gabo kwauron nata ba ko? Nayi murmushi na ce, in bai ishe ta ba sai ta sayà da kudinta ta kara, ya ce to haka. 34 Mun kammala komai ne muka shiga falon Babana ni da shi muka sake. gaisawae na isar da gaisuwar Ado a gare shi. Wai shi har yanzu yana fushi dani ne ko? Nayi maza na ce mishi a'a Baba, ya zubo min ido yana kallona, nan take kuma ya zubo min hannayenshi alamar dakwa. "Kul ki ka kawo min iya shege, in ba fushi yake yi dani ba don me tunda ya tafi bai sake waiwayowa ba, ko a waya bai taða nemana ba'?" Cikin natsuwa da nuna ladabi na ce, ba zai yi fushi da kai ba Baba, to shi a wa ma da zai ce zai yi fushi da kai? Shi din kullum a cikin fadar alherinka yake. Yana kuma gaya nin cewar ya karu da ilimi iri- iri a wurinka na darasin rayuwa, yasha gaya min cewar kai ne mafi alherin mutuIIn da yasa ni wanda bai taba kyashin na kasa dashi ya samu alheri a tare dashi ba. "Bai yi fushi da kai ba Baba, sai dai kuma zai ji nauyin kiranka a waya,. watakila so yake ya samu damar da zai zo gabanka ya roke ka gafara kan kuskuren da ya aikata maka." To wane kuskure ya aikata min Humaira? Da ya rike min ke? Shi mijinki tun kafin ya aure ki ai ni da na dauke shi to balle kuma da yake aurenki yake kuma rike min da ke cikin rufin asiri a yanzu." 35 Dadi ya kämä ni na ce to zan gaya mishi ya daina tsoron kiranka Baba zai. kuma kira ka, to to to gaya mishi. Bayan wannan hirar nabi sai na isar da sakon Ado gare shi na ce, amma ya ce kar in gaya mata sai in kai din ka yarda ka aminoe, don haka sai in ka yarda ne zata ji Baba. Yarda? Yarda kai Humaira in da ina da hali kamar da da bara ban biya mata ba? To bani da hali, komai da ki ka sani babu shi, babu shi Baba? Nayi mishi tambayar a firgice, ya ce ai babu ba I gani ba? Ina ki ka ga ina zuwa? Nayi salati na ce yaya aka yi Baba? Na shiga hankaling sosai don jin äbin da ya same shi. Sai kawai. naji ya ce min Baba da lorahi, hannu biyu na saka na dafe kai3a, cikin tsananin kaduwa. Bayan tafiyar mijinki sai wannan ja'irar matar muguwa ta tasa i a gaba akan in maida su makwafin mijinki a kasuwa. Ta tasa ni a gaba da fitintinu iri-iri sai da na kái su kasuwar, ba aje ko ina ba sai na gane kasuwar tawa ba za ta juri ta'adin da ako yi mata ba don haka sai na rufe ido nayi ta maza na kore su na kuma haramta musu zuwa kasuwa. Ni da uwarsu muka shiga wani Irali na babu dadi, ga can kasuwar ma babu dadi, tunda na riga na samu matsala, abokaina duk sun yi gaba sun bar ni, don 36 haka sai na ce to wadannan gidaje da mijinki ya dawo min dasu tunda dama ban san da su ba, bari in sanya su a kasuwa in karbi kudinsu in kara jari don in koma harkar sosai. An kawo min kudin gidajennan da kwana biyu don mutum daya ne ya saye su, barayi suka zo min gidan nan da daddare suka shigo min nan. Kin ga kin gani ya nuna min wani shafcecen tabo a keyarshi wanda na tabbatar ban san shi dashi ba ya ce su suka buga in karfen da suka zo dashi suka bincike min daki suka dauki kudi suka bar ni nan a kwance a sume. Sai daga baya sai da asiri ya tonu aka samu aka kama guda daya, sai ya ce wai su Ibrahim da Baba ne suka turo su zo suyi min satar. Ni kam kuka sosai na kama yi saboda bakin ciki da tausayin Babana, tabbas Mama ta cuci Baba na, don kuwa ita tayi mishi sanadin lalacewar 'ya' yanshi. yayan da kowa yasan babu abinda bai yi akan su ba, don su zama mutanen kirki. Bata aike shi ba, bata kuma bar shi yayi shi kadai ba, kullum gini yake yi tana rusawa share hawayenki kiyi shiru, Humairah ai ya wuce. Ya wuce, kana zaune baka komai Baba? Yayi murmushi ya ce to ba gani a raye ba? Da sun yi nasarar kashe ni ko nakasa ni a wani wuri fa? Na sake fashewa da wani sabon kukan. 37 Baba Yahya ne ya iso saboda kiran da Babana yayi mishi, matar Sarkin Noma ne ta iso, nayi murmushi na soa gaishe shi ai tunda naga tsaraba na ce to ta Dabai ta iso kenan? Babana ya kyalkyale dadariya, ya ce ai sunan da ka sanya mata kenan? Baba Yahya ai ni sunanta kenan a wurina tunda dai ta ki zama cikin mu ta koma cikin danginta, to ba zan kirata da wani suna ba, sai wannan ina ta ke? Babana ya daga murya ya kira Zubaida da ke goye da ita ta kawowa Baba Yahya ita ya karbe ta cikin farin ciki yana fadin ka gani ba, wannan da ganinta ai kasan gidan noma ta fito, taci hatsi ta koshi. Baba ashe abinda ya faru kenan mu ba mu sani ba? Na tanbayi Baba Yahya cikin natsuwa don in yi mishi jaje, sai ya ce min kece ba ki sani ba Aisham, amma ko sanda muka je wurinku, ni da Mallam ai mijinki ya yi mana jajen al'amarin ya ce min Innarku ce ta gaya mishi. Mamakin Ado yayi matukar kama ni, me yake nufi da wannan abin da yayi bai gaya min ba, bai kuma yi wa Babana jaje ko a waya ba? Maganar tafiyar Inna da ya soma yi wa Baba ya katse tunanin nawa, ni kam in ban da alheri Ado ya yi wa Innata ai da na karbe kudin na mayar mishi dasu, ban ji dadin yanda yayi ko in kula da abin da ya 38 samu Babana ba. Baba Yahya ya yi matukar murna, ya yi ta addu'a yana sanya albarka, ya rungumi kudi ya tafi dasu, wai zai je yayi duk wani abin da ya dace a gama komai sai bayan tafiyar tashi ne ma maganar ta watsu a cikin gida. Mama tayi matukar kidimewa, hankalinta ya tashi ta shiga rusa kuka tana zage-zage, Zubaida kuwa sai faman tsalle take yi tana murna tana fadin yau fa ga inda haihuwar 'ya mace tayi rana. An mallake ta ita kuma ta mallako wa uwarta mijinta, Inna kam ba zan iya kwatanta farin cikinta ba, kan ka ce meye wannan yan uwanta har sun cika gida da kuma makwabta, har lokacin Mama ba ta daina kuka da zage-zagen da take yi ba. Babana yaje ya daga labulenta ya ce mata, ji mana Majadan, kin san dai dama na gaya miki sharadin zamanki a gidan nan yanzu shi ne ki zauna da kowa lafiya, don ba. zan iya lamuntar hayaniya ko tashin hankali a cikin iyalina ba. Don haka in kin ga kina da matsala ko za kije gidan ku ne? tayi maza ta suro gyalenta ta yafa ko gama rufe jiki bai yi ba saboda nadewan da yayi tana fadin ebh, ai gara min hakan yafi min wannan zaman da nake yi cikin bakin ciki, wulakanci da kuma zalunci. Ni kam ai ba zan taba yafe aka ba, sai kaga 39 8akamakon...Babana ya bi ta da kallo yace, ke Majadan ki taimake ni in kin je gidan naku kar ki dawo." Cak! Marma ta tsaya, ban san tunanin me tayi ba, sai kuma naga ta juyo ta shige dakin nata tayi shiru. Kwanana biyu a gida na soma zaga dangi yan uwa da kuma abokan arziki, har giyade na tafi da zani kuwa mun tafi ne da su Atika da Aliya da Sa'adatu. Kan hanyarmu ta dawowa daga Giyade na yi wa yan uwana magana kan halin da Babanu yake ciki na zaman rashin abin yi, bai kamata mu bar shi a haka ba. Aliya ta kalle ni cikin natsuwa ta ce, ni kam Anti ban ga abin da ya shigar damu cikin wannan maganar ba, musamman ke matsalarsu shi da matarshi da 'ya'yansu, mu kam ai ko da yake harkar ma anyi lokacin da abinci ma aka hana shi. Ba mu koshi da abin da ya faru nayi ta kawo mishi kaji yana ci har ya murmure, ba shi kenan ba? Innarmu bata cikin matsala, ba kua zata sake shiga ba da yardar Ubangii, to su karata mana ko kuwa Anti? Ta zubawa Atika ido, Atika ta tabe baki ta ce, uhn, kyale Anti kawai in kudin sunyi miki yawa ne ki kawo a rinka juya miki su zasu yi amfani a gaba. Na zuba musu ido ina mnamakin yanda ko kadan basa tausayin wahalar da Babanmu ya shiga kan in yi 40 musu wata magana sai Atika ta ce min ni ina ce shi ya kore ki ke da mijinki don taji dadi. Kuje ku kuma ku wulakanta sannan bayan tafiyar taku kin san abin da ya faru? Nayi maza na ce mata a'a, ta ce ina ce sakin Inna yayi? Da karfi na kurma wa Atika ihu tare da fadin kar kiyi min haka Atika, ta ce to tabar maganar. Ta ci gaba da baiwa Baba nono wanda ni na mika mata shi ta sake waiwayowa tana kallona cikin natsuwa ta ce min. Ina ce sai da suka yi mishi abin da suka yi mishin ne da ya kori uwarsu a gidan shi ne yazo wai inna ta koma, su Baba Yahya suka ki da Alhaji Babba, shi ne mai babban allo ya ce a'a ta koma dakinta ta zauna saboda in muka je gidan mu samu dakin da muka shiga, muka zauna. Amma ba za ta koa ba sai yaje ya daidaita da matarshi ya dawo da ita tukuna, ya hada su dukansu yayi hakuri ya zauna dasu don sun riga sun zama bangaren rayuwarshi. Inna tana da matsala ne? bata da ita, kullum Yaya Ado yana yi mata aike tana gaya mana ni ta bangare na mijina ba mai sakin kudi ba ne, saboda yana taka tsan-tsan dukiyar ba tashi ba ne ta Baba ce. Ama ya samar min da wata hanya da ake juya min kudi, ina armfana ina yi mata abin da nake iyawa, Aliya ma tana yi mijin tama yana yi darna kuma 41 danta ne tana kuma da 'yan uwanta ga shagonta na dinki. Kin ganta da matsala ne? na girgiza kai a hankali cikin sanyin jiki, can' cikin zuciyata kuma na gane abinda yasa Ado bai taba furta min abinda ya farun ba, tunda na Innan ma bai gaya min ba. Mun dawo gida da yamma gaba daya nuka dawo sai dare mazansu zasu zò su dauke su. Sa'adatu tana goye da Umahmnah, ni kuma in rungume da Babaa akan kafadata, yayin da Atika da Aliya suke rike mana da kayan tsarabar kauye da muka dawo dashi. A tsakar gida muka samu Babana ya kwance buhun shinkafa yana aunawa can gefe kuma ga doya ya kasata kashi uku, Mama tana tsaye tana kallon abin da yake yi. Karo na farko da na ganta a tsakar gida tun da nazo, da sauri naje na kwantar da Baban Atika a daki na dawo na karbi mudun a hannunshi ina aunawa yana nuna min in da zan saka. Kin ganni ina awo ba Humairah? Na ce mishi eh Baba. Ya ce to daurowa yake yi a daure, Alkali kin gane? Na ce mishi eh, Baba. Ya ce to kin ga wannan buhun shinkafar da wannan doyar kawo min su aka yi kyauta Na yi wa wanda ya kawo din addu'a, Babana ya amsa da amin. Kafin ya ci gaba da yi min bayani. Yanzu komai raba shi nake yi a gidan nan in kasa 42 kashi uku in baiwa kowa nashi ya adana a wurinshi saboda Inna ce zan ajiye ayi amfani da shi gaba daya. To sai a biyo dare a kwashe aje a Boye ana baiwa kattin banza kin ga haka zai yiwu? Duk da Mama tana wurin bai hana ni cewa a'a ba, a zuciyata na ce ke ki ka koya mishi cewa ana kwashe mishi hatsi ana 6oyewa. Shi yasa nake rabona daidai da daidai rabo na adalci in kasa kashí uku kowa ya dauka, ko kuwa? Na ce haka ne, nayi kamar in ce amma da an dan yi wa adalcin kwaskwarima, don ya kara tafiya daidai. Tunda ita Zubaida babu da ko daya a dakinta, ita ita kadaice sai kuma ake yi mata rabo na daidai tsakaninta da Innata mai ya'ya uku da kuma Mama mai 'ya'ya uku manyan mutane duk da ita hudu ga kuma jikoki guda bakwai. Da nayi wani tunanin sai naga to menene nawa a ciki in ja bakina kawai in yi shiru mana, mai ya kare musu a tsakaninsu. Na daga ido na kalli Mama da tun sanda Babana ya ce mata dauki take kallon kason ta rasa wanda zata zaba. Furfura na gani a girarta da kuma gashin idonta. Gabana ya fadi na ce ashe a kan yi furfura har a gashin ido? Lemon da nayi mata a tsakar gida yau ya Kara bayyanar min da sirrin al'amarinta gaba daya. Gaba daya ta canza, gaba daya tsufa ya yanko ya 43 afka mata, sai ka ce wacce tayi tamanin alhalin kwata-kwata shckarun Mama in tayi da yawa ne zata yi hamsin koda biyu, shekaru biyu kawai da suka wuce ai gamu dinta take a cike ga kyau ga zati ga kwalliya, ga iya isa da nuna gadara. A zuciyata na Kara tabbatarwa kaina da cewar babu abin da yaff bakin ciki nukurkusa dan Adam, musamman ma amce ace tana fuskantar bakin ciki kan haihuwarta da kuma aurenta wanda abin da ya samu Miama kenan a lokaci daya. Tunda yanzu dai a zahiri yake a bayyane in akwai abin da Babana yake zaune dashi akan lalura to Mama ce de 'ya' yanta wadanda a baya kuma su ya ray tsawon rayuwar shi yana so yana fifitawa yana yiwa hidina da dawainiyar ba tare da yana tunanin akwai wasu masu hakki a bayan nasu ba. Babana yaja tsaki saboda kallon kashin da Mama ke ta yi, ki dauka mana. Yayi maganar cikin tsawa, idonta yana kan na gabanshi, ta nuna da hannunta ga wanda nake so. Haushinta ya kama shi an ki a baki wannan din na gabanki za ki dauka. Na ce yi hakuri Baba, bari a kwashe mata wannan din, nasa hannu na soma diban doyar ina kai mata kofar dakinta su Buhari suna karasa mata dashi cikin daki. A zuciyata tunani nake yi a irin iyalin da ke dakain Mama, 44 Wannan kason da aka bata kwana nawa zai yi mata? Da na dan yi wani tunani kuma sai naga to Mama ma dai ba abin tausayi ba coe, sai dai kawai mutum ya tausayawa wanda yake tare da ita saboda shi din dan uwanshi ne. Amma in ba haka ba ai tukunyar gidanmu tana hade ana girki gaba daya na wajo ma in ya shigo gidan mu zai ci ya koshi, Babana yana cikin harkarshi bai da wata matsalar babu. A wannan lokacin tasa iko ta raka tukunyar ta ce kowa yayi girkin shi don kawai ta ganawa Inna azaba, ga bakin cikin kishiayr da tasa aka yi mata, ga hakkokinta na aure duk ta danne sai wanda tsananin rabo yasa aka bata. Amma bai isheta taga bari ta ganawa 'ya'yanta azabar yunwa.watakia tana ganin ta hakanne kawai zata iya korarta, to wahala kam mun sha daidai wargwado, amma bata yi nisa mai yawa ba sai ta wuce maha ta kuma wucewa uwarmu ta kuma juyo ta dawo mata ta inda bata taba zato ba. Wai ace mutum bai san yayi adalci ba? An ce a karkace za'a tashi amma shi kullum aikinshi kenan zalunci, cuta, a raina na ce yau kenan ki ka san wannan. Zai yi magana nayi maza na ce mishi, kayi hakuri Baba. Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce, in yi hakuri ta zage ni? Na ce eh ai babu komai, ya ce to 45 shi kenan. Nasa hannu na sake kwashe kashin da yafi dama-dama bna kaiwa Zubaida. Na kirą, Sa'a ta kwashéwa nnarmu na karshen tunda dama kason nashi hawa-hawa ne, wani yafi wam na' kuma sân Zubaida yaso ya baiwa babba, ita Mama dan Rararain Innarmu ta dauki na tsakiya sai Mama taki. Shi wansan rabo da ki ka ga ina yi, na ce eh Baba, ya kale ni yà cc shi ne kaso na gaskiya, da sauri na ce mishi haka ne Baba. Ba tare da na tambayi dailin shi na fadin hakan ba, sai naji yace min ita wannan yarinyar ya nuna min dakinta, nayi murmushi na ce anti? Yayi maza ya ce min eh, na ce eh, ya ce shi yaroh yasan babu ne? Nayi maza nå ce mishi a'a Baba bai sani ba, ya ce to kin ga dole a bata da yawa, na ce haka ne. Ya sake nuna min dakin Marma da dan yatsanshi, na ce eh, alamar na gane. Ya rage inuryà ye ce ni ne zan zauna ina ciyar ta ya'yan gidan wasu da kuma zäurawa? Nayi maza na ce, a'a Baba, ba zai yiwu ba. Amma itama Habiba auren ya mutu ge? ya girgiza kai nuna alamar bai mutu ba, ya ce amma an samu ta koma da kyar ta haihu a can taje tayi fada da uwar miji akan naman suna. Daga cikin dakinta Zubaida ta daga murya ta ce fada ko duka? Dukan uwar mijin tayi, nayi kamar . 46 ban ji ba, don bana son hirar tamu ta zama sanadin fitina. To ita Innarkı ko ban bata ba tana da shi, wani lokaci ma in naga zata kure min Zubaidan ta rasá, shiga wurinta nake yi in debo mata na ce haka né Baba. Da iyakacin gaskiyata :sai naga hikiar rabon nashi, don haka ko babu adalci a ciki to daj akwai dabara tunda shi ka adalci ai bai wuce baiwa mai hakki hakkinshi ba. Rannan muna kwance ni da Inna alkan gadonta bayan su Atika, sun tafi gidajen su sun bar mu, hirą muke yi kan al'amuran da yanda rayuwa ke tatiya, Inna ta kalle ni tayi murmushi ta ce "Sanda ku ke yara yan kanana a lokacin da nake ganin tanfar abinda ke faruwa a, kaiga ba zai taba wucewa ba. Kullum 'naje gaban Mallam mai, babban allo ina kuka zaunar da ni yake yi ya yi ta bani hakuri, sai ya ga natsawata ta dawo jikina.sai ya ce min, wadannan yaran da ki ke haifa Binta ai kawayenki ne. Kwana nawa ne, in Ubangiji ya amfana miki su za ki ga sun girma sun zama abokan mu'amalar rayuwarki? To amma fa sai kin yi hakuri, sai kin zauna kin yi tarbiyarsu ta yanda Ubangiji zai taimake ki su zama mutanen kirki. To amma fa sai kin yi hakuri, ki zama ke din bata kanki ki ke yi ba, don kuwa in ki ka yi kuskuren 47 da suka lalace, sai ya girgiza kai nuna alamar abinda zai biyo bayan hakan ba karami ba ne. To gashi nan a yau, ta sake wani murmushin kafin ta ce na godewa Ubangiji da ya sanya ni na zamo mai bin umarnin iyaye, na ce ban taba sabawa umarnin nasu ba komai zafinshi a kaina. Ta kalle ni ta ce na kira mijinki dazu don in yi mishi godiya, bai bari mun yi tmaganar ba, na roke ki kiyi mishi biyayya iya iyawarki, ki kuma zauna da kowa nashi bisa gaskiya da adalci. In hali yasa shi kawo miki abokiyar zama, to duk yanda ki ka kai da kinta kar ki zalunceta, kar ki danne mata hakkinta, na ce mata to Inna. Washegari da safe ina tashe da kwanonon dafafiyar kaza mai nonon Rakui da Innan ta dafa min, wai da ita zan karya. na rike da wayar Inna ina kokarin kiran Ado, don mu gaisa. Na kai wayar kunnena ina sauraror ya dauka, na kalli Inna cikin natsuwa na ce, ni wannän na menene ne Inna? Ban fa ga alamar za ta yi wani dadi ba. Inna ta ce, a to ko babu.dadi dai cinyeta aka ce kiyi ki sha romon, na saké kalionta in ji waye Inna? Ta ce Aliya, ita ta kawo ta ce in dafa miki wai ba za ta iya ba ki da hannunta tana jin kunya. Ado ya dauki wayar yana jin ni ce ya rage fara'a, na gaishe shi yaya su Bala dai suna lafiya? Ya ce yau ne ya kamata kiyi waya ki tambaye shi? Ai na kuma 48 gane ki wato ke in ki ka samu 'yan uwanki to zance kuma ya Rare, kowa ma za ki iya mantawa da shi. Na rasa abinda zan yi in wankc kaina, sai na tuna na ce, to kawu ka ki ka sai min waya, zan yi ta bin wayoyin mutane ne ina kiranka, ni kunyar hakan nake ji. Ya dan ii sanyi, ina Umahrnah? Ko tana wurin uwarta? Na ce mishi eh, ba ki sani ba Humairah, sai bayan da ki ka taho naje gida kan wani abin da ya kai ni, sai na gane nayi kuskure. Da sauri na tambaye shi, kuskuren me kayi? Inna ma ta kallo ni don jin yarda na ambaci kuskuren, ya ce kwanakin da na baki sunyi min yawa, zan koma Dabai wannan satin saboda aikin gonata ki dawo gida kawai. Gabana yayi matukar faduwa, na ce haba Kawu, yau ne ma fa nake da kwanaki shida a garin ran. Ba za ki dawo. din ba kenan? Na ce a'a ba wai ba zan dawo ba ne, amma ni gaskiya...bai jira jin gaskiyar tawa ba ya kashe wayar. Inna ta kalle ni so yake ki koma gobe? Na bata rai saboda ran nawa ya baci, na ce ban sani ba tunda ya kashe, to kira shi mana kiji, ya baro ki kin zo lafiya cikin farin ciki da alhairori iri-iri ai ba za ayi sanadin bacin ranshi ba. Na sake kiranshi, nayi zaton ba zai dauka ba, sai naga ya dauka. A hankali na ce mishi kayi hakuri in 49 ranka ne ya 6aci, ko da bana kusa dashi nasan murmushi yayi. Inna tana nan kenan? Na ce mishi eh, ya ce nasan ita ce zata ce ki bani. hakuri tunda ke ba dabi'arki ba ce, Ban.yi magapa ba shiru nayi ina sauraronshi. Ki dawo gida awai Humairah, kin san tunda muka yi aure bamu taba yin nesa da juna haka ba, abin yayi min tsanani da yawa, nafi sabawa da pi in tafi in barki a gida ina jin.marmarinki sai in juya, amma ba ke ki tafi ki bar ni ba. Da kyar Ado ya yarda ya janye maganar tafiyar daga kwana bakwai, ya maida ita kwana tara. Shi kenan sai kawai na soma shiry-shiryen komawa gida, ciki har da karasa zuwa wuraren 'yan uwan da, ban je ba. Inna kuma a gida tana tashi zan koma dakina. Duk da naje gidan mai babban alo, tun washe garin zuwana gida na sake komawa wajen shi don ba zai yiwu in zo in tafi ban gaya mishi halin da na baro gidan mijina dà 'yan uwanshi ba, don ya bani shawara ko kuma ąaddu'a. A gidan mai babban allo ina zaune gabanshi shi da uwargidanshi Hajiya 'Yar Dubu, matarshi ta sakun lalle, matar da ya yi sa'a ta. zame mishi uwargida ta gaskiya, wacce ta danne al'amarin kishi tsakaninta da kowa ta tsaida adalcin da yayi sanadin da gidan ya zama dunkulallen gidan da babu 50 bambanci tsakanin ya'yan nan da na can. Ta sauko da Umahmah daga bayanta ta kar6i uwa zam-zam wurin mai babban allo, ta kwankwada mata kafin ta mika mishi ita, ta sake neman wuri ta zauna cikin natsuwa ta ce min aure suke so yayi ba kuma zasu barku ku zauna lafiya ba, sai sun ga sun sa shi yayi. Ba su kadai ba ne mafi yawancin 'yan uwan miji ai zuwa suke in dai zasu ji ka shiru da dan uwansu sai suce fin Karfinshi aka yi ko da kuwa hakuri ka ke yi. Nayi maza na ce mata, haka ne Hajiya, ta ce to ke ni ganau ce ba jiyau ba, kar ki yarda ki shiga layinda ba na gaskiya ba ne, don ka mallake miji ka hanashi tsaida adalci tsakanin iyalinshi, ka hana shi yiwa kowa adalci. In dai ba ka mallaki 'ya'yanka ka hana su lalacewa ba, baka kuma mallaki hikima da dabarar hana alhaki kama ka ba, ai kayi shirme. Na ce haka ne Hajiya, ta ce to ladabi da biyayya tsakaninki da mijinki, yi nayi bari na bari, in yana fada a bashi hakuri ba yana fada ana fada ba. Su kuwa 'yan uwan miji nan da ki ke kallon su fita harkarsu kawai za ki yi, da wuya kwarai ki ga wata mata da zata ce miki bata da tabonsu, sai dai aniyarsu kawai ta bisu. Mai babban allo ya yi murmushi alamar yasan wani abu ko in da addu'ar ta Hajiya ta dosa, bai ce 51 komai ba sai da ya ji hirar tamu tazo karshe sai ya ce min ke Aishatu. Nayi maza na ce mishi na'am Mallam, ya ce to gyara zama da kyau sai kiji abin da zan gaya miki, na sake cewa to tare da yin abin da ya ce min din. Cikin natsuwa ya soma yi min magana, kin ga wadannan mutane da ki ke tare da su? Na ce mnishi eb, ya ce to je ki maza ki gyara abinda ke tsakaninku Ba mijinki ne zai gyara miki ba, ba kuma shi ne zai rinka tare miki fada tsakaninki da su ba, in dai ba shima nema ki ke ki maida shi ya zama abin da ya zama ba. Ai ke mace ce suma mata ne, halinku daya, dabi'arku daya, rashin kirkinku daya. Dangin miji ba mutanen kirki ba ne, amna wuria matar da bata yi wa kanta adalci ba. Ama in zata yi wa kanta adalci to zata gane su din "yan uwane na gaskiya, abokan zama na amana. Tasan yanda ta tyi ta zäuna da su lafiya bisa girmamawa da mutuntawa da adalci, ba don komai ba sai don tasan ita din atà wani Bangaren wata rana dangin mijin wata ne ko kuma üwar mijin wata, to me zai hana ka yi wa wasu adalci don kai ma naka in sun zo suyi maka? Yanzu dan karamin misali zan yi miki, Hadiza ni na haife ta? Na daga ido na kalle shi don jin ya kira Hajiya Kubra Hadiza, ya ce ba sunanta kenan ba? 52 Nayi maza na ce sunanta ne, ya sake tambayata ni ne na haife ta? Na ce a'a, ya gyada kai ya ce ai kin san gidan ubanta, kin san iyayenta, tunda kuna zuwa. Na ce mishi eh, ya zuba min ido yana kallona, kafin ya ce min to da wata yar da ta fi ta a nan gidan? Nayi maza na ce mishi a'a, ya ce to da ta dauke mu a yanda mafi yawancinku ku ke daukan dangin miji zamu zama bhaka mu da ita? wo en Na ce a'a, ya ce to dubi tsakaninta da uwarki ita tafi kowa kusa da ita, ba haihuwa uwarki tayi ba, ba daga gidansu tazo da ita ba, kanwar mijinta ne ta maida ita yarta, ta hada damu duka ta rike mu da gaskiya don ta yarda mu ne 'yan uwan da tafi bukatar zaman lafiya da su. Ranta ba ya baci ne? Yana baci, tunda mijinta shima shi ne amma bata taba tsallake ni taje takai kararshi wurin mahaifinta ba, duk da ni ban taba zaunar da shi a gabanta nayi mishi fada kan laifinshi da ta kawo in ba. Sai in ta tafi in yi mishi nasiha, in gaya mishi ya yi hankali da gidanshi, kuma ko da mijinta ya soma yi mata kishiyoyi bata canza ba, ta kuma san daga nan gidan ne aka sa shi ya yi mata amaryarta ta farko. To yau me gari ya waya? Da tayi hakuri ta yi wa kowa adalci ta zauna da kowa da amana har kishiyoyinta yau waye gidan? Shiru nayi ina kallonshi, da kanshi ya ce, ita ce 53 don kuwa ita ce wuar Alhaji Abba, ko shi kadai ta haifa kuwa kin san tayi haihuwa mai albarka, balle ga su Ahmad ga su nan da yawa don ita kadai mutun takwas yanzu take da su. Ko ba ka sónta zaka je gaishe ta don tasa baki danta ya yi maka alfarmar da ka ke nema a wurinshi, tunda babu abin da ya ke so da girmamawa irinta. Don haka je ki ki gyara tsakaninki da kowa ki zauna da kowa lafiya kiyiwa kowa adalci. Na ce to, ai ba na gane abinda zan yi usu ne Mallam, ni a ganina muna iyakacin kokarinmu ni da mijina a kansu, tsanata kawai suka yi. Wani murmushin ya sake kafin ya ce, to bari dai in dan sa ki a hanya, kin ga dan uwa na Musulunci kawai? Ina nufin ba dan uwan da hakki biyu ya hada ku ba, hak kin Musulunci da hakkin makwabtaka. Na ce mishi eh, ya ce to yana da wasu hakkukuwa guda biyar da suka zama wajibi akan ka kai Musulmi. Hakkukuwan kuwa su ne, na farko in ya yi sallama ka amsa, idan yayi atishawa ya yi hamdala kayi mishi addu'a ta nemar mishi gafarar Ubangiji, in ya yi rashin lafiya kaje har in da yake kwance ka gaishe shi. In ya rasu ka halarci zana'idarshi, in ya gayyace ka cin abincinshi kar ka ki uwa, kin ji su su biyar? Na ce eh Mallam, ya ce to yan uwantakan Musulunci ne yake da wadanran hakkokin. 54 To ina ga 'yan uwantakar da ta zama bayan na Musulunci akwai na makwabtaka? Kin taba sanin hakkin makwabci akan makwabci? Ban kai ga ba shi amsa ba sai ya ci gaba. Ya ce, to ga kuma uwa uba na zumunci, babu abin da ke ruguza bawa irin shi, akwai kuma alhairori da yawa ga wanda yayi hakuri ya yi shi ya bada hakkin shi. Wasu Malaman sai suka ce tun a duniya ake amfana da tukucin shi, ayi ta jan kwanakin mai yin shi don ya dade yana yi, wasu suka ce a'a ba kara mishi kwanaki ake yi ba ayukanshi na lada ake nunnunka mishi. Wasu kuma suka ce zuriyarshi ce bata tabewa, sai ayi tayi mata albarka, to wanne ne a ciki in anyi mana ba a so? Na ce babu, ya ce to kiyi hankali da su, don hakki uku suke da shi a kanku. Hakkin Musulunci, hakkin makwabtaka da kuma hakkin zumunci, na ce mishi to Mallam. Na sake kallonshi cikin natsuwa na ce mishi, to ba ni addu'a Mallam. Ya yi murmushi ya ce wadancan da na baki kin raina su? Shiru nayi ban ba shi amsa ba, sai na ji ya ce je ki ki rike su sun ishe ki istigafari. Hailala, Salatin Manzon Rahama, kiyi tayin su gwargwadon iko sa ki cikata da la'hau'la 100. Nasha gatya miki ita kadai in ki ka rike ta ta isa, 55 magani dari babu daya take yi wa mai karantata karami daga cikin maganin nata kuma shi ne bakin ciki. Nayi wa Mallam godiya nayi mishi fatan alheri, nayi sallama da shi da iyalanshi na fito daga gidanshi cikin zuciyata ina tunanin babu abin da ya dace damu illa mu tashi kawai mu bar gidannan muyi nesa da kowa balle hakkin wani yaje yana hawa kan mu, kuma wai komai mugun halin mutum sai ace wai sai ka ba shi hakkinshi. To in kayi nesa da shi ba ka huta ba? Sai da na biyo gidan Anti Ramlah na shaida mata tafiyar tawa kafin na isa gida. A gida Inna sai shiri take yi gaba daya 'ya'yan da aka haifa da Umahmah mata biyu Nusaiba da Hindu ya'yan Ruwaila da Ade da kuma da namiji daya na amaryar gidan Usman. Sayayya mai kyau Inna tayi musu iri kuma daya, tsofaffin gida kuma duka atamfofi dattawan gidan shaddodi yadi biyar-biyar matan gidan da a hira ne kawai na gaya wa inna yawan su na kuma ce mata cikinsu mata biyu ne kawai ba su haihu ba. Tayi dariya ta ce, lalle gidan naku gidan yawa ne, gaba daya dakunan sai da ta baiwa yaro daya riga ai kyau na kalli irin lodin tsarabar da ta tara wai duka na mutanen gida ne, na ce mata aa Inna, to ni da zan zo me suka ba ni suka ce in kawo miki? 56 Nan da nan fuskarta ta yamutsse alamar maganarta bata yi mata dadi ba, nayi maza na ce mata to kiyi hakuri. Ana gobe zan tafi gidanmu ya cika makil da 'yan uwa wai an zo min wunin sallama wasu kua sun zo ne yi wa Inna taimakon aikin abin tsarabar da zan tafi da shi. Muna gefe ni dà Anti Ramlah wacce tazo min da mai kitso,da kuma lalle su suna ta aikinsu mu kuma hirarmu muke yi. Ai naso in zo miki da kaza mai nonon rakumi ban samu nonon ba ne. Na ce ar na ci, da sauri ta ce min a ina ki ka samu? Na ce, Aliya ce ta kawo, Anti Ramlah ta ce, kai Hajiya Aliya fa ta kile ko da yake dai ai sirikar Hajiya Kubra ce. Gyaran jiki sosai aka yi min kafin aka yi min adon lallen dan daidai mai kyan gani da sha'awa, sannan aka yarfa min kitso. Azahar bata yi.ba sai ga Bala da direban da ya kawo ni sun iso, Inna tana ta dariya kai Bala har kun iso? Bala yana fara'a don sun riga sun saba da inna saboda jan shi a jiki da take yi. Nan da nan ta shiga ina aka saka dashi da direban kafin yamma komai ya kammala, dubulan, nakiya, alkaki, tayota, tuwon madara, kwakumeti, babu abina da Inna da masu taimakonta basu yi ba. Da yamma kuma sai ga Hajiya Kubra an kawo ta 57 a sabuwar motar da Alhaji Abba ya saya mata, sai da ta shiga suka gaisa da Mama kamar yanda ta saba sannan ta shigo wurin Inna. Kwalla guda tazo dashi shake da soyayyan naman rago, ga kuma danbun naman abokitin kwallan ga kuma man. shanu da yaji ki kaiwa mijinki. Wannan nashi ne, ki kuma gaya mishi na gode, Ubangiji ya yi wa zuriyarshi albarka, zan kuma zo da kaina in yi mishi godiya, na ce mata to. Washegari tun safe aka gama shiri' na shiga wurin Babana muka dan yi hira na bashi hakuri akan al amura na kawo abin da zan iya bashi na bashi duk da dai nasan ba komai zai yi mishi ba sái dai kuma ya ji dadi yayi tasa min albarka. Itama Mama na shiga nayi mata sallama na ce mata ni zan tafi, kallona kawai take yi watakila kalmar da zata yi amfani da ita ne a kaina ta rasa, na mike muka yi sallama da su Habiba na mika wa 'ya'yan Sha'awa dubu biyu na ce su raba. Habiba ta biyo ni tana yi min rakiya zuwa ko far gida, in da 'yan uwa duk suke tsaye suna jiran fitowata. A cikin zaure na tsaya don yin magana da ita, saboda ta hakura ta sauke girmen kai ta sassauto har dakin Inna ta biyo ni tana yi min sannu da zuwa, har ina jin Mama tana tambayar ta kema kin bi ne saboda yar wainar da take baki? 58 Na kalle ta cikin natsuwa na ce mata, in hali yayi kin koma dakinki kiyi hakuri, Habiba saboda kema kin san wannan zaman naku ba tsari ba ne, tayi maza ta ce min haka ne Humairah, na gode. Na ciro dubu hudu na milka mata na ce kiyi hakuri godiya tayi tayi min, na juya zan tafi tana bina kice ina gaida Kawu, na ce zai ji. ln kin samu mai zUwa ki aiko min da zani don zannuwan nawa sun fara yin sanyi. Na ce to, ai kwauron baki ki ka yi Habiba da kin gaya min da wuri duba miki, to amma yanzu kinga kayana har an riga an daure su. Adam da Baba Karami suna tsatsaye ga Sa' adatu tana rungume da Umahmah 'ya'yan makwabta ma duk suna tsaitsaye, na sake yin sallama da Baba na shiga mota muka kama hanya daidai karfe bakwai da rabi na safe. A gida rannan muka yi sallar azahar a gidan kuma na samu Ado shima kuma a safiyar ya iso don haka tsaf na samu dakin yayi matukar farin cikin dawowan namu, ya kuma yi magana mai yawa kan irin hidimar da Inna da 'yan uwanta suka yi. Nan da nan na shiga rabon tsaraba nan da nan aka shiga zirga-zirgan zuwa yi min sannu da zuwa, sai ka ce ba ni ce na tafi ana amsa salamar tawa da kyar ba, na ce kai akwai hikima mai yawa a cikin al'adar bahaushe ta yin tsaraba. 59 Ni kuwa duk wanda yazo sai na mika mishi wani abu yara in sun shigo in debo tuwon madara ko kwakumeti in danka musu. Dare nayi Ado ya tasa ni a gaba ya soma bari yana rawar jiki yana marairaita, tanfar dai wani lokaci mai tsawo muka yi ba mu hadu ba. Na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi ni fa ji nake ma kamar abinnan yazo min da sauri, ya tsuke fuska yana fadin wasa kenan, ki ce min duk wannan kwalliyar da kyale-kyalen a haka nan za su tashi? Rannan sa ar da muka yi ni da Ado shi ne na samu ya saiwa Umahmah dan gadon jarirai a ciki tun farko ya sanyata ban da haka kuma dakin namu can gefe yake babu ai jin abiri da muke ciki. nna ce ta kara gyara min ke, shiru nayi ban tanka mishi ba. nna tana sona Humairah, ya gama maganganun shi, ban yarda na ce mishi komai ba. Washegari da wuri na fita na gaida kowa na kaiwa Goggo Ayalle Umahmah na kai mata ita tare da danbun nama da man shanu har da yaji, na kuma ce mata 6oye Goggo don ku kadai na baiwa daga ke sai baba, ya kamata to wannan tsaraba dama ai ba na kowa da kowa ba ne. Tun daga ranar ban sake ganin wani yaro ya shigo wurina na kore shi don takamar na gyara wurina ba, wai kar su lalata min. Sai dai ma in nei abinda na mika mishi don ya 60 kara mike kafa yayi zamanshi. Sannu a hankali 'sai wurin nawa ya zama wurin wasansu, kasancewata ba mai jurar magana ba ce in dai ba da mijina zan yi tayin maganar ba. Sai na soma ce musu ku kawo littattafanku muyi karatu, kan kace meye wapnan? Kowa ya dawo Makaranta da matsalar shi zai zo wurina Maman Umahmah. Rannan na ce musu kai kar wanda ya sake kiranaa da wannan sunan. Ado yana jin mu da su ya ce dawane suna ki ke so su kira ki? Na ce oho, ya ce to ku rinka kirantada sunan tsofafi Goggo na ce oho ya i min, tun daga ranar gaba daya yara Oggo suke ce min in amsa. Cikin hikima na baiwa Ado shawarar mu tashi mu koma wai Wurin, da sauri ya tambaye ni muje ina? In bar dangina in je ina? Naja bakina nayi shiru cikin zuciyata dai na san ina da aiki tunda ba zai yarda ya tashi ba, don haka na dauki ataki na gyara mu'amalla tsákanina da manya kamar yanda na samu da yara. Kullurm Juma'a in zan je gaida Goggo zan kai mata goro murza-murza ko kuma abin sayen goron, bini-bini kuma zan lallu6e abin dadi cikin hijabina in kai mata. Itama Ruwailah haka, danma kuma ina jin ta gaji 61 da zaman namua haka, don haka tunda taga na dan yi sassauci sai tayi maza ta saki. Bini-bini zata leko wurina. Goggon yara nace ko da abù kaza ne a wurinki? In ce mata eh, ko inf ce a'a ajea sayo mana in mika mata kudin tayi godiyá ta tafi. Gari yana wayewa kumă žata turo a daukan mata Umahmah ta hada da Nusaiba tayi musu wanka ta bar su a wurinta. Rannan ba karamin tashin hankali Ado yayi min ba, akan ya gane na koma yin mu'amallah da Ruwaila nayi tayi mishi kuka, ita ta riga kowa karbanmu a gidan nan abin da ya faru bayan häkan in aka bar shi zai wuce ka bar ni in yi mu'amalla da kowa don kaima ka sanmu natsuwa. In yaso taji dadin koya miki iya shege ba? Na ce to in ta koya min nan dauka mana ai jiki magayi, da nayi maka ka kyale ni ne? wacce irin azaba ce ba ka gana min ba? Ado ya kalle ni yayi murmushi ya ce ni kar ki kulla min sharri. A haka na lallaba Ado ya bar ni na soma shiga harkar cikin gida, ina zuwa wurinsu muna hira, iyaka dai ina kula da bakina bana kuma yarda da zaman dakin wata. A haka sai na soma shiga ayyukansu zan yi musu tankade na tuwo ko na abin kadi zan zuba garin tuwo suyi tuki zan zuba abin kadi suyi kadin zan yi sharar 62 wurin girki. A haka rannan sai na karbi girkina daga hannun Furerah ban kuma yarda mun 6ata ba, don haka sai muka samu saukin zaman mu'amalla kuma ta gyaru duk da dai nasan gyaruwar mu'amallar bata kawar da Su daga dokin ganin Ado yayi aure ba. Sai dai kuma an daina yin maganar a kan idona, nima kuma nayi sassauci mai yawa a kan hakan, saboda na riga na yarda da cewar a yau don Ado yayi auren shi bai zalunce ni ba. Shi yakai min Inna Makkah, ta sauke farali ko wannan kadai yayi min ni ya biya ni, balle kullum a cikin hidimarta yake ita da kaņnena. A wannan lokacin ne Ado ya soa gini a cikin gida ciki da falo ne guda biyu manya, daya da kicin da bayan gida a cikin shi, daya kuma babu ga kuma wani daki guda daya suma biyu a jere. Yana soma ginin gidan gaba daya ya dauka aure zai yi ya gano wata kenan, ai kin ga namiji ba? Tuntuni tana zaune a tsukakken daki bai yi mata gini ba sai yanzu da ya gano wata kuma ki duba ki gani tun ba aje ko ina ba yana yiwa amaryar gini irin na zamani mai hade da kicin da bayan gida a ciki. Ita kuma nata babu bayan gidan bare kicin din, ban ce komai ba ban kuma taba daga hankalina har wani ya gane ba, na bar wa zuciyata komai. Rannan dai muna tare da Adon a daki, laptop din 63 shi yake dubawa a dalilin ba wani kula juna sosai muke yi ba, saboda wai na bata mishi rai nima naja nayi shiru ban Bada, hakuri ba don fushin ya dan yi tsawo saboda wasu dalilai nawa. Ina jin dai aure ka ke shirin yi ko? Shi yasa ka ke yi min abubuwan da ka ke yi barin abinda yake yin yayi ya dago ya kalle ni me na yi miki? Na daure fuska na ce, gashi nan wułakanci iri-iri, wanne da wanne? Nayi shiru, ya ce ai kin lissäfo su tunda ki ka ambaci wulakanci saï kin gaya min. Shim nayi ban tanka mishi ba, ya gaji ya ce in kuma kece ki ke yi min wulakancin saböda kin ga na kasa yin auren"to zan yi wa kaina maganin abin saboda na lura raini ya sbiga tsakanina da ke ba kya ganin mutuncina. Kullum kawu ya soma yi minirin wadannan kalaman kuka nake yi doń ba sa yi min dadi na kuma kasa sabawa da su In yi mata biyu mana nima in ji dadi in wannan bata tattake ni ba a yau to gobe wata zata yi. A lokacin da Ado ya gama gininshi wanda ya y matukar yin kyau ya kuma kawata wannan ciki da talon mai kicin da bayan gida da kayataccen tails da rufin silin irin na zamani. Sauran kuma ya yi musu suminti jiranshi kawai nake yi ya ce min ga ranar aurenshi ga kuma ni dakin da ya bani. 64 Ana cikin haka, rannan sai gashi rannan yazo da kujeru ana zubawa a falon nan ya sanya darduma ya kawata wurin sosai. Mamaki ya kama ni na ce. To wannan sai ya gama sanya musu komai ne za su bashi 'yar ko yaya? Ni dai ban ce komai ba, tunda dai na tseguntawa Inna maganar, ta ce in zuba mishi ido na ce mata to na zuba. Da daddare ranar muna hira ya ce min ni fa gado bai damen ba, nafi jin dadin kwanciyar katifa shi yasa bai sayi gadon ba, amma in kina so a sai miki. Na ce a'a a sai min gado kawu ai mutuncin daki ne ya ce to shi kenan. Kwana biyu daga nan na tare a sabon dakina ciki daya guda daya ya mayar min da shi aji don karatunmu da yara har bencina da black boad yayi mana daya dakin kuwa ya gyara shi don baki ya bar daya ciki da falon. Sai suka koma cewa sai ya gama gyara wannan din tukuna zai yi auren gashi ya killace min wurin da yar katanga amma duk da haka ban daina shiga can cikin gida nayi abubuwan da muka saba ba. Kaka tana zuwa ciki da falon Ado ya bayyanawa mutanen gida cewar don buhunan hatsinshi ya tanade shi tun da rumbunan da yake amfani da su basa isan shi. A wannan lokacin ne kuma ya sanya ni na fara karatuna na (N.C.C) a makaranta nan a Zariya kullum 65 nake zuwa ina dawowa. A wannan lokacin harka sosai yake yi don tun a shekara ta biyu da soma aikin shi ya zama mataimakin (Princepal) a makarantaryanmata ta kafur a yanzu kuwa shi ne (Princepal) na makarantar gozaki. Ban shekara cur ina zuwa Zaria ba ya sai min motar hawa ya kuma koya min duk da shi din har yanzu babur din shi yake burgawa yaje duk in da za shi, ko kuma ya hau motar haya in kuma ina gida ya ce min in kai shi. Umahmah, Nusaiba: da Hindu tare da Usman makaranta daya ya sanya su, don haka kullum in zan fita da safe nike kai. su in wuce Zaria in lokacin tashinsu ya yi kuma 'sai. Bala yaje ya dauko su a motar haya. Rannan na dawo daga Zaria da yamma a gajiye nake sosai saboda muna cikin karatu mai zafi, ina zaune ina dama furar da zan sha don ragewa kaina yunwar da nake ji sai ga Ruwailah ta shigo min da dan waken da ta ce wai don ni tayi na karba cikin farin ciki ina mata godiya. Na soma ci, lomar farko da ta biyu da nayi abin gwanin dadi, sai kawai naji ta ce min ni fa wata magana naji na ce to ba za ka ji za a cuci naka ko ana cutar shi ba kayi shiru. Dole ka gaya mishi ko da kuwa ba jin dadin 66 maganar zai yi ba, sai da naji cikina ya ba da sautin kulululu don tsoron abin da take shirin gaya min din. Sai kawai naji ta ce min wai ashe Baban yaran nan cikina ya sake ba da wani sautin na kulululu, tunda nasan sunan da take kiran Ado kenan, wai ashe matar nan da ake cewa ya ajiye yana karyatawa wai har ta haihu. Karfin hali nayi na iya karasa tauna dan waken da ke bakina, na hadiye ban tofo shi waje ba, cikin natsuwa na daga ido na kalle ta. Na ce mata shi. Baban yaran nan wani irin mutum ne Yaya Ruwaila da ban isa in tuhume shi kan abinda yake yi ba? Kin san kowane mutum da yanda yake, da irin lagon da matarshi take samu akan shi, to shi wannan wanda nake da shi a kan shi bana in tuhume shi ba ne in akan wannan ne ban isa ba. Don haka ko kawo min dan ya yi ya ce in rike ba zan tambaye shi inda ya samo shi ba, musamman ma da yake nasan ba kan shi farau ba, don haka ko kin ji irin wadannan maganganun daina gaya min su kawai. Wai dama kai da naka ne kar kaji ana cutarshi kayi shiru, na ce eh ai dama, to bani da iko akan shi ai kin ga gaya min din bai yi min amfani ba kenan. Sai dai ma kawai ya yi dalilin tashin hankalina ke kuma nasan ba za ki so ganina cikin tashin hankali ba tayi maza ta ce yo to ina fa? Da haka sai na kashe bakin Ruwailah akan dauko 67 min wani labari ta kawo min. Na kara haihuwa da namiji muka samu na roki Ado ya sanya min sunan Babana ya ce min to sai kawai ranar suna naji yana fadin sunan yaro Yahya ban ce mishi komai ba tunda shi ma uban nawa ne Baba Yahya kuma yayi matukar jin dadin takwaran da Ado ya yi mishi don tasowa ya yi yazo har Dabai wai yazo ganin takwaran nashi. Rannan ina tare da yara a aji karatu muke yi saboda wunin na ranar Lahadi ne tun safe kuma Ado yana gida sai da yayi azahar ya fita, don haka nima da muka yi azahar din sai na ce mu shiga ajin zuwa lokacin La'asar sai mu fito muyi sallah su taya ni aikin abinci. Muna cikin karatun sai ga wani yaro dan makwabta da nake kina Baba saboda sunanshi Surajo, ya shigo da sauri sai da ya gaishe ni sannan ya ce min Goggo wai kinyi bako wai a gaya miki wai yayanki ne daga Bauchi. Yana yi min maganar cikin wani yana kamar tsoro ko kunya. Jin da nayi ya kira Bauchi ya sani nuna mishi kofar baya na ce mishi jeka ka shigo min da shi ta wancan kofar, ya ce min to. Ya tafi ya dawo ya zuba min ido, kafin ya ce "Goggo kila ma fa karya ne, nayi murmushi na ce je ka dai ka shigo min da shi." 68 Na ci gaba da toayuwa a wurin don ganin wanda zai kawo min din, ai kawai gashi ya shigo min da Yaya Ibrahim. Ysna ganina ya zube a kasa wai ni yake gaisarwa, gaisuwar girmamawa, sannu Yaya sannu dai, ina wumi yaya aka ji damu? Zuba mishi ido nayi ina kalion shi, gaba daya yayi baki, baki ya gama rubewa ko'ina a jikinshi tabo ga wani katon yanka ya raba goshinshi biyu. Yau kuma ni ka ke kira yaya? Nayi mishi tambayar don in hutar dashi girman da yake ta kokarin bani sai kawai naji yayi maza ya ce, au Baba-Baba kiyi bhakuri ai mancewa nayi nake kiranki Yaya. Sallamar yara naji na bar Hasiya na ce ta kula min da girkina naje na budewa Yaya Ibrahim dakin baki na sauke shi a ciki na kai mishi abinci da na sha na kuma zauna don mu gaisa dashi gaisuwa irinta yan uwantaka. Yana kai lomar abincin bakinshi ya sake canza min suna Anti ai baki san abinda ya faru da ni ba, ai hatsari nayi na rantse miki, Anti ai in ban da rabon za'a sake shan ruwa a gaba ba ai da yanzubabu ni. Ai mota da ta fadi damu ai ni kadai na tsira shi ne naji wadannan raunukan gama wani ko warkewa bai yi ba, ya kwace min wani shafcecen ciwo a kwaurinshi babu ko kyan gani tausayinshi yayi matukar kamani sannu Yaya lbrahim na soma gaishe 69 shi. Kan ka ce meye wannan ya lamushe abincin da na kawo mishin na fita don in karo mishi sai kawai nazo na samu wai har ya fara bacci, don haka na koma naci gaba da aikin abincina cikin zuciyata dai tausayin Yaya Ibrahim yafi konai damuna. Ko ina Baba yake ko suna tare bari ya tashi daga bacci sai in tambaye shi. Wajen karfe biyar da rabi Ado ya dawo gida da sauri naje na same shi na gaya mishi albishirinka, ya ce goro na ce mishi su Yaya Ibrahim da tunda suka tafi ake cewa ba a taba jin ga wanda ya ce ya gansu ba. Ya ce, eh na ce to gashi nan yau yazo, yana ina? Na ce gashi can yana bacci a dakin baki, ba ka ga ciwanwukan da ke jikinshi ba, hatsarin mota suka yi. Ya ce, ayya! Ya wuce ya shiga can cikin daki, nima amsawar tashi ta ban haushi, na juya na nufi kicin din tsakar gida wanda nake aiki a ciki. Ban yi aune ba, ban san yanda aka yi ba sai kawai na jiwo ihu mai tsananin firgitarwa, na zare ido tare da kasa kunne don kokarin tantance daga ina ihun yake fitowa, ban gane ba. Daga ina ne Hasiya? Cikin natsuwa naji ta ce min watakila Baba ne yake dukan bakon nan don naga ya shiga dakin da dorina a hannunshi. Da gudu na nufi dakin ban san yanda aka yi ba 70 ganina kawai nayi a kwance kan Yaya Ibrahimn na rufe shi da jikina, gigitaccen ihun da na kurtna shi ne ya fahimtar da Ado har dani a dukan da yayi Ado yana haki yana tambayarshi me ya kawo ka gidana? Nima kazo ne kayi min abinda kuka yiwa ubanku? Hannu biyu na saka Da rufe baki na zaro ido jikina sai rawa yake yi saboda tsoratar da nayi da irin zagin da Ado yake yi mishi, amma ko a jikinshi muna da gai daku ne uwarku ce 'yar uwata itama bata takowa in da nake ba balle ku. Fita ka bani dan iska... nayi maza nace ni dan uwana ne wurina yazo na soma kuka don ban taba ganin duka da wulakanci irin wanda Ado yayi mishi ba. To nemi inda za ki kai shi ki kai shi amma in ki ka bar min shi a gidannan kin sanni da kyau lokacin da zan turo N.D.L.A su kama shi ba za ki sani ba, sai dai kawai ki neme shi ki rasa. Kuka sosai na soma yi na ce mu tafi Yaya Ibrahim tunda dan uwana ba zai iya zuwa wurina ba ai nima bani da wurin zama ya ce eh baku dashi kuje. Tbrahim yaja ya tsaya a'a Anti ba zan zo in same ki a gidan mijinki in kashe miki aure ba, kiyi zaman ki kawai bar ni ni in tafi aini kadai ya kora na çe a'a tare ya kore mu. Na tasa Yaya Ibrahim a gaba muka fita muka bar gidan, Ado ko Baba Yahya ban dauka ba saboda 71 Zuciyata takai natuka wa en zafi wulakancin da Ado ya yi wa Ibrahim ba shi ya yi wa ba ni ya yi wa tunda dan uwana ne wana ne uban mu daya mu kuma da yä zauna a namu gidan rayiwar yanci yayi babu wani wanda ya wulakanta shi. " Har mun shiga mota mun zauna muna jiran direba yazo mu tafi, sai gá Baba Tanirnu da saurinshi yana bin motocin da ke todi yana leka cikin su har yazo kan tamu yana ganina ya ce, fito k fito nan. Muka fita muka bi bayanshi, ba ki kyauta min ba, ko kadan ba ki kyauta min ba. Ban taba sanin ba ki dauke mu iyaye ba sai yau. Čabana ya fadijin maganar tashi, in kin dauke ni matsayin uba ba za kiyiumin haka ba, na soma yiwa Baba Tanimu kuka saboda jin abin da yake fada. Yaya za ki. fita ki bar dakinki da sunan 6acin rai ba ki sanar dani ba'? Wato nayi kadan ko? Har muka isa gida bai bar maganar ba. Cikin zuciyata nayi nadama da na tuna mai babban allo ya gaya min cewar Hajiya Kubrah bata taba tsallake shi taje ta kai kara gun nata iyayyen ba. Saboda ta yarda shi din ubanta ne. Muna shiga gida Ado muka fara gani zai fita da Baba Yahya a hannun shi, mutumin banza mutumin wofi, wato ban isa a zo wurina ba sai kayi hukunci da kanka? Wato ni ban isa ba? Wato in ban da yarinyar nan Hasiya tayi hankali 72 tazo ta gaya min da sai kawai 1yaycn yarinyar nan su ganta a gida ni ban san komai ba, to. ina amfanin girman nawa kenan? Kayi hakuri Baba, Ado ya ba shi hakuri ya hada mu yayi mana fada, ya kuma hana Ado korar Yaya Ibrahim ya ce mishi wurina yazo ba wurinshi ba, ya bar shi tunda dan uwana ne, muka dawo muka zauna, amma ni da Ado ta ciki-na-ciki. Rannan da daddare muka yi mummunan tashin hankali ni da Ado yayi min wulakanci irin wanda bai' taba yi ba. Ai ke ba ki san kowa ba sai kanki, shi yasa ba ki san girma da darajar kowa ba in ba naki ba ne, ba a bakin ki naji labarin irin lalacewar da Mama ta yi ba? Har kina gaya min wai wadaman mazaunan na Mama da take juijuyawa tana tafiyar takama duk sun zagwanye sunz ama kamar fata ko tsunma? Sannan ina zaune ni Adamu ina zaune a inda kii ka amsa wayar da Atika tayi miki tana baki labarin Mama ta fadi har ta samu stroke tana asibiti, ba ki ji kunyata bare tsorona ki ka bude baki ki ka cewa Atika ke duk abinda zai samu Mama ba zai dame ki ba. In da abin zai tsaya ne a kanta ita kadai. ba zai shafi 'ya'yanta ba. Yaya Habiba ta koma dakinta aka ce miki eh, ki ka ce to madallah. Kina nufin don naki rabuwa da ke kamar yanda 73 Mama tayi min umarni shi kenan hakan yana nufin bana sonta ko bana ganin girma da darajarta? Idanuwanshi suka baiyanar da bacin rai mai tsanani wanda yayi dalilin da náyi magana naja bakina nayi shiru saboda a yanzu tsoroni abinda zai taba lafiyar jikina nake yi. Na kuma san na saki baki na fadi maganganu iri- iri akan Maman a gabanshi ban taba sanin basa yi mishi dadi ba sai yau. Rainà ni ki ka yi yasa kike iya fadin mugum'abu a kanta a gabana ko kuwa ke din kin manta ne cewa ita din madadın uwa take a wurina? Shiru nayi ban iya ce mishi komai ba. Ibrahim ba zai zauna mih a gida ba na gaya miki, don ba za su pakāsa min yar uwa suyi sanadin shigarta cikin musibar rayuwa ba, sahman su zo min gida su zauna don sùna gadarar ga ki a gidan, in da ba su lalace ba in da ba su maida kansu sika. zama abin da suka zaa.ba, Babanku zai rinka yi mata abin da yake yi mata a yanzu? Wai har yana gayawa mutane ita din macuciya oe shi da ita wa ya cuci wani? A ina aka ce wa namiji ya bari mace ta... da sauri na kátse Ado. Na ce, a'a ya ya haka? Me Babana ya yi maka? in anyi wa Mama...kan in karasa ya wanke ni da mari, ai ba za ki sake zaginta a gabana ina kallonki ba, ai kun riga kun kure ni. 74 Yau ma Baba Tanimu ne ya raba ni da Ado. Kwanaki kadan bayan nan ma aka sake masifar Ado ta ishe ni naje na kai karar shi wurin Baba Tanimu ya hada mu ni dashi duk gaba daya bayanin akan Ibrahim ne. Baba Tanimu ya ce to ke ki bar shi mana kawai ya kore shi ba yarshi ce ta haife shi ba? Na ce a'a Baba ba wurin shi yazo ba, wana ne sune ya'yan Babana manya ba asan in da dayan yake ba, shi yazo wurina a kore shi, in shima ya tafi bai sake dawowa ba fa? Na yarda tunda gidán shi ne yasa mishi ka'idar zama' in bai bi ba shi kenan, amma ba kora ba, in an bar shi ma in yaga zai tafi sai ya tafi don kan shi. Baba Tanimu ya ce, gaskiya' ne, kasa musu ka'ida ita dashi in basu bi ba ni ne zan kore shi ba kai ba. Ado ya ce, za'a rinka salloli biyar dashi a Masallaci, Baba ya ce ko ba ka nan zan sa maka ido kan wannan, ban yarda kuma asha ko da sigari ne ba a cikin gidana, balle wani abinda yafi sigari. Kina ji? Baba Tanimu ya tambaye ni na ce mishi eh Baba. Sai me kuma ya sake juyawa wajen Ado, Adon ya gyara zaa ya ce, zama kawai zai rinka yi a gida ban da fita in kuma ya ki ya fita to kar ya dawo. A baka maganar ta dan lafa ni kuma na tasa Yaya Ibrahim a gaba kullum ina kaf-kaf-kaf dashi ina 75 tsoron kar yayi abinda za a ce yayi laifin kora tunda maganar tana gaban Baba, ba zan iya jayayya da shi ba. Kwanaki kadan da ya yi yana tsare a gida sai da jikinshi ya canza ya soma yin kyau. Rannan ne nemi Yaya Ibrahim na rasa, ban gan shi ba baya cikin gida ba kuma lokacin Sallah ba ne balle in ce yana masallaci. aNa kesa buda bakina in tambayi wani shi, don kar ya yada maganar cewar ba a gan shi ba har Ado ko. Baba suji, don haka naja bakina nayi shiru nayi ta leke-leke ko zan hango shi har dai na hakura. Ina zaune tsakar gida sai gashi ya shigo layi yake yi nayi salati mai karfi ya waiwayo ya kalle ni "Anti Humairahhh ki shouumn kawai kin gane? Ki rabu da wannan mugun mutumin muuu dah yah zan... Nayi maza na tura shi dakinshi na tura mishi abincin shi wanda sakwara ne da miyar taushen da aka yi da kayan ciki da busasshen kifi naja kofar na rufe shi a ciki ina ta addu'ar kar Ado ya dawo ya ce ina yake? Washegari da Asuba Ado yana fita Masallaci da yake yana fita da wuri tun kafin kiran Assalatu nayi maza na tashi naje na shiga dakin Yaya Tbrahim. A kwance shame-shame na same shi, yayi filo da sakwarar da na mika mishi, ko loma daya bai yi ba, a tsorace na tashe shi ya wastsake na nuna mishi 76 abinda yayi, shima ya tsorata. Na sa shi yayi wanka kafin ya fita Masallaci aka yi sallar Asuba dashi ya shigo gida ya gyara dakin nashi. A haka ina zaune da Yaya Ibrahim kullum ina kab-kab-kab ina kuma addu'a har nayi sa'a zaman nau ya mike ya soma wastsakewa daga abubuwa masu yawa. Natsuwa ta soma zuwa mishi, har dai daga baya ya yarda ya koma makarantar addini da ta boko. Ado ya yarda da zamanshi a gida, ya saki jiki dashi ya soma jan shi zuwa gona da ma wuraren harkokinshi, har ma daga baya yake iya tura shi ya wakilce shi kan al'amura masu yawa. Shekaru goma cif sun cika daga wannan ranar ta daidaituwar al'amuran Yaya Ibrahim. Shekaru goma sha biyar kuma kenan na aurena da Ado, auren da kaddara da rabo na abubuwa masu yawa suka tilastawa Mama yin sanadin shi. A yau ni din mahaifiyar 'ya'ya biyar ne cif na Kawu Ado, cikinsu akwai namiji guda daya Baba Yahya, sai kyawawan 'yan mata guda hudu, Umahmah ita ce ta farko, sai Baba Yahya bayanshi ne kuma muka samu Zainab da Khadija da Fadima. Wadanda mahaifinsu ya zaban musu Sunayen nasu saboda kaunar da yake yi wa yayarsu Umahmah, don haka ya ce to tunda a tarihin da ya 77 karanta na Umahmah Zainab yar Annabin Rahama ce mahaifiyarta ita kurma Zainab kowa yasan 'yar Nana Khadija ce. Sannan ita Nana Fadima sonta da take yi wa Umahmah ne ya sanya ta bar wa mijinta wasiyyar auren Umahmah bayanta, to bari ya jera mana Sunayen. Haka don neman albarkar masu sunan na ce mishi to Kawu don haka Ado bai taba yiwa kowa takwara ba tun bayan wanda yayi wa Baba Yahya. Duk kuma da wadannan 'ya'ya biyar din da ke gare ni shekaru kusan biyar ne kuma yau rabona da haihuwa a dalilin son miji da neman gindin zama a wurinshi ya sanya ni shiga harka ta bin tsarin iyali. Mahaifar tawa a daure take, watakila in ban dá haka da yanzu an wuce biyar an kai shida ko bakwai ko ma takwas ko da yake dai ina da sani da kuma Imani na cewar babu wani wanda ya isa ya hana wani zuwa duniya a lokacin da kaddarar zuwanshi tazo. Don haka na yarda nayi hakan tunda abin da maigidan yake so in yi kenan ni kuma kullum a kan bin ra'ayinshi nake matukar dai bai zamo sabo ba tunda nasan ni din ni kadai ke gare shi a gida ko a waje ba mai leke-leke ba ne. Yanda na zamo mahaifiyar ya'ya biyar a cikin gida, to a waje shima mai gidan al'amura masu yawa ya sanya a gaba farko dai a yau shi din shi ne 'Dr. 78 Ado Sulaiman', don kuwa digiri uku ne da shi. A yanzu yana aiki ne tare da hukumar inganta ilimin makarantun primary ta kasa. Shi ne kuma mamallakin shahararriyar gonar nan ta "HUMAIRAH FARM'. Wacce ita ce kadai gonar da a nan kurkusa tayi fice wajen bayar da kayayyakin amfani irin na lambu rani da damina, irin su (Brocooli, Beetroot, Asparagus, Aborigine, Cabbage, Kore ja, ko na Chinese, carrot, ganyen celery, cucumber, lettuce, da abubuwa masu yawa da suka danganci lambu, ga kuma 'ya'yan bishiya irin su gwanda, abarba, lemo, gwaiba, da makamantansu, wadanda duka ana' tafiyar dasu ne bisa tsarin nomna irin na zamani. Haka nan wannan babbar gona ko kusa harkarta da dawainiyarta bai fitar da Ado daga cikin harka ta noma damina ba, wanda da shi dama ya fara. A yanzu shi din manya-manyan gonaki ya mallaka na noman masara, dawa, wake, ga kuma fadamun noman shinkafa da rake wadanda mutane da yawa suke taimakon shi tafiyarwa. Amintattun yaran da ya rike irinsu Bala wanda bayan kammala hada haddar Alkur'aninshi, Ado ya trua shi ya dan karanci Boko har ya zamo ya mallakii ilimin digiri akan aikin gona da kuma wasu yaran da anbatonsu zai y yawa... Ina zaune cikin katafaren gidan da sanda na yi 79 wa Ado rakiya zuwa kasar Singapore ne na dauko sanfurinshi bana komai na aikin hukuma bayan kanmaluwar karatuna na N.C.C. nayi aikin karantarwa a makaran tar primary ta Dabai na tsawon shekaru bakwai. Ado ya bani umarnin' ajiye aikin don in zauna a gida in yi aikin da yati kowanne dacewa da ni, wanda yafi kowanne zamo min dole don shi ne in ban bayar dashi baza a tambaye ni. Shi ne aikin tarbiya, tarbiyar 'ya'yan da ke gare mu wadanda ba biyar din da na ambatan wa kaina ne kawai tarbiyarsu ta hau kan nawa ba, manyan yanmata kadai guda hudu ne da ni ga Umahmah ga Hindatu ga Nusaiba ga 'yar gidan Furerah da ta haifa bayan haihuwarsu da shekara daya har tayi min takwara da ita. Da zan taso duk na hada su muka dawo a maza kuma ga Usman sai Baba Yahya sai kuma wasu yaran da Adon ne ya kawo su gidan to ga kuma su Nana. Bisa wannan dalilin ne maigidan ya zaunar dani yayi min gamsasshen bayanin da ya sanya ni gamsuwa da barin aikin nawa na zauna a gida nake sa mana ido kan al'amarin tarbiyar ya'yanmu. Ganin da yayi na hakura da albashin nawa da nake samu wanda yasan amfaninshi wurina yana da yawa, tunda yasan ina da iyaye da 'yan uwa da dangi 80 wadanda nake tafiyar da al'amuran da ke tsakanina da su na zumunci ba tare da shi1 yasan yanda aka yi ba. Sai yaga na hakura na bari na kuma ja bakina nayi shiru, ban taba tanbayarshi yaya za ayi ba? Ya sanya shi yi min tukuici da gonar HUMAIRAH FARM. Ina zaune a falona ina karatun littafin (Riyadus- salihin) babin godiya kan ni'imomi nake karantawa, Baba Yahya ya shigo da gudu, can bayana ya tsallaka ya wuce ya buya. Sai ga Umahmah ta biyo shi a fusace, ga dukkan alamu tsokanarta yayi, ta bude baki da nufin yin magana fushin nata yayi tsanani, na daga ido na kalle ta cikin natsuwa na ce mata. "Umahmah sau nawa zan gaya miki cewar Ubangiji yana son masu hadiye fushinsu, nan da nan ta 'sauka, ta kalle ni cikin ladabi ta ce na hadiye Goggo, na ce to ai kin san kuma yana son masu yafiya, ta ce na yafe mishi. Na ce to kuma har ila yau yana son masu kyautatawa na kasa da su, tayi murmushi ta ce to Goggo ya biyo ni yazo ya karba. Tana barin dakin na kamo Baba Yahya na jawo shi gabana, kumnenshi na kama na rike da hannuna ina ja yana bin hannun nawa yana fadin kiyi hakuri Goggo, na zaro ido ina kallon shi sau nawa nake gaya 81 maka ba sa'o'inka ba ne? Sau nawa nake gaya maka da Hindu da Umahmah da Nusaiba shekaru uku-ukı suka baka? Don haka ka daina tsokanarsu, ka daina yi musu rashin kunya." Jin da ya yi na ce da jan kunnen nashi ya sanya shi tunanin da dokar da yasan an kafa min, cikin natsuwa ya ce Goggo Babana ya hana ki kama min kunne saboda yana min ciwo. Na saki kunnen nashi cikin sauri na ce, to ama ba zai hana in saka, in saka tsallen kwado ba ai, tunda kai baka son a tsokane ka amma ka iya tsokana. Sun ce maka superdi ka gaya mishi ya ce kar a sake. Sannan sun ce maka Tanko ka sake gaya mishi ya hana, to zan gaya mishi ni da kaina ba ka da aiki in ka zauna a gida sai tsokanar yayunka kawai kake yi, don haka ya zabi abinda za'a rinka yi maka cikin biyu, ko dai ya bari in rinka sa Yaya Bala yana tafiya da kai gona ko kuma a gida Yaya Usman ya rinka horar da kai yana saka tsallen kwado. Cikin natsuwa ya kalle ni ya ce, kiyi hakuri wahala zan sha in an sani tsallen kwado, nayi nauyi da yawa, na ce to bi bayan 'yar uwarka kaje ka bata hakuri, ya ce min to. Ya tashi ya fita. Yana fita ya bar dakin, na amsa wayar Yaya Ibrahim daga Kaduna, Anti Humaira ina kwana? Nayi murushi na ce lafiya Yaya Ibrahim, ya ya gida? 82 Ya ya yaran? Ya ce, lafiyarsu kalau, na ce to Mamansu fa? Ya ce ga ta nan tana jin ki, wai tana gaishe ki, na ce to na gode ina amsawa. Yaya Ibrahim ya ki ya. daina kirana Anti Humaira, duk da a yau shi din wani irin kammalallen mutum ne natsattse, mai addini, mai mutunci da ganin girman na gaba dashi, don haka ba kirana Anti Humaira akan yanayin shirme irin na baya ba ne yana dai kiran nawa ne kawai saboda sunan da ya zabi kirana da shi kenan. Yayi aurenshi tun a lokacin da ya gama karatunshi na (N.C.C) saboda sanin da nayi cewar shi din ba yaro ba ne karami, yana bukatar aure ya sani tsayawa wajen ganin yayi auren yana koyarwa yana kuma taimakon Ado kan al'amuranshi. Da haka ya soma rike iyalinshi daga baya na bashi shawarar janyewa daga harkokin Adon don ya tafi yayi nashi na karishi saboda lura da jaruntakar shi da nayi. Kan haka na tasa Ado a gaba sai da ya ware dukiya mai dan nauyi ya bashi nima na tattara abinda na iya tattarawa na hada na mika mishi ya soma harkokinshi na kasuwanci. A yanzu yana zaune a Kaduña a gidanshi na kanshi da ya gina da matarshi Rumana da 'ya' yanshi maza guda uku. 83 Dama na ce bari in tambaye ki yaya jikin na Mama? Na ce da sauki sosai, ya ce to ki rinka hakuri fa, ko kuma in ce kiyi ta karawa tunda nasan kina yi. Nayi murmushi na kawar da zancen ta hanyar tambayarshi an samu sakon nawa kuwa? Ya ce eh an samu, na ce to in Rumana zata zo sai tazo min dashi, zata zone? Nayi murmushi na ce ba za ta zo duba mu ba ga Mama ta dawo? Ya dan yi murmushin ya ce, to' to shi kenan sai ta zo din na ajiye wayar can cikin zuciyata nasan tsanar da Mama ke nunawa Rumana ke damunshi, ita kuma Mama tana tsanar Rumaia dama Ibrahim din baki daya ne har da ma 'ya'yan da suka haifan saboda ni. Saboda tayi juyin duniya Ibrahim ya dauke ni kamar yanda ita da sauran ya'yanta suka dauke ni ya ki, don haka taki shi ta hakura dashi akan idona akan idonshi. Ado yayi dariya ya ce ai ta kwarc ki Mama daina barin Humnairah tana kara kwararki. Daina bar mata abin da ki ke so, ki rinka yarda kawai ke da ita kuna haduwa kan abin da ki ke son tunda kaddara ta riga ta hada ki ke da ita. Gaskiyar Ado ne kaddara ce ta hada ni da Mama kaddarar kuma ta kaddara min mallakar mutanen da take matukar so a rayuwarta don haka kiyayyata da ita maimakon raguwa kullum karuwa take yi ban Kara sani da fahintar hakan ba. 84 Sai a shekarun baya-bayan nan shekarun da Ado ya sake komawa cikin al'amuranta saboda yawan rashin lafiyar ta da kuma wulakanci mai tsanani da ta fuskanta a wurin Babana ga shigar ya'yanta cikin matsalolin aure da ma rayuwa. Ganin da yayi zata tozarta, ya sanya shi yin tattaki zuwa har gidanmu tafiyarshi gidan na farko kenan tun bayan barin gidan da yayi yaje ya daukota ya kawo ta yayi jinyarta sai da ta warke tayi garau ta samu lafiya ta murmure tayi kiba tayi kyan gani. Sannan ya maida ita dakinta bayan' ya gyara mata shi yasa mata duk wani abin da ta bukaci a sanya mata, ya daurawa Anti Sha'awa aure ya kwashe ya' yanta ya maida su gidan ubansu ya baiwa Habiba jari mai karfi don yin sana'a, tunda a gidan su kullum fada ake yi akan abinci sannan ya dawo. Amma duk da haka bai sa Mama ta samu zaman lafiya a dakinta ba gatan da ta ga ta samu wurin Ado da kulawar da taga yana yi mata ta hanyar yi mata aiken kudi akai-akai saboda maganinta da ma wasu al'amuran rayuwarta. Sai ya sa ta yunkurin sake tasa mutane a gaba da fitina, shi kuwa Babana ya ce ina? Ai wannan zamanin ya wuce, bai zai yiwu ba, ba zan lamunci hayaniya da fitina ba, ba kuma zai yarda a tasa mishi wata mata a gaba ba tunda a yanzu kam a zahiri ai Zubaida ce. ta damu Mama. 85 Sai dai idan nayi nazari naga ta kasa hakura da kiyayyar da-take yi min yanda take kina kuma haka take kin Umahmah, sai in gane ta hakura da Innan ne kawai saboda ta gane tafi karfinta bata kuma kallon inda take. A wannan lokacin kullum wurin Ado Mama ke kawo karar Babana, kullum kuma karar ba ta wuce ba ya shiga dakina ya dade kamar nasa, ba ya saurarona ba ya bani hakkina. Rannan ina jin kan Ado ya daure ne da al'amuran, bai fahimce su da kyau ba, yasa shi kallona cikin natsuwa ya ce min ni me Mama ke nufi da wadannan kalmomin, na sauraro da hakki ne? Ko tana nufin har yanzu itama bata daina ba ne? nayi shiru nayi kamar ban ji shi ba, can cikin zuciyata na ce ai da ita ka kira ka tambaya. Ba ki ji ina magana da ke ba ne? tunda ba zai yiwu in gaya mishi. abinda ke zuciyartawa ba tunda nasan yin hakan bacin rai zai zama, sai kawai na maida maganar wasa na ce mishi, towwwo! Wato in mutum ya girma sai ya hakura? Kenan nima in shirya, ya yi maza ya jawo ni jikinshi yana dariya tare da fadin a'a-a'a ai ke ban da ke a cikin Humairah tunda ke ai ke kece. Zuwa can yaja tsaki an jima ya sake jan wani tsakin ina dai jin shi ban tambayi dalili ba, can anjima abinda ke damun nashi ya kasa zama yayi 86 Shiru a cikinshi. Sai naji ya ce kwata-kwata Mama bata fahimci rayuwa ba. Ba ta ma san yanda rayywar take ba, ai baka cin zamaninka ka ce zaka ci na wani, ya sake jan wani mummunan tsaki sannan ya ci gaba, ke kuma kin ci naki kin hana wasu cin nasu. Kin kama hakkokin mutane kin daddane kin yi samadin da abubuwa da yawa suka caccabe, kin hana 'ya'ya jin dadin rayuwarsu saboda baki yi musu tarbiyar da ta dace da su ba. Ga alhakin Jama'a da ki ka yi ta diba amma wai har yanzu ba ki fahinci komai ba? Wai lokacin saduda ma bai zo miki ba? Haka ake rayuwa Humaira? Nayi mishi murmushin yake naja bakina nai shiru. Ya zuba min ido yana kalloma amma kin san bana so in yi magana ayi min shiru ko? Nayi murmushi na ce kayi hakuri Kawu mu bar wannan zancen kawai muyi wani tunda ni ai ba ni da bakin magana kan wannan batun. Saboda dai ka riga ka karantar da ni na gane wata gaskiyama fadanta rashin kunya ne. Yayi murmushi saboda yasan nasha fadar gaskiya akan Mama in muna hira ya ce shi na zaga dai haka na daina. Ya ce, to naji kawo mana wani zancen muyi funda na kawo nawa kin ce a'a, na matsa jikinshi 87 kawai na soma yi mishi abubuwan da na san sun fiye mishi hirar dadi da kuma muhimmanci. Tun sanda Mama ta sake dawowa cikin al'amarin aurena ban samu wani cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali ba saboda har a yau dinnan bata hakura ba burinta bai wuce na taga, ta ga bayan auren nawa ba saboda kullum tana gidana. Nata gidan da tsawon rayuwar kuruciyarta take kirarin nata ne, mijin ma nata ne wanda duk zai zauna da su kuma sai dai yayi hakuri, to zaman cikinshi ya gagare ta, a yanzu a shekarunta na girma, shekarun da a su ne ya kamata ace gidan ya zama nata dop tafi bukatarshi. Shi kuma Ado a baki ne kawai yake fadan halin Mama kaga kamar babu wanda ya kai shi sanin halin nata bale ya fishi arnaidan ta zaunar dashi ta gaya mishi abin da ta gaya mishi ta kulla abinda take son kullawa. Sai ka gan shi yana huci yana zare ido, yana fadin maganganu da in ba ayi hankali ba ráyuka zasu yi matukar baci. Haba Humaira! Haba wannan abin tausayi har ina? Zaman gidanku kuma ya gagareta da gimanta ta baro dakinta ta dawo nan, nan din ma zai gagare ta ne? To in nan ya gagare ta taje ina? Rannan dai danne ziciyata kawai amma kiris ya rage in ce mishi 88 to ta shiga daniya Mama. Rannan ma da wata matsala ta sake samun Mama ta sake yanke jiki ta fadi, stroke dinta ya dawo, da sauri na yi wa Adon waya ya dawo. amma abin mamaki wai da ya tambaye ta abinda ya faru da yake bakinta bai mutu ba, sai ta ce mishi ni ce nayi mata sanadin hakan. Watakila tayi zaton daga fadin hakan zai ce min zo ki tafi gidanku, bana auren yanda ta saba ganinn ana yi wa 'ya'yanta, sai kuma maganar ta kare ayi min fada ya kuma shirya ya turata ita tare da Suwaiba wacce bar yanzu aure ya gagare ta, to sun je sun dawo gamu nan kuma muna zaune tare a gidan. Wadannan dalilai da nake issafawa sai suka sa auren nawa ya zamo auren da a daidai lokacin da mutancn waje suke yi min hangacn jin dadi da farin cikin da ke cikinshi saboda nasarorinshi na zahiri da suke baiyane. Ni kuma da nake ni ce a cikinshi cikin zuciyata nasan yanzu ne nake zaman hakuri mai yawa, sai dai kuma ban taba yarda fitintinun da ke kewaye dani a cikin nashi sur sani na taba cewa da na sani ba, a kullum na gayawa mai babban allo matsalolina ko a waya ne. Hakuri zai yi ta bani yana gaya min cewar shi dan Adam haka rayuwarsu take, yakan girma ne yana tare da matsalolinshi, don haka in yi ta hakuri. Dadin 89 abin dai kawai a wurina shi ne duk kokarin Mama ta kasa shiga tsakanin Kawu Ado da Innata ta 6ata. Tayi-tayi abin ya gagara, tayi juyin duniya ta rasa yanda zata yi, bata ma kara tsinkewa da al'amarin ba ta kara tsorata dashi sai a lokacin da Adon ya zartarwa Sa'a hukuncin aurar da ita ga babban amininshi Barrister Tukur Usman. Wanda yasan Sa adatu tana da saurayin da take So bai ma tsaya wajen yin shawara da kowa ba, izini kawai yaje ya nema a wurin Baba. Sai kaWai ya fadi daurin auren kowa yaji, Mama tayi bakin ciki kanar zata mutu ta tasa shi a gaba tana kuka ga Suwaiba shekara da shekaru babu aure, ka samo mutumn mai muhimmanci irin wannan ka dauki wata Sa'a ka bashi don dai kai sun shanye ka ba ka ganin kowa ba ka son kowa sai su? Ya ce ba samo shi nayi ba Manma Aminina ne yya kuma yi min kukan matsalolin gidanshi ne ya roke ni in ina da wata "yar da na san me tarbiya ce in yi mishi hanayrta yana so. Kin ga kuma yana cikin damuwa ba zan kara mishi damuwarshi ba, ban yi mishi adalci ba in nayi mishi hakan. Yanzu ita Sa'a ba damuwa bace sai Suwaiba? Yarinyar da bata son auren ban ganta tana yin kuka a gabanka ba, yayi murmushi ya ce ai iyakar dai abinda zata yin kenan Mama. 90 Ba za a kai ta gidanshi ta ki bin umarninshi ba, be za te je tayi mishi rashin kunya ko wulakanci ba, ba za taje ya ce mata yi ta ki yi ko bari ta ki bari ba, sabods du a dakinsu uwarsu tana da tasiri mai karfi akan 'ya'yanta. Tana kuma da halin girma nayi wa surnıki adalci, ni kadai nasan irin taimakon da tayi min akan aurena, su Suwaiba kuwa ba haka suke ba Mama, ina jin ta rannan tana gaya miki ko taje gida bata gaida Babansu ko kallonshi bata yi, saboda bata da lokacinshi. Shiru kawai nayi muku, to yaushe zan dauke ta in baiwa wani? In dai ba so nake in taje tana w&stsakewa daga halin rashin mijin da take ciki ba ta Soma cin mutuncinmu ni dashi. Shi yasa na barta ta kawo shi ita da kanta, kayan dakin dai zan bayar. Hidima ta ban mamaki Ado ya yi wa Sa'adatu, a lokacin auren nata irin hidimar da ko auren su Umahmah ya tashi yi in yayi haka ya ci a yaba mishi. Magana guda daya da ya gayawa Sa'adatu a ranar da za'a kaita gidan mijin nata kuma ita ce dai ta gamsar da ita tayi amfani da ita aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake nema bai taba kawo karanta wurin Adon ba balle maganar ta wuce ta kai ga Innarmnu. Maganar kuwa ita ce hukunci na zartar miki Sa'a 91 irin wanda uba ne kadai ke da ikon yiwa 'yarshi hakan in har anyi mata tarbiyar da ta dace da ita duk kuwa da ni din ba mahaifinki ba ne, na kuma san hakan sai dai nasan ke din yarinya ce da aka yi wa tarbiyar sanin darajar na gaba. Na kua san ina da gira da mutunci a wunnki sai nake ganin kamar ba zan yi iko dakc kiyi sanadin da zan tozarta wurin mutuin da nake da kima a wurinshi ba, don haka in kin ji ku zauna lafiya. Shekaru biyu kenan da yin auren Sa'a ta haifi danta Adam, har sun yi aikin Haji ita da Inna tare ya biya musu suka tafi babu wanda ya taba jin wata magana surukuta mai dadi suke yi shi da Ado. Ire-ircn irin wadannan al'amuran sune suke kara sanya ni hakuri da kokarin danne zuciyata a kan al amura masu yawa ina kawar da ido akansu. Amma duk da haka wani abin kure hakuri ake yi, saboda a hali irin nawa halin da kullum Inna ke yi min kirarin rashin hakuri a kan shi sai in rinka ganin bai dace in yi hakuri da dole in kuma yi da abinda bai zame tnin dole ba. Dawowan Mama gidan Ado yayi dalilin da itama Suwaiba ta dawo gidan da zama don ta ce ba za ta iya ZAInan gidan ubanmu ba, in kuma da mutumin da ke taimakon Mama kina a zahiri to Suwaiba ce. Kan ya' yana a hade yake, don ko da sun yi wayon sanin 1yayensu tun kan mu taso to a zaman da 92 ake yi dai kansu a hade yake, don ba a bambanta su da komai ba, komai tare ake musu, suma duk abin da zasu yi tare suke yi ba su da wata matsala ko wata damuwa. Amma zuwan Suwaiba sai ta tasa min su a gaba da iya shege iri-iri, dan kankanin abu ne na yara zasu yi sai ta ce uhun, wai su masu gida ko? Saboda ita gidan ubanta ne yasa take yi muku haka, ta bugi Umahmah ko Mama ta buge ta bai taba damuna ba, don nasan duk tsiyarsu ba za su gana mata %50 din abin da suka gana min ba. Don haka ko a jikina saboda na riga nayi ilimin sanin cewar zaluntar yaro bai cutar dashi da komai sai dai ma ya zamo mishi wani alheri a rayuwarshi ta gaba. To amma neman da take yi na ta rinka 'shiga tsakanin Umahmah da dan uwanta tana batawa shi ne abin da naji ba zan lamunta ba, tunda abin da ke afruwa a tsakaninsu din hali ne kawai na kuruciya. Suna mata tana musu kamar yanda take yi tsakaninta da kanmenta, da ni ce na haife su, gara wadancan ma duk sun fi karfinta in dam be za'ayi dukanta zasu yi. A duk lokacin da maganarsu tazo gabana kuma na kan yi hukunci ne bisa cewar ta basu hakuri don ita ce karama duk da mafi girman da aka yi mata na kwana bakwai ne. 93 Ba kuma don komai nake yi hakan ba sai don in hada kansu su zama abu daya, su sani su kuma yarda da cewar yancin da ita take dashi a gidan bai wuce wanda suke da shi ba. Don haka rannan da na sake jin Suwaiba tana shiga naganar Su tana cewa ai tunda kuka zo zaman maula a gidan ubanta sai kuyi jayin bakuri da ita sai na gangara daga inda nake. Naje na shiga wurin nasu Suwaiba tana ciki na tambayi yaran abin da ya faru suka mayar min na kalli, Suwaiba na ce mata a wannan bayanin ne ki ke, fadin wannan maganar wa wadaanan yan yaran ya'yan cikinki? Sau nawa ki ka haifi wadannan? To bana so kar in sake ganin ki a wurinsu bana son ganin kina shiga min harkar yara, ta ce har da taki ma na daina, na ce to da yafi miki daidai. Tun daga ranar ta daina gaishe ni, in na gaishe tan ma ta amsa a laiace ba fita tana kallona bata yi min sallama ba ta dawo kuma a lokacin data ga dama. Naga zata zubarwa mijina da mutuncin da ake ganinshi da shi tunda ba wani shiga na mutunci take yi ba shi kuma ba zaunin gida bane balle yasa abinda take yi. Don haka nayi mata magana kan ta daina yawan fita, ina take zuwa tunda ni da ita ai ba wasu dangi 94 muke da su a Dabai ba, balle ta ce min wurin 'yan uwanmnu take Zuwa. Sai kawai tavi min maganganun da na kalle su a matsayin rashin kunya, gudun 6acinrai sai yasa Ado yazo gida daga Abuja, sai na ce mishi ga abinda ake ciki don ya sani. Sai kawai ya ce min kai Humaira, kananan maganganu irin wadannam rinka hutar dani kawai ki daina gaya min su ko dai kiyi maganin abin kawai da kanki ko kuma hanya mafi sauki shi ne ki gayawa Mama. Nasan zata tsawatar na ce mishi to duk da ba dadin hakan naji ba. Rannan sai wani abu ya sake hada ni da Suwaiba, naje na samu Mama ina gaya mata, sai kawai ga Suwaiba tana biye da ni tana magana har tana tafa hannu, ni fa sai dai in za ki mutu ki mutu in za ki yi rai kiyi rai. Don duk tsiyarki ba zan bar gidan ba ba wurinki na zo ba, ba kuma don ke nake zaune ba, kin ce in daina kula 'yarki na hada na ce har kema bana kulaki, bana shiga harkarki, ba na shiga harkar 'ya'yanki dukkansu wurin Mama nazo gida kuma gidan Kawuna ne. Na kalli Mama, wacce tayi shirù tana kallon tsiwar da Suwaiba take yi min, na ce Mama kina jin ta? Sai kawai naji taja nin tsaki ta ce min 95 Ke tafi can ni ki bani wuri da fitinarki ta tsiya, ke yanzu ai na riga na gane ki gaba daya burinki bai wuce kiyi min abin da hawän jinina zai tashi ba ya karasa ni in mutu, in yaso burin uwarki ya cika a kaina. Na kalli Mama nayi murmushi na ce lnnata ai bata da sauran buri akan ki Mama, tunda gidan da ki ke yi mata gadara a kanshi kina fadin naki ne ya zama nata, mijin da ki ka kwace mata gashi can kin baro mata shi saboda ya gagare ki. Nan kurna da aka dawo aka zauna nawa ne, tunda mai kishiyoyi da 'ya'yan miji ma takan nishadi in ta samu wuri ta ce gida da mnijin nata ne ita kadai balle ni da ni kadai din ce. Mama ta kama kuka, Suwaiba kuma ta kama maganganu ba dai ita kadai ce a gidan ba wooo! Na ce ai ita bata dame ta ba, ba kin san gidan ba? Ai kin san bata kishi da ita. Ai Inna bata da sauran kishiya, dama Mama ce matsalarta, tun kuma daga ranar da tayi kuskuren kin jin kashedin da masoyanta suka rinka yi mata, ta dauki Ado ta danka min shi a hannuna da nufin zaluntar uwata, nayi wuf na kama shi na dunkule shi wuri daya na dankawa Innata shi bata sake zamowa matsalarta ba. Na wuce su nayi tafiyata cikin zuciyata ina fadin Mama dai kam yau na zage ta duk abinda Ado zai yi 96 kuma sai yayi kawai mu gani. Ban dade da fitowa daga dakin nasu ba sai ga Suwaiban tazo ta wuce ni ta fita nayi waya na ce wa maigadi ya kulle gidan kar wanda ya sake shigowa kowane ne sai an gaya min, ya ce min to. Sai da aka yi sallar magariba Suwaiba ta dawo maigadi ya ki bude mata kofa tayi juyin duniya ya ki, Mama ta turo keken ta na guragu don bata riga tayi karfi ba tukuna, tazo ta same shi ka bude mata na ce. Cikin stawa take ba shi umarnin, ya ce Goggo ce ta ce kar a bude, tayi-tayi abin ya gagara sai ga ta a kofar dakina na ce kisa a bude wa Suwaiba gida ko? Cikin tsawa tayi maganar na ce to, ba ta kuma zaci to din zance ba na kali Hindu na ce mata jeki ki ce wa solori ya bude mata kofar, tana gaya mishi ya bude, Suwaiban ta shigo. Muna nan a haka Suwaiba bata sake fita ba don tasan taná fita zan sa a kulie har Ado ya dawo, shigowar dare yayi na kuma riga na shiryawa zuwan nashi, don sabuwar kaza ce a jikina. Kwanaki uku kuma kenan tunda naci ka riga ta jika a kidime kwarai ranar ya kwana, Humaira, na ce mishi naam ya kara matsowa jikina va kankae kina da wani sirri a tare da ke Humairah da wani lokaci ki ke kidiar da ni, ki rinka sanya ni ina jin tanfar dai ke din budurwa ce. 97 Shiru nayi ban tanka mishi ba. Washegari da safe sai da na slirya mishi abin karyawanshi ya gama komai ya yi wanka ya kintsa aiken Mama biyu ta waya wai tana son ganinshi, amma bai samu fita daga dakin nawa ba sai gab da azahar. Don haka sai da yaje yayi Sallah ya dawo sannan ya shiga wurin nata, ya dan dade kafin yayi waya wai in je. A dakin na same su ranshi a 6ace kwarai da alamar ya ji maganganu iri-iri, amma duk da haka ya kalle ni saboda kwalliyar da nayin yasan táshi ce. Meke faruwa ne Hurmaira? Cikin natsuwa na ce mishi kamar me? ya ce ina nufin mc ya hada ki da Mama? Nayi maza na ce babu komai. Mama tayi maza ia ce ba ki zagen ba za ki ce mishi babu komai? Suwaiba ta ce wai ita ga mu...Ado ya yi maza ya katse ta in ki ka zage ta a gabana ranki zai 6aci, na kalle shi cikin natsuwa na ce mishi. Ni babu abin da ya hada ni da Mama tunda ba abokiyar magana ta ba ce, uwata ce kai ne ka ce in wani abu ya faru tsakanina da Suwaiba in daina gaya maka, in kawo kara wurinta zata tsawatar mata. Ya ce haka ne, na ce to karar na kawo sai Suwaiba tayi min rashin kunya a gabanta nayi mishi bayanin komai har kawo kan abin da ya faru duka, 98 sai dai na ki yarda da cewar ni maganganu da Mama nake yi na ce da Suwaiba ne. Ado yayi shiru na lokaci mai tsawo saboda ranshi ya 6aci kwarai, don kwa ko ban amsa da Mama nake yi ba ai shi ya ji abinda na fadan sai dai kuma nasan zai san ita Mama ita ta fara tsokanata. Shiru yayi cikin matsanancin tunani, yayin da ni kuma nayi shiru cikin natsuwa ina sauraron abinda zai ce, sai Mama ta fara yi mishi bayani, ita Humairah bata gane ba ne ita so take duk wanda zai zauna a gidan nan sai ya yarda ta maida shi talolo kamar yanda ta maida wannan yaron. Ado ya daga kai ya kalle ta ya ce wa Ibrahim? Tayi maza ta ce ebh, shi to ita kuma Suwaiba ba za ta yarda da hakan ba, don ita ba sakarya ba ce irin shi, -ba ruwinta tazo ba ba don ita tazo ba. Tunda gidan nan ba nata ba ne ita da yan dakinsu da zata ce sai ita da su ne za su zauna a ciki, gida ai naka ne amma take bugun kirgin nata ne yayi maza ya katseta ba bugun kirjin bane nata ne kuma tunda suwaiba tace ba wurinta tazo ba. Kema kin fada ba wurinta tazo ba, to ta bar mata gidanta kawai, azo a zauna a gida ace ba wurin matar gida aka zo ba wurina aka zo'ni mazaunin gida ne? Humairah ai bata adawa da 'yan uwanta, Mama da ke take yi shi yasa da ta samu damar gaya mii magana ta gayaa miki, ba kuma zan kyale ta kan 99 rashin kunyar da tayi miki ba. Ai ta zauna da Ibrahi babu abinda bata yi mishi ba, ta kuma zauna da Kaltume da ya'yanta tsawon wata goma bata ji ko ganin wani abu mara dadi ba, saboda bata da matsala dayan uwanta. Don hakka Suwaiba suna da gidan uba ta koma can ta zauna. Mama ta ce uhun, za ka kore mu dai kawai tunda kasan hakanne zai fi yi mata daidai, ai kaima kasan ba zan zauna a in da Suwaiba ba za ta zauna ba in dai ka ce ta tafi to tare zamu tafi. Ya ce to shi kenan Mama, in kun ga hakan yafi miki sai ki bita ni dai nasan ban ce ke ba amma Suwaiba kam a gabana ta amsa ta ce ba wurin Humairah tazo ba, to in wurina ne ni bani da gida zaman nata ya isa haka ta tafi kawai. A ranar Suwaiba ta tafi, ina jin Mama tana gaya mata inda zata, wai kar ta ce gidanmu ban san yanda aka yi ba sai kuma gata ta gama bin dangi ta gaji ta koma gidan namu. Ta bude dakin Maman ta shiga ta zauna ita kadai, Innar tawa kuma ita ce dai mai daukar dawainiyartata. Barin Suwaiba gida sai Ado ya dorawa diyarshi dawainiyar baiwa Mama magani da safe da yamma tunda da rana kam bata nan tana makaranta, sai ni in je in bata. Tunda Ado ya dorawa Umahmah wannan 100 dawainiyar ya hadata da aiki saboda kullum taje baiwa Mama magani tunda ba maganin ba ne kawai sai ta motsa mata jiki, to bata fitowa sai da kuka. Tunda ba za ta gama ba sai ta jawo wata sanda da ta sunne a gefen gadon nata ta rafke ta dashi wai tayi mata mugunta. Kullum tazo ta gaya min zante mata to kiyi hakuri Umahmah ai kin san bani na saki wannan aikin ba ko? Ta ce min eh. Rannan ina dakin Ado da rana saboda yazo gida week end na kalli agogo na ce mishi bari in je in baiwa Mama magani lokaci ya yi, ya ce a'a babu inda za ki yanzu Umahmah taje ta bata na ce ishi to. Sai ga Umahmah ta dawo tana kuka da iyakacin Rarfinta, sallama biyu tayi kafin Ado ya bani izinin amsawa da bata umarnin shiga inda muke din. Durkusawa tayi a kasa tana cewa, Baba ka taimake ni ka ce ni da Hindu da Nusaiba ne zamu rinka baiwa Mama magani da motsa jiki, kowa sau daya a wuni tunda su ba ta dukansu. Amma ni kullum sai ta buge ni. Da sauri ya ce duka Umahmah? Ta ce ch, ka gani? Yanzu ma ta buga min sanda a dan yatsana yayi maza ya kama hannun nata yana dubawa ban san abin da ya tuna ba sai kawai naga ya yi murmUshi. Ya ce, Mama kenan, ba kya iya tashi kiyi komai 101 ba kya iya yi wa kanki komai amma kin ajiye sanda don dukan wadanda ki ke son duka? Ya dago ya kalli Umahmah ya ce, Umahnmah, tayi maza ta ce na'am Baba, ya ce daga yau na sauke miki nauyin kulawa da Mama da maganinta da motsa jikinta, duk ba naki ba ne. Zai zamo na Mamanki bari ke in dora miki nauyin kulawa da Maman naki kin san irin abincin da na canza mata don gyara min jikinta? Tayi maza ta ce eh Baba. Ya ce to ki rinka shirya mata shi kina bata ita zata kula min da Mama. Umahmah tayi dariya cikin tsananin farin cikin canjin da ta samun ta ce mishi sau goma zan rinka bata ko sau ashirin Baba? Ya ce, a'a Umahmah ai rage kiba da rage teba nake so tayi ba karawa ba, don haka sau uku kadai za ki bata, ta ce mishi to. Tana murna tana tsalle don dadi, tasa kai ta fita. Tun daga nan bai wa Mama magani da motsa mata jiki ya dawo kaina. Gaskiya ne, tunda Ado ya tilasta ni janyewa daga cin abinci mai nauyi irin namu na dafawa na janye daga cin nama mai yawa, na koma cin irin ganyayyakin da ake nomawa a gonar Humaira Farm'. Nayi matuka zabge jikina, tebar da na ajiye tayi matukar sauka na rasa nauyi mai yawa a tare dani 102 daga kilo sittin da biyar zuwa saba' in na dawo arba in da bakwai zuwa hamsin. Na kurma tsaya akan motsa jikina safe da yamma, don in kara gyara jikin nawa ta yanda mai gidan zai samu yanda yake so. Masani da motsa jikin Mama na gama na dawo nazo na samu Umahmah tana zaune tana jiran zuwan nawa, wai abincina ta shiryo ta kawo min, kin san Goggo nasa miki 'Asparagus' sanda daya Brocooti daya ganyen celery danyen dankalin turawa guda uku, cherry tomatu biyu, Beef tumatu biyu, cabbage dan madaidaici, kwai dafaffe biyu Na ce to na gode Umahmah bari in yi wanka tukuna in fito ta ce min to, har nayi wankan nazo na gama ci tana jirana in kawo miki madarar shanu na dafa miki? Na ce kawo min taje ta kawo min a kofi ina karba na kafa kai na kwankwade, ta zuba min ido tana kallona tayi murmushi ta ce, Goggo ke kam kwankwadar madara ki ke yi nace eh, Umahamah kin san mu komai addininmu ya koya mana yanda zamu yi shi. Don haka madara kwankwada muke yi, ruwa musha a hankali, sai zuma kuma mu lasa, kin gane? Tayi maza ta ce min eh. A wannan lokacin ba Ado ba da dama kullum jikina abin jin dadin shi ne kowane lokaci kuma cikin 103 tattalin jikin nawa yake don ya kara jiyar dashi dadin da yake nema. Ni da kaina ina jin dadin jikin nawa, ya yi min warai-wasai, bana tare da wani nauyi, kullum kuruciyata kara bayyana take, kwalliyar da na dama nake yi saboda ina daukar kowane iri. A daidai irin wannan yanayin ne da lokacin wani irin lokacin da nake ganin tanfar ban taba samun wata dama ta mallakar mijina kamar shi ba. Ado ya dawo daga tafiya zuwa kasar Thailand in da ya tafi taron kärawa juna ilimi kan noman Rania kasashe masu tasowa, saboda a wannan lokacin ya shiga kungiyoyin manoma daban-daban cikin kasa da waje. Kwalliyar mini siket da wata 'yar shirmanmiyar riga nayi mishi, shi ne kuma ya taho min dasu in na tsaya cewa nayi kyau ma nayi shirme. Kallona Ado yake yi yana karawa, watakila ji yake tanfar ya kama ni yayi ta lashewa tun lokacin yin hakan bai yi ba. Ban fa bai wa Mama maganinta ba, fuskarshi ta dan yannutse alamar ba ta maganin ya somma shiga mishi cikin harkokin rayuwarshi. Bari dai zan nemi wacce zata rinka yi min wannan aikin ina biyanta, don na riga na fara gundura da yanda hakan yake shiga lokataina. Nayi murmushi na ce, ai ba wani dadewa ma ake 104 yi ba, minti arba'in da biyar ne kawai. Ya kalli agogon hannunshi kafin ya sake kallona, ai ba zan iya jiranki minti arba'in da biyar ba, sai in ga kamar awa arba'in da biyar din ki ka yiwo, muje in raka ki. Na mike tsaye da nufin zuwa dauko alkyabbata da gyalenta in sanya in rufe kwalliyar tawa, tunda nasan ba zai yiwu in iya shiga wurin Mama a haka ba. Hannu ya saka ya jawo ni na fada jikinshi, Humairah kina kallon yanda ki ka zama kuwa a madubi? Ko ban kalla ba ai kana gaya min kuma in dai nayi maka ka gamsu to ai shi kenan ya ishe ni. Kin yi min na gamsu Humairah, kin zama tanfar wata yar yarinya mai shekaru ashirin da biyar. Nayi dariya na ce, goma fa ka rage min Kawu, ya ce uh ba ki i ashirin da biyar din ba, babu mai ganinki ya ce kin wuce hakan, don haka bar gonman kawai a gefe in kin ga dama ma ki dora min a kaina tunda ni kam ni ne... Nasa hanu a bakinshi na ce na ce baka yi ba kawu, ganinka nake tanfar yau ne nmuka faro komai in don wannan tebar taka ne bata yi maka komai ba in ban da mutunci da kwarjini da ta kara maka. Ado ya kyalkyale da dariya ya ce, muje ki bata magani mu dawo na sanya alkyabbata na rufe kaina da gyalanta muka fita muka nufi dakin Mama, tana ganinmu ta rushe da kuka. 105 Ni kam nasan ganin da tayi mana tare ne yasa ta kukan gashi kuma na dan makara kan lokacin da na saba zuwa bata maganin, amma Ado da bai gane hakan ba rarrashi ya rinka yi yana bata hakuri tare da tambayarta damuwarta. Wani abu ke miki ciwo Mama? Tayi jagwale ta. kara maida kanta ta kara zama abin tausayi, ta girgiza kai uh'uh wasu hawayen suna kara zubowa, to menene? Kiyi magana mana Mama, ganin kidimewar tashi a kanta ya kara bata dama ta sake rushewa da wani sabon kukan. Cikin kukan naji tana cewa, wai burinta ne kawai ta gane ba zai cika ba a kanshi har ta mutu, da sauri Ado ya zaro ido yana kallonta cikin kidima tare da tambayarta menene burin nata? To ba Ado ba, ko ni da ba wani damuwa nayi da lamarinta ba, mu'amallah kawai nake yi da ita don ta zame min dole, 6oyewa kawai nake yi nake kuma kin yardan wa zuciyata dauke ta ita din damuwa ta ce tunda nasan damuwarta a kaina tafi wacce nake da ita a kanta yawa. Kasake nayi ina kallon Mama tare da sauraron abin da zai fito daga bakin nata a matsayin shi ne burin nata, sai kawai naji ta kekkebe baki ta ce, wai in ganka da mata biyu, kadan ya rage in yi subutan hannu in buge bakin Mama da abin da nake rike da 106 shi na gwajin jininta. Sai na daure kawai cikin zuciyata dai gaya mata nayi ai ke da burinki za ki mutu Mama, Ado kuwa shiru yayi na wani lokaci mai tsawo, cikin wani yanayi da yafi kama da tausayinta ne yafi komai kama shi. Zuwa can sai naji ya bude baki ya ce mata kiyi hakuri Mama in har na samu yanda zan yi to ba zan bar ki har ki mutu da wannan burin ba, zan cika miki shi nan ba da dadewa ba, in har muna raye dukkan mu, kiyi hakuri. Cikin yanayin shagwaba ta ce mishi, to. Hannu yasa ya karbe abubuwan da na zo dasu din na amfanin nata yayi mata komai saboda jikina ya riga yayi min sanyi, na riga na gane wannan burin na Mama na son ganina da kishiya. In ba wata kaddarar ba zai cika a kaina, don kuwa kalaman da yayi amfani da su wajen bata hakurin sun sha bamban sosai da wadanda na saba jin shi yana yi mata a duk lokacin da tayi mishi magana kan ya kara auren. Mafi yawancin lokaci murmushi yake yi ya ce Mama kenan, ba wai bana son yin auren ba ne, ko kuma na kasa yin shi lokacin yin nashin ne kawai bai yi ba, don haka kiyi hakuri. Ita kuma tayi ta zuga tana kokarin tunzura shi kan wai ya kasa ne, sai ya ce to Mama in na kasa ma 107 ai ba wani abu ba ne dama karawan ba na kowa da kowa ba ne na wanda yaga zai iya adalci ne, in ba za ka iya ba sai ka zauna da guda dayarka kawai. Ni da in yi biyun in zo ina zaluntar wata ko ana zaluntarta ina kallo na rasa yanda zan yi ai gara min in yi ta zamana a haka. Sai taja tsaki ta ce ai kuwa da ka ji kunya. To yau ba haka aka yi ba cewa yayi in har ya samu yanda yake so nan ba da dadewa ba zai yi sanadin cikan burin nata. kenan yayi nufin yi shi kuma mutum ne mai yin aiki da abinda ya fada. Tashi muje Humairah, kalmarshi da naji kenan na dawo cikin natsuwata na fahimci ya gama yi mata abinda ya kawo mu din. Sai dai duk da na gane abinda yake shirin yin ban muna mishi wani canji ba. Iyaka dai bayan ya samu bacci ya dauke shi, maimakon nima in yi nawa baccin don in samu hutun da ya dace da jikin nawa tsunduma nayi cikin tunani mai yawa, in saka wannan in kwanče, in saka wanca. Mama zata yi min sanadin kishiya a daidai lokacin da ni da mijina muka dunkule muka zama abu guda daya, ya zama ni a zama shi. Zata sa shi kawo min wata cikin gidana don ta samu hanyar wargaza min gidan, tayi min sanadin fitina, tayi dalilin da nima zan kasa zaman gidan mijina kamar yanda itama nata gidan mijin ya gagare ta. 108 Tunda a yanzu din nan a yanda najin zuciyata, ai ba zan iya zama da wata kishiya ba, bai yi min ita tuntuni ba sai yanzu da na gama mike kafafuna, ya ce in nade hanyoyi iri-iri kawai nayi ta tunanowa na yanda zan yi in hana Ado yin auren saboda in ga burin na Mama bai kai ga ci ba. Sai dai tayi ta zama dashi yana cinta ita kadai a ranta, tayi ta fama dashi tuni Ruwailah ta fado cikin raina, kiranta zan yi in yi mata maganar tunda ni da ita yanzu a dunkule muke, ta kuma san hanyoyin shiga da fita iri-iri, bari dai ya kuskura ya ce min yana neman aure, zai ga abin mamaki. Mun soma zama da Ado a cikin wani yanayi da shi bai san me nake ciki ba nasa ido da 'yan rahoton da na kewaye shi da su akan dan kiris in suka ji to suzo su gaya min sai kawai aka yi waya da daddare kan cewar mai babban allo bai da lafiya. Babana ne kuma yayi wayar, jikina ya dauki rawa nan take na soma yin kuka duk da ina jin Babana yana gaya mishi cewar a'a da sauki gashi nan ma ita Binta tana ba shi kunu ina jin dai jikin girma ne kawai ya yi addu'ar Ubangiji ya ba shi lafiya. Ya juyo ya kalle ni. Mallam mai babban allo kar yayi ciwo? In ban da mai babban allo an yi mishi kira mai kyau gashi ya rayu cikin addini ga kuma gatan ya'ya da jikoki a kewaye dashi an ce miki kananan shekaru ne dashi? 109 Ya fa haura tamanin da dadewa, ban daina kukan ba tunda a kam nasan komai tsufan mai babban alle ina son shi ina kuma son rayuwarshi kullum fatana da addu'ata Ubangiji ya kara mishi lafiya ne. Miko annunshi yayi yana share min hawaye tare da fadin sai ki himmatu muyi sammako da sassafe muje mu dubo shi, in yaso ai daga can sai in wuce tunda ina da tafiya a gabana. Ke kuma in ki ka kwana sai ki dawo na ce mishi to, amma ai gara muje da yara koda su Nusaiba ne kawai tunda kana jin irin fadan da yayi min wancan karon na kar in sake zuwa mishi gida ban kai mishi yara ya gansu ba. Koda bai da lafiya in ya gansu zai ji dadi, ya ce min to. Kan ayi sallar Asuba mun gama komai, suma yaran da za'ayi tafiyar dasu sun gama, Mama kuwa naje na gaya mata na kuma ce mata ko zamu tafi tare ta ce ina? Ba za ta ko ina ba da wannan jikin nata na ce to. Nayi mata addu'ar samun karin lafiya na bar wa masu aikina guda biyu Sadiya da Tabawa sallahun kula da Mama da sauran yaran da ke gidan, muka Idar da sallar Asuba muka tashi. Computer Hiace Bus mai cin mutum goma ne muke tafiyar a ciki, dama kuma Adon ya sai min ita ne saboda tafiya gida da yaran, ni da shi da Baba Yahya ne a baya sai yan matan su hudu a tsakiya, sai 10 kuma Usman da dircba a gaba. Ni kam dama tunda muka taso ban saki jiki nayi wata magana ba in dai ba wata tambaya aka yi min ba, lazimina kawai nake yi. Ado yana ta amsa wayoyinshi daga wurare daban-daban, kamar yanda dama al'adarshi take saboda yanayin mu'amallar shi da Jama'a. Ana cikin haka naga ya amsa wata waya da naji ya ce ikon Allah! To muna nan akan ya na daga ido na kalle shi banga wnai abu ba sai naji ya sake yin wata wayar, kai Bala ka bar abin da ka ke yi kaje gida ka dauki motata ta hawa ka debo min sauran yaran nan kuzo ku same ni a Bauchi. Ban yi mamakin umanin da ya yi wa Balan ba, don nasan tsakaninsu ya wuce duk yanda ake zato, mu'amallah yake yi dashi irin na da da uba, tunda takai ma ya gaya min ya gayawa Umahmah cewar Bala shi ne mijin da zai bata in har lokacin auren yazo muna raye. Na daga ido na kalle shi cikin natsuwa, na tambaye shi wani abu ya faru ne? ya ce me ki ka gani? Na ce uh'uh nayi shiru naci gaba da abinda nake yi, shima ya kashe wayoyin nashi ya kara gyarawa Baba Yahya jinginon da yayi a jikinshi yana bacci wai don ya kara jin dadi. Jimawa can sai naji ya ce min ke a rayuwari ai ke 'yar gata ce Humairah nayi maza na ce mishi da 111 aka yi me? ya ce to kin rayu tare da uwa da uba da Kakanni na bangaren uwa da uba. Ki duba kiga Hajiyar Giyade irin yawan ran da baiwar Allahn nan tayi, bara ne fa ta rasu. Nayi maza na ce mishi eh, ai daga rasuwar tata ne ma na kara tsorata da rashin lafiyar Mallam. Ya kalle ni cikin natsuwa ya cc min, to ki kara tsorata Humairah, Mallam zai yi ta zama a duniya ne, jikokinshi na farko-farkon fa sa'o'in Inna ne, mutumin da yayi irin wannan yawan ran ya bar zuriya mai albarka irin ta Malla ya'ya da jikoki da ya'yan jikoki ba a san yawansu ba. Su Nusaiba nan duk ba yawan ranne yasa suka san shi ba, ke kina zama kiyi nazari da tunani kan ya' yan da suka rayu rayuwa irin tawa Humairah? Nayi maza na daga ido na kalle shi ya ce, ni kam ai maraya ne Humaira, tunda ban san mahaifiyata ba. Babana ya rasu tun ban isa komai ba, a haka na taso a tsakanin gidajen 'yan uwa da makwabta babu wanitsayayyen da za ka gani a tsaye akan al'amarinka, haka nayi ta dibi-dibin da nayi karatun primary da secondary a lalace. Saboda ina ganin wasu yaran unguwar yan kadan suna zuwa a irin wannan lokacin ne fa Mama tazo ta tafi dani, kafin zuwana hannun Mama ban taba dandanar wani abu mai sunan dadi ba. To ke fa? A cikin gatanki ki ka rayu mutanen da 112 suke sonki suna kewaye dake, don haka kar muje gida ki samu jikinshi yayi tsanani kice zaki yi ta rusa kuka wannan al'ada ce ta jahiliyya wacce kuma aka hanata. Cikin natsuwa da sanyin jiki na kalle shi na ce jikin nashi yayi tsanani kenan ko? Bai yi musu ba ya ce ch, gaba daya muka kama bakunanmu mnuka yi shiru, sai addu'a kawai muke yi. Mun isa Bauchi wajen sha daya da rabi ne na safe saboda samnmakon da muka yi, ga kuma mota lafiyayya uwa uba kuma shi ne mun godewa Ubangiji ya tsare mana hanyar. Tun daga karya kwanan layin runfuna ne a kakkafe, Jama'aa ciccike har lokacin kuma Jama'a isowa suke tayi, jikina ya dauki rawa kar-kar-kar. Ado ya kama ni ya rike a jikinshi. Kiyi hakuri Humairah, tun a hanya an gaya min Mallam lokacin shi ya yi, ban gaya miki ba ne don kar tafiyar ta zamo mana mai tsanani da yawa, kiyi kuka ta hanyar zubar da hawaye ba laifi ba ne, amma kar kiyi wani abinda ya sabawa Shari'a. Tunda kullum a cikin karatu ki ke, karatu na addini. To shi karatu da ki ke ganinshi yanda duk ya kai da yawa to bai da wani amfani matukar mai shi din ba zai yi aiki da abinda ya sani ba. Shi yasa ma sai aka ce mana babu wani sani sai 113 wanda aka yi aiki dashi. Ade yana yi min wadanan bayanan tuni ni kam awaye da majina zuba kawai suke yi min. Jama'a suka tartaso don ganin isowar Ado, suna yi mishi sannu da zuwa Alhaji, barka da isowa, abin da suke fada mishi kenan yana amsawa, amma hankalinshi yana kaina, na yanda zan yi in wuce cincirindon Jama'ar da ke zaune in shiga gida. Rike Mamanku Nusaiba, tayi maza ta kama ni ta rike ungo jakar nan Hindatu, itama ta karba, to maza Umahmah kuje. Haka muke wuce in na wuuce inda maza suke 'yan uwana suka atre ni don an riga an ji isowata. Muna shiga gida na saka kuka sosai sai dai ban yi ihu ko wani abin da ya saba ba, na riga na sani ihu ko sabo ba zai dawo min dashi ba, ba zai amfanar da mu da komai ba šai dai ma ya zame mana wani sanadi. Ubangiji ya gafarta mana. "Sannu da zuwa Hajiya." Mafi yawan mutane abinda suke fadi kenan, ina amsawa. Manya kuma da suka fi kowa sanin abinda ke tsakanina da mai babban allo suna ganina cewa suke yi. Uh uhun, sai hakuri Humairah, yau kin rasa Mallam, wannan maganar ita ce tafi komai Rara 114 tayar min da hankali ia karyar min da zuciya gaba daya gidan a cike yKe har tsakar gida babu masaka tsinke. Tabarmi ake ta shisshimfidawa saboda iyali sun riga sun hadu. amma kowa yana cikin natsuwarshi babu koke-koke, babu maganganu a koma gefe ana ta hira ana ba da labari a gidan mutuwa. Kowa cikin natsuwarshi yake, in ma yana istigifari ko salatin Manzo ko kuma yana zaune cikin jimami saboda yasan tilas watarana shima zata zo kanshi. Dakin Hajiya 'yar dubu na fara shiga can kusa da ita naje na zauna saboda tana hango ni ta shiga kokarin samar min wurin zama a kusa da ita din, kama ni tayi ta rungume a jikinta tana fadin sai hakuri, sai hakuri sai hakuri. Bar kukan haka kuyi tayi mishi addu'a,. Ina share hawaye ina ce mata ban gan shi ba ne Hajiya da na ganshi wata kila da ya gaya min wani abu, ta ce da kin ganshin ma maganar guda daya ce, ita yayi ta nanatawa kuyi hakuri da gidajen aurenku, kuyi bakuri da zumuncinku, bai fadi komai ba bayan wannan. Ranar da mijinki yazo kuwa lafiyar shi kałau sun kai awa biyu a falon shi su biyu ya hana a shiga 115 bayan tafiyar nashi ne ya soma kukan ciwon kai ashe tafiya ce tazo ban cewa Hajiya 'yar dubu ban san Ado yazo wurin mai babban allo ba, shiru kawai nayi. Yan uwa suka yi ta baro in da suke suna zuwa yi min ta'aziyya da na natsa nima sai na mike naje na yi wa wadanda suke gaba dani lokacin ne naga inda su Nusaiba suka yi masauki, wurin Hajiya Kubrah. Anyi zaman makoki kwana uku amma Jama'a sai tururuwa suke yi suna ta isowa a cikin gida ana ganin kamar za a kara zuwa bakwai sai kawai Alhaji Maikudi ya shigo ya kara gaida Janma'a ya ce to yau kowacce ta shirya ta tafi dakinta ya isa haka. Duk inda muke ba zamu fasa yi wa Mallam addu'a ba, har sai ranar da tamu tazo ta same mu, muka ce haka ne. Muka tashi daga gidan rasuwa muka bi Inna zuwa gidanmu, can ma gida yayi matukar cika saboda su Bala da yara sun iso har iyayen Balan ma Sun zowa Ado ta'aziyya, ga Yaya Ibrahim da iyalanshi gaba daya, ga su Ruwailah har da su Baba Tanimu. Ga mutanen arziki kawayena da a yanzu nake mu'amallah dasu matan abokan Ado, Babana va 116 shiga dawainiya da Jama'a, Zubaida ma haka, tun da ita kam Sa'a can dakinta ma ta sauka gaba daya. Shigowa nayi wurin Inna na samu Kawu Ado da abokinshi na tuntuni, Mallam Umar wanda yanzu shi da Inna babu wanda yasan tsakaninsu, saboda mu'amallar dukiyar da suke yi. Suna zaune kan shimfida a kasa su biyun ita kuma Inna tana daga can cikin daki kusa da bakin kofar dakin tana rike da labulen don ta rinka hangen su don suji dadin maganar da suke yi. To mutuwa kam ba an riga an yi ta ba, Mallam Umar sai yasa a fasa abin da aka sa a gaba? Ya ce a'a Inna a dai bar shi a hakan kawai na juya na fita na basu wuri cikin zuciyata dai ina mamakin abinda aka sanya a gabad a ya sanya Inna fadin mutuwar Mallam ba za ta bana ayi ba. Nasan lalle yana da muhimmancia wurinta. Kwananu biyu a gida na kwashe iyalina muka koma gida muka je muka samu Mama wacce ba sai na tsaya fadin mutuwar Mallam tayi matukar faranta mata rai ba, a zuciyata na ce uhun murnar mutuwa kam ma ai murnar banza ce, tunda kai ma mai murnar ba ka tsira ba, wani naka ma bai tsira ba. Kwananmu biyu da komawa, Ado yayi tafiyarshi wacce dama zai yi rasuwar Mallam tasa 117 ya daga, ni kam ina gida tare da iyalina tunda Mallam ya rasu na kara maida komai ba komai ba. Kullum sai na tuna shi, na tuna kalamanshi musamman nasihohinshi da mafi yawancin lokaci yake yawan nanatawa, wannan duniyar ai ba komai ba ne, dan dadinta kuma takaitacce ne. sAl' amuran cikinta kuwa in har kana da hankali to na tsoratarwa ne, ina iyayenmu suke? Ai muna kallonsu suka kare ba mu yi komai ba don ba mu da ikon yin to haka randa tazo kanmu to gashi kuwa tazo din yau baya nan. Duk yawan iyalinshi kuma taruwa kawai muka yi muka yi kuka muka tashi wannan kadai ya ishi bawa tsoro. Sati biyu da tafiyar Ado ya dawo ya kwana a gida gari ya waye daga ni har shi ga dukkan alamu muna cikin jimami don 'yan abubuwan da suka gudana a tsakaninmu duka babu wani matsanancin nishadi a ciki. Tun kwanaki fa naso muyi wata yar magana da ke rasuwar da aka yi ne yasa na dakatar da al'amuran zuwa wannan lokacin. Na zuba mishi ido ina kallonshi cikin natsuwa da sauraro. Sai naji ya ce min kin san abokina na ruwan bungo da matanshi da iyalinshi duka na ce mishi eh, ya ce ke da kanki ne kike gaya min cewar 118 suna da kokari wajen kula da tarbiyar 'ya'yansu, na ce haka ne. Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce min, to tun kwanakin baya kamar sati shida da suka wuce nayi mishi waya na ce mishi in akwai yarinya budurwa a gidanshi ina so. Abinda naji a zuciyata yafi karfin a kira shi faduwar gaba, na dai daure kawai na zuba mishi ido ina kallonshi cikin wani yanayi da ban tabbatar ba a-farke nake ko a mafarki nake oho? Ni da ke muna da fahintar juna, kanmu a hade yake bamu da wata matsala a tsakaninmu, yarinyar da zan kawo ba wata yarinya ba ce da ba ki san tarbiyarta ba, kin san iyayenta kin san komai dinsu. Har ma kuna mutunci ke da su. Yar wajen Hannatu ce, bana so ki dauki wani abu da tsanani ko kiyi tunanin saboda wani zan yi musamman da yake na sha gaya miki cewar ina son mata biyu amma ba zan yi ba, sai adaidai lokacin da ke da kanki za ki shaida cewar nayi miki adalci. Ban san yanda aka yi ba, sai kawai na tambayi Ado to adalcin me kayi min a yau da zaka kawo min ita? Ban san shi ba in kuma akwai shi nuna min shi. Shiru yayi yana kallona, bai tanka ba, tuni naji, wani abu yana motsi cikin Jikina daya sani 119 shure mishi abin karyawan nashi da kafata na mike tsaye ina fadin, ai tuni nasan abutarka da Mallam Haruna in ba sa'a nayi ba tsiya zata zame min. Baka da hira sai ta ya yanshi ni ina nasan su balle in san wata tarbiyar su da ka ke cewa na gaya maka? Ina ruwana da su, Mama ce ta saka kayi aure don burinta ya cika ba kuma zai cikan ba a haka zata mutu. Kar ki zagi Mama Humairah, saboda bana so kiyi sanadin da maganar zata lalace a tsakaninmu, kar ki neme ni da fitina tunda ni ba ita nake nema da ke ba. Ki bari mu tafiyar da al'amuranmu yanda muka saba yi saboda yaran nan sun riga sun fara wayo bana so su shaida wani sabani a tsakaninmu. Na mulmulo wani irin mahaukacin ashar irin wanda ban taba ba na antakawa yaran na ce su sheda komai, saboda ka shirya cutata wannan mutuwar tsohuwar tasa ka kayi aure mugu...caraf yayi ya kama min baki ya rike, yana sakin bakin kuma ya faska mishi mari. Kafin ta sa ni auren wata ai ta sani aurenki,. kenan ba yau na fara yi mata biyayya akan aure ba. Hannu biyu na saka na kama rigar Ado na rike na ce to a saken kawai tunda ai bayan umarnin aurena ta baka umarnin sakina sake ni kawai a yau 120 kowa ya huta. Kama hannayená nayi yá tattara su wuri daya ya hada su a jikina, ya hankada ni nayi tsalle na kife can gefe. Ya kama hanya yayi tafiyarshi Ana cikin haka sai ga su Ruwailah sun iso da su Furerah, Jama'ar cikin gida gaba daya sai 'yan kadanne ba su zo ba, gaba daya labarin auren Ado ya bazu ko'ina. Don haka suka zo su jajanta min al'amarin tunda su din a yau nawa ne a bangarena suke. Muna zazzaune jungum-jungum gaba daya mun buga uban tagumi, kowa da lissafin da zuciyarshi take yi, na hanyoyin da zamu bi auren ya wargaje kafin ranar daura shi. Sai da Sa'adatu ta iso tana rike da hannun danta sun sha kwalliya sai walkiya suke yi. Hajiya sannu da zuwa, suka soma gaishe ta tana amsawa a lalace, a wulakance na zuba mata ido ina kallonta. A zuciyata ina tambayar kaina dama yarinyar nan ta iya yi wa mutane irin wannan wulakancin r ni ban sani ba? Wai ita matar me kudi ko? To bari Ana gama gaisuwar ta mike ta nufî can cikin daki ta bar mu, don haka muka ci gaba da tattauna al'amuranmu irin masoya sai gata ta sake fitowva fuskarta a murtuke kai duk ku watse ku bar gidan nan ko kuma in kira Yaya Ado in gaya mishi 121 abinda naji kuna tattaunawa a kai. A fusace na ce mata, ke Sa'a za ki ci mutuncin mutanena ne a gabana? Kina hauka ne? za ki kawo min iskanci ne da rashin kunya? Nan da nan ta kama kuka haba Anti, kishiya musiba ce? Da in za' ayi miki ita sai ki birkice ki fita hankalinki ki tara mutanen da zasu yi miki karya? Su wacece bata da kishiya a cikinsu? In kura tana maganin zawo tayi wa kanta mana, kin san ki ga yawa wani gaskiya ya ji amma in gaskiyar tazo kanki ba za ki iya aiki da ita ba? Na wanke Sa'a da mari mai kyau saboda maganganun nata sun zama rashin kunya a wurina. A'a-a'a to mu kam barî mu tafi, su Ruwailah suka soma zare jiki suna shiga suna gaida Mama daga can kuma sai su wuce, ta sake kallona cikin natsuwa ta ce min. Sai dai kiyi hakuri Anti, ko kuma ki mike kiyi ta dukana amma zan gaya miki cewar wannan kishin naki bai dace da ke ba, don kuwa yafi kama da kishi irin na jahilan mata, ba matan da suka karanta addini suka san shi ba. Ita kaddara yarda da ita ai sharadi ne na cikar Imani, kaddarar kuma wacce ka ke so ne da wacce ba ka so, kan ayi miki kishiya ai Anti Aliya aka fara yi wa ba kya nan ne lokacin yasa baki ga bukin 122 da muka yi ba ita irin kishin Innarmu take ji ke kua kina yin irin na Mama. Na kalli Sa'a cikin tsananin fushi na ce, ranki zai 6aci fa, ta ce kiyi hakuri. Ado ya shigo, Sa'a tana ganin shi ta soma murmushi, Yaya ashe kana gida? Ya ce, mata eh, yasa hannu ya dauki danta ya rungume a jikin shi, me yaron nan yake ci ne haka? Ta taya shi murmushin da yake yi ta ce ai shekaran jiya naji Barisster yana cewa wai wannan yaron irin Baba Yahya zai yi. Ado ya kyalkyale da dariya ya ce, ina ruwan Super D. Ta gaishe shi cikin ladabi tana tambayarshi yaya ashe hidima tazo? Bai amsa ba ya dan kalle ni kun tattauna ne da yayar taki? Ta ce uh uhn ai ni ba wurinta nazo ba, ba ita nazo wa bukin ba. Ni ki ka zowa kenan? Tayi maza ta ce mishi eh, ai shi yasa nazo da wuri don in akwai wani abin da za'a shirya mishi sai a shirya. Dadi ya kama Ado ya ce to muje wurina mana ki sauka a can ai akwai daki, kya so ki zauna a nan? Ya mike ya daukan mata danta ita kuma taja jakarta suka tafi, ina kallonta sai da ta shiga wurin Mama ta dade kafin ta fito ta shiga wurin nashi, a zuciyata nace lallai Sa'a ba karamar mara mutunci ba ce, amma barta ni da ita ne. 123 Daga can nesa ne kawai nake hangen Sa'adatu da irin kaiwa-da-komowan da take yi tsakanin wurin Ado, wurin yara, da kuma na Mama da ma kuma ita din aminiyar yara ce. Amma ni ko kallon wurina bata yi, sai mamakinta nake ji wato ita wannan saboda Ado abokin mijinta ne shi kenan ta koma bangarenshi kenan? Wajen karfe hudun yamma sai ga Hajiya Aliya da 'ya'yanta guda biyar maza biyu mata uku da kannen mijinta biyu yan mata ya'yan amaren Hajiya Kubrah. Tana ganina ta kalle ni ta ce yaya haka Anti? Nayi murmushi na ce babu komai Aliya, me ki ka gani? Ta kalli 'yanmatan da tazo dasu har da ya'yan nata ta ce wa Umahmah da tazo gaisheta kuje tare ki kuma maida su yan gida tayi murmushi ta ce Inna ai ba baki ba ne ta ce eh amma ki kara, suka tafi. Sa'adatu ta hauro saboda ganin zuwan Aliyan, na gaya mata abinda Sa'an tayi tun kan Sa'a tayi magana Aliya ta kalle ni ta ce haba Anti, in ki ka ce haka za ki yi ai mu da uwarmu ki ka tozarta babu irin mutanen da ba mu tarawa yaya Ado a gidan nan ba sanda yayi hidimar Sa'a ya kuma yi. mana goma shatara ko ma ashirin da tara ta arziki. 124 Sai kuma yanzu hidima tazo kan shi zai yi kice za ki tsuke fuska ko ayi tashin hankali da ke?2 Gaskiya ba ma ciki, shi kishin mafi ba yanda ki ka ga na gidanmu yake ba, ki kama mijinki kawai ki rike gam a hannunki, ba wai ki rike shi a jiki ki hana shi zuwa wajen wata matar ba. Ki hanata hadakinta a'a ki bar mishi jikinshi yayi ta yawo yaje wurinta ya ji dadi yayi abinda yake so ya more, Ubangiji ne ya halatta mishi ita, amma ke kina rike da zuciyarshi in da duk yaje yana tunawa da ke in zai yi magana sunanki zai ambata, in zai fadi alheri naki ya sani. Sannan ko mu yanzu a gidan namu ba ki ga yanda Inna ta maida gidan ba, Zubaida da 'ya'yanta ai basa gabanta, tuni ta sake hada girkin gidan tunda Mama ta fita ta bar musu gidansu ke. baki ga yanda Baba ya yi gwanin kyau ba? Sa'a ta ce a to, shi Yaya Ado ma ba zai takuru ba tunda ba ki ga abinda ke cikin wurin nashi ba wal kawai in kin ganshi sai kin yi mamaki, gashi kuma naji yana maganar kayan daki ina jin shi ne mai yi. Na ce to ba gashi ba tun ba a yi auren ba zai fara zalunci. Aliya tayi maza ta ce zalunci anti? Yanzu ke akwai wani abinda Yaya Ado zai yi waa wata mata ki ce ya zalunce ki? 125 Sunkuyawa fa yayi ya yi noma yana yarfe gumi ya tara kudin ya biyawa umarmu kujera taje ta sauke faralinta, bayan nan ki ka biya mata da kudin aikinki, yazo ya mallaka miki gonar da a yanzu duk shekara ki ke kaita Ummura da watan Azumi kin kai Baba kin kai mai babban allo. Ba daga gidanmu ki ka zo da gonar ba sannan in kin manta in tuna miki ba ki zo gidan shi da kayan daki ba, kuma in ba ki sani ba in gaya miki ba fa tsoronki yake ji ba. Yana jin kunyar ki ne saboda kin yi sa'a yana sonki yana kuma ganin darajar iyayenmu, to taimake mu ki bar shi a haka kar ki kure hakurinshi don ko su Ahmad da suke 'yan uwanmu ne in suka balle hancin tsiya ba dadinsu ake ji ba. Sa'a tayi mazá ta ce, na dai gode. Ado ya shigo daga waje da sauri da alamar yaga zuwan nata, Hajiya Aliya ashe kema kina tafe tun yau? Ta ce eb, Inna ce ta roke shi ya bar ni in zo da wuri don in kawo maka wannan sakon. Sako? Yayi tambayar cikin tunani, ta ce eh, tayi maza ta jawo katon akwatin da ta zo dashi wanda nayi zaton kayanta ne da na ya'yanta a ciki, tana bude shi ta soma zaro atamfofi tsala-tsala duka super guda shida, manyan lesuna hudu da kuma shaddoji masu tasa guda biyu. Tana gama zaro su ta ce wai in ji ta a kawo maka 126 ka zuba akan na lefe. Wani irin matsanancin dadi ne ya kama Ado, a hankali ya nemi wuri ya zauna a bakin kujcra cikin natsuwa ya ce, Aliya, tayi maza ta amsa na'am Yayya, ya ce mahaifiyarku tana da girnma a wurina, saboda ita din wata irin mata ce da samun irinta yake da wahala. Ina matukar girmamata sbaoda halayenta na girma da mutunci ga ta da adalci ga na kasa da ita, amma Humairat bata gane abin da nake nufi ba. Naje na same ta ita da mai babban allo nayi musu maganar zan yi aure amma ina so suyi wa Humaira magana don bana son matsala a cikin iyalina. To kan akai ga hakan ga Mallam babu shi, ni kuma a yanzu ba zan je in kai kararta wurin Inna ba, zan bar Inna kawai tunda nasan ita bata manta mahaifinta ya rasu ba, kamar yanda ita Humaira ta manta. Aliya tayi maza ta ce, itama bata manta ba Yaya, ya ce ta manta tunda ta bude baki ta zage ni ta ce in tuna mata da adalcin da na taba yi mata don ita bata san shi ba. Aliya tayi salati ta ce, in ita ta mantra su mu ba mu mance ba, ba kuma zamu mance ba. Amma maganar zagi kar ka rinka fada yaya, ya ce kar in ce ta zagen Aliya! Ta zagi Mama a gabana ta kuma durawa ya' yana ashar a gabana? 127 In haka ake karatu zan barta tayi ta zaryar makarantar addini? Aliya ta ce ai matsalarmu kenan yin aiki da abin da muka sanin gashi kuma kullum ana gaya mana cewar mu mata babu abin da yake saurin kai mu wuta irin kafurcewa ni' ima. Amma kayi hakuri ya ce to yaya zan yi? Alamar dai ranshi ya baci sosai da abinda nayi mishin. Gaba daya 'yan uwana har Atika da ta iso bata goyi bayan yanda naso mu yiwa bukin ba, itama cewa tayi mutuncinmu zamu zubar, don haka rungumar hidimar suka yi da hannu bibiyu suka kankane komai, wanda ba haka Mama taso ayi ba. lta taso ne a warc ga 'yan uwan Ado da nawa sia ita ta jagoranci hidimar Ado sai taga ba haka ba ne. Dangin Inna da na Babana da suka zo min bukin ba za su lissafu ba, su Habiba da Anti Kaltume ma muna hade dasu, Sha'awa da Suwaiba ne suka koma wai su suná dangin miji. Ga kawaye na zamani, kawayen da aka yi bayan daula ta sau, don haka hidima sosai aka yi. Kane-kanen da Sa'a tayi kan hidimar Ado ba karamin taimako ko amfani yayi min ba, ba don ina ganin kO za a zarce ni da wani abu ma to ba wani mai yawa ba ne sai dai duk da haka zafin yana nan a can ciki zuciyata tafasa take yi. Wani lokaci ni da kaina ma mamakin kaina nake ji, saboda a farkon rasuwar mai babban allo na dauka 128 babu wani abin'da zai sake samuna in ji zafinshi, sai gashi maganar auren Ado yayi min wani irin dukan da ya kidimar dani. Ya mantar dani wast abubuwa masu yawan gaske, kai kishi al'annsrin shi yana da girma, sai dai kawai hakuri. Tsananin batin rai ne yayi min yawa, bakin ciki ya addabi 2mciyata. yayi dalilin da ya sa na kame bakina na kulie shi nayi shiru na daina fadin komai in ban da 'la'haula wala kuwata." Hidima irin wacce Ado yayi tana da yawa, wane ta bukin Sa'adatu, da nake ta bada labari, iyaka dai kawai na sani ko da nake wurina a kammale 'yan uwana su Habibah su Aliya, Atika, Anti Kaltume, Sa'a sune suke tsarc da komai. Anyi daurir aure an kuma ce min har sü Babana da su Baba Yahya da su Alhaji Maikudi duk sun zo wa Ado daurin auren. Da daddare kúwa ana idar da Sallar Magariba amarya ta iso, duk wacce taga amaryar sai naji tazo tana fadin kai mazan nan sai fa a bar su kawai, ban dai san me suka gam ba. Sannan koda nasan gidan Mallam Haruna da iyalinshi na kasa gane ita wannan yarinyar da aka ce wai sunanta Balkisu, saboda ni nafi sanin uwargidan gidan Hannatu da 'ya'yan dakinta. Wannan kuwa an ce yar amaryar gidan co Mamya wacce ko gaisuwa da ita ban cika yi ba, don ba 129 kasafai ka ke ganinta a waje ba. Taro ya tashi, Jama'a sai iatiya suke tayi saura wadanda suka rage saura kadan Hajiya Kubra ta shigo wurina tana murmushi, yau uwarki har da goggoro ta daura. Nayi maza na tambaye ta wacce a cikin iyayen nawa? Ta ce wacce uwa ke gare ki da ta wuce Mama? Na tsuke fuska na ce Mama kuma Hajiya? Tayi maza ta ce eh, ita uwarki ce kar kuma ki yarda ki biye mata akan komai. Kiyi hidimarki kawai, wannan yarinyar kuma kar ki yarda kuruciyarta tasa ki zalunceta, shi kuma mijinki ki kara mutunta shi don ki karawa kanki girma da daraja albarkar 'ya'yanku ma ta karu, na ce to Hajiya na gode. Dare yayi babu kowa a gidan, ina kivance kan gadona tun bayan fitar Ado daga dakin da yazo yayi min sai da safe, ban iya motsawa na tashi naje na kulle kofar tawa ba, sai kallon agogo kawai nake yi ina lissafin cikin zuciyata a sanin halin Ado da nayi yanzu ya gama kaya ne yana yin kaza. Ina cikin haka ne kawai naga yarinya ta fado min daki da gudu a firgice kwarai take, tayi matukar tsorata da abinda ta gani, tsallake ni tayi ta wuce can bayana ta makure wuri daya. Na waiwaya na kalle ta, 6ari take yi kar-kar-kar daga ita sai yar wata lalatacciyar shimi ne a jikinta, 130 ga nonuwanta nan ba suma karasa fitowa sosai ba, Yarinya ce 'yar karama da ba ta wuce shekara sha hudu zuwa biyar ba. Kamar dai ace sa'ar Umahmah, kyakkyawar yarinye don kuwa zafin kishinta bai iya rufe min ido ya hana'ni ganin kyan nata ba. Na tuna sanda dima. nawa nonuwan suke kamar nata.. Cikin zuciyata na co, kai lalle Ado! Ado nabaiji ne, yau ne na gane me yake nufi da yawan ambaton kanshi namiji da yake yi, sai gashi ya shigo yana daure da rigar baccin da ke jikinshi da belt Muna hada ido dashi ya sakar min wani lallausan murmush, a zuciyata na ce shi ma yasan ya cuce ni, ya gama de ni. To zomarna Humaira, ya juya ya fita ban yi jayayya da shi ba na bi bayanshi zuwa tsakar gida dan fito min da yarinyar nan sai ki auro kofarki, ki kulle, ai dare yayi me ki ke yi har yezu idenki biyú? Na harare shi na çe, kai vie ka,ke yi? Yayi. murmushi ya ce to naji fito mii da ita don kin ga na riga nayi niyya zan shiga dakinta. Na ce toai bani na kawo ta ba, ka shiga ka dauke ta mana. Cikin natsuwa ya ce ina jin kunyarki ba zan iya ba, shi yasa nake so kiyi in adalci ki bani ita. Na wuce shi naje nayi kwanciyata gabana sai faduwă yake yi, kar dai Adó ya shigo min dakin nan ya ce zai fitar da yarinyar nan don ban san abinda zai faru ba. 131 Sai aka yi sa'a har gari ya waye bai shigo ba, sai dai kuma in bata jin zirga-zirgar, shi nayi zaton ko lemon tsami yake nema da jar kanwa bai samu ba. Washegari da safe na kammala abin da zan yi na sallah da jan carbina na mike zan fita don shiryawa yara abin karyawa da tafiyarsu makaranta. Sai na kalli Bilkisu na ce mata ke je ki đakinki kin ji, yanzu ba zai zo miki ba balle ya taba ki tunda gari ya waye ta ce min to. Tuni su Nusaiba suna kicin suna kokarin kammala komai, don sallamar kannensu kafin suma su sallami kansu, saboda sun riga sun saba ko ban fito ba ba za su yi komai don haka ina shiga akan kammala suka gama suka tafi. Suna fita suka bar gidannan sai kawai na hango wucewar Ado zuwa dakin yarinyar nan kan kace meye wamnan sai kawai na jiwo ihunta akidime. Jikina ya rinka rawa nayi matukar kidia na gigice na rinka jin tanfar wani abu yana yi min yawo a jiki, ya rasa hanyar fita, waiyo! Wayyo!! Wayyo!!! Abin da kawai nake fadi kenanz uwa can nayi sa'a wani tunani yazo min na bar waiyo na koma 'lahaulah'. Ban san tsawon lokacin da na dauka ina cikin wannan kidimar ba, sai kawai na ji ni jike sharkafda gumi, na mike naje nayi wanka na yiwo alwala nayi nafila raka'a hudu nayi addu'o'i na shafa na zauna gaban madubi ina shafa mai ina kallon kaina a 132 madubin. Ko da bani da nonuwa a tsaitsaye i din kuma ba zai yiwu ace Ado zai yi wuju-wuju dani ba, a cikin ganiyar kuruciyata nake na kuma riga na zaina mace mai daraja wato dai mata irin na zsmani da kana ganinsu ba sai an tsaya yi maka bayani ba. Don baka na tsayarwa raina da cewar da wuni in wani ya ce bai sonka to lokacin ne wani kuma zai ce shi da kwana yake kaunarka, don haka ba zan lamunci irin wannan matsanancin bakin cikin ba daga gare shi, don zai iya nukurkusani ya karya min zuciyata. Kwalliya sosai na tsaya nayi ba don komai ba, ba kuma don kowa ba sai don in tabbatar wa kaina cewar kuruciyar da nake kirawa kan nawa tana nan. Daga ido nayi na kalli agogo da nufin in ga lokaci don fitar da nake son yi in bar gidan ya gama abin da yake a dakin ya fito bai same ni ba, sai kawai naji gabana ya fadi Sha daya da rabi ne lokacin dora abincin ranar gidan yayi, gashi mai girkin bata zo ba, na ce tay1 hutun kwana biyu don ta huta wahalar hidimar da aka yi kenan, in har ban tsaya ni nayi girkin ba yara za su dawo gida basu samu abin da suka ci ba. Kan haka na fito na shiga kicin na soma aikina abincin gidana bakina da zuciyata basu daina ambaton lahaula' ba. 133 Duk da ban shiga kicin din don kowa ba sai don yaran da nake gudun kar su dawo gida basu samu abincin da zasu ci ba, ban kuma iya yin girkin yaran kawai na fita na bar sauran mutanen gida ba. Don ban saba ba, ba kuma zan iya barin iyalin gidana da yunwa ba, don haka sai kawai na shiga aikin girkin sosai, gefe daya ina yin dafaduka mai hade-haden kayan lambu gami da naman rago a ciki. Daya gefen tuwon shinkafa ne miyar agushi, wanda nima shi nake sa ran zan ci don in rage matsananciyar ramar da nayi a kwanakin maganar aurennan zan ci abincin girki na kwana biyu. Na sake yin farfesun kayan ciki da na yi wa hadi sosai na kuma yi na kaji saboda Balkisu, a dalilin nanata min da zuciyata take yi cewar ita yarinyar bata yi min komai ba, bata da wani laifi a wurina, ba ita ta kawo kanta ba, ba ita taga mijina ta ce tana so ba. Sannan kwata-kwatanta bata wuce Umahmah ba, ashe kuwa ko don Umahmah ta samu wadanda zasu yi mata adalci a rayuwa zan yi wa Bilkisu. Na hangi fitowar Ado daga dakin ban san sanda bakina ya ce mishi dan iska ba, sai da na tuna mijina ne nayi maza nayi tayin istigfari. Yara suka shigo da gudu suna murnar ganina a kicin din su, na shiga zuba musu ina mika musu da kananan na fara kafin na is kan nmanyan. Ado ya shigo ya same ni ina magana da su 134 Umahmah dukansu saboda na lura in ba yi nayi da gaske ba shiga za su yi cikin lamarin da ba nasu ba ne, suyi kane-kane. Babu wani zumudin bukin da suka yi sai ma da Sa'adatu tayi musu kaca-kaca ne suka je suka yi kwalliya. v Nusaiba ai kun san Babanku yayi aure ko? Hindu ta ce eh Goggo, amma ai mun girmeta ma, na rage fara'ata na ce uwarku ce, ko kun girme ta zaku girmamata don matar Babanku ce, balle ma ba ku girme ta ba, za dai kuyi sa'anni ne kawai. a Ina maganar ina zuzzuba musu farfesun a kwanuka daban-daban ina ajiyewa, ga kuma abincin shima duk na zuba musu shi na sake bude oven na dauko wata katuwar kaza da na yi wa gashi na musamman na hada na sake jawo flask na cika da ruwan tea mai citta na ce ku diba kuje ku same ta bakuwa ce ku sata taci abinci ta kuma sha tea suka ce to, suka diba suka tafi. Ado ya matso kusa dani, nawa abincin fa? Ban iya yi mishi magana ba, na dauki na Mama na tafi wurinta sai da nayi sallama sau biyu bata amsa ba, nasa kai na shiga tunda nasan tana ji na. Sannu Mama, ta ce yauwa sannu kadai, ta bude ido sosai tana kallon irin kwalliyar da nayi, na zauna ina bata abinci, Ado ya biyo ni yana tambayata ina abincin shi? Kan in yi magana Mama ta ce mishi har 135 ka fito daga dakin amaryar ne? Shima bai amsa ba balle ni, to kaima kenan ana jin haushinka ba a baka abinci ba to balle kuma ita wannan aure ai fata dai kawai Ubangiji yasa ba asarar dukiya aka yi ba, tunda ban ga alamar yayi wani tasiri ba. Na fito daga dakin Mama na dawo nawa nayi maza na dauki gyalena zan fita, sai ga Ado ya shigo ina za ki Humaira? Maimakon in tsaya gaya mishi inda zanin sai kawai na soma yi mishi kuka. Kuka kuwa mai tsananin gaske, saboda bakin cikia shi ya ishe ni, kiyi hakuri, hakuri yake ta bani sai da ya ga na dan natsu sai ya ce min ban fa yi miki wani aibu ba Humairah, ban kursa zalunce ki ba, ba kuma zan zalunce ki ha. Saboda ban yi aure don na gundura da ke ko kin ishe ni ba, nayi ne don ina son karawa yin hakan kuma ba laifi ba ne, gode ni'imar da aka yi min nayi Na roi alfuoarki ki ba ni mu zauna lafiya kar kiyi min abin da k: ka san úa car ba kya yi min. Kar ki fita ba da izinina va, zan hakura da komai amma ban da wannan, in ki ka dan yi hakuri da ni kadan nayi miki alkawarin zan yi mai yawa da ke. In ki ka dan kawar min da kai ki ka yi min kawaici na miki alkawarin zan ji kunyarki, in kuma yi ta girmamaki, saboda ke din dama kina da girma a wurina. Yanzu muje ki bani abinci yunwa nake ji, 136 nace ai ya kare, ya sake kallona cikin natsuwa kafin ya ce min Humairah kenan. Kina ganin idan ki ka azabtar dani da yunwa da akwai wata riba da hakan zai kawo miki? Ai yanda ki ka shirya abin da ya dace ki ka tura wa Balkisu tare da yara sa'o'inta don su debe mata kewar zaman gidan su saboda kin yarda bata yi miki laifin komai ba, ba ita ta kawo kanta bani naje na kawo ta. Haka ya kamata ki yarda nima da na kawo ta ba laifi nayi ba, Humairah. Sannan ko da nake ni na ajiye ku dukanku kin fi kowa sanin ina gudun bacin ranki, ina tsoron ganin fushin ki. Ina yin komai ko barin komai don neman zaman lafiya dake, to na roke ki kar kiyi amfani da damar da ki ke da ita a kaina don ki kuntata min ki hana ni morar halal din da aka halalta min. Kalaman nashi suka dan sani natsuwa, naje na dauko daya kazar da na bari a cikin oven din na kai mishi falonshi tare da ruwan matsattsen lemo, to zauna mana na ce mishi IRa zuwa na dawo wurina ina shiga wayata na dauka saboda rurin da take yi. Gabana ya fadi kar dai wani laifin aka je aka cewa Inna nayi take nemana? Jikina a sanyaye na Soma amsa wayar tata, sai naji ta ce min, taro ya tashi lafiya? Na ce lafiya Inna. Ta ce, to Ubangiji yayi miki albarka, ke da zuriyarki, ya saka miki da alheri, ya kuma baki 137 hakuri da juriyar rike girmanki, na ce to amin Inna. Muka dan fara hira da ita har na dan saki jiki na gaya mata wulakanci da cin mutuncin da Ado yayi min, na shiga dakin matarshi da rana tsaka, sai da tayi ajiyar zuciya kafin ta ce min. Kar ki rinka kokarin shiga tsakaninshi da ita, babu ruwanki kamar da ido kawai kan al'amarin nasu kamar yanzu ne kawai sai ki ka zafin shi yana ta raguwa a zuciyarki. Yafi Yafi ace za ki rinka damywa da su ku rinkka samun matsala ke dashi har ita yarinyar tayi wayon da zata gane kina da damuwa a kanta, sai ta raina ki. Kin ga abu ya baci kenan, aa ce haka ne Inna. Muka dan yi shiru kadan sia naji ta nişa ta ce ai kishiya zafi ne da ita, sai kayi hakuri in ba haka ba sia ki ga ka gudu ka bar ladanka. Na ce ai aima dazu ji nayi kamar in gudun, tayi aza ta ce kar ki fara ai gidanki ne kiyi mata adalci, kawai Ubangiji zai hore miki zama da ita na ce to. Dama Inna ta bani sosai na in saki jiki in yi magana da ita. Magana kuma ba irin ta uwa da 'ya ba kawai, a'a har da zancen kawa da kawa aminan juna tana yi min magana in muka soma gaisuwa zata sako min maganar kishi'. Watakila don tasan shi ne babbar matsalata ta lokacin ni kuma da yake na riga na kidime bana iya 138 boye mata zafin da nake ji, in yi tá gaya mata abinda nake ji da yanda zuciyata take tafarfasa in fadi maganganu masu zafi a kanshi. Rannan ma dai da'yake na riga na tunzura da yawa saboda abin da nake ganin yanayi da tayi min wayar ce mata nayi, kai ni kam Inna to me zan sake yi da Kawu ne kuma? Me zai sake yi min in ga ya burge ni kuma a rayuwar nan Inna? Ai ni kwata-kwata gaba daya ya riga ya fita kaina babu abinda na tsana irin in ga wulgawarsu ko in ji maganarshi balle in gan shi ya shigo in da nake, sai in ji kamar in mike kawai in rufe shi da duka in yi ta duka. Dariyar da tayi ne yasa na katse zancen nawa, nayi shiru, me yayi miki da zafi ne haka Baban Umahman? Na dan yi murmushi saboda jin sunan da ta kira shin na ce bare-barenshi ne yayi yawa Inna. Ba ki ga irin rawar jikin da yake yi akan yarinar nan ba, shi yasa ma na ce ni kam ko ya sake dawowa wurina ba zan sake sauraronshi ba, tunda dai abin nashi haka ne na hakura dashi na bar mata shi na yafe, suje can su karata kawai To in ki ka yi hakd ai ba kiyi mana adalci ba, nayi maza na ce kamar ya ya Inna har da ke a ciki? Tayi murmushi ta ce, dani kai tsundum a ciki, ke din ai tanfar uwa ki ke a gare ni a yau, zaman lafiyarki da kwanciyar hankalinki a gidan aurenki yana nufin 139 al'amura masu yawa a gare ni, don nasan shi ne kwanciyar hankalin 'ya'yanki. Ni nasan babu wani bare-baren da rawar jikin da zai yi akanta da har zai tsole miki ido, in ba kin bar abin da yake gabanki kin maida hankalinki a gare su ba. Me zai mata ya kai wanda ya yi miki? Ai babu shi, maganganu masu dadi tayi ta yi min har dai na ahkura na yarda da cewar wai duk abin da yake yin bai kai wanda ya yi min ba, amma ni kam in ban da Innan ce ta gaya min haka da ban yarda ba. Don gani nake tanfar babu ma in da aka taba yin irin abin da shi yake yi din. A haka sai gashi ya dawo dakin nawa, kashedin da 'Inna tayi min na cewar matukar ba-shi ne ya kawar da kai daga gare ni ba, to kar in bijire mishi dashi nake shirin yin aiki. Don haka nake ta fatan shi din da kanshi ya fita hanyata tunda ni kam a yanzu nafi so ya bar ni kawai. Zo nan kiji Maman Umahmah cikin zuciyata na ce wani,wayon zai yi min don kuma ya kan kira ni Maman Umahmah ne a irin lokutan da yake-ganin tanfar al'amura suna shirin cabe mishi a tsakaninmu. Ai babu wata amaryar da zata yi irin amarcin da ki ka yi a hannuna, Humairah ke ce fa, ya. soma lissafo min alarmura masu dadi da suka gudana tsakanina da shi a lokacin amarcin da muka yi sannan ya kalle ni ya ce to a yanzu wanne nake iyawa a ciki? 140 Sannan ke ce Humairah da na kamu da sonki sai na iya tsayawa na nunawa kowa har da wadanda bai kamata in yi musu wannan tsaurin idon ba, cewar ke din ke kadai nake so, ke kadai nake bukata. Zan kuma iya barin kowa saboda ke a yanzu wa zai sani in yi irin hakan? Ado ya soma lissafo min al'amura da tun ina jin shi ne kawai har ya soma sani murmushi har ya sani na hakura na fidda komai çikin raina nasa hannu biyu na karbi al'amarin aurena. Shi da kanshi Ado ya fahinta tare da sanin cewar Inna tayi tasiri mai yawa a cikin harkar zamantakewar rayuwar aurena dashi da kuma amaryar da yayi, don haka kullum a cikin girmamata yake, kullum kara ganin mutuncinta yake yi. A kullum kuma in ya bude baki zai fadi wani abu game da ita, to alherinta da karemcinta gami da adalcinta ga suruki shi ne abinda yake bayar daa labarinta akai. Rannan na wuni cikin farin ciki da zumudi saboda Ado ya gaya min zai tafi Abuja gobe, a dalilin hutun da ya dauko ya kare, dadi ya kama ni a Zuciyata na ce zan dan huta da ganin mu'amallarshi da 'yar yarinyar nan da ko kunyar tubewa a gabanta ba yayi, duk da karancin shekarunt. Tsananin farin cikin nawa ne yasa na yi wa Inna waya nake bata labarin da zai yi, sai ta ce min ba da ita zai tafi ba kenan? Nayi maza na ce, a'a shi kadai 141 zai tafi, ta ce to me zata yi miki a gidan ba shi ita kawai ya tafi da ita, ai kawaici yayi miki kin ga kumnà ki sata ta bishi da kanki yafi ace shi ne ki ka kure hakurinshi ya ce zai tafi da itan. Ko ba zai iya yin hakan ba ne? na ce zai iya wanda yafi wannan a ta ce to kin gani. Duk da bana son tafiyar tasu tare na daure nayi abinda Innan ta ce in yi. Dadi yayi matukar kaa shi sai dai ya daure ya hadiye ya biyo ni dakina yana muzurai, to tunda kin ce dole sai an tafi da wannan yarínyar ai sai kije ki ga shirin nata wannan wani shiri zata iya? Na ce mishi to. Duk da ni na ce ayi tafiyar tare da ita bayan tafiyarsu kuka nayi tayi, to ina ga in da shi ne kawai ya zartar da hakan? Bayan tafiyar tasu ne Innan tayi min waya don jin lafiyata, na ce mata sun tafi Inna amma nayi kuka. Tayi murmushi ta ce share hawayenki ki wastsake babu wani abinda zai je ya yi har ya kusa da kusan-kusan abinda yayi miki, ko yake yi miki a yanzu. Na ce Inna kenan, ta ce eh ai gaskiya ce kawai mai ita kuma yana iya yiwa kanshi hukunci. Sai mutum bai cin zamaninshi ya hana wani cin nashi zamanin, ai kin ci naki Maman Umahmah kina a kai tunda me akai da maza? Don haka itarna barta taci irn nata saboda naki zamanin vavi tsawo ya 142 kuma yi karko mai kyau. Amma menene? Me zai je yayi sabo? Wane dare ne jemage bai gani ba? Ai sai na ranar mutuwarsa ke ce fa aka bashi ke yana da shekaru talatin kina da shatara, kin san muhimmancin shekaru talatin wurin da namiji kuwa shekaru ne na kamala da cikar halittarsa. Shekaru ne na ganiyar karfi, shekaru ne na abubuwa masu yawa da ba zai yiwu in yi ta lissafo miki su ba, sannan a wancan lokacin bai da wani nauyi kece ke kadai, bai da wani uzuri sai naki, bai da wata bukata sai taki, bai da wani abinda yake so sai ke gaba daya lokacinshi naki ne, gabba daya hidimarsa taki ce. Ba yanzu da ya riga ya gama mallakar hankalinshi nauyin Jama'a da kuma abubuwa masu yawa suka hau kanshi ban da haka kina ma da wasu darajojin a wurinshi ke kadai ce zai yi surukata da uwarki irin surukutar da yake yi dani ba zai sake yiwa uwar wata hakan ba. Saboda ya riga ya girma sannan ban da wadannan duka sai kuma ki ka yi sa'a ki ka zama kece ki ka zamo mishi uwar Umahmah, ki ka sake zuwa ki ka haifan mishi Baba Yahya. Ko wadannan biyun kawai ki ka tsaya akai ai kin san kin haifi abin da yake so, to balle gasu Zainab, ga Khadija ga Fatima, don haka kar ki yarda ki mance 143 ni' imomin da aka yi miki kije kina sa ido kan abin da bai taka kara ya karya ba. Kullum ki tasa al'amarin ya'yanki a gaba kar ki zalunci dan kowa balle sakaiya ta taba miki yayanki, nayi aza na ce to Inna. Kullum kalaman Inna suna kwantar min da hankali su sanyaya min zuciyata su kara min son ya'yana da ganin darajar su, ba.wai son 'ya'ya irin na rashin kwaba ba, a'a son 'ya'ya irin na hakura da abinda ka ke so ko yin abin da baka so saboda su saboda rayuwarsu ta gaba ta inganta. Kalaman nna ne suka kara sanya ni na yarda na gane na kara hakuri na kara kyautatawa mijinam, ita kuwa matarshi na maida ita tanfar yar uwa bani da wata ita balle in je ina sha'awar zaluntarta, musamman kuma da yake nafi kowa sanin mijin nawa Dr. Ado Sulaiman zai yi min kawaici ya ji kunyata ne ya kuma yi ta girmamani kan abin da yaga ina yi na adalci, amma ba zai taba yarda da zalunci ba. Rannan da daddare muna hira da Inna a waya saboda hirar tamu ta zama ka'ida yanzu kullum sai mun yi, na ce mata ai dazu na fita Inna. Tayi maza ta tambaye ni, ina ki ka je? Na ce robar nan naje na cire, Inna tayi dariya ta ce kishi dai ya motsa kenan, na ce ba kishi ba ne Inna, na dai gaji ne kawai, ta ce ai shi din ne dai. 144 Na numfasa na co mata ni wanne yafi ne cikin biyun nan Inna? Tunda ke su duka biyun kin san yanda suke kin zo kin samu an kuma zo an same ki? Tayi murmushyi ta ce, ni kam a wurina ai dace ne kawai. Tunda ita rayuwar gaba dayanta sa'a ne, na tuna mata da kalaman Mama a da cewar da take yi 'ya'yanta ba za suje gidan kowa ba zuwa za'ayi á same su, tayi dariya ta ce ba gashi ba, kuma da aka zo aka same sun sai aka kore su Saboia sun kasa yin hakuri? Na ce haka ne, ta ce ai babu mai cin ribar rayuwa sai yayi hakuri, na sake cewa haka ne. Mama tayi ta zuba ido tana kasa kunne ko zata ji wate rigima ta tashi tsakanina da Ado, shiru babu wata matsala, saboda yona matukar jin kunyata da ganin girmana a dalilin na yarda da shawarar da ya bani na in dan yi mishi kawaici da kuma kara. Sai kuma hankalinta yayi matukar tashi ta rinka fadin maganganu wannan aure da aka yi ai ba aure ba ne an kawo 'yar mutane an ajiye a gida ana cutar ta. Rannan ina daga falona na ganta ta fito kan keken guragunta, tana tura tayoyinshi da hannunta kofar dakin amarya taie ta tsaya saboda ba za ta iya tura shi yı shiga ba. Ni yarinyar nan ana baki abinci kuwa? Ban ji abinda BilkisD ta ce mata ba na dai ga 145 kawai ta gyada kai ta ce au to, ta juya ta tafi. Ban san yanda aka yi ba, daga tsayuwar bakin kofa tayi magana sai kuma abu ya dawo in ta zo bakin kofar ta tsaya sia ta kira Balkin ta tura ta su shiga ciki. Ni kam ko a jikina saboda da na gaya wa Inna ma abin da Maman take yi dariya tayi ta ce ai babu abu mai dadi a rayuwa irin ka rayu kana addini kana kuma yarda da kaddara na ce haka ne Inna. Rannan sai kawai aka yi kacibis tsakanin Mama da Ado a dakin amarya, shi zai shiga ita kuma z ata fito ina jin shi yana fadin a'a-a'a Mama, ai kin ji sauki tunda ki ka iya fitowa daga dakin ki ki ka zo har nan ai shi kenan magana ta kare. Mama tayi maza ta ce, a'a wane sauki? In ban da karfin hali don in zo in duba wannan yarinyar abincin da ake bata ne nake ganin kamar ba ya isanta, ya ce eh wannan duk ai alamar samun lafiyarki nce tunda gashi har kina iya shiga harkar da ba taki ba ce. Don haka sai ki shirya za ki koma dakinki, Mama ta soma kuka tana bashi hakuri, ya ce a'a aiu ba za ki kasa zaman lafiya a naki gidan ki zo nima ki bata min nawa ba. Dama kwanaki an kira ni a gidan su aka yi min wasu maganganun da nayi zaton da hannunkii a ciki, tun a lokacin na gaya wa Mallam Haruna cewar ni ban saba da irin wadannan maganganun ba. Ban iya yin irin wannan surutun ba na kuma 146 gayawa ita Balkin cewar in aka sake kirana a gidan Su kan wasu maganganun da ban san da su ba zata koma gidansu. To ashe kece Mama, don haka zan kira Baba an jima in gaya mishi yasa ayi miki fentin dakinki ga ki nan zuwa, ai ba rabuwa ku ka yi ba. Na dai kyale ki a nan din ne kawai don na gane ba kya son zaman can din amma ba zai zama dalilin da kuma za ki nemi kulla min fitina a cikin iyalina ba. Mama tayi kuka har ta gaji ta bai wa Ado hakuri, har taji babu dadi ya ce a'a Mama ki koma dakinki kawai ita mace ai bata da wani wurin da ya fiye mata dakin mijinta daraja in kina da matsala kawai ga sabuwar waya nan na saya miki ki kira ni ki gaya min, nima kullum zan rinka kiranki muna gaisawa. A haka Ado ya kammala mata shiri ya kuma sani wai ni da yara muyi mata rakiya na ce mishi to, muka je muka kwana muka dawo. Sai bayan dawowan nawa ne naji labarin wa duk wanda yazo sai ta gaya mishi cewar ni nasa Ado ya kore ta. Bayan kuma ita din ita ce tayi sanadin aurena da shi, amma a yau na shiga tsakaninta da dan uwanta na raba su. Ni kam tunda nayi sa'a Mama ta yi wa dan uwanta abinda ya tattara ta ya maida ita inda dama mazauninta yake, sai naji sakat na samu sa' ida, na gane ashe ba kishiya ce ma babbar matsalata ba, ta 147 rayuwa Mamace to na rabu da ita shi kenan zance ya kare. **. * *. Shekaru biyar ne yau tunda Dr. Ado Sulaiman ya yi min amaryarshi ta farko Hajiya Bilkisu bayan ita ya kara bayan wannan ma ya sake karawa. Don saukin ma su din basu zauna ba can ta bare musu suka watse, kenan in ana sabawa to na saba a yanzu ma naji yana cewa da wata akan hanya. Duk da har yanzu na kasa daina kishin mijin nawa, ban cika jin zafin shi sosai ba, saboda ya riga ya samu daukaka mafi yawancin aurenshi na baya- bayan ba shi yake nema ba, yana zaman zaman shi ne kawai za ki ji an ce Dr. ga wata tsuleliya an baka. Shi kuwa sai ya ce wai mutumin kirki baya maida hannun kyauta baya, don haka nake yi mishi sassauci mai yawa. Amma wai duk da hakan da nake yi in sun fitan sai ka ji su da iyayensu dama Mama suna ta yada zance cewar wai din ni nake hana shi zama da amaren nashi saboda fin karfin da nayi mishi. Iyakar sa'ar da nayi ita ce ni dashi da akwai fahimtar juna mai yawa a tsakaninmu, a duk lokacin da ya ji ana yada irin wadannan maganganun zaunar dani yake yi ya rarrashe ni. Rabu da su Humairah, toshe kunnuwanki kawai 148 kiyi kamar ba ki ji su ba, ni kam ai nasan kaina na kuma san ki nasan kishi mai tsananin zafi da na fuskanta a wurinki, ai wanda ki ka nuna ne akan auren Bilkisu. To ba gashi kin yi mata adalcin da ku ke zaune lafiya tana kuma ganin girmanki ba? Surukuta ce irin ta iyayensu ban saba da ita ba surukuta irin ta zamani wace babu kawaici ko kara a cikinta. Kuma babu kunya balle nuna sanin ya kamata, na riga na saba da surukuta irin ta Inna wacce komai suruki yayi wa 'yarta ba za ta daga ido ta kala ba, sai dai in shi da kanshi ya yi tunani. Kunyar kanshi ya kama shi kullum tsakaninta da yarta nuni ne na alheri bi mijinki, kyautata mishi, kiyi mishi biyayya, saboda girman hakkinshi da yake kanki yawa ne da shi. Bisa wannan dalilin ne yasa har yanzu dai ni da Bilkisun mu biyun ne dai a gidan na Dr. 'ya'yanta biyu dukan su maza, Sulaimañ da Adam. Nima na kara daya da kyar bayan nasha kafirar wahalar da na kubuta da kyar saboda matsalar da na samu da mahaifar tawa. A dalilin kaka ba ihata robar nasara da nàyi don haka ina da mai sunan Babana Sirajo wanda Sulaiman ya girma da shekara daya shima ya girmi Adam da shekara daya. To har yanzu dai itama uwar tasu shuru ban sani ba ko itama ta yarda da hikimar ta 149 maigidan ne na bin tsarin iyali don a samu wadataccen lokacin kulawa da juna. A wannan lokacin gaba daya 'yanmatan gidan nawa su Umahmah, Nusaiba, Hindatu da Aisha suna dakunan mazajensu har da rabo a tsakani saboda Ado yayi musu auren ne da sha bakwai-bakwaj. Sai dai har yanzu suna can suna ci gaba da karatunsu a Jami'o'i daban-daban, shima kuma mai daukan nauyin, shima Baba Yahya yana kasar Malesia ya tafi karatun digirin shi na farko kan aikin zane. Sai su Zainab, Khadija da Fatima sune suke Makarantar secondary ta Marigayiya Hajiya Maryam Babangida, don haka a gidan a yanzu Sulaiman ne kawai sai Sirajo da Adam. Wadanda guda biyun farkon Sulaiman da Sirajo a wurina suke duk inda zani kuma tare dasu nake zuwa, Adam ne a wurin uwarshi. Gonata tayi matukar bunkasa, don' haka a yanzu a shekarun da nake da su guda arba'in mafi yawañcin al'amurana da lokutana da farin cikina kan tafi ne kan abin da ya shafi 'ya'yana, 'yan uwana, iyayèna, gonata, hidimomina, .kwalliyata, karatuna da har yanzu ban daina ba, da wasu abubuwan da suka danginci hakan. Aure-auren da Ado ya tsunduma yi a shekarun bayan nan sun kara fahimtar dani cewar a shekarun 150 mace na girmanta tana bukatar farin cikin abubuwa da yawa da nasarorinsu kafin tata nasarar ta tabbata. Babba daga ciki kuwa shi ne nasarar 'ya'yana ta kintsuwarsu, su kama hanya ta zama mutanen kirki, wannan shi ne gaba da komai a wurinta, sabanin lokacin kuruciyarta da zaman lafiyarta da mijinta kawai ke gamsar da ita har kullum rayuwar Mama kan zame min darasi saboda masu hikima. Sai suka ce wanda duk bai hankalta ya lura da abinda ya samu wani ya zamo mishi darasi ba, to wani zai lura da abinda shi zai same shi ya hankalta dashi ya koyi darasin rayuwa. Rugujewar rayuwar Mama ta rasa farin ciki, kwata-kwata mijinta ya subuce mata, gidan da take gadara dashi ayfi karfinta ya faru nhe a dalilin rugujewar al'amarin ya'yanta har a yau kuma a haka take a zaman hakuri a zaman babu, yanda za' ayi tunda har yanzu ita da Babana dai gasu nan ne kàwai har yanzu babu wanda yasan inda babu yake. Har yanzun su Anti Sha'awa basu wuce zawarci ba, tunda tayi aure yáfi a kirga, Suwaiba sai kwanan nan ta sau wani Dattijo ya aure ta bayan 'bukin su Umahmah daga Giyade matanshi uku ita ce ta hudu. Tana can Giyade a gidan kauye ga iyali wannan dalili yasa ban taba yarda na sa kaina cikin 'damuwar aure-auren Ado ba, balle in rinka daga ido ina ganin abinda yake yi da 'yan kananan matanshi, har in je 151 ina neman in takurawa wani ko Wata. Da na daga ido ni'imomin da aka yi min nake kalla in tuna rayuwata da ta mahaifiyata a lokacin kuruciyata, rayuwar rashin yanci, Kaskanci, wulakanci, rayuwar da uwarmu zaune kawai take tanfar ba matar gida ba ce. Mu ma 'ya'yanta ba a dauke mu wasu 'ya'ya ba, sai gashi a yau duk ya wuce, ina tuna wannan sai in yi ta yiwa Ubangiji godiya, in na ga ma kamar Ado zai yi wani 6are-6aren da zai 6ata min ko ya.daga min hankali a kan wata. Tattara shi nake yi in sa shi a.gefe bana kallon abin da yake sai shi da kanshi yaga kamar abin nashi zai wuce makadi da rawa sai ka ganshi yayi maza ya dawo yana fadin ni me nayi wa yarinyar nan ne nake ganin kamar sha min kamshi take yi tana wani shasshare ni? Ya rinka lallami kenan da kalamai masu dadi, na fa je wajen Inna tana gaishe ki ko Umahmah ta ce kaza, don yanemo dalilin da hira zai yi nisa, sannan a hakan sai in ji itama matar gidan da ake ganin zaman lafiyar tamu tana korafin ai ba shi da wani zance sai nata in ma labari ya zauna zai, baki to ba ki sanin yanda ake yi sai kiji labarin ya koma nata da iyayenta ko da 'ya'yanta. A haka sai na kara fahimtar cewar shi dai namiji mai mata biyu ko uku a tsakani kawai yake, bai cika 152 samun gwaninta mai dorewa wurin guda daya ba, in dai har akan adalcin ya tsaya ba karkata yayi ba. Don haka yana da kyau wata tafi wata hakuri, da kuma dan saurara mishi don a samu saukin al'amura kan haka na sake yankewa kaina hukuncin kara hakuri da mijin nawa a kowane lokaci a kuma kowane hali. Rannan mun ziyarci kasar Malesia ni da shi don kaiwa Baba Yahya ziyara, mun ziyarce shi, a makaranta ya kuma biyo mu masaukinmu don yi mana hira suna zaune shi Babanshi kan kujera guda daya irin zaman da suka saba yi tun yana dan yaro dan karami. Ado yana rungume da kafadar shi yayin da shi kuma ya kwanto da nashi kan kafadar Baban a haka sukc hirarsu, ni kam ina can a gefe kan wata kujerar ni kadai kallonsu kawai nake ina tunani gaba daya Baba Yahya ya sauya ya zama tanfar ba shi ba. Ga wanda yayi shekaru bai ganshi ba, zai yi wuya a yau ya ganshi ya gane shi. Gaba daya ya zube kibar tashi babu ita, tebar shi ta zama kamar ba a taba yin ta ya zama wani -dan dogon saurayi dan sirirn wankan tarwada, kamanannin nashi na yanzu sun fi kama da kamannin Kawu Ado a farkon zuwanshi gidanmu. Hira sosai suka yi da Babanshi tattaunawa suka yi tayi kan karatun nashi da kuma bambancin 153 nomanmu na kasashen Africa da kuma na kasashen da suka samu ci gaban zamani, tunda shima Baba Yahya aikin gonar yazo karantawa. Sai da yaga dare ya fara nisa sannan yayi mana sallama da nufin komawa cikin makaranta in da yake zaune. Ado ya mike ya tsaya yana kallona bari in raka shi cikin makarantar in dawo na ce mishi to a dawo lafiya. Ba mu baro kasar Malesia ba sai da muka kai ziyara wasu manyan gonaki da Baba Yahya ya ba shi shawarar ziyara saboda itama Malesia tana cikin kasashe da Gwamnatocinsu ke bayar da muhimmanci kan aikin gona. Mun dawo gida babu dadewa muka nufi Bakori saboda saukan ruwan saman da aka samu da ya gamsar da noma na soma shukan wannan shekara. Wata sabuwar gonar Ado ya bude a can ta noman masara zalla wacce ba zai yiwu in tsaya in dewatanta girmanta ba, a bisa tsarin da aka shirya kuma za a rinka noma masarar ne sau biyu maimakon sau daya. Ina tsaye tarc da 'ya'yana Sulaiman da Sirajo muna kallon aikin da ake yi Sirajo ya wage baki da karfi yana hamma. Na kalli Sulaiman da ke rike da hannun Bala na ce mishi dubi irin hammar da Kaninka ke yi saboda baka koya mishi ladabin 154 hamma ba. Yayi maza ya kalli Sirajo ya ce mishi, kai ba haka ake yi ba in zaka yi hamma rufe baki ake yi don kar shedan la'ananne ya shiga bakin in da hannun dama zaka rufe sai kasa tafin hannu in kuma da hannun hagu ne sai kasa bayan hannu. Ado ya Zubaida yaron ido yana kallonshi cikin murmushi yayin da Bala ke kallon shi yana fadin ashe Babangidan Malami ne, da kuwa har naji Umahumah tana fadin wai zata zo ta kwashe ku a gaban Goggo don ta lura shagwabarku tayi yawa saboda wai ba irin tarbiyar da aka yi mata ake yi muku ba. Ado ya kyalkyale da dariya ni kam cikin zuciyata tunani nake yi na ranar da Ado ya kawo min Bala da Hamza a matsayin 'yan almajiraina gaskiyar da Bala ya riki Ado da ita, tayi dalilin da ya so shi ya sanya shi karatun boko. Bayan yayi haddar Alkur'ani har daga baya ma ya bashi diyarshi Umahmah bayan ga mutane da yawa 'ya'yan manya shi kam Ado ya ce ai babu wani babban da ya fiye mishi Bala tunda makarancin Alkur'ani ne kuma mai gaskiya ne. A zuciyata na sakefadin babu abin da tafi yawa babba a lokacin da yake zaune da na kasa dashi illa adalci don bai san abin da gòbe zata haifar ba. Kallon Baban na sakeyi cikin natsuwa na ce 155 mishi Bala, yayi maza ya amsa cikin natsuwa da nuna ladabi ya ce min na'am, na ce mishi yanzu a irin wannan aikin da kuke yi a gonakinku kuna da wani- shiri da kuke yi na taimakon kananan manomna? Cikin ladabi Bala ya ce min ba wannan ne asalin taimakon da kananan manoma ke bukata ba Goggo saboda injinan da muke amfani da su wajen yin kaftu kunya da shuka injina ne da suke karawa manomi kashe kudade masu yawa a gonarshi saboda suna tono kasa tun daga can cikinta. Ita kumna kasar wannan da muke takawa tafi kowacce kasa danko da kuma sinadarin da amfani ke bukata, shi karamin manomi yafi bukatar shanun garma, muna kuma bada su bisa farashi mai rangwame har ma mu daga kafa muyi lamuni matukar mun san za'a biya mu muna bada taki bisa farashin da Gwamnati take bayarwa. Haka nan da akwai kungiya da gonarmu ke jagoranta da take karbanwa kananan manoma rancen da babu ruwa a ciki. Ado ya galla min harara alamar muna takaicin shi a zahiri ya ce kai ke ka surukutarki ba irin ta Inna ba ce jeka wurin aikinka kaga abinda suke yi ka ji Engineer Bala yayi min sallama ya tafi. Yana barin wurin na kallo Ado na ce mishi tausayin kananan manoma nake ji Dr. jaruman manoma irin su, Baba Taniu wadanda jaruntakar 156 rayuwarsu ke farewą kan gona guda daya babu wani ci gaban da suke samu. Ado ya ce ch, Humairah ai kin san duk wani abinda ilimi zai yi aiki a cikinshi to kuwa za ki tarar da banbanci mai yawa tsakaninshi da abin da karfi ne kawai jagoranshi. Na cc to in kuwa haka ne Kawu ai yana da kyau kuyi ta janyo hankalin masu ilimin mu na arewacin kasar nan da su dawo su tsunduma sosai cikin harkar noma tunda nikam a wurina banga sana'ar da ta fita riba ba, musamman a wannan lokacin damnu Jama'ar arewa uke cikin halin da muke ciki. Muke fuskantar abinda muke duskanta muke kuma ganin abinda muke gani, gaba daya arewarmu ta zama tanfar ba ita ce arewar da iyayenmu ke bamu labarinta ba ita da shugabanninta. A yau mun zama komai na koma baya namu ne rashin kishin kai namu ne, rashin aikin yi ma namu, talauci ma nau, rashin ilimima namu rashin mafadi ma namu rashin hadin kai namu, rashin tsaro ma namu, rashin zaman lafiya... Ado ya katse ni ta hanyar fadin komai a Humairak, sannan da za'a kama aikin gonan gadan- gadan fa da kin ga anyi magana mafi yawancin matsalolin namu kamar talauci da rashin aikin yi wadannan guda biyun kuma in da za ayi maganinsu. To da sun isa su zama sanadin da za'a sau saukin 157 fitintinu da tashin-tashina, musamman ma da yake ita arewa ai ta taba yi an gani, an taba yin lokacin da kasar nan gaba dayanta ta dogara kacokan kan tattalin arzikin da ake samu a arewa wanda Noma ne. Cikin natsuwa na ce haka fa aka ce kawai Kawu ya dan yi tsaki nuna alamar tsananin damuwarshi da 6acin ranshi kan sakacin damu da kanmu ne muka yi wa kanmu da kuma saki na dafen da muka yarda aka yi mana kafin ya sake sakin ajiyar zuciya mai karfi. Sannan ya ce Ubangiji dai yana kallon komai yana kuma sane da komai ya kuma san dalilin da komai yake faruwa, mu kuma yasan gare shi muka dogara gare shin kuma muke neman taimako muna rokonshi ya taimake mu ya sanya mana sauki cikin wadannan al'amura da suka addabe mu suka addabi yankinmu na arewa. Ya dawo mana da zaman lafiya da duk wani abin da muka rasa albarkar Alkur'anin da muka yi Imani da shi muke kuma karanta shi kullum. Nayi maza na ce amin Kawu. ** A gida a zaune nake ni kadai cikin falona saboda yara suna makaranta, Bilkisu tana nata wurin yayin da maigidan ya nufi Abuja tare da sabuwar amaryarshi mai shekaru sha bakwai, tunani nake yi kan shekaru ashirin da daya na rayuwar aure na da 158 Ado, auren da ya sha gwagwarmaya da kwaramniya iri-iri. Ya fuskanci matsaloli tun daga na iyaye har kawo kan dangi da abokan zama kafin ya tsunduma, cikin matsalar kishi ko in ce kishiyoyi. Wadannan matsalolin da kwaramniyar duka basa iya sani in rufe in mance alheri, jarumtaka da tsayuwar mijin nawa a kaina balle ina daukarshi ina jefa shi cikin mazan da ake cewa wai su din ba 'yan goyo ba ne. A'a, ni kam nawa mijin da na goya shi ban ga komai ba sai alheri har ma nake ganin tanfar da dai ace shi din shi kadai halinshi kan gamsar har ya iya wanke laifuffukan da sauran yan uwanshi kan yi wa sauran mata, to da sai in ce wa 'yan uwan nawa mata cewar ai babu wani goyo mai dadi irin goya NAMIJI. Don kuwa shi namijin ba kowa ba ne face wani cikakken mutum kammalalle, jarumi mai fuskantar kowane irin al'amari da karfin zuciyarshi, mai iya Juyawa daga wani mataki ya koma wani ba tare daa yana waiwaye ba. Mai tarar kowane irin wahala da jaruntakarshi don ya zamo kariya ga na kasa da shi mai sanin ya kamata wanda kuma yake iya saka alheri da alheri. Ni kam a wurina wannan shi ne namiji. Na gode. 159 Mu sake gamuwa dàku cikin wani sabon littafin nawa IN KUNNE YA JI...' Hausawa suka ce wai jiki ya tsira, da ikon Allah zamu sake haduwa daku nan ba da dadewa ba, cikin yardar Ubangijinmu. Kafin nan ina yi muku sallama tare da cewa; (Wassalau alaikum) Allahumma iah sahala illa maja'altahu sahalan, wa'anta taj'alul hazana izah shi 'ita sahalan." Na gode. Hafsat Chindo Sodangi. 17/1/2013 160