MIJIN-TA-CE 2 NA HAJ. HAFSAT C. SODANGI (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) Haqqin Mallaka (m) Hafsat Sodangi Copyright© Hafsat Sodangi GODIYA Godiyata har kullum ga Ubangijinmu take, shi kaxai Subhanahu wata’ala, mai kowa mai komai, Makaxaicin Sarki wanda ya ni’imta al’ummar Annabi (S.A.W) da Wata mai albarka na RAMADAN. Tsira da Aminci su tabbata ga Manzon tsira, Manzon da babu wani bayanshi, Manzon da ya zo mana da Alqur’ani mai tsarki, Manzon Rahama Muhammad (S.A.W) da Alayensa da Sahabbansa da waxanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa ranar Alqiyama. DON MAKARANTANA Godiya mai yawa gare ku makaranta littattafaina na kusa da na nesa, Ubangiji ya saka muku da mafificin sakamako, na gode. GAISUWAR SADA ZUMUNCI Ga Hajiya Asma’u Bello Bala Rabe da Iyalin ta (USMAN XANFODIO UNIVERSITY, SOKOTO) da Haj. Mami Xan Hassan (Maryam), itama da iyalanta. Da Dr. Fatima Ibrahim Khalil ta (Jami’ar Maiduguri), itama da nata iyalan. Da Aminiya Hajiya Iyatu Abba (B.R.C Bauchi), itama da nata iyalin. Na gode, Allah ya bar zumunci, amin. MIJIN-TA-CE 2 N a xaga ido na kalli Inna da hankalinta in yai dubu duka ya tashi, na ce “A’a Inna, to menene na wannan tashin hankalin? Mu bar mishi gidan mana ina ce shi kenan magana ta qare?” Tayi maza ta riqe baki nuna girman lamarin, ta ce “Magana kuwa bata qare ba, yau in da ni kaxai ya ce in bar mishi gida to da ta kwana gidan sauqi, amma budurwa kamarki ace ta bar gidan ubanta a dalilin shi xin da kan shi ya koreta ai ba qaramin al’amari ba ne, vata suna ne ba kaxan ba. Sai ayi ta nanata zancen har ‘ya’ya da jikoki, don haka ina ganin dai to maimakon ayi haka bari in koma kawai in ce mishi ko shi xin zai baki mijin da yaga ya dace tunda ai Mahaifinki ne uba kuma dama yana da wannan damar.” Da sauri na ce mata, “A’a Inna, a’a ni kam gara kawai ki bar ni in yi tafiyata ban san abinda na yi wa Baba ba ya tsane ni, ya tsani farin cikina.” Tayi maza ta daka min tsawa, ta hanyar faxin “Ke kama bakinki, kiyi shiru baka gaya wa Mahaifinka magana ko da kuwa me yayi maka?” Na ce mata “Haba Inna, in ban gaya wa Baba magana ba me zan yi ba shi ya ja ba? Tayi maza ta wafce min bakina da duka abinda ya yi dalilin dana soma kuka sosai. Tun ina yin kukan tana kallona har ta gaji ta soma rarrashina, daga baya ma ta shiga taya ni kukan, muka yi har muka gaji muka yi shiru don kan mu. Na fito tsakar gida zan yi mana wanke-wanke daga nan in yi wanki sai na ji muryar Anti Kaltume a falon Mama alamar tazo gidan kenan, dama kuma su xin don sun zo wuni gida basa zuwa su gaida Inna sai in ta ji muryarsu ne zata leqa ta ce musu “A’a su Kaltume kun zo ne? su ce mata eh, su gaisa. In kuwa lokacin tafiyarsu yayi to in dai ba tana tsakar gida ba ne sanda za su tafin tayi musu sallama to zata shafa ne kawai bata gansu ba sai ta gane sun tafi. Na wanke kunfan hannuna na nufi xakin Mama da nufin gaida Anti Kaltume, don ita tana cikin ‘yan dama-daman ‘ya’yan Mama, tafi Anti Sha’awa yi min adalci sanda nake qarama, sai kawai na ji ta itama tana cewa. “Uh’uh Mama bar mata ‘yarta, taje can tayi sha’aninta ita da ‘ya’yanta, mu ma a nan muyi namu, ai ba a qwacewa uwa ‘ya’ya, Mama ko an qwace su zasu koma.” “Ko zan bar mata sauran dai wannan kam zan tabbatar na riqe ta a hannuna saboda in har na barta taje ta sake, to ba qaramin iya shege zata yi ba.” Nayi sallama na gaida Anti Kaltume, na xan yi ma xanta da take goyo wasa itama kuma sai kallona take yi, tanfar dai wacce bata gama sanina ba, ‘yar gari wato kenan yanzu kin girma kin daina zuwa wurin mutane ko? Nayi murmushi na ce, “Anti kenan, ban fa daxe sosai ba ai ban kai wata biyu ba.” Ta miqo min hannayenta duka biyu alamar daquwa. “Wata biyun ne ba ki daxe ba? Ki zo kiyi min wanki kayan dattin ‘ya’yanki sun taru.” Na ce, “To Anti.” Na tashi na tafi. Ko kaxan bana jin qyashin zuwa gidan Anti Kaltume in yi mata wanki ko ma wani aikin da yafi wankin wahala, saboda ita akwai hikima cikin lamarinta, tunda ta gane ina jin zafin zagin uwata da ake yi a gabana ta yi maza ta daina sava min, Anti Sha’awa da sauran yaran. Ina fitowa daga xakin naji Anti Kaltume tana sake cewa, “Ba fa zai iya da ita ba Mama, wahala kawai za a sha ki bar mata ita suje can su qarata, in taso uwarta ba laifi tayi ba, mu ma duk muna sonki.” Mama tayi maza ta daka mata tsawa “Tafi can shashasha, duk ‘ya’yana sun goyi bayan abinda na shirya sai ke saboda ke dama dole ce tasa ki ka yarda na haife ki in ban da haka da can wurin su kika faxo wani so ki ke yi min?” Komawa nayi xakinmu wurin Inna don ya zama min dole in zaiyane wa Inna irin maganganun da nake ji tunda ga irin furucin da Babana yayi na in fidda miji cikin kwanaki uku ko kuma mu bar mishi gida. Inna ta kalle ni cikin nutsuwa ta ce min, “Haka ne?” na ce mata “Eh.” Ta ce, “To babu laifi.” Tasa hannu ta xauki wayarta ta soma magana da Mamanta Hajiya Kubra, izini take so ta neman mata wurin Babanta don ta koma gida. “Me ya yi zafi haka?” ta kwashe bayani duka tayi mata, ta ce, “To zan yi mishi bayani in ji abin da zai ce, amma kafin nan sai ki sanar da Mallam Yahaya don kar ayi abin da zai ce ba a sanar da shi ba.” Ta ce, “To.” Suna gama maganar, Inna tayi fulashin xin Baba Yahaya, ya kirata shima tayi mishi bayani, ya ce “To ai ba za’a bar gida akan maganar fitar da miji ba, ta fitar mana.” Inna ta gaya mishi gaskiya ai ni xin bani da kowa ga kuma maganar da Ado ya yi wa abokinshi da kuma waxanda Mama ke ta faxi.” Ya xan yi tsaki ya ce, “Bana son ki da irin waxannan maganganun Fatima, bana so in ace ance-ance yana fitowa daga bakinki.” Ta ce mishi “To.” Rannan da daddare sai ga Jamilu xan Amaryar Hajiya Hairan yazo har cikin xakinmu ya shigo ya durqusa ya gaida Inna, ya ce mata ni da Yaya ne, Inna ta ce wannan yaron?” yayi maza ya ce, eh, ta ce to ina yake, ya shigo mana.” Ya ce, a’a yana waje yace ne wai in shigo in kira mishi Humaira. Daga ni har Inna kallon juna muka yi, don mun gane ma’anar kiran, Baba Yahaya ne ya turo babban xan shi sa’an Ibrahim xan Mama na biyu, don shi manyan ‘ya’yan mata ne Salisu su wanda Hajiya Hairan ke kira yaron nan, har su Inna duk suke taya ta shine xan shi namiji babba yazo neman aure na. Salisu yana xaya daga cikin yaran da kullum Babana ke bada labarin natsuwarsu a duk lokacin da takaicin Baba da Ibrahim ya cika mishi ciki, yana shekarar qarshe ne a karatun da yake yi kan harkokin kasuwanci a Jami’ar Abubakar Tafawa Valewa, wato (A.T.B.U). Sannan babu inda Baba Yahaya baya tura shi kan harkokin shi, sannan shine yake tafiyar da al’amuran gidansu gaba xaya, in dai akan yara ne da yake su gidan su babu ruwansu da ‘ya’yan wannan xakin da na wancan gaba xaya abin da suka sani shi ne ubansu xaya to magana ta qare. Bare-bare sosai muka kama yi ni da Inna muna murna da farin ciki, yau na yi saurayi nima gashi an zo ana kirana. To shirya mana ki tafi yana jiranki kuma, na xan yi murmushi nan take kuma kunya ta kama ni. Hijabin dana cire da nayi sallah kawai na sake maidawa na fita. Yana tsaye a qofar gidanmu daga can gefe tanfar dai wani baqo, na xan matsa kamar zan qarasa kusa dashi na kuma kasa, saboda kunya da kuma jin nauyi. Ya xan zuba min ido kaxan cikin yanayin murmushi, shima dai kunyar yake ji ban fa tava zuwa taxi ba, ‘yammata na gaya min yanda ake yi in an zo. Na taya shi murmushin da yake yi na ce mishi “Ai nima ban tava taxin ba.” Yayi dariya cikin wani yanayi da na san dariyar rinjayarshi tayi, ya ce, “Au to shi kenan ki ce min mu duka sabbi ne, na sake taya shi wani murmushin na ce mishi eh, mu duka sabbin ne. Ya ce, to kin gani Humaira dama can mu ‘yan uwan juna ne, ko da Baba bai turo ni yau ba ma aka xaura mana aure aka kawo min ke ai ina zaman kamar zamanmu lafiya zamu yi, to zamu ce auren dole aka yi mana? Na ce, a’a ai ma ba irin tarbiyar da aka yi mana ba kenan.” Yayi maza ya ce “Yauwa, Humaira to na gode miki da ki ka san hakan, to in je in ce wa Baba dai ba matsala kenan? Nayi murmushi na ce mishi, eh, babu matsala ya ce to shi kenan, yasa hannu a aljihun shi ya miqo kuxi zai bani na ce mishi a’a, ai tsakaninmu babu haka, ba sai ka bani kuxi ba, sai da ya kalli kuxin dake riqe a hannun nashi ya saki wani lallausan murmushi kafin ya ce min. Da dai ace kuxina nayi nufin yi miki kyautar da su ki ka faxi haka to da sai in mayar dasu kawai cikin aljihuna in tafi, to amma kuxin Inna ne addu’a kuma mai yawa tayi musu kafin ta bani su. Na shiga xakinta zan yi mata sallama sanda zan taho nan sai ta xauko su ta bani na ce mata a’a Inna Baba ma ya bani kuxin ya ce in riqe na ce mishi don kuxin da zan yi mata kyauta ina da su ba sai ya bani ba, sai ta ce min sa hannu biyu ka karvi waxannan nawa ne in kaje su nake so ka bata. Don haka sa hannu biyu ki karve su daga hannun surukarki suka fitom hannu biyu na saka na karve su tare kuma da yi mishi godiya mai yawa. Habiba ta zo wucewa zata shiga gida, ga alama itama daga wurin saurayinta ta fito, duk da Salisusu ba baqonta ba ne sun kuma gaisa dashi amma bai hanata waiwayowa bayan ta wuce. A cikin gida Inna ta xaure fuska bata so karvar kuxinshi da nayi ba, don haka nayi mata bayani, tayi murmushi ta ce, to miqo min su nan in adana su don basa cikin ire-iren kuxin da kike sayo sabulun wanka da na wanki.” Rannan kwana muka yi ni da Inna muna qus-qus-qus xin mu cikin farin ciki da jin daxi, hirar abotar Babana da Baba Yahaya Inna ke yi min, tana qara gaya min cewar shi kaxai ne abokin Babana tun suna yara da ya qi yarda suyi vatawar da zasu rabu ko ya zo gida an yi kaca-kaca bai hana shi kuma gobe ya sake dawowa. Har irin tsayuwar da yayi kan neman auirenta sai da ta gaya min da ta gama kuma sai ta ce to gashi yau daga kai mishi wannan magana ya turo xan shi kan maganar aurenki, yanda ya rufa min asiri shima Ubangiji ya rufa mishi, na ce amin Inna. Abin mamaki gari na wayewa sai ga Alhaji Tijjani makwabcin Alhaji Mai kuxi shi da Limamin unguwar su sun zo wurin Babana wai sun zo ne a madadin Alhaji Mai kuxi don su nemar wa Alhaji Abba izinin aurena wai da Hajiya Kubra ta yi wa Alhaji Mai kuxi bayanin abin da Inna take ciki da wa’adin da Babana ya bayar lokacin uma Alhaji Abban yaje gidan sia ya roqi mahaifinshi ya turo a tambayar mishi izinin auren nawa. Shi yana sona.” Inna tayi dariyar jin daxi, farin ciki mai yawa ya kama ta, ta xaga hannu sama tayi ta addu’a da ta gama sai ta waiwayo ta kalle ni ta ce min “Amma fa ba zaki canza wannan yaron ba don Alhaji Abba yazo ba duk da shi xin xan uwana ne amma kuma akwai mutunci da ganin girma mai yawa tsakaninmu da Mallam Yahaya, da kuma hajiya Hairan don haka kan Salisusu kawai za ki tsaya, na ce mata to Inna. Ba mu san yanda aka yi ba, sai kawai muka jiwo Mama tana sakin manya-manyan ashar a tsakar gida, tare da faxin “Lalle ana munafurci a garin nan, jiya yaron nan Salisusu yazo yau kuma ga waxannan sun zo, to raba musu ita biyu za ayi kenan ko?’ Mama wai fa don ace tayi farin jini ne, in ji Habiba. Mama taja tsaki ta ce, farin jinin gidan uwar wa? A yanzu ko Samari goma aka turo mata rana xaya ai an yi aikin banza tunda dai turo su aka yi, ban da haka kuma shekara nawa aka yi a gidan nan ana hidimar arziki a kanku ina nunawa uwarta bata tava cewa ga nata ba? Magana kamar wasa, Mama ta shiga kai-kawo mai tsanani, kowane lokaci tana tashe da Babana tana gaya mishi abinda take gaya mishi, sai dai kuma babu wanda yasan me take faxan sai su biyun suka san abinda suke yi. Aike akan aike daga gidan Baba Yahaya da kuma Alhaji Mai kuxi, Babana ya qi ya tanka, rannan Baba Yahaya yazo da kanshi a tsakar gida ya samu Babana, don haka shima a tsakar gidan ya zauna sai da ya gaisa da duk mutanen gidan kowacce ta nufi xkainta, sannan ya kalli Babana ya ce mishi. “Wurin ka fa nazo kan maganar yaran nan.” Baba ya gyara zama ya xaure fuska alamar rashin wasa kafin ya ce, “Ina sauraronka.” Baba Yahaya yayi kamar bai gane abinda yayin ba, ya ce mishi an turo mutane wurin ka daga wurina da kuma wurin Alhaji Mai kuxi da fari ka ce a saurare ka don zaka yi shawara tukunna akai, daga baya kuma da aka sake turowa sai ka ce wai saboda ka raba faxa a tsakaninsu duka ka zartar da hukuncin yi mata miji kai da kanka. Wanene mijin da ka zavan matan? Ai mu dukan mu muna da ‘yancin ka gaya mana don mu ma iyayenta ne ba kai kaxai ke da ita ba, kuma kasan zaka iya zar tar da wannan hukuncin a kanta ma Alhaji menene na bata wa’adi har kana cewa in ba haka ba ita da uwarta su bar maka gida?” Maganganu masu yawa Baba Yahaya ya yi ta sakewa Babana, ya kuma ja ya tsaya akan ba zai bar gidan ba, sai Babana ya gaya mishi mijin da zai ba ni, da Babana ya ga da iyakacin gaskiyarshi yake yi, gashi kuma tuni ya riga ya amba ci ranar bikin matsowa kuma take yi, sai yaga to bari kawai ya fexe komai ya ji ya huta da voye-voyen da yake yi. Ina daga xaki nayi kasake ina sauraron in ji ya ce Nasiru ne abokin Ado, na kuma zuba wa Inna ido ina kallon irin sauraron da take yi, daga tsakar gida sai kawai na ji ya ce, wai Ado ne. A daidai lokacin da Baba Yahaya ke tambayar shi Ado? Ita Inna rafka salati tayi yayin da ni kuma na qurma musu ihu ina daga cikin xaki. Baba Yahaya ya ce, “wannan kuwa shi ne zance, me ka ke so ka yi wa Binta ne Alhaji? Ai kuma dai ba zai yiwu ba don ba zan qyale ka ba saboda kowa yasan in da maganar taka ta dosa da kuma abin da yasa kayi ta. Tuntuni Ado yana gidan nan bai ce yana sonta ba, ba ka yi niyyar ba shi ita ba har ka zartar musu da hukuncin bar maka gida, sai da aka ga masu son aurenta sun zo na gaskiya sai kuma a koma a cuno maka shi ace ka bashi ita don a samu a yi ta sa uwarta baqin ciki? To kun yi kaxan. Ya tashi ya fita a fusace, Mama ta bishi da kallo kafin taja wani mummunan tsaki daga baya kuma ta saki wani lallausan murmushi ta ci gaba da abinda take yi. Ni da Inna hankalinmu yayi matuqar tashi, in ban da kuka babu abin da nake yi, Inna kuwa ta shiga tattara kayanta tana kintsa abinda yake buqatar kintsi alamar kenan in har Baba Yahaya bai yin nasarar hana Babana haxa aurena da Ado ba, to zata tasa ni a gaba mu tafi mu bar mishi gidan. Da yamma bayan Sallar La’asar na shirya na fita gidan Mallam mai babban allo, na tafi na gama rattaba mishi komai yana sauraro yana kuma shan furarshi bai fasa ba, babu alamar damuwa ko wani vacin rai a tare dashi. Bai kuma ce min komai ba sia da na gaji na ce mishi to Mallam kana jina ba ka ce min komai ba. Lokacin ne ya xago kan shi ya kalle ni wani irin lalataccen kallo ya yi min sai da ya gama share furar da ta tava lavvan bakinshi sannan ne ya ce min ba kun zartar da abin da zaku yi ba ne ke da uwarki, ga kuma Yahaya yana taimakonku shi ne ku ka zo ku ka gaya min. To ni meye nawa a ciki? Ba sai ku je kuyi abinda zaku yi ba? Na soma yiwa Mallam mai babban allo kuka yayin da shi kuma ya shiga yi min faxa abinda ya yi dalilin da kukan nawa ya qaru. “Kin tava ganin in da mai Doki ya koma kuturi? Ya ce zai ba da ke ga Ado ace bai isa ba to sai waye ya isa? Sai ku da Yahaya? Haka kawai don kun samu mutum mai haquri sai kuma ace iya shegen da za’ayi mishin har da na wulaqanci da rainin hankali? Ita uwarki ita ta ce miki ta zavi mijin da zata aura? Ko shi Yayanta bai kawo nashi gwanin ba? Na ce mishi a’a ni ga nawa gwanin da nake so a ba, ya kuma bada ita a dole duk da a lokacin auren tsinken zabori ban bada ba, amma na gwada iko na cewar ni ne uba mahaifi. Shi kuwa Alhaji Surajo ke da uwarki kun ce bai da irin wannan ikon a gidan shi saboda shi ba uba ba ne ko? Tashi ki bani wuri, ya yi min umarnin ta hanyar tsawa. Ina miqewa yana magana zata zo nan uwar taki ta same ni, sakarya kawai sha-sha-sha, in ban da sakaryar uwa wa ke taimakon ‘ya bijerewa uba ana karo ne tsakanin qwai da dutse? To in ma cutarku ake son yi sai me? Don an cuce ku, kuma sai me? Kafin ayi muku ba a yi wa mutanen kirkin da suka fiku ba? Bai wuce ba? Abin mamaki itama Hajiya ‘Yar dubu rannan taya shi yi mana faxan tayi, har tana faxin shi lamarin aure ma ai ya wuce duk yanda ake zaton shi, sai dai addu’a kawai, in ban da a gidan ku a ina ake yin haka? Uba ya ce ga yanda zai yi ace wai bai isa ba? Ko da yake ba laifinku ba ne ku kaxai, na shi yafi yawa don shi yayi sakacin da mace tasha gabanshi sai abinda taso yake yi.” Mai babban allo ya shiga yi mata faxa kan hakan da ta faxa, ni kuwa nayi gaba na bar su tunda dai na gane ba goyon baya zan samu ba. Kin yi mishi bayanin kuwa? Inna tayi min tambayar a sanyaye saboda ganin yanda nima jikina yayi sanyi, na ce mata eh, amma dai kar kije. Tayi shiru tana kallona, zuwa can ta ce min shi Baba ba zai fahimci yanda abin yake ba, na ce mata eh. Ilai kuwa rannan dare nayi sai ga Suwaiba ta xaga labulen xakinmu babu sallama babu komai ba tare da ta gaida kowa ba ta ce min, wai in ji Kawu Ado wai kije yana kiranki.” Muka yi shiru ni da Inna, ta juya ta tafi na kalli Inna na ce mata, bari in je in ji abin da zai ce min, ta ce min to. A zauren gidanmu na same shi tsaye cikin kwalliya, sai wani qamshi yake yi tanfar wani wanda ya zo taxin gaske, sai dai ba don taxin yayi kwalliyar ba, xabi’arshi ce yin hakan don a yanzu ko Babana bai kai Ado sanya yadi mai tsada ba, muka xan yi shiru kaxan na xan wani lokaci kafin na kawar da shirun ta hanyar tambayarshi. “An ce kana kirana?” ya ce min “Eh” na ce to lafiya? Ya ce, qalau, taxi zamu yi. Na sake kallon shi a sakarce na ce taxi wane iri? Ya ce taxin aure, na ce to muyi in ji, ya ce ai gashi nan muna yi.” Na gane shima irin zuwan da nayi shima shi yayi, don haka sai na ce mishi Ado, ya ce Humaira, na kawar da duk vacin ran da nake ciki don in samu gaya mishi abinda zan gaya mishi, na ce mishi yanzu nan kai idan aka baka ni aka ce ka aura sai ka aura? Cikin natsuwa ya ce min qwarai kuwa, na sake zuba mishi ido ina kallonshi na ce mishi saboda me zaka yi hakan? Saboda baka jin kunya? Saboda baka jin tausayi? Saboda ba ka damu ba kai kayi ta taimako ana yin cuta? Ko kuwa saboda me? Cikin natsuwar shi ya sake cewa, saboda ni namiji ne, na sake tambayarshi saboda kai namiji? Ya ce min eh, na ce mishi to babu laifi to amma zan aike ka wurin waxanda suke saka kana yi, waxanda suka turo ka kazo ka aureni, don ku qara cutarmu saboda duk abinda ku ka haxu kuka yi mana ni da uwata bai ishe ku ba. Ka gaya musu ni na ce wannan karon ba za ku yi nasara ba, don ba zan qyale ku ku sake sanya uwata cikin wani vacin ran ba. Don haka in har zaka ji shawarar da zan baka to kayi maza ka ce musu ka fasa ba kaso, don kar suyi dalilin faxawar ka cikin wawakeken ramin da ba za su iya fiddo ka ba. A hankali ya ce min, babu komai don an yi hakan na ce to shi kenan, na juya zan shiga gida, ya ce to tsaya ai da sauran bayani, na ja na tsaya ina kallon shi menene bayanin? Kuxi ya ciro ya miqo min dunbus a hannunshi ya miqo min tare da faxin kuxin taxi zan baki. Sai da na kalle shi na kalli kuxin sannan na sake kallonshi na ce mishi ai baka da su, baka da ko kwabon da zaka bani in karva, don duk wani abin da kake dashi kake barazana ka ke wani menene? Na ubana ne, sannan ina so in sanar da kai don nasan komai hatta asara-asarar da kake cewa an yi da kuxin kujerar Innata da aka baka kaje ka biya mata kujerar Hajji kaje ka dawo ka ce kayi sujada an xauke kuxin sai daga baya kai da Mama kuka ce kun je qauye kun sayar da gonakinku na gado ku ka sai gida. Nasan komai.” Ya ce to ai yayi kyau gara da ki ka san komai, ungo kawai ki karva in baso kike kiyi na kenta ba, na ce ai babu komai tunda yanzu dai ka mako na karvi kuxin hannun ka wanke kifi aka yi da ruwan jikinshi cikin dukiyar ubana ka ke fantamawa don haka riqe ka qara ci, na wuce shi nayi tafiyata. Tunda Ado ya kira ni na amsa kiranshi sau xaya ban sake ba, ko a hanya muka gamu wucewa kawai yake yi nima in wuce. Muna cikin haka muka wayi gari Anti Sha’awa da ‘ya’yanta guda uku sun kwana a gida ga dukkan alamu kuma ba lafiya ba ne, yaji ta yiwo don ina jin Mama tana yiwa Babana bayanin dalilin yajin nata, tana faxin wai ka ji min xan iskan mutumin nan mara mutunci Alhaji, Zubaida tana daga kicin ta ce assha surukinne kuma xan iska? Ban kulata ba don har yanzu bana shiga harkarta, gaisuwar safe ce kawai take haxa ni da ita daga nan babu qari, na dai lura kawai na gane ita da Mama sun xan yi tsami sai dai ban san dalilin tsamin nasu ba, kawar da kunnuwana nayi daga sauraron Zubaida na maida su wajen Mama da Babana. Wai ashe aure yake nema ka ji xan iska, ko yaushe ya gama ciyar da na gidan? Oho!. Babana ya xan yi maganar da ban ji ba sia na ji Mama ta soma cewa, ina Alhaji? Ai ma ba zai yiwu ba kar ma ka fara sai ka ce wata mara gata? Ai sai ya zo nan shi da kanshi sai mu ji dalilin qara auren nashi, menene ba a mishi ta ina aka gajiya mishi? Ko kuma dai neman fitina? Ba’a gama kada wata ba ana cewa wata ma ta tuve, ai zamu gamu ni dashi zai gane karon babu daxi in don yaga ina yi mishi lako-lako ne. Haka Babana ya haqura ya qyale Anti Sha’awa a cikin gidan nan yana kallonta ita da ‘ya’yanta har tsaraba yake kawo musu bai kawowa nashi ‘ya’yan ba, tana yiwa kowa kallon uku kwabo sai tayi ta habaici tana faxin maganganu kan aurena da Ado, wai daga rufa mana asiri da aka yi amma muna wani iya shege in ban da Mama ma ai Kawu Ado ba mijina ba ne, don yafi qarfina kamar in ce to aba shi daidai dashi mana nima abar ni da daidai ni sai Inna ta ce min kul, ja bakinki kiyi shiru na ce mata to. Kwanan Anti Sha’awa uku a gida mijinta bai zo ba, bai yi aike ba, hankalinsu gaba xaya ya soma tashi don sun saba in ta yiwo yaji ya yi ta zirga-zirga safe da yamma yana kawo hasafi ana wulaqantawa ana tambayarshi baka bayar a gida ba sai da aka zo nan? Ai ya zama aikin banza. Shi kuma ya yi ta bada haquri yana rantsuwar babu ne amma in akwai ai babu wanda zai fi maigida son ya yi wa iyalinshi alheri. Mama tana faxin ba dai kai ba kam don kai kam ba mai alherin ba ne. Rannan da yamma sai ga Baba Yahaya yazo gidan, sallama xaya ya yi ya shigo cikin gidan bai jira sai an amsa mishi ba yana riqe da wani qunshi na tsohon buhu a hannunshi na fito daga kicin da sauri don in karvi buhun a hannunshi, sai kawai naga Innar Giyaxe tana biye dashi tukuf-tukuf. Tsalle na buga na kuma kurma ihu da qarfina kafin na kankameta ina faxin “Kai ku firfito ga Hajiyar Giyaxe tazo.” Da gudu aka yi ta firfitowa yi mata oyoyo, ni kuma Baba Yahaya ya tsare ni da ido yana yi min daquwa hannu bibiyu don Atika ta riga ta karve buhun da ke hannun nashi. Kaga min ja’irar yarinya kina hauka ne ko kuwa qara sa mana ita za ki yi? Na sake ta cikin sauri a hankali cikinladabi na ce mishi Baba kayi haquri. Na kama tafin hannunta na riqe tana qoqarin qwacewa qyale ni ni kar ki matse ni, na ce haba Hajiyata ai tamu da ke bata vaci, har xakin Mama na kaita don nasan can ne masaukin nata a can muka tattaru gaba xayanmu muna ta hargowar yi mata oyoyo rabonta da gidan anyi matuqar daxewa. Mama ta shiga hidimar yi mata hidima sai ina aka saka da ita take yi, itama dai nasan ta gane Baba Yahaya ne yaje ya xaukota ba kuma kan komai ba sai kan maganar aurena da Ado. Rannan ni da Inna muka kwana muna murna tunda ga Hajiyar Giyaxe tazo ai kuma zance ya qare ana baiyana mata komai zata hana auren. Rannan kwananta biyu a gidan tasha farfesu ta kuma wastsake gajiyar girma, idanuwanta sun buxe sosai ta soma gane kan gidan da kyau, ina cikin wanke-wanke na ji ta tana tambayar Babana ni wannan yarinyar Sha’awa me take yi ne a gidan nan? Ya xan yi ‘yan wasu maganganu da ita da kanta na ji tana cewa, ban fa ji ba to balle kuma ni da nake nesa. Sai ga Baba Yahaya yana sallama ta amsa mishi tare da yi mishi sannu da zuwa, sai albarka take ta sanya mishi tare da tambayarshi iyalin sun je gida lafiya ya ce mata lafiya qalau sun ce a gaishe ta, ta ce to tana amsawa, Allah dai yayi musu albarka ya kuma amfana su, Babana ya ce amin. Sai da aka xan yi hira sosai sannan Baba Yahya ya gyara zama ya ce mata, to Inna ko da naje na xauko ki akan ki zo kiyi mana baqunta saboda kin daxe ba ki zo mana ba, to ba baquntar kaxai ba ce tasa na xauko kin, tayi maza ta gyaxa kai tare da mamula bakinta ta ce, nayi zaton hakan nayi zaton da wani abu wataqila tsakaninka da xan uwan naka ko kuma tsakaninshi da iyalin shi. Baba Yahaya ya sake gyara zama kafin ya ce mata kan maganar auren Humaira ne, Hajiyar giyaxe ta ce Humaira, Humaira ya ce mata Aisha, ta ce af to, tayi shiru tana sauraronshi ya gama rattaba mata ba yanin komai sai dai ya yi qoqarin cire sunan Mama a ciki wataqila don yasan ba wani son Mama take yi ba, wataqila kuma bai son nuna mata gajiyawar xanta kan riqon gidan shi. Sai da ta gama sauraronshi tsaf yayin da ni da Inna da su Atika muke xakinmu muna sauraro cikin murna da farin ciki zata zartar da hukunci na adalci a tsakaninmu suma su Mama da nata iyalin suna wurin su don daga ita sai Babana da kuma Baba Yahaya ne a tsakar gidan. Muna cikin sauraronta sai muka ji ta ce mishi, kan wannan maganar ne kaje ka xauko ni Yahya? Cikin ladabi ya ce mata eh, Inna sai kawai muka ji ta ce to ai kuwa dai baka kyauta min ba, ashe waxannan yara ba ‘ya’yanka ba ne ina dalilin da ba zaka zartar da hukunci a kansu ba? Ina dalilin da za ku zauna kuna kace-nace dashi akan wannan ja’irar yarinyar mai bakin ido? Ba ga sauran ‘yanmata a xakin uwarta ba? Ko su me zaku yi da su? Su masu son auren nan ai duka sun cancanci a basu wa za’a ba wa za’a hana? Yanzu shi wannan yaron na gidan nan in an hana auren nan ba a ji kunya ba? Ai sai yaga kamar don ba ku ku ka haife shi ba gashi kuma a gabanku ya girma yana kuma hidimarku ai shi ne ma gidan tunda bini-bini za ka ji Ado dai, Ado dai, Ado dai. To kuma sai ku hana shi aure Yahya? Ai bai yi ba ni da Inna da su Atika muka zaro ido don jin ba zamu samu goyon baya ba, sai dai dole muka yi shiru muna ci gaba da sauraro, su waxannan ‘yanmata guda biyu da suka saura a xakin Fatsuma tunda su na majadan sun samu nasu mazan ko? Baba Yahya yayi maza ya ce eh, sun samu, ta ce to su sauran na xakin nata Atika da Aliya ko? Ya ce “Eh, sunan su kenan ta ce to ka baiwa Salisu su xaya shima xan wan uwar tasu da ya zo nema ka bashi xaya ai ina ganin ma gaba ta kai su sun zo neman baqa an ba su farare. Aka xan yi dariya saboda rahar da tayi, Baba Yahya ya ce, Inna baqar nan fa gida ta xauko Innar giyaxe tayi shiru cikin yanayin murmushi don kuwa kowa yasan Babana kuma da mahaifiyarshi yake yi. Baba Yahya ya soma magana cikin farin ciki alamar shi kam ya gamsu da hukuncin da ta zartar, ya ce to ba zan ba Alh. Abba ita ba, Inna Ahmad zan baiwa Aliya don shi ne saurayi a cikinsu, ta ce wannan kuma kai ta shafa. Inna ma nasan ta xan samu sassaucin damuwarta, sai dai kuma nasan babu yanda za’ayi taji daxin haxa ni da Ado da za’ayi, don haka sai nayi maza na nuna mata murnata a zahiri na ce ai shi kenan ma Inna tunda gashi daga Salisusun har Ahmad duka naki ne, ka kuma da Aliya za’a ba su, Inna tayi magana cikin natsuwa tana kallona cikin wani yanayi ta ce min, to amma ke fa? Ki auri wannan yaron? Kin ga zan samu natsuwa cikin zuciyata? Ai da Atika ko Aliyan aka ba shi, ai da gangan Mama take yin abin da take yi, baqin ciki take so ta sani na ce uh’uh Inna kar kiyi maganar nan har wani ya ji ni da su Atika da Aliya duk xaya ne a wurinki, kuma gara ni in auri Ado da su su aure shi saboda ni ce babba ban da haka ma kuma nafi su sabuwa da wahalar Mama, don haka gara ni xin kiyi haquri kar kuma ki nuna baki gamsu da abinda tayin ba, dukkanmu naki ne Inna dukkanmu kuma xaya ne sannan waxanda za’a basun suma naki ne. Ta ce, “Haka ne, Allah na gode maka ni da nake ta fatan ko ke kaxai in samu ayi auren ki gashi a sanadin auren naki ‘yan uwanki ma duka sun samu auren, Allah Ubangiji ya yi miki albarka, ya kuma rufa miki asiri, nayi murmushi na ce amin Inna. Na sake maida kunnuwana can tsakar gida inda nake jiwo Hajiyar giyaxe tana sakin maganganu masu zafi, saboda hakan ne yasa ka zubawa ‘yarku mai yaji ido tana zaune a gida? Baba Yahya yai shiru kamar ruwa ya cinye shi. Can anjima ya soma magana saboda yasan shirun da tayi alama ne na wai shi take sauraro, ya ce to Inna in na ce komai na gani sai nayi magana ba fa ba jituwa zamu yi da shi na gaya miki abinda ya faru sanda nazo da maganar yaran nan da aka kawo min labarin abinda suke yi zuwa nayi da qarfina don musan matakin da zamu xauka a kan su tun abin bai yi nisa ba sai uwar su ta ci mutuncina a gabanshi ta ce wai duk tsiyata dole in ga ‘ya’yanta in kuma haqura da su tunda an riga an haife su ba kuma zai yiwu in dunqule su in maida su inda suka fito ba. Hajiyar Giyaxe ta ce, to kayi haquri, ni da kaina na baka haquri in cin mutunci tayi kuwa to ba kai tayi wa ba kanta tayi wa, gyara kayanka kam ai baya zama sauke mu raba, ba ga ta nan gasu ba, ko ni xin nan da ban san shaye-shayensu na zamani ba ina ganinsu na gaya musu kai ba sigari kaxai suke sha ba suka ce shi kaxai ne nace to bai karve su ba, su daina don duk sun rine sun zama wani iri. Sannan ko ba komai waxannan yaran su Salisusu ai sa’o’insu ne shi Baba ma ya girme shi to ba gashi nan ba ya natsu ya zama babba har ga aure zai yi su wake ta tasu? Dama shi mutum in yayi kos xin iya shege ai in ya riqa sai ya koma yiwa kanshi, don haka ba don su taimake ni kasa a mayar da wannan yarinyar xakinta. Ya ce to Inna, yanzu in na tashi daga nan zan tafi can gidan mijin nata in neme shi muyi magana in yaso da daddare sai in turo masu maida ita su maida ita, ta ce mishi to, tayi tasa mishi albarka Babana kuwa tayi mishi tas. Ba akan komai ba sai akan irin mu’amallarshi da Baba Yahaya ta ce shi kaxai ya riqe abotar da don ta Babana da tuni sun rabu. Mama tayi ta kuka tana faxin wai dama can Hajiyar Giyaxe ba sonta take yi ba, ita kuwa Hajiya ko kallonta bata yi ba balle ta damu da kukan da take yi. Mama bata xauki cewar da Hajiyar Giyaxe tayi na a baiwa Ahmad da Salisusu Atika da Aliya da sauqi ba, da farko tayi maganar qanqantarsu da Babana ya gayawa Hajiyar Giyaxe sai ta ce ai ita sanda aka kaita gidansu shekarunta goma sha xaya ne ba gata ba me ya same ta? To balle Aliya mai sha huxu a kaita xakinta kawai ta sake dawowa da maganar hidimar da za’ayin wai an riga anyi nisa babu su a ciki gashi ana matsalar kasuwa tunda kwanannan ma akayi wata asarar. Don haka a xan xaga nasu bikin don a samu a xan tanadan musu wani abu, da Babana ya sake yi mata wannan maganar sai ta ce mishi kira min iyayen yaran in ji ta bakinsu, Mama da Inna suka zo Mama ta sake rattaba mata bayani da dalilan son xagawan da ta waiwayi Inna sai ta ce ita ana ta ayi hidimar ba tare da su an sanya su cikin waxanda za’ayi wa sayayyar ba, tunda ba a faro dasu ba a xaura musu aurensu kawai a kai su xakunan mazansu arzikin gidan miji ai yafi na gidan iyaye, don haka kar ayi musu komai ko da kuwa tabarma ce. Innar Giyaxe ta ce, na gode miki ‘yar nan, Allah dai yayi miki albarka, je ki abinki kin ji Inna ta tashi ta tafi ta kalli Babana ta ce mishi kar kayi sayaiyar da su sun yafe a xaura musu auren a kai su gidajensu tunda uwar suma ta ce bata son sayaiyar, don haka na umarce ka ka aurar mata da ‘ya’yanta in kuma bani ka ke nema da magana ba. An maida Anti Sha’awa gidan mijinta ko kwana bakwai ba ayi ba sai ga goro an kawo wai na tarewar amaryarta rana ita yau. Hajiyar Giyaxe ta ce, uhun ka gani ba? Gajiya yayi da irin qarantarku da kuke mishi, don haka zai yi wa kanshi maganin iya shegen ‘yarku ku kuma kun kama ta kun riqe kuna jira sai yazo, to ba don Yahaya yaje ya bashi haquri yasa an maida ita ba da amarya ta tare ita tana wurin yaji kaga kuma da girma ya faxi. Ko da yake yanzun ma dai sai dai ayi sha’ani. Rannan Mama ta wuni tana zage-zage, tana faxin kaga min ja’iri mara mutunci bai da ko kwabo naja na tsaya na ce sai shi bayan ga mutanen da suka dace a ba su shi ne tun ba a gama fita daga zaman talaucin da ake yi ba zai kwaso wata tsiya ya kawowa mutane? Zubaida ta ce ai sai dai kar a kuma don wannan kam ya riga ya kwaso. Gaba xaya Babana hidimarshi da maganarshi ta zama ta hidimar bikin da ya sanya a gaba na ‘ya’yanshi mata guda biyar, ga kumaxan shi na riqo wato qanin matarshi Ado, wai shima shi ne mai yi mishi komai sadaki da zannuwan aure duka ina jin mama tana cewa wannan kuxi da ka bayar na sayaiyar zannuwan auren Ado ai ba za su yi ba Alhaji, haka fa kayayyakin xakin yarannan da hikima na qarasa yi musu sayaiyar. Inna mai ‘ya’ya uku rus cikin lamarin ba a ko sha’awa da ita hankalinta kuma a kwance hidimarta kawai ta sanya a gaba. Tuni tayi kasafi na abinda zata baiwa kowacce a cikinmu cikin ‘yan kuxinta da cikinmu ya rage mata da suke wurin juyi. Sai dai ni kam ba kayan xaki take shirin saya min ba, don Mama ta riga tayi furuci maganar kuma ta riga ta bayyana har mutane da yawa sunji ta cewar auren nawa da Ado za a yi shi na wata uku ne kawai, watanni ukun suna cika zai sako ni in dawo gida in yaso sai ya nemi wata qalleliyar yarinyar ya aura tunda ma ai kan nawa auren ko me aka yi bai da asara don ko qwandalarshi ba zai kashe ba, Babana ne zai yi mishi komai. Ado ya yarda da wannan qa’ida da Mama ta sanya mishi, ya kuma yi rantsuwar yi mata duk abin da take so akan auren dama kuma kowa yasan shi xin mai yi mata biyayya ne. Bisa wannan dalili ne Inna da ‘yan uwanta suka tsaida shawarar ni kar a saya min komai na kayan xaki ta saya min zinari tunda qadara ce ban da haka kuma zan yi kwalliya. Kwanakin bikinmu sun matso gaba xaya abinda yai saura bai wuce kwana bakwai ba, hidima ta riga ta soma kankama in Mama tayi sammako ta fita tun safe to bata dawowa sai dare, wai tana can wurin hidima. Inna ma dai da bata zuwa ko’ina itama tata hidimar tayi nisa don Hajiya Kubra tana tsaye akan al’amarinta gashi kuma ta tsaya wajen ganin an haxawa Innar gudumowa mai yawa shi kam Alhaji Abba ma shi ta xora wa hidimar gadaje da kujerun su Atika, don haka masu matuqar kyau aka saya. Rannan da hantsi na fita naje gidan Anti Ramla don ita tayi kirana wasu ‘yan dabaru wai take son koya min na yanda zan yi in zauna da Ado, tunda ga abinda ake cewa wai auren na kwana casa’in ne tana gama gaya min abinda zata gaya min xin nayi mata godiya na fito ba wani daxewa nayi ba da barin gida amma abin mamaki da yake an ce wai baya bata kaxan sai nazo na samu yanayin da na bar gidanmu ya canza, ganin mutanen gidan nayi a tsaitsaye kowa sai zare ido yake yi yana rarraba su. Da sauri naja na tsaya ina tambayarsu me ya faru? An yi wani abu ne?ko wani ya rasu ne? shiru sai kallona ake yi na ce ha’a to menene haka? Zan fara kuka don ban san me ya faru ba gashi kuma ban ga Babana a cikin gidan ba, sai kawai Zubaida ta ce min ba fa wani abu ba ne maneman Suwaiba ne suka tuiro wai a xaga musu nasu bikin don ba su samu xaki ba, shi ne da aka ce musu a’a bikin ya riga yazo kuma ba ita kaxai ba ce don haka ba zai yiwu ba maganar xagawar shi ne suka ce to sun fasa auren. A zuciyata na ce ina ma ni ce! Duk da irin rashin kyakkyawar mu’amallar da ke tsakanina da su ban ji daxin hakan ba, don haka sai na wuce naje na shiga xakin Mama don in yi magana da Suwaiba, kukan da take yi ya wuce gaban bayani, nayi qoqarin rarrashinta, naga ba za ta gane ma ina magana ba, don haka na haqura na fito cikin zuciyata dai na ji tausayinta don ta riga tasa rai da yawa akan auren. Can cikin zuciyata na ce, oh’oh ko menene mai daxi haka cikin auren da za’ayi mishi irin wannan son? Oho. Ko kwana xaya da faruwar abin bai cika ba sai kawai Mama ta soma yin waya tana gaya wa mutane cewar bikin babu shi kwata-kwata ma ba za ayi ba don ba zai yiwu ayi biki babu Suwaiba a ciki ba. Kan ka ce menene wannan sai ga Babana shima yana qoqarin gamsar da Mahaifiyarshi dalilan da suka sa shi zai xaga bikin zuwa wani lokaci gaba kaxan, ita kuwa ta ce ina! Akan mutum xaya sai a fasa bikin ‘yanmata huxu? Ba zai yiwu ba sai dai ko ita Suwaiba da uwarta su fito da wani mijin kafin ranar don a haxa har da ita ko kuma ayi babu ita. Hakan kuma aka yi ranar xaurin aure yazo an kuma xaura auren ‘yanmata guda huxu babu Suwaiba a ciki, don ita da Mama sun kasa fiddo da wani mijin ko da kuwa cikin ‘ya’yan dangi ne, a zuciyata na ce oh’oh wato Inna dai ba qaramin rufin asiri ke gare ta ba da aka bata wa’adin kwanaki uku in kawo miji aka kuma kawo har guda biyu da aka hana su ni kuma aka ba su qannena suka karva saboda ba donni da qannena dama za su yi auren ba don ita Innan ce sanin halinta da suka yi mutuncinta da kuma haqurinta. Anyi biki irin wanda ba’a zata ba, zan ma iya cewa ba a tava yin irin shi ba a unguwarmu gaba xaya saboda ba Mama da Babana ne kaxai tsaye akan bikin ba, balle don sunyi mishi saki lecece ya kasa yin armashi. Baba Yahaya da Alhaji Maikuxi sunyi wa bikin hidima ta ban mamaki dangin Inna rannan basu wani saurari dokar Babana ta hana su zuwa mishi gida ba, tururuwa kawai suke yi suna shigowa Inna tana can cikin xakinta ko ganinta ba’ayi. Itama Mama danginta da qawayenta sun zo da yawa, to amma kuma ta riga taki bakin sai zage-zage da neme-nemen tashin hankali take yi, Inna Balki ta ce kar wanda ya kulata ai mu ba ma hidimar arziki muyi faxa. Duk wani abin da suke buqata shigo dashi kawai suke yi ko loma xaya na gidan basu nema ba balle aje ana vacin rai. Ni kam nayi kwalliya ko in ce mun yi kwalliya don kuwa Atika da Aliya kayan aure aka yi musu tanfar ba za su qare ba, saboda yawa to amma kuma nima dama Innata da Hajiya Kubra sunyi min tanadin kayan ado masu daraja, don haka ko kallon akwatin da Mama ta bayar guda xaya na kayan aurena da zannuwa biyar a ciki babu wanda ya sake yi. Sai ma da Hajiya ‘Yardubu taga irin wulaqancin da ake yi wa Akwatinne taja shi ta adana tana faxin “Wannan akwati fa ba shi ne auren ba, miji shi ne aure. Gaba xaya aka fara magana shima mijin ai ba auren yake nufi ba, Hajiya ba ki ji abinda suke faxi ba ne cewa a kwana casa’in zai qare? Tayi murmushi ta ce, to ko na kwana bakwai ne in ya zamo mai albarka ai shi kenan, ba dai an xaura ba? Suka ce, “Eh” ta ce to ai shi kenan.” Cikin kwanaki biyun da bikin ya kankama wato Juma’a da Asabar hidimar da aka yi ba qarama ba ce, abin mamaki kuma shima Ado yayi hidima yayi ado yayi gayya, danginshi na uba da abokanshi masu yawa suka zo, qanin Mahaifinshi ne wai ya karvar mishi auren. Ranar Asabar da daddare Amare gaba xaya aka kai su gidan mazajensu, sai dai ni kam fita da ni kawai aka yi daga gidanmu aka sake shiga dani xaya gidan namu. Inna Balki tana zaune a gefena kan wata ‘yar tabarma da muka samu a shimfixe don Mama bata sa anyi jere ba, ta ce sai gobe, sannan gaba xaya kayan alatun da Ado ya kamata wurin shi da su ta kwashe wai sunzama nata tunda yayi aure. Ta xan faki idon mutanen dake cike a xakin ta matso da bakinta kusa da kunnena ta ce min, mijin naki fa xazu na ganshi da yazo angwanci santalelen saurayi ne, ina ganin maimakon fito-na-fito da rashin kirki ko za ki gwada yi mishi kirki ne? nayi maza na ce mata a’a bana son shi ba zan zauna dashi ba, ta gyaxa kai ta ce to shi kenan, amma baki ga kamar…kan ta gama nace mata bar shi kawai Inna ba zan iya zama dashi ba, ta ce to yanda tayi dai muna miki addu’a na ce to na gode. Waxannan suka kawo ni suna barin gidan abokan Ado suka shiga kai-kawo suna tambayar ‘yanmata, abinda suke buqatar a kawo musu. Wata zaqaqura ta ce musu katifa don ba mu ga yanda za’ayi amarya ta kwanta kan wannan tsohuwar tabarma da aka yar a qasa ba, suka ce kin faxi gaskiya ‘yanmata, suka juya suka fita. Jimawa can sai gasu da qatuwar katifar sunbuqa sabuwa dal a cikin ledarta, har bargo shima sabo duniyar kule kan ka ce meye wannan sun wadata wurin da kayayyakin ciye-ciye da shaye-shaye iri-iri. Washegari ranar Lahadi rannan wuni muka yi daga ni sai qawayena sai dangin su Mama da suke shigowa jifa-jifa ganin amarya sai ko ‘ya’yana su dake kai-kawo amma dangin Inna babu wanda ya leqo don su dama sun ce sun gama da gidanmu tun jiya sun dai zo sun sheda xaurin aure, to yau za su yi hidimar su a tsakanin gidajen amaren su Atika da Aliya da kuma gidan mai babban allo, don su a wurin su shima Salisusu xa ne saboda Baba Yahaya. Har bayan Azahar ba a zo aka yi min jere ba, abincin ranar ma ba a kawo ba, wataqila don sun leqo sun ga angwaye sun kawo abin karyawa shi yasa ko suke zaton za su kawo na rana oho. ‘Yanmata suka nemo redio suka shiga sanya kaset suna cashewa, don su xebewa kansu takaicin zaman shiru. Sai bayan La’asar lokacinne naga ana shigowa da wasu katakwaye da ‘yan kujeru waxanda rabon da inga irin su tun a hotunan mutanen da, tunda nasan ko a qauye ba za ayi amfani da waxannan ba yanzun. Nan da nan masu jere suka yi jere suka gama ko awa xaya basu cika ba suka yi tafiyarsu dama kuma ‘yan uwan Maman ne masu jeren. Wajen qarfe shida saura kwata na yamma sai ga Anti Ramla ta shigo tasha kwalliya tayi matuqar yin kyau da kyar maganar take fitowa ga alama ba qaramin jiki ta ji ba a bikin, menene wannan? Ta shiga waige-waige tana qara kallon xakin na ce mata kayan xaki ne ta kwashe da dariya ta ce, kanta kayi wa kamata ta muzanta tunda shi ne zai hau kai ya kwanta ko kuwa na ce mata eh. Ta ce, kai baki ga gidan su Aliya ba da Atika, nayi murmushi na ce sun yi kyau ko? Ta ce ai ba a magana, Salisusu yana faxamar mada na ce sabon gidan Baba Yahaya kenan, ta ce eh to ita kuma Atika tana C.B.N Quarters, Alhaji Abba ya baiwa Ahmad vari xaya amaryar shi shima tana xaya, na ce kai sun more gidaje, ta ce eh an kuma yi musu kaya, don ban da na Alhaji Abba shima Alhaji Babba yayi musu wasu gadaje da kujerun a zuciyata na ce Alhaji Maikuxi kenan. Labari sosai ta bani na irin hidimar da aka yi na bikin Atika da Aliya, nayi murna sosai don nasan Inna tana cikin farin ciki. Daga baya ne kuma na ji tausayi, sai dai maimakon in ji tausayin kaina tausayin Babana ne ya kama ni. Gaba xaya abokanshi a yanzu arzikinsu ya zarce nashi, saboda suna da tsayayyun ‘ya’yan da suka tallabawa neman arzikin su a lokacin da suka soma buqatar hakan saboda shekaru sun soma yi musu yawa. Shi kuwa bai samu nashin sun kintsa ba, balle shima suyi mishi irin wannan taimakon sai Ado. Ado kuwa ta’adin da suke yi mishi shi da Mama yawanshi ba kaxan ba ne. “Tashi kiyi kwalliya ga waxannan kayan Hajiya Kubra ta ce in zo miki da su.” Na ce mata “To.” Sai da na sake wanka na zauna na sake shafa mai tana taya ni don mun riga munyi matuqar shaquwa da ita, sannan na sanya sabbin under wears waxanda suma a cikin kayan tazo dasu na sanya kayana tare da ‘yankunne da abin wuya tare da wasu banguls xin a hannuna su zobuna sai sheqi nake yi ina xaukan ido tanfar dai wata amaryar gaske. Sai da ta gama feshe ni da turare ta ko’ina sannan ta kalle ni tayi murmushin gamsuwa ta miqe tsaye da nufin tafiya nima na miqe tsaye da nufin yi mata taku zuwa qofar xaki, waiwayowa tayi cikin natsuwa kafin ta ce min “Kai kin yi kyau Humaira, kuma ke xin amarya ce ta sosai da sosai, sannan angon ki ma ango ne na gaske abu guda xaya da ya rage ku shi ne baku da haxaxxen gida baku kuma da kayan alatu amma wannan duk ba komai ba ne in har kun yarda zaku mallakawa junanku kawunanku zaku more aurenku a haka.” Nayi maza na ce, “Haba Anti Ramla, yaya kike irin wannan maganar kamar ba ki san komai ba?” ta xan yi murmushi tare da tave baki ta ce, “Nasan komai Humaira, amma dai kuma nayi miki sha’awar yaronne very handsome, very gentle.” Na ce, a hakan ko?”ta ce, eh, na ce to sumu-sumu kasau ne kin ji, in kin san abinda ya yi wa Inna da wanda yake yiwa Babana za ki san ko yaya yake ni xin bani da buqatarshi ba kuma zan buqace shi ba. Ta ce, “To shi kenan abinda ki ka gani dai tunda mai xaki ai shi yasan inda ke yi masa yoyo. Amma dai in har kin san baki da buqatarshi xin da gaske to ki riqe budurcinki kar ki bar shi ya tava don shi xin shi ne komai xin mu.” Na ce mata, “To.” Ta tafi tana jaddada min, kar fa in yi sakarcin da zai cuce ni tunda ga abinda uwar goyonshi ma take faxa, cewar auren nasu na kwana casa’in ne, na ce mata yauwa ko nan aka tsaya zaki gane ba wani abin da zan yi dashi, tayi maza ta ce haka to amma fa sai kin yi jarumtaka mai yawa don su xin ba wani kirki ne da su ba, haka nan kunyarsu ma ‘yar qanqanuwa ce, na ce to.” Na juya zuwa can cikin xaki, cikin zuciyata ina tunanin yanda za’ayi Ado ya ce yana son wani abu daga gare ni, kai haba shima ba zai fara ba zai jira ne kawai wa’adin kwana casa’in xin da Mama ta xibar mishi su cika ya sallame ni, shi kenan burinsu ya cika na zama bazawara tunda ma ga irin lalataccen kayan da suka yi min, ba don ayi amfani da shi suka yi ba, abu mai xan fasali da yake cikin gidan to a kicin yake shi ne coler da frich sai ko frizer waxannan kuwa Baba Yahaya ne yayi mana dukkanmu. Abokan ango suka rako angon don sayen baki, kayayyakin sayen baki sosai suka zo da shi, qawaye kuma suna faxin abin da za’a basu na sallamar qawaye suka kawo suka basu bayan an xan yi raha da barkwanci suka sallame su, suka tafi daga baya suma suka yi ‘yan nasihohinsa da addu’o’i, suka shafa. Ado ya yi musu rakiya ya dawo xakin. Yana dawowa ya cire hularshi da babbar rigarshi ya jefar kan kujera guda xaya ga alamar dama ya riga ya gaji da su, ya shiga banxaki ya gama abinda zai yi ya fito cikin natsuwa ya kalle ni. “Xan tashi mana Amarya kiyi alwala don mu gabatar da Sallar nafila.” Lokacin ne na gane bayan wankan da yayi har da alwala ya xauro. Ganin ban tanka mishi ba ya sanya shi tsayawa yi min bayani, akwai alheri mai yawa cikin irin wannan nafilar da aka kwaxaitar da ma’aurata game da samunsu, na ce au haba? Yayi shiru yana kallona sai dai fara’arshi ta xan ragu, a lalace na ce mishi har da auren kwana casa’in cikin irin auren da ake yiwa wannan nafilar? Yana daga tsayen ya ce min, “Ai lokaci ne zai bayyanar da wannan, don haka tashi kiyi alwala muyi sallar.” Na ce to ban yi niyya ba.” Yayi sallar nafila raka’a biyu ya xora shafa’i da wuturi akai ya yi addu’o’in shi ya shafa, sannan ya miqe ya jawo ledar kayan ciye-ciye da suka zo da ita, ya matso kusa da ni. “Sa hannu mu ci ko kin fi so in ba ki?” da sauri na kalle shi na ce mishi, kai kar fa ka ce zaka maida ni wata ‘yar yarinya qarama, yayi maza ya ce haka ne ke a yau ba yarinya qarama ba ce ya ture ledar can gefe ya fasa cin abin da ke ciki ya miqe ya fita sai gashi ya dawo xakin daga shi sai wata lalausar rigar bacci da ya riqe da belt xinta. Gabana yayi mummunan faxuwa, me wannan mutumin yake nufi? Nayi maza na mike tsaye ina ja da baya har na kai ga tava bango, zuba min ido yayi yana kallona kafin ya buxe baki a hankali cikin natsuwa yana tambayata me ki ke yi haka kamar wata qaramar yarinya? Nayi maza na ce mishi kar ka tava ni, kai ma kasan bai dace ka tava ni ba in har kana da gaskiya da adalci. To in ba ni da gaskiya da adalci fa Humaira zan iya tava ki? Kasa bashi amsa nayi yayin da jikina kuma ya xauki rawa sosai saboda tsoratar da nayi dashi, don haka nan take na ji babu abin da nake son yi irin in yi kuka. Kukan da yaga ina yi sosai-sosai ya sanya jikinshi ya xan yi sanyi, ya koma bakin gado da nufin zama yana tava gadon ya valle. Ado ya miqe tsaye ya zuba wa gadon ido ya xaga zanin gadon ya kalli katifar ya ce, “A’a kamar zai yi magana sai kuma naga ya kame bakinshi yayi shiru iyaka dai bai sake yin wani abu ko cewa komai ba sai bayan da ya gama fitar da gadon tare da ‘yar katifar dake kanshi, sannan ya dawo ya jawo katifar da muka kwana akai jiya ya kwantar yayi shimfixa akai sannan ya sake kallona ya ce min. “To zo ki kwanta.” Naci gaba da tsayuwar da nake yi, ya kalle ni ya ce min “Ai in ina so zan zo nan inda kike in xauke ki, don haka zo ki kwanta kawai ba zan tava ki ba, magana kawai zamu yi.” Na xan taho a hankali jikina kuma a takure na xan xofanu gefen katifar yayin da shi kuma ya zauna a tsakiyarta ya baje qafafuwanshi ya zuba min ido yana kallona, menene matsalarki Humaira? Nayi maza na ce mishi bani da ita, ya ce to me yasa ba kya son in tava ki bayan kuma kin sani sarai tun jiya ke xin a matsayin matata kike? Na xago ido na kalle shi wasu sabbin hawayen suka sake zubowa sharrr daga idanuna na ce mishi na roqe ka ko baka tava yiwa kowa adalci ba kayi wa wannan auren adalci, kar ka tava ni tunda kaima kasan komai.” Ya ce, “Ban san komai ba, sai kin gaya min.”Na ce “Kaima kasan ba da gaske kake nufin zaman ba.”Ya ce, “Wannan kuma abinda ya shafe ni ne ni da zuciyata, abinda yake naki guda xaya ne shi ne nayi miki umarni ki amsa, na ce ba zan iya ba.” Ya ce, “To saboda me?” ban san yanda aka yi ba sai kawai naji bakina yana yi mishi lissafi “Saboda baka tava gaida Innata ba, baka tava girmamata ba, baka tava xaga ido ka kalle ta da nufin mutuntata ba, tsawon zaman ka da ita in ban da tattalin vacin ranta ya qaru babu abinda ka rinqa yi. Sai kuma ka tava mata ni?” na sake xago ido na kalle shi hawaye suna gudu a idona shar-shar-shar cikin wani yanayi da yafi kama da na shanye halin da ake ciki, ko voyewa. Ya ce, “To ai na ce miki ni xin namiji ne.” na tambaye shi me ake nufi da namiji? Ya ce min, jarumi, na ce tabbas na yarda kai xin jarumi ne, na miqe na bar mishi katifar na fito falon na hau kan ‘yar kujerar ulun da ke wurin na xan xofanu ban wani yi motsi mai qarfi a kanta ba saboda tsoron kar itama ta wargaje kamar yanda naga gadonta ya yi. Rannan dai kusan kwana nayi idona biyu saboda tsoron Ado da abinda yake shirin yi abinda ban tava tsammanin hakan zai faru ba a tsakaninmu, to sai dai kuma shima Adon da baya cikin tsoron barazanata bana zaton ya runtsa, don ina ta jin motsinshi. Ana kiran Sallar farko ya tashi ya shiga yayi wanka ya yi alwala ya fito falo inda nake “ki shiga kiyi wanka kiyi Sallah.” Ban amsa ba, ban kuma qi yin abin da ya ce in yin ba, saboda ciwon da jikina ke yi ga gajiyar biki ga kuma kwanan takura da nayi, ido kuma biyu da kamar nayi bacci ne ma to da da xan sauqi. Na idar da sallar Asuba na xan kishinfixa gefen katifar ina sauraron shigowar Ado daga Masallaci, ban san yanda aka yi ba sai kawai na farka naga gari ya waye sosai, na miqe na shiga banxaki don in rage nauyin dake marata, lokacin ne naga aikin da Ado ya yi ina bacci jarkoki cike da ruwa ga wata qatuwar randa itama ya cikata da ruwa donni ko kayan aiki ba ayi min ba. Mama ta ce, wai uwa ce mai yin wannan ita kuma Inna bata yi ba, ta ce tunda ba da niyyar a zauna suka yi auren ba to babu abinda zata kai musu sai cin-cin da alkaki da kayan rabon da za’a baiwa iyayenshi wannan kam a wadace aka yi aka kuma basu suka tafi cikin murna.” Ta window nayi leqe saboda jin maganar da Ado keyi shi da Baba ne a tsakar gida wai yatsa yake nunawa Baba alamar kashedi. “Ba fa zan lamunci abinda ku ke yi a cikin gidannan ba kai da Ibrahim, saboda a yanzu ba ni da ku ba ne kawai, matata tana ciki.” Gabana ya yanke ya faxi da qarfi saboda jin yanda ya ambaci matata xin cikin wani yanayi. Haushi da takaici ya kama ni, na yanda yake gwadawa Baba Isa da gadara, bayan kuma gidan ubanshi ne, a zuciyata na ce in ban da su Baba sun zama abin da suka zama yaushe za ace wanda yake zaman cin arziki a gidan ku zai yi muku haka? Ko da dai a matsayin Kawunsu yake ai da sai dai ayi zaman ganin darajar juna da mutuntawa. Tsintsiyar zabori Ado ya saka ya wanke gidan gaba xaya ya gyara duk wani abin da yake buqatar gyarawa, sannan ya shigo xaki bai kalle ni ba ya ce min za ki rinqa gaisawa da Baba da Ibrahim ne a matsayinsu na yayunki, amma ban yarda ki ga wani abokinsu ki gaishe shi ba, ban kuma yarda wani abu ya kai ki xakinsu ba ko menene shi. Matuqar kuma ba wani aiki za ki yi ba, to bana son zamanki a tsakar gida in kuma hakan ya kama to ki sa gyale ko hijabi ki rufe jikinki, na ce tafxijam gidan nan ai gidanmu ne ni da su kuma ‘yan uwan juna ne, ubanmu xaya babu wani wanda zai zo ya saka mana dokoki don kawai yazo cin arziki ya samu shiga. Bai kula ni ba. Ina zaune a falo shima ya fito falon a dalilin shigowar da Sa’adatu tayi ta kawo mana abin karyawa, Mama ce ta aiko ta xan kununa a kofi da qosai guda uku qanana a takarda nashi kuma a wani kyakkyawan food flask an cika shi tam ga yaji a gefe ga kuma kununshi a wani kyakkyawan jug tare da kofin xiba asha, shima mai kyau. Na kawar da kaina gefe na ce hu’un, ai Babana kam kirkinshi yana da yawa, kowa yazo cin arziki gidan shi zai ci ya qoshi. Da sauri ya tambaye ni menene? Alamar bai ji abinda na faxin sosai ba, yana jin na soma kamo bayanin zan maimaita mishi sai kawai naji kau, ya warware hannunshi ya wanke ni da mari, ban tava zaton zai iya yi min hakan ba, don haka a kixime na qurma mishi ihu, yanda Sa’adatu tayi tsalle tayi waje a tsorace tun saukar marin da ta gani haka shima ya miqe ya tsallake komai ya fita ya bar min xakin bai sha kunun ba. Hannu biyu na saka na rungume fuskata tare da shafa inda ‘yan yatsunshi suka kwanta a gefen fuskata, can cikin zuciyata kuma faxi nake yi lalle mutumin nan ba qaramin artabu zamu yi dashi ba. Ya mare ni a gaban qanwata saboda baya tsoron kowa? Tafxijam, na sake jinjina abinda yayin cikin zuciyata, bai wani daxe ba ya dawo fuskarshi a xaure sosai nima na xaure tawa fiye da tashi ya ajiye kayan da ya shigo dasu kayan tea ne da kayayyakin amfani dangin su sabulu da omo da izal gami da detol. Sai kuma wani yaro da ya biyo shi da katon xin ruwan eva ya karvi tare da faxin yauwa Sadiqu ko ba Sadiqu sunanka ba? Yayi tambayar ta hanyar nuna alamar wasa ga yaron, ya buxe food flask xin ya dunbuzo qosai ya cika wa yaron nan hannu dashi sannan ya zauna yana karyawa sai da ya gama ya shiga ya shirya ya yi kwanciyarshi, sannan ya fito. Kwana uku a jere bana magana da Ado, bana ko kallon inda yake shima baya shiga harkata, zaman a haka ya xan fi min daxi da sauqi fiye da ranar kwananmu na farko, don haka na qudurawa raina ci gaba da daina kula shi. Rannan ya dawo da yamma yayi min sallama ban amsa ba, ya nemi wuri ya zauna maimakon yayi abinda yake gabanshi kamar yanda yake yi a sauran kwanakin, sai ya ce min gaba a Musulunci kwana uku ne, in ya wuce haka ya zama haramun, don haka wacce muke yi wa juna yau ta qare, na kawo qarshenta ta hanyar ce miki Assalamu alaikum” nayi shiru ban amsa ba ya ce min ko ki amsa ko kar ki amsa wannan ke ta shafa, ya ci gaba da al’amuranshi. Ganewan da nayi cewar ba zai yarda gabar ta ci gaba ba yasa da aka aiko Baba Qarami ya kawo mana abincin dare don Sa’adatu bata yarda ta sake shigowa gidan ba, tunda taga marin da yayi. Ina buxe abincin naga irin salon da aka yi na buxe baki zan sake jera mishi wasu baqaqen maganganu saboda in samu mu xora akan na da, sai ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min, kina so ki sha wahala kenan, in ki ka ce za ki rinqa gaya min magana ai ba auren ‘yan iska nayi ba, ba kuma auren nayi a bisa wata mummunar manufa ba balle in zuba miki ido ki rinqa zagina, ko ki bari ne girma da arziki ko ki ji a jikinki.” Shiru nayi na kame bakina saboda na gane Inna ce sai na faxi abinda nayi nufin faxan, tolalle kuwa da gaske zan ji a jikin, don ban ga alamar abin zai tsaya ga mari kawai ba. Ban sani ba ko shirun da nayi ne ya xan bashi wata dama ta tambayata xazu naga fura da nono a frizer, a ina ki ka samu? Ban kalle shi ba na ce mai babban allo ne ya bayar aka kawo min, to xan dama min mana insha, yanayin da yayi maganar a ciki yasa na xebo na zo na dama na miqa mishi. Sai da ya kusa shanyewa na tuna ban sa mishi sugar ba, nayi maza naje na xauko kwalbar sugar na kawo mishi tare da gaya mishi cewar kayi haquri ban sa sugar ba, na riga na saba da shan furar mai babban allo, ya ce eh ai hakan ma daxi ne da ita na ce uh na qi yarda maganar ta qara nisa. Rannan na kwana bakwai a gidan Ado, a lissafi ne kawai suke guda bakwai, amma a tsanani sun fi kama da watanni. A daddafe muka kai waxannan kwanakin, shi xin bai yi gaba ba a kaina ba sai dai da gani har shi mun kai wani hali na tsananin wahala da galabaita. Ni dai ina cikin wani hali na tsananin ciwon jiki a dalilin wasan mugunta da wani lokaci yake yi min, ga kuma tsananin ciwon kai saboda rashin samun barci. Yayin da shi kuma Ado yake kwana zirga-zirgar shan kanwa da su andur lever sold. Kwana muke wani yanayi mara daxi, amma gari na wayewa sai ya maiyace ya maida komai ba komai ba ya ci gaba da murmushin shi, ya shirya da safe zai fita har ya gama komai sai ya waiwayo ya kalle ni ya ce min “Anya kina da kirki kuwa Humaira? Nayi maza na ce mishi ba ni da shi, ya ce to da alama kam amma in ban da haka yau kwanaki bakwai a nan gidan ga Hajiyar Giyaxe a cikin gida bata tava shigowa wurinki ba kema ba ki neme ta ba, sannan baki tava xiban ko da ruwan gidanki ne a kofi ki ka aike mata da shi ba. Anya! Bakya lura ki ga kamar sa’a kika yi tayi yawan ran da taga aurenki? Sannan in kika yi sakacinda ta tafi ba ta ci abincinki ba sai yaushe kike ganin zata dawo taci? Yaushe? Jibi ko gata ko baxi? Shiru nayi ban tanka mishi ba, shima bai matsa sai na bashi amsar ba, yasa kai ya fita yana fita sai ga Sa’adatu ta shiga da sauri na tare ta cikin farin ciki ina tambayarta me yasa ba kya shigowa Sa’adatu? Sa’adatu sai yau?” A hankali ta ce, “Inna ce ta hana ni, yanzu ma yaya Ado ne ya ce min kina nemana, da sauri na tambaye ta me yasa Inna zata hana ki zuwa wurina? Ta ce na gaya mata kin zagi Yaya Ado shi kuma ya mare ki, shi ne ya ce to kar in sake shigo muku gidanku.” Nayi kamar in sake tambayarta wani abu sai kuma dai na fasa a dalilin shekarun nata ba wasu masu yawa ba ne tara ne da ita. Na jawo kazar da Ado ya kawo min jiya da daddare ban ci ba, na tura mata tare da kayan tea. “Zuba yanda ya yi miki ki sha Sa’adatu, yi nayi wai don in burge ta in yaso in ta gama sai in ce mata taje ta turo min su Baba Qarami sai ta kalle ni ta ce min, na riga na qoshi. Da sauri na ce mata, naman kaza ne fa Sa’adatu, don nasan ita xin mai kwaxayin naman ne sai ta ce eh na qoshi ai muma muna dashi.” Na ce, “To shi kenan Sa’adatu, ki gaida Innan ko?” na ce mata “To.” Ta tashi ta tafi cikin zuciyata sai murna nake yi, Inna ma al’amura sun fara canza mata, ko a ina take samun kuxi yanzu? Tunda nasan dai duk abinda take dashi ta kashe sai kuma na tuna ai surukaye ne da ita ga Ahmad xan wanta ga Salisusu xan Baba Yahaya na kuma san dukansu zasu ji da ita. Na fito tsakar gida sanye da doguwar shimi a jikina wacce ta xan fara jiqewa kaxan a dalilin wankin kayan su Baba Qarami da na sa aka kawo min nayi shanya na ke yi a igiya yayin da su Baba da Ibrahim suke xakinsu suna sharholiyarsu tare da abokansu, sai ga Ado ya shigo riqe da ledojin sayaiya biyu a hannunshi. Yana ganina fuskarshi ta sauya ban ce miki a tsakar gida kisa gyale ko hijabi ba? Nayi shiru ban amsa mishi ba, ya sake yi min tambaya cikin tsawa, “kina so ne wani ya ganki a haka?” na ce, “A’a, to su waye za su ganni ba yayuna ba ne?” Yayi maza ya cukume ni ya shaqe yana faxin “Har abokansu da suke cikin xakin ma yayunki ne?” nayi shiru ina zaro ido cikin yanayin tsoro yana sakina ya nufi xakin su Baba ya xaga labulen. “Kai duk ku fito nan bana hana ku shigowa gidan nan kuna mana shaye-shayenku ba?” “A’a Kawu, sigari ne kawai.” Abokansu ne masu bashi amsa, daidai suna fitowa suna barin gidan sum-sum ya sake biyo ni xaki bayan ya gama dasu ya same ni kwance a kan katifa ga cefane na kawo ki tashi kiyi girki, na ce ba zan yi ba na riga na fasa, ya ce kije kiyi ta fasawa. Ya juya ya fita. Ado yayi matuqar tasa Baba da Ibrahim tare da abokansu a gaba har sai da Mama tayi mishi magana akan su sai kuma ya sake dawowa kaina da wasu dokokin nashi masu tsananin bi. Rannan ya dawo gida da rana T.V da kafet Plasma tare da rediyo C.D da kafet na tsakiyar xaki alamar dai so yake ya xan gyara falon saboda rashin fasalin shi ya yi yawa, yana barin gidan sai ga Suwaiba ta shigo, bayan tunda aka yi bikinmu bata shigo min ba, amma kullum tana barin unguwar taje gidan Habiba. Ban ji tayi min sallama ba, don haka na ci gaba da kwanciyata akan katifata a xaki ba tare da na tanka mata ba, ta shiga kunne-kunne da jone-jone ina jin ta sai naji qawarta tana ce mata mun shigo gida babu sallama babu gaisuwa mun kama yiwa matar gida tave-tave. Sai kawai naji Suwaiba tana ce mata, “to nata ne? na Kawunmu ne ba ki ji Mama ma tana cewa duk abinda zan tava a gidan in tava shi cikin gadara na Kawuna ne ba? Ita fa ga irin kayan da aka yi mata can.” Ina jin haka nasan da hannun Mama cikin rashin mutuncin da tazo zata yi min, don kuwa ita dai nasan a yanzu tsorona take ji, a zuciyata nayi tunanin wata qila ta turo ta ne ta tsokane ni don muyi faxa da ita ta fake da wannan tasa Ado ya sake ni, don kuwa ko shekaran jiya ta shigo har gidan har cikin nan falon na gaishe ta taqi ta kula sai da Adon ya ce mata ana gaishe ki Mama sannan ta amsa. Ina cikin xaki ina jin ta tana tambayar shi anya muna nan akan alqawarinmu kuwa Adamu? Yayi murmushi ya ce, me ki ka gani Mama? Ta ce vare-varen da ka soma yi ne yake bani tsoro, ya sake kallonta cikin natsuwa ya ce mata, ai ba na vare-vare Mama, me ki ka ga nayi? Ta ce me ka ke zuwa yi xakin uwarta? Cikin natsuwa ya ce mata gaisuwa ce kawai Mama don akwai nauyi mai yawa ace ‘yarta tana gidan nan a matsayin matata amma ace ba na gaishe ta.” “Matarka Ado? A gabana ka ke kiranta matarka? Kaga yanda kasa na ji faxuwar gaba kuwa?” yayi maza ya shiga bata haquri, yana faxin ya yi kuskure ba kuma zai sake ba, ya yi ta lallava Mama tana ta faman tashin hankali da faxin wai ya wulaqantata tunda ya kira ni matarshi a gabanta, da kyar ya samu ta haqura ya miqe ya rakata har gida. Don haka da na ji kalaman Suwaiba na gane turo ta aka yi sai na fito na same ta hannu na saka na kashe kallon na zare soket xin na ce, ko na Kawunki ne na hana ai na mijina ne xakinmu xaya ni dashi, shimfixar mu kuma xaya ni dake wa yafi iko da kayanshi?” Ta ce, “Au, kwana nawa zaki yi a gidan nashi? Ai za ki fito.” Na ce to ko zan fito dai ai an xaura ya karva bai ce baya so ba, gashi kuma har yana zaryar gaida uwata.” Suwaiba tasa kuka ta fita wai nayi mata gori an ce ba a sonta. Ban san yanda aka yi ba sai kawai na hango Mama tana shigowa gida da sharveviyar dorina da gudu na fito daga xakin ban yarda ta ritsa ni a xakin ba. Muka shiga kai-kawon zagaye gida a qoqarinta na son kama ni, ina yi kuma ina ihun wayyo Mama kiyi haquri kar ki buge ni, ko zan samu makwabta su jiwo mu su kawo min agaji. Ganin ba za ta iya kama ni ba yasa ta shiga qwalawa Ibrahim da ke gida kira wai yazo ya riqe mata ni, da gudu na yanka nayi waje don nasan zai iya kama mata ni xin don ta buge ni, karab muka haxu da Ado a zaure. Lafiya? Da sauri ya tambaye ni bayan ya buxe hannayenshi gaba xaya ya tare hanyar da nake nufin wucewan, jikina yana rawa kamar yanda muryata ma take yi saboda na riga na tsorata, Mama ce tasa Yaya Ibrahim ya kama mata ni wai zata buge ni. Shiru ya yi na wani xan lokaci nuna alamar nazari kafin ya buxe baki cikin natsuwa ya ce min “To mu koma ciki.” Kuka na soma yi mishi saboda na riga na tsorata ba kuma na son gidan dama kuma a matuqar takure nake. “Kiyi haquri mu koma cikin tare in kin yi min haka zan ji daxi don zanga kamar kin mutunta ni ne.” mun juya zamu shiga cikin gidan muka ji Mama tana cewa Ibrahim ai ni na fasa kwana casa’in xin ma da na xiban mishi tunda tun ba aje ko’ina ba har ya fara canzawa, ni ina tunani kar ma dai washa-washan da nake ganin uwar a ciki kwanannan shi ne. Tana ganin na shiga ta katse maganarta tana tambayarta ai dawowa ki ka yi? Ai kuwa za ki…bata gama ba Ado ya shigo, ni na dawo da ita Mama ai bai kamata ta fita ta bar gidan Babana nan ba nine nan na ce ta tafi taje duk inda zata auren nata ya ishe ni haka, ai rannan ma da nayi maka magana kan zaman naku ya ishe ni cewa kayo to ko za’a rabu da ita ai za’a rabun ne akan tayi laifi, ba haka kawai ba, to yau tayi sai ka sallame ta. “Me tayi?” ya buqaci sanin cikin natsuwa, Mama ta kwashe bayanin da Suwaiba tayi mata ta gaya mishi. Ya ce, “Kiyi haquri Mama, amma ya yi daidai ace an sake ta akan Suwaiba? Ni nafi so ki bari sai tayi wani abinda ya shafe ni ko ya shafe ki wanda kowa ya ji da ma yasan muna da hujja ba za’ayi ta zarginmu ana vata mana suna ba, amma Suwaiba ai qanwarta ce kuma ni Kawunta ne mutane ba za su gamsu da hukuncin saki akanta akan Suwaiba ba, sannan kai Ibrahim kar ka fara ace maka ka kama ta ka mata.’ Da sauri Mama ta tambaye shi to don me zaka faxi haka shi ba wanta ba ne?ya ce wanta ne Mama amma ita xin matar aure ce, shi auren kuma Amana ne, daga nan kuma zuwa ranar da zan ce bana yin shi to zan tsare wannan Amanar, don haka kar ya fara yin hakan kawai, kalaman na Ado da yanayin da fuskarshi ta nuna yasa daga Mama har Ibrahim jikinsu yayi sanyi, a hankali ta matso kusa da shi tana tambayar shi anya Adamu ba suyi maka komai ba? Anya ba xanxani haukaci aka sa maka ba? Tsoro fa nake ji kar su juyar min da kai, su qwace ka, dubi yanda ranka ya vaci akan al’amarin ta wai har ni ka ke wa faxa? Ya ce, Babu mai qwace miki ni Mama, kuma ni ba a kanta raina yake vaci ba, aurena da yake kanta ne ba zan iya yin haqurin da za’a wulaqanta min shi ba, ace Ibrahim ya kama matar da aurena yake kanta Mama don a bugeta? To me ya hana shi ni ya buge ni? Ni fa inda ana mutunta min aurena to da wata qila sai ayi a gama komai cikin hanzari, in ta yi laifi a matsayinta na matar aure a gaya min a ga abin da zan yi, ba a xauko bulala ace za ayi mata duka ba, wannan wulaqanta min aure ne. Hukuncin hukuntata nawa ne nima kuma na iya dukanta tunda kema kin ce an gaya miki sau biyu ina mata duka a zuwan da tayi, har ki ka qara jaddada min in ci gaba da haka, don kar ta ce zata raina ni na ce miki a’a ba zan bar ta ta raina ni ba, ai da gaske nake yi ba zan barta ta raina ni ba, haka kema ba zan barta ta raina ki ba, to amma kuma ba zan bar wani itama ya wulaqantata ko ya hanata ‘yancinta na matar aure ba, ba kuma don ita ba sai don aurena da yake kanta. Amma ta rasa yanda zata yi da wannan curarren bayani nashi na ba don ni ba don auren shi yake yi, ya saki auren kuma ya qi ya ce sai an yi laifin da ya dace ayi sakin ko kuma a saurari zuwan kwanaki casa’in xin da aka ambata tun farko. A haka Mama ta haqura ta tafi gida bayan ya yi mata alqawarin yana idar da Sallar Isha’i zai shigo ya same ta don su qara tattaunawa. Mama tana barin gidan ya kalle ni fuskarshi a xaure ya ce min, ke haka ake yi? In an zo za’a buge ki ba za ki yi maza ki shiga xakinki ko kicin ki kulle kanki ba har kafin in dawo sai kiyi waje da gudu? Kina da hankali kuwa? Ke kin san darajar kanki kuwa? Hawaye suka soma zuba a idona, ya roqi in mutunta shi nayi mishi hakan yanzu kuma ya zo zai yi min faxa. Yanayin fuskarshi ya xan sauya a hankali kuma ya soma yin magana, yi haquri kar kiyi kuka nasan kin tsorata ne to amma ya kamata ki san kina da daraja jikinki ba jikin da ya dace ayi ta buxewa ba ne wasu da ba su dace ba suna ganinshi, kishi mai yawa nake yi a kanki ban san dalili ba, da dai ace kin tava barina na tava ki ne to wataqila da nima na yarda da maganar Maman cewar xanxani haukaci aka yi min. To ban xanxani komai ba Humaira, kowa ya gane abinda nake ciki vare-vare nake yi akanki amma babu ruwanki, na ce akan aurenka dai, yayi maza ya ce eh akan aurena, to amma waye auren nawa? ban tanka mishi ba, shima ya kawar da zancen ta hanyar tambayata yanzu nan har yau ma ba za ki yi girki ba? Tsakanin gobe da jibi ne fa naji Baba ya ce wai Hajiyar Giyaxe zata tafi, da sauri na ce mishi kai? Ya ce, uhun, dama zata yi ta zama ne? na xan kalle shi kaxan kafin na kawar da kaina gefe, wani lokaci na kan ji kamar in saki jiki kawai da Ado muyi zamanmu, to amma in nayi wani tunanin sai kuma in ga to ai zan iya sakin jikin nawa dashi muzo muna cikin zaman kwanaki casa’in su cika ace min ki tafi aure ya qare, in akayi haka wa aka cuta? Ni tunda ni ce zan rasa wani abu shi bai rasa komai ba, to in kuma ma ba ace min in tafi ba zama da Ado yana nufin ci gaba da zama cikin ukubar Mama da wulaqantawarta, don haka sai in ga to gara min kawai in ci gaba da jajircewa har lokacin rabuwarmu tazo in je in yi aurena na ‘yanci da mutuntawa da ganin darajar mahaifiyata. Na shiga kicin da nufin yin girki karo na farko a rayuwar aurena ni da Ado cikin kwanaki goma shataran da muka yi tare saboda in yi girkin da zan aikawa kakata Mahaifiyar Baba abincina don kar ta tafi bata tava cin girkina saboda na yarda da maganar da Ado ya gaya min cewar yawan rai ne ya sata ganin auren nawa, don shekaru tamanin da huxu ke gare ta, bai kamata in bari ta tafi bata xanxani girkin nawa ba, tun da ban san randa zata sake zuwa ba. Na fara shirye-shiryen xora girkin kenan bayan na gama tsabtace wurin, sai Ado ya leqo cikin natsuwa ya ce min ko za ki yi ne har da mai babban allo? Ban tanka ba ya juya ya tafi, ga dukkan alamu dai ya ji daxin ganina a kicin xin, shawarar da ya bayar ta sanya ni faxaxa girkin sosai. Tuwon semovita nayi miyar kuka don a sanina tuwo shi ne abincin da yafi daxi yafi sauqin ci a wurin Hajiyar Giyaxe, to ko shima mai babban allon yasha gaya min cewar a dole yake cin wani abinci matuqar ba tuwo ba ne. Na kammala komai ya kuma yi daxi sosai, don wadatattun kaji na zuba a cikin miyar ina tunanin Inna gama in aika a gayawa Inna ta bani inda zan zuba abincin sai ga Ado ya shigo da su food flask har guda uku da wasu kwanukan silver masu murfi masu kyau set biyu da dinner set guda xaya. Nasa hannu na karvi wasu, wasu kuma shi da kanshi ya shigo ya ajiye su ya kuma koma gefe ya tsaya yana kallon yanda nake malmala tuwon ina naxe shi cikin leda ina ajiyewa cikin food flask da kwanukan da ya kawo. Wannan na waye? Ya buqaci sani ba tare da na kalle shi ba na ce mishi nasu Yaya Ibrahim, to wannan fa? Ya sake nuna wani, na gaya mishi na ce na Baba ga na Hajiyar Giyaxe da na gidan mai babban allo da ka ce a sa. To na Inna da Mama fa? Na ce ai wannan da na ce na Baba ne malmalar ciki na da yawa duk mai so sai ya xiba, ya ce to ya yi ina gama zuba miya nasa manshanu da yaji, Ado ya juya zai kira Yaya Ibrahim ya xaukan musu nayi maza nace mishi a’a bari shi zan je in kai musu jin haka da yayi ya sa shi xiban kwanukan a hannunshi yaje har xakinsu ya kai musu. Cikin zuciyata ni kam ina jin takaicin yanda Ado ke tafiyar da su Ibrahim duk da dai shi xin qanin mahaifiyarsu ne, to amma kuma na sani in banda su xin sun lalata kansu da shaye-shaye da qin karatu da zaman rashin sana’a babu yanda za’ayi ya rinqa yi musu haka. Koda yake akwai adawa mai yawa a gidanmu tsakanin ‘ya’yan wannan xakin da na wannan wanda nake ganin kamar Mama ce tayi dalilin aukuwar hakan, ko da yake dai Maman da kuma Babana suna faxin cewa wai Inna ta ce tayi sanadin faruwar komai to amma kuma hakan ba zai hana zuciyata sa min cewar Baba da Ibrahim dama duk wani xa da Mama ta haifa ‘yan uwana ne ba don haka ina jin ciwon rashin kintsuwarsu musamman da yake ‘ya’yan abokan Babana da yawa sun yi gaba sun bar su na kuma san Babana baya jin daxin hakan, iyaka dai ya kama bakinshi ya yi shiru ya zuba ido kamar yanda nasan shima Adon a farkon al’amarin nasu bai xauki al’amarin nasu da sauqi ba. Na sha jin shi yana kai qararsu wajen Baba kan suna shan wani abu bayan sigari, don haka ayi bincike a san abinda suke ciki don a san matakin da za’a xauka tun kafin abin yakai ga lalacewa. Daga ranar da na ji Mama tana tambayarshi ne a’a har da kai ma Ado da nake ganin kamar kai nawa ne zaka tsaya ka taya ni faxa da masu neman qulla musu sharri don su haxa su da mahaifinshi kuma kaima zaka shiga cikinsu? Ai ba a haka, ai ban kawo ka don kai ka samu shiga a wurin ubansu su kuma ka shiga tsakaninsu dashi ka vata ba, matsayinka daban nasu ma daban su ‘ya’ya ne, ya ce haka ne Mama nayi kuskure kiyi haquri daga ranar ne nasan ban sake jin bakin Ado yana magana kan abin da suke yi ba tun daga shaye-shayen, qin zuwa Makaranta, tarkacen abokai da kuma ‘yanmatan da suke kwasowa sai dai kuma a yanzu kam nasan ba ni kaxai ce na gane matsayin da Ado ya ajiye su ba, nasan Mama ma ta gane na kuma tabbatar ta fini jin zafin hakan to amma kuma ban san yanda aka yi ba taja bakinta tayi shiru tana kallo. Maimakon a wancan lokacin ne ya kamata tayi shiru ta bar Ado ya taya Babana sa ido akan ‘ya’yan nashi. Ado ya sake shigowa kicin xin yana tashe da Sa’adatu, “Nuna mata na Hajiyar Giyaxe in yaso na Baba da na mai babban allo sai ni in kai musu.” Na ce, “A’a in ka bar shi ma sai ta kai musu duka.”ya ce, “To bari ni da kaina in tambaye ta don kar ki xora mata abin da ba za ta iya ba, za ki iya Sa’adatu?” tayi murmushi tare da gyaxa mishi kai alamar tasan wasa yake mata, cikin zuciyata nace kai yaro kenan, wai har ta saki jiki da Ado bayan tsawon rayuwarta bata tava ganin yana wata mu’amalla da ita ba in ban da a ‘yan kwanakin nan. Sai da ta kai na Hajiyar Giyaxe ta dawo sannan na tambaye ta Babanmu yana ina ne ta ce xakin Mama, na ce to can za ki kai mishi, ta ce to. Na kammala komai nayi wanka tare da yin kwalliya mai kyau ta hanyar gyaran jikina sosai, sai dai ban sanya wasu kaya masu yawa ba, doguwar riga ce kawai baqa sai dai bata da nauyi ko kaxan, duk abinda nake yi Ado bina kawai yake yi da kallo sai da yaga ya gama komai har na nufi katifata ina shirin kwanciya shi ne ya tambaye ni. “Mu namu abincin fa, ba ki kawo mana ba kuma kina shirin kwanciya?’ na ce, ai ba ka ce in yi da mu ba, waxanda ka ce in yi wa girkin su na yi wa.” Ya ce, to babu laifi.” Na hau katifata na kwanta na jawo bargona mai laushi na ruhu yayin da Ado ke zaune kan kujerar ukun dake falo wacce a kwanakinnan, nan ya mayar wurin kwanciyarshi, ina jin shi yana daidaita tashar talabijin ta hanyar yin amfani da rimot kafin ya ji fitarshi kusan minti talatin kafin ya sake shigowa. “Humaira!” sau biyu ya kira ni kafin ya soma tambaya “Na dai san idonki biyu ba wani bacci kike yi ba, tunda da za ki ji motsina firgigit zaki yi ki tashi, ki fito nan muyi magana.” Na bi umarnin da ya bayar xin ba tare da na yi magana ba, gasasshiyar kaza na samu ajiye a gabanshi. “Zauna mu ci tunda ai ba zai yiwu ki kwana da yunwa ba ko?” na ce “Ai na qoshi.” Ya yi maza ya xago kai ya kalle ni, kina nufin ke kin ci tuwon kenan ni kaxai ne ba ki baiwa ba?’ na ce, a’a ban ci ba, ya ce zauna muci. Yasa wuqa ya raba kazar biyu ya turo min tawa yaja tashi nasa hannu zan xauka in tafi kamar yanda na saba yayi maza ya kama hannuna ya zaunar dani tare da faxin zauna a nan kici. Ai magana na ce miki zamu yi ina zaune ina kallon shi yana cin tashi kazar har ya gama ya xora robar ruwan swan ya tashi yaje ya wanke hanunshi yayi brush sannan ya dawo ya zauna yana hamdala sai da ya xan xauki lokaci kaxan kafin ya ce min ban fa shirya yin wasa da aurena ba Humaira, don haka ina ganin bai dace ace kina ta cutar da ni ba. Cikin natsuwa na tambaye shi, cutarwar me nake yi maka? Ban wani tsaya dogon bayani ba sai ya ce min, kina cutar da ni mana, ai kema kinsan komai tunda ke ba yarinya ba ce ‘yar qanqanuwa kin san abin da kike yi sarai, ban kalle shi ba na ce mishi to in ina cu tar da kai ba sai ka maida ni in da ka xauko ni ba? Ko kuma na menene damuwar? Kaima dama auren kwana casa’in aka ce maka kayi, to in kayi na kwanaki sha tara ai ka kyautata baka yi ta wahalar da ni ba balle in yi ta cutar da kai tunda itama mai auren dama ta ce maka tuni ya riga ya ishe ta.” A natse ya ce min, auren ai nawa ne kuma tun kwanakin baya sai na roqe ki cewar in muna magana to ta rinqa tsayawa a tsakaninmu mu biyu kar ta rinqa shafar ko da na qasa damu ne, balle na sama damu, na ce to a ma daina yin magana mana a rinqa qirgen kwanakin kawai zuwa lissafin casa’in xin.” Ya ce, a’a ba zan iya ba ba zai yiwu in yi ta zama da ke ina zuba miki ido kina zaune a gidana, nayi maza na xaga ido na kalle shi na ce mishi gidanka? Yayi maza ya ce min eh, gidana ne, na yamutsa fuska na ce, wai….bai bari na gama maganar ba yayi maza ya katse ni ta hanyar tambayata wai me? Faxi in ji qarasa abinda ki ke son faxan in dai har ke xin mara kunyar gaske ce.” Ban iya qarasawan ba ta hanyar furta kalma sai dai kuma ban bar shi haka ba murguxa mishi baki nayi, yayi maza ya cafke bakin nawa ya riqe da ‘yan yatsunshi ya matse tare da faxin mara kunya kawai wacce bata san rarrashi da ban baki ba tafi gane ayi tsiya-tsiya da ita tukuna. Washegari da sassafe ina zaune a tsakar gida ni kaxai duk da matsanancin hadarin dake haxuwa a garin wanda yayi dalilin tasowar iska mai tsanani cikin zuciyata tunani nake yi irin abinda ya faru tsakanina da Ado jiya da daddare, abin da na tabbatar kawia shi ne in ban da al’adar da ya gananwa idonshi a zahiri da babu abin da zai tsare shi daga yin abinda ya shirya xin. Can cikin zuciyata na sake tunawa da Anti Ramla da irin yanda ta rinqa jaddada min cewar kar in yarda in bar Ado ya tava budurcina tunda dai na riga na ce ba sonshi nake yi ba, ba zan zauna dashi ba sannan suma mun riga mun san ba da manufar suka karvi auren nasu ba, aure ne kawai suka yi da nufin vata suna don kawai a maida budurwa ta zama bazawara. A wannan lokacin ban yi tunanin wani abu ne mai tsanani ba yin hakan, musamman da yake nasan babu wata alaqa dake shiga tsakanina dashi, to ashe wai ba haka ba ne, ban san dalili ba ban san abinda yasa ya matsa ya takura rayuwarshi kan sai lalle ya tava ni ba, don ya cika burin Mama ne ko kuwa dai da gaske son nawa ya soma yi kamar yanda yake yawan nanata min? Na sake zurfafa cikin wani tunani don in tantance tsakanin son da Ado yace yana yi min da kuma sha’awa kamar yanda Anti Ramlah ta tava yi min bayanin su ban iya gane komai ba illa iyaka dai nasan ko ma wanne yake yi min a cikin biyun to ya soma kanshi cikin fitina don kuwa yayi matuqar takura kanshi barci yayi matuqar yin qaranci a gare shi. Kallo xaya zaka yi mishi ka gane walwalarshi ta ragu, gashi kuma rama ta bayyana a fuskarshi. Ina cikin wannan zaman sai ga Sa’adatu ta shigo rungume da wata qatuwar leda, na tabbatar Ado ne ya aiko ta sai da ta shiga xaki ta ajiye sannan ta fito ta gaishe ni ta miqe zata tafi, nayi maza na ce mata zo mana Sa’adatu, ni hayaniyar me jiya na rinqa ji tana tashi a cikin gidanmu? A hankali ta ce min, Anti Zubaida ce suke faxa da Mama, shi ne Anti Suwaiba ta shigan wa Maman da sauri na ce mata Mama kuma? Ta ce min eh, nayi maza na ce mata me ya haxa su Sa’adatu? Ta ce ban sani ba amma dai na ji tana cewa Inna wai Mama macuciya ce tayi qaryar ta bar mata ko menene? Ni ban gane ba, cikin zuciyata na gane da magana bai wuce Zubaida ta gane Mama irin rashin adalcin ta ba. Na yi murmushi kafin na sake kallon Sa’adatu na ce mata, yanzu kuma Zubaidan tana magana da Inna ne? ta ce, eh daga kwana ukun can ne take samun Inna in ta ganta a kicin tayi ta mata magana ita kuwa sai ta ce mata ai zaman aure sai an haxa shi da haquri, nayi dariya na ce Inna kenan ki ce ina gaishe ta in wankin ya haxu ta baki ki kawo min ta ce to ta tafi. Ruwa ya xan fara saukowa sanda Ado ya shigo gida ga dukkan alamu kuma ranshi a vace yake duk da shi xin ba mai yawan fushi ba ne, na kuwa gane hakan ne ta dalilin yawan baqaqen maganganun da nake gaya mishi don wai in tabbatar mishi da qiyayyar da ke tsakanina dashi. Shi kuwa maimakon ya vata rai sai ya ce min ai shi auren namu ba yin shi aka yi a dalilin so ko amincewa ba anyi shi ne kawai bisa qa’ida ta rabo da kuma qaddara, don babu wanda yasan menene a tsakanin, don haka mu baiwa juna lokaci kawai. Tashi nayi na bi bayan Ado, zuwa cikin xakin duk da lokacin da ya shigo bai ma kalle ni ba balle ya yi min wata magana, ina shiga xakin nayi mishi sannu don dai in samu ya saki jiki in tambaye shi abinda nake son sani. Ni me ya haxa Mama ne kuma da wannan yarinyar Zubaida? Yayi maza yayi min wani lalataccen kallo kafin ya tambaye ni, to ina ruwanki? Hakan da yayi, ya yi matuqar vata min rai, amma sai na danne na ce Mama kenan, ai munafurcinta da sharrinta da mugun abin ta da iya…ban kai ga qarshen maganar ba na ji caraf Ado ya cukume ni ya shaqe da hannunshi, za ki zage ta ne a gabana? Kina nufin ke xin rashin kunyarki har ta kai ki kalli idona ki zageta? Ya sake ni ya tsare ni da idanuwanshi wata qila don ganin na shiga mutsu-mutsun qoqarin qwatar kaina saboda wahala, kina nufin don kin zama matata sai ki zagi Mama akan idona ina kallonki?” Duk da ban wastsake daga wahalar shaqar da ya yi min ba, ban yarda nayi shiru ba sai da na ce mishi ai ni ba matarka bace ba kuma zan yarda in zama ba, bai kula ni ba ya wuce ya shiga cikin xaki ya barni a nan ina kuka sai da ya sake fitowa falon na gane wanka yayi. Can gefe ya koma ya zauna kan kujerar dake wurin sannan ya xago ido ya kalle ni cikin natsuwa ya soma cewa ai na riga na roqe ki cewar ko bamu mutunta juna ba a zaman da zamu yi to mu mutunta auren dake tsakaninmu, mu kuma girmama shi, mutunta aure da girmama shi yana nufin mutuntu ta, duk wani abin da ke buqatar mutunci da ke zagaye da shi haka nan a girmama duk wani abinda ke buqatar girmamawan dake tare dashi Mama ai uwa ce a wurinki aurena da ke kuma ya sake maida ita surukarki sannan ni bani da wata wacce ta fita mahaifiyata ta rasu ita ce uwata ba zan iya ba ba kuma zan yarda ba ki rainata ina gani balle har rainin ya kai ga zagi ina ji, na ce eh ai shi yasa nima nace maka ba zan iya zama da kai ba don nafi buqatar auren mutumin da zaiga girma da mutuncin Mahaifiyarta ba. Ai ni ban raina Inna ba ban kuma tava yi mata wani abu wanda yake na raini ko rashin mutunci ba in ke kin xauka a haka to ita Inna na gode bata xauka a hakan ba domin ranar da na fara shiga xakinta na gaishe ta na roqe ta ta yafe min abubuwan da suka faru a baya a tsakanina da ita na kuskure ta ce ban mata komai ba, kuma a tsakanina da ke da ki ke ganin nayi matana kamar yanda nima zuciyata ta qi yarda da cewar ban yi matana ba, sai na roqe ki ki bani dama irin wanda ta bani kiyi min adalci irin wanda ita xin tayi min, ki kuma yarda da yawan ce mikin da nake yi cewar ni xin namiji ne ma’ana zan iya juyawa a kowane lokaci daga wani matsayi in koma wani, ban ce mishi komai ba. Kwanaki biyu a jere harkokinshi kawai yake yi bai kula ni akan wani abu ba, iyaka dai nasan yasa min ido mai yawa kan al’adar da nake yi, ya kuma hana kawo min abincin da ake yi daga cikin gida, wai na riga na fara girkina duk kuma da ba yin girkin nake yi ba. Rannan ya shigo gida bayan sallar Isha’i, tuni nima na riga nayi sallata na hau kan katifa nayi kwanciyata naja bargo na kululluva zuwa zan ya shigo riqe da leda a hannunshi abinda za’aci ya kawo har kin kwanta ne? na ce mishi eh, tashi kici naman nan tunda xuminshi kar yayi sanyi nace ai na qoshi, ya ce to ba laifi, kin yi wanka ne kin yi sallah? Nayi shiru kamar ban jishi ba, ya ce ba kya jina ne? ko ba na ce bana so in yi tayin magana kina jina kina kin amsawa ba? Kinyi wankan al’ada ne?na ce ba yau na ke yi ba, ya ce to ban yarda ba ki tashi kiyi yanzu, na ce ha a nuka ake yi ba sai ta xauke ake yin wanka ba? Ya ce ko ta xauke ko bata xauke ba yanzu za ki yi wankan wacce irin al’ada ce haka har kwana shida? Tashi kiyi wanka kawai ko kuma in ganta da idona kamar yanda rannan na ganta. Rikici mai yawa ne ya faru tsakanina da Ado saboda qoqarin da nayi wajen ganin na hana shi ganin abinda yake son ganin kallona yayi, ya yi murmushi bayan ya tabbatarwa kanshi da abinda yake son tabbatarwar, nayi matuqar tsorata da abinda ke shirin faruwa na takura na maqu re a jikin ban go a daidai lokacin da na xaga ido na kalle shi naga abinda yake yi tsoro ya sake kama ni hawaye suka soma zuba daga idanuna, bai fasa abinda yake yi ba savanin sauran kwanakin da suka gabata da in ya ganni ina kuka yake haqura ya qyale ni, kayi haquri kar ka tava ni. Nayi maganar cikin wata irin murya da ta riga ta tsorata da abinda ke shirin samunta kiyi haquri ki bar ni in tava ki, ya faxi hakan a daidai lokacin da ya miqo hannayenshi a gare ni, kuka sosai na soma yi mishi ina roqonshi yayi min adalci kar ya tilasta ni yin abin da bana so yayi murmushi ya ce babu komai don na tilasta ki tunda na riga na gane ke xin baki da ra’ayi baki da wani abin da ki ke yi don kanki, kina bin umarnin da ake baki ne. Kin kuma san ba zai yiwu ni dake mu haxu muna bin umarnin wani mutum wanda shi a gidan shi yake nashi zaman auren lafiya duk irin nashi mas’alolin amma mu a namu gidan yayi uwa yayi makarviya wajen ganin bamu zauna lafiya ba, tuni na bar kukan da na ke yi na koma sauraron kalaman Ado saboda na qara tsorata da kalaman nashi, ai nayi haquri na kuma tilasta zuciyata yin haquri akan dole saboda na xauka ra’ayinki ne ki qi yarda da ni ki qi bani haxin kai a duk lokacin da na nemi kiyi min hakan. To amma kuma a ‘yan kwanakin nan sai na gane saki ake yi don naji wayar da ki ka amsa kwanci wanda a ciki ake jaddada miki kar ki yarda in tava budurcinki, to ai nawa ne, domin aurena ya bani shi ba zai yiwu ba kuna zuane a xakina a gidana kina bin umarnin wata naki savanin.” Na kawar da kai game da ke don ki fahinci cewar ba dudurcinki nafi nema ba a yanzu abinda nafi nema shi ne fahimtar juna, tsakanina da ke don shi yafi komai a wurina, to amma tunda akwai wasu a bayan fage masu zuga ki to shi kenan na haqura da fahintar zan karvi budurcin in yaso sai fahintar ta biyo baya tunda na gane kin qi yarda mu fahinci junanne don kina ganin in anyi hakan akwai wani abinda zai biyo baya. Gaba xaya na firgita, hankalina kuma yayi matuqar tashi da na gane Ado ya ji wayar da Anti Ramlah tayi min wacce na amsa a kicin ranar da nake yin abincin da aka kaiwa su Hajiyar Giyaxe, jikina yana rawa na ce mishi kayi haquri, bai kalle ni ba ya ce min kema na roqe ki kiyi haquri yau kaxai ai ni kin sha bani haquri ina haqura, don haka nina yau na roqe ki kiyi min haquri. Ganin da nayi Ado bai da shirin haqura nema ma yake yayi amfani da qarfi wajen raba ni da budurcina sai naji gaba xaya hankalina ya tashi, na shiga tunane-tunanen da neme-nemen hanyoyin da zan bi wajen ganin na kuvutar da kaina daga gare shi, ina cikin hakanne wata shawara da Anti Ramla ta bani na kuma yi amfani da ita ta faxo cikin raina. Kar ka taba ni, kashedi mai qarfi nayi mishi cikin tsananin firgita saboda na kai matuqa wajen tsoron abinda zai faru in har bai yarda ya qyale nin ba, bai ji ba baya ma saurarona abinda ya sanya a gaba kawai yake shirin aiwatarwa. A kiqxime cikin tsananin tsoro na shiga miqa hannuna karqashin filo ina lalube kan ka ce meye wannan na jiwo motsin abinda na ke neman wanda na daxe ina voye shi, saboda maganin vacin rana irin wannan na gwada fin qarfi da nuna zalunci da rashin adalci a zahiri. Ado bai ankara ba saboda hankalinshi ya riga ya tafi inda ya tafi, sanda na jawo abin daga qarqashin filo na kuma taqarqare da iyakacin qarfina na kwantara mishi aka. Sai da yayi tsalle kafin ya kai ga faxuwa a qasa cikin wani irin sauti mai tsananin firgitarwa, yana faxuwar ni kuma nakoma na kwanta cikin tsananin gajiya sai haki nake yi, ina maida numfashi a dalilin ya riga ya gajiyar da ni. Ina kwancen ina tunanin in ya tashi me zai faru a tsakaninmu? Ina qarawa gudumar da nayi dukan da ita riqo mai qarfi ta yanda in ya sake tasowa zan sake gunduma mishi ita akan nashi, sai kuma na ji shiru bai motsa ba, shirun yayi min yawa ta yanda har na kasa jurewa, na taso na leqo don ganin wane hali yake ciki. Yana kwance a qasa shame-shame babu alamar numfashi a tare dashi, a firgice sosai na soma qurma ihu da iyakacin qarfina, ina faxin waiyo Ado, waiyo Kawu waiyo ka tashi ka zauna in ganka a zaune ka yafe min wannan muguntar da nayi maka. Nan take wani tunani yazo min da gudu na shiga bayan gida, bokitin ruwan da na fara cin karo da shi, shi na fara jawowa ban yi tunanin yawan ruwan ba na kwara mishi shi gaba xaya cikin tsananin firgitan da ban tava ganin wanda ya yi shi ba. Wani irin firgitaccen motsi yayi da ya qara tsorata ni da gudu na valle qofarnayi waje naje ina dukan qofar su Yaya Ibrahim da kyar suka buxe suka fito. Bayan sun tabbatar ba zan iya hangen abin da ke cikin xakin ba, ke menene haka? Yaya Ibrahim ne ya fara tambayata cikin tsananin kaxuwa na ce musu Ado, ne ku zo ku ganshi Baba ya ce ka ji ‘yar iska wai Ado take ce mishi ko da yake shima maganinshi kenan muje suka taso ni a gaba zuwa xakin, suna ganin halin da yake ciki suka juya da gudu, Mama kawai Mama kawai za ku kashe mata qaninta don kun ga yana ji da ita dama auren haxin baki ne, ni kam na takura wuri xaya in ban da kuka babu abin da nake yi. Suna barin xakin na faxi jikin Ado ina ta faman kuka ina roqonshi gafarar abinda nayi mishi, tsorona kar ya rasa rayuwarshi a sanadin abinda nayi mishi ne ba tsoron abinda Mama zata zo tayi min ba. Ina cikin haka naji kamar an yi min magana, a firgice na ce iye, na’am? A hankali ya buxe baki ya ce min yi maza ki kulle qofa kar Mama ta shigo ta same ki, da gudu naje na kulle qofar na dawo na durqusa a gaban Ado, kuka sosai nake yi yayin da shi kuma yake kwance bai motsa ba lokacin ne na gane tsoratar da nayi ne ya hanani gane ya farfaxo, tun sanda na ji atishawa da hamdala sai nayi zaton ko daga wani wuri ne. Muna cikin haka na ji isowar Mama tana faxin “Lallai yau za’ayi wacce za’ayi, buxe min qofar in ga abin da yake ciki in bai tashi ba ai sai dai in haxa su za’ayi a haxa su gaba xaya in kuma nayi sa’a ya tashi to uwata zata ci gari na wayewa kuma zan tattara ta koma xakin uwarta.” Gwam-gwan-gwan, duka suke yi da iyakacin qarfin su nayi matuqar tsorata don ji nake yi tamfar zasu valla qofar su shigo, don haka na tsallaka can bayan katifar na maqure. Ado ya tashi zaune nayi matuqar qara tsorata saboda ganin da nayi tanfar zai buxe qofar ne saboda yawan kiran da Mama ke mishi “Adamu! Adamu!! In kana nan amsa mana in ji ka.” Cikin qarfin hali ya ce, “Lafiyata qalau Mama, je ki gida kawai sai da safe.” Da kyar ta haqura ta tafi saboda ganin da tayi ya qi yarda da buxe qofar. Har gari ya waye ban tashi daga inda nake takuren ba, yayin da shi kuma Ado ya koma falo ya zauna ban san me yake yi ba sai da na ji an yi kiran Sallar farko ban ga shigowarshi don yin alwala ba, lokacin ne na miqe da kyar na tashi saboda ciwon da jikina nima ke yi min na leqa shi yana zaune ne kan kujera ya kuma kwantar da kanshi akan masagalin kujerar ya kuma xora hannayenshi duka biyu a kan nashi alamar dai ya addabe shi da ciwo. Durqusawa nayi da gwiwoyina duka biyu na ce mishi “kayi haqurin abin da nayi maka.” Da iyakacin gaskiyata haqurin kawai nake bashi ba tare da wani tunani ba, don na riga na tsorata na kuma yi nadamar xaukan wannan mummunan shawara da nayi, na yi amfani da ita da Ado bai farfaxo ba to da wanne hali zan shiga? Ba abinda Mama zata yi ne matsala ta ba, girman laifin ne na tsorata dashi. “Kayi haquri.” Bai amsa ba, bai kuma motsa ba daga yanayin kwanciyar tashi, shiga Masallaci da ya ji anyi shi ne abinda yayi dalilin miqewar shi ya nufi banxaki sai da yayi wanka sannan yayi alwala ya fito yayi raka’atil fijr, sannan yayi sallar Asuba ya idar yana jan carbi nima na idar na shafa fatiha sannan na kalle shi na sake ce mishi “kayi haquri ka ji?” bai kula ni ba. Aka soma buga qofa da qarfi kamar na jiya da daddare, gwan-gwam-gwan. Ya miqe ya buxe, Mama ta shigo da xamarar gyale a qugunta riqe kuma da sharveviyar dorina a hannunta, nayi maza naja can baya na maqure a jikin bango sai faman kaxuwa nake yi, don in ta soma dukana yau ban san wanda zai qwace ni ba, tunda shima Adon bai huce ba daga mummunan abinda nayi mishi. Yau za ki gamu da ni, yau za ki san vakko miya ce in ma uwa ki ce ta turo ki ku kashe min shi to zaku san qarya ku ke yi yau zan yi maganinki ke da iyayenki masu koya miki mugun abu.” Me ya faru Mama? ya yi maganar cikin natsuwa, ta xago ido ta kalle shi kamar zata yi mishi magana sai kuma ta fasa, wataqila don ganin da tayi tanfar vata lokacinta zata yi, don haka ta zabura ta xago bulalar da niyyar sharva min, ni kuma na takure ina sauraron ta inda zan ji saukarta, sai kawai na ji shiru. Mama tayi maza ta waiwaya don ganin abinda ya riqe mata bulalarta ta baya, taga Ado a tsaye da bakin bulalar a hannunshi, sake min bulalata, tayi mishi maganar cikin tsawa, nan da nan yayi hakan tare da faxin na sake Mama, amma kiyi haquri kar ki ce za ki tava ta, ai in mun yi faxa ba rama min zaki yi ba, nima da kaina in kin bar ni zan rama ai ba fin qarfina tayi ba. Ran Mama ya kai matuqa wajen vaci, da ta gane ba zai barta ta buge ni ba, ta shiga zage-zage tana haxawa har da shi a ciki, kiyi haquri Mama, kar ka sake bani haquri, tayi maganar cikin tsawa da fusata, kiyi haquri Mama, ya sake bata haquri. A hankali kuma cikin natsuwa da nuna ladabi har ta xan sassauto tayi kamar zata juya ta fita, muje gida yanzu ina zuwa Mama, kamar ta yarda zata yi hakan sai kawai naga ta juyo da iyakacin qarfinta ta xaga dorina zata sharva min, da sauri ya sake kama dorinar ya riqe, ta sake juyowa tana kallon shi cikin qarin fusata, zaka riqe min bulalar ne kuma? Cikin natsuwa ya sake ce mata, mace a gidan mijinta Mama ya kamata ace tana da ‘yancin walawa, hukuncinta ya zamo a hannun mijinta ne kawai ba wai duk wani wanda ta yyiwa wani abu sai kawai ya zaro bulala ya ce zai buge ta ba, ba tare da ya sanar da mijin ta ba. To ai nan ba gidan ka bane, balle ka ce na mijinta ne, cikin hanzari ya ce haka ne. Mama ta ci gaba da maganganu gidan mijina ne ni naga dama kai da ita ku ke zaune a gidan ita xin kuma ni naga dama ne na ce a baka ita ko nawa ka kashe a cikin hidimar auren? Ya ce, babu, ta ce to babu inda zani yau sai ka rubuta takarda ka sake ta tukunna tunda dama komai akan alqawari muka yi shi da kai, ya ce haka ne to kije gida ina zuwa. Ta sake faxin babu inda za ni ai gidan mijina ne in naga dama na ce a nan xakin zan kwana kana da yanda zaka yi dani ne? A hankali cikin natsuwa ya ce mata babu, ya waiwayo ya kalle ni a inda nake takure ya ce min shiga ciki. Nayi maza na tashi na shige cikin na bar shi a nan don yin hakan ya fiye min sauqi akan zaman da nake yi a cikinsu, ina ganin abinda ke faruwa. Ina so tabar min gidan a yanzu tunda na mijina ne, ya ce ai na ji Mama, amma na roqi arzikin ki xan yi haquri kaxan ki xan saurare ni ba wani lokaci mai tsawo zata xauka a cikin gidan ba. Mama tasa kai ta fita, shima Ado ya koma ya zauna akan kujera, ni kuma ina can cikin xaki maqure wuri xaya, qirjina sai faman bugawa yake yi val-val-val saboda ban tava ganin abinda ya firgita ni irin na jiya da yau ba, Ado da Mama suna kace-nace bayan kowa yasan kullum Ado akan bin umarnin Mama yake. Wajen qarfe takwas da rabi na ganshi yana shiri kamar in tambaye shi ina za shi? Sai kuma na fasa, saboda yanda fuskarshi take xaure gashi kuma dama ban saba yi mishi irin waxannan tambayoyin ba. Yana fita daga gidan na koma can cikin xaki na zauna ina tunanin in yanzu Mama ta shigo ko ya ya zan yi da ita? Oho. Sai kawai naji sallamar Hajiyar Giyaxe da sauri na fita naje na tare ta, tana riqe da food flask xin da aka kai mata abinci a hannunta, nasa hannu na karvi food flask xin tare da faxin, gani ga ki amma ba ki tava shigowa ba sai yau, don na kai miki tuwo kin ji miyar amayar mai zaqi shi ne ki ka kawo min food flasks? To bari yau ma zan sake aiko miki da wani tuwon don gobe ma ki sake shigowa ki kawo min kwanon. Tayi murmushi ta ce, oh’oh-oh’oh, ni ba don kwanonki na shigo ba, zuwa nayi don maigidan ya ce min in zo in zauna mishi a gidan kafin ya dawo.” Cikin zuciyata na gane abinda yasa Ado yin hakan, shima tsoro yake kar bayan shi Mama ta shigo ta same ni ni kaxai. Muna zaune da Hajiyar Giyaxe mu biyu hira muke yi bayan nayi mata abin karyawa ta karya ta qoshi, sai sakucen haqoranta take yi da tsinken sakace a dalilin farfesun kaza da tasha, sanin da nayi cewar tun asalin dama can Hajiyar Giyaxe tana son Innata tana kuma matuqar sona ya sani sakin jiki da ita sosai, har na kwashe bayanin duk abin da ke tsakanina da Ado, da abin da ya faru daren jiya da abinda yasa ya turo ta taya ni hira duk na gaya mata, don kuwa neman abokin magana nake yi saboda damuwa tayi min yawa. Hajiyar Giyaxe tayi min wani lalataccen kallo ta ce, to abinda ya rinqa yi wa uwarki ba sa shi aka yi ba? Yanzu ma kuma za’a sa shi yayi ne? ba gashi nan ba a yanzu kullum yana kai-kawo a tsakani kuma da ban sani ba ai nasan ba da gangan yake yin abinda yake yin ba, to kuma in ban da shirmenki da kayi cuta ka cuci abokin zamanka ai gara shi ya cuce ka, tunda babu wani abin da ba ayin sakayya akanshi musamman ma ace shi wannan abin kan lamarin aure ne. yanzu ace Innarku bata soma ganin sakayya ba? Innarku fa surukaye uku tayi rana xaya, wane arziki ne ya wuce wannan? Kuma kana ganinta ma a cikin gidan ai kasan walwalarta ma ta xan sauya jinin jikinta ma ya soma dawo mata saboda wahalarta ta soma raguwa, gashi yanzu kullum zaka ganta a wadace cikin harka ni a zatona ma na ce ko mijinki ne oho, na ce anya shi ne kuwa surukayen nata waxancan xin ai dukansu ‘ya’yanta ne, ta gyaxa kai ta ce oho ban sani ba, amma ina ganin mijinki ma yana cikin aini ba yarinya ba ce nace haka ne Hajiya. Hajiyar Giyaxe ta gyara zama ta ce, to ko wannan tijara da ja’irar yarinyar nan mara kunya tayi wa Babanki da wannan mata shekaran jiya in ban da alhakin Innarku da ya kama su me ya kawo hakan? Nayi maza na vallo varin goro na miqa wa Hajiyar Giyaxe ta shiga goga shi a magogin goronta tana watsa shi a bakinta, ni kuma na qara mannewa da jikinta kafin na qara tambayarta ni me ya haxa su ne Hajiya? Ta ce, uhun in ban da iya shege menene wai kama su tayi suna yin wani abu ranar girkinta bayan kuma dama da nata girkin da natan duk ita kaxai aka haxawa, na sunkuyar da kaina qasa cikin yanayin jin kunya, cikin zuciyata dai cewa nake yi lalle yarinyar nan da kafirin iya shege take, yanzunnan Babana ta yiwa irin wannan iya shegen? Ita kuwa Hajiyar Giyaxe babu ruwanta, sai bayanin ta take yi amma da maganar tazo wurina na gaya musu dukansu ita mijin nata na gaya musu dama gulma da munafurci ne ya saku yin hakan, don ku cutar da Binta, to gashi nan abin ya koma kanku. Ni kam ban yarda na tofa cikin wannan zancen ba, illa iyaka dai na amsa sallamar Hajiya ‘Yar dubu, itama riqe take da food flask xina a hannunta na kalle ta nayi dariya nace, kema kwanona ki ka kawo min? ta ce, oh’oh, wane kwano ne zai fiddo ni a ruwan nan? Uwarki ce tayi wa Mallam waya ta ce mishi wai mijinki babu lafiya, gabana ya yanke ya faxi me Inna ke nufi da wannan wayar da tayi kar dai itama zafina take ji? Ina yake yanzu, ko yana ciki ne a kwance? Tayi tambayar bayan sun gama gaisawa da Hajiyar Giyaxe, sun yiwa juna ban gajiyar biki har tana faxin ai ban san kina nan ba Hajiya da na zo miki hira, Hajiyar Giyaxe ta ji daxin hakan da ta gaya mata ta kwashe zance duka ta yi wa Hajiya ‘Yar dubu, har da yiwa bayanin kwaskwarima na ce ah Hajiya…kan in faxi abinda zan faxa Hajiya ‘Yar dubu ta daka min tsawa ke tafi can ki baiwa mutane wuri akan zai tava ki ne ki ka kwantara mishi qarfe kina neman kashe shi? To zauna ya bar ki ba shi kenan ba sai ki rinqa jiqawa kina sha ko ki kai inda za ki kai. Hajiyar Giyaxe ta ji takaicin maganar, ta ce a’a Hajiya wannan ai ba zancen da za ki yiwa yarinya ba ne, sai kiyi mata faxa kawai irin wanda ya dace da ita. Rannan cikin dare na yi wa Inna waya don in gaisheta, bata xauka ba kamar yanda dama kullum nake mata washegari ma da sassafe na kira ta bata amsa ba, gashi kuma ina ji ta bugo waya ta gaida Ado da jikinshi, a zuciyata na ce ha’a to me na yi wa Inna? Me babban allo yazo gaida Ado wai da jiki, ya gaya mishi gani nan zuwa zai turo ni don in gaishe shi amma naje zauren shima ban same shi ba ya tafi. Na dawo xaki na zauna zuciyata takai matuqa wajen vaci, me nayi musu? Me nayi kowa yake fushi da ni? Ban san yanda aka yi ba kawai naji hawaye suna zuba a idona, kuka na soma yi sosai. Ado ya juyo ya kalle ni, me ya same ki Humaira? Me ya saki kuka kuma yanzu? Ko kuma kin tuna da irin takurawar da nake yi miki ne? rarrashin da yake yi min ya sanya ni buxe baki na ce mishi ban san dalili ba ne kowa sai jin haushina yake yi. A hankali ya ce min haba Humaira, kowa fa kika ce, kenan har da ni cikin masu jin haushin naki? Na gyaxa kaina nuna alamar eh har dashi. Ya ce, uh’uh ni bana jin haushin ki,ina dai so ne kawai in xan rinqa danne zuciyata ina yin haquri kar in rinqa yawan sakin jikina ta yanda zan yi tasa rai a kanki ina matsa miki tunda na gane da gaske kike yi ba kya son haka xin. Ban tankawa zancen nashi ba, iyaka dai na riga na sawa zuciyata wani al’amari tunda na gane har da Inna cikin masu fushi da ni akan Ado, bata lura da irin tasa Ado a gaba da Mama tayi ba kan sai lalle Adon ya sake ni. Kwana wajen huxu a jere daga wurin Inna ake kawowa Ado abincin dare na kuwa gane hakanne a dalilin Sa’adatu da ke kawowa da ganin irin kwanukan da ake zubo mishin kuma kasan ba qaramin girma Adon yake dashi ba a wurinshi, yana gama cin abincin in ya gama abin da zai yi zai duqunqune kan ‘yar kujerar da ke falon yayi kwanciyarshi iyaka dai bai cika yin wani barci ba, bini-bini kuma zan gan shi yana jiqa jar kanwa ko andre lever sold yana sha. Rannan cikin dare ruwan sama mai qarfi ne yake sauka kamar da bakin qwarya, ina kwance can cikin xaki akan katifata bayan na shafe jikina da mayuka masu qamshi da qara laushin jiki sai da na feshe jikina sosai da turare mai sansanyar qanshi, sannan na shige cikin bargona na ruhu. Ina jin yanda ruwa ke sauka da kuma sauraron tsawar da aka yi ina mai karanto addu’o’in da ake yi lokacin saukan ruwa, ko kuma tsawa. Ni kin kawar min da kofin da kanwar nan ke ciki ne? a hankali na ce mishi eh, ai ban san kana so ba ne ya ce ina so mana Humarai, ai kema kin san ina da buqatarta, gashi yanzu ruwan sama yayi qarfi yaya zanyi in je kicin in samo wata? Na ce to ko in zo in kawo maka wata, ya ce bar ta kawai zan yi haquri tunda ga ruwa yayi qarfi. Kwanaki kusan tara a jere babu abinda ban yi ba, wanda zan sa Ado ya tanka min na jan hankali da hila don dai in samu in sallama mishi kaina tunda na gane abinda nayi mishin ne ya sanya Inna har yanzu bata xaukan wayata, amma ya qi. Yana ganina a kusa dashi da lalatacciyar shiga sai yayi maza ya kawar da kanshi ko ya haye kan doguwar kujerarshi ya ja abin ruhuwa ya lulluva ya ce, wai bacci yake ji. Da rana kuma yana Azumi. Cikin zuciyata na ce to ko dai ya tsorata da abinda nayi mishi ne yake ganin kamar a yanzu ma in ya matso kusa dani zan sake maimaita mishi? Gashi Mama ta tasa shi a gaba kullum sai ta shigo gida ta tasa shi a gaba kan sai lalle ya sallame ni, ita auren nawa ya riga ya ishe ta gara kawai a yanzu don in ance sai an kai kwana casa’in to bata san me zamu sake yi mishi ba cikin waxannan kwanakin. Yana faxin kiyi haquri Mama, ba yau ba sai ka ji ta soma rattabo mishi maganganu tana tuna mishi sanda ta xauko shi daga qauye da irin wahalar da yake ciki a wancan lokacin da kawo shi gidanmu da tayi ta maida shi abin da ya zama a yau amma yake nema ya butulce mata saboda aurena. Shi kuwa sai ya ce mata ai ban manta ba, Mama na gode miki da wannan taimako da ki ka yi min ina kuma yi miki addu’ar sakaiya ta gari, ban da haka ma tun kafin kiyi min hakan ke xin uwa ce don haka ne ma a yau bani da wata uwar da ta fiki, to in har hakanne me yasa nake cewa ka sake ta kana qi? Sai ya ce ai shi aure ajali ne dashi in wa’adinshi ya cika sai kaga kamar a mafarki. A wannan lokacin tausayin Ado nake ji, don na tabbatar da daxin komai yake ji ba don gaba xaya al’amuranshi sun sauya, yin su kawai yake yi amma can cikin zuciyarshi ina ganin kamar akwai wani abin da yayi matuqar takura mishi gashi kuma yana dawowa gida daga kasuwa zan ganshi yana wasu abubuwa waxanda shi kaxai yasan me yake yi. A wannan lokacin al’amuranshi da yawa sun sauya, mafi yawancin lokaci a yanzu ya koma shigowa gida ne wajen sha xaya da rabi ko sha biyu duk da ba wata jituwa mai yawa ba ne tsakanina dashi, wannan sabuwar xabi’ar tashi ba daxi take yi min ba, amma nayi kamar ban san me yake yi ba, don kar ya xauka na wani damu dashi. Rannan tun bayan Sallar Magriba ruwan sama ya kece kamar da bakin qwarya, amma Ado bai shigo gida ba da ya idar da Sallar Isha’i, har wajen sha biyu saura kwata na dare, kamar in kulle mishi qofa don in hana shi shigowa xakin in ya dawo, sai naga to na menene yin hakan? Ai kulawama yabawa ne. Da safe ma haka daga sallar Asuba bai sake shigowa ba sai da ya shigo don yin shiri ya fita kasuwa ban ce mishi komai ba, zai kawo cefane in yi girki amma ba zai tambayi nashi abincin ba, in na ajiye ma ba zai tava ba, a zuciyata na ce shima dai zaman namu ya ishe shi hanyoyin rabuwa yake bi wataqila jira yake yi Mama ta sake bashi wani umarni mai qarfi kafin yayi sakin don tasan dai saboda ita yayi. Muna cikin wannan zaman da Ado na kowa ta kanshi yake yi, duk rashin mutuncin da yake tatawa kuma kallonshi kawai nake yi, iyaka dai ina yi ina lissafin kwanakin da suka saura casa’in xin su cika. Ina zaune a tsakar gida bayan fitarshi kasuwa sai ga wayar Inna ta shigo, ina vare-vare cikin yanayin rawar jiki na xauki wayar a dalilin na kirata yafi sau talatin bata amsa ba, Hello Inna salamu alaikum.” Duka gaba xaya na haxa mata saboda zumuxi, bata tsaya amsa gaisuwata ba sai ta soma tambayata ni wane irin zama ku ke yi ne ke da wannan yaron? Da sauri na tambaye ta, wane yaron Inna? Ta ce, mijinki mana, cikin zuciyata nace to itama Inna mijina take kiran Adon? Kafin in soma yi mata bayani kan munanan xabi’unshi da nake shirin gaya mata don in roqe ta ta qara tsaya min da addu’a akan rabuwarmu don ta zo cikin sauqi ba tare da ya cutar dani ba, sai na ji ta soma cewa “kin ga ki shiga hankalinki da ni fa.” Cikin hanzari na tambaye ta me nayi Inna?” Maimakon ta bani amsa faxa ta soma yi mu ma fa da ki ke ganinmu ba ma wulaqanta aure mutuntashi muke yi in miji ya zalince mu, kuma mu zuba mishi ido saboda mun san watarana ba zai yi ba, mu wulaqanci ne kawai ba ma yarda da shi ba kuma mayi wa wani, to amma ke na menene yana iyakar qoqarinshi a kanki kullum sai kin wulaqanta shi, kin ci mutuncinshi, da sauri na tambaye ta, me nayi mishi Inna? Tun bayan wannan abinda ya faru na sake yin wani abu ne? ko shi ya kawo karata wurinki don ya haxa ni dake, kiyi ta fushi da ni? Tunda ai dama can Inna kin sani ba, son mu yake yi ba babu kuma abinda bai yi ba wajen ganin ya taimaka an quntata mana sai kawai nayi ta soma faxin kinci gidan ku na ce miki kinci gidanku da wannan bayanin da kika tsaya kina yi min Inna sake ji an ce min anga mijinki a waje bayan qarfe tara na dare yana zaune to ni dake ne sakarya kawai mara hankali zaku hankatashi ne? Tuni na soma yiwa Inna kuka sosai ita kuwa bata kula da kukan nawa ba faxa kawai take yi, nan da gobe kamar yanzu in ban ji kin xauki matakin gyara al’amari a tsakaninku ba to zaki yi mamakin abinda zan yi akanki ta ajiye wayarta. Kuka sosai na zauna nayi saboda na gane itama Inna a yanzu so take in miqawa Ado kaina bata damu da abinda zai biyo bayan hakan ba bata tsaya nayi mata bayanin da zai fahimtar da ita gane shima adon bai da wani kwaxayi mai qarfi a kaina ba tunda ai nayi mishi tayi na saki shi ne bai kula ba, to sai kuma yanzu da zaman namu yayi matuqar yin xaci bama tsami ba sai ta ce ta bani daga nan zuwa gobe da safe to me take so in yi mishi? Na zauna nan wurin zuciyata sai kake sake take yi ta saqa wannan ta kwance ta saqa wancan ko abincin rana rannan ban yi ba saboda zuciyata a quntace take. Wajen qarfe shida na yamma ya dawo gida, alamar dai daga kasuwa yake don dama lokacin dawowarsu kenan. Ban iya xaga ido na kalle shi ba, saboda raina yayi matuqar vaci da abinda yayi min na haxa ni da Mahaifiyata da yayi, ban tava sanin Inna tana iya fushi dani ba in ban da a ‘yan kwanakin nan a kuma sanadin aurenshi, auren da a farkonshi daga ni har ita qin shi muke yi muna neman tsari dashi har ma ni ce mai danne zuciyata in bata haquri akai, to ko kuma menene yayi mata daxi da auren a yanzu oho? Har bayan Sallar Isha’i ni da Ado babu wanda ya ce wa wani ci kanka, kowa sha’anin gabanshi kawai yake yi, ya fito daga wanka ya sanya kayanshi ya fesa turare kamar dai yanda ya saba yi kullum shirin fita yake yi kamar dai kar in ce mishi komai in bar shi yayi tafiyarshi sai kuma na tuna Inna da kalaman kashedin da tayi min na in ta sake jin an ganshi a waje bayan taran dare zan gamu da ita. A zuciyata na ce uhun in ban da Inna mutumin da ya riga ya mallaki haqoranshi talatin da biyu wanda ba wani ganin juna da mutunci dama can muke yi ba xan gara ma a xan zaman wuri xaya da muka yi shi ne ma aka xan yi wa juna xan alheri a ciki shi ne wai zata yi fushi da ni saboda shi na sani nima wani lokaci nakan xan ji tausayin shi, saboda matsin lambar da yake fuskanta a wurin Mama a kaina. Wacce ita xin kuma da gaske madadin uwa take a wurinshi suna kuma son juna yana girmamata babu wanda yayi zaton zai iya bijirewa umarninta a kaina, to amma duk da haka ina ganin ni an takwaran ace dole ni ce zan nemi shiri dashi ba a daidai kuma lokacin da yake fito min da halaye iri-iri. Qirjina sia harbawa yake yi val-val-val saboda tsananin qin yi mishi maganar da nake shirin yi, sakai yayi ya fita ya miqo hannu zai ja qofar ya rufe a daidai lokacin da na buxe baki na ce mishi ina magana, yaja ya tsaya nuna alamar wai ni yake sauraro. Sai da ya ji ban sake cewa komai ba lokacinne ya sake dawo da kanshi cikin xakin, kin ce kina magana? Ban iya cewa komai ba in ban da hawayen da suka soma zubowa daga idona, shar-shar-shar tanfar dai ba kukan na wuni ina yi ba. Maida qofar yayi a hankali ya rufe sannan ya juyo gare ni, me ya faru Humaira? Baki da lafiya ne? ban iya ce mishi komai ba, babu abin da yake cin zuciyata irin tilasta nin da Inna tayi sai na nemi shiri dashi bayan kuma tasan me hakan yake nufi, ta kuma xiban min qanqanin lokaci na na yin hakan, ganin da na yi ya nufe ni da shirin tava ni ya sani kai gwiwoyina qasa na durqusa ban daina kukan da nake yi ba. Hannu biyu ya saka ya jawo ni jikinshi nayi maza na zame, me nayi miki Humaira? In wani laifi nayi miki yasa ki wannan kukan na roqe ki kiyi haquri, ki kuma gaya min shi don gobe kar in sake yi miki shi. Rarrashin da yayi min ne yasa ni gaya mishi cewar yana haxa ni da Mahaifiyata. Da sauri ya ce min ban tava yin hakan ba Humaira, ai nasan tana sonki ba zan vata ki a wurinta ba, ban da haka ma yaushe ne na soma mu’amalla da ita da har zan je ina kai sukarki wajenta? Me ya faru wanda yasa ki ka ce ina haxa ki da ita? Ban kalle shi ba na ce mishi ta ce ni nake saka yawon da ka ke zuwa, ya xan yi murmushi kaxan ya ce bana fita yawo Humaira, hira nake zuwa shagon Sani mai shayi, wurin taruwar samari ne mu xan yi hira in xan ji xan sauqin zuciyata, kema in bar ki ki xan sake. Ba zan iya zama dake shiru ba in yi ta zuba miki ido ban kula ki ba, gashi kuma a yanzu ina cikin wani hali na canka-cakare, ban san abinda nake ciki ba a yau, ban kuma san abinda zan fuskanta ba, iyaka dai kawai nasan ina cikin wani irin ruxani da ban tava shiga ba, wanda kuma na shige shi ne a sanadin aurenki da nayi. Hausawa suna faxin wai tsalle xaya mai jefa mutum rijiya, ya kuma yi dubu bai fito ba. Wani lokaci naka yin tunani in ce da dai ace na sani to da naji kashedin da kika yi min na cewar kar in karvi aurenki in nayi wannan tunanin sai in ce da nayi hakan wataqila da ban samu kaina cikin halin da nake ciki ba, wataqila da rayuwata bata canza ba daga yanda take wataqila da yanzu ina nan ina zamana lafiya ina tafiyar da harkokina cikin kwanciyar hankali da gamsuwa. A duk lokacin da tunani ya tsananta gare ni na rasa yanda zanyi in warware wa kaina matsalolin da na samu kaina a ciki, sai in ce wa kaina to in sauwaqe miki auren mana in zauna lafiya tunda dama ba da wata kyakkyawar manufa aka karvi auren ba, to in kuma nayi wannan tunanin sai kuma in samu kaina da tambayar kaina, in na yi hakan zan koma kamar yanda da xin nake? Zan iya fidda ke cikin raina, in koma walwala da nishaxi kamar da? In zan yaudari kowa ba zan yaudari kaina ba, ina son zama dake sai dai kuma abubuwan da nake ciki da barazanar da nake fuskanta za su bar mu mu zauna tare? To in ina cikin wannan barazanar me ya kamata in yi? Shine haquri, haqurin kuma yana nufin dole sia na rinqa yin nesa dake saboda kar in aikata miki abinda zai zamo rashin adalci in tilasta ki yin abinda bakya so duk da nayi qoqarin yi miki hakan a baya dalilai biyu ne ko uku suka ingiza ni yin hakan. Na farko dai tsananin matsuwar da nayi a ikanki na biyu jin hirar ku da nayi da Ramla sia na gane har da ita ke zuga ki na uku kuma shine ban hango abinda na hango ba a yanzu, ban ce mishi komai ba, ban kuma tsaya tambayar shi abinda ya han go ba, iyaka dai kawai na miqe na shiga banxaki nayi wanka na fito xaure da farin tawul a qirjina, har lokacin yana zaune a inda na bar shi can cikin xaki na wuce na zauna a bakin katifa bayan na ajiye kayan shafana kusa da ni. Ko ba ka ce kana sona ba ma ya riga ya zama min dole in baka kyautar kaina tunda abinda Inna take so kenan, zuciyata ce tayi min waxannan kalaman. Ina magana ne na xan xaga murya kaxan na gaya mishi bai vata lokaci ba ya shigo, kallo xaya yayi min ya kawar da kanshi gefe me ki ke so in yi miki Humaira? Ban kalle shi ba na ce mishi mai zaka shafa min, ya sake kallona da xan guntun tawul xin da ke jikina ya durqusa a gabana yana faxin ba shafa man ba ne matsalar Humaira, abinda nake tunani shine kanwa ko andre lever sold ba za su yi min wani amfani ba, na ce to shi kenan nasa hannu na lakato man zan shafawa kaina, sai kawai naga ya karve man ya xaga hannayen naw aya sagala akan kafaxar shi wai don ya ji daxin shafa min man sosai. Har Asuba tayi ban iya daina kukan da nake yi ba, saboda dalilai guda biyu, na farko dai in ma Mama taci galaba a kan Ado ta tilasta shi sakina in zama qaramar bazawara kamar yanda dama can tayi buri tunda nasan tana da qarfi akan al’amarinshi, ko kuma aurena dashi ya ci gaba kamar yanda ya kwana yana yi min alqawarin in kwantar da hankalina in saki zuciyata muyi zamanmu lafiya babu abinda zai samu aurenmu. Babu mai sa shi ya rabu dani ya kuma godewa Inna da ta sanya ni nayi mishi alherin da nayi mishi, to in auren namu ya ci gaba da akan son ran Mama ba tunda nasan ba za ta tava son zamana da xan uwanta tunda tun asali ma ba don a zaunan ta sa shi yin auren ba, zan samu zaman lafiya da kwanciyar hankalin da nake buqatar samu a rayuwar aure na ko kuwa na rinqa zama cikin fitinar Mama kenan tayi min ta yi wa mahaifiyata? Shi kuwa Ado wanda ya kwana cikin matsanancin farin ciki gani yake yi tanfar matsananciyar wahalar da na gamu da ita a wurin shi ne ta sanya ni kukan da nima na kwana ina yi, don haka ya kwana yana rarrashi da ban baki da faxin kalamai masu nauyi tare da alqawarin zai tabbatar min da cewar shi xin namiji ne. Na idar da Sallah kenan sai ga Hajiyar Giyaxe ta shigo, na tabbatar Ado ne ya turo ta, kai lalle Ado namiji ne ko ya ya aka yi yaje gaban Hajiya yayi mata wannan bayanin? Oho. Cikin zuciyata ne kawai nayi wannan tunanin, oh’oh sannu Humaira sannu kin ji? Sannu Aishatu sannu da haquri kin ji? Allah dai yayi miki albarka, ya kuma qara rufa wa uwarku asiri ku dukanku ukun, haka aka yi haka nan aka same ku lafiya lafiya sai alheri.” Sunkuyar da kaina qasa nayi ban iya ce mata komai ba, saboda tsananin kunya ai ma kin yi qoqari kin taimaki kanki kin yi abin da ya dace ayi miki, to amma duk da haka sake shiga ki qara wani wankan don ki qara gasa jikinki sosai, ban yi musu da ita ba. Ado ya shiga kai-kawo da hidimomi iri-iri ko kunyar su Hajiyar Giyaxe da Hajiya ‘Yar dubu da suka zo gidan baya yi, wai har hira yake yi da su Hajiya ‘Yardubu ta kalle ni ina makure wuri xaya saboda zuciyata ta qi yi min daxi, ta qi yarda da cewar in sake ta tayi walwala taji daxin al’amuranta, musamman da yake na jiwo maganganun da Mama ta gayawa Ado sanda ya shiga wurinta da safe bayan Hajiyar Giyaxe tazo wurina saboda akwai haxakar bango tsakanin cikin xakina da nata. Amma wai sai Hajiya ‘yardubu ta kalle ni ta ce min oh’oh mahaqurci dai mawadaci, wannan fa shine wai komai wayon amarya a sha manta, to yau dai Adamu ya zama miji qarya kuma ta qare. Kuka sosai na kama yi ita kuwa Hajiyar Giyaxe ta soma yi mata magana Hajiya ke dai munin nan naki bai da wani daxi, zo ki tafi gidanki kije wurin naki mijin ki bar min Aishana ta huta, qaryarta bata wani qare ba me akai kuma da maza, da za ki ce mata wani qarya ya qare?” To haka al’amarin ya zama, shiryawata da Ado sai ta haifar da al’amura masu yawa a ta vangarena dashi dai sai nake ganin tanfar ba a tava son wata ‘ya mace kwatankwacin irin son da Ado ke nuna yana yi min ba, ko kuma don ban tava sanin yanda son yake ba ne, ban kuma tava yin dacen ganin wacce ake son ba ne? oho. A tsakaninshi da Mama kuma abin ya qara cavewa har ya shiga zullumin shiga cikin gida da dai ace yasan in bai shiga ba ita ba zata zo ba to da ya rinqa daxewa bai shiga don maganganun ba su da daxi, to qa’ida ne kullum sai ta shigo da safe da daddare sannan a gabana ma gaya mishi take yi ba fa a kanta muka soma ganin yarinya takai budurcinta ba, duk ‘ya’yan xakina da kake gani ‘yanmata aka same su yauwa ba sabon ba ka tava mace ka haukace. To wannan ma har wata mata ce da za’a ruxe akanta? Yayin da itama Mama take wannan tashin hankali itama Inna nata sha’anin take yi, aike biyu tayi tana tambayar Ado ya bada lokacin da ya ga ya dace azo ayi min jere a sanya min kayana don mu ma mu ji daxin zama a inda muke, shi kuwa sai yayi murmushi ya ce a gayawa Inna tayi haquri kawai ta huta ai shi xin mace ya nema ya kuma samu an bashi, don haka ya gode da alherin da aka yi mishi maganar kaya kuwa a bar su ba shi da buqatarsu waxanda aka kawo mishi sanda aka kawo mishi matar shi sun ishe shi. Kusan sati biyu ne da faruwar abin da ya faru a tsakanina da Ado tun lokacin nan kuwa ban sake yarda ya tava ni ba, tun yana haqurin har dai na qure haqurin nashi, don haka akan dole jiya da daddare na haqura na qyale shi yayi yanda yaso, wanda ba ni da na ji a jikina ba shima yasan ba qaramin takura nayi ba. Amma duk da haka da gari ya waye na fito na kama ayyukana na gida, don dai in samar mishi da kwanciyar hankalin cewar bai qware ni ba, duk da ni kam nasan ya qware nin, ina sunkuye ina qarasa wanke wurin da nayi wanke-wanke ban san hawa ba ban san sauka ba kamar daga sama sai kawai naji saukar bulala a jikina da iyakacin qarfina na qurma ihu. Ina xaga ido naga Mama ne mai dukan, kuma na yanka da gudu na nufi xakina saboda neman mafaka, da saurinta ta biyo ni tana faxin “Ja’ira mai gadon raba zumunci, ai ni ba za a kawo min wannan iya shegen ba, a hanya muka gamu da Ado ya fito daga xakin cikin sauri daga shi sai gajeran wando Boxers fari sol, hannu ya saka ya tare ni ya hana ni shiga xakin ya maida ni bayan shi na tsaya, me ya faru Mama?” yayi tambayar cikin natsuwa duk da dai fuskarshi ta riga ta baiyanar da motsuwar zuciyarshi. “Kaga ja’iri mara kunya, a gabana ka ke tava ta?” tayi maza ta sake xaga hannu zata sharvo min bulalar ya tare da hannunshi, “Matata ce ai Mama don na tava ta ba wani laifi nayi ba, sannan na fara gajiya Mama, zuciyata ba za ta iya ci gaba da xaukar irin wannan abin ba, kin yi sammakon zuwa dukan yarinyar nan alhalin ba ki san yanayin da ta kwana a ciki ba, ko tana da lafiya ko bata da ita.” “A’a qarya kake yi gaya min dai abin da kake son gaya min xin, ja’iri mara kunya mara mutunci akan wannan ja’irar yarinyar? Ai in ba hanzarin raba ku nayi ba to in ba sa’a nayi ba ina zaune ne kawai zanga ka rufe ni da duka.” Ta sake sharvo bulalar ban san yanda aka yi ba sai kawai na ganta a hannun shi, “Haba Mama, wannan fa bulalar doki ce kike duikanta da ita.” Ban ita nan.” Tayi mishi irin tsawar da bata tava yi mishi ba, a’a Mama ba zan baki wannan bulalar ki buge ta ba. Bayan bata yi miki komai ba, in kuma tayi miki ma ai ni ya kamata ki gaya wa in yi mata nasiha sai in bata ji ba ne zan sake dubawa in ga wani matakin da zan xauka amma ba duka kan wannan ba, ai ba zai yiwu a buge ta tana budurwa sannan yanzu ma tana matar aure tana hidimar mijinta da xaukar xawainiyar shi ace za a buge ta, ko nima da nake matsayin mijinta in tayi min laifi a yanzu haquri zan yi tunda nima akwai abubuwan da nasan haquri zata yi dani a kansu. Ni ban tava ganin ana bin matar aure gidan mijinta a buge ta ba sai ita, gaskiya ni kar a sake yi min haka Mama, na roqe ki don bana so. Kasaqe Maman tayi tana kallon Ado, cikin kaxuwa da mamaki. Ai in bar maka ita ta sangarce ta lalace kenan, tafi qarfinka taje tana rabaka da ‘yan uwanka tunda su abinda suka fi iyawa kenan? Ya ce, a’a ni ban san abinda suka fi iyawa ba, Mama na dai san haqququwana da ke kanta tana qoqarin tsare min su, maganar zumunci kuma ba ita ce ta haxa ni da su Ibrahim ba mata suka kawo Baba kuma ya ce bai yarda a rinqa shigo mishi da matan banza cikin gidan shi ba.” Kasaqe Mama tayi tana sauraron Ado cikin kaxuwa da mamakin kalaman bakinshi, uh yanzu nasan kasan mace, tasa kai ta fita kamar ace tayi fushi zance ya qare amma ina? Da daddare nayi wanka ina zaune gabanshi yana shafa min wani mai a tabon shatan dukan Maman da ke jikina, yana yi yana faxin nan da shekara guda in muna raye ba za ki ga tabo a jikinki ba Humaira, tunda ni me za ki yi min in buge ki? Ai in ma kin yi min laifin dukan to bai wuce in yi kamar zan kaxe miki qura da bakin rigata ba, tunda nasan ba za a xauki wani lokaci mai tsawo ba zan dawo miki da lalurata. Muna cikin haka sai ga Mama ta shigo har can cikin xakin, tana ganinmu ta soma faxin uhun, ni fa nasan ba haka kawai kake yin abinda kake yin nan ba, don haka na yafe maka duk laifuffukan da kayi a sanadin zuwanta gidannan in ma haxin baki suka yi na su vata tsakanina da kai to ba su isa ba, ba za su raba mu ba. Rubuta mata takardarta kawai in tasa ta a gaba in kai wa uwarta ita don in gaya mata gata nan na kashe wannan wutar aniyar kowa kuma ta bishi, kamar dai in ce amin sai na fasa saboda Ado da kuma ita Mamar kanta don haka sai na faxi kawai a zuciyata. Shiru Ado yayi yana jinta bai tanka ba tayi rarrashi da ban baki iri-iri bai motsa ba, da ta tunzura da shirun nashi sai ta ce mishi, amma dai ka san dagewa kan zama da itan yana nufin ne kayi zavi tsakanina da ita. Yin wannan zavin kuma ba qaramin fitina zai zama maka ba, don zaka fita daga gidan nan zaka fita daga cikin harkokina, za kuma ka fita daga cikin dukiyar mijina da ka yi wa kane-kane, sannan ko kayi hakan zan kuma iya bi ta wata hanyar da zan rabaka da ita da qarfi tunda in kai ban gaya maka ka ji ba shi uban ta ai zan gaya mishi ya ji. Ya ce mata haka ne.” Muna cikin haka ne sai kawai ga Suwaiba ta shigo da gudu, “Mama wai ki zo da sauri ga Anti Habiba tazo.” Suna barin xakin, Ado ya kalle ni cikin wani yanayi da yafi kama da na tausayin kai, cikin qarfin hali ya tambaye ni in na ce miki ina sonki za ki gamsu? Da sauri don in kwantar mishi da hankali na ce mishi me zai hana? Ya sake kallona cikin natsuwa ya ce, “Duk abubuwan jin daxin da nake ganin kamar yau ma za ki daure kiyi haquri dani in same su sun rushe ko? Nayi murmushi na ce, sai dai in kai ne baka so.” Ya saki wani lallausan murmushi ya ce, “Humaira in tambaye ki mana?” na ce to, dama dai kayi sa’a in san amsar tambayar, kin tava sanin wani abin da yafi aure daxi? Nayi dariya na ce in dai auren na namiji ne kamar ka to ina ganin kamar babu. Daxi ya kama shi, ya jawo ni jikinsa. Rannan kwana muka yi ni da Ado tanfar dai dama mu xin ba baqin juna ba ne, tanfar kuma ya mance da kasadin da Mama ke yawan yi mishi na cewar tari mai qarfi in kayi a wannan xakin ina jin shi, don haka babu wani abin da ku ke ciki wanda ban sani ba. Harkar gabanshi ya yi, nima kuma ban takura mishi ba, saboda a yanzu nima ba zai yiwu in ce ba na sonshi ba, ban da haka kuma na riga na gane Inna tana son auren namu a yanzu in kuwa haka ne to zan yi komai wajen ganin Mama bata qwacewa Inna mijinta ta kuma sake hana ta jin daxin surukinta ba. Washegari da safe Ado ne ya shiga gida don gaida iyayenmu, ya dawo yake gaya min cewar, kin ji ashe wai zuwan nan da Habiba tayi jiya uwar mijinta ce ta kora ta bayan mijin ya naxa mata dukan tsiya, kuma don wulaqanci baki ga doguwar wasiqar da suka haxo ta da ita ba, wai ta zauna a gida daga nan zuwa watanni uku don ta koyi tarbiyya. Na kalli Ado kawai cikin zuciyata kamar in faxi wata magana sai kuma na tuna ba zai yarda in gayawa Mama wata magana ba, don haka naja bakina nayi shiru na vuge da cewa kai abin bai yi daxi ba, yaushe aka yi auren da har za’ace a dawo gida ayi zaman wata uku? Ya ce, to ai kin san bakinta itama kuma ba kunya ne da su ba, na dia ja bakina nayi shiru. Kiyi abin karyawa da ita na ce to. Tun daga lokacin ya zama min qa’ida inna yi girki bayan abincin da nake zubawa na cikin gidanmu zan kuma zuba na Habiba daban. Ado ne yasa ni yin hakan ga kuma kwanukan su Ibrahim safe, rana da dare, amma duk da haka ban fita ba a wurin Mama, wai ban sa mata nata kwanon daban ba, na sata a haxaka sai kace ni tawa uwar ba a haxakan na sakata ba. Saboda gudun fitina, bayan kuma ni nasan zai yi wuya Inna taje tana wani xiban abincin da na aika dashi a kunya da kara irin nata ma ba za ta je tana yin hakan ba. Tuni dama Mama ta riga ta yaxa rashin jituwar dake tsakaninta da Ado, bata bar shi ya zama sirri ba a tsakaninsu, don haka kowa yasan da maganar, ta xauka hakan zai zamo tozartawa ga shi Adon ko kuma Innata ace ta mallake mata qani ta rabata dashi, ta sani ba kanta ta jawa magana ba, don kuwa mutanen da suka santa suka san komai na sirrin zaman gidanmu da dalilin da ya sata tasa Ado aurena sai albarka suke sawa Adon suna faxin mun gode mishi kaga min jarumin yaro ai gara da yayi mata haka. Wannan magana da ta riga ta bayyana kowa ya san da ita yasa dawowar Habiba gida ya zamo abin gulma abin tattaunawa a tsakanin mutane wasu ma faxi suke yi to ai gashi nan tana qoqarin fidda wata ga tata nan an korota. Baba Yahya da kanshi ya nemi wani abokinshi ya xauki Habiba a motarshi suka je har gidan don maida ita xakinta, daga nan su baiwa uwar mijin haquri, tunda dai an yi sa’a hutu suka bayar basu furta kalmar saki ba. Amma uwar mijin Habiba tayi qememe ta qeqasa qasa ta ce ai tunda da bata hutun nan sai tayi shi in dai ba sun gwammace auren ya mutu ba ne, tunda dai ai sun san ‘yarsu zata gidan wasu, amma basu tsaya suka yi mata tarbiya ba. Shi kuwa uban mijin da suka koma ta wurinshi ko zai yi halin maza ya ce a’a tunda an riga an kawo ta to shi kenan iyaka dai a kwave ta don gaba kar ta qara sai yace tunda hukuncin da Hajiya ta zartar kenan sai dai ayi haquri aje kawai in lokacin yayi a dawo da ita. Wurin Ado naji labarin saboda abinda aka yin yayi matuqar vata mishi rai, ni kam murmushi na xan yi can cikin zuciyata dai cewa nayi ashe dai ba Babana kaxai aka yi wa irin wannan kamun kazar kukun ba. Duk da irin hidima da xawainiyar da nake yi da Habiba saboda tausayinta da nake ji gashi kuma na gane xan qaramin ciki ne da ita koma bata nake yi ko ba ta zo ba in aike mata dashi don nasan tana buqatar kulawa ta musamman amma bata gamsu ba haka Mama gaba xaya jin haushina suke yi tanfar dai ni naje na fito da ita daga gidan mijin nata. Kullum dai ta shigo xakina sai ta zagi xakin sannan shigarshi babu qa’idar sallama a wurinta, sau biyu tana samuna kan shimfixa tare da mijina amma hakan bai hanata shigan mana xaki babu sallama ba. In kuma abu ta gani ko na xiban mata sai tasa hannu ta kwashe sauran. Rannan dai abin nata ya ishe ni ta shigo falo babu sallama bata ganni ba ta biyo ni can cikin xaki bayan kuma tasan Ado yana gida muna tare a ciki, don haka na kalle ta na ce mata “Habiba kar ki sake shigo min xaki babu sallama, bana so kuma in kin yi sallamar ma ban yarda dan baki ganni ba ki biyo ni cikin xakina, don kuwa wurin sirrina ne ni da mijina.” Sai da tayi wa xakin kallon banza sannan ta tambaye ni, meye a cikin wannan sukurkutaccen xakin naki da babu komai a ciki sai ‘yan tarkacen kujerun da?” na ce ai ba kayan xaki ne aure ba, Habiba da sune to da tuni anyi nasarar korata daga gidan da kuma ba a koro wasu daga nasu gidajen ba, don haka aure daban kaya daban in ana maganar aure kuwa to miji shi ne maganar in aka yi dacen samun shi to shi kenan zance ya qare. A fusace tace mijin da kike gadara da shi xin dai ai kawunmu ne kuma kema dolenki sai kin fito, na ce oho kin dai riga ni fitowar sannan ko Kawunki ne ba mijin ba ne tunda ba za ki yi abinda nake yi dashi ba, don haka kar in sake ganin kin zo kin xaukar mun wani abu ba ki sanar da ni ba. Kin kuwa san duk yanda ki ka kai da gadara da abinshi saboda kusancin da ke tsakaninku, baki kaini ba, tunda kin sha faxo mana xaki babu sallama, kina ganin mu a shimfixa guda xaya, ko ba haka ba? Gidan Kawu ai ba abin gadara ba ne gidan miji shi ne abin gadara ba ki ga ni daga shigowana sai nayi kane-kane na kankane komai ba? Na wuce zan kai abinda na qwace a hannun nata kicin in ajiye. Ado ya leqo daga xaki “Ke Humaira menene haka? Maida mata dasu, na ce to na kawo na bata ta karva ta fita ta tafi sai kuma gata ta dawo ta dangwarar mun da su ta juya ta tafi tana maganganu kici ki qara kece baquwar daxi na ce eh ni ce baquwar su na kuma gode da na yi sa’a na samu a gidan mijina.” Nayi ta zuba ido ko zan ga Mama ta shigo da bulala ko kuma ta turo a kira mata Ado don ya amsa tambayoyi kan abinda ya faru tsakanina da Habiban, ban ji ba, a zuciyata na ce ta haqura kenan, sai da na gama abincin dare na aike musu da shi naga an dawo min da abincin gaba xayan shi wai in ji Mama ace min bata so in haxa duka in cinye ita tun kafin asan za’a haifi uwata ta same ta ne a duniya tana cin abinci, abincin ma kuma mai daxi tunda ita tuni tun da daxewa a cikin rufin asirinta take raye. Na kalli Suwaiba da ta rattaba min bayanin nayi murmushi da gangan na kalle ta na ce mata Kawu mijina ne ina kuma son shi kamar kamar in yi ya ya? Ni kaxai nasan yanda nake jin shi a cikin raina, don haka babu wani abin da wani nashi zai yi min in ji takaici, balle Mama wacce uwata ce sannan da umarninta ne aka yi min wannan aure mai daxi ki bata haquri kafin in zo da kaina in bata. Ta juya ta tafi ga alama kuma ta gane gatsen da nayi mata, na sake zuba idon ganin Mama ta shigo bata shigo ba. Cikin zuciyata nace in ma dai savanin Mama da Ado yayi tsananin da ta fita harkarshi ko kuma tana nan tana shirya abinda take shiryawa. Ko da yake dai a yanzu itama tana da matsalolin da suke kewaye da ita, ga Suwaiba da aka qi karvar aurenta daga dalilin xaguwa ga Habiba an ce ta dawo gida ta qara koyon hankalin zama da manya, ga Zubaida da yanzu ta watse musu kusan kullum sai ka ji ta tana zuba rashin kunya a cikin gida wai da Mama take yi daga baya kuma ka ji faxan ya rikixa ya koma tsakaninta da su Habiban. Ga al’amarin su Yaya Ibrahim da ya riga ya baiyana har duk mutanen unguwa sun gane kusan kullum sai wani dattijo mai mutunci cikin mutanen dake ganin bari su bada haqqin maqwabtaka yayi sallama da Babana akan su yana tambayar shi anya Alhaji haka za’ayi ta zubawa yaran nan ido ba za a xauki matakin da ya dace ba? Ga Anti Sha’awa daga zuwan Amarya kuma wai komai ya susuce mata, bini-bini sai ka ganta a gida ita da ‘ya’yanta wai tayi yaji saboda wai mijin yana nuna bambanci a zahiri, sai Maman ta kwaveta ta ce mata ta koma xakinta kawai taje ta duba taga irin matakin da ya dace ta xauka saboda a yanzu ba zai yiwu tazo ta zauna a gida ba, tunda ga Hajiyar Giyaxe ga kuma maganar Suwaiba da Habiba. A duk lokacin da na tuna Mama da irin iko da gadaran da ta gwada na ganawa wanda bata so azabar yunwa da ta wulaqanci da duka sai in ji kamar zan ji daxin abubuwan da suke faruwa da ita, wanda nasan mafi yawancin mutane dariya suke yi mata sai dai kuma in na tuna ‘yan uwana ne sannan Babana ba jin daxin hakan yake yi ba sia in ji tausayi ya kama ni, in ce ina ma dai a kanta abin yake faruwa ba akan ‘ya’yanta ba. Rannan Ado ya dawo gida bayan Azahar, cefane ya sake kawowa mai yawa sosai da sauri na fito daga xaki na karve shi guda xaya, xayan kuwa qin bani yayi yace muje in kai miki wannan. Muna tafiya yana tambayata sau nawa ki ka yi aman bayan fitana? Na ce, a’a ban ma sake ba ina jin fa dama tin nan ne ya xaga min hankali don nafi son da safe insha kunun gyaxa da alala, ya ce to ki jiqa gero mana, na ce to ko kuma in ce Inna tayi min qullin, ya ce a’a ina dalili baki taimake ta kin yi mata ba sai ki sa ta aiki? Ban yi magana ba na soma fiddo cefanen don in san irin adanar da zan yi mishi, tunda ko jiya yazo da wani sai na ji ya ce min za ki yi miyar ne ta soyu da kyau ta yanda zata daxe bata yi komai ba, ta Haiyar Giyaxe ce gobe zata tafi. Da sauri na xago kai na kalle shi, tafiya zata yi?ya ce ina laifi goben ta ce watanninta uku kenan a gidan, na ce sai tayi ai kwanci tashi babu wuya, amma kuma har na soma kewarta tun kafin ta tafin. Ya ce, to ko zan je ne in gaya mata ta haqura ta bar tafiyar sia kin haihu an yi suna tukunna? Shiru nayi ban amsa mishi ba saboda ina jin kunyar irin wannan zolayar da yake yi min. Da wuri sosai na gama aikina na kawo mishi ya gani, ya ce min to sai ki shirya in anyi Sallah sai muje tare kiyi mata sallama, na ce to. Cikin zuciyata ina murna zan shiga gidanmu har inga Innata, bayan kwanaki tamanin ban ganta ba, duk da ga ni gata saboda bata shigo ba nima bai bar ni na shiga ba. A wani gefen kuma ina fargabar ganin Mama saboda mun yi kwanaki ba mu sa juna a ido ba. Wanka nayi sosai na xau kwalliya mai kyau sai sheqi nake yi ina xaukar ido, doguwar riga ce a jikina ta shadda gwan shep xinta yayi matuqar fitar da surata da kyau ga xinkinta yayi matuqar kwanciya. Ado ne ya saya min shaddojin guda biyu ya bayar aka xinka min su, na sanya qananan ‘yan kunne da abin wuyansu waxanda suma shi ya saya min su a dalilin sha’awar da suka bashi sai dai a hannuna ne na sanya wara-waran daham da zobunansu na kuma xaura wani xan siririn agogo da zoben G.L, suma kyautar Adon ne. Ya kalle ni cikin wani yanayi da na tabbatar nayi matuqar burge shi, ya ce “Ba za ki fesa turare ba ne? ai gida kawia zamu shiga.’ Na ce ‘uh’uhn bana son turaren na jikinka ya ishe mu, bai ce min komai ba in ban da kallona da ya sake yi. “Xan kawo min turame biyu cikin kayan aurenki aro.” Nayi murmushi na ce, zan fa xunka su, ya ce eh na ji kawo min dai, naje na kawo mishi akwatin ya zubawa zannuwan ido yana kallonsu, babu wata atamfa a ciki da ta wuce dubu xaya da xari biyar, ni nafi zaton ma zannuwan da dangin uban Ado suka zo dasu daga qauye ne na gudummuwa Mama ta zuba a cikin akwatin ta xora sabulai da man shafawa ta bayar. Zavo min guda biyu masu kyau a ciki, nasa hannu na zavo mishi su ya kuma gamsu da zaven da nayi mishin ya sake maida kallonshi kan abinda ya saura a ciki, dama zannuwan shida ne? na ce a’a takwas dai kwanaki baka ari guda biyu ba? Ya ce, af, haka aka yi to zuba min waxannan sabulan da man in haxa mata, na ce to ai ka kwashewa Hajiyar Giyaxe kayan auren nawa. Ya ce eh ai ba kya son su, da kina son su da tuni kin xinka su kin saka, na ce to ai yanzu ina son su zan kuma xinka su in xaura don ma dai bani da keke ne da da kaina zan xinka abina. Bai amsa ba iyaka dai ya tasa ni a gaba muka fito, bayan yasa makulli ya kulle qofar xakinmu ya kuma sake kulle qofar gida. Na sake xaga ido na kalle shi daidai sanda yake kulle qofar gidan, idanuwanmu suka haxu na xan kawar da kaina gefe ya ce, uh sai dai ki faki ido ki kallan mun kwalliyata amma ba ki san ki ce tayi miki ba, ban tanka mishi ba iyaka dai nasan yayi kyau ba kaxan ba. A tsakar gida Hajiyar Giyaxe tana alwala ta amsa sallamar da muka yi tare da yi mana oyoyo mai yawa, na ce hala Hajiya Sallar Isha’i zata yi? Ta ce uh’uh me zan zauna yi har yanzu ban yi Sallah ba? Alwalar kwanciya nayi, na ce to kwanciyar ma har da alwalarta? Ta ce eh, muka bi bayanta zuwa xakinta wanda dama shi ya fi kusa da qofar zauren gidanmu har muka shiga bata gama yi mana bayani kan muhimmacin wannan alwalar ba, muna zama kan shimfixar da tayi mana ta koma bakin gadonta ta zauna tana kallonmu. Ni in ce ko dama iya shege ne kawai ya saki yin abinda ki ka yi ba qin auren kike yi ba? Na yamutsa fuska naqi yin magana, yayin da Ado ya ke dariyar maganar tata da tambayar ta me ki ka gani Hajiya? Ta ce eh to abin ne nake kallon shi wani iri, ashe dama ana so ake kaiwa kasuwa, an je don iya shege har ana qwale miji da guduma, yanzu kuma sai naga ana ina aka saka dashi ba aso ko quda ya sauka akan shi. Ado ya kama dariya yayin da ni kuma na shiga shure-shure cikin yanayin shagwava da jin kunya ina cewa bana so Hajiya, bana so. Kin gani Hajiya za ki sa ta tayi shure-shure duk ta shuire kwalliyarta ta lalace, yana maganar yana kallona cikin murmushi ga alama daxi ya kama shi an ce ina wai ina aka saka dashi, ai ni da cewa nayi Hajiya tafiya tun yanzu ba za iki bari sai wata daga cikin amaren ta sauka anyi suna kafin ki tafi ba? Hajiyar Giyaxe ta qyalqyale da dariya ta ce, kai dai gaya min kawai in sani cewar taka amaryar tana kan hanya.’ Xaure fuska sosai nayi naqi kulawa da zancen nasu, iyaka dai na jawo kayan da muka zo mata da su na ajiye mata a gabanta na kuma ciro kuxin da ya bani ya ce in bata na haxa tayi ta godiya tana sa mana albarka, tayi man addu’ar samunzaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma zuriya mai albarka. Ado ya ce amin. Ta miqe ta xebo wasu kayan tana nuna mana daga gidan Atika aka kawo su, nayi murna nayi musu addu’a na tashi na bar Ado yana sa hannu a aljihu alamar zai mata wata kyautar ta daban. Ina barin xakin Hajiyar Giyaxe can wurin Mama na shiga, samun Babana da nayi a xakin baisa ta sake min fuska ta amsa gaisuwar da nake yi mata ba, shima Babana amsa gaisuwar tawa a yanaayin kadaran-kadahan na dai san sau biyu na ganshi yana fakon idon Mama yana kallona. Ga dukkan alamu kuma nasan canzawar da nayi ne yafi komai bashi mamaki, gashi kuma nayi kwalliya ta xaukar hankali, ban wani ja zance yayi nisa ba, saboda ganin irin karvar da suka yi min na miqe na fita. Ban tambayi su Habiba ba don kuwa nasan dukkansu suna jin shigowata suka yi kamar basu ji ni ba. A kusa da qofar xakin Inna na ci karo da wani lafiyayyen injin xin wanki mai matuqar kyau sai da na qare mishi kallo sannan na shigo cikin xakin nata tana zaune kan kujera, gaskiya ne da Hajiyar Giyaxe ta ce min ta fara murmurewa. Ina murmushi na miqa hannu na xauki Adam karo na farko da na ji ina son shi tare da sunan da aka sanya mishin. Na sake kallonta cikin murmushi na ce “Inna rowar yaron nan take yi sai in yi ta aiken a kawo shi kina hanawa, bata kula zancen ba, ta miqe taje ta kawo min yugurt mai sanyi mara sugar ta ajiye min, nayi murmushin farin ciki saboda ganin canjin da ta samu, na ce Inna ashe injin xin wanki kika samu shi ne nake ta aiken ki ba da kayan wanki in yi miki kina cewa babu, ba ki gaya min ba. Wa ya saya miki? Ahmad ne ko Salisusu? Ta waiwayo a hankali ta kalle ni cikin natsuwa ta ce min shi mijinki fa? Ba kiyi tunanin shi ya saya min ba, sai ki ce Ahmad ko Salisusu? Shiru nayi ban ce mata komai ba, itama ta xan yi shiru sai jimawa kaxan ta kalle ni ta ce min to, wanda ba kya zaton ne ai na xauka ya gaya miki ne shi yasa ban ce Sa’adatu taje ta gaya miki ba. Amarya ce yau a gidan tayi maganar cikin murmushi nima na xan yi mata murmushin kaxan ta shigo har cikin falon Inna ta zauna muka gaisa, ta miqe zata fita tana faxin kai amma xinkin nan naki yayi min kyau a ina aka yi miki? Na ce a’a ban sani ba, haka naga an kawo su a xinke ta sake cewa kai ai auren wayayyen miji mai son matarshi daxi ne dashi. Shiru nayi ban tanka mata ba, ta fita na kalli Inna cikin mamaki na ce har cikin xakin nan yanzu Zubaida take shigowa? Bata tanka ba ta ce min sha nonon mana, na ce uh’uh Inna ina dashi a gida ta ce haka ne ai daga wurin naku aka kawo to me za ki ci? Na ce ban son komai Inna sai dai ina so kiyi min qullin kunu tayi maza ta kalle ni tana tambayata yau kuma qullin kunu kike so? Naga kuma aike ba mai san kunu ba ne shiru nayi ban ce mata komai ba, itama sai kallona take yi na kuma san kyau taga nayi. A’ah auren naku fa ya xan kwana biyu kai tafiyar lokaci bai da wuya, na ce me ki ka gani Inna? Ta ce, to ko wannan canzawa da kika yi ai ya isa a san ba shekaranjiya bane ban ce mata komai ba, ta xan sake yin murmushi ta ce ai dama tunda naga maigidan yana maida jikinshi na ce to an zauna lafiya kenan. Shi dai aure ai kin san ba komai ba ne illa yi nayi bari na bari in zaka zauna da mutane kuma to ka zauna da su akan gaskiya nace to Inna. Ado yayi sallama ya shigo Inna tana yi mishi sannu da zuwa ga dukkan alamu dai ya zama xa sosai wurinta cikin zuciyata nace kai Ado ma dai da qoqari yake ko da dai shi da bakinshi ya sha kiran kanshi da ‘namiji’. Inna su sa’a basu taso ba ne? ta ce mishi eh in ma sun tashin ba su riga sun iso ba ya zauna suna hira da jin hirar tasu kasan sun riga sun zama abokan hirar juna sosai, a hirar da suke yi na fahimci Ado ne ya sanya Sa’adatu da Baba qarami a Makarantar Islamiyar unguwarmu ban dai tsoma musu baki cikin maganganun su ba. Suka yi hirar su suka gama da ya ce mata zamu tafi sai ta ce mishi da jira nake yi Sa’adatu ta shigo don ta raka ku da kai da kafin nan ko sai da safe a kawo muku? Ya ajiye xan makullen da ya kulle qofar gidan ya ce mata gasi in ta dawo ta kai mana ta rufe gidan ta kawo makullin nan sai mun dawo zan zo in karva ta ce mishi to muka fito. Ba mu dawo ba sai wajen goma da rabi na dare saboda unguwannin masu yawa muka je har gidan mai babban allo da gidan Alhaji mai kuxi da gidan Musa abokin Ado wanda shima bai daxe da zama ango ba, a hanya muna dawowa tun daga nesa Ado ya hangi Mama a tsaye a qofar gida cikin damuwa yake ta nanata faxin me kuma ya fito da Mama waje tare da waxannan sakarkarun yaran? Dama dai ayi sa’a ba wata fitina suka xauko mana ba na ce to amin muna isowa yayi maza ya fito daga cikin taxin in ban da ma na tsaya na xauko mana ledar sayayyar da yayi mana da mai taxi ya tafi dashi. Lafiya kike tsaye a waje a cikin sanyin nan Mama? Ina fa lafiya tana faxi tana qara tafa hannu tare da salati, me ya faru Mama? Ya qara tambaya don ya san abinda ya farun, uhun xaukan wa kaina abinda yafi qarfina nayi na xauko fitina na saka cikin al’amarina yana nema kuma ya buwaye ni ya buwayi duk wani nawa. Cikin natsuwa Ado ya tambaye ta fitinar sai kawai ta nuna mishi ni, yayi kasake yana sauraronta tana gaya mishi nema take sai ta raba ka da zumuncinka ba kuma zai yiwu ba, ba zan barta tayi nasara ba, don babu inda na ji an ce don mutum bai yi aure ba ba zai shiga aljanna ba. Buqata dai kawai mutum ya kama kanshi ne ba a qi aure kuma a rinqa leqe-leqe ba, to amma zumunci fa? Sau nawa ka ji ana cewa wanda bai yi shi ba ko yaje zai wuce saboda a yakanshi sun kai sai makaran zumuncin ya kamo shi ya hana shi wucewa? Tana rufe baki don hutawa Ado yayi maza ya tambaye ta me aka yi ne Mama? Ta ce, ai dama nasan ba za ta yi akan sanin ka ba, to dubi qofar gidan yanda ta kama shi ta kulle ta bar su suna tsaye a waje don su ce kaina ku samu matsala a tsakaninku. Ado yayi mata rantsuwa ya ce mata ba ita ce ta rufe gidan ba, ni ne Mama, ya kuma gaya mata yanda aka yi duk har ya bar key xin a cikin gida nan da nan kuma ya tura ni na shiga na karvo na samu tana cewa haba Ado, yau ku ke tare da su in ba ita ta saka ba yaya za’ayi ayi haka? Ni kam cikin zuciyata na ce Mama kenan, wanda take so ya more baya laifi a wurinta, komai yayi sai ta ce ba shi ba ne in ma shi da kanshi ya ce shi ne taga zai xorawa kanshi laifin da bata so ya xauka sai ta ce to sa shi akayi. Ado yayi ta bata haquri har dai ya samu ya lallavata ta shiga gida. Muna shiga xakinmu ya kalle ni cikin natsuwa ya tambaye ni “Humaira za ki iya zaman qauye kuwa? Da sauri na bugi qirjina na ce qauye? Ya amsa eh, na ce hu’un su qauye manya, to ni me ma zai kai ni wani qauye? To ko Giyaxe abinda yasa take yi min daxi ai saboda Hajiya tana can ne. Bai sake yin maganar ba, iyaka dai rannan nasan Ado bai wani yi bacci sosai ba duk da ya saba yin bacci mai nauyi dake baiyanar da alamar gajiyarshi a duk lokacin da al’amura suka afru a tsakaninmu, amma a yau har cikin dare da na farka idon shi biyu na ganshi. “Lafiya baka yi bacci ba?” Ya ce, min lafiya, tunaninki ne ya hana ni yin bacci, ya kamata in samar mana wani wuri da zamu zauna cikin ‘yanci da kwanciyar hankali Humaira, bai kamata ace kowane lokaci kina cikin fitina da fargaba ba, musamman a wannan lokacin da kike da juna biyu.” Juyawa nayi naci gaba da baccina na qi kula zancen nashi saboda bana son kirana mai juna biyu da yake yi. Tun washegarin ranar dai na lura Ado yana yin wasu abubuwa da suka fi kama da lissafe-lissafe da kuma kintse-kintse sai dai da yake gaba xaya al’amarin ya tafi ne kan takardu sai ban maida hankalina wajen neman sanin abin da yake ciki ba tunda dai bai ce min ba sai nima ban tambaya ba. Kwana biyu da tafiyar Hajiyar Giyaxe ina zaune a falonmu ni da Ado in har da wata rana da na soma tunanin lalle juna biyu yana nufin wani abu mai girma da muhimmanci da wahalarwa kamar yanda kullum Ado ke gaya min, to ranar ne don kuwa wuni nayi a galabaice saboda amai, ko abincin rana ban iya girkawa ba balle na dare. Ado ya dawo daga kasuwa da yamma ya same ni a kwance nayi mishi bayanin abinda ake ciki ya ce to abin da nake faxin zai tabbata kenan? Ya sake kallona ya ce min to sannu kin ji Humaira? Na ce mishi to ya sake kallona ya ce min amma in na roqe ki ai zaki iya yi min wani alheri guda xaya ko? Na ce mishi eh, ya ce to wanka nake so kiyi ki sanya min wannan rigar a jikinki in ganta, xazu naje na karvo ta daga wurin xinki in kin iya yi min haka shi kenan don ta rashin girki babu komai, sai in fita in je in nemo mana abinda zamu ci na ce mishi to. Muna zaune da Ado bayan nasha kwalliya cikin sabuwar rigar da ya karvo min daga wurin tela ta xinkin kanfala ‘yar asali, sai kallona yake yi yana murmushi ke kin gan ki kuwa? Ban ce mishi komai ba iyaka dai kawai nima nasan nayi kyau, to me dame kike so in je in kawo miki?na xan rage fara’a kaxan na ce mishi ni dama ka bar ni haka kawai tunda lalurar ciki take ai ba a biye mata…zai ci gaba da yi min magana sai ga Suwaiba ta shigo da gudu, murna take yi farin ciki mai yawa ne ya bayyana a fuskarta wai in ji Baba wai ku zo yanzu-yanzun nan kai da ita. Tana faxin hakan ta juya da gudu ta tafi tanfar dai wata yarinya ‘yar qarama, Ado ya waiwayo ya kalle ni, nima kallon nashi nayi ko lafiya? Na ce ba zan iya sani ba sai mun je mun ji. Nasa hannu na xauki gyalena, ya kalle ni cikin sanyin jiki ya ce ko dai za ki bari ne in je in ji tukuna? Na ce to ai cewa tayi muje tare kar ka je kai kaxai xin kuma ya zama maka laifi, ya ce haka ne to muje. Muna shigowa gida Babana muka fara gani a tsakar gida sai Mama da kuma Innata da ke can wajen bakin qofarta ga dukkan alama kuma kiranta aka yi ta fito. Muna shiga gidan muka tafi qasa don gaida Baba, amma maimakon ya amsa gaisuwar da Ado ke yi mishi sai ya kalle ni ya ce min, ke ga xakin uwarki can tafi ki shiga, kaima ga taka uwar nan jeka wurinta shi kenan kowa ya riqe nashi, magana kuma ta qare dama ita ta ce a baka ita na baka yanzu kuma ta ce ta gano munafurci da raba zumunci in raba na raba magana ta qare kar in sake jin wani ya ce wani abu zan sava mishi. Cikin kaxuwa mai yawa Ado ya ce ka raba min aure Baba me nayi maka? Baba bai tanka mishi ba ya wuce ya shiga wurin Zubaida, ga alama a wurinta yake. Inna ta biyo bayana zuwa cikin xaki don ni kam ma ban wani tsaya jin komai ba, tuni na haye kan gadonta na kwanta sai Ado da Mama ne a tsakar gida, “kin sa Baba ya qwace min mata Mama? Ta ce ka kwantar da hankalinka ai dama ni nasa shi ya baka ita yanzu kuma ba ka san wacce zan sa a baka ba nan da kwana tara ma za’ayi komai tunda na riga na gama komai ai ba zan barka ka zauna haka ba, tunda nasan ka riga ka xanxani daxin mace. Ba ke ki ka bani Humaira ba Mama kaddara ce ta bani ita ba kuma zan rabu da ita ba, ba kuma na son kowace iri za ki sake bani in gidan da ki ke cewa zan bari ne akan zama da ita zan bar shi zan fita daga harkokin da kike cewa zan fitan miki, zan fita daga dukiyar tashi abinda ba a tsammani na zan mayar dashi zan riqe Humaira ne kawai Mama don ita kaxai xin nake buqata a yanzu. Kai Ado, tayi mishi tsawa mai qarfi zaka zage ni ne? yayi maza ya ce ba zan zage ki ba don ke uwata ce amma kuma ba zan yarda ki raba ni da matata ba, Mama ban ga abinda tayi miki ba ina kuma sonta. Ni kuwa ina shiga banxakin Inna na kama aman tun daga falonta har bayan gida da sauri Inna ta biyo bayana tana qoqarin taimakona. Ado kuwa ya juya ya fita ya bar gidan ban san inda ya tafi ba sai dai bai xauki lokaci mai tsawo ba sai gashi ya dawo, kayayyakin ciye-ciye yaje ya sayo min har cikin xakin da nake kwance ya shigo bai saurari maganar da Mama ke yi mishi na kar ya shiga xakin nan ba haquri yake ta bani wai in kwantar da hankalina kar in ce zan xaga hankalina. Nayi murmushi na ce babu komai ni kam ai dama a nan nake su suka xauke ni suka baka ni in sun ce in sake dawowa ba zan zarge su ba don haka kaima kayi haquri, ya ce min to me kike so in kawo miki yanzu? Na ce babu komai kar ka damu ai ga Inna in ina son wani abu zata yi min, ya ce to sai da safe. Tunda Ado yasa kai ya bar gida cikin dare a cewar sai da safe bai sake dawowa ba, babu ma wanda ya ce ya ganshi a unguwar don ina jin Mama tana tambayar ‘ya’yanta sun ga Kawunsu kuwa? Su ce mata a’a Inna ma tayi ta neman shi a waya amma babu layinshi, ya rufe. Ina jin ta tana faxin ni Binta wannan yaro ko ina ya shiga haka oho. Ban dai ce mata komai ba amma ni kaina a cikin damuwar nake don kuwa nasan yana cikin vacin rai mai yawa. Cikin zuciyata dai addu’a sosai nake yi mishi don kuwa ina matuqar tausayin halin da ya samu kanshi a ciki wanda kuma a dalilin aurena ne ko da dai na sani a farkon al’amarin ni suka yi nufin cutarwa, amma hakan ba zai rage min komai a tausayinshi da nake ji ba tunda nima a yanzu ba zan iya cewa ba na son shi ko kuma ban damu dashi ba. Rannan da safe muna karyawa ni da Inna na kalle ta cikin natsuwa na ce mata “Yau kam in Ado bai zo gida ba Inna zan fita in neme shi a irin gidajen abokanshi da muka jejje, ta ce to ya yi kyau kam hakan duk dai ke ma ba lafiya ke gare ki ba, amma abin ai yayi tsanani daga sai da safe abu ya tafi har kwana uku? Muna cikin wannan maganar sai muka jiwo Babana a tsakar gida yana cewa Mama, yaron nan fa Ado ko kasuwa ba ya zuwa, ta ce rabu dashi ja’iri mara kunya da butulci wai shi nan yayi fushi ne a dole ga mai zafin rai ya bar gida, aje a nemo shi in yaso ya samu hanyar cewa sai an mayar mishi da ita sannan zai dawo to yaje duk inda za shi an hana shi itan yafi ruwa tafiya. Inna ta ce uh’uhun abin tausayi yana zaman zamanshi dai aka tsoma shi cikin wannan fitinar da ba a sa shi wannan auren ba ai da yana nan yana harkokinshi da ya saba cikin kwanciyar hankali, kema da yanzu kina naki xakin, shiru nayi ban ce mata komai ba. Sa’adatu ce ta shigo gida da gudu rungume da qatuwar Jakar da kayana yake ciki wanda kayana ne na gida da kayan da nayi biki da su a ciki don tun ina gida nake amfani da Jakar. Hajiya Kubra ce ta bani ita, tana ajiye Jakar a tsakar falon Inna ta sake komawa da gudu na jawo Jakar kusa da ni nasa hannu na buxe ta ina dubawa duk wani abu nawa da naje gidan da shi da wanda ya saya min da kanshi ya tattara min ya saka a ciki har da akwatin sarqoqina don dama yasan in da nake voye su, na miqa wa Inna akwatin sarqoqin tare da yi mata bayani gaba xaya kayana ne Ado ya tattara ya aiko min da su. Ta xan yi shiru cikin tunani kafin zuwa can ta ce duk abinda yayi niyyar zartarwa don ya samar wa kanshi kwanciyar hankali da ya rasa muna yi mishi addu’a ta fatan alheri ba kuma zamu ji zafin shi ba. Cikin zuciyata na ce itama Inna ta hango abinda na hango kenan, cewar Ado zai haqura da aurena ne yasa ya tsintsinto kayana ya aiko min dasu. Muna cikin haka sai ga Sa’adatu tana shigo da kayan kallon shi da ya saya bayan auren mu a dalilin Mama ta ci gadon nashi na samartaka, Inna tayi maza ta ce a’a wannan ai ba nan za ki kawo ba can xakin Mama za ki kai mishi, ta ce a’a nawa ne bani ya ce yayi in sa a xakinmu in rinqa kallo. Da sauri Inna ta ce a’a shi da yake cikin wannan hali yayi kyauta da kaya mai daraja haka? Na ce, a’a Inna bashi ya bata ba? Ta ce to ina yake yanzu? Ta ce na dai ganshi ya baiwa Yaya Ibrahim makullan gidan ya ce wai yaba Mama shi kuma ya hau mashin ya tafi. Inna ta sake cewa kai wannan al’amari yakai inda yakai, yaron nan yana cikin wani hali kuyi mishi addu’a. Sa’adatu ta ce wa Inna shima ya ce in gaya miki kiyi haquri kuma kiyi mishi addu’a ta ce to ni me yayi min ma? Nan da nan kuma ta shiga jero addu’o’in da yace tayi mishin, zuwa can kuma ban san tunanin da tayi ba sai naji ta ce ni in da zai samu ya kama muku haya a wani wuri ai da nasa an gyara muku gidan ba kaxan ba ta shiga bani labarin irin gadaje da kujerun waje da Alhaji Abba yasa ake kawowa Hajiya Kubra wai don itama ta rinqa juya kuxi a hannunta. Inna tana faxin haka sai zuciyata ta shiga raya min irin qayataccen gidan da zata shirya mana in har Ado ya kama mana haya da zai yi hakan kuwa ko da wane irin daxi zamu ji ni da shi oho? Washegari da safe ne Ado ya sake zuwa unguwar har ya shigo gida sai da ya fara shiga wajen Babana ya gaishe shi sannan ya shiga ya gaida Mama ya fito zai shigo wurinmu ina jin Mama tana ce mishi ai na xauka ba za ka sake shigowa gidan ba ne saboda an qwace maka Inna Majandi, in kuma baka daina shigowa kana shiga wannan xakin ba to zan sa mai gidan ya hana ka shiga mishi gida, ban ji ya ce mata komai ba. Inna ta amsa sallamar da yayi ya shigo suna gaisawa naji tana tambayar shi lafiya dai ko? Ya ce qalau Inna, na xan yi zirga-zirga ne saboda in warware wasu abubuwa wasu kuma in kammala su, na kuma gama shi ne nazo in yi miki bayani, ta ce mishi to, daga ni har ita muka shiga sauraro don mun fi zaton takardar sakin aurena ya kawo min, sai na ji ya ce akwai wasu sharuxxa da kwanaki aka sanya min akan aurena ban sani ba ko rashin cika su ne yasa Baba ya baiwa Humaira umarnin dawowa gidan don haka na tsaya naga na cika su. Inna tayi shiru alamar shi take sauraro shima kuma da yake yasan hakan sai kawai ya ci gaba da yi mata bayani na farko akwai maganar gida cewar in bar shi na biyu akwai jarin Mama da nake juyawa sai na uku shi ne in fita gaba xaya daga cikin kasuwancin Baba. Inna ta ce tow, ya ce to waxannan xin duka na shirya yin su don haka ne ma naje nayi wa Baba Yahaya bayanin komai ya kuma ce min in zo yana zuwa in na zo xin kuma kafin ya iso to in shaidawa Liman da Malam Harisu makwabcinmu don su zo su taya shi zama shaida na zan mayar musu da abinda suka nemi in mayar musu don suma su bani matata da suka karva. Inna ta sake cewa haka ne, ya ce to bayan wannan ma Inna akwai gidajena guda biyu da nake karvar hayarsu da bus da take yi min zirga-zirga ina kuma da shago da ake yin xikin a ciki shi wannan shagon nawa ne da kuxina na gado na saye shi na kuma zuba kekunan, Musa ne yake lura da komai nashi, don shima gwanin tela ne ban kuma tava samun matsala da shi ba, yasan komai nawa na gaya mishi abinda ya saba bani ya rinqa kawo miki ki rinqa sayen sabulun wankin yara, su kuma gidajen da motar zan mayar wa Baba da abinshi don a cikin dukiyarshi na saya. Inna tayi maza ta ce a’ah to in kayi haka kai kuma fa? Ba wahala kayi wa dukiyar ba, ka kuma yi tattali?ya ce eh, amma ban same su ta hanyar da ta dace ba, don haka zan mayar mishi zan je in nemi nawa ni dai in suka yarda muka rabu lafiya dasu suka bani matata na tafi da ita to shi kenan komai mai sauqi ne, sai da tayi tayi mishi addu’a da godiya kan alherin da yayi mata sai ta ce mishi to in ka xauki matarka ina za ku koma? Sai da ya xan yi shiru tanfar dai nauyin abinda zai gaya matan yake ji zuwa can sai naji ya ce mata qauyenmu zan koma, da gudu na fito daga xakin da nake kwance ina riqe da xankwalina a hannuna durqusawa nayi da gwiwoyina biyu a qasa na ce mishi qauye? Bai kalle ni ba bai tsaya amsa maganar da nayi mishi ba sai kawai ya ci gaba da yiwa Inna bayani, dangin mahaifina mutane ne masu karamci da zumunci, na kuma yi miki alqawarin matuqar ina raye cikin lafiyata to ba zan bar Humaira ta shiga cikin matsalar da zata dame ta ba, don haka na roqe ki ki qara yin haquri ki kuma yafe min abubuwan da nayi miki. Cikin wata irin murya mai rauni naji Innan tana ce mishi to amma kai ma na roqe ka kayi haquri ka fara tafiya tukuna in yaso daga baya sai kazo ka xauketa. Maimakon ya ce wa Inna to sai kawai naji ya ce mata a’a Inna, ai in nayi haka ya zama min kenan tanfar na rasa komai bayan kuma don in same ta ita kaxai xinne yasa na bayar da komai xin da nake da shi saboda haka zan tasa ta a gaba ne mu tafi. Ina jin ya faxi haka ban jira amsar da Inna zata bashi ba sai na ce mishi a’a babu wani qauye da zan bika mu tafi, ban tava zuwa qauye nayi kwanakin da suka wuce guda bakwai ba, bana iyawa. Sai kuma haka kawai in bika can in zauna? Ba a can aka haife ni ba mahaifiyata ma ba a qauye aka haife ta ba. Ado ya tashi ya fita saboda jin sallamar Baba Yahaya, ya barni a nan ina durqushe ban gama lissafa mishi abinda na fara ba, yana barin xakin Inna ta kalle ni ta ce qauye kuma? Wannan wace irin fitina ce? Maimakon ta saurari amsar da zan bata tunda naga kamar tayi min tambaya ne sai kawai naga ta rushe da kuka, kuka kuwa mai tsanani irin wanda ban saba ganin tana yi ba. A tsakar gidanmu gaba xaya mutanen da Ado ya nema sun hallara ana zazzaune har da Babana wanda yasha mur sosai don nuna alamar babu wasa, Mama ma tana gefe tun kafin a kira ta ta fito ta zauna. Liman yayi addu’a ta fatan a dace da duk abin da za’ayi ya zaman ya zamo shi ne mafi alheri kuma ayi komai lafiya a tashi lafiya aka shafa da amin. Baba Yahya ya kalli Ado ya ce, to me ya faru ne Ado? Ado ya gyara ya soma rattabo bayani tun farko yanda aka yi Mama tasa shi karvar aurena al’amuran da suka yi ta faruwa bayan auren da sharuxxan da ta sanya mishi na cewar za su faru in har ya ce zai ci gaba da zama da ni da kuma yanda Babana ya kira mu muka zo ya ce ni in shiga xakin uwata shima ya shiga na tashi uwar shi kenan ya raba aure, magana ta qare. Kowa yaje ya riqe tashi. Ya ce, to shi ne nace wataqila rashin cika waxancan sharuxxa da aka gaya min ne yasa aka zartar min da wannan hukunci, don haka na kira ku saboda ku shaida zan cika sharuxxan dan nima a bani matata in tafi da ita, kowa ya yi shiru yana sauraron abin mamakin da Ado ya rattaba yayin da shi kuma Babana ya shiga faxin lalle kai xin nan butulu ne ban sani ba, Mama kuwa kuka ta kama yi tana faxin wai bata tava zaton Ado zai qulla mata sharrin da ya qulla mata ba. Liman ya katse su ta hanyar cewa, to amma wannan lamari da ban mamaki yake, ashe bani da Alhaji Yahaya ba ne muka je ba da haquri don iyayen mijin ‘yar uwarta su barta ta koma xakinta ta zauna suka qi muka dawo muna vacin rai da baqin cikin wulaqancin da aka yi mana na qin yarda ta koma ba? Baba Yahya ya ce eh, to shi ne kuma kai da kanka kake cewa a dawo maka da wannan ka raba auren Alhaji a ina ne uba ya samu ikon qwace ‘yarshi daga wurin mijinta, alhalin ba mijin ne yace baya yi ba, ai daga faxin ka bayar an ce an karva to baka da sauran iko, kai Ado kana son matarka ka kuma shirya cika sharuxxan duk tsananinsu don a baka ita? Cikin ladabi ya ce eh Mallam, to kawo su. Ado ya shiga miqa takardu yana bayani har da na gidajen nashi da motar ya ce ita kamma direban ya ce min ya kawo ta suka ce eh mun ganta bayanin kuxi a banki da na hannun mutane da wanda su kuma ake bin su bashi duk ya bayar. Mallam Harisu ya ce amma Alhaji yanda yaron nan yasan komai na kasuwar nan taka da kuma dawo da wannan dukiya da yayi wacce da can baka san da ita ba baka ga kamar ka yafe mishi ka bashi matarshi suci gaba da zamansu kaima kuci gaba da harkokinku bai fiye maka ba? Tunda kowa ya san shi ya san shi ne a tare da kai babu kuma wanda bai san jarumtakar shi ba yana rabuwa da kai fa wasu a kasuwar a kuma kusa da kai za su qwace maka shi ba kuma zaka ji daxin hakan ba, kan Babana ya buxe baki yayi magana sai Mama tayi caraf ta ce, to ya tafi mana da can da babu shi Alhaji bai nemi kuxinshi ya samu ba? Wannan neman kuxi da yake yi mishi ma ai neman kuxi ne na kashe mu raba, Baba Yahaya ya ce eh da ki ka sa shi yin hakan ba in ba haka ba a ina ki ka samu wannan dukiya da ya dawo miki da ita? Me ki ke dashi? Ko kina so ne in tuna miki da…da sauri Liman ya ce a’a Alhaji kai kuma me ya kaika yin haka? Baba Yahaya ya ce abin baqin ciki ne da matar nan Mallam, gaba xaya ta hana gidan nan zama lafiya, ka duba yanda aka yi da dalilin da yasa ta qulla wannan aure da kuma abin ya juya ta inda bata zata ba maimakon tayi nadama kan muguntarta tayi ta istigafari sai kuma ta tasa xan uwanta a gaba da masifa, to za ki rasa shi za kuma kiyi kuskure don shi ne komai na hidimar gidanku ke da mijinki. A wurinka ba, kai kake ganin hakan ai ku ku ka shiga tsakanina dashi, Baba Yahya ya ce to ai shi kenan kai Ado a ina ka samu inda zaka koma xin? Ado ya sunkuyar da kai qasa ya ce can nake so in koma wurin dangin ubana, yana faxin haka Mama ta qyalqyale da dariya ta ce qauye kenan? Ai da can xin ku ka fi dacewa. Gaba xaya wurin yayi tsit saboda babu wanda ya zaci Ado qauye zai ce zai kai ni, shiru aka yi na wani lokaci mai tsawo kafin Mallam Harisu ya gyara zama ya ce wa Ado, ka gani Ado in wani abu irin wannan ya faru haquri ake yi a kwantar da hankali a natsu kafin a san kuma inda za’a fuskanta. Kai yaro ne mai natsuwa da girmama na gaba da kai, kowa ya sanka saboda kana da kwarjinin jama’a ka iya zama da su lafiya, kayi karatu.” Baba Yahaya yayi maza ya ce mishi ai digiri biyu ne da shi a yanzu, da sauri Mallam Harisu ya ce to ka gani? Babu wani dalilin da zai sa don wannan abin ya faru ka ce zaka bar birni ka koma qauye. A nan ma za ka yi harkokinka zaka samu kuma abokan harkar. Za kuma ka nemi aiki ai kayi ilimi shi qauyen nan da ka ke gani ka riga ka baro shi da daxewa ba iya zaman cikin shi zaka yi ba, don ka riga ka manta da rayuwar can duk da dai nasan kana yawan zuwa to sannan ita Humaira fa bata san qauye ba kar ka manta da wannan. Gaba xaya aka sake yin shiru na wani tsawon lokaci saboda Ado ya ki tanka maganar da Mallam Harisu yayi mishi, sai Baba Yahaya ya kawar da shirun da tanbayar cewa to ko kuma zaka fara tafiya ne kai kaxai ka barta a nan sai kaje ka gano yanda zaman naku zai yiwu in yaso sai ka dawo ka xauke ta? A hankali ya ce, a’a Baba, nafi so in tafi da ita, nafi so a bani ita, wataqila taurin kan Ado ne ya fusata Babana ko kuma yawan tsakin da Mama ke ja ne oho. Don jin shi kawai aka yi ya kama faxa yana faxin babu in da zaka tafi min da ‘ya ai bamu yi da kai akan in anyi auren qauye za ka xauke ta ka kaita ba, shi kuma Liman ya ce a’a wannan kuma ai ba magana ba ne shi dai a roqe shi cikin biyu yayi xaya, ko dai shi ya fara zuwa kafin ya dawo su tafi tare ko kuma kai Alhaji Yahaya ya yarda ka bashi aron wurin zama da shago a kasuwa tunda mun san duk abinda yake hannunshi ne ya kawo.” Baba Yahaya yayi maza ya ce har kayan zan sa a bashi in yi mishi lamuni ai duk an san shi, da Liman ya waiwayi Ado don jin abinda ya zava sia ya shiga basu haquri yana faxin shi a yanzu zai fi son a bashi matarshi ya tafi da ita wurin dangin ubanshi. Baba Yahaya ya ce to ina ganin tunda yarinyar nan itama tana da hankalinta da wayonta a kira ta tazo nan muji ra’ayinta, in ta yarda zata bi ka qauyen shi kenan, amma in bata yarda ba ba za mu tilastata ba, Babana yayi maza ya ce bin shi kuma yana nufin ta tafi kenan ba za ta sake dawowa ba. Ado ya xaga ido ya kalli Baba Yahya cikin natsuwa da ladabi yayin da tsoro ya baiyana qarara a idonshi ya ce mishi na roqe ka Baba kar ka bata zavi akan aurena, don zata ji tsoron maganar da Baba yayi mata. Baba Yahaya ya ce ba zavi ba ne haqqinta zamu bata in ta ce zata bi ka shi kenan, amma in ta ce ba za ta bi ka ba ba zamu sa ta ba, domin ya kamata ace kaima kayi sassauci akan tafiyar taka tunda mun maka alqawura mun baka zavi mun kuma roqe ka a matsayinmu na waxanda suka haife ka, amma baka yarda ba to hakan ba yana nufin ita xin zamu tirsasata ba ne. Mama tayi dariya tare da gyaxa kai ta ce ai gara dai kuma ku gani wai shi nan a dole shi mai taurin kai ne. Fitowa nayi a xaki a dalilin kiran da aka yi min har kafin fitowar tawa kuma Inna bata daina kukan da take yi ba, tana faxin qauye kuma? Haba wane irin qauyea? Na durqusa a qasa da gwiwoyina duka biyu cikin sauraron abinda Baba Yahya zai gaya min, zuba min ido yayi yana kallona cikin wani yanayi da yake baiyanar da tausayin shi a gare ni, ni baki da lafiya ne ma ko Humaira? Na ce mishi eh Baba, sai da ya qara xaukan wani lokaci mai tsawo cikin nazari da tunani kafin ya daure ya ce min to Humaira kin dai ji duk abinda muke ciki da mijinki, amma a yanzu zavin ya rage naki, za ki bishi ku koma can qauyen nasu? In za ki bishi to babu laifi ba zamu hana ki ba, domin aure ne shi kuma aure babu inda ba ya kai ‘ya mace, sannan mijinki yaron kirki ne jarumi kuma mai neman na kanshi, ni nafi kyautata kyakkyawan zato a gare shi, in kuma ki ka ce ba za ki bishi ba to babu mai sa ki saboda mu xin iyayenki ne zamuyi miki adalci baki san komai ba game da rayuwar qauye a xauke ki a kai ki can ki koma da zama ba zai zamo mai sauqi ba a gare ki. Don haka me ki ka ga ni, za ki ko ba za ki ba? Ya waiwaya wurin sauran jama’ar da suke tare ya ce ko ba haka ba Jama’a? suka yi maza suka ce wannan shi ne gaskiya, ya sake waiwayowa ya kalle ni ya ce, To Humaira zavi yana wurinki, yi maza ki gaya mana wanda ki ka xauka don ki kawo mana qarshen wannan kai kawo kin ga ai tun safe muke wurin nan ko kasuwa ba mu samu mun je ba. Xago ido nayi da nufin baiwa Baba Yahya amsa sai ka rab idanuwana suka haxu da na Ado, ni yake kallo ko qibta idon nashi baya yi saboda tsananta kallon da yayi, maqwalwuyanshi sai kai kawo yake yi alamar tsananin damuwa da alama kuma wata maganar yake son gaya min wataqila da ya san zavin zai zo wurina da yayi hanzarin gaya min ita tausayinshi yayi matuqar kama ni da na tuna kalmomin da ya furtawa Inna cewar tafiya babu ni xin zai zamo mishi tanfar ya rasa komai, gaskiya ne tafiya babu ni tanfar rasa komai ne a wurin Ado, tunda ya bayar da komai nashi to amma kuma anya tausayin hakan ya isa yasa in zavi Ado in bar kaina, da mahaifiyata? Anya tausayin nashi ya isa ya hana ni tausayin kaina da mahaifiyata? Bin Ado qauye kenan yana nufin rayuwata ta shiga wani hali musamman ma da yake nasha jin mawaqanmu na Hausa masu basira suna faxin wai kowa kaga ya bar birni ya koma qauye to wannan zaman duniya tasa ce ta gigita. Ban da wannan ma ni da kaina na sani ba sai an gaya min ba, shigana cikin matsala yana nufin Inna ma tana cikinta tsundum, na kuma sani da ita ce ta samu damar da aka bata irin wannan zavin da aka bani da tuni ta kawo qarshen maganar ta hanyar faxin babu inda zani. Waxannan dalilai sai suka sanya ni cikin wani hali na kai-kawo da bugun zuciya wanne zan zava? Rufe ido zan yi in zavi kaina da kwanciyar hankalin Innata in bar Ado da xan guntun kunyarshi da xan vacin ranshi ya kama hanya yayi tafiyarshi qauyensu ko kuwa? Tunda ai yayi kyakkyawar rayuwa babu ni, gaba xaya son da yake tutiyar yana yi min kwata-kwatanta daga wata uku ne, a baya ni xin ba komai ba ce a wurinshi, sannan dukiyar da yake ikirarin mayar wa don ya same ni na sani jarunta ne yin hakan, to amma kuma ai ta wani vangaren taimakon kanshi yayi tunda dama bata hanyar halal ya same ta ba, tana cikin asarorin qarya da aka yi ta cewa Babana yayi. Sannan ko Ado bai tafi da komai ba zai tafi da iliminshi wanda babu wanda ya isa ya qwace mishi shi digiri biyu kuma ke gare shi, sannan ban da waxannan dalilan duka bani da tabbacin cewar zan samu karvuwa wurin ‘yan uwan Ado da yake ikirarin maida ni cikinsu in suma suka zamo min kamar Mama fa yaya zan yi haka nan shi kanshi Ado wane tabbaci ke gare ni akan shi tunda tun ina ‘yar qaramata nake jin iyayena mata suna faxin wai shi xa namiji ba xan goyo ba ne, to musamman ma kuma wannan da shi da kanshi ne yake yi wa kanshi kirari da cewar shi xin namiji ne. Iyayena kuwa da dangina tuni suna sani zama da su yana nufin zan ci gaba da zamana a cikin gatana musamman Innata wacce nasan babu wani wanda zai cike mata girbina balle ya xebe mata kewata tun daga ranar da ta haife ni take sona kowa kuma ya san hakan, kowa ya bada wannan shaidar cewar Inna bata tava son wani xa kwatankwacin son da take yi min ba, haka nan zan ci gaba da rayuwa ta a birnin da na sani, birnin da aka haife ni, birnin da na rayu, zan ma iya komawa Makaranta in yi karatuna tunda ina da wannan burin. Mama kuma in babu auren Ado a kaina ba za ta sake takura min ba don kuwa ba zan sake yarda ba saboda a yau kan ungulu ya riga ya waye xan auren nan da nayi na kwanaki tamanin da bakwai ba qaramin buxe min ido yayi ba. Tuni zuciyata ta shiga kai-kawo mai tsanani na kasa gane menene abin yi? Wanne zan yi? Wane zan bari? Hankalina ya yi matuqar tashi na rasa wanda zan zava cikin niyun Inna da sauran dangi tare da Babana mai faxin bin Ado yana nufin na bar gidanshi kenan zan xauka in bar Ado? Tunda shi Ado ai zai tafi da iliminshi ban da haka ma zan haifar mishi abinda yake cikina yazo ya xauka abin shi, ko kuwa Adon zan bi min soyayyar wata uku muje can qauyen nasu cikin danginshi mu yi zamanmu? Duk yawan kirarin da yake yiwa kan shi na cewar shi xin namiji ne, alhali kuma mu mata mun sha jin iyayenmu mata suna jaddada mana cewar shi namijin ba xan goyo ba ne…? Mu haxu a littafi na uku jama’a don jin kafin nan in ku ne wanne zaku zava cikin biyun? Godiya mai xinbin yawa a gare ku bisa qaunar da kuke nunawa rubutuna. Na gode da zumuncinku, Ubangijinmu Allahu ya sada mu cikin Aljannarsa ta Firdausi don rahamarsa, Ubangiji yasa mu dace da samun dukkan alherin da yake cikin wannan wata mai albarka na Ramadan, watan da Manzon Rahama (S.A.W) ya ce watan Alqur’ani ne. 10/9/1433 Hijira 29/7/2012 miladiya Taku Hafsat Chindo Sodangi 07035586299