© HASKE WRITERS ASSOCIATION. _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO......* *MIJIN MATACCIYA.....!*💞💞 _*NA*_ *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad-Ummishatu* بسم الله الرحمن الرحيم،رب اشرح لي صدري، ويسر لي امري،واحلل عقدة من لساني،يفقهوا قولى. اللهم ربنا إنك جامع الناس ليوم لا ريب فيه إن الله لا يخلف الميعاد، الحمد لله رب العالمين. *Shafin farko sadaukarwa ne gareku mudubi na,wato allon kwaikwayo na Anty fauziyya D Sulaiman & Anty juwairiyya A Girei madallah da ku iyaye na gari.* *Kina raina Phertymah Xarah,fatan alkhairi agareki ahar kullum.* *1* ~~~ *Cikin dimuwa,damuwa da tashin hankali mai tsanani yasake damke hannayenta dake cikin nashi wani irin gumi na keto masa tamkar anyi masa b'arin ruwa aka, idanuwanshi jajur suke sannan kuma sun kankance mutuka, Anata bangaren itama hakan take domin inbanda hawaye babu abinda take fitarwa, kwalla ce ke ta faman tsiyaya daga cikin kwayar idanuwanta, "Wai wannan wanne irin shashanci ne haka....? Kai balarabe bazaka kyaleta ayi maza aje ayi mata aikin nan da za ayi mata ba?" Muryar wata yar dattijuwa ya karade wurin da suke, tamkar ansake fama masa wani Miki dake tare dashi haka yayi domin rikon da yayi mata yanzu har yaso yafi na dazu, cikin jarumta da dauriya gamida juriya irinta maza yayi mata wani basaraken murmushi mai tafiya da hankalin duk wata ya mace, cikin karfin hali da kokarinsa na hadiye kukan dake gab da balle masa ya saka kwayar idanuwanshi cikin nata sannan cikin sanyin muryarshi wadda ta hadu da yanayi na tashin hankali da yake cikin yace, "Is ok my heart.....daina wannan kukan haka,insha Allah zaki shiga lafiya sannan zaki fito lafiya domin kullum addu'ar da nake yimiki kenan.... Allah yayi miki albarka yar aljannah insha Allah tare zaku fito da kyawawan twins dinmu masu kama dake....." Kawar da kanta tayi daga kallonshi tana zubar da hawaye, "Kayya.....kayyah Rabin raina,bana jin zan sake rayuwa dakai acikin duniyar nan....nidai kawai ka yafe min,ka yafe min duk laifin da nayi maka a iya zaman mu sannan koda na mutu to ka sanyawa yaranmu sunan da kayi min alkawarin zaka sanya musu....ina tsananin sonka mijina...." Bai kai ga buda baki ba yaga ta sake burkicewa ciwon haihuwa yadawo mata sabo fil fiyeda dazu babu bata lokaci ma'aikatan lafiya dake tare dasu sukayi azamar tura gadon da take kwance akai zuwa dakin da za ayi mata aiki wanda har lokacin yana rike da hannunta dukkaninsu suna hawaye amma sai dai shi nasa hawayen azuci yake yi ahaka aka shigar da ita cikin dakin shikuma dan dole yaja burki daga bakin kofa bawai dan yasoba. Daga wajen da yake tsaye yagagara zama sai faman sintirin kaiwa da komowa yake yi yanata faman hade hannayensa wuri daya yana runtsewa gamida da runruntse idanuwa acikin zuciyarsa kuwa baida addu'ar da ta wuce, "Ya Allah ka sauki Ramlat lafiya,ya Allah kafito min da abinda ke cikin cikinta lafiya......" Haka yaketa faman fada har tsawon mintuna talatin, Yakumbo mariya tayi tayi dashi akan ya nemi wuri ya zauna amma yakasa tamkar wani sabon soja haka ya dake yanata kaiwa da kawowa,zuwa can yajuya ya kalli wurin da yakumbo mariya ke zaune bayan ya duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunshi wanda ya nuna kimanin karfe 11:30 nadare,cikin sassarfa kamar kazar da kwai ya fashewa aciki yanufi wurin yakumbo mariya,cikin russunawa yace, "Yakumbo bari naje nayi salla ina dawowa...." "Ko kaifa,yawwa dan albarka, maza kaje kayi mata addu'a domin ita tafi bukata a wannan lokacin..." Batare da yasake furta komai ba yajuya yatafi domin zuwa inda zaiyi sallar. Binsa da ido yakumbo mariya tayi tana girgiza kai domin tasan halinsa yawan magana ratataa baya cikin dabi'arshi da tsarinsa bare kuma yau da zuciyarshi ke cikin alhini da tashin hankali, wannan yaro dai ba asan adadin son da yake yiwa Ramlat ba sai shi sai ubangijinsa tunda shine yasan zuciyar kowa. Tunda yayi alwala yashiga masallaci yake salla wadda yake jimawa cikin kowacce sujjada saida yayi salla raka'a hudu sannan yadaga hannu yayi addu'a bayan ya shafa ya mike a kasalance yana gyara kafar wandon jeans din dake jikinsa,haka kawai yaji ya nemi nutsuwa atare dashi yarasa gashi zuciyarshi tayi wani irin nauyi sai bugawa takeyi da karfi fat fat tamkar zata faso kirjinsa tafito,cikin mawuyacin hali da yanayi yafito daga masallacin yana dafe goshinsa wanda yadauki zafi haka siddan,jan kafarsa yarinka yi wacce tayi masa tsananin nauyi kamar jini irin ya taru dinnan sosai ahaka yanufi wurin da yabaro yakumbo mariya, Hangota yayi atsaye da alama shi take jira dama cikin sauri ya karasa wurinta, "Mu'azzam Ramlat ta haihu,anciro yara biyu mace da namiji amma macen bata zo da rai ba sai namijin kadai...." "Suna ina yanzu yakumbo? Ina ita Ramlat din?" "Muje ka gansu,Ramlat kuma ba afito da ita ba tukunna har sai nan da wani lokaci..." Shuru yayi baice komai ba yabi bayanta zuwa inda tashiga,yara kam tubarkalla jajur dasu kamar shi sannan tun daga yanzu zaka gane tsananin kyawun da Allah yayi musu amma ita macen babu rai sai iya namijin kadai keta yan callare callaren kukanshi, "Allah yasa haka shi yafi alkhairi, Allah ya raya mana namijin....." Yakumbo ta fada tana karbar macen daga hannunshi, "Amin Yakumbo...." "Na kira su Zaid insha Allah nan bada jimawa ba zasu karaso...." Jijjiga kai kawai yayi yafita bayan ya dauki namijin yaganshi. Tun bayan da aka gama yiwa Ramlat aiki har asubah bata farfado ba, karshen tashin hankali kowa dake wurin yashiga musamman ma shi uban gayyar dan dakyar ya iya zuwa yayi sallar asubah yana sallamewa ya fito yadawo wurinsu amma tun daga nesa ya fahimci kamar akwai matsala domin yanda ya hango mutane na rusar kuka sannan wasu sunyi cincirindo sun rufe gadon da Ramlat ke kai,jin kansa kawai yayi yana faman juya masa kamar fanka nan yazube ya fadi awurin,kinkimarsa akayi zuwa emergency domin bashi agajin gaggawa. Tunda aka kwantar dashi ake faman yimasa karin ruwa wanda ake gaurayawa da wasu allurai aciki,bai tashi bude idonshi ba sai misalin karfe 5 na yamma, Cikin zafin ciwon da yake ciki ya yunkura yatashi duk da jikinsa babu wani sauran karfi, Zaid ne yanufoshi cikin sauri yana fadin, "Sannu yaya Khalil....tsaya jikinka babu karfi" Kallonsa yayi da raunannun idanuwanshi sannan cikin sanyin murya yace, "Zaid muje gida....kaini inga Ramlat..." Zaid zaiyi magana suka hada idanuwa yasan babu abinda yayan nasa ya tsana irin gardama, lallabawa sukayi suka nufi gida wato family house dinsu tare da sauran yan uwa wadanda ke tare dasu, Iske gidan sukayi cike dam da mutane babu masakar tsinke anata karbar gaisuwa,shi dai yasan tafiya kawai yake yi amma bazaice ga inda yake zuwa ba kai daga karshe ma gani yayi ganinshi ya dauke gaba daya saboda yagama tabbatar da cewa Ramlat ta rasu,dakin Zaid aka kaishi can aka cigaba dayi masa kare karen ruwa kowa shi yake tausayawa ganin halin da yashiga domin har yafi iyayen Ramlat din shiga rudu da dimuwa,duk wanda yazo gaisuwa idan najikine sai yashiga ya dubashi shi baima san inda yakeba. Bayan kwana uku da rasuwar Ramlat ya farfado yasamu kansa hankalinsa yadawo gareshi tun da yabude ido kuma yake kuka kamar wani karamin yaro,kowa shi yake bawa hakuri amma angagara gane kansa, hajiya Raihan mahaifiyar Ramlat tare da Alhaji Tamim maihaifin Ramlat shiga wurinsa sukayi suna bashi baki tare da yimasa nasiha amma duk abanza,daga karshe yayan mahaifiyarsa wanda suke kira da Abban London shine yashiga wurinshi ya zauna gefensa cikin nasiha yace, "Ibrahim kayi hakuri ka rungumi k'addara domin kowa da kagani na haka ne,kayiwa Ramlat addu'ar samun rahamar ubangiji sannan kayi hakuri domin duk abinda Allah yayi akan bayinsa to shine daidai....ba aja da hukuncin ubangiji,idan kaci gaba da irin haka to Allah zai iya yin fushi dakai domin baka karbi k'addara ba ko kamanta Allah yakan jarrabemu da rayuka? Yau ina mahaifinka? Ni ina nawa mahaifan? Mahaifinka ma ya mutu kuma kayi hakuri to meyasa yanzu zaka gaza? Dan Allah kadaina duk wadannan abubuwan ka daure kayita addu'a insha Allah zaka samu madadinta koma wacce tafita....." Tunda Abban London yasoma maganar bai kalleshi ba sai lokacin jin yace wai zai samu madadin Ramlat koma wacce tafita,tab ina ai shikam yasan bazai taba samun ko kwatankwacin rabinta ba shiyasa ma shida aure yanzu haihata haihata sai dai yaga anayi amma yagama aure aduniya idan yamutu yaje lahira sa hadu da Ramlat dinsa su cigaba da rayuwar aurensu a aljannah, Har Abban London yagama nasiharsa yafita baima saniba kasancewar yafada kogin tunanin da yasaba. Ganin al'amarin nasa bamai sauki bane yasa hajiya Zaitun mahaifiyarshi sanya limamin dake jansu salla agidan yimasa taimako koda na addu'o'i ne dama kuma babu laifi nasihar Abban London ta dan shigeshi domin har ansamu ya fito daga dakin Zaid yaje wurin jaririnshi dan kimanin kwanaki biyar daukar jaririn yayi yai masa huduba yana fitar da kwalla, "Menene sunanshi...?" Babbar yayarshi wato anty saudat ta bukata, "Sulaiman Aryan..." Daga haka yamika mata shi yatashi yafita,makabarta yasaka Zaid ya rakashi ya nuna masa kabarin Ramlat tun daga wannan lokaci kuma yasamu wurin zuwa sai yaje yasaka kabarin agaba yayita kuka har akayi sadakar bakwai gashi ba ci ba sha sai idan an takura masa hajiya tazo da kanta sannan zai yarda yasha ruwan tea amma rabon da yasakawa cikinsa abinci har yamanta. Yauma saida yajima agaban kabarin yana rusar kuka kamar daga sama yaji andafashi ta baya cikin hawaye yajuya,wani mutum yagani tsaye dan dattijo dashi cikin taushin murya dattijon yace, "Kayi hakuri bawan Allah....ka dauki k'addara wannan kukan da kake zuwa kullum kanayi ba mafita bace mafita guda daya ce itace addu'a...." Gyada kanshi yayi ya goge hawayensa yana furta "nagode....nagode" Juyawar da zaiyi yaga wayam babu dattijon nan babu alamarsa, addu'a yayiwa Ramlat sannan yamike yana fadin, "Insha Allah zaki zama abar tunawa acikin zuciyata akoda yaushe Ramlat....bazan manta dakeba da yardar Allah, Allah yasa kina aljannah kina hutawa kin manta da wahalar rayuwar duniya...." Motarshi yanufa yabude yashiga yanufi gida,duk mutane sun tattafi sai wadanda ba arasa ba wato na jiki jiki,yana yin parking masu tsaronsa dake zaune acan gefe suka mike suka nufoshi domin a yan kwanakin nan yahanasu binsa shi kadai yake zuwa kabarin Ramlat, Falon hajiya Zaitun ya nufa amma sai karar jiniyar motocin gwamnati suka cika gidan da ma unguwar gaba daya hakan ya tabbatar masa da cewa mai girma gwamna ne yazo yimasa ta'aziya, Fita yayi yaje ya taryeshi yashigar dashi zuwa dakin saukar baki nan yayi masa ta'aziya sannan ya bukaci ganin jaririn da marigayiyar tabari, Zaid ne ya dsukoshi yakawoshi wurin mai girma gwamna nan ya karbeshi yayi masa addu'a sannan yabada shi yayi musu sallama yatafi bayan ya ajiye kudi daruruwa. Cikin gida yashiga bayan tafiyar mai girma gwamna,zazzaune yasamu kowa afalo ana yin sallama da iyayen Ramlat wadanda zasu bar gombe ayau zasu nufi gida wato jos,da alama kuma dama shi kadai ake jira, Zama yayi a kasa kusa ba Abban London wanda ke sanye cikin kayan gida amma na sarauta sai dai yau babu jibga jibgan rigunan nan da yasaba sawa shiyasa yafito a siririnsa, "Ibrahim Allah yakara mana hakurin jure rashin Ramlat yakuma raya abinda tabari,mu zamuje mu tafi amma zamu tafi da jaririn sai mu kula dashi awurinmu....." Alhaji Tamim maihaifin Ramlat yafada yana kallonshi, "A'a Abba ina neman alfarmar ku kubar min yarona zan rikeshi awurina insha Allah kuma zan rinka kawo muku shi kuna ganinsa...." "To shikenan hakanma babu aibu fatanmu dai Allah ya rayashi" Kowa dake wurin da Amin ya amsa, "To yanzu waye zai shayar dashi? Sai kabawa Humaida ko Lubnah tunda sune suke shayarwa...." Inji anty saudat, Ai shi sai lokacin ma yatuna da batun shayarwa shi baida ra'ayin kowa ya shayar masa da yaronshi madara zai rinka bashi, "A'a madara zai rinka sha..." Yafada atakaice sannan cikin sauri yasake kallon anty saudat, "Da wata cikinsu ta shayar dashi?" "Babu wadda ta shayar dashi madara ake bashi dama ana sone asanar dakai first sai wata cikinsu ta daukeshi" "Basai andaukeshi ba abar min shi ni zan kula dashi" "Kai ina ka taba jin namiji yakula da jariri? Kanada nonon da zaka bashi ne? Wadannan da akace kabawa wata cikinsu ba yan uwanka bane uwa daya uba daya ba?" Yakumbo mariya tafada cikin fada,shiru yayi baice komai ba amma shikam harga Allah bazai iya bawa wani rainon yaronshi ba shine zai kula da kayansa, "Tunda kai ba mace bane tofa ya zama dole kabawa wata cikin yan uwanka ko yan uwan matarka akula da shi...." Yakumbo mariya tasake fada tana kallonsa, Idonshi rau rau cikin rawar murya yace, "Yakumbo kuyi hakuri karku rabani da Aryan bazan iya jurewa ba na rokeku da girman Allah kubar min shi..." Yakumbo mariya ta bude baki kenan zata sake magana Abban London yayi gyaran murya yace, "Ya isa haka tunda hakan yake so to muyi masa yadda yake so din ina ganin zaifi,Allah yaraya mana shi mudai shine fatanmu....." Gaba daya akan hakan aka tafi,aranar yaje babban store ya lodo duk wani abu wanda jariri ke bukata,madara kuwa yasiyota tafi gaban abinda tafi,umma barira k'anwar abbansu yadauka ta dawo family house dinsu gaba daya da zama tana tayashi kula da Aryan dayake ita din ahalin yanzu bata da aure kuma duk yaranta sun manyanta dama guda uku ne,shine da kansa ke yiwa Aryan wanka ya shiryashi yabashi abinci duk wani abu na kula da jariri ya iya ahalin yanzu kamar dama can yajima yanayi,indai kaga umma barira tayiwa Aryan wanka ko tsarki ko wani abu mai kamada haka to Khalil baya nan amma indai yana nan shine ke yimasa komai gaba daya rayuwarsa yanzu ta ta'allaka ne akan kula da Aryan ko aikinsa yar sama sama yake yimasa cikin haka har Aryan din yacika shekara daya nan kuma su yakumbo mariya suka sakashi agaba da maganar lallai lallai lokacin da zaiyi aure kuma yayi domin bazai yuyu yayita zama babu mace ba,duk lokacin da suka yi masa irin wannan maganar tayar masa da hankali sukeyi yayita kuka har takaishi da kwanciya a asibiti,daga karshe suka yanke shawarar hadashi aure da kanwar matarshi margiyaya mai suna zulaiha amma fafur yaki aminta wai shi bazai iya auren kanwar Ramlat ba yana jin kunyarta koda bata raye daga karshe dai sai hakura sukayi suka zubawa sarautar Allah Ido suka cigaba da rakashi da addu'a domin duk wadda aka samo masa akan za ahadasu aure baya yarda idan kuma ance yasamo da kansa sai yace shi baida wannan lokacin haka dai suka kyaleshi suna tayashi da addu'a. *** BAYAN SHEKARA SHIDA.............✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 : ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO....* *MIJIN MATACCIYA....*💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* WATTPAD:-ummishatu بسم الله الرحمن الرحيم. *3* Washe gari ** ~~~Tunda yafara tafiya akan titi kowannensu yayi shiru babu wanda yayi magana har saida sukayi tafiya mai nisa sannan ya dan kalleta inda take zaune agefen kujerarshi hannunta rike da wayarta tana dubawa, "Hanan.... Bakice komai ba fa kinyi shiru kin barni da nazari....." "Ai nayi magana mujahid kawai dai baka ji dadinta bane,nafada maka kayi hakuri ka jira nagama service dina sai ka turo iyayenka,to inma banda abinka kai da kayi hakurin shekara da shekaru ai bana tunanin hakurin shekara daya zai zame maka damuwa, wallahi insha Allah kamar yaune zamu yi aure......" Dan sassauta gudun da yake yi yayi sannan ya kalleta cikin sanyin jiki, "Wallahi ni gani nakeyi kamar baza muyi auren nan ba hanan shiyasa kika ga duk hankali na yatashi....." "Hmm kajika da wata magana kuma.... Dan Allah kadaina wannan maganar" "Shikenan nadaina" Da wannan maganar yana ta faman nanata ta suka isa unguwar kurna gidan anty salaha wato babbar yayar su Hanan,saida Hanan ta shigar da mujahid suka gaisa sannan yayi musu sallama yatafi amma da yamma zai sake dawowa ya dauki Hanan. Agidan anty salaha dinma dai maganar guda daya ce shine ta tafiya service wuni sukayi suna wannan hirar har lokacin tafiyar Hanan yayi nan ta kira mujahid yazo ya dauke ta anty salaha nata fadan wai karfi da yaji ta maida mujahid driver dariya Hanan tayi tace wai ai dama namiji bawan matane idan bai kyautata mata ba tunda yana sonta har sai yaushe?,haka dai suka karasa gida cikin farin ciki da kaunar juna bayan mujahid ya dan yimata siyayya ahanya. Acikin yan kwanakin Hanan tagama hada komai nata da take bukata kullum cikin lissafi take su shamsu na tayata ai kuwa aranar da akayi posting ta duba dash board dinta nan taga ankaita Abuja tsalle ta daka sannan ta dire tana fadin "yes" murna kamar zata taka rawa nan ta soma kiran yan ajinsu wadanda suke mutunci tana tambayar inda aka kaisu sai dai fin rabi duk sunansu bai samu fitowa ba yanzu sai zuwa batch na gaba wadanda sunan nasu kuma yafito duk wasu garuruwan aka turasu ita kadai aka tura Abuja sai ko wasu yan department din wadanda bama lallai ta sansu ba. Aranar da za ashiga camp din aranar ta shirya ta tafi,da tare da shamsu zasu tafi zai rakata amma ganin Abuja ne yasa aka barta ta tafi ita daya shamsu sai tsokanarta yake yi yana cemata gaskiya ba karamar sa'a tayiba domin Abuja special posting ake turawa can ba kowa ake kaiwa ba amma fi tura yaran manya wurin,ita dai yau baki har kunne zata tafi camp,wata dirkekiyar trolley ta tafi da ita wadda ta hade gaba daya kayanta aciki amma sauran abubuwan bukata kamarsu bokitin wanka da makamantansu tace sai taje can zata sissiya,har tasha shamsu ya rakata yasata a motar Abuja direct sannan yatafi, mujahid kuwa daga can inda yake wato jahar yobe yakirata awaya yafi sau 30 acewarsa shi da yasan cewa ita daya zata tafi da baiyi tafiyar nanba da yajira yarakata, murmushi tayi tace masa babu matsala insha Allah zata kular masa da kanta. *** Tunda yadawo daga makaranta ya hakimce akan kujera yana ta faman buga tv game dinshi umma barira tayi kiransa har ta gaji yaki tashi suje tayi masa wanka tabashi abinci yaci, D'an turo baki yayi lokacin da umma bariran ta shigo takai hannu ta kashe game din da yake yi, "Ka tashi muje kaci abinci nace ko,ga David can tun d'azu yagama hada abinci amma inata kiranka kayi kunnen uwar shegu....." Shure shure yafara yi zaiyi kuka ganin ta kashe masa game dinsa,zama tayi akusa dashi sannan cikin fara'a tace, "Yawwa yaron babanshi,maza tashi muje kaci abincin kafin abbanka yadawo yakaika unguwar ko?" Daga kai yayi yana dariya, "Umma Daddy ai zai siya min doki ko?" "Ehh zai siya maka duk wanda kake so" Makalkaleta yayi ta daukeshi suka fita zuwa dining area wanda ke hade da kitchen dinsu,kan kujera ya haye umma barira ta zuba masa abinci tabashi abaki sannan ta daukeshi zuwa dakinshi tayi masa wanka bayan ta shiryashi ne Khalil yakira waya nan suka lalace wurin hira shida Aryan tamkar sun shekara basu ga juna ba sai surutu Aryan din keyi masa shi kuma yana biyeshi dakyar umma barira ta sa Khalil ya katse wayar shi kuma dan rigimar tata nan ya kwanta yafara bacci. *** Tunda tagama registration tasaka white take faman daukar hotuna wadanda tayisu sunfi guda 50 wani ita daya wani kuma itada sabbin kawayen da tayi wato Khadija da hajara,tun lokacin da tafara hotunan take ta turawa shamsu da mujahid, kayan kam ba karamin karbarta suka yi ba dan duk inda ta gifta sai kaji ana cewa "yarinya mai kyau", dan hijabin dake jikinta iya kafadarta ne baida girma sosai sai farar t shirt ta kamfanin Polo da farin wando wanda ya tsaya iya kwaurinta tasaka farar safa da farin combos sannan ga yar karamar jaka daure a kugunta. Ba kadan ba tayi mutukar kyau wanda har ita da kanta ta shaida hakan. Tun shigarta camp bata taba karbar abincin da ake rabawa aciki ba maami market take shiga ita da su khadija suje suci abinda suke so su biya kudi,gashi ta samu wani guy ya makale mata wai shi Ashraf wanda ko ba afada mata ba tasan dan masu ido da kwalli ne kai kusan ma yaran dake camp din duk yayan masu fada aji ne dan sai yanzu take gasgata maganar da yaya shamsu yafada mata cewar special posting ake turawa camp din Abuja, Tana son ta shiga parade domin yana burgeta amma Ashraf ya hana ta sai hakura tayi,haka zai jata zuwa maami market yayita kashe mata kudi itada friends dinta,gaskiya taji dadin zaman camp dinnan da tayi domin tayi shi ne cikin walwala da jin dadi babu abinda take yi sai dai taci abinci ko wankin kayanta biya take yi awanke mata baya ga cin abinci babu abinda take yi koda yaushe tana clinic ita da Ashraf suna hirar duniya, ranar da akayi canival day kuwa aranar tasan Ashraf ya danganci sarauta domin shigar yayan sarauta yayi,ita kam kayanta na hausawa ta saka ita da kawayenta atamfa dinkin riga da skirt harda mayafi ranar ma sunsha hotona kamar babu gobe. Saida suka yi sabo da mutane sosai acikin satin ukun da sukayi a camp,ranar talata suka fita inda aka tutturasu duk guraben da yakamata,abin haushi duk cikinsu kowa inda aka turashi daban amma duk da haka sun yanke hukuncin cewa zasu zauna awuri daya ita da su Khadija wato a corpers lodge din da aka tanada musamman dan yan kano, Haushi kamar ya kasheta lokacin da taga wai makaranta aka turata su kuma su hajara duk ministries aka kaisu, Ashraf kuwa mutuminta yana babbar fada domin shi dama sai da ya zabi inda yake so sannan ya gayawa babanshi kuma can din aka kaishi, Su hajara nata tsokanarta suna kiranta da malama ta shirya ta nufi makarantar domin yin report,tun acikin taxi take faman mita acikin ranta domin gaskiya Abuja akwai tsadar rayuwa yanzu daga inda mai taxi ya daukota zuwa makarantar da zai kaita yace sai tabashi dari bakwai wai da dan nisa ita dai duk abinnan yafara damunta gaskiya ba zata iya wannan tsadar rayuwar ba idan taga babu haza itama redeploy zata yi. Lokacin da taje makarantar yar kauye ta zama domin bata taba ganin hadaddiyar makaranta makamanciyar wannan ba a tarihin rayuwarta, makarantar ta hadu ta tsaru fiye da hasashen mai karatu,gata tana da girman gaske gashi ta kawatu ta ko ina kamar a k'asar turai gaskiya wannan makarantar ko shakka babu zata yi tsada domin taci kudinta, Tana tafe tana sake yaba kyawu da tsarin makarantar acikin zuciyarta,a k'asa take tafiya saboda mai taxi din da ya kawota tun daga gate suka rabu,taji dadin ganin wasu mutum biyu sanye da kayan hidimar k'asa irin nata domin itanma sanye take da uniform dinta riga mai tambarin NYSC da wandonta sai farin hijabi marar girma yayinda ta daura rigar jacket din a kugunta sannan tasha farar safa da farin takalmi wato dai ta zama fully kitted gwadas da ita gwanin ban sha'awa dan kayan sun sake fito da ita sosai. Su ukune kacal yan hidimar k'asar da makarantar ta nema da kanta aturo mata su saboda tana da bukatarsu kamar yadda aka saba,suna zaune itada sauran corpers din su uku suna dan tattauna rayuwar camp wanda ke da alhakin karbarsu yafito daga office din principal yana basu hakuri akan bata musu lokacin da ya danyi, Kamar daga sama tana tsaka da bincika handbag dinta domin ciro biro da kuma posting letter dinta taji an rungumeta ta baya juyawar da zatayi taga wani kyakkyawan yaro mai mutukar kyau da daukar hankali, "Momy.... momy uncle yace min kin mutu.... Momy dama baki mutu ba? Kizo muje wurin daddy...." Daure mata kai maganganun yaron sukayi wanda har saida ta sake kura masa ido ta kalleshi,farine sol yaron sanye cikin uniform dinshi tsaftacacce yasha stocking ga suma akanshi antaje masa ita tayi kyau gwanin burgewa,tana kokarin yi masa magana chioma taja hannunta sakamakon kiran da senior master yayi musu nan ta wuce office din senior master batare da ta kara bi ta kan yaronba,yana kokarin binta shi kuma principal yafito nan ya rakashi class da kanshi............✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO.....* *MIJIN MATACCIYA...!*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad:-ummishatu* بسم الله الرحمن الرحيم. _*Har yanzu yan shidan haske masu dauke da fararen alqaluma na cigaba da kawo muku hazikan littattafai guda shida reras masu dumi da sanyi wadanda suka hadar da Gidan rina,hayatuddin,izzata,Da ciwo a zuciyata,tana k'asa tana dabo da kuma Burin zuciya ta,bugu da kari zaku samu wadannan dadadan labaran akan farashi mai sauki daidai da aljihunku naira 500 kacal,burin haske akoda yaushe shine ta saku dariya,maza garzaya ki nemi naki domin da abaka labari ai gara ka bayar,haske maganin duhu.*_ *4* ~~~Koda tafito daga office din senior master bayan yagama accepting dinsu bata ga wannan yaron ba na dazu amma kuma maganganun yaron nata kai kawo acikin kwakwalwarta musamman ma maganar da yayi da yanda yazo ya riketa kamar dama can yasanta, Da tunanin yaron da bata san ko waye ba tabar makarantar ta nufi zonal office domin taje tayi documentation zuwa gobe kuma sai ta nufi gida kanon dabo domin anbasu hutun sati biyu kowa yaje gida ya kintso sai yadawo da shirin zama,duk da bata son koyarwa kuma bata sha'awarta amma wannan kam tana jin zataji dadin aiki dasu domin makarantar ta azo agani ce kuma class biyu kacal aka bata wato JSS 2 da JSS 3 inda zata rinka koyar dasu darasin turanci dama abinda ta karanta kenan wato BSC English. Aranar ta gama harhada kayanta domin da safe sammako take son yi zuwa gida bata son takai rana ahanya,mujahid kuwa kamar sun shekara basu ga juna ba yadda yabi ya rikice mata ya dameta da waya ba dare ba rana yana tambayar yaushe zata tafi idan babu dama shifa sai yazo da kanshi dan yaganta. Sassafe ta fita ta samu taxi yakaita tasha inda zata shiga motar kano kuma cikin nasara tana zuwa motar ta cika dama mutum daya ake jira babu bata lokaci suka dauki hanyar kanon dabo tumbin giwa. *** A guje yashiga cikin babban falon gidan yana kiran "Daddy.... Uncle..... Papa..." "Kai Aryan menene haka kake gudu sai ka yanke jiki ka fadi ko?..." "Umma Ina Daddy na?" Dariya umma barira tayi ta mika hannu ta jawoshi jikinta, "Banda abinka dan jikalle na ina zaka samu ganin babanka yanzu? Tun fa kafin ka tashi daga bacci yafita yace zaije waccan kasar arnan ni banma rike sunan garin ba,ai ko zai shigo gidan nan to ba yanzu ba...., Maza muje acire kaya ayi wanka azo aci abinci ayi shirin islamiyya malam yana nan zuwa" Bata fuska yayi kamar zai saka kuka jin abinda umma barira tace,shi Daddyn sa yake son gani,shi yake son fadawa abinda yagani yau,da gudu ya shige dakinsa ya dauki kantamemiyar wayarshi ya zauna akan gado yana neman layin baban nashi amma bai samu ba ahaka umma barira tazo ta iskeshi nan ta karbe wayar ta ajiye asama sannan tajashi zuwa toilet tayi masa wanka ta shiryashi sai rakwarkwabe fuska yake yi irin baya so dinnan. Misalin karfe 1 na dare ya shigo gidan tare da mukarrabansa, direct sashensa yashiga yayi wanka yasaka kayan baccinshi masu silbi riga da wando maroon colour,ga abinci nan akan table kala daban daban wanda duk aciki baya jin akwai wanda zai iya ci, da kanshi yashiga kitchen ya hada coffee sannan yafita ya nufi dakin Aryan, A gefen gadon Aryan din ya zauna yana dan kurbar coffee din dake hannunshi yana yi yana nazarin d'akin,ga littattafai nan acan k'asa kan center carpet da alama home work yayi yagama kuma shine ba adebe littattafan ba yabarsu awurin, Da kanshi ya tattarasu yasaka masa cikin school bag dinshi sannan yasake komawa gefenshi ya zauna tare da kunna yar karamar fitilar dake girke gefen gadon Aryan wato bedside lamp. Cikin magagin bacci yaron yafarka ganin Khalil zaune kusa dashi yasashi kokarin tashi zaune,mayar dashi Khalil yayi ya kwantar tare da dan rungumoshi jikinsa cikin sanyin murya yana fadin, "Koma kayi baccinka Aryan...., Nazo ne inganka dama,yi bacci kaji yaron kirki" "Daddy naganta yau..... Kace min ta mutu ashe bata mutu ba Allah naganta" Duk a tunanin Khalil magagin bacci ne yasa Aryan wadannan surutan na shirme shiyasa yayi gaggawar dakatar dashi ta hanyar fadin, "Shhhhhh,Nace kayi bacci ko? Kar nasake jin bakinka awurin" Maida idanuwanshi yayi ya rufe yana motsa baki alamun yana son yin magana amma babu damar yi,shafar kanshi Khalil yafara yi tun daga sumarshi har zuwa fuskarshi alamar so da kulawa mintuna kadan yasake komawa bacci,sai da yaga yayi nisa acikin baccin sannan yayi masa addu'a ya shafe masa jikinsa dashi sannan yakashe masa bed side lamp din da ya kunna yatashi ya fita bayan ya lullube shi ya rufe masa kofar dakin, Bedroom ya wuce direct ya nemi wuri ya zauna saman kujerar dake can girke gefe daya da center table a gabanta,lumshe idanuwanshi yayi take tunanin da yasaba bijiro masa ya fara bijirowa kwakwalwarshi kamar koda yaushe wato tunanin matarshi Ramlat margayiya, "Allah sarki Ramlat kin tafi kin barmu da kewarki da tunanin ki da kaunarki da kuma begenki da kishirwar ganinki..... Sai dai kash nasan bazan sake ganinki ba sai a darus salam,Allah ya jikanki,yaron mu ma da bai sanki ba kullum cikin mafarkinki da begenki yake...." Daurewa yayi ya hadiye hawayen dake barazanar zubo masa,ahankali ya jingina da jikin kujerar ya kwanta sannan ya lumshe idanuwanshi yana tunani aranshi. Tsawon mintuna masu yawa ya dauka yana tunanin daga karshe dai ya tashi yashiga bathroom duk zufa ta jikeshi tamkar yana gaban wuta,ruwan sanyi ya sakarwa kansa bayan ya kunna na'urar dake bada ruwa. Ruwa yayita kwararawa kansa sai da yaji dan dama dama sannan yafito bayan ya daura alawala, Wani kayan yasake sakawa sannan ya tsaya gaban mahaliccinsa kamar yanda yasaba akoda yaushe,sallah yayita yi har karfe 3 na dare tayi sai lokacin ya kwanta bacci amma kuma baccin ya gagreshi sai tunani dake ta addabar ruhinsa daga karshe dai yayi nasara baccin ya daukeshi bashi ya farka ba sai asubah. Bacci yasake komawa bayan yayi sallar asubah,yana cikin bacci yaji Aryan yana tashinsa, "Daddy kace min mommy na ta mutu kuma jiya naganta a school..... Papa naga mommy jiya katashi kaji..." Cike da bacci a idonshi ya bude idanuwansa yatashi zaune yana kallon Aryan wanda ke sanye cikin uniform din makaranta sai kamshin turaren silver boy yake yi idanuwanshi sunsha kwalli baki, murmushi Khalil yayi sannan yajawoshi jikinsa ya rungume, "Good morning lovely son...." "Daddy naga mommy jiya a...." "Mu fara gaisawa first sai ka fada min,ko baza ka gaida ni ba yau?" "No Daddy zan gaida ka, Good morning" "Morning my love,how was your night? Wa kace kagani jiya?" "Uncle mommy na mana wadda kake nuna min a hoto har kace min ta mutu lokacin da za a haifeni..." Dan jimm Khalil yayi yana nazarin maganar da Aryan yafada,lumshe idanuwanshi yayi ya shafi sumar Aryan, "To naji Aryan...ai idan aka mutu ba a dawowa ita kuma mommy dinka ta mutu" Bude baki Aryan yayi zai sake magana Khalil ya dakatar dashi sakamakon kaiwar da idonshi yayi kan agogon dake ajiye kan bed side drawer,karfe 7:40 agogon ya nuna, "Aryan ya isa maza jeka ka tafi school kaga ka kusa makara" Kiss yayi ma yaron a kumatu sannan ya saukar dashi daga kan gadon yana tambayar shi yaci abinci? Daga masa kai yayi alamar ehh, "Me kaci?" Yasake tambayarshi yana son kawar da damuwar dake saman fuskar yaron, "Potatoes smiley & egg muffin" "Good boy,umma ta hada maka da chocolate ko?" Kai ya daga masa,kumatunshi yaja sannan ya rakashi ya koma ya kwanta bayan ya rufe kofar d'akin nashi,wani baccin yake son yi amma yasan ba mai yuyuwa bane domin yau yanada commitments da yawa gashi yana son ya je gombe ayau yadawo duk da dama yasaba hakan, hakura da baccin yayi yatashi yayi wanka ya shirya cikin fararen kaya yafita dama already table ashirye yake amma iya ruwan tea kadai ya iya sha yafita yaje ya gaida umma barira daga nan yafita office,a office dinma babu abinda yaci duk da ankawo abinci conference room din nasu,bashi yabar office ba sai 6 na yamma wato dab da magriba,daga can wani uzurin yasake wucewa bai fito ba sai misalin karfe 8 da kusan rabi kai tsaye kuma gobe suka nufa. Lokacin da yashiga family house dinsu a gombe tuni wasu ma har sunyi bacci agidan amma dai hajiya Zaitun wato mahaifiyar su bata kai ga yin baccin ba hakama sauran yanmatan gidan duk suna tare a falonta suna hira, Zama yayi agefen yanmatan gidan wato mufida da zarah da Sarah wadanda duk yan riko ne hajiya ke rikesu amma ita Zaid ne dan autanta, "Mufida ku kawo min abinci inci wallahi rabona da abinci har na manta....." Tashi suka yi dukansu suka fita ita kuma hajiya tasamu wuri ta zauna tana kallon d'an nata wanda aganinta yanzu duk ya lalace yaki yin kiba amma da ba haka yakeba, "To ba dole kayita zama da yunwa ba mu'azzam tunda ka ki yin aure ka zabi yin rayuwa kai kadai babu mace... Yanzu da kana da aure yaushe matarka zata barka da yunwa wuni guda..." Bai kai ga yin magana ba su mufida suka shigo kowaccensu rike da food flask,tuwon shinkafa suka kawo masa miyar taushe sai gasasshen nama da kunun aya mai sanyi wanda yaji kwakwa da madara da dabino sosai,saida yaran suka fita sannan ya kalli hajiya bayan yafara kwasar girkin dake gabansa, "Wallahi hajiya ba rashin aure ne ke hanani cin abinci ba, lokacin cin abincin ne ma babu kwata kwata, rabona da gida fa tun karfe 8 nasafe ahakanma dan dai ina daurewa ne bana son yin nesa da Aryan amma da wallahi sai inyi kwana biyu banje gidanba...., Ni yanzu ma banida lokacin aurenne gaba daya" "To koma dai yaya ne ai gara ace kana da matar akan ace babu Khalil,kai kaine babba kuma kana nema ka zama babban kwabo...... Ko tafiye tafiyen k'asashen wajen nan da kake yi acan kake aikata son ranka?" Cak ya tsaya daga cin abincin da yake yi sannan cikin sanyin murya yace, "Wallahi tallahi hajiya ni harkokin aikina ke fitar dani waje bawai wani abuba,haba hajiya ai ko dan Ramlat bazan iya aikata mummunan laifi kwatankwacin wannan ba..." "Nima bance kana aikatawa ba amma dai yadace kayiwa kanka fada,mutum ya radi kansa tun kafin duniya ta radeshi, mutane suna ganin kana da kudi da komai na rayuwa amma baka da mata to gani zasuyi kamar wani abu kake aikatawa agefe..." "Hajiya wallahi duk lokacin da kika yimin maganar auren nan jinina ne yake hawa saboda bana sonta..." "Ai shikenan,to Lubnah ta haihu yau da safe ta samu yarta mace,sai ka samu lokaci kaje kayi mata barka" "To insha Allah, Allah yaraya,zan dawo inyi mata barka idan nasamu lokaci, Ina zaid kuma" "Ai yatafi Abuja tunda rana,baku hadu bane?" "Bamu haduba ai rabona da gidan tun 8 nasafe" Hira ya zauna suka sha da hajiya sosai kai idan ba sani kayi ba sai kace agarin zai kwana,karfe 1 da yan mintuna suka kama hanyar Abuja, Lokacin da yashiga part dinsa a mutukar wahale yake ga gajiya ga kuma damuwar dake addabar mararsa,cire rigar jikinshi yayi yarage daga shi sai iya singilet da dogon wando,wayarshi ya dauka ya kira number nura PA,mintuna kadan sai ga nuran yashigo, Cikin mawuyacin hali ya kalli nura, "Nura ina zaka samo min kanwa ko lemon tsami?" "Ranka yadade kanwa kuma? A wannan daren? Ai yanzu babu inda za asamu kanwa acikin garin Abuja,dama dama lemon tsamin ma" "Je kasamo min lemon tsamin" Sake gyara kwanciyar shi yayi bayan nura yafita yana dafe da mararsa wacce ke murda masa wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa baya son yaci abinci ya koshi domin duk ranar da ya koshi to sai ahankali.......✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO....* *MIJIN MATACCIYA....*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad:-ummishatu* بسم الله الرحمن الرحيم *Alqaluma shida daga k'ungiyar haske na nan na cigaba da baje kolin basirarsu cikin farashi mai sauki daidai da aljihunku, akan naira dari biyar kacal zaku samu labarai guda shida cis wadanda suka hadar da Gidan rina, Hayatuddin, Izzata,Burin zuciya,Tana k'asa tana dabo,sai kuma Da ciwo a zuciyata,karku bari abaku labari,burin haske gamsar daku cikin nishadi da farin ciki.* *5* ~~~*T* amkar zaiyi kuka haka ya zama kwakkwaran motsi yana neman ya gagareshi,yana baje saman Rug din dake shimfide tsakiyar falonshi yana shan sanyayyiyar iskar _air condition_ din da ta wadata falon da sanyi marar karfi wanda bazai cutar da jiki ba, Juyi yake tayi shi kadai bayan ya tasa kansa da daya daga cikin pillows din dake kan kujerun falon sannan ga wani pillow din guda daya shima ya saka kasan kafafunshi, Tsaki yaja yakuma karawa, yayi tsaki awurin yafi sau 30 saboda bacin rai, "Mtswww shima nura yaje ya wani nemi wuri ya zauna kamar an aiki bawa garinsu.....mtsawww duk abinda mutum bazaiyi da kansa ba ai dama wahala gareshi dan sai abinda yagani kawai" Juyi yayi yakoma kan damtsen hannunshi na dama dayan hannun kuma na kan mararsa, Ahaka ya kwashe fiyeda mintuna 20 sai lokacin nura yabude kofa yashigo yana fadin, "Tuba nake yallabai....wallahi ba asamo anan kusa bane amma dai gashi andace" Tashi zaune yayi dakyar idonshi a lumshe ya karba kawai batare da yace ko uffan ba, Har nura yajuya zai fita ya dakatar dashi ta hanyar fadin, "Bani wuka a kitchen...." "To yallabai" fita nura yayi yashiga kitchen yaje kan kitchen wire ya ciro daya daga cikin wukaken dake jere akai yakoma ya kai masa lokacin kuma yana jingine da jikin kujera sai faman ajiyar numfashi yake yi, Karbar wukar yayi shi kuma nura yajuya yafita. Lemon tsamin ya yanyanka wurin guda uku take ya matse su abakinsa ya shanye yana mai yamutsa fuska saboda tsami,tamkar abin shiri cikin mintuna kadan yajishi garau ya dawo cikin nutsuwarsa, bedroom dinshi yawuce yaje yayi wanka yasa kayan bacci sannan ya fita zuwa dakin Aryan,shi kadai yasamu yana kwance yana bacci bayan ya gama game domin ga ga game dinnan na tayi ko kashewa baiyi ba, sannan ga text books dinshi nan suma bisa saman gadon, Sai da ya kintsa masa komai sannan yayi masa kiss a kumatu yafita. Bedroom dinshi ya shiga ya kwanta bayan yayi shafa'i da wutri domin yau kam bacci yakeji da gaske bada wasa ba saboda jiya bai samu bacci ba yanda ya kamata kuma yau da safe ma haka,duk da gobe babu aiki ana yin public holiday amma shi yana da tarin ayyuka wanda dole sai ya fita yaje ya gabatar dasu, pic din Ramlat ya kalla sannan ya kwata ya lumshe idanuwansa bayan yayi addu'ar bacci. Washe gari da safe asubanci yayi yafita daga gidan tun kafin mutanen gidan su tashi, shiyasa lokacin da Aryan ya tashi kuka yafara yi bayan yaje bedroom din Khalil bai ganshi ba shi ina Daddynshi? Sai da Zaid yafito yayi masa wayo sannan ya hakura daga karshe Zaid din ya daukeshi suka fita tunda yau babu makaranta. Duk da Khalil ya fadawa Aryan cewa ya daina maganar yaga mommynshi a makaranta ba ita bace ita ta rasu bai hakura ba kullum cikin maganar yake kuma idan yaje makaranta yakan duba gaban staff room wai ko zai ganta, kullum sai yaduba wurin amma bai sake ganinta ba, Khalil kuwa har yagaji da maganar nan gashi da zarar Aryan yayi masa maganar sai yaji damuwar sa da raunin dake cikin zuciyarsa sun dawo sabo fill. Yau ma da suke zaune a falonshi shida Aryan da Zaid Aryan yana game a wayarshi sai yasaka pause yajuya ya kalli Khalil wanda ke magana da zaid yana cewa, "Ai Zaid mutane ne kadai ke ganin kamar muna jin dadi amma wallahi azahirin gaskiya wahala muke sha,sam fa mutum baida hutu sannan baida lokacin kansa kana gani kai kanka tunda kazo bamu haduba bamu zauna dakai ba sai yau.... Kai ai wannan rayuwa tana da wahala" "Daddy..... Mommy" Jin abinda Aryan yafada yasashi juyawa ya kalleshi shi wallahi yasoma gajiya da wannan maganar mommy din domin bata masa rai ma take yi, "Daddy zamuje da mommy new york?" "Ban saniba,ba nafada maka idan kagama exams dinka zan kai ka can ba? Kamin shiru da bakinka" Shiru yayi ya kama bakinshi kamar yadda Khalil yasaba sashi idan ya hanashi surutu sai yasashi ya kama bakinshi. *** A bangaren Hanan kuwa cike da farin ciki da murna ta isa gida tana ta dokin ganin mutanen gida kamar irin ta shekara dinnan bata gansu ba domin dama ita bata saba yin tafiya taje wani wurin tayi kwanaki ba shiyasa wannan dan sati uku zuwa hudun da tayi take ganin kamar watanni ne tayi batare da taga yan gida ba. Tun aranar mujahid yazo domin shima cike yake da dokin ganinta, Kamar yadda ta kawowa kowa dake gidan tsarabar turare shima mujahid haka ta kawo masa turaren secret man, Tallafe kumatunsa yayi yana kallonsa saboda azahirin gaskiya tayi bala'in kyau domin da alama weather din garin Abuja ta karbi fatar jikinta tayi wani luwai luwai sai sheki take yi tana kyalli, "Wai yallabai menene ka tisani agaba kana kallona kamar yau kafara ganina?" Murmushi mujahid yayi sannan ya janye idanuwanshi daga kanta ya mayar kan sitiyarin motarshi, "Wallahi kinyi kyau ba karya,gaskiya Abuja ta karbeki,ko can zamu zauna ne?" Yar dariya tayi sannan ta shafi fuskarta, "Wai haka ma su yaya shamsu suka ce,wai nayi kyau kamar bani ba yar dukununun fatata duk ta haska tayi kyau ashe da gaske ne...." "Allah dagaske ne kinyi kyau amarya ta kamar irin kin fara cin amarci dinnan..." "Uhmmm zaka fara ko,kai a kullum baka da magana sai ta aure" "To bashi ne araina ba? Ai dole intayi miki maganarsa ko zaki ji tausayina ki bani dama" "To nidai yanzu gobe kazo ka kaini gidan anty salaha inje mu gaisa inbata labarin Abuja" "Duk yanda kikace haka za ayi da girman kujerarki...." Cikin sati biyun da tayi a kano ta harhada kayanta jimilla gaba daya wadanda zata tafi dasu sannan ta sissiya wadanda take da bukata,ranar da zata tafi yaya shamsu ne da mujahid suka kaita basu suka baro garin abuja ba sai magriba yayinda ita kuma ta zauna zaman shirya kayanta a daya daga cikin dakunan dake cikin quarters din makarantar domin yanzu tabar Lodge hukumar makarantar bright future tabasu masauki a quarters din malamai wanda ke dauke da komai na more rayuwa, Wallahi sosai abun ya burgeta kuma yayi mata dadi haba zatayi service a dadi komai yana zuwar mata cikin sauki duk ma dai da term din yakare domin exams za afara to amma yazama dole su kasance suna kusa. Washe gari ashraf ne ya tadata daga bacci wai zaizo yaganta kafin yabar Abuja,tana fitowa daga wanka yakaraso kaya kadai tasa tafita ta sameshi waje yana jiranta,suna tsaye dashi suna hira motar Khalil tashiga cikin makarantar inda zasu ajiye Aryan sannan yawuce kaduna shida nura PA,duk da ba akusa suke ba ahakan Aryan ya hangota,kama hannun Khalil yayi yace, "Papa kalli mommy can...." Khalil bai kulashi ba ya saka hannu cikin aljihunsa ya ciro wayarshi ya soma latse latse har suka ajiye Aryan bai kulashi ba sai babbata rai Aryan din ketayi, Tun daga ranar walwalar Aryan ta ragu ahaka har suka fara exams ita kuwa Hanan bama sosai take shiga cikin makarantar ba saboda jarabawa akeyi aikin da ake basu kadanne ba wani aiki sukeyi sosai ba amma dai suna yin nasu daidai gwargado,ana yin hutu ta tattara nata inata ta nufi gida kanon dabo. *** Tunda aka gama exams Aryan ke faman yiwa Khalil rigima akan maganar mommynshi, Aryan irin yaran nanne da basa mantuwa kai sai ma ka manta da abu shi bai manta ba, Rarrashinsa Khalil yafara yi yana cemasa, "Kamanta da maganar mommy dinnan kaji yaron kirki,ana yimuku hutu zan kaika Jos kaga yan uwan mommynka sannan zan kaika gombe wurin hajiya ai zakaje ko? Daga nan zan daukeka mu tafi new york inda zaka kare hutunka gaba daya acan,kullum zamu rinka zuwa central park kana shan ice cream...." Makale kafada Aryan yayi yana turo baki, "Ni wurin mommy nake so..." "Kai..... Shut up.....ba na hanaka wannan maganar ba? Get out of here ko in bugeka,marar jin magana" Tsawar da Khalil yayi masa ce ta razanashi yafita da gudu yaje ya zauna a falo yana kuka abunka da yaran hutu wadanda basu saba ba take temperature din jikinsa ta sauya kansa yafara ciwo shikenan sai numfashi sama sama, Shi kuma uban na can dakinshi yagama shiryawa zai fita zai tafi kano ta'aziyar baban wani classmate dinshi,duk atunaninshi Aryan na wurin umma barira,har zai fita ta kofar side dinshi sai yafasa domin bai yiwa umma barira sallama ba, Ta babban falo yabi acan ya hango Aryan sheme saman carpet yana wani irin abu kamar mai iska,kansa yaje ya dagashi duk hankalinsa atashe,baima tsaya ya saurari fitowar umma barira ba yanufi waje dashi, Asibiti suka kaishi nan aka fara bashi taimakon gaggawa,shidai a iya saninshi Aryan lafiyayyen yarone bashi da wata lalura sai dai ko boyayyiya wacce bata bayyana ba, Abinda likita yafada masa ne yayi mutukar girgizashi wai zuciyar Aryan yar mitsitsiya ce sannan dole aguji bacin ran shi adaina hanashi abinda yake so,to ai dama Khalil a iya saninshi abinda Aryan yakeso yake masa dan shi ko fada bai yarda wani yayiwa yaronsa ba, Aranar da daddare aka sallamesu,tunda suka koma gida yaketa nan nan da Aryan ranar ma tare suka kwana,da zarar yayi masa maganar mommy kuwa sai yace ehh zai nemo masa ita duk inda take,abun har mamaki yabashi saboda irin yanda yaga yaron yanata murna yana farin ciki,shima farin cikin yaji ya samu kansa aciki domin farin cikin Aryan shine nasa, Aryan ya cancanci dukkan soyayyar da ta dace daga gareshi domin yarasa mahaifiyar shi a lokacin da yake tsananin buk'atarta baiji dumin jikinta ba haka kuma bai sha ruwan madarar dake fita daga jikinta ba shiyasa yanzu dole ya zame masa uwa kuma uba dole yasamar masa da dukkan farin cikin da yake buk'ata koda kuwa hakan zaisa shi yarasa nasa farin cikin......✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO.....* *MIJIN MATACCIYA....*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad:-ummishatu* بسم الله الرحمن الرحيم *6* ~~~*R* anar hutu Khalil da kansa yakai Aryan makaranta saboda tunda suka tashi daga bacci yaga alamar da rigima Aryan din yatashi dan sai wani tutturo baki yake yi breakfast ma saida lallami yasamu yaci amma da umma barira tayi tayi dashi ya zauna yaci yaki ci daga k'arshe ta kira Khalil awaya,yana kwance yana bacci yaji karar wayar landline ta cika masa kunne wacce ke ajiye saman drawer din gadonshi,dole tasa yatashi ya daga wayar domin yasan daga cikin gidan ake kiransa ko securities ko wani daga cikin jama'ar dake cikin gidan addu'ar shi dai bata wuce Allah yasa ba baki yayi ba da sanyin safiyar nan domin ko wanka baiyi ba, Muryar umma barira yaji tana cewa, "Mu'azzam zo kaji da wannan kinibabben yaron naka dan ni bazan iya ba nayi lallashi har nagaji yaki jin lallashina tunda kai kaine ubansa kila zaiji naka....." Jin abinda umma barira tace yasashi yin murmushi mai dauke da sauti yasauka daga saman gadon yana kokarin zira silifas dinshi dake ajiye gaban gadon domin tana gama fadar abinda ta fada ta katse layin, Gaban closet dinshi yaje ya tsaya yacire farar riga armless din dake jikinsa yasaka jallabiya kalar ruwan kasa sannan yafita, A babban falo yasamesu suna drama umma barira nata tura masa soyayyen dankalin turawa wanda ya wadatu da kwai ga plantain shima agefe da wainar kwai sharba sharba amma yaki ci sannan ga tea dinshi nan a dan karamin cup dinshi, Umma barira na ganin yashigo ta mike ta nufi cikin falon tabar dining room din tana fadin, "Khalil wannan yaron naka dan jakar ubane ayita shan kansa amma yana sake botsarewa.....to nidai nayi nawa jeka kaima ka gwada taka sa'ar" Murmushi Khalil yayi yana kallon Aryan wanda ke zaune saman dining yana ta turo baki, "Ai ni dama tunda naga har yanzu bai shigo dakina ba nasan da walakin.... Bari naje na bashi abincin....." Daga haka yawuce wurin Aryan ya zauna akusa dashi sannan ya dagashi ya dora kan cinyarsa, "Baba na yau kuma abinci ake yiwa yaji? Uhmmm? Yau fa za abaku hutu amma banga kana murna ba.... Kana da kiwar zuwa school Aryan,nifa when i was young kamarka banyi gardamar zuwa makaranta ba..." "Papa ni bazan ci wannan ba..." "To me zaka ci? Fada min maza adafa maka kaci ka tafi school ka karbo report card dinka" "Noodles...." "To ai mai saukine bari adafa maka within 5 minutes...." Tashi yayi yafita ya kira kuku nan da nan kafin wani lokaci ya dafa noodles din mai kunshe da vegetables aciki da kifin gwangwani sannan ga soyayyen kwai akai, Zama yayi yabashi abaki yaci ya koshi sannan yaje ya kaishi da kansa daga nan ya juyo gida domin kamar koda yaushe yauma yana da inda zaije. Tunda yafita bai samu dawowa ba sai misalin karfe 10 saura na dare yayi mamaki sosai da yaga wai idon Aryan biyu a wannan lokacin baiyi bacci ba,yana ganinshi ya ruga da gudu ya rungumeshi yana rike da report card dinshi a hannu,daukarshi Khalil yayi yana karbar report card din,fuskarshi ce ta fadada da murmushi da fara'a har yakai bakinshi kan goshin Aryan yayi masa kiss, "Yaron kirki this time around baka yarda suhail ya kwace maka first position din ba?? Kayi kokari,zan yi maka duk abinda kake so kaji...me kake so?" Kwantar da kanshi yayi jikin kafadar uban sannan ahankali yace, "Mommy..." "To Aryan din Daddy..." Tare dashi sabe a kafadarshi yawuce bedroom dinshi ya ajiye shi saman gado shi kuma ya fara kokarin rage kayan jikinsa. Bayan yayi wanka yayi shirin bacci yana zaune saman Rug da Aryan kan cinyarsa yana bacci umma barira ta kira waya tana tambayar ko suna tare da Aryan domin ta shiga dakinsa bata ganshi ba kuma baya wurinta,niyyar tsokanarta yayi yace, "Umma baya wurina ni nan ni kadai ne" "To sai ku bazama nemansa domin nima baya tare dani" "Umma kenan kin ganshi nan yana bacci,hira ma muke yi yayi bacci ya barni..." "Aima yayi kokari da har kadawo ka sameshi ido biyu shida kafin 8 wani lokacin yayi bacci amma yau ya dan taba baccin rana wuni yayi yana bacci inajin shiyasa baiyi na daren da wuri ba" "Ai nima nayi mamakin ganin idonshi biyu lokacin da na shigo" "Ina ruwan mai gida" Katse wayar yayi yana dariya shi bama dan yayiwa Aryan alkawari ba da ya turasu umarah shida umma barira,babu abinda zaice da ita sai godiya domin tana tsananin kaunar gudan jininsa ko ita ta haifeshi sai haka abinda hajiya mahaifiyar shi zatayi masa shi umma barira take yimasa duk tsawon lokacin nan da ta dauka tare dasu shekara da shekaru bazai iya cewa ga laifinta ba kullum cikin tattalinsu shida yaronsa take. Cikin dakinshi yakai Aryan suka kwana tare,bayan kwana biyu da yiwa su Aryan hutun makaranta Khalil yasa umma barira ta shirya kayanta da na Aryan shima ya shirya nasa suka nufi gombe domin shima ya dauki hutu a office,tun da suka je gomben ma bai zauna ba kullum cikin karbar baki yake da yawon gaishe da yan uwa da abokan arziki,duk wasu dangin hajiyarsu da dangin abbansu sai da yaje ya gaidasu tare da yimusu rabon masu gidan rana,kwanansu uku a gombe ya dauki Aryan suka tafi jos wurin iyayen Ramlat,shi a hotel ya sauka bayan yakai Aryan gidansu Ramlat sai dai kullum yana zuwa gidan domin ya duba Aryan,harga Allah yana jin dadin irin yanda ummi kanwar Ramlat ke kula da Aryan sannan duk itace ke wahala da tiriniyar kaishi gidajen yan uwa,har gobe iyayen Ramlat basu daina kwadayin sake hadashi aure da itaba amma shi bazai taba iya auren ta ba da ace zai iya to da ya aureta ko dan kulawar da take yi da dansa. Kwanansu biyu a garin jos daga can suka wuce Calabar babban birnin jahar cross river domin ya fahimci Aryan yana son yaje yaga yan uwanshi wato yaran Khalid cousin dinshi,kwanansu daya da yini daya adaren ranar suka tashi suka nufi babban birnin new york. Kamar yadda yasaba duk lokacin da suka tafi hutu shida Aryan yakan samu lokaci sosai ya zauna tare da yaron suyi ta hira yana bashi labaru na ban dariya da nishadi da tatsoniyoyi kala daban daban hakan ba karamin sake kara musu shakuwa da sakin jiki da kusanci yake yi da yaron ba, sannan yakan ware musu lokaci a kullum su fita su zaga gari su je wuraren shakatawa da wurin wasannin yara domin debewa Aryan kewa banda shagunan sayar da kayayyaki da yake kaishi ya siyo masa duk abinda yake so. Wannan karon ma hakance ta faru a k'asar new york,duk inda yadace yakai Aryan yakaishi sannan sun samu lokaci sosai wurin kasancewa da juna,sunsha hotuna har sun gaji dama Khalil yakan tafi da yar karamar camera saboda daukar hotunan tarihi, Satinsu uku sannan suka fara haramar dawowa,saida suka je babban kantin sayar da kaya dake cikin birnin Khalil ya jibgo masa kayan sawa da takalma dan hatta school bag dinshi da combos da sauran kayan sawarshi duk acan yasiyo masa, Baiyi wata tsaraba mai yawa ba sai yan abubuwan da ba arasa ba ya sissiya daga nan suka nufo gida Nigeria,a Abuja suka sauka dama tun da Khalil yace gobe zasu dawo umma barira ta shirya ta tafi Abuja dan haka can suka tarar da ita, Daga Aryan tayi ta rungume suna dariya gaba dayansu yana sanye da dark blue din jeans da jar t shirt ta kamfanin polo sai jan takalmi shima na kamfanin polo,yanda yayi wannan shigar shima uban ita yayi sak jeans da t shirt duk irin na Aryan. Bayan sun dawo sai da sukaje gombe suka gaida hajiya sannan suka juya aranar,ranar Monday Aryan suka koma school shi kuma Khalil yakoma office shikenan yazama busy kullum bashida hutu. A bangaren Hanan itama ta shirya ta koma Abuja bayan hutu yakare nan kuma akaje aka fara koyar da dalibai babu kama hannun yaro duk sai ta zama busy itama saboda marking din script din dalibai kadai ya isheta shiyasa yanzu bata da lokaci sosai. Shi kam Khalil Aryan ne ya bi duk ya dameshi da maganar mommy gashi baya samun lokaci sosai amma kullum yaron cikin maganarta yake daga karshe da yagaji sai yatura PA dinsa yace yaje ya binciko masa koma wacece wannan yarinyar da Aryan keta faman magana akanta kullum. Cikin kwanaki biyu kacal nura yazowa da Khalil amsa lokacin Khalil din yadawo daga bauchi yana dan hutawa acikin falonsa,dan russunawa nura yayi sannan yace, "Ranka yadade sunanta Sa'adatu mustapha mai jama'a taura,mahaifinta haifaffen garin taura ne,amma yanzu haka suna zaune acikin garin kano a unguwar sabon titi mandawari...." Dan murmishi Khalil yayi yashafi sumar kanshi sannan yace, "Ashema 'yarmu ce,to ai ta kwana gidan sauki,nura kana iya tafiya, nagode" "Nabarka lafiya yallabai" daga haka yajuya yafita, murmushi Khalil yasake yi akaro na biyu yana jin dadi har can cikin kasan ransa zaiyi surprising Aryan,zai kawo masa Mommy har gida ya ajiye masa ita yayita kallonta hakan ita kadaice mafita. Acikin satin yaje har gombe yasamu hajiya da Abban London da maganar ai kuwa zo kaga murna wurin iyayen nasa musamman ma hajiya da dama tafi kowa matsuwa da damuwar rashin auren nan nasa,washe gari Abba da kansa ba sako ba yashirya ya tafi kanon dabo neman aure, Da dafarko shi mahaifin Hanan ma yayi zaton ko batan kai akayi amma da Abba yayi masa bayani sai ya fahimta yagane ba batan kai aka yiba,nan yace yabada auren hanan ai ko da ace akwai wani to zai iya hanashi yabawa Khalil bare ma babu,shi ai Khalil nasa ne atakaice dai Abba bai baro kano ba sai da ranar auren Khalil sannan abbanta yace Khalil din yasamu lokaci yaje su gana. Yan hidimar k'asa kuwa ana can Abuja ana hidimtawa k'asa yanda ya kamata,kullum suna mak'ale da mujahid awaya dawowarta kuwa zuwansa biyu kullum cikin maganar tabari yatura gidansu yake amma ta murje idonta tace sam ita ba yanzu ba. Wata ranar alhamis sukayi waya da abbanta nan yake cemata, "Uwar masu gida ki daure ki samu kizo acikin weekend dinnan domin inada muhimmiyar magana dake sannan kuma zamu samu bakuncin manyan mutane" "To Abba insha Allah gobe dama nake son tahowa" Tunani tai tayi aranta bayan sun gama waya da abba,to ko suwaye manyan bakin da zasuyi kuma oho,ko menene dalilin da yasa Abba yace taje gida oho,ko wacce muhimmiyar magana zasuyi da yace mata zasuyi duk Allah masani amma gaba daya hankalinta yatafi gida kawai so take ta ganta acikin garin kano,aranar taje tayi yar siyayyar kayan marmari domin yin tsaraba dama anyi musu alawee tun ranar Monday,washe gari tun 7 tafita taje tayi signing sannan ta tafi tasha ta hau mota cikin lokaci k'ank'ani mota ta cika fam suka kama hanya.......✍️ _Game bukatar biyan kudin wannan book din zai turo naira 200 ta Account number dina 3112877210 Aisha Ibrahim first bank,sai atura shaidar biya ta wannan number din 07044644433 ko kuma atura MTN recharge card zuwa wannan number din 07044644433 sai atura shaidar biya ta the same number da aka tura katin nagode._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:06 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO.....* *MIJIN MATACCIYA.....*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad-ummishatu* *Alqaluma shida daga k'ungiyar haske na nan suna cigaba da baje kolin tasu basirar,nemi naka kaima adama dakai cikin farashi mai rahusa.* *7* ***Har motarsu ta isa kano tunani daban daban bai daina kai kawo acikin ranta ba,duk ta kasa samun nutsuwa sai tufkawa da warwarewa take ta faman yi tana son gano dalilin wannan kiran gaggawar da Abba keyi mata wanda abisa dukkan alamu akwai abinda ke faruwa ko kuma yake shirin faruwa. Ita dai har motarsu tashiga kano ta sauka ta tare mai napep ta shiga zuwa gida zuciyarta bata daina yimata wasi wasi ba,alla alla takeyi taganta agida dan taga abinda ke faruwa shiyasa jiki a sanyaye ta shiga gidan bayan ta sallami mai napep din da ya sauketa, Mamaye ce kadai tana kwaba fulawar da zatayi dan wanke a kofar kitchen abisa dukkan alamu shima yaya shamsu baya nan,ganin fuskar mamaye awashe sannan kuma asake alamun babu matsalar komai yasata ta danji sanyi acikin ranta, Kayanta ta shigar cikin daki sannan ta dawo wurin mamaye suka fara gaisawa, "Mutanen Abuja kinsha hanya kuma kun fito da wuri..." "Ehh wallahi mamaye tun wurin 7 fa muka fito dan ni ko karyawa ma banyi ba" "To ai akwai ruwan zafi a flask sai kije kihada shayi kisha" "To bari insha abisa lalura amma shan shayi da rana ai sai ahankali" Daga haka ta tashi tawuce falo ta hado tea ta dauko bread ta sake dawowa wurin mamaye. Sai la'asar sannan abbba yadawo lokacin suna zaune da mamaye da yaya shamsu suna hira, Wurin Abba taje suka gaisa sannan suka dan taba hira kadan har zata tashi abba ya dakatar da ita, "Uwar masu gida sai kuma kikaji kira ko?" "Ehh Abba dama nima ina son inzo gidan inganku ai" "To wani abokina ne kuma aminina ya nemi wata alfarma awurina wadda nikuma bazan iya kin yimasa itaba,ya bukaci inbashi aurenki nikuma bazan iya hanashi ba...." Jin abinda Abba yace yasata zaro ido tare da jin firgici gamida gagarumar faduwar gaba,bata san lokacin da tace, "Abba abokin ka?" "Ehh uwar masu gida... abokina amma nasan insha Allah zaki sameshi kamar yadda kike so,zaki ji dadin kasancewar shi mijinki, matarsa ce ta mutu a lokacin haihuwa,dansu daya kacal wanda ta mutu ta bari...." Kamar wacce aka zarewa laka ajikinta haka taji bata san lokacin da hawaye ya ziraro ta idanuwanta ba, "Abba kuma shine da kansa yaganni yace yana sona?" "Shine Hanan,shi yaganki anan Abuja,acan yake da zama minister ne,shine ministern yada labarai,matasa,raya al'adu da wasanni,yanemi da inbashi aurenki kuma na bashi nan da sati uku za adaura muku aure,sai kije kifara shirye shiryen da duk ya kamata.... Allah yayi miki albarka" Bata iya cewa komai ba ta tashi tafita idanuwanta cike da hawaye tausayin kanta da kuma mujahid take yi,yanzu me zata cewa mujahid? Da wacce kalma zata dosheshi har tayi masa bayani? Da wacce kalma yadace tayi amfani wurin sanar dashi wannan bakin labari? Daga mamaye har yaya shamsu babu wanda tayiwa magana tawuce daki taje ta kwanta tasoma shakar kuka,duk tsawon shekarun da suka dauka tare da mujahid bata taba jin sonshi ba sai yau da taji zata rasashi,wata zazzafar soyayyar shi take jin tana shigarta babu k'akk'autawa, Tajima tana kuka kafin mamaye tashigo ta zauna gefenta tasoma bata baki, "Hanan kiyi shiru wannan kukan baida wani amfani,kiyi shiru ki mika al'amuranki ga Allah ki nemi alkhairinsa da kuma albarka acikin aurenki...." Kamar jira take tasake fashewa da wani hargitsattsen kuka mai tsayawa arai, "Mamaye abokin Abba ne fa wai,wai abokin Abba,mamaye yanzu ni anyi min adalci kenan idan aka aura min wannan mutumin? Mutumin da ya haifi yani? Mutumin da yafara ban kwana da duniya yana kusantar kabari,inama laifin abani zabi idan ina sonshi a aura min idan bana so abarni amma sai kawai ayi min dole ayanke hukunci batare da anji ra'ayina ba...." "Ki daina fadin haka Hanan,iyaye sunada damar zabawa yaransu mazaje hakan bai saba ka'idar musulunci ba,kiyiwa mahaifinki biyayya sannan kiyi addu'a insha Allah bazaki tabe ba" "Mamaye nidai har ga Allah bana sonshi, tayaya zan auri sa'an babana? Abokin Abba fa,sa'an abba ne fa mamaye, yanzu Abba yarasa wanda zai aura min sai abokin sa?" "To ni me kikeso inyi akai Hanan? Yariga da ya yanke hukunci,aikin gama yagama, k'addara tariga fata sai dai kawai kidau hakuri kiyita addu'a, Allah ya zaba miki abinda yafi alkhairi a rayuwarki" Daga haka mamaye ta tashi tafita tabarta tana ta faman gursheken kuka kamar ranta zai fita, Wannan wacce irin k'addara ce? Ita mema yakaita Abuja yin service gashi nan mutum yaganta yazama silar rushewar farin cikinta, duk yanmatan Abuja yarasa wacce yagani yake so sai ita? Dan dai kawai yana da kudi sai yarinka amfani da damarsa yana taka duk wanda yaso? Insha Allah sai Allah yasaka mata,ita dai tasan Abba bawai kudi yabi ba wurin aurar da ita ga wannan bawan Allah,koda yake yace abokinsa ne watakila wannan shine dalilin da yasa ya bayar da ita batare da yajira yaji ra'ayinta ba. Wayarta ta dauka tana share hawayen dake zuba daga idanuwanta tana face hancinta da tissue,text massage ta turawa mujahid kamar haka, _Ban taba sanin cewa bakaine abokin rayuwa ta ba sai yanzu da k'addara ta gifta,ashe ba Kaine mijina ba shiyasa kayita bina akan zaka turo gidanmu amma naki gashi yanzu Abba ya bayar dani ga abokinsa,ya zanyi mujahid? Wallahi ina tsananin sonka musamman ma yanzu da ake neman rabamu._ Ai tunda mujahid yaga massage dinta hankalinsa shima yabar jikinsa,jiki yana rawa yakirata,shiru yayi yana sauraren sautin kukanta da yacika kunnuwanshi, Daga shi har ita sun kasa cewa komai ita sai kuka takeyi murya adashe, Cikin sanyin murya mai kunshe da damuwa yace, "Hanan kiyi shiru....kiyi hakuri ki daina kuka kinji,ni nafi cancanta da inyi kuka bake ba domin wallahi ko tantama banayi soyayyar da nake yimiki ta ninka wacce kike yimin.... Ina sonki fiyeda tunaninki,kullum da sonki nake kwana nake tashi...." "Mujahid tsohone fa,wai minister ne a Abuja, Abba baiyi min adalci ba,abokinsa fa zai aura min" "Hanan ina son ganinki,yaushe zan ganki?" "Mujahid sai dai mu hadu agidan anty salaha kaga bazai yuyu kazo nanba Abba yaganka,idan nafita zan kiraka" "Shikenan babu matsala amma ki daina kuka kinji" Shiru tayi ta katse wayar amma maganar ta daina kuka kam tasan abune wanda bama zai taba yuyuwa ba, ai dole tayi kuka rabuwa da masoyi sai dole bawai dan ana so ba, mujahid ako ina zata kirashi masoyinta domin yana tsananin kaunarta kamar ita kadaice macen da tayi saura a duniya, Kuka kam tayi shi ta kara har tagaji, zuciyarta koda yaushe cikin kunci take da radadi Allah ya isa kuwa tayiwa abokin Abba tafi sau dubu domin shine mutum na farko da yafara yunkurin rabata da farin cikinta, Washe gari ta tashi da niyyar zuwa gidan anty salaha amma Abba yace babu inda zataje tajira saboda zatayi bako domin yau angon yace zaizo su gana,tamkar zata fashe haka tazama saboda tsabar cikar da tayi. *** Tunda ya fadawa Aryan cewa nanda 3 weeks zai kawo masa Mommyn shi yaron ke cikin farin ciki marar misaltuwa, Dadi ne ya lullube zuciyar Khalil sosai saboda ganin Aryan cikin farin ciki,aranar ya shirya yatafi gombe yaje yaga Abba suka tattauna akan yanda abubuwan zasu kasance anan Abba kece masa sai yasamu lokaci yashirya yaje su gana da yarinyar,yadai ansawa Abba da toh amma harga Allah ba zuwa zaiyi ba shi ina yaga wani lokacin zuwa zance wurin budurwa yanzu? Acikin ayyukan sa wanne zai tsallake yatafi hira? Duk ma ba wannan ba shifa auren nan kawai zaiyi shine saboda Aryan bawai saboda kansa ba shi idan dan ta shine shida aure sai dai yaga anayi amma ayanzu kam babu macen da ta isa, Maimakon yaje sai kawai yatura PA dinsa yaje yaga Hanan sannan yakai mata sako, Lokacin da nura PA yaje Hanan a murtuke taje ta sameshi a dakin saukar baki dake kofar gida,motar ma da yazo da ita kawai abar kallo ce saboda kyanta da tsaruwarta,duk azotanta akwai ubban gayyar sai taga sai iya mutum daya, Dan russunawa nura yayi sannan yace, "Ranki yadade barka da fitowa,ayi mana afuwa yallabai bai samu damar zuwa ba da tare zamu zo dashi to sai kuma meeting na gaggawa ya sameshi,amma duk da haka ga sako yabayar inkawo miki...." Envelope ya ajiye mata da wata babbar leda, "Babu komai.." shine kadai abinda tace bayan yagama rattabo mata bayanin. Daga haka yamike da niyyar tafiya domin tuni dama tun kafin fitowarta yaci snacks da drinks din da aka tanadar masa, "Amm yawwa sannan yace idan kina bukatar ganin hotonshi sai in......" Tun kafin ya karasa ta dakatar dashi, "Bana bukata...." Mamaki ne ya addabi ruhin nura PA ita kuwa wannan yarinyar ya take kokarin yin sakarkaba? Ya take kokarin yiwa kanta asara? Ita da Allah yayi mata gam da katar da kabakin arziki ya zabota cikin dubban mata amma shine take nema ta butulce? Saka takalmansa yayi sannan yasake dan russunawa, "Na barki lafiya ranki yadade" "Nagode,ka gaida gida" Fita nura yayi babu jimawa itama ta tashi tafita batare da ta dauki kayan da nura ya ajiye mata ba sai yaya shamsu ne lokacin da yashiga ya fito mata dasu yabita cikin gida ya kai mata, Tana daga kwance cikin daki tajiyo muryar abba yana cewa, "Uwar masu gida kina ina? Inbanda shirmenki uwata kuma akawo miki kaya ki taho ki baraso acan? Ai sai ki dauka ki duba haka akeyi" Fita tayi ta saka hannu biyu ta karbi kayan awurin Abba sannan tajuya takoma daki zuciyarta nayi mata wani irin tukuki........................✍️ _Ga wadda keda bukatar biyan kudin littafin mijin matacciya sai ta aiko da naira 200 ta account 3112877210 Aisha Ibrahim first bank sai atura shaidar biya ta wannan number din 07044644433,ko kuma katin waya na MTN zuwa ga 07044644433 sai atura shaidar biya ta wannan number din da aka tura katin,domin neman Karin bayani za a iya tuntubar marubuciyar kai tsaye ta wannan number 07044644433._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO.....* *MIJIN MATACCIYA......*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *8* ***Kamar tayi fatali da kayan da ya aiko mata haka taji nan ta watsar dasu saman gado takoma gefe ta kwanta,tsabar yawan kukan da takeyi yanzu har takai takawo ma bata iya kukan sai dai tayi girim tana tunani wanda hakan ba karamin daga hankalin mamaye yakeyi ba ita tsoronta ma kar hawan jini ko ciwon zuciya ko kuma wata lalurar mai kama da haka ta kama mata yarinya hakanne ma yasa mamaye tasamu Abba da maganar tace masa kodai zaiyi hakuri ya janye maganar auren nan yabawa minister hakuri saboda yarinya bata so ita kuma tana gudun fadawarta mawuyacin hali, Budar bakin Abba sai cewa yayi ai muddin idan suka ga ba ayi auren nanba tofa kwanan dayane acikinsu ya kare amma shi ko bayan ransa bai yarda Hanan ta auri wani miji bayan abokinsa ba,shine kadai mijin da ya zaba mata kuma ya yarda ta zauna dashi, Haka mamaye tafito jiki babu kwari domin Abba fada yayi ta yimata yana cewa ya zata biyewa shirmen Hanan duk da ta girma ai har yanzu bata san abinda zai amfaneta agaba ko sabanin haka ba tunda abinda babba ya hango daga zaune yaro ko yahau rimi ba lallai ya hangoba,shi yasan mijin da yadace da hanan sannan yasan waye ya kamata yazama tare da ita shiyasa yayi mata wannan zabin. Kasancewar yanzu bata iya kuka yasata yin shiru tana sauraren fadan da mamaye ke yimata cikin lallami da nasiha tana cewa ta daure ta cije tayiwa mahaifin ta biyayya insha Allah zataji dadi agaba sannan zatayi farin ciki ko dan biyayyar da tayiwa mahaifin ta sannan mamaye ta kara da fadin, "Insha Allah Hanan sai kin yi alfahari da mahaifin ki,sai kinyi dariya agaba ko dan bin umarnin mahaifinki da kikayi kika masa biyayya,iyaye ba zasu taba cutar da yayansu ba sai dai abisa kuskure,duk abinda kikaga mahaifinki yayi to yayi miki ne dan soyayyar da yake yimiki,ke kanki shaida ce mahaifin ki yana tsananin sonki saboda ma soyayyar da yake yimiki da ace bani na haifeki ba to da bazan iya zama daku ba domin yafi fifitaki akaina... Ko kin manta yanda kuke hade min kai keda shi...?" Murmushi mamaye tayi,itama Hanan din murmushi tayi tana tuno shekarun baya nan abubuwan da suka faffaru abaya suka soma dawo mata kamar yanzu ne suke faruwa, Kamar yanda mamaye taso haka ta dan saki ranta tana hira har da su dariya idan mamaye ta fada mata wani abu,sai da aka kira sallar magriba sannan suka tashi,ita da yake bama sallar zata yi ba kitchen tawuce ta zubo abinci dan kadan domin yanzu bata iya ci dayawa,sai da tagama cin abincin sannan takoma cikin daki nan ta bude sakon da minister ya aiko mata, Ledar tafara budewa nan taga tamfatsetsiyar sabuwar waya kirar kamfanin Samsung mai mutukar kyau da daukar hankali harda sim card aciki, Tabe baki tayi cike da jin haushi tace, "Tsabar ya rainawa mutane hankali da wayo shine shi baizo ba saboda yafi karfin yazo sai aikowa yayi,kuma ko waye yace masa bani da arzikin waya da har zai siyo ya bayar akawo min.... Saboda ga yar talakawa ko" kwafa tayi da karfin gaske sannan ta bude envelope din tana tsaki, Kudi tagani bugun Abuja sababbi fil yan dubu dubu wanda bazata iya kiyasta adadinsu ba sannan kuma ga dan karamin card nan ajiki anrubuta, _Ibrahim Sulaiman I._ Sai phone number dinshi a k'asa, maganar PA ce ta fado mata inda yake cemata, "Akwai number dinshi ajiki yace idan kina da bukatar magana dashi ko wani abu mai kama da haka sai ki kirashi...." Ita bazata kirashi ba amma dole ce zata sa tayi hakan ko dan tunatar dashi kuskuren da yake neman tafkawa dan kawai yana da kudi,saboda kawai yana da dama shine zaiyi amfani da karfin mulkinsa wurin musgunawa wasu, Number wayar tashi ta kwafa tasoma kira domin so take ta fada masa maganar da zata bakanta masa rai watakila ma idan yaji haushi yace yafasa tunda bata da kunya, Saida ta kira wayar sau hudu amma bata shiga sai dai ta danyi wata yar kara sai ta yanke,tsaki taja ta harhada kan kayan ta mayar dasu cikin leda tana kokarin tashi tajiyo karar shigowar text massage, Kamar bazata duba ba sai kuma ta dauka tana dubawa, _Am Little busy now,text me please._ Shine abinda taga anturo da wata special number mai dauke da 33333, tunani tafara yi to waye kuma wannan? Zuwa can tagane minister ne,kai duk yanda akayi shine tunda ita dai yau bata kira kowa ba sai shi,kai shi dinne ma, Saida ta duba number tasake dubawa sannan ta mayar masa da reply, _Ya kamata dai idan angirma asan angirma,duk zawarawan duniyar nan da rikakkun yanmata ka rasa wacce zakace kana so sai ni,nidai ka cuceni kuma kasani kawai zanyi zaman biyayya ne bawai dan ina soba saboda ni inada wanda nake so,idan kuma dan kana da kudine to ni kudinka baya gaba na._ Shine abinda ta rubuta ta tura masa amma shiru babu amsa har tagaji ta daina ma tsammanin zai turo mata da reply, "kaji irin wulakancin nasu ai" tafada aranta kafin ta tashi taje tashiga wanka,har tagama komai nata ta shirya ta kwanta mutumin nan baibi ko ta kanta ba,har tagama yanke tsammanin zai kulata domin 11 tawuce. *** Lokacin da Hanan ta kirashi yana cikin meeting da yan uwansa ministoci,shi a ka'idar wayarshi idan ka kira asalin layinshi bazai shigaba sai dai idan text massage kayi masa to wannan zai shiga har yagani amma idan kira kayi to bazai shigaba amma dai zai ga kiran a dayan layinshi da akayi forwarding kiran zuwa can,to idan yasanka zai kiraka ta special line dinshi idan kuma bai sanka ba shikenan sai yakyale,itama Hanan dalilin da yasa ya san itace shine abbanta yatura masa number din tunda jimawa tun bayan lokacin da yabashi aurenta da yakirashi domin yimasa godiya yatura masa number dinta wai ko zai kirata shi kuma baice a'a ba amma aganinshi me zai kirata yace mata? Shi baida bukatar number dinta saboda baida case da ita, To yau yana tsaka da meeting yaga kiranta shine yayi mata text, lokacin da ta dawo masa da reply ma shi ko budawa baiyi ba saboda lokacin har yasake shiga wani meeting din da masu bada shawara ta musamman akan harkokin wasanni da matasa gashi yan jarida suna waje sunyi cincirindo suna son ganawa dashi dangane da wani rade radi dake ta faman kaiwa da kawowa acikin gari na cewa wai gwamnatin tarayya zata sauke wasu masu ruwa da tsaki a harkar gwamnati har su dari daya, Gaba daya bai samu kansa ba sai wurin misalin karfe 11 sai a lokacin yabar office bayan yagama ganawa da yan jarida yanufi gida, Agajiye yake mutuka sannan ga ciwon baya dake dan damunsa da kuma ciwon kirji shiyasa tun kafin yakarasa gida yasa nura yakira masa likitansa wato Dr Al'amin, Duk jikinsa jinsa yake babu karfi ga rashin cin abinci,yana komawa gida yayi wanka yasa jallabiya da gajeren wando aciki,a dan karamin falon shakatawarshi ya zauna ya hada coffee mai zafi yasha yana gama sha yaji amai na kokarin fito masa, bathroom din dake cikin falon yashiga yayi aman sannan yadawo falon ya zauna daidai lokacin da PA yashigo yana sanar dashi zuwan Dr cemasa yayi yashigo sannan ya dan kishingida jikin kujerar da yake kai, Sai da Dr yagama dubashi sannan ya daure masa hannunshi da wata yar roba yana duba jijiya saboda anan ne zai dan yimasa allura sannan zai kara masa wani dan karamin ruwa leda daya, Sai lokacin ya dauki wayarshi yasoma duba sakon da aka tutturo masa nafi yawa friends ne da masu neman taimako ahaka har yazo kan na Hanan,ganin abinda tace abin yaso ya bata masa rai,wai yara kanana sai su zagi mutum dan kawai maganar aure ta hadasu, yanzu ita wannan yarinyar ko ahanya ta ganshi ta isa ta fada masa wannan maganar ba dan maganar aure ta shiga tsakani ba? _Ok_ shine abinda yatura mata kawai,yaci gaba da karbar ruwan dake shiga jikinsa wanda Dr ke kara masa,ajiye wayar yayi agefe ransa adan bace, "Ranka yadade wallahi stress ne kawai ba wani abuba, sannan kuma yallabai maganar nan tawa dai kamar koda yaushe,dole fa sai ansamu abokiyar debe kewa..... Saboda agaskiya kana bukatar mace ko dan lafiyarka" Shiru Khalil yayi yana dan sake jingina sosai cikin kujera, so yake idan yagama da Dr yaje yaga Aryan saboda yau throughout bai ganshi ba,yadai ganshi da safe kafin yafita lokacin ko ma tashi daga bacci baiyi ba kasancewar yau asubanci yayi. Wurin karfe 12 saura sakon minister yashigo wayar Hanan dama har lokacin bata yi bacci ba,tana dubawa taga ok,ranta yayi mutukar baci,inbanda rashin mutunta dan adam Menene zai ce mata wani ok, Tsaki tayi tasake tura masa da wani text din, Bai kulata ba sai da Dr yatafi shima PA yatafi, bedroom din Aryan yaje ya dubashi sannan yakoma part dinshi yawuce bedroom ya kwanta domin Dr yace yadan samu bacci akalla na awanni shida. Massage din da yaji yashigo tun dazu ya duba, "Again?" Yafada ganin Hanan ce ta sake turo masa da reply, Budewa yayi ya tsurawa sakon nata ido cikin nutsuwa, " _Ni dai ancuceni anrabani da wanda nake so saboda kawai budurwar zuciya,angirma ma ba za a hakura ba,yadai dace idan angirma asan angirma._" Afili ya karanta sakon kamar yana karantawa wani,wai shine mai budurwar zuciya, murmushi yayi saboda shi abinma dariya yaso bashi,sai dai gaskiya turancinta ya burgeshi saboda duk sakonnin tana turosu ne da harshen turanci da alama dai ta kware a fannin, Bai cemata komai ba ya ajiye wayar tashi saman bedside drawer sannan yakashe bedside lamp din dake gefen gadonshi ya lumshe idanuwanshi saboda son bin umarnin Dr,yana son ya dan samu bacci kamar yadda Dr yace......✍️ _Ga mai bukatar siyan littafin mijin matacciya zai tura naira 200 ta account dina 3112877210 Aisha Ibrahim first bank sai atura shaidar biya ta 07044644433,ko kuma recharge card na MTN ta wannan number din 07044644433 sannan sai atura shaidar biya ta number da aka turawa._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO.....* *MIJIN MATACCIYA......*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *9* ***Baccin shi ya takarkare ya shaka kamar babu gobe sosai kwakwalwarshi da gangar jikinsa suka huta daidai yanda ake bukata shiyasa ras yatashi da asubah yayi salla sannan yasake dan komawa ya kwanta hankalinsa kwance wani lafiyayyen baccin yasake kwasheshi bashi yasamu farkawa ba sai misalin karfe 8 nasafe lokacin tuni andade da kai Aryan makaranta shi kansa yayi mamakin dalilin da yasa Aryan yau bai shigo dakinsa ba to kodai yazo yana bacci kuma bai samu nasarar tashinsa ba? Wanka yayi yashirya cikin dark blue din shadda sabuwa fil sannan yafita,kamar koda yaushe table ashirye yake tsaf da kayan karyawa kala kala, Shi arayuwarsa yana mutukar kaunar Irish amma yanayi yasa baya zama yaci yau dai ya zauna akan table domin karyawa saboda jiya Dr Al'amin yayi masa maganar rashin cin abinci kuma hakan na iya haifar masa da wata matsalar duk da dama matsala kam sai dai ayi fatan sauki amma yana tattare da ita, Soyayyen dankali da kwai ya dan zuba sannan yahada coffee kamar yadda yasaba,dan ci yayi ba wani mai yawa ba sannan yasha coffee yana shirin tashi umma barira tashigo ganinshi saman table yasata dan murmusawa tana cewa, "Mu'azzam yau ansamu damar cin abinci?,ai gara ka rinka dan ci ko kayi kumari..." Murmushin shima yayi yasauka kasa ya gaidata sannan yamike yana fadin, "Wallahi kuwa umma, yau banga mutumin ba ko laifi nayi shiyasa ba ako lekani ba?" Dariya umma tayi taja kujera ta zauna, "Ai Aryan yau akwai abinda ya dauke masa hankali amma yashiga wajen naka bai dai tasheka bane...." "Nima nayi wannan tunanin nace duk yanda akayi yashiga bedroom din nawa tashina ne dai baiyi ba,umma ni bari inwuce wallahi mutane na can suna jirana a office tun 7" "To shikenan adawo lafiya, Allah ya tsare yabada sa'a, Allah yadawo dakai lafiya" "Amin umma nagode,sai nadawo" Juyawa yayi yabi ta kofar babban falo yafita,duk da bai son maganar Hanan tazama issue acikin al'amuransa dan baida lokacinta amma sai da ta zama,abun ya tsaye masa arai bai san dalili ba,wai shi ta kira da mai budurwar zuciya,kasa yakice maganar yayi acikin ransa haka ya wuni da ita. *** Amarya Hanan kuwa kowa yaganta yasan acikin bacin rai take domin fuskarta babu walwala sam, ga haushin rashin baccin da bata samu jiyaba saboda bakin cikin abinda minister yayi mata, dama su masu kudin nan wulakanci garesu basa ganin kowa da gashi sai junansu, Tana ta faman babbata fuska ta shirya ta tafi gidan anty salaha can ta iske mujahid yana jiranta cikin motarshi a kofar gidan. Bude side din mai zaman banza tayi tashiga ta zauna take tafara hawayen da tajima tana dakonsu acikin zuciyarta, Tagumi mujahid ya rafka yana kallonta shima nasa idanuwan jajur kamar ya hadiyi kunama,shi kansa badan dauriya da juriya irin na maza ba da tuni yajima da fashewa da kukan amma dai yadaure,sunfi mintuna goma zaune shiru babu wanda yayi ko tari acikinsu sai sautin kukanta da yake fita kadan kadan, "Hanan.... Ki daina kukan nan da kikeyi domin ahalin yanzu shi yafi komai tayar min da hankali... Kiyi shiru kinji,kiyi shiru kiji abinda zan fada miki" Ahankali take rage sautin kukanta har tasamu nasarar tsayar dashi gaba daya sai ajiyar zuciya da takeyi kadan kadan, "Kiyi shiru kinji...., Kin dai san ina sonki kuma najima ina son mallakarki a matsayin matata amma yau gashi k'addara na neman rabamu..... Kiyi shiru kar ki sake yimin asarar hawayenki" Ajiyar zuciya ta ja mai karfi sannan ta kalleshi da idanuwanta wadanda suka yi ja, "Mujahid ni wallahi idan bada kai ba bazan iya rayuwa ba, wallahi kai nake so...." "Hanan nima ke nake so amma babu yanda zamuyi,kiyi hakuri ki yiwa iyayenki biyayya idan har na zugaki ko na goya miki baya kan ki bujirewa umarnin iyayenki to ban yimiki adalci ba sannan son da nake yimiki na karya ne,wallahi dagaske nake sonki kuma tsakani da Allah,tunda har k'addara ta raba to ni ina ganin kawai muyi hakuri kuma muyi wa juna addu'a da fatan alkhairi....." Wani kallo tayi masa mai cike da ma'anoni daban daban kafin daga bisani ta daure fuska cikin fushi da bacin rai tasoma magana, "Dama ashe son da kake ikirarin kana yimin duk na karya ne kuma na yaudara,idan dagaske kana sona meye naka na fadin haka? Maimakon ka nemo mana mafita shine zaka ce wai inyi hakuri indauki k'addara, mujahid ni zaka yaudara? Ni zaka rainawa hankali? Wannan shine irin soyayyar da kake ikirarin kana yimin? Yayi kyau kuma nagode" Bata saurari bayaninsa ba ta balle murfin motar tafita ta nufi cikin gidan anty salaha tana sake rushewa da wani sabon kukan mai cin rai. Ganin shigowar ta tana kuka yasa anty salaha dake wanke wurin da tagama wanke wanke dakatawa da abinda takeyi ta nufi wurinta hankalinta atashe saboda duk zatonta ba kalau ba, "Hanan.....meya faru kuma? Wanine ya mutu ko hatsari akayi? Ki fada ni abinda yafaru kin barni atsaye cikin zulumi..." "Anty wai dama haka k'addara take? Idan ta afko maka kowa sai yajuya maka baya? Gaba daya sai ka kasa gane kan kowa? Wai haka k'addara take?" Ajiyar zuciya anty salaha ta sauke sannan ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tana kallon Hanan wacce har lokacin bata bar kuka ba, "Hanan dan Allah ki dauki wannan auren amatsayin hanyar samun aljannar ki,ki dauka cewa wani nauyine iyayenki suka dora miki suke son ki sauke shi,kiyi hakuri dama shi aure mukaddari ne daga Allah,aduk inda mijinka yake sai yazo ya sameka anyi,kuma ke ki godewa Allah ma domin yayi miki gatan da ba kowa yayiwa ba,duk cikin danginmu da kawayenki babu wacce ta taba aurar babban mutum sai ke, minister fa Hanan,kin kuwa san suwa ake kira da minister? Wallahi ba kananan mutane bane....." "Anty ni babu ruwana da wani arzikinsa ni wallahi mujahid nake so,mujahid shine sa'an aurena shine yaro shine muka jima tare mun san halin juna mun san sirrin juna babu abinda bamu saniba na junanmu....." Sakar baki anty salaha tayi tana kallonta sannan cikin faduwar gaba tace, "Hanan kar dai ko wani abu ya taba shiga tsakaninku da yaron nan..?" Cigaba tayi da kukanta tana jin wayarta ana kiranta taki dagawa tasan bazai wuce mujahid ba, "Tambayarki nakeyi,wani abu ya taba shiga tsakaninku?" Girgiza kai tayi alamar a'a sannan taci gaba da kukanta,anty salaha zama tayi taci gaba yimata nasiha tana kwantar mata da hankali. Dakyar ta daina wannan kukan ta share hawayen ta,wuni guda tayi agidan anty salaha har lokacin mujahid bai bar kiranta ba amma taki dauka yakirata yafi sau 20,sai magriba takoma gida, Tunda ta koma kuma taci gaba da kuncinta har lokacin bacci yayi nan ta shirya ta kwanta bakin ciki kuma yace muje zuwa,saida taci kukanta ta share sannan ta dauki wayarta, _Akwai Allah._ shine kadai abinda ta turawa Khalil ta ajiye wayar. *** Yana kwance saman Rug da laptop agabanshi Aryan na gefenshi yana bacci yaji shigowar text,bai duba ba har saida yagama abinda yake yi sannan yadauki wayar yaduba ganin abinda tace yasashi girgiza kai sannan yasoma tura mata da reply, _Nifa bawai yimin kikayi ba, kawai zan aureki ne saboda ki rike min yarona amma ni bakida wani abu da zai burgeni ko yaja hankali na atare dake infact ma ni banko san kamanninki ba bare insan ya kike,soo kisan inda yake yimiki ciwo._ Tunda Hanan taga wannan sakon nasa bacin ranta yasake nunkuwa zuciyarta har tafarfasa take yi dan bacin rai,wai ita zai cewa saboda ta rike masa yaro zai aureta,mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki nan tasoma kokarin mayar masa da reply dama haushinsa takeji saboda girman kansa da wulakancinsa dan ko sako ne sakonshi baya wuce layi biyu, _Nima ai ba sonka nakeba kuma da kake maganar zaka aureni saboda in rike maka yaro to ni ba yar aiki bace kuma ba baiwa bace tun wuri ka nemi mai rike maka yaronka._ Wannan karon sakon nata ya bata masa rai fiye da wancan,wai wannan yarinyar dame take tak'ama da har take fada masa maganganu kanta tsaye ko tsoro bata ji kamar wata sa'arshi,dan kawai yace zai aureta sai aka fada mata sonta yake? Shi yanzu aduniya ai babu yarinyar da zata ja hankalinsa har ya sota,tsaki yayi ya ajiye wayar agefe yatashi ya shiga bathroom.................? *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO....* *MIJIN MATACCIYA.....*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *Wattpad-ummishatu* *10* ***Kamar ya rabu da ita dan har ya shimfida Rug din salla yaji bazai iya kyaleta ba duk da yasan ko tantama baya yi a haihuwar kaji ya haifeta amma gara dai ya nuna mata ita ba kowan kowa bace agareshi. Sai bayan da yagama da ita sannan yaje ya tada kabbarar sallar da yayi haramar yi, Har lokacin ita kam bata jin ta huce wani irin zafinsa take ji kamar taje har inda yake ta shakeshi saboda yashiga hakkinta da yawa,tana tsaka da sharar hawaye taji shigowar wani sakon wanda ko tantama batayi daga gareshi ne,yanzu kuma Allah ne kadai yasan irin bakar maganar da yaturo mata tunda ta lura shima dan zafin kaine bai da hakuri kamar ba babban mutum ba, K'wafa tayi sannan cikin bacin rai tace "Ai wallahi idan tsoho baiji kunyar hawa jakiba to kuwa jaki bazai ji kunyar yin totso dashi har ya damfara shi da kasa ba,duk abinda zaka fada am too much ready in baka amsa daidai da maganar ka..." Text massage din nashi ta bude nan ta soma karantawa afili, _Ki dauki kanki bakida maraba da mai rainon yarona, sannan ina son infada miki akwai dokoki da sharruda masu yawa wadanda zan kafa miki akan yarona mutukar kika bisu zamu zauna lafiya amma karya doka daya daidai take da rugujewar dukkan dokokin da kika bi,idan har kina son aji kanmu dake to ki gwada saka kafa ki shure daya daga cikin dokokin._ Ranta idan yayi dubu to ya baci saboda wannan sakon da yaturo mata,ai kuwa wallahi sai dai ayi wacce za ayi amma ita ba yar raino bace, Kiris dama take jira shiyasa ganin wannan sakon nasa yabata damar amayar da abinda ke nukurkusar zuciyarta, Ko bayan da ta tura masa sakon ji take bata huce ba daga cin mutuncin da yayi mata gashi yana yin komai nasa isa isa iko iko,tasan dan girma kam ya girme mata nesa ba kusa ba to amma Menene zai rinka nuna mata gadara harda wani cewa a yar aiki ya dauketa kamar wata baiwar da yasaka kudi yasiyo a kasuwa zai tsaya yana fadin wai zai kafa mata dokoki da sharruda, Sakon mujahid ne yashigo mata cikin wayarta adaidai wannan lokaci,ji tayi tausayinsu shida ita duk ya mamaye ilahirin zuciyarta baki daya saboda tasan yanda batayi bacci ba shi dinma gashi can kwance bai samu baccin ba duk kawai dan mutum daya,gaskiya saima Allah ya saka musu ita da mujahid,duk tsawon shekarun da suka dauka suna shirya yanda rayuwarsu zata kasance idan sunyi aure yau kwatsam rana daya wani tsohon banza can mai budurwar zuciya yazo ya rusa musu mafarkin su da suka dade suna yi, Bude sakon tayi tana kuka kamar wata mai arahar hawaye, _Dan Allah wify karki cigaba da wannan fushin dani,ki tsaya ki saurare ni,sanin kankine ina mutukar sonki kuma wallahi har na mutu da sonki dankare cikin zuciya ta zan koma ga mahaliccina,dan Allah ki daina fushi dani kijira kiga irin matakin da zan dauka._ Sai lokacin taji ta dan samu nutsuwa jin mujahid yace akwai abinda yake shiryawa, sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske tayi sannan tasoma kiran wayar mujahid din,ada kam ji take bata wani damu dashi ba amma ahalin yanzu tana jin soyayyar sa kamar idan babushi aduniya bazata iya rayuwa ba,ita kanta bata san yaushe wannan soyayyar ta shigeta ba sai yanzu, bata san yaushe tafara son mujahid har haka ba a iya saninta dai sai da aka fara turka turkar auren nan sannan wannan matsananciyar soyayyar tasoma tasiri agareta. Bugu uku taji ya katse kiran sannan ya kirata,dauka tayi tai kasa da dasasshiyar muryarta wacce ke fita dakyar kamar wacce mura taci karfinta, "Wify meyasa baki tsaya kinji uzuri na ba,meyasa kika dauki fushi dani har haka? Kema kin san ai ina sonki,u know how much you mean to me and i soo much loves you...." "To ai dafarko dinne sai naga kamar baka damu da rabamun da za ayi ba shiyasa,naga kamar ni daya keta haukana you didn't make any effort..." "No wify,ba haka bane,gashi kina gani nakasa bacci...,akwai abinda nake shiryawa, kawai all what i want from you is ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa kima daina nuna kwata kwata cewa kina cikin damuwa,nikuma ina can bayan fage ina shirya abinda nake shiryawa..." Dan murmushi tayi mai dauke da jin dadi sannan cikin sanyin murya tace, "Ok har naji relief wallahi,gobe insha Allah zan koma Abuja saboda ban dauki excuse ba nataho dama kawai nataho weekend ne fa" "Babu matsala zamu hadu before kitafi,yanzu ki kwanta kiyi bacci kinga 2 ta kusa" Sallama sukayi ta katse wayar tana jin farin ciki yana ziyartar birnin zuciyarta,haba har taji sanyi aranta. *** Kamar kada ya bude sakon nata amma sai ya dake yabude aransa yana fadin "wannan yarinyar bata da kunya sam" Yana budewa yaga tace, _Girma dai ya fadi kasa wanwas masu budurwar zuciya._ Tsaki kawai yaja ya kashe wayarsa yayi kwanciyar sa bisa luntsumemen gadonshi mai azabar laushi,shi idan ta barshi da abinda ya dameshi ma ya isheshi bawai sai ta kara masa da tata matsalar ba domin shekara da shekaru acikin matsala da damuwa yake kawai yana daurewa ne amma acan kasan ransa babu kwanciyar hankali ko jin dadi atare dashi, Bai kara bi ta kanta ba domin aganinsa ai ita ba sa'ar kace nace dinsa bace,nawa take da har zai zauna yana haka da ita? Ai ubanta shi shine abokin yinsa bawai itaba kuma duk ranar da ta kara yunkurin yimasa rashin kunya zai fada mata ubanta shine daidai shi bawai ita ba. Washe gari kamar yadda yasaba 9 yabar gida ya nufi kaduna saboda yana da wani muhimmin taro da zai halarta sannan kuma aranar yana son zuwa gombe zaije ya duba jikin hajiya haka kuma zai ga kayan aurenshi da aka gama hadawa cikin kwanaki kadan, Wurin lokacin sallar la'asar yabar kaduna suka tasamma gombe wanda basu suka isa garin ba sai bayan magriba, Saida suka fara yin salla a masallaci sannan yashiga cikin gidan,akwatuna ne gasu nan set biyu a falon hajiya Zaitun hadaddu dasu masu tsada kowanne damfare da kaya dan ko rufuwa ma basayi saboda tsabar cika, Wuri yasamu ya zauna kansa babu hula suna gaisawa da hajiya wacce ke kishingide saman kujera. "Mu'azzam dama kayanne nake son kazo ka gani kafin aje akai musu kasan abubuwan nakune duk cikin gaggawa kuka yisu kun debi lokacin auren kadan amma hakanma yayi daidai gara ayi ayi kawai..." "Hajiya ai Abba ne ya bukaci hakan amma nidai bani nace asa rana kadan hakaba" "To ai babu aibu hakanma,ni dama kullum fatana inga kayi auren nan zaman ka kai daya babu aure baya min dadi yana damuna wallahi.....ga kayan nan bari yaran nan suzo su bude maka kagani" "Toh hajiya..." Tashi tayi tafita zuwa kitchen da kanta ta harhado masa abinci ta kawo masa,tuwon accha miyar busasshiyar kubewa sai dafaffen zogale wanda aka kwadantashi da kuli kuli,dafaffen kwai,tumatur, cucumber da sauran kayan lambu,sai bottle water da kunun aya da zobo, "Hajiya duk wannan abincin ni daya.." "Ehh ai gara kaci dan yanzu Allah kadai yasan rabonka da abinci Khalil,shiyasa nake murna da zakayi auren nan domin nasan idan kasamu mai nutsuwa zata kula da abincin ka" Filet din zogalen da ta kwadanta masa yaja gabansa yafara ci,mazauna gidan sai shigowa akeyi ana gaisheshi kamar yadda aka saba duk ranar da yazo, Sosai yaci zogalen da yawa ya sha zobo kadan domin shi yana son irin wadannan kayan marmarin kamar kwadon yakuwa,kwadon rama, kwadon zogale da sauransu, Su mufida ne suka zo suka bubbude masa kayan wanda shi bama wani gani yayi sosai ba kawai dai dan kar hajiya tace bai gani bane,yana jin ankira salla yatashi yafita masallaci dama neman hanyar tashi yake domin yagaji da kallon kayan gashi sunki karewa, Yana fitowa suka hadu da Zaid wanda shima shigowar shi gidan kenan,musabaha sukayi Zaid ya gaisheshi sannan suka shiga masallaci tare, Lokacin da yakoma ciki bayan yafito daga salla sallama yayiwa hajiya akan zaije asibiti yaduba sirikin Abban London wanda ke can kwance a asibitin kudi baida lafiya kuma ta can zai wuce Abuja, kudi ya ajiye mata mai yawan gaske saboda hidindimun da ba arasa ba musamman ma yanzu da biki yake dososu. Jama'a cankam a kofar gida yagani lokacin da yafito dama duk ranar da yazo hakace take faruwa shiyasa saida yayi rabon kudi sannan yawuce suka nufi asibitin standard dake nan cikin garin gombe,acan dinma duk da asibitin kudine sai masu hali ke zuwa saida yabi yayi rabon kudi sannan yabar asibitin,shi haka rayuwarsa take Allah bani inbayar ne da yasamu zai rabar,matasa kuwa suna morewa duk ranar da suka samu ganinsa shiyasa a gombe da mai matasa ake kiransa. K'arfe 1 na dare yashiga gidansa acikin Abuja,gidan shiru kamar koda yaushe,ji yayi cikinsa yana yimasa wani irin ciwo amma haka ya lallaba yayi wanka yasanya farar jallabiya yafita zuwa dakin Aryan,yana kwance ga tulin tady nan akan gadon kamar hauka Kuma manya manya,kwashe tady din yayi ya matsar masa dashi gefe sannan yayi masa addu'a yafita, Acikin daren yakira Dr Al'amin saboda dagaske cikinsa ciwo yake yi bada wasa ba kuma yakasa gane musabbabin faruwar hakan..........✍️ _Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO.....* *MIJIN MATACCIYA.....*💞💞 *_NA_* _*UMMI A'ISHA*_ *Wattpad-ummishatu* *11* ***Zuwan Dr Al'amin yasashi fitowa daga cikin bedroom dinshi zuwa falo inda yake zaune yana jiransa, Fitowarsa ta sa Dr Al'amin mikewa tsaye dan girmamawa,kan daya daga kujerun dake kawace afalon yasamu guda daya ya zauna, "Dr ciwon ciki ke damuna tun bayan dawowata gida..." "Ayya Allah yabada lafiya yallabai amma yau me da me kaci?" "Da safe tea kadai nasha sai dazu da naje gombe shine naci zogale da tuwo dan kadan...." "To ai ranka yadade ga inda matsalar take nan,dan abubuwan da kaci dinne suka dan ruda maka cikin naka gashi dama bai saba ba" "Wallahi duk ya takura min gashi bacci nake son inyi" "Babu damuwa Allah yakara lafiya bari yanzu inbaka magungunan da zaka sha insha Allah zaka samu bacci..." Lumshe idanuwanshi yayi ya dan kishingida jikin kujerar yana sauraren Dr Al'amin, sai da yagama hada mishi magungunan sannan yatafi, Cikin bedroom yakoma bayan tafiyar Dr yayi shirin bacci ta hanyar saka gajeren wando na bacci sannan ya dauko robar ruwa guda daya daga cikin bedside fridge dinshi,zama yayi yasha maganin da Dr yabashisannan ya kwanta yana lumshe idanuwanshi cike da bege da kuma tunanin Ramlat, Allah sarki Ramlat Allah dai yasa tana gidan aljannah,shi kam yasan shima har yakoma ga mahaliccinsa bazai iya mantawa da Ramlat ba kullum da tunanin ta yake kwana yake tashi. *** Duk da tana cikin damuwa sai dai yau bacin ranta ya ragu da damuwar ta amma fa duk da haka dai sai ahankali yanayin nata, Karfe 8 nasafe ta kammala shirinta tsaf na komawa Abuja sai kuma satin biki sannan zata dawo, Dakin Abba taje tayi masa sallama nan yasake dan yimata nasiha sannan yasaka mata albarka ta taso tafito, sallama tayi dasu mamaye yaya shamsu ya rakata tashiga napep zuwa tasha inda zata shiga mota, Tun tana cikin napep din sukayi waya da mujahid kan cewa zasu hadu a tasha inda zata shiga mota,tana zuwa shima babu jimawa sai gashi ya karaso cikin motarshi, Karasawa tayi wurinshi ta bude gaban motar ta shiga tana dan harararshi,take away din dake ajiye seat din baya ya dauko ya mika mata saboda dama yasan bata ci abinci ba, "Good morning my love,gashi kici...." Dan makale kafada tayi sannan ta kawar da kanta saida ya dan yimata magiya sannan ta yarda ta karba koda ta buda dankali da kwai tagani nan tafara ci mujahid na sake kwantar mata da hankali yana cemata insha Allah akwai matakin da zai dauka yana nan yana shirinsa a boye ita kanta zata sha mamaki, wadannan kalaman nasa ne suka sake sakawa zuciyarta nutsuwa har taci abincin da yakawo mata da yawa dan kadan ta rage yabata ruwa tasha,5k yabata wai tayi kudin mota amma dakyar ta karba daga nan ya rakata mota sukayi sallama dan tuni motarsu ta cika. Agajiye lis ta isa dan karamin d'akinta dake quarters din malamai,salla kawai tayi ta dafa noodles ta kwanta domin ta huta wanda ba ita ta tashi ba sai la'asar lis wannan dinma wayarsu hajara ce ta tada ita bayan ta dauka suke cemata wai zaman wuri dayane ya ishesu yau suna son su kawo mata ziyara, Tashi tayi tai wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga ta atamfa sannan ta dora musu abinci kafin su karaso, Tana shirin sauke sphagettee jalop din da ta dafa mai dauke da kifin gwangwani su hajara suka karaso,sunyi murnar ganin juna sosai saboda rabonsu da haduwa tun ranar clearance na wancan watan dan wannan watanma basu haduba saboda ba rana daya sukayi ba, Har magriba suna tare amma sam bata sanar dasu cewa za ayi mata aureba. Sha'anin gabanta kawai takeyi dan koda anty salaha ma ta kirata akan maganar gyaran da sauran abubuwan gyara da ake yiwa amarya cewa tayi bata so,anty salaha kuwa tace to ko bata so ita zata yimata inyaso ta zubar, "Ai kuwa wallahi zan zubar,inma anyi auren kenan" tafada cikin kunkuni,anty salaha na jinta amma dai bata yi magana ba kawai sai ta kashe wayarta, Agefe guda kuma mujahid naci gaba da bata tabbaccin sai maganar aurenta da minister ta rushe,sai yahana wannan auren indai yana raye to baza ayishi ba sai dai afasa da minister shi ayi dashi wadannan kalaman nasa ne ke sakawa zuciyarta cikakkiyar nutsuwa da farin ciki shiyasa take abinta gaba gadi,kallon kowa take yanda gida suka dauki abin da muhimmanci gashi komai akayi sai yaya shamsu ko anty sun kira sun fada mata dan ko dazu saida anty ta kirata wai za akawo lefenta gobe gasu agida sai aikin nama suke yi amma snacks sun bada kwangila sun biya ayi musu, Baki ta tabe aranta tace sayi sa gama aure dai ba yinsa za ayiba kamar yadda mujahid ya saba sanar da ita kuma wani sharri na Shaidan ayanzu kusan kullum sai sunyi waya da mujahid fiye da sau biyar sabanin da wanda ada idan ya kirata ma ganin nacinsa take yi amma yanzu ko bai kirata ba ita tana kiransa saboda wani sonshi ne kullum ke kara shigarta. Kamar yadda anty salaha ke sanar da ita ankawo kaya kuma anyi bajinta anyi rawar gani kowa yaga wannan kayan yasan babu karya ankashe masu gidan rana dan har da kudin dinki dubu dari, kuma gashi biki ya matso dan haka yakamata ta dawo gida tazo ayi abinda yadace, Kuka ta fara yi ta kira mujahid tana fada masa abinda ke faruwa nan yace mata babu komai tayi yanda suka ce din hakan bazai basu matsala ba, hutu taje ta rubuta har na tsawon sati uku domin bikin saura sati daya da kwanaki biyu, Kamar wacce idan ta tafi ta tafi kenan haka ta harhada kan kayanta tsaf washe gari ta nufi kano. Bayan ta koma gida aboye suke haduwa da mujahid suna yin hira yana sake kwantar mata da hankali,tun ranar da ta koma kuma anty salaha tafara kawo mata kayan gyara irin na amare amma bata sha sai dai ta faki ido ta zubar,gaba daya gidan shirin biki akeyi ganga ganga bugu da kari ansake gyare gidansu tsaf yasha fenti yasha gyara na musamman. *** Duk shirye shiryen da can gida gombe ke faman yi shi kuwa mai gayya mai aiki wato ango yana nan Abuja yana harkokinsa domin ayyuka sun sakoshi gaba bashi can bashi nan kullum cikin yawon ayyuka yake bashi da kwakkwaran lokacin kansa kullum da garin da zaije banda yawon taruka da bude ayyuka da yake halarta, A gaggauce yake fitowa daga tamfatsetsen dakinshi hannunshi rike da agogon azurfa na Rolex yasha skye blue din shadda mai tsada da kyau, Yana tafe yana kokarin daura agogon sukayi kicibus da Aryan wanda ke sanye cikin kayan shan iska kasancewar weekend ne babu school, Rungumeshi ya ida yi sannan ya daga kai yana kallonshi, "Papa...... Zan bika wurin mommy" Murmushi yayi ya daga shi sama ya rikeshi yana kissing din face dinshi, "Good morning my lovely son...., Waye yace maka wurin mommy zanje? Zanje lokoja ne fa,ba gombe zanje ba" Makale kafada Aryan yayi ya sake rikeshi kamar zaiyi kuka, "Zan bika Daddy,ni ka kaini wurin mommy,hajiya tace ankusa kawota nan" Kan dining ya nufa dasu yana murmushi wallahi shi har mantawa yakeyi da wani batun auren nan saboda sam bashine agabansa ba shi sabgogin gabansa ma sun isheshi domin yawa garesu wanda idan har ba mai cikakkiyar lafiya kamarsa ba to mutum bazai iyaba shi dinma da yake da lafiyar ya aka kare stress da zama babu cin abinci kusan koda yaushe cikin kara masa drip ake shiyasa amafi yawan lokuta yafi danganta wannan mukamin nasa da wahala, Zama yayi saman kujera ya dora Aryan akan glass table din yana kallon shi, "Aryan kabari inje lokoja indawo zanzo indaukeka muje gombe din but yanzu ka zauna gida kaga anjima kadan lesson teacher dinka zaizo..." Bata fuska Aryan yayi yasoma murtsuka ido, Dakyar yasamu ya lallasheshi yakaishi wurin umma barira sannan yafita ta kofar baya. A lissafinsa ma shi baza ayi bikin nan yana k'asar ba domin zai tafi kasar Spain shida yan wasan kwallon kwando inda za aje akara wasan kuma yana son ya halarta domin yana da muhimmin abinda zai gabatar acan,sai dai yana shakkar sanar da hajiya duk da harka ce ta aiki watakila tayi fada tace dan me zai tafi bayan gashi bikinsa za ayi, addu'ar sa dai Allah yasa kar tayi fadan. Aranar saida yaje gombe kuma basu tafi da wuriba dan ko lokojan da yaje bai dawo ba sai karfe biyar na yamma,suna zuwa Abuja suka dauki Aryan suka wuce, Koda sukaje gombe tuni yaga shirye shirye sunyi nisa domin ita hajiya da gaske ta dauki lamarin bada wasa ba shiyasa yayi ta fargabar sanar da ita tafiyar da zaiyi daga karshe dai yaja bakinsa yayi shiru ya zabi yasanar da ita daga baya ta waya, Sai bayan karfe tara sannan suka baro gombe lokacin tuni Aryan yajima da yin bacci ajikinsa, PA dake gaban mota yayiwa magana, "Gobe in Allah yakaimu zan aikeka kano,hajiya tace aje akaiwa yarinyar nan kudin menene wai ita da friends dinta...." "To yallabai Allah yakaimu" Shiru yayi bai kara cewa komai ba sai tunani fal da yasoma zagaye ilahirin kwanyarsa. *** Amarya Hanan kam tana cike da damuwa duk da mujahid kullum na sake bata kwarin gwiwar cewa aurenta ba tabbatacce bane dan haka ta kwantar da hankalinta tajira taga abinda zai faru, Duk da idan taji yafadi haka takan ji ranta yayi sanyi amma hakan baya hanata shiga damuwa da jin faduwar gaba mai tsanani akoda yaushe, Yau tunda sassafe taji abba na barwa mamaye sallahun wai ta fada mata zatayi bako,ranta bakikkkirin ta wuni tana jiran taga wannan bakon da zaizo tunda tasan dai bai wuce tsohon banzan nan wato angon. Wurin misalin karfe 2 na rana nura PA yazo,ranta ahade kamar kullum taje bayan sun gaisa yazaro envelope yabata yana cewa, "Ranki yadade gashi inji yallabai saboda yan hidindimun da zakuyi keda kawayenki, sannan yace idan kuna bukatar wani abu sai ki sanar dashi" Karba tayi fuska ahade tace, "Bama bukatar komai kawai dai kafada masa inada bukatar yaje asibiti yayi gwajin cutar HIV,sai yabada result din akawo min...." Jin abinda tace yabawa nura PA mamaki amma baice komai ba kuma gaskiya bazai iya fadin wannan sakon nata ba dan yayi masa mutukar nauyi,tayaya zaije yafadawa uban gidansa haka? Dan russunawa yayi sannan yace, "Ai ina ganin ranki yadade gara dai kawai ki fada masa da kanki ko ta waya ne saboda ni din ba lallai nasamu ganinsa ba" "Ok to ni zan fada masa" Daga haka tajuya takoma cikin gida tana kunkuni,kudi ne cikin envelope din da yabata har kimanin dubu dari yan dubu dubu sabbi fil ita tama yi mamakin ta yadda akayi kudin yashiga cikin envelope din, Aranar anty salaha tasa aka fara yimata gyaran jiki wanda Hanan bawai ason ranta bane amma ko ba komai dai za agyara mata fatarta duk da auren bamai yuyuwa bane. Mujahid ke kaita gidan gyaran jikin sannan ya daukota yadawo da ita gida,tayi tayi dashi akan ya sanar da ita plan dinshi amma yaki kullum sai dai yace mata kawai ta zuba ido zata sha kallo, K'unshi da saloon ma da kin yi tayi sai da mujahid ya lallabata shine ma yakaita kuma yajira ta har ta gama sannan yadawo da ita gida lokacin bikin yarage saura kwana biyu. Kamar yadda nura PA yace mata ta fada da kanta da kan nata kuwa ta fada dan sako ta turawa gogan tana rubutawa tana tsaki aranta tana cewa, "Ance shekararsa wurin 9 babu mace wai tunda matarsa ta mutu,to waye yasan abinda yake aikatawa tunda da kudinsa gashi a Abuja yake zaune babu dangin iya bare na baba, watakila ma a hotel yake yin gaba daya weekend dinshi,kai may be ma bazai rasa karuwar da ya ajiye ba za ma ta iya yuyuwa baturiya ce" Ita kadai taketa wadannan maganganun har ta tura masa text din sannan ta ajiye wayar ta tashi tafita tsakar gida inda take jiyo hayaniyar su anty salaha wadanda keta aiki. *** Kamar yadda ya shirya sai ana igobe zai tafi k'asar Spain sannan ya sanarwa da hajiya ai kuwa tafara fada tana cewa to kuma auren nasa fa? Taya zasu yarda su bashi aure adaura babu ango? "Hajiya "yar abokina ce fa yarinyar,kuma wallahi wannan tafiyar dole sai dani za ayita shiyasa" Jin abinda yace yasa hajiya sakin ajiyar zuciya sannan cikin mamaki ta furta, "Yarku mu'azzam? 'yarku fa? To ai shikenan" "Yawwa hajjaju adai yimin addu'a da fatan alkhairin da aka saba" Addu'a tai tayi masa sannan sukayi sallama,katse wayar yayi yana murmushi acikin ransa kuma yana cewa, "Ga inda nasarata take, addu'ar hajiya itace take zame min jagora adukkan nasarorin da nake samu cikin rayuwata" Yana kokarin tashi daga office kuma sakon marar kunyar nan yashigo kamar yadda yake kiranta domin tuni ya rada mata wannan sunan acewarsa bata da kunya ko kadan,dubawa yayi aransa yana cewa yau kuma dame tazo? _Ina bukatar HIV test result dinka before adaura aure._ Tsaki yaja yamike daga kan kujerarshi yana danna kararrawar dake kan teburinshi alamar yana kiran masinjanshi sannan cikin sanyin murya yana fadin, "Wannan yarinyar baki da hankali,you are very stupid" Saida yabar office sannan yatura mata da reply _'Ok'_ shine kadai abinda yatura mata saboda baida lokacinta shi idanma bata saniba to da asuba zai bar k'asar baida lokacin zuwa yayi wani HIV test sai dai kar subashi auren, Toma wai yarinyar nan me take nufine da sai yayi HIV test? Ko suna tsammanin shi mazinaci ne? Mtswwww tsaki yaja daga nan bai kara bi ta kanta ba har yabar kasar. Ayau itace ranar da za adaura auren Ibrahim Sulaiman Ibrahim da Sa'adatu mustapha mai jama'a daurin auren da yatara manya manyan yan siyasa da masu rikeda manya manyan mukamai na k'asar Nigeria, Amarya acike take famm sakamakon wayar mujahid da taketa kira bata samuba duk da kusan kwana sukayi suna waya daren jiya tana ta bashi labarin wulakancin da minister yayi mata wai tace yayi HIV test yaki yayi yace mata kawai ok,ita wallahi bata sonshi ita mujahid take so kuma kowa haushinta yakeji ana cewa ga arziki Allah yakawo mata har gida amma ta runtse ido,arziki na binta tana gudu. K'arfe 11 na rana ake son adaura auren da tuni ma andaura ana jiran waliyyin ango yakaraso ne wato Alhaji Idris kanwa tsohon gwamnan jihar gombe,dama Abban London tuni yajima da karasowa shida tawagarsa, Zuwan waliyyin ango yayi daidai da isowar mujahid wanda yacaba ado tamkar shine angon tare da zugar abokansa dake take masa baya..........✍️ _Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *MIJIN MATACCIYA.....*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *WATTPAD-UMMISHATU* _Alhamdulillah wannan shine karshen Dandanon da zan baku (free pages) duk mai bukatar karanta cigaban labarin sai yaturo da 200 ta account din 3112877210 Aisha Ibrahim first bank,sai atura shaidar biya ta wannan number 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta wannan number din,dan neman karin bayani sai a tuntubi marubuciyar kai tsaye ta wannan number din 07044644433._ *13* ***Kwana tayi tana kuka sam bacci baiga idonta ba, abubuwa biyu ke sakata kuka abinda mujahid yayi mata da kuma abinda minister yafada mata dagaske dai raino zataje tayi masa na yaro,kaico,kaiconta inama iyayenta sun san manufar wannan auren nata,inama sun san abinda ke lullube da wallahi tasan ko za ayi kuli kulin kubra dasu bazasu yarda ayi wannan aurenba amma da yake wasu mutanen Allah yahore musu baiwar iya tsara mugunta da cuta shine aka rufi kura da fatar akuya aka yiwa iyayenta ungulu da kan zabo su sunata murna yarsu ta auri babban mutum basu san nan kuwa a matsayin yar raino ta fito ba,ai kuwa minister zaisha mamaki domin zata saka kafafunta duka biyu tayi kolin kolin fatali da wadannan sharrud'an nasa inyaso idan yaji haushi ya korata gida. Da bacin rai da bakin ciki ta wayi gari wanda ko diss bata samu bacci ba,wanka tayi bayan tayi salla wanda su anty salaha ne suka tilastata bayan sun shigo cikin dakin,humrah masu sanyin kamshi da jan hankali suka shasshafa mata sannan tasaka kaya wadanda suma suka sha turare na daukar hankali, Doguwar riga zuwa gwiwa tasaka da zaninta duka na atamfa orange and blue colour bayan sun gama shiryata tasaka su sarka da dan kunne akayi knocking a kofa aka shigo yanmata ne guda uku wato mufida da Sarah da Zarah kowaccensu dauke da madaidaitan warmers masu kyau iri daya,kasa kasa take kallon yanmatan wadanda daga gani kasan jin dadi da hutu sun jima da samun muhallin zama a jukkunansu, Kayan breakfast ne suka kawo musu sannan suka gaggaishesu sai kallonta suke suna dan magana kasa kasa shiyasa taji duk sun isheta domin ta tsani kallo,kamar sun san abinda ke cikin ranta suka tashi suka fita. Abincin karyawa ne na gani a na fada domin farfesun koda ne da soyayyar agada sai wainar kwai fal sannan ga wainar shinkafa itama da zuma ga kuma kayan tea da ruwan zafi agefe abinci dai kaca kaca gashi nan sai wanda ka zaba ita kam ruwan tea din kadai ta iya sha sai da anty salaha suka bude mata wuta sannan tasamu ta danci farfesun kuma suka tilasta mata saida tasha romon tass,sake gyara mata jikinta sukayi suka nada mata lafaya suka fita zuwa dakin hajiya Zaitun, Ita ma taci ado Sosai cikin wani leshi, kama Hanan tayi ta rungume tana dan shafa bayanta ahankali take yimata magana, "Barka da zuwa cikinmu Sa'adatu,lale marhabun dake,kinyi dace da miji mai biyayya ga iyayensa bawai dan nina haifeshi ba a'a sai dan kawai halinsa ne,ko kai ka haifi mutum halinsa shi zaka fada,ki zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya duk abinda yayi miki wanda ba daidai ba ki sanar dani,tsawon shekaru kusan bakwai kenan rabonshi da mace tunda matarsa ta mutu wurin haihuwar yaronsa shikenan bai kara aure ba nayi nayi amma baiyi ba sai yanzu bagatatan yazo min da maganar ki kuma gashi da yake Allah ya kulla anyi, Allah yayi miki albarka, Allah yayi miki albarka....." Wadannan sune kalaman mahaifiyar sa wanda harda kwalla take yi lokacin da take fada mata domin duk da fuskarta arufe take amma tana fuskantar komai kuma tana jin lokacin da matar Yakumbo ke cewa, "Haba hajiya kema kukan zakiyi Khalil din da ba shine auta ba......." Sun dan jima awurin hajiya sannan akace sufita domin tafiya Abuja,kamar jiya yauma zaid ke jan motar da take ciki tun daga garin gombe har Abuja wanda tafiyar awanni kadance ta kaisu,tana jin anyi parking gabanta ya tsinke ya fadi, Da addu'a abakinta ta taka tashiga da k'afar dama wadda iyaye keta nanata mata wadanda ke tare da ita, Masha Allah, Masha Allah,shine abinda kunnuwanta keta jiye mata lokacin da suka shiga gidan gashi babu laifi tafiya taki karewa abisa dukkan alamu gidan da zurfi dan harda su hawa bene taji anyi daga bisani aka danyi yar tafiya taji anbude wani daki sun shiga wanda sanyi da kamshi ya cikashi kai gaba daya cikin gidanma sanyi da kamshi ne acikinsa dan tunda suka shigo taji yana shigarta,abakin wani luntsumemen gado taji an zaunar da ita kan wata hadaddiyar katifa mai sifrin tamkar kahau irin gadon nan na da irin na karfen nan wanda zakaji yana tsalle dakai, Har lokacin bata bude fuskarta ba tana jin lokacin da su anty badi'a suka shigo anty badi'a tazo kusa da ita ta zauna cikin rada take cemata, "Wallahi yarinya kin more da gida, aljannar duniya,kinga gidanki kuwa Hanan? Wallahi girman wajen nan ya isa mata hudu su zauna basu takura ba, Allah yasa rabonki ne yasa gidan zamanki ne har abada, Allah yasa mutuwa ce kadai zata raba..... Ai tun dazu muna kasa muna ta santin wannan aljannar duniyar, Masha Allah wallahi gidanki ko a London iyakaci kenan sannan gaki ga Villa...." Ai Hanan ji tayi kamar ta dora hannu aka saboda takaicin wadannan addu'o'in na anty badi'a danme zata rinka yimata addu'ar kare rayuwarta a wannan gidan da yafi kurkuku tsanani agareta babu kunya bare tsoron Allah aranta ta rinka cewa, "Ba amin ba" Tana tukunkune atakure har saida dakin yarage daga ita sai su anty salaha sannan ta bude fuskarta,tamkar amafarki tajita lokacin da tayi ido hudu da dakin da ake kira da mallakinta bata san lokacin da ta furta, "Masha Allah" Ba kadan ba taga dakin yayi bala'in haduwa gashi tangamemen gaske duk kayan ciki dark purple ne masu dan sirki sirkin haske ko ina sai sheki yake magana ta gaskiya bata taba cin karo da furnitures makamantan wadannan ba wurin kyau da haduwa, sunkuyar da kanta tayi saboda bata son su gane dakin take kallo tabari har sai sun tafi sai ta bude idonta ta kashe kwarkwatar idonta dakyau gida kamar akasar turai?. Saida suka ci abinci sukayi sallar azahar sannan yan kawo amarya aka fara haramar tafiya nanfa Hanan tace bata san zance ba domin zama tayi ta rinka rusar kuka ahaka suka tafi suka barta, kwanciya tayi saman gadonta tana cigaba da kukanta cike da kunar rai har tayi tagaji tunda babu mai rarrashinta dan abisa dukkan alamu ma ita kadai ce agidan sai ko ma'aikata domin bata ji motsin ko kare ba duk da cewa ma gidan yana da girma da fadi ko da ace akwai wani ciki ba lallai kasani ba indai bawai yashigo side din da kake bane,ita kam ko tantama batayi tasan ita kadaice cikin wannan katon gidan domin dazu lokacin da suna kan hanya tana ji zaid yana waya da wani wanda bata san ko wanene ba yana cewa wai su umma barira da Aryan na tsohon gida ita amarya yanzu sabon gida za akaita amma suma su umma barira din nanda anjima ko gobe za akawo su sabon gida basu karasa parking din kayan su bane. Saida tayi kukanta ta gaji dan kanta sannan ta tashi da niyyar yin alwala domin la'asar ta kusa zaman dirshan tayi tana bin d'akinta da kallo wanda ya amsa sunan aljannar duniya, mai karatu Hanan bata san ta inda yadace tafara kwatanta muku haduwar da d'akin baccinta yayi ba domin komai yajine ba karya komai yadace da muhallin da aka ajiyeshi tun daga kan labulayenta gadonta wardrobe dinta,da komai dake cikin dakin sannan daga can dan gaba kadan da gadonta wasu hadaddun kujeru ne guda uku suma dark purple an dan yi circle dasu an ajiye glass table a center sai wurin yabada ma'ana tamkar dai aturai sannan ga wurin sallarta nan an tanada ga katuwar tv ta bango da dan karamin fridge kawai dai komai yaji ne fa,sauka tayi ahankali da niyyar zuwa toilet nan ta tsaya yin wani kallon domin shi kansa bathroom din nata da glasses aka zagaye shi marassa duhu sai dai ba lallai ne ka iya hango mutum ba idan yana ciki amma ta yuyu zaka iya ganoshi tsaff,kamar mai shirin daukar kwai haka takama kofar bathroom din ta tura ahankali tashiga,bandaki kamar wani filin shakatawa? Ta fadi hakan aranta domin shima an kawatashi an shiryashi sannan anzuba daula acikinsa kamar ba wurin wanka da fitsari ba,irin haduwar da bathroom dinnan yayi fadarshi bata bakine yahadu fiye da duk yanda zaka kissimashi cikin ranka,ita dai gidansu ba hamshakan masu kudi bane shiyasa sai da tabi komai asannu gudun kada tayi barna domin wasu abubuwan ma yaune tafara ganinsu haka dai ta lallaba tayi alwalar tafito tazo ta bude wardrobe ta ciro hijabi daga cikin jakunkunanta wanda su anty salaha suka saka mata cikin wardrobe dinta dazu. Rasa wacce irin addu'ar da zatayi tayi saboda ita dai bata son zaman gidan nan ko kadan bare tayi addu'ar Allah ya tabbatar da ita agidan,daga karshe dai sai kawai ta roki Allah da ya zaba mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta, Saman gado taje ta hau ta kwanta domin bata san abinda zatayi ba ayanzu juyi kawai tashiga yi tana ta tunanin rayuwa wai yau itace acikin wannan gidan wanda ko acikin mafarkin ta bata taba mafarko gida makamancinsa ba a tarihin rayuwarta,duk da gidan ya cancanci akirashi da aljannar duniya ita kam bata yiwa kanta fatan tabbata acikinsa, nasihar Abban ta ce ta fado mata inda yake cewa, "Hanan ki yiwa mijinki biyayya kibishi sau da k'afa ban yadda kiyi ko musu dashi ba sannan ban amince miki kiyi koda yaji ba bare ki nemi saki a hannunshi,kada naji kuma kada nagani,duk ranar da kika zo gidan nan da sunan yaji to ba zamu kwashe dakyau ba,mijinki shine aljannarki domin tana karkashin kafarsa ne dan haka kiyi masa biyayya iya iyawarki daidai gwargwadon yanda zaki iya..... Allah yayi miki albarka" Wasu tagwayen hawaye ne suka zubo mata sakamakon tuno wannan nasihar ta abbanta da tayi,to wai ita yanzu ta ina yadace tafara ne? Wanne irin zama zatayi a wannan gida? Wanne irin zama zatayi da abokin mahaifinta? Wacce irin rayuwa zatayi da dansa da sauran jama'ar da ke rayuwa cikin wannan gida? Menene makomar rayuwarta? Wadanne irin kalubale ke jiran rayuwarta saboda auren babban mutum da tayi shin zai dauke mata dukkanin bukatunta ko kuwa zai yi watsi da lammuranta? Wadannan tambayoyin sune keta circulating acikin kwakwalwarta wanda ta gagara bawa kanta amsa.....................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: ©? *HASKE WRITERS ASSOCIATION.* _(Home of expert & perfect writers)_ *D'AND'ANO......* *MIJIN MATACCIYA.....*💞💞 *_NA_* *_UMMI A'ISHA_* *WATTPAD-UMMISHATU* *12* ***Wata zazzakar guda ta jiyo babu k'akk'autawa wata mata wacce Allah yabaiwa baiwar hanci ta dage sai rangada ta take yi kamar anyi mata bishara da kujerar hajji ko ta umarah kafin daga bisani tafara jiyo maroka suna faman yin kirari,tsam ta dakata daga kokarin saka sarkar da take yi awuyanta, "Ayyiriyiriyiriiiiiiiiiiiii....... Aure ya kullu,amarya Sa'adatu rai yakaiki..... Allah yasa gidan zamanki ne..... Ayyiririiiiiiiii" Matar da keta faman rangada guda agufi agufi tafada tana sake bude makogaro wurin rero wata gudar, sake saurarawa tayi dakyau har tana mika kunne domin jiyo abinda marokan nan ke fadi, " _Sa'adatu sa'ar mata, Sa'adatu mai sa'a babu shakka kin tako sa'a da auren baya goya marayu dan mulki kuma jinin sarauta, yagaji arziki da sarauta dan na gada ba dan na koya ba, wato Alhaji Ibrahim Khalil ga kudi ga mulki... Ina amarya Sa'adatu,kifito kibani kyautar mota da kujerar hajji amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida...._" Ai bata iya karasa jin karshen kirarin da marokan nan ke zuba mata ba jikinta yahau rawa wanda har kyakkyawar sarkar hannunta na neman sulmiyewa,anty badi'a yar gidan yayar mamaye itace tayi gaggawar riketa sannan ta rike sarkar tasoma kokarin saka mata, Ita anty badi'a duk azatonta rudewar Hanan akan an daura auren ne bata san ita jin sunan wanda aka daura auren dashine ya rudata ba saboda taji ana ambaton wani daban sabanin mujahid. Hawaye ne suka shiga wanke mata fuska babu k'akk'autawa kamar anballe bakin fanfo, Jin shigowar anty salaha yasata juyawa tana tambayar ta domin zuciyarta na fada mata kamar fa kunnenta karya yayi mata bai jiyo mata daidai ba, "Anty dawa aka daura auren? Da mujahid?" Wani kallo anty salaha ta watsa mata sannan ta fusge hannunta tana harararta, "Waye wani mujahid? Dama ya kawo miki kayan aure ne? Mtswww" Daga haka anty salaha ta dauki abinda zata dauka tayi waje tabarsu ita da anty badi'a wacce ke faman rarrashinta amma ina hawayen dake kwaranya daga idanuwanta sun kasa tsayawa, tambayar kanta take faman yi to ina plan din da mujahid keta ikirarin ya hada? To kodai plan din baiyi aiki ba? Inama zata farka taga acikin mafarki take,inama inama....!!! Wani kukan ta sake fashewa dashi ta fada saman gado ahaka aka aiko kiranta,tashi tayi tafita tana sanye da wani dandatsetsen leshi baki mai adon pink ajiki yasha manyan stones wadanda suka kara haskashi kuma suka fito da tsadarsa fili,pink din takalmi ne akafarta wacce tasha lallen amare ja da baki,kai gaskiya ba dan wannan yanayin da take ciki ba da ita kanta sai ta yabawa kanta da kanta saboda tsabar haduwar da tayi. Su Abba tasamu zaune da kaninsa baba mahe nan suka zaunarta suka yimata nasiha akan tayiwa mijinta biyayya sannan kuma ga sadakinta nan har naira dubu dari,da wani kukan ta sake fita ai kuwa cincirindon matan dake tsakar gidan suka hau guda suna fadin, "Ke kikace kina so da bakice kina so ba da ba abaki shi ba...." Ko takansu bata bi ba tawuce daki tana matsar kwalla ita yanzu gaba daya tarasa me zata kira wannan abun,wai mujahid meya faru ne da har plan dinsa yarushe? Tasan inbanda mujahid din babu wanda zai iya bata amsar wannan tambayar tata gashi ita yanzu ma kwata kwata bata san inda wayarta take ba, Zama tayi gefen gado taci gaba da kukanta,kowa yazaci kukan rabuwa da gida take yi amma ita kadai tasan dalilin kukanta,dakyar anty badi'a takawo mata maltina da madara tasata agaba tasha saboda yau bata ci abinci ba. Bayan misalin karfe 3 aka gama shirya amarya tsaff inda za atafi garin gombe da ita ta can kuma za awuce da ita gidan mijinta dake garin Abuja, Zaid ne ke jan tsadaddiyar motar da amaryar ke ciki ita da iyaye wadanda zasu rakata sai faman sharbar kuka take ta cikin mayafin dake lullube da ita, Daf da magriba suka shiga garin gombe ita dai bata iya gane komai amma tana jiyo hayaniyar jama'a wacce daga ji tasan suna da yawa sannan tana ta jiyo kade kade da raye raye gamida bushe bushe, fuskarta a rufe aka shiga da ita sashen uwar ango wato hajiya Zaitun wacce ke hakimce afalo ita da wasu hamshakan mata wadanda akalla zasu kai su biyar zuwa shida,biyu daga ciki matan Abban London ne daya kuma matar Alhaji Idris kanwa ce sai yakumbo da anty saudat banda wasu matan da yanmata dake biye dasu sai faman daukarsu ake yi awaya, Gaban hajiya Zaitun aka kaita ta zauna nan hajiya Zaitun din ta kama hannayenta wadanda suka kawatu da lalle ta rike tana saka mata albarka tare da addu'ar samun zaman lafiya mai dorewa agidan aurenta, daga bisani kuma aka gudanar da addu'o'i bayan anshafa hajiya Zaitun tace akai amarya ta huta taci abinci tayi wanka bayan tayi salla domin ta sha hanya ta gaji tana bukatar hutu inyaso gobe sai atafi da ita dakinta. Hakan akayi yakumbo ta kamata zuwa wani daki marar tarukuce ciki domin iya wani kantamemen gado ne kadai aciki sai mirrior da bedside drawers shikenan sai carpet dake shimfide gaban gadon amma fa ba karya dakin ya hadu yayi kyau fiye da hasashen mai hasashe, Sai bayan da yakumbo tafita sannan anty salaha da anty badi'a suka shigo dauke da dan madaidaicin akwatin kayanta, Salla ta farayi sannan suka zuba mata abinci shinkafa da chicken pepe soup,ita dai dakyar ta daure ta dan ci abincin wannan dinma saboda tana gudun fadan anty salaha ne domin tasan matsawar bata ci ba to sai anyi fadan da aka saba, Tana jinsu ita da anty badi'a sai faman yaba karamci da dattako irin na surukan nata suke yi suna cewa tayi dace tayi sa'a Allah ya zabeta yabata abinda ba kowacce mace ce zata samuba wato miji na kwarai da danginsa na arziki masu sonta da mutuntata,ita dai jinsu kawai take yi bata cewa komai amma can kasan ranta wani irin tafarfasa zuciyarta keyi alla alla take taji daga mujahid tana son jin abinda yafaru har hakan ta kasance. Sai bayan da tayi wanka ta shirya cikin jar night gown mai santsi tasha humra da turare kai kace angon yana nan wannan kuma duk aikin anty badi'a ne wai ko ango baya nan ai gara ta kasance cikin kamshi, Saman gado ta haye zata kwanta anty badi'a ta kalleta, "Ke Hanan bafa kwanciya zakiyi ba kinaji, lecture zamu yimiki yanzun nan dan gobe iyanzu kina dakin miji..." "Kibarta badi'a,saura kije ki samu wuri ki yita kwasar bacci babu kula da miji,mijinki dai kinga ba yaro bane da hankalinsa kuma saboda tsabar son da yake yiwa matarsa ance tunda ta rasu baiyi aure ba anbishi anyi anyi dashi akan yayi aure amma yaki dan haka idan har kikaje kika tsaya kallon ruwa wallahi kwado ne zaiyi miki kafa tunda shikam already da kudinsa kara aure ba wuya zaiyi masa ba..." "Kwarai kuwa maganar salaha na kan hanya,ki zauna ki nutsu ki koyi dabaru da salo na rikon miji yarinya wallahi aure babu abinda yafishi dadi mutukar akayi dace da abokin zama na gari,maza na son macen da ta iya kula dasu wacce zata rungumesu ta rarrashesu kamar baby,suna son mai kunya mai girmama su da mutuntasu amma fa bance kije kiyi masa dinkim a master bedroom ba,acan zagewa zakiyi kifito a yar bariki sak kima fishi rashin ta ido kin gane? Yanzu dama nasan baza ki iya hakanba saboda rashin sabo da kuma kunya amma ahankali ahankali kina sakin jiki dashi kina sake samun wayewa aharkar dan wasu abubuwan ma shi zai koya miki to daga nan fa kema sai kifara naki salon tunda anriga da anzama daya babu kuma sauran kunya..... Inbaki wasu sirrika akan maza? To bude kunnenki dakyau kiji yarinya" Nanfa anty badi'a tafara farfada mata abubuwan da yadace ta rinka yimasa wadanda maza keso ita wallahi duk sunsa kunya ta kamata gashi ma ita hankalinta ba awurinsu yakeba kadan kadan dai take jinsu amma gaba daya tunaninta yatafi ga mujahid su kam babu maganar kunya bare boye boye sai fada mata abubuwan da yadace tasani suke yi musamman ma anty badi'a wacce ta takarkare tana yimata dalla dalla yadda yadace ta kula da shinfidar mijinta da yadda yadace ta sarrafashi a wannan lokacin daga karshe ta rufe da yimata bayanin irin kulawar da zata bashi a lokacin da take yin period domin mata da yawa na daukar last position a wannan yanayin,lumshe idanuwanta ita dai tayi wani bayanin tana jinsa yayinda wani kuma bata ji, "Yar kare kike wani sissinne kai kina rufe idanuwa nan da yan wasu kwanaki zamuji ki difff da zarar kin shige gidan miji...." Inji anty badi'a wacce ta dan daki kafadarta kadan, "Ke kyale asara,kuma irinsu sunfi zakalkalewa ba" Anty salaha tafada tana sake kishingida,ita dai bakam tayi tana jinsu sunata sake karawa maganganun nasu haske ta yadda zata fahimta sosai ahaka akayi knocking anty saudat tashigo,duk kallonsu yakoma kanta,baka ce siririya doguwa sosai tana sanye cikin material pink colour, "Manyan yayu ataimaka abar mana amaryar mu ta huta haka tasamu dan bacci inji hajiya,ga dakinku can inda zaku kwanta" Ai wani sanyi Hanan taji jin zasu fita su barta ita kadai, "To ba matsala muje,amarya ga wayarki may be zaku dan taba hirar dare da ango kar mu tauye muku hakki...." Anty badi'a ce tayi wannan maganar sannan ta fito mata da wayarta ta mika mata,sake tukunkune fuska tayi saboda bata son anty saudat dake tsaye bakin kofa taganta. Tattarawa sukayi gaba daya suka fita suka barta nan ta duba wayarta jikinta har wani tsuma yake saboda yanda take hanzarin taba wayar,miss called sama da guda 15 tagani sai massages guda biyar bata bi ta kan massages din da miss called din ba tafara kiran layin mujahid amma duka akashe,ji tayi kamar ta fashe da kuka amma babu hali sakamakon wani dunkulen abu mai kamada curin karago da yazo ya tsaya mata a kirji ya tokare mata makoshi, Miss calls din tabi ta duba kusan fin rabi kiransa ne sai na sauran abokan arziki wanda bata tsaya bi ta kansu ba, massages takoma dubawa nan taga sakon bank guda daya anturo mata alawee sai sakon minister shima guda daya sauran kuwa duk sakon mujahid ne, Na mujahid din tabi tafara karantawa daya bayan daya gaba daya jikinta sai yayi mata sanyi tamkar bata da sauran laka ajikinta wai ashe duk abubuwan da mujahid yajima yana fada mata gaba daya zirata yayi akwali yarufe wai dama wallahi baida niyyar yin wani abu dan yahana aurenta da minister kawai yayi hakane dan ya kwantar mata da hankali amma kamar yadda yafada mata abaya shi mai taimaka mata ne dari bisa dari tayiwa iyayenta biyayya bazai taba goyon bayanta wurin bujirewa umarnin iyayenta ba saboda soyayyar gaskiya yake yimata kuma har gobe yana sonta,ayau dashi aka daura auren ta domin ya halarta kuma yayi musu addu'a ita da mijinta Allah yabasu zaman lafiya dan Allah tayiwa mijinta biyayya fiyeda yadda taso yiwa shi mujahid din sannan ta sani ko gobe aurenta ya mutu wanda baya yimata fatan haka ashirye yake da ya aureta yakaita gidansa domin yana sonta har gaban abada, Wadannan kalaman nasa sune suka kashe mata duk wata kafar laka dake jikinta sannan kuma suka tsayar da tunaninta cak na dan wani lokaci tabbas abunda mujahid yayi abune da yadace ta yaba masa kuma taji dadi amma kasancewar akwai Shaidan sai taji samm hakan bai burgeta ba ita wani haushi ne ma ya turnuketa dan me mujahid zai yaudare ta yamayar da ita karamar yarinya wacce bata san ciwon kanta ba? Wallahi da tun farko tasan wannan tuggun yake hada mata da tuni ta samarwa kanta mafita amma dan mugunta bai sanar da itaba sai a kurarren lokaci, lokacin da bata da matakin dauka, Sakon minister ta bude tana jin kwalla na ciko mata ido wanda sai lokacin hawayen suka samu zarafin fitowa, _Kamar yadda na fada miki zan kafa miki dokoki akan yarona,nafarko ba a dukan min yaro,ba a zaginsa,ba a yimasa tsawa sannan duk abinda yake so abashi,kuma ki sani ko harararshi kikayi zai sanar dani._ Ganin abinda yaturo mata yasata wurgi da wayar can karshen gado amma dai Allah yaso bata kai ga faduwa kasa ba,fashewa tayi da kuka aranta tana cewa wannan shine inuwa zafi rana kuma k'una........✍️ _Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *Littafin mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *14* ***Tun bayan tafiyarshi k'asar Spain ya tsinci kanshi cikin yanayi na rashin lokaci duk da a bangare daya yayi tafiyar ne dan ya kebance kanshi wuri daya kwakwalwarshi da gangar jikinsa su samu hutu koda babu yawa amma baiyi katari da samun hakanba har sai bayan yan wasu kwanaki da zuwanshi k'asar. Ranar da aka daura aurensu da Hanan Khalid ne yafara yimasa albishir ta hanyar turo masa da sakon karta kwana ta wayarshi, Lokacin yana kwance adaki mai lamba 9 cikin babban hotel din da ya sauka wato luxury 5 Stars hotel wanda ke cikin tsakiyar birnin na spain wato birnin Madrid,yana ganin sakon sai yaji hankalinsa ya dugunzuma mutuwar Ramlat ta dawo masa sabuwa kamar yanzu ne akayi ta, Samun kansa yayi da zubar da hawaye kamar wani karamin yaro kankani,mutuwa mai yankan kauna,mutuwa yanke buri,bai taba kawowa Ramlat mutuwa ba a lokacin da ta mutu amma wai sai mutuwar kawai yaji,a wannan lokacin saida rayuwar da suka gabatar tare ta dawo masa tun daga ranar da yafara ganinta har izuwa ranar da aka daura musu aure da irin tsaftacacciyar rayuwar da sukayi tare har izuwa samun juna biyunta da kuma mutuwarta duk saida suka dawo cikin kwakwalwarshi a wannan lokacin,wai yau gashi shine aka sake daura masa aure da wata saboda rashin Ramlat da ace Allah yabarshi da Ramlat dinsa ai shida kara aure har abada saboda ita kadai ta isheshi rayuwar duniya dai wadda ba matabbaciya ba. A zamansu da Ramlat yasha fada mata cewa bazaiyi mata kishiya ba ita kadai ta isheshi a lokacin sai tayi murmushi tace wannan fa tatsoniya ce kawai yake yimata ba komai ba,idan kuma Khalid na nan sai yarinka tsokanarta yana cewa ai karya Khalil din yake yi bayan shi yake ma rakashi zance ta shirya kwana kwanannan zasu kawo mata amarya, A takaice dai ranar wuni yayi acikin daki wani lokacin yayi kuka wani lokacin kuma yayi murmushi tamkar wanda ya zauce ko yasamu tabi,amma ta wani bangaren yana jin sanyi acikin ransa idan yatuna da ya cikawa Aryan burinsa dan irin farin cikin da zaiyi sai Allah. Bai samu fita ba sai bayan da yayi sallar magriba bayan yayi wanka, kananan kaya yasaka jeans da t shirt dukkansu bakake sannan ya dora jar jacket asama bayan yasa bakin takalmi sau ciki,amafi yawan lokuta irin wannan shigar yake yi aduk lokacin da yabar gida Nigeria, kananan kaya yake sakawa sai yakoma Nigeria ne yake saka manyan kaya kuma shima bai fiya amfani da babbar riga ba a'a sai dai doguwar riga da wando da hula su yafi ta'ammali dasu, Wayarshi ya dauka yafita bayan yasaka hular dake jikin jacket dinshi yarufe kansa,saida yabar harabar hotel din domin dan mike kafarsa sannan yakira Aryan yasan dai lokacin ba afi la'asar ba a Nigeria tunda akwai dan banbancin lokaci, Zama yayi kan wani bridge sannan ya kalli screen din wayar domin video call yakira,ganin Aryan yayi da hijabin umma barira ajikinsa yana kan cinyarta dare dare, "Papa Uncle...... Daddy" "Aryan,shine ka haye min kan cinyar gyatuma saika karasa mata kafafun ko? Oya tashi maza dagata" Kafada ya makale yana dariya, "No Papa.....uhm uhm" "Bar ja'iri dai ai sai na kaishi an aske masa wannan sumar tashi dake kansa" umma barira ta fada cikin tsokanar Aryan ai kuwa sai yafara kuka yana cewa baza ayi masa aski ba dan tunda aka haifeshi ba ataba yimasa aski ba tun bayan na suna har yau dinnan sai dai ataje sumar wani lokacin kuma akaishi saloon a dan gyara masa ita shikenan saboda shi kansa baban shima ba askin yake yiba sai dai gyaran fuska amma shima kansa haka yake, "To ya isa kyale umma babu mai yiwa abbana aski..... Daina kuka" "Papa momy tazo ko? Zamuje wurinta nida umma balila" Dariya umma barira tayi ta d'aukeshi cancak ta dora saman kujera tawuce gaban gado ta zauna tana cewa, "Daina bata min suna dan nema.." "Momy tazo tana sabon gida,are you happy?" "Yes Daddy,ka siyo mata kaya mai kyau" Kamar yadda ya tsammata sai da yagaji da surutun Aryan dan har saida yaji yamanta damuwar da ya wuni acikinta, Aryan na debe masa kewa Sosai aduk ranar da yasamu kansa cikin damuwa da zarar ya kasance da yaron sai yaji hankalinsa ya kwanta ko dan irin son da yake yiwa yaronne oho. *** Zaman kadaici,shiru da rashin sanin abinyi takamaimai shine ya taru ya dabaibaye Hanan wacce ke kwance cikin daki lamo ita kadai batare da abokin hira ba har magriba tayi tana kwance saman gado bata ma san magribar tayi ba saida ta kunna wayarta wacce ke kashe da niyyar kiran yaya shamsu taji ko Allah yasa sun isa gida sai lokacin taga ashe har lokacin salla yayi,yaya shamsu takira bugu uku ya dauka, "Yaya shamsu kun karasa gida ne?" "Ehh" Shine kadai abinda yafada yakashe wayarshi saboda baya son tayi masa kuka yasan yanzun nan zata fara koke koken nata, Itama tasan dalilin da yasa yakatse wayar kenan duk da haka saida taji hawaye sun zubo mata tamkar ruwan zafi saboda duminsu,kiran mujahid tayi amma har lokacin wayarshi akashe take,lallabawa tayi ta tashi tashiga bathroom tayi alwala tafito tayi salla nan ta zauna awurin bata tashiba har lokacin sallar ishah yayi,mikewa tayi ta gabatar da sallarta sannan ta tashi takoma saman gado,gaba daya tagaji da kwanciyar ma amma kuma babu yanda zatayi babu yanda ta iya,sake tashi tayi ta canja kayan jikinta izuwa na bacci riga da wando lainon c green rigar mai botira ce da gajeren hannu shi kuma wandon dogo ne, kwanciya tayi duk ranta tsoro fall amma tasan insha Allah babu abinda zai sameta saboda katon gida irin wannan akwai security duk da dai Allah ne mai karewa ita abinma mamaki yake bata wai itace daren farkonta ya kasance ahaka,lallai Allah shine mai tsara rayuwa amma ko amafarki bata taba tunanin wai daren farkonta zaizo ta wannan sigar ba. Tajima tana juye juye amma kasancewar akwai ramukon bacci da yawa akanta bata san lokacin da bacci ya dauketa ba wato shiyasa bacci yakeda dadi domin akwai wani sirri acikinsa duk damuwarka ko ciwo ko bacin rai kana mantasu a lokacin da kayi bacci baka tuna komai har sai ka farka, Hakance tafaru gareta itama domin tunda tayi bacci tasamu nutsuwa tayi baccinta cikin nutsuwa da kwanciyar hankali wanda ba ita ta tashi ba sai bayan asuba wannan dinma tasowar hadirine yatasheta saboda iska,salati tayi tai maza tashiga bandaki tayi alwala tafito lokacin tuni anfara ruwa misalin karfe 6 da kwata na safe, Sai bayan da tayi salla sannan tashiga wanka tafito,make up kit dinta ta bude ta dan shafa lotion tasaka powder sai kwalli shikenan ta saka kayanta shadda brown colour da sarka da dan kunne ta dan fesa turare sama sama sannan ta bude kofa tafita domin wata lafiyayyar yunwa take ji duk hanjin cikinta sun sarke da juna,tamkar sakaliya yau haka ta zama sakamakon ganin haduwar da falonta yayi yasha purple colour din furnitures hatta wallpaper din dake bangon falon purple colour ne amma mai dan haske sannan ga wata tangamemiyar plasma ajiye wacce ke barazanar cinye bangon da take,agaskiya gidan yayi kyau ya hadu kuma ya tsaru sannan ankashe miliyoyin kudi wurin shiryashi, ita kanta cikin falon nata wurin bedrooms hudu ne aciki banda kitchen da store da dining area haka dayan part dinma dake opposite da nata,daga tsakiya kuma akwai wani dan corridor mai dauke da wasu hadaddun kujeru kai daga ganin wurin kasan anyi ne domin shakatawa dan ga flowers nan masu kamshi shuke agefe cikin tukwanen kasa wacce aka yiwa fenti da golden gashi yadda aka you roofing din wurin dabanbanci da sauran domin wannan anyishi ne da wani style mai ban sha'awa sosai ya burgeta dan daga nan inda kake ma kana iya hango cikin unguwar ta glasses din dake zagaye da wurin kana iya hango kyau da tsari irin na unguwar wacce ke dauke da manya manyan gidaje kerarru ga korayen ciyayi da shuke shuke da suka yiwa unguwar kawanya, gaba kadan kuma wata kyakkyawar kofa ce katuwa mai dauke da security code ajiki amma ita arufe take balle taga abinda ke ciki dan haka tajuya ta nufo kasa, babban falon dake kasa shima yana dauke da kitchen da store da dining room sannan ga guest room, atakaice dai gidan yakai part 4 waje waje ko ina kuma a tsare wani wurinma bata san dashi ba. Babu kowa cikin falon sai sanyi da kamshi dake ta faman tashi ta ko ina, kan dining ta duba abinci ne reras cikin warmers mai kyau kala kala wanda ita abinma har yaso bata tsoro to ina za akai wannan abincin sai kace wanda mutane goma zasu ci bayan bata ji motsin kowa ba? Lallai masu kudi suna shagalinsu a duniyar nan ta Allah, Zama tayi ta debi dankali da kwai sai farfesun kayan cikin saniya dan su kadai zata iya ci,tana ci tana sake karewa falon kallo wanda yake kamar baza amutu ba dan tsabar haduwa tab irin wannan gidan idan mutum ba mai cikakken imani bane ai sai yamanta da mutuwa domin zai shagaltar dashi shi kansa dining area din abun kallo ne kujerunshi na karfe ne milk colour sai wani show glass mai fadi da girma glass da glass anzuba kwanukan cin abinci duk na tangaran plates, spoons, cups da sauran kayan amfani irinsu dinner set. Bayan tagama ci ta mike ta dauraye hannunta da bakinta awurin wanke hannu wanda aka tanada a dining area din dan hadda sabulun wanke hannu ajiye awurin nan ta matsa ruwa yafito ta wanke hannunta sannan ta leka cikin kitchen din wanda ke tafare da kayan amfani na wuta dan gaba daya electric ne kayan ciki gashi kuma babba dashi ba karami ba kayan ciki kuwa yaci ayiwa yanmata biyar aure dashi cikin wadata kuma,mayar da kofar tayi ta rufe takoma sama tana mai sake jinjina wannan gida acikin ranta,da ace wanda ta aura take so ko yaro ba tsoho ba ai zata fantama ta wataya to amma ina k'addara tariga fata. Rasa abinda zatayi tai daga karshe tasaka wayarta a charge tabi lafiyar kujera ta hakimce tana sake bin falon nata da kallo to kenan ma har kayan dakin shi minister dinne yayi amma dai zata iya yuyuwa shima abbanta yayi mata,to aure ne babu shiri dududu ko wata daya fa ba ayiba da maganar akayi aure shiyasa komai babu shiri, Dan sakin ranta tayi sakamakon kiranta da mutane keta faman yi awaya suna yimata Allah yasanya alkhairi wasu kuma suna yimata korafin kin sanar dasu bikin nata da batai ba ita dai bata cewa komai sai dai tayi shiru ko ance Allah yabada zaman lafiya bata cewa amin, su Khadija kuwa wadanda sukayi zaman camp tare sunce insha Allah zata gansu tunda dai tana Abuja. Wuni guda ta kwashe tana shan baccinta salla kawai ke tada ita,bayan tayi sallar la'asar ta yi wanka ta sake shiryawa cikin atamfa exclusive irin na cikin lefenta,dinkin riga da zani ne pieces simple daurin dan kwali tayi sannan ta shafa turare,tun safe rabonta da abinci shiyasa ta nufi downstairs domin cin abinci ai kuwa gashi nan jere an ajiye wurin kala biyar,shinkafa fara da plantain sauce,sai amala da miyar yauki,ga gasasshen kifi wanda yaji vegetables washa washa ga jalop cous cous,sai farfesun kaza da wasu ganyayyaki wadanda bata gane Wadanne bane, Shinkafar ta diba a plate tafara ci tana hadawa da gasasshen kifin,wato daga safe zuwa yanzu shine har aka kara zuba wasu abubuwan cikin show glass dinnan domin da safe iya dishes ne da ire irensu aciki amma yanzu harda kayan hada shayi irinsu madara, corn flakes, golden moon,da biskit kala kala wanda ake hadasu da tea asha, Tana daf da gamawa taji karar kararrawa abakin kofar falon wato door bell,tana yunkurin tashi aka sake dannawa,mikewa tayi ta nufi bakin kofar dan ganin waye dukda babu hijabi ko mayafi ajikinta amma tasan kayan jikinta basu da matsala.................✍? *_Ummi A'isha_*👌🏻 8/14/20, 10:07 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *15* ***Cikin nutsuwa take takawa har ta isa bakin kofar daidai lokacin aka sake dannawa, budewa tayi ta dan ja baya,umma barira ce da nura PA yana dauke da Aryan a kafadarshi da alama ma Aryan dinne ke ta faman daddanna door bell din, Kasancewar ita ba saninsu tayiba yasa ta dan saki fuska tana yimusu sannu da zuwa, Aryan kuwa sauka yayi daga hannun PA ya ruga jikinta ya rungume ta, bata da zabin da yawuce itama ta rungumeshi din amma bawai dan son ranta ba, Kaya aka rinka shigowa dashi wanda yake mallakin su umma bariran da Aryan,sai lokacin ta fahimci ko suwaye domin dama taji Zaid yana waya yana fadar cewa zasu dawo gidan da zarar sun kammala shirya kayansu nan suka sake sabuwar gaisuwa da umma barira ta tsugunna har kasa ta gaida umman, Suna zaune a falo PA nata shigarwa da umma kayanta cikin daya daga cikin bedroom din dake kasa bayan angama kaiwa Aryan nasa dake sama, Sosai take ankare da yaron wato Aryan wanda yayi dare dare kan cinyar umma barira sai game din Angry run yake ta faman yi awata waya hadaddiya wacce bata da masaniyar ko ta waye, "Umma kema akai miki kayanki upstairs....." Taji Aryan din yafada yana turo baki alamun shagwaba, "A'a Aryan ni ina kasa yaushe zan hau sama intakura muku" Jin abinda tace yayi wurgi da wayar yasoma rigima shi ala dole itama umma sai ta hau sama,wani irin haushin yaron Hanan keji gaba daya anbi anbata yaro an sangartashi dan kawai uwarshi ta mutu? Yaro sai tabarar tsiya duk anbarshi babu gwaba? Dan karamin tsaki taja tana kallonsu umma nata kokarin rarrashinsa amma yana ta botsarewa,cigaba tayi da kallon dramar tasu amma fa yaron akwai masifar kyau ko tantama batayi tasan mahaifiyar shi ya iyo dan wallahi kamar dan larabawa yake ko turawa, Dakyar umma ta rarrasheshi ya hakura ita dai Hanan haushi ne ya hanata magana domin dama haushinsa take ji tunda ta sanadiyyar shi ne ubansa yaje ya aurota har da su kafa mata dokoki akansa. Har lokacin sallar magriba yayi suna babban falon kasa zaune lokaci zuwa lokaci suna dan taba hira shikuma Aryan na kwance yayi pillow da cinyar umma yanata game dinshi,ganin lokacin salla na neman wucewa yasa umma barira fadin, "To kai sulaimanu dagani inje daki inyi salla karka karasa min k'afar" Mikewa umma tayi domin shiga daki shikuma Aryan yana cewa, "Ni bazan bikiba mommy zanbi" "Ehh kuje umma ta gaida Aysha" umma tafada tana wucewa daki,ita kam Hanan bata kulashi ba da taga zai biyota ma harara ta zabga masa jikinsa yana rawa yabi bayan umma yafasa binta,sama ta hau tana ta faman mita, "Haka kawai kunbi duk kun bata yaro kamar shi kadaine maraya mtswwww nidai wallahi bazanyi tolerating wannan nonsense dinba" Bedroom dinta ta shiga tayi alwala tafito aranta tana cewa idan uban naka yaji haushi ya sallame ni inbar muku gidanku sai yaci gaba da lallaba ka yana tattalinka. Aryan kuwa da kuka yashiga dakin umma wacce ke kan rug din salla tana yi,shi tunda yafado duniya bai san wani abu waishi takura ko kiyayya ba,kowa cikin nuna masa so yake da kauna ko harara bai santa ba sai yau da yaga Hanan tayi masa shiyasa tun daga lokacin yafara jin tsoronta,saida umma ta idar da salla sannan tasoma rarrashinsa daga karshe taci nasara bayan tace masa suje tabashi tuwo yaci dama akwai shi da son tuwo yana mutukar kaunar tuwo yaron yafi sonshi fiyeda komai adangin cima, Saida umma ta sake masa kayan jikinsa daga jeans da t shirt zuwa riga armless da gajeren wando sannan suka fita,akasa suka zauna bayan umma ta zubo tuwon nan tafara bashi abaki yana ci tana hada masa da ruwa amma shi hankalinsa gaba daya yana kan wayar dake hannunshi,ahaka Hanan ta sauko ta samesu tana sanye da babban hijabi hannunta rike da casbaha tana ja ahankali,zama tayi akan kujera tana kallonsu kamar tasamu tv domin sai umma ta dan rarrashesa sannan yake yarda yana karbar tuwon, Kamar a mafarki kuma sai taga yana murna yana dariya yana fadin, "Papa..... Daddy" "Yes son how you? Me kaka cine haka?" Khalil yafada wanda ke kwance kan gado yana kallon Aryan da umma agefenshi ta video call din da yakira, "Daddy tuwo umma take bani.... Kuma da dad'i" Dariya Khalil yayi yana kallon fuskar Aryan Sosai, "Boy meyasa kayi kuka? Waye ya taba min kai?" Kafin Aryan yayi magana umma tayi karaf tace, "Rigimar tashi ce kawai ta motsa kasan halin mutumin idan yan rikicin suna kusa,muma ai gamu asabon wuri Masha Allah wallahi wuri yayi kyau mu'azzam Allah yasanya albarka" Duk abubuwan da akeyi Hanan na saman kujera tana kallo amma ita bata jiyo maganar Khalil din tunda ba akusa take ba. Sunfi mintuna talatin suna wannan wayar dan har Hanan ta ci abinci tagama tawuce sama tabarsu har lokacin Aryan yanata hira da Abban nashi, lallai Allah kadai yasan irin son da wannan mutumin ke yiwa Aryan gaba daya parlors din gidan hotunan yaronne akakkafe wanda sam da bata lura dasu ba kun san ance hankali shine gani ita dai dakinta ta koma tayi sallar ishah tayi wanka tayi shirin bacci tabi lafiyar gado. Washe gari kasancewar da akwai makaranta kafin ma tafito tuni har anshirya Aryan antafi kaishi shiyasa lokacin da ta fito iya umma kadai ta tarar tana karyawa,gaisheta tayi sannan itama tawuce kan table tana ta mamakin wai su ma'aikatan gidan nan ba aganinsu ne sai dai kawai kafito ka tarar da aiki angama? Dan hatta shara dasu mopping duk anyi ansaka turaren kamsasa daki sai faman tashi yake,bayan tagama takoma wurin umma anan ma take tambayar ta ma'aikatan gidan nan umma tafara bata labari ai su da asubah suke aikinsu suyi su gama,sun jima tare da umma suna shan hira wanda hakan ba karamin debe mata kewa yayi ba,suna tare Khalil yakira umma suka gaisa cikin fara'a umma ke cemasa mutumin ai yatafi makaranta sai anjima za aje adaukoshi,tana jin lokacin da umman ke cemasa amarya fa ko abata waya? Sai yace a'a itama zai kirata ita kuwa Hanan tasan ba kiran nata zaiyi ba shiyasa da umma ta fada mata acikin zuciyarta tace yarike kiransa itama ba nema take yiba. Sun jima tare da umma suna hira daga daren jiya izuwa yau kadai taji ta saki jiki da matar kuma har sabo yashiga tsakaninsu kamar dama can sun dade tare,wurin azahar ta koma sama tayi wanka tayi salla ta dan kwanta ita fa gaba daya ta kosa hutunta yakare ta koma school saboda bazata iya wannan kwanciyar ba ace mutum babu abinda zaiyi sai dai yaci ya kwanta? Tunda fa tazo gidan nan babu abinda take yi daga gyaran d'akinta sai gyaran falo da toilet shikenan aikin sai kwanciya alhali ita bata saba wannan rayuwar ba,ita tasaba ta wuni tana aiki tana kujiba kujiba takai can ta kawo nan amma yanzu wani lokaci yazo mata wanda bata duk wadannan abubuwan. K'arfe 2 na rana tasake sauka k'asa lokacin tuni har Aryan yadawo daga makaranta PA yaje ya daukoshi yana zaune a falo daga shi sai gajeren wando duk uniform din nashi da takalmi da school bag duk ya zubarsu anan, harararshi tayi bayan ta zauna nan yashiga taitayinshi yadaina abinda ta sameshi yana yi wato baza kayan wasanshi irin fruits din roba dinnan na wasan yara harda su wuka wacce ake yanyankawa to su ta iskeshi yana barbazawa duk yana neman hargitsa falon,kalar tausayi yayi ya rakube jikin kujera yana wasa da wayarshi, Jin motsi a dining area yasata waiwayawa nan taga kuku yana shirya abinci dama tunda ta sauko take jin kamshi ya cika falon,yau dai taga ma'aikacin gidan guda daya, muryar kukun tajiyo yana gaidata nan ta amsa cikin harshen turanci domin bai iya hausa ba sunanshi John,tana ji yanata jan Aryan da wasa amma baiyi magana ba Aryan din bayan kuma surutu ne da yaron kamar aku, Tana can tana faman kallon yanda john ke shirya table cikin kwarewa da sanin makamar aiki Khalil yakira Aryan kuri yayi yana kallon yaron saboda sam babu fara'a atare dashi fuskarshi kamar zaiyi kuka tambayar shi yafara yi wai waye ya tabashi? Ko yunwa yake ji? Yaci abinci? Ina umma barira? Duk wadannan tambayoyin babu wanda ya amsa sai murza ido da yake ta faman yi yana son yin kuka,kasa da murya Khalil yayi yace, "To albishirinka lovely son.... Gobe zata zama rana ta musamman agareka.... Ai kasan babu school gobe ko? Gobe zanyi surprising dinka da wani abu,maza jeka ka kaiwa umma wayar.." Tashi Aryan yayi da gudu yana murna yahau sama nan Hanan tabishi da kallo, dakinshi dake sama yashiga wanda sam Hanan bata ma san dashi ba can ya iske umma tagama gyara masa dakin tana karasa shirya masa kayansa cikin drawer,wayar yabata yana ta murna, Bayan umma tagaisa da Khalil cikin damuwa Khalil din yace mata, "Umma ni kwana biyun nan haka haka nake ganin yaron nan babu walwala kamar yana cikin damuwa ko baida lafiya ne?" "A'a lafiyar shi kalau wallahi kuma babu abinda ke damunshi kai dai ka saki ranka ka kwantar da hankalinka wuri daya" Bazaiyi musu da umma ba shiyasa yayi shiru amma ko jiya fa da yaga yaron da daddare saida jikinsa yabashi cewa kuka yayi yau kuma gashi yaganshi yazama wani soo silent kamar wanda aka takure wuri daya, sallama sukayi umma ta mikawa Aryan wayar suka ci gaba da magana da tsohonshi Khalil sai janshi yake da hira tun bai sake ba har yasake yafara nuna masa dakinshi da umma tagama gyara masa yana ta murna yana cewa Khalil dakinshi na yanzu yafi na tsohon gida kyau ahaka Hanan ta shigo ta samesu saboda taji shirun yayi yawa kuma agabanta Aryan ya iyo sama da gudu shine da taji shiru tabiyo bayanshi, kasancewar yabar kofar dakin abude shiyasa tagane inda ya shiga,koda ta shigo cikin dakin sakin baki tayi kawai ta tsaya cak tana kallon ikon Allah domin abinda idanuwanta suka gane mata yayi bala'in bata mamaki.....................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *16* ***Sakin baki kawai Hanan tayi tana kallon irin uwar dukiyar da aka narkar wurin shiryawa Aryan dakinsa,dakin ya hadu ne yasha furnitures masu tsada da burgewa irin yanda ake shirya dakunan yara akasar turai ko India, Wani dan karamin gado ne hadadde pink & purple colour da drawers dinsa sai mirrior wanda aka daurashi a jikin bango gashi gaba daya bangon dakin an zaneshi da zanen su butterfly da sauran zane na daukar hankalin yara da kaloli daban daban har da wurin karatunshi acan gefe ansaka table da yar karamar kujera kai dakin dai yagama haduwa karshe, Tsabar mamaki kasa magana tayi sai faman bin ko ina na cikin dakin take yi da kallo yayinda ita kuma umma barira ke kokarin karasa shirya masa takalmansa saman shoe rack, "Masha Allah Aryan wannan dakin naka na yanzu yafi na tsohon gida kyau ko?" Umma ta tambayeshi cikin tsokana,yana rike da wayarshi yaturo baki, "Uhm uhmm ni nafi son wancan" "To basai kaje ka koma ba dan nema,ni katashi ma inshiryaka maza malamin islamiyya zaizo yanzu kar yazo baka shirya ba..." Ita dai hanan wuri tasamu ta zauna tana kallon wannan ikon Allah yaro karami amma dan daurewa karya kugu shine harda wani dakinsa kuma dakin ma ba ashiryashi da wasa ba dagaske aka shiryashi domin anci mutuncin naira dagaske ba kadan ba. Agabanta umma ta buda drawer din kayan shi domin ciro masa kayan da zata saka masa,kayane iya ganinka wani kayanma wannan sai yafi shekara bai maimaita shi ba saboda tsabar yawansu dan hatta uniform din makarantarshi gashi nan yafi set goma,gaskiya yaron nan dan gata ne na ajin karshe ubanshi naji dashi kuma yana nuna masa tsantsar so shi ko tunanin gaba ma bayayi? Tabe baki tayi ta tashi tafita bayan ta fadawa umma dama sawun Aryan din tabiyo da taji shiru bai koma ba, k'asa ta sauka ta hau kan table domin cin abinci, spaghetti and cheese bagels taga ni sai egusi soup and eba ga kuma jalop rice with jerk chicken salad, sannan ga goat meat pepe soup, Eba din ta zuba da miyar egusi tasoma ci tana yi tana hadawa da juice mai sanyi,gefe daya kuma tana mamakin yadda akayi wannan kukun ya iya girki har haka sai kace yaje catering school dan ko mace bazata nuna masa kwarewa wurin girki ba,tun kafin ta kalli wurin tasan sun sauko domin tana jiyo karadinsa da karar takalminsa, gaskiya umma barira na da hakuri dan wannan Aryan din dan rigima ne, Su dinma kan dining din suka hau umma nata rigima dashi akan sai yaci abinci saboda baya son cin abinci dan wani lokacin ma lunch box dinshi yanda yatafi dashi school haka zai dawo dashi bai ko buda ba, Tana jin umma nata lallaminsa har aka samu yaci eba ta hada masa da karamin juice na kwali sannan yafita domin tuni malaminsa yazo yana can yana jiransa. Ita dai tana son tayiwa umma barira magana akan Aryan amma kuma bata san ta inda yadace tafara ba domin irin wannan wani lokacin kai zakayi magana da zuciya daya kuma gaskiya zaka fada amma sai aga kamar da biyu ka fada saboda ba kai ka haifi yaroba shiyasa ma kawai taja bakinta tayi shiru suka yi wata hirar ba wannan ba, Suna zaune cikin falo bayan sun gama cin abinci nura PA yashigo dauke da kayan wasan Aryan wanda yabaro a tsohon gida wai Aryan dinne yace akawo masa kayansa shine fa akaje aka debosu cikin mota Hilux guda ahakan ma ba duka ya debo ba yabar wasu acan, Daki guda taga anbude anan k'asa kusa da na umma barira ciki nura keta kai kayan ashe dama akwai wasu aciki kiriga guda sababbi babu abinda babu,motoci ne,babur,jirgi,bindiga,duk na roba gasu nan jingim kamar dakin wasan yara,ganin haka sai ta kara shan jinin jikinta akan lamarin daga karshe ma tashi tayi takoma sama bata san lokacin da aka gama shigowa da kayanba. Washe gari bayan tafito da safe misalin karfe 11 iya umma kadai tasamu kishingide cikin d'akinta tana jan charbi,shiga tayi suka gaisa sannan umman ta kara da cewa, "Nima yanzun nan nashigo ai mutumin na raka yashiga mota babanshi ya iyo waya tunda asuba wai ashirya shi za akaishi wurin faretin yara yana son gani wai yau babu makaranta ranar yarace...." "Allah sarki shi faretin yake so? Ko harda shi a masu yi?" "A'a gani kawai zaije yayi ai uban yahana shi yi da harda shi ake zaba sai uban yace bazai yiba kin san hutsu ne wani lokacin..." "Ai kuwa dai naga alama" Ta fada acikin zuciyarta amma afili sai tace, "To Allah yadawo dashi lafiya,bari naje inyi breakfast nima fitowata kenan" Fita tayi ta hau kan dining domin karyawa,to ko mujahid yasake layi ne dan ko dazu sai da ta kirashi amma wayarshi akashe kamar koda yaushe,tsaki tayi taci gaba da cin abincinta tana jin duk zaman gidan har yafara isarta tun ba aje ko inaba,to zamane wuri daya kuma gashi babu abinda zakayi sai dai kaci kasha ka kwanta daga nan babu wani motsi da zaka yi,ita wallahi son fita ma take yi ta dan ga gari, A kasalance ta koma sama ta kwanta a falonta wayarta ta dauka ta siyi data wai ko zata dan rage zafi domin ta gaji da zaman shirun nan wai ahakanma dan da su umma, group dinsu na WhatsApp ta duba wato Abuja Kopa kamar yadda sunan group din yake wai ashe anfara clearance tun jiya amma bata saniba kuma babu wanda yafada mata,dan tsaki tayi ta mike tana tunanin ko a ina kakinta ma yake oho dan bata san duniyar da yashiga ba,bata san ta inda yadace tafara nemanshi ba, Bedroom tashiga tafara dubashi amma sai dakyar ta ganshi duk ya yi squeezing yanzu dole sai angogeshi,fita tayi wurin umma tana tambayar ta a ina zata samu ta dan goge kayanta? Nan umma ta karba tace idan PA yazo zata bashi sai yabawa mai wanki idan angoge za akawo mata, godiya ta yiwa umma sannan ta juya tasake komawa inda ta fito. K'arfe 2 da kusan rabi na rana su Aryan suka shigo shida PA yana kan kafadar PA ya daukoshi kamar wani yaron goye,zuwa yayi ya haye kan umma barira bayan nura ya saukeshi shikuma yafita, "Dan albarka andawo? Me ka kawo min?" Inji umma, "Kayan dadi..." Shigowar nura ta katse musu hirar da suke yi wanda ke rike da kaya niki niki na kwalam da makulashe cikin manya manyan ledoji masu dauke da tambarin ihsan confectionery, Uniform din Hanan umma tabaiwa PA yabawa mai wanki ya wanke mata ya goge sai yahado da kayan Aryan ya kawo, nura na shirin fita Hanan ta sauko lokacin umma nata tiriniyar bubbude kayan da PA yashigo dasu,vanilla ice cream ne manya manya sai chocolate suma manya manya da sauran tarkacen kayan ciye ciye da su snacks,fada umma tafara yi tana cewa Aryan, "Kai ja'iri ba babanka ya hanaka shan wadannan kayan sanyi da zakin ba? Shine shikuma nura ya biyewa son ranka yasiyo maka ko?" "Umma Papa ne yace asiya min shima yakusa dawowa" "Karya kake Khalil bazai ce asiya maka wannan kayan zakinba" Ai jin umma ta ambaci Khalil sai yafara kuka wai danme zata fadi sunan babansa sai dai itama tace Daddy ko Papa,dariya umma tayi ta soma rarrashinsa tana cewa, "To ai nikuma ba babana bane ba akanme zance masa baba?" "Babanki ne..." "To naji baba nane nima shikenan?" Hanan kallonsu take yi kawai amma acan kasan ranta ji take yi kamar taje ta kwada masa mari saboda b'acin yaron da sangartarshi yayi yawa yanzu meye abin kuka anan daga magana dan anfadi sunan Khalil? Wallahi ba dan tana jin kunyar umma barira ba da sakashi zatayi agaba ta yita fadin sunan uban nashi inyaso yayi kukan jini. Wadannan kayan da yazo dasu su yasha yaki cin abinci umma sai kyaleshi tayi,malamin islamiyyarshi ma da yazo kin fita yayi nanma umman tayita binsa amma yaki harda yimasa barazanar zata fadawa abbansa amma abin mamaki da Khalil din yakira waya umma tana cemasa, "Ka ganshi nan tunda yadawo daga wannan cindirin de din yaki dadi sai rigima yaketa yi yaki yaci abinci sannan ga malaminsa can yana jira shima yaki zuwa" Murmushi Khalil din yayi yace da umma, "Umma children's day fa ake cewa,tunda baya son zuwa karatun yau akyaleshi gobe sai yaje nima insha Allah yau da tsakar dare zan dawo yanzu haka ma ina dan shisshirya kayana da nazo dasu ne" "Ai kuwa Aryan yafada nazaci ko shirmensa ne,to Allah yadawo daku lafiya" "Amin umma nagode, bawa Aryan din" Duk abubuwan da ake yi Hanan dake can karamin falo tana jiyowa amma iya maganar umma kadai take ji, da alama dai shi yake bata yaronshi da kanshi ba umma ba dan umma na iya bakin kokarin ta akan Aryan. Tabe baki tayi aranta tana cewa sudai suka sani ita kam yar kallo ce. *** Misalin karfe 3 nadare agogon Nigeria suka sauka afilin tashi da saukar jirage na Nmandi azikiwe international airport dake garin Abuja,kai tsaye tsohon gidanshi yawuce domin shi komai nasa yana can bai dauke ko tsinkenshi zuwa sabon gida ba kuma bai san ranar komawa ba tunda aganinsa mai zaije yayi agidan alhali ba Ramlat ce aciki ba, Wanka kadai yayi da ruwan dumi sannan yazura farar jallabiya tas yafita yana rike da wani dan karamin akwatin adana zobe amma daga gani kasan yashaki kudi, Kasancewar ya danci abinci acikin jirgi baya jin yunwa dan haka yashiga mota suka nufi sabon gidanshi dan bazai iya hakuri baiga Aryan ba har gari yawaye, Nura na gaba yana yimasa jagora har cikin gidan,gidan yayi masa yadda yake so kuma anshirya shi yanda yabada umarni babu ta inda aka kuskure,dakin Aryan yabude yashiga ganinsa yayi yana kwance yana bacci amma ba kamar yadda ya saba ganinsa ba yau sai yaga yaron ya danyi masa wani iri,sumbatar goshinsa yayi da kumatunsa sannan yashafi kansa,akwatin zoben dake hannunsa yabude yaciro wani dan karamin zoben azurfa mai kyawun gaske dan har kana iya hango haskenshi acikin duhun tsabar shekin da yake yi,kama hannunshi na hagu yayi yasaka masa zoben wanda ke dauke da wani farin stone wanda yakara masa kyau da kwarjini,koda yaushe yana ta son yasiyo masa sakamakon wanda ke yatsan Aryan din tun yana jariri tuni yayi masa kadan yacire masa shi to bai samu wanda yayi masa bane sai wannan lokacin, Tashi yayi ya dan zazzaga yaga yanda dakin Aryan din yake sannan yafita yaja masa kofar bayan ya lullube shi da bargonshi mai tsananin laushi, Bai sake shiga ko inaba yafita yakoma mota suka bar gidan yanufi tsohon gidansa, kwanciya ya danyi ko zai dan samu bacci kafin asubah ta karasa domin da safe yana da tafiya zaije jihar katsina. Da safe bayan yashirya yana kokarin saka farin takalminsa sau ciki sakon Hanan yashigo da kamar bazai bi takai ba sai kuma ya duba bayan yagama saka takalmin, _Zanje clearance NYSC sectariat._ _Ok._ Yatura mata kawai yadauki hularshi yafita yanufi office. *** Tunda taga reply dinshi taji ranta yabaci, karasa shiryawa tayi tasaka uniform dinta tafito sanye da milk colour din hijabi, Bata samu kowa ba sai kayan breakfast jere saman table,taosted bread taci da ruwan tea sannan tashiga dakin umma barira wacce ke kwance bayan tagama shirya Aryan yatafi school gaisawa suka yi sannan tacewa umma zataje clearance tadawo ba jimawa zatayi ba, "To sai kin dawo,ashe mai gidan shima yadawo daren jiya ko... Ai sai dazu Aryan ke nuna min zoben da yazo masa dashi kuma shine kamar gari bazai waye ba aka kasa hakurin bari sai yau... Tunda yadawo nima wajen gobe zanje ingano gida in danyi kwana biyu sai indawo" Shiru Hanan tayi saboda ita bata san cewa wai minister yadawo ba au ashema yana garin take wani tura masa text massage,dan murmushi ta kakalo tayi sannan tace da umma, "Umma menene kuma na zuwa gida dan kawai yadawo,dan Allah karki tafi ki zauna muyi zamanmu" "A'a wallahi ai idan naje can dinma ba dadewa zanyi ba,kwana biyu kurum zanyi indawo" "To ai shikenan umma,bari naje nadawo" Fita tayi nan suka yi kicibus da PA wai oga ne yaturoshi tafito yakaita unguwar, batace komai ba tabishi harabar gidan mai dauke da sassa daban daban gaskiya gidan nan katone ga haduwa da yayi securities kuwa abakin gate kamar gidan wani shugaban k'asa sai yau ta taba fitowa shiyasa ta kame a owners corner tana kallon unguwar tasu har suka je bright future ta karbi clearance form daga nan yakaita NYSC sectariate tayi thumbprint sannan ya maido da ita gida sai lokacin yake fada mata wai oga na can office yana jiransu da zarar yakoma zasu tafi unguwa ita dai bata ce komai ba ta bude kofa ta fita. Kamar yadda umma barira ta fada haka ta matsa sai ta tafi gida wai tayi kwana biyu kun san iyayenmu akwai kara da alkunya ita gani take zata shiga hakkinsu ta takura musu tunda amarci zasuyi,shi kansa Khalil din baya nan tunda yadawo daga Spain sau daya suka hadu sai driver yatura mata da mota yaje ya dauketa suka nufi gombe lokacin Aryan yatafi makaranta, Koda yadawo daga makaranta baiga umma barira ba kuka yafara yi gidan shiru babu wanda yasan ma yanayi haka Hanan ta sauko ta sameshi kallonsa kadai tayi yaron yashiga taitayinsa jikinsa duk yafara rawa,da kansa ta turashi yaje ya cire uniform dinshi sannan ta tayi masa wanka,wani irin mugun tsoronta yaron yake ji domin baiga fuska ba ko abinci tana zuba masa ya dauka yafara ci duk yau babu wannan shagwabar da surutun da yasaba yiwa umma barira da kuwa ummance da sai sunyi daga da ita kafin ya yarda yaci abincin, Gaba daya Aryan ya takura yazama marayan gaske kalar tausayi,malamin islamiyyarshi na zuwa yatafi yau babu game babu wasa babu kallon carton,sam Hanan bata wasa dashi,washe gari ita tatashi tayi masa shirin makaranta yatafi kuma babansa bai samu zuwa ganinsa ba ranar yadai kirashi awaya, Cikin kwanaki biyu kacal Aryan yazama abun tausayi aranar da daddare misalin karfe 2 nadare Khalil yashiga gidan dawowarsa kenan daga gombe yaje ya dubo hajiyarsa,gani yayi Aryan duk ya sauya dan ko dazu awaya yayi mamakin yanda yaga yaron ya zama wani silent kamar bashi ba, Aryan ba irin yaran nanne masu kunci ba amma cikin yan kwanakin nan yafara zama haka shiyasa abin ke taba zuciyar Khalil,a lokacin bai tashe shi ba amma yadau alwashin sai ya tambayi yaron abinda ke damunshi,tashi yayi yafita yayi tafiyarsa tsohon gida. Washe gari bayan antashi daga school office yasa aka kawo masa Aryan ba akaishi gida ba, Tare ya zuba musu abincin da PA ya karbo musu daga gida saboda Aryan,daukar shi yayi yadora saman cinyarshi suna facing juna gani yayi da alama yauma Aryan yayi kuka,cikin damuwa ya dan girgizashi, "Abba na meke damunka? Andukeka a makaranta ne?" Girgiza kai Aryan yayi kamar zaiyi kuka dan har yafara murza ido da hannunshi, "To meke damunka? Maza fada min,kaida na kawo maka mommy gida,ko baka farin ciki da zuwanta?" Daga kai yayi alamun ehh tun daga nan Khalil yasa alamar tambaya jikinsa yabashi akwai wani abu dake faruwa...............✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *17* ***Sake tsare Aryan yayi da idanuwanshi yana son gano dalilin da yasa yaron yashiga cikin damuwa kwana biyu tunda ya tambayeshi yaki fada masa damuwarsa, Kama hannunshi yayi yana murza diamond ring din dake yatsanshi, "Aryan me mommy din take yimaka? Tana dukanka ne?" Girgiza kai yayi alamar a'a, "Tana zaginka ko?" Nan dinma girgiza kan yayi wai a'a, "To me take yimaka? Fada min bazan fada mata ba" "Nidai uncle umma tadawo....umma nake so" "Umma zata dawo ayau dinnan ma kuwa Aryan amma matsalar baka fada min abinda mommy din keyi maka ba,ko baka son inje umarah dakai bana?" Kwantar da kanshi yayi jikin uban yana murza idanuwa, "Ina so..." "To me take yimaka?" "Babu komai" "To shikenan,bari nakira PA yazo maza yatafi gombe yanzu yaje ya dauko umman" Tunda Aryan yaji haka yashiga murna umma zata dawo wanda har abin yaso bawa Khalil mamaki to ko dama rashin umman ne ke sashi cikin wannan damuwar? Babu mamaki saboda umma bata nanne yasa yaketa wadannan shiriritar tunda da ita yasaba, Kasancewar shima Khalil din fita zaiyi yanada ganawa ta musamman da shugaban kasa yasashi bawa PA Aryan akan yakaishi gida amma Aryan ya tubure akan shi lallai lallai sai yabi nura dauko umma,cewa nura yayi su tafi taren amma dan Allah kar suyi dare ahanya. Hanan na gida bata san abinda ke faruwa ba ita dai taga Aryan bai dawo gida ba daga baya kuma sai malamin islamiyyarshi da yazo yana jiranshi yace PA ya kirashi yace yatafi wai Aryan na tare da babanshi a office ita sai a lokacin ma taji abinda ake ciki, Tabe baki tayi ta zuba abincin ta a plate tawuce sama ta shiga falonta tana ta jan tsaki ita kadai, "Haka kawai kun dauki son duniya kun dorawa yaro kamar akanka aka fara haihuwa,bama dole yaro ya sangarce ba tunda ba a tsawatar masa...." Saida tagama cin abincin sannan ta zage tafara gyara falon saboda da alama masu aiki iya kasa kadai suke gyarawa sai ko dakin Aryan amma ita nata basa ko shigowa ma shiyasa ta dage ta shareshi tsaff duk da ba wani datti yayiba tayi mopping ta kunna turaren wuta a burner take falon ya dauki kamshi kamar me, toilet ta shiga ta yi wanka tafito bayan ta shirya cikin doguwar riga yar kanti marar nauyi dark blue ta dauko wayarta ta kira number mujahid kamar a mafarki sai taji ta shiga amma har tayi ta katse bai dauka ba sake kira tayi nan dinma har ta tsinke bai daga ba, Kwalla ce taji tafara zubo mata daga idanuwanta dan wallahi har yanzu bata ji alamar sonshi yaragu daga cikin ranta ba kuma bata jin zata iya daina kaunarsa a rayuwar da zata gabatar agaba, Text massage ne yashigo wayarta nan ta dauka ta duba mujahid ne yaturo mata, _Hanan dan Allah kiyi hakuri ki yafe min sannan ki zauna da mijinki lafiya wannan itace alfarmar da nake bukata kadai daga gareki._ Wasu hawayen ta sake jin suna kokarin zubo mata wai kowa sai yace ta zauna da mijinta lafiya bayan mijin ko sanin kamanninsa ma bata yiba ita yanzu da zasu hadu a hanya tasan sai yawuce ta wuce dan dukkansu ba sanin fuskokin juna suka yiba ita wallahi wannan mutumin yagama cutarta,kamar dama wacce take jira nan tasha kukanta tagama sannan ta sauka kasa har lokacin Aryan bai dawo ba babu shi babu alamarsa amma tunda dai ance tare yake da babanshi shikenan. Haka tayita kaiwa da kawowarta ita kadai acikin gidan har magriba tayi tunda ta shiga daki kuma bata sake fitowa ba har akayi sallar ishah,saida ta tashi ta gabatar da ishah din sannan tafita falonta dake sama,tv ta kunna ta kamo tashar da ake nuna fina finan India sabbi da tsofi bugu da kari akwai fina finai masu dogon zango da tashar ke nunawa dan debe kewa, Zama tayi zaman dirsham tana kallon film din da suke nunawa a wannan lokacin mai suna Viva,kallon shine ya dauke mata kewa dan ko tashi bata son yi har saida taga karshen film din nan ta kalli agogo domin yunwa take ji tana dan sunkurinta haba ashe dole taji yunwa domin karfe 10 daidai yanzu lallai tajima azaune dama karatu da kallo haka suke idan suka dauke maka hankali sai ka raba dare batare da kasani ba, Tashi tayi da niyyar zuwa kasa domin zubo abinci wanda zata dan sakawa cikinta,duk da dare ne saida ta yafa mayafi ajikinta sannan ta sauka,gidan shiru kamar koda yaushe sai ko uban hasken fitilu tarwal tamkar rana dan ko allurarka ce ta fadi to babu shakka zaka ganta hankali kwance,falon sai tashin kamshi yake yi kamar koda yaushe kan dining table din kuwa jere yake da abinci reras kamar yadda John yasaba shiryashi, Tuwon semovita tagani miyar okra,sai sphagettee with beef stew,fish and yam stew sannan ga balangu jalop,fish and yam stew ta zuba a plate sannan ta debi balangun taje fridge ta dauki ruwa da juice takoma sama ta cigaba da kallonta tana tsakurar abincin ta ahaka har ta cinye,ita dai gashi ahaka kamar babu abinda ta rasa amma azuciyarta tana jin tabbas ta rasa wani muhimmin abu atare da ita mai mutukar muhimmanci, K'arfe 10:30 su umma barira suka dawo lokacin kam tuni Aryan yajima da yin bacci dan lokacin da suka shigo ma PA ne ya daukoshi yashigo dashi falon kasa ita kuma umma ta karasa dashi dakinsa ta kwantar dashi bayan ta canja masa kayan jikinsa, Falon Hanan ta nufa a karon farko dan ba taba shigarshi tayi ba sai yau,har lokacin Hanan na zaune ta kurawa tv na mujiya amma fa acan zahiri bawai kallon take yi ba kawai tunanin yanda rayuwarta ta sauya a lokaci kankani take yi,ita da tajima tana lissafin sai tagama karatu tagama NYSC sannan zatayi aure ashe abin ba haka yake ba, Jin ana yin knocking yasa ta dan firgita sai kuma tajiyo muryar umma tana cewa "Ko har matar gidan ta kwanta ne?" Mikewa tayi taje ta budewa umma kofa fuskarta dauke da murmushi, "A'a wallahi umma idona biyu ashe kune kuka dawo...." Karasa shiga cikin falon umma tayi tana cewa, "Ehh wallahi ai mutumin nawa ne yatada rikici sai da akaje aka dawo dani,basu ma sameni anan cikin gombe dinba ina can Billiri gidan dan uwana ziyara acan suka je suka rakato ni..." "Allah sarki,ai gara da kika dawo umma amma kin tafi ki barmu?" "Ai ba tafiya nayi ba 'yarnan,zuwa nayi indawo" "To ai shikenan umma barka da dawowa ya mutanen gida? Kin baro kowa lafiya?" "Lafiya lau,suna agaggaisheki" "Ina amsawa" Kasancewar umma ta gaji daga haka ta tashi ta tafi taje tayi shirin bacci ta kwanta. Ita kuwa Hanan batayi bacci da wuriba yau tasamu kallo saida takai 1 na dare tana kallo a d'akinta,daga k'arshe ta kashe ta kwanta, Daidai lokacin kuma Khalil yashigo gidan bai shiga ko inaba sai dakin Aryan kadai daga nan yafito ya dan zazzaga gidan sannan yatafi domin agajiye yake shima. Washe gari misalin karfe 8 yashiga gidan lokacin har ankai Aryan makaranta,dakin umma yashiga kamar koda yaushe yana sanye da farar shadda kar tasha aiki da coffee colour din zare yadora hula itama coffee yar bama sai kamshin turaren gentleman yake yi wanda yake fita daga jikinshi, Zama yayi suka gaisa da umma sannan cikin fara'a yace, "umma sai kuma kika ga anje andauko ki...... Wallahi Aryan ne yakasa sakewa da bakya nan" "Ehh mu'azzamu haka nura ya sanar dani,amma ai da kun barni na danyi koda kwana biyu ne itama matar gidan ta dan sake" Dariya yayi saboda jin abinda ta fada dama yasan dalilin da yasa ta tafi kenan ganin yadawo ne, "A'a umma ai babu komai kiyi zamanki wallahi,nima kaduna zanje yanzu amma sai na fara zuwa office tukunna zan gana da manema labarai" "To Allah ya kiyaye hanya yabada sa'a,sai ka dawo" "Amin umma,mutumin yatafi makaranta ko?" "Tun dazu ai yajima acan,yatafi yana ta rikicin wai sai anhada masa harda wannan lemon madarar da ka hana abashi cikin lunch box dinsa" "Kar arinka bashi umma saboda rana wallahi" "Ehh ai shiyasa ban bashi ba nadai lallabashi nabashi dayan" Fita yayi yatafi abinshi bai ko nemi inda matar gidan takeba kai to ai shi da zaka saka wuyansa gaba gabas bazaice maka ga kalar amaryar nan ba, ita kuwa umma har yau bata san ba agidan yake kwana ba duk d'aukarta agidan yake. Hanan sai wurin karfe 11 sannan tafito bayan tayi wanka ta shirya cikin wani jan swiss material dinkin doguwar riga,umma ta iske tana falo tana sak'a muficin roba da alama jiya ta taho da kayan yin, Tea ta hado ta dawo wurin umman ta zauna suna hira, "Ashe maigidan kaduna zaije ko? Ai kullum baya rabo da tafiye tafiye,ayi mutum kullum da inda zaije bashida ranar hutu? Wannan aiki nasu da wahala yake" Jin abinda umma tace yasa Hanan fuskarta akan baban Aryan umman ke magana, murmushin yake tayi amma bata nuna cewa bata saniba, "Wai nikam umma meyasa auren da yafi na yanzu kwanciyar hankali ne dan Allah? Auren yanzu da yawa wallahi ana dai zaune ne kawai amma bawai dan ana jin dadinsa ba", ita kanta bata san lokacin da tayiwa umma wannan tambayar ba kawai dai kun san abinda ke ran mutum wani lokacin sai ya amayar dashi yake jin dadi, "To ai mu ada kinga akwai biyayya mijin ma ba saninsa kayiba shima bai sanka ba iyayene zasu hada kuma baka isa kace kai bahaka ba koda kuwa kana da naka zabin haka zaka hakura ka karbi nasu,ka isama kace kai ga wanda kake so? Ai idan kayi haka kayi rashin kunya,haka zaka yi hakuri kuma sai kiga nasu zabin yafi nakan" "Amma dan Allah umma ya kuke ji idan akayi muku auren dolen nan lokacin" "Wallahi bama jin komai 'yarnan tunda dama abune da aka riga aka saba sannan kin san mutanen da akwai biyayya ba irin na yanzu bane,dan ni kinga lokacin da aka kaini daki wallahi ban taba ganin mijinba sai lokacin shima haka kuma haka muka zauna acan muka saba muka so juna har lokacin da mutuwa ta raba,amma ku yanzu mazajen da kuke so din kuke aura amma babu zaman lafiya,mu hadamu akeyi hadin iyaye amma Sai mu zauna lafiya ba fada ba yaji bare aje garin saki da yawa mutuwa ce ke rabawa amma ku yanzu aure wata biyu wata uku sai afara yaji ko ma auren yamutu gaba daya,mu ada bamu san wannan ba,miji yana girmamaki yana girmama iyayenki kema kuma haka sannan kina yimasa biyayya babu reni amma yanzu ku auren ma yazama na zamani..." Sosai yau Hanan suka sha hira da umma wacce ke zaune tana ta sak'ar muficinta to babu abinyi idan kuma kafiya kwanciya jikinka sai yayi ciwo. Har lokacin da Aryan yadawo suna tare umma nata bata labarin auren da, Aryan baiko nufeta ba umma yanufa dama da ita yasaba shima kuma yaro yasan mai yimasa inda ake kaffa kaffa dashi yake zuwa shiyasa Aryan baya ko rabarta. Aranar da yamma su Khadija suka yimata waya wai zasu zo tabasu address din gidan,itama saida ta dan tambaya sannan ta tura musu,tana falo ita da umma shikuma Aryan yana can ana koya masa karatu wani mopol yashigo falon da kayansa na aiki ya tsuke harda bindiga rataye ajikinsa, Dan russunawa yayi sannan yace "madam kina da baki kin san da zuwansu?" Ita wallahi sai yau tasan dan zakayi bako sai ka sanarwa securities,mantawa ma take yi da agidan da take nan dai tace masa ehh tasan da zuwansu,fita yayi yaje yashigo dasu sannan yajuya yasake fita, Mamaki ne yaso kashe su hajara saboda ganin irin aljannar duniyar da Hanan ke ciki haba ai ko haka Allah yabarka sai ka gode masa domin ya daga darajar ka,gaisawa sukayi da umma daga nan takaisu sama falonta ai sai suka sake zama kauyawa sunata yimata murna ita kuwa sai tabe baki take yi bayan tagama cika musu gabansu da kayan ciye ciye da abinci da fruits da juice kala kala, Ita haushi ma take ji yanda suke ta ikirarin wai tayi sa'a tayi dace,ita da ta auri tsoho komai kudinsa wallahi gara ta auri yaro sun mutu cikin talauci, dariya hajara tayi tace, "Lallai yarinya baki san talauci ba,wallahi yau da gobe tafi karfin wasa,ai inda kudi bacin ranki kadanne koda bakya sonshi amma komai son da kake yiwa mutum mutukar akwai babu tofa babu zaman lafiya wallahi talauci shi yafi komai hana aure ya zauna lafiya" "Ki kyaleta hajara,ke nidai ki taimaka min ki hadani da wani acikin abokanshi nima infaso...." Khadija tafada tana kashe ido daya dan ita har zuciyarta dagaske take ita kuwa Hanan wallahi duk haushi suke bata haba me za ayi da auren tsoho ai wallahi akwai matsala yanzu ko abune yatashi na friends kowacce zataje da dan mijinta yaro mai jini ajika kai sai aganka da tsoho? Tsohonma wai abokin babanka,ai ita dai wannan minister ya cuceta wallahi, Duk maganganun da su hajara keyi ta bayan kunnenta yake shiga har suka gama suka tafi bayan ta cika musu leda da kayan kwalliya,ita dai yanzu alla alla take takoma school taci gaba da zuwa PPA dinta ko ta samu abinyi........................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *18* ***Haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum Hanan cikin kunci take sam bata jin dadin zaman gidan minister amma na waje koda yaushe cikin tayata murna suke ana cewa tayi sa'a kuma tayi dacen gidan miji, duk da suna zaune da umma lafiya kuma cikin mutunta juna amma wani sa'ilin ji take yi kamar ta dora hannu aka ta fasa ihu dan tsabar takaici,saida hutunta yakare ta soma zuwa school sannan ta dan fara samun nutsuwa domin kullum idan ta fita bata dawowa sai 2 na rana duk ta zama busy bata samun zama sai weekend Aryan kuwa tare suke tafiya school dashi kullum amma babu ruwanta dashi sam bata sakar masa fuska bare ya kawo mata wargi, A bangaren oga Khalil shi dinma hakan take domin har yau bai san ko kalar Matar da ya aura ba dama kuma shi ba mazauni bane kullum yana da inda zaije baya shigowa gidan sai dare darenma ba na kusa ba da yazo zaiga Aryan shikenan sai yayi tafiyarsa yakoma tsohon gida amma bai taba kwana a wannan sabon gidan ba umma kuwa yakan zo wani time din da sassafe ya gaishe da ita sannan yawuce bai taba neman hanan ba kuma bazai taba nemanta ba domin bashida matsala da ita shi yanzu matsalar shi ciwon cikin da ke neman zame masa karfen kafa domin kusan kullum cikinsa yake kuma gashi yasha magani yasha magani har yagoda Allah. Hanan har yau bata ji son mujahid yaragu daga cikin zuciyarta ba kusan kullum sai tayi masa text massage amma baya yimata reply ita kuma kamar yanda kasan asiri yayi mata haka ta makale masa. *** Mujahid Dauriya kawai yake yi amma tun ranar da Hanan ta sanar dashi maganar bikinta hankalinsa yayi masifar tashi domin akanta yafara yin soyayya kuma ita yake so bai taba son wata mace ba sai ita,bacci wannan baya iyawa yanda ya kamata, Yana zaune cikin falon mami mahaifiyar shi ya rafka uban tagumi yasaka abinci agaba amma tsabar damuwa ya kasa ci ahaka mamin tazo ta iskeshi idanuwanshi jajur yakasa cin abinci sai faman tunani yake yi,zama mami tayi ta dafashi tana son jin damuwarsa, "Mujahid meke damunka ne? Kwana biyun nan duk baka da kuzari lafiya kuwa?" "Babu komai mami...." Ya fada yana kokarin hadiye kwallar dake kokarin sauko masa, "A'a wanne irin babu komai bayan gashi nan ina ganin damuwa baro baro atare dakai,ka fada min abinda ke damunka,idan baka fada minba wa zaka fadawa?" Tallafe kumatunsa yayi da hannuwanshi guda biyu, "Mami Hanan din da nake baki labarinta itace aka yi mata aure....." "Aure? Aure fa kace, yaushe?" " tun sati biyu da suka wuce nikuma wallahi narasa yadda zanyi indaina sonta" Shiru mami tayi tana nazari amma tunda yafada mata cewa wai anyiwa Hanan aure tasamu kanta cikin bacin rai domin mujahid din yana tsananin son wannan yarinyar amma shine zata yaudarar mata yaro tasashi cikin matsala da damuwa alhalin ita kuma tana can tana more tata rayuwar, Shafa kansa tayi acikin ranta tana tunanin abinda yadace tayi domin bazata taba zura idanu tilon danta yashiga cikin matsala ba akan wata, "Dauki abincin kaci mujahid..... Insha Allah sai Allah yayi maka sakayya,dauki kaci..." Ba dan yana so ba haka yadauki abincin yafara ci sai dai ko lauma uku kwakkwara baiyi ba yaji wani azababben amai yana taso masa babu shiri yabar abincin yatashi yanufi bedroom din mami yashiga toilet dinta yasoma yunkurin yin amai wanda ke fitowa dakyar harda jini jini,ai hankalin mami wacce ke biye dashi idan yayi dubu saida ya tashi babu shiri ta kira driver suka tafi asibiti mujahid rai a hannun Allah, Saida yashafe fiye da sati daya a asibitin yana samun kulawa daga ma'aikatan jinya sannan yafara samun lafiya,kullum yana ganin kiran Hanan da sakonninta amma baya bi ta kai saboda yanzu matar aure take bai kamata yarinka kulata ba amma shima kawai danne tashi zuciyar yayi bawai dan yadaina jinta acikin ranshi ba. *** Zaman Hanan agidan minister har yau jiya iyau domin babu wani sauyi sannan bata taba ganinsa ba shima haka shi dai Khalil akwai ranar da yashigo da sassafe ita kuma ranar zata fita CDS tana sanye da uniform ya hango shigarta mota shikuma yana cikin motarshi mai dauke da bakaken gilasai yana kishingide a owners corner kamar koda yaushe,suna yin parking ita kuma motarsu na fita daga cikin gidan dama yanzu anware musu motarsu ita da Aryan mutumin nata wanda har yau baya ganin dariyarta kullum cikin cimasa magani take shiyasa yake bala'in jin tsoronta wanda har yau babanshi bai saniba dan da ace yasani da tuni yajima da daukar matakin da yadace. Kasancewar tana jin haushin uban shiyasa shima dan take jin haushinsa ga shegen surutu da shagwaba awurin wannan yaron amma uban baya gani bini bini zaka ji yakira dan awaya yana tambayar sa ko akwai wani abu? Ita kanta wayar Aryan din ta dubunnan kudice kuma ba uwar komai yake yi da itaba sai game sai waya da uban ita dai wallahi tana jin haushin wannan abu amma tunda ba danta bane ido ne nata,gashi da yadawo daga makaranta zai shiga dakin da kayan wasanshi suke a kasa yayi kaca kaca dasu yahau na hawa ya bata na batawa. Yau kam ta kama weekend tunda asuba Khalil yatafi gombe zai halarci wani daurin aure da yaso yatafi da Aryan to kuma yasan time din bai tashi daga barci ba, Hanan kuwa tun da tatashi ranta abace yake saboda weekend ne yanzu zata yita zaman wuri daya daga nan har monday,gashi tunda tazo garin nan batayi kitso ba kanta atsefe tagaji dashi kuma ahaka,text massage ta turawa minister akan tana son fita kitso,shi kam da yake yana can gombe kuma tare da mutane bai ko samu zarafin duba wayar ba saboda jama'ar da yake tare dasu daga wadannan sun fita wadannan zasu shigo kuma duk lokacin da yaje gombe hakane,zakayi mamakin irin mutanen dake tururuwar zuwa wurinshi duk ranar da yaje garin. Shirun da Hanan taji yayi mata sai tasake kufula ta tunzura dama ta jima da yimasa zargin girman kai wato yanada wulakanci da girman kai anata tunanin dan ko massage sai ya gadama yake amsawa,shiyasa a kule ta wuni ranar da rana ma saida yunwa ta ciyota tazama weak sannan ta sauko kasa Aryan na zaune falon yabaza kayan wasa baja baja yanata wasanshi umma kuma na bedroom tana dan taba baccin kalula, Kan dining Hanan ta hau ta zuba alalan kwai mai dauke da kayan lambu da sos tana ci, Aryan ne yacika falon da wata irin kara sakamakon bindigar wasanshi da ya kunna kai sai ka rantse karar bindigar gaske ne nan yacikawa Hanan kunne da kara ita kuma dama a kule take, "Kai......kashe karar nan" Ta fada cikin fada amma bai kasheba saboda shi bai jita ba sau kusan uku tana yimasa magana amma bai jiba ita kuma ta zaci yana jinta ya kyaleta dan haka ta tashi afusace ta nufe shi tana zuwa ta daka masa wata gigitacciyar tsawa da ba ataba yimasa irinta ba, "Kai...... Kashe wannan abun naka duk kabi ka wani cikawa mutane kunne shashasha kawai...." Dama Aryan tsoronta yake hakan da tayi masa sai yasake tsorata da sauri ya kashe jikinsa na rawa, "Bar nan....fice daga nan" Tashi yayi da sauri garin yabar wurin yataka wani abu daga cikin kayan wasan nasa santsin tiles yajashi suuu yatafi ya fadi kansa ya bugu da kujera ji kake gummm shikenan ya fadi awurin babu numfashi....................✍️ _*Ummi Shatu*_👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *20* ***Da hasken wayarshi ta hannu yayi amfani wacce ke cikin aljihun gaban rigarsa,caan ya hangosu kwance saman gado sunyi kai da kafa,sake lumshe idanuwanshi yayi sannan yasoma takawa ahankali har ya isa gaban gadon,kamshin dakin nata sai yaji ya banbanta da irin wanda falon nata keyi, bai tsaya kallonta ba yayi abinda yakaishi kawai wato kallon sha lelensa Aryan,ita kam gaba daya lullube take da duvet tun daga kafafuwanta har zuwa kanta dan haka babu abinda zaka iya gani atare da ita sabanin Aryan da dama tun can asali baya son a lullubeshi idan yana bacci sai ko idan baccin nasa yayi nisa, Shafa fuskar Aryan din yayi sannan yayi kissing dinsa a goshinsa shima ya lullubeshi, ahankali yajuya yafita daga cikin bedroom din amma can kasan ranshi wani dadi ne ke ziyartarsa ganin irin kulawar da Hanan ke bawa Aryan, Allah sarki ashe ya dauki hakkin yarinyar ne da har ada yafara zargin ko itace ke takurawa dan gaban goshin nasa,ashe ba haka bane ita tayashi ma sonshi takeyi, Zuciyarshi fes yabar gidan yanufi tsohon gidansa inda karfi da yaji can yake rayuwarsa shi daya,wanka yafara yi sannan yahada coffee yasha duk jikinsa jinsa yake yi yana yimasa ciwo kamar wanda ya wuni yana yin aikin karfi, shiyasa ma yau bai samu zarafin yin tsaiwar dare ba kawai dai ya zauna ya karanta abinda ya sawwaka cikin littafi mai tsarki daga nan yayi alwala ya kwanta. Su Hanan kuwa babu wanda acikinsu yasan cewa wai Khalil yazo gidan sai da suka fito da safe sannan suka ga tsarabar da yakawo musu adaren jiya wato fura da nono sai fruits kala kala harda apple mango irin manya manyan mangoes dinnan, ita umma barira har yau bata san cewa ba agidan yake rayuwarsa ba kuma bata san akwai wata akasa tsakaninsa da Hanan ba da za ta tsawatar musu kuma ta dauki mataki. Yau ita dai hanan da farin ciki ta tashi,ruwan wanka ta hadawa Aryan sannan ta d'aukeshi duk da bai tashi ba ta nufi cikin toilet dashi tana sakashi cikin bahon wanka mai dauke da ruwan dumi ya bude manyan idanuwanshi irin na ubanshi domin babu ta inda yabar babanshi a kamanni, "Mommy....." "Good morning cutie" Kwantar da kanshi yayi acikin ruwan nan tayi saurin rikeshi tana dariya, ahaka tayi masa wankan suka fita, direct dakinshi ta wuce dashi domin shiryashi, saida tafara jona masa wayarshi a jikin charge sannan ta zauna ta shafa masa mai ta fesa masa turare sannan ta saka masa uniform, ahankali take taje masa kanshi wanda ke mutukar bata sha'awa, ohh duniya kenan Allah baya barin wani dan wani yanzu gashi shi Aryan uwar ta tafi ta barshi bai ko santa ba shiyasa bahaushe ke cewa da na kowa ne saboda sai ka haifeshi amma baka mora ba wanda zai mora daban,insha Allah tayiwa kanta alkawarin kula da rayuwar Aryan ko dan lalurar dake tattare dashi kuma insha Allah zata soshi zata kula dashi fiyeda yanda zata kula da dan cikinta, K'asa suka sauka ta bashi breakfast yana ci sai lokacin umma barira tafito ganinsu cikin shiri suna karyawa yasata yin murmushin jin dadi sannan cikin farin ciki tace, "A'a d'a da uwa har anshirya ne anfito?" "Wallahi kuwa umma ai idan muka zauna sanya sai mu makara azo ana tare mu" "Ahh gaskiya kam,kai dan albarka yau babu magana? Zanfa daina mijin dakai" "Ai sai muma mu samo wata umma" Dariya sukayi dukkaninsu cike da raha suka rabo bayan Aryan ya gaisa da abbanshi wanda ke can gida kwance har lokacin bai fita ba saboda gajiyar daren jiya bata sakeshi ba har yanzu shiyasa bai bar gida ba yau sai 10. *** Mujahid yajima yana jinyar son Hanan acikin zuciyarsa,kullum baida aiki sai dai ya tisa hotonta agaba yana kallo duk yabi ya susuce yafita hayyacinsa,ada ya zaci zai iya daurewa ashe abin ba haka yake ba sai yanzu yagane gaskiyar son da yake yimata, Kullum idan yaga sakonta sai yaji kamar ya mayar mata da amsa domin yanda take ji shima fa hakan yake ji acikin ransa koma fiye da haka,nan dai zuciya ta soma zugashi akan kawai ya fara kula Hanan suje suyi rayuwarsu, gashi akwai yar uwarsa mai sonshi sumayya amma shi hankalinsa baya kanta yana kan Hanan kuma tajima tana sonshi tun yana jami'a agidansu take kasancewar shi kadai ne awurin iyayensa shiyasa suka dauki sumayya suke rikewa, Zaman asibitin da yayi ma tare sukayi jinyarsa da mami amma har yafara samun lafiya baya sakar mata fuska saboda shifa ba sonta yake ba,yau ma yana zaune a falonshi yana kallon hoton Hanan sumayya tabude kofa tashigo tana sanye da Arabian gown maroon colour,sake hade rai yayi kamar yaga mutuwarsa domin aduniya yaki jinin wannan yarinyar sumayya, Kayan breakfast din dake hannunta ta ajiye masa tana sussunkuyar da kai alamun kunya, "Yaya mujahid ga breakfast dinka inji mami..... sannan tace....tace wai ka daure ka kaini school..." Idan kujerar da yake kai ta amsa to shima ya amsa mata,tafi minti biyar atsaye awurin baice mata uffan ba daga karshe yaja wani dogon tsaki yawuce cikin bedroom dinshi batare da ya ko kalleta ba,jagwab ta tafi ta zauna bisa kujerar da yatashi tana dafe kanta wanda yafara sara mata wasu hawaye ne suka shiga kai komo akan kuncinta wanda ko tantama babu na bakin cikine,inama tana iyawa da ta cire son ya mujahid daga cikin zuciyarta amma tasan hakan bamai yuyuwa bane tunda ba ita ta dorawa kanta ba. *** Lokaci kankani shakuwa da soyayya mai tsanani ta shiga zukatan Hanan da Aryan,yanzu yaron yasaba da ita sosai kuma yana sakewa da ita kamar umma, dukkan al'amuransa wadanda ada umma ce keyi masa ayanzu Hanan ce ke yimasa,itace wankansa, shiryashi zuwa makaranta,yanke masa farce itace ke bashi abinci abaki yanzu komai ita keyi masa kuma har cikin zuciyarta yanzu tana son Aryan kamar zata lasheshi dan so,shima Aryan din yanzu ya shaku da ita komai ita yake nufa, A yanzu kam tana jin dadin zaman gidan fiye da farkon zuwanta dama gidane babban gida babu abinda babu na fannin more rayuwa babu ce kawai babu agidan amma komai da kasani akwaishi ga swimming pool,ga wani daki mai dauke da kayan motsa jiki ga library babba mai dauke da littattafai iri iri, can ta kofar baya kuma idan kabi akwai hadadden garden dan debe kewa mai dauke da tsintsaye aciki ga Giggs da dawisu dake sake kawata wurin,agaskiya gidan akwai abubuwan dauke kewa da kadaici sai dai har lokacin tana kewar gida dan duk bayan kwana bibbiyu take kiran mamaye da Abba su gaisa shi kuwa yaya shamsu kusan kullum suna hade ta online. Har tsawon wannan lokacin Khalil da Hanan basu taba ganin juna ba saboda shi baya shigowa gidan sai sunyi bacci kuma idan yaje ma iyakarshi dakin Aryan da yaje yaganshi zai tafi idan kuma awayane tashi hanan take yi tabar wurin amma tsakaninta da Aryan yanzu akwai kauna mai girman gaske dan har shi Khalil din yafara fuskantar hakan saboda komai sai yaji Aryan yace mommy ce tayi masa idan abu yaci sai yace itace tabashi yaci,tsakaninsa da ita sai dai yaji sunanta abakin Aryan amma ko awaya bai taba jin muryar taba itama haka shi kuma dama ba mazauni ba yau yana wancan gari gobe yana waccan k'asa. Tana kwance a d'akinta bayan ta idar da sallar la'asar tana karanta wani novel din turanci (Tiers of betrayal) gaba daya hankalinta yatafi ga karatun da take yi taji Aryan ya fada kanta, Ajiye wayar tayi tana rungumoshi jikinta, "Cutie what happened?" Kiss yayi mata agoshi sannan ya rungume ta, "Uncle yace ba gobeba wata goben birthday dina kuma Uncle Zaid zaizo yakaimu aje ayi party..." "Woww.....my boy zai kara girma" Rungumeshi tayi tana tambayar shi me yafi so wanda zata bashi a matsayin gift da yake yaro akwai shirme wai sai yace cake yake so,dariya tayi tace insha Allah zata yimasa cake, Khalil kuwa washe garin ranar yatafi kasar Italy kuma aranar da yamma sai ga Zaid yazo saboda wai shine zai kai Aryan wurin birthday dinshi idan ranar tayi, Sai yau Hanan ta taba ganin Zaid saboda ranar bikinta bata samu damar ganinsa ba tana kunshe cikin mayafi,tunda Aryan yaga Zaid ya makale masa suna ta tafawa da yin games kamar wani abokinsa,shima Zaid yanada haske amma ba sosai can ba kana dai ganinsa kaga bufulatani,gaba daya tana ta tunanin abunda yadace ta bawa Aryan amatsayin birthday gift dinshi amma ta rasa me zata bashi daga karshe dai sai ta turawa da Khalil text message, _Ina son zan fita zuwa super market nida Aryan_ Shine abinda yaga ta turo masa, lokacin da yaga sakon nata yana daki ya idar da salla, reply yatura mata, _me akeyi a supermarket din? Ki kular min da yaro saboda ban fiya barinsa yana fita any how ba._ Yana gama tura mata yakira Zaid yace yakaisu supermarket din sannan dan Allah ya kula da Aryan Sosai, Shiryawa Hanan tayi tasha bakar doguwar riga mai stones tayi rolling tafita kasa inda Aryan da Zaid ke jiranta,umma suka yiwa sallama sannan suka tafi supermarket din,duk abinda Aryan keso barinsa tayi ya dauka sai da yagama jidar abubuwan da yake so sannan taje wurin biya ta ciro ATM card dinta tabasu suka cire kudinsu ta POS,duk kayan ciye ciye da zaki Aryan ya diba dan harda su ice cream,daga can kai tsaye gida suka wuce dama Khalil sai kiran Zaid yake awaya yana tambaya yaji ko sun koma gida saboda shi duk lokacin da aka fita da Aryan hankalinsa baya kwanciya har sai yaji sun koma gida. Washe gari yakama ranar birthday din aryan kuma tun safe Zaid yafita karfe 2 yakira Aryan awaya yace wai mommyn shi ta shiryashi zaizo masa da kayan da zai saka,suna bedroom dinshi bayan tayi masa wanka Zaid yashigo ya kawo masa wasu tsadaddun kaya shi ba yadi ba kuma ba shadda ba yasha dinki na musamman kalar kayan ash colour ne amma anyi masa kwalliya da baki,ga takalminsa shima baki Aryan yayi kyau kamar babu gobe, Itama Hanan shiryawa tayi cikin doguwar riga mai shegen kyau ja tayi rolling kamar abun shiri sai kuma mararta tafara yimata wani azababben ciwo dole sai hakura tayi tace suje, Zaid ne yadebesu a mota banda umma ita kam cewa tayi adawo lafiya,daga shi sai Aryan suka tafi excellent square garden acan ne aka shirya party din cikin wani kayataccen hall mai masifar kyau, Hall din yasha decoration tako ina ga cakes nan manya manya wurin guda hudu kowanne kalarshi daban amma ajiki anrubuta HBD Aryan,yara da manyan dake wurin kwata kwata basu fi guda goma ba nan akayi aka gama saboda Khalil yanata yiwa Zaid takarar wai karsu yarda sukai dare shiyasa ana yin magriba suka tashi bayan anyanka cake anci ansha. Har suka dawo Hanan na kwance adaki tana fama da kanta saida taji dawowarsu ne ma sannan ta samu dan karfin fita dan ganin gifts din da aka kakkawowa Aryan wadanda ke zube afalonta Zaid yashigo dasu, gifts ne sama da guda goma ko wanne anyi raping dinshi da raping sheet mai kyalli sannan ga manya manyan cakes dinshi nan wasu an yanka wasu kuma ko tabawa ba ayiba banda sauran snacks da drinks, PA ne yazo falon kasa yakira zaid yabashi wani sungumemen gift din shima anyi raping dinshi wai inji oga wato Khalil, Hanan na zaune da Aryan akan cinyarta suna cin cake Zaid yakawo sakon,itace tafara budewa gift din Khalil din tana cewa Aryan, "Bari mufara ganin na Daddy ko" Da wani dan karamin greeting card tafara cin karo wanda ajiki aka rubuta, _Hope your birthday blossoms into lots of dreams come true! May today be filled with laughter and love. Happy Birthday and many happy returns of the day._ Murmushi tayi bayan ta gama karanta masa,wani babban enlargement din hoto tagani mai dauke da hoton Aryan atsakiya yayi kyau sosai ajiki anrubuta HBD boy,sai kuma wani dan karamin akwati koda ta bude agogon diamond ne kirar carat watch sai walwali yake aciki anninke wata yar karamar farar takarda ce wadda ajiki akayi rubutu da biro kamar haka, _I may not be celebrating your special day with you but I want you to know that I am thinking of you & wishing you a HAPPY BIRTHDAY._ _papa_ Murmushi tayi ta daura masa agogon wanda kamar angwada da hannunsa,gaskiya babansa rikakken dan boko ne jibi rubutu kamar ba hannune yayi ba sai kace injine ya rubuta,raba dare sukayi suna santin gifts din da Aryan yasamu musamman ma na wurin Dad dinshi ga kuma na sauran mutane dan wasu ma ko budesu basu yiba..................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *19* ***Duk da cikin bacin rai take sai da hankalinta yayi mugun tashi domin gani tayi Aryan yayi wanwars baya ko motsi wanda da alama suma yayi ko kuma rai ne yayi halinsa, Rasa ma inda zata dosa tayi waje ko ciki? Da gudu ta nufi kofar da zata sadata da waje amma sai takasa bude kofar ma da yake arude take sai kokarin budewa take amma ta kasa,kamar daga sama Allah ya kawo mata security guda daya wanda yanufo cikin gidan,cikin rudu da rikicewa dan ko maganar ma ta kasa tafara nuna masa Aryan wanda ke can cikin falo asheme kamar wanda ya mutu, A mutukar hanzarce suka shiga ya daukoshi,umma na can daki tana bacci bata san abinda ke faruwa ba har suka tafi asibiti,suna zuwa Dr Al'amin ya karbeshi dama shine family Dr dinsu nan yashiga bashi agajin gaggawa ita kuwa Hanan na waje ta rasa inda zata tsoma ranta tun daga yanzu tafara nadamar abinda ta aikata, bawai matakin da minister zai dauka shine tsoronta ba a'a shi dama tasan dole ne ya daureta har igiya tayi rara amma tsoronta kashe dan mutum da tayi, Tafi awa tana kaiwa da komowa tasan idan minister yaji abinda yafaru ai yau sai kwanan prison tunda ta tabo shalele,yaron da yake jinsa kamar ransa, tana nan tsaye tana ta faman kaiwa da kawowa saiga umma barira da daya daga cikin securities din gidan itama ya kawota hankali atashe, "Sa'adatu..... Me yasamu Aryan din? Ni natashi daga bacci na duba naduba ban ganshi ba sai da nafito nemansa wai ko yafita karatu sai suke fada min kun taho asibiti, me yasameshi?" "Umma faduwa yayi yabuge da kujera,wallahi babu abinda ya sameshi bayan wannan...." Kafin umman tasake magana sai ga Dr Al'amin yafito, "Insha Allah nan da anjima ko zuwa dare zamu iya barinku ku tafi gida saboda ya farfado dama ba wani abu bane furgici ne da tsoro da ya shigeshi shi ya haifar masa da wannan suman amma insha Allah babu komai zai tashi normal..." Sai lokacin Hanan taji hankalinta ya dan kwanta ta samu yar nutsuwa da taji cewa bai mutuba yana numfashi,umma kuwa ai arikice take dan kallo daya kadai zaka yimata ka fahimci hakan,tana dai tsaye ne kawai amma hankalinta yagama tashi, Wurin Aryan din suka shiga suka iskeshi yana bacci amma ga numfashinsa nan yana fita yanda ake bukata, dukkansu jugum suka yi babu wanda yake cewa uffan har tsawon wani lokaci. Koda Aryan din ya tashi jikin umma yaje ya boye yana leken Hanan cike da jin tsoronta, murmushi Hanan tayi masa idanuwanta jajur sanadiyyar kukan da tayi, Hannu ta mika masa, "Zo mana cutie" Kin zuwa yayi har suka tafi gida yana nanuke da umma suna zuwa gida suka iske miss calls din Khalil yafi abinda yafi yakira Aryan yakira umma saboda tunda yakira Aryan yaji bai sameshi ba yakira umma yaji ko lafiya ita dinma shirun yaji, Hanan kam sai sake shiga jikin Aryan take tayi tana son yaron yasaba da ita yadaina tsoronta yasake da ita kamar kowa tunda lalura tashigo ciki dan a mota har suka zo gida umma nabata labarin dama haka yake yi tun yana jariri idan yayi kuka yayi kuka sai kajishi difff yasuma shiyasa uban baya son bacin ransa, Chocolate ta debo masa irin wadan taga umma na bashi idan zai tafi makaranta, "Cutie zaka sha wannan?" Girgiza mata kai yayi alamar a'a da tace yazo yakarba sai ya makale kafada yahaye kan cinyar umma, Bata hakura ba taje ta zubo masa tuwon semovita miyar egusi wanda ke cikin fridge a ajiye saida ta dumama masa sannan ta zubo cikin plate ta kawo inda yake zaune yana ta danne danne awayarsa yaran yanzu kamar da ilmin danna waya ake haifarsu saboda yanda yaketa latsa wayar sai ka rantse babba ne, "Cutie zo inbaka tuwo kaci kaji...." Kallon umma yayi sannan ya kalleta,make kafada yayi, "Ni umma ce zata bani" "A'a ni zan baka yaron kirki dan babansa,zo kaci kaji,akwai dadifa tuwone ko incinye abuna? Kaga zan cinye to..." Kamar baya son zuwa haka ya sauka daga kan cinyar umma wacce ke cemasa maza yaje yaci,tafiya yake kamar yana taka kwalba ahaka yaje wurinta,murmushi tayi ta dorashi kan cinyar ta tafara bashi abaki yana ci,tashi umma tayi tabarsu tashiga daki tana waya da Khalil wanda ya kara kiranta tana dauka tajishi arikice, "Umma meya samu Aryan ne? Na kira aka ce mun kunje asibiti..." "Waye yafada maka Aryan muka kai? Matarka muka raka kanta na ciwo kuma tasamu sauki" Ajiyar zuciya taji yasaki mai karfi, "Allah yabata lafiya,yanzu ina Aryan din?" "Gashi can tare da ita afalo tana bashi abinci" "Ok to bari na kirashi" Suna zaune tana ta bashi tuwon yana ci yana game din Disney magic awayarshi amma yafi maida hankali kan game din haka dai take ta lallaba shi tana bashi,kiran Khalil ne yashigo sai jinsa tayi yana fadin, "Papa...." "Na'am Aryan...." Bata jiyo maganar uban ta iya Aryan take ji kawai, "Ina kaje dazu na kiraka baka nan?" Khalil ya tambaya dan son tabbatar da gaskiyar abinda daya daga cikin securities din yasanar dashi, "Munje asibiti nida umma da Mommy" Wani sanyi Hanan taji jin ya kirata da mommy ashe haka iyaye ke jin dadi idan 'yaya suka kirasu da wannan sunan? "Shikenan naje gombe idan zan dawo me zan kawo maka?" "Yogurt....." "To shikenan sai nadawo" Katse wayar yayi yajuya ya kalleta, "Na koshi" Murmushi tayi ta shafa kansa, "Daure ka cinye dai cutie nah" Karba yayi taci gaba da bashi har sai da ya cinye din sannan ta d'aukeshi suka haura sama, dakinshi ta kaishi tayi masa wanka ta sake daukoshi zuwa cikin dakin ta zauna ta shirya shi yasha turare,pink din riga t shirt ta saka masa da bakin jeans ta daura masa belt,akan cinyarta ta dorashi tana gyara masa sumarshi, "Kai wai ba a yimaka aski ne cutie?" Jijjiga mata kai yayi alamar a'a baya so,dariya tayi ta d'aukeshi suka fita zuwa falonta,carton ta kunna masa a tv dinta itama tashiga ta watsa ruwa ta fito, doguwar riga ta saka marar nauyi sannan ta dawo wurinsa bayan ta dauko robar ruwa, "Mommy Daddy yace min kin mutu...." Cak ta tsaya daga shan ruwan da takeyi ta kalleshi tabbas yataba fada mata haka, "Yaushe Daddyn ya fada maka" ta tambayeshi tana janyoshi jikinta, "Da dadewa ya nuna min wani hoto yace na mamata ne awurin haihuwata ta mutu bayan an fito dani mu biyu sai dayan ya mutu itama mommyn sai ta mutu sai ni dashi kadai....." Hawaye taji yana kokarin zubo mata wanda bata san ko na menene ba amma tausayin yaron taji akaro na farko sannan taji tana nadamar abubuwan da tayiwa yaron na rashin jansa ajikinta da sakar masa fuska, Allah sarki maraya, "Kuma sai naganki a school...." Shafa kansa taci gaba dayi cikeda tausayinsa tana jin kaunar yaron na sake shigarta ta ko wacce kafa. Ranar tare dashi suka kasance har lokacin bacci yanata bata labari da yake yaro ne mai wayo da surutu,bacci ma adakinta yau yayi ta kwantar dashi Misalin karfe 1:30 Khalil yadawo daga gombe kuma basu zarce ko inaba sai sabon gida domin yazowa da Aryan da tsarabar da yace yakawo masa. Agajiye yake lilis dan kana kallonsa ma zaka fahimci hakan,cikin fridge yasaka masa su fura da nonon daya kawo masa sauran kayan kuma sai yadora musu kan dining,duk da yasan Aryan din yayi bacci amma haka yanufi dakinsa,amma yana shiga yaga wayam baya ciki,gabansa ne yaji ya fadi nan yafita agigice da kamar yashiga dakin umma sai kuma yasake komawa sama ya nufi falon Hanan wanda bai taba shiga ba sai yau, Wani kamshi ne mai sanyaya zuciya da narkar da ita gamida saukar mata da nutsuwa ya bakunci hancinsa dayake turaren wutar da take amfani dashi mai masifar kamshi ne daya daga cikin irin gudunmawar da anty badi'a ta kakkawo mata,sai da ya lumshe idanuwanshi sakamakon irin kasalar da kamshi da sanyin falon ya haifar masa dashi, kofar bedroom din nata yabude zai shiga amma duhu didim babu haske ko kadan...................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *22* ***Bai kokalleta ba kai da alama ma kamar bai san tashigo cikin dakinba domin shi ta lafiyar dansa yake yi gaba daya hankalinsa na kansa, Tana tsaye tana kallonsu shida Dr Al'amin wanda keta kokarin kwantar masa da hankali ta hanyar yimasa bayanin cewa wai jikin Aryan dinma ai da sauki akan yanda aka kawo shi,shi dai Khalil duk bai gamsu ba domin irin yanda yaga ramar da yaron yayi sannan duk yafige yayi wani iri kamar wanda ya shekara yana jinya gara kawai yafita dashi waje aje can adubashi, sakin hannun Aryan din yayi yajuya suka fita shida Dr Al'amin domin Aryan bacci yake tayi. Awaje ya tsaya wurin su umma da hajiya yana yimusu bayanin gaskiya daga yau zuwa gobe zai fita da Aryan k'asar chairo ko India domin lalurar yaron ta tayar masa da hankali,wuri hanan tasamu ta zauna kamar wata munafuka sai faman rabe rabe takeyi, "Banki ta takaba Khalil amma da dai ka dan sake basu lokaci nan din tukunna dan ni wallahi bana son harka da turawan nan,nan dinma likitocinmu babu abinda basa yi sai dai ko da yake ku kuna dashi shiyasa fitar bata yimuku wahala...." "Shikenan hajiya amma fa duk kiduba kiga yanda Aryan yakoma..." "Hakane,mudai muyi fatan Allah yabashi lafiya" "Amin hajiya,bari naga Dr Al'amin" A office ya iske Dr Al'amin yanata yan rubuce rubuce ajikin file din Aryan,abunku da dan jarida zama yayi ya tsare Dr Al'amin da tambayoyinsa masu zafi wadanda sunfi guda goma daga wannan sai wannan daga karshe yatashi yafita yasake komawa wurin Aryan, Hanan na zaune gefensa ta rafka uban tagumi,atsaye ya tsaya kyamm yanata faman safa da marwa hannuwanshi goye a bayansa,ta gefen ido take kallonsa wallahi ba dan kar tayi karya ba sai tace bata taba cin karo da halittar da ta dauki hankalinta kamar tashi ba,bata taba ganin namiji mai kyau da kwarjini da kuma cikar haiba kamarsa ba. Gaba daya ta raja'a a kallonshi bata ko kiftawa yayinda shi kuma hankalinsa kacokan ya tafi kan abinda yadace yayi wurin samowa Aryan lafiya baima san tanayi ba domin hankalinsa ba akanta yake ba dan baiko san da itaba awurinma, Tunda yazo bai matsa ko nan da canba salla kawai ke fitar dashi,har lokacin magriba yayi,lokacin su hajiya suka dawo asibitin itada Zaid ita kuma Hanan suka tafi gida ita da umma barira,tun acikin mota take jin zuciyarta na addabarta da tunaninshi wanda bata taba jin irin hakanba akan wani namiji a iya tsawon rayuwarta,daga kallo daya da tayi masa duk tabi ta rikice ta gigice ta kuma dimauce, Kasa katabus tayi kamar wacce aka zarewa laka daga jikinta motsi kadan sai taga fuskarshi ko shi kanshi yana kaiwa da kawowa cikeda damuwa a dakin da Aryan yake,ji take yi kamar ta koma taje taci gaba da kallonsa babu ko kiftawa,haka dai tasamu tayi bacci sama sama amma bawai cikakken bacci mai cike da nutsuwa ba,washe gari da sassafe ta tashi ta shirya ta hada breakfast din da John yashirya acikin basket wanda zata tafi dashi asibiti ita da umma, Arabian gown ta saka pink colour tayi rolling tasa hill sannan suka tafi PA yajasu, tunda suka shiga suka san abu yasake rikicewa domin Aryan sai razana yake kamar wadanda Aljanu suka shafa abun dai babu dadin ji gaba daya uban yashiga wani hali. Abu kullum gaba yake kara yi duk Aryan yabi yayi wani irin baki kamar bashi ba,cikin sati daya kacal yazama duk wani iri baya ko iya tashi zaune ga firgita da yake ta faman yi ko bacci yake yi sai aga yanata firgita hakan yasa hajiya cewa su tattara su koma gida dan da alama wannan ciwon ba ciwon asibiti bane dan haka suje gida ayi magani,suna komawa gida aka fara maganin gida amma duk shi dinma jiya iyau Khalil kam ba acewa komai domin karshen tashin hankali ya shigeshi, Waya Hanan tayiwa abbanta ta sanar dashi lalurar Aryan nan yafada mata duk abubuwan da yadace tayi kafin yasamu yazo, Dakin Aryan ta nufa bayan tagama wayar da abbanta ta iske Khalil zaune gefen Aryan wanda ke kwance yayi baki sosai, tunda yazo k'asar ko kalma daya bata taba hadasu ba sai yau dinnan, Durkusawa tayi agabansa kanta a kasa tace, "Abban Aryan nayi waya da abbanmu kuma na fada masa irin lalurar da Aryan ke ciki yace asamo ruwan zamzam sai ahada da ruwa inkaranta masa ayoyin warware sihiri sai abashi yasha sannan ashafe masa jikinsa dashi dan abisa dukkan alamu sihiri ne....." Baice mata komai ba sai kai da ya daga mata,nan take yaciro wayarshi ya turawa da Zaid massage akan yaje yasamo pure zam zam mai kyau ba fake ba,tashi hanan tayi takoma bedroom dinta taje ta dauko littafin ta na ayatusshifah,tana zaune tana duddubawa Zaid ya leko yasanar da ita yakawo zamzam din, magunguna kam Aryan na shansu dan gasu nan jarka jarka anata kawowa daga wurare daban daban, Cikin babban jug ta zuba zamzam din ta hada da normal bottle water ta dauka ta kakkaranta ayoyin karya sihiri kamar yadda Abba yasanar da ita bayan ta gama ta mikawa Zaid, shida Khalil suka daga Aryan suka bashi yasha sannan suka shafe masa jikinsa dashi tas,tun atake awurin suka fara ganin alamar sauki domin yabude idonsa harda yin magana yana kiran Daddyn sa duk da maganar bata wani fita sosai. Tunda Hanan taga haka sai suka mayar da ruwan wannan addu'ar yazama shine ruwan shan Aryan kuma alhamdulillah sauki yana samuwa dan ana ganinsa,bayan kwana biyu Abban Hanan yazo duba Aryan sannan yataho masa da wasu magungunan irin na musulunci musamman na karya sihiri,dama yan dubiya kam suna shansu dan kullum gidan baya rabo da baki yan zuwa dubiya danginsu Khalil kuwa kusan babu wanda baizo ba, Mamaki ne ya lullube Hanan saboda ganin yanda abbanta da Khalil keyi tamkar wasu abokai,yau shine karo nafarko da zata shiga sashen Khalil wanda tun bayan dawowarsu daga asibiti yakoma can tunda dama ashirye yake babu abinda ba asaka ba shine dai kawai baiga damar dawowa ba sai yanzu da Aryan baida lafiya sannan yadawo dan aganinsa Menene amfanin shi yana gabas dansa yana yamma baya ganin motsinsa, Fruits da drinks ta jera cikin farantin silver ta dauka ta nufi sashen oga,suna daga ciki suna hangota tana tahowa amma ita bata ganosu sakamakon daga waje glass din mai duhu ne taciki kuma mai haske ne sosai kana kallon na waje tsaff,riga da zani ne ajikinta na atamfa tasaka hijabi,hanan taso tayi kauyanci domin bata san ta yanda zata bude kofar falon nashi ba tana tsaye da faranti a hannunta yataso da kansa yazo ya bude mata bata hanya yayi tawuce ciki sannan ya rufe kofar yabi bayanta,agaban abbanta ta dire farantin tana jin wani farin ciki yana mamaye ta tare da kaunar mahaifin ta wanda tasan har duniya tatashi banda Allah babu wanda zaiyi mata ko rabin gatan da yayi mata,tashi tayi tanufi kofar fita tana zuwa ta danyi tsamm da ranta tana kallon madannan dake gefen kofar bawai dan ta saniba kawai tayi shahada ta danna green din nan take taga kofar ta bude,kasa ta sauka taje ta harhado abinci kala daban daban wadanda John ya dafa saida ta dauko komai sannan ta sake komawa, yanzun ma shine yataso yasake bude mata sannan ta shiga, fruits din da ta kai musu ta iske suna sha da fork kowannensu, Sunkuyar da kai tayi ta soma gaida abbanta wanda fuskarshi ta cika da fara'a dan bakinsa yaki rufuwa, "Lafiya kalau uwar masu gida,mun sameku lafiya ko? Ya jikin yaron naki? Allah yabashi lafiya, Allah yasa takin arzikine" "Amin Abba" Magungunan da yazo dasu yafirfito dasu wadanda yawancinsu da zuma da zaitun da habbatussauda aka hada yana yimusu bayanin yanda zasu yiwa Aryan amfani dasu,sai bayan da yagama yimusu bayanin sannan ya kalli Khalil wanda ke sanye da farin yadi tsadadde dinkin boda yace, "Dama ahar kullum ina fada maka yaron nan sai shima ka kula dashi da addu'o'i da zikirin safiya da maraice,wani abun idan kai anyi maka aka ga bai sameka ba to za a iya komawa ayiwa danka,kai kam bani da jaa akanka kana da kariya sosai atare dakai saboda duk wanda yayi riko da ibada ya tsaida salla kuma ya kiyayeta sannan yake yawaita tsayuwar dare da sadaka kuma yabi iyayensa to babu mahalukin da zaiyi nasara akansa sai dai makiya su gaji su barshi dan yafi karfinsu to amma shi sulaimanu ai kaga yarone dole sai ankula dashi, Allah yabashi lafiya kuma insha Allah nasamo bakin zaren,insha Allah zai samu waraka,sihiri ne akayi masa kuma mace ce tayi amma idan nace gata to nayi karya,amma tabbas mace ce dan naganta acikin mafarki,wato kasan wani sihirin akwai addu'ar da akeyi ayi salla raka'a biyu to Allah yana haskawa mutum inda aka yimasa sihirin idanma binnewa akayi duk za anuna maka wurin...." Daga Hanan har Khalil jikinsu ne yayi sanyi Sosai, Hanan aranta cewa takeyi wannan wanne irin rashin imani ne da mutum zai nemi halaka dan tahalikin yaron da baiyi masa laifin komai ba? Ita kuwa wannan matar me Khalil yayi mata da har take kokarin hucewa akan dansa? Kwalla taji ta ciko mata ido bata gogeba saida tabarta ta sauka, Shi kam Khalil shiru yayi yana tunanin to wacece wannan? Zuwa caan ya sauke ajiyar zuciya ya tankwashe kafafuwanshi yana lankwasa yan yatsun kafarshi domin yagano ko wacece, Abba ne ya kalli Hanan sannan yace, "Yanzu kiyi azamar zuwa kibashi magungunan nan yasha sannan ki shafe masa jikinsa da wadannan mayukan,insha Allah zai samu waraka" "Toh Abba" Tashi tayi ta dauki maganin tafita,sai bayan da ta fita sannan Khalil ya kalli Abba yace, "Nagode madallah malam, Allah yasaka maka da alkhairi,kuma ba dan kar kace nayi zargi ba wallahi har nagano wadda tayi min wannan abun...., bazai wuce yesmin ba,tajima tana bibiyata kuma ita ba da aure take sona ba a'a da sabon Allah nikuma ba halina bane,babu wanda bai san zaman kanta take yiba...., Yanzu last zuwan da nayi Denmark sai da tabini hotel din da nasauka....." "Ai shiyasa nake fada maka dole sai ka dage da addu'a da rokon Allah saboda mata iri iri zasuyi ta kawo maka farmaki sai dai Allah ya tsareka ya kareka daga kaidinsu...." "Amin" yafada yana sunkuyar da kanshi kasa,shi dai Abba cigaba da bashi shawarwari yayi ta yi yanda zai cigaba da neman tsari daga kowacce irin mace. Hanan na zuwa dakin Aryan ta samu hajiya da umma atare dashi,sune suka taimaka mata tabawa Aryan magungunan yasha sannan ta shafe masa jikinsa da wadanda abba yace mata na shafawa ne,kuma sauki kam ana samu sai godiyar Allah dan ko minti 20 baiyi da shan maganin ba yace zaici abinci wanda rabon da yaci anjima,abinda yake son ci Hanan ta tambayeshi yace shinkafa dama akwai shinkafa acikin abubuwan da John yadafa yau dan haka ta sauka da sauri taje ta zubo masa a plate ta kawo,itace ta zauna ta bashi abaki kuma babu laifi ya dan ci dayawa daga nan bacci yakoma ita kuma tafita taje d'akinta tayi wanka sannan tayi sallar la'asar,wurin Aryan ta sake komawa tasamu suma su umma har lokacin suna tare dashi yatashi daga baccin da yake yi yanata game a wayarshi, gefenshi ta samu ta zauna ta dora kanshi saman cinyarta tana tofa masa addu'a ahaka Khalil yabude kofa yashigo ya samesu ganin Aryan yana game yaji dan sanyi sanyi acikin ransa,hannu yakai saman goshin Aryan yace, "Sannu abba na,jiki yafara sauki ko?" Kai Aryan ya daga sannan yace, "Uncle zaka tafi dani Italy ko?" "Zanje dakai duk inda kake so abbana, Allah dai yabaka lafiya" Daga haka yajuya yafita yakoma wurin Abban Hanan wanda ke can yana jiranshi, ita kuwa Hanan tana wurin Aryan har magriba tayi dan anan ma dakin Aryan tayi sallah tana idarwa taji shigowar text cikin wayarta, _Kizo abbanki na kiranki._ Shine abinda taga minister yaturo mata tashi tayi tafita saida tafara shiga bedroom dinta ta shafa turare sannan tafita tana sanye da doguwar riga yar kanti da farin hijab ajikinta, tsayawa tayi bakin kofar tana wurwurga ido shin ina zata taba? Jan ta danna sai kuwa kofa tabude,ahankali cikin nutsuwa take takawa har zuwa cikin hadadden falon nashi wanda yafi kowanne falo dake gidan haduwa,komai nashi farine tas babu sirki,hatta Rug din dake shimfide a tsakiyar falon farine sai dai an diddiga masa kalar baki dan sake fito dashi,falon tafkeke ne na gaske amma sai dai babu tarkace masu yawa acikinsa,iya kujeru ne wato (Turkish Sofas) farare guda biyar sai glass tables manya da kanana an a'ajjiye su a muhallin da yadace dasu sannan ga kayan kallo manya manya sai fridge acan gefe daya sannan ga dining table da yan kujerunsa kwaya hudu shima farare acan gefen dama,daga gefen hagu kuma wasu fararen kujerunne kwaya biyu masu laushi an ajiyesu da farin Rug dan karami a tsakiyar su sai center table atsakiya,kai falon dai yayi ba karya kuma ya hadu karshen haduwa,ga toilet nan aciki sannan sai kofar bedroom dinshi agefe ta can bangare daya kuma kofar da zata sadaka da valcony ce wadda aka shiryata domin hutawa dan yanzun ma haka su abba acan suke suna hira, Hanan tsaye tayi domin bata san inda zata nufaba, maganar su tajiyo suna kokarin shigowa, "A'a ashe ma ga mai babban sunan har ta karaso" Tajiyo muryar Abba yana fada cikin raha shi dai minister bata ji me yace ba, Abban ne yafara shigowa ya nemi wuri ya zauna sannan itama ta zauna akasa tana sunkuyar da kanta, Sake sabuwar gaisuwa sukayi da abba sannan suka cigaba da hirar gida wanda ba karamin dadin hakan Hanan tajiba shi kuwa Khalil har har lokacin yana valcony yana shan iska daga Allah bai shigo falonba sai da yaji ana kiran sallar ishah, Hanan tasake sosai da abbanta yashigo,dan satar kallonsa tayi taganshi sanye cikin wasu kayan wadanda ba na dazu ba saboda yanzu milk colour din shadda ce ajikinsa sai kyalli takeyi dinkin half jamfa yayi kyau yayi kyau har ya gaji, "Bari muyi salla ko..." Taji abbanta yafada,tashi tayi tana fadin, "To Abba,bari naje na kawo muku abinci" Fita tayi sukuma nan cikin falon suka tada kabbarar sallarsu ita kuma tawuce kitchen taje ta zuzzubo musu abincin da aka shirya na dare,suna salla duk ta kawo ta ajiye musu sannan tafita. Bata sake komawa sashen minister ba sai wurin karfe 9 shi lokacin ma yana d'akin Aryan tare dashi dasu hajiya yadora Aryan din asaman cinyarsa yana yin game awayarsa,bata ga abbanta ba sai kayan kawai ta debo ta fito dasu tasan watakila abban yana masaukinsa dan dakyar ma ya yarda zai kwana da cewa yayi ayau zai koma, Dakin Aryan ta shiga inda su hajiya ke ciki itada umma dakin gauraye da kamshin turaren Khalil na no 1 wanda ya mamaye dakin gaba daya,sai bayan da ta rufe kofar dakin sannan idanuwanta sukayi arangama dashi zaune dare dare bisa kan gadon Aryan ga kuma Aryan din akan cinyarshi,zama tayi gefen umma tana satar kallon Khalil wanda ke cikin blue din riga ta polo sai dogon blue din wando mai santsi,kamar lokacin da tafara ganinsa yanzu ma shagala tayi da kallonsa yana ta yiwa Aryan wasa wanda ke yin game, "Mommy zan sha ruwa..." Taji Aryan yafada, Tashi tayi ta dauko masa ruwan maganinsa wato ruwan addu'a taje ta mika masa,karba yayi yatashi zaune yasha sannan yakoma ya kwanta,ayanda ta lura Khalil ba mai yawan magana bane domin idan aka bata dama tsaf zata kirge adadin maganarsa tun shigowar ta dakin,iya umma da hajiya ne kawai ke ta hirarsu. Sai da Aryan yayi bacci sannan Khalil yafita,bayan fitarsa da yan mintuna itama tafita ta nufi bedroom dinta,shirin bacci tayi ta kwanta tana lumshe idanuwanta cike da begen Khalil....................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *21* ***Khalil na kwance kan gadonshi adakin hotel din da yasauka yana kallon pics din birthday din Aryan duk da baya nan aka gabatar da party din amma zaid yayi kokari kamar yana nan saboda yanda aka shirya abin cikin kyau da tsari bugu da kari kuma gashi yaga fuskar Aryan cikin farin ciki sosai hakan kadai da yagani yaji inama shima yana wurin ko kuma inama zai iya yin fuffuke yatashi da yaje anyi dashi,har yagama kallon pics din baiga Hanan ba koda yake ai ba saninta yayiba kuma ta yuyuma babu ita awurin. Hanan kam har washe gari ma bata samu fitaba dan har lokacin bata jin dadin jikinta tadai shirya Aryan ta hada masa komai yatafi school,kuma har yaje yadawo tana kwance a bedroom dinta tana kallon hotunanshi dake cikin wayarshi wadanda sunfi dari,kuma duka nashi ne shi kadai bata ga na babanshi ba duk shi kadai ne akasashe daban daban gaskiya yaron nan ya zagaya duniya domin tun baifi shekara biyu ba ta ga uban yafiffitar dashi manya manyan k'asashen labarawa da na turawa dan wasu hotunan ga larabawa nan wani kuma turawa zaka gani gasu nan dai burjik wani kuma a saudiyya ne dan ga ka'aba nan da sauran kyawawan wurare dake cikin birnin k'asar,ta shagala sosai da kallon hotunan shiyasa har Aryan yadawo bata saniba tana ta kallon hotunanshi shida wasu yara kyawawa suma guda biyu kamarshi mace da namiji taji shigowar Aryan yana zuwa ya haye kanta kamar yadda yasaba, rikeshi tayi tana murmushi, "Welcome back my Cutie..." Kankameta yayi suna dariya pic dinshi da yaran nan ta nuna masa tana tambayarshi suwaye wadannan sai yace mata wai nawwar ne da Naina yaran Abba Khalid wai yan uwanshi ne, lallabawa tayi ta tashi taje tayi masa wanka bayan ta cire masa uniform dinshi tabashi abinci yaci sannan yafita islamiyya wurin malaminsa. Bayan birthday din Aryan da kwana biyu Zaid yakoma gombe yanzu gida yarage sai iya Hanan da Aryan da umma barira,duk wani abu da yashafi Aryan yanzu Hanan ce keyi masa itama shagwabashi yanzu takeyi sosai wanda har Khalil yasan da haka dan komai sai Aryan yace masa wai mommyn shi ce tayi masa idan abinci ne sai yace itace tabashi shi kansa yasan tana kulawa da yaron Sosai ba kadan ba. *** Har yanzu sumayya bata samu ta shawo kan mujahid ba domin kullum cikin wulakantata yake yauma hakance tafaru tana daki tana ta sharbar kuka mami ta shigo ta zauna gefenta,cikin lallashi tace, "Sumayya daina kuka kinji,yi hakuri,ki daina sakawa kanki damuwa akan mujahid kedai kawai kici gaba da addu'a idan har mijinki ne babu makawa sai ya aureki....kiyi shiru kinji" Kai ta daga alamun to,haka mami taci gaba da rarrashinta daga karshe ta tashi tafita,tana fita ta dauki wayarta ta kira k'awarta muhibba ta zayyane mata dukkan abunda yake faruwa sannan cikin kuka ta karasa maganar tata da fadin, "Muhibba da me Hanan tafini da yake wulakanta ni akanta bayan ma tayi aurenta ita ta manta dashi amma shi kullum cikin kallon hotonta yake...." "Babu da abinda tafiki sumy,ki kwantar da hankalinki kiji abinda zan fada miki....." "Ina jinki muhibba" "Yawwa kema ki shareshi ki fita harkarsa kuma ki daina kulashi,ki nuna masa idan dashi ko babu shi zaki iya rayuwa,ki shareshi fa sosai dan shima yana sonki bawai ke kadai ke haukan sonshi ba saboda duk wanda kake so wallahi shima yana sonka sai dai ko wani dalili ya hanashi bayyanawa amma dan so shima yana sonki,ki danne zuciyarki ki shareshi shi da kansa zai sauko" Shawarwari sosai muhibba tabata kan yanda zata share ya mujahid har sai yakawo kansa da kanshi,ita dai sumayya ji take yi kamar bazata iya ba saboda irin yanda a kullum wutar son mujahid ke ruruwa a cikin zuciyarta gashi shi kuma yayita disgata agaban kowaye babu ruwansa dazu fa agaban yan aikin gidan yayi mata rashin mutunci dan kawai tashiga dakinsa abinda yasata kuka kenan amma insha Allah zata danne zuciyarta tabata hakuri ta gwada aiki da shawarar muhibba. *** Bayan birthday din Aryan da sati daya Khalil yadawo nan yakawowa Aryan tsaraba mai tarin yawa ta takalma da jeans da t shirts masu tsada, Kullum baya shiga gidan sai cikin dare misalin karfe 1 ko 2 wani lokacinma har 3 dan sai kowa yayi bacci agidan,bai jima da dawowa ba yasake komawa k'asar Italy amma kullum suna makale awaya shida Aryan wanda ada yamakale masa wai sai yabishi dakyar ya shawo kansa ta hanyar cemasa ankusa yin hutun makaranta ana yin hutu zai fita dashi duk k'asar da yake so. Khalil baifi sati daya da tafiya ba Aryan yawayi gari da wani zazzabi mai zafi ga tari da ciwon kirji babu shiri aka kira Dr Al'amin yana zuwa da yadubashi yace su tafi asibiti dan dole sai ya kwantar dashi, Asibitin suka tafi dukkaninsu cike da damuwa da tashin hankali ita kam umma ma kashe wayarta tayi dan kar Khalil yakirata haka ta Aryan dinma arufe take,kwantar dashi Dr Al'amin yayi yafara bashi taimakon gaggawa, Aranar da yamma sai ga Zaid yazo kamar yanada masaniyar abinda ke faruwa,can asibitin yabisu dan ajikinsa ma aka debi jinin da aka karawa Aryan din, Khalil shi bai san abinda yake faruwa ba amma haka kawai yaji jikinsa duk babu dadi kamar irin baida lafiya dinnan alhalin kuma shi lafiyar sa kalau amma dai jikinsa yayi masa wani irin sanyi kalau haka dai ya daure yaci gaba da al'amuransa wadanda suka kaishi, Yana ta kiran Aryan awaya kuma baya samunshi haka itama wayar umma bata shiga daga karshe sai Zaid ya nema dan jin meke faruwa amma sai Zaid ya ce masa wai babu komai da ya tambayi Aryan sai yace bacci yake yi,cewa yayi to ya gaidashi shida umma sukayi sallama, Duk dangi kuwa babu wanda bai san rashin lafiyar Aryan ba Khalil kadai aka boyewa saboda ba ason afada masa saboda kar hawan jininsa ya motsa,tun a washe garin ranar da aka kai Aryan asibiti hajiya tazo Abuja suna tare a asibitin suna kula dashi, Zaid kuwa sai hanya hanya yake yiwa Khalil idan ya kirashi yace ya hadashi da Aryan sai yace yana toilet ko yace yana bacci ko kuma yace wai yana makaranta,da Khalil ya tambayeshi to me yasamu wayar Aryan din da yasa baya samu idan yakira sai yace wai ai swimming pool tafada a hannun Aryan shiyasa ta daina yi nan Khalil yace masa to idan yadawo ya daukeshi suje wurin siyar da wayoyi ya siyo mishi duk wacce yakeso komai tsadarta da toh Zaid ya amsa masa sukayi sallama suna yin sallama yakashe shima tashi wayar gaba daya. Yau kam tashin hankalinsu yafi na kullum domin tunda garin Allah yawaye Aryan yake ta faman suma daga safe zuwa yamma ya suma yafi sau biyar,shi kansa Dr Al'amin yagama shiga tashin hankali saboda yanda jikin Aryan yarikice Sosai, Hanan shawara tayi da zuciyarta bata sanarwa da kowaba aranta tace gara ta fadawa Khalil abinda ke faruwa tunda boyewar bata da amfani da afada masa mutuwar dansa gara afada masa rashin lafiyarsa yazo ya ganshi kar aje yamutu, Text massage ta tura masa tana turawa ta kashe wayarta itama, Khalil na kwance yakasa bacci dan a yan kwanakin nan sam baya iya bacci gashi dai lafiyarshi kalau amma kamar baida lafiya yake jinsa,jin shigowar sako yasashi kallon agogo,karfe 3 da kusan kwata dan asubah ma ta kusa,daukar wayar yayi yabude sakon nan yaganshi kamar haka, _Abban Aryan kazo gida domin Aryan ba lafiya muna asibitin Dr Al'amin._ Yana gama karantawa yaji yashiga cikin tashin hankali,acikin wannan daren yafita akayi cuku cukun jirgin da zai tashi da asubah zuwa Nigeria,bai dauki komai ba sai wayoyinshi yanufi Nigeria. Kamar yadda babu wanda yasanar dashi rashin lafiyar Aryan shima babu wanda ya fadawa cewa yabaro Florence yataho Nigeria har saida jirginsu ya sauka sannan yakira PA yace yazo ya d'aukeshi, Kai tsaye asibitin suka wuce PA ne agaba sai securities dinshi abaya shi kuma yana tsakiyarsu, "Ni wallahi bana son yaron nan Khalil yaji maganar nan saboda hawan jininsa" umma barira tafada cikin damuwa domin dukkansu suna waje su hudun zaune kofar dakin da Aryan ke ciki kan wasu kujerun karfe wadanda aka tanada awurin domin zama, "Ai gashi nan ma dan halak" Zaid yafada yana mikewa tsaye, Hanan kam kanta asunkuye yake ta dunkufar dashi bayan tasha kukanta ta more dan har idanuwanta sunyi jajur ga shi sunyi luhu luhu,wani arnan kamshi ne yafara kaiwa kofofin hancinta sumame wanda ya tilastata ta dago kanta domin ganin mamallakin wannan kamshi, Dakatar da securities din nashi yayi yakarasa wurinsu umma shi kadai,ai Hanan ji tayi tai suman zaune, dama wannan shine minister? Shine mahaifin Aryan? Shine abokin Abbanta? Mamaki ne ya mamaye dukkan ilahirin zuciyarta domin bata taba zaton zata ganshi hakaba kyakkyawa mai cikar halitta da kwarjini ba,kamarshi daya da Aryan da Zaid amma duk ya kere su a kyau domin farine kal dogo Sosai dan har ya dan rankwafa ma'abocin bakar suma wuluk mai matsakaicin jiki, fuskarshi dauke take da manyan eye balls farare tas ga hanci kamar biro bakinshi kuwa dauke yake da lips masu taushi suba red ba kuma su ba pink ba akwai saje a fuskar tashi wanda yataho har zuwa habarshi yahade da dan kyakkyawan gemunsa amma bawai buzu buzu da yawa ba a'a dan gwanin sha'awa dashi kuma shine ya karawa fuskar tashi kyau da annuri, kuruciyarshi afili dan sam babu maganar tsufa atare dashi sannan jin dadi da hutu sun sake fito da kuruciyarshi da kyakkyawar halittar shi dan duk da yana yawace yawace baya zama wuri daya amma hakan bai samu nasarar hana jin dadi da hutun da yake ciki bayyana agareshi ba,bafulatani ne na usul daga kallonsa zaka fahimci hakan,samun kanta tayi da nadamar yimasa rashin kunya da tayi abaya ita wallahi ta zaci zata ganshi tsoho kuma mummuna ashe abin bahaka yake ba sai gashi ta ganshi mai kyakkyawar halitta ma'abocin cikar haiba da kwarjini,shagala tayi da kallonsa domin tunda yazo ya dauke mata hankali wanda bata farga ba har saida yagama gaisawa dasu umma yanufi dakin da Aryan ke ciki batare da yako kalleta ba dan shi hankalinsa ma bai kai kanta ba, firgigit tayi daga duniyar da tatafi kamar kazar da kwai ya fashe mata aciki haka ta mike jiki babu kwari tabishi cikin dakin...........✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:08 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *23* ***Juyi tayi ta dauki karamin pillow guda daya ta rungume acikin zuciyarta tana hango kyakkyawar fuskarshi, murmushi ta saki ita kadai kamar wata tababbiya saboda tuno rashin son hayaniyar shi da tayi ga masifar jan ajin tsiya kamar wata mace wanda hakan ba karamin kyau da kwarji yake kara masa ba,wai meke shirin faruwa da itane? Ta tambayi kanta bayan ta tashi zaune, "He's cute....." Tafada ahankali bayan ta koma ta kwanta tasake rungume pillow, "Ban taba ganin namiji dan gayu handsome kamar shi ba" ta sake fada afili tana sakin murmushi,gaskiya Khalil yahadu yahadu irin haduwar da tafi gaban kwatance domin sai wanda idanuwansa yagane masa kawai,juye juye tayita faman yi takasa bacci sai Khalil da take ta faman gani a idon zuci dakyar tasamu bacci ya lallabo ya saceta. Shima Khalil anasa b'angaren bayan yagama nafilfilinsa lokacin da ya kwanta kasa bacci yayi kawai tunanin abinda yesmin tayi masa yake yi wato ta zabi ta kashe masa d'ansa saboda bata samu abinda take so ba daga gareshi,ita sabon Allah take son ya yarda suyi ta yi shikuma hakanne bazai taba iya aikatawa ba,sau da dama tana zuwa office dinsa amma baya saurararta,gashi dai babbar mace ce amma kuma sam bata da nutsuwa dan babu halin mata na kirki atare da ita gashi abanza tana neman illata masa yaro wallahi ba dan Abban Hanan yabashi baki yace yarabu da itaba da sai sunyi shari'a da ita,bacin rai bai barshi ya runtsa ba sai tsakiyar dare. Washe gari Hanan da farin ciki ta tashi cikin nishadi tayi wankanta ta shirya cikin riga da skirt na English wears sannan ta saka dan madaidaicin pink din hijabi ta fita lokacin umma na kwance adakin Aryan dama tare suke kwana sai da Hanan ta shiga sannan umma tafita,daga Aryan Hanan tayi wanda zata yiwa brush nan taga abunda yayi masifar tsorata ta har ta nufi kofa da gudu dan kiran umma ko hajiya amma tana bude kofar sukayi gware da Khalil wanda ke kokarin shigowa cikin dakin ganinta da yayi kamar a razane yasashi riketa kamar yanda ta rikeshi, "Menene...?" Itace tambayar da yayi mata,cikin razani ta nuna masa Aryan jikinta na rawa, "Wani abune a karkashin Aryan" Sakinta yayi ya nufi Aryan, shima saida abin yaso tsoratashi domin wata sab'a ce daga jikin Aryan din tafita doguwa sambel kamar muciji bakikkkirin da ita,karasa cire masa sabar yayi yafita aransa yana tunanin wato duk wanda yayiwa Aryan wannan abun da niyyar kasheshi watakila yayi kuma sai Allah bai lamunce masa ba, Ita kam duk tsoro ya isheta sai sannu take yiwa Aryan,bayan tagama yimasa brush ta zubo masa kindirmo cikin cup ta hada masa da maganin da Abba yace ta rinka hadawa da nono tana bashi da sassafe kafin yaci komai saida ya shanye sannan tafita ta nufi kan dining domin hadawa su Abba breakfast tana tafe tana murmushi sakamakon tuno abinda yafaru dazu da tayi, rikon da mutumin nan yayi mata ya tsaya mata arai,hannunsa masu masifar taushi da laushi kamar auduga. Ita kadai take ta sakin murmushi har tasamu ta gama jera musu breakfast din saman babban faranti, Sama ta hau ta nufi sashen Khalil,kamar jiya suna zaune shida Abba sai hira suke sha fuskokinsu dauke da fara'a, Tsugunnawa tayi ta fara gaida Abba sannan ta gaishe da Khalil wanda hankalinsa ke kan wayarshi yana turawa secretary dinshi na office sako, Dan shiru tayi tana sauraren tattaunawarsu da Abba wadda bata shafeta ba su ta shafa domin bata ma gane kan zancen nasu ba, da gefen ido take satar kallon Khalil wanda ke sanye cikin farin yadi mai laushi wato tissue amma kai daga gani kasan naira tayi kuka domin yanayin yadin ma daban yake, "Uwata tashi maza kema kije ki karya sai ki dawo muyi sallama saboda tafiya zanyi..." Idanuwanta narai narai ta mike tafita daga khalil har Abba binta sukayi da kallo bakar body hug ce ajikinta sai purple din skirt wacce ta baje daga kasa, Tana fita wurinsu umma ta wuce wadanda ke dakin Aryan can takai musu kayan karyawar suka ci domin hajiya ita ba ruwanta duk da cewa tana dan kunyar Hanan din, Suna zaune su umma nata hira ita kuma ta na shirya Aryan wanda tayiwa wanka kuma dayake yau jikin nasa da sauki da kansa ya taka har zuwa cikin bathroom, Wayar landline dake ajiye gefen gadon Aryan ce tafara rurin neman agaji, Hanan ce ta dauka tana mamakin to ko waye kuma, shiru tayi batace komai ba caan taji muryar Khalil, "Zo abbanki na kiranki....." "Tohm ina zuwa.." Baice komai ba yakatse wayar, hanzartawa tayi ta karasa shirya Aryan sannan ta fita, Zaune ta samesu shida abbanta saman kujera suna yin magana amma zuwanta yasa suka bar maganar abba ya fuskanceta yana murmushi, "Uwata ni zanje inkoma sai ayita hakuri da rayuwa kinji...., Ayita hakuri da duk halin da aka samu kai domin rayuwar gaba dayanta hakuri ce kuma kici gaba da yiwa mijinki biyayya banda sabawa umarninsa,kamar yanda na fada miki abaya ban yarda ki saba masa ba mutukar idan umarnin nasa ba shari'a ya sabawa ba...." Tuni har kwalla ta ciko idanuwan Hanan tun bayan da Abba yasoma yimata wadannan nasihohin, "Toh Abba insha Allah zanbi umarninka kuma zan kiyaye su...." "To Allah yayi miki albarka, Allah yabaki zuri'a kema wadanda zasu yimiki ni zanje inkoma....". Juyawa yayi ga Khalil wanda ke zaune ya tallafe kumatunsa da hannunshi guda daya dayan kuma yana lallatsa wayarshi ba komai kuma yake yiba sai game irin games din da Aryan ke yi idan ya karbi wayarshi,ahaka sai kace ba yajin abinda suke fada amma kuma yana sauraronsu sarai, "To kai moddibo ni zanje inkoma fa,bako zaiyi halinsa" Kashe wayar yayi sannan ya kalli Abban Hanan wanda ke kokarin mikewa tsaye, "Ba zaka sake kwana ba,ai mu bamu gaji dakai ba tukunna" "Duk da haka gara naje na karasa ai idan nace zan zauna har sai lokacin da zaku gaji dani to ai magana ta baci moddibo" "To muje kaga Aryan sai mu wuce...." Hanan na jinsu kuma tunda taga abba yamike tafara sharar hawaye kamar wata karamar yarinya,cikin bedroom dinsa yawuce shi kuma Abba yayi hanyar fita,tana nan zaune tana hawaye sai gashi yafito rike da hularshi a hannunshi,ganinta tsaye tana kuka kuma bata fita ba yazo zai wuce, "Ko zaki bishi ne?" Shine abinda taji yace kuma bai jira amsarta ba yayi waje abunshi. Itama bin bayanshi tayi abunka da dogo kamin ta fito har yayi mata nisa,a dakin Aryan ta iskesu Abba nayiwa Aryan wasa ya kama hannunsa yana yimusu sallama ita kam har lokacin kuka take yi,akan idonta Abba yayi musu sallama yatafi,yanzu inbanda aure mai zai rabata da abbanta amma gashi yazo yatafi yabarta, Tunda Khalil yafita bata kara samun damar ganinsa ba domin duk da yana cikin gidan amma baya ganuwa saboda bakin da yaketa faman yi agida,su kansu cikin gidan kullum cikin baki suke yan dubiya dayawa Hanan ba saninsu tayi ba sai su umma ne da hajiya ke yimata bayanin ko su waye,yan makarantar su Aryan ma sunzo sun dubashi daga students har malaman nasu duka. Yau ma haka suka tashi da bakin daga wadannan sun tafi wasu zasu zo, Abba Khalid ne yau kuma yazo da iyalansa da matarsa Muneerat da yaransa guda biyu Nawwar da Nainah,yau kam Hanan taga su Nawwar din da Aryan kullum ke maganar su kuma take ganinsu a hoto tare dashi,suma yaran kyawawa ne kamar ba yaran hausawa ba koda yake maman nasu kamar irin shuwah shuwah dinnan take sai dai bata da sakin jiki da saurin sabo dan ko magana kayi mata sai dai tayi murmushi ita dai Hanan haka ta sauketa tana ta nan nan dasu shi kuwa Aryan ganinsu Nawwar ai tuni yasake warewa dan har yajasu dakin kayan wasanshi suna can suna fama. Bayan sallar la'asar sun gama lunch kenan ita da Muneerat adakinta ta kwaso kayan zata kai kasa tahango Khalid da Khalil awurinsu Aryan wadanda suka fito da kekunan Aryan suna yi acikin falon, Khalid na fadin, "A'a lallai sauki yasamu,marar lafiyar nake gani akan keke?" "Ai nafada maka da kunyi zamanku yasamu lafiya fa..." Khalil yabashi amsa, "A'a sai munzo mun ganshi ai mun jima bamu ganshi ba dama..." Hanan karasawa wurinsu tayi ita yanzu ne ma taga Khalil amma yau koda wasa bata ganshi ba inbanda yanzu, kamar kullum yana sanye da farar shadda shi kam da alama yana son fararen kaya koda yake farin abu dama na masu tsafta ne dan kazami bai isa ya saba yanzun nan sai aganeshi,dan dukawa tayi ta gaida Khalid wanda ya riko hannun Aryan yana tambayar shi yajiki,dan juyowa yayi yana amsa gaisuwar tata, "Lafiya lau madam,ya hakurin zama da wannan sarkin yawon?ki rinka bashi query idan yaki zama agida..." Khalid yafada cikin barkwanci,ita dai shiru tayi ta dan saci kallon Kahlil wanda kamar bai san ma abinda suke fada ba yana tsaye ya dauki Nainah yana tambayar ta wai zatazo hutu suyi wasa da Aryan? "Ya kuma jikin Aryan? Naga ma ai yasamu sauki to Allah yakara masa lafiya" Sai lokacin ta amsa da "Jiki ai yayi sauki,amin ya Allah,mun gode madallah" Juyawa tayi ta koma sama wurin Muneerat duk da ba wata hira zasuyi ba babu jimawa saiga su Aryan sunzo suna kiranta wai tazo inji Abba zasu tafi kar suyi dare ahanya,rasa abinda zata bawa Muneerat tayi sai kawai ta diddibar mata irin humra dinta ta aure acikin kwalabe madaidaita, A babban falon kasa ta iskesu suna yin sallama dasu hajiya sannan ga kayan dubiya nan anata shigowa dasu wanda Khalid din yakawo kwalayen kayan ciye ciye daban daban da katan katan din lemuka jibgi guda,hannu Khalil yasa a aljihu yaciro rafar kudi yan dubu dubu guda biyu ya mikawa su Nawwar wai susha sweet shima Khalid din duk uban wannan kayan da yakawo sai da yabaiwa Aryan kudi wai yasai alawa bayan gata nan yakawo kaya guda, sallama suka yimusu suka tafi kuma tare suka fita da Khalil din........✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:09 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *24* ***Tun bayan tafiyar su Khalid Hanan bata kara saka Khalil a idonta ba sai washe gari wannan dinma yana kokarin fita ne yashiga wurinsu hajiya ya gaida su daga nan yawuce office wai yana da meeting din gaggawa da shugabnnin wata k'ungiyar matasa, Hanan na dakin zaune itada Aryan suna cin plantain yashigo wanda tun kafin ya karaso kamshinsa na no 1 yariga shi zuwa, "Mutumin nan dan gayu ne na ajin karshe" Hanan tafada acikin zuciyarta domin yayi kyau ba karya cikin farin lallausan yadin dake sanye ajikinsa harda hula amma babu babbar riga ajikinsa,zama yayi suka gaisa dasu hajiya sannan ya mikawa Aryan hannu suka gaisa yana amsa gaisuwar Hanan wacce ke gaisheshi kuma dama gaisuwar bata wuce guda biyu daga ina wuni lafiya shikenan, Bai jima ba adakin yafita,itama hajiya tun aranar tafara Shirin tafiya domin jikin Aryan yayi sauki sosai kuma sannu ahankali duk farinsa da kamanninsa sun fara dawowa har wata yar kiba yafara yi saboda zaman wuri daya sannan ga kulawa da yake samu daga Hanan dasu umma har kumatu yafara yi, A kowacce rana Hanan cikin tunanin Khalil take ita kanta tana mamakin yanda tafara damuwa dashi har haka bayan shikuma ba ta ita yakeba domin babu ruwanshi da ita ko maganar shi atakaice take sau da dama idan yana gida suna tare dasu umma sai dai su,su umman suyi ta hirarsu shikuma yayi shiru yana jinsu sai ta kama yake saka baki. *** Shawarar muhibba sumayya ta dauka duk da tana son mujahid amma haka ta daure tafara shareshi,ko sun hadu a kitchen ko falo ko compound din gidan yi take yi kamar bata sanshi ba ko bata ganshi ba sai takai makura sannan suke gaisawa gaba daya tayi watsi dashi duk da wani lokacin har kuka takeyi saboda irin yanayin da ta samu kanta na son maso wani. Shi kuma abun duniya ne yataru ya dameshi sakamakon daina ganin text din Hanan da yayi,to ko lafiya? Kodai mijinta yaga irin sakonnin da take turo masa kullum ya kwace wayar tata? Wadannan tambayoyin kullum su yake yiwa kansa gashi yasaba da ganin massage din nata shiyasa yakasa samun nutsuwa yana jin kamar wani abune marar dadi ya gifta ko kuma ya faru da ita,kullum cikin duba wayarsa yake waiko zaiga sakonta idan kuwa yaji k'arar shigowar text jikinsa har rawa yake yi atunaninshi ko itace sai ya duba sai yaga sabanin haka nanfa abun yayita damunsa daga karshe ya yanke shawarar kiranta duk da yasan hakan haramun ne amma haka yarufe ido ya kirata,har wayar tayi ta katse bata dauka ba nan yasake kira nan dinma no answer saida yakira sau biyar sannan ya hakura ya hada Kai da gwiwa ya rafka uban tagumi. *** Bayan Sati Biyu Jikin Aryan yayi kyau kusanma za a iya cewa yagama warkewa gaba daya dan har ana maganar zai fara zuwa makaranta domin ana gab da fara exams,ganin yasamu lafiya yasa hajiya komawa gombe itama dama shi Zaid yajima da komawa tun lokacin da Aryan din yafara samun lafiya,ai Hanan ji tayi kamar kada hajiya ta tafi saboda tana mutukar jin dadin zama da ita babu tsangwama babu sa Ido da takurawa irin na wasu surukan,ita abubuwa da yawa ma hajiyan ke matsanta mata akai dan ko abinci ta rinka cewa taje ta zauna taci abinci tabar hidima dasu haka ita kam bazata fadi kiyayyar uwar mijiba duk da zaman nasu baiyi nisaba. Tunda hajiya ta tafi kuma yarage sai su kadai da umma shima Khalil ba ganinsa akeyi ba domin ankoma gidan jiya dan harma yasake fallawa yakoma Florence wato k'asar italy dan dama bawai yagama abinda yaje yi bane lalurar Aryan ce ta dawo dashi amma koda yaushe yanzun ma suna makale awaya, Ita kam Hanan tana cikin wani hali domin ta samu kanta dumu dumu da tunanin Khalil wanda ke neman tarwatsa kwakwalwarta kullum ita kenan cikin tunani tarasa meke damunta gashi shi bama ya nan kuma koda ace yana nan dinma ba ganinsa take samun yiba sosai sai antaki sa'a,ranar da mujahid yafara kiranta tana gani taki dauka saboda kamar yadda yataba fada mata akan tayiwa iyayenta biyayya ta zauna da mijinta lafiya to ayanzu ta daura aniyar yin hakan idan kuwa hakane to babu bukatar sufara kiran juna awaya yanzu. Lokuta da dama tana jin Aryan na yin waya da Khalil amma bata tunanin ya t'aba koda tambayar ta amma fa kullum kuma koda yaushe zaka samesu suna video call da d'ansa,ranar da su Aryan suka fara exams ranar yadawo da daddare yasauka a Abuja su PA sukaje suka daukoshi,tana son taje tayi masa sannu da zuwa domin idonta biyu yadawo amma bata son yin abinda ajinta zai zube a idonshi, shiyasa itama ta shareshi kamar yanda shima ya shareta. Washe gari da sassafe suna yin breakfast zasu tafi school sai gashi ya sauko sanye da kananan kaya kuma da alama dasu yayi bacci riga ce jersey fara sol da dogon wando shima fari mai sulbi sunkuyar da kanta tayi aranta tana tunanin wai Wadanne kayane suka fi karbar wannan bawan Allahn? Duk wadanda yasa kyau suke yimasa daga manyan har kananan,bata farga ba taji maganarshi akusa dasu yana yiwa Aryan magana da harshen turanci wai ko bai san yadawo bane yaga bai ganshi yaje bedroom dinshi ba da safe, Makalkaleshi Aryan yayi yana murna dagashi yayi cancak daga kan kujerar da yake zaune akai ya rungumeshi yana kissing dinshi, "Uncle ka siyo min abunda nace kasiyo min?" "Nasiyo maka Abba na,ai dole insiyo maka,kaje school ka dawo zaka ganshi" "Thank you Papa..." "You are always welcome lovely son" Saida tajira suka gama sannan ta gaidashi,kamar kullum adan ciki ciki ya amsa sannan yawuce yafita daga falon yayi waje,ita kanta tsarin rayuwarshi na burgeta saboda baida girman kai irin na wasu masu kudin sannan bai dauki rayuwarsa da zafiba dan ko yanzu da yafita takalmin roba slippers ne akafarshi amma fa yayi kyau yafito sosai ko dan jiya yadawo daga waje ne oho amma yayi kyau, Suna fita suka shiga mota kasancewar daga bakin kofa ake ajiye musu motar shima Khalil din haka ne anan ake ajiye masa motarshi yana fitowa sai dai yashiga,daga cikin mota ta hangoshi caan nesa da su da mutane sun yanyameshi ko su wanene oho,kwalla taji ta ciko mata ido tayi saurin gogewa dan kada Aryan yagani. Bayan dawowarsu daga makaranta tana kwance adakinta tana duba scrip din yara tagaji ta ajiyesu gefe ta kwanta tana hutawa Aryan yashigo da gudu hannunshi rike da wata kyakkyawar yar karamar laptop irin wacce ake siyawa students, ash colour ce mai mutukar kyau ashe dama shine sakon da Aryan ke tambayar Khalil da safe,karba tayi tana fadin, "Woww.... Yaron babanshi yasamu sabuwar laptop,inye,to maza tafi library kaci gaba da karatu sai anjima sai kafito ka huta kayi game na 15 minutes" Da gudu yafita ita kuma tashi zaune tayi ta bude laptop din tana dubawa babu komai aciki sai games kala kala da cartoons sai kuma pictures, pictures din tafara bi daya bayan daya tana gani duka na Aryan da Khalil ne tun yana rarrafe gasu nan yayiyyi musu selfie,shagala tayi da kallon hotunan domin mafi yawa daga ciki tare suke kuma sunyi shiga iri daya wato dai atakaice anko yake yi musu dan ko kananan kaya ne yasa sai taga shima Aryan din irinsu yasaka masa, tajima akan wani hotonsu duk sunsha bakaken suit da blue din t shirt aciki sun daura necktie rike da hannun juna awani katafaren wurin shakatawa wanda bata san kowacce k'asa ce ba amma duk fuskokinsu cike da fara'a dan har hakoran Aryan sun bayyana wanda ya daga kansa yana kallon uban, kowannensu idanuwanshi sanye da bakin gilashi wanda yasake kara musu kyau, "Fatabarakallahu ahsanul kaliqin....." Tafada tana sake zooming din hoton,tana zuwa kan na gaba taga ashe na baya ba wani kyau yayiba akan na yanzu domin shi na yanzu bakaken wanduna suka saka da jar t shirt sunsa p cap suna zaune akan wata gada cikin babban birnin k'asar ingila dan gashi nan akasan hoton anrubuta London Vive,haka tayita rudewa tana kasa banbance wacce shiga ce tafi yimusu kyau domin wani shigar manyan kaya sukayi iri daya har hula wani kuma jallabiya ma suka saka iri daya da yar karamar hularta amma yawanci a saudiyya ne suka yi wadannan shigar, "Aryan dan gata" Ta furta hakan acan kasan makoshinta sakamakon ganin pic din birthday dinshi na cika shekara biyar da tayi,shima ankon sukayi da uban kowa yasha bakin jeans da maroon din riga suna bawa juna cake abaki duk suna yin dariya.................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:09 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *25* ***Har Aryan yadawo bata samu zarafin gama kallon wannan pictures dinba wadanda ke shirin zautar da ita hakika sai yaune ta sake tabbatarwa da kanta cewa Khalil dan kwalisa ne kuma cikakken dan gayu sannan idan har ba fada maka akayiba wallahi baza ka taba cewa Aryan danshi ne na cikinsa ba duk da suna mutukar kama da Aryan din amma fuskar Khalil babu girma atare da ita yarinta ce fal kwance akai, Jin Aryan yafada kanta yasata ajiye laptop din tana dubanshi, "Wai har kayi me cutie?" "Mommy har nagama karatun" Kanshi ta shafa sannan tace, "A'a cutie baka gama ba ka dai fito break ko?" Kai ya daga mata yana kaiwa babban dan yatsanshi baki hannun ta buge saboda yanzu dabi'ar da ya ke neman koya kenan shan hannu tun bayan rashin lafiyarsa amma da ba haka yake ba, "Cutie ba na hanaka shan hannu ba? Ka daina kaji yaron kirki..." Kai ya daga mata yana jan hannunta,tashi tayi tabishi suka sauka k'asa ta kofar baya suka bi suka fita sune har garden gashi garin da alamar hadari kuma yagama haduwa, Acan ruwan ya iskesu,da gudu suka shigo ciki ita kam cikin ruwan ta shiga ta hanyar shiga cikin wani dan karamin fili dake tsakanin part din Khalil da nata,filine fetal an shuka flowers kala kala awurin amma babu kasa gaba daya rufe yake da interlock an kawatashi yadda yakamata, Sosai take jin dadin ruwan yanda yake sauka ajikinta, Aryan ne shima yashigo yana ta tsalle acikin ruwan yana jikasu, Shigowar shi kenan cikin sashensa yashiga bedroom dinshi yasoma rage kayan jikinsa farar t shirt da bakin dogon wando yasaka yana son shiga yayi wanka kamar ance ya kalli window yanufi gaban windown yana shirin rufewa, Hanan ya hango a kasa ita da Aryan cikin ruwa suna ta wasan banza atoh wasan banza mana tunda wasan ruwa suke yi, wannan yarinyar bata da hankali yanzu da taja masa yaro takaishi cikin ruwa idan mura ta kamashi ko zazzabi fa? Da sauri yabar wurin window din yafita daga dakin ya sauka zuwa kasa a hanzarce, Sam Hanan bata san cewa yadawo gidan ba saboda lokacin dawowarshi baiyi ba dan sai dare kuma darenma bawai na kusa ba, "Aryan..... what are you doing there?" Dukkansu juyawa sukayi wurin da suka jiyo maganar shi,shi dinma tsaye yayi yana kallonsu cike da takaici dan gaba daya sun jike jagaf,kunya da tsoro taji sun rufeta lokaci guda,shi kam kama kunnen Aryan yayi guda daya yana yimasa fada, "Idan nasake ganin kayi wasan ruwa nida kaine..." Juyawa yayi ga Hanan, "Nan gaba idan zakiyi wasan ruwanki kiyi ke daya karki sake kai min yaro cikin ruwa..." Daga haka yahaura sama yana cewa Aryan yaje umma ta sauya masa kayan jikinsa,jan hannunsa Hanan tayi suka je dakinsa ta sauya masa kaya bayan ta goggoge masa jikinsa,kayan sanyi ta saka masa sannan itama tawuce d'akinta taje ta cire nata kayan ta sauya wasu,tun daga wannan lokacin bata sake ganinshi ba shima haka,duk abin duniya ya taru ya isheta yayi mata yawa,haka dai taci gaba da daurewa tana yin al'amuranta amma can kasan ranta akwai damuwa atattare da ita. Kusan kullum sai sun gaisa da yan gidansu musamman ma mamaye haka itama anty salaha jifa jifa suna gaisaw musamman ma ta chat. A kwana atashi har su Aryan sun gama exams dinsu kuma ranar Friday ake sa ran yin hutu, kasancewar hutun azumi za ayi Khalil yana da burin kaisu gombe sai suyi azumi da salla acan shikam duk Ramadan umarah suke tafiya shida Aryan sai ankusa salla suke dawowa wani time dinma sai bayan sallar sannan suke dawowa, Ranar Friday akayi hutu bayan anrabawa yara results dinsu,tun a makaranta Hanan taga result din Aryan kuma tayi farin ciki sosai domin ya dauki first position kamar yanda yasaba, Khalil kuwa da yagani farin doki yabada aka siyo masa domin Aryan na masifar son doki tun yana dan mitsitsi. Tunda akayi hutu kuma sai zaman gida babu wurin zuwa duk zaman nan yabi ya ishi Hanan,kullum kai kenan agida babu fita sai hira da umma da koyar da Aryan dan dama tun bayan warkewarsa take koya masa littafin (hisnul ad'fal) wato littafi mai dauke da addu'o'in yara wadanda zasu rinka yi dan samun kariya, Sati daya da yin hutun taga text din Khalil wai ta shirya zasu tafi gombe kuma acan zasu yi azumi,wani dadi taji ya lullube ta domin tasan zaman gombe zaifi na Abuja dadi saboda can akwai mutane ba kamar nan ba,duk wani abu wanda tasan zata bukata ta dauki abinta haka shima Aryan ta shirya masa nasa kayan,ranar asabar da daddare bayan Khalil yadawo daga office suka dauki hanyar gombe, Aryan ne agaba sai shida ita abaya ita kuma umma motarta daban,tunda Hanan ta shiga cikin motar tayi shiru ta kasa ko kwakkwaran motsi amma fa motar ta tafi da ita domin sanyin AC kadai ke shigarta gashi hatta kujerar motar wani azababben laushi gareta wannan motar ita dai aganinta bata da maraba da jirgin sama kawai dan dai shi asama yake ne ita kuma a kasa,tv taga ya kunna wacce ke cikin motar,daga shi har ita babu mai cewa koda uffan sai dai yana ta amsa wayoyi lokaci zuwa lokaci,wani abu da yasake burgeta shine duk inda sukaje check point ba a tsayar dasu da sunzo zasu wuce shiyasa tafiyar tasu tayi sauri gaskiya masu kudi suna cikin ni'ima domin suna fantamawa son ransu ashe shiyasa Khalil bai jin wahalar tafiya kullum yana bisa hanya, Suna shiga garin gombe duk da cewa dare ne amma mutane sai faman daga musu hannu suke gashi dai na waje ba ganin na ciki yake ba tun daga nan Hanan tasan jama'ar garin na sonsa kuma suna yinsa domin masu babura rakasu suka yi har kofar gida,ita kam ta bude ido tana ganin yanda garin yake domin wannan shine ganinta na farko dan lokacin da aka kawota tana amarya babu abinda ta samu damar gani shiyasa yau take ta baza idanuwa tana kallo. Suna shiga cikin gidan securities suka fito suka bubbude musu kofa ita abinma kusan mamaki yake bata wai yau itace cikin wannan daular ana girmamata kamar wata matar governor,kai tsaye cikin gidan suka shiga tare da umma da Aryan, Duk yanmatan gidan suna tare da hajiya ana sauraren zuwansu ganin Aryan dake gaba yasa yanmatan rige rigen zuwa daukarshi shi kuma sai ya gudu ya haye kan cinyar hajiya yana boye fuskarshi cikin jikinta, "Ja'iri ashe dai baka manta dokaka da kasar da suka taba yiba,sarkin wayo" Inji hajiya, Kowa dake wurin dariya yayi,a kasa Hanan ta zauna tana gaida hajiya,duk da hajiyan tace ta koma kan kujera ta zauna amma taki anan taci gaba da zama zuwa can aka fara shigo musu da kayayyakin su wanda suka zo dashi, ita kuwa Hanan tuni ancika mata gabanta da kayan cima iri iri hajiya tana ta cewa taci abinci taje ta huta, abincin suka ci ita da Aryan sannan suka wuce dakin dake ciki wanda ko lokacin da tana amarya anan aka sauketa,wanka tayiwa Aryan tayi masa shirin bacci ya kwanta sannan itama taje tayi tazo ta kwanta ta san idan ba wani iko na Allah ba sai Khalil yashigo dakin nan komai dare yaga Aryan saboda tun da sukazo basu kara sakashi a idanuwansu ba yana can tare da baki tunda baya rabuwa dasu. Kamar Hanan ta sani kuwa domin tun bayan zuwansu Khalil salla kawai yasamu yayi daga nan yaketa ganawa da baki bai samu kansa ba sai karfe dayan dare saura yan mintuna gashi cikinsa inbanda yunwa babu abinda yake ji,kuma dadin dadawa ma kofa gaisawa da hajiya basuyi ba, Tunda yaji part din hajiya shiru yasan kowa yayi bacci agidan amma yana shiga ita ya sameta ido biyu tana zaman jiran zuwanshi yaci abinci kuma su gaisa,kansa babu hula ya zauna nan kasa inda Hanan ta zauna dazu, "Hajiya mun sameku lafiya?" "Lafiya lau Khalil ya fama da jama'a? Ga abinci zuba kaci" "Hajiya ai fama da jama'a kam sai godiyar Allah wallahi rabona da abinci tun wani ruwan tea da na sha da safe a office da meatballs guda biyu shikenan,ko gidana sai dazu da zamu taho nasamu naje daga can muka iyo nan.... Kai rayuwar nan tana da wahala babu komai acikinta face gwagwarmaya da fafutuka astagfirullah" "To ya za ayi Khalil sai dai fatan lafiya da taimakon ubangiji,nauyine Allah yariga da ya dora maka kana yaronka dakai sai dai fatan Allah yabaka ikon saukeshi" "Amin hajiya,nauyifa mutum da kuruciyarshi da komai wallahi,duk cikin ministocin nan nine yaro wasunsu ma sun kusa haifata ni wallahi banma san ta yadda akayi na zama ba...." Dariya hajiya tayi ta dan kishingida ajikin kujera, "To inbanda abinka Khalil shi hukuncin Allah ai ba ruwansa da girma ko shekaru,haka Allah ya tsara maka, Allah dai yabaka ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyanka" "Amin hajiya,shi wannan yayi bacci ko?" "Ehh Aryan ba,yayi bacci ai tunda jimawa,kuma nace maimakon ka kai matar taka sashenka shikenan sai akawota nan?" Dan shiru yayi ya shafi kansa sannan ya ce, "Hajiya wanne bangaren nawa kuma bayan daki dayane aciki,muje muyi zaman takura haka kawai...." "Idanma babu dakin ba matarka bace? Ko zaman gaban takura zakuyi kuyi mana ai canne yafi dacewa da ita,kuma kasan ai daki dayanne amma ka daukosu kuka taho" "Gaskiya hajiya daki daya yayi mana kadan" "To ba sai kasake gina muku waniba tunda kana da halin yi amma dai babu tsari ace kana can matarka tana nan,yanzu idan kana bukatar tayi maka wani abu sai kazo kana tasota daga nan tana tafiya can?" "Hajiya ni kwana nawa ma zanyi agarinne? Dududu kwana hudu fa zanyi ko biyar mutafi umarah nida Aryan...." "Kaida Aryan? Ita kuma matar taka fa? Wa zaka barwa ita?" Shiru yayi yana tunanin abinda yadace yafada wanda hajiya ba zata yimasa fada ba,ruwa ya dan kurba sannan yace, "Ai hajiya bana visa dince tayi wahala kuma da har ita naso hadawa amma abun ya faskara mukuma ai kinga permanent Visa garemu shiyasa..." "Ai shikenan amma gaskiya banji dadin tafiya kubarta ita kuma ananba da zakuyi gaskiya...." "Hajiya kiyi mana addu'ar dai Allah yasa hakanne yafi zama alkhairi" "To amin, Allah yadawo daku lafiya, Allah yatsareka ya kareka ya tsare maka dukiyarka da zuri'arka, Allah ya rabaka da mugun ji da mugun gani ya shiga lamarinka akoda yaushe...." "Amin hajiya..." Saida yakai wurin karfe 2 na dare shida hajiya sannan yatashi yafita ya nufi bangarensa aransa yana tunanin ai kamar fa tunda yazo baiga Zaid ba anya kuwa yana nan? Kai duk yanda akayi zaid baya garin nan dan kuwa da yana nan da yaganshi. Duk jikinsa a gajiye haka ya lallaba ya daure yayi wanka yasaka kayan bacci yahaye gado yana kallon agogo,karfe 3 saura na dare,yanzu hajiya da take cewa ya hada daki da yarinyar can ai da takurashi za ayi haka kawai abanza shi harma mantawa yake yi da wai ita matarsa ce kawai abinda yasani ya kawowa Aryan friend wanda zata rinka debe masa kewa. Washe gari ya dan samu zarafin komawa baccin safe, Aryan kuwa tunda yatashi Hanan ta shiryashi cikin kananan kaya bakar t shirt ta polo da blue din jeans tasa masa combos shima baki bata sake ganinsa ba dan wurin hajiya yaje ta can ya gudu wurin babansa dan shine ma ya tashi Khalil din, rungumeshi yayi yana shafa sumar kanshi, "Waye ya yi maka wanka?" "Momy ce.." "Uhmm dan gatan mommy..." "Mommy tana sona..." Murmushi Khalil yayi ya tashi zaune yana daukar wayarshi domin kira yashigo, "Hajiya ina kwana...... lafiya lau....gashi muna tare dashi ai......ehhhh....kokon dai hajiya.....to shikenan sai na shigo" Daga haka ya katse wayar yabawa Aryan shikuma yashiga bathroom domin yin wanka,har yafito ya shirya Aryan na kwance kan gadon yana ta faman matse matse awayar kamar tashi cemasa yayi kar dai ya yarda yayi masa deleting din wani abu garin wannan matse matsen nasa,shiryawa Khalil din yayi cikin wata farar shadda yasha turare,ba dan hajiya tace yajira akawo masa breakfast ba da fita zaiyi. Hanan tunda ta gama shiryawa tayi zamanta adaki saida hajiya ta turo mufida kiranta sannan tafita,wata dark purple din atamfa ce ajikinta doguwar riga tasha turare mai sanyin kamshi,gaida hajiya tayi sannan hajiya ta nuna mata breakfast din Khalil wai idan tagama karyawa shima taje ta kai masa mufida ta rakata ko zarah,tea ta hada ta sha ta danci awarar da aka soya da kwai sannan ta tashi suka fita ita da zarah dauke da kayan breakfast din Khalil, Part din nashi dan karami ne bawani babba ba saiko kayan alatu da yasha,suna zaune falo shida Aryan wanda keta waya dasu Nawwar awayar Khalil daga jin Khalid ya kirashi suna magana shikenan yakafa rigimar sai anbashi ana bashi kuma suma su Nawwar din suka karbe kan wayar tun dazu suketa hirar da taki karewa domin sai labari suke ta bawa juna,durkusawa zarah tayi ta gaidashi sannan ta ajiye kayan dake hannunta tafita,itama Hanan din gaisheshi tayi suka gaisa kamar yanda aka saba ina kwana lafiya shikenan,ta mike zata fita taji yace, "Zo nan" Dawowa tayi ta zauna amma baice da ita komai ba saima kayan breakfast dinshi da yajawo yabude ya tsiyayi koko a cup sannan ya bude flask din soyayyiyar awara da kwai ya diba a plate ya zuba vegetables sos akai yasa spoon yafara ci,duk sai taji ta takura domin basu taba zama haka su biyu ba awuri duk da Aryan yana wurin, Ganin wayar Aryan ba mai karewa bace yasa Khalil kwace wayar ya kashe yace maza ya zauna suci abinci shi baya son cin abinci sai anyi masa dabara,yanzun ma saida dabarar shima yabashi yaci. Suna zaune shiru amma jifa jifa Aryan na yin surutunshi ahaka akayi knocking a jikin kofa, zaid ne amma ganinsu duka sai yakoma Khalil nata kiransa amma bai dawoba,ita dai duk da tana jin dadin zaman wurin amma ta kosa ta tafi domin zuciyarta kamar zata faso kirjinta tafito dan tsananin bugun da takeyi,saida suka gama sannan yace sutafi cikin gida ita da Aryan,shikuma yafita tun daga nan kuma ganinsa yayi mata wahala dan bata ganinsa sai kowacce safiya da zarar yafita kuma shikenan dan lokacin da yake shigowa da daddare tuni sun kwanta,ita kanta hajiya fadan da take yimasa kenan wai bata ga yana jan matarsa ajiki yana kiranta suna hira ba shi kuma sai cewa yayi wai ai duk sanda taje wurinshi da safe kai masa abinci suna tattaunawa. Kwanansu hudu da zuwa yace ashiryawa Aryan kayansa saboda zasu iya tafiya a kowanne lokaci, lokacin ana saka ran ganin watan Ramadan nan da kwanaki biyu zuwa uku,daren asubar da zasu tashi tana daki kwance har tayi shirin bacci hajiya ta aiko kiranta,koda taje hajiya cewa tayi wai ta je wurin Khalil ta kwana acan suyi sallama, innalillahi ita dai gashi ba damar tayi musu da hajiya gashi bata jin zata iya zuwa gareshi a wannan lokacin,jiki a mace ta tashi takoma dakin da ta sauka tafi minti goma tana tsaye tana kallon Aryan dake kwance yana bacci sannan ta dauki hijabi har kasa tasa ta fita rike da wayarta a hannu,gidan tamkar rana dan tsabar haske baka jin motsin kowa sai karar injin bada wutar lantarki da ke tashi,tana sake kusantar sashen nasa faduwar gabanta na karuwa jikinta na rawa ahaka taje,ta jima tsaye a bakin kofar falonshi tarasa ta yadda zata shiga ciki,dakyar tayi ta maza ta bude kofar ta sa kai tana jin numfashinta yana tsinkewa kamar zai fice gaba daya.....................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *26* ***Kasa daga kafarta tayi daga nan inda take tsaye bayan tashiga cikin falon nasa wanda kamshinsa ke kai komo acikinsa, Wuri ta samu ta zauna saman kujera tana kallon kowacce kusurwa da lungu dake cikin falon wanda yake dan madaidaici sai dai kuma antsarashi yadda yadace dan yayi mata kyau kamar irin dan bangaren nan na ango da amarya auren saurayi da budurwa, ango da yar amaryar sa ya ishesu rayuwa kafin su tara 'yaya,komai na ciki milk ne and coffee colour gashi tsaf tsaf babu datti babu kura yayi kyau gwanin ban sha'awa. Idonta ne yakai kan wayar Khalil dake kan wani center table na glass dake can gefe daya take ta sake jin faduwar gabanta ta karu da kaso tamanin cikin dari na wadda takeji dazu, Fitowarsa kenan daga wanka yasaka farar jersey mai ratsin blue agefe da gefenta sai wandon rigar shima fari amma dogone dan har ya rufe gwiwarshi,falo yafita domin dauko daya daga cikin wayarshi da ya ajiye acan,yana fitowa yaganta zaune ta tukunkune cikin hijabi ba dan yasan da zuwanta ba da babu abinda zai hana ya tsorata to dan dai hajiya ta sanar dashi ne dazun nan da yashigo tagama kora masa jawabin wai yakamata matarsa taje suyi sallama kuma yaji ko tana da wata damuwa, "Kowacce irin sallama hajiya take son muyi oho..." Yafada acikin ransa yana kokarin daukar wayarshi,cikin sanyin murya yaji tana gaisheshi nan ya amsa kamar koda yaushe cikin rashin son doguwar magana,ita dai tun kallon farko da tayi masa bata sake kallonshi ba domin yau yasake yimata kwarjini fiye da sauran ranakun baya gashi kayan jikinsa sun dan kamashi. Wuri shima yasamu ya zauna afalon yadora kafa daya akan daya yana duba tulin sakonnin dake cikin wayar wadanda aka turo masa kuma mafi yawa ba sanin wadanda suka turo yayi ba, Hanan gyangyadi tafara domin tuni 12 ta dan gota ita kuma ba saba dogon zama tayiba karkarinta takai 11 wannan dinma sai da dalili amma wani lokacin 10 tayi baccinta saboda fitar sassafe. Lura yayi da gyangyadin da take yi dan haka yayi mata magana cikin muryar sa mai cike da sanyi,taushi da kuma gardi, "Shiga ciki ki kwanta..." Taji yafada amma bawai dan yasoba domin harga Allah shifa takurashi akayi da aka turo masa yarinyar nan,yanzu dole sai taje ta hau masa kan gadonsa shikuma abarshi yayi kwanan takura a falo, Kasancewar itama bawai awani sake take dashi ba yasata girgiza kanta tace,"A'a nanma ya isa" Iya nan din da ta furta kawai ya iyaji dan haka yaci gaba da abinda yake tsawon mintuna goma yagama yatashi yawuce cikin bedroom dinshi harda rofo kofa,saman gadonshi ya haye yai kwanciyar sa bayan ya kara karfin na'urar sanyaya daki,itama Hanan anan ta bingire kan 3 sitter bacci yayi gaba da ita,ba ita ta tashi ba sai asubah kasancewar tasaba tashi yau dinma lokacin salla nayi ta tashi duk jikinta ciwo yake yimata saboda baccin da tayi a takure shikuwa wuyanta ya kage bata ko iya juyashi Sosai sakamakon pillow da tayi da hannun kujera,fitowarshi taji daga cikin daki,sanye yake da jallabiya kalar ruwan kasa hannunsa rike da casbaha,ganinta zaune alamar ta tashi yasashi wucewa yafita zuwa masallacin da ke cikin gidan,tana ganin haka itama taja jikinta tafice ta nufi bangaren hajiya sadaf sadaf kamar wata marar gaskiya,da sand'a ta shiga dakin da ta sauka tasamu Aryan yanata sharar baccinsa cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi tashiga toilet, brush tayi sannan tayi alwala tafito,nan inda tayi salla anan wani bacci mai shegen dadi yayi awon gaba da ita,cikin baccin ta soma wani mafarki da wata mata wai ita Hanan din tana rike da Aryan suna ta gudu cikin dokar daji ita kuma matar tana binsu wai ala dole sai ta kwace Aryan daga wurinta,gudu take cin karfinta har tazo wani bakin ruwa mai yawa ga kuma matar ta kusan cimmusu firgigit tayi ta tashi sakamakon tashinta da Aryan din ke yi,janshi tayi tana dudduba jikinsa domin taga ko lafiya yake gaba daya ta gama jikewa jagab da gumi,ganinshi tayi ras saima fararen hakoransa da yake washe mata yana nuna mata sabbin kaya yan kanti da hajiya tasaka masa, Window ta kalla nan taga rana har tafito sosai tayi mamakin irin baccin da tayi daga yar kwanciya, sauri sauri tayi wanka tafito ta shirya ta saka atamfa pink colour dinkin riga da skirt wadanda suka yimata caras cass,tana kokarin fesa turare zarah ta shigo cikin dakin rike da farantin abinci, "Anty ina kwana? Yau kin makara,ga breakfast dinki inji hajiya" Da fara'a itama ta juya ta kalli zarah wacce ke kokarin ajiye mata farantin akan rug din dake gaban gado, "Lafiya lau zarah,wallahi na makara ina kokarin fitowa ma da yanzu,bari to nafara karyawar" Fita zarah tayi tana murmushi ita kuma Hanan tayi sakare aranta tana fatan Allah yasa dai kar su hajiya su zargi wani abu akan makarar nan tata tunda jiya taje wajen Khalil. Aryan ta kira suka zauna tare suka karya da wainar shinkafa da miyar agushi sai kunun gyada da shinkafa da tea da bread ga kuma wainar kwai agefe,sai da suka koshi damm sannan tafita duk kunya ta cika mata ciki domin aganinta hajiya zata tsammaci dan taje wurin mijine shiyasa ta makara amma koda ta fita hajiya fuska asake kuma awashe ta karbi gaisuwarta har tana cemata umma barira ta tafi funakaye tace afada mata sai nan da sati biyu sannan zata dawo, Tana zaune tare dasu hajiya Khalil yashigo cikin ash din shadda yau ne kadai Hanan zata ce ta ganshi da wasu kaya sabanin farare tun daga ranar da ta fara ganinsa, "Hajiya zamuje mu wuce....Sai Allah yadawo damu" Taji yafada yana zama kujerer dake kusa da ta hajiya, "To mu'azzam Allah yadawo daku lafiya, Allah ya kiyaye hanya" Tashi hajiya tayi tabasu wuri wai ko zasu tattauna wani abu da matarsa, "Ina kwana?" Hanan ta fada tana wasa da yan yatsun hannunta kanta akasa, "Lafiya lau...." Daga haka bai kara cewa komai ba sai waya da taga ya daga yana magana cikin sanyin murya da rashin hayaniya, "Kana jina..... Na warewa PA dina komai awurinsa zaka karba,akwai kayan marayu yadina da shaddodi da atamfofi bandir dari biyar biyar na zawarawan da mazajensu suka rasu ma haka da tsoffi,sai kayan abinci shima shinkafa da hatsi da masara da sugar da man gyada shima kowanne guda dari biyar biyar akai musu a rarraba dan Allah.... Idan kuma akwai wani abu da kuke bukata kayi wa PA dina magana zai sanar dani komai...amin....Amin nagode" Saida ya gama wayar sannan ya juya ga Hanan wacce har lokacin kanta na kasa aranta tana jin dadin abinda taji Khalil din yayi wato taimakon marayu da marassa karfi acikin wata mai falala kuma gashi harda kayan salla gaskiya yayi kokari dole yarinka ganin budi cikin harkokinsa domin taimakawa marayu da yake yi, muryar sa tajiyo yana cemata, "Idan kina bukatar wani abu ki fadawa hajiya zata baki..." Ganin yamike yasa itama ta mike tana jijjiga kai, "Tom, Allah yadawo daku lafiya" "Amin" Kai tsaye dakin hajiya yashiga suka fito tare tana rike da Aryan, rungume ta Aryan yayi suka yi sallama sannan suka fita, itama bin sahun masu yimusu rakiya zuwa compound din gidan tayi tana rike da hannun Aryan,sai bayan da suka ga tafiyarsu sannan suka koma cikin gida kowannensu zuciyarshi cike da kewa musamman ma ita wacce tayi mugun sabo da Aryan. Kamar yanda ta tsammata hakance ta faru wato daren yau sai takasa bacci tunanin Khalil da gudan jininsa Aryan sune suka tsaya mata arai tana jin kamar tayi tsuntsuwa taje garesu, Haka tayita kewarsu cikin kwanakin har zuwa ranar da Aryan ya kirata lokacin kwanansu hudu da tafiya kuma ranar aka kai azumi na farko,sunsha hira sosai da Aryan da yake gwanin surutu ne, Haka rayuwa tayi ta tafiya idan tace acikin zaman da takeyi a gidansu Khalil wani yataba sab'a mata ko yayi mata ba daidai ba to tayi karya,kusan kullum suna gaisawa da yan gidansu ranar ma abbanta yake sanar da ita wai Khalil ya aika musu da kayan azumi da na salla ita dai batace komai ba domin rabonta dashi tun ranar da yatafi umarah sabanin d'ansa da kullum sai sun gaisa,hajiyarsa kuwa tana tattalinta kamar me kullum Cikin hidima da ita ake babu abinda take yi sai dai taci ta kwanta dinkin sallah kuwa kaya kala biyar hajiya ta bada aka dinko mata da mayafinsu da takalmi ko kadan hajiya bata yi la'akari da cewa wai anyi mata lefe mai uban yawa ba. Ana saura kwana biyu salla su zarah suka matsanta mata wai dole sai sunje gidan kunshi tare,ita wallahi a budget dinta babu wani maganar yin kunshi amma irin yanda suka bi suka takura mata yasata yarda zasuje din, Khalil tayiwa text cewa zata fita zataje gidan kunshi,kamar koda yaushe ok kawai yace mata hakan ya tabbatar mata da cewa kenan yabarta taje, Su hudu suka tafi sukaje akayi musu jan k'unshi mai hade da baki kuma tun safe suka bar gidan amma har la'asar suna gidan kunshin hajiya ajima kadan ta kira tace har yanzu ba agama ba saboda Hanan ce kadai keyin azumi acikinsu ranar su dukansu su ukun basa yi ita Sarah dama sam bata ma yin azumi saboda lalurarta ba mai cikakkiyar lafiya bace ita. Sai da aka kusan shan ruwa sannan suka baro gidan kunshin nan suna dawowa gida ana shan ruwa sai dai fa amma mai kunshin ta iya kwararriya ce sosai domin duk ta rangade musu kafafuwa da hannaye sai yanzu suka fahimci dalilin da yasa kunshinta keda tsada ashe ta iyane sosai,washe gari kuma kitso aka zo aka yimusu har gida mai kitson hajiya itama ta iya babu laifi, Bayan ansha ruwa an idar da sallar tarawih suna baje falon Hanan tana kwanciyar gajiya saboda azumin yau dinnan tajishi sosai bada wasa ba kamar bazata kai ba gashi wani abun al'ajabi azumin bana bata sha ko daya ba bata taba fashin shan azumi ba sai wannan karon ita wani lokacin ma azumi sai tasha sau biyu farkonshi da karshensa amma wannan karon bata shaba kwata kwata,babu ko dan kwali akanta hancinta yafara jiyo mata kamshinsa na turaren no 1 ai kuwa wannan turare yaci sunansa domin no 1 dinne wurin zama ajikin mutum dan yariga da ya zauna ajikinsa, Muryarsa tajiyo yana dososu yana yin magana awaya cikin kwantacciyar muryar nan tashi mai ratsa zuciyar duk wani wanda ke sauraronta, "Ehh wallahi dawowa ta ma kenan yanzun nan muka sauka...... Ai dama ta gombe natafi wannan karon.... Ehh insha Allah anan zamuyi sallah.... Ok har kashigo ne?..... To Allah yakawoku lafiya" Sam bata yi yunkurin tashiba dan tasan ba iyawa zata yiba,karadin Aryan suka jiyo shida Zaid wanda ke rike da hannunshi,ayanda take akwancen nan haka suka shigo suka isketa sai dan kwali kawai da taja ta rufe kanta duk su zarah sannu da zuwa suka shiga yimasa ita kuma Aryan yazo ya murkusheta yana murna da farin cikin ganinta,ita ma sannu da zuwa tace dashi idonta na kan farar kafarshi dake sanye cikin takalmi half cover fari tatas,da yawwa kawai ya amsa mata yawuce ciki, Suna nan zaune Aryan yasasu agaba da labari Khalil din yafito tunda yatafi kuma shikenan sai kayansu aka shigo dashi shi kam har yayi wani wurin,tsaraba kam Hanan tasha ta wacce Aryan yakawo mata kuma ba komai bane sai tarin chocolate kala daban daban da dabino shikenan,shi kuwa uban gayyar babu wanda yasiyowa koda tsinke amma ya sissiyo zam zam da su dabino Sosai shi dama haka tafiyar shi take baya iyo tsaraba idan kaga yasiyo abu to Aryan ya tahowa dashi yanzunma ga kayan wasa nan iri iri yatahowa da Aryan, Washe gari yakama ranar salla, babbar Rana kuma mai bikin daya rana haka kuma mai dogon baya,kowa kagani cikin farin ciki da nishadi yake,ita tayiwa Aryan wanka sannan tayi masa shirin masallaci domin tare da Daddynshi zasu tafi,wata arniyar shadda aka dinka masa skye blue riga da wando da babbar riga harda hula dinkin yar bama,da takalminsa sau ciki baki mai masifar kyau,saida ta fesheshi da turare sannan ta yiyyi masa hotuna daga nan yafice yanufi bangaren mahaifin sa, Ita kam dama bata da niyyar zuwa masallaci sallar idi wankanta tayi ta shirya cikin leshinta dan ubansu golden colour dinkin bubu wanda yayi mata kyau sosai,daurin dan kwalin maryam babangida tayi sannan ta yafa farin mayafi ta fita,tunda aka sauko daga sallar idi gidan ke daukar baki wasu dayawa ma bata sansu ba gashi sai raye raye da bushe bushe ake ta faman yi agidan abinci kuwa kala kala gashi nan sai wanda ka zaba cikin manya manyan warmers wanda aka iyo musamman dan ranar yau,ita dai tuwon shinkafa taci ta kora da lemon jarka, Bayan ta dan nutsu ta kira duk yan uwa da abokan arziki tayi musu barka da sallah bayan tagama ta yafa mayafi tafita kanta babu dan kwali sai mayafin da ta lullube kanta dashi tana fita falo idanuwanta suka sarke da nashi wanda ke zaune falon hajiya shida Khalid suna cin abinci wata faduwar gaba ce mai tsanani ta ziyarceta cikin gaggawa ta sauke nata idon k'asa,gaishesu tayi sannan ta juya da niyyar komawa amma sai tajiyo muryar Khalid yana cewa, "Ahh madam dawo mana mu gama gaisawa..." Dawowa tayi ta zauna duk atakure tana jinsu sunata hira amma muryar Khalid tafi tashi dan shi Khalil ma kamar adole yake yin maganar, "Wai kasan yarinyar nan me tace min last time? Wai su Nawwar da Nainah sun isheta bata son ta sake haihuwa ita planning zata yi kaza da kaza ko kasan asatin da ta fara planning din a lokacin ta samu ciki....." "Baka yi da wasa ba kenan....." Khalil yafada yana dariya ciki ciki,ita Hanan bata ma ji abinda Khalil din yafada ba kawai dai taji Khalid yace, "Atoh ba kai ka tsaya wasa ba...." "Kai ai gashi nan kayi dagaske..." "To anfada maka ni rago ne irinka? Kai a wannan fannin ai lazy ne...." "Na taba yi agabanka ne ka gani?" "Ai alamar karfi tana ga mai kiba,madam saifa kin hadawa wannan tuzurun da yan dabaru ko ya samu yarinka yin abin arziki" Khalid ya karasa maganar yana kallon Hanan wacce sam bata fahimci inda zancen nasu ya dosa ba kasancewar bata jin abinda Khalil yake fada domin maganar tashi k'asa k'asa yake yinta yanda bazata jiba,jin Khalid na shirin yimasa b'arin zance yasashi daga manyan idanuwanshi ya kalleta kamar ance ta kalli wurin da yake nan suka hada ido bakinshi kawai taga ya motsa amma bata ji abinda yace ba sai dai jikinta yabata cewar cewa yayi "Tashi daga nan",jikinta yayi lakwas kamar anyi mata duka tayi azamar tashi ta wuce ciki ba tare da jinkirin ko sakwan daya ba....................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *27* ***Kai tsaye daki ta wuce wurinsu zarah wad'anda ke ta faman daukar hotuna kamar babu gobe,zama tayi cikinsu sai dai gaba daya hankalinta yana can tare da Khalil wato yau dinnan mutumin ya tsokano kyau kamar dan shi kadai aka kera shaddar da ke jikinsa wadda ta kasance irin ta Aryan sak domin anko suka yi yahadu yau dinnan karshen haduwa, Acan falo kuwa bayan Hanan ta tashi tabar wurin Khalid kallon Khalil yayi yace, "Anya kuwa mutumin nan? Anya kuwa?" "Anya me?" Khalil ya bukata cikin rashin son maganar tayi nisa, "Gaskiya Khalil ya kamata ka gyara nidai bazan gaji da fada maka gaskiya ba amma yadai dace kayi abinda yadace a lokacin da ya dace,ina dalilin kullum shekaru na tafiya sannan ka kawo yarinya karama ka ajiye a tangamemen gida amma ka kasa kulawa da da ita...." "Itace ta fada maka bana bata kulawa?" "Sai ta fada? Ai basai ta fada minba,haba Khalil wai kai wanne irin mutum ne, wannan abun fa da kake yi hadda zalunci idan baka saniba domin itama tana da hakki akanka amma haka kawai dan wani banzan tunani irin naka da taurin kai ka zauna kana cutar da yarinya.... wallahi kaji tsoron Allah" Shiru Khalil yayi masa hakan yabawa Khalid damar cigaba daga inda ya tsaya ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, "Kaga malam dan Allah ka rabu dani bana son hayaniya,ko insakar maka ita ka aurane tunda kace ni zaluntarta nake yi? Kai sai ka aureta kayi mata adalci" Khalil yafada yana cigaba da cin abincin dake gabanshi kuma sai ka rantse da Allah bashi ne yayi maganar ba, jijjiga kai Khalid yayi domin yafi kowa sanin Khalil tun kuruciya suke tare, tare suka taso suka yi karatu suka yi komai kuma asalima ai sunansu iri daya shima Khalid din sunanshi na gaskiya Ibrahim duk sunan mutum daya suka ci wato kakansu na wurin uba (moddibo),to dukansu sunanshi aka saka musu tunda 'yayan wa da kani suke amma mahaifin su Khalil shine babba, "Allah dai yana gani ai..". Inji Khalid,shiru Khalil yayi masa yana duba agogon Rolex dinshi dake daure a hannunshi karfe biyar har da kusan rabi yana son yatura adauko Aryan amma baya son Khalid yaji babu dadi domin Aryan din na can tare da su Nawwar daga karshe dai ya zabi yin shiru zai bari zuwa magriba inyaso sai ya tura Zaid ya daukoshi. Su Hanan kuwa sake sabon shiri suka yi suka fita kallon wasannin da ake gabatarwa acan filin fada dama kuma babu wani nisa daga nan gidan zuwa filin fadar,basu suka dawo gida ba sai dab da sallar magriba. Suna shiga gidan Zaid na dawowa shida Aryan hango Hanan da yayi da gudu ya balle murfin kofa ya fito yaje ya rungumeta,rikeshi tayi tana dariya, "Cutie ina ka tafi yau kabarni ne da kewa?" "Gidansu Nawwar Uncle yakaini" "Kuma shine babu sallama cutie? Tafiya babu ko sallama?" "A'a" Bata sake yin magana ba tana rike da hannunshi zasu shiga part din umma ta hango abban nashi yafito da alama masallaci zaije domin gashi nan yana gyara hannun rigarshi wanda ya nannade wurin alwala,sakin Aryan tayi dalilin jiyo kiranshi da uban keyi wai yazo suje salla,ita kam kada kanta tayi zuwa ciki. Daren yau kamar abun hadin baki dukkaninsu su biyun basu samu bacci ba kowa damuwarsa ce ta hanashi runtsawa ita Hanan tunani da begen ganin Khalil ne ya sa bacci ke neman gagarar idanuwanta,bata gajiya da kallon bawan Allahn nan bata san dalili ba koda yake Allah ne ya kamata tunda abaya babu irin fariya da cika baki da rashin kunyar da bata yimasa ba shiyasa akace kar ka raina mutum ko kuma ka wulakantashi musamman ma wanda baka sani ba ko baka taba ganiba dan Allah na iya jarrabarka da kaunarshi bayan kun hadu,duk da ita dai har yau bata gama tabbatarwa da kanta cewa ta kamu da sonshi ba amma ta damu dashi tunanin sa ya sako ta agaba ta yadda bata yin kwakkwaran minti daya ba tare da ta tuna dashi ba to wai meke damunta ne?. Shi kuma Khalil maganganun da Khalid ya farfada masa sune suka nemi hanashi bacci wai harda cewa yana zaluntar yarinyar mutane dan haka yaji tsoron Allah, Juyi yayi akan luntsumemen gadonshi sannan yaja dan guntun tsaki ya harde hannuwanshi a kirji, "Ko me yake son inyi mata oho..." Yafada acikin zuciyarshi yana sake yin wani tsakin, "Ka bata hakkinta na aure tunda itama mutum ce....." Maganar Khalid ta sake dawo masa tamkar yanzune yake fada masa, "Inbata hakkinta? Kai gaskiya bazan iyaba...... Ni in rab'i wata mace wadda ba Ramlat ba? Gaskiya bazan iyaba, Ramlat ita kadai ce matar da zan iya wannan rayuwar da ita kuma tunda ta rigada ta tafi ta barni shikenan zan ci gaba da hakuri har zuwa lokacin da nima nawa wa'adin zai cika...." Ya fada yana lumshe idanuwanshi nan kwalla ta ziraro masa ta gefen idonshi,har yau yakasa mantawa da Ramlat dinsa sannan yakasa daina zubar da hawayensa aduk lokacin da ya tunota,yana yiwa Ramlat son da shi kansa bai san wanne iri bane,akan ya je ya hada jiki da wata macen wadda ba Ramlat ba gara ya zauna bukatar hakan ta zama ajalinsa dan ita kadaice daidanshi a wannan bangaren wannan shine hukuncin da ya yankewa kanshi. Washe gari da safe da dan ciwo ciwon kai kadan kadan Hanan ta tashi sakamakon rashin samun isasshen bacci da bata yiba,tana zaune ita kadai a falon hajiya saboda su Sarah sunbi umma barira Billiri sai zuwa gobe zasu dawo yanzu gidan babu kowa daga ita sai hajiya sai Aryan sai masu aiki shi Aryan ma tun bayan da tayi masa wanka ya tafi wurin abbanshi bai dawo ba har yanzu, Text ne taga ya shigo wayarta sai da ta dan ja lokaci sannan ta duba saboda ta zaci ko mujahid ne domin shima yanzu baya kwana biyu batare da yaturo mata da sako ba, _Ki shirya zan fito yanzu zamuje unguwa._ Shine abinda taga Khalil yaturo mata,tashi tayi ta shiga cikin bedroom ta sake gyarawa ta kintsa sannan ta fito yau shigar shadda tayi kalar ruwan shanshanbale wadda tasha aiki dinkin riga da zanine yayi kyau sosai,sarka da dan kunne da abun hannu ta sassaka sannan tayi dauri wanda yadace da zamani kuma dan yayi da ka ganta dai kaga amarya wacce ludayinta ke kan dawu. Tana zaune bakin gado tana yiwa yaran anty salaha voice note ta WhatsApp tajiyo kamshin turaren shi yana gabato ta, Bude kofar dakin yayi bayan ya danyi knocking sau biyu bai jira tabashi izini ba kuma yabude ya sako kanshi ciki aranta tace to me amfanin knocking din tunda bai jira izini ba? "Fito mu wuce...." Daga haka yajuya yana gyara zaman hular dake kansa, hajiya suka yiwa sallama sannan suka fita da ita dashi da Aryan hajiya sai faman fara'a take yi,yau dama kaya yan kanti ta sakawa Aryan yan ubansu jeans da t shirt jeans din baki da belt dinshi sai brown colour din riga t shirt wadda ajiki aka rubuta 123,sai bakin combos sabo dal,shi kuwa uban farar shadda ce ajikinsa zubin dinkin birni yasha hula sai zuba kamshi yake yi,dukkaninsu baya suka shiga shi kuma Aryan ya shiga gaba yana mikewa tsaye saman kujerar, Gidan Abba Idris suka fara zuwa wanda ke can sabuwar GRA,gidan babban gidane mai dauke da sassa daban daban, bangaren uwar gidan suka fara zuwa wacce ta karbi Hanan hannu bibbiyu da yake mace ce mai fara'a,shi kuma dama uban gayyar yana can wurin Abban suna gaisawa,bayan tafito daga sashen uwar gidan aka rakata na amaryar itama ba laifi tana da karbar baki,tana zaune ita da Aryan da wasu yara agidan wanda tafi kyautata zaton jikokin gidanne dan harda wadda bata d'ara Aryan a shekaru ba aka leko kiranta wai tafito su tafi,kudi matan gidan suka bata da turaruka,har falon Abba kuma aka rakata suka gaisa shima yabawa Aryan kudi wai gashi nan barka da salla shima khalil rabon kudin yayi agidan kowa da nasa sannan suka tafi,gidan anty Fatu kanwar hajiya suka je wannan kam har falonta Khalil yashiga suka gaisa itama yayiwa yaranta rabon kudi sannan suka fito, Hanan ta lura shi mutum ne mai son zumunci da kaunar yan uwansa domin duka kannensa babu gidan wanda basu jeba yakai mata ziyara, ba dan mai zumunci bane ai hakimcewa zaiyi sai dai shi aje asameshi tunda shine babba kuma yana da kudi amma babu ruwansa yakanje ya gaidasu lokaci zuwa lokaci kuma duk sallar duniya karama ko babba indai yana k'asar sai yaje gidajensu yayi musu barka da salla haka idan anyiwa su Aryan hutu shima kaf dangi sai ya zagaya dashi anganshi sannan yake barin k'asar dashi gaskiya ya rike yan uwanshi kuma ya rike girmansa ya zame musu babban wa uba. Gidan mai martaba suka je wato fada bayan sun fito daga gidan hamida kanwarshi, Hanan aranta tambayar kanta take tayi to ko dai duk cikin gombe yan uwansu Khalil ne? Saboda sunje gidaje sunfi 20 idan lissafawa zata yi,lallai sai yanzu ta yarda da maganar da taji marokin nan nayi ranar daurin aurenta yanata yiwa Khalil kirari wai ya gaji mulki kuma yagaji sarauta ashe kuwa dagaske hakanne dan tagama kamar gaba daya masu arzikin garin danginsu ne, Bayan fitowarsu daga fada inda aka hado ta da kayan kamshi kaya guda su turaren wuta,turaren kaya,ban daki da na jiki gidan Khalid suka wuce ta fahimci hakanne dalilin waya da taji yana yi da Khalid din yana cewa gasu nan zuwa, Acan suka yi sallar magriba duk da Muneerat matarshi bata da saurin sabo amma hakan bai damu hanan ba tayi mata uzuri saboda kowa da irin halinshi. Sai da suka ci abinci sannan suka fito domin tafiya,a compound din gidan suka tarar da su Khalil tsaye shida Khalid suna yin magana amma basu san kowacce iri bace saboda basa jiyo abinda suke fada, sallama sukayi musu suka tafi su Nawwar nata yiwa Aryan bye bye wai suma sai sunzo. Tunda suka koma gida hanan tashiga daki ta kwanta ga gajiyar yawon da suka sha ga ciwon mara saboda tsallaken watan da tayi bata yiba shiyasa take dandana kudarta,tana cikin wannan halin taga text din Khalil wai ta shirya gobe zasu koma Abuja,kasa tashi ta shirya kayan tayi ahaka su zarah suka dawo suka sameta wad'anda suka dawo daga Billiri tare da umma barira...........................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:11 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *28* ***Tana daga kwancen tana fama da ciwon mara wanda ke nukurkusar ta su zarah suka shigo ita da mufida kowaccensu da alamun gajiya atare da ita, Cikin wannan hali ta janyo wayarta tana sake duba sakon nashi wanda yarubuto mata, _ki shirya kayanki gobe da safe zamu wuce Abuja._ "Anty mun dawo..." Mufida ta fada tana kokarin zama gefen gadon nata batayi magana ba sakamakon yawu da ya tarar mata abaki,tashi tayi taje ta zubar ta dawo ta kwanta, Wasa wasa tashin zuciya ya sako ta agaba ga shegen rashin dadin baki dake damunta kamar wata mai ciki haka yawu zai yita cika mata baki dayake wani lokacin period yana da wannan tsiyar duk sai yamayar dakai mai laulayin dole,zuwa bayan ishah har ta galabaita dan sai da lamarin ya kaita da yin amai,amai tayita kwarawa kuma tana gamawa cikin ta shima ya rude ta sake komawa cikin toilet din ai tuni su mufida suka tafi suka kaiwa hajiya tsegumin ai ga Anty can tana ta amai bata da lafiya,hajiya tare da umma ai da hanzarinsu suka taho kamar zasu tashi sama, Tana kwance ta sauya kayan jikinta sakamakon wanda ke jikin nata sun baci da aman da tayi,cikin rudu hajiya da umma keyi mata sannu tana daga musu kai tana kokarin yin magana wani aman yasake turnuko mata cikin sauri ta tashi ta nufi toilet taje ta yi acan, Fita hajiya tayi ta kira Khalil awaya lokacin shi yana can ma tare da baki suna ganawa, "Mu'azzam kabar duk abinda kake yi maza kazo matarka babu lafiya amma ka fara kiran likita tukunna...." Abinda yaji hajiya tace kenan sannan ta katse wayar, Zaid ya kira yace yaje ya dauko Dr, Hanan na kwance saman gado tana ta karkarwar sanyi suka shigo shida Dr din kowa fita yayi yabasu wuri,yana gaba Dr yana biye dashi abaya,ajiye dan first aid box dinsa yayi likitan yana dan yimata tambayoyi, "Akwai juna biyu ne?" Girgiza kai tayi idanuwanta arufe, "When last kika ga al'adarki?" "Last month banyi ba" Tabashi amsa cikeda kunya saboda Khalil dake tsaye kyam yana sauraren su, "Dama kina tsallaken wata ne?" Girgiza masa kai tayi kuma cikin yamutsa fuska tace "A'a" "Akwai amai?" Kai ta daga masa, "Akwai ciwon kai?" Girgiza kai tayi alamar babu, Dafa wuyanta yayi yaji akwai zazzabi sannan ya dan dudduba idanuwanta bayan ya dan bubbudesu. Magani ya soma duba mata yana cigaba da bayanin cewa ai ba wata matsala bace dama dayawan mata sukan samu irin wannan laulaye laulayen lokacin da zasu yi period, Khalil na tsaye yana daddana wayarshi kamar baya jinsu,ganin hankalinsa yana kan waya yasata dan bude idanuwanta ta kalleshi sannan ta mayar dasu ta rufe,saida yagama hada maganin tsaf sannan ya bata yace taci abinci komai kankantarshi sai ta sha magani daga haka suka fita shi Khalil bai ce komai ba,afalo ya tarar dasu hajiya dukkaninsu zaune suna jiran fitowarsu cewa yayi bari ya sallami Dr yadawo,baifi minti biyar da fita ba sai gashi yadawo amma bai samensu ba sai acikin bedroom din da take ciki ya iskesu anata lallabata ana tambayar wai me take son ci akawo mata? Tsayawa yayi ya harde hannuwanshi akirjinsa yana kallon ikon Allah domin su duk atunaninsu juna biyu Hanan tasamu wai dan sunga tana amai basu san lalurar su ce ta mata ba duk wata, "Ki daure kici wani abu kinji.... Kinga ai yanzu dole sai kin kula,me za akawo miki?" Hajiya ta bukata cikin kulawa, "Custard powder kadai zan sha itama kar asa sugar....." Ta fada cikin rashin kwarin jiki, "Ke zarah maza tashi kuje ku hado mata custard..." Inji umma barira, Shi abinma sai yaso bashi dariya saboda yanda duk su hajiya suka bi suka rude sunata lallabata,sai da tasha custard din tasha magani sannan suka fita suka barta, Shima yana shirin fita hajiya tazo ta dakatar dashi, "Khalil nace yaushe matar taka tafara wannan laulayin ne? Idan tana yawan yin aman ai sai insa asamo mata magani,kasan masu juna biyu sai da kula" "Toh hajiya" Daga haka yasamu tabarshi yafita,kulawa sosai ake bawa Hanan dan da safe ma kafin su tafi hajiya nata jawa Khalil kunnen yarinka kulawa da Hanan,da tafiyar ma hajiya cewa tayi sai abari wai har Hanan din ta warware sai da Hanan din tace mata ai itama akwai abinda zatayi idan taje Abujan zatayi clearance to jin haka yasa hajiya amincewa suka kama hanya suka tafi tana sake jaddada wai arinka kulawa da Hanan shi dai bai ce ba juna biyun bane yai shiru yana binsu da ido. Duk da cewa bata baccin mota yau kam ta yi shi dan tunda suka baro gombe take tikar bacci har lokacin da suka shiga garin Abuja lokacin anata sheka uban ruwa dan tun daga farkon abuja ake zubashi, Har suka shiga cikin compound din gidan Hanan bata saniba domin tana can tana ta sharar baccinta,sai da Aryan ya bude murya yace, "Mommy ki tashi anzo gida..." Firgigit tayi ta mike domin kamar acikin mafarki taji maganar tashi,a dan tsorace ta juya ta kalli Khalil wanda ke zaune kusa da ita,tashi tayi tafita ta nufi ciki tana dan dingishi tana zuwa bedroom dinta ta rage kayan jikinta ta sake kwanciya domin a mutukar gajiye jikinta yake tamkar anyi mata dukan tsiya. Ta jima tana bacci dan sai la'asar sannan ta tashi tayi wanka ta fita wurinsu umma da ke babban falon kasa ita da Aryan wanda ke ta wasa da keken sa,itama zama tayi bayan ta zubo abinci dama aikin kenan daga ci sai bacci bayan shi babu abun yi. Haka rayuwa taci gaba da tafiya su Aryan tuni sun koma makaranta shi kuma Khalil yakoma kan harkokinsa shima dan ko ganuwa ma bayayi kullum da inda zaije, Hanan kuwa tun bata damuwa rashin daidaituwar dake tsakaninta da Khalil har tafara damuwa,bata da aiki sai na tunaninsa da mafarke mafarke akansa gaba daya ta rame ta kanjale gata dai a katon gida lafiyayye zata ci zata sha ba aikin komai take yiba amma da yake akwai damuwa acikin zuciyarta shiyasa duk ta zuke dan ko ganinsa ma bata yi tsakaninta dashi text massage ne idan tana son wani abu ko kuma tana son zataje wani wuri kuma duk abinda ta nema ko ta bukata baya hanata yana sawa a kawo mata, Shima anasa b'angaren har gobe bai daina kukan rashin matarsa ba domin halin da yake ciki yafara damunsa ada yayi tunanin zai iya rike bukatarsa ba tare da shiga wani hali ba amma yanzu ya ga abun yana neman faskara domin kullum cikin shan pills yake wai ko zaiji dama dama gashi yana yin azumin litinin da alhamis amma duk jiya iyau, Hajiyarshi kuwa duk lokacin da yaje gombe cikin tambayar sa yajikin Hanan take yana dai kulawa da ita ko? Wannan zuwan da yayi last kuwa hajiya harda bashi sassake sassake na gargajiya wai maganin laulayine na masu ciki yana tsayar da amai da sauran su shidai baice komai ba ya karbo yataho dashi da yazo sai yabawa umma saboda su Hanan basa nan suna makaranta ita da Aryan, "Umma gashi wai maganin Sa'adatu ne idan ta dawo sai kibata....." "Na menene?" Umma ta tambayeshi, "Maganin laulayine wai inji hajiya...." "Au toh toh, Allah yasa adace Allah sarki dama ai yarinyar nan duk ta zuke ta lalace wallahi cikin nan na wahalar da ita... Allah dai yaraba lafiya" "Amin" ya amsa daga nan yafita, Bayan su Hanan sun dawo tana falo tana tsara lesson plan dinta umma tazo ta kawo mata maganin da Khalil yakawo karba kawai tayi tace ta gode,kwalla taji ta ciko mata ido sakamakon damuwar dake ranta gashi kullum mujahid cikin turo mata da massage yake amma tayi biris dashi bata kulawa wallahi kallo daya idan kayi mata zaka fahimci tana da damuwa,sau da dama sai taji kamar ta tura masa da text massage ta fada masa sirrin zuciyarta amma sai taga rashin dacewar hakan,idan tayi haka ta disga kanta kuma bata siyawa kanta daraja ba. Yau dai tana cikin farin ciki saboda zuwan anty salaha yayarta dan rabonta da ita tun bikinta yau watanni shida kenan kuma wata tara da fara service dinta dan saura yan watanni su gama, Binta da kallo kawai anty salaha keyi saboda yanda taga ta rame tayi kanjal kanjal da ita kamar ba itace cikin wannan daular ba, "Gaskiya Hanan banji dadin ganinki ba haka, wannan uwar ramar da kikayi duk ta mecece? Baki rasa ciba baki rasa sha ba meyake damunki?" Dan jimm tayi dan ta rasa me zata cewa anty salaha,ada tana ta kukan bata son minister bata kaunar shi ayanzu kuma kukan tsananin sonshi da kaunar shi take duk da shi nasa hankalin ba akanta yake ba ko ganinsa yanzu bata samun yi,sai tayi sati daya ko fiye da haka bata ganshi ba,da yake bata da abin fada haka taja bakinta tayi shiru tana sauraren fadan da anty salaha keta faman yimata tana cewa yadace dai yanzu ace ta kwantar da hankalinta ta yi zamanta agidan mijinta tunda ita anty salaha bata san abinda ke cikin ranta ba. Kwanan anty salaha biyu sannan ta tafi kuma ko haduwa basuyi da Khalil ba dan baya nan sai kudi da ya aiko PA dashi ya kawowa Hanan dan tayi masa massage cewa anty salaha tazo. Tun bayan tafiyar anty salaha tasake shiga cikin damuwa sosai kamar wacce ke cikin kurkuku haka take jinta gaba daya yanzu ta rasa abinda zatayi taji dadi,da yake ranar weekend ne kuka kawai ta zauna tanayi adaki ahaka Aryan yaje ya sameta,ganin tana kuka yasashi fita da gudu zuwa part din Khalil dama suna tare tun safe a dakinshi,yana kwance kan gadonshi sanye da kananan kaya yana aiki a system dinshi dalilin da yasa ma bai fita ba kenan sai ganin Aryan yayi yafado yana fada masa wai ga mommy can tana kuka adaki suje yagani,rufe system din yayi yasa slippers dinshi suka fita suka nufi bangarenta........................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:12 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *29* ***Tana kwance tana sharbar kuka kamar wacce aka daka haka suka shiga suka tarar da ita,wuri Khalil ya samu ya zauna bayan yacewa Aryan yaje wurin umma ya gaidata saboda yau bai sauka downstairs ba kwata kwata, Dan bude idanuwansa yayi akanta yana kallon yanda take kuka duk tabi ta cika masa kunne domin kukan yana dan fitane da sauti, "Me yafaru kike kuka....?" Ya tambayeta idanuwanshi na zagaya dakin yana kallonsa komai dai neat ya ganshi babu Kaya awarwargaje,jin muryar sa yasata rage kukanta amma ta kasa magana sai shassheka take yi, "Bakya jine? Ina tambayar ki me aka yimiki kike kuka? Ko ciwon Marar ne?" Yasake fada cikin fada kadan domin shi ya tsani kuka babu gaira ba dan dalili musamman ma na karamin yaro ko mace mutane biyun nan yana da weakness akansu, "Babu komai..." Ta bashi amsa tana jan hanci amma acikin zuciyarta ji take inama zata iya da ta ce masa "sonka da kaunar ka ne" Sai dai amma tasan abune da bazata taba iya furta masa ba duk kuwa da cewa yana azabtar da zuciyarta, "Kukan jin dadi kike yi?" Taji ya fada kuma wannan karon idanuwanshi suna kanta kyarr hakan yasa ta kasa bashi amsa saima sake tukunkune kanta da tayi, "Duniyar ce tayi miki dadi shine kika zauna kina yiwa mutane kuka?" Mikewa tsaye yayi har yana shirin fita idonsa ya sauka kan maganinta da ke ajiye saman mirror wanda hajiya ta bada akawo mata, karasawa yayi ya dauka yana dubawa, "Meye wannan kuma?" Daga idanuwanta tayi wadanda suke jajur ta kalleshi, "Maganin laulayi nane..." Juyawa yayi ya kalleta cike da mamaki har bai san lokacin da yafurta, "Laulayi?" "Ehh mana,ba ana bawa masu ciki maganin tsayar da amai da tara yawu ba shine nima aka kawo min nikuma na ajiye kafin infara....." Sosai maganganun ta suka bashi mamaki har baima san lokacin da yayi murmushi ba unexpected murmushin ya subuce masa "lallai yarinyar nan yar drama ce" yafada acikin ransa amma afili sai ya ajiye maganin ya kalleta, "Kin kyauta...." Daga haka yafita daga cikin dakin yana mamakin bakin Hanan wato magana ta fada masa kenan ko yaya? Itama mamakin kanta da kanta take yi yanda ta iya bude baki ta fada masa haka amma ai gara da ta fada masa tunda ai shine yayiwa su hajiyan karyar wai tana da ciki saboda kar su zargeshi da tauye mata hakki, Tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka da ruwan dumi sannan tafito ta zira doguwar riga ta koma ta kwanta yau ita haushin kowa take ji shiyasa ma bata fita ba tunda ta tashi adaki yau tayi rayuwarta umma barira ma da taji shiru sai dakin ta biyota tana tambayar ta ko lafiya bata fito ba yau? Cewa tayi babu komai kawai dai bata jin dadin jikinta ne, "Sai hakuri ai,rainon ciki haka yake sai anhada da hakuri idan ba haifeshi akayi ba lafiya bata fiya samuwa dari bisa dari ba......" Shiru tayi tana sauraren umma kuma tana jin tausayin su acikin ranta saboda su duk sun zaci cikinne da ita dagaske basu san gadar zare ce Khalil ya shirya musu ba. Haka taci gaba da zaman takura wanda ba kowa ne ya takurata ba itace kawai ke takura kanta. *** Mujahid Duk da cewa idan yayiwa Hanan text massage yanzu bata kulashi hakan baisa ya daina ba, sannan baya jin zai karbi bukatar sumayya har ya amince yafara soyayya da ita, Rashin kulashin da Hanan keyi shi yafi komai daga masa hankali ahalin yanzu duk da dai dama bawai kalaman soyayya yake tura mata ba gashi ko ta WhatsApp bata kulashi daga baya ma sai yaga kamar tayi blocking dinshi nan abu ya sake hadar masa goma da ashirin, Sumayya kuwa ganin tana ta faman shassharreshi tana dauke masa kai ba kamar yadda ta saba ba ada hakan ko ajikinsa sai dai wani lokacin sai yakanji babu dadi irin yanda yarinyar ko kallo bai isheta ba gaisuwa ma sai ta gadama take gaisheshi, Yau da yake weekend ne yana kwance falon mami da remote hannunshi yana kallon kwallon kafa ta bude kofa ta shigo bata ko kalleshi ba tawuce sai yaji hakan ya kona masa rai fiye da tunaninsa,har shi zata zo ta wuce bata gaisar ba? Bai gama hucewa daga wannan fushin ba yadawo daga masallaci sallar azahar yazo ya tarar dasu ita da mami tana cemata taje dakinshi ta dauko mata bedsheet dinshi zata hada cikin kayan wanki budar bakinta sai cewa tayi, "Mami ni bana shiga dakinsa yanzu sai dai intura mai aiki ta dauko miki...." "Yaushe kika daina shiga dakin yayan naki sumayya? Dan uwanki ne fa" Kafin tasake magana ya sako kai yashigo dama yana tsaye yana ji, yarinyar nan bata taba bashi haushi irin na yau ba, "Ke je ki zubo min abinci idan kin gadama...." Yafada yana kishingida saman kujera,kamar bata so haka ta tashi ta wuce kitchen tana ta turo baki alamar dole aka yimata,kwafa yayi da karfi ya kalli mami yace, "Wallahi na kusa balla yarinyar nan tunda bata da kunya,wai ni ban isa ta gaida ni ba? Dazu fa ina zaune tazo ta wuce kamar bata ganni ba...." Murmushi mami tayi tace, "To me yakawo maganar ballawa dan kawai bata gaida ka ba.." "Ai dama mami duk kece kike goyon bayanta wallahi" Daidai lokacin sumayya ta fito rike da plate din Brown rice with prawn, mango and avocado salad,ajiye masa tayi agabansa tajuya zata tafi tana sake turo baki, "Ke zo nan...dauko min juice adakina cikin fridge...." Tana sake turo baki tajuya ta wuce,dariya mami tayi tana fadin "To nima sai ki taho min da nawa aiken da nayi miki dazu kika turje wai ke bakya shiga sai kace dakin surukinki". *** Kwanci tashi yanzu saura wata daya su Hanan su kammala service dinsu,rabon da ta sa Khalil a idonta kuwa anfi sati domin shi baya ma nan yaje k'asar Cameroon kwananshi shida acan sai jiya da daddare yadawo, Cikin sanyin jiki da damuwa take shiryawa tana ta sakin dan karamin tsaki ada bata da burin da yawuce taganta sanye da kayan NYSC tana yin service amma yanzu da tafiya tayi tafiya bata da babban buri wanda yawuce taga tacire wadannan kayan ta karbi certificate dinta a hannu, "Mtswwww wallahi na tsani lectures dinnan na tsiya haka kawai dan kar abar mutum yahuta...... Kaki zuwa kuma suce zasu baka query" Wani tsakin ta sake ja sannan ta mike tasa kakinta, farin hijabi ta dauka tafito ta tsuke cikin kayanta na NYSC harda takalmi jungle boot a kafarta ta rataya hijabinta a kafada tana saukowa daga sama zuwa downstairs,itafa yanzu duk NYSC dinnan ta fita ranta ji takeyi kamar ta janyo ranar P. O. P dinnan nasu ayi ayi a bata kwalinta amma haka kawai sai gayyar lectures din dole, Tana saukowa shi kuma yana fitowa daga bedroom din umma,tsayawa sukayi dukkaninsu suna kallon juna na tsawon wasu yan mintuna, "Ina kwana....?" Ta fada cikin duburburcewa sakamakon hada idanuwa da suka yi, "Lafiya lau....." Daga haka ya gegeta yawuce ya haura sama,binsa tayi da kallo har sai da ya bacewa ganinta,kai ai dole ma ta lalace bata taba sanin cewa so cuta ne ba sai yanzu,ashe dama haka mutum yake ji idan yakamu da son wanda bai damu dashi ba? Haka masoyin da ake nunawa halin ko inkula yake kasancewa cikin damuwa da bacin rai? Tun daga lokacin bata kara sakashi a idonta ba sai ranar wata laraba taga text dinshi wai ta shirya zasuje gombe kuma aranar zasu dawo anyi haihuwa, Laila ta haihu yar abban London hajiya ce tace masa lallai lallai yakai matarsa itama tayi barka ko kuma taje suna da hakane zata san dangi suma su santa, Da yake ranar aikine Aryan baya nan yana school,shiryawa tayi taci kwalliya cikin atamfa exclusive koriya dinkin riga da skirt kamar yadda ta saba dinkunanta, green din mayafi ta yafa sannan ta dauki handbag wadda ta dace da shigarta haka ma takalminta, tana falon k'asa zaune ita da umma tana jiransa amma har azahar shiru wai meeting yakeyi da mr president daga k'arshe dai sai PA yaturo wai yazo ya dauketa yakaita office dinshi sai su wuce ta can basai yadawo gida ba, Office din nashi yayi masifar haduwa kamar kar ka fita daga ciki dan tsabar kyau baya ciki yana can meeting dan haka ta shiga ciki ta zauna a inda aka kebance dan baki na musamman, kamar yanda yake babu hayaniya to haka office din nasa shima babu wasu takarcen hayaniya aciki,komai atsare kuma ashirye,kan table dinsa kuwa kambun girmamawa ne sunfi abinda suka fi irin wadanda ake bashi sannan ga hotunanshi nan manya manya kafe acikin office din wani shi kadai wasu kuma tare da mutane,wasu kuma tare da matasa yan kwallo,kan teburinshi kuwa wani dan karamin frame ne mai dauke da hoton Aryan ajiki, "Ohh ni Sa'adatu wannan bawan Allah yana kaunar d'an nan nasa...... Har a office dinma?" Tana nan zaune tana zaman jiransa duk tagama kosawa duk da cewa ga kayan kallo nan tv katuwa nata faman aiki ankamo tashar labarai ga fridge can kuma shima gefe guda dama kishin ruwa take ji dan haka ta mike ta nufi fridge din da kanta tana zuwa ta budeshi nan ta ganshi tafare da kayan sanyaya makoshi iri iri sai dai kuma abinda idanuwanta suka gane mata sune suka yi sanadiyyar tsayawar numfashinta cakk take ta firfito da ido kamar zasu fado kasa dan tsananin firgici da tsoro.....................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:12 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *30* ***Jikinta rawa yashiga yi babu bata lokaci cikin hanzari ta mayar da fridge din ta rufe ta koma ta zauna tana al'ajabin wannan lamari me neman sakata cikin wasi wasi, "Giya?..... Dama minister mashayin giya ne? Kai anya kuwa iyayensa da abbanta sun sani? Kai ko iyayenshi sun sani abbanta bai saniba dan idan har yana da masaniyar haka to babu abinda zaisa ya dauki auren yarsa ya baiwa mashayi..... Innalillahi" Ta fada acikin zuciyarta tana mai rafka tagumi saboda takaici da nadamar fadawa tarkon sonshi da suka lullubeta lokaci guda, Gaba daya ma ta rasa abinda zatayi taji sanyi acikin ranta,gaskiya Abban Aryan yayi bala'in bata kunya,ohh Allah kowa dai ka gani kabarshi ayanda ka ganshi domin Allah kadai shine yasan sirrin cikinsa da wajensa,ai ko cikin mafarki bata taba kawowa kanta cewa wannan bawan Allahn zai sha giya ba ashe ashe, Zaman jiransa taci gaba dayi duk zaman yasoma gundurarta domin ta gaji da jira,ta saka ta warware ahaka yashigo office din tare da wasu mutum biyar wadanda take kyautata zaton cewa bakinsa ne, kasancewar tana wuri daya babu wanda yayi mata magana saida yagama dasu ya sallamesu sannan yamike daga kan kujerarsa ita kuma sai daure fuska take yi kamar me, "Muje ko....." Daga haka yayi gaba itama ta mike tabishi abaya securities suka dafa musu baya, Har acikin mota babu wanda yace uffan saida suka fara tafiya sannan yayi magana hankalinsa yana kan wayar dake hannunsa, "Me zaki kai mata?" Shine tambayar da taji yayi mata idanuwanshi akan screen din wayarsa,saida ta dan yi jimm sannan tabashi amsa, "Duk abinda yasamu...." Bai sake magana ba itama haka asalima dauke kanta tayi zuwa glass din motar tana kallon birnin abuja domin bata taba zuwa nan haka ba sai yau,awani katafaren supermarket taga sun tsaya,dan karkacewa yayi yana laluba aljihunsa duka guda biyun, "Ohh Allah ashema kudin nawa sun kare...." Yafada yana kokarin ciro yan canjin da suka rage masa ajikinsa domin duk ya rabar da kudin mawa masu neman taimako da bakin da suke zuwa office gaisuwa, Sabbin yan dubu dubu taga ya mika mata amma bai kai rafa guda ba sai dai da dan yawanshi badai zata iya kiyasta ko nawane adadinsu ba, "Gashi ki siyo mata abinda kika ga yadace..... Karki zauna ki bata min lokaci inada abinyi" Hannu biyu ta saka ta karba sannan tafita wasu daga cikin securities din suka take mata baya har zuwa cikin supermarket din,duba abunda yadace ta siya tafara saboda nafarko dai tasan tunda danginsu masu kudi ne idan ta siyi atamfa watakila arena ko akushe dan haka sai kawai ta yanke shawarar siyan kayan babies, Hadaddun rigunan jarirai ta siya guda biyar masu tsada sannan ta siyi takalma da socks dinsu set daya sannan ta kara da kayan shafe shafen yara irinsu sabulun wankansu,turare,man shafawa,powder da sauransu shima set daya, atakaice dai tayi siyayya ta kusan fin dubu hamsin,kuma kayan bawani dayawa fal bane ba a'a kawai dai da yake masu tsada ne shiyasa, Tana shiga mota aka mika mata kayan ta ajiye atsakiyarsu, "Gashi...." Sannan ta mika masa canjinsa da yayi saura wanda shima bata san ko nawa bane, "Ga guntun canjinka" "Ajiye awurinki" Yabata amsa atakaice yana kokarin kara wayarshi a kunnenshi, "Na'am Aryan..... Andawo daga school ko?...... Kaci abinci?......Ka koshi sosai?...... Yawwa lovely son......ok bye bye.....i love u too" Tana jinsa har yayi wayar tashi yagama,yana gamawa ya mayar da ita aljihunsa ya ajiye ya sake ciro dayar itama yashiga latsawa,yanda ya manta da lamarinta itama haka ta manta da nashi ta jinginar da kanta jikin kujera bayan ta lumshe idanuwanta cike da takaicinsa duk kamshinsa yabi ya rikitata ya cika mata hanci,ba dan kar tayi karya ba to da zata iya cewa tunda take bata taba jin kamshi mai dadi mai sanyaya rai da zuciya kuma mai saka nutsuwa kwatankwacin nasa ba,wato kamshin nasa ne na dabanne ko acikin dubbai. Har suka hari gombe zaman kurame suke yi sai shi da yake yin waya jifa jifa dan daga tahowarsu zuwa yanzu taji yayi waya yakai sau goma, lallai mulki ba sauki ne dan koda amsa waya aka barka anbarka da aiki tuk'uru, Basu suka shiga garin gombe ba sai la'asar,gidan Laila suka fara zuwa wato mai jego,tare suka shiga ciki ita dashi dan shine ma yayi mata jagora saboda ita ba taba zuwa tayi ba wancan karon da suka je barka da salla basu samu damar zuwa gidan laila dinba dayake sunyi yawo da yawa ranar, Yanayin yanda taga gidan ya tabbatar mata da cewa itama Laila din wani hamshakin take aure dan gidanta kadai abin kallo ne,a falo aka yi musu masauki mai dauke da kayan alatu,suna zaune tana kan kujerar da take kusa dashi laila tafito rike da jaririnta wanda ke nannade cikin towel mai laushi, "Oyoyo yaya Khalil..... Sannunku da zuwa" Laila ta fada fuskarta dauke da fara'a lokacin da tayi ido biyu dasu, "Laila maman 3" Ya fada yana murmushi, karasawa tayi ta mika masa jaririn tana yiwa Hanan barka da zuwa,zama tayi da kyar tana dan ciccije baki, Khalil ta fara gaisarwa sannan ta juya suka gaisa da Hanan cikin sakin fuska, Basu fi mintuna goma ba agidan suka fito dan ruwa kadai suka sha suka yimata sallama suka fita bayan Hanan ta ajiye mata kayan barkar da ta tafi mata dashi, Daga can gidan su Khalil suka wuce acan suka yi sallar la'asar suka ci abinci hajiya sai kaffa kaffa take yi da Hanan tana ta tambayar ta wai ko akwai abinda take so? Shi kam shiru yayi yana saurarensu yarasa wanne irin so hajiya ke yiwa yarinyar nan dan tunda taji zasu zo tayi musu tanadi shiyasa da zasu tafi harda su garin kubewa busasshiya da garin kuka da su daddawa ga kindirmo mai kyau da sauran kayan gargajiya wai tasan mata masu juna biyu akwai kwadaye kwadaye to gashi nan ko zata bukaci wani abu aciki ta huta nema,duk yadda Khalil yaso dakewa kasawa yayi dan saida ta kaishi da yin murmushi yawuce yabarsu suna sallama, Kofar gidansu lokacin da suka fito cike yake dam da mutane yara da manya da matasa,hakuri yace abasu zuwa nanda kwana biyu zai dawo,gaskiya yan gombe suna yinsa kuma suna kaunar sa sai yau ta sake tabbatar da hakan domin har suka bar cikin garin mutane suna biye dasu sunyi convoy ashe dama kusan duk lokacin da zaizo haka suke yimasa sai sun rakashi har gida idan kuma zai tafi nanma sai sun rakashi wajen gari sannan suke komawa. Wannan karonma kamar dazu haka tafiyar tasu ta kasance baya da amsa waya babu wani abu da yake yi,ita kam duk zuciyarta babu dadi inbanda kuna babu abinda take yi,bacin ran abinda ta gani dazu yaki gogewa cikin zuciyarta, Bayan sallar magriba suka shiga garin Abuja wanda ke dauke da daddadar iska tana kadawa garin lullube da ni'imar ubangiji,ajiyeta suka yi daga nan ko gidan bai shiga ba suka sake juyawa zasu koma office a wannan lokacin, A dakin umma ta samu Aryan da umman yana kwance yayi pillow da cinyarta yana game a wayarshi sai shagwaba yake tayi umma nata shan kansa tana lallaba shi yaci abinci wai sai yagama game, shigowar Hanan ta sashi zabura ya yar da wayar yatashi yaje ya rungumeta yana yimata oyoyo,itama rungumeshi tayi tana shafa kumatunsa, "Cutie" "Mommy sannu da zuwa" "Yawwa cutie nah" "Sannu da zuwa,to kaga shikenan ma tunda ga ummanka ta dawo nima sai inhuta" inji umma barira, Dariya Hanan tayi ta kama hannunsa, "Au umma haka zakice? Mai gidane fa" "Wannan mai gidan ai rigimamme ne kyaleshi" Dariya Hanan tayi taja Aryan suka hau sama domin ko salla bata yiba,sai da ta kammala sallolinta sannan suka koma dakin umma can suka raba dare suna hira dan har 11 lokacin tuni Aryan yajima da yin bacci, Saida ta kaishi dakinshi ta kwantar dashi sannan ta wuce zuwa nata,sam babu alamar bacci acikin idonta tunani ne kawai keta mutsuttsukar zuciyarta,ta rasa dalilin da yasa abun ya tsaye mata arai har haka ko dan tana yimasa kallon mutumin kirki na arziki ne shiyasa yanzu abun ke damunta? Tasan watakila yanzu ya shigo gidan tunda 12 tayi,text massage ta rubuta ta tura masa, Fitowarsa daga wanka kenan yana saka kayan baccinsa yaji shigowar text dinta,karasa shiryawa yayi ya dauki wayar yazauna gefen gado, _Dan Allah ina son yin magana dakai Abban Aryan amma ina so kayi min kyakkyawar fahimta...._ Shine abinda yaga Hanan ta turo masa,dan yatsanshi yakai bakinsa yana shafa lips dinsa,magana to wacce irin magana take son yi dashi? Kodai har yanzu bata saduda bane ta rungumi k'addarar ubangiji, _Ok,ina jinki._ Dama tasan amsar dai bazata wuce haka ba tunda shi kamar dogon bayani wahala yake bashi,sake gyara kwanciyar ta tayi ta tura masa da reply kamar haka, _Dan Allah kana shan giya ne?._ Ganin sakonta yasashi bude idanuwanshi sosai sannan ya tura mata da, _Zo ina son ganinki._ Gabanta ne taji yafara faduwa jin wai tazo yana kiranta,a tsorace tasaka rigar saman kayan baccinta sannan ta yafa mayafi ta fita,wata iskace mai sanyi da dadi ke kadawa sannan ga sararin samaniya yayi kyau taurari sun kara masa ado da k'awa, ta samu damar ganin hakanne dalilin fitarta kuma dan gaban corridor din da zai sadaka da sashen Khalil open ne babu roofing awurin shiyasa zaka samu damar ganin sararin samaniya, Tamkar marar gaskiya haka ta shiga falon nasa wanda yake shiru dan babu kowa aciki,Allah ya sota ta taho da wayar ta da bata san yanda zatayi ba,text ta tura masa cewar gata tazo tana falo,kimanin mintuna biyu taji motsin fitowarsa,kallo daya tayi masa ta sunkuyar da kanta kasa, sanye yake da kayan bacci na maza white colour riga da wando masu santsin gaske, Zama yayi a opposite dinta yana rike da wayarshi, "Kika ce ina shan giya ko me?" Shiru tayi tana wasa da yan yatsunta, "Ba kiji ne?" Dago kai tayi ta kalleshi nan taga idanuwanshi kyarr akanta ya tallafe kumatunsa gaba daya da hannuwanshi, "Ina ji...." "Waye yafada miki ina shan giya...?" "Babu kowa..." "To meyasa kika yimin wannan tambayar?" Duburburcewa taso yi saboda tambayoyin nasa na neman yimata yawa to abunka da kwararren tsohon dan jarida, "Meyasa kika yimin wannan tambayar? Kin taba ganina ina Shane ko kin taba ganina acikin maye?" Girgiza kai tayi alamar a'a, "To why did you asked?" "Gani dama nayi dazu a office dinka acikin fridge...." Shiru yayi yana kallonta baice komai ba har saida ta fitar da tsammanin zaice wani abu sai kuma taji yace, "To abinda kika gani ba giya bane,lemo kika gani saboda ni babu abinda ya hadani da giya banko taba dandanata ba bare insha,ki rinka tabbatar da ingancin magana kafin kiyi comment akanshi...... Bakauyiya kawai kinga lemo kince giya" Duk da bata gane ayanayin da yayi maganar ba shin cikin bacin raine ko sabanin haka ita dai hakuri ta fara bashi, "Kayi hakuri bazan kara ba" Sai da ta sake maimaitawa sannan yamike yana fadin, "Is alright" Fita yayi tabi bayansa,shi dakin Aryan ya hara ita kuma ta wuce nata tana jin nutsuwa na saukar mata, murmushi tayi da tuno sunan da ya kirata dashi wai bakauyiya gaskiya taji kunya dan tabbas kam bata karanta sunan lemon ba kawai dai taga kwalba kuma green an kawatata,ashe dan Allah wai lemo ne dole ne yace da ita yar kauye. *** Yau ne su Hanan ke yin Pop dinsu ranta fari tass taje ta karbo certificate dinta wahala dai ta kare hutu zai samu zata huta da wannan gayyar fita PPA da CDs dinnan masu hana mutum isasshen bacci,hotuna suka sha Sosai ita da friends dinta yan batch dinsu wadanda suka gama tare da ta dawo gida ma sunyi da Aryan yafi kala ashirin,shima uban gayyar lokacin da takai masa certificate din "congratulations" yace da ita kadai. Bayan kwana biyu da gamawar su kuma duk sai taji babu dadi domin tayi bacci har ya isheta wuni take yi tana bacci yanzu har takai minzalin da ko baccinma bai fiya daukarta sosai ba, Satinsu biyu da gama service tana daki tana gyara wardrobe dinta umma ta shigo mata agigice cikin tashin hankali da dimuwa hannunta aka......................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:12 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *31* ***Sake gigicewa tayi ta rikice ganin umma na hawaye tuni jikinta ya dauki rawa dan tasan babu ko tantama mutuwa akayi kuma abu mai yuyuwane kila ace minister ne ya mutu, "Umma waye ya mutu? Shikenan ya mutu...." Goge hawayenta umma tayi cikin damuwa da yanayin dimuwa tace, "Ba mutuwa bace amma har gara mutuwar Allah na tuba, Aryan ne ba aganshi ba tunda aka tashi daga makaranta wai ance wasu ne sukaje suka daukoshi daga makarantar wadanda ba asan ko su waye ba....." "Innalillahi....." Hanan ta fada gaba daya idanuwanta awaje,haba shiyasa taji shiru bai dawoba aranta har tana cewa ko kuma dai yadawo ita dince bai shigo wurinta ba, Hawaye take son yi amma tashin hankali ya hanata sai yau ta tabbatar da cewa yaron yashiga ranta fiye da tunanin ta domin jin numfashinta take yi kamar zai dauke, Fita umma tayi ita kuma ta samu gefen gado ta zube bayan ta kifa kanta, innalillahi kawai take ambata ahaka taji anbanko kofar d'akinta anshigo kafin ta daga kai taga waye taji anshakota, Khalil tagani tamkar wani mahaukaci saboda yanda duk ya furgice ya rude, bata taba sanin haka ya iya fada da daga murya ba sai yau, "Da sa hannunki acikin b'atan d'ana ko babu.....?" Yafada yana jijjigata kamar zai ballata idanuwanshi aburkice kamar wanda yasha wani abu,sake rikicewa tayi ta gigice tama rasa amsar da zata bashi, "Dake nake magana,nace da sa hannunki cikin batan yarona?" Yasake fada cikin karaji, Girgiza kai tashiga yi muryarta na rawa, "Wallahi tallahi ban san komai ba akai Abban Aryan, wallahi babu hannuna, taya za ahada baki dani acutar da Aryan...." Sake wujujjugata yayi sannan cikin kausashasshiyar murya yace, "Wallahi idan har bincike na ysnuna min cewa akwai sa hannunki sai na kasheki....." Daga haka ya hankadata kan gado yajuya yafita da sauri gudu gudu,sai lokacin ta samu damar fashewa da kuka ai daga ganin yanda yakeyi kasan yashiga rudu jifa harda maganar kisa,kuka take yi sosai, Shima Khalil yana can anbaza jami'an tsaro kowanne lungu da sako dake cikin garin, yan gombe kuwa tuni labari yaje musu wai ansace Aryan,sai wayar umma da Hanan ake kira amma duka wayoyinsu akashe shi kuwa dama Khalil ba asamu call forwarded wayarshi ke nunawa. Har magriba gidan tsit kowa yana cikin daki abun duniya ya isheshi daga ita har umma babu wanda yaci koda kwayar abinci haka shima Khalil yana can yanata yawo daga nan sai nan har gidansu principal din Aryan yaje yace Wallahi idan dansa bai fitoba sai yarufe wannan makarantar tunda har cikin makaranta akaje aka sace Aryan bawai fitowa yayi wajeba,shi dai principal hakuri kawai yake bashi yana cewa insha Allah Aryan zai bayyana,masu gadin makarantar kuwa da securities sunsha tambayoyi kamar babu gobe dan tambayoyin da Khalil ya tsaresu yana yimusu ko agaban alkali ba lallai ayi musu itaba,Emah kuwa ranar yaga tashin hankali saboda shine drivern Aryan shine ke kaishi school yadawo dashi saboda shi PA abubuwan sunyi masa yawa, Emah sai da yaji kamar ya gudu kauyensu dake can anambra state kawai dai dan yasan ko ya gudune oga sai ya nemoshi shiyasa ya zauna amma daga lokacin da yaje dauko Aryan bai ganshi ba zuwa yanzu ya zagaya bandaki yafi sau goma. Hanan tana d'akinta ta idar da sallar ishah lokacin misalin karfe 11 na dare umma ta shigo wai tazo suje asibiti ankwantar da Khalil baida lafiya hawan jininsa ya kada shi, Wani tashin hankalin hankula suka sake shiga domin Khalil baya ko gane wanda yake kansa dayake hawan jini shima akwai kisan mummuke,daren yau dai yanda suka ga rana haka suka ganshi Hanan tayi kuka har ta gaji, Washe gari da sassafe su hajiya suka bayyana a asibitin kowa jikinsa a sanyaye kuma fuskarsa dauke da alhini,kamar masu zaman makoki haka suka zama,shi kuwa Khalil yana can Dr Al'amin yana fama dashi dan acewar Dr nisan kwana ne da Khalil amma da ace mai kararren kwana wannan ciwon yasamu to da yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba, Kwanansa biyu a asibitin sannan ya dan farfado duk da baya gani yadda ya kamata haka kuma jinsa ma ya danyi kasa amma ahakan yake son wai sai yatashi yatafi neman Aryan, Zaid ne ya rirrikeshi yace yayi hakuri shi zaije neman nasa yanzu, Zaid yana fita yasake yunkurin tashi ta hanyar riko Hanan wacce ke zaune gefe, "Karki barshi yatashi.... Idan yatashi faduwa zaiyi" Anty saudat ta fada sannan ta fita daga cikin dakin, Riskeshi Hanan tayi ta mayar dashi ta kwantar kwalla tana fita daga cikin idanuwanta, "Kayi hakuri Abban Aryan insha Allah, Allah zai bayyana shi,mutane sunata addu'a suma kuma jami'an tsaro suna iyakar bakin kokarin su dan ko dazu saida ministan tsaro yazo yace afada maka ka kwantar da hankalinka kaci gaba da addu'a insha Allah suna gab da samo Aryan......" Lumshe idanuwanshi yayi wasu zafafan hawaye suka zubo masa duk sai Hanan taji tausayinsa ya kamata saboda duk abinda zaka ga babba yana kuka to abin ba karami bane, lallabashi aka yita yi har yasamu bacci, Aranar abbanta shima yazo ya jajanta musu dama kuma mutane nata zuwa kamar anyi musu busa,asibitin kullum cika yake dam da matasa da manyan mutane sai yanzu ta sake tabbatarwa da cewa Khalil mai jama'a ne kuma ana sonsa shiyasa idan Allah yabaka dama to kayi iya bakin kokarin ka wurin kyautatawa mutane dan tayuyu zaka bukacesu agaba sai suma su taimakeka a lokacin da kake neman taimakon da kudinka baza suyi maka ba dan wani taimakon kudi bai isa yayi ba sai dai jama'a ce zasuyi maka. Kullum cikin garin Abuja sake baza jami'an tsaro ake sannan gaba daya kafafan yada labarai koda yaushe maganar batan Aryan ne to abunku da dan masu abun,shi kuwa Khalil ya dan fara samun sauki sakamakon ruwan zamzam da Abban Hanan yasa aka nemo ya hada masa maganin hawan jini na musulunci gaskiya zamzam maganine sosai kuma sadidan. Cikin Kashi dari kashi 70 na hawan jininsa ya sauka dan tangararau yake ganin komai yanzu sannan kuma yana jin komai radau kamar da sai dai tarin damuwa dake sakashi zubar da hawaye da rashin cin abinci,idan yatuno Aryan yana hannun wadanda ba asan ko su waye ba sai yaji kamar ya hadiyi zuciya ya mutu dan bacin rai, damuwarsa bai san inda yaronsa yakeba bai san wanne hali yake cikiba sannan bai saniba ko yana raye ko ya mutu shi idanma mutuwarce to har gara Aryan ya mutu agabanshi yakaishi ya binne hankalinsa zaifi kwanciya akan ace bata yayi gaba daya, wannan al'amari shi yake sake daga masa hankali har baya kunyar zubar da hawayensa agaban koma waye dan da yan jarida suka zo asibitin domin ganawa dashi kasa cewa komai yayi inbanda kwalla da yayita fitarwa sai fitar da yan jaridar akayi daga dakin,gashi ko bacci baya samu sai idan allura Dr Al'amin yayi masa shine zai dan samu bacci akalla na awa shida zuwa bakwai, Yau kam saida safe yasamu baccin saboda jiya da daddare kasawa yayi duk da cewa anyi masa allurar, Hanan na zaune kasa kan sallaya tana kallonsa wallahi duk tausayi yake bata idan ta kalleshi dama shi ba jiki ba kuma gashi yasake ramewa cikin kwanaki hudu kacal,yana sanye da farar t shirt da bakin jeans duk yasake zama yaro sakamakon ramar da yayi,ahankali taga ya bude idanuwansa sai kuma taga ya mayar dasu ya rufe hawaye na zirarowa ta gefen idonshi, Tashi tayi ta matsa gaban gadon ta durkusa akan gwiwowinta ta kai hannu kan nashi wanda ke soke da cannula ajiki,bai bude idonsa ba kuma bai motsa ba,kwantar da murya tayi koda yake dama muryar tata akwance take sakamakon kukan da itama ta shassha, "Dan Allah Abban Aryan kayi hakuri muci gaba da addu'a insha Allah Aryan zai bayyana kuma baza su samu ikon cutar dashi ba domin yana tare da kariyar ubangiji....." Shiru tayi tana sake zuba masa ido ji take yi kamar ta rungume shi ajikinta taci gaba da rarrashinsa kamar jariri,jin za abude kofa ashigo yasata dan matsawa, Khalid ne yashigo shima hankalinsa duk yatashi dan shi bai san hakan tafaru ba sai jiya da daddare dama matsalar zaman nesa kenan sai ayi abu agida kai baza ka ji ba shiyasa har gobe yake takaicin zaman Calabar dinnan da yakeyi domin abubuwa da dama baya sanin anyi sai yazo yake ji, Zuwan Khalid dinnema yasa Khalil ya dan samu saukin damuwarsa kasancewar wani lokacin childhood friend dinka yana da abubuwa daban daban wad'anda zai yimaka har yasamo kanka,duk da dai akwai damuwar amma ya dan ji saukinta. Bayan sallar la'asar kawai sai ganinsa suka yi yafito daga cikin dakin da yake kwance yana bacci,kowa tashi tsaye yayi har securities dinsa, Khalid ya kalla, "Bani aron key din motarka zanje wani wuri indawo...." Kowa dake wurin zaro ido yayi nan aka fara tambayar ina zashi? Hajiya kuwa tiburewa tayi tace babu inda zaije idan kuwa ya dage sai ya tafi to dole yatafi da masu kula dashi shi kuma yace A'a,dafashi Khalid yayi yace, "Haba Khalil.... Ina zaka je acikin wannan halin kuma? Kafa san yanda kuke koda yaushe mutane suna fakonku..... Dan Allah ka koma ka kwanta" Hannun Khalid yaja suka shiga dakin mintuna biyu suka sake fitowa, "Hajiya babu matsala insha Allah kubarshi yaje yadawo din..." Khalid yafada cikin kwantar da hankali, Duk da haka dai hankula basu kwanta ba da fitarsa shi daya nan suka dunguma suka bishi har harabar asibitin inda yashiga motar Khalid mai dauke da bakaken gilasai,yafita daga cikin asibitin kamar zai tashi sama saboda yanda yake sharara gudu,zuba ya hara cikin kankanin lokaci ya isa yana tuki yana duba wayarshi yana bin direction din da aka bashi har ya isa wani hamshakin tangamemen gida,horn yayi wasu garada su kimanin guda biyar suka zo suka bude dukkaninsu fuskokinsu rufe da mask, ahankali yatura hancin motar tasa ciki sannan yayi parking yafito, Sakashi suka yi atsakiya suka yimasa jagora har cikin wani kerarren falo mai dauke da Royal furnitures,juyawa sukayi suka fita yarage saura shi daya acikin falon, Minti biyar yana tsaye hannayensa cikin wandon jeans din dake jikinsa yaji wani azababben kamshi yasoma ziyartar hancinsa ahankali cikin takun jan hankali da kasaita ta bude kofa tafito tana taunar cingum, Daga idonsa yayi ya kalleta tana sanye cikin kayan bacci na daukar hankali farare tatas wadanda babu abinda suka boye na daga kyakkyawar surar da Allah yayi mata,doguwar rigace iya gwiwa da yar top dinta asama wacce ta tsaya iya kirjinta, "Yesmin......" Yafurta akan labbansa, "Barka da zuwa fadata mai girma minister....." Ta fada cikin jan hankali tana kokarin zama kan daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya, "Yesmin...... Ina kika kai min yaro na?" Ya fada fuskarshi babu rahma ko kadan, "Karka damu yaronka yana nan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali..... Babu abinda ya sameshi" "To me kike nufi da hakan da kikayi? Me kike bukata daga gareni?" Ya bukata cikin bacin rai domin tuni hakan ya bayyana akan fuskarshi, "Yawwa sai yanzu kazo gabar da najima ina son kazo...." Mikewa tsaye tayi tana karairaya da salo na jan hankalin duk wani da namiji mai cikakkiyar lafiya, "Abinda najima ina so daga gareka tsawon shekara da shekaru....." Marairaicewa tayi harda kwallar karya da yaudara,ta matsa dab dashi kamar zata rungumeshi, "Dan Allah Khalil kaji kaina....,ka taimaka min kada ciwon sonka ya zama ajalina.....pls....pls" Juya mata baya yayi domin yasan idan yaci gaba da kallonta ahaka za a iya samun matsala domin tausayin ta zai iya shigarshi shi kuma baya son yaji tausayin ta adaidai wannan lokacin, "Yesmin abinda najima ina fada miki yau ma shi zan sake jaddada miki.... Bana zina ban taba yinta ba kuma bana sha'awar inyi har tsawon karshen rayuwa ta.... Ina yarona yake? Kifito min dashi dan shine yakawo ni bawai bukatar ki ba...." Dan lumshe idanuwanta tayi sannan ta budesu akanshi wannan fa wani lakani ne aka jima da bata akanshi kuma dole sai yayi zina da ita sannan maganin zaiyi tasiri har yayi aiki gashi wannan itace damarta ta karshe idan har hakanta bai cimma ruwa ba to komai zai rushe, "Gashi can cikin wancan dakin...." Ta nuna masa dakin dake kusa da wanda tafito daga cikinsa, Cikin jarumta da rashin tsoro ya dirfafi dakin, "Sadauki..." Tafada ahankali tana kokarin bin bayansa wannan yana daya daga cikin abubuwan da ke kara ingizata duniyar son taga ta mallakeshi domin baida tsoro ko kadan ga nuna shi namiji ne agaban ko waye, Cikin kwarin gwiwa Khalil yabude kofar dakin yashiga mai dauke da duhu dan kamar ba a halicci haske ba aduniya haka dakin yake,laluben makunnar hasken dakin yafara yi amma yarasa sai shashimawa yakeyi yana kiran, "Aryan..... Aryan" Haske ne yaga ya gauraye dakin cikin sauri yajuya ya kalli kofa,yesmin yagani tsaye tana rike da key din kofar dakin sannan ta cire yar rigar saman rigar baccinta gaba daya kirjinta yafito fili ta yar raga ragar dake saitin kirjin rigar, "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un...." Yafada yana juya mata baya, murmushi tayi ta kai hannu zuwa ribon dinta dake daure da yalo yalo gashin kanta nan tacire ribom din ta jefar ta baza gashin nata ya sauka saman kafadarta,takawa tafara yi ahankali tana dosarsa maganganun malaminta na sake fado mata "Sai kin yi zina dashi tunda bai taba yin zina ba sannan bukatarki zata biya..." Lumshe idanuwanta tayi cikeda kwarkwasa takai hannu zuwa gareshi......................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din. *32* ***Dafa kafadarshi tayi sannan cikin sanyin murya mai dauke da tsantsar yaudara yaji tace, "Wai meyasa kake guduna ne Ibrahim? Gaka dai ahaka kamar wayayye..... Kana da kudi,kyau, kuruciya uwa uba ga mulki to meyasa bazaka more rayuwarka kaji dadi ba? Sai yaushe ne zaka waye? Idan baka huta yanzu ba sai ka tsufa ko yaya?" Lumshe idanuwanshi yayi domin tab'ashin da tayi ji yake yi kamar ta watsa masa garwashin wuta ajikinsa, "Yesmin..... Ki nuna min inda yarona yake kawai domin ni ba wannan ne ya kawoni ba..." Rigar baccin dake jikinta ta soma sabulewa tana kokarin shan gabansa, "Me kake ci na baka na zuba? Zaka ga yaronka amma har sai nima ka amince da bukata ta..." Bude idanuwanshi yayi da zummar balbaleta da fada amma abinda idanuwanshi suka gane masa yasashi saurin runtse idanuwanshi yana furta, "Wa'iyazubillahi.... Yesmin dama bakida hankali? Ke wacce irin sakarya ce?" Rabon da yaga sankaceciyar budurwa tsirara har yamanta sai yau da yayi mummunan gani sanadiyyar ta, Kokarin rungumeshi take yi yayi gaggawar matsawa nan ta sake matsowa yasake matsawa bata hak'ura ba ta sake yunkurin matsowa bai san lokacin da ya dauketa da wani gigitaccen mari ba abunka da bahago bai iya duka ba shiyasa sai da taga wasu taurari sun gilma ta idanuwanta sannan taji jinta ya dauke na dan lokaci, kuncinta ta dafe tana kallonsa cikin mamaki da bacin rai, "Ibrahim ni ka mara? Dan kawai na nuna soyayya ta agareka?" "Na mareki..... Ai kadanma kika gani tunda ke wawiya ce dakikiya marar tunani... Ina yarona yake? Wallahi idan baki fito min dashi ba sai nayi miki dukan kawo wuka,sai nayi shari'a dake ke saima na kasheki......sai nayi ajalinki....." "Ka fita waje zaka samu yaronka acan amma ka sani Wallahi sai kayi nadamar abinda kayi min....sai ka san ka mareni kuma ka wulakanta ni" Bai sake tanka mata ba yawuce ta yafita tare da bugo kofar dakin da wani mugun karfi,abakin kofa yaga biyu daga cikin garadan nan na dazu masu kama da samudawa,wani mugun kallo yayi musu sannan ya ratsa ta tsakiyarsu yawuce yana kaiwa tsakiyar falon yaga Aryan yataso da gudu yazo ya rungumeshi yana kiran, "Daddy.... Uncle...." Rungumeshi shima yayi sannan ya durkusa gwiwowinsa akasa yana dudduba jikin Aryan din, "Abba na babu abinda suka yimaka? Sunyi maka wani abu?" Jijjiga kai yayi yana sake makalkale Khalil,daukarsa yayi yajuya ya kalli bakin kofar dakin nan yaga yesmin tsaye tare da garadanta tana yimasa wani kallo mai cike da ma'anoni kala kala,fita yayi yabude motar da yazo da ita ya saka Aryan sannan ya bude side din driver shima yashiga ya zauna yayi reverse da mugun gudu yafita yabar gidan, "Aryan ya akayi ka bari suka sace ka? Haba Aryan kaida nake ganinka kamar mai wayo ashe bahaka bane...." "Daddy da aka tashi daga school ne sai naga mota irin tamu kuma wani mai kamada Emah yazo yakama hannuna shine nabishi muka tafi....." "Kaima dai soko ne Aryan,you are such an idiot....daga ganin mutum sai ka bishi? Suna baka abinci kana ci?" Kai ya daga babu bakin magana duk ya tsure dan yasan watakila sai Khalil ya zaneshi saboda duk wannan soyayyar da yake yimasa fa idan yayi laifi babba to rufe ido yake ya zaneshi da belt shiyasa tun yanzu tsoro ya darsu a zuciyarsa dan yasan zaisha duka. Can asibiti kuwa hankula sun sake tashi domin anata kiran wayar Khalil baya dagawa kuma gashi shiru shiru bai dawo ba, hajiya fadi take, "Sai da nace yaron nan kar yadauki motar nan ya fita amma ina sai da yafice.... Ko meyasa yakeda taurin kai oho" Suna tsaye carko carko kowa na fadin albarkacin bakinsa Khalid ya koma gefe ya dauki wayar da Khalil ke yimasa, "Ya andace kuwa?" "Ehh gashi na taho dashi dagaske ai itace ta saceshi,ku tattaro ku taho gida kawai..." Katse wayar Khalid yayi yakoma wurin su hajiya yace suje su tafi gida shima khalil din ya tafi gida ansamo Aryan dan tare suke nan sukaje suka dudduru amota suka nufi gida tare da securities dinsa. Shi kam tun daga zuba yake haduwa da jami'an tsaro amma da zarar sun tsayar dashi yana sauke glass idan sukayi ido hudu sai su matsa gefe suna fadin "sorry sir" Duk mamakin ganinshi shi kadai sukeyi ba tare da securities ba gashi mugun gudu yake yi dan shi sam bai iya jan mota a hankali ba gudu yake kamar zai tashi sama, Yana zuwa gidansa kuwa wani uban horn yashiga zubawa duk yabi ya cikawa masu tsaron kofar kunne sukuma basu san shi bane, full light yayi ya haskesu hakan ya kular da ben daya daga cikinsu ya taso da sauri yana gyara zaman bindigarsa akafadarsa alamar zaiyi rashin mutunci,tun kafin ya karasa Khalil ya sauke glass din zuwansa keda wuya yaga Khalil idonshi na kallon gate din yana mamakin wannan lamari wai shi da gidansa amma anbarshi yana jira sai sun gama shuka rashin mutuncinsu sannan zasu bude, Da gudu ben yaje yabude gate din sannan ya matsa gefe yana neman afuwa, Khalil baiko kulashi ba ya saka hancin motar zuwa cikin gidan,shi kuwa ben alama yarinka yiwa sauran da baki wai ogane fa da kansa a wannan motar, Yana kokarin fitowa daga cikin motar bayan yayi parking securities din suka karaso suna yimasa sannu da zuwa da tayashi murnar bayyanar Aryan wanda yafito rike da school bag dinshi, Ciki suka shiga yawuce part dinshi Aryan na biye dashi, Yana bathroom yana wanka su hajiya suka shigo dukkaninsu sashen Khalil suka shiga har Hanan ganin Aryan aka shiga yiwa juna barka da taya juna murna,a lokacin Hanan taje tayi masa wanka tasako masa kananan Kaya har lokacin suna part din Khalil acikin falonsa sai ciye ciye akeyi cikin farin ciki, Khalil ta kalla yana sanye da jajayen jersey da dogon wando da juice a hannunshi yana kurba,kan cinyar Khalil Aryan yaje yahaye ya zauna ana shan hira ohhh wai yau sune cikin farin ciki haka kamar ba sune kwanaki biyu da suka gabata suke cikin damuwa da zubar da hawaye ba. Raba dare suka yi a b'angaren Khalil dan ita kam Hanan saima tafiya tayi ta barsu lokacin karfe 11 na dare,wanka tasamu tayi da ruwa mai dan zafi sannan ta saka rigar baccinta ta kwanta, Su hajiya kuwa har wurin 1 na dare suka kai daga bisani suka tafi suka bar Khalil da Khalid, kallon Khalil Khalid yayi yace, "Malam ni zo ka nuna min nawa makwancin nima inje insaka hakarkarina dan gobe asubanci zanyi inbar garin nan.... wallahi hutun kwana daya kacal suka bani..." "Ga bedroom nan kana gani kaje ka kwanta mana..." Khalil ya fada yana nuna masa da hannunshi, "Dan Allah ni ka kaini dakin da zan kwana,ya zaka nuna min master bedroom dan wulakanci? Idan matarka tazo fa.... Kasan kai babban mutum ne sai dai abiyoka" "To nidai bani da wani dakin idan ba wannan ba..." Tashi Khalid yayi yana kokarin cire rigar jikinsa yanufi cikin dakin yana fadin, "Ni dai nashiga ciki idan zaka takura kuma saika bakunci dakin matarka" Banza Khalil yayi dashi yaci gaba da danne dannen wayarshi. Bayan wasu mintuna da shigar Khalid shima yatashi yashiga,kwance yasamu Khalid yana waya da matarsa Muneerat sai wani lankwashewa juna murya suke yi tamkar saurayi da budurwa, Gefen gadon yasamu ya lallaba ya kwanta kanshi yana dan sara masa Allah sarki Ramlat yanzu da tana raye da shima yana da gata irin gatan da duk wani magidanci yake samu idan har ya amsa sunan dan gata awurin matarsa, Abubuwane suka shiga dawo masa kamar yaune suke faruwa,tuno lokacin da suke samari yashiga yi Khalid haka zai raba dare yana waya da budurwa shi kuma abinda bai iyaba kenan dan sam baida jimirin yin waya sai idan ta zama dole amma zai iya wuni yana chaten ta waya yafi yimasa sauki akan yayita magana,yanata tunane tunanensa shi dai ahaka bacci ya d'aukeshi yabar Khalid yana ta fama, dayake rabon da yasamu bacci mai dadi tun gabannin sace Aryan shiyasa yau ya nutsu yayi daga shi har Khalid din da yake ta kurin zaiyi asubanci duk makara suka yi dan har aka fito daga masallaci basu saniba,koda Khalil ya farka tuni gari yayi haske fayau sai dai shi nasa dakin kamar dare, fitilar dakin ya kunna ya mike yashiga bathroom yayi wanka sannan yayi brush da alwala yafito rike da dan karamin towel yana sake goge jikinsa, "Khalid...... To sai ka tashi ai kayi salla ko har yanzu ana nan dai hali bai canja ba? Ka raba dare kana soyayya kuma ka kasa tashi sallar asubah..... Kanata cika bakin asubanci zakayi waye waye ni dama kawai jinka nake yi ai" Tashi Khalid yayi yawuce cikin bathroom,sai da yayi wankan shima sannan yafito saboda ason samunshi yana yin salla zai wuce,jam'i suka yi duk da sun makara bayan sun idar Khalid yace, "Ranka yadade ni baka karasa sanar dani abinda yafaru ba jiya ina gama waya naga har kayi bacci...." "Khalid Wallahi yarinyar nan a daki ta sakani ashe wai wayo zata yimin tace Aryan yana ciki ashe karya take,intakaice maka labari dai wallahi niked tayi agabana...... Dakyar na kwaci kaina" "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,ai wasu matan hatsabibai ne nake fada maka,makirci dama ta shirya sai dai Allah ya cigaba da tsareka daga sharrinsu...." "Amin Khalid ni wallahi narasa gane da me nafi sauran naza da kowacce mace ke kawo min farmaki,kaga idan office naje suna biye dani,idan kasar na bari suna biye dani duk inda naje suna bina...... Ni Wallahi mulkin nan duk ya isheni baida wani dadi ko kadan sai tarin stress da wahalhalu" "A'a ka daina fadin haka,mulki fa Allah ke baiwa wanda ya zaba kuma yaso,kai dai kaci gaba da addu'a... Amma ya kamata ka dauki mataki akan yarinyar nan gaskiya ko dan saboda gaba" "Ehh akwai matakin da zan dauka amma ina sone inyi magana da lawyer dina first inyaso sai inji shawarar da yake ganin yadace mubi...." Wayarshi ya dauka yana duba time 6:30, text ya turawa Hanan akan ta kawowa Khalid breakfast tafiya zaiyi, Allah yaso ta tashi kuma wayarta a kunne take,sauka tayi zuwa kitchen ta samu john na ta aiki yana soya dankali sannan gefe daya yana hada vegetables sos, diban wanda ya tsame tayi sannan ta harhada masa sauran kayan tea ta dauka ta haura sama,a bakin kofa ta jira bayan tayi knocking domin har yanzu bai bude kofar ba,fitowa yayi yazo ya bude mata tawuce ciki yana biye da ita,kan dining table ya nuna mata taje ta dora kayan sannan ta juyo ta dan kalleshi yana kokarin kunna tv da remote a hannunshi, "Ina kwana?" "Lafiya lau....." Juyawa tayi zata fita taji muryar Khalid yana cewa, "Madam mun saki fitowa da sassafe ko?" "Lahh ai babu komai,ina kwana?" Suna gama gaisawa tayi waje domin Khalil sai daddaure fuska yake yi dan baya son Khalid yayi masa baran barama ya jawo masa reni, Aranar suma su hajiya suka tafi gombe,duk da anga Aryan Khalil bai fitaba dan Dr Al'amin har gida yazo ya dubashi yace ya dan bari tukunna har sai yakara warwarewa, Manena labarai da yan jarida har gida suka biyoshi suka ji ta bakinsa dangane da batan Aryan da kuma yanda akayi aka ganshi,bai fito fili yasanar dasu yanda aka ganshin ba kawai dai ya basu tabbaccin cewa masu yin garkuwa da mutane ne suka saceshi kuma yana kan yin bincike dan gano ko su wanene,bayan tafiyar yan jarida ya kira emah yasake tsareshi da tambayoyi domin Aryan yace wani ne mai kama da Emah din yazo ya kama hannunshi yakaishi mota to shikuma wannan din yake son gano ko waye saboda yanzu duniya ba abar yarda bace kana tare da mutum sai a iya hada baki dashi a cutar dakai, sai da yagama yiwa emah tambayoyi masu kada masa yan hanji sannan ya sallame shi yatafi yana fita ya danko kunnen Aryan guda daya har cikin bedroom dinshi belt ya dauka yana tambayar shi, "Nan gaba zaka kara bin wanda baka saniba? Zaka kara bin mutumin da baka san ko waye ba?" Girgiza kai Aryan yayi yana fadin, "Allah Daddy bazan sake ba...." Zaneshi yayi sannan ya sakeshi, cikin fad'a yace, "Get out of here wawa kawai...." Fita Aryan yayi yana kuka yatafi wurin Hanan, bata taba ganinsa yana kuka haka ba sai yau tunda tazo gidan,daukarsa tayi tafara lallashinsa tana tambayar meya sakashi kuka, "Uncle ne ya....zaneni...." Gwalalo ido Hanan tayi dama Khalil yana dukansa? Tohh ashe dai duk soyayyar yana daukar mataki, rarrashinsa taci gaba dayi har yayi shiru bacci ya d'aukeshi. Tana can wurin umma suna hira Aryan yasauko yazo ya hau jikinta duk jikinsa zafi alamar zazzabi, daukar shi tayi ta nufi sashen uban dashi,samunshi tayi zaune da laptop dinshi kan glass table agabanshi yana aiki, wannan mutum dai ko shine agogo sarkin aiki sai haka dan koda yaushe cikin aiki yake, Daga ido yayi ya kallesu itada Aryan wanda ya kwantar da kai a kafadarta, "Ka taba jikin Aryan kaji kamar zazzabi yake yi....." Mika hannu yayi ya karbeshi, "Na zaneshi ne shiyasa watakila zaiyi zazzabin...." Shiru tayi bata ce komai ba ta tsaya tana kallon su yana ta tattaba jikin Aryan yana fadin, "Am sorry lovely son, zazzabi ne ko? Bari inkira Dr yazo yabaka magani kaci abinci?" "Baici abincin ba,yanzun nan yatashi" Hanan ta bashi amsa dan tasan Aryan cewa zaiyi yaci saboda baya son cin abinci, "Ok je ki kawo masa" Fita tayi shikuma yakira Dr Al'amin ita dai tana ta mamakin Khalil saboda a tsananin son da taga yana yiwa Aryan to bata taba tsammanin Wai zai iya saka hannu ya dakeshi ba. Zazzabin kwana biyu Aryan yayi sannan yakoma school domin yawarke garau haka shima uban ya warware domin har ya soma fita office. A ranar da yamma mummunan labari ya sameta wai wata matashiya takai Khalil kara babbar kotu akan yunkurin yimata fyade adaren ranar larabar da ta gabata..........................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *33* ***Tsoro,mamaki da kuma damuwa sune suka taru suka rufe Hanan lokaci guda,jin wai wata matashiya takai Khalil kara kuma da laifin yunkurin yimata fyade kai jama'a wannan abu da me yayi kama, Rasa abinda zatayi tayi kawai sai ta nemi wuri ta zauna nan cikin falonta tayi tagumi,to shin dagaske ne kodai sharrine kawai wannan matar take kokarin yimasa dan dukda cewa ita bata wani zauna tare dashi na tsawon lokaci ba amma sai taga kamar baida lokacin aikata hakan,shiru dai tayi da bakinta bata ce komai ba sannan kuma babu wanda ta fadawa ahaka Aryan yashigo ya sameta yadawo daga makarantar yamma wato islamiyya wadda shi agida ake yimasa tashi, Kafin kace me tuni labari ya karade kafafan yada labarai wai Khalil yayi yunkurin yiwa yesmin fyade agidanta dake can zubah, nanfa wad'anda basu sanshi ba suka fara Allah wadai dashi wadanda suka sanshi kuma suka fara karyatawa suna fadin ai wannan shaci fadine kawai irin na wasu matan marassa tsoron Allah amma Khalil bazai aikata hakaba dan haka wannan labarin baida maraba da kanzon kurege. Khalil Kam shi bama ya k'asar dan haka baima san abinda yake faruwa ba yana can Seoul babban birnin k'asar Korea, Khalid ne yaci karo da posting din a Instagram shine yayi gaggawar Kiran Khalil yana tambayar sa, murmushin takaici Khalil yayi zuciyarsa na tafarfasa saboda bacin rai, "Wallahi wannan karon sai na nemi hakkina awurin yarinyar nan...... Text massage fa tayi min Khalid cewa inje inkarbo Aryan wai yana wurinta kuma kar natafi da securities saboda wani dalilinta marar amfani kuma na yarda natafi ahakan ni daya.... Taje tayita kaiwa k'arar dan Allah karta fasa amma nima yanzu zata ga the other side of me...." Kitt ya kashe wayarsa cikeda bacin rai saboda yasan zubar masa da mutunci kawai yesmin ke sonyi, so take ta goga masa bakin fenti abanza gashi yan media sam basu iya daukar abuba sai ayita yamididi dakai ana nuna ka kamar watan ramadan, tamkar Khalid ya bude kofar kiran Khalil nanfa yan uwa da abokan arziki suke ta go slow din kiransa daga kiran wannan yashigo sai na wannan, Bai dauki kiran kowa ba sai na anty saudat babbar yayarshi wacce yake bi,yana dagawa yaji ta rufeshi da fada tana cewa abinda yayi ya kyauta kenan? Yanzu yadace da girmansa da komai arinka buga labarinsa a jaridu da mujallun k'asar nan cewar yayi yunkurin ketawa mace hadddinta? Fada anty saudat take yi ta inda tashiga ba ta nan take fita ba dayake itama mafadaciya ce akwai fada babu laifi, kwata kwata taki tabarshi yayi magana sai zuba masa ruwan masifa take dama shima to afusace yake dan haka ya katse kiran dan ta cika masa kunne da fadanta, Sake kira tayi tana jin ya daga tafara fadin, "Ibrahim ni kake kashewa waya? Ni ka katse mawa waya saboda na kiraka ina fada maka gaskiya?" "To danme zaki kirani ki sakani agaba kina wani yimin fada kamar karamin yaro? Ba zaki tambayeni kiji abinda yafaru ba...." "Anki atambayeka din..." "To kar Allah yasa ki tambaya din,duk abinda kikaji akaina ance hakane ina shikenan? Ko da...." "Kaje kayi fin haka ma idan kaso sunan wa zaka bata? Ba sunanka bane...." Yana jiyowa daga kusa da ita ana yimata magana kan cewa bai kamata ba wannan abun da sukeyi kamar wasu kananan yara yasan bazai wuce mijinta ba dan kamar muryarsa yaji yana cemata tayi shiru,"Ni baka jin abinda yake fada min? Ba kanina bane shi? Akan me zai rinka gaya min kananan maganganu?" Shi dai katse wayar yayi yana kokarin ajiye ta kiran lawyer dinshi yashigo wato Barrister muhsin nan ya dauka ya zayyanewa barrister duk abunda yafaru sannan yakara da cewa, "Barrister nima ashigar min da Kara a nema min hakkina na sace min yaro da tayi har tsawon kwana biyar wanda sanadiyyar hakan har saida ta kaini ga kwanciya a gadon asibiti, sannan a nema min hakkina na bata min suna da tayi..." "Babu matsala ka kwantar da hankalinka insha Allah komai zai daidaita kuma sai tayi nadamar abunda ta aikata,ai bata san me ake kira da shari'a ba shiyasa har tayi saurin kai k'ara...". Barrister muhsin yabashi tabbaci sallama suka yi suna gama waya da barrister ya kashe wayar gaba daya bayan ya sakata a flight mood. Kwana biyu da faruwar lamarin ya dawo Nigeria yaci gaba da gudanar da harkokinsa, Hanan na son tambayar sa dangane da rade radin da ake tayi akansa amma bata ga fuskar yin hakan ba domin Khalil wani kwarjini gareshi na musamman idan har ya tsare gida to sai kaji tsoron tunkararsa ko kai waye dan su kansu yan jarida suna ta son suji ta bakinsa amma abun ya gagara. Dawowarsa da kwana biyu yatafi gombe saboda anshirya family meeting akansa amma iya manyanne babu yara, Abban su Khalid tsareshi yayi da tambayoyi to amma da yake mutum idan da gaskiyar sa baya tsoron amsa kowacce irin tambaya haka ya amsa musu dukkan abunda suka tambayeshi daga karshe tattaunawar ta tashi bayan kowa ya yarda dashi. Daga wurin family meeting din nasu gidansu yawuce duk da sun hadu da su hajiya acan sai da suka sake zama da hajiya suka tattauna sannan yatafi ya koma abuja, Haka dai labari yaci gaba da yaduwa har aka fara zaman kotu shi dai baya samun halattar zaman kotun sai lauyansa shine ke ruwa da tsaki domin acewar lauya shi Khalil ayyukansa bazasu bari ya samu damar zuwa ya zauna a kotu ba. Ita kam Hanan zaman gida da rashin sanin takamaimai abinyi sune suka taru suka sakata agaba,wata zuciyar sai tace mata kodai ta koma masters degree dinta ne koda kuwa online ne,gashi yanzu inbanda kwadayin zuwa gida babu abinda take yi tana ta son taje gidansu dan wani lokacin har mafarki take yi saboda tsabar yanda ta saka abun aranta haba aima tana ganin kamar tayi kokari wata tara fa yanzu rabonta da gida tasan da akusa da gida tayi aure ai da tuni taje gida yafi akirga,tana son tambayar Khalil amma tana jin tsoro dan tunda abun nan yafaru yasake zama wani marar son magana,daurewa dai tayi ta rufe ido tayi masa text wai tana son taje taga yan gida,reply yadawo mata dashi lokacin yana wurin wani taro acan garin yola shida mataimakin shugaban k'asa, _Me akeyi agidan?_ Shine tambayar da taga yayi mata, murmushi tayi aranta tace "wai shi dai mutumin nan baya rabo da tambaya ne? To kawai sha'awar zuwa gidan nakeyi" hakan kuwa ta tura masa amma sai taga yadawo da reply yace wai ba yanzu ba,ranar Hanan harda kukanta au dama haka mata keji idan suka bukaci futa aka hanasu? Wallahi sai yanzu take nadamar zaman gida da tayi ta rinka kunshe kanta agida bata fita ko ina daga makaranta sai gidan anty salaha dama ita ba kawaye gareta ba sai abokan mutunci balle ta rinka yawon bin gidan kawayen,ranar har yajin cin abinci tayi sai uban kuka da tasha dan har agaban Aryan tayi. Bayan sallar ishah Khalil yadawo gidan, Aryan na dakinsa yana game din zumah a laptop dinshi khalil yafito daga wanka sanye da rigar wanka ajikinsa, "Papa..... Mommy yau tayi kuka.... Kuma taki taci abinci..... Bata da lafiya" Dakatawa yayi da goge kanshi da karamin towel da yake yi ya kalli Aryan, "Jeka ka kirawo min ita...." Tashi Aryan yayi ya fella da gudu yafita ita kuma tayiwa Aryan wayone da yake tambayar ta wai meyasa take kuka sai tace bata da lafiya ne,tana zaune falo tana kallon tashar Bollywood inda suke haska wani film _Ek villain_ Aryan yashigo yana kiranta, "Mommy kizo inji Daddy... Uncle ne yake kiranki" Daga haka yanda take ta mike tabishi saboda doguwar rigace ajikinta yar kanti da bakin siririn mayafi akanta sai kawai ta cire mayafin ta warwareshi ta yafa akanta, Lokacin da suka shiga a falo ta tsaya bata bi Aryan zuwa bedroom din Khalil ba,agaban mirror Aryan ya sameshi yana fesa turare hannu daya kuma yana gyara sumar kanshi, "Unlce tazo..... Taki shigowa" Murmushi Khalil yayi yace "Abbana baki abun magana,akwai ka da surutu yaron nan kamar zaka sauko da sarki daga kan doki,jeka wurin umma tana kiranka" Shi dai Aryan daukar laptop dinshi yayi yafice,da yaje falonma bai tsaya ba wai Daddy yace yatafi wurin umma, Tafi mintuna goma azaune bai fito ba Wallahi wannan mutumin da jan ajin tsiya yake da mulki ta raya hakan aranta,bata gama tunanin hakanba taji motsin fitowarsa,farar riga t shirt ce ajikinsa ta kamfanin Nike sai bakin wando jeans kamar yadda yasaba shigarsa amafi yawan lokuta,gaba daya kamshinsa ya karade farfajiyar cikin falon, "Ina wuni....?" Ta fada kanta akasa,dan kallonta yayi sannan ya amsa, "Lafiya lau..." Daga haka babu wanda yakara magana acikinsu har tsawon wasu mintuna, "Me ya sameki kike kuka? Bakida lafiya ne?" Jin tambayar da yayi mata yasata girgiza kai alamar A'a, "Lafiyar ki lau kika zauna kina yiwa mutane kuka?" Shiru tayi bata amsa masa ba domin tasan ai yasan dalilin kukanta bashine ya hanata zuwa gida ba da ta tambayeshi,tasan Aryan ne zai fada masa cewa tayi kuka, Shiru yayi yana dan nazarinta kadan,shi baya son ta tafine tabar Aryan domin akwai shakuwa mai karfi tsakaninsu,yanda ta damu da yaron haka shima ya damu da ita, "Ko akan na hanaki zuwa gidane? Shikenan bari zan kira Abban naki infada masa...." Nan dinma shirun tayi duk da taji abinda yace wai zai kira abba yafada masa,bata yi magana ba dan haka yace, "Tashi kije..." Tashi tayi tawuce tafita,tana fita kuma kamar daga sama taji wata kara taratsatsaaaa gaba daya glass din wurin ya tarwatse awurin ya watsu jikinta babu shiri ta durkushe awurin saboda azaba, Khalil dake zaune a falonshi shima yajiyo karar tarwatsewar glass dan haka da sauri yatashi yafita domin duba abinda yafaru,yana fita yaganta durkushe ga gilasan nan tarwatse awurin da sauri ya nufeta dan ganin halin da take ciki.......................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *34* ***Kamar acikin mafarki taji ya rikota ya dagota hankalinsa amutukar tashe saboda ganin irin yawan glass din da ya tarwatse,cikin tashin hankali yake furta, "Ya yanke ki?...... Ya sameki?" D'aga kai tayi cikeda azaba sakamakon jin glasan da takeyi acikin jikinta,fuuuu taga ya jata zuwa cikin falonsa kuma tun daga cikin falon yasoma cire dan mayafin dake lullube kanta, Tiryan tiryan yarinka janta har zuwa cikin bathroom din dake cikin falon domin aganinsa shi yafi kusa fiyeda wanda ke cikin dakinsa duk hankalinsa yagama tashi wanda bata san dalili ba, Suna shiga cikin bathroom din yasoma cire mata mitsi mitsin gilasan dake wuyanta domin kaifine dasu kamar anfeke ita kanta tana jin radadin shigarsu acikin jikinta kuma sunfi shiga wuyanta da bayanta,lumshe idanuwanta tayi jin yana kokarin cire rigar jikinta,duk sai taji kunya tabi ta dabaibaye ta ganin da gaske cirewar yayi yana cigaba da cire mata glass din,a lokacin da yake kokarin cire mata doguwar rigar jikinta sauran gilasan dake jikin rigar sun zuba cikin farar bra din dake jikinta nan taji shima kirjinta yadauki radadi amma bata fatan azo gabar da zaice nan dinma sai ya cire,shi bama ta jikinta yake yiba ta ganin yarabata da wadannan mitsi mitsin gilasan yake yi domin suna iya kashe mutum har lahira shiyasa bai tsaya wata wata ba yafara kokarin cire bra dinma, hannu biyu tasa ta kare kirjinta bai kulaba yaci gaba da abinda yake yi domin harsu cikin gashin kanta duk gilasan sun shiga kuma ciresu dole saida dabara dan ahakanma gashi nan wurare da dama duk sun dan yanyanketa, Ganin ya maida hankali kan gashin kanta yana ciccirosu daya bayan daya yasata dan daga ido ta kalleshi nan shima ta hango glass din a wuyansa abinka da farar fata shi har yankan ya bayyana,hannu ta mika tama manta ahalin da take ciki ta zaro glass din, "Kaga ashe kaima ya yankeka...." Sai da ya tabbatar da ya cire mata su tass sannan ya kalleta cikin sauri ta kare kirjinta da hannunta,kawar da kanshi yayi, "Kiyi wanka ina zuwa bari zan kira Dr ya dubaki..." Daga haka yajuya yafita wayarshi ya dauka yabi ta kofar baya yasauka k'asa yana tafe yana yiwa Dr Al'amin text akan yazo cikin sauri yana nemansa, Securities dinsa na hangoshi lokacin da yake kokarin fitowa nan sukayi saurin mara masa baya,dama shi idan abu yafaru da kansa zaka ganshi yafito,idan kaga Khalil agidanshi zakayi mamakin jin wai shine minister,saboda irin yanda yake gudanar da sabgoginsa da al'amuransa da lokacin da yana tsohon gida sai kaje ka samesu shida Aryan suna yin ball wani lokacin harda yaran neighbors idan sun shigo, Wurin chief security yaje yarinka yimasa fada yana cewa menene aikinsu agidan idan har abu irin wannan zai rinka faruwa,kenan zamansu bashi da wani amfani matsawar ba zasu rinka kulawa da kyau ba,yanzu gashi nan an iyo jifa ya fasa glass har yasamu Hanan,da Aryan ne ma awurin haka zai sameshi ko shi kansa,shi dai chief security hakuri kawai yake bashi yana cewa insha Allah haka bazata kara faruwa ba kuma yanzunma zai zurfafa bincike har sai yagano musabbabin faruwar hakan, Wanka Hanan tayi kamar yanda yace ta dauki towel dake rataye cikin bayin ta daura ta kwaso kayanta da ta cire ta fito sadaf sadaf kamar wata marar gaskiya,ganin baya cikin falon yasata fita ta wuce part dinta tana zuwa ta saka doguwar riga mai gajeren hannu ta dauki turare tafesa nan taji kamar tayi kuka sakamakon zafin da taji ajikinta ta manta ashe ta yanyanke, muryar Aryan tajiyo afalo kuma da alama shida umma barira ne dan itama tajiyo maganar ta,dan karamin gyale ta dauka tafita, sannu umma tayi mata tana cewa ashe abinda yafaru kenan yanzu Khalil ke sanar dasu a k'asa, Suna nan zaune tare da su umma yaturo mata da text wai taje yana kiranta,tashi tayi ta fita nan taga wurin da glass din ya tarwatse har an tattare an share an gyara numfashi ta dan ja ahankali dama ai wannan kasada ne wato siyan mai yarda inbanda kasada taya za ace gaba daya ayi katanga da glass,ace ko ina glass ne ai dole wata rana irin haka ta rinka faruwa,tare da Dr Al'amin ta samesu zaune shi yanata matse matsen waya yana duba posting din da S A na labarai yayi akan yajin aikin da likitoci ke son tafiya,zama tayi ta gaida Dr Al'amin wanda ke murmushi yana fadin, "Amarya ashe abinda yafaru kenan..... To Allah ya kiyaye gaba,insha Allah zan baki magani saboda jikinki da glass din ya shisshiga" "Tohm" ta fada batare da ta daga kanta ba saboda ita kunyar hada ido take yi da Khalil, magunguna Dr Al'amin ya harhada mata yabata tana karba ta tashi sim sim ta fita saboda bata son su sake yin ido hudu da Khalil kuma, Har ta koma sashenta umma barira da Aryan na nan suna jiranta suna kallon tashar MBC 3 inda Aryan ke kallon cartoon sunata drama da umma tana cewa ita wadannan robobin masu kama da aljanu sun isheta ya canja shikuma yaki ya kama remote ya kankame yana zaune daram akan cinyarta, Abinci ta zubo taci sannan tasha magungunan da Dr Al'amin yabata, Aryan ta dauka takaishi dakinsa ta kwantar sannan ta fito tazo tayi shirin bacci ta kwanta,tunanin Khalil ne yafara yawo acikin kwanyarta yana kaiwa da kawowa, hannayensa masu taushi da laushi duk da rikon da yayi mata dazu bada wata manufa bane amma tajishi har cikin ranta,kuma har yanzu tana jinsa, lumshe idanuwanta tayi tana sakin murmushi ita kadai sakamakon tunowa da tayi yanda dazu ya rude lokacin da abin yafaru,rufe idanuwanta tayi da tafukan hannayenta kamar yana ganinta saboda kunya, "Yanzu shikenan ya ga jikina" Da tunaninsa tare da sabuwar kaunarsa fil bacci yazo yayi awon gaba da ita. Khalil bayan fitar Hanan kallon Dr Al'amin yayi yace masa baya jin dadin jikinsa yabashi pills, Kallon mamaki Dr Al'amin yafara yimasa kafin daga bisani ya cire farin gilashin dake fuskarshi, "Amma ranka yadade anya kuwa bazaka hakura da shan relief pills dinnan hakaba.... Kar muje kuma ya fara haifar maka da matsala saboda kajima fa kana shan shi for over 5 years..... For how long zaka yita amfani dashi bayan kuma yanzu kana da iyali..... Ai sai ita ka cutar da ita...." "Wai wadannan suratan duk waye ya tambayeka? Nifa pills kadai na bukata ba dogon bayani ba..." "Sorry sir...." Dr Al'amin yafada yana kokarin fito masa da pills din,karba yayi sannan ya sallameshi yatafi,saida yasha pills din sannan yashiga bedroom dinsa,kai tsaye bathroom yawuce yacire kayan jikinta ya sakarwa ruwan sanyi,yajima yana kwarawa kansa ruwan sanyi sannan yafito yana daure da towel,zama yayi gefen gadon yana dafe kansa da hannayensa guda biyu,hoton Ramlat kawai yake gani acikin zuciyarsa, Hanan tayi kama da Ramlat dinsa ata wurare da dama,shi ba Hanan dince ta jefashi cikin wannan halinba,matarsa da yatuno shine silar samun kansa cikin wannan yanayi amma ita Hanan tausayi da kuma kaunar da take yiwa Aryan ne yasa shi dazu yaji hankalinsa yatashi lokacin da glass ya fashe kuma ai ko babu komai yanzu a karkashin kulawarsa take dan haka dole ne ya kula da ita,rasa abinda yake yimasa dadi yayi domin ko pills dinma yau ji yayi kamar baisha ba dan babu abinda ya canja na damuwar da yake ciki,kwanciya yayi saman gadonshi mai laushin gaske duk aikin bada sanyin da na'urar sanyaya dakin keyi shi gumi yake yi kamar ana gasashi cikin oven,yau yasha wahala dan saida ya gwammace kida da karatu daga karshe dai ya lallaba yatashi yasa jallabiya da short din wando sannan yafita, kitchen yasauka yaje yaduba fridge cikin sa'a yasamu lemon tsamin da yaje nema nan take ya yanka yashanye guda daya sannan yakoma sama,abin salla ya shimfida yahau yasoma sallar nafila. Tunda wannan abun yafaru shikenan Hanan ke kunyar sake cin karo da Khalil dama kuma shi ba mazauni bane hakan yakara nisanta fuskokinsu da haduwa da juna,wurin da glass din yafashe kuwa tuni har an dauko ma'aikata sun gyara sun saka sabon glass awurin, Text ta sake turawa Khalil akan maganar tafiyar ta kano dan gano gida amma sai yayi mata reply da wai ba yanzu ba,to wai sai yaushe zataje gidanne? Ranar ma tayi kuka dan har yafi na waccan ranar da ya hanata zuwa,ita zaman gidanne ma gaba daya ya isheta babu inda mutum zaije ko makota bazai fita ya shiga ba kai wannan zaman baiyiba gaskiya,haka tayita rayawa aranta,ko kuma dan shi baya zaman gidanne shiyasa yake ganin kamar zaman dadinsa sukeji?. Khalil yau tun yana office yake jin zazzabi yana neman saukar masa amma dai yayita daurewa ga mura dake damunsa tun jiya amma ita bata yi tsanani ba sai yau din yake jin tafara takura masa, K'arfe 10 yau ya koma gida bayan ya gama ganawa da lauyansa wato barrister muhsin wanda ke cigaba da kareshi akan karar da yesmin ta shigar, barrister muhsin yace masa akwai alamun nasara sosai dan reshe ne ma ke neman juyewa da mujiya duk da ita ce tayi k'arar, Yana komawa gida ya ajiye wayoyinsa yasaka su a flight mood sannan ya canja kayan jikinsa ya shige bargo ya kwanta domin izuwa yanzu zazzabin yagama rufeshi ga mura wacce ke haddasa masa tari da atishawa harda ciwon kai. Washe gari yakira likita yazo ya dubashi sannan yatafi ita Hanan bata san yana gida ba ranar dan babu inda yafita da yayi bakima hakuri yace abasu saboda bazai iya fita ba,zuwa yamma dai zazzabin ya sauka sai iya murar kadai gashi baya kaunar shan maganin murar nan dan duk sai yabi ya kashe masa jiki kuma yayita sakashi bacci,ko yau dinma wuni yayi yana bacci kamar wani dan kwaya,da suka yi waya da Khalid yake dubashi shine Khalid din yake tsokanarsa wai ayi masa farfesu mana dahuwar kalwa da attaruhu yaci Wallahi da haka zai fatattaki wannan murar, shawarar Khalid ya dauka dan haka da yasamu yatashi yayi wanka yayi salla sai yafita da niyyar yaje k'asa ya sanar da umma dan baya son kunna wayarsa yanzun nan mutane zasu dameshi da kira,ahankali yake takawa saboda jikinsa babu karfi sosai,ta gefen part din Hanan yajiyo k'arar kida dan haka yakoma yabi ta wurin domin dubawa, muryar m Sharif ce ta fara dukan kunnuwanshi cikin wakarsa ta _hafiz_ koda ya leka Hanan ya hango ita da Aryan sun takarkare sai casa rawa suke yi................................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *35* ***Samun wuri yayi ya harde hannuwanshi akirji yayi crossing legs dinsa ya jingina yana kallonsu,daga ita har Aryan din basu san yana tsaye awurin ba har saida wakar ta kare wata ta shiga nan fa hanan tafara bi tana wata irin rawa ahankali idanuwanta arufe "Sabon salon soyayya na kirkiro.... Kai zan yiwa amma sai munje gida.....sabon salo...sabon salo.... Sabon salo" Juyowar da Hanan zatayi taga mutum jingine yana kallonsu,guduwa tayi ta shige cikin bedroom dinta,sai lokacin shima Aryan ya hangoshi da gudu yatafi ya rungumeshi, "Papa...." "Sakeni Aryan kar ka kada ni mana,tun jiya baka ganni ba amma shine baka nemana ko?" Girgiza kai Aryan yayi,"Ina nemanka Daddy" Kama hannunsa yayi suka sauka k'asa wurin umma barira nan yake sanar mata da bukatar shi na son yimasa farfesu ko wanne iri amma yasha daddawa da attaruhu saboda mura ke damunsa, daga nan sama yakoma shida Aryan yana yiwa Aryan takarar kar ya dameshi da surutu baida lafiya idan kuma ya dameshi koroshi zaiyi, bedroom dinshi suka wuce kai tsaye ya kwanta saman gado shima Aryan yabishi ya kwanta akanshi, murmushi yayi ya rungumeshi yana cemasa, "Wato duk da nace maka karka dameni shine saida ka fara ko? Zan koraka wurin mommy yanzun nan kuje can kuci gaba da rawarku tunda rawa momyn ke koya maka..." "Daddy tana koya min karatu ma" "Me da me take koya maka? Fada min inji" Kamar Aryan jira yake yafara jero masa irin karatuttukan da Hanan ke koya masa tiryan tiryan, "Tana zaneka idan bakayi karatu ba ko?" "A'a bata zaneni....." Yabashi amsa yana sake hawa kanshi wai zaiyi doki. Hanan sai da ta tabbatar da cewa Khalil yatafi sannan tafito ta sauka k'asa,a kitchen ta samu umma tana gyara kaji manya manya wad'anda zata yiwa Khalil farfesu dashi, karba tayi tana tambayar umma saboda tunda tazo gidan bata taba ganin umma barira a kitchen ba tunda akwai kuku, "Ai kin san mu'azzamun baya jin dadi mura ke damunsa to shine yace ayi masa farfesu mai yaji dahuwar kalwa..." Dariya Hanan tayi jin umma tace wai dahuwar kalwa,ita kam agida duk lokacin da wani ke yin mura mamaye wani shayi take dafawa na na'a na'a sannan yasha kayan kamshi, Gyare kajin tayi guda uku manya manya sannan ta hada kayan kamshinta ta dafasu rigib sannan ta dora shayin bayan ta gama ta zuba masa ta zubawa umma nata ta dauka ta nufi dakinsa,suna falo shida Aryan bayan sun idar da salla,shi yana saman kujera shikuma Aryan yana kasa yana wasa akan rug sai burgima yake yi,da sallama a bakinta ta shiga ta jawo glass table din dake gefenshi ta dora masa akai sannan tafara gaisheshi, "Ina wuni....?" "Lafiya lau..." "Ya jiki?" "Da sauki" "Allah yakara sauki" "Amin" Daga haka ta kwashi yanmatan kafafunta ta fita. Farfesun yabude tun kafin yakai bakinsa yawunshi ya tsinke,kasa ya sauko ya tankwashe kafafuwansa yasoma yaga yana ci dama kuma gashi yadahu sosai irin yanda ake so kuma farfesun yasha kayan kamshi da daddawa sosai,tare da Aryan suka kusa cinye naman dan sai da kowannensu yaji ya koshi sannan suka hakura Khalil ya rufe sauran ya ajiye,shi duk a tunanin sa umma barira ce ta dafa bai taba kawowa Hanan bace,tun bayan da yagama cin farfesun yaketa fama da face facen hanci, Aryan yatura zuwa cikin bedroom dinshi ya dauko masa tissue,babu laifi yaji dadin naman domin yaji yajin da yaci yafara yimasa amfani. Har lokacin bacci yayi suna tare da Aryan wanda tuni shi yajima da yin bacci ma, Hanan na kwance dakinta abun duniya ya taru yayi mata yawa,inbanda tunani da begen Khalil babu abinda ke damun zuciyarta,tana tsananin sonshi da bukatarshi wanda har bata san yanda zata kwatanta ba, Tashi tayi daga kwancen da take domin ta kasa yin baccin,kamar wacce akace tafito ta bude kofa tafito sanye da night gown dinta milk colour,gaban corridor taje ta dan jingina da jikin karfen da ke kewaye da wurin tana jin iska tana kadata tamkar zata dauketa,kanta ta daga sama tana kallon taurari wadanda suka yiwa sararin samaniya ado suka kara haskashi,daidai lokacin shikuma Khalil yafito rike da Aryan a kafadarshi zaije ya kwantar dashi acikin dakinsa,har yazo ya wuceta bata sani ba saboda hankalin ta baya wurin yana can wata duniya ta daban mai cike da soyayya, kauna,shauki da kuma bege,babu abinda take son kasancewa tare dashi ahalin yanzu sama da Khalil kuma tasan bazata taba gajiyawa da shiba domin kallonsa kadai zai dauke mata hankali ya debe mata kewa sannan zai nisantata da dukkan damuwa. Ahankali yake tahowa yana dosota amma bata saniba har yazo inda take tsaye kanta asama idanuwanta kyarr tana kallon sararin samaniya ko kiftawa bata yi,akusa da ita kadan ya tsaya yakai hannunshi yadafa karfen dake wurin shima sannan yakai dubansa izuwa sama dan ganin abinda take kallo wanda ya shagaltar da ita har haka, Samun kansa shima yayi da jin dadin kallon da yake yiwa saman nan ya lumshe idanuwanshi sannan yabudesu yasake kai dubansa izuwa sama,shi dan soyayya ne kuma ma'abocin sonta akoda yaushe irin wannan yanayin shi ake kira da lovers moment domin idan masoya guda biyu suka samu kansu a irin wannan yanayin sukan manta da kowa da komai, sannan sukan manta da damuwarsu da duk wani abu da ka iya kawo musu cikas acikin duniyar soyayyar su, Sake lumshe idanuwanshi yayi sakamakon wata irin iska mai dadi da ratsa jiki da ta shigeshi,a wannan lokaci bazai iya fada maka takamaimai halin da gangar jikinsa da ruhinsa ke ciki ba,fata yake inama yabude idanuwansa yaganshi tare da Ramlat,inama ace yaga Ramlat akusa dashi koda cikin mafarki ne, Saura kadan Hanan ta fasa ihu saboda ganin mutum da tayi akusa da ita wanda sam koda wasa bata ji zuwanshi ba saboda tana can duniyar tunani, "Abban Aryan...." Ta fada bakinta na dan rawa,juyowa yayi ya jingina ya harde hannuwanshi akirji yana kallon ta bayan yayi crossing legs dinsa kamar yadda ya saba tsayuwarsa,kallonshi take yi daga sama har kasa kamar yaune tafara ganinsa, bakin dogon wando ne ajikinsa na sport sai farar t shirt ta kamfanin Adidas kafarshi sanye da takalmi slippers dama shigarshi kenan kullum fari baida kayan da suka wuce wadannan ko meyasa oho, "Abban Aryan yaushe kazo nan?" Ta bukata bayan ta rufe bakinta da hannayenta, "Kina can duniyar tunani...... Tunanin saurayinki wanda na rabaku kike yi ko?" Sake rufe idanuwanta tayi da dukkanin tafukan hannayenta tana girgiza masa kai alamar A'a, "Fada min gaskiya karki yimin karya...." "Hmmmm" tafada tana gyara tsayuwarta, "Nasan zafin rabuwa da masoyi.... Nasan irin radadi da azabtuwar da zuciya kan shiga aduk lokacin da ka rasa wanda kake so..... Nasan kema acikin wannan yanayin kike rayuwa ahalin yanzu..... Har yanzu kina kukan rabaki da masoyinki da nayi...." Lumshe idanuwanta tayi take wasu hawaye suka gangaro mata wanda ba na komai bane face na tsantsar soyayyar da take yimasa,inama zata iya,inama tana da dauriya da kwarin gwiwar da zata iya duban kwayar idonshi ta fada masa ita shi take so shi take kauna ba waninsa ba,inama,zata iya kallonsa cikin ido ta sanar dashi akansa ne zuciyarta ke shiga duk wadannan abubuwan da ya zayyana, Ganin hawaye na bin kumatunta ya sake tabbatarwa da kansa cewa abinda ya fada ko kuma yake hasashe gaskiya ne domin gashi nan har kuka take yi saboda fama mata raunin dake zuciyarta da yayi, "Hmmmm...... Wai meyasa masoyi bai fiya kasancewa da masoyinsa ba har tsawon lokacin da yadace?..... Me yasa aduk lokacin da kake tare da masoyinka sai wata k'addara ta rabaku?...... Meyasa yawancin masoya basa samun happy ending?......" Kawar da kansa yayi ya furzar da wata zazzafar iska kwayar idanuwanshi har ta sauya daga launin fari zuwa ja, karfen wurin ya dafa yana jin tamkar ya fashe da kuka,ita kuwa Hanan dama kukan take wanda zata iya kiranshi da kukan bakin ciki wai Khalil shi duk azatonsa kukan soyayyar wani take yi ba soyayyar shi ba,meyasa yakasa ganewa cewa ita shi take so? Wanne irin makaho ne shi da ya gagara gane tsantsar soyayyar da take cikin idanuwanta wanda take yimasa? "Kiyi hakuri kowa da yadda Allah ke tsara masa rayuwar sa.... Wasu masoyan sukan kasance da juna tamkar tif da taya ko kuma kamar wata da zara amma lokaci guda sai wata k'addara ta rabasu.... Babu abinda yafi zama da masoyi dadi nasani..... Sannan babu abinda yafi rabuwa dashi daci,tashin hankali da shiga damuwa.... Nasan kina cikin damuwa amma ki kara hakuri har zuwa lokacin da Allah zai kawo karshen zamanki atare damu...." Wata faduwar gaba ce tasoma ziyartarta jin abinda yafito daga bakinsa wai karshen zamansu,ita da take fata da burin kasancewa tare dasu har karshen rayuwar ta amma yana yimata maganar rabuwa da ita,bata san lokacin da kuka ya subuce mata ba.... Dagowar da zatayi taga wayam babu Khalil babu alamarsa har yabar wurin,da kuka ta koma dakinta ta fada kan gado taci gaba da rusar kuka. Shima Khalil cike da damuwa yashiga sashensa ya yada zango a falonsa ya zauna cikin tsantsar damuwa da radadi,wai ma meyasa yabi ta son ran Aryan ya auro yarinyar nan? Meyasa ya rabata da masoyinta wanda take so dan kawai biyan bukatarshi alhali kuma yasan zafin radadin rabuwa da wanda kake so? Shi dai gashi Ramlat bata raye amma kullum cikin damuwar rashinta yake wani lokacin har zubar da hawaye yake yi to inaga Hanan wacce ita masoyin yana raye amma aka rabata dashi ai dole tayi kuka idanma akwai abinda yafi kuka dole tayi, Zamewa yayi ya kwanta kan doguwar kujera idanuwanshi suna kallon sama, tambayar kansa yake shin menene mafita? "Ka saketa kawai...." Zuciyarshi tabashi amsa tana sake karfafa masa gwiwar aikata hakan domin hakan shi kadai ne mafita kawai,sabanin haka kuwa zai sa yazama azzalumi mai son kansa kuma marar tausayi,tashi yayi dakyar ya nufi cikin daki zuciyarsa na raya masa wani abu..........................✍️ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: 36 ***Tafiya yake yana hada hanya har yasamu ya cimma lafiyayyen gadonshi wanda yasha shimfidu masu laushi sannan ga pillows nan sama da guda goma manya da kanana kuma kaloli daban daban, Zama yayi akai sannan ahankali ya zame ya kwanta yana jin jikinsa duk asanyaye, agogon dake ajiye kan bedside drawer dinshi ya kalla nan yaga karfe 11:30 yasan dare yayi amma yazama dole ya kira Khalid acikin daren nan ba sai zuwa gobe ba,yana da bukatar neman shawarar sa da kuma jin ta bakinsa kafin ya zartar da hukuncin da yake ganin shine daidai. Kiran layin Khalid yasoma yi yana jin zuciyarsa kamar zata fashe dan tsabar nauyin da tayi masa,cikin dan magagin bacci Khalid ya daga wayar, "Khalid zan saketa...." Shine abinda kunnuwan Khalid suka jiye masa ai bai san lokacin da ya wartsake ba yayi zunbur ya tashi yabar cikin bedroom dinsu gudun kada ya tada Muneerat,a falo ya zauna sannan cikin damuwa yace, "Khalil what are you saying?...... Me ya faru?" "Khalid zan saki yarinyar nan kawai inaga hakan zai fi...." "Wai meya faru? Wani abun tayi maka mai girma har haka?" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tashi zaune ya dafe kanshi da hannunshi guda daya, "Babu abinda tayi min kawai dai naga kamar na shiga hakkinta ne kuma na zalunceta domin na kawota gidana na rabata da wanda take so...." "Itace ta fada maka haka?" Khalid ya bukata, "Ba ita ta fada minba amma dai kamar alamun hakan sun bayyana atattare da ita...." "Kaga malam wannan ba hujja bace, bai kamata ka yi haka ba kaifa babban mutum ne Khalil karka manta, yanzu gaba daya idanuwa akanka suke da zarar kayi abinda bai kamata ba za afara yadawa ana yin yamididi da kai.... Ai gara ka ci gaba da zama da ita har zuwa ranar da zata mance da masoyin nata akan ka saketa ka mayar da ita yar karamar bazawara..... Khalil kasan zawarci kuwa? Kasan radadin da iyaye ke ji aduk lokacin da aka sakar musu yaya? To Wallahi duk amincin da ke tsakaninku da mahaifin ta daga ranar da ka sakar masa 'ya shikenan sai wani kadari na Allah kuma.... Kayi tunani" Shiru ya dan yi na wani lokaci tabbas yasan abinda Khalid yafada gaskiya ne to amma ya zaiyi da halin damuwar da ya jefata? Idan har ya zama silar rugujewar farin cikinta bazai taba yafewa kansa ba, "Kayi hakuri ka kwanta ka manta da kowacce irin damuwa ka samu bacci brain dinka ta huta inyaso gobe sai mu karasa magana....." "Shikenan Khalid thank you, thank you for always being with me.... Indeed I have no words to thank you.... Sai da safe" "Don't mention it Khalil,you are always welcome...." Katse wayar Khalil yayi sannan cikin karfin hali yasamu yayi addu'ar bacci ya kwanta wai ko Allah zai sa yasamu bacci,duk tunane tunanen da ke zuwar masa cikin rai a daidai wannan lokaci kin yi yayi da haka yasamu bacci yayi gaba dashi. *** Sosai sumayya taga alfanun daukar shawarar muhibba da tayi,ita kanta bata taba sanin tana da kwarin gwiwar iya yin haka ba sai yanzu,gaba daya ta fita sabgar mujahid babu ruwanta dashi wani lokacin ma shine zai yita takalarta har yasamu suyi fada,fada kam yanzu tsakaninsu kullum ne babu ranar banza da zata zo ta wuce basuyi wannan fadan nasu na sabo ba, Sai dai kwana biyun nan yanzu ba sosai yake ganinta ba sakamakon exams da suka fara a makaranta,kullum tana cikin makaranta suna karatu bata dawowa gida da wuri,ranar da suka gama exams kuwa aranar ta tattara ta tafi katsina gidan iyayenta, mujahid duk sai yaji gidan babu dadi musamman ma idan yana son abu to sai dai yasaka yar aiki ko kuma yayi da kansa haka ma aikin nata da take yi wani lokacin mami shi take sawa yanzu yauma shi yayiwa mami guga ya goge mata kayanta duk gugar gashi babu dadi stones everywhere injishi da fada,tun yana daukar abun da wasa har yaga bafa na wasa bane,dan haka yacewa mami wai zaije ya dauko sumayya a katsina,ranar da safe ya shirya yatafi bayan yasha manyan kayansa brown colour din shadda da hularta,baisha wahalar samun gidanba saboda dama ya sanshi suna zuwa tare da mami,har ciki yayi sallama ya shiga sumayya na ta shan bacci a falo tana kan doguwar kujera,kafarta ya buga nan tayi firgigit ta juyo kamar a mafarki taganshi tsaye, "Tashi mu tafi....." Mutsuttsuke idonta tayi tana son gasgata shin dagaske mujahid ne ko kuwa mafarki take yi? "Nine nan daina wani kallo na" Dan turo baki tayi ta zuro kafafunta kasa tana harararsa. *** Kamar yadda Khalid yafada masa washe gari wasai yatashi zuciyarsa babu wani sauran damuwa ko gurbataccen tunani haka itama murar tashi yau ya danji dama dama shiyasa ma ya shirya yafita office,ita kuma Hanan da damuwa ta wayi gari duk abunda takeyi tana yinsa ne cikin rashin walwala, wai meyasa ya kasa fahimtar ta ne? Meyasa yakasa gane son da take yimasa duk nauyinsa? Ranar dai haka ta wuni babu farin ciki dan adaki ma ta wuni taki fitowa, Tsawon Kwana biyu basu hadu da Khalil ba gashi ita kuma gaskiya ganin gida ta ke son taje tayi domin zamanta anan bata ga abinda take tsinanawa ba inbanda zaman kashe wando babu abinda take yi. Waya suka yi da anty badi'a nan take fada mata cewa tana son ta dan shiga makarantar koyon abubuwa irinsu hada sabulai,turaren wuta da sauransu koda kuwa irin na online dinnan da akeyi ne shine anty badi'a ta hada ta da wata mata wai ita hajja hasinah kwararriya wurin koyar da mata abubuwa daban daban,kuma wani abun dadi ma kina zaune daga gida zaki koyi abubuwa masu tarin yawa matsawar kin maida hankali. Zunzuruntun kudi ta biya har naira dubu ishirin tayi registration saboda online classes ne nan hajja hasinah ta sakata a cikin group inda aka fara gudanar da lectures,irin tsarin yanda ake koyarwar abun yayi mutukar burgeta domin ana yin komai dalla dalla yanda zaka gane kuma ka fahimta, Yanzu kam zaman banza ya ragu domin koda yaushe tana rike da wayarta da littafin da ta tanada musamman dan rubuta muhimman abubuwan da aka koyar gudun kada ta manta tunda shi dai WhatsApp baida tabbas, Ganin yanda take bobboye kanta a daki yanzu bata fitowa falo sosai sannan bata biye Aryan suyi wasa sosai sai Khalil yafara zargin to ko dai dan ya hanata zuwa ganin gidane shine abin yake damunta? May be hakane zuciyarshi ta raya masa saboda duk lokacin da zaiga Aryan yana wasa a falon kasa ko falon sama shi kadai yake gani bai fi ita yaganta sau daya ko sau biyu ba, Yau garin Abekuta yaje inda matasan yankin suka shirya masa wasan kwallon kafa da kambun girmamawa da zasu bashi kuma bashi yadawo Abuja ba sai misalin 11 harda rabi na dare,acikin daren saida ya je office yayi signing wasu mails da aka aiko masa sannan yanufi gida,wanka yayi ya sha coffee mai zafi sannan ya nufi part din Hanan,yayi mamaki lokacin da yaga haske dal tako ina acikin sashen nata wannan alamu ne dake nuna cewa batayi bacci ba idonta biyu, Zaune take kan gadonta tana rubuta abubuwan da aka koyar dasu yau wanda bata samu damar rubutawa ba sakamakon baccin rana da tayi kuma koda ta tashi da yamma garden suka shiga ita da Aryan suka je suka shantake acan har magriba, Knocking yayi wanda yasa Hanan taji tsoro ya shigeta,shiru yaji ba a amsa ba dan haka ya sake bugawa, ahankali ta sauko daga kan gadon cikin sanda sadaf sadaf tazo bakin kofar zata leka, bude kofar yayi nan taga cewa shine, kallon kallo suka tsaya suna yi dan rabon da suga juna face to face tun ranar nan, "Sannu da zuwa" ta fada tana sunkuyar da kanta kasa, "Yawwa...." Tsaye suka yi awurin cirko cirko shi dai bai shiga cikiba haka kuma bai koma waje ba, "Ki shirya jibi zaki je ganin gida......" Da mamakinsa sai yaga ta dago fuskarta cike da farin ciki ta kalleshi, "Nagode" Baice komai ba yajuya yatafi nan tabishi da kallo yauma dai fararen kayanne na gado farar riga t shirt mai gajeren hannu da farin wando,cike da murna taje ta fada saman gado ta rungume pillow cike da farin ciki ranar dai tsabar murna bacci kadan tayi,washe gari kuma ta fara hada kayanta akwati guda kamar wacce zata yi watanni ko shekara,ranar wuni tayi tana fara'a kamar anyi mata albishir da kujerar hajji, Washe gari da safe bayan Aryan yatafi makaranta itama suka kama hanyar kanon dabo,karfe 11 da kusan rabi suka isa kano ai Hanan kamar zata tashi sama haka take ji dan tsananin farin ciki, Lokacin da suka je gidansu kaya taga ana ta fitowa dasu ana shigarwa,kayan abinci ne,atamfofi bandir bandir da shaddodi na maza, "wadannan kuma na menene?" Ta tambayi kanta dan Khalil bai fada mata ba, Da tsallenta da gudunta ta shiga gidan taje ta rungume mamaye tana murna,shamsu dake tsaye shikam matsawa yayi yana fadin, "A'a karki kada ni ki jamin zama wuri daya" Bakinta yau yaki rufuwa kuma ta kasa zama wuri daya ta shiga nan ta fita nan haka ta rinka yi saboda bakuwa ta zama agidan,har Abba yadawo bata samu zama ba sai lokacin ne suka zauna, "Uwar masu gida ina kuma kika baro dan naki Sulaimanu?" Dariya tayi aranta tana cewa Allah sarki Aryan, "Abba suna nan lafiya duk suna gaisheku" Har dare bata san ma'anar wadannan kayan da tazo dasu ba,text tayiwa Khalil tana tambayar shi wad'annan kayan da ya hadota dasu na menene? Sai lokacin ya tuna ashefa baiyi mata bayani ba shi yasaba duk lokacin da Ramlat zata je gida yana yimata tsaraba wadda zata kaiwa yan uwa da abokan arziki, reply ya mayar mata dashi, _Tsaraba_ Shine kadai abinda ya rubuta,tambayarsa ta sake yi wai to kwana nawa zatayi nan ya dawo mata da reply wai sati daya marairaicewa tayi kamar yana ganinta wai dan Allah tayi sati biyu shi kuma yace A'a,damunsa Aryan yayita yi shi kuma wai zaiyi waya da mommy,saida ya kira masa ita sannan yabarshi,tashi yayi ya wuce bedroom dinshi. Tana kwance suna shan hirar yaushe gamo da mamaye tana ta zuba shagwaba wai mamaye bata je gidanta ba, gashi ankusa shekara tana cikin yin wannan mitar kira yashigo cikin wayarta nan ta dauka tun kafin tayi magana taji muryar Aryan, "Hello mommy...." Murmushi tayi ta amsa masa ko gaisheta baiyi ba yasoma bata labari yadawo daga makaranta umma tabashi abinci yaci kuma yaje islamiyya,uncle yadawo daga office ya kawo masa shawarma da tsire,labarai dai kala kala, "Ina uncle din yake?" "Yana daki yace kar na dameshi da surutu" Dariya tayi saboda abisa dukkan alamu kam Khalil ba mai son hayaniya bane sai wacce ta zama dole shiyasa take mamakin yanda yake yi da bakin matasa a office duk lokacin da suka kawo masa ziyara kila wannan dalilinne yasa baya rabuwa da ciwon kai kullum cikinsa yake, Sun jima suna waya da Aryan har saida Khalil yafito nan tajiyo muryar shi yana tambayar Aryan wai har yanzu basu gama hirar da mommyn ba?lumshe idanuwa tayi tana murmushi sakamakon jin muryar sa da tayi tasan yanzu yana can sanye da farar t shirt da bakin wando ko fari tunda shigar tashi kenan kullum babu sauyi, sallama sukayi da Aryan ta kashe wayar. Sabo turken wawa bata taba sanin cewa tayi mugun sabo da gadonta ba sai yau domin kasa bacci tayi sai juye juye kadai taketa faman yi tana tuno abun kaunarta, fuskarsa, muryar shi da dukkan yanda yake gudanar da komai nashi cikin jan aji da nutsuwa, murmushi tayi ta rungume pillow ahankali cikin rada ta furta "I love you minister"........................✍? *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *37* ***Baccin yau tayi shi ne cike da nutsuwa,kewa da kuma shauki,hakanne ma yazama silar faruwar wani mafarki mai dadi acikin baccinta, Khalil ta gani zaune akan wasu duwatsu agaban bakin wani tafkeken kogi,shi kansa ruwan yana da daukar hankalin duk wani ma'abocin kallonsa ko kuma wanda yasamu kansa a wurin. K'ananan duwatsu yake ta dauka yana cillawa cikin ruwan,yana sanye da farar t shirt da bakin trouser fuskarshi boye cikin bakin gilashin da ya karbeshi yayi masa kyau ainun,ita kuma tana zaune gefe daya can nesa dashi itama sanye cikin farar doguwar riga amma kuma tana ta kuka tsawon lokaci shi kuma yaki ya ko kulata bare ya bata hakuri, Tsawon wani lokaci bai juya ya ko kalleta ba sai tajiyo wata kara daga bayanta kafin ta juya tuni yayi kukan kura yayi tsalle yazo ya fizgota jikinshi ya rungume yana kakkareta alamar baya son wani abu ya sameta ko ya tabata,zuwa cann bayan dan wani lokaci ya dago kanta yana kallon kwayar idonta sai dai ita bata iya ganin nashi idon sakamakon bakin gilashin dake sanye a fuskar tashi,cikin muryar shi mai taushi da dadin saurare yace, "Sa'adah...... Kin zaci bana sonki ko?..... Gashi ke kuma kina sona.... Shi so sirri ne dake boye cikin zuciya...... Wani mutumin yana mutukar kaunar ka amma yakan boye hakan acikin ransa batare da ya bayyana maka ba....." Sakinta taga yayi ya durkusa akan gwiwowinsa irin yanda indiyawa keyi hannunshi guda daya yakai ya kamo nata yayi kissing dinshi sannan ya bude baki cikin salo mai burgewa yace, "Nima ina sonki......! I love you sa'adah......" Wata iskace mai karfi da dadi ta taso wacce ke barazanar yin awon gaba da ita cak taji ya dagata yasata cikin jikinsa ya lullube ta da yalwataccen kirjinsa, Juyi kawai take yi daga kwancen da take saboda har lokacin cikin mafarki take tana rungume a kirjinsa suna juyawa iska na kadasu tana shakar kamshin jikinsa mai saukar da nutsuwa, "Hanan..... Hanan...." Ahankali ta bude idonta nan taga mamaye tsaye da carbi a hannunta gari har yayi haske alamar ta makara, "Wai kinyi sallah ma kuwa?" Girgiza kai tayi ta sauka daga kan gadon tana jin wani sabon shaukin kaunarsa acikin zuciyarta. Kamar mahauciya ko sabon kamu haka ta zama ranar domin wuni tayi tana murmushi bata da aiki sai murmushi ita kadai,da zarar ta tuno wannan mafarkin da tayi sai murmushi ya kufce mata haka tayi ta fama tana buri tare da fatan mafarkin ya zama gaske, Yauma sunyi waya da Aryan kuma sun jima yana yimata surutu dan har da sanar da ita wai Daddy bashi da lafiya yana yin ciwon ido dayake yau khalil da ciwon ido ya tashi gaba daya idanuwan sunyi jajur kuma suna yimasa radadi ga dan kunbura da sukayi, Bayan sun gama waya da Aryan sun gaisa da umma barira ta katse wayar tana tunanin taya yadace ta duba Khalil? Shin kiransa zatayi ko text massage zata tura masa? Ita fa gaba daya Khalil dinne kunyarsa take ji idan ta tuna irin diban albarkar da tayi masa abaya, shiyasa ba kyau saurin yanke hukunci ita dai gashi yanzu zuciya ta kaita ta barota aruwa,shiru tayi tana nazari to idan ta kirashi me zata ce masa? Kawai gara tayi text din zaifi sauki dama dadin text massage kenan zaka iya fadawa mutum abinda kake so wanda bazaka iya fada ba idan waya kuke, shawarar zuciyarta tabi ta tura masa massage din. Khalil yana zaune kan gadonsa da laptop a cinyarshi gefe daya kuma Aryan ne shima yayi matashin kai da kafarshi idanuwanshi sanye da farin glass sakonta ya shigo bai samu damar budewa ba saboda yana aikine mai muhimmanci,sai bayan da ya gama ya dauki Aryan yaje ya kwantar dashi a dakinsa ya shiga kitchen ya hado coffee mai zafi sannan ya koma bangaren sa, glass din idonshi yacire saboda dama saboda hasken system din shiyasa yasaka,wayar ya dauka yana zaune kan sofa yana kurbar coffee dinshi bude sakon yayi nan yaga daga Hanan ne wani dan kyakkyawan greeting card pic yagani mai kyau mai dauke da flowers jajaye ajiki sannan anyi rubutu kamar haka, _If these flowers were wishes, then my wish for you is to get well soon._ Shiru yayi kamar wanda yake kokarin gano wani abu daga jikin sakon zuwa can yasaki ajiyar zuciya sannan yatura mata da reply, _Thanks_,bata damuba saboda dama tasan halinsa sakonshi bai wuce ok, alright, thanks etc. *** Cike da mamaki sumayya ke kallon mujahid tun bayan da suka kamo hanyar kanon dabo tumbin giwa koda me kazo anfika, Wai yau itace mujahid yaje tahowa da ita takanas har garin katsina,hannu takai kan radio din cikin motar zata kunna, "Karki kunna min...." Fasa kunnawa tayi ta kawar da kanta tana hararar gefe, "Ke haka akeyi sai ki wani taho gida ki nemi wurin zama ki shantake..... Kinma manta da mutane gaba daya" Sai lokacin ta kalleshi tana kokarin turo masa baki, "Suwaye mutanen? Mami ce kuma kullum muna gaisawa ta waya" "Ohh mami kadai kika sani? Idan kika kara turo min bakin nan sai kinga yanda zanyi dake...." Bata kara magana ba taja mayafi ta rufe fuskarta zatayi bacci, "Karki yarda kiyi min bacci a mota,ki bude idonki kar ki jamin ace satoki nayi...." Gaba daya ita mamaki mujahid ke bata wai shine yaketa takalarta da janta da surutu haka mujahid din da ada ko magana tayi masa sai ya gadama yake amsawa idan kuma bai gadama ba harara ce ke rabasu amma wai yau shine keta janta haka,har suka je kano yana janta da magana,agaban wani dan karamin restaurant ya tsaya ya fita yana cewa ta jirashi idan kuma tafito ta bata to babu ruwanshi, murmushi tayi ta dauke kanta bayan wasu yan mintuna yadawo dauke da wata yar kyakkyawar leda wadda aka zubo masa snacks aciki harda drinks guda biyu, "Amshi kici yar kauye dake kawai...." "Yan kauye dai" "Keda wa?" Ya bukata yana kokarin yiwa motar key, "Nida kai tunda duk tushenmu daya..." Murmushi yayi ya harareta, "ke dai yarinya" Lumshe idanuwanta tayi ta jingina da jikin kujera tana yiwa Allah godiya acikin ranta da yakawo mata wannan rana cikin sauki batare da tasha doguwar wahala ba. *** Kullum sai sunyi waya da Aryan da umma barira haka shima Khalil tana kokarin tura masa massage tana tambayar idanunshi domin har yanzu bai samu lafiya ba sai dai da sauki za ace, Acikin gidajen dangi da yan uwa da sauran abokan arziki babu inda bata je ba kuma duk inda taje sai takai turamen atamfofi da shadda ita kanta tana jin farin ciki da dadin abinda tayi domin ta dadadawa mutane da yawa ta hanyar basu wannan shaddar da atamfar,gidan anty salaha kuwa kwana biyu tayi acan anty salaha sai mitar uwar ramar da tayi take tayi tana cewa taki ta kwantar da hankalinta ta zauna lafiya agidan mijinta tayi kiba bayan bata rasa komai na jin dadin rayuwa ba idan kuma saboda tsufan minister ne take sawa ranta damuwa ai akwai matan da suka auri mijin da yafi nata tsufa, murmushi Hanan tayi sannan tace, "Ai anty bama tsoho bane wallahi,matashi ne mai jini ajika son kowa kin wadda ta rasa.... Bari ki ganshi fa" Hotunanshi da tayi saving a Instagram ta budewa anty salaha ta mika mata wayar tafara gani daya bayan daya, "Ikon Allah.... Hanan yar baiwa.... Ke yanzu dama wannan balaraben ne mijin naki? Allah mai yadda yaso.... Hanan ki godewa Allah" Haka anty salaha keta faman santin Khalil ai da taga pic din Aryan sai ta sake rudewa tana cewa sai kace jinin larabawa? Ita dai hanan dariya take yi saboda itama farkon ganinsu tayi wannan santin da rudewar amma ta boyewa anty salaha halin da take ciki na tsananin son Khalil wanda shikuma abisa dukkan alamu bai ma san tanayi ba. Satinta daya agida PA yaje ya daukota kamar yadda Khalil ya fada mata,harda kukanta itada mamaye ita tanayi mamaye nayi, tsakanin d'a da mahaifi, K'arfe biyar na yamma suka shiga garin Abuja lokacin anyi ruwa an dauke amma garin awadace yake da ni'ima mai yalwa ga iska mai dadi tana kadawa, lumshe ido tayi ta bude lokacin da suka shiga unguwar su tana zaune ta kame a owners corner,unguwar shiru babu hayaniyar komai ga shuke shuke sunyi shar shar luf luf dasu, tangamemen gidansu suka shiga har bakin kofar shiga PA yakaita yayi parking, tunda Aryan ya hangota yabaro malamin islamiyyarshi yataho yana yimata oyoyo karatun da bai koma ba kenan,murna da umma barira da Aryan kamar sayi me saboda gidan duk sororo yayi musu lokacin da bata nan itama umma ba abokin zance sai kayan kallo da radio,har dare suna tare a dakin umma ga tsarabar da ta kawo musu nan iri iri da na ciye ciye da kayan amfanin gida, Bayan sallar ishah tafito daga wanka ta shirya cikin riga da wando na bacci blue colour,yau jin kanta take yi wata iska na shigarta sakamakon kitson da tayi kafin ta taho dan rabonta da kitso tun kafin bikinta dan tunda tazo Abuja ba ayi mata kitso ba ita dai umma ita keyi mata tunda ta dan iya, Aryan ne yashigo rike da balloon yana son hurawa ya kasa yabata wai ta hura masa awurin Daddy ya karbo,karba tayi ta kama hannunsa suka koma kasa wurin umma,itace har 12 saura adakin umma suna hira daga k'arshe tayiwa umma sallama ta tashi dama tun dazu takai Aryan dakinshi, Tun da ta shawo kwana iskar dake kadawa tafara kawo mata kamshinsa cikin hancinta ai kuwa tana taka kafar bene tajiyo takunshi shikuma yana kokarin saukowa,sai da ta lumshe idanuwanta sannan ta budesu daidai lokacin ta hangoshi yana sanye da farar t shirt da bakin dogon wando hannunshi rike da dan karamin coffee flask yana kurba idanuwanshi sanye da bakin glass...........................✍? *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: 38 ***Ahankali take hawa steps din shikuma yana saukowa cikin kwarjini da cikar haiba,yana kara dosota kamshinsa na kara kusanto ta kasala na kara lullubeta, Dan sunkuyar da kanta tayi lokacin da suka zo kusa da juna, "Ina yini uncle?" Ta fada muryar ta na dan sassarkewa wanda ita kanta ba zatace ga dalili ba kawai dai abinda ta sani shine kusan duk lokacin da zata ganshi to sai ta tsinci kanta cikin wannan halin koma fiye da haka domin nutsuwarta tafiya take tabarta har sai baya nan sannan take dawowa gareta, "Lafiya lau.... Ya mutanen gida?" Ya amsa yana cigaba da tafiyarsa batare da ya tsaya ba, "Suna lafiya,ya jiki?" "Alhamdulillahi...." Yabata amsa lokacin har ya dan gota ta, "Allah ya kara sauki" Ta sake fada duk da bata da tabbaccin ko zai jiyo abinda ta fada,ahankali taci gaba da tafiya cikin ranta tana jin wani abu yana tsirgawa cikin magudanar jininta,kamar wannan shigar da yayi sak ita taganshi da ita cikin mafarkin da tayi kwanaki biyar da suka wuce, Bedroom dinta ta shiga ta sulale gefen gado asanyaye ta kwanta tana jin damuwa na lullube farin cikin da take tare dashi yanzu,da ace Khalil na sonta ko yana jin wani abu agame da ita da yanzu suna can tare amma sai dai kash ba itace a gaban sa ba abisa dukkan alamu. Washe gari haka ta tashi sukuku danma dai online classes dinsu na dan debe mata kewa domin abubuwan da take koya a group din Allah yayi yawa dasu ko a fannin girke girke ta koyi girki kala kala wadanda ba zasu lissafu ba ita kuma dama Allah ya dora mata jarabar son girki dan sam bata ganin wahalar sa amma abun haushi tun da tazo gidan Khalil iya farfesu kawai ta taba girkawa komai kuku ke dafa musu,wuni tayi adaki tana tsara abubuwan da zata bada a sissiyo mata domin hada turaren wanka da humrah wadanda hajja hasinah ta koyar musu,ita nata take son tayi daban mai kamshi na musamman wanda duk wanda yaji zai so, Zuwa yamma ta bawa Emah driver yatafi kasuwa domin harhado mata kayan,daga nan falon kasa ta zauna wurin umma barira dake zaune tana sakar maficin roba anan take jin wai Khalil yau minna yatafi gaisuwa,dan tabe baki tayi cike da bacin rai amma bata nunuwa umma ba. Zuwa dare Khalil yadawo kuma yau da wuri yadawo sakamakon takurawar da idonshi yayi masa wani irin radadi da zugi yake yimasa ta ciki, Yana zaune falonsa jikinsa sanye da jallabiya umma barira da Aryan da Hanan suka shiga domin dubashi,waya suka iske shi yana yi yana cewa, "Khalid kace mata nifa bana cin mike..... Ehhh...to shikenan muna zuba ido....ok thank you" Jin sunan wanda ya ambata yasake tabbatar musu cewa da Khalid yake yin waya nan Aryan ya tubure yahau rigimar shi sai anbashi yayi magana dasu Nawwar,mika masa wayar Khalil yayi sannan ya maida hankalinsa ga su Hanan wadanda ke zaune ita umma tana saman kujera ita kuma Hanan tana k'asa kan Rug. Da umma suka fara gaisawa tana tambayar ya idon nashi saboda yau da sassafe yafita, tissue ya yaga yana dan goge idon nashi sannan ya dagosu jajur yana kallon umma ita kuma Hanan tana kallonsa tana ganin yanda idanuwanshi suka yi ja, "Wallahi umma idonne ma ya takura min nadawo gida amma ban gama aikiba a office kawai dai tahowa nayi.... Ina saka masa magani amma kamar bana sakawa" "Ai likitan ido ya kamata ka gani mu'azzam..." "Ai shi nagani umma, Dr Al'amin ne ma ya hada ni dashi..." Sai da Hanan tajira suka gama da umma sannan ta gaishe shi,sau daya kurum ya kalleta daga nan bai kara ba sun dan jima wurinsa suna hira da umma sannan suka fita, Washe gari da burin yin aiki ta tashi tana son hada humrah da turaren wanka kuma cikin nasara ta yisu kamar dama can tajima tana yi,gaba daya sashenta gaurayewa yayi da kamshi kamar me ita kanta kamshin take yi saboda kayan hadin da tayi amfani dasu masu kyau ne da tsada sannan ta dan kakkara da wasu turarukan wanda ma hajja hasinah bata saka musu suba, lokacin da ta kammala saida ta yiyyi wa kayan hotuna sannan ta turawa hajja hasinah,kowa na gidan saida ta diba masa ta saka masa acikin toilet daga Aryan har umma har Khalil shi amma Khalil a toilet dinshi na falo ta ajiye masa dan ba taba shiga master bedroom dinshi ma tayiba har yau bata san kalar bedroom dinsa ba ita kuma humrar dama kanta ta hadawa shiyasa bata bawa kowa ba,ji tayi idanuwanta suna yi mata kekayi nan ta sosa kamar kuma dama jira suke suka fara yimata radadi sai kuma hawaye kafin dare itama tuni har ido ya ruruce yahau ciwo ya kada yayi jajur, lokacin da umma tagani cewa tayi to awurin Khalil ta dauka sai akira mata likita itama yadubata, itama tasan awurin nashi ta dauka dama tun lokacin da sukaje falonsa ta kalli kwayar idanuwanshi tafara jin nata kwayar idon suna dan tsikarinta kadan, Har 12 dare bata yi bacci ba sakamakon ciwon da idanuwanta keyi ganin babu haza yasata yimasa text wai bata da lafiya ciwon ido ke damunta ko zai taimaka ya Kira mata Dr? Reply taga yayi mata da wai tazo, Tashi tayi ta sauka daga kan gadon ta saka hijabinta da silifas tafita,yana kishingide akan kujera kafarshi daya saman center table yana kallon CNN ta bude kofar ta shiga bakinta dauke da sallama, idanuwanshi akan TV ya amsa batare da ya kalleta ba. Wuri ta samu ta zauna can nesa dashi sosai amma duk da haka sai da hancinsa ya jiyo masa masifaffen kamshin humrar dake tashi jikinta,shiru yayi ya dan lumshe idanuwanshi na dan wani lokaci sannan ya kalleta da lumsassun idanuwanshi wadanda suka kara yin jaa,saurin kawar idonta tayi daga kanshi dan tunda ta zauna take kallonsa kamar zata cinyeshi, " Me kika ce....?" Taji ya tambayeta bayan ya dauke idonshi daga kanta, "Idanuwana ke ciwo..." Tabashi amsa tana wasa da bakin hijab din jikinta, "Me yasamu idon?" Ya sake tambaya, "Awurinka na dauka..." Jin abinda tace yasashi daga ido ya kalleta, "Awurina kuma?" "Uhmmmm" Shiru yayi na dan wasu mintuna sannan cikin rashin daga murya taji yace, "Shiga bedroom dina zaki ga magani ki dauko...." Har ta mike bata san me ya tuna ba taji yayi saurin cewa, "Zauna kawai bari in dauko.." Daga haka yatashi yawuce cikin bedroom dinshi nan tabishi da kallo farar t shirt ce jikinsa da farin wando wanda da kadan yawuce gwiwarsa shima fa ta lura idan yasamu dama akwai gayu idan zai fita ne kullum cikin manyan kaya, Koda yashiga cikin dakin sai da yatsaya gaban bedside drawer dinshi wanda ke dauke da hoton Aryan da hoton Ramlat cikin wasu frame kanana guda biyu masu kyau,ya dan jima yana duban hoton kamar mai son gano wani abu aciki sannan ya dauki maganin yafita, Tana zaune inda yatafi ya barta zama yayi saman kujerar da yake zaune tun farko, sannan ya dora mata maganin kan center table din gabanshi, "Zo ki dauka" Anutse ta tashi tazo ta dauka tana kallonsa alamun neman karin bayani, "Ki disa a idon naki idan zaki kwanta" "To kai kuma fa?" Ta fada muryarta na rawa kamar wacce ke jin tsoron fada, "Ba matsala kije dashi" "Nagode,sai da safe" Kai kurum ya daga mata ta juya ta fita tana jinjina rashin son magana irin na wannan bawan Allah dan idan yana yinta kamar anyi masa dole. Kamar ciwon idon nasu layi yake bi washe gari shima Aryan yatashi da shi duk idanuwan nashi a like haka suka yita fama har tsawon sati biyu umma ce kadai bata yi wannan ciwon idon nasu ba, Abangaren abubuwan da take koyo kuwa yanzu tasake bada himma sosai kuma alhamdulillah ta koyi abubuwa masu yawa kuma tana ma kan koyo wani abun burgewa ma shine ta kan jajurce wurin gwada dukkan abun da aka koyar dasu, Yauma kamar kullum tana zaune falon kasa itada umma kowa yana aikinsa maganin zaman banza,ita umma tana karasa mificin da take sakawa ita kuma Hanan tana sabulun gyaran jiki wanda hajja hasinah ta koyar dasu cikin satin nan,muryar Aryan tajiyo yana ta zuba surutun nashi ko shida waye oho, "Kinji d'an naki can ko wa ya samo yabaro karatun islamiyyar tashi kuma?" Umma ta fada tana kokarin bantarar goronta,kafin Hanan tayi magana tuni anbude kofa, dukkansu ita da umma d'aga ido sukayi suka mayar da hankalinsu kan wad'anda ke shigowa,Zaid ne rike da trolley yana janta Aryan na biye dashi shida wata kyakkyawar matashiyar mata sai zuba mata surutu yake yi, Ganinsu yasa umma fadada fara'arta tana fadin lale marhabun da mutanen gombe,itama Hanan ba abarta abaya ba wurin yimusu barka da zuwa, Kujera duk suka samu suka zazzauna ana kokarin gaisawa,jin muryar matar yasa Hanan dan sake kallonta lokacin da taji umma tace, "Maamy mutanen London..... Saukar yaushe?" "Ai zan kai 3 weeks da dawowa.... Koda yaushe Khalil na mitar wai bana zumunci naki zumunci shiyasa shima ya shareni ko Aryan baya kai min to yanzu gani nazo har gida....." "Allah sarki ai kuwa kin kyauta.... Sannu da zuwa" "Ina yini?" Hanan ta fada tana kallon ta,dan murmushi maamy tayi sannan ta amsa cikin fara'a, "Lafiya lau.... Mun sameku lafiya?" "Lafiya lau" Hanan ta amsa mata tana tattare kayanta tunda dama ta gama,sama ta haura domin kai kayan bayan sun gaisa da zaid, lokacin da take saukowa tana jiyo muryar Zaid yana cewa umma, "Ai ni umma kasa gane Anty maamy nayi Yaya Khalil ma nasan dakyar idan zai ganeta dan tafi 4 years rabonta da kasar nan" Dariya maamy tayi ta cire farin glass din dake idonta, "Zaid kaima fa baka da dama" Ita dai hanan samun wuri tayi ta zauna tana kallonsu da sauraren hirar da suke yi yayinda ita kuma Aryan yazo ya haye cinyarta. Kasancewar ga dakuna nan reras agidan daki guda aka warewa anty maamy ta shigar da kayanta lokacin anata kiraye kirayen sallar magriba,suma su Hanan basu zauna ba kowa dakinshi yawuce domin gabatar da salla shikuma Aryan suka fita tare da Zaid, Hanan bata samu fitowa ba sai bayan sallar ishah saboda tana can dakinta tana chaten da su salaha tana tuttura musu abubuwan da ta gwaggwada na daga cikin wad'anda ta koya,bayan sallar ishah tafita domin cikinta yafara kiran ciroma,tana sanye da dark blue din doguwar riga yar kanti da hijab asama,falon babu kowa hatta umma bata fito ba,zama tayi kan dining bayan ta debi abincin da zata ci,tana tsaka da cin abincinta Zaid suka shigo shida Aryan,suna zama saiga umma itama tafito nan suka cigaba da hirar su suna cin abinci, K'arfe 9 tabar falon takoma sashenta bata sake fitowa ba sai 11 saura lokacin Khalil yadawo suna can falonshi gaba dayansu harda umma,sashen nashi itama ta nufa jikinta na fitar da wani kamshi mai sanyi,cikin nutsuwa ta bude kofar falon ta shiga abinda idanuwanta suka gane mata shine yasanya ta taji jikinta yayi sanyi cikin rashin kwarin gwiwa ta juya zata koma...........................✍? _Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:13 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *39* ***Muryar umma tajiyo tana kiranta lokacin da take kokarin komawa, "Sa'adatu ina kuma zakije.....? Ki karaso mana ayi dake" Babu musu tafasa fita ta shiga,kujera ta samu ta zauna tana kallon kowa, Khalil ne zaune kan doguwar kujera shida Aryan wanda ke bacci akusa dashi sai Anty maamy dake kujerar kusa dashi tana sanye cikin brown colour din doguwar riga sai Zaid dake kujerar kusa da ita amma shi gaba daya hankalinsa yana ga wayar dake hannunsa yana daddannawa ita kuma na zaune opposite dinsu tana kallonsu,akusa da umma Hanan ta zauna tana yiwa Khalil sannu da zuwa sannan tana sake kallon Anty maamy dan sai yanzu ne ma tayi mata kallon tsaf,doguwa ce sosai dan idanma Khalil zai fita tsayi to da kadan zai fita, fatarta mai haske ce sosai wadda hutu da jin dadi suka sake haskaka ta, siririya ce Sam bata da kiba amma fa kuma tana da masifar kyau kamar ita tayi kanta tana da diri da sura, Hanan wani abu taji ya tsaya mata arai sakamakon murmushin da taga Khalil nayi lokacin da suke yin hira da Mami, "Maamy uwar son girma.... Wai dan Allah har yanzu baki daina son girman nan ba? Lokacin da kina yarinya fa har kuka kike yi idan akace kece karama acikinmu...." Wata dariya mai kayatarwa maamy tayi sannan cikin murmushi tace, "Woohhh Khalil ka iya bada mutane wallahi,yanzu da girmana kake fada min haka agaban Zaid..... Kana gani na kusa diban surukai,sahla fa jss 3 take Jawad jss 2 faruk ne kadai a primary school" "To kuma shine me? Kaji yarinyar nan da wata magana,to nida Khalid da ace da wuri mukayi aure da ba tuni mun aurar da 'yaya ba....." "To wai Khalil da kai da Khalid din da me kuka fini? How many years kuka ban? Da me kwado yafi gaya ne wai?" Dariya Khalil yayi yasake kishingida jikin kujera alamar yana jin dadin wannan hirar, "Wai dan Allah shekararki nawa? Fada min" "Am 39 by the way...." "Lallai maamy kina da son shekaru,to yarinya ai ko mu bamuyi 39 ba 38 muke har yanzu.... Ke ai ba zaki fi 36 ba ko 35..." "Haba haba Ibrahim....haba Ibrahim ya zaka fadi haka? Nice 35 ko 36? Gaskiya nafi haka" "Au wai ko dan kinga kin hayayyafa kin tara yara shine kike karawa kanki shekaru? Saboda kinga su sahla sun fara girma ko.... To ai ba anan takeba" Hanan kallonsu kawai take yi dan bata taba sanin cewa Khalil yana iya yin hira doguwa kamar wannan ba sai yau gaskiyar bahaushe da yace kowa da abokin zancensa,yau kam shi cikin nishadi yake da alama dan harda dariya yakeyi Hanan har tambayar kanta take yi wai dama mutumin nan yana hira? Kuma koda wasa bata taba bashi shekaru har 38 ba dan wallahi da za sata agaba ace ta kiyasta shekarunsa da ko tantama bata yi zatace 32 ko 33 domin jikinshi da fuskarshi duk basu nuna yafi hakanba, "Wai ma yaushe muka daina tsallakar dake kwata ne maamy? Idan kin manta in tuna miki" "Ibrahim kenan.... Ka manta lokacin da nake tare maka fada ko? Ka manta lokacin?" Dariya Khalil yayi, "Gaskiya maamy ki rage son girma dan wallahi duk shekarunki mu dai mun girme miki nida Khalid" "Da shekara daya da rabin? Shekara daya da rabi ne fa Ibrahim" "Zan fadawa Khalid ai duk abun da kika ce" "Shima saida muka yi dashi ai zuwan nan da nayi gidanshi,ku son girma gareku bayan kuma tuni na kwace muku girman,yanzu dole ku bani girmana" Murmushi Khalil yayi nan suka cigaba da hirar kuruciya har suka gangara suka koma ta duniya su Hanan dai na zaune suna jinsu saida dare ya raba sannan suka fara tafiya daya bayan daya,umma ce ta fara tafiya sannan Zaid,ita kam Hanan tana nan zaune koda za su kwana anan tayi alkawarin sai taga tafiyar maamy sannan zata tafi dan haka kawai taji bata jin dadin yanda Khalil yasake yabiye maamy suna hira duk da tasan yar uwarsa ce amma bata san ta ina suka haduba kuma da alama tare suka yi kuruciya suka tashi tare dan har hirar zuwa makaranta lokacin da suna kanana sukayi. Bayan fitar anty maamy itama tashi tayi ta dauki Aryan tafita sai da tafara kaishi dakinshi tukunna sannan ta wuce nata,bata san dalili ba amma baccinta kadan tayi ko me yasa oho kuma saida ma tajima kafin ta samu ya dauketa saboda tana ta tunane tunane marassa amfani zuciyarta sai faman sake baci take yi, Washe gari haka ta tashi shima babu walwala ahaka ta shirya Aryan sannan takoma part dinta bayan yatafi makaranta,wanka itama tayi ta shirya cikin atamfa exclusive riga da skirt sannan tasha humrarta da sauran turarurruka masu dadi,fita tayi dan ta sauka k'asa tana fitowa ta hango anty maamy ta glass ta nufi part din Khalil, kamar ta bita amma sai ta nufi kasa tana duba agogon dake daure a hannunta karfe 9 saura wasu mintuna, A babban falo ta iske umma da Zaid na kokarin yin breakfast Zaid rike da waya a hannunshi yana sakale da earpiece, gaisheta yayi duk da ahaife kamar zai girme mata amma dai yana bata girmanta,ruwan tea kawai ya hada da sauran kayan soye soyen da John yayi ya dauka yawuce dakinsa dake nan k'asa. Kallon umma barira Hanan tayi bayan Zaid yatashi, "Umma ina kwana? Ya gajiyar zama wuri daya?" "Alhamdulillahi Sa'adatu,ya akaji da dawainiyar gida da kulawa da Sulaimanu?" Murmushi Hanan tayi amma batace komai ba, hira suka cigaba dayi ita da umma jifa jifa har sukaji alamun saukowar Khalil,tare suka jero shida anty maamy wacce ke sanye da doguwar riga ta bacci ta yafa babban mayafi shi kam farin tsadadden boyel ne ajikinsa wanda yasake fito dashi dass kuma ya amsheshi, Tun kafin ya karaso kamshinsa yafara karasowa, Hanan tun bayan kallo daya da tayi musu bata kara sake kallon su ba,tana ji suna gaisawa da umma yana sanar mata da wai Legos zaije amma by flight kuma insha Allah ayau zai dawo, "Ranka yadade wannan charger din abar min mana sai ka nemo wata...." Anty maamy tafada tana daga charger din dake hannunta, "Kinma isa..... Aro nabaki kina gamawa ki mayar min" "Dan Allah ka nemo wata Ibrahim.." "A'a indai bada a nemo miki,amma nidai ki mayar min" "To babu matsala...., Allah yatsare saika dawo" Har tajuya zata tafi ta sake dawowa, "Am Khalil dan Allah acikin motocin gidan nan za a ara min daya inaso zan fita anjima....zanje gidan wata friend dita" "Babu matsala ki fadawa Zaid sai ya d'auko miki...." Daga haka yafita itama ta wuce daki, Hanan dai sama sama ta yi breakfast dinnan ta tashi ta koma part dinta wanda ita kanta bata san abinda ke damunta ba, Tunda ta kule acikin part dinta bata fito ba sai la'asar iya umma kadai ce agidan da ta tambayi umma su Zaid fa sai tace ai tun dawowar Aryan suka fita su uku har Aryan din da anty maamy saboda dama yau babu islamiyya tunda alhamis ce,bata kara magana ba taje ta zubo sakwara da miyar egusi ta dawo ta zauna, "Wai umma meye dangantakar Abban Aryan da anty maamy?" "Kakanninsu daya,da uban maamy da uban Khalil ai uwa daya uba daya suke.... Dukkaninsu 'yayan moddibo ne,Asalinsu, Ibrahim moddibo haifafen garin Billiri ne dake nan gombe sana'arshi a wannan zamani kiwo domin Allah ya hore masa dabbobi masu tarin yawa kusan yana daya daga cikin mutanen da ake lissafawa wadanda keda tarin arziki a wannan karnin domin yana da yawan shanu,tumaki, da kuma jakuna,matarsa daya maryo da yara hudu Sulaiman shine dan fari sai Idris dake bi masa sannan sai mariya sai kuma karamarsu muzayya, Duk cikar gombe da batsewarta babu wanda bai san moddibo ba domin mutum ne sananne kuma malami domin lokacin da yaransa suka fara girma yabaro Billiri yadawo cikin garin gombe da zama nan yasake bude tsangayarsa inda almajirai ke taruwa suna karatu,anan 'yayansa duka suka yi karatu na allo da na zamani amma na allon yafi yawa dan iya Idris ne kadai yasamu nasarar yin karatun boko mai yawa amma yayansa Sulaimanu shi iyakacinsa primary, Anan cikin gombe duk sukayi aure shi Sulaimanu yar gidan sarauta ya aura yar sarki gaba da baya wacce take sonsa dalilin zuwa fada da suke yi tare da mahaifin sa moddibo saboda aminin sarki ne a wancan lokaci dan shine limamin gidan sarki ma ko ina sarki zaije suna tare to kinji inda ita zaituna suka hadu da Sulaimanu mahaifin mijinki har akayi aure kuma aka samesu su biyar da saude dashi ibrahim mijinki da Lubnah da Humaida da kuma zaidu mai sunan kakan hajiya zaituna wato sarki zaidu na uku,Shi kuwa Idris can yawon karatunsa a k'asar borno ya samo tasa matar labibah wacce ta kasance shuwah wanda ana kyautata zaton ma asalinsu larabawan sudan ne zama yakawo su nan k'asar maiduguri suka zo suka zauna,bayan andaura musu aure nan gombe suka dawo suma suka zauna ga dakin zaituna ga na labibah kowacce tana zaune da mijinta lafiya,kuma yanda kan mazajensu yake ahade haka suma suka hada kansu kin san zama irin na da ya banbanta da na yanzu,ita zaituna duk da kasancewar ta yar sarki jikar sarki bata dauki girman kai ta dorawa kanta ba tare suke yin girki da sauran aikin gida ita da labibah har Allah yabawa kowaccensu rabo bayan zaituna ta yaye babbar yarta ta farko saude na biyunne sukayi rainon ciki lokaci daya dan kusan tare suka haihu tsiran na kwana biyar ne kowaccensu ta haifi danta namiji kuma duk aka saka musu sunan moddibo wato ibrahim amma shi Khalil da yake shine babba shi sai moddibo yasa masa Khalil shikuma dayan Khalid to tare suka taso suka yi wasan kasa suka yi komai da kika sani tare shekararsu daya da watanni biyar labibah ta haifi maamy to itace aka sakawa sunan maryo mahaifiyar su Sulaimanu shine suke kiranta da maamy,itama acikinsu Khalil ta taso tare suka tashi har girma,to da yake kin san shi Idris yayi karatun zamani babu laifi to shine yashiga siyasa ka'in da na'in kuma da Allah ya dafa masa sai yasamu karbuwa,jinin moddibo akwai albarka kowa yana son Idris dan har mukamin governor yarike kuma shine yajawo Khalil ajikinsa yadorashi shima aharkar siyasar duk da shi Khalil din bawai dan yana da sha'awar hakanba dan har commissioner na yada labarai yayi masa lokacin mulkinsa shekararsa hudu yana rike da commissioner na yada labarai matasa da wasanni saboda abinda yakaranta kenan a makaranta,to lokacin da aka gyara kundin tsarin mulki akace anbawa yan k'asa da shekara 40 damar rike mukamin ministoci saboda suma yara zasu iya a lokacin Alhaji Idris yatura Khalil kuma da yake Allah ya tsaga da rabonsa kin ganshi nan sai yasamu dan yanzu akalla ba a kasaru ba mun shafe fiye da shekara biyu a nan kadanne bai karasa uku ba,maamy yar uwarsa ce sosai yaranta uku amma yanzu babu auren dan tafi shekara uku ma bata tare da mijinta, zawarci take yi....." Ajiyar zuciya Hanan ta sauke bayan umma ta kammala bata tarihin su Khalil,to ita yanzu me yadace tayi? Ta ina yadace tafara? Wanne mataki yakamata ta dauka............................??✍? *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *40* ***Sakin fuskarta tayi bata bari umma barira tagane komai ba dan bata nuna mata cewa tana tare da damuwa ba,har magriba suna tare da umma suna shan hira da yake umman gwanar hira ce,suna kokarin tashi su shiga salla su Anty maamy suka dawo tana rike da hannun Aryan wanda keta tsallen rashin ji, Damm Hanan tayi tana kallon anty maamy wacce ta hade cikin bakar riga gown mai stones ta dan yafa mayafin rigar akanta kuma hakan ba karamin kyau yayi mata ba sai dai ko hassada irin ta mai ita, Sannu da zuwa suka yimusu Hanan bata jira komai ba ta tashi ta hau sama tare da Aryan,bayan sun idar da salla acikin dakinta Aryan sai labari yaketa bata na unguwar da suka je dan har abokan wasa yasamu agidan shiyasa fitar tasu tayi masa dadi ita dai hanan saurarenshi take tana jinjina kai amma idan taga fitar tana neman tayi yawa to zata sanarwa ubanshi dan babu abinda yayi mata zafi kar abu yafaru Khalil yazo yana ganin laifinta saboda shi ba sakaka yake bari ana fitar masa da yaro ba dan kullum ma sai yayi wannan takarar yanzu ne ma ya hakura ya daina, Sai bayan da tayi sallar ishah sannan ta fito nan ta iske umma da su Zaid ana shan hira harda anty maamy,itama zama tayi akayi da ita sune har wurin 11 dan saida Khalil yadawo tukunna sannan hirar ta tashi. Haka dai aka cigaba da lallabawa Zaid kam tuni yakoma gombe yabar anty maamy wanda hakan gaskiya bai yiwa Hanan dadiba domin bata son zaman anty maamy atare dasu bawai dan kasancewar ta bazawara ba a'a sai dan zata rusa mata target dinta,zata bata mata plan dinta,ahalin yanzu ita babban burinta shine ta yanda zata ja mijinta ajiki su shirya yasaki jiki da ita suyi rayuwa irin ta ko wanne ma'aurata shiyasa zaman anty maamy atare dasu kamar karan tsaye ne agareta, gashi kullum suna tare da Khalil idan har yana gida sai dai idan baya nan amma idan yana gida zaka samesu zaune shida maamy suna hira har abinci maamy ke zubo musu tare amma kowa da flate dinsa hakan ba karamin bawa Hanan haushi yake ba, Yau ma suna zaune a falonshi misalin karfe 10 na dare sai hira suke yi da maamy hirar sharrin da yesmin tayi masa yana bata labarin irin yanda kotu ta wankeshi dan ankusa kawo karshen k'arar, Dariya maamy tayi sannan cikin tsokana tace, "To kai ka aureta mana....". Dan rausayar da kai yayi yana wasa da wayar hannunshi, "Nida ke waye yafi dacewa yayi aure yanzu? Ke yakamata kiyi aure ai maamy" Dan murmushi mai ban sha'awa tayi sannan ta kalleshi, "Aure fa kace Khalil..... Hmmm aiki jaa" "Ba wani aiki ja,kawai acikin zawarawan nan naki ki bawa wani dama,in bahaka ba ni sai infito" Dariya maamy tayi harda rike ciki, "To dama dama kai din..... Zaka iya fitowa" Duk da awasa suka yi maganar sai kuma sannu ahankali take shirin fara zama babba, Hanan bata da masaniyar hakan amma jikinta yana bata kamar akwai wani abu tsakaninsu, Shi Khalil rabonshi da soyayya ko wani abu mai kama da haka tun Ramlat tana raye,wata kulawa ta musamman maamy ke bashi ko office yafita tana dan yawan kiranshi awaya suna hira tayi masa fatan alkhairi kuma idanma basu samu damar yin wayar ba to tana tura masa da text message idan kuma yadawo gida zasu kasance tare suna hira amma aboye kamar soyayya suke yi saboda dama tun asali tun kuruciya maamy budurwarsa ce itace budurwarsa tafarko a tarihin rayuwarsa irin saurayi da budurwar nan na wasa dan ko abu yaci sai ya rage mata, Khalid kuwa bai isa ya tabata agabanshi ba dan baya mantawa sunsha kai ruwa rana akan hakan sunsha dambe da Khalid akanta idan ya mareta ko ya daketa to lokacin da yake da wuri ake yiwa yara mata aure shiyasa aka aurar da ita dan shi lokacin bai isa aureba kuma iyaye ma basu san sunayi ba amma da ansani ta yuyu asamu mafita lokacin, Tuna hakan da yayi sai yaga ai gara kawai ya komawa maamy domin dama can akwai tsohuwar soyayya kuma ita ba karamar yarinya bace bare suyi ta samun sabani,da hankalinta tasan menene aure kuma ta san yanda zata zauna dashi da irin kulawar da yadace tabashi,dari bisa dari yaji zuciyarshi ta gamsu da hakan,bai fito fili ya fadawa maamy abinda ke cikin ranshi ba itama haka amma dai suna dan nunawa juna alamu ko kunyar fitowa su sanarwa da junansu sirrin zuciyoyin nasu suke yi oho. Hanan gaba daya ta susuce ta sake tsangwamar kanta sai kara lalacewa take yi dayake ita budurwa ba kamar bazawara ba ai wayon ma ba daya bane haka sanin sharruda da ka'idojin auren ma duk ba daya bane,ita abinda ke sake daga mata hankali shine irin yanda Khalil da maamy suka dinke har wani fita suke yi tare,idan zaije office tace zata bishi akwai inda zasu sauketa tace zataje saloon abubuwa dai iri iri,gaba daya hanan bata da kwanciyar hankali, Yauma asama ta samesu falonshi suna hira da system akan cinyarshi maamy na zaune kujerar dab dashi irin zaman masoya dinnan,wani abune ya tokare kirjin Hanan rufe idonta tayi taje ta zauna akan kujerar da yake zaune akai ya tankwashe kafarshi daya akan kujerar dayar kuma tana kasa,sanye yake da fararen kananan kaya jeans da t shirt fuskarshi tasha kyau kamar ya shafa mai da powder, Bata taba sanin cewa zata iya haka ba sai yau saboda Khalil din kwarjini yake yimata dari dari take yi dashi,bata taba attempting zama kusa dashi irin wannan ba sai yau,zama tayi gefen shi gata gashi jikinsu na gogar juna hannunta kan tafin kafarshi dake lankwashe amma wannan bata saniba ta zaci jikin kujerar ne, Juyawa yayi shima ya kalleta da mamaki acikin ransa, idanuwanshi kuma na nuna neman Karin bayani tunda watakila da abinda tazo fada masa tunda har tayi irin wannan zaman, "Uncle..... Banda lafiya" Ta fada tana marerecewa saboda tana masifar jin haushin lankwasa murya da anty maamy keyi idan tana yimasa magana kuma bata son zaman nan da sukeyi tare akujeru makusantan juna,tunda ita matarsa ce ai game din tazo da sauki ita zata iya yimasa abinda ita maamy bata isa tayi ba idanma ta gwada yi to shari'a ce zata hau kanta, Katse abinda yake yi yayi ya kalleta cikin sanyin muryar sa yace, "Me ya sameki?" Dan jimm tayi saboda ta rasa karyar da zata yi masa zuwa can ta tuno da datsewar da Aryan yayiwa dan yatsanta tun shekaran jiya ajikin kofar bathroom dinshi amma bawani sosai bane sai dai wurin ya kunbura kuma yaji ciwo,yatsan ta mika masa tana cewa, "Ka gani.... Datsewa nayi jikin kofa" Zai iya cewa this is the second time da ya taba riketa nafarko lokacin da glass ya fashe ya watsu ajikinta sai wannan na yanzu,jan dan yatsan yayi cikin sauri ta shige jikinsa domin wani irin azababben radadi taji kamar yatsan zai cire dan saida tayi nadamar nuna masa,yana kara ja tana sake shiga jikinsa dan har jefar masa da laptop tayi kasa, tsakaninta da Allah take yin kukan da take yi saboda zafi abunka da yan auta shagwababbu kuma sakalai LoL..... Maamy yi tayi kamar bata gansu ba,da yake akwai shekaru da kuma wayewa sai kawai ta mike fuskarta awashe tace, "Khalil bari inje in kwanta kaina ciwo yake yi yau banyi baccin rana ba,see you tomorrow" Yana rike da hannun Hanan wacce ke cukwikwiye ajikinsa ya kalli maamy, "Yau da wuri haka? Alright Allah yabaki lafiya, Allah ya kaimu goben,saida safe" Anty maamy bata kara cewa komai ba haka bata kallesu ba ta wuce ta fita,maida kallonsa yayi kan Hanan wacce ke sharbar kuka kamar yana kwakwale mata ido, "Targade fa kika yi...." Dago jajayen idanuwanta tayi ta kalleshi haba gaskiya mana taji ciwon yaki wucewa kuma bata iya amfani da yatsan, "Gobe da safe zan fadawa nura ya samo miki mai gyara sai agyara...." D'aga kai tayi amma takasa ko kwakkwaran motsi domin bata son matsawa daga jikinsa ji take inama zata tabbata ahaka, "To dagani....." Taji yafada yana kokarin dauko system dinshi dake kasa, Kunya ce taji ta lullube ta nan ta matsa tana rufe idanuwa da tafukan hannunta,duk da ba hira suke yi ba amma sai da takai 12 saura a wajensa sannan ta tashi ta tafi ta kwanta,kasa baccinma tayi dan haka ta kunna data ta shiga WhatsApp,sakon hajja hasinah tagani ta private tana tambayarta lafiya kuwa 2 days ta daina participating a group? Dan duk abinda za ayi da tana cikin sahun yan gaba gaba masu gwadawa da kuma bada himma amma yanzu shiru kamar bata nan,bata da kawaye na jiki ko aminiya wanda zata fada mata damuwarta anty salaha kuma idan ta fada mata fadane zata sha shi kamar babu gobe har ta goda Allah,anty badi'a kuma yanzu bata da waya a hannunta shiyasa ta yanke shawarar sanar da hajja hasinah watakila zata taimaka mata da shawarwarin da suka dace,nan tayi mata voice note ta tura mata ta zayyane mata matsalar da take tare da ita sannan ta kare maganar da fadin, "Nikuma wallahi anty ina sonshi tun ranar da na fara ganinsa to kuma shi baya sona hankalinsa da tunaninsa na ga matacciyar matarsa,ga wannan anty maamy din tazo duk tana neman kankane min miji dan Allah kibani shawara" Kashe data dinta tayi bayan tagama yiwa hajja hasinah bayanin komai,daga nan tayi addu'a ta kwanta. Shi kuwa Khalil bayan yashiga bedroom zai kwanta da misalin karfe 1 miss called din maamy yagani,bai kiraba saboda yasan yanzu kila tayi bacci,kwanciya yayi ya lumshe idanuwansa,ya kamata kawai ya auri maamy domin rabonshi da wata ya mace shekaru kusan bakwai bayan kuma yana da cikakkiyar lafiya sannan sau da dama halin bukatuwar yana damunsa yana takura masa yana hanashi sakat gara kawai yayi auren ai arashin uwa akanyi uwar daki,insha Allah cikin kwanakin nan zai fasawa maamy sirrin dake ranshi. Da asubah bayan Hanan ta idar da salla take ganin sakon hajja hasinah inda itama ta turo mata da voice note kuma har lokacin tana online,budewa tayi tafara saurara, "Hanan naji sakonki kuma matsalar ki matsala ce babba kuma ba babba ba,tun farko sakacinki yajawo haka.... Ai baka sallama namiji musamman ma miji irin naki,maza da ake rikesu hannu bibbiyu gudun kada su zame, gaskiya kinyi kuskure babba amma akwai abubuwan da idan kinyi zaki iya gyarasu watakila amma fa dole sai kin dage,sai kuma kin mike tsaye kinyi iyakar iyawarki,yanzu da farko dole sai kin kula da abincin sa,sai kin kula da al'amuransa na yau da kullum sannan uwa uba shimfidarsa wanda wannan shine matakin karshe..... Ki fara sanin wanene ma shi tukunna? Me yafi so? Wadanne abinci yafi so? Me yafi burgeshi? Wacce irin hira ke sakashi nishadi?, Me yafi daukar hankalinsa? Wadannan sune assignment dinki ayanzu kuma sune zaki nemo dan ta nanne kadai zaki samu solution,dan haka ina yimiki fatan nasara dan daga yanzu dinnan zaki fara....." Wata iska mai zafi hanan ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya lallai kam wannan babban assignment aka bata mai chaja kwakwalwa da sata nazari gamida tunani,to yanzu ta ina yadace tafara..............................✍? *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *41* ***Tafi mintuna goma zaune batare da tasan ta ina yadace tafara ba ganin wankin hula na shirin kaita tsakar dare yasata mikewa daga zaunen da take ta cire hijabin jikinta tafita tamkar kazar da kwai ya fashewa aciki, kitchen dinta da ke makare da kaya wanda musamman aka tanada dominta a matsayinta na matar gida tayiwa tsinke, to yanzu ita me zata dafa tunda takamaimai bata da masaniyar me yafi so yaci da safe? Amma dai wallahi hajja hasinah ta hadata da assignment me zafi, Tana nan tsaye harabar kitchen din tana tunanin me yadace dabara ta fado mata,gwara kawai tayi abincin kala biyu daya na gargajiya daya kuma na zamani inyaso duk wanda taga yaci to shi yafi so, Hakan kuwa tayi nan ta zage ta soma girkinta cikin jin dadi da farin ciki domin girki yana daya daga cikin abubuwan da ke sakata nishadi a lokacin da take gabatar dashi,wainar semovita tayi za aci da suga kuma abarta tayi kyau kamar ta shinkafa tayi laushi libis sai kunun gyada da ta dama haka kuma ta soya dankali da sos wadda taji kwai nasha nasha, Agaugauce ta je ta shirya Aryan bayan tagama aikin danma dai ba wani mai yawa tayiba shiyasa bai dauki dogon lokaci ba,tana gama shirya Aryan ta kamo hannunshi suka sauko kasa wanda tuni kuku yajima da shirya table, breakfast ta bashi yaci sannan ta shirya masa lunch box dinsa yatafi,yana tafiya takoma sama ta shiga wanka shima bata zauna tajima acikiba tayi tafito aranta tana jinjina kokarin iyaye mata musamman wadanda suka tara 'yaya ko kuma haihuwar tayi musu sammako,ka kula da yara sannan ka kula da ubansu kai gaskiya isn't easy,shiryawa tayi batare da bata lokaci ba cikin orange colour din atamfa mai bala'in kyau,dinkin fitted ne shiyasa yayi mata tsantsam ajikinta,bata yi wani dogon lissafi ba wurin kalmasa dan kwalinta ba kawai dan cokara shi tayi tafita kuma hakan sai yabada style mai kyau, Yau kam ta shirya baiwa Khalil surprise dan duk abubuwan da ta dafa kwasarsu tayi ta kai sashensa ta jejjera bisa table din cin abinci sannan ta nemi wuri ta zauna nan cikin falon, agogon hannunta ta kalla bayan ta zauna karfe 8 saura mintuna biyar,kai amma gaskiya tayi kokari kuma aikin nata ma yayi sauri sosai,yau kam sai dai anty maamy tazo ta isketa duk sammakonta ehe. Bata jima zaune afalon ba taji alamun bude kofa, kamshinsa ne yafara sanar da ita fitowarshi kafin shi din ya bayyana,sanye yake cikin farin yadi na maza dandakeke mai mutukar kyau mai laushi shara shara, yana tafe yana kokarin balle hannun rigarshi,mamaki yaji ya kamashi kwarai da gaske sakamakon ganinta da yayi zaune cikin falon,mikewa tsaye tayi daga zaunen da take alamar girmamawa, Da idonsa yake neman karin bayanin ganinta da yayi a daidai wannan lokaci,kasa tayi da kanta ta dan duka ta gaisheshi, "Ina kwana?" "Lafiya lau..." Ya amsa mata idanuwanshi na kaiwa kan dining, warmers yagani jere akai da sauran kayan karin kumallo,agogon hannunshi ya kalla sannan ya dan yi guntun tsakin da bata san dalilinsa ba, "Waye ya kawo wancan abincin?" Ya bukata batare da ya kalleta ba domin hankalinsa na kan wayar dake hannunsa, "Nice....." Ta bashi amsa cike da kwarin gwiwa domin ta dauri aniyar canja komai a tsakaninsu, Bai kara magana ba ya nufi saman kujera ya zauna yana ta danne dannen waya da alama wani yake nema amma wayar taki shiga dan sai dan guntun tsaki yake ta ja yana kara wayar a kunnensa,zuwa caan taji yafara magana fada fada, "Wai ina kaje ne inata kiran wayarka tun asubah amma taki shiga?........ Kana jina...... Ya isa...... Yanzu yanzun nan katashi kaje store ka dauki abinci ka kai gidan yaran nan........ Abincinsu yakare tun jiya....... Kawai ka wani kashe waya tun 11 ana ta nemanka wayarka akashe........ Ka tashi yanzu kaje karka bata min lokaci...." Daga haka ya cire wayar daga kunnenshi yana jin kamar an dauke masa wani nauyi dake kansa, haba har ya dan ji sanyi amma ace anbar yara marayu babu abinci ai akwai matsala,ita dai hanan ba gane kan zancen nashi tayi ba saboda bata san da wanda yake wayar ba kuma bata san akan wanene ba, Ta glass ta hango anty maamy na tahowa hannunta rike da karamin flask din coffee zata kawowa Khalil mikewa tsamm Hanan tayi ta koma kusa dashi aranta tana cewa ai kuwa yau sai dai ayi wacce za ayi amma Khalil bazai sha wannan coffee dinba breakfast din da ta kawo masa zai ci, "Ga breakfast din can kar ya huce......." Ta fada cikin marereta, baice komai ba kuma bai tashi ba yaci gaba da danne dannen wayarshi, falon shiru baka jin sautin komai sai kukan dawisu dake tashi daga bayan dakin baccinsa,ahaka anty maamy tashigo nan Hanan ta dan sake matsawa dab dashi wanda har sai da hakan yaso batawa anty maamy rai, Fuskarta babu yabo babu fallasa ta karasa cikin falon tana dan basarwa,sanye take da doguwar riga ta material multi colour rigar mai burmemen hannu ta yafa siririn bakin mayafi akanta, karasawa tayi ta zauna kujerar gefensu, "Ibrahim har kafito kenan....." Daga ido yayi ya kalleta, "Maamy..... Kin tashi lafiya.... Wallahi nafito..... Zanje kwara state ne" "Allah ya kiyaye hanya...." Ajiye masa flask din tayi agabansa, "Ga coffee din..." "Ok thank you.... Sai dai ma nafita dashi office nasha acan" Hanan na jinsu batace ko uffan ba kuma da yake yau yan rashin kirkin na kusa ko gaida anty maamy bata yiba sai wani daddauke kai take yi ita ala dole ankula mijinta, "Me da me aka kawo kan table din can?" Taji Khalil yana tambayar ta,wata irin mikewa tayi babu zato yaji ta kamo hannunsa mai tsananin taushi, "Uncle kazo ka gani mana....... Kai fa na dafawa" Ba Khalil ba ita kanta anty maamy saida taji mamakin wannan lamari,jingina tayi jikin kujera yanda zata cigaba da kallon scene din da kyau, Duk da baya wani sakar mata fuska mikewa yayi yabi bayanta zuwa kan dining din wanda har lokacin tana rike da hannunshi,wani irin shock take ji kamar anjona mata electric amma ta kasa sakinsa har sai da ya zauna saman table din, Tea yace ta hada masa rabin cup amma ganin kunun gyadar da tayi sai yace tabar tea din ta zuba masa kunun,da kunun da waina ta saka masa yaci sai wani kwarkwasa take yi wanda hakan ke baiwa anty maamy dariya, lallai yaro yaro ne,yaran yanzu akwai rawar kai da feleke ita ala dole mai miji sai wani karairaya take yi mijin da ba ma lallai ta burgeshi ba,mikewa tsaye anty maamy tayi domin ta gaji da kallon dramar tasu, "Ibrahim bari naje na kwanta.... Zamuyi waya anjima" "Ok mammy thank you" Fita tayi Hanan tabita da harara aranta tana cewa ai wayar ma insha Allah baza ayita ba,shi kam har ga Allah yaji dadin waina da kunun da yasha haba amma ace kullum tea tea babu wani canji,mikewa yayi yawuce cikin bedroom dinshi tana ganin haka tayi wuff ta mike taje ta dauki flask din coffee din da anty maamy ta kawo taje ta tuttuleshi cikin sink din dake dinning area din, Fitowa yayi tsaf cikin shirinsa na fita sai zuba kamshi yake yi,tsaye take hannuwanta abaya tana wasa dasu, "Amm........ Am nace...... Maganar mai gyaran targaden da kace....." Shiru ya dan yi na dan wani lokaci kafin ya daga ido ya kalli side din da take, "Za aturo shi...." "Nagode..... Adawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya...." "Amin,nagode" Ya fada a takaice sannan yawuce zai fita har yaje bakin kofa yajiyo, "Yawwa bani wannan flask din wanda maamy ta kawo min coffee" Dauka tayi ta nufeshi ta mika masa batare da ta nuna wata alama ba wacce zai sa ya zargi tana da masaniya akai,hannu yasa ya karba sai kuma yaji empty,dan jijjigawa yayi yana son ya tabbatar da abinda yaji nan kuwa yaji wayam babu komai, "Ya najishi empty??" Ya fada ahankali amma kasancewar akusa take dashi taji abinda yace, "To ko dai dama bata saka maka komai ciki ba?" Ita kanta ta san wannan tambayar da tayi masa ta rainin hankali ce, baice mata komai ba ya mika mata flask din yawuce yafita tana biye dashi abaya kamar wata bodyguard,sai da ta rakashi har kasa suka gaisa da umma barira sannan yafita,sai lokacin tajuya ta koma sama saboda dama bata son ya hadu da anty maamy ne a kasa shiyasa ta zame masa jela, Falonshi ta gyara masa ta tsaftace shi tas amma bata yi garajen shigar masa cikin bedroom ba,sai dai amma abinda yakama tun daga kan falonshi zuwa bathroom din dake cikin falon da sauran lungu da sako dake harabar sashen nasa duk ta samu nasarar kalkalesu tsaf, Bayan ta gama gyara nata sashen kasa ta sauka wurin umma wacce ke kishingide a d'akinta,anty maamy kuma na falo tana rike da novel na turanci tana karantawa, tsaki Hanan tayi aranta tace to ko me anty maamy din take jira da taki tafiya ta share daki ta zauna? Shifa Zaid kwata kwata ma kwananshi biyu ya tafi amma ita anty maamy taki tafiya koda yake ai gidan dan uwanta ne ta sake fadin hakan acikin ranta,dakin umma ta shiga bayan ta shigar musu da sauran kayan breakfast din da Khalil yarage, Zama tayi suka fara cin wainar da ta yiwa Khalil itada umma,umma na sake kara mata haske akan irin kalolin girke girken da Khalil yafi so wanda shi yafi son abincin gargajiya dan bai ki ya yi breakfast da dumamen tuwo ba ko koko da kosai watikil wannan ne dalilin da yasa bai cika cin abinci ba yake zama da yunwa saboda su ma'aikatan gidan sunfi maida hankali wurin girke girken zamani,murna tayi sosai saboda jin wannan daddadan labari daga bakin umma. Bayan mai gyaran targade yazo yayi mata sama ta koma ta shiga dakinta ta samu dan karamin littafinta da biro ta soma tsara jaddawalin girke girken da zata rinka yi asati duk na gargajiya amma zata dan rinka hadawa da na zamani shima ba wani mai yawa ba,bayan tagama kwanciyar ta tayi ta huta har azahar tana kwance,bayan ta idar da salla sai maganar anty maamy ta fado mata wacce tayiwa Khalil da safe wai sai sunyi waya, Wayarta ta jawo ta shiga ta tura masa massage tunda dai ita bazata iya kiranba domin koda ta kirashi bata san abinda zata ce masa ba. Khalil na zaune tare da mukaddashin mai girma gwamnan jihar kwara sakon Hanan yashigo, _Uncle ya hanya? Ya aiki? Allah yataimaka ya tsareka ya dawo mana dakai gida lafiya._ Mamaki da al'ajabi sakon Hanan suka bashi,to wannan yarinyar lafiyar ta kuwa? Domin daga jiya zuwa yau gaba daya ta sake canjawa fiye da da,sai kace ba itace ta rufe ido a kwanakin baya ta rinka yimasa ruwan tijara da rashin kunya ba,to yanzu kuma ko me ya canjata? Oho, Reply ya tura mata kamar yanda yasaba da Thanks kawai sannan yaci gaba da harkokinsa. Hanan kuwa sai la'asar ta shiga kitchen ta shirya lafiyayyen tuwon semovita dinta miyar ganye, sannan ta sake dama kunun gyada wanda yasha lemon tsami sai kamshi yake, Bayan tagama Aryan taja suka tafi garden suka haye lilo nan suka shantake har magriba sannan suka shiga cikin gida,anty maamy ce kadai a falon kasa tana daddanna waya,ganin Aryan yasata kiransa ita kuma Hanan ta wuce sama bata bi ta kansu ba,salla tayi bayan ta idar ta yi zamanta a daki tana kallon wani kayataccen labari mai dogon zango na hausa,anan Aryan yazo ya sameta suka cigaba da kallon tare. Misalin karfe 9 Khalil yashigo gidan,babu wanda yasan ma yadawo,wanka yafara yi,yafito yana shiryawa anty maamy ta kirashi,dauka yayi yana tsane jikinsa da dan karamin towel, "Hello.... Ka shigo ne?" "Hy mimimi......" Murmushi anty maamy tayi ta shafi gashin kanta dake bude tana kwance saman gado, "Kai baka rabo da tsokana Ibrahim,ka dawo dinne?" "Ehh.... yanzun nan nashigo nayi wanka" "Ok....to ya? Zamu je dinne?" "Uhmm bari na shirya,bani 10 minutes" "Ok" Katse wayar yayi yaci gaba da shiryawa,mintuna kadan ya karasa shiryawa bama zaka taba ganewa shi bane sai dai idan kayi masa kyakkyawan sani, Itama Anty maamy dan sake gyarawa tayi sannan ta fito,da motarshi sukayi amfani suka fita PA yana jansu yayinda su kuma suka kame agidan baya bodyguards dinshi na biye dasu, Wani Park suka je kayatacce ma'abocin sanyi da sanya nutsuwa,zama sukayi suna fuskantar juna da wani dan table a tsakiyar su, "Maamy...." Yakira sunanta cikin taushin murya,daga idonta tayi ta kalleshi fuskarta cike da annuri, "Khalil...." "Maamy bazan boye miki sirrin dake cikin zuciya ta ba..... Ni dake ina kyautata zaton duk abu iri daya muke ji agame da juna....." Dan murmushi tayi sannan ta tallafi kumatunta da hannunta guda daya tana kallonsa, "Amma wai me ya rabaki da uban yayanki? Saboda a iya sanina dake ke macece mai hakuri though dai zaman aure yana da banbanci da kowanne irin zama" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dan lumshe idanuwanta ta budesu akansa, "Khalil mahaifiyar shi ce ta rabamu,bata sona aduk shekarun da muka shafe tare da danta,ni babu abinda ya hadani da Bilal..... Mahaifiyar shi ce bata kaunata kuma ta sanadiyyar ta nabar gidan" Jijjiga kai yayi sannan yayi murmushi mai dauke hankali, "To insha Allah yanzu zaki samu uwar mijin da take ji dake take kaunarki kamar ranta...... Maamy shin zaki iya karasa sauran kwanakin da suka rage miki a duniya tare dani?" Duk da tajima tana zargin jin wad'annan kalaman daga bakinsa amma bata tsammaci zata jisu da gardi da zaki irin haka ba, Rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta cikin farin ciki tana jin iska na kadata kamar tana yawo cikin gajimare, "Woww........ Khalil..... Wadanne irin dadadan kalamai ne wadannan? Wow....." Murmushi yayi ya dan kalleta bayan ya rausayar da kanshi gefe daya, "To ko dai ban samu karbuwa bane?" Murmushi tayi wanda har fararen hakoranta suka bayyana, "Hmmmm..... Anya kuwa ban yimaka tsufa ba?" Harararta yayi hararar dake cike da ma'anoni daban daban, "Nawa kike da har zaki yimin tsufa,nine ma dai nake tunanin kamar zan iya yimiki tsufa" Wannan karon dariya tayi sannan ta kalleshi, "Kai ai har yanzu kamar yaro ne,ban san menene sirrin ba amma baka canjawa" Murmushi yayi yana wasa da agogon hannunshi, "Maamy kenan.... Ai kin fini kuruciya,wai dan Allah yaran nan waye zai zaci naki ne? Saifa wanda yasani" Dariya tayi suka cigaba da koda juna daga bisani ya kalleta, "Me kike so inbaki a matsayin sadaki...?" Dan jimm tayi alamar tunani,zuwa can ta kalleshi, "Ring..." "Na gold ko na azurfa?" "Diamond gold" "Angama ranki yadade,kamar nan da yaushe kika shirya yin auren ne?" "Ka bari zamuyi wannan maganar daga baya" Misalin karfe 11 suka koma gida, Hanan tun 10 take jiran dawowarsa taci gayu cikin English wears riga da skirt,kamar wacce akace ta sauka kasa tana saukowa suna shigowa,tsayawa tayi tana kallonsu maamy sanye cikin bakar doguwar riga mai adon stones ja ajiki ta yafa jan mayafi marar nauyi,shi kuma Khalil kananan kaya ne ajikinsa jeans da riga long slif mai dogon hannu da p cap duk bakake,kafarsa sanye da bakin combos,sosai yayi kyau abunka da farin mutum cikin bakin Kaya............................✍? _Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *42* ***Yi tayi kamar bata gansu ba ta wuce dining area taje ta bude fridge ta dauki kwalin lemon abarba guda daya sannan takoma sama tuni lokacin maamy ta shige dakinta shi kuma Khalil yawuce part dinsa zuciyarsa cike da abubuwa guda biyu wato damuwa da kuma farin ciki,bangare daya na zuciyarshi yana farin ciki zai samu abokiyar rayuwa sannan daya bangaren kuma yana bakin cikin tunawa da mosoyiyarshi Ramlat wacce ta tafi ta barshi cikin shauki da kewarta, Zama yayi a falonshi ya cire p cap din dake kansa ya ajiye sannan yafara kunce igiyoyin dake jikin takalmin combos din dake kafarshi daidai lokacin Hanan ta turo kofa ta shigo tana mai yimasa sallama, Daga kansa yayi ya kalleta sannan ya amsa mata sallamar yana zare takalman daga kafarshi, "Masha Allah...." Ta fada acikin ranta saboda yanda yayi kyau ya sake ja cikin kayan jikinsa,zama tayi dan can nesa dashi cikin sanyin murya mai cikeda tsantsar ladabi gamida biyayya tace, "Sannu da zuwa uncle...." "Yawwa" ya fada atakaice domin zuciyarshi ce ke wani irin hautsinawa tana yimasa kuna,yarasa meyasa aduk lokacin da yaso yin maganar da ta shafi aure yake samun kansa cikin wannan mummunan halin, Bata yi kasa agwiwa ba ta sake kwantar da murya tace, "Ga abinci can saman table,ko akawo nan...?" Girgiza mata kai yayi sannan ya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanuwansa,shi kadai yasan abinda yake ji kuma yasan abinda yake damunsa shiyasa kadaici kadai yake bukata daidai wannan lokaci, Ganin yaki kulata yayi shiru baya ko motsi yasata fahimtar cewa yau fa yan miskilancinne akusa wannan dalilinne yasa ta tashi tafita ta nufi sashenta tana zuwa tayi shirin bacci tayi kwanciyarta,sai sake sake take yi a cikin zuciyarta tana ta tambayar kanta to yaushe Khalil suka fita da maamy? Ina sukaje? Tambayoyin da ta rinka jujjuyawa kenan cikin ranta amma bata da amsarsu shiyasa zuciyarta ta cika da kunci da bacin rai,da damuwa aranta ta samu nasarar yin baccin ranar. Washe gari kamar jiya yauma tunda ta tashi da asubah bata sake komawa bacci ba kitchen ta shiga bayan ta kammala taje ta shirya Aryan shirin makaranta,suna falon kasa tana bashi breakfast yana ci lokacin ba afi 7:30 ba anty maamy tafito zata hau sama, Hanan tasan bazai wuce wurin Khalil ba shiyasa ta gaggauta karasa bashi breakfast din taja hannunsa zuwa sama tana cewa, "Zo muje kayiwa Papa sallama sai kazo akaika school" Khalil na zaune afalo sanye da farar t shirt da bakin trouser wanda yawuce gwiwarsa da kadan da laptop gefenshi yana duba wani sako ta email dinsa maamy ta bude kofa ta shiga, "Ranka yadade har antashi?" "Ba dole na ba maamy.... Mai girma deputy president da kansa yaturo min sako ai dole intashi" "Haka kam.... To yakake?" Ta fada tana kokarin zama gefen kujerar dake kusa dashi, "Alhamdulillah,kefa?" "Lafiya lau wallahi Khalil" "Any problem?" Ya bukata idanuwanshi na kan system dinshi, "Ehh to.... Dan Allah idan zaka fita zaku yi dropping dina wurin saloon ina so zanyi kitso...." Daidai lokacin su Hanan suka shigo kuma kunnuwan Hanan sun samu nasarar jin kalaman maamy,sam Hanan bata nuna tajiba suka gama abinda zasuyi taja hannun Aryan suka fita, Bata sake komawa part din Khalil ba sai bayan da tayi wankanta ta shirya ta saka wata pink and blue colour din atamfa riga da skirt sannan ta nufi wurin Khalil tana rike da kayan breakfast dinshi,baya cikin falon lokacin da ta shiga sai dai ga system dinshi nan da wayoyinshi zube saman kujera,fita tayi tai maza taje ta ci nata breakfast din cikin sauri sannan ta dawo tana shigowa yana fitowa sanye cikin farin yadi tissue,bai san ko yaushe Hanan ta koyi wannan abun arzikin ba ko da yake ai kullum mutum girma yake yi hankali na kara shigarshi, Kan dining din ya karasa ya zauna tana biye dashi abaya,dumamen tuwon daren jiya tayi masa da kunun gyada sai yan soye soyenta da tayi,ga mamakinta sai taga ya wanke hannu ya zuba dumamen tuwon yana ci,wai dan Allah Khalil wanne irin mutum ne shi mai saukin kai haka? A wannan level din nasa da wanine ai ko kallon tuwo bazai yiba bare har yaci, Shiru ne ya mamaye wurin sai shi dake ta faman cin dumamen sa,dan ajiyar numfashi tayi sannan tace, "Uncle zan bika.... Ina so zanje gyaran gashi da k'unshi dan Allah sai ku saukeni......" Shiru yayi bai amsa mata ba dan yi yayi ma kamar bai jita ba,ita maamy tace zata bishi itama wannan yanzu tazo tace wai zata bishi to wa zai dauka acikinsu? Tunda shi dai bazai taba hadasu gaba daya su fita tare ba,kuma idan yatafi da Hanan yabar maamy bai kyauta ba haka idan yatafi da maamy yabar Hanan to yayi ganganci ko kuma yaso kansa dayawa saboda ko babu komai Hanan matarsa ce kuma dole akirata da wannan sunan, "Kaji uncle......" Muryarta ta katse masa tunaninsa, "Ba yau ba..." Shine amsar da yabata yana wanke hannunshi cikin sink,bata kai ga kara magana ba anty maamy ta shigo taci wata bubu na wani dan ubansun leshi baki mai adon pink sai kyalli yake ta dan yafa mayafi akanta da alama dai tafi son shiga irin wannan, "Khalil ka gama ne muje?" Shiru yayi na wasu mintuna sannan yace, "Maamy kiyi hakuri bazai yuyu mu fita tare ba saboda inada urgent meeting yanzun nan,but zan turo miki driver idan hakan yayi miki....." "No kabarshi kawai babu matsala bari sai infita da kaina kawai" "Ok" Juyawa tayi tafita ita kuma Hanan tafita fuuuu itama alamun wai tayi fushi,bai bi ta kanta ba yawuce yafita shima. *** Tun bayan dawowar sumayya daga katsina abubuwa suka fara canjawa tsakaninta da mujahid,sai yayita janta yana tsokanarta koda kuwa bata kulashi ba,haka makaranta shine yake kaita ya koma ya daukota,gashi babu dama yaganta da saurayi sai ya koreshi duk wanda yazo wurinta sai ya koreshi,sosai abin yake bata mamaki duk da ta dan fahimci inda yasa gaba amma bata yi saurin bada kai ba, Yau daga makaranta dan ajinsu ya rage mata hanya domin sun gama lectures daya lecture din ance malamin bazai zo ba,suna zuwa kofar gida tana shirin fitowa mujahid na fitowa daga ciki, parking yayi yaje wurinsu yace tafito, tambayar ta yafara yi wai wanene wannan? Meye hadinta dashi da har zai kawota gida a mota? "Course mate dinane fa ya mujahid.... Rage min hanya yayi" Zura kansa yayi cikin motar yace, "Barka dai.... Dan Allah daga yau karka kara rage mata hanya,koda kuwa itace ta bukaci hakan,kana iya tafiya" Fuskantarta yayi wacce ke tsaye baki bude saboda tsabar mamaki, "Daga yau sai yau kar na kara ganinki acikin motar wani da sunan wai yarage miki hanya.... Kina jina?" "Haba dan Allah ni wai meyasa kake takura minne? Menene dan anrage min hanya? Ni wallahi....." "Zaki wuce kishiga ciki ko sai na baki mari...." Wucewa tayi tana kunkuni sai bubbuga kafa takeyi,har yashiga motarsa zai fita ya kashe yafito yabita cikin gidan can dinma sakata yayi agaba da dokoki wai babu ita babu kula kowanne namiji ta inda yake shiga ba tana yake fita ba da ya isheta da fada mikewa tayi tsaye cikin fada tace, "Wai menene naka idan na kula wani namiji? Ina ruwanka dani?" Kallonta yayi idanuwanshi cikin nata sannan ya dan sassauta muryarshi, "Saboda ke tawace..... Ke tawace ni daya sumayya,bazan iya jure ganinki tare da wani da namiji wanda ba niba" Ai rasa abinda zatace tayi,ta ma rasa wanne irin farin ciki zatayi gaba daya, kwalla ce ta ji ta ciko mata idanuwanta saboda tsabar farin ciki,dama tajima tana mafarkin jin wadannan kalaman daga bakinsa amma bata tsammaci jinsu kwana kusa ba,bata zaci zata jisu a daidai wannan lokacin ba,rufe bakinta tayi da dukkanin hannayenta guda biyu. *** Ta jima akwance tana kuka tun bayan fitowarta daga part din Khalil ta kwanta tana kuka,haba wannan cin fuska da tozarci har ina? Dan kawai anty maamy tana matsayin kanwarsa sai yarinka fifitata akanta? Duk yanda akayi ba a iya yan uwantaka al'amarin nasu ya tsaya ba sai dai idan akwai wata akasa,ita tana nan tanata wahalar dawainiya da soyayyar shi bai tsaya ya kulata ba a matsayinta na matar aurenshi amma yaje yana kula da wata mace dan kawai yana takamar jininshi ce, Sam Hanan bata iya samun abu ba shiyasa wuni tayi tana kuka kuma har lokacin bata jin zuciyarta ta huce daga bacin ran dake makale dankare acikinta, Aryan tunda yadawo daga makaranta yake son ta tashi suje garden su hau lilo kuma ta koya masa karatun hisnul ad'fal amma taki tana nan dai kwance kamar ruwa kan gadonta duk idanuwanta akode, Duk da bawai azumi take yiba amma wuni tayi bata ci komai ba bata saniba yaturo andauki anty maamy din ko bai turoba oho musu,bayan tayi sallar magriba wanka tayi ta saka riga da wando na English wears jeans da t shirt ta dan yafa mayafi ta fita ai karuwancin kowama ya iya kunya ce da kara ke sawa ake nuna kamar ba a iya ba,azo har gidanta anemi takura mata? Wallahi bazai yuyu ba ai tunda anty maamy tasata kuka wallahi itama sai ta sakata kukan kuma shima Khalil din zai gane shayi ruwane dan sai yagane kurensa,umma kadai ta samu a falon kasa sai Aryan dake kan kekenshi yana ta faman zagaye harabar falon,zama tayi suka gaisa da umma anan umman ke tambayar ta wai ko lafiya kuwa kodai jikinne? Murmushi kawai tayi aranta tana tunanin wai har sai yaushe su umma zasu farga su gane cewa babu juna biyu a tattare da ita? Tashi tayi zuwa dining area ta hado golden moon cup biyu ita da Aryan domin shima gwaninshi ne yana son golden moon haka zata yita hada musu suna sha kamar wasu yan boarding,suna nan falon suna taya Aryan kallon cartoon anty maamy ta shigo tabe baki Hanan tayi ta kawar da kanta gefe acikin zuciyarta tana cewa ashe ma bata nan ko ina taje kuma oho? Itama Anty maamyn umma kadai ta kula sai Aryan tawuce bedroom daga nan bata sake fitowa ba,har 10 suna falon kasa da umma suna hira ganin karfe 10 ya dan gota kuma batayi sallar ishah ba yasata hawa sama dan tayi,tana tashi Khalil na shigowa,ai tun ahanya Aryan yasoma tsegunta masa wai mommy tanata kuka tun da yadawo daga school yau ko karatu bata koya masa ba blah blah, Bayan sun shiga falonshi text massage ya tura mata wai tazo, shareshi tayi ta sake gyara zamanta saman kujerar da take zaune tana kallon tashar zee world,har yayi wanka yafito bata zo ba ga Aryan nan yayi bacci kasa kan rug acikin falonsa,da kanshi yafita ya nufi sashenta, knocking yafara yi sannan yabude yashiga duk zatonta Aryan ne shiyasa bata ma ko dago ba daga kwancen da take da pillow akirjinta ta rungume, Kamshin turaren sa tafara ji sai kuma tajiyo muryar shi, "Baki ga kiran da nayi miki bane nace kizo?" Bata rai tayi sannan ta tashi zaune tana sake babbata fuska, "Zo...." Daga haka yajuya yafita ta tashi tabi bayansa tana gwada tafiyarsa harda wani dan sakin doro take yi,shi dai baima san tanayi ba,suna shiga part dinsa bedroom yawuce zai dauko system dinshi ita kuma ko zama batayi ba ta hango anty maamy rikeda karamin flask tana tahowa tashi tayi taje ta sakawa kofar lock,ta dawo ta zauna, knocking anty maamy tafara yi amma Hanan taki budewa zuwa can dai ta tashi taje ta bude amma tayi bake bake akofar ta yadda mammy bazata iya wucewa ba, "Lafiya?" Hanan ta fada tana kallon gefe, "Matsa inwuce..." "Ki wuce ina? Haba anty dare ne fa,ai wannan lokacin na ma'aurata ne,muna cikin tsaka da raya sunna kinzo kin katse mana jin dadi......." Daga haka ta mayar da kofar ta rufe ta sake danna lock ta wuce ciki tabar anty maamy tsaye baki abude.........................✍? *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* 43***Tana iya hango anty maamy daga zaunen da take wacce takaici ya hanata ko motsi daga inda take tsaye kawai mamakin maganganun da yarinyar nan ta fada mata take yi,ta dan jima atsaye sannan taja kafafunta wadanda suka yimata nauyi ta kara gaba zuciyarta cike famm da takaicin furucin da hanan tayi mata, Hanan sake gyara zamanta tayi tana hango lokacin da maamy ta juya ta koma inda tafito dama allah allah takeyi ta tafi kafin Khalil yafito yaganta yaje da kansa yabude mata kofar,ai kuwa tana tafiya sai gashi yafito yana yin waya da alama ma wayarce ta tsayar dashi cikin dakin dan har yanzu bai gama ba,zama yayi a kujerar da yafi zama wacce ke kallon kofa,jin ya ambaci barrister muhsin yasata fahimtar cewa da lawyer dinsa yake yin waya, Aryan ta dauka ta fita zata kaishi dakinshi ta kwantar dashi kafin Khalil yagama wayar da yake yi,saida ta zauna tayi zaman canjawa Aryan kaya sannan ta fita,part din Khalil ta sake komawa sai kunkumbura baki take yi ita kadai, Ayanda ta tafi ta barshi haka ta dawo ta sameshi sai dai yanzu ba waya yake yiba laptop dinshi yake dubawa,a kasa ta zauna tana wani turo baki, "D'anki yace yau ma kinyi kuka,meya faru?" Yafada idanuwanshi na kan system dinshi kyarr, Jin abinda yace yasata sake turo baki amma batayi magana ba,ai yafi dan dako sanin tasha,yafi kowa sanin abinda yasata kuka tunda shine sila, "Uhmmmm....?" Ya sake fada batare da ya kalleta ba, "Da safe ne na tambayi zuwa saloon aka hanani....." Murmushi yayi jin abinda tace, lallai yarinyar nan yar yice, "Shine kika zauna kina kuka?" "Uhmm" Shiru yayi yaci gaba da abinda yake yi tsawon mintuna biyu taji yace, "Jeki ki hado min coffee ki kawo min" Tashi tayi tafita aranta tana mitar dama dan dai yasata aikine kawai yaje ya tasota, kitchen dinta ta shiga,tana cikin hadawa taga diff an dauke wuta akaro nafarko tun bayan zuwanta gidan bata taba ganin an dauke wutaba sai yau, wayarta ta kunna da ita tayi amfani ta karasa ta dauka ta fita wato da ita maamy kawo mishi tayi kenan to sai dai taje tasha kayanta yau bazai sha ba. Daga shi sai gajeren wando ta sameshi lokacin da ta koma amma jin motsinta yasa shi lulluba t shirt dinsa a kirjinsa,sai tsaki yake yana kiran wani awaya wanda bata san ko waye ba,shi kwata kwata baya shiri da zafi duk da ba wani jikin azo agani gareshi ba amma jin zafine dashi to sai Allah yarufa masa asiri ya iyoshi agidan hutu kullum yana cikin AC, "Wai meke faruwa da Gen dinne?........ Ok tom" Daga haka taga ya katse wayar yamike daga kan kujera yashiga bedroom dinsa,ruwa yaje ya watsa ya fito yana fitowa wuta tazo dama wai Gen din aka yiwa juye, jallabiya yasa yafita har lokacin tana zaune tana jiransa, "Gobe za akaiki saloon din...." Kamar tace ta fasa sai ta amsa masa,cewa yayi ta tashi taje ta kwanta,tashi tayi ta fita sai faman cika take tana batsewa kamar zata fashe, bai san har lokacin akule take dashi ba shiyasa ma ai yau ko girkin bata yimasa ba ita maamy din da ta fita awurinsa ba sai tayi masa ba. Juyi ta fara yi lokacin da ta kwanta domin yin bacci sai dai sam baccin yaki zuwa maimakon ma taji alamunsa sai tunanine taji yana bijiro mata adaidai wannan lokaci,bata taba ganin namijin dake burgeta yana jan hankalin ta ba kamar Khalil tsawon rayuwarta, musamman ma yau da ta ganshi cikin yanayin da bata taba ganinsa ba koda yake bama shiba bata taba ganin babban namiji baligi ahaka ba dan ko yaya shamsu zata iya bugar kirji tace bata ganinsa yana zama haka, Wani irin bege da shaukine ke fusgarta agame dashi,jin zuciyarta takeyi tana wani irin harbawa da karfi, runtse idanuwanta tayi tana fatan bacci ya dauketa ko wai zata samu ta huta da wannan tunane tunanen amma hakan bai samuba har wurin k'arfe 1:30 dakyar da addu'a tasamu tayi bacci a wannan dare, Washe gari bayan ta shirya Aryan yatafi makaranta itama shiryawa tayi cikin wata jar atamfa mai zanen camera ajiki,sashen Khalil ta wuce dauke da kayan breakfast a hannunta,tana shiga ta wuce kan dining ta soma shirya masa tana gamawa ta koma ta rufe kofa b'am ta dawo ta zauna tasan yanzu haka anty maamy tana kan hanyar zuwa sai kace wata matarsa kullum tana manne dashi,wani dogon tsaki taja saboda kishin da ke ciciyar zuciyarta wanda ita bata ma gane ba kawai dai tasan tana masifar jin haushin anty maamy sannan tana jin haushin yanda take shisshigewa Khalil duk da yar uwarsa ce, "Keda wa?" Juyawa tayi sakamakon jin muryarshi da tayi abayanta yana tsaye ya dafa kujerar da take kai shirye yake tsaf cikin shirin fita office yau kam yafi koda yaushe yimata kyau saboda abaturensa yafito sak domin suit yasaka bakake amma farar t shirt mai dogon hannu wacce keda kwala yasa aciki, "Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakkyawar halitta.... Masha Allah" Ta furta can kasan makoshinta,kasa dauke idanuwanta tayi daga kansa ahaka suka gaisa ya nufi dining tabishi,dan wake da yaji da man gyada da vegetables ta zuba masa harda dafaffen kwai sai kunun farar shinkafa mai dauke da gyada da madara,kai masha Allah shima hakan yaketa nanatawa cikin ranshi saboda tsabar dadin da abincin yayi masa,yana masifar son irin girke girken nan amma baya samu sai idan yaje gombe, Kiran Khalid ne yashigo cikin wayarshi saboda tun daren jiya yatura Khalid din text massage yana yimasa maganar daidaita kansu da sukayi da maamy yanzu wani abu kadai yake jira sai yasanar da gida,yasan Khalid zaiyi farin ciki saboda dama maamy kanwarsa ce shikuma amininsa ne, "Kai baban yan uku ya akayi?" Khalil yafada cikin raha, "Lafiya lau babban mutum,ya aiki? Ya Aryan?" "Yatafi school...... Kaga sakona ko?" "Ehh naga abin farin ciki,wai ya akayi hakan ta kasance? Kodai kun tuna tsohuwar soyayya ne?" Kamar tv haka Hanan ta sakashi gaba tana kallonsa, Kai wannan mutum da kyau yake,ga nutsuwa ga kuma aji,shagala tayi da kallonsa shiyasa ma bata samu damar ganin tahowar anty maamy ba kawai sai knocking dinta taji,da hannu Khalil yayi mata alama wai taje ta bude,mikewa tayi cike da bacin rai ta nufi kofar tana harare harare ita daya,tana zuwa ta tsaya bakin kofar kamar yadda tayi jiya,anty maamy tasha kwalliya cikin doguwar riga ta shadda hadaddiya peach, "Anty maamy gaskiya bazan boye miki ba kina shiga hakkinmu..... Wai meye tsakaninki da mijina da har zaki rinka shigowa part dinsa kullum? Nidai agaskiya kina takura min sannan kuma nagaji...." Murmushin takaici anty maamy tayi, "Bani wuri inwuce ni ba gunki nazo ba gurin mijinki nazo" "Toh ai duk daya..... Koba wurina kika zoba tunda kika zo wurin mijina ai baki nemi zaman lafiya ba,nifa kina shigar min hakkina kuma bazan lamunta ba..... Nayi kara nayi kara har nagaji" "To yanzu zaki bani hanya inwuce ne ko yaya?" "Gaskiya sai dai ki koma inda kika fito dan wallahi bazaki shiga ba,haba ya wai nida gidana nida mijina amma ahanani sakewa?" Turata anty maamy tayi zata wuce nan kuwa ta dage karfinta ta dawo da ita baya tana kokarin mayar da ita waje abu sai yakoma fada fada kokawa kokawa,wayar da yake yi ya katse yamike domin kamar hayaniyar su yake jiyowa,mamakine karara ya bayyana akan fuskarshi lokacin da ya iskesu suna kai ruwa rana ita Hanan ta daddage tayi bake bake abakin kofa tana hana maamy shiga ita kuma maamyn itama ta dage tana kokarin ita alallai dolen dole sai ta shiga, "Maamy..... Menene haka?" Yafada idanuwanshi akansu su duka biyun, "Wai daga nazo inaso zan shiga wurinka shikenan yarinyar nan ta daddage ta hana wai bazan shiga ba...." "Meya faru?" Ya maida kallonsa kan Hanan gaba daya wacce ta bata fuska ta hade rai tana ta faman gurmude gurmuden baki sai karkada jiki takeyi alamar masifa da bala'i karara,jin tambayar da yayi mata yasata kallonshi sannan ta kawar da kanta gefe tana hararar anty maamy, "Abinda ta fada maka shi akayi,ba ita kafara tambaya ba....?" Bashiba ita kanta maamy saida kalaman Hanan suka bata mutukar mamaki kuma suka daure mata kai mutuka gaya,yanzu yarinyar nan ce ke fadawa Khalil haka agabansa bawai abayan idonsa ba? Shi kuwa dama yasan hali yasaba da rashin kunyarta sai dai ma yabawa wani labari shiyasa abin bai wani dameshi ba sannan shi mutum ne mai hakurin gaske sau tari sai dai mutum ya cuceshi amma shi yakan jima kafin ya nunawa mutum rashin hakurinsa, "Ehh ai ta fada min kuma naji nata yanzu naki nake son ji shiyasa na tambayeki....." "Takura min take yi duk lokacin da ta shigo min b'angaren mijina,jiya cikin dare tazo nace bazata shiga ba yauma ta sake dawowa to menene ma'anar hakan? Wannan safa da marwa din ya isa haka...." "To yanzu me kikeso ayi? Yar uwata ce fa" "Duk da yar uwarka ce ai bai kamata ta rinka shigo mana ba anyhow,ya za ayi ace ni banda sirri? Shikenan kuma har turakar mijina sai wata mace tagani? Ni karta kara shigowa sashenka idan gaisawa ne tajira duk lokacin da ka sauka k'asa sai ku gaisa...." Shi gaba daya ma mamaki Hanan take bashi saboda yanda ta fututtuke ta hakikice tana tada jijiyar wuya wai harda cewa maamy karta kara shigar mata turakar miji, "Yanzu ke idan akayi hakan kin kyauta kenan? Fada da bakuwa? Kwana nawane zata taf...." "A'a wannan yanzu ba bakuwa bace ai tajima da zama yar gida....yau kwananta nawa agidan?" "To yanzu dai kar na kara ganin kinyi mata irin wannan babu ruwanki da ita,ba wurinki take zuwa ba wurina take zuwa...." "To wallahi ni bazan zauna da ita ba agidan nan,zanje intafi gidanmu inyaso ita taci gaba da zama tare daku......." Fuuuuhhh tayi waje tabarsu awurin tawuce sashenta hawaye na karakainar zubowa daga cikin idanuwanta,tana zuwa ta janyo babban akwati daga cikin na lefenta tasoma kwaso kayanta na sawa tana zubawa aciki wanda kawai cakuda su take tana hautsinawa aciki babu wani jerawa ko shiryawa, Jiki asanyaye maamy tajuya tabar Khalil tsaye ta sauka kasa zuciyarta duk babu dadi, Kai tashin hankali baiyi ba arayuwa me za ayi da bacin rai, Shi kuwa Khalil ciki yakoma ya dauko wayoyinsa yasaka bakin takalmi sau ciki yafito yasauka kasa,a babban falon kasa yasamu Hanan da umma barira wacce keta faman riketa tana bata hakuri akan ta janye maganar tafiya gidan da ta dage sai tayi amma taki sai jan uban akwati take yi, "Wai meya faru ne? Mu'azzam meke faruwa?" Umma barira ta tambaya tana kai dubanta gareshi, "Umma ni bazan zauna tare da anty maamy ba,sai dai azabi daya ya zauna tsakanin nida ita acikin gidan nan.... Wallahi tafiya zanyi" Lamarin Hanan gaba daya mamaki yake bashi wai yarinya duk tabi ta burkice tace ita lallai lallai sai maamy tabar gidan,to wai menene azuciyar yarinyar nan? Kafin yayi magana fuuhhh yaga taja akwati ta nufi kofa ita kuma umma ta tsaya cak tana kallonsu tama rasa me zata tsara balle tasamu ta cewa,bin bayanta yayi tana ta kokarin yafa jan mayafin dake hannunta cak numfashinta yanemi daukewa sakamakon rikon da taji yayi mata wanda har saida yayi sanadiyyar haduwar jikinsu wuri daya...............................✍? *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: *Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din.* *44* ***Fuskarta ya tallafe da dukkan hannayensa guda biyu masu tsananin taushi hakan yasa ta lumshe idanuwanta wanda yayi sanadiyyar zubowar wasu tagwayen hawaye ajere, "Meyasa bakya jin magana ne? Kina musu dani ko? Ga gardamar tsiya kamar sabon angon jaki...... Kina son infadawa abbanki?" Girgiza kai tayi tana cigaba da b'arin hawaye afuskarta, "To yanzu da kika debi wadannan uba uban kayan cikin akwati ina zakije? Kin gaji da zama da mune?" Kai ta sake girgiza masa har lokacin idanuwanta a rufe suke sai hawaye dake ta faman malala, "Kar ki tafi ki daure ki zauna ko dan d'anki Aryan.... Yanzu idan yazo ya iske bakya nan wanne irin hali kike tsammanin zai shiga? Kar ki tafi kibar d'anki idan kuma kin dage sai kin tafi to kibari yadawo sai ki hada masa nasa kayan kutafi duk inda zakije tunda ni kin gaji da zama tare dani...." Sai lokacin ta bude idonta ta kalleshi shima ita yake kallo ko kiftawa bayayi ita dai tasan kawai yafada ne amma ya za ayi yabata Aryan yace wai sutafi duk inda zataje ai ko giyar wake yakesha bata jin zata yi masa tasiri anan, Kai ya jijjiga mata alamar tabbacin abinda yafada,daga haka ya saketa daga rikon da yayi mata yawuce yafita yana kokarin gyara necktie dinshi, Tafi minti biyar tsaye wurin ta kasa koda kwakkwaran motsi har umma barira ta karaso tazo tana mai sake bata hakuri akan karta tafi tunda bada mijinta sukayi fada ba to babu amfanin tabar gidan wai da sunan yaji, Juyawa tayi ta ja akwatinta ta nufi ciki dakyar ma take jan akwatin saboda kayan da ta loda ba kadan bane sai kace wacce idan ta tafi zatayi shekara agidan,har bedroom dinta umma ta rakata tana sake bata baki tana cemata kowa kagani agidansa hakuri yake yi amma akwai matsalar da take tare dashi, Bayan fitar umma Data ta kunna awayarta ta hau online saboda tana son ta dan debewa kanta kewa amma acan kasan ranta ta kuduri aniyar itafa bazata cigaba da zama da anty maamy ba sai dai ayi wacce za ayi. Har Khalil yaje office bai daina mamakin abinda Hanan tayi ba,to wai me zai kira wannan lamarin nata dashi? Kishi ko kuruciya? Gaba daya yarinya ta dage sai ta kori maamy daga gidan,yana shiga office kiran maamy yashigo masa, dauka yayi muryarshi asanyaye kamar kullum, "Ibrahim ni nagama shirya kayana zan wuce gombe......" Dan jimm yayi sannan yace, "Ban gane zaki wuce gombe ba..." "Ehh zan koma gidan ubana mana,inbanda matarka ta samu dama wai har ni zata yiwa gorin gida? Taje ta tambaya waye ubana,kai kanka kasan ubana yanada gidajen da bazasu lissafu ba,ni kaina inada gidaje sunfi goma mallakina amma wai ni ake yiwa gori akan gida nida gidan mijina akasar turai yake amma wai yau saboda nazo gidanka karamar yarinyar da bata fi sa'ar autar gidanmu ba take kokarin wulakanta ni..... Nagode" Kitt ta katse wayar,rabuwa yayi da ita bai kara kiranta ba saboda yasan yanzu ranta abace yake ko daga kalaman da take yi yasan akule take maamy kuma badai zuciya ba,rabuwa yayi da ita har zuwa yamma lokacin da zai tashi daga office inyaso sai yabita can gomben ya wanke kansa. Misalin karfe 6 yatashi daga office kuma direct hanyar gombe suka kama wanda basu suka isa ba sai bayan sallar magriba,salla yafara yi sannan ya karasa gidan Alhaji Idris kanwa mahaifin maamy,bai samu abban agida ba kasancewar baya gari, Jawad yatura yace yayi masa sallama da momyn su nan Jawad din ya ruga da gudu ya nufi can cikin gida, Maamy tana gaban mirror tana tsala kwalliya tamkar wata budurwa dan ko da wasa bata daukar kanta a matsayin wata babba ta azo agani duk da tana da samarin yaya da budurwar 'ya, "Mommy kizo inji uncle Khalil...." "Yana ina?" "Yana falon abba na kasa" "Ina zuwa to" Fita jawad yayi ita kuma ta tashi ta karasa shiryawa cikin doguwar riga ja tasha turare sannan ta dauki dan siririn mayafinta ta fita tana takunta mai cike da nutsuwa da daukar hankali, Zaune ta sameshi ya dora kafarshi daya akan daya yana duba wayarshi,zama tayi gefenshi bayan tayi masa sallama, "Haba amarya irin wannan fushi haka kuma? Sai kace dani akayi fadan....." Wani kallo tayi masa kafin ta rausayar da kanta gefe, "Ai wannan matar taka sai Kai..... Kasan wani abu? Wallahi bazan zauna gida daya da ita ba, tun wuri ma ni ka sama min gida amma banda wannan..... Ban son rashin kunya" Murmushi Khalil yayi ya shafi sajensa, "Kinji tsoro kenan?" "Ba maganar tsoro anan fa Ibrahim gaskiya ce" "To Allah dai yabaki hakuri,dan Allah ki dauki abinda yafaru yau amatsayin ba komai ba saboda kinga ita yarinya ce,yanzu ne ma take sanin yaya rayuwar take......" "Nifa banda case da ita,kawai nidai bukatata awurinka shine karka hadamu gida daya dan bazamu zauna lafiya ba...." "Baki da matsala a wannan bangaren Maryam,insha Allah zanyi yanda kike so......., Yanzu ina son zan karasa wurin hajiya mu gaisa sai inkoma Abuja,dan nan nafara zuwa" "Ayya babu matsala,ka gaida min da ita" "Zata ji insha Allah, shikenan intafi an sallameni?" Murmushi tayi ta dan fara idanuwanta alamun shagwaba, "Da ance maka kai mai laifine?" "Ehh mana ranki yadade..... Za dai muyi waya insha Allah" "To babu matsala yallabai,muje in taka maka" Har inda motocinsa ke ajiye ta rakashi aka bude masa yashiga sannan tajuya tawuce cikin gida,shikuma suka nufi gidan hajiya can dinma bai wani zauna ba dan ana kiran sallar ishah yafito bayan sun gabatar da salla suka juya abuja zai koma ya tarar da yar rigama Hanan,karo na farko da yayi tunanin abinda ya shafeta har yayi dariya shi daya,gaskiya yarinyar nan case ce,wai,wayarshi ya ciro ya soma kiran layin Aryan. Ita kuwa Hanan bayan tafasa tafiya ta mayar da kayanta ciki sai da ta zauna ta sha kukanta sannan tayi shiru wannan dinma zuwan umma ne wacce ta tisata agaba tana ta faman bata hakuri tana cemata shi dama zaman aure gaba dayansa hakurine yafi yawa acikinsa kai bama iya zaman aure ba ita kanta rayuwar gaba dayanta hakuri ce dan haka ta dauki wannan abun da yafaru amatsayin ba komai ba kuma taci gaba da yiwa mijinta biyayya, Tsamm tayi ta tsaida hankalinta da tunaninta wuri guda tana mai cigaba da jujjuya maganganun umma acikin ranta duk da cewa umman adunkule ta bata maganar bawai zama tayi tai mata ita dalla dalla ba amma akwai alamar tana bukatar tayi wa dukka maganganun duba na tsanaki domin umma cemata tayi taci gaba da kyautatawa mijinta saboda zuciya ahar kullum tana son mai kyautata mata sannan ta guji fushi da bacin ransa,to tayaya zata guji wadannan abubuwan? Dole tana bukatar daura damarar kulla abota da hakuri da gujewa duk wani abu da ka iya bata ransa sannan umma tace duk runtsi duk tsanani karta karaya daga fafutukar yakin neman cikar burinta taci gaba da fadawa Allah dukkan bukatunta haka kuma ta jajurce ta tsaya tsayin daka har sai hakarta ta cimma ruwa, Murmushi tayi aranta tana tambayar kanta to kodai umma ta fahimce cewa tana son Khalil? Ko umma ta gano sirrin da taketa boyeshi acikin zuciyarta ita kadai wanda bata fatan wani mahaluki ya fahimta baya gashi wanda take yi dominsa? Cigaba tayi da aikinta acikin tamfatsetsen kitchen dinta mai dauke da komai da komai na bukata wurin girke girke,dama tasan bazai dawo da wuriba shiyasa itama bata tarki aikin da wuriba har sai da tabari la'asar tayi liss sannan tafara,tuwon semovita ta dora saboda Aryan yanata damunta da tambayar wai "mommy tuwo zaki dafa mana?" Wannan dalilinne yasata dora tuwon semovita miyar shuwaka, farfesun zabbi da kuma kunun shinkafa. A kitchen magriba tayi mata,agurguje ta karasa aikace aikacenta sannan ta kwashi na umma ta kai mata can ta isketa tana ta drama da mutumin nata Aryan ita dai da yake bata yi salla ba komawa sama tayi taje tayi wanka sannan tayi salla bayan ta idar ta koma k'asa dauke da tuwon da zata bawa Aryan, Anan umma ke sanar da ita tafiyar anty maamy wadda sam ita Hanan bama tasan cewa ta tafi ba sai yanzu da umma ke bata labari, "Allah yaraka taki gona......" Shine abinda Hanan ta fada acikin zuciyarta,afili kuwa sai kawai tayi murmushi tana sauraren umma, Yau sun jima sosai da umma wacce keta yiwa Aryan tatsoniya har saida yayi bacci,daukarshi Hanan tayi a kafadarta ta nufi dakinsa dashi ta kaishi ta kwantar,daga can kuma part dinta ta wuce tana kallon agogon dake kan wayarta karfe 11 na dare harda wasu mintuna,shirin bacci tafara yi itama bayan tagama ta saka dogon hijab ta fita,kanta tsaye sashen oga ta nufa wanda dawowarsa kenan dan ko minti biyar baiyi ba da shigowa cikin gidan,wani abun mamaki kuma wai sai yanzu ne taji tana jin kunyar abunda yafaru da safe sai yanzu take jin kunyar rufe idanuwanta da tayi ta zazzaga masa rashin ta ido, Tana shiga falon yana fitowa jikinsa sanye da rigar wanka fara, hannunshi rike da charger da alama wayar shi zai saka ajikin chaji, sunkuyar da kanta kasa tayi tana yimasa sannu da zuwa daga bisani ta mike tafita domin kawo masa abinci kamar kuwa tasan dama yunwa yake ji saboda rabonsa da abinci tun wanda yaci da safe. Yana zaune yayi nisa kadan aduniyar tunanin da ya tafi tabbas yana son maamy bawai so irin can mai zurfin nanba amma kuma wani lokacin sai yaji kamar yafasa auren nan domin shi yanzu gaba daya mace bata gabansa bawai dan baya bukatarta ba a'a saboda kawai ruhinsa da tunaninsa gaba daya kacokan suna ga Ramlat,iya gangar jikinsa ce kadai anan ita kanta wannan yarinyar Hanan kawai yana zaune da itane saboda Aryan,amma har gobe Ramlat ce abirnin zuciyarsa, shigowar Hanan bayan tayi masa magana shine yayi sanadiyyar dawowarshi daga tunanin da ya zurfafa acikinsa, Cikin sanyin jiki da na murya yace ta zubo masa tuwon guda daya,zubo masa tayi sannan ta zuba masa kunu cikin cup da farfesun da tayi agefe takai masa gabansa,samun wuri tayi ta zauna duk da ta dan fara jin bacci sama sama domin 12 ta kusa,lura da gyangyadin da yaga tana yi yasashi fadin, "Je ki kwanta sai da safe,nagode......" Tashi tayi tana lullumshe ido ta fita,tana zuwa daki ta fada kan gado tana zare hijabin dake jikinta babu jimawa bacci ya dauketa, Shi kuwa Khalil yana can yana sakawa da kwancewa yarasa meyasa aduk lokacin da maganar aure ta fara shiga tsakaninsa da wata mace sai yasamu kansa cikin mugun hali sai yaji gaba daya kunci da damuwa sun rufeshi koda yake yasan hakan bai rasa nasaba da tsananin kaunar da yake yiwa Ramlat,lumshe idanuwansa yayi yana mai barwa Allah zabi,idan har aurensa da yar uwarsa maamy alkhairi ne to Allah ya tabbatar idan kuma babu alkhairi Allah ya canja musu da mafi alkhairi. 3:30 AM Daidai wannan lokaci Hanan ta farka daga nannauyan baccin da take yi,yanda taga yanayin d'akin nata sai ta dan tsorata domin kamar anshigo mata dan ga kofar dakin nan abude alhalin kuma ita ta rufe sai dai bata saka mukulli ba,wuta ta kunna ta sad'ad'a taje ta rufe da key sannan ta wuce bathroom tayi abinda zatayi ta gama tazo ta sake kwanciya tana dauko wayarta daga karkashin pillow dan ganin time, text massage taga anturo mata da kamar ba zata budeba sai kuma ta bude nan taga abunda yayi nutukar razanata kuma yasata cikin tunani sakamakon ba sanin wanda yaturo sakon tayi ba...................................✍? *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: 45 ***Gabanta ne yasoma faduwa saboda sako aka turo mata mai cike da kalaman soyayya tsantsa wanda kuma ba sanin number din tayi ba,kasa komawa bacci tayi tanata faman sak'awa da warwarewa,to ko waye wannan kuma? Innalillahi,shine abinda take ta faman nanatawa acikin zuciyarta,shiru tayi tana tunanin abinda yadace tayi daga karshe dai ta tattara sakon da mai turo sakon ta watsar da tunaninsu tayi kwanciyarta tana fatan sake komawa wani baccin, Daidai wannan lokacin shikuma Khalil ya idar da sallolinsa na dare kamar yanda yasaba yahaye saman gado ya kwanta yana son ya huta, tunani kwaya daya shine keta faman kaiwa da kawowa cikin kwakwalwarshi wato tunanin auren maamy,yanzu shikenan ta tabbata yaci amanar Ramlat? Yanzu shikenan ya saba alkawarin da yajima yana yiwa Ramlat akan bazai taba auren wata 'ya mace ba bayan ita? Shi yanzu abinda yafi damunsa kenan dama ita Hanan ba a ta ita domin yanada hujja da dalilin aurenta,har yayi bacci tunanin dake cikin ransa kenan. Washe gari karar shigowar text massage ne ya tada Hanan daga bacci,bata budeba tawuce toilet kai tsaye domin ta so ta makara,cikin sauri sauri ta ke gabatar da komai har ta kammala sannan ta shirya Aryan,sai da yahau sama yaje wurin abbanshi sannan yazo yawuce makaranta,ita kuma daki ta koma tayi wanka tafito sai lokacin ta bude sakon da aka turo mata tun dazu, number din jiyace kuma yanzun ma sakone na barka da safiya mai dauke da kalaman soyayya,lumshe idanuwanta tayi aranta tana fatan inama inama.... Inama ace wanda zuciyarta take bege take mutukar kauna shine ke turo mata wadannan kalaman ai da tayi tsalle akan kaya saboda tsabar farin ciki. *** Rayuwa haka taci gaba da tafiyarwa Hanan cikin gidan Khalil duk da babu wani sauyi a zamansu amma idan tace bata jin dadin zaman gidan tayi karya,har ila yau Anty hasinah naci gaba da bata shawarwari da kwarin gwiwar hanyoyin da yakamata tabi domin mallaka da siye zuciyar mijinta wanda amafi yawan lokuta tafi kwatanta shi da bahago,miskili kuma murdadde domin kamar bai san wadannan abubuwan da take yimasa ba shiyasa duk tabi ta kare ta sake bushewa saboda tsananin damuwa domin ita tana sonshi kullum ta Allah da sabuwar soyayyar shi take wayar gari amma kamar shi baya ganewa, sannan wani abun karin takaicin shine wasu zafafan massages da ake turo mata kullum safe da rana da dare wanda takasa gane ko waye sai dai tanata addu'ar Allah yasa muradin ranta ne. Abinda Hanan bata saniba shine shikam Khalil tuni shirye shiryen bikinsa da anty maamy yayi nisa domin har sun kai maganar gaban iyaye bayan sun gama shirya yanda suke son abunsu ya kasance,duk da wani lokacin idan ya kadaice kansa ya zauna sai yayita tambayar kansa Wai meyasa zaiyi auren nan ne? Wani bangare na zuciyarsa na son yayi auren yayinda wani bangaren kuma ke adawa da hakan, Daurewa dai kawai yakeyi akan maganar auren nan tunda har anyanke lokaci bayan babbar salla da sati uku kamar yadda ita amarya maamy ta bukata,shima uban gayyar hakan yayi masa shiyasa ya sanar da Abban London wanda shine zai nema masa auren kuma gaba daya family kowa yayi farin ciki da murnar wannan al'amari dake shirin kulluwa nan wasu cikin dangi ke fadin ai dama tun suna yara budurwar shi ce ashe da rabon aure,ita Hanan koda wasa bata san abinda ke faruwa ba saboda dama can shi zuwa gombe bata yimasa wahala shiyasa yanzun ma idan yace yatafi gombe bata jin komai aranta, Yau kam tun kafin ta kwanta bacci ta gama shirya kayanta saboda Khalil yace mata ta shirya gobe zasu tafi gombe saboda acan zasuyi salla shi dama agida yake salla karama da babba, Washe gari tare da Aryan suka je school dinsu ta rakashi saboda ranar za abasu hutu,taji dadin zuwan da tayi sosai domin daliban makarantar sun shirya wasanni kala kala dan nishadantar da iyayen yara wadanda suka samu damar halattar bikin rufe makarantar, K'arfe 2 saura suka dawo gida nan suka fara zaman jiran Khalil saboda sai yataso daga office zasu tafi ai kuwa kamar yadda Hanan ta tsammata sai dab da magriba yazo nan suka tattara suka tafi,umma barira da Aryan motarsu daya shikuma oga da Hanan suma mota daya suka shiga dukkansu sun kame agidan baya,zaman kurame yau dinma sukeyi kamar koda yaushe,ajiyar zuciya Hanan ta dan ajiye sannan ta saci kallon sa tace, "Abban Aryan nidai da son samune inyi salla a kano....." Idonshi na kan jaridar daily trust dake hannunsa yabata amsa da, "Saboda wanne dalili?" "Nafa jima rabona da gida....." Ta fada cikin shagwaba, "Shine kadai dalilin?" "Dan Allah....." Shiru taji yayi hakan ya tilastata itama yin shirun tana zunburo baki duk da tasan ba ganinta yake yiba. Bayan sallar ishah suka shiga cikin gombe kai tsaye cikin gida suka wuce tun daga lokacin basu kara ganin Khalil ba dan ko shiga gidanma baiyi ba lokacin, wannan karonma sun samu tarba ta girma da karamtawa daga daukacin jama'ar dake rayuwa agidan lokacin salla saura kwana biyu kacal, Tun bayan zuwansu rabonta da Khalil dan ko da safe lokacin da takai masa breakfast baya nan har yafita sai ajiye masa tayi afalo tadawo,suna tare dasu Sarah da Rufaida hajiya ta dauko musu mai k'unshi tana ta yalyala musu text massage din Khalil yashigo wayarta gashi lokacin kunshin kafarta bai busheba bakin amma jan yayi dan harma ancire, _Zo ina part dina._ Abinda taga yarubuto kenan,babu yanda zatayi haka dole ta tashi da kwayayyen zani tabi ta baya saboda mutane ta nufi sashen nasa,yana baje falo yana cin kilishi cikin wata babbar takarda da waya a kunnenshi,wuri ta samu ta zauna tana kallonsa kallo na kurulla aranta tana gulmarsa ita daya wai har yanzu bai fara furfura ba domin babu ko kwaya agashin kansa, "Idan kin gama gulmar ga kayanku nan keda Aryan....." Jin abinda yafada yasata saurin dauke idonta daga kan sumarshi, "Gulma kuma uncle?" Bai bata amsa ba maimakon haka ma sai taji yace, "Wannan menene aka mammanna miki?" "Lalle ne fa...." Jijjiga mata kai yayi, nannade kilishin da yake ci yayi yasaka mata cikin leda sannan ya mika mata,karba tayi ta tattara kayan da yakira da nasu ita da Aryan tafita. Bata kara sakashi a idonta ba sai ranar salla yasha manyan kaya farare tas andawo daga masallaci dama ita bataje ba saboda ta tashi tana fashin salla,gidan gaba daya cike yake da baki daga wurare daban daban sai rabon kudi da danyen nama yake yi domin ya yanka shanu da raguna sun kai talatin duk wanda yazo maroka da mabukata sai ancika masa leda Viva da nama,sai bayan da yayi sallar la'asar sannan yafita. Wannan karonma kamar karamar salla sun yi ziyarce ziyarcen gidajen dangi da yan uwa,washe garin salla suka tafi katsina gidan yayarshi saudat wannan shine karon Hanan nafarko da taje gidan anty saudat kuma ta karbeta hannu bibbiyu basu wani jima sosai ba suka tafi nan kuma kano suka wuce direct gidansu Hanan ai tun acikin mota hanan ke murna kamar zatayi tsalle, Ta samu gidansu cikin wadata da walwala domin suma saniya suka yanka da raguna guda biyu kuma duk Khalil ne yakawo banda kayan salla da ya aiko dasu wadanda za arabawa dangi,wuni guda yabarta tayi agida dan har gidan anty salaha suka je a tsattsaye daga nan suka juya gombe,yauma Hanan harda kukanta wanda bai san ko kukan me zai kirashi ba shin kukan shagwaba zai kirashi ko kukan sakarci? "Ke Wai bakya girma da kuka?" Taji yace da ita lokacin da take share hawaye da gefen mayafinta,dole yafadi haka mana tunda shi yana zuwa gida yana ganin kowa nashi aduk lokacin da yaso ta ayyana hakan acikin ranta. Washe garin salla da kwana uku suka koma Abuja inda akaje aka cigaba da zama irin na da,gashi kullum mai turo mata sakon nan bai daina ba yi yake ita kuma bata ko bi takai dan bata san waye ba, Bikin maamy da Khalil kam kullum kara karatowa yake yi domin saura sati daya da yan wasu kwanaki angama komai sadakine kadai yarage Khalil bai bada ba amma har gidan da maamy zata zauna da komai da komai yagama shiryashi. K'arfe 11 saura minti shida agogon bangon dake cikin falonsa yanuna,zaune yake akan sofa yana sanye da farar t shirt mai tambarin Nike ajiki da farin dogon wando mai santsi yana tura wasu bayanai ta laptop dinshi, Hanan yake ta jira ta kawo masa coffee din da yaturata ta hado masa amma shiru kamar wacce aka aiki bawa garinsu, Bai kai ga gama tunaninsa ba ta turo kofa tashigo,sanye take cikin kayan bacci riga da wando marassa nauyi shiyasa ta dora dogon farin hijabi akai,gabansa takai ta ajiye kan center table sannan ta nemi wuri ta zauna, "Gashi...." Kai ya daga mata sannan cikin taushin murya yace, "Thank you" Shiru tayi kawai ta dan yi murmushi tana mai cigaba da satar kallonsa,zuwa can ta mike saboda bacci take ji, "Saida safe...." "Ok Allah yakaimu" Ya furta yana binta da manyan idanuwansa masu haske, yarinyar tana dan bashi tausayi kadan saboda yanda take dawainiya da Aryan da kuma shi kansa wani lokacin domin kullum cikin fama take da girkin abincin da zai ci da gyaran sashensa kamar wata house girl,watsar da tunanin yayi yaci gaba da aikinsa yanayi yana kurbar coffee din da ta ajiye masa wanda bashi yagama ba sai misalin karfe 1 na dare, Tattare komai yayi zai wuce bedroom dinshi nan yaji k'arar wayar Hanan wacce ta manta,idonsa ne yakai kai bayan tagama kara alamar shigowar sako,komawa yayi ya dauki wayar zuciyarshi na tambayar shi to waye yaturowa yarinyar nan sako adaidai wannan lokaci? Tambayar da yaketa yiwa kansa kenan saboda ko babu komai ai a karkashin ikonsa da kulawarsa take dan haka wajibine yasan dukkan motsinta da kuma mu'amularta da kowa, ajiye wayar yayi tare da sauran wayoyinsa akan gado yawuce bathroom yaje ya dauro alwala yafito,fitowarsa tayi daidai da shigowar wani sakon cikin wayar Hanan,zama yayi gefen gadon ya dauki wayar tata luckily babu wani lock ajiki nan yabude sakonnin yasoma karantawa idanuwanshi aware bakinsa abude alamar mamaki..............................✍? _Book din mijin matacciya na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:14 AM - Ummi Tandama: 46 ***Idanuwansa aware bakinsa abude alamun mamaki yasoma bude sakonnin yana karantawa daya bayan daya wadanda ke dauke da kalamai na soyayya, Kasancewar abun yayi mutukar bashi mamaki shiyasa bai tsaya wuri daya ba dan koda yagama karanta wanda aka turo yanzu cigaba yayi da bude sauran sakonnin dake cikin inbox din nata yana dubawa,shi kansa bai san dalili ba amma dai bai ji dadin wannan al'amari ba sam baiji dadin ganin sakonnin da yagani ba saboda har da na mujahid duk yagani,to Hanan wacce irin yarinya ce? Koda yake dama yajima da fahimtar cewa akwai wanda take so wanda ta mallakawa zuciyarta shikuma yazo yayi musu karfa karfa ya aureta, Gaba daya ji yayi kansa ya kulle yarasa ma wanne irin mataki yadace ya dauka akanta,ya za ayi tana gidansa karkashin ikonsa a matsayin matarsa amma wani gardin banza acan waje yana turo mata sakonni makamantan wadannan? Raba dare yayi yana binciken dashi kansa baiga alfanunsa ba acikin wayar tata ko ina saida yaduba hatta nata sakonnin da ta tuttura saida yabude yagani bayan ya gama ya kashe wayar ya ajiye cikin bedside drawer sannan ya kwanta zuciyarshi cunkushe da fushin da bai san hujjarsa ba. Hanan bata da masaniyar abinda ke faruwa shiyasa bayan tayi sallar asubah ta wuce kitchen kamar yadda ta saba ta dorawa oga breakfast,tana ta tunanin to a ina ta ajiye wayarta saboda ta duba bata ganta ba babu inda bata duba ba daga karshe ta tuno cewa ai a sashen Khalil ta barta jiya da daddare,cike da kwarin gwiwa ta kammala komai kamar yadda ta saba taje ta shirya Aryan yatafi makaranta sannan itama ta shirya ta nufi bangaren Khalil. Ta jima zaune kadan a falon nashi tana dakon jiran fitowarshi,misalin karfe 8 taji alamun fitowarshi,duk da dama can shi ba ma'abocin dariya satataa bane amma yau kam kallo daya tayiwa fuskarshi ta gane akwai matsala saboda irin yanda yatsare gida ya hade bangon gabas da yamma ya daure fuskarshi tamau, Cikin sanyin jiki da tsoro bayyananne ta gaidashi, "Uncle ina kwana?" Sai da ya dan ja lokaci kafin ya amsa mata da, "lafiya" Daga haka yawuce yayi waje yana kara waya a kunnenshi ko kallon inda ta ajiye masa abincinsa baiyi ba saboda amugun kule yake da ita,ita mahaukaciyar inace da bata san darajar aure ba har zata rinka musayar kalamai da wani katon banza awaje? Shiyasa ya zama dole agareshi ya dauki matakin da yadace, Hanan abun duniya ne taji yataru yayi mata yawa domin sam bata da masaniyar abinda ke wakana,ita dai kawai abunda ta sani shine yanzu Khalil ya canja completely yana yin wasu abubuwa fushi fushi,zafi zafi dan ko abincinta yadaina ci tsawon kwana uku kenan sannan ko gaisheshi tayi asama yake amsawa kamar zai mareta to wai me yake faruwa? Ita ba abinda yafi tayar mata da hankalima kamar yajin cin abincinta da yayi domin haka zata zage ta bata lokacinta ta shiga kitchen ta shirya masa abincin da ta san zaiyi farin ciki dashi amma yanda ta ajiye masa haka zata samu abinta ta dauko bai ko taba ba, gashi wayarta tana son tambayarsa amma tana tsoro domin wani irin kwarjini gareshi na innanaha. Khalil kuwa ya zabi ya hanata wayar ne har zuwa lokacin da zai gama fahimtar komai saboda bazai yuyu ya zuba ido tayita aikata son ranta ba, Maganar aurenshi da maamy kuwa ankammala komai sai daurin aure kawai da yarage sadakinta ma yayi order dinsa dubai tun kwanaki biyu da suka wuce aka kawo masa dan haka yau bayan yatashi daga office yawuce gombe domin kaiwa maamy zoben, Bayan sallar magrib yashiga gidansu maamy din yana shiga ya isketa zaune tare da abbansu jawad wato tsohon mijinta, kamar zasu mari juna suka gaisa abban su jawad yatashi yafita,da alamar tuhuma akan fuskarshi yake kallon maamy kafin ya furta, "Wannan fa?" "Ibrahim kenan.... Abbansu jawad ne fa....,Yazo ganin yaranshi" "Ehh nasani,but da nashigo ban ganshi tare da yaranshi ba da ke naganshi" "Su dinma da suna tare damu basu jima da fita ba saboda zamu tattauna akan makomarsu wato inda yadace su zauna a hannunsa ko a hannuna....." "To yanzun a ina kuka yanke hukunci zasu zauna?" "Nidai idan son samuna ne shine su zauna anan wurin iyayena shikuma yaki yarda wai ala dole lallai lallai sai nabashi yaranshi ya kaiwa mom dinshi wacce nasan gallaza musu kawai zatayi" "To ke meyasa ba zaki rikesu ba?" Dan Damm tayi sannan ta saki murmushi, "Ibrahim kenan,taya zan rikesu alhali ubansu na raye? Da dai ace baya raye ne shine zan iya daukarsu intafi dasu gidan aure na" "Kar ki damu indai dan tani ne,maamy nima fa mai rike yaranki ne koda kuwa babu aure tsakaninmu....... Babu matsala kina iya rikesu" "Allah sarki Khalil..... Can't wait lokacin da zamu zama ma'aurata" Murmushi yayi ya kalleta, "Wanne albishir za ayi min?" "Farin ciki kawai...." Murmushi yayi baice komai ba,har suka gama hirar yatafi bai nuna mata zoben ba ko yamanta ne ko kuma meyasa oho shi dai yasan dalili. Karfe 11 yashiga gidansa a abuja, Hanan na zaune taji shigowar shi yau kam ta daura damarar sai taji daga gareshi, mintuna 30 tabashi yagama kintsawa sannan sai taje gareshi taji abinda ke faruwa da har yadauki fushi da ita, Tana ganin mintuna 30 sun cika ta tashi ta fita tana sanye cikin kayan bacci ta dora hijab akai,falon nashi ta shiga wanda ya wadatu da kamshinsa mai sanyaya zuciya da tsayawa arai,bata fi mintuna biyu da zama ba taji fitowarsa yana magana awaya cikin sanyin murya, "Khalid maganar aure na da maamy ne...... Dazu naje na sameta tare da baban yaran nan nata,ni banda problem akan yara zan rike mata amma inda problem din yake shine....." Ai bata jira taji karshen bayanin nasa ba ta tashi jiri na d'aukarta kamar zata fadi tafita daga sashen nasa gaba daya. Wani irin kuka ne yaci karfinta kuma tun kafin ta shiga bedroom dinta ya subuce mata,haba ashe da walakin,ashe dama can akwai wata akasa shiyasa anty maamy tazo gidanta ta tare tun kafin adaura musu aure da Khalil,ashe sun jima suna cin amanarta bata saniba, Kukan rashin sanin mafita tayita faman yi gashi babu waya a hannunta bare ta bukaci shawarwarin yan uwa da abokan arziki,kusan kwana tayi tana kuka sai da asubah ta iya samun bacci. Haka ta wayi gari kamar wata marar lafiya gashi sam babu farin ciki atare da ita danma dai kafin ta tashi umma tuni ta shirya Aryan yatafi makaranta,kasa cin abinci tayi sai ruwan tea kadai da ta iya kurba,tsawon kwanaki biyu tana fama da rashin cin abinci da kuma rashin bacci wanda yayi sanadiyyar haddasa mata ciwon kirji da zazzabi, Da farko zazzabin baiyi zafiba amma magriba nayi sai ya tsananta jikinta kamar ana kada mata mazari saboda tsananin rawar sanyin da take yi,waya umma tayiwa Khalil ta sanar masa akan ya turo musu Dr,babu jimawa sai ga Dr Al'amin din yazo nan ya dubata yayi duk abunda yadace yatafi, Wani bacci ne mai dadi ya kwasheta bayan tafiyar Dr nan umma taja hannun Aryan suka fita suka barta dan ta samu bacci,shi kuwa Khalil lokacin da umma ta kirashi awaya tana fada masa rashin lafiyar Hanan yana can gombe tare da maamy wacce gyaran jikin da aka fara yimata na dilke da halawa yasa ta sake fitowa dauu kamar wata balarabiya ga wani azababben kamshi da ke tashi daga jikinta kamar masana'antar sarrafa turare, K'arfe 12 yasamu shigawo gida domin bai baro gombe da wuri ba,wanka yafara yi yasaka k'ananan kaya na bacci sannan yafita zuwa part din Hanan domin ganin yanda jikin nata yake tunda lokacin da umma ta kirashi awaya tace masa jikin Hanan din ya dan tsananta, Kamar koda yaushe wani sanyayyen kamshi ne yafara yimasa maraba lokacin da yashiga falon nata,kai tsaye bedroom dinta yabude yashiga,tashinta kenan tana zaune tsakiyar gado ta jingina tana tunanin ta yanda zata sauka domin ta hado tea saboda yunwa kuma take ji, Kamar wanda baya so haka ya karasa gaban gadon fuskarshi babu yabo babu fallasa, sunkuyar da kanta kasa tayi saboda tsoro da kwarjinin shi take gani, "Ya jikin?" Taji ya fada yana tsaye yakama kugunshi ya rike, "Da sauki..." Ta fada muryarta adashe sakamakon yawan kukan da tayi, "Me yafaru naganki a zaune kuma?" "Yanzu natashi tea nake son zan sha...." Dan shiru yayi sannan ya kalleta, "Zaki iya zuwa ki hado ne?" Kai ta girgiza masa batare da ta kalleshi ba, Juyawa yayi yafita ya sauka k'asa,tea din ya tsiyaya cikin cup ya hada mata yaji madara da milo sosai dan ba karamin kauri yayi ba sannan ya daukar mata snacks yakoma sama,har lokacin ta zaune kamar yadda take dazu, Mika mata yayi ya nemi wuri ya zauna gefen gadon domin sai yaga ta rame sosai,to ko dama tajima tana zazzabin ne bai saniba? Harga Allah bata son tea dinnan da ya hado mata saboda yasaka madara ita kuma saboda zazzabin da take yi bata ko kaunar taji karnin madarar gashi yazuba da yawa da ace itace zata hada to da ruwan bunu zata hada tasha shi bak'i,daurewa tayi kawai tafara sha ahakan tana rintse idanu,tasha yakai rabi ta yunkura zata ajiye ya kalleta, "Wa kika ragewa wannan din? Shanyeshi" Jin abinda yace yasata fasa ajiye cup din taci gaba da sha tana jin zuciyarta tana tashi amai yana taso mata, yunkurin amai ne ya addabeta har bata san lokacin da ta rikeshi ba saboda babu tazara sosai tsakaninsu,tare ta wankesu da aman wanda yaki karewa domin gaba daya tea din da ta sha sai da ta amayar dashi, lokacin da tagama aman jikinta duk ya saki babu karfi ko kadan,lagwaff ta sakeshi ta kwanta tana jin wani sabon zazzabi na shigarta,mikewa yayi yafita, bedroom dinshi yaje ya wanke jikinsa ya sauya kaya sannan yadawo tana nan kwance kamar yadda yatafi yabarta, Baida zabin da yawuce ya gyara ta ya tsaftace wurin da ta bata, tunanin ta inda yadace yafara yayi nan yafara da kan gadon sannan ya dagata itama,tana son tayi masa gardama amma kuma tana tsoro domin yau akwai wani kwarjini na musamman akan fuskarshi,yar doguwar rigar jikinta ya cire ya goggoge mata jikinta sannan ya bude drawer dinta yaciro mata wata,tun dazu ya lura da ita sai faman kakkare kirjinta take yi tanata bobboyewa ko ta manta da yataba ganinta ahakane oho? Amma wanne dare ne wanda jemage bai ganiba ya furta hakan acikin ransa,yana gama saka mata rigar ta tukunkune taja bargo ta rufe jikinta tana rawar dari, Sai da yagama tsaftace duk wurin da ta bata da aman sannan yafita zuwa sashensa, kwanciya yayi amma ba bacci yake ba,bayan kamar mintuna 30 yasake tashi yafita yaje ya dubata,bacci ya samu tanayi dan haka yakoma sashensa shima ya kwanta zuciyarshi cunkushe da tunani iri iri................................✍? _Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 47 ***Haka yaci gaba da jinyarta amma koda yaushe fuskarsa ahade babu fara'a alhalin ita kuma bata san abinda tayi masa ba shikuma yaki yasanar da ita sai faman fushi yake yi, Duk abinda tace tana so yana mutukar yin duk iya iyawarshi wurin nemo mata amma fa tsakaninta dashi babu sakin fuska dan komai yana yine kamar irin anyi masa dole dinnan, Kwananta biyu akwance ta dan fara samun sauki,itama gaba daya acike take dashi sakamakon auren da taji zai yi kuma wai anty maamy zai aura,tana ta son ta kira abokan shawararta su dan tattauna su bata shawarar da ta dace amma babu waya a hannunta kuma tsoron tambayar Khalil take yi,rasa yanda zatayi tayi daga karshe sai umma barira ta samu da maganar lokacin ita kadaice adakinta tana sauraren fm radio shi kuma Aryan yatafi makaranta,tashi zaune umma tayi daga kishingiden da take sannan cikin alamun tausayawa da tausasa harshe tace, "Kiyi hakuri Sa'adatu,tabbas kishiya nada ciwo kuma tana da zafi shiyasa ba kowacce mace ce take iya cin rabarta ba, da yawa mata a kishiya jarrabawar su take sai dai amma basu fiya cin wannan jarrabawar ba saboda gajen hakuri da kuma hawa dokin zuciya..... Idan akayi hakuri kuma aka kai zuciya nesa wallahi ba kishiya ba ita kanta rayuwar gaba daya mai wucewa ce,kina zaune mijin zai dawo ya sameki kuma har ma ki zama alkali atsakaninsu amma fa sai kin kai zuciyarki nesa, mutukar baki nutsu kin kama mutuncin kanki ba to a irin wannan gabar ne miji yake rainaki,danginsa suke rainaki,kishiya take rainaki,ke hatta sauran abokan arziki rainaki sukeyi mutukar baki ja girmanki kin yiwa fushinki da zuciyarki linzami ba,shi wannan zafin kishin da kan tasowa mata a lokaci guda shine ke sanadiyyar sasu aikata abinda zasu zo suna nadama da dana sani tsawon shekaru dan da yawan mata a wannan lokacin suke barin damarsu,miji yayita rarrashinsu amma suna fandarewa har shima yagaji yayi watsi dasu daga karshe idan ba ayi sa'a ba shikenan ansamu hanyar lalacewar zamantakewar da aka gina shekara da shekaru....." Sake gyara zama umma barira tayi sannan ta fuskanci Hanan, "Shawarar da ni dai zan baki 'yarnan shine..... Kishiya bata cinye uban kowa ba kuma kema bafa zata cinyeki ba,kiyi hakuri kici gaba da kyautatawa mijinki,nima na zauna da ita nasan zafinta kuma nasan ciwonta amma da nayi hakuri wallahi komai sai da ya zamto tarihi,to kema haka taki zata zama tarihi kamar ba ayiba......." Jijjiga Kai Hanan tayi alamar gamsuwa da bayanan umman shiyasa neman shawarar manya amafi yawan lokuta take da dadi domin ko basu magance maka matsalarka ba zasuyi maka bayanin da kai kanka sai kaji dadi zuciyarka tayi sanyi, "Nagode umma kuma insha Allah zanyi yanda kika ce......" Cigaba da bata shawarwari umma tayi har tsawon wani lokaci kafin ta tashi ta shiga kitchen domin dorawa Khalil abinci ada tayi fushi tace bazata sake yimasa girki ba sai dai wacce zai auro din idan tazo ita taci gaba dayi masa amma kalaman da umma tayi amfani dasu wurin bata shawarwari sune suka sanyaya mata zuciya har taga rashin dacewar hakan ta sauya shawara, Tasan daga shi har dan gaban goshin nasa zasuyi farin ciki da abunda zata girka musu yau shiyasa ta bada himma ta zage wurin ganin ta nuna kwarewarta a wannan fannin, Zuwa yamma ta kammala komai nata suna tare da Aryan a falonta suna yin game,kokari takeyi taga tayi yaki da duk wani bacin rai tare da damuwa dake kokarin yiwa zuciyarta tsinke har yasamu wurin zama wannan dalilinne yasa take ta biyewa Aryan suka taru suka zama mashirmata. Tun kafin Khalil yadawo ta shirya masa table bayan ta gyare masa sashensa tsaf yasha turaren wuta dan sudan mai bala'in kamshi,bayan sallar ishah yasamu zarafin dawowa kasancewar yau yaje garin zamfara ya halacci wani taro, Kamar yadda yasaba wanka yafara yi yashirya cikin kananan kaya sannan yafito falo hancinsa na shakar kamshin turaren da Hanan ta saka masa sannan wani abun sha'awar shine yanda ta kawata table din sannan ta armasa shi da warmers masu kyau kanana,zama yayi yana budewa nan yaga funkaso ne yatashi sosai sannan yayi kyau sai miyar agushi tasha alayyahu itama tayi kyau sosai tun a ido gashi ta wadatu da naman kaji,sai lafiyayyen zobon da ta hada wanda yaji flavors daban daban ya wadatu da kankana da cucumber aciki,zuba funkason yayi yafara ci wanda yayi daidai da shigowar Aryan cikin falon, cinyarshi ya haye shima yasaka hannu yafara cin funkason wanda tunda aka sauke yake ci amma yakasa koshi gashi kuma baiyi wani auki sosai ba dan hatta umma ma saida ta bukaci kari akan guda hudun da Hanan ta zuba mata shi kansa Khalil din kwaya uku yasamu, "Abba na ba kaci naka bane? Wannan fa nawane nima zanci....." Makale kafada Aryan yayi yaci gaba da ci yana surutu, "Nima zan kara ci uncle......." Tare suka cinye sannan Aryan yafice,shikuma zama yayi nan falonshi aranshi yana tunanin to ko menene kuma yafaru da Abba Idris ke nemanshi? Dan dazu yayi masa text massage akan yaje gombe yana son ganinshi gobe yasan dai baya wuce maganar aurensu shida maamy,wayarshi yatashi yashiga bedroom dinshi yadauko yafito yasoma kiran layin maamy amma number busy,ajiye wayar yayi saboda yasan idan tagama zata kirashi amma kuma ga mamakinsa har ya kwanta bacci bata kirashi dinba shima kuma bai sake kiranta ba. Washe gari asubanci yayi yafita ta can office yawuce gombe domin amsa kiran Abba Idris wanda yake matsayin uba agareshi, Bayani cikin nutsuwa abba Idris yayi masa akan maganar aurenshi da maamy cewa tsohon mijin maamyn wai yadawo yanata bibiya sai takoma d'akinta kuma dama tun farko matsalar ba daga gareshi bane daga mahaifiyar shi ne dan haka shi Khalil yayi hakuri yabarwa Abban jawad domin mammy takoma gidan tsohon mijinta,dama Khalil yasan za arina kuma za ayi haka dan tunda yaga take taken tsohon mijin mammy yasan da wata akasa,duk da baiji dadin abinda yaji ba amma godiya yayiwa Abba kuma yanuna baiji zafi ko ciwon abinda yafaru ba sai dai har acikin ransa baiji dadin boye masan da mammy tayiba shi baya son boye boye da nuku nuku cikin sha'aninsa koda yaushe yafi son mutum yazama open amma babu komai dan koba alaka ta so maamy ai yar uwarsa ce ta jini, sallama yayiwa abba yatafi batare da yashiga cikin gidanba. Wannan al'amari shine sanadin rushewar maganar aurensa da maamy wanda ita Hanan bata saniba duk atunaninta maganar aure har yanzu tana nan daram shiyasa taci gaba da kyautata masa da yimasa duk wani abu wanda zai faranta ransa,ranar da aka daura auren mammy sai ranar Hanan tasan anfasa auren da Khalil dan abakin umma barira taji bayan umman sun gama waya da hajiyarsu Khalil,wani sanyi da annuri da farin cikine yarinka ratsa zuciyar Hanan da kuwa duk zuciyarta ta shiga cikin wani hali,babu bata lokaci ta shiga cikin kitchen domin jinta take yi awartsake yanzu,tuwon dai nasu na gado ta dora musu shida Aryan saboda basa gajiya dashi nan ta lailayashi tayishi lafiyayye miyar busasshiyar kubewa mai tsananin yauki wacce tasha kifi wadatacce,man shanu ta soya bayan ta sauke girkin, Tun kafin Khalil din yadawo su umma ke santin wannan tuwon ita da Aryan ita dai Hanan dariya kawai tayi ta haura sama,bayan sallar magriba Khalil din yadawo daga gombe amutukar gajiye ga wata yunwa dake ciciyarshi,kayan jikinsa ya sauya daga manya zuwa kanana sannan yazo yahau table nan yafara kwasar girkin Hanan wanda ke barazanar cire masa kunne dan tsabar dadi,yana dab da kammalawa Hanan tashigo itada Aryan wanda ta sakoshi agaba wai ya tayata tambayar Khalil wayarta da yarike ya hanata tun sati biyu zuwa uku da suka gabata, Ganin sun hade kai yasashi kallonsu yana cigaba da cin tuwonsa, "Papa....." Kallon Aryan yayi sannan yakai laumar tuwon da ya debo, "Menene?" Kallon Hanan yayi sannan ya kalli Khalil, "Mommy infada?" Girgiza masa kai tayi, "Kabari har sai yagama cin abinci tukunna" "Kai fadi..... Menene?" "Uncle mommy ce tace wai kabata phone dinta...." Yaji abinda Aryan din yafada sarai amma sai bai kulasu ba kawai yaci gaba da cin abinsa har ya kammala lokacin tuni har lokacin sallar ishah yayi dan haka bai zauna a falonba yamike zuwa cikin bedroom dinshi hakan ya tabbatarwa da Hanan cewa bazai bata ba shiyasa kafin yafito ta tashi tafita shikuma Aryan yabishi zuwa cikin bedroom din tare sukaje salla suka dawo,itama sallar taje ta yi,bayan ta idar ta na zaune kan abin salla Aryan yashigo yace taje Daddy yana kiranta,tashi tayi batare da ta cire hijabin jikinta ba tabishi suka tafi, Yana hakimce kan sofa ya dora kafarshi daya akan center table yana ta faman yimata bincike awayar tata,zama tayi akujerar dan nesa dashi kadan, "Me kuke cewa dazu keda d'anki?" Taji yafada har lokacin idanuwanshi na kan wayarta yana ta faman yimata bincike ita dai fatanta Allah yasa kar ya kalle mata sirrin da ta ajiye a WhatsApp,dan duk ranar da hajja hasinah tayi posting din abu mai amfani starring dinsu takeyi ta adana bata gogewa, "Baki jine?" "Inaji..... Cewa nayi ka taimaka kabani wayata zanyi amfani da ita gida....." Bai amsa mata ba har tsawon mintuna biyu sannan cikin alamar tuhuma taji yace, "Waye mujahid?" Sosai tambayar tabata mutukar mamaki sannan lokaci guda saima ta nemi amsar da zata bashi ta rasa dan sai ta kasa gane wayema mujahid? "Ina tambayar ki waye mujahid?" Shirun taso sake yi amma kuma ganin ya tsareta da idanuwanshi mayalwata yasata yin kasa da kanta sannan tace, "Dan makarantar mu ne..." "Kar kiyi min karya dan already nasan gaskiya,kawai ina son sake tabbatarwa ne,wayeshi?" Ji tayi yawun bakinta na neman kafewa, "Ya taba cewa yana sona......" "Tsohon saurayinki ne kenan?" Taji yafada bayan yaja wasu sakwanni, "Uhmmm" "Bai san kinyi aure bane?" "Yasani..." "Ok" Daga nan cigaba yayi da tambayar contacts dinta kusan kowa sai ya tambayeta waye shi sai dai abinda yabata mamaki shine sam bai tambayeta waye wannan wanda yake turo mata text massage dinba ko bai ganiba? "Ita wannan hasinah din itace malamar ku kenan?" Taji yafada babu zato babu tsammani, sunkuyar da kanta kasa tayi tana jin kunyar duniya na lullubeta saboda tasan yaga abinda taketa addu'ar Allah yasa kar yagani, Baiyi mata maganar ba ya mika mata wayarta bayan ya gama karanta duk abinda idonshi yasauka akai, Hannu biyu tasa ta karba ta tashi tafita cike da murna tana zuwa part dinta ta saka wayar a charge tashiga wanka,bayan tafito tagama shirin bacci ta dauki wayar ta kunna data ta leka WhatsApp domin sosai tayi missing dinshi shiyasa har 12 saura takai yau a online,kai ashe waya ma rahama ce bata san da haka ba har saida Khalil ya kwace mata wayarta. Washe gari Khalil yabar kasar yatafi k'asar Rwanda,tunda yatafi kuma ta shiga missing dinshi har ta kasa hakuri sai da ta tura masa massage, Yana kwance adaki har yafara bacci yaga massage din nata murmushi yayi ya mayar mata da reply, _Me kika fi missing atare dani?_ Itama murmushin tayi lokacin da taga tambayar da yayi mata saima ta rasa amsar da zata bashi dan haka tayi shiru kawai. Satinshi daya yadawo,aranar da yadawo bai shigo gidanba sai dare bayan duk sunyi bacci washe gari da safe yatafi gombe bayan yadawo da daddare yakira Hanan falonshi, "Ki shirya gobe za muje gombe Muneerat ta haihu....." Ya fada yana rike da wata jotter da pen yana rubutu amma bata san abinda yake rubutawa ba, Tun adaren tayi shirinta ta hada kayanta set biyu sai ko kayan bacci da inner wears,humrar da hajja hasinah ta kawo mata ranar da tazo ta saka cikin akwatin kayanta sai da ta tabbatar tagama hada komai sannan ta kwanta, Washe gari bayan ankai Aryan makaranta Khalil yaje office yafito suka nufi gombe bayan sunje store ta sai kayan baby,duk yau tunda ta tashi jikinta babu dadi ahaka dai suka karasa da rana fatse fatse nan ta samu tarba kamar yadda aka saba yimata,saida suka fara zuwa gidan Khalid suka ga baby anan Muneerat ke yimusu albishir din wai sunan Khalil Khalid yasakawa jaririn,ba karamin dadi Khalil yajiba nan ya ajiyewa Muneerat damin kudin da Hanan bata san ko nawa bane amma dai yan dubu dubu ne sabbi fil dasu,daga nan suka tafi cikin gida can Hanan ta samu tarba ta musamman awurin su hajiya da su zarah, bedroom din da take sauka idan tazo yauma anan aka sauketa,tunda tazo tashiga cikinsu sarah suna shan hira har dare, Khalil kuwa dama bata kara sakashi a idonta ba kuma shima agarin zai kwana. Misalin karfe 11 da wurin rabi tana kwance suna chaten da yaya shamsu nan yake sanar da ita rashin lafiyar abbansu wai ciwon koda sunje asibiti yau,ai agigice tasa hijabi ta fita ta nufi bangaren Khalil tana hawaye, Fitowarshi falon kenan bayan yafito daga wanka yashirya bata tsaya yin knocking ba ta bude kofar ta shiga, kallonta ya tsaya yi yana son jin ba'asin kukanta, "Abba nane baida lafiya wai ciwon koda..... Dan Allah kasa akaini kano yanzu" haka take ta fada sam taki barinsa ma yafurta koda kalma daya saiko uban hawayen dake ta faman bin kumatunta kamar anballe bakin fanfo,hannunta yakama akaron farko ya zaunar da ita kusa dashi har jikinsu na gogar juna saboda kusancinsu kuma har lokacin yana rikeda hannunta,hakuri yasoma bata domin dare yayi yanzu bazai yuyu akaita kano a wannan lokacin ba,kuka ta fashe dashi hakan yabashi damar sakata acikin jikinsa yana rarrashinta,tun shigowar ta kamshin jikinta ke neman rikita masa lissafi domin humrar hajja hasinah yau ta shafa wato giredi nan da nan ta tayar masa da hankali,ita kuwa yau mamakinsa ne ya cika mata zuciya ganin ya biye mata harda rarrashi shiyasa ta bararraje taci gaba da shagwabarta.......................✍? _Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 48 ***D'aukarta yayi gaba dayanta ya dorata kan cinyarsa wanda hakan yayi mutukar bawa Hanan kunya sosai, rungume ta yayi cikin jikinsa yana shafar bayanta alamar rarrashi,ji tayi kamar ta nutse kasa saboda tsananin kunya,shi kuwa gogan hankalinsa ne yakai kololuwar tashi saboda sosai kamshin jikinta ya rudashi kuma ya jefashi cikin kogin bukatarta, Cikin dabara yasamu ya rabata da hijabin da ke jikinta wannan ba shine karo nafarko da yafara ganinta ahaka ba amma wannan yana da banbanci da na lokutan baya,sosai yau dinnan Khalil ya dauki dumi domin wata irin matsa yayi mata sai faman aikin sinsinar jikinta yake yi sakamakon kamshin da jikinta keyi wanda ke kara masa kaimi yana ingizashi gareta,cak yatashi da ita yanufi cikin bedroom dinshi yana rike da ita,ita kam idanuwanta arufe suke ta runtse su dan ba zata iya hada ido dashi ba cikin wannan yanayi, A saman katafaren gadonshi yayi musu masauki bayan ya rage hasken dakin izuwa haske marar karfi, jikinta har rawa yake yi saboda rashin sabo ga kuma tsoro duk da cewa abun yazo mata bagatatan batare da shiri ba,tun kafin ya aiwatar da kudirinsa shima nasa jikin ya dauki rawa babu bata lokaci wani matsanancin zazzabi da ciwon kai suka rufeshi nan take batare da ya cimma burinsa ba, Kasa aikata komai yayi sai ko uban kakkarwar sanyi da gangar jikinsa keyi kamar ana kwara masa kankara, "Sa'adatu lullube ni........ Sanyi nake ji" Gaba daya duk ta rude itama ganin abinda ke faruwa domin wani irin rawa jikinsa keyi, lullubeshi tayi da bargo amma yanda yake jin sanyi na kadashi gani yake yi kamar bata rufa masa komai ba shiyasa yayi azamar jawota jikinsa ya rungume jikinsa ya dauki zafi sosai, Haka suka kasance zuwa wani lokaci yanata kakkarwa har lokacin yana rungume da ita kamar zai mayar da ita can cikin cikinsa,ya dan fara samun bacci sama sama ciwon ciki ya turnikeshi kamar zai mutu har da su yunkurin amai amma kuma yakasa, Hanan kuka tafara yi tana son ta tashi taje cikin gida ta kira su hajiya amma ya riketa tsam kamar me,kuka take ta faman yi tana yimasa sannu shi kam ko magana ma yakasa yi sai yunkurin amai yake ta yi cikinsa na murda masa haka suka kusan kwana dan sai kirjin asubah sannan yasamu ciwon ya lafa masa har bacci yayi nasarar daukarshi,sakashi agaba Hanan tayi tana kallonsa cikin tausayawa har lokacin yana manne da ita yana bacci,ita kam sai bacci barawo domin tana cikin hali na zullumi dan yanda taga Khalil din yayi ba karamin tayar mata da hankali yayiba dan kamar wanda zai mutu haka yazame mata fa, Misalin karfe 7:30 na safe ta farka nan idanuwanta suka sauka akan bawan Allah Khalil da keta faman baccin wahala duk yagama jigata takai kimanin mintuna biyar tana kallonsa sannan da dabara ta raba jikinta da nashi ta tashi, kayan baccinta ta maida jikinta sannan ta shiga bathroom,bata wani jima acan sosai ba tagama abinda zatayi ta fito tazo tayi salla,bayan ta idar ne ta samu zarafin kallon dakin,daki kam komai yaji ne babu ma abinda yafi burgeta irin dan karamin farin gadonshi wanda ke girke cikin dakin,mikewa tayi ta nufi bakin gadon nan idonta yasauka kan wani madaidaicin hoto dake ajiye kan bedside drawer dinshi,zama tayi ta dauki hoton tana dubawa bakinta abude mamaki karara kwance saman fuskarta domin badan tasan cewa ba ita bace ta dauki wannan hoton to da babu abinda zai hana tace itace saboda tamkar kara aka tsaga da ita da wacce ke jikin hoton tana sanye cikin purple din atamfa tana dariya, Allah mai iko to ko wannan itace mahaifiyar Aryan? Ta kissima hakan acikin ranta,tajima tana kallon hoton kafin ta ajiyeshi ta juya ga Khalil wanda ke kwance ya dunkule wuri daya,so take ta tasheshi yayi salla amma tana tsoron kar kuma yatashi da ciwon cikin tunda ansamu ya lafa masa, Bargon da yake ciki ta dan yaye tafara tashinsa har lokacin jikinsa akwai zafi sosai,riga mai nauyi yasa ta dauko masa yasaka sannan ta rikeshi ya sauka daga kan gadon yashiga bathroom,daurewa kawai yayi yai sallar amma shi kadai yasan abinda yake ji,tun akan abin sallar yafara rike ciki dakyar ta taimaka masa yakoma saman gado ya kwanta nan tafita zuwa cikin gida da sauri domin sanarwa dasu hajiya. Cikin lokaci k'ank'ani aka kira Dr yazo yafara dubashi amma ciwo kamar karashi akeyi,gaba daya hankula sun tashi musamman ma Hanan da hajiya,wurin azahar yasamu ciwon cikin ya lafa dan har yasamu damar yin bacci, Hanan na zaune awurinsa yaya shamsu yakirata awaya saida taji hankalinta yatashi gabanta ya fadi nan ta amsa wayar jikinta na rawa tunda shima Abban nasu tasan baida lafiya, "Yaya shamsu yajikin Abban?" "Jikinsa da sauki Hanan gamu ma agida..." "Kajini shiru banzo ba ko? Shima Abban Aryan ne yatashi da ciwon ciki shiyasa wallahi amma zanzo..." "A'a kiyi zamanki ki kula dashi tukunna.....ga Abban ma" Jin Abba ya karbi wayar yasata fashewa da kuka, Nan Abba ya dan kwantar mata da hankali yace mata yama samu lafiya dan har fita zaiyi anjima,saida suka gaisa da mamaye sannan sukayi sallama ta kashe wayar ta zubawa Khalil ido kamar lokacinne tafara ganinsa, tausayinsa take ji har can cikin ranta wanda bata san daliliba koda yake kila tausayin yanada nasaba da irin son da take yimasa, Zuwa la'asar ya farka da wani azababben ciwon cikin ga yunkurin amai amma yakasa yin aman ganin dai abun kamar gaba yake kara yi Zaid ya kwashesu suka nufi asibiti can aka bashi gado aka kwantar dashi,daren ranar kuwa daga shi har Hanan basu runtsa ba saboda murkususun da yaketa faman yi sai asubah sannan yasamu bacci, Misalin karfe 7 nasafe su hajiya suka zo harda wani dattijon bafulatani tare suka shiga cikin dakin sannan ya tsaya akan Khalil yana kallonsa har na wani tsawon lokaci daga bisani yajuya ya kalli hajiya ya kalli Hanan sannan yace, "Wannan aikin shaidanu ne,ko shakka babu sihiri ne kuma mai karfin gaske sai dai Allah yabamu nasarar warwareshi cikin sauki...., Yanzu hajiya abani kwana uku zanje innemo makarin wannan asirin dake jikinsa,amma zan aiko jikina salisu zai kawo masa tsumin da zaisha saboda wannan ciwon cikin dake damunsa, Allah yabashi lafiya...." "To shikenan nasalla,mun gode, Allah yasa adace,mun gode" hajiya ta fada tana sharar hawayen dake idonta,ita dai Hanan tana tsaye tarasa ma wanne irin tunani zatayi,shikuma Khalil haka rayuwarshi take daga acutar dashi sai acutar da danshi to duk suwaye keyi masa wadannan abubuwan? "Makiya mana" zuciyarta tabata amsa,wuri ta samu ta rafka tagumi tanata tunane tunanen da bata san dalilinsu ba, Zuwa yamma aka kawo sakon tsumin da za abawa Khalil wanda duk yayi wujiga wujiga dashi babu ci babu sha sai wahalar ciwo,tunda yasha maganin yasamu saukin ciwon cikin domin ba kamar jiya ba yau har yana iya tashi yayi salla kuma ansamu yasha ruwan zafi, Hanan kam koda yaushe cikin hawaye take lallai dan adam ba abakin komai yake ba komai kudinsa komai mulkinsa yanzu shi Khalil ga kudin ga mulkin ga zaratan masu tsaron lafiyarsa amma duk ciki babu wanda ya isa ya dauke masa ciwon dake tare dashi sai sarki Allah. Cikin kwanaki biyun da suka yi a asibitin za a iya cewa da sauki tunda yana tashi kuma yana iya cin abinci sai dai fa yunkurin aman da yaketa yi kuma yakasa yinsa,yana kwance yanzunma bayan yagama yunkurin aman Hanan na yin salla nasalla yashigo dauke da wata yar batta irin wacce fulani ke zuba ruwa aciki, gaisheshi Hanan tayi sannan tabashi kujera ya zauna yana fuskantar Khalil, "Moddibo......... Insha Allahu andace kuma anyi nasara domin ansamo makarin cutar dake jikinka shekara da shekaru,amma sai kayi hakuri da abinda zaka ji daga gareni,matarka itace tayi maka sihirin mallaka,sihirin da bazaka taba kusantar wata 'ya mace ba koma bayan ita,idan har kayi koda yunkurin aikata hakanne to zaka iya rasa rayuwarka......." Shiru Khalil yayi yana nazari acikin ransa,yanzu Ramlat itace ta aikata masa wannan mummunan aikin? To saboda me? Awanne dalili? "Saboda ta kasance ita daya tilo acikin zuciyarka da rayuwarka mana...." Zuciyarshi tabashi amsa, "Ba dan Allah yasa hajiya ta kirani ta sanar daniba to da haka zska kare rayuwarka sai dai wani kadari na ubangiji..... Yanzu ga wannan tashi kasha" Idanuwansa fal da hawaye yatashi zaune ya karbi maganin yakafa kai yafara sha amma ko hadiya uku kwakkwara baiyi ba yaji wani mugun amai yataso masa,karbe maganin nasalla yayi ita kuma hanan ta taso da sauri, "Samo masa wani abu amai zaiyi..." Cikin sauri ta dauko wata silver ta kawo masa riketa yayi bayan ta zauna akusa dashi nan yaci gaba da kakarin aman kamar zai amayar da dukkan abinda ke cikin cikinsa gaba daya,zuwa can yasoma wani irin amai domin gashi ne curi curi yake amayar dasu abun ba kyan gani gwanin ban tsoro,yasha wahala mutuka sannan yasamu nasarar amayar da gashin tas nan nasalla yakarba yafita harabar asibitin yaje ya binne yasake dawowa, Daga Hanan har Khalil mamakine keta faman dawainiya dasu saboda jin abinda nasalla yace,kai amma gaskiya mata na aikata kuskure,yanzu wannan daukar hakki har ina? Ita gashi wacce ta aikata hakan tariga da tabar duniyar to koma dai tana raye ai da cutarwa, Shi kuwa Khalil abin yatsaya masa arai haba shiyasa ranar da Ramlat zata rasu ta rinka neman gafararsa tana cewa ya yafe mata to ko dama wannan yafiyar take nema? Gaskiya mata ba abun yarda bane, Ramlat ta cutar dashi da yawa sannan ta cutar da wani ma tunda kila ba dan Allah yakawo karshen abunba da ahaka zai kare rayuwarsa, Adaren ranar aka sallamesu suka koma gida domin jiki yayi sauki kuma ansamo bakin zaren,wanka yashiga yayi yafito yana zaune bakin gado yana rike da turare Hanan tashigo dauke da tiren abinci ganinshi babu riga yasata niyyar komawa da baya, "Shigo mana...." Yafada kamar wani marar lafiya koda yake marar lafiyar ne amma dai muryarshi ta sake yin sanyi kalau, Kanta a kasa ta ajiye masa ta mike zata fita, "Ina zaki je?" "Zan koma canne..." "Can ina?" Ya tambaya bayan yasoma fesa turaren ajikinsa, "Wurin su hajiya" Shiru yayi baice komai ba har saida yamike tsaye domin dauko rigar da zai saka sannan taji yace, "Ki shirya gobe dasafe za akaiki ki gano abbanki" Cikin fara'a da farin ciki yaga ta dunkule hannayenta wuri daya sannan tace, "Tom nagode" Daga haka ta tashi tafita kuma bata kara komawa sashen nasa ba ita dama tun can asali tayiwa Khalil uzuri duk wannan faman shassharetan da yakeyi bai wani dameta sosai ba ashe ashema bai laifinsa bane bawan Allah, Shima anashi bangaren tunanine kala kala yaketa shiga yana fita cikin kwakwalwarshi,gaskiya Ramlat tayi masa abinda bai taba tunanin zatayi masa ba amma ya yafe mata kuma yana yimata fatan samun rahamar ubangiji. Daren ranar sam bacci baiga idonsa ba sai bayan da yayi sallar asubah sannan ya dan samu baccin,ita kuwa Hanan da wuri tagama shirinta zuwa karfe 8 suka kama hanyar kano saboda aranar zasu dawo, Lokacin da taje gida ta samu jikin abbansu da sauki babu laifi sai lokacin taji hankalinta ya kwanta domin taganshi kalau dashi nan aka shisshigo da kayayyakin da tazo dashi, agurguje tajewa anty salaha sannan suka juya gombe ita da sabon drivern Khalil mai suna attahir. Tana komawa gombe adaren ranar suka koma Abuja domin acewar Khalil yana da uzururruka da yawa acan, Karfe 9 da wasu mintuna suka shiga gida cikin murna su umma suka zo suka taryesu ita da Aryan wanda har lokacin baiyi bacci ba, Ita dai sashenta ta wuce shikuma Aryan yabi abbanshi part dinsa, Wanka tafara yi sannan ta gabatar da sallolinta tana idarwa ta sauka kasa ta nemawa kanta abinda zata sakawa cikinta,tana kokarin tashi taji shigowar text massage, _Zo ki dauke Aryan._ Ganin abinda Khalil yaturo mata yasata mikewa direct tawuce part dinsa, Aryan na falo kwance kan sofa shi kadai,daukarshi tayi tafita zuwa dakinsa taje ta kwantar dashi,takoma nata har ta kwanta taji shigowar wani text massage din, _Had'o min coffee._ Mikewa zaune tayi tana kunkuni ita kadai, "Shima Abban Aryan akwai saka aiki wallahi,sam bazai bar mutum ya huta ba" K'asa ta sauka ta hada masa coffee din sannan ta wuce part dinsa,baya cikin falon dan haka taje gaban kofar bedroom din nasa akaro nafarko dan ba taba shiga tayiba, knocking tayi har zata juya tajiyo muryar shi yana cewa, "Come in" Dukan uku uku kirjinta yafara yi sannan wani dan banzan tsoro ya shigeta lokaci guda,kamar wata sakarya haka ta tsaya kafin daga bisani ta kama kofar dakin ta murda tashiga............................✍️ _Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Aisha_*👌🏻 8/14/20, 10:15 AM - Ummi Tandama: 49 ***Yau kam tantagayyar yar kauye Hanan ta koma lokacin da ta shiga bedroom din Khalil, bedroom din ya hadu ya hadu karshen haduwa,komai na ciki farine kama tun daga kan tafkeken gadon baccinshi kirar Turkish bed sai wani dan karamin wurin hutawa mai dauke da kyawawan fararen kujeru zagaye da center table atsakiyarsu,gaba daya idanuwanta sun kasa tsayawa wuri daya sai kaiwa da kawowa suke yi a sassan bedroom din, Yana kishingide kan wani lilo wanda ke can nesa da gadonshi hannunshi rike da novel na turanci wanda da alama karantawa yake yi,sanye yake da riga armless marar nauyi da kauri sai bakin wando mai santsi, Cikin sassarfa ta dosheshi hannunta rike da coffee din,jikinta har wani rawa yake yi kadan kadan wanda bata san dalili ba,harga Allah a daidai wannan lokacin da Khalil zaice takoma inda tafito da zata fi yin murna da hakan,kamar wanda zai zaneta ko zai rufeta da duka yau haka take jin bala'in tsoronshi, Har kasa ta durkusa lokacin da ta karasa gareshi wanda ita kanta bata san dalilin hakanba, hannunta taji ya hada dashi lokacin da ta mika masa coffee din,dagota yayi ya zaunar da ita kan lilon a gefenshi sannan ya ajiye coffee din kan stoll, Tun shigowar ta kamshin dake manne jikinta yake barazanar tarwatsa kofofin hancinsa dan mutukar sanyi da dadi,tamkar wacce aka zarewa laka ajikinta haka tazama yau dan sam bata cikin nutsuwarta gaba daya, Wata irin fargaba da tsoro ne keta faman shigarta tun bayan shigowarta cikin dakin,tajima tana burin wannan rana sannan kuma ta dade tana rokon Allah akan yanuna mata ranar nan amma yau sai gashi tana jin inama tana da damar mayarda hannun agogo baya,inama wannan ranar takoma da tayi dunbin farin ciki domin babu komai cikinta inbanda tsoro,damuwa da tarin zulumi, "Uncle zan koma....... Bacci nake ji....." Ita kanta bata san lokacin da ta furta hakanba, Littafin hannunshi taga ya mika mata, "Babu inda zakije,yau hira zaki tayani and tare zamu kwana......" Tamkar zakaran da aka tsoma cikin ruwa yayi tsumu tsumu haka tayi jin abinda yace ya sake rikitata da burkitata wannan fa shi ake kira da bazata,ita dai yau tana tsoron wannan rana,jin ya rungumo kafadarta ya karata da jikinsa yasata saurin kallonsa, murmushi yasakar mata cikin rada taji yace, "Meke tsorataki ne? Dama haka kike da tsoro?" K'asa tayi da idanuwanta saboda bazata iya cigaba da kallonsa ba, "Fara karanta min wannan novel din...... Am all ears" Littafin tabi da kallo kamar wata sokuwa, "Ke nake jira....." Taji yafada cikin muryar rada,kasa karanta littafin tayi domin gaba daya tagama tsorata dashi,lallai komai dokinka da wannan ranar dolenka kayi ladab idan tazo, "Bani littafi na tunda ba zaki karanta minba...." Karba yayi ya ajiye saman stoll sannan ya dauki coffee dinsa da ke ta faman turiri ya bude yafara kurbarsa da zafinsa wanda hakan har mamaki yaso bata, Sai da yashanye tass sannan ya ajiye dan karamin flask din saman stoll yajuya ya kalleta,cikin azama tayi kasa da idanuwanta, "Tunda kin ki karanta min novel to bani labari...." "Bacci nakeji...... Dare yayi" Agogo ya kalla sannan ya kalleta, "Nikuma yanzu dare na yafara, sai 2 ko 3 nake kwanciya bacci..." Ido ta zaro sannan ta toshe bakinta da hannunta guda daya, "Uncle dan Allah inje in kwanta?" Yunkurawa yayi yatashi daga kan lilon yana kallonta, "Ai nafada miki yau tare zamu kwana,oya tashi muje" Kasa tashin tayi saboda tsabar fargaba da tashin hankali,har yasoma tafiya ya juyo yaga ta nan zaune bata ko motsa ba,dawowa yayi da baya bata farga ba taga ya tarairayeta gaba dayanta yanufi kan gadonshi da ita nan jikinta ya cigaba da rawa kamar mai rawar sanyi,ajiyeta yayi sannan ahankali taji yace, "Yi baccinki anan....." Daga haka yashige cikin bathroom ita kuma taci gaba da tsittsilla ido tana bin dakin nashi da kallo,wai tayi bacci to tayaya zata iya bacci anan? Ahaka taga yafito ya karasa kan abin sallarshi da alama alwala ya dauro,salla taga yayi raka'a biyu duk yanda akayi shafa'i da wutri zai gabatar, Anashi bangaren shima yana son yace ta tashi suyi sallar nafila amma ganin irin tsoron da ya bayyana atare da ita yasashi kawai ya rabu da ita sai shi kadai yayi nafilfilinsa bayan ya idar da addu'o'insa yamike ya nufi gadon,tana ganin haka ta mayar da idanuwanta ta kulle cike da fargaba,gaba daya hasken dakin ya kashe sai wata yar blue light marar haske nan Hanan ta sake samun kanta cikin faduwar gaba tare da zulumi, Abayanta taji kwanciyar shi sannan cikin nutsuwa ya juyo da ita suna fuskantar juna, "Wannan hijabin zai takura miki..." Bai jira cewarta ba yacire hijabin ya ajiye agefe sannan yajata ya sakata cikin jikinsa, Ji tayi kamar ta saki fitsari awando saboda fargaba da tsoro da suka taru suka kanainayeta shi kansa ya lura da hakan shiyasa saida ya hada da dabaru da wayo, bakinsa taji yana laluben nata wanda ke kamshin splash kamshin kadai ya isa ya sanyawa mutum nutsuwa acikin zuciyarsa,shikuwa tun bayan lokacin da yarabata da hijabin jikinta wani sanyayyen kamshi ke barazanar rusa masa tunani nan duk yabi ya susuce, Kuka kam ta shashi har ta goda Allah,har komai ya kammala bata daina wannan kukan ba domin jinta take kamar ana kokarin rabata da numfashinta saboda duk ta jijji rauni ayanda yazo mata kamar sabin shiga shima haka ya zama yau, Rungumeta taji yayi acikin jikinsa cikin muryarshi wacce bata fita sosai yana rarrashinta, " Kiyi hakuri kinji...... Nine ko? Sorry,ke dince kinada gardama sa'adah,sannu yi shiru bazan kara ba......" Wadannan sune kalaman da yaketa faman rada mata acikin kunnuwanta ahaka har bacci ya kwasheta,sai da ya tabbatar tayi baccin sannan yatashi yashiga toilet yau kam mararsa sakayau yake jinta sakamakon fitar da abinda yajima yana damunsa da yayi tsawon shekara da shekaru,bazai taba mantawa da wannan ranar ta yauba acikin tarihin rayuwarsa, Fitowa yayi bayan ya tsaftace jikinsa sannan yabi gefenta ya kwanta bayan ya sauya kayan jikinsa, "Sarkin tsiwa..." Yafada ahankali yana kokarin sakata ajikinsa,yamutse fuska yaga tayi cikin baccinta sannan ta turo masa dan madaidaicin bakinta, kissing din bakin nata yayi kafin ya lumshe idanuwansa yana rungume da ita tsantsam akirjinsa, Wani baccin dadi ne yayi awon gaba dashi mai cikeda dunbin ni'ima marar misaltuwa domin rabonsa da yasamu bacci mai dadi irin wannan tun Ramlat tana raye,baccinsa yasha na dan wani lokaci daga bisani yatashi yashiga toilet domin tuni anjima da fitowa daga masallaci, bude ido Hanan tayi tana jin jikinta duk yayi tsami ahankali ta lallaba ta maida sutturarta ta dauki hijabinta ta fice daga dakin tana dingisawa dakyar lokacin da taje corridor kuwa saida ta tsaya ta dan huta sannan ta karasa part dinta,kai tsaye toilet ta shiga ta tara ruwan zafi sannan ta shiga ciki, Wanka tayi tai brush sannan tafito har lokacin tana jin zafi da radadi ajikinta ahaka ta canja kaya tayi salla bayan ta idar taje ta rufe kofarta tun daga falo sannan ta dawo tabi lafiyar gado ta lulluba ta kwanta babu jimawa wani bacci mai dan karen dadi ya kwasheta. Shi kuwa Khalil bayan yafito daga bathroom dinshi sai yaga gadonshi wayam babu Hanan babu alamarta, "Har ta gudu kenan....." Yafada acikin ransa, Salla yayi sannan ya nade bedsheet din da ke kan gadon yawuce dashi toilet wanka yayi yafito yashirya cikin sauri saboda yanada meeting na musamman da mr president sannan da yuyuwar zai iya barin k'asar ayau zuwa k'asar Denmark, Suit yau yasha yatsuke kuma ba karamin kyau yayi ba,agogonshi ya daura sannan yafita,tun daga corridor yafara jiyo karadin Aryan wanda Attahir sabon driver ke rike da hannunshi cikin shigar kayan makaranta, "Good morning Papa" Aryan yafada tare da rungumeshi, "Morning lovely son" "Uncle yau mommy ba itace ta shiryani ba umma ce,wai mommy ta makara..." "Ehh Aryan,maza kaje akaika school kada kayi late...." Part din Hanan ya nufa bayan su Aryan sun koma kasa,kofar tata akulle take gamm nan yayita faman knocking amma shiru domin tana can cikin bedroom dinta tana ta sharar bacci bata ma san yana yi ba, Gajiya yayi da knocking din yawuce domin har yaso ya dan makara. Hanan kuwa ba ita ta tashi daga bacci ba sai misalin 12 na rana wannan dinma yunwace ta tada ita,dan mayafi kadai ta yafa sannan ta sauka kasa,umma na babban falon kasa tana sakar tabarma,saida suka gaisa sannan tawuce dining table ta zauna tayi breakfast,bayan ta gama ta sake komawa wurin umma,duk yanda taso da ta boye yanayin da take ciki saida umman ta gane dan har magana tayi mata tace ta daure ta gasa jikinta sosai da ruwan zafi zata ji dadi,cike da kunya ta tashi ta koma sama tana jin dan zazzabi zazzabi ajikinta amma bai sauka sosai ba,shawarar umma tabi ta sake gasa jikinta sosai da ruwan zafi daga nan tasake kwanciya kafin lokacin salla yayi,wani sabon baccinne yasake daukarta cikin baccin zazzabi ya dan rufeta wanda ita kanta tasan na tsananin wahalar da ta shane,har Aryan yadawo daga makaranta tana kwance cikin bargo da zazzabi ajikinta bata samu fitowa ba sai zuwa bayan magriba lokacin ta danji dama dama atare da ita. Khalil kuwa yau bai samu zama ba duk da yana cikin sabgogi masu tarin yawa amma yana ta gwada kiran layin wayar Hanan amma akashe baya samunta daga karshe lokacin da sukayi waya da Aryan shi ke sanar dashi wai bata da lafiya lokacin da Khalil din ya tambayeshi wai ina mommy,suna gama waya da Aryan yaturawa Dr Al'amin text massage akan yaje yaduba Hanan saboda shi bazai samu damar komawa gidanba dan ta can office zasu wuce airport. Hanan bata san cewa Khalil yasan rashin lafiyarta ba,bayan tayi wanka tayi salla ta sauka kasa har lokacin jikinta akwai zazzabi kadan duk kuma tayi sanyi komai tana gudanar dashi cikin rashin kuzari,suna zaune falo Aryan nata wasa akan dokin robarshi Dr Al'amin yazo,gyara mayafinta tayi sannan tace yakaraso, "Ranki yadade oga ne yaturo ni yace bakida lafiya inzo indubaki...." Jin abinda Dr yace bayan sun gaisa sai duk kunya ta kamata to shi Abban Aryan din waye yasanar dashi bata jin dadi? Kodai shi da kansa yasan dole hakan tafaru tunda yasan abinda ya aikata? Cike da kunya tayiwa Dr bayanin yanda take ji nan ya hada mata magunguna yabata yatafi, Abinci ta dan ci sannan tasha maganin tasake komawa sama ta kwanta,haka taci gaba da kwanciyar nan har zuwa dare kuma sai lokacin ta kunna wayarta domin tana son kiran gidansu dan taji ya Abba yakara ji da jiki, Mamaye ta fara kira bayan sun gaisa sannan ta kira abbaa wanda ke tare da yaya shamsu sun dan jima suna hira daga bisani sukayi sallama,suna gamawa ta ajiye wayar tashiga wanka, lokacin da tafito tana tsaka da shirin bacci kiran Khalil yashigo,rasa yanda zatayi ta dauki wayar tayi domin wata irin matsananciyar kunyarsa take ji har kiran ya katse bata iya dagawa ba,wani kiran ne yasake shigowa akaro nabiyu wanda shi kansa Khalil bai san dalilin zuciyarsa na nacewa lallai lallai sai taji halin da Hanan take cikiba wai yau shine harda kiran ta sau 2 gaskiya taciri tuta domin hakan ba dabi'arsa bace, Wayar ta d'aga amma ta kasa cewa komai sai shiru da tayi,numfashi ya dan sauke ahankali daga kwancen da yake sannan cikin taushin murya yace, "Bacci kike yine?" Jin abinda yace yasata furta, "A'a" Ahankali, "Me kike yi?" "Wanka nayi ina shiryawa....." "Inzo in tayaki?" Shiru tayi sakamakon jin abinda yace,gaskiya mutumin nan shima A ne, "Uhmmm?" Taji yasake bukata,kasa magana tayi amma dai tana rike da wayar a kunnenta, "Ya jikin naki?" "Da sauki...." Ta fada muryarta na dan rawa, "Kinsha maganin?" "Uhmmmm" "Allah yakara lafiya...." Shiru tayi ba amsa,jin har lokacin ta kasa sakewa dashi yasashi yimata sallama ya katse wayar,karasa shiryawa tayi ta kwanta aranta tana sake jinjina rashin kunya irinta da namiji,shikuma Abban Aryan irin nasa salon muguntar kenan yasha coffee mai zafi yakare akanta,lumshe idanuwanta tayi tana murmushi duk da tasha wahala amma moment din yayi mata dadi sannan zata yita ajiyarshi acikin kwakwalwarta har zuwa karshen rayuwarta,da tunanin daren jiya bacci yasamu nasarar yin gaba da ita. Washe gari ras ta tashi sai dai dan abunda ba arasa ba kuma yau dinma wuni tayi akwance wayarta akashe dan har ta kwanta bacci bata bude ba,shi kansa Khalil sai awurin umma yaji lafiyar ta jin umma tace masa lafiya lau yasashi sauke wani gwauron numfashi sannan yayi mata sallama ya katse wayar, Washe gari tunda ta tashi take shargallenta domin ta wartsake ta warke ras yanzu bata jin ciwon komai kuma sunsha wasansu da Aryan dayake weekend ne,har bayan sallar ishah suna tare afalonta dake sama suna kallo saida yayi bacci sannan tashiga wanka bayan ta kaishi cikin bedroom dinta ta kwantar dashi,rigar bacci ta saka bayan ta shafa humrarta mai sanyin kamshi, wayarta ta landline dake ajiye kan bedside drawer itace tafara ruri nan ta dauka dan jin waye domin dai duk yanda akayi acikin gidanne, "Meyasa wayarki akashe? Hado min coffee ki kawo min yanzu....." Jin muryar khalil yasata jin cikinta ya tsure to yaushe yadawo? Gashi kuma wai takai masa coffee,ita fa bata manta da kaiwa coffee din ranar nan ba,anan cikin bedroom dinta tabar Aryan ta saka hijab har k'asa sannan tafita zuwa kitchen, mintuna kalilan tagama hada masa ta dauka tafita,yauma baya cikin falo yana can cikin bedroom dinshi hakan yasake tsinkar mata da gaba,cikin fargaba da tsoro tashiga bedroom din nashi nan dinma baya ciki,ajiye masa coffee din tayi tana kokarin juyawa takoma taji motsin fitowarsa daga toilet,tunda tajuya sau daya ta kalleshi bata sake marmarin kallonsa ba, "Ina zakije kuma? Taji ya tambayeta idanuwanshi akanta, "Uhmmm...... Dama.... Dama Aryan zanje inkai dakinshi" "To je ki kaishi ki dawo" Kai ta daga sannan ta fita amma bata da niyyar dawowa dan harga Allah ita yanzu tsoron Khalil take yi,shiyasa lokacin da ta koma bata dauke Aryan din ba tabarshi adakinta zasu kwana tare, Shiru shiru Khalil yaga bata dawoba har yagama komai nasa, k'arfe 1 na dare agogon kan bedside drawer dinshi yanuna turaren midnight mai tsadar yasake fesawa sannan yafita yanufi part din Hanan, Ganinsu kwance tare da Aryan yasashi yin dan murmushi, Aryan din ya dauka yafita dashi yakaishi dakinsa ya kwantar sannan yadawo bedroom dinta,bacci take yi sama sama taji kamar andauketa,jinta tayi kamar acikin mafarki shiyasa tasake kankameshi tana shakar kamshin jikinsa bayan ta lafar da kanta cikin kirjinsa. Yana rike da ita akirjinsa har part dinshi cikin bedroom dinshi,akan gadonshi ya kwantar da ita nan ta wartsake daga baccin da take yi jin ya ajiyeta,dan bude idonta tayi kadan nan ta hangoshi yana kurbar coffee daga tsayen da yake rike da kugunshi da hannunshi guda daya cigaba tayi da kallonsa har ya shanye,sai da taga ya ajiye yana kokarin juyowa sannan tayi gaggawar rufe idanuwanta, murmushi yayi yarage hasken dakin sannan ya nufi kan gadon, Kamar yadda ta tsammata yauma bai saurara mata ba ko kadan dan gaba daya gajiyarshi akanta ya sauketa,tasha kuka har muryarta ta dashe,kamar yadda take zargin da biyu yake shan coffee din nan da alama zarginta yazama gaskiya dan da asubah ma sai da yafita da kansa yaje kitchen ya hado yazo yasha tana kallonsa,rage mata yayi itama yamika mata wai tasha, girgiza kai tayi idanuwanta har sun tara kwalla, "Kisha zakiji dama dama...." Tana kokarin sake yin musu yaje yakai cup din bakinta nan ta tashi tasha duk da bawai so take yiba. Dana sanin shan coffee din ta tsinci kanta tanayi domin wahalar yanzu har tafi ta daren jiya sai dai shi uban gayyar taga kamar yanzun yafi zakewa fiye da jiyan, jikinta duk yayi tsami ahaka bacci ya dauketa tana rungume ajikinsa yana dan jijjigata alamun lallabawa. Misalin karfe 9 nasafe ta samu nasarar tashi daga daddadan baccin da ya dauketa mai cikeda hutu domin ko babu komai jikinta da ruhinta sun dan huta,idanuwanta ne suka sauka akan Khalil wanda ke tsaye gaban mirror yayi crossing legs dinsa yaharde hannuwanshi a kirjinsa sanye cikin farar t shirt da farin wando,yanda take kallonshi haka shima yake kallonta kamar zai hadiyeta, "Good morning" Taji yafada ahankali cikin muryarshi mai sanyi da taushi gamida zaki haka kuma mai cikeda dadin saurare,kai kawai ta daga masa tasoma yunkurin sauka daga kan gadon nashi ma'abocin girma da laushi, "Hey..... Where are you going?" "Bedroom dina zan tafi" "No,kwanta ki huta anan" Matsawa kusa da ita yayi ya tarairayeta ya sake kwantar da ita sannan yaja duvet ya rufeta, abayanta tajishi shima ya kwanta sannu ahankali ya rungume ta bayan yakai fuskarshi saman tata,irin yanda ya kanannadeta ya kanainayeta ko kwakkwaran motsi ta gagara yi,jin dumin jikinshi da sanyin kamshinsa da ya cika mata hanci bata san lokacin da bacci ya sake d'aukarta ba,shima baccin yayi cikin farin ciki da nutsuwa har zuwa 12 na rana,itace tafara farkawa har lokacin tana kanannade cikin jikinsa sai faman sharar baccinsa yake yi,dan murmushi tayi wanda ita kadai tasan dalilin yinsa sannan ahankali ta daga ido ta kalleshi domin yanzu suna kallon junane,idonshi taga shima yabude wad'anda ke cike da bacci da ido yake tambayar ta menene? Kai ta girgiza masa hakan yabashi damar sake matseta ajikinsa yana shirin komawa wani baccin, "Uncle yunwa....." Bude idonshi yayi ya kalleta babu shiri ta dauke nata idon, Dan sakinta yayi daga rikon da yayi mata hakan yabata damar tashi duk kunya ta cikata dan dakyar take iya kallonshi, ahankali ta sauka daga kan gadon tafita ta nufi sashenta,ada babu abinda take buri kamar zuwan wannan lokaci sai gashi yazo yanzu kuma tana fatan samun rangwame,wanka tashiga tafara yi sannan bayan tafito batare da ta ko shirya ba ta nufi kitchen taje ta hada tea tafara sha sannan takoma bedroom dinta ta shirya sama sama saboda yunwar da takeji,riga da skirt ta saka na atamfa coffee colour sannan ta shafe jikinta da turare tafita duk jikinta babu karfi sosai, K'asa ta sauka taje ta zuba abinci sannan ta shiga wurin umma suka gaisa nan umman ke bata labarin mutumin nata Aryan wanda saida yagama casa rigamarsa sannan ya tafi makaranta,dariya Hanan keyi har tagama karyawa sannan tafita ta nufi dining table, Khalil ta shiryawa nasa breakfast din kan wani babban faranti dan tasan shima da wahala idan ya karya,kinkima tayi ta nufi sama, lokacin da ta shiga baya cikin dakin da alama wanka yashiga,ajiye masa tayi akan center table tana kokarin fita yafito, "Ina zaki? Zo..." Ahankali tajuyo bayan tayi kasa da kanta ta nufeshi,zama yayi gefen gado sannan yakamo hannunta da nashi, "Dauko min cream din can na shafa...." Asanyaye ta karasa gaban mirror ta dauko ta dawo batare da tasake kallonsa ba saboda iya farin wandone ajikinsa iya rabin cinyarsa, hannunta yasake kamawa sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa, "Yaufa muna da baki amma kinsa na manta...." Ya karasa maganar yana kallon agogon dake ajiye kan bedside drawer, dan kallonsa tayi jin abinda yace wai itace tasa yamanta shi dai yasa,jin ana kiran sallar azahar yasashi tashi domin shiryawa dama ita kam tajima tana neman hanyar guduwa hakan yabata damar tserewa, Cikin kwanaki biyu kacal har Hanan ta sauya,duk da ta rame amma hakan bai hana fatarta yin fresh ba dan har wani sulbi take yi tana sheki gefe daya kuma ga fargaba da ladama dake sake tsurar da ita tana faman karewa kamar kudin guzuri kana ganinta kaga amarya domin tayi wani irin kyau na musamman, Yau dai takama ranar juma'a kuma yau Khalil yace mata su abbanta zasu zo shiyasa tun bayan fitar Khalil din ta shiga kitchen ta dorawa su abba girki,misalin karfe 1 na rana suka karaso shida yaya shamsu,murna wurin Hanan ba a magana nan ta shiga gabatar musu da kayan motsa baki da abinci, Tana tare dasu suna gaisawa Abba nasanar da ita dalilin zuwansu Khalil yakaraso wannan dalilinne ma yasa bata gama jin abinda Abba keson sanar da itaba. Ita dai ta lura tsakanin Khalil da abbanta akwai aminci mai karfi domin yau dinma sai hira suke yi cikin raha da farin ciki kuma hatta abinci ma tare suka ci, Bayan sallar la'asar Khalil yace ta fito suyi sallama dasu abba zasu wuce,wasu hawaye ne suka fara kokarin zubo mata tun kafin ta karasa, "Uwar masu gida.... Mijinki yadage akan lallai lallai sai naje k'asar chairo anduba ni saboda wannan ciwon nawa duk da nace masa yabar kudinsa amma yadage..... Kici gaba da yiwa mijinki biyayya, Allah yayi muku albarka,tare da shamsuddini zamu tafi" "To Abba Allah yasa aje asa'a, Allah yabaka lafiya..." Hawaye ne suka cigaba da wanke mata fuska har su Abba suka tafi tare da Attahir drivern Khalil wanda yadauki Aryan suka tafi,duk abinda take yi Khalil na ganinta,ganin ta zauna kan kujera tana kuka yasashi karasowa hannunta yakamo ya hadata da jikinsa ahaka yanufi sashensa da ita..................................✍? _Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/15/20, 3:50 PM - Ummi Tandama: 50 ***Tana rungume ajikinsa har cikin falonshi wanda ya wadatu da sansanyan kamshi mai dadi, Zama yayi kan kujera ya zaunar da ita ajikinsa yana kallonta, "Wannan kukan na menene.....? Meyasa wai bakya girma da kuka ne?" Jin abinda yace yasata sake bare baki taci gaba da kukanta,kukan ne ya tsaya cak sakamakon harshensa da taji kan fuskarta yana kokarin lashe hawayen dake gudana kan fuskarta, cigaba yayi da lashe mata hawayen daga karshe ya tsaya akan dan kyakkyawan bakinta dake karawa fuskarta kyau da annuri, Sun jima kadan aduniyar masoya mai cike da tsantsar so,kulawa da kuma farin ciki marar yankewa,dago lumsassun idanuwanshi yayi ya kalli nata idanuwan dake lumshe tayi luff tana amsar sakonnin da yake kokarin bata, hannunshi cikin rigarta yafurta, "Tashi kije ki hado min coffee....." Bubu shiri ta bude idonta,hada ido sukayi ta mayar da nata ta rufe tana makale masa kafada alamun A'a, murmushi yayi yashafi kanta, "Yaushe kika fara kiwa?" Shiru tayi bata ce komai ba,saida ya tabbatar ta saki zuciyarta kukan yatafi sannan yafita,ita kam cigaba da kwanciyar ta tayi har tsawon wani lokaci,saima da su Aryan suka dawo ne sannan ta samu ta tashi tabishi zuwa dakin kayan wasanshi wanda har aka kira magriba suna ciki bata saniba lokacin Khalil har yadawo yaje ya dauro alwala yashiga part dinta bai gansu ba,da yaje wurin umma shine take sanar dashi wai watakila suna garden ko kuma yaduba su dakin kayan wasan Aryan, Yana bude kofar dakin kuwa ya hango Aryan akan dokin wasanshi mai taya ita kuma tana zaune kan kekensa,ta bayanta ya lallaba yaje ya rufe mata ido,wani gwauron numfashi taja sannan cikin faduwar gaba tace, "Uncle...." Sakamakon kamshin turaren jikinsa da taji, "Baku san lokacin salla yayi bane? Wasan ya isa haka sai kuma gobe, Aryan zo mutafi salla..." Mikewa tayi daga kan keken babu zato taji ya hadata da jikinshi ta baya bayan yakamo waist dinta,kwacewa tayi ta gudu tafice daga cikin dakin, Alwala taje itama tayi tai salla duk mamakinsa yacika ruhinta lallai ashe shima Khalil dan yine amma shine take yimasa kallon salihi,miskili ma'abocin girman kai da dagawa koda yake duk wanda bai fahimceshi ba kallon da zaiyi masa kenan saboda shi ko magana bai fiya sakin baki yayita yinta ba komai atakaice yake fadarshi,wurin umma ta sauka wanda can ta iske Aryan umma nabashi tuwo, Bayan sallar ishah sashen Khalil suka shiga ita da Aryan,zaune suka sameshi da laptop akan cinyarshi ga kuma waya makale a kunnenshi yanayi, "Agogo sarkin aiki....." Ta fada acikin ranta,samun wuri tayi ta zauna idanuwanta akan TV amma jikinta na bata idanuwan Khalil akanta suke domin duk tajita atakure takasa sakewa,dan satar wurin da yake tayi nan taga yayi mata kyarr da ido ko kiftawa bayayi,amma koda suka hada ido sai ya basar,tun safe ya lura da ita bata sakin jikinta yanda yakamata sai wani dingishi dingishi take yi tana tafiya kamar wacce ke taka kaya, Sai bayan da yagama wayar sannan yamayar da hankalinsa kan Aryan wanda ke kokarin yimasa ta'adi ajikin laptop dinshi,tana jinsu bata tanka ba har tsawon wani lokaci ahaka bacci ya dauke Aryan yana kan cinyar Khalil, "Zo...." Taji yace idanuwanshi na kan system dinshi,kamar bata so haka ta tashi ta nufeshi tanata faman harararshi ta gefen ido saboda ita kadai tasan irin wahalar da yabata duk yabi ya raunatata, "Gani...." Daga kanshi yayi ya kalleta sannan ahankali yace, "Wai meke damunki ne naga kina yin komai sanyi sanyi.... Baki jin dadi ne?" Saida ta dan turo baki sannan tace, "Ni lafiyata kalau..." Murmushi yayi acikin zuciyarsa yace, "to za ayi min halin ne na rashin kunya?" Amma afili kuma sai yace, "To shikenan tunda lafiyar ki kalau" Aryan ta dauka ta fita,saida ta kaishi dakinsa ta kwantar dashi sannan ta wuce nata part din ta yi wanka da ruwan zafi sannan tazo ta shasshafa turare da humra masu kamshi sosai wadanda ke sanyawa zuciya nutsuwa,wata farar rigar bacci ta saka marar nauyi sannan ta dora dogon hijabi pink ta fita bayan ta dauki wayarta,ita kanta bata san dalilinta na zuwa sashensa ba amma dai haka kawai ta tsinci kanta da nufar sashen, Lokacin da ta shiga bedroom din nasa yana gefen gado kwance yana waya da sabon PA dinsa,katse wayar yayi sannan ya mika mata hannu,cike da kunya ta kama nasa nan yajata jikinsa, "Tashi ki kawo min coffee...." Makale kafada tayi kamar dazu, "Jikinane babu karfi,bacci kuma nake son inyi" Duk da taji abinda yace kin tashi tayi domin atsorace take dashi, "Ok ni bari naje da kaina..." Tun kafin ya karasa ta rikeshi gam gam ta yadda bazai iya tashi ba, "Nidinma banida ikon zuwa da kan nawa?" "Uhmm" tafada tana mai daga masa kai, "To shikenan kwanta kiyi bacci...." Kin kwanciyar tayi har saida ta tabbatar cewa dagaske shima baccin zaiyi, ajikinsa ya rungume ta tsantsan yana shakar kamshinta. Hakace taci gaba da faruwa duk Hanan tabi ta sakawa ranta tsoro da fargaba wannan dalilinne yasa har gobe bata dan murmure ba gaba daya ma ji take yi kamar ta tafi gidansu ta huta amma abun haushi ranar da Khalil yasa aka kaita kanon ma wuni guda tayi ta dawo yaki yabarta ta kwana haka ta kwana tanata yimasa buntsire buntsiren baki tunda tafi kowa sanin dalilin nashi na hanata ta kwana, Bayan zuwanta kano da kwana biyu suka tafi gombe gaba dayansu saboda bikin saukar alqur'ani da zasu halarta na su Sarah,tunda sukaje hajiya ta sake jan Hanan ajikinta domin ta sake karewa amma kuma tayi kyau ba laifi,ranar walimar kuwa har anty maamy Hanan tagani amma ko gaisawa basuyi ba saboda suna zazzaune su uku da Lubnah da Muneerat da anty maamy tazo sai kawai ta tsallake Hanan ta gaggaisa da sauran tabe baki Hanan tayi aranta taje aje dai tunda ba aurar mata miji ba, Washe gari khalil yace su shirya zasu koma nan hajiya tace A'a yaje shi kadai su Hanan yabarsu su dan huta tunda ba zuwa suke yiba sai ta kama,badan yasoba haka yasa Aryan agaba suka tafi saboda shi yana zuwa makaranta, Hanan kam murna tarinka yi har acikin zuciyarta dan ko babu komai zata huta da fitinar Khalil, Tun bayan tafiyar su hajiya ta maida hankali wurin kulawa da Hanan tana sake gyara ta ta hanyar sawa ahado mata tukudi na musamman domin wannan ramar tata bata yiwa hajiya dadi, kullum suna waya da Khalil da Aryan wanda gidan sam baya yimusu dadi saboda rashinta, Satinta biyu Khalil yazo daurin aure kuma yasamu ya karaso gidan lokacin da yaga Hanan sai yaga ta dan murmure ba kamar daba, murmushi yayi ya shafi kumatunta yana fadin, "Yar gidan hajiya me hajiyan take baki ne kike cika haka?" "Bacci" Wani murmushin yasake yi, "Bacci take barinki kiyi? Wato nan kuma dani akeyi kenan ana nuna min nine ke hanaki bacci ko? Zaki dawone" Makale kafada tayi tana cewa saita fadawa hajiya,ranar ma duk yanda yaso sutafi tare da ita sukoma Abuja hajiya cewa tayi yabarta ta kara kwana biyu,bai damuba saboda shi kadai yasan shirin da yakeyi. Bayan tafiyar shi da kwana uku yaturo driver yazo ya tafi da ita wai akwai inda zata rakashi,aranar da ta koma aka gama dukkan shirye shirye bayan sallar magriba driver yakaita airport wanda wannan shine karo nafarko da zata hau jirgin sama atarihin rayuwarta,gabanta sai dar dar yake,tana shiga taganshi tsaye yana jiranta sanye da kananan kaya jeans da t shirt,tare suka zauna ga kujerarshi ga tata yana rike da hannunta, "Yau kuma gudu ya kare ko? Zamuje inda babu hajiya ai sai muga ta karyar gudu" "Dan Allah kayi hakuri....." Tafada idanuwanta na cikowa da kwalla, "Ban hakura..." Kuka tafara yi hakan yabashi damar dan rungume ta kadan yana shafar bayanta babu bata lokaci bacci ya dauketa ba ita ta tashi ba saida jirginsu ya sauka, Yana rike da ita har cikin motar da zata sadasu da lafiyayyen hotel din da zasu sauka,ita kam yar kauye ta zama domin bata taba ganin hadadden birni makamancin wannan ba ko acikin mafarki kasa boye kauyancinta tayi har saida takaita ga tambayar shi lokacin motarsu na tsakiyar titi suna lilawa, "Uncle nan inane?" "Rome...... K'asar Italy" Lumshe idanuwanta tayi ta kwantar da kanta akafadarshi bayan ta makaleshi kamar tana jin tsoron kada wani ya kwace mata shi,basuyi wata doguwar tafiya ba suka isa hotel din da zasu sauka. Ayanda ta dan lura kamar yana mutukar son k'asar Italy domin yana yawan zuwa akai akai, Lokacin da suka shiga masaukinsu amutukar gajiye suke duk da cewa dai ba wani aiki suka yiba inbanda zama to amma zaman ma wani lokacin sai ahankali, Itace tafara shiga bathroom domin yin wanka shikuma yana zaune yana duba wayarshi wacce take akashe tun bayan shigarshi jirgi sai yanzu ya kunna,sak'onni ne rututu suketa kokawar shigowa har har Hanan tafito kasancewar ba wani jimawa tayi ba kawai ta dan watsa ruwane ajikinta gashi tana fashin salla, Yana zaune inda ta tafi tabarshi ta bude trolley bag dinta ta ciro pad da pant,dan daga kai yayi ya kalleta ganin pad din dake hannunta yasashi dan tsuke fuska,dan karamin tsaki yaja sannan ya ajiye wayoyinshi yawuce bathroom yana wani ciccin magani, Kafin yafito ta samu ta shirya agaugauce tana kokarin saka night gown yafito saida ya harareta sannan taji yace, "Karki saka wannan rigar baccin bana bukata...." Daga haka yawuce gaban kayansa yabarta tsaye rike da riga ahannu, kayan baccinsa ya dauka zai saka hakan yasata juyawa tafita zuwa falo ta nemi wuri ta zauna ita bata saka rigarba sannan kuma ita bata ajiye ba, Shi kam bayan ya gama shiryawa cikin fararen kayan baccinsa sallolin dake kansa yasoma gabatarwa,yana cikin sallar Hanan tashigo cikin dakin fuskarta awani rakwarkwabe kamar zata fashe da kuka,gefen gado tasamu ta zauna har lokacin tana rike da rigarta ahannu,tana nan zaune tana dan gyangyadi ya idar da sallar baiyi mata magana ba yatashi yafita mintuna kadan yadawo dauke da abinci, "Sauko kici abinci...." Batare da tayi musu ba ta sauka ta zauna suka fara cin abincin sai wani shasshan kamshi yake yi domin shi duk zatonshi Allah ya amshi addu'ar shi tasamu juna biyu tun a first night ashe da sauranshi, Shine yafara tashi sannan yahaye gado ya bararraje yana latsa wayar shi ahaka itama tagama ta zauna saman gadon adan darare kamar mai jin tsoron wani abu, hannu yamika mata kamar koda yaushe takama sannan yajata jikinsa ya rungume cikin sanyin murya taji yana cemata, "Tunda ga duvet yau bana bukatar wannan rigar baccin taki mai takura mutum......." Ita kam ji tayi kamar ta nutse saboda tsananin kunyarshi,wai meyasa shi baya jin nauyinta ne? Har yagama rashin kunyarsa ita dai bata motsa ba haka idanuwanta ma bata budesu ba gashi inbanda bacci babu abinda take bukata amma koda tayi korafi sai cewa yayi ai yanzu lokacinsa ne ba lokacin bacci ba. *** Kimanin watanni bakwai kenan da bikin mujahid da sumayya wacce yanzu haka take dauke da cikinta dan kimanin watanni bakwai din kuma tuni har ya bayyana tunda jimawa, Zaune take afalo tana gogewa mujahid k'ananan kayanshi gefe daya kuma tana kallon tashar dake haska finanan turanci inda take kallon wani kayataccen Nigerian film mai suna the perfect couples,ahankali taga yabude kofa yashigo,musayar murmushi suka yiwa junansu sannan yazo ya dan rungumeta kadan ta bayanta, "Matar alkhairi sannu da kokari....." "Sannu da zuwa mijin arziki" Dariya yayi yashafi cikinta, "Ya babynmu?" "Baby na lafiya dazun nan tagama motsi" Murmushi yayi yai zaman dirsham shima kamar yadda yaga tayi sannan ya karbi gugar yaci gaba dayi, "Kin san wani abu? Har yanzu inata nazarin sunan da yadace musakawa babynmu....." "Wanne kake ganin zamu saka mata" Kashe iron din yayi ya zuba mata ido, "Akwai sunan da najima inada burin sakawa 'yata (Sa'adatu Hanan)" Murmushi tayi ta gyara zamanta sannan ta kalleshi tana murmushi, "To yanzun me zai hana ka cika wannan burin naka kayi mata takwara?" "A'a ni tsorona kar kice da biyu nasaka sunan Hanan" "Kaji yaya mujahid da wani magana,to ni ina ruwana dan kasawa yarka duk sunan da kayi niyya? Ni ai nadaina kishi da Hanan" Murmushi yayi yasake rungumeta yana saka mata albarka tare da addu'ar sauka lafiya. *** Washe gari Hanan bata tashi daga bacci da wuriba kasancewar ga uwar gajiyar da take addabarta sannan ga rashin bacci akan lokaci wannan dalilinne yasa har k'arfe 9 nasafe takai tana bacci batare da Khalil ya tasheta ba sanin ba salla zatayi ba, ahankali take bude idonta kamar bata so ko mai tsoron ganin wani abu tayi luff cikin bargo,bata ga Khalil ba hakan yabata damar cigaba da kalle kallenta acikin d'akin ahaka har idanuwanta suka sauka akan tamfatsetsen mirror din dake cikin dakin, _Good morning beautiful!_ Abinda taga anrubuta kenan baro baro ajikin mirror din da red din janbaki, murmushi tayi ta tashi zaune tashiga wanka tana sake yaba kyau da haduwar hotel din wanda Allah ne kadai yasan adadin kudin da Khalil din yabiya,cikin farin ciki da annashuwa tayi wanka tafito tazo ta shirya cikin wata bakar riga iya gwiwa,tana kokarin fesa turare yashigo dauke da breakfast a hannunshi,tsayawa yayi kawai yana kallonta saboda ba karamin kyau tayiba, Kayan hannunshi ta karba sannan ta danyi dage ta yiwa kumatunsa kiss, "Good morning Uncle" Rungumeta yayi yana shafar kumatunta, "Morning mai period,how was your night?" Murmushi tayi ta lumshe idanuwanta saboda ta lura period dinnan nata ya tsaya masa arai kuma yana jin haushinsa dan tun jiya yaketa faman yin tsaki da yaga pad,zaunar da ita yayi kan cinyarsa sukayi breakfast daga nan kwanciya suka sake yi har lokacin sallar azahar,zuwa yamma taci gayunta cikin jar doguwar gown mai stones tayi rolling suka fita,shi kansa Khalil din shima kananan kaya yasaka da black face ya sakaye fuskarshi,yana rike da hannunta suka rinka zuwa wurare daban daban na shakatawa da debe kewa sunata yin video call da Aryan,gaskiya k'asar tayi mata kyau sannan ta burgeta domin birnine na can kololuwar karshe basu suka koma gida ba sai karfe dayan dare amutukar gajiye. Ai ita kam kasa tabuka abun arziki tayi duk da taga shi lamarin nasa ba sauki,hannayenta ya kama gaba daya yakai jikinsa cikin rada yake cemata, "Ke yar kauye ce......, Kamar kina tsoron tabani,ko har yanzu kunyar ce bata gama sakinki ba? Kin barni inata wahala ni kadai bayan ba wani abu zan samuba...... Kema kiyi wani abu" Ahankali hudubar su anty badi'a tafara dawo mata cikin kwakwalwarta tiryan tiryan wacce suka yimata a gombe lokacin da za akawo ta,ji tayi kamar yanzu ne suke yimata amma kuma bata san ta yadda zata tunkareshi da wannan babban lamari ba saboda wallahi tana bala'in jin kunya ga tsoro wanda bata san ko na menene ba, "Wai ke waya fada miki idan akazo wannan bangaren ana jin kunya? Idan haka zaki rinka barina babu kulawa,babu tarairaya sai dai kisaka ni gaba da kuka muna komawa gida zanyi aure......" Ai tana jin haka bata san lokacin da ta bude idanuwanta ta kalleshi ba, "Aure uncle......?" Ta tambayeshi bakinta har yana rawa,juyawa yayi yai rigingine batare da ya kalleta ba yace, "Yes aure...... Kuma bazawara zan aura wacce tasan aure tasan yanda zata kula dani" Shiru tayi tana kallonsa nan zuciyarta tasoma bugawa da wani irin karfi wanda tafi kyautata zaton na tsantsar kishine,gaskiya tana da zafin kishi na ajin karshe akansa,shima sanin tana da zafin kishin ne yasashi fadin haka ko wai zata nutsu ta gyara tunda yaga abin nata kamar harda sakarci, Nutsuwa tayi tana saurarar fadan da zuciyarta keyi mata "kema hanan kina abu kamar wawiya, tunda har yafito ya nuna miki ga abinda yake so meyasa bazaki daure ki cije kiyi masa ba? Gashi nan ai kuna komawa gida yace zaiyi aure waya sanima ko mijin anty maamy ya mutu ya aureta shikenan kin zama yar kallo...." Wata kwalla taji ta zubo mata nan ta share kwallar sannan cikin sanyin murya tace, "Uncle..... Kayi hakuri bazan sakeba" Shiru taji yayi mata cikin dar dar taja jikinta zuwa gareshi ta rungumeshi tare da yimasa wani lafiyayyen kiss a kumatunsa irin yanda yake yimata, rungume ta taji yayi sannan cikin farin ciki taji yace, "Yawwa to ko kefa,amma da kamar ba yar makaranta ba..... Ai ko a school ana practical ko?" Kai ta daga masa, "To kema lokacin da zaki fara practicing abubuwan da na koya miki yayi.... Don't be shy" "Kai Abban Aryan akwai rashin ta ido...." Ta fada acikin zuciyarta,kamar mai shirin taba wutar lantarki haka take tabashi awani d'arare,haka dai da taimakon sa da komai ta dan tabuka abun arziki, rungume ta yayi yana cemata har yanzu batayi wani abun azo ayaba mata ba,yana shafar kanta har bacci ya dauketa shi kam tashi yayi ya tsaftace jikinsa ya dan gabatar da sallolin nafilfili zuwa karfe 3 na dare yaje ya kwanta abayanta tare shiga cikin jikinta sosai. Tsabar gajiyar da tayi ai har gari yawaye bata ko juya ba,shima Khalil din yau saida yamakara sallar asubah. Ta rigashi tashi,bayan tafito daga wanka tana shiryawa shima yafarka,wankan yashiga shima yayi yafito rike da dan karamin towel daga shi sai gajeren wando, Zaune yaganta tana kokarin daure gashinta ta saka wata yeluwar riga mai budadden kirji amma dan kauyanci sai ta saka mayafi karami ta rufe kirjin nata, zama yayi gefen gado yace, "Zo kibani wannan jakar....." Tana zuwa ya yaye mayafin yana fadin, "Ba kiji abinda nafada miki jiya ba ko? Kina son nakara auren dai kenan....." Girgiza kai tayi tana bata fuska,kan cinyarsa yadorata sannan cikin taushin murya yace, "Zan auro yar birni tunda ke yar kauye ce,zan auro wacce ta iya soyayya,wacce zata rinka barmin surarta abude koda yaushe ina gani ba irinki da kike rufewa ba...." "Nadaina....." Ta fada tana turo baki,shiru yayi mata yamaida kallonsa kan kirjinta wanda ya bayyana ta saman rigar da ta saka, "Kaji uncle...." Kunya ce ta kamata lokacin da ta fuskanci abinda yake kallo,babu yanda ta iya haka ta daure ta biyeshi kafin daga bisani sukayi breakfast bayan yayi sallar azahar suka fita. Yauma kamar jiya sunsha yawace yawace dan basu suka dawo ba sai karfe 1:30 nadare, kuma yau dinma bai barta tasamu bacci ba sai wurin karfe 3 saura kwata shiyasa washe gari babu inda suka je a masauki suka wuni suna shan baccinsu sai da daddare ne suka samu dan fita gaban harabar hotel din suka mike kafa suka dawo, Hanan dai tana jin dadin kasar saboda ko ina ya hadu ashe shiyasa Khalil idan yazo yakoma suke ganin ya canja yayi kyau kamar wanda aka canjawa halitta ko fata. Yau kam tun asubah suka fita tana sanye cikin purple din Dubai gown ta dan yafa mayafi karami akanta kafarta tasaka takalmi toms shima purple sai yar karamar side bag wacce ta rataya hannunta cikin na Khalil wanda yake sanye da fararen jeans da t shirt fuskarsa boye cikin bakin gilashin ido mai dan girma,kai masha Allah dan kasa boye farin cikinta tayi sai daukarsu selfie take ta faman yi har suka shiga cikin wani kyakkyawan jirgin ruwa mai daukar akalla mutane goma,tana zaune gefenshi ga kugunta ga nasa ya rike waist dinta da hannayensa kanta bisa kafadarshi. Sunyi doguwar tafiya har gari ya waye rana ta dan fito duk da bawai ranar mai kwal dinnan bace,awani hamshakin katafaren bakin ruwa suka sauka gaba daya ruwan kalarsa blue ce mai sheki da daukar ido sai ambaliya yake yi ga mutane tsilla tsilla suna hada hadarsu,kamata Khalil yayi yafito da ita yana rike da hannunta, "Wai uncle ta ina duk kasan wadannan wuraren.....?" "Tun ina yaro nake mafarkin zuwa wadannan manyan biranen na duniya tare da wata cute baby....." Wani kyakkyawan masauki wanda aka gina akan tsauni atsakiyar ruwan suka je can Hanan tayita baje idanuwa tana kallo gaba daya takasa bambance tsakanin can Rome inda suka sauka da nan Florence ina ne yafi wani haduwa, Gaskiya Khalil yayi kuma ya hadu domin ya zagaya da ita taga wurare ta karkashe kwarkwatar idonta sosai kuma ayanda ta lura shima dan harka ne wato dan soyayya ma'abocin son ashana da iyali,basu suka koma Rome ba sai dab da asubah,ko ba afada mata ba tasan gogan nata mutum ne mai son yawace yawace da harkar bude ido saboda ko agida Nigeria ba zama yake ba bare nan da yakeda yancin zuwa duk inda yake so. Kwanansu biyu adaki babu inda suke zuwa tun bayan dawowarsu daga Florence sai dai suci abinci susha soyayya suyi waya da yan gida, Yammacin yau yagama shirya musu kayansu tsaf suka kara gaba zuwa birnin Venice dake nan k'asar ta Italy, Hanan duk da tana cikin murna da farin cikin zuwa wuraren da bata taba mafarkin zuwa ba amma adarare take da Khalil saboda yau zata samu tsarki duk da kwana biyu tasake dashi tunda suna zaune daki daya zasu kwana tare zasu tashi tare su wuni tare, Yanzunma awani dan karamin hadadden hotel suka sauka,bayan sunci abinci sunyi salla Khalil yafita shi kadai yace ita ta kwanta tayi bacci,baccinta kuwa tasha kamar yadda yace,zuwa magriba yadawo hannunshi rike da wayarshi suna yin video call da Aryan,karbar wayar tayi suna yiwa juna dariya itada Aryan ko dariyar ta mecece oho,har Khalil yayi wanka yafito yayi salla basu gama wayar ba da zasu ci abincine yakarbe wayarshi ya kashe. Shiru tayi tai jugum tana jimamin wannan lamari Khalil yace tare zasu yi wanka saboda ya kyalla ido yaganta tana yin salla, tunaninta ne yatsaya daidai lokacin da yashigo cikin dakin kasa tayi da idonta lokacin da taga yana kokarin rage kayan jikinsa, "Oya muje...." Tashi tayi kamar kazar da kwai ya fashewa aciki tawuce gaba yana biye da ita abaya har cikin bathroom din wanda ya hadu karshen haduwa,janta yayi cikin ruwa bayan ya warware towel din jikinta,tun tana jin kunya har ta warware ta saki jiki,daman yau kam ita kanta tasan babu daga kafa domin kamar Khalil baida hakuri da kawaici a wannan bangaren,duk da yau taji lamarin da sauki sai dai amma akwai tarin gajiya da tarin bacci wadanda suka hadu suka yimata rubdugu shiyasa ta wuni tana bacci washe garin ranar. Zamansu a Venice yafi na ko ina tsaya mata arai domin acan ne suka fi kulawa da juna da tattala juna tunda yanzu tafi sakewa dashi wannan kunyar tata da Khalil ke kira da kauyanci ta dan rageta,kayan shan iska take sakawa na wulakanci suyi ta shanawarsu da daddare kuwa sallama take yi da kowacce irin suttura komai kankantarta domin saukakawa gwarzon nata, Tunda Khalil yafada mata saura kwana biyu su koma gida duk take jin babu dadi kamar kar su tafi saboda yanzu tayi sabo dashi ta shaku dashi yanzu suna komawa gida zai fara yimata wahalar gani sai dare yau yana kano gobe yana bauchi,zama yayi kusa da ita yana murmushi shigowar shi kenan, "Hey...... Meyake damunki ne?" Shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka, "Nasan idan muka koma gida zan daina ganinka koda yaushe......" Murmushi yayi yakama hannunta yana matsawa ahankali, "Kekuma kina son ganina koda yaushe ko?" Kai ta daga masa kwalla na shirin sauko mata,hadata yayi da jikinsa yana bubbuga bayanta alamar kulawa da rarrashi, ahankali ya zaro wani dan karamin akwati daga cikin aljihunsa ya bude yaciro dan karamin zoben gold mai mutukar kyau ya kama yatsanta,saida yafara zira zoben cikin yatsanta na tsakiya sannan ta dago tana kallonsa cikin farin ciki tasake rungume shi tana cewa, "Thank you uncle...." "I love.....you....." Yafada kamar mai koyon magana ai duk sai taji ta rude jin abinda yafito daga bakinsa kamar cikin mafarki,fuskarshi yasake mika mata taci gaba da yimasa ruwan kiss tako ina. Ranar alhamis da yamma suka sauka a Nigeria,tsayawa kawai Khalil yayi yana kallon Hanan da Aryan lokacin da suka rukunkume juna suna murna,kamar yadda Hanan ta tsammata washe gari Khalil yasoma tafiye tafiyen nasa da yasaba kullum baya dawowa gidan sai dare wani lokacin ma sai tayi bacci. Wannan watanma da yaga tana period sai duk yabi ya bata rai ya tsuke fuska daga karshe sai cewa yayi umarah zai tura hajiya da umma barira da Aryan suje su tayashi da addu'a tasamu ciki tunda har yanzu yaji shiru,zaro ido Hanan tayi sannan cikin mamaki tace, "Kai uncle dan rashin kunya hajiyan zaka fadawa haka?" "Ni ai babu maganar da bamayi da hajiya,barima kiga..." Ganin zai dauki wayarshi yasata rigashi dauka ta gudu,silifas dinshi yasaka yabi bayanta har zuwa sashenta,tsaye ya sameta a corridor tana yimasa bincike awayar, "Duk abinda kika gani babu ruwana bincikenki ne yaja miki dan nayi budurwa jiya" Murmushi tayi tai tsalle ta dale bayansa tana tambayar shi wai ina nura PA saboda kwana biyu bata ganinsa,riketa yayi Sosai abayanshi sannan yabata amsa, "Na koreshi tun tuni......" "Saboda me?" "Saboda naga yana kokarin shiga gonata......." "To Uncle kuma basai kabarshi ba iyakaci fa idan yagama nomanshi ya....." Bata karasa ba taji ya birkitota tadawo gaba, makalkale shi tayi da kafafuwanta idonta cikin nashi yake kallonta, "Kin kuwa san abinda kike fada? Shine fa wannan da yarinka yimiki text massage dinnan,harda sake sabon layi saboda yazaci bazan ganeshi ba....." Shiru tayi aranta tana cewa lallai kam biri yayi kama da mutum ashe shiyasa idan yashigo cikin gidan koda yaushe idonshi akanta. Kamar yadda Khalil yace saida yatura hajiya da umma barira umarah amma banda Aryan saboda shi lokacin suna yin exams a school shiyasa Khalil yajira sai bayan yagama,suna yin hutu kuwa suka tafi tasu umarar shida Aryan da Hanan,bayan sun gama suka nufi k'asar Scotland daga can kuma suka wuce Australia, Hanan kam taga manya manyan biranen duniya kuma tasha tarairaya wurin Khalil,tun daga can take jin jikinta yana wani canja mata bata jinsa daidai amma dai bata fadawa Khalil ba har suka dawo gida Nigeria nan abu yaci gaba da karuwa kasala da ciwon jiki ga kuma yawan bacci dake damunta ganin duk kuzarinta ya ragu yasa Khalil kiran Dr Al'amin,test din farko da Dr yayi mata ya fahimci tana da juna biyu, Khalil ji yayi kamar ya goyata har Aryan yarinka fadawa wai yakusa yasamu sister ko brother,ita kam kyautar wata dambasheshiyar sarkar diamond yabata kuma tun daga ranar kulawar da yake bata ta karu lallaba ta yake yi kamar kwai. Koda cikin yagirma kuwa ai Hanan daina fita tayi wai ita kunya take ji kaza da kaza dariya Khalil yarinka yimata shikam yawonsa bashi nan bashi can yau yana wannan kasa gobe yana waccan...................................✍? _Wannan littafin na kudine game bukatar siya sai atura 200 ta account din Aisha Ibrahim, 3112877210 first bank,sai atura shaidar biya ta WhatsApp number dina 07044644433 ko kuma atura recharge card da shaidar biya ta number din._ *_Ummi Shatu_*👌🏻 8/17/20, 9:07 PM - Ummi Tandama: *Littafina na kudine ga duk wacce keda bukatar karantawa saita turo naira 200 ta account dina 3112877210 Aishatu Ibrahim first bank,sai aturo shaidar biya ta wannan number din 07044644433 ko kuma recharge card na MTN ko atuntubi marubuciyar kai tsaye ta wannan number din 07044644433* *51* ***Fad'ar irin kulawar da Khalil ke baiwa Hanan bata bakine ko kuma kauyanci domin yanzu ne tagane ainihin irin soyayyar da yake ikirarin yana yimata kuma hatta hotunan Ramlat da ada yake ajiye dasu akan drawer gefen gadon baccinsa ayanzu duk ya kwashesu ya adana a inda yadace, Hanan haihuwa ko yau ko gobe domin cikinta yagama tsufa kuma ya isa haihuwa,tunda ta tashi yau dai haka haka take jin jikinta amma da yake bata san takan abunba shiyasa bata kawo cewa haihuwa bace kuma dama jiya a sashen Khalil ta kwana shikuma sai shegen rashin hakuri duk da ga halin da take ciki lallabata yake yasha sha'aninsa, asubanci yayi yau yafita zaije kasar Ghana, Abinci ta zubo soyayyen dankali da farfesun hanta ta zauna kenan agefen kujera taji wani abu ya tsurkuneta haka dai ta daure ta cuccusa dankalin tasha ruwa nanfa taji ciwo kamar karuwa yakeyi kafin wani lokaci har ciwon ya tsananta,umma ta kira awaya babu bata lokaci suka tafi asibitin da take zuwa awo wato alkhairi clinic and maternity, Tun safe take nakuda amma har dare bata haihu ba, khalil yana can amma hankalinsa yana gida musamman ma da yakira hanan bai sameta ba wayar umma da Aryan kuma duk ba adauka idan yakira, daren ranar Hanan bata yi bacci ba saboda da ciwon nakudar ta kwana zuwa asuba ta haifo katon jaririnta sambalele,dakyar ta iya bacci saboda azabar da take ji atare da ita karshe ma saida aka hada da yimata allurar bacci,sai lokacin umma tasamu zarafin kiran yan uwa da abokan arziki ta sanar musu da haihuwar Hanan, ai tun aranar yan uwa suka yiwa garin Abuja cincirindo dan asibitin cika yayi taf da yan uwan Khalil da na Hanan shima Khalil adaren ranar yadawo, lokacin da yashiga d'akin tana kwance angama yimata karin ruwa tana bacci,goshinta yayi kissing ya shafi kumatunta sannan yafita cikeda farin ciki marar misaltuwa,ita Hanan bata san yanayi ba saboda baccine take yinsa kamar wata yar kwaya ga uban ciwon dake damunta wanda bai saketa ba har yanzu. Washe gari tunda sassafe Khalil yadawo asibitin shida Aryan,zuba musu Ido kawai tayi tana kallonsu saboda yadda suketa murna suna kwakwume da jaririn wanda Khalil yayiwa huduba da Muhammad Ayaan, Kwananta uku suka koma gida kuma aranar kaf yan gidansu suka zo kafatanin ilahirinsu dan harda mamaye,ganin girman jaririn yasa anty salaha cewa ai dole tasha wahala ji jariri kamar dan kwana arba'in? Ita dai bata ma magana dan ko zama saida dabara sakamakon irin uban dinkin da tasha,tafiya ma wannan ba son yinta take yiba sai ta zama dole, Lura da yanda take ciccije lips idan tana zaune ko tana tafiya Khalil yayi nan yasata agaba da tambayar menene matsalar? Turo baki tayi cikin shagwaba tace, "Nida aka dinkeni kamar bayan kwarya......" "Insha Allah anyi nafarko kuma anyi na karshe ai hakan bazata sake faruwa ba..." Jin abinda yace yasata yin watsi ma da maganar saboda duk tunaninta bazai iya yin abinda yafada ba bata san shi abinda yake nufi ba shine bazai sake barinta ta haihu a k'asar nan ba gara yafitar da ita k'asashen ketare koda kuwa tattalin arzikinsa zai kare. Haka dai akayi suna aka gama mai jego babu cikakkiyar lafiya,anty salaha da umma barira sune ke tare da ita suna kula da ita,bayan suna da kwana biyu taji kamar akwai matsala nan ta fadawa anty salaha babu shiri suka koma asibiti wani dinkin aka sake yimata domin wancan ya warware,da kuka suka dawo gida tana ta kuka ahaka Khalil yazo ya sameta. Zama yayi kusa da ita ya rungumota jikinsa yana rarrashinta, "Uncle zafi mutum kamar zai suma ko zai mutu ni wallahi bazan kara haihuwa ba ma......" "A'a sa'adah,wahala ai mai wucewa ce insha Allah bazaki sake shan wahala kamar wannan ba wurin haihuwa..... " Dakyar yasamu ya rarrasheta ta yi shiru ta daina kukan nan aka cigaba da lallaba ta su umma na kulawa da ita,shi kuwa jariri dayake yana samun abincinsa yana koshi nan da nan yasake zama kato dan ko Aryan baya iya daukarsa sai dai idan yana zaune abashi shi,itama mai jegon ba abarta abaya ba wurin murmurewa da sake kara samun kumari domin itama ta cika tayi kiba kamar ba itaba sai yanzu ta yarda da batun mutane da suke cewa kudi na gyara mutum haka duk muninka yana kara maka kyau,kafin arba'in tasamu ta warke tayi fess da ita amma duk da haka bata sakin jiki da khalil kuma shima baya takurawa saboda yana son ta huta sosai,kullum da daddare dai yana kasancewa dasu itada Aryan da Ayaan su raba dare a sashensa suna hira,anty salaha kuwa ganin Hanan ta warke yasata tattarawa ta tafi saboda tabar yara agida duk hankalinta yana garesu, Tunda anty salaha ta tafi kuma Hanan ta koma sashen Khalil da kwana itada jararinsu can suke tafiya suyi baccinsu cikin nutsuwa da kulawa domin ko tashin dare Ayaan yayi zaiyi rigima khalil ke daukarsa ya rarrasheshi. Watan Ayaan biyu Hanan ta shirya ta tafi gida kuma itace har gombe domin ziyara tayi ba kadanba saida tayi sati biyu taje nan taje can duk wasu danginta da na Khalil lungu da sako babu inda bata je ba takai Ayaan anganshi wanda kamarsu daya da Aryan saboda duk Khalil suka debo, Kafin ta baro gombe saida aka yimata kunshi da kitso sannan Zaid ya mayar da ita, lokacin da ta koma bata samu Khalil ba domin yatafi k'asar chairo wanda bata san dalili ba,gyara jikinta taci gaba dayi har izuwa ranar da zai dawo,bayan dawowarta da kwana biyu shima ya sauka amma office yawuce bai karaso gida ba sai dare, Kwalliya taci sosai cikin doguwar riga ta material tasha turare mai sanyin kamshi,yana dauke da Ayaan a kafadarsa wanda ya karbeshi hannun umma Aryan na biye dashi, A sashensa ya sameta tana shirya masa table ganin irin adon da ta caba yasashi yin murmushi ya nemi wuri ya zauna, "Sannu da zuwa uncle...." "Yawwa.... Irin wannan kwalliya haka? Ko anshirya karbata ne yau?" Murmushi tayi ta karasa kusa dasu, "Kai uncle....." "Ai tambaya nayi,kuma shiyasa nayi miki da yaren da Aryan bazai ganeba, anshirya karbata yau?" Kafada ta makale tace "A'a" "Karya kike yau dai dole akarbeni tunda ai anhuta kuma zafin haihuwar yatafi...." Dariya tayi ta mika hannu ta karbi Ayaan tana fadin, "Zo nan mubar uncle yaje ya shirya yazo yaci abinci..." Tare suka rankaya zuwa dakin nasa banda Aryan wanda yakoma wurin umma,ita ta taimaka masa yayi wanka sannan ya shirya cikin kayan shan iska saboda shi mutumne mai jin zafi gashi baida wata kiba ta azo agani amma sai jin zafi,falo suka koma ta bashi abinci yaci daga nan tatafi sashenta domin yin shirin bacci. Yau kam tayi shirin da Khalil bazai kirata da yar kauye ba itama yar birni ta zama domin rigar baccin da ta saka kadai ta isa tabbatar masa da haka kuma kalar da yafi murada ce wato fari, Yana zaune rike da wani littafi a hannunsa kishingide saman sofa acikin bedroom dinsa ta shiga,bayan ta kwantar da Ayaan ta nufeshi,acikin jikinsa ta zauna tana cire hijabin dake jikinta, "Wow....... Kinyi kyau" yafada yana shafa kitson kanta,tun anan labari yasoma canjawa har suka dangana ga gadon barcinshi amma kuma yau sam ta lura kamar baida kuzari kai kamar ma dan ita yake jagorantar tafiyar bawai dan kanshi ba, "Uncle ko inkawo maka coffee din ne?" "No" Ita dai yau ganinsa take yi kamar wani marar lafiya kuma duk zumudinsa yau kam jikinsa asanyaye yake, Bayan wani dogon lokaci tayi bacci ta farka ta ganshi zaune ya tallafe kumatunsa da hannunshi abin yayi mutukar bata mamaki, cike da bacci ta tashi zaune, "Uncle wai lafiya kuwa? Meke damunka ne?" Kamata yayi suka kwanta ya kwantar da kanshi a kirjinta bayan ya rungume ta, "Babu abinda ke damuna,muyi bacci..." "A'a uncle wallahi da akwai abinda ke damunka..." "Babu" Jin yaki fada mata yasata tureshi ta mike zata bar dakin tana masifa, "Tunda baka daukeni abokiyar shawararka ba,kuma baka kallona a abokiyar tayaka farin ciki ko sabanin haka...." Tashi yayi ya rikota dakyar ya kwantar da ita tana ta zizzillewa,binta yayi ya saka mata nauyinsa ta yadda bazata iya tashiba, "Nifa bazan kwana adakin nanba...." Dariya yayi sannan ya shafi kumatunta, "Kwana kuma na nawa sa'adah? Jiya kam ai kin kwana saura yau kuma..." "To ba ka ki ka fada min damuwarka ba" "Sa'adah banda lafiya......... Insha Allah zan koma chairo next month zasuyi min surgery....." Tashi zaune tayi yunkurin yi ya hanata babu bata lokaci tafara hawaye tana ta tambayar rashin lafiyar dake damunsa amma yaki fada kawai dai yace mata wai wani abune shima bai san menene ba zasu yimasa aiki,dakyar ya lallaba ta suka koma bacci,tun daga ranar hankalinta yaki kwanciya duk tabi ta damu dan gani takeyi kamar mutuwa zaiyi yabarta,shima kuma komai nashi cikin sanyin jiki yake gudanar dashi dan daga karshe ma cewa yayi zaiyi resigning yabar aiki hajiya ta hanashi,haka dai yaci gaba da fita aiki kusan kullum yana fama da zazzabi mai zafi, Lokacin da zai koma chairo din tare da Hanan suka tafi kuma aranar da suka je aranar aka yimasa aikin,yasha wahala ba kadan ba amma kuma anyi cikin nasara nan tayita zaman jinyarsa har yafara samun lafiya,kullum cikin amsa wayar yan uwa daga gida Nigeria take,satinsu uku acan ya warke garau kuma yaji sauki sai lokacin yake sanar da ita wai cancer ce ta kamashi amma bata girmama ba ita aka cire masa, Gida suka koma yaci gaba da al'amuransa gefe daya kuma yana kulawa da iyalinsa, itama dagewa tayi tana kulawa dashi domin bata son wata ta kwace mata shi bugu da kari kuma mijin matacciya take aure idan batayi da gaske ba zaiyita kewar matarsa da tunaninta, abinda bata saniba shi yanzu baida lokacin kara aure ko kula mace awaje saboda atsarinshi mace guda daya ta isheshi rayuwa. Ganin wanda takeyi dominsa baya ta kowacce mace sai iya ita kadai yasata sakin jikinta nan tafara kasuwancinta tabude restaurant da boutique mai hadeda wurin saloon da gyaran jiki da kwalliya duk na manyan mata,idan Khalil ya tsareta da tambayar wai me zatayi da kudi sai tayi dariya tace abunda akeyi dasu nan kuwa iyayenta take taimakawa wanda bata da kamarsu kuma duk da Khalil na iya bakin kokarinsa amma itama gara tayi nata haka kuma sauran yan uwa da abokan arziki ai basai tazo tana cemasa bani bani ba lokuta da dama da nata take yin amfani. Rana tsaka kuma Khalil ya daukesu ya mayar dasu k'asar Paris saboda karatun yaransa itama ba abarta abaya ba ta fada tata makarantar inda taci gaba da karatu kuma su basu cika zuwa bama sai shine ke zuwa,amma wannan karon saida yayi 3 months bai jeba,kuka Hanan tasaka masa awaya washe garin ranar sai gashi yazo lokacin dama har ta yaye Ayaan, A bedroom dinta ya sauka tunda dama 2 bedrooms ne daya nata daya nasu Aryan, "Wai sai yaushe za abawa su Aryan kani ne..." "Hum um babu rana,garinsa da nisa...." "Garinsa akusa yake ai kuwa saboda saida nataro gajiya ta gaba daya sannan nataho" Turo baki tayi tana harararshi, "Muda ka manta ma damu kaje kayi zamanka...." "No,ni na isa mantawa da zuciyata......... Zo kiji wani abu" Janyota yayi ya rungume ta yana fada mata irin girman matsayinta cikin zuciyarshi daga karshe kuma yashiga nuna mata a bayyane da bakinsa da hannayensa da dukkan gangar jikinsa gaba daya yana kara jaddada mata shi nata ne ita daya haka kuma ta daina kiransa da mijin matacciya shi mijin rayayyiya ne domin tuni ya maye gurbin Ramlat da Hanan tsakaninsa da Ramlat addu'a ce amma Hanan itace abokiyar rayuwarsa har gaban abada zai cigaba da kulawa da ita da nuna mata kauna da soyayya har tsufansu, wannan karon akasar Paris tasamu ciki kuma acan ta haihu cikin kulawar doctors da Khalil wanda ya tayata nakuda ta haifo yaronta santalele wanda gaba daya su Aryan suka tare masa kyau domin tamkar balarabe haka yake nan Khalil yayi masa huduba da Abubakar saddiq yana tsokanar Hanan wai wannan karon babu kukan dinki to sai muce Allah yaraya yakaro kazantar daki. ALHAMDULILLAH Godiya ta tabbata ga ubangiji Allah madaukakin sarki wanda yabani ikon kammala wannan littafi mai suna mijin matacciya, Allah ya yafe mana kuskuren dake ciki ya hadamu acikin ladan gaba daya tare daku masu karatu,kamar yadda nafada book dina na kudine duk wadda ta karanta batare da ta biya ba to yar uwa kisani Allah yana kallonki,bawai book dina kadai ba duk book din da akace na kudine yakamata mu kiyaye daukar hakkin wani domin Allah yana gafarta abinda ke tsakaninka dakai bawa amma baya yafe hakkin wani murinka tunawa da wannan,ina mutukar godiya ga masoyana wadanda ke nuna min kauna kuma suke tare dani koda yaushe Allah yabarmu tare,sai mun hadu acikin labari nagaba,taku ahar kullum kuma akoda yaushe Ummi A'isha nagode. _*Ummi Shatu*_👌🏻