[2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ SADIYA ABDULRAZAƘ *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 1 Dare mahutar bawa, ta wata fuskar kuma rigar mugu, lokacin da dubban mutane suke samun damar ajiye haƙarƙarinsu bayan shafe tsayin awanni cikin yini suna gwagwarmayar rayuwa, walau ta waje ko ta cikin, a daren yau ba haka kalmar take ba a wajen Maryam domin kuwa ba ta damu da agogo ba a lokacin da ta tashi mijinta suke ta zabga tijara cikin talatainin daren, sakamakon binciken da ta yi a wayarsa ta ga bidiyoyin banza, inda a ce kishi cuta ne to za ta iya cewa ita shi ne kaɗai cutarta, wacce take wujijjiga ta, ta zabtare jarumtarta, ta kuma rufe ido wajen yankawa namiji kazar rashin daraja, su haɗu su figeta tare. "Maryam idan kika sake danganta ni da kalmar mazinaci a bakin aurenki! Na faɗa miki yau na siyo wayar, ban zauna na bincike ta...". A matuƙar harzuƙe ta katse mijin nata da faɗin"An faɗa ɗin mazinaci! Sai me idan ka sake ni? Ai ba a bakinka na fara jin kalmar saki ba, kuma ba ta damuna, don miji goma ba uba goma ba ne!". Ya ce"Tabbas wanda bai ji bari ba zai ji woho! Babu abin da ba a faɗa mini ba kafin na aure ki na cewar ba kya zaman aure kuma ba za ki iya ba har abada, amma tsautsayi da ƙaddarar wannan cikin jikin naki ya sa na ƙi saurara". Ta ce"Ka ma daina ƙalawa ƙaddara sharri, ka ce dai saboda son zuciyarka ka aure ni, duk kuwa da tsanar da tsohuwarka ta yi mini". Ya ce"Maryam! Ki je na sake ki saki ɗaya". Ta ce"Tabbatar mini kake yi ko kuwa saki ka ƙara a kan saki? Ka san dai tun da ka lanƙaya kalmar kiranka mazinaci da mutuwar auren ban fasa ba na sake furta maka, saki na farko ya tabbata, yanzu kuma ka sake yin ɗaya, biyu kenan, saura igiya ɗaya, duk da ko ka mayar da ni ba komawa zan yi ba, domin jaki shi yake maimaita aji!". A fusace ya ce"Dama wane tsautsayin ne zai saka na mayar da ke? Ki fice mini daga gida kafin na shayar da ke mamaki!". Ta yi wata dariyar rainin hankali na ce"Hehehe! Amma ai ba ƙarfe uku na dare ka auro ni ba, sannan a wajen ɗaurin auren ba a ce mini za ka sake ni na koma gidanmu uku na dare ba". Ya ce"Ki fice mini daga gida tun kafin zuciya ta ɗebe ni a yi ɓatacciya!" Ta ce"Don Allah idan ta ɗebe ka kar ta sauke ka sai ka kashe ni, wallahi idan ba uwata Hansatu ce ta taso daga ƙabari ba babu wanda ya isa ya saka ni barin gidan nan a yau!". Nasiru ya yi ƙwafa ya bar mata ɗakin, ya shige falo ya kwanta a doguwar kujera, yana ji a ransa ta ci darajar tsohon cikin da yake jikinta, da sai ya lakaɗa mata mugun duka samfurin tashi ki sha kunu, ya yi nadamar auren Maryam, duk da dama abu ne da ya tsammata, amma bai san girman rashin kirkinta ya kai haka ba sai da ya aure ta zama ya yi zama, yau dai duk haƙurinsa ta ƙure shi mai afkuwa ta afku. Ita kuwa Maryam baccinta ta kwanta hankali kwance, don wannan shi ne karo na uku da ta ji kalmar saki daga bakin miji, ko na farko bai ɗaɗata da ƙasa ba ballantana wannan da za a ce abun ya zama jiki. Har makara ta yi sallar asuba saboda dama shi ne take tashinta, ƙarfe shida ta yi sallah, ta shiga kitchen ta dafa indomi da shayi, ta cika cikinta sannan ta koma ɗaki ta hau haɗa kayanta, ta kusa gamawa ta kira wayar babarta, tana ɗagawa ta ce"Babarmu za a samu mai mota kuwa?" Daga can ɓangaren Uwani ta tashi zaune tana cewa"Maryam! Me kike nufi?" Maryam ta ce"Ya sake ni, jiya tsakar dare". Uwani ta ji farinciki ya yi dirar mikiya a zuciyarta, ta ce"Maza hanzarta ki haɗa kayanki, yanzu zan fita na samo mai mota, duk wanda ya rasa ki shi ya yi asara!". Maryam ta yi murmushi tana ƙara jin ƙaunar babar tasu, ta ƙarasa haɗa kayan, tana wanka ta ji tsayuwar mota tare da bugun gida, sai kuma sallamar Lami da Dije ƙawayen babarmu na kurkusa, ta fito tana yi musu sannu da zuwa, suka shiga kwashe kaya mai motan ya shigo yana taya su fita da kayan gadon, sai a lokacin Nasiru dake falo ya fito, ya same ta ranta fess tana saka kaya, ga kayansa da ta juye su cikin babbar rigarsa wacce ya yi fitar ɗaurin aurensu da ita, ta ajiye masa su a gefe, ransa a ɓace ya ce"Ina takarduna?" Ta ce"Suna ciki har takalma". Ƙwafa kawai ya yi ya fice daga gidan, zuciyarsa a dagule, a ƙofar gida ya zauna har suka gama kwashe kayan tsaf, Maryam ta fito ta yi tsaye a kansa da ƙaton cikinta ta ce"Nasiru ya za a yi da batun cikin nan? Jaririn zan kawo maka bayan na haihu ko kuwa ciniki za mu yi ka dinga biyana ina shayar maka da shi?" Ya ce"Allah Ya sauke ki lafiya sai a san abun yi". Bai jira cewarta ba ya shiga gidan ya saka sakata, ɗakunan wayam babu komai sai ƙunshin kayansa, ya fara tunanin yanzu yau a ina zai kwana? Katifa zai fito ya shimfiɗa ko tabarma? Gabaɗaya ya ji tsanar gidan ta kama shi tun kafin a je ko'ina tabbas mutum rahama ne ko da ba zaman lafiya kuke yi ba, ya kullo gidan ya tafi gidansu don sanarwa iyayensa, wanda ya san ba za su tausaya masa ba, sai dai su bi shi da Allah Ya ƙara, tun da tun farko sun nuna masa Maryam ba matar aure ba ce ya ce ya ji ya gani. A ɓangare Maryam, da gudu Uwani ta tare ta ta rungume tana cewa"Ƴata ta dawo kusa da ni, wallahi Maryam ko ƴaƴan da na haifa a cikina ba na yi musu son da nake yi miki, saboda kin fi su bin umarnina sau da ƙafa, zo ki huta ki sanar da ni abin da ya faru". Cike da ƙaunar babar tasu ta bi ta ɗaki, Uwani ta ce "Kwanta ki huta, bari na taya su shigar da kayan, ai kina kirana na ce to ban ga ta zama ba, na tashi na share ɗakinki tass, bari na sako miki ɗumamen tuwo". Maryam ta ce"A ƙoshe nake babarmu, sai da na yi girki na ci, cikin kayan ma akwai kayan abinci da yawa, don shekaran jiya ya yo mana siyayyar wata, na kwaso su duka ko ashana ban bari ba". Uwani ta ce"Allah Ya yi miki albarka ƴata, duk wanda ya rasa ki shi ya yi asara, wallahi har mamakin yadda kullum kike ƙara kyau da zama matar manya nake yi? Ban da kin ce kina so kuma ni ina son farincikinki dama ina ke ina Nasiru? Waye ubansa ma?" Daga haka ta fita ta shiga ɗakin Maryam ɗin, don taya aminanta aiki. Maryam ta ajiye hijjabinta, ta miƙe ƙafa wannan ne karo na biyu da aurenta ya mutu da ciki, sam ba ta jin nadamar ɗaukar mutuwar aure ba a bakin komai ba, tun da ba ta fuskantar tsangwama a gida ko ta nemi wani abu ta rasa kamar yadda ta ji an ce zawarawa suna fuskantar wannan ƙalubalen, ta yunƙura ta tashi don zuwa ta taya su aikin don ta ga har yanzu babarsu ba ta shigo ba shaidar ba su gama ba, ta fito ta ga labulen ɗakin a sake, saura taku biyu ta shiga ɗakin ta ji suna magana ƙasa-ƙasa, Maryam tana da wata al'ada ta laɓe, wannan duk wanda ya zauna da ita tabbas zai santa a kan haka, yanzu ma laɓewar ta yi daidai sanda babarsu take cewa"Lami wallahi Maryam ta yi ta aure-aure kenan, alƙawari na ɗauka ba za ta taɓa zaman aure ba, wannan ba na uku ba ne? Ku ci gaba da taya ni lissafi sai ta yi aure goma muddin ina raye! Wannan ce kaɗai fansar da zan ɗauka na cin amanar da uwarta ta yi mini, ina ma Hansatu tana raye ta ga yadda ƴarta za ta zamewa maza tamkar banɗakin kasuwa?" Sai suka saki shewa Lami tana cewa"Wallahi Uwani ba ki da dama!". Wani irin tashin hankali ne ya ruftowa Maryam, da ƙyar ta ja ƙafa ta koma ɗaki ta zauna jagwab, wani irin sanyi jikinta ya yi har ma zuciyarta, ta shiga tariyo maganganun masoyiyar babarsu tana yi musu sukola mai inganci, babar nan tasu mai kirki da ƙaunarta wacce ta sha cewa ta fiye mata mahaifiyarta tun da ba ta girma tare da ita ba, ashe wannan ƙaunar tata a gare ta duka ta bogi ce? Ta shiga tunanin me yasa za ta yanke mata wannan hukuncin? Ashe burin kashe mata rayuwa take yi take yaudararta da sunan inganta mata rayuwa? Ba kasafai Maryam ta fiya yin nadama a kurakuranta ba, amma yau ta ji nadamar biyewa babarsu, a hankali ta furta"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ta shiga tunanin mafita, yanzu ya za ta yi da wannan bita da ƙullin da ake binta da shi? Tabbas da a ce ba babarsu ce ta yi mata wannan abun ba da tuni yanzu wata maganar ake yi ba wannan ba, sanin hali ya fi sanin kama, babarsu ita ce malamarta a duk wani halinta na rashin mutunci, don haka ba za ta iya karawa da ita ba, to ta ina ma za ta fara? Tana cikin wannan tunanin ta ji tana yi wa ƙawayenta sallama da godiya, ta shigo ɗakin ta kalli Maryam sheƙeƙe ta ce"Maryama! Ba dai damuwa kike saboda mutuwar aure ba?" Hawayen da ba ta tsammata ba ne suka sakko mata, Uwani ta dafe ƙirji tana cewa"Yau ga muguwar shekara, inji kwaɗo da ya faɗa ruwan zafi, ke Maryam da gaske mutuwar aure kike yi wa kuka tun daga yanzu?" Ta ƙarasa maganar tana zama a kusa da ita, ta kamo hannunta ta ce"Maryam, wai ina huɗubata a gare ki? Ko yanzu kin ajiye maganata ta miji goma ba uba goma ba ne? Uwar me Nasiru yake ba ki da har za ki yi kukan rashin shi a rayuwarki?" Maryam tana danne zuciyarta don ta yi alƙawarin ba za ta bari babarsu ta san ta san manufarta a gare ta ba, ta ce"Babu komai babarmu, wallahi tausayin ɗan da zan haifa kawai nake yi, Al'amin yana can yana rayuwa ba tare da ni ba, wannan ma haka ce za ta faru, a ce na yi ta haɗawa ƴaƴana ƴan uba?" Uwani ta ce"Au ke wannan ne kaɗai tunaninki? To mene ne da ƴan uba? Ke matsala kuke samu da naki ƴan uban? Ke uwa ce, addu'arki kaɗai ƴaƴanki suke buƙata, matuƙar dai su ma kin ɗora su a tarbiyyar da na ɗora ki ta jajircewa da ƙwatarwa kai ƴancin rayuwa, wallahi ba za su yi kukan rashin uwa ba kamar yadda ke ma ba na fatan ki yi shi ko bayan raina". Maryam ta ce"Hakane babarmu na gode, bari na je na kwanta". Ta tashi ta fita, Uwani ta bi ta da kallo tana mamaki da fargabar abin da ya sanyaya mata jiki. Kwanciya ta je ta yi ta shiga tunanin baya, ta tuna ranar aurenta na farko da huɗubar babarsu a gare ta. Kowace amarya musamman wacce ta kasance buduruwa da aka yi mata auren fari, takan shiga damuwa da jin kewar rabuwa da gidansu da iyayenta a ranar da za a kai ta ɗakin mijinta, takan yi kuka ko da kuwa tana son wanda za ta aura ɗin, jikinta ya yi sanyi har ma wata takan ji dama ba ta yi auren ba, saɓanin Maryam da har yanzu da ta samu labarin motocin ɗaukarta ita da ƴan rakiyarta sun zo garau take jinta, babu wata fargabar shiga sabuwar rayuwa ko wani ƙalaubalen da za ta iya fuskanta a gidan aurenta, babu ruwanta da kewar iyayenta don ita ba mutum ba ce mai saka abu a rai, sabgar gabanta kawai take yi. "Don Allah Maryam ki saka mayafinki, ki rufe fuskarki, ga shi nan za a kai ki wajen Baba ya yi miki nasiha" Cewar ƙawarta Aisha tana miƙo mata mayafinta. Ta ce"Wai ni kam Aisha shi rufe fuskar nan dole ne? Baban zan ji kunya ko shi Nazifin da ya aure ni?" Ta yafa mata mayafin tana dariya, daidai lokacin da ƴan'uwa suka zo suka ɗagata don kai ta gaban babanta, nasiha sosai Baba ya zage yana yi mata, kanta a sunkuye tana sauraron shi, kalamansa suna shiga ta nan suna fita ta can, domin duk wata nasiha da ta gamsu da ita a rayuwar aure masoyiyar babarsu ta gama yi mata ita, _"Maryam ki riƙe wannan kalmar da zan sanar da ke ruƙo ba na wasa ba, miji goma ba uba goma ba ne! Ita rayuwar aure ba a yi ta don ƙunci ko tauye hakki ba, ba a yi ta don haihuwa da rainon ƴaƴa kaɗai ba, sai don samun ƴancin kai da soyayya daga wajen miji, duk macen da mijinta ya yi wani abu dake nuna ba ta isa ba a wajen shi, ko kuma ya kalli wata macen bayan ita to tabbas sunanta bora! Da a kira ki da bora gara a kira ki da bazawara, saboda haka ina ba ki shawarar kar ki sake ki ɗauki raini daga wajen miji ko danginsa, ko da hakan zai yi silar mutuwar auren, ni fa da a ce kin yi wuni ɗaya a gidan aurenki cikin baƙinciki gara a ce kin yi auren wuni ɗaya mijin ya sake ki! Don haka ki ɗaura ɗamarar samarwa kanki aji da ƴanci daga wajen mijinki, zawarci ba komai ba ne"_. "Maryam! Ba dai kuka kike yi ba?" Muryar yayana Sunusi ta ziyarci kunnenta, yana tambayar da mamaki da kuma izgili. Ta ɗago ta buɗe fuska da soyayyun idanunta fess ta ce"Kukan me zan yi Sunusi? Kawai dai na rufe fuskar ne". Ta ƙarasa maganar da gadara tana juya masa kai gefe. Ya ce"Ai na yi zaton kuka kike yi, in ce uban wa za ki yi wa? Hmm wannan aure Allah dai ya ba da zaman lafiya kawai, amma Nazifi ya ɗakko Dala da gammo". Baba ya ce"Sunusi ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru, Maryam tashi ki je, Allah Ya kai ki a sa'a". Suka tashi aka yi ɗakin babarsu da ita, tana zaune cikin ƙawayenta, ta zauna kusa da ita, ta kama hannunta ta ce"Babarmu zan tafi". Ta yi murmushi ta ce"Maryam duk wata nasiha da zan yi miki ai na gama ta, kar dai ki zubar da karatuna kawai shi ne fatana". Ta kawo bakinta saitin kunnenta ta ce"Miji goma ba uba goma ba ne!". Ta gyaɗa mata kai cike da gamsuwa tana murmushi, yayin da matan ɗakin suke binsu da kallon burgewa, na ƙaunar dake tsakaninsu da babarsu wacce ba ta ɓoyewa har kullum ƴaƴanta ƙawayenta ne, ita ta ja mayafinta ta rufe mata fuska aka fitar da ita waje. Aka saka ta a mota lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba aka tafi da ita gidan mijinta wanda ya kasance zaɓinta, domin duk cikin samarin da suka nuna mata so Nazifi ne yake daidai da ra'ayinta, ba don komai ba sai don shi ne mai sauka a kan ra'ayinsa ya bin ra'ayinta ko da ba ya so, shi ne mai yi mata biyayya da kwantar da kai tamkar uwarsa, sakamakon sonta da ya zame masa tamkar wata jarabawar rayuwarsa. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 2 Ƴan kai amarya da rakiyar ƴan ango kowa ya watse, wannan washe bakin da wasu kalaman soyayya bai damu Maryam ba, burinta kawai ta ji dalilin da ya sa ya rufe wani ɗaki guda ɗaya a cikin gidan, wanda tun da aka je jeri ya ce musu ban da ɗakin nan, ta sakko daga gadon da take a zaune, ta fice, ya bi bayanta yana cewa"Alwala za ki yi?" Tana ƙarewa gidan kallo ta ce"A'a ina ganin yanayin gidan ne". Ɗakuna uku ne sai kitchen da banɗaki a tsakar gida, ɗaya aka saka mata gado, ɗaya kujerunta, ta ce"Ni kam Nazifi wannan ɗakin da ka cewa ma su jeri ban da shi mene ne a cikinsa? Ko aure za ka ƙara?" Ya yi ƴar dariya ya ce"A haba dai aure! Ko auren zan ƙara ai dai kin san ba yanzu ba, kuma idan hakane me zai hana ki saka kayanki sai auren ya kusa sannan ki kwashe?" Ya yi wata dariya ya ce"To ballantana ma ban da ra'ayin ƙara aure, ai ba irinki ake yi wa kishiya ba my Love". Maryam ta taɓe baki ta ce"Ni dai ba ka ba ni amsar tambayata ba, me yasa ka kulle? Ko turakarka ce ai dai ka buɗe ko labule na saka maka". Ya ce"'A'a ma wallahi ba turaka ba ce, ki yi haƙuri ban faɗa miki ba, dama Gwaggo ce za ta dawo nan da zama, don ma ba a gama ginin da wuri ba, da sai ta riga mu tarewa, yanzu kuma da ta ga abun ya zo dab sai ta ce idan an gama bikin kin tare sai ta dawo". Wani abu ya daki zuciyar Maryam, wai ita yake nufi ta zauna gida ɗaya da uwar miji, tun tana amarya? Ta ce"Wai kana nufin da Gwaggo za mu zauna? To inda take a da me ya same shi?" Ya ce"Ai kin san dama gidan haya ne, ina da burin gina mata gida, to da na ci rabin ginin nan na ce mata nata ne, sai ta ce sam ita dai na yi aurena na tare idan ya so sai na ba ta ɗaki ɗaya ta zauna, gobe za ta dawo in sha Allah". Kamar wacce aka fizgi zancen daga bakinta ta ce"Kuma tun gobe?" Ya ji tambayar ba ta yi masa daɗi ba, da alama dai Maryam ba ta maraba da mahaifiyarsa, ya ce"To ai dayake ita kaɗai ce dama a gidan, sai wata jikarta ƴar yayana ita kuma yarinya ce, kin ga tare muke kwana a gidan, yanzu kuma ba na nan, akwai dai ƙanwata wacce take makarantar kwana, kin ga yanzu sai ita kaɗai, ba na son barinta ita kaɗai a gidan, shiyasa na ce gobe sai ta taho". Maryam ta jinjina kai ta ce"To Allah Ya kaimu". Ya amsa da"Amin my Love, ki yi alwala, ni ma bari na yi". Ta ce"A'a ni na yi sallar isha'i yanzun nan". Ya ce"To ai ta godiya ga Allah za mu yi". Ta ce"Ka bari dai gobe ma yi". Ya ce"Da dai kin daure mun yi yau ɗin, don ina cike da ɗokin kasancewa da amaryata, kin ga ya kamata mu fara gabatar da sallar tun da sunna ce". Maryam ta kyaɓe fuska kamar mai ƙyamar wani abu ta ce"Wallahi kar ma ka saka rai, don yau a gajiye nake, sai dai mu bar wa gobe". Ransa bai so ba, amma ba ya son takura mata, don haka ya ce"Yau da gobe ai duk ɗaya, ni bari na yi nafila". Ya ɗauki buta ya shiga banɗaki, ita kuma ta koma ɗaki da sauri, ta ɗauki wayarta ta kira babarsu, ta ɗaga tana cewa"Maryam lafiya kuwa da daren nan?" Maryam ta ce"Babarmu kin ji wata sabuwa? Wai ashe wannan ɗaki da ya kulle na babar shi ne a nan gidan za ta dawo ta zauna". Uwani ta dafe ƙirji ta ce"Na shiga uku! Me kika ce Maryam? Hauka ake yi? To wallahi ba ki samu gidan zama ba, kada ma ki miƙe ƙafa!". Ƴarta Mardiyya da take kwance tana shirin yin bacci ta ce"Haba babarmu! Yanzu Maryam ɗin da aka kai yau kowa yana murnar ta yi aure kike cewa ba ta samu gidan zama ba? Me ta ce miki?" Uwani ta ce"Maryam ki kwanta kin ji, gobe za mu yi waya, akwai ƴan sa ido a ɗakin" Ta kashe wayar tana tsuke fuska. Mardiyya ta tashi zaune tana cewa"Wai me ta kira ta ce miki?" Uwani ta ce"Mardiyya ba na son shiga shara ba shanu, ina ruwanki ne?" Mardiyya ta ce"Gaskiya da ruwana! Ya za a yi a ce awanni da kai ta ɗaki har ta fara kiranki tana kawo miki ƙorafi? Ke kuma ai bai kamata tun yanzu ki ce mata ba ta samu gidan zama ba, ki duba ki ga fa duk mun yi aure sai ita kaɗai a gidan nan, ana ta murna ita ma ta yi kuma sai ki ƙi ƙarfafarta ta zauna? Me yafu ma wai?" Uwani ta ce"Mardiyya me kike nufi ne? Na fa fi ku damuwar ganin Maryam ta yi aure ta zauna, gani na yi kamar ba ta yi dace na, wai ashe wannan ɗakin da kuka ce ya ce ban da shi a jere babar shi ce za ta dawo ta zauna". Mardiyya ta ce"To sai me? Ita Naziyya da take zaune da uwar mijinta a gida ɗaya mene ne ya same ta?" Ta ce"Babu komai, amma ita ai kin ga kowa da ɓangaren shi, ita kuwa Maryam ga ɗaki ga ɗaki fa suke, suna shaƙar numfashin juna, a kan idonta fa za su shiga wanka su fito, ko leda ya shigo da ita idonta a kai, to kuwa ina za su more amarci?" Mardiyya ta yi ƴar dariya ta ce"Ta ina za su shaƙi numfashin juna kamar a ɗaki ɗaya za su kwana?" Uwani ta ce"Ke dalla can rufe min baki, ku da ba ku san komai ba". Mardiyya ta koma ta kwanta tana cewa"Allah Ya kyauta". A ɓangaren Maryam amarya haka suka kwana tana tunanin irin zaman da za su yi da mahaifiyarsa, da yake babu nisa tsakanin gidansu da gidan su Nazifi ta san mahaifiyar tashi, sai dai taƙaimaimai ba za ta ce ga halinta ba, tun da su kaɗai ne a gidansu ballantana wani ya ga wani halin nata mara kyau, ita dai ta saka a ranta babu ruwanta da babar shi tun da ba a kanta za ta zauna ba, kowa ya yi ta kansa, sai dai fa ba za ta ɗauki raini ba, duk abin da ta ga an yi mata ba daidai ba ba za ta yi shiru ba, don gidan aurenta ne tana da cikakken ƴancinta, Gwaggo ta ja girmanta ita ma ta ja ƙanƙantarta. Haka shi ma Nazifi ya kwana da tunanin Allah Ya ba su zaman lafiya da mafimtar juna a zaman su da Gwaggo, yana son Gawaggo yana son Maryam don haka dole zai yi wa kowa adalci don ganin sun zauna lafiya. Washegari da safe suna cikin karyawa sai ga kiran Gwaggo, ya ɗaga suka gaisa ta ce"Nazifi ka manta da mu ka tafi aiki ne?" Ya ce"A'a ina gida yanzu dai zan fito". Ta ce"Ikon Allah! Yanzu ƙarfe tara kana gida Nazifi? Daga yin auren jiya za ka watsar da aikinka kenan? To ni dai na shirya ina jiranka". Ya ce"To ga ni nan zuwa". Maryam tana jiyo sautin muryar gwaggo da tattaunawarsu, ta jinjina kai kawai tana ayyana lallai wannan tsohuwar a tsaye take, to ai kuwa muddin tare za su zauna dole sai ta zaunar da ita, zaman dirshan ma kuwa. Bayan ya fita ta wanke kofunan da suka ɓata, ta share gidan ta koma ɗaki ta kwanta, sai ga sallamar Nazifi tare da Gwaggo tana cewa"Gafaranku dai!". Maryam ta tashi zaune tana taɓe baki, tana ji suna ta shiga da kaya ɗakin nata, ba ta fito ba sai da ta ji an buɗe mata kitchen, ta fito tana ɗaura ɗankwali da rarraba ido, Gwaggon ce ta buɗe har ma ta shige, kamar ta bi ta sai dai ta daure ta koma falo ta zauna, Nazifi ya shigo yana cewa"Maryam ki fito ku gaisa mana". Ta ce"Ai za mu gaisa ita da ba yau za ta tafi ba, ba gobe ba, gaggawar ta mene ne?" Ya ce"Hakane". Ta ce"Na ga an buɗe min kitchen? Me ake nema?" Ya ce"Tukwanenta da kwanuka ta ajiye". Ta ce"Ok". Ya daɗe da fita sannan ta fito ta shiga ɗakin Gwaggon, ta yi sallama Gwaggo ta amsa tana yi mata kallon tsaf, Gwaggon irin uwayen nan ce masu kishin ɗansu haka siddan, kuma haka kawai ta ji Maryam ba ta yi mata ba, saboda rawar jikin da Nazifi yake yi a kanta, Maryam ta gaisheta, ta amsa babu yabo babu fallasa, ga jikar tata a kusa da ita, wacce take ta kallon Maryam ɗin ba tare da ta gaishe ta ba, yarinyar za ta kai shekata tara, a ganinta ai ta san gaida manya, ta tashi za ta bar ɗakin Gawaggo ta ce"To mu fa ba mu karya ba muka taho". Maryam a zuciyarta ta ce'To zumuɗin uban me kuke yi?' A fili kuma ta ce"To" A daƙile ta tashi ta fita tana tura baki gaba, saboda ita fa gani take takura ne zaman uwar shi a gidanta, shayi ta dafa dama biredi biyu ya shigo da shi jiya, ta kai mata ta ajiye ta fice, ta same shi yana shirin fita, ya ce"Zan fita, zan aiko da cefane, sai ki dafa da ɗan dama tun da ga Gwaggo kuma na san za a yi baƙi ma ko?" Ba ta ce komai ba, har ya gama shirinsa ta ce"A dawo lafiya". Yana fita ta ɗauki waya ta kira babarsu, sun gisa ta ce"Ya kuka kwana?" Maryam ta ce"Lafiya ƙalau, amma fa kin ga tsohuwar nan har ta dawo, ta jera kayanta, wai abun takaici har kitchen ma haɗawa za mu yi, haka ta kwaso jiki don sauri ko karyawa ba ta tsaya ta yi ba". Uwani ta rafka salati da sallallami kamar wacce ta ji mutuwa ko tashin hankali ta ce"Har ta dawo gidan, kenan amarcin ma a gabanta za ku ci!? Maryam wannan wane irin gidan aure kika faɗa, anya ba za ki yi bore ba kuwa?" Maryam ta ce"Bari dai na ga yadda zaman zai kasance, idan na ga ba zan iya ba wallahi sai dai na bar mata gidan, yanzu ma har yana cewa ba yi girki da yawa, ga baiwa an kawo musu". Uwani ta ce"To ai shikenan, idan dai kin ga da matsala kar ki yi shuru ki cuci kanki, aure irin wannan da aka fara shi da matsala babu inda yake zuwa, idan kuwa kin ga ya yi nisan zango to tabbas durƙushe matar aka yi, irin matan da suke ɗaukar miji kamar rayuwarsu, ke kuwa daraja da ƙimarki ta fi gaban nan wallahi, ƴata wanke hannu ka taɓa ce ta wuce zaman haƙuri a gidan miji wallahi". Maryam ta ji daɗin maganganun babarta mai sonta, tana murmushi ta ce"Zan dai ga take-takensu tukunna". Uwani ta ce"Yawwa, kuma kin san su iyayen miji idan kika nuna musu ke mai haƙuri ce da biyayya to fa tamkar kin ce musu ke bola ce a zuba miki kowace ƙazanta, wallahi ke ce ƴar iska a idonsu, don haka idan ta yi miki kallon yamma ki yi mata na arewa, wannan cewata ce". Maryam ta naɗe huɗuba tass a kanta, suka yi sallama, ta ɗakko kazarta ta jiya da ba ta ci ba ta fara ci. Wajen sha ɗaya babarsu ta aiko mata da sauran kayanta, da kuma kula fal da jar miya wacce ta ji nama, shi ma Nazifi ya aiko cefane, sai ta soya naman da ya kawo ta ajiye ta dafa taliya ta ɗauki wata kula cikin tarkacen kayan Gwaggon da ta ajiye a kitchen ɗin ta zuba mata, ta yi sallama ta kai mata, tana ajiyewa Gwaggo ta buɗe ta ce"Kuma kya zuba miyar a kai?" Maryam ba ta ce komai ba ta fice daga ɗakin, har zuciyarta take jin haushin matar kuma daidai take da zamaninta, dayake tana ta yin baƙi taliya leda uku da ta dafa ta ƙare, dab da magriba ta dafa macaroni leda ɗaya, ta raba gida biyu ta zuba mata rabi ta bar wa Nazifi rabi, don ita ba ta jin yunwar ma, da ta kaiwa Gwaggo ta buɗe ta gani, sai ta tura kular gefe. Ana idar da sallar isha'i Nazifi ya dawo gidan, da ledojinsa biyu, ya siyo musu balangu da biredi ne, ya fara shiga ɗakin mahaifiyarsa da sallama, ta amsa tana yi masa sannu, ya ce"Yawwa sannu Gwaggo, ga wannan". Ya miƙa mata biredin da balangu, ta buɗe ta ce"Allah Ya amfana, dama ban ci komai ba". Da mamaki ya ce"Ba ki ci abinci ba Gwaggo?" Ta taɓe baki ta ce"To ka san ni ba cin kayan basir ɗin nan nake yi ba, da rana ta dafa taliya, da daddare ta dafa macaroni, ni gaskiya ba zan iya wannan rayuwar ba, gara ma tun wuri ka auno garin tuwo, idan ba za ta ci ba ni ta dinga dafa mini, na fi gane na ci tuwona idan zan kwanta, da safe na ci ɗumame". Jikinsa ya ɗan yi sanyi, ya ce"To babu damuwa in sha Allah gobe zan siyo, amma dai yau ɗin ki daure ki ci macaronin". Ta ce"To bari na gani". Ya fita ya shiga ɗakin Maryam, tana kwance tana kallon hotunan biki a wayarta, ya sakar mata murmushi ya zauna a kusa da ita cike da shauƙin sonta, yau dai ta karɓe shi sun sha amarcinsu, sanda suka fito suna alwala ma sai da Gawaggo ta leƙo ta ce masa"Alwalar me kuke yi? Me kake yi a waje ba ka yi sallar isha'i ba?" Cike da kunya ya ce"Na yi sallah Gwaggo kawai dai zan kwanta da alwala ne". Ta taɓe baki ta koma ɗaki, haka da komai ya wakana ya ji kunyar fita yin wanka, sai ya bari sai tsakar dare sosai sannan ya fita ya yi, kuma ya yi taka-tsan-tsan sosai wajen zubar da ruwa ta yadda ba sosai za a jiyo ƙara ba, bai saka a ransa Gwaggo za ta saka musu ido ba, kawai dai shi ne yake jin kunya. Ita kuwa Maryam da asuba ta yi nata wankan, lokacin ya tafi masallaci, Gwaggo da ta makara yau ta fito don shiga banɗaki ta ji ƙarar ruwa ana yin wanka, ta ce"Waye a ciki? Waye yake wanka da asubar fari?" Wani ƙululun baƙinciki ya tsayawa Maryam a wuya, sai da ma ta ɓata lokaci sosai sannan ta fito tana haɗe rai. Gwaggo ta ce"Ashe ke ce". Ba ta kula ta ba, ta shige ɗaki. Da sassafe ta ji motsin an buɗe kitchen, don tun asubar ba ta koma bacci ba, tana dai kwance tana jira gari ya waye ta fita, ta fara tunanin me tsohuwar nan za ta yi a kitchen? Jin shiru ba a rufe ƙofar ba ya tabbatar mata har yanzu ana cikin kitchen ɗin, ta tashi ta fito ranta yana ɓaci, daidai sanda Gwaggo ma ta fito daga ɗakinta, tana cewa"Haka kawai kun ƙule a ɗaki kun bar mutane da yunwa? Yasmin!" Ta doshi kitchen ɗin tana ƙwalawa jikarta kira. Ko kallon arziƙi ba ta yi wa Maryam ɗin ba, ita ma kuwa ta bi su kitchen ɗin, zaune ta samu Yasmin ɗin a kan turmi ta saka kwanon naman da Maryam ta soya jiya da rana a gaba tana ta ci har ta kusa cinyewa, ranta ya ɓaci don dama ita ba ta cikin jerin mutane masu haƙuri, ta ce"Kutt! Ke uban wane ya ce ki shigo mini kitchen har ma ki ɗauki abu ki ci?" Gwaggo ta ce"Ke dakata! Kar ki zagar mini ita, don ta ci naman da ba da kuɗinki aka siya ba?" Nazifi da y ƙaraso kitchen ɗin yanzu ya ce"Me yake faruwa ne?" Takaici ya hana Maryam cewa komai, saboda ba ta son nunawa babar shi halinta tun yanzu, sai kawai ta jinjina kai ta fice daga kitchen ɗin. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 3 Ɗakinta ta shiga ta riƙe ƙugu tana huci kamar mai jiran dambe. Nazifi jiki a mace ya ce"Gwaggo ya kamata ki nunawa Yasmin kuskurenta fa, wannan ai ba ɗabi'a ba ce mai kyau ta dinga ɗaukar abin da ba a bata ba". Gwaggo ta ce"Au! Nazifi kenan dai ka goyi bayan matarka ko? Yanzu ƙarfe nawa? Ƙarfe bakwai da rabi kun ƙule a ɗaki kuna ta bacci ba ta fito ta sallame mu ba? Saboda na dawo gidanka da zama sai karatun yarinya ya ɓalɓalce? Ai shikenan". Ta faɗa tana rausayar da kai kamar abar tausayi. Sannan ta ja hannun Yasmin tana cewa"Mu je ki shirya sai na ba ki kuɗi ki sayi koko a hanya". Nazifi ya shiga ɗaki ya samu Maryam kamar za ta fashe, ya ce"Maryam yarinyar nan ba ta yi daidai ba, amma ke ma bai kamata ki yi magana ba, da sai ki faɗa min na tsawatar mata, kin san tana zuwa makaranta to don kar ta yi latti ne ya sa ta nemi abin da za ta ci". Ta ce"Ka ga dakata Nazifi! Ta ya zan san tana zuwa makaranta alhalin a sharuɗan auren ba ka sanar da ni har da kula da wasu ba?" Ya ce"Gwaggon ce wasu?" Ta ce"Duk yadda ka ɗauka!". Ya jinjina kai ya ce"To ki yi haƙuri ki je ko shayi ne ki dafa musu tun da akwai biredi, amma daga yau sai ki dinga tashi da wuri, tun da ita Gwaggo ta fi son karyawa da abinci ko kunu da ƙosai, shi ma sai idan babu ɗumamen tuwo, na manta na faɗa miki anjima zan auno gari, ita ta fi son tuwo". Maryam ta ƙanƙance ido ta ce"Ni Nazifi na tambaye ka mana". Ya ce"Ina ji". Ta ce"Ku nawa aka aurawa ni? Kuma sannan zaman wa nake yi?" Ya ce"Maryam! Kina nufin mahaifiyata ba ta da matsayin da za ki yi mata hidima?" Ta ce"Ba zancen matsayi ake yi ba, ka ga ba na son abin da za a zo ana jin kanmu, tun wuri gara mu baje ta a faifai kowa ya ɗauki rabonsa, kai ka auro ni, zamanka nake yi, wallahi babu wacce za ta mayar da ni baiwa, to tsaya na tambayeka ma, da Gwaggo take gidanta kafin ta dawo nan wace take yi mata girki?" Nazifi ransa ya ɓaci sosai, amma ya san halin matarsa ba a yi mata hayaniya, kuma ba zai so su fara samun matsala tun yanzu ba, ya ce"Kin ga zauna mu yi magana ta fahimta". Ta zauna tana ɗauke kai. Ya ce"Gwaggo fa uwata ce, idan kika kyautata mata ni kika yiwa, kuma ladanki yana wajen Allah, sannan ke ma za ki so idan zama ya haɗa babarki da surukarta ta kyautata mata..." Ta katse shi da faɗin"To yaushe aka fara rayuwar aure a barzahu? Ni uwata ta gama tata rayuwar kuma babu surukar da ta takurawa". Ya ce"Kenan uwata takura miki ta yi?" Ta ce"Za dai ta fara". Nazifi ya ce"Maryam ina sonki, amma gaskiya son bai kai yadda zan bari wani raini ya shiga tsakaninki da mahaifiyata ba". Maryam ta ce"Sanin kana sona ne yasa na amince na aureka, amma ai kai ma ka san ka so kanka da yawa, a ce daga zuwana gidan na hau hidima da jama'a? Wai har wani tuwo zan dinga yi ina ɗumame?" Ya ce"To ai ban ce ke za ki ci ba, ita za ki yiwa". Ta ce"Nazifi idan kana so mu sasanta aurenmu ya yi ƙarko to ka yiwa sharaɗin da zan kafa assam'u wa ɗa'a". Kallonta kawai yake yi, ta gyara zama ta ce"Ka ga dai a wajen ɗaurin aure ba a ce zan dinga kula da Gwaggo da jikarta ba, cewa ma aka yi za ka kula da ni, ni ban ce ba zan zauna da mahaifiyarka ba, amma sai dai mu rayu kamar ƴan zaman haya, idan gari ya waye ta fito na fito za mu gaisa, ta yi girkinta na yi nawa, zan iya zubawa a roba na bata don zaman tare da fita haƙƙin maƙobtaka, sannan zancen haɗa kitchen ba zai yiwu ba, tun da ga abin da hakan ya fara haifarwa, gaskiya ta haƙura ta mayar da kayanta ɗaki, ko ka ɗan buga mata rumfa a tsakar gidan, sannan wannan yarinyar kar ta ce za ta dinga shigo mini ɗaki, don na lura ba ta da kunya, kowa ya yi harkarsa, ka yiwa Gwaggo cefanenta da ban nawa da ban, ta yi girkinta na yi nawa, idan ka yi haka za mu zauna lafiya". Nazifi ya ce"A gaskiya Maryam wannan ba tsari ba ne, kuma ni zan ji nauyin faɗawa nahaifiyata haka". Ta ce"To salun-alun ka sallame ni tun tafiya ba ta fara miƙawa ba, sai na tafi gidanmu, don mutuwar aure ba komai ba ce". Ya ce"Ni ba haka nake nufi ba, zan ji ta bakinta dai, yanzu ki dafa shayin". Ta tashi tana taɓe baki ta shiga kitchen ta ɗora shayin, a nan ta zauna ta kira lambar babarta, tana ɗagawa ta ce"Babarmu ni fa zan taho gida". Uwani da take zaune tana shan kunu ta ce"To abun ya ƙi ko?" Maryam ta kwashe komai ta faɗa mata, Uwani ta ce"Tabɗijan! To shikuwa Nazifi kwana-kwanar me yake yi? Ai gara ma ya fito fili ya sanar da duniya ƴar aiki ya ɗakkowa uwarsa! Maryam da ƙuruciyarki da kyaunki za ki ƙare a gidan da za ki dinga yin bauta? Ga ɗakinki ga na suruka, to wannan uban gwanjon da kike ta siya na ƙananun kaya duk ita za ki yi wa kwalliya ashe? Yanzu ya amince da sharaɗinki ko kuwa?" Ta ce"Ya dai ce za su tattauna". Uwani ta ce"To su tauna sa kyau ta yadda za su ji daɗin haɗiyewa, Maryam idan fa kin ga da takura ki kamo hanya ki taho gida, don ba gajiya muka yi da ke ba, muka ba shi". Ta ce"Bari dai na ga yadda za su tsara, wallahi ba sai kin ce na taho ba, don indai haka zaman aure yake to gara ma na dawwama a gabanki". Suka yi sallama, ta juye shayin a flas, ta zuba na Gwaggo a ƙaramin flas ta a ajiye, ta ɗauki nasu ta tafi da shi ɗaki, ba ta same shi a ɗakin ba, sai ta fito ta ga takalmansa a ƙofar ɗakin Gwaggon, hakan ya tabbatar mata yana ciki, ta yi saɗaf-saɗaf ta je ta laɓe a jikin labulen ta kasa kunne, daidai sanda Gwaggo take cewa"Yanzu dai Nazifi kenan ka zo ka faɗa mini na takura muku kai da matarka na bar maka gidanka ne ko?" Muryarsa cike da damuwa ya ce"Subhanallah! Kar Allah Ya kawo ranar da zan yi wannan tunanin, kin san Maryam yarinya ce..." Ta ce"Kai dakata, Allah Ya sa a nonon uwarta ka tsigota ka kawi gidan nan, mu sanda muka zauna da surukanmu wace bauta ce ba mu yi ba? Tuwon dawa kwano biyar nake tuƙawa, bayan na yi daka na yi surfe na niƙa, idan ban da lalacewar zamani har yarinyar da aka auro shekaran jiya ce za ta kafawa miji wani sharaɗi kuma akan mahaifiyarsa? Nazifi ka fice min daga nan zan haɗa kayana na tafi kawai". Maryam ta ja wata ajiyar zuciya a hankali jin Gwaggo za ta tafi, Nazifi ya ce"A'a babu inda za ki je, ni fa ba haka nake nufi ba, shikenan zan fahimtar da ita za ta dinga yi miki komai, ki yi haƙuri, bari na karɓo miki shayin". Maryam ta yi wuff ta shige ɗaki, zuciyarta tana zafi, a ranta tana ayyana ta ga wanda zai sauka a kan bakansa tsakaninsu, ya shigo yana cewa"Ina shayin nata?" Ba tare da ta kalle shi ba ta ce"Yana kitchen". Ya ce"Ai da sai ki kai mata, don Allah Maryam ki zauna lafiya da babata, wallahi ba ta da wata matsala". Ba ta ce komai ba, ta fara haɗawa kanta shayin, sai da suka gama karyawa ya shirya fita aiki, amma ya kasa yiwa Maryam bayanin Gwaggo ba ta amince ba, saboda yadda ya ga ta yi kicin-kicin da fuska, sai janta yake da wasa ta ƙi sauraronsa, ganin sai kame-kame yake yi yasa ta cewa"Wai ni kam ba fita za ka yi ba?" Ya yi murmushi ya ce"Au korata ma kike yi?" Ba ta ce komai ba. Ya ce"Maryam kin san dai ina sonki, ina son zama da ke, dalilin da yasa na zaɓi aurenki kenan, to kin kafa sharuɗa na samu Gwaggo amma ita ba ta amince ba, ni sai nake ganin ta fi mu gaskiya, don Allah ki yi haƙuri ki yi yadda ta tsara ɗin, wallahi kamar kin yiwa mahaifiyarki ne lada za ki samu, kuma ni ma za ki samu ƙima da mutunci a idona". Ta ce"Wato da ba ni da mutunci ko?" Ya ce"A'a ina nufin za ƙaru". Ta ce"Nazifi ina ga zan tafi gidanmu sai hakan ya fi kawo masalaha, sai ka auro wata ta zo ta yi mata hidima, matsalar da aka samu fa duk kai ka ja, ka ga ba ka faɗa min zaman mutum biyu zan yi ba, dama da ba zan ma fara aurenka ba, don abin da zai yiwu shi ake yi". Ransa ya ɓaci ya ce"Maryam ina lallaɓa ki ne saboda a zauna lafiya fa, amma na ga abun naki sai gaba yake yi, kin san dai yanzu ni mijinki ne ina da ikon saka ki da hana ki, don haka umarni zan ba ki yanzu, ya zama dole ki kula da mahaifiyata, ki yi mata biyayya, indai kin yarda aljannarki tana ƙarƙashin ƙafata, na ji ita ba ta isa da ke ba, amma ni ai na isa da ke, to ni za ki yiwa ba ita ba". Maryam kallon shi kawai take yi da maɗaukakin mamaki, don bai taɓa faɗa mata maganganu kai tsaye haka ba, wato yanzu yana ganin tun da ya aure ta zai iya taka ta yadda ya so, bai ma tsaya jiran amsarta ba ya fice, a ransa yana jin babu daɗi, amma dole ya nuna mata muhimmancin mahaifiyarsa. Ita kuwa yana fita ta kira babarta, ta zayyana mata komai, ta ƙara da faɗin"Ni zan haɗa kayana na taho". Uwani ta ce"Kul! Kar ki taho yanzu, ƴan gulma sun tashi daga bacci, ki yi haƙuri sai dare, ana sallace sallar magriba ki taho, ba ki ga wajen zama ba Maryam". Ta tashi ta haɗa kayanta cif a kwati ƴar tsakiya, ta gyara ɗakin ta fito tana wanke-wanke tana jin waƙoƙi a wayarta, tana bin waƙar cikin nuna ko ajikinta, wani jinta take a sama ta yadda take jin tana da gatan da ba za ta ɗauki raini daga wajen kowa ba, ta gama ta shiga kitchen ta tattaro kayan gararta danginsu cincin da dubulan ta kawo su ɗaki, tana ci tana chart har sha ɗaya ta yi, sai ga ɗan aike da ledoji wai ga shi inji Nazifi, ta buɗe ta ga ledar farko kayan miya ne da nama, sai kuma garin masara da na alkama, ta yi wani murmushi na takaici ta ɗauki ta kayan miyan ta kai kitchen ta garin kuma ta je ajiye a ƙofar ɗakin Gwaggo, ta koma ɗaki ta ci gaba da harkokinta, sai sha biyu da rabi da Yasmin ta dawo daga makaranta, ta ci karo da kedar, tana buɗewa take cewa"Gwaggo wannan ledar fa?" Gwaggo ta ce"Leda kuma?" Yasmin ta ce"Ai garin tuwo ne ma, kuma kika ajiye a waje?" Gwaggo ta fito tana cewa"Garin tuwo kuma? Sai ta ƙwalawa Maryam kira, ta fito tana ɗaura ɗan kwali, Gwaggo ta ce"Wnnan fa na ga an ajiye a ƙofar ɗaki?" Maryam ta ce"Ƙila ɗan aike ne ya kawo". Ba ta jira cewarta ba ta koma ɗaki, tana jin Yasmin tana tambayar me aka dafa? Gwaggo ta ce"Shiga kitchen ɗin ki duba" Ta koma ɗaki tana mamakin kalal surukar da Allah Ya haɗata da ita. Maryam tana jin ƙarar buɗe kitchen ta fita, ta samu Yasmin tana buɗe-buɗe, ta haɗe rai sosai ta ce"Ke ƙalau kuwa? Uwar me kika ajiye da za ki ɗauka?" Yasmin ta ce"Ba dai uwata ba". Mamaki ya kama Maryam ta ce"Zaginki na yi? To na zage ki ɗin uwarki da ubanki! Na fi ki iya rashin kuya, a fagen nan ke jikata ce ba ƴata ba, fice ko na kikkifa miki mari!". Yasmin ta fita tana kwarara ihu kamar wacce aka cirewa ido, Maryam ta fara kwashe kayan abinci na gararta tana kaiwa ɗaki, har ta gama Yasmin ba ta fasa ihu ba, Gawaggo kuma ba ta fito ta ce komai ba, tana zaune sai ga kiran Nazifi, tana ɗagawa ya ce"Amma Maryam sai da na faɗa miki babu ruwanki da yarinyar nan, akan me za ki dakar musu ƴa?" Ta yi tsaki ta kashe wayar, saboda ba ta da lokacin tsayawa faɗa musu ba ta kai ga dukanta ba, abu ɗaya da ta sani dai shi ne auren nan ba mai yiwuwa ba ne, dole a kira ta da ƙaramar bazawara, don ko miji bai isa ya saka ta ciwon kai ba, ballantana kuma uwarsa da wata ƴar tsakuwar jikarta. Ya yi ta kira ba ta ɗaga ba, hakan ya sa ya taho gidan don kukan da ya ji Yasmin tana kurmawa ta waya da yadda Gwaggo take ta masifa ya tada hankalinsa. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 4 Yana shigowa gidan ya shiga ɗakin Gwaggo, da yake Maryam ta ji sallamarsa sai ta tashi ta fito, ta je ta laɓe tana sauraron su, Gwaggo tana ta tsara masa son ranta kamar a gabanta aka yi, sai da ta ji ya ce"Ki yi haƙuri don Allah Gwaggo bari na je na same ta". Sannan ta yi wuff ta shige ɗakinta, ta haɗe rai tana jiran ta ga ta inda zai fara, ya shigo da sallama, ransa a ɓace yake da abin da ta yi, amma sai ya kasa karaɓus saboda yana son Maryam, ya zauna a sanyaye ya ce"Maryam don Allah ki rufa mini asiri ki fita daga harkar yarinyar nan". Ta ce"Na fita daga harkarta fa ka ce, kamar dai wata sa'ata, yarinyar da a haihuwar kaji na haife ta amma ta yi yunƙurin zagina..." Ya katse ta da faɗin"To kin ji ke ma yunƙuri kika ce, ba ta zage ki ba, a kan me za ki dakar musu ƴa?" Ta ce"To shi yunƙurin ba raini ba ne? Ai wallahi inda ta zage ni sai bakinta ya yi jini, kuma ni fa ban dake ta ba, sharri ne kawai ta so ƙullawa, kuma sai dai ya ƙare a kanku don yau zan bar muku gidan". Ya yi murmushi ya ce"A haba, da wasa kike yi, babu inda za ki tafi ki bar ni". Ta ce"Wallahi Nazifi da gaske nake, ba zan iya ba, bari na faɗa maka gaskiya inda na san haka zan samu gidanka da ban aureka ba, a ce daga aure sai saka ni ɓacin rai ake yi?" Ya ce"Ki yi haƙuri don Allah! Komai zai daidaita in sha Allah, kuma ke ma fa har da laifinki, kin ƙi kwantar da hankalinki, yau da wuri zan shigo mu sha shagalinmu amaryata". Ta taɓe baki, don ba ta da lokacin ɓatawa wajen nuna masa dole yau za ta tafi gida. Ya ce"Kin yi girki? Na aiko cefane za ki iya yi mata tuwon yau ko sai gobe? Kin ga cikinta ita kaɗai ne ko kaɗan ne kin ji Sweety". Takaici ya kamata, ta kwanta tana cewa"Don Allah ka tafi harkarka". Shi ma ya kwanta kusa da ita yana cewa"Ba zan tafi ba, kin ga yi haƙuri tashi mu shiga kitchen ɗin tare sai na taya ki". Ta ce"Wallahi Nazifi ba zan yi tuwon nan ba". Zai yi magana suka ji Gwaggo tana ƙwala masa kira, ya tashi ya fita jiki a mace. Gwaggo ta ce"Nazifi tun da ka zaɓi matarka ta huta ni na wahala to mu je ka koya min yadda ake kunna gas ɗin, sai na ɗora". Ya ce"Haba Gwaggo za ta yi, duk fa ba yadda kike tunani ba ne, kin san Maryam tana da aljanu shiyasa wani abun sai an yi mata uzuri". Gwaggo ta ce"Allah Ya sa tsamiya ce a kanta, wa za ta faɗawa aljanu? Ni da nake da guda saba'in a kaina na gado, zaman gidan nan fa idan ba zai yiwu ba tun wuri ka faɗa min na koma inda na fito". Inda za ta koma ɗin tabbas da zai ji daɗin hakan, amma ba zai iya nuna mata yana so ta tafi ba, don haka ya ce"Ki yi haƙuri Gwaggo, bari na samo miki tuwon, gobe sai ta dafa miki". Bai jira cewarta ba ya fita daga gidan. Ya siyo mata tuwon ya kawo ya koma kasuwarsa, ba tare da ya sake shiga ɗakin Maryam ba. Can da magriba Maryam tana sallayar da ta idar da sallah ta jiyo hayaniyar Gwaggo tana cewa"Wallahi Yasmin idan fitina za ki yi sai ki bar gidan nan, ga tuwo ki ce sai kin yi girki, alhalin ba iya kunna gas ɗin kika yi ba?" Yasmin ta ce"Wallahi na ga yadda ake kunnawa, idan na kunna sai ki dafa min indomin don Allah, idan kuma so kike na kwana da yunwa shikenan". Gwaggo ta ce"Rufa min asiri na mutu babu hakkin kowa a kaina, ungo siyo ashanar, don wannan matar ƙila ɓoyeta ta yi". Maryam ra ƙufula, sanda ta fito Yasmin har ta fice, tana dosar kitchen ɗin ta fara jiyo ƙarar gas ɗin shuuuu alamar ta kunna shi, kuma wai ta tafi siyo ashana, a ranta ta ayyana lallai dole dai ta bar gidan nan, don ba ta shirya mutuwa ba, ta kashe gas ɗin ta fito ta ja ta tsaya a ƙofar kitchen ɗin. Sai ga Yasmin ra dawo da saurinta, ta yi turus ganin Maryam a ƙofar kitchen, ta haɗe rai ta shiga ɗaki, sai ga Gwaggo ta fito tana gyara ɗaurin zani, Maryam ta ɗauke kai kamar ba ta ganta ba, Gwaggo ta ce"Baiwar Allah za ki iya ba mu waje ko?" Ta ce"Gwaggo ba zai yiwu a kunna gas yanzu ba, ya kamata ku fara sanin yadda abun yake kafin ku fara amfani da shi, wallahi yanzu idan aka kunna gas ɗin nan gobara ce za ra tashi gagaruma ku mutu, don haka ko za a kunna shi a yau dole sai warin iskar nan da ya fita ya baje". Ta ce"Ke Yasmin daga yau kar ki sake gwada kunna gas ko a wani wajen, ba haka ake yi ba". Gwaggo ta tafi ɗaki tana cewa"Oh! Ni kam Nazifi wa ya auro ne? Yau ni za a faɗawa zamani? An hana ni abinci kuma an hana ni dafawa? Ba laifinki ba ne". Maryam ta ce"A'a Gwaggo ku zo ku kunna, sai dai na ce Allah Ya ji ƙanku, don ni yanzu zan bar muku gidanku ma". Daga haka ta shige ɗaki, ta ɗauki akwatinta ta saka wayarta a jakar hannu ta fice, Gwaggo ta bi ta da kallon mamaki, sai kuma jikinta ya yi sanyi, ita dai ba ta ga abin da aka yi da zai saka ta yi yaji ba, "Daga kunna gas? Allah Ya kyauta" Ta faɗa tana shigewa ɗakinta. A ɓangaren Maryam ranta fess ta ƙarasa gida, duk da tana ɗan fargabar abin da Baba zai ce, faɗa ne ta saba da shi musamman ta wajen shi, kuma shi Baba yana da wani hali wanda yake burge ta, idan ya yi maka faɗa da nasiha a kan abu, ka ƙi yarda ko ka ƙi dainawa, shikenan sai ya ce ka fi ƙarfinsa ya zare hannu a tafiyarka, sam ba zai takura maka ka yi dole ba, shiyasa take ganin ba zai takura sai ta koma gidan Nazifi ba. Ai kuwa da Baban ta fara cin karo, a ƙofar gida ta same shi, suna tattaunawa da wani maƙocinsu, dama gaida manyan unguwa ba ɗabi'arta ba ce, don haka kanta tsaye ta wuce su ta shiga gidan, Baba da ya gane ta sai da gabansa ya faɗi, ya bita da kallo. Tana shiga da sallama Uwani ta tare ta ta rungume tana cewa"Sannu da zuwa, maza shige ɗaki, ai ba neman kai muke yi da ke ba" Ta yi maganar tana jan akwatin zuwa ɗaki. Maryam ta shiga ta ajiye hijjabinta, ta kwanta a gado, Uwani ta shigo tana cewa"Kuma Nazifin yana kallo kika taho?" Ta ce"A'a ba ya nan, sai dai ya dawo ya ga wayam". Uwani za ta yi magana suka ji sallamar Baba, ya ɗaga labulen ɗakin yana cewa"Wace ta shigo yanzu kamar Maryam?" Uwani ta ce"Ita ce, zama ya ƙi daɗi, tun a daren da aka kaita suke ƙunsa mata baƙinciki ba ta huta ba". Baba ya ce"Ban gane zama ya ƙi daɗi ba, amma dai kin manta kwana biyu da kaita gidan miji ko? Da har za ta kwaso ƙafa ta dawo ta shimfiɗa miki ƙarairayi ki yarda. Ke ta shi ki fice ki koma gidanki". Uwani ta rafka salati har da tafa hannu kafin ta ce"Wallahi Malam irinku ne masu siyar da ƴarsu a gidan auren, ta yi ta bauta da sunan zaman aure, ai aƙalla ka tsaya ka ji me ya dawo da ita tukunna kafin ka kore ta". Ya ce"Wane irin rashin haƙuri ne zai sa ta dawo gida kwana biyu da aure?" Ta shiga tsara masa ƙarya da kashi-kashi, har da cewa yau ɗin Gwaggon har marinta ta yi a gaban shi bai ce komai ba, ga shi kullum sai ta yi mata tuwo, ga jikarta tana zaginta. Baba ya yi shiru yana nazari kafin ya ce"Uwani duk da hakan wannan bai kai ta taho gida, ko waya ce sai ta yi wani ya je a sasanta yanzu idan aka fahimci har ta zo gida me duniya za ta ce?" Uwani ta ce"Ita fa rayuwa indai za ka biyewa duniya za ka ƙare a wahala ne, ina ruwanka da duniya ko mutanen cikinta, yadda za su yi suka don ta dawo haka za su yi idan miji da uwarsa sun kassara ta". Tsaki Baba kawai ya yi, don ba ya iya doguwar ja in ja, ya fice daga gidan. Uwani ta ce"Maryam dole fa ki buɗe baki ki ƙwatarwa kanki ƴancinki, idan ba haka ba wallahi kwasarki zai yi ya maida ki, ƙarama da ke da ƙuruciya ki ƙare a wahala da uwar miji? Duk yadda za a yi ki ce ba za ki koma ba, kar ki sake ki sare, don auren kwana biyu mene ne marabarki da buduruwa? Yanzu wani saurayin zai aure ki wanda ya fi shi komai, Allah Ya sa dai bai ɗora miki idda ba". Ta tsare ta da ido tana jiran amsarta, Maryam ta ce"Sai dai kar a kuma". Uwani ta ce"Ya cuce ki! Allah Ya saka miki". Nazifi yana komawa gida ya tarar an karo ƙofar ɗakin Maryam, ga shi dai ba lokacin sanyi ba ballantana ya ce shiyasa ta rufe, sai ya raya a ransa ko bacci ta yi da wuri, duk da sai yanzu ake kiraye-kirayen sallar isha'i, ya fara shiga ɗakin Gwaggo da sallama, ta amsa ya shiga ya zauna yana yi mata sannu, ta ce"Ni kam Nazifi matarka wace iri ce? Daga magana a kan kunna gas shikenan ta haɗa kaya ta bar gidan?" Gabansa ya faɗi ya ce"Ta bar gidan kuma?" Gwaggo ta ce"Ka ga Nazifi ni kam zan bar gidan nan, na tabbata Auduwa bai saka ƴan haya a gidanmu ba, ka taimaka ka yi masa magana na koma, idan na mutu ni kaɗai shikenan, ko na kumbura babu wanda ya sani duk tsiya dai kafin na fashe na ishi duniya da wari wani zai shigo ya gan ni". Nazifi ya ce"Haba Gwaggo wannan wace irin magana ce kike yi?" Ta ce"Ka ga ka je ka dawo da matarka, gobe zan bar gidan nan, yanzun ma don dare ya yi ne, ka faɗa mata ta yi haƙuri ni ba baƙuwar zafi ba ce". Nazifi ya tashi ya fita jiki a mace, a ƙofar gida ya tsaya ya kira lambar Maryam, ta ɗaga ya ce"Maryam kina ina?" Ta ce"Gidanmu". Ya ce"Don Allah me yasa za ki yi mini haka? Me ya yi zafi?" Tsaki kawai ta yi ta kashe wayar, ya bi wayar da kallon mamaki, bai taɓa zaton da gaske za ta iya yin yaji a kwana biyu da aurensu ba, ya mayar da wayar aljihu ya kama hanyar gidansu. Yana ƙarasawa yayanta Sunusi ya zo shiga gidan, suka gaisa yana ce masa"Ya Maryam ɗin? Ko wani abun za ka karɓar mata?" Nazifi ya yi yaƙe ya ce"Ai tana ciki ma, zuwa na yi mu tafi". Sunusi ya zaro ido ya ce"Kamar ya tana ciki? Uban me ta zo yi?" Nazifi ya fara kame-kame kafin ya ce"Ba wata matsala ba ce, za mu sasanta". Sunusi ya shiga gidan ransa a ɓace, ya fara ƙwalawa Maryam kira, ta tashi zaune tana harare-harare, Uwani da ta fito daga banɗaki ta ajiye buta a fusace ta ce"To Allah Ya dawo da kai! Lafiya kake yi mata kiran mafarauta? Uwar me ta kashe maka?" Ya ce"Yanzu na ga mijinta a ƙofar gida, wai babarmu uban me ya dawo da ita tun yau?" Ta yi masa daƙuwa ta ce"Ubanka ne! Kuma wa ya sako ka a wannan rigimar?" Da mamaki ya ce"Rigima fa kika ce? Lallai, kenan nufinki waje za ki ba ta ta zauna? Ke Maryam!" Ya ƙarasa yana shiga ɗakin, kamar zai dake ta ya ce"Uban me ya haɗa ku da shi, da har kika kwaso jiki kika dawo?" Ta yi banza da shi, tana turo baki, ya ce"Ai dama na san zai yi wuya ki zauna wallahi, idan na ce da motsi a kanki sai a ce ba haka ba, to ga shi dai an fara gani, sai ki wuce ga shi can yana jiranki a ƙofar gida". Uwani ta ce"Kai Sunusi ka kiyaye ni fa! Ka fita daga idona na rufe, ina ruwanka da zancen nan wai?" Ya ce"Allah Ya kyauta". Ya shiga ɗakinsa. Uwani ta saka hijjabi ta fita, ta samu Nazifi tsaye yana jira, ya tsuguna ya gaishe ta, sannan ta ce"Ka shigo daga ciki, magana ai ta wuce ƙofar gida". Ya bi bayanta yana sunne kai ƙasa irin na surukai. A tsakar gida ta shimfiɗa tabarma, ya zauna sannan ta shiga ɗaki ta ce da Maryam"Ki fito, kuma saura ya yi miki kallon soyayya ki haƙura, shi fa aure irin wannan da ya fara da matsala wallahi matsalar nan ba ta taɓa ƙarewa, sai dai ta yi ta girmama, ki tsufa a haka kina shaƙar baƙinciki, idan kuma kin ji kin gani to sai ki bi shi ki koma". Maryam ta tashi ta fito, suka zauna aka ƙara gaisawa, Uwani ta fara magana"Nazifi ka ba ni mamaki, ka yi mana bazata! Ashe kai uwarka ka aurowa ƴata ba ka yi bayani ba? Ta ya za ku rufar mata da bauta ba ta da hutu ta ko'ina? Ka ga a gidan nan ma da na saka Maryam aiki gara na yi, saboda ba na so ta wahala, a gaskiya wannan zama naku ba mai yiwuwa ba ne, tun da abun har ya kai ta fara dukanta to kawai ka sake ta kowa ya huta tun ba ku fara tara zuri'a ba". Gabansa ya faɗi ya ce"Duka kuma? Maryam Gwaggon ce ta dake ki?" Ta ɓata rai ta kau da kai gefe. Uwani ta ce"To ƙarya za ta yi mata kenan?" Ya ce"A'a kawai dai na yi mamaki ne, saboda ita Gwaggon ba ta ce mini an yi haka ba". Ta taɓe baki ta ce"Dama mutum zai yi ya ce ya yi ne? Nazifi don Allah salun-alun ka furta mata kalmar saki, ba sai ka wahalar da shari'a ba". Ya ce"Haba Umma wannan ai ƙaramar matsala ce wacce za a magance ta, abun bai kai na rabuwa ba". Ta ce"Ban ga alama ba! Uwarka ce fa, ba za ka taɓa canzata ba, don haka ita ya kamata ka zaɓa ba matarka ba, yanzu idan ta kwashe maka albarka kana ganin zan bar ƴata ta ci gaba da zama da kai da rashin albarkar uwa? A'a ba zai yiwu ba, ka rabu da ita kawai shi ne maslaha". Nazifi ya ce"A yi haƙuri don Allah, indai babata ce ta ce ma gobe za ta bar gidan, shikenan babu wani abu da zai sake tasowa kuma in sha Allah". Uwani ta ce"To ai gata nan, idan za ta koma shikenan!" Ta tashi ta shiga ɗaki. Ya kalli Maryam ya ce"Haba Maryam, yanzu wannan har ya kai ki taho gida? Wannan ƴar matsalar da za mu daidaita a tsakaninmu?" Ta ce"Kai kake mata kallon ƙaramar matsala, ni kam babba ce a wajena". Ya ce"Wannan ma ai abun kunya ne a ce har kin yi yaji, ki rufa mini asiri ki zo mu koma". Ta ce"Abun kunya ya wuce na zuwan uwa ta zaune a gidan yara?" Maganar ta dake shi sosai, ya ji haushi amma ya dake ya ce"To ki tashi dai mu tafi". Ta ce"Nazifi wai da wane yaren ake yi maka bayani? Aka ce maka wannan auren ba mai yiwuwa ba ne ba fa! Don haka ka sallame ni kawai". Ya ce"Ba dai Gwaggo ba ce? Za ta tafi ai na faɗa miki". Ta ce"Ni ko ta tafi na fasa auren, ka sallame ni idan kana son zaman lafiya". Nazifi ya ce"Shikenan bari na tafi, zuwa gobe idan kika huce na dawo mu yi magana". Ta ce"Nu babu wata hucewa da zan yi, za dai ka ɓatawa kanka lokaci". Ya fice daga gidan yana jin ransa babu daɗi. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 5 A hanya ya tsaya ya siyawa Gwaggo tuwo ya tafi da shi gidan, ya miƙa mata ya zauna ya yi shiru, ta ce"Nazifi, ko daga gidan nasu kake?" Ya ce"Daga can nake". Ta ce"Ya kuka yi?" Ya ce"Wallahi ita da babar tata sun ƙi fahimtata, wai zancen ma na sake ta suke yi". Gwaggo ta ce"La ila ha illallahu! Saki kuma? Duk saboda ni? Ka ga taya ni haɗa kayan nan na bar maka gidanka yau, ba ka ba ta haƙuri ba ka faɗa mata ni ba baƙuwar zafi ba ce?" Nazifi ya ce"Na faɗa mata za ki tafi tun da haka ta zaɓa, amma duk da haka zancen rabuwa take yi". Ta ce"To Allah Ya kyauta". Ganin ta janyo tsohuwar akwatinta ta fara haɗa kaya jikinsa ya yi sanyi kamar an zare masa laka, zuciyarsa kuma ta fara kumbura, sai a yanzu ne ma yake ganin Maryam da uwarta fa sun ci mutuncinsa, ya tuna ƙima sa daraja irin ta uwa, ya tuna goyon ciki, haihuwa har zuwa shayarwa da raino, ga kula da tarbiyya da karatunsa Gwaggo ba ta gajiya ba, anya kuwa idan ya zaɓi ra'ayin wata mace wacce suka haɗu rana tsaka ya wofantar da mahaifiyarsa zai gama da duniya lafiya? Sai ya ji tausayinta ya kama shi, har ya ji gara ya zaɓi rayuwa babu aure a kan ya zama silar ɓacin ranta, ya matsa kusa da ita, ya mayar da kayan ya zuge akwatin ya matsar gefe, sai ya sunkuyar da kai, Gwaggo ta kafe shi da kallo, ya ce"Gwaggo babu inda za ki je fa, ke uwata ce ba a canza uwa, amma ana canza mata, babu macen da za ta raba ni da ke dare ɗaya, zan iya rayuwa babu auren ma gabaɗaya matuƙar ina tare da albarkarki". Ita ma sai jikinta ya yi sanyi, ta ce"Nazifi ba zai yiwu ka ƙi aure saboda ni ba, wallahi so ne yasa na zaɓi zama a kusa da kai, ka sani duk cikinku na fi sonka, ba zan so abin da zai takura rayuwarka ba, saboda haka gara na tafi ɗin kawai tun da haka ta zaɓa". Ya ce"Gwaggo wallahi ba za ki tafi ba, indai ba za ta zauna da ke ba a gidan nan, to tabbas zan haƙura na sake ta kamar yadda ta ce". Gwaggo ta ce"A'a kar ma ka fara, ba zai faru ba ma, tun da ka ce sai na zauna to zan kwashe kayana daga kitchen ɗinta, sannan zan dinga girkina a murhuna, idan ta ga dama ma ko gaishe ni kar ta yi, tun da ba zamana take yi ba, indai hakan ya yi mata shikenan". Ya ce"Wallahi da na san haka Maryam take da ba zan fara aurenta ba" Gwaggo ta ce"Ka daina yiwa kanka baki, ai idan ka lura har da ƙuruciya da rawar kai irin ra yaran zamani, Allah dai Ya kyauta". Ya ce"Amin, bari na siyo miki tuwon". Ta ce"To kai me ka ci?" Ya ce"Tun kunu da na sha a kasuwa". Da sigar tsokana ta ce"Kai dai sunanka angogu ba ango ba, to ko ƴar taliya za ka dafa mana? Ka ga Yasmin tuwon rana da ka siyo ma ba ta ci ba, ka ganta ta yi lakur ko motsin kirki ba ta iyawa saboda yunwa, ba mu iya kunna gas ɗin ba, kuma matarka ta ce za mu babbake, na ce to mu bar shi tun da ba mu san kalar kaifin bakinta ba". Ransa a ɓace ya ce"Kamar ya za ku babbake?" Ta kwashe labarin yadda aka yi da Yasmin ta zo kunna gas ɗin ta faɗa masa, ya ce"Tabb ai kuwa da kun babbake ɗin, gaskiya kar yarinyar nan ta sake gwada irin wannan tsautsayin, nawa take da za ta ce za ta yi girki?" Ya tashi ya shiga kitchen ɗin, sai bai ga kayan abincin ba, ya koma ɗaki nan ma bai gani ba, saboda Maryam a cikin sif ta loda su ta kuma rufe ta zare mukullin ta tafi da shi, abun ya ba shi mamaki, kamar ya kira ta ya tambaye ta, sai kuma ya ga ai ba shi ya siyo ba dama gararta ce, don haka ya fita ya siyo taliyar ya dafa musu, suna ci suna fira cike da nishaɗi kamar suna gidansu na da. Ƙarfe tara ya yi mata sallama ya tafi ya kwanta, sai dai ya kasa baccin, ya shiga tunanin yadda rayuwar aurensa ta fara da ƙalubale, yana son Maryam sosai, har zuciyarsa yake son ƙare rayuwarsa da ita, sai dai ya fara tunanin ita ba son shi take yi ba, tun da har wannan ƴar matsalar za ta saka ta ce ya sake ta, wajen goma da rabi ya kira ta a waya, har sau uku ba ta ɗaga ba, ya kunna data ya ganta a online, kamar ya yi mata magana sai ya fasa, ta ajiye wayar yana jira gobe ta yi, ya je ya ji yadda za su kaya da ita, don shi dai bai shirya rabuwa da ita ba. A ɓangaren Maryam kuwa bayan tafiyar Nazifi, Uwani ta saka ta a gaba da zuga, tana nuna mata ya zama dole ta haƙura da auren nan indai tana son kanta da arziƙi, ta na ta nuna mata mutuwar aure ba komai ba ce, ballantana ita da ba ta haihu ba ma, nan da nan wani da ya fi shi zai fito ya aure ta, ta nuna mata da ka yi rayuwar aure cikin ƙunci da rashin ƴanci gara a ce ka ƙi zaman auren ma, ai dai ka san kana da cikakken ƴancinka. Shi kuwa Baba bai sake bi ta kanta ba, ya zuba ido ta ga gudun ruwansu. Tsaf ta kwashe karatun da aka biya mata, don haka har ta fara jin tsanar Nazifi shi da auren nasa duka, ta kuma saka a ranta ba za ta koma ba, dole ya sake ta, shiyasa tana kallon kiransa ma ta ƙi ɗagawa, lafiya ƙalau ta shari baccinta sai ta ji kamar dama ba aure ta yi ba, unguwa kawai ta je ta kwana biyu ta dawo gidan babarta mai ƙaunarta. Washegari Nazifi tun safe ya kira ta a waya ba ta ɗauka ba, haka dai ya tafi kasuwa, sai la'asar ya tashi ya dawo gida ya yi wanka ya canza kaya ya tafi gidan nasu, da ita ya fara cin karo bayan ya shawo kwanar kayin nasu, tana tsaye a ƙofar gidan kusa da su, ta yaye hijjabinta ta baya gabaɗaya bayanta a waje, ga shi riga da siket ɗin jikinta sun ɗame ta sosai, tsaye take a kan yarinyar da take soya awarar siyarwa a ƙofar gidan, ta ɗauki ɗaya a cikin ɗan kwandon, ta kai bakinta kenan suka haɗa ido da Nazifi wanda ya tsaya yana kallonta ransa a ɓace cike da takaici. Wani haushinsa ya kamata, ta tsaya tana ƙare masa kallo kamar yadda yake kallonta, Nazifi dogo ne siriri, baƙi ba wani kyakkyawa ba ne, shi ba kuɗi ba, sai yau ma ta ji haushin kanta, ta fara tunanin me yasa ma ta aure shi? Kamar wacce aka yiwa asiri, idonta ya rufe saboda ganin son da yake yi mata. Ta yi tsaki bayan ta karɓi awarar da yarinyar ta miƙo mata, ta juya ta fara tafiya, kamar ba ta san wajenta ya zo ba. Ya bi bayanta yana kiran sunanta, ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ƙarasa ya tsaya a gabanta yana kallonta zuciyarsa cike da sonta, ya ce"Amma Maryam kar ki manta yanzu ke matar aure ce fa, bai kamata ki ɗage hijjabinki haka a titi ba, duk wanda ya kallar mini ke a haka wallahi ya cuce ni". Ta yi masa wata kafirar harara ta ce"Malam me yake tafe da kai?" Ya daure ya yi murmushin yaƙe ya ce"Ango ya zo wajen amaryarsa a tambaye shi dalili? Zuwa na yi mu tafi mana". Ta gyara tsayuwarta ta ce"Nazifi kana son kanka da arziƙi? To ka taƙaitawa kanka wahala ka sake ni, zan faɗa maka a taƙaice, wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe, ko uwata za ta taso daga ƙabari ba zan koma gidanka ba, ka ga wannan bayanin da na yi maka? Indai ba ka fahimce shi ba, to ba za ka taɓa fahimta ba, ka ga kenan ba ni da lokacin ɓatawa wajen sauraronka". Ransa ya ɓaci, a ɗabi'arsa shi mutum ne mai saurin fushi, amma yakan danne zuciyarsa idan yana gaban Maryam, ya ce"Ki yi haƙuri Maryam, indai a kan Gwaggo ne ta amince da wannan sharuɗan da kika kafa da farko, za ta dinga girkinta, kuma ta ce ma za ta kwashe kayanta daga kitchen ɗin". Ta yi wata shegiyar dariya ta ce"Yanzu da kuka ji uwar bari kenan! To sai ka koma ka faɗa mata kun makaro, ita dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa, da ace ka amince tun a lokacin da an yi hakan, amma ka yi sake yanzu auren duka ya fita daga raina, kuma wallahi babu wanda ya isa ya saka ni na ci gaba da yi, don Allah Nazifi idan ba takarda ka zo kawo mini ba kar ka sake zuwa wajena, ni zan fi so ma ka turo min da sakin ta waya saboda ba na son ganinka". Ganin ya daskare ya kasa cewa komai, sai ta yi tsaki ta shige gidan, ya rasa ma me yake yi masa daɗi, me kuma zai ce mata ta yarda ta koma? Ya lura ita ma babarta ba son ci gaban auren take yi ba, don haka ya yanke ba sai ya sake tuntuɓarta ba, kawai sai ya zauna a ƙofar gidan yana jiran Babanta ya dawo, ya saƙa wannan ya ware wancen har aka kira magriba, ya shiga masallaci ya yi, ya dawo ya zauna, babu jimawa kuwa sai ga Baban ya dawo. Ya tashi da sauri, ya rusuna yana gaishe shi, Baba ya amsa yana cewa"Kamar Nazifi ko?" Yana rusunar da kai ya ce"Ni ne Baba". Baba ya ce"Sannu da zuwa". Ya ce"Yawwa". Ya ce"Wajen Maryam ka zo? Ka shigo daga ciki". Nazifi ya ɗan sosa kai ya ce"Ai wajenka na zo, ita mun yi magana tun ɗazu, kai na zauna jira". Baba ya ce"To shigo daga zaure". Suka shiga, Baba ya shiga cikin gidan ya ɗakko tabarma, ya dawo ya shimfiɗa suka zauna, Baba ya ce"Wai mene ne yake faruwa tsakaninku?" Nazifi ya zayyana masa komai, sai Baba ya ji akwai ragi a maganarsa ba kamar yadda Uwani ta faɗa masa har da dukan Maryam mahaifiyarsa ta yi ba, ya ce"Sun sanar da ni, to kai yanzu wane mataki ka ɗauka?" Ya ce"Ita Maryam ɗin tun farko ita ce ta ce ta yarda za su zauna da Gwaggo amma kowa ya yi harkarsa, kowa ya yi girkinsa, to da farko ban amince ba, shi ne abin da ya tada tarzomar, duba da ganin mahaifiyata ce, tana da cikakken iko a gidana, kuma ta cancanci mutuntawa daga matata, amma da na ga hakan ya ƙi kawo maslaha sai na ce na amince da sharaɗin nata, ita ma kuma Gwaggon ta amince, amma dai har yanzu Maryam ɗin ta ƙi ta nuna saki kawai take nema". Baba ya ce"Saki!? Kai ɗan yau ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, ka ga ni fa shiyasa ba na saka baƙincikin ɗan yau a kaina, sai su kashe ka a banza, kuma dama Maryam ta fita da ban da ƴaƴan gidan nan, za ta aikata, auren ma da ya ta yi?" Nazifi ya ce"Sai haƙuri Baba". Baba ya tashi ya ce"Jira ni kaɗan". Ya shiga cikin gidan ya ƙwalawa Maryam kira, har ta tashi Uwani ta mayar da ita ta zaunar tana tsuke fuska ta ce"Malam lafiya?" Ya shigo ɗakin yana cewa"Uwani wannan wane irin shirme ne haka? Ya za ki ɗaurewa yarinya ta samu saken cewa ba za ta koma ɗakin mijinta ba?" Maryam kamar za ta yi kuka ta ce"Baba ni fa wannan zaman ba zai yiwu ba". Ya ce"A kan me? Ba matsalar babar shi ba ce? Ai ya karanta mini komai, ya ce zai bi sharaɗin da kika kafa da farko, ku zauna da uwar tashi ba ruwan kowa da kowa, sai kace wasu facaloli, kai Allah Ya shirya yaran zamani, maza saka hijjabinki ki wuce ku tafi". Uwani ta ce"Haba Malam don ka ga ba ni na haifi yarinyar nan ba, shiyasa ba za ka ƙyale ni na ƙwatar mata ƴancinta ba?" Ya ce"Ko wacce kika haifa ce haka zan yi mata, ni ba na ma taɓa sakawa a raina ba ke kika haifi Maryam ba, tun da ba kya wani abu na nuna bambanci, amma kin san wannan zaman nata ba shi da wata fa'ida". Ya kalli Maryam ya ce"Ba ki tashi kin saka hijjabin ba?" Ta tashi a zabure kamar wacce za ta kai wa wani duka, tana turo baki da haɗe gira ta saka hijjabin ya fita ta bi bayansa, ya ce"Ina akwatin?" Ta ce"Gobe a kawo mini". Uwani takaici ya rufe ta, sai take jin kamar da zuciyarta za ta tafi, sam ba ta so hakan ba, so ta yi a yita ta ƙare, auren nan ya mutu a cikin satin nan, duniya ta shaida. "Maryam!" Ta ƙwala mata kira murya a shaƙe. Ta koma ɗakin tana share hawayen da ya zubo mata, idan ta tuna haka za ta tsufa cikin bauta da rayuwar ƙunci sai ta ji har gara mutuwa a kan gidan Nazifin. Uwani ta ja hannunta har ƙuryar ɗaki ta ce"Ba kuka za ki yi ba, ki koma ɗin amma ki ɗaura ɗamarar yi musu gashin ƙuma shi da uwar tashi, kada ki sake ki saurara musu, musamman ita uwar, saboda idan ta ga abun ba na ƙare ba ne, ita ce za ta saka dole ya sake ki, sannan kada ki sake yarda ku haɗa shimfiɗa, idan kuma kin je kin sakar masa jiki kin samu ciki kin ga kanki kika cuta, ki yi zaman zawarci da ciki". "Ke Maryam!" Muryar Baba ta katse musu tattaunawar. Wannan karon tare suka fito Uwani tana cewa"Allah Ya ba da sa'a Maryam". Suka tarar da Nazifi a zaure, Baba ya ce"Tashi ku tafi Nazifi, Allah Ya rufa asiri". Ya tashi ya naɗe tabarmar yana cewa"To Baba na gode, Allah Ya saka". Ya yi gaba, Maryam ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nisa da gidan suka kusa kai wa titi sannan ya tsaya har ta ƙaraso, saboda su samu damar jerawa. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 6 Yana ɗan murmushi ya ce"Ki yi haƙuri Maryam komai zai wuce in sha Allah!". Ta yi banza da shi. Ya ce"Ni fa ba nufina kawowa Baba ƙararki ba, da na san ma zai tilasta miki ki koma da ban zo ba, na fi so ki dawo mini ta daɗin rai ba dole ba". Nan ma dai ba ta kula shi ba, sai ma ƙara sauri da ta yi, yana biye da ita har suka ƙarasa titi, a ranta tana ayyana zai gane kuskurensa na kafewa sai ya zauna da ita, a cikin adaidaita sahu ma da ya kamo hannunta fizgewa ta yi tana aika masa mugun kallo, ya ce"Kin ce abinci kuwa? Ko na tsaya mu siya?" Ta yi kamar ba ta ji shi ba, sai ya kama kanshi ya ƙyale ta, ya ciro waya ya kira Gwaggo, ya ce"Gwaggo na siyo miki tuwon ko sai na zo na dafa mana wani abun?" Ta ce"La ai ni yau na yi tuwona, ina ka tsaya ne?" Ya ce"Ga ni nan a hanya". Ya ajiye wayar yana kallon Maryam wacce ta haɗe fuska tamkar ba ta taɓa dariya ba, shi mamaki ya ƙi barinsa yadda soyayya take neman rikaɗa ta zama ƙiyayya, sun sauka a bakin titi, sai ya tsaya don ya siya mata wani abun, ita kuwa ba ta jira shi ba ta wuce gidan, a buɗe ƙofar take ta tura ta shiga ko sallama babu, har tana cin karo da kofin sulba da Yasmin ta bari a tsakar gidan, tana jin Yasmin ta ce"Gwaggo kamar wani ya shigo". Gwaggo ta ɗan ɗaga murya ta ce"Wane ne a nan?" Ta ce"Ƙila tumakai ne, je ki kora su". Haushi ya kama Maryam, wacce ta ja ta tsaya a ƙofar ɗakinta, saboda mukullin yana wajen Nazifin, Yasmin ta fito ta haskata da fitila ta ce"Au!" Sai ta koma ta ce da Gwaggo"Maryam ce fa ta dawo". Gwaggo ta ce"Au kuma shi ne babu sallama?" Daga nan Nazifi ya shigo da sallama, Gwaggo ta amsa daga ɗaki, ya ƙarasa wajenta ya miƙa mata ledar hannunsa guda ɗaya, ta kau da kai gefe ba ta karɓa ba, sai ya ajiye su a ƙasa ya ciro mukulli ya buɗe mata ɗakin, ta shiga, ya ɗakko ledar ya ajiye mata ɗaya, ya ɗauki ɗayar ya shiga ɗakin Gwaggo, ya zauna yana cewa"Sannu da gida". Ta ce"Yawwa, ashe ɗakkota ka yi". Ya ce"E wallahi, kun gaisa?" Gwaggo ta ce"Ba ta shigo ba". Ya ce"Bari na kira ta". Ta ce"Nazifi ba na son tada zaune tsaye, me gausuwarta za ta yi mini? Tun kafin a haife ta ake ta gaishe ni, kuma har yau ban rasa masu gaishe ni ba". Ya ce"Ki yi haƙuri Gwaggo". Ta ce"A'a haƙuri ita ya kama ai, ga tuwonka nan" Ta ƙarasa tana miƙa masa kulolin da suke ajiye a gefe. Ya ce"Bari na yi sallah tukunna, kin ga har an shiga". Ya fito ya yi alwala ya tafi masallaci. Kafin ya dawo Maryam ta fito ta yi alwala ta yi sallah, ta rufe ƙofarta, ta saka sakata, ta ɗauki ledar, tsire ne a ciki da lemon jarka, ta cinye tass ta sha lemon ta kwanta, tana ta tsara nau'in wulaƙancin da za ta fara aiwatarwa a gidan har bacci ya ɗauke ta. Shi kuwa yana dawowa daga masallaci ɗakin Gwaggo ya shiga, ya zauna suna fira yana cin tuwon, har tara ta gota, sannan ya tashi ya yi mata sai da safe. Ya ga Maryam ta rufe ƙofa bai kawo komai ba, a zatonsa turo ta kawai ta yi ba ta saka sakata ba, amma sai ya tura ya ji ta a rufe, da mamaki ya fara ƙwanƙwasawa ya ji shiru, ya fara kiran sunanta ƙasa-ƙasa don kar Gwaggo ta jiyo shi ta gane halin da ake ciki, ƙarshe ya kira wayarta tana ta ringin ba ta ɗauka ba, ya rubuta mata gajeren saƙo ya ce"Don Allah ki buɗe kar a fahimci wani abun". Shiru babu amsa, da ya sake kira ma sai ya ji wayar a kashe, haka ya shige falo ya rufo ƙofar ya kwanta da kayan jikinsa, a ransa yana ta mamakin kalar zuciyarta, da ƙyar bacci ya ɗauke shi. Da asuba da ya dawo daga masallaci ya yi zaton zai ga ɗakin a buɗe, amma sai ya gan shi a rufe, har ya yi tunanin ko ta makara ne? Sai kuma ya ga alamar ruwan alwala a takalminta da yake ƙofar ɗakin, ya jinjina kai ya shiga falon ya zauna, yana ta saƙa da warwara har gari ya waye, ya ji motsin Gwaggo ta fito hura wuta, sai ya fito ya gaishe ta, ya kalli ƙofar ɗakin har yanzu ba ta buɗe ba, ita ma Gwaggo ta kalli ƙofar don a zatonta yana ciki bacci suka koma, ta bi shi da kallo ganin ya koma falo. Har takwas ta gota Maryam ba ta buɗe ƙofa ba, shi kuma wanka yake so ya yi ya canza kaya ya tafi kasuwa, ya kira wayarta, yanzu ta shiga amma ba ta ɗauka ba, ya yi mata text ya ce"Maryam wai mene ne haka? Ki buɗe mini ƙofa mana, wanka zan yi na tafi kasuwa". Can anjima ya ji ƙarar buɗe ƙofar, yana fitowa yana banko ƙofar ta rufe, ya bi kayan da ta jeho waje da kallo, duka jakar kayan shi ne, dama bai samu nutsuwar jera su a cikin sif ɗin ba, mamaki ya daskarar da shi, sai ya yi saurin ɗaukar jakar ya shige falo don kar Gwaggo ta fahimci wani abu, ya ajiye ya fito ya yi wanka ya canza kaya, ya shiga ɗakin Gwaggon, ta miƙo masa kofin kunu da ɗumamen tuwo a roba, ya ce"Alhamdulillah Gwaggo". Ta yi masa wani kallo ta ce"Kana nufin haka za ka fita ba ka ci komai ba? Ko teburin mai shayi za ka je?" Tun da ta ce hakan ya san ta gane wani abu a tsakaninsa da Maryam, don haka ya sha kunun, ya ba ta ɗari biyar ta yi cefane ya yi mata sallama, ya tafi, ta bi shi da kallon tausayi don zuwa yanzu ta gama saddaƙarwa ɗanta bai yi dacen mace ta gari ba, tana fatan idan da alkhairi a zaman nasu Allah Ya daidaita, idan kuma babu alkhairi Allah Ya kawo rabuwar cikin sauƙi, amma ta ji haushin rufe ƙofar da aka yi wa ɗan nata mai haƙuri. Ransa babu daɗi ya je kasuwa ya kama harkokinsa, komai yake yi yana tunanin me zai yi ya shawo kan Maryam su daidaita? Saboda yana sonta shi bai shirya rabuwa da ita ba, ko sati ba a yi da aure ba a ce a rabu? Sau ɗaya rak suka haɗa shimfiɗa da ita, kenan duk kuɗin da ya kashe daga neman auren zuwa auren ya yi asararsu a banza? Gaskiya ba zai yiwu ba, ko ta kama dole zai rabu da ita sai ya mori kuɗinsa tukunna. Maryam sai ƙarfe goma ta fito, shi ma yunwa ce ta fito da ita, ta ga Gwaggo a tsakar gida tana wanke wake, don gyara shi take yi ta yi garinsa saboda yin ƙosai da safe, kallo ɗaya ta yi mata ta ɗauke kai, ta shige kitchen, ita ma Gwaggon ba ta kula ta ba, ta tsaya tana ƙarewa kitchen ɗin kallo, babu sauran kayan Gwaggo a ciki, ta ƙarasa ta dafa shayi da indomi, ta gama ta fito ta koma ɗaki, yanzu ta bar ɗakin a buɗe, tana gama karyawa ta fito ta share iya ƙofar ɗakinta, sannan ta shiga wanka da guntun tawul ko kunyar Gwaggo ba ta ji ba a matsayinta na surukarta sai ma ita ce ta kau da kai, tana Allah Ya kyauta a zuciyarta. Tun da ta shiga ɗaki ba ta fito ba sai azhar ta fito za ta yi girki ta ga babu kayan miya, ta saka hijjabi ta je ta fita, ta yi ta yawo a unguwar har ta samu inda ake siyarwa ta siyo ta koma gida, daidai lokacin Nazifi ya sauka daga adaidaita, hannunsa ɗauke da ledar cefane, da bai yi niyyar kawo mata cefanen ba saboda abin da ta yi masa, sai kuma ya duba ya ga ai haƙƙinsa ne, ya kamata shi ya sauke nashi ko da ita tana tauye masa, kuma maslaha yake nema bai kamata ya yi abin da za a ce ga laifinsa ba, shiyasa ya yo cefanen, sai kuma ya ganta a waje. Kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kai za ta shige gidan, ya tare hanya yana cewa"Maryam daga ina kike?" Ta harare shi za ta gota ta gefen shi ta wuce, ya ce"Tambayarki fa nake yi, ina kika je babu neman izini?" A fusace ta ce"Kenan ba ka yarda na gama aurenka ba, shiyasa har kake tunanin idan zan yi wani abu sai da izininka!". Yana saita ɓacin ransa ya ce"Mu shiga mu yi magana". Ya matsa ta shige, ɗakin nata ya dosa, yayin da ita kuma ta shiga kitchen ta fara gyara kayan miya, ya na ta zaune yana jiran shigowarta ya ji shiru, sai da ya ji ta fara daka sannan ya fito ya shiga kitchen ɗin ya tsaya yana kallonta, ta gama dakan ta ɗauku ruwan da ta wanke kayan miyan ta watsa masa da gayya, ya matsa gefe yana cewa"Subhaballah! Mene ne haka? Maryam ƙalau kike kuwa?" Ta ce"Gobe ma Gwaggon zan watsawa shi". Nan ransa ta ɓaci ya ce"Ke Maryam kar fa ki ga ina lallaɓa ki, ki yi zaton za ki taka mahaifiyata na rabu da ke..." Ta katse shi da faɗin"Ai ban ga alamar ka san darajarta ba, kuma wallahi ko ita ce ta zo ta yi mini tsaye a kai sai na watsa mata". Ya ce"Me kike so da ni?" Ta ce"Ka sake ni!". Ya ce"Ba zan sake ki ba, ki ma daina wannan tunanin, don ba sadaƙa aka ba ni aurenki ba". Ta ci gaba da aikin gabanta, ya ce"Wallahi ban yi zaton haka daga gare ki ba, na faɗa miki indai Gwaggo ce ta ce kowa ya yi sabgarsa, ba ki ga ta kwashe kayanta ba ma ta bar miki kitchen ɗi ba?" Ta yi banza da shi. Ya ce"Jiya kika kulle ƙofa, idan Gwaggo ta gane hakan kin ga ba za ta ji daɗi ba, sai ta ga kamar har yanzu ba ma zaman lafiya, ko me za mu yi don Allah kar ki sake yi mini haka, mu yi abun mu a ɗakinmu mu biyu". Nan ma dai ba ta kalle shi ba. Ya ce"Kenan kayan miya kika siyo? Ki yi haƙuri ai ga shi ma na siyo miki, bai kamata ki fara fita tun yanzu ba, har gara ki aiki Yasmin". Ya ce"Mun shirya ko? Me kike dafa mana?" Ganin dai da gaske ba za ta kula shi ba sai ya fice daga kitchen ɗin, ya shiga ɗakin Gwaggo yana cewa"Bari na koma, cefane na kawo mata". Cike da tausayin shi ta ce"Allah Ya tsare". Da ta gama girkin ta juye a kula ta kai ɗaki, dama iya cikinta ta dafa wanda zai ishe ta har dare, ta ci ta ƙoshi, ta kira babarsu a waya suna ta fira, tana ba ta labarin abin da ya faru tsakanin jiya zuwa yau, ta ƙara zugata sosai ta ce ita ma Gwaggon ta fara taɓa ta don sai ya fi fusata. Da magriba da ya dawo ya shigo ɗakin, ya ƙaraci surutunsa ba ta ce masa ƙala ba, sannan ya tambayi abinci ba ta ba shi ba, har aka kira isha'i yana zaune, yana tafiya masallaci, ta fito ta yi alwala ta sakawa ɗakinta sakata, da ya dawo ya ga ta rufe ƙofar sai da gabansa ya faɗi, ga shi ba ya son ya cikata da bugun ƙofa har Gwaggon ta gane, sai ya shiga ɗakin nata, ya zauna shiru, ta ce"Nazifi ka ci abinci kuwa?" Ba don yunwar yake ji ba da zai yi ƙaryar ya ci, sai ya girgiza kai alamar a'a, ta miƙo masa kula tama cewa"Shiyasa na dafa muku shinkafa kai da Yasmin". Ya ɗauka ya ci, ya gama ya zauna shiru, yau ya kasa taya ta firar ma, saboda hankalinsa ba ya kanta, yana can wajen tunanin mafita a wannan auren nasu, har tara ta yi, ta ce"Ka je ka kwanta mana Nazifi, na ga kamar ba ka jin daɗi ko?" Ya ce"To sai da safe". Ya tashi ya fita, ya je a hankali yana buga ƙofar ɗakin, wanda Gwaggo tana ji, dama ta na son tabbatar da jiya a falo ya kwana, don haka ta leƙo kaɗan, ta kuwa gan shi tsaye, can kuma sai ya juya ya shiga falon ya rufe ƙofa, ita ma ta rufe ƙofarta tana jin tausayin shi, sai ta ji nadamar zuwa gidan tun farko, da ta sani ta yi zamanta a gidanta ƙila da haka ba ta faru ba. Washegari ma haka ce ta faru, da safe a ɗakin Gwaggo ya karya ya fita, ƙarfe tara Maryam ta fito ta gama karyawa ta shiga kitchen tana wanke-wanke, ta gama ta fito da ruwan, ta samu Gwaggo duƙe tana sharar tsakar gidan, ta ɗaga ruwan ta sheƙo shi duka a kanta, Gwaggo da ta samu saukar ruwan babu zato firgita ta yi, ta ɗago da mamaki take kallon Maryam, Yasmin kuwa salati ta rafka har da ɗora hannu a ka, ta ce"Kai Gwaggon kika watsawa ruwa?" Ita kuwa Maryam kamar wata makauniya kuma kurma haka ta koma kitchen ɗin ta fara sharewa, ta gama ta zo ta wuce ɗaki, har lokacin Gwaggo tana tsaye mamaki ya daskarar da ita, ta jinjina ki ta shiga ɗaki ta zauna jaɓar, saboda ba za ta iya ƙarasa sharar ba, a ranta tana ta tunanin wace irin mara kirki Nazifi ya kawo cikin rayuwarsa? Yasmin ta ce"Ruwa fa ta watsa miki Gwaggo". Gwaggo da zuciyarta take a kumbure ta ce"Babu komai Yasmin". Ta shiga haɗa kayansu, ta ɗauki waya ta kira lambar babban ɗanta Shazali, suka gaisa ta ce"Don Allah zan iya samun ɗaki a gidanka ko na sati ɗaya ne?" Ya ce"Gwaggo kamar ya? Mai zai hana? Ai ke kika ƙi tun farko". Ta ce"To ga ni nan zuwa". Ta ajiye wayar, tun da Shazali ya gina gidansa ya ware ɗaki ɗaya har banɗaki ya yi a ciki ya ce nata ne, amma ta ƙi zama saboda tunanin Nazifi bai yi aure ba ba za ta koma wani gidan ta bar shi ba, kuma ba za ta so ya koma gidan yayan nashi da zama ba, daɗin daɗawa ita ba ta son nisa da Nazifin ta fi son zama a gidansa, saboda shi ya fi kwanta mata a zuciya duk cikin ƴaƴan nata, ashe hatsabibiyar matarsa ba za ta bari burinta ya cika ba. Ƙatuwar akwatin kawai ta ɗauka, ta rufe ɗakin suka tafi, Maryam tana leƙe ta gefen labule ta ga sanda ta ja akwatin suka fice, ta yi wata shegiyar harara tana cewa"Da kika ce za ki jure!". Bayan sallar magriba Nazifi ya dawo daga kasuwa, da mamaki ta fara cin karo, na ganin ƙofar ɗakin Gwaggo a rufe, ya san ko ba ya nan idan za ta je unguwa tana faɗa masa, ya kalli ƙofar ɗakin Maryam ya gan shi a buɗe, sai ya ƙarasa ya ɗaga labulen, tana zaune tana chart, ya ce"Maryam unguwa Gwaggo ta tafi?" Ta ce"Dama ajiyarta ka ba ni? Ko ita ƙaramar yarinya ce da zan saka mata ido a kan shige da ficenta?" Ya ce"Ke dakata! Maryam kin fa fara fusata ni a kan mahaifiyata, wallahi kar ki yarda ki kai ni bango!" Ya yi ƙwafa ya saki labulen. A tsakar gidan ya tsaya ya kira lambarta, ta ɗaga ya gaishe ta kafin ya ce"Gwaggo unguwa kika je ne?" Ta ce"E Nazifi ina gidan shazali". Ya ce" Ba ki taho ba? Ba na son kina kaiwa dare a waje". Ta ce"Ai a can zan kwana, gobe idan Allah Ya kaimu sai ka haɗo sauran kayana ka kawo mini nan ɗin, don hakan zai fi". Gabansa ya faɗi ya ce"Gwaggo me hakan yake nufi? Me ya faru?" Ta ce"Idan ka zo goben ka ji". Ta kashe wayar, ya kasa zama, ya fice daga gidan yana fatan Allah Ya sa ba Maryam ce ta yi mata wani laifin ba. Ya shiga gidan, suka gaisa da matar yayan nasa, a tsakar gida ya tarar da yara suna cin abinci, Yasmin ta yi farat ta ce"Yaya Nazifi ka dawo? Mun dawo nan da zama, matarka ce ta watsawa Gwaggo ruwan wanke-wanke, ta hiƙewa jagab!" Wani tashin hankali ya rufto masa, ya ce"Ruwan wanke-wanke!?" Yana zazzare ido kamar yarinyar ce ta yi masa laifin. Ya shiga ɗakin da aka ce masa Gwaggon tana ciki, tun kafin ya zauna ya ce"Gwaggo da gaske ruwa ta watsa miki?" Ta ce"Zauna Nazifi". Ya ce"Ina zuwa". Ya fice daga gidan cikin sauri, a hanya sai ya kasa haƙuri, kawai ya ciro wayarsa ya rubutawa Maryam gajeren saƙo "Na sake ki saki ɗaya". Tana cikin chart ta ga shigowar saƙon, gabanta ya ba da rass, kafin kuma farin ciki ya biyo baya, ta tashi ta zauna ta ƙara tashi, ta ma rasa me za ta fara yi, ta ina za ta fara haɗa kayan? Sai ta kira lambar babarta a waya, tana ɗagawa ta ce"Albishirinki!" Ba ta jira amsarta ba ta ce"Ya gaji ya sake ni!". Uwani ta miƙe tsaye cike da farinciki ta ce"Alhamdulillah! Ƴata ta rabu da ƙaya ta samu ƴancinta, maza tashi ki haɗa wata akwatin, dama ga wata a nan, gobe tun safe za a siyar da kayan ɗakin nan". Maryam ta ce"Ina sha Allah! Wallahi sai na ji kamar an cire mini wata ƙaya". Uwani ta ce"To ai irin wannan auren sartse ne, idan kika rabu da shi dole ki ji haka". Ta ajiye wayar ta shiga haɗa kaya. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 7 A zuciye sosai Nazifi ya ƙarasa gidan, ko sallama bai yi ba ya banka ɗakin Maryam, ba ta ɗago ta kalle shi ba ta ci gaba da aikinta ranta fess, ya ce"Ke Maryam akan wane dalilin kika watsawa babata ruwan ƙazanta?" Ta ɗago tana hararar shi cike da tsiwa ta ce"Ƙila tare mini hanya ta yi". Tass! Ya ɗauke ta da wani zazzafan mari, ta tsaya tana mamaki ya ƙara sauke mata wani, yana nunata da yatsa a fusace kamar zai tsokane mata ido ya ce"Wallahi uwata ta fi kowa a wajena, ke ba ki kai wacce za ta wulaƙanta uwata ba, duk duniya ma babu indai ina raye ina kuma da ikon rama mata..." Ta katse shi da faɗin"To ai ba ka rama mata ba, wanke-wanke za ka yi ka watsa mini ruwan na yi tsumu-tsumu kamar an tsoma kaza a ruwa shi ne zan san ka rama mata". Tana rufe baki ya naushi bakin nata, ya ce"Wallahi ni dai na yi asarar kuɗi da lokacina wajen aurenki, maza ki tattara gayyar tsiyarki ki bar mini gidana". Har ya juya zai tafi, sai kuma zuciya ta ciyo shi, ya tuna yadda ya dinga sintiri a ƙofar gidansu yana yi mata wahala, yana yi mata ladabi kamar uwarsa, ya tuna kuɗin da ya kashe a kayan lefe, da shagalin bikin, da ya san wacce zai aura ai da a kasuwa ya saka kuɗin ya ƙara jari ya ciji leɓe, sannan ya dawo kamar an jeho shi, tana duƙe tana haɗa kaya, ya yi mata wani dundu a bayanta, sannan ya rufe ta da duka ta ƙo'ina yana cewa"Wallahi sai na daki kuɗina, ƴar wahala wacce ba ta san halacci ba!". Maryam ma ta taso tana kai masa duka daidai iya ƙarfinta, sai dai ƙarfin ba ɗaya ba ne, idan ta dake shi ma ita ce take jiggata hannunta saboda ƙaƙƙarfan ƙashi kawai take duka, don haka cikin ƙanƙanin lokaci Nazifi ya yi mata lilis ya tara mata gajiya, fuskarta kuwa har ta kumbura, dama naushin da ya yi mata bakinta ya fashe, bai bi ta kan ashar ɗin da take ƙundumawa Gwaggo ba, ya fice daga gidan, saboda idan ya biyewa zuciya sai ya kashe ta, tun da ta lura bakinta ba zai yi shiru ba. Kuka sosai Maryam ta ci kafin ta saka hijjabi ta tafi gida, don fasa haɗa kayan ma ta yi, yana daga runfar maƙotansu a zaune, dama jira yake yi ta fice ya zo ya rufe gidan, sai da ta yi nisa sannan ya shiga, sai ya ga kayan duka a baje ba ta haɗa ba, nan ya yi tozali da tarin kayan lefen da ya haɗa mata, zuciya ta faɗa masa ya ragewa kansa zafi a kansu, ai kuwa ya ɗauki atamfofi guda biyar, leshi guda biyu, ya kwasarwa Yasmin kayan kwalliya, sannan ya rufe ɗakin ya tafi gidan Gwaggo, a hanya ya tsaya ya samu leda ya zuba kayan, ya zauna a gaban Gwaggo cike da kunyar abin da matarsa ta yi mata ya ce"Gwaggo don Allah ki yi haƙuri, na ja miki tozarci, wallahi inda na san haka za ta faru da tun farko ma ban yi auren nan ba". Gwaggo ta ce"Ba komai Nazifi, kowa da irin halinsa, ba ga shi na bar mata gidan ba? Yanzu sai ku zauna lafiya". Ya ce"Haba Gwaggo, ai ko ita ta gwal ce wallahi ba za ta yi miki wannan abun na iya ƙara kwana ɗaya da ita ba, na sake ta". A ranta ta ji daɗin yadda ɗanta ya nuna tana da muhimmanci a wajensa, ta ce"Na gode Nazifi, Allah Ya shi albarka, amma da ba ka rabu da matarka ba, tun da na tafi ƙila ku ci gaba da zaman lafiya, dama fa ba lallai ne sai matarka ta so danginka ba, wata nagartar tata za ka duba sai ka yi haƙuri da wani halin nata". Ya ce"Haba Gwaggo ina nagarta ga wacce za ta iya wulaƙanta mahaifiyarka? Ba fa zama za ki yi a gidan nan ba, kin ga idan sun gama kwashe kayanta sai ki koma, ba na son su zo wani ya ganki ya zage ne, amma da a yau ɗin za ki koma, gara na haƙura da auren matuƙar za ki zauna lafiya". Ta yi murmushi ta ce"Ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,nan gaba sai ka ga ka samu wacce za ta bi ra'ayinka". Ya ce"To Allah Ya sa, ga wannan kayan Gwaggo kya ɗinka". Ta karɓi ledar da ya miƙo mata, tana cewa"To daga ina kuma? Na ga sallah da saura". Ya ce"Na lefen yarinyar nan ne, na kwaso saboda na rage asara". Gwaggo ta yi ƴar dariya ganin yadda ya yi maganar bil haƙƙi, ta ce"Nazifi kenan, idan ka yi wani abun sai ka ce yaro ƙarami, yanzu dai ka san wannan wata fitinar ka siyo ko? Lefenta ai haƙƙinta ne ka je ka mayar mata, ni ba yafe". Zai yi magana ta ɗaga masa hannu ta ce"Ka je ka mayar". Ya ce"To". Daga nan suka shiga fira, ta ba shi abinci ya ci, sai tara da rabi ya koma gida, washegari da safe ya haɗa kayan shi ya saka a ɗakin Gwaggo ya kulle, ya ɗauki kayan da ta ƙi karɓa ya tafi da su kasuwa, sai ya bawa wani mai kanti dake kusa da su mukullin gidan, ya ce idan wasu sun zo ya ba su. Ita kuwa Maryam da kuka sosai ta shiga gidan nasu, lokacin Baba yana tsakar gida yana cin abinci, Uwani da take ta jiran dawowar tata ta miƙe tana rafka salati kamar ba ta san komai ba ta ce"Ba dai yaron nan sakinki ya yi ba?" Baba ya yi mata wani kallo bai ce komai ba, tun da ya san dama sakin suke so. Maryam ta shige ɗaki tana ƙara sautin kukanta, Uwani ta mara mata baya, tana cewa"To ai ya isa haka, na ji daɗi da kika shigo da kukan kissar nan wallahi, kin ga babanki zai ce ba da son ranki komai ya faru ba". Ganin Maryam ta ƙi daina kukan kuma ta ƙi ɗagowa sai ta sha jinin jikinta, ta ce"Maryam to ko dai kina son mijinki?" Sai a lokacin ta ɗago, Uwani ta yi arba da kumburarriyar fuskarta, ta ce"Innalillah wa inna ilaihi raji'un! Faɗuwa kuka yi a adaidaita sahun?" Tana kuka ta ce"Dukana ya yi". Uwani ta ji daɗi a ranta, ta ce'Allah Ya ƙara, kaɗan ma kika gani'. A fili kuwa ta ce"Duka!? Duka dai wanda na sani?Me kike yi da ba ki ɗauki turmi kin rotse shi ba?" Sai ta yi waje tana"Malam! Mun shiga uku...". Baba ya katse ta da faɗin"Kun shiga uku dai". Ta ce"Shigo ka ga fuskar yarinyar nan, bayan sakin da ya yi mata, har da yi mata dukan kawo wuƙa, fuska ta kumbura kamar an saka mata yis". Baba ya ci gaba da cin abincinsa bai ce komai ba. Ta ce"Ga duka ga tsinka jaka? Wallahi ba zata saɓu ba bindiga a ruwa, sai na bi mata kadinta!". Ta shiga ɗakin, ta tashi Maryam zaune tana cewa"Bar kukan haka, wallahi sai na ƙarti daidai da shi sun yi masa duka, ke dai tun da kin rabu da ƙaya Alhamdulillah!". Ta fita ta kunna wuta, ta ɗora ruwan zafi, daidai nan Sunusi ya shigo, Baba kuma ya fita, ko sallamar da ya yi ba ta amsa ba, ta tare shi da faɗin"Sunusi ka ga abin da wannan tambaɗaɗɗen yaron ya yi wa ƴar'uwarka? Ya yi mata dukan mutuwa sumanta uku, kuma ya sake ta, da ƙyar ta kawo kanta gidan nan tana jiri tana faɗuwa". Ya ce"Subhanallah! Ya sake ta kuma? Ko fa sati ba a yi da auren ba, gobe Lahadi shi ne zai cika sati ɗaya cif". Uwani ta ce"Ubanka kai da satin, ina maka zancen duka wato kai mutuwar auren ce ma ta dame ka!". Ya ce"To babarmu kin san wane tudu da gangare suka hau har ya dake ta? Kin san fa Maryam ba ta da kunya, ƙila zagin shi ta yi". Ta ce"Kai dalla gafara, kar na gwabje ka, ashe dai bayan raina ba za ka iya ƙwatarwa ƙannenka ƴanci ba, Allah wadaran naka ya lalace". Sunusi ya buɗe ɗakinsa ya shige, ita so ta yi ya fusata ya kwashi abokansa a daren su je su yiwa Nazifi duka, ashe ba zai iya komai ba. Sai da ruwan ya yi zafi sosai sannan ta juye a baho ta kai banɗaki, ta shiga ɗakin ta taso Maryam ta ce"Maza ki je ki yi wanka, ki gaggasa jikinki sosai da zani, idan ba haka ba ba za ki iya bacci ba, Allah Ya saka miki". Maryam ta yi wanka, ta zuba mata abinci ta ci, ta kwanta nan take kuwa sai bacci ya ɗauke ta. Washegari Uwani ta kira ƙawayenta da maƙota suka je suka kwashe kaya tass, a ranar kuwa ta siyar da su aka ajiye kuɗin. Sai bayan kwana biyu da Maryam ta nutsu sannan ta gane an kwashi wasu daga cikin kayan lefen, amma dai ta yi shiru ba ta ce komai ba, don ta fi tunanin a cikin masu kwaso kayan ne wata ta ɗiba. Nan fa ta gyara zaman idda, ta manta da ta taɓa rayuwa da Nazifi, kullum Uwani ƙara koyar da itw darussa take yi, ita kuma tana kwashewa tana adana su a kanta, a haka har ta gama iddarta, ta ɗiɗɗinka kayan lefenta, tana shiga tana fita, sai Uwani ta ba ta shawarar ta fara sana'a don zawarci sai da sana'a, da fari Baba ya hana ya ce ba za ta yi ba, to akwai ƙawarta da take siyar da abinci a tashar kusa da layin nasu, Maryam sai ta tsiri cin kwalliya ta je ta zauna kawai a wajen, suna kwashewa da maza, Baba ya yi faɗan har ya watsar, ƙarshe abokinsa ne ya ba shi shawarar gara ma ya barta ta fara sana'ar don a san zaman tashar nata mai dalili ne, don haka ya barta, ta fara dafa shinkafa da taliya tana kaiwa tashar, uwar kwalliyar da take ci da tsaftarta, uwa-uba kuma yadda take ƙawata abincin, da yadda take sakin baki su yi ta fira da maza shi yake ƙara janyo mata hankulan maza, da ta fito za ta siyar ta koma gida, ta ƙirga ribarta cass ta adana, nan da nan kuwa zawarawa suka fara tururuwar zuwa wajenta, amma sai Uwani ta nuna mata kar ta sake ta ce za ta yi aure yanzu, ta bari sai ta tara wani abu tukunna, don haka duk wanda ya zo da zancen aure sai ta saita masa hanya, wanda kuma dama su ƴan a bi yarima a sha kiɗa ne, ƴan rage dare sai ta yi ta cin kuɗinsu, amma hakan ba ya saka ta bawa wani jikinta, sai dai ta yi ta maka wayo, har ka gaji ka kama gabanka. Ta kusa shekara a gida, ta haɗu da wani Hamza, lokaci ɗaya ta ji tana ƙaunar shi, kuma za ta iya auren shi, don haka duk yadda Uwani ta so nuna mata ba yanzu ba, ba ta yarda ba, ƙarshe dai ta rabu da ita, suka sasanta tsakaninsu, babu jimawa Hamza ya turo manyansa, bayan gabatar da bincike an ga ba shi da matsala aka saka ranar aurensu wata biyar, suka ci gaba da soyayyarsu suna kuma shirin aure. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 8 A wannan karon Uwani ta dage sosai wajen yiwa Maryam karatunta, ta riga ta gama hawa gada ɗoɗar, ta yarda zawarci ba komai ba ne, don haka ba za ta ɗauki raini ko tauye haƙƙi daga wajen miji da danginsa ba, tun da miji goma ba uba goma ba ne. Kusan rabin kayan ɗakin da kuɗinta ta yi shi, Hamza bai yi lefe ba, kuɗi ya bayar ta sayo kaya ta ɗinɗinka, aka ɗaura aure aka kai amarya ɗakinta, gida ne madaidaici, mai ɗauke da babban falo da ɗakuna uku a cikinsa, sai kitchen da banɗaki, gidan ya yi kyau babu laifi komai fess. Maryam tana son shi, don Hamza ɗan soyayya ne, sosai take tarairayarta hakan ya ƙara mata ƙaunar shi a zuciyarta, kuma ƴan'uwan shi ma suna sonta suna ba ta kulawa da janta a jiki, don sai da ta yi sati ɗaya ta fara girki, tun washegarin ranar da aka kaita ake aiko musu abinci daga gidansu, fal kula su ci su zubawa baƙi, na safe kawai take yi, ga gararta da ta zo da ita, cefane kawai yake yi a yi lafiyayyen girki. Uwani tana ta baza kunne da ido ta ji ta inda matsala za ta ɓullo ta ji shiru, ta sha ƙara jaddadawa Maryam idan da matsala fa kar ta ɓoye ta cuci kanta, amma sai ta ce mata lafiya ƙalau suke zaune, takaicin duniya ya ishe ta kuwa, kullum da lamarin take kwana. Watan Maryam ɗaya a gidan ta samu ciki, mai masifar laulayi kuwa, ga kwaɗayi sosai, sai ta ce a siyo mata abu idan aka kawo kaɗan za ta ci ta fara kwara amai, ga muguwar kasala ta sa kwalliyar ma ta daina yi, kuma ta tsani Hamza ya matso kusa da ita, sai ta ji ba ta son warin jikinsa ko da kuwa yanzu ta fito daga wanka, indai za su kasance to fa sai ta yi ta kwara amai, ƙarshe sai take komawa wani ɗakin ta kwana, tun Hamza yana daurewa har abun ya fara ba shi haushi, duk wata ƴar soyayya da kulawa ta daina ba shi. Watarana ya sameta kwance a ɗaki, yana haɗe rai ya zauna ya ce"Tashi za mu yi magana". Ta tashi tana kallon shi, ya ce"Maryam na ga wannan cikin yana wahalar da ke, kalli yadda duk kika rame kika zama wata iri, duk kin kojale..." Ganin yana maganar yana taɓe baki kamar mai ƙyamarta ta katse shi da faɗin"Hamza! Ni kake cewa na kojale? Kar fa ka manta ko me ya same ni sanadin cikinka ne, dama na lura wani kallon rainin hankali kake yi mini kwana biyun nan!". Ta ƙarasa maganar a hasale. Ya ce"Kin ga ni ban ce ki ɗaga mini murya ba, masalaha ce na zo da ita". Ta yi shiru tana sauraron shi . Ya ce"Maryam kin ga fa har yanzu ba a yi wata biyu da aurenmu ba, ɗan amarcin nan ba mu ci ba, ni da na so a ce matata sai ta yi shekara ɗaya ko wata shida haka kafin ta samu ciki, kin ga lokacin an ci amarci an fara marmarin samun ɗa ko ƴa, amma yanzu kalle ki fa don Allah, ni yanzu a shawarata kawai a cire cikin nan, tun da ba ƙwari ya yi ba, sai na siyo miki ƙwaya ki dinga amfani da ita, idan aka kwana biyu kika huta kamar nan da wata shida haka sai ki ɗauki wani cikin, don ni gaskiya yanzu duk na takura gidan ma ba daɗi yake yi mini ba". Haushi ya kamata ta ce"Ka gama?" Ya ce"Na gama". Ta ce"Hamza ashe haka kake ba ka da kirki ba ka san ya kamata ba? Yanzu idan da tausayi ina ta wahala da cikinka za ka kalle ni ka ce na cire shi? To bari ka ji na faɗa maka, ko cikin shege na yi ba zan cire shi ba sai na haife shi, ballantana na halak, idan ka ga ba za ka iya zama da ni a haka ba ka sallame ni, ba a kanka na fara rabuwa da miji ba, miji goma ba uba goma ba ne!". Tun da ta furta masa ba shi da kirki ya kafe ta da ido cike da mamaki, duk da ya san Maryam ko a wajen siyar da abinci ba kanwar lasa ba ce amma bai yi zaton za ta iya kallon mijinta ta ce masa ba shi da kirki ba, ya ce"Kina cikin hayyacinki kuwa? Ni ne ba ni da kirki?" Tana yi masa wani mugun kallo ta ce"Akwai ƙarshen rashin kirkin da ya fi wannan? Ina fama da cikinka a maimakon ka tausaya mini sai ka ce a cire?" Ya ce"Kin ga, ni fa ba tausayinki ne ba na yi ba, kawai dai dama can na tsara idan na yi aure matata ba za ta haihu da wuri ba". Ta ce"To da ka san haka me ya hana ka zuge tazugen wandonka? Ai ka ga da ba zan ma samu cikin ba ballantana ka ce a zubar na ƙi". Ya yi shiru ya rasa abun cewa, ta ce"Hamza! Na aureka ne saboda ina sonka, wallahi son da nake yi maka ba zai saka na ɗauki wulaƙanci daga gareka ba, idan ka san ba za ka iya ba tun wuri ka sallame ni, na je na raini cikina a gaban iyayena". Tsaki kawai ya yi ya tashi ya fita. Yana fita kuwa ta ɗakko waya, ta kira babarta ta juye mata komai, Uwani a zaune take amma sai da ta miƙe tsaye, a ranta tana faɗin 'lokaci ya yi' Ta ce"Innalillahi! Ke dai Maryam ba kya dacen mazan aure, shi kuma ba ya son haihuwa? To ai har gara ma Nazifin shi matsalar babar shi ne, shi fa miji da ba ya son haihuwa ya fi uban kowa matsala a rayuwar aure, kin ga wannan maganar ma ai ba ta waya ba ce, gobe zan zo mu baje ta a faifai, ina! Ai ba ki ga wajen zama ba". Maryam ta ce"To Allah Ya kaimu". Haka kuwa aka yi, washegari da yamma ta je gidan nata, tana ganinta ta fara salati tana tafe hannu ta ce"Maryam kin ga yadda kika zama kuwa? Kamar wata horuwa! Mun shiga uku, nan duk cikin ne babu yunwa?" Ba ta ce komai ba, ta gaishe ta ta kawo mata ruwa da abinci, ta ce"Ai Maryam ba zan iya cin komai ba, wai me ma kika ce mini? Har ya ce a cire cikin?" Ta ce"Haka ya ce, ni kuwa babu mai saka ni na cire cikin nan wallahi!". Uwani gabanta ya faɗi jin ba za ta yarda a cire cikin ba, ta san halin Maryam sarai idan ba ta son abu babu wanda zai mata dole, sai dai da siyasa da dabara. Ta ce"Maryam kin san matsalar wanda ba ya son haihuwa kuwa? Kin ga na farko dai idan kika samu ciki a wulaƙance zai dinga kallonki, ga wahalar laulayi ga wulaƙanci da rashin kulawa, irin su gani suke ma asara ce su kashewa cikin kuɗi, sai ki ga mace idan ba sana'a take yi ba zuwa awo ma ya gagare ta, wani kuma hanawa zai yi ko da kuɗin nata, ke akwai wacce tana naƙuda mijin ya kulleta a ɗaki tana ihu tana magiya har sai da ta haifo ɗan ya mutu sannan ya buɗe..." Dariyar da Maryam ta yi ce ta katse ta daga shararo ƙaryarta, ta ce"Maryam! Dariya ma kike yi?" Maryam ta ce"To ai abun dariya ma ya bani, ya rufe ta a ɗaki fa?" Ta ƙara sautin dariyar ta ce"Lallai wannan ba shi da kirki, ai kuwa da ni ce idan na fito kai ma sai na shaƙe ka ka mutu". Uwani ta ce"Kina wasa da iskancin maza, to ai ni ba ma wannan gaɓar ce ta fi damuna ba, kin san kuwa idan aka haifi ɗan shi da babu duk ɗaya a wajensa? Wallahi ko sutura ba yi masa zai yi ba, wani ma sai ki ga yana tsangwamar yaron kamar ba jininsa ba, wani agolan ma ya fi shi gata, sannan kina nan zaune sake da baki zai auro yarinya ta yi planing su yi ta soyayyarsu suna ƙunsa miki takaici". Maryam ta ce"Kamar dole? Wallahi babu namijin da zai yi mini haka". Uwani ta ce"To kuwa maganin kar a yi kar a fara, muddin ba za ki iya ɗaukar wannan ba gara ma ki cire cikin nan, kuma ki nemi saki, don haihuwa da irin wannan mijin ba ƙaramar matsala ba ce". Maryam ta ce"Ni fa ba zan cire cikin nan ba, haka kawai nake jin ina son abin da zan haifa, idan na haihu komai sai ya biyo baya". Uwani ta ce"Kina nufin za ki jure cin mutuncin shi kafin haihuwar?" Ta ce"Ba zai ma fara ba". Duk ta inda Uwani ya ɓullo sai Maryam ta kauce, saboda ita ba za ta zubar da ciki ba, don haka Uwani ta tattara ta tafi, lokacin dab da sallar magriba. A ƙofar gida suka yi kiciɓus da Hamza zai shiga, ya rage tsayi ya gaishe ta, ta amsa tana cewa"Ya mai jikin?" Ya ce"Da sauƙi". Ta ce"Ai yau dai na ce bari na zo na duba ta, ashe haka ta zama ta yi yarab kamar haihuwa ta goma? Na ci to Hamza dai sai haƙuri ba a samu damar angwancewa ba, to wannan yaushe mutum ta tada komaɗarsa? Ana ta jigilar amai da yawu". Hamza ya ce"Wallahi kuwa, sai haƙuri". Ta ce"Haƙuri ya zama dole ai, tun da abun nata na gado ne, uwarta ma fa haka ta yi, idan ta samu ciki duk haƙurin Malam sai ya ƙosa, ƙarshe daina rabon kwana yake da ita, kuma ba ma wannan ba, haka take haifo ɗan a yaƙune da cutar tamowa, duk mutuwa suka yi sai Maryam ɗin ce ta rayu, amma fa ta ci wuya, an kashe kuɗi maƙudai, idan aka kwantar da ita kamar gawa, a yaƙune, uwar ta sha mantawa ta fizgota ta yi zaton zani ne babu mutum a ciki". Hamza ya cika da mamakin surutun matar nan, gefen zuciyarsa kuwa cike yake da tsoron kar a haifo masa ɗa irin wannan. Ta ƙara da faɗin"Kai dai ka fara banki kawai, don da alama ita ma gado ta yo, sai anjima Allah Ya sawaƙe". Ya ce"Bari na raka ki titi". Suna tafe tana ƙara zuga shi da ƙarairayi kala-kala, shi kuwa ya hau kai ya zauna daram, ya sake jin haushin Maryam da ƙin zubar da cikin da ta yi, ya samar mata adaidaita sahu ya biya kuɗin sannan ya koma gida. Ya tarar da ita tana sallah, ya yi alwala shi ma ya fita masallaci, da ya dawo ya zauna ta kawo masa abinci, ya ci kaɗan, saboda yanzu abincin nata ma ƙyanƙyamin shi yake ji saboda amai da tofe-tofen yawun da take yi, shi a yadda yake jin labarin haihuwa wannan jinin biƙin da sauransu bai ma san yadda zai zauna da ita inuwa ɗaya ba idan ta haihu, dole dai ta tafi gida dab da za ta haihu, idan ɗan ya yi wata uku sai ta dawo, saboda shi ko wata mata ce a unguwarsu take siyar da wani abu, daga ranar da aka ce ta haihu to fa ya daina siyan abu a wajenta, ƙyanƙyami yake ji, har sai ya manta ɗan ta ɓa girma sannan ya ci gaba da siya, ballantana kuma a ce matarsa wacce dole ya ci abincinta. Ya yi nisa a duniyar tunani ya ji muryar Maryam ta ce"Wai me yasa yanzu ka rage cin abinci?" Ya ce"Babu komai". Sannan ya tashi ya fice daga gidan. Tun daga ranar ya yi mugun jan baya da ita, duka ya canza mata, a da yana biyo ta ɗakin da ta koma da kwana su kwana tare ko ba ta so, daga baya ya daina, tsakaninta da shi da safe idan ya fito zau tafi aiki ya zauna ya karya, da yana dawowa ya ci na rana daga baya ya daina, sai na dare shi ma ba kullum yake ci ba, sannan ba ya dawowa gidan da wuri, sai ya kai sha biyu a waje, kuma tun da gara ta ƙare ta lura shi mutum ne mai maƙo da bin diddigin abinci, idan ya auno shinkafa kwana ɗaya sai ya yi ta mitar ta ƙare da wuri, ya ce duk cikin nan ne yake saka ta cin abinci, idan ta yi faɗawa Uwani ba ta ba ta shawarar komai sai ta cire ciki, wanda ita kuma ba ta so, don haka ma ta daina faɗa mata komai, jira take kawai ta haihu ya sake ta ta ƙara gaba. Cikin yana wata biyar wataran ya shigo mata da balangu da lemo, ta manta rabon da ya siyo mata nama, ko ƴar kankana da lemon nan ba ya siyo mata, cike da marmari kuwa ta cinye tass, ta shanye lemon dama jarka ɗaya ne, babu jimawa kuwa ta fara jin ciwon mara, abu kamar wasa ciwon yana ra ƙaruwa, fitsari ya matseta, tana shiga banɗaki ta ga jini, ga shi ita kaɗai a gidan, ta nemo wayarta don ta sanar masa ta rasa ta, don ya ɗauka ya fita da ita, a tunaninta ba za ta nemi wata mafitar ba sai ta zauna har cikin ya zube. Da ta ga abun ba na wasa ba ne, sai ta saka hijjabinta ta tafi gidan iyayen shi, da yake ba su da nisa, a jigace ta shiga gidan, tana shiga ta durƙushe a gaban Umman shi dake zaune a tabarma tare da ƙannen shi, da yake da hasken wutar nefa ta gane ta, ta ɗago ta tana faɗin"Maryam lafiya?" Ta ce"Marara ciwo take kuma na ga jini". Umma ta hau salati ta ce"Tashi mu tafi asibiti wannan ai ba ƙaramar matsala ba ce". Suna zuwa aka ba ta maganin da aka yi nasarar tsayar da jinin, suka ba ta gado, sai a lokacin Umman ta kira Hamza a waya, ta faɗa masa asibitin da suke, ya ce ga shi nan zuwa, a ransa yana addu'ar Allah Ya sa cikin ya zube. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 9 https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee Lokacin da ya ƙaraso asibitin Maryam tana kwance luf an saka mata ƙarin ruwa, ya shigo yana cewa"Umma wai me yake faruwa?" Ta sake sanar masa a yadda Maryam ta zo, ta ɗora da faɗin"Kai ina ka shiga?" Ya ce"Yanzu shikenan cikin ya zube?" Ta ce"A'a Allah Ya taƙaita, amma ga scanning sun rubuta a yi". Ta miƙa masa takarda, ya karɓa jiki a suluɓe yana jin babu daɗi na rashin cikar burinsa. Maryam ta ce"Ina wayata?" Ya ciro daga aljihu yana miƙa mata ya ce"Dama na ga cajin ya yi ƙasa kuma ba su kawo wuta ba, shi ne na kai miki". Ta ji sam ba ta yarda ba, ta ce"Amma Hamza wannan lemon da ka ba ni akwai wani abun a ciki ko?" Ya kalli Umma da ta kafe shi da ido, ya fara muzurai ya ce"Kamar ya? Ban gane ba". Ta ce"To ya za a yi a ce daga shan lemo sai ciwo?" Ta kalli Umma ta ce"Dama fa ba son cikin yake ba, ya ce na zubar na ƙi yarda, kuma ma na manta rabon da ya shigo min da ɗan wani abun motsa baki, sai yau ɗin ya kawo min balangu da lemo, kin ga tun da ba son cikin yake ba ai zai iya saka min maganin ma". Hamza ya fara zabure-zabure ya ce"Wai kamar ya? Me kike nufi ne?" Umma ta ce"Lallai biri ya yi maka da mutum, za ka aikata Hamza, na sanka dama ba son haihuwa kake yi ba, amma kuwa idan haka ta tabbata sai dai na ce Allah Ya shirye ka, Ya ganar da kai gaskiya! Ke kuma Allah Ya saka miki". Ya ce"Wallahi Umma ban zuba mata komai ba". Ta ce"Allah Ya san komai". Sai ya fice ya bar asibitin. Umma ta je gida ta kwaso ƴan abubuwan buƙata tun da sun ce sai gobe za a sallame ta, ƙanwar shi ce ta kwana da ita, washegari da safe aka yi scanning aka ce cikinta lafiya ƙalau, ashe ma ƴan biyu ne, kowa ya cika da farinciki ban da Hamza da ya ƙara sarewa da lamarin, mai ɗa ɗaya ma ya aka cika ballantana biyu? Ai kwamacala kawai za a yi masa a gida kafin su girma, ya kasa ɓoye baƙincikinsa har sai da Umma ta gane, ta san halinsa ta san haihuwa ba ta dame shi ba, ta zaunar da shi ta yi masa nasiha sosai, ya ce shi fa bai ce ba ya son haihuwa ba, da aka sallame su ƙanwarsa ce ta zauna a gidan har sati biyu, ba ta faɗawa Uwani wannan abun ya faru ba ma, har ta warware, laulayin ma yanzu ya tafi sai amai da ba ta daina ba har yanzu, da ta yi masa zancen zuwa awo ma cewa ya yi wannan awon kawai yawo ne, sai da ta haɗa shi da Umma sannan ya barta ta fara zuwa. Da daɗi da ba daɗi cikin Maryam ya shiga wata na tara, idan ka ganta kamar ba ita ba, ta kumbura ta cika fam, hanci ya bubbuɗe, duk ta gaji da cikin, ko fita ba ta son yi sai a filin tsakar gida take ɗan zagaye tana tattaka ƙafarta, Hamza idan ya kalle ta wani mugun haushinta yake ji, shi kam inda ya san haka za ta samu ciki da wuri har gara ma bai yi auren ba, babu wani amarci da ya sha sai na laulayi. Wataran tana zaune a falo ya zo ya zauna ya ce"Maryam ya kamata ki tafi gida haihuwa ko? Tun da an shiga watan". Ta yi wani murmushin takaici ta ce"Hamza ba don cikin jikina ba a cikin maza kai ba kowan kowa ba ne a wajena da har sai ka kore ni zan bar maka gidanka". Ya ce"Ni kike faɗawa haka?" Ta ce"Bari dai Allah Ya sauke ni lafiya sai mu tattauna, ni ba wannan ba, ban ga fa wani shiri da kake yi na haihuwar nan ba, ko riga ɗaya b a siya ba, me kake nufi?" Ya ce"Kin ga kin haihu ban siya ba?" Ta ce"Sai na haihun? To cikin kayanka sai ka zaɓo wanda ƴaƴan za su saka na tafi da shi a sibiti kafin ka siyo musu". Ya ce"Kin ga ni na riga ma na faɗawa babarki gobe za ki koma gida, kuma zan bada kuɗin kayan yaran kafin ki haihu". Bai jira cewarta ba, ya tashi ya fice. Ta ɗauki waya ta kira Uwani, suka gaisa ta ce"Kin gama shiryawa?" Maryam ta ce"Shiri na me?" Uwani ta ce"Ba mijinki ya ce yau za ki dawo gida ba?" Ta ce"E, yanzu zan tashi na shirya". Ta ce"To sai kin ƙaraso". Ta haɗa kayanta a akwati, ta ɗauki waya ta kira Hamza, ya ɗaga ta ce"Na gama shiryawa zan tafi". Ya ce"To ki gaida gida, ki biya ta gidan Umma ki ajiye mini mukullin". Ta ce"Kana nufin ba za ka zo mu yi sallama ba? Kuma haka zan tafi ziƙau-ziƙau ko ɗan kayan shayi ba za ka siya mini ba? Sannan ma ni ko kuɗin adaidaita sahu ba ni da shi". Ya ce"To wane kayan shayi kuma sai ka ce wacce za ki tafi daji ba gida ba? Su a gidan naku ruwa ake sha? Kuma ni ban da ko sisi". Ta ce"Ka ga Hamza dakata mana! Kar ka sake ka zage ni ballantana iyayena!". Ya ce"An zage ki ɗin me za ki yi?" Ta ce"Ramawa zan yi fiye da wanda ka yi mini, don kai mijina ne ba ubana ba!". Ya yi tsaki ya kashe wayar, ta mayar da akwatinta ɗaki, ta zauna ranta a ɓace tana mamakin wai ita ce namiji yake yi mata haka, kamar wanda ya asirce ta, ji take har yanzu ba ta son rabuwa da shi, kuma babu wata hujja da zuciyarta take ba ta sai na cikin nan na jikinta, don haka ta bari har zuwa ta haihu ɗin ta gani, shin da gaske cikin ne sila ko kuwa Hamza ne ya samu nasarar canza mata tunani? Azhar ta yi ta tashi ta ɗora girki, saboda ta yi alƙawarin ba za ta tafi ba sai ya yi mata siyayya kuma ya ba ta ɗan kuɗi ta riƙe a hannunta, ta gama cin abinci ta yi wanka ta kwanta baccinta, sai la'asar ta tashi, ta idar da sallah Uwani ta kira ta a waya, ta ce"Ya na ji shiru? Ko sai yamma?" Ta ce"Ai na fasa tahowa yau". Ta ce"To! Sai yaushe?" Ta ce"Sai yadda ta yiwu". Ta ce"A kan me?" Ta ce"To ya ce ko kuɗin babur ba shi da shi, ballantana ya yi min ƴar siyayyar tahowa gidan, sannan ko tsumma bai siya ba, babu rigar da za a tafi da ita asibiti, sai na zuba masa ido?" Uwani ta ce"Kayyasa! Amma wannan yaron akwai mara kirki, kodayake laifinki ne ɓa wallahi, ni na rasa irin son da kike yi masa ba". Maryam ta ce"Ta ya zai zama laifina?" Ta ce"To akan me ba za ki yi masa kaca-kaca ba? Wannan wane wulaƙanci ne a ce ciki har ya shiga watan haihuwa ba a sayi komai ba? Haihuwar fari fa za ki yi Maryam, ko so kike mutane su samu abun faɗa a kanki? Wallahi da ki haihu ya zo ya ja mana abun kunya, gara ma mu san auren ya mutu wannan an san dama ba mijinki ba ne, ke ba ki ga Murja ba haihuwar fari yadda ta dinga tatso kuɗi a jikin mijinta hatta yajin da na yi mata da kuɗinta ne, to ba ki Murja komai ba? Shi kenan ki yi ta zama da wannan ƙaddararren auren". Maryam ta ce"Ai shiyasa na ce ba zan taho ba sai ya zo". Uwani ta ce"Ki miƙe tsaye ki tada masa da hankali kar ki yarda ki dawo gida haka hannu na dukan cinya". Ta ce"To bari ya dawo". Suka yi sallama, kalaman Uwani sun ƙara tunzurata don haka ta cika ta yi fam tana jiran dawowar shi, ƙarfe tara ya dawo unguwar, ya biya ta gidansu don ya karɓi mukullin gidansa, Umma ta ce"Wane irin mukulli kuma? Ina Maryam ɗin ta tafi?" Ya ce"Au ba ta kawo mukulli ba? Gida ta tafi ai, kin ga ta yi nauyi idan ta haihu ta yi arba'in sai ta dawo". Umma ta ce"Ikon Allah! Ku mazan zamani da ba kwa yarda mace ta tafi goyon ciki? Hamza anya kuwa? Kuma da sai ta tafi haka ko sanar da ni ba za ka yi ba?" Ya ce"To ai ga shi yanzu kin ji, kuma goyon ciki ai ba komai ba ne". Ta ce"Amma ni dai da ta haihu a ɗakinta, idan aka yi suna sai ta koma gidan". Ya ce"A'a ta je ɗin kawai babu komai". Ta ce"To Allah Ya sauketa lafiya". Ya yi mata sallama ya fita. A ƙofar gida ya tsaya ya kira lambar Maryam,har ta fara bacci ma, ta ɗaga cikin muryar bacci, ya ce"Mayam kina ina?" Ta ce"Ina gida mana". Ya ce"Wane gidan?" Ta ce"Gidanka mana". Ya ce"To me ya hana ki tafiya?" Kawai sai ta yi tsaki ta kashe wayar, ta tashi ta je ta cire sakatar ƙofar ta dawo ta kwanta. Babu jimawa ya shigo gidan, ya same ta a ɗakin ya ce"Wai ni me ya sa ba ki tafi ba?" Ta yi kamar ba ta ji shi ba, tana jin takaici wai ita miji yake nunawa yana son ta yi nesa da shi ƙiri-ƙiri babu sakayawa. Ya ce"Magana fa nake yi miki". Ta tashi a fusace ta ce"Hamza idan ka yi haƙuri zan bar maka gidanka har abada, amma sai na haihu, kuma dalilin ƙin tafiyata ai na faɗa maka sai ka yi mini siyayya, sannan ka sayi kayan jarirai". Ya ce"Amma ai ce miki na yi zan aiko ko?" Ta ce"Don ka yi magana dole ne na amince? Idan ji ya zama dole ai babu inda yarda take zama dole". Ta juya ta kwanata. Ya fice daga ɗakin yana tsaki. Da ya ga dai har ta ƙara kwana uku ba ta da niyyar tafiyar, sai ya same ta suka zauna ya ce"Wai me da me kike buƙata?" Ta ce"Za ka siyo kayan shayi na gwangwani fa ba irin wanda kake kawo mini ba, sannanza ka siyo kwalin indomi, da golden morn, sannan kayan jariran wanda mace da namiji za su iya sakawa kala uku, ka ga kenan shida za ka siya tun da su biyu ne". Kalmar biyun nan ta saka gabansa faɗuwa, saboda har yanzu kuɗin abun yanka ma ɗaya ya tanada, shi ma lissafinsa tunkiya zai siya haka ƴar madaidaiciya. Ta ci gaba"Ka ga za ka siyo tawul masu kyau kowa biyu, sai saitin kayan sanyi da saitin man shafawarsu, wannan su za ka siya kafin na haihu, idan na haihu aka ga me aka samu sai a san yadda za a haɗa kayan barka". Ya ce"Wannan lissafin nawa ya kama?" Ta ce"Oho! Ka ba da dubu ɗari sai a je a ji". Ya yi mata wani mugun kallo mai ɗauke da manufar ba ki da hankali, ya ce"Dubu ɗari?" Ta ce"To ka je ka siyo mana". Ya tashi ya fice, a ranar ya siyo komai da ta lissafa, amma duk masu sauƙin kuɗi ya zaɓo, ya kawo mata ya lallaɓata ta tafi. Uwani da ta ga kayan ta rafka tagumi har sai da Maryam ta tsargu, kafin ta ce"Maryam wane irin miji ne wannan da kike son rayuwa da shi? Wannan kayan tsohon ya yi masu mugun arha ya siyowa ƴaƴansa na fari? To sai dai mu ce Allah Ya kyauta". Maryam dai ba ta ce komai ba. Daga nan kuma sai Uwani ta tsiri saka ta ta cewa Hamza ya siyo mata nama, ko kayan marmari haka, idan ta kira shi ta faɗa masa sai ya fara masifa yana cewa shi fa ba shi da kuɗi, wataran zai kawo, wataran kuma ya ƙi kawowa, Uwani kuwa ta samu abun mita, ta yi ta masifa tana tsinewa auren, a haka dai har aka cika sati biyu, ranar tsakar dare Maryam ta fara naƙuda, Baba ya ce ga maƙotansu wani matashi yana da adaidaita sahu a kira shi su tafi asibitin, amma fir ta ƙi ta dinga kiran Hamza a waya, shi kuwa yana ganin kiran jikinsa ya ba shi ba lafiya ba, ya san dai ƙarshen zance cewa za a yi Maryam za ta haihu ko kuma ta haihu, don haka ya ƙi ɗagawa, sai ma ya saka wayar a silent ya ci gaba da baccinsa, dole dai aka bi maganar Baba, suka tafi asibitin a hanya tana ta zagin Hamza Baba yana kwaɓarta. Sai da asuba Maryam ta haihu, ƴaƴanta mace da namiji, sai dai macen ta zo babu rai, sai namijin ga shi nan ma sha Allah, sai da gari ya waye ta kira lambar babar Hamza ta bawa Uwani, ta faɗa mata an sauka lafiya, ta ce"Ki sake kiran shi shi ma". Uwani ta ce"Kin san kira nawa na yi masa jiya? Yanzu da ya tashi sallah ai zai ga miss call idan shi mutumin kirki ne ai sai ya kira!". Bakwai da rabi Hamza ya zo asibitin tare da babar shi, suka kawo musu abun karyawa, a gaban babar shi Uwani ta caccake masa tass na rashin ɗaga wayar, ita kuma tana ta ba ta haƙuri, aka tafi da gawar yarinyar aka binne, sai da yamma aka sallami Maryam ta koma gida. Sun ga tijara kafin ranar suna ta zo, don yanzu Uwani karɓar lambar shi ta yi, abu kaɗan ta kira shi ta ce ana buƙatar abu kaza, ranar da bai kawo ba ta yi ta tsine masa ƴaƴanta suna yi mata nasiha, amma kamar suna zugata. Ranar sunan ma sai da ta raina abun yankan, kayan fitar suna ma kala ɗaya ya yi mata, wata atamfa ce aka sako ta a cikin kayan barka, don haka ita Maryam a ranta ta ƙudure wannan zuwa gidan da ta yi, ta zo kenan babu zancen komawa, don wannan idan ta ci gaba da zama da shi gorin Uwani ma kawai ya ishe ta. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* PAGE 10 https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee Hamza sai ya bushi iskarsa yake leƙowa gidan har aka yi arba'in ɗin Al'ameen, ga wani raini da ya yiwa Uwani, saboda yawan roƙon shi da take yi, da yadda take raina ƙoƙarin shi, har wani kallon gani-gani yake yi mata idan ya je gidan. Uwani tana sane ta ce Maryam arba'in biyu za ta yi, saboda ta dinga ja masa rai har ya gaji auren ya sire masa, ba ta san kamar an zuga zugagge ba ne, don shi ma ba son ci gaba da zaman yake yi ba, Baba da ya yunƙuro a kan sai ta koma ɗakinta Uwani ta sanar masa ba ta da lafiya fa, ɗinkin da aka yi mata sanadin haihuwar nan bai warke ba, kuma likitocin sun yi gargaɗi da kakkaurar murya a kan kar ta koma sai bayan wata uku, su kuwa yaran zamani masu do a tsakar ka idan ta koma sai dai komai ya faru, don haka Baban ya ƙyale su ya zuba ido. Watanta biyu a gida Hamza ya zo da daddare, sun gaisa yake cewa"Maryam yaushe za ki koma ne? Sannan ina ga fa sai dai ki koma gidanmu da zama..." Ta katse shi da faɗin"Ban gane ba!". Ya ce"Ai ganar da ke nake yi". Ya ce"Kin ga dama kuɗin hayar ya ƙare, kuma ni ba ni da kuɗin da zan sake biya, sannan ma ina son tafiya wata ƙasar neman kuɗi, ana kan yi mini hanya, kuma ko ba wannan ba ni dama fa a zamanmu haƙuri kawai nake yi da ke, saboda tsakani da Allah ba ki da kunya, ba ki da tarbiyya ba ki san girmana ba a matsayina na mijinki". Maryam ta yi mamaki sosai, don ko da wasa ba ta taɓa tunanin gidan nan ba na shi ba ne, sanda yana neman aurenta ya ce mata na shi ne ya gina tun da jimawa sai ya saka ƴan haya a ciki, yanzu ya tashe su tun da ya yi aure, ta ce"Hamza idan za ka kore ni ba sai ka yi mini ƙarya da gida ba naka ba ne, idan ka yi haƙuri dama ni ma wannan zaman da nake yi ba ni da niyyar komawa, saboda haka ka sallame ni kafin ka tafi inda za ka je". Ya ce"Wallahi ba gidana ba ne, ki tambaya ki ji, kuma sannan ni fa ba ni da manufar rabuwa da ke, sai dai idan ke ce kika zaɓi hakan". Ta ce"E ni ce na zaɓa ɗin, ka sake ni". Ya ce"To gobe zan aiko miki saƙo". Ya tashi ya fice, a tsakar gida ya samu Uwani zaune, ta ce"Ka fito?" Ko kallonta bai yi ba ya yi dogon tsaki ya fice. Ta shiga ɗakin dafe da ƙirji tana cewa"Na shiga uku ni Uwani, Maryam me zan gani? Mijinki ne yau ya yi mini tsaki, a gobe kuma sai duka, wallahi saura zagi da duka, Maryam wa kika kwaso mana ne haka?" Jin shigowar saƙo wayarta ya sa ba ta kula Uwani ba, tana dubawa ta ga daga shi ne, ya rubuto mata ya sake ta saki ɗaya, ta nunawa Uwani wayar ba ta ce komai ba, ta ce"To rubutu nake gani, kuma kin san ni ba iya karatu na yi ba, na mene ne?" Ta ce"Shi ne ya turo mini saƙo wai ya sake ni saki ɗaya". Uwani ta sauke ajiyar zuciya ta ce"To Alhamdulillah! Tsaki da ya yi mini kuma ya je don kansa, tun da dai ya sallame ki ni ya biya ni!" Ta zauna tana cewa"Maryam ki kwantar da hankalinki, wannan ba komai ba ne, in sha Allah nan gaba za ki samu miji na kere sa'a, wanda za mu yi alfahari da aurenki". Maryam ta ce"Allah Ya sa". Bayan kwana uku da sakin sai ga babar shi ta zo gidan, Uwani ta yi kicin-kicin ta tarbe ta a tsiyace, saboda kar ma ta yi zancen kome, irin yadda take amsa mata gaisuwa a daƙile kamar mai gyambo a maƙoshi har Maryam ɗin sai da ta ji babu daɗi, saboda ta zauna da matar lafiya ba ta da wata matsala, babar Hamza ta ce"Ashe haka abu ya faru, ɗan yau dai ka haife shi ba ka haifi halinsa ba, wallahi Hamza bai yi shawara da ni ba ya yanke hukunci, don Allah ku yi haƙuri". Uwani ta ce"Ai ba komai ba ne a wajenmu, duk wanda ya rasa Maryam shi ke da asara, don haka shi za ki bawa haƙuri". Ta ce"Ai kuwa ba a ce ba komai ba ne, aure irin wannan da albarkarsa har an fara samun rabo..." Uwani ta katse ta da faɗin"Cewa za ki yi har an samu rabo, idan kika ce an fara da saura kenan za a ci gaba, kin ga mun gode amma don girman Allah ki ƙyale yaron nan sa hukunci shi, don ba a yi wa yaran zamani dole". Ta ce"Haka ne, to Allah Ya rufa asiri". Uwani ta gyara zama ta ce"Dama ai jira nake a cika sati na ga ƙarshen abun, da ba ki zo ba dama zan zo". Babar Hamza ta ce"To lafiya dai ko?" Uwani ta ce"Ƙalau, dama a kan wannan yaron ne, na ce ya za a yi da shi? Za ki karɓa ne ko kuwa biya za ku dinga yi tana shayar muku da shi?" Ta ce"A haba dai ga uwarsa a raye ai bai kamata a raba shi da nonon uwa ba, sai a dinga ba ta wani abun". Ta ce"To nawa za ku na badawa? Kin ga bayan shayarwa ma a kwai omo, sabulu, famfas kafin kuma ya fara cin abinci". Maryam da duk matar ta ba ta tausayi ta ce"To babarmu ai ba sai an wani tsadance ba, ko me suka kawo Allah Ya saka masa albarka, ni ma fa ɗana ne". Uwani ta galla mata harara, ita dai ta yi musu sallama ta tafi, ta ce gobe za ta dawo idan suka yi magana da Hamza. Tun daga nan duk sati biyu sai babar Hamza ta zo ta gansu, wataran kuma ta tiso shi a gaba su zo tare, su ba su kuɗin shayarwa. Babu laifi Maryam ta samu kulawa sosai a wajen Uwani, yanzu hankalinta a kwance yake tana ra rainon ɗanta da yake ta ƙara girma da wayo. Al'amin yana da wata biyar ta ce za ta fara bussiness da kuɗin da ta siyar da kayan ɗakinta, Uwani ta so daƙile ta, ta nuna mata wannan fa duk cake ne ba samun ciniki ake ba, har gara ma siyar da abincin, ita kuma Maryam ta ga ya za a yi ta sana'ar abinci da ƙaramin ɗa, to da yake Uwanin ta san idan Maryam ɗin ta coge ba a iya ture ta sai ta rabu da ita, ita take zuwa kasuwa da kanta tana yo sarin abubuwa iri-iri, ta tallata a maƙota da kuma status kuma Alhamdulillah Allah sai Ya sakawa abun albarka, Uwani tana kallo take ƙirga ribarta tana adanawa. Da ta yaye Al'amin sai ta daina zuwa kasuwar da shi, ta fara ɗaukar wanka don shirin fara zawarci, ai kuwa zawarawan suka fara layi, tana ta cafke musu ƴan canji,domin ta koyi roƙo sosai, idan ma kai faƙiri ne ko marowaci soyayyarku da Maryam ba ta taɓa yin ƙarko, bani-bani ne zai kore ka, idan gari ya waye dare ya yi ba su ci kaza ko balangu ba ita da Uwani to sai dai idan ita ce ba ta so ba, ma'ana idan ba ta bawa kowa damar zuwa ba, amma muddin ka ce ga ka nan tafe to za ta lissafo maka abin da za ka taho da shi, ai kuwa har wata ƙiba ta fara yi, ta yi kyau abunta. Ba ta tsayar da mijin ba, tana ta tantancewa dai, yayin da ƴan'uwanta ƴaƴan Uwani suke yawan yi mata nasiha kan auren shi ne rufin asirinta, idan a gaban Uwani ne kuwa nan za ta hayayyaƙo tana cewa su ba su san ƙaddara ba? Ai ita Maryam ƙaddararta kenan, shi ma Baba ya fara matsa mata, don haka ta tsayar da wani Nasuru, a kasuwa suka haɗu, ya faɗa mata ya taɓa yin aure ƴaƴansa biyu suka rabu da matar, Nasuru ba shi da rowa, sosai yake sakar mata kuɗi, kuma ba shi da wata makusa a halitta, ta ji tana son shi za ta iya auren shi, don haka ta ba shi dama ya turo bayan ta gama shirinta. A wannan karon wata biyu aka saka, aka ɗaura aure, aka mayar da Al'amin wajen babar Hamza ta ci gaba da kula da shi, a wannan karon Uwani ta san babu buƙatar yiwa ƴar tata wata huɗuba domin ta riga ta haddace karatunta, musamman ma a wannan zawarcin da ta yi ta ƙara samun gogewa ta rayuwa, don haka hankalinta kwance yake, ta san yadda ta tafi haka za ta dawo. An kai amarya lafiya, zamansu da Nasuru lafiya ƙalau babu wata matsala daga farko, haka kuma shi yana son haihuwa ba kamar Hamza ba, don da ta samu ciki ya nuna mata kulawa sosai, bai taɓa nuna ƙosawa da yanayin laulayinta ba. Yaran shi suna zuwa gidan, wani lokacin ma har su kwana biyu idan sun zo ranar Juma'a sai ya mayar da su ranar Asabar, a yadda ta lura da alamunsa yana son yaran su zauna a wajenta, ita ma kuma ba ta ɗauki hakan a komai ba, tun da ba ƙananu ba ne sosai ballantana ta ce za ta ci kashinsu da fitsari, babban shekararaa tara, sai ƙanwarsa shekararta baƙwai, to da yake komai na gidan aurenta a tafin hannun Uwani yake ita ce ta nuna mata sam kar ta sake ta riƙe masa ƴaƴa, ɗan kishiya ruƙon mai haƙuri ne, ta zuga ta a kan idan ta haihu tana kallo zai yi ta fifita yaran a kan wanda za ta haifa, saboda an fi marmarin ɗan fari, haka dai ta harhaɗa mata raunana hujjoji marasa tushe bare makama, sai ta hau kai ta zauna ta fara baya-baya da yaran. Nasuru ɗan kasuwa ne, dole ba zai rabu da mata a waya ba, musamman yanzu da kasuwancin ya koma na online, sannan da daddare ne yake samun damar zama ya nutsu ya duba saƙƙonnin da bai duba ba, sannan ya yi ta saka hotunan kaya a groups ɗin shi, ita kuma Maryam wannan karkata da yake yi a kan waya yana mugun ba ta haushi, ko kuma ta ga wata ta kira shi suna magana, duk da ga shi a zahiri tana ji zancen kaya ake yi, amma sai ta yi ta yi masa tijara tana cewa ƙarya yake yi alaye yake yi mata, kurman baƙi ne kawai suke yi saboda a gabanta ne, kuma da fari ba haka take yi ba, ta yarda da shi sosai, nan ma Uwani ce ta zuga ta ta ɗora ta a keken ɓera ta ce duk ƙarya ce, dama ƴan kasuwa ba a isa a raba su da mata ba, ga su da watsewa da masu abinci, har da cewa Allah Ya sa ma bai ɗebo mata alaƙaƙai ba. Tun daga ranar da Maryam ta ji haka shikenan ta kasa zaune ta kasa tsaye a gidan aure, ta matsewa Nasuru lamba take tuhumarsa babu dare babu rana, dayake yana sonta haka yake ba ta hujjojin kare kansa, daga ƙarshe ma ta ce munafurci ne yasa yake saka password a waya dole sai ya cire, kuma ta cire ɗin saboda a zauna lafiya, don haka ta samu damar bincikar wayarsa kullum, tsakar dare za ta tashi ta ɗauki wayar ta fice falo ta yi ta bincikenta, yana kallonta amma bai damu ba tun da ya san babu komai ba rashin gaskiya da za ta gani. Ana haka ne ya sayi wata waya sakan a wajen abokinsa, ya ɗora wani daga cikin layinsa a kai, da yamma ya karɓi wayar bai ma duba ya ga mene ne a ciki ba, ashe da fina-finan batsa kala-kala, ta ɗauki wayar ta duba ta gani, shi ne ta tashe shi tsakar dare suka yi tijara har ya sake ta, tana ganin ba komai ba ne don aurenta ya mutu, sai kuma ta dawo a ranar ta san matsayinta da gadar kwalin da Uwani ta sakawa rayuwarta ta hau kai ta kwanta a rashin sani. Wannan shi ne abin da ya faru a baya, yanzu za a ci gaba da labari. 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee PAGE 11 Wunin ranar Maryam ba ta bar zuciyarta ta huta ba, tunani kawai take yi na irin zuciyar wasu mutanen, ta ɗauki Uwani tamkar mahaifiyarta, tana yi mata kallon gatanta, kusan ma za ta iya cewa ta fi sonta fiye da mahaifinta, saboda yadda take riƙe ta da amana, tun tana yarinya take kula da ita bayan rasuwar mahaifiyarta, ba ta taɓa ganin wani abu na nuna bambanci a tsakaninta da ƴaƴan da ta haifa ba, kuma da yake ita ma Maryam tana da sakin jiki da mutane da surutu sai ya zamana ba ta rakuɓewa kamar na ƴaƴan da babu uwarsu a gida, sabgarta kawai take kamar Uwani ce ta haife ta. Ita Hansatu mahaifiyar Maryam ƙawar Uwani ce tun ta ƙuruciya, kowa ya san amincinsu komai tare suke yi, ƙawance irin na da mai cike da tsafta da yarda da juna, musamman da suka kasance maƙota, ga gida ga gida, Uwani ta samu miji da wuri ta yi aure, saɓanin Hansatu da ta samu jinkirin aure, har ana cewa aljani ne ya aure ta sai da ta girma Uwani ta yi haihuwa uku sannan ta samu miji, shi ma abokin mijin Uwanin ne, wanda bai yi auren wuri ba shi ma abun ya damu iyayensa, kawai sai mijin Uwani ya yi wani tunani, ya ce tun da ƙaddararsu ta zo ɗaya da Hansatu kawai a haɗa su a gani ko za a dace, kamar wasa aka haɗa su suka fara soyayya, kuma sai abun ya ɗore har aka yi aure, wata biyu da auren Hansatu da Malam Habu Allah Ya yi masa rasuwa, sanadin hatsarin mota, da yake direba ne shi, yana kai kaya Legas. Nan fa marasa ilimi suka ƙara gasgata lallai aljani ne ya auri Hansatu, bayan ta fita daga takaba babu zato babu tsammani mijin Uwani ya ce zai aure ta, Uwani irin matan nan ne ma su tsananin kishi don haka ta girgiza matuƙa da jin zancen, ta tada hankali ta ce ba ta san zance ba, a cewarta Hansatu fa aljani ne ya aure ta, idan ya aure ta shi ma mutuwa zai yi, shi kenan ya bar ta da marayun ƴaƴa, ta ci kuka ta yi magiya, shi kuwa namiji idan ya so ƙara aure babu mai hana shi sai Allah, don haka ya ɗaura ɗamara, musamman da ya kasance ita Hansatu tana son shi ta karɓe shi hannu biyu-biyu, duk kuwa da caccakar da ake ta yi masu a gari ita da iyayenta na cewar za su yi auren cin amana, a haka dai aka yi auren nan tun da Allah Ya ƙaddara, kuma ana yi aka samu rabon cikin Maryam. Sam ba a ga miciji a zaman nasu, duk yadda Hansatu ta so su sasanta Uwani ta ƙi ba ta dama, masifar yau da ban ta gobe da ban, a haka har aka haifi Maryam, sai kuma Allah Ya jarabci Uwani da son Maryam, idan ta rarrafo ta fito waje haka za ta ɗauke ta, sai ta ga fitowar Hansatu sannan ta ajiye ta ta shige ɗaki, to da Maryam ta girma take shiga ɗakin Uwani sai suka ja ta a jiki sosai, yaran suka haɗe kansu kamar ba ƴaƴan kishiyoyi ba, shekarar Maryam bakwai a duniya mahaifiyarta ta rasu, wajen haihuwa ta biyu, dama tun farkon cikin ya zo da matsala, kuma Allah Ya yi cikin ma abokin tafiya ne, ba ta haihu ba ta rasu, kuma dama tun da ta fara naƙuda aka tabbatar ɗan ya mutu a cikinta. Kowa ya ji tausayin ƴar marainiyar nan Maryam, mutane sun yi mamakin yadda Uwani ta saka ta a jikinta ta rungume tsam, ta hana dangin babarta tafiya da ita, dama shi ma Baba ya hana, saboda ya san kishin Uwani da uwar kawai take yi tana son ƴar, haka aka bar mata Maryam, ana ta yabonta a gari, ita kuwa ta haɗe ta da ƴaƴanta aka ci gaba da yaruwa. Sai dai me? Mayam ita ce ƙarama a kan ƴaƴan Uwani Mardiyya da Murja, amma samari ita suke hari tun tana ƙwailarta, ita a tunaninta Maryam za ta yo ƙashin baƙin jini irin na babarta, sai ga shi ta ga saɓanin hakan, nan hassada ta fara shiga zuciyarta sannu-sannu, ta fara jin haushin Maryam ɗin, su kuwa su Mardiyya ba su damu ba, don sun ɗauki Maryam ƙanwarsu kamar uwa ɗaya suke, sai Uwani ta dinga nuna musu suna cikin matsala sanadin haka, a cewarta babarta ce kafin ta rasu take yi mata maganin farinjini, su dai ba su saka a ka ba. Da farko sai ta samu Baba kamar abun arziƙi take nuna masa illar wannan farin jinin na Maryam, ta ce tana da ƙuruciya mazan za su iya amfani da wannan damar su hillace ta, saboda haka a samu wani Malamin wanda zai iya dakatar da maza daga kanta zuwa sanda za ta yi hankali ta isa aure, Baba ya nuna sam bai yarda ba, duk da shi ma abun yana ba shi tsoro, musamman da ya kasance ita ta fi ta zakka da sauran yaran gidan, ita ba ta jin magana sosau, ga yawon bin gidajen ƙawaye, wani feleƙe da rawar kai da son girma ga kwalliya kamar babbar budurwa, Baba ya ce ko maza dubu ne za su zo babu wani dakatarwar Malami da ake buƙata, tun da dai ba zance ta fara yi a ɓoye ba, to a barwa Allah komai, kuma ba yanzu zai yi mata aure ba ai, sai ta gama sakandari, haka Uwani ta haƙura ta bar zancen. Amma ta kasa haƙura, sai da ƙawarta ta zuga ta ta karɓo rubutun farinjini take bawa ƴaƴanta ba tare da sanin Maryam ba, a haka dai har suka samu mijin, a rana ɗaya aka haɗa na Mardiyya da Murja, dama daga su sai Maryam sannan ƙaramar ƴarta Fatima, wanda tsirarsu kaɗan ne da Maryam, don bai kai shekara ba. To ita ma Maryam ɗin da yake ba ta jin magana, sam babu auren a gabanta, duk wanda zancen aure ne ya kawo shi ba ta fiya sauraron shi ba, tun ba a farga ba har aka gane, Uwani ta fara farinciki tana tunanin ƙila ita ma ƙaddararsu ɗaya da mahaifiyarta. A hankali shaiɗan ya tunzurata, take tuna auren da ta kira da na cin amanarta da aka yi tsakanin ƙawarta da mijinta, ta ji a ranta lokaci ya zo da ya kamata ta ɗauki fansa a kan Maryam, ta yi ta tunanin abin da za ta yi mata, kafin ta yanke shawarar hana ta zaman aure, ba ta yin shirya kuma ba ta so ta yi a kan Maryam, sannan idan ta yi mata cutarwa ta ƙiri-ƙiri mutane za su gane da wuri, a yi mata terere, ta ruguje yardar da aka yi mata akan Maryam, shiyasa ta ga gara ta yi mata kisan mummuƙe, ta so a ce ta ƙi aure kamar babarta, yadda za ta fake da dama gado ta yi, sai ga shi ta tsayar da Nazifi, don bayan auren ƙanwarta Fatima sai Baba ya matsa da zancen auren nata. Tabbas Maryam ta shiga ƙunci, ta ji baƙinciki da takaici, ta yi kuka tsakar dare ta share, wanda ta saka a ranta ba za ta sake hawaye saboda butulcin babarsu a gare ta ba, sannan ta saka a ranta ko da wasa ba za ta taɓa nuna mata ta san mummunan ƙudirinta a kanta ba, Uwani ta nuna mata so, ko da a ce ba so ba ne duka taku ne to fa tabbas ta yi ƙoƙari, don wasu ba sa iya sarrafa kansu har su danne ƙiyayyar mutum, sannan ta kasa yarda ma da cewar Uwani ba ta sonta, kawai ta fi yarda da shaiɗan ne da zugar ƙawayen banza ya sa take aikata mata haka, ko kuma ta ce ta aikata haka a baya, saboda komai da Uwani ta yi mata na hana ta zaman aure ya wuce a zuciyar Maryam, ta saka a ranta yanzu sabuwar rayuwa za ta fara yi, sai yanzu ta gane tabbas ta yi kuskure, ta kuma yi nadama. Baya ta wuce, yanzu ta gaba ake yi, gaba ake iya gyarawa ba baya ba, don haka dole za ta yi gyara a rayuwarta, yanzu ita dai ba za ta fito ƙarara ta nunawa Uwani ta ajiye zancenta na miji goma ba uba goma ba ne, saboda shi maƙiyi ba ka ba shi ƙafar sanin abin da yake ranka, saboda kar ya canza taku ya shigo maka ta bayan gida. A wannan daren Maryam ta ɗaukarwa kanta wani alwashi, ta ƙudure a ranta tabbas sai ta ba wa Uwani kunya, sai ta rusa mata burikanta, kuma ta hanya ɗaya hakan zai tabbata shi ne ta ɗaura ɗamarar jure zaman aure, ta saka a ranta za ta yi aure na mutu-ka-raba, idan ta gama idda ta yi aure ko wa ta aura, kuma ko wace matsala ta tarar a gidan auren, za ta yi haƙuri da ita, za ta zauna ta jure duk wani ƙalubale, kawai saboda mafarkin Uwani ya zama ƙarya. Duk da tana kallon abun da kamar wuya gurguwa da auren nesa, saboda ta riga ta ginu a kan kalaman Uwani na ƙanzon kurege, ta san ba abu ba ne mai sauƙi a ce a lokaci a ɗaya ta sauka daga kan wannan hanyar da ta yi nisan tafiya a kanta, wannan ƙudurin da ta ɗauka daidai yake da mayar da kanta ƙasƙantacciya, a yanayin halittarta dama can ba ta da haƙuri, to ta ya za ta koyi wannan haƙurin ta dinga jure halin mijin da za ta aura ko yaya yake? Wannan shi ne babban ƙalubalen da take ganin za ta fuskanta, amma ta saka a ranta za ta jure ta kuma haɗa da addu'ar Allah Ya tallafe ta Ya zama gatanta. Duk wata jarumta da dauriya Maryam ta yi, wajen nunawa Uwani ba ta gano komai na shirinta a kanta ba, ita kuwa Uwani da ba ta san wainar da Maryam take toyawa a zuciyarta ba sai ta ci gaba da biya mata karatunta, wanda sai yanzu ne Maryam ta ƙara gasgata lallai ita doluwa ce a baya ta yi wasa da damarta. Ba ta ma gama tsinkewa da lamarin ba sai ranar da Murja ta yo yaji, saboda mijinta zai ƙara aure, ta ce ita wallahi sai dai ya sake ta, tun kafin Uwani ta ce wani abu a kai Maryam ta yi farat ta ce"Lallai wannan miji naki akwai ɗan banza! Duk zamanku nai ƙara aure ba sai yanzu? Wallahi kar ki yarda, da ki zauna da kishiya gara ki yi zaman gida, ai miji goma ba uba goma ba ne". Uwani ta yi wuƙi-wuƙi ta ce"Amma Murja wa za ki barwa ƴaƴanki?" Maryam ta ce"Ƴaƴa kuma ai dama tarbiyyarsu a hannun Allah take, ta bar masa su can su ƙarata ya riƙe su, ta nemi wanda ya fishi ta aura, ai wallahi wanda ya rasa Anti Murja shi ya yi asara, kalle ta fa sankaɗaziyya da ita, ƙila ma ta samu wani saurayin ya yi wuf da ita". Murja ta yi dariya ta ce"Kai Maryam, ni kuwa wani saurayi ne zai kwashe ni? Kina kallon yadda wahala ta fara mokaɗar da ni?" Maryam ta gyara zama har da kamo hannun Murja ta ce"Wallahi Anti Murja ni nan na yi miki alƙawarin sai na samo miki miji na gagari ko ba saurayi ba, ke dai ki yi ƙoƙari ya sake ki kawai, ina haihuwa na tsige yaron ko yarinyar mu fara falla zawarci, yasin sai na wayar da ke, idan kika fantama a gari sai an taro ki, wai wa ya ga Anti Murja a gaban motar wani Alhajin!". Ta kwashe da dariya tana kallon yadda fuskar Uwani ta nuna rashin jin daɗi, hakan kuwa ya ƙara raunana zuciyarta tabbas wata kishiyar uwar ba uwa ba ce, kuma ba za ta zama uwar wani ba har abada. Maryam ta dage ta dinga zayyanowa Murja jawabai, tana kwaɗaita mata yadda rayuwar zawarci take, Uwani ƙarshe tashi ta yi ta fice daga ɗakin, ta fara kiciniyar ɗora girki gabanta yana faɗuwa da fargabar kar fa Maryam ta yiwa Murja huɗuba, ta zo ta kashe aurenta ta rasa miji, tun da dama can sai da ta basu rubutun farinjini suka samu mijin, tana buduruwa ma kenan, ina ga yanzu da ta yi haihuwa huɗu? Lallai dole ta yi wa tufkar hanci, amma ta yadda Maryam ba za ta gano komai ba. Ta ƙwallawa Murjar kira, ta fito, Uwani ta rufe ta da faɗa"Kin shige ɗaki kin bar ni da aiki, ni zan yi muku girkin kenan ko? Sai surutan banza kuke yi kamar yau kuka taɓa sanin juna?" Maryam ma ta fito, Uwani ta ƙaƙalo murmushi ta ce"La Maryam ba da ke nake ba, ke ai kin yi nauyi, ina ke ina aiki? Ki koma ki yi kwanciyarki". Maryam ta koma tana tunanin shin ta zuga Murja ta kaso aurenta saboda Uwani ta ɗanɗani baƙinciki, ko kuwa Murjar za ta kalla da matsayin ƴan'uwantaka da ke tsakaninsu ta ƙyale ta? *Mun kusa gama free page fa, za ku iya biyan kuɗin karatunku 500 kacal ta nan* 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay Ko ta nan 1869739740 Sadiya Abdulrazak access bank 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee PAGE 12 Jin shiru babu motsinsu a tsakar gidan sai ta leƙo ta kuwa ga wayam, alamun suna cikin ɗaki, ta fito ta nufi ɗakin ta laɓe jikin labule tana sauraron su, daidai sanda Uwani take cewa"Shi ne za ki biyewa shirmenta? Ita ba ki ga kalarta ba? Kin manta da farinjininta? Ko kin manta sai da na karɓo muku taimako kafin ki samu mijin? Kina buduruwa ma kenan, ina ga kin zama bazawara? Maza ki tattara ki koma ɗakinki, kishiya ba kanki farau ba, ni ma na zauna da ita ballantana ke!". Murja ta ce"Amma babarmu..." Ta daka mata tsawa ta ce"Rufe mini baki! Wallahi sai kin koma, uzuri ɗaya kawai zan yi miki za ki zauna har sai ya zo biko, amma yana zuwa to wallahi ƙafarki ƙafar shi, ni za ki ja wa abun magana a gari?" Daga nan Maryam ta ja ƙafa ta koma ɗaki jiki a sanyaye, sannan ta yi kokowa da zuciyarta da take ta faɗa mata ta zuga Murja, ta raya a ranta ƴar'uwarta ce, idan ta cuce ta kanta ta cuta, haka kuma idan an kasa gulmarta a tire ba za ta ji daɗi ba, don haka ta share su, kwananta biyu a gidan mijin ya zo, ai kuwa ko Baba ma bai shiga zancen ba, ita ce ta sasanta su, ta bi shi suka tafi, suka ci gaba da zamansu shiru abunsu. Nasiru ya zo ya kawowa Maryam kayan abinci, sannan ya ba ta kuɗi don a yi siyayyar jariri, a haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah Ya sauke ta lafiya, ta haifi ɗanta namiji, aka yi suna yaro ya ci sunan mahaifin Nasiru Yusufa, suna ce masa Abba, duk wata sai ya zo ya ba ta dubu ashirin, amma sam bai yi zancen kome ba, wanda a lokacin a yadda Maryam take ƙishin yin aure da burin ta yi zaman aure babu abin da zai hana ta yarda ta koma gidan nasa, sau tari takan tuna da Nazifi ta ce dama ya dawo ya ce ta koma da za ta zauna da Gwaggo lafiya, to amma damarta ta wuce sai dai ta gaba, sai ta ci gaba da kula da ɗanta, ta kuma koma kasuwancinta, tana ra adana ribarta. Taimako ɗaya da Allah Ya yi mata ma shi ne tana da farinjinin masoyan, wannan karon ma tun kafin ta yaye Abba maza suka fara sallama da ita, sai dai ta ce musu sai ta yaye ɗanta. Akwai wani Alhaji Haruna da suka haɗu da shi a kasuwa, ya fi kowa naci cikin masu sonta, don har cewa ya yi zai aure ta a hakan, amma ta ce a'a sai ta yaye, ita bai ma wani kwanta mata sosai ba, saboda yana da matarsa da ƴaƴa huɗu, ita kuma tana da kishi, sam ba ta son zama da kishiya, amma ta sani tun da ita ma yanzu ba buduruwa ba ce dole ta jingine burinta a gefe, aurenta uku da ƴaƴa biyi ba zai yiwu ta ce sai saurayi ba, don haka take ɗan kula shi. Sanda ta yaye Abba ta fara zancen aure sai Nasiru ya ce to zai ɗauki ɗansa, don har ma ya yi wani auren, nan Uwani ta fara subaɗaɗi tana cewa a bar mata shi, a cewarta yaron ya shiga ranta, ba za ta iya rabuwa da shi ba, ita kuma Maryam ta fi zargin wannan dubu ashirin ɗin da yake kawowa duk wata ce ta ruɗe ta, don haka ta ce a'a gara ya ɗauke shi ɗin, ba ta so a ɗora mata wahala, haka dai Nasiru ya ɗauki ɗansa, gidan iyayensa ya kai shi, tun da ba a daɗe da yin auren na shi ba, kar ya hana su cin amarci, duk sati ake kawo mata yaran nata su wuni wataran ma su kwana ɗaya sai a mayar da su, tana jin babu daɗi a ranta, saboda fargabar yadda tarbiyyar yaran za ta kasance, idan ba ƙaddara ba me zai saka uwa tana raye a raba ta da ɗanta? Haka dai take danne damuwarta tana bin su da addu'a, kwanciyar hankalinta ɗaya ce duk mariƙan yaran suna son su, ba ta ga alamar wahala a tare da su ba. Wata ɗaya da mayar da Abba, Alhaji Haruna ya zo da zancen aure faka-faka, ya ce sati biyu za a saka, Maryam da yake har lokacin ba sosai take son shi ba sai ta fara yi masa kwana-kwana, a wannan karon aure take son yi na har abada, saboda haka yana da kyau ta samu wanda zuciyarta ta amince da shi ɗari bisa ɗari, shi auren wanda kake yi wa so sahihi fa yana da alfanu, saboda idan zama ya yi zama saɓani ya fara shiga tsakaninku wannan son da kake yiwa mutum yana taka muhimmiyar rawa wajen haƙurtar da zuciyarka ka ci gaba da zama da shi, kana jure wasu abubuwa, saɓanin wacce ta yi auren manufa babu son miji a zuciyarta, daga wannan abin da ta aure shi don shi ya gushe, shikenan sai ta tsane shi, tun da dama babu so tun farko, idan kuwa ka tsani mutum ba za ka taɓa yi masa uzuri ba, komai ya yi na laifi sai ka yi masa hukunci. Ƙiri-ƙiri Uwani ta nuna ba ta son wannan auren, saboda ganin yadda Alhaji Haruna yake son Maryam kamar bai taɓa aure ba, sai bushasha yake yi mata da kuɗi kamar ba ya so, da alama duk ya fi mazajen ƴaƴanta rufin asiri, dama mijin Mardiyya shi ne abun tutiyarta da nunawa a gari ƴarta ta yi goshi tana auren mai kuɗi, sai ga shi Maryam za ta dusashe tauraruwar Mardiyyar, don haka ta ɗauki hassadar duniya ta saka a ranta, ta yi ta zuga Maryam a kan kar ta aure shi, ta ce"Ke yanzu Maryam da ajinki da kyaunki da komai za ki auri babban mutum mai mata da ƴaƴa huɗu? Ni sai nake ganin kamar kin faɗo" Maryam ta yi murmushi ta ce"Ba faɗuwa ba ne babarmu, kin ga zaman gidan ba shi da wani amfani, kuma idan kika duba kika gani ni ma fa kullum ƙara girma nake, ban yi ƙanƙantar da za a ce Alhaji ya yi mini girma ba, saboda haka wannan ba komai ba ne, Allah dai ya ba mu zaman lafiya". Uwani ta ce"Amma Maryam za ki iya zaman kishi kuwa? Ba mu san halin matarsa ba". Ta ce"Babu ruwana da ita, ba zamanta nake yi ba, idan kin ji kanmu to ita ce ta so hakan". Duk inda ta yi sai Maryam ta tare, haka dai ta rabu da ita ta zubawa sarautar Allah ido, tana jira a yi auren ta ji ta ina matsala za ta fara, ita dai ta san a yadda ta tafi haka za ta dawo, ko ta dawo da ciki ta ƙara haihuwa a gida, haka za ta yi ta rabon yara gida-gida. Sai da Alhaji Haruna ya je wajen Baba da ƙoƙon bara kan a yi wa Maryam magana ta amince da auren da wuri, saboda babu amfanin jinkirtawar, Baba ya zaunar da Maryam ya yi mata nasiha sosai, saboda ya yaba da hankalin mutumin, kuma shi ma a yanzu ya fi so ta auri babba, kamar zai fi haƙuri da halinta, saɓanin yara da ƙuruciya kawai ake zabgawa a zaman auren, ya faɗawa Maryam shi Alhajin ya ce zai yi mata komai na kayan ɗaki, don haka ba ta da wani uzuri na cewa ba ta shirya ba, ta ce shikenan ta amince, Baba sai ya bi ta da kallon tausayi, ba ya jin daɗin wannan mace-macen auren nata, ga shi kwana biyun nan ya ganta duk a sanyaye kamar tana da wata damuwa, duka ta rage tsiwa har ma yawon bin ƙawaye. Yayin da Maryam ta amince da auren Alhaji Haruna, shi kuma yana can ana gumurzu a gidan shi, matar shi Rabi masifaffiyar mace ce, tun da ya yi zancen ƙara auren shikenan ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai tijara take yi, amma shi ya ce mata aure babu gudu ba ja da baya, sai ya yi, wannan ne karo na uku da yake niyyar yin aure, amma sai ta je gidan su yarinyar ta tada tarzoma har a fasa, don haka wannan karon sai ya zaɓi sanarwa Maryam halinta. Ranar ya zo zance yake cewa"Maryam a gaskiya ba zan ɓoye miki ba, matata ba tana da kishi sosai, tun tuni nake son ƙara aure ta hana ni, dama kuma dai lokaci bai yi ba, amma a yanzu ina ji a jikina ke ɗin ce ta aure in sha Allah! Saboda na shirya fito na fito da ita a wannan karon". Maryam ta ce"A'a don Allah ka lallaɓata, kar ka rabu da matarka saboda ni". Ya ce"Ba zan rabu da ita, amma aure dai babu fashi, ke kuma sai ki shirya zama da ita, kar ki ce za ki rabu da ita ta ci tuwo a kanki, ku zauna lafiya dai kawai saboda ni ma hankalina ya kwanta, tun da kin ga gida ɗaya za ku zauna". Maryam ta ce"Ni idan da hali ka raba mana gida mana". Ya ce"Wallahi haka na tsara tun farko, ginina na mata biyu ne ita ma ta sani kuma tun da na gama ginawa na sanar mata zan ƙara aure". Ta ce"To shi kenan, Allah Ya sassauta zuciyarta". Ya amsa da amin, sannan ya nuna mata vedion gidan a waya, gida ne babba mai kyau, daga farfajiyar tsakar gida babba sai a shiga babban falo, mai ɗauke da manyan kujeru, kayan kallo da firji komai dai an saka falo ya haɗu, akwai dining a ciki, sai kitchen da banɗaki, sannan a shiga cikin gidan, ɗakin da zai saka Maryam ɗin ne a farko, ciki da falo da banɗaki a ciki, ita ma na uwar gidan haka yake, sai ɗakin shi da kuma ɗakunan yara guda biyu, sannan wani banɗakin a tsakar gida, ga bantileson mai ɗauke da shuke-shuke da famfuna, gidan ya burge ta, ta miƙa masa wayar tana cewa"Ma sha Allah ya yi kyau". Ya ce"Zuwa gobe jibi za a gama kayan ɗakinki, sai a saka, zan ba ki kuɗi sai ki sayi kayan kitchen ko? Gobe muka yi da ƴan gidan namu za su kawo kayan lefe". Ta ce"Allah Ya kaimu". Ya ɗan yi jim kafin ya ce"Don Allah ku yi haƙuri da abin da ƙila ƴan'uwana za su iya yi a yayin kawo lefen, kin san da yake Sauda ƴar'uwata ce, auren gida aka yi mana, kuma ita Innar tawa ita ta riƙe ta tun tana ƙarama, da ta isa aure ta aura min, to yanzu haka tana nan tana taya ta kishi, don ban faɗa miki ba ne ba ma, amma Sauda ta yi yaji tana can gidanmu, kuma Innar ta goya mata baya ta ƙyale ta, sannan akwai wasu ƙananun maganganu da suke yi, wai ai ba zaman aure kike yi ba, ko na aure ki za ki fita, sai dai kin toshe kunnuwanki gaskiya". Jikin Maryam ya ɗan yi sanyi ta kasa cewa komai ta tafi duniyar tunanin kalar zaman da za su yi. Alhaji ya ce"Maryam kin yi shiru, ina son ki, kuma sannan zan kwatanta adalci daidai gwargwadon iyawata a tsakaninku, ba zan ga wata ɓaraka na ƙyale ba, amma kin san komai sai kin yi haƙuri kafin ki ci riba". Ta ce"To Allah Ya ba mu zaman lafiya bakiɗaya". Suka yi sallama Maryam ta shiga gida a sanyaye, da a da ne da tuni ta juyewa Uwani komai, amma a yanzu sai ta yi shiru ta bar abun a cikinta tana fatan Allah Ya ba su zaman lafiya. Washegari ƴan kawo lefe suka zo, mata ne su biyar, suka kawo akwati guda huɗu, kuma babu laifi ya saka mata kaya sosai, duk da sun rage a cewarsu ai wannan kayan bai cancanci bazawara ba, ƴan'uwa da aka gayyato karɓar lefe da ƙawayen Uwani suna ta ɗaga kaya suna cewa"Ma sha Allah! Kaya sun ce". Wata cikin masu kawo kayan ta taɓe baki ta ce"Iyyi kaya sun yi fa! Sai fatan Allah Ya sa kunun banza ya ƙare a farau-faru ɗin banza". Wata ta ce"A to, tun da dai amaryar an ce ba mazauniya ba ce a gidan aure". Wata cikin dangin babar Maryam ta ce"Daɗin abun dai shi ya gani ya yaba, sai a bar shi da zaɓin shi". Wata ta ce"Kuma mutuwar aure ai ƙaddara ce, ƙaddara kuwa tana kan uban kowa, ko a yau idan uban mutum ya kwanta ya mutu uwarsa ta zama bazawara". Wata cikin masu kawo kayan ta hasala ta ce"Kin ga kar ki zage ni, wallahi kar ki sake, dama an faɗa mana ba gidan arziƙi ba ne, ƙaddara ce da biyewa zuciya ya kawo shi". Nan aka fara maganganu, hayaniya ta kaure a gidan, aka rabu baran-baran dutse a hannun riga, ko tukuici ba a samu damar ba su ba, suka tafi. Wannan abu da ya faru ya ƙarawa Maryam baƙinjini a wajen dangin Alhaji Haruna, musamman mahaifiyarsa da ta cika ta yi fam kamar za ta yi bindiga, musamman idan ta kalli Sauda da yaran a gida, a cewarta ya zaɓi wata mara tarbiyya ya watsar da matarsa ta ƙuruciya da ƴaƴansa, don haka fushi take yi da shi sosai. A haka dai Alhaji ya toshe kunnensa, suka yi ta hidimar gabansu shi da Maryam, har ranar auren ta zo, aka ɗaura aurensu, an yi yini a gidan su Maryam saɓanin shi da babu abin da aka yi, ko abincin ƴan ɗaurin aure a can gidan matar baban shi aka yi, shi dai yana ta zumuɗin zuwan amarya babu abin da ya dame shi. Bayan sallar isha'i aka ɗauki Maryam aka kai ta gidan miji a karo na huɗu, wanda take fatan ya zama na ƙarshe da za a sake ɗaura aurenta, ma'ana wannan aure ne ta yi na mutu-ka-raba. (To fa! Ya kuka hango zaman Maryam a irin wannan gidan?) Littafin nan na kuɗi ne a kan naira 500 kacal! 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3 PAGE 14 Suna ƙule a ɗakinsu baban nasu ya dawo, Maryam ta tare shi ranta fess, ta haɗa masa ruwan wanka ta kai banɗaki, abin da ba ta taɓa yi wa sauran mazan da ta aura ba, ko ruwa a buta ba ta taɓa zuba musu ba, amma shi wannan da yake zaman gaskiya ta zo ta ɗaura ɗamarar yi masa hidima iyakar iyawarta, tsaf ta taya shi shiryawa bayan ya fito, sannan ta ja hannunsa kamar wani ɗanta zuwa falo, ta kawo masa tuwon, tana ba shi a baki suna ta firarsu cike da nishaɗi, har ya yi mamakinta saboda shi kansa ya san kafin auren ba wani son shi take sosai ba, kiran sallar magriba ne ya tashe shi, ya yi alwala ya tafi masallaci yana jin shi fess da shi, ya manta rabon da ya samu kulawa da soyayya irin wannan, sautari sai bayan magriba yake yin wanka saboda sai ya ce Sauda ta dafa ruwan take dafawa, wataran ma a haka yake kwanciya ko ya yi da na sanyi, sannan Momy ce mai kai masa abinci dining, idan ma ya shiga ɗakinsa yana wani aikin ko kuma ya shigo da wata damuwar, babu ruwan Sauda da zuwa ta ji dalilin ƙin fitowarsa, sai dai ta aiko masa da abincin ɗakin nasa, sannan babu ruwanta da tambayar shi fita unguwa, indai ka ga ta tambaye shi sai dai idan nesa sosai za ta je, gidan Inna kuwa idan za ta je tun rana idan ta tafi sai dare idan ya je yi mata sai da safe su taho tare, babu ruwanta da me zai ci ranar, babu dai wata kulawa akwai matsaloli birjik, wanda shi ne dalilinsa na son ƙara auren, kuma tun yau ya fara tunanin za a samu canji in sha Allah! Ya dawo daga masallaci Maryam ta ga bai yi maganar yaran ba, ta dai leƙa bayan fitarsa ta ce duk su yi alwala su yi sallah. Ta ce"Alhaji dama ina so mu yi magan a kan yaran nan". Ya ce"To, wasu yara?" Ta ce"Yaranka". Ya ce"Me ya faru? Ba za ki samu matsala da su ba in sha Allah! Kin ga ma yara ne, uwar ma don Allah ki kau da kai ga matsalolinta". Ta ce"Ba wata matsala ba ce, ka ga yau taliya na dafa da safe, na ba su suka ce wai ba sa cin taliya, sai kowaccensu ta shiga zaɓar abin da take so, ni kuma na ga ba zao yiwu na yi girki har kala huɗu ba, ko hakan bai zama almubazzaranci ba ai ka ga ni ma ina buƙatar hutu, tun da ba bautarsu na zo yi ba, sannan ba ma tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓin abin da za su ci, na ce su tsayar da guda ɗaya, suka ce tuwo, shi ne na yi, loma ɗaiɗai suka yi suka ce mini ba daɗi, ƙarshe sai suka sha golden morn suka ƙule a ɗaki". Alhaji ya ce"Ikon Allah! Wai kina nufin su yaran suna gidan nan? Waye ya kawo su?" Maryam ta ce"Wai dama ba ka sani ba? Daga makaranta mai adaidaita sahu ya kawo su". Ya ce"Yanzu suna ina?" Ta ce"Suna ɗaki". Ya shiga ƙwala musu kira ransa a ɓace, suka fito, Kausar da Momy suka haɗa baki wajen faɗin"Abba yunwa muke ji, ba mu ci komai ba". Ya daka musu tsawa da faɗin"Ku nemi wajen zama!". Suka zauna duk suka sha jinin jikinsu, saboda Abban nasu ba mai yawan faɗa ba ne. Ya ce"A cikinku waye ba ya cin taliya? Yaushe kuka daina cin taliya?" Duk suka yi shiru suna raba ido. Ya ce"Wato ku har kun yi girman da za ku yiwa babba rashin kunya? Ku sa ta yi tuwo ku ce babu daɗi?" Ya kalli Maryam ya ce"Idan akwai ki sako musu". Ta tashi ta je ta ɗakko shi a yadda suka bar shi, ta ajiye, ya saka su a gaba sai ga shi sun cinye tass, har da ƙari, ya yi mamakin dalilin da ya sa suka yi mata haka, ya zaunar da su ya yi musu nasiha sosai, ya nuna musu ita ma Maryam babarsu ce, duk abin da suka san ba za su yiwa babarsu ba to kar su yi mata, suka ce to, sannan ya saki jiki da su suka yi fira, Maryam ta ce su je ta yi musu wanka, ba su yi musu ba suka wuce, sai a lokacin ma ta sa suka yi home work, ƙarfe takwas Abba ya ce su je su kwanta, ita kuma Maryam ta kwashi unifom ɗinsu ta tafi wankewa, sai ga shi sun yi wankin a tare da Alhaji suna yi suna fira. Ita kuwa Momy suna shiga ɗaki ta ɗauki wayar ta sanarwa Sauda duk yadda aka yi, Sauda ranta ya ɓaci matuƙa ta ji kamar ta taso ta taho gidan yanzu, ta fara tunanin wato daga zuwanta za ta sa ya tsani ƴaƴansa har yana yi musu faɗa? Nan gaba ai sai duka, kenan ya goyi bayanta nan gaba ko ita ce da laifi tana kallo za a tauyewa ƴaƴanta haƙƙi, ai kuwa ba zai yiwu ba, ta fara tunanin hanyar da za ta bi don ta hana su cin amarci, sai dai yaran sun yi ƙanƙantar da za ta saka su yi wata kissar, don haka kawai ta yanke gara ta dawo su fara gabza yaƙin, ta ce wa yarinyar ta yi haƙuri su kwanta, amma kar su sake bari ta yi musu wanka, ita ta yi da kanta sannan ta yiwa ƙannenta. Washegari haka Maryam ta yi sammakon tashi saboda yaran, don tun a daren ya faɗa mata girki biyu ake yi da wanda za su ci, da wanda za su tafi da shi, ta dafa shayi ta soya doya da ƙwai ta saka musu a lunch box ɗin, sannan ta tafi ɗakinsu, ta tarar Momy ta yi wanka za ta fara yiwa sauran, Kausar tana cewa ita ba za ta yi mata, ta ce"Ya za a yi ki yi musu? Ke ma ai ba wuce wankan kika yi ba, ku wuce na yi muku". Momy ta ce"Mu fa Ummanmu ce kawai take yi mana wanka". Maryam ta ce"Tun da yanzu ba ta nan ai dole ku bari na yi muku". Ta ce"Mu dai a'a". Maryam ta juya ta fita, ta sanarwa da mahaifinsu, da mamaki ya ce"Ha'a, wai me yasa yaran nan suke haka ne?" Ya fito ya zo ɗakin, ya ce"Ke Momy! A kan me ba za ta yi muku wanka ba?" Ta ce"Ummanmu ta ce kar mu yarda da ita". Maryam ranta ya ɓaci ta ce"Ai shikenan". Ta juya ta bar ɗakin. Ya ce"Ummanku? Au haka ta tsara muku? Abin da ta turo ku ku yi kenan? To zan haɗu da ita! Ku saka kayan naku a haka ku tafi, idan ta damu sai ta dawo ta dinga yi muku wankan". "Maza ku saka ku fito, mintu uku na baku". Ya ƙarasa a tsawace yana jin dole ya takawa Sauda burki don ba za ta lalata masa tarbiyyar yaransa ba. Yana fita Momy ta shiga banɗaki ta kira Sauda ta sake faɗa mata, ai kuwa ta hasala tana ta zage-zage. Suka fito kowaccensu babu sakewa, sai a lokacin suka gaishe shi, ya amsa kafin ya ce"Kun gaishe da Antinku?" Duk suka yi shiru, sannan suka gaishe ta ɗaya bayan ɗaya, suka karya mai adaidaitansu ya zo suka tafi makaranta. Sun gama karyawa ya ce da Maryam"Don Allah ki yi haƙuri, yara ne kin san duk yadda aka tsara musu ba za su yi nazari ba, amma zan same ta na yi mata magana, idan ba za ta barki ki yi yadda ya dace da su ba, to ta zo ta zauna da su". Maryam ta ce"Allah Ya kyauta". Kafin ya tafi kasuwa ya tsaya a gidan nasu, ya gaida Inna, ya samu Sauda tana karyawa, ko kallon shi ba ta yi ba, ya ce"Yawwa Sauda na ga kin aiko mini yarana, ina son ki sani Maryam za ta iya riƙe su fiye da yadda kike kula da su, sai dai ki sani indai kin bar mata su to fa sai dai ki koma gefe ki yi kallo, ba zai yiwu tana tufka kina warwarewa ba, saboda shirme kin zauna kina tsarawa yara shirmen banza, to matata uwa ce a gare su, ya zama dole su yi mata biyayya tun da ni na haife su!". A hasale Sauda ta ce"Ita ta haifar mini su? Wallahi babu shegiyar da ta isa ta tsarawa ƴaƴana yadda za su yi, yarinyar da ba ta samu tarbiyya ba tun daga tushe, har kana kallona kana faɗa mini kalmar matarka?" Sai kuma ta saki wata dariya mai kama da ta tsantsar baƙinciki ta ce"Heee masu mata manya! To a yi mu gani idan tusa za ta hura wuta, yarinyar da ba ta zaman aure har wata abar alfahari ce? To sai ka jira ka ga zaman ya yiwu kafin ka fara wulaƙanta ni ka watsar da ƴaƴanka!". Ya ce"Ni dai na faɗa miki, idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba!". Ya fice ya barta tana ta bambami. Inna duk a gabanta a ka yi komai, ba ta ce wani abu ba, dama idan da sabo ta saba da faɗan nasu, sai da ya fita ta ce"Sauda a nan fa ba ki da hujjar da za ki saka yara su raina matarsa, idan har ba kya son ta shiga sabgar yaranki to ya zama dole ki koma kansu ki ci gaba da kula da su, kin ga dai yadda ya gigice a kan yarinyar nan yake rawar kai, kina nan a zaune za ta gama mallake shi da kissarsu ta zawarawa, irin wannan gogaggun yaran da suke yin aure-aure wallahi ki kiyaye su,sai kin tashi a tsaye kin ɗaura ɗamara, saboda haka ni yanzu umarni nake ba ki ba shawara ba, ki kama hanya ki koma ɗakinki a yau, ki kula da ƴaƴanki, sannan ki yi iya yinki na ganin ba ta mayar da ke bora ba, kar ki yarda ta ƙwace miki mijinki da gidanki". Sauda ta ce"Shi kenan Inna an jima zan koma". Inna ta ce"Ko ke fa, wannan ai kina nuna mata ta fi ƙarfinki ne ba za ki iya da ita ba, saboda haka ki koma ki nuna mata gida naki ne, kuma miji da ƴan'uwan shi ma naki ne!". Sauda ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta tashi ta shige ɗaki. Zama ta yi ta kira ƙawarta a waya ta sanar da ita za ta koma, ta ɗora da faɗin"Don Allah ya za a yi ki haɗa ni da wannan mai maganin? Na san shegiyar tana nan ta gigita shi, bazawara ana marari za a samu miji". Aliya ta sheƙe da dariya ta ce"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna mini ranar da Sauda za ta nemi maganin gyara zama". Sauda ta ce"Au shaƙiyanci za ki yi mini kenan". Ta ce"To ai ke ce kullum cikin kuri kike kina da ni'imarki ba sai kin sha komai ba, yanzu kika dawo hanya Hajiyata, zan turo miki lambarta". Sauda ta ce"Malama yanzu fa nake so, zai yiwu ta aiko mini kayan a yau?" Aliya ta ce"In sha Allah!". Tana turo mata, ta kira ta a waya, suka yi ciniki gabaɗaya irin wanda ake cewa ban da me kishiya su ta siya na dubu ɗari, kuɗin gudunmawa ne dangi suka haɗa mata don ta yi gyaran dama, da yamma aka aiko mata da kayan, ta gama shirinta tsaf jira kawai take yi ya zo yi wa Inna sai da safe ta bi shi su tafi. Yau ɗin Maryam shinkafa da miya ta yi, da alama yaran ba ma su taurin kai ba ne, don kuwa yau babu wanda ya yi magana a kan abinci, kowa ya ci, sannan sun tsaya ta yi musu wanka, ban da babbar da ta ce ita ce take yi da kanta dama, sai ta rabu da ita, amma dai sam sun ƙi yin fira da ita, don haka ita ma ta ke ta harkar gabanta. Da yamma da ya dawo sai da ya tambaye ta yaran, ta ce babu wata matsala, ya yi wanka ya ci abinci, ya fita sallah ya dawo, dama idan zai fita sallar isha'i da mota yake fita saboda daga can yake wucewa gidan Inna ya yi mata sai da safe, don haka yau ma ya wuce, ya ɗan zauna bayan sun gaisa, hat yanzu ta ƙi dawo masa kamar baya, babu wata fira haka dai babu yabo babu fallasa, ya tashi zai tafi ta ce"Ka zauna". Ya zauna yana sauraronta. Ta ce"Sauda za ta bi ka ta koma kan ƴaƴanta, saboda haka kar na ji kar na gani, ka zama mai adalci a tsakaninsu, kar sabo ya sa a watsar da tsoho, ta farkon dai ita ce dahir ɗinka, ba zan ɗauki wulaƙanta mini ƴa ba wallahi, don haka ka ja kunnen yarinyar nan, ta kula ta kiyaye, tun da zuwa ta yi ta tarar da ita da ƴaƴanta, ba ta san faɗi-tashin da aka yi kafin ka kai matakin da kake a yanzu ba". Ya ce"To Inna za a kiyaye in sha Allah!". Ya tashi ya fita yana yi mata sai da safe, ya ɗan jima a motar kafin Saudar ta fito da akwatinta, ta buɗe motar ta shiga ya ja suka tafi, babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka ƙarasa gidan, lokacin yaran suna ɗaki, Maryam kuwa tana hakimce a babban falo cikin wata fitinanniyar rigar bacci, suka shigo da sallama, niyyarta idan ya shigo ta je yin oyoyo amma sai ta yi turus ganin shi tare da wata wacce ba sai an faɗa ba ta san matarsa ce, sai da gabanta ya faɗi, ta daure ta ce"Sannunku da zuwa". Alhaji kuwa ya bi ta da kallon burgewa, wankan ya burge shi, don Sauda babu ruwanta da wani wankan dare ballantana kuma kayan bacci, dogayen riguna ne marasa nauyi kayan baccinta tun da ta fara haihuwa, ya haɗiyi wani yawu muƙut wanda har Sauda ta ji sautin, zuciyarta ta ƙara kumbura, ta kasa shigewa kawai tana tsaye tana ƙarewa Maryam kallo, sai Alhaji ne ya katse shirun nasu da cewar"Na barki ke kaɗai a gida". Sauda ta yi masa mugun kallo ta ce"E tabbas ita kaɗai, tun da a yanzu ita kaɗai kake kallo a mutum, su ƴaƴan naka ba mutane ba ne, komai ma ya same su ta matarka kake yi! Hmm!" Ta wuce fuuu ta yi cikin gidan. Ya yi murmushin yaƙe ya ce wa Maryam"Kin ga Sauda ta dawo ko? Don Allah ku zauna lafiya, kin ga ma tun da ta dawo kan yaranta za ki fi kula da ni sosai ko?" Ta yi farr da ido ta ce"Ƙwarai kuwa, zo ma mu je ka gani". Ta yi ɗakinta, shi kuwa ya bi bayanta kamar raƙumi da akala, a gaban Sauda suka shige ɗakin nata, wacce ta fito daha ɗakin yaranta za ta shiga nata, ta manta rabon da ya shiga ɗakinta, sai dai ita ta bi shi nashi ɗakin idan ya kira ta, amma shi ne ya zo ya shige ɗakin amarya ko kunya ba ya ji, ta yi ƙwafa tana cewa"Lallai akwai aiki a gabana, tsohuwar kilaki ya kwaso". Ta gagara zama a ɗaki, ko wanka ta kasa yi, sai leƙe take yi tana jiran fitowarsa amma shiru har ƙarfe sha ɗaya ta yi, ga shi ko sallar isha'i ba ta yi ba, kuma ta kasa yi, saboda tana son tabbatarwa da gaske a nan zai kwana? Shi kuwa Alhaji yana can Maryam ta saka shi a kwana ta kalallame shi, ta kanainaye shi har ya manta ma a ɗakinta yake. Ƙashe dai sai sha biyu Sauda ta haƙura da leƙen ta yi sallah, ta kwanta, sai ta gagara yin bacci gabaɗaya ya ƙaurace mata, ta fara tunanin yanzu fa yana can tare da ita, lallai namiji ba shi da kunya, can dai ta fara tunanin ya za ta yi ta hana su sukuni, ta tashi ta fito a hankali ta shiga ɗakin yaranta, ta haska su, sai baccinsu suke yi hankali kwance, ta shiga tashinsu bisa shawarar zuciyarta, ta dinga jijjiga su duk suka tashi suna murza ido, ta sakawa fuskarta alamun firgici ta ce"Ku tashi don ubanku, aljanu ne suka shigo gidan! Suna ɗakin nan a ƙarƙashin katifarku!". Ai kuwa a tare suka fara ihu, ta ce"Ku kwanta ba za su yi muku komai ba". Suka fara kuka suna rirriƙe ta suna cewa a ɗakinta za su kwana. Ta fizge tana cewa"Suna can a ɗakina sun cika ɗakin kowa ya yi ta kansa". Ta fice a guje suka mara mata baya, amma kafin su shiga ta banke ƙofarta ta saka sakata, gabaɗaya suka ruɗe suka dinga ihu a mugun firgice kamar za su shiɗe. A tare Maryam da Alhaji suka fito a ruɗe, suka tarar yaran suna ta buga ƙofar ɗakin babarsu, fitowarsu ya sa suka yi wajensu suna shigewa jikinsu cikin matsanancin kuka, Alhaji ya ruɗe ya fara tambayarsu me ya faru? Suka ce"Aljanu, Abba aljanu a ɗakinmu". Gabansa ya faɗi ya ce"Aljanu kuma? Me kuka gani?" Inaa sun ruɗe, sai a lokacin Sauda ta fito tana cewa"Mene ne?" Suka yi kanta suna kuka. Alhaji ya ce"Kin ji wai aljanu". Ta ce"Aljanu kuma?" Ya wuce ɗakin a tsorace yana addu'a, ya haska bai ga komai ba, ya dawo a sanyaye ya ce"Abun ya bani mamaki wallahi". Sauda ta ce"To kar dai fa ture aka fara yi musu". Ya ce"Wane irin ture? Waye zai yiwa yaran nan ture?" Ta ce"Wanda suka tsonewa ido mana, an ga yara sun cika gida tubarkalla ana son haukata su don kar ƴaƴana su moru". Alhaji ya ce"Subhanallah! Kar na sake jin magana irin haka!". Ya janyo yaran yana cewa"Tsorata kawai kuka yi babu komai a ɗakinku kun ji? Ku je ku kwanta zan yi muku addu'a". Sauda ta ce"Au da gaske sai ka kora su, saboda kar kwanan ɗakin amarya ya wuce ka? Hmm dama uwa ce ba ta gudun ƴaƴanta duk runtsi, ku shigo nan!". Ya ce"Ba za su shiga ba! A ɗakin nasu nake so su kwana ina son fahimtar wani abu ba ne kafin Allah Ya kaimu gobe na kira malamai a yi addu'a". Maryam ta ce"Allah Ya rufa asiri". Ta koma ɗakinta, ita ma duk sai tsoron gidan ya kama ta. Ya saka su a gaba suna turjewa suka shiga, ya zauna ya kunna karatun qur'ani a wayarsa, yana addu'a yana tofa musu, amma da bacci ya fara ɗaukarsu sai su zabura su farka suna maƙale shi, a haka suka kwana, ita kuwa Sauda ta yi baccinta ranta fess, tun da dai ta haramta musu wannan daren to ita fa buri ya cika, kuma ta saka a ranta yanzu aka fara wasan, ta ɗau alƙawarin sai ta fitini gidan gabaɗaya, sai kwana a ɗakin shi ya gagari Maryam, kafin ta tankaɗa ƙeyarta waje. LAST FREE PAGES! A NAN ZAN TSAYA DA FREE PAGE, DAGA WANNAN SHAFIN DUK WANDA KUKA GANI A PAID PAGE NE, ƳAN'UWA KU BIYA KU KARANTA CIKIN AMINCI, YANZU ZA A FARA WASAN NAN, TAFIYA TA KISHI MAI CIKE DA ƘULLA-ƘULLA TURA ƊARI BIYAR ƊINKI TA NAN KI SHA KARATU CIKIN AMINCI. 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay 08028966015 [2/11, 4:53 PM] Sadiya abdulrazak: *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* https://chat.whatsapp.com/G08KLEmlF3gJ3X4npkfIee PAGE 13 Alhaji Haruna har zuciyarsa ya yi niyyar kamanta adalci, saboda haka duk da Sauda tana gidansu da ya tashi siyan kazar amarci haka ya siya da nata kashin, dama a baya kashi biyi yake siya da nata da na Innarsa, yau kuwa sai ya sayi kashi uku, ya tafi gidan don ya yiwa Inna sallama kamar yadda ya saba a kowane dare, lokacin tara saura kwata, ya same su a falo, ya ƙarasa a sanyaye ya zauna yana gaishe da Inna, ta amsa fuska babu walwala, ga yaran can rakuɓe a gefe, sun nuna kamar ba su san shi ba, saɓanin da, da idan ya shigo gida a guje suke rige-rigen zuwa gare shi, yaran su huɗu ne, Momy ita ce babba shekararta goma sha ɗaya, sai mai bi mata Kausar, shekararta takwas, sai Ummi shekararta shida, sannan Nana mai shekara huɗu, daga kan Nana ya ce mata ya kamata ta ɗan yi planing don mahaifarta ta huta, ta biye masa ta saka inplan na shekara uku da ya yi expire ta cire ta sake saka wani, don haka yanzu take ganin dama shi burinsa ta tsaya da haihuwar saboda amaryarsa ta zo ta zazzago masa ƴaƴa, kallo ɗaya ta yi masa ta kau da kai gefe, saboda mugun haushin shi da take ji, ya ce da babbar ƴar"Momy ko gaisuwa babu?" Sai ta waiwaya ta kalli mahaifiyarsu, saboda tun da suka yi yajin nan kullum sai ta zaunar da su ta faɗa musu babansu yanzu ya daina son su dukansu, shiyasa zai ƙara aure, kuma shi ya kore su dukansu, sannan amaryar da zai aura muguwa ce, kashe ta za ta yi ta zama ita ce uwarsu, kuma dukansu za ta dinga yi, tana hana su abinci, shi kuma baban nasu ba zai yi komai ba, saboda ya daina son su, haka dai ta tsara musu abubuwa kala-kala daidai da tunaninsu, su kuwa hakan ya sanya musu damuwa da jin tsoron baban nasu. Sai da ya yi magana sannan suka fara gaishe shi ɗaya bayan ɗaya, ya amsa yana ce musu"Ya makaranta?" Sauda ta yi wani huci kamar zakanya ta tashi buguzun-buguzun ta bar falon, kasancewarta mace mai ƙiba kuma doguwa, ya bi ta da kallo, sai ya ajiyewa Inna ledarta ya bi bayan Sauda ɗin, zaune ya tarar da ita ta naɗe hannu a ƙirji, ya yi sallama tana kallon shi yana kallonta ta ƙi amsawa, ya zo ya zauna a gefen katifar da take, sai ta miƙe za ta fita, ya ce"Kin ga Sauda zauna mu yi magana". Ba ta zauna ba, amma ta fasa fitar,shi ma sai ya tashi tsayen ya ce"Ni fa ban ƙara aure saboda kin gaza mini ba, sai don ina da ra'ayin yin hakan, kuma dama can mata biyu ne a ƙaddarar aurena, idan mai afkuwa ta afkuwa ya kamata ki ajiye komai a gefe, ki koma ɗakinki, ni sai nake ganin ba girmanki ba ne a ce yarinyar nan ta zo ta tarar kin yi yaji, kamar hakan zai janyo miki raini". Ta yi shiru dai ba ta ce komai ba. Ya ci gaba da faɗin"Maryam ƙanwarki ce, kuma tana da sauƙin kai, za ku zauna lafiya in sha Allah, ni dai yanzu ki wuce mu tafi gida kawai, wannan abin da kika yi sai ki jawo mini zagi a gari, nan kuwa ba ni na kore ki ba". Ta ce"Babu inda zan je, ka je ka zauna da wacce ka zaɓa, kuma sannan zan aiko maka da yaranka, tun da ita ka zaɓa kake ganin za ta iya sai ta riƙe maka!". Ya ce"To shikenan, ni dai ba zan yi miki dole ba, musamman ma da Inna ta goya miki baya, saboda haka ki yi duk yadda kika tsara, amma ki sani ni dai ba zan sake ki ba". Ta ja dogon tsaki. Ya ce"Akwai abin da kuke buƙata?" Sai a nan ta ce"Ba na buƙatar komai daga gareka, kai kanka bana buƙatarka ballantana abun hannunka, ita da kake baƙo a wajenta ka je can ka yi mata komai!". Ya yi ɗan murmushi ya ce"Sauda kina da kishi, amma ban taɓa zaton za ki bar gidanki saboda kishiya ba, wai har kina barazanar za ki ba ni ƴaƴana, to ki ba ni, zan riƙe su". Ya ajiye mata ledar hannunsa, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya ajiye mata ya fice, bai tarar da kowa a falon ba, sai ledar da ya ajiyewa Inna, cike da dumuwa ya bar gidan. Amma ko da ya je gida ya tarar da amaryarsa sai ransa ya yi fess, yana son Maryam sosai, suka sha amarcinsu hankali kwance har ta mantar da shi yana cikin damuwa. Washegari ya tafi kasuwarsa, ita kuma ta gyara gidan, tana ta baƙi jefi-jefi da maƙota da ƴan'uwa, maƙotan dai duka ƙawayen Sauda ne, don haka gulma ce kawai take kawo su, kowacce idan ta shiga ta ganowa idonta sai ta kira Sauda ta yi mata sharhi, wanda hakan bai ƙara mata komai ba, sai baƙinciki da tsanar Maryam ɗin, ita kuwa Maryam dama ta yi tunanin za a yi hakan, don haka babu wata mace da ta sakarwa fuska, kadaran-kadahan take karɓarsu. Wajen ƙarfe biyu ta gama girki tana sallah ta ji ana buga gidan, an daɗe ana bugun saboda tana tayar da sallar aka fara, da ta idar ta taho da sauri ta buɗe, sai ta ga yara ne su huɗu da unifom a jikinsu, jikinta ya ba ta ƴaƴan mijinta ne, sai mai adaidaita sahun da ya ajiye su ya ƙaraso da waya a kunnensa yana cewa"Ai ga shi ma ta buɗe". Don kuwa da ya ga yaran suna ta bugawa ba a buɗe ba, sai ya kira Sauda ya faɗa mata, ta kuwa harzuƙa ta miƙe tsaye tana zage-zage da cewar gidan ubanta ne da za ta hana su shiga? Ya miƙawa Maryam babbar jakar dake hannun shi yana cewa"Ga shi mamansu ce ta ce na kawo su". Maryam ta karɓa ta ce"To ka gaishe ta". Ta kalli yaran ta ce"Ku shiga, sannunku da zuwa". Babu wanda ya amsa, ballantana su gaishe ta, wannan huɗubar mahaifiyarsu ce, suka shige ɗakin kwanansu, Maryam ta biyo su da jakar kayansu ta ajiye tana cewa"Ku cire unifom, sai na yi muku wanka ku canza kaya ko?" Momy da take babbar ta ce"A'a, mun yi wanka da safe". Ta ce"To ku canza kaya ku fito ku ci abinci". Suka fara kiciniyar cire kayan, ban da Momy da ta ja ta tsaya tana ta ɓata rai, sai da Maryam ta fita sanan ta fito da duka kayan cikin jakar, sai ga waya keypad ta bayyana, ta ɗauka ta shige banɗaki, ta danna ta kira babarsu a waya, Sauda tana ganin kiran ta miƙe ta shige ɗaki, don ko Inna ba ta san da wannan shirin nata ba, tana ɗagawa ta ce"Momy yaya aka yi?" Momy ta ce"Ta ce mu yi wanka na ce mata mun yi, shi ne ta ce mu fito mu ci abinci". Sauda ta ce"To ko me ta dafa ku ce ba kwa ci, kowa ya zaɓi abin da yake so ya ci, kin ji ko?" Ta ce"To, amma wallahi Nana ce uwar kwaɗayi, na san ci za ta yi". Ta ce"Ki gargaɗe ta, ki ce idan ta ci za ta mutu, ta ce doya take so ta ci, ku kuma ku zaɓi wani abun kowa na shi da ban". Ta ce"To" Ta ce"Ki ɓoye wayar nan fa sosai, ki saka a ƙarƙashin katifarku, kuma kar ki fita ko falo da ita". Ta kashe wayar ta fito ta faki idon ƙannen nata ta ɓoye, sannan ta ba su kayan da za su saka, ta zaunar da su ta ce"To Umma ta ce ko me ta dafa kowa ya ce ba ya ci, ke Nana ki ce doya da ƙwai za ki ci, ke Kausar ki ce shinkafa da wake, ke ke kuma Ummi ki ce shinkafa jollop, idan kuma shinkafar ta dafa sai ki ce macaroni, wallahi Umma ta ce duk wacce ba ta ce haka ba sai ta ci ubanta". Duk suka gyaɗa kai, sannan suka fito a tare, Maryam tana falo tana chart, ta ce"Kun fito?". Ba su ce komai ba, ta tashi ta shiga kitchen ta juye musu taliyar da ta dafa da miya, leda ɗaya ce dama ta dafa ko ci ba ta yi ba, plate biyu ta yo ta kawo ta ajiye a gabansu tana cewa"Ku yi maza ku ci". Daidai lokacin kiran Uwani ya shigo wayarta, ta ɗaga tana gaishe ta, Uwani ta ce"Oh! Maryam har na fara kewa, ya kike ya gidan?" Ta yi ƴar dariya ta ce"Lafiya ƙalau". Ta ce"Babu wata matsala dai ko? Kin san zama da kishiya". Da a da ne sai ta faɗa mata ga shi har yaran shi sun zo, amma yanzu kuwa ta ce mata babu komai, kuma ba ta ma faɗa mata uwar gidan ta yi yaji ba, ko da ƴan kai amarya suka zo ma duk a zatonsu ɗaki ta shiga ta kulle saboda kishi. Suna gama wayar ta juyo ta ga yaran ba su da niyyar sakkowa su ci abincin, ta ce"A'a! Ya ba ku fara ci ba? Ko sunayenku ba ku faɗa mini ba ma, ku gama ci ku zo mu yi fira ko?" Momy ta ce"Mu ba ma cin abinci a ƙasa sai a dining, kuma ba ma son taliya". Ta ce"Ba kwa son taliya? Kwata-kwata ba kwa ci a gidan?" Ta ce"E". Maryam ta ce"To me za ku ci?" Momy ta ce"Ni tuwo nake so". Ummi ta ce"Ni kuma jollop ɗin shinkafa". Nana ta ce"Ni doya da ƙwai". Kausar ta ce"Ni shinkafa da wake, da mai da yaji da salak da tumatur da albasa, da cocomba". Ta ƙarasa da karsashi, don dama Momy kowa abin da ta san ya fi so ta ce ya faɗa. Maryam ta tsaya kallon su da mamaki, ba sai ta wahalar da kanta da tunani ba, saboda ba zai taɓa yiwuwa ta biyewa yara ta yi girki kashi-kashi ba kamar wata ƴar aiki, girki kala huɗu? Sannan wannan ai ba tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓar abincin da za su ci, don haka ta ce"Duk na ji, amma fa sai dai ku zaɓi abu guda ɗaya dukanku, saboda kun ga idan na yi girki har kala huɗu na yi almubazzaranci, don haka ku tsayar da abu ɗaya". Duk sai suka kalli Momy tun da ita ce shugabar tawaga, ta ce"To ai mu ba ma cin taliya". Ta ce"Na ni ba za ku ci taliya ba, ku zaɓi kala ɗaya sai na dafa muku". Ta ce"Sai dai a yi mana tuwon shinkafa miyar agushi". Maryam ta ce"Ni ba ni da agushi, sannan ba zan takurawa babanku ba yana kasuwa, amma akwai wake, zan yi muku miyar wake". Da gaske Nana ba ta cin miyar wake, don haka ta taɓe fuska za ta fara kuka ta ce"Ni dai ba zan ci ba". Kausar ta ce"Nana ba ta cin miyar wake". Maryam ta ce"Zan dafa mata indomi". Ta wuce kitchen ɗin, a ranta tana mamakin yadda aka sangarta yaran, ita idan ƴaƴanta ne gaskiya ba za ta saki fuskar da za su yi mata haka ba, amma su ma ɗin muddin a wajenta za su zauna to kuwa tabbas sai ta saita su. Ta ɗora tuwon da yake ta tarar da komai har farar shinkafar da akwai, da yake gas ɗin mai huɗu ne tana wanke waken sai ta ɗora miyar, sannan ta zauna ta ci taliyar. Tana tafiya kitchen Momy ta tashi ta shige ɗakinsu, ta ɗauki waya ta shiga banɗaki ta kira Ummansu, tana ɗagawa ta zayyane mata komai, Sauda ta ce"Amma dai Allah Ya yi miki albarka Momy, yanzu kin san yadda za a yi?" Ta ce"A'a". Ta ce"Idan ta gama tuwon ku yi loma ɗaya ku ce babu daɗi ku ba kwa ci kun ji ko? Ko kun ji daɗi fa kar ku ci". Momy ta ce"To Umma yunwa muke ji fa". Ta ce"Idan kun ƙi ci sai ku shiga kitchen ku ɗauki golden morn ku haɗa ku sha, idan ya dawo ku ce masa ba ku ci komai ba yunwa kuke ji, ku ce ba ta ba ku tuwon ba". Momy ta ce"To". Amma a sanyaye, saboda yunwa take ji. Sauda ta ce"Ki yi haƙuri kin ji ƙawata, ni na san me zan siya muku". Ta ce"To". Ta ajiye wayar, sai da Maryam ta koma kitchen sannan ta sake tsarawa yaran, ta ce inji Umma, ta ce sai sun ƙi ci za ta dawo, ai kuwa suka yarda. Sai da ta sauke tuwon ta dada indomin saboda ta manta, ta zubo ta kawo musu,lokacin har ƙarfe uku ta gota, ta ajiye ta ɗakkowa Nana indomi, ita kam ana ajiyewa ta fara ci ta manta da gargaɗin yayarsu saboda yunwa take ji, kuma dama duka-duka shekararta huɗu, su kuwa manyan ba su saɓa ba, loma ɗaya kowa ya yi a layi, idan wannan ya ci, sai wannan ya ci, sai suka tsaya suna kallon tv, Maryam ta ce"Ya dai? Ku ci mana". Momy ta ce"Ni dai ba na ci, na ji babu daɗi, ko Kausar?" Su ma suka haɗa baki wajen faɗin"E babu daɗi". Ran Maryam ya ɓaci, lallai sun yi sa'a a wannan karon zama ta zo na mutu-ka-raba, da babu abin da zai hana ta fesawa babbarsu mari, ba ta ce komai ba, ta kwashe ta kai kitchen, babbar ta shige ɗaki, duk suka bi ta, babu jimawa kuma ta fito ta shiga kitchen ɗin Maryam ta bi bayanta, ta tarar tana haɗa golden morn, ta haɗa shi kofi uku ta ƙwala musu kira, suka fito suka ɗauka suka koma ɗaki, ita kuwa Nana sai ta zauna a nan falon tana kallo. Maryam ta cika da mamakin yaran sosai, ta kuma saka a ranta ta san zaman da za ta yi da su. Da yamma da ta yi baƙi sai ta ba su taliyar, tuwon kuma ta rufe musu shi, tana jira babansu ya dawo ta sanar masa ta ga matakin da zai ɗauka. LITTAFIN NAN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 500 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay 08028966015 *MIJI GOMA...* _(BA UBA GOMA BA NE)_ *SADIYA ABDULRAZAƘ* *Ƴan magana dai sun ce "Miji goma ba uba goma ba ne" Shin kun yarda? Sannan mene ne hikimar wannan maganar? Kun yarda da ingancinta? Ta kai a kafa hujja da ita a ƙi zaman aure?* Marubuciyar ZUCIYAR MACE WUTAR ƘAIƘAYI DA WALAKIN... WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE. da sauransu *FIRST CLASS WRITERS* https://chat.whatsapp.com/BuEB69AOiqBKg0PMiBzdG3 PAGE 14 Suna ƙule a ɗakinsu baban nasu ya dawo, Maryam ta tare shi ranta fess, ta haɗa masa ruwan wanka ta kai banɗaki, abin da ba ta taɓa yi wa sauran mazan da ta aura ba, ko ruwa a buta ba ta taɓa zuba musu ba, amma shi wannan da yake zaman gaskiya ta zo ta ɗaura ɗamarar yi masa hidima iyakar iyawarta, tsaf ta taya shi shiryawa bayan ya fito, sannan ta ja hannunsa kamar wani ɗanta zuwa falo, ta kawo masa tuwon, tana ba shi a baki suna ta firarsu cike da nishaɗi, har ya yi mamakinta saboda shi kansa ya san kafin auren ba wani son shi take sosai ba, kiran sallar magriba ne ya tashe shi, ya yi alwala ya tafi masallaci yana jin shi fess da shi, ya manta rabon da ya samu kulawa da soyayya irin wannan, sautari sai bayan magriba yake yin wanka saboda sai ya ce Sauda ta dafa ruwan take dafawa, wataran ma a haka yake kwanciya ko ya yi da na sanyi, sannan Momy ce mai kai masa abinci dining, idan ma ya shiga ɗakinsa yana wani aikin ko kuma ya shigo da wata damuwar, babu ruwan Sauda da zuwa ta ji dalilin ƙin fitowarsa, sai dai ta aiko masa da abincin ɗakin nasa, sannan babu ruwanta da tambayar shi fita unguwa, indai ka ga ta tambaye shi sai dai idan nesa sosai za ta je, gidan Inna kuwa idan za ta je tun rana idan ta tafi sai dare idan ya je yi mata sai da safe su taho tare, babu ruwanta da me zai ci ranar, babu dai wata kulawa akwai matsaloli birjik, wanda shi ne dalilinsa na son ƙara auren, kuma tun yau ya fara tunanin za a samu canji in sha Allah! Ya dawo daga masallaci Maryam ta ga bai yi maganar yaran ba, ta dai leƙa bayan fitarsa ta ce duk su yi alwala su yi sallah. Ta ce"Alhaji dama ina so mu yi magan a kan yaran nan". Ya ce"To, wasu yara?" Ta ce"Yaranka". Ya ce"Me ya faru? Ba za ki samu matsala da su ba in sha Allah! Kin ga ma yara ne, uwar ma don Allah ki kau da kai ga matsalolinta". Ta ce"Ba wata matsala ba ce, ka ga yau taliya na dafa da safe, na ba su suka ce wai ba sa cin taliya, sai kowaccensu ta shiga zaɓar abin da take so, ni kuma na ga ba zao yiwu na yi girki har kala huɗu ba, ko hakan bai zama almubazzaranci ba ai ka ga ni ma ina buƙatar hutu, tun da ba bautarsu na zo yi ba, sannan ba ma tarbiyya ba ce yara su dinga zaɓin abin da za su ci, na ce su tsayar da guda ɗaya, suka ce tuwo, shi ne na yi, loma ɗaiɗai suka yi suka ce mini ba daɗi, ƙarshe sai suka sha golden morn suka ƙule a ɗaki". Alhaji ya ce"Ikon Allah! Wai kina nufin su yaran suna gidan nan? Waye ya kawo su?" Maryam ta ce"Wai dama ba ka sani ba? Daga makaranta mai adaidaita sahu ya kawo su". Ya ce"Yanzu suna ina?" Ta ce"Suna ɗaki". Ya shiga ƙwala musu kira ransa a ɓace, suka fito, Kausar da Momy suka haɗa baki wajen faɗin"Abba yunwa muke ji, ba mu ci komai ba". Ya daka musu tsawa da faɗin"Ku nemi wajen zama!". Suka zauna duk suka sha jinin jikinsu, saboda Abban nasu ba mai yawan faɗa ba ne. Ya ce"A cikinku waye ba ya cin taliya? Yaushe kuka daina cin taliya?" Duk suka yi shiru suna raba ido. Ya ce"Wato ku har kun yi girman da za ku yiwa babba rashin kunya? Ku sa ta yi tuwo ku ce babu daɗi?" Ya kalli Maryam ya ce"Idan akwai ki sako musu". Ta tashi ta je ta ɗakko shi a yadda suka bar shi, ta ajiye, ya saka su a gaba sai ga shi sun cinye tass, har da ƙari, ya yi mamakin dalilin da ya sa suka yi mata haka, ya zaunar da su ya yi musu nasiha sosai, ya nuna musu ita ma Maryam babarsu ce, duk abin da suka san ba za su yiwa babarsu ba to kar su yi mata, suka ce to, sannan ya saki jiki da su suka yi fira, Maryam ta ce su je ta yi musu wanka, ba su yi musu ba suka wuce, sai a lokacin ma ta sa suka yi home work, ƙarfe takwas Abba ya ce su je su kwanta, ita kuma Maryam ta kwashi unifom ɗinsu ta tafi wankewa, sai ga shi sun yi wankin a tare da Alhaji suna yi suna fira. Ita kuwa Momy suna shiga ɗaki ta ɗauki wayar ta sanarwa Sauda duk yadda aka yi, Sauda ranta ya ɓaci matuƙa ta ji kamar ta taso ta taho gidan yanzu, ta fara tunanin wato daga zuwanta za ta sa ya tsani ƴaƴansa har yana yi musu faɗa? Nan gaba ai sai duka, kenan ya goyi bayanta nan gaba ko ita ce da laifi tana kallo za a tauyewa ƴaƴanta haƙƙi, ai kuwa ba zai yiwu ba, ta fara tunanin hanyar da za ta bi don ta hana su cin amarci, sai dai yaran sun yi ƙanƙantar da za ta saka su yi wata kissar, don haka kawai ta yanke gara ta dawo su fara gabza yaƙin, ta ce wa yarinyar ta yi haƙuri su kwanta, amma kar su sake bari ta yi musu wanka, ita ta yi da kanta sannan ta yiwa ƙannenta. Washegari haka Maryam ta yi sammakon tashi saboda yaran, don tun a daren ya faɗa mata girki biyu ake yi da wanda za su ci, da wanda za su tafi da shi, ta dafa shayi ta soya doya da ƙwai ta saka musu a lunch box ɗin, sannan ta tafi ɗakinsu, ta tarar Momy ta yi wanka za ta fara yiwa sauran, Kausar tana cewa ita ba za ta yi mata, ta ce"Ya za a yi ki yi musu? Ke ma ai ba wuce wankan kika yi ba, ku wuce na yi muku". Momy ta ce"Mu fa Ummanmu ce kawai take yi mana wanka". Maryam ta ce"Tun da yanzu ba ta nan ai dole ku bari na yi muku". Ta ce"Mu dai a'a". Maryam ta juya ta fita, ta sanarwa da mahaifinsu, da mamaki ya ce"Ha'a, wai me yasa yaran nan suke haka ne?" Ya fito ya zo ɗakin, ya ce"Ke Momy! A kan me ba za ta yi muku wanka ba?" Ta ce"Ummanmu ta ce kar mu yarda da ita". Maryam ranta ya ɓaci ta ce"Ai shikenan". Ta juya ta bar ɗakin. Ya ce"Ummanku? Au haka ta tsara muku? Abin da ta turo ku ku yi kenan? To zan haɗu da ita! Ku saka kayan naku a haka ku tafi, idan ta damu sai ta dawo ta dinga yi muku wankan". "Maza ku saka ku fito, mintu uku na baku". Ya ƙarasa a tsawace yana jin dole ya takawa Sauda burki don ba za ta lalata masa tarbiyyar yaransa ba. Yana fita Momy ta shiga banɗaki ta kira Sauda ta sake faɗa mata, ai kuwa ta hasala tana ta zage-zage. Suka fito kowaccensu babu sakewa, sai a lokacin suka gaishe shi, ya amsa kafin ya ce"Kun gaishe da Antinku?" Duk suka yi shiru, sannan suka gaishe ta ɗaya bayan ɗaya, suka karya mai adaidaitansu ya zo suka tafi makaranta. Sun gama karyawa ya ce da Maryam"Don Allah ki yi haƙuri, yara ne kin san duk yadda aka tsara musu ba za su yi nazari ba, amma zan same ta na yi mata magana, idan ba za ta barki ki yi yadda ya dace da su ba, to ta zo ta zauna da su". Maryam ta ce"Allah Ya kyauta". Kafin ya tafi kasuwa ya tsaya a gidan nasu, ya gaida Inna, ya samu Sauda tana karyawa, ko kallon shi ba ta yi ba, ya ce"Yawwa Sauda na ga kin aiko mini yarana, ina son ki sani Maryam za ta iya riƙe su fiye da yadda kike kula da su, sai dai ki sani indai kin bar mata su to fa sai dai ki koma gefe ki yi kallo, ba zai yiwu tana tufka kina warwarewa ba, saboda shirme kin zauna kina tsarawa yara shirmen banza, to matata uwa ce a gare su, ya zama dole su yi mata biyayya tun da ni na haife su!". A hasale Sauda ta ce"Ita ta haifar mini su? Wallahi babu shegiyar da ta isa ta tsarawa ƴaƴana yadda za su yi, yarinyar da ba ta samu tarbiyya ba tun daga tushe, har kana kallona kana faɗa mini kalmar matarka?" Sai kuma ta saki wata dariya mai kama da ta tsantsar baƙinciki ta ce"Heee masu mata manya! To a yi mu gani idan tusa za ta hura wuta, yarinyar da ba ta zaman aure har wata abar alfahari ce? To sai ka jira ka ga zaman ya yiwu kafin ka fara wulaƙanta ni ka watsar da ƴaƴanka!". Ya ce"Ni dai na faɗa miki, idan kuma kin ƙi ji ba kya ƙi gani ba!". Ya fice ya barta tana ta bambami. Inna duk a gabanta a ka yi komai, ba ta ce wani abu ba, dama idan da sabo ta saba da faɗan nasu, sai da ya fita ta ce"Sauda a nan fa ba ki da hujjar da za ki saka yara su raina matarsa, idan har ba kya son ta shiga sabgar yaranki to ya zama dole ki koma kansu ki ci gaba da kula da su, kin ga dai yadda ya gigice a kan yarinyar nan yake rawar kai, kina nan a zaune za ta gama mallake shi da kissarsu ta zawarawa, irin wannan gogaggun yaran da suke yin aure-aure wallahi ki kiyaye su,sai kin tashi a tsaye kin ɗaura ɗamara, saboda haka ni yanzu umarni nake ba ki ba shawara ba, ki kama hanya ki koma ɗakinki a yau, ki kula da ƴaƴanki, sannan ki yi iya yinki na ganin ba ta mayar da ke bora ba, kar ki yarda ta ƙwace miki mijinki da gidanki". Sauda ta ce"Shi kenan Inna an jima zan koma". Inna ta ce"Ko ke fa, wannan ai kina nuna mata ta fi ƙarfinki ne ba za ki iya da ita ba, saboda haka ki koma ki nuna mata gida naki ne, kuma miji da ƴan'uwan shi ma naki ne!". Sauda ta jinjina kai cike da gamsuwa, ta tashi ta shige ɗaki. Zama ta yi ta kira ƙawarta a waya ta sanar da ita za ta koma, ta ɗora da faɗin"Don Allah ya za a yi ki haɗa ni da wannan mai maganin? Na san shegiyar tana nan ta gigita shi, bazawara ana marari za a samu miji". Aliya ta sheƙe da dariya ta ce"Alhamdulillah! Allah na gode maka da ka nuna mini ranar da Sauda za ta nemi maganin gyara zama". Sauda ta ce"Au shaƙiyanci za ki yi mini kenan". Ta ce"To ai ke ce kullum cikin kuri kike kina da ni'imarki ba sai kin sha komai ba, yanzu kika dawo hanya Hajiyata, zan turo miki lambarta". Sauda ta ce"Malama yanzu fa nake so, zai yiwu ta aiko mini kayan a yau?" Aliya ta ce"In sha Allah!". Tana turo mata, ta kira ta a waya, suka yi ciniki gabaɗaya irin wanda ake cewa ban da me kishiya su ta siya na dubu ɗari, kuɗin gudunmawa ne dangi suka haɗa mata don ta yi gyaran dama, da yamma aka aiko mata da kayan, ta gama shirinta tsaf jira kawai take yi ya zo yi wa Inna sai da safe ta bi shi su tafi. Yau ɗin Maryam shinkafa da miya ta yi, da alama yaran ba ma su taurin kai ba ne, don kuwa yau babu wanda ya yi magana a kan abinci, kowa ya ci, sannan sun tsaya ta yi musu wanka, ban da babbar da ta ce ita ce take yi da kanta dama, sai ta rabu da ita, amma dai sam sun ƙi yin fira da ita, don haka ita ma ta ke ta harkar gabanta. Da yamma da ya dawo sai da ya tambaye ta yaran, ta ce babu wata matsala, ya yi wanka ya ci abinci, ya fita sallah ya dawo, dama idan zai fita sallar isha'i da mota yake fita saboda daga can yake wucewa gidan Inna ya yi mata sai da safe, don haka yau ma ya wuce, ya ɗan zauna bayan sun gaisa, hat yanzu ta ƙi dawo masa kamar baya, babu wata fira haka dai babu yabo babu fallasa, ya tashi zai tafi ta ce"Ka zauna". Ya zauna yana sauraronta. Ta ce"Sauda za ta bi ka ta koma kan ƴaƴanta, saboda haka kar na ji kar na gani, ka zama mai adalci a tsakaninsu, kar sabo ya sa a watsar da tsoho, ta farkon dai ita ce dahir ɗinka, ba zan ɗauki wulaƙanta mini ƴa ba wallahi, don haka ka ja kunnen yarinyar nan, ta kula ta kiyaye, tun da zuwa ta yi ta tarar da ita da ƴaƴanta, ba ta san faɗi-tashin da aka yi kafin ka kai matakin da kake a yanzu ba". Ya ce"To Inna za a kiyaye in sha Allah!". Ya tashi ya fita yana yi mata sai da safe, ya ɗan jima a motar kafin Saudar ta fito da akwatinta, ta buɗe motar ta shiga ya ja suka tafi, babu wanda ya ce wa wani ƙala har suka ƙarasa gidan, lokacin yaran suna ɗaki, Maryam kuwa tana hakimce a babban falo cikin wata fitinanniyar rigar bacci, suka shigo da sallama, niyyarta idan ya shigo ta je yin oyoyo amma sai ta yi turus ganin shi tare da wata wacce ba sai an faɗa ba ta san matarsa ce, sai da gabanta ya faɗi, ta daure ta ce"Sannunku da zuwa". Alhaji kuwa ya bi ta da kallon burgewa, wankan ya burge shi, don Sauda babu ruwanta da wani wankan dare ballantana kuma kayan bacci, dogayen riguna ne marasa nauyi kayan baccinta tun da ta fara haihuwa, ya haɗiyi wani yawu muƙut wanda har Sauda ta ji sautin, zuciyarta ta ƙara kumbura, ta kasa shigewa kawai tana tsaye tana ƙarewa Maryam kallo, sai Alhaji ne ya katse shirun nasu da cewar"Na barki ke kaɗai a gida". Sauda ta yi masa mugun kallo ta ce"E tabbas ita kaɗai, tun da a yanzu ita kaɗai kake kallo a mutum, su ƴaƴan naka ba mutane ba ne, komai ma ya same su ta matarka kake yi! Hmm!" Ta wuce fuuu ta yi cikin gidan. Ya yi murmushin yaƙe ya ce wa Maryam"Kin ga Sauda ta dawo ko? Don Allah ku zauna lafiya, kin ga ma tun da ta dawo kan yaranta za ki fi kula da ni sosai ko?" Ta yi farr da ido ta ce"Ƙwarai kuwa, zo ma mu je ka gani". Ta yi ɗakinta, shi kuwa ya bi bayanta kamar raƙumi da akala, a gaban Sauda suka shige ɗakin nata, wacce ta fito daha ɗakin yaranta za ta shiga nata, ta manta rabon da ya shiga ɗakinta, sai dai ita ta bi shi nashi ɗakin idan ya kira ta, amma shi ne ya zo ya shige ɗakin amarya ko kunya ba ya ji, ta yi ƙwafa tana cewa"Lallai akwai aiki a gabana, tsohuwar kilaki ya kwaso". Ta gagara zama a ɗaki, ko wanka ta kasa yi, sai leƙe take yi tana jiran fitowarsa amma shiru har ƙarfe sha ɗaya ta yi, ga shi ko sallar isha'i ba ta yi ba, kuma ta kasa yi, saboda tana son tabbatarwa da gaske a nan zai kwana? Shi kuwa Alhaji yana can Maryam ta saka shi a kwana ta kalallame shi, ta kanainaye shi har ya manta ma a ɗakinta yake. Ƙashe dai sai sha biyu Sauda ta haƙura da leƙen ta yi sallah, ta kwanta, sai ta gagara yin bacci gabaɗaya ya ƙaurace mata, ta fara tunanin yanzu fa yana can tare da ita, lallai namiji ba shi da kunya, can dai ta fara tunanin ya za ta yi ta hana su sukuni, ta tashi ta fito a hankali ta shiga ɗakin yaranta, ta haska su, sai baccinsu suke yi hankali kwance, ta shiga tashinsu bisa shawarar zuciyarta, ta dinga jijjiga su duk suka tashi suna murza ido, ta sakawa fuskarta alamun firgici ta ce"Ku tashi don ubanku, aljanu ne suka shigo gidan! Suna ɗakin nan a ƙarƙashin katifarku!". Ai kuwa a tare suka fara ihu, ta ce"Ku kwanta ba za su yi muku komai ba". Suka fara kuka suna rirriƙe ta suna cewa a ɗakinta za su kwana. Ta fizge tana cewa"Suna can a ɗakina sun cika ɗakin kowa ya yi ta kansa". Ta fice a guje suka mara mata baya, amma kafin su shiga ta banke ƙofarta ta saka sakata, gabaɗaya suka ruɗe suka dinga ihu a mugun firgice kamar za su shiɗe. A tare Maryam da Alhaji suka fito a ruɗe, suka tarar yaran suna ta buga ƙofar ɗakin babarsu, fitowarsu ya sa suka yi wajensu suna shigewa jikinsu cikin matsanancin kuka, Alhaji ya ruɗe ya fara tambayarsu me ya faru? Suka ce"Aljanu, Abba aljanu a ɗakinmu". Gabansa ya faɗi ya ce"Aljanu kuma? Me kuka gani?" Inaa sun ruɗe, sai a lokacin Sauda ta fito tana cewa"Mene ne?" Suka yi kanta suna kuka. Alhaji ya ce"Kin ji wai aljanu". Ta ce"Aljanu kuma?" Ya wuce ɗakin a tsorace yana addu'a, ya haska bai ga komai ba, ya dawo a sanyaye ya ce"Abun ya bani mamaki wallahi". Sauda ta ce"To kar dai fa ture aka fara yi musu". Ya ce"Wane irin ture? Waye zai yiwa yaran nan ture?" Ta ce"Wanda suka tsonewa ido mana, an ga yara sun cika gida tubarkalla ana son haukata su don kar ƴaƴana su moru". Alhaji ya ce"Subhanallah! Kar na sake jin magana irin haka!". Ya janyo yaran yana cewa"Tsorata kawai kuka yi babu komai a ɗakinku kun ji? Ku je ku kwanta zan yi muku addu'a". Sauda ta ce"Au da gaske sai ka kora su, saboda kar kwanan ɗakin amarya ya wuce ka? Hmm dama uwa ce ba ta gudun ƴaƴanta duk runtsi, ku shigo nan!". Ya ce"Ba za su shiga ba! A ɗakin nasu nake so su kwana ina son fahimtar wani abu ba ne kafin Allah Ya kaimu gobe na kira malamai a yi addu'a". Maryam ta ce"Allah Ya rufa asiri". Ta koma ɗakinta, ita ma duk sai tsoron gidan ya kama ta. Ya saka su a gaba suna turjewa suka shiga, ya zauna ya kunna karatun qur'ani a wayarsa, yana addu'a yana tofa musu, amma da bacci ya fara ɗaukarsu sai su zabura su farka suna maƙale shi, a haka suka kwana, ita kuwa Sauda ta yi baccinta ranta fess, tun da dai ta haramta musu wannan daren to ita fa buri ya cika, kuma ta saka a ranta yanzu aka fara wasan, ta ɗau alƙawarin sai ta fitini gidan gabaɗaya, sai kwana a ɗakin shi ya gagari Maryam, kafin ta tankaɗa ƙeyarta waje. LAST FREE PAGES! A NAN ZAN TSAYA DA FREE PAGE, DAGA WANNAN SHAFIN DUK WANDA KUKA GANI A PAID PAGE NE, ƳAN'UWA KU BIYA KU KARANTA CIKIN AMINCI, YANZU ZA A FARA WASAN NAN, TAFIYA TA KISHI MAI CIKE DA ƘULLA-ƘULLA TURA ƊARI BIYAR ƊINKI TA NAN KI SHA KARATU CIKIN AMINCI. 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay 08028966015