**𝙼𝙸𝙵𝚃𝙰𝙷𝚄𝚉𝚉𝙰𝚁𝙱𝙸𝙻** 𝙻𝙸𝚃𝚃𝙰𝙵𝙸 𝙽𝙰 𝙱𝙸𝚈𝚄 2 𝙿𝙰𝚁𝚃 𝙰 𝙽𝙰 𝙰𝙱𝙳𝚄𝙻'𝙰𝚉𝙸𝚉 𝚂𝙰𝙽𝙸 𝙼𝙰𝙳𝙰𝙺𝙸𝙽 𝙶𝙸𝙽𝙸. 𝚃𝚈𝙿𝙸𝙽𝙶 𝙰𝙷𝙼𝙰𝙳 𝙼𝚄𝙽𝙽𝙸𝚁. 𝙿𝙾𝚂𝚃𝙸𝙽𝙶 𝙽𝙰𝙹𝙸𝙱𝚄𝙻𝙻𝙰𝙷 𝙼𝚄𝙷𝙰𝙼𝙼𝙰𝙳. 𝙺𝚞𝚢𝚒 𝚑𝚊𝚔𝚞𝚛𝚒 𝚋𝚊𝚢𝚊𝚗 𝚝𝚜𝚊𝚠𝚘𝚗 𝚕𝚘𝚔𝚊𝚌𝚒 𝚋𝚊𝚔𝚞 𝚜𝚊𝚖𝚞 𝚙𝚘𝚜𝚝𝚒𝚗𝚐 𝚍𝚒𝚗 𝚕𝚒𝚝𝚝𝚊𝚏𝚒 𝚋𝚊, 𝚝𝚘 𝚊𝚖𝚖𝚊 𝚒𝚍𝚊𝚗 𝚔𝚞𝚔𝚊𝚢𝚒 𝚕𝚊'𝚊𝚔𝚊𝚛𝚒 𝚍𝚊 𝚒𝚛𝚒𝚗 𝚛𝚊𝚢𝚞𝚠𝚊𝚛 𝚍𝚊 𝚊𝚔𝚎 𝚌𝚒𝚔𝚒 𝚠𝚊𝚍𝚍𝚊 𝚝𝚊𝚔𝚎 𝚌𝚒𝚔𝚎 𝚍𝚊 𝚖𝚊𝚝𝚜𝚊𝚕𝚘𝚕𝚒 𝚑𝚊𝚔𝚊𝚗 𝚋𝚊𝚣𝚊𝚒 𝚋𝚊𝚔𝚞 𝚖𝚊𝚖𝚊𝚔𝚒 𝚋𝚊. 𝚝𝚘 𝚊𝚖𝚖𝚊 𝚒𝚗𝚜𝚑𝚊 𝙰𝚕𝚕𝚊𝚑 𝚢𝚊𝚗𝚣𝚞 𝚣𝚊𝚔𝚞 𝚌𝚒𝚐𝚊𝚋𝚊 𝚍𝚊 𝚓𝚒𝚗 𝚖𝚞 𝚔𝚊𝚖𝚊𝚛 𝚢𝚊𝚍𝚍𝚊 𝚊𝚔𝚊 𝚜𝚊𝚋𝚊. 𝚖𝚞𝚗𝚊 𝚏𝚊𝚝𝚊𝚗 𝙰𝚕𝚕𝚊𝚑 𝚢𝚊 𝚝𝚊𝚒𝚖𝚊𝚔𝚎 𝚖𝚞, 𝚢𝚊 𝚔𝚞𝚖𝚊 𝚔𝚊𝚛𝚎 𝚖𝚞 𝚍𝚊𝚐𝚊 𝚍𝚞𝚔𝚔𝚊𝚗 𝚜𝚑𝚊𝚛𝚛𝚒 𝚗𝚊 𝚑𝚊𝚕𝚒𝚝𝚝𝚊. 𝙼𝙰𝚁𝚄𝙱𝚄𝙲𝙸𝙽 𝚈𝙰𝙲𝙸 𝙶𝙰𝙱𝙰 𝙳𝙰 𝙲𝙴𝚆𝙰.... Lokacin da suka baro masaukinsu,asuba bata yi ba domin har ynx akwai sauran duhu a gari.Gaba daya gudajen mutane a rufe suke birnin yayi tsit kamar ba mutane a cikinsa domin ba'a jin sautin komai face haushin karnuka daidaiku.Tsoho rafkanagu,hajarul mukurus da Ruziyal ne suka biyo hanya a cikin wannan lokaci saboda suje fadar sarki Muzuluch don suji karshen hikayar bawa Mozur da gimbiya suhaila gaba daya Daren jiya ba suyi barci ba sbd kawai dokin gari ya waye su dawo fada.Gashi yanxun ma sun kasa hakura garin ya waye,suna tafe suna hira inda hajarul mukurus ya dubi Ruziyal yace,"Anya kuwa tun daga hikayoyin sarki Dujalu zuwa wannan ta ynx akwai wadda tafi hikayar bawa Mozur da gimbiya suhaila dadi"?. Ruziyal yayi murmushi yace,"Haba Hajarul mukurus Ashe ka manta da hikayar masunci lamlas kenan da kuma attajiri kuffuru bin Aljar.Ai duk sunfi wannan hikayar ta bawa Mozur saidai kuma hikayar bawa Mozur ta fisu daukar hankali da Sosa zuciya musamman yadda sarki Muzuluch ya yanke Mana labarin a daidai haduwar sarauniya Ashikatul Ashiriya da sarki saubatul Azman a bakin kogon Baitul Husuk.Dole ne mutum yaso yaji yadda zata qarke,shin za'a yi yaki a nan wajen ko kuwa za'a shiga cikin kogon ne don a debo wannan dukiya?,Shi kansa kogon mutum zaiso yaji yadda cikinsa yake haka kuma mutum zaiso yaji abinda zai faru idan gimbiya suhaila ta gama baiwa kuyanga suzaila labari.Tsoho rafkanagu yayi gyaran murya yace,"Duk da dai baku sa dani ba a cikin hirar taku bari nayi muku karambani.Maganar gaskiya hikayar bawa Mozur tafi duk sauran hikayoyin dadi,alajabi da kuma darasi.Domin a labarin ne mutum zai gane cewa kuskure ne ka wulaqanta mutum dan uwanka don zai iya zama wani abu a nan gaba.Kamar yadda boka hazaru ya baiwa suhaila labarin cewa nan gaba Mozur zai zama sarki,haka kuma labarin na nuni da cewa tsananta gaba da mutum kuskure ne tun daga yadda suhaila ta tsani bawa Mozur amma sai gashi a karon banza ta Sami ciki da shi harma ta haifi da mai kamanninsa sak.Hajarul mukurus yace,"hakika zancen ka dutse ne nima na amince". Haka dai su Ruziyal suka cigaba da hira har suka qofar fada.Da zuwa suka iske ba'a bude gidan sarautar ba,kuma ga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikin su.Rafkanagu ya matsa kusa da masu gadin yana dogara sanda cikin tafiya da kyar ya dube su yace,"Ya ya na ku bude mana kofa mu shiga cikin fada mu zauna mune baqin sarki wadanda yake bawa labari". Daya daga cikin masu gadin ya dube shi yace,"Baba ai saidai kuyi haquri domin lokacin bude fada baiyi ba.Idan za ku iya jira ku zauna anan ku jira,idan kuma ba zaku iya ba to ku koma masaukinku in yaso in an jima kwa dawo". Rafkanagu yayi ajiyar zuciya yace,"Yaro ai mun fito kenan ba zamu koma ba.Gwara dai mu zauna mu jira". Nan dai suka zauna har lokaci yayi,sannan aka bude qofar suka shiga ciki suka zauna a gefe guda. Sarki Muzuluch bai fito ba sai bayan sa'a uku.Da fitowarsa kowa ya miqe tsaye sai daya zauna akan karaga aka zazzauna.Sannan kuma fadawa suka fara kwasar gaisuwa har aka zo kansu Ruziyal.Koda sarki Muhucul ya dubi fuskokinsu Ruziyal sai ya bushe da dariya.Sannan yace,"Yaku wadannan baqi,menene ya hanaku yin barci jiya"?. Cikin mamaki su Ruziyal suka dubi juansu suka kasa cewa komai.Sarki Muhucul ya sake bushewa da dariya karo na biyu yace,"Na san abinda ya hanaku yin barci,ba komai bane face dokin son jin qarshen hikayar bawa Mozur da gimbiya suhaila.To kusha kuruminku yanxun nan zan cigaba da baku wannan labari,kuma indai lokaci baiyi halinsa ba za kuji qarshen labarin gaba daya". Sarki Muhucul yayi gyaran murya sannan ya fara bayani kamar haka:- "Bayan anyi kallon kallo tsakanin gimbiya Ashikatul Ashiriya da sarki saubatul Azman sai sarauniya ta bushe da dariya tace,"Ya kai tsohon mijina kayi sani cewa duk wani shiri naka a kaina ba zaiyi tasiri ba.Ba zai yiyu ka rabani da 'yata ka rabani da dan uwana,sannan kuma kace zaka rabani da dukiyata.Kota halin qaqa saina ga bayanka,domin bani da maqiyin daya fika a doron kasa.Dukiyar da ka dade kana begenta yau zaka ganta da idanun ka,Amma saidai ka kalle ta da idanu badai ka taba ta ba ko ka mallaketa". Koda Ashikatul Ashiriya tazo nan a zancenta sai sarki saubatul Azman yayi murmushi yace,"Yake Ashikatul Ashiriya kiyi sani cewa yar da kike tutiyar cewa taki ce ba jinin ki bace,domin kuwa inda jinin ki ce ba zata guje ki ba ta taho wajena.Haka kuma dan uwan da kike tutiyar cewa dan uwanki ne yau ya zabi ya bar gidanku ya tafi wata duniyar ya zauna da dukiya ba da sarauta ba saboda kishin karagar da kike kai.Kinga kuwa ashe bai kamata kiyi gaba dani ba akan yarki da dan uwan ki,saidai kiyi gaba dani akan dukiyar ki". Koda jin wannan batu sai itama Ashikatul Ashiriya tayi murmushi tace,"Ya kai saubatul Azman kayi sani cewa shi dan uwa rabin jiki ne ko ya guje ka dole ne ka so shi,tunda hannunka baya rubewa ka yanke.Batun 'yata daka ce ba jinina ba ce,mene ne hujjarka"?. Shaubatul Azman ya bushe da dariya.Sannan ya bata labarin lokacin data haihu tare da kuyangarsa.Sannan yayi rantsuwa da darajar abin bautarsa yace,"Wannan labari gaskiya ne". Koda fadin haka sai idanun Ashikatul Ashiriya suka ciko da kwalla ta dubi shaubatul Azman tace,"Hakika ka cuce ni da ka bani 'yar wata na shayar da ita a matsayin tawa ta cikina.Na rantse da girman birnin Kisra saina dandana maka azabobi bisa wannan laifi". Kafin Shaubatul Azman yayi wani yunquri tuni dakarun Ashikatul Ashiriya sun yanyame shi da dakarun nasa aka daddaure su da sarqa.Ashikatul Ashiriya tasa aka gurfanar da Suhaila a gabanta tace,"Yake Suhaila kiyi sani cewa na rene ki da zuciya a matsayin 'yar cikina kuma kin tsotsi nonona.Na kula da rayuwar ki da lafiyar ki tun kina jaririya har izuwa girmanki,yanxu da butulci zaki saka mini kenan?,ya kamata ace kin mini kara ko dan saboda halaccin dana miki a rayuwa.Tabbas kema kin cancanci sakamako kwatankwacin abinda kika aikata". Nan take sarauniya ta bada umarnin a daure gimbiya suhaila cikin sarqa.Dakaru kuwa suka bi umarni da gaggawa.Daga nan saita kirawo jarumi Haiman ta dora hannunta guda a kafadarsa tana mai murmushi a gareshi tace,"Ya kai dan uwana kayi sani cewa kai jinina ne,kuma komai zaka yi min dole ne dauki haquri don haka na yafe maka wannan laifi daka yi a gareni,kuma ina roqonka daka bini zan sauka daka kan karaga na baka". Yayin da jarumi Haiman yaji wannan batu sai idanun sa suka ciko da kwalla take yayi nadamar abinda yayi,ya nemi gafarar Ashikatul Ashiriya.Kawai saita rungume shi tana kuka.Ba zato ba tsammani sai Ashikatul Ashiriya ta zaro wuqa cikin shammace ta cakawa jarumi Haiman a ciki.Haiman ya sulale kasa ya fara shure shuren mutuwa.Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan.Koda jarumi Miqdad yaga abinda ya faru ga abokinsa Haiman,saiya kwalla ihu yayi ya rusa kuka a cikin ragar qarfen da aka sa shi. Ashikatul Ashiriya taxo kan Haiman Wanda yake magagin mutuwa ta tsaya tana mai zubda hawaye tace,"Ya kai dan uwana kayi mini gafara na kasheka da hannuna.Ka sani cewa rayuwar ka hadari ce ga tawa.Ina son mulki fiye da komai a rayuwa ta.Tabbas in dai kana raye wata ran saika rabani da shi saidai zan kasance mai matuqar bakin ciki tun da yanzu bani da sauran dan uwa na jini a duniya". Tana gama fadin haka ne idanun Haiman suka rufe komai na jikinsa ya daina motsi.Nan take tasa aka dauko gawarsa aka dunguma izuwa gaban qofar kogon Baitul Husuk.Sarki Shaubatul Azman,Jarumi Miqdad da gimbiya suhaila kuwa aka taho da su a daddaure har bakin kogon.Da zuwa sai Ashikatul Ashiriya ta kama hannun Haiman ta soka dan yatsansa a cikin rami guda dake jikin qofar.Sannan ta soka nata dan yatsan a cikin rami na biyu.Yin hakan ke da wuya sai hayaqin nan da kuma walqiyar nan dake sararin sama bisa ganuwar Baitul Husuk suka bace bat.Wani zagayayyen qarfe mulmulalle dake cikin qofar ya zagaya da gudu.Sannan wasu manyan sakatu daga ciki suka zare kansu.Take qofar kogon Baitul Husuk ta fara budewa a hankali.Shi kansa budewar katuwar qofar ya isa abin al'ajabi.Tsaitsaye a bakin qofar wasu dakarun yaki ne na aljanu gasu nan birjik sunyi dogon layi ba adadi.Gaba dayansu a qame suke kamar gumaka,ko motsi basa yi amma fa idan ka dubesu sau daya ba zaka sake kallon su ba saboda kwarjinin su da ban tsoro.Cikin kogon kuwa babu kasa ko ina dutsen lu'u lu'u ne a shimfide kamar dama can haka aka halicci wajen.Kafin Ashikatul Ashiriya ta shiga cikin kogon saida tayi wurgi da gawar dan uwanta Haiman.Sannan ta shiga cikin kogon Baitul Husuk aka bi ta a baya duu gaba daya. Kogon Baitul Husuk a haskake yake da wani irin haske na musamman Wanda ko allura ce ta fadi kasa sai an ganta.Duk da cewa kogon yakai shekaru dubu a kulle babu kura a ciki,kuma babu yana.Ko ina ka duba fes fes yake banda qamshi babu abinda ke tashi.Duk inda mutum ya duba dukiya ce baja-baja mai tsananin tarin yawa kuma duk dangin Zinare, lu'u lu'u,yaqutu,jauhar,zubardaji,murjani da sauransu.Kai inda za'a Kai shekara daya ana diban wannan dukiya ba zata qare ba.Kayan qawa gasu nan iri-iri harda Wanda mutum bai taba gani ba.Saida kowa ya shiga kogon sannan kofar ta rufe kanta da kanta. Nan fa aka zazzaro idanu cikin rudewa da mamaki.Nan fa jama'a suka dasawa dukiya wawa suna ihu kamar mahaukata.Saida Ashikatul Ashiriya ta daka tsawa sannan kowa ya shiga taitayinsa.Nan take ta bada umarnin kowa ya cika jaka da dukiya.Nan fa aiki ya samu,wasu ma saisu cika yadda baza su iya dauka ba,dole sai sun rage.Haka dai miliyoyin jama'a suka yi ta facakarsu kai ka ce kasuwar duniya ce a wajen. It's kuwa Ashikatul Ashiriya sai ta sami wuri ta zauna fadawanta suka kewaye ta ana fadanci sai kyalkyala dariya take da farin ciki da ta dubi tarin dukiyar da aka diba ta tuna cewa duk tata ce,kuma in an koma gida a baitul malinta za'a zuba wannan dukiya.Haka kuma duk sa'ar data buqatar qari sai a dawo a diba.Abinda ta mance shine ynx fa kofar kogon ta rufe kuma ba zata taba buduwa ba sai an sake zura dan yatsan ta guda dana dan uwanta Haiman Wanda tuni ta kashe shi tayi wurgi da gawarsa a kofar kogon kafin a shigo.Duk wannan buduri da mutanen Ashikatul Ashiriya ke yi Jarumi Miqdad da sarki saubatul Azman da gimbiya suhaila na kallo amma basu da ikon diban komai kasancewar a daure suke.Shi kuwa littafin nan na sihirin shiga kogon Baitul Husuk na tare da gimbiya suhaila ta boye shi a cikin rigarta. Saida aka shafe kwana uku cur miliyoyin jama'ar na dura dukiya cikin jakunkuna.Sannan kowa ya gama cika jakarsa.Nan take Ashikatul Ashiriya tasa aka zo da sarki Shaubatul Azman, Jarumi Miqdad da gimbiya suhaila aka kwance su,sannan aka sake daure su a jikin wasu manyan dirkoki na cikin kogon.Ashikatul Ashiriya ta dube su daya bayan daya ta bushe da dariya tace,"Ya ku maqiyana kuyi sani cewa anan zamu barku cikin wannan kogo kuyi ta zama a haka har yunwa da qishirwa su kashe ku.Da wannan kalami nake muku bankwana da taya ku murnar mutuwa a sauqaqe". Koda gama fadin haka sai kowa ya bushe da dariya.Nan take sarauniya ta bada umarnin a tashi a fita daga cikin kogon don a koma birnin Kisra.Kamar tururuwa na fitowa daga cikin raminta haka mutane su kayi ta tafiya suka nufi bakin qofar.Saida aka shafe awa bakwai ana tafiya sannan kowa ya isa bakin qofar aka tsaya akayi cincirindo domin qofa a rufe take.A sannan ne Ashikatul Ashiriya ta tuna cewa dole saida dan yatsan dan uwanta Haiman kofa zata budu.Nan fa hankalinta ya dugunzuma ta kwarara uban ihu Wanda ya firgita kowa.Ashikatul Ashiriya ta dubi fadawanta ta sanar da su halin da ake ciki.Nan fa ido ya raina fata kowa yayi tsuru tsuru murna ta koma ciki.Ashikatul Ashiriya tasa dan yatsan ta ita kadai da nufin kofa ta bude amma sai kogon ya cika da wata irin qara mai cika kunne.Nan take sandararrun Aljanun nan suka bude idanuwansu wato dubunnan masu tsaron Baitul Husuk.Babu wanda ya lura da hakan. 𝙼𝚄 𝙷𝙰𝙳𝚄 𝙰 𝙿𝙰𝚁𝚃 𝙱 𝙳𝙾𝙽 𝙹𝙸𝙽 𝙲𝙸𝙶𝙰𝙱𝙰𝙽 𝚆𝙰𝙽𝙽𝙰𝙽 𝙺𝙰𝚈𝙰𝚃𝙰𝙲𝙲𝙴𝙽 𝙻𝙰𝙱𝙰𝚁𝙸. 𝙽𝚊𝚓𝚒𝚋𝚞𝚕𝚕𝚊𝚑 𝙼𝚞𝚑𝚊𝚖𝚖𝚊𝚍😎😍**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU. PART B NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI. TYPING AHMAD MUNNIR. POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️🙏😄 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.. Koda Ashikatul Ashiriya taga babu abinda ya faru sai ta sake sa dan yatsan nata a karo na biyu.Nan fa Aljanun suka motsa hannanayensu dake ruqe da makamai.Sai da kowa yaji wannan motsi amma ba'a gane ko na mene ba.Ashikatul Ashiriya ta sake zura dan yatsan ta a karo na uku.Faruwar hakan ke da wuya sai Aljanun nan suka zama rayayyu gaba dayansu.Kawai sai suka afkawa mutane da sara. **************** Nan da nan kogon ya hargitse da ihu,masu gudu na yi,masu faduwa a mace na yi.Gimbiya suhaila da jarumi Miqdad kuwa na daure a jikin sarqoqin gini haka ma Shaubatul Azman.Kiri-Kiri suna ganin halaka,amma babu damar su gudu su ceci kansu.Sarauniya Ashikatul Ashiriya kuwa da rarrafe ta shiga cikin wani saqo na kogon,ai kuwa sai wasu daga cikin fadawanta suka bi ta da gudu suna tunanin cewa wata hanyar ce daban ta tsira.Abin da basu sani va shine sun sake kai kansu cikin wata babbar masifar ne wacce za su gwammace gwara su tsaya a baya Aljanun su kashe su. Haka dai Aljanun suka dinga ragargazar jama'a kafin kace wani abu tuni fadar ta cika da jini male-male.Wasu daga cikin dakarun sun yi qoqarin su yaki wadannan Aljanun amma ko kadan basu sami nasara ba,domin Sara da Suka baya tasiri a jikin su.Sai dai kaga mayaki ya yarda makaminsa ya take da gudu amma sai Aljanun su cafko shi da hannu daya su tsarge shi da takobi su yar da gawarsa.Kai a wannan rana mun ga tashin hankali domin munga yadda aljanu ke daukan rayukan miliyoyin mutane kamar suna zubar da kwayoyin hatsi. Ana cikin wannan badaqala ne takobin wani aljani ta sare sarqar da aka daure jarumi Miqdad.Ai kuwa nan take sarqar ta tsinke.Ko da Miqdad yaga ya kubuta sai ya daka tsalle sama ya doki wani aljani dake shirin sare sarki Shaubatul Azman da kafa biyu.Aljanin ya bugu da dirkar gini takobinsa ta su6uce kasa.Cikin zafin nama Miqdad ya dauki takobin ya hau Aljanun da sara.Bisa mamaki sai muka ga duk aljanin da ya sara sai ya kama da wuta,ya kone qurmus ya zama toka.Nan take Miqdad ya gano cewa sirrin na jikin takobin Aljanun.Cikin zafin nama Miqdad ya sare sarqoqin da suka daure Shaubatul Azman da wadanda suka daure ni muka ku6uta.Da karfin tsiya Miqdad ya qwato wadansu takubban guda biyu daga hannun Aljanun ya bamu ni da Shaubatul Azman yace mu kare kanmu.Nan fa muma muka shiga ragargazar Aljanun.In ka dauke mu ukun babu wani mahaluqi mai iya ta6uka komai a wajen.A haka dai muka kutsa ta cikin Aljanun muna saransu suna saranmu har muka sami damar shiga saqonnan inda su Ashikatul Ashiriya suka bi. Wani irin saqo ne mai zururun lungu,kuma mai dubu ba don muna riqe da takubban Aljanun nan ba da baza mu iya wucewa ba.Hasken takubban ne ya ringa haska mana hanya.Tun da muka shiga wannan saqo muka tsira daga wadancan aljanu,amma muna ta jiyo ihun mutane da karar takubban Aljanun alamun cewa har ynx Aljanun kisa kawai suke ba sassauci.Sai da muka yi tafiyar sa'a guda a cikin wannan saqo.Sannan muka iso wata babbar haraba inda muka iske wani wawakeken rami mai cike da tafasashshiyar dalma tana za6al6ala.Hucin zafi na fesowa daga cikinta tare da hayaki.A cikin ruwan dalmar akwai wasu manyan sandunan karfe da yawa da suka yi tsiri sama.Fadin saman nasu na da fadi kadan.Dole ne mutum ya tattaka wadannan sandunan karfe idan yana son ya tsallake wannnan kogin darma.Sannan ya cigaba da tafiya akan turba. A cikin kogin darmar ne muka ga gawar mutum biyar daga cikin fadawan Ashikatul Ashiriya suna nutsewa.Nan fa muka tsaya muka dubi juna cikin shakka da tsoro.Jarumi Miqdad ya dubi kogin darmar nan da kuma sandunan dake cikinsa a tsaitsaye yayi nazarin su sosai.Sannan yace, "Kuyi sani cewa bamu da wani za6i face mu bi ta cikin kogin darmar nan muna masu taka kan sandunan nan.Amma fa ku sani cewa ba kowace sanda ake takawa ba,domin wata idan aka takata nutsewa kasa zata yi da mutum ya fada cikin kogin darmar nan ya narke.Babu mamaki Ashikatul Ashiriya ta san sirrin Baitul Husuk shi yasa ta iya wucewa ta nan,amma da sai mun iske gawarta a cikin kogin darmar nan." Koda fadin haka sai na girgiza kaina nace,"Ko shakka babu sarauniya ta san sirrin kogon nan,domin ta taba bani labarin cewa ta haddace duk abinda da ke rubuce a cikin wannan littafi da ake kira Mabudin arzikin Kisra." Koda nazo nan a zancena sai jarumi Miqdad ya dube ni yace,"Ina wannan littafin shin ba yana tare dake ba?" Koda jin haka saina tuno da littafin da yake cikin rigata.Cikin sauri na laluba aljihunan rigar tawa.Ai kuwa sai gashi na fiddo littafin.Miqdad ya karbi littafin ya bude har izuwa shafi na uku,saiga hoton wannan kogin darma.A kasan hoton anyi bayani kamar haka: "Ya kai bakon wannan kogo kayi sani cewa baza ka iya shallake wannan kogin darma ba face ka bi takan wadannan sanduna na cikinsa.Dole ne ka rufe idanun ka yayin da zaka taka sandunan kuma ka tabbata cewa idan ka taka sandar farko ka tsallake ta biyu kafarka ta dira akan ta uku.Haka zaka yi tayi harka fita daga cikin wannan kogi na darma mai tsawon kamu dari uku.Kuskure daya na nufin ajalinka." Koda jarumi Miqdad ya gama karanta wannan jawabi sai muka dubi juna muka yi ajiyar zuciya.Cikin karayar zuciya na dubi jarumi Miqdad nace,"Ni kam bazan iya hawa wadannan itatuwan ba idanu na a rufe dole ne nayi kuskure na halaka." Na juya ga mahaifina Shaubatul Azman ina mai zub da hawaye nace,"Ya kai Abbana kayi sani cewa anan ne zanyi bankwana da kai ina mai yi muku fatan nasara,ni kam tawa ta kare." Shaubatul Azman ya rungume ni muka fashe da kuka a tare.A lokacin ne jarumi Miqdad ya janyeni daga jikin Shaubatul Azman ya jani gefe guda muka fuskanci juna muna tsaye daf da daf.Miqdad ya kuramin idanu yace,"Yake Suhaila ina so ki dubi cikin idanu na da kyau ki gayamin abinda kika gani a cikinsu." Na dubi idanun da kyau.Sannan nace,"Naga kauna da yarda a cikinsu." Miqdad yayi murmushi yace,"Kin amince dani akan bazan cutar dake ba?" Nace na amince. "Abinda nake so dake shine ki ayyana a ranki cewa zamu samu nasarar shallake wannan kogin na darma bisa son cikar burin dake zuqatan mu.Zaki hau kan kafaduna ynx ki zauna kina mai rufe idanun ki.Ni kuma zan haye dake izuwa karshen wannan kogi na darma.Lallai kada ki kuskura kisa tsoro a zuciyarki,ko kuma ki bude idanun ki yayin da muka tsallake wannnan kogi na darma,domin yin haka zai janyo halakar mune." Koda Miqdad ya gama wannan jawabi sai ya dubi Shaubatul Azman ya ce,"ya shugabana shin zaka iya kiyasta yawan sandunan karfen nan da suke jere a layi daga farkon kogin nan zuwa karshen sa?" Shaubatul Azman ya dubi sandunan ya gansu reras ba adadi iya hangen sa.Ya kada kai yace,"Ba zan iya ba." Miqdad ya kama kafadunsa yace,"ya shugabana na san cewa kai namiji ne mai dakawa maza gumba a hannu,ina son ka tuno da irin gwagwarmayar daka sha a rayuwar ka,ka dauka a ranka tamkar ynx kake yinta.Abinda nake so dakai ka biyoni a baya kana mai runtse idanun ka kuma kayi amfani da Kunnenka sosai wajen jin sautin inda na dora sawuna.In dai kayi haka albarkacin abin bauta zamu shallake wannan kogi na darma." Miqdad na gama fadin haka ya tsuguna a gabana ya umarce ni da na hau kan kafadarsa.Cikin kwarin zuciya da aminci na hau kan kafadar tasa na zauna.Sannan na maida littafin nan cikin rigata na ajiye.Ba tare da fargabar komai ba jarumi Miqdad ya nufi kogin darma gadan gadan Shaubatul Azman na biye damu.Koda muka zo daf da kogin sai Miqdad ya kurawa sandunan ciki idanu tsawon lokaci yana nazarin tazarar dake tsakanin kowanne.Sannan ya kiyasta iya adadin su a zuciyarsa.Kawai saiya rufe idanun sa.Sannan ya umarce mu damu rufe idanuwan mu ni da mahaifina Shaubatul Azman.Take muka bi umarnin sa,kuma ya fara hawa kan sandunan yana tafiya a nutse kamar akan turba yake. Shaubatul Azman kuwa ya biyo bayansa duk inda Miqdad ya dauke sawunsa sai Shaubatul Azman yasa nasa a wajen.A haka dae muka yi ta tafiyar har ya rage saura taku biyu kacal mu haure kogon darmar.Anan ne Shaubatul Azman yayi kuskure maimakon yasa kafarsa akan sanda ta uku saiya dora akan ta biyu.A lokacin kuwa mu muna kan sanda ta karshe.Sa'adda Shaubatul Azman yayi kuskuren tuni kunnen Miqdad ya kai masa saqon kuskuren.Har Shaubatul Azman yayi kasa zai fada cikin kogin na darma sai jarumi Miqdad yayi sauri cikin zafin nama ya durqusa ya cafo shi da hannu daya.Sannan ya miqe tsaye a haka ruqe da shi,kuma ba tare da ya bude idanun sa ba ya daka tsalle ya dirga can gaba kan turba. Muna dirga muka bude idanun mu cikin tsananin mamakin juriya da bajintar jarumi Miqdad.Nan take naji son jarumi Miqdad ya shiga cikin zuciya ta ya mamaye ta gaba daya.Ban san sa'adda na daka tsalle na rungume shi ba ina farin ciki.Shima Shaubatul Azman sai ya taho garemu ya rungume mu gaba daya.Shaubatul Azman ya dubi Jarumi Miqdad yace da shi, "Ya kai wannan gwarzon sadauki ina son ka gaya mini abubuwan da kake son na saka maka da su idan har munyi nasarar fita daga cikin kogon nan." Koda jin wannan batu sai jarumi Miqdad yayi murmushi yace,"ya shugabana kayi sani cewa bana buqatar komai face abu guda kuma ba zan sanar da kai shi ba har sai mun tsira." Shaubatul Azman yayi murmushi yace,"to shikenan muje zuwa." Nan dai muka qara nausawa cikin kogon muka bi wata hanya daban mai surquqi.Wannan hanya bata da duhu,kuma ta cikin wani kwararo ake bi wanda ba dama mutum ya wuce a tsaye saidai ya sunkuya. Miqdad ya wuce gaba ina biye da shi.Sannan sarki Shaubatul Azman.Sai da muka sake yin tafiyar rabin sa'a sannan muka iso maqura ashe akan wani kogon dutse muke,wanda qarqashin sa wata masifaffiyar gagarumar wuta ke ci.Babu yadda za'a yi mutum ya wuce face yabi ta cikin wutar.Daga inda muke zuwa qarshen wutar yake ya kai kamu dari biyar.Nan fa muka tsaya muka yi duru-duru.Daga can sai muka hango alamun rigunan dakarun Ashikatul Ashiriya a cikin wutar basu gama cinyewa ba, kuma ga su nan birjik babu adadi.Al'amarin daya dugunzuma hankalin mu kenan.Na dubi jarumi Miqdad nace,"ya kai Miqdad ta ya ya zamu iya haure wutar nan?" Miqdad yace,"ina littafin nan yake?" Take na sake zura hannu cikin aljihun rigata na dauko,Miqdad ya kar6a ya bude shafin da wutar take ya karanto jawabi kamar haka: "Ya kai bakon wannan kogo kayi sani cewa ba zaka iya haure wutar nan ba face ta saman gininta.Za kaga wadansu karafa a manne jikin ginin sama farare da baqaqe a cakude.Lallai fararen zaka rinqa kamawa kana tafiya.Ma'ana kafafunka na reto a kas,kuma idanun ka a rufe.Idan ka kuskura kayi kuskure ka kama bakin qarfe, karfen zai tumbuko daga cikin gini ka fado qasa cikin wutar nan ka kone." MU HADU A PART C DON JIN CIGABAN KAYATACCEN LABARI... Najibullah Muhammad**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU💯🙏 PART C🗡️🗡️ AUTHOR: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 TYPING: AHMAD MUNNIR. POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Koda Miqdad ya gama karanta wannan jawabi sai na tsuguna qasa cikin karayar zuciya na dago kai na dube shi nace,"zai fi kyau ku bar ni anan don dole ne ma nayi kuskure.Dubi fa yadda dubunnan karafan nan suke a cakude farare da baqaqe.Kuma koma banyi kuskure ba ai kafin mutum yakai karshe saiya gaji da tafiyar a haka ya fado." Miqdad ya tsuguna a gabana yace,"ya ke suhaila kiyi sani cewa ba zan iya tafiya ba na barki.Idan kuwa za ki hallaka a cikin kogon nan zan so mu halaka tare.Ni na san cewa dani da mahaifin ki zamu iya ketare wannan wuta albarkacin abin bautar mu.Tun da kin tsorata ni zan tsallakar dake ta hanyar ki rungume ni a kirji kuma ki daure jikin ki da nawa.Idan har zaki fado cikin wutar nan saidai mu fado tare." Koda gama fadin haka saina dube shi nace,"haba ya ma za ai mu tsira da wannan dabarar? Ka tuna fa cewa nauyin jikin ka ma kadai zai gundureka ballantana ka kara da nawa nauyin." Miqdad yace,"karki damu ina son ki yarda da ni kisa a ranki lallai zan iya." Nayi shiru ina mai nuna alamun rashin gamsuwa,yayin da mahaifina Shaubatul Azman ya fuskanci haka sai shima ya durqusa a gabana ya kama kafaduna.Sannan yace,"yake 'ya ta ki saki jikinki ki tuna irin hadarin da ke can baya na kogin darma,amma saida Miqdad ya hayar dake.Tabbas na san zai iya kubutar dake." Wannan jawabi ne yasa jikina yayi sanyi na aminta.Kawai sai na yarda na rungume Miqdad shi kuma Shaubatul Azman sai ya kwance rawanin sa ya daure jikina dana Miqdad tamau.Koda yin hakan sai ya dubi Miqdad yayi murmushi,sannan yace,"idan har ka tserar da rayuwar 'ya ta daga wannan hadari ka biya sadakin aurenta." Cikin tsananin mamaki da farin ciki na dubi Shaubatul Azman na kama dariya,shima sai ya kama dariyar.Miqdad yayi murmushi yace,"ai kuwa zan nemo wannan sadaki ta kowane hali iyakar qoqarina." Nan take jarumi Miqdad ya runtse idanun sa sannan ya daka tsalle sama ya kamo fararen qarafa biyu.Sannan ya cigaba da tafiya a sama yana kama karafan dake gaba.Sai da Shaubatul Azman ya lura da yadda jarumi Miqdad ke sauya hannayensa wajen kamo karafan.Sannan shima yayi koyi da shi.Idan muka yi tafiya mai dan tsawo saiya tsaya ya huta,sannan ya cigaba da tafiyar.Babu abinda ya bani mamaki face yadda ya jure nauyina da kuma gajiyar.Saida muka isa daf da karshen wutar nan sai rawanin dani a jikin Miqdad ya kwance.Ai kuwa saina su6uto na yi yo kasa.Cikin zafin nama na ruqo kafafun Miqdad sai gashi ina reto a sama kamar zan fado. Nan fa na rikice na dunga kwala ihu.Miqdad ya daka min tsawa yace,"ki nutsu ko na karkada kafafuna ki fada cikin wutar." Da jin wannan batu sai na yi tsit.Miqdad yace,"haba gimbiya 'yar sarakai wadda ta gaji zuciyar maza.Ki cigaba da kama kafafuna kina hawowa sama ni kuma zan taimaka miki na dawo dake kan kirjina.Idan kika yi haka zan gamsu cewa kema kina son ki ceci kanki,kuma kin cika mace mai zuciyar maza." Koda jin haka saina ji wani sabon qarfi ya shige ni gami da kwarin gwiwa.Nan take na cigaba da hawa kan kafafun nasa duk da cewar shima reto yake a sama.Saida na kai iya kugunsa sannan yasa hannu daya ya dagoni sama ya dorani a kirjinsa ni kuwa na qara maqalqale shi.Duk wannan abu dake faruwa idanun mu a rufe suke kuma sarki Shaubatul Azman bai qaraso inda muke ba.Nan da nan muka dirga a karshen wutar bisa turba.Koda Miqdad ya ga cewa har ynx Shaubatul Azman na can baya sai ya sake tsalle ya ruqo karafan nan na sama ya koma da baya cikin sauri kamar dama can ya laqanci tafiya a wajen yasa Shaubatul Azman a kirjinsa kamar yadda yayi mini ya taho da shi da sauri suka riskeni.A wannan lokaci ne na jinjinawa Miqdad na dube shi nace da shi,"hakika ka cika gwarzon jarumi mai matuqar sadaukan taka da juriya." Miqdad yayi murmushi sannan ya kama hannuna ya jani da gudu muka kara nausawa cikin kogon Shaubatul Azman na biye da mu. Haka dai muka cigaba da riskar abubuwan hadari iri-iri har kala goma a tsawon kwana biyu.Kuma cikin sa'a duk muka tsallake su dayan mu bai halaka ba.Amma fa munga gawarwakin fadawan Ashikatul Ashiriya da yawa ba adadi.Ba zato ba tsammani sai muka tsinci kanmu a wata makekiyar fada wacce ta cika ta batse da dukiya ninkin baninkin dukiyar da muka gani a farkon shigowa wannan kogo na Baitul Husuk.Ni kam babu abinda ya fi bani mamaki face girman kogon domin har ynx a wani bangare dabam muke bamu shiga wasu wuraren ba.Har na kutsa kai zan shiga cikin dukiyar nan sai Miqdad yayi sauri ya ruqo hannuna kuma yayi wa Shaubatul Azman nuni da cewar duk muyi shiru mu daina motsi.Cikin sanda jarumi Miqdad ya nufi cikin wasu tukwane marasa adadi wadanda a cike suke taf da sulallan zinare.Miqdad ya zare takobin sa ya soka cikin sulallan.Kawai sai muka ji ihu daga cikin tukunyar.Miqdad na zare takobin saiga jini a jikin ta. Nan da nan dakarun Ashikatul Ashiriya suka rinqa fitowa daga cikin tukwanen sulallan suka afka mana.Ashe tuntuni sunji motsin tahowar mu shi yasa suka yi lam6o.Nan fa wuri ya hargitse sarki Shaubatul Azman kuwa ya kaiwa Miqdad dauki aka fara azababben yaki.Ni kaina mayakiya na zama a wannan lokacin na dunga sara da suka saiga shi kuwa ina zubar da maza dama na dade da koyon yaki a wajen jarumi Haiman amma ban taba jarraba jarumtata sai a sannan.Muna cikin tsakiyar artabu da wadannan tsirarun dakarun ne na hango Ashikatul Ashiriya a can sama cikin wani daki tana karanta wadansu dalasimai na tsafi.Ai kuwa fara karatun nata ke da wuya sai wani irin haske mai tsananin qarfi ya haskake wajen da ake yaki gaba daya.Take kowa ya qame aka zama kamar gumaka ni kadai ce ban komai ba. Ashikatul Ashiriya ta kyalkyale da dariyar qeta ta juyo ta dubi inda muke kawai sai ta hango ni a tsaye na ruqe quguna da hannu biyu ina kallonta.Cikin tsananin mamaki ta dube ni ta daka min tsawa tace,"ya akai ke baki qame ba?" Maimakon na bata amsar tambayar saina zaro littafin nan na sirrin arzikin Kisra daga cikin rigata na nuna mata ina mai murmushi nace,"ya ke wannan sarauniya kiyi sani cewa indai ina tare da wannan littafi babu wani sihiri na cikin kogon nan da zaiyi tasiri a kaina." Yayin da Ashikatul Ashiriya ta ji haka saita fashe da kuka sannan ta dube ni tace,"yake 'ya ta ashe kin manta da duk irin son dana nuna Miki a rayuwa.Ki tuna cewa nonona kika sha kika girma har kika kawo iyanzu.Na kasance a cikin tsananin qaunar ki tun daga quruciyar ki don haka har abada ba zan cutar da ke ba.Ina mai roqonki daki kawo mini wannan littafin yanzu nayi alqawari ba zan cutar da ke ba kuma zan cigaba da riqeki a matsayin'yar cikina." Koda Ashikatul Ashiriya ta zo nan a zancenta sai na kyalkyale da dariya nace,"haba sarauniyar yaudara kiyi sani cewa na sanki na san halinki,idan kika qi abu har abada baza ki so shi ba,kuma nima kin koya mini wannan hali.Na rantse da son da nake wa mahaifina yanzu haka na tabbatar da cewa yaudara ta kike so kiyi in baki wannan littafi don ki halakar dani,kuma ki sami damar fita daga cikin kogon nan don haka ba zan ba ki ba.Ina tabbatar miki da cewa ajalinki na cikin kogon nan." Koda jin wannan batu sai sarauniya Ashikatul Ashiriya ta zare takobin ta ta rugo gareni tana qaraji da nufin ta sare ni.Nima saina ruga gareta muka hadu a tsakiya muka fara dauki ba dadi.Nan fa muka rinqa kaiwa juna sara da suka.Hannuna guda na ruqe da takobi,dayan kuma na ruqe da wannan littafi na Mabudin arzikin Kisra.Bisa mamaki saina ga ta quntata ni ta hanani sakat,domin ta fini kwarewa a iya sarrafa takobi nesa ba kusa ba. Nan da nan ta rikirkita ni har ta sami nasarar yi mini yanka guda biyu.Daya a damtsen hannu,daya kuma a cinya.Al'amarin daya sa nayi ihu na fadi kasa ita kuwa saita matsoni tana kyalkyala dariya lokacin dana ke ja da baya.Ashikatul Ashiriya ta ce,"haba yarinya ai duk wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi.Na rantse da darajar karagata koda Haiman na kara ba zai samu nasara ba a kaina bare ke." Ina cikin jan jiki da baya ne bayana ya tokare da bango babu damar gudu.Koda ganin haka sai Ashikatul Ashiriya ta qara bushewa da dariya tace,"yauwa yanxu kam na rutsa ki kuma cikin ruwan sanyi zan kashe ki na dauke wannan littafi." Take ta daga takobin ta ta kawo mini sara da nufin ta tsarge ni biyu.Cikin zafin nama na kare saran da littafin nan na Mabudin arzikin Kisra.Ko da takobin ta sari littafin sai hasken nan mai qarfi ya sake baibaye kogon gaba daya.Take ruhin kowa ya dawo aka cigaba da yaki.Ashikatul Ashiriya tayi sauri ta ruga cikin dakin nan don ta karanta wadansu dalasimai na tsafi.Ai kuwa saina bita da gudu na sa kafata na harde ta ta fadi qasa takobin ta ta su6uce daga hannun ta.Kawai saina daka tsalle na dira a kanta muka cigaba da kokawa mu murgina nan,mu hautsina can. Nan fa ta samu ta hau ruwan cikina ta rinqa naushina a fuska ta hada mini jini hanci da baki,sai dana suma.Sannan ta dagani kuma ta cire littafin nan daga hannuna.Cikin sauri ta rinqa bude shafukan littafin harta zo kan shafin karshe inda aka yi bayanin yadda za'a bude wata kofa ta fita daga cikin kogon da kuma yadda za'a qone kogon gaba daya.Ashikatul Ashiriya ta karanta wadansu kalmomin tsafi saiga wadansu raquma da alfadarai sama da guda dubu dari uku sun bayyana.Bayyanar su keda wuya sai dukiyar nan ta cikin tukwane ta dora kanta a kansu.Ashikatul Ashiriya ta sake karanta wadansu kalmomin sai wata katuwar kofa ta bayyana ta bude kanta.Cikin sauri Ashikatul Ashiriya ta kada raquman nan da alfadaran suka fara fita wajen Kogon Baitul Husuk dauke da dukiyar.Ita ma saita ruga da gudu izuwa kofar don ta fice.Har yanzu ana ta fafata yaki da su jarumi Miqdad sai ragargazar maza yake baima lura da abinda ya faru gare ni ba,bare ya hango Ashikatul Ashiriya wacce ta nufi kofar fita da gudu. A dai dai wannan lokaci ne na farfado daga dogon suman dana yi,kuma a sannan ne Ashikatul Ashiriya ta isa bakin kofa.Tana zuwa tayi arba da jarumi Haiman tsaye a gabanta ruqe da zabgegiyar wuqa.Cikin tsananin tsoro da fargaba ta ja da baya tana mai nuna shi da dan yatsanta wanda ke karkarwa tace, "Ashe ba kai na kashe ba tun gabanin shigowar mu cikin kogon nan?" Jarumi Haiman yace,"kwarai kuwa ni kika kashe amma ban mutu ba,kece dai za ki mutu yanzu." MU HADU PART D DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCIYAR HIKAYAR.**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU. PART D ❤️❤️ NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴 TYPING AHMAD MUNNIR ☺️ POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️ MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Cikin zafin nama Ashikatul Ashiriya ta yunqura ta zare wata qaramar wuqa daga qugunta ta kai masa sura a kirji.Haiman ya goce wuqar ta soki iska.Kafin ta sake wani yunqurin tuni ya kir6a mata tasa wuqar a kirji.Wuqar ta nutse a cikin kirjin nata ta fadi qasa jini na 6ul6ulowa tana kakarin mutuwa,har ynx bata saki wuqar dake hannun ta ba.Haiman ya sunkuya a kanta yace,"wannan shine sakamakon 'yar uwar data nemi hallaka dan uwanta saboda mulki da dukiya." Kafin Haiman ya gama rufe bakinsa Ashikatul Ashiriya ta luma masa wuqar nan dake hannun ta a maqoshin sa,take ya fadi qasa matacce.A lokacin ne na qaraso wajen na fusge littafin nan daga hannun ta kuma na doki hannun ta mai ruqe da wuqa da qafata.Wuqar tayi can gefe guda.Ashikatul Ashiriya tayi dariyar qarshe tace,"yake 'ya ta kiyi sani cewa ban mutu raguwa ba,jaruma ce ni wadda na kashe daya daga cikin manyan jaruman duniya wato dan uwana Haiman.Kiyi sani cewa ga dukiyar nan bisa raquma da alfadarai duk taki ce ke kadai,amma ki sani kema ba zaki gama rayuwar ki ba ta duniya sai qunci da bakin ciki sun riske ki.Tuni na gama shirya hakan cikin sihirin tsafi.Da wannan kalma nake miki bankwana a ci duniya da tsinke lafiya." Ashikatul Ashiriya na gama fadin haka idanun ta suka qafe komai nata ya daina motsi.A dai dai wannan lokaci ne jarumi Miqdad da sarki Shaubatul Azman suka gama karkashe sauran dakarun Ashikatul Ashiriya.Sannan suka taho gareni.Koda jarumi Miqdad yaga gawar Haiman kusa da gawar sarauniya saiya durqusa ya dago da gawar Haiman ya rungume ta.Sannan ya fashe da kuka yana mai cewa, "Shi kenan na rasa abokina,na rasa aminina." Nan dai muka yi ta rarrashin sa har ya daina kuka.Sannan muka tsaya saida duk raquman nan da alfadaran nan masu dauke da dukiya sama da dubu dari uku suka gama fita daga cikin kogon Baitul Husuk,sannan muma muka fita.A bakin kogon na tsaya na bude littafin nan zuwa shafin karshe na karanta wadansu kalmomin tsafi.Take kogon ya fara ruftawa cikin kasa.Kasa ta kama girgiza bisa dole muka ruga da gudu tare da raquman mu da alfadaran mu.Har muka yi nisa daga wajen kogon nan bai gama nutsewa ba a cikin kasa. Daga inda muke muna iya hango nutsewar kogon.Anan ne na tsaya na dubi jarumi Miqdad da mahaifina Shaubatul Azman ina mai murmushi kawai saina rungume su muka kama tsalle gaba daya cikin matuqar farin ciki.Mu uku kacal muka tsira daga cikin miliyoyin mutanen da suka shiga cikin kogon Baitul Husuk.Ba tare da 6ata lokaci ba muka kada raquman mu da alfadaran mu muka yi ta tafiya har muka iso birnin mahaifina Shaubatul Azman.Anan ne aka daura aurena da jarumi Miqdad. Bayan an daura aurene yayi sallama dani yace zai tafi kasar su in yaso na riske shi a can.Lokacin da Miqdad yaje birnin Shauqib inda dan uwansa ke mulki saiya iske ana yaki har an kashe dan uwan nasa.Nan take ya kai dauki ya kashe abokan gabar gaba daya.Bisa wannan dalili ne aka ba shi mulkin kasar.Saida ya kwana ashirin akan mulki sannan mahaifina Shaubatul Azman yasa aka shirya mini tafiya tare da dakaru dubu dari 'yan rakiya.Sannan ya bani dukkanin raquman nan da alfadaran nan masu dauke da dukiya muka tafi ga mijina sarki Miqdad.Bamu shigo nan birnin Shauqib ba sai la'asar sakaliya.Raqumana da alfadarai na kuwa sai da kwanaki bakwai suka shude suna shigowa cikin garin sannan suka qare saboda yawa. Koda gimbiya suhaila tazo nan a labarin ta sai kuyanga suzaila tayi ajiyar xuciya tace,"ya shugabata a gaskiya kinyi butulci ga sarki Miqdad domin ba don shi ba da baki kawo iyanzu ba.Ya kamata ace kinso duk abinda ya ke so.Ki tuna baqar wahalar daya sha a yakin da yayi a cikin garin ku,duk saboda ke kuma ki tuna yadda ya saida rayuwar sa a cikin kogon Baitul Husuk.Ina mai shawartar ki kije ki nemi gafarar sa bisa qin bawa Mozur da kika yi tunda farko." Koda zulaiya ta gama wannan jawabi sai Suhaila ta kama dariya tayi ta dariyar kamar ba zata daina ba.Al'amarin daya firgita Zulaiya kenan ta miqe tsaye zata gudu.Cikin zafin nama Suhaila ta cafkota ta shaqe mata wuya da hannu biyu.Tun Zulaiya na harba kafafunta da hannayenta harta kasa motsi harshenta ya zazzago waje.Suhaila tayi jifa da gawar Zulaiya tace,"wace ce ke da har za ki bani shawara akan abinda ya dace nayi? Ke baiwa ce ya kamata ace kin tsaya iya matsayin ki." Tana gama fadin hakan ne ta miqe tsaye ta shige cikin turakar ta.Nan da nan fadawa suka dauke gawar Zulaiya suka tafi da ita.Wannan shine abinda ya faru ga Suhaila matar sarki Miqdad bayan ta gama bada labarin yadda ta hadu da sarki Miqdad har ta zamo matarsa. A can nahiyar kasashen baqaqen fata kuwa a cikin birnin Malhiya inda sarki Amzadu ke mulki anan ne bawa Mozur ke bauta a wani 6angare na gidan sarautar.Da yake Mozur ya kasance kakkarfa sai aka kaishi cikin wani wani dakin wata na'urar dutse wadda ake nuqa hatsi da ita.A kalla sai kato arba'in sun taru suke iya juya dutsen dake nuqa dawar,amma bawa Mozur shi kadai yake juya dutsen kuma saiya yini yana aikin da kato arba'in za suyi cikin kwana biyu. *********** Tunda aka siyo bawa Mozur a birnin Shauqib aka kawo wannan daki na nuqan hatsi bai ta6a fita wajen dakin nan ba na tsawon wata tara.Kai bai qara ganin hasken rana ma ba.Ko yaushe yana cikin aiki.Da daddare ne kadai yake samun damar hutu,kuma sau daya ake ba shi abinci da ruwa.Wani lokacin idan bawa Mozur ya tuno da irin rayuwar sa ta da sa'adda yake can kasar Shauqib tare da sarki Miqdad saiya fashe da kuka domin ya san cewa ya rasa babban masoyi,wanda har abada ba zai sake samun kamar sa ba.Kuma rayuwar sa tazo karshe domin karfinsa gaba daya a cikin daki na nuqan hatsi zai kare. Sarki Amzadu nada wata kyakkyawar 'ya budurwa 'yar shekara goma sha takwas wacce yake matuqar kauna,ana kiran ta da suna gimbiya Laslaiya.A iya rayuwar gimbiya Laslaiya babu abinda take so face kallon 'yan kokawa.Bisa wannan dalili ne take shirya wasan kokowa bayan kowane kwana talatin.Duk wanda yaci gasar sai ta kawo kyautar dukiya mai tsananin yawa ta ba shi.Jaruman dake wannan kokowa sukan zo ne daga kasa-kasa. Akwai wani babban bafaden sarki Amzadu mai suna Azmandu wanda shine da alhakin kula da gidan nuqan hatsin sarki inda bawa Mozur ke aiki.Duk sa'ar da za'a yi wannan gasa ta kokawa ya kan tafi neman babban jarumi yazo da shi,domin idan jarumin yaci gasar ya sami dukiya mai yawa suyi kashe mu raba.Yanzu anyi gasar har sau uku amma duk jaruman da yake kawowa basa nasara.A ranar da ya rage saura kwana bakwai ayi gasa ta gaba sai hankalin Azmandu ya dugunzuma saboda jin cewa dukiyar da gimbiya Laslaiya zata bayar a wannan karon tafi ta duk wadda ta bayar a baya.Ba wani abu ne ya tayar da hankalin Azmandu ba face sanin an gama qureshi bashi da sauran wani jarumi wanda yake ganin zai iya cin gasar saboda an kawo zakwaquran jarumai fitattu wadanda suka yi shuhura a wasu 6angararo na duniya. Gefen magriba ne Azmandu ya shigo cikin ɗakin nuƙan inda bawa Mozur ke kishingiɗe yana hutawa saboda gajiyar aikin da yayi.Azmandu ya kewaya cikin ɗakin yaga cewa Mozur ya niƙa buhun hatsi da yawa sama da yadda ya saba yi a kullum.Koda ganin haka sai yayi murna nan take yasa aka ƙarowa Mozur abinci da ruwan sha ishasshe.Sannan ya zauna kusa dashi yana tambayar sa yace, "Ya kai Mozur ya akayi yau kayi aiki mai yawa fiye da yadda ka saba yi?" Koda jin wannan tambaya sai Mozur yayi murmushi yace,"ya shugabana kayi sani cewa a duk sa'adda raina ya ɓaci ina iya yin abinda kowa zaiyi mamaki.Kayi sani cewa a yau na tuno da wani tsohon mai gidana ne wanda ke matuƙar ƙaunata fiye da komai a rayuwar sa amma saida matarsa ta rabamu.Sa'adda na tuno da irin makircin data ƙulla mini ne don ta kashe ni nayi ta aiki a ɗakin nan fiye da yadda na saba yi." Koda jin wannan batu sai Azmandu yayi shiru yana tunani.Daga can ya dubi Mozur yace,"shin ka taɓa yin wasan kokowa kuwa a can garinku?" Mozur yace,"eh na taɓa yi sau ɗaya harma na ci gasar." Yayin da Azmandu yaji haka sai murna ta kamashi ya dubi Mozur yace,"ina son na shigar dakai cikin gasar kokawa wadda gimbiya Laslaiya ke shiryawa a kowanne kwana talatin,zaka iya?" Cikin murna Mozur yace,"ƙwarai kuwa zan iya kuma zan baka mamaki." Ba komai ne yasa Mozur yake son a shigar da shi wannan gasa ba sai don kawai ya sami damar fita daga cikin wannan ɗaki yaga hasken rana wanda rabonsa da shi yau wata tara kenan da ƴan kwanaki. Tun daga wannan rana ya dinga ɗokin zuwan ranar gasa,saboda jin daɗin hakanne ya cigaba da hazaƙar aikinsa fiye da yadda ya saba.Azmandu kuwa yasa a rinƙa bashi abinci mai kyau kuma isasshe.Nan da nan jikin Mozur yayi kyau a cikin kwana bakwan ya zamana ya mayar da duk komaɗar jikinsa da ramarsa.Kyawunsa da kwarjinin sa suka ƙara bayyana ƙarara. Da ranar gasa tazo tunda sassafe Azmandu yazo ya riski Mozur ya kawo masa abinci da abin sha na musamman tare da waɗansu kyawawan tufafi.Bayan Mozur yaci ya ƙoshi sai Azmandu ya bashi waɗannan tufafin gasa,sannan ya dube shi yace,"ya kai Mozur ka sani cewa kai bawa ne na sarki kuma a ƙa'ida bai kamata na ciyar da kai abinci mai kyau ba kuma isasshe,amma gashi tun daga ranar daka yi aikin nan mai yawa kawo iyanzu ban fasa ba.Idan har kana son na cigaba da kyautata maka dole kayi iya ƙoƙarinka kaci gasar wannan kokawa.Kai in dai kaci wannan gasa nayi maka alƙawari zaka rinƙa samun hutun kwana uku a sati,kuma duk sanda kake da muradin mace zansa a kawo maka ɗaya daga cikin bayi na." Koda jin haka sai bawa Mozur yayi murmushi yace,"ni kuwa da izinin abin bautata mai girma Lazzatul sakaru saina sami nasara a cikin wannan gasa." Haka dai Azmandu da bawa Mozur suka cigaba da tattaunawa har lokacin tafiya fada yayi inda za'a gabatar da wannan gasa ta kokawa. MU HADU A PART E DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCIYAR HIKAYAR.**MIFTAHUL-ZARBIL** LITTAFI NA BIYU✍️✍️❤ PART E 👌✌ NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI✍️✍️ TYPING: AHMAD MUNNIR. POSTING:NAJIBULLAH MUHAMMAD 🙂❤👌 Tom jama'a kyan alkawari cikawa, kamar yadda na maku alkawarin kawo maku cigaban wannan littafin a yau din nan, to gashi na cika. Allah ya Temake mu akan cika duk irin alkawarin da muka ɗauka. MARUBUCIN YA CI GABA DA CEWA.. Koda jin haka sai bawa Mozur yayi murmushi yace,"ni kuwa da izinin abin bautata mai girma Lazzatul sakaru saina sami nasara a cikin wannan gasa." Haka dai Azmandu da bawa Mozur suka cigaba da tattaunawa har lokacin tafiya fada yayi inda za'a gabatar da wannan gasa ta kokawa. Lokacin da su Mozur suka isa ƙofar fada sun makara domin tuni an fara gasar kuma wasu jarumai biyu ne akan wani faffaɗan gini mai tudu suke kafsawa.Jama'a sun kewaye wannan tudu an cika maƙil sai shewa da ihu da tafi ake yi.Daga can ɓangaren gabas kuwa nesa kaɗan sarki Amzadu ne da ƴarsa gimbiya Laslaiya zaune bisa karagar mulki dakaru sun kewaye su suna kallon wannan kokowa.Kallo ɗaya mutum zai yiwa gimbiya Laslaiya ya san cewa yau tana cikin matuƙar nishaɗi domin fuskar ta cike take da murmushi da annuri. Gimbiya Laslaiya ta kasance kyakkyawa ta kwatance domin Allah yayi mata kyakkyawar surar ƙirar kalangu.Tana da dogon gashi baƙi siɗik mai ƙyalƙyali wanda ya sauko har ƙasan cibiyarta,tana da dara daran idanuwa,ɗan ƙaramin baki da dogon hanci.Ƙirjinta cike yake taf,kuma tana da tsukakken ƙugu.Ƴan yatsun hannayenta dogaye ne zara zara gwanin ban sha'awa kuma tana da dogon wuya.Duk da kasancewar ta baƙar fata ba balarabiya ba,bata da duhu ta kasance wankan tarwaɗa.A zahirin gaskiya babu wani ɗa namiji da zaiga gimbiya Laslaiya bata ɗau hankalin sa ba. Koda shigowar Azmandu da Mozur cikin wannan taro sai Azmandu ya kama hannun Mozur ya kaishi wajen alƙalan gasar ya gabatar dashi a matsayin sabon gwanin sa.Cikin mamaki alƙalin gasar wanda ake kira Daraz ya dubi Azmandu,sannan ya ƙarewa Mozur kallo ya bushe da dariya yace,"haba Azmandu ya zako zo mana da wani ƙaramin mutum haka kace shine gwanin ka? Anya kuwa ka dubi jaruman bana da kyau?" Azmandu ya waiga inda jaruman suke tsaye wajen su talatin.Gaba ɗayansu gabza gabzan ƙarti ne masu ƙwanji da murɗaɗɗen jiki,babu wanda girmansa bai ninka na bawa Mozur ba sau uku.Azmandu ya haɗiyi miyau gami da ajiyar xuciya yace, "Ba komai ɗan hakin daka raina shi ke tsone maka ido,kai dai kawai ka shigar dashi cikin gasar." Nan take Daraz ya ƙara bushewa da dariya yace,"lallai yau da rabon zaka ji kunya kenan amma tunda kace a shigar dashi zan shigar." Daraz ya dubi Mozur a wulaƙance yace,"mene ne sunanka?" "Suna na Mozur bin Miƙdad."Ya bashi amsa. Daraz ya sake tambaya yace,"daga wace ƙasa?" "Daga birnin Shauƙib." Koda jin haka sai Daraz ya ƙurawa Mozur idanu cikin yanayin mamaki har saida Mozur ɗin yace da shi,"Ina zan tsaya?" Sannan ya nuna masa inda jaruman gasa ke tsaitsaye suna kallon waɗanda ke kafsawa.Kai tsaye Mozur ya tafi inda jaruman suke ya shige cikin su ya tsaya.Jaruman kuwa suka rinƙa kallonsa cikin mamaki don basu san dalilin da yasa yayi wauta ba ya shigo cikin su.Tsayuwar Mozur keda wuya sai idanun sa suka kai inda sarki Amzadu da gimbiya Laslaiya ke zaune.Koda yayi arba da Laslaiya sai ya ƙura mata ido yana mai mamakin tsananin kyawunta.Nan take ya tuno da gimbiya suhaila ya kasa tantance wadda tafi kyawu tsakanin Laslaiya da Suhaila,amma sai yace a ransa,"ni dai inda zaɓi za'a bani dana zaɓi wannan baƙar fatar ƴar uwata,domin tafi burgeni akan suhaila." Yana gama faɗin haka ne hankalin sa ya koma kan jaruman dake kafsawa a kan wannan gini mai tudu.A lokacin ne ɗaya daga cikin su mai suna Zarto ya ɗaga abokin gwamin nasa sama ya dunga hajijiya dashi har saida ya jigata shi sannan ya kwaɗa shi da ƙasa.Take jarumin ya sume fili ya cika da shewa aka yi ta yiwa Zarto tafi. Zarto ya kasance ƙaton gaske domin duk cikin ƴan kokawar babu mai girmansa da kwarjinin sa.Lokacin da Mozur yaga Zarto saida zuciyar sa ta kama bugawa da ƙarfi domin yasan cewa ka ba'a gwada ba linzami yafi ƙarfin bakin kaza.Nan dai Zarto ya sauko daga kan tudun gumurzu ya koma cikin jarumai ya tsaya.Shi kuma waccan jarumi da suka kafsa da Zarto sai da aka yayyafa masa ruwa sannan ya farfaɗo.Alƙalin gasa ya ƙara kiran wani jarumi waishi Kambus. Kambus ya hawo kan tudun kafsawa yana mai tafiyar taƙama,jin kai da hura hanci.Shima Kambus ƙato ne na gaske domin da kaɗan Zarto zai fishi,amma kuma yafi Zarto tsawo sosai.Ba zato ba tsammani sai Mozur yaji an kirawo sunan sa cewa ya hawo kan tudun kafsawa shine zai kara da Kambus.Nan fa hankalin Mozur ya dugunzuma,amma sai ya dake ya hau kan tudun cikin ƙarfin hali.Koda ya tsaya a gaban Kambus sai ya zamo kamar ɗan tsako a gaban shirwa domin tsawon sa ma iya cibiyar Kambus ya tsaya. A wannan lokaci ne gimbiya Laslaiya ta ƙurawa Mozur idanu tana mai mamakin tsautsayin da ya shigo da shi cikin wannan gasa domin shine mafi ƙanƙanta a cikin jaruman.Kambus ya sunkuyo da kanshi ƙasa fuskar sa ta tsaya daf da Mozur yana muzurai yace,"kai ɗan tatsitsi mai tsautsayin wahala wane irin karambani ne ya shigo dakai cikin wannan gasa?" Mozur yayi murmushi yace,"neman suna da neman arziki ne ya kawo ni kamar yadda ya kawo ka." Kambus ya ƙyalƙyale da dariya kuma ya murtuke fuskar sa a lokaci guda yana mai cewa,"yaro kayi ganganci,yau zan koya maka darasi domin kasan cewa bakin rijiya ba wajen wasan ka bane." Kafin Mozur yace wani abu tuni Kambus ya shaƙo wuyansa da hannu ɗaya saiga Mozur na wutsil wutsil da ƙafafu a sama kamar jelar ɓera a bakin kyanwa.Nan fa filin wajen ya cika da dariya,kowa sai ƙyaƙyatawa yake.Azmandu ne kaɗai sai kuma gimbiya Laslaiya wacce ta shiga cikin tashin hankali saboda tausayi.Shima Kambus sai yayi ta ƙyalƙyala dariya yana zagaya wa akan tudun kuma yaƙi sakin wuyan Mozur. Nan da nan idanun Mozur suka yi ƙulu ƙulu suka yi jawur.Koda yaji numfashin sa na neman ɗaukewa saiya harzuƙa cikin tsananin zafin nama ya tattare ƙarfinsa gaba ɗaya yasa hannu biyu ya ɓanɓare hannun Kambus daga wuyansa kuma yayi wurgi da Kambus can gefe ɗaya.Saiga Kambus na katantanwa a ƙas.Al'amarin daya jefa kowa cikin mamaki kenan filin gaba ɗaya yayi tsit kuma sai da kowa ya miƙe tsaye aka zubawa Mozur idanu ana mai al'ajabinsa.Shi kuwa Azmandu saboda farin ciki bai san sa'adda ya kama wuyan alƙalin gasa ba yana tsalle da shewa.Kamar haɗin baki sai kowa ya kama yiwa Mozur tafi.Gimbiya Laslaiya kuwa saita miƙe tsaye daga kan karagar ta tana ta tafi da kallon jarumi Mozur tana murmushi. Koda ganin haka sai sarki Amzadu ya kamo hannun ta ya zaunar da ita yana mai harararta.Laslaiya ta nutsu ta kau da kai gefe ɗaya.Dama ƙa'idar wannan gasa itace indai mutum ya faɗi ƙasa to an cinye shi.Koda Kambus yaga yaje ƙas sai idanun sa suka ciko da ƙwalla saboda tsabar takaicin cewa ƙanƙanin mutum kamr Mozur ya kayar da shi.Haka dai Kambus ya sauka daga kan tudun cikin jin kunya da baƙin ciki har yana kuka.Bai tsaya a filin ba gaba ɗaya ya bar wajen gasar.Nan dai aka cigaba da wannan gasa.Duk wanda Mozur ya kara da shi sai yayi nasara.Sai da takai ta kawo cewa gaba ɗayan jaruman nan na tsoron kafsawa da Mozur face mutum ɗaya wato Zarto,kuma ba'a haɗasu ba sai a zagayen ƙarshe na gasar.Koda ƴan kallo suka ga jarumi Mozur da jarumi Zarto tsaye a kan tudun kafsawa sai filin ya kaure da shewa da ihu kowa na zaɓin gwanin sa.Wasu suce Zarto ne zaiyi nasara a wannan gasa,wasu kuma suce Mozur ne.Nan fa ƴan caca suka fara fito da kuɗaɗe don neman sa'a.A wannan rana ƴan caca sun zuba dubunnan dirhami masu yawa akan wannan gasa. Zarto da Mozur suka fara kallon kallo.Sannan suka hau zagaya filin kowannen su zuciyar sa ciki da saƙe saƙen hanyar da zaibi ya sami nasara.Cikin shammace Zarto ya kawowa Mozur cafka da niyar ya rungume shi ya matse shi.Mozur ya goce cikin zafin nama ya wuce ta tsakankanin ƙafafunsa.Takaici ya kama Zarto ya ciza yatsa domin a tarihin kokawarsa bai taɓa kaiwa wani wannan hari ba ba tare da ya sami sa'a da nasara ba.Zarto ya juya ya sake fuskantar Mozur ya sake kai masa irin wannan hari a karo na biyu.Ai kuwa sai Zarto ya sami nasarar damƙar Mozur ya zamana ya matse masa baya da hannu biyu.Mozur ya kwarara ihu saboda tsananin jin zafin ruƙon da yayi masa. Al'amarin da ya razana kowa kenan a wajen.Gimbiya Laslaiya kuwa bata san sa'adda ta miƙe tsaye ba zumbur cikin alamun razani.Sarki Amzadu ya sake danƙwafar da ita zaune yayi mata raɗa a kunne yace,"idan kika sake miƙewa kin gama kallon gasar kenan." Cikin fushi Laslaiya ta kau da kai ta cigaba da kallon abinda yake faruwa.Mozur yayi iya ƙoƙarinsa akan ya ɓamɓare hannayen Zarto daga bayansa amma ya kasa kawai sai ya yiwa Zarto karo da ka a fuska.Bisa dole Zarto ya saki Mozur ya dire ƙasa da ƙafafunsa.Fuskar Zarto ta cika da raɗaɗi har idanun sa suka rufe ya zamana yana ganin mutane dishi dishi,saida ya girgiza kanshi sannan ya watstsake.Zarto ya ruga kan Mozur yana ruri da nufin ya sunkuce shi.Saida ya rage saura taku ɗaya ya riskeshi Mozur yayi tsalle sama ya shallake Zarto ya dira a bayansa.Cikin zafin nama ya juya ya shaƙo wuyan Mozur da hannu biyu saiga Mozur yana wutsiltsila ƙafafu yana kakarin mutuwa.Zarto ya ƙara haɗa ƙarfinsa duka yana mai daɗa shaƙe Mozur.Tabbas niyarsa kawai ya kashe Mozur murus har lahira. Nan da Mozur ya fara ƙoƙarin ɓanɓare hannun Zarto amma saiya kasa.Nan da nan idanun Mozur suka wurƙile suna nuna alamun suma.Laslaiya dai bata san sa'adda ta fara zubar da hawayen tausayi ba.Gashi a ƙa'idar wannan gasa ba'a raba faɗan face ɗaya daga cikin ƴan kokawar yaje ƙasa.A zahiri dai mutane suna iya ganin wutsil wutsil ɗin ƙafafun Mozur da motsin hannuwansa kamar ba suma yayi ba amma a baɗini ƙanin suma yayi,inda ya shiga tunanin irin haɗarurrukan da ya shiga a can birnin Shauƙib a lokutan da gimbiya Suhaila tasa aka yi masa dukan kawo wuƙa don a kashe shi da kuma lokacin data sa aka ɗaure shi a cikin buhu aka jefa shi cikin tsakiyar teku.Koda Mozur yazo nan a tunanin sa sai zuciyarsa ta kama tafarfasa ya watstsake.Take wani sabon ƙarfin na musamman ya shige shi,kawai sai aka ji ya kwarara uban ruri lokaci guda ya ɓanɓare hannuwan Zarto daga wuyansa kuma ya sunkuci Zarto cikin zafin nama yayi sama dashi ya dinga hajijiya da shi. **************** A wannan lokaci ne gimbiya Laslaiya ta bushe da dariyar farin ciki tana yiwa Mozur tafi.Mozur yayi ta hajijiya da Zarto a sama saida ya fita daga haiyacinsa sannan ya kwaɗa shi da ƙasa.Gaba ɗaya filin ya ruɗe da shewa da tafi.Jama'a suka ruga kan tudun da ake gasa suka ɗaga jarumi Mozur sama suna cilla shi a cikin iska yana dawowa kan hannuwansu ana yi masa jinjina.A sannan ne Mozur da gimbiya Laslaiya suka ƙurawa juna ido yaga tana yi masa tafi fuskarta cike da annuri amma kuma ga hawaye na zuba a idanun nata.Al'amarin da yayi matuƙar jefa Mozur cikin tsananin mamaki da damuwa kenan.Nan take aka kira Azmandu yazo gaban gimbiya Laslaiya ya kwashi gaisuwa.Sannan ta sunkuya ta ɗauki ƙatuwar jaka cike da dirhami ta miƙa masa.Azmandu ya karɓi jaka ya fara tiƙar rawa cikin tsananin farin ciki.Sannan ya ruga inda jarumi Mozur ke tsaye ya rungume shi yana mai yi masa jinjina.Sarki Amzadu ya kama hannun gimbiya Laslaiya suka nufi cikin gidan sarauta dakaru na biye da su.Laslaiya tayi ta waigen jarumi Mozur suna kallon juna tana murmushi a gareshi har ta ƙule ya daina ganinta. Lokacin da Mozur da Azmandu suka koma cikin gidan nan inda Mozur ke bauta sai suka zauna don su huta.Azmandu yasa aka kawo musu abinci iri iri da kayen shaye shaye kala kala,don suyi walimar wannan nasara da suka samu.Nan take Azmandu ya kama ciye ciye,shi kuwa Mozur saiya zubawa abincin idanu ya kasa ci,kuma ba komai yake gani ba a cikin abincin face fuskar gimbiya Laslaiya.Zuciyarsa cike da wasu wasi yana mai tambayar kansa cewa me yasa gimbiya ke yi mini murmushi haka? Kuma mene ne dalilin zubar hawaye a idanunta? Amsar da ya kasa samar da ita kenan a cikin ƙwaƙwalwarsa.Koda Azmandu ya lura da halin da Mozur ya shiga saiya dubeshi yace, "Ya kai wannan jarumi tunanin me kake haka wanda ya hanaka cin abinci alhalin yau ranar farin ciki ce a gare mu ko kuwa wani abun kake da buƙata ka kasa sanar dani?" Koda jin wannan tambaya sai jarumi Mozur yayi ajiyar zuciya yace,"ya shugabana kayi sani cewa bana buƙatar komai daga gareka kuma babu abinda nake tunani face yadda al'amuran rayuwa ta suka kasance a da da yanzu." Da jin haka sai Azmandu ya bushe da dariya sannan yace,"ashe kuma bayi kukan shiga damuwa da tunani irin wannan?Ai inda ni bawa ne har abada bazan yarda na sa wani abu a raina ba,wanda zai dame ni,tunda nasan cewa a cikin bauta rayuwa ta zata ƙare." MU HAƊU A PART F DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCEN LABARIN.**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU✍️✌ PART F ❤❤ NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI🧝‍♀️ TYPING AHMAD MUNNIR. POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD. MARUBUCIN YA CI GABA DA CEWA... Ai inda ni bawa ne har abada bazan yarda na sa wani abu a raina ba,wanda zai dame ni,tunda nasan cewa a cikin bauta rayuwa ta zata ƙare." Mozur yayi murmushi yace,"ya shugabana kayi sani cewa ita rayuwa bata da wani haƙiƙani akan kowa.Da mu daku duk ɗaya ne domin bawa na iya zama sarki,haka kuma sarki na iya zama bawa." Koda jin wannan batu sai Azmandu ya furzar da abincin dake bakinsa cikin fushi yace,"wannan wace irin maganar banza kake yi? A ina ka taɓa ganin sarki ya zama bawa? Ai abinda ba zai taɓa yiwuwa bane,domin ko tarihin labarun da suka shuɗe ban taɓa jin haka ba." Nan dai Azmandu ya rufe Mozur da faɗa yayi ta bambami har ya gaji.Sannan ya tashi ya fice cikin fushi ba tare da ya kammala cin abubuwan dake gabansu ba.Shi kuwa Mozur saiya kishingiɗa ya lumshe idanun sa ya cigaba da ganin hoton fuskar gimbiya Laslaiya a cikin zuciyarsa. Kamar yadda jarumi Mozur ya kasance cikin sabon yanayi na tunani da rashin sukuni haka gimbiya Laslaiya ta kasance domin ita ma dai a wannan rana ko ruwa bata iya sha ba bare cin abinci.Idan ta kwanta sai taji kwanciyar ba daɗi don haka saita miƙe zaune. Zaman ma saita ji ba daɗi kawai saita tayi ta kai komo a cikin harabar gidanta ta kasa zaune ko tsaye. Duniyar gaba ɗaya ta yi mata zafi. Tana cikin wannan hali ne mahaifiyarta Zalisha ta shigo ta risketa. Kallo ɗaya Zalisha ta yi wa Laslaiya ta fuskanci cewa lallai tana cikin damuwa. Nan take Zalisha ta kama hannun Laslaiya ta jata izuwa cikin ɗakinta ta zaunar da ita a gefen gado suka fuskanci juna. Zalisha tace,"yake 'ya ta ki yi sani cewa babu abinda nake so a duniyar nan sama da ke,kuma duk abinda kike so shi nake so,haka kuma wanda kike ƙi dole na ƙi shi. Yake 'ya ta haƙiƙa yau kina cikin damuwa don haka zuciya ta ta sosu ina umartarki da ki hanzarta sanar dani abinda ke damunki,domin na amince miki shi yanzu take." Sa'adda Zalisha tazo nan a zancen ta sai Laslaiya tayi ajiyar zuciya. Sannan tace,"yake ummina ki yi sani cewa babu abinda ke damuna face son ganin jarumin da yaci nasarar gasar kokawa a yau." Koda jin haka sai mamaki ya kama Zalisha tace,"wane ne wannan jarumin?" Haka kuma mene ne sunansa?" Cikin yanayin damuwa Laslaiya tace,"ban san kowane ne shi ba,amma naji ana kiransa da suna Mozur,kuma sarkin gida Azmandu ne yazo da shi filin gasa." Koda jin haka sai Zalisha tace,"ai kuwa kamar na taɓa jin sunansa a cikin gidan sarautar nan amma dai bari dai nasa a bincika...." Nan take Zalisha ta kira wata baiwa Amaratu tace da ita ta ruga gidan sarkin gida Azmandu tace yazo yanzun. Amaratu ta ruga da gudu don cika umarni. Jim kaɗan sai ga ta ta dawo tare da Azmandu. Azmandu ya ƙaraso da sauri izuwa gaban Zalisha ya faɗi ya kwashi gaisuwa cikin biyayya da sunkui da kai ƙas. Zalisha ta dube shi tace,"ya kai Azmandu kayi sani cewa ban kira ka nan dan komai ba don sai ka yi mini cikakken bayani. Ina son nasan wanene Mozur jarumin da yaci gasar kokawa a yau." Azmandu ya ɗago kai ya dubi Zalisha yace, "Ya shugaba ta Mozur ba kowa bane face bawanku wanda ke aikin niƙan hatsin gidan nan. Kiyi sani cewa yau watansa tara cif a cikin ɗakin hatsi bai taɓa fita ba sai yau tun daga ranar da aka kawo shi daga birnin Shauƙib sa'adda aka siyo shi a matsayin sa na bawa." Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zalisha da Laslaiya, saboda daɗewar Mozur a cikin gidan sarautar tasu amma ko sau ɗaya basu taɓa ganin sa ba. Zalisha tace,"yanzu yana ina?" "Yana cikin ɗakin aikinsa."Azmandu ya amsa. Koda jin haka sai Zalisha ta miƙe tsaye.Sannan ta kamo hannun Laslaiya ta tashe ta tsaye,kuma ta dubi Azmandu tace, "Na umarce ka da ka kaimu wajen Mozur yanzu-yanzu." Cikin biyayya Azmandu yace,"an gama ya shugaba ta." ********************************* Nan take Azmandu ya wuce gaba Zalisha da Laslaiya suka bishi a baya suka yi ta tafiya cikin gidan sarautar suna ratsawa ta saƙo-saƙo,lungu-lungu. Sai da suka yi 'yar tafiya mai tsawo. Sannan suka iso gidan da bawa Mozur ke ciki. Ko ina ka duba dakaru ne a tsaitsaye riƙe da makamai suna kula da ma'aikata.Kuma sai mutum ya wuce ƙofofi goma sha biyu. Sannan zai isa ƙaton ɗakin da bawa Mozur ke ciki. A bakin kowace ƙofa dakarun tsaro ne a tsaitsaye guda goma sha biyu. Duk ƙofar da aka zo sai Azmandu ya ƙwanƙwasa yayi magana. Sannan za'a leƙo ta wata 'yar ƙaramar taga a tabbatar da cewa shine ɗin sannan a buɗe. Duk inda suka shiga aka ga Zalisha da Laslaiya sai ayi mamakin zuwan su kuma ai yi ta gaishe su cikin girmamawa. Ba wani abu ne yasa ake mamakin ganin su a wannan waje domin tun da aka gina wajen tsawon shekaru arba'in baya ba su taɓa kawo ziyara ba sai yau. Shi kansa sarki Amzadu bai taɓa shigowa wajen ba. Mozur na kishingiɗe yana tsakiyar tunanin gimbiya Laslaiya sai yaji an buɗe ƙofa an shigo. A firgice ya ɗago kai ya dubi bakin ƙofar, domin a saninsa kullum sau ɗaya tak ake buɗe ƙofar a miƙo masa abinci kuma saida yamma gefen magriba ba kamar yanzu ba da hantsi. Kwatsam,sai ga gimbiya Laslaiya,Zulaisha da sarkin gida Azmandu sun shigo. Ba tare da ɓata lokaci ba Azmandu ya gabatar da Zalisha a wajen Mozur. Sannan yace, "Wannan kuwa gimbiya Laslaiya ce wadda na san ka ganta a yau wajen gasar kokawa." Mozur ya risina ya kwashi gaisuwa a gare su. Zalisha ta ƙarewa Mozur kallo sai ta ji ya kwanta mata a zuciya.Cikin murmushi ta dube shi tace, "Ya kai wannan jarumi ka yi sani cewa na rako 'ya ta ne Laslaiya domin ta gana da kai,don haka yanzu zamu baku dama ku zanta." Tana gama faɗin haka ta juya ta yiwa Azmandu inkiyar su fita. Bada gardama ba Azmandu ya wuce gaba ta bi bayansa. Sai da suka je bakin ƙofar ɗakin. Sannan Zalisha ta waigo tace da Laslaiya, "Karki daɗe sosai, domin mahaifin ki zai iya neman ki." Laslaiya tayi murmushi tace,"ba zan daɗe ba." Bayan fitar Zalisha da Azmandu sai Laslaiya da Mozur suka dubi juna suna murmushi aka rasa wanda zai ce ƙala har kunya ta kama Laslaiya ta kau da kai ga barin kallon sa. Sannan tace, "Daman can kai ɗan kokawa ne?" Mozur yace,"A'a,amma na taɓa shiga gasar kokawa sau ɗaya sa'adda nake can birnin Shauƙib a daular Larabawa." "Ina ne asalin garin ku?" Laslaiya ta sake tambaya. Mozur yace, "A gaskiya ban sani ba,ni dai kawai na taso na tsinci kaina a birnin Shauƙib a hannun wani attajiri wai shi Abulkhairi. A lokacin ban fi shekara bakwai ba,tun a sannan nake yi masa aikin bauta. Wata rana sai sarki Miƙdad ya kawo masa ziyarar bazato koda ya ganni sai yaji yana sona don haka sai ya siye ni da tsada,kimanin dirhami dubu ɗari uku ya tafi da ni gidansa. Daga wannan rana ya cigaba da kula da ni ya zamana kullum ni ke kula da turakarsa na shareta na tsaftace ta har dai ya aminta dani nake dafa masa shayi. Kai har ta kai cewa abinci ma ni ke dafa masa kuma ni kaɗai ne zan ba shi abu yaci ko ya sha. Hatta matarsa gimbiya Suhaila bai sakar mata al'amuran sa ba kamar yadda ya sakar mini. Sai da ta kai ta kawo cewa babu wani sirri na sa da ban sani ba. Wannan shine iyakar labarin asali na wanda zan iya baki." Laslaiya tace, "To yaya aka yi kuma aka siyo ka a matsayin bawa har aka kawo ka wannan nahiyar tamu ta baƙaƙen fata alhalin tafiya ce mai tsawo?" Koda jin wannan tambaya sai jarumi Mozur yayi ajiyar zuciya yace, "Ya shugabata kiyi sani cewa amsar wannan tambaya taki daidai yake da na baki gaba ɗayan tarihin rayuwa ta. Idan kuwa nace zan baki wannan labari sai mu kwana anan ban gama ba." Laslaiya tayi murmushi tace, "Ai kuwa ko ba yau ba sai naji wannan labari daga bakin ka. Ya kai wannan jarumi kayi sani cewa a iya rayuwa ta ban taɓa ganin mutumin dana ji ya burgeni ba face kai. Ka sani cewa tun rabuwa ta da kai ɗazu a filin gasa na kasa samun sukuni, domin zuciya ta ta cika maƙil da begen ka,idanu na kuwa suka cika maƙil da hawayen rashin ganin ka. Gaba jikina ya kama karkarwa saboda rashin jinka a kusa. Ina mai sanar da kai cewa a halin yanzu ina ji a cikin raina cewa ba zan iya yin rayuwa ba muddin babu kai. Lallai kaine zaka zamo abokin rayuwa ta. Shin zaka iya gaya mini yadda kake ji a zuciyar ka dangane da ni?" Yayin da gimbiya Laslaiya tazo nan a zancenta sai mamaki ya ƙara turnuƙe jarumi Mozur kuma hankalin sa ya dugunzuma domin ya san cewa Laslaiya ta naɗa gammo don ɗaukar dutsen da yafi kowane dutse girma a duniya,haka kuma tana shirin jefa rayuwar sa ne a cikin bala'in da bai taɓa shiga ba,don sai ya gwammace mutuwa da rayuwar sa. Cikin alamun karayar zuciya Mozur ya dubi gimbiya Laslaiya yace, "Yake wannan 'yar sarki kiyi sani cewa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa,don haka tafi ƙarfin taɓawar yaro. Ina bawa ina 'yar sarki? Haƙiƙa nima na kasance a cikin irin halin da kika tsinci kanki na yawan tunani da bege to amma fa dole ne mu haƙura da juna in ba haka ba kuwa zamu jefa kanmu cikin rayuwar ƙunci,wataƙila ma ta zama sanadin nadama ga ɗaya daga cikin mu." Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa gimbiya Laslaiya tace, "Ya kai Mozur kayi sani cewa in dai a kanka ne ba zan taɓa yin nadama ba koda kuwa zan rasa rayuwa ta. Kayi sani cewa daga yau na ɗaura ɗamarar yaƙi da duk wanda ke son rabani da kai. Idan har kana sona da gaskiya kaima ka ɗora taka ɗamarar. Na barka lafiya sai nazo ganin ka a karo na biyu." Laslaiya na gama faɗin haka ta juya ta fita ta bar Mozur a tsaye ƙiƙam kawai sai ya bita da kallo cikin tsananin damuwa zuciyarsa cike da fargaba. **************************** Sa'adda Zalisha da Laslaiya suka koma gida suna shiga cikin turakar Laslaiya suka tsaya cak a razane sakamakon ganin sarki Amzadu zaune a bisa gado ya ɗora ƙafarsa ɗaya akan ɗaya fuskarsa a murtuke babu alamar annuri. Zalisha da Laslaiya suka yi ƙerere ido ya raina fata. Sarki Amzadu ya dubi Zalisha yace, "Amma dai kin bani kunya. Ban taɓa zaton cewa tunani da hankalin uwa zai zo ɗaya dana 'ya ba. Ya kamata ace kin fita basira da hango abin da ita ba zata iya hangowa ba. Ya za'a yi ace a matsayina na sarki mai daraja da ɗaukaka 'ya ta tace tana son bawa. Bawan ma baƙo,kuma maƙasƙanci mai aikin niƙan abincin mu. Haba!! Haba 'yata ki tuna cewa 'ya'yan sarakai kyawawa sun zo sun biɗi auren ki,amma duk kin ƙi su. Saboda son da nake miki ne na ƙyale ki da zaɓin zuciyarki kuma yanzu saiki rasa wanda zaki zaɓa sai maƙasƙancin bawa. Na rantse da darajar abin bauta babbar wuta saina datse wannan soyayya dake tsakaninki da bawa Mozur ta kowanne hali." Koda sarki Amzadu yazo nan a zancen sa sai gimbiya Laslaiya ta fashe da kuka. Ita kuwa Zalisha sai ta matsa gabansa cikin ɓacin rai ta dube shi tace, "Ya kai mijina yanzu kenan ka zaɓi kare martabar Mulkin ka fiye da farin cikin 'yarka guda ɗaya kacal a duniya?" Cikin fushi Amzadu ya miƙe tsaye yace, "Ƙwarai kuwa,daga yau ku sani cewa ina kishin daraja da darajar mulkina fiye da yadda nake kishin ku." Yana gama faɗin haka ya nufi ƙofar fita daga ɗakin. Har yasa ƙafarsa ɗaya waje sai ya waigo ya dubi Laslaiya yace, "Zan sa kyawawan matakan tsaro akan ki don kada kije inda Mozur yake idan kuwa kika matsa har kuka sadu saina kashe shi." Amzadu ya juya ya fice daga ɗakin. Yana fita Laslaiya ta ruga ga Zalisha ta rungume ta tana kuka,ita kuma ta shiga rarrashin ta. A wannan rana dai yadda Laslaiya taga rana haka taga dare, domin kwana tayi tana kuka. Sai da ya zamana kullum bata da aikin yi face zama da tunanin jarumi Mozur. Abinci kuwa sai Zalisha tayi matuƙar takura mata sannan take cin ƙanƙani. Koda ta sami kwana bakwai a cikin wannan hali sai ta rame ta fita hayyacin ta. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Zalisha kenan ta kirawo sarki Amzadu don yaga halin da Laslaiya ta shiga. Yayin da sarki Amzadu yaga yadda Laslaiya ta zamo wato a rame,kuma a firgice. Sai ya ƙyaƙyale da dariya. Sannan ya dubi Laslaiya yace, "Yake 'yata kiyi sani cewa ko zaki zamo ƙwarangol ba zan amince kiyi soyayya da bawa Mozur ba bare har kuyi aure." Sa'adda Laslaiya taji wannan batu sai tayi murmushi tace, "Ya kai Abba na kayi sani cewa bana fatan ka tausaya mini bisa duk irin halin da zan shiga,amma ina da burin ka sanya ni cikin kabarina da hannun ka idan ciwon son Mozur ya zamo ajali na." Koda jin wannan batu sai sarki Amzadu yayi shiru ya kasa cewa komai. Cikin sanyin jiki ya nufi ƙofar fita daga ɗakin. Zalisha ta ruga da gudu ta sha gabansa tana mai fashewa da kuka tace, "Ya kai mijina kayi tunani mai kyau bisa wannan al'amari. Ya kamata ka hanzarta ceto rayuwar wannan 'ya tamu guda ɗaya kacal a duniya tun gabanin lokacin nadama bai zo ba." Maimakon sarki Amzadu yace wani abu sai ya hankaɗe Zalisha ta faɗi ƙasa. Nan yasa ƙafa ya shallake ta ya tafi abinsa. Zalisha da Laslaiya suka ƙara fashewa da kuka a tare lokaci ɗaya. Daga wannan rana al'amura suka ƙara dagulewa har ta kai cewa Laslaiya ta kwanta cuta aka yi ta magani amma a banza. Shi kuwa sarki Amzadu wannan al'amari na ta nuƙurƙusar zuciyarsa amma ya rasa hanyar da zaibi ya magance matsalar domin ko zai mutu ba zai iya bari Laslaiya ta auri bawa Mozur ba. Al'amarin jarumi Mozur kuwa shima duk ya rame ya ƙara baƙi,kuma ya tara gashi a fuskar sa saboda baƙin cikin rashin ganin Laslaiya da kuma yawan tunanin ta. A koda yaushe a cikin tunaninta yake dare da rana koda kuwa yana kan aiki ne. Sau tari sai ayi tayi masa magana amma baya jin mai maganar face an taɓa jikinsa saboda tsananin tunani. Duk wanda ya dubi jarumi Mozur a wannan lokaci dole ne yaji tausayinsa. Babu abinda yake ƙara ɗaga masa hankali face jin labarin irin halin da gimbiya Laslaiya ke ciki na rashin lafiya duk saboda shi. Ba wani ne ke kawo masa wannan labari ba face Zalisha da kanta. Bisa wannan dalili ne Mozur ya fara tunanin hanyar da zaibi ya gudu daga cikin wannan gida inda aka tsare shi,amma sai yaga cewa babu dama domin akwai cikakken tsaro. Babu yadda za'a yi ya wuce ta ƙofofin nan guda goma sha biyu waɗanda ke ɗauke da zaratan dakaru sha bibbiyu dukkanin su na riƙe da muggan makamai. Haka dai Mozur ya cigaba da zama a cikin ƙunci har ya rage saura kwana goma ranar gasar kokawa ta kewayo. Koda sarki ya fuskanci kusantowar ranar sai ya kira Azmandu yace da shi, "Ya kai sarkin gida kayi sani cewa ba zan hana wannan taro ba na gasar kokawa kuma bazan hana ka zuwa da bawa Mozur ba, domin idan nayi hakan duniya zata zage ni bisa abinda aka saba yi na al'ada a ƙasa ta. Na yarda ka fito da Mozur ranar wannan gasa,amma sai na zuba masa dakaru dubu arba'in masu tsaronsa don kada ya gudu. Kuma a ɗaure za'a zo da shi cikin sarƙoƙi a hannayen sa da ƙafafuwan sa da kuma wuyansa. Ba za'a kwance shi ba face zai kafsa da abokin gwaminsa. Yana gama kafsawar sai a ɗaure shi. MU HADU A PART G DON JIN CIGABAN WANNAN HIKAYAR TA MOZUR✍️✍️😁😁👌**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU ✍️✍️ PART G ❤❤💯 NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🧝‍♀️🧝‍♀️ TYPING AHMAD MUNNIR.. POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 🥰🙏 Marubucin ya CI GABA DA CEWA.. Kuma a ɗaure za'a zo da shi cikin sarƙoƙi a hannayen sa da ƙafafuwan sa da kuma wuyansa. Ba za'a kwance shi ba face zai kafsa da abokin gwaminsa. Yana gama kafsawar sai a ɗaure shi. Ba za'a gushe ana yin hakan ba har sai an kammala wannan gasa. Ka sani cewa wannan karon gimbiya bata da lafiya tana kwance,don haka nine zan wakilce ta wajen bayar da kyauta ga wanda yaci gasar." Koda sarki Amzadu yazo nan a zancen sa sai Azmandu ya sunkui da kansa a ƙas yace, "Ya shugabana kayi sani cewa duk yadda kake son a tsara wannan al'amari haka za'a yi." Sarki Amzadu ya bushe da dariya harda doka ƙafa. Sannan ya kira sarkin yaƙinsa sadauki Akurga yace da shi, "Na umarce ka daka shirya dakaru dubu arba'in waɗanda za suyi wa Mozur rakiya daga cikin gidan nuƙan abinci zuwa filin gasa don kada ya sami ƙofar guduwa." Akurga ya rusuna yace, "An gama ya mai duniya." Nan take sarki Amzadu ya miƙe ya shiga gida,fada ta watse kowa ya kama gabansa. Da ranar gasa tazo sai filin fada ya cika maƙil da jama'a ko'ina ka duba kawunan mutane ne birjik ba adadi. Wannan karon dai jaruman kokawar basu da yawa,ba sufi su ashirin ba kuma akwai jarumi Zarto a cikin su. Ga wanda baisan Zarto ba in ya ganshi a wannan lokaci ba zai gane shi ba saboda ya ƙara girma fiye da wancan karo da aka yi gasar har jarumi Mozur ya cinye shi. Akwai alamun cewa wannan karon Zarto ya dawo da cikakken shirin,don ya karɓi kambun gasar daga hannun Mozur. Har sarki Amzadu ya fito daga cikin gida ya zauna akan karaga don kallon wannan gasa ba'a kawo jarumi Mozur ba. Wannan tasa jikin mutane yayi sanyi ya zamana ba'a wata hayaniya a filin gasar da kambama jarumai domin kowa so yake kawai yaga hallarar jarumi Mozur musamman masu goyon bayan jarumi Zarto saboda sun ci burin cewa wannan karon suke da nasara. Har an kirawo jaruman farko sun hau tudun faɗan za su fara kafsawa sai aka hango dakaru dubu arba'in sun sako jarumi Mozur a tsakiya yana tafe yana jan sarƙa wacce ta ɗaure hannayen sa da ƙafafuwan sa kuma ta zarge wuyansa. Duk da cewar fuskar Mozur ta cika da gashi kuma ya rame sai da masoyansa suka shaida shi. Nan da nan filin ya kaure da shewa aka rinƙa ambaton sunansa ana cewa, "Mozur! Mozur!! Mozur!!!" Sautin wannan kiran suna ne yabi iska ya riski dodon kunnen gimbiya Laslaiya wacce ke kwance akan gado magashiyan tana jinya a cikin gidan sarautar. Rabonta da miqewa zaune kwana ashirin da bakwai kenan. Koda taji ambaton wannan suna na masoyinta sai ta miƙe zumbur ta fara waige-waige domin a tsammanin ta yana kusa ne. Laslaiya ta dubi gabas da yamma,kudu da arewa ba taga kowa ba a cikin ɗakin data ke wannan jinya ba face wata baiwa guda ɗaya wadda ke kula da ita. Ita ma kuma ta kishingiɗa a jikin bango barci ya kwashe ta,wataƙila saboda gajiyar aiki ne. Gaba ɗaya gidan sarautar yayi shiru kamar babu mutane. Sautin nan na kiran sunan Mozur ya cigaba da yawo a kunnen Laslaiya. Nan take ta tuno cewar ai yau ne ranar zagayowar gasar jarumai. Kawai sai Laslaiya ta ruga da gudu ta nufi hanyar fita daga cikin gidan sarautar. A wannan lokaci wata doguwar farar rigace kawai a jikin ta mai shara-shara wadda ke nuna duk ilahirin surar jikinta babu takalmi a ƙafarta kuma babu wani ado a tare da ita. Tana gudu gashin kanta na tarwatsewa a cikin iska. Haka dai tayi ta gudun tana wuce tsirarun bayi da dakarun gidan masu hidima, kuma duk suka kasa ganewa cewa gimbiya Laslaiya ce a cikin wannan hali, saboda an san cewa ita kwance take cikin matsananciyar rashin lafiya. A can filin gasa kuwa koda sarki yaga an zo da jarumi Mozur sai yace a janye kafsawar waɗannan jarumai na farko da suka hau kan tudu don buɗe taron a fara da karon jarumi Zarto da jarumi Mozur. Koda jin haka sai jama'a suka sake ruɗewa da ihu da shewa domin dama kowa ya ɗagu saboda yaga yadda za'a yi wannan mugun karo ya zo. Ba tare da ɓata lokaci ba aka kwance jarumi Mozur daga cikin sarƙa aka rako shi har bakin wannan gini mai tudu na gasa. Mozur ya taka matattakala ya hau kan tudun. Sannan jarumi Zarto ya hawo suka fuskanci juna aka fara kallan-kallo. Nan da jama'a suka ƙara kaurewa da shewa. Ko shakka babu ya karaya da wannan karo da zai yi da jarumi Zarto domin yasan cewa akwai yunwa a jikin sa da kuma ƙarancin lafiya. Sai dai duk da haka masoyansa na ɗan ƙara masa ƙwarin gwiwa, saboda ganin yadda suke masa jinjina. Ba tare da ɓata wani lokaci ba aka buga gangar fara gasa. Yin hakan ke da wuya Zarto ya juya ya dubi sarki Amzadu yayi sujjada a gare shi yana mai kwasar gaisuwa. Sarki Amzadu ya duƙar da kansa ƙasa kaɗan alamar ya karɓi gaisuwar. Sannan ya nuna masa inkiyar ya kashe jarumi Mozur murus har lahira ta hanyar nuna kaifin hannu a wuya. Zarto ya jinjina kai gami da murmushi alamar cewa ya fahimci buƙatar sarki. Cikin zafin nama ya ruga ga Mozur. Kafin Mozur yayi wani yunƙuri tuni Zarto ya matse shi da hannu biyu a gadon bayansa. Mozur ya fara ihu saboda tsananin zafi da zugi tamkar ƙasusuwan bayansa zasu kakkarye. Nan fa Mozur ya cigaba da ƙoƙarin ya cire hannayen Zarto daga ruƙon da yayi masa amma ya kasa. Mozur ya yiwa Zarto karo da ka a fuska har sau huɗu,amma a banza,baiji komai ba bare ya sake shi. Nan fa Mozur ya cigaba da rusa ihu saboda azabar da yake ji a bayansa. Shi kuwa Zarto sai ƙara taƙarƙarewa iya ƙarfin sa kuma yana bushewa da dariya. Saida kusan rabin sa'a ta shuɗe a haka Mozur bai fasa ihu ba shi kuma Zarto yaƙi ya sake shi. A wannan rana dai Mozur yaci baƙar wahala tamkar zai mutu. Da ƙyar ya samu ya ware 'yan yatsun hannunsa ya luma su cikin ƙwayar idanun Zarto. Zarto yayi ihu ya saki Mozur saboda raɗaɗin da yaji a cikin idanun nasa. Mozur ya tafi taga taga zai faɗi amma sai ya daure ya tsaya da ƙafafunsa. Koda ganin haka sai masoyansa suka kaure da shewa aka hau yi masa tafi. A lokacin ne Zarto ya dawo cikin hayyacinsa idanunsa suka buɗe. Cikin tsananin fusata da shammata ya sake rugawa ya shaƙo wuyan Mozur shaƙa bata wasa ba. Nan take idanun Mozur suka zazzaro kamar zasu faɗo ƙasa ya fara wutsil-wutsil da ƙafafuwan sa da kuma hannayen sa. Tun yana motsa su da ƙarfi ya fara ɗaga su da ƙyar wata irin kumfar wuya da majinar wahala suka fara dalala. Nan take gana ɗaya jikin masoyan jarumi Mozur yayi sanyi,wasu ma suka fara kuka don gani suke tabbas mutuwa zai yi. ************** Sarki Amzadu kuwa banda ƙyaƙyata dariya babu abinda yake yi. A daidai wannan lokaci ne gimbiya Laslaiya ta iso filin gasar cikin matsiyacin gudu. Koda tayi arba da jarumi Mozur a hannun Zarto taga halin da ya shiga sai ta kwarara ihu tana mai kiran sunan Mozur. Cikin shiɗewa Mozur ya jiyo wannan kira kuma ya shaida muryar mai kiran. Ba zato ba tsammani,sai aka ji Mozur ya kwarara uban ihu shima yana mai kiran sunan Laslaiya. Nan take ya ɓanɓare hannayen jarumi Zarto daga wuyansa da ƙarfin tsiya. Sannan ya ɗaga shi sama ya dinga wulwula shi kamar yana wasa da majajjawa. Lokaci guda kuma ya damfara shi da ƙasa. Bisa tsautsayi sai Zarto ya cake da ka. Take wuyansa ya karye ya mutu,ko shurawa bai yi ba. Faruwar hakan ke da wuya gimbiya Laslaiya ta ruga da gudu ta hau kan matattakala ta isa kan tudun da Mozur ke tsaye. Da zuwa ta faɗa kan ƙirjinsa suka rungume juna cikin tsananin farin ciki. Sarki Amzadu ya miƙe zumbur a fusace yana mai bawa dakaru umarnin su hallaka jarumi Mozur. Kafin dakarun suyi wani yunƙuri sai aka hango ƙura ta turnuƙe gabas. Nan fa kallo ya koma gabas ɗin kowa ya tsaya ƙyam. Kawai sai aka ga ashe wasu dubunnan mayaƙa ne a sukwane bisa dawakai suka kawo farmakin sumame. Nan fa gari ya ruɗe,waje ya hargitse akayi ta gujeguje da iface-iface. Shi kansa sarki Amzadu da rarrafe ya samu ya ruga ya kama doki ya hau. Sannan ya sukwani dokin a guje izuwa cikin gidan sarautar baima kula da batun 'yarsa ba, gimbiya Laslaiya. Su kuwa dakarun nan guda dubu arba'in waɗanda aka sasu tsaron jarumi Mozur sai suka riga suka tari waɗannan baƙin mayaƙan sumame aka fara kafsa yaƙi. Koda jarumi Mozur yaga yadda waje ya hargitse sai ya ɗauki gimbiya a hannunsa ya ruga da ita zuwa inda wani farin doki ke ɗaure. Koda ya iske dokin sai ya ɗora gimbiya akai. Sannan shima yayi tsalle ya haye kan dokin ya fincike igiyar aka. Sannan shima yayi tsalle ya haye kan dokin ya fincike igiyar da ta ɗaure ƙafar dokin da ƙarfin tsiya har turken da aka ɗaure igiyar a jiki ya tumɓuko daga cikin ƙasa. Mozur ya zunguri dokin da ƙafafunsa ya sukwane shi a guje. Maimakon subi hanyar cikin gari sai suka kewaye ta bayan dakarun dake gabza yaƙi da mayaƙan sumame suka nausa cikin daji suka yi ta gudu ba ƙaƙƙautawa. Al'amarin sarki Amzadu kuwa lokacin da suka isa fada shi da fadawansa cikin gudu sai suka tsaya aka fara shirye-shiryen yaƙi,don akwai waɗancan dakaru dubu arba'in na ɗaukin gaggawa, domin kuwa mayaƙan sumamen na da matuƙar yawa fiye da ƙima. Nan da nan aka shirya dakaru masu yawa aka yi hawa har da shi kansa sarki Amzadu inda ya bayar da umarnin cewa lallai a nemo jarumi Mozur da gimbiya Laslaiya a duk inda suke kuma a ƙarar da waɗannan abokan gaba da suka kawo farmakin sumame. Nan take sarkin yaƙi ya jagoranci dubunnan ɗaruruwan mayaƙan garin suka sukwani dawakai cikin matsanancin gudu suka nufi ƙofar filin fada inda ake yaƙi. Idan mutum yaga wannan zuga a wannan lokaci sai yayi zaton mayaƙan duniya ne kaf suka fito yaƙi. Ƙarar kofaton dawakai ma kaɗai ya isa ya firgita mutum bare kuma ihun mayaƙan da kuma ƙarajin su wanda ya cika garin gaba ɗaya ya firgita ƙananan yara da mata suka kama koke-koke. Tsofaffi kuwa suka tsure da gudawa.😅😅 Lokacin da mayaƙan kawo ɗauki suka iso filin yaƙin sai suka iske an yiwa 'yan uwansu lugude an karkashe su saura ƙalilan. Nan fa aka sake kaurewa da sabon yaƙi. Karafkiyar ƙarafa ta yawaita. Jini ya ringa fallatsa yana malala a ƙas. Nan fa kasuwar ɗaukar rayuka ta kama ci. Masu ƙarfi da jarumta suka rinƙa ciniki ba sassautawa. Jarumi Mozur da gimbiya Laslaiya kuwa saida suka kwana suka yini suna tafiya akan dokin nan tana kwance akan ƙirjinsa basu tsaya ba saboda gudun kada a biyo bayansu a cim masu. Saida suka iso wani ƙaramin gari dake cikin nahiyar ƙasar. Sannan suka tsaya gaban wata rijiya suka sauka. Anan ne suka sha ruwa,suka zauna suna kallon juna. Koda suka ga yadda kowannensu ya rame sakamakon ƙuncin rashin ganin juna sai suka fashe da kuka. Gimbiya Laslaiya ta rungume Mozur tace, "Ya kai masoyi na haƙiƙa na san mun shiga cikin mugun ƙunci da azabar cutar bege. Amma yanzu ina jin farin ciki tamkar ban taɓa shiga damuwa ba, saboda kasancewa tare da kai a yanzu. Lallai kuwa ba zan sake yarda wani abu ya raba mu ba face mutuwa." Jarumi Mozur ya janye jikinsa daga cikin nata suka fuskanci juna. Sannan yace, "Ya ke abar begena dare da rana kiyi sani cewa zuciya ta da raina sun kori komai daga cikin su. Ba za su bar abin da ya kai ƙwayar zarra ba face ke. Ina tabbatar miki da cewa ji da gani na , tafiya da kwanciya ta begenki ne ke musu jagora dare da rana. Nayi miki alƙawari daga yau ko ruwa ko iska ko wuta ko guguwa,komai yawan bala'i da masifa ba zan yarda mu rabu ba face babu ruhin numfashi a cikin gangar jikina." Koda jin wannan batu sai farin ciki da daɗi suka lulluɓe gimbiya Laslaiya ta sake rungume Mozur. *** Koda sarki Muhucul yazo nan a labarin sa sai yayi shiru ya dubi su Ruziyal yace, "To lokaci yayi halinsa,anan zan dakata sai gobe kuma idan muna raye ku dawo na cigaba da wannan labari." Yana gama faɗin haka ya miƙe ya shiga gida,fada ta watse kowa ya kama gabansa aka bar su Ruziyal a zaune cikin matuƙar damuwar rashin jin ƙarshen wannan labari. ******* Al'amarin su aljani Markahus sabus kuwa bayan sun sami nasarar ɗebo narkakken dutse daga cikin dutsen da yafi kowane dutse girma,sai aljani Durmazalu ya cigaba da tafiya da su a cikin sararin samaniya. Sai da suka yi tafiyar sa'a bakwai cif. Sannan suka sauko ƙasa suka dira akan wani ƙaramin tsuburi. Saukar su ke da wuya aljani Durmazalu yayi gyaran murya yace, "Ya ku abokan tafiya ina kira a gare ku da kowa ya shirya, domin yanzu ne zamu yi tafiya mai haɗarin gaske fiye da wadda kuka gani a baya. Kuyi sani cewa yanzu ne zamu shiga cikin ƙarƙashin ƙasa don mu isa duniyar ƙarshe mu ɗebo dutsen wuta. Ina sanar da ku cewa ita dai wannan duniya ta ƙarshe itace ta bakwai kuma kafin mu risketa sai mun ratsa ta cikin duniyoyi shida a cikin kowacce duniya akwai irin halittun da ke cikin ta,kuma duk sun kasance masu ƙarfin mulki da ƙarfin sihiri. Bai zamo lallai ba mu wuce ta cikin waɗannan duniyoyi shida lafiya. Babu mamaki wasun mu su hallaka ko kuma mu duka mu halaka. Saboda bala'in dake tattare da waɗannan halittu na duniyoyin ƙassai. Ina mai shawartar mu damu jajirce,musa a ranmu cewa muna tare da nasara in kuwa zuciyoyinmu suka karaya ba zamu taɓa samun dacewa ba." Koda aljani Durmazalu yazo nan a zancen sa sai markahus sabus,boka jinshan,durfus,boka sulbaini da yarinyar nan ta birnin duwatsu wato salusa suka yi tsuru-tsuru da idanu,tsoro ya baibaye su kuma hankalin su ya dugunzuma don basu san irin bala'in da zasu riska ba a cikin duniyoyin ƙassai. Ba tare da ɓata lokaci ba Durmazalu ya nutse cikin ƙarƙashin ƙasa ɗauke da su markahus sabus,yayi ta tafiya. Saida suka yi tafiyar kwana uku. Sannan suka iso duniya ta ɗaya wadda ake kira Madinatul Aslik. Koda bayyanar su a cikin wannan duniya sai duk suka zama ƙauyawa suka kama kalle-kalle suna masu mamakin irin gine-ginen birnin da suka tsinci kansu a ciki da kuma irin halittun dake rayuwa a cikin sa. Shi dai wannan birni na Madinatul Aslik an gina gidaje a cikin sa da zallan darma. Ko ina ka duba a garin babu ƙasa saidai ka taka shimfiɗaɗɗiyar darma mai kama da tabarma, domin za'a iya naɗeta. Babu wani wuri wanda za'a iya yin shuka bare tsuro ya fito. Su kuwa halittun sun kasance 'yan wadanni dugul-dugul babu wanda tsawonsa ya wuce kamu ɗaya,kuma sun kasance'yan ƙanana sirara,shafal-shafal basu da nauyi. Babu abin mamaki face yadda suke iya ɗaukan gunguma-gunguman ƙarafa. Wani ƙarfen ma ko markahus sabus bai isa ya iya raba shi da ƙasa ba,bare su boka jinshan 'yan ƙananan alhaki. Fuskokin waɗannan halittu irin na mutane ne haka ma hannayen su da ƙafafuwan su,amma kuma wani irin dogon baki ne da su,wanda daga ƙarshen sa yayi doro da tsini,kamar bakin aku,kuma ƙwari ne da shi kamar ƙarfe,duk abinda suka caka da shi take abin zai huje ya burma koda kuwa dutse ne. Gaba ɗaya ƙarfin waɗannan halittu a jikin bakin na su yake, domin ƙarafan ma da suke ɗauka masu nauyi da bakin na su suke ɗauka. Basu da abin hawa kamar dawakai,ko jakai,amma suna yawo ne akan wasu irin manyan jemagu masu siffar ban tsoro. Koda ganin dirar aljani Durmazalu a cikin wannan birni ɗauke dasu markahus sabus sai mutanen garin suka tsaya cak suka daina komai suka zuba musu na mujiya. Su kuwa sai suka cigaba da tafiya bisa ƙafafunsu. Su shiga nan su fita can. Su dai ba su yiwa kowa magana ba, kuma babu wanda yayi musu magana. Duk ta inda suka ratsa sai a tsai da harkoki ayi ta kallon su. Haƙiƙa su markahus sabus sun ga abubuwan al'ajabi a cikin wannan duniya fiye da sauran abubuwan da suka gani a baya tun farkon shigowar su cikin wannan aiki na nemo abubuwa uku don ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL. Babu abinda yafi basu mamaki face wata siririyar kwalba wacce mutanen wannan birni suka ajiye ta a tsakiyar birnin. Saboda tsananin tsawon kwalbar sai kaga kamar zata tokare da hadarin sama. Idan kuwa mutum yace saiya kewaye kwalbar to tabbas sai ya kwana arba'in yana zagaya ta bai dawo kan inda ya fara ba. Ita dai wannan kwalba a cike take da ruwa,kuma anyi wani famfo a jikin ta wanda ke zubar da ruwa. Kowa saika ga yazo ya tari ruwan yayi gaba don amfanin kansa. A lokaci guda sai mutum dubu su zo su ɗiba suyi gaba,amma ruwan baya ƙarewa duk da cewar girman kwalbar baikai na mutum ɗaya ba,kawai dai tsawo gareta. Markahus sabus ya dubi kwalbar da kyau yace, "Jau wanda bai yawo ba a duniya bai more kallo ba. Kun ga inda labari aka bamu aka ce akwai wannan kwalbar ba zamu yarda ba,amma tunda da idanun mu muka gani dole mu gasgata." Kafin wani daga cikin su boka jinshan yace wani abu sai suka ga anyi musu ƙwawanya. Wasu mutanen garin ne cikin shigar mayaƙa kimanin su dubu bisa jemagun nan. Ko sillan kara babu a hannunsu,amma kuma bakunan su sun fi na sauran mutanen garin tsawo da faɗi. Kafin su aljani Durmazalu suyi wani yunƙuri tuni an cafkosu da bakuna ɗaiɗai an ɗora su akan jemagun an cilla da su da gudu a cikin sararin samaniya ba tare da ɗayansu ya iya ƙoƙarin gudu ba. ******************** Aljani Durmazalu ya dubi girman halittar jikinsa mai ɗauke da fukafukai miliyan ɗaya yaga cewa girman sa bai amfane shi da komai ba,tunda ga ƙananan halittu sun kama shi tamau a hannu ya kasa motsi. Kawai sai ya fashe da kukan takaici. Markahus sabus ya dube shi ya ƙyaƙyale da dariya yace, "Yau fa ake yinta ga zaki a hannun kyanwa,harma kyanwar ta sashi kuka. Ashe dai ba girma ne ƙarfi ba. Daga yau kuma babu batun kuri ko cika baki, domin baba ma da babansa."😅😅😅 Durmazalu ya dubi markahus sabus ya daka masa harara. Sannan yace, "To ƙaramin mara kunya ai dama ni banyi kuri ba tunda farko, domin saida na gaya maku cewa komai zai iya faruwa ga dukkanin mu ban ware kaina ba nayi kuri." Haka dai aka cigaba da tafiya da su har izuwa wani lokaci mai tsawo. Sannan aka iso wani babban gida wanda babu mai girmansa a duk faɗin birnin. Gidan ya kasance an gina shine da farar darma. Duk iya yawon markahus sabus a duniya bai taɓa ganin gida mai girman wannan ba. Koda aka shigar da su cikin gidan kuwa sai gashi ana ratsawa da su ta cikin waɗansu ƙayatattun fadoji na alfarma. Mu HADU a part H DON JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LITTAFIN NAJIBULLAH MUHAMMAD🥰**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU 🤝😍 PART H 😊 NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 😎 TYPING AHMAD MUNNIR🤝 POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 💪 Note: kuyi hakuri akan rashin isasshen posting akan lokaci. Kuyi sani cewa hakan ya faru ne sakamakon yanayin rayuwar da ya, Wanda ku kanku kunsan halin da ake ciki. Don haka ku rinka yi mana uzuri. A koyaushe muna fatan Allah ya taimakemu tare da fatan Allah ya tattara mu a cikin gidan Aljannar Firdausi Nuzila🤝😍🩷🙏 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Duk iya yawon markahus sabus a duniya bai taɓa ganin gida mai girman wannan ba. Koda aka shigar da su cikin gidan kuwa sai gashi ana ratsawa da su ta cikin waɗansu ƙayatattun fadoji na alfarma. Kowace fada guda ɗaya ta ninka fadar nan ta Baharzus sau uku a girma,kyau da ƙayatuwa. Saida aka wuce fadoji shida sannan aka tsaya da su a ta bakwai. Ita dai wannan fada ta bakwai ta kasance uwa ga sauran fadoji shida na baya,kuma duk abinda ke cikin ta fari ne sol babu baƙi ko wata kalar dabam. Abubuwan al'ajabi kuwa gasunan birjik ba adadi, domin anan ne suka ga kifaye na yawo a fili ba a cikin ruwa ba,haka kuma suka ga mutum mai rabin jikin zaki. Wato kansa da hannayen sa ne na mutum,amma daga cibiyar sa zuwa gangar jikinsa da ƙafafuwan sa duk na zaki ne,haka ma ƙirjinsa irin na zaki ne wanda ke cike da gashi. Wannan mutum na kishingiɗe bisa wata doguwar kujera ta alfarma ya riƙe wani babban tambulan cike da ruwan inibi yana sha,kuma yana karkaɗa jelarsa alamar yana jin daɗin ɗanɗanon ruwan inibin a bakinsa. Koda aka shigo dasu markahus sabus cikin wannan ƙasaitacciyar fada sai mutumin nan mai rabin jikin zaki ya washe fuskar sa da murmushi ya ajiye tambulan ɗin ruwan inibin akan ƙaramin tebur dake gabansa. Sannan ya dubi su markahus sabus yace, "Lale marhaban,ina mai yi muku barka da zuwa birnin Madinatul Aslik yaku hadiman boka Shamharu." Cikin tsananin mamaki su markahus sabus suka dubi juna. Sannan suka maida hankalinsu ga mutumin suka yi shiru. Caraf sai markahus sabus yace, "Ya kai wannan sarki mai karamci,ya akai ka san da zuwan mu nan kuma yanzu me kake nufin aiwatarwa da mu har da kasa aka kamo mu aka gurfanar damu a gabanka?" Koda jin wannan tambaya sai mutumin ya bushe da dariya. Sannan yace, "Ya kai markahul sabus kayi sani cewa ni sunana Sarudul Makam kuma nine sarkin wannan duniya ta Madinatul Aslik. Babu wani sarki a cikin duniyar sama ko ta ƙasa ko ta tsakiya wanda bansan da zamansa ba,kuma bansan da shirin sa ba,ko burin rayuwar sa. Kuyi sani cewa duk abinda ya faru gareku naji kuma na gani a cikin madubin tsafina. Yanzu haka kun fito ne daga birnin duwatsu inda kuka samo narkakken dutsen da yafi kowane dutse girma a duniyar ku. Yanzu kuma kuna son ku wuce izuwa duniyar ƙarshe ta nan ƙasan bakwai,don ku ɗebo dutsen wuta. Idan kuka sami nasara ne zaku je ku ɗebo rabin ruwan tekun duniyar ku. Sannan ku kaiwa Shamharu waɗannan abubuwa uku,don ya ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da ita ne zai buɗe fadar Saukatul Askur ta sarki Azmul gallar,don ya ɗauko kundin tsatsubansa ya karance shi saboda ya sami sirrikan tsafinsa. Ko ba haka bane?" Markahus sabus yace, "Zancen ka dutse ne." Sarudul Makam ya sake bushewa da dariya yace, "Kuyi sani cewa gaba ɗaya duniyoyin nan guda bakwai dake nan ƙarƙashin ƙasa na ƙarƙashin ikon mahaifiyata,kuma duk 'yan uwana ne ke mulki a sauran duniyoyi shida. Rana guda aka haife mu mu bakwai,amma nine na fara fitowa daga cikin ta,sai kuma Saradul Hasal, Saradul Algaz, Saradul Hisnu, Saradul Badal da kuma Saradul Imzan,wanda shike sarautar duniyar ƙarshe. Ina mai sanar daku cewa gaba ɗayan mu mu bakwan nan bama ga maciji kuma kowa na ƙoƙarin kashe kowa. Ba komai ne ya haddasa haka ba face kishi akan mulki. A da can kafin mutuwar mahaifiyar mu duniyoyin bakwai a ƙarƙashin wannan duniyar tawa suke,kuma mahaifiyar mu ke mulkin ta. Amma da ta kwanta ciwon ajali sai ta raba mana duniyoyin ta baiwa kowa guda ya mulka,don gudun rigima a tsakanin mu. A halin yanzu kowa daga cikin mu so yake ya haɗe duniyoyin bakwai ya mulka shi kaɗai. Kun ga kenan dabarar da tayi ba tayi amfani ba tunda dai rigima ta karƙe a tsakanin mu. Nayi bincike na gano cewa sai nayi wani aiki sannan zan iya mallakar waɗannan duniyoyi shida kuma aikin ba zai yiwu ba saida taimakon halittu irin ku. Don haka ni yanzu zuwan ku nan rahama ce a gare ni,don tamkar cikar buri na ne. Lallai bazan bari ku gusa daga nan ba face kun bani haɗin kai nayi wannan aiki tare da ku." Koda sarki Sarudul Makam yazo nan a zancen sa sai markahus sabus yayi ajiyar numfashi yace, "Ya kai wannan sarki ina son na nemi wata alfarma guda ɗaya a wajen ka kafin ka sanar damu wannan aiki da zamu tayaka." Sarudul Makam yace, "Faɗi abin da kake buƙata." Markahus sabus yayi gyaran murya sannan yace, "Ya kai wannan sarki kayi sani cewa a duniya babu abinda nake so kuma nake matuƙar son gani face gimbiya Sima. Ina son ka sanar dani halin data shiga,tun daga lokacin dana rabu da ita. Tunda kace ka san duk abinda ke faruwa a ko'ina a cikin kowacce duniya." Koda jin haka sai sarki Sarudul Makam ya ƙyalƙyale da dariya sannan yace, "Ai wannan aiki ne mai sauƙin gaske,kuma ina yima albishir da cewa bama gaya maka zanyi ba. Zan nuna maka al'amarin ne a zahiri yanzu take kaga duk abinda ya faru gareta." Nan take Sarudul Makam ya shafi wani jan allon tsafi,saiga hoton abubuwan da suka faru ga gimbiya Sima na zayyana daki-daki tun daga lokacin da markahus sabus ya tafi da ita gida wajen mahaifiyarsa Samaratu kawo izuwa lokacin da aka yi gagarumin yaƙin nan nasu aljani Abtarul Hudeis da su sarki Lu'umanu sa'adda Hubairu da gimbiya Sima za suje garin nan inda gidan kayan tarihi suke har kuma izuwa lokacin da aka ɗaura auren gimbiya Sima da jarumi Hubairu a birnin Laharim aka kafa tutar musulunci a garin. Koda markahus sabus ya gama ganin waɗannan abubuwa,sai idanunsa suka ciko da ƙwalla ya fara zubar da hawaye,don yasan cewa shike nan ya rasa gimbiya Sima har abada. Nan dai markahus sabus ya shiga tunani a zuciyarsa yana mai cewa yanzu mene ne amfanin rayuwar sa tunda dai duk gwagwarmayar da yake yi akan gimbiya Sima ne,kuma gashi ya rasa ta. Markahul sabus ya tuno da wahalar da yasha a hannun sarki Lu'umanu kuma ya tuno da gwagwarmayar da yayi da dodo kiryanu sa'adda yaje ɗebo tsumi. Haka kuma ya tuno da yadda rayuwar sa ta kasance a hannun matsafan duniya sai yawo ake da shi a kaishi can a wulla shi can ba shi da wani iko nasa. Ya sake yin nazari akan hanyar da zaibi ya kuɓuta sai yaga ai a duniya babu waɗanda suka gagari matsafa face ma'abota addinin Musulunci, tunda yanzu ma gashi a zahiri yaga yadda su Abtarul Hudeis suka sami nasara akan su Lu'umanu. Nan take markahul sabus yaji zuciyarsa ta aminta da addinin musulunci, kuma yaji yana son shiga cikin addinin sai dai kash bai san yadda zai shiga cikin addinin ba. Sarki Sarudul Makam ya dakawa aljani Markahus sabus tsawa yace, "Tunanin me kake yi? Bani hankalin ka nan don kaji aikin da zamu yi yanzu. Wannan aiki ba komai bane face zamu tafi tare daku izuwa waɗannan duniyoyi guda shida dake ƙasan wannan, domin mu yaƙe su ɗaya bayan ɗaya,mu kashe na kashewa mu kama na kamawa,har dasu 'yan uwan nawa kuwa. Sannan ku shiga cikin baitul malinsu ku ɗauko mini wasu ƙahonni na zinare guda shida. Ma'ana a cikin kowacce baitul mali akwai ƙahon zinare guda. Idan aka haɗa jimila ne zai zama shida,idan na mallaki waɗannan ƙahonni guda shida zan soka sune anan cikin tsakiyar duniya ta. Sai na yi hakan ne zan iya mulkar waɗannan duniyoyi guda shida. Kuyi sani cewa waɗannan ƙahonni guda shida 'yan ƙanana ne mitsi-mitsi,amma mu ba zamu iya taɓa su ba da hannuwan mu. In kuwa muka taɓa su take zamu narke mu zagwanye. Ba komai bane ya haddasa hakan ba face cewar mu a jikin mu babu jini face ƙashi da tsoka zalla. Kuma dole sai mai jini a jikine zai iya taɓa waɗannan ƙahonni." Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama su markahul sabus. Boka Jinshan ya dubi sarki Sarudul Makam yace, "Ya zaka ce babu jini a jikin ku?" Sarudul Makam yayi murmushi yace, "Ai dama nasan ba zaku amince ba,don haka yanzun nan zan nuna muku zahiri." Nan take Sarudul Makam ya ɗauko wata zureriyar wuƙa ya feraye hannun sa saiga ƙaton nama ya zaftaro yana lilo,amma ko ɗigon jini babu face ƙasusuwa da jijiyoyi ba kyan gani. Cikin sauri su markahul sabus suka kau da kansu ga barin kallon hannun. Sarudul Makam ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya kamo yankakkiyar tsokar dake reto a jikin hannunsa ya maida ita mazaunin sa. Take wajen ya haɗe kuma ya shafe kamar ba a taɓa yanka ba. Al'amarin daya ƙara baiwa su markahul sabus mamaki kenan. Boka sulbaini ya dubi Sarudul Makam yace, "Ya kai wannan sarki shin mutanen dake sauran duniyoyin ƙasa duk irin ku ne?" Sarudul Makam yace, "A'a ba irin mu bane. Kuyi sani cewa duk mutumin daku ka gani anan ɗana ne ko kuma 'yata. Ma'ana duk nine na haifi gaba ɗayan mutanen wannan duniyar tare da matata guda ɗaya. Kuma ga matar nan tawa a tsaye a gaban ku." Sarudul Makam yayi nuni izuwa ga wata wadar tsohuwa tukuf. Launin jikinta gaba ɗaya ja ne jajur. Kuma haka duk mutanen garin suke. Sarudul Makam ya cigaba da cewa, "Idan kuka je duniya ta biyu zaku iske cewa launin mutanen garin gaba ɗaya fari ne, saboda haka launin matar Sarudul Hasal take. Matar Sarudul Algaz shuɗiya ce,matar Sarudul Hisnu baƙa ce,matar Sarudul Badal koriya ce,matar Sarudul Imzan kuwa ruwan ɗorawa ce. A taƙaice dai kowacce jama'a yanayin mahaifiyar su ne." Salusa ta tsoma baki cikin wannan zance tace, "Ya kai wannan sarki na fahimci cewa makami baya tasiri a jikin ku,ta yaya zaka yaƙi sauran 'yan uwanka dake cikin duniyoyin shida?" Sarudul Makam yayi dariya yace, "Haƙiƙa babu wani ƙarfe da zai iya tasiri a jikin mu domin ko an daddatsa mu anyi gutsin gutsin da mu sai jikin mu ya haɗe ya manne,kamar yadda yake. Bari na baku misali ku gani." Nan take Sarudul Makam ya sake luma waƙunnan a cikin ramin idonsa guda ya ƙwaƙulo ƙwayar idon ya ajiye ta akan tebur. Kogon ramin idon yayi zururu babu kyan gani. Koda Sarudul Makam ya durƙuso da fuskarsa ƙasa daf da kan tebur ɗin sai ƙwayar idon nasa tayi tsalle ta koma cikin gurbin ramin idon da kanta. Sarudul Makam ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuskar sa a lokaci guda. Kawai sai ya buɗe wata akwati ya ɗauko wata irin takobin haske. Ita dai wannan takobi in ka taɓa ta da hannu sai kaji baka taɓa komai ba,amma a zahiri surarta ta haske ce. Ƙotarta kawai ake iya taɓawa asan an taɓa ta. Sarudul Makam yace, "Kunga wannan takobin ta musamman ce nine na ƙirƙire ta daga cikin sirrikan tsafina. Da wannan takobi ne kaɗai za'a iya kashe irin mutanen mu, domin duk wanda aka sara da ita take zai zagwanye ya narke. A halin yanzu na ƙera irin wannan takobi guda miliyan dubu ɗaya da ƙwaya biyar. Ina dakarun yaƙi guda miliyan dubu ɗaya cif kunga kenan akwai sauran takobi guda biyar,kuma ba ta kowa bace face taku ku biyar ɗin nan,dama na tanade su ne saboda ku don nasan cewa kuna tafe." Cikin matuƙar tsoro boka sulbaini ya dubi sarki Sarudul Makam yace, "Au kana nufin cewa muma zamu tayaku yaƙin ne?" "Ƙwarai kuwa,idan ma baku jagoranci yaƙin ba ba za mu yi nasara ba. Kunga shike nan muna gama yaƙin sai nasa a ɗebo muku duwatsun da kuka zo nema a can duniyar ƙarshe ku yi tafiyar ku salin alin cikin kwanciyar hankali." Koda jin wannan batu sai markahus sabus yayi tsaki yace, "Ina fa batun salin alin kace dai bayan mun sha muguwar wuya ko kuma bayan mun halaka?" Sarudul Makam ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Koma mene ne ai ba kuda zaɓi dole ne kuyi yadda na tsara in ba haka ba kuwa yanxun nan na azabtar daku da irin azabar da baku taɓa ɗanɗana ta ba." Salusa tace, "Kai kuwa wace irin azaba ce wannan wadda bamu taɓa ɗanɗana irin ta ba?" Sarudul Makam yayi murmushi yace, "Karki damu yanzun nan zan jarraba miki ita." Nan take sarki Sarudul Makam yasa aka zo da wata ƙatuwar kwalba wadda aka rufe ta da wani irin faifai na ice. Kawai sai yasa aka kama Salusa da ƙarfin tsiya aka sata a cikin kwalbar aka rufe da wannan faifai. Yin hakan ke da wuya sai jikin Salusa ya fara daddarewa yana sala sala kamar ana feraye ta da zabira. Nan fa Salusa ta rinƙa ihu saboda tsananin azaba,saida ta suma. Sannan ne sarki Sarudul Makam yasa aka fito da ita daga cikin kwalbar. Salusa dai bata farfaɗo ba sai bayan sa'a guda. ########### Sarudul Makam ya dubi su markahul sabus yace da su, "Duk wanda yayi mini gardama daga cikin ku haka zan yi masa." Ya sake nuna salusa da ɗan yatsa yace, "Ke kuma idan baki gamsu ba da wannan azabar akwai wadda ta ninka ta sai a jarraba miki ita kiji nata ɗanɗanon." Cikin tsoro da kuka salusa tace, "Kayi mini rai haƙiƙa na gamsu da wannan ma." Markahul sabus ya bushe da dariya sannan yace, "Amma dai salusa kinyi wauta koda yake ban yi mamaki ba domin 'yar fari ce ke zaki iya yin abinda yafi haka,amma in banda wauta wa zai nema wa kansa wahala." Gama faɗin haka ke da wuya sai Sarudul Makam yace, "Yanzu za a kai ku masauƙin ku don ku huta,amma ku kwana da shiri domin gobe da safe zamu yi shiri mu tafi wannan yaƙi." Nan take dakarun nan da suka zo da su suka sake surarsu suka ɗora su akan manyan jemagun nan. Su kuwa jemagun sai suka buɗe fukafukansu suka yi sama. Sannan suka cigaba da tsala gudu a sararin sama. Saida akayi tafiyar daƙiƙa ɗari sannan aka sauke su markahul sabus a masaukensu. Masaukin ya kasance wani tamfatsetsen gida mai tsananin girma da faɗi domin aljani Durmazalu bai isa ya ƙure ƙarshen sa ba a cikin sa'a uku duk da cewa kuwa yana da fukafukai miliyan ɗaya. Shi dai wannan gida a cike yake da hadimai sai tafiyar da aikace-aikacen su kawai suke. Bayan an kai su markahul sabus cikin wani babban ɗaki sai aka kawo musu abinci da abin sha kala biyu. Kalar farko irin na mutane ne irin su boka jinshan. Kala ta biyu irin na aljanu ne. Nan take suka kama ci da sha aka bar salusa ita kaɗai a gefe guda tayi zugum da tagumi kamar zata fashe da kuka kuma dama ga raɗaɗin ciwon jikinta,ga yunwa ga ƙishirwa. Nan fa tausayin ta ya kama markahul sabus yace, "Yake salusa taso mana kizo muci abinci." Salusa ta gyaɗa kai tace, "Ai ni babu abinci na anan. Ni kam ina ganin cewa sarkin nan fa baya ƙaunata kawai so yake ya halaka ni. Ku dubi fa yadda jikina ya zama sala-sala." Rufe bakinta keda wuya sai ga wani hadimi ya shigo ɗauke da wani ƙaton faranti. Akan farantin dafaffiyar dalma ce ke fitar da tururi. Kai tsaye hadimin ya ajiye farantin a gaban salusa. Koda taga abinda ke cikin farantin sai tasa hannu biyu ta rinƙa ɗiba tana shanye wa. Da yake jikinta na dutse ne sai ruwan darmar data sha ya rinƙa manne jikin nata. Cikin 'yan daƙiƙu kaɗan duk ciwon jikin nata ya ɓace ɓat. Kawai sai su markahul sabus suka ji tayi wata irin gyatsa mai kama da rurin giwa. Tana gama gyatsar ta dubi jikinta taga ya warke sumul gaba ɗaya, kawai sai ta bushe da dariyar farin ciki. Tayi ta ƙyalƙyala dariyar kamar ba zata daina ba. Dariyar ce ta baiwa su markahul sabus dariya suma suka hau ƙyaƙyatawa. Kashe gari da sassafe sarki Sarudul Makam yasa aka zo aka ɗauki su aljani Durmazalu aka tafi dasu izuwa can fadarsa. Da zuwa suka iske dakaru miliyan dubu ɗaya a tsaitsaye a jere kan layi,sahu sahu kowannensu riƙe da takobin haske. Sarki Sarudul Makam na tsaye a gaban su yana kallon yawansu da kuma daidaiton tsayuwar su. Koda aka zo da su markahul sabus sai aka gurfanar dasu a gaban sa. Nan take ya ɗauko takubban haske guda biyar ya rarraba musu. Sannan ya umarce su dasu shiga cikin sahun mayaƙan. Ba tare da fargabar komai ba suka bi umarni. Kawai sai sarki Sarudul Makam ya fara bayani kamar haka: "Yaku mayaƙana kuyi sani cewa a yau ne ranar da zamu jajirce iyakar jajurcewar mu. Yau ne ranar da zamu zamo iyaye ga sauran duniyoyin dake ƙasanmu,kuma yau ne ranar ƙwatar ranmu da cikar burin mu. Ina mai kira a gare mu gaba ɗaya damu sallama rayuwar mu don kare mutuncin mu. A matsayina na mahaifin ku ina mai horonku da kada ɗayan ku yaji tsoro ya gudu daga filin daga. Kuyi sani cewa kamar yadda muke wannan shiri na son mallakar sauran duniyoyin nan haka suma suke nasu shirin na son mallakar mu. To amma sunyi sake ɗan zaki ya girma,kuma sun manta da cewa wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi. Ya ku 'ya'yana kuma mayaƙana kuyi sani cewa ga baƙi nan su biyar a tare damu, waɗannan baƙi sune za suyi mana jagora a cikin wannan yaƙi kuma su kaɗai ne zasu iya shiga cikin baitul malin duniyoyin ƙasa su ɗauko mana ƙahonnin nan guda shida." Lokacin da sarki Sarudul Makam ke wannan jawabi sai su boka jinshan suka nutsu suna sauraronsa. Koda jin cewa sune zasu jagoranci wannan yaƙi sai markahul sabus ya matsa daidai kunnen boka jinshan yayi masa raɗa yace, "Ya kai jinshan kayi sani cewa nifa ina ganin cewa mutanen nan fa sun raina mana hankali. Ya za'a yi mu da bamu da ƙarfi da kuma taurin rai irin nasu,amma suce wai mune zamu jagoranci wannan yaƙi?" Jinshan yayi ƙwafa yace, "Kaidai bari kawai ai ni tun jiya na gama suƙewa inda nasan cewa nafi ƙarfin mutumin nan da tuni nayi wa shege dukan tsiya na koya masa hankali, gajeren banza me kamar a kife da kwando🤣🤣🤣🤣(kuji pah boka jinshan da ƙarfin hali🤣🤣shi ya manta cewa shima gajere ne kamar waziri kuddaru 🤣🤣) To in banda ma rainin wayo ya mu da aka turo mu wani aikin kai kuma saika tsare mu kace sai munyi maka naka aikin. Sannan zamu aiwatar da namu?" Markahul sabus yace, "Ai abin ma ya wuce rainin wayo saidai a kira shi fin ƙarfi da zalunci." Suna cikin wannan magana ne sarki Sarudul Makam ya gama jawabi kuma ya bada umarnin a tafi izuwa duniya ta biyu. Kawai sai aka ga wata wawakekiyar ƙofa ta buɗe saiga jemagu na ta tuttuɗowa daga cikin ta har saida guda miliyan dubu ɗaya suka shigo kuma dukkanninsu suka sauko ƙasa suka tsaitsaya cak a waje guda. Nan da nan mayaƙan nan guda miliyan dubu ɗaya kowa ya hau kan nasa jemagen. Mu hadu a part I don Jin cigban wannan Kasaitaccen labarin.**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU 2❤️ PART I 💪✋ NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 😎 TYPING AHMAD MUNNIR 🤝 POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD 💪 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Kawai sai aka ga wata wawakekiyar ƙofa ta buɗe saiga jemagu na ta tuttuɗowa daga cikin ta har saida guda miliyan dubu ɗaya suka shigo kuma dukkanninsu suka sauko ƙasa suka tsaitsaya cak a waje guda. Nan da nan mayaƙan nan guda miliyan dubu ɗaya kowa ya hau kan nasa jemagen ya zauna. Babu abinda zai baiwa mutum mamaki face kowa ya san nasa jemagen, domin idan mutum yayi kuskure ya hau wanda ba nasa ba,sai kaga jemagen yayi wani irin ruri. Cikin sauri mutum zai sauka yaje ya nemi nasa. Bayan kowa ya gama hawa nasa jemagen sai kuma aka ga waɗansu jemagun guda biyar sun shigo. Su dai waɗannan jemagu sun fita dabam da sauran, domin sun kasance masu irin siffa dabam,kuma duk farare ne. Da shigowar jemagun sai suka sauka a gaban su markahul sabus suka yi layi. Sarudul Makam ya dubi su markahul sabus yace, "To ga naku ababen hawan ai saiku hau." Ba tare da wata gardama ba suka hau. Daga nan sai Sarudul Makam ya kawo takubban haske da garkuwoyi ya rabawa su markahul sabus. Sannan yace, "Ina yi muku fatan nasara, domin yanzu nasarar ku itace nasarar ku bisa abinda kuka zo nema." Sarudul Makam ya matsa kusa da boka jinshan yace, "Idan ka dawo saika koya mini hankali kayi mini shegen duka koh?" Koda jin haka sai mamaki da kunya suka kama jinshan ya sunkui da kansa ƙas. Sarudul Makam yayi murmushi sannan ya zunguri ɗaya daga cikin jemagun dake ɗauke dasu markahus sabus. Nan take jemagun biyar suka tashi sama suka wuce kan gaba. Sannan sauran jemagun guda miliyan dubu ɗaya suka bisu a baya. Sarudul Makam ya tsaya yana kallon su sa'adda suke ficewa ta cikin wawakekiyar ƙofar nan har saida suka ɓace masa da gani. Sannan ya tuntsure da mahaukaciyar dariya cikin tsananin farin ciki yana mai cewa, "Shikenan burina ya gama cika wannan karon." Haka dai markahul sabus suka cigaba da tafiya a cikin ƙarƙashin ƙasa,sai da suka yi tafiyar kwana uku. Sannan suka iso birnin Sarudul Hasal wanda ake kira Madinatul Hiluz. Birnin Madinatul Hiluz ya sha bambam da birnin Madinatul Aslik inda sarki Sarudul Makam ke mulki, domin su gidajensu an gina sune da zallan fararen duwatsu,saidai suma babu ƙasa ko tsirrai sai wannan farin Dutse wanda ya malale ko'ina. Lokacin da su markahul sabus suka shigo cikin wannan birni na Madinatul Hiluz tsakiyar dare ne,don haka garin yayi tsit,kamar ba mutane kuma garin gaba ɗaya a haskake yake babu duhu. Mutum bazai taɓa ganewa cewa dare ne ba face ya ɗaga kai sama yaga ƙananan taurari a cikin sararin sama. Sannan ya hango su markahul sabus kamar tsuntsaye suna shawagi a sama. Su dai su markahul sabus sun zama tamkar makafi domin jemagun da suke kansu ne ke musu jagora sai inda suka nufa dasu. Lokacin da jemagun suka iso wani gabjejen fili mai tsananin faɗi da tsawo sai jemagun suka sauko ƙasa gaba ɗayansu suka jeru a layi suka kafa sansani. Koda su markahul sabus suka duba can gaba nesa da su cikin babban filin sai suka hango cincirindon mayaƙan sarki Sarudul Hasal tamkar yuyar ƙudajen duniya. Al'amarin daya firgita su markahul sabus kenan,zuciyoyin su suka fara duka. Markahul sabus ya dubi boka jinshan, sulbaini, salusa da kuma aljani Durmazalu yace, "Ku dubi mayaƙan can fa yanzu dasu zamu yi yaƙi ai yawansu ya ninka namu sau ɗari. To wai shin sun san da zuwan mu ne har suka yi shiri haka?" Kafin wani daga cikin su Jinshan yace wani abu sai suka ga wani doki mai fukafukai ɗauke da sarki Sarudul Hasal ya ratso ta tsakiyar yuyar waɗannan mayaƙa a sama ya taho gare su sai daya rage saura kamu bakwai a tsakaninsu. Sannan dokin mai fukafukai ya sauko. Nan fa aka fara kallon kallo tsakanin sarki Sarudul Hasal dasu markahus sabus. Gaba ɗaya surar jikin Sarudul Hasal iri ɗaya ce sak data Sarudul Makam tamkar Hassan da Hussaini. Inda suka bambanta kawai shine,shi Sarudul Hasal kunnen sa na hagu a yanke yake, kuma an huda kunnen an maƙala masa wani ƙaton yari mai ƙawanya. Bayan Sarudul Hasal ya ƙarewa su markahul sabus kallo sai ya tuntsure da dariya. Sannan ya daka musu tsawa duk suka firgice,hantar cikin su duk ta kaɗawa suka ji kamar su ruga. Jinshan, Sulbaini, Durmazalu da kuma Salusa suka fara ɓoye fuskokinsu. Markahul sabus ne ya tsaya ƙyam bai firgice ba. Sarudul Hasal yace, "Ya ku waɗannan 'yan tatsitsan halittu yanzu kune jaruman da ɗan uwana Sarudul Makam ya turo don ku yaƙe mu,ku shiga baitul malin mu ku ɗauko ƙahon zinare? Ƙaryar ku tasha ƙarya, domin ko shi da kansa yazo nan mun fi gaban nan bare ku da waɗannan 'yan mayaƙan nasa da basu taka kara sun karya ba." Cikin ƙwarin zuciya da tarar aradu da ka markahul sabus ya dubi Sarudul Hasal yace, "Ya kai wannan sarki kayi sani cewa ba'a sanin maci tuwo sai miya ta ƙare. Haka kuma ai ba yawa bane alamun nasarar yaƙi, domin mazajen ƙwarai masu zuciyar dutse ƙalilan na iya samun rinjaye akan mazaje masu zuciyar ƙarmami komai yawansu." (Gaskiya markahul sabus ya faɗi magana 😅😅😅) Koda jin wannan batu sai zuciyar Sarudul Hasal ta kama tafarfasa tamkar ƙirjin sa zai tsage ta faɗo. Daga inda yake tsaye markahul sabus na iya hango yadda ƙirjinsa nasa mai cike da gashi irin na zaki ke hurowa kamar zai kumbura ya fashe. (Ran maza ya ɓaci, markahul sabus ka taɓo tsuliyar dodon dake tsaka da barci😥) Duk da dakakkiyar zuciya irin ta markahul sabus sai da gabansa ya faɗi shima yaji kamar yayi tsalle ya durga daga kan jemagen sa ya ruga da gudu,amma sai ya dake ya ƙaddara a ransa cewa tabbas yau mutuwarsa tazo. Sarki Sarudul Hasal ya ɗagawa jama'arsa hannu alamar a afkawa su markahul sabus. Sannan ya zaburi dokin sa. Nan take dokin ya zabura a sukwane ya durfafo inda su markahul sabus ke tsaye cikin matsiyacin gudu har yana tashi sama yana sauka suma kuwa dakarun nasa sai suka rufa masa baya sai ga dawakai masu fukafukai a sama tamkar gaba tsuntsayen duniya ne ke taron biki. Koda ganin haka sai markahul sabus ya waiga ya dubi su Durmazalu yace, "Ya ku 'yan uwana kuyi sani cewa yau fa mun gamu da gamon mu. Batun gudu ko ɓuya babu shi kuzo kawai muma mu tare su ayi karon batta ai ita kanta mutuwar ma mutuwa take." Jinshan yace, "Wace ce kuma mutuwar ka santa ne?" Markahul sabus yace, "Ai ba komai bane mutuwar ba face bala'i da masifa kasan kuwa idan tsanani yayi tsanani suma cinye kansu suke yi." Yana gama faɗin haka ya ɗaga takobin sa ta haske yayi kururuwa ya zunguri cikin jemagen da yake kai kawai sai jemagen ya ruga da gudu ya tunkari su sarki Sarudul Hasal. Nan da nan sauran jemagun suka rufa masa baya. Tun gabanin a haɗu wuri ya cika da ruri da kururuwar mayaƙa na ta cin burin a gwamutsu don a fara tamore. Koda ya rage saura kamu ɗaya a haɗe sai sarki Sarudul Hasal yayi tsalle sama ya bar kan dokin sa ya bangaji markahul sabus da ƙirjinsa na zaki. Markahul sabus yayi tsalle ya faɗo ƙasa sumamme. (😳😳😳😳😳😳 Gaskiya markahul ya gamu da gamon shi kuwa, gaskiya halittun duniyar ƙasa akwai masifa) **************** Al'amarin daya firgita su Durmazalu kenan suka yinƙura da nufin su juya da baya sai aka afka musu da sara bisa dole suka tsaya suna kare kansu da maida martani. Nan fa wuri ya hargitse. Cikin daƙiƙu kaɗan aka sumar dasu Durmazalu ya rage saura dakarun sarki Sarudul Makam da kuma su Sarudul Hasal ana ta artabu. Idan takobi ta haɗu da takobi sai kaga walƙiya da tartsatin wuta na tashi. Duk wanda ya sake kuwa aka sari jikinsa take yake narkewa walau a cikin mutanen sarki Sarudul Makam ko a cikin mutanen Sarudul Hasal. A wannan yaƙi dai Sarudul Hasal ne ya zama GAGARABADAU domin duk inda yasa a gabansa saidai kaga yana karkaɗe maza suna zubewa ƙasa matattu, domin yafi kowa ƙarfi,ƙwarewa, juriya da kuma jarumta. Sai da aka samu sa'a biyar ana wannan yaƙi su markahul sabus basu farfaɗo ba daga dogon suman da suka yi,kuma duk wannan dudufniya akan su ake yi in ba don ma gawarwakin waɗansu sun danne su ba da tuni an karairaya su. Koda ya rage baifi saura mutum dubu ɗari huɗu ba daga cikin mayaƙan Sarudul Makam,sai sarki Sarudul Hasal ya juya da baya ya cigaba da ragargazar maza yana ihu da kururuwa mai firgitarwa,yana neman inda su markahul sabus suke. Kamar haɗin baki sai su markahul sabus suka farfaɗo a lokaci guda. Cikin sauri suka tutture gawarwakin da suka yanyame su suka miƙe tsaye. Koda suka yi arba da sarki Sarudul Hasal bisa dokin sa mai fukafukai ya durfafo su yana ihu riƙe da takobi a sama sai suka ruga da gudu cikin tsananin tsoro suna ihu suna waige, domin mutuwa suka gani muraran. Markahul sabus ne a ƙarshen baya yana waigowa yaga Sarudul Hasal a saman kansa ya ɗaga takobin sa zai fille masa kai. Saboda tsananin razana markahul sabus bai san sa'adda yace, "Ya ubangijin musulunci ka cece ni daga wannan bala'i." Gama faɗin hakan ke da wuya takobin Sarudul Hasal ta dira a wuyan markahul sabus. Wata ƙara ta faru tamkar dutse aka sara. Take takobin Sarudul Hasal ta narke. Shi kuwa markahul sabus sai yaji wani irin ƙarfi ya shige shi wanda bai taɓa jin kamar sa ba. Kawai sai ya shaƙo wuyan sarki Sarudul Hasal suka kama kokawa da naushin juna. Nan fa Sarudul Hasal ya raina kansa don cikin ƙanƙanin lokaci markahul sabus ya haɗa masa jini da majina. Dakarun Sarudul Hasal kuwa suka yi caa akan markahul sabus suna saransa,amma kamar susa suke masa,baima kula dasu ba, kawai sai yaci gaba da tumurmusa Sarudul Hasal. Da yaga yana neman ɓata masa lokaci sai ya ɗaga shi sama ya fyaɗa da ƙasa ya take wuyansa da ƙafa guda. Koda ya kama hannunsa guda yaja da ƙarfi sai hannun ya tumɓuke daga gangar jikin. Sarudul Hasal ya kwarara ihu saboda tsananin zafi da zugi. Markahul sabus ya cigaba da tsintsinka shi saida yayi filla filla dashi. Koda ganin yadda akayi da Sarudul Hasal sai gaba ɗaya mayaƙan nasa suka fashe da kuka suka yi caa kan markahul sabus. Yayin da markahul sabus yaga sunyi nasa rubdugu sai ya ƙwaci takubba biyu a hannunsu ya ci gaba da ragargazar su shi kaɗai ya zama shaiɗani a tsakiyar su ya rinƙa cinikin mutuwa. Su boka jinshan kuwa da sauran tsirarun dakarun Sarudul Makam suka koma gefe ɗaya suna kallon ikon Allah, domin al'amarin ya wuce sanin su. Markahul sabus bai gushe ba yana saran mayaƙan nan ba har sai bayan sa'a biyar. Sannan ya ƙarar dasu gaba ɗaya. Yana gamawa da sune ya faɗi ƙasa, saboda tsananin gajiya ya kama haki da numfarfashi. A lokacin ne su boka jinshan suka rugo gareshi don su rungume shi,amma sai Durmazalu ya cafkosu da hannu ɗaya su ukun yace, "Akul kuka raɓe shi. Kuyi sani cewa a halin yanzu markahul sabus ya zama ma'abocin addinin musulunci, domin sunan ubangijin musulunci ya kira ya sami wannan gagarumin ƙarfi mai ban al'ajabi. Duk wanda yaje kusa dashi daga cikinmu ƙonewa zaiyi tunda mun kasance ma'abota tsafi. Abin da zamu yi kawai mu lallaɓa shi har mu gama ɗebo ƙahonhunan nan guda shida." Koda jin haka sai boka sulbaini yace, "To mai ze hana ne muma mu bada gaskiya ga wannan addini na musulunci tunda gashi yanzu a zahiri mun ga ƙarfin ubangijin sa. Kuma in ba don markahul sabus ya kirawo sunan sa ba,da tuni yanzu gaba ɗayan mu mun hallaka." Koda jin wannan batu sai aljani Durmazalu yace, "Duk wanda yayi yunƙurin karɓar wannan addini a cikin ku saina hallaka shi. Dole ne kubi a sannu mu kammala wannan aiki wanda mai girma shamharu ya turo mu." Sa'adda markahul sabus yaga su Durmazalu sun noƙe a baya sunƙi zuwa wajen sa sai ya miƙe tsaye ya taho inda suke. Kafin ya iso daf dasu sai aljani Durmazalu yace, "Dakata anan karka ƙaraso nan wajen mu." Cikin mamaki markahul sabus yace, "Don me zaka ce kada na ƙaraso wajen ku ashe ku ba 'yan uwana bane abokan tafiyata?" Durmazalu ya bushe da dariya. Sannan yace, "Ai daga yau ka zamo dodo a garemu domin kana kusantar mu zamu ƙone, domin ka zama ma'abocin addinin musulunci. Abin da nake so da kai shine muje yanzu kayi mana jagora mu ɗauko ƙahon zinare a cikin baitul malin wannan gari in yaso mu wuce izuwa sauran duniyoyin guda huɗu mu ɗauko ragowar ƙahonnin. In dai muka sami nasarar hakan da wannan ƙarfi naka muma zamu bada gaskiya da wannan addini na musulunci." Yayin da markahul sabus yaji wannan batu sai mamaki ya kama shi daya ji cewar shi yanxu ya zama musulmi alhalin kuma bai san yadda ake shiga addinin musulunci ba,amma kuma ya san cewa tabbas yanzu yayi imani da ubangijin musulunci. Markahul sabus ya dubi aljani Durmazalu yace, "Idan har kun amince zaku bada gaskiya ga addinin musulunci bayan nayi muku jagora mun ɗebo ƙahonnin na amince nima." Ba tare da wani ɓata lokaci ba markahul sabus ya wuce gaba su Durmazalu suka bishi a baya har izuwa cikin baitul malin sarki Sarudul Hasal,suka ɗauko ƙahon zinare. Sannan suka fito. Daga nan kuma suka sake nutsewa cikin ƙarƙashin ƙasa suka isa duniya ta uku anan ma aka tafka gagarumin yaƙi,kuma markahul sabus ne sanadin nasarar yaƙin aka ɗauko ƙahon zinare aka wuce izuwa duniya ta huɗu. A haka dai saida suka je har duniya ta bakwai suka sami nasarar ɗauko ƙahonnin shida suka dawo da baya suka kawowa sarki Sarudul Makam. Cikin tsananin murna ya karɓa. Sannan yasa aka ɗebo duwatsun wuta aka basu suka yi sallama dashi suka tafi suna murna shima yana yi. Koda suka fito daga cikin ƙarƙashin ƙasa kafin wani daga cikinsu yayi wani yunƙuri tuni aljani Durmazalu ya fesawa markahul sabus wani shuɗin hayaƙi. Take markahul sabus ya faɗi ƙasa sumamme. Durmazalu yayi sama dasu boka jinshan tare da duwatsun wuta suka ƙule a cikin gajimare suka bar markahul sabus anan cikin daji a kwance bai san halin da yake ciki ba. Wannan shi ne abinda ya faru gasu markahul sabus bayan sun sami nasarar samo abubuwa guda biyu,waɗanda shamharu ya tura su samowa,don a ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da itane za'a buɗe fadar sarki Azmul gallar a ɗauko kundin tsatsuban sa. MU HADU A PART J DON JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LITTAFIN.**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU🤝❤️ PART J ❤️💯🩷 NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑 TYPING AHMAD MUNNIR 🤝 POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️💯 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA... Wannan shi ne abinda ya faru gasu markahul sabus bayan sun sami nasarar samo abubuwa guda biyu,waɗanda shamharu ya tura su samowa,don a ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da itane za'a buɗe fadar sarki Azmul gallar a ɗauko kundin tsatsuban sa. ******************** Al'amarin su Jafar kuwa lokacin da iskar kundin tsatsuba ta watso su waje cikin tasu duniyar sai suka faɗo gaban kundin tsatsuba,kuma shafi na ɗari uku da ashirin da huɗu ne a buɗe. Nan fa suka kama haki da numfarfashi kamar ran su zai fita. Koda Jafar ya dubi Yalisa da Gulzum sai tsoro ya kama shi. Ba komai bane ya haddasa hakan ba face ganin Yalisa ta ƙara girma sosai,ta zama cikakkiyar budurwa,shi kuma Gulzum furfurar kansa ta ƙaro. Kamar yadda Jafar ya tsaya yana kallon su cikin mamaki suma haka suke kallon sa cikin matuƙar mamaki domin shima ya girma,ya zama saurayi harda gashin baki a fuskarsa da wani ɗan ƙaramin saje. Gaba ɗaya kamannin Yalisa dana Jafar sun sauya sun ƙara kyau. Kamannin Gulzum ne kaɗai basu sauya ba face wannan ƙarin furfura da ya samu. Jafar ya dubi Yalisa yana mai nuna ta da hannu yace, "Yalisa kece kuwa?" Itama sai ta nuna shi tace, "Jafar kaine kuwa?" Nan take suka rungume juna suka kama kukan farin ciki shi kuwa Gulzum sai ya bushe da dariyar murna. Sannan ya dube su yace, "Ai nasan dole ne kuyi mamakin yadda kuka yi saurin girma haka,amma bai kamata kuyi mamaki ba idan kuka yi la'akari da yawan shafukan da muka shiga a cikin kundi. Ku duba da ku gani a cikin shafi na ɗari uku da ashirin da huɗu muke yanzu. Wannan na nuni da cewa yanzu mun sami shekara shida da 'yan watanni a cikin kundi duk da cewar yanzu a cikin gaggawa muke karatunsa,amma bamu isa mu ragewa kanmu lokaci ba ko mu ƙara,dole ne sai mun yi shekara ashirin cif a cikin sa. Sannan zamu kammala karanta shi." Koda jin wannan batu sai jikin Jafar dana Yalisa yayi sanyi gaba ɗayan su suka koma gefe ɗaya suka zauna cikin matuƙar damuwa,duk suka yi zugum suna tunani mai zurfi. Koda ganin haka sai tausayin su ya kama Gulzum ya ƙaraso garesu ya dafa Yalisa yace, "Ya shugaba ta wai shin tunanin me kuke yi ne haka ke da Jafar?" Yalisa tayi ajiyar numfashi tace, "Ni kam ba komai nake tunani ba face mahaifina wanda yau rabona dashi shekara shida kenan. Haƙiƙa inda nasan wannan al'amari zai kasance mini da ban nemi na karanta wannan littafi ba." Sa'adda Yalisa tazo nan a zancen ta sai hawaye ya zubowa Jafar yace, "Yake masoyiya ta kiyi sani cewa nima tunanin nawa mahaifin nake, kuma nayi nadama bisa halina na rashin jin magana da karambani, domin karambani na bai haifar mini da komai ba face tsananin wahala, ƙunshi da tashin hankali. In da nasan cewa zan shiga cikin wannan hali da ban nemo ki ba,mun ɗauko wannan tsinannan littafi ba." Sa'adda Jafaru ya faɗi haka sai hawaye ya zubowa Gulzum ya rungume Jafar yana mai cewa, "Ya kai abokina ka sani cewa ita kazar wahala in dai mutum ya yankata dole ne ya ƙarasa fige ta. Inda muna da rabon barin wahala da tun haɗuwar mu da jarumi Hubairu zamu rabu da ita, domin da tuni mun karɓi addinin musulunci a hannun sa. In kuwa mun karɓi addinin musulunci da baza mu buɗe kundin tsatsuba ba har mu fara karanta shi." Koda Jafar yaji wannan batu sai yayi shiru yana mai nazari a cikin ƙwaƙwalwar sa. Daga can saiya janye jikinsa daga na Gulzum ya dube shi. Sannan ya dubi Yalisa yace, "Kun san wani abu kuwa?" Su biyun suka kaɗa kai alamar basu sani ba. Jafar yace, "In da ace zamu sake saduwa da jarumi Hubairu da mun bada gaskiya ga addinin musulunci,kuma mun nemi gafarar sa bisa cin amanar sa da muka yi, domin ni yanzu ina ji a cikin zuciya ta cewar wannan addini na musulunci shine gaskiya. Tsafi da bautar gumaka kuwa ba komai bane face toshewar basira da ɓata. Ku tsaya kuyi tunani inda tsafi gaskiya ne ya za'a yi mu kasa ceton kanmu daga cikin wannan bala'i tunda ke Yalisa kin gaji tsafi. Kuma me yasa duk irin ƙarfin tsafin sarki Lu'umanu jarumi Hubairu ya sami nasara akan sa?" Sa'adda Jafaru yazo nan a zancen sa sai jikin Yalisa dana Gulzum yayi sake yin sanyi sosai suka yi shiru basu ce komai ba. Har Yalisa ta buɗi baki zata ce wani abu sai kundin tsatsuba ya buɗe kansa izuwa shafi na ɗari uku da ashirin da biyar. Saiga hoton wani babban birni mai ƙayatattun gine-gine. A ƙasansa anyi rubutu kamar haka:- -------------------------------------------------------------- *"Wannan birni, birni ne na wuya da daɗi,an ƙirƙire shi kimanin shekaru dubu baya. Mai karatu shigo cikin sa kasha kallo"* -------------------------------------------------------------- Koda siririyar muryar nan ta gama karanta wannan jawabi sai iskar cikin kundi tayi fitar burgu ta zuƙe su Jafar suka zama 'yan mini-mini suka shige cikin sa. Kawai sai tsintar kansu suka yi a tsakiyar wannan babban birni. Birni ne mai ban sha'awa da ban mamaki. Gaba ɗaya gidajen garin an gina sune da tubalin zinare,kuma duk iri ɗaya ne babu wanda yafi wani faɗi ko tsawo. Ko'ina ka duba wata irin ciyawa ce ta lulluɓe ƙasa mai tsananin taushi da daɗin takawa. Wani abin mamaki shine mutanen garin gaba ɗayan su yara ne ƙanana waɗanda ba sufi shekara bakwai bakwai ba,kuma duk kansu ɗaya shekarun su ma ɗaya. Gaba ɗayan su kyawawan 'yan matane babu namiji ko guda ɗaya. Abinda zai ƙara baiwa mutum mamaki shine suna ta aikace-aikace irin wanda manyan mutane masu ƙarfi ke yi. Kai wani aikin ma ko aljani Gulzum aka sada shi dashi sai ya jigata ainun. Koda ganin su Jafar sai yaran nan suka yanyame su suna shewa da murna kuma suna tattaɓa jikin Jafar da Yalisa suna masu mamakin ganin irin surar jikin su. Wasu suka yi ta taɓa ƙirjin Yalisa wasu kuma suka rinƙa taɓa gashin bakin Jafar da sajensa. Al'amarin daya fusata Jafar kenan ya daka musu tsawa. Bisa mamaki sai Jafar yaga duk sun razana suna ja da baya sun daina taɓa su. Ba zato,sai ƙofar wani gida ta buɗe sai ga wata doguwar mace kyakkyawa 'yar kimanin shekaru arba'in ta fito. Kallo ɗaya zaka yi wa matar ka san cewa tana da nasaba da waɗannan yara, domin kamar su ɗaya da ita. Matar ta tsaya ta ƙarewa su Jafar kallo. Sannan tayi murmushi tace, "Marhaban da manyan baƙi ina yi muku barka da zuwa birnin jinsi ɗaya. Ku biyo ni izuwa cikin gidana domin mu tattauna muhimman al'amura." Tana gama faɗin haka ta juya ta nufi cikin gidan data fito daga ciki. Ba tare da wata fargaba ba su Jafar suka bi ta a baya. Da shigar su cikin gidan sai kansu ya ɗaure, saboda ganin irin kayan da aka shirya a wani tangamemen falo. Duk wani abu na jin daɗin rayuwar duniya akwai shi a ciki. Abinci,abin sha kuwa gasu nan iri-iri harda wanda su Jafaru basu taɓa gani ba a rayuwar su duk da irin yawon da suka sha a cikin kundin tsatsuba. Duk abinda su Jafar ke buƙata ba sai sun ɗauko ba da hannun su. Suna miƙa hannu abin zai taso da kansa ya dira a hannunsu. Bayan sun ci,sun sha,sunyi hani'an sai matar nan ta sake dubansu tayi murmushi. Sannan tace, "Yaku waɗannan manyan baƙi masu daraja kuyi sani cewa ni sunana Hasiyatul Lauras. Gaba ɗaya yaran nan da kuka gani a cikin garin nan 'ya'yana ne ni na haife su. Duk shekara ina haihuwar 'ya'ya dubu arba'in kuma ban taɓa haihuwar ɗa namiji guda ɗaya ba. Waɗannan 'ya'ya nawa basa girma iyakar girman su kenan yadda kuka gansu. Wannan al'amari na jefa ni cikin matuƙar baƙin ciki duk da cewar bamu rasa komai na jin daɗin rayuwa ba. Ina matuƙar son naga na haifi ɗa namiji kuma ina son ya kasance 'ya'ya na suna girma,amma abu ya gagara. Yaku waɗannan baƙi kuyi sani cewa ba wani abu ne ya haddasa mini wannan masifa ba face wani azzalumin sarkin dodanni wanda yake zuwa mini duk shekara yana saduwa dani. Yana gamawa dani zai tashi yayi tafiyarsa. Bayan tafiyar da da tsawon rabin sa'a saina fara haihuwar'ya'ya har saina haifi guda dubu arba'in. Shi dai wannan sarkin dodanni komai nasa irin na mutane ne face hannayen sa da ƙafafuwan sa waɗanda suke irin na goggon biri. Ko'ina a jikin sa gashi ne. A fuska ya kasance kyakkyawa kuma babu gashi a fuskar sa. Ya kasance murɗaɗɗen ƙato mai tsananin ƙarfin damtse. Babu wani makami dake tasiri a jikin sa bare yayi masa lahani. Idan zaizo ya kan zone tare da mutanen sa waɗanda suka kasance irin sa kuma sukan zo bisa dawakai su da yawa,ba zan iya misalta muku adadin su ba. Kafin kuzo nan nayi mafarki da zuwan ku,kuma a cikin mafarkin an nuna mini cewa kune zaku yaƙi wannan dodo da jama'arsa kuyi mana maganinsu. Kuyi sani cewa duk abinda nayi mafarkin sa wannan abu yana faruwa a gaske don haka ni yau ina cikin matuƙar farin ciki da ganin ku." Yayin dasu Jafar suka ji wannan batu sai suka dubi juna cikin matuƙar mamaki. Sannan Jafar ya dubi Hasiyatul Lauras yace, "Yake wannan mata mai baiwar haihuwa kiyi sani cewa mu bamu mayaƙa ba,ta yaya zamu iya tarar wannan basamuden dodo alhalin kince makami baya tasiri a jikin sa da kuma na jama'arsa. Kuma kince baki san yawan adadin su ba? Ai ko ba komai sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi bare ma mu bamu da ƙarfin." Hasiyatul Lauras tace, "Ni dai bani da wata shakka akan ku,na tabbatar da cewa zaku iya kawar da dodo Abulungu da jama'arsa indai kuna da niyya saidai idan ba kwa son ku taimake ni. Ku sani cewa idan ma baku yaƙi dodo Abulungu ba indai ya iske ku anan sai ya kashe ku, domin bai yarda yaga wata halitta kusa dani ba,face waɗannan 'ya'ya nasa." Koda Hasiyatul Lauras tazo nan a zancen ta sai Jafar, Yalisa da Gulzum suka sake duban junansu cikin tsananin damuwa. Yalisa ta cizi yatsa tace, "Kash! Sai mutum baya nan sannan ake sanin muhimmancin sa. Yau ga ranar Mazalish inda tana nan yanzu ne zata yi tunanin dabara cikin gaggawa." Jafar yace, "Ƙwarai kuwa ai rashin Mazalish a gare mu ba ƙaramar asara bace." Shi kuwa Gulzum sai ya matso ƙwalla daga cikin idanun sa yace, "Haƙiƙa kowa ya tuna da bara baiji daɗin bana ba." ************************ Jafar yayi shiru ya sake shiga sabon tunani da nazari. Daga can sai ya dubi Hasiyatul Lauras yace, "Yake wannan mata shin a wani lokaci su dodo Abulungu ke zuwa?" Hasiyatul Lauras tace, "Su kanzo ne duk ƙarshen shekara da magriba kuma yau saura kwana goma cif su zo." Yayin da Jafar yaji wannan amsa sai yayi shiru ya sake yin tunani. Sannan yace, "Kince ƙarfe baya tasiri a jikin su,to shin suna iya lalata ƙarfe ne da ƙarfin hannun su?" Hasiyatul Lauras tace, "A'a basa iyawa,amma dai suna zuwa riƙe da muggan makamai wasu ma ko a labari ban taɓa jin masu kaifin su ba da tsinin su." Jafar yayi murmushi. Sannan ya dubi Hasiyatul Lauras yace, "Abinda nake so dake shine ki tara 'ya'yan nan naki gaba ɗaya ki gaya musu cewa su fara shiri zamu yaƙi su dodo Abulungu nan da kwana goman kuma kisa a ƙera mana ragar ƙarafa mai yawa wacce da itane zamu kama su Abulungu mu rinƙa watsa musu wuta suna ƙonewa. Ina ganin da wannan dabara ne kaɗai zamu iya samun galaba akan su." Koda jin wannan batu sai Yalisa, Gulzum da Hasiyatul Lauras suka cika da tsananin mamakin irin basirar Jafar da yadda yayi tunanin wannan hikima a cikin ƙanƙanin lokaci haka. Daga wannan rana 'ya'yan Hasiyatul Lauras suka fara ƙera ragogin ƙarfe. Sannan aka tanadi gunguma-gunguman itatuwa aka kunna gagarumar wuta. Kuma sai akayi waɗansu majajjawa na ƙarafa waɗanda za'a rinƙa watsawa mutanen dodo Abulungu ɗanyen mai da wannan wuta. Ita dai wannan wuta kullum ƙara zuba mata gunguma-gunguman itatuwa ake tana ci dare da rana. Jafar ya raba 'ya'yan Hasiyatul Lauras izuwa kaso uku. Kaso na ɗaya aikin su shine hawa kan bishiyoyi su ɓuya. Da zarar mutanen Abulungu sun zo wucewa su jeho musu ragogi. Kaso na biyu aikinsu kuwa shine watso wannan ɗanyen mai. Su kuma kaso na uku aikin su shine watsa musu wuta. Jafar ya samu wani ƙaton kulki ya baiwa Gulzum yace, "Kai kuma ka ruƙe wannan idan kaga mutanen Abulungu a cikin raga waɗanda wuta bata kama ba kayi ta dukan su da wannan kulki ka kashe na kashewa ka sumar dana sumarwa." Ba tare da gardama ba Gulzum ya karɓi kulkin yana mai murmushi,amma zuciyarsa cewa yake, "Anya kuwa shegen yaron nan ba mugunta ya shirya mini ba. Idan kuma garin dukan dodannin sun kamani fa? Shikenan tawa ta ƙare." (😂😂😂😂Kai dai Gulzum akwai shegen tsoro yasin😂) Haka dai aka cigaba da shirye-shirye har kwanaki goma suka cika. A rana ta goman ne tunda yamma suka samu wurare suka ɓuya wato suka yi lamɓo suna jiran ƙarasowar su dodo Abulungu. Har magriba tayi shiru ba'a ji motsin komai ba. Al'amarin daya sa su Jafar suka ƙosa kenan domin sun matsu waɗannan abokan gaba suzo domin ganin mugun tanadin da suka ya isa su gama da su. Bayan an saka jimawa kawai sai aka jiyo ƙarar sawun kofaton dawakai daga can nesa. Jim kaɗan kuma sai ƙarar tayi yawa ta matso kusa kuma ihun dodannin da gurnanin su ya cika dodon kunne da kuma hayaniyar dawakansu. Koda su Jafar suka hango yawan waɗannan dodonni sai suka firgice,ƙiris ya rage basu tsure da gudawa ba, domin sun san cewa wannan shiri da suka yi bai isa ya gama da waɗannan miyagun dodonni ba. Har Yalisa da Gulzum sun yunƙura zasu ruga da gudu sai Jafar ya daka musu tsawa yace, "Ina zaku? To ku sani cewa idan ma kuka gudu kunyi gudun banza tamkar ma kun fallasa kanku ne yadda za'a yi saurin hallaka ku. Kawai ku tsaya mu jarraba iyakar sa'ar mu. Ai da mu mutu ragwage gwara mu mutu jarumai." A daidai wannan lokaci ne wata zuga mai yawa ta dodanni tazo zata gifta sai masu raga suka watso ragogin su akan su. Nan take ragogin suka lulluɓe su suka rinƙa faɗowa ƙasa daga kan doki. Kafin su miƙe tsaye kuwa aka rinƙa watso musu ɗanyen mai da wuta. Nan fa dodannin suka rinƙa kamawa da wuta suna ci kamar ƙarmami suka rinƙa ihu da ruri mai razanarwa. Da yake dodo Abulungu na daga can baya sai ya ɗaga hannu sauran dakarun sa suka tsaya cak. Shima ya tsaya yana mamakin wannan baƙon al'amari domin tunda yake zuwa wannan birni fiye da shekaru arba'in baya ba'a taɓa kawo masa hari ba sai yau. Abulungu ya hanga da kyau yaga ashe 'ya'yan sune da kansu suke yiwa jama'arsa wannan ɓarna. Nan take ya baiwa mutanen sa masu kwari da baka umarnin su ruga su harbo dukkanin yaran nan dake kan bishiyoyi masu jeho raga. Nan take 'yan kwari da bakan suka zaburi dawakansu suka durfafi yaran. Tun daga nesa suka fara harba kibiyoyi saiga yaran na faɗowa ƙasa matattu. Da yake suma yaran suna da yawa basu fasa jeho ragar ba, suma masu watso ɗanyen mai da masu watso wuta basu fasa ba. Nan fa wuri ya ƙara hargitsewa da ihun dodannin dana yaran aka rinƙa gasar ɗaukar rayuka. Har yanzu dodo Abulungu na daga can baya a tsaye kan doki da wasu fadawan sa da kuma dubunnan dakaru suna kallon abinda ke wakana. Babu yadda mutum zai iya gane ɓangaren da suka fi mutuwa tsakanin mutanen dodo Abulungu da mutanen su Jafar. A wannan lokaci Gulzum ya taka muhimmiyar rawa, domin ya ragargaji dodannin nan da wannan ƙaton kulki dake hannun sa. Da yawa sun baƙunci lahira wasu kuma yayi daga-daga da sassan jikin su ba zasu taɓa moruwa ba. Jafar kuwa yana daga cikin masu watsawa dodannin ɗanyen mai ita kuma Yalisa tana cikin masu watsa wuta. Koda dodo Abulungu ya fuskanci cewa babu alamar nasara ga mutanen sa saiya fiddo da wani ƙaho ya busa. Faruwar hakan keda wuya mutanen nasa dake artabu dasu Jafar suka juya da baya a guje suka koma wajen Abulungu 'yan kaɗan dasu alamar cewa an kashe su da yawa. SAI MU HADU A PART K DON JIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LABARIN MAI CIKE DA DIMBIN ABIN AL'AJABI, JARUMTA, DA SOYAYYA. Najibullahi Muhammad**MIFTAHUZZARBIL** LITTAFI NA BIYU 🤝❤️ PART K 🥰🤝 NA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 👑 TYPING AHMAD MUNNIR 🤝🥰 POSTING NAJIBULLAH MUHAMMAD ❤️❤️💯 ONE LOVE 💕😘 MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.... Faruwar hakan keda wuya mutanen nasa dake artabu dasu Jafar suka juya da baya a guje suka koma wajen Abulungu 'yan kaɗan dasu alamar cewa an kashe su da yawa. Koda Abulungu yaga haka saiya kwarara ihu cikin tsananin baƙin ciki. Daga can ya ɗago kai ya dubi sauran dakarun nasa dake baibaye dashi yace, "Yaku mayaƙa na abin dogaro na kuyi sani cewa haƙiƙa yau Hasiyatul Lauras ta shirya mana mugun nufi na ƙarar damu,amma duk yadda aka yi ta samu taimakon wasu baƙin halittun, domin bata da basirar shirya wannan hikima. Abin dana ke so daku yanzu shine mu tattara waje ɗaya gaba ɗayan mu,mu haɗa ƙarfi waje guda mu shige su lokaci guda,don ayi ta ta ƙare." Koda jin haka sai dodannin suka fara jeruwa sahu-sahu a waje guda. A can ɓangaren su Jafar kuwa tuni sun fara murna,don a zatonsu dodannin sunji tsoro sun gudu,don haka sa'adda suka ga dodannin na jeruwa a sahu-sahu sun ɗauka tafiya zasu yi su bar garin. Ba zato, ba tsammani kuma sai suka ga dodannin sun taso musu a sukwane gaba ɗayansu ba'a rage ko guda ba. Nan fa su Jafar suka tsure. Ita dai Hasiyatul Lauras da rarrafe ta ruga cikin gidanta ta maida ƙofa ta rufe. Jafar da Yalisa kuwa sai suka ruga bayan Gulzum suka ɓuya. Sauran yaran nan kuwa masu jeho ragogi da masu watso mai da wuta ko gezau basu yi ba sai kawai suka tsaya suna jiran isowar abokan gaba. Koda ganin yadda waɗannan yara suka dake suka cire tsoro a zuciyarsu sai Gulzum yaji shima ya daina tsoron komai. Take yaji ƙwarin gwiwa da ƙarfi ya shige shi. Kawai sai ya kama wata ƙatuwar bishiya ya cisgota daga cikin ƙasa ya ruƙe ta a matsayin makami ya zamana yana da makami biyu kenan,wato ga ƙaton kulki,kuma ga bishiya. Da isowar dakarun sai wuri ya ƙara hargitsewa da ihu da kururuwa. Dodanni na mutuwa yara na mutuwa. Nan fa aljani Gulzum ya zama kamar ifritu a tsakiyar dodannin nan ya dinga ragargazar su da kulki da bishiya. Duk inda yakai duka saidai kaga suna zubewa ƙasa matattu ko sumammu. Duk wannan ɗauki ba daɗi da ake yi Jafar da Yalisa na kan kafaɗar Gulzum sun maƙalƙale sunƙi yarda su sauko ƙasa. Sa'adda Jafar yaga yaran nan suna ta ƙoƙari duk da cewar ana ta kashe su sai kunya ta kama shi ya dubi Yalisa yace, "Yake masoyiya ta a gaskiya zamu ji kunya idan har aka samu nasara a yaƙin nan bamu taɓuka komai ba. Zaifi kyau muyi iya yinmu koda kuwa zamu hallaka." Ba tare da wata gardama ba Yalisa ta karɓi wannan uzuri nan take suka daka tsalle daga kan kafaɗar Gulzum suka kaiwa yaran ɗauki. Wannan karon sai Jafar ya shiga cikin masu watso wuta ita kuma Yalisa ta shiga cikin masu watso ɗanyen mai. Ai fa sai wurin ya ƙara hautsinewa fiye da da, domin Jafar da Yalisa sunfi waɗannan yara zafin nama. Shi kuwa dodo Abulungu yana cikin ragargazar yaran ne ya hango Jafar, Yalisa da Gulzum yaga irin ɓarnar da suke ta wuce misali sai yayi kururuwa ya zaburi dokin sa ya durfafi Gulzum, saboda ganin cewa yafi ɓarna. Koda ya riske shi sai suka kaure da matsiyacin faɗa. Abulungu ya dinga kaiwa Gulzum sara da suka da wata irin lafceciyar adda mai girma da kaifi. Gulzum ya dinga karewa da kulkin ƙarfen dake hannunsa kuma yana maida martanin duka da bishiyar dake hannunsa. Duk da girma irin na aljani Gulzum dodo Abulungu ya fishi faɗi da tsawo. Nan fa suka yi ta Artabu harya zamana kowannensu ya fara gane kuskurensa, domin dodo Abulungu ya samu nasarar yankar Gulzum har sau uku da wannan lafceciyar adda. Shi kuma Gulzum ya mammaka masa bishiyar nan a fuska ya haɗa masa jini da majina. Fuskar dodo Abulungu duk ta kumbura ba kyan gani. Cikin tsananin fushi dodo Abulungu ya shammaci Gulzum ya danƙara masa sara a ƙafa. Take wajen yayi rami jini yayi tsartuwa sama. Gulzum ya kwarara ihu saboda tsananin zafi da zugi ya durƙushe a ƙasa,amma sai shima ya shammaci Abulungu ya danƙara masa bishiyar nan a ƙoƙon gwiwarsa. Take ƙafar Abulungu ta karye ɓas shima ya faɗi ƙasa yana mai kwarara uban ihu. Koda jama'ar Abulungu suka jiyo ihun sarkin sai suka ruga inda yake suka ɗauke shi suka juya da baya gaba ɗayansu suka sake runtuma wa da gudu suka bar birnin gaba ɗaya,ɗayansu bai tsaya ba face matattun dake kwance fululu a ƙasa. Nan take Gulzum ya faɗi ƙasa sumamme saida su Jafar suka watsa masa ruwa. Sannan ya farfaɗo. Daga nan 'ya'yan Hasiyatul Lauras da ita kanta suka fara haƙa kabarurruka suna binne gawarwakin yaran da suka mutu suna kuka. Abin dai abin tausayi.😢😢 Babu wanda zai ga sa'adda yaran ke binne 'yan uwansu bai zub da hawaye ba. A wannan lokaci ne Hasiyatul Lauras ta kawo magani aka sanya wa masu raunuka hadda aljani Gulzum, amma duk da haka bai dawo cikin hayyacinsa ba. Sai bayan sa'a uku a cikin falon Hasiyatul Lauras. Bayan farfaɗowar Gulzum ne Jafar da Yalisa suka ruga gareshi suka rungume shi suna kuka, saboda ganin halin daya shiga. Gulzum ya dube su sa'adda shima idanunsa suka ciko da ƙwalla yace, "Yaku 'yan uwana ku daina kuka saboda wannan hali dana shiga, domin ni namiji ne kuma an san namiji sha gwagwarmaya ne. Koda na mutu a wannan yaƙi bai kamata ku damu ba tunda nima na salwantar da rayuka da yawa. Yanzu babu abinda ya kamace mu face tunanin yadda zamu sake tarar waɗannan mugayen dodonni, domin tabbas sai sun dawo mana." Koda jin haka sai hankalin Jafar, Yalisa da Hasiyatul Lauras ya dugunzuma aka rasa wanda zai ce ƙala. A sannan ne Jafar ya fara da cewa, "Tunda aka fara yaƙin nan bai ga Salusa ba." Nan take ya tambayi Yalisa da Gulzum ko sunga Salusa? Gulzum ya sunkui da kansa ƙas cikin alamun karayar zuciya yace, "Ai salusa ta mutu kuma dodo Abulungu ne yayi mata wawan duka aka take kanta ya rugurguje duk da cewa kuwa na dutse ne, domin tarwatsewa yayi, yayi filla filla. Yanzu haka gawarta na nan a inda muka gwabza yaƙi ni da Abulungu." Yayin da Gulzum yazo nan a bayanin sa sai jikin Jafar da Yalisa ya ƙara yin sanyi kuma suka sake tsorata ainun da wannan bala'i da suke ciki. Saida Gulzum ya kwana bakwai yana jinyar jikinsa. Sannan ya sami ƙwari,harma yake iya takawa da ƙafarsa. Tsawon waɗannan kwanaki ana ta ƙera sababbin ragogin ƙarfe da kuma majajjawar watsa ɗanyen mai da wuta. Ice kuwa saida aka tara wanda inda za'a shekara ana ƙonawa bazai cinye ba. Wannan karon dai sai Jafar ya bada shawarar a rarrabu wuri-wuri ayi kwantan ɓauna. Ma'ana kada a tsaya a waje guda saboda ya san cewa suma su dodo Abulungu da sabon shiri zasu zo kuma da sabuwar hikima. Su Jafar dai suka zamo kullum a cikin shiri da jira,don sun san cewa lallai su dodo Abulungu zasu iya zuwa a koyaushe. Saida aka kwana goma sha huɗu ana jiran aga ɓullowar su dodo Abulungu amma shiru ko alamar su babu. ********************* A can kogon dutsen dasu dodo Abulungu ke ciki kuwa sai da Abulungu ya kwana tara a kwance yana jinyar fuskarsa da ƙafarsa. Sannan ya warke,harma ya iya tashi ya taka sawayensa. Koda Abulungu yaga ya samu lafiya sai ya zabura da nufin ya ɗau kayan yaƙin sa ya koma birnin Hasiyatul Lauras ya yaƙe su shi kaɗai. Cikin sauri matarsa dodanniya Kurdisa ta ruƙo hannun sa tace, "Haba mai gidana kayi sani cewa ba'a ramuwa ranar gaba. Ai zuwa da shiri yafi zuwa da wuri. Ina mai sanar da kai cewa tabbas waɗannan abokan gaba ba zasu zauna haka ba,sai sunyi mana mugun tanadi don haka ya zama wajibi muma muyi musu tanadin da basu taɓa zato ba,yadda muna riskar su zamu gama dasu a cikin ƙanƙanin lokaci." Abulungu yayi ƙwafa yace, "Ai ni babu abinda ke mini takaici face ganin cewa da 'ya'yan cikina muke wannan yaƙi." Kurdisa ta bushe da dariya tace, "Ai maganin mai kwaɗayi kenan. Inda ka haƙura dani kaɗai muna haihuwar dodanni irin mu ai da haka bata faru ba. Yanzu gashi kaje ka haiƙewa bil'adama ta haifo 'ya'yan dake neman zama sanadin ajalinka. In ba don ina tsoron kada a cuci 'ya'ya na a mayar dasu marayu ba ai da ba zan yarda a cigaba da yaƙin nan ba. To kai kaɗai ne babba namiji a garin nan kuma kaine uban kowa,kaine kuma mai basirar kare mu daga kowane irin haɗari." Sa'adda Kurdisa tazo nan a zancen ta sai Abulungu yace, "Haƙiƙa kinyi gaskiya kuma na samu darasi don haka daga yau ba zan sake yarda na haiƙewa wata mace ba,in ba ke ba." Nan take Abulungu ya tara gaba ɗaya mutanen sa waɗanda suka kasance 'ya'yan sa ne kaf yayi musu bayani cewa kowa ya fara shiri nan da kwana goma za'a koma birnin Hasiyatul Lauras ɗin. Koda jin haka sai aka ruɗe da shewa ana kururuwa da ruri ana murna. A sannan ne ya zayyana musu duk irin sabbin dabarun da za'a yi da kuma irin makaman da za'a tanada don a samu nasara a wannan yaƙi. Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga aikin ƙera sabbin makamai. Saida aka kwana tara ana ta shirye shirye, sannan komai ya kammalu. A daren kwana na goma ne dodo Abulungu da jama'arsa suka kai sumame birnin Hasiyatul Lauras. Kuma da tsakar dare suka shiga don ma kada a ji motsin tahowarsu. Sai suka fara tafiya a dudduƙe da laɓe-laɓe domin a tunaninsu su Jafar na barci a cikin wannan lokaci. Abinda basu sani ba shine tun daga ranar da akayi wancan yaƙi aka daina barci a birnin. Lokacin da su Abulungu suka shigo tsakiyar birnin suna duƙe-duƙe da laɓe-laɓe kawai sai suka ji an fara watso musu raga,ɗanyen mai da wuta. Wannan karon harda manyan duwatsu aka jeho musu yana ragargazar su. Kafin su ankara anyi musu muguwar ɓarna. Nan take Abulungu ya bada umarnin a koma da baya da gudu. Ai kuwa nan da nan suka juya basu tsaya a ko'ina ba sai inda suka baro manya-manyan dawakansu masu kama da giwaye. Da zuwa suka haye dawakan suka sake zaburo su a sukwane suka durfafo birnin Hasiyatul Lauras. Suna isowa yaƙi mummuna ya sake ɓarkewa. A wannan rana anci kasuwar mutuwa domin dubunnan ɗaruruwan rayuka sun salwanta tsakanin jama'ar dodonni da jama'ar Hasiyatul Lauras. A lokacin ne Jafar da Yalisa suka shiga mugun hali na tsakanin mutuwa da rayuwa, domin duk jikinsu raunuka ne jini na zuba. Jiri na ɗibarsu,suna faɗuwa,amma a hakan suka cigaba da gumurzu. Aljani Gulzum kuwa da dodo Abulungu dama yau sun fito ne da niyyar ko rai ko mutuwa,amma ba gudu ba ja da baya. Sai daya zamana dukkanin su sunyi fata-fata da juna, kowannensu ya sami saɓawar kamanni. Tun suna iya yin yaƙin a tsaye suka koma yi a durƙushe. A ƙarshe ma suka zub da makamansu suka kama kokawa suna cizo da yakushin juna. Abulungu ya cafki kunnen Gulzum na hagu ya ciza da haƙoransa. Sannan ya fincike shi da ƙarfin tsiya. Gulzum yayi kururuwa yayi tsalle sama ya faɗo ƙasa tim saboda tsananin zafin daya ji. (Wannan ya tunanin da boka karluz 😅😅😅,bambancin da aka samu shine,boka karluz dodon ne yayi watanda da kunnensa😅😅) Koda Abulungu yaga ya samu wannan nasara sai ya ƙara mirginowa ya kaiwa hannun Gulzum wawura da gatso gatson haƙoransa. Cikin zafin nama Gulzum ya goce shima ya kaima Abulungu cizo a marainan sa. Ai kuwa yayi sa'ar damƙar su. Take Gulzum ya taune su suka farfashe, ihun da Abulungu yayi saida ƙasa ta kama girgiza. Nan da nan idanun sa suka ƙafe jikinsa ya sandare,komai nasa ya daina motsi. Koda Gulzum yaga ya samu nasarar kashe Abulungu sai ya miƙe tsaye wuf ya kwarara kururuwa cikin ƙarfin hali da ƙwarin zuciya ya sungumi kulakensa biyu ya cigaba da ragargazar dodonnin nan. Suma su Jafar koda suka ga an kashe Abulungu sai ƙarfi yazo musu suka cigaba da kashe dodannin. Su kuwa dodannin gaba ɗaya suka rasa kuzari tunda suka ga an kashe ubansu don haka sai suka fara ƙoƙarin guduwa,amma damar hakan bata samu ba,don kewaye su su Jafar suka yi suka yi ta ragargazar su. Ana cikin haka ne aka ga dodanniya Kurdisa tayi wani sabon ayarin dodannin jagora bisa kan dawakai ba adadi sun kawowa su Abulungu ɗauki. A sukwane suka durfafo inda ake wannan yaƙi. Tun daga nesa Kurdisa ta hango gawar mijinta ai kuwa nan take ta haukace ta dunga ihu tana ƙarawa dokin ta ƙaimi,don ta riski su Gulzum. Koda su Gulzum suka hango wannan gagarumin ayari sai suka yarda dukkanin makamansu suka saduda,don sun san cewa tabbas ajalinsu yazo. Saida ya rage saura baifi zira'i ashirin ba tsakanin su Kurdisa dasu Jafar kawai sai aka ga ƙatuwar macijiyar nan ta sarki Azmul gallar ta bayyana a gaban su Kurdisa. Cikin razani dawakan nasu suka rinƙa turjiya suna juyawa da baya a guje,amma sai macijiyar ta sauko da kawunan ta ta rinƙa haɗiyar su Kurdisa daga su har dawakansu tayi ta tsince su ɗaya bayan ɗaya sai data ƙarar dasu gaba ɗaya babu wanda ya tsira. Bayan ta gama lanƙwame sune ta juyo da kanta guda ta ƙare wa su Hasiyatul Lauras kallo,koda taga Jafar, Yalisa da Gulzum saita haɗiye su. Sannan ta ɓace ɓat. ***************************** Su Jafar dai sai gani suka yi an watsar dasu a tsakiyar fadar sarki Azmul gallar yana tsaye a kan su. Azmul gallar ya dubi su Jafar ya ƙyalƙyale da dariya, sannan ya murtuke fuska yace, "Sannun ku da hanya." Jafar ya miƙe tsaye yana mai riƙe ƙugunsa da hannu biyu ya dubi Azmul gallar cikin alamun raini yace, "Ya kai wannan sarki mene ne yasa baka ceto rayuwar mu ba da wuri sai bayan da kaga munsha baƙar wahala kamar zamu mutu?" Sa'adda sarki Azmul gallar yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariya yace, "Ai ba zan iya ceto ku ba,face bayan kunsha wuya ainun, domin haka ƙa'idar kundin tsatsuba take. Idan kuwa nace zan cece ku da wuri nima hallaka zanyi, domin fadar nan tawa gaba ɗaya ma ragargajewa zata yi, komai na cikinta ya ƙone. Ni yanzu burina kawai kuyi sauri ku kammala karatun wannan littafi, domin sirrin shamharu ya bayyana gareni kafin ya gama haɗa abubuwa uku da zai ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL, wacce da ita ne zai iya buɗe fada ta inda nawa kundin tsatsuban ke ajiye ya ɗauko ya karanta. Kuyi sani cewa a halin yanzu Shamharu ya tura su aljani markahul sabus nemo abubuwa ukun kuma har sun samo guda biyu saura guda ɗaya rak,wanda shine rabin ruwan tekun duniyar ku. Tabbas idan baku gama karanta kundi ba kafin su samo rabin ruwan tekun tawa ta ƙare. Don haka dole ne na ƙara saurin tafiyar ku a cikin kundin tsatsuba domin ku kammala karatun da wuri. Ku sani cewa tafiyar su markahul sabus ta sami matsala domin a halin yanzu markahul sabus ya zama ma'abocin addinin musulunci don haka aljani Durmazalu ya sumar dashi sun gudu sun barshi a can cikin wani jeji. Abinda da Durmazalu bai sani ba shine wannan rabin ruwan tekun ba zai ɗebu ba sai sunyi da gaske,amma inda suna tare da markahul sabus zai iya taimaka musu su ɗebi ruwan a sauƙaƙe." Sa'adda sarki Azmul gallar yazo nan a zancen sa sai Jafar ya dube shi yace, "Ya kai wannan sarki kayi sani cewa mu yanzu mun shiga cikin kundin tsatsuban shamharu munga irin bala'in dake ciki,kai kuma naka kundin mai ya ƙunsa?" Koda jin wannan batu sai sarki Azmul gallar ya ƙyaƙyale da dariya, sannan yace, "Ni nawa kundin tsatsuban babu komai a cikin sa face labarun nan na da dana yanzu na abubuwan al'ajabi dana tausayi waɗanda suka faru a tsakanin bil'adama tun daga kan mutanen farko kawo izuwa na yanzu. Kuyi sani cewa a cikin wannan kundi nawa akwai hikayoyi guda dubu a cikin sa,haka kuma a cikin kowace hikaya akwai labarai dubu. Idan har kuna son kuji kaɗan daga cikin irin waɗannan hikayoyi masu daɗaɗan labarai,ku nemi wani littafi mai suna "HIKAYA DUBU." Yanzu littafin HIKAYA DUBU na nan a cikin birnin Misra a cikin gidan tarihin su a ƙarƙashin wata akwatu wadda aka sa wani gunki mai suna SARUƘ. Wannan littafi ba zai taɓa ganuwa ba a wajen kowa ba sai nan da shekaru arba'in masu zuwa,don haka bana tsammanin zaku kai wannan zamani saidai 'ya'yan ku. Zaku iya bar musu wasiyya don suje su duba littafin su karanta daɗaɗan Hikayoyin dake cikin sa. Da wannan jawabi nake muku sallama sai mun sake saduwa a karo na uku." Sarki Azmul gallar na gama wannan jawabi ne macijiyar nan ta sake haɗiye su Jafar suka tsinci kansu a gaban kundin tsatsuba,kuma shafi na ɗari uku da ashirin da biyar ne a buɗe. Take shafin ya karanto kansa,sannan ya zuƙe su suka faɗa cikin kundi. Haka dai suka yi ta tafiya a cikin kundi suna haɗuwa da masifu kala-kala a wurare dabam dabam sai da suka shiga har cikin shafi na ɗari shida da hamsin. Sannan aka sake watso su tasu duniyar ta cikin kundin tsatsuba. Wannan shine abinda ya faru gasu Jafar bayan sun baro birnin Hasiyatul Lauras inda suka yi mugun artabu da dodo Abulungu a cikin kundin tsatsuba. (Wanda yanzu kuma sun zo shafi na ɗari shida da hamsin). ***************************************** Al'amarin bokanya Samaratu kuwa wato mahaifiyar markahus sabus lokacin data baro fadar shamharu sai tayi ta tafiya har ta iso duniyar ƙasa. Sannan ta nufi garinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sauka a tsakiyar farfajiyar gidanta. ####################### To masu karatu,iya inda nawa littafin MIFTAHUL ZARBIL na biyu 2 ya tsaya kenan,sauran duk sun falle,wannan iya rabin littafin ne. Amma bari nayi muku summarizing ɗin abinda ya faru a iya na littafi na biyu 2. *************************** Bokanya Samaratu ta isa gidanta,sannan kuma tayi bincike akan ɗanta wato markahul sabus,taga duk abinda ya faru dashi tun daga lokacin da suka samo narkakken dutse,zuwa duniyar ƙasa wato inda suka samo duwatsun wuta ma'ana duniyar su Sarudul Makam da 'yan uwansa. Har taga lokacin da yayi imani da ubangijin musulunci har kuma sa'ilin da aljani Durmazalu ya shammace shi ya sumar dashi da wannan shuɗin hayaƙi. Wannan al'amari ya jefa bokanya Samaratu cikin tsananin baƙin ciki inda ta cika da tsananin fushi ta tafi neman markahul sabus don ta tilasta shi ya fita daga musulunci. In baku manta ba,a cikin littafin matsatsubi na uku 3 boka shamharu ya kama su markahul sabus harda Samaratu inda ya tura su su samo abubuwa ukun da zai ƙera kubar MIFTAHUL ZARBIL dashi,amma ya riƙe Samaratu a wajensa yace saidai idan sun kammala aikin su sannan zai sake ta kowa ya kama gabansa. Wannan kenan. Toh da yake ban karanta miftahul Zarbil na ɗaya 1 ba,ni dai abinda na fahimta shine Shamharu ya tafi izuwa wata hallarar tsafin sa inda ya bar bokanya Samaratu anan fadar sa ta Bahar zus. Inda bansan ya akayi ba Samaratu ta kuɓuta sannan ta samu wani gagarumin ƙarfi har siffar jikinta ta sauya har fuka fukanta suka zamo guda miliyan ɗaya,sannan kuma ta hallaka gaba ɗaya dakarun shamharu dake bahar zus. Ban san ya shi kuma Lu'umanu ya kuɓuta ba. Wannan kenan. To Samaratu ta tafi neman markahul sabus don ta tilasta shi ya fita daga musulunci. To shi al'amarin markahul sabus kuwa,bayan ya farfaɗo kawai sai ya duba yaga ba abokanan tafiyar sa,anan ne yayi tunanin tabbas yaudarar shi suka yi. Kurum sai ya tsaya yana tunani,daga ya nufi birnin Teheran,wato birnin sarki Lu'umanu saboda yadda Lu'umanu ya kulle shi a kurkuku tsawon shekaru hamsin in ban manta ba. Shi kuma Lu'umanu bayan ya baro fadar Bahar zus sai shima ya nufi birnin sa na Teheran,da ya isa sai ya iske har sun naɗa sabon Sarki. Nan take Lu'umanu kuma ya bayyana,koda suka ganshi sai dukkanin su suka firgice,babu wanda yafi tsorata face wanda aka naɗa a matsayin sabon sarki. Anan Lu'umanu ya tambaye shi akan wannan babban ganganci da yayi,sai sabon sarkin yake sanar dashi cewa ai rabon shi da birnin tsawon shekara shida kenan. Abin ya baiwa Lu'umanu mamaki,yace raina masa hankali yake son yi,inda sabon sarkin ya gabatar da shaidar shi wato wani zaki wanda yake a cikin gidan sarautar. Shi kuma Lu'umanu tabbas yasan zakin domin da hannun sa ya kamo shi tun yana ƙarami kuma gashi zakin yanzu ya girma sosai. Anan Lu'umanu ya yarda amma da yake azzalumi ne sai ya dubi sabon sarkin yace,duk da haka hukuncin kisa ne a kansa tunda ya zauna akan karagar sa😂😂😂. Harya ɗaga takobin sa zai sare kan sabon sarkin nan sar kurum ga markahul sabus ya diro, sannan ya nuna Lu'umanu da ɗan yatsa yace shine ya kulle shi a kurkuku a cikin akwatin ƙarfe shekaru masu tsawo,amma daga yanzu zaluncin ya ƙare,kuma muddin yana so ya ƙyale shine ya karɓi addinin musulunci, Lu'umanu yace bai san zance ba,shi da musulmai sai yaƙi. Anan ne suka kaure da faɗa,su faɗa nan su faɗa can,a inda markahul sabus ya tumurmusa Lu'umanu ya shaƙe shi,har Lu'umanu ya fara kakarin mutuwa ne kurum sai markahul sabus yaji an sure shi anyi sama dashi. Shi kuma Lu'umanu ya tsaya yana shafa wuyan sa. Karku manta,ni dai ban san ya akayi Lu'umanu ya tsira ba harya dawo Teheran,amma dai wannan asalin Lu'umanu ne, ma'ana asalin ruhinsa ne a gangar jikin sa. Shi kuma markahus sabus sai da akayi can sama dashi sannan ya ganshi a cikin kejin ƙarfe sannan yaga mahaifiyarsa. Anan nake maku sallama da fatan Alheri, tare da fatan idan an samu MIFTAHUZZARBIL na uku to zaki GA mun ci gaba da yardar Allah. Nagode. Najibullahi Muhammad #legends