[1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu 1&2 Da sunan Allah mai Rahma mai jin qai,ina sake yiwa Ubangiji godia daya nuna min ranar dazan fara posting wannan labarin lafiya,littafin ME 'DEBE KEWA na dad'e da fara rubutunsa,tun kafin na rubuta littafin MAWAHIB nake faman rubutu akan littafin ME 'DEBE KEWA,idan har akwai wani sharri wanda zai amfani al'umar Annabi asandin wannan labari,ina roqon Allah karya bani damar dazan kaishi qarshe,ina roqon Allah yasa na rubuta abinda zai amfani al'uma baki d'aya,Alkhairin dake cikin wannan labarin ina roqon Allah ya sadamu dashi,ina roqon ku kada kuyi amfani da qyale-qyalen dakukaci karo dashi acikin wannan labari,kuyi amfani da darasin da littafin yazo muku dashi,ina Addu'ah ga duk wasu mata iyayenmu da qannanmu,da yayunmu masu juna biyu ubangiji Allah ya saukesu lafiya,wanda suka rigamu gidan gaskiya da wanda sukai rashin iyayensu Allah yaji qansu yayi musu Rahma,Allah yasa Aljannah ce makomar mu baki d'aya,Allah yayi mana tsari da talauci,Allah ya sauqaqa mana wannan yanayi na matsin rayuwa damuke ciki. ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,naso in kawo muku shi tun 2023 kamar yanda na saba kawo muku littafi sau biyu a shekara,amma Allah bai nufa ba sakamakon wasu uzurirrika dakuma salon bincike da labarin yazo min dashi. Akwai wanda suke siya littafi na,saisu koma gefe su dinga siyar dashi,ban yarda ba,ban amince ba,ko kad'an daga cikin labari na ban yarda ajuyamin ba bare asiyar dashi,babu kyau shiga haqqin mutum bare kuma d'an uwanka musulmi. Wannan labari gaba d'ayansa na sadaukar dashi ga dukannin masu Suna BILKISU,yanda sunan littafin yazo ME 'DEBE KEWA, ina Addu'ah Allah yasa ya 'DEBE muku KEWA. Lokacin dana rubuta littafin MAWAHIB,dayawa daga cikin masoyana suna min complain littafin yayi tsada,dan Allah na rage suna so su siya,harma da wanda suke cewa dan Allah inci gaba da rubuta labari akan farashin 300 Naira,nikuma ina ganin ai dad'in labari shi kesa mutum ya siyeshi ko naira nawa aka sa,to kunfi qarfina 😣, dama saboda ku Amnah take rubuta littafi,idan babu Readers babu rubutu,kamar yanda kuka roqa gashinan littafi daidai da aljihunku,dan Allah idan kinsan zaki siya ne domin ki dinga fitar min dashi zuwa group to wallahi na haqura da 300 dinki😭 Ku riqemin amana dan Allah,duk wacce taga tayimin magana ta private ban saurareta akan lokaci ba,tayi haquri,tayi haquri,tayimin uzuri dole zan saurare ta saboda Amina ta kowa ce,ta dukkanin fan's dinta ce🥰 ME 'DEBE KEWA naira 300 ne kacal,duk wanda yakeson wannan labari zai iya yin payment ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Tareda turo shedar biya ta wannan number 08033300034 masu tura kati transfer kokuma photon Kati,zaku iya turowa ta wannan number 08033300034 _____ Garin Malam...Hadejia Area,Jigawa State. { 1986.} Shekaru Talatin da Bakwai baya. Gidane d'an qarami wanda yake d'aukeda d'aki qwaya d'aya jal ginin qasa,be samu arziqin samun Katanga irinta d'akin ba,wato katangar qasa,saide yasamu arziqin samun katangar zana,ita kanta zanar da'akai katangar da'ita batakai har qarshe ba saida kara aka qarasa ta. Gidan abushe yake qaraf bashida komai face wata madedeciyar bishiyar maina me mutuqar sanyi,kana ganin gidan kasan gidan wani mashahurin talaka ne futuk wanda bashida cin yau bare na gobe. Kyakykywar mace me shekaru aqalla talatin da biyar tagama share gidan daqyar saboda tsohon cikin datake dauke dashi me mutuqar girma haihuwa yau ko gobe,gumin fuskarta ta share,ta nufi qasan bishiyar gidan ta zauna tana maida numfashi tareda lumshe idonta tanajin dad'in is'kar datake kad'awa,jingina tayi da jikin bishiyar hakan yasa d'an kwalin dake d'aure akanta yazame yafad'i,wani uban gashi me sheqi da bala'in tsawo ya bayyana,gashin nata baqi ne sid'ik,ita kanta idan ka kalleta karon farko zaka tabbatar matar manya ce,asalin kalar farar fatarta zaisa kagane cewa ba 'yar Nigeria bace. Ahankali tajuya ta kalli d'akinsu da tsakar gidan wanda babu komai yaqare,babu abinda zata samu tasa acikinta,amma duk da haka cikin dauriya ta shafa qaton cikinta tace"kayi haquri kaji,Babanka zaizo yakawo mana abinci" Kafin ta d'auke hannunta daga kan cikin,mijinta yashigo gidan bakinsa d'auke da sallama,tun kafin ya qaraso inda take yagama qare mata kallo yana sake yiwa Allah godia daya azurtashi da Samun mace kamarta, yasan cewa banda qaddara da qudurar ubangiji itadin ba sa'ar aurensa bace,amma sai gashi ubangiji bai dubi hakanba, ya mallaka masa ita amatsayin mata d'aya tilo. Zama yayi kusa da'ita har jikinsa yana gogar nata,ya kalleta cikeda kulawa da tsantsar so sannan yace"Mai Gadon zinare yakike zaune haka kai babu dankwali?" Murmushi tayi dimples dinta suka bayyana,wanda suka sake qawata kyawun fuskarsa na asalin buzuwar qasar Nijar,cikin shauqin qauna tasaka hannunta tafara tattare dogon gashinta,cikin sauri yasaka hannunsa yana tayata tattare gashin,cikin jin dad'i tace"Malam zafi naji,bansan lokacin da dankwalin yafad'i ba,da alama de yau kasamo mana abinci,na ganka da farinciki" Murmushi yayi,sannan yasake gyara zamansa yana fuskantarta "wato Bilkisu duk lokacin dana tuna inada mace kamar ke acikin gidana,hankali na yana kwanciya,duk rashin kud'i na da talaucina,inde na kasance tare dake kina 'DEBE MIN KEWA,ina farinciki ne saboda nasamo mana kud'i masu yawa har kimanin naira dubu d'aya" ya qarasa maganar yana futo da kud'in daga aljihunsa ya ajiyesu agabanta. Takardun naira ashirin-ashirin ne dayawa sai kuma qwandaloli da ficika. Kyawawan fararen idonta ta zaro,cikin tsananin mamaki dakuma ganin yawan kud'in yasa ta kalli mijin nata tace"Malam Ina kasamo wannan kud'ad'en masu yawa haka?" "kekena nasiyar Bilkisu,lissafa kigani cefanan kwana nawa zai mana?" Manyan idonta ta lumshe sannan ta bud'e,taja hannunsa guda d'aya tad'ora akan qaton cikinta,cikin damuwa ta kalli mijin nata tace"dani da d'ana zamu jure duk wata yunwa amma ba zamu jure ganinka babu abinda kake sana'ah dashi ba,yanzu daka siyar da kekenka dame zaka dinga dako kana samo mana abinci?,meyasa kasiyar?" Kansa ya sunkuyar qasa cikeda damuwa da rashin sanin makomarsa,cikin nata ya shafa sannan yace"Bilkisu bake kad'ai bace,idan ban sai dashi ba mezan baku kuci?" Hannunta tad'ora akan nasa hannun wanda yake kan cikinta sannan tayi murmushi dimples dinta suka futo ta kalli cikin idonsa tace"shima yaron cikina zaiyi haquri,yasan cewa yau Babansa bai samo mana abinci ba" Cikin jin d'adi ya kalli fuskarta yace"Bilkisu waye yace miki namiji zaki haifa ne?" Cikinta ta shafa cikin kulawa dajin dad'i tace"Babu Wanda ya fad'amin,amma Ina fata,Ina Addu'ah Allah ya azurtani da d'a namiji,zan saka masa sunan mahaifina sannan kuma sunan fiyaiyen halittafi Annabi Muhammad (s.a.w)" Murmushi yayi,ya kalli cikinta sannan yace"Bilkisu ko mace kika haifa,ko namiji, zanyi farinciki da duk abinda kika haifamin,kuma ko abinda na mallaka zai qare gaba d'aya,insha Allah abinda zamu haifa sai yayi karatun Boko,kwanaki dana shiga qasar Hadejia,Naga wani yaro matashi yasa wannan baqaqen kayan(Suit) irinta manyan ma'aikata,yana magana yana zaro turanci sai abun ya birgeni,naji duk duniya babu abinda nakeso irin boko,amma tunda ni Allah yasa banida rabon yin boko har iyayena suka rasu, insha Allahu zan tsaya tsayin daka,Inga jinina yayi karatun boko,sannan...." Kafin yaci gaba da magana suka jiyo ana kwad'a sallama a qofar gida. Tashi yayi yafita,yana zuwa qofar gidan nasa yaci karo da mutane kusan su bakwai,d'aya daga cikinsu mai kimanin shekaru ashirin da takwas yace"Malam MANU kud'in bashin mu mukazo kar6a,duk wanda kagani anan yaji labarin kasaida keken kane shine ya biyo bayanka kabashi haqqinsa,amma inaso kafara sallamata saboda bashina yakusa shekara biyu a kanka kullum kalmar haquri kake fad'amin" Malam Manu yayi shiru kamar an doka masa sanda,yasauke wata nannauyar ajiyar zuciya yad'ago kansa ya kallesu yace"jama'ah,dan Allah kuyi haquri,ku rufamin asiri kamar yanda Allah yarufa muku,wallahi zan biyaku bashin ku,bamuda abinda zamu ci nida iyalina...." 'Daya daga cikinsu wanda yadan manyanta yace"kaga dakata malam Manu,yaushe mukai dakai zaka biyani kud'ina?" Cikin sanyin jiki yace"Tun wata uku dasuka wuce yadace nabiyaka" Cikin rashin tausayi mutumin yameqa masa hannu sannan yace"to Alhamdulillah,qirgosu naji d'uminsu..." Malam Manu baisake cedasu komai ba yajuya yashigo gida,baqin ciki da taqaici yasa baisan lokacin dayaji wani irin hawaye mezafi yazubo daga idonsa ba. Tana ganin haka tasan cewa ba qalau ba,tashi tayi daqyar ta qarasa wajansa,cikin damuwa tace"Malam meyake faruwa? Yanaga jikinka a sanyaye mutuwa akayi?" Hawayen idonsa yashare daqyar sannan yace"Bilkisu masu kar6ar bashi ne,nabasu haquri sunqi tafiya,Ina murna na saida kekena zamu samu abinci ashe duk da haka ban tsira ba,bamuda komai a gidannan wanda zan d'aga in siyar,babu abinda yarage min saide wannan kayan na jikina zan saida musamu muci abinci" Ya qarasa maganar yana mata nuni da kod'ad'd'an yadin dayake jikinsa. Cikin son kwantar masa da hankali tace"ya'isa,kayi haquri kadena kuka Ina zuwa" Dan kwalin kanta tacire,dogon gashinta na asalin buzuwa ya bayyana,ta warware dankwalin tayafashi akanta sannan ta qarasa qofar gidan da sallama, d'aya daga cikinsu ne yazaburo tun kafin tayi magana yace"kudin ne?" Yayinda sauran suka qura mata ido suna kallonta saboda tsananin kyawunta dasuka gani,cikin zuciyarsu kuwa mamaki suke dama acikin wannan qauyen nasu na Garin Malam ashe akwai matan India aciki?🤔 Murmushin qarfin hali tayi tace"A a, kuyi haquri,dan Allah ku qara masa lokaci insha Allahu zai biyaku kud'in" Wanda yafara tambayarta kud'in da farko yanzu ma shine yasake yimata magana yace"kinga...idan kud'in ki kazo kawowa to kawo kiwuce, idan ba kud'in kika kawo mana ba,juya kituro mana Sulaimanu" Murmushi tayi idonta na kawo ruwa,sannan ta meqa musu dubu d'ayan hannunta wanda malam Manu yabata,cikin rawar murya tace dasu "gashi" Babu musu suka kar6a, lokaci d'aya hawaye yazubo daga cikin idonta zuwa kan farar fatar fuskarsa,hawayen ta goge tace"dan Allah kubamu ko naira ashirin ne mu sayo wani abun muci..." ko sauraren ta ba suyi ba suka fara fad'a akan kud'in kowa yanaso a bashi kasonsa aciki,saboda kud'in sunyi kad'an akan yanda sukebin Malam Manu bashi, ahankali ta girgiza kanta tajuya tadawo gida tana jiyo hayaniyar su suna fad'a akan yanda za'a raba kud'in. Zama tayi akusa dashi baisan ma ta'iso ta zauna ba yayi nisa acikin tunanin halin dasuke ciki,shiba kowa ba duk danginsa sun rasu, ita ba kowa ba dan'uwan ta qwaya d'ayane shima yana qasar nijar,ya kalli katangar gidansa ta Kara da zana gaba d'aya duk ta mutu gara ta cinyeta kad'an yarage afara ganinsu daga waje,kana ta6ata zata Iya fad'uwa. Maganar data masa ne yasa yadawo hayyacinsa,yasaka hannu yagoge hawayen idonsa bayan yagama jin kalaman ban haquri daga matar tasa. Wani yaro ne yayi sallama da wata roba a kansa,yana zuwa yabata robar yace"Balki ME GWANJO waiga niqa inji innata" Cikin sauri ta kar6i niqan tareda ladan niqan nata naira goma,ta dubi yaron tace"to Ashiru kadawo anjima kad'an ka d'auka mata" Yaron Yajuya yafice da gudu,batayi qasa a gwiwa ba tatashi takoma wajan datake niqa da dutsin niqa irinna da can,tsumma tasa tagoge jikin dutsin, sannan tafara zuba geron akan dutsin, tadora wani dutsin d'an qarami Wanda ake riqe shi da hannu, sannan tafara niqa musu geron,yunwa tasa cikinta ya murd'a,lokaci d'aya wani irin hawaye yazubo mata,tasaka bayan hannunta ta share taci gaba da niqan. Tsaf tagama yin niqan burabusko ta ajiye musu agefe, sannan ta dawo wajan Malam Manu dayayi tagumi hannu bibbiyu yayi zurfi cikin tunani tazauna sannan tabashi naira goman da Ashiru yakawo mata ladan niqan datayi, ta meqa masa kudin tace"Malam kayi haquri kadena tunani dan Allah,duk wani tsanani yana tareda sauqi,kaje ka siyo mana gari da siga ashago sai musha" Cikin sauri ya kar6i kud'in sannan yatashi tsaye yace"to Bilkisu,ubangiji Allah yayi miki Albarka" Cikin kulawa ta amsa masa,sannan ta kwanta tana maida numfashi tareda shafa qaton cikinta tanajin tsananin qaunar cikin tana sake ratsata. Malam Manu bai jimaba yadawo hannunsa daukeda garin kwaki da siga,shine yajiqa musu,yadawo yazauna akusa da'ita yace"Bilkisu tashi musha gaarin" Saida ta runtse idonta sannan tatashi daqyar,tazauna tafara sha. Canjin hannunsa daya rage na qwandala biyu ya'ajiye agabanta yace"ki adana wannan canjin a wajanki ko zaki sai wani abu,garin nera biyar nasiyo mana,da siga na naira uku,yau nayi muku horon yunwa keda abinda ke cikinki Bilkisu kiyi haquri" Cikin kulawa tace"Babu komai malam" Basu sake magana ba har suka kammala cin garin, sannan yayi mata sallama yafita nema,sai alokacin tasamu nutsuwa,qarfin jikinta yadawo harta samu damar gyangyad'i anan qasan bishiyar. Baidawo gidan ba sai yamma lis,hannunsa d'aukeda baqar leda,alokacin tana zaune tana tunanin yanda zatayi tasamu kudi taje tasaro kayan gwanjo kamar yanda tasaba siyarwa kafin jarinta ya karye. Zama yayi kusa da'ita yace"Bilkisu ga gaarin kwaki nasake samo mana" Wani irin farinciki ne ya wanzu a fuskarta,ta kalleshi da kulawa "Ina kasamu kudi Malam?" Cikin farinciki yace"bakin titi naje na zauna, sai Allah yakawo wani baqo,na kar6i kayansa nayi masa dako,yad'auki naira hamsin yabani,shine naje shago nasiyo mana garin kwaki dashi,kinga ai zamu dade muna ci" Gaarin taduba tagani sannan tamaida dubanta gareshi tace"ai kuma babu abun had'i malam,ko zaka daure kamaida masa saiya rage gaarin yasako mana siga na canjin?" Saida malam Manu yayi jimmm...sannan yace"eh kema kuma kince wani abu,to bari naje nakai masa,duk abinda kikace ai haka za'a yi Mai gadon zinare..." Murmushi tayi batare datace masa komai ba,har yaje yadawo tana tunanin mafita akan yanda za'a yi tasake Samun jarin kayan gwanjo amma tarasa mafita. Bayan sunyi shirin bacci da daddare tanajin yanda yake shafe mata jikinta da Addu'ah,ta kalli kyakykywan Black Beauty d'in mijin nata tana yaba irin kulawar dayake bata duk da bashi dashi,cikin qasan zuciyarta tanajin qaunar sa tana sake ninkuwa aranta,cikin kulawa dawata irin soyaiya tace"SULAIMAN...." Cikin sauri ya kalleta,saboda zai Iya cewa yadad'e rabon dayaji Bilkisu takira sunansa kai tsaye,saide Malam,amma yasan cewa duk yanda akayi maganar dazata fad'a masa tabbas mai muhinmanci ce,cikin kulawa yace"na'am mai gadon zinare" "inason ganin qanina FAROUQ,inaso bayan na haihu kayimin qoqari nasamu naje naganshi,idan ba'a samu kud'in ba,to kasamu ko saqon wasiqa ne atura masa,baisan inada ciki ba,tabbas da yasan halin danake ciki,zaizo yaganni" "Bilkisu wannan ne abun dakike buqata?" Ahankali ta d'aga masa kanta alamun amsawa. Ajiyar zuciya yasauke yace"nayi miki alqawari insha Allah zanyi abinda kikace Bilkisu,kina haihuwa dazaran kin zubar da wanka zamu shirya ni dake muje can nijar d'in kiga danginki,kinga nima nasake ganin FAROUQ d'in,rabona dashi tun bayan aure na dake" Daganan yad'aga hannayesa yayi karatu yatofa acikin hannun nasa, sannan yasake bin jikinta yana shafa mata addu'ar har hannunsa yasauka akan manya-manyan nashanunta,wani irin numfashi ta sauke najin dad'i,tanajin yanda yake murza mata nashanunta ko kad'an batayi kuskuren hanashi ba,daga baya ya lalla6a ya kwanta,yanaci gaba da abinda yake har yayi nasarar futo dasu waje yad'ora bakinsa akai,wani irin numfashi taja med'an qara wanda yake nuni da cewa taji dad'in abinda yafara d'in,wannan dalilin yana d'aya daga cikin abinda yasa take qaunar Manu,kuma tayi haqurin zama dashi saboda shid'in ba baya bane ta wannan Fannin,ya'iya sarrafa mace sosai. Tsawon lokaci yana abu d'aya kamar jariri,ahankali tasaka hannayenta tariqe fuskarsa dashi,cikin sanyin murya me cikeda kasala dajin dad'i tace"meyasa Manu na baya gajiya da shan wannan abun ne?" Murmushi yayi yace"ajinina abun yake Bilkisu,bazan Iya daina soba,koda abunda yake cikinki yazo wannan duniyar,bazan Iya barmasa yadinga sha shi kad'ai ba"(🙈) Murmushi tayi me sauti,bata qara cemasa komai ba,hakanne yabashi qwarin gwiwar jiyar dasu wani irin dad'i wanda yasa suka manta da hali dakuma quncin rayuwar dasuke ciki. Washegari da safe garin kwakin daya siyo musu jiya shi suka jiqa sukasha,sannan yayi mata sallama yafita,bai dad'e da fita ba aka kawo mata wankau,babu musu ta kar6a tazauna tafara wanke musu kayan tana daga zaune,tana cikin shanya kayan wankin aka sake kawo mata surfen dawa,shima ta kar6a ta surfa ta bushe musu,tanemi waje ta zauna ta qirga kud'ad'en data samu yakama naira dari biyu da hamsin,kudin ta ajiye agefenta, sannan ta zubawa tafin hannunta ido tana kallon yanda hannunta yayi wani iri,uwa uba gefen hannunta duk yayi kanta gashi hannun yayi wani irin tauri kamar ba hannun mace ba,amma data tuna yawan kudin data samu har d'ari biyu da hamsin sai hankalinta ya kwanta ta manta da batun halin da hannun nata yake ciki,taji komai yawuce. Hijabin ta ta d'auka tazura, sannan ta nemi niqab dinta ta d'aura,tafuto tanufi gidan Tabawa me kayan gwanjo,gaba d'aya kudin hannunta tabata,tasiyo wasu daga cikin kayan gwanjo na yara,bata koma gida ba saida tabiya wajan wata tela tarage mata fad'in kayan,sannan ta nufo gida tashiga maqotanta tana shaida musu cewa ankawo kayan gwanjo. Bayan Malam Manu yadawo ta nuna masa,yayi farinciki sosai yayi mata Addu'ah akan Allah yasa albarka, Washegari da safe bayan malam Manu yafita itama shiryawa tayi kamar kullum tasaka niqab dinta tashiga cikin gari,tana tafiya ahankali tana shiga gida-gida tana tallar gwanjon kayanta,kasancewar yanayin damuna ake ciki hakan yasa bata dawo gida da kaya ko d'ayaba,dukansu ta saida su tas. Cikin farinciki tadawo gida ta zauna ta qirga kud'in da ribar data samu dakuma uwar kud'in gaba d'aya kud'i suka koma naira d'ari bakwai,cikin farinciki ta d'aga hannunta tafara godewa Allah bisa ni'imar dayayi mata,dakuma nasibin datake dashi akan kayan gwanjo. Malam Manu kuwa bai nufo gida ba sai yamma lis, yana cikin tafiya yaga mutane sunsha gabansa,cikin tashin hankali yaja yatsaya saboda ganin gaba d'ayansu babu wanda baici bashi awajansa ba,ciki harda Aminu me shago wanda yaje ya kar6i bashin alabo a wajansa tun Bilkisu tana laulayin ciki,cikin qarfin hali malam Manu yace"Aminu ya akayi kukasha gabana kuka tareni haka babu magana,aiko hannu kwabani mu gaisa ko?" Cikin tsantsar rashin kunya Aminu yace"Malam Manu munji labarin ka saida kekenka harka samu sukunin biyan bashi amma mu dayake munyi shiru mun zubama ido shine kahanamu namu kud'in,to munga alama kud'ad'en mu kariga kaci ham,ba futowa zasuyi daga hannunka ba,danhaka gara muyi maka dukan kud'inmu ko zamu huce taqaici..."(🙆🏻‍♀️) Cikin sauri Malam Manu yace"ku tsaya kuji,kuyi haquri nayi muku bayani wallahi suma wanda suka kar6i kudin..." Basu bari Malam Manu yagama magana ba suka rufeshi da duka saida suka kaishi qasa,daqyar wani tsoho daya dawo daga gona ya qwaci malam Manu a hannun su,gaba d'aya sun nuna masa jiki,gefen bakinsa ya fashe saida wannan tsoho yabashi sauran ruwa irin wanda ake tafiya dashi gona ya wanke bakinsa, sannan yabashi haquri suka rabu. Koda ya koma gida bai fad'awa Bilkisu abinda yafaru ba saboda kada hankalin ta yatashi,cikin sanyin jiki Yanemi waje yazauna jikinsa ko'ina yana masa ciwo,umarni yabata tadafa masa ruwan wanka,cikin farinciki kuwa tatashi tadora masa ruwan, yaga sai fara'ah takeyi kamar gonar auduga da alama zata bashi wani daddad'an labari ne,ido yazuba mata yana aikin kallonta,yana tuna irin baiwar da Allah yayi mata na kyau dakuma shi Karan kansa baiwar da ubangiji yamasa na Samun ta amatsayin mata, ya tabbatar da'acikin birni suke babu yanda za'a yi manyan masu kudi su barshi ya auri Bilkisu,duk wani kai kawo datake yana kallonta kamar yasamu tv. Koda yafuto daga wanka shiru yayi yana kallonta yayi jirim...kamar wanda aka masa albishir da mutuwar sa. Baiwar Allah Bilkisu batasan yana mata wannan kallon ba,saida ta juyo ta fuskanceshi sannan tace"Malam meyafaru?naga yanayin ka ya sauya meyake damunka?" "Bilkisu duk lokacin danake tare dake inajina wani mutum na daban,kina 'DEBE MIN KEWA aduk lokacin dana kasance cikin qunci ko tunani,babu abinda yake damuna Ina tunanin hanyar dazanbi ne domin insamo kud'in dazan siya miki raagon suna tunda kin shiga watan haihuwar ki" Murmushi tayi ta kalleshi tana sakin ajiyar zuciya tace"saboda wannan kake tunani? to Abishirinka,ga kud'in kayan gwanjon dana siyar d'azu naira d'ari bakwai ne,ka ajiyesu awajanka kafara tarawa insha Allahu zamu tara kud'in abun suna" Cikin farinciki ya kar6i kud'in yana kallonta yace"Bilkisu bai kamata ki tara kud'in abinda zamu siya ayi miki yanka dashi ba,wannan haqqinane amatsayina na uba" Cikin rashin damuwa tace"karka damu Malam,zan iya sadaukar maka da komai nawa inde zamu taru mu rufawa kanmu asiri,kasaki ranka muyi farinciki malam,ubangiji yana sane damu" Cikin farinciki Malam Manu yace"hakane Bilkisu,Allah yayi miki Albarka,Allah yabaki abinda kikeso duniya da lahira Bilkisu" Cikin farinciki tace"Amin Malam" Kallon kud'in hannunsa yayi,yad'ago kansa ya kalleta lokaci d'aya jikinsa yayi sanyi,kallonta yake kamar ba gobe,saide kwata-kwata batasan yanayi ba,zuciyarta tana cikeda farinciki ta kyautatawa mijinta, tasa shi walwala,akoda yaushe fatan ta tayi sana'ah ko zasu samu su rufawa kansu asiri shiyasa kowa yasanta a unguwar inde aikin hannu ne,babu abinda batayi,itace niqan dutsi,wanki, surfe,dakuma saida kayan gwanjo idan tasamu ribar kud'i me yawa. Da daddare shine yayi mata Addu'ar bacci kamar yanda suka saba,sama-sama take jinsa yana tofa mata Addu'ah saboda agajiye take tilis nan da nan wani irin nannauyan bacci ya kwasheta. Yayinda Malam Manu yakasa runtsawa yasata agaba yana kallonta kamar bai ta6a ganinta ba,jikinsa yayi mutuqar sanyi,ahankali yasaka hannunsa ya shafa cikinta,sannan ya shafa fuskarta, wani irin hawaye yazubo daga idonsa,yadad'e yana hawaye har kusan qarfe uku nadare,ahankali yatashi yaduba takarda ad'akin,akwai wata tawada ta rubutu itama yad'aukota yayi rubutu ajikin takardar da Ajami. kasancewar a wannan lokacin be'iya Boko ba,amma yasan yanda zaiyi rubutu da Ajami,hawayen idonsa ya share ya ninke takardar ya ajiyeta agefen fuskarta,yabude dakin yafuto, ya qarewa gidan nasu kallo, yafashe dawani irin kuka sannan yafice daga gidan cikin sauri.(😭) Kiran sallar farko ta farka taji ana sheqa musu ruwan sama,tashafa gefenta bataji malam Manu ba,sai tayi tunanin ko yana tsakar gidane yana tattara musu 'yan tarkace,tasake juyi daqyar saboda girman cikinta, taci gaba da baccinta,bata sake farkawa ba saida gari yayi Haske,cikin fad'uwar gaba ta yunqura tatashi tana salati saboda wani irin mummunan mafarki da tayi,saita danganta hakan da rashin yin sallar asuba da batayi ba akan lokaci,tamiqe tana hamma ta tattare dogon gashin kanta daya warware saboda bacci,tafuto tsakar gida taga yanda tabar komai jiya,haka yake yana nan yanda yake,a fili tace"to malam kode shima yau ya makara ne? bai tasheni sallah ba,ga gida yana nan yanda na barshi na kwanta,kode yana band'aki ne?" Ta d'aga murya tace"malam!!" Taji shiru,ta d'auki buta tashiga band'aki tagama uzurinta tafuto tayi alwala tayi sallah,bayan ta idar da sallar haka nan ta tsinci kanta da rashin kwanciyar hankali,malam bai ta6a fita yaqi sanar da'ita inda yaje ba,koda tana bacci zai tasheta yafad'a mata,to ina yaje haka? Cikin hanzari tatashi tafuto tsakar gida gabanta yana fad'uwa,mayafin da tayi sallah dashi shine ajikinta tashin hankali yasa ko takan niqab d'inta batabi ba,suba wani d'akuna ne dasu ba bare tace yashiga ciki,d'akinsu ne qwaya daya jal kuma baya nan,qofar gida tafuto tana faman kiran sunansa, sai dube-dube take tana fad'in "Malam...!!" Amma shiru kakeji,wasu d'aid'aikun masu tafiya gona sai kallonta suke saboda sunga abun mamaki,basu ta6a tunanin akwai kyakykywar halitta kamarta acikin qaunyensu na Garin Malam ba,wani me Keke yazo wucewa shima zai tafi gona tsabar waigowar dayake yana kallonta har fad'uwa yayi sakamakon cin karo dayayi dawani tsoho. Tana ganin abunda yafaru tasan cewa itace sila,cikin sauri taja mayafin jikinta ta6oye fuskarta,sannan tajuya takoma gida,d'akinsu tashiga tafara tattare musu kayan Shimfid'arsu,anan idonta yasaauka akan wata farar takarda,gabanta ne yafad'i da ganin takardar cikin sauri tad'auka sannan ta bud'eta,lokaci d'aya taci karo da rubutun mijinta Malam Manu inda ya rubuta mata cewa ( KIYAFEMIN ) jikinta ne yafara rawa,taji numfashinta yana sama kamar zai d'auke,hakan yana nufin kenan Manu yagudu yabarta,daqyar tasamu ta fuzgo numfashinta tareda sakin wata irin gigitacciyar qara,wanda yajawo hankalin maqotanta. (so sad😭,sorry Mama Bilki) Littafin ME 'DEBE KEWA na kud'i ne,300 Naira kacal👌🏻 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034 Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu 3&4 maqotanta sunyi tunanin naquda ce ta taso mata,hakan yasa suka shigo a fujajan,anan suka tarar da bilkisu tana kuka tad'ora hannunta akanta,d'aya daga ciki ce tafara bubbuga bayanta alamar lallashi tace"Balki me gwanjo kiyi haquri,ciwo ba mutuwa bane" Cikin kuka da baqin cikin halin da tashiga tace"Manu ya gudu yabarni Bintu,bai duba maraicina ba yatafi yabarni da tsohon ciki" Wadda Bilkisu takira da Bintu saita zabura taja gefe guda jikinta yana rawa,d'ayar maqociyar tata kuwa duka hannunta biyu tasa tarufe bakinta hawaye yana zuba a'idon ta,cikin kuka tafice da gudu tabar gidan taje tafad'awa mijinta halin da'ake ciki. Kan kace me,labari yaje kunan mai Gari,Bintu tana rungume da Bilkisu tana lallashinta saide itama hawaye take zubar wa tana fad'in"kiyi haquri me gwanjo,insha Allahu muna nan tare dake bazaki tagayyara ba" Sallama suka jiyo daga qofar gida,Bintu taje taduba,mutumin dayake tsaye yace"kece Balki me gwanjo?" Bintu ta girgiza kai hawaye yana zarya daga idonta tace"Balki tana ciki" "kice mata megari yana kiranta,maqocinta yakai masa labari yanzu" Bintu batace masa komai ba tajuya,takamo hannun Bilkisu suka futo idanun nan nata yayi jajir abunka da farar mace,zama sukai agaban megari yayinda idanun fadawansa yadawo kan Bilkisu,wasu suna mata kallon qurulla wasu suna mata kallon tausayi, maigari yayi gyaran murya yace"Munsamu labarin abinda yafaru,kiyi haquri insha Allahu za'a ga mijinki,haqiqa Sulaimanu bai kyauta ba,kuma dole zai kar6i hukunci mai tsanani daga fada,maqociyarki fatsime tafad'awa mijinta Haruna gashinan a zaune,Haruna yazo fada ya sameni yafad'a min abinda yake faruwa,bamuyi qasa a gwiwa ba mun tashi matashi me hanzari akan Keke, mun turashi Garin Gandun Galadima yaje yanemo Sulaimanu,nasan duk inda Sulaimanu yake,bazai wuce garin Gandun Galadima ba" Rufe bakin megari keda wuya,dan aikensa yadawo,lokaci d'aya idanun fada yakoma kansa,cikin ladabi matashin yadubi maigari yace"Allah yaqarama lafiya mun bincika cikin Gandun Galadima kaf....babu malam Manu babu dalilin sa,da yiyuwar yayi nisa ranka ya dad'e" Bilkisu tanajin bayanin wannan matashi kanta yasara,cikinta yayi wata irin juyawa,lokaci daya tasaki qara tafara naquda afadar megari,nan take megari ya kalli Bintu da Fatsime maqotan Bilkisu yace"ku qarasa da'ita cikin gidana ta sauka acan har mugama binciken inda Sulaimanu yake" Babu musu fatsime da Bintu suka kama Bilkisu datake d'aga qafa daqyar saboda naquda tazo mata gadan-gadan sukai cikin gidan megari da'ita. Da taimakon 'Dayyaba matar maigari su Bintu da Fatsime suka had'u suka dinga tausar Bilkisu har Allah ya sauketa lafiya,ta haifi d'anta namiji kyakykywa dashi masha Allah,kallo d'aya zaka yiwa yaron kaji yashiga ranka,fari ne tas qato,babu abinda ya dauko na mahaifinsa sai yatsun qafarsa sak irinna Manu,babu rama atareda yaron 6ul6ul dashi kamar ba rainon Gaarin kwaki ba, bayan sun tsaftace su itada yaran haka ta rungume shi a qirjinta tana hawaye,gashi de abinda take fatan haifa Allah yabata,saide babu Manu,baisan me suka haifa ba,baisan awanne hali take ciki ba,baisaniba tana raye kota mutu ta dalilin haihuwar d'ansa,hawayen idonta ta share tazuba wa yaron ido tana kallonsa yayinda yafarka daga baccin dayake shima idonsa cikin nata,wani hawayen ne yasake zubo mata tana kallonsa tana murmushi ga hawaye,Fatsime ce tashigo takawo mata kunun kanwa,suka zauna agabanta suna sake bata haquri dakuma tabbacin insha Allahu za'a ga mijinta. Sai dare aka kawo mata dahuwar Jan nama umarnin maigari kenan,haka take cin naman amma daqyar take iya had'iyeshi saboda jin wani irin abu aqarqashin wuyanta wanda takeji kamar dutsi ne awajan tsabar damuwa. Washegari ma tasamu kulawa wajan matar maigari anyi mata wankan jego irinna mutanan da,taci dumaman tuwon dawa dakuma kunun kanwa,babu 6ata lokaci kuwa ruwan nonon ta yake zuwa yaronta yanasha yana qoshi. Da misalin qarfe goma shad'aya na safe kira yasameta daga maigari,wannan lokacin bayan Fatsime da Bintu maqotanta harda ita kanta 'Dayyaba matar maigari suka nufi fada,yaronta yana rungume a qirjinta ta qanqameshi,bayan sun zazzauna maigari yadubeta yace"Balki saide kiyi haquri,mun tura mutanan mu Garin Galadima jiya ba'a ga Malam Manu ba,munsake tura mutane cikin garin Hadejia da Gaarin Gabas,har zuwa Birniwa,amma babu labarin Mijinki Manu,wasu daga cikin masu zaman fada sunbawa fada shawara asake bincikawa, duk da haka fada batayi qasa a gwiwa ba munsake tashin mutane sun nufi yamma har zuwa garin Gujungu,amma babu Manu, babu Labarinsa" Lokaci d'aya Bilkisu tafashe da kuka harda shashsheka. 'Daya daga cikin masu zaman fada ya gyara zaman sa ya kalli Bilkisu sannan yakai dubansa wajan Maigari yace"Allah yaqara ma lafiya ai tunda akayi irin wannan nema ba'aga Manu ba to haqiqa yagudu yabi duniya,akwai manema aure dayawa anan,saboda haka kawai karaba wannan auren nasu,saita samu miji kamar de nid'innan sai tayi aurenta"(😲🤭) Cikin tsawa Megari yace"Rufe mana baki Bala" Yajuya ya kalli Bilkisu yace"Balkisu nasan danginki suna qasar Nijar,zakiyi haquri ki zauna damu har aga mijinki? Ina miki albishir zamu harhad'a miki kud'i kidinga sana'ar saida kayan gwanjo,tunda med'akina tafada min cewa duk garin nan,bayan Tabawa me saida kayan gwanjo babu wanda yakaiki samun nasibi akan saida gwanjo,zaki zauna tare damu?" Ba tareda tunanin komai ba,Bilkisu tagoge qwallar data taru a'idon ta tace"Zan tafi qasarmu Ranka yadade" Megari yace"to kiyi haquri kizauna damu idan anyi suna saiki tafi,kafin nan kema kin sake samun qwarin jikinki" Bata iya amsa masaba tatashi suka koma cikin gidan maigari,domin kuwa idan tace zatayi magana haqiqa kuka ne zai biyo baya. Zaman Bilkisu agidan maigari babu laifi,tana Samun kulawa kamar tana gidan iyayenta,matar maigari 'Dayyaba cikin kwana shida ta koya mata yanda zata dinga wankan yaronta,Bilkisu tanajin bala'in qaunar d'anta,koda yaushe idon yaron qur akan uwarsa kamar ba haihuwar kwana shida ba,haka itama Bikisun kullum idonta a kansa tanajin wani irin nishad'i idan ta tuna ko bata da kowa to tabbas tana dashi,tasan cewa koda kowa zai gujeta shikam yana tareda ita,ita kanta 'Dayyaba matar maigari jitake kamar ta qwace wannan yaro na Bilkisu,yaron abun sha'awa fari qal dashi kamar Mamansa. Yauda safe tanayi masa wanka tana masa surutu kamar tana magana dame hankali,bayan tasakashi acikin zani ta lullu6eshi tana qoqarin shafa masa mai ajikinsa ta kalleshi cikin sanyin jiki tace"Babanka yagudu yabarmu,nasan kai bazaka gudu kabar Mama bako?Mama tana sonka,karka gudu kabarta kaji? idan kabarni bazan iya jurewa ba,nima ina tareda kai Babana,yanda Babanka yagudu yabarmu insha Allahu saimun bashi kunya,insha Allahu saika mulki mutane dayawa a duniyar nan,kaine d'ana,d'anda nafiso fiyeda komai a rayuwata...." tana kaiwa nan ta sunkuya ta sumbaci goshin yaron. 'Dayyaba matar maigari tashare hawayen tausayin Bilkisu,sannan tajuya ahankali tafasa shigowa cikin dakin bayan tagama jin duk maganganun da Bilkisu take yiwa yaronta. Washegari tacika kwana bakwai da haihuwa,kuma a ranar aka sanyawa yaron Bilkisu suna MUHAMMAD kamar yanda ta buqata,yaro yaci sunan mahaifinta,Megari yasa mutanan gari sukayi karo-karo aka hada mata kudad'e masu yawa aka bata,a ranar kuma aka kira me photo yayiwa yaronta photo yace zaije cikin garin Hadejia ya wanko mata photon gobe zai kawo mata,a ranar taso tafiya amma saboda photon ta tsaya tasake kwana,washegari da safe kuwa me photo yakawo mata,tashirya yaronta tagoyashi,sannan itama ta shirya suka futo. Ba'iya maqotanta ne suka futo domin yimata rakiya ba,harda matar maigari da sauran 'yan unguwa duk suka futo qwansu da qwarqwatarsu domin yin sallama dame gwanjo,bayan tayi sallama da Megari tasake yimasa godia tajuya ta kalli gidansu,ta tuna irin rayuwar dasukai itada Sulaimanu,taji hawaye yanason taruwa a'idon ta amma ta daure batayi kuka ba,tasake tuna lokacin da iyayenta suke raye,suka damqa amanarta a hannun Manu,ashe Manu talauci zaisa ya gujeta,a wannan lokacin kam saida ta zubar da hawaye,tana kuka mutanan arziqin qauyen suna kuka haka tahau mashin suka tafi. Bayan sun futo daga Garin Malam, suka wuce Garin Galadima, sannan suka dauki hanya har zuwa cikin garin Hadejia, a Hadeja tahau motar Maigatari,bayan mota tacika,direba yaja Mota sukabi ta hanyar malam madori,tacikin Gumel suka shiga garin Maigatari daga nan suka d'auki hanyar bodar dazata kaisu cikin qasar Niger. *** *** *** Lagos Nigeria Alhaji ALIYU MEKU'DI yana tsaye agaban matarsa tana shirya shi,gefe guda kuma yana qare mata kallo yanajin tsananin qaunarta duba da yanda bata ta6a gajiyawa wajan yimasa hidima tun bayan da'aka d'aura musu aure tsawon wasu shekaru masu yawa. Wani tsadaddan turare ta d'auka mai mutuqar tsada tafara fesa masa ajikin d'anyar shaddar sa wadda kallo d'aya zaka yiwa shaddar kasan cewa ba shaddar yara bace saide manyan attajirai,cikin murmushi ta kalleshi cikeda soyaiya tace"yau ina cikin farinciki mijina abin Alfahri na zai sake bud'e sabon Company aqasar Niger,ina Addu'ah Allah yadawo min dakai lafiya Alhaji,ubangiji Allah yabaka nasara akan wannan sabon company dazaka bud'e,Allah ya kauda ma idon maqiya" Cikin jin dad'in addu'ar ta yasaka hannunsa yajata jikinsa ya rungume ta,hannayen sa duka biyun suna kan bajajjen hips d'inta,cikin tsantsar soyaiya yace"Amin My Dear,kema Allah yabaki abinda kikeso" Ahankali tazame jikinta daga nashi,tasaka hannayen ta duka biyun ta riqe fuskarsa dashi sannan tace"Haihuwa....,Fatana na haihu dakai,nima inga 'yata ko d'ana suna amfani da sunan ALIYU MEKU'DI,kyakykywar nasaba,kyakykywan tushe, wannan kad'ai zai zama abun Alfahri agareni" Murmushi yayi yakai hannunsa ya d'ora akan qugunta,yayinda hannayenta suke kan fuskarsa har yanzu,cikin jin dad'i yace"ZALIHA muci gaba da Addu'ah,Allah yana sane damu" Qwalla ce tacika idon matar tasa wadda yakira da suna Zaliha...kafin yabata amsa landlines phone d'in dake d'akin irin tada can tafara qara,saida ya sunkuya yayi kissing fuskarta sannan yaje yad'auki wayar. Tsawon mintuna biyu yana magana a wayar sannan yakashe yadawo wajanta yace"Aminina Alhaji Auwal yakirani,ya fad'amin already angama komai nikadai suke jira,ki kula da kanki Zaliha,banaso kisa damuwa aranki kinji ko?" Zaliha tatashi tsaye ta fuskanci mijin nata sarqar gwal din dake wuyanta sai walwali take, ahankali kuma cikin kissa tace"idan bakaso nasa damuwa araina to kada ka saurari matan qasar Nijar,ina tsoro kada wata buzuwar ta qwace min mijina....,sannan inaso kabani dama idan kadawo inje in dauko yaro ko yarinya agidan Marayu,ina son Baby Alhaji" Murmushi yayi sannan yace"inde hakan kikeso zamuje ki za6i duk yaron daya miki Zaliha,please ki kula da kanki banda sa damuwa" Yana fad'ar haka bai saurari amsar taba yajuya yafice daga falon nasu. Yana futowa babbar harabar gidan nasa wadda tayi kama data shugaban qasa,guard's d'insa suka taso suka rufa masa baya har zuwa wajanda aka adana motocinsa domin yimasa rakiya Airport,briefcase d'in hannunsa wani guard ya kar6a sannan aka bud'e masa mota yashiga suka futo daga gidan dawani irin gudu. Adede lokacin SULAIMANU mijin Bilkisu wanda yazo garin tun kwanaki hud'u dasuka wuce, yazo wucewa zai tsallaka titi,lokaci d'aya motar da'akejan Alhaji Aliyu Mekud'i tabigeshi. Cikin sauri suka ja wani irin birki,Alhaji Mekud'i yabude motar da kansa ya futo yadafa Malam Manu yace"bawan Allah bakaji ciwo bade ko?" Malam Manu daya gama galabaita duk kamanninsa sun fara sauyawa saboda damuwa dakuma yunwa,ya dubi Alhaji Mekudi yace"Alhaji karka damu,banji ciwo ba" Alhaji Mekudi yad'aga kansa ya kalli direban sa yace"kadinga driving da nutsuwa mana" Cikin rawar jiki driver yace"to Alhaji tuba nake,kayi haquri" Alhaji Mekudi baice komai ba yasake kallon guards dinsa dasuka furfuto daga Mota sai zare ido suke suna gyara bindigar hannunsu yace"ku kaishi gida a bashi abinci da masauqi naga kamar yana cikin damuwa,idan nadawo daga Niger zan ganshi" Yana fad'ar haka bai saurari amsar su ba yaduba tsadaddan agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yakoma cikin Mota aka rufe masa murfin motar sukaci gaba da tafiya. Yayinda d'aya daga cikin guard yayi sauri yakama hannun Malam Manu sukai cikin katafaren gidan Alhaji Mekudi dashi. (Ina labarin Bilkisu me gwanjo a Hanyar tafiya qasar nijar?🤔) *** *** *** Bayan sun bar cikin Maigatari suka wuce boda suka fice daga Nigeria gaba d'aya suka shiga cikin qasar Niger, a qasar Niger sun wuce 'Garin Isah',suka wuce 'Katurje',sunyi nisa sosai da barin 'Katurje' acikin daji motarsu ta lalace sakamakon fashewar taya,dole sai futowa sukayi suka nemi wata bishiya suka zazzauna,bayan Bilkisu dawata tsohuwa gaba d'aya motar duk maza ne,hakan yasa itada wannan tsohuwar suka koma gefe,nesa da maza kad'an sukai zaman su suna zancensu kad'an kad'an. Kafin asamu masu gyara suzo an d'auki tsawon lokaci sosai daga baya aka sabunta musu wata tayar sukaci gaba da tafiya. Kasancewar bata futo da wuri ba kuma ga yanayin jiran fasinjoji kafin sutaru mota tacika hakan yasa dare yayi musu ahanya,har wasu daga cikin fasinjoji sun kama bacci amma idon Bilkisu biyu,akan idonta suka shiga cikin garin 'Washawa' suka wuce garin,jaririn hannunta ne yafara kuka kamar wanda take mintsininsa,tsohuwar datake gefenta wadda take d'an gyangyadi kad'an-kad'an tabud'e idonta tace"bashi yasha mana" Cikin sauri Bilkisu tagyara mayafin jikinta tasaka masa nono a bakinsa amma kwata-kwata yaqi kamawa,saima wani sabon kuka dayasake fashewa dashi duk ya gigitata,hawaye ne yacika idonta cikin ranta take tunanin tome yakeso? haka ta d'auke shi daga kan cinyarta tamaida shi kafad'arta tana jijjigashi amma yaro yaqiyin shiru. Suna gab da shiga cikin garin 'Dungas' Direban motar yataka wani irin mahaukacin birki sakamakon ganin wasu d'irka d'irkan 'yanfashi agabansa,yana taka birkin mota 'yan fashin suka yiwa motar su Bilkisu qawanya,wani babba daga cikinsu da muryar sa ta 'yan daba marar dad'in ji yace"qananun 'yan'iska kowa yafuto yazube aqasa" Ya kalli yaransa yace"aje a futo dakomai na guzurin su akawo min shi nan" Lokaci d'aya mutanan Mota suka fara salati,masu bacci idonsu yabud'e ras, yayinda gaban Bilkisu yayi wata irin bugawa,tasake qanqame Muhammad ajikinta,gaba d'aya ilahirin jikinta yad'auki rawa,batayi qoqarin 6oye kud'in hannunta ba,sai photunan da'aka yiwa Muhammad tayi sauri ta 6oye su acikin bujen siket d'inta naciki wanda yakeda aljihunsa irin wanda mutanan da suke sakawa domin 6oye kud'in su. Gaba d'aya motar aka futo dasu kan titi, yanda taga suna gabzawa maza bindiga akansu kai yana fashewa da jini hakan ne yasake tsoratata tasake qanqame d'anta suka dunqule waje daya ita da wannan tsohuwar, ga Muhammad sai tsala wani irin kuka yake kamar tana dukansa,maza biyu ne suka shiga cikin motar suka kwashe komai da komai na guzurin matafiya,suka zube shi agaban ogansu. 'Daya daga cikin yaran ne yakalli inda su Bilkisu suka dunqule itada tsohuwa yace"ke dan uwarki ki rufewa yaron nan baki komu tattakaki anan wajan" Lokaci d'aya itama tafashe da kuka,ganata gana Muhammad,tasaka hannunta tarufe masa baki,numfashin yaro yafara sama-sama kamar zai mutu cikin sauri tabud'e masa bakinsa. d'an fashin daya ga taqi bin umarninsa cikin 6acin rai ya hasketa dawata fitilarsu me shegen haske,adede lokacin Bilkisu ta sunkuyar da kanta qasa tana jijjiga yaronta,mayafin kanta yad'an zame yayi baya kad'an sakamakon sunkuyar da kannata datayi,hakanne yasa d'an fashin yayi tozali da gashinta wanda yake sheqi da qyalli,yadawo da fitilar kan fuskarta ya haska kyakykywar fuskarta,lokaci d'aya yasaki murmushi yace"oga gawata zazzafa fa..." Ogan su dayake zaune akan wani qaton itace,yadaka mata tsawa yace"Ke!! ajiye yaron nan kizo nan" Bilkisu ta kalli qasa taga rairayin qasa tayaya zata kwantar da yaronta aqasa? batayi musu dasu ba tatashi ta nufi inda Ogan yake,saide yaronta yana hannunta saima sake qanqameshi da tayi,sai jan zuciya yaron yake saboda kukan dayasha. Agabansu ta tsugunna,Ogan ya kalleta yayi wani irin hadiyar yawu, cikin tsananin sha'awa yace"yaronki yana kuka futo da nono kibashi yasha,inkin gama dashi nima kibani" Yafad'i haka yana kwashewa dawata irin mahaukaciyar dariya,yaransa ma suka fara tayashi. Hawaye ne yafara zarya a'idon ta,bakinta yafara karkarwa takasa yin magana. Wannan tsohuwar dasuka taho tare tad'aga murya tace"yaro kayi haquri karka cutar da'ita,ku kar6i duk abinda kuke so a wajanta dan Allah karku cutar da'ita" Oga yanajin haka yadaga bindigarsa baiyi wata-wata ba ya harbi tsohuwar nan,lokaci d'aya rai yayi halinsa(😭) Bilkisu tana ganin haka tasaki kuka me sauti,shima Muhammad dayake hannunta yaci gaba da kuka,yayinda mazan dasuke qwance aqasa jikinsu yasake d'aukar rawa ganin yanda akai kisan kai awajan amma kamar sun kashe kiyashi. Muryarta tana rawa tahad'a hannunta biyu waje d'aya tace"dan darajar Allah kuyi haquri,kuyi haquri ku qyalemu mutafi karku kashemu" Ogansu yayi wata irin dariya yabuga qafarsa aqasa yace"kibamu wani abun,saimu qyale ku kutafi" Cikin sauri tace"kun qwace mana komai,banida abinda zan baku,dan Allah kuyi haquri" 'Daya daga cikin yaran Ogan nasu dayake zaune akusa dashi da alama shine na hannun daman oga ya kwashe dawata irin dariya yace"kaji fa,wai batada abinda zata bawa oga,baki ji abinda matacciyar tsohuwar can tafad'a ba? mu kar6i komai a wajanki amma kada mu cutar dake,yanzu oga na zai kar6i komai kuwa" Yana fad'ar haka ya fuzge mayafin jikinta,dogon gashinta ya bayyana,Bilkisu tasake qanqame Muhammad a hannunta na dama,yayinda takai hannunta na hagu tacikashi da rairayin qasar wajan,ogansu baiga abinda tayi ba ya sunkuya yakai hannu zai ta6a gashin kanta tafaki idonsa ta watsa masa wannan rairayin qasar a'idon sa, sannan ta kwasa aguje tafara wani irin mahaukacin gudu kamar wanda tashiga gasar tseren gudu,lokaci d'aya suma yan fashin suka mara mata baya suka bita da mahaukacin gudu. Gudun datake ne yasa dogon gashinta yabazu a bayanta, yayinda wani ya rufe mata fuska amma bata damu ba haka taci gaba da gudu ko sanin inda zatasa qafarta batayi,wahalar da Muhammad yaji hakan yasa yaci gaba da kuka,yayinda kukan yaron yasa 'yan fashin suke binta duk inda tayi,dole qanwar naqi,dole Bilkisu tasa hannunta tarufe masa baki ganin kukan nasa shine yasa suke gane inda take,taci gudu sosai harta 6acewa ganinsu,tasamu bayan wata bishiya ta 6uya,adede lokacin suma 'yan fashin sukazo wajan sunata dube-dube,Bilkisu tana ganinsu tasake rufewa Muhammad baki yayinda wahala tasa yaron nan take ya suma(🙆🏻‍♀️😥) Ta waiga gefenta,cikin sa'ah taga wata hamshaqiyar Mota a adane,da alama motar wasu matafiya ne suka tsaya uzuri,ahankali tafara tafiya tana nufar inda motar take,taku take sid'af sid'af ahankali hartaje wajan motar,duka glasses d'in motar a rufe suke,tana ganin idan tashiga cikin motar tarufe,ba zasuji kukan yaron ba,batasan cewa shikam yaro yariga ya suma ba(😭) Cikin ikon Allah tana bud'ewa motar ta bude alamun ba'a kulle motar ba,tana shiga cikin motar wani irin qamshi me dad'i ya bugeta da wani sanyi-sanyi da motar takeyi alamun ba'a dad'e da kashe esin ciki ba,ahankali ta ajiye Muhammad tasaka hannu zata rufe motar wannan 'yan fashin suka ganta,cikin 6acin rai suka qarasa suka fuzgota,d'ayan yasaka hannunsa ya rufe motar ga Muhammad acikin Mota (🙆🏻‍♀️) Janta sukai can bayan bishiyar data 6uya musu,Mayafin jikinta dayake hannunsu wanda suka fuzge matashi d'azu,dashi sukai amfani suka d'aure mata baki,yayinda mutum biyu suka rirriqe mata hannayenta tabaya,ogansu ya matso cikin zilama yad'ora hannayen sa duka biyu akan qirjinta yafara murzawa,baqin ciki yasa tasaki wani irin kuka gashi sun rufe mata baki,hawaye sai zarya yake a fuskar ta yayinda take girgiza masa kai alamun a'a,tanajin wani irin baqin ciki kamar zata mutu. Adede wannan lokacin Alhaji ALIYU MEKU'DI,yazo yabud'e motarsa yashiga ya zauna ya kunnata,danjar mota takawo haske alamun mota tatashi,gaban Bilkisu yayi wata irin fad'uwa ganin an kunna motar kuma Muhammad yana ciki,lokaci d'aya ta zaro manyan idonta waje,tafara fuffuzgewa daga hannun su,amma sai suka sake riqeta,hasken wannan fitilar motar shine yasake haskawa har taga number motar,tanaji tana gani mota tafara tafiya,ganin yanda taqi tsayawa waje d'aya sai faman fuzge-fuzge take hakan yasa oga ya wanke fuskarta da wani zazzafan mari,zafin Marin yasa ta sunkuyar da kanta qasa,dogon gashinta ya sakko ya rufe mata fuska,tad'ago kanta da sauri ta kalli motar tagade da gaske fa motar nan tafiya take gakuma d'anta yana cikin Mota,lokaci d'aya tasa qafarta tadaki abunsa(🍌) Tsananin azabar dayaji ne yasa ya janye hannunsa daga kan qirjinta yamaida hannun zuwa gabansa ya tsugunna yana runtse ido,ganin Mota tafara nisa yasa Bilkisu ta qwace ta kwasa aguje tabi bayan motar,tacire mayafin dasuka rufe mata baki tayi wulli dashi,tabi bayan motar da mahaukacin gudu tana kuka tana fad'in " d'ana,d'ana yana ciki,Muhammad karka tafi kabarni,...." Tasake daga murya tace" me Mota ka tsaya!!! " Amma inaaa,Alhaji mekud'i kokad'an baiji taba,saima gudu daya qarawa motarsa sakamakon lokacin tashin jirgin su yana gab da qurewa gashi ko cikin Nigeria bai shigaba bare yaqarasa jihar kano yagana da wasu baqi sannan yahau jirgin zuwa Lagos,haka Bilkisu tasake bin bayan motar da gudu tana d'agawa Mota hannu tana magana kamar ta6a66iya. kasancewar gudun mutum dana mota ba d'ayaba,hakan yasa Bilkisu tanaji tana gani,Mota tatafi da d'anta idonta akan Number wannan Mota,lokaci d'aya ta tsugunna awajan tasaki wani irin qarajin kuka me tsoratar wa,adede lokacin kuma 'yan fashin suka sake zuwa zasu kamata, a wannan yanayin zuciyar Bilkisu ta bushe,ta tsinke,bata tsoron koma mezai faru yafaru,wani qaton itace dayake gefenta tad'auka tayi kukan kura ta maka musu shi,sannan tasaki itacen ta gudu,bata hango nisan tafiyar da tayi tana gudu ba,harta qaraso cikin Garin 'Dungas' a wahale,alokacin masallatai suna kiran sallar farko,tana tafiya tana had'a hanya kamar 'yar maye,ga dogon gashin kanta yayi buzu-buzu ya hargitse yana rufe mata fuska kamar na mahaukaciya,saida tazo qofar gidansu idonta ya rufe ruf...tadena ganin komai tazube awajan Sumammiya. (so Sad....😭Sorry Bilkisu) (masu karatu karfa ku manta har yanzu labarin 1986 mukeyi shekaru talatin da bakwai dasuka wuce Kenan 🤒yauwa) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne, 300 ne kacal 0164549488 Amina muhammad GTbank Tareda turo shedar biya ta wannan number 08033300034 Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu 5&6 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Alhaji Aliyu Mekudi,yayi nisa atafiya yaji kamar motsi abayan motarsa,juyawar da zaiyi yayi tozali da jariri wanda ubangiji cikin ikonsa yasa ya farfad'o da kansa sai d'aga qafafu da hannu yake sama irinna jarirai. Alhaji Mekud'i yataka wani irin birki ya futo daga mota yazo yabud'e gidan baya,idonsa ya sauka akan kyakykywan yaro masha Allah fari tas dashi,gabansa yayi wata irin fad'uwa ganin jaririn kyansa yayi yawa kamar ba d'an Bil Adama ba,yakai hannu zai d'auki yaron hannunsa yafara karkarwa,haka ya daure yad'auki yaron wanda yunwa tasa yasaka d'an yatsansa a bakinsa yanata tsotsa,Alhaji Mekudi yasake kallon jariri yace"innahu min sulaimana wa'innahu bissmillahirrahmanirrahim" Yayi tunanin ba d'an mutum bane Aljanine. Yajuya ya kalli gabas da yamma yaga babu kowa,to waye zai saka masa jariri amota idan ba aljannu ba?(🤔) ga yaro kwata-kwata babu inda zakace bahaushe ne saide Balarabe duk yanda akayi yaron aljannu ne. Cikin sauri ya lalla6a kamar yana tsoron aljannun zasu kamashi yamaida yaron cikin mota yarufe, yakoma yatada mota yajuya baya zaije inda ya ajiye motarsa ko Allah zaisa aljannu suzo su dauki d'ansu,cikin gudu yaja motar yajuya,saide yana zuwa wajan yaga babu kowa,yaduba yasake dubawa babu alamun komai, yabude murfin motar gidan baya yakoma gefe ya yatsaya yana jira masu d'a su dauke d'auke d'ansu, wato aljannu. Saide tsawon mintuna babu abinda yafaru,saima wasa da Muhammad yakeyi da yatsansa abakin sa idonsa abude kar ko alamun kuka bayayi. Alhay Mekudi daya gaji da jira yakoma wajan motar yasaka hannunsa ya d'auki Muhammad,yad'aga shi sama sannan yace"ya ubangiji na,haqiqa ni bawankane mai yawan godia agareka,na kasance tsawon wasu shekaru Ina neman haihuwa ubangiji Allah baka bani ba,amma rana irinta yau ya Allah ka azurtani da wannan wanda bansan daga inda yake ba,Allah nagode maka da wannan kyauta dakamin,bazan baka kunyaba wajan yiwa yaron nan tarbiya kamar nine na haifeshi,haqiqa zan riqe amanar wannan yaro kamar yanda kayiwa sauran iyaye umarni su riqe amanar 'ya'yansu" Ya sauke hannunsa qasa yasaka Muhammad a qirjinsa ya rungume shi,sannan ya zagaya dashi yabude motar yasaka shi a cinyarsa, yaci gaba da driving. Da yaron a hannunsa ya gana da wasu baqin turawa akano,saida yagama dasu sannan yanufi Airport d'in Malam Aminu. Lokacin daya qarasa filin jirgin already har jirgin dazaibi yatashi, saida yasake yin booking yajira lokaci yacika, sannan jirgin su yasake tashi zuwa Lagos.(👋🏻) *** *** *** Niger Republic Azabure Bilkisu me gwanjo tafarka daga baccin datake,gefenta ta kalla tana dube-dube da alama Muhammad take nema,ganin babu Muhammad babu dalilinsa sai qaninta dayaci uban wani nad'in rawani irin wanda buzaye sukeyi, da matar qaninta wadda take Sanye da laffaya ruwan toka dasuke gefenta babu kowa,hakan yasa tagane cewa ba mafarki takeba da gaske ne shima Muhammad yatafi,shikkenan yatafi yabarta,cikin d'acin zuciya da qunci tafashe dawani irin kuka,matar qaninta ta dafa kafad'arta cikin sigar lallashi tace"Yaya kiyi haquri kidena kuka,tunda Allah yakawo ki gida lafiya ai Alhamdulillah" Qanin nata ma yadubeta cikin hausarsa da bata goge sosai ba yace"kiyi shiru" Daga haka baisake cewa komai ba ya kalli matarsa JAMILA,wadda yasha fama yayi yaqi da samari bila'adadin domin ya aureta saboda yanda takeda tsananin kyau,hakanne ma yasa mahaifinta yasa mata suna Jamila,yayi ajiyar zuciya yace"JAMI, ki kula da'ita nizan fita nema..." Jamila ta kalleshi tagyad'a kanta sannan tace"to FAROUQ saika dawo" Farouq yasa hannu yad'auki butar shayinsa dawata jaka 'yar qarama arataye a wuyansa, yafice daga gidan. Tun bayan fitar Farouq Bilkisu me gwanjo take hawaye,idonta yayi jajir kawai hawaye ne masu zafi suke zarya akan kuncinta,tsabar kuka har muryarta ta dashe,jamila tayi lallashin tayi ban baki amma Bilkisu shiru,har zuwa la'asar hawaye take,haka kuma taqiyin magana,taqi cewa komai, kawai de ta zubawa waje d'aya ido tana kallo ga hawaye yana zuba,agefe guda kuma ga nonon ta dayake zubarda ruwa kasancewar anwuni ba'asha ba. Sai yamma lis,farouq yadawo,ya kalli Yaya Bilkisu sannan ya maida kallonsa ga Jamila yace"Jami,yanaga Yaya a zaune tayi shiru har yanzu kukan takene?" Jamila ta kalleshi tace"ka ganta nan tunda kafita har yanzu kuka take taqicin komai sannan kuma taqiyin magana" Farouq ya girgiza kansa ya zauna a kusada Bilkisu sannan yacewa Jamila"had'o mata shayi" Jamila tatashi da sauri tahad'owa Bilkisu shayi acikin wani d'an qanqanin kofi irin wanda buzaye suke amfani dashi,tazo ta ajiye mata shayin itama tazauna awajan. Farouq ya kalli Bilkisu yace"Yaya kid'auki shayin nan kisha hanjin cikinki ya warware" "na salwantar da d'ana" Shine kawai abinda Bilkisu tace. Jamila ta kalli Farouq tace"kamar fa bata cikin hayyacinta,Yaya da batada kowa kana jifa maganar yaro takeyi" Farouq ya jinjina kansa yace"um ina tunanin haka,inaga iftila'in data had'u dashi ahanya shine bai barta ba,bari inje wajan liman yabani rubutu na kawo mata tasha ko Allah zaisa tadawo hayyacinta" *** *** *** Lagos Nigeria Gudun kada mutane Susan abinda yake faruwa hakan yasa Alhaji Mekud'i yana sauka a Airport babu wanda yasan da dawowar sa kai tsaye yawuce gidan yayarsa qwalli d'aya aduniya wadda suke uwa d'aya uba daya kuma iya sukad'ai suka rage a duniyar wato YAYA MARIYA,ita kanta gidan datake ciki abun kallo ne,basai an fad'aba kasan cewa gidan ya amsa sunansa na gidan yayar Mekudi. Tana ganinsa da yaro tatashi tsaye ta tareshi tareda fad'in "Mekudi ina kasamo yaro haka tubarkalla masha Allah?" Zama yayi acikin luntsuma luntsuman kujerun falon sannan yayi kissing Muhammad yace"Allah ne yabani shi Yaya,kar6eshi kisa masa albarka" Cikin sauri Yaya Mariya ta kar6i yaron fuskarta fal farinciki tana fadin"ikon Allah,Aliyu wannan yaron aid'an larabawa ne,Ina kasamo shine?" Murmushi yayi, sannan yatashi yaje inda wayar gidan nata take ajiye yakira layin gidansa yacewa zaliha matarsa lalle lalle duk abinda take tabari tasa driver yakawo ta gidan Yaya Mariya, kasancewar gidan babu nisa hakan yasa nan da Nan Hajiya Zaliha matar Alhaji Aliyu Mekudi tazota cikin sauri, bayan sun gaisa nan take Alhaji Mekudi yafara basu labari tiryan-tiryan yanda akai yasamu wannan jariri. *** *** *** Niger Republic Bayan Farouq yakawo mata rubutu Jamila tajuyeshi a kofi takawowa Bilkisu tace"Yaya gashi ki kar6a kisha" Bilkisu ta kalli Jamila dajan idonta tace"ina hayyacina,lafiyata kalau Jami,talauci yasa Sulaimanu yagudu yabarni da tsohon ciki,na haihu kwana tara dasuka wuce,ahanyata ta zuwa nan munhadu da 'yan fashi....." Tsaf Bilkisu ta zayyane musu abinda yasameta har kukan da yaron yake tayi ahanya har zuwa lokacin data qwace daqyar daga hannun 'yan fashi.... Tun kafin ta qarasa basu labarin Jamila take kuka,shi kansa Farouq saida ya goge qwallar tausayi daga idonsa,cikin jajircewa irinta maza ya dubeta yace"ki kwantar da hankalin ki Yaya,insha Allahu d'anki yana cikin aminci,yanzu babu wani abu dakika riqe amatsayin shaida wanda zamuyi bincike dashi ko Allah zaisa mugane inda yaron yake? " Cikin sauri Bilkisu ta goge qwallar idonta tazana masa number motar aqasa,batajin ko nanda shekara d'ari ne zata manta number wannan mota, bayan ta rubuta masa ta kalleshi tace"motar baqar kala ce da'ita,katemaka min Farouq" Farouq ya girgiza kansa yace"kiyi haquri Yaya,insha Allah gobe zanje police station inyi report,za'a ga d'anki da iznin Allah" Sai alokacin tayi wata irin ajiyar zuciya,sannan Jamila tagoge hawayen idonta tabata shayi tasha. *** *** *** Lagos Nigeria Hajiya Zaliha takama jariri ta rungume sai walwala takeyi bakinta yaqi rufuwa kamar gonar audiga,Yaya Mariya ta kalleta tace"to Zaliha,Kinga de kundad'e kuna neman haihuwa Allah bai kawo ba,yanzu gashi sama taka kin samu yaro,dan Allah Zaliha, kiriqe yaron nan amana, bashida kowa saimu,idan muka riqe shi da gaskiya muma saiki ga Allah yatemakemu ta dalilin sa" Cikin tsananin farinciki Hajiya Zaliha ta kalli mijinta Aliyu Mekud'i da yayarsa Hajiya Mariya sannan tace"Yaya insha Allahu bazan baku kunya ba,zan riqeshi irin ruqon da mahaifiyarsa zata masa" Alhaji Mekud'i yayi wata irin ajiyar zuciya,dama Sam baya jin Zaliha, yasan bazai samu matsala da'ita ba kamar yanda yasani tana bala'in qaunar Yara. Yaya Mariya ta kalleshi tace"to Alhamdulillah,Aliyu kar6eshi kayi masa hud'uba, sai kaje masallaci atara mutane suma su shaida sunansa" Cikin farinciki Alhaji Mekudi ya kar6i jaririn daga hannun Zaliha wadda takeji kamar tagama samun komai a duniya tunda gashi Allah yabata yaro. Cikin ikon Allah Alhaji Aliyu Mekudi yayiwa yaro hud'uba da suna JAWAD, yad'ago kansa ya kallesu yace"daga yau sunansa Jawad A. Mekudi" (Muhammad d'inmu yakoma Jawad 😭) Farinciki ya wanzu a fuskar Yaya Mariya da Hajiya Zaliha,Yaya Mariya tace"masha Allah, Allah yaraya mana Jawad" Alhaji Mekudi yace"Amin ya Allah yaya" Itama Hajiya Zaliha tace"Allah yarayamin Baby na" Cikin farinciki suka amsa mata gaba dayansu,daga nan yadauki yaron yafita masallaci dashi,abunka da me kudi nan da nan aka siyo goro da alawa aka rabawa mutane a masallaci,liman ya kar6i yaro yayi masa Addu'ah yasa masa albarka,sannan Alhaji Mekudi yadawo gidan yayar tasa, basu zauna ba, kai tsaye asbiti suka wuce duka su ukun,wani qwararran doctor yaduba Jawad ciki da waje ya tabbatar musu da cewa yaron yanada cikakkiyar lafiya babu abinda yake damunsa,daga nan likitan ya rubutawa Hajiya Zaliha magungunan da zatayi amfani dashi ruwan nono yazo domin taci gaba da shayar da Jawad. Sai dare suka dawo gidansu shida Zaliha,kasancewar dare ne hakan ne yasa ba kowa ne yaga Jaririn dake hannun Hajiya Zaliha ba. Saida yaraka su ciki sannan yasake futowa driver ya dauke shi suka fita da mota guda biyu,kai tsaye sayaiyar kaya yafara yiwa Jawad,hatta da d'an qaramin gadon kwantar da jarirai irinna turawa saida aka hado dashi,siyaiya aka yi masa ta hauka kamar a yarinta zai tabbata bazai girma ba,duka mota biyun dasuka fita da'ita saida suka cikota da kayan Jawad,bayan sun dawo gida yatsaya a farfajiyar gidan mutane suna sake yimasa Allah sanya Alkhairi akan sabon kamfanin dayaje qasar Nijar yabude,yayinda ma'aikata suke shigar da kayan siyaiyar tasa zuwa cikin falo. Bayan yadawo falo yana zama guard dinsa guda daya yashigo falon cikin ladabi ya rissina yace"Yalla6ai ya za'ai da mutumin da muka kusa kadewa jiya,kace a bashi masauqi idan kadawo zaka ganshi" Alhaji Mekudi yadafe goshinsa da hannunsa yace"subhanallah, na manta dashi wallahi, jeka shigo dashi" Cikin sauri guard din yajuya,yayinda Alhaji Mekudi yajuya yana bawa Hajiya Zaliha datake sanyawa Jawad pampers labarin abinda yafaru jiyan. Cikin mintuna qalilan aka gabatar masa da Malam Manu wanda kwana daya kawai harya fara sauya wa black beauty din fatarsa taji esi da naman kaji,Alhaji Mekudi yazuba wa Malam Manu ido yana kallonsa,yayinda Malam Manu ya shagala a kallon kyakykywan yaronda Hajiya Zaliha take sakawa wata hadaddiyar singlet ta jarirai,jiyake kamar ya dauwama yana kallon yaron,yaji lokaci d'aya wata matsananciyar qaunar yaron tana ratsa shi. Alhaji Mekudi yace"bawan Allah daga ina kake? Sannan tunanin mekake kana tafiya haka akan titi har mota tazo tabigeka baka sani ba?" Malam Manu yayi shiru cikin yanayin damuwa,bai dauki wannan bigeshin da mota tasoyi abakin komai ba face haqqin Bilkisu daya fara bibiyarsa,ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yace"Ina tunanin aikin dazan nema nafara ne intara kudi sannan in koma wajan iyalina,ni mutumin jihar jigawa ne,nabar iyalina a halin babu,damuwa tamin yawa ganin tunda nazo cikin garin Lagos babu wata sana'ah dana samu domin in riqe kaina, tunani yamin yawa hakan yasa bansan motarku tazo kusana ba" Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya,Hajiya Zaliha tayi kissing goshin Jawad tasakashi a qirjinta ta rungumeshi tana shashshafa masa baya tana so yayi bacci, sai lalla6ashi take saikace d'an gwal (😚). Kallon Manu yayi bayan yagama ajiyar zuciyar yace"to zan baka aikinyi insha Allah, kaga nima asali na dan arewa ne, nema ne yakawo ni garin nan har Allah yasa nan garin yazama kamar shine tushena yanzu,zaka iyayin driving din mota?" Cikin sauri Manu yace" zan'iya Alhaji,a dacan ai na'iya tuqin mota kafin iyayena su rasu" Alhaji Mekudi yace"to zan baka driving,sannan akwai wajan zama, zaka dinga zama anan tare damu insha Allah" Cikin sauri Manu yasake rissina wa duk da yana zaune, yayi godia Iya godia, Alhaji Mekudi ya kalli guard dinsa yace"aje anuna masa masauqinsa " Guard d'in ya amsa cikin biyaiya,sannan yasaka malam Manu agaba zasu fita daga falon, saide kafin su fice saida Malan Manu yasake juyawa ya kalli Jawad dake kwance a kafad'ar Hajiya Zaliha. Washegari tun safe har azahar ruwan nonon Hajiya Zaliha baizo ba,saboda wannan dalilin Alhaji Mekudi ko office baije ba,Hajiya Zaliha kuwa hawaye tafara ganin Jawad din yafara galabaita,dole saida aka kira doctor gida yazo yasake dubashi yafada musu yunwa yakeji,gashi nono yaqi zuwa,hakan yasa likitan ya rubuta musu Kala kalar madara ta jarirai,Alhaji Mekudi yabada umarni akawo wannan madara, aikuwa nan da nan aka kawowa Jawad madara katan katan,Hajiya Zaliha tahad'a masa tafara bashi,nan take yafara sha babu musu,sai alokacin hankalinsu ya kwanta. *** *** *** Niger Republic A6angaren mutanan Niger kuwa tun safe da Farouq yafita da number motar wajan police yanaso yaji yanda za'a yi,Bilkisu taqi ci taqi sha tana jira yadawo taji Ina aka tsaya,Jamila sai kallonta take cikin tausayawa,duk da bata haihu ba taji zafin rashin wannan yaro jitake kamar d'anta ne aka tafi dashi. Farouq yana dawowa Bilkisu me gwanjo tamiqe tsaye tanufeshi tana fadin"Farouq ya ake ciki?" Cikin sanyin jiki Farouq yace"Yaya abun nanfa ba d'an qarami bane,naje nayi report sannan na basu number motar sun tabbatar min cewa ba motar qasar Nijar bace,motar daga Nigeria take,wai wani gari Lagos, kuma nima sai bayan nakai musu naga sunan garin sannan natuna ba motar qasar nan bace,tashin hankali ne ya hanani fahimta tun jiya dakika rubuta min,amma kiyi haquri sunce zasu tura wasiqa zuwa hukumar garin ko Allah zaisa adace...." Tun lokacin dayace ance motar qasar Nigeria ce, daga nan tadena fahimtar komai tasan cewa a Nigeria ma taji labari ana cewa Lagos da nisa,sai an kwana ake zuwa,tasan cewa shima Muhammad shikkenan yatafi yabarta,lokaci d'aya idonta ya rufe ruf...tadena ganin haske sai duhu.... Cikin sauri Jamila tatarota tana fadin"innalillahi Farouq riqeta karta fadi tasuma fa" Farouq yayi azamar tareta shida Jamila, suka samu suka kwantar da'ita akan tabarmar kaba wadda take shimfide a saharar tsakar gidan nasu, Jamila ta debo ruwa tashafa mata,lokaci daya taja wani irin numfashi tafarka azabure tana fadin "Muhammad!!!" sannan tafashe dawani irin kuka,Jamila ta goge hawayen idonta, cikin muryar kuka tace"Yaya kiyi haquri,inda rabo watarana zaku had'u,kisa dangana aranki Yaya ubangiji shine yasan nufinsa akan hakan" cikin tashin hankali da damuwa Bilkisu tafara magana tana fad'in"yanzu shikkenan na salwantar da d'ana dakaina? nasan cewa bazai soni ba, bazai yafemin ba" Cikin sauri dakuma juriya irinta maza Farouq yace"Yaya meyasa zakice bazai soki ba? akwai yaron da uwa zata haifa sannan yazo yaqi uwarsa?" Cikin kuka Bilkisu tace" Farouq ban shayar dashi ba tayaya zai soni? koda zai soni ba kamar yanda natsaya na shayar dashi tsawon shekara biyu ba,nasan yanzu duk inda yake bashida lafiya,baisha isasshen nono ba,ba lalle yayi basira kamar sauran yara sa'anninsa ba,ba zaiyi kuzari kamar suba,bazai tashi da qawazucin uwa ba..." Jamila ta girgiza kanta cikin muryar kuka tace" karkice haka Yaya,jariranda uwa take mutuwa tabar su kuma su tashi da basirar sufa Yaya? ubangijin daya rabaki da d'anki zai azurtashi da wad'annan abubuwan dakika lissafa koma fiyeda haka..." (karfa ace inason kashe Bilkisu saboda yanayin rayuwa ato nasan hali😂) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name https://chat.whatsapp.com/GnQsZx4Pn7QHpdshIPWwtu 7&8 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. ___ Shima Farouq yayi ajiyar zuciya ya kalleta yace"abinda Jami tafad'a miki hakane Yaya,kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki,ki daure ki kar6i wannan qaddarar a yanda tazo miki,Yaya kefa musulma ce,nasan ki da haquri ko a baya,yanzu ma ki daure kici gaba da haqurin" Bayan yayi shiru itama Jamila tad'ora daga inda yatsaya,haka suka zauna su biyun sukai amfani da kalamai masu dad'i da hikima suna yi mata nasiha suna qara lallashinta. Aranar babu inda Farouq yasake fita,yazauna agida yana taredasu,sai yamma yafita kai tsaye yaje wajan limamin unguwarsu yayi masa bayanin halin datake ciki,yanemi yabashi taimakon wasu addu'o'in wanda zai dinga yimata ko Allah zaisa ta kwantar da hankalin ta,babu musu kuwa liman yazauna ya rubuta masa addu'o'i kala-kala,sannan yayi masa rubutun dangana yace akai mata tasha, sannan kullum ya dinga zuwa yana kar6a mata rubutun. hakan ce ta kasance kuwa,kullum Farouq zaije wajan liman ya kar6o mata rubutu,agabansa zata shanye sannan ne hankalinsa zai kwanta,cikin ikon Allah da taimakon Farouq Bilkisu tafara dawowa cikin nutsuwarta,tadena suma tadena kuka. **** Haka kwanaki suka dinga tafiya suka koma satittuka har zuwa watanni,acan Nigeria kuwa har Jawad yafara rarrafe,abincin sa idan za'a bashi ma'aikata kusan guda uku ne suke kula da abincin,idan yafara 6arna babu wanda yake masa magana,ko anyi magana tofa Hajiya Zaliha zatace a barshi yayi wasansa qwaqwalwar sace take bud'ewa a wannan lokacin,ma'aikatan gidan mata suna so su dinga d'aukar sa saboda yanda yake basu sha'awa amma basu Isa su doshi inda yaron yakeba Hajiya Zaliha zata hana,komai sai ita,haka idan anayi masa wani abu kamar wanka kokuma idan yana wasa yad'an bige hannunsa yafara kuka,ma'aikaciyar datake kula dashi alokacin batayi saurin daukar mataki akan kukan Jawad ba, to kai tsaye Hajiya Zaliha zata koreta daga aiki,kwata-kwata batason ganinsa yana kuka,da Jawad yayi kuka gara taita korar ma'aikatanta.(🙆🏻‍♀️) Lokacin da aka sakashi a makaranta yana playgroup motoci guda biyar ne suke kaishi,haka guda biyar ne suke zuwa d'aukoshi gaba d'ayansu security ne acikin motocin suna bashi kariya,har gaban motar Hajiya Zaliha zata kaishi tasa shi a motar har motarsu tafita daga get d'in gidan bata daina yimasa bye bye. Lokacin daya fara koyon magana da sunan MAMA yafara a bakinsa,amma Hajiya Zaliha saita hanashi cemata Mama saide Mummy. **** Niger Republic Acan Nijar kuwa Bilkisu takasa sukuni, koda yaushe zaka sameta shiru babu um bare um-um,yauma photon Jawad ne a hannunta tana kallon photon da'aka yi masa tun yana jariri kafin subar jihar jigawa,photon ma ko kala babu irin farin photon nan ne nada fari marar kala. Jamila datake zaune agefenta tana tufke dogon gashinta wanda yazo mata har gadon bayanta,ta kalli Bilkisu sannan tayi wani irin murmushi na damuwa,cikin lallashi tace"Yaya Photon nanfa ba yaron ne zai futo daga ciki ba" Hawaye yazubo daga idonta,tasaka hannunta ta share hawayen " yatafimin da d'ana..." Abinda tace kenan. Jamila ta matsa kusa da'ita tace"Yaya kiyi haquri,kwana biyun nan kinsake saka damuwa aranki kamar baya,tun safe kin riqe photon nan kinkasa saka komai acikin ki ina tsoro kada ulser ta kamaki yaya" Cikin sauri tasaka bayan hannunta ta share hawayen,sannan tamaida photon ma'adanar sa ta6oyeshi,ta dauki butar shayinsu ta zuba tafara sha. **** Lagos Nigeria Lokacin da Jawad yayi shekara uku,a lokacin yana yawo ko'ina yana gudu,haka kawai Alhaji Mekudi da Hajiya Zaliha zasu sa ad'aukeshi a kaishi wajan wasan yara,awajan wasan ma duk inda yatafi da gudu guard din dasuka rakashi suke binsa su kamo shi,ko da yaushe idonsu yana kansa saboda kada wani abu yasame shi,sosai suke masa gata kamar d'an shugaban qasa. A shekarar 1996 Jawad yayi shekara goma,har zuwa wannan lokacin Malam Manu yana taredasu,yanzu yazama shine yakejan Alhaji Mekudi zuwa duk inda zasu. Har zuwa wannan shekarun Malam Manu bai koma gida ba,bai nemi Bilkisu ba. daga wannan lokacin ne kuma abun mamaki Alhaji Mekudi yake daukar Jawad da kansa ya kaishi kasuwa,ya had'ashi da wasu 'yan kasuwa su dinga d'ora masa tallar pure water,gashi tun yana yaro kasancewar kafin ya nemi abu anyi masa hakan yasa yazama baqin miskili,duk lokacin da Alhaji Mekudi ya kaishi yayi tallar pure water baya fad'awa Mummy,haka kullum yake sashi agaba ba tareda wasu security ba ya kaishi a wuni ana dora masa tallar pure water yana yawo dashi cikin kasuwa waje-waje yana siyarwa,saida yagama gogewa a fannin saida ruwa sannan yafara daukar sa yana kaishi wajan dako,kullum zai kaishi wajan 'yan dako yashiga cikinsu shima yayi dako yasamu kudinsa. Da Hajiya Zaliha taga fitar tasu tafara yawa kai tsaye ta tambayi Alhaji Mekudi cewa Ina yake kai Jawad ne? Shima Alhaji Mekudi kai tsaye yafuto fili yafad'a mata wajan dako da tallar ruwa yake kaishi, Hajiya Zaliha tanajin haka tafashe da kuka harda shashsheka. Alhaji Mekudi yakama hannayen ta yariqe ya sassauta murya yace"Zaliha, ki saurareni dakyau,sonake nakafa Jawad dakyau yanda zai zama cikakken mutum yasaba da gwagwarmayar rayuwa,abinda nake kaishi yakeyi yanzu nima dashi nafara har Allah yakawoni wannan matsayin a yanzu,inaso Jawad ya goge a fannin kasuwanci karki manta yaron nan shine goben mu,idan muka ce ahaka za'a ci gaba tayaya zaisan rayuwa har ya'iya kula damu idan muka tsufa?,duk abinda kikaga inayi kiyi haquri nasan kinajin ciwo to kiyi haquri ki kawar dakai" Hajiya Zaliha bata sake magana ba, amma qunci iya qunci tana jinsa,a wannan lokacin ne kuma kasuwancin Alhaji Mekudi yasake ha6aka,yana harka da manyan mutane yasake bude wasu kamfanunnika a jihohi daban daban na Nigeria harma da qasashan qetare,yazama babban mutum ganinsa sai ansha wahala saboda yanda yamaida kansa busy saboda aikin,ya mallaki abubuwan duniya dayawa kama daga jiragen ruwa,dana sama,helicopter,babu wanda Alhaji Mekudi bashi dashi,ganin capital d'in Nigeria yakoma Abuja yabar Lagos kuma yana harkoki dayawa a Abujan hakan yasa suka tattara suka bar Lagos da zama suka koma Abuja. Shekarar dasuka koma Abuja a shekarar Hajiya Zaliha tasamu ciki ta haifi d'anta namiji aka sanya masa suna FU'AD. 2003 Alhaji Mekudi yatura Jawad karatu qasar Italy. **** Tsawon wannan shekarun Bilkisu ta d'auki dangana tasawa ranta haquri akan 6atan yaronta,Farouq yabata Jari taci gaba da saida kayan Gwanjo. A da mutane suna cewa tanada nasibi akan saida kayan gwanjo bata tabbatar da haka ba sai yanzu,gida gida take shiga takai tallar kayanta kuma nan da nan kayan zasu qare tasake saro wasu,zamansu lafiya kalau itada Jamila,tana al'amuran rayuwarta cikin kwanciyar hankali saide fuskarta babu walwala,babu fara'ah,haka babu yawan magana,abinda tasa agaba kawai shine saida kayan gwanjo,nan da nan kuwa sunanta na BILKISU ME GWANJO yadawo. Acikin shekarar 2005 Allah yabawa Jamila ciki,Farouq da Bilkisu me gwanjo sunyi farinciki,gaba d'aya su ukun kowa yana qoqarin ganin sun taru sun kula da cikin Jamila kasancewar sun dad'e shekara da shekaru babu haihuwar,cikin ikon Allah 2006 Jamila ta haihu,tahaifi 'yarta mace mai tsananin kyau kamar Jamila,babu abinda yarinyar ta d'auko na ubanta,komai da komai na Jamila ne,uwa uba gashin kan yarinyar yayi yawa,idan 'yan barka sukazo ba koda yaushe suke nuna yarinyar ba saboda bakin mutane. Ranar suna aka sanyawa yarinya suna INAAS ma'ana (ME 'DEBE KEWA). Tunda aka haifi Inaas Bilkisu tafara walwala saboda gani take kamar Muhammad d'inta ne lokacin dayake yaro,tana tsananin qaunar yarinyar, Jamila bata mata komai,kullum Bilkisu ce takewa Inaas wanka,wanki da duk wani abu daya shafeta. 2007 Jawad yagama Degree dinsa,adede lokacin shekarar Inaas d'aya a duniya,a wannan yanayin ne kuma tashin hankali ya sauka a gidansu Bilkisu,inda suka wayi gari sukaga Jamila tarasu sakamakon zazza6in kwana d'aya (😭) Sun shiga tashin hankali sosai,daga nan ne ruqon Inaas yadawo hannun Bilkisu,Farouq yace yabata ita halak malak. 2010 Jawad yagama masters dinsa,alokacin shekarar Inaas hud'u,tayi bala'in wayo ga surutu kamar aku,gashi de gidan nasu babu mutane daga Bilkisu sai Farouq amma idan tazaro wata maganar tafad'a sai Bilkisu tayi mamaki. Tun tana shekara hud'un gashinta ya sauko har d'uwawunta,haka Bilkisu zata sa abu ta rage mata shi saboda yayi yawa,rana guda take warewa tazauna kawai wannan ranar ta gyaran gashin Inaas ce,sau tari idan tana gyarawa yarinyar gashinta ba kowa ne yake zuwa ranta ba sai Jamila mahaifiyar Inaas,itama haka take fama da gashi kamar 'yar India. Inaas tashiga ran Bilkisu,tanaji da'ita kamar Muhammad d'inta,ta shagwa6a yarinyar kamar goyon kaka,tun Inaas tana qarama Bilkisu ta lura yarinyar tanada masifar kyau mai fizgar mutum,wanda kallo d'aya zaka mata kaji tatafi da imanin ka,haka kawai sai tasa yarinyar agaba tana kallonta tana tunani inama ace Muhammad d'inta yana nan ta had'ashi aure da Inaas? Farouq daya dawo daga makarantar kud'i (private school) inda yake koyarwa ya dinga yiwa Bilkisu magana amma Inaaaaaa!,Bilkisu tatafi tunani tana kallon Inaas datake wasa tana tunanin inama ace d'anta yana nan, Farouq yadafa ta,tayi firgigit tadawo hayyacinta,yayi zaton tunanin d'anta takeyi,hakan yasa ya sassauta murya cikin lallashi yace"kiyi haquri insha Allah watarana zakiga d'anki" A shekarar 2014 Jawad yagama p.h.d dinsa a fannin kasuwanci,saiya kasance tundaga Degree har master's zuwa p.h.d gaba d'ayansu a fannin kasuwanci yayi bisa umarnin Alhaji Mekudi Alokacin Inaas tana primary,surutu sai abinda ya qaru,duk lokacin da za'a rubuta sunan 'yan surutu a aji to kana dubawa zakaga sunan tane nafarko (😂) ______ 2024 (yanzu kenan,nagama baku labari, mun bar shekarun baya mundawo zamanin mu,zamu cigaba da labari taurarinmu sun girma💃🏼) Agidan Alhaji Mekudi kula da komai yadawo hannun Jawad,duk wasu takardu na kadarorin Alhaji Mekudi sunkoma sunan Jawad,acikin shekaru 37 d'innan arziqinsu yaci uban nada, Jawad yatsaya tsayin daka babu abinda yake face kasuwanci,tun kafin amaida sunan kadarorin izuwa sunansa haka yake aiki baya zama, bayan komai yadawo qarqashin sama bai zauna ba,saima himma daya qara, saida ya kasance Jawad yanada resuna na kamfanin-nikansa sama da guda talatin aduniya,yana zuwa manyan qasashe daban-daban,har yanzu yana nan yanda yake tunda can baya magana,babu abinda yaragu daga miskilancinsa sai qaruwa ma da abun yayi kasancewar tun yana yaro kafin yanemi abu,anriga anyi masa basai yabude baki yayi magana ba,hakan yasa yasake zama miskilin gaske,matsalar sa d'aya bashida kirki a fannin kasuwanci,inde zakai wasa da aikinka to bazaka shirya dashi ba. Manya-manyan 'yan kasuwa da 'yan siyasa sun san Jawad amatsayin shugaban kamfanin jiragen sama,idan aka had'a kud'ad'en dukkanin kasuwancin sa za'a iya cewa yana samun ribar million dubu talatin a kowacce shekara,kasancewar tun yana qarami yatashi da koyon kasuwanci hakan ne yasa yazama me mutuqar basira a fannin kasuwanci, tun zamowarsa mamallakin dukannin company's dinsu daga nan yafara ruguza kishiyoyin kasuwancin sa,kafin abokan kasuwancin sa su farga har ya musu tazara bakajin sunan kamfanin kowa saina Jawad Mekudi,duk yanda d'an kasuwa yakai gayin takarar kasuwanci dashi to lokaci d'aya Jawad zai daqusheka ta hanyar rage farashin kayan kamfanin sa nad'an wasu lokaci,daga nan kuma mutane su dinga tururuwar neman kayan kamfanin sa,hakan yasa sauran manyan qasashen duniya sukasan da Jawad Mekudi. Lokacin dayayi Degree na farko akan kasuwanci yayi project dinsa,lokacin dayayi masters akan kasuwanci yayi project dinsa,haka p.h.d dinsa ma, bayan yagama karatu saida ya rubuta littattafai dadama duka a fannin kasuwanci domin na qasa dashi su amfana da irin salonsa. Yawan ayyukan dayake dasu hakan yasa yana iya kaiwa kusan shekara ko fiye da haka baishigo Nigeria ba. Jawad yahad'u sosai maqura,d'an gayu ne nabugawa a jarida,uwa uba ga kudi,ba qaramin d'aukan hankalin 'yanmata yake ba. Shine matashi na farko dayake d'aya daga cikin masu manyan kamfanin nika acikin Nigeria dama wasu qasashen. *** *** *** Niger Republic Zuwa wannan shekarar damuke ciki ta 2024 Inaas tacika shekara goma sha takwas,tayi Candy shekara d'aya data wuce,tagirma ta zama budurwa me bala'in kyau kamar mamarta Jamila,yawan gashin ta tun tana qarama har yanzu gashi yana nan har gadon bayanta,tanada tsananin kyau me daukar hankali,rana d'ai-d'ai ne ba zakaji sallamar samari a qofar gidansu ba amma Bilkisu tahana ta kula kowa,idan Inaas tafara zuba surutu saika dakatar da'ita hakan yasa takeda mutane sosai,shagwa6ar da Bilkisu tasaba mata dashi tun tana qarama hakan yasa data girma ma tacika shagwa6a,batajin kunyar kowa agaban kowa saita fara buga qafafu tana yiwa Mamanta Bilkisu shagwa6a,Allah yayi mata baiwar surar jiki da qira,uwa uba diri kamar budurwa me shekaru dayawa,tanada madedetan nashanunta wanda bazaka kirasu yan qananu can ba,kullum suna nan atsaye daram wanda yaci ace tun tuni tafara saka musu brezia amma qememe Inaas taqi sakawa ko irin na kayan gwanjonsu ne dasuke siyarwa,Bilkisu tayi mata magana harta gaji tarabu da'ita,gani take atsaye suke mezaisa tadinga saka wata brezia tana fama. Sana'ar saida gwanjonsu tana nan sunayi babu abinda suka daina,sunan Bilkisu yakoma Bilkisu Me gwanjo,yayinda ita kuma Inaas yawancin mutane suke kiranta da 'YAR ME GWANJO. kowanne lokaci Inaas bata kunyar kowa haka zata d'auki kayan gwanjonsu takai musu gida-gida kuma dayake tanada surutu nan da nan zatayi ciniki tadawo gida. Sun tashi daga garin Dungas,sunkoma cikin Niamey,sakamakon aiki da Babanta Farouq yasamu yana koyarda yaran wani attajiri mesuna ALHAJI AUWAL..., " (me karatu in baku manta ba Alhaji Auwal shine aminin Alhaji Mekudi,wanda yakira Alhaji Mekudi awaya cewa angama kammala komai na aikin kamfaninsa kawai shi ake jira yazo yabude,yazo nijar yabude kamfani a hanyarsa ta dawowa gida ya tsinci Jawad,to Alhaji Auwal yadauki Farouq Baban Inaas aikin koyawarwa,yana zuwa kullum yana yiwa yaransa lesson, kasancewar sa tsohon malamin makaranta) Farouq yanema musu d'an qaramin gidan haya daidai na talakawa gida,gidan nasu yana daga can baya-bayan gari inda babu cukowar mutane dayawa a unguwar. Suna rayuwar su cikin farinciki,Inaas bata barin Bilkisu tayi tunani tana qoqarin sanyata farinciki,tasan ba'itace ta haife taba,haka tasan labarin 6atan yaron ta,tasan komai kasancewar Bilkisu bata 6oye mataba,hakan yasa tadage wajan ganin ta maye mata gurbin d'anta data rasa,tana sata tanajin idan d'anta ya6ata to tanada wata yarinyar yanzu. Kamar kullum,cikin sauri tashigo gidan nasu tana qwalawa Bilkisu kira "Ammiy.., Ammiy!" Cikin sauri Bilkisu tafuto daga d'aki tana sake gyara d'aurin dankwalinta,tana nan har yanzu kyawunta bai gushe ba,mace mai haquri da hangen nesa,jikinta yana nan da kyansa kamar ba'ita ta haifi Jawad d'an shekaru 37 ba,kafin tayi magana Inaas tasaki kayan gwanjon su aqasa yayinda ta damqawa Bilkisu wasu takardu a hannunta,ita kuma tashige bandaki da gudu saboda wani mugun fitsari datake ji. Bilkisu taja kujera ta zauna,ta ajiye takardun agefe sannan tabude qullin kayan gwanjon nasu tana dubawa. Inaas tafuto daga bandaki tad'aga bakin buta ta wanke fararen qafafunta,sannan ta tsugunna tafara alwala,dogon gashinta kuwa Ammiy ta nannad'e matashi a qeyarta kamar ribon,saida tagama alwala sannan tadawo kusada Ammiy ta zauna tace"Ammiy albishir..." Bilkisu tayi ajiyar zuciya tasan halin Inaas yanzu haka surutu zata fara, danhaka ta katseta tace"kafin albishir d'in de,yanaga kayan kin dawo dasu kwata-kwata baifi qwaya biyar kika siyar ba?" 'Dan qanqanin bakinta taturo gaba cikin shagwa6a sannan tace" Ammiyyyyy...." taja sunan,sannan taci gaba da fadin"Ammiy ina miki maganar albishir kinata gwanjo,to kwanan nan za'a daina cemiki Me gwanjo nima adena cemin 'yar me gwanjo,nasamu aiki a kamfanin Mekud'i Oil,danaje na zauna Ina tsara wani ma'aikacin nasu,wallahi yana ganin takarduna ya kaiwa manager,bayan sunmin gwaje-gwaje kawai saiji nayi ance an daukeni" Bilkisu ta zaro idonta cikin farinciki sannan tasaki murmushi tace"Inaas da gaske kinsamu aiki a wannan babban kamfanin? kai Alhamdulillah,to kuma sai akai Yaya? bani labari mana" Inaas ta kwashe da dariya sannan tace"bakece kikemin maganar ban saida kayan gwanjonmu ba,to ai ajiyar kayan nabayar awani gida natafi kamfanin na basu takarduna,da har yafara yatsina fuska wai da secondary zamu daukeki aiki?" (ta gwada yanda mutumin yake magana)sannan taci gaba da fad'in "nikuwa danaga zai kwafsa min ai tuni nagyara zama naketa zuba masa zance wallahi Ammiy sai gashi yanata dariya,yanzu gobe babu zuwa tallar gwanjo,nazama ma'aikaciyar kamfani" Ammiy tayi murmushi tana kallon Inaas tanajin wani irin farinciki,akoda yaushe tana Alfahri da Inaas,ajiyar zuciya ta sauke tace"to Allah yasanya Alkhairi,kidinga nutsuwa de idan kinje ba kowa zaki dinga sakewa dashi kina wannan surutun naki ba" Inaas tayi fari da idonta tace"angama Ammiy" Bilkisu tamiqe takawo mata abincinta, bayan tagama cin abincin tayi sallah, sannan suka zauna Bilkisu tafara gyara mata gashin kanta,already gashin nata a wanke yake,saita had'a wani turaren wuta na gashi me mutuqar qamshi,ta warware mata gashin tataje mata shi,gashin nata yayi wani irin tsawo har yanaso yawuce gadon bayanta yata6o mata duwawu kamar lokacin datake qarama, bayan tagama taje mata tadaga gashin sama tasaka turaren wuta aqasa tana turara mata gashin, yayinda Inaas ta lumshe idonta tanajin dadin yanda Ammiyn take gyara mata kanta. *** *** *** UAE. (Abu Dhabi) Ya kasance kowacce rana baya cikakkiyar awa biyar,batare da yaji muryar mahaifinsa ba,duk yawan ayyukan dake gabansa kokad'an baya sakaci da kiran Daddy,yana qaunar mahaifin nasu,kallo d'aya yayiwa P.a dinsa dake tsaye agefensa p.a yagane abinda yake nufi,cikin sauri yakira masa Alhaji Mekudi. Adede lokacin Alhaji Mekudi yana cikin mota Malam Sulaiman yana jansa da sauran motoci a bayansu zasuje d'aurin auren yaron wani Sanata. Cikin sauri Alhaji Mekudi yad'auka tareda fadin"Jawad" Daga nasa 6angaren ya lumshe idonsa sannan yace"Daddy good afternoon" Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya,maimakon ya amsa masa gaisuwar tasa saiyace"Jawad Ina hanya zanje wajan d'aurin auren yaron Senator Hamza" Jawad yanajin haka yasake lumshe idonsa fuskar nan tasa kokad'an babu walwala akanta,yasan cewa Daddy Ishara yake masa akan shi yaqi aure gashi zaije d'aurin auren yaron abokinsa. Shima maimakon yabawa Daddy amsa sai yace"Daddy i hope you're fine...." Alhaji Mekudi yace"maganar danakema kenan? yaushe zaka shigo Nigeria? ya kamata ka sassautawa kanka wannan aikin kadawo gida ka ajiye iyali kuma,Jawad shekarunka 37 yanzu,sai yaushe zakai aure? mahaifiyar ka kullum maganar datake kenan". ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name https://chat.whatsapp.com/FzjixDJbvvWCUd7az9a0K0 9&10 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. ___ Runtse idonsa yayi sannan yabud'e,yanda ayyuka suke hanashi samun sukuni ina yaga lokacin dazaima fara duba yarinyar dayake so?,ita kanta soyaiyar idan yahad'u da yarinyar ma bazaice ga yanda zaiyi ba,ko irin kula 'yanmatan da samari sukeyi alokacin dasuke taashan balaga shikam baiyi ba,abinda yasani kawai shine kasuwanci,dashi aka bud'e masa ido,akan turbar kasuwanci aka fara d'orashi,baida lokacin dazai bawa mace,idan yace zai'iya kulawa da'ita ma to yayiwa kansa qarya,ahankali yayi ajiyar zuciya sannan yace"Daddy i don't have any girl friend,nabaku dama,kuza6omin duk wadda tamuku" Alhaji Mekudi yakashe wayar cikin taqaici,sannan ya lumshe idonsa, Malam Manu dayake driving yanajin duk abinda yake faruwa,yayi murmushi yace"Alhaji aida kun barshi yakawo wacce yakeso da kansa,'ya'yan yau idan sukaqi mace abun ba dad'i,Jawad d'in har yanzu ai yaro ne,nawa yake?" Alhaji Mekudi yabude idonsa yayi wani murmushi irin nasu na manya najin dad'i,duk wanda zai shagwa6a masa Jawad d'insa yana sonsa,aduniya in kanason kwanciyar hankalinsa to ka yabi d'ansa Jawad,ya kalli Manu driver yace"Man Sulaiman bakasan halin d'annaka ba,idan muka barshi to ina tabbatar ma ahaka zamuyi ta tafiya ba zaiyi auren ba,saboda agabanka yatashi shiyasa kake masa kallon qaramin yaro,duk sa'anninsa fa sunyi aure,wani lokacin idan na nutsu nayi duba akan sabgoginsa sai naga idan yazo qasar ma ko sau d'aya ba zakaji yana wayar nan irinta samari kaji Jawad yana waya da mace ba,sai Inga kamar ko bashida sha'awa ne"(🙈) Malam Manu yayi murmushi baice komai ba,ganin yanda salon maganar Alhaji Mekudin ta sauya wannan maganar kuma tsakanin sane da d'ansa. Alhaji Mekudi ya kalli Malam Manu wanda yake driving cikin qwarewa,yatuna lokacin daya daukeshi aiki alokacin baqi ne,amma yanzu ya washe yakoma chocolate,girma yafara futowa ajikin sa,amma yanayin jin dad'i da hutun dayake samu yasa girman ya 6uya,ga wani haqorin makka daya saka tun zuwansa Hajji da umara wanda Alhaji Mekudin shine yabiya masa,haqorin Makkan yasake qawata haqoransa yayi masa kyau sosai,ya sassauta muryarsa duk da su biyu ne amotar yace"nikam Man Sulaiman tsawon shekarun nan damuke tare banta6a jin kayi min maganar iyalinka ba,bakada yarinya ne ko yaro?sannan meyasa bazaka d'auko matarka kuci gaba da zama tareda muba?" Gaban Malam Manu yayi wata irin bugawa,jikinsa yafara rawa cikin sauri yataka burkin mota yafashe da wani irin kuka,cikin sauri motocin dake biye dasu na security suma suka taka burki sannan suka futo da sauri suka fara duba motar ko wani abu ne yasamu Alhaji Mekudin. Alhaji Mekudi yazuge glass d'in motar yayi qasa,sannna ya kallesu yace"no problem we're fine" Security suka juya cikin sauri suka koma motarsu,Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya ya kalli Malam Manu, wanda kai tsaye bazai ce Malam Sulaiman ba saide Man Sulaiman, yace"Man Sulaiman meyake faruwa haka?kode nayi laifi ne dalilin tambayar danayi ma?" Cikin sauri Malam Manu ya girgiza kansa,sannan yashare hawayen idonsa yace"kodaya Alhaji,bakamin laifin komai ba Alhaji,tsakanina dakai saide nace Allah ya azurtaka da Aljanna mad'aukakiya,Alhaji kakaini Hajji,kakaini Umara,kabani muhalli nazauna tare daku,kabani ci da sha da kudi,saide duka abinda nasamu banida kwanciyar hankali,haqqin iyalina yana nan yana kan bibiyata,bana cikakkan kwana uku banyi mummunan mafarki ba" Alhaji Mekudi yace"subhanallah duk me yayi zafi haka?" Malam Manu yace"Alhaji na gudu nabar iyali na da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe,talauci yamin katutu,bamuda cin yau bamuda na gobe,har takai takawo idan naci bashi banida wanda zai biyamin nima bazan Iya biyaba saide ayimin dukan kudin,iyayen Bilkisu sun damqamin amanarta a hannuna kafin su rasu,naci amanar Bilkisu natafi nabarta,bansani ba tana raye kota mutu,abinda tahaifa yana nan koya mutu,duk lokacin dana daura aniyar zuwa gida sai inji gabana yana faduwa inji tayaya ne zan iya kallon Bilkisu in fuskanceta in nemi yafiyarta? da hannunta take aikin qarfi tatara mana kudi muyi buqatun gida dashi,kai hatta kudin motar dana samu nagudu Lagos itace tabani su alokacin kudin sunada daraja tace nafara tarawa dan musamu abinda za'a yankawa yaron cikinta na suna,Bilkisu tanada haquri,ta yarda dani,tana mutuqar sona amma duka na rusa komai,bazan iya kallon idon Bilkisu ba,hakan yasa nakasa zuwa gida nazauna anan ina jira kafin Allah ya dauki raina" Alhaji Mekudi yacire medical glass din idonsa yagoge qwalla sannan yamaida glass din yace"Ash'sha,Man Sulaiman kayi kuskure,ai ba'a gudun annoba,Allah yana sane da halin dakuke ciki especially ma kaida Allah ya azurtaka da mace irin wannan,ya kamata ka shirya kaje ka fuskanci iyalinka karoqesu gafara sannan ka daukosu kudawo nan gaba dayanku" Malam Manu yagoge hawayen idonsa yace"to Alhaji,insha Allah zanyi yanda kace, nagode" Daga nan yaja motar suka qarasa wajan d'aurin auren,saide kafin su qarasa har anriga an d'aura sai gaggaisawa dasukai da mutane. Da daddare wajan qarfe takwas,Alhaji Mekudi yana zaune acikin tangamemen falonsa na sama,wanda yaji wasu lafiyayiyun kujeru 'yan gajeru ruwan cement,fruit ne agabansa yanasha yayinda Hajiya Zaliha take gefensa a zaune tana ganin labarai a bbc. Tasake zama hamshaqiyar uwa matar Alhaji,haka kuma uwar Alhaji,wuyanta da zoben hannunta da awarwaron hannunta gaba daya na gold ne,stone work din jikinta sai walwali yake. Alhaji Mekudi ya'ajiye fork din hannunsa wanda yake daukan apple dashi, ya kalli Hajiya Zaliha yace"d'azu munyi magana da yaron ki,nayi masa maganar aure yace yabamu dama munema masa,lokaci yayi daya kamata ace yayi aure,muma muga 'yan jikokinmu agidan" Hajiya Zaliha tasaki murmushin farinciki sannan ta d'aga hannunta sama tace "Alhamdulillah,Alhamdulillah,yau-yau d'innan kuwa zansa abinciko min yaran garinan,daga kan 'ya'yan 'yan kasuwa har zuwa na siyasa duk zanyi magana sai muga wacece ta dace dashi" Alhaji Mekudi yagyad'a kansa cikin gamsuwa da bayanin nata yace"hakan yayi,nima munyi magana da Aminina Alhaji Auwal,saboda haka zan kira Jawad d'in insashi yakira can Nijar d'in su gaisa da Fauziya da Ummi ko za'a dace sai muyi musu had'in gida" Hajiya Zaliha tace"hakanma yayi,nima daga nawa 6angaren zanta bincikawa,har muga abinda hali zaiyi, idan yaza6i 'ya'yan Alhaji Auwal d'in shikkenan,idan kuma na nan Nigeria yaza6a shikkenan" Sunacikin wannan farinciki gidan tv na bbc suka fara karanta labarin Babban matashin d'an kasuwa Jawad Mekud'i yabiya wa yaran talakawa daliban University's kudin registration kimanin naira million talatin. Alhaji Mekudi yayi murmushi yad'auki wayarsa yakira Jawad,bugu biyu Jawad yad'auka,cikin miskilancinsa kamar bayason yayi magana yace"Daddy..." Alhaji Mekudi yace"yanzu nake ganin labarai kabiyawa yara kudin Registration,ka kyauta sosai,musanman yanzu dana samu labari ana cewa kud'in karatun yara yaqaru,kaci gaba da taimako idan da hali,na tabbatar kaima Allah zai taimaka maka" Cikin tsananin biyaiya yace"ok Daddy insha Allah" Alhaji Mekudi yasake cewa "yawwa idan kasamu dama kakira Babanka na Nijar yanzu-yanzu ku gaisa" Cikin mamaki Jawad yace"Daddy Babana?" Yayi tambayar cikin sigar rashin gane wanda ake magana a kansa. Alhaji Mekudi yagane hakan,dan haka yace"Aminina Alhaji Auwal na Nijar" "Daddy i don't have...." Cikin sauri Alhaji Mekudi ya katse shi yace"you don't have his number,hakane?" Cikin sauri Jawad yace"Yes Daddy" Alhaji Mekudi ya girgiza kansa yace"you don't have a girl friend,you don't have his number,Jawad kai shikkenan komaima babu?,rayuwa zata iyu da haka? kaida ya kamata ace kacemin kanada number sa kana kiransa ma kuma gaisawa, wanne irin zumunci ne wannan,?zan turoma number sa yanzu,saika kirashi" Yana fadin haka yakashe wayar, Jawad ya lumshe idonsa mecike da jin bacci,dan yanzu haka qarfe goma shadaya dayane na dare a agogon qasar Dubai. Bayan yagama waya da Jawad kai tsaye Alhaji Auwal yakira, bayan sun gaisa yace masa "nasa Jawad yakira ka,idan yakira,ka had'ashi da yaran gaba d'ayansu su gaisa ko Allah zaisa su daidaita kansu da d'aya daga cikinsu" Alhaji Auwal yayi godia daga nan suka kashe wayar. Bayan Alhaji Mekudi ya ajiye wayarsa agefe Hajiya Zaliha tagyara zamanta ta kalleshi tace"Alhaji yaron nan fa yana kashe kudi dayawa" Alhaji Mekudi yayi mata wani irin kallo sannan yace"gaskiya kam,amma kuma maimakon raguwa kullum kud'in sake qaruwa suke,kinga amfanin taimako ko?" Hajiya Zaliha tayi wani irin murmushi mai ciwo ganin cewa cikin hikima Alhaji Mekudi kamar magana ya gwa6a mata,kokadan bataji dadi ba,tasaki ajiyar zuciya tasake cewa"to Alhaji mezai hana muyiwa Jawad magana Fu'ad ma a bashi wani 6angare na dukiyar yana juyawa?" Kai tsaye yace"Fu'ad be goge akan kasuwanci ba" Cikin damuwa ta sauya salon zancen nata tace"hakane,to amma Alhaji aikin yayiwa Jawad yawa,kana gani kwata-kwata baya samun damar da zaizo ya zauna tare damu,yaron nan tun yana qarami kakaishi wata qasa ka ajiye,yagama karatu ka d'orashi akan harkokin ka nacan,qarshe ma duka dukiyarka ka maidata hannunsa komai da komai yazama nasa,tokai mezai hana ka dinga tayashi dawani abun ko shima zai samu ya huta ya dinga zuwa gida muna ganinsa akai-kai yanzu fa tsakaninmu da d'anmu saide gani daga nesa,saide mu ganshi a tv" Alhaji Mekud'i yasaki ajiyar zuciya sannan ya fuskanceta yace"nina tsufa,har yaushe ne zanci gaba da wannan harkar kasuwancin? Fu'ad kuma bai karanci kasuwanci ba idan zaiyi kasuwanci ma saide yayi abu daka,Jawad d'in de shine matashi beyi yarinta da kasuwanci da gwagwarmaya ba kuma baiyi tsufa ba,shine matashi sabon jini wanda zaiji da matasa da manyan 'yan kasuwa,ina ganin mubarshi yayi abinda yaga yadace kawai, maganar namaida sunansa akan dukiyata kuma idan kin manta bari in tuna miki yaron nan karki manta bashida gadona ko d'aya,kuma dukiyar tareda shi na tarata,abar maganar dukiya ko wani qyale-qyalen duniya ma mune iyayen Jawad,bayan mu bashida kowa,sannan karki manta Fu'ad da Jawad abu d'aya ne,yarannan sun taso suna son junansu,ko bayan babu ranmu NI DAKE,nasan cewa Jawad zaici gaba da kulawa da dan'uwan sa,hakane?" Sai alokacin Hajiya Zaliha tasaki wata irin ajiyar zuciya,sannan tace"eto hakane kuma,to shikkenan,Allah ya tayashi ruqo,Allah yatemaka" **** Acan Dubai kuwa Jawad yasa p.a dinsa yakira masa number da Daddy yaturo masa,kasancewar Alhaji Auwal yasan da kiran nasa hakan yasa bayan sun gaisa dashi yakira yaransa 'yanmata guda biyu yace"ku kar6i waya ku gaisa da yayanku" Babbar ce tafara kar6a wato fauziya,ta gaida shi taji baya magana dajan zance irinna samari daga lafiya,sai kina karatu ko?,sai ok.... (♀️🤭) To itama dayake bawani yawan magana ne da'ita ba kasancewar ta 'yar Alhaji Auwal babban attajiri a qasar Niger,abunka da 'ya'yan manya tataso cikin gata,sai kawai tace masa "ga qanwata Ummi bye bye" (🤭) To itade Ummin tad'an jashi da surutu har tana tambayarsa yaushe zaizo qasar tasu,kasancewar bai iya qarya ba hakan yasa babu 6oye-6oye yace mata "babu rana"(🙆) Baby dake zaune agefe 'yar gidan Antyn su ce,jikar gidan ce,tana zaune agefe tana jinsu dataga zasu kaiwa Alhaji Auwal waya cikin sauri ta wullar da teddy din hannunta tace"Anty Ummi bani shi,bani shi" Ummi ta kalli Baby da sauri tana ganin ikon Allah, tasan halin Baby da surutu amma batayi tunanin abun nata yakai haka ba,babu musu tabata wayar. Baby ta kara wayar a kunnanta tace"Hello Yaya,ni ba kace abaka niba gashinan ni nace subani kai,Sunana Baby" Jawad yadaga girarsa guda d'aya yasaki wani miskilin murmushi,daga ji yarinyar irin yaran nan ne masu surutu da shiga rai,ahankali yace mata "ni Sunana Jawad Mekudi" Baby tace"nasani,Yaya Jawad kasan me?jiya aka kaini wajan wasa,nayi wasa nahau doki,saboda nice nazo ta d'aya a ajinmu,kai nanawa kazo?" Jawad yayi murmushi yace"nine na biyu,kinga kece first nikuma second" Baby ta qyalqyale da dariya tace"to kaima ankaika wajan wasa ne?" Wannan lokacin ma murmushi yayi yace"Daddy na bekaini ba, yace dole sainazo na d'aya,amma zan dage next time naqwace miki position d'inki nima sai akaini wajan wasa" Baby tace"tabdi,wallahi bazan yarda ba,to bari kaji Kullum idan Uncle Farouq yazo nice nake fara yimasa bayanin lesson d'in dayayi mana abaya,nafi kowa qoqari,bazaka qwace min position ba" Kai tsaye Jawaad yace mata "waye Uncle Farouq?" (masu karatu Uncle Farouq d'innan da yarinyar nan take maganar sa shine Farouq mahaifin Inaas,Qanin Bilkisu me gwanjo,inba ku manta ba nace muku yana yiwa yaran Alhaji Auwal lesson,yawwa🤒) Baby tace"shine yake mana lesson,shima yace nice best student d'insa" Jawad yayi murmushi ya girgiza kansa yace"ok,tokici gaba da karatu,idan kika sake zuwa ta d'aya zan kawo miki chocolate da kaina" Cikin murna Baby tasakar masa kiss ta wayar sannan tatafi da gudu ta kaiwa Alhaji Auwal wayarsa. *** *** *** Abuja Nigeria Washegari sassafe Man Sulaiman yayi sallama da Abuja yatafi Jigawa kamar yanda Alhaji Mekudi yabashi shawara jiya. Kasancewar jirgi yabi hakan yasa wajan shabiyu na rana ya isa garin,tunda yashigo garin yake kalle-kalle yana tuna baya,agefe guda kuma banda fad'uwa babu abinda gabansa yakeyi,duk wanda yake had'uwa dasu babu wanda yasani shima babu wanda yagane shi,kai tsaye gidansa yanufa anan yaga gida yazama gidan tarihi domin kuwa sai fili,d'akinsu qwaya d'aya na qasa shima babu yazube,nan take ya zube awajan yadira gwiwar sa aqasa yafashe dawani irin matsanancin kuka,hakan yasa yara suka fara taruwa a kansa ana kallonsa,daga nan manyan gari sukaji labari suka nufo wajan,d'aya daga cikin manyan ne yace"kamar Malam Manu" Man Sulaiman yad'ago kansa da sauri ya kalleshi,kallo daya yayi masa yagane shi, cikin kuka yace"nine malam jafaru" Mutumin da'aka kira da malam jafaru yace"ikon Allah,ashe muna raye Allah zai nuna mana wannan ranar,Malam Manu Ina kashige?munyi tunanin kaida Balki Me gwanjo rai yayi halinsa" Cikin sauri malam Manu yanufeshi yace"Ina take? Bilkisu tana raye? meta haifa malam jafaru?" Malam jafaru yagoge qwallar idonsa yace"malam Manu kad'au haqqi,Balki me gwanjo tatafi,haqqinta bazai barka ba,mu qarasa wajan Maigari sai kaji komai" Tunda malam jafaru yace Balki me gwanjo tatafi daga nan jikinsa yayi sanyi,saboda yayi tunanin tafiyar mutuwa yake nufi. Lokacin dasuka qarasa wajan Megari saiyaga ba Megari daya sani da bane,wancen Megarin yamutu,d'ansa ne akan kujerar yanzu,bayan kowa ya nutsu ya zauna daya daga cikin tsofaffin fada wanda yana raye akayi komai,ya girmi Manu sosai, tsoho ne, ya kalli Man Sulaiman yace"kalleni nan Manu,bakaji kunyar zuwa garin nan ba? Manu me Balki tama har haka dazaka gudu kabarta,Ina kakeso taje? gidan uwaka kakeso tatafi bayan kasan bayan kai batada kowa agarin nan? meyasa bazaka sata agaba kutafi ko nanda bangon duniya bane? to Balki ta haihu,da haifi d'anta namiji kuma Washegarin suna takama hanya tatafi qasar su,marigayi Megari yace tazauna damu abata jari har Allah yadawo dakai lafiya idan kana raye,amma Balki tace gida zata tafi,saboda haka bamu saniba itada abinda ta haifa suna raye ko sun mutu,sai kaje can qasar Niger din kaita bilayin nemanta qila ma idan kun had'u tahad'o maka matasan unguwa suyima shegen duka"(🤭😳😂) Malam Manu ya sunkuyar da kansa qasa yana kuka,sosai yake kuka harda shashsheka yakasa cewa komai. Maigari yayi gyaran murya yace"ayi haquri Baba Muntari,komai yawuce tunda gashi yatuba yadawo mahaifarsa,saide muyi masa Addu'ah Allah ya baiyana masa iyalinsa idan tana raye" Gaba daya fada aka amsa da "Amin" Megari ya kalli wani yaro yace"zakariyya a rakashi cikin gidana abashi masauqi da abinci" Ahankali malam Manu yadago kansa yayi godia sannan yace"inaso nafara biyan bashin dana tafi nabari akaina" Megari ya kalleshi yace"kaje kahuta Kaci abinci tukunna, zaka biyasu insha Allahu" Malam Manu yatashi aka kaishi gidan Megari dakin da ake saukar baqi,yayi wanka yaci abinci yazauna yayi shiru yana tunanin baya,lokaci zuwa lokaci yanajin hawaye yana zubowa daga idonsa,acikin wannan garin yahadu da iyayen Bilkisu sun kawo tallar magani,kafin su rasu suka bashi ita tareda amanarta,a wannan Garin iyayen Bilkisu suka rasu,yasan cewa tanada qaninta wanda suke uwa daya uba daya dashi wato Farouq,yasan Farouq sosai tun kafin a bashi Bilkisu,bayan iyayensu sun rasu sai shi Farouq yakoma Niger,yanzu shekaru talatin da bakwai baisan ta'ina zai fara neman Bilkisu ba,dole zaije qasar Niger cikin garin Dungas yanemota aduk inda take, hawaye suka sake zubo masa,yabuga kansa da bangon dakin yanajin kamar yadawo da baya gaba. Saida yayi sati daya agarin,duk wasu abokan sa nada dasuka gujeshi yanzu duk sun dawo,duk wani bashi da yasan ana binsa saida yabiya harda ninki,idan dubu daya kake binsa zai ninka maka saboda darajar kudin da d'in dana yanzu ba d'aya bane,abinda dubu d'ayan da zata maka yanzu saide dubu uku ko hud'u. Filin gidansa yasa mutane suka sake gyara shi aka fara yimasa ginin cement,samarin dasuka suka masa dukan kudin bashi a wancen lokaci yanzu d'aya bayan d'aya suka dawo suna bashi haquri. Saida yayi kwana goma cif,sannan yadora wani abokinsa akan harkar ginin gidansa, shikuma yayi sallama da mutane cikin aminci. Daga nan kai tsaye qasar Niger yanufa,bai zame ko'inaba sai garin Dungas,saida yayi kwana biyu yana tambayar su Bilkisu da Farouq amma babu wanda yagane su saboda kawai suna yake fada babu inkiya,yasha wahala kafin yasamu wanda yagane su Bilkisu,hakan yasa mutumin yayi masa jagora har gidansu Bilkisu,saide basa gidan wasu 'yan haya ne aciki,maqotan su sun tabbatar masa cewa su Bilkisu sun saida gidan tun shekarun baya,sunkoma cikin Niamey da zama. Man Sulaiman yarasa yanda zaiyi,acikin Dungas ma yayi kwana biyu yana nemansu,to idan yashiga Niamey ta'ina zai fara nemansu? wa zai kama?,hakan yasa yabi jirgi yakoma Abuja da nufin idan yasake shiryawa saiya dawo ya bazama neman Bilkisu. *** *** *** Niger Republic Tana dawowa daga wajan aiki tafara warware laffayar jikinta fara,ya kasance sai wata riga aciki 'yar qarama,ta zauna a kusada Bilkisu tace"Mom kinsan me?" Bilkisu tace"baki abun magana, yau kuma da mom kika dawo abakinki?" Inaas tace"emana,ai talaucinmu bazai hanamu walwala ba" Bilkisu tazuba mata ido tana kallonta,tana ganin tsantsar kyawun Inaas,kyawu me fizgar duk wanda yayi tozali da'ita,cikin farinciki tace"fad'amin,meyafaru yau kuma? yaya aikin naki?" Inaas tace"yawwa Ammiy,aiba dole sai masu kudi ne sukeda damar dazasu ce mummy ba,muma zamu iya fad'a,aikina lafiya kalau,dad'i nakeji wata yakusa qarewa,nakusa jin qaramm.... albashi ya fad'o in siyo mana kayan kallo,kede kimin Addu'ah kawai" Bilkisu tayi murmushi tace"tunda kikace zaki siyo mana kayan kallon nan nasan zaki iya Inaas,kina qoqarin sanyani farinciki,Allah yasa shima idan yana raye,yana qoqarin saka nakusa dashi a farinciki,saboda daga ke har yayanki Muhammad kuna zagaye da sanyawar albarka ta,kullum cikin saka muku ita nake babu ranar banza, Allah yasake yimuku albarka,yarinyata 'yar albarka ce,nasan duk mijinda kika aura yayi sa'ah" Farinciki yakama Inaas,tana so taji Ammiy tana yabonta tana zuzutata fiyeda mijinda zata aura, cikin farinciki ta rungume ta, sannan tayi cikin daki. *** *** *** Zaune yake akan kujera,fuskarsa babu walwala kawai aiki yake yamaida hankalinsa kacokam kan laptop din dayake daddannawa qirar apple,yayinda guards guda biyu suke tsaye a kansa gaba d'ayansu su biyun suna sanye da baqaqen suit,p.a dinsa yana gefe shima a tsaye yana shafa wata babbar iPad d'in Jawad. Yashiga cikin yanar gizon Jawad d'in yana fada masa abubuwan dake faruwa dakuma saqonnin da'aka tutturo masa,bayan yaci karo dawani posting da'akai a Instagram yadago ya kalli maigidan nasa yace"yalla6ai gawani masallaci yazube,mazauna wajan suna buqatar a tallafa musu zasu sabunta ginin" Ba tareda yadago kansa ba,idonsa akan computer gabansa yace"atura musu" Cikin sauri p.a ya russuna yace"ok sir" Yaci gaba da duba saqonnin yana bawa mutane amsa, saida yadauki kusan minti ashirin sannna yasake kallon Jawad yace"yalla6ai gawani shafi sun dora photon wani yaro qashin bayansa yasamu matsala sakamakon daukar buhun shinkafa,za'a yi masa aiki ana buqatar one million naira,yanzu sun had'a seven hundred thousand Naira " Wannan lokacin ma batare daya kalleshi ba yace"atura musu two million,please p.a kayi abinda yadace, banason magana" p.a yanajin haka yayi gum da bakinsa (🤫) Da yamma kamar yanda yasaba da gashi sai wani gajeren wando yashiga cikin swimming pool din gidan yana swimming,yadade sosai yanayi sannan yafara taka wata matattakala zai futo,yana futowa ruwan dabe gama barin jikinsa ba yake tsiyaya aqasa,yayinda lafiyaiyar farar fatar jikinsa take daukan ido tana wani irin shinning,yayinda gajeren wandon jikinsa yaffida shatin abubuwan sa muraran(🙈) Kasancewar yashiga ruwa. yana qarasa futowa wayarsa tafara qara,p.a ya matso da sauri yabashi,guard dinsa kuma sukai sauri suka sanya masa wata farar riga ta towel kawai shide hannunsa yabude musu sukuma suka zura masa rigar daga bayansa. Wayar yakara a kunnansa, daga dayan bangaren baby tace"Hello Yaya" Yasan cewa su Daddy basu da wata yar'uwa sai Yaya Mariya kuma batada qananun yara,haka Mummy batada wata alaqa da yara,hakan yasa mamaki ya kamashi jin muryar yarinya tana kiransa,cikin mamaki da rashin sani yace"wacece?" Daga d'ayan bangaren Baby tace"oh kama manta dani Yaya? Baby ce,Babyn Niger,yaushe zakazo kakawo min chocolate din?" Lokaci d'aya yatuna da yarinyar,yasaki wani irin murmushi sannan ya zauna yace"Baby waye yabaki number ta?" "wajan Papa naje yabani,Yaya zakazo gobe? inaso inganka inaso kakawo min chocolate" Cikin sauri Jawad yazaro idonsa yace"gobe gobe Baby? kinga nayi miki alqawari very soon zanzo,amma sai kinyi qoqari a school kinzo ta d'aya" Cikin zumud'i tace"to zaka siyomin teddy?" "harda jirgin sama metashi Babyna,zan daukeki mutafi Europe kiyi wasa" Cikin farinciki yarinyar tace"to Yaya saikazo,I luv you bye bye" Bata jira amsar sa ba ta kashe wayar,Jawad yasaki ajiyar zuciya yana murmushi,sannan yabawa p.a dinsa wayar tareda fadin "kiramin Daddy" P.a ya kar6i wayar yafara neman layin Daddy cikin ransa yana mamakin yanda Yalla6ai Jawad yake son mahaifinsa,wani lokacin ko awa uku ba'a yi zaice akira masa shi. *** *** *** Niger Republic Tsaf tagama shiryawa cikin baqar laffaya,laffayar ta tsufa amma ta goge ta sosai babu alamar datti ko tattarewa ajikinta,ta dauki kibiya ta tsaga dogon gashinta tarabashi abiyu,sannan tafuto tsakar gida wajan Babanta da Ammynta ta tsugunna agaban Bilkisu sannan tace"Ammiy dauremin" Babu musu Bilkisu tasa hannu ta daure mata gashin nata sosai yanda bazai kunce ba,tamiqe tsaye tasake gyara laffayar sannan ta kalli Bilkisu tace"to Ammiy nikam nagama bani kud'in kayan gwanjon" Bilkisu tace"kije ki kar6o kawai sai akai mata kud'in daga baya idan ansamu" Cikin sauri tace"kai Ammiy dan Allah,ni wallahi banason naje nace mata tabamu kayan nan babu kud'i,nikam Allah ki kawo kudin natafi" Tafadi hakan cikin sigar shagwa6a. Cikin sauri Bilkisu tajata jikinta cikin sigar lallashi tace"kinga ya'isa haka,haba Inaas,kayan nanfa duk sati muke kar6a,kuma bamu ta6a cinye mata kudi ba,yau d'aya de fisabilillah kije ki kar6o mana,itama ai tasan za'a bata ko?,yi maza kije ki kar6o karkuma ki tsaya awani wajan" Dan qaramin bakinta taturo gaba sannan ta amsa mata tatafi. Bayan fitar Inaas,Farouq dayake zaune yana karatun qur'ani yasaki ajiyar zuciya bayan yagama kallon dramar tasu yace"Yaya kenan,kina mata irin wannan soyaiyar tayaya zaki barta tayi aure?" Bilkisu ta zauna ta fusukance shi tace" nikaina ina tunanin wannan ranar wallahi,nikam Farouq auren nan dolene ne sai anyi?" Farouq yace"aure ba wajibi bane Yaya, amma sunnah ce mai qarfi" "to gaskiya banajin Inaas zatayi aure, gara tabarshi tunda kaima yanzu gashinan kace ba dole bane,banaso tayi nesa dani,shiyasa nake Addu'ah Allah ya bayyana min d'ana inbatashi insa abata agaba inta kallonta" (🤭) (tab jama'ah gida nawa za'a raba mana Jawad dinmu ne? 🤔Mummy zata nemo masa mace,Daddy yanaso yabashi auren 'yar amininsa, gakuma oga kwata-kwata itama tana so tabashi Inaas 😂, masoyan me debe kewa suma saisu kawo tasu shikkenan yacika sunnah hudu cif 😂😃💃🏼) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name 11&12 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. https://chat.whatsapp.com/LJeNOKMt7ZvJ7Hlu7btQw9 ___ Cikin tausayawa Farouq ya girgiza kansa yace"uhm" Cikin ransa kuwa yana mamakin soyaiyar d'a da uwa wato har yanzu bata cire ran zataga d'anta ba,tsawon shekaru talatin da bakwai tana sa ran ganin d'anta. Da daddare dukansu su ukun suna zaune afalo yayinda Abban Inaas yake qoqarin had'a sababbin kayan kallon da Inaas tabada kudin albashinta na farko aka siyo musu. Wani yaro ne yayi sallama daga tsakar gida yace"wai ana sallama da 'yar me gwanjo inji Is'haq" Sunan Is'haq din karaf a kunnan Bilkisu,tasan yaron sarai,a'unguwar yake gidansu babu nisa da nasu gidan, iyayensa aikin gadi suke agidan wani me kudi. Kai tsaye ta d'aga murya tacewa yaron"kaje kace bata nan" Farouq ya kalleta da sauri Sannan ya kalli Inaas dake zaune tanata zumudi ayi ahada musu kayan kallon yace"ke tashi kije" Inaas bataso zuwa ba,amma sanin halin Abban nata sarai zai'iya wanka mata mari shiba kamar Ammiy bane hakan yasa tamiqe babu musu tafita ranta duk babu dadi saboda gaba daya hankalin ta yana kan kayan kallon nan,so take ahada musu suma sufara kallo irinna mutane. Inaas tana fita Bilkisu ta kalli Farouq tace"nifa yaron nan banaso ka d'aure gindi yaci gaba da zuwa qarshe yarinya tafara sonsa kazo min da maganar zamu bata shi,harga Allah banaso ta aureshi shiyasa duk lokacin dayake turowa kiranta nake bashi uzuri,ko kad'an banason tayi irin rayuwar danayi,ai Ina shiga gidansu,su kansu gidan nasu sai suyi sati basu d'ora tukunya ba,ina tsoro itama kartaci gaba da sauraron sa azo ayi aure qarshe itama miji ya gudu yabarta kamar nawa mijin" Farouq yayi ajiyar zuciya yace"Yaya babu fa wanda yasan mijin da yarinyar nan zata aura sai Allah,aure ai nufin Allah ne idan shi dinne Allah yarubuta zata aura babu yanda zamuyi duba da yanda yake wannan nacin zuwan kullum,da talaka da me kudi duk abu d'aya ne,zata iya yiyuwa ma talakan yafi me kudin daraja awajan Allah,kiyi mata Addu'ah kawai" Bilkisu tayi shiru batace dashi uffan ba,sai karkad'a qafa take alamun ranta de baiso ba. Adede lokacin Inaas tadawo domin kuwa suna fara zancen tabashi uzuri tace masa yadawo daga baya yau tanada uzuri,saboda sai maganganu yake mata amma hankalin ta gaba daya yana gida wajan kayan kallo. Zama tayi fuskarta d'auke da fara'ah ganin kayan kallo sun tashi ga mutane nan tana ganinsu tar-tar atashar Tauraruwa tv. Tajuya ta kalli Bilkisu tace"Ammiy Ina sake tara wani kudin, zan sauya miki kayan daki" Bilkisu tace"hakama kinyi qoqari Inaas,Allah yayi miki albarka,nasan da yayanki yana nan bazai bari kiyi komai ba amatsayin ki na mace,shine zai kula dake..." *** *** *** Tun bayan kiransa da doctor yayi yasanar dashi rashin lafiyar Daddy jiya, hakan ne ya hanashi sukuni saida ya diro qasar yau Acikin private jet din gidansu me sunan mahaifinsa yazo,tun miqewarsa daga cikin jirgin zai futo gaba d'aya ma'aikatan jirgin suka fara rissina masa cikin girmamawa. Yana futowa yashaqi is'kar Nigeria ya lumshe idonsa,rabon sa da qasar tasa kusan shekara daya da wani abu kenan, yayi bala'in kyau cikin suit ruwan toka,fatarsa tayi luwai luwai gawani glass da yasa me launin jan duhu wanda yasake qawata farar fatarsa,fuskarsa kamar kullum babu fara'ah kana ganin fuskar kasan cewa babu wasa,sajen dake fuskarsa yasake futo masa da zahirin kyansa,guards dinsa dake tsatstsaye cikin sauri suka fara gaida shi saide baice dasu komai ba sai hannu daya daga musu kawai,kai tsaye yanufi manyan motocin da sukazo daukar sa guda takwas wanda kowacce number motar take dauke da sunan J.MEKU'DI tundaga number one har zuwa number eight,kai tsaye aka bude masa motar tsakiya wadda take daukeda j.mekudi number 6,yashiga bayan motar ya zauna sannan suka dauki hanyar gida,kafin su qarasa gida sai kallon agogon hannunsa yake yana ganin kamar ba tafiya sukeba,fatansa daya ya ganshi agida gashi ga Daddy yanaso yaga halin dayake ciki,cikin damuwa ya furzar dawata irin is'ka daga bakinsa. Motocinsa suna tsayawa 'yan jarida sukaiwa wajan caaaa,suna qoqarin yanyame jikin motar,yayinda get din gidan yake budewa da kansa har motocin suka qarasa cikin gidan,guard guda biyu suka qaraso da sauri suka bude masa motar,yan jarida suna ganin futowar sa suka matso kusa da get din,lokaci d'aya security suka fara dakatar dasu. Magana yake ta hanyar d'an qaramin farin Bluetooth din kunnansa,yajuya bayansa yabawa get din gidan baya kad'an,masu bashi kariya suna tsaye sai zare ido suke duk da idanun nasu yana daukeda baqin gilashi,hannun kowa dawata irin bindiga. Daga cikin wayar dayake yi ne aka sanar dashi cewa angano mutane guda hudu dasuka hada kai da ma'ajin kamfani suka saci wasu kudad'e kimanin million arba'in a kamfanin sa dake Kano state,fuskarsa babu annuri yace"daga kan manager na campany dasu mutum hud'un gaba daya atuhumesu sudawo da kudin sannan asabunta kujerar su da wasu ma'aikatan a sallamesu,sannan kayi magana da P.a yaduba jadawalin lokutan danake free,yasamun ranar dazan zauna dasu" Wayar yakashe yacire Bluetooth din yabawa p.a wanda ya matso da sauri ya kar6a,sannan yad'aga kansa ya kalli 'yan jarida yajuya bayansa yayiwa p.a dinsa magana yace"abarsu su shigo" Dama jira suke,ana basu dama kuwa suka qaraso dayawa daga cikinsu suka fara fadin "Yalla6ai,Yalla6ai" Kafin daga bisani wata daga cikin su tadaga murya tace"yalla6ai ko zaka iya bamu minti biyar?" Hannunsa guda daya yazura acikin aljihun wandon sa sannan yace"nabaku minti uku" Cikin sauri ta kalli camera man d'insu sannan tafara magana tana fad'in"masu sauraren mu kuna kallonmu kai tsaye daga gidan hamshaqin d'an kasuwa wato J.mekudi,wanda kukafi sani da Jawad Aliyu Mekudi,ayau muna sanar daku zuwan Babban d'an kasuwan mafi qarancin shekaru acikin jerin manyan 'yan kasuwa na wannan qasa" Tayi sauri tajuya ta kalli Jawad tace"ranka yadade Jawad,a shekara sau daya kake zuwa Nigeria,idan kayi zuwa biyu saida dalili,kwatsam sai gaka a Nigeria yau,shin wannan zuwan naka na bazata ko zaka fada mana dalilinsa? kazo ne domin gina wani kamfani kokuma kazo ne domin tsoratar da abokan kasuwancin sa?" Kai tsaye Jawad yace"nazo ganin mahaifi nane, baida lafiya" Wani daga cikin maza yayi sauri yace"yalla6ai yaushe zaka bamu dama mu tattauna dakai agidan radion mu?" Agogon hannunsa ya kalla ganin minti hud'u tayi,ya kalli me tambayar yace"next time" Abinda yace kenan daga haka bai sake cewa komai ba yajuya cikin takunsa na qaqqarfan namiji ingarma yayi ciki,yanajin yanda 'yan jaridar suka dinga fad'in "Yalla6ai,Yalla6ai" amma bai juyoba. Tafiya yake yana kallon gidan nasu wanda yake gida gari guda ga grass carpet amalale ta ko'ina,saikayi tafiya me nisa kafin ka qarasa apartment din gidan, manyan Sojojin dasuke shawagi agidan hannun kowanne yana riqe da bindiga d'aya bayan d'aya suke qarasowa wajansa suna masa barka da zuwa. Ya waiga ya kalli gefen damansa yatuna lokacin dasuka dawo Abuja da zama,yatuna lokacin dasuke buga ball shida Daddy da Mummy cikin farinciki ba kamar yanzu ba da bashi da lokacin kansa. Yana qarasawa had'ad'd'an falon nasu ma'aikatan dake goge-goge sai ganinsa sukai cimbau,cikin sauri suka fara gaida shi amma bai amsa ba,ko kallonsu ma baiyi ba yayi sama yana tafiya gudu-gudu sauri-sauri harya qaraso cikin dakin Daddy,a kwance ya hango shi akan had'ad'd'an gadonsa,Fu'ad yana zaune agefensa yayinda Mummy take tsaye,tana ganinsa tasaki murmushi tace"Jawad..." Cikin sauri ya qarasa wajanta ya rungume ta tareda lumshe idonsa na tsawon wasu second,sannan yad'ago fuskarta yace"Mummy kina lafiya?" Cikin farinciki tace"kafin kazo de ina jinya,amma yanzu dana ganka na warke Jawad" Murmushi yasaki sannan yayi kissing hannunta,yanufi wajan Daddy,kafin ya zauna a gadon saida yacire jacket d'in jikinsa ya ajiyeta akan had'ad'd'iyar kujerar dake ajiye agefen gadon Daddy,yabar iya tacikin kawai, hakan yasa dantsan hannunsa yasake futowa muraran a murd'e kamar zai fasa rigar tasa,ya qaraso gadon ya zauna yakama hannun Daddy yariqe daduka hannunsa biyu damuwa qarara ta bayyana akan fuskarsa. Kafin yayi magana Daddy yace"meyasa kazo?" Jawad yace"Daddyyyyy" yaja sunan,sannan yaci gaba da fad'in"Ina tunanin ajiye aikina Daddy,saboda bana samun lokacin zama dakai,bana baka kulawar data dace amatsayina na babban d'anka" "naji sauqi Jawad,kuma koda bayan raina karkayi watsi da ayyukan ka,kaci gaba da abinda yadace,kaci gaba da kula da dukiyar ku,kaja qaninka jikinka" Jinjina kansa yayi alamun amsawa sannan yakai dubansa wajan Fu'ad yace"meyake damunsa ne?" Fu'ad yad'an sosa tulin sumar kansa irinta samari yace"Yaya babu komai fa,zazza6i ne,kuma Alhamdulillah dasauqi sosai" Sai alokacin yasaki wata irin ajiyar zuciya,yasaka hannunsa yadauki file din Daddy na rashin lafiya yafara gani,sannan yasa Fu'ad yakira masa likitan sukai magana dashi kasancewar duka nasa wayoyin suna hannun p.a Saida Daddy yayi bacci sannan Mummy tace"Fu'ad ka raka yayanka daki shima yahuta tunda Daddynku yasamu bacci" Fu'ad yamiqe ya kalli Jawad yace"yaya muje" Jawad yayi masa wani irin kallo irin shine babban nan harda cewa muje,sannan yawuce yayi gaba shima Fu'ad din ya mara masa baya suka futo,Hajiya Zaliha ta tsugunna tayi kissing goshin mijinta, sannan taja masa blanket tafuto daga dakin itama. Yana shiga dakinsa wani qamshi me dadi yabugi hancinsa alamun Mummy tana sawa ana gyara masa dakin duk dadewar dayake baya qasar,babban falo ne isasshe wanda aka qawatashi da kayan more rayuwa kamar ba dakin namiji ba,sai wani qaton daki me fad'in gaske wanda kake hango hadaddan gadonsa acan qarshan dakin,photunan sane birjik adakin wanda yayi su lokacin yana karatu,wasu yayi su ne da maza, wasu kuma da mata wanda photon yake nuni da matan duk sun maqale ajikinsa. Wajan ajiye glasses yanufa kasancewar sa ma'abocin saka glasses hakan yasa shi kansa wajan ajiye glasses din wani ado akayi wa wajan hawa-hawa kowanne step Kala-kalar glass ne na zamani, ajiye glass din yayi sannan yacire agogon dake daure a hannunsa ya qarasa inda yake ajiye agogo gasunan agogon kana ganinsu tacikin glass a zahiri kamar ka meqa hannunka ka dauka,amma babu hali saida ya danna wani dan qaramin remote sannan wajan agogon suka bude yacire na hannunsa yasaka shi aciki, agefensa wajan ajiye turare ne kamar shagon saida turare domin kuwa ajikin bangon dakin akayi wata yar kanta anyi mata gida-gida irin yanda shagon masu saida turare suke yi,haka aka ware masa su gasunan kala kala sai wanda yaza6a,agefen hannun hagunsa wajan ajiye takalman sane suma birjik anyi musu kanta kamarta turare an ajiyesu a jejjere,shi kansa zai iya cewa wani takalmin ma ba lalle yata6a saka shi ba. Wanka yayi ya shirya cikin qananun kaya nashan is'ka,yana futowa yaga p.a dinsa afalo da alama waya ce zai kawo masa, a wannan lokacin baya jin zai iya magana da kowa,lokacin Daddy ne kawai. Danhaka yabashi umarni yakashe duka wayoyin sa. Mummy tana ganin futowar sa tasaki murmushi tana jin qaunar Jawad d'in har cikin ranta,cikin farinciki takamo hannunsa suka qarasa dining tafara bashi abinci cikin kulawa,saida suka gama sannan suka koma d'akin Daddy har Fu'ad,acan suka zauna tare dashi harya farka yaji jikin nasa yasamu kuzari sosai,bai nemi su fita daga d'akinba yabarsu sukaci gaba da zama dashi yanajin wani irin farinciki yau gashi ga matarsa gakuma duka 'ya'yansa maza suna tare dashi,hakan yasa yakejin dad'i sosai har fuskarsa ta nuna hakan. Misalin qarfe tara na dare yana zaune afalon su yana vedio call da computer sa dake gabansa, yayinda Mummy take gefensa tanajin dad'i yanda ahalinta ya had'u ga 'ya'yanta nan agabanta tana ganinsu tanajin dad'i kamar yanda take muradi koda yaushe, Fu'ad kuma yana kwance acikin kujera yana daddana wayarsa,yayinda tangamemiyar plasma ta falon take aiki Mummy tana ganin labarai kamar yanda al'adar gidan take da wahala kaga suna kallon shirme. Ita kadai ce hankalin ta yake kan kallon,lokaci zuwa lokaci tana kai dubanta wajan Jawad wanda yake vedio call d'insa cikin nutsuwa,kayan jikinsa ta kalla ba shigar dazu ce ajikinsa ba,wannan karon wando ne three quarter ajikinsa sai riga marar hannu wadda ta bayyana masa manyan dantsan hannunsa ma'abocin d'aga qarfe. Coffee d'in gefensa yad'auka yayi sipping kad'an,sannan yaci gaba da magana ta computer tasa. P.a ne yashigo falon ya russuna yayiwa Mummy barka ta amsa da fara'ah a fuskarta,sannan yasake rissinawa yabawa Jawad waya,fuskarsa babu walwala kokad'an ya kalli p.a yace"P.a kamar nace kakashe wayoyin nan ko?" Cikin ladabi yace"Yalla6ai naga wayoyin suna qoqarin wuce awa uku ne a kashe,Ina tsoro karmu rasa wata damar ta wani kiran me muhinmanci" Ajiyar zuciya yasaki sannan ya lumshe idonsa yabude ya dauki wayar bayan yabawa baturen dasuke vedio call dashi haquri akan yabashi minti d'aya. Jawad yana waya,yayinda p.a yake shafa iPad din hannunsa cikin qwarewa,saida yagama wayar yabashi sannan cikin ladabi yasake kallon Jawad din yace"yalla6ai Mr.Joshua yaturo saqo ta Email yana gayyatarka a matsayin babban baqo zuwa wajan taron dazai qaddamar na had'akar kamfanin sa,yaji labarin kashigo qasar" "kafada masa nadauki nauyin d'akin taro da abinda kowa zaici yasha awajan" Cikin sauri p.a ya rissinar da kansa alamar amsawa,daga nan Jawad yadauki computer sa yaci gaba da vedio call d'in yatashi yabar falon yakoma sama wajan Daddy,anan yatarar dashi har yayi bacci,hakan yasa shima yakoma yayiwa Mummy saida safe sannan yawuce d'akinsa ya kwanta. Cikin dare ya farka cikin mawuyacin hali na tsananin sha'awa,daqyar ya'iya tashi ya lalubo maganin sa yasha,kamar yanda ya kusan zame masa jiki baya daukan tsawon lokaci batare da yasha maganin ba. Kan gadon yakoma yaja fillo yayi masa wata irin mahaukaciyar runguma fuskar sa sharkaf da gumi,sannan wani irin baccin wahala yasake daukan sa. Washegari sassafe suka fara motsa jiki shida Fu'ad awani d'an qaramin waje da aka qawatashi da kayan motsa jiki kala kala,dayake asama wajan yake hakan yasa suke hango komai dake wakana a gidan,shide Fu'ad yagama nasa waya ce a hannunsa yana chat yayinda hannunsa na dama yake riqeda cup din coffee yanasha ahankali, amma shi oga Jawad kamar ansake zigashi,kasancewar babu riga ajikinsa hakan yasa murd'ad'd'un dantsan hannunsa suka sake bayyana,fatarsa sai sheqi take,saida yagaji dan kansa sannan yakoma kan kujerar dake gefe ya zauna yana maida numfashi,d'an qaramin gajeren wandon jikinsa tagaba yabaiyana abubuwan sa muraran. (🙈) Saida ya nutsu sannan ya kalli Fu'ad wanda hankalinsa kacokam yakoma kan chatting din dayake,yabugi kafad'ar Fu'ad d'in sannan yace"muwuce" Babu musu Fu'ad yatashi sukai ciki. Awajan yin break gaba d'ayansu su hud'un harda Daddy wanda yaji sauqi duk suka had'u suka zauna,Mummy tatashi zata zubawa kowa abincin sa Jawad yayi sauri yatashi yahanata zubawa,yadauki plate d'in kowa yana zuba masa. Fu'ad ya kalleshi da farinciki yace"abun mamaki yau Yaya ne atare damu" Jawad ya kalleshi yace"yes kuma ba saboda kai ba,saboda iyayena nad'auki hutu nad'an wani lokaci domin na zauna tareda Mummy da Daddy na" Gaba d'ayansu suka saki murmushi Fu'ad yace"dama aini zuwana na musanman ne,bazaka had'a zuwana danasu ba" Mummy takai masa hannu zata murde masa kunne ya kauce yana dariya. Cikin farinciki suka kammala break din nasu suka bar Mummy awajan yayinda suka futo compound din gidan duka su ukun Daddy yana tattaki ko zaiji dadin jikinsa, tafiya suke ahankali suna zagaya gidan Daddy yana musu zance cikin hikima duk rabin zancen nasa yanayi ne akan yanda zasu had'e kansu karsu yarda wani abu yarabasu, saida suka gama zagaya gidan sannan suka zauna a wasu fararen kujeru had'ad'd'u wanda suka sake qawata grass carpet din wajan,Daddy yaci gaba dajan yayan nasa da zantuka har suma suka saki jiki fira tayi fira sai dariya suke kwasa gaba dayansu. Sun dauki lokaci awajan a zaune me aiki takawo musu madara dafaffiya acikin jug na glass,da kofuna guda uku akai,bayan tatafi Daddy yazuba musu madarar da kansa sannan yafara bawa Jawad sai Fu'ad,haka ya dinga basu madarar da kansa kamar wasu qananun yara,zuciyar Jawad wasai yanason irin wannan yanayin wanda zai kasance da iyayensa cikin walwala. Man Sulaiman ne ya qaraso wajansu cikin girmamawa yafara gaida Alhaji. Daddy yana ganinsa yabashi hannu sukai musabaha sannan yace"Man Sulaiman tunda kadawo bamu had'u ba kasan nima jikina babu dadi" Malam Manu yayi murmushi ya kalli su Jawad cikin sauri ya russuna qasa da nufin gaida Jawad d'in,Jawad yana ganin haka cikin sauri shima yatashi ya ruqo kafad'un Man Sulaiman ya hanashi gaidashi saboda yanda yake ganin girman mutumin,uwa uba baya iya tsayawa yayi doguwar magana dashi zaiji gabansa yana fad'uwa,cikin girmamawa yace"Subhanallah Uncle yahaka?" Cikin tsananin qaunar Jawad d'in wanda tun yana yaro Allah yasanya masa qaunarsa,Man Sulaiman yace"babu komai Jawad,Allah yayi maka albarka" Jawad ya amsa azuciyar sa,yanajin dad'in duk lokacin daya had'u tsohon direban na Daddynsa bashida aiki sai sanya masa albarka. Bayan Fu'ad ya gaida Man Sulaiman Daddy ya kalleshi yace"yaya mutanan gida? ya'ake ciki dangane da iyalinka?" Cikin sanyin jiki Malam Manu yace"Alhaji saide ka tayani da Addu'ah,tatafi qasar su,amma anfada min abinda tahaifa namiji ne,bansani ba itada yaron suna raye ko rai yayi halinsa,na shirya naje har garin nasu,saide an tabbatar min cewa sun tashi daga garin" Daddy ya girgiza kansa ransa babu dad'i yace"kayi haquri" Abinda ya'iya fad'a kenan,saboda rashin iyali ba qaramin abu bane, baisan kalmomin da zaiyi amfani dasu ya lallashe shiba,Malam Manu yace"insha Allahu Alhaji nagode" Yajuya ya kalli su Jawad yace"Jawad,Fu'ad,ku tayani da Addu'ah kunji?" Jawaad dabai gane kan zancen nasu ba yagyad'a kansa alamun amsawa. Malam Manu yana tafiya Daddy ya kalli Jawad da fu'ad yace"Abun tausayi,yabani labarinsa tsautsayi da talauci yasa yabar garin su,yabar matarsa da tsohon ciki,yafad'a min yanajin kunyar had'uwa da'ita,nikuma nayi masa nasiha nasa shi yaje ya taho da'ita idan tana raye,to kunji yaje itama bata nan tatafi qasar su dama ba 'yar Nigeria bace" Tsananin mamaki ya kama Jawad,tayaya mutum zai tafi yabar mace da tsohon ciki Daddy yakira hakan da talauci? wanne irin rashin tawakkali ne wannan? cikin damuwa ya kalli Daddy yace"yagudu yabarta? wannan ganganci ne da rashin tawakkali,but Daddy why all this?" ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name 13&14 https://chat.whatsapp.com/LJeNOKMt7ZvJ7Hlu7btQw9 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. ___ Daddy yace"qaddara da talauci ai babu abinda basa sawa Jawad,talauci masifa ne,musanman awajan mata,kaga talauci yanasa mace takoma neman maza,talauci yanasa wasu yaran su fara sata,annabi da kansa ya nemi tsari da talauci,mutane dayawa idonsu yana rufewa akan neman kudi,abunda basu sani ba shine shi talauci da arziqi duk na Allah ne,idan ubangiji ya qaddara zakayi kudi to zakayi,kamar ajali ne muddin idan yazo to babu makawa,shiyasa a kowanne lokaci nakeso ka kasance kana taimaka wa mabuqata inde kanada hali,taimakon dakake saika ga ta hanyar wannan taimakon kasamu aljanna" Jawaad yayi shiru yana jinjina kansa amma yana mamakin wanne irin talauci ne zaisa karabu da matarka duk irin zaman da kukai na aure?. P.a d'in Jawad ne ya qaraso wajan kamar kullum hannunsa d'auke da takardu dakuma wayoyi,tun daga nesa Fu'ad ya hango shi yasosa girarsa guda d'aya sannan yayi qasa da kansa yana dariya yasan cewa inde anga p.a to anga aiki (😂) Yana qarasowa yagaida su sannan ya kalli Jawad yace"yalla6ai mun kar6i saqon gayyatar kane zuwa wajan bud'e sabon masallaci wanda katura musu tallafin gini" Cikin 6acin rai Jawad ya kalli p.a yace"kamarya kenan? waye yace musu nine na basu kudin? meyasa aka fad'a musu?" Daddy yayi murmushi ya girgiza kansa sannan ya kalli p.a yace"kace dasu zaizo" Cikin sauri Jawad ya kalli Daddy yace"Daddy ban son zuwa" Daddy yace"kayi haquri mana,ka daure kaje ko awa d'aya ne kabasu" Jawad yajuya ya kalli p.a wanda yayi tsumu-tsumu a tsaye,sannan yace"ranar yaushe ne zan halacci taron Mr.Joshua?" P.a yace"duka rana d'ayane da wannan Yalla6ai" Jawaad ya runtse idonsa yace"ka kwa6a min aiki p.a, please jeka" Babu musu p.a ya juya yabar wajan. Suma basu tashi daga wajan ba saida sukaga Daddy yadan warware yaji dad'in jikinsa sosai sannan suka dawo ciki. Jawad kai tsaye dakin sa ya shige yayi wanka yadauro alwala domin tafiya masallaci,bayan yadawo daga masallaci yaga har lokacin Mummy bata falon,hakan yasa kai tsaye yawuce d'akinta,adede lokacin ta'idar da sallah tana zaune akan sallaya tana karatun Alqur'ani,jingina yayi da jikin qofar yana sanye da Riga da wando qanana amma rigar yadora mata 'yar sama yabar 'yar saman abud'e bai rufe botir d'inta ba,yahard'e hannunsa a qirji,yacire glass din idonsa yasoke shi agaban rigar jikinsa ta ciki sannan yazuba mata ido yana kallonta ganin har lokacin batasan yashigo ba. Yadade a tsaye har ta gama karatun sannan ta daga hannyenta sama tafara Addu'ah a baiyane cikin yaqini tace"ya Allah ka aurar min da Jawad dina,Allah yasa muna raye muga jikokin mu" Wani irin murmushi yasaki sannan ya qaraso cikin dakin yazauna agabanta,yakama hannyenta yariqe yakai bakinsa yayi kissing hannun nata sannan yace"Mummy aure fa lokaci ne" Dan qaramin tsaki tasaki tace"Jawad kullum haka kake fada,lokaci yayi Jawad" Murmushin qarfin hali yayi yace"Mummy aina baku dama,duk lokacin da kuka shirya nima I'm ready" Lokaci d'aya farinciki ya wanzu a fuskarta,ta kalleshi dakyau tace"Allah yayi maka albarka Jawad,insha Allahu baza muyi ma za6on tumun dare ba" Murmushi yasaki sannan yatashi yakoma kan gadonta ya kwanta yana qoqarin kunna plasma din dakin. **** Kamar yanda p.a yasanar dashi, ranar da za'ai taron bude masallaci,hakan yasa ya shirya tsaf suka tafi shida Fu'ad da sauran guards dinsa,gaba daya mota uku suka dauka,waje na musanman aka bar masa acikin masallacin wanda Iya tsaruwa ya tsaru,malamin addini yanata wa'azi akan falala da dunbin ladan da'ake samu idan angina masallaci,Jawad yayi shiru yanajin wa'azin,cikin ransa yana tunanin yanzu duk wannan ladan da'ake magana akai Shima fa ubangiji yabashi ko? sai hakan yasake qarfafa masa gwiwa dangane da taimako,bayan yagama fad'ar falalar gina masallaci saiya gangaro wajan falalar sharar masallaci da ladan da'ake samu idan an tsaftace shi,daga qarshe ganin matasa dayawa a masallacin sai wa'azin nasa ya gangaro kan batun aure wanda yake magana akan matasa wanda Allah yabasu damar aure su daure suyi aure domin rage zinace-zinace adoron duniya,bawai lalle saika samu yanda kakeso sannan ne zakayi aure ba,daga nanfa jikin Oga Jawad yayi sanyi yaji kamar danshi ake wa'azin.(🤭) Tunani yafara aransa yana tuna dalilan da yasa baiyi aure ba tun tuni,nafarko kasuwancin sa,na biyu baima san soyaiyar ba bare yaga wata wadda zata dauki hankalinsa,na uku be'iya soyaiya ba tayaya zaija hankalin yarinyar? Nahudu ba lalle yasamu irin yarinyar dayake so ba,yanason matarsa ta kasance marar dogon karatu wanda idonta bai bude dayawa ba,yanason mace mai gashi yanda zai kama ya dinga wasa dashi,yanason gashin turawa da larabawa,yana birgeshi sosai,amma Allah bai bashi damar riqewa yayi abinda yakeso dashi ba,saboda shiba manemin mata bane,sannan bayason matarsa tayi aikin gwamnati ra'ayinsa ne wannan kudin daya tara ya'ishesu rayuwa,yasan cewa su Daddy zasu nemo masa mata,kowacce irin yarinya suka kawo masa zai Iya rayuwa da'ita amma ya kasance tanada gashi dakuma sauran abubuwan more rayuwa najikin mace,yasan cewa bazasu Samo masa irin matar dayake so ba wato marar dogon karatu, yasan gogaggiyar 'yar Boko za'a samo masa,babu kuma yanda zaiyi tunda shine yabasu dama su za6a masa,saide yayi haquri ya yarda ya aure ta ahakan,saide da sharadin babu aiki,matar J.mekudi saide tabada umarni bawai wani daga sama yabata ba. gaba daya sai jikinsa yagama sanyi bayan yasan cewa bafa lalle ne yasamu irin wannan yarinyar ba saide in qasar zai bari,ya lumshe idonsa yana tuna irin tsawon shekarun daya dauka yana faman shan maganin kwantar da sha'awa duk saboda wad'annan dalilan nasa, wazai aura? tanada abunda yakeso? Baigama dawowa daga tunanin dayake ba yaji p.a dinsa yana fadin "muje Yalla6ai" cikin sauri yadawo hayyacinsa yaga har angama wa'azin,Fu'ad dake gefensa sai fara'ah yake yana fadin "Yaya yau kasha Addu'ah" Kai tsaye wajan motarsa yanufa amma mutanan garin suka nuna suna so suje dashi gida yaci abinci kafin yawuce,ganin dukansu tsofaffi ne hakan yasa baiyi musu ba yabisu suka qarasa wani had'ad'd'en gida inda aka tanadar musu abinci kala kala,da naman kaji,da naman sa,saide Jawad baici komai ba saide yadauki gorar ruwa ta faro yasha d'an kadan,yayinda Fu'ad da sauran guards dinsa da p.a suka nutsu suka kwashi girki abun su. Washegari da safe gaba d'ayansu su hud'un sunacin abinci a dining, Jawad yana sanye cikin qananun kaya nashan is'ka kamar kullum,Mummy datake kusada Jawad itace take bashi abincin da spoon din hannunta,yayinda shima Daddy yake sakawa Fu'ad abaki, abun gwanin sha'awa basai an fada makaba zakasan cewa akwai tsananin Qauna a tsakanin iyayen da yaran nasu. Daddy yabude wata yar madedeciyar iPad yakamo pictures din 'yanmata tsala-tsala sunsha kyau,jikin nan an matse shi da dinkin zamani,ya kalli Jawad yace"yaran sanatoci ne,da yaran ministoci da 'ya'yan sarauta,akwai guda ukun farko acikin su yaran gamna ne kaduba kagani idan akwai wacce tama sai muje dasu Man Sulaiman da abokaina anemo ma aurenta" Dam!!! gaban Jawad yafadi,gashi de shine da kansa yabasu za6i su za6o masa matar amma saida yaji gabansa yafadi. Kafin Jawad yayi magana Mummy tace"haba Alhaji,duk da muna son abun nan aida an barshi yad'an huta tukunna,duka-duka yaushe ne yazo qasar?" Bata jira amsar da Daddy zai bata ba tamaida kallonta wajan Jawad tace"ci abincinka yarona" "shekara kusan Arba'in shine kike kira yaro? yanda kike masa kullum kina shagwa6a shi hakanne yasa yake daukar kansa yaro,tunda yazo qasar nan ban ganshi da manyan kaya ba,inda ya ajiye iyali yaga matarsa da qaton ciki kokuma yaga matarsa da Baby dole zai nutsu ya dinga saka manyan kaya yazama cikakken magidanci" Cewar Daddy. Jawad yajuyo ya kalli Daddy yanason ya kaucewa maganar yanmatan,sannan yasake juyawa ya kalli Fu'ad yace"shaddar wanne Campany ce takeda kyau?" Fu'ad da dariya ta kamashi ya kawar dakai yayi murmushi sannan yace"zanyi magana ad'inkama Yaya" Jawad ya sunkuyar da kansa qasa ransa duk ba dadi,sai yanzu ne yagane kuskuren sa nacewa su nema masa auren, daya sani yayi ta basu haquri har zuwa lokacin dazai samu wata. Daddy yagane saboda maganar matan dayayi masa ne yasa yaketa hura hanci,kokadan babu damuwa aransa yasake tura masa wayar yace"gasunan duba" Fuskarsa adaure yadauki wayar cikin sauri far-far yayi scrolling screen din,sannan ya ajiye kansa aqasa yace"basuyi ba" Daddy ya kalleshi yace"hmm" Sannan yaci gaba dacin abincinsa. Mummy tasaki ajiyar zuciya tace"to Jawad mezai hana inyi magana da Uncle dinka Bature Yaya na,sai a nema maka auren Amal?" duk ransa babu dadi haka ya sassauta muryar sa duk da baisan yarinyar ba, yace"shikkenan Mummy tunda za6inki ce na Amince" Fu'ad dake zaune yasaki murmushi,yasan Amal sosai yana bibiyarta ashafinta na tik tok, cikin sauri yadauko photon ta yadora a status dinsa yayi kalamai wanda yake nuni da cewa itace yarinyar da yayansa zai aura. Adede lokacin Yaya Mariya yayar Daddy tana zaune a gidanta tana zuba iko, wayarta a hannunta tana duba saqonni,ganin Fu'ad yayi status da photon mace hakan yaja hankalin ta hartaje tabude tagani,lokaci d'aya ranta ya6aci,idonta ya rufe da masifa, ta wullar da wayar tata can gefe,tafara girgiza qafarta. Daddy yayi ajiyar zuciya sannan yace"Alhamdulillah,Allah ya tabbatar da Alkhairi" Mummy tace"Amin ya Allah Alhaji,nasan shima Jawad zaiji dadin zama da'ita inde anyi auren,zai yaba da kyawawan dabi'un ta,lokaci daya zai sota" Fuska babu walwala Jawad yace"no Mummy,zan aure ta ne saboda ke,Mummy niban ta6a soyaiya ba,ban'iyaba,abinda nasani kawai shine kasuwanci,babu yarinyar danake tunanin zanso ta" Mummy tayi ajiyar zuciya ta kalli Jawad tana girgiza kai jikinta duk a sanyaye,taga alama rigima kawai yakeji. P.a ne yashigo falon bakinsa dauke da sallama ya rissina awajan Jawad yace"yalla6ai,shugaban babban kamfanin taliya na qasar Masar Sheik shamiy,yaji labarin kashigo Africa yaturo maka da saqon gayyatar shan shayi,zan'iya duba jadawalin lokutan dakake free sai a afada masa ranar da zakaje?" Ba tareda ya kalli P.a ba,cikin 6acin rai yace"Shan shayi ko maganar kasuwanci? P.a bakasan hutu nazo bane?" Cikin fishi yamiqe yabar dining din yanufi hanyar zuwa dakinsa ransa fal qunci dama ga maganar auren nan da'aka masa. baiyi nisa da tafiya ba,wayarsa tafara qara,cikin sauri p.a yasake cewa"yalla6ai ana..." Kafin ya qarasa cewa ana kira,cikin jin haushi yajuyo yace"waye kuma? ko Sheik Shamiy dinne?" P.a daya lura yau Yalla6ai akusa yake ya sassauta murya yace"daga qasar Niger ne" Kai tsaye yace"kashe waya" Daga nan yayi dakinsa bai sake futowa falon ba sai dare,kuma babu wanda ya nemeshi saboda sun San cewa akusa yake,da alama kadan yake jira yace yafasa auren, sukuma suna so yayi auren. Da daddaren ma ransa babu dadi fuskar nan a murtuke haka yake zaune afalo yayi shiru duk abun duniya yataru yamasa yawa. p.a yashigo falon yace"yalla6ai ana waya daga Niger,number d'azu ce aka sake kira" Babu musu Jawad ya kar6a,sannan yad'auka bakinsa d'auke da sallama,daga can 6angaren Alhaji Auwal yace"Jawad nakiraka da safe zan baka Baby itace ta dameni saina kira mata kai batajin dadi ne sai maganar ka take" Cikin sanyin jiki Jawad yace"Ya Salam nayi busy ne da safe, please Papa bata wayar" Cikin sanyin jiki Alhaji Auwal yace"Jawad saide kayiwa Baby Addu'ah Allah yamata rasuwa yanzu-yanzun nan,ka fad'awa mahaifinka kace nakira wayarsa bata shiga ba" Lokaci d'aya Jawad yaji kansa yayi masa wani iri dummm!, Baby tarasu? lokaci daya yafara fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,please Papa inaso inzo suturar ta qarfe nawa za'a yi?" Alhaji Auwal yace"sai gobe dasafe insha Allah kamar qarfe takwas" Jawad yakashe wayar yadafe kansa yana tuna irin alqawarin dayayi wa yarinyar baicika ba,gashi de baisan taba,bai ta6a ganin taba amma mutuwar ta tadakeshi. Mummy ta kalleshi tace"waye yarasu?" Jawad yad'ago kansa yace"jikar Alhaji Auwal ce,abokin Daddy na Niger" Daddy yace"ayya, to ainima bazan zauna ba,saimu shirya muje goben" Jawad yace"Daddy zaka Iya ne? jikinka yagama warware wa?" Daddy yace"a a karka damu, na warke sosai Jawad" Jawad yayi ajiyar zuciya yabawa p.a wayar sannan yace"ashirya mana tafiya zuwa qasar Niger gobe da sassafe" P.a ya kar6i wayar sannan yajuya yafita. **** Washegari sassafe ya shirya cikin shadda milk color harda babbar riga yayi bala'in yin kyau kamar ka saceshi ka gudu,yana sakkowa falo yaci karo da Hajiya Mariya yayar Daddy. Mamaki ya kama Jawad me yakawo Mama gida da sassafen nan,itada sai an dad'e ma kafin a ganta agidan,saide in wani muhinmin abu ne yafaru,cikin sauri ya qarasa wajanta tun kafin yagaida ta tana ganinsa tace"ina uwar taka?" Jawad yayi saurin yin qasa da idonsa ganin akusa take,tuni ya rissina qasa cikin nutsuwa yad'an motsa lips dinsa sannan yace"Hajiya Mama ina Kwana?" Hajiya Mariya bata amsa gaisuwar tasaba cikin masifa tace"Uwar taka tana gani da idonta za'a baka wannan yarinyar?" Tafad'i hakan tana nuna masa photon Amal dake screen d'in wayarta,saide kansa aqasa baima dago ba bare ya kalleta. Cikin Masifa Hajiya Mariya tasake daga murya tace"yarinyar da batada tarbiya?,kullum tana cikin yin raye-raye a tik tok yara suna nunamin rawar datake tana nunawa duniya jiki shine za'a dauko a liqa maka?" Shide Jawad yayi shiru baice komai ba,har lokacin kansa yana qasa baice da'ita uffan ba kasancewar yasan halin ta masifaffiya ce. Adede lokacin Mummy tafuto daga daki itada Daddy wanda yagama shiryawa zasu wuce Niger,Hajiya Mariya ta kalli Mummy tasan sarai tanada nasaba da Amal amma sai tace"da ke kinsan yarinyar ne kokuma asama-sama kika santa da zaku bashi ita?" Mummy ta sunkuyar da kanta,tarasa a'ina Yaya Mariya taji wannan maganar. yayinda Hajiya Mariya ta kalli Daddy tace"ban yarda da wannan hadin ba,aje asake bincike akan yarinyar tukunna" Tajuya ta kalli Jawad dahar yanzu kansa yake qasa ta tsatstsare shi da'ido tace"kokaine kaganota ahakan kaji kagani kana sonta harka kawo ta gida?" Jawad yayi shiru kansa yana qasa saboda babu ladabi babba yana fada kayi magana,musanman ma ita datake gaba da mahaifin sa,shi baisan dalili ba,amma yarasa meyasa koda yaushe Hajiya Mariya take nunawa kamar tafi kowa sonsa,wani lokacin qiri-qiri zata dinga yin abu kamar tafi Mummy sonsa. Kafin wani daga cikinsu yasake yin magana p.a yashigo yace"yalla6ai mungama shirya komai kai muke jira,sannan akwai baqin manoman dakace asanar dasu suzo yau zaka gansu sunyi magana zasu taso yanzu" Sai alokacin Jawad yadago kansa yace"kafad'a musu nadage ranar dazan zauna dasu,saika basu wani lokacin daya dace" Daddy yayi ajiyar zuciya ya zauna sannan ya kalli Jawad yace"tashi kuje Jawad,kayimin ta'aziyya awajan Alhaji Auwal d'in tunda Yaya tazo zan zauna zamuyi magana da'ita,nina haqura dazuwa" Babu musu Jawad yamiqe,ya kalli Hajiya Mariya cikin ladabi yad'an motsa lips dinsa sannan yace"Kihuta lafiya Mama" Daganan yabi p.a suka wuce. Daddy ya kalli yayar tasa ya sassauta murya yace"yaya zauna muyi magana,abun duk bana zafi bane" Cikin fishi Hajiya Mariya ta nemi waje ta zauna bayan tagama yiwa Hajiya Zaliha wani irin kallo. *** *** *** Yana futowa zuwa Compound guard's dinsa suka fara take masa baya har zuwa wajanda aka a dana motoci domin kaishi Airport,d'aya daga cikin guard yabude masa motar yashiga,Man Sulaiman yaja motar suka tafi,Jawad yayi shiru ya lumshe idonsa yana zaune abaya,kwata-kwata yakasa sakewa ganin wanda yadauko shi,kokadan bayason ganin mutumin yana aiki bare kuma ace shine wanda zaijashi amota,haka nan yake jin qimar mutumin aransa,saide labarin sa da Daddy yabasu na gudun iyalinsa kwata-kwata baima sa dadi ba. Har suka je Airport shide Jawad baisaki jikinsa sosai ba,har saida jirginsu yatashi. Bayan wani lokaci jirgin su ya sauka a Aeroport International Diori Hamani Niamey Niger Airport,kamar ansan da zuwansa nan da nan 'yan jarida sukai masa caaaa, sai hasken camera ne yake tashi ta ko'ina ana masa photo, yayinda guard's d'insa suke hana mutane tunkarar inda yake,bai saurari yan jaridar ba kasancewar jana'iza ce takawo shi idan yayi wasa kuma bazai samu ba. Yanajin yanda wasu mutane suke tambayar sa ko zasu iyayin salfie? amma Jawad ko juyowa baiyi ba. Motocin gidan Alhaji Auwal ne suka zo suka daukeshi zuwa gidan,yana zuwa kuwa babu dadewa akayiwa Baby jana'iza aka kaita gidanta na gaskiya,sannan suka dawo suna kar6ar gaisuwa, manyan mutane wanda sukasan Jawad d'in sai zuwa suke suna gaidashi,shi kuwa yaci wannan babbar riga ya hakimce kamar wani magidanci. Gidan rasuwar yacika sosai da mutane kai kace shi kansa Alhaji Auwal d'in ne yarasu,ma'aikatan gidan sai futo da katan-katan d'in ruwan gorar DALLOL suke,ana rabawa mutane masu zuwa gaisuwa. Farouq Abban Inaas shima yana zaune daga can gefe tare da wasu mutanan suna kar6ar gaisuwa,abakin nakusa dashi yaji suna qus-qus suna cewa wannan matashin nakusa da Alhaji Auwal wanda mutane suke zuwa suna gaidashi shine mamallakin kamfanin Mekudi Oil na qasar,shine Babban d'an Alhaji Mekudi abokin Alhaji Auwal. Abban Inaas yakai dubansa inda su Jawad da Alhaji Auwal suke zaune,yaga yanda manyan mutane suke zuwa gabansa su tsugunna su bashi hannu su gaisa mamaki yasake kamashi,dama wannan matashin yaron shine shugaban kamfanin Mekudi oil? dama tun lokacin da Jawad d'in yazo gidan ya ganshi tareda wasu gabza gabzan muqarrabai dasuke take masa baya anan yasake tabbatar wa koma waye wannan yaron to tabbas wani babban mutumin ne. Bashida damar zuwa rumfar dasu Jawad d'in suke zaune ta manyan mutane,aida ya matsa kusa ya ganshi sosai a zahiri,ko watarana a tarihi zaice shima yaga me kamfani Mekudi Oil, amma yanzu saide gani daga nesa. Har dare Jawad yana tareda Alhaji Auwal,yaso sukoma Nigeria a ranar saboda kwata-kwata bayajin dad'in jikinsa tunda yashigo qasar,masifar fad'uwa gabansa yakeyi kamar ana doka masa wani abu a gefen zuciyarsa,hakan yasa yace zai tafi,to amma Alhaji Auwal ya hanashi tafiya,shikuma bazai iya musu dashi ba saboda shima kamar Daddynsa ne. Washegari yana tashi da safe aka aiko masa da kayan sakawa wata suit ruwan toka mai mutuqar kyau,cikin sauri yake shiryawa yanaso yabar qasar saboda har yanzu bai daina jin wannan fad'uwar gaban irinta jiyaba,yayi Addu'ah yayi Addu'ah amma abu shiru yaqi yadena. Duk da cikin sauri ya shirya,hakan bai hanashi yin wani irin kyau me masifar daukan hankali ba,iya ruwan tea kawai yasha yamiqe zasu wuce,Alhaji Auwal ya kalleshi dakyau sannan cikin bada umarni yace"Jawad kafin ka wuce ya kamata kashiga kaga kamfaninka na Mekudi Oil kaga abubuwan dasuke faruwa,nadad'e ban kaiwa kamfanin ziyara ba,amma tunda kashigo qasar yanzu,saika shiga kaga meyake wakana,inyaso saika dawo kuyi sallama da sister's dinka saiku wuce okay?" Ya qarasa zancen yana nuna masa yaransa 'yanmata guda biyu wanda suka ta6a yin waya da Jawad din tun kafin yazo Nigeria. Kansa aqasa cikin nutsuwa da kamewa irin tasa yace"to Papa" Sannan yamiqe yafice,yana fita yaga motoci guda uku ajere suna jiran futowar sa da alamu Alhaji Auwal yariga yafad'a musu,tun kafin ya qarasa suka bud'e masa mota,sannan yashiga suka fice daga gidan. suna tafiya ahanya yana kallon Agogon dake d'aure a farar fatar hannunsa wadda tacika da gargasa,yasaki d'an qaramin tsaki gaba d'aya ransa adagule yake saboda yaso yanda yatashi sassafen nan kawai yawuce Nigeria, yajuya gefensa ya kalli window yana ganin yanayin garin gwanin birgewa,duk yanda yake yawon zagaya kamfanin nikan nasu shi bai ta6a tunanin zuwa na Niger ba. Qarfe bakwai da rabi daidai suka iso kamfanin,aka bude masa ya futo hannunsa guda daya zube cikin aljihun wandonsa yana tafiya yana qarewa kamfanin kallo, yayinda guard's d'in dasuka rakosu suke tafiya cikin sauri suna masa nuni da hanyar dazaibi. Suna qarasawa ciki aka yi sauri aka kawo masa kujera yazauna yad'ora qafa d'aya kan d'aya,dayawa daga cikin ma'aikatan kamfanin duk basu qaraso ba,fuskarsa ad'aure babu walwala yakalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa sannan yasaki wata is'ka me zafi ya furzar,qarfe bakwai da minti arba'in tayi amma har yanzu de baya ganin ma'aikata suna cincirindon shigowa. Kamar manager yasan tunanin dayake shima sai gashi yashigo alokacin,ai yana ganin fuskar Jawad lokaci daya jikinsa yad'auki rawa,ya qarasa wajansa yana gaidashi,Jawad ya kalleshi baice dashi komai ba kuma bai amsa gaisuwar tasaba sai agogon hannunsa daya kalla. Daga nan ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa d'aya bayan d'aya,ganin yanda manager yayi tsumu-tsumu agaban Jawad lokaci d'aya suka gane shine de mutumin dasuke jin labari yashigo Niger,shine J.mekudi,mamallakin kamfanin Mekudi Oil. Duk ma'aikaci ko ma'aikaciyar data shigo haka zasuyi qasa da kansu sum-sum su wuce cikin kunya ganin oga kwata-kwata yakawo musu ziyarar bazata,kuma ya riskesu dayawa daga cikinsu duk sunyi latti. Jawad ya kalli manager yace"bani bayanan kamfani zan duba" Cikin sauri manager yakoma yashiga office d'insa yad'auko masa wasu file-file's da wata computer yakawo masa,sannan yasake tsayawa agefe kamar yanda guard's d'insa suka maqale a tsaye. Kundin shigar da bayanan kamfani yafara dubawa a nutse,adede lokacin aka gabatar masa ruwan gorar DALLOL mai mutuqar sanyi jikin gorar har ra6a yake,tareda wasu lemuka aka ajiye agaban kujerar dayake zaune,saide Jawad kota kan ruwan baibi ba. Duk wannan buduri da'ake Hajiya madam Inaas 'yarme gwanjo bata qaraso kamfanin ba. Yadad'e yana ganin yanda ake shigarda bayanan daki-daki abun ya birgeshi,har wajan qarfe takwas dawasu mintuna yakai yana ganin bayanan sannan yad'ago kansa ya kalli manager anan yaga yanda ma'aikata dayawa suke had'a kai suna qus-qus,saide baisan me suke cewa ba ya d'auke kansa daga garesu. a nasu 6angaren kuwa gulmar sa suke suna yaba irin tsantsar kyan dayake dashi,'yanmatan dasuke aiki a kamfanin sai qasa da murya suke suna fad'in "wallahi ya had'u sosai". Jawad yayi ajiyar zuciya bayan yagama kallon manager sannan yad'an motsa lips dinsa yace"komai yayi kyau,yanda ake shigar da bayanan company daki-daki yayi kyau sosai,but waye yake shigar da bayanan? naga yayi qoqari sosai aikinsa yana kyau" Cikin sauri Ilyasu manager yafara rawar baki yakasa magana,Inaas ce me wannan aikin,gashi har yanzu bata qaraso kamfani ba,daqyar ya'iya kallon Jawad yace"yalla6ai ba... bat bata qaraso ba" Cikin tsananin mamaki Jawad ya kalli agogon hannunsa yaga qarfe tara saura ,sannan ya kalli manager,kafin yayi magana p.a d'insa dayake tsaye agefensa yabashi waya alamun ana kiransa,Jawad ya kar6i wayar yakara a kunnansa,daga d'ayan 6angaren shugaban kamfanin gidan radio da television ta qasa yafara roqon sa yace"Ranka ya dad'e daga nan ORTN ne,Office de Radio et Television Nationale,gidan radio da television na qasa,munji labarin ka shigo qasar ne idan babu damuwa muna so kabamu minti talatin zamuyi muyi fira dakai". Kai tsaye Jawad yace"ok ganinan zuwa" Yakashe wayar yamiqawa p.a,sannan yadawo da kallonsa ga manager yace"mace ce take shigar da bayanan?" Manager yakasa magana sai kansa daya gyad'a kawai alamun hakane. Kai tsaye ya kalli assistant manager dayake tsaye agefe yace"bani bayanan takardun ta" Cikin sauri assistant manager yagabatar wa da Jawad photo copy na takardun Inaas,Jawad yaqarewa takardun kallo,takardun sunyi kyau sosai,saide iya secondary ne, cikin mamaki yadago kansa ya kalli manager yace"S.s.c.e? a kamfanina? meyasa zaku dinga d'aukar irin wad'annan sakarkarun aiki a kamfani babba kamar wannan?,qualification dinta bekai ba,sannan bata zuwa aiki akan lokaci" Cikin rawar jiki manager yace"kayi haquri Yalla6ai yarinyar ce abun tausayi wallahi,sannan munga tanada sani ne sosai akan tattara bayanai,idan kaduba wasu daga cikin sauran companies zakaga ana iya samun irinsu,basuda dogon karatu amma sunada basira da qwarewa akan aiki" Jawad ya kalli manager fuskarsa babu walwala yace"magana nake akan kamfanina,menene alaqata da sauran companies dan sun d'auki irinsu? ni d'an kasuwa ne, bazan lamunci wannan ba,afad'a mata na sallameta daga aiki takoma makaranta"(🙆🏻‍♀️) (shikkenan tafaru ta qare,d'an aikin kamfanin da muka samu ma an koremu 😣😫😥) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub ✍️ [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name 13&14 https://chat.whatsapp.com/LJeNOKMt7ZvJ7Hlu7btQw9 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. ___ Daddy yace"qaddara da talauci ai babu abinda basa sawa Jawad,talauci masifa ne,musanman awajan mata,kaga talauci yanasa mace takoma neman maza,talauci yanasa wasu yaran su fara sata,annabi da kansa ya nemi tsari da talauci,mutane dayawa idonsu yana rufewa akan neman kudi,abunda basu sani ba shine shi talauci da arziqi duk na Allah ne,idan ubangiji ya qaddara zakayi kudi to zakayi,kamar ajali ne muddin idan yazo to babu makawa,shiyasa a kowanne lokaci nakeso ka kasance kana taimaka wa mabuqata inde kanada hali,taimakon dakake saika ga ta hanyar wannan taimakon kasamu aljanna" Jawaad yayi shiru yana jinjina kansa amma yana mamakin wanne irin talauci ne zaisa karabu da matarka duk irin zaman da kukai na aure?. P.a d'in Jawad ne ya qaraso wajan kamar kullum hannunsa d'auke da takardu dakuma wayoyi,tun daga nesa Fu'ad ya hango shi yasosa girarsa guda d'aya sannan yayi qasa da kansa yana dariya yasan cewa inde anga p.a to anga aiki (😂) Yana qarasowa yagaida su sannan ya kalli Jawad yace"yalla6ai mun kar6i saqon gayyatar kane zuwa wajan bud'e sabon masallaci wanda katura musu tallafin gini" Cikin 6acin rai Jawad ya kalli p.a yace"kamarya kenan? waye yace musu nine na basu kudin? meyasa aka fad'a musu?" Daddy yayi murmushi ya girgiza kansa sannan ya kalli p.a yace"kace dasu zaizo" Cikin sauri Jawad ya kalli Daddy yace"Daddy ban son zuwa" Daddy yace"kayi haquri mana,ka daure kaje ko awa d'aya ne kabasu" Jawad yajuya ya kalli p.a wanda yayi tsumu-tsumu a tsaye,sannan yace"ranar yaushe ne zan halacci taron Mr.Joshua?" P.a yace"duka rana d'ayane da wannan Yalla6ai" Jawaad ya runtse idonsa yace"ka kwa6a min aiki p.a, please jeka" Babu musu p.a ya juya yabar wajan. Suma basu tashi daga wajan ba saida sukaga Daddy yadan warware yaji dad'in jikinsa sosai sannan suka dawo ciki. Jawad kai tsaye dakin sa ya shige yayi wanka yadauro alwala domin tafiya masallaci,bayan yadawo daga masallaci yaga har lokacin Mummy bata falon,hakan yasa kai tsaye yawuce d'akinta,adede lokacin ta'idar da sallah tana zaune akan sallaya tana karatun Alqur'ani,jingina yayi da jikin qofar yana sanye da Riga da wando qanana amma rigar yadora mata 'yar sama yabar 'yar saman abud'e bai rufe botir d'inta ba,yahard'e hannunsa a qirji,yacire glass din idonsa yasoke shi agaban rigar jikinsa ta ciki sannan yazuba mata ido yana kallonta ganin har lokacin batasan yashigo ba. Yadade a tsaye har ta gama karatun sannan ta daga hannyenta sama tafara Addu'ah a baiyane cikin yaqini tace"ya Allah ka aurar min da Jawad dina,Allah yasa muna raye muga jikokin mu" Wani irin murmushi yasaki sannan ya qaraso cikin dakin yazauna agabanta,yakama hannyenta yariqe yakai bakinsa yayi kissing hannun nata sannan yace"Mummy aure fa lokaci ne" Dan qaramin tsaki tasaki tace"Jawad kullum haka kake fada,lokaci yayi Jawad" Murmushin qarfin hali yayi yace"Mummy aina baku dama,duk lokacin da kuka shirya nima I'm ready" Lokaci d'aya farinciki ya wanzu a fuskarta,ta kalleshi dakyau tace"Allah yayi maka albarka Jawad,insha Allahu baza muyi ma za6on tumun dare ba" Murmushi yasaki sannan yatashi yakoma kan gadonta ya kwanta yana qoqarin kunna plasma din dakin. **** Kamar yanda p.a yasanar dashi, ranar da za'ai taron bude masallaci,hakan yasa ya shirya tsaf suka tafi shida Fu'ad da sauran guards dinsa,gaba daya mota uku suka dauka,waje na musanman aka bar masa acikin masallacin wanda Iya tsaruwa ya tsaru,malamin addini yanata wa'azi akan falala da dunbin ladan da'ake samu idan angina masallaci,Jawad yayi shiru yanajin wa'azin,cikin ransa yana tunanin yanzu duk wannan ladan da'ake magana akai Shima fa ubangiji yabashi ko? sai hakan yasake qarfafa masa gwiwa dangane da taimako,bayan yagama fad'ar falalar gina masallaci saiya gangaro wajan falalar sharar masallaci da ladan da'ake samu idan an tsaftace shi,daga qarshe ganin matasa dayawa a masallacin sai wa'azin nasa ya gangaro kan batun aure wanda yake magana akan matasa wanda Allah yabasu damar aure su daure suyi aure domin rage zinace-zinace adoron duniya,bawai lalle saika samu yanda kakeso sannan ne zakayi aure ba,daga nanfa jikin Oga Jawad yayi sanyi yaji kamar danshi ake wa'azin.(🤭) Tunani yafara aransa yana tuna dalilan da yasa baiyi aure ba tun tuni,nafarko kasuwancin sa,na biyu baima san soyaiyar ba bare yaga wata wadda zata dauki hankalinsa,na uku be'iya soyaiya ba tayaya zaija hankalin yarinyar? Nahudu ba lalle yasamu irin yarinyar dayake so ba,yanason matarsa ta kasance marar dogon karatu wanda idonta bai bude dayawa ba,yanason mace mai gashi yanda zai kama ya dinga wasa dashi,yanason gashin turawa da larabawa,yana birgeshi sosai,amma Allah bai bashi damar riqewa yayi abinda yakeso dashi ba,saboda shiba manemin mata bane,sannan bayason matarsa tayi aikin gwamnati ra'ayinsa ne wannan kudin daya tara ya'ishesu rayuwa,yasan cewa su Daddy zasu nemo masa mata,kowacce irin yarinya suka kawo masa zai Iya rayuwa da'ita amma ya kasance tanada gashi dakuma sauran abubuwan more rayuwa najikin mace,yasan cewa bazasu Samo masa irin matar dayake so ba wato marar dogon karatu, yasan gogaggiyar 'yar Boko za'a samo masa,babu kuma yanda zaiyi tunda shine yabasu dama su za6a masa,saide yayi haquri ya yarda ya aure ta ahakan,saide da sharadin babu aiki,matar J.mekudi saide tabada umarni bawai wani daga sama yabata ba. gaba daya sai jikinsa yagama sanyi bayan yasan cewa bafa lalle ne yasamu irin wannan yarinyar ba saide in qasar zai bari,ya lumshe idonsa yana tuna irin tsawon shekarun daya dauka yana faman shan maganin kwantar da sha'awa duk saboda wad'annan dalilan nasa, wazai aura? tanada abunda yakeso? Baigama dawowa daga tunanin dayake ba yaji p.a dinsa yana fadin "muje Yalla6ai" cikin sauri yadawo hayyacinsa yaga har angama wa'azin,Fu'ad dake gefensa sai fara'ah yake yana fadin "Yaya yau kasha Addu'ah" Kai tsaye wajan motarsa yanufa amma mutanan garin suka nuna suna so suje dashi gida yaci abinci kafin yawuce,ganin dukansu tsofaffi ne hakan yasa baiyi musu ba yabisu suka qarasa wani had'ad'd'en gida inda aka tanadar musu abinci kala kala,da naman kaji,da naman sa,saide Jawad baici komai ba saide yadauki gorar ruwa ta faro yasha d'an kadan,yayinda Fu'ad da sauran guards dinsa da p.a suka nutsu suka kwashi girki abun su. Washegari da safe gaba d'ayansu su hud'un sunacin abinci a dining, Jawad yana sanye cikin qananun kaya nashan is'ka kamar kullum,Mummy datake kusada Jawad itace take bashi abincin da spoon din hannunta,yayinda shima Daddy yake sakawa Fu'ad abaki, abun gwanin sha'awa basai an fada makaba zakasan cewa akwai tsananin Qauna a tsakanin iyayen da yaran nasu. Daddy yabude wata yar madedeciyar iPad yakamo pictures din 'yanmata tsala-tsala sunsha kyau,jikin nan an matse shi da dinkin zamani,ya kalli Jawad yace"yaran sanatoci ne,da yaran ministoci da 'ya'yan sarauta,akwai guda ukun farko acikin su yaran gamna ne kaduba kagani idan akwai wacce tama sai muje dasu Man Sulaiman da abokaina anemo ma aurenta" Dam!!! gaban Jawad yafadi,gashi de shine da kansa yabasu za6i su za6o masa matar amma saida yaji gabansa yafadi. Kafin Jawad yayi magana Mummy tace"haba Alhaji,duk da muna son abun nan aida an barshi yad'an huta tukunna,duka-duka yaushe ne yazo qasar?" Bata jira amsar da Daddy zai bata ba tamaida kallonta wajan Jawad tace"ci abincinka yarona" "shekara kusan Arba'in shine kike kira yaro? yanda kike masa kullum kina shagwa6a shi hakanne yasa yake daukar kansa yaro,tunda yazo qasar nan ban ganshi da manyan kaya ba,inda ya ajiye iyali yaga matarsa da qaton ciki kokuma yaga matarsa da Baby dole zai nutsu ya dinga saka manyan kaya yazama cikakken magidanci" Cewar Daddy. Jawad yajuyo ya kalli Daddy yanason ya kaucewa maganar yanmatan,sannan yasake juyawa ya kalli Fu'ad yace"shaddar wanne Campany ce takeda kyau?" Fu'ad da dariya ta kamashi ya kawar dakai yayi murmushi sannan yace"zanyi magana ad'inkama Yaya" Jawad ya sunkuyar da kansa qasa ransa duk ba dadi,sai yanzu ne yagane kuskuren sa nacewa su nema masa auren, daya sani yayi ta basu haquri har zuwa lokacin dazai samu wata. Daddy yagane saboda maganar matan dayayi masa ne yasa yaketa hura hanci,kokadan babu damuwa aransa yasake tura masa wayar yace"gasunan duba" Fuskarsa adaure yadauki wayar cikin sauri far-far yayi scrolling screen din,sannan ya ajiye kansa aqasa yace"basuyi ba" Daddy ya kalleshi yace"hmm" Sannan yaci gaba dacin abincinsa. Mummy tasaki ajiyar zuciya tace"to Jawad mezai hana inyi magana da Uncle dinka Bature Yaya na,sai a nema maka auren Amal?" duk ransa babu dadi haka ya sassauta muryar sa duk da baisan yarinyar ba, yace"shikkenan Mummy tunda za6inki ce na Amince" Fu'ad dake zaune yasaki murmushi,yasan Amal sosai yana bibiyarta ashafinta na tik tok, cikin sauri yadauko photon ta yadora a status dinsa yayi kalamai wanda yake nuni da cewa itace yarinyar da yayansa zai aura. Adede lokacin Yaya Mariya yayar Daddy tana zaune a gidanta tana zuba iko, wayarta a hannunta tana duba saqonni,ganin Fu'ad yayi status da photon mace hakan yaja hankalin ta hartaje tabude tagani,lokaci d'aya ranta ya6aci,idonta ya rufe da masifa, ta wullar da wayar tata can gefe,tafara girgiza qafarta. Daddy yayi ajiyar zuciya sannan yace"Alhamdulillah,Allah ya tabbatar da Alkhairi" Mummy tace"Amin ya Allah Alhaji,nasan shima Jawad zaiji dadin zama da'ita inde anyi auren,zai yaba da kyawawan dabi'un ta,lokaci daya zai sota" Fuska babu walwala Jawad yace"no Mummy,zan aure ta ne saboda ke,Mummy niban ta6a soyaiya ba,ban'iyaba,abinda nasani kawai shine kasuwanci,babu yarinyar danake tunanin zanso ta" Mummy tayi ajiyar zuciya ta kalli Jawad tana girgiza kai jikinta duk a sanyaye,taga alama rigima kawai yakeji. P.a ne yashigo falon bakinsa dauke da sallama ya rissina awajan Jawad yace"yalla6ai,shugaban babban kamfanin taliya na qasar Masar Sheik shamiy,yaji labarin kashigo Africa yaturo maka da saqon gayyatar shan shayi,zan'iya duba jadawalin lokutan dakake free sai a afada masa ranar da zakaje?" Ba tareda ya kalli P.a ba,cikin 6acin rai yace"Shan shayi ko maganar kasuwanci? P.a bakasan hutu nazo bane?" Cikin fishi yamiqe yabar dining din yanufi hanyar zuwa dakinsa ransa fal qunci dama ga maganar auren nan da'aka masa. baiyi nisa da tafiya ba,wayarsa tafara qara,cikin sauri p.a yasake cewa"yalla6ai ana..." Kafin ya qarasa cewa ana kira,cikin jin haushi yajuyo yace"waye kuma? ko Sheik Shamiy dinne?" P.a daya lura yau Yalla6ai akusa yake ya sassauta murya yace"daga qasar Niger ne" Kai tsaye yace"kashe waya" Daga nan yayi dakinsa bai sake futowa falon ba sai dare,kuma babu wanda ya nemeshi saboda sun San cewa akusa yake,da alama kadan yake jira yace yafasa auren, sukuma suna so yayi auren. Da daddaren ma ransa babu dadi fuskar nan a murtuke haka yake zaune afalo yayi shiru duk abun duniya yataru yamasa yawa. p.a yashigo falon yace"yalla6ai ana waya daga Niger,number d'azu ce aka sake kira" Babu musu Jawad ya kar6a,sannan yad'auka bakinsa d'auke da sallama,daga can 6angaren Alhaji Auwal yace"Jawad nakiraka da safe zan baka Baby itace ta dameni saina kira mata kai batajin dadi ne sai maganar ka take" Cikin sanyin jiki Jawad yace"Ya Salam nayi busy ne da safe, please Papa bata wayar" Cikin sanyin jiki Alhaji Auwal yace"Jawad saide kayiwa Baby Addu'ah Allah yamata rasuwa yanzu-yanzun nan,ka fad'awa mahaifinka kace nakira wayarsa bata shiga ba" Lokaci d'aya Jawad yaji kansa yayi masa wani iri dummm!, Baby tarasu? lokaci daya yafara fadin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,please Papa inaso inzo suturar ta qarfe nawa za'a yi?" Alhaji Auwal yace"sai gobe dasafe insha Allah kamar qarfe takwas" Jawad yakashe wayar yadafe kansa yana tuna irin alqawarin dayayi wa yarinyar baicika ba,gashi de baisan taba,bai ta6a ganin taba amma mutuwar ta tadakeshi. Mummy ta kalleshi tace"waye yarasu?" Jawad yad'ago kansa yace"jikar Alhaji Auwal ce,abokin Daddy na Niger" Daddy yace"ayya, to ainima bazan zauna ba,saimu shirya muje goben" Jawad yace"Daddy zaka Iya ne? jikinka yagama warware wa?" Daddy yace"a a karka damu, na warke sosai Jawad" Jawad yayi ajiyar zuciya yabawa p.a wayar sannan yace"ashirya mana tafiya zuwa qasar Niger gobe da sassafe" P.a ya kar6i wayar sannan yajuya yafita. **** Washegari sassafe ya shirya cikin shadda milk color harda babbar riga yayi bala'in yin kyau kamar ka saceshi ka gudu,yana sakkowa falo yaci karo da Hajiya Mariya yayar Daddy. Mamaki ya kama Jawad me yakawo Mama gida da sassafen nan,itada sai an dad'e ma kafin a ganta agidan,saide in wani muhinmin abu ne yafaru,cikin sauri ya qarasa wajanta tun kafin yagaida ta tana ganinsa tace"ina uwar taka?" Jawad yayi saurin yin qasa da idonsa ganin akusa take,tuni ya rissina qasa cikin nutsuwa yad'an motsa lips dinsa sannan yace"Hajiya Mama ina Kwana?" Hajiya Mariya bata amsa gaisuwar tasaba cikin masifa tace"Uwar taka tana gani da idonta za'a baka wannan yarinyar?" Tafad'i hakan tana nuna masa photon Amal dake screen d'in wayarta,saide kansa aqasa baima dago ba bare ya kalleta. Cikin Masifa Hajiya Mariya tasake daga murya tace"yarinyar da batada tarbiya?,kullum tana cikin yin raye-raye a tik tok yara suna nunamin rawar datake tana nunawa duniya jiki shine za'a dauko a liqa maka?" Shide Jawad yayi shiru baice komai ba,har lokacin kansa yana qasa baice da'ita uffan ba kasancewar yasan halin ta masifaffiya ce. Adede lokacin Mummy tafuto daga daki itada Daddy wanda yagama shiryawa zasu wuce Niger,Hajiya Mariya ta kalli Mummy tasan sarai tanada nasaba da Amal amma sai tace"da ke kinsan yarinyar ne kokuma asama-sama kika santa da zaku bashi ita?" Mummy ta sunkuyar da kanta,tarasa a'ina Yaya Mariya taji wannan maganar. yayinda Hajiya Mariya ta kalli Daddy tace"ban yarda da wannan hadin ba,aje asake bincike akan yarinyar tukunna" Tajuya ta kalli Jawad dahar yanzu kansa yake qasa ta tsatstsare shi da'ido tace"kokaine kaganota ahakan kaji kagani kana sonta harka kawo ta gida?" Jawad yayi shiru kansa yana qasa saboda babu ladabi babba yana fada kayi magana,musanman ma ita datake gaba da mahaifin sa,shi baisan dalili ba,amma yarasa meyasa koda yaushe Hajiya Mariya take nunawa kamar tafi kowa sonsa,wani lokacin qiri-qiri zata dinga yin abu kamar tafi Mummy sonsa. Kafin wani daga cikinsu yasake yin magana p.a yashigo yace"yalla6ai mungama shirya komai kai muke jira,sannan akwai baqin manoman dakace asanar dasu suzo yau zaka gansu sunyi magana zasu taso yanzu" Sai alokacin Jawad yadago kansa yace"kafad'a musu nadage ranar dazan zauna dasu,saika basu wani lokacin daya dace" Daddy yayi ajiyar zuciya ya zauna sannan ya kalli Jawad yace"tashi kuje Jawad,kayimin ta'aziyya awajan Alhaji Auwal d'in tunda Yaya tazo zan zauna zamuyi magana da'ita,nina haqura dazuwa" Babu musu Jawad yamiqe,ya kalli Hajiya Mariya cikin ladabi yad'an motsa lips dinsa sannan yace"Kihuta lafiya Mama" Daganan yabi p.a suka wuce. Daddy ya kalli yayar tasa ya sassauta murya yace"yaya zauna muyi magana,abun duk bana zafi bane" Cikin fishi Hajiya Mariya ta nemi waje ta zauna bayan tagama yiwa Hajiya Zaliha wani irin kallo. *** *** *** Yana futowa zuwa Compound guard's dinsa suka fara take masa baya har zuwa wajanda aka a dana motoci domin kaishi Airport,d'aya daga cikin guard yabude masa motar yashiga,Man Sulaiman yaja motar suka tafi,Jawad yayi shiru ya lumshe idonsa yana zaune abaya,kwata-kwata yakasa sakewa ganin wanda yadauko shi,kokadan bayason ganin mutumin yana aiki bare kuma ace shine wanda zaijashi amota,haka nan yake jin qimar mutumin aransa,saide labarin sa da Daddy yabasu na gudun iyalinsa kwata-kwata baima sa dadi ba. Har suka je Airport shide Jawad baisaki jikinsa sosai ba,har saida jirginsu yatashi. Bayan wani lokaci jirgin su ya sauka a Aeroport International Diori Hamani Niamey Niger Airport,kamar ansan da zuwansa nan da nan 'yan jarida sukai masa caaaa, sai hasken camera ne yake tashi ta ko'ina ana masa photo, yayinda guard's d'insa suke hana mutane tunkarar inda yake,bai saurari yan jaridar ba kasancewar jana'iza ce takawo shi idan yayi wasa kuma bazai samu ba. Yanajin yanda wasu mutane suke tambayar sa ko zasu iyayin salfie? amma Jawad ko juyowa baiyi ba. Motocin gidan Alhaji Auwal ne suka zo suka daukeshi zuwa gidan,yana zuwa kuwa babu dadewa akayiwa Baby jana'iza aka kaita gidanta na gaskiya,sannan suka dawo suna kar6ar gaisuwa, manyan mutane wanda sukasan Jawad d'in sai zuwa suke suna gaidashi,shi kuwa yaci wannan babbar riga ya hakimce kamar wani magidanci. Gidan rasuwar yacika sosai da mutane kai kace shi kansa Alhaji Auwal d'in ne yarasu,ma'aikatan gidan sai futo da katan-katan d'in ruwan gorar DALLOL suke,ana rabawa mutane masu zuwa gaisuwa. Farouq Abban Inaas shima yana zaune daga can gefe tare da wasu mutanan suna kar6ar gaisuwa,abakin nakusa dashi yaji suna qus-qus suna cewa wannan matashin nakusa da Alhaji Auwal wanda mutane suke zuwa suna gaidashi shine mamallakin kamfanin Mekudi Oil na qasar,shine Babban d'an Alhaji Mekudi abokin Alhaji Auwal. Abban Inaas yakai dubansa inda su Jawad da Alhaji Auwal suke zaune,yaga yanda manyan mutane suke zuwa gabansa su tsugunna su bashi hannu su gaisa mamaki yasake kamashi,dama wannan matashin yaron shine shugaban kamfanin Mekudi oil? dama tun lokacin da Jawad d'in yazo gidan ya ganshi tareda wasu gabza gabzan muqarrabai dasuke take masa baya anan yasake tabbatar wa koma waye wannan yaron to tabbas wani babban mutumin ne. Bashida damar zuwa rumfar dasu Jawad d'in suke zaune ta manyan mutane,aida ya matsa kusa ya ganshi sosai a zahiri,ko watarana a tarihi zaice shima yaga me kamfani Mekudi Oil, amma yanzu saide gani daga nesa. Har dare Jawad yana tareda Alhaji Auwal,yaso sukoma Nigeria a ranar saboda kwata-kwata bayajin dad'in jikinsa tunda yashigo qasar,masifar fad'uwa gabansa yakeyi kamar ana doka masa wani abu a gefen zuciyarsa,hakan yasa yace zai tafi,to amma Alhaji Auwal ya hanashi tafiya,shikuma bazai iya musu dashi ba saboda shima kamar Daddynsa ne. Washegari yana tashi da safe aka aiko masa da kayan sakawa wata suit ruwan toka mai mutuqar kyau,cikin sauri yake shiryawa yanaso yabar qasar saboda har yanzu bai daina jin wannan fad'uwar gaban irinta jiyaba,yayi Addu'ah yayi Addu'ah amma abu shiru yaqi yadena. Duk da cikin sauri ya shirya,hakan bai hanashi yin wani irin kyau me masifar daukan hankali ba,iya ruwan tea kawai yasha yamiqe zasu wuce,Alhaji Auwal ya kalleshi dakyau sannan cikin bada umarni yace"Jawad kafin ka wuce ya kamata kashiga kaga kamfaninka na Mekudi Oil kaga abubuwan dasuke faruwa,nadad'e ban kaiwa kamfanin ziyara ba,amma tunda kashigo qasar yanzu,saika shiga kaga meyake wakana,inyaso saika dawo kuyi sallama da sister's dinka saiku wuce okay?" Ya qarasa zancen yana nuna masa yaransa 'yanmata guda biyu wanda suka ta6a yin waya da Jawad din tun kafin yazo Nigeria. Kansa aqasa cikin nutsuwa da kamewa irin tasa yace"to Papa" Sannan yamiqe yafice,yana fita yaga motoci guda uku ajere suna jiran futowar sa da alamu Alhaji Auwal yariga yafad'a musu,tun kafin ya qarasa suka bud'e masa mota,sannan yashiga suka fice daga gidan. suna tafiya ahanya yana kallon Agogon dake d'aure a farar fatar hannunsa wadda tacika da gargasa,yasaki d'an qaramin tsaki gaba d'aya ransa adagule yake saboda yaso yanda yatashi sassafen nan kawai yawuce Nigeria, yajuya gefensa ya kalli window yana ganin yanayin garin gwanin birgewa,duk yanda yake yawon zagaya kamfanin nikan nasu shi bai ta6a tunanin zuwa na Niger ba. Qarfe bakwai da rabi daidai suka iso kamfanin,aka bude masa ya futo hannunsa guda daya zube cikin aljihun wandonsa yana tafiya yana qarewa kamfanin kallo, yayinda guard's d'in dasuka rakosu suke tafiya cikin sauri suna masa nuni da hanyar dazaibi. Suna qarasawa ciki aka yi sauri aka kawo masa kujera yazauna yad'ora qafa d'aya kan d'aya,dayawa daga cikin ma'aikatan kamfanin duk basu qaraso ba,fuskarsa ad'aure babu walwala yakalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa sannan yasaki wata is'ka me zafi ya furzar,qarfe bakwai da minti arba'in tayi amma har yanzu de baya ganin ma'aikata suna cincirindon shigowa. Kamar manager yasan tunanin dayake shima sai gashi yashigo alokacin,ai yana ganin fuskar Jawad lokaci daya jikinsa yad'auki rawa,ya qarasa wajansa yana gaidashi,Jawad ya kalleshi baice dashi komai ba kuma bai amsa gaisuwar tasaba sai agogon hannunsa daya kalla. Daga nan ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa d'aya bayan d'aya,ganin yanda manager yayi tsumu-tsumu agaban Jawad lokaci d'aya suka gane shine de mutumin dasuke jin labari yashigo Niger,shine J.mekudi,mamallakin kamfanin Mekudi Oil. Duk ma'aikaci ko ma'aikaciyar data shigo haka zasuyi qasa da kansu sum-sum su wuce cikin kunya ganin oga kwata-kwata yakawo musu ziyarar bazata,kuma ya riskesu dayawa daga cikinsu duk sunyi latti. Jawad ya kalli manager yace"bani bayanan kamfani zan duba" Cikin sauri manager yakoma yashiga office d'insa yad'auko masa wasu file-file's da wata computer yakawo masa,sannan yasake tsayawa agefe kamar yanda guard's d'insa suka maqale a tsaye. Kundin shigar da bayanan kamfani yafara dubawa a nutse,adede lokacin aka gabatar masa ruwan gorar DALLOL mai mutuqar sanyi jikin gorar har ra6a yake,tareda wasu lemuka aka ajiye agaban kujerar dayake zaune,saide Jawad kota kan ruwan baibi ba. Duk wannan buduri da'ake Hajiya madam Inaas 'yarme gwanjo bata qaraso kamfanin ba. Yadad'e yana ganin yanda ake shigarda bayanan daki-daki abun ya birgeshi,har wajan qarfe takwas dawasu mintuna yakai yana ganin bayanan sannan yad'ago kansa ya kalli manager anan yaga yanda ma'aikata dayawa suke had'a kai suna qus-qus,saide baisan me suke cewa ba ya d'auke kansa daga garesu. a nasu 6angaren kuwa gulmar sa suke suna yaba irin tsantsar kyan dayake dashi,'yanmatan dasuke aiki a kamfanin sai qasa da murya suke suna fad'in "wallahi ya had'u sosai". Jawad yayi ajiyar zuciya bayan yagama kallon manager sannan yad'an motsa lips dinsa yace"komai yayi kyau,yanda ake shigar da bayanan company daki-daki yayi kyau sosai,but waye yake shigar da bayanan? naga yayi qoqari sosai aikinsa yana kyau" Cikin sauri Ilyasu manager yafara rawar baki yakasa magana,Inaas ce me wannan aikin,gashi har yanzu bata qaraso kamfani ba,daqyar ya'iya kallon Jawad yace"yalla6ai ba... bat bata qaraso ba" Cikin tsananin mamaki Jawad ya kalli agogon hannunsa yaga qarfe tara saura ,sannan ya kalli manager,kafin yayi magana p.a d'insa dayake tsaye agefensa yabashi waya alamun ana kiransa,Jawad ya kar6i wayar yakara a kunnansa,daga d'ayan 6angaren shugaban kamfanin gidan radio da television ta qasa yafara roqon sa yace"Ranka ya dad'e daga nan ORTN ne,Office de Radio et Television Nationale,gidan radio da television na qasa,munji labarin ka shigo qasar ne idan babu damuwa muna so kabamu minti talatin zamuyi muyi fira dakai". Kai tsaye Jawad yace"ok ganinan zuwa" Yakashe wayar yamiqawa p.a,sannan yadawo da kallonsa ga manager yace"mace ce take shigar da bayanan?" Manager yakasa magana sai kansa daya gyad'a kawai alamun hakane. Kai tsaye ya kalli assistant manager dayake tsaye agefe yace"bani bayanan takardun ta" Cikin sauri assistant manager yagabatar wa da Jawad photo copy na takardun Inaas,Jawad yaqarewa takardun kallo,takardun sunyi kyau sosai,saide iya secondary ne, cikin mamaki yadago kansa ya kalli manager yace"S.s.c.e? a kamfanina? meyasa zaku dinga d'aukar irin wad'annan sakarkarun aiki a kamfani babba kamar wannan?,qualification dinta bekai ba,sannan bata zuwa aiki akan lokaci" Cikin rawar jiki manager yace"kayi haquri Yalla6ai yarinyar ce abun tausayi wallahi,sannan munga tanada sani ne sosai akan tattara bayanai,idan kaduba wasu daga cikin sauran companies zakaga ana iya samun irinsu,basuda dogon karatu amma sunada basira da qwarewa akan aiki" Jawad ya kalli manager fuskarsa babu walwala yace"magana nake akan kamfanina,menene alaqata da sauran companies dan sun d'auki irinsu? ni d'an kasuwa ne, bazan lamunci wannan ba,afad'a mata na sallameta daga aiki takoma makaranta"(🙆🏻‍♀️) (shikkenan tafaru ta qare,d'an aikin kamfanin da muka samu ma an koremu 😣😫😥) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub ✍️ [1/20, 08:44] My Number: 💝 *ME 'DEBE KEWA*💝 ('yar me gwanjo) Writing By Amnah El Yaqoub Dedicated to Bilkisu's name 15&16 https://chat.whatsapp.com/LJeNOKMt7ZvJ7Hlu7btQw9 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yanzu muna posting free page ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. ___ Yana fad' ar haka yamiqe,guad's d'insa suka mara masa baya,yayinda manager da manya-manyan ma'aikatan kamfanin suka masa rakiya zuwa wajan motocinsa,saida sukaga fitar sa sannan sukai shirin juyawa kowa yana ajiyar zuciya, daga nan baki yabud'e aka fara maida zance. Motocin Jawad suna fita adede lokacin Inaas tazo,ma'aikatan da sukasan ankoreta sai qus-qus suke suna gulmar ta harda masu nunata da hannu, Ilyasu manager ya kalleta yace"Inaas saide kiyi haquri ki koma gida shugaban wannan kamfanin Jawad Mekudi yakawo mana ziyarar bazata,yaga takardun ki yace ya sallameki daga aiki kuma yace afad'a miki ki koma makaranta" Inaas tazuba wa manager ido tana kallonsa takasa magana,duk tsananin surutun ta bata ta6a tunanin akwai ranar da zatazo afad'a mata magana ta kasa maida martani ba.(😂) Ahankali tasaki ajiyar zuciya ta kalli manager tace"to nagode" Daga haka bata sake cewa komai ba tajuya tabar kamfanin,tsabar taqaici aqafa tatako zuwa gida ranta baqiqqirin tana tafe tana tunani ta saqa wannan ta kunce wancen,idan a lami lafiya ne bazatayi wannan doguwar tafiyar aqafa ba,amma yau tashin hankali yahanata ganin nisan tafiyar. Su Jawad kuwa suna barin kamfani kai tsaye wajan wani baturen qasar france suka qarasa suka tattauna dashi akan wasu abubuwa,sannan p.a dinsa yatuna masa maganar zuwa gidan television d'in da zasuyi fira dashi,hakan yasa yamiqe,yabawa Baturen hannu suka sake gaisawa sannan yayi masa sallama suka d'auki hanyar gidan television d'in. sunyi nisa atafiya sosai motar da Jawad yake ciki ta tsaya adede layin gidansu Inaas,driver yayi-yayi ya kunna mota kwata-kwata mota taqi tashi,hakan yasa ya futo yaduba yaga ruwan ciki ne yaqare kuma babu ruwa acikin motar. Sauran motocin guda biyu suka tsaya kowa ya futo zuwa wajan Jawad,ahankali shima yabud'e ya futo,baisan dalili ba adede lokacin kuma gabansa ya tsananta fad'uwa sosai,ya kalli yanayin unguwar yaji hankalinsa ya kwanta da wajan yanason yad'an sha is'ka kad'an,hakan yasa ya kalli sauran guard's d'in yace"kuyi gaba kawai babu damuwa,ku sanar dasu ina qarasowa,p.a katsaya tare dani" 'Daya daga cikin drivers d'in dasuke jan sauran motocin yace"ranka yadad'e ko zaka shigo nan saimu qarasa dakai duba da yanayin wajan nan akwai sahara dayawa gashi rana tafara futowa" Jawad yayi murmushi yace"no ba damuwa,aiba wata matsala bace, ruwa ne kawai,zamu taho yanzun nan,kuje kawai" Babu musu drivers sukaja suka tafi gidan tvn domin isar da saqon Jawad nacewa yana hanya. Direban dayake Jan motar yabud'e booth d'in motar yad'auki wata gora yace"bari asamo ruwa acan, nasan baza'a rasaba" Cikin sauri shima p.a yabi bayansa, Jawad yasaki ajiyar zuciya tareda kallon agogon hannunsa yaga sunada sauran lokaci kafin afara shirin,yafara kallon yanayin wajan babu gidaje dayawa sosai amma akwai sahara awajan sosai. Daga can nesa ya hangota tana tafiya aqasa cikeda wahala dakuma tsantsar gajiya,tun barowarta daga kamfanin bayan taji baqin labari sai yanzu Allah yayi taqaraso gida,baqar laffaya ce ajikinta wadda tasake qawata farar fatarta,tundaga nesa yake qare mata kallo yana kallon d'an qaramin bakinta yanda yake motsi da'alama magana take ita kad'ai duba da yanda take maganar tana watsa hannayenta biyu alamun 6acin rai,tun kafin taqaraso wajansa yashagala a kallon kyakykywar fuskarta,haka yaci gaba da kallonta kamar zai cinye ta,da alama baima san ya lula duniyar kallon nata ba. Harta qaraso kusa dashi bata daina surutu ba,tagefensa tazo zata wuce tana masifa kota kansa batabiba bare tasan wanda yake tsaye kusa da qofar gidan nasu, haka taci gaba sababi tana fadin"kora daga kamfani aiba kora daga duniya zuwa lahira bace" Ganin zata wuce shi hakan yasa yad'an motsa lips d'insa,cikin sauri yace"am...kinga,naceba..." Inaas tajuyo ta kalleshi cikeda masifa dakuma taqaicin ankoreta daga aiki tace"kace me?" Jawad yadan motsa lips d'insa kamar baison magana saikuma yace"please inason ruwa ne" Inaas ta kalli idonsa tace"ruwa? anan wajan? to babu" Mamaki yakama Jawad,yad'an saci kallon dan mitsitsin bakinta yace"kinga driver na yacemin za'a iya samu,but har yanzu kuma ba sudawo ba,kuma babu ruwan gora a motar" Inaas tasaki ajiyar zuciya ta nuna masa wata hanya tace"idan kabi nan hanyar,saika miqe kasha kwana zaka iya samu anan" Jawad ya kalleta da mamaki 'yar qarama da'ita sai zaro magana take,yace"okay kuma da kinsani d'in but why zakiqi sanar dani tunda farko?" Ganin kamar yana tuhumar tane saboda taqi nuna masa inda zai samu ruwan hakan yasa ranta yasake 6aci,dama ga abinda aka mata a kamfani,itama a zuciye take,6acin rai takeji sosai,hakan yasa ta kalleshi tace"da kacemin in fad'ama inda zaka samu ne? ruwa kace min kanaso,koni ce ruwan?" Lumshe manyan idonsa yayi sannan yabud'e,ransa yafara 6aci,yarinyar tafara kaishi bango,hakan yasa yace mata "kinga ya'isa!, idan baki dainamin wannan shirman ba zan kakkaryaki anan"(🙆) Kai tsaye Inaas tace"tome kake jira?" Jawaad ya kalleta fuskarsa ad'aure babu walwala yasaka hannunsa yafara qoqarin cire suit d'in jikinsa yace"okay kina tunanin bazan iya bane?" ba tareda shakka kojin tsoro ba Inaas tace"ikon Allah,kaji mutum,daga had'uwa? daga tambayar ruwa saika koma yimin abu har kana qoqarin cire riga saikace wani d'an dambe? to Bismillah,kallon me kake? me kake jira kadakeni mana,nima inda Yayanah yana nan baka isa kanuna min hannu ba,Ammiy na tace inda yana nan shine zai kula dani,basai kacire rigarka ka nunamin qwanji ba, tsaya na kawo ma ruwan badan halinka ba" Tana fad'in haka tayi wuf tashige cikin gidansu domin kuwa bilhaqqi ta tsorata da yanda taga yana qoqarin cire suit d'in musanman yanda ta hango murd'ad'd'an dantsan hannunsa,kawai hargagi take masa dan karya raina ta. Yana ganin shigar ta gidan yasaki ajiyar zuciya sannan yasaka hannunsa yabude gaban motar yana dube-dube,adede lokacin takawo masa ruwan d'an kadan kamar ya roqa,batare dayayi magana ba ya kar6a yafara zubawa a motar. Inaas ta kalli motar sannan tasa qafa tadaki tayar gaban motar tace"idan na mallaki irin wannan motar nikuma shikkenan zama ya qaremin,yawo zanyi tayi waje-waje,kasan me? Ammiy na tace duk wanda ya aureni yayi sa'ah saboda nid'in tadaban ce,na tabbatar mijina saiya samu motar datafi wannan had'uwa" Jawad da surutun yarinyar yafara damunsa ya rufe gaban motar yana girgiza kansa,yabata kofin data kawo masa ruwan sannan ya kalli hannunsa cikin qenqemi saboda robon daya bude mota da kansa harya manta,yadubeta yace"ruwan yaqare,inaso na wanke hannu na" Kai tsaye Inaas tayi gaba ta nufi gidansu tareda fad'in"biyoni" Babu musu Jawad yabi bayanta suka qarasa cikin gidan nasu,yana saka qafarsa agidan yaji gabansa yayi wata irin muguwar fad'uwa kansa yasara,amma bai kawo komai aransa ba ganin tunda yashigo qasar jiya yake jin irin wannan yanayin. Inaas tadaga murya tace"Ammiy!, ga baqo" Bilkisu dake zaune akan kujera tad'ago idonta ta sauke shi akan had'ad'd'an gaye,matashin d'an kasuwa,ingarman namiji,miskili,Jawad d'in Daddy da Mummy kuma Muhammad din Bilkisu. lokaci d'aya taji gabanta yayi wata irin fad'uwa har saida tasa hannunta a qirjinta,shima a nasa 6angaren zuba mata ido yayi yana kallonta tana sanye cikin baqar doguwar rigar gwanjo,kanta yana d'aure da d'an kwalin rigar,yayinda ta tsaga dogon gashinta tarabashi abiyu ta daure sauran abaya,amma daga gashin gaban goshin ta kana iya ganin yanda gashin yake arabe ta hanyar tsagar. Lokaci d'aya yaji matar tashiga ransa ta birgeshi,da alama batada hayaniya kamar wannan ficiciyar yarinyar marar kunya. Cikin sauri taqaraso wajansa cikin sanyin murya tace"sannu da zuwa" Jawad saiyaji hausarta a goge ras kamar tasa,ba kamar hausar Inaas ba. Ammiy tajuya ta kalli Inaas tace"daga ina kika samo baqo?" Inaas tace"awaje na tsinceshi,hannunsa zai wanke wai,dan 'wai' zance saboda kinga hannun nasa nan ras babu abinda ya sameshi amma ahaka zai wanke" Bilkisu tayi murmushi sanin halin 'yartata, tawuce tad'ebowa Jawad ruwa,ta kalleshi cikin kulawa tace"zona zuba ma ka wanke hannun" Cikin sauri Jawad ya matso ya tsugunna agabanta,Ammiy tazuba masa ruwa yafara wanke hannayen sa sosai,yana wanke hannun amma idonta gaba d'aya yana kansa tana kallon yanda yake komai a nutse,ko kad'an takasa janye idonta daga kansa, yana gama wanke hannun tamiqe zata maida kofin kan randa,cikin sauri Jawad ya kar6i kofin har hannunsu yana haduwa waje daya,yamaida kofin kan randa. Inaas tazuba musu ido tana kallonsu sai wani abu suke kamar basa son rabuwa da juna. Jawad kotakan Inass baibi ba ya kalli Bilkisu yace"MAMA nagode,sai anjima" Gaban Bilkisu ya yanke yafad'i,MAMA? ta maimaita sunan a bakinta,lokaci d'aya tatuno da yaronta Muhammad,mama shine sunan da taso yakirata dashi idan ya girma saide kuma Allah bai nufa ba,haka tunda ya 6ata babu wanda yata6a kallonta yace da'ita Mama sai yau da wannan yaron yafad'a mata,ta tuna lokacin datake wa Muhammad dinta wanka tana fad'a masa kada shima ya gudu yabar mama,mama tana sonsa idan ya gudu bazata iya jurewa ba,tasaki ajiyar zuciya ta kalli Jawad taga harya juya zai fice daga gidan tayi sauri tace"tsaya yaro,zokasha shayi saika tafi" Cak! Jawad yaja yatsaya yaji kwata-kwata yakasa yin musu da matar. Bilkisu tayi sauri ta Shimfid'a masa tabarmar ta mai kyau tace"zoka zauna" Babu musu Jawad yadawo ya zauna yanata kallonta. Inaas datasan cewa ita Ammiy zata ce tahada masa shayin hakan yasa ta dauko butar shayin zata hada masa,cikin sauri Ammiy tace"bani nahad'a masa dakaina" Inaas ta kalleta da mamaki,duk wani baqo da zaizo gidan kullum saide tace Inaas ta had'a musu shayi,amma abun mamaki yau itace da kanta take qoqarin had'a wa wannan baqon,babu musu tabata butar shayin ita kuma takoma gefe ta zauna ranta duk ba dadi. Jawad ya kalli yanda Ammiy take had'a masa shayi cikin nutsuwa, tazuba masa a dan qaramin kofin shan shayi irinna buzaye,sannan ta qarasa tabashi,tazauna kusada Inaas tamaida nutsuwarta gaba daya kan Jawad,tunda yashigo gidan takejin wani irin nishadi wanda rabon da taji nutsuwa da nishadi irin wannan tun kafin Malam Manu ya gudu yabarta. Cikin farinciki ta kalleshi dakyau tace"yarona kaima anan qasar kake ne?" Jawad yayi murmushi ya ajiye kofin shayin hannunsa sannan tace"a a,ni d'an Nigeria ne Mama" Wannan sunan na Mama daya sake fad'a saita sake jin wani irin dad'i,tasaki ajiyar zuciya tace"masha Allahu,nasan Nigeria sosai,nima nazauna acan shekarun baya,Yaya matarka?,tana lafiya?" Jawad yasake murmushi sannan yace"Mama ai banda aure" Bilkisu tasaki 'yar qaramar dariya sannan tace"ikon Allah,ashe yaron nawa tuzuru ne,to Allah yabaka mace tagari,yanda kake da nutsuwa Allah yabaka nutsats-tsiyar mace,nasan duk yarinyar data aureka tayi sa'ah,babu wata budurwa dazata kai matarka sa'ah saboda tayi dace da miji nagari" Inaas tanajin haka tacuno bakinta gaba cikin shagwa6a tace"Ammiyyyy.....,nimafa irin wannan maganganun kike fad'a min" Bilkisu ta kalleta tayi murmushi tace"to sarkin Kishi,fad'amin waye yata6amin ke tunda kika shigo naga ranki a6ace,Yaya wajan aikin naki meyasa kika dawo dawuri yau?" Cikin tsananin damuwa Inaas tace"Ammiy ai sun koreni,wai shugaban kamfanin ne yazo koya sunansa ko Jawad? oho masa de, shine yace afad'amin yakoreni daga kamfanin sa wai in koma makaranta,wallahi Ammiy duk randa naganshi da idona,saina saka hannayena nashaqe masa wuya"(🙆🏻‍♀️) Tafad'i hakan tana dunqule hannayen ta alamar yanda zata Shaqe wuyan Jawad. Jawad dake shan shayi lokaci d'aya gabansa yafad'i,cikin sauri ya kalleta tare zaro idonsa. cikin ransa yake magana dama itace?,shiyasa tazo wucewa tagabansa dazu take sababi tana fada tana cewa kora daga kamfani aiba itace kora daga duniya zuwa lahira ba? nan take yaganeta,tabbas itace wadda akace masa tana shigar da bayanan kamfani yace afad'a mata ya sallameta. Inaas taci gaba da fad'in"wallahi Ammiy wannan Jawad d'in ko, tunda naji sunansa nasan cewa bashida mutunci,daga sunan mutum nake gane me mutunci da marar mutunci,yanzu daya koreni dan Allah Ammiy tayaya ne zan tara wani kud'in in sauya miki kayan daki?, nayi alqawari duk ranar danayi kudi,saina gina kamfanin Oil guda dari ta yanda zan fuskanci Jawad inyi gogayya dashi" Bilkisu tayi murmushi kamar bataji haushin korar da'aka yiwa Inaas dinba,domin ta kwantar mata da hankali hakan yasa tace"to ayi haquri mana,saida nace miki kitashi dawuri ki tafi karki yi latti, kika tsaya zaman wanke kai,ina me tafiya wajan aiki yaga lokacin tsayawa wanke kai? ai shikkenan saiki yi Addu'ah Allah yakawo miki wani aikin,matso na turara miki gashinki karna sakejin kinsa damuwar hakan aranki kinji ko?" Inaas tayi qwafa,sannan tace"shikkenan Ammiy" Bilkisu tatashi taqara zubawa Jawad wani shayin wanda baimasan ya shanye nacikin kofin ba saboda yanda yaji d'and'anon shayin yayi masa dad'i sosai. Bayan tazuba masa shayin ta d'auko turaren wutan datake turara dogon gashin Inaas dashi kasancewar basuda halin zuwa wajan saloon, zama tayi sannan ta janye laffayar daga kan Inaas,dogon gashinta ya bayyana a fili,tasaka hannunta ta warware mata gashin nata,sannan tasake taje mata gashin, tafara turara mata shi. Jawad dake zaune yasaci kallon su lokaci d'aya idonsa yayi arba da dogon gashin Inaas,ahankali yazaro idonsa gabansa yana fad'uwa, aransa yana fad'in yanzu duk wannan gashin natane?,yasake qarewa gashin nata kallo yaga de tabbas natane. Inaas tad'an juyo ta kalleshi cikin sauri ya janye idonsa,cikin zuciyarsa kuwa fal mamakin yawan gashin yarinyar yake. Inaas kuwa qare masa kallo take talura kamar yana cikin damuwa,bayan damuwar ma da alama bashida lafiya,yana tattare dawata irin cuta,wato miskilanci,wannan ma babbar rashin lafiya ce. 'Dauke kanta tayi daga kallonsa. yayinda shikuma Jawad zuciyarsa tasake tunzurashi akan yasake kallon abun dayake mutuqar so tun kafin yabar gidan,wato dogon gashi. (🤫🙈) Ahankali yad'an juya yasaci kallonta kamar yana tsoron karta kamashi yana ganinta, idonsa ya sauka akan d'an qaramin bakinta,yadade yana kallon bakin tsiwar tata, ahankali yamaida kallonsa zuwa dogon gashinta,adede lokacin Inaas ta juyo ta kalleshi,karaf idonsu yafad'a cikin na juna,Koda wasa Jawad yakasa dauke idonsa daga kanta,nan take wata irin fad'uwar gaba ta ziyarcesu lokaci d'aya. Ammiy kina zaune yaranki suna satar kallon juna 😍😫 Jama'ah nace ba?🤔 Wai yaushe wannan baqon namu na zaune daya koremu daga aiki kuma yazo yake shanye mana shayi zai tashi yatafi ne? 🤔 Mezai faru idan Inaas tagano cewa Jawad din data gama ciwa mutunci shine a zaune a gefenta yagama Jin komai? 🤔 Yaya batun hadin auren Jawad da Amal?🤔 Tayaya Bilkisu zata gane cewa Jawad shine Muhammad dinta?🤔 Yaya haduwar Bilkisu da malam Manu? 🤔 Duk kubiyoni 💃🏼, Basai na fada ma,duk me bibiyar littafi na yasan cewa akwai soyaiya, wannan Karon ma akwai zazzafar soyaiya agaba,makirci,dakuma tirka tirka. Yanzu ne labarin zai fara,yanzu ne zamu nutsa cikin zallar soyaiya dakuma qalubale,munji labarin tasowar taurarinmu munji haduwar su to yanzu ne wasan zai fara,littafin nan yanada yawa,tundaga kan free page zaku gane haka,ban taba rubuta free page me yawa kamar na wannan littafin ba. Wanda suke siyan littafi na ba gajiya wa nagode banda kamar ku akoda yaushe.🙏 Alhamdulillah, 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼anan na kawo qarshan free page,duk wanda yakeso ayi tafiyar dashi yazo yayi payment. ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,yau free page yaqare. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. idan kinsan zaki sai littafi nane danki fitar min dashi to nagode na haqura da Dari ukun ki,wanda suka siya ma Allah ya musu albarka. Wanda zamu rabu dasu daga nan wato iya free page, saimun hadu a sabon novel dina mesuna MATAR ABBANA,nagode 🙏 Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. 31&32 Lokaci d'aya Jawad ya6ata ransa tareda d'auke kai kamar bashine yagama qare mata kallo ba,saide kawai yabita da wani irin kallon qasa-qasa irin kallon gefen idonnan kamar an masa dole saiya kalleta. Maganar su p.a daya jiyo daga waje,itace tasa yamiqe ya kalli Bilkisu sannan yace"Mama zantafi,nagode da kulawar ki" Bilkisu ta kalleshi fuskarta fal murmushi sannan ta kalli Inaas tace"ke riqe gashinki naraka yarona waje" Inaas tayi sauri ta riqe gashinta saboda idan bata riqe shi ba zai iya shafar qasa tunda a zaune take,kallon Jawad tayi wanda yatsaya tsayin daka shi ala dole jira yake Ammiy ta rakashi saikace yasan Ammin tata. Cikin shagwa6a tace"Ammiy towai kinsan shine? kibarshi yayi tafiyarsa" Jawad ya kalleta fuska babu walwala sannan ya kawar da kansa,ya lura yarinyar batajin magana,saide kuma abun mamakin maganar Inaas din batasa yatafi ba,saida yatsaya Ammiy taqaraso wajansa sannan cikin lallashi tacemasa "muje yarona,rabu da'ita" Saida Yajuya yasake kallon Inaas wadda batasan yanayi ba, sannan cikin sauri Yajuya yayi gaba yana zura hannunsa d'aya cikin aljihun wandon sa. P.a da driver suna ganinsa suka qaraso da sauri suna bashi haquri,baice dasu komai ba yajuya yasake kallon Ammiy wadda take tsaye daga qofar gida,yarasa meyasa yakeji kamar bayason barin matar,kafin yace wani abu Bilkisu ta d'aga masa hannu sannan tace"Allah yatsare hanya,Allah yayima albarka" Cikin jin dadi yace"Amin Mama" Daga nan driver yabude masa motar yashiga suka tafi,saida suka qule sannan Ammiy tasaki ajiyar zuciya tadawo ciki zuciyarta fal da farinciki,ta zauna taci gaba da turarawa Inaas gashinta,Inaas tace"Ammiy daga ganin baqo? keda bakya yiwa mutane haka amma wannan sai qara liqe masa kike?" Bilkisu tayi murmushi tace"ina laifi dannayi masa hakan? bakya ganin yaron yanada nutsuwa sosai?" Inaas da mamakin Ammin nata yagama kasheta tayi ajiyar zuciya tace"nagani kam,naga nutsuwa Ammiy...". Cikin jin dadi Bilkisu tace"ai shine abinda nake fad'a miki,kuma da alama babban mutum ne,naga ana bud'e masa mota da rawar jiki,kuma abokan tafiyar tasa banji sun fad'i sunan saba kowa Yalla6ai yake cewa,kinga yatafi ma ni kwata-kwata na manta ban tambayi sunan saba,Shima kuma bawan Allah babu magana shima bai tambayi namu sunan ba" Inaas de datake cikeda mamaki tace"aikam hakane babu magana gashinan gim azaune" Abangaren su Jawad kuwa kai tsaye gidan tvn dazasuyi fira dashi nan suka wuce,yana qarasawa guards suka matso da gudu suka bude masa mota, sannan suka qarasa ciki domin fara gabatar da shirin. Tsawon minti talatin firar tasu ta d'auka sannan yawuce gida,daya koma gidan ma bai zauna ba yasake shiryawa ya futo zai wuce Nigeria,gaba d'aya 'yan gidan na Alhaji Auwal sukai masa rakiya zuwa wajan motocin dazasu kaishi Airport,Ummi sai fari take masa da'ido tana masa yanga,shikuwa bihim baima gane metake nufi ba. Yayinda fauzy yayar Ummi ta dakata daga gefe ta hard'e hannunta a Qirji tana kallonsu,dama itama 'yar shan qamshi ce kamar shi, Ummi tafita sauqin kai. Saida motocin suka fice daga gidan sannan suka juya ciki,kafin motocin su Jawad su qarasa Airport Fu'ad yakira wayar Jawad,p.a dake zaune agaban motar yajuyo yabashi wayar,yana d'auka Fu'ad yace"yaya zan wuce Germany ba lalle kadawo ka sameni ba" Jawad yayi murmushi yace"ok har birthday party d'in naka yazo?" "yes Yaya" "ok kanada kud'i enough awajanka?" Fu'ad yace"yes Yaya akwai,kuma shaddodinka ankawo sun zama ready,Yaya I will miss you,but bazan dad'e ba zan dawo may be 2 to 3 day's" Cikin sauri Jawad yace"no Fu'ad,karka damu kayi zamanka kahuta sosai,lokacin danake kamar kai niban samu damar wannan hutun ba,saboda haka kayi rawa,kayi yawo,kahuta sosai saika dawo" Cikin farinciki Fu'ad yace"thank you Yaya,I'm proud of you" Jawad yayi murmushi yakashe wayar yabawa p.a sannan ya jingina da motar ya lumshe idonsa,yana ganin fuskar Bilkisu acikin idon zuciyar sa. Bayan sun dawo Abuja kai tsaye d'akinsa yawuce,yayinda Daddy da Mummy suke zaune afalo. Alhaji Auwal yakira wayar Alhaji Mekudi,bayan sun gaisa sungama yiwa juna jaje akan rasuwar Baby, Alhaji Mekudi yace"Jawad yadawo gida yanzu,ina fatan sun daidaita da Ummi ko fauziya" Alhaji Auwal yayi murmushi irin nasu na manya yace"Inaaa!, banga alamar hakaba Alhaji,ina ganin kawai arabu dasu,suma zansa musu rana da samarin su nanan Niger kawai,kasan sud'in gaba d'ayansu daga Jawad d'in harsu fauziyan dukansu qananun yara ne,kada a takura musu su shiga damuwa". Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya cikin damuwa,ko kad'an baiso hakan ba, yaso ace sun sake had'a danqon zumunci tsakanin sa da aminin nasa,cikin damuwa yace"to shikkenan Alhaji,Allah yasa hakane yafi Alkhairi" Bayan sun gama wayar Hajiya Zaliha tace"Alhaji banji kace komai akan maganar Jawad da Amal ba,Yaya Mariya tazo tace ita bata amince ba,Alhaji ina laifin Amal? yanzu Yaya Mariya tana nufin kenan d'an'uwana bai iya bada tarbiya ba?" Alhaji Mekudi yayi murmushin su na manya yace" Zaliha kenan,wani lokacin kina yin abu kamar bakisan halin Yaya ba,sanin kanki ne Jawad tun yana yaro take ji dashi,kamar yanda na lalla6a ta shekaran jiya insha Allah idan auren ma yataso zanji da'ita, tunda de kedin kinga yarinya kuma yarinya tayi miki to shikkenan,shima yaron da kansa yace tunda za6inki ce bashida damuwa to dan Allah kibar maganar nan" Hajiya Zaliha tayi ajiyar zuciya tace"to shikkenan Alhaji,yawuce" *** *** *** Niger Republic Da daddare suna zaune suna kallo itada Ammiy bayan sun idar da sallar isha'i,ganin babu abinda ake a tashar tauraruwa sai tallace-tallace hakan yasa Inaas ta d'auki remote ta sauya tasha zuwa gidan television na qasa,adede lokacin aka hasko fuskar Jawad yana zaune yayi kyau cikin suit dinsa ta d'azu da safe da yabar gidan nasu,gaban Inaas yayanke yafad'i tazaro idonta waje,takamo hannun Bilkisu tace"wanake gani haka Ammiy?"(😳) Bilkisu ma tazubawa Tv ido tana kallo,tabbas yaron da yabar gidansu ne d'azu dasafe,to meyake a tv ko aikin jarida yake?(🤔) Kafin su sake magana matar datake zaune akan kujera tana fuskantar Jawad da alama itace zata masa tambayoyi ta kalleshi fuskarta fal murmushi,sannan ta juyo kad'an ta kalli camera tace"masu kallo barkanmu da sake kasancewa acikin wannan shirin namu mai suna 'musan junanmu', ayau mun kar6i baquncin shahararran d'an kasuwa,wanda ya qirqiri kasuwanci dayawa afad'in duniya,jagoran talakawa,wanda ya kasance yana taimakon talakawa,matashin da yake samun nasara a kasuwancin sa,shugaban kamfanin Mekudi Oil, wato JAWAD MEKU'DI" Inaas tanajin sunan Jawad tamiqe tsaye tad'ora hannunta akanta tafara zagaye falon nasu tana fadin"innalillahi!,shikkenan Ammiy,shikkenan na kashe kaina,ko sunyi niyar mayar dani aiki wallahi yanda na zauna naci masa mutunci yanaji na sarai dole su fasa" Ammiy ta gagara magana saboda tsananin mamaki,ta tattara hankalin ta kacokam tamaida kan tv,tunani take aranta yanzu dama yaron nan shine shugaban kamfanin Mekudi oil? Inaas takoma ta zauna adede lokacin da matar tasake kallon Jawad tace"Mr. Jawad,kwatsam saigaka a qasar Niger,muna tunanin idan har hamshaqin d'an kasuwa kamarka zai shigo qasar Niger to muna fatan zaka sake kawowa qasar wani cigaban ne kamar yanda kakawo mana kamfanin ka a baya kuma har yanzu oil din Mekudi yana nan ana damawa dashi acikin jerin mayukan da'ake amfani dasu a qasar Niger" Jawad yayi murmushi d'an kad'an sannan ya motsa lips dinsa kamar bayason magana yace"ziyara ce kawai takawoni dakuma ta'aziyya" Zamanta tagyara sannan tace"Allah yaji qan rai, Mr. Jawad,kamfanin Mekudi oil ya shahara,sannan yagama kerewa dukkanin sauran kafaninnika na oil's dake cikin qasar Niger,yana d'aya daga cikin jerin manyan kamfanin nika dasuka samu damar shiga cikin jerin kamfanin nika aduniya, kunada resuna na Mekudi oil samada guda talatin a qasashen aduniya ciki harda qasar Niger,Mr. Jawad menene sirrin nasarar ka?" (Ammiy na tace duk wanda ya aureni yayi sa'ah,saboda nid'in tadaban ce ....) Maganar Inaas ce tafad'o masa cikin ransa,cikin sauri yayi nasarar kawarda tunanin yarinyar aransa sannan ya girgiza kansa ya kalli 'yar jaridar yace"sirrin nasarata shine addu'ar mahaifiyata" "mezaka cewa sauran matasa 'yan kasuwa masu tasowa? Wacce shawara zaka basu?" "Ina bawa matasa shawara su tashi suyi aiki tuquru domin inganta gobensu,abaya babu abinda banyi ba domin in temaki kaina,suyi qoqari,su tashi tsaye, su jajirce,insha Allah ubangiji zai taimakesu" "Mr.Jawad,kasancewar ka babban d'an kasuwa,sananne a'idon duniya,mutane dayawa suna saran ganin matarka,wacce me sa'ar ce tayi nasarar sace zuciyarka? shin babu 'yanmatan ne, kokuma kaine baka ra'ayinsu?" Kallonta yayi yace"Jawad d'an kasuwa ne, babu abinda na'iya sai kasuwanci,har yanzu de babu yarinyar datayi nasarar sace zuciya ta" "Mr. Jawad,kashiga cikin jerin hamshaqan masu kudi a Africa,menene burinka nagaba?" Murmushi yayi wanda yasake futo da tsantsar kyawun sa sannan yace"babban burina shine in shiga cikin jerin masu kudin Duniya" 'Yar jaridar tayi murmushi tace"muna tayaka Addu'ah Allah yacika ma wannan burin naka,mungode sosai da ziyara,muna fatan zuwa gaba zamu sake kar6ar baquncinka" Kansa yagyada mata alamun insha Allah,daga nan tarufe tattaunawar tasu da fatan Alkhairi. Har inda yafuto zai shiga motarsa domin yatafi gida saida suka nuna,da yanda wasu daga cikin yan jarida suka tareshi yake yi musu sign,wasu kuma selfie suke dauka dashi. Saida yagama da jama'ar sannan yanufi mota yayinda guards kusan guda goma sha biyar suke kakkareshi saboda kada acutar dashi, cikin sauri aka bude masa mota yashiga sannan suka tafi. Inaas ta janye tagumin datayi da hannu bibbiyu bayan tagama kallon firar su Jawad da yanda taga guard's suna take masa baya, ta tuna dazu dasafe lokacin da take gwada yanda zata Shaqe masa wuya idan taganshi,harce masa tayi bashida mutunci,meya kaita? Ita 'yar wacece? ina ita ina takalar wannan mutumin da fada? dama ance idan baka san mutum ba kada kayi gaggawar cimasa mutunci,ta lumshe idonta taja wata irin ajiyar zuciya sannan ta bud'e idonta tajuyo ta kalli Ammiy taga sai murmushi take,cikin muryar shagwa6a tace"Ammiy sai murmushi kike kamar ba shine ya koreni daga wajan aiki naba" Bilkisu ta kalleta tace"ina kallon sane, kalar fatarsa kamar ta d'ana, fari tas dashi,nasan nima da Muhammad d'ina yana nan,zuwa yanzu zekai shekarun wannan Jawad d'in" tasake kallon Inaas sosai sannan taci gaba da fad'in "kinga dalilin dayasa banason kidinga wannan shegen surutun naki agaban baqi ko? yanzu de gashinan kingama zageshi tsaf,kuma yanad'e wannan zagin tas a kunnansa,keda aiki a kamfanin sa kuma shikkenan zance yaqare yariga yazama tarihi,shiyasa naga kafin yatafi yajuyo sai kallonki yake ashe shi sake ganeki yake da kyau ko wataran zaki koma masa kamfani dan yasan irin hukuncin dazai miki" Inaas taturo bakinta gaba cikin shagwa6a tace"to Ammiy korata fa yayi" Bilkisu tace"to ai saiki yi tunda bazaki rissina ba" *** *** *** Washegari da rana ya shirya tsaf ya futo domin cin abinci,haka kawai yake jinsa cikin nishadi, kafin yaje qasar Niger zuciyarsa cike take fal da d'aci ahaka yatafi saboda maganar yarinyar da shine yace yabasu dama su nemo, kuma sun nemo din amma yana fishi akan haka,amma tunda yabar qasar Niger din yadawo Nigeria yakejinsa cikin walwala,dazaran yatuna da Matar nan data bashi shayi sai yaji hankalinsa ya kwanta,sai yaji wata irin nutsuwa wadda bai ta6a jin makaman ciyar taba. Kai tsaye dining yawuce anan ya tarar da abinci kusan kala biyar, Mummy ta kalleshi da kulawa tace"wanne kakeso nabaka dana?" Saida ya qarewa abincin kallo sannan ya za6i guda daya,mummy ta matso tafara bashi abincin da spoon,yanaci yanajin dadin girkin har wani lumshe ido yake, hakan da Hajiya Zaliha tagani shine yasake tabbatar mata yanajin dadin abincin,dan haka tasake tura masa abincin yaci yanda ransa yakeso. P.a ne ya qaraso wajansu ya rissina cikin girmamawa yabawa Jawad wasu takardu yace"yalla6ai ana buqatar saka hannunka anan" Babu musu Jawad ya kar6a yaduba sannan yasaka masa hannun, shikuma yafita. Man Sulaiman ne yashigo falon,cikin girmamawa ya gaida Hajiya Zaliha,ta amsa masa. Jawad ya kalleshi yace"Uncle Ina wuni" Man Sulaiman ya kalli Jawad da tsantsar soyaiya yace"lafiya kalau Jawad,sannu da hutawa" Jawad baice masa komai ba yadai dauki tissue yafara goge bakinsa. Hajiya Zaliha ta kalli Man Sulaiman tace"Man Sulaiman dan Allah gidan gona zakaje, fruits din gidan nan yaqare, kaje kadebo wasu" Cikin murmushi yace"to Hajiya insha Allah, za'a debo yanzu" Yajuya yafice daga falon cikin sauri. Lokaci d'aya Jawad yaji ransa yayi wani irin baqi,inda yanada iko dayace ya sallami malam Sulaiman saboda tun yana yaro yake ganinsa agidan har kawo yanzu, zuwa wannan lokacin ya kamata ace anbarshi haka da ire-iren wannan aiken. Hakan yasa ya kalli Mummy wadda hankalin ta yakoma kan waya fuskarsa cikeda damuwa yace"Mummy please kudena aiken wannan mutumin dan Allah,banajin dad'i kokad'an wallahi,idan yana aiki inaji ajikina kamar nine nake aikin, yanda yake faman driving kullum jinake kamar da ga66an jikina yake amfani ba nasa ba,banajin dad'i kokad'an, shekarun sa sunja yakamata kubarshi haka Mummy" Cikin sauri Hajiya Zaliha ta kalleshi. ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 41&42 Cikin sauri Hajiya Zaliha dake zaune agefensa ta kalleshi sannan ta ajiye wayar hannun ta tadawo kusa dashi ta zauna, tadora hannunta akan kafadarsa tace"duk menene yayi zafi haka Jawad? shine abinda kakeso kawai?" "yes Mummy" "toya isa,kada kasa damuwa aranka saboda hakan ok?" Kansa yagyada mata cikin nutsuwa,sai yanzu ne yaji wata irin nutsuwa acikin ransa. Da yamma yasan Daddy baya nan,hakan yasa yayi shigar qananun kaya farar fatar qafarsa tana sanye cikin wani takalmi me mutuqar laushi irinna zaman falo,computer sace akan cinyarsa yana aiki cikin nutsuwa,sosai yake jin dadin aikin nasa musanman idan yatuna da Mummy ta masa alqawari Man Sulaiman yadena ayyukan dayake. Wata matashiyar budurwa ce tashigo falon bakinta daukeda sallama,hankalinsa yana kan computer ya amsa mata sallamar da muryarsa qasa-qasa, sannan yadago kansa yazuba mata ido jin muryar yarinyar tanada zaqi sosai kamar ta yarinyar dayaje yasha shayi a gidansu a qasar Niger (🙆🏻‍♀️🤭😳) Har yarinyar taqaraso cikin falon, bai janye idonsa daga kanta ba,so yake yaga yanda muryarta take kama data yarinyar nan ta Niger shin a fuska ma suna kama? Mummy data futo daga dakinta ta kalli Jawad tana murmushi ganin yanda yazubawa yarinyar mutane ido yana kallo,har zata masa magana saita rabu dashi tana so taga gudun ruwansa. Jawad kuwa bakin yarinyar ya kalla sannan yatuna da d'an qaramin bakin Inaas,yaga ba irinsa bane, ahankali ya girgiza kansa, yasake kallon daurin dankwalin yarinyar irin wanda ake fitarda gashi ne, ya kalli gashin nata, yatuna irin yawan gashin Inaas yaga wannan kamar na qari tasaka saboda wanda ya futo daga bayan yafi gashin gaban goshin ta baqi,cikin sauri ya girgiza kansa sannan yamaida idonsa kan computer sa yaci gaba da aiki. Hajiya Zaliha tayi murmushi tadaga murya tace"Jiddah kin qaraso?" Yarinyar tayi murmushi tace"eh wallahi Hajiya Ina wuni?" Mummy ta amsa mata, sannan tajuya ta kalli Jawad wanda hankalinsa yake kan computer kamar ba shine yagama qare mata kallo ba tace"ina wuni?" Idonsa akan computer sa batare da ya kalleta ba yace"lafiya" Hajiya Zaliha tajata suka shige daki,basufi minti biyar da shiga ba suka futo hannun yarinyar daukeda leda, dazata wuce tasake kallon Jawad tace masa"sai anjima" Amma Jawad yayi gim kamar badashi take ba, Hajiya Zaliha tayi murmushi Sannan ta zauna agefensa tace"yakaga wannan yarinyar? tayima ne insa Alhaji yayi magana da babanta sai afasa waccen maganar ta aurenka da Amal?" Jawad yadan 6ata fuska sannan yace"Mummy already nabaki za6i" Murmushi tayi cikin jin dadi,sannan ta wuce hanyar kitchen. Da daddare yana zaune a falonsa dake sama, ba main falon qasa na kowa da kowa ba,coffee ne agabansa yakesha kad'an kad'an,yadauki remote zai kunna kallo ya kalli labarai lokaci daya maganarta tafad'o masa. (kasan ne? mamana tace duk wanda ya aureni yayi sa'ah,saboda nidin tadaban ce...) Yafasa kunna kallon yakoma ya jingina da jikin kujera ya lumshe idonsa,maganarta tasake fad'o masa. (yanzu daya koreni da wanne kudin zan sake miki kayan daki?) Furzar da is'ka yayi daga bakinsa sannan ya runtse idonsa,ahankali ya motsa lips dinsa qasa-qasa yace"sun kyautata min" Kwata-kwata sai yaji kallon yafita daga ransa,mutanan dasuka yimasa irin wannan karamcin basu cancanci haka daga gareshi ba,idan da albashin nata suke amfani wajan siyan abinci hakan yana nufin ya toshe musu hanyar cin abinci kenan? shikuma yazo gidansu ya zauna mahaifiyar ta tayi masa kirki, ta yi masa karamci kamar d'anta. Ya dade yana tunani,baisan tsawon lokacin daya dauka ba har yaji bacci yafara daukan sa, da wannan tunane-tunanen yayi bacci. Washegari abokinsa Na'im yakawo masa ziyara, suna zaune a compound din gidan cikin wata yar qaramar rumfa irinta hutawa, guard guda biyu suna tsaye daga bayansu,ga computer agabansa abude da alama wani aikin yake zuwan Na'im dinne yasa ya dakata da abunda yake,daga gefen Na'im gorar ruwan Faro ne guda biyu dakuma Apple manya-manya mai launin ja acikin wani tsarararren plate. P.a ne ya qaraso wajansu ya rissina cikin ladabi yabashi wasu takardu sannan yace"yalla6ai wannan takardun suna buqatar saka hannun ka" Kar6ar takardun yayi yana fadin"takardun menene p.a?" "takardun da kukai agreement ne akan daukan sababbin ma'aikata" Shiru yayi yana sake duba takardun sannan yayi masa sign din, yahada da wasu takardun dake gabansa yabashi yace"kahada da wannan c.v din nawasu yarane danake dubawa, idan nagama da Na'im saika dawo min dasu" Cikin biyaiya yace"okay sir" Sannan yajuya yabar wajan. Jawad yagyara zamansa ya fuskanci Na'im yace"naje qasar Niger gaisuwa" Na'im yadauki tuffa guda d'aya yakarya sannan yamaida nutsuwar sa kacokam ga Jawad yace"yeah naga tattaunawar da gidan tv sukai dakai" Jawad ya motsa lips dinsa kamar bayason magana,har Na'im yafitar darai zai masa magana sai caan yaji Jawad d'in yace"yarinyar ta had'u,idan nacema had'uwa to ina nufin maqurar had'uwa,komai nata gwanin birgewa,har tsawon wasu lokaci surutun yarinyar ya 'DEBE MIN KEWA"(🤭) Na'im yasake kallon Jawad da tsananin mamaki sannan yasaki murmushi yace " you're talking about lady Jawad,are you serious?" Jawad yagyara zamansa yace"yeah,hatta ahalinta na lura sunada d'abi'u masu kyau especially mahaifiyar ta,gidan nasu babu kowa,babu hayaniya,inaji kamar naci gaba da zama da matar har abada,kamar kada nafuto daga gidan,tabani shayi,tazuba min ruwa na wanke hannu na,tasake bani shayi, kaiii tayi min kirki de wanda yasa har yanzu tunaninsu duka su biyun yakasa barin zuciyata" Cikin mamaki Na'im yace"ikon Allah,but tayaya ka'iya shan abun hannunsu? baka tsoron su cutar dakai?" Jawad yadaga kafadarsa alamun rashin damuwa sannan yace"no,hankali na ya kwanta da matar gaskiya" Na'im yayi murmushi yasake gyara zamansa sannan yace"but ita kuma yarinyar fa?" Cikin rashin sanin yana bayyana abinda yake cikin ransa, zuciyarsa d'aya yace"bana tunanin akwai ta biyun ta wajan kyau,surutun ta ya 'DEBE MIN KEWA tsawon wasu minute's din" Na'im yasaki wata irin dariya yace"wow!!,you're in love Jawad...." Cikin sauri Jawad yace"no" Na'im yasake cewa "seriously you're in love Jawad" Shima Jawad cikin comfidence yace"no,Na'im" *** *** *** Niger Republic Kayan gwanjon dake kanta tasauke agaban matan gidan bayan tayi sallama,Hajara tafara kunce kayan tareda fadin "Me gwanjo yau keda kanki?" Bilkisu tace"to yazanyi? dole ne mufuto nema" Hajara tadaga wata riga me kyau tana jujjuya ta tareda fadin"yau ina 'yar taki? kobata nan?" Bilkisu tace"tana can tana bacci dayake yanzu ba zuwa kamfani,banaso na tasheta daga baccin ta yau nabarta tahuta tunda kullum itace take zarya" Hajara tace"hakane kam ai tana qoqari ma,yau dinma dakin bari tatashi ai zata zagaya da kayan naku" Bilkisu tace"yaushe zan bari sai rana tatake zata futo talla,najira najira naga bata tashi ba saina qyale ta nafuto, baccin babu inda zai kaimu,gara mutashi mu nemi na aure" Hajara tasake daga wani wando na yara ta ajiye shi akan cinyarta sannan tace"auren 'yar me gwanjon?ikon Allah auren ta zakiyi kenan tun yanzu?" Bilkisu tace"aure kuwa,ada kam banyi niyar aurar da'ita ba,yanzu kuwa na cire wannan tunanin araina,saboda naga yarinya tun ba'aje ko'inaba ta had'a wannan uban nonuwa,kinga kuwa yaushe zan sata agaba ina kallonta?,dauki abinda zaki siya in qara gaba" Hajara tayi murmushi tace"ai Inaas din takice nima de naga saurin girman ta,batafi shekara sha takwas ba amma kamar wata babbar budurwa, nadauki guda uku, za'a aiko miki kudin" Bilkisu tace"to nagode" Tatashi ta dauki qullin kayan gwanjon ta tashiga gida nagaba. *** *** *** Abuja Nigeria Washegari aka kai goron Jawad gidansu Amal,duk wasu kudi da al'ada ta nuna Alhaji Mekudi ya bayar,bai bar gidansu Amal ba saida aka saka ranar Jawad da Amal tsawon sati biyu kacal, Alhaji Mekudi yanemi hakan ne domin yanaso idan Jawad zai tafi to yatafi tareda iyalinsa. Washegari goro yasamu Yaya Mariya,batayi qasa a gwiwa ba tadira agidan Alhaji Mekudi,a falonsa na sama ta sameshi, bayan ya gaidata ta kalleshi tace"yanzu Aliyu kade dage sai an had'a auren Jawad da wannan yarinyar? Fisabilillah menene hadin Jawad da wata Amal? yarinyar nan ba sa'ar auren Jawad bace, Jawad yafi qarfinta nesa ba kusa ba, uban yarinyar nan babu abinda ya'iya sai shegen son kudi kamar shine yafi kowa son kudi aduniya,itama kanta Zaliha tasan da haka,kawai son kanta ne ya rufe mata ido" Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya yace"yaya shi aure ai babu ruwansa da wannan,idan kika duba zakiga kwata-kwata Jawad bashida niyar aure, mun zuba masa ido mun barshi yana yawo agari Yaya karki manta fa mutanen gari zasu iya zaginmu,ita kuma Zaliha tahada Jawad da Amal ne domin tasake qarfafa zumunci" Cikin damuwa Yaya Mariya tace"dan de Zaliha tadage ne akan auren nan saboda yarinyar nan dangin su ce, amma banda haka ina Jawad ina wata Amal nafadama yarinyar nan kullum tana nan tana raye-raye a tik tok, rawa ta fitsara babu mutunci aciki" Alhaji Mekudi yace"to mubawa Zaliha dama Yaya,idan muka bari akai auren muma kamar munyi mata kara ne duba da yanda ta riqe wannan yaron Yaya kema fa kinsan komai" Ajiyar zuciya ta sauke tace"Allah ya kyauta, ai sai ayi musu auren, amma de zansa aci gaba da sawa yarinyar ido gaskiya" Alhaji Mekudi yayi na'am da shawarar data yanke, daga nan suka futo daga falon nasa zuwa qasa, anan suka tarar da Hajiya Zaliha a zaune afalo, tana ganin futowar su ta kalli Yaya Mariya tace"Yaya ina kwana" Hajiya Mariya taci gaba da tafiya batare da ta tsaya ba ta amsa tace"lafiya" Daga nan tafice tabar gidan. Washegari Fu'ad yadawo,duk da Jawad yasan da batun saka ranar kokadan bai fadawa Fu'ad ba,ayyukan dake kansa gaba daya sunsa ko tunawa da batun auren ba yayi,shikuwa Fu'ad tunda yaji batun saka rana yafara tsare-tsare kamar shine angon, haka yasa Jawad agaba har dakinsa yana tambayar sa wanne irin shagali za'a yi awajan bikin, amma Jawad baice komai ba,saboda yana daukan auren da zaiyi ne amatsayin kawai yayi aure iyayensa su dena yimasa maganar mata,har yau baije inda yarinyar take ba, haka bai buqaci number wayar ta danya kirata su gaisa ba,babu abinda ya sauya daga al'amuran dayake yauda kullum. Alhaji Mekudi yayiwa Fu'ad waya cewa su shirya shida Jawad zasuje wajan rantsar da dan abokinsa anbashi minister. Fu'ad yamiqe yace"yaya Daddy yace mu shirya zamu fita,zanje dakina na shirya I'm waiting for you" Yana fadin haka yafice da sauri,Jawad yayi ajiyar zuciya yatashi yafara shiryawa shima,daya daga cikin shaddodin da Fu'ad yasa aka dinka masa yadauka yasaka,farar shadda ce wadda tayi masa kyau ta kar6i kyakykywar fatar jikinsa,idan wani ya ganshi babu tantama zaice shidin ango ne, yatsaya agaban mirror yana gyara zaman hular tasa, Daddy ne yayi sallama yashigo dakin nasa anan ya ganshi yana fama da gyaran hula yace"mekake jirane Jawad? kawai saka hula ma saiya daukeka wasu mintunan? banason wannan shirman,qananun kaya da zaman qasar waje yasa kana nema ka manta da al'ada" Yafadi hakan yana saka hannunsa yasake gyara masa Zaman hular sannan suka futo. Afalo ya tarar da Fu'ad harya shirya,shima manyan kaya yasaka saide shi bai saka babbar riga ba, Jawad kuwa yasa, sallama suka yiwa Daddy da Mummy sannan suka futo yayinda Hajiya Zaliha tabisu da kallon sha'awa. Suna futowa compound guard suka qaraso da sauri suka rufa musu baya Fu'ad yana tafe yana danna wayarsa, yayinda Jawad yake takunsa na qaqqarfan namiji ingarma maiji da kansa. Malam Manu suka tarar a tsaye ajikin daya daga cikin jerin motocin da'aka shirya domin fita dasu, Jawad yana ganinsa ransa yayi baqiqqirin, suna qarasawa wajan Guard yabude musu bayan motar suka shiga, Malam Manu yashiga yazauna Fu'ad yana gaida shi. Jawad yadaga kansa ya kalli Man Sulaiman yace"Uncle fita ka koma ciki kawai,sai aturo wani driver yakaimu" Malam Manu yayi murmushi yace"Jawad aini nasa kaina zan kaiku,Hajiya ta dade da fadamin kace nadena aikin komai, to zaman danake waje daya yafara damuna, kabarni muje daku inda zakuje, inajin nutsuwa araina duk lokacin dana daukeka dakaina amota nakai ka har inda zakaje" Jawad ya kalleshi da mamaki,menene hadinsa da maganar malam Manu dayake cewa yanajin nutsuwa idan ya kaishi wani waje shida kansa? Saikace irin uba da d'a? to ai ko Daddy bai ta6a cewa yanajin nutsuwa duk lokacin dasukai tafiya tareda shi ba. Ajiyar zuciya yasauke yace" Alright,we can go" Cikin farinciki Malam Manu yaja motar suka fice daga gidan. Sunyi nisa atafiya motocin su suka fara rage gudu suna tafiya ahankali qarshe ma sai suka tsaya saboda yanda garin yacika sakamakon taron yan siyasa,Jawad ya kalli baqin agogon dake daure a farar fatar hannunsa yayi tsaki,Fu'ad ya kalleshi yace"yaya kagaji ne?" "no Fu'ad banason jira ne" Fu'ad yayi murmushi yace"yaya kaida zaka fara zuwa zance ai dole yanzu ka koyi yanda ake jira,wallahi na matsu ranar nan tazo" Man Sulaiman dayake gaban mota hannunsa yana kan sitiyari yayi murmushi yanajin yanda firar yan'uwan take kasancewa,gashi de bawani tsiran shekaru ne a tsakanin suba amma sosai Fu'ad yake girmama yayan nasa. Jawaad ya kalli Fu'ad yace"ko naje wajanta bazan jirata ba"(😳🤭) Fu'ad yayi wani malalacin murmushi yace"yaya kenan,dan de bakaga Amal bane shiyasa kake fadar haka,nina ta6a ganinta sau daya lokacin munje gidan nida Mummy kaikuma baka qasar alokacin,tanada kyau sosai, amma fa gaskiya andade, to kaga sanin dana mata da kenan, zuwa yanzu kuma Yaya zaka ganta? ada canma tun kafin na ganta adanginmu suna cewa duk yanmatan family din su Mummy babu mai kyanta to inaga yanzu? kaga kuwa kaima Yaya idan kaje zance dole zaka jirata kodan kaga wannan kyakykyawar da'ake cewa baya'ita a dangi, wai Yaya saina tsaya Ina siffantama itama? nasan ma ka dade da ganinta awaya yau kwana nawa da saka muku rana?" Jawad yayi ajiyar zuciya yace" ban gantaba,but inaso duk lokacin da zan ganta tota kasance..." saiyayi shiru yana hango Inaas acikin ransa, yatuna kalar farar fatarta sannan yaci gaba da fadin"ta kasance fara"(🤭) Fu'ad ya gyara zama yayi murmushi yana kallon Jawad ganin yau kamar an yiwa yayan nasa baki sai sakin zance yake da alama yafara nisa.(😂) Jawad kuwa baima lura da kallon mamakin da Fu'ad yake masa ba, haka yariga ya manta cewa Malam Manu yana cikin motar, dan haka zuciyarsa daya yasake tafiya duniyar tunanin 'yar me gwanjo, yatuno dogon gashin ta, sannan yasake kallon Fu'ad yace"gashinta ya kasance dogo har gadon baya"(🤭) Fu'ad yanajin haka yazaro idonsa waje yana kallon yayan nasa. Jawad yasake tuno d'an qaramin bakin Inaas sannan yace"kuma bakinta ya kasance d'an qarami, surutun ta yazama yana 'DEBE MIN KEWA akoda yaushe" (Man Sulaiman kanajin d'anka yana sakin zance ba zakayi masa gyaran murya bane? 🤔) (munkusa shan bikin Jawad 💃🏻💃🏻) (Inaas ya kamata fa ki sakarwa Jawaad dinmu mara yayi fitsari 😎😂) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍ [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Masu turomin 500 da masu turomin data duk da kunsan bahaka ne kudin littafin ba, nagode Allah yasaka da Alkhairi,Allah yabar zumunci,wanda suka sai littafina badan ya musu dadi ba saidon qaunar su agareni banida bakin dazan gode muku,koda yaushe bakwa gajiya da zaran nafara littafi zakuce kunaso ku siya,nagode sosai,Amina tana tare daku yanda kuke tare da'ita, nagode🙏 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 ___ Man Sulaiman yanajin duk abinda Jawad yagama fada akan irin matar dayakeso,lokaci daya matarsa Bilkisu tafad'o masa arai,yanda Jawad ya siffanta sai yaji gaba daya kamar siffar Bikisun sa yafad'a,cikin sauri yafaki idon yaran yagoge hawayen daya zubo masa. Fu'ad dayayi tagumi hannu bibbiyu yana sauraren yayan nasa yasaki ajiyar zuciya yace"yaya,duk yanda ake fadar kyan Amal adangi to ko kama qafar wannan batayi ba,yanzu babu irin wannan yarinyar daka siffanta Yaya, babu irinsu ko kad'an " Jawad ya kalleshi ya motsa lips dinsa kamar ba zaice komai ba,sai can kuma yace"akwai" Fu'ad yace"amma larabawan qasar Dubai ko? yaya siffar aljana fa kagama zayyanowa"(😂) Jawad ya motsa lips dinsa kamar zaiyi magana amma baice komai ba, ya lumshe idonsa yatuno Inaas,yasake tuno yanda ake turara mata wannan dogon gashin nata. Yanaji Fu'ad yana cewa"ai Yaya yanda ka lissafo irin yarinyar da kakeson ka aura dinnan da'ace nima zan samu irinta tuni zanyi wuf da'ita" Ya fadi haka yana kallon gefen Jawad sai yaga ashe ma idonsa a rufe yake, kenan shi yagama tashi maganar shikuma yaje yayi tayi ko? Jawad kuwa Cikin ransa yake tunani, baisan menene soyaiya ba,baisani ba wanne alamomi zaiji domin yasan yakamu da son mace kobe kamu da son taba, abinda yasani kawai shine kasuwanci, dashi aka raine shi,tun yana yaro dashi yabude ido. A hankali yabude idonsa ya kalli Fu'ad yace"Fu'ad wanne alamomi mutum yakeji yagane yanason mace?" Fu'ad yayi murmushi ganin yau de yayan nasa da gaske yake, yagyara zamansa sannan yace" wow! Yaya gaskiya you're in love...,nafarko zakaji fad'uwar gaba, yawan tunanin yarinya, kaji komai tayi tana birgeka,kaji zuciyarka kanason kasancewa da'ita,kaji komai nata yana birgeka" Jawad ya jinjina kansa yayi shiru kamar ba zaice komai ba, sai can yace"ok thanks" Malam Manu dake driving duk yana jinsu,yayi tunanin Jawad din zai sake cewa wani abu kuma sai yaji shiru,Jawad kuwa lumshe idonsa yayi yana tunanin maganar dasukai shida Na'im,wannan kalmar da Na'im yafada masa rannan cewa he's in love, gashi yauma ita Fu'ad yafada mata,son qaryata abinda yakeji din yayi, hakan yasa ya girgiza kansa batare daya furta komai ba. Bayan sunje wajan, saida suka gama uzurin su sannan suka juyo gida ba tareda 6ata lokaci ba. Tunda suka dawo gida yashiga dakin karatu yafara aiki,yaduba wannan takarda yaduba waccen,yaduba computer yayi danne-danne,yakoma kan takarda, haka yamaida kansa busy sosai har zuwa dare wajan qarfe goma nadare yanata aiki babu abinda yake tadashi sai sallah, kasancewar yayi busy dayawa hakan yasa da daddare yagaji sosai, yana zaune afalon dakinsa p.a yana fada masa wasu bayanai idan yace a shigar dasu saiya amsa masa da baki, shikuma p.a saiya shigar. Bayan sungama p.a yashiga yanar gizonsa zai duba saqonni,anan yaci karo da saqon wata sabuwar number,kai tsaye yaduba sunan wanda yaturo saqon anan yaci karo da sunan Amal,tun bayan lokacin da'aka sakawa ubangidan nasa rana yake jin sunan Amal din, hakan yasa cikin girmamawa da farinciki ya kalli Jawad yace"yalla6ai madam taturo saqo" Jawad daya jingina ajikin lafiyaiyar kujerar falon ya lumshe idonsa yabude bakinsa kamar baison magana yace" who's she?" P.a yace"Madam Amal" Jawad dayaji sunan saida ya danyi jimmm sannan yayi ajiyar zuciya yace"kuyi magana" Mamaki yakama p.a, yayi wani sararo yana kallonsa,matarda zai aura guda? anya kwa Yalla6ai yanason hadin nan? ganin bashida damar yimasa wannan maganar hakan yasa p.a ya amsa mata sallamar tata sannan yace"yakike?" Daga 6angaren Amal datake kwance male-male akan lafiyaiyan gadonta tace" I'm fine Yaya Jawad,Mummynku tacemin zakazo na shirya zuwanka,but bakazo ba,yakamata kazo Ina missing dinka" tatura masa saqon sannan tasake rungume fillo tana jiran reply dinsa. P.a ya dan kalli Jawad yaga har yanzu idonsa a lumshe,yanaso ya tambaye shi wacce amsa zai bata? zaije dinne kokuma zai bata lokaci ne? ahankali yayi gyaran murya sannan yace"yalla6ai tace tana kewar ka,sannan Hajiya tace zakaje amma baka samu zuwa ba wai yaushe zakaje?" Idonsa har lokacin a lumshe yake,yabude bakinsa ahankali yace"kace mata ( koh?)" (koh?) p.a ya maimaita Kalmar a bakinsa, yanzu duk wannan dogon jawabin datayi amsar itace 'koh?' Babu yanda ya'iya haka ya turawa Amal amsa yace"koh?" Amal tasaki wani irin murmushi sannan tafara typing cikin sauri tabashi amsa tace"ina so kazo naganka,ko abokinka, zamuyi maganar anko" P.a ya kalli Jawad yace"yalla6ai madam tana so taganka,zakuyi maganar anko" Idanun Jawad a lumshe yace"banda lokacin zuwa p.a,nawa take buqata?" P.a ya kalleshi da sauri yaga idonsa a lumshe har yanzu,Amarya guda ace babu lokacin zuwa wajanta?, Anya?🤔 Ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan ya janye idonsa daga kan Jawad yamaida kan wayar hannunsa ya turawa Amal cewa"nawa kike buqata?" Amal taga amsar tayi murmushi tace"million daya" P.a yasake kallon amsar data bashi,ya daga kafadunsa alamun babu damuwa sannan ya kalli Jawad yace"yalla6ai tace 1 million" "kafada mata Mummy zata bata" Cewar Jawaad. P.a yatura mata amsa,bayan tagani tajuya fararan idonta sannan tasake turo masa wani saqon tace"to yaushe zakazo? inaso musha ice-cream tare" P.a yayi murmushi bayan yagama karantawa,da alama madam din tasu batasan waye ogan nasu ba,Ina Yalla6ai Jawad yaga lokacin ire-iren wannan abubuwan? duk da yasan cewa abu ne me mutuqar wahala hakan ta'iyu,baiyi qasa a gwiwa ba ya kalli Jawad yace"yalla6ai Madam tace tana so kusha ice-cream tare" Sai alokacin Jawad yabude idonsa me cikeda gajiya,ya kalli p.a yace"Ina naga lokacin fita shan ice-cream p.a? ko batasan cewa chat dinma badani take yiba? kafada mata banda lokaci,shi kansa chat dinma banda lokacin sa dakai take magana"(🙆🏻‍♀️😳) P.a de yayi shiru yana sauraren Jawad,tayaya zai fada mata haka ai da nauyi, ba zataji dadi ba, danhaka saiya tura mata "lol" Amal ta karanta amsar da'aka bata,tasake turo wani saqon tace"da alamu bazaka samu zuwa ba,baka tambayi photo naba?" P.a ya kalli Jawad yace"yalla6ai Madam tana neman iznin turo photo,taji baka tambaya ba" Ataqaice Jawad yace"taturo" P.a yafada mata,aikuwa dama kamar jira take taturo wasu shedanun pictures,p.a yana bude photunan yazaro ido jikinsa ya dauki rawa ganin duk rabi nonuwanta sun futo waje,hannunsa yafara karkarwa yana qoqarin bawa Jawad wayar, Jawad da baisan halin da p.a yashiga ba ko ajikinsa,p.a yamiqo masa wayar yace"yalla6ai gashi taturo" Jawad bai kar6i wayar ba yace"kaduba photon kagani tana da gashi har gadon baya?" Cikin sauri p.a dayake Allah-Allah Jawad ya kar6i waya ya girgiza kansa yace"a a Yalla6ai gashinta bekai gadon baya ba" Jawad yasake cewa"bakinta dan qarami ne?" Nanma p.a yace"a a Yalla6ai" "Yaya kalar fatar ta?" Cikin sauri p.a yace"fara ce Yalla6ai, ga wayar duba kagani da kanka" Yabashi wayar jikinsa yana rawa cikin sauri yafice daga falon nasa yana mamakin wannan Amarya ta Yalla6ai Jawad,kawai daga cewa turo photo saiki turo irin wannan photon tun kafin ma a daura auren? Jawad ya yashiga yaduba photon nata yaga kwata-kwata batada abubuwan daya lissafa irinna yarinyar nan ta qasar Niger(🤭) Yadauke idonsa daga kan fuskarta yamaida zuwa suturar jikinta anan yaci karo da manya Mayan nashanun ta,saida gabansa yayi wata irin fad'uwa,saboda bayason ganin irin wannan photunan yasan cewa shi mabuqaci ne, yanzu ma dabaya kalla kusan kullum yana fama da shan magani inaga kuma yana ganin irinsu? Kai tsaye yayi mata reply yace"thanks" Sannan yagoge chatting din gaba daya ya lumshe idonsa yafara tunani,dama haka ake soyaiyar? babu wani nishadi da mutum yakeji? ajiyar zuciya yasauke,sannan yatafi tunanin inda zuciyarsa tafi karkata wato wajan yarinyar nan ta qasar Niger. Yadade yana tunanin Inaas,lokaci daya maganar Fu'ad tafad'o masa,lokacin dayake cemasa ( duk yarinyar dakake so zakaji kana yawan tunaninta...) Cikin sauri ya girgiza kansa,a fili yace"kai bahaka bane..." *** *** *** Niger Republic Tana zaune tazubawa kayan gwanjon dayake gabanta ido,gidan tela zata kai za'a rage wand'anda Bilkisu take d'ad'd'aga wa tana nuna mata"Kinga wannan kar arage shi dayawa,manya zasu iya sakawa" tasake d'aga wasu kayan tana nuna mata tace"wannan kuma kinga ai madedeciya ce,sai arage ta sosai masu yara zasu siya" Inaas tagama jin bayanin nata, tayi ajiyar zuciya tace"Ammiy wai dan Allah ahaka zamu qare ne? mu kenan kullum tallar gwanjo nida nakeso musamu kudi dayawa a sauya wannan kayan dakin namu,da wannan cinikin gwanjon tayaya zamu samu kudin?" Bilkisu tayi ajiyar zuciya tace"Inaas, nita kayan dakinki nakeyi ba nawa ba,yanzu ni in sauya kayan daki ince nayi me? nida ba miji ba inani Ina wani sauya kayan daki,kayan dakinki ne agabana nida mahaifinki, musamu kafin lokacin bikin kema amiki kaya me tsadar gaske,d'an aikin kamfanin dakika fara muna murna shima yanzu babu,da ina tunanin inje ni dake da babanki mubawa manajan kamfanin haquri ko Allah zaisa su maida ke, to shugaban kamfanin yazo har gida kingama yimasa zagin duniya,kinga kuwa Ina zamu samu gwarin gwiwar zuwa basu haquri?,ko munje musu kamfani idan yaji labari zai musu waya yace karsu maidake,inda ace baki cimasa mutunci bane ma toda sauqi,amma lokacin dazai tafi ma inaji kina cewa dole ne saina rakashi? kuma shima yanajin ki sarai,shiyasa nake hanaki wannan shegen surutun naki, dan wata rana sai kinja anzo har gida an kamamu" Inaas tahade girar sama data qasa,dan qaramin bakin nan nata tacunoshi gaba,batace komai ba ta dauki qullin kayan gwanjon nasu tadora akanta sannan tafice daga gidan fiya-fiya cikin sauri kamar zata tashi sama. *** *** *** Abuja Nigeria Washegari sassafe yatashi,ya shirya tsaf cikin baqar riga, baqin wando,fuskarsa tana sanye da glass jan duhu kamar kullum, yayi kyau sosai sai zuba uban qamshi yake gefe guda kuma farar fatarsa tafuto sosai acikin kayan. Wayoyi ne a hannunsa guda biyu yana tahowa main falon gidan nasu yana magana qasa-qasa,gakuma takardu yana dubawa gaba daya yaraba hankalinsa biyu, ga waya ga duba takardu,atsakiyar falon yatsaya yana magana tareda cigaba da duba takardun,Mummy tataso hannunta daukeda cup din tea tanufeshi tana bashi tea din da spoon, babu musu yake bude bakinsa take bashi tea din saide saiya dan rissina mata sannan take bashi kasancewar yafita tsawo. Wayar yakashe sannan suka zauna akan kujera taci gaba da bashi tea din,Daddy dayake zaune a dining yana breakfast ya kalleshi dakyau yace"idan kunje gonakin nan fa kakula dakyau" Cikin nutsuwa yad'ago kyawawan idonsa ya kalli Daddy sannan yace"okay Daddy" Daga haka yamiqe zai fice, Daddy ya kalleshi yace"yazaka fita bayan ko tea din baka gama shaba? Koma ka zauna,ayyukan nan sunada yawa Jawad bazasu qare ba,wannan dalilin ne yasa nakeso ka ajiye iyali,inda kayi auren ka toda tun aciki matarka zata baka breakfast bazata yarda ka futo bakaci komai ba" Jawad yakoma ya zauna tareda murmushi kad'an. Mummy tajuya ta kalli Daddy tace"Alhaji ai komai yazo qarshe,kwana nawane yarage ayi masa auren? ni munyi magana da Amal dinma, tacemin tayiwa Jawad maganar kudin ankon biki suna buqatar million goma sha biyar itada qawayenta" Jawad yayi jimmm! yana tunani,million goma sha biyar kuma? just anko kawai million goma sha biyar har mezasu saka itada qawayen nata? idan bai manta ba ai million daya yarinyar tace tana buqata,kamar haka p.a dinsa yafada masa,kuma p.a yasan aikinsa, bazai fadi ba daidai ba. Daddy ya kalli Jawad ko zaiyi magana dangane da kudin da Hajiya Zaliha tafada,but yaga Jawad din yayi shiru kamar yana nazari,to ganin yadade baiyi aure ba, kuma Jawad yasan meyake akan kashe-kashen kudi hakan yasa yayi shiru, duba da cewa Hajiya Zalihan tace ita yarinyar sunyi magana da Jawad din. Jawad yadawo daga tunani kafin yayi magana wayar gefensa tafara qara,Mummy tasa hannu ta kashe wayar, sannan tace"lokacin cin abincinka ne yanzu" Ko minti uku ba'a yi ba,p.a yashigo dakin bayan yagaida Mummy da Daddy ya rissina yabawa Jawad waya yace"yalla6ai ana kira" Mummy tadafe goshin ta da hannunta tana girgiza kai alamun baza'a barshi yayi breakfast din bade. Jawad yayi d'an qaramin murmushi yace"Mummy kibarshi naqoshi" Yajuya ya kalli Daddy yace"Daddy saina dawo" Daddy yace"Allah yadawo daku lafiya Jawad,kafin kasa musu hannu ka tabbatar idan kabasu kudin to noman zasuyi,wasu idan sukaga anbasu kudin taki saisu kashe kudin suqi yin noman" Cikin nutsuwa ya amsa masa sannan yayiwa Mummy bye bye suka fice daga falon,zasu wuce wajan manoman dasukazo kwanaki ganinsa, akan aron kudi dazasu kar6a awajansa zasu sai takin gona, idan sunyi noman zasu dawo masa da kudin takin. *** *** *** Niger Republic Da daddare suna kallo wani yaro yashigo kiran Inaas,babu musu tamiqe ta dauki mayafin abayar jikinta baqa tayafa sannan ta fice,kamar yanda ta tsammata yauma Is'haq dinne,yau bata koma da wuri ba, sun dad'e suna zancen su sannan tayi masa sallama yadauki kyautar kudi yabata,da farko qin kar6a tayi saida yadage sannan ta kar6a takoma gida. Kudin daya batan ta ajiye agaban Bilkisu sannan tace"Ammiy gashinan, Is'haq ne yabani" Bilkisu ta kalli kudin tayi ajiyar zuciya sannan tace"Allah yabaki miji nagari"(😂🙆🏻‍♀️🤭) Farouq dake zaune yayi murmushi tareda girgiza kansa,da alama de har yanzu Is'haq begama samun kar6uwa awajan Bilkisu ba. Har suka gama kallon suka kwanta Bilkisu bata daina tunanin wannan saurayi na Inaas ba,yanzu shekarar Inaas goma sha takwas,tunda basuda halin dazasu tura ta makaranta to gara tun kafin zaman gidan nata yayi yawa ita ba aure ba ita ba karatun ba gara kawai ayi mata aure,kullum sake zama budurwa take,wannan yaron Is'haq yadage,idan kuma yace zai futo ayi aure tasan cewa Farouq bashi ita zaiyi,harga Allah ita kuma batason Inaas dinta tayi irin rayuwar datayi shekaru talatin da bakwai baya. Bata samu ta runtsa ba har tsakiyar dare tana tunane-tunane, daga qarshe tatashi Inaas suka fara gabatar da nafilfili, bayan sun idar haka Bilkisu tadaga hannunta sama tana Addu'ar data saba wato Allah ya bayyana mata d'anta,sannan Allah yabawa Inaas miji nagari (😂) *** *** *** Abuja Nigeria Bikin Jawad yanata matsowa,gida anata murna musanman Mummy da Fu'ad. A6angaren ango kuwa kana ganinsa kasan cewa auren baya gabansa,uzurin gabansa kawai yake,Amarya bata sake nemansa ba, shima bai nemeta ba, haka Mummy ma bata sake yimasa maganar taba, tun lokacin datayi maganar zata bawa yarinyar million goma sha biyar tun daga lokacin babu wanda yasake yimasa maganar ta,har yanzu bata kirashi tace anbata kudin ba, bata kirashi tafada masa cewa million dayan data fara tambaya ta yimata kad'an ba shiyasa tanemi qari, shiruuu babu wata magana. Yauda safe yana gama motsa jiki yazauna awajan yana qarewa gidan nasu kallo yanda sojoji suke shawaginsu a compound din gidan,p.a yana tsaye daga bayansa yana duba wasu file. Fu'ad yazo wajan ya ajiye wa yayan nasa Coffee me zafi akusa da computer sa datake ajiye awajan, sannan yajuya yafice daga wajan. Jawad ya kalli coffee din yanaso yasha amma kuma zuciyarsa tana tunzurashi akan yayi abinda take so. Ajiyar zuciya yayi sannan ya kalli p.a yace" p.a,kiramin manajan kamfanin Mekudi oil na qasar Niger" Cikin sauri p.a yace"ok Yalla6ai" Sannan yasaka hannunsa akan iPad din hannunsa cikin qwarewa yakamo number wayar manaja sannan ya doka masa kira, saida manager ya dauka sannan yabawa Jawad wayar yace"gashi Yalla6ai" Jawad ya kar6i wayar sannan yace"manager" Cikin sauri manager yace"na'am Yalla6ai,barka da wannan lokaci, Allah yasa de ba laifi mukayi ba" Jawad ya girgiza kansa kamar manager yana kallonsa sannan yace"katuro min jadawalin sunayen ma'aikatan ku tareda bayanan su yanzu yanzu" Cikin sauri manager yace"angama ranka yadade" Jawad yabawa p.a waya sannan yaja computer gabansa yashiga cikin Email dinsa yana sauraron manager, ba'a dauki tsawon lokaci ba kuwa sai gashi sun shigo, cikin sauri yafara dubawa har hakan yabawa p.a mamaki,tsaf ya dinga bin d'an qaramin photon dayake kan bayanan kowa, amma baiga nata photon ba,ko tsayawa ya karanta sunayen ma'aikatan ba yayi, kawai Iya photon yake dubawa, cikin 6acin rai yarufe computer yasaki tsaki tareda lumshe idonsa yana shafa goshinsa da hannunsa alamun damuwa. Cikin wata irin murya ya kwadawa p.a kira kamar p.a din baya gefensa. P.a yace"na'am Yalla6ai" "asake kiramin manager" Cikin sauri p.a yasake dokawa manager kira,manager yana ganin wani kiran jikinsa yayi sanyi, yayi tunanin wani za'a sake kora acikin su, ahankali yadauki wayar, p.a yabawa Jawad waya,ahankali Jawad yace"wannan sunayen ka tabbatar iyakar ma'aikatan dakuke aiki tare dasu kenan?" Manager yace"eh gaba daya ne Yalla6ai,kowa da kowa yana cikin list din dana turoma,saide wanda aka kora daga kamfani ne kawai babu sunayen su" Cikin masifa dawani irin 6acin rai Jawad yace"A a, to saboda me babu bayanan wanda aka kora? idan kuma suka aikata laifi awani wajan da sunan kamfanin mufa?" Cikin sauri manager yace"ayi haquri Yalla6ai bayanansu yana nan bari aturo maka" Batare dayace komai ba yakashe wayar tareda dungurar da'ita ya lumshe idonsa,p.a ya kalleshi yarasa dalilin damuwar ogan nasa kawai saboda sunayen ma'aikata,yasaka hannu ya dauki wayar adede lokacin kiran manager yashigo, ya shaidawa p.a cewa yaturo saqon. P.a ya kalleshi cikin ladabi yace"yalla6ai anturo saqon Cikin sauri Jawad yabude idonsa sannan yabude computer cikin wata irin qwarewa yafara shafata yana ganin bayanan ma'aikatan d'aya bayan d'aya,har saida yaci karo da nata bayanan,gabansa yayi wata irin faduwa, cikin sauri yashiga yayi zooming din photon ta,kyakykywar fuskarta ta bayyana qarara,yazubawa fuskar tata ido yana kallo yasaki ajiyar zuciya yanajin wani irin nishadi aransa. P.a dayake tsaye abayansa yasaki wani irin murmushi bayan yaga photon yarinyar da Yalla6ai Jawad din yazubawa ido yana kallo,sai alokacin yagano wayo da dabarar Yalla6ai Jawad din. Shikuwa Jawad saida yagama kallonta tsaf, sannan yasaka hannunsa akan torch screen din computer yadan maida photon nata baya, sannan yaduba qasan photon inda sunanta yake,cikin ransa ya maimaita kalmar sunan nata INAAS OMAR FAROUQ,yasaki wata irin ajiyar zuciya a fili, sannan yasake zooming photon yaci gaba da aikin kallonta. Fu'ad yadawo wajan cikin hanzari hannunsa riqeda waya yace"yaya!" Shiru Jawad bai amsa ba,p.a ya kalleshi yace" Yalla6ai ana magana" Amma kwata-kwata Jawad baisan sunayi ba, gaba daya daga tunanin sa har zuciyarsa sunakan photon Inaas. Fu'ad ya qaraso yata6a kafadarsa yace"yaya!!" Sai alokacin Jawad yayi firgigit yazabura yadawo daga duniyar tunanin daya tafi,cikin sauri ya rufe computer tasa,dariya tana so takama p.a amma haka yayi fuska ya maze. Fu'ad ya zauna kusada Jawad yace"yaya,munyi magana da mawaqin dazai yi muku waqar bikinku, yace yaturo ma wayar kaduba kaji idan tayi shikkenan, idan batayi ba sai asake wata, amma nafada masa idan zaizo ya gabatar da waqar kada yazo da mutanan dasuka wuce biyar, saboda a America Mummy takeso ayi dinner,kuma awajan dinner za'a saka waqar,already an qayyade adadin mutanan da zasuje" Jawad yad'aga kafadunsa alamun rashin damuwa yace"inde kaji waqar tayi ma is okay Fu'ad" Fu'ad yace"okay yaya" Sannan yajuya yatafi, bayan Fu'ad yatafi Jawad yamiqe tsaye ya kalli p.a yace"p.a, akiramin manager" P.a yayi sauri yakira masa manager,bayan manager yadauka Jawad yakirashi da asalin sunansa yace"Ilyasu" Manager yace"na'am Yalla6ai" Jawad yace"yarinyar nan da'aka kora yakamata tadawo bakin aiki"(🤭) Ilyasu manager yace"to Yalla6ai angama" Jawad yayi shiru nawasu second,shibe kashe wayar ba,shi beyi magana ba, haka shima manager daga nasa 6angaren bashida ikon dazai Iya kashewa Yalla6ai Jawad waya,haka yatsaya qam da waya a kunne. Saida yadauki minti d'aya, sannan yasake cewa "ilyasu" da girmamawa manager yace"na'am Yalla6ai" Jawad yace"ba aikinta nada zata koma ba,Ina nufin abata aiki mekyau,babban office inda yadace". (🙆🏻‍♀️🤭) (manager yau kaga ta kanka kaima😂irin wannan kira haka) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 17&18 Lokaci d'aya ilyasu manager yagano shi,yayi murmushi ya jinjina kansa yana tunani tofa shi da alama lokacin qarin girman sa yazo,to amma lokacin daya koreta daga aiki aibata zo kamfanin ba, a'ina yaganta? a'ina suka had'u? to koma de menene yakamata ya dinga shigewa yarinyar nan idan tadawo bakin aiki ko Allah zaisa shima asan dashi(🤭) cikin ladabi yace"to Yalla6ai,yanzu-yanzu za'a tura mata letter tadawo bakin aikinta" Jawad baice komai ba yakashe wayar yana sakin wata irin ajiyar zuciya,sai yaji ransa yayi sakayau kamar yasauke wani nauyi daga kansa,daga nan yayi gaba domin zuwa daki yayi wanka ya shirya kafin lokacin yin break fast dinsa yayi. P.a yayi murmushi ganin tabbas da gaske Yalla6ai Jawad yakamu da soyaiya,ko banza shima zai d'an huta da wannan aikin nasu dasuke fama dare da rana babu hutu inda ace sunada iyali to wataran za'a ce adan huta saboda a kula da iyali,ya sunkuya yadauki computer Jawad din sannan ya biyo bayansa. *** *** *** Niger Republic Qarfe tara na safe,suka jiyo ana doka sallama a qofar gidansu,Bilkisu datake gyaran waken awara tad'aga murya tace"Inaas zoki duba ana sallama" Inaas tafuto daga daki tayafa mayafi ta leqa qofar gidan,wani matashi tagani a tsaye ya jingina da motarsa, ta kalleshi tace"kaine kake sallama?" Yace" eh, dama daga kamfanin Mekudi Oil ne,akace nakawo miki wannan letter,koba kece Madam Inaas ba?" Inaas ta kalleshi dakyau tace"nice Inaas de,amma ba madam ba, muga wasiqar" (😂) Yabata takardar hannunsa wanda manager da kansa yazauna ya rubuta yakuma gargad'eshi akan ya girmamata idan yakai mata,sannan yayi magana da'ita cikin ladabi domin itadin ba qaramar mace bace yanzu. takardar tagama karantawa tsaf, sannan ta kwashe dawata irin dariya tace"waini za'a yaudara" ta kalleshi tareda bashi takardar tace"kakoma ka cewa wanda yabaka wannan saqon inada hankali,baza'a min shigo-shigo ba zurfi ba" Dan aiken yatsaya saroro yana kallonta,ita kuwa bata lura da kallon dayake mataba tasake yin wata dariya tace"tabdi,saikace wata marar wayo ni zan yarda inkai kaina inda za'a kashe ni" Mekawo saqo yayi ajiyar zuciya yace"Madam manager nefa yabani saqon da kansa,kuma yace nabaki hannu da hannu,saboda haka saqo yazo hannun ki,ni kinga tafiya ta nabarki lafiya" Yafadi haka yana qoqarin juyawa zai shiga mota,Inaas tace"tsaya tsaya ka kaimasa takardar sa" Bilkisu da taji shirun yayi yawa taqaraso bakin qofar gidan tace"meyake faruwa ne?" Yajuyo ya kalli Bilkisu ya gaidata sannan yace"manager ne yabani saqo nakawo mata,shine tace lalle saina kar6a na maida masa,nikuma bazan Iya maida masa ba" Bilkisu tace"jeka mungode" Babu musu yashiga motarsa yatafi, tajuya ta kalli Inaas tace"takardar menene?" Inaas tabata takardar tace"duba kigani Ammiy waini za'a rainawa hankali saikace marar wayo" Bilkisu tace"takarda duk turanci mezan fahimta aciki? kifadamin ta mecece?" Inaas tace"wai turomin sukai in koma bakin aikina,kuma Ammiy kingani fa harda qarin matsayi tsabar yaudara,sarai nasan cewa wannan Jawad din dayazo rannan shine yayi wannan aikin,ai yajini lokacin danake cimasa mutunci,so yake na koma inyaso idan naje su had'u sukamani sumin shegen duka,ni kuwa babu inda zanje Ammiy" Bilkisu ta kar6i takardar ta kalla kamar tana fahimtar abinda aka rubuta sannan tadago kanta ta kalli Inaas tace"kin tabbatar abinda yake cikin takardar kenan aiki suka maida ke da gaske?" Inaas tace"emana,gashinan harda haquri suka bani akan korar dasuka min" Bilkisu taja hannunta suka dawo cikin gida suka zauna sannan tace"toke wannan ai abun farinciki ne Inaas,na tabbatar yaron nan Jawad ba zaice ki koma aiki kawai danya kamaki ya dakeki ba,idan yayi niyyar dukanki ai yasan gidanku,har nan zaizo yakama ki yadaka,yaron nan yanada nutsuwa Inaas, kuma yanada hankali,sannan yasan Alkhairi, da alama shimfidar fuskar dana masa ne yasa yace kidawo bakin aiki,ai kinga amfanin mutunta d'an Adam ko?" Inaas tayi shiru tana nazari,tayi ajiyar zuciya tace"to Ammiy ai nayi tunani dukana zaisa ayi,saboda ranar nan har cemasa nayi yana kama da 'yan dambe,yace zai dakeni nace tome yake jira yadaken mana" Bilkisu tazaro idonta waje tace"wai keda shidin duk kukai hakan?"(😳) Inaas tafara zare ido alamun tsoro kana ganinta kasan a tsorace take,tace" eh wallahi Ammiy,kuma bakiga dantsan hannun saba gabjeje lokacin daya fara cire suit dinsa ya'iyo kaina, shiyasa nace miki da biyu aka turomin wasiqar nan, ni nasan mena aikata" Bilkisu ta jinjina kanta sannan tace"kema na hanaki surutun nan naki kinqi ji,dan Allah kidinga sawa bakinki linzami,ki shirya gobe kije aikinki, amma de ki kasance a ankare,dakinga wata alama ta duka toki fece,karki tsaya ata6a lafiyar ki"(😂) Inaas ta jingina kanta alamun amsawa sannan tace"to Ammiy,aikuwa kinban dabara takalmi zansa marar tudu, zaifi dad'in gudu" Suna cikin wannan zance Abban Inaas yadawo,Bilkisu ta zayyane masa komai shima yasake bata qwarin gwiwar zuwa kamfanin. *** *** *** Abuja Nigeria Hajiya Zaliha tasake gyara daurin da kwalin kanta na gogaggun matan manya, yatsun hannun nan nata duk zoben gold,Jawad yana kwance a kujera yana kallon labarai, yayinda Fu'ad yake danna waya agefe,Daddy kuma yana gefen Hajiya Zaliha. Biron hannun ta ta ajiye sannan ta kalli Daddy yace"Alhaji munyi magana da mahaifin Amal dakuma ita yarinyar,tace tana buqatar million goma na gyaran jiki,sannan zasuyi ladies party itada qawayenta gaba daya wajan partyn da abunda za'a ci asha zasu kashe million dari,sai bridal shower zasu kashe million hamsin,sannan tanaso ayi wasan polo zasuje su kalla itada Jawad din,shima suna buqatar kudi,sai maganar kayan lefe" Tayi wani miskilin murmushi Sannan taci gaba da fadin"wannan kam bansan nawa zamu kashe ba" Daddy yasha ruwan dake gabansa sannan yace"duk kudin dakuke buqata ki dauka kiyi uzurin ki dashi kawai,auren Jawad ne, dole zamu kashe kudi,yanzu ne fa zamu aurar da yaro muma, ranar damuke jira ce tazo, dole za'a yi abinda akeso, sonake duk qasar nan dama sauran qasashen duniya su san da wannan aure" Fu'ad ya jinjina kansa yayi murmushi hankalinsa yana kan waya. Shikuwa Jawad fuskarsa a cunkushe take, kokadan babu walwala kamar de yanda take kullum,ana magana akan aurensa amma kamar ana magana akan mutuwar sa. *** *** *** Niger Republic "Farouq zuba cikon daga nan,wajan zaifi kyau sosai" cewar Ammiy. Farouq yasake debo wasu duwatsun yazuba a'inda ta nuna masa,yasake kallon tsakar gidan nasu koda wani wajan dayake buqatar ayi masa ciko, adede lokacin Inaas tadawo daga wajan aiki,Bilkisu tana ganinta ta qarasa wajanta tana kallon jikinta tareda fadin"babu wanda yata6a ki deko?" Inaas tayi murmushi wanda yasake qara mata kyau sannan tace"Babu abinda akamin Ammiy,bakiga yanda ake ji dani ba,manager da kansa yaketa nan-nan dani,bansan dalili ba sai wani girmama ni yake, yanuna min sabon office dina,amma aikin da wahala saida yasake koyamin yanda zan dinga yi,Infada miki Ammiy office din ga esi,harda wani dan qaramin fridge aciki, ga ruwa da lemuka aciki,kingama nataho miki da wasu lemukan ma kema kisha,gobe ma idan na koma zan sake d'ebo miki wasu"(🙆🏻‍♀️) Bilkisu tafara tafa hannu tana fadin"yanzu Inaas lemukan office din kika d'ebo?,Ina kikaga ana haka? oh ni Bilki me gwanjo yau naga takaina" Inaas taturo bakinta gaba cikin shagwa6a tace"to Ammiy sai insha lemo kekuma inbarki baki shaba? nide gashinan ku shanye keda Abba" Tafadi haka tareda ajiye musu lemukan sannan tawuce ciki. *** *** *** Abuja Nigeria Tunda yaga anata shirye shiryen biki yaji hankalinsa yatashi,ga Na'im dayake ta damunsa akan abubuwan dazasu tsara,hakan yasa yabar Abuja yakoma Lagos yake harkokin sa,bai tashi shirin dawowa daga Abuja ba saida biki yarage saura kwana bakwai shima saboda Mummy tana ta kiransa ne,saide wani abu guda daya dayake bashi mamaki shine yanda yarinyar har yanzu bata sake yimasa magana ba duk da bikin yazo kusa,to saiyayi tunanin tunda auren had'i ne may be itama bataso,hakan yasa yashareta,bazai takura mata ba kokadan,idan zaman auren ma taji zata takura zai iya sauwaqe mata. Cikin nutsuwa suke tafiya yana zaune abayan mota shi kadai, yadora computer akan cinyarsa yana danne-danne, p.a da driver suna gidan gaba, wayarsa ce tayi qara p.a yajuyo yabashi, bayan ya dauka daga can 6angaren akace"Yalla6ai dama maganar takardun nan ne dakace yau mu tuna maka idan kagama dubawa" Cikin nutsuwa murya qasa-qasa yace"nagama dubawa zaku Iya zuwa ku kar6a,na shigo Abujan ma" Cikin girmamawa suka kashe wayar sannan shima ya ajiye tasa agefe yaci gaba da shafa computer sa. Suna dawowa gida yaga babu kowa afalo,yayi mamaki sosai ganin falon nasu baya rabo da mutane,cikin sauri yawuce dakinsa ya watsa ruwa a gurguje yadawo falon yazauna yana ganin labarai inda ake sanarwa cewa ga jihohin dazasu Iya samun ambaliyar ruwa idan damuna tazo,remote yadauka ya canza channel sannan yasaka hannunsa yadauki inab guda daya yasaka a bakinsa, yajuya gefensa yaji de gidan shiru har yanzu babu wanda ya futo, cikin sauri yatashi yanufi dakin Mummy yaga wayam babu kowa, yajuya yashiga dakin Fu'ad nanma baya nan, hakan yasa kai tsaye yawuce dakin Daddy, yana shiga yaga Fu'ad agefe yayi tagumi, yayinda Mummy take rusgar kuka tana share hawaye da dan kwalin ta,Daddy kuwa yana zagaya falon nasa fuskarsa cikeda damuwa. Lokaci d'aya jikin Jawad yayi sanyi ya qaraso cikin falon yanufi Mummy yana fadin"mummy meyafaru kike kuka? waye yata6a ki?" Daddy yajuyo ya kalli Jawad tausayin sa ya kamashi,gaba daya yaron tausayi yake bashi,nafarko har zuwa wannan lokacin baisan asalin suwaye iyayensa ba,yanzu ma gawata qaddarar tasake samunsa,ganin Hajiya Zaliha tana kuka takasa jurewa tayi magana hakan yasa Daddy yadaure yace"Jawad saide kayi haquri Allah yayiwa Amal rasuwa yanzu,gaba dayanmu mun rasa ta'ina zamu iya kiranka muyi maka wannan maganar, ga biki ya matso,ina fatan zaka kar6i qaddara da hannu biyu" Jawad yadago ya kalli Daddy cikin sanyin jiki,lokaci daya chat dinsu yafado masa,sai yaji bai kyauta mataba datace suje susha ice-cream yanuna baida lokaci,yana qin aure ashe ashe yarinyar ma ba zataga bikin ba,toko alamun mutuwar tafara ji shiyasa bata sake nemansa ba? Ahankali yafurta kalmar "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" Sannan yazauna kusada Mummy ya rungume ta yana bubbuga bayanta alamun lallashi saboda yasan cewa Mummy tafi kowa qwallafa rai akan auren nan,kuma dole zataji mutuwar saboda yanda ta shaqu da Uncle Bature mahaifin Amal din, cikin sigar lallashi yace"Mummy kiyi haquri kidena kuka,muma jiran tamu mutuwar muke, kiyi haquri" Hajiya Zaliha tasa hannu tasake rungume Jawad tana kuka tace"kaima kayi haquri Jawad,kai akaiwa rashi kayi haquri Jawad" Jawad baice komai ba sai kansa daya jinjina kawai. Hajiya Zaliha tadauki wayarta takira Yaya Mariya yayar Daddy, bugu daya Yaya Mariya ta dauka, Hajiya Zaliha tace"Yaya idan kingama Ina jiranki kizo muje gidan suturar nan" Yaya Mariya tace"innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ni Mariya waye yarasu?" Hajiya Zaliha ta share hawayen idonta tace"Amal ta rigamu gidan gaskiya Yaya" Cikin sauri Yaya Mariya tace"ke dakata Zaliha!!,wacce Amal kike magana akai?, tarigamu gidan gaskiya kamar Yaya? ba dazu-dazu aka nunamin Amal din tana live video na tik-tok ba? kode wata Amal din kike nufi?" Hajiya Zaliha tace"wallahi Yaya da gaske nake,Amal ta mutu,yanzun nan Yaya Bature yakirani yake sanar dani hakan" Yaya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"shi Baturen ne yace 'yar tasa tamutu? nadade da sawa a dinga bimin diddigin yarinyar fa, kuma tunda akasa ranar aurenta da Jawad kullum saitayi video na fitsara ta dora a shafinta na tiktok,ga wasu filla-fillan motoci da yarinyar take hawa kullum da irin motar dazata sake posting tana yawo da qawaye a mota saikace yar gidan shugaban qasa,zanje har gidan Baturen yanzu inje Inga gawar Amal din da idona" Tana fadin haka ta kashe waya. Lokaci d'aya gaban Mummy yayi wata irjn bugawa,kanta ya Sara, amma babu wanda ya lura da hakan. Jawad ya sunkuyar da kansa qasa bayan dukansu sungama jin komai kasancewar babbar waya babu rufin asiri, kwata-kwata yarasa meyasa Yaya Mariya take haka,mutuwa aita wuce wasa,ya za'ai mutum bemutu ba kuma mahaifinsa da kansa yace ya mutu?. Daddy yace"Allah yarufa asiri" Ya kallesu gaba dayansu yace"muje falo sai nayiwa Man Sulaiman magana shida maqota su shirya suzo muwuce gidan suturar gaba daya, karmu rasa jana'iza. Babu musu dukansu suka nufo Babban falon qasa. **** Kai tsaye Hajiya Mariya ta yiwa Sojan dayake mata aiki waya,shine tasa yake kula da duk wani shige da ficen Amal,haka yayi following nata ako wanne kafar sada zumunta datake amfani, duk wani abu datake posting yana gani, shikuma idan yagani zai turawa Yaya Mariya,tunda akasa ranar auren hankalin ta bai kwanta da yarinyar ba,saboda ko a vedio wani lokacin duk da maza takeyi tana ganin hakan kamar wayewa ce, abun yana yiwa Yaya Mariya ciwo, Jawad nutsatstse, shiba magana ba,shiba hayaniya ba,idan aka bashi yarinyar kamar da cutarwa aciki, to amma ganin yarinyar yar gidan yayan Zaliha ce kuma Daddy yabata haquri, hakan yasa ta danne komai tazuba musu ido. Wayarsa tana shiga yadauka, Hajiya Zaliha tace"Yaya batun aikin dana baka?" Cikin ladabi yace" Hajiya anakan yi, yanzu haka ma Ina tareda ita,taje super market" Yaya Mariya tasaki wata irin ajiyar zuciya tace"ka tabbatar Amal din kagani da idonka?" Yace" yes Ma" Cikin 6acin rai tace"wanka mata mari kasakota amota kutaho gidan ubanta,nima ganinan zuwa" Babu musu wannan soja yanufi Amal gadan-gadan,yana zuwa kawai gefen rigar sa yadaga yanuna mata wata bindiga sannan yasauke rigar sa yayi mata nuni da mota, babu musu Amal tashige mota shima yashiga yazauna ya futo da bindiga yana shafata yadaka mata tsawa yace"muje gida" Cikin sauri Amal tata da mota jikinta yana rawa suka nufi gidansu. Suna zuwa bakin get suka tarar da Hajiya Mariya tana tsaye tana jiran su sai kaikawo take, tana ganin su ko jira batayi sun bude motar ba tabude dakanta takamo hannun Amal tajata suka shiga gidan,babu kowa agidan sai yan tsirarun mutane da basu fi mutum goma ba, suma duk yan'uwansa ne dangin su Hajiya Zaliha babu maqota babu yan'unguwa tabbacin abun dama shiryaiye ne. Kota kansu batabiba taja Amal sukayi ciki,saida ta dire Amal a falonsu sannan ta daga murya tace"Bature!!!" Cikin sauri Uncle Bature da matarsa suka futo jin kiran kamar bana hankali bane,yana ganin Amal yatsaya yayi turus, yarinyar daya turata gidan abokinsa yace karta kuskura tafuto waje menene yakaita futowa har wannan masifaffiyar matar taganta? Yaya Mariya ta nuna Uncle Bature da hannu tace"kaikam Bature anyi girman banza wallahi,karasa wacce zaka ha'inta sai qanwar ka, toka sani kanka kayiwa, dama banda Zaliha ta dage me Jawad zaiyi da wata Amal,inde Amal ce gatanan kadena d'ora mata mutuwa kwanan ta bai qare ba,gata nan saika jiqata kasha,duk kud'ad'en da'aka turo maka kuma kayi gaggawar maida su" Alhaji Bature dayaga bashida wata mafita asirinsa yariga yagama tonuwa saiya fara kuskurin kunya da fadan qarfin hali yace"ke dakata Mariya,yazakizo har cikin gidana kina fadamin maganar da kikaga dama? ko cewa nayi Amal tamutu ta rayo babu abinda yamiki zafi yarinya de 'yata ce,kuma dakike maganar Zaliha Zaliha aida ita muka shirya komai, dan haka idan kin shirya tonamin asiri ne toki had'a da matar qaninki ki tona mana asiri gaba d'aya,Amal kuma dama banda niyyar bata DAN TSUNTUWA" Wannan furucin na Alhaji Bature yadaki Yaya Mariya,har saida taji wani jiri-jiri yana dibarta, numfashinta yafara yin sama, amma tsabar masifar datakeji haka ta kalleshi tace"okay haka kace ko? to gaba dayanku daga kai har Zalihan na isheku riga da wando,matsiyata dangin maciya amana, kuma insha Allahu saikunga irin matarda Jawad zai aura,saiya auri wacce ta ninka Amal sau dubu" Tana fadin haka tajuya tafice tabar gidan,Sojan daya biyo Amal suka dawo gida tabawa key din motar ta tace"kaini chemist mafi kusa" Cikin sauri ya kar6i key din yashiga yaja motar aguje suka nemi chemist, yana tsayawa tafuto tashiga ta kar6i maganin hawan jini tasha,saboda tabar nata agida, kuma tabbas wannan mummunan labarin da taji tasan cewa zai Iya tada mata hawan jinin ta, batafi minti biyar ba tafuto tace masa yakaita gidan Aliyu Mekudi. Ahanya kawai lumshe idonta tayi tana maimaita hailala aranta har sukazo gidan Alhaji Mekudi,anan taga ana sake goge motoci da alama gidan rasuwar qaryar zasuje. Tana qarasawa falo kuwa taga Daddy da Fu'ad da Jawad duk sun gama shiryawa zasu tafi. ta kalli Daddy tace"Aliyu Ina zuwa?" Yanda yaji muryar ta tayi magana hakan ne yasake tabbatar masa da cewa ba lafiya ba, yace"gidan rasuwar zamuje Yaya" Yaya Mariya ta girgiza kanta tace"bade gidan rasuwa ba,saide kace gidan tantirai kokuma kace gidan dangin tantirai"(🙆🏻‍♀️) Fu'ad da Jawad suka hada ido kowa fuskarsa daukeda tsananin damuwa. Yaya Mariya ta kalli Daddy tace"yarinya tana nan da ranta da lafiyar ta bata mutu ba ina tunanin ma tafika lafiya,ubanta de yace bazai bamu yarsa ba, kudi da'aka tura musu kuma sun cinye bazasu biya ba,amma maganar mutuwar yarinya babu ita, Amal tana nan araye saide tahadu da iyaye tsofaffin najadu..."(🙆🏻‍♀️) Daddy yace"Subhanallah..." Jawad da Fu'ad kuwa ganin cewa maganar ba qarama bace, hakan yasa suka tashi suka basu waje suka wuce sama,Jawad baisan dalili ba haka nan yake jin ransa sakayau kamar ancire masa wata qaya daga jikinsa. Yaya Mariya saida ta tabbatar su Jawad basa nan sannan ta kalli Hajiya Zaliha suka hada ido,Hajiya Zaliha tayi maza ta sunkuyar da kanta qasa,Yaya Mariya tasaka hannu ta goge hawayen taqaici tace"zaliha kin bani mamaki,nayi tunanin da Jawad,da duk abinda ya mallaka naki ne...." (yara marayu wanda basu tashi da iyayensu ba, da wanda aka tsinta Allah ya bayyana muku iyayenku idan da rabon haduwar ku da juna😭😭😭) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Idan kika karanta min batare da kin biya ba keda Allah saboda ban yafe ba👌🏻 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 Wani irin hawaye mezafi yazubo daga idon Hajiya Zaliha tasa hannunta tashare hawayen idonta. Yaya Mariya taci gaba da fadin"mekike tunani idan yaron nan Jawad yasan abinda kuka aikata keda d'an uwanki? ganinki yake amatsayin mahaifiyar sa wacce tafi kowa sonsa aduniya menene kudi Zaliha?" Daddy yayi ajiyar zuciya yace" Yaya kin barni aduhu,kiyimin bayanin abinda yake faruwa" Yaya Mariya ta kalleshi tace"da niyya tayi wannan hadin auren,sun shirya hakane itada Bature domin su samu yan kud'ad'en su, kuma sun samu, domin kuwa Bature yacemin kudi sun riga sun riqe bazasu bayarba,yace kuma bazai bawa Amal dan tsuntuwa ba, saboda haka nina gama yanke hukunci Jawad yahado kayansa yadawo gidana, nizan masa ruqon d'a, ba ruqon d'an tsuntuwa ba" Daddy yana gama jin wannan bayani yaji kansa yayi wani dumm! kamar an buga masa wani abu, ya runtse idonsa cikin baqin ciki sannan ya kalli Zaliha yace"hakane wannan maganar Zaliha?" Hajiya Zaliha ta share hawayen idonta sannan tace" ka gafarce ni Alhaji" Sannan tajuya tasake kallon Yaya Mariya tace"kema Yaya kiyimin aikin gafara,Yaya Bature ne yake fadamin cewa ina zaune Alhaji ya maida duka kadarorin sa sunan Jawad,kamata yayi ace shida Fu'ad kowa yanada damar da zaiyi amfani da dukiyar bawai Iya Jawad ba,tun bana amincewa da maganganunsa har shaidan yayi nasara akaina,nayiwa Alhaji magana akan yanda ya bawa Jawad dukkan kadarorin sa kamata yayi abasu shida Fu'ad,Alhaji ya nunamin da Jawad da Fu'ad duk d'aya ne,saida natura masa kud'ad'en yariqe gaba daya ya hanani komai,qarshe ma yace idan kuskura nasake yimasa maganar kudin to zaizo har wajanku ya tonamin asiri" ta qarasa maganar tana share hawayen idonta. Daddy yayi ajiyar zuciya yace"Zaliha bansan meyake damunki ba,idan yaron nan yaji abinda kikayi mekike tunani zai dauka? har abada banaso Jawad yasan cewa ba nine mahaifinsa ba saboda ubangiji shine yasakamin qaunarsa araina,yanzu gashi kin fitar da maganar damuke 6oyewa kowa,kinfadawa Bature Jawad ba danmu bane,ban ta6a tunanin haka daga wajanki ba,shi da Fu'ad ni duk d'aya na dauke su,kuma ko bayan raina nasan Jawad bazai yada dan'uwan sa ba,kinyi min maganar kudin nan nafada miki da Jawad da Fu'ad duk dayane,Jawad zai kula musu da kudin su sannan yaron nan nafada miki ko mutuwa nayi bashida gadona,Zaliha yaron nan ATM dinsa yadauka yabaki kiyi abinda kike buqata da kudi tome wannan kudin zai qara miki? naga alama tunda kika samu Fu'ad shikkenan shi Jawad din kin yadashi,danhaka ki dauki yanaki yanaki kibarmin gida kije caaan! ki zauna da Alhaji Bature ni bazaki rabamin kan 'ya'yana ba" Cikin sauri Mummy ta dago kanta ta kalli Alhaji Aliyu Mekudi cikin tsananin mamaki. **** Tunda suka shiga dakin Jawad, Fu'ad ya zauna fuskarsa cikeda alhini ya kalli Jawad yace"gaskiya uncle Bature yayi qaranta,saida aka tura masa wannan uban kudin?" Jawad dayake kwance yayi matashi da hannunsa ya motsa lips dinsa kad'an sannan yace"ra'ayin sane" Fu'ad yace"ni Yaya sainagama kamar baka damu ba" Jawad yasaki wani irin murmushi sannan yace"gaskiya I'm happy sosai da hakan tafaru" Fu'ad yadauki fillo yajefa masa cikin taqaici sannan yafice daga dakin, yana fita yaga har lokacin Yaya Mariya tana nan itada Daddy a zaune afalon saide babu Mummy, falon ya qarasa yanufi fridge zai bude yadauki ruwa adede lokacin Mummy tafuto hannunta janye da trolley tana share hawaye,Fu'ad yadago da sauri ya kalleta fuskarsa daukeda mamaki,Fridge din yafasa budewa yanufeta yana qoqarin riqe jakar kayan nata yace"Mummy meyafaru ina zakije?" Daddy da fuskarsa tayi baqiqqirin ya kalli Fu'ad fuska babu alamun wasa yace"kai saketa ka koma ciki" Gaban Fu'ad yayi wata irin faduwa,hakan da Daddy yayi shine ya tabbatar masa da cewa lalle ba lafiya ba, saboda bai ta6a ganin sunyi hakan ba, cikin sauri ya juya aguje yayi dakin Jawad,adede lokacin Jawad yafara duba computer sa zai nemo picture din Inaas ya kalla,sai ga Fu'ad aguje yashigo dakin, cikin firgici yace"yaya!! Mummy" Jawad yafasa daukan computer yadago da sauri ya kalli Fu'ad yace"meyafaru? meyasameta?" Cikin sauri Fu'ad yace"gida zata tafi,nahana ta tafiya Daddy yace nabarta tatafi" Gaban Jawad yayi wata irin fad'uwa yace"what!?" Baijira amsar Fu'ad ba yafice daga dakin cikin gudu, yana zuwa falon yaga tana qoqarin ficewa,cikin sauri yacinmata yariqe jakar yace" Mummy what happened? ina zakije?" Hajiya Zaliha ta share hawayen idonta takasa had'a ido da Jawad,muryar ta can ciki tace" Jawad kayi haquri" Cikin damuwa yace"Mummy wai meyake faruwa ne? meyasa kike bani haquri? please dawo,bani jakar" Mummy takasa bashi jakar kuma takasa tafiya,Jawad yajuya ya kalli Daddy sannan yace"Daddy kayi mata magana zata tafi fa,wai meyake faruwa ne?" Daddy yace"kabarta taje,ba buqatar cigaba da zamanta" Jawad ya lumshe idonsa cikin damuwa yabude ya kalli Yaya Mariya yace" Hajiya Mama kisa baki mana" Yaya Mariya tace"to Jawad kace karta tafi kuma taqi ji basai kabarta taje ba" Wani irin taqaici yakama Jawad,yarasa meyake damun Daddy da wannan rikicacciyar tsohuwar. Ya girgiza kansa yadauki jakar cak,sannan yakamo hannun Mummy suka wuce dakinta, suna zuwa dakinta tafada jikinsa tasaki wani irin kuka,haqiqa tasan cewa abunda tayi bata kyauta ba,sauqinta daya Alhaji dakuma Yaya Mariya basu fadawa Jawad din abinda tayi ba. Jawad yasake rungume ta yana lallashin ta,Fu'ad ya kallesu yace"Mummy kiyi shiru please" Bata saurari Fu'ad ba taci gaba da kukan ta,Jawad yajata suka zauna abakin gado yafara bubbuga bayanta sannan cikin sigar rada yace"Mummy kiyi shiru,babu inda zakije muna nan tare dake idan yadage akan saikin tafi to tare zamu tafi" Ahankali tasaki ajiyar zuciya sannan tace"kayi haquri Jawad" Jawad yadafe goshin sa da hannunsa yace"Mummy haqurin nan ya'isa haka,bakimin komai ba,kuma bazaki min ba,babu wata uwa dazata yiwa d'anta laifi Mummy, maganar Daddy kuma zamuyi settling komai nida Fu'ad,ki kwanta kihuta please" Wani irin tausayin Jawad din da tsananin kunyar sa ya kamata,ahankali tagyada masa kanta alamun amsawa sannan ta share hawayen idonta tana sakin wata irin ajiyar zuciya sannan ta kwanta akan gadon,yatashi yaja mata blanket ya rufe mata qafafunta sannan ya kalli Fu'ad yace"muje" Futowa sukai suka zauna afalon anan suka tarar Yaya Mariya tana sallama da Daddy zata tafi gida,Daddy yajuyo ya kallesu yaga sun zauna kowa ya tsare fuska su ala dole gaadin uwarsu suke, ko idan yayi niyar korar tata sune zasu hanashi oho(😂) Bayan yaraka Yaya Mariya ma daya dawo falon shima waje ya nema ya zauna yadora qafa daya kan daya babu wanda yacewa wani uffan tsakanin shi da su,haka akai zaman kurame afalon kowa da abinda yake ransa. Saida aka kira sallar magrib suka tashi daga falon suka wuce masallaci, dasuka idar da sallar ma basu dawo ba saida sukayi sallar isha'i, dasuka dawo dinma a falon suka zauna anan Na'im yakira Jawad yace gashinan zuwa,Jawad yaji dadin wayar tasa,hakan yasa yatashi ya kunna musu kallo har Na'im din yazo sukaci gaba da fira suna kallon labarai. Daddy yashigo ya gansu, Na'im yatashi ya gaidashi, sannan Daddy yawuce sama, bai dade da zamaba Mummy ma tafuto tawuce dakin Daddy domin sake bashi haquri,Jawad yaganta, hakan saiya masa dadi koba komai insha Allah zuwa wayewar gari zasu daidaita kansu. Har wajan qarfe tara na dare suna falon a zaune, har lokacin Mummy bata futo daga dakin Daddy ba, saida suka gama kallon labarai sannan Fu'ad ya sauya tasha yajuyo yana kallon Na'im tareda fadin"babu wasu zafafan yanmata ne? tunda Yaya yagwada na family ba'a dace ba yanzu saimu koma wajan bare" Na'im yace"kamarya? mekake nufi?" Fu'ad yayi murmushi yace" wallahi anfasa bikin Yaya, but issue ne na family dinmu kasan halin auren dangi" Na'im ya girgiza kansa alamun rashin jin dadi sannan ya kalli Jawad yace"sorry bro...,banji dadi ba wallahi, ko shiyasa naga kayi shiru kabarmu munata zuba?" Jawad ya kalleshi ya shafa sumar kansa yace" no,ni dadi ma naji da'aka fasa,ni har yanzu babu macen da take gabana" Fu'ad yayi murmushi ya jinjina kansa baice komai ba, yayinda Na'im yasaki dariya yace"kaide bakaga wata zazzafar bane,akwai yanmata masu aji wallahi,kazo kayi biyaiya in hadaka da d'aya" Jawad yamiqe yadauki wayarsa yana fadin"banda lokacin wannan shirman" Fu'ad da Na'im suka saki dariya,Na'im yace"kajishi,shifa ala dole d'an kasuwa ne baya soyaiya saide kasuwanci,yanda yake da naci akan kasuwancin sa irinsu ne masu naci awajan wacce suke so,idan ya had'u da wacce yakeso wallahi liqe mata zaiyi" Jawad ya harari Na'im yawuce dakinsa,yayinda Fu'ad yasa dariya, daga nan sukaci gaba firar su su biyu. tunda abun nan yafaru Mummy ta zama silent,agaban yaran nasu basa nuna komai,saide bayan idon yaran batada aiki sai bawa megidan nata haquri,haka idan tayi sallah koda yaushe Addu'ah take akan Allah yasake shiryata,Allah ya hade mata kan zuri'arta,tsawon wannan yan kwana biyun Jawad jinsa yake kamar anyi masa albishir da gidan Aljannah,musanman idan yatuna cewa babu maganar aurensa tariga ta rushe, agefe guda kuma zuciyarsa tanata azalzalarsa akan kallon pictures din Inaas,shi kansa yasan cewa wannan tunanin nata yafara kawo masa naqasu aharkarsa tayau da kullum a fannin kasuwancinsa. Yauda safe yashirya tsaf cikin qananun kaya wanda yayi masa mutuqar kyau,yasauko qasa anan yaga Daddy yashirya cikin manyan kaya kamar yanda yasaba, ga Mummy ta riqe masa jaka,Man Sulaiman yana gefe shima yayi kyau cikin manyan kaya,Jawad ya gaida Man Sulaiman wanda yazubawa Jawad din ido tun saukowar sa yanajin qaunar yaron aransa. Ya matsa kusada Daddy yace"Daddy zakayi tafiya ne?" Fuska babu alamun wasa Daddy yace" eh zamuje nijar ne,daurin auren fauziya da Ummi yaran Alhaji Auwal" Jawad yace"Daddy baka fadamin ba,aida na shirya munje" Daddy yace"kaje Ina? basai kaje ba, gashinan zamu tafi tareda Man Sulaiman zai rakani,Jawad da hankali na yaushe zan sake turaka gidan Alhaji Auwal? last time da biyu na turaka ko Allah zaisa kaza6i daya acikin yaran,amma sai kaje kadawo babu wani sakamako" Jawad yayi sauri ya sunkuyar da kansa qasa yana shafa qeyarsa,sai yanzu ne yatuno wannan d'aya yarinyar Ummi tanata fariii da idonta lokacin dasuka rakoshi wajan mota, ashe abinda take nufi kenan,to ai shi baisan hakan wani abu daban take nufi ba(🤭) Yasake shafa qeyarsa yace"Daddy tuba nake" Daddy ya girgiza kansa yace"yazanyi dakai Jawad? zamuje nida Man Sulaiman,zamuyi kwana biyu,sai ayi mana Addu'ah" Jawad yace"ok Daddy,Allah yadawo daku lafiya, nima inaso gobe zan wuce insha Allah" Mummy ta kalleshi tace"A a,da yaushe kazo dazaka koma? bazaka bari Daddynka yadawo ba?" Jawad ya kalleta cikin sigar lallashi da kwantar da hankali yace" Mummy nima banson tafiya,but yakamata naje ne,akwai wata makaranta dana ginawa marayu a Kuwait, yaran sun shirya min Birthday party na tareda su, gobe da daddare zanyi meeting da wasu baqi a Indonesia,jibi kuma zan qarasa Kuwait makarantar" Mummy ta jingina kanta tace"to shikkenan Allah yakaimu goben" Jawad ya amsa mata sannan ya amshi jakar hannunta ta kayan Daddy, suka fice shi dasu Daddy, saida yaga fitar su daga get din gidan sannan yadawo ciki. *** *** *** Niger Republic Tunda suka sauka a qasar Niger Man Sulaiman jikinsa yayi sanyi qalau,domin kuwa rabuwar sa da matarsa Bilkisu saita dawo masa sabuwa fil,yau gashi a qasar ta amma bashida yanda zaiyi yaganta. Alhaji Auwal yayi musu tar6a mai kyau saboda jin dadi yarasa Ina zai d'orasu,daga qarshe aka kai su dakin baqi na musanman kafin zuwan ranar daurin aure,daga qarshe shima Alhaji Auwal din saiya dawo wajan aminin nasa Alhaji Mekudi suke sake tattauna yanda za'a kar6i sauran baqi masu zuwa daga wasu qasashen,da daddare angwayen sukazo har gida suka gaida Alhaji Mekudi bisa umarnin Alhaji Auwal kasancewar Alhaji Mekudi shine zai zama waliyin fauziya,ita kuma Ummi wani Qanin Alhaji Auwal din ne waliyinta. *** *** *** Indonesia Washegari sassafe Jawad yabar qasar ya gudu Indonesia kamar yanda ya fadawa Mummy,tunda suka sauka yashiga meeting bai samu kansa ba sai yamma lis,kai tsaye gidan daya sauka suka qarasa,shida guard dinsa guda biyu sai kuma p.a dinsa na amana. kowa wajan hutawa yanema,Jawad yashige dakinsa yayi wanka yaci abinci sannan ya kwanta yana hutawa idonsa a lumshe,wani irin tunanin tane yake addabar zuciyarsa har yanajin kamar zai Iya shiga wani hali idan bai d'orata a'idon sa ba. a hankali yasaki wani dan qaramin tsaki yasake juyi akan faffadan gadon nasa,yana tuna surutun ta da tsiwar ta,ahankali yasaki murmushi sannan yasake juyawa yana rungume fillo a qirjinsa yanajin tamkar ita dince ajikinsa (🙆🏻‍♀️🙈) haka ya dinga juyi agado yanata aikin tunanin ta,wanda inda abaya ne baya 6ata lokacinsa akan tunanin mace saide ya6ata lokacinsa akan tunanin kasuwanci. Da daddare bayan sunyi dinnar yakoma dakinsa yasake wanka,ya futo cikin wasu qananun kaya wanda suka bayyana qaqqarfan jikinsa,afalon ya zauna tareda kunna kayan kallo yana kallon abinda yasaba wato labarai. P.a ya matso gabansa ya ajiye masa wasu uban takardu. Sannan yashige kitchen din falon yahado masa coffee yana turiri ya ajiye masa,yaja gefe yakoma shima yana nasa aikin na shigar da wasu bayani. Jawad yayi ajiyar zuciya yadauko biro yafara duba takardun cikin qwarewa,lokaci zuwa lokaci yana shan coffee din gabansa kad'an-kad'an, ko awa daya baiyi da fara duba takardun ba,Inaas tafad'o masa,ahankali ya lumshe idonsa sannan yadora hannunsa akan goshinsa, babu musu ya ajiye biron hannunsa ya kalli p.a dayake tsaye cak yana aikin danne-danne da iPad din hannunsa. Yace"p.a bani computer" Cikin sauri p.a ya ajiye iPad din hannunsa yadauko computer Jawad ya ajiye masa agabansa sannan yabude masa ita, yakoma yatsaya. Cikin sauri Jawad ya kunna computer yashiga cikin wata folder nan take photon Inaas ya bayyana,yayi wata irin ajiyar zuciya wadda tasa daga p.a har guard dinsa guda biyu hankalinsu yadawo kansa. P.a yayi murmushi cikin ransa yana jinjina wa miskilanci irinna ogan nasa,da alama yayi nisa a soyaiyar wannan yarinyar amma kuma ya gagara tunkararta yafada mata abinda yake zuciyarsa. Jawad yazubawa photon nata ido yana kallo kamar yau ne karon farko daya fara ganinta,sosai ya shagala da kallonta da alama ya manta cewa yana tareda guards dakuma p.a, saida yagama kallonta tsaf sannan yasaki ajiyar zuciya ya rufe computer. Yajuya ya kalli p.a dinsa sannan yace"P.a!" P.a yace"na'am Yalla6ai" Jawad ya danyi murmushi sannan yace"jibi munada taron Birthday na a qasar Kuwait,da zatazo da abun zaifi armashi"(🤭) Daya daga cikin guards din yace"with dou respect sir,kabamu dama muje mukawo ma ita"(🙆🏻‍♀️) Jawad yajuya ya kalleshi ya girgiza kansa alamun shawarar tasa batayi ba, sannan yajuya ya kalli p.a yace"ayi abinda yadace p.a" Yana fadawa p.a haka, yakoma cikin kujera ya jingina tareda lumshe idonsa,yana fatan p.a yasamo masa maslaha. Cikin sauri p.a yace"angama Yalla6ai" Tab din hannunsa yafara shafawa cikin qwarewa yanemo number ilyasu manager Mekudi Oil na qasar Niger. Ilyas yana ganin kiran,cikin sauri yadauka tareda girmamawa yace"yalla6ai barka da dare" P.a yace"kana magana da p.a dinsa,Yalla6ai Jawad zaiyi bikin qarin shekarun sa jibi a qasar Kuwait,kamfanin ku yana d'aya daga cikin wanda suka samu kyautar tickets din mutum biyar domin halartar taron" Ilyasu manager yayi shiruuu yatafi tunani,kyautar tickets har na mutum biyar zuwa qasar Kuwait? tabbas wannan kyautar tickets din da biyu,haqiqa Yalla6ai Jawad son Inaas yake,tunda yake bai ta6a zuwa Kuwait ba,amma gashi ta dalilin Inaas an aiko musu da kyautar ticket harna mutum biyar bama nata ita kadai ba,harda qarin wasu mutum hudu,lalle in hakane yakamata ya dinga girmamata sama da qasa(🫡) p.a dayaji shiru yace"Hello!" Daga dayan bangaren ilyasu yace"angama sir, sannan muna so amiqa mana godia wajan Yalla6ai Jawad" P.a yakashe wayar ba tareda yabashi amsa ba,daga nan maida hankalinsa kan iPad dinsa yana qoqarin yin magana akan tickets din. Jawad yasaki wata ajiyar zuciya jin wannan dabara ta p.a,shiyasa akoda yaushe yake alfahri dashi, yanajin dadin aiki dashi, yabude lumsassun idonsa ya kalleshi yace"P.a" P.a yace"na'am Yalla6ai" Jawaad yasake gyara zamansa cikin darura yace"P.a kana ganin zatazo kuwa?" (eto 🤔) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Idan kika karanta min littafi ba tareda kin biya ba keda Allah saboda ban yafe 👌🏻 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 ___ Cikin yaqini p.a yace"insha Allah zatazo Yalla6ai,gashinan Ina qoqarin yimusu booking din tickets" yafadi haka yana maida hankalinsa kan iPad din dake hannunsa. Jawad yayi ajiyar zuciya sannan ya lumshe idonsa,gabansa yana tsananta fad'uwa yana tsoron ace yarinyar nan batazo ba. *** *** *** Niger Republic Ilyasu manager baiyi qasa a gwiwa ba yahada meeting din gaggawa,duk wanda yashigo dakin taron cikin ransa yana mamakin cewa wanne irin taro ne haka yataso na gaggawa,zama sukai akan dogon table din dasuke zama domin meeting yayinda aka ajiyewa kowa gorar ruwan DALLOL agabansa,bayan kowa ya nutsu manager yayi gyaran murya sannan yace"nataraku anan ne domin in sanar daku cewa munsamu saqo daga mamallakin wannan kamfani wato Yalla6ai Jawad Mekudi,zaiyi taron qarin shekara a qasar Kuwait,Allah da ikonsa kamfanin mu yana cikin wanda zasuje wannan qasa domin tayashi murna..." Gaban Inaas yayanke yafadi,tunda ya ambaci sunan Jawad takejin fad'uwar gaba, amma saita maze ta sunkuyar da kanta qasa. Manager yaci gaba da fadin" munsamu kyautar tickets na mutum biyar,saboda haka wannan kamfanin namu yayi selecting mutum biyar din dazasu je ciki harda Inaas Omar Farouq " Cikin sauri Inaas tadago kanta tana kallon manager,gabanta yaci gaba da faduwa hannunta yafara rawa. Ahankali surutu yafara tashi adakin meeting din nasu kowa sai qus-qus yake dana kusa dashi suna sake tabbatar wa cewa lalle da gaske zargin da'ake ya tabbata, manager son Inaas yake (😂🤭) duba da yanda mamallakin kamfani Jawad Mekudi yazo yakoreta aiki,amma manager yadawo da ita,kuma daya dawo da ita dinma sai wani nan-nan yake da'ita yana bata girma kamar wata 'yar wani. Manager yaci gaba da fadin"idan akwai me magana kokuma wanda zai bada wata shawara dangane da wannan tafiya zai iya magana" Daya daga cikin maza yadaga hannu alamun yanada abun fada,hankalin manager da sauran mutane yadawo kansa,yayi gyaran murya sannan yace"gaskiya munji dadin wannan al'amari,wannan ma wata babbar nasara ce da kamfanin mu yasamu wanda abaya bamu ta6a samun irinta ba,saide inaso nabada shawara akan yakamata kamfani ya shirya masa wata 'yar kyauta wadda za'a kai masa domin nuna jin dadinmu akan wannan gayyata" Manager ya jinjina kansa yace"wannan hakane,zamuyi qoqarin hakan insha Allah,sannan duk wanda wannan tafiya tafad'o kansu,zasu Iya tafiya gida su shirya,idan lokacin tashinmu yayi,saisu futo mu wuce" Yadauki wata takarda ya karanto sunayen mutum biyu maza,sai shi na uku,sai wata mace saboda yasan halin ta batada surutu kuma tanada kamun kai sosai babbar mace ce,itace ta hudu, saikuma Inaas ta biyar. Daga nan taro yatashi,Inaas tawuce office dinta ta dauki Jakarta tafuto tarufe office din sannan ta nufi gida jikinta a sanyaye,har yanzu mamaki take to ita awa? dazata shiga cikin jerin wanda za'ai wannan tafiyar dasu? sannan manager bai ta6a nuna mata wata alama da zatayi zargin sonta yake ba,tunda tadawo bakin aikinta taga yana girmamata abun har tsoro yake bata. Tana shigowa gida taga Abbanta yaci manyan kaya yanad'a rawani a kansa irinna buzaye da alama fita zaiyi,Bilkisu datake gefe a zaune tana ninke kayan wanki tadago ta kalleta tace"yanaga kindawo jiki a sanyaye bade korarki sukayi ba?" Abbanta ma yanemi waje ya zauna yana jiran amsar ta. Zama tayi agefe jikinta duk a sanyaye sannan tace" Ammiy wannan Jawad din da yazo gidannan kin tuna shi ko?" Cikin sauri Bilkisu tace"sosai kuwa,menene ya sameshi? aiba cutar dashi akayi bako?" Abban Inaas da ita kanta Inaas din duk sai suka kalleta da tsananin mamaki,ganin daga cewa Jawad duk tabi ta rude tana tsoro kar ace wani abu ne ya sameshi. Inaas tace"A a babu abinda aka masa,wai shine zaiyi Birthday awata qasa,sai akace zamuje muyi masa murna muma" Cikin sauri Abbanta yace"ban fahimta ba,yanzu dama ita taya murna harta wuce a kirashi awaya kokuma atura masa saqo dole sai anje har wata qasa? toki fada musu babu inda zakije" Cikin ladabi Inaas tace"to Abba" Sannan ta dauki wayar Ammiy,tabude Jakarta ta dauki wata takarda wadda number manager take ciki sannan ta kirashi, yana dauka tace"yalla6ai dama zan baka haquri ne ko za'a sa sunan wata a gurbina saboda Abbana yace inbaka haquri ba zanje ba" Manager yanajin haka gabansa yafadi,shi ya'isa yaje wannan qasa babu wannan yarinyar?(🤔) Cikin sauri yace"kinga Inaas,bai wuce awa biyu yarage ba jirginmu zai tashi,ki cewa Abbanki yajirani agida, gani nan zuwa" Inaas tace"to Yalla6ai" Sannan ta kashe wayar ta kalli Abbanta tace"Abba nafada masa,yacemin infada ma dan Allah kajira shi zaizo yanzu" Abbanta baice komai ba,itama daga haka bata sake cewa komai ba tawuce daki. Bilkisu tasaki ajiyar zuciya tace"Farouq dakayi haquri taje,Inaas ba zatayi wani abu ba kaide barta a surutun ta kawai,amma kasan cewa ba zatayi shashanci ba,sannan yaron nan ni sheda ce yanada hankali wallahi,kuma tafiyar nan bafa ita kadai akace mutura masa ba,da mutane zasuje,idan wani abu kake tunani me wannan yaron zaiyi da Inaas? ai munsani cewa yafi qarfinta ruwa ba sa'an kwando bane,amma bai kamata dama ta samu, sannan kaikuma kahana ba,inde ka yarda da tarbiyar dana bawa Inaas to karkaji ko d'ar aranka,zataje ko'ina kuma ta dawo lafiya,bare ma yaron nan wallahi naga a nutse yake,bashida hali marar kyau" Farouq ya kalli Bilkisu ya girgiza kansa yace"Yaya kenan, sai yabonsa kike kamar kin zauna dashi tsawon shekaru kin karanci halinsa" Bilkisu tayi shiru ta qyaleshi bata sake magana ba. Inaas tafuto ta dauki buta tawuce bandaki, adede lokacin kuma manager ya Parker motarsa a qofar gidan,yadaga murya yayi sallama, Abban Inaas yatashi yafita waje yabashi hannu suka gaisa, sannan yace"Bissmillah shigo daga ciki mana" Bilkisu tatashi tayafa mayafi sannan ta Shimfida musu tabarma suka zauna,takawo shayi me zafi ta'ajiye masa. Abban Inaas yace"yanzu Inaas tazo min da wata magana,to ba komai ne yasa nace ba zataje ba kasan yanzu kiwon mutum ake ba dabba ba,kadauki 'ya mace katura wata qasa ba tareda muharramin taba akwai matsala,shiyasa nace ba zataje ba" Manager yayi murmushi yace"wannan haka yake,kayi gaskiya, kuma kowanne uba dole zaiyi wannan tunanin,amma inaso kabani amanar Inaas,zan riqeta amana tunda dani za'a yi tafiyar nan zamuje lafiya mudawo lafiya insha Allah,yanda nazo gida na dauketa,dakaina zan dawo da'ita gida, insha Allah nayima alqawarin babu abinda zai sameta" Abban Inaas yayi ajiyar zuciya sannan yace"to Alhamdulillah,yanzu kaga hankali na zaifi kwanciya" Yadaga murya yace"Ke kina ina? futo kutafi" Inaas tafuto daga bandaki ta wanke hannunta,sannan tashiga daki ta sauya kayanta tafuto,manager yatashi shima Abban nata yatashi tsaye yace"nima wajan daurin aure zanje gidan Alhaji Auwal, yau za'a daura auren yaransa,aida har Airport din zamuje na rakaku" Manager yace"ato muje mana tunda hanya ce saimu saukeka,nima badan wannan tafiyar tamu ba aida zan halarci daurin auren" Abba yace"to shikkenan nagode sosai muje" Suna fita, Bilkisu ta janyo Inaas takama kunnanta ta riqe dakyau sannan tace"kishiga hankalin ki dakyau kina jina?" Cikin sauri Inaas tadora hannunta akan kunnanta tana runtse ido tace" to Ammiy" Bilkisu tasaki kunnanta sannan tace"idan kunje babu ruwanki da wannan surutun naki,ki zauna awaje daya ki nutsu kiyi shiru kinji?"(😂) Inaas tace" to Ammiy,dama ni babu ruwana da kowa" Bilkisu ta kalli kyakykywar fuskar 'yar tata sannan tasa hannunta tana sake goge mata fuskar tana cewa"wannan fuska taki ko kwalli baki saka mataba,bare powder,kinde ji menace miki ki nutsu idan kinje,ungo wannan kudin ko zakiga abu ki siya a hanya" tafadi haka tana zaro kudi agefen zaninta, Inaas ta kar6a tafice, Bilkisu ta taraka ta har bakin mota tana daga musu hannu, saida sukai nisa ta daina ganinsu sannan ta juyo gida ranta fes kamar ba wata qasa 'yar tata tatafi ba, musanman idan tatuna wajan Jawad tatafi haka kawai sai taji hankalin ta ya kwanta, domin kuwa kokad'an bata yiwa yaron kallon tantiri. Har qofar gidan Alhaji Auwal manager ya ajiye Abba, sannan Abba yayi mata nasiha yashige gidan, ita kuma suka tafi itada manager idonta yana kan gidan tana kallon tsantsar kyau irinna gidan kana gani kasan ba gidan qaramin Mekudi bane. Tayi tunanin Airport zasu wuce,sai taga sun dauki wata hanya saida sukaje wani shago yatsaya yajuyo ya kalleta yace"kishiga cikin shagon nan Hajiya Halima ma tana ciki,kuyi sauri kufuto" Inaas kanta ya daure, tarasa me zatayi a shagon? amma ganin yace mata Hajiya Halima tana ciki,kuma tasan Hajiya Haliman itace wacce akace zasu tafi tareda ita,hakan yasa tafuto tashiga cikin shagon, tana shiga Hajiya Halima ta nunawa masu shagon Inaas tace"yauwa gata nan ma ta qaraso" Matar ta kalli Inaas tace"sannu da zuwa yanmata zauna mufara" Inaas tarasa meza'a fara,taja kujera ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido. Dogon gashinta suka kunce kasancewar a wanke yake hakan yasa suka shafa mata mayuka aka sake taje shi da hand rayer, yasake miqewa yayi kyau,akayi mata light makeup, sannan suka bata wata hadaddiyar laffaya baqa,wadda taji duwatsu sai walwali take,aka bata yar fos tariqe tareda takalmi mai kyau,bayan angama data kalli kanta a madubi ita kanta tasan cewa bata ta6a yin masifar kyau irin wannan ba. Saide tarasa dalilin wannan gyara dasuke mata. Suna futowa manager dayake zaune amota ya kalleta yayi saurin kawar da kansa tun kafin ma yaji aransa cewa Inama ace zata zama mallakinsa.(🤭) Sai yanzu ne yasake yarda cewa lalle Yalla6ai Jawad baiyi za6en tumun dare ba,duk wanda ya kalleta karon farko babu qarya zaice ita din matar manya ce. Tunda suka sauka a qasar Kuwait,Inaas taketa kalle-kalle, har wasu had'ad'd'un motoci sukazo suka dauke su,mazan sai firar su suke yayinda Hajiya Halima take ta danna waya,Inaas kuwa da batada waya hankalin ta yana kan window tana bawa idonta abinci,kai tsaye wani gida aka wuce dasu,suka yada zango a babban falon,abinci aka kawo musu da lemuka da ruwa,sukaci suka sha yayinda Inaas tafi maida hankali wajan cin nama,daga nan mazan suka fita,Hajiya Halima tahau WhatsApp tana voice note da mutanan gida,Inaas kuwa tashi tayi tai sallah sannan tadawo falon ta gyara zamanta ta lumshe idonta lokaci daya bacci ya dauketa. Batasan tsawon lokacin data dauka tana bacci ba saiji tayi Hajiya Halima tana tashinta,cikin murmushi tace"Inaas tashi zamu tafi wajan Birthday din" Inaas tatashi,ta dauki fos dinta zata wuce Hajiya Halima tace"haba Inaas kamar ba yanmata ba,zona gyara miki fuskar taki mana" Kasancewar ta babbar mace, hakan yasa Inaas din ta tsaya, babu musu Hajiya Halima tasake gyara mata fuska,Inaas tafuto tai ras da'ita, sannan takamo hannunta suka futo. Suna barin gidan,kai tsaye makarantar marayun aka wuce dasu,alokacin yamma tayi sosai, suna shiga cikin makarantar Inaas taga yara sai wasa suke sunyi mutuqar kyau cikin uniform dinsu,matan anyi musu parking din gashin su yaran gwanin sha'awa,tasaki wani irin murmushi najin dadi,motarsu tana tsayawa tafuto tashige cikin yaran tana jansu da wasa,baqar laffayar jikinta tasake haska farar fatarta sai dariya take lokacin dasuke jefowa juna ball itada yaran. P.a dayake tsaye da wasu guards yana hangota yasaki murmushi ganin plan dinsa yayi,sannan ya qaraso wajansu Hajiya Halima da manager yayi musu iso wajan da za'a yanka cake din. Jawad kuwa yana cikin aji tareda wasu yara yana zaune a kujerar baya yana ganin yanda malamin yake koyarda yaran,kasancewar yana daga gefen window lokaci daya yaji wata dariya tana tashi da wata irin murya me dadi,ahankali yajuya kansa ya kalli gefen window din, nan take yayi arba da'ita, adede lokacin ita kuma ta sunkuya zata dauki ball din laffayar kanta tadanja baya,gashin gaban goshinta yadan futo, tasa hannu daya tasake jan laffayar ta sukaci gaba da ball din sai dariya take,lokaci daya wani irin murmushi ya qwace masa,cikin ransa yace"yes!" Alokacin wata malama tazo tafara kora yaran zuwa wajanda za'a yanka cake, hakan yasa Inaas tabar wajan itama tafara tafiya ahankali tana kallon sauran ajujuwan yanda aka qawatasu kamar ba koyarwa ake ba. tana zuwa dede ajin da Jawad yake ciki tafara leqawa ta window tana hango yaran dake cikin ajin,tana d'aga idonta zuwa can qarshan ajin anan idonta yayi tozali dashi,cikin sauri ta daga masa hannu ta washe bakinta cikin farinciki tace"sannu de!"(🙋🏻‍♀️) Jawad yanajin ta yasan cewa dashi take,amma saiyayi kamar badashi take ba yayi fuska,muddin yace zai kalleta to za'a iya samun matsala domin kuwa idan yadora idonsa akanta bazai iya dauke wa ba. Inaas kuwa tayi tunanin baiji taba,hakan yasa tasake daga murya tace"yalla6ai" Ahankali yadago kansa ya kalleta fuskarsa babu walwala kamar ba shine yayi murmushi dazu ba saboda ganinta. Kallonta yayi cikin abun da baifi second ba,ya janye idonsa,Inaas ta kalleshi tayi shiruuu,tatafi tunani,sai yanzu tatuno rabuwar su ta qarshe, ta tuna yanda take cika baki idan ta ganshi saita shaqe masa wuya,lokaci daya ta nutsu,ahankali tafara ja da baya sum-sum tabar wajan takoma wajansu Hajiya Halima. Saida aka jira sauran yaran malamin yagama yimusu lesson din sannan suka futo gaba dayansu harda Jawad din hannunsa guda daya yana zube cikin aljihun wandon sa,idonsa yana Sanye da glass jan duhu kamar kullum,yana zuwa wajan cake din yafara gaisawa da jama'ah anata yimasa Allah ya sanya alkhairi, ta gefen idonsa yake satar kallonta yaga sai fara'ah take kamar Birthday dinta ake,wani irin murmushin gefen baki yayi yanajin dadin yanda murmushin ta yake 'DEBE MASA KEWA. wata malama ce ta matso kusa dashi tabashi wata 'yar qaramar wuqa tace"Mr. Jawad" Cikin sauri yadawo hayyacinsa,ya kar6i wuqar,sauran yara dalibai suka matso suka tayashi riqe wuqar suka yanka cake din tare,jama'ar wajan suka fara yimusu tafi ciki harda Inaas. yara biyu ne suka saka masa cake din abaki,wayoyi da camera kuwa sai haske suke saboda yanda ake daukan sa a photo. Shima yayanka yasaka musu abaki,sannan aka fara photuna da mutane,Inaas tana gefe tana murmushi bata shiga cikin photo ko daya ba,saide wanda aka kira yake daukan photo awajan hankalin sa yafi karkata kanyi mata photon wanda ita kwata-kwata batasan ma yanayi ba. Saida aka gama photuna sannan mutane suka fara tafiya wani waje can baya duk de acikin makarantar ne,domin cin abinci,manager yayiwa Hajiya Halima rada a kunne yayi gaba,Hajiya Halima tayi murmushi sannan ta qaraso wajan Inaas tabata wayarta tace"Inaas naga bakiyi photuna ba,ga wayata ki dauka idan mukaje gida saiki nunawa Mamanki" Cikin farinciki Inaas ta kar6i wayar, tafara yin selfie,ta matsa kusa da sauran cake din tana daukan photo awajan,Jawad yana tsaye agefe yana kallonta cikeda shauqi hannayensa zube cikin aljihun wandon sa,ganin photunan nata bazasu qare ba hakan yasa yayi gyaran murya, cikin sauri Inaas tad'ago,waigawa tafara yi taga babu kowa,wajan wayam! kamar anyi shara saisu biyu kadai,kowa yatafi wajan cin abincin da'aka shiryawa baqi. tadaga kanta ta kalleshi,cikin sauri tasake yin qasa da kanta,gabanta yafara fad'uwa,Jawad yazuba mata ido yana kallonta kamar zai cinyeta,ahankali ya motsa lips dinsa kamar zaiyi magana,saiya fasa, saida yadauki wasu second din, sannan yayi magana murya qasa-qasa cikin sigar rad'a yace"Whare is your Mom?" shine abinda yafara tambayarta,kanta aqasa batayi kuskuren kallonsa ba tace"she's fine" Ahankali yafara takowa harya matso gab da'ita qiris yarage jikinsu yahad'u,tanayin qwaqwqwaran motsi jikinsu zai had'e,hakan yasa gabanta ya tsananta fad'uwa,tasake yin qasa da kanta takasa hada ido dashi,shikuwa idonsa yana kanta,yanda ta sunkuyar da kanta hakan yasa dogon gashin idonta yahadu waje daya suka sake qawata kyawun fuskarta,yamaida kallonsa kan d'an qaramin lips dinta,wata irin nutsuwa da shauqi suka sake mamaye shi yaji kamar yasaka ta cikin jikinsa,daqyar ya daure ya d'an saita kansa sannan yasake yin qasa da muryar sa yace"Whare is my Birthday gift?". *** *** *** Niger Republic Cikin farinciki aka gama d'aurin auren Fauzy da Ummi yaran Alhaji Auwal,Alhaji Mekudi bakinsa har kunne yana fara'ah kamar wanda ake auren Jawad,Man Sulaiman yana gefensa yaci manyan kaya yasake zama wani cikakken mutum magidanci me 'yan canji,Alhaji Mekudi sai gaisawa yake da jama'ah shida Man Sulaiman,Alhaji Auwal yana gefensu yanata amsa wayar masu kira suna yimasa Allah ya sanya alkhairi wanda basu samu zuwa daurin aure ba. Farouq Abban Inaas ya qaraso wajan Alhaji Auwal yabashi hannu suka gaisa cikin farinciki yace"Alhaji Allah yasanya Alkhairi,Allah yabawa su fauziya zaman lafiya Allah yasa gidansu ne" Alhaji Auwal yayi dariya yace"Amin Amin Uncle din yara, nagode sosai,ga abokina ku gaisa" Yafadi haka yana nuna masa Alhaji Mekudi,sannan ya kalli Alhaji Mekudi yanuna masa Farouq yace" wannan shine malaminsu fauziya da Ummi,shine yake zuwa har gida yana musu lesson tun kafin su tafi Maryam abatcha University" Tunda Farouq yajuyo,Man Sulaiman yaqame a tsaye,idonsa qurrr akan Farouq,baya tunanin ko shekara hamsin yayi zai kasa gane Farouq,sannan bugu da qari Farouq din yana nan yanda yake saide fari daya sake saikuma yanayin shekaru dasuka qaru. Farouq yabawa Alhaji Mekudi hannu suka gaisa, sannan yabawa Man Sulaiman hannu suka gaisa yayi gaba, kwata-kwata baigane shiba,kudi da jin dadi dakuma haske daya qara yasa koda wasa baigane shiba. ganin de da gaske Farouq din bai ganeshi ba, hakan yasa yayi sauri yabi bayansa yabar Alhaji Mekudi awajan yana gaisawa da wasu mutane. Yana zuwa dab da farko yameqa hannu ya ruqo rigarsa yace"Farouq!" Farouq yajuyo yace" na'am" Man Sulaiman yace"Farouq wai baka ganeni ba? Manu nefa,Malam Manu naku" Cikin sauri Farouq yasake kallon sa,sai yanzu ne yagano kamar sa amma da qyar,saboda kafin ma Bilkisu tadawo qasar nijar shikam yadade rabon sa da Manu tun lokacin da akai bikinsu shida Bilkisun shikuma yadawo gida nijar. Ya kalleshi yasake kallonsa sannan yace"okay" yayi gaba yabarshi awajan(😂🙆🏻‍♀️) Cikin sauri Malam Manu yasake binsa ya ruqo shi,cikin rawar murya wadda take dab daya fara zubar da hawaye yace"Farouq wai baka gane menake nufi bane? ninefa Manu mijin yayarka Bilkisu,Farouq Ina Bilkisu? Bilkisu tana raye?" Farouq yaja yatsaya ya kalleshi yace"to dana ganeka sokake na goyaka?" yana fadar haka yasake yin gaba, yabarshi a tsaye awajan. Qwalla tacika idon Man Sulaiman,yayi sauri ya maidata,yabi bayan Farouq,akan idonsa Farouq yahau machine shima yayi sauri yahau wani sukabi bayan Farouq. Ana ajiye Farouq a qofar gida shima Malam Manu aka sauke shi,Farouq ya kalleshi ya watsar, yashige gida ya barshi a tsaye anan. Cikin sauri shima Man Sulaiman yasakai yashiga gidan,adede lokacin tana tsaye tana shanyar kayan wanki,jikinta sanye da riga da zani na atamfa,Man Sulaiman yana ganinta wani irin hawaye yazubo masa,baisan lokacin daya dira gwiwowinsa aqasa yayi kneel down ba tareda fashewa dawani irin kuka yasaka hannayen sa a fuskarsa yana shashshekar kuka. Bilkisu ta juyo ta kalleshi,kallo daya tayi masa tagane shi,bata tunanin cewa ko shekara d'ari Manu zaiyi basu had'uba zata Iya manta fuskarsa,tayi sauri ta kawar da fuskarta taci gaba shanyar kayanta ko takan Man Sulaiman bata sake biba,ta tattara shi ta watsar dashi kamar anshuka dusa awajan haka ta share shi tana sabgoginta. Farouq yaja tabarma yazauna yafara warware rawanin kansa ko inda Man Sulaiman yake shima bai kalla ba,daga ita har Farouq din kowa abun gabansa kawai yake. ( uba yana gida yana kukan nadama,😆😥 shikuma d'a yanacan yana yad'a manufa😂🤭🙈) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Idan kika karanta ba tareda kin biya ba keda Allah saboda ban yafe 👌🏻 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 17&18 Yatsun hannunta take ja ahankali duk ta rasa sukunin ta,tanemi surutu, da zaqin baki da tsiwar ta tarasa,gaba daya yayi mata wani irin kwarjini,ahankali tace"yana...yana...um birthday gift din yana wajan manager" Ahankali yasaki wani irin murmushi wanda yasa Inaas takusa sumewa a tsaye,cikin sigar rada yace"no,ni naki nakeso" Ahankali tagyada kanta alamun amsawa,amma takasa yarda tad'aga ido ta kalleshi, cikin nutsuwa ya sunkuya ya yanko cake din dake gabansu yanufi bakinta dashi sannan yace"open your mouth" Inaas sai taji maganar tasa kamar saukar aradu,cikin sauri tadago kanta ta kalleshi gabanta ya tsananta fad'uwa,idanunsu yahadu dana juna,cikin rawar murya tace"yalla6ai a a kabar...." Kafin tagama cewa ka barshi,yadora yatsan hannunsa guda daya akan lips dinsa yace" shiiii...." alamun tayi shiru,sannan yanufi bakinta da cake din,ahankali tabude d'an qaramin bakinta yasaka mata cake din,cikin darura tafara tauna cake din me mutuqar dadi,yadauki tissue yagoge hannunsa,sannan yazura hannunsa acikin aljihun wandonsa yazaro wata sarqar gold me masifar kyau,yanufeta da'ita,a wannan lokacin kam kusancin nasu yayi kusanci hakan yasa har jikinsa yafara gogar nata,jikin Inaas yafara rawa, shi kansa yaga yanda take karkarwa amma saiya maze kamar baigani ba,yasaka hannunsa na dama ya janye laffayar dake kanta,kyakykywan gashinta ya bayyana saide an nad'eshi abaya anyi mata ribon dashi, idonsa akan gashin nata yanaji kamar ya d'ora hannunsa akai, amma yahana kansa aikata hakan saboda yanzu ma jikinta yana irin wannan rawar idan yadora hannunsa ajikinta sai yaya kenan? Sarqar yadaga yasako mata ita a wuyanta,sannan ya daura mata sarqar tanajin yanda hucin numfashin sa yake sauka akan wuyanta saboda ya sunkuyo yake kallon kyakykywan wuyan nata,saida yagama kallonta sannan yaja laffayar tata idonsa akan gashinta yamaida mata ya rufe mata kanta yace"tunda kin hanani birthday gift,ni ga nawa nan" Cikin sauri ta gyada masa kanta sannan tace"nagode Yalla6ai,zan iya tafiya?" Kai tsaye yace" a a,haka zaki tafi baki bani kyauta ba baki bani cake ba?" Gabanta yasake fad'uwa,tadago kanta ta kalleshi,da idonsa yayi mata nuni da cake din dake gabansu,sannan yace"idan kika bani saiki tafi" Inaas tarasa yaya zatayi, tarasa meyake mata dadi,tana so tabar wajan, bata so wannan ke6ewar tasu tasa yayi mata wani abu,ahankali tajuya ta kalli ko'ina taga babu kowa awajan,cikin sauri ta sunkuya ta yanki cake din dan qarami sannan ta nufi bakinsa dashi,babu musu ya rissina ya daidaita tsawon su sannan yabude bakinsa tasaka masa cake din ya lumshe idonsa yana taunawa,Inaas ta kalleshi tarasa menene abun lumshe ido acin cake... Adede lokacin p.a ya qaraso wajan, cikin sauri Inaas ta janye idonta daga kallon Jawad, ta sunkuya ta dauki tissue din wajan ta goge hannunta kamar yanda taga yayi,p.a ya kalli Jawad cikin ladabi yace"yalla6ai ga saqon" Jawad ya kar6i ledar,sannan yayi magana da p.a qasa-qasa, Inaas batasan me yace masa ba, tagade p.a din yajuya yabar wajan yanufi hanyar da mutane suka tafi wajan cin abinci. Saida yaga 6acewar p.a sannan yasake matsowa kusa da ita yasaka hannunsa ya ruqo nata hannun,lokacin d'aya sukaji wani irin shocking, Inaas tafara qoqarin qwace hannunta amma saiya sake riqe ta sakamakon wani irin laushi dayaji hannun nata yanayi,yaso ace su tabbata ahaka har zuwa wayewar gari,amma babu yanda ya iya,dole zaibarta tunda lokacin tashin su yakusa,ledar da p.a yakawo masa yadauka yasaka mata acikin hannun nata, sannan yazaro wani kati mai daukeda numbers dinsa ajiki yabata, yace"please ki gaida Mama,kifada mata nayi KEWAR TA " yana fada mata haka ya juya yabar wajan da sauri hannunsa zube cikin aljihun wandonsa yana tafiyar sa irinta qaqqarfan namiji ingarma. Inaas tabishi da kallo harya 6acewa ganinta sannan ta lumshe idonta tasaki wata irin ajiyar zuciya,taji kanta yasara,gumi ya wanke mata goshi kasancewar bata ta6a yin kusanci dawani namiji kamar haka ba,sannan wani namiji bai ta6a riqe mata hannu ba,kafin tagama tunanin taji muryar Hajiya Halima wadda p.a yaje yaturo ta wajan, tana cewa"Inaas mekikeyi anan ke kadai? zomuje mutafi kici abinci kowa yana can banda ke" Inaas ta kalleta sannan taja ta tsaya ta ajiye ledar hannunta aqasa, sannan tafara qoqarin cire sarqar da Jawad yasaka mata tana cewa"wannan sarqar cire ta zanyi, babu ruwana wallahi Abbana dukana zaiyi idan yaji waye yabani" Hajiya Halima data riga tasan komai saita nunawa Inaas kamar bata ganeba tace"sarqar mecece wannan din, waye yabaki?" Inaas ta kalleta kamar zata fashe da kuka cikin rawar murya tace" shine yabani,Yalla6ai Jawad ne" Hajiya Halima tayi murmushi tace"to meyasa zaki cire? kinsan darajar wannan sarqar kuwa? to kudinta albashin kine na duka tsawon rayuwarki,ai kyauta ce, babu kyau maida hannun kyauta baya,shima Abban ki ai yasan kyauta ce bazai miki komai ba,karki yi kuka kinji,zomuje kici abinci naji manager yana cewa munkusa tashi" Inaas ta gyada kanta sannan tayi sauri ta maida qwallar idonta, ta dauki ledar daya baya suka tafi,kafin su qarasa Hajiya Halima tace"menene acikin ledar?" Inaas tabata ledar tace" nima bansani ba" Hajiya Halima ta bude ledar taga kwalin waya ne sabuwa dal,wayar sak irinta Jawad ce,tayi murmushi tace"ai waya ce,ungo jakata ki riqe saiki saka wayar taki aciki karma mutane su ganki da leda suce waye ya baki" Cikin sauri Inaas ta kar6i hand back din tata, tajefa kwalin wayar aciki, sannan ta rataya jakar a kafadarta suka tafi wajan cin abincin,suna zuwa kuwa taga kowa sabgar gabansa yake anata ciye-ciye,Yalla6ai Jawad yana can qarshan table din yana cin abinci cikin nutsuwa ko dago ido baiyi ya kalli inda Inaas take ba,bazaka ta6a cewa akwai wani abu a tsakanin suba,kokadan bai bada wannan damar ba,inka dauke manager,Hajiya Halima,p.a dakuma guards dinsa, babu wanda yayi zargin wani abu. Abincin ma dan kad'an taci, ko yaya tayi motsi sai yanayin su na dazu itada Yalla6ai Jawad yafado mata,ko minti ashirin batayi da zama ba,sukai shirin tafiya,har wajan motocin dazasu shiga Jawad da tawagar sa suka musu rakiya,p.a yabi kowa a cikinsu yabasu envelop wadda kana gani kasan kudi ne aciki,saide envelope din Inaas daban take. Jawad yana tsaye daga can gefe shida guard,hannunsa guda daya yana cikin aljihun wandonsa,fuskarsa babu fara'ah haka idonsa yana sanye da glass jan duhu, yana ganin yanda p.a yake sallamar su,gaba daya ya tattara nutsuwar sa akanta,haka idonsa akanta harta shige cikin mota sannan yayi ajiyar zuciya yajuya ciki, suma aka dauke su aka nufi Airport dasu,acan Airport dinma basu wani dade ba jirgin su yatashi suka nufo jamhuriyar Niger. *** *** *** Niger Republic tana gama shanya kayanta tawuce zata shige daki,cikin sauri Man Sulaiman yatashi yabi bayanta ya tsugunna yariqe qafafunta yana kuka,tanajin yanda hawayen sa yake d'iga akan qafarta. Farouq yana zaune agefe saiya gyara zamansa ya kishingid'a yana daga kwance yana kallonsu uffan baice musu ba. Bilkisu taja qafarta taja takasa qwace wa daga ruqon dayayi mata,cikin kuka yace"Bilkisu dan Allah ki yafemin, Bilkisu nasan cewa nime laifi ne a wajanki,kiyi haquri ki yafemin,Bilkisu idan baki yafemin ba haqqin ki bazai daina bina ba,dan darajar Annabi Muhammad s.a.w Bilkisu kiyi haquri kidawo mugina sabuwar rayuwa domin ingoge kuskuren dana aikata miki Abaya,naje gida neman ki,anfada min cewa kintaho nijar,Bilkisu nazo nan qasar nayi kwana biyu ina neman ki, bansameki ba,sannan acan gida sun fad'a min cewa kin haihu,kin haifi da namiji,Bilkisu ina gudan jinina yake nima in ganshi ko zanji dadi?" Kallonsa tayi fuska babu alamun karaya tace"Manu,saboda ka hadani da darajar Allah da ma'aiki ne yasa nayima magana,amma banda haka, banida wata alaqa dakai dazata sa magana ta hadamu,yaro dakake tambaya ka dade da salwantar da danka,ta dalilin ka na rasa dana,Manu bazan ta6a yafema ba, tun kafin in dauko wuqa Manu ka sakarmun qafata inwuce"(😳🙆🏻‍♀️) Manu yajuya ya kalli Farouq dayake kwance yana jinsu kamar baya wajan,cikin hawaye yace"Farouq kasa baki dan Allah, katayani neman yafiyar Bilkisu,inaso tabani dama nagyara kuskure na,tun bayan barin Bilkisu daga cikin rayuwata har yanzu bana bacci cikin nutsuwa,katayani bata haquri Farouq" Kafin Farouq yayi magana Bilkisu ta waiga gefenta tazaro wata wuqa tanufo Manu da wannan wuqa gadan-gadan.(🙆🏻‍♀️) Cikin sauri yasaki qafarta yayi baya,cikin 6acin rai tasa gefen zaninta ta goge inda yasa hannu yariqe mata qafar sannan tayi wani irin tsaki tashige ciki tareda rufo qofar. Wani irin kukan baqin ciki da nadama yakama Man Sulaiman, duk irin soyaiyar da Bilkisu take masa yau shine take goge inda hannunsa ya ta6a jikinta, rayuwa kenan. Farouq yatashi zaune yace"katashi kaje,idan tahuce saika dawo kuci gaba"(😂🤭) Manu ya kalli Farouq yatashi ya futo daga gidan yana goge hawayen idonsa, yarasa Ina Farouq yanufa,da alama yana goyon bayan yayarsa,shida ya nemi taimakon sa maimakon yabata haquri wato shine yake cewa yatashi yaje idan tahuce saiya dawo suci gaba,bashida niyar bata haquri kenan saide yadawo suci gaba daga inda suka tsaya. Tunda Manu yafice yabar gidan, Bilkisu bata sake futowa tsakar gida ba, tana daki tana uzurin ta,saide in an kira sallah zata futo tayi alwala saita juya takoma daki, Farouq yanaso yayi mata magana amma kuma yana shakkarta,saboda yasan halin yayar tasa zata jima tana haquri dakai amma inde kakai haqurin ta qarshe to tana daukan zafi sosai, hakan yasa baice da'ita uffan ba,har saida aka kira sallar magrib yaje yayi sallah yadawo, anan yaganta ta shimfida babbar tabarma tana zaune a tsakar gida da 'yar qaramar wayarta a hannunta tana danna wa,zama yayi shima a gefenta sannan yace"yaya yanzu mekike ganin za'a yi?" Bilkisu ta kalleshi tace" game dame kenan?" Farouq ya daure duk da yana shakkarta ya cije,ya dake kamar baya tsoron yimata magana sannan yace"dangane da Manu,agidan Alhaji Auwal nahadu dashi,ban bashi fuskar dazai min doguwar magana ba,ashe ya biyo bayana bansaniba,tun acan gidan Alhaji Auwal din naga nadama acikin idanuwan Manu,ni aganina Yaya da kinyi haquri kin saurare shi tunda bakisan dame yazo ba,bakisan dalilin da yasa ya gudu yabar kiba,Yaya ubangijin daya haliccemu mafa muna aikata masa laifi wani da saninmu, wani babu saninmu, amma kuma idan muka roqeshi gafara yana gafarta mana,kiyi haquri Yaya kibashi dama kamar yanda yafada din domin ya wanke laifin sa a wajanki, tsawon shekarun nan dakika rabu dashi har yanzu babu wani namiji dakika bawa dama ya aure ki,aganina ki koma gidan uban danki,kuci gaba da Addu'ah har Allah yasa idan da rabo kuga d'anku". Bilkisu ta kalleshi tace"kagama?" Duk da yana shakkarta haka yadago ya nuna mata shi cikakken namiji ne ya kalleta babu alamun tsoro yace"nagama saura naki" Bilkisu tace"to tunda sauran nawane,saika barni inyi abinda nayi niyya, Farouq da alama bakada hankali,mutumin daya gudu yabarni da tsohon ciki,na mutu kona rayu duk daya awajansa,shine kake cewa in koma gidansa? dana dauki shekaru naqi yin auren cemaka akayi Manu nake jira? ta dalilin safa nataho nan, har na rasa Muhammad dina,yanzu shi Manu in banda tsaurin ido irinna maza har yanada qwarin gwiwar dazai iya kallon idona yace in koma gidansa? yanda yasa nayi asarar d'ana shima yayi asara ta wallahi" Ta qarasa maganar tana karkad'a qafa. Adede lokacin Inaas tayi sallama tashigo gidan, manager ilyasu yana bayanta. Cikin murna ta qarasa ta rungume Ammiy,Bilkisu tabita da kallo ganin kayan data fita dashi ranar dazasu tafi, ba shine ajikinta ba,Inaas ta kalleta dakyau tace"Ammiy meya sameki naga kamar kina cikin damuwa?" Bilkisu tayi shiru kamar bataji tambayar da Inaas din take mata ba, tajuya suna gaisawa da Ilyasu manager, Abba ma yabashi hannu suka sake gaisawa, yayinda Ammiy tatashi takawo masa ruwa. Ilyasu yasha ruwan sannan ya kallesu yace" to Malam Farouq kamar yanda nayi alqawari gashi nacika,nadawo da Inaas gida lafiya,kuma Yalla6ai Jawad yace yana sake yimuku godia Allah yabar zumunci" Farouq yayi murmushi yace"qwarai kacika alqawari,sannunku da zuwa,Yaya hanya to?" Ilyasu yace"Alhamdulillah hanya lafiya,mungode sosai, bari in wuce" Ammiy tace"har tafiya zakayi?" Ilyasu yace"eh wallahi naga dare yayi" Inaas tatashi ta rakashi qofar gida sannan tadawo gidan ta zauna ta kalli Ammiy tace"Ammiy meyake damunki?,waye yata6a min ke?" Kai tsaye Bilkisu tace"Sulaimanu ne yazo" Cikin rashin sani Inaas tace"waye Sulaimanu?" Bilkisu tace"tsohon mijina,Baban Muhammad" Cikin sauri Inaas tace"kaiiii Alhamdulillah,wallahi naji dadi Ammiy inama ace ina nan yazo dana ganshi, dama ban ta6a ganinsa ba" Bilkisu ta kalleta da tsananin taqaici sannan tace"toke da miye hadinki dashi dakike wani washe baki kina cewa baki ta6a ganinsa ba? d'ansa na cikinsa ma bai taba ganinsa ba tunda guduwa yayi yabarshi tun kafin yazo duniya"(🤭😂) Inaas tanajin wannan amsa da Ammiy tabata saita nutsu tayi shiru,da alama akusa take,saida ta dauki minti biyu sannan ta sassauta murya alamar lallashi tace"Ammiy,koba komai shifa Baban danki ne,kin riga kin hada alaqa dashi tunda duk runtsi idan an ganshi za'a ce shine Baban danki,Ammiy bansan ki da fishi ba,kiyi haquri ki yafe masa Allah yanason ba yinsa masu haquri Ammiy" Hawaye yacika idon Bilkisu,tanaso ta tsaida su amma saida sukai nasarar zubowa ta kalli Inaas tace"Inaas ta dalilin sa fa narasa Muhammad dina,kema kin goyi bayan mutumin daya gujeni saboda talauci?" Inaas ta matsa ta rungume ta sannan tace" Ammiy idan da ya gujeki saboda talauci ai har yanzu mu d'in talakawa ne,yanzu ma ai gashinan yadawo gareki duka de acikin talaucin" Bilkisu batace komai ba ta dauki ruwan da manager yasha yarage, ta matsa gefe ta wanke idonta, sannan tayi ajiyar zuciya ta kalli Inaas tace"ya hanya? Ina Jawad yake? yana lafiya?" Cikin sauri Inaas tace" yana nan kalau Ammiy,shima muna haduwa yace ina kike? kuma wai ince miki yayi KEWAR KI" Bilkisu tayi murmushi tace"Allah sarki Jawad yaron kirki,Allah de yayi masa albarka,Allah yakare shi aduk inda yake" Farouq ya kalleta da tsananin mamakin yanda take zubawa Jawad Addu'ah saikace wani d'anta. Inaas tayi murmushi tace"Amin" Sannan ta dauko ledar gefenta tace"wannan ma shine yabani,harda sarqar wuyana" Bilkisu da Farouq suka bude leda,tsaleliyar wayarta qirar iPhone tafuto fili,Farouq ya jujjuya wayar yagani sannan ya ajiye,yabude envelope din daya gani aciki,daloli suka bayyana sababbi fil amiqe" Cikin sauri Bilkisu ta zaro idonta waje tace"duk wannan din na menene haka? wannan dalar amurka cefa,mezaki da wannan uban kaya? sarqar wuyan naki ma naga kamar sarqar gold ce" Inaas tace"eh haka Hajiya Halima ma tace,waita gold ce, kuma tanada tsada" Bilkisu ta jinjina kanta sannan tace"tab lalle Jawad yayi qoqari,wannan kashe kudin ai yayi yawa,kinga yanzu shikkenan kema kinyi waya saiki dauka kije daki idan ankawo wuta saiki saka caji" Farouq yayi sauri yaja wayar gabansa yace"ta dauki me?, wai Yaya kina tunanin a banza zai kashe mata wannan uwar dukiyar ne? dole akwai abinda yake nema a wajanta,saboda haka ba zatayi amfani da wannan wayar ba,kudin ma a ajiye shi duk lokacin da Allah yasa suka sake had'u wa adauki kudinsa a bashi,ni tsoron masu kudin nan nake,bare kuma shi Jawad din kansa,yaron nan ranar da akai rasuwa agidan Alhaji Auwal ina ganin yanda manyan qasar nan suke zuwa har gabansa su rissina su gaidashi nasan cewa ba qaramin mutum bane,saboda haka gaskiya ina tsoron wannan al'amari Yaya" Bilkisu ta kalleshi tace" Farouq bangane ba zatayi amfani da waya ba, Jawad nefa yabata" Cikin sauri Farouq yace"shi Jawad din Muhammad dinki ne? ni Yaya kwata-kwata nakasa gane miki akan wannan yaron,daga ganin yaro sau d'aya shikkenan kin dauki yarda kin bashi,haka lokacin da yarinyar nan tazo da batun tafiyar nan tasu kika daure mata gindi wai ai Jawad ne babu komai kawai taje ta yaron yanada nutsuwa,Yaya kidawo hayyacinki Jawad fa ba Muhammad dinki bane bare kiyi masa shaidar kirki" Bilkisu ta kalli Inaas tace" ai shikkenan, ke sai kiyi haquri da wayar,idan Jawad din yazo karma ki masa zancen waya,nida kaina zan fada masa cewa ubanki ya hanaki amfani da wayar saboda yana zarginsa"(😂🤭) Inaas tatashi tawuce ciki ta dauki buta tashige bandaki, yayinda Farouq yadauke wayar da envelope din kudin yayi cikin dakinsa dasu yana mamakin yayar tasa akan wannan Jawad din,har yanzu de dayayi mata wannan dogon bayanin ita bataga laifin Jawad din ba. Da daddare bayan ta watsa ruwa taci abinci ta kwanta tayi shiru tana tunanin sa aranta,sarqar daya daura mata takamo ta riqe da hannunta tana shafa sarqar tana tuna lokacin datake saka masa cake abaki,ta tuna d'an qaramin lips dinsa wanda yake kama da nata lips dinta,ta tuna kyakykywan sajen daya sake qawata fuskarsa,tayi murmushi tasake gyara kwanciyar ta,ahankali tayi magana can qasan maqoshinta tace"yalla6ai Jawad ya had'u sosai,maqurar had'uwa shidin had'ad'd'e ne". (Inaas yadai🤔) Mutara zuwa gobe🙏🏻 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME DEBE KEWA,300 ne kacal,ba dubu daya bane ba dari biyar bane 300 ne kacal idan kika karanta ba tareda kin biya ba keda Allah saboda ban yafe,ki biya ki karanta cikin salama👌🏻 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034. Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 ___ Yau kwana biyu kenan da dawowar Inaas gida,tun ranar data tafi Jawad yake saran zata kirashi,yanason jin muryarta, yanason yasake magana da matar data had'a masa shayi koda na second biyar ne,yanason jin muryar matar sosai,baisan meyasa matar ta tsaye masa arai ba,yanajinta wata ta daban acikin zuciyarsa. Yafi minti talatin yana zagaye dakinsa dagashi sai dan qaramin gajeren wando,hakan daya tsaya shine yasake baiyana qaqqar fan jikinsa cikinsa har wani hawa-hawa yake kamar dan wasan dambe,ayyukan sa da sukai masa yawa hakan yasa baya riqe wayarsa wayoyin suke tsayawa awajan p.a, amma yau wayoyin suna hannunsa saboda yana tsammanin kiran Inaas,amma haka yagaji da zagayen dakin yagaji bata kiraba,cikin damuwa yashiga wanka yana addu'ar Allah yasa ya futo daga wanka yaga missed call dinta. *** *** *** Abuja Nigeria Daddy ya kalli Man Sulaiman yace"yanzu kaga Man Sulaiman wannan auren damuka dawo shekaran jiya, naso ace Jawad ya auri wannan babbar yarinyar fauziya,saboda batada hayaniya,zasu zauna lafiya,kuma zumuncin mu zai sake qarfi tsakani na da Aminina Alhaji Auwal saboda tun muna matasa tare muka fara fafutukar kasuwanci dashi har Allah yadafa mana,to amma kasan halin yaron naka firrr yaqi, gashi har tayi aurenta" tunda Daddy yafara wannan maganar kwata-kwata Man Sulaiman baisan me Daddy yake fada ba,zuciyarsa tatafi wajan Bilkisu, tun bayan tahowarsu daga Niger kowanne cikin dare baya bacci sallah kawai yake yana sake godewa Allah akan bayyana masa Bilkisu dayayi. Daddy dayaji shiru yajuyo ya kalli Man Sulaiman yana nazari a kansa,kafin yayi magana wani gurd yazo wucewa sukaci karo da Man Sulaiman, sai alokacin Man Sulaiman yadawo hayyacinsa,cikin sauri yabawa guard din haquri,Daddy yayi ajiyar zuciya sannan yaja hannun sa suka qarasa wajan wasu had'ad'd'un kujeru farare wanda suka qara qawata grass carpet din wajan, suka zauna sannan Daddy yace"Man Sulaiman meyake damunka? tun dazu inama magana amma hankalin ka baya kaina kwata-kwata,tunanin mekake haka?" Man Sulaiman ya kalli Daddy yace" wallahi Alhaji cikin matsal..." kafin ya qarasa cewa matsala wani irin kuka yazo masa,bai iya hana kansa ba saida ya rushe da kuka,Daddy yace"Subhanallah,Man Sulaiman kuka fa kake,meyake faruwa ne?" Man Sulaiman yagoge hawayen idonsa yace"Alhaji zuwan mu Niger naga matata,da qyar nasamu qwarin gwiwar kallonta,na roqi tayafe min taqi,na roqi Alfarma tayi haquri tazo mu zauna domin in wanke laifina a'idon ta amma bata bani damar hakan ba" Daddy ya jinjina kansa ya kalli Man Sulaiman yace"amma ka tabbatar ita kagani da idonka Man Sulaiman?" "itace Alhaji,ko shekara dubu nayi,inde zan sake dora idona akan Bilkisu to tabbas zan ganeta,itace" Daddy yace"to amma ina labarin yaron data haifa? ka ganshi?" Man Sulaiman ya girgiza kansa,wani sabon hawaye mezafi yazubo masa,yace"bangan shi ba,banasa ran zan ganshi inajin saide a lahira,domin kuwa Bilkisu ta tabbatar min da cewa yaron ya salwanta, sannan nima banga kowa agidan ba bare ince shine,daga ita sai qaninta Farouq,haka shima dan'uwan nata naga yana goyon bayanta" Daddy yace"Subhanallah,Hasbunallahu wa ni'imal wakeel,haqiqa Man Sulaiman kana ganin qaddara,kayi haquri kayi Addu'ah har Allah yabaka damar cinye wannan jarabawa,maganar qaninta kuma dole zaibi bayan yar'uwarsa,saboda abunda yafaru aiba qarami bane,yanzu kayi haquri kaje ka kwanta kahuta, qwaqwalwar ka tasamu nutsuwa,gobe da sassafe saika shirya muje,zanje dakaina zamu taru mubata haquri insha Allah komai zai wuce" Cikin sauri Man Sulaiman ya tsugunna zaiyi wa Daddy godia,Daddy yayi sauri ya ruqo kafadunsa yace"A a tashi-tashi, ai mun zama daya Man Sulaiman, babu damuwa kaje kahuta" Malam Manu yasake yiwa Daddy godia sannan yatafi,shima Daddy yawuce ya qarasa ciki. Yana zama afalo yakira Yaya Mariya,yayi magana da da'ita, Hajiya Zaliha tazo takawo masa ruwa yadauka yasha,ta zauna akusa dashi ta kalleshi tace"Alhaji lafiya de ko? naga kamar akwai abinda yake damunka" Daddy yayi ajiyar zuciya yace"wallahi batun Man Sulaiman ne yake ta6ani,yana cikin matsala,yana buqatar taimakon mu" Hajiya Zaliha tace"meyake faruwa haka Alhaji?" Kafin Daddy yayi magana Yaya Mariya tashigo falon nasu a fujajan, tanemi waje ta zauna tace"Aliyu meyake faruwa haka katasoni daga gida Ina fatan de bawani abune yasamu Fu'ad da Jawad ba?" Hajiya Zaliha tace"Yaya nima yanzu naganshi haka kamar marar lafiya,nayi masa magana yace lamarin Man Sulaiman ne" Daddy yayi ajiyar zuciya sannan ya kwashe komai yafada musu tun daga farko duk da sunsan labarin Man Sulaiman din,sannan ya qarasa da fadin"yanzu maganar danake muku daurin auren da mukaje Niger gidan Alhaji Auwal,to yaga matar tasa,saide yabata haquri taqi haqura,maganar cikin daya gudu yabarta dashi kuma ta tabbatar masa cewa yaron ya6ata, ta nemeshi ta rasa" Gaban Hajiya Zaliha da Yaya Mariya yayi wata irin bugawa,lokaci d'aya suka hada baki wajan fadin"ya6ata?" Daddy ya jinjina kansa alamun tabbatar wa. Lokaci d'aya Hajiya Zaliha tafashe da wani irin kuka,cikin kuka tace"ni de wallahi ba Jawad dina bane,suje can su nemi d'ansu" Yaya Mariya ta daka mata harara tace"da kina son nasa amma kika fifita danki a kansa? idan Fu'ad ne zaki masa abinda kika yiwa Jawad ne?" Daddy ya girgiza kansa sannan yayi murmushi irinna manya ya kalli Hajiya Zaliha yace"wacce irin magana kike haka Zaliha? daga cewa yaron Man Sulaiman ya6ata shikkenan saiki kawo maganar Jawad? yara nawane suke 6ata anemesu arasa wasu a asbiti wasu azo har gida asace su, wasu kuma wata qaddarar tasa arasa su, sai kawai wannan ne zai zama dansu? kokadan ni ban kawo hakan araina ba, ko wani waje najeni naji mutane suna maganar Yara yan tsuntuwa kokadan bana kawo Jawad a cikinsu,manta wa nake cewa ba nine na haife shi ba, kuma ina fatan inci gaba da wannan mantuwar har abada,sannan bamusan dalilin 6acewar nasu d'an ba,kuma bana sonji,ina tsoron ranar da Jawad zaisan cewa ba nine mahaifin sa ba, tabbas ina tsoron wannan ranar, yanzu abinda yasa nataraku anan shine inaso ku shirya muje mutaru abawa wannan baiwar Allah haquri tayi haquri tazo suci gaba da zama da Man Sulaiman" Yaya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"to Allah yarufa asiri,Allah yabaiyana mata d'anta, idan kuma ya mutu Allah yaji qansa ,idan yana raye Allah yasa yana gidan da zasu riqe shi kamar dansu,kar ayi masa irin ruqon Jawad"(🤭) Ta qarasa maganar tana hararar gefen Hajiya Zaliha. Daddy ya girgiza kansa yace"yaya ayi haquri mana,kuskure de anriga anyi,kuma Zaliha ta tuba,inada yaqinin insha Allah zuwa gaba bazata sake aikata haka ba" Yaya Mariya tayi ajiyar zuciya tace"Allah yasa,yanzu yaushe zamu tafi?" Daddy yace"gobe dasafe insha Allahu" *** *** *** Niger Republic "Inaas yaufa kin makara,tun dazu kike nuqu-nuqu bazaki futo kitafi aiki ba,a'irin haka ne wancan lokacin kikaja suka koreki ai" Farouq daya futo shima yana sake gyara nad'in rawaninsa na asalin buzaye ya kalli Bilkisu yace" a a, Yaya kuda kuke da Jawad,aina zata sai wajan azahar zaki mata magana tafuto tatafi aikin"(😂) Bilkisu ta kalleshi ta gyada kai ganin magana yafad'a mata saboda yaga tana son Jawad din,tasake daga murya tace" 'yar me gwanjo bazaki futo kitafi ba kinaji ana fada mana magana?" Inaas tafuto tayi kyau sosai cikin shigar ta ta kullum wato laffaya,dan qaramin bakinta taturo gaba tace" kai Ammiy dan Allah, kuma har yanzu de wannan sunan yana nan?" Kafin Bilkisu tayi magana,akayi sallama aka shigo gidan,Alhaji Auwal ne agaba,sai Alhaji Mekudi,Hajiya Aisha matar Alhaji Auwal,Hajiya Zaliha, Yaya Mariya,dakuma Man Sulaiman a qarshe. Inaas taja ta tsaya ganin baqin fuska sai shigo musu gida suke,Bilkisu tana ganin Man Sulaiman tayi sauri ta dauke kanta kamar bata ganshi ba. Farouq kuwa yana ganin uban gidansa wanda yake yiwa yaransa lesson wato Alhaji Auwal,cikin sauri ya qarasa wajansa yace"Alhaji sannunku da zuwa" Alhaji Auwal ya kalli Farouq yace"A a,Uncle din yara wai dama gidanka mukazo?" Farouq yace"eh Alhaji,ai anan nake" Yajuya ya kalli Inaas yace"Ke shimfida musu tabarma" Inaas ta ajiye jakar hannunta sannan ta dauko babbar tabarma ta shimfida. Hajiya Zaliha tunda suka shigo idonta yake kan Inaas,kyawun yarinyar da nutsuwar data gani atare da'ita lokaci d'aya ya fuzgeta har taji tana yiwa Jawad sha'awar ta(😲) Tana so ta wanke laifin datayi wa yaron ta hanyar nema masa matar data dace. Zama sukai Inaas ta gaida su sannan ta wuce zata tafi aiki,Alhaji Mekudi ya kalleta yace"dawo ki zauna mana,ina zakije haka?" Inaas tayi murmushi tadawo ta zauna acan gefe kusa da Bilkisu. Bayan anyi gaishe-gaishe Alhaji Auwal ya kalli Alhaji Mekudi, sannan ya nuna Abban Inaas yace"Alhaji wannan shine yake yiwa yarana lesson,kullum zaije sugama karatunsu sannan yayi mana sallama yatafi" Alhaji Mekudi yayi murmushi ya kalli Hajiya Aisha matar Alhaji Auwal yace"Hajiya kice zanyi muku fashi" Hajiya Aisha tayi murmushi tace"aiba komai Alhaji" Duk wannan abun dasuke kan Bilkisu yana qasa,batasan dalilin da yasa Sulaimanu ya kwaso mata wannan gayyar yakawo mata ba. Yaya Mariya ta kalli Alhaji Mekudi tace"Bissmillah Aliyu" Alhaji Mekudi yadago kansa ya kalli Bilkisu,tun a fuskar ta yasan cewa da alama tanada haquri,tanada innocent face,yanaso ya roqeta amatsayin sa na Alhaji Mekudi,mashahurin mutum wanda babu wanda baisan dashi ba afad'in Africa da kewayanta, saide bayaso tayi masa Alfarma amatsayin kasancewar sa wani babban mutum,gara tayi masa Alfarma amatsayin sa na mutum kamar kowa,hakan yasa ya6oye mata cikakkan sunansa na Alhaji Mekudi, yadubeta yace"Bilkisu Sunana Alhaji Aliyu,ni mutumin Nigeria ne,atare dani akwai Yayata uwa daya uba daya,gakuma matata Zaliha,inada yarana guda biyu maza,sannan nazo qasar nan ne nida dangina saboda ke....,bayan mun sauka a Airport naqarasa gidan Aminina gashinan a zaune Alhaji Auwal da matarsa Hajiya Aisha,kamar yanda nace munzo qasar nan ne saboda ke,to saboda ke din mukazo amma ta dalilin Man Sulaiman..." Bilkisu tanajin haka qwalla tacika idonta,batason mutane su shiga cikin matsalar ta itada Sulaimanu ,menene amfanin kawo mata wannan mutanan? shida ba mutumin arziqi ba tayaya ya hadu da mutanan arziqi? Inaas tanajin wannan Alhaji yace sunzo ta dalilin Man Sulaiman tasan cewa Man Sulaiman dinnan shine Manu mijin Ammin ta,ahankali tadago kanta ta kalleshi, kansa yana qasa,cikin nutsuwa tatashi tashige daki ganin maganar tasu ta manya ce,saide daga cikin d'akin tana Iya jiyo abinda suke fada. Alhaji Mekudi yayi ajiyar zuciya yaci gaba da fadin"Bilkisu gaba dayan mu munzo ne domin mu taya Man Sulaiman baki haquri,dukkan mu munsan komai,munji abinda yamiki, sannan munji batun 6atan yaro muna qara baki haquri,haqiqa kinyi haquri,amma inaso ki qara haquri,ki qara haquri Bilkisu,Man Sulaiman din dakika sani abaya,yanzu bashi bane,yatuba yayi nadama Bilkisu,inaso ki yafe masa sannan keda d'an'uwanki da yarinyar ki muna so kubimu mukoma Abuja muzama ahali d'aya,domin kuwa ni Man Sulaiman kamar dan'uwana na daukeshi,shekaru talatin da bakwai dasuka wuce direba na yakadeshi,nafuto daga mota na bashi haquri,nace a kaishi gidana, bayan wasu kwanaki nazauna dashi,yayimin bayanin dalilin da yasa yabar ki,kuma ko alokacin akwai tsantsar damuwa atare dashi,kiyi haquri Bilkisu,ki yafe masa, sannan ki kar6i roqona inaso na maida aurenku kuci gaba da rayuwa kamar baya" Tsakar gidan yayi tsit bakajin motsin kowa sai kukan Bilkisu dake tashi,sosai take kuka harda shashsheka,Yaya Mariya ta kalleta cikeda tausayi tace"kiyi haquri Bilkisu,karki duba baya,idan kikace zaki tuna baya, bazaki iya yafe masa ba" Bilkisu dake faman kuka ta gyada kanta alamun amsawa sannan tace"nayafe masa Alhaji...,Allah ya yafe mana baki daya" Cikin sauri Man Sulaiman ya goge hawayen idonsa yanajin wata irin nutsuwa tana kwaranya acikin zuciyarsa. Alhaji Mekudi yayi murmushi yace"to Alhamdulillah,kin kyauta,Allah yasaka miki da Alkhairi,to Yaya batun mayarda auren ku?" Bilkisu ta goge sauran hawayen ta idonta,fuskarta ba yabo ba fallasa tace" a a,abar wannan maganar Alhaji" Alhaji Mekudi yasake yin murmushi,ya kalli Hajiya Zaliha,kafin yayi magana Hajiya Zaliha tace"Bilkisu mungode sosai,Allah yasaka da Alkhairi,maganar aure baza'a tilasta miki ba,zamu baki lokaci duk lokacin dakika ga yadace saiki taimaka ki koma dakin ki,amma yanzu de maganar tafiya tare daku zamu tafi,muna fatan kun yarda damu kuma zaku bimu" Bilkisu ta kalli Farouq tace"kuyi magana dasu" Farouq ya kalli Alhaji Mekudi yace"Alhaji bazamu dora muku nauyi ba? tayaya harmu uku zamu tashi daga wata qasa mu koma gidanku cinmu da shanmu yahau kanku?" Alhaji Auwal yayi murmushi yace"Uncle din yara karka damu,tunda abokina ne da kansa yace ku koma, to banaso ku watsa masa qasa a'ido,ku daure kutafi tare dasu" Farouq ya kalli Alhaji Mekudi yace"to Alhaji mungode,Allah yasaka da Alkhairi,Allah yaraya bayanka,mungode" Alhaji Mekudi yace" a'a babu damuwa,ai mun zama daya,Man Sulaiman yawuce haka awajena" Ya kalli Alhaji Auwal da Man Sulaiman yace"muje waje mubasu waje su shirya saimu wuce ko?" Alhaji Auwal da Man Sulaiman da Farouq duk suka fice,a kabar iya matan agidan. Bilkisu tashiga daki domin tarkata yan kayansu,Hajiya Zaliha tamiqe tacire Mayafin ta tace"bari naje nataya ta had'a kayan" tafadi haka tana shigewa cikin falon nasu,Yaya Mariya ta miqe qafa a tabarma tacire mayafi tadaga murya tace"Zaliha bafa komai zaku dauko ba,kawai Iya d'an abun amfani wanda suke so zaku dauka,amma karsu dauki ko sutura,idan munje can sai ayi musu wasu" Hajiya Zaliha tace"eh Yaya nagane" Yaya Mariya tasake daga murya tace"ina yarinyar nan take ne,zoki bani buta nakama ruwa" Inaas tafuto da sauri tazubo mata ruwan takawo mata,Yaya Mariya ta kalleta tace"yanmata ya sunan kine?" Inaas tayi murmushi tace"Sunana INAAS" Yaya Mariya tace"masha Allah,munzo zamu rabaki da samarin ki ko? karki damu zaki samu wasu samarin a Nigeria,muma munada samari guda biyu a gidan namu sai wanda kika za6a"(🤭) Hajiya Aisha da hankalin ta yake kan waya ta dago ta kalli Yaya Mariya tace"haba Yaya,haka yayan nawa suka koma kuma?" Yaya Mariya tace" ato tunda sunqi sukawo matar aure ai kinga sai yan matan sufara tsabar su" Inaas tayi murmushi takoma daki sukaci gaba da hada yan kayansu,duk abinda Ammiy ta dauko sai Hajiya Zaliha tahanata dauka acewarta basa buqatar komai,zasu samu komai acan,bawani kayan kirki suka dauka ba,yawanci abubuwan su ne masu muhinmanci, musanman Bilkisu ba komai ta dauka ba sai photunan Muhammad dinta wanda aka masa tun lokacin haihuwar sa. Agurguje suka kammala komai,Ammiy da Inaas da Hajiya Zaliha suka shiga maqota sukai musu sallama,sannan Farouq yakira me gidan hayar yayi masa bayani zasu tashi,sannan suka dunguma suka tafi gidan Alhaji Auwal,acan suka huta sukaci abinci,Inaas takira wayar manager a wayar Ammiy tayi masa cikakkan bayani akan komawarsu Nigeria, takuma bashi haquri akan rashin sanar dashi da batayi ba dawuri itama abun yazo matane baga tatan, har yamma lis suna gidan Alhaji Auwal har saida aka nema musu tickets sannan sukai bankwana da Niger suka nufi Nigeria. *** *** *** Lokacin dasuka sauka dare yayi,amma duk da haka daga Bilkisu har Farouq da Inaas babu wanda bai tsorata da ganin girman gidan ba,Inaas da Bilkisu suka sake qanqame hannun juna ganin yanda sojoji suke shawagi a harabar gidan kowa hannunsa daukeda bindiga. Farouq kuwa duk da yana zuwa gidan Alhaji Auwal za'a iya cewa yasaba da ganin babban gida,saide bai ta6a ganin irin wannan gida gari guda haka ba,baisan cewa wannan shine katafaren gidan Alhaji Mekudi ba,baisan cewa wannan shine gidansu Jawad dinnan de dayace kada 'yarsa tayi amfani da kyautar sa ba. Daga Hajiya Zaliha har Alhaji Mekudi da Yaya Mariya saida suka rakasu har part dinsu dayake kusa danasu Hajiya Zaliha,Inaas tana liqe ajikin Bilkisu hannunsu yana cikin na juna sai kalle-kallen hadaddan falon suke, wanda yaji komai da komai najin dadin rayuwa,Alhaji Mekudi yace"to Alhamdulillah,Bilkisu wannan shine masaukin ku,akwai dakuna dayawa sannan akwai abubuwan buqata aciki,Man Sulaiman zai dawo nan shima yaza6i daki daya saikuci gaba da zama tare,sannan muna sake baki haquri akan duk abubuwan dasuka faru,yanzu ma kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki ku zauna tare damu" Bilkisu ta gyada kanta sannan tace"Alhaji mungode,wannan dawainiyar tayi yawa Alhaji,yanzu Ina zamu kai wannan uban dakuna da wannan tangamemen falo,Alhaji dame zamu saka maka?" Yaya Mariya tace"kuyi masa Addu'ah Bilkisu,ladansa yana wajan Allah" Farouq yace"gaskiya Alhaji badan badanba, zan iya cewa babu irin ka a duniyar nan,bamu hada dangi dakai ba,baka sanmu ba, amma kayi mana abinda ko wani dan'uwan namu ne ba zaiyi mana haka ba, mungode Alhaji,Allah yasaka da Alkhairi " Alhaji Mekudi yace"Haba Malam Farouq,yazakace kuba dangi na bane? ai nayi tunanin cewa tsawon shekaru talatin da bakwai danayi tareda Man Sulaiman munriga mun zama d'aya ni dashi,danhaka kuma daga yau kun zama ahalina,Allah yabamu zaman lafiya" Gaba dayansu suka amsa da "Amin" Daga nan Alhaji Mekudi yamiqe,Yaya Mariya da Hajiya Zaliha ma suka musu saida safe da niyyar idan sunje su aiko musu da abinci,Man Sulaiman yatashi yasaci kallon Bilkisu aikuwa karaf idonsu yahadu dana juna tayi sauri ta watsa masa wata irin harara,cikin sauri ya janye idonsa yabi bayansu Alhaji Mekudi. Farouq da komai yafaru akan idonsa ya kalli yayar tasa yasaki murmushi. Inaas tana ganin babu kowa tatashi tsaye cikin murna tafara warware laffayar jikinta tana duba d'akunan cikin farinciki tace"wayyo Allah Ammiy zoki gani wanne d'akin zamu za6a?" *** *** *** Yana tsaye acikin wani hadaddan jirgin ruwa yayi kyau sosai cikin qananun kaya nashan is'ka,wandon duka dukansa iyakar sa gwiwar sane, yayinda rigar ta kasance marar hannu,cikin ruwan yake kalla amma hankalinsa kwata-kwata baya wajan, kawai idonsa ne awajan,zuciyarsa da tunanin sa sun tafi wajan kiran waya,kowanne lokaci yana nan yana dakon ranar dazata kira wayarsa. Yayi ajiyar zuciya ya furzar dawata irin is'ka me zafi daga bakinsa,yadawo yanemi waje ya zauna,wata baturiya taqaraso tazuba masa lemo tajuya takoma cikin jirgin,Jawad bai kalli inda lemon yake ba yahade hannunsa biyu yayi tagumi, kana ganin fuskarsa zakasan cewa yana cikin damuwa. P.a ya kalleshi cikin girmamawa yace"yalla6ai lafiya kuwa?meyake damunka?" Batare daya kalleshi ba yace" ina cikin damuwa P.a,please ina buqatar ke6ewa" Yana fadin haka yatashi yakoma cikin jirgin yashige wani dan daki ya kwanta tareda lumshe idonsa. P.a ya girgiza kansa,tabbas koma menene wannan ba qaramin abu bane yake damun Yalla6ai Jawad,duba da ko yana cikin damuwa ba kasafai ake iya gane halin dayake ciki ba. Basu bar ga6ar ruwan ba sai yamma,kai tsaye gida suka wuce,Jawad yayi wanka yasake shiryawa cikin qananun kaya saide wannan lokacin wandon jeans yasaka amma tsawon wandon yadan wuce gwiwar sa da kad'an amma bai qarasa har can qasa irin kowanne wando ba,sai rigar me hade da hula wadda tasake qawata kyawun halittarsa. Waya ce a maqale a kunnansa yana waya da Mummy,adede wannan lokacin Mummy ta kaiwa su Bilkisu abinci itada yan aikinta, tadawo tayi wanka ta kwanta taji kiran Jawad din, a wannan lokacin qarfe tara na dare a agogon Nigeria,bayan sungama gaisawa tana so tafara yimasa zancen zuwansu Bilkisu,P.a yakawo masa waya,cikin sauri yayi mata saida safe yakashe ya kar6i wayarda P.a yake bashi dawani irin sauri yayi tunanin Inaas ce take kiransa (🤭) Yana dauka yaji ba'ita bace,lokaci daya 6acin rai ya bayyana a fuskarsa,tsabar baqin ciki ko magana yakasa yi,daga dayan 6angaren akace"Yalla6ai dama maganar wannan gwanjon kamfanin daka siya ne na Suleja, angama duk wani gyare-gyare nashi,an sabunta komai taron budewa kawai yarage sai batun aiki" Jawad ya runtse idonsa,sai yanzu ne yagane cewa haqiqa yarinyar nan tayi masa illa arayuwarsa da kuma kasuwancin sa,tunanin ta da begenta dakuma kewar ta yasa gaba daya yama manta da batun bude kamfanin da'akai gwanjonsa ya siya,batare daya bude idonsa ba yace"ok thank you I will call you back" Yana fadar haka ya wullar da wayar ba tareda yakashe taba. P.a ya kalleshi yasaka hannu yadauki wayar yakashe ta,sannan yakoma gefe yatsaya. Daya daga cikin guard daya fahimci kamar Jawad din yana cikin damuwa, ya qarasa ya kunna kayan kallo yakoma gefe,Jawad yazubawa TV ido yarasa meyake masa dadi,jiya ke a zuciyarsa idan baiji muryarta ba, to zai iya fuskantar wata matsalar a zuciyar sa. Tsawon lokaci yana kallo ganin babu abinda yake fahimta hakan yasa ya kalli p.a yace"P.a" P.a ya qaraso da sauri yace"na'am Yalla6ai" Jawad yameqa masa hannu sannan yace"bani computer" Cikin sauri p.a yabashi computer,yabude ta ya kunna sannan yakira Fu'ad vedio call. Fu'ad dayake kwance a dakinsa yana chatting kasancewar shabiyu na dare ne a agogon Nigeria hakan yasa yayi mamakin ganin kiran Yayan nasa, cikin sauri yadauka suka zubawa juna ido kowa yana ganin dan'uwan sa tartar babu alamun rashin network. Fu'ad yace"yaya baka kwanta ba? i hope you're feeling better" Jawad ya lumshe idonsa sannan yabude yace"yes,mekake yi yanzu?" Fu'ad yadan daga kafadarsa yace"nothing Yaya,just ina chat ne da friend's" Jawad yayi masa wani irin kallon kama raina min hankali,Fu'ad yayi murmushi ya shafa sumar kansa batare dayace komai ba,Jawad yace"ina Mummy dazu muna waya,munyi sallama da'ita da sauri-sauri,tana lafiya ko?" Fu'ad yace" she's fine,dazu suka dawo,kasan sunje Niger,da'ita da Daddy,da Hajiya Mama,da Uncle Sulaiman,wai ina tunanin kamar ko anga matar Uncle Sulaiman din ne,ina tunanin haka de gaskiya, ban tsaya na saurari zancen nasu ba" Cikin rashin damuwa Jawad yace"ok,yayi..." Kafin yaci gaba da magana p.a yakawo masa waya yace" Yalla6ai ana kira" Cikin sauri Jawad yakashe computer tasa sannan yarufeta, yatashi tsaye ya kar6i wayar,gaba daya tunanin sa yagama bashi Inaas ce ta kirashi,hakan yasa bayan ya kar6i wayar idonsa ya rufe ko number bai kalla ba,yad'an matsa gefe d'aya yasake sassauta muryar sa yace"Barka da dare" Daga dayan bangaren yaji muryar wani Baturen qasar America yana masa magana,Jawad yanajin haka yaji kansa yasara,yanzun made ba ita bace? ahankali yasake lumshe idonsa,yayinda yaji wani irin jiri yana d'ibarsa,duk yanda yaso yatsaya da qafafunsa yaji ko kad'an yakasa hakan,lokaci daya yazube awajan. Cikin sauri p.a yasaki wayar hannunsa yayi kansa shida sauran guards din dasuke tsaye afalon,cikin tashin hankali p.a yafara jijjigashi yana fad'in "Yalla6ai!! Yalla6ai!!!" (Hmmm to P.a,yaufa Yalla6ai saide kuyi haquri domin kuwa Inaas ta kwantar mana dashi 🤒😘😗) ( new P.a kina ina haka abubuwa suka fara ta6ar6are muku?🤔😂 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍ [1/20, 08:44] My Number: ME DEBE KEWA 300 ne kacal,ki biya ki karanta cikin salama,idan kika karanta min batare da kin biya ba keda Allah saboda ban yafe 👌🏻 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 17&18 Cikin sauri wani guard ya dauki waya yayi kiran Doctor,sannan suka daukeshi cak,duk kuwa da kasancewar sa qaqqarfan namiji,suma masu bashi tsaron ba baya ba, kai tsaye dakinsa suka kwantar dashi,P.a yana qoqarin shafa masa ruwa a fuskarsa,likitan ya'iso, dayake asbitin nasu akusa yake,Likita ya ajiye qaramar jakar hannunsa sannan ya nutsu yafara duba Jawad,yadade yana masa gwaje-gwaje sannan ya daura masa ruwa guda daya,yayi allura acikin ruwan, sannan yahada kayansa yamiqe ya kalli P.a yace"rashin samun hutu ne yasa yakasa controlling kansa,jikinsa da qwaqwalwar sa suna buqatar hutu,aikin dayake yayi yawa,a bashi wasu yan kwanaki yahuta zai dawo normal,idan ya farka akirani" P.a yabawa Likita hannu suka gaisa,sannan suka fita ya rakashi, dakin da Jawad yake ciki suka rufe suka koma falo suka zauna,yayinda P.a yaci gaba da kula da komai. Duk bayan awa daya P.a yana zuwa ganinsa,da ruwan yaqare ma shine yacire masa,sannan yasake gyara masa blanket din dakyau ya futo daga dakin. Saida Jawad ya debi kusan awa biyar yana bacci sannan yafarka ahankali,yabude idonsa ya kalli Plasma dake aiki adakin amma babu qara kokadan,yaja lallausan blanket din daya rufa dashi ya rungume shi a qirjinsa, yazubawa Plasma ido yana karanta labaran da'ake saide baya fahimtar rubutun,kawai karanta wa yake amma ba zaice ga abinda ya fahimta ba,hankalinsa da tunanin sa gaba daya yatafi wajanta,meyasa taqi nemansa awaya? ko yayi mata laifi ne?,meyasa takeson daukar fansar fadansu dakuma 6oye musu koshi waye ranar da suka fara haduwa ta hanyar qin kiran wayarsa? meyasa? yasaki ajiyar zuciya ya lumshe idonsa, sannan yajuya gefensa yadauki wata babbar waya yabude,wata folder yashiga nan take pictures dinta suka bayyana,wanda akayi mata su dayawa ranar Birthday nashi, amma babu guda daya da tasan cewa an dauka da saninta. Dan qaramin lips dinta yazubawa ido kamar zai cinye shi,yasake gyara kwanciya tareda sake rungume Blanket din jikinsa yanajin dama ace itace, yasake kallon photon nata dakyau,ahankali ya motsa lips dinsa kamar zaiyi magana amma baice komai ba,sai can yazubawa kyawawan idanuwanta ido yace"kece ME 'DEBE MIN KEWA" Ahankali ya matso da photon nata dab da fuskarsa,sannan ya lumshe idonsa yadora lips dinsa adede nata,yasakar mata wani irin kiss.(🙈) Tsawon wasu mintuna ya6ata yana aikin kallonta,sannan yatashi ahankali yashige toilet yayi wanka,ya dauro alwala ya futo jikinsa d'aure da towel fari qal,hakan ya bayyana lallausan baqin gashin dake kwance a faffadan qirjinsa,wata jallabiya yasaka yatada kabbarar sallah,saida yarama duka sallolin da'ake binsa sannan ya zauna a yabude qur'ani yana karantawa. P.a yashigo dakin hannunsa daukeda coffee ya ajiye masa, sannan yajuya yafita falo yakira Likita,yawuce Fridge yadebo masa Fruit,yahado masa da abinci madedeci yakawo masa dakin sannan ya zauna ya kalleshi yace"yalla6ai yajiki?" Saida yakai qarshan shafin dayake karantawa sannan ya rufe qur'anin yadubi P.a yace"Naji sauqi P.a,dama ciwon kaine kawai" Likita ne yashigo dakin, Jawad ya kalleshi yayi masa murmushi sannan yabashi hannu suka gaisa, Likita yasake dudduba shi, sannan ya kalleshi yace"babu wata damuwa yanzu,amma nabaka hutun kwana biyar, kafin ka koma bakin aiki" Jawad ya jinjina kansa sannan yabashi hannu suka sake gaisawa,suka fice shida P.a daga dakin,suna fita Jawad ya jingina da gadon ya lumshe idonsa, sannan yabude da sauri yatashi yagyara zamansa yafara shan coffee din. *** *** *** Abuja Nigeria Washegari sassafe aka kawowa Hajiya Zaliha order kayan datayi,suna breakfast su uku ita da Daddy da Fu'ad,daya daga cikin me aikinta tazo ta rissina tace"Hajiya munkai musu abincin" Hajiya Zaliha tace"ok Ladi zaki iya tafiya" Bayan sungama cin abinci,Hajiya Zaliha ta kalli Fu'ad tareda nuna masa kayan dake zube akan kujera tace"Fu'ad dauki kayan can muje wannan Plat din nan nakusa damu" Fu'ad ya kalleta yace"Mummy ko insa akai miki?" Hajiya Zaliha ta kalli cikin idonsa tace"kadauki kaya muje nace" Daddy yayi murmushi yana jinsu,Fu'ad yatashi yakwashi kayan,itama ta dauki sauran suka tafi wajansu Bilkisu. Suna zuwa kai tsaye suka shiga falon,Bilkisu tana zaune akan hadaddiyar kujera tana kallo,yayinda Inaas take tsaye akusa da TV kanta ko dankwali babu tana qoqarin sauya channel, Farouq kuwa idonsa yana kan Alqur'ani yana karatu. Suna jin sallamar Hajiya Zaliha gaba dayansu fuskarsu ta washe da annuri,Inaas tataho da sauri ta kar6i kayan hannun Hajiya Zaliha,Fu'ad yazubawa Inaas ido yana kallonta,cikin ransa yake tambayar kansa anya mutum ce kuwa? Har Inaas suka gaisa da Hajiya Zaliha Fu'ad bai bar kallonta ba kuma bai daina tunani ba,saida Hajiya Zaliha ta kalleshi tace"Fu'ad Inaas tana gaidaka" Cikin sauri yadawo hayyacinsa sannan yace"sannu yakike" Inaas tayi murmushi tace"lafiya" Hajiya Zaliha ta kalli Bilkisu da Farouq sannan ta nuna musu Fu'ad tace"wannan shine qaramin yaro na,sunansa Fu'ad,Yayansa baya nan yana qasar waje" Cikin kulawa Farouq yace"Masha Allah,sannu Fu'ad" Fu'ad yayi sauri yayi qasa da kansa yana sosa qeyarsa, sannan ya rissina ya gaida Farouq, yajuya yasake gaida Bilkisu itama ta amsa masa cikin kulawa. Zama sukai akan kujera Hajiya Zaliha ta kalli Bilkisu tace"Bilkisu ga kaya,zaku iya amfani dashi kafin akawo musu dinkunan ku,naza6i wasu kaya nace a dinka muku,amma yanzu de ga wasu kayan nan kufara dasu" Bilkisu tafara duba kayan tana dagawa dogayen riguna ne Abaya masu kyau,da takalma,da mayuka na gyaran jiki dana gashi,da hand drayer, dakuma jallabiya da takalman maza da alamu wannan na Abban Inaas ne. Bilkisu ta dago kanta ta kalli Hajiya Zaliha tace"Hajiya kayan nan ai sunyi yawa,Ina zamu kaisu Hajiya? Ina laifin ma guda bibbiyu?" Hajiya Zaliha tasaki murmushi sannan ta miqe tsaye tace"to nide kinga tafiya ta" Fu'ad ma yamiqe yabi bayan Hajiya Zaliha yana satar kallon Inaas wadda bakinta yakasa rufuwa da ganin kayan nasu. Bilkisu da Farouq suka biyo bayan Hajiya Zaliha har Compound suna zuba mata godia kamar ba gobe. *** *** *** Yasaba duk lokacin dabai fita wani waje ko office ba to yana aiki a Computer sa agida,hakan ce ta kasance yauma,babu inda yafita saboda hutun dole da Likita yabashi,computer sa tana gabansa a ajiye, saide maimakon yayi aiki,photon ta yazubawa ido yana kallo,har mamakin kansa yake yanda yarinyar ta hargitsa masa lissafi,yana mamakin yanda soyaiyar ta take nema ta maidashi mahaukaci qarfi da yaji,tayaya ne zai sameta awaya? ta wacce hanya zai yi magana da'ita,? yanason jin muryar mahaifiyarta but ta yaya?, ahankali yarufe computer sannan yakoma cikin kujera ya kwanta yayi luf. *** *** *** Abuja Nigeria Tsawon wasu kwanaki dasukai agidan Fu'ad baisake saka Inaas a'idon sa ba,da niyya yake futowa Compound yayi shawagi ko zai hango ta amma kokadan baya ganinta. Zuwa wannan lokacin kuwa daga Bilkisu har Inaas sun sake yin fresh dasu,cimar dasuke ci yanzu, dakuma hutun dasuke basa fita ko da yaushe suna waje daya, hakan yasa fatar jikinsu tasake yin kyau uwa uba mayukan dasuke amfani dashi na gyaran jiki,yau tagaji da zaman waje daya,tafuto daga falon nasu tana zagaya compound din gidan,jikinta sanye da wata Atamfa mai kyau dinkin doguwar riga,kayan yayi mata kyau sosai kasancewar bata saba saka irin kayan ba, lungu da saqo takebi tana ganin gidan sai nishadinta take tana kalle-kalle,hakan da takeyi sai yaja hankalin security na gidan dayawa,kowa sai kallonta yake saboda sude a sanin su babu yarinya budurwa agidan, saide baqin dasuka zo ne tareda Alhaji, Inaas kuwa ko ajikinta, batasan ta dauki hankalin mazan dasuke tsatstsaye a Compound dinba, saida tagama kalle-kallenta sannan takoma falo, tana zama Man Sulaiman yashigo falon hannunsa janye da jaka Farouq yana biye dashi,Inaas tatashi da sauri ta kar6i jakar hannunsa takai masa wani daki kusa da dakin Ammiy. Man Sulaiman yasaci kallon Bilkisu yaga tasake yin wani irin kyau tasake zama cikakkiyar matar manya kamar de baya,kasa janye idonsa yayi daga kanta,tayi mutuqar kyau cikin leshi riga da zani, taja wani daurin dankwali kamar ba'ita ba,wata sabuwar qaunar tace ta sake ninkuwa a ransa,Farouq ya kalleshi yayi murmushi yawuce kan kujera ya zauna,Bilkisu tadago kanta ta kalleshi sau daya ta watsar kota kansa bata sake biba, cikin sauri shima ya janye idonsa sannan ya zauna daga can gefe nesa da'ita,ya kalleta adan tsorace yace"Bilkisu ina kwana" Batare data kalleshi ba tace"Lafiya" Man Sulaiman yayi ajiyar zuciya yace"dama Alhaji ne yace Inaas dinki takai masa takardunta zata koma makaranta" Bilkisu batace masa uffan ba,asalima ko inda yake bata kalla ba,ba zakace da'ita yake magana ba,Farouq zaiyi mata magana saide kuma dawowar Inaas falon yasa yayi shiru ya sauya akalar zancen da fadin"Allah yasaka masa da Alkhairi,zata kai masa" Yajuya ya kalli Inaas data zauna yace"ai Takardunki suna nan ko?" Inaas tace" eh Abba suna nan" Yace"to Alhaji yace ki shirya su kikai masa zai nema miki makaranta" Cikin farinciki Inaas tace"to Abba" Man Sulaiman ya kalli Inaas da murmushi a fuskarsa,yaga alama dole saiya kama qafar yarinyar nan sannan zai iya samun kan Bilkisu,duba da yanda yaga tanaji da yarinyar, cikin sakin fuska yace"Inaas kinajin dadin garin ko?" Inaas ta kalleshi tace"Eh Uncle inaji" Bilkisu tajuya ta watsawa Inaas harara,harda wani Eh Uncle ko'a'ina yazama Uncle dinta oho. Man Sulaiman yayi murmushi yace"to Alhamdulillah,anjima saiki shirya muje nakai ki yawo kiga gari kinji?" *** *** *** Tunda yarasa mafita akan yanda zaiyi yayi magana da da'ita hakan yasa yasake shiga damuwa yarasa gane kansa,bayan kwanaki biyar din da Likita yabashi yasake warware wa sosai yakoma bakin aikinsa,saide ga wanda ya sanshi kallo daya zaiyi masa yagane cewa Jawad din yana cikin damuwa,saide yanayin fuskar sa da kullum take daure babu fara'ah hakan yasa ba zakace yana cikin damuwa ba, saboda dama haka yake kullum babu fara'ah. Yaci gaba da harkokin kasuwancin sa saide gefen zuciyarsa yana jin wani irin zafi wanda yariga yasani cewa hakan baya rasa nasaba da rashin jin muryar Inaas. P.a ne yakawo masa waya,ya karba yakarata a kunnansa, daga can 6angaren akace"Yalla6ai maganar kamfanin nan fa jibi ne ranar budewa" Jawad ya lumshe idonsa sannan yabude,yasaka hannunsa yadafe goshin sa, cikin damuwa yace"banace a sauya date din ba,? why not amaida zuwa next year? banason shiga Nigeria kwana kusa saboda inada ayyuka?" "Ranka ya dade kayi haquri de,mun riga mungama sanarwa jibi ne taron,uwa uba duk wasu mutanan mu dasuke qasar waje suma an sanar dasu" Fuska babu walwala yace"ok I will be there insha Allah" Daga haka yabawa P.a wayar yaci gaba da aiki da computer. Washegari sassafe suka shirya da shirin zuwa Nigeria agama taron bude kamfani subar qasar,kokadan bashida niyyar yin kwanaki samada uku a Nigeria,baison zuwa qasar kokadan,yaso ace de abar batun budewar zuwa next year. Suna sauka a Airport guards suka bude masa mota yashiga baya yazauna computer sa tana kan cinyarsa yana dube-duben wasu ayyuka. Kasancewar zuwan dayayi zuwa ne wanda ba'a san dashi ba, hakan yasa suna qarasowa gida sukaga yan Jarida danqam abakin get din gidan,kowa yanaso yaji ta bakinsa,bai saurari ko mutum daya daga ciki ba yayi umarnin cewa abasu haquri, baya cikin yanayin dazai iya magana dasu,motocin dasuka dauko shi suna tsayawa ya futo yayi gaba yana tafiya hannunsa guda daya yana cikin aljihun wandon sa, yayinda daya hannun yana riqe da waya akan kunnansa, cikin sauri yake tafiya yana waya da wasu baqi dazasu samu damar halartar taron da za'a yi gobe,yanda yake tafiya da cikakken kuzari ba zakace shine kwanaki biyar baya aka bashi hutun dole ba. Yana qarasawa cikin hamshaqin falon nasu Mummy ta taso da sauri tatare shi tana murmushi har saida ta sadashi da qirjinta ta rungume shi,Fu'ad ya kar6i briaf Case din Jawad a hannun P.a, yawuce da'ita yakai masa dakinsa,Daddy yayi murmushi yace"yanaga ka d'an rame? meyake damunka? zo,zo,zoka fadamin" Yafadi haka yana meqawa Jawad hannu, Mummy ta riqe hannun Jawad suka qarasa wajan Daddy. **** Acan Plat din su Bilkisu kuwa,da daddare duka su hudun suna zaune afalo,ko kad'an basuji labarin zuwan Jawad ba,suna zaune afalonsu sunata zance,Man Sulaiman qasa-qasa suke magana shida Farouq suna tattauna wa akan yanayi dakuma halin da qasarmu take ciki,suna firar su suna cin abinci, Man Sulaiman ya kalli Inaas datake gefen Bilkisu, saida yafara satar kallon Bilkisun sannan yace"Inaas kin kaiwa Alhaji MEKU'DI takardun naki kuwa?" gaban Inaas yayi wata irin bugawa,Abban Inaas ya dakata da cin abincin dayake yazubawa Man Sulaiman ido,yayinda Bilkisu ma ta qwara masa ido, gaba dayansu suna neman qarin bayani,cikin mamaki Abban Inaas yace"Alhaji Mekudi kuma? wai dama shine?" Gaban Inaas ya tsananta fad'uwa,yayinda Bilkisu ta zubawa Man Sulaiman ido,tunda abun nan yafaru ita de da kanta bata ta6a yimasa magana ba, amma yau saita tsinci kanta da jefa masa tambaya tace"wai Mahaifin yaron nan Jawad? to yanzu ina Jawad din yake? yana nan lafiya?" Farouq yazubawa Yayar tasa ido yana kallo, yarasa meyasa Yaya Bilkisu ta damu sosai da lamarin Jawad,baisani ba ko haduwar jini ce. Inaas kam idonta yana kan Man Sulaiman tana jira taji amsar dazai bayar. Man Sulaiman kuwa ganin yau Bilkisu ta masa magana,hakan yamasa dadi,ya tabbatar Addu'ar dayake akan Allah ya huci zuciyarta tafara kar6uwa,yajuya ya fuskanci Bilkisu yace"Jawad ai baya zama,a shekara befi yazo qasar sau d'aya ba" Cikin sauri Inaas tace"to inje nakai masa takardun yanzu?" Man Sulaiman yace" yanzu dare yayi Inaas,kibari gobe saiki kai masa insha Allah" Cikin ladabi ta amsa masa sannan tatashi ahankali tashige dakinsu tafara bincike saida ta nemo katin da Jawad yabata wanda yake daukeda numbers dinsa,tazubawa katin ido kamar tanaso ta haddace numbers din jiki,ahankali tasaki ajiyar zuciya,tajuya gefen damanta ta kalli wayar Bilkisu,tanaso ko sau daya ne takira shi a wayar tayi masa godia akan kyautar dayayi mata,tanaso ko sau daya ne takirashi su gaisa,amma bazai iyu ta qetare Umarnin Mahaifinta ba,ahankali tatashi tamaida katin inda take 6oye shi,sannan tawuce toilet domin ta watsa ruwa. **** Qarfe shadaya da kwata suna zaune shida Daddy afalon Daddy din,Alhaji Mekudi yazubawa d'an nasa ido yana nazarinsa,ya tabbatar akwai abinda yake damunsa,amma zurfin ciki irinna Jawad sunyi masa tambayar duniya yaqi fada musu komai. Daddy yadauki ruwan Zam-Zam din dake ajiye a gefensa awata qatuwar gora ya tsiyaya yasha, sannan yasake kallon Jawad yace"Man Sulaiman yaga matarsa" Cikin ladabi Jawad yace"Eh Fu'ad yafada min Daddy" Daddy yagyada kansa sannan yace"sun dawo nan muna zaune tare dasu gaba daya,akwai Qanin Matar Man Sulaiman yana nan Sunansa Farouq, inaso idan kungama taron bude kamfanin nan gobe, ka bashi aikin daya dace dashi,yayi karatu me Zurfi tun irin karatun shekarun baya, amma bai samu kyakykywan aikin gwamnati ba hakan yasa yake yiwa yaran Alhaji Auwal lesson, na rabo shi da aikinsa,bai kamata in hanashi wani aikin ba" Jawad yayi shiru yana tunani, yatuna lokacin dasuke waya shida Baby kafin ta rasu, har take cemasa Uncle Farouq ma yace tafi kowa qoqari,ikon Allah ashe shidin Qanin matar Man Sulaiman ne,Allah da iko yake,ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yace"to Daddy insha Allah za'a yi abinda yadace" Washegari bayan sungama Breakfast Bilkisu taga Inaas sai walwala take,batasan menene dalilin farincikin yarinyar ba,saide tana hasashe cewa tun lokacin da Man Sulaiman yace nan gidansu Jawad ne daga lokacin ne taga Inaas din tanata nishadi,mamaki ya kamata,to kode son Jawad din take? Man Sulaiman ne ya futo cikin Shiri ya kalli Abban Inaas yace"Farouq mu wuce wajan taron nan,dazu Alhaji yakirani yace akwai taron bude kamfani da za'a yi, yanaso muma muje" Farouq yadauki tissue ya goge bakinsa sannan yamiqe suka fice daga falon,ahanya Man Sulaiman yakalli Farouq yace"jiya muna zancen Jawad kaji ashema yashigo qasar jiyan,kuma shine ma zai bude kamfanin" Farouq yayi murmushi yace"Allah sarki, Allah yasanya Alkhairi" Bayan sun qarasa wajan bude kamfanin,suma suka samu waje suka zauna kamar kowa. Wajan yayi kyau sosai,manya manyan 'yan kasuwar qasashen duniya sunzo,Jawad yamiqa hannu daya daga cikin guard dinsa yasaka masa Scissors, sannan yayanka zaren da akai docoration,lokaci daya aka dauki tafi fuskar kowa d'aukeda farinciki,sannan suka nemi wajan zama kowa ya zazzauna,me gabatar da taro yafara gabatar da Jawabi daki-daki kamar yanda suka tsara,saida akayi abinda ya dace sannan me gabatar da Jawabi yace"Dayawa daga cikinmu nan munsan wanda muke zaune anan domin sa,muna kira ga Babban d'an Kasuwa Mr. Jawad Mekudi,mamallakin kamfanin Oil da Kala-kalar meterial,shugaban masana'antun Jiragen ruwa dana Sama,muna kira ya futo fili yazo yayi Jawabi ga taro" Cikin nutsuwa Jawad yatashi,yayi mutuqar kyau cikin wata baqar Suit,ahankali ya qarasa yatsaya a'inda aka tanada domin magana,ya kalli mutanan wajan ganin yanda waje yayi tsit kowa yana so yaji nasa Jawabin. Abban Inaas dayake zaune kusa da Man Sulaiman ya zubawa Jawad ido yana kallonsa,mutumin dayake hanga daga nesa ranar da'akai rasuwa agidan Alhaji Auwal,wai yau shine agabansa a zahiri tsakanin sa dashi bai wuce taku goma ba,yatuna kyautar daya bawa 'yarsa Inaas,Masha Allah Yalla6ai Jawad ya hadu sosai,shi din mutum ne mai kwarjini da haiba,haqiqa baiyi kuskure ba daya hana 'yarsa kunna waya,domin kuwa ruwa ba sa'an kwando bane, auren qwarya tabi qwarya irinsu Yalla6ai Jawad sukeyi. Jawad ya katse masa tunani ta hanyar fad'in" Assalamu Alaikum jama'ah,nasani cewa dayawa daga cikin mutanan dasuke zaune anan kusan kowa yasan cewa nine Jawad Mekudi,Jawad d'in da mutane da 'Yanmata suke muradi da rububin son haduwa dashi,saide a zahiri da bad'ini wanda yafi kowa sanina shine mahaifina,dashi muke fafutuka wajan ganin munzo wannan matsayin,shine ya dafani har na kawo yanzu,shine ya riqe hannu na ya koya min kasuwancin danake Alfahri dashi a yanzu,shine ya tsaya min harna kawo hakan,taimakon Allah dakuma aikin danake ba Dare ba Rana shine ya ha66aka kasuwanci na,Ina Addu'ah da kuma fatan kasuwanci na yaci gaba da ha66aka ta yanda zan zamo d'aya daga cikin manyan mutum goma na masu kudin Duniya" Yana kawowa nan,gaba daya waje yadauki tafi,wata Baturiya ta matso kusa dashi tabashi wasu file file na takardu tace"yalla6ai Jawad wadannan takardun suna buqatar saka hannun ka" Babu musu Jawad ya kar6i takardun yasaka hannu,sannan yakoma wajan zamansa,ba'a dauki tsawon lokaci ba aka kammala taro lafiya. Bayan sun dawo daga wajan taro suna zaune afalo gaba dayansu,Jawad yana daddana waya, yanajin wata irin fad'uwar gaba atare dashi,yarasa meyasa tun da safe yake jin wata irin fad'uwar gaba,rabon dayaji wannan fad'uwar gaban tun zuwansa qasar Niger. Daddy ya kalli Jawad yace"yaya maganar Farouq damukai dakai jiya? Ina fatan baka manta dashi bako?" Jawad yace" ban manta ba Daddy,already nasa sunansa acikin jerin wanda za'a bawa babban muqami a kamfanin,za'a bashi MD na kamfanin insha Allah" Daddy yayi murmushi yace"to Alhamdulillah,Allah yayi ma Albarka" Jawad ya amsa da "Amin Daddy". Da daddare yana zaune a Compound da guard guda biyu a tsaye a bayansa,ice-cream ne agabansa yana sha lokaci zuwa lokaci yana kallon Plat din da Daddy yace masa iyalan Man Sulaiman suna ciki,yana iya hango hasken fitilar falon saide akwai labule ba sosai ake hango cikin falon ba. Yajuya gefen hannun hagunsa yaga yanda sojoji suke shawagi agidan,yajuya ya kalli P.a bayan yagama yanke shawarar zuciyarsa, sannan yace"P.a" P.a yace"na'am Yalla6ai" Jawad yace"ka shirya mana tafiya zuwa qasar Niger gobe da sassafe idan Allah yakaimu" P.a yayi d'an qaramin murmushi bayan yagano shi yace"angama Yalla6ai" Yadade a zaune awajan yanashan is'ka sannan yayi sallama dasu P.a yayi ciki. Washegari tunda sassafe yatashi yahau shirin tafiya Niger,yariga yagama yanke hukuncin zuwa ya tunkare ta,yanaso yaje ya ganta ko wannan zafin na gefen zuciyarsa zai daina damunsa(🤭) Yasa kaya kusan Kala biyar yana cirewa,duk wanda yasaka saiya ga beyi masa kyau yanda yakeso ta ganshi ba, daga qarshe yasaka wata farar shadda wanda akayi mata aiki da zare ruwan toka,ba qaramin kyau shigar tayi masa ba,tsananin kyawun sa yasake futowa kamar sabon ango haka kayan yayi masa kyau sosai. A gaggauce ya futo daga dakinsa,ko agogon hannu bai daura ba,yana sakkowa falo yana d'aura agogon hannunsa,Fu'ad tun shekaran jiya baya gida yaje gidan wani Uncle dinsu. Mummy tana jera abinci Jawad ya gaida ta a gaggauce yana qoqarin ficewa daga falon,kana ganinsa basai anfada maba kasan cewa yanda yake zuba saurin nan to tabbas akwai wani waje muhimmi da zaije. Cikin sauri Mummy ta kalleshi tace"ina zakaje haka kake ta wannan saurin ne? ko Breakfast bakayi bafa" Cikin gaggawa yace"Mummy zanje wajan wani taro ne,sauri nake"(🤭😳) Yafad'i hakan yana qoqarin wucewa, cikin sauri ta ruqo hannunsa tace"tsaya kasha kunun Madara saika tafi" Jiyayi kamar yafashe da kuka wannan d'an jinkirin da Mummy zatasa yayi,babu yanda ya'iya haka yatsaya ta dauko kunun madarar tafara bashi,ahankali yakeshan kunun yana tauna kwakwar dake ciki ahankali kamar bayaso,a tsaye yakeshan kunun,hakanne yasake tabbatar wa da Mummy cewa lalle wannan taron da Jawad zaije ba qaramin taro bane.(😂) Adede lokacin Inaas tashigo falon bakinta dauke da sallama,hannunta daukeda Takardunta wanda Daddy yace takawo masa,tunda sukazo gidan bata ta6a saka riga da siket ba sai yau,tana Sanye cikin Riga da siket na wata Holland Atamfa, dinkin ya zauna ajikinta sosai, hakanne yasa Hips dinta wanda Jawad bai ta6a sanin tana dashi ba ya futo sosai acikin siket din kamar Hips din babbar mace yanda tacika siket din nata dam, idon Jawad ya sauka akanta,gabansa yayi wata irin fad'uwa,lokaci d'aya ya qame a tsaye idonsa qyam akanta,tunani yake ita din ce kokuma de gizo tafara yimasa? Wayar dake hannun sa tayi qara,hakanne yasa yadawo hayyacinsa yadauki wayar saide idonsa yana kanta yakasa janyewa,daga can 6angaren P.a yace"yalla6ai jirgi yazama Ready,kai muke jira" Idon Jawad akan Inaas kai tsaye yace"anfasa tafiya" (😳🤭😂🥰uhm banda tacewa yau) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍ [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 31&32 Ganin yanda yazubawa waje daya ido kamar yama manta da abinda yake sha hakan yasa Hajiya Zaliha ta juya ta kalli abinda yake gani,nan take taga Inaas a tsaye,kan yarinyar aqasa tana dan jujjuya takardun hannun ta,tunda tashigo taga Yalla6ai Jawad gaba daya sai jikinta yafara rawa,tanemi qwarin gwiwar ta tarasa. Hajiya Zaliha tayi murmushi tace" Inaas yau kece? meyasa bakyason shigomin ne?" Inaas tayi murmushi ta qaraso wajan Hajiya Zaliha tace" Mummy Ina kwana?" Cikin jin dadi Hajiya Zaliha tace"Lafiya kalau Inaas ya samari?" Inaas tayi sauri tarufe fuskar ta da hannunta cikin kunya sannan tace"dama na kawowa Daddy takardu nane" Mummy tameqa hannu ta kar6i takardun Inaas sannan tace"bari nakai masa,amma karkije ko'ina, yau anan zaki wuni,dama nayi waya me qunshi zatazo tamin kema sai tayi miki" Tajuya ta kalli Jawad daya qame a tsaye mamaki yagama kasheshi,alamu de sun nuna masa dama can suna cikin gidan nasu,hakan yanuna sune iyalan Man Sulaiman kenan dasuka dawo nan,Mummy ta bashi cup din hannunta tace"Jawad riqe cup dinnan ka qarasa da kanka 'yata tazo" Jawad ya kar6i cup din yariqe,yayinda Hajiya Zaliha tawuce sama da sauri zuwa dakin Daddy. Inaas tana ganin tafiyar Hajiya Zaliha tazaro idonta ta kalli Jawad, cikin sigar rad'a tace"yalla6ai,dama kana nan?" Jawad ya rissina ya ajiye cup din hannunsa,cikin wani irin farinciki yayi taku daya ya qarasa wajanta,ido yazuba mata yafara qare mata kallo da gasken de itace,wani irin farinciki ya kamashi har saida fuskarsa ta nuna,cikin jin dadi yashafa sumar kansa sannan yasaki wata irin ajiyar zuciya, yad'aga kansa ya kalli babban falon nasu yaga cctv Camera dake falon bata kansu,babu 6ata lokaci yayi sauri ya fuzgota,lokaci d'aya tafad'a kan faffad'an qirjinsa,cikin jin dadi yayi mata wata irin runguma ya lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya kamar yaron dayayi wuni d'aya baisha nonon uwarsa ba. (🙈) Inaas tazaro idonta waje, yayinda gabanta yafara wata irin mahaukaciyar fad'uwa,bata ta6a aikata hakan ba,abin yazo mata wani irin sabon abu ne awajan ta wanda saide taga anayi a tv,hannunta aware suke takasa koda yunqurin dorasu ajikin Yalla6ai Jawad,meyasa yake son karya mata duk wata Garkuwa ta jikinta? meyasa duk lokacin dazata had'u dashi yake zuwa mata da sabon abu wanda qwaqwalwar ta take kasa dauka? jikinta ne yake wani irin mazari,shi kansa Jawad yanajin yanda jikinta yake karkarwa,amma maimakon yasaketa,saima yasake qanqameta sosai a qirjinsa yanajin yanda nashanunta suke ta6o masa faffadan qirjinsa,daga ita harshi sunji alamun tahowa falon,hakan yasa Inaas tafara tureshi daga jikinta, amma Yalla6ai Jawad ko gizau beyi ba, saima idonsa daya sake lumshe wa,cikin wani irin yanayi yad'ora lips dinsa daidai saitin kunnanta,cikin wata irin murya me kashe jiki yace"pleace karki sake yin nesa dani,inaso ki kasance ME 'DEBE MIN KEWA" Yana fad'a mata haka yayi sauri yasake ta yakoma kan kujera ya zauna yadauki wayarsa saika rantse da Allah ba shine ya aikata hakan ba. Jikin Inaas sai karkarwa yake tana neman hanyar guduwa,shikuwa gogan ko ajikinsa yana zaune yamaida hankalinsa kan waya sai ajiyar zuciya yake saki cikin tsananin farinciki,saide bazaka gane yana farincikin ba ta hanyar fuskarsa,domin kuwa fuskarsa tana nan babu alamun wasa. Hajiya Zaliha ta qaraso falon tayi turus awajan,ta kalleshi da tsananin mamaki tace"Jawad? menake gani haka? kaida kake gaggawa? meyasa baka tafi wajan taron ba?" Koda wasa Jawad bai kalli inda Inaas take ba,yanda ya maze yayi fuska bazaka ta6a zargin cewa ma magana ta had'asu ba,ya kalli Mummy yace"bawani taro bane mai muhinmanci nafasa zuwa"(🤭) Mamaki yasake kama Mummy tace"kaid'in Jawad?" Jawad ya sunkuyar da kansa qasa tareda sosa kansa,sannan ya maida hankalinsa kan waya. Hajiya Zaliha tayi ajiyar zuciya takamo hannun Inaas tace" mu zauna Inaas,nabarki a tsaye shima kuma wannan baimiki kara yace ki zauna ba" Jawad yadan saci kallon Inaas,adede lokacin itama ta kalleshi, idonsu yana haduwa Inaas tayi sauri ta janye nata idon. Daddy ne ya sauko falon yayi shirin sa tsaf cikin manyan kaya,yazauna a kusa da Jawad sannan ya kalli Inaas yace"yanmatan Mummy zance ne ko yanmatan Ammiy?" Hajiya Zaliha tayi murmushi,yayinda Inaas tayi sauri ta sauko daga kan kujera tace"Daddy ina kwana?" Daddy yayi murmushi yace"lafiya kalau,naga takardun ki yanzu,Mummynku takai min,nagani sunyi kyau sosai,wacce irin makaranta kikeso a nema miki?" Gaban Jawad yayi wata irin fad'uwa,annurin fuskarsa ya 6ace 6at,tunani yafara aransa, wacce irin makaranta kuma? meyasa takeson tayi karatu? idan maza suka ganta fa? duk wahalar dayasha yayi nasa karatun hakan bai ishesu ba shida ita,? itama saitayi? dole ne karatun?. Inaas tayi murmushi batace komai ba,Daddy yajuya ya kalli Jawad yace"Jawad wannan qanwar ka ce,Qanin matar Man Sulaiman shine mahaifinta,nabaka labarin dawowar su nan,shine nakeso takoma makaranta,kayi bincike kaga wacce makaranta yadace a nema mata,saikayi magana da shugaban makarantar" Nan take Jawad yagane cewa kenan mahaifin Inaas ya bawa matakin MD jiya,to idan Qanin wannan matar shine mahaifin Inaas,wacece mahaifiyar ta? Ina take? Daddy yaji shiru Jawad ba amsa yata6oshi yace"Jawad!!" Cikin sauri Jawad yace"ok Daddy" Sannan yadan dago kansa ya kalli Inaas,kamar ba Daddy ne agefensa ba yazuba mata ido yana kallonta,Inaas ta kalleshi sau daya tayi sauri ta sunkuyar da kanta qasa, Duk wannan maganganun dasuke Inaas tana jinsu,saide ba komai take fahimta ba,abinda Yalla6ai Jawad yamata shine abinda yafi tsayawa aranta,me Yalla6ai Jawad ya aikata? meyake nufi da maganar sa?. Me qunshi ce tayi sallama tashigo falon,Daddy yatashi yayi Dining,ta rissina ta gaida su gaba dayansu,Hajiya Zaliha tace"kifara yiwa yata" Tana fadin haka tajuya wajan Daddy domin zuba masa abinci. Me qunshi ta zauna tafara zanawa Inaas a farar fatarta,Jawad yadauki wayarsa cikin dabara yafara yiwa Inaas photo,ta dan dago tasaci kallonsa, yayi sauri yasake dauka,cikin sauri ta sunkuyar da kanta,tazubawa zanan fulawar da'ake mata ido,hakan datayi sai dogon gashin idonta yahadu waje d'aya,nan take Jawad yasake yimata wani photon. Haka ya zauna afalon shi baitashi yaci abinci ba, shi bai koma dakinsa ba, haka shibai fita ba,yanaji aransa cewa kasancewar ta awajan duk ya wadatar dashi wannan abubuwan. Saida aka gama mata qunshi duka hannayen ta,kasancewar akwai sanyin esi afalon nan da nan kuwa qunshi ya bushe,aka fara yiwa Hajiya Zaliha nata,Inaas ta kalleta tace"Mummy zanje wajan Ammiy" Cikin farinciki Hajiya Zaliha tace"bazaki zauna muyi firar mu ba?" Inaas tayi murmushi,haqiqa taso ta zauna,saide zaman Yalla6ai awajan yasa a takure zata zauna,hakan yasa tace"Mummy anjima zan dawo" Hajiya Zaliha tace"to saikin dawo,ki gaida Ammiyn taki" Inaas ta amsa mata,sannan tadan juya ta kalli Jawad,cikin sauri ya d'ora yatsun hannunsa biyu akan kunnansa alamar ta kirashi.(🤙) Inaas kam kokadan batada nutsuwa aranta,Allah Allah take ta fice daga falon,hakan yasa tafice da sauri kamar wacce ake kora,ahanya tana tafiya kana ganinta zakasan cewa babu nutsuwa atare da'ita. Tana komawa falonsu ta zauna kusa da Bilkisu tana nuna mata zanan qunshin hannunta tace"Ammiy kinga qunshi na" Bilkisu ta kalli qunshin tace"masha Allah,kice ke gayu kika tsaya aka miki shiyasa naji ki shiru" Maimakon tabata amsa saita marairaice ta shagwa6e fuska sannan ta kalli gefen da Abban ta yake zaune yana shan shayi tace"Ammiy dan Allah abani wayata kinji" Abban ta ya kalleta sannan ya kalli Bilkisu, kai tsaye yace"abata" Bilkisu tayi murmushi tace"to" Sannan tatashi tayi daki,Inaas ta doru a bayanta,suna zuwa daki Bilkisu tabata wayar,tayi sauri ta yage ledar dake jikin kwalin sannan tabude kwalin tafuto da wayar,ta sakata a caji. Tunani tafara tana so ta kirashi amma kuma wayar ba caji,hakan yasa ta dauki wayar Ammiy zata kirashi,kafin tayi kiran tajuya tana fuskantar Bilkisu sannan tace"Ammiy,wai idan mutum yace yanaso ina d'ebe masa kewa,meyake nufi?" Mamaki ya kama Bilkisu,iya saninta de Inaas bata kula kowa,waye zaiyi mata wannan maganar,? cikin hikima tace"waye yafad'a miki hakan?" Inaas taturo d'an qaramin bakinta gaba cikin shagwa6a tace"Ammiy dan Allah" Bilkisu ta ruqo hannunta,tajata jikinta cikin sigar lallashi tace"Inaas,kinada wacce tafi ni ne?" Cikin sauri Inaas ta girgiza kanta,alamun babu. Bilkisu tace"to fadamin waye yafada miki hakan?" Cikin rawar murya Inaas tace"Ammiy dama...dama....Yalla6ai Jawad ne ya...ya..." tanaso tace ya rungume ni,saide tana shakkar fada saboda ta tabbatar idan ta fada daga Ammiy har Abbanta sai sunyi mata shegen duka, hakan yasa takasa gaba ta kasa baya,takasa fadar komai. Bilkisu tasake matse hannun Inaas dake cikin nata tace"yayi me? me Jawad din yayi?" Saida ta daidaita kanta sannan tace" dama Yalla6ai Jawad ne ya fadamin haka dazu danaje wajan Mummy" Bilkisu ta runtse idonta, sannan tasaki ajiyar zuciya ta bude ta kalli Inaas tace"yana nufin koda yaushe ki kasance tare dashi,kidinga yimasa wasu abubuwan wanda zai dauke hankalinsa ya daina tunanin komai,bansani ba Jawad yana sonki ne kokuma sa6anin haka,amma koma menene banason alaqar soyaiya ta shiga tsakanin ki dashi,Jawad yafi qarfinmu Inaas,kinga de inda suke rayuwa,nasani cewa tabbas banaso ki auri talaka futuk wanda basu da cin yau bare na gobe,saboda ina guje miki irin rayuwar auren danayi abaya,banaso kisha wahala irin wacce nasha,karki ga nace banaso ki auri talaka kiyi tunanin sai me kudi nakeso ki aura,a a, ina nufin nafiso ki auri tsaka-tsaki,kamar de mu d'innan,koda kin fara son Jawad,kiyi qoqari ki cireshi aranki kirufa mana asiri Jawad yafi qarfin mu,kinga de inda suke rayuwa,basai nasake tunatar dake ba kinsan komu su waye, duk da inason yaron acikin raina bazan daure miki gindi ki saurareshi ba,ina gudun zuciya,kada mutane suce daga zuwanmu gidansu har munyi shige da fice kin auri d'an gidan" Lokaci d'aya jikin Inaas yayi sanyi,kokadan ba zatayi jayaiya da maganar Ammin ta ba,amma taso kiransa,saide maganganun Ammiy yasa tafasa kiran nasa, cikin sauri ta rungume Bilkisu,saida tasamu nutsuwa sosai, sannan ta saketa tashige toilet domin wanke qunshin hannunta. Jawad kuwa ganin cewa yafada mata suyi waya,hakan yasa har dare yana jiran kiranta,yasaba barwa P.a wayoyin sa, amma yau duka suna wajansa saboda yana tunanin kiran Inaas,saide har yayi shirin kwanciya shiru bata kirashi ba,har wajan shadaya na dare yana tunanin zata kirashi amma shiru,ahankali yatashi ya qarasa jikin window din dakin, ya janye labulan windon yazubawa Plat dinsu Inaas ido kasancewar dakinsa yana sama sai yake hango Plat din nasu sosai,ganin duhu yahade ko'ina hakan ne ya tabbatar masa da cewa sunyi bacci,badan yaso ba haka yadawo yakashe wutar dakinsa yashige cikin bargo ya kwanta,kokadan baiji dadin rashin kiran nata ba, saide daya tuna cewa yanzu suna tare da'ita a gida,sai hakan ya dan kwantar masa da hankali. Washegari da safe Hajiya Zaliha takira wayar Ammiy tace idan sun gama abinda suke suzo,cikin nutsuwa kuwa suka shirya itada Inaas suka tafi bayan sungama aikin komai. Suna zuwa falon Hajiya Zaliha tace"haba Bilkisu,menene amfanin zaman namu tare? kudinga shigowa mana muna wuni tare" Bilkisu tayi murmushi tace"to Hajiya insha Allah zamu dinga shigowa" Fu'ad dake cin abinci a Dining yana hango Inaas yayi sauri yatashi yadawo falon ya zauna,yagaida Bilkisu, ta amsa masa cikin sakin fuska, yajuya ya kalli Inaas yace"ke kuwa shiru ake jinki kod'an leqowa bakyayi" Inaas tayi murmushi tace"jiyama fa nazo,nadade anan" Fu'ad yace"ok jiya bana nan,naje unguwa,yakike ya zaman Nigeria, akwai dadi?" Inaas Uwar surutu dama abokin zance take nema,hakan yasa tagyara zama suka dinga zance itada Fu'ad kamar dama can sun san juna,Hajiya Zaliha da Bilkisu suma suna nasu zancen na duniya, Fu'ad da Inaas kuwa zance yayi zance Fu'ad yace"bani number ki"(🤭😂) Inaas kuwa tsabar ta dade bata samu abokin zance wanda zasu dade sunata zuba ba,hakan yasa tasake sosai da Fu'ad,tace"ai in fadama banida Sim card,kaga wayar ma jiya daqyar na kunna ta,saida nasa Email dina sannan ta bude,har yanzu narasa gane kan wayar,bansan ya take ba" Tafadi haka tana bashi wayar ta. Fu'ad yana ganin wayar yace"laaa ai irin wayar Yaya Jawad ce dake,wallahi irin tasa sak,yanzu yana bacci bai tashi ba,idan kika ganshi duk abinda baki gane ba, ki tambayeshi zai gwada miki komai,amma kiyi ahankali bayason surutu,idan kika bashi kikaga yana cika yana batsewa toki kar6e wayarki salin-alin kibar wajan, bashida da niyar koya miki"(😂) Inaas ta kalleshi tace"to" Fu'ad yace"Ina da wani sabon sim card bari in kawo miki saiki yi amfani dashi" Bai jira amsar taba yanufi dakinsa da sauri yadauko mata sim din yakawo mata,shine yasaka mata, sannan yayi kira yadauki number shima yayi saving a wayar sa,ya kalli dogayen gashin idon Inaas yace"yanzu shikkenan kema kinyi waya saiki dinga waya da samarin ki,ko babu?" Yayi mata tambayar yanason jin ko akwai samarin,idan babu yasako kansa yafara kafa tasa gwamnatin. Inaas tayi murmushi shima yana kallonta yasaki wani irin murmushi. adede lokacin Jawad yasauko daga sama,kasancewar jiya baiyi bacci dawuri ba yana faman juye-juye da tsammanin kiran Inaas,hakan yasa bai tashi dawuri ba sai yanzu ya futo, yana sanye cikin wando three quarter, da riga marar hannu,da murmushin Inaas da Fu'ad yaci karo,hakan yasa nan da nan yaji wani irin zafi agefen zuciyar sa,ya d'aure fuska yaqaraso cikin falon,saide ganin Ammiy yasa nan da nan yaji 6acin ran nasa yana raguwa. Ammiy ta daga kai ta kalli Jawad dayake saukowa,lokaci daya gabanta yayi wata irin fad'uwa,shima Jawad a nasa 6angaren hakan ce ta kasance,yarasa meyasa duk lokacin dayaga wannan matar yake tsintar kansa cikin fad'uwar gaba,haka yazuba mata ido yana kallonta har yaqara so cikin falon. Mummy tayi murmushi ta kalleshi tace"Jawad katashi?" Saida ya tsugunna sannan yadan kalli Bilkisu kad'an yace"MAMA barka da safiya" Cikin jin dadi Bilkisu tace"sannu Jawad" Jawad ya amsa mata yana qoqarin komawa wajan Mummy,Bilkisu tasake kallonsa, taga yanda dantsan hannunsa yake a mummurd'e tace"Baba nah wannan hannu a dinga rufeshi mana" Jawad yayi d'an qaramin murmushi baice komai ba. Inaas tasaci kallon dantsan hannun Jawaad taga yanda yawani murde,ta d'an jinjina kanta ta tuna ranar da suka fara haduwa take cewa yazo ya daketa mana meyake jira? Tayi sauri ta kawar da wannan tunanin sannan ta dan kalli idonsa tace"ina kwana?" Jawad yayi kamar bai gantaba,yadauke kansa sannan ya amsa mata da qyar yace"lafiya" Yatashi yakoma can gefen Mummy ya zauna,Fu'ad ma yatashi yakoma wajansa. Ko minti biyar Jawad baiyi da zama ba,aka kira wayarsa,fuska babu walwala yadauka yafara magana akan zakkar dazasu fitar,yadan jima yana magana fuskarsa babu walwala, ransa baqiqqirin musanman idan yatuna irin murmushin datake wa Fu'ad sai yaji ransa yana zafi,saida yagama wayar sannan yakashe. Me aiki takawo masa abinci ta ajiye sannan tajuya tabar wajan cikin sauri, wayarsa yaci gaba da dannawa kamar baiga abincin da'aka kawo masa ba,d'ayar wayarsa dake ajiye agefe ta dauki qara, yadauka tareda dora qafar sa daya kan daya yafara magana"idan kunje kusamu Hakimin garin kuyi magana dashi,iya yara marayu kawai zaku dauka,wanda basu wuce shekara biyar ba,za'a dauki photonsu ahada da bayanan su, sannan kowanne mutum daya a cikinsu insha Allah zamu bashi kudi amatsayin zakkar da zamu fitar, abawa kowanne yaro dubu tamanin amatsayin kudin islamiya,amma ku sanar dasu cewa muna so nanda wata uku wadannan yaran su haddace uzu biyu na Alqur'ani,please kuyi yanda nafada muku ok?" Yana gama wayar yakashe ta sannan ya kalli Fu'ad yace"kaje dakina zakaga wata jaka,ka kaiwa Alhaji Isah" Fu'ad yatashi yace"ok yaya" Sannan yanufi dakin Jawad,yana zuwa kuwa yaga jakar,saida yabude yaga kud'ad'e ne aciki sannan ya rufe ya futo,yana zuwa falo yayi sallama dasu Mummy yafita, Hajiya Zaliha taji dadin hakan,tana so koda yaushe taga Jawad din yana qoqarin saka Fu'ad wasu abubuwan dan shima Fu'ad din yazama Busy. Jawad ya ajiye wayar hannunsa,yayi ajiyar zuciya sannan ya saci kallon Inaas,karaf akan idon Mummy,shikuma baisan Mummy tana ganinsa ba,haka ya dinga kallon Inaas din qasa-qasa, saide har yanzu fuskarsa babu walwala. Mummy tayi murmushi ta kalli Inaas tace" Inaas matso ki zubawa Yayanki abinci" Cikin daure fuska Jawad yace"no Mummy,ta barshi kawai" Bilkisu ta kalli Inaas taga itama tahade rai da alama de su sukasan abinda ya hadasu,tayi murmushi ta kalli Jawad din sannan tace"Jawad bari nazo nabaka" Jawad ya kalli Bilkisu,yaji kokad'an bazai iya yin musu da matar ba,har tazo ta zauna akusa dashi bai iya yunqurin hanata ba,itace da kanta tazuba abincin,sannan tasaka hannunta acikin abincin ta debo ta nufi bakinsa dashi,babu musu yabude bakin tasaka masa abincin yafara ci,nan take yaji wata irin nutsuwa, hakan yasa yasauke wata irin ajiyar zuciya kamar wanda yadauki tsawon lokaci yana kuka. Idon Jawad akan Bilkisu sai kallonta yake, yanajin wani irin sonta acikin zuciyarsa,Bilkisu kuwa batasan kallonta yake ba,fuskarta kadaran kadahan take bashi abincin,shikuwa sai faman kallonta yake yana ji kamar su tabbata ahaka,kowanne lokaci Mummy da spoon take bashi abinci,amma yau gashi wannan matar da hannunta take bashi abinci,kuma yake jin abincin yamasa dadi fiye da qima. ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta baki biyani haqqina ba banyafe ba nabarki da Allah 👌🏻 300 ne kacal ki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034 *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 31&32 Yayi mamakin irin Abincin dayaci,Abinci yaci wanda rabon sa dayaci abinci mai yawan haka harya manta,har zuwa wannan lokacin idonsa yanakan Bilkisu,yanajin matar sosai aransa,tana birgeshi,shide baice mata ya qoshi ba,itace da kanta taga hakan zai iya wadatar dashi,danhaka ta dauki tissue din gefensu ta goge masa bakinsa,sannan ta dauke abincin ta wuce kitchen dashi,daga can ta wanke hannunta. Mummy ta kalli Jawad tace"masha Allah Jawad kaine kaci abinci haka?" Bilkisu data futo daga kitchen tace"bayason cin abinci ko?" Mummy ta jingina kanta cikeda tabbatar wa tace"ina harkokin sa ma suka barshi yaci abincin?inkinga yatsaya ya nutsu yaci abinci sosai to na matsa masa ne" Kafin Bilkisu tayi magana wayar Inaas ta dauki qara,tana dubawa taga Fu'ad ne yake kiranta,lokaci daya fuskarta ta washe,ta miqe tsaye ta dauki wayar tana shirin ficewa daga falon sannan tace"Hello Yaya Fu'ad" Jawad ya runtse idonsa,ransa ya sosu da wannan kiran waya,nan take gefen zuciyarsa yafara yimasa wani irin zafi,lokaci daya ransa yayi baqiqqirin. Cikin damuwa yatashi yabar falon yawuce sama,saide babu wanda ya lura da irin yanayin daya shiga. Da daddare suna zaune afalo shida Mummy,kallo sukeyi amma hankalin ta yana kan Jawad,tun dazu dasafe da taga irin yanda yake satar kallon Inaas taji aranta ko son yarinyar yake? tun ganin farko datayi wa Inaas taji yarinyar ta birgeta,nutsuwarta tayi mata,taji tana yiwa Jawad sha'awar ta,to Jawad din nata ne ba'a gane kansa,wani lokacin ba'a yimasa gwaninta inde akan mata ne,amma yakamata tashiga cikin lamarin. Jawad kuwa cikin yanayin damuwa yawuce dakin karatun sa,wani littafi ya dauka zai fara dubawa, yabude littafin kenan, sai tunanin ta ya fad'o masa,meyasa shi taqi kiransa? meyasa takira Fu'ad amma shi ko sau d'aya duk tsawon lokacin nan taqi nemansa? ya runtse idonsa yasaki wata irin ajiyar zuciya, sannan yayi qoqari ya kawarda tunanin ta aransa,ya ajiye littafin hannunsa yabude computer,yadauko wasu takardu suma yabude su zai fara dubawa,yatashi yabude wani fridge dake can gefe yadauko gorar ruwa guda daya,yadawo ya zauna zai fara aiki,lokaci daya wannan kyakykywan murmushin nata datake yiwa Fu'ad dazu yafado masa arai,cikin taqaici yakawarda computer gefe har hakan yasa takardun suka zube aqasa amma bai damu ba. Wayarsa tafara qara,yaduba yaga Na'im ne,ahankali yadauka yayi shiru baice komai ba,daga can 6angaren Na'im yace"yanzu nake gani a labarai kashigo qasar" A taqaice Jawad yace"yes" Na'im yace" Alright,nima gobe zan shigo qasar insha Allah" Yanzun ma Jawad a gajarce yabashi amsa yace"ok" Na'im yayi mamaki,danhaka yace"what happen to you?" Batare da 6oye-6oye ba,kai tsaye Jawad yace"wata yarinya ce" Wata irin dariya takama Na'im,saida yagama shan dariyar sa sannan yace"Jawad fa d'an kasuwa ne,babu abinda yasani sai kasuwanci,ciki harda soyaiya" Jawad ya runtse idonsa,batare dayace komai ba qit yakashe wayarsa yatashi ya futo daga dakin karatun yadawo falo. Mummy tadaga kai ta kalleshi,daga gani yana cikin damuwa saide idan an tambayeshi ma zaice babu komai, kokuma yace yanayin aiki ne kawai, ahankali tatashi tawuce dakinta,ta dauko wani turaren qamshi mai bala'in dadi,takawo masa turaren alokacin harya sake shigewa cikin kujera ya kwanta kamar wani maraya, ta kalleshi tace"Jawad ka kaiwa Bilkisu wannan turaren kace tayi amfani dashi yanada dad'i" Idonsa yafara d'agowa ya kalli turaren,kamar bashida niyyar kar6a,saikuma ya kar6a yatashi yafice daga falon baice mata uffan ba. Mummy ta bishi da kallo, ta d'aga hannunta sama tace"Allah,Allah ka shirya min Jawad dina,Allah karage masa wannan miskilanci kasa yadawo normal mutum kamar kowa" Daddy dayake saukowa daga sama yanajinta yayi murmushi yace"to Amin,amma kema kinsan da kamar wuya,dama can haka halin danki yake". Mummy tajuya da sauri ta kalli Daddy. Jawad kuwa yana futowa Compound din gidan yanufi Plat din su Inaas, yana tafiya ahankali kamar baison tafiya,Sojojin dake shawagi agidan sai gaidashi suke yana daga musu hannu,yana gab da shiga cikin falon yaji gabansa yana fad'uwa,yarasa dalilin wannan fad'uwar gaba dayake ji duk lokacin da zai tunkari wadannan mutane. Da sallama abakinsa yashiga falon,saide babu kowa sai qarar tv dake aiki afalon,yazauna a kujera yana qarewa falon kallo kokadan bashida makusa,yana juyawa gefensa yaga wayar Inaas a ajiye, cikin sauri yadauki wayar,yana dubawa cikin sa'ah yaga babu password akan wayar,cikin sauri yashiga cikin contact dinta,yaduba number Fu'ad yayi deleted dinta, sannan ya maida wayar yanda ya ganta ya ajiye. Shiru-shiru yana zaune babu wanda ya futo,yamiqe tsaye yadauki remote ya sauya channel zuwa labarai,yana ajiye remote din Bilkisu tafuto daga daki,cikin tsananin mamakin ganinsa tace"Jawad? kaine kazo? meyasa ka zauna afalo baka shigo daki ba?" Jawad ya ajiye remote din sannan ya danyi murmushi ya tsugunna har qasa yace"Mama ina wuni" Farinciki yakama Bilkisu,tanajin dadin yanda yake kiranta da Mama,tun farko haka taso Muhammad dinta ya dinga kiranta, amma kuma Allah bai nufa zata rayu tare dashi ba. Cikin sauri tasa hannunta akan kafadarsa tace"tashi ka koma kan kujera" Babu musu Jawad yatashi,yarasa meyasa matar nan take yimasa abubuwa kamar wani d'anta,fisabilillah shida yake nema yace a nema masa auren 'yarta tayaya suruka zata dinga ta6a jikinsa? (🤔🤭😂) Yana zama akan kujera itama Bilkisu ta zauna ta kalleshi fuskarta fal da fara'ah tace"kaci abinci? mekake so nakawo ma?" Jawad yayi murmushi kai tsaye yace"shayi" Domin kuwa har gobe, yakasa manta dad'in wannan shayin data had'a masa lokacin dayaje gidansu a Niger. Bilkisu tatashi tawuce kitchen tafara hado masa shayin,tarasa meyasa take jin Jawad aranta,itade tunda Allah yadora mata shi a'idonta shikkenan taji tana qaunar yaron,baza'a ta6a fada mata laifin Jawad ta dauka ba,tanajin farinciki aduk lokacin data kasance tare dashi. Shayin tahado,takawo masa falon ta ajiye, sannan ta kalleshi da murmushi tace"kona baka?" Jawad yayi murmushi yace" A a Mama,zansha" yadauki cup din yafara shan shayin a hankali,sannan yabata turaren qamshin yace"gashi inji Mummy" Bilkisu ta kar6i turaren qamshin tabude shi ta shaqa taji wani qamshi me dad'in gaske,sannan tadago kanta ta kalli Jawad tace"kaiii amma yanada qamshi,shaqi kaji..." Tafadi hakan tana nufar hancin Jawad da turaren tanaso shima yaji qamshin(😂) Jawad yayi murmushi yace"um da qamshi" Cikin murna tace"kace mata nagode sosai,bari inje daki insaka manashi dakinmu yayi qamshi,kayi zamanka kasha shayin a nutse kaji ko?" Jawad yace"to Mama" Yamaida hankalinsa kan labarai, yana gani yana shan shayinsa ahankali. Bilkisu tashiga daki ta kunna musu turaren wutar,sannan tayi nocking toilet tad'aga murya tace"Inaas futo kiji turaren qamshin da Hajiya ta aikomin me dadi" Daga cikin toilet din Inaas tayi gyaran murya sannan tace"gani nan zuwa Ammiy" Bilkisu tafuto daga dakin tadawo falo ta zauna suna kallo itada Jawad,lokaci zuwa lokaci tana kallonsa tanajin nutsuwa dakuma hankalin yaron yana birgeta. Acikin daki kuwa Inaas tana futowa daga wanka taji wani irin qamshi tace"kai amma gaskiya wannan turaren inajin na qasar waje ne" Tafadi hakan tana qoqarin futowa daga dakin,ta riga tasan cewa babu kowa,Abbanta da Man Sulaiman basa dawowa sai can dare,tasan cewa daga ita sai Ammiy,hakan yasa tanufo falon kanta tsaye (🙆🏻‍♀️) Tana futowa tace"Ammiy naji tura...." Kafin tagama cewa Turaren,idonta ya sauka acikin na Jawad,gabanta yayi wata irin bugawa,qafafunta suka fara rawa,tanaso tajuya daki taji kamar an riqe mata qafa. Jawad yazuba mata mayun idonsa yana ganin tsantsar kyawun Inaas ba tareda kaya ba,farin towel din data daura yayi mata kyau sosai, farar fatar jikinta sai wani sheqi takeyi,gabansa yafara faduwa saboda wannan shine karon farko dayaga mace ahaka,saide a Tv,dogon gashin kanta baqi duk ya liqe ajikin kafadarta kasancewar sa ajiqe. Madedetan nashanunta suna tsaye cak acikin towel din,bai ta6a sanin haka kyawun surar ta yake ba,saboda koda yaushe cikin kaya yake ganinta. Lokaci d'aya yaji yanayinsa yana sauyawa,fad'uwar gabansa ya tsananta. Cikin wani irin ihu Inaas tajuya daki da gudu,yayinda Jawad yashafa sumar kansa ya ajiye cup din yayi sauri yafice daga falon. Bilkisu tayi ajiyar zuciya tarafka wani irin tagumi da hannunta bibbiyu(🙉) Wannan mayen kallon dataga Jawad yanabin Inaas dashi ta tabbatar idan shidin mabuqaci ne to zaiyi wahala ya kwana lafiya,tana lura dashi tunda yarinyar tafuto yadena shan shayin yazuba mata ido yana kallonta,yanda taga qwayar idon Jawad,sai hakan ya tuno mata da zamanta da man Sulaiman a shekarun baya,idan yana buqatar ta haka shima yake binta da wannan mayen kallon kamar wani mayunwacin zaki wanda yadade yana farauta bai samu abinci ba. Kanta taji yasara,ahankali tatashi tabi bayan Inaas daki. Jawad kuwa yana komawa Plat dinsu ko tsayawa afalo baiyi ba kai tsaye yawuce dakinsa da dan gudu,Mummy ta bishi da kallon mamaki,saide kafin tayi magana Jawad yawuce dakinsa ya murzawa qofar key,wani irin numfashi yake saukewa ya tsugunna awajan,yadade baisha maganin komai ba,amma yau akwai matsala,gashi maganin nasa yaqare,toilet yashige ya watsa ruwa ko zaiji sauqi saide baiji wani abu daya ragu daga cikin abinda yakeji ba,har yanzu santala santalan fararen cinyoyin ta gizo suke masa acikin zuciyar sa,ko towel din jikinsa bai cire ba yakife akan gado yashige cikin blanket jikinsa yana wata irin rawa. Yadade acikin wannan yanayin,baisan tsawon lokacin daya dauka acikin wannan halin ba,wani irin wahalallan bacci ya daukeshi,saide mafarkin dayayi da'ita shine ya haddasa masa lalata towel din jikinsa gaba d'aya.(🙈) Dawani irin zazza6i yatashi,yayi tunanin yanayin daya shiga daren jiya yariga yawuce,saide yana dora hannunsa akan qasan mararsa yaji babu wani sauyi,yanda ya kwanta jiya,haka yauma yatashi, daqyar yatashi yawuce toilet yayi wankan tsarki,sannan ya futo yasaka wata Jallabiya,ya kalli jikinsa yaga bazai iyu yafita sallah masallaci ahaka ba,idan yafita ahaka kowa zai gane halin dayake ciki saboda yanda gaban jallabiyar tasa yatashi sosai,dan haka yatada kabbarar sallah,yana idarwa yacire Jallabiyar yakoma gado ya kwanta, sannan ya turawa family Doctor dinsu saqo,ta waya. Saida gari yayi haske sannan Daddy yadawo daga masallaci,ya kalli Mummy datake zaune afalo hannunta d'aukeda carbi tanaja,yace"Naga Fu'ad a masallaci, amma banga Jawad ba,meyasa baije masallaci ba?" Mummy ta kalleshi tace"Alhaji kuda kuke fita tare ni ina daki tayaya zansan baije masallaci ba? Allah yasa lafiya, bari naduba dakinsa Allah yasa de yana lafiya" Tafadi hakan tana miqewa,adede wannan lokacin likita yashigo falon,Daddy ya kalleshi, itama Mummy ta kalleshi tace"Doctor meyake faruwa?" Doctor yabawa Alhaji hannu suka gaisa,sannan yace"naga text din Yalla6ai Jawad ne,baya jin dadi" Cikin sauri Mummy tayi dakin Jawad,Daddy da Likita ma sukabi bayanta. Jawad yana kwance cikin Blanket dagashi sai gajeren wando, yanajin budewar qofa yayi sauri yagyara kwanciyar sa yanda baza'a ga halin dayake ciki ba. Mummy tana shigowa tasa hannu zata bude bargon, Jawad yayi sauri yariqe sai iya kansa ne yabari ya futo. Fuskarsa ta shafa tace"meyake damunka? meyasa baka kiramu ba?" Jawad yadan lumshe idonsa yabude sannan ya motsa bakinsa a hankali yace"Mummy zazza6i ne kawai sai ciwon ciki" Daddy ya kalli likita yace"duba shi" Likita ya kalli Mummy yace"Hajiya adan samo masa ruwan tea yasha,zanyi masa allura ne" Mummy tatashi tafice daga dakin,Daddy yanemi waje ya zauna, saqo yashigo wayarsa yadauko wayar daga Aljihunsa yana duba saqon. Likita ya janye bargon har zuwa gwiwar Jawad,cikin sauri Jawad yaja bargon yasake rufe jikinsa yana kallon gefen da Daddy yake zaune yana hamdala aransa da Daddyn baiga komai ba, Daddy kuwa tun shigowar su da Mummy ya fahimci halin da Jawad din yake ciki,tun da yaga zata bude bargon amma Jawad din yayi sauri yariqe, tun daga nan yasan cewa matsalar tasa ta buqata ce,hakan yana nufin yaron nasa lafiyarsa kalau kenan,duk da bashida lafiya hakan yayiwa Daddy dad'i, yasake kallon Jawad ya kawar da kansa amma bai nuna yasan komai ba,yamaida hankalinsa kan wayar hannunsa. Likita ya tatta6a jikin Jawad yaji babu zafi sosai. Mummy tashigo takawo masa tea,yatashi a hankali ya kar6a yasha,sannan likita yamasa allura. Daddy ya kalli Mummy yace"muje" Suka futo daga dakin,suna fita Jawad ya lumshe idonsa sannan yasaki ajiyar zuciya yakoma ya kwanta. Likita yabude jakar daya shigo da'ita,yadauko masa magungunan daya saba bashi yace"ga maganin Yalla6ai,sannan insha Allah zuwa anjima zakaji komai yakoma yanda yake" Jawad ya kar6i maganin ya ajiye,sannan yace"thank you Doctor" Likita yasake hada allurar bacci,yayi masa, sannan ya futo daga dakin. Jawad ya lumshe idonsa yanajin wani irin bacci yana fizgar sa,saide jin dad'insa d'aya,abinda yake tsaye qyam yake barazanar tona masa asiri yafara kwanciya.(🙈) Wunin ranar bacci yake sadidan,Fu'ad yashigo dakin yadade a zaune amma Jawad bai tashi ba,daga qarshe ma saiya kwanta agefen Jawad din. Sai bayan azahar Jawad yatashi,yaduba gefensa yaga Fu'ad yana bacci. Yatashi a hankali yajishi komai normal kamar yanda likita yafada masa,kai tsaye toilet yashige yayi wanka yafuto ya Shimfida sallaya ya tada kabbarar sallah. Kafin ya idar Mummy da Daddy suka shigo dakin,yana idarwa sukai masa sannu, sannan Mummy tafara bashi abinci. Washegari da yammah Na'im yakawo wa Jawad ziyara,suna zaune a Compound din gidan akan wasu had'ad'd'un kujeru,P.a yana tsaye agefen Jawad yana duba wasu takardu. Guard guda uku suna tsaye daga gefe suma,Jawad yadauki lemon gabansu yasha dan kad'an,babu laifi ya warke ras ba kamar jiya ba,wani ma ba zaice shine ya kwanta jinya jiya ba. Inaas tafuto daga Plat dinsu sanye cikin wata Abaya kalar blue,daya daga cikin Abayoyin da Mummy ta siya musu,tayi mutuqar kyau kamar Balarabiyar qasar larabawa,wajan Hajiya Zaliha zasuje itada Bilkisu saide tabar Bilkisun abaya zata zubawa Farouq abinci, ita kuma ta'iyo gaba. Tun kafin tayi nisa take qarewa Sojojin dakuma guard din dake zagaye a gidan kallo, tunani tafara yanzu duk wannan masu tsaron sama da mutum dari,akan mutum hudu kawai,Daddy,Mummy,Jawad dakuma Fu'ad. Tayi ajiyar zuciya taci gaba da tafiya ahankali,dayawa daga cikin masu tsaron ta dauki hankalin su,sai kallonta suke. Tun daga nesa ta hango Jawad a zaune shida wani wanda batasan ko waye ba,ta tuna abinda yafaru shekaran jiya da daddare yanda yagama qarewa jikinta kallo babu kaya,cikin sauri ta janye idonta tadena kallonsa,bazata iya had'a ido dashi ba. Shima Jawad a nasa 6angaren tunda tafuto daga Plat din nasu yaganta,amma saiyayi kamar bai ganta ba. Tazo wucewa ta gefensu,Na'im yayi arba da'ita,lokaci daya tadauki hankalin sa,yabita dawani irin kallo,Jawad yana ganinsa amma bai nuna masa komai ba, saide acan qasan zuciyarsa wani irin zafi yakeji,wannan kallon nata da Na'im yake wani haushi ne yake nuqurqusar sa. Na'im yajuyo ya kalli Jawad yace"Abokina kaga wata fine girl,wacece?" Kai tsaye Jawad yace"Oho" (🤭) Wata irin Dariya takama P.a, ya kawarda kansa gefe yayi murmushi,sannan yaci gaba da duba takardun hannunsa. (Easy jawad😂) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta ba tareda kin biya ba keda Allah saboda ban yafe ba 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 31&32 Na'im bai lura da yanayin da Jawad yabashi amsa ba yatashi tsaye yace"ina zuwa" Kai tsaye yabi bayan Inaas yasha gabanta,Inaas da batasan da zuwansa ba cikin sauri taja baya tayi turus tana kallonsa da mamaki,Jawad ya d'an juya ya kallesu fuskarsa baqiqqirin sannan yadauke kansa,Na'im ya kalleta yace"Sannu 'Yanmata" Inaas tace"yauwa" Jawad yana jinsu,domin kuwa tazarar dasuka bashi batada yawa. Na'im yace"anan gidan kike ne?" Inaas ta girgiza masa kai sannan tace"baqi ne" Na'im yayi murmushi tareda rausayar da kansa yace"idan bazan takura miki ba inaso kibani number ki,akwai wata shawara dazan baki" Mamaki ya kama Inaas,tafara tambayar kanta wacce irin shawara zai bata? tasaki ajiyar zuciya sannan tace"to gashi dauki" tafadi hakan tareda bashi wayarta,cikin farinciki kuwa Na'im yasaka number sa a wayarta yayi kira, yaga tata number,sannan yabata da tsananin farinciki yace"thank you" Awannan lokacin idan ran Jawad yayi dubu toya 6aci,agabansa yarinyar nan ta dauki number ta tabawa wani,meyasa duk alamomin daya nuna mata takasa fahimtar sa? yaya takeso yayi ne? lokaci daya yaji ransa yasake mugun 6aci, yaji bazai iya jurewa ba, gara ya tunkare ta fuska da fuska ayita taqare, baiyi tunanin komai ba yatashi tsaye zai bi bayan Inaas,sai ga Ammiy tazo wucewa,yana ganinta yayi saranda,yafasa bin bayan Inaas din. Cikin nutsuwa ya rissina ya gaisheta,Na'im ma da baisan wacece ba shima ya gaidata, sannan ya kalli Jawad yace"Abokina nawuce" Jawad baice dashi uffan ba, yana tsugunne awajan har saida Ammiy ta wuce sannan yayi wata ajiyar zuciya mai nauyi yakoma wajan zamansa ya zauna. P.a yaga yanayin da Jawad din yake ciki,hakan yasa ya rissina cikin girmamawa yace"yalla6ai ayi mata uzuri yarinya ce,indai za'a dinga yimata dabara irin haka,to haqiqa kowanne yaro zai iya samun number ta,idan kabani dama ina ganin ya kamata a sauya mata waya da Sim card" Jawad ya lumshe idonsa yabude,yakai tsawon minti biyu baiyi magana ba,sai kuma can yace"ba buqatar hakan P.a" Sannan yamaida hankalinsa kan wata takarda yana karantawa,har saida aka kiran sallar magrib, Sannan suka bar wajan suka wuce masallaci. Adakin Hajiya Zaliha Bilkisu da Inaas sukai sallar magrib, Sannan suka dawo falo,Hajiya Zaliha ta kalli Inaas wacce ta maida hankalin ta kan tv tace" 'yanmatana yakamata kishirya keda Ammin ki kuje Shopping ko?" Bilkisu ta kalleta tace"Haba Hajiya,duk wannan d'awainiyar? munada sauran kayan miya a fridge,sannan 'ya'yan itatuwan ma suna nan dayawa suma" Hajiya Zaliha tace"duk da haka de ai ba zaku rasa abinda zaku siyo ba" Kafin Bilkisu tayi magana,Daddy yashigo tareda Jawad,Inaas tayi sauri ta sauko daga kan kujera ta gaidasu, saide bata yarda sun hada ido itada Jawad ba,Daddy yace"Inaas kallo ake" Cikin murmushi tace"eh Daddy" Daddy yanemi waje ya zauna,sannan Bilkisu ma ta sauko daga kujera ta gaida shi,ya amsa mata cikin kulawa. Jawad yawuce zai tafi dakinsa,Daddy ya kalleshi yace"kai zonan" Cikin ladabi ya dawo ya tsugunna agaban Daddy tareda fadin "Gani Daddy" Daddy ya kalleshi yace"yaya maganar makarantar danace ka nemawa Inaas? tayaya zaka bar yarinya ta zauna haka agida batada aiki sai kallo?" Jawad ya sunkuyar da kansa qasa yarasa meke masa dadi,baqin ciki ya hanashi magana. Daddy ya kalleshi yace"kayi shiru" Jawad yadago da kansa ya kalli Daddy yace"Daddy ai angama bada addmisson,yawanci duka University's dinmu nagida suna first semester ne yanzu" Daddy ya jinjina kansa sannan yace"to anema mata awata qasar" Gaban Jawad yayi wata irin fad'uwa,lokaci d'aya yayi kicin-kicin da fuskarsa. Bilkisu ta kalli Jawad tayi murmushi,tariga tagama ganoshi Kishi ne yake damunsa,da alama bayason maganar karatun nan,in hakane kuwa lalle Jawad yanason Inaas,saide batun aure ne hakan bamai iyuwa bane,kowa yasan cewa ruwa ba sa'an kwando bane. Hajiya Zaliha ta kalli Daddy tace"idan yakoma bakin aikinsa ai saiya nema mata a qasar dayake yawan zama,kaga saitayi karatun ta akusa da Yayanta ,duk abinda zata buqata Yayanta yana kusa" Bata jira amsar da Daddy zai bata ba tamaida kallonta wajan Jawad dayake tsugunne har yanzu kansa yana qasa tace"Jawad kaje ka shirya,kazo kakai Qanwarka shopping itada Mamanta" Daddy yayi murmushi irinna manya bayan yagama gano inda Hajiya Zaliha ta dosa. Hajiya Zaliha ta kalli Inaas tace"Inaas shiga dakina kisake kwalliya kafin Yayanki ya futo" Inaas tamiqe tsaye tadawo kusada Bilkisu ta ajiye wayarta,Sannan tashige dakin Mummy,Jawad da kansa ke qasa ta gefen idonsa yake kallonta yaga inda ta ajiye wayar tata,yadago kansa ya kalli Daddy yaga Daddy yana kallo a TV,yayinda Mummy da Bilkisu suke firar su,hakan yasa yafaki idonsu yayi sauri ya ajiye wayarsa awajan,yadauki ta Inaas yawuce da'ita dakinsa, tunda wayoyin iri daya ne yasan cewa bazasu gane bata Inaas bace awajan. Yana shiga dakinsa baibi takan wani shiryawa ba, zama yayi akan gado yabude wayar tata,yaje yayi blocking number Fu'ad data Na'im,sannan yacire Sim Card d'in ya kakkarya shi mitsi-mitsi.(🙆🏻‍♀️😫) Sai alokacin yayi wata irin ajiyar zuciya, yaji ransa sakayau bashida wata sauran damuwa,yatashi yasake shiryawa cikin Riga da wandon jeans,rigar baqace mai had'e da hula,yayinda wandon tsawon sa yawuce gwiwar sa, amma baikai can qasa yanda wando yake saukowa ba,yadauko glass dinsa dake qara masa kyau yasaka,wato jan duhu, sannan yasauko zuwa qasa,yana zuwa yazauna akusa da wayar daya bari, babu wanda ya lura da abinda yake, hakan yasa ya ajiye wa Inaas tata wayar, shikuma ya dauko tasa,yana hamdala a ransa ganin babu wanda yakirashi bare asirinsa ya tonu. Saida Inaas ta dauki lokaci tana kwalliya,Sannna tafuto tayi kyau sosai kuwa,Jawad yayi mata kallo daya yadauke kansa yatashi yafice daga falon,Sannan Bilkisu tamiqe sukayiwa Mummy sallama sukabi bayan Jawad. Suna futowa Compound din suka hangeshi yana zagaya wajan alamun bayason jira,suna qarasowa guard yabude musu gidan baya suka shiga,driver zaija Jawad yabashi hannu yace"bani key" Driver ya kalli Jawad ya rissina yace"yalla6ai kaida kanka? kabari akaiku mana" Jawad ya girgiza kansa yace"karka damu,bani" Babu musu yabashi key din,Jawad yabude gidan baya ya kalli Inaas fuska babu wasa yace"ke dawo gaba" Cikin sauri Inaas tazuro qafafunta tafuto daga motar,shida kansa yabude mata gidan gaba kusa dashi, sannan tashiga shikuma ya rufe ya zagaya yashiga,yaja motar,sannan motar guard dinsa ta take musu baya. Tafiya suke amma motar shiru babu motsin komai, Bilkisu ta kalli Jawad ta kalli Inaas tayi murmushi Sannan ta maida kallonta zuwa window. Inaas tajuya tadan kalleshi tana so tayi surutu amma babu damar yi,domin kuwa fuskarsa ahade take,kuma so take tayi magana, tsabar babu abokin surutu harjin ta take a takure,hakan yasa tajuya ta kalli window tana ganin dogayen gidaje tana magana ita kadai.(😂) Jawad yajuya ya kalleta ya girgiza kansa,sun kusa qarasawa super market d'in wayar Jawad tayi qara,yadauka tareda sallama. Daga d'ayan 6angaren akace "Yalla6ai daga gareji ne,inaso kazo kaga wad'annan motocin da alama Alhaji ya manta dasu,idan kagani sai kuyi magana dashi inyaso ko gwanjon su ne sai ayi" Jawad ya d'an motsa bakinsa kad'an,sannan yace"ok zan qaraso yanzu,nafuto zanje unguwa,zan qaraso nagansu,insha Allah" Yafad'i hakan tareda kashe wayar,yarage gudu sannan yakira wayar P.a wanda suke cikin daya motar suna bin bayansu Jawad. P.a yana dauka Jawad yace"P.a. zamu fara zuwa gareji kafin muje super market" Cikin girmamawa p.a yace"ok Yalla6ai" Jawad ya d'an kalli Inaas yana sakin ajiyar zuciya a 6oye,sannan yaqara gudun motar ya kallo Bilkisu ta glass yace"Mama zamu d'an biya ta wani gareji" Bilkisu tace"Babu komai Jawad,Allah yakaimu lafiya" Jawad ya amsa da "Amin" sannan yafigi motar dawani irin gudu,suka dauka hanyar zuwa gareji,ba suyi tafiya mai nisa sosai ba suka qaraso cikin garejin,Jawad ya kashe motar,sannan ya futo yanufi wajan wasu motoci masu yawa ajere. Inaas ta sauke glass din motar qasa,yanda zata ga ko'ina,tajuyo ta kalli Bilkisu dake baya tace"Ammiy ki sauke naki kema kiga duniya" Bilkisu tayi murmushi ta sauke glass din,tana iya hango Jawad da sauran guard dinsa,saikuma wani tsoho ma'aikacin garejin yana sanye dawani uniform irin wanda ma'aikatan gareji suke sakawa. Bilkisu ta qarewa motocin dasuke jere ido kowacce mota tana cikin riga,ta jinjina kanta tana fadin "ikon Allah" Acan wajansu Jawad kuwa,bayan yagama jin bayanin tsohon ma'aikacin garejin yayi ajiyar zuciya yace"yanzu Baba mekake ganin za'a yi da wad'annan motocin,? idan akwai masu buqata kuyi magana dasu kawai" Ma'aikacin garejin yacire rigar wata tsohuwar mota sannan ya kalli Jawad yace"yanzu kaga wannan motar,takai samada shekara talatin anan,tunda tasamu matsala Alhaji yakawo ta ya ajiye,bai sake bibiyar taba..." Gaban Bilkisu yayi wata irin bugawa idonta akan number motar da'ake nunawa Jawad,kanta yayi wata irin sarawa, jikinta yafara wata irin rawa tad'aga hannunta dayake rawa kakar-kakar tana nuna motar..., ko shekara dari tayi bata tunanin zata manta da wannan number motar,motar data saka Muhammad dinta aciki,motar da tanaji tana gani aka tafi da d'anta akan idonta. Bakinta ne yake rawa tana so tayi magana amma takasa,sai faman nuna motar take da hannu,wani irin hawaye me zafi yazubo daga idonta,numfashin ta yafara yin sama yana qasa. Acan waje kuwa Jawad yagama magana da me garejin yabashi hannu suka sake gaisawa,sannan yajuyo suka nufo mota,guard yabude wa Jawad mota yashiga, sannan yatada motar suka fara shirin barin garejin,har zuwa lokacin Bilkisu tana nuna wannan motar da hannunta,saida suka fice daga wajan sannan ta sauke hannunta,zuwa wannan lokacin idonta yayi jajir saboda kuka,Mayafin Abayar dake jikinta ta janyo tarufe bakinta dashi ta dora kanta akan cinyarta tana gunjin kuka,Inaas tajuyo baya ta kalleta tace"Ammiy najiki shiru" Cikin sauri Bilkisu ta goge hawayen idonta sannan tadago kanta tana qoqarin daidaita kanta,ta kalli gefen window tana kokarin daidaita kanta,ta maze kamar ba kuka take ba,saide inda acikin Haske suke,kallo daya zaka mata kasan cewa ba qaramin kuka tasha ba. Sun dauki hanyar Super Market Bilkisu ta kalli Jawad dake driving cikin nutsuwa,ta daidaita muryarta yanda bazasu gane halin datake ciki ba tace"Jawad motar da'aka nuna maka ta waye?" Inaas tajuyo ta kalli Ammiy da tsananin mamakin tambayar motar,tasan cewa Amminta bata mu'amula ko wata sabga ta mota. Jawad yana driving batare daya juyo ba yace" wata tsohuwar motar Daddy ce" Gabanta yasake faduwa,takai hannunta kan qirjinta ta dafe,sannan tace"Jawad ka tabbatar motar mahaifinka ce?" Jawad ya d'an juyo ya kalleta yace"Motar Daddy ce Mama,amma shima kansa ya manta da'ita,ta dade a wannan wajan" Wani sabon hawaye me tsananin zafi yazubo daga idon Bilkisu,tasa hannu ta goge,duk yanda take qoqarin 6oye kukan ta kasawa tayi,cikin muryar kuka tace"Jawad kanada Yaya Namiji ne?" Cikin sauri Inaas tajuyo ta kalleta tace"Ammiy!!, yanaji muryarki kamar kina kuka? menene yasame ki?" Jawad yataka wani mahaukacin birki yajuyo ya kalli Bilkisu yace"Mama kuka kuma?" Cikin sauri Bilkisu ta goge hawayen idonta sannan tace"A a, karku damu,babu komai fa,ba kuka nake ba,wani abu ne yafad'a cikin idona" Jawad yabude motar ya futo,yabude seat din baya sannan ya kalleta yace"are you sure babu damuwa Mama?" Bilkisu tayi murmushi tace"babu komai Jawad" Jawad ya gyada kansa,sannan yazuge mata glass din motar,Bilkisu tana ta kallonsa wasu sababbin hawaye suna sake zubo mata,Inaas tana kallonta,tasan cewa tabbas akwai abinda yake damun Ammin,batason Jawad yasani ne,sannan abun mamakin taga idon Ammin nata akan Jawad, kuma hawayen ta bai daina zuba ba,Jawad kuwa bai lura da halin da Bilkisun take ciki ba,bayan ya rufe mata glass din yamaida mata qofar ya rufe, sannan yakoma yaja motar sukaci gaba da tafiya. Bilkisu tayi qoqari ta saita kanta,ganin duka yaran kamar kukan nata yadaga hankalin su. Sun kusa zuwa Super Market d'in Bilkisu ta kalli Jawad tace"Jawad baka bani amsa ba,kanada Yaya namiji?" Jawad ya girgiza kansa yace"A a,banida Yaya,nine Babba sai Fu'ad" Cikin sauri tace"yaushe aka haifi Fu'ad?" Kai tsaye Jawad yace"Shekarar sa Talatin,tsakanina dashi shekara bakwai ne" Idonta a kansa cikin hikima tasake cewa "masha Allah,amma kai menene kwanan watan ranar haihuwar ka?" Mamaki ya kama Jawad,baisan meyasa take masa wannan tambayoyin ba,cikin rashin damuwa yace"goma ga watan January aka haifeni,a shekarar 1986" Bilkisu ta runtse idonta,tanajin bayanin Jawad ta fahimci komai,ta riga tagane cewa Jawad shine Muhammad dinta,d'aya ga watan January ta haife shi,kuma tara ga watan January ya6ata,hakan yana nufin da date din ranar da Alhaji ya tsince shi yake amfani,ta zuba masa ido tana kallonsa,hawaye ya dinga zarya akan kuncinta wani nabin wani,shekaru talatin da bakwai suka dawo mata sabbi fil,kuka take amma murmushi ne a Shimfide a saman fuskar ta,ashe wannan dalilin ne yasa takejin Jawad aranta,inde tunanin ta,da lissafin ta yazama gaskiya tabbas Jawad shine Muhammad dinta. Tayi sauri ta goge hawayen idonta lokacin dasuka tsaya a gaban Super Market d'in,guard suka bude musu motar suka futo,Jawad ya kalli Bilkisu data zuba masa ido tana sake qare masa kallo yace"muje Mama" Wannan Mama daya fada,shine yasa wani hawayen yasake tahowa zai zubo mata, tayi sauri ta maidashi, wannan Mama daya fada,shine yasa tatuna lokacin da yana yaro,tana masa wanka tana magana dashi, tana fada masa cewa Mama tana sonsa,cikin ranta take sake godewa Allah,tana kuma Allah-Allah suyi sukoma gida domin ta zauna da Alhaji. Guard din cikin daya motar gaba dayansu suka tsare gaban Super Market da bindugu a hannun su,yanda Bilkisu taga guards din suna girmama Jawad saita tuna lokacin dayake qarami take masa Addu'ah cewa insha Allah saiya mulki mutane dayawa, gashi maganar ta tana neman tabbata. cikin nutsuwa suka shiga ciki,suna shiga Inaas tafara kalle-kalle saboda wannan shine karo na farko data ta6a zuwa irin wannan wajan,wajan ya had'u sosai ba qarya,wani had'ad'd'en Gaye yana tsaye agefe yabada a.t.m dinsa acire kudin siyaiyar dayayi yazubawa Inaas ido yana kallonta,duk inda ta juya idonsa akanta,kallon farko yayi mata ta dauki hankalin sa. Inaas ta matsa kusa da Bilkisu tace"Ammiy me yasamu idonki,? nasan kuka kikayi ko? meyafaru Ammiy ko wanine yamiki wani abu?" Kafin Bilkisu tayi magana Jawad da kansa ya turo wani kwandon zuba kaya yace"Mama muje" Bilkisu tayi murmushi tayi gaba itada Inaas,shikuma Jawad yaturo kwandon yana binsu Abaya idonsa yana kan Inaas yana ganin yanda Abayar jikinta take nuna yanda Hips dinta yabaje acikin Abayar,yatuna irin wahalar da yasha saboda ganinta da towel,cikin sauri ya dauke kansa kada asake shiga irin makamancin wannan yanayin(🙈) Turare suka dauka dakuma mayukan shafa wa irin wanda sukaga Hajiya Zaliha ta siya musu,Jawad ya kalli yanda suke za6ar kayan kamar suna tsoron kashe kudin sai daukar abu suke guda d'ai d'ai,daga nan wajan qananun kayan mata suka qarasa,Bilkisu taga wasu bra masu kyau,tunda tariga tagano cewa shi din d'anta ne,babu buqatar wani 6oye-6oye,daga Inaas d'in,da Jawad d'in,duka nata ne,hakan yasa ta kalli Inaas tace"Inaas dauki brezia"(😂🙈) Jawad yayi sauri ya sunkuyar da kansa qasa cikin kunya. Inaas tajuya ta kalli gefen Jawad,ta runtse idonta wata irin kunya ta kamata,meyasa Ammiy zata mata haka? Ta kalli Bilkisu cikin shagwa6a tafara bubbuga qafafunta aqasa,kamar zatayi kuka tace"Ammiy ni...ni...ni me zanyi da'ita?" Jawad yadago da idonsa dake cikin glass ya kalleta,tayi bala'in yimasa kyau yanda take shagwa6ar. Bilkisu tace"me ake dashi? shekara da shekaru inayi dake akan kidinga sakawa kinqi, dauki nace!" Ina taturo d'an qaramin bakinta gaba cikin shagwa6a tace"to Ammiy tamin girma fa" Jawad ya d'an dago idonsa yasauke su akan nashanunta,bai ta6a lura cewa bata saka bra ba,abubuwan nata a tsaye suke car,kuma tana qoqarin 6oye su yanda mutum bazai gane bata saka ba,yanda yazubawa nashanun nata ido yana kallo hakan yasa yaji wani irin abu zirrrrr tundaga kansa har zuwa tafin qafar sa. Ammi ta kalli Jawad taga inda idonsa yake,tayi murmushi ta janye idonta daga kansa,taga alama kamar ya manta inda yake,fata take aranta Allah yasa baiyi gadon zilamar ubansa ba(🙈🙊) Ta katse masa kallon nasa ta hanyar fadin"Jawad za6awa qanwarka brezia" Cikin sauri Jawad yajuyo ya kalleta,wata irin kunya ta kamashi,kode ta kamashi yana kallon abubuwan 'yarta? Bilkisu tagyada masa kanta alamun tabbatarwa,kamar me tsoron ta6awa haka yakai hannunsa yadauki wacce yake ganin zatayi mata daidai,yasaka acikin kwandon,sannan yasake qaro mata wasu kalolin masu kyau,Inaas tayi masa wani irin kallo ta jefeshi da wayar hannunta,cikin shagwa6a tayi gaba. Daga nan wajan kayan cefane sukaje,Jawad yaga suna daukar normal kayan Miya irinna kowa,ya kalli Bilkisu ya nuna mata irinna qasar waje yace"Mama bakwa amfani da irin wannan?" Bilkisu tayi murmushi tace"Jawad bamu saba cin irin wannan abubuwan ba" Jawad ya girgiza kansa sannan yasaka hannu yadauka yasaka musu yace"kufara koya yanzu" Saida suka gama siyan komai,sannan sukaje Jawad yabiya kudin,suka futo,har zuwa wannan lokacin idon Bilkisu akan Jawad,har yanzu takasa gaskata cewa yanzu wannan ingarman yaron shine Muhammad dinta,Garin kallonsa tayi tuntu6e zata fadi,cikin sauri Jawad ya tarota zuwa jikinsa,Bilkisu tasake rungume shi,wani irin sabon hawaye yazubo daga idonta. Saida yaji ta daidaita sannan yacire ta daga jikinsa yace"Bakiji ciwo ba Mama?" Bilkisu tace"Babu komai Jawad" Tajuya suka shige mota,Jawad yaja yayi gaba,suma guard dinsa suka shige mota sukabi bayansu. Gayen dayaga Inaas tun dazu, Shima yayi sauri yashiga tasa motar yabi bayansu. Ahanya idon Bilkisu yana kan window tana share hawaye kad'an kad'an,har sukazo gida bata daina kuka ba,suna tsayawa kuwa itace tafara fita daga motar tayi ciki dawani irin sauri. Tana shiga falonsu taga babu kowa hakan yasa tashige daki ta kulle kanta tasaki wani irin kuka harda shashsheka,sosai take kuka kamar ranta zai fita,lokaci daya idonta ya kunbura yayi jajir kasancewar ta farar mace. Saida tagama shan kukan ta,sannan tashige toilet ta dauro alwala tazo tata da kabbarar sallah,ta dade a tsaye tanata karatun sura,sannan ta qarasa sauran raka'at din, tayi sallama ta daga hannunta sama tana sake yiwa ubangiji godia. Tatashi tafuto falo taga Farouq,da Man Sulaiman a zaune,tunda tafuto Man Sulaiman yazuba mata ido yana kallonta kokadan yakasa dauke idonsa akanta. Bilkisu ta kalli Inaas dake zaune tana ganin kayan dasuka siyo yanzu,tace"Inaas kije ki taya Yayanki Jawad fira mana" Cikin sauri Inaas ta kalli Bilkisu,itace tayi mata fada akan babu ruwanta da Jawad,itace tahana ta yin waya da Jawad,menene ya sauya Ammiy lokaci daya haka? meyasa take qoqarin cusata wajansa ayau d'in? meyasa take nunawa kamar itada Jawad din duk abu d'aya ne? Ganin cewa batada bakin da zatayi mata wannan tambayoyin,hakan yasa tamiqe ta dauki wayarta tatafi Plat din Mummy. Inaas tana fita Farouq ya kalli Bilkisu yace"Meyasa kikeso biyewa yarinyar nan ne Yaya? ba wannan bama menene yafaru naga idonki haka? kinyi kuka Yaya,rabonda naganki cikin irin wannan yanayin na kuka tun bayan shekara talatin da bakwai" Wani sabon hawaye yazubo daga idonta,tasa hannu ta share sannan ta kallesu tace"naganshi" Man Sulaiman yayi sauri yace"waye? wa kika gani Bilkisu?" Bilkisu ta dago idonta ta kalli Man Sulaiman,kokadan bataso ya dinga kiran Sunanta haka kai tsaye,saboda yana ta6a zuciyar ta,tun a shekarun baya ma idan yace Bilkisu jitake kamar yafi kowa iya kiran sunan nata(🙊) Bata kula hawayen dayake zubo mata ba bare ta goge,ta kalli cikin idon Man Sulaiman tace"Naga d'ana... inaso ka temaka ka kiramin Alhaji" (ina fatan wannan labari yana DEBE MUKU KEWA💃🏻 Nace ba🤔new P.a yaya batun Sim Card din da Yalla6ai ya karya ne? 🤔sabo zaku nemo kokuma baqin Hali ne yasa kuka karya? 😂 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,karki karanta littafin Allah ya'isa,ki siya ki karanta cikin salama inba haka ba kuma keda Allah 👌🏻 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 31&32 Tana shiga falon Mummy Fu'ad yasaki murmushi yace"Inaas kin 6uya,ko neman mutum awaya bakya yi,idan nakira wayarki kuma bata shiga" Inaas tayi sallama ta qarasa wajansa tana kallon gefen da Jawad yake zaune,su biyu ne kadai afalon,ta zauna kusa da Fu'ad tace"Yaya Fu'ad dan Allah ka dubamin wayata,Sim Card dina ya sauka,na kashe wayar na kunna ko zai dawo amma bai dawo ba" Jawad yayi musu kallo d'aya itada Fu'ad din,yata6e baki yaci gaba da shan lemonsa. Fu'ad ya kar6i wayar yaduba yaduba yace"kai yanaga kamar wayar taki babu Sim aciki" Cikin mamaki Inaas tace"Babu Sim kuma? to wallahi nide ban cire Sim ba,banma san yanda akeyi ake duba wajan Sim ba" Fu'ad yaduba wajan saka Sim Card yaga babu Sim, ya kalleta yace"ai babu Sim,wa kika bawa aron wayarki? inde kin bayar to ancire miki" Inaas ta girgiza kanta tace"gaskiya babu wanda nabawa,toni yanzu ya zanyi?" Taqarasa maganar cikin shagwa6a. Fu'ad yayi murmushi yace" inada wasu adaki na,bari inje in kawo miki " Cikin farinciki tace"to Yaya Fu'ad nagode" Fu'ad yatashi yatafi dakinsa,adede lokacin Mummy da Daddy suka sauko daga sama,sakamakon kiran da Man Sulaiman yayi musu awaya cewa akwai magana mai muhinmanci dasuke so suyi gaba d'ayansu. Mummy ta kalli Jawad,tasake kallon Inaas tayi murmushi,duk da zaman nasu kowa harkarsa yake, hakan ba qaramin dadi yayiwa Mummy ba,tace"Inaas fira kuke ne?" Inaas tayi murmushi tayi qasa da kanta cikin kunya saboda Daddy daya kallesu yawuce shima. Falon ya kasance saisu biyu,Jawad yadago yasaci kallonta,adede lokacin itama ta kalleshi,cikin sauri kowa ya dauke idonsa. Fu'ad yadawo yasaka mata Sim Card din sannan yace"Daddy yamin waya inje gidan Hajiya Mama in dauko ta,ai kina nan babu inda zakije ko?" Inaas tace"eh ina nan" Fu'ad ya kalli Jawad yace"Yaya saina dawo" Jawad yace"ok" Inaas tafara duba wayar tata,taga Sim gashinan a fuskar wayar alamar yahau,ta girgiza kanta cikin mamakin waye zai cire mata Sim Card,wata waqa ce acikin wayar tata qwaya daya,ta kunna tana danji,ko minti daya batayi da fara ji ba,Jawad yatashi tsaye ya kalleta yace"miye hakan kikeji kamar kinajin wata duniya?kinajin muryar qaton gardi ko kunya bakyaji ki kashe wayar nan yanzu-yanzu,ki goge wannan waqar,mene abun birge wa ajin waqar gardi?" Inaas ta kalleshi taturo d'an qaramin bakinta gaba,menene laifi dan mutum yaji waqa? Jawad ya daure fuska yayi gaba zai wuce dakinsa. Cikin sauri Inaas tatashi tabi bayansa,tace"Yalla6ai" Jawad ya runtse idonsa,bayason jin wannan Yalla6ai din datake fada,yakamata tagane cewa ita din daban take da sauran mutane masu kiransa da suna Yalla6ai, yajuyo yazuba mata mayun idonsa. Inaas ta kalleshi sannan tayi qasa da idonta tace"Yaya..." Jawad yayi ajiyar zuciya yaharde hannunsa ya qirjinsa yanajin wani irin tsantsar nishadi kasantuwar su su biyu afalon, cikin wata irin murya yace"what?" Cikin shagwa6a tace"toni ba Ammiy ce tace nazo na tayaka fira ba" Wani irin yanayi ya rufe Jawad,sakamakon wannan shagwa6ar datayi masa,ya d'an lumshe idonsa yabude,yanaji kamar ya fuzgota jikinsa,cikin wata irin muryar rad'a wadda daga ita sai shi ne zasuji maganar juna yace"ki dameni da surutu de...,fadamin meyasa bakyason kiran wayata?" Inaas taji wani irin zirrrr ajikinta saboda yanda yake mata maganar cikin rad'a,batare data kalleshi ba tadan juya fararen idonta,bataso tace masa Ammiy ce da Abban ta ne suka hanata kira,hakan yasa tace masa"katin daka bani ne yafadi" Jawad yasake gyara tsayiwarsa idonsa akanta yace"saboda baki daukeni da muhinmanci ba?" Mamakin maganar sa yasa tadago da kanta ta kalleshi, Jawad yaci gaba da kallonta,yanda suka tsaya suna fuskantar juna face to face, hakan ba qaramin dadi yake masa ba,hakan ne yasake bashi damar qare mata kallo,idonsa akan d'an qaramin lips dinta wanda yakeji kamar ya shanye wannan sauran lipstick din na bakinta. Inaas da batasan cewa lips dinta yake kallo ba tace"nifa ba haka bane,lokacin da muka dawo na ajiye katin inda yadace,kuma Abbana yace wayar daka bani tayi girma karna fara amfani da'ita,kuma ni tun alokacin nakeso na kiraka,kuma dazan kira din saina rasa katin,naduba-naduba banganshi ba, to dan Allah ya zanyi?" Tafadi hakan tana kallonsa,Jawad yayi ajiyar zuciya ya dauke idonsa daga kan lips dinta,duk wannan dogon bayanin kawai dan an rasa kati ne? yarinyar nan akwai surutu. Yanda take kallonsa shima haka yazuba mata ido yana kallonta,Inaas tana kallon tsantsar kyau irinna Yalla6ai Jawad,haqiqa duk wacce ta aure shi,tasamu miji na bugawa a jarida saide zata sha fama da yanmata a kansa, Yalla6ai Jawad ya had'u iya haduwa,baida makusa ko d'aya. Yayinda Jawad kuwa tunani yake ta wacce hanya ya kamata ya bayyana mata yanda yake jin ta aransa? meyasa takasa gane alamomin dayake nuna mata? Why?. **** Har Plat din su Bilkisu Fu'ad yaraka Yaya Mariya,yayi mamakin ganin iyayen nasu gaba daya a zaune afalon,ya tsugunna ya gaida su sannan ya futo yana fatan cewa Allah yasa lafiya ce tahada su awajan. Kai tsaye mota yakoma yafita yanaso ya siyo musu ice-cream shida Inaas su sha tare.(🙊) Yaya Mariya ta kalli Alhaji Mekudi,sannan ta kalli Man Sulaiman da Abban Inaas tace"meyake faruwa haka ina zaman zamana agida Fu'ad yazo yacemin kunason ganina?" Alhaji Mekudi ya dubi yayar tasa yace"Wallahi Yaya nikaina bansani ba,ina zaune Man Sulaiman yamin waya cewa akwai maganar dayake so muyi me muhinmanci,bayan munzo kuma saiya sake cemin in daure kema inkiraki,inajin de batun aurensu ne shida Bilkisu yataso,da alama komai yawuce sun gama daidaita kansu,amma de gashinan ki tambayeshi" Ya qarasa maganar yana d'an murmushi. Yaya Mariya ta kalli Man Sulaiman tace"Sulaiman meyake faruwa? kuyi min bayani" Man Sulaiman yayi ajiyar zuciya yace"Wallahi Yaya,muna zaune nida Farouq,Bilkisu tafuto daga daki cikin kuka,take fada mana cewa taga yaronta,sannan kuma dan Allah in taimaka inkira mata Alhaji,to ganin cewa maganar ba qarama bace,hakan yasa na cewa Alhaji kema kizo ayi komai agabanki amatsayin ki na Babba" Yaya Mariya tayi wata irin ajiyar zuciya sannan ta kalli Bilkisu wadda take zubar da hawaye,cikin sigar lallashi tace"Bilkisu,fadamin a'ina kikaga yaron ki? muddin acikin qasar nan yake,to zamu tsaya miki muga mun qwato miki yaron ki,fada mana a'ina kika ganshi?" Bilkisu tadago fuskarta wadda tayi jajir,hatta kumatunta duk yayi ja alamun tasha kuka,ta kalli Alhaji Mekudi tace"Alhaji,shekaru talatin da bakwai dasuka wuce,tara ga watan d'aya,a shekarar Alif d'ari tara da tamanin da shida, cikin dare,adede qauyen Dungas na qasar Niger,na ajiye yarona Muhammad acikin mota me d'aukeda lambar qasar Nigeria cikin garin Lagos,mun fita nida Jawad d'azu,naga wannan motar a gareji,Jawad ya tabbatar min motarka ce,Alhaji dan girman Allah kafadamin ina yarona Muhammad yake?,yamutu ko yana raye? katemaka ka fadamin Alhaji" Ta qarasa maganar tana saukowa daga kan kujera ta zuba gwiwar ta aqasa tareda hade hannunta waje d'aya (🙏🏻) Tana roqonsa. Gaba daya sai falon yayi tsit...,shashshekar kukan Bilkisu ne kawai yake tashi,yayinda Man Sulaiman yayi qasa da kansa shima yana goge hawaye,haqiqa ya zalunci Bilkisu,baisan iya gararin datayi ba lokacin daya gudu ya barta. Daddy ya runtse idonsa yakasa dago ido ya kalli Bilkisu,yadade a wannan yanayi,haka duk tsawon lokacin daya dauka baice komai ba Bilkisu tana tsugunne agabansa kamar me neman gafara tana aikin kuka. Daddy yadago kansa ya kalli Bilkisu da idanunsa wanda sukai jajir yace"Bilkisu kece...?" Bilkisu tagyad'a masa kanta,idonta yana tsiyayar da hawaye,cikin kuka tace"Alhaji ka temaka min,inason dana" Tana fadin haka,numfashinta yafara sama-sama tana qoqarin faduwa awajan tanajan numfashi da qyar kamar zata shid'e. Dawani irin gudu Man Sulaiman yataso zai rungumota tafad'o jikinsa(🙆🏻‍♀️) Lokaci d'aya yatuna cewa yanzu fa Bilkisu ba matarsa bace,yanzu ba da bace,hakan yasa yaja yayi turus,yayinda Hajiya Zaliha da hawaye yake sauka a tata fuskar,tayi sauri ta ruqo Bilkisu suka koma kan kujera suka zauna,tana goge mata hawayen idonta. Daddy ya kalli Bilkisu yace"Bilkisu bayan nagama jin dukkan hujjojinki,hakan ma ya gamsar dani,basai kin tsugunna agabana kina roqona akan haqqin ki ba,a wannan ranar bayan na zaga nakama ruwa,kai tsaye nashiga mota ta natafi,saboda saina shigo cikin kano sannan zan hau jirgin dazai kawoni Lagos,bansan cewa akwai mutum acikin mota ta ba,saida nayi nisa naji motsin jariri,na dakata nazo na daukeshi,muka dawo inda na ajiye mota ta saide banga kowa awajan ba,hakanne yasa na daga yaron sama nayiwa Allah godia bisa kyautar dayayi min wadda mun dade muna neman haihuwa nida matata Zaliha amma Allah bai bamu ba,hakan yasa muka rungumi wannan kyauta da Allah yamin amatsayin yaron mu,a halin da'ake ciki yanzu Bilkisu JAWAD shine yaron ki" Cikin sauri Man Sulaiman ya kalli Alhaji,hakan yana nufin Jawad yaronsa ne? Cikin Jawad ne ajikin Bilkisu ya gudu yabar su? still abinda ya gudu yabari shine yadawo yake aiki a qarqashin sa? ashe wannan dalilin ne yasa yakejin Jawad acikin zuciyarsa? Lokaci d'aya yafashe dawani irin kuka,sosai yake kuka kamar ransa zai fita,tunani yake meya aikata haka? meyasa yayi sanadiyar rabuwar uwa da d'anta? Farouq ya matsa yafara bubbuga bayansa alamun lallashi,shi kansa abun ya daure masa kai,sai yanzu ne yagane dalilin da yasa ko kad'an Bilkisu batason laifin Jawad. Bilkisu ta share hawayen idonta tana jan wata irin ajiyar zuciya idanunta duk sun kumbura,Hajiya Zaliha ta goge hawayen idonta sannan ta kalli Bilkisu dake gefenta tace"yanzu Bilkisu Jawad dina shine Muhammad dinki? dan Allah Bilkisu na roqeki kada ki qwace Jawad daga wajena,ki fada masa komai,kiyi masa komai duk abinda kika so,amma dan Allah karki rabani dashi,wallahi tallahi ina sonsa" Cikin kuka Bilkisu ta rungume Hajiya Zaliha,sannan tace"har gobe,har abada Jawad nakine Hajiya" itama Hajiya Zaliha bata jira komai ba tasake rungume Bilkisu sukaci gaba da kuka,sosai suke kuka kamar anyi musu mutuwa,babu wanda basu karya wa zuciya ba afalon. (bari mu leqo wad'ancan tsuntsayen soyaiyar 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️) **** Bazata iya jure kallon cikin idon Yalla6ai Jawad ba,tanajin kamar wani abu ne yake futowa daga cikin idonsa yake shigewa cikin nata idon,cikin sauri ta janye idonta daga qwayar idonsa. Ahankali Jawad yatako ya matso dab da ita qiris yarage yahad'e jikinsu waje d'aya,cikin sauri Inass tayi qasa da kanta,gabanta yafara fad'uwa,tanajin yanda kusancin nasu yayi kusanci dayawa,cikin wani irin salo Jawad ya sassauta muryar sa takoma rad'a, sannan yace"mekike so?" Inaas ta girgiza kanta alamun babu komai,daga nan tafara tunani me zata ce masa? ce masa zatayi yana birgeta? kokuma ce masa zatayi shid'in had'ad'd'e ne? tasan cewa yayi mata nisa,nisan da koda wasa ba zatayi kuskuren saka sonsa acikin zuciyar taba,saboda ta riga tagama gane cewa shi d'in yayi mata nisa. Ahankali tajuya zata tafi,yayi sauri ya fuzgota tafada jikinsa,tanajin yanda numfashinsa yake bugar gefen wuyanta. Ahankali Jawad yafara matso da fuskarsa dab da tata fuskar,sannan ya lumshe idonsa ya karkatar da kansa,yanufi lips dinta gadan-gadan zaiyi kissing,tana ganin abinda yake qoqarin yi,tazaro idonta, cikin sauri ta qwace daga jikinsa tabar wajan da gudu, ta nufi qofa, zata fice daga falon. Jawad yazuba hannunsa acikin aljihun wandon sa yana sakin ajiyar zuciya, yabi bayanta dawani irin kallo mai cikeda shauqi sai hadiyar wani irin yawu yake(🙈) Cikin qasan maqoshinsa yace"i luv her..." Inaas takama handle din dakin zata fita,aka turo qofar falon dawani irin qarfi,cikin sauri tayi baya tana tunanin duk wanda yabude qofar nan,afusace yake. Kafin tagama tunanin datake wani Babban mutum yashigo dagashi sai Jallabiya kana ganinsa kasan cewa ba'a hayyacinsa yake ba,yadaga Murya cikin Masifa yace"ina Zalihan take!!?" Jawad ya kalli Uncle Bature mahaifin Amal yarinyar daza'a hadasu aure aka fasa,cikin mamaki yace"Uncle meyake faruwa?" Cikin Masifa Uncle Bature yace"dakata Jawad,waye Uncle d'in naka? kaje can kanemi Uncle d'inka,wallahi tallahi nafi qarfin zama Uncle d'in d'an tsuntuwa..." Inaas datake tsaye abakin qofa ta kalleshi da sauri tana bude baki cikin tsananin mamaki. Jawad ya qaraso wajansa yace"what? mekake magana akai Uncle?" Cikin tsananin Bala'i Uncle Bature yace"wato saboda nace bazan baka 'yata Amal ba,nakuma bugi Qirji nace wa Zaliha na cinye kudin data bani shine hakan bai isheku ba saida kuka sa akaje aka bankawa gidana wuta komai da komai ya qone ban tsira da komai ba,to inaso kasani,kaiba kowa bane face d'an tsuntuwa,bazan had'a jini da kai ba,taqamar kade shine kanada kudi kanada masu tsaya ma amatsayin iyaye,to kasani ko duk abinda na mallaka zai qare wallahi, tallahi sai kotu tabimim haqqina akanku..." Jawad ya runtse idonsa yanajin kansa yayi nauyi kamar an d'ora masa wani gingimeman dutse,me Uncle Bature yake fad'a haka? Meyake shirin faruwa dashi ne? Lokaci d'aya yafara ganin duhu-duhu ga jiri yana dibarsa,yaji falon nasu yana juyawa,hakan yasa yafara laluben kujera yanaso ya dafata gudun kada yafad'i. Inass tajuya ta kalli yanayin da Jawad yake ciki kamar wanda yasha wani abu na maye kamar ma shirin faduwa qasa yakeyi. Cikin wani irin gudu tafi ce daga falon ta nufi Plat dinsu. Adede wannan lokacin Yaya Mariya ta kalli Bilkisu da Hajiya Zaliha dakuma Man Sulaiman dasuke faman kuka ta goge qwallar idonta tace"kukan nan ya'isa haka,tunda an fahimci juna ubangiji ya kamata muyiwa godia,tunda komai yazo cikin sauqi" Kafin wani daga cikinsu yayi magana Inaas ta banko qofar falon har tana fad'uwa qasa,cikin tashin hankali tafara nuna musu qofar falon da hannunta amma takasa magana. Abban ta yatashi yadawo wajanta ya jijjigata yana fadin"ke meyake faruwa? me aka miki?" Cikin tashin hankali Inaas tace"Yaya Jawad ne....shida wani afalo...Yaya Jawad ne....Abba idonsa yana rufewa zai fad'..." Kafin Inaas tagama cewa zai fad'i,Bilkisu ta miqe,cikin sauri Yaya Mariya tace"Subhanallah" tamiqe suka fice da sauri suka nufi falon Mummy. Suna zuwa falon sukaga Jawad yakama gwiwar sa yariqe yana qoqarin fad'uwa. Bilkisu da Mummy sukai kan Jawad,Man Sulaiman yana tsaye agefe har lokacin hawaye yake daukewa daga fuskar sa. Daddy yayi qarfin halin d'ago Jawad sannan yace"meyake faruwa Jawad?" Cikin tashin hankali Jawad ya kalli inda yake jin maganar Daddy sannan yace"Daddy bana gani...,duhu nake gani" Cikin 6acin rai Daddy ya kalli Bature yace"wallahi,tallahi Bature duk abinda yasamu yarona,saina makaka a Court anyi maka daurin rai agidan yari" Yaya Mariya ta kalli Uncle Bature tace"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un...ni Mariya yau nake ganin Bala'i,yau kuma masifa ta sauka a gidanmu,Bature meya kawoka gidannan? Bayan cin amanar da kuka mana mekake nema kuma?" Adede lokacin Fu'ad yadawo,hannunsa riqeda ledar daya siyo musu ice-cream,yana shigowa falon yatsaya yayi turus ganin mutanan gidan ba lafiya,ga Inaas agefe sai kuka takeyi,ga Mummy da Bilkisu da Daddy sun rirriqe Jawad kowa hankalinsa atashe. Uncle Bature ya kalli Yaya Mariya yace"cin amana yawuce wanda kukamin,dan me zaisa aje a qonamin gidana saboda na hanashi auren Amal? shi awa zan dauki yartawa qwalli d'aya jal na bashi,asalinsa nasani kokuma tushensa nasani dazan had'a 'yata da d'an tsuntuwa? Wallahi kotu ce zata rabani daku" Fu'ad yasaki ledar hannunsa yace"What? Uncle mekake fada haka?" Lokaci d'aya Yaya Mariya data gama jin dalilin komai,ta hayaiyaqo masa da masifa tace"yanzu ko naji,lalle Bature ka tabbatar min da cewa kai jahili ne,inde baka yarda da qaddara ba,naji dadin wannan gobara saboda dama kariga kahada kudin ka da kudin haram,Allah ne yabi wa Jawad haqqin sa,Amal kuma kaje kajiqata kasha,wallahi tallahi Jawad yafi qarfinta,dama can ba kalar aurensa bace,kotu kuma ka dade baka kaiba,daga kotun farko har kotun qoli daidai muke dakai" Cikin 6acin rai Uncle Bature yace"Mariya haka kikace?" Yaya Mariya tace"ban'isa nafadi hakan bane?" Ta daga murya tace"security!!!" Cikin sauri wasu sojoji guda biyu suka shigo. Yaya Mariya ta nuna musu Uncle Bature tace"ku kamashi kuma sa duka ku wullar dashi awaje,tayaya zaku dinga barin mahaukata suna shigo muku gida?" Uncle Bature Yajuya ya kalli Yaya Mariya da tsananin 6acin rai,kafin yace wani abu Sojojin nan suka d'aga shi sama cak, sukai waje dashi. Daddy yajuyo ya kalli Abban Inaas yace"Farouq matso mu kaishi daki" Jawad yadago kansa,ya kalli Daddy da idanunsa dasuka rine sukai jajir yace"Daddy me kuke 6oyemin ne? da gaske ne abinda Uncle Bature yaje fada ba kune iyayena ba?" Daddy ya sunkuyar da kansa qasa cikeda taqaicin abinda Bature yayi,yaso ace sun zaunar da Jawad din cikin fahimta sun sanar dashi komai. Wani irin hawaye yazubo daga idon sa,baya jin ko Man Sulaiman dayayi silar zuwan Jawad duniya zai kaishi son yaron,yana qaunar Jawad tun ranar farko da Allah yabashi shi. Kokadan bai hana kansa zubar da wannan hawaye ba. Ganin Daddy ya sunkuyar da kansa qasa yana hawaye babu amsa,hakan ne ya tabbatar wa da Jawad cewa kenan gaskiya Uncle Bature yafada. Yajuya yasake kallon Mummy,hawaye yazubo daga idon Hajiya Zaliha ahankali ta kawar da kanta gefe takasa kallon Jawad din,bata sake tabbatar wa tana qaunar Jawad ba sai yau,yayi mugun bata tausayi. Hakan daya gani daga wajansu shine yasake tabbatar masa cewa tabbas shi d'in ba dansu bane,may be ma bashida iyaye kokuma agidan marayu suka dauko shi. Cikeda damuwa ya runtse idonsa yanajin duniyar gaba daya ta masa qunci,to su waye iyayensa? meyasa suka rabu dashi? daqyar ya'iya bude idonsa wanda yake jin yanason rufewa ya sake kallon Mummy da Daddy yace"Mummy,Daddy! kufadamin su waye iyayena?" Hawaye yazubo daga idanun Bilkisu,ta matso ta riqe fuskarsa da tafin hannunta biyu sannan ta kalli cikin idon Jawad,cikin muryar kuka tace"nice mahaifiyar ka,nice na haifeka,ina sonka sama da kowa a Duniyar nan" Inaas da Fu'ad da basusan abinda yake wakana ba,suka dago kansu da sauri suka kalli Bilkisu. Jawad kuwa yanajin furucin Bilkisu ya lumshe idonsa,wani irin hawaye me d'umi yazubo daga idanunsa,ahankali yafurta kalmar "MAMA" ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan baki biyaba kika karanta min littafi to ban yafe ba👌🏻 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 17&18 Hawaye yazubo daga idon Bilkisu,cikin kuka yace"na'am Muhammad" Jawad ya lumshe idonsa,wani irin hawaye me d'umi yazubo daga idanunsa. Daga wannan lumshe idon dayayi, baisake budewa ba yaji qafafunsa bazasu iya daukarsa ba,daga nan yazube awajan bai sake sanin meke faruwa ba. Cikin sauri Fu'ad yayi wani irin tsalle sai gashi a gaban Jawad yataroshi,Daddy da Man Sulaiman da Farouq suka qaraso suka kinkimi Jawad sukai sama dashi,Mummy da Bilkisu da Inaas dakuma Yaya Mariya sukabi bayan mazan. Wannan shine karon farko da Inaas da Bilkisu suka ta6a hawowa sama,Inaas de saida tadan gwada halin nata,domin kuwa sai kalle Kalle take sosai tabawa idonta abinci saboda abinda ba'a saba gani bane,tundaga falon sama har cikin dakin na Jawad sun kai maqurar haduwa, an tsara shi dakyau kamar baza'a mutu ba. Kwantar dashi sukai akan gado,sannan Fu'ad yakira wayar likita,dukansu kowa yayi shiru ya nemi wajan zama sukai jugum-jugum har likita yazo ya dubashi,bayan yagama dubashi ya kalli mazan dakin yace"babu abinda yake damunsa,kawai yaji wani wani abu ne wanda yabashi tsoro,insha Allah idan yafarka zai tashi lafiya" Daddy yace"to Alhamdulillah likita,mungode sosai, Allah ya tasheshi lafiya" Likita ya amsa masa, sannan yayi musu sallama yatafi. Yaya Mariya tasaki ajiyar zuciya tace"Bature! Bature!! Bature ba mutumin kirki bane,Allah ya shirye shi idan me shiryuwa ne,idan kuma bazai shiryu ba daidai nake dashi" Mummy tayi qasa da kanta,har gobe tana nadamar abinda suka aikata abaya itada Yayan nata,yaro yana zaune dasu zuciya d'aya,yanzu gashi saboda jin cewa su din ba iyayensa bane shine yashiga wannan hali,dole ne tasake neman gafara awajan ubangiji ta kuma nutsu taja yaranta jikinta. Yaya Mariya ta kalli mutanan dakin baki d'aya tace"to Bilkisu ku zauna tare dashi keda Zaliha,bari mu barshi yahuta" Cikin sauri Hajiya Zaliha ma tatashi tace"A a Yaya,yau kam itace tafi cancanta ta zauna dashi,taja shi ajikinta ta lallashe shi" Daddy yace"hakane kam,Man Sulaiman kaima matsa kusa ku zauna tare" Man Sulaiman ya girgiza kansa ahankali yace"Haba Alhaji,ni dakai awajan Jawad duk d'aya ne,yanda zaka fita nima fita zanyi,ita Bilkisun de ta zauna, zata iya kulawa dashi,Allah yasaka muku da Alkhairi Alhaji,Allah yabiya ku da gidan aljanna" Ya qarasa maganar yana fashewa da kuka. Daddy yadan bubbuga gefen kafadarsa yace"ya'isa haka Man Sulaiman" Daga nan kowa yamiqe,Bilkisu ta qarasa kan gadon Jawad din ta zauna ahankali,Inaas ta qaraso wajanta tace"Ammiy kidena kuka, murna zakiyi" Bilkisu tayi murmushi ta kalleta tareda shafa kanta tace"to Inaas,kije ki kwanta karki manta kiyi Addu'ah kinji?zan zauna tareda Yayanki" Inaas tace"to Ammiy" Sannan itama ta futo tabiyo bayan su Yaya Mariya,saida tasake yiwa Ammiy bye bye da hannunta,sannan taja musu qofar tarufe. Fu'ad ya dauki Yaya Mariya zai maida ta gida,Mummy kuma suka wuce daki itada Daddy,itama Inaas tabi bayan Abban ta da Man Sulaiman suka nufi nasu Plat din. Tana zuwa dakinsu tamurzawa qofar key,sannan ta jingina ajikin qofar tana sakin wani irin murmushin jin dad'i,Yaya Jawad shine Yayanta? kenan shiyasa Ammiy take sonsa? Cikin wata irin murna tayi jifa da Mayafin Abayar dake kanta tahau kan gadon nasu ta dinga tsallen murna. **** Qarfe goma da rabi na dare Bilkisu tajuya ta kalli Jawad wanda yake bacci har yanzu,ta kalli yatsun qafarsa har yanzu de sak irin yatsun qafar Man Sulaiman ne,hawaye yazubo daga idonta tayi sauri ta goge su,sannan tasake matsawa kusa da Jawad din tadauke kansa dake kan fillo tadawo dashi kan cinyarta,ahankali ta dora hannunta akan lallausar sumar kansa ta dinga shafawa,bata cikakken minti d'aya batare data sake kallonsa ba. Har wajan shabiyun dare Jawad bai tashi ba,har zuwa wannan lokacin kuma Bilkisu bata daina shafa sumar kansa ba,jitake kamar a mafarki wai yau itace tareda d'anta,bayan shekaru talatin da bakwai yau Allah ya bayyana mata d'anta. Cikin wata irin murya me rauni tace"Baba na ina kashiga? ina ka shige kabar Mama tsawon wannan shekarun?" Hawaye yacika idonta,ba tareda data goge hawayen ba taci gaba da fadin"meyasa na aikata haka? meyasa na salwantar dakai?" Hawayen ta ya d'iso akan fuskar Jawad,tunda tafara magana yana jinta,shi kansa hawaye yake,itama tanajin yanda hawayensa yake sauka akan cinyarta. Ahankali yasaka hannayen sa a bayanta dede qugunta,yasake rungume ta yana sakin kuka kamar ba Yalla6ai Jawad ba. Daga ita harshi kuka suke,cikin kuka yace"Karki sake tafiya ki barni Mama...." Bilkisu dake kuka tace"bazan sake ba Jawad,ina tare dakai bazan sake yin nesa dakai ba,Mama tana nan bazata sake barin d'anta ba" Jawad yasake Rungume ta sukaci gaba da kuka,sun dade suna kuka sannan tayi shiru,shima ta share masa hawayen idonsa,taci gaba da fadin"ba'asan raina narabu dakai ba,lokacin da nabar jigawa state munshigo Niger ahanya yan fashi suka taremu, sun nunamin suna so suyi fasiqanci dani,nikuma na bijire musu,hakan yasa na gudu,sukabi bayana zasu kamoni,gashi sai kuka kake,duk inda sukaji kukan ka saisu biyoni,nasa hannu na na rufema baki naga kana qoqarin shid'ewa, hakan yasa danaga mota a ajiye agefe kuma duka glass din motar a rufe suke sainayi sauri nasaka ka aciki na rufe motar, ashe yan fashin sun ganni,sukazo suka Jani cikin duhu suka rufemin baki na, akan idona Alhaji yaja mota yatafi,gashi kana cikin motar, ganin Antafi min da dana hakan yasa naji wani irin qarfi naqwaci kaina a wajansu nabi bayan motar da gudu,saide tuni Alhaji yamin nisa,Nashiga matuqar damuwa alokacin dana rasaka,bansan adadin kwanakin danayi kewarka ba,har bayan wasu shekaru ban dawo daidai ba,saida Jamila matar qanina Farouq ta haifi Inaas,sannan ne Inaas taci gaba da 'DEBE MIN KEWARKA,daga qarshe Jamila mahaifiyar Inaas ta rasu,Farouq yabani Inaas Halak Malak, amma duk da haka na nunawa Inaas cewa tanada Yaya namiji,duk wahalhalun damuke sha nida ita ina fada mata cewa da yayanta yana nan bazai bari tayi aikin komai ba,kaida ita duk daya ne awajena,kaci gaba da kula da qanwar ka kaji?" ta qare maganar cikin sigar lallashi. Ahankali Jawad yatashi zaune,yakama fuskarta ya riqe da hannunsa biyu, yazuba mata ido yana kallonta cikin tsananin soyaiya dakuma farinciki, sai yanzu ne yagane dalilin dayasa gabansa yake faduwa duk lokacin dazai kusanci matar, sai yanzu ne yagane dalilin dayasa yake jin nutsuwa aransa duk lokacin datake kusa dashi,cikin yaqini yace"zan kula daku Mama,daga yau babu wanda ya'isa ko kallon banza yamiki bare yayi tunanin keta miki haddi,kiyi haquri, ki qara haquri ki yafewa Babanah" Bilkisu a rungume Jawad ajikinta tace"Allah yayi maka Albarka Muhammad" Jawad ya lumshe idonsa yanajin wata irin nutsuwa ajikinsa wadda tunda yake bai ta6a sanin cewa idan uwa ta rungume d'a haka akeji ba. Acikin qirjinsa yasa ta,dukansu suna zaune,sun jingina da jikin gadon,ahaka wani irin bacci me dadi ya daukesu. **** Washegari sassafe Inaas tatashi tataho wajan Ammiy,saide alokacin basu farka daga bacci ba itada Jawad,kuma babu wanda yayi yunqurin tashin su,dan haka ta wuce kitchen wajan Hajiya Zaliha tana ganin yanda suke irin nasu aikin breakfast din na yan gayu,daga nan itama tasaka hannu sukaci gaba dayi tare da masu aikin suna sake koya mata wani abun, ga Inaas da shegen surutu abu kad'an idan taga bata ganeba sai an dakata da aiki anyi mata bayanin sa. Wajan takwas da rabi Ammiy ta sauko daga sama,tabar Jawad adaki zaiyi wanka yashirya,Hajiya Zaliha dake zaune tayi murmushi tace"Bilkisu kin tashi? yaya Jawad din yake?" Ammiy ta nemi waje ta zauna yace"lafiya kalau yake Hajiya,yanzu ma na barshi zaiyi wanka,nima zuwa zanyi nayi wanka na shirya" Hajiya Zaliha tace"A a,ki dakata kici abinci tukunna,yau harda 'yar dakina a kitchen din,ta dage saitayi aikin breakfast din itama" Bilkisu tayi murmushi ta daga muryar ta wadda tafara dashewa saboda kuka tace"Inaas!!" Cikin sauri Inaas tafuto daga kitchen bakinta a washe,tace"Ammiy kin tashi?,ina kwana?" Cikin farinciki tace"natashi lafiya Inaas,ina Abban ki?" Kafin Inaas tabata amsa wani guard yashigo falon ya rissina awajan Hajiya Zaliha yace"Hajiya wani matashi ne yazo yace yanason magana da Inaas" Cikin sauri Hajiya Zaliha da Bilkisu suka hada baki wajan fadin"Inaas kuma?" Guard din ya jinjina kansa alamun tabbatar wa,Bilkisu tace"Inaas da bata fita tayaya wani zaizo wajanta?" Hajiya Zaliha tace"A a,ai bamusan waye ba" Tajuya ta kalli Inaas tace"jeki gano ko waye" Inaas ta gyada kanta,sannan ta warware Mayafin Abayar data daura akanta,tabi bayan guard din. A Compound taci karo dawani matashin saurayi dan gayu,cikin mamaki ta qarasa wajansa bakinta dauke da sallama,yadubeta da wani irin murmushi sannan yace"sannu da zuwa gimbiya" Kalmar daya fada ta gimbiya ta daure wa Inaas kai tace"Nice Gimbiya?" "Yes,kece mana,amma fa Gimbiyar zuciyata,ni Sunana Haneef,mahaifina sanan nan mutum ne a wannan garin,ina aiki agarin nan sannan lokaci zuwa lokaci ina zuwa qasar India order kaya,bazan 6oye miki ba tun lokacin dana ganki keda Yayanki da Mamanki a Super Market naji kin kwanta min,naji cewa tabbas na samu matar aure,najira ku awaje har kuka gama abinda kuke kuka futo,na biyo bayan motarku,har naga gida,Allah da ikonsa ina zuwa danayi wa security kwatancen ki, sai suka cemin sunan ki Inaas,ina fatan zaki kar6i soyaiya ta?" Inaas tayi ajiyar zuciya sannan tace"to nagode,amma inaso kabani lokaci zanyi tunani kuma zanyi shawara da Mamana" Cikin jin dadi Haneef yace"Hakan ma yayi,kuma kin birgeni,inason mutum mai mutunta mahaifiyar sa" Inaas tayi murmushi d'an kadan sannan tace"to zan wuce gida nagode" Cikin sauri Haneef yace"to kinga,please Number kifa?" Yafad'i haka yana miqo mata wayarsa. Inaas ta kar6a ta saka masa number,sannan tajuya takoma ciki. Tana zuwa falon Bilkisu tace mata"ke waye yazo wajanki?" Inaas tayi murmushi tace"Ammiy ashe jiya da mukaje Super Marke wani ya ganni,shine ya biyo bayan motar mu yaga gidannan,shine yazo yacemin sunansa Haneef kuma shima anan garin yake,wai yana sona,nace masa nide sainayi shawara dake tukunna,shine yace na bashi number ta, nabashi nayi masa sallama na taho" Dukkan wannan bayanin da Inaas takeyi gaba daya sun shiga cikin kunnan Jawad tsaf,yagama jin komai,fuskar nan tasa kuwa tahadu tayi baqi kamar hadarin dake shirin sauko da ruwa,babu wanda yasan ya qaraso wajan saijin maganar sa sukai yana fadin"ke wato ko wanne jaki,da kowanne mahaukaci,da kowanne daqiqi yace yanason ki saiki tsaya harma ki bashi number ko?" Cikin sauri Hajiya Zaliha da Bilkisu suka juya suna kallon Jawad,Hajiya Zaliha ma duk da bataji dadin zuwan baqon Inaas dinba haka ta daure ta kalleshi da kyau tace"Haba Jawad!,meyayi zafi haka?" Jawad dayake ji gaba daya duniyar ta masa zafi saboda jin Inaas tayi saurayi ya kalli Hajiya Zaliha kamar zai fashe da kuka yace"Haba Mummy,wannan abun kunya ne awajena,wani yazo ya tsallake ni,duk irin tsaron gidannan,yazo yace yana sonta" Bai saurari amsar Mummy ba yajuya ya kalli Inaas yace"kifada masa karya sake zuwa,idan kika sake saurarar sa saina kakkarya ki" Cikin sauri Inaas tatashi tafice daga falon da gudu cikin wani irin kuka. Bilkisu ta girgiza kanta ta kalli Mummy tace" Hajiya kijawa danki kunne,mu bamu saba da irin wannan fad'an ba,bari naje na lallashi abata" Tafadi haka tareda miqewa tabi bayan Inaas. Jawad ya zauna cikin 6acin rai yace"Mummy ina Daddy?" Hajiya Zaliha tayi ajiyar zuciya tace"Daddynka yafita shida Fu'ad da Man Sulaiman,zasuje dubiya ne,sun jiraka baka tashi daga bacci ba,nace zan je na tasoka amma ya hanani tashinka,amma nasan sun kusa dawowa saboda ko Breakfast ba suyi ba suka fita" Jawad yayi ajiyar zuciya yace"Allah yasawaqe" Mummy tace"Amin ya Allah,muje nabaka abinci" Babu musu Jawad yamiqe suka nufi Dining,Mummy tana tambayar sa yanayin jikin nasa. **** Ganin Inaas bata falo hakan yasa Bilkisu tabi bayanta zuwa daki, tana shiga kuwa ta ganta a kwance akan gado tanata faman kuka,Bilkisu tajata jikinta tafara bubbuga mata bayanta alamun lallashi sannan tace"kukan nan ya'isa haka Inaas,menene abun kuka saboda Yayanki yayi miki fada? so kike yabarki kizama marar jin magana?,shi dinfa yayanki ne,tunda bayaso daga yau kidena kula samarin" Inaas dake kuka cikin shagwa6a tace"Ammiy shima fa ba sona yake ba,kuma ya hanani kula wasu" Bilkisu ta lumshe idonta,taja Inaas jikinta ta rungume ta,ita kanta tarasa dalilin da yasa Jawad din yadauki irin wannan zafin haka,kawai saboda ta kula saurayi,haka ta dinga lallashinta harta samu tayi shiru. **** Acan falon Mummy kuwa saida ta tabbatar Jawad ya qoshi,sannan tabar Dining din tawuce daki zata dauko wayarta. Shima Jawad tashi yayi yadawo kan kujera ya zauna,yana juyawa yaga wayar Inaas agefe,cikin sauri yabude wayar yafito da Sim Card dinta ya karya shi. Karaf akan idon Mummy wadda ta futo daga cikin dakinta,tana ganinsa yagama karya layin,sannan ya ajiye ya koma gefe ya zauna kamar ba shiba. Tasaki murmushi taqaraso zuwa falon tana kallon Jawad,yanzu kam tagama gane cewa tabbas Kishi ne yake damun Jawad. Hakan yana nufin yanason Inaas din kenan,miskilanci dakuma zurfin ciki ne ya hanashi bayyana mata. Ta dubeshi zatayi magana sai su Daddy suka shigo falon,Jawad yana ganin Daddy yatashi ya nufeshi ya rissina ya gaida shi,sannan ya gaida Man Sulaiman. Daddy ya kama hannun Jawad yace"muje can wajan Bilkisu akwai maganar danake so muyi" Babu musu Jawad yabi bayansa,sannan Mummy da Fu'ad da Man Sulaiman suka suka biyo bayansu. Suna zuwa falon,sukaga Farouq ne kawai a zaune,bayan sun zauna Farouq yakira Bilkisu da Inaas dake cikin daki, suma suka futo falon baki d'aya,Inaas ta saci kallon gefen da Jawad yake zaune ta murguda masa baki,sannan ta zauna agefen Bilkisu,Jawad sarai ya ganta,bai nuna alamun komai ba ya sunkuyar da kansa qasa,Mummy dake kallon Inaas da Jawad tayi murmushi tana girgiza kai. Daddy ya kalli kowa sannan yace"Farouq bude mana taro da Addu'ah" Abban Inaas yace"salati goma ga Annabi....S.A.W" Saida suka gama Addu'ah suka shafa, sannan Daddy yace"Dukkannin ku,kunsan dalilin taruwar mu anan,naso tun daren jiya munyi wannan zama amma hakan bata samu ba,Jawad kayi haquri,kowanne bawa dakake gani da irin tasa qaddarar,Allah yasoka taka qaddarar mai kyau ce,domin kuwa bakayi maraici ba,sannan adede lokacin da kasan cewa ba mune muka haife ka ba alokacin ne kagano su waye asalin iyayanka,hakan bawai yana nufin mu din mun tashi daga kan yanda muke bane,ina roqon Alfarmar iyayenka akan subarmin kai muci gaba kamar yanda muka saba,babu wanda yasan wani abu yafaru a wannan ahali namu, banaso kuma asani,mu riqe sirrin juna mu taru mu rufawa kanmu asiri,Bilkisu da Man Sulaiman kuma gasunan kajasu a jikinka,haqiqa sun soka,bakada tamkar su,gasunan saboda ka 6ata har yanzu Bilkisu taqi su daidaita kansu amaida wannan aure, inajin de kaine zaka qarasa sauran aikin" Daddy ya qarasa maganar cikin barkwanci, gaba d'aya falon saida kowa yadan daara,yayinda Bilkisu ta kauda kanta gefe tana karkad'a qafa. Man Sulaiman yasaci kallonta ta watsa masa wani irin kallo. Daddy ya kalli Farouq yace"to Abban Inaas nadawo gareka,Inama albishir danka yabaka matsayin MD na sabon kamfanin daya bude,nan da wasu yan kwanaki zaka fara fita aiki insha Allah,kafin asamo wa Inaas wata sabuwar Antyn" Farouq yayi murmushi yace"Alhaji mungode sosai,irinku basuda yawa awannan lokacin,Allah ya rayama zuri'arka,haqiqa bamuda bakin dazamu gode muku,Allah yaqara hade kan wannan ahali daga yanzu har zuwa qarshan numfashinmu" Gaba d'ayansu suka amsa da "Amin" Farouq ya maida kallonsa wajan Jawad yace"Jawad nagode sosai da irin wannan muqami,insha Allah bazan baka kunya ba,zamuyi aiki yanda ya kamata" Jawad yayi sauri ya sunkuyar da kansa qasa,wata irin kunyar surukin nasa tana mamaye shi. Daga nan gaba dayansu suka futo daga falon,a kabar Jawad da Bilkisu da Man Sulaiman. Inaas takama hannun Mummy ta riqe suka futo yayinda Fu'ad yake janta da zance aikuwa tasamu abinda takeso nan da nan tasaki jiki tana zuba surutu. Bayan anbarsu su uku afalon babu wanda yayi yunqurin yin magana,Jawad yatashi yakoma kan kujera kusada Bilkisu ya zauna,yakama hannunta ya riqe yace"Mama ki yafewa Uncle,nikaina kwanaki can bayan naji abunda yafaru awajan Daddy banyi wa Uncle uzuri ba,Bansan cewa qaddarar akaina take faruwa ba,dan Allah Mama kiyi haquri nasan kinsha wahala,amma kiyi haquri amaida muku aurenku,nima hankali na zaifi kwanciya Mama" Bilkisu ta kalli Jawad tace"Muhammad,nifa na riga na dade da yafewa mahaifinka,maganar aure ce de nace bazan sake aurensa ba,lokacin daya tafi yabarni da cikin ka yayi tunanin wannan ranar ne? qarewa kudin dana bashi nace ya dinga tarawa har zuwa lokacin dazan haihu mu sai abun suna dashi,da kudin ya gudu,yatafi yabarni nida kai ko tausayi babu,in aure shi ince na auri me?" Cikin sauri Man Sulaiman yace"kice kin auri mutum,kuma mutum cikakke wanda kika samu santalelan yaro dashi" Jawad ya runtse idonsa ya bude yace" Mama,abar kaza cikin gashinta,babu dad'i tone-tone"(😂) Bilkisu tace"kanajin abinda yake fada fa,in banda yaci darajar ka tayaya zan dinga magana yana bani amsa bayan laifin dayamin,gara a fige kazar kowa yahuta" Jawad yace"A a Mama,abarta de cikin gashin ta,idan kikai tunani kin riga kin hada jini dashi,Mama zamanku ahaka nima bazanji dadi ba,kowanne iyaye suna zaune tare saboda 'ya'yansu da dad'i ba dad'i,kiyi haquri ki yafe masa amaida aurenku kada mutane sumin dariya" Cikin rawar murya Bilkisu tace"amma kanajin abinda yake fadamin fa, meyasa shi bazaka masa fad'a akan laifin dayayi min ba,lokacin da kana jariri nayi ma hud'uba cewa duk lokacin daka girma saimun bawa Babanka kunya,ashe bazaka tayani ba?" Jawad ya lumshe idonsa,yabude,yajuyo ya kalli Man Sulaiman sannan yace"Uncle Please...,Kabawa Mama haquri" Babu musu Man Sulaiman ya sauko yadawo gabanta,ya tsugunna, sannan yakama fararen qafafunta ya riqe,ya sassauta murya yace"Bilkisu...kiyi haquri,inaso ki yafemin amaida mana aurenmu kodan saboda Jawad" Jawad ma ya kalleta ya marairaice yace"Plaese Mama,Allah yanason masu yafiya" Bilkisu tayi ajiyar zuciya sannan ta kalli Man Sulaiman tace"shikkenan na amince,kaje amaida auren,kaci darajar d'anka" Tana fadin haka tatashi tawuce daki,Jawad yayi murmushi ya shafa sumar kansa shima yatashi ya futo yabar musu Plat din. Yana futowa Compound yasaki wata irin ajiyar zuciya yanaji aransa kamar ya sauke wani irin babban nauyi daga kansa,kai tsaye wajan P.a yawuce,suka fara rage wasu ayyukan cikin kwanciyar hankali. Jawad baisamu kansa ba sai yamma lis gab da magrib,hakan yasa suka wuce masallaci shida P.a sukai sallar magrib da isha'i,sannan yadawo gida,yana shigowa falo yaci karo da Inaas tana kuka,sai zuba shagwa6a take tanata faman kuka, ya tsaya ya harde hannunsa a qirjinsa yana ganin yanda Mummy da Mama Bilkisu suka rikice akanta sai tambayarta suke abinda aka mata. Ya girgiza kansa ya d'aure fuska yazo yawuce su zaije dakinsa,babu buqatar ya tsaya awajan,idan ya tsaya ma tayaya ne zai iya lallashinta? ko kad'an baisan yanda zai lallashi mace ba,macen ma budurwa,saboda tun asali Mummy da Daddy basu yi masa rainon da zaiyi kuka ba,bare yasan yanda ake lallashin. Yanajin Inaas tana magana cikin shagwa6a" Ba Aljannu ne suke ta6a min waya taba,duk lokacin dana sake sabon Sim sai sun karya min shi" Mummy ta kalli Jawad dayake shirin hayewa sama,ta d'aga murya tace"Aljannun nan kam nima abun nasu yafara yimin yawa,kuma sai sun kalli ko'ina,sunga babu me kallonsu,saisu karya Sim Card din suyi wulli da wayar" Jawad yanajin abinda Mummy tafada gabansa yafadi,ya runtse idonsa batare daya juyo ba. Mummy tasake kallonsa tace"Jawad" Ahankali kamar bayason had'a ido da'ita yajuyo yana sosa kansa,yace"Na'am Mummy" Mummy tanuna masa Inaas tace"kaita wajan wasa tad'an sha is'ka" Inaas ta kalleshi da idanunta dasuka cika tab da qwalla,ta tuna masifar daya mata dazu da safe, cikin shagwa6a tace"Mummy ni bazan jeba,yayi tafiyar sa" Jawad yasake daure fuska yayi mata kallo daya yace"nabaki minti biyar" Bilkisu ta kalli Inaas tace"kinga tashi kutafi,banason musu" Inaas taturo d'an qaramin bakinta gaba sannan tatafi tafice tabi bayan Jawad. Suna fita,Bilkisu tace"narasa yanda ake Sim Card din nata yake karyewa,kusan sau biyu kenan ko uku" Hajiya Zaliha tace"Hmm Jawad nefa" Bilkisu tafara tafa hannaye tana fadin"Amma kiduba kiga yaron nan yanda yawani maze kamar ba shiba?"(🤔) **** Ahanya suna tafiya kowa yayi shiru babu wanda yayiwa dan'uwan sa magana,fuskarsa ad'aure ya d'an juyo ya dubeta,yaga itama tata fuskar ad'aure take,idonta yana kan window ko kad'an taqi kallon inda yake ta hard'e hannunta a qirjinta, ya danyi qasa da idonsa kad'an zuwa nashanunta,yanda ta hard'e hannun nata hakan yabawa doguwar rigar ta damar futo da shacin brar dake jikinta,ahankali ya d'an lumshe idonsa yahadiye wani irin saliva,sannan yaci gaba da driving dinsa. Har sukaje wajan baice da'ita komai ba,haka itama,wajan ya birgeta sosai,taji dadin yanda ake jere mata ice-cream kala-kala sai wanda taza6a,banda kayan maqulashe dangin gishiri,yanda guard suke zagaya wajan suna basu tsaro hakan ne yasa babu wani saurayi dayayi gigin kawo kansa wajanta. Qarfe tara dawani abu suka dauki hanyar dawowa gida,har zuwa wannan lokacin babu wanda yace da dan'uwan sa uffan a tsakanin su. Suna tsayawa agida tayi sauri zata bude motar ta fice,yayi caraf ya ruqo hannunta,tajuyo ta kalleshi. Ya tsatstsareta ta da idanunsa, cikin muryar rad'a yace"Meyasa bakya son zaman lafiya me?" Inaas taturo d'an qaramin bakinta gaba,tatuno masifar daya dinga zuba mata yau da safe,lokaci daya qwalla ta cika idonta,ahankali ta zama hawaye ta sauko akan kumatunta, takai hannu zata share yayi sauri ya riqe hannun nata, sannan yakai nasa hannun ya goge mata hawayen,cikin muryar sa me kamar rada yace"Banason ganin fuskarki haka,idan kina murmushi kinfi kyau,murmushinki yana 'DEBE MIN KEWA,kidena sauraran samari, inde zaki dinga rabawa maza number ki sau dubu,to zan dinga karya layin ki sau dubu..." Cikin sauri ta kalleshi tace"dama kaine?" Jawad ya murza hannunta dake cikin nasa,wanda hakan yasa dagashi har ita suka tsinci kansu acikin wani irin yanayi sakamakon yanda yake murza tafin hannun nata,ya lumshe idonsa ya bude sannan cikin shaqaqqiyar yace"Yes nine..." Inaas ta kalleshi tace"to meyasa?" Kai tsaye ya kalli qwayar idonta yace"Saboda ina sonki..." (to tsuntsayen soyaiya, nabarku lafiya🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️) Yaude Jawad yafad'a 😂inajin yaga uwar bari ne ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍ [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne, kibiya ki karanta cikin salama,idan kika karanta baki biya ba keda Allah 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. 17&18 Daddy ya kalli Man Sulaiman yabashi hannu cikin farinciki yace"to Alhamdulillah,Allah yasanya Alkhairi Man Sulaiman,Allah yabaku Zaman lafiya,sannan ka kiyaye duk wani abu da kasan cewa zai 6ata ran Bilkisu,ita din abar tausayi ce" Man Sulaiman yayi murmushi yace"ai Alhaji ban ta6a ganin Bilkisu tayi irin wannan 6acin ranba tunda nake,ban ta6a bata haquri sau d'aya taqi haqura ba,amma tunda naga nine nake bawa Bilkisu haquri har tsawon lokaci taqi haqura,hakan yasa dole zan sake kiyaye wa inyi taka tsantsan da'ita,yanzu de gashinan Allah ya temakeni Jawad yana saka baki ta haqura" Murmushi Daddy yayi yace"to Alhamdulillah,Allah yabada Zaman lafiya,sai a kula da Amarya,nima bari nawuce" Daga nan Daddy yawuce,shima Man Sulaiman yanufi wajan amaryar sa. Daddy yana zuwa falo Mummy tahada masa dinner,yana faraci yace"ina yaran nan suke ne?" Mummy tace"Fu'ad kam yafita yawonsa,Jawad kuma sun fita shida Inaas,har yanzu basu dawo ba" Cikin mamaki Daddy yace"naga motocin dayake fita a Compound,gaskiya sun dawo, may be sun wuce wajan Bilkisu ne" Mummy tace"eto inaga,Allah yasa de sun daidaita kansu da yarinyar nan,Alhaji inaso Jawad yayi aure wallahi,amma shi naga ko ajikinsa" Daddy yayi murmushi yace"waye yafada miki cewa ko ajikinsa? shima ai yanaji ajikinsa,tun kwanaki naso inyi masa maganar Inaas din cewa idan yasan yana sonta toya fadamin,to bansamu zama dashi ba,saboda naga nace masa ya nema mata makaranta yatsaya yanamin kuskunda,tundaga nan na fahimci kamar de qoqarin dakike masa akan yarinyar yafara tasiri,to ki zauna dashi idan yashigo kuyi magana,inde yana sonta to ga mahaifin yarinyar nan muna tare dashi agida,kinga sai ayi komai tuwona maina,muma mufara ganin yan jikoki agidan namu,idan kuma yasan baya sonta toki fada masa yayi gaggawar futo da matar aure,dan bazan cigaba da saka masa ido yana zaune babu aure ba,ga mata nan dayawa sai wacce ya za6a bazai iyu ya dinga shiga halin buqata har abun yakai ga ganin likita ba" Mummy ta kalleshi da sauri tace"Jawad dinne yake ganin likita Alhaji? Yaushe? nifa nayi tunanin ma yaron nan ba qalau yake ba,gashinan de mutum cikakke,babu abinda Jawad ya nema yarasa,amma ko kad'an mata basa gabansa,har gara Inaas dinma itace naga kamar yana kishin ta,jiyama datayi baqo karka ga yanda ya rufeta da fada kamar zai kai mata duka,yarinyar ma saida ta tsorata da fadan nasa, domin kuwa da kuka tabar falon nan" Daddy yayi murmushi yace"kalau yake,lafiyar sa kalau sai iskanci,kwanaki can nima na ta6a yin wannan tunanin,nayi maganar da Man Sulaiman nace ina tsoro ko Jawad bashida sha'awa kwata-kwata,to saida likita yazo gida duba shi rannan sannan ne na tabbatar lafiyar sa kalau shegen miskilanci ne ya hanashi sauraren yanmatan,to tun a wannan lokacin naso nayi masa magana amma wani abun ya dauki hankali na" Mummy ta jinjina kanta alamun tabbatar wa,ta tuna lokacin tanajan bargon dayake ciki shima yayi sauri yaja bargon bai barta ta bude ba,tasaki ajiyar zuciya tace"Allah yarufa asiri,zanyi magana dashi" Daddy yace"Amin ya Rabbi,Yaya Mariya tace agaida ki,daga can muke nida Man Sulaiman,a masallcin gidanta aka maida aurensa da Bilkisu" Cikin farinciki Mummy tace"au har an maida auren? to Alhamdulillah" Daddy yace"an maida,bayan mun idar da sallah aka maida,Yaya Mariya tasake yimasa gargadi akan Bilkisu sannan muka dawo gida,kinga ikon Allah duk tsawon wannan shekarun da suka dauka basa tare da juna tun kafin a haifi Jawad, sai gashi basu shirya da juna ba saida Jawad din ya shirya su da kansa" Mummy tayi dariya tace"Ai yaron naka ba daga nan ba" **** Cikin sauri Inaas ta zaro idonta sannan ta kalli cikin qwayar idon Jawad,gabanta yayi wata irin fad'uwa,sakamakon jin Kalmar da batayi tunani ba. Shima zuba mata ido yayi,yayinda har lokacin hannunta yake cikin nasa yana murza mata shi,cikin wata irin murya acan qasan maqoshinsa yasake tabbatar mata yace"ina sonki INAAS" Yana fad'a mata haka yaja hannayen ta zuwa qirjinsa,yanda ya dora masa hannunta akan faffadan qirjinsa hakan yasa taji yanda bugun zuciyar sa ya tsananta,nan da nan jikinta yafara karkarwa. Ahankali Jawad yafara matso ta har saida ya kasance tanajin yanda numfashin sa yake sauka akan fuskarta, Inaas tana ganin yafara kawo fuskarsa dab da tata,ta runtse idonta tafara girgiza masa kai,cikin sauri tace"A a,Yaya..." Cikin wata irin shaqaqqiyar murya yace"Plaese Kiss d'aya kawai" Cikin sauri ta girgiza masa kanta tace"nide a a,kabari banaso,ni ban ta6a yiba" Jawad yayi d'an qaramin murmushi yazuba mata ido ganin yanda jikinta yake rawa gashi ta maqe ajikin murfin mota ta runtse ido,ahankali yace"waye yace miki ni d'in nata6a yi? ki bude idonki kiyi min..." Gabanta yasake tsananta fad'uwa ganin yanda yacire kunya kamar ba shiba yake nema yayi mata wannan abun, cikin fad'uwar gaba tace"nide a a" Jawad ya lumshe idonsa,sannan yabude yace"kiss me... inba hakaba ni zan miki" Cikin sauri itama tasake cewa"nide a...." Kafin tagama cewa a a,Jawad yahade bakinsu waje daya,abun yazo wa Inaas a bazata,bata ta6a tunanin Yalla6ai Jawad zai iya hakan ba. Jawad kuwa idonsa ya lumshe, yakama harshanta yanasha cikin kwanciyar hankali. Kasancewar motocin dayake fita dasu dukansu baqin glass ne dasu hakan yasa kokadan babu wanda yasan wainar dasuke toyawa acikin motar shida ita. Inaas tabude idonta tazaro shi waje cikin tsananin tsoro,jikinta yadauki rawa bata wasa ba,lokaci daya tafara qoqarin qwace hannunta dake cikin nasa,Jawad yanajin haka yasake riqe duka hannayen nata da hannunsa guda daya,yahanata damar qwacewa,yayinda yakai daya hannun nasa yariqe kanta dashi yaci gaba da kissing bakinta kamar yasamu sweet. Baisan cewa abinda akeji ba kenan,baisan cewa haka gangar jiki take sauya wa ba,baisan cewa haka kiss din yake da dadi ba,ya shagala mutuqar shagala,hakan yasa gaba daya jikinsa ya mutu,yana tsoron kada asamu matsala fiye da haka,ahankali yabude qwayar idonsa mecike da fitina dasukai wani irin jaaa, ya kalleta har lokacin bakinsa yana cikin nata,yaga har yanzun idonta a rufe suke,ya danyi murmushi, sannan daqyar ya'iya zare bakinsa daga cikin nata,yasaka hannunsa daya yacire key din motar,Inaas tanajin wannan alamun tasan cewa yabude motar,aikuwa cikin sauri tafuto ta kalli Compound din gidan taga babu mutane akusa da motar Jawad din,tasaki wata irin ajiyar zuciya,tafara zuba uban sauri bata tsaya ko'ina ba sai cikin falonsu. Tana zuwa kai tsaye daki tawuce wani irin zazza6i me zafi yarufeta,har yanzu a tsorace take da abinda Jawad d'in yamata. Shikuwa Jawad saida yagama saita kansa,sannan ya futo daga motar,kai tsaye Plat dinsu yawuce domin yaje ya watsa ruwa,yariga yasan cewa wanka ya wajaba a kansa (🙈) Yana shiga falo Mummy tace"kadawo?" Jawad ya d'an sosa kansa sannan yace"yes Mummy mun dawo yanzu" Mummy tace"Alhaji yacemin yaga motarka kun dawo tun dazu,nayi tunanin ai kuna wajan Maman Inaas" Gaban Jawad yayi wata irin fad'uwa,cikin sauri yafara kame-kame yace"eh...aaaa mun dawo,but...but ita tawuce wajan Mama,nikuma na tsaya dasu P.a ne" Tariga tasan cewa Jawad bazai mata qarya ba,hakan yasa cikin gamsuwa da maganar tasa tace"ok,muje daki zamuyi magana" Yace"ok Mummy" Yafadi haka yana wucewa cikin dakin nata. Itama tayi ajiyar zuciya tabi bayansa,tana shiga daki ta zauna akan gado,yayinda Jawad yake zaune akan lallausan carpet din dake malale adakin,ta kalleshi tace"an maida auren Mama da Uncle" Cikin sauri ya kalleta, sannan yayi d'an murmushi yace"Allah yabasu Zaman lafiya" Mummy tace"Amin ya Allah,Jawad ya maganar Inaas ne?" Jawad ya sunkuyar da kansa qasa baice mata komai ba. Mummy tasake kallonsa tace"ko baka sonta Jawad?" Cikin sauri yace"Mummy I luv her...." Mummy tayi murmushi tare da sakin wata irin nannauyar ajiyar zuciya,sannan tace"to kaga tunda abu ne na gida ba buqatar atsaya 6ata lokaci,zanyi wa Alhaji magana,shima yasamu Farouq da Man Sulaiman da Yaya Mariya suyi magana,inyaso ko 4 Week's ne sai asa" Gaban Jawad yafadi,anya a yanda yake ji d'innan zai iya haqurin sati hudu? Ahankali yadago kansa ya kalli Mummy kamar zai fashe da kuka yace"Mummy 4 week's fa yayi yawa,me za'a jira? samari fa sai kawo mata hari suke"(🙊😂) Mummy tayi murmushi ta dauki fillon dake kan gado zata bugeshi dashi, cikin sauri yatashi yafice daga dakin yana dariya. Kai tsaye dakinsa yawuce yashige toilet yayi wanka,ya tsarkake jikinsa,sannan yashirya yasauko yaci abinci da kansa,yayinda Mummy take kan kujera tana kallo fuskarta cikeda Farinciki saboda zancen dasukai da Jawad na aurensa. Bayan yagama cin abincin ta kalleshi tace"muje wajan Amarya Jawad" Jawad yayi murmushi yatashi suka tafi wajan Bilkisu. Suna zuwa kuwa suka sameta afalo a zaune tana shan shayi,Jawad ya zauna kusa da ita cikin tsokana yace"Ammiy Amarya" Bilkisu tayi murmushi tace"ga qanwar ka can adaki zazza6i ya rufe ta" ta kalli wajan Hajiya Zaliha tace"sannu da zuwa Hajiya" Hajiya Zaliha tace"subhanallah,haba Bilkisu 'yar tawa ba lafiya kuma kika zauna kinashan shayi? kude buzaye ba'a rabaku da shayi" Bilkisu tayi murmushi tace"Hajiya wallahi zazza6in bana kirki bane, 'yar taki ce batajin magana,kullum saita kunna esi sannan zatayi bacci,fisabilillah jikin dabai saba da esi ba yaushe lokaci daya zaka dage saika ji? sanyin esi ne ya kwantar da'ita" Kafin Mummy tayi magana sukaji Jawad yana magana da family Doctor dinsu. Zama yayi,amma yayi shiru kana ganin yanayinsa kasan cewa yana cikin damuwa,saida yaga zuwan likita sannan yasaki ajiyar zuciya,Bilkisu tace"kuje Jawad tana cikin daki" Gaba dayansu suka shige dakin har Hajiya Zaliha,Bilkisu kuma ta biyo su abaya. Likita yana dubata yace"wannan ba zazza6in maleria bane,may be gajiya ko tsoro,ko wani abu de,nayi mata allurar paracetamol insha Allah zuwa safiya zataji dadin jikinta" Cikin damuwa Jawad yace"no Doctor idan akwai damuwa kafadamin,ko nan India ne sai akaita adubata sosai,kasan zazza6in yanzu zuwa yake yadawo"(🤭) Likita yace"ba buqatar hakan Yalla6ai,insha Allah zuwa safiya zataji dadin jikinta" Jawad yabashi hannu suka sake gaisawa,sannan likitan yafice daga dakin. Mummy tataso tadawo kusa da Inaas ta zauna agefen kanta tasa hannu ta shafa wuyanta sannan cikin damuwa tace"ikon Allah,qalau-qalau ku fita amma kuma adawo da zazza6i?"(😂) Ta kalli Jawad tace"Jawad dauketa muje dakina takwana acan,abar Maman nata tahuta" Jawad yasa hannu yadauketa cak,yaji babu nauyi,yajuyo zasu fice daga dakin ya kalli Bilkisu yace"mubar Mama tahuta,saida safe Mama" Bilkisu tayi murmushi tana mamakin wad'annan mutane,yanzu wannan zazza6in ne suke magana ko akai mutum India? to idan ciwo ne me tsanani sai ina kenan? (🤔) Dakin Mummy suka shiga,ya kwantar da'ita,Mummy taja mata blanket sannan tafice daga dakin. Mummy tana fita,Jawad ya janye blanket din yazuba mata ido,Inaas tad'an bude idonta da qyar ta kalleshi,suna had'a ido dashi tayi sauri ta runtse idonta. Jawad yayi murmushi yace"Ke haka akeyi? daga d'an yin abu sai jinya? idan mukai aure fa?" Kafin tayi magana Mummy tashigo dakin,takawo mata coffee me zafi tace"Inaas tashi kisha Coffee,nasa miki wani maganin zazza6i aciki" Inaas tatashi ahankali ta gyara zamanta,Jawad ya kar6i cup din daga hannun Mummy,sannan Mummy tajuya tafice tabar musu dakin. Shida kansa yafara bata coffee din,saida takusa shanye wa sannan ta kalleshi tace"Yaya nide kadena min wannan kiss din,ni wallahi ban sababa,zakasa na suma" Cikin sauri Jawad ya kalli qofa sannan yadora hannunsa akan bakinsa yace"shiiiiii!,banason surutu so kike Mummy tajimu? open your mouth" Cikin sauri tabude bakin nata,yad'ebo coffee a spoon yasaka mata,ta shanye,sannan yaja tissue agefe yagoge mata bakinta,yace"ni bazan sake ta6aki ba,gashinan daga d'an yin kiss Mamanki tana cewa Sanyin esi ne ya kwantar dake jinya,batasan Sanyin kiss ne ya kwantar dake ba"(🙊) Inaas ta dan turo qaramin bakinta gaba,sannan ta sauya a kalar zancen nasu tace"Yaya dama ka'iya bada abinci abaki? naga kullum saide abaka,yaushe kafara koya?" Jawad ya girgiza kansa yayi shiru,mai hali baya fasa halinsa,tana halin jinya ma bazata daina surutu ba(😣) Jin yayi shiru hakan yasa Inaas cigaba da fadin"meyasa idan Inama magana saika dinga shareni?" Jawad ya lumshe idonsa yabude,sannan yasaka hannunsa daya yadafe kansa(🤦🏻‍♂️) Babu zato taji yasakar mata wani kiss din a kumatun ta. Sannan yace"maganin surutu" Cikin sauri Inaas ta zaro idonta waje,bata sake cewa komai ba tayi sauri tashige cikin bargo har kanta,bata sake sanin meyake wakana adakin ba,sai can bacci yafara daukar ta sama-sama takejin maganar Jawad din da Mummy dakuma Fu'ad. **** Bayan sun idar sa sallah kamar yanda ma'aiki ya koyar,Man Sulaiman yayi musu Addu'ah,suka shafa,Bilkisu ta miqe zata haye gado,Man Sulaiman yayi saurin ruqota yace"ina zakije Bilkisu? ki zauna muci wannan abubuwan mana" Bilkisu ta juyo ta kalli gasassun kajin dake gabansa tace"Wanne irin kaji kuma Manu? kamar wasu qananun yara?" Cikin wani irin Salo wanda yasan cewa ko a shekarun baya ma idan yayi mata yana karya mata garkuwar jiki ya marairaice yace"Bilkisu ai nidin har yanzu yaro ne a wajanki"(🤭) Bilkisu tayi murmushi tahaye gado tayi kwanciyar ta,shima baisa naman ko daya a bakinsa ba yakashe wutar dakin yarage kayan jikinsa sannan yahaye gadon,duk da yana d'an shakkarta haka ya daure bai jira komai ba yadora hannunsa agefen wuyanta yana shafa wa,tanajinsa batayi yunqurin hanashi ba saida taji yana neman hargitsa mata lissafi sannan ta riqe hannunsa. Cikin wata irin murya Man Sulaiman yace"Bilkisuuuuu...." Yaja sunan nata,sannan yaci gaba da fadin"Bilkisu shekaru talatin da bakwai ba nan bane,kada ki haramta mana abinda Allah ya halasta mana,kinsani nima nasani cewa tsawon lokacin nan babu abinda yasake faruwa irin wannan,kibari mu Raya sunnar ma'aiki Bilkisu" Lokaci d'aya Bilkisu tasaki hannunsa,hakan ba qaramin dad'i yayi masa ba,daga nan labari ya sauya,daga nan komai ya kunce musu,man Sulaiman kuka yake wiwi yana wani irin sambatu saboda an dade ba'a had'u ba,jin dadin Bilkisu d'aya shine d'akin Man Sulaiman din agefe yake,banda haka babu abinda zai hana Farouq yajuyo kukan sambatun sa,ada idan hakan tafaru itace take qoqarin rufe masa baki, saide wannan lokacin itama ta kasa ta6uka komai,domin kuwa ita kanta sheda ce Man Sulaiman gwani ne wajan sarrafa mace ada ma kenan,yanzu kuwa abun nasa yawuce tunanin Bilkisu, tunda yadora bakinsa akan qirjinta yake sha kamar yaron goye, tariga tasan dama shi din mayen wannan abubuwan ne,yanda yake sarrafa ta cikin Salo sai taji ashe da d'inma ba komai ya'iya ba akan yanzu(🙈🙊) **** Washegari da safe Mummy tana falon Alhaji,ta dubeshi tace"Alhaji munyi magana da Jawad jiya,ya fadamin yana son Inaas,sannan yanaso asaka lokacin bikin qasa da sati hudu" Daddy yayi murmushi yace"Haba Hajiya,tayaya zaki biye masa ace asaka ranar aure qasa da sati hudu? a barshi de asaka wata d'ayan,karki manta fa akwai mutanan mu dazasu halarci bikin daga qasar waje,idan aka saka biki qasa da sati hudu tayaya zasu samu visa akan lokaci,dole wasu bazasu samu daurin auren ba,nikuma inaso kowa da kowa yazo ahadu ayi farinciki,inaso ayi gagarumin biki wanda duniya zata shaida nayi auren babban d'ana" Mummy tayi ajiyar zuciya tace"Alhaji nan fa jiya kagama cemin,akan yanayin buqata likita yazo har gida yaduba Jawad,to yanzu mutane zamu duba kokuma lafiyar yaron mu? duk zurfin ciki da miskilanci irinna Jawad tunda naga shine da kansa yace asa masa ranar aure kafin wata d'aya,Alhaji ai inaga abun yakai maqura" Daddy ya danyi jimmm sannan yace"eh hakane kuma,to shikkenan babu damuwa,sai asaka ko 2 week's ne,inyaso sai asanar da batun saka ranar da wuri,dan mutane su fara shirin zuwa tun yanzu" Cikin farinciki Mummy tace"to Alhamdulillah,Allah yanuna mana" Daddy yace"Amin" Sannan yadauki wayarsa dake gefe yakira Abban Inaas,bugu daya kuwa Abban Inaas dake Breakfast afalo shi kadai,yadauki wayar. Alhaji Mekudi yace"Farouq kayi magana da Man Sulaiman ina jiranku zamu je gidan Yaya Mariya,yaronka yaga yarinyar ka,muna so atsaida magana d'aya" Farouq yayi murmushi yace"to Alhaji,gamu nan zuwa" Daddy ya kashe wayar. Daga 6angaren Farouq shima ya ajiye wayar yana murmushi,cikin ransa yanajin dadi abun yataso kenan,ya kalli qofar dakin Man Sulaiman yaga har yanzu shiru bai futo ba,har gara Bilkisun ta futo tahada Breakfast sannan takoma, shikuwa Man Sulaiman tun daren jiya bai leqo ko falo ba,sallar asuba ma bai ganshi a masallaci ba.(😂🙊) Yadaga kafadunsa alamun rashin damuwa,sannan yadauki wayarsa yakira Bilkisu yace"Yaya kiyiwa Man Sulaiman magana Alhaji yana jiranmu zamuje gidan Yaya Mariya" Bilkisu tace"ai yashiga wanka ma,gashinan zuwa insha Allah" Bayan ta kashe wayar ta kalli Man Sulaiman daya maqale ajikinta tace"Abban Jawad katashi ka shirya,baccin ya'isa haka" Man Sulaiman yasake qanqameta,cikin jin dadi yace"Bilkisu rabon danayi irin wannan baccin na yau wallahi harna manta,tun lokacin dana rabu dake nake cikin damuwa,idan na kwanta bacci na dinga mugayen mafarkai kenan,yau kuma abar danake so tadawo gareni,ki barni naji d'umin jikinki zuwa azahar saimu fita falon"(😳🤭) Bilkisu tayi murmushi tace"Bafa guduwa zanyi ba,ina nan,kuma kaga nariga nace masa kana wanka,Alhaji ne yake jiranku" Man Sulaiman yayi miqa,sannan yatashi badan yaso ba yawuce Toilet,ita kuma tafara gyara d'akin. Bayan ya futo itace ta tayashi ya shirya cikin sauri,yayi kyau sosai cikin manyan kaya,sai qyallin amarci yake,yanufi qofa zai fice, yajuyo ya kalli Bilkisu bakinsa cikeda fara'ah kamar gonar audiga yace"ikon Allah,to Bilkisu, nizan fice, babu damuwa de ko?" Bilkisu tayi masa wani irin kallo sannan tayi murmushi tace"saika dawo" Man Sulaiman yasake bude baki cikin walwala yajuyo yadawo cikin dakin yace"babu matsala de? to bari in fice,saina dawo d'in,Bilkisu Bilkisu,Bilkisu tawa me gadon zinare"(😂) Bilkisu tayi murmushi bayan yafita,ta girgiza kai tana mamakin yanda Abban Jawad din yake wasu irin abubuwa kamar ba shiba. Bayan sun fita shida Farouq kai tsaye wajan Alhaji sukaje,suka dunguma suka tafi gidan Yaya Mariya Mama ga kowa. Acan aka saka ranar auren Jawad da Inaas sati biyu masu zuwa,kasancewar harda P.a din Jawad akaje,hakan yasa yanajin saka ranar uban gidan nasa,yayi maza yayi posting a shafikansu na kafafen sada zumunta. (jama'ah Amarya Hajiya Ammiy tana gayyatar kowa da kowa zuwa wajan bikin 'ya'yanta💃🏻) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍ [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. 17&18 Kasancewar lokacin bikin Jawad da Amal babu wanda yasan da batun auren nasa sai su yasu 'yan gida,yanzu kuma anga P.a din Jawad din da kansa yayi posting nanda 2 weeks Jawad zai zama ango hakan yasa 'yan Jarida suka samu nayi,kan kace me,lokaci daya labarai ya watsu ko'ina ciki harda gidajen tv,Alhaji Bature yana ganin labaran yata6e baki,banda Babban yayansu ya haneshi akan maka Jawad din akotu bisa zargin qona masa gida,da babu abinda zai hana su shiga wannan kotun daya ambata. Kasancewar tasha bacci sosai bayan sallar asuba hakan yasa duk budurin da'ake bata sani ba,ahankali tatashi da Addu'ar tashi daga bacci a bakinta,tajuya gefenta taga an ajiye mata wani kaya daga gani aikin Mummy ne,tasaki murmushi tatashi tashige toilet tayi wanka da ruwa me d'umi,ta dad'e tana cikin ruwan d'umin sannan tafuto taji jikinta sakayau bata tareda wani zazza6i ko alamar sa. Mayukan Mummy ta shafa sannan ta saka kayan data ajiye mata,riga da wando ne masu d'an karen kyau, tajuya a gaban madubi ta dubi kanta,taga yanda hips dinta yabaje sosai ajikin wandon,gashi wandon ya kamata,ita kanta batasan cewa tanada irin wannan kyawun ba. Ahankali tafara jujjuya agaban madubi, ta kalli nan ta kalli can kamar 'yar Babyn roba. Jawad dake tsaye abakin qofa yana kallon zallar baiwar Inaas wadda take juyi batasan yashigo ba,sosai yake qare mata kallo,idonsa yana sauka akan nashanunta yaji wani irin abu,yaji kamar yaje yakai musu hannu,yanda ya gansu a tsatstsaye hakan yasake tabbatar masa cewa bata saka bra ba,yamaida kallonsa zuwa farar fatar ta wadda take wani irin shinning alamun hutu yafara zama ajikinta,ya kalli hips dinta yana mamakin dama haka yake? bai ta6a ganinta a zahiri haka ba, har wani karkatar dakai yake yana sake qare mata kallo,yana ganin wannan surar tayaya ne zata barshi yayi aiki? Wani irin saliva ya had'iye me cikeda jaraba sannan yasaki ajiyar zuciya,hakanne ya tona masa asiri Inaas taji motsi tajuyo da sauri,tana ganinsa ta runtse idonta tayi sauri ta tsugunna sannan taja hijabin Mummy dake kan sallaya tazura. Jawad ya d'an ta6e baki sannan ya qaraso cikin dakin ya zauna akan Carpet, Inaas ta zauna akan gadon can nesa dashi,ahankali ya d'an matsa kusa da'ita,sannan ya kalleta yace"Meyasa kikeson zama nesa dani? so kike duk abinda zan fada miki sai anjimu? matso kusa! " Ahankali ta matso kusa dashi kanta aqasa,ita tana kan gado yayinda shikuma yake zaune a qasanta,yayi ajiyar zuciya yace"kidena zama nesa dani" kanta aqasa batare data kalleshi ba tace"bagashi na matso ba?" Yayi d'an qaramin murmushi sannan yace" kisaki jikinki ni babu abinda zan miki,kalli can" Yayi mata nuni dawani waje,ahankali takai idonta wajan,anan taga 'yar qaramar camerar tsaro,yajuyo ya kalleta yace"akwai 'yar leqen asiri" Gaba dayansu sukayi murmushi atare. Yayi qasa da muryar sa ya sassautata,sannan ya kalleta cikeda so yace"sallama nazo nayi miki,inaso natafi,because bana Samun damar yin ayyuka yanda yadace,idan naci gaba da zama a qasar nan zaki karya min dukkan qwarin gwiwa ta" Inaas tayi murmushi tayi masa wata irin hararar masoya,wadda ita kanta batasan tayi ba. Ya kalleta daga fuskarta har zuwa qafarta duk da tana cikin hijabi yace"kinyi kyau da wannan shigar" Ahankali Inaas tace"ni banda kyau ai" Cikin sauri Jawad yace"inji waye? bakisan duk wanda ya ra6eki shima sake kyau yake ba? shi kyan da kansa hassada yake miki,ban ta6a ganin abu me kyau kamar ki ba,zan wuce Saudia inyi wa ubangiji godia daya bani sarauniyar matan duniya, amma kafin nawuce Saudian zan tsaya a Cairo tsawon awa uku zuwa hudu ,zanyi wani meeting" Cikin kulawa Inaas tace"Allah yadawo dakai lafiya" Jawad yayi murmushi yace"Amin Amarya" Inaas ta kalleshi da mamaki,wacce irin Amarya kuma? meyake nufi da haka? Wayarsa ya dauka yayi kira,daga d'ayan 6angaren ana dauka Jawad yace"P.a. a turawa ma'aikata saqon gaggawa,muna da meeting yanzu-yanzu" Cikin sauri P.a yace"ok Yalla6ai" Yajuyo ya kalli Inaas bayan yakashe wayar sannan yace"bazan dawo ba sai lokacin bikinmu,akwai kudi a dakina idan kina buqatar cash,abubuwan buqata na biki kuma,ga card dina,ko zaku sai wasu abubuwan keda Mama,inaso da anyi bikin nan mutafi qasar waje,saboda harkokin kasuwanci na dayawa suna can,banaso ko kwana daya mu qara inde anyi mana aure,amma kafin natafi inaso kifadamin cewa kina sonah" wata irin kunya ta kama Inaas,tarasa gane ina maganganun sa suka dosa,yanzu kuma yana maganar wata kalma ta daban. Ahankali Jawad yamiqe tsaye,itama tatashi tsaye,ya kalleta yace"ina jinki" Cikin sauri tasa hannunta biyu ta rufe fuskar ta dashi,sannan tace"Ina sonka Yaya" Cikin jin dadi ya lumshe idonsa,yanason jinta ajikinsa amma babu dama saboda cct camera dake dakin,hakan bai masa dadi ba,ahankali yataka ya matso kusa da ita yayi kissing goshin ta,sannan yace"muje" Inaas ta bude idonta,adede lokacin plasma dake manne adakin Mummy tanayi kad'an kad'an ta hasko photon Inaas da Jawad ana sanar da saka ranar aurensu. Sai alokacin Inaas tagane inda kalaman Jawad ya dosa,Jawad ya dauke kansa daga kan tv sannan ya kalleta yace"baki mana Addu'ah ba" Ahankali tace"Allah ya sanya Alkhairi" Cikin jin dadi ya amsa mata,sannan suka futo daga dakin,suka wuce qaramin falon Mummy sannan suka futo Main falo na gidan. Anan sukaci karo da 'yan'uwan Mummy maza guda hudu a zaune afalo tareda Mummy,Inaas ta rissina ta gaida su,Mummy tace"kin tashi kokuma yatashe ki? yaya jikin naki?" Inaas tayi murmushi tace"natashi Mummy,lafiya kalau na warke" Daga nan ta rissina ta gaida baqin dake zaune, sannan tafuto daga falon tatafi wajan Ammiy Jawad yanemi waje ya zauna suka gaisa da baqin,sannan Mummy ta kalleshi tace"Su Kawu Amadu ne,sunzo ne suyima Allah yasanya Alkhairi,sunji labarin saka ranar bikinka" Jawad yayi murmushi ya kallesu yace"nagode sosai kawu,gashi kunzo kuma ina kan hanya,zanyi tafiya ne,da munsha fira" Mummy ta kalli Jawad din cikin jin dadi,duk da tasan cewa shi din ba ma'abocin magana bane amma yana qoqarin yaga ya wanke kansa awajanka. Kawu Amadu yace"ai babu komai Jawad,Allah yayi maka albarka,wannan abu da Bature yayi maka kayi haquri,dan kansa,wata rana sai labari,amatsayin mu na dangin mahaifiyar ka muna sake baka haquri a madadin Bature" Jawad yayi qasa da kansa yace"A a babu damuwa kawu,komai yawuce" Yatashi tsaye yajuya ya kalli Mummy yace"Mummy zan tafi,kimin Addu'ah,sannan su kawu su bada motocin su amaida su gida,su kuma su wuce su za6i sababbin motoci awajan AHMAD MUHAMMAD MARZUQ" (Dana Sani,star...,my first novel) Cikin farinciki kawu Amadu yace"ikon Allah Jawad harda wahala haka? to mungode,Allah yaqara arziqi" Jawad yace"Amin kawu,ku samu P.a na awaje zai baku dubu hamsin-hamsin saiku sha mai" Cikin sauri suka kalleshi da tsananin mamaki dakuma tsantsar farinciki,lokaci daya suka fara qoqarin saukowa daga kan kujera zasu masa godia. Jawad yana ganin haka yayi murmushi yayi sauri ya futo daga falon,kai tsaye yawuce wajan Bilkisu,anan ya tarar da Inaas tana shan shayi,Man Sulaiman yana kallo,yayinda Bilkisu take karatun Hisnul Muslim. Tana ganin shigowar Jawad ta ajiye littafin,shima kai tsaye wajanta ya qarasa ya zauna, sannan ya kalli Man Sulaiman wanda ya sauya yayi wani irin fresh kamar ba shiba,da alama Uncle din yaji dadin auren nasu,yadan sosa kansa sannan yace"Uncle ina kwana,barka da hutawa" Man Sulaiman yace"sannu Jawad,ina zakaje haka na ganka cikin shiri?" "zan tafi ne,zan koma bakin aiki kafin ranar tazo" Man Sulaiman yayi murmushi yace"to Allah yadawo mana dakai lafiya,Allah yakareka Jawad" Jawad yace"Amin Uncle" Yajuya wajan Bilkisu ya riqe hannunta yace"Mama zan tafi,babu abinda kike buqata ko?" Bilkisu tadora hannunta akan sajen fuskarsa ta shafa cikin kulawa tace"Jawad mezan buqata bayan kasancewar ka atare dani?,Allah yadawo mana dakai lafiya,ka kiyaye kaji....?" Jawad yadaga kansa yace"insha Allah Mama" Inaas tajuyo ta musu wani irin kallo tace"Yaya d'an gata,sai lalla6aka Ammiy take kamar kaine Auta,bayan nice Autarta" Jawad ya kalleta da sauri yace"oh bakinki yabude yanzu ko?" Inaas tayi masa wata irin hararar soyaiya tana turo bakinta gaba. Shima kallon soyaiya yazuba mata,sannan yamiqe yafuto, Man Sulaiman yabiyoshi zai masa rakiya. Bilkisu ta girgiza kanta tana murmushi bayan tagama ganin irin kallon soyaiyar da Jawad yazubawa Inaas ko kunyarta baiji ba,to wannan agaban idonta ne suke jifan juna da irin wannan salon soyaiyar,to idan kuma bayan idonta ne yaya kenan?(🤔) Acan Compound suka tarar da Daddy taredasu kawu Amadu,Jawad yayi sallama da iyayen nasa,guard dinsa suka bude masa mota yashiga suka tafi. Bayan Daddy yadawo falo tunda ya zauna yaketa amsa kiran mutane masu yimasa Allah ya sanya Alkhairi. Mummy ta kalleshi tace"Alhaji tunda ka zauna kake waya,yau mutane sun hanaka nutsuwa,tun da safe kake falon baqi daga wannan yatafi sai wannan" Alhaji Mekudi ya kalli Hajiya Zaliha yace"ni kaina abun yana bani mamaki,kuma duka fa 'yan Allah ya sanya Alkhairi ne, sunji batun saka ranar Jawad, bansan cewa mutane suna daakon zuwan ranar auren Jawad har haka ba" Kafin Mummy tayi magana,wata wayar tasake shigowa,yadauka cikin murmushi yana fadin"Alhaji Mudan mutanan Ghana" Alhaji Mudan yayi murmushi irinna qosassun masu kudi sannan yace"Mekud'i da kansa..." Gaba dayansu suka sa dariya,Alhaji Mekudi yace"to Yaya kasuwanci, ya Ghana?" Alhaji Mudan yace"Alhamdulillah kasuwanci suna tafiya sosai,da taimakon yaronka Jawad yanzu nima yarona shima yayi nisa a nasa kasuwancin" Daddy yace"to Alhamdulillah,Allah yayi musu Albarka" Alhaji Mudan yace"Amin Alhaji,yauwa yanzu nake gani a labarai ansa ranar auren Jawad,shiyasa na kira da wuri in sanar dakai cewa na dauki nauyin esin d'akin dinner,da kujerun zama, tareda kyautar da za'a rabawa jama'ah" Alhaji Mekudi yace"Alhaji Mudan ayi haka? meyasa kuke so kumin komai ne? d'azu-d'azu Alhaji Hadi yamin waya yace kada asaiwa Amarya komai na lefe kawai afada masa size dinta zai aiko komai daga Dubai,ga Alhaji Auwal yace kada nasa hannu na akan bikin nabar masa komai a hannunsa zai shigo jibi,kaima kuma yanzu kafadi haka" Alhaji Mudan yace"Haba Alhaji Mekudi,Jawad ai yaron mu,karka manta kayimin fiye da haka abaya" Alhaji Mekudi yayi murmushi irin nasu na manya sannan yace"to godia nake Alhaji Mudan,godia nake" Daga nan yakashe wayar,ya kalli Hajiya Zaliha yace"sai yanzu ne nake tunanin gara da bamu fadi bikin Jawad na farko ba,domin kuwa Alhaji Bature da ba qaramin kunyatani zaiyi ba a'idon mutanan nan" Mummy tayi ajiyar zuciya sannan tace"Alhaji,nikaina yanzu hankali na yafi kwanciya akan Inaas din,bansan me Yaya Bature yayimin harya yaudareni na dinga tura masa wannan kud'ad'en ba" Ta qarasa maganar cikeda hawaye,tana nadamar abinda ta aikata. Alhaji Mekudi yace"Haba Hajiya Zaliha,meyasa kike haka ne? komai fa yariga yawuce,kigodewa Allah tunda Jawad din baisan komai ba,yanzu shima Baturen ba gashi nan kudin sun qone ba? ai matsalar haram kenan,gashi shikuma Jawad din yanata Samun cigaba kina ji de yanda mutane suke tururuwar yimasa komai na hidimar bikin,dan Allah kidena kukan nan" Ya qarasa maganar yana janta jikinsa yana lallashin ta,Hajiya Zaliha tayi shiru tasake yin luf a qirjinsa(🙊🙈) Washegari Bilkisu tana zaune afalon Mummy dawata qawar Mummy din da tazo domin jin yanda zasuyi tsare-tsaren biki. Hajiya Zaliha tace"yanzu de tunda bamuda isasshen lokacin,kamata yayi afara yiwa Amarya gyaran jiki kona kwana goma ne,da ina tunanin aturo mana me gyaran jiki daga Sudan,tazo ta dinga yimata har zuwa lokacin bikin" Bilkisu tace"Hajiya dakin bar maganar gyaran jikin nan,hakan ma ai qalau take,me za'a gyara?" Mummy tace"a a Bilkisu,yarona zanyi wa komai,bazai iyu mubarta haka kamar marar gata ba" Hajiya Zainab tayi ajiyar zuciya tace"ni kuma inaga da anbar maganar ta Sudan dinnan,tunda suma yanzu qasar tasu zaman lafiya yayi qaranci,ya kamata abawa mutanan mu na'nan qasar dama,suma suzo ayi tafiyar nan dasu,gasunan munada masu gyaran jiki dayawa muma, a dauko me gyaran jiki daga maiduguri,adauko wata daga katsina,adauko wata daga Sokoto,su hadu su baje kolin basirarsu akan Amaryar mu,bana mantawa akwai wata me gyaran jiki da aka ta6a daukowa ta yiwa wata yarinyar Deputy govnor gyaran jiki wallahi Hajiya Zaliha bakiga yanda jikin Amarya yakoma ba,kamar ka ta6a jikinta jini yafuto,jikin yarinya yayi luwai-luwai duk inda Amarya ta gifta qamshi ne yake tashi awajan,maganar maganin mata kuwa ba magana,suna dashi ingantacce mai kyau,saboda haka itama Inaas din su za'a dauko suzo har gida su mata,alokacin nikaina saida nasai magungunan mata a wajansu,kuma na gwada sunada kyau sosai,kinga suna had'in amare kala-kala akwai (Gumbar Mallaka) ,yarinya zata mallake shi babu me shigowa sai ita kadai,haka sai abinda takeso zaiyi,akwai wata Gumba Sunanta (karya gado) ,a daren farko ango saiya karya gado,saboda yanda gumbar take, akwai (a Ciji kunne), inba sa'a akaci ba ango a daren farko saiya gama cije yarinya saboda dadi,sunada hadin (Bita makewayi),ko toilet tashiga,yana nan biye da'ita,bazai bari tayi nesa dashi ba. sannan akwai hadin (Bita Zai-Zai),tome zamu nema kuma awata qasa daban?" Bilkisu tayi ajiyar zuciya ta jinjina kanta bayan tagama jin bala'in da ake shirin d'urawa 'yarta,ta kallesu tace"Hajiya Zainab karfa garin neman gira arasa ido,yarinyar nan budurwa ce,idan ya kashe min ita ince mene? Ina ganin babu buqatar wad'annan magungunan,abar batun wani Bita zai-zai wallahi yanzu ma duk inda tayi binta yake"(😂) (jama'ah kunga laifin Ammiy? 🤔🤔😂) Mutara zuwa yammah🙏🏻 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/20, 08:44] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta baki biyaba keda Allah saboda ban yafe ba. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 _____ Hajiya Zainab tayi murmushi tace"mutunci zamu kankaro mata,Bilkisu saifa kinyi haquri anbawa yarinyar nan magungunan nan,saboda shima Jawad ya d'in ya more gajiyarsa" Hajiya Zaliha tayi murmushi tace"Hajiya Zainab,magungunan sunyi yawa gaskiya,babu batun wata mallaka,da kai da kaya duk mallakar wuya ne,da yarinyar da yaron dukansu namu,ade bata wanda ya kamata kawai,inkin duba shima fa Jawad din ya dade baiyi aure ba,bana tunanin zaiyi mata da sauqi,aji tausayin yarinya arage magani" Hajiya Zainab tayi ajiyar zuciya tace"naji wannan,toya maganar kayan lefe" Hajiya Zaliha tace"mungama da wannan Fannin,Abokin Alhaji zai turo su daga Dubai,amma nima anan zan qara abunda nake ganin yakamata a qara" Hajiya Zainab tace"to ba damuwa,sai muyi maganar kayan da Amarya zatayi amfani dasu,kuma mu bincika muga wacce me makeup ya kamata mu dauko" Sai alokacin Bilkisu tasaki wata irin ajiyar zuciya,dataji cewa za'a rage wannan kayan matan daza'a bawa Inaas,tana kuma yiwa Inaas din Fata Allah yasa Jawad din bai dauko jarabar Ubansa ba.(🤭) **** Lokacin daya sauka a Cairo,ko minti ashirin baiyi da sauka ba,Na'im yakirashi,P.a ya meqo masa waya,ya kar6a yace"Na'im" Na'im yace"Na'am late commer,yanzu nake gani a social media"(😂) Jawad yayi murmushi yace"tanan ka 6ullo?" "Emana,J. yanzu kasan cewa kana son yarinyar nan amma shine kabarni naje na kar6i number ta? da mun dedeta kanmu Yaya kenan?" Jawad ya d'an motsa lips dinsa kad'an sannan yace"ai ban baku damar daidaita wa ba,what next?" Murmushi Na'im yayi yace"dan kasuwa da soyaiya" Jawad ya lumshe idonsa yabude sannan yace" Na'im,what next,if you don't have anything to say,I will...." Kafin Jawad yagama magana Na'im yayi dariya yace"Allah ya shirye ka J,yanzu yaushe zaka dawo mufara shirye-shirye?" Jawad yace"Na'im kana nan meyasa zan dawo da wuri? kuyi komai tareda Fu'ad kawai" Na'im yace"ok bye" Daga nan yakashe wayar yabawa P.a Washegari aka saiwa masu gyaran jiki tickets, suka nufo garin Abuja,daki na musanman Mummy ta ware musu,aranar basu fara yiwa Inaas aikin komai ba,sai washegari da safe suka fara,dukansu sun samu hadin kai,kowa takawo fasaharta sun hada sun tashi abu mai kyau guda daya,Inaas de binsu take da kallo kawai,tana mamaki dama a Nigeria ma idan za'a yi biki sai anyi wadannan abubuwan?. Da daddare misali shabiyu na dare yakira wayarta,saida yayi mata 3 missed call sannan ta dauka cikeda muryarta me bacci. Daga nasa 6angaren wata irin wawiyar ajiyar zuciya yasaki yace"harkin kwanta bacci?" Sai alokacin tabude idonta ta kalli fuskar wayar taga number qasar waje,sannan ta maida kanta kan fillo tace"na kwanta Yaya,ya gajiya ya hanya?" "babu gajiya,na nemeta na rasa tunda naji muryarki" Inaas tayi murmushi tana jinjina kanta cikin mamaki,yanda yake maganar kamar ba shiba,cikin jin dadi tace"banason sharri Yaya,tayaya daga jin voice dina zakaji babu gajiya?" Jawad yasake shigewa cikin blanket dinsa mai laushi yace"serious fa,ina Mama?" "Ammiy bata nan taje dakin Abba" "ok,kenan saike kadai kenan?" Inaas tace"um" Yayi murmushi yace"Meyasa bazaki kirani inzo in tayaki bacci ba?" Inaas tabude bakinta da sauri cikin mamaki, sannan cikin shagwa6a tace"Yayaaaa" Taja sunan nasa. Jawad ya lumshe idonsa yace"Plaese,inason jinki acikin jikina,inason in dora kaina akan cinyarki nayi bacci,nifa maraya ne" Inaas batasan lokacin data saki dariya ba tace"who is maraya? kai ko ni?, kai dan gatane nesa ba kusa ba, kuma kanada iyaye har guda hud'u dukansu suna raye" Murmushi yayi yace"wayo zaki min? ok fadamin, ya shirye shiryen biki,? me kika fara shiryawa?" " Yaya ai Shiri yana wajansu Ammiy,ni babu abinda nake,ande fara yimin gyaran jiki" Cikin jin dadi ya lumshe idonsa,yace"wow,idan za'a yi miki zan kiraki vedio call Inga yanda ake miki,inason nasake ganin wannan kyakykywan surar taki kamar yanda naganki adakin Mummy" Inaas ta zaro idonta cikin tsananin mamakin Jawad din,tarasa meyasa yau din yake mata wasu irin baaqin kalamai,wanda abaya zata iya rantse wa cewa shi din bazai iya zaro irin wannan manyan kalmomin masu nauyin fada ba, cikin tsananin kunya tashige cikin bargo ta rufe kanta kamar yana ganinta sannan tace"Yaya nide saida safe gaskiya" Jawad yayi murmushi cikin wata irin muryar shagwa6a wadda Inaas bata ta6a sanin yanada itaba yace"kiss me please,zanyi bacci me dadi idan kikamin" Inaas tasa tafin hannunta ta rufe idonta dashi duk da tana cikin bargo,tace"Yaya kana bani kunya fa,wai meyake damunka ne?" Daga nasa 6angaren ya lumshe idonsa cikin zallar buqatarta yace"Ke ce..." Dan qaramin bakinta taturo gaba tace"ni ban iyaba" Ajiyar Zuciya yasaki yace"rufe idonki" Cikin sauri ta rufe idonta tace"na rufe,meyafaru?" Baice da'ita komai ba yafara sakar mata wani irin kiss ajajjere. salon yanda yake yimata Salo ne wanda zaisa dole ya karya mata dukkan wani qwarin gwiwar ta,Salo ne wanda zaisa dole jikinta ya kar6i saqonsa,yanda yake yin kiss din dawani irin Salo saitake jin kamar ajikinta yake mata hakan,batasan lokacin data rungume fillon gefenta ba,ko kad'an bata bude idonta ba,Jawad yana jiyo yanda yanayin saukar numfashinta yafara sauya wa,ya tabbatar cewa taji dadin saqonsa. Ahankali Inaas tafara janye wayar daga kunnanta,saboda wani irin yanayi data jita aciki wanda bata ta6a tsintar kanta a cikinsa ba,hakan yasa tayi qundunbala ta kashe wayar tasake rungume fillon jikinta,batasan lokacin da bacci ya dauketa ba. Shima anasa 6angaren hakan ce ta kasance,yanajin ta kashe wayar ya lumshe idonsa dake cike tsananin buqata,daqyar yasamu yayi bacci,lokacin sallar asuba daya tashi saida yayi wanka,sakamakon yanayin yanda yatashi ya ganshi yayi jalaf...(🙈) Cikin wasu yan kwanaki gyaran jikin Inaas sai wanda yagani,sosai suke gyara ta abun har mamaki yake bawa Hajiya Zaliha da take tunanin dauko masu gyaran jiki daga qasar Sudan,ashe muma acikin gida ba baya ba,iya gyaran jiki kawai suke mata sai maganin sanyi,haka na tsugunno dana turare dana wanka duk babu wanda Inaas bata gani. Man Sulaiman yaje gida Jigawa ya taho da gayyar yan'uwa da abokan arziqi,maza da mata,acikin matan harda Bintu da Fatsime maqotan Bilkisu na da,wanda suka taimaka mata sukai kaita wajan Maigari ranar da Man Sulaiman ya gudu yabar gari,dakuma 'Dayyaba matar maigari wadda ta kar6i haihuwar Bilkisu acikin dakinta. Lokacin da suka sauka afalo Man Sulaiman shida kansa ya gabatar musu da abinci, sannan yatafi falon Hajiya Zaliha yakira Bilkisu,suka taho harda Hajiyan. Bilkisu tana ganin matar maigari wato 'Dayyaba ta qame awajan a tsaye tace"Yaya 'Dayyaba ke nake gani ko wata?" 'Dayyaba tayi murmushi tace"nice Balki,ashe da rabon zamu sake ganinki Balki? ina kayan gwanjo Balki? kinganni tareda Fatsime da Bintu maqotanki,kin sheda su?" Bilkisu tajuya ta kalli matan guda biyu dasuke zaune agefe,kwata-kwata bata ganesu ba saida 'Dayyaba tace mata Fatsime da Bintu ne,wahala tasa sun sauya,wahala tasa sun tsufa,bazaka ta6a cewa su d'in kusan sa'annin ta ne ba. Wani irin kuka ya tahowa Bilkisu,cikin gudu ta qarasa wajansu suka fashe da kuka,kamar dakin makoki haka suka maida falon sai kuka suke kamar ransu zai fita,mazan dasuka taho dasu mutum uku sune suka fara basu baki. Hajiya Zaliha ta goge qwallar idonta tace"kuyi haquri ku daina kuka Bilkisu,murna zakuyi kuma kuyiwa Allah godia tunda gashi yasake hada fuskar ku da Alkhairi" Bilkisu ta share hawayen idonta sannan tace"Haka ne,Hajiya bazan iya kwatanta miki irin halaccin su agareni ba,sune suka kar6i haihuwar Jawad,suka yanka min ragon suna,jama'ar gari suka had'a min kudin mota natafi qasar mu" Hajiya Zaliha tace"Allahu akbar,Allah abun godia,sannunku da zuwa" Bintu tace"sannu Hajiya" 'Dayyaba tace"Balki Muhammad din naki suna kuka sauya masa ne? naji kina cewa jawal" Bilkisu tayi murmushi jin yanda 'Dayyaba tafadi sunan,tamayi kokari,ko a wancen shekarun na baya ita din babba ce,kuma mutane suna girmamata kasancewar ta matar maigari,tace"Haka muke kiransa,an6oye Muhammad din, sai muke cemasa JAWAD" Fatsime tace"Balki kiga jikinki fes dashi kekam yarinya ma kika sake komawa wallahi" Gaba daya falon sukai dariya,Man Sulaiman yaji kansa yasake girma anyabi matar tasa,shi kansa yasan cewa shi me sa'a ne,domin kuwa Samun mace kamar Bilkisu sai me sa'ah. Bilkisu ta kalli mazan wanda bata ganesu ba tace"Meyasa bakuzo da Megari ba?" Gaba dayansu sai sukai shiru aka rasa me bata amsa,sai 'Dayyaba ce tace" Allah sarki,Balki Alhaji aiya dade da rasuwa,yanzu babban d'anane akan kujerar,kinganshi nan" Ta qarasa maganar tana nuna mata wani matashi daga cikin mazan guda uku dasuke zaune. Nan take tayi musu ta'aziyya,sannan sukai masa Addu'ah, daga nan kuma fira ta 6alle ana bawa juna labarin baya. Washegari baqin Niger suka iso,ciki harda Maman Is'haq saurayin Inaas,da mutanan dasuke mutunci dasu maqota,sai matar Alhaji Auwal,suma baqin Niger ba'a barsu Abaya ba,domin kuwa kullum da daddare idan Inaas zata kwanta sai sun bata magunguna masu kyau tasha irin nasu na qasar Niger,Bilkisu dai nata idanu,tariga ta saddaqar cewa Inaas zata d'and'ana kudarta awajan Jawad. Mutanan Niger sosai suka yiwa Bilkisu gudunmawa amma taqi kar6a sai kad'an daga ciki ta kar6a. A satin biki baqin qasar waje suka iso,gida yacika yayi dam da jama'ah,Hajiya Zainab tayiwa Inaas sababbin qawaye yan Boko mutum hudu,biyu yaranta ne,sauran biyun kuma yar gidan minister ce da yar gidan tsohon matemakin gwamnan jihar kaduna. Idan mutum yazo gidan zaiyi tunanin anfara bikin,duk baqin kusa suma sunzo,Yaya Mariya ma ta debo tawagar ta sun dawo gidan gaba daya. Tunda biki yarage saura kwana hudu,Hajiya Zaliha tahana Inaas fita ko'ina,tana can wajan masu gyaran jikinta suna jiqata da humra kala-kala,tayi masifar kyau yanda mutane basa zato. Ana saura kwana biyu Jawad yasamu ya qwato kansa yashigo qasar,so yake yayi tozali da Inaas, ba qaramin kewar ta yayi ba, hakan yasa kai tsaye yawuce wajan Bilkisu,yana shiga falon ya ganshi acike da jama'ah,kowa sai kiransa yake yana gaida su,haka yasamu yashiga dakin Bilkisun,ya tsugunna yagaida mutanan daya ganta tare dasu. Bilkisu tayi murmushi tace"yanzu ka sauka Jawad?" Jawad yadan juya gefe yana kalle kalle ko zaiga Inaas amma shiru ba bayani,yayi qasa da kansa yace"yanzu muka sauka Mama,mun same ku lafiya?" Bilkisu tace"lafiya kalau, Jawad wadannan yan'uwanka ne daga jihar jigawa,dukansu kamar dangin Babanka suke,sune suka kar6i haihuwar ka ranar dana haifeka" Cikin sauri Jawad ya kallesu. Fatsime taqura masa ido tace"ikon Allah Muhammadu kaine ka girma haka?Bintu kinga Muhammadun Balki" Tafadi haka hawaye hana zubowa daga idonta. Bintu tace"ikon Allah kenan Fatsime,sainaga kamar yau aka haife shi,girman d'an mutum ba wuya" 'Dayyaba tayi murmushi tace"Muhammadu kayiwa mahaifiyar ka biyaiya kaji? tayi qoqari a kanka kuma tasha wahala ita din abar a tausaya wa ce" Jikin Jawad yayi sanyi qalau,yaji wata irin soyaiyar Bilkisu tasake ninkuwa acikin zuciyarsa, haqiqa Mama taga rayuwa,daga yanda mutanan nan suke magana kadai zai tabbatar masa cewa tayi garari abaya. Cikin nutsuwa yace"insha Allah zanci gaba dayi" Bilkisu tace"kaci abinci kuwa?" Yace"A a Mama, yanzun nan na shigo,ko wajan Mummy ban shiga ba,zanje nafara yin wanka tukunna" Tace"to shikkenan,itama qanwar taka tana can wajan Hajiyan" Ahankali yayi wata ajiyar zuciya a 6oye,sannan ya kalli baqin nata yace"akwai abunda kuke buqata ne akawo?" Cikin sauri Bintu tace" a a Muhammadu,wallahi bamason komai,Balki tana bamu duk abinda muka nema" Cikin nutsuwar sa ya gyad'a kansa alamun amsawa sannan ya kalli Bilkisu yace"Bari inje Mama" Bilkisu tayi masa Addu'ah sannan yatashi ya futo daga dakin,yanajin wasu mata afalon suna cewa "wannan ko shine angon?" Yaji wata daban daga gefe tace"eh shine,yanzu yazo yawuce,kina daki kina waya lokacin" Shide cikin sauri yayi wuf yafice daga falon. Ta qofar baya yasamu yashiga yahaye sama,sannan yakira Mummy wadda ta kacame cikin baqi,sai itace ta bishi dakin nasa,yana ganinta ya rungume ta yace"Mummy I'm hungry,yarinyar nan takawo min abinci" Mummy tace"yarinya takawo abinci kokuma Mummy takawo? Inaas bata gidannan,saide zuwa jibi idan an daura aure zaku hadu awajan dinner,hayaniya zata samata ciwon kai shiyasa na tura ta gidan qawata" Jawad yaji wani irin fad'uwar gaba yaji kamar ya rusa kuka,haka dan dole yace"to Mummy abincin" Hajiya Zaliha tajuya tafice daga dakin,shima yashiga wanka. Washegari aka yiwa Amarya qunshi,ja dakuma baqi,aka gyara mata dogon gashinta aka turara mata shi da wasu sinadaran qamshi,sannan tayi wanka da ruwan lalle, mai kwalliya tazo tafara aikinta. Garin Abuja yacika da manyan baqi,duk wasu mutane na qasar waje sun iso aranar,qalilan ne zasu qaraso gobe. Washegari daurin aure manyan 'yan siyasa dakuma manyan 'yan kasuwa sun halarci Central mosque na Abuja inda za'a daura aure acan,dayawansu sunzo ne domin taya Alhaji Mekudi murnar auren Babban d'ansa da za'a yi. Jiragen sama sai shawagi suke basai mutum ya tambaya ba anriga ansan cewa bikin Jawad Mekudi ake. Man Sulaiman shine Waliyin Amarya,yayinda Alhaji Auwal yazama waliyin ango,ba'a dauki wasu tsawon lokaci ba bayan angama abinda addini ya tanada domin dauren aure nan da nan aka daura auren Jawad Aliyu Mekudi da Amaryar sa Inaas Omar Farouq akan sadaki naira Million d'aya,lakadan ba ajalan ba. Kasancewar akwai baqi na nesa wanda zasu juya zuwa qasar su,hakan yasa daga wajan daurin aure aka fara wucewa da baqi zuwa hall din da zasuyi dinner, andauki lokaci sosai mutane suna tafiya wajan,saide duk wanda kagani kallo daya zaka masa kasan cewa wani qusan ne. wajan yayi kyau ya tsaru iya tsaruwa da adon furanni,anyi komai da tsari kasancewar abun sune na Manya,ga abinci nan kala kala ruwan gorar faro da lemuka kamar banza. Sai a wannan lokacin Jawad yaga Inaas,yanda tayi masifar kyau hakan yasa yaji wani irin Kishi ya kamashi,shi kansa daya Santa ba qaramin gigitashi tayi ba,doguwar riga ce ajikinta fara daga Bayan rigar ansaka mata net yana bin bayanta har qasa,yayinda Jawad yayi mutuqar kyau cikin manyan kaya farare,hannunsa cikin nata suka shigo,bayan sun zauna aka fara gabatar da taro,yanda manyan yan siyasa suke tiqar rawa abun har mamaki zai baka,daga baya aka kira ango da Amarya suka futo fili,aka kunna musu hayaqin soyaiya,hannun Jawad yana kan hips dinta,yayinda ya dora fuskarsa akan tayaya yana mata magana qasa-qasa wanda su kadai sukasan me suke fada,wata waqa ce take tashi awajan me sanyi wadda babu tashin hankali acikinta sai zallar kalaman soyaiya da'ake fad'a. Na'im babban abokin ango yataso tareda abokan Jawad yan qasar waje,suka fara yimusu kari da dala, yayinda Fu'ad yataso dawata jaka me d'aukeda kudi yana watsa musu cikin farinciki. Lamarin daya jawo cece-kuce a social media,ta wani Fannin kuma zallar kyawun Amaryar Jawad din yasa wasu yan bani na'iya a social media suke fadin cewa da alama Jawad din wata qasar larabawa ya tsallaka yasamo matar. Qarfe goma daidai aka gama dinner kai tsaye falon Daddy Hajiya Zaliha ta wuce da Amarya,ba tafi minti goma da kaita ba,Jawad yashigo ya zauna akusa da'ita,Man Sulaiman da Abban ta da Bilkisu da Daddy da Yaya Mariya duk suka had'u,nasiha suka musu,tareda jan kunne da gargadi akan su had'e kansu suyi zaman lafiya. Abban ta ma yayi musu nasiha,itade Inaas kanta yana qasa cikin net. Acan Compound kuma su Na'im da Fu'ad suna waje tareda sauran abokan ango,suna fafatawa da qawayen Amarya akan kudin siyan baki,bayan dogon kace nace wani abokin Jawad yayi magana guda d'aya yace tunda harka ce ta manyan yara abasu million biyar,nan take aka tura kudi ta account din babbar qawar Amarya,ita kuma ta kar6i account number kowa zatayi magana da Amarya sannan a turawa kowacce qawa nata. Bayan angama yimusu nasiha Hajiya Zaliha takamo Amarya suka futo,yayinda Jawad yabi bayan Bilkisu domin yin sallama da baqi, Su Fatsime da Bintu suna zaune sunata fira,Jawad ya tsugunna yayi musu godia akan halartar taron da sukai,sannan ya kalli Bilkisu yace"Mama kifada musu daga nan zasu wuce Saudia tare daku idan kunyi Umarah saisu wuce gida" 'Dayyaba ta fashe da kuka tace"Allahu akbar,haihuwa me rana,yau Muhammadu ne yabiya mana Umarah,Allah yayi maka albarka Muhammadu" Cikin nutsuwa Jawad ya amsa mata,daga nan suka futo shida Bilkisu har zuwa gaban motoci,Bilkisu ta rungume Inaas tayi qasa da murya a setin kunnanta tace"Inaas banda wasa da abubuwan dana fada miki kinji ko? ki nutsu ki kula da Yayanki kiyi masa biyaiya" Cikin sauri Inaas da tasha kuka saboda zafafan nasihohin da iyayen nasu suka musu tace"wai ina zamuje ne Ammiy?" Bilkisu tace"mijinki yace yanaso kutafi qasar Qatar daga wajan dinner,Daddy yace bazai iyu ba dole saikun dawo gida kunyi sallama da mutane tukunna,muma cikin satin nan zamu wuce Saudia bayan mun gama sallamar baqi" Inaas tafashe da kuka tasake rungume Ammiy cikin kuka tace"to haka akeyi,kawai kuma Ammiy saiku barshi daga daura aure yatafi dani,meyasa bazamu zauna tare daku ba? Ammiy gaskiya ni bazan bishi ba" Hajiya Zaliha ta kallesu tace"to ya zamuyi Inaas? mijinki ne yace yafi so kutafi yau,dole zaki yiwa mijinki biyaiya" Daddy ya kallesu yace"me ake jira ne? Man Sulaiman shiga mota muje" Man Sulaiman da Abban Inaas da Daddy suka shiga mota,Inaas tana kuka Bilkisu tana kuka haka sukaja mota suka tafi, yayinda Jawad yashiga daya motar,iya maza ne kawai suka rakasu Airport,Mummy da Bilkisu da Yaya Mariya suna gida. Saida jirgin su yatashi,sannan Daddy da Abban Inaas da Man Sulaiman suka juyo gida. har cikin jirgin ma Inaas kuka take sosai,Jawad ya kalleta ya lumshe idonsa,sannan yajata jikinsa ya shigar da'ita cikin faffadan qirjinsa ya rungume ta yana sakin ajiyar zuciya. Sunyi tafiya me nisa sannan suka sauka cikin dare,P.a da sauran guard dasuka riga su zuwa,sune sukazo Airport daukarsu,Inaas kam batasan sunzo ba,tunda tajita ajikin Jawad batasan lokacin datayi bacci ba.(🙈) Hakan yasa yadauketa cak daga cikin jirgi zuwa mota,saida suka sauka awani hadaddan gidansu wanda yayi shahararran kyau sannan yafara qoqarin tashinta daga bacci,amma bata tashi ba,hakan yasa guard dinsa suna bude masa mota yasake dauko ta cak suka futo,saida ya danyi tafiya kad'an zuwa hanyar da zata kaisu falo sannan yajuyo yace"P.a" Cikin sauri P.a ya qaraso yace"na'am Yalla6ai" Yadan motsa lips dinsa kad'an sannan yace"zaka iya barin wayoyin ka a kunne kaci gaba da tafiyar da al'amura,amma ni ka kashe wayoyina"(🙊) Cikin girmamawa P.a yace"ok sir" Sannan Yajuya yana murmushi. Jawad kuma ya qarasa ciki,Suna shiga cikin falo ya rufe qofar sannan yazubawa kyakykywar fuskarta ido yana kallon yanda take bacci ajikinsa tayi luf kamar tasamu katifa. Yayi murmushi ya qarasa ciki ya zauna akan wata irin hadaddiyar kujera sannan ya sunkuyar da kansa yadora lips dinsa akan nata lips d'in yayi kissing,amma shiru Inaas bata tashi ba,hakan yasa ya lumshe idonsa yamaida bakinsa kan nata yakama lips dinta na qasa yana tsotsa cikin wani irin salo kamar maye. Jin kamar a mafarki anasha mata baki hakan yasa tafarka a zabure,adede lokacin yabude rinannun idanunsa yasaka shi cikin nata idon,cikin wata irin murya acan qasan maqoshinsa yace"ina miki barka da shigowa gidanki,Mrs. J. Sulaiman" Inaas ta yunqura tatashi ta zauna sosai akan cinyarsa tafara waige waige tana qarewa falon kallo yanda aka kafa photunan ta tako ina,tsananin mamaki ya kamata ganin wani photon tun ranar da sukaje wajan Birthday dinsa,wani tasan anyi wani bata sani ba,wani kuma ranar da ake mata qunshi ne afalon Mummy,sosai aka yiwa pictures din editing ta ko'ina itace a manne afalon. (Qarfi da yaji ango ya dauke Amaryar sa ya barmu da hayaniyar biki 🤔🤔) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍ [1/20, 14:36] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne, idan kika karanta baki biyani haqqina ba banyafe ba nabarki da Allah 👌🏻 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. ____ Sosai Bilkisu take kuka adaki tun bayan tafiyar Inaas,baqinta 'yan biki sai haquri suke bata,amma kokadan batayi shiru ba,hakan yasa d'aya daga cikinsu tatafi wajan Hajiya Zaliha ta sanar da'ita,bayan Hajiya Zaliha tazo dakin tanemi waje ta zauna abakin gadon ta dafa Bilkisu,da muryarta wadda take gab da dashewa saboda yawan magana tace"Bilkisu har yanzu de kukan ne? kiyi haquri mana aure fa yagaji haka" Cikin kuka Bilkisu tace"Hajiya dede da kwana d'aya,ban ta6a rabuwa da Inaas ba tunda mahaifiyar ta tarasu,tare muke komai,tare muke shawara,kullum tana gefena" Fatsime tace"to Balki aure ai ya gaji haka,bare ita data auri dan'uwan ta,menene zai dameki?" Hajiya Zaliha tace"Bilkisu saide kiyi kukan rabuwa da Inaas saboda sabo,amma ba saboda ta fada hannun Jawad ba,na tabbatar zai bata kulawa fiye da wadda kike bata,kidena kukan haka dan Allah" Bilkisu ta gyad'a mata kai alamun amsawa,sannan suka dinga bata baki harta dan ware akaci gaba da fira. *** *** *** Saida tagama kallon photunan tsaf sannan ta juyo ta kalleshi,ya lumshe idonsa sannan yasake maidata cikin jikinsa yacusa hancinsa cikin wuyanta yana goga mata dogon hancinsa awuyan nata yana shaqar qamshin dake tashi ajikinta,ahankali tasaka hannunta tad'ago masa kansa alamun yadena abunda yake,hakan yasa yad'ago kansa yadauketa cak,suka nufi dakinsa, ya direta akan gado sannan yace"ga toilet nan,ki shiga kiyi wanka,muyi sallah,muci abinci mukwanta muhuta" Yafadi haka yana qoqarin cire agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Inaas ta gyada masa kai,sannan tatashi tashige toilet din,tasa mukulli ta rufe qofar saboda tsaro. Tacire kayanta ahankali sannan ta nufi wajan kunna ruwa tarasa yanda zatayi ta kunna,saboda babu irin toilet din a house(😂) Ta ta6a tasake ta6awa taji shiru ruwa baizo ba alamun de bata kunna daidai ba,hakan yasa ta kalli toilet din sosai taga wasu towels kala-kala acan gefe,taja guda daya ta daura,ta dauki dankwalin kanta data cire ta yafa ajikinta sannan tabude toilet din tadan leqo kanta tace"Yaya!" Jawad daya cire babbar rigar jikinsa yajuyo ya kalli toilet d'in yace"what" Tace"nakasa kunna komai,bansan ya zanyi ba" Jawad yayi murmushi yatashi yanufo ta,tana ganin zai shigo toilet tasake matsawa can gefe tana saka hannu tana rufe fararen cinyoyinta,ya kalli cinyoyin nata yazuba musu ido sannan ya kawar da kansa yace"keda gidanki tayaya zaki kasa gane komai? zoki gani" ya qarasa maganar cikin bata umarni. Inaas ta matso kusa dashi yafara nuna mata komai,sannan yabata dama ta kunna yagani,tasa farin hannunta me zanan ja da baqin lalle tafara gwada masa yanda taga yayi,ya kalli hannun nata yanaji kamar yadora hannunsa akai yatsotse qunshin,sannan yamaida kallonsa zuwa qirjinta saboda yanda yake d'an hango shi ta saman towel din,yakawar da kansa daqyar, yayi qoqarin seta kansa yace"yayi" Yajuya ya futo daga toilet d'in. Inaas tasaki wata irin ajiyar zuciya,sannan ta kulle qofar tafara wanka. Akan gadon ya zube yana maida numfashi,daqyar ya lallashi kansa ya daure,yadauki remote ya kunna kayan kallon dakin, yarage volume, yajirata harta futo daga wankan,yanajin motsin futowar ta yajuyo yazuba mata ido,kasa janye idonsa yayi akanta,saida wani 6angaren na zuciyar sa yatuna masa cewa ba suyi sallah ba, sannan yatashi yashige toilet din,agurguje yayi wanka ya futo qugunsa daure da towel,dantsan hannunsa dasuke a mummurde ya futo fili,gawani gashi baqi me laushi da ya kwanta akan faffadan qirjinsa,Inaas data maida kayan jikinta tana ganinsa ahaka tayi sauri ta runtse idonta,ya kalleta yayi wani miskilin murmushi sannan yabude wardrobe yadauko riga yasaka,itama ya dauko mata wasu riga da wando me santsi ya ajiye agabanta. hararar kayan tayi,taqi dauka tasa,ya kalleta yace"kisa kaya ga hijab can a wardrobe kisa kizo muyi sallah. Yana fadar haka yatada kabbarar sallah,ganin hankalinsa baya kanta hakan yasa tatashi tashige toilet tasaka kayan,dogon wando ne, sai rigar me qaramin hannu da botir qanana ajere agaban rigar,ta kalli qirjinta acikin rigar taga sun sake futowa sun tsaya sunyi carrr,saboda rigar me santsi ce,gashi batasan saka bra,haka ta futo da sauri ta dauko hijab din sannan tazo ta bishi sukai sallar. Bayan sun idar yayi musu Addu'ah sosai,sannan yatashi yadauko musu nama da fruit,ya ajiye agabanta, ya meqa hannunsa yacire mata hijabin jikinta yadauketa ya d'orata akan cinyarsa,yadauko naman guda daya yace"bude bakin" Cikin kunya Inaas tasa hannu ta rufe fuskarta,yasaki ajiyar zuciya yace"dan Allah kirage kunyar nan,because wallahi ina cutuwa" Batare data bude fuskarta ba tace"ai Ammiy na tace kunya adon mace" Jawad yazuba mata ido yana kallonta yace"oh... Really? kuma to harda mijinki a kunyar? inkuwa hakane shikkenan Mama ta kasheni"(😂) Inaas ta janye hannunta taturo bakinta gaba tana masa wani irin kallon shagwa6a me kamada harara. Ya girgiza kansa yace"bude bakin nace" Ahankali tabude masa bakinta, yasaka mata naman, shima yafara ci,saida sukaci naman sosai, sannan yafara bata fruit din,ganin kamar tafi son tuffa hakan yasa yafi bata ita,yanda yaga tana tauna ahankali kamar da niyya take yi hakan ne yafi komai daukar hankalinsa,yazuba wa d'an qaramin bakinta ido yana kallo,daya saka mata wata tuffar tana fara ci yadora bakinsa akan wuyanta yafara sha,Inaas ta zaro idonta kamar zatayi kuka tace"Yaya wuyanane fa" Kallonta yayi cikin shaqaqqiyar murya yace"kici tuffa dinki mana" Yafadi haka yana cigaba da shan wuyanta saboda yanda ta zauna akan ainahin cinyarsa hakan ba qaramin illa yamasa ba. gaba daya ilahirin wuyanta saida ya bishi ya tsotsa sannan yadawo kan fuskarta,qarfi da yaji haka ya hanata shan fruit din,saboda tundaga idonta,har hancinta babu inda yabari ko'ina yake kissing, hakan yasa ta rabu dashi ta rufe idonta tana jin ikon Allah,banda tasan cewa Yaya Jawad dan'uwan tane, jinin tane, to da babu abinda zai hana tace maye ne(🙊) Lokacin daya saka bakinsa cikin nata kusan sumewa yayi,ahaukace yake kissing dinta kamar ance masa zata gudu,laushin lips dinta danasa yasa yake jin kamar su kadai ne a duniyar. daqyar yadauketa yakashe wutar dakin ya kwantar da'ita akan gado,rigar jikinsa ya cire,yaja musu bargo me tsananin laushi,cikin jikinsa yasata,cikin zafin nama ya kaiwa nashanunta dasuke tsone masa ido wata irin damqa,Inaas ta runtse idonta saboda yanda taji zafi,tadora hannunta akan nashi hannun dake kan boobs dinta tafara janye hannunsa amma ko alamar motsi bataji hannun yayi ba,tanajin yanda yake murza mata su kamar da gayya yake hakan,hakan yasa tafashe masa da kuka,tafara qoqarin qwacewa tafuto daga blanket din amma ya riqe ta,sai motsi suke tacikin bargo kamar yan dambe(😂) Cikin wata irin murya tame kama da fitar hayyaci yace"ki nutsu babu abinda zan miki,bakiga dogon wando nabaki ba?" Inaas kam tashin hankali bai barta tagane meyake nufi dawani dogon wando ko akasin haka ba,cikin kuka tace"Yaya zafi fa" Jawad ya lumshe idonsa,sannan yasaka hannunsa biyu ya yaga rigar jikinta,botir din gaban rigar duk suka watse akan gadon,yacusa hannunsa cikin tulin gashin kanta yafara sosa mata kanta sannan yadora bakinsa akan nashanunta yafara sha bil haqqi. Tsawon lokaci yadauka yana sha tun tanajin dadi yanasha ahankali har abun yafita aranta saboda yanda suke mata wani irin zugi,ganin tayi hargagin tayi kukan bai barta ba, hakan yasa ta rabu dashi saide hawaye dasuke tsiyaya tagefen kunnanta. yadade yana sha,yanajin wani irin dad'i sannan shida kansa yacire bakinsa daga kai,yajata jikinsa ya rungumeta yana sakin wani irin numfashi a jejjere,cikin fitar hayyaci yaja hannunta yadora a qasan mararsa. Tanajin inda yakai mata hannunta gabanta yayi wata irin fad'uwa,jikinta yafara karkarwa, bata ta6a shiga tashin hankali irinna yau ba,tsananin mamakin Jawad din ya kamata,saita fara qaryata kanta cewa kode dama can haka yake bashida kunya? cikin sauri tafara qoqarin dauke hannunta daga wajan. Jawad yabude jajayen idonsa ya kalleta yaga yanda tahada wata Uwar zufa saboda ta riqe abunsa, yayi wani murmushin jin dadi sannan yasake riqe hannunta yahanata dauke wa daga wajan. Tashin hankali de Inaas tagama ganinsa awajan Jawad,gani take da wanne irin ido zata sake kallonsa Kenan? tana jin yanda yake motsa hannunta akan abunsa yana qoqarin d'orata akan hanya,yayinda hannun nata yake wata irin rawa,saide Jawad bai bata damar da zata cire hannun taba,yadora bakinsa akan kunnanta yana tsotsa ahankali, yayinda yasakar mata ragamar komai yanajin yanda take masa aqasan mararsa kamar zai shid'e,ta dade tana abu daya, sannan taji yayi mata wata irin runguma yana sakin numfashi a jejjere. tun ranar dayayi kissing dinta yaga ta kwanta zazza6i daga ranar yayi alqawari zai dinga binta daki-daki kada yaje mata kai tsaye ya kashewa Ammiy 'yarta. Inaas ta runtse idonta sakamakon yanda ya rungume tan yahada fatar qirjinsa da nashanunta,taji wani irin zafi saboda yanda nipple dinta suke mata wani irin rad'ad'i. Saida yaji ya d'an samu nutsuwa sannan ya maida ta kansa,ya kwantar da kanta akan faffadan qirjinsa yana kawar da dogon gashin kanta gefe,yayi kissing gashin nata,sannan ya dinga shafa gadon bayanta har wani irin bacci me dadi ya dauke su. Basu tashi sallar asuba ba,gaba dayansu sun makara,abu biyu ya had'e musu, ga baccin gajiya gakuma wani baccin na daban daya zo musu a bazata kasancewar basu ta6a kasance wa da juna haka ba,haka alerm ya qaraci kid'ansa yagama babu abinda sukaji. Saida gari yafara haske kafin Inaas tafarka,tad'an motsa kad'an tajita male-male akan qirjinsa,sai yanzu tatuna da abinda yafaru jiya,gabanta yafadi da taji babu rigarta ajikinta haka shima babu riga ajikinsa. Jawad ya yi wani irin juyi takoma qasa shikuma yahau kanta yazuba mata idonsa mai cikeda bacci yace"kin tashi?" Idonta aqasa ta gyada masa kai alamun amsawa. Ya matso da fuskarsa yayi kissing wuyanta cikin muryar rad'a yace"ya daren jiya?" Cikin tsananin kunya Inaas ta kawar da kanta gefe,tace"ba dadi" Jawad ya dage girarsa d'aya yayi mata wani irin kallo sannan yace"muje muyi wanka,lokacin sallah yawuce,ni ban ta6a makara sallah ba,gashi daga zuwanki kinsa na makara" Inaas taturo d'an qaramin bakinta gaba batace masa komai ba sai ma cikin bargo data sake shigewa sakamakon babu riga ajikinta,Jawad ya yagata. Saida taga yashige toilet din sannan tatashi da sauri tasaka rigar data cire jiya,sannan tafara d'ebe botir din rigarta dasuka watse jiya,saida ya futo daga wankan itama tashige toilet din ko kad'an bata yarda ta kalleshi ba. Yanzun ma shine yajasu sallah,bayan sun idar yayi musu Addu'ah sannan yamiqa mata hannunsa,babu musu tasaka nata hannun acikin nasa,ya tasheta tsaye yakai hannunsa zuwa bayan rigarta yayi qasa da zif din rigar,farar fatar jikinta ta bayyana ciki harda na shanunta,tayi sauri ta runtse idonta, yayinda Jawad yazuba musu ido yana kallonsu cikeda fitina,batasan meyake ba,saide taji saukar harshansa akan na shanunta yakama kansu yana mata wata irin zuqa,batare daya cire bakinsa akansu ba yadauketa suka koma gado,yauma kamar daren jiya haka ya dinga sha yana mata wani irin salo kala-kala,saide najiya kukan hawaye take masa,amma yau kuka take sosai sakamakon bata daina jin zafin jiya ba, gashi yau yadora daga inda yatsaya,hakan yasa take kuka sosai harda sheshsheka tana qoqarin ciro masa kansa dayake kan nashanunta,amma saiya sa hannunsa daya yariqe hannaye ta, yayinda dayakai daya hannun yana share mata hawaye,yakasa dauke bakinsa daga kai,bare yasamu qwarin gwiwar dazai bude baki yabata haquri. Yanaji tayi kukan ta tagama tafara jan zuciya amma bai daina abinda yake ba,saida ya yi yanda yakeso sannan yacire bakinsa daqyar yajata jikinsa yana bubbuga bayanta alamun tayi shiru. Tsawon kwana hudu horon da Jawad ya dinga yimata kenan,safe,rana,yamma,dare,asuba, abinda yake yi kenan, abun har mamaki yake bawa Inaas koda yaushe baya gajiya da shan nashanunta,hakan yasa kwata-kwata tadena saka bra saboda zafi da nipple din ta suke mata,saide ta zauna babu bra. saide kuma kallo daya zakayi wa nashanunta zaka tabbatar nipples dinta sun sake futowa sosai,haka zaka dinga ganin tsininsu tacikin riga. Yau shiryawa sukai suka fita shan is'ka tun safe,riga da siket ne ajikinta,sai wata hula me malafa da adon fulawa ajikin hular,dogon gashinta yabazu a gadon bayanta,suna cikin jirgin ruwa daga sama a kwance awata doguwar kujera,babu riga ajikin Jawad sai gajeren wando me fad'i,fuskarsa tana sanye da glass jan duhu kamar kullum,wayar Inaas ce a hannunsa yana sake gwada mata wasu abubuwan wanda baya iyaba, yayinda wata hadaddiyar computer take gefe suna kallon photunan bikin su hankalinsu kwance sai nuna mata manyan mutane yake na qasar waje dana cikin gida Nigeria wanda ko kad'an bata sansu ba lokacin bikin,inzai yankata bazatace gawani babba a Nigeria ba Saboda ba'a qasar take ba,yanda suke nishadi suna murmushi ba zakace yayan hausa wa bane musanman idan ka kalli shigar su. Wayar Inaas tafara qara alamun kira yashigo,Jawad yana ganin number Daddy yayi murmushi ya d'an shafa sumar kansa, saboda tunda suka taho babu wanda sukai waya dashi,shi yace P.a yakashe wayoyin sa,wayar Inaas dinma yakashe ta mata ita,cikin kunya yadauka tareda fadin"Daddy barka da safiya,ya Saudia?" "Alhamdulillah kuna lafiya?" "lafiya Alhamdulillah yasu Mummy da Mama?" Daddy yayi murmushi yace"lafiya muna tare dasuma,gasunan ku gaisa" Mummy ta kar6i wayar tace"Jawad ya Qatar din?,ina Inaas?" "Alhamdulillah Mummy,gatanan tana lafiya,ina Fu'ad?" "Fu'ad yana harami munbar shi acan,muma yanzu muka dawo,yacemin wai wata yarinya yagani acikin qawayen Inaas shine zaiyi Addu'ah kafin yafad'a mata yana sonta"(😜) Jawad yayi murmushi,suma daga nasu 6angaren dariya sukayi sannan aka bashi Bilkisu da Man Sulaiman da Abban Inaas suka gaisa,yabawa Inaas wayar itama ta gaida su,tana jin muryar Bilkisu taji hawaye yana shirin zubo mata,Jawad ya girgiza mata kansa,cikin rawar murya me kama da son fashewa da kuka tace"Ammiy ina kewarki,yaushe zaki zo?" Bilkisu tayi murmushi tace"to menene abun kuka kuma? baga yayanki nan atare dake ba?" Cikin shagwa6a tace"Ammiy to ai Yayan kullum kullum...." Cikin sauri Jawad ya zaro idonsa sannan yakashe wayar yace"Asiri zaki tonamin?" Inaas tace"nima wallahi bansan zan fada ba" Dariya maganarta tabashi,ya lakace mata hanci yace"yanzu fisabilillah a wannan abun menene abun zafi? nida nake lalla6a ki ma" Inaas ta kalleshi da sauri tana turo masa baki gaba,ahankali ya matsa yayi kissing kumatunta sannan sukaci gaba da ganin photunan. Saida sukai kusan kwana goma Jawad baiyi mata komai ba,duk wani Salo da yasan zaibi domin yaga ta kwantar da hankalin ta tasake dashi yabi,kuma yaga cigaba sosai,domin kuwa hankalin ta yafara kwanciya sosai,hakan daya gani shine yabashi qwarin gwiwar tunkarar ta da abunda yakeji. da daddare tayi tunanin yanda yasaba shan nashanunta suyi bacci tayi zaton yauma hakane,saide taji yau din da banbanci ta yanda yake abu kamar mayunwacin zaki,lokacin da taji kamar yana karanta addu'ar saduwa da iyali fashewa tayi da kuka,Shima a nasa 6angaren kukan yasaka mata,domin kuwa maqurar haquri yayi haquri,ayau d'in jinsa yake idan beyi ba to zai iya Samun matsala,hakan yasa yaci gaba da sha'anin sa,dad'in daya fara ji lokacin dayake qoqarin shigar ta shine yasa baisan lokacin daya kaiwa gadon wani irin duka ba yana sakin wata irin qara, yasha wahala sosai kafin yasamu ya kutsa kansa ciki,yana fara shiga daya fara jinsa cikin qoramar ta, yasaki wani irin qara tareda kuka yana surutu kan gari. Inaas ta dinga doke-doke tana tureshi amma Jawad ko gezau,saima hannunta daya riqe yaci gaba da fafatawa,Inaas kuka harda majina,babu wanda bata kiraba a gidansu,tajiqe fillon datake kai jagab da hawaye. Tsawon lokaci ya dauka yana abu daya,sannan ya kawo,daga nan yakoma gefe guda yana maida numfashi,saide har yanzu abunsa yana nan yanda yake,babu alamar rissinawa.(🙈) Inaas tasha kuka ta qoshi,murya harta dashe, ahankali yajata jikinsa yana bubbuga bayanta,cikin wata irin murya yace"kiyi haquri,bafa duka nashiga ba" Inaas tanajin haka tasake fashewa da kuka tace"Yaya dan Allah karka kasheni,dan Allah ka maidani wajan Ammiy,nina haqura da auren"(🙆🏻‍♀️) Saida yagama sauke numfashi sannan yakamo hannunta yadora acan qasan mararsa yace"ya kikeso nayi da wannan abun? um? kinaso na mutu?" Cikin sauri ta girgiza masa kanta,ahankali wasu hawaye masu zafi suka zubo daga idonsa,tanajin yanda hawayen sa yake sauka akan tata fuskar,cikin muryar kuka yace"Love kinada dadi sosai,dan Allah kibari na qara,wallahi yanda nakeji zan'iya mutuwa" Cikin tashin hankali tafara girgiza masa kanta alamun rashin yarda,cikin wani irin kuka yace"Plaese" Bai bata damar sake magana ba yahade bakinsu waje d'aya,yayinda hannunsa yake kan nashanunta yana musu matsar kayan wanki. wannan Karon Kam yanda yakeji yasa yacire tausayi yashiga gaba daya kansa tsaye,lokacin daya yaji shi acan ciki yanda yakeso, wani irin ihu suka saki atare,Inaas tana sakin wannan ihun bata sake sanin inda kanta yake ba ta sume,yayinda Jawad yake ihun dadi yana dukan gado,banda su kadai ne agidan babu abinda zai hana kowa yaji su,sosai yake ihun kuka yana dukan katifa kamar mahaukaci,saida ya raba dare yana abu daya sannan yasaki wani irin ihun kuka harda shashsheka ya rungume ta tsam ajikinsa batare daya zare jikinsa daga nata ba,saida ya nutsu yaji yadawo hayyacinsa sannan yazare jikinsa daga nata yaga komai ya rissina yakoma yanda yake(🙈) Ya kalli jikinta sai alokacin yaga yanda gefen cinyoyinta da nashi suka 6aci da jini. Gabansa yayi wata irin fad'uwa,kansa ya sara,cikin sauri yaduba ta,sai alokacin yaga bata motsi,cikin tashin hankali yadafe goshinsa da hannunsa, sannan ya dauketa suka shige toilet,saida tajita acikin ruwan d'umi sannan yafarka idonta yana tsiyayar da hawaye saboda murya ta riga ta dashe babu damar kuka, Koda tayi kukan ma toba sauti. Kokadan batason kallonsa,hakan yasa kallo daya tayi masa ta lumshe idonta tana tuna irin azabar da tasha a wajansa. Saida yayi mata wanka sannan shima yayi har lokacin idonta a rufe,dauko ta yayi suka fice daga dakin yakaita dakinta ya kwantar da'ita sannan yadawo yagyara wajanda suka 6ata, yakoma dakin datake. Zama yayi akusa da'ita yashafa fuskarta da idonta yake lumshe,yadora fuskarsa akan tata yace"I'm sorry Love" Tana jinsa bata bude ido ta ganshi ba,sai hawaye daya zubo daga idonta. Cikin tashin hankali ya runtse idonsa,yasauko daga kan gadon yayi kneel down yace"kiyi haquri ki yafe min kinji,wallahi banida nutsuwar dazan iya haqura dake,kin riga kingama dani,kiyimin uzuri saboda bazan iya haquri dake ba" Duk maganganun dayake tanajin sa bata bude idonta ba saide tana sauke ajiyar zuciya ahankali. Wayarta ya dauka yakira P.a Cikin tashin hankali P.a ya dauki waya saboda ganin kiran waya da layin matar Yalla6ai kuma kiran ma cikin dare. Jawad yanaji p.a yadaga yace"P.a" cikin girmamawa P.a yace"na'am Yalla6ai" Jawad ya d'an runtse idonsa kamar bayason magana sannan ya motsa lips dinsa yace"P.a ina buqatar Doctor" P.a yasaki murmushi a 6oye sannan yace"ok Yalla6ai" Yakashe wayar yafara qaqarin kiran Doctor. Jawad ya futo daga dakin yadawo falo yana zagaye falon cikin tashin hankali,tunda yaga wannan jinin dayawa hankalinsa yakasa kwanciya. Saida Doctor tashigo sannan hankalinsa ya kwanta yakuma jinjina wa aikin P.a da alama ya fahimci abinda yafaru. Cikin dakin yayi mata jagora yanuna mata Inaas sannan ya futo yabar su,likitan ce tasake sakata acikin ruwan d'umi ta dade aciki, sannan tabata magani tasha, cikin nutsuwa tafara yimata dinki,sosai ta tausayawa Inaas din,saide kuma duba da yanda taga Yalla6ai din tasan cewa dama dole yarinyar zata d'and'ana kud'arta,saboda shi din ba namiji ne kamar kowa ba. Saida tagama yimata dinki tsaf,sannan takira shi,cikin girmamawa tayi masa bayanin cewa yabarta tahuta zuwa sati daya kafin yasake nemanta,zuwa lokacin ya dinga sakata acikin ruwan d'umi har wajan data mata dinkin ya warke. Cikin girmamawa shima yamata godia, yafada mata cewa P.a zai sallameta. Kan gadon yahawo ya rungume ta adede lokacin,time din kiran sallar farko yayi,yanajin yanda jikinta yayi zafi sosai alamun zazza6i,cikin kunnanta yafara yimata rada yace"kiyi haquri,Yaya ya6ata miki rai ko?" Babu 6oye-6oye cikin sauri ta gyada masa kanta,yayinda hawaye ya silalo daga idonta. Yasaka hannu ya goge mata hawayen sannan yayi kissing fuskarta yace"na daina,bazan sake ba kinji?" Ahankali ta gyada masa kanta,yayi murmushi yace"kinsan me?" Ta girgiza masa kanta,ya d'ora bakinsa akan kunnanta yace"infada?" Tasake gyada masa kai. Yayi murmushi yace"kinada dad'i sosai,wallahi kamar na mutu dan dad'i haka naji,Allah bansan inda kaina yake ba" Cikin sauri takai masa duka a qirjinsa,yasaki dariya, ya rungume ta yana shafa dogon gashinta,ahankali wani irin baccin wahala ya dauketa. Sai alokacin yasaki wata irin wawiyar ajiyar zuciya,ya kwantar da ita, sannan yashiga toilet yayi alwala yazo yatada kabbarar sallah. Tundaga wannan ranar Jawad bai sake neman Inaas ba kamar yanda likita tafada masa,bayan kwana biyu P.a yasake turo likitan,hakan ba qaramin dadi yayiwa Jawad ba,yakuma qudurta aransa cewa dole za'a yiwa P.a qarin Albashi.(🤭) Sosai likitan tasake duba Inaas ta kuma basu shawarwari sannan tatafi,daga 6angaren Inaas hakan ba qaramin dad'i yamata ba,domin kuwa ruwan d'umin datake shiga yasa taji wajan yafara warke wa,amma bata nuna masa hakan ba,Jawad kuwa tunda ya d'and'ana yaji yanda take da mugun dad'i,hakan yasa kwana biyun da baiyi ba yakejinsa atakure. Babu inda yake rage zafi sai waje d'aya,shine idan yanashan nashanunta,idan yafara sha yadora ita kuma ya dora mata hannunta acan qasan mararsa tana masa wasa hakan ne yake sa yaji yad'an samu nutsuwa shima ba kamar yanda yasoba. Kwanansu biyar a wannan halin,zuwa yanzu Inaas hartana tunanin gara ma tafada masa gaskiya ta warke,saboda gaba daya kan nononta wani irin zafi suke mata,idan yafara sha tun tanajin dadi tana lumshe ido harsai ta dawo tana runtse idonta,Jawad baya wasa da wannan 6angaren tarasa meyasa?🤔 Washegari Kwanansu shida dayin first night dinsu,aranar ne kuma suka kar6i baquncin mutanan Saudia. Daddy,Yaya Mariya,Mummy,Bilkisu,Man Sulaiman,Abban Inaas,dakuma Fu'ad. Inaas tana ganinsu tafashe da kuka,Bilkisu tagoge qwallar idonta tace"kukan menene to? bagamu munzo ba?" Jawad yayi murmushi ya shafa sumar kansa yace"kukan shagwa6a nefa Mama" Inaas ta kalleshi ta sakar masa wata irin hararar shagwa6a. Cikin jin dadin yanda taga Inaas din ta sauya tayi Shar da'ita Bilkisu tace"gaskiya yafad'a mana" Inaas ta goge hawayen idonta ta tsugunna ta gaida iyayen nata maza,kowa ya amsa mata cikin farincikin yanda suka ganta kalau da'ita da alama amarcin ya kar6eta. Inaas takoma kusa da Ammiy tace"Ammiy muje kiga dakina" Bilkisu ta miqe suka tafi dakin Inaas,saboda itama so take su ke6e ta tambaye ta taji ko akwai damuwa? domin kuwa wannan kukan data taresu dashi ya tsaya mata arai. Suna shiga daki kuwa Inaas tajata suka zauna agefen gado Sannan ta rungume ta, tasake tafashewa dawani irin kuka,Bilkisu tafara lallashin ta tace"ya'isa, fadamin meyake damunki Inaas? menene matsalar?,naga jikinki bai nuna kina cikin damuwa ba,meyake faruwa?" Cikin kuka Inaas ta fara qoqarin d'age rigar ta sama,zata nunawa Bilkisu nashanunta. (🙈🤭🙊🙆🏻‍♀️) Mummy da Yaya Mariya dasuka shigo dakin cikin sauri Mummy tace"nashiga uku karki bude,karki bude" Inaas ta kallesu da fuskarta sha6e-sha6e da hawaye tace"Ammiy zafi sukemin,wajan yayi ja,Allah Ammiy wuni Yaya yake yanasha" Yaya Mariya ta zauna tace"kai wannan masifa dayawa take,zamani kenan,mazan yanzu 'yan zamani babu abinda suka bari,komai najikin mace sai sun moreshi tsaf,inba hakaba mu lokacin mu ina mukasan wannan jarabar kaiba jinjiri masha nono ba? saikiyi haquri ai, be'isa yaye bane aka yayeshi, idan kin lura wani lokacin aiba miskilanci ne kad'ai yake damun saba,bayan miskilanci harda rashin wayo atare dashi,saboda baisha nonon uwarsa ya qoshi ba, shiyasa gashinan abun tausayi duk sauran abokan sa sun fishi wayo da surutu,saboda haka kibashi abinda yakeso shine gatan da zaki masa, yaron dabe sha Nonon uwarsa ya qoshi ba ina yasamu wani gata? tunda abun jaraba ce kibarshi yasha yasamu kuzari"(😂) Cikin sauri Inaas da Bilkisu da Mummy suka kalli Yaya Mariya,ganin ko kad'an ba taga laifin Jawad dinba,ita akoda yaushe Jawad baya laifi a wajanta. Bilkisu tasake kallonta da kyau tace"haba Yaya saikace wani jariri?" Yaya Mariya tamiqe tsaye tace"tome maraba?" (Yaya Mariya tace a bashi yasha yasamu kuzari 😂😂😂wannan tsohuwar bataji) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍ [1/21, 13:10] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta min littafi baki biyaba to ban yafe ba keda Allah. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 31&32 Ammiy ta lumshe idonta,cikin ranta tace gaado ba karambani ba,tasaki ajiyar zuciya tabude idonta, sannan ta girgiza kanta cikin kulawa ta kalli Inaas tace"kiyi haquri kinji?" Tana fadin haka tatashi tafice daga d'akin. Bayan Ammiy ta fita,Mummy tasaki ajiyar zuciya sannan ta riqe hannayen Inaas,tace"wakika fadawa wannan maganar bayan mu?" Inaas ta share sauran hawayen idonta tace"Babu kowa Mummy,babu wanda yake zuwa" "toko wasu sunzo karki sake fada musu sirrin mijinki kinji? Jawad yana sonki Inaas,cikin lallami zaki dinga tunatar dashi cewa kefa abinnan kina cutuwa,nasan cewa kobe dena dukaba to zai rage,kuma karki yarda ki nuna masa gajiyawarki a Shimfida,idan baizo wajanki ba wajan wa zaije? kiyi haquri nan d'an wani lokaci zakiji komai yawuce, kinji?" Ta qarasa maganar cikin sigar lallashi. Inaas tace"to Mummy" Daga nan suka futo daga dakin,a kitchen ta hango Bilkisu,hakan yasa tatafi wajanta suka yi sauri suka shirya abinci me dan ruwa-ruwa, suka kawo falon kowa yafaraci ciki harda su Daddy. Jawad idonsa akan Inaas,wannan yan minutes din dayayi baiji ta ajikinsa ba sai yake jinsa a takure,har tunani yake to idan yakoma aiki yaya za'a yi kenan? Hada ido sukai shida Mummy, ta kamashi yana kallon Inaas din,cikin kunya yadauke kansa tareda shafa sumar kansa,yajuya ya kalli Fu'ad yace"Ya zancen yarinyar?" Fu'ad ya ajiye cup din lemon dake hannunsa yace"tahadu Yaya,ba qarya kyakykywa ce,dan tafi wannan yarinyar haduwa" Ya qarasa maganar yana nuna Inaas. Inaas ta dago kanta ta kalleshi sannan tayi masa harara taci gaba da cin abincin ta. Yaya Mariya tace"to ba haduwar bade,kyawun hali" Fu'ad yace"aaaaa Hajiya Mama ai wannan ta dade da wuce wajan,idan kikaga yanda take gaida manya kamar zata musu sujjada abun sai wanda yagani" Mummy ta dauki fillon kujera ta jefa masa tace"to rasa kunya" Daddy yayi murmushi,Man Sulaiman yace"Allah yasa adace Fu'ad" Haka suka dinga fira gaba dayansu,kowa fuskarsa dauke da farinciki har kusan awa biyu da rabi sannan suka fara shirin tafiya,dama transit din awa uku suka samu,idon Inaas yayi qwalqwal kamar zatayi kuka, hannunta cikin na Ammiy suke tafiya ahankali zuwa wajan motoci,Ammiy tayi qasa da murya tace"kidinga haquri kinji?" Inaas tace"to Ammiy, kuma yaushe zaku dawo?" "Inaas inde zamuzo saide kawai ki ganmu,yanzu ma ai kinga bakisan zamu zo ba,to ki kwantar da hankalin ki nafiso idan zamu dawo naganki kin sake qiba kinyi 6ul6ul abinki,Abban ki yafara shirin aure,ki masa Addu'ah, zai auri qanwar mijin Yaya Mariya" Wannan maganar itace tasa ran Inaas yayi fari,cikin farinciki tace"to zan masa Ammiy,Allah yabasu Zaman lafiya" "Amin ya Allah Inaas,toki koma ciki" Inaas ta qarasa wajan Abban ta ta masa sallama, Shima yayi mata fad'an da ba'a rasa ba sannan takoma jikin motar ta tsaya wajan Ammiy. Mummy kuwa kunnan Jawad ta riqe sannan taja shi gefe tace"Jawad kabi yarinyar nan ahankali,banason sake jin wata matsalar please" Jawad daya runtse idonsa yadora hannunsa akan kunnan data riqe masa,wata irin kunya ta kamashi,yasan cewa Inaas tafada musu komai,saide yana fatan ace Ammiy bataji ba, ahankali yace"ok Mummy" Daga nan sukai musu sallama suka tafi,har suka fice daga gidan Inaas bata daina yimusu bye bye ba. Yayi ajiyar zuciya yajuyo ya kalleta,sannan yasa hannu ya dauketa cak,har cikin d'akin sa,rigar wanka yabata tasaka tana turo baki cikin shagwa6a,rigar tayi mata masifar kyau saboda launin baqa ce,farar fatar jikinta tasake haskawa sosai aciki,gaba daya cinyoyinta awaje suke,daga kan qasanta ne zuwa qirjinta rigar ta tsaya,shi kam wani d'an qaramin wando ne ajikinsa ya kamashi sosai bashida da banbanci da pant din maza. Daukarta yayi, yayinda ta saqalo hannun ta tabayan wuyansa,ta 6oye fuskarta cikin qirjinsa. Har suka shiga cikin ruwan bata dago kanta ta kalleshi ba,acikin ruwan ya nutsa su gaba daya hakan yasa tadago kanta da sauri,yasaki wani irin murmushi ganin yanda dogon gashinta ya jiqe saita qara yimasa kyau sosai. Ya rungume ta ajikinsa yace"shine kika had'a min taron dangi ko? thanks God danma Ammiy bataji ba" Inaas ta kalli faffad'an qirjinsa tace"inji wa? bud'e mata ma nayi niyyar yi" Jawad ya runtse idonsa yace"innalillah...Love kin kashe ni,shiyasa naga tanamin wani kallo haka harara-harara,amma Hajiya Mama bata nunamin komai ba" Inaas tace"ai ita baka laifi awajanka" Jawad yasaki ajiyar zuciya yajata jikinsa suka sake shigewa cikin ruwa sannan yace"Tana sona sosai matar" Ya qarasa maganar yana damqar nashanunta,sosai taji zafi hakan yasa takai hannunta kan nasa hannun ta janye masa hannunsa cikin shagwa6a tace"Yaya da zafifa" Cikin muryar rad'a yace"kin cika rowa love,bakya barina ina ta6awa,shiyasa suke miki ciwo" Wani d'an qaramin hawaye ne yazubo mata,cikin rawar murya tace"ba ina baka ba" Jawad ya kalleta yadora harshansa akan kumatunta ya lashe hawayen,cikin shaqaqqiyar murya yace"ni yamin kad'an,alhaki nane yasa yake miki ciwon" Cikin shagwa6a tace"to bada zafi kake ta6awa ba..." Cikin ruwa yasake maida su,yadora ta akan jikinsa sannan yadora harshansa akan kunnanta yace"meyasa bazaki na dakatar dani ba?" Cikin sauri tace"naga har dukan...." Kafin tagama cewa duka, yahade bakinsu,saide baiyi mata komai ba,da idonsa yayi alama akan tayi komai,hakan yasa ta lumshe idonta tafara tsotsar lips dinsa ahankali,Jawad yaji wani masifaffan dad'i,hakan yasa yasaki wani irin numfashi, yasa hannunsa yaciro duka nashanunta ya futo dasu waje yana wasa dasu ahankali yanda ba zataji zafi ba, hakan kuwa ba qaramin dad'i yamata ba,domin kuwa batasan lokacin dataci gaba kissing dinsa ba cikin wani irin salo wanda ita kanta batasan cewa ta'iya ba. Idon Jawad yayi wani irin ja,wanda hakan yasa Inaas taji wani irin tausayin sa. Cikin sanyin jiki yazare bakinsa daga nata,yamaida shi kan nashanunta yana sha ahankali,ya d'an d'ago idonsa ya kalleta yaga ta lumshe ido,ahankali yacire bakinsa sannan yamaida shi kan kunnan ta cikin rad'a yace"haka kikeso na dinga yimiki?" Cikin jin dadi ta gyada masa kanta da sauri. Shima lips dinsa ya d'an motsa kad'an,sannan yamaida kansa wajan yaci gaba da abinda yake. Sun dade acikin ruwan,saida suka gama wasan su sannan sukaita wasan watso ruwa ya watso mata itama ta watso masa,sai ga Inaas ta ware tanata dariya,daga baya suka fice suka koma ciki. Da daddare ma hakan ce ta kasance,saide ya sauya salon komai kamar yanda Mummy tayi masa kashedi,ahankali yake bin komai ba kamar baya ba yana abu kamar yana tsoro zata gudu ta barshi. Yanda take jin dadin wasan nasa hakan yasa batama san lokacin daya shige ta ba,kawai jinsa tayi acikin jikinta, ta runtse idonta saboda zafi. Duk da cikin nutsuwa yake yi yau,hakan bai hana taji zafi sosai ba,ko kad'an bataji banbancin sa dana farko ba,kawai de na farko yanayin komai ne da zafi-zafi, yanzu kuma yana yi cikin nutsuwa a hankali,tanajin yanda yake ihun dad'i yana dukan katifa,banda hawayen sa daya jiqe mata fuska,babu irin alqawarin da baiyi mata ba,. Itade idonta a runtse yake tana ta yatsina fuska babu wani dad'i datake ji,yayinda shikuma yake jin kamar baya cikin duniyar,musanman yau da batayi wani hargagi nason qwace wa ba,ta tsaya ta barshi yayi abunsa yanda ransa yakeso. Ya dade yana abu daya,kafin yaji nutsuwa ajikinsa,numfashi yaketa saukewa ajere, sannan ya raba jikinsa da nata yakoma gefe fuskarsa cikeda murmushi saide har lokacin idonsa a lumshe suke,saida yaji nutsuwa sosai sannan ya kunna wutar dakin yabude qafafun Inaas yaduba wajan yaga baiji mata ciwo ba,yayi wata irin ajiyar zuciya sannan ya rungume ta yana kissing ko'ina na jikinta. Bai sake maimaita wa ba sai bayan sallar asuba,haka shima ta daure bata nuna masa taji zafi sosai ba. Daga nan suka fara bacci musanman ita baccin gajiya yayi gaba da'ita me masifar nauyi. Satin su biyu suna murzar juna,tun Inaas tana tunanin zai d'an d'aga mata qafa yana tsallaken rana harta daina tasa aranta kullum ne saiyayi kuma ba sau daya ba. Har zuwa lokacin Jawad bai koma aiki ba,p.a ne yake yin komai,saida sukai sati hudu cif sannan ne yafara shirin komawa bakin aiki,adede lokacin kuma da daddare suna kwance tana jikinsa suna kallo Daddy yakira waya,bayan sun gaisa Daddy yace"Jawad ya kamata ka maida Inaas makaranta fa,tunda kuna tare kamar yanzu ne zakaga har karatun nata yayi nisa" Jawad ya d'an runtse idonsa yace"to Daddy za'a nemo mata" Bayan yakashe wayar Inaas ta kalli yanda ya6ata fuska,tasan cewa kawai ya amsawa Daddy ne, amma kokadan bayason tayi karatu tarasa meyasa bayaso, tayi ajiyar zuciya tasake rungume shi sannan takai hannunta cikin lallashi tafara shafa kyakykywan sajensa tace"menene abun damuwar bayan kariga ka mallakeni? kariga kazama ni nazama kai,mun zama abu guda,bana tunanin zan iya hulda da kowa sai wanda ka amince min tukunna,kayi haquri mana Yaya" Jawad yana jinta yayi shiru kamar baiji me tace ba,yasaka hannu ya janye mata hannunta daga kan sajensa. Inaas tasake yin ajiyar zuciya ganin har yanzu be sauko ba,cikin dabara tadora hannunta daya akan Qasan marar sa ta d'an matsa masa shi a hankali yanda saqon zaije masa,sannan ta saqalo kafadarsa da d'aya hannun nata,idonta cikin nasa taci gaba da matsa masa qasan marar tasa,Jawad ya lumshe idonsa cikin jin dadi,ahankali yasake bude mata cinyoyin nasa(🙈) Inaas tayi murmushi ganin saqon datake turawa yafara kar6uwa, Sannan ta matsa tayi kissing fuskarsa, cikin kissar tausasa harshe tace"Babu ni babu hulda da kowanne irin namiji,ni taka ce kai kadai,dukkan abinda na mallaka naka ne Yaya,kadena tsoron wani abu akan karatun nan,Yaya kana faranta min,kamin abubuwa dayawa najin dadin rayuwa,banida damuwar komai, dan haka shima karatun bazanji komai ba idan ka hanani,saide ma inyiwa Allah godia bisa ni'imomin dayamin ciki harda na mallaka min kai dayayi amatsayin mijina...." Jawad yasaki ajiyar zuciya yanajin yanda kalaman nata suka ratsa shi kuma suka sa hankalinsa ya kwanta,hannunta dayake kan qasan mararsa ya dauke yariqo hannun ya tura mata shi can cikin wandon sa yanda zaiji yanda yakeso(🙈) Inaas tayi murmushi tana kallonsa,rungume ta yayi cikin sigar rad'a yace"amma ai baki ta6a cemin ina jiyar dake dad'i ba sai yanzu dayake kinason karatu ko? Love baki rasa komai ba,kina dani,har jikokin mu bana tunanin zasu kasa jin dadin rayuwa kamar mu,babu abinda zance wa Allah sai godia saboda bayan kudin Daddy nikaina bansan adadin abunda na mallaka ba" Inaas tayi murmushi tayi kissing faffadan qirjinsa sannan tace"to yau Nafad'a ma Yaya,kana jiyar dani dad'i sosai,kaidin jarumi ne fiyeda sauran mazan duniya,ka'iya aiki sosai,babu macen da bazatai fatan kazamo mijinta ba,saide nariga nayi musu nisa,ni kadai zaka dinga yiwa aikina cikin dare da duk lokacin danaso,kuma karatu Yaya ai saide inyi dan korar jahilci,sannan kuma saboda yaranmu" Jawad yayi mata wani irin kallo yace"yarinyar nan dama kin iya wadannan kalaman amma shine bakya min?" Inaas ta rufe fuskarsa acikin jikinsa cikin wata irin kunya,tana son karatu sosai,dole zatayi yanda zatayi domin ta shawo kansa ya amince da batun karatun,har yanzu bata jin dad'i idan suna mu'amula,saide tanajin dad'i sosai idan suna wasa,ita kanta tasan cewa kawai zigashi tayi dan yaji dadi, kuma gashinan ta d'ana tarkon ta ya kama, domin kuwa yaji dadin yanda take yabonsa akan shi din jarumi ne ko a Shimfida. Tayi murmushi tace"bahaka bane yaya" Cikin jin dadin saqon dayake kar6a acikin hannunta tacan qasa yace"to tunda kin tabbatar ina miki aiki kema yau saiki nunamin naki aikin" Inaas ta kalleshi cikin shagwa6a tace"to Yaya ka amince da karatun?" Kallonta yayi da idonsa dasuka fara sauya launi yace"ya zanyi? tunda kinaso har master's zakiyi insha Allah, but banson Yayan nan,daga Yalla6ai kindawo Yaya,please inaso shima Yayan nan acireshi" Cikin jin dadi Inaas ta rungume shi tasakar masa kiss sannan tace"thank you Qauna" Jawad yayi murmushi bayan yaji sunan data sauya masa, sannan ya zuba mata ido yana kallonta,hakan yasa tagane cewa jiranta yake,cikin kunya tafara yimasa duk abinda tasan cewa yana so,sosai yake jin dadin yanda take masa komai,yasakar mata jikinsa yabata ragamar komai, banda numfashi babu abinda yake saki, saida tafiya tayi nisa sosai sannan shikuma yaci gaba dayin komai cikin sauri-sauri. Bai nema mata makarantar ba saida sukai wata uku cif a Qatar,zuwa lokacin jikinsu ya murje,amarci ya kar6esu,sunyi wani fresh dasu kamar basu ba. Qarfi da yaji Jawad yasa Inaas ta zama 'yar hannu,sosai takejin dadin abun yanda ya kamata,acikin wata ukunnan idan be nemeta bama ita da kanta zata lalla6o sai sunyi sannan zataji dadi, yariga yayi mata wannan horon,tasake yin qiba tayi kyau sosai,kusan wata biyu kenan rabon datayi period,sau d'aya tayi tunda sukazo qasar, ko kad'an Jawad bai sani ba,yama manta da batun period saboda dad'in dayake kwasa,kullum sake qara dadi take hakan yasa yakeji da'ita kamar ya lashe ta,yana jin dadin yanda take so suyi abun,sosai suke murzar juna shi da ita, wannan sauyin dayake ji ajikinta hakan yasa ya mantar dashi komai,ko tunanin tana period ko batayi ba yayi kwata-kwata,dad'in sa kawai yake kwasa. Daga nata 6angaren dabata gani ba tafara shiga damuwa, hakan yasa tahau internet tayi search anan taga bayanin da yasa gabanta yafadi,wato ciki,to amma datayi tunanin ance masu ciki suna laulayi kokuma jinya kuma ita babu d'aya wanda tayi sai zazza6i kad'an shima idan tasha paracetamol sai taji ta ras, kuma ba taga cikinta ya futo yayi qato ba kamar na masu ciki, saide kwad'ayi datake yi,tarage cin abinci saide kayan maqulashe,saita wuni tana ciye-ciye kuma ba abinci ba kawai tarkace, hakanne yasa hankalin ta ya kwanta bata dauki hakan amatsayin ciki ba, uwa uba a bayanin data gani a goggle sunce mace tana iya tsallaken wata batayi period ba, hakan yasa hankalin ta ya kwanta,tadena tunanin komai. Tafara zuwa makaranta cikin kwanciyar hankali,kullum sai sun sauketa a makaranta shida sauran guard dinsa sannan su wuce wajan aiki,idan tagama lactures dinta zai turo mota amaida ta gida. Bayan wata hudu sukai exam din first semester,adede lokacin yakama watansu bakwai a qasar,ranar dasuka gama exam din tayi photuna da qawayenta sosai,sannan tayi masa waya yaturo akazo aka dauketa aka kaita gida. Kwanciya tayi akan doguwar kujera bayan tacire kayan jikinta,ta dauki apple tanaci,photunan nasu take kalla,wani photo da'aka mata ita kadai tad'an dage laffayar jikinta shine yasa tatashi zaune dawani irin sauri,gabanta yana fad'uwa,cikinta ne taga yaqara girma sosai ya kumbura duk da acikin photo ne ana iya ganinsa,jefar da wayar tayi,sannan tatashi zaune tabude cikinta tazuba masa ido taga ciki de gashinan ya kumbura,yanzu yafi acikin photon futowa saboda acikin photo ta daure cikin da laffaya,tsananin mamaki ya kamata,a fili tace" ha'a to meyake faruwa ne? what's wrong with me?" Tasa hannunta akan cikin ta d'an daki cikin kad'an tana so ta tantance kumbura tayi kokuma me? yaushe har cikinta yazama haka bata lura ba? metake tunani? har wanne irin karatu ne zaisa takasa gane yanayin jikinta? tasake dukan cikin nata akaro na biyu taji wani irin abu acikinta zil-zil kamar motsin maciji,lokaci daya ta dora hannunta akanta ta fashe dawani irin kuka. Adede lokacin Jawad yashigo gidan,cikin sauri ya qarasa wajanta, cikeda tashin hankali yace"love menene?" Cikin sheshshekar kuka tace"Yaya cikina,sai kumbura yake,idan na daki cikin saina dinga jin kamar maciji ne acikina" Gaban Jawad yayi wata irin mummunar fad'uwa yazaro idonsa waje yace"innalillahi Snake"(😳) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/22, 15:46] My Number: Cikin kuka ta gyad'a masa kanta tana kallonsa. Jawad yayi sauri yabude cikin nata sosai,lokaci d'aya shima gabansa yafad'i,da sauri yakai hannunsa kan cikin sannan yadago kansa ya kalleta tace"kinga don't cry,ya'isa tashi muje asbiti" Cikin kuka tatashi tasake daura laffayar jikinta sannan suka fice cikin tashin hankali. Har sukaje asbitin bata daina kuka ba,bayan sun fadi matsalar datake damunta kai tsaye scanning aka mata,lokaci daya saiga Baby,Jawad ya zaro idonsa yana gani,sannan yajuya yana kallon likita da mamaki, itama Inaas anata 6angaren cikin sauri tafara qoqarin tashi daga kan gadon. Jawad ya rufe fuskarsa da hannunsa yana yiwa Allah godia,likita ta kalleshi tace" She's a Baby girl" Jawad ya janye hannunsa daga kan fuskarsa,Inaas taga hawaye a kwance a fuskarsa, abun yasake bata mamaki, tasa hannu tafara share masa hawayen. Likita ta basu shawarwari akan kada ta dinga yawan aiki sosai,ta kuma bata wasu magungunan wanda zasu taimaka mata ita da Babyn ta. Ahanya yana driving hannunsa yana kan cikinta yana shafa wa,suna zuwa gida kuwa ya dauketa suka shige ciki,akan gado ya kwantar da'ita, sannan yawuce toilet ya dauro alwala yazo ya gabatar da sallah raka'ah biyu, yayiwa ubangiji kirari,yayi musu Addu'ah akan Zaman aurensu,sannan yayi mata Addu'ah ita kadai,akan Allah ya sauketa lafiya, ya shafa Addu'ah yadawo kan gadon ya zauna yajata ya d'orata akan cinyarsa,yayi kissing goshin ta hawaye sabo yana sake zubowa daga idonsa. Inaas tasa hannunta tadago fuskarsa sannan tasa bakinta ta shanye hawayen tas yanda taga yanayi mata shima,cikin sigar lallashi tace"Qauna ...kukafa kake tun a asbitin nan" Kallonta yayi cikin farinciki yace"Allah yayi miki Albarka Love kinmin komai,kinbani komai,yanzu nanda wata uku zuwa hudu munzama mu uku" Inaas tayi murmushi,tace"hakane,Allah yakawo ta lafiya" "kinga yanzu kunyi hutu,to babu batun aiki,kibi duk do kokin da'aka gindaya mana" Inaas tagyada masa kanta tana kallonsa da murmushi a fuskarta,tasaka hannunta cikin sumar kansa ta dinga shafawa,jin dadin hakan yasa yashige cikin jikinta duk da tana kan cinyarsa ne,fuskarsa yafara goga mata a wuyanta,Inaas ta lumshe idonta tanajin yanda yake busa mata iskar numfashi akan wuyanta,daga nan ya gangaro zuwa ga abinda yafi so,yacire laffayar tata, sannan yayi sama da rigar ta,yadora bakinsa akan nashanunta yafara zuqa ahankali,atare suka saki wani irin numfashi, Inaas tasake rungume kanshi tayi luf acikin qirjinsa. Daga nan labari ya sauya Salo,farinciki Samun Baby yasake samarda wani farincikin a gangar jiki da zuciyar su,saida sukayi kusan round uku, sannan suka haqura. sai kiran wayoyin sa ake amma shiru kakeji baisani ba, kasancewar suna silent. Da daddare suna zaune afalo akan doguwar kujera qafafunta suna kan cinyarsa yana matsa mata su, yayinda hankalinsu yake kan labaran da'ake karantawa,hannunta yana riqe da cup cikeda fruit salat. Daya daga cikin Wayoyinsa tafara Haske alamun kira yashigo,yaduba da sauri yaga abokin aikinsa ne,sun dade suna waya sannan yakashe ya dinga bin missed call din d'aya bayan d'aya yana kiransu, daga nan yakashe wayar baki daya,yadauki wata wayar daban yakira Bilkisu. Bugu uku ta dauka tace"Jawad" Cikin farinciki da kulawa yace"na'am Mama,Albishirinki" Inaas tanajin haka tazaro idonta sannan tafara yimasa alama yayi shiru karya fad'a,Jawad yayi mata wani irin kallo sannan yace"Mama nanda wata uku...." Saiyayi shiru. Bilkisu tace" meyafaru fadamin,me za'ai nanda wata ukun?" Jawad yayi murmushi yace"zaki zama kaka" Bilkisu ta lumshe idonta cikin farinciki,kasancewar babbar waya ce a wajanta yanzu,kana iya jiyo abinda ake fada, hakan yasa cikin sauri Hajiya Zaliha datake zaune agefenta ta qwace wayar tace"Jawad menake ji haka?" Jawad ya d'an sosa kansa kad'an,sannan yace"Mummy kin kusa samun jika,nanda 3 months" Cikin farinciki Mummy tace"Jawad tome kuke jira? kakawo ta gida ta haihu mana" Gabansa yafad'i,cikin sauri yace"But Mummy she's fine fa" Cikin muryar rashin wasa Mummy tace"Jawad,bazai iyu fa yanda kake shekara bakazo gida ba itama kace haka zaka mata,dole zaka bar yarinya tazo gida" "to Mummy karatu fa take,kune kukace nasata a makaranta,idan tagama karatun nanda 4 years sai tazo gidan" Mummy tace"dama take takenka Kenan? to karna sakejin wannan maganar,dazu da safennan Fu'ad yanuna min picture's din data turo masa sun gama first semester,tunda hutu suke yanzu kakawo min yarinya ta haihu agida kaji Nafada ma" Cikin 6acin rai yace"ok Mummy" Sannan yakashe wayar ya kalli Inaas yace"Kinji wata sabuwa kuma" Yana fadar hakan yakoma cikin kujera ya runtse idonsa cikeda damuwa. Inaas ta sauke qafafunta daga kan cinyarsa, ta matsa ta rungume ta tafara lallashin sa,daga wannan lallashi kid'an ya sauya salo,rawar ta sauya,shida yake mita yana complain baison kawo ta gida sai gashi shine yadawo yana ihun dad'i saboda yanda take tafiyar dashi cikin wani irin salo wanda baisan inda takoyi hakan ba. Sosai yake bata kulawa tunda suka gano cewa tanada ciki,har yanzu batacin abinci sosai saide kayan qwalam,kullum sai Yaya Mariya takira su taji lafiyar Inaas din,itace take hanata yawan shan zaqi dakuma abubuwa masu sanyi kamar ice-cream,Jawad baya barin ta tayi komai idan wani abu take buqata saide yayi musu order kawai,bai sake bi takan maganar dawowar ta gida ba,haka itama Mummy ta zuba masa ido tana so taga gudun ruwansa. 6angaren aurataiyarsu babu abinda ya canza, saima naci da Jawad din yasake qarawa babu ranar dayake iya haquri ya d'aga mata qafa,kasancewar itama ta zama yar hannu hakan ba qaramin dadi yake mata ba,sai yanzu nema takejin tsantsar dadin,abaya duk haukan ta take,kullum suna manne da juna,basu da wani lokaci ke6a66e wanda basa wannan abun saide in baya gida. Saida cikinta yacika wata bakwai sannan Daddy yayi masa waya akan yazo zaije tareda su Man Sulaiman a nemawa Fu'ad da P.a dinsa aure a Kaduna state,yasan da biyu suka shirya masa wannan tafiyar,bai Isa yaqi tafiya da'ita ba,tunda yaga alama zuba masa ido sukai akan maganar kawo ta gida haihuwa. Hakan yasa suka shirya tafiya Nigeria,Inaas tayi mutuqar kyau cikin laffayar ta milk color,ta rataya yar qaramar hand back ta gayu a kafadarta, yayinda hannunta yake riqe da babbar wayarta tana danne danne,lokacin dasuka sauka a Nigeria sosai yan Jarida suka so kashe mata ido ta hasken camera,hannunta yana cikin na Jawad yayinda ya kama gefen laffayar ta ya riqe saboda tanada tsantsi kuma da tsawo zata iya jan qasa,sai kakkareta yake kamar wata zinariya. Har wajan motocin dasukazo daukarsu yan Jarida suka bisu, amma Jawad bai basu damar magana dashi ba,kan kace me, labari ya watsu a media,daga masu cewa Amarya taji kudi tayi qiba abunta,sai masu cewa kamar ma ciki ne da'ita, wasu kuma suce batada cikin komai kawai qiba tayi da alama Jawad din ya'iya kiwo,saide wasu manyan mata iyaye masu bibiyar kafafen yad'a labarai kallo daya sukewa Inaas din sugano tanada ciki tsoho ma kuwa,suma daga nasu 6angaren suna ganin da alama Jawad d'in ya'iya aiki(🙈) Acikin mota ajiyar zuciya ta saki tadora kanta akan kafadarsa,cikin kulawa yayi mata rada acikin kunanta yace"sorry" Inaas ta gyad'a masa kanta,ya sunkuya yayi kissing kanta,sannan yadora hannunsa akan cikinta yana shafawa har sukaje gida. Awajan adana motoci sukaga iyayen nasu a tsaye da alama jiran zuwansu suke,motar tana tsayawa Jawad yayi kissing bakinta sannan yabude mata motar tafita,shima ya futo daga d'aya 6angaren. Cikin farinciki Inaas ta rungume Bilkisu,sannan ta rungume Mummy. Yaya Mariya ta ruqo hannunta tana kallon yanayin jikin nata tace"sannu Inaas,Allah ya raba lafiya,muje ciki" Gaba dayansu falon Mummy suka wuce,fuskar kowa d'aukeda farinciki,abinci sukaci saide Inaas kam nama kawai taci tasha ruwa,Jawad yana cin abincin yana satar kallonta,saida Fu'ad yayi masa rada yace"yaya Daddy fa yana kallonka" Sannan ne yadan sosa kansa,ya daidaita kansa yamaida hankali kan cin abincin. Shine yafara tashi,idonsa akanta yawuce sama domin ya watsa ruwa yayi sallah. Itama Inaas adakin Mummy tayi sallah,batayi wankan ba,tadawo falo ta zauna sunata fira,har Jawad ya sauko yadawo falon suna nan,sai qarfe goma Yaya Mariya tatafi gida abokin rakiyar tata ya rakata, wato Fu'ad. Su kuwa sai wajan goma da rabi sannan Bilkisu tayi musu saida safe,Inaas ma tamiqe taqi kallon inda Jawad din yake ma,tabi bayan Ammiy,Jawad ya dinga binta da kallon mamaki har suka 6acewa ganinsa. Mummy ta juyo ta kalli Jawad tace"Jawad kashe kayan kallon nan kaje ka kwanta,naga alama kamar baka gaji ba, kuda kukai doguwar tafiya" Ransa duk ba dadi yatashi yakashe kallon sannan murya ciki-ciki yace"saida safe Mummy" Mummy tayi murmushi tace"Allah yakaimu" Saida taga hawan sa sama sannan tayi ajiyar zuciya tawuce dakinta,tasan sarai saboda Inaas tatafi ne shiyasa yake wannan fishin,bazai iyu ta hanata tafiya ba saboda ko Yaya ne ya kamata ace anbarta da Bilkisun suyi firar yaushe Gamo. Suna zuwa daki tacire kayanta tashiga toilet tayi wanka da ruwan d'umi,tana futowa Ammiy tabata mai ta shafa,sannan tahado mata turaren wuta irin nasu na Niger ta turara jikinta,tasaka kayan bacci tafara qoqarin daure dogon gashinta,tajuyo wajan Ammiy tace"Ammiy daure min" Bilkisu ta kalli cikin Inaas din taga ciki da girmansa sosai,laffayar da tasa ce ta 6oye cikin,amma yanzu da tasa doguwar riga ta bacci marar nauyi gashinan ya futo zahiri. Ta kar6i ribon din hannun Inaas din tace"Kafin kiyi aure ban huta da daure wannan gashi ba, yanzun ma bazaki barni nahuta ba? acan qasar taku waye yake daure miki?" Inaas tace"haka nake barinsa Ammiy,idan na daure ma Yaya zaice bayaso" Bilkisu tayi murmushi takama gashin nata ta daure mata,suka kashe wutar dakin suka kwanta,sannan tace"ai babu matsala azaman naku ko?" Inaas tace"A a Ammiy babu komai wallahi,Yaya yanamin duk abinda nakeso,ko nan da can baya barina inje,ko aiki ne saide shi yayi,girkin ma banayi dayake likita ta hanani aiki,saide yayi mata order abinci" Bilkisu tasaki wata irin wawiyar ajiyar zuciya,hankalin ta yasake kwanciya,duk da suna cikin duhu haka ta fuskanci Inaas din tace"to kinga wannan abun nake hango miki tun farko,shiyasa banso alaqarku keda yaron nan Is'haq ba,nafiso Kiji dad'i agidan aurenki banaso ko kad'an kiyi irin rayuwar danayi saide in Allah ne yariga ya qaddara miki,kinga ni lokacin danake d'aukeda cikin mijinki,bama samun abinda zamuci,daqyar babansa yake nemo mana garin kwaki,shi zamu jiqa muci,wani lokacin ma duk da inada tsohon ciki sainayi wankin kudi,kokuma nayi niqan Lada,sannan zan Samo mana abinda zamu dan tarkada muci,shinkafa kuwa bama ganinta,abincinmu daga qanzo sai garin kwaki..." Taqarasa maganar tana share hawaye,Inaas ma hawayen ta share tace"Ammiy kiyi haquri,kidena tuna baya,yanzu ba gashi Yaya Jawad yana yi mana komai ba?" Bilkisu ta share hawayen ta tace"hakane kam,kinga katin bankin daya baki lokacin bikinku yace ko zamu cire kudi dana yi masa maganar katin qin kar6a yayi,daga qarshe yacemin duk abinda ya mallaka wanda yasani da wanda bai saniba yabani shi,nace masa samunsa agareni yafiyemin dukkan wani qyale-qyalen duniya" Inaas tace"ai Yaya yahadu,wallahi bashida matsalar komai Ammiy" Bilkisu tayi murmushi ta dungure mata kai,suka sa dariya daga nan sukai Addu'ah suka fara bacci. Qarfe daya na dare wayarta dake vibration tafara haskawa,Bilkisu tayi juyi taga wayar Inaas din ana kira,tad'an ta6ata tace"Inaas tashi ki dauki waya" Inaas takai hannu ta dauki wayar cikin muryar bacci tace"Qaunah" Jawad ya lumshe idonsa yace"Love nakasa bacci" Idonta a lumshe tace"Meyasa?" Jawad yace"ina gefen window ina hango falon ku,kifuto falo kibude window naganki,ko zan'iya baccin" Ahankali tad'an bude idonta sannan tatashi tafuto daga dakin,tazo falon ta yaye labulan window ta hango shi daga can sama yana tsaye, tace"kaganni?" "yes naganki,meyasa zakibi Mama? yanzu biyu saura,kuma a'irin wannan lokacin kin riga kin san memuke yi,kin saba min da abun dad'inki,yanzu gaba daya na a firgice nake wallahi,narasa nutsuwa, tun dazu sai juyi nake nakasa bacci" Inaas tayi ajiyar zuciya tayi qasa muryarta cikin rad'a tace"Qaunah,yanzu fa muna gida,dole haquri zamuyi" Cikin sauri yace"what!? mekike nufi?,kasheni zakiyi?" Idonta ta lumshe tabude tace"bahaka nake nufi ba,Qaunah kasanfa bazai iyu ba,da kunya inbika sama mu kwanta tunda su Mummy suna nan" Cikin sauri yace"ok,to zan dinga biyoki wajan Mama" Cikin sauri tace"Qaunah tareda itafa nake kwana,kawai mudinga fita wani wajan idan mukai abinda zamuyi saimu dawo" Jawad zaro idonsa waje yace"muje ina? to duk inda nasa qafata agarinnan sai yan Jarida sun sani,nide kawai kisan yanda zaki dinga yin dabara muna haduwa,wallahi zan'iya cutuwa,yanzu haka nasan cewa yau bazan fita sallar asuba ba,saboda idan nafita za'a gane halin danake ciki" Inaas ta lumshe idonta tace"toya zamuyi? nide bazan yarda kazo nan ba,saboda dakunan mu babu space sosai tsakanin na juna,duk abinda zakayi wallahi Uncle da Mama da Abbana duk sai sun jika,kuma kaima Qauna baka iya abun sirri ba,saika dinga ihu kana dukan gado kamar wani d'an dambe" Jawad ya motsa lips dinsa sannan yace"to waye yake sani hakan? ba kece ba? dama aina dade da sanin cewa kallon d'an dambe kikemin,kawai fada ne bakya yi, ranar dana fara ganinki abinda kika fadamin kenan" Inaas tayi murmushi tace"siffar mijina ne hakan,shi din jarumi ne,inaji dashi fiyeda yanda nakeji dakaina,yanzu de abinda za'a yi shine duk lokacin danaga Ammiy tayi bacci zan futo,kaima idan kaduba kaga Mummy da Daddy sunyi bacci kazo mu hadu ta qofar bayan Plat dinku, sai muje dakinka,kafin asuba saina dawo" Jawad yayi wata irin ajiyar zuciya sannan yace"i luv you so much love" Daga nan yasakar mata kiss yakashe wayar. Takoma daki tashiga toilet tayi fitsari,sannan ta kwanta a gadon tana tunanin mijinta. Sai alokacin Bilkisu taci gaba da bacci,itama tashi tayi takasa komawa saida taji Inaas din tadawo daki sannan hankalin ta ya kwanta.(🙊🙆🏻‍♀️) (kuyi haquri da wannan ba yawa, idan nace saina gama rubuta page din zan turo to zaku iya kaiwa qarfe goma kuna jirana,ku rage wannan mu hadu zuwa safe insha Allah 🙏🏻saida safenku nagode ❤️ Amnah El Yaqoub ✍🏻 [1/23, 08:05] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. 17&18 Washegari dasafe a wajan Mummy sukai breakfast,Abban ta da Uncle Sulaiman sun fita zasu taho dawani abokin Alhaji tareda shi zasuyi tafiyar zuwa kaduna. hakan yasa itada Ammiy suka tafi wajan Mummy,bayan Daddy yagama cin abincin sa ya kalli Mummy yace"ina Jawad ne? banganshi a masallaci ba,dana dawo ma banganshi ba,yanzu qarfe takwas,kuma su man Sulaiman suna dawowa zasu wuce,meyake ne haka bai futo ba?" Mummy tace"jiya da daddare idonsa qyamas yake babu alamun bacci,saida nace yaje ya kwanta sannan yatafi daki,nasan baiyi bacci da wuri ba,shiyasa yake ramuwar bacci" Daddy ya kalli Inaas datake shan tea yace"jeki taso shi kice yashirya dawuri suna dawowa daga dauko abokina bazasu jira shi ba ko baiyi wanka ba haka zai bisu su tafi" Bilkisu tayi murmushi,yayinda Inaas tatashi tana tafiya daqyar ta nufi sama dakin Jawad. Mummy tace"Alhaji ace ko baiyi wanka ba sai tafiya? babu maganar cin abinci?" Daddy yace"banaso yasa iyayen nasa jirane,inaso kuma yashige gaba ayi komai dashi akan neman auren,musanman saboda P.a dinsa, kinga gara a dinga yin komai dashi, because sune manyan gobe agidan" Mummy tace"eh hakane kuma,gara a dinga saka su acikin sabgar tun yanzu" **** Inaas tana shiga ta ganshi a kwance cikin bargo yana matse qafafunsa,cikin sauri ta qarasa gadon tace"Qauna lafiya? meyake damunka? Daddy yace ba kaje sallar asuba ba meyafaru?" Ahankali yad'ago kansa ya kalleta da Jan idonsa,lokaci daya tagane yanayin da mijinta yake ciki,cikin sauri tace"Subhanallah meyasa bazaka kirani ba?" Cikin shaqaqqiyar murya yace"bansan ma ina na jefa wayar ba,yau sallar asuba adaki nayi,kinganni fa tayaya zan fita ahaka?" Yafadi hakan yana yaye mata bargon dayake ciki,gabanta yafad'i saboda yanda taga yanayinsa babu sauqi,ta matsa kusa dashi tayi kissing goshinsa tace"sorry,kuma su Uncle idan suka dawo Daddy yace kaduna zaku tafi" Jawad yace"bazaniba Love" Cikin sauri tace"A a sai kaje,bani minti goma kaga" Tana fadar haka tatashi ta kulle dakin sannan tadawo tacire rigar jikinta,Jawad duk yana kallonta,yana jinta tashige cikin bargon tana yi masa wani irin salo,daga nan al'amari ya sauya,Jawad ya dinga abu daya saida yaji ya d'an samu sassauaci,bai haqura ba daga nan yafara qoqarin sake wani round din,Inaas dataga abinda yake qoqarin sake yi tace"su Uncle fa karsu dawo" Cikin sauri yace"bazasu zoba yanzu zan gama" Tana jinsa yayi abinda yakeso,sannan ya qanqameta zai fara sakin ihu tayi sauri ta rufe masa baki,saida suka nutsu,taga yana hawaye,tagoge masa hawayen tace"me yafaru kuma?" Jawad yayi kissing dinta yace" hawayen farinciki nake bisa ni'imar da Allah yamin ya mallaka min ke,Allah yayi miki Albarka,wallahi naji dad'i sosai" Inaas tayi murmushi tatashi tace"jekayi wanka Yaya,karsuzo" Saida yayi wata irin miqa,sannan yatashi yashige toilet. Itama tashi tayi tagyara jikinta,sannan tamaida kayan ta tagyara gadon tsaf,yana futowa yace"kishiga kiyi wanka saimu fita tare" Cikin sauri tace"wallahi idan nayi wanka zasu fahimci abinda yafaru,ka shirya ni zan wuce dakin Ammiy inyi wankan" Cikin sauri ya shirya tana taimaka masa,cikin d'an qanqanin lokaci ya shirya cikin shadda light blue da babbar riga,suka futo,sai tashin qamshi yake,fuskarsa cikeda walwala. suna saukowa Daddy ya kalli Jawad yayi ajiyar zuciya,yasan cewa duk abinda zai hana Jawad zuwa masallaci ba d'an qarami bane,saboda tun yana yaro baya wasa da lokacin sallah,hakan yasa ya fahimci Jawad din yana buqatar matarsa ne,shiyasa ya tura masa ita,kuma da alama ta warware komai,saide yaji dadin yanda suka 6oye sirrin su babu wata alama dazaka gani daga wajan Inaas din wacce zata nunama yaran sunyi wani abu. Ko minti daya ba suyi da saukowa falon ba su man Sulaiman suka dawo,hakan yasa Inaas ta zame tabar falon ta gudu toilet din Ammiy zatayi wanka,Daddy dayaga fitar ta yayi murmushi kawai. Cikin sauri Jawad yaci abinci daga nan suka nufi kaduna state. Bayan sun tafi Bilkisu tatafi domin tabar Hajiya da Daddy suma su huta, tana shiga daki taga Inaas tafuto daga wanka tana busar da gashin kanta da handrayer,lokaci daya tagano su,ta riga tagama yarda Jawad gadon ubansa yayi,domin kuwa har zuwa yanzun shima uban ba yayiwa Bilkisun ta sauqi,cikin dare idan tatafi dakinsa saisu raba dare yana abu daya kamar ba tsoho ba. Tayi ajiyar zuciya ta zauna a gadon tana qoqarin kunna kallo bata nunawa Inaas d'in tagane komai ba. Basu koma wajan Mummy ba sai wajan yamma,farfesun jan nama ne agaban Inaas tanaci ahankali, yayinda Hajiya Zaliha take cewa" Bilkisu ni kayan Babyn nan menene ba'a siyo bane?" Bilkisu tace"Hajiya duk yawan kayan nan ai bana tunanin akwai abinda bamu siyo ba, bayan taku siyaiyar nima awajena fa akwai wasu kayan" Mummy tace"duk da haka sai nake ganin bazai hana mu qara wasu ba,kamar sunyi kad'an" Bilkisu tayi dariya tace"Hajiya yanda kike yiwa yarinyar nan tanadi Allah yasa de kartazo ta qwace miki Alhaji" Inaas tayi dariya bayan tagama jinsu. Adede lokacin Alhaji Bature yayi sallama yashigo falon,abayansa wata yarinya ce budurwa tana biye dashi. Hajiya Zaliha tana ganinsu gabanta yafad'i,domin kuwa ba Alkhairi a ganin Yaya Bature. Bilkisu tana ganinsa ta sunkuyar da kanta qasa,sarai tagane shi, shine mutumin daya zo ya musu tijara,Inaas ma tana ganinsa tagane shi saboda ranar da yazo yafad'a wa Jawad maganganu suna tare,kawai de macen dasuke tare ne bata ganeta ba. Hajiya Zaliha tace"Yaya yau kune atafe?, sannunku da zuwa,ku zauna,Amal qaraso ki zauna mana" Gaban Inaas yayi wata irin fad'uwa,tun ranar da taji sunan Amal ta riqe sunan a kanta,itace da za'a bata Yaya Jawad,lokaci d'aya ta dauke kanta daga wajansu tamaida kan kayan kallo. Bilkisu tace"sannunku da zuwa" Tafadi haka tana miqewa,ko sauraren amsarsu batayi ba,bowl din gaban Inaas ta dauka tawuce kitchen taqaro mata wani farfesun,tadawo ta ajiye mata tace"ki cinye shi gaba daya" Mummy tajuya ta kalleta tace"idan ta cinye ma ai akwai fruit dinta dana had'a mata tun dazu ba tasha ba,sai tasha ko kad'an ne, kada Babyn ta zauna da yunwa" Bature ya jinjina kansa ganin kotasu basayi gaba daya sun maida hankalinsu akan yarinyar dayake gani da qaton ciki. Yayinda Amal taji kamar taje ta Shaqe Inaas din kowama yahuta, sai wani nan-nan suke da'ita da yanzu fa ita za'a yiwa wannan Kulawar. Alhaji Bature yace"zaliha munzo amma kuma baki tambayeni menene yake tafe dani ba" Mummy ta kalleshi,tace"af Yaya kuyi haquri,kunsan sha'anin me juna biyu dole saida kulawa,menene yake faruwa?" Alhaji Bature yagyara zamansa zaiyi magana saigasu Jawad sun dawo,tare suka shigo da Daddy fuskarsu cikeda Farinciki da alama sun samu nasarar abinda sukaje nema, mamaki ya bayyana qarara akan fuskokin su,Jawad yabashi hannu suka gaisa kamar babu abinda yata6a hadosu,Fu'ad kuwa sannu yayi musu kawai. Amal tana ganin Jawad tafara gyare gyaren mayafi har saida Mayafin jikinta ya sauka daga gaban qirjinta,nonuwanta duk suka furfuto tanayi tana satar kallon Jawad. Inaas da hankalin ta ke kan Amal din tana ganin duk abinda takeyi. Daddy ya kalli Alhaji Bature yace"Bature meyafaru?" Alhaji Bature yace"Alhaji Mekudi dama wajanku nazo,saboda maganar gaba dayanku tahada daku,maganar gobara danayi har nazo nan nace zankai kotu, na janye ta, yan'uwa sun min fada sun nunamin ni daku ai duk daya ne,hakan yasa na haqura na janye,yanzu de inaso komai yawuce,ina roqon ku garafa ku yafemin,d'an jarin nan idan da hali atemaka min,Amal kuma dama yarku ce,gatanan na kawo muku ita sai abata Jawad d'in,itama ai qanwar sa ce" Cikin sauri Jawad yadago kansa ya kalli Uncle Bature sannan ya maida kallonsa wajan Amal,anan yayi tozali da nashanunta,yafara tunani ita bayan budeshi datakeyi acikin photo a zahiri ma haka take ashe? Inaas ta kalli yanda Jawad din yake kallon Amal,wani irin Kishi ya kamata,ahankali tatashi tsaye sannan ta gyara mayafin rigar jikinta tafice daga falon. Fu'ad yayi d'an qaramin murmushi ganin madam ta shaqa,yamaida kallonsa wajan Jawad,yaga shima binta yayi da kallo harta fice daga falon. Daddy yayi dariya yace"to wannan maganar kam aiba tawa bace Bature,duk abubuwa guda biyun daka nema d'aya ne nake tunanin zan'iya yima shine nabaka Jari,Shima saika jirani naduba nagani ko zaka samu,maganar Amal kuma ga Jawad dinnan agabanka" Bature ya kalli Jawad yayi murmushi yace"yarona Jawad kayi haquri ka manta baya kaji,nasan nayi kuskure amma ina nema daka yafemin, yanzu me kace game da qanwar ka Amal?" Jawad ya kalleshi cikin kwanciyar hankali yace" Uncle dama ni bance ina sonta ba,zan aure tane saboda Mummy na,yanzu kuma tasake kawomin wata yarinyar gashinan kana gani kasan komai kuma,na aure ta,ina tunanin zatafi rufamin asiri tunda ita jininace" Bilkisu tasaki ajiyar zuciya tana d'an murmushi ahankali. Daddy ya kalli Alhaji Bature yace"to kaji,bari inje dakina in duba ma ko zaka samu jarin ko dubu dari ce" Alhaji Bature ransa baqiqqirin yakalli Amal yace"Ke tashi mutafi,dama saida nace ko munzo bazasu amince ba kika dage sai munzo,Jawad dinnan ko dan gwal ne yakamata ki haqura dashi tunda dama can nine dalilin haduwar ki dashi, yanzu daga ganinsa a TV shida matarsa sun zo shikkenan kikabi kika rikice" Yajuya ya kalli Daddy yace"Alhaji kabar dubu darinka,idan qari kake buqata zanyi dako na aiko ma dawata dubu darin" Yana fadin haka ya miqe suka fice daga falon, Amal sai share hawaye take tana dana sanin biyewa mahaifinta datayi a baya saboda kudi harta bari Jawad din ya kubce mata. Daddy ya girgiza kansa yace"bazai sauya bafa,dan in gwada shi yasa nace masa dubu dari amma ba hakan zan bashi ba,Bature bazai sauya ba" Abban Inaas yace"Alhaji da anyi haquri inde zai iyun ayi musu auren tunda naga yarinyar kamar tana son shi" Jawad ya kalleshi da sauri,cikin daure fuska yamiqe yabi bayan matarsa. Daddy yayi murmushi ya nuna masa Jawad da hannu yace"kaga amsar maganar taka ko?" Man Sulaiman yayi murmushi yace"Allah yasa mudace" Hajiya Zaliha tasaki ajiyar zuciya tace"Allah ya shirye shi" **** Yana shiga falon bai ganta anan ba,hakan yasa yaduba dakin Ammiy nan ma bata ciki,yaduba d'ayan dakin nakusa dana Ammiy yaganta aciki tana gyara kayanta,ya rufe dakin yasaki ajiyar zuciya hannunsa zube cikin aljihun wandon sa. Dakin yafara qarewa kallo da alama ba'a zama aciki kawai kayan Unborn Babyn sune adakin saikuma wasu daga cikin kayanta. Ya kalleta yace"aikin mekike haka bayan kinsan cewa likita ta hanaki aiki?" Batare data kalleshi ba tace"qasarmu zan tafi,tunda nan d'in kasamu wacce zata dinga 'DEBE MA KEWA" Jawad ya lumshe idonsa yabude yasaki ajiyar zuciya yace"meyake damunki ne Love? why all this? mekike fada haka?" Cikin masifa ta juyo ta kalleshi tace"karka nunamin bakasan komai ba,ina ganinka kana qarewa jikinta kallo" Cikin sauri ya qaraso wajanta yariqe hannayen ta yace"bahaka bane,tata6a turomin photo naga alokacin awaje suke,kuma yanzu ma naga ko kunyar su Daddy batayi shima tasake barinsu awaje" Cikin 6acin rai tace"ohh shine kake qare musu kallo? ashe kasaba gani bansani ba,har turoma photo take" Taqwace hannunta taci gaba da saka kayanta cikin jaka. Jawad yace"sau daya nefa,kuma tun da dadewa tun kafin ku dawo nan,sannan ni dazu ban kalli abunta ba" Tana saka kayanta ajaka tace"ka kalla mana,idan baka ganiba tayaya zaka San cewa a photo tana budewa a zahiri ma tana budewa,kaga kuwa ai kana gani" Jawad ya rungume ta tabaya yadora kansa akan wuyanta,yayinda hannunsa yake kan qaton cikinta yana shafawa,cikin muryar lallashi yace"kinga....,nagani ko ban gani babu abinda zanyi da wancen yarinyar,bata gabana daga ita har mahaifinta,na d'aga musu qafa ne saboda shi d'in Yaya ne awajan Mummy amma da sojoji zansa suyi musu dukan tsiya" Ya janye hannunsa daga kan cikinta ya dorashi akan nashanunta yana musu wata irin murza wacce yasan cewa tanaso,sannan yafara kissing wuyanta cikin wani irin salo yace"Love bayan ganaki kullum kina bani ina abinda nakeso dashi mezan yi dana wata? uhm...?" Yafadi hakan yana sake aika mata dawani irin saqo,Inaas ta lumshe idonta cikin shagwa6a tace"to meyasa zaka kalleta...nide karabu dani" Shima idonsa a lumshe yace"ni ban kalleta ba,please kiyi haquri,komai yariga yawuce,ni bazan aure ta ba" Tabude baki zata masa magana yayi sauri ya sanya bakinsa cikin nata,daga nan nan mitar taqare,tanajin yanda yake sarrafa mata nashanunta cikin salon qwarewa,kafin daga qarshe ya futo dasu yafara sha ahankali,Inaas ta rungume kansa tana sosa masa cikin sumar kansa idonta a lumshe tanajin wani irin dadi. Ganin al'amarin nasa yana sake gaba,hakan yasa tafara qoqarin tureshi,cikin wata irin murya yace"haquri zan baki fa....,please ki barni mana" Inaas tace"Qauna ka manta inda muke ne? idan Abbana da Uncle suka dawo fa?" Cikin damuwa yace"basa nanfa,sun san cewa ina nan,bazasu zoba, nide ki barni nabaki haquri kinji...? dan Allah kinji Love?" Yafadi haka wani irin hawayen fitina yana sakkowa daga cikin idonsa. Hakan data gani yasa tarabu dashi,suka Haye kan gadon daga nan komai ya sauya Salo. Kusan awa biyu da futowar Jawad daga falon,iyayen nasu sukaci abinci acan falon Mummy,daga nan suka fice saboda ankusa fara kiran sallar magrib,hakan yasa Bilkisu ma tataho saboda tayi haramar sallah. Tana sako qafarta falo taji kamar ana doke-doke,gabanta yafad'i taji tsoro kode Jawad biyewa Inaas yayi suke fada harda doke-doke? saboda taga futowar ta daga falon ranta a6ace,kuma tasan cewa shima Jawad din daya futo wajanta zaizo,cikin tashin hankali ta qarasa kusa da d'akin datake jin doke-doken,tasa hannu zata kama handle din d'akin adede lokacin gabanta yayi wata irin fad'uwa sakamakon muryar Jawad data jiyo yana kuka cikin fitar hayyaci yana fadin"kiyi haquri...kin haqura ko?, Wayyo Allah love dadi zai kasheni,kiyi haquri bazan sake ba....,Allah nadena kallon kowacce mace kinji....,Wayyoooo" Yafadi Wayyo din yana dukan katifa. Ammiy ta zaro ido tasaki handle da sauri ta matsa tabar wajan,bata shiga dakinta dayake kusa dasu ba,kai tsaye tawuce d'akin Man Sulaiman tashige toilet dinsa tafara haramar alwala. Har aka idar da sallar isha'i tana cikin dakin bata futo ba,tana zaune tana tasbihi Man Sulaiman yashigo dakin yafara qoqarin cire babbar rigar jikinsa yana fadin"gaskiya iyayen yaran nan nan sunyi mana karamci sosai,bamu bar gidansu bafa saida aka saka rana nan da wata d'aya,abun yamana dadi sosai" Bilkisu tace"Allah yasanya Alkhairi,ai bayan kun fita Hajiya take cewa zuwan Alhaji Bature yasa ko tambayar ku yanayin tafiyar bamu yi ba" Man Sulaiman yace"to ya za'ai,sha'anin mutane sai haquri,yau anan kike zaune kenan? dana shigo banganki a falo ba nayi tunanin har yanzu kina can wajan Hajiya" Bilkisu tace"A a ina nan,nabarwa yarana falon" Man Sulaiman ya kalleta yace"kamarya? babu kowa afalon fa" Ajiyar zuciya tayi tace"Alhaji yaron nan kuwa anya bazan zauna dashi nayi magana dashi ba? yarinya da tsohon ciki amma ace babu haquri acikin lamarin sa? wallahi nayi tunanin fada suke da doke doke,gaba daya baisan meyake fada ba,kuma wannan abun arasa inda za'a yi sai nan?" Man Sulaiman yayi murmushi bayan yagano manufarta, yace"karki fara yimasa magana,kibar yarona yahuta,nan da can 6angaren Hajiyan duk d'aya,kibarshi yaci gaba da aiki babu batun d'aga qafa tunda hakan ba matsala yake kawowa yarinyar ba" Bilkisu tace"amma mahaifin yarinyar nanfa yana nan,idan mu kadai ne dasauqi" Man Sulaiman ya jinjina kansa sannan yace"eh kuma hakane,to amma nasan cewa shima Jawad din ba zaiyi abinda zai shafeshi shida Farouq din ba,sannan tare mukai sallar isha'i da Jawad din fa,magrib cede bamuyi dashi na, amma tare mukai sallah yanzu,kidena tunanin komai,nasan zasu dinga qoqarin 6oye sirrin su" Bilkisu tayi ajiyar zuciya tace"to shikkenan,Allah yasa". Tunda wannan d'an sabanin yafaru a tsakanin su basu sake samun wani sabanin ba,koda yaushe Jawad yana qoqarin ganin ya faranta mata,haka itama, 6angaren auratayya sun riga sun tsara abun su da daddare zata taho ta hanyar baya zai tarota su tafi dakinsa,su kwana suna abunda suke so,lokacin kiran sallar farko zai rakota tadawo ta kwanta,dasafe taita rama baccin gajiya,saida cikinta yacika wata takwas,sannan Daddy yayiwa Jawad maganar kowama aiki,saide Jawad din yayi masa bayani akan yanaso Inaas ta haihu yana gida,shiyasa ma yabar P.a dinsa acan saboda yaci gaba da kula da komai,duk abinda yake faruwa suna magana,kada yadawo sai lokacin bikin sa, shikuma zai zauna yaci gaba da kula da komai na nan Africa. Hakan yasa Daddy ya haqura da batun tafiyar sa,saide ahakan ma baya zama,duk qasashen dasuke Africa wanda yake da huldar kasuwanci dasu kullum yana can yana ganin yanda abubuwa suke gudana,sau daya yaje Niger inda yaqara wa Ilyasu Manager babban muqami,hakan ba qaramin dadi yayiwa ilyasu ba,cikin ransa yaji dadin daukar Inaas aiki saboda yasan komai ta dalilin ta yasamu. Bayan sati d'aya Jawad yana zaune a compound din gidan yana vedio call a Computer shida P.a ga wasu takardu dayawa agabansa da alama aiki zaiyi, daga can gefensa wasu guards ne a tsaye,suna zare ido. Inaas ta qaraso wajansa jikinta sanye da dogon hijab ta ajiye masa lemo sannan ta zauna tana duba takardun tana jira yagama magana. Lemon data kawo masa yadauka yasha,sannan ya sallami P.a ya kalli qaton cikin Inaas,idan lissafin su yazama gaskiya saura sati uku ta sauka,yayi mata Addu'ah acikin ransa sannan yace"madam" Inaas tayi masa hararar wasa sannan tace"yau kuma?" Murmushi yayi yadaga kafadarsa yace"har gobe,karki hargitsa min takardu na" Dan qaramin bakinta taturo gaba cikin shagwa6a tace"nasanfa aikin,ko inci gaba kagani?" Cikin rashin damuwa yayi qasa da muryarsa yace"why not? idan kika kasa kuma kika maida min aiki baya saina fanshe da daddare" Wani kallon soyaiya tayi masa sannan taja computer gabanta tafara aikin,mamaki ya kama Jawad ya kalli computer sannan ya kalleta yace"waye ya koya miki? Idan inayi la6ewa kike yi kina kallo na ko?" Cikin murmushi tace"satar amsa ma kenan,babu wanda ya koyamin,lokacin daka qaramin matsayi a wannan kamfanin na Niger,Manager yafara koyamin" Lokaci d'aya ransa ya6aci yace"kamarya ya koya miki? Meyasa bazai sa wata mace ta koya miki ba?" Cikin sauri tayi kwana tace"Bafa ni kadai bace Qauna, mu uku ne duka mata,kuma ko kallon inda nake ba yayi" Sai alokacin Jawad yasaki ajiyar zuciya sannan yace"naji,bani aikina karki wahalar min da Baby na" Inaas tatura masa computer sa sannan tace"Qauna yaufa sati biyu kenan da qarewar hutun mu,an koma second semester" Cikin nutsuwa yazuba mata ido yana kallonta sannan ya jinjina kansa yace"zanyiwa P.a magana yaje makarantar, saiki dinga karatun anan gida, idan kin haihu lafiya,bayan kin haihu saimu koma,nasan zuwa lokacin ba za'a fara exam ba" Inaas tasaki ajiyar zuciya sannan tace"i luv you Qauna,banda kamar ka wallahi,Allah yabar min kai ni kadai" Tafadi hakan tana qoqarin tashi d'aqyar. Jawad yayi murmushi yace"wato kalaman cin hanci ne wannan ko?" Itade Inaas batace masa komai ba tawuce ciki. Acikin wannan satin aka fara shirye shiryen bikin P.a da amaryar sa Fadila,sai kuma Fu'ad da amaryar sa Noor,Inaas taso ayi komai da'ita saide hakan bai samu ba,domin kuwa Jawad kafawa yayi yatsare babu abinda zatayi,duk yan biki dasukazo kowa yanayi mata Addu'ah da fatan Alkhairi. Ranar daurin aure aka hada aka daura dana Farouq Abban Inaas,da Amarya sa Surayya yarinya 'yar shekara talatin,banda mijinta daya rasu da yanzu itama tana gidan mijinta,to kuma Yaya Mariya tana yiwa Abban Inaas din maganar Surayyan saiya amince,itama Surayya ganin bawani tsufa yayi ba kuma ga kudi ga kyau nan da nan ta amince aka wuce wajan. Gidan yacika maqil da jama'ah Jawad yazama busy komai shi Daddy yake sakawa,Bilkisu ce take kula da 6angaren abincin baqi, babu irin naman da babu saide na mutum,anyi karamci sosai a bikin. Acan kaduna sukai taron dinner inda yan wasan hausa sukaje suka baje kolin basirar waqoqi,daga nan aka taho da Amare. Kai tsaye aka wuce da Amaryar P.a hadaddan gidanta, shikuma Fu'ad wani Plat din daban yakoma, haka Shima Abban Inaas shida matarsa. Fu'ad yaso yakoma wani gidan daban, danyayi amarcinsa yanda yakeso,saide Daddy ya hanashi,acewarsa Jawad ma bai barshi yafita daga family house ba,hakan yasa Fu'ad yayi zamansa. Cikin kwanciyar hankali aka gama biki lafiya,Surayya matar Abban Inaas tunda taga Inaas din taji tana qaunar yarinyar,lokaci daya taja Inaas din ajikinta suka hade kansu. Satin bikinsu daya,Fu'ad yadauki matarsa suka tafi Honeymoon. Washegari dasafe Inaas tanata bacci adaki sai wajan shadaya na safe tatashi sakamakon Yaya Jawad bai barta ta runtsa ba,tayi tunanin zuwa yanzu zai harta,saboda yanayin girman cikinta,to amma saita ga ya sauya style, yanda cikin bazai takura shi ba. wanka tayi ta shirya,sannan tafuto falo tafara cin abinci. Bata dade da zamaba Jawad yashigo,Bilkisu ta kalleshi tace"daga ina haka kamar an koroka?" Jawad ya kwanta akan doguwar kujerar falon sannan yadora kansa akan cinyarta yace"Mama nagaji,wallahi daga kamfani nake tun sassafe nafita,bacci nakeji" Bilkisu tace"to tayaya zakayi bacci bakaci abinci ba?d'aga min cinya kaje kuci abinci kaida matarka" Jawad ya yamutsa fuskarsa cikin shagwa6a ya rungumota ta hanyar zagayo da hannunsa ta qugunta yace"Mama idan natashi zanci" Bilkisu tayi murmushi ta girgiza kanta,sannan tadora hannunta a kansa tana shafa sumar kansa,shekaru talatin da bakwai baya suna sake dawo mata. Inaas ta daga murya tace"shagwa6a master" Jawad yana jinta yayi shiru,itama Bilkisun murmushi tayi tarabu da'ita. Sosai yayi bacci akan cinyar tata,baccin yamasa dadi yanda baya zato,bai tashi ba, itama bata tasheshi ba har qarfe biyu na rana,ahankali yayi juyi sakamakon muryar Abban Inaas dayaji afalon. Bilkisu tafara shafa masa sumar kansa hakan yasa yaqi tashi dan karta daina. Abban Inaas yayi murmushi yace"yau kujerar Inaas aka qwace kenan" Inaas ta kalli Jawad tayi murmushi Sannan tatashi tawuce kitchen zata hadowa Abban ta shayi. Bilkisu tace"yau kam yabawa qanwar sa hutu shine akan kujerar,yana ganka kai kadai? ina Surayya?" "tana daki Yaya,banma shiga wajanta ba, nafara biyo nan ne mugaisa tukunna" Cikin jin dadi Bilkisu tace"Allah sarki baiwar Allah, babu ruwanta kamar Marigayiya Jamila,kuma sainaga kamar suna yanayin kama da Jamilan ma" Farouq yayi ajiyar zuciya yace"Yaya nima yanayin danaga tanayi da Jamilan shiyasa na amince zan aure ta,amma har yanzu banajin zan samu kamar Jamila,kullum cikin kallon mata nake ko zanga mai kama da Jamila sak,amma ban ta6a ganiba, inda naganta da tuni nayi aure,saide inajin dadi idan naga Inaas,saboda kamar mahaifiyar ta kullum sake bayyana take atare da yarinyar" Jikin Bilkisu yayi sanyi tace"jamila kam mutum ce,amma kuma fa duk shaharar da kyawun Jamila yayi,Inaas tafita kyau" Farouq yayi dariya yace"A a Yaya, karki ziga yarki,har yanzu banta6a ganin mace wadda samari suke tashin hankali akanta kamar Jamila ba,Yaya Nasha wahala fa kafin na sameta" Bilkisu tayi murmushi kafin tayi magana Inaas takawo masa shayi,bayan tagama jin duka firarrakinsu, tausayin Abban nata yasake kamata. Zama tayi akusa da Jawad ta mintsine shi aqafarsa,ahankali yabude idonsa ya kalleta,Bilkisu tace"shikkenan kin tasheshi kin huta" Inaas tace"Ammiy kutashi kuyi sallah mana,dama aiba cinyarsa bace" Ta qarasa maganar cikin shagwa6a Jawad yatashi suka gaisa da Abban Inaas,sannan yashige d'akin Ammiy zaiyi alwala,itama tatashi tashige dakin Man Sulaiman domin tayi sallah. Bayan sati uku,Inaas tana falon Mummy suna fira,itada Mummy da Jawad, Fu'ad yakira wayarta suka sha firar su, bayan ta kashe wayar sukaci gaba da fira har qarfe goma na dare, Mummy tayi musu sallama tawuce dakinta, Jawad yakashe kayan kallon ya dauki Inaas cak suka haye sama,suna zuwa dakinsa tashige toilet wanka,shikuma yadauki computer yabude yana tura wasu saqonni. Har Inaas tafuto daga wanka tashirya cikin doguwar riga me fadi Jawad yana zaune da computer agabansa,tafe she jikinta da turare sannan tazo ta rungume shi ta baya duk da tsinin cikinta yahana rungumar sosai. Cikin farinciki tayi kissing wuyansa sannan tace" d'an kasuwa,lokacin bacci yayi" Ahankali ya rufe computer sannan yajuyo shima yayi kissing wuyanta yace"Matar d'an kasuwa sainaji d'umin Baby na tukunna" Daga haka yature computer gefe,ya d'orata akan cinyarsa,yaraba su da kayan jikinsu,cikin fitar hayyaci yafara aiwatar da komai a zaune,Inaas bata ta6a sanin akwai wannan style dinba sai yanzu,a zaune yayi komai sannan ya dauketa suka koma kan gado yakoma second round,tanajin yafara abu da zafi-zafi taji marar ta ta riqe,bayanta ya amsa,lokacin d'aya taji wani irin ciwo na fitar hankali,tabude baki tasaki wani irin ihu sakamakon wani irin abu dataji ya taho mata gadan-gadan yana neman rabata abiyu,lokaci daya qaran ihun nata ya ratsa ko'ina nagidan,cikin azabar ciwo tace"Yaya zan mutu,cikina" Gaban Jawad yafad'i,cikin sauri yazare jikinsa daga nata,yaga tafara zubar da jini hakan yasa nan take yagane cewa haihuwa ce tazo mata, cikin sauri yanufi qofar dakin zai bude jikinsa ko kaya babu(🙊😳🙆🏻‍♀️) Saiya dawo baya da sauri ya zura gajeren wando yasaka Jallabiya,yadauko mata rigar ta jikinsa sai rawa yake yana saka mata,cikin kuka tace"Yaya bayana zan mutu" Mummy data futo daga dakinta cikin tashin hankali tafara buga qofar tana fadin"Jawad! Jawad!!" Jawad da jikinsa ke rawa yace"asbiti zamuje,yi haquri kidena kuka,bazaki mutu ba" Yafadi hakan yana qoqarin daukarta. Inaas tahada wani irin gumi,dogon gashinta ya barbaje,cikin azaba tace"Yaya karmuje ko'ina, kabarni namutu anan, mutuwa zanyi" Gaban Jawad yafadi,yatuna zancen mutuwar mahaifiyar ta,gaba daya saiya sare,lokaci daya hawaye ya wanke masa fuska. Mummy tasake buga d'akin,cikin tashin hankali ya qarasa da Inaas din a hannunsa yabude qofar,ya kalli Mummy fuska cikeda hawaye yace"Mummy wai mutuwa zatayi?,Mummy mukai ta asbiti bazata mutu bako?,nashiga ukuna duk nine najawo mata" Ganin baya hayyacinsa yasa Mummy taja hannunsa qasa harya sauke Inaas d'in,gaba daya hannunsa ya6aci da jini, cikin sauri taduba tace"Jawad ai haihuwar tariga tazo,kiramin Maman ka yi sauri" (mata masu juna biyu ubangiji Allah ya saukeku lafiya,Allah yabaku lafiya😥🤲🏻) ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/23, 13:28] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. *👭GARKUWAR MATA👭* *Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci* *GA* *Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa* Rage tumbi💯 Nono💯 Sanyi💯 Karin kiba💯 girmar hips💯 Ni'ima💯 Sabulai💯 Humra💯 Turarukan wuta💯 Matsi💯 Miski💯 Dilka💯 Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI 08089965176 07084653262 17&18 Saida yajuyo yasake kallonta,yaga hawaye yayi mata jaga-jaga a fuska,sannan yajuya yafice da sauri,afalo sukaci karo da Daddy,shima zai qarasa wajansu Mummyn. Tun kafin ya qarasa suka had'u da'ita ahanya,cikin tashin hankali tace"Jawad naji qara,hankali na yakasa kwanciya ina Inaas take? tana lafiya?" Kafin yabata amsa taga hannunsa alamun jini,hakan yasa suka qaraso da sauri,koda suka zo dakin suna temaka mata akan tayi nishi ga kai nan yataho,Inaas kasawa tayi,ga jini yana zuba,hakan yasa suka nufi asbiti cikin wannan dare. Babu wanda yasan meke faruwa daga Daddy sai Mummy saikuma Bilkisu da Man Sulaiman,Fu'ad da matarsa basa qasar,yayinda Abban Inaas Plat dinsu yake can gefe akwai d'an nisa kad'an,shiyasa basuji abinda yafaru ba. A asbiti suna zuwa aka kar6eta cikin sauri sukayi ciki da'ita,wani Doctor yaja Jawad cikin office dinsa ya taimaka masa ya wanke hannunsa inda ya6aci,sannan ya gyara jikinsa yadawo wajan yayi qasa da kansa yana Addu'ah Allah ya sauketa lafiya,ba naqudar ce kadai take bashi tsoro ba,yadauki laifin komai ne ya d'ora a kansa,da bai nemeta ba da cikin kwanciyar hankali ciwon naqudarta zai tashi,ahankali yaji d'umi akan hannunsa, hakan ya tabbatar masa cewa kuka yake,qarin tashin hankalinsa idan yatuna yanda take fada masa cewa mutuwa zatayi,gaba daya sai kalaman nata suka sanya ya masa jiki. Man Sulaiman ya zauna akusa dashi yana bashi haquri. Da taimakon Allah da taimakon Doctor's Inaas ta haifi Baby girl dinta,aka gyara su tsaf, sannan aka maida Inaas dakin hutu,tunda aka gyara Baby su kansu Doctor's din jinjina kai suke,tun yarinya tana qarama ake ganin zallar kyau atareda ita ga hanci kamar ba jaririya ba,sosai Babyn take kuka amma Doctor's sai kallonta suke kamar su saceta,haka suka futo da Babyn tanata kuka suka nufi familyn Mekudi dasuke zaune jugum-jugum,adede lokacin Abban Inaas da Surayya suka qaraso saboda Man Sulaiman yamasa waya. Gaba dayansu suka taru suka rufe Baby kowa yana kallonta yayinda hannu sai rawa yake kowa na jira a bashi ita ya dauka. Jawad ne ya kar6eta,hawaye masu d'umi suka zubo daga idonsa,yayi kissing Babyn,sannan yabawa Daddy ita, yawuce wajan Doctor's ya kalli daya daga cikinsu yace"zan iya ganin Maman Babyn?" Likita tace"zaka iya Yalla6ai,amma tana bacci kada a tasheta" Cikin sauri Jawad yayi ciki. Daddy ya qarewa Baby kallo yace"masha Allah,fa tabarakallahu ahsanul qaliqin,to Zaliha nifa nadawo nan" Gaba daya sukasa dariya,Abban Inaas ya kar6eta,kallo daya yayi mata yad'ago kansa ya kalli Bilkisu yace"Yaya wannan ai photo copyn Jamila ce" Bilkisu tayi murmushi tace"gaskiya kam,duk photunan Jamila tana yarinya itama kamar hakan de take" Addu'ah yayiwa Babyn sannan yabawa Man Sulaiman shima yamata Addu'ah,daga nan Su Mummy suka kar6eta. Jawad yana shiga dakin yaganta tana bacci,tana Sanye cikin wata riga doguwa me fadi ta asbiti,sai wata hular net me shara-shara sosai take bacci kamar ba gobe. Ya qarasa ya zauna akusa da'ita ya sunkuya yayi kissing goshinta, ya sanya mata Albarka, sannan yasaka hannunsa cikin nata yazuba mata ido yana kallonta tsantsar soyaiyar ta tana sake ninkuwa acikin zuciyarsa. Mummy tashigo itada Bilkisu suka ajiye Babyn acikin gadonta kusa dana Inaas,sannan Mummy ta shafa kan Jawad suka fice daga dakin tunda ba'a so a tasheta. Jawad yatashi tsam yadauko Babyn ya kwantar da'ita ajikin Inaas sannan yasaka hannunsa ya rungume su gaba daya ya lumshe idonsa. Sai bayan sallar asuba tatashi bayan gari yafara haske,ahankali tabude idonta ta saukeshi akan na Jawad,suka zubawa juna ido kamar zasu cinye kansu,hawaye yazubo daga idonta,Jawad ya matsa yayi kissing goshinta sannan yasake rungume su yace"Allah yayi muku albarka sweet,Allah yabarmu tare har gidan aljanna,kiyi haquri akan abinda yafaru ki rufamin asiri..." Ya qarasa maganar hawaye yana zubo masa daga idonsa. Cikin sauri tarufe masa baki,tana girgiza masa kai,yayi qasa da kansa ya dauko Babyn daga tsakiyarsu yace"kinga Babyn mu,kalla kigani tana kama dake,riqe Mamanki kisa mata Albarka" Cikin sauri Inaas ta kar6i Babyn hawaye yana sake zuba daga fuskarta,taji dadin yanda Jawad yakira Babyn da Maman ta,taji qaunar Babyn tana ratsa ta,yanzu irin wannan wahalar Maman ta tayi akan ta? lokaci daya sabon kuka yazo mata,cikin kuka tabude bakinta tace"Allah yayi mata Albarka,Allah yaji qan Mamana" Jawad yayi sauri ya goge mata hawaye,sannan yayi caraf yakama lips dinta na qasa yafara tsotsa,ahankali itama takama nashi nasama tanasha,saida ya tabbatar ta daina kukan sannan yazare bakinsa daga nata,yayi kissing Babyn,ya futo daga dakin yana fadawa su Mummy ta farka. Gaba dayansu suka shigo dakin ciki harda Doctor's din dasuka kar6i haihuwar ta,saida suka dubata suka tabbatar tana lafiya sannan suka fara qoqarin ficewa daga dakin,daya daga cikin Doctor's din ta dauko waya zata dauki photon Babyn,amma qiri-qiri Jawad ya hanata,Man Sulaiman yajasu gefe ya kar6i account number su nan take sukaji alert me nauyi,Daddy ma yayi murmushi yace"idan kun tashi daga aiki kuje gida ku kar6i tawa kyautar" Cikin farinciki suka fice daga dakin. Sai wajan qarfe tara nasafe aka sallamesu daga asbitin,'yan Jarida kuwa sunyi cincirundo agaban asbitin Jawad yarasa yanda akai sukaji,hakan yasa yaja Mayafin Mama Bilkisu yasake rufe Baby ruf babu wanda zaice Babyn tana hannunta. Har suka shiga mota qara da hasken camera ne yake tashi,Inaas de an dauki photon ta,amma babu wanda yaga Baby. Kafin azahar duniyar yana gizo ta dauka matar Jawad Mekudi ta haihu,photunan uwa da uba sai yawo suke,amma babu Photon Baby,harda masu dubo date din bikin suna cewa wata daya Inaas din ta qara akan na aurensu sannan ta haihu. Mutane sai kiran Jawad suke suna masa murna banda saqonni da'ake ta turo masa bayan sun samu labarin haihuwar awajan P.a lokacin da yayi posting ashafukan su inda yace ayiwa Babyn Addu'ah. Babu wanda baya nunawa Inaas gata,tana dakin Mummy anayi mata wankan jego irinna mutanan da,kullum Jawad yana wajan Babyn bashida aiki sai kissing dinta ko kunyar Mummyn bayaji. Saida ya shawarci Daddy akan sunan da zaisa wa yarinyar,sannan yayi mata hud'uba da JAMILA. Ranar suna kuwa aka rad'awa yarinyar suna Jamila,za'a dinga kiranta da Beauty a cewar Jawad d'in. Bilkisu tafi kowa farinciki,saboda har yanzu tana tuno irin zaman dasukai da Jamila. sassafe P.a yasake yin posting sunan Baby,dakuma sunan da kowa zai dinga kiranta dashi. Wannan posting na p.a saida wasu mutanan sukayi screenshot dinsa aka dinga dorawa a status ana rubuta comment aqasan screenshot din wannan yace da alama anhaifo balarabiya,wannan yace kaji wani suna wai Beauty to waye ba Beauty ba? Yayinda wasu suke cewa da alama de yarinyar ba qaramar kyakykywa bace shiyasa iyayenta suka 6oyeta sukaqi nunawa duniya photon Babyn. Tun safe Jawad yake jin alert yanata shigowa wayarsa wannan yace kudin Baby ne asiya mata chocolate wannan yace kudin keken koyon tafiyar Baby ne,wannan yace kudin pampers din Babyne,sosai yan'uwa da abokan arziqi sukai masa kara akan haihuwar Beauty. Kayan Baby dana maijego tun su Mummy suna gani har suka gaji dagani,banda kyautar da Inaas tasamu daga wajan Jawad din dakuma mutane,abun har yayi yawa. Bayan suna da kwana uku Jawad yabar qasar,kullum suna yin video call yana ganin Baby da Maman baby,Mummy tana jinsu saide ta to she kunnanta tana mamakin yaran zamani,wannan Jawad kenan shida baya magana baya shiga wasu sabgogin to idan Fu'ad ne Yaya za'a yi kenan?(🤔) Wannan karon Bilkisu ce da kanta ta zage take gyaran 'Yarta,gyara take mata na haqiqa irinnasu na Niger,kafin wata daya kuwa sunyi shar dasu itada Baby,sai alokacin su Fu'ad suka dawo,Baby tayi wani sabon uban, domin kuwa Fu'ad ma kullum yana wajan Baby bashida aiki sai de yayi ta yimusu photo, tun yarinya bata tsaida idonta akan camera harta saba.(🤭) Duk yanda yake daukar yarinyar a photo bai ta6a d'orawa awata kafa da za'a ce ga Babyn Jawad ba,saboda lokacin haihuwar duk yana ganin surutun da'ake tayi a yanar gizo akan rashin posting photon yarinyar. Bayan sunyi arba'in Jawad yadawo,suka shirya gaba dayansu gidan suka hau jirgi iyasu yasu family suka tafi jigawa. Acikin jirgin ma saida aka daukeshi photo kowa yana ganinsu yasan suna cikin kwanciyar hankali,Inaas kamar ba haihuwa tayi ba,duk wanda yaga wannan photo saiya fara dubawa ina zaiga Beauty? amma shiru kokadan babu alamar ta,hakan yasa wasu suke cewa to da alama de yarinyar wani ciwon ne da'ita shiyasa ba'a son nunawa duniya(😂) A dutse suka fara sauka,sannan suka shiga motoci suka nufi Hadeja,ta Gujungu sukabi,suka wuce qayyuka dayawa su marke,yalo,kwanar Auyo, suka shiga cikin Hadejia sannan suka dauki hanyar garin Galadima,suka wuce garin Galadima suka qaraso cikin Garin Malam. Ba qaramin tarba suka samu ba daga wajan mutanan gari,Bilkisu dake gefen Jawad tayi qasa da murya tace"Muhammad ga asalin garinku" Jawad yayi murmushi yanajin qaunar garin acikin zuciyarsa,kwanan su d'aya agarin,amma saida Jawad yayi qoqarin yin wani abu amatsayin sa na d'an garin,yabada aiki aqara musu famfon ruwa,titi babu kwalbati nanma yabada aikinsa,aka janyo musu sabuwar kwalta,sannan ya kar6i takardun samari masu n.c.e dakuma degree domin taimaka musu wajan daukarsu aiki. Wannan abubuwan da Jawad yabari ayi,ba qaramin cece-kuce ya janyo ba tsakanin Garin Galadima dakuma garin su Jawad din wato Garin Malam,suma yan Garin Galadima suna gani ai yaci ace suma anyi musu hakan suci albarkacin maqotaka,tunda sai an fara wucewa ta garin su, sannan a shiga Garin Malam din,su kuwa yan Garin Malam har wani buda hanci suke su ala dole Jawad d'in d'an garin su ne. Saida suka sake kwana acikin masarautar Hadejia sannan Washegari suka koma Abuja cikeda KEWAR karamcin dasuka samu daga Masarautar Hadejia. *** *** *** Bayan shekara uku. 'Dakin taron yacika sosai da jama'ah,na gida dana qasar waje,iyaye da yan'uwa da abokan arziqi,Na'im yana zaune shida matarsa agefe wadda take d'aukeda d'an qaramin ciki,Bilkisu tasake yin qiba hutu yasake zama da kuma jin dadi,Man Sulaiman yana gefenta sunyi shar dasu babu alamun tsufa atare dasu, Yayinda Mummy da Daddy ma suke zaune agefe d'aya fuskar kowa da farinciki,Abban Inaas yana Sanye cikin Suit yasake yin kyau kamar Balarabe,suna zaune hannunsa yana cikin na Surayya, Fu'ad da Noor ma suna zaune sunyi bala'in kyau da Baby boy dinsu me kamada Noor sak d'an shekara biyu. Kowa ya matsu afara taron hakan yasa Daddy yafara dube-dube yanaso yaga a'ina Jawad ya la6e ne kowa yanata faman jiransa? Tawagar mutanan daya hango sun shigo hall din dakuma yanda yan Jarida suketa faman daukarsa photo kamar shugaban qasa ne yashigo hakan ne yadauki hankalin jama'ah. Jawad ne yashigo cikin hall din yayi bala'in kyau cikin manyan kaya farare tas,Inaas tana gefen sa tasa farar laffaya me adon stone hannunta na hagu tana riqe da Babbar wayarta dawata hand bag me mutuqar kyau. Yayinda hannunta na dama take riqeda da hannun Beauty na hagu,shima Jawad ya riqe hannun Beauty na dama,ahankali suke tafiya saboda tafiyar Beauty tafiyar yara ce,daga Jawad har Inaas hankalinsu yana kan Babyn su fuskarsu cikeda Farinciki. Wannan shine karon farko dasuka nunawa duniya fuskar 'yarsu,saboda tsabar son labari irinna d'an jarida lokaci daya suka tsugunna dede tsowon yarinyar suka dinga yimata photo sai qaran camera wajan yake,yarinyar bata sababa,hakan yasa ta qamqame Inaas cikin tsoro,yarinyar tayi mutuqar kyau sosai cikin doguwar riga fara me adon net,net din rigar yabaje daga qasa,rigar batada hannu,sai dogon gashinta da akayi mata parking dinsa,anyi mata kwalliya harda janbaki pink,ba qaramin kyau tayi ba,sai yanzu ne mutane dayawa suka sake sanin dalilin da yasa Jawad yake 6oye yarsa,kuma sai yanzu ne sukasan cewa ashe ga dalilin dayasa yace za'a dinga kiranta da Beauty,haqiqa yarinya taci Sunanta. Ganin yanda ake cincirundon daukar Beauty a photo yaqi qarewa hakan yasa wani guard din Jawad din ya dauketa,yakaita wajan Fu'ad,Beauty tana ganin Young Mekudi wato takwaran Daddy yaron Fu'ad sai hankalin ta ya kwanta bata sake bi takan nata iyayen ba,daga nan kuma photo yadawo wajansu Fu'ad,saida suka gaji suka daina dan kansu. Bayan bude taro da Addu'ah Jawad yayi wa mutanan dasuka samu damar halartar wannan taro wanda dubban ma'aikatan sa suka shirya masa domin tayashi murna, kasancewar cikin wannan watan yasamu shiga jerin cikin sunayen mutum goma na masu kudin duniya. Yayi godia,yayi godia bisa wannan taro sannan yaqara da yiwa gomnatin Nigeria godiya bisa hadin kai dayake samu daga wajanta,yakuma yiwa gomnati alqawarin zai sauke farashin wasu kayan masarufi domin talakawan Nigeria,tareda daukan matasa aiki domin a ragewa gomnati wani nauyin. Daga qarshe yadauki duk wasu kula da harkokin kasuwancin sa na Africa ya damqashi a hannun qaninsa Fu'ad,daga rana irinta yau,Fu'ad shine yake da haqqin komai da komai na Africa,shine zaici gaba da kula musu da wannan 6angaren,shikuma Jawad zaiji da kasuwancin su na sauran qasashen duniya,wannan hukunci da Jawad ya yanke ba qaramin dadi yayiwa iyayensa ba,lokaci daya hall yadauki tafi. Fu'ad yatashi ya rungume Yayan nasa,yan Jarida suka samu nayi,sai daukarsu ake a photo. Daga nan suka dawo suka zauna akaci gaba da taro har aka gama taro lafiya. Bayan sun dawo gida suna zaune suna kallon labarai babu abinda ake nunawa sai photon Beauty,dayawa daga gidan TV da Radio maganar da ake kenan,mutane dayawa suna ganin matakin da Jawad din ya dauka na 6oye yarsa hakan shine daidai. Inaas ta sanya kayan bacci takawo wa Jawad coffee tace"yalla6ai gashi" Jawad ya kalleta dawani irin murmushi me salo daban daban yace"anjima zaki min bayanin dalilin dayasa kika fadi sunan nan" Inaas tayi masa hararar soyaiya, kafin tayi magana Beauty datake zaune tana sanye cikin Riga da wando na bacci irinna yara tana ganin photunan bikinsu Inaas a computer ta juyo ta kalli Jawad tace"Dad gaka ga Mom,amma babu ni" Jawad ya kalli Inaas yayi murmushi sannan yamaida dubansa wajan Beauty yace"yes,lokacin Mom dinki tanajin zafi" Beauty bata fahimci meyake nufi ba,tace"Dad zafi ake ko?" Jawad yayi dariya yace"eh" Beauty ta maida hankalinta kan kallon photunan,Inaas ta harari Jawad ta zauna agefensa,yayinda ya zuro hannunsa ta bayan qugunta ya rungume ta,Inaas tayi qasa da murya tace"miye hakane?" Kallonta yayi,cikin sigar rad'a yace"Matar Yalla6ai,Yalla6ai fa a hannu yake,yau satina d'aya da dawowa har yanzu babu wani labari,Beauty bata bacci dawuri,bana samun damar dazan huta dake,kinsan cewa kuma nayi qoqari ba d'an qarami ba,see my legs" Inaas tayi ajiyar zuciya ahankali takai dubanta zuwa tsakanin cinyoyinsa,lokaci d'aya ta tabbatar da maganar sa duk da yana Sanye cikin sutura hakan bai hana idan ka kalli wajan kakasa gane halin da mijin nata yake ciki ba,saida tagama ganin yanayin sa sannan yamaida qafafunsa ya had'esu waje d'aya ya6oye abunsa. Ta saussauta murya zata masa magana saide kafin tace wani abu Beauty tataso tazo wajan Jawad tahaye jikinsa itama tace"Dad" Jawad ya had'esu duka su biyun itada Inaas ya rungume sannan cikin soyaiya ya kalli Beauty yace"Na'am Beauty" Cikin sauri tace"Dad a school dinmu ko,? idan nace my name is Beauty sai school mates dina suce wai Beauty is not a name,Dad why?" Jawad yariqe fuskar Beauty yayi kissing goshinta sannan yace"Ki dinga fad'a da comfidance d'in ki cewa your name is Beauty,Dad dinki ne da kansa yasa miki Sunanki Beauty Because You're Beautiful" ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻 [1/24, 20:34] My Number: ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,idan kika karanta ba tareda kin biya ba keda Allah saboda ban yafe miki ba. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. 31&32 Jin jina da dubun godia agareku,haqiqa kun taka rawar gani wajan taimako na ta hanyar bincike wajan ganin na kammala wannan littafi. Sister Wasila nagode da yanda kika taimakeni wajan fadamin abubuwan da bansaniba na qasarku,gidan radio na qasa,al'adu dakuma ruwan dakuke amfani dashi(DALLOL) yanda mutanan qasar Niger su manager suke bawa Jawad gorar ruwan Dallol,nima muddin nazo qasar Niger zan nemi ruwan gorar Dallol nasha 😜 ban manta dakaiba Yaya salahuddeen yanda ka taimaka wajan fadamin wasu daga cikin sunayen garuruwan qasar Niger,da taimakon labari ya qara armashi😍 Saboda haka na sadaukar da page izuwa gareku💃🏻. ____ Beauty zata sake magana Inaas tace"shiru!,muje ki kwanta" Jawad yamiqe da Beauty a hannunsa suka wuce daki,saida suka lalla6a ta tayi bacci,sannan Jawad yaja Inaas jikinsa ya rungume ta tabaya,rad'a yafara yimata a kunne yace"yarinyar nanfa surutun ki tabiyo,idan tafara magana abun har mamaki yake bani,kema haka kike kina qarama ko?" Cikin shagwa6a Inaas tace"nifa bahaka nake ba" Cikin jin dad'in shagwa6ar tata ya lumshe idonsa,ahankali yafara kissing dinta cikin jin dad'i,batare da 6ata lokaci ba itama tasaki jiki suka fara mayarwa juna martani,saida suka gama fita hayyacinsu Jawad yafara sakin wani irin nishi,hakan yasa Beauty tatashi,cikin muryar bacci tace"Mom" Daga Jawad,har Inaas sai kowa yayi d'if suka dakata da abunda suke,ahankali Inaas ta matsa daga jikinsa takoma can gefe kusada Beauty tana bubbuga bayanta,Beauty tashige jikin Inaas ta qanqameta sannan taci gaba da bacci. Jawad ya lumshe idonsa yana sakin numfashi a jejjere,ahankali ya matso jikinta daga bayanta yaci gaba da shafa wuyanta,cikin rada yace"kidawo mana" Inaas ta kalli Beauty duk da duhu ne sannan ta girgiza masa kanta alamun a'a,cikin 6acin rai ya kaiwa gadon duka sannan yajuya bayansa yadena kallon inda suke kwata-kwata,gaba d'aya hankalin sa atashe yake,sai had'a uban gumi yake yana cizon lips,da qyar yasamu yayi bacci bayan yaga itama Inaas din ba tashi take ba, ta kama 'yarta sunyi baccinsu. Da asuba baije masallaci ba,afalo yayi sallah,ko takan Inaas baibi ba yatashi yashiga toilet yayi alwala yawuce falo,har gari yafara haske yana zaune akan sallaya yarasa mafita,wayarsa dake gefe tayi haske alamun shigowar saqo,saqon yaduba yaga P.a ne yake sanar dashi yau sunada meeting da manyan 'yan kasuwar Malesia,saboda haka jirgin su zai tashi qarfe goma nasafe. Jawad ya runtse idonsa,yakai hannu yata6a qasan mararsa yaji bawani sauqi tun daren jiya,haka ya sunkuyar da kansa qasa yarasa tunanin da zai kama. Inaas tafuto falon zata duba fridge ta ganshi a zaune,cikin mamaki tace"Qauna dama bakaje masallaci b...." Kafin ta qarasa maganar da zatayi yawani irin fuzgota,tafad'o kansa,nan take yafara yamutsa ta,batayi masa musu ba,domin kuwa itama kanta a hannu take,sosai take tayashi gudanar da abubuwan,hakan yasa yafara zame mata kayan jikinta,lokaci d'aya,sukaji Muryar Beauty tana fad'in "Mom,natashi" Cikin sauri Inaas tatashi tsaye tana gyara hijabin jikinta,yayinda Jawad yaji wani irin abu yatsaya masa awuya,jiya ke kamar ya fashe da kuka. Inaas ta qarasa wajan Beauty tace"kin tashi? muje ki gaida Dad sai ayi wanka ko?" Beauty ta qarasa wajan Jawad ta shige jikinsa tace"Dad,inaso muyi wasa" Jawad da idonsa yake a lumshe cikeda 6acin rai yace"Beauty...please leave me alone" Beauty taturo mitsitsin bakinta gaba,kamar yanda uwarta takeyi sak,sannan ta kalli Inaas tafashe da kuka. Inaas tajata jikinta tafara lallashinta tace"yi haquri,muje kiyi wasan dani,Dad baida lafiya" Cikin kuka tace"ni da Dad d'ina nakeso muyi" Inaas ta lumshe idonta tabude sannan ta sunkuya dede tsawon yarinyar yace"Beauty,bakyason Dad ya warke?" Cikin kuka tace"ina so" Inaas tace"to kije wajan Mama,kice kinzo kuyiwa Dad Addu'ah keda ita,ta dinga fada miki addu'ar kunayi tare,kafin kidawo ya warke,saikuyi wasan ok?" Cikin sauri Beauty ta goge hawayen idonta sannan taje wajan Jawad tayi masa kiss,tafice da gudu daga falon tatafi wajan Mama Bilkisu. Inaas tasaki ajiyar zuciya ta kalli Jawad tace"wai dan Allah Qauna meyake damunka ne? kaine ka sabawa yarinyar nan da wasa dakai,meyasa zaka dinga yi mata magana haka? zatayi tunanin wani abu kokuma tasa damuwa aranta" Cikin 6acin rai Jawad yamiqe tsaye yace"amma nafada miki halin danake ciki,almost 8 day's ina yin bacci daqyar,kinsan yanayi na,amma haka zaki juya min baya ki rungume 'yarki kuyi bacci,danayi bacci da karnayi duk ba damuwar ki bace,ai kinsan hanyoyin da zakibi yarinyar taje wani wajan,amma bakiyi ba,yanzu dakika so ba gashinan kina mata magana ta jiki ba,yanzu kinji dad'i?,anjima zan bar muku qasar,saiki sata agaba kiyi ta rungume ta kinajin dad'i" Bai saurari amsar ta ba yawuce dakin yafara loda kaya acikin jaka kamar wanda zaiyi tsaraba da kayan. Inaas tabiyo bayansa daki ta dakata daga bakin qofa tana ganin yanda yake loda kaya ajaka daga gani ba'a hayyacinsa yake ba,6acin rai ne yasa shi loda wannan uban kayan shida ko wacce irin tafiya zaiyi baya daukan komai bayan takardu? Jawad yana ganin shigowar ta d'akin yaci gaba da sababi yana fad'in"kwana takwas mutum yana fama da abu d'aya saikace marar iyali? garama mutun yayi tafiyar sa,ko aure ne mutum yaje yanema" Inaas ta harde hannunta a qirjinta ta kalleshi,taga abun nasa sai qara gaba yake,sai wata magana yake yana fad'in mutum,mutum, tasaki ajiyar zuciya tace"Qauna wai dama an ta6a fad'ama cewa ina tsoron kishiya ne?"(🤭) Cikin 6acin rai ya kalleta yace"ok haka kikace?" Tace"yes" Baisake cemata komai ba yaci gaba da loda kaya ajaka,Inaas tajuya tafice tabar masa dakin,taje ta rufe qofar falon nasu da key,sannan tabude fridge ta dauko wani tsumi wanda aka aiko mata shi daga Niger,yanayin aiki cikin sauri,ta d'aga bakin gora tasha sosai,sannan ta maida cikin fridge takoma dakin, Jawad yanajin shigowar ta ko kallon inda take baiyi ba,kayan jikinsa yafara cirewa zai shiga wanka,saida ya cire kayan yarage daga shi sai gajeren wando,sannan yanufi toilet din,Inaas ta kalleshi,takai dubanta zuwa ga gajeren wandon sa gashinan qiri-qiri tana ganin komai gajeren wandon bai rufa masa asiri ba saima qara tona masa asiri dayayi saboda bashida kauri santsi ne da wandon. tasaki ajiyar zuciya, shida yake cikin wannan halin shine yake fada yana sababi. Yakama handle din toilet din zai shiga tayi sauri ta qarasa ta rungume shi tabaya,ta dora kanta abayansa,sannan takai hannunta kan qasan marar shi tariqe sosai tana yi masa wani irin matsa,cikin wata irin murya tace"fishi baya yimaka kyau Qauna..." Jawad dake cikeda 6acin rai ya lumshe idonsa saboda dadin dayake ji sakamakon yanda take masa,yanaso yaraba jikinsa da nata amma yakasa,so yake ya tureta daga jikinsa ya nuna mata laifin data masa amma kokadan yakasa sakamakon yanda ta riqe abunsa tanayi masa wani abu wanda baisaba ji tanayi masa makamancin haka ba. Daqyar yabude bakinsa cikin muryar kasala yace"bari...,kibari fa nace" Yafadi hakan yana sakin wani irin numfashi tareda sake lumshe idonsa. Cikin shagwa6a Inaas tace"ni bazan bari ba..." Wani irin numfashi Jawad ya sauke cikeda jin dad'in abinda take masa yace"niki denamin banaso faaaa...." Inaas tad'an kalli idonsa taga a lumshe idonsa yake kuma sarai yanajin dad'in abinda take masa,hakan yasa cikin wani irin salo tasakar masa kukan shagwa6a wanda yasake jefa shi cikin tsananin buqatar ta, cikin muryar jin dad'i yace"me kike buqata namiki danki rabu dani?" "nide ka barni nikad'ai,kadena min zancen kishiya" Cikin jin dad'i yace"saboda kinga kin riga kin zama ni shiyasa kika raina Yayanki ko?" Qafafunta tafara bubbuga wa aqasa cikin shagwa6a tana sake goga masa nashanunta a bayansa sannan tace" Yaya na dena fa" Idonsa a lumshe yace"ni banga hakan ba,ki nuna min a aikace nagani" Murmushi tasaki tace"yanzu zaka gani" Tana fadin haka taja gajeren wandon nasa yayi qasa. Basusan cewa sun dauki lokaci suna abu daya ba saida suka kalli Agogo,sannan ne ya dauketa cak fuskarsa cikeda annuri suka shige toilet sukai wanka,bayan sun shirya taga ko kallon jakar kayansa daya hada ba yayi tace"Qauna ga jakar kayanka fa" Jakar ya kalla yace"kinga ni bansan ma nahada kayan ba,maidasu kawai" Inaas tayi murmushi tamaida kayan,sannan tahada yan qananun abubuwan datake buqata tace masa "muje Qauna,nikam nagama shiryawa,idan muka yiwa Ammiy sallama saimu dauki Beauty mutafi" Cikin mamaki ya kalleta yace"ina zakije? hutun fa?" Ajiyar zuciya tayi ta kalleshi tace"mijina yafiyemin duk wani hutu da zanyi,zan bika mukoma na haqura da hutun,saimu koma muhuta tare" Cikin jin dadi ya rungume ta,daga nan suka sauko qasa,abinci suka fara ci, yayinda Mummy take bawa Jawad abaki. Adede lokacin su Bilkisu suka shigo,Beauty tatafi da gudu wajan Jawad tace"Dad ka warke ko?" Jawad ya shafa fuskar Beauty sannan yace"sosai Babyna" Yadauketa ya d'orata akan cinyarsa. Bayan sungama cin abinci Inaas ta kalli Ammiy da Mummy tace"nafasa yin hutu Ammiy,zamu koma yanzu" Bilkisu tace"yanzu-yanzu? ko sati biyu fa bakuyi ba" Jawad yace"wallahi Mama anyi min kiran gaggawa ne,inada meeting anjima" Mummy tace"to Allah dai yatsare,Allah yakare mana ku" Atare suka amsa da "Amin" Jawad yayi gaba yana kiran wayar Fu'ad,cikin sauri Inaas ta shirya Beauty suka futo gaba dayansu harda Noor matar Fu'ad dakuma Abban ta da Anty Surayya,Daddy yana tareda Jawad agaban motar,yayinda Inaas take gefen Bilkisu,saida taga babu kowa akusa dasu sannan tace"Ammiy akwai matsala idan mun sauka zan kiraki" Bilkisu ta riqe hannunta tace"fadamin meyake faruwa?" Inaas ta qaqaro murmushin dole tace"Ammiy bawani abu bane babba,ki kwantar da hankalin ki,zan kiraka idan munje" Bilkisu tasaki ajiyar zuciya sannan tace"dazaran kun sauka ki kirani" Inaas tace"to Ammiy" Daga nan ta rungume ta,taqarasa wajan su Mummy ta rungume Mummy da Noor da Anty Surayya,sannan ta yiwa iyayen nata maza sallama tashige mota,Shima Jawad saida ya qaraso ya rungume Mummy,sannan ya qarasa wajan Bilkisu itama ya rungume ta tsam ajikinsa tareda lumshe idonsa yace"Mama ki mana Addu'ah,wannan lokacin ba zamu dawo da wuri ba,zamu dade sosai" Bilkisu ta shafa bayansa tace"adduah kullum ina cikin yimuku ita kaida qanwar ka Muhammad,ka dinga haquri da'ita kaji? Inaas yarinya ce,Allah ne yabata haihuwa da girman jiki dawuri,kaja qanwar ka a jikinka karnaji wata magana" Jawad yasaki wata irin ajiyar zuciya sannan yace"insha Allah Mama,sannan idan kina buqatar wani abu kimin waya" Daga nan yasaketa yashige mota suka tafi,babu wanda yabar wajan saida sukaga ficewar motarsu daga gidan tukunna. Suna sauka a Malessia yawuce wajan meeting,sun dauki lokaci sosai suna meeting sannan yadawo gida agajiye,kwanan su daya Washegari suka koma Qatar. Saida tasake gyara gidanta tsaf,tashirya shi yatafi wajan aiki,sannan tasamu nutsuwa ta zauna ita kadai bayan tahada Beauty da kayan wasa, takira Bilkisu. Cikin sauri Bilkisu ta dauka tace"Inaas kin sa nakasa nutsuwa,fad'amin menene yafaru? banason jin matsala a tsakanin ku kokadan" Inaas tasaki ajiyar zuciya ta lumshe idonta sannan tace"Ammiy Yaya ne" Cikin sauri Bilkisu tace"me Yayan naki yayi? Fad'amin" Inaas tace"Ammiy mun samu sa6ani ne dashi tun muna gida,shine yake cemin zai iya qara aure,hankali na yatashi Ammiy,ina tsoro karya fara kula wata" Bilkisu ta lumshe idonta tasaki ajiyar zuciya bayan taji kanun zancen sannan tace"Inaas,duk irin son da namiji yake miki karki sake kisa aranki cewa bazai qara aure ba,soyaiyar da Babansa ya nunamin ban ta6a tunanin cewa zai iya tafiya yabarni ba,saboda haka ki nutsu,ki iya takunki,idan ma auren zaiyi ai duk wacce ta'iya allonta saita wanke,fadamin menene yasa yafada miki hakan? yace miki yafara neman auren ne?" Cikin sauri Inaas ta goge hawayen idonta sannan tace"A a Ammiy,Beauty ce bata bacci da wuri,idan yazo wajena yarinyar bata barinsa,saida mukai haka dashi lokuta da dama,har mukazo gida hakance take ta faruwa har yazo yana yiwa yarinyar fad'a,kuma bai ta6a yimata fad'a ba,shine nayi masa magana akan fad'an dayayi mata,shine yace min shiya gaji,yanada iyali kamar bashida su,ya dinga fada shine yace garama yaje yanemi aure kawai" Taqarasa maganar tana sake fashewa da kuka harda shashsheka. Bilkisu tayi shiru tana jinta,saida tabarta ta danyi kukan,nauyin zuciyar ta yaragu,sannan tasaki ajiyar zuciya tace"Kukan ya'isa haka,yanzu ina Jamilan take?" Inaas ta share hawayen idonta tace"tana falo na kunna mata kallo, nabata kayan wasa" Bilkisu tace"to ai wannan matsalar da kin fad'amin ita da tun tuni kin kawar da'ita da kanki Inaas,meyasa kuke kwana tare da'ita? shekara uku yakamata kidena kwanciya da'ita,sannan tanada bala'in wayo ga surutu,duk wani abu dazakuyi kidinga taka tsantsan da yarinyar karta ga wata alama" Inaas tace"Ammiy tun kafin takai haka nace masa zata dinga kwanciya ita kadai shine yacemin tayi qanqanta mu barta ita kadai,wai bazan bar masa Babynsa ita kadai ba rashin tausayi ne" Bilkisu tace"to dole yanzu ki barta ita kadai,inda baku fara fuskantar wannan matsalar ba toda sauqi,yarinyar nan da wayon ta,da surutun ta,an dade da yayeta sannan wayon ta zaisa wasu suce tafi shekara uku,idan baku dena kwana da'ita ba to duk abinda taji, kota gani kunayi kusa aranku zata fadawa wasu,saboda haka ki lalla6ashi ki nuna masa illar kwanciya tareda ita" Inaas tasaki ajiyar zuciya me nauyi sannan tace"to Ammiy,kuma batasan yin bacci da wuri ma" Bilkisu tace"seta mata komai zakiyi Inaas,tun yanzu ya kamata kidinga tsara mata lokacin bacci dana tashi,tana yin baccin rana ne?" Inaas tace"eh tana dawowa daga school nake sata tayi bacci saboda qwaqwalwar ta tahuta" Cikin sauri Bilkisu tace"toki dena, karki sake bari tayi baccin rana,sannan duk inda qarfe takwas na dare yake kije kisata ta kwanta kiyi mata Addu'ah,wannan gajiyar datayi da rana shine zaisa nan da nan bacci me nauyi zai dauketa,ki gwada wannan shawarwarin,idan sunyi shikkenan,idan ba'a dace ba saiki sake kirana" Inaas tasaki ajiyar zuciya tace"to Ammiy insha Allah zanyi tun daga yau ma" Bilkisu tayi murmushi tace"yawwa,kuma adena tsoron kishiya,koya sake yimiki zancen ki danne kishi ki nuna masa kinaso yayi auren,kuma duk lokacin daya zo miki da buqata ki nuna masa aike kinma fishi,dayake miki mita yana cewa mutum yanada iyali kamar bashi dasu saiki nuna masa cewa kema ai hakan kika gani,ki nuna masa ko de bayarda Beuaty din zakuyi tadawo Nigeria danki dinga sauraren sa? Idan kika nuna masa kin fishi shiga damuwa akan komai to jikinsa zaiyi sanyi,ki tabbatar kinsa ya manta da wannan furucin nasa na batun qarin aure, dole saikin koyi kissa qarfi da yaji kinji abinda nafad'a miki ko?" Inaas tayi murmushi tace"naji Ammiy,saikin jini" Bilkisu tace"to Allah yayi muku albarka,Allah yasake had'e min kanku" Inaas tace"Amin Ammiy" Sannan ta kashe wayar tayi ciki. Bilkisu tadafe kanta a fili tace"kaii yaran zamani,wannan yaro ka gado jarabar ubanka qarfi da yaji,haba wannan abu har ina" Man Sulaiman yana jinta yayi murmushi,baice mata komai ba. **** Inaas tana komawa falo taga Beauty harta fara bacci,cikin sauri ta qarasa ta tasheta,yarinyar sai shagwa6a take mata amma haka ta hanata wannan bacci,qarshe ma qananun kaya tasaka musu suka futo compound d'in gidan suna wasa,har wajan yamma batabar Beauty tayi bacci ba. Jawad bai dawo da wuri ba sai dare,kafin yadawo Inaas ta shirya cikin wasu arnan kayan bacci,tasha magungunan ta masu kyau da inganci tana lalla6a Beauty kamar yanda Ammiy tafada mata. Yana shigowa falon alokacin Beauty har bacci yafara nisa,hakan yasa Inaas ta kalleshi tace"Zan kaita dakinta,acan zata kwana yau" Jawad daya qura mata ido yana ganin yanda kayan baccin nata yayi mata mutuqar kyau,bai iya yimata musu ba, har takai Beauty daki tadawo falon,itada kanta tabashi abinci, sannan sukaje yayi wanka,tun kafin yasaka kayansa yana daure da towel dauketa cak,ya zauna abakin gado sannan ya d'orata akan cinyarsa,yazura hannunsa cikin rigar baccin ta yayiwa nashanunta wata irin damqa sannan yace"yau mun yaye Beauty ne?" Inaas tayi masa wani fari da'ido sannan ta saqalo wuyansa da hannayen ta tace"Naga alama Dad dinta bazai yaye taba,nikuma ina cutuwa sosai idan tana nan, mijina bayamin service yanda nakeso" Wani irin dad'i yakama Jawad,har ya kasa 6oye hakan akan fuskarsa,yayi sama da hannunsa dake cikin rigar ta yakama nipples dinta yana murzawa sannan yace"tunda Mom dinta tafad'i haka shikkenan,bazan shiga haqqin Mom dinta ba,za'a dinga service dinta yanda takeso,Love inaso kibani dama idan kin qare semester dinki ta qarshe,inaso in dauko Junior yaron Fu'ad,zasu dinga tafiya makaranta shida Beauty,inaso in kula da yaron ta yanda zai gajeni nida Daddy,yanda Fu'ad yasaka masa sunan Daddy inaso in tabbatar da wannan sunan,inaso sunan ALIYU MEKU'DI,yasake dawowa akaro na biyu,inaso in yiwa yaron horo irin wanda Daddy yamin,inaso yazama Babban d'an kasuwa fiye da ni da Daddy, amma idan kin bani dama" Inaas tayi murmushi tace"Qaunah ni duk wannan maganar nariga nagama amin cewa,inaso mutane sudena kiransa da junior, nanda wasu yan shekaru su dinga kiransa da YOUNG MEKU'DI, but.... nide kaji dani yanzu,a hannu nake fa" Cikin tsantsar jin dadi Jawad yayi mata wani irin kallo,ahankali ya matso da fuskarsa harya had'e fuskokin su,yajefa bakinsa cikin nata,Inaas tana jinsa bata fara maida masa martani ba,saide kuma tana tuno shawarar da Bilkisu ta bata,cikin sauri ta hanashi komai,taci gaba da sarrafa shi cikeda zafin nama,hakan ne yasake tabbatar wa Jawad cewa lalle da gaske take,ashe yana shiga haqqin ta batare daya sani ba,ashe itama abun yana damunta,ashe kwanciyar su tareda Beauty ba qaramin jin dadi yake ragewa kansa ba. Lokaci d'aya yasaka hannunsa yayaga rigar jikinta,ya qwace bakinsa daga cikin nata yadora shi kan nashanunta,kasancewar sun dade basu sake kamar haka ba, hakan yasa gaba daya suka fita hayyacinsu sai nishi suke suna surutai,da tafiya tayi tafiya sai Jawad yakoma yin ihu sakamakon wani iri dad'i dayaji saboda magungunan data sha. Sai wajan qarfe uku na dare sannan suka gama round na uku,Inaas ta gaji mutuqar gajiya amma ko kad'an bata nuna masa ba,saima kallonsa da tayi cikin qwarin gwiwa tace"Qauna bade kagaji bako? nide...uhm" ta qarasa maganar cikin shagwa6a. Jawad yasake rungume ta yace"Love ashe haka nake shiga haqqin ki bansaniba? kiyafemin kinji?" Inaas tayi qoqari ta 6oye gazawarta bata bari yagano taba,tasaki wani irin murmushi sannan taja hannunsa ta d'ora akan nashanunta,babu musu Jawad yafara matsawa cikin dad'i sannan ya kalleta yace"Love yau kin fita daban,qarfi da yaji kin goge min hadda,kin shafe min batun qarin aure daga cikin qwaqwalwa da zuciya ta" Inaas tayi murmushi tace"yaza'ai nayi wasa da kyautar da Allah yamin? Qauna banason gazawata tasa ka qara aure,saide ka qara dan niyyar kanka" Jawad yasake matsa nashanunta sannan yace"kicire wannan batun aranki Love,6acin raine yasa nafad'a,kin riga kinzama ni,rashi na akusa da mahaifiyata yasa kece kikaci gaba da 'DEBE MATA KEWA,kika zama kamar qawarta,tayaya zan iya kawo wata matar tashiga tsakanin wannan aminan guda biyu?,bazan iya yiwa Love d'ina kishiya ba,because you're so sweet takowanne 6angare,har gida ake kawomin photunan mata amma ke kad'ai nagani a cikinsu,inaso kisani aiki nama bazai bani lokacin kallon mata ba,ke kad'ai kin isheni,wannan abun nede bansan yaushe zai isheni ba...." Yaqarasa maganar yana shafa qasan mararta. Inaas tasaki wata irin wawiyar ajiyar zuciya sannan tace" I'm ready ai, muje round na hud'u " Jawad yace"Really?" Inaas ta lumshe ido ta bude sannan tace"yeah..." Cikin son tabbatar wa Jawad yace"Are you sur...." Kafin yagama cewa sure,Inaas ta had'e bakinsu waje d'aya.(🙈) (to da alama de wannan round d'in nasu bazai qare ba🤔saboda haka Amina de da gudunta🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️tatafi round d'in hutu,sai mun had'u a sabon littafi na nagaba me suna MATAR ABBANA, insha Allah. TAMMAT BI HAMDULLAH Anan na kawo qarshan wannan littafin nawa mesuna ME DEBE KEWA,ina fatan ya DEBE MUKU KEWA yanda ya kamata. sannan idan da wanda na 6atawa rai sanadin wannan labarin to yayi haquri ya yafemin d'an Adam ajizi ne.🙏 mutanan da suka nunamin soyaiya suka sai littafi na banida bakin dazan gode muku,wasu sun siyane saboda yanda aka saba da juna, wasu sun siya saboda dadin labarin, wasu sun siya saboda soyaiyar su agareni,wasu sun siya fiyeda yanda na yanke kudin labarin,wallahi banida bakin dazan gode muku,tunda nake rubuta littafin kudi ban ta6a haduwa da fan's din dasuka riqemin Amana basa fitar min littafi kamar Kuba,hakan ba qaramin dadi yamin ba,duk da nasan cewa Ana fitar dashi din,Danni ma da idona nagani, amma beyi fitar da mutum zaiyi tunanin ba littafin kudi bane,wallahi naji dadin hakan yanda bakwa zato. Gashi anyi littafi lafiya angama lafiya babu wani tashin hankali babu raina juna,anfara lafiya angama lafiya babu wanda akai tashin hankali dashi hakan yamin dadi sosai,yanda muka hadu acikin wannan littafi ubangiji Allah ya hadamu acikin aljanna madaukakiya, ubangiji Allah yabarmu tare,Amnah tana tare daku akoda yaushe,ina yinku sosai. Kada ku manta da MATAR ABBANA,yana nan zuwa😜 Nagode 🙏 ME 'DEBE KEWA littafin kud'i ne,inde baki siyaba kika karanta min banyafe ba, keda Allah. 300 ne kacal,zaki biya ta wannan account number 0164549488 Amina muhammad GTbank Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034 Tareda shedar biya ta wannan number 08033300034. Amnah El Yaqoub✍🏻