NAGODE BOOK 2 PAGE 1 "Alhaji! Alhaji!! Alhaji!!!" Taratsi da kwaroroton Binta ya maido shi daga cikin duniyar tunanin daya lula. Ya yunƙura ya zauna da kyau yana cije baki saboda yanda bayansa ya ƙage, baya iya dogon zama tun Hatsarin daya samu shekaru goma da suka wuce a hanyarsa ta zuwa Kaduna Jana'izar Alhaji Zakariyya Mahaifin Binta shikenan yake fama da Baya dukda iyakar bincike ance babu abinda ya samu bayan nasa amma kam yana ji a jikinsa ga kuma shekaru da suka miƙa wannan yana daga abinda yake ƙara ta'azzara masa ciwon. "Alhaji lafiya kuwa? Nakusa minti goma tsaye akanka ina magana kayi shiru badan idonka a buɗe yake bama ai ɗauka zanyi ka mutu" Bintan ta sake faɗa tana zama a gefensa. Ya tsura mata ido, ya rasa dalilin daya saka ranar Allah ba zata fito ta koma ba tareda Binta ta kawo zancen mutuwarsa ba, ya rasa meya tsare mata a duniya da take cike da burin taga ya kau. "Kaci abinci ma kuwa? Koda yake la'asar sakaliya yaci ace kaci abincin rana ai" tayi tambaya kuma ta bawa kanta amsa tana tashi tsaye ta nufi firjin dake cikin Makeken Bedroom ɗinsa me kama da Turakar wani sarki. Ruwan gora ta ɗauko da Kofin tangaran da suke jere a saman firjin ta dawo ta zauna tana tsiyaya masa data gama ta miƙa masa babu musu ya karba dan yana buƙatar ruwan. "Ya kukayi to? An samu kuɗin sun fito?" Ta jefa masa ainihin maganar data shigar da ita gurin nasa. Ya kurɓe ruwan yana gyara zama yace "Ba'a samu ba, yace besan inda suka shiga ba kuma na yarda Aminu baze yimun sata ba dan haka maganar ta ƙare dukma wanda yayi sama da faɗi dasu shida Allah kuma a sannu wata rana asirinsa ze tonu" "Kace me? Miliyan dubu dari biyun harda ɗori kake cewa kabar mutum da Allah akanta Lallai ma Alhaji, tsaya ma, yanzu kai har kana da bakinda zaka shaidi Aminu? Yaushe ka zauna dashi da har kasan halinsa da zakace bazeyi maka sata ba?" Binta tayi maganar a zabure. Alhaji Audu ya kalleta sheƙeƙe yace "Waini nawane kasonki cikin kuɗin nan Binta da duk kika bi kika tashi hankalinki kamar ma kin fini damuwa da abinda ya faru?" "Ni kuwa nake da kaso a ciki, karka manta Yara goma na ƙyanƙyashe maka a gidan nan ga Takwas nan a raye cikinsu kuma Zarata shida duk mazane kaga kuwa ni nake da Kaso a cikin dukiyarka kuma bazan zuba ido ina kallo a ringa damfararmu sannan kayi shiru kace ka bar mutum da Allah ba" ta bashi amsa tana kaɗa jiki tareda juya ido kamar wata ƙaramar yarinya, ya buɗe baki ze bata amsa sallamar Momy ta dakatar dashi seya haɗiye abinda yayi niyyar faɗa ɗin ya amsa sallamar ta ƙaraso ciki hannunta ɗauke da ƙaton Try. Akan Centre table dake tsakiyar ɗakin ba tareda ta nuna tasan da zaman Binta a gurin ba ta kalli Alhajin fuska babu yabo babu fallasa tace "Ai bansan ka dawo ba seda nake nake cewa shiru kace kuma ba daɗewa zakayi ba sannan Baba Bilki tace ai ko taji shigowarka tunɗazun ta zata na sani shiyasa batayi mun magana ba" abincin ta shiga zubawa ta gama jere komai ta sauke kulolin daga kan Teburin sannan ta tura masa shi gabansa yanda zeji dadin cin Abincin. Wani ruwan ta sake dakkowa daga firji ta ajiye masa Binta dai kallonta take tana zare ido a ranta tana tunanin wai ya akayi ta gaza korar wannan sailubar matar har suke dosar shekaru Arba'in tare a matsayin Kishiyoyi? "Bari nayi sallar La'asar se naci abincin" Alhaji Audu ya faɗa kafin ya yunƙura ya shige banɗakin dake manne da ɗakin barcin nasa. Momy ta zauna kan doguwar kujera kwaya ɗaya dake cikin ɗakin Hajiya kuma har sannna tana zaune kan gado tana ƙarewa Momyn kallo kamae wata farin shigar Maita har Audu ya fito ya tada sallah ya idar ya hau kan abincinsa Binta na zaune ita kuma Momy bata ce mata ta fita ba dukda zaman nata ya ɓata mata rai. Har a yanzu da shekaru suka miƙa tsakanin ita ko Rabi babu wadda ta isa ta shiga Turakar Alhajin a ranakun girkin Hajiya Binta amma ita ko a kwance suke tana iya faɗo musu a yanzu ne kuma Alhaji Audun yake son ya gyara wannan barakar har yake ƙoƙarin taka mata burki wasu lokutan sedai a banza domin ta rigada ta raina shi, bashi da wani kwarjini ko Martaba a idonta da zw ce tayi abu tayi ko ya hanata ta hanu har ila yau kuma zancen tayi laifi ya mata faɗa kamar yanda yake musu fa babu shi, ita lamarin Alhaji da Hajiya Binta ma har rasa matsayin da zata ajiye shi takeyi dan ko a labarai bata taɓa cin karo da Macen da take zuba sharafi a gidan Auranta irin Hakiya Bintan ba. "Ina kin gaka abinda ya kawoki?" Muryar Audu ta ratsa kunnuwansu, Momy na danna waya ta ɗago so take ta fahimci dawa yake a cikinsu? Ita me girki ko kuwa Binta data zo ta tasasu gaba? Hamshaƙiyar kuwa ƙara gyara zama tayo dan a tsammaninta da Aishar yake seda ya sake maimaita maganar yana kallon idonta kafin ta ankare, ta buɗe baki zata faɗa masa ba dadi se kuma ta gimtse data tuna tanada shirin da take so ta cimma seta miƙe tsaye tana murmushi tace "Ai to bari naje, duk na shafa'a ne wlh se naga kamar a Ɗakina nake". Tana dafda fita daga ɗakin wayar Momy tayi ƙara alamar shigowar kira, Hajiya ta fice amma ta coge a bakin ƙofa ta kasa kunne, abin ya rigada ya zame mata Ɗabi'a ko ace ciwo, gulma da Laɓe, tsabar yanda ta ɗorawa kanta bala'i ko a hanya take tafe taji wasu na ƙusƙus seta dakata ta kasa kunne ko ba zataji ko ta fahimci abinda suke faɗi ba, ga zargi da tsarguwa ko yayan cikinta taga suna magana seta tsargu da ita suke ko wani abun suke shiryawa. A cikin ɗakin kuwa a speaker Momy ta saka wayar saboda kunnenta dake mata ciwo kwana biyu bata kara wata a kunnen muryar Ahmad ta ratso wayar yana cewa "Momy, kin masa maganar kuwa?" "Tukunna dai, wai idan sauri kakeyi haka ka tareshi da kanka kayi masa maganar mana seni zaka mayar yar aikenka" ta bashi amsa. Daga waje Binta ta sake manna kunne a jikin ƙofa tunda taji muryar Ahmad da kuma cewar anyi magana wace maganace? Abinda take so kunnuwanta su zuƙo mata kenan. Ahmad ya sake marairaicewa Momy yana cewa "Haba sweet mother, haba rabin raina kinsan dai bazan iya tunkararsa ba kuma na gaya miki Jafar ya masa magana yace he will get back to us yanzun kusan one month kenan bamuji komai daga gareshi ba and time is really against me Momy, idan baze samu ta hanyar sa ba na sani na nemi wani Alternative ɗin kinji Mamana? Ya ƙarasa maganar kamar ze saka mata kuka yana idarwa kuma tari ya sarƙe shi" "Bakaje Asibitin da nace kaje ba kenan?" Ta jefa masa tambaya ba tareda tabi ta kan maganar da suka fara ba, Ahmad da tarin ya tsagaita masa yace "Naje wlh Momy an rubutamun magani na ma farasha, kiyi masa maganar yanzu dan Allah kinji" "Zanyi" ta faɗa a taƙaice daga nan ta kashe wayar. Alh Audu na cin abincinsa kuma yana sauraron duk wayar da sukeyi tuni kuma ya fahimci zancen da tunin da Ahmad ɗin yake magiyar tayi masa. Ruwa yasha yana kallonta yace "Shi baze iya zuwa ya sameni muyi magana ba se ya ringa turomun yan aike?" "Wane shi? Wannan ai se Yayan gida Yayan So" ta bashi amsa hankalinta na kan wayarta se yayi shiru yana kallonta, a yan shekarun nan Aishar ta fara canzawa, idan tayi wani abun se yaga kamar ta fara gajiyawa dashi ne kamar me neman wani dalili da ze janyo saɓani a tsakaninsu. Ajiyar rai yayi yace "Ai shikenan, kice masa gobe ya sameni a gidan Gona na Kwanar Dawaki se mu tattauna maganar kuma yazo da takaddun" "Baka da lambar wayarsa kaima kenan?" Ta faɗa tana tsareshi da ido, tamke fuska yayi be kuma bata amsa ba ya shige banɗaki wanko hannu. Tayi tsaki a ranta wani abu me ɗaci yana taso mata seta miƙe ta shiga tattara kwanukan daya gama dasu ta ɗora akan Try ɗin data kawo su ta fita. A bakin ƙofa sukayi kiciɓus da Hajiya dake dakon jiran a faɗi gundarin abinda take so taji buƙatar da Ahmad ɗin yake nema a gurin Alhajin da har yace ya sameshi a gidan Gona. Kardai fa tufka take ta baya tana warwarewa tana nan tana haƙilon ganin sun danne komai Aisha ta ringa mata zagon ƙasa suna wawasa ita da Yayanta? Dole ta Ƙara saka idanu kenan akan harkar shige da ficen gidan da duk abinda yake faruwa wannan maganar ma da ba'a ƙarasa ba seta bi diddiginta tunda sunan Jafar ya fito a ciki shi zata tambaya dukda dai shegen Yaro ne ba lallai ya faɗa mata ba tunda sirrin ubansa Ahmad ne. Tana ganin Momyn ta ɗan diririce se kuma ta waske ta tura ƙofar irin dawowa ta sakeyi zata shiga. Momyn ta kaɗa kai kawai ta wuce, ba yau Hajiyar ta sababa Laɓe ya zame mata ɗabi'a. Hajiya na ganin Momy ta sauka ta juyo itama ta fice dan akwai abinda yake a gabanta yanzu kafin ta juya takan zancen Ahmad ɗin, ɗakinta ta wuce ta tarar da YAKUBU na cin abinci, Hajiya ƙarama na tsaye gaban console mirror dake falon tana gyara ɗaurin kallabinta. Ganinta yasaka Binta sakin fuska ta washe haƙwaranta duka, guda biyu data sakawa Haƙorin Makka na zinari sunata ƙyalli, Umarar Bara da sukaje ta cire Asalin guda daya na bakinta daya cinye aka saka mata biyun. "Kinyi kyau uwar masu gida, yau zuciyar mahassada sedai ta buga dan baƙin ciki" Hajiyar ta faɗa tana ƙarasawa kusa da ita. Hajiya ƙarama ta saki murmushi kafin ta shiga juyawa dan ta nunawa Hajiyar kwalliyarta dakyau, Fitted gown ce ta wani cotton London Brocade a jikinta dark blue me zanen flower sea green da fari a jiki, kudinsa ya tasamma dubu sittin, Jafar ne ya aikowa da Hajiyar su sun kai guda goma yace a ɗinka mata dogayen riguna saboda laushinsa yasan zeyi dadin sakawa shine Hajiya ƙaramar ta kwashe uku dan tasan ba ɗinkawa Hajiyar zatayi ba ta kai aka mata lalatattun dinkuna a ciki wannan fitted gown din itace me ɗan dama dama dan ta rufe mata jiki gaba daya illarta kawai shape dinta daya bayyana ƙarara. "Kin fa gama haɗewa Yar nan babu makusa" Hajiyar ta sake faɗa tana bata hannu suka kashe daidai nan wayarta tayi ƙara, sunan Abba Tee ya bayyana akan screen ɗin. Tsanar dadi harda wani maƙale hannaye Hajiya tayi sama kamar Kangaroo bakin nan ko har maƙogaronta ana hangowa, Hajiya ƙarama ta amsa wayar cikin muryar shagwaɓa kamar zata fashe da kuka tace "Harka iso" "Yes Babe, ina waje" ya bata amsa daga cikin wayar, ta sake narkewa tana cewa "Baka shigo ciki ba? Issa baya nan ne? Kayi horn ze buɗe maka Get ya shogar dakai palour kafin na fito" "He isn't here, oh kamar gashi nan wani Buzu ko? ya buɗe Get ɗin bari na shigo" " Saurayin ya sake Faɗa kafin ya katse wayar. Hajiya ta sake bata hannu suka kashe tana cewa "Wai, Allah ya taimakemu, maza kije ki ƙara turare, duba ɗakina akwai wannan Disaina da kike nacin na baki na gurin Yayanki ki ɗauka, bari na duba abincin idan sun kammala" "An gama kumai har na shirya a Try kaowa kawai za'ayi" Inji Hajiya ƙarama "Yauwa yar gari, jeki to kar yayita zama Allah ya bada sa'a" cewar Binta. Hajiya ƙarama ta wuce ɗaki ta ƙaro turare kamar yanda Binta tace ta fito tana takun yauƙi Albarkatun jikinta na motsawa danma kayan jikin nata sun matseta kam hakan ya rage musu samun damar rangaji yanda ya kamata. Yanda Yaran Alhaji Audu Maza suke Dogaye ginannu idan ka cire Ahmad daya ɗauki Jikin Aisha bashida ƙiba sam haka beyi irin tsahonsu ba to Matan ma duk haka suke dogaye masu cikakken jiki, Allah ya taimake su da ƙira mai kyau ta jiki data fuska musamman da dukansu se akayi katari suka ɗauko fuskar Dada, Farare tas ɗin cikinsu Amina, Aslmaiyya da Hajiya ƙarama da yan Biyun Hajiya Rabi Baba Bilki takance kamanninsu kwabo da kwabo da Dadarsu. "Yauwa, saura kuma ki sake maimaita abinda kikayi wancan karon kika saka yayi fushi, kina kallo dai har dubuta dari Turai ta damfareni, koda yake kwalliya ta biya kuɗin sabulu tunda an janyoshi yazo, soyayyar nan ta zamani ke sekace ba wayayya ba da ita ake kama samarin nan, banda abinki waye ze kwasheki haka siɗan ba tareda ya tabbatar kin iya kalar soyayyar da yake da buƙata ba, yar rungumar nan da kis ne dai Allah na tuba ai ba wani abu bane, ban dai ce kije ki buɗe kafa ba ki saka mu shiga uku kuma kuyi a hankali Alhaji ma sama ze iya saukowa kowan...." "Hajiya!" YAKUBU da ke cin abincinsa tun shigarta be tanka maganar da sukeyi ba ya kira sunanta cikin ɗaga murya me kama da tsawa dan a firgice daga ita har Hajiya ƙaramar suka kalleta kowacce na tsammanin da ita yake. Farantin gabansa ya ture ya miƙe tsaye fuskar sa tamkar zatayi aman bacin ran daya turnuƙeshi lokaci daya. Ya nuna Hafsatu da yatsa yana cewa "Ashe abinda ake faɗa akanki gaskiya ne? Iskancin da aka ce kinayi dagaskene saboda kin shahara yanzu har cikin gidan ubanki kika kawo saurayi zakuyi iskanci?" Kai ta shiga girgiza masa tanaja baya domin Yakubu bashida daɗi, ba su ba uwar data haifeshi ma shakkarsa takeyi dan Lamarinsa me girma ne. Hajiya Binta ta dake tana hararar sa tace "Kai bana son ɗiban Albarka, a gidan uwar masu faɗar aka ganta tana iskancin? Koda uban wani tayi a cikinsu da har suke bayar da shaida? Bakaji me nake faɗa bane? Ce mata nake fa ta saki jiki dashi ita ai gida huma ce duk samarin da kake gani suna zuwa suna tafiya ai ƙin basu fuska takeyi shi yake korarsu. Shifa wannan ɗin in gaya maka, Yaron Alhaji Mudi Tanko ne tsohon Senet piresiden kuma yanzu haka takarar gwamna yake a Garinsu, can kwanaki bana muku zancen sa ba har yazo sau ɗaya shine ya tafi be sake dawowa ba? Ai in gaya maka wannan shashashar yarinyar ce ta kusa kwafsa mana, wai fa ɗaukarta yayi sukaje Otal ya kama Ɗaki, daga cewa su shiga ciki shikenan ta gudo wai har da ce masa ita ba yar iska bace se kace yace mata wata tsiyar ze mata idan suka shiga. Shiko yayi fushi ya tafi, dakyar fa yanzu seda na baiwa Turai dubu ɗari ta kaiwa Malaminta akayi aiki akansa shine fa ya zo yanzu, faɗan da nake mata kenan kar a maimaita ta wnacan karon a samu a kamashi a hannu ya fito ayi zancen Auren nan masu yi mun dariya su sha kunya suji da ƙaryar sarauta suzo suga Arziƙi a inda yake dan duk na samu labarim gidansu ba ƙaramar wadaƙa ubansu yakeyi idan ya tashi Aurar da Yara ba". Yanda take maganar hankali kwance tamkar me faɗar wani abin Arziƙi, Yakubu yayi sakato yana kallonta a ransa kuwa kokwanto yakeyi akan Hajiyar ce ta haifi Hafsatu ko kuwa Riƙonta takeyi? Anya uwa zata yiwa yarta irin wannan huɗubar kuwa? "Zatayi mana, mussamman uwa irin taku da take bautawa duniya da abinda yake cikinta" zuciyarsa ta bashi amsa. Seya ja numfashi ya furzar kafin ya zabura ya nufi ƙofa, cikin Hajiya ƙarama ya kaɗa, Hajiya kuwa yatsine fuska tayi tace "Ke da Allah rabu dashi, ance masa bansan duk abinda sukeyi bane su? Duk fa haka suke lallatse yammatan suma suna basu kuɗi balle ke da Aurenki ma zeyi jeki abinki manta dashi kar kuma ko manta uar soyayyar nan da ake nunawa a fim irinta zaki masa kinji ki hargitsa masa tunani yayi maza maza ya turo azo ayi magana kar zancen Auran Aslamiyya ya riga naki tashi". A saluɓe Hafsan ta fita duk karsashin da take dashi ya barta. A ƙofar fita daga ainahin cikin gidan taci karo da Ali Daya daga cikin Ma'aikatan gidan me kula da shuke shuke, da gudu ya taho badan ta matsa masa ba da tuni yayi tafiyar gari da ita. "Yawwa Hajiya kiyi sauri, ga Alhaji Yakubu can yana dukan baƙonki" ya faɗa yana haki. Ƙirji ta dafe tana zaro ido daga inda take kuma tana iya jiyo ihun kukan data tabbatar na Abba Tee ne da kuma hargowar Yakubu yana faɗin "Daga yau ka sake zuwa wani gida ka yi iskanci da ƙanwar wasu". Da gudu ta juya ciki tana kuka tana kiran Hajiya. Binta nacan tana gyara zaman kofunan da za'a kaiwa Baƙon tana kwararaqa me aikinta Ashar akan wai bata goge su dakyau ba so take yace musu ƙazamai sega Hafsa na kuka jage jage, bata ko iya sauraronta gaba daya ba tayi waje cikin tashin hankali tana kiran Yakubu. Yakubu kuwa dukan Ɗa da Uba yakeyiwa saurayin Hafsatu ya fasa masa baki da hanci ga hauri yana kai masa a ƙafafu yana kiran seya karya su yaga da wanda ze ringa yawon iskancin Hajiya ta iso ta cakumeshi tana zaginsa se kuma ta saka kuka tana cewa "Shikenan kaima an taɓa ka, nidai yanda naga ka fito ido a jirkice daman kamar wanda iska ta shafa nasan da walakin, ni aka tozarta a gidan nan ko? Anga Asirin da akayiwa Yata yaƙici kullum sababbin Manema take samu shine aka biyo ta wannan hanyar ko? To wlh mu zuba mu gani, bana Boka bana Malam amma ko wanene ya taɓani seyaji a jikinsa" se kuka wiwiwiwi. Ma'aikatan gidan gaba daya sukayi dafifi suna kallon ikon Allah, Drama a gidan dai ba sabon abu bace ta safe daban ta rana daban ba kuma sa gundira da tirka tirkan gidan domin kullum sabon abu suke gani. Audu da hayaniyar ta fito dashi ya isa gurin cikin dakakkiyar murya yake tambayar abinda ya faru se sannan kuma Abba Tee ya samu ya miƙe ya nuna Yakubu yace zasu gamu seya san shiya taɓa, Yakubu ya zabura ze sake damƙarsa ya taka ya gurin motarsa da sauri ya shige yana cigaba da faɗin "We shall meet in court, zaka san ni ka daka se ka gane baka da wayo". Cikin tsawa Audu ya bawa ma'aikatan umarnin su watse kowa ya juya gurin aikinsa. Ya kalli Hajiya dake kuka har sannan Hafsatu ta runguketa itama tana kukan kafin ya mayar da hankalinsa kan Yakubu yana tambayarsa meya faru? Waye wancan ɗin kuma meya haɗa u harta kai ga duka? Kafin ya bashi sa Hajiya tayi zuruf tace "Me kuwa ya haɗasu? Magautane sukayi masa turen Aljani haka kawai ya rufeshi da duka saurayin Hafsa ne fa, anga Allah ya fito mata da Miji na nunawa Sa'a shine aka bi yanda akayi shima aka koreshi kuma wlh ba'a taɓa banza ba ko wacece a cikin matanka tayi abin nan ta kwana da shirin zubin Adashi tayi ɗauka kuma dole, ka wuce kai kuma ka kwanta kana tsaye kana wa mutane muzurai ko Aljani ƙarƙuzu ne wlh sekaci ubanka sannan ka koma kan wadda ta aiko ka" ta faɗa tana aikawa da Yakubu wata harara me tafe da gargaɗi. Juyawar yayi kamar yanda tace ya fice daga gidan gaba ɗaya ita ma suka koma ciki da Hafsa dake kuka har sannan. Alhaji Audu ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi yana kallon Ma'aikatan gidan da duk suka maida hankali kamar masuyin wani abun ya tabbatar kuma kunnuwa da hankulansu har sannan yana kansu, an gama na ɗazu ga wata an sakeyi kuma, idan ba'ayi sa'a ba kafin kwanciyar bacci se an kuma kafta wata Drama. A sanyaye ya ringa taku ya fita ya shiga Masallacin dake manne da gidan tunda Magriba ta kawo kai saura mintina kaɗan a kira. Carbi yake ja amma ya lula cikin tunanin daya aureshi, bashi da damar yayi shiru haka nan ko yayi tunanin abu me daɗi kullum se damuwa se ɓacin rai daga wannan se wannan. Wayar sa dake gaban Aljihu ta ɗauki Ƙara ya zarota, Alƙali Yakubu ne, miƙewa yayi ya fice daga cikin masallacin ya tsaya daga gefe lokacin wayar ta katse dan haka yabi bayan kiran. A taƙaice suka gaisa, Yakubun ya tambayeshi yanda Zaman su ya ƙare da matsaya akan zancen kuɗin. "Mun rigada mun gama magana yayi rantsuwa akan bashi ya ɗauka ba kuma na yarda amma na sauke shi daga kujerar Takwaranka ze riƙe na lokacin kafin musan abinyi" Audun ya faɗa masa. Daga ɗaya ɓangaren Yakubu yace "Idan har ka yarda dashi menene dalilin daya saka ka dakatar dashi daga aiki kuma?" "Haka dokar take a rubuce, duk wanda aka kama da laifin cin hanci ko yiwa Kamfani zamba hukuncinsa korace sannan ze maido da duk abinda aka rasa, bamu baƙaci ya mayar da komai ba amma an dakatar dashi saboda idan banyi haka ba kamar na buɗe Ƙofa ne ga sauran kowa ze iya wasarere da dukiyar Kamfani saboda yasan babu matakin da za'a ɗauka akansa, kuma dalilin daya saka bamu buƙaci ya maido da kuɗin ba saboda Bincike ya tabbatar da basu shiga account ba, a rubuce ne kawai akwai su kuma idan aka tattara lissafi ya kamata ace suna ciki sedai am rasa ta inda suka maƙale". Dariya jawabin Audun ya bawa Yakubu ya dara kafin yace "Ai shikenan, tunda har ka gano da kanka inda matsalar take ina ganin babu laifin Aminu kamata yayi ka tattara shuwagabannin kowanne ɓangate su gabatar maka da lissafinsu da kansu sannan ka haɗa dashi wamda suka bashi daga nan za'a tantance me laifi da me gaskiya, most especially guraren da kuke generating kuɗi sosai Oil da sauran Mineral su ya kamata ka tsananta bincike akai na tabbata daga nan matsalar take" Yakubun ya bashi shawara daga nan suka ɗan tattauna wasu batutuwan kafin sukayi sallama dalilin sallah da aka kira. A cikin gida kuwa a tsakar gida Hakiya ta kafa kujera tana zazzaga bala'i, daga Momy Har Anty babu wadda ta leƙo ballantana ta tanka mata daman da Baba Bilki tana nan ne itace zata kulata to tana gidan Sarki matarsa ta haihu ita take zauna mata. Har aka kira sallar Magriba batayi shiru ba bakinta har kumfa yake yawu na sarƙeta amma taƙi haƙura ita kanta Hajiya ƙaramar datayi iyakar yinta akan Hajiyar tayi shiru taƙi ɗaki ta shige tana cigaba da kukan Asarar da Yaya Yakubu ya janyo mata, ita ai bata ce masa zata biye ta zancen Hajiya ba domin da tana hawa layin data ke ɗorata da tuni ta daɗe da zama riƙaƙƙiyar karuwa a cikin gida domin abinda Hajiyar take nuna mata kullum shine tayi komai ba komai bane muddinba bude ƙafa zatayi ba. Ta rasa irin tunani da son zuciyar Hajiya, bata duba mutunchinta ko zunubin da zasu ɗauka da ita me aikatawar da ita data turata burinta kawai ta cafko musu Dan Attajiri wanda ya kere Mijim Anna dana Khadija da kuma saurayin da yake neman Aslamiyya tunda bata samu yanda take so akan Nazira data janyowa Nakasar data so ta hanata Auruwa daga ƙarshe Audun ya haɗata da wani Yaronsa babu laifi yana da abin hannunsa daidai Misali shima kuma yana sonta. Ita Anna Ɗan Sarkin Zazzau ta aura Khadija kuma Wani Matashin Ɗan Kasuwa me jida Yayan Banki duk su biyun suna cikin daula da jin daɗin rayuwa ita Khadija ma zamansu rabi da rabi ne a Nigeria sunfi zama a Dubai wannan Daula da Yayan Momy suke ciki ta tsolewa Hajiyar Ido, sannan ga Auren da Sarki yayi ya Auro wata halfcast Ambariyya, Mamarya ce Bahaushiya yar Nigeria Babanta kuma Balaraben Qatar ne Hamshaƙin me Arziƙi Bikin Sarkin da yanda Uban Amaryar yayi wasan kuɗi ya gigita Hajiyar, ada tana hura hanci akan Matar Zakariyya da Matar Naziru yan manyan gidaje ne tana habaicin kaf Yayan gidan babu wanda ya auro Ya daga gida kamar nasu se gashi Sarki ya goge mata hadda ya auro Balarabiya wannan yasa ta sake cin buri akan Hafsa seta auri Mijin daya doke nasu Khadija sannan Jafar shi ze wanke mata takaicin Sarki ya samo wata tsaleliyar Baturiya ko Indiya shida yake sananne a Duniya ma ai Matar da ze Aura se an ganta kawai yanzun hankalinta yafi karkata akan Hafsa tayi Aure se kuma ta mayar da hankali kan Autarta Sarah. PAGE 2 Kiran sallar Magriba ne ya tasheta badan ta gaji da zazzagar da takeyi ba ba kuma ta gama ba zata cigaba. Ta bubbuga sallarta domin babu nutsuwa tattare da ita ko kaɗan tana idarwa ko salati bata iya tsayawa tayiwa Annabi ba taja waya ta shiga kiran Tirau. "Yaushe zaki dawo? Akwai matsala" ta faɗa ba tareda ta tsaya sun gaisa ba. "Jibi in Allah ya yarda, jirgi muka rasa yau shiyasa ma bamu taho ba se jibin muna Jidd ma, wlh ansha dake, da uwa kuɗinki matar nan ki biya mu tafi abi mu kikaƙi, tafiyar nan tayi daɗi yanda baki zato keni ban taɓa umarah me daɗin wannan ba yanzu ma muka dawo daga kanti munyo siyayya naga wasu riguna har zan kiraki idan kinaso a siyo miki na tuna da dai kyautace zaki karba koda yake ko kyautar ce babu lallai ki saka ma sedai ki Ajiye har su daddage su zama gari" Turai ta bata amsa cikin dariyar shaƙiyanci. Binta taja tsaki tace "Ai shikenan se kun dawo ɗin, idan kuma naga bazan iya jira ba zanje gurin Hajiya Halima kawai muyi maganar ai tasan gidan Malamin nan naki ko?" "Daɗina dake rashin saiti wani sa'ilin wlh Binta, ce miki nayi ina haɗen Malami da ƙawaye? To ai ko ke abinda yasa kikaga ina kai matsalarki gurin Malamina saboda nasan ba layinki bane dole tasa kike leƙawa kuma ba zakimun yankan baya ba. Ki kuskura ki kaiwa Halima matsalarki zaki gane baki da wayo wlh ke baki san da yawa neman hanyar ganin bayan mu akeyi bako? To idanbata kaiki inda za'ayi miki magani ba ta kaiki inda za'a ƙara dagula miki lissafi ai. Maganar Hafsatun ce ko yaya? Ba jiya kince mun yau yaron zezo ba? Be zo bane ko yaya? Amma abin da kamar wuya ace be zo ba dan kiranyen da Malam ya masa idan kinga be zo ba to a kabari yake dan wlh aikin da aka masa irinsa akeyiwa Riƙaƙƙun masu laifo kiji ance sun gudu daga Magarƙama to Aljanu ake turawa su ɗauko su, yauwa ya wancan zancen kuɗin komai ya tafi daidai ko? Dan ko ɗazu seda Malam ya mun tunin kasonsa nace masa ban dawo ba bamu zauna naji yanda ake ciki ba tukunna". "Uhm kedai Turai Allah ya kaimu jibin ku dawo ma zanta, maganganun da yawa ni na rasa ma abinda zanyi wlh" Bintan ta faɗa kamar abar tausayi, Tirai ta sheƙe da dariya tace "Ai Binta lamuranki kamar me bakin uwa, kiga abu rumi rumi an ƙullashi se yayi kamar yaci komai ya watse gaskiya ki tashi tsaye magauta sunga gadon barcinki lokacin daya kamata ki huta yazo, Yayanki sun kawo ƙarfi amma kuma kwanciyar hankali taƙi samuwa? Allah ya kaimu jibin to mu dawo zuwa gata seki shigo muji yanda ake ciki" daga nan sukayi sallama ta rafka tagumi tana tunani. Masifar gidan da kullum gaba takeyi ba baya ba ta sakata fara abinda bata da ra'ayi akai kwata kwata wato Bin Malamai, tun Kissar tana ci a sannu ta dena tasiri saboda an kai gaɓar da wata kwarkwasa ko kisisina ta dena tasiri akan Audun, sabgar Kasuwancinsa kawai ya saka a gaba, shekarun baya lokacin da yake ta tiri tiri da ƙoƙarin ganin BECHI GROUP OF COMPANIES ya tsaya da ƙafarsa lokacinsu ma wahala yake masa, ga tafiye tafiye ko yana ƙasar ma se su kwana su wuni basu sakashi a ido ba a wannan lokacin ne kuma tayi Arziƙi domin itace akan komai, Ashana idan babu a gidan gurinta za'a nema cefane se abinda taga dama za'a kawo ta ringa tara kuɗi tana siyar Kadarori, Filaye, gidaje ta zuba yan haya da kuma sarƙoƙin gwal wanda ba sakawa take ba suna nan narke a drawer wani Design dinma wanda suka ƙirkireshi sun manta da Kalarsa. Da su Zakariyya suka gama makaranta kuma dukda daman tun suna ciki take cusa su akan harkokin Audun kullum tana nuna masa ya kamata ace ya sakasu domin sune magadansa tun yanzu ya kamatu su san komai da yanda ake gudanar dashi ba wai se rana tsaka ne zasu kama abin ba, tun baya sakar musu har yazo dakansa ya yarda yana da buƙatar su horu akan sabgar kasuwancin nasa domin Bare ze iya ha'intarsa wata rana kamar yanda yake gani ga Abokanan kasuwancinsa da suka tashi tare da yawa sun durƙushe kuma idan aka bi kadi daga ƙarshe yakan kasance wasu daga cikin ma'aikatan gurin ne da suka fitar da sirrunsu ga abokanan Hamayya har hakan ya janyo durƙushewar gurin amma se tunanin sa be kawo masa cewar ba su kaɗaine yayansa ba ko kuma ba su kaɗai ne magadan nasa ba kamar yanda take faɗa, burinta ya cika suka samu gurin zama dukda da farko sun fara ne a ƙanana ma'aikata tafi tafi suna haɗa tuggu da manaƙisa irin wadda suka sha a Nono har suka saka aka tunɓuke asalin waɗanda suka da muƙamansu na yanzu suka maye gurbinsu. Aminu da Alhaji Babannan Alƙali Yakubu ne ya cusa su a gurin da kansa, duk kuma bala'inta haka tayi ta haƙura wannan tasa ta matsa Yakubu ƙarami sukayi yanda sukayi har suka ciccibashi ya kai matsayin mataimakin Accountant General wato mataimakin Aminu a birinsu na ganin a sannu sun tunɓuke Aminun se Yakubun ya maye gurbinsa ta haka suka shirya wannan ƙulla ƙullar suka zabtare lissafi wanda daman aikinsu kenan yawan kuɗaɗen da suka zabtare ne yasaka har ta tashi aka gane aka kuma ɗora laifi kacokan akan Aminu dukda daman kuɗin babu su, lissafi ne kan lissafi tsoho da sabo suka harhaɗa ya bada wannan Adadi amma Asalin abinda suka kwasa Naira Biliyan daya ce kuma tana kwance cikin boyayyen Asusun Crypto wanda Naziru ya buɗe musu, Asusu ne irin wanda ba'a iya tracing koda an tura kuɗi ba za'a iya bibiyar su aga inda suka tafi ba can suke tura duk wata Albarkar office da suka samu kafin su zauna su ukun, ita Hajiyar, Zakariyya da Nazirun ayi kasafi kowa a tura masa nasa dan hatta da su ɗin ba wai ta yarda data bar kuɗinta a hannunsu bane, wani sa'ilin ma Ruwan Cash take karɓowa ta zube a ɗaki abinta tayi ta shafasu tana jin daɗi. To wani sa'ilin kuma idan Al'amura sun cukurkuɗe mata ta rasa mafita se Turai tace suje gurin Malam, tun akan Muƙamin Yakubun da Audu yaso yayi mata buyagi yaƙi yarda Turai tace ta kawo kuɗi, har yarjejeniya sukayi akan odan aiki beci ba zata maido mata kuɗinta se gashi tana zaune Audun ya kira Yakubun wannan tasa ta fara amanna da sabgar dukda ko buƙatar ta taso ba ita take zuwa ba, Turai take bawa kuɗi aje a mata abinda ya dace tunda sabgarta ce, ta daɗe dayin amannan da Bin Malamai harda Bokaye zuwa gurinsu takeyi shiyasa har kawo yanzu Ta kanainaye Ali, shekaru an tasamma Hamsin amma se yanda tayi dashi ƙarin Aure da yake da burin yi tunda jajayen sahu ta hana haka yake ta gurgura rayuwa ga kuɗi ya tara mata ita da yayanta suna wadaƙa Yau tana waccen ƙasar gobe tana wannan kayan Alatu kuwa kullum cikin siya takeyi dan ita ba irin Binta bace tana cin kuɗinta Binta kuwa har yau har gobe abin naira goma sabo idan ka ganta dashi to Yaranta suka siya mata shi ko ma ace Jafar dan shine duk abinda ya gani na kwalliyar jiki a gurin hamshaƙan mata ze siyawa Hajiyar abin takaici kuma ba zata saka ba musamman idan taji kuɗin kayan, suturu da sauran kayan Ado da kuɗi kam ta tarasu babu Adadi har tsokanarta Faisal yake yana cewa "Hajiya idan kika mutu zamu ja kaya da yawa dan wlh inaga kason abinda zamu samu na gadonki se yafi na Alhaji" duk ranar da yayi mata wannan maganar kuwa Ashar da tsinuwa babu wadda baya sha tace sedai ubansa ya mutu tamkar ita ɗin zata zauna gadin duniya ne. Bayan sun gama waya da Turai ta miƙe tayi sallar Ishar da aka idar tuni, tana zaune a gurin takaicin duniya ya isheta, jibgin kayan snacks da Kaji da akayiwa Abba Tee take tunawa ya zatayi dasu harda irin shinkafar Larabawan nan da ake dafawa da naman Rago yayi ligib aka masa yanzu duk sun tashi a banza ta saka ran ze cakewa Hafsatu kuɗin da zasu maida wanda aka kashe harda riba se gashi wancan Dan is** yaron ya janyo mata Asara. Tsaki ta rafka yanda kasan wata riƙaƙƙiyar tsaka, ita kaɗai taci gaba da bala'i daga zaunen da take tana dannanwa Yakubu Ashar. Faisal ya shiga kamar an jefoshi, ya kalli Hajiyar ya kalli cikin falon ganin ita kaɗaice zaune kuma tana ta faman sababi yasa ya matsa gabanta yana cewa "Hajjaju, kinƙi yarda Jayy ya kaiki Asibitin da yace, lamarin nan naki fa kullum ƙara gaba yakeyi gara a tari abin tun beyi nisa ba" "Dan ubanka Faisal kaima mahaukaciyar kake so kace mun?" Ta faɗa tana miƙewa tsaye, Faisal yayi wata dariyar shaƙiyanci yaja ja da baya dan ya san tana iya kai masa duka yace "Ni ba haka nake nufi ba, bafa ciwon hauka bane Ciwon damuwa akace kamar yana damunki kuma idan yayi yawa ne yake komawa haukan kinga ba zamu so haka ta kasance ba gara ki daure aje Asibitin nan asan abinda za'ayi dan wlh daga mutum yana zama shi kaɗai yana maganganu kodai wata rana aganshi warwas a ƙasa ya mutu ko kuma aga ya zura da gudu saitinsa ya kwance.." Be dire maganarsa ba ta fashe da kuka tana cewa "Sedai kaga hauka ko mutuwa a kanka dan iska kawai, fice mun daga ɗaki kafin nayi maka baki" "Allah huci zuciyarki ni ban faɗa dan kiyi kuka ba, ɗaki kuma sedai kiyi haƙuri amma yau a nan zan kwana bazan shiga can ba akwai tamu da Salim" yana gama faɗa mata ya shige kitchen da lafcecen takalmin Salim daya sace. Abincin daya gani a gyare ya ɗebi iyakar abinda ze isheshi ya shaƙo plate ya fito har sannan Hajiya na kuka da faɗe faɗen maganganu marasa daɗi akan Yakubu daya fara jangwalota da kuma Faisal ɗin daya ɗora nasa wanda kuma be kyautu ace uwace take danganta Yaranta da irin kalamanba. Kan kujera ya haye abinsa bayan ya kunna Tv ya ƙure volume abinda ya fito da Hafsatu ya hau cin abincinsa ya gama ya gyara zama yana kallo, duk Tijarar da Hajiyar take zuba masa be tanka ba harta gaji dan kanta ta wuce ɗaki ta barshi anan bacci ya kwasheshi dan ko giyar wake yasha bazeje ɗakinsu ya tarar da Salim ba tsaf seya masa dukan mutuwar da yace ze masa. Washe gari da safe zuwan Alhaji Zakatiyya ne ya wankewa Hajiya Binta baƙin cikin data kwana dashi jiyan, dukda sun fara maganar a waya tunjiya amma da yazo yayi mata bayani dalla dalla na yanda komai ya faru se ranta ya sakeyin fari ƙal. "Ai ni wani tunani nakeyi, anya wannan shegen yaron ma ze bamu haɗin kai idan ya hau kujerar? Jiyan nan fa kar kaga tijarar daya mun a gidan nan ya zubar mun da mutunchi a gaban maƙiya" nan ta bashi labarin yanda sukayi da Yakubu jiya, Zakariyya ya jijjiga kai yace "Haba kema Hajiya wani sa'ilin se ki ringa abunda be kamata ba, yanzu saboda Allah wannan tarbiyyace? Ko yar wani kikaga zatayi abinda be kamata ba ai hanawa zakiyi amma kike ingiza yarki ta aikata wannan ba daidai bane sam wlh kuma koni da ace na tarar da yaron sena ballashi wlh itaka kuma se naci uwarta dama ana yawan kawo mun zancen bataji na zata hassadace kawai akeyi mata ashe da gaskene to dan ubanta kawai zamu nemo koma waye mu aurar da ita mu huta kafin ta janyo mana abin kunya a gari". Baki sake Binta ta ringa kallonsa har ya kai aya kamar zatace wani abu kuma seta haɗiye ta bar maganar tace "Ai shikenan, zancen ya wuce, yanzu dai a aikamun da kasona a akawun kai a kawomun kash kawai na ringa ganinsu inajin ɗuminsu kusa dani" "Miliyan dari ukun za'a kawo miki cash Hajiya?" Zakariyya faɗa cikin mamaki, ta harareshi tace "Bangane dari uku ba? Wai nawane kuɗinma da kake kiran wata dari uku za'a bani?" Cikin ɗaga murya tayi maganar yayi saurin yi mata alama da tayi shiru saboda motsin taɓa ƙofa dayaji, Yakubu Bechine ya shiga fuskar nan a turɓune kamar ta Audu, Binta ta lafta tsaki tace "Dallah rabu dani yaji mana, nama zata wani barene ze shigo" "Barka da safiya Hajiya, Zakariyya Sannu" ya gaishe su daga tsayen da yake. Hajiyar ta harareshi bata amsa ba dan a cike dashi akan abinda yayi jiya Alhaji Zakariyya kuwa wani banbarakwai yaji daya kirashi Zakariyya gatsal kamar wani sa'ansa, yanzun shigowarsa ya haɗu da Ahmad ze fita shi kuma, seda ya kusa kaiwa ƙasa kafin ya gaishe shi kuma da Yaya ya kirashi ya amsa masa a wani wulaƙance yana shan ƙamshi kamar wanda yazo masa maula kuma yaron ko a jikinsa ya wuce abinsa har yana masa fatan fitowa lafiya daga gidan se yanzu Yakubu ƙaninsa ciki ɗaya ze masa wannan gaisuwar se kace wasu Abokanai? Koda yake ai Yakubun ma ya mutuntashi tunda Faisal da ido kawai ya kalleshi sanda ya shigo ita kanta Hajiyar be tsammaci ya gaisheta ba ya fita dan da ganinsa lokacin ya tashi ma daga barci. "Tambayarka nake nawane kuɗin?" ta sake nanata masa seya sauke ajiyar zuciya yace "To nidai abinda yace mun kenan kuma baze yuwu a saka kuɗin lokaci ɗaya ba saboda kinga yanzu EFCC ta tsaurara da binciken shige da ficen kuɗaɗe a Account ɗin mutane kar mu jefa kanmu a matsala gara a ringa sakawa da goma da biyar har ayi balancing" "Zezo ya sameni kuwa, a gidan ubanwa kasafin ya zama dari uku? Nida nake lissafin kusan dari bakwai shine zaku cemun wata dari uku? Nifa shiyasa naƙi jinin haɗa sabgar kuɗi da Naziru dan macuci ne, tsayin lokaci kullum yace ana juya kuɗin za'a turo ina nan galahanga kenan kuna can kuna sharafinku se yanzu zaku ɗan yafutamun abinda kuka ga dama shiyasa naji ance ka siyawa Matarka motar Miliyan Ashirin shi kuma yana rabon kujerun Umarah ko ni dana hada pulan ɗin ban san komai ba kun ninkeni a baibai" murya a sama take maganar babu ɗar ko shakkar wani ya jita Zakariyya kuwa daga inda yake zaune har zufa ta fara keto masa ta tsoron kar wannan fallasar ta Hajiya ta janyo musu tonon Asiri tun ba'aje ko ina ba, muakutawa yayi cikin rage sauti yace mata "Yanzu dai kiyi haƙuri na gaya miki yace ze zo kuyi magana tafiyar gaggawa yayi zuwa Legos amma Litinin ze dawo ba jimawa zeyi acan ba" "Ai ko bezo ba ni zanje har gida na sameshi, yo hauka akeyi mu damfari ubanku sannan ku zagayo nima ku cuceni" ta sake sakin wata maganar "Dan Allah Hajiya kiyi ƙasa da muryarki kar a jiyo me muke ciki" Alhaji Zakariyya ya sake faɗa, Yakubu daya haɗo shayi yana daga kan Dining yana jiyosu ya kuma fahimci tsaf inda suka dosa a maganar tasu, daman ya zargi saka hannun yan uwan nasa a manaƙisar da akayiwa Aminun amma be kawo dagaske an ɗebi kuɗin ba ya zata lissafi kawai suka ƙara masa. Kwankwaɗe shayinsa yayi ya taso yana cewa "A fitar dani ko wallahi na fasa ƙwai" "Dan uwarka ka yanka Kaza ƙarewar fasa ƙwai, kai baka san a cike nake dakai ba ko? Ka bari mu haɗe seka gane baka da wayo wlh" Be kalleta ba, Alhaji Zakariyyan yake kallo yace "Ko a tabbatar dani AG ko wlh na fasa tayi wari kowa ya rasa dan naji ƙishin ƙishin idan Aminu ya tafi wani bare ake shirin kawowa". Zabura Binta tayi da jin wata sabuwar lukutar Masifar kuma dake shirin danno kai, wani kuma? Wa za'a kawo? Kodai Ahmad ne? Kenan maganar da akeyiwa Alhaji tuni akanta kenan yace ya sameshi yau a gidan gona? Lallai bataga ta zama ba wai an saci zanin mahaukaciya. Wayarta ta raruma, Jafar zata kira tunda dashi aka ƙulla komai, ta kira sau uku bata shiga su Yakubu duk suka tsaya suna kallonta ganin yanda ta ruɗe se kokawa take da waya "Wai wa zaki kira? Badai Alhaji ba?" Yakubu ya tambayeta, seta miƙa masa wayarta tana cewa "Kunno mun Jafar na gaza samunsa yasan komai akan maganar nan dashi ake ƙullata". "Aikuwa ba zaki same shi a waya yanzu ba dan suna da wasa ƙarfe sha daya, lah lokaci yayima an fara ina tsaye bari kawai na kalla a nan" Yakubun ya bata amsa bayan ya dire mata wayarta a gabanta ya matsa gaban Cinema Tv bango guda wadda Jafar ya sakawa Hajiyar saboda tace wai bata ganinsa dakyau a tsohuwar tata. Tv na daidaita kuwa kamar me daukar hoton wasan Kwallon da ake yasani ya haskowa Hajiya Binta fuskar JAFAR BECHI tarr kamar ze fito ta cikin gilashin Tv. Zabgegen saurayi irin ƙirar Yayan AUDU BECHI, dogone sosai jikinsa nada ɗan kauri dukda ba za'a sakashi a layin masu ƙiba ba amma a murɗe yake koda gani ba se an gaya maka yana motsa jiki dakyau ba. Fatarsa nada haske sosai dukda ba fari bane sedai hutu da zaman Turai ya bashi wata kala me kyau kuma me wuyar samu a cikin mutane, ba wani shahararren kyan fuska yake dashi ba Aa daidai Misali ne irin na Maza gayu da yanayin muhalli da wankan da yakeyi ne yasa har Mata suke iya sakashi a jerin Maza masu kyau wanda ake gwarama kai akansu , ga duk wanda yasan Hajiya Binta Musamman a zamanin ƙuruciya kai tsaye ze tabbatar da JAFAR din jininta ne dan zubin fuskarsu daya idan ka cire Idanun Gidan BECHI daya samu se labbansa wanda Binta tace irin na Alhajinsune, duk tana jika dai da itan yake kama kenan. Jafar ɗin na tsaye a coner ya take kwallo da ƙafarsa ta hagu idanunsa kuma na kan saitin inda yake so ya bugata. JC ce a jikinsa Jaa me ratsin fari ta club din Arsenal wadda ke dauke da Number 7, a bayan rigar an Rubuta JAAY, wani murmushi yake saki daidai sanda Referee ya busa whistle gaba ɗaya yan ƙwallo suka shiga tara tara kowa na jiran ya jefo ta inda yake ya kama, baya yaja kaɗan ya buga ball ɗin daga inda yake ta ringa kurɗaɗawa ta tsakakanin ƙafafuwan yan wasan aka rasa wanda ze taketa har seda ta dangana da cikin raga shikansa Goalkeeper kamar an riƙe masa hannu da ƙafafuwa ya kasa tareta har ta shige, ihun yan kallo na cikin Tv tarefa na ZAKARIYYA BECHI da YAKUBU BECHI ya cika falon, Hajiyavkanta da take cikin ruɗu fuska a ɗaure bata san sanda ta saki dariya ba tana cewa "Ai na sani, sedai idan ba Jafaru na ba be taba kama kwallo ya saka ba tareda ya kaita raga ba, kai Allah dai yacigaba da tuntuɗo maka Albarka ɗan nan Allah ya cigaba da tsole idon maƙiya" Ɗa guda tilo kenan cikin rayayyu tara da take dasu wanda take ɗaga hannu ta roƙar masa nasara a gurin Allah ta kumayi masa addu'ar fatan nasara tareda saka Albarka, yana kuma ganin hasken hakan domin Uwa duk yanda take Uwa ce kuma tasirin harshenta nada girma. Jafar ɗin me shekaru Ashirin da bakwai a duniya yanzu ya kai matsayi mai girma a duniyar kwallon ƙafa. Matashin Dan wasa ne da ake ji dashi a faɗin duniya wanda kowanne Club suke zawarcinsa, idan ka cire Messi da Ronaldo JAAY shi yake take musu baya a duniyar kwallon ƙafa a yanzun. Ubangiji ya hore masa baiwar sarrafa kwallo, duk rintsi duk tsanani idan JAAY ya karbi kwallo seya kaita ga inda ya hara kafin ya haƙura, juriyarsa da Nacinsa da kuma ƙoƙarinsa na haɗakan Yan Team ɗinsa Abokanan taka ledars shiyake ƙara masa ƙima a idon duniya domin kowa ya shaida wannan jajircewar tasa ce ƙashin bayan cigaba da Nasarorin da duk wani club dayake taka leda a ciki yake samu. Cikin farin ciki suka haɗu suna kallon Wasan, harda Hafsatu da Sarah dake bacci ihun su Yakubun ya taso su ko karyawa basuyi ba suka haɗu aka cigana da kallon. BECHI FARM Kamar yanda Alhaji Audu yace Ahmad ya sameshi a gidan gona haka ce ta kasance, Alhajin ya riga Ahmad isa saboda baƙi da yayi ze gana dasu acan wanda shine musabbabin daya saka yace Ahmad ya tarar dashi a can ɗin, sanda ya isa Alhajin na tsakiyar tattaunawa dan haka yayiwa kansa masauki a daya daga cikin falukan da suke gidan gonar idan kaga tsaruwarsu zaka ɗauka a cikin gida kake ba wai gidan gona ba. Yana zaune cikin zullumi rungume da takaddun tsarin abinda yake so ya gudanar, zuciyarsa fal wasi wasin yarda ko akasin haka daga gurin Alhaji, idan Alhajin be yarda da buƙatarsa ba a ina ze samu gurin da ze aiwatar da aikinsa tamkar wanda yake nema a gurin Alhajin? Gajiya yayi da zama da tunani ya tashi ya fita yana zagaya gidan gonar, sashen tsuntsaye ya tafi, acan ya shantake yana kallon Halittun ubangiji, tsuntsaye gasu nan kala kalanda Alhajin yake kiwo danginsu Dawisu, Aku, Kanari da sauran tsuntsaye masu tashi kala kala a keji nan su ga kuma tattabaru nan irin ƙasashe daban daban Jikinsu kaɗai abin sha'awa. Kukan tsuntsayen da surutun masu kula da gurin ne ya ɗebe masa kewa har besan lokacin daya ɗauka ba seda wani daga cikin yaran Alhajin yayi kiransa. Masaukin daya tarar da Alhajin yafi kowanne haɗuwa a gidan gonar, yana zaune kan Luntsumemiyar Rolar chair two sitter irin zaman da yayi da suturar da take jikinsa kamar wani basarake seya cike kujerar gaba daya kwarjininsa ya cika falon. Tamkar beran da ruwa yayiwa duka haka Ahmad ya raɓe daga gefen kujera yana gaida Alhaji. "Ka tashi ka zauna a sama, meye haka kakeyi kamar wanda yazo Maula?" Alhajin ya faɗa cikin muryarsa me razana Maza. Ahmad ya sake yin ƙasa dakai cikin tsantsar ladabi yace "Aa Alhaji nan ma yayi, be kamata kana zaune akan kujera nima na zauna ba" "Umarni na baka ba shawara ba" ya sake faɗa a dake, wani sashi na zuciyarsa kuma yana tsinkewa, Ladabin Ahmad daban ne kaf a cikin Yayansa 28 yayi zarra wanda yake take masa baya kuma Jafar ne wanda zama da Ahmad ɗin ya washsheshi shima ya rabautu da kyawawan ɗabi'u. Kamar wanda ya zauna akan wuta haka Ahmad ya ɗosana mazaunansa akan kujerar jininsa yana sake tsinkewa, falon yayi shiru, motsin ƙofa da aka buɗe ya saka Ahmad ɗin zabura kamar mara gaskiya ganin Kuku ne ya shigo yana tura abinda ake ɗoro abinci akai yasa ya maida kansa ya sauke Ajiyar zuciya a hankali. A nan tsakiyar falon kan Ledar da Kukun ya shimfiɗa ya jera abincin daya shigo dasu. Seda ya gama ajiye komai daya kamata kafin ya juya ya fita bayan ya sanarwa da Alhaji komai ya kammala. Alhajin ya sauka ya zauna a ƙasan ya tokare hannunsa ɗaya da Tum Tum ya shiga serving kansa abincin Ahmad yayi sauri ya sauka ya karɓa. Ganin duk ire iren abincin da Alhajin yake ci yanzun ne dangin Alkama dasu Acca se kayan ganye sakamakon Sugar daya gamu dashi ya saka masa komai madaidaici yanda ze iya ci kafin ya koma ze zauna Kukun ya sake shigowa da madaidaicin Tray ya ajiye a gaban Ahmad ɗin ya sake fita. "Ga irin naku nan" Alhaji dake cin Funkaso da akayi da garin Alkama da wata miyar tantaƙwashi ga shayin Goruba yana kurɓa ya faɗa. Ya buɗe baki da niyyar yace ya ƙoshi amma kallon da Alhajin yayi masa ya saka ya buɗe abincin. Soyayyar jollof din Basmati ce se kaza guda gasashshiya da kuma coslow. Favorite ɗin Ahmad kenan shinkafa balle ga Kaza mutuniyarsa a gefe daman be karya ba ya fito dan haka tuni ya manta da surukutarsa da Alhajin ya hau zuba loka. Seda suka ƙoshi ƙat, Kuku ya sake zuwa ya kwashe komai ya dire musu kayan marmari da tataccen ruwan Inibi me sanyi, Alhaji nata satar kallon Ahmad kamar yanda shima yake satar kallon Alhajin. Dukda wata magana bata shiga tsakaninsu ba har suka gama cin abincin amma duk su biyun yanayin ya musu daɗi domin wannan shine karo na farko da suka taɓa haɗa muhallin cin abinci tun tasowar Ahmad ɗin sedai su hangeshi sunaci da Hajiya tareda Yayanta, sanda suna yara idan ta kira Jafar yazo suci abinci suka tafi tareda Ahmad ɗin haka zatayi ta zaginsa ta koreshi shi kuma Jafar ya saka kuka yabi bayansa wata rana haka da duka zata tisa Jafar ɗin seya zauna dukda bazeci abincin ba domin basa raba kwano da Ahmad da suka fara girma kuma da lokacin cin abincin wanda sukafiyi da dare ya kusa ze ja Ahmad su bar gidan ma doke ta haƙura ta barshi kuma duk abinda akeyi Alhajin be taɓa magana akai ba, ashe haka cin abinci tareda Mahaifi yake da daɗi? Ya raya a ransa. "Ina sauraronka, menene abinda yake tafe da kai?" Alhajin ya soko ainin abinda ya tarasu. Ahmad ya zaro takaddun daya zo dasu. Filla filla yayi musu a gaban Alhajin zane ne a jiki da guntayen rubutu yayi ta maza ya shiga yi masa bayanin abinda yake shirinyi. Tsarin taswira ne na katafaren Shopping Mall dayake da ƙudirin buɗewa, burinsa ne tun yana yaro provision store yake bashi sha'awa. Sanda suna Goron Dutse kafin su taso har Tireda ya kafa a ƙofar gidansu yake siyar da alawowi harda su Maggi da Omo, sau Biyi Audu yana sakawa a jijjigeta amma idan aka cire Yau in Allah ya yarda kwana biyu yayi yawa zega sabuwa a karo na uku harya niyyata ze cire ranar a kan Idon Ahmad ɗin yace masa "Dan Allah Alhaji karka ciremun, idan ma kuɗin haya kake so na ringa biya zan baka idan na tara kuɗi jarina yayi yawa, so nakeyi idan na girma na gina babban Shop da za'a ringa siyar da komai da komai" wannan maganar ta sanyaya masa jiki tasa ya fasa abinda ya niyyata wanda a sannan ma Binta ce tace masa Aisha ta saka Ahmad ya buɗe tiredar saboda aga gazawarsa ace ya kasa daukar ɗawainiyarsu, maganganun Yaron kuma se suka tuna masa da sanda ya daura ɗambar cika nasa burin sanda yake yaro yanzu da Ahmad ɗin yake nuna masa abinda yake so yayi se abinda ya faru kusan shekara Ashirin kenan ya dawo masa. A nutse ya ringa kallon komai yana kuma sauraron bayaninsa, ya fasalta masa guri da girman filin dayake da buƙata danyin ginin. "Shin kana da kuɗin da zaka gabatar da duk wannan aikin daka ɗauko?" Alhajin ya tambayeshi, Ahmad ya haɗe yawu kafin yace "Da akwai tanadin da nakeyi dukda nasan baze isheni nayi koda rabin abinda nake da buri ba a yanzu, amma a hankali ina sha Allah ina saka ran zan samu" "Ok, to me kake so nayi maka kenan?" Alhajin ya jefa masa tambayar me kama da rainin wayo, jikinsa yayi sanyi dan be hango alamar samun nasara ba amma ya daure yace "Wannan filin na cikin gari inda ake ajiye manyan Motoci da nake so idan da Hali a bani Aro tunda an dena amfani dashi". "Aro?" Alhajin ya tambayeshi kamar da mamaki, kansa na ƙasa ya ɗaga masa shi da tabbatarwa seya gyara zama yace "Se kum me?" Muryarsa na rawa kamar a tsorace ya sake cewa "Sannan idan da hali a gina mun, se muyi lissafi a yankemun abinda zan ringa biya duk shekara har na mallakeshi ya zama nawa". Shiru ya ratsa tsakaninsu fin tsahon minti goma sha biyar har Ahmad ya yanke ƙauna daga samun Amsa me daɗi Alhajin kuwa kallonsa yakeyi yana nanata kalmar Aro da yace ya bashi na guri sannan ya yanka masa abinda ze ringa biya kuɗin hayar daya ambata tun yana yaro kenan ze ringa biyansa, kenan a matsayinsa na Mahaifinsa baze iya roƙarsa ya mallaka masa gurin kyauta ba ko kuma ya gina masa irin yanda sauran Yaransa Yayan Binta sukeyi ko su ɗauki abinsa ma suyi amfani dashi ba tareda saninsa ba? "Idan ya tambayekan zaka yi masa hakan ne?" Zuciyarsa ta tambayeshi se ya rasa amsar da ze bawa kansa dan haka yaja numfashi yace "Shikenan, ina fatan kana da Lawyer? Ka haɗa duk wata takadda data kamata ka kaiwa Barr, kuyi magana dashi daga nan ka samu Mr Lee ku tsara yanda construction ɗin ze kasance da abinda za'a kashe daga nan se a tattara lissafin, darajar filin dai shekara goma baya an taya Miliyan dari ban siyar ba, nasan yanzu ya ninka haka sau goma ko fiye da haka tunda kasan inda yake kaima kwaɗayin kyawun location ɗin ne yaja hankalinka dan haka zan bar maka shi a Dari biyu, ka gayawa Barr, sannan ka fara haɗo kuɗin filin tukunna koda rabine sannan zan yarda na fara gina maka". Wani sanyi ya ratsa zuciyar Ahmad, ya shiga zuba masa godiya, seda ya gama kuma kwakwalwarsa ta shiga aiki na gaske, Miliyan dari biyu da Alhaji ya ambata kuɗin fili seya biya sannan za'a fara gini a ina ze nemota? Tanadinsa ƙarƙaf idan ya haɗa baze fidda kuɗin filin ba, amma ya yarda a ransa Allah zeyi masa ze kawo masa hanyar da ze samu abinda ze cika burinsa. PAGE 3 Daga gidan gona kai tsaye gidan Anty Manfusa Inda ya ajiyw Momy dan tare suka fito. Yayi masu bayanin yanda sukayi da Alhajin dan Anty Manfusan na cikin waɗanda zasu saka hannun jari idan Allah yayi buɗewar shopping mall ɗin. "Wato uban nan naku lamarin sa yana matuƙar bani mamaki, yanzu ba'a rufa wata guda ba Yayansu Nihal (Dan Mijinta ne) yake cemun Anyi musu ƙarin kuɗin hayar shaguna a plaza, da aka kawo musu takaddu yaga an canza sunan da yake jiki wai yanzu ta zama ta NAZIRU BECHI, a yanda akace wai siya yayi gurin Alhajin wasu kuma sunce bashi yayi, nima yana faɗa nace wlh ƙaryane bashi yayi saboda rashin tsoron Allah duk girman plazar nan ace ya bawa Naziru shikaɗai shagunan ciki fa sunyi hamsin? nifa da nice a matsayinki wlh da tuni gayyar ta watse dan bazan zauna ana wannnan kutumar ubancin inyi shiru ba" "To banda abinki Manfusa Naziru ai Ɗansa ne yana da damar mallaka masa duk abinda yayi niyya" Momy ta bata amsa. Manfusa ta harzuƙa tace "Shi Ahmad ɗin ai Agola kikaje masa dashi shi yasa ze kasa bashi kyaitar fili, tsabar zalunci kuma ya lafta kuɗi har Miliyan ɗari biyu ce masa akayi Ahmad ɗin barawo ne irin sauran Yayansa da ze mallakin waɗannan kuɗin a shekarunsa? Ko kuwa saboda yana rayuwarsa cikin rufin Asiri bai taɓa neman wani abu a hannunsa ba?" "Hakan ma da yayi nagode Anty dan wlh idan a gurin wani ne darajar filin nan ta zarce haka ko a haya za'a bani a gine dai a shekara Miliyan Hamsin sen bayar da ita wlh kinfa san location kafin ni nasan manyan Organization da suka nema ya hanasu har Gwamnati seda taso ta kwace gurin Baba Alƙali ne ya tsaya masa Allah ya taimaka aka bar masa in sha Allahu in har muka samu abinda muke so shekara biyar tayi yawa zamu mallakeshi ya zama namu kawai dai kuyi ta tayamu da Addu'a" Ahmad ya yayyafawa wutar masifar data fara ruwa, dole tayi shiru tunda uwa da Ɗan da take haƙilo akansu abinma.be damesu ba. A hanyar komawa gida Momy take ce masa "Nifa ubana ina tsoron mutanen gidanku akan maganar gurin nan, ban manta ba Yayanku Zakariyya ya taɓa nemar ya bashi ya gina Hotel yaƙi, baka tsoron idan sunji suyi maka lamɓo se ka saka kuɗinka su zugashi ya kwace?" "Momy, dan Allah ki kyautata zato akan abin nan ki cire duk wani wasi wasi daga ranki. Nida ke duk mun sani Alhaji kaifi ɗayane, idan da beyi niyyar bani ba koda ace duniya zata taru akansa wlh baze bayar ba haka nan yanzu daya ce ze bada bana tsammanin da akwai abinda ze canza masa ra'ayi akan hakan, ki kwantar da hankalinki" "Ai shikenan, Allah yasa tabbatar da Alkhairi" "Amin Momy, abinda ya kamata ki faɗa kenan" daga nan suka shiga wasu hirarrakin harya sauketa gida ya juya yana so yaje yaga Barr Ansaruddeen Kalam, Childhood friend ɗinsa ne kuma shiya Aminta dashi da zama Lawyersa, a gidan Barr yayi Magriba da isha suna tattauna yanda za'ayi da takardun daya kamata su haɗa kafin su zauna da Lawyer Alhajin. Cikin hukuncin Allah yarjejeniya ta ƙullu tsakanin Alhaji Audu Bechi da Ahmad Bechi, kowanne bangare ya gamsu da tsarin da akayi har kuma BECHI CONSTRUCTIONS sun aza harsashin gini bisa Jagorancin Mr Lee, Injiniyan da yake shugabantar bangaren gine gine da ƙere ƙere na BECHI GROUP OF COMPANIES kujerar da Hajiya Binta take hari domin kuwa tuni ta matsantawa Faisal tafiya bangaren Engineering ɗin yanzu haka yana shekara ta biyu ne a Civil Engineering, burinta daya gama kuma a tunɓuke Mr Lee ya koma ƙasarsu Faisal Bechi ya maye gurbinsa. Ubangiji ya sirrinta Al'amarin ta yanda har gini yakai Linta Hajiya da Yayanta basu san abinda ake ciki ba, koda yake Yakubu Bechi ya sani saboda buƙatar fitar da kuɗin da aka kai kan Teburinsa dan tuni ya maye gurbin Aminu Bechi. Yakubun be fiya shiga sabgar da bata shafeshi ba, a barshi dai da son kansa dan haka muddin Abu ba wai ya shafi personal Interest nasa bane baze ce komai a kai yanzun ma haka ce ta faru yayi shiru ya saka hannu kawai kamar yanda aka buƙata be kuma tattauna maganar da kowa ba. Yanda akayi Labari ya isarwa Hajiya Binta kuwa hanya ce ta bida ita ta gurin da filin yake zataje gaisuwar Lantana wadda Allah yayiwa Rasuwa, Hajiyar bata yada Lantana ba a wannan bangaren kam tayi Alƙawari dan Lantanar tsautsayi ta gamu dashi a shegen yawonta mota ta kaɗeta shikenan ta gamu da Ƙafa, shekararta goma a zaune kafin Ajali ya sauka Bintan na leƙata lokaci lokaci duk kuma sanda ta wuce seta kalli wannan fili tana wassafa burinta akansa. A Zoo road yake, zuciyar Kasuwanci, kanta takeyiwa tanadi zata gina plaza ta zuba shaguna wanda ko iyakarsu me kadararta tasan ba ƙananan kuɗaɗe zata ringa shaƙa duk shekara ba. Jiki na rawa ta samu Alhaji Zakariyya da zancen waya tada gini a wannan filin? "Badai siyar dashi yayi bamu sani ba? Ka nema ya hanaka ina fakonsa shine ze siyar? To duk wanda ya siya ma kuwa ya siyi Asara dan ciniki be yuwu ba" Inji Hajiya Binta. Alhaji Zakariyya da har ya fita shiga ruɗu domin a halin da ake ciki a yanzun ya karɓi kuɗi a hannun Lebanese da suke son gurin zasu gina Hotel dan bashi zeyi ginin ba kuma ya musu Alƙawarin kafin watan da ake ciki ya ƙare zasu fara aikinsu se kuma yake Jin wata magana daban. Bangaren Land and properties ya tafi ya samu Alhaji Musbahu, basa shiri saboda duk sanda suka tashi cefanar da wani abun muddin basu kai masa takadda ta gaske me ɗauke da signature Chairman ba baya basu Approval, Zakariyyan kuma baya duba Girma ko Shakarun Alhaji Musbahun haka ze zageshi a gabansa yace ai bashida gadon ubansu balle ya ringa hanasu Taɓa dukiyarsu, yau ɗin se gashi harda risinawa ya gaidashi kafin ya tambayeshi suwa aka bawa Filin da har suka fara gini" "Ban sani ba, kaje ka samu uban naka kaitsaye, ku masu jiran Gado ma kuke ɗauka kuyi yanda kuka so da guri balle me abun daya tara da guminsa?" Amsar da Alhaji Musbahu ya bashi kenan shima kuma ita ya mayarwa da Hajiya. Ranar akayi dacen itace da Girki dukda Alhaji Audu baya gari ya tafi Umara amma a daren ranar ake saka ran dawowarsu shida Hajiya Rabi da Yammatan gidan duka suka tafi Umara wanda Albarkacin Tafiyar da za'ayi da Hajiya ƙarama da Sarah, wanda ze buga musu Visa da karanbaninsa ya haɗa da duka sauran Yara Matan da suke a gidan se kuwa gashi Alhajin bece komai ba akai. Amma fa seda akayi uwarka ubanka da Hajiya Binta kafin tafiyar ta yuwu harda Allah ya isa yanda kasan kuɗinta aka ɗiba akayi tafiyar dasu. Babu shirin da tayi na cewar yau Megidan ze dawo tunda ya tafi ma sau biyu sukayi waya Albarkacin zata bashi sautin Dogayen Rigunan Gumama wanda take bulalawa a tsakar gida tayita yawo kamar Maroƙiya, idan tacewa Hafsatu ko Sarah su siyo mata cewa zasuyi ta tura da kuɗi shiyasa ta aikawa da Alhajin hotunan kalarsu kamar wani Yaronta tace guda biyar za'a siyo, da taji shiru be duba saƙon ba shine ta kirashi, na biyun ma tinin an siya tayi masa yace Eh Alhalin ko downloading yaga me ta tura beyi bama. Ƙarfe goma na dare jirginsu ya sauka kafin a gama dakko musu kayansu su tafi gida sha biyu saura shi Alhajin dama VIP lounge na Arrival ya shige abinsa yace idan sun gama a sanar masa dan baze tafi ya barsu su duka mata ba ga dare, Ahmad ne kaɗai ya tsaya Tarbarsu a samarin gidan, a cikin gida kuma Momy ta musu ɗan abin taɓawa dukda dawowar darece amma tasan Alhajin baya cin abincin jirgi ko China zeje sedai yasha ruwa ko shayi shiyasa ta tanadar masa abinda zeci dukda ba girkinta bane sedai ganin Yau Hajiyar ko Hanyar kitchen bata kalla ba yasa tayi, kamar ma dai bata da lafiya ne dan karaɗin da take isarsu dashi a gidan ma yau shiru kunnuwansu sun samu sa'ida. A Ɗakinsa Momyn ta shirya masa komai ta bari tayi masa sannu da zuwa daga bakin ƙofa ta wuce Ɗakinta da Yammatanta da suka ruƙunƙumeta suna faɗin sunyi kewarta. Dukda darene haka ma'aikatan gidan Maza suka ringa shiga Babban Falo suna masa sannu da zuwa, Hamshaƙai kuwa, Yakubu, Faisal da Salim harda Mu'allim suna Ɗakunansu babu kuma wanda yake bacci a cikinsu daga masu chatting se masu waya da Yammata gara Mu'allim ɗin ya fita ya tarbi uwarsa ya rakata cikin gida kafin ya koma yaci gaba da Chatting, Tashen Balaga yake akayi rashin sa'a kuma Yayyensa da suke kewaye dashi babu wani gwani da ze kwafi abin Arziƙi a gurinsa shiyasa shima yake nema ya tashi da Ɗabi'u irin na gidansu da ya zame musu Gado wato halin ko in kula. Hajiya Binta bata saurara ko Babbar Riga Alhajin ya cire ba yana sallamar Masu aiki ya hau sama ta dirar masa a Ɗaki, ransa a jagule da rashin ganin sauran Yaran dake cikin gidan tamkar yanda Ahmad yazo ya tsaya kuma yaga motar kowannensu a ajiye dan ya kafa dokar hana yawon dare ƙarfe goma ake rufe masa Get ba shiga sedai fita duk kuma wanda ya kwana a waje shi yasan ta yanda yake hukuntasu kuma sun biyu suna bin dokar. "Yawwa Alhaji sannunku da sauka, nace ɗazu naje Goron dutse se nabi ta Zoo road zan karbi saƙo, base naga gini tsiriri a filin kaba? Ni na gaza fahimtar ma me ake ginawa yo bulune ta ko ina an tayar da katangu inaga hawa uku ma aka ɗora bene a gurin" Hajiya ta faɗa tana zama idanunta kuma akan kwanukan da Momy ta ajiye. Alhaji ya shiga kacaniyar zare kayan jikinsa, sati biyun nan yaji dadinsu ya samu lokaci da Amaryarsa dan har wani ɗan kumari yayi yanzu ya dawo zata fara ƙwarzabarsa, ita bata tarairayeshi ba sannan ta addabi masu tarairayarsa ta hana musu sukuni. Seda ya cire rigarsa ta rage singlet da Wandon dakakkiyar Gedzenar jikinsa kafin ya janyo teble ya bude Casserole ɗin da Momyn ta ajiye, Irin dankalin nan na yan gayu da ake soyawa sama sama sannan a gasa yaji Albasa da Koren tattasai da Yellow da zafinsa alamar yanzu aka gama ko akayi Microwaving ƙamshi na tashi. Ya tsiyaya Shayin dake cikin yar buta yayi bismillah ya faraci ba tareda ya bata amsa ba. A daren take son jin yanda ake ciki dan haka tayi shiru ta tuno da tsohuwar kissa ta matsa tana cewa "Yi haƙuri duk na sha'afa banma ce maka ga abinci ba, Allah sa be huce ba dan na daɗe da gamawa". "Da dai harshena ya dena tantance ɗanɗano sena yarda, sannan yaushe kika fara siyan irin kwanukan nan? Ina cewa kikayi na yara ne sedai a siyawa su Dada ko kuma kin canza shawara kinbi sahun su Aisha tsofai tsofai daku kuna Asarar kuɗi a siyan kayan kitchen?" Alhajin ya mayar mata da martani yana murmushin rainin hankali. Tayi tsam, har yar kunya ce ta kamata wato yasan ba ita ta ajiye ba kenan? Amma seta waske tajira harya cinye tas ya shiga banɗaki ya kuskuro baki ya zauna a bakin gado yana duba wayarsa. Maganar ta sakw soka masa hankalinsa naga saƙonnin da yake dubawa yace mata "Ahmad ne ze bude kanti a gurin". Ruwa take sha babu shiri ta ƙware nan ta shiga tuttula tari kamar zata amayo kayan cikinta Alhajin na jera mata sannu. Seda ya lafa mata ido da fuska sunyi jajir se sauke numfashi takeyi dan ta shaƙu amma bata daddara ba ta kalli Alhajin tana zaro ido tace "Ban fahimci Ahmad ne ze buɗe kanti ba? Ka gane inda nake maka zance kuwa? Filin Mota fa nake magana bawai wani guri daban ba" "Nan ɗin nima nake miki zance ai, ba kince kinga ana ta gini ba? Shopping Mall ze buɗe a gurin" ya sake bata amsa. Yanzun ta tabbatar da ya gane inda take nufin kuma gaskiyar zancen yake gaya mata. A fusace tace "Ahmad ze buɗe shopping Mall ko zaka buɗe masa? Ni zaka ninke a baibai wannan filin zakace ka bawa Ahmad ya bude kanti a ciki ina nan da Me sunan Alhaji yace yana son gurin cewa kayi da tanadin da kakeyi akai ashe Ɗan gidan Aisha kakeyiwa tanadi zaka buɗe masa kanti?" Hankali kwance dan seda ya kishingida kafin ya bata amsa yace "Ko kaɗan yanda dai kikaji nace miki shi ze buɗe to hakan ne nidai na bashi fili mun kumayi Agreement harya biyani wani kaso zan gina masa gurin a hankali idan kasuwa ta kafu ze ringa biyana har mu warware" Data rasa abin ce masa se kawai tace "Ai shikenan" ta fice daga ɗakin. Da Asubar Allah ta tattago Naziru da Zakariyya ta shaida musu abinda akw ciki, suka ƙule a ɗaki suna ta ƙulleƙullen yanda za'ayi a rusa maganar amma sun gaza samo hanya domin a yanda Alhajin ya iya bata amsa jiya tasan ba wata magana da zata faɗa yanzu ta samu shiga a gurinsa. Idan ya murɗe barinsa takeyi domin a garin tace seta latsa dole se ayi rashin sa'a kwaɓarta tayi ruwa shiyasa yanzun ma kamar zatayi kuka tace "Kubar komai a hannuna zan barshi dai yanzu tunda naga kansa yana hayaƙi amma zan maidashi hankalinsa ne kuma wlh ba Ɗan Aisha ba ko ubanta ne yayi kaɗan daya mallaki gurin nan se an karɓeshi". NAZIRU da yayi shiru yana ta tunani ya gyara zama yace "Wani tunani nayi, tunda kince yace miki ba kyauta ya bashi gurin ba na tabbatar kuma dagaske ba kyautar bane, me ze hana mu bi abin a siyasance? Nasan dai a shekara goma Ahmad indai ba Naman mutane ze ringa siyarwa ba a gurin nan baze haɗa kuɗin filin nan da ginin da za'ayi masa ba..." "Kai na rabaka, ka dena ganin yaron nan yana yawo tsalo tsalo dashi wlh neman kuɗine ya hanashi ƙiba, yanda kasan wannan tsohon haka yake babu sana'ar da baya gwadawa" Alhaji Zakariyya ya tare Nazirun. Seya ja tsaki yace "Ka dakata Malam kaji point ɗina, i know what I'm saying, kai kasan nawa ake taya filin nan Tsohon nan yaƙi siyarwa? Kuma kaidai kasan riba kawai ya sani babu batun faɗuwa ko mu da yake mana Gwanjon kayansa ai saboda uwarmu ta iya ƙasarta ne, ni shirin dana hasaso yanzu as i was saying a shekara goma Ahmad baze biya kuɗin gurin nan ba shi kuma Tsohon nan nasan duk Nacinsa shekara biyar gaba ma yaci ace ya dunguri ƙasa dukda ma naga Sugar nasa da hawan jinin wani sanɗa sukeyi sunƙi su rarakeshi yanda ya kamata ya buɗa mu samu muja kaya. Yawwa maganata a nan a bar maganar akwace guri ko wani abu, da zarar Alhaji ya sheƙa lokacin kuma Ahmad ya gama wahala da gurin ya rayashi kawai zamu tayar da rigima muce guri na Alhaji ne, babu ruwanmu da ko nawa sukayi yarjejeniya ya biyashi bamu san anyi ba dan haka guri yana cikin lissafinmu". "Ji banza, kai matsalata dakai wani lokacin se ka ringa magana kamar wani ɗan ƙwaya wlh, da kake cewa idan Alhaji ya wulla semu tada rigima ana maganar yanda za'ayi guri ya zama mallakinmu kana kawo shirme ko kuwa ka manta bamu kaɗai Alhajin ya haifa ba idan anzo rabon kowa se an fitar masa da kasonsa dai dai da namu?" Naziru yaja hanci irin yanda masu zuƙar hoda sukeyi ya wani karkace yana hararar Zakariyya yace "Kai ai kanka baya kawo wuta ne kwata kwata, kaji da Kuɗin mutane daka karba nasan sune matsalarka yanzu, zancen Gado kuma ai me sauƙi ne. Karka manta Yaya Tara ne a Ɗakin nan namu mu shida Maza a ciki munfi yan kowanne ɗaki yawa sannan mu muke da ruwa da tsaki a duk wasu sabgogin megidan nan, karka manta Kadarorin da uwar kuɗin kansu se abinda muka ga dama muka fito dashi za'a raba kuma ba wanda ya isa ya ɗaga mana yatsa" "Wannan gaskiyane" Hajiya da tunda ya fara maganar batace komai ba ta faɗa tana gyara zama dakyau dan tafi jin dadin wannan Haɗi na Naziru. "To idan suka haɗe mana kai fa? Kasan dai in suka haɗu sun nunka mu a yawa Mazansu da Matansu" Alhaji Zakariyya da yake jin shawarar Naziru bata kwanta masa ba ya sake faɗa, ta yaya za'ayi a zauna lissafin jiran Alhaji ya mutu? Cewa yayi yau ko gobe ze mutu? "Kai kana bani ciwon kai wlh, a gidan nan kake zancen haɗin kai? Ko mu da muke Abokanan cin mushe muke cin dunduniyar junanmu ballantana kake maganar waɗanda a cikinsu akwai wanda suka fi shekara basu ga fuskar junansu ba, ni kana haɗuwa da Hussaini kuwa? Kasan zuwana Legos na ƙarshe kawai Mr Oniye ya ambato mun sunansa, wlh na manta a gidan nan munda wani Hussaini se lokacin wai yaron nan lasisin fitar da Mai ya taceshi yake nema bama ya siya a nan ba" A tare Hajiya da Zakariyya suka zabura suna haɗa baki gurin cewa "Hussainin?" "Wlh fa, i was shocked irin kamar na faɗa tsakiyar transformer, kai nifa abun nan ma ya fara rikitamun lissafi ta yaya za'ayi ne mu mukeda kuɗi da iko from no where yaran nan su ringa fasowa suna mana over taking?" Nazirun ya sake faɗa, Zakariyya ya dunƙule hannaue yana kaɗa ƙafafu kamar mejin fitsari Hajiya kuwa kasa haɗiye kyashi, hassada da baƙin cikinta tayi kawai ta fashe da kuka tana cewa "Nidai Binta ina ganin ta kaina a gidannan, na gama da Hadiza dakyar bangama da matsalar Aisha ba gata Zubaida tana neman ɓullo mun niko me nayiwa wani da wannan bala'u suke rikirkitomun haka wani bin wani?" Haka taro ya watse dalilin wata sabuwa data bullo. (Ai daman duk wanda yace tukunyar wani ba zata tafasa ba to fa tasa ko ɗumi ba zatayi ba). A bangaren Aminu Bechi tsohon AG kuwa cikin hukunci irin na ubangiji barinsa BECHI GROUPS ba'a ko cike sati ba yana zaune ya fara samun gayyata daga kamfanonin da suke hamayya da BECHI GROUPS din, wasu sun so jansa ne domin su samu damar da zasu karya BECHI GROUPS saboda sunsan dole yasan sirrinsu ciki da waje kuma korar sa da akayi tana iya saka yayi fushi ya nemi ɗaukar fansa a kansu sedai Aminunba haka yake ba, koda cewar beji daɗin abinda ya faru dashi ba kuma yana da wani Rauni daban a zuciyarsa gameda Chairman ɗin BECHI GROUPS wannan bazata saka ya ha'ince su ba domin karya Alhaji Audu daidai yake da karya kansa dan ko babu komai Uba yake a gurinsa shiyayi silar zuwansa duniya wanna ta saka ya karbi aiki a wani ƙaramin Kamfani dan be kai sauran da suke farautarsa ba, Albashinsa be kai wanda ake biyansa a baya ba amma a hakanma ya godewa Allah tunda ya ishe shi yacigaba da biyan buƙatunsa na yau da kullum dan shi bashida burin ya tara kuɗi daman shiyasa tanadinsa ƙalilan ne, jin daɗi makura yana bawa Iyalansa a duk sanda dama ta zo kuma ya tabbatar ko be mutu ya bar musu komai ba wannan farin cikin da ya sanyasu sanda yana raue zasu ringa tunawa suna masa Add'u, abinda ya rasa daga nasa Mahaifin. Rayuwa taci gaba da tafiya, wanda yake binta a sannu tazo masa da sauƙi, wanda suka ɗauketa da girma tana cigaba da kwallo dasu bugu ta kowanne bangare har ana rasa na inda za'a tare se fatan ubangiji ya kawo sauƙi. A cikin shekara daya da wasu watanni ginin katafaren Shopping Mall ɗin Ahmad ya kammala. Gini ne akayi shi badai ya gini ba, tsari da taswirar gurin kaɗai ta isa ta sakaka ka shiga kayi siyayya ko badan kana ra'ayin hakan ba. An fitar da komai a tsare, bangare bangare daga na kayan Abinci na dafawa dana kwalama dangin su Alawa su Biscuit, kayan sakawa na manya da yara, kayan amfanin gida daga kan sumunti har zuwa ƙarshen abinda ake buƙata domingida ya amsa sunansa na gida da akwai a gurin, kai babu ce kawai Ahmad ne zuba a gurin ba, kuma wani abin jin dadi yanda ya faɗaɗa komai ya bawa Yan uwa da Abokanan Arziƙi damar shiga su saka hannun jari, bashida kuɗin da ze raya gurin shi kaɗai dan haka yayiwo gayya. Yan uwansa na gidansu kaf babu wanda be samu akan maganar ba ya kuma tallata masa idan akwai abinda yake so ya zuba ya kawo amma kaɗan daga ciki suka amsa tayin. Takanas yaje har Bechi ya samu Alhaji Babannan wanda seya shekara biyar be taka ƙafarsa a gidansu ba seda babban dalili koda yake waɗanda suke cikin Kanon ma ba zuwa suke ba se su ɗin dai da iyayensu suke cikin gidan su kadai suke dabdalarsu idan kaga wani a cikin sauran tofa ba ƙaramin abu ya faru ba tunda Alhajin yayi musu Aure shikenan kowa ya sallami kansa. Ahmad ya samu Alhaji Babannan akan zancen Shinkafa wadda yakeyinta sosai kuma yana jin yanda ake yabon irin da yake amfani dashi ana siyan shinkafar sosai dan kamfanunuwa ne suke kwasheta da yayi girbi dan hatta da BECHI RICE suna siyan shinkafar Babannan ɗin saboda ingancinta. "Ina ganin Yaya me ze hana kaima ka samu Alhaji kuyi yarjejeniya kamar yanda mukayi dashi, a maimakon ka ringa siyar da shinkafar daka Noma ya gina mala kamfani ka ringa sarrafata da kanka ana packaging kai tsaye kana siyarwa zakafi ganin ribar abinda kakeyi sosai kaga se a ringa ajiyewa a gurinmu masu siyan ɗaɗɗaya yan sari kuma suzo kamfani gurinka" shawarar da Ahmad ɗin ya bashi kenan. Alhaji Babannan ya murmusa kawai, shiɗin bashida yawan magana tamkar marigayiya Bara'atu amma kuma dafin da yake cikin zuciyarsa yasa maganganun bakinsa basu da daɗi sam. "Kaine mara zuciya da har abin hannunsa ya tsole masa ido ka iya neman Alfarma a gurinsa, yanda beyimun abinda ya zama wajibi na haƙƙina akansa ba bana fatan Allah ya kawo wani abu da ze sakani neman Alfarma a hannunsa komai ƙanƙantarta, abinda nake samu ya isheni rufin Asiri a duniya dan haka ka tashi ka tafi" amsar da Ahmad ya dawo da ita kenan tana masa nauyi a cikin zuciya ya kuma kasa amayar da ita ga kowa domin shi ubangiji ya hore masa ƙarfin zuciyar iya sirri komai girmansa komai ƙanƙantarsa. Be daddara ba ya samu Ali ɗan uwan Aminu, bayan aikin kamfani yana siyan gyada ya kai kamfani a fitar masa da Mai yayi packaging ya siyar, a cikin waɗanda suke uba daya banda Jafar da baya cikin lissafinsu Alin na da saukin Hali se Hassan su biyun daman yasan da wuya suƙi tayin nasa Alin ya yarda yayi murna sosaima har yake cewa daman ya gaji ya fara tunanin haƙura da harkar saboda yanda yake shan wahala da mutane idan suka karɓi kayan kafin kuɗinsa ya fito. Hassan kuwa Magunguna yace ze zuba a bangaren Pharmacy da aka ware yace kuma ze tuntuɓi Hussaininsa wanda ko Lambar wayarsa Ahmad ɗin yace baya samu zeyi masa magana ko kuɗine se su haɗa su buɗe Pharmacy ɗin. "Amma Ahmad idan ban shiga abinda be shafeni ba da se nace me yasa kayi register Kamfaninka da BECHI AND SONS sannan kayi Naming Mall ɗinka BECHI SHOPPING MALL? why not AHMAD BECHI SHOPPING MALL If you must include the Bechi a cikin sunan? Ni kaina dana buɗe Clinic ɗina da BECHI HOSPITAL I'm regretting kuma ina shirye shiryen chanza masa suna soon" Dr Hassan ya faɗa, Ahmad ya ɗanyi shiru yana mamakin dalilin wannan maganar lura da hakan yasa Dr Hassan yi masa ƙarin bayani yace "Magana tazo mun cewar yan gidanku sun cewa duk mu gama wahalarmu a ƙarshe komai da muka tara ya zama nasu mun sauƙaƙa musu ma da mukayi naming property namu da na Alhaji, dukda ni nasan ko sarautar hauka suke taƙama da ita babu wanda ya isa yazo anywhere near my property yayi claiming cewar nasa ne saboda uban nasu ma besan sanda na gina abuna ba balle su" Dr Hassan ya faɗa cikin zafin rai. "Kayi haƙuri Yaya ka tausasa kalaminka akansa ko babu komai mahaifinmu ne Allah kuma babu ruwansa da wani abu da yake tsakaninka dashi wannan kyautatawa da bayar da girman dole kayi masa" Ahmad ɗin ya tareshi cikin ɗar ɗar domin dama damarsa ya gani akan Alhaji Babannan da har ya iya yi masa togaciyar. Ajiyar zuciya Dr ya sauke kafin yace "Hakane, thaks for reminding me, amma kamar yanda nake gaya maka kai kana tsakiya, you still didn't own the property hundred percent, and you know that Man, he can be cunning, ina tsoron ya maka shigo shigo babu zurfi yayi ta kwace maka kuɗi daga ƙarshe ya barka da rigima da Yayansa ko kuwa ya baka papaers ɗin guri komai is in your name now?" Ahmad ya girgiza kai a hankali alamar Aa, zuciyarsa naso ta kama zancen Dr Hassan sedai amintacciyar na jaddada masa babu yanda za'ayi Alhaji yayi haka, yama za'ayi hakan ta faru? Ya tabbatar suffar da suke ɗorawa Alhajin bashida ita haba da kuwa ya cika ƙarshen Azzalumi a duniya ace ya rasa wa ze damfara se Ɗan cikinsa kai wannan abin ko a labari be taɓa jin anyi irinsa bama. A sanyaye yace masa "Bai bani papers ba amma komai da mukayi a rubuce ne akwai copy a gurina da Lawyer na shima haka, sannan Baba Alƙali ya sani, Baba Abdullahi ma ya sani Barr Aminu ma ya sani da Baba Musbahu duk suna cikin shaidu" "Cikin yaran gidan fa ya sanarwa da wani?" Dr Hassanya sake tambayarsa. Duk se Ahmad ya nemi daya hargitse da tambayoyin Hassan ɗin shaiɗan ya nemi daya fara rawar disco a zuciyarsa yana kawo masa wasi wasi. Kamar maraya yace "Aa bansani ba ko ya gaya musu dai Amma Yaya Yakubu ya sani Jafar kuma tare muke shirya komai" "Jaay, dazun na gama kallon maimaicin wasansu he is really making us proud, kaga a gidan Alhaji Audu, ku biyun nan ne kaɗai abinda zance yamun na kirki daya haifeku ko babu komai My two half brothers are something to write about" Inji Dr Hassan, se Ahmad ya fara tattare takaddunsa cikin alamar haramar tafiya amma Dr ya hanashi yace se yayi Dinner tukunna. Tare sukaje sallar Magriba da Isha'i sukaci abinci sunyi hira sosai sun kuma samu fahimtar juna daya tashi tafiya ya rabawa yaran Dr kuɗi dan yau be fito da Chocolate ba ko a mota bashida sannan ya kama hanyar gida yana tafe yana tunanin irin Daɗin da rayuwar gidansu zatayi da ace guri ɗaya suke zaune gaba ɗaya, se ya ringa ganin kaman samun daidaito a gidansu ze zama abu me sauƙi amma duk sanda ya zauna da wani a cikin yayyensu seya fuskanci abun ya shallakewa tunaninsa, tabbas Allah ya azurta Alhajinsu da zuri'a sedai ya watsata, haɗuwarta kuma se ikon Allah. A yan ɗakin Hajiya Yakubu ya amsa tayinsa ya zuba zunzurutun kuɗi ba kayaba an kumayi komai a rubuce ta yanda za'a ringa bashi ribar abinda aka samu, shikaɗai ya zuba jari se Jafar wanda daman dashi ake tafiyar, yayi supporting Ahmad ɗin da duk abinda ze iya shima kuma ya zuba kayan ƙwallo da kayan motsa jiki a yanzun shima yana kan tsarin buɗe Academy ta Ball ne under his NGO wanda ze ƙaddamar idan yazo Bikin buɗe shopping Mall ɗin Yaya Ahmad da yace ko za'a bashi query se yazo be kuma sanar da kowa zuwansa ba banda Ahmad ɗin domin muddin Hajiya taji seta hana. Abinda ya matuƙar bashi takaici duk bayan daya gama zagaya sauran yan uwa ya dawo kan yan cikin ɗakinsu da yake tsammanin bashida matsala dasu se gashi sunyi disappointing nashi. Kaitsaye Sarki yace he should count him out akan duk wani abu me kama da joint business shi kuma Salim da yake yazo ya ringa zama a gurin ranar da bashida lectures a makaranta se cewa yayi sedai idan shi za'ayiwa Manager to ya yarda amma bazeyi yaron shago ba. "Kai baka san kasuwanci ba, se kaje ka haɗo dame ƙashin tsiya komai ya rushe a barka a ciki bazanyi wannan abunba I'm going to send you something ka ƙara jari ni yanzu hankalina ba'akan Business yake ba because I'm going in to politics" zancen Sarki kenan, Ahmad besan sanda yace "Saboda shirme kabar Business ka koma siyasa? Ka kwashe kuɗinka fa kenan kaje ka zuba a cacar da baka da tabbacin samun nasara who does that? " "Kai zaka gayamun abunda zanyi kenan?" Sarkin ya faɗa yana tsareshi da ido, Ahmad yayi shiru, basa faɗa irin na sako da sako amma fa basa ga Maciji sam, ba sarki kaɗai ba harda Salim kullum cikin faɗa suke Sarki na ganin Ahmad ya rainashi yana shigar masa rayuwa a son ya nuna masa daidai ko rashin daidai shi kuma Salim yace Ahmad ya takura masa ya tsaneshi komai yayi abin faɗane a gurinsa bayan kuma Ahmad ɗin duk ya fisu gaskiya shi Sarki tunda Abokai suka masa famfo suka ce ya shiga siyasa shikenan lissafinsa ya kwance Salim kuma da Faisal basu da saiti sam shiyasa yake matsanta musu yanzu shi a ɗakinsu Momy da yan uwansa mata ne abokanan hirarsa da shawara Mazan kowa kansa hayaƙi yakeyi. Cikin nasara akayi bikin buɗe BECHI SHOPPING MALL, da yawan mutane kam sun ɗauka mallakin Alhaji Audu Bechi ne dukda sunan AHMAD BECHI dake matsayin CEO dayawan mutane ma se sannan sukasanshi a matsayin ɗan Alhaji Audun, wani abun mamaki duk tarin Yayan Audu ba kowa ya sansu ba idan ka cire waɗanda suke cikin kamfani. Abinda ze baka mamaki shine hatta JAAY da yake sananne kuma shahararre a duniya mutane basu san Ɗan Audu Bechi bane saboda da yawa suna ɗaukar Alhaji Muhammad Babban Yayansu Binta wanda ya tafi dashi UK a matsayin shine mahaifinsa dan yawan ganin hotonsu da akeyi tare acan, ganinsa da akayi a Taron buɗe Mall ɗin Ahmad da yawa sun bashi expression na cewar Abokin Ahmad ne, ko kuma wani abu na daban ya kawo shi gurin. Au na manta ban faɗa muku bala'in da aka kwasa da Hajiya akan zuwan Jaayy ba, ayi shiru kawai amma Ahmad ya kwashi tsinuwa saboda ta dalilinsa Jaayy ze rasa Miliyoyin da akace mata kullum ana bashi. PAGE 4 BAYAN WANI LOKACI. Ahmad Bechi na tsaye a sashen siyar da kayan yara na BECHI SHOPPING MALL daga inda jerin kayan jarirai na sakawa dana amfaninsu, riguna yake dubawa da hannu ɗaya ya dafe wayar dake kunnensa da ɗayan hannun da suke magana da Jafar. Yaja tsaki a karo na uku tunda ya fara duba kayan, daga cikin wayar Jafar yace "Yah Ahmad what is wrong with you? Tun ɗazun kake sasi?" "Don't tell me u still can't pronounce Tsa Jafar?" Ahmad ya faɗa cikin muryar raha, daga can Jafar ya ƙume, bece masa komai ba dan yasan yanzu ze fara tsokanarsa. Tun suna yara harshensa bashi da Tsa, tun ana zaton yarintace dan shi be fara magana irin sosai da wuri ba har yakai shekarun daya kamata ace ya iya furta kowacce kalma amma baya iya faɗin Tsa, sedai kaji yana Fisari, Samiya, Sugunna da sauransu abunna bashi haushi idanana kwaikwayon maganarsa shiyasa yayi shiru dan yasan yanzu Ahmad ze fara jansa ne. "Bari nayi switching to face time call please ka tayani differentiating kayan Baby Boys dana girls, ni duk iri ɗaya suke mun, tace pink for girls blue for boys kuma I'm seeing both colors a kowanne sample na kaya" Ahmad ya kawar da shirun jafar ɗin, "To kai kenan ma da kake ganinsu, ka ɗauka duk wanda ya maka kyau kawai ko ka tambaya wani a kusa da kai, ina yaran da suke tsawaya a counter?" Jafar ya bashi amsa, "Kasan na manta dasu wlh, barina kira Majid kawai ya haɗamun kayan daman aikinsa ne" "And u are there stressing ur self, Yah Ahmad ka fara tsufa fa, ya kamata kayi yunƙuri ka samo mana mata mu sha biki dan Allah" Jafar ya faɗa teasingly, Ahmad yayi murmushi yace "Za'a samu soho a sakaninmu..." "Stop it" Jafar ya tareshi Ahmad ya fashe da dariya yana waiwayen inda ze gano Majid karaf idanun sa suka sauka kan wata Budurwa dake nan tsaye ta jingina da bango ta harɗe hannayenta a ƙirji, kallonsa tayi da alama dariyarsa ce ta janyo hankalinta suna haɗa ido ta juya bayan data masa wani kallo me kama da harara wanda yaji dirarsa har tsakiyar zuciyar sa. "I will call u back, Jafar" ya faɗa be jira amsarsa ba ya kashe wayar ya jefata a Aljihu daidai nan kuma Majid ya iso gurin yana bawa wata Mace me ciki haƙuri akan daɗewarsa, Kwalin Gadon Jarirai ne a hannunsa da alama a store ya ɗakko, daga nan yaci gaba da haɗa mata kayayyaki tana nuna wanda take so yana ɗaukowa. "Kalli wannan Sunyi kyau?" Matar ta nunawa Budurwar dake tsaye ba zaka taɓa cewa tafiyarsu ɗaya ba saboda yanda ta kame gefe tana ta muzurai kamar wadda akayiwa wani abun, "Sunyi kyau Anty, dan Allah ki barsu haka mu tafi ma sake dawowa wani lokacin duk na gaji" ta bata amsa. "Aiko babu inda zanje sena gama siyan komao dan ba lallai na sake samundamar fitowa ba shiyasa ma nace kai tsaye mu taho nan dan nasan komai da nake so zamu samu in kuma ban ƙarasa ba waye ze zo ya siya mun?" Matar ta faɗa tana cigaba da duba kayayyakinta, Budurwar ta narke fuska kamar zatayi kuka tace "Wlh zanzo na siya Miki amma ki barsu haka yanzu mu tafi dan Allah" "Ai se kiyi, in kinga na bar nan to na gama abinda ya kawoni ne ahto" Me cikin ta sake faɗa tana yin gaba abinta da alama wasu kayan ma zata tafi nema, ta kusada Ahmad ta gifta, fuskarta a sake ganin yana ta kallonta yasa tace masa "Sannu" se ya shiga sosa kai, besan sanda ta iso inda yake ba kuma bawai da niyya yake kallonta ba, wani abu yake so ya tantance, idan ba idanunsa ne suke gizo ba gani yayi kamar mutum ɗaya da kaloli biyu a gabansa. Ita da budurwar kamar an tsaga kara, hatta da muryoyinsu, banbancinsu Budurwar fara ce tas ita kuma tana da duhu dan bama za'a kirata wankan Tarwaɗa ba, Baƙace amma kyakykyawa ce tagaske Tabarakalla dan hartafi farar kyau sanda tazo kusa dashi sosai kuma ya fahimci ta girmewa waccan sosai, ba ita ba shikansa da alama zata iya girmarsa dukda da tana da kyan jiki. "Kamar ku ɗaya" ya faɗa mata kamar wani yaro yana nuna ƙanwar tata data zabga tsaki har inda suke tsaye sun jiyota. Matar ta sake faɗaɗa murmushinta tace "Haka ake faɗa, amma na fita kyau ai" ta matsa gaban kayan da yake ta juyawa duk Unisex ne, suna waya da Jay yana jagwalgwala kayan. Nazira ce ta haihu yake so yaje yaga baby shine yake so ya zaɓi kayan da ze kai mata ya kira Aslamiyya tace masa Anything pink is for girls blue na maza shine fa duk ya rikice ya rasa me ze ɗauka kusan minti sha biyar yana abu ɗaya. Ganin ta ciro wasu tana dubawa ya saka yace mata "Yawwa dan Allah Anty wanne ne na mata wanne na Maza?". Tayi murmushi har haƙoranta suka fito kafin tace "Wannan duk unisex ne, ana iya sakawa kowa kawai dai kasan Pink da blue color an fi sakawa Mace ko Namiji amma bayan su kana iya ɗaukan ko wacce kala zeyi, haihuwa akayi maka?" Kai ya girgiza mata yana murmushi yace "Aa, ai banida Mata. Yayata ce ta haihu baby girl nake so naje na ganta shine zan kai mata gift, ko zaki tayani zaɓa toh idan ban takuraki ba?" "Allah ya raya, ya kawo mata ta gari babu damuwa guda nawa kake so kuma kamar na wane kuɗi?" "Haba Anty Sauda jiranki fa nakeyi shine zaki shiga wata sabgar kuma da bakizo ba waye ze zaɓar masa kayan? Duk ma'aikatan gurin nan ke kaɗai ya gani da zece ki tayashi ɗaukar kaya ko kuwai neman gurin zama?" Ƙanwar tata ta faɗa cikin bacin rai. A fili Ahmad yace "Ikon Allah" yana kallonta yayarta me suna Sauda ta lafta mata harara kafin tace "Wai ni dole na miki da ki biyoni ne ko yaya? Idan ba zaki iya jira nagama abinda nake ba FATIMA ga hanya yi tafiyarki mana" Majid da se lokacin ya lura da Ahmad ne a gurin ya saki abinda yakeyi da sauri ya isa cikin ladabi yana cewa "Ranka ya daɗe wani abun kake buƙata?" "No, cigaba da aikinka kawai babu matsala ga Anty zata tayani zaɓa" ya sallameshi. Bata tafin ba se ƙara lafewa bango da tafi tana cika tana batsewa kamar fulawar dataji yeast. Anty Sauda kuwa ta cigaba da ɗaga kaya tana zaɓar nata dana Ahmad da yace kala biyar yake so. "Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" yayi mata godiya, Majid ya karɓi kayan yayi masa gaba dasu shi kuma ya kalli Fatima dake dabda fashewa yace "Ki zauna kar ƙafarki ta gaji bari a kawo miki ruwa me sanyi kisha". Sanin idan ta buɗe baki ba zata bashi amsa me daɗi ba tasa tayi ƙwafa kawai ta sake tsumewa. Seda Antynta ta gama jan ranta iyaka kafin aka tattara mata kayan da ta siya aka kai gurin biyan kuɗi lokacin tuni Ahmad ya biya nasa an kai masa mota yana ƙarasa wani abu kafin ya fita, ko tsinke ya ɗauka a gurin seya saka kuɗin balle ma wani yayi tunanin zuwa yace ze ɗibi bati kamar yanda Salim yaso ya fara masa sanda yake zuwa seya kwaso Abokanansa su ɗebi abu ayita rigima dasu a gun biyan kuɗi yace shiya basu ba zasu biya ba securities su hanasu fita, seda Ahmad ɗin yayi masa kaca kaca a gurin sannan ya samu salama dalilin kuma daya saka Salim ɗin ya bar aiki a gun wanda daman Momy tayi masa dole. Suna tsaye a bakin titi suna jiran abin hawa, Fatima nata zabga Mita Anty Sauda kuwa ta mata shiru kamar bada ita take ba, iyakar zafin ranar dake ratsasu ya isa sunfi Awa guda cikin sanyin Raɓa kuma sanda suka shiga rana bata take kamar haka ba seda suka fito suka ganta ƙwal da alamun hadari ze iya haɗuwa zuwa jimawa. Wani abin takaici kamar an hana masu Adaidaitan hanyarsu zuwa duk wanda suka tare da sunce MARMARA zece ba nan yayi ba, wanda zasuje kuma da mutum a ciki su kuma ga kaya drop ma yaƙi samuwa kamar wanda akawa baki. Suna nan tsaye kamar Fatima zata fashe ga rana ga babban abinda ya dameta ita, yanayin da take ji a jikinta ta tabbatar period ze iya zuwar mata a kowanne lokaci dukda gobe take saka ran zuwansa shiyasa ma bata fito a shirye ba amma suna shiga gurin nan taji jikinta ya fara sauyawa irin yanayin da takeji idan jinin ze zuba dan bata wani laulayi ko ciwon Mara sedai taji jikinta na mata wani Yamm kamar tana jin sanyi dataji haka tasan any moment ze iya zubowa to wannan yanayin takeji shiyasa duk ta takura tun shigarsu gurin Miskilanci kuma ya hana tayiwa Anty Saudan bayani se baƙin rai takeyi tana tsaki. Wata dalleliyar mota Ford fara tas ta giftasu se gata ta dawo da baya a hankali ta tsaya a gabansu, Ahmad ya sauke glass, fuskarsa me ɗauke da murmushin yan Aljanna ta bayyana ya kalli Fatima suka haɗa ido yanda tayi seda ya kusa bushewa da dariya amma ya kanne ya maida dubansa ga Anty Sauda. "Bari na rage muku hanya to nima cikin garin na nufa" Ya faɗa bayan da Anty Sauda ta masa bayanin sun rasa abin hawan hanyarsu ne, Fatima ta zabura tace "Yi tafiyarka zamu samu" Anty Sauda ta galla mata harara ƙasa ƙasa tace "Duk saboda ke yake wannan abun kiyi dagaske harya fusata ya tafi" "Allah ya kiyaye ni beyi mun ba" abinda Fatiman ta faɗa ya isa kuma har kunnen Ahmad dake ƙoƙarin saka musu kaya a booth securities biyu da suka hangoshi suka taho da sauri suna tayashi. Murmushi yayi da jin furucin Fatiman, sam kuma ransa be ɓaci ba illa ma burgeshi data ƙarayi domin ta nuna ita ɗin Macece me ra'ayi wani abu da ta gani tattare dashi be ruɗeta ba dukda yasan basu da masaniyar shine mamallakin gurin da sukayi siyayyar. Akan shiga motar ma seda akayi daga da ita Anty Sauda ta balbaleta da masifa Ahmad ya shiga tsakani yana bata haƙuri tareda lallashin Fatiman kan ta shiga su tafi, shikam Ajinta burgeshi yakeyi saɓanin sauran Matan da suke zuwa gurin kaga Mace har Mace amma babu Aji, wasu takanas suke zuwa ganin CEO saboda an san kusan koyaushe yana zaune a office ɗinsa indai yana Kano, wasu ma zuwa suke da ƙaryar kaya zasu kawo, ba kuma zasuyi magana da Sales Manager ba seda CEO kai tsaye da Ma'aikatan suka gane me yake kawo su se suka fara hanasu suce basa karban kaya a hakan wasu zasu zauna a waje jiransa muddin anga motarsa a Parking lot kiran waya kuwa seda ya maida layinsa private idan beyi saving Number ba kira baze shiga ba sannan ya samu Sa'ida, kuskurensa saka Main Line ɗinsa akan Banner su. Suna tafe suna yar hira da Anty Sauda har suka isa bakin titi inda ze ajiyesu dan Mota bata shiga har cikin layinsu, Anty Sauda ta fita ta kira yara suka fara kwashe mata kayanta, seda suka gama tas ta kalli Ahmad tace "Mungode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" "Amin Anty, Allah kuma ya raba lafiya, gashi banga gidan ba balle nazo cin naman suna" "Seka karbi number waccen, idan na haihu seta sanar maka ko?" Cewar Anty Saudan. Ya juya ya kalli Fatima yana cewa "Kodai ki bani da kanki, kalli fa yanda ta haɗa fuska Allah sa ba tunanin yanda zata shaƙeni takeyi ba , daman idan kin haihu karki bari ta fara ɗaukan Babyn kar yayo gadon rashin fara'arta ". Fatiman na zaune tana kuma jinsu kamar an dasata a gaban motar, tasan me afkuwa ta afku shiyasa ta kasa motsawa daga inda take. Abinda ta guda da hawa lift ɗin kenan, idan da Napep suka hawo bakinta alaikum se samu hanyar kurɗawa ya kaisu har ƙofar gida data sauka ta afka kuma ba lallai kujerarsa ta nuna ba sabanin ta Ahmad da take fara tas ita kam yau ina zata kai wannan abin kunyar staining a motar jama'a daga Rage hanya? Ya miƙawa Anty Sauda wayarsa ta sanya masa number Fatima wadda tare suka siyi layin banbancin lambobin ƙarshene kawai da tata shiyasa ta riƙe kafin ta sake masa godiya ta shige layi ba tareda tabi takan Fatima ba. "Ko ba tare kuke ba?" Ahmad ya faɗa yana karantar fuskarta, dukda be santa ba amma wannan fuskar tata da akwai abinda yake damunta ba iyakar Miskilanci bane". Fatima ta yunƙura domin babu amfanin zaman da takeyi a cikin motar. Ta kalli kan layinsu dukda tsakiyar ranace ƙwal amma munafukai yan saka'ido na nan suna bin inuwar gefen Titi a haka zata ratsasu ta wuce? Jakarta ta buɗe da dabarar kiran Anty Sauda ta bada Hijabi A Miƙo mata tazo mata, da zasu fita harta saka Hijabinta haka nan ta canza kaya ta saka Abaya Light blue ashe rabon abin kunya ya jata da Hijabi ne Asirinta a rufe kota bata masa kujera shamiƙewa zatayi ta tafi dan ba sake haɗuwa zasuyi ba balle taji kunya. Takaicinta ya ƙaru sanda ta zaro wayar taganta a mace, ita dai yau bata fito da sa'a ba. Ta kalli Ahmad fuska a marairaice, so take tace ya bata aron wayarsa amma ina hali irin nata na shegen Miskilanci ya hanata se kawai ta rungume jakarta jin ya yiwa motar key da alamun ya gaji da jiranta ne ze tafi da ita ko yaya ta kama murfin motar ta buɗe, tana zura ƙafafunta waje Ahmad dake lura da duk motsinta yaga abinda take boyewa, da saurin gaske ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta da ƙarfi. Ta dakata ɗin tareda kallonsa yace mata "Me yasa tun a Mall bakiyi magana an baki pad kin gyara jikinki ba? Da a haka zaki keta titi ki wuce waɗannan Mutanen?" Mutanen daya faɗa ta kalla. Suna nan tun tsayuwarsu a motar suka baza idanuwa suna naɗar rahoton gulma da munafunci wanda sukafi ƙwarewa akai. Fita yayi daga motar ya buɗw booth, tana tunanin Pad ɗin ze ɗauko mata ko me? Koda yake a yanzu ai pad bata da amfani a gurinta ta samu abinda zata rufa ta isa gida kawai take da buƙata kuma wayar tasa dai itace mafitarta. Tana saƙa abinda zatayi ya dawo da leda a hannunsa ya miƙa matata karɓa ganin kamar yadin Hijabi ko Abaya. Hijabi ta gani data warwarshi har bata sanda ajiyar zuciya me Nauyi ta kwace mata ba, ta zura a jikinta kafin ta saci kallonsa kamar mara gaskiya tace "Nagode" "Babu damuwa, but next time idan kina cikin yanayin buƙatar taimako kiyi magana bakiyi ɓacin rai kina kumburi ba" "Toh" kawai tace masa kafin ta fita tana waiwayen inda ta zauna ya baci sosai kuwa kamar ma da gayya Jinin yazo da yawa dan ya kunyatata. Murmushi Ahmad ya rakata dashi harta ƙulewa ganinsa, harya tada motar se kuma wani tunani ya saka ya gyara parking ya sauka yabi cikin Layin da sukayi. Beyi nisa da yawa ba ya tambayi wasu yara gidansu Fatima sukace basu santa. Ya riƙe ƙugu yana kallon Lokon da ya tabbatar idan ya ƙureshi ze tsinci kansa ne a wata unguwar daban ba wadda yake ciki ba, hagu da dama kuma layukan duk basa ɓulla ya tabbatar gidansu na daga cikinsu, harya haƙura ze juya tunda ya samu number wayarta sega wani saurayi ya fito daga wani gida da bokitin Markaɗe ya tareshi yana tambayarsa gidansu Fatima. "Farace sosai?" Yaron ya tambayeshi ya gyaɗa masa kai alamar itace, yaron ya ƙwalawa ɗaya daga cikin yaran dake wasa kira yace "Ka rakashi gidan Malam bakanike" "Bansan gidan ba" yaron ya faɗa yana zabura ze koma gun wasansa wanda ya kirashin ya talle masa ƙeya yace "Gidan su Jafarun ne zakace baka sani ba banza gidansu yar Fara fa" "To ai haka zaka ce mun ba yanzu Anty yar Faran ta wuce ba da Antynsu me Mota sun taho da kaya da yawa mu muka kai mata gidan ma ta bamu Cakulat" yaron ya sake faɗa kafin yayi gaba yana tsalle, Ahmad ya zaro dari biyar a aljihunsa ya bawa babban yaron kafin yabi bayan wancan. Da yar tafiya daga Titi zuwa gidansu a can cikin Lokon suke har sun kusa shiga Alfindiki ma daɗin da sukaji lokon gaba ɗaya lailaye yake da Interlock ga Fitulun Solar da alamu basu da matsalar haske har tsakar gida sun huta da kunna fiti. A ƙofar wani gida yaron ya tsaya. Daga yanayin ginin zaka fahimci gidan masu ƙaramin ƙarfi ne, ya sallami Yaron da alawoyin dake cikin Aljihunsa sannan ya juya ya tafi daman gurin kawai yake so ya gani. Babu ƙyama ya saka Ruwa daya zubawa Omo da freshner ya goge kujerar tsaf, ya maimaita gogewar har sau uku kafin ya saka clean ruwa ya goge sannan ya sake fesa Freshner akai sa'annan ya ya tayar da mota ya bar gurin. Yana tuƙi yana tunanota, yanda take haɗa fuska tana motsa ƙaramin bakinta ba ƙaramin kyau tayi masa ba. Ya tuna idanuwanta sanda ta rasa mafita ya bata Hijabi, muryarta a karaye da tace masa ta gode har zuwa tafiyarta a sanyaye kamar wadda batada laka. Zuciyarsa ta ringa ayyano masa gidan data fito, yanayi na suffa da tsarin halitta daga ita har Yayarta be taɓa hango daga irin wannan unguwar suka fito bama balle wannan gidan, seya tuna da wani abokinsa Munir da ya taɓa ce musu Mata da suka amsa sunan Mata na cikin Lungu. "Kunga unguwannin nan da muke gani as no go, wlh mata nacan, kaga yarinya kamar ita tayi kanta gashi sun ƙoshi da tarbiyya kawai dai basu kai wayewar da muke kwaɗayi ba amma ni dai idan na tashi aure Lungu zanje na samo mata wadda zan ringa Faɗawa magana taji da ɗan kuɗina ƙalilan Alaji a hankali na wayar da ita yanda nake so" inji Munir ɗin to yau ya gasgata zancensa domin Fatima dai kodaga Villa ta fito ta isa Mace kuma za'a nunata a ko ina ba tare da anji kunya ba, shikam yaga Mata dukda tace be mata ba, ze tabbatar da se yayi matan dan baze bari ta wuceshi ba, ita ɗin tayi daidai da tsari da ra'ayinsa. Yama manta da zeje gidan Nazira seda ya ganshi a ƙofar gidansu tukunna ya tuna, kwakwalwa duk tunanin Fatima har ya fara loosing focus. Gidan ya shige akan se da dare idan ya fita seya kai mata kawai. Haka ya ƙarasa yinin ranar har gizo take masa muryarta na masa amsa kuwwa. Ahmad be taɓayin budurwa da yaji ta shiga zuciyarsa farat ɗaya a ganin farko ya sakawa ransa ya samu mata ba se akan Fatiman. Mutum ne shi da idan abu ya shiga ransa tofa se Allah, Fatiman kuma abin nata yazo masa da gaske, daga haɗuwa yini ɗaya harya fara tsara rayuwar da zasuyi tare, har tunani yakeyi idan da gaske tace beyi mata ba wani kalar garari rayuwarsa zata shiga dan ya rigada ya kwallafa rai a kanta, shi kuma duk abinda ya saka rai da samu baya taɓa saduda har seya mallaki wannan abun. Yaya zeyi idan ya gaza cin galabar zuciyar Fatima ta Aminta dashi. Seda yayi sallar Isha'i ya tafi gidan Nazira, ya tarar da Matan Naziru Uwargidan Anty Mardiyya da Amaryar da yayi kwanannan Yusra wato Yuseebaby Shahararriyar yar rawar Nanayece a Sabuwar Manhajar Tiktok, su suka fara yankewa bin waƙa ana rawa a tiktok ɗin cibi. Allah kaɗai yasan inda Nazirun ya yayibota kuma da yake me uwa a bakin murhune duk sukar da abokanan Alhaji suka ringa kawo masa akan Yarinyar wadda kowa ya bada shaidar bata jin magana cewa yayi tunda me Auranta yaji ya gani ai shikenan, Karuwa ma idan ta tuba ana auranta balle ita da babu wanda ze kawo shaidar cewa tana Alfasha, Yarinyar da har video take iyayi da undies ta ɗora a Tiktok amma Alhajin ya murje ido yace babu komai ya aureta, koda yake umarnin Hajiya domin ita yarinyar tayi mata, yanda tayi suna tayi shura tana da followers bila Adadin a duniya baki ɗaya ba iyakar Nigeria ba ga uwarta tana da kuɗi suna da ƙaton gida wanda akace ire iren Alhazan da take hulɗa dasu ne wani ya gina musu gidan, hatta Kawunta daya bawa Nazirun Auranta se bayan anyi Baba Alƙali ya binciko cewar ƙaryane ashe ba ɗan uwanta bane tsohon saurayinta ne. Mahaifinta kuma yana raye sukace ya rasu, mutumin Sokoto ne, gajiya yayi da halin uwarta ya saketa tun Yusran na yar yarinya ta taho da ita Kano ta tashi a sakalce yanda dai take yanzu, to Me aure da iyayensa sunce sunji sun gani duk wani me abin faɗa dole ya kama bakinsa. Sanda Ahmad ɗin ya shiga falon Nazirar ma tarar da ita yayi ta jera Yayan Nazirar Su uku yammata babbar ta riƙe yar Babyn ta kunna waƙa tana musu Video suna rawa Nazirar da Mardiyya da wata da be sani ba suna zaune suna hira daga gefe, ransa ya baci, tun batafi wata da shiga gidansu ba ta fara koyawa Yaran gidan wannan iskancin raye rayen ana video, seda ya kwace wayar Maimuna data Sarah, ita Aslamiyya tumda ya mata gargaɗi ta dena. Wayar Sarah ko awa batayi a hannunsa ba Hajiya tazo ta fara Tijara Momy tace ya basu wayarsu. Maimuna ma taurin kai tayi masa taci gaba dayi wai a Draft take saving randa ya ɗauki wayarta ya gani shikenan ya kasheta ya ajiye seda tayi wata uku taji jiki kafin ya bata to basu Kaɗai ba Babbar Yar Alhaji Zakariyya ma tana nan ance ta fara zama sananniya a Tiktok ɗin dukda dai ubanta yace wai tallan kaya takeyiwa Mamanta dake tana siyar da Dogayen riguna da sauran kayan kwalliyar Mata, amma fa rawa take tiƙa abinta kuma duk wani trend daya fito sune akan gaba gurin yi abin dai se a hankali. Bayan sun gaisa ya Naziran yace mata "Amma Anty kina kallo take ɗaukan video yaranki harda Baby zata saka a Tikto, baki san duk a nan yara suke kwaso baki kowa idan ya gani da me faɗar Alkhairi dame bakin sharri wani ma yabawa zeyi amma idan bakinsa bame kyau bane se kiga wani abu ya faru, ya kamata dai ku ringa kiyayewa, ko su wanda suka kawo Tiktok ɗin wayanda suka san abinda sukeyi a cikinsu basa exposing yaransu ƙanana ko zasu musu video basa nuna fuskarsu amma kalli yanzu dan Allah Nur ai ta wuce shekarun da zata ringa daukar hoto babu kallabi bare har a ɗorata a Tiktok". Mardiyya tace "uhm" domin abune dayafi ƙarfinta tayi magana su koma gida ta haɗa mata tuggu gurin Mijinsu se ɗayar matar ce tace "Nima dai na faɗa, Malamai ma nata wa'azi akan wannan shagalar data zo mana wlh, gaba ɗaya yara sun lalace, tun suna ƙanana an cire musu kunya ana sakasu suyi ta raye raye ana ɗorasu a duniya haka zasu tashi basajin nauyi ko kunyar yin rawa a ko ina ko a gaban wa kuma ta bakinka dame baki mai kyau da mara kyau kowa ya tanka Allah dai ya kiyaye. Kaganni ni ko saka hoton jinjiri a status na kiyaya wlh, nan wata ƙawata ta haihu, bakuga yaron ba Tabarakallah Masha Allah kyakykyawa kamar ɗan larabawa. Ta ringa turashi group group na makaranta, na kasuwanci, na Novel ne groups ɗinta na WhatsApp babu inda bata tura hoton Yaron nan ba kowa kaya kaya anata yabawa wasu na cewa basu taɓa ganin Jinjiri me kyansa ba, in taƙaita muku wlh Yaron nan kamar wasa ya fara rashin lafiya, Asibiti har Saudiyya suka kaishi anyi gwaje gwaje ance komai lafoya ba'asan abinda yake damunsa ba yaron nan be samu lafiya ba har seda ta Allah ta kasance shekarar sa Ɗaya ya mutu kuma bata daddara ba yana Jinyar tana sake tura hotonsa wai a tayasu da Addu'a Allah ya bashi lafiya, shin idan ka haihu ba zaka iya faɗa haka kawai ba dolene se ka tura hoton Yaro ko Yarinya a group? Kasan iya inda ze tsaya mutane da Aljanu masu ido biyu da masu huɗu duk suyi ta kalle maka Yaya to yi ta kanki dai ki karɓe jinjinniyarki idan ma su manyan ba zaki hanasu ba ita dai bata san komai ba kar a fara ɗura mata sheɗanci a kwakwalwa". Yusra fa ta shaƙa tayi fam musamman da Nazira tace ta goge Video dan idan Babansu ma ya gani tasan se yayi faɗa ai ta zata a WhatsApp status zata ɗora shiyasa ma batayi magana ba. Ta ringa hararar Ahmad domin shiya zo da wannan sanaben, shidai ko kallonta beyi ba dan ko gaisawa basuyi ba ya gama abinda ya kaishi gidan ya tafi. Yana cin abinci a falon Momy yana bata labarin zuwansa gidan Nazirar Jay ya kirashi, a speaker yasa wayar yana ci suna magana har zasu kashe Jay ɗin yace "Yah Ahmad waye ka gani ɗazu that you hanged my call?" Ahmad ya saki wani murmushi, shauƙi ya kwasheshi harya manta a inda yake. Wani baya yayi ya tallafe ƙeyarsa da hannu biyu yace masa "Addu'arka ce ta karɓu, muna wayar nan naga wata tsaleliyar budurwa ta sace mun zuciya, I'm telling you my brother na samu matar Aure" Ihu Jay ya fasa, a kwance yake akan tamfatsetsen gadonsa cikin apartment ɗinsa a birnin London amma haka ya tashi yana ihu yana tsalle kamar wani ƙaramin yaro. Ahmad kuwa besan katoɓarar da yayi ba seda ya ɗaga kai suka haɗa ido da Momy, a sittin ya fice daga falon seda suka kwana biyu suna wasan ɓuya dakyar tayi Bikonsa amma dukda haka sun zama kamar surukai baya iya haɗa ido da ita. PAGE 5 MARMARA GIDAN MALAM HAFIZU BAKANIKE Jiki a sanyaye kamar kazar da ruwan sama ya buga ta shiga gidan bakinta ɗauke da ƙaramar sallama. Anty Sauda na tsaye bakin fanfo tana wanke hannu bayan ta gama jajjefa ɗan waken da Ummansu tayi abincin rana, giftawar Fatiman kawai ta gani ta shige ɗaki dan bataji sallamar ba, bata daɗe a ɗakin hannunta riƙeda Kwandon kayan wankanta se zani da ledar pad har sannan tana sanye da Hijab ɗin daya mata kyau matuƙa ta raɓe Anty Saudan zata shige banɗaki "Ina kika samo Hijabi kuma?" Antyn ta tambayeta ta shige ba tareda ta bata amsa ba. Taci Sa'a ruwan fanfo yazo ta tara bokiti dukda bata son wanka da ruwan sanyi kwata kwata komai zafi dole haka ta watsa dan babu lokacin da zata tsaya ɗumama ruwa yanzu. Bayan ta gama ta wanke rigar ta da kayan cikin da suka ɓaci, faɗin irin yanayin da take ciki kan wannan abin kunya daya sameta ɓata lokacine, tunani takeyi wa ze gyara kujerar da ta ɓata? Da kansa ze goge ko car wash ze kai? Ita kam yau taga ta kanta Period ya kwafsa mata wai ma Allah yasa ba idon sani bane babu lallai su sake haɗuwa yanzu da be bata Hijabin nan ba ya zatayi? "Ko ina ya samu Hijab ma oho" ta faɗa a fili tana shanya kayanta akan igiya. Anty Saude tayi rashe rashe cikin barander ga Zobo me sanyin gaske gabanta tana sha tana kallon Fatiman ta sake shigewa ɗaki, seda ta kimtsa kanta sosai kafin ta fito har sannan ranta babu daɗi ta zauna kan Tabarmar kusada Anty Sauda. "Wai wane isakanci ne yake damunki AFEEYA ina ta miki magana kina mun banza, wani sabon raini ne yake neman shiga tsakaninmu ko yaya?" Anty Saudan ta faɗa a ɗan fusace. Idanun Fatima sukayi rau rau har muryarta na rawa tace "Toni me zance miki? Duk bake kika jawo mun ba ina tace miki mu taho gida kikaƙi har seda kikaja na ɓata jikina shima na ɓata masa mota" Anty Sauda ta buɗe baki da mamaki tana kallonta kafin tace "Lallai yarinyar nan, duba nakeyi da zansan matsakarki ko kuwa ɗinke miki baki akayi da bazaki gayamin abinda kike ciki ba? Yanzu staining kika masa a mota? Innalillahi Afeeya kin tafka abin kunya staining a motar saurayi haɗuwar farko gaskiya abu beyi daɗi ba ka kujerunsa farare tab" bata gama rufe baki ba se ga hawaye sha sun fara zubowa Afeeya kamar an kunna fanfo abin ma se ya bawa Anty Sauda Dariya ta cigaba da Tirata tana faɗin ta kwafsa "To waya baki Hijabi kuma?" Ta tambayeta cikin kukan Afeeya tace "Shiya bani mana, harda cewa wai meyasa tun a can gurin ban tambaya an bani pad ba?" Anty Sauda cikin jimami kamar gaske tace "Ai gaskiya ne, kinga ranar Gayu ai gobe ma idan kina Al'ada ki sake saka kaya masu haske ki fita babu Hijabi, ni wannan daya bakin ma ɗinkin yamun kyau, idan ya kiraki ki tambayarmun shi inda ya siya". Kuka AFEEYA ta dage tanayi kamar yarinya tsa tsani raini yanzu ga ƙarshen raini can wani Namiji yaga jinin Al'adarta ita kuma Anty Sauda harda cewa wai ya kirata, ai wlh koya kira blocking zatayi babu ma zancen ko gaisawa suyi balle ya tuno abin kunyar da tayi a motarsa. Sallamar Ummansu ce tasa ta tsagaita kukan da takeyi, bata ma san bata gidan ba se yanzun data shigo. Umman ta zare Hijabin jikinta ta saƙale jikin igiya tana kallom Afeeyan tace "Uwannan lafiya? Meya faru kike kuka? Ina kuma kika tsaya Yayarki ta rigaki shigowa gida?" Se maganar Umman ta sake tunzurata kukan ya ƙara ƙarfi, ta gaya mata bata son wannan sunan wai Uwannan amma Umman taƙi bari kamar da gayya ma take kiranta haka dukda Baffa da kansa yace ta dena amma taƙiji. Anty Sauda ce tayi mata bayani, Umman ta haɗiye dariyarta tace "To kuma shine abin kuka? Lalura ce shima ai ya sani. Kima godewa Allah daya sa yana da abinda ze baki ki suturta kanki, kina kukan dan shi kaɗai ya gani to da kuma kin keto Titi da abin ashe ba zaki sake fita ko ƙofar gida ba saboda kunyar yan unguwa" maganar Umman Gaskiya ce wannna tasa ta haɗiye kukanta ta zubo abimci tana ci tana sauraron hirar Umman da Anty Sauda. Har dare ta kasa sakewa duk motsi seta tuno Ahmad da yanda ya ringa kallon gurin data ɓata Allah kaɗai yasan tunanin da yakeyi a ransa. Da Mijin Anty Sauda yazo zasu tafi haka suka sake kinkimar kayan da suka siyo ɗazun aka kai Mota, Afeeya nata mitar mema yasa ta kawo su gidan da se ta barsu acan su mata Delivery kai tsaye ba seta wahalar da mutane anyi ɗauka biyu ba. Har Anty Saudan ta zauna a motar ta yafito Afeeya tana cewa "Ya kiraki kuwa?" "Wa?" Ta tambayeta kamar bata gane wanda take nufi ba. Anty Sauda ta lafta mata harara tace "Saura ki masa wulaƙancin da kika saba yiwa samari" "Ai daman na gaya miki beyi mun ba" amsar data bata tana tura baki ta koma gida. Dagaske take har ranta Ahmad beyi mata ba a matsayin saurayi. Bashida makusa a halitta domin kyakykyawane daidai misali amma magana ta domin Allah yayi mata ƙarami shi ba wani tsayi can ba kuma bashida jiki sannan da ganinsa sanyi ƙalau ne se yanda mace tayi dashi kuma ya fiya Fara'a gaba ɗaya be kama hanyar Mijin da take buri ba. AHMAD Yar matsala suka samu ta rikicewar lissafi a Shago wannan ya ɗauke masa hankali haryasa be samu damar kiran Fatima ba har akayi sati guda da haɗuwarsu badan ya manta da ita ba ko bata ransa Aa sedan yana da buƙatar nutsuwa gurin warware abinda yake a gabansa. Seda ya samu komai ya koma kan layi kafin ya dawo lissafin Fatiman har yayi niyyar kiranta sedai kamar Almara ya nemi number da yayi saving da hannunsa sama ko ƙasa ya rasa. Yayi mamakin yanda akayi ta goge amma ya godewa Allah daya sa yayi basirar bincikar gidansu tun waccen ranar. Da Magriba ranar Juma'a bayan ya dawo daga sallah ya niyyatu zuwa gidan idan yaso ya sakw karɓo number dan dagaske yakeyi yaga fure kuma bazeyi saken da zata kufce masa ba. Fuskar daya gani a gurin Yayarta ta tabbatar masa Fatiman a kasuwa take, ma'ana wani bai rigashi ba ko ba'ayi mata baiko da wani ba domin yanayinsu basuyi kama da wanda zasuyi kwashe kwashen samari ba. Tsaf ya shirya cikin Manyan kaya ya kafa hula shida kansa yasan yayi kyau ya ringa murmushi yan fesa turare yana hasaso fuskarta ya zata karɓeshi? Da tace beyi mata ba dagaske takeyi har ranta ko kuwa dai irin abin nan na yammata ne? Wayarsa dake ajiye ce ta ɗauki ƙara ya janyota ya duba Momy cw take kira dan haka ya ɗaga da sauri yana sallama. "Yaya Ahmad wai ni ina saƙona daka karɓomun kai baka ce mun gasu ba nima na sha'afa fin sati se yanzu da nake so nayi amfani dasu na tuna" Momy ta faɗa bayan data amsa sallamarsa. Tana cewa saƙo ya gane wanda take nufi, Hijaban daya karɓo mata ne a gidan *UMMU-MAHEER ME HIJABS ƊIN YAN GAYU* wanda harya ɗaukarwa Fatima a ciki. "Yanzu zan kawo miki Momy na mantane wlh" ya faɗa da sauri kuma ya ɗauki muƙullin motarsa ya fita daga ɗakin suka kusa yin karo da Lawan, Autan Hajiya Binta a Maza ya taho hannu biyu riƙe da Tab yana buga game kamar wani yaro ƙarami yayi diri diri shi bai kauce ba be kuma matsa bayaba. Haushi ya ƙume Ahmad, ga sauri yanayi a fusace yace masa "Ni zan kauce maka ka wuce kenan?" Lawan ɗin yayi muimui da baki kafin ya raɓe gefe, Ahmad yayi ƙwafa ya wuceshi dan yana da abinyi yanzu amma tabbas se koma ta kansa wannan rainin da yaron ya ɗauko baze zuba Ido ya barshi ya tashi a haka ba kamar sauran Yaran gidan idanba haka fa Zayyad da yake ƙarami a gidan duka shima haka ze taso da Tarbiyyarsu, Matan tasu rashin kunyar da sauƙi da wuya suyiwa Mazan sedai a tsakaninsu amma su waɗannan da suke tashi yanzu shida Mu'allim jin kansu suke daidai dai da uban kowa daman Salim Da Faisal sun rigada sun ƙafura tuntuni. Ledar Hijaban ya ɗauka, guda goma ne ya bawa Fatima ɗaya ya wuce ciki a tsakar gida suka ci karo da Hajiya idanuwanta akan Ledar hannunsa tamkar zata huda tashiga taga abinda yake ciki haka take kallon Ledar ko gaisuwar da yake mata bataji ba balle ta amsa dan haka yayi gaba shina ya kusa shiga ɗakin Momy ya jiyota tana cewa "Au Amadu, kana kallona ka wuce ko gaisheni ba zakayi ba" "Ya fa gaisheki Hajiya kinata kallon Ledar hannunsa" Sarah ta bata amsa aiko ta kai mata duka ta kauce nan ta shiga sababi tana cewa "Dan uwarki dake nake? Ko kin koma Amadu bansani ba shegiya me shegen shishshigi a abinda ba'a sakata ba kuma da idon ubanki kika ga ina kallon kayan hannunsa?" Hajiya Rabi na daga cikin falonta inda ta idar da sallah tana lazumi hayagagar Hajiyar ya na neman ya raba mata hankali dan ta jikin window ta take tsaye, rabon ayi yasa ta leƙa kaɗan tacewa Hajiyar tayi haƙuri tayi shiru nan ta juya kanta ta dirar mata cin mutunchi da gorin da bata gajiya dayi mata. "Itama Rabi banda neman magana waya kaita tanka mata? Yau Allah ya taimakemu tun safe kunnuwanmu shiru rabon dai se an mana na dare" Momy ta faɗa sanda Ahmad ya dire ledar hannunsa a ƙasa ta jata gabanta tana fito da kayan ciki. Hijabai tara ta gani, ta fara ciresu daga ledojinsu tana duba yadin, fuskarta a washe tace "Kaji laushin yadin nan ga kyau a ido waye zece ba Ɗan Egypt ɗin bane?" Ahmad ya ja guda yana dubawa yace "Wai daman ba order kikayo ba?" "Inafa order? Yadin gidane wlh a gurin Hajiya Hauwa nake ganin ire irensu harta bani guda biyu naji daɗin ɗinkin sosai yanda yake zama a jiki be matse ba kuma baya bin Jikin mutum ga matured style na hannaye nima na ɗauka na wajene tace mun wata Matace takeyinsu sunanta *MARYAM FAROUK amma anfi saninta da UMMU-MAHEER (07061838488) indai Hijabi ake magana daga Normal Hijab me Hannu ko Mara hannu, Jilbab, ko two pieces Gown da V hijab to idan ka sameta an rufe magana, ga yadikan da take amfani dasu ka gansu nan dai ga kyau ko ba'a faɗa ba zasuyi quality sannan ga sauƙi shiyasa nace ta bani number ta kawai na siya na huta da jigilar siyowa daga Egypt ɗin nan kuma babu lallai mutum ya samu yanda yake so". "Gaskiya sunyi kyau sosai nima idan zan siyi Hijabs zaki bani number ta" yayi suɓutar baki, Momyn tayi dariya tace "Wato kowacece wannan bata kama da sauƙi ba, to Allah ya nuna mana lokaci dama ai ita zan bawa order Hijaban Lefenka da Jafar, ni guda tara ma na gani inaga tayi kuskuren lissafi ne" Ahmad ya shafa kansa cikin kunya yace "Aa Momy ni na ɗauka ɗayan" "To seka turamun kuɗina kuwa, ina zakaje haka naga kasha kwalliya da daren nan ko gurin yar tawa zakaje?" Ta sake faɗa tana kallonsa daga sama zuwa ƙasa ganin harda hula ya kafa, seya juya ya nufi ƙofa yana cewa "Kai Momy, nidai sena dawo kiyimun addu'a" "Allah ya tsare ya dawo dakai lafiya" "Amin Momyna" ya amsa daga nan ya fice da sauri yana jin Hajiya na kwala masa kira yaƙi tsayawa dan ɓata masa lokaci kawai zatayi ya sani. Daidai inda ya saukesu waccen ranar yayi parking, akwai wutar Nepa ga kuma fitilun Solar a cikin layukan dan haka hankali kwance ya ringa kutsawa harya isa ƙofar gidansu. A kan Dakali dake ƙofar gidan ya zauna ganin gurin fes yake babu datti kamar yanda Dandamalin Ƙofar gidan yake har zuwa cikin soron da shima yake shafe da sumunti da fasassun Tiles ko ina tas. Hangen yaron daze tura yayi masa sallama da ita yakeyi sega wani Saurayi da zasu iyayin Sa'anni koya girme masa da kaɗan ya fito daga gidan yana ganinsa ya fahimci ɗan gidannan kamarsu ɗaya dasu sedai shima be kaita haske ba amma yafi waccen Yayar tasu haske. Ya miƙawa saurin daya dakata hannu sukayi musabaha. "Baffa za'ayi maka sallama dashi?" Saurayin ya faɗa dan dukda ya ganshi Matashi be kawo gurin Afeeya yazo ba tunda yasan samarinta a waya suke kiranta da wuya a aiko yaro sallama kuma ya dade a cikin gida harya fito beji tayi waya ko tayi zancen zatayi baƙo ba. Ahmad kuwa ji yayi kamar ya masa wata tunasarwa daya manta. Tabbas da mahaifinta ya kamata ya fara magana ya nemi izinin nemanta kamar yanda Shari'a ta tanadar dan haka yayi murmushi yace masa Eh. Saurayin ya juya, a bayan rigar Jessy dake jikinsa yaga an rubuta JAY amma bata Arsenal bace ta club ɗin unguwa ce amma ya tabbatar sunan daya gani baya rasa ace Fan ɗin Jafar ɗinsa ne. Saurayin ya fito ya sanar masa da Baffan yana zuwa daga nan ya wuce inda zashi, babu jimawa Sega wani Dattijon ya fito a ƙalla zeyi shekaru sittin da ɗoriya yana da matsakaicin jiki tamkar dai Ahmad ɗin, babu wata shahararriyar kama tsakaninsa dasu Fatiman seta jini da kuma fatarsa me duhu da Anty Sauda da saurayin da yaji ya ambata da Jafaru suka ɗauka. "Samari kaine Jafaru yace kanaa sallama dani?" Baffan ya faɗa. Ahmad ya zube a ƙasa kamar ze kwanta ya shiga gaisheshi Baffa se cewa yake ya tashi karya ɓata kayansa amma ya ƙi tashin. Bayan gaisuwar shiru ya biyo baya, Baffa na kallonsa da sauraron jin me yake tafe dashi Ahmad kuma nauyin Dattijon da kunya irin tasa yasa ya kasa magana seda Baffan yace "Inajinka samari lafiya dai ko? Fuskar taka ta kwantamun gaskiya ko maganar gyaran Mota ce?" "Aa Baffa, bamu taɓa haɗuwa bama. Daman wata yarinya na gani kuma akace a nan gidan take, shine nake so nayi tambaya naji ko da maganar wani a ciki" ya tattara ƙarfin guiwa ya faɗa. Baffa yayi murmushi Ahmad ɗin kuma ya burgeshi domin ya nuna shi ɗin mai tarbiyyane kuma yasan shari'a. Gyara tsayuwa Baffa yayi yana kallonsa yace "Madallah, naji daɗi kwarai da kayi abinda ya kamata kuma ina mai sanar dakai Yarinya tana da manema amma har yanzu dai babu wanda magana me ƙarfi ta ƙullu tsakaninsu dan haka kana da dama ka gwada taka sa'ar idan da rabo se Allah yasa a dace, amma Yaya sunaka? Kuma kai ɗin ɗan garin nan ne ko Ina?" Daɗi ya kama Ahmad jin amsar Baffa ya sake sunkuyar da kai yana murmushi yace "Eh, ni ɗan garin nan ne. Mahaifina sunansa Alhaji Audu Bechi sunana Ahmad" "Alhaji Audu Bechi dai dana ke jin sunansa?" Baffa ya faɗa cikin mamaki, Ahmad ya gyaɗa kai cikin tabbatarwa yace "Eh shi, ni Ɗansa ne". "Toh, toh masha Allah, amma yaro ita Mamana ka gani ko kuwa wata ce tazo gurinta kaga ta shiga nan gidan?" Baffa ya sake tambayarsa dason tabbatarwa domin sunan Mahaifinsa daya kira ya sakashi kokonton Anya wanda ya fito daga babban gida kamar wannan ze biyi yar Talaka irinsa yace yana sonta da aure? "Sunanta dai Fatimaz tareda yayarta Anty Sauda na gansu" Ahmad ya bashi amsa wannan ya tabbatar masa dagaskw ita Fatiman dai ya gani. Numfashi yaja kafin ya fara magana yana cewa "Tabbas Yatace wacce ka gani, sedai kuma a matsayi da irin gidan daka fito bana tsammanin zaka zo gida kamar nawa kace kaga yarinya kana so ba kuma da aure, dan haka ina roƙonka da kayi haƙuri idan wata sharholiya ce ta kawoka gurinta ka tafi domin nasan maganar Aure ba zata taɓa yuwuwa a tsakaninku ba saboda banbanci matsayi da kuke dashi, a zamanin nan da Masu kuɗi suke kyamatar talakawa bana zatom koda har zuciyarka da gaske kake son Fatima Iyayenka zasu goyi bayan daka Aureta kadai ga gidansu ka kuma ganni nine mahaifinta ni ba kowa bane sana'ar gyaran Mota nakeyi da ita nake cida Iyalina na shayar dasu kar wani kyau ko zubin Halittarta ya ruɗeka, ni bana son tashin hankali da abinda ze janyo Kace nace, a Ƙasar nan babu wanda besan sunan Mahaifinka ba bana tsammatar mutum kamar shi ze yarda ya haɗa zuri'a da Talaka kamata". Cikin mutuwar jikin da maganganun Malam Hafizu Ahmad ya buɗe baki dakyar yace "Amma Baffa banji daɗin da kayi mun zaton wani abu na daban ya kawoni gurin Fatima ba aure ba, dukda kaima kana da naka uzurin amma Baffa da Mai kuɗi da talaka duk Allah yayisu babu wanda yafi wani a gurinsa se wanda yafi tsoronsa da kiyaye dokokin Allah. Sannan babu wata Aya ko Hadisi ko shari'a data haramta Aure tsakanin Mai kuɗi da Talaka, kuma Baffa Mahaifina baya daga cikin irin waɗannan mutanen da suke kyamatar wani saboda banbancin matsayin abun duniya ko Mulki, a auratayya bayan Ingancin Asali da Tarbiyyar gidan da aka nemo Auran muddin Ma'aurin yana so bashida damuwa baze hana ba. Nine Ɗa na goma sha ɗaya a jerin Maza, yayyena Tara sunyi aure ɗayane beyi ba a cikinsu kuma harda me mata uku sannan kowa da irin gidan da yayo aure babu kuma wanda Alhajinmu ya taɓa hanawa ya auri Matar da yake so ba na tabbatar kuma ba za'a fara a kaina ba In sha Allahu". Malam Hafizu ya sakw jan numfashi yace "Karka fahimceni a baibai Yaro, tabbas ba kowanne me kuɗi bane yake da hali na ƙin Talaka amma kuma kuma masu irin waccen Ɗabi'ar su sukafi yawa. Abinda yasa kuma nake maka togaciya saboda bana so azo a maimaita abinda ya faru akan Yayarta, Mijin da ya aureta yayiwa Iyayensa ƙarya akan Asalinta saboda ya samu su barshi ya aureta ba tareda qata tangarɗa ba, aure kuma ba'a ɓoye ɓoye domin komai daren daɗewa se gaskiya ta bayyana dan haka abu ɗaya da nake so kaje ka nemi Yardar Iyayenka ka gaya musu yar wa kake nema kake kuma so ka aura kar kayi musu ƙarya idan har ka samu Amincewarsu ni banida matsala ya rage tsakaninka da yarinya kus samu daidaito namu mu rakaku da Addu'a" Daga haka Baffan yayi masa sallama ya koma gida Ahmad guiwoyi a sage ya koma gida gashi bega Fatima ba be kuma samu number tata ba balle ya kirata. Yasan bashida matsala ko kaɗan da Momy, Besan ya ze tunkari Alhaji da zancen aure ba yanzu dukda yasan abu me me wahala ace Alhaji ze hanashi Auran koma wacece ya kawo tunda ya bari an auri me rangwamen Asali ma ai baze hanashi Auran Fatima ba. Ranar kwana yayi yana saƙa ta inda ze fara, ze gayawa Momy sannan ze nemi shawarar Jafar su biyun sune manyan Abokanansa kuma duk shawarar da suka bashi yasan zata bulle masa. Sha biyun dare ta haura amma haka ya dannawa Jafar kira, Macece ta ɗauki wayar cikin harshen turanci ta sanar masa Jafar ɗin yana wanka amma karyewar harshenta ya tabbatar da ba Asalin Baturiya bace tana da wani yaren daya fi zama a harahenta sosai, yana jiyo tsawar da Jafar ɗin ya buga mata akan me yasa zata amsa masa waya. "I'm sorry Yah Ahmad and wlh ba abinda kake tunani bane, she is only a friend tayi visiting ɗinane and she is leaving now" Jafar ya faɗa bayan daya karɓi wayar a hannunta. Ahmad ya sauke numfashi irin na disappointment kafin yace "Nidai bazan gaji da tuna maka kaji tsoron Allah ba, karka bari ɗaukaka ta saka ka manta wanda yayi maka komai ka kuma saka masa ta hanyar saɓa masa da aikata abubuwan da yayi hani dasu sannnan Jafar ka sani Zina bashi ce, muna da ƙanne Mata, zamuyi aure mu haifi Yaya karkayi abinda zaka janyowa Yaranmu da basuji ba basu gani ba su biya bashin da basu suka aikata ba, i called you to discuss something important but since you are busy may be we takl about it some other time" yana gama faɗar haka be jira ta bakin Jafar ɗin ba ya kashe wayarsa ransa duk babu daɗi. Ya sani a ƙadamin da Jafar yake ko be nemi Mata ba Mata zasu nemeshi, koshi da be kaishi Ɗaukaka da samun suna ba a yanzu fama yake da Mata masu binsa ƙafa da ƙafa da sunan so wasu kai tsaye suke faɗin ko ba aurensu zeyi na su ƙulla Alaƙa kawai, balle Jafar dake tsakiyar Mata kala kala na kowacce yare da ƙabila wanda kowa ze so ace yana da Alaƙa dashi. ya rasa irin lalacewar da zamani yayi yanzu Maza sun dena neman Mata da fasiƙanci Matan ne suke kai kansu da kansu wasu dan neman abin duniya wasu kuma ka rasa ma me suke nema domin idan kuɗi ne suna dashi kai Allah yasa mu dace kawai. Yanajin wayarsa tana ƙara, Jafar ne haƙuri kuma ze bashi to amma idan ya aikata abinda yake guje masan ai bashi ze bawa haƙuri ba Allahn sa daya batawa ze nemi gafararsa. Jafar daya gaji da kira ya turo masa Text message yana cewa "Wallahi Allah Yah Ahmad i have never cross any girls boundary, only kiss and some fore play, shima zan dena in sha Allahu". "Oh zaka dena bama ka dena bako? Duk zina sunanta Zina babba ko ƙarama, Jafar live your life as you want it ban hanaka na ina sauke haƙƙi ne a matsayina na ɗan uwanka shi yasa nake tunatar dakai abinda yake daidai da ba daidai ba" ya turawa Jafar ɗin. Jafar ya karanta saƙon duk hankalinsa ya tashi bama komai yake ganewa ba kuma iyakar Gaskiyarsa yake faɗawa Ahmad ɗin, yana ƙoƙari gurin kama kansa shiyasa ko Budurwa bayayi just friends dan karma shauƙin soyayya yasa ya manta Morals nasa ba irin tarkon da Mata basa haɗa masa yasan Allah ne yake kareshi har cewa akeyi ko Gay ne shi saboda baua harkar Mata wannan tasa a shirmensa saboda ya kori sharrin da ake nema a laƙa masa ya fara ɗan biyewa Matan suna dan Romance shima bada kowacce ba saboda he is very selective when it comes to Mace, yana da ƙyama kuma sosai dan haka bada kowa ze iya haɗa jiki ba balle wani abu ya shiga tsakaninsu. Duk rantse rantse da magiyar Ahamd ya ɗaga waya beci galaba ba haka ya haƙura shi kuma Ahmad ya masa hakane saboda ya ƙara nisantar abinda bashi da kyau saboda yasan baya son fushinsa, idan ka cire Hajiya Ahmad ne mutum na biyu da yake jin maganarsa ya kumayi abinda yace masa with out second thought dan yama fi jin Maganar Ahmad ɗin akan ta Hajiyar dan ita sakin layinta yayi yawa wani abun idan ta gaya masa sedai kawai yace mata toh amma bazeyi ba saboda ba abu bane me kyau. Washe gari ya samu Momy da maganar, tayi murna sosai ta kuma yi Addu'ar Allah ya tabbatar da Alkhairi. "Banda abin Mahaifinta Talauci se yasa ka kasa auran yarsa se kace kai ɗin ƙaeuna ne ya haifeka? Wannan ba wata matsala bace ka samu Alhajin ka gaya masa" "Momy aike zaki gaya masa" ya faɗa yana langwaɓe mata, ta harare shi tace "Har se yaushe zaka fara tun karar mahaifinka kana magana dashi? Sanda ka sameshi kan maganar Fili cizonka yayi ko duka? Aure fa zakayi idan baka shirya ba ai shikenan karka gaya masa". Duk magiyarsa Momyn tayi rantsuwa akan ba zata gayawa Alhaji ba ya sameshi da kansa. Ba samun Alhajin ne baze iya ba domin akan Fatima ya shirya tunkarar kowa sedai tsoro da taraddadin amsar da Alhajin zw bashi wadda ba lallai tayi daidai da muradinsa ba shi yasa yake shakkar samunsa. Da kunnensa wata rana bayan Mahaifin Hajiya Rabi yazo Masa Maular daya saba zuwa da farar safiya ya sallameshi ya tafi, yana tsaye daga bayan Alhajin ya jiyoshi yana magana shi kaɗai yana cewa Da ace yana da damar maida hannun Agogo baya da be auri yar wannan mutumin ba, me za'ayi da Auren Talaka? Baze bari wani cikin yayansa ya maimaita kuskuren da yayi ba to amma tsakanin Mahaifin Hajiya Rabi dana Fatima ai akwai banbanci. Mahaifin Fatima nada Sa'arsa kuma ya tabbatar ko bashida ita kamalarsa ta wuce ace ya ringa zuwa gidan Siriki Maula amma Mahaifin Anty Rabi fa? Dama ai Alhajin ya sanshi yasan sana'arsa ce roƙo kuma da biyu ya masa tayin auran yarsa shi ma ya kasa haɗiye kwaɗayinsa ya aura gashi yanzun ya addabeshi Farar Asuba idan ta raya masa ze wanko ƙafa yazo gidan yau yace sun tashi basu da abinda zasu ci gobe yace wani cikin Yaransa bashida lafiya yana neman na kaishi Asibiti da siyan magani bayan duk watan duniya ko bezo ba Alhajin zeyi masa aiken kuɗi dana Kayan abinci, ita kanta Hajiya Rabin duk a ƙoƙarin kare mutuncin kanta dana Iyayen nata kome ta samu kai musu takeyi amma dukda haka bata tsira ba zuciyar Mahaifin nata ta rigada ta mutu da roƙo da banbaɗanci idan beyi ba baya taɓa jin daɗi. PAGE 6 Duk Ahmad ya rasa me zeyi, Jafar ne last hope ɗinsa shi kuma kwana biyu yana fushi da shi, seda aka kwana uku da wancan abun kafin ya sakko ya kulashi bayan ya tabbatar masa ya sallami yarinyar da yace daga Spain taje gurinsa, wai Model ce kuma Actress sonshi takeyi kamar me zuwan tama be sani ba Abokinsa ne yayi setting komai kawai dawowa yayi daga field ya ganta a apartment ɗinsa, baya so ya wulaƙantata shiyasa ya barta tayi kwana biyu ya sallameta amma haka ba zata sake faruwa ba. Shima Ahmad ya gaya masa maganar Fatima data Mahaifinta Jafar ɗin yace "Amma Yah Ahmad duk matan da suke Kano ka rasa wa zaka so se Daughter Mechanic? Yar Talaka For heaven sake me take dashi? Sannan har Babanta ya zauna ya gaya maka wasu magana haka se kace ze baka Gold, duk ina Babes ɗin da suke nacin sonka? Ina su Najiba Shaka, Ina Khulsum Galadima yarinyar nan loves you dearly kuma dai duk abinda zaka nema gurin matar Aure tana dashi hankali har yayi mata yawa plus akwai zumunchi tsakaninku and if ba ita ba why not Zahidah Ab..." 'Jafar! Fatima nake so ba wata ba kuma a gurina tafi duk waɗannan da kake jerowa yanzun. What is wrong with her father been a Mechanic? Kanikanci ba sana'a bane? Talauci Fasadi ne? Karka shiga layin da bansanka akai ba kaima ka shiga sahun irin waɗanda suke kyamar wani Abokin Halitta saboda fifikon Arziƙi, idan na samu matsala daga kai i will loose hope dan nasan sauran ma babu me goyamun baya so please Jafar mu ajiye maganar Matsayi ko sana'ar Mahaifinta mu fuskanci ta yanda zan samu amincewar Alhaji akan maganar nan" Ahmad ya dakatar da Jafar. Daga can ɓangaren Jafar ya fesar da iska daga bakinsa he can't believe simplicity irin na Yaya Ahmad har ya kaishi ga faɗawa soyayya da yar me gyaran Mota, Mechanic fa Yah Ilahi wace irin yarinya ce har haka da ta saka Ahmad ya manta waye shi ya manta gidan daya fito zece ita yake so?" "Kayi shiru ko baka da abinda zaka faɗa mun?" Ahmad ya sake magana jin bece komai ba se sannan Jafar ɗin yace "Gaskiya Yah Ahmad nidai idan shawara kake nema a gurina i will say just late that girl go, karka saka kanka matsala itama ka sakata. Iyakar problem ɗin gidanmu ya isa, kana kallon Maman Mu'allim ban sani ko yanzu ba amma sanda nake gida nasan rana daɗɗayane batayin kuka saboda abinda take gani a cikin gidan nan and sauƙinta ma is because Alhaji yana sonta I'm sure shiyasa takai yanzu a gidan nan. Look at Anty Mardiyya ko cikin Co Inlaws ba kowanne taro take iya zuwa ba because of the humiliation she faced, haka kake so itama matarka ta tashi ana wareta kullum ana zaginta?" "I'm different from Alhaji And Yaya Naziru, babu wanda ya isa ya wulaƙanta matar Aure na na ɗaga masa ƙafa suma su suka bada damar da ake raina matansu kuma ni ba zan zama irin su ba" "Zakayita faɗa da yan uwanka kenan saboda matarka?" "Bazanyi faɗa da kowa ba kuma bazan bayar da hanyar da kowa ze taka matata ba, look Jafar duk ba wannan ta saka na kiraka ba, I have already made my mind so no going back. Nayi magana da Momy ta saka mun Albarka akan maganar i wanted her to talk to Alhaji about it amma tace ba zatayi ba nina sameshi na masa magana kuma ni bansan ta inda zan fara ba, idan yace Aa bansan ta yaya zan roƙeshi ba shiyasa nake so kai kayi masa maganar Dan Allah" Ahmad ya faɗa cikin sigar roƙo. Yanzu fa kake cewa ka shirya facing kowanne challenge amma kace ba zaka iya yiwa Alhaji Maganarta ba kaga kenan kaida kanka kasan maganar bame yuwuwa bace Alhaji baze karɓeta ba, kuma ni yanzu da kake so nayi masa magana idan nayi and it turns out Negative response nasan ni zaka ɗorawa laifi saboda na nuna maganar batayi mun ba, kayi haƙuri for the fist time bazan iya maka abinda kake so ba, kamar yanda Momy tace ka sameshi da kanka, Yah Ahmad is high time you stand for your self. Alhaji fa ba Dodo bane bare ka ce tsoronsa kake ji, go meet him ka gaya masa buƙatarka but it should be you and him alone, karka bari maganar nan ta fita asan wa kake nema, Allah ya bada sa'a but i will pray you change your mind kafin ka sameshi because magana ta Allah banji yarinyar tayi mun ba" matsayar Jafar akan zancen Fatima kenan. A karon farko Ahmad yayiwa wani mutum ƙarya, ya kasa samun Alhajinsu da maganar se kawai ya yanke komawa gidansu Fatima ya kuma tabbatarwa da Mahaifinta yayi magana da nasa Iyayen kuma sun yarje masa daya nemi auranta. A zuciyarsa ya tabbatar Allah baze bashi kunya ba tunda Aure yake so yayi ba wani mugun abu ba, kafin sanda zasu buƙaci ya turo ze san yanda zeyi da Alhaji, idan ma bashi ba Baba Alƙali ze kaiwa maganar Auransa kawai. "Amma da akwai magana guda, Mamana Karatu takeyi, ta ƙare shekarar farko zasu shiga ta biyu yanzu suna hutu ne saura yan kwanaki su koma A can Jami'ar Zaria take Karatun" Malam Hafizu ya faɗa masa. Ahmad dake durƙushe yana faman sunne kai yace "Babu komai Baffa, gidanmu gidan Karatu ne. Idan Allah ya nufa zamuyi aure Fatima tana cikin makaranta bbau damuwa zanyi duk abinda ya kamata gurin ganin bata takura ba ko Karatunta be samu matsala ba, sannan idan ta zaɓi har seta kammala kafin muyi Aure zan iya haƙuri na jira lokacin, fatana kawai na samu Amincewarta da taku" "Allah ya shige mana gaba ya sa a ƙulla Alkhairi, bari na shiga ciki na turo maka ita" cewar Malam Hafizu daga nan ya shige gida. Tun zuwan Ahmad na farko Malam ɗin ya sanarda ita daya wassafa mata kamaninsa ta ganeshi tunda ba sanin sunansa tayi ba. A lokacin ji tayi kamar tacewa Baffan nata ya sallameshi kawai yace ya mata Miji, tsakani da Allah be mata ba, kuma ita da wanne ido ma zata sake kallonsa bayan wancan abinda ya faru shi ma ya zeyi mata haka ya dawo? Dataji shiru be kirata a waya ba ta zata ya janza shawarane ashe shi me gaba ɗaya ya shirya mata biyowa ta hannun Baffa. Tana jin yanda Baffan yake ta yabon Kamalarsa da hankalinsa sannan ya gayawa Umma yanda sukayi da abinda yace masa, Jiki a sanyaye ta fita, Dogon Hijabin datayi sallah dashi ne a jikinta, bata tsaya gyara fuska ba balle akai ga fesa turare ko sauran Al'adu da yammata sukeyi idan zasu fita hira haka ziƙau ɗinta ta fita abinka kuma da jiki kalar Madara a hakan ma tayi kyau abinta. A cikin gida kuwa bayan fitar Fatima Umma tayi jugum kafin ta kalli Malam tace "Ban tsammaci yaron nan ze dawo ba, Anya kuwa Malam ba'a yi ɗage da yawa ba? Ɗan gidan Alhaji Audu Bechi yazo neman Auran Afeeya, wannan fa ba irin Mijin Yayarsu bane idan ma ana maganar masu Arziƙi irinsu Alhaji Audu a ƙasar nan Sirikin Saudatu inaga ai ko gurin baze leƙa ba, gaskiya ni koda da sahalewar Iyayensa ba zanso wannan Auran ba, Malam kafa san irin zamanin da muke ciki yanda Aure ya zama ƙwarya tabi ƙwarya duk kuma wadda tayi kuskuren faɗawa gurbin da ba nata ba zata fusakanci ƙalubale" Ki kyautata zato ki kumayi Addu'a Allah ya zaɓa mata binda yafi zama Alkhairi, sannan ki tuna shi yaga Afeeya yace yana sonta bawai tura masa ita akayi ba, Nutsuwa da Kamalar yaron ta burgeni idan har Allah ya zaɓa matashi a matsayin miji zanyi mata murna kwarai dan daga ganinsa mutumin kirki ne" inji Baffa. Umma ta nisa tace "Toh, Allah ya zaɓa mafi Alkhairi amma dai Alhaji Audu Bechi fa.." "Ai kingama magana tunda kika miƙawa Allah zaɓi sedai mu zuba ido muci gaba da Addu'a kawai" Baffan ya sake tareta. Seda Fatima tafi minti biyar tsaye a soro kafin ta hada courage ta fita, wata irin kunya da nauyin sake haɗa ido dashi takeji tasan yana ganinta wancan abun ne zero faɗo masa a rai, da dai taga babu sarki se Allah yasa ta fitan, Ahmad na jingine jikin katanga ta raɓe gefensa tana yar siririyar sallama kai a ƙasa tamkar wadda ya kama tana gulmarsa. Murmushinsa me kyau yayi ya amsa mata sallamar kafin ya tsaya dakyau yana fuskantarta, har sannan kanta a ƙasa murya a sanyaye ta gaidashi "Hajiya Fatima, se yanzu sarautar ta sakeki kenan har ina shirin na ƙaraso soron na taroki ai" ya faɗa cikin raha. Bata tanka ba haka nan bata ɗago kanta ba, ya waiwaya ya kalli Dakalin gurin kafin ya kalli mutanen da suke wucewa kamar an basu gadi duk wanda yazo seya zura musu ido sannan ya wuce se ya kalleta yace "Mu zauna a nan ko mu tsaya cikin soron?" "Bari na kawo maka abin zama" ta faɗa kafin ta juya cikin gidan ranta babu daɗi, shi gurin zama ma yake nema, ita data fita da niyyar su ƙarƙare kuma yana neman yaja maganar da tsayi. Kujerun roba ta kawo guda biyu ta saka a Soron ta koma ta dauko pure water da Zobon da Ummansu take siyarwa ta haɗo masa da ƙaramin kofi dukda bata da tabbacin zesha. Seda ta aje komai kafin tace ya shigo, yana ta doka murmushi kamar sabon Ango ya zauna, kallonta kaɗai nishaɗi yake bashi musamman yanda take sunne kai yasan meye dalilinta naƙin haɗa ido dashi amma a ganinsa wannan ai ua wuce, banda abinta idan Allah yayi wata rana na jikinta ma ai wanke mata zeyi balle gurin da ta ɓata. A taƙaice yayi mata bayanin kansa da dalilinsa na zuwa gurinta. "Kema se ki bani taƙaitaccen bayani akanki" ya faɗa yana ƙarewa fuskarta kallo. Kyakykyawace Masha Allah komai na fuskarta ɗan daidai hasken fatarta kuma ya ƙara ƙawata kyan nata, tana da tsayi dan ko ze fita da kaɗan ne sannan ba ramammiya bace kuma bata da ƙiba, baze iya ƙiyasta shekarunta ba saboda suffarta irin wadda bata nuna shekaru ce, se kayi wa mutum kallon yaron idan kaji ainihin shekarunsa kuma kayi mamaki. Yanayin zubin jiki da fuskarta yafi kama dana Jajayen Buzayen Niger ko kuma Fulanin Mambila, sannan daga yanayin goshinta ya fahimci tana da kufar gashi, kuma irin me Laushin nan dan gashin goshin nata a kwance yake luf kamar na Jariri sabuwar haihuwa gashi baƙi siɗik. "To ai kasan sunana Fatima kuma nan ne gidanmu" maganarta ta maido shi daga tunanin daya tafi. Ya saki murmushi, jan Ajin nata ya fara yawa, ya zata kuma tunda har yaga mahaifinta kuma zata ɗan sake masa tasan dai bada wasa yake yi ba. Ya gyara zama yace "Nasan sunanki Fatima kuma naga gidanku amma ai ni ba iyakar abinda na faɗa miki a kaina ba kenan, na gaya miki mena karanta, aikina har adadin yan gidanmu da wanda nafi so seda na gaya miki fa" Tayi shiru tana jinsa, idanun daya zuba mata su sukafi damunta da alamu kuma idan ba magana tayi ba baze dena kallonta kamar ze hango yan cikinta ba dan haka tace "To ai ni banida wani abu da zan gaya maka ne, amma dai kamar yanda nace maka nan ne gidanmu, mu uku ne ai kaga Anty Sauda itace babbarmu se Yah Malam.." "Jafar? wanda yayi mun sallama da Baffa?" Ya katseta, kai ta ɗaga masa kafin taci gaba da cewa "Shi nake bimawa, ni kuma banida ƙani ko ƙanwa, ina makaranta a Zaria Level two zan shiga ina karantar English Literature, bayan Baffa da Umma dasu Anty Sauda Ina da Best Friend Badar i think iyakar abinda kake buƙatar sani akaina kenan" ta ƙarasa tana yamutsa baki. "Masha Allah ku uku kacal a gidanku kenan, ashe ke ɗin Autace shiyasa shagwaɓarki tayi yawa, shekarar ki nawa toh" "20" ta bashi amsa a gajarce tana ci gaba da murza zoben hannunta. Sukayi jugum shi yana kallonta ita kuma tana faman juya Zobe, wayarsa dake Aljihuce ta katse musu shirun ya cirota ya duba, Jafar ne yake kiransa, ya nuna mata screen ɗin wayar yana cewa "Jafar ne yake kirana". Tankar wadda take zaune akan ƙaya ta miƙe da sauri tace "Ka amsa toh, bari naje ciki kafin ka gama". Kallonta yayi kaɗan ya kasa fassara yanayinta amma dai kamar she is not comfortable with him, ya mata uzurin haɗuwar farko ne dan haka ya miƙe shima yana laluba Aljihubsa yace "Ai inaga zan wuce kawai idan naje gida se na kirashi wayarmu bata yankewa da wuri ga dare ma ya farayi karna zaunar dake a waje" Kuɗi ya zaro masu yawa daga Aljihun nasa ya miƙa mata yana cewa "Kinsan farin shigan zuwa hira ne ni, bansan me akw tafiya dashi zance ba kiyi haƙuri ga wanan kisha Sweet kafin na sake zuwa" "Nagode" ta faɗa ba tareda ta karbi kuɗin ba se wani kallo da ta musu ta ɗauke kai kamar taga wani abunda bata so. Wayarsa ya sake miƙa mata uace ta saka masa Number ta wancan ta goge, nan ma seda taji jum sannan ta karba, ta saka number ta mayar masa. Akan kujerar data tashi ya ajiye mata kuɗin ya juya yana cewa "Zan kiraki idan na isa gida se kiyi saving number ta. Ki gaida Umma, se na sake dawowa" Ganin ta tsaya kamar wata sokuwa kawai tana kallonsa yasa yayi murmushi ya fice daga soron yanajin wayarsa nata ƙara yasan Jafar ne bala'in wutar ciki ne dashi yanzu idan ba ɗauka yayi ba ya ringa kira kenan ga Mita kamar Mace. Jiki babu ƙwari ta haɗe kujerun ta ɗauke farantin ruwan da be ko taɓa ba daman tasan ba sha zeyi ba Umma ce tace ta kai masa. Iyayen nata na yar hirarsu ta shiga. Seda ta ajiye kujerun a mazauninsu kafin ta isa gaban Baffa ta Zube kuɗin da Ahmad ya bata. "Wannan fa?" Baffan ya tambayeta yana kallon kuɗin, a sanyaye tace "Shi ya bani wai bezo da komai ba danaƙi karɓa shine ya ajiye akan Kujera ya tafi" "Toh madallah amma idan ya sake dawowa ki gaya masa na hana karki Ƙara karɓan kuɗinsa" Baffan ya faɗa ta amsa da "Toh Baffa" kafin ta miƙe tsaye zata wuvmce yace mata "Kwashe kije dasu ai ke aka bawa" "Ni babu abinda zanyi dasu Baffa" ta bashi amsa tana juyawa. "Zo nan Mamana, me yake damunki? Ko wani abu yayi miki?" Baffan ya sake dakatar da ita saboda lura da yanayinta sam ba daidai take ba, murmushi ta ƙaƙalo tace "Babu komai Baffa kaina ne yake sarawa zanje na ƙarasa shirya kayana sena kwanta" "Toh Allah ya sawwaƙa ki samu magani kisha kafin ki kwanta ɗin idan be dena ba da safe se kije Asibiti, sannu ko" Baffa ya faɗa cikin tausayawa. Seda ta shige sannan Umma ta gaya masa abinda take zaton shine sikar tsumewar Fatima. Yayi murmushi yace "Ina ruwan Mamana, wato kunya ce duk ta dabaibayeta, to ya za'ayi abu ya rigada ya faru ta yuwu ma ya manta idan kuma ya ganota ya samu abin tsokanarta ai" tana jiyo Baffan daga ɗakiz harta hasaso Ahmad ya dawo da zancen ai lumewa zatayi a ƙasa kawai ta huta. Harta bacci ya fara fizgarta wayarta ta tayar da ita, Data ta a buɗe yake dan haka taga sunan Ahmad Bechi a truecaller, kamar ba zata ɗauka ba se kuma zuciyarta ta kwabeta kan wulaƙanci babu kyau. "Allah yasa ban tasheki a barci ba" ya faɗa bayan data amsa wayar, cikin muryar da bacci ya fara tasiri a cikinta tace masa "Aa". Ahmad ya gyara kwanciya akan Gadonsa, tunda ya shiga gida suke waya da Jafar daya kai masa ƙarar Hajiya wai ta kirashi akan seya Rantawa Faisal Kuɗi ze fara harkar Crypto kuɗaɗe kuma ba Ƙanana ba take cewa ya bashi ita lissafin Ribar da Faisal ɗin yace mata kawai za'a samu takeyi bata hango Risk da yake tattare da sabgar ba kuma wai rance bama kyauta take nufi harda bashi zuwa lokacin da ze turo kuɗin shine ya kawowa Ahmad ƙararta ita da Faisal ɗin se kace ze iya masa wani abu akai be samu sun gama maganar ba se yanzun yana ta Allah Allah kar tayi bacci ba suyi magana ba. "Kara zakiyi mun amma muryarki ta fallasaki, kiyi baccinki toh in Allah ya kaimu da safe sena kiraki ƙarfe nawa kike tashi daga bacci?" "Ko yaushe ma" ta bashi amsa cikin ƙaguwa, ya fiya tambaya take ayyanawa a ranta. Ahmad naso suyi hira dan so yake ta sake dashi da sauri amma kuma bayaso ya shiga haƙƙinta dan haka ya mata sallama akan ze kira da safe dukda bata gaya masa sanda take tashi ba ya kuma jaddada mata kan tayi saving number sa. Tsaki tayi bayan ta kashe wayar baccin data fara ya gudu se ta shige WhatsApp tana duba saƙonni kafin baccin ya dawo. Dm na samari gasu nan babu Adadi unread messages ɗinta sunfi dari duk ta tsallake ta wuce kan number Badar dataga ta mata magana da ita suke hira daman baccin ya kwasheta. "Al'amin yace inya kiraki wayar bata shiga, a WhatsApp kuma baki buɗe chat ɗinsa me yasa?" "Blocking ɗinsa nayi" ta bawa Badar ɗin amsa ganin tana online. Tana turawa kuwa ta buɗe ta shiga yi mata voice. "Kina kuwa yanda ya gigice Afee zuwansa fa gidan nan biyu yau wlh se in kira masa ke a wayata na kira kuma bata shigo ba lokacin wai me ya haɗaku ne? Dan Allah ki tausayawa guy ɗin nan wlh Al'amin yana sonki sosai fa" cewar Badar. "Uhm duk ya gama haukansa can ya nemi daidai shi a gaba, wai ni Badar shikenan Namiji baze so ni saboda Allah ba se dan wata buƙata ta daban? Ki faɗamun tsakaninki da Allah ko da akwai wani abu da nakeyi mara kyau da yake Attracting yan iskan Maza zuwa gareni? Ni kenan duk wanda zece yana sona seya nemeni da lakata me nakeyi daya sa suke mun kallon Mara kamun kai Badar?" Fatiman ta mayar mata da Voice note muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka saboda zafin abinda take ji a ranta. Allah ya mata farin jini bana wasa ba, bata taɓa fita ta dawo gida Namiji be tsaidata ko an biyota gida ba amma duk wanda ta kula take ganin kamar zasu samu daidaito da tafiya ta fara nisa se ya kauce layi ya shigo mata da wani zancen na daban. Tun abin baya damunta har yazo ya fara bata tsoro ta yaya za'ayi ace duk wanda yazo yana sonta seya nemi ya taɓa jikinta se kace ita kaɗaice Mace a duniya ko kuwa duk suma sauran Matan haka ake musu?? "Na gaya miki Afee wannan matsalar fa bake kaɗai ta shafa ba, abinda yasa kuke mun kallon Masifaffiya kenan na kasa tsaida saurayi ko ɗaya saboda ni bana iya shiru, mutum na zuwar mun da shirme a take nake tsigaleshi gara nayita zama single dina har Allah ya kawomun Mijin Aure na na gaske, ke kuma duk wanda yazo miki da suffar Salihai seki saki jiki se mutum ya nuna miki true color kizo kina ciwon rai kenan shima Al'amin ɗin shegene da gemunsa kamar Na Allah ai da kin gayamun da wuri wlh da daya zo ɗazun sena wulaƙantashi dan iska shege me ci da buguzun da fuskar Salihai" Badar ta hau spark daga nan suka cigaba da tattauna abinda yake damunsu ya kuma zama ruwan dare a zamanin nan. Samari sun zama abinda suka zama kawai, sun maida mata tamkar wasu Takalma da zasu ce se sun gwada sun samu wanda yayi musu daidai kafin su siya a irin haka waɗansu da ƙadda take hawa da wanda suke kasa jure jarabawar ubangiji yayi musu suga kamar idan Saurayin ya gudu ba zasu samu wani ba se su bayar da kai bori ua hau wanda daman samarin yan latsine da sun samu abinda ya kawosu su fece shikenan se a shiga lahaula da Innalillahi Allah ya rufa asiri. Soyayya ta ƙullu tsakanin Fatima da Ahmad ko ace farashin soyayya nata hauhawa a zuciyar Ahmad domin abinda yakeyi yafi kama da One sided Love sedai ya kasa fahimtar hakan. Kwana uku tsakanin zuwansa na farko ya sake komawa daga nan kuma ya mayar da zuwan nasa sau biyu a sati bayan nan kuma kullum a ƙalla ze kirata waya sau uku yaji ya take, kulawa da tattali duk irin wadda yasan zata farauto masa da zuciyarta yana mata amma ko a jikinta shan ƙamshin nan ma ƙaruwa yake ko a waya idan suna magana yanayin da take amsawa tamkar bata so amsarta bata wuce Eh ko Aa shi zeyita zuba surutu inya gaji yace tana jinsa tace Wh bata da abin cewa ne shi yasa tayi shiru hakan kuma yake jurewa baya fushi yana cigaba da lallaɓata. A cikin haka suka koma makaranta wanda taji daɗin hakan sosai saboda ko babu komai zata huta da zuwan da yakeyi sannan zata samu uzurin da zata ringa gujewa wayarsa yanzu dan a gida Idan ya kira Umma data fahimci Ahmad ɗin be samu karɓuwa gurin Fatiman ba ita take takura mata tayi ta mata faɗa idan ta bar wayar tana ƙara ko yazo ta tsaya nuƙu nuƙu taƙi fita. Ta kance mata wulaƙanci babu kyau, bata san abinda Allah ya tsara ba kuma ita bataga makusarsa ba da zatace beyi mata ba dan a zuwansa na biyu ya shiga har ciki ya gaidata itama data ganshi ta fahimci nutsuwa da Kamalar da Malam yace yana da ita. Yaro ne amma Allah ya hore masa nutsuwa da dattako daya zarce shekarunsa kuma duk wasu iyaye na kwarai tabbas zasuyiwa Yarsu sha'awar samun Miji me kulawa tamkar Ahmad ɗin. Bayan sun koma makaranta haka zeyita kiranta ba zata ɗaga ba, tun su Badar basu sanda Ahmad ba dan bata gaya musu ba har suka gane dalili wata raba ya kirata tana sallah Badar ta amsa wayar suka gaisa ya kama sunanta shikenan hira ta ɓarke, Fatima bata so ba domin muddin Ahmad yayiwa Badar tasan ta shiga uku, takura kam ko ruwa me daɗi ba zata barta tasha a dalilin Ahmad ba shiyasa take ta ɓoyewa gashi yanzu Badar ɗin ta ganoshi. "Dukda banga guy ɗin nan ba tun daga voice ɗinsa nasan ya haɗu, wato Afee kin iya catching Big Boys matsalar duk yan iska ne in disguise Allah yasa dai wannan na Allah ne dan wlh daga magana a waya harya burgeni yana da nutsuwa ga kirki, waye shi? A ina kuka haɗu" Badar ta tambayeta bayan ta gama waya da Ahmad ta bashi uzurin abinci zataci shi kuma ya shaida mata ze fita Jafar ne yazo ze ɗauko shi daga Airport. "Ya samu hutu ne shine yazo Gaisuwar Rasuwar Brigadier General Baballiya Bechi, ƙanin Alhajinmu sa sukayi Hatsarin jirgi last two weeks ai kinji labari ko?" Abinda ya gaya mata da duk ya saka taji kunya kenan. Sanda akayi rasuwar ta gani a SM, kuma anyita surutun a gari kan set up ne akayi musu ba wai Accident bane ba ance akwai wani sirri da suke shirin bankaɗawa na wata badaƙala data faru shine kafin nan masu laifin suka kawar dasu, tunda taga Bechin a ranta ta kawo yana da alaƙa da Ahmad kuma ta gani ya saka a Status harya tura mata cewar an masa rasuwa kunyar data ji yanzu irin gaisuwar da tayi masa ta "Allah ya jiƙan rai" kawai tace, babu wani sympathy babu nuna concern na cewar Kawunsa ne na kusa ya rasu tana ganin shiyasa yanzu yake gaya mata Jafar yazo dan tasan Mutuwar me muhimmanci ce a gurinsu tunda har na wata ƙasar ya taho ita kuwa ba wanda ta gayawa a gidansu ma balle ko a waya su masa gaisuwa. Hoton Ahmad kawai ta nemo ta miƙawa Badar data addabeta da waya, cikin Mamaki take kallonsa tace "Ahmad Bechi? Wlh Afee kinyi Miji kinsan kirkin mutumin nan kuwa?" "A ina kika sanshi?" Ta tambaya tana tsare Badar ɗin da ido wani abu da bata taɓa tsammatar zata jishi akan Ahmad ɗinba ya taso mata wato kishi. "A IG mana, ai ina following ɗinsa" b Badar ta bata amsa. Seta tsume fuska tace "Shine har kika san kirkinsa daga ganinsa a IG kuma" "Ai mutumin kirki baya ɓuya, kuma idan da kinsan yanda mutane suke yabonsa da bakiyi mamakin dan nace yana da kirki ba, kin san yanda yake taimako kuwa? Ke dai Allah yana sonki Afee, kinga ya canza miki da abinda yafi duk shegun da kika rasa Alkhairi wlh ki gode masa" "Allah ya saka mu a danshinku Afee, ke kam Allah ya taimakeki da jinin manyan mutane, Bechi Family fa?" Ilham roommate ɗinsu ta faɗa nan suka shiga hirar caaa caaa kowa na tofa Albarkacin bakinsa. Ahmad Ƙarfe biyu ya fita ɗakko Jay wanda suka samu delay na jirgi daga Abuja zuwa Kano, tun daren jiya ya sauka daga London, ya biyo jirgin Abj to Kn na sha biyu da rabi na rana basu taso ba se biyu da wasu mintina uku saura suka sauka a Kanon. Beyi mamaki daya kira Yah Ahmad yace masa already yana cikin Airport ɗin ba. Be taɓa barin sa yayi jira muddin yana gari shi ze zo ya ɗaukeshi kafin Jirginsu yayi Landing Ahmad ya isa Airport wani sa'ilin har Abujan yake zuwa ya taro shi su taho Kanon Tare. Cikin tsananin murna da ɗokin ganin juna suka rungume juna kowanne yana jin soyayyar ɗan uwansa na sake ratsa Jini da jijiyarsa. "Kullum ƙara girma kakeyi da fresh, look at you, idan muka jera za'ace kai Yayana ne na uku ma" Ahmad ya faɗa cikin zolaya yana kallon Jay daya ɓata fuska irin na sangartattun yara wai yace masa tsoho. Kuma da gaskiyar Ahmad ɗin, A tsaye Jay yake gansansan kamar ya haɗa jini da samudawa koda yake jinin Binta da Audu fa kowanne ba baya bane a garin jiki. Suna tafe suna hira gwanin sha'awa har suka isa gida. Hajiya na tsaka da shiri domin wannan karon ta rantse gayya zasuyi suje taro Jay ɗin se Kano gaba ɗaya ta san da ya dawo. Idan zezo gida babu wanda yake sani, ko a jirgi badda kama yakeyi saboda ya tsani irin taro da hargowar da mutane sukeyi duk sanda suka ganshi a cika guri ayita ihu ana ɗaukar hotuna dashi ayi blocking masu uzurirrika shiyasa kusan shekara biyar kenan ya canza salon zuwansa Nigeria, hatta da manager sa na nan wrong schedule yake bashi dan shi yake sanarwar Jay ɗin na tafe ya haɗa masa mutane shiyasa ya zaɓi boye zuwansa, Ahmad kaɗai yake gayawa se idan ya dawo a kwashi tsiya da tsiyataku da Hajjaju dan idan zezo Yau ce mata yakeyi se Jibi sedai ta ganshi kamar dirar kirsimeti. Zuwansa na ƙarshe waccen shekarar na buɗe Shagon Ahmad daman bata san da zancen ba ganinsa kawai tayi, ta zabga tijara ta kuma ce Alhaji yayi mata tsakani da Ahmad ya fita a sabgar Ɗanta, ta yaya za'ayi idan ba mugunta ba ya saka ya baro gurin sana'arsa dan yayi Asarar miliyoyin da ake biyansa? Ta kuma ce zancen Ahmad shi kaɗai ya ɗauko shi daga iyafot ya kau, duk in ze sake zuwa zuga za'ayi dangi da Abokanan arziƙi aje a taroshi jama'a su san yana da gata ba wai ace kamar shi sananne a duniya idan zezo gida ya ringa shigowa kamar Ɗan fashin da ake fako a kama. Shine dalilin daya saka ta haɗo Jama'a kenan dangi da Abokanan Arziƙi, jira takeyi ayi La'asar su ɗebi motoci a tafi Iyafot ɗauko Jafaru, yau ɗin har kwalliya taci, ta saka Sabuwar Atamfarta Super Sheraton, kusan shekarar ta uku a ɗinke, da siyanta kuma zatayi biyar ko Shida ta sallah ce da Alhaji yayi musu sauran da yuwuwa sun dade da bayar da tasu amma ita se Yau Allah ya nufa zata saka shima da fari wani Lace ta saka, sabone amma ajiya tasa ɗinkin ya fita a yayi, tun ana style me Umbrella da hannu me ɗorin Kafaɗa, ga wata uwar boader Lace da aka tattara a wuya da bakin Hannu, da ace Zallar Lace ɗin aka ɗinka mata ko ya shekara goma zata saka abinta dan babbane, Design ɗin Lace kuma baya tsufa sedai ɗinkin jikinsa ya nuna shekarunsa. Turai ce ta kalleta sanda ta fito ala dole ta ƙure gayu ga Sarƙar Zinare irin design ɗin Saudiyya damɓasheshiya ta sauka har kan ƙirjinta, jan hannunta Turai tayi da sauri suka koma ɗaki tana cewa "Haba Binta, yanzu saboda Allah da wannan shigar zaki tafi tarar Jafar ɗin se kace wadda ta fito daga riga? So kike ki ja masa abin magana a ɗauke ku hoto a yaɗa a a duniya duk suturunki keko ki rasa wanda zaki saka se wannan Matsiyacin Lace ɗin dan girman Allah ina zaki kai ubannin suturun da kike dasu ne?" Hajiya ta yamutsa fuska tana kallon Turai tace "Karki gaya mun mara daɗi mana, me Leshi na yayi? Ina a gurinki na siyeshi ko a lokacin ai ya haura ɗari balle yanzu indai ba cutata kikayi ba kuma" "Shekararki nawa da siyansa? Ni wlh har na manta da nayi irin Leshin nan bana zaton wadda na bawa ma har yanzu yana nan be zama tsumma ba, yanzu dai duk ba wannan surutun ba su Hajiya Rafi'a da Hajiya Zuwaira duk suna falo yanzu suka iso se kin raina kanki idan kikaga kwalliyarsu, yayayenau kansu da sukazo dasu bakiga yanda suka sha kwalliya ba se ke da ake taron saboda ke ce zaki fita a haka kamar mara kan gado dan Allah wuce ki sauya Kaya, ki nemo na mutunchi wannan rakwacam ɗin sarƙarma kiyiwa girman Allah ki tattarosu muje gurin Alhaji Mansur a narkasu, a maida miki ƙirar zamani". Badan taso ba shine ta canza da Atamfar dukda itan ma Turai tace ba tayi ba, gafa kayan nan a jibge amma ta bari ta zaɓa mata ma tace Aa, da babu gara babu daɗi Atamfar Ɗinkin doguwar rigane an mata Bead work a wuya da bakin hannun, Sarƙar ce dai tace ba zata cire ba, tilas Turai ta barta, a neman mayafi kuma aka tafka abin kunya dan Hajiya dai bata da Mayafin fita Taro, ƙarshe se a gurin Momy Turai taje da kanta ta Aro mata Jaka da Takalmi kuma aka samu a gurin Hajiya ƙarama. "Wlh Binta ki canza hali, wannan tsumulmula har ina? Kuɗi kina dasu kamar su kasheki amma ace ko jikinki ba zaki iya kashewa ba wannan wace irin rayuwa ce? Yanzu tsabagen zubar da ƙima Gyalen da zaki saka ki fita kunyar Ɗanki ma baki dashi se an aro a gurin kishiya wannan abin takaici har ina?" Turai ta dasa mata mita, Binta dake kiciniyar Rataya Jaka a hammata ta buɗe baki zata bata amsa suka jiyo ihun Yara ana oyoyo Uncle Jay, Hajiya ta zabura tayi waje dan ta tabbatar da abinda take jiyowa, Jafar ɗin da ta gama haɗa jama'a da motoci zasu tafi tarowa ko kuwa wani daban suke nufi???? PAGE 7 "Jafaru, ni uwarka ka yaudara wannan karon ma kace mun biyar na yamma jirginku ze sauka seda na gama tattara jama'a zamu tafi taronka mu nunawa Duniya gatanka shine zaka tozartani Ko La'asar bata rufa ba ka diro a gidannan wato ka sanar da Amadu shi da yake ƙanin ubanka yaje ya dauko ka ko?" Hajiya ta faɗa tana zarewa Jafar idanu. Sakin Yaran Yayyensa da suka ruƙunƙumeshi suna masa oyoyo yayi ya nufeta fuska ɗauke da murmushi cikin shagwaɓa yana cewa "Haba Hajiyata, dawowana lafiya ai shine komai yanzu, maimakon ki tareni da warm hug se ki farayi mun faɗa kuma?" "Ka matsoni sena kwasheka da mari wlh, kai kuma me kama da dido dido, sau nawa zan faɗa maka ka fita daga sabgar Jafaru? Shin wai Aisha ta haifamin shine ko Yaya? Nace ka fita daga sabgata data Yayana Amadu amma kaƙi kaji shin ana dolene? To kaji da kunnenka duk bala'i da tuggunku sedai ya ƙare muku amma babu tsafi ko Asirin da zeci Jafaru wlh balle har kuga ya samu nakasu. Ɗaukaka da cigaba a rayuwa yanzu ya fara ganinta duk nasan shirinku da liƙe masan da kakeyi ba wai ban sani ba Asirin da kayi ka lashe masa zuciya ma ina kan karyashi kuma idan na juyo takanka ba zaka ji da daɗi ba" "Haba Binta wannan wane irin abune kikeyi dan girman Allah? Meye amfanin wannan faɗe faɗen da kikeyi? Jafar dai gashi ya dawo lafiya me kuma kike da buƙata?" Turai ta katse Hajiya daga Hauragiyar da takeyi se kuwa ta zabga mata harara tace "Babu ruwanki Turai, idan ba zaki tayani ba to kija bakinki kiyi shiru" "Allah ya sawwaƙa miki, Sannu da zuwa kaji Jafar yi wucewarka can Ɗakinku, idan kuma zaka fara shiga ku gaisa da iyayenka da suka zo tarbarka toh, sannu da hanya" Hajiya Turai da bataji kashedo ba ta faɗa tana nunawa Jafar Palour Binta wanda jama'ar ciki sukayi shiru suna saurar abinda yake faruwa a wajen, Mutan gidan kuwa daman sun san za'a rina dan haka abin bezo musu a bazata ba. Jafar ya kalli Hajiya dake tsaye kamar sojanniya se numfarfashi take tana dannanwa Ahmad da yayi ƙasa da kansa harara, cikin sigar rarrashi Jafar ɗin yace mata "Please mana Hajiyata, ki saki fuskarki, change of schedule muka samu na flight and na manta ban sanar miki ba. Believe me Yah Ahmad ma be sani ba seda na sauka Kano. You Know i Miss you so much shiyasa ba zan iya jira ba kuzo da yawa ba shiyasa kawai na kirasa nace yazo ya ɗauko ni amma ba laifinsa bane Allah nike da laifi amma kiyi haƙuri bari na koma Abuja kawai gobe sena dawo kizo keda jama'arki ku taroni" ya faɗa bayan daya isa dab da ita. Hararar da takewa Ahmad ta mayar kansa kafin tace "Billahillazi karka ɗauka kaci banza baka isa ka tozartani a banza Ƙawayena su tafi suna gulmata ba sannan na ƙyakela muje cikin" "Ai wanan unnecessary drama taki ce zata saka a tafi ana gulmar taki, sabida Allah meye abin tashin hankali a nan? Daman banda ɗaurawa kai ke kika saba taroshi ko yaya? Wlh Yaya Binta bakya gudun abin magana da abin sakawa kai ciwon kai a duniyar nan, duk inda zaman lafiya yake kin ɓauɗe masa" Munira ƙanwarta da batayi niyyar magana ba sedai ganin Abin na Yayartata na neman zarce misali yasa ta fito tana mata maganar. Fuuuu Hajiya ta shige ɗaki Jafar ya kalli Ahmad yace "I'm sorry Yah Ahmad ni na jawo maka" "Kaidai jeka kafin Hajiya ta canza maka wannan fuskar taka babu ruwana bari naje wani guri bazan jima ba zan dawo" Ahmad ya bashi amsa yana juyawa ya fice daga gidan. Dukda yayi ƙoƙarin danne ɓacin ransa Amma Jafar ɗin seda ya fahimta, ya sani dole kalaman Hajiyar su sosa masa rai shi kansa beji daɗi ba amma yasan idanyace wani abu baya ga kalmar lallaɓi da banbaki a yanzu ƙara tunzurata zeyi tayi musu zazzafar Tijara a gaban mutane. Jiki a sanyaye ya bi bayan Hajiyar, Yaƙe kawai ya ringayi yana gaisawa da tarin matan dake zaune falon Hajiyar, ya so ya gane wasu amma ya manta sunayensu wasu kuma sababbin fuskane a wajensa dan Hajiya badai tara ƙawaye ba ga Yayayensu da suka kwaso sekace Biki keyi yanzu da tana nufin waɗannan jama'ar zata kwasa su tafi Ɗaukoshi daga Airport ɗin?. Abinda ya sake ɓata masa rai yanda Yayan Ƙawayen Hajiyar suketa wani abu kamar masu shafar Jinnu, se ɗaukar hotuna suke da video ana sakoshi a ciki wasu ma yaga kamar Live sukeyi a IG suna faɗin gasu a gidansu Jay sunzo taron shi. Ƙasa Ƙasa yake jan tsaki yana durƙushe tsakiyar Mata kowacce da kalar soki burutsun hirar da take jefa masa da tambayoyi kamar sun aikeshi ya dawo, ba Hajiyar ba ba Ƙawayen nata ba babu wadda tayi tunanin a gajiye yake ko yana da buƙatar yaje ya huta seda Hajiya Turai ta fito daga Kitchen taje tana shirya abincin da za'a rabawa Jama'ar da Hajiya ta tara abin Allah arziƙin Jay yau ba Ƙaramin Better tasa aka shirya a gidan ba harda Rago aka gasa. "Kana tsugunne Jafar ai se Ƙafafunka su gaji tashi kaje ka huta kaida ka shawo tafiya" Turai ta faɗa, ya saci kallon Hajjaju da ta zauna ta haɗe fuska tana juya ƙafa da gani lissafa yanda zataci ubansu daga shi Har Ahmad ɗin daya rusa mata shiri takeyi. "Tashi kaje mana kake kallona da wasu idonka irin na Ubanku" ta faɗa tana zaburo masa. Ya miƙe yana shafa kai, daidai nan Faisal Bechi ya shigo yana kwalawa Hajiya kira yana cewa "An fa gama saita komai har Photographer ya iso Allah dai yasa ma a barku ku shiga Airport ɗin irin wannan gayya se kace masu taro Governor.." Se kuma ya dakata saboda ganin Jay a gabansa, ya buga tsalle kamar yaro ya ɗaneshi yana ihu. "Get off me my friend, kai baka zaka girma da shirme ba ko?" Jafar ya faɗa yana tureshi. Bakin Faisal kamar ze yage yace "Welcome brother, ni na sani sedai ba Jafar Bechi ba wlh se kayi disappointing Hajiya amma fa ka kwafsa kai kasan irin Grand welcome da aka shirya maka kuwa yau?" "Matsa na wuce" Jafar ya tureshi jin yana neman ɓallo masa sabon ruwa Faisal yabi bayansa yana kyalkyala dariyar mugunta yana gaya masa irin shirin da Hajiya tayi. Ɗakin Momy ya wuce, tana zaune kan kujera da waya a hannunta tana dannawa Khadija, Aslamiyya da Maimuna duk suna falon suna kallon Tv duk Drama da aka kwasa suna zaune basu fita ba balle su tanka Jafar ya shiga da sallama suka amsa masa a tare kowannensu fuskarsa na faɗaɗa da murmushi. Gaban Momy ya wuce ya zauna dab da Ƙafafunta yana kallon Step sisters ɗinsa fuska ɗauke da murmushi. "Barka da dawowa Sheikh Jafar" Momy ta faɗa cikin raha. "Mun same ku lafiya Momy?" Ya mayar mata ta amsa da "Lafiya lau, ya ka baro abokanan sana'arka da gurinsu Yaya Muhammadu?" "Duk suna lafiya suna gaisheku" "Madallah sannu da zuwa" ta sake faɗa kafin ta miƙe ta shiga kitchen, bata jima ba ta fito me aikinta Amira na biye da ita da babban Try ta ajiye a gaban Jay kafin ta gaishe shi ta koma. Ya miƙawa Nu'ayma Babyn Khadija hannu ta tafi kamar zata faɗi dan tafiyar tata batayi kwari ba, Khadija, Maimuna da Aslamiyya suka haɗa baki gurin yi masa sannu da zuwa ya amsa musu kafin yace da Khadija "Yaya Khadija ya yara? Ina Alhaji?" "Yana Islamiyya se sun tashi idan an ɗauko shi zasu biyo ta nan mu wuce". "Kasha ruwa, ga mutuminka nan Coconut Juice" Momy ta faɗa ganin yana ta wasa da Nu'ayma be taɓa abinda aka ajiye masa ba. "Yah Jay sha kaji dan Allah ni nayi fa" Maimuna ta faɗa cikin zumuɗi ta sauka ƙasan ta tsiyaya masa a Cup ta bude kwanon da aka zuba kayan maƙwalashe tana cewa "Har small chops ɗin ma ni nayi fa" "Kice kin zama Chef babu labari? Me ya samu wayarki na dena ganinki Online?" Ya faɗa yana karɓan Cup ɗin da ta zuba masa Lemon, seta kalli Momy, Momyn tace "Kya kalleni? Ki gaya masa abinda kikayi Ahmad ya kwace wayar mana" "Ai base ta faɗa ba ma Momy tunda kikace Yah Ahmad ne nasan tayi abu mara kyau ne, Any Juice ɗin yayi daɗi sosai, and this too" ya nuna Chocolate cake dake hannunsa. "Thank u, shine Yah Aslamiyya yace ba zakaci ba wai beyi daɗi ba" "Zanci mana har Token zan baki ma for the good job". Gwalo tayiwa Aslamiyya Momy da Khadija na musu dariya Faɗan sako da sako sukeyi kamar kaji. A cikin zuciyar Jafar kuwa abinda ya sabaji a duk sanda yake cikin ɗakin Yauma yaki, ina ma ace shima ɗan ɗakin ne? Duk sanda ya zo Nigeria irin wannan tarbat yake samu a gurin Momy. Ita zatayi masa maraba ta bashi abinci Hajiya kuwa se Hayagaga ta cikashi da tambayoyi da ƙorafe ƙorafe, ruwa seya tambaya kafin zata tuna ya kamata a bashi babu ruwanta da duba daga wani guri me nisa yazo yana da buƙatar hutu da kulawa Aa matsalolinta kawai sune a gabanta. "Bari naje nayi sallah an kira La'asar" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy tace "Tam, zasu Miƙo maka abinci Gas ne yayi mana tsiya amma an gama ƙarashene kawai" "Nagode, Yah Khadija kafin ki tafi kimun magana" daga haka ya fice daga falon. Seda ya leƙa Hajiya Rabi, a mutunce suka gaisa se sannan Yaranta suka samu sukunin yi masa sannu da zuwa suma, ya kama hannun Zayyad suka fita tare zuwa masallaci. "Idan kina Ƙaunar Allah Binta ki zauna, mene haka? Waike bakya kunyar idon mutane ki ringa abu kamar wata zararriya?" Turai ta faɗa tana tare Ƙofar uwar ɗakin Hajiya dake shirin fita ta raba hali, Jafar na fita tacewa Aidah, Jikarta Babbar Yar Nazira ta bishi taga inda zashi ilai kuwa tace mata ya shiga ɗakin Momy ta zabura zata fita Turai ta hanata shine ta turata ɗaki suketa tata burza tun dazun lokacin daya ɗauka a ɗakin be fito ba shi ya saka Harzuƙata, ta window taga fitowarsa da shigarsa Gurin Hajiya Rabi shine ta zabura zata tareshi ta tsigaleshi taji tsakanin Aisha da Rabi ko da akwai wadda ta tayata ɗaukar cikinsa ko ɗawainiyar rainonsa ne bata sani ba dayafi mutuntasu da girmama su akanta? "Turai kirabu dani, ni ban iya haɗiye baƙin ciki ba sena Amayar dashi, ke ni fita ki sallami kowa ma ta wuce gidanta zaman me kuma za'a mun tunda wanda ake taron danshi ya watsa mun ƙasa a ido, sallami kowa dan Allah na samu sararin huce fushina yanda ya kamata" Hajiya ta faɗa a fusace tana fuzgewa daga riƙon da Turai tayi mata. "Kamar ya in sallamesu ni na tara miki su ko yaya? Sannan Ai kya jira su gana cin abinci ko ba'ace su tafi ba kowa kama gabanta zatayi tunda ba yinin Biki bane balle ace se rana ta faɗi idan kuma zaki fita ki korasu daman ba baƙon abu bane a gurinki ai siyar da hali" Turai ta mayar mata itama a fusace kowa ta kalli Bango tana hura hanci. Jafar kuwa daƙyar ya ƙwato ya fito daga Masallaci, ɗakinsu shida Ahmad ya wuce. Ya saki murmushi ganin yanda aka canza tsarin ɗakin daga zuwansa na last year ya canza musu Gado da Labulaye da Carpet harda penti aka sake sabo ga kyawawan Food warmers da Jug a ajiye yasan aiken Momy ne. Seda ya sakawa Ƙofa Key kafin shiga wanka. A cikin kayan Ahmad ya nemi marasa nauyi Three quater Kaki da Armless shirt ya saka ya dirarwa Abincin. Tuwo ne da Miyar Agusi, taji Wasulla na ruwa dana ƙasa wato Momyn kamar tana shiga zuciyarsa duk zuwa seta tareshi da abinda yake da burin ci idan yazo gida. Sosai yaci tuwon ya sha Juice ta ture kayan gefe ya kishingiɗa jikin gado yana jin jikinsa ya cika da yawa, shida abinci me nauyi kamar tuwo se yazo Nigeria shina baya ci da yawa saboda Diet ɗinsa. Wayar Ahmad ya kira, "Ina Get" Ahmad ya faɗa bayan daya amsa wayar dan idan be ɗaga ba Jay kira zeyi tayi baze barshi ba. Ragowar Abincin daya rage Ahmad yaci suna hira Salim ma ya shigo se Lawal da Mu'allim da suka shiga suka gaida shi suma suka kuma gaya masa mutane na jiransa a ƙofar gida. "Ka ce musu na fita" Inji Jafar. Ahnad na siɗe hannu yace "Sun fika sanin whereabouts ɗinka ai, garama ka tashi kaje kafin Alhaji ya dawo ya tarar da taro a Ƙofar gidansa ya dirar maka daga dawowa" "Yana nan da halinsa kenan be canza ba? Is high time da muma ya kamata mu mallaki gidan kanmu haka a dena zuba mana Iko, small thing ze fara badai a gidana za'ayi this ba? A gidana kuke mun that?" Jafar ya faɗa yana mimicking muryar Alhaji Audu. Ahmad dasu Salim sukayi dariya, dole ya fita ya sallami Fans ɗakyar kafin ya koma ciki Matan da Hajiya ta tara nata fitowa kowa na kama gabanta ya ɗauke kai kamar be gansu ba yanajin Yannatan na kiran sunansa amma ya share. Shi ko ƙawar hira be hango a cikinsu ba balle Alaƙar da iyayensu suke son ƙullawa dashi. Bayan Magriba suka shirya shida Ahmad sukaje gidan Late Brigadier General Baballiya Bechi yayiwa Matarsa da yaransa Ta'aziyya, daga can Ahmad yace su biya gidan Baba Alƙali sukayi rashin Sa'a baya nan yana Abuja se washe gari ze dawo inji Mama Balaraba, dukda basu tarar dashi ba amma suka zauna har kusan 11 suna can dan idan sukaje gidan nan basa iya fita da wuri daman musamman da suka tarar da Fadlan ya fara caccakar Jay akan Premier League wai suna kwan gaba kwan baya, se sunyi sama se su diro ƙasa sun kasa yin abin kirki. Drama Jay da Fadlan daman bata ƙarewa tunawa da dokar Alhaji Audu ta hana kaiwa dare a waje yasa suka tafi a 11 ɗin. "So we go cross fence today" Jay ya faɗa sanda suka tarar da Kantamemen Get ɗin gidan a garƙame, Ahmad yace "Da rabon kayi kwanan Cell kuwa, gidan Alhajin Bechin zaka haura? To sauka nayi tacan farkon Layi karma yace tare muke" suka fashe da dariya suna tuna wani lokaci zamanin yarinta Jafar da yarbanzar ƙiriniya Hajiya bata nan ta kukke ɗakinta ya shiga ta window wai ze ɗakko Uniform ɗin Islamiyya ya shiga amma fitowa ta gagara a zatonsa bata saka key ba a Ƙofar ze buɗe ta ciki ashe ta murza Key abinta haka ya zauna ɗaki har Magriba akayi sa'a Alhajin ya riga Hajiya dawowa akace ga Jafar can ya haura ɗaki ya kasa fitowa Alhaji ya tubure se an kirawo yan sanda kafin a buɗe ƙofa se su tuhumi Jafar dalilin daya saka ya haura masa gida dakyar fa Aka bashi baki ya ɗauko spare key ya buɗe shi amma yaci duka a gurinsa ranar. Horn Ahmad ya danna, Issa ya leƙo ganin motar Ahnad ya buɗe Ƙofar, "Da alama Alhaji baya gari" Ahmad ya faɗa bayan da ya ajiye mota. Issa yace "Aa, mun faɗa masa kunje gidan Alhaji Soja kuma kunayin dare acan shine yace idan kune a buɗe, idan ba ku bane kowaye ya kwana ga waje, kuma Alhajji Yaƙubu bayaga gida? Ko bashi a Kano baki ɗayane?" Ya tambayesu. "Ohna manta ko banga Yah Yakub ba, ko baya nan?" Jafar ya faɗa Ahmad yace "I'm not sure da safe dai mun haɗu, ta yuwu yayi tafiya ko kuma Gidansa ze kwana kasan Yah Yakub ya zama jan wuya Alhaji ya saka masa ido kawai" "Kodai Hajiya ta tsaya masa ba?" Inji Jafar daga nan suka wuce ɗaki, yana so yaje gurin Hajiyar amma yasan tashin hankali ze siyo da se ta hana kowa bacci a tsanake gara ya bari ayishi ido na ganin Ido. Ƙofar falon Alhaji da suka gani a buɗe tasa suka fahimci yana ƙasan dan haka suka shiga sedai suna saka kai duk su biyun sukayi dana sanin shiga a lokacin, Hajiya na zaune da akama su take jira, Jay ya juya ze koma Ahmad ya rufa masa baya ta tashi da hanzari ƙiris ya rage ta hantsila tana cewa "Gasu nan, ka gani ko ya janyeshi sunfita ze fara koya masa yawon Iskancinda yakeyi, wlh tallahi kayi mun tsakani da Aisha da zuri'arta ta fita a sabgata idan ba haka ba ta bari na waiwaya kanta wlh na lahira se ya fita jin daɗi. Banda tsabagen an juyar masa da hankali Jafaru ne zezo ƙasar nan ya shiga sabgoginsa tamkar na mutu baya tunawa dani? Kalleshi fa, kai da gani kasan ba a hayyacinsa yake ba to na rantse da Allah duk abinda mutum yake taƙama dashi na dameshi na shanye kuma se na nuna muku ku baku san komai ba ƙananan yan banza ne ku, dallah wuce ka bawa mutane guri kana wani sunkuyar da kai kamar na Allah kai kuma shigo nan" ta dakawa Ahmad tsawa. Daman neman hanyar tsira yake dan haka da sauri ya wuce ya bat Jafar a gurin. A gurguje yayi shirin bacci yana sake gwada kiran Fatima. Tun da rana da sukayi magana yace mata ze ɗauko Jafar ya sake kiranta kusan sau huɗu bata amsa ba, sanda suka fita tareda Jafar ya kirata tace she will call him back tana abune amma shiru yanzu kuma neman abinda ze hana maganganun Hajiya tasiri a zuciyarsa yakeyi shiyasa ya kasa jirn ta kirashi kamar yanda tace yake sake kiranta. Ko dazun ma da rana sanda ya ɗauko Jafar fita kawai yayi daga gidan ya tafi can bakin titi daya gwada wayar Fatima be samu ba ya zauna yana ƙirga motocin da suke wucewa har zuciyarsa tayi sanyi shine ya dawo gidan. Yaja tsaki yana cilli da wayarsa akan gado dalilin kiranta daya sakeyi sau biyu bata ɗauka ba, wlh da ze iya cire sonta daya masa kamun kazar kuku daga zuciyarsa daya haƙura da yarinyar. Duk wasu alamu na nuna rashin karbuwarsa a gurinta ta gwada masa, ya rasa Aibunsa daya saka Fatima ba zata so shi ba, shiɗin da Mata suke bi kamar ƙuda da Alawa shi Mace take wulaƙantawa gaskiya So baya kyautawa sam. "Lafiya kake tsaki Yah Ahmad ga wayanka kuma a ƙasa?" Jafar daya shige fuska tayi jaa ya faɗa, Ahmad ya kalli ƙasan dayace, ashe wayar can tayi tsalle ba kan Gadon ta tsaya ba. Ya sake yin tsaki ya ɗauka, Screen ɗin ya tsage, sabuwar wayace Dal Samsung ƙirar shekarar Kwanansa huɗu da bareta, guda biyu ya siya ze bata ɗaya idan sun dawo hutu ko yaje Zarian ko screen guard be saka mata ba gashi takaicin Fatiman ya saka ya fasata. Dannawa yayi ya tabbatar iyakar Screen ne faɗuwar ta taɓa be shafi Sensor ba dayaga lafiya lau take ya ɗorata kan Bedside ya kwanta. Jafar daya gama shan Rap a gurin Hajiya abin takaici Alhaji na zaune yanajin yanda take aibata Ahmad tana ɗora masa Alhkin wai son ya rabata da ɗanta amma ya gagara cewa komai harta gaji ta barshi ya taho. Wanka yayi ko ze samu sauƙin bacin ran da yake cikiz Ahmad daya kasa bacci abin tausayi ya sake ɗaukar waya yana gwada number Fatima tana ta ƙara amma bata ɗaga ba. Tashi yayi ya shige banɗakin da Jafar ya fito. Jay ya zauna a bakin gado ya ɗauki wayar Ahmad. Tunda suka fita ya lura da yana ta trying qata number idanbata shiga ba yayi tsaki ya ajiye waya har a gidan Baba Alƙali hankalinsa rabi baya tare dasu shida Fadlan ya barsu sunata surutu. Call log ya shiga sunan FATIMA ya fara cin karo dashi da wata Red heart a gaba. Yaja tsaki a fili yace "She must be that Mechanic daughter, har take da guts ɗin wulaƙanta Yah Ahmad". Haka kawai ya sake danna kiran number zuciyarsa na tafarfasa addu'a yake Allah ya bashi sa'a ta ɗaga, cikin ikon Allah kuwa ringing uku yaji an ɗaga, Fatima tsaye a gefen Tukubar Sambo me Mac Dee tana jiran a sallami Badar. Test garesu har biyu a gobe dan haka tunda yamma suka fita karatu. A silent ta saka wayarta shiyasa bata ji kiran Ahmad na farko ba, da sukaje sallar Magriba kuma taga missed calls, fa sukaje sallar isha ma ya sake kira tace she will call back amma ta manta bata kirashi ba kamar yanda Badar tace saboda baya gabanta shiyasa har take mantawa da abinda ya shafeshi. Kiran da yake tayi mata na yanzu kuma ta na gani dan wayar na hannunta da ita take karatu ƙyuyar ta tashi ta fita daga class ɗin ta amsa wayar ya saka taƙi dagawa ganin yanata kira yasa tayi rounding off suka fito dan daman Badar tace ta gaji bacci takeji, suna tafe seda suka wuce FSLT Badar tace wai yunwa takeji zataci Mac Dee shine suka zarce gurin Sambo a gaban Social Centre tana ta Allah Allah a sallamesu ta shiga hostel ta kirashi sega kira ya sake shigowa wannan dalilin yasa ta ɗauka muraya a sanyaye cike da gajiya da bacci tayi masa sallama. "Dallah riƙe sallamarki Malama, who the hell do you think you are da har zaki ringa wulaƙanta mutum kamar Ahmad? Do you even deserve to date someone like him? Koda yake daman haka kuke Yayan Talakawa yayan Matsiyata ku ba kowan kowa ba se shegen girman kai da isa kamar wasu sarakai. Imagine Yar Mechanic, bawai me Gyaran Mercedes Benz ko wata Lambo or Tesla ba just a common mechanic may be ma Motorcycle yake gyarawa not even cars shine kika samu damar raina Ahmad Bechi saboda he stop so low yace yana sonki. I even began to think anya ba Asiri kikayi masa ba? Ke koma dai Mayyace ke because they way Ahmad is behaving yafi kama da someone that is possed. "What ever you have done to him bear it in your mind bazaki Aureshi ba, in har ina raye i will make sure that ko Inuwar Ahmad baki tsaya tareda ita ba balle har kiyi tunanin Auransa. Look for your mate ki kuma sakar masa Soul idan kuma ba haka ba zanyi maganinki, ni Jafar Bechi i will be the end of you akan Ahmad zan iya sacrificing life ɗina kuma bazan saka ido ina kallo yayi wasting rayuwarsa on worthless thing like you ba ku....." "Jafar..." Ahmad daya fito daga wanka ya kira sunansa cikin ƙaraji kafin ya kwace wayarsa. Ya duba screen tabbas da Fatima yake magana ita yake faɗa wannan kausasan maganganun daya taraddashi yana faɗa. Na ƙarshen ma yaji Allah kaɗai yasan me yace mata daga farko. "Fatima, i will call you please. Karki bari maganarsa ko guda tayi tasiri a zuciyarki ina ganin shaye shaye ya fara, let me deal with him first zan kiraki kiyi haƙuri dan girman Allah kinji?" Ahmad ya faɗa, be jira amsarta ba saboda yand aya rikice ko kashe wayar beyi ya ajiyeta ya fuskanci Jafar da idanunsa suke ci da wutar Bala'i. "Why Jafar? Me yasa zakayi mun haka? Kasan wacece ita? Kasan matsayinta a gurina?" Ya faɗa yana kallo Jafar, a fusace Jafar yace "Koma wacece ita ta wuceni a gurinka ne? Ni Yah Ahmad kake tunanin shaye shaye nakeyi saboda na gayawa waccen bastard ɗin gaskiya ta shiga hankalinta? Do you think i can withstand seeing you being disrespected by that local champ? No kuma kaima you must come back to ur senses wlh ba zaka auri waccen yarinyar ba da bata san mutunchinka ba. Duk matan duniya kowace kake so ka nemo i will stand with you but not her not Fatima or what ever her name is" "I will slap you wlh ka sake zaginta Jafar, Fatima is my Life, matar da nake burin na aura ce in har kana so na dole ka sota duk yanda take and you must respect her as much as you respect me. Tsaya Jafar yaushe ka zama haka? Yaushe ka fara kyamatar Talaka? Juat tell me the truth, Do you hate Fatima for not been from prestigious family like yours ko kuma saboda bata sona?" "Akan Mace zaka Mareni Yah Ahmad, macen da bata san mutunchinka ba?" Jafar ya faɗa yana nuna kansa mamaki sosai a muryarsa. "Answer me Jafar akan me ka tsaneta kafin nan zan tabbatar maka da ka cancanci Marin ko kuma ba haka ba" Ahmad ya mayar masa tasa muyar cike da tabbatarwa. Kawai se Jafar ya jijjiga kai ya nufi ƙofa yana cewa "Wlh ko kowa ya yarda ka aureta bazan bari ba, bata isa ta shigo ta lalata abinda Allah haɗa ba, babu matar da zata lalata zumunchin da yake tsakanina dakai kuma Mayyace Ta kama maka Soul, first thing tomorrow morning Bechi zan tafiz ai da muna Yara ance da akwai Sarkin Mayi acan, I'm going to report her to him duk ma inda ta kai Kurwanka seta dawo dashi I promise". Fatima ko tayi tsaye da waya a kunne tana sauraron Jafar, ta ma kasa fahimtar kalamansa da inda suka dosa, ta fahimci ba muryar Ahmad bace abinda take tambayar kanta waye wannan??? Zagin Mahaifinta da yayi shi ya karya mata zuciya har bata san hawaye ya fara saukar mata ba seda Badar ta taɓata akan su tafi taga tana kuka da waya a kunna wannan yasa da sauri ta zare wayar ta saka a speaker don a zatonta ko wani Bad news ake gaya mata daga gida nan ta tsinci faɗan Jafar da Ahmad dan lokacin ya gama zazzaga mata tijara Ahmad ya kwace wayar. "Atleast he stood for you, shi kuma ko wanene wannan da yake iƙirarin indai yana raye ba zaki Auri Ahmad ba Bi'iznillahi da ransa yanaji yana gani zaki Aureshi sedai baƙin ciki ya sa ya haɗiye zuciya ya mutu. Ke kuma banza kin tsaya kina kuka, me yasa baki cuccusawa uwarsa Ashar ba? Dallah muje ni kar kisa na huce haushi na akanki kin wani tsaya kina kuka wlh na ɗauka mutuwa aka kira a gaya miki daga gida, daman idan baki nemo mana number sa munci Kutumar ubansa ba to naki zanci Soloɓiyon banza kawai". Badar ta ringa masifa iyakar Ƙarfin ta har suka isa Ɗaki ita kuma Fatima tana kuka. Yar Matsiyata, mayya daya kirata yafi komai yi mata ciwo a rai, shi be san ba son Yayan nasa takeyi ba bare har yaci mata mutunchi akansa? Koda ace tana son Ahmad wannan dalilin ya saka ko zata mutu seta rabu dashi wlh. Wayarta ta ɗauka take tayi blocking ta kumayi deleting number Ahmad, an gama chapter sa domin ba ayi wasu Ahali fa zasu wulaƙanta mata Baffanta ba kuma ko Ahmad ne Autan Maza sedai ta mutu batayi Aure ba. PAGE 8 Sosai Ahmad ya ɗauki fushi da Jafar akan abinda yayiwa Fatima, dukda shi Jafar ɗin ya sauke kai ya bashi haƙuri inda suka sake fafatota da yace se ya kira Fatima ya bata haƙuri ai ita yayiwa laifi nan fa Jafar ɗin yace muddin ba Momy bace bazeyi ba, sedai idan sanadin haka yasa Ahmad yace shi ba jininsa bane amma wlh baze bata haƙuri ba, da niyyar sati uku yazo Nigeria dalili wannan ɓarakar yasa kwana goma yayi a daddafe ya tafi kuma duk gida seda aka gane akwai matsala tsakanin Jay da Yah Ahmad ɗin nasa dan muddin yana gari duk inda zaka gansu tare suke amma wannan karon kowa sabgarsa yakeyi. Momy ta tambayi kowannensu akan meya faru amma sukace mata babu komai, ta haɗasu tayi musu Nasiha akan karsu bari shaiɗan yayi tasiri a cikin zukatansu, su ɗin sun kasance abin misali cikin zuri'ar Audu Bechi karsu yarda seda girma ya fara zuwa kuma su kama wata hanya ta daban. "Na san abu biyu shaiɗan yake saurin samun gakaba akan mutum ta dalilinsu, Mace da Kuɗi, karku bari ɗaya daga ciki ya haɗaku kuyi Ƙoƙari ku sasanta kanku" tace musu duk suka amsa mata da "In sha Allah" amma suna fita kowa ya kama gabansa. Ahmad yanda ya kasa samun Fatima a waya shiya sake dugunzuma hankalinsa har yake ƙara tasirin fushin Jafar a zuciyarsa, Allah ya sani yana sonta, so me tsanani da yake jin tamkar idan be sameta ba ze iya rasa ransa. Daya kasa samun wayarta tilas ya shirya ya tafi Zaria abinda ya Ƙara tunzura Jafar shi kuma tsanar Fatiman ta ninku a zuciyarsa tunda har ta zama silar ruguza Alaƙar sa da Ahmad yayi rantsuwa ba zata shiga zuri'arsu ba domin Allah kaɗai yasan abinda zata haifar musu. Shirin komawa ya shigayi duk da kwanakin daya niyyata basu cika ba kawai gara ya tafi dan baze jure abinda Yah Ahmad yake masa akan Mace ba, Macen ma wadda bata kai matsayin ace Ahmad ɗin ya haukace haka akanta ba. Har hasaso kamanninta yakeyi Ƙila wata baƙace mummuna da fuskarta kamar ta shafa Baƙin Man da Babanta yake ta'ammali dashi, kai Yarinyar nan ma dole asiri tayiwa Ahmad kuma tilas ya karyashi. Hajiya kuwa ranta ƙal tamkar zata taka rawa data fahimci yanda abu yayi zafi tsakanin Jafar da Ahmad. Dubunta Hansin ta bawa Turai taje mata gun Malam akan ayiwa musu Farraƙu domin taga alamun Amadun yana neman yasa kwaɓarta tayi ruwa kuma aiki yaci. Duk wani buri da tanadi da take dashi akan Jafar in har yana tareda Ahmad ba zata samu cikar burinta ba Jafar kuma shine makamin ƙare danginta a yanzu. Tana da shiri da kuma tsarin ganin ya zama makwafin Alhaji. Da akwai matattarar sirrin Alhajin inda duk wani abu mai muhimmanci daya shafi rayuwarsa yake da wanda su suka sani harma da wanda basu sani ba takaddun Kadarorinsa na gida dana Ƙasashen waje duk a nan ya ajiyesu. Wata Safe box ce a cikin Wardrobe ɗinsa ta kaya. Safe ce da akayita da wani irin matakan tsaro ta yanda duk tsiya da bala'i muddin ba wanda ya kulleta ba shi kaɗai ze iya buɗewa babu ta yanda za'ayi lalata tsaronta kuma ba zata fasu ba. Tasha ta saita Kemarar wayarta ta yanda zata ɗauko mata Ɗalamisan da Alhajin yake buɗe gurin dasu amma abu ya faskara kamar ma ba wani abu da yake dannawa se daga baya ta fahimci kwayar idonsa ce mabuɗin gurin, kenan babu ta yanda za'ayi ta buɗu indai ba shine da kansa ba. Hankalinta yana Ƙololuwar tashi idan tayi tunanin yanzu ace ya faɗi ya mutu ta yaya zasu buɗe gurin su kwashe wasu abubuwan da bazasu so ace sun fito a rabon gado ba sedai ita da Yayanta su handame? Da fari taso ta tattauna maganar da Zakariyya da Naziru taji ko suna da Mafita, sedai ta fasa hakan saboda ta sani a yanzu ita dasu shegen Sama ne uake dukan na ƙasa, kowanne ƙoƙarin ya gina kansa yakeyi idan kuma ya samu dama ya tattare komai shi kaɗai shoyasa ta fasa sakasu a cikin shirinta. Jafar kaɗai ta aminta da sakashi gaba akan cimma wannan ƙudurin nata, shi take so ya zama magajin Alhaji domin tayi ammanna duk cikin Yayansa babu wanda ya aminta dashi har zuwa yanzu ya sanar dashi ta yanda za'a buɗe ma'ajiyar bayan ransa. So takeyi ta sake cusa Jafar ɗin jikin Alhaji ta fili data baɗini ta yanda ze Amince dashi ya damƙa wannan Amanar a hannunsa ya zama shine Magajinsa, ita kuma da wannan damar ta samu Jafar ɗin ya gama sanin komai game da Alhajin shikenan burinta ya cika domin se yanda tayi da Jafar ɗin da kuma dukiyar Alhaji sedai wannan muradi nata baze cika ba muddin Jafar yana tare da Ahmad, shi yasa bataji komai ba da Turai tace ta bada kuɗi zata je mata inda suka kai sunan Abba T saurayin Hajiya Ƙarama domin dukda dukan daya sha a hannun Yakubu be haƙura ba, ya dawo amma a can gidan Haj Turai sukeyin Hira ko kuma su fita yawo gari maganar da ake yanzu ma Bayan sallar Azumi yace Iyayensa zasu zo tambayar masa Auranta. Babu wanda ya san zancen a gidan kosu Naziru Hajiyar bata gayawa ba tace sedai aji komai katsahan tunda har a yayan cikinta akwai masuyiwa Hafsatun baƙin ciki. Ahmad na Zaria Jafar ya tafi dan tarewa yayi a Hotel kullum haka ze je Samaru ya wuni a Faculty of Art yana bibiyar ta inda ze gamu da Fatima amma taƙi yarda su haɗu se ranar daya kwana uku ne ya samu nasarar ganinta sammako ya buga tun bakwai yaje ya zauna a bakin Class ɗin da zasuyi Lecture, a gurin wani Guy ya samu Time table ɗinsu bayan daya nuna masa hotonta ya tabbatar masa ya santa bata zuwa Class kwana biyu amma na goben ya tabbatar zata zo indai tana Makaranta dan Malamin baya wasa Individual Attendance yake ɗauka and is automatic carry over idan mutum yayi missing wannan tasa ya tafi da wuri, 8 zasu shiga amma 7 bata gama rufawa bama ya kafa ya tsare a bakin Ƙofa. Yana tsaye a gurin suka zo ita da Badar da wasu yammata biyu, bata ganshi ba se Badar ce ta nuna mata shi tana cewa "Kinga Ahmad" "Ahmad?" Ta maimaita da mamaki tana kallon inda take nuna mata se gashi kuwa a tsaye ya zuba hannaye a Aljihu yana binta da kallo suna hada ido maganganun Jafar suka fara dawo mata tamkar a lokacin yake faɗarsu wannan tasa tayi saurin ɗauke kanta ta doshi class ɗin da sauri dan ba zata bari ya tareta ba amma kafin ta shiga yasha gabanta. "Ka matsamun na wuce" ta faɗa ba tareda ta bari sun haɗa ido ba saboda yanayinsa da yake neman karya mata lago ya samu galaba akanta. "Zan jiraki a waje ku gama" ya faɗa a sanyaye yanajin tamakar ya rungumeta saboda So, taja baya saboda kusancinsu yayi yawa tana cewa "Karka jirani dan ko ka zauna bazan saurareka ba" "Shikenan, zan shigo Ajin na roƙi Lecturer ya bani dama a gaban kowa nayi magana dake hakan ya miki?" Yanda yayi maganar ta fahimci ze aikata abinda yake nufi dan haka tace "Karka shigo, ka jirani a waje" "Good girl" ya faɗa yana mata murmushin ƙarfin Hali, kansa ciwo yake masa be taɓa zaton haka so yake dagaske ba. Fatima ta wuce, Badar ta matso fuskarta ɗauke da fara'a, she is lively ko yaushe fuskarta a washe take kamar ta Ahmad ɗin muddin ba an tsokalota bane. "Hi" ta faɗa tana waving masa, "Hello Badar" ya mayar mata yana ɗaga mata hannun shima bakinta har kunne jin ya ambaci sunanta, ashe dai Fatima ta bashi labarinta. "Karka damu, just give me your number, kaje ka samu comfortable guri ka zauna i will bring her to you damun gama Class" ta faɗa tana bashi wayanta. Ya karɓa ya shigar da Digits ɗinsa kafin ya mayar mata yace "Nagode Badar, i will be in Shinkafi Elite, zan jiraku a can" "Ayt, se munzo" ta sake ɗaga mishi hannu kafin ta shiga Ajin ta zauna kusada Fatima dake leƙensu ta window, duk a kan Idonta Badar ta bashi wayarta tana ganin yanda suke ta wani Murmushi duk seta tsargu. Badar batace mata komai ba har akayi Lecture aka gama suka fito, tana lura da yanda take satar kallon gurin da alama Ahmad yake nema amma bata ganshi ba A zuci Badar tace "Munafuka kawai tana so tana kaiwa Kasuwa". Suna tafe duk Fatima bata da laka, tunani takeyi ko ya tafi? ƙila ya haƙura da itan kawai tunda har ya karɓi number Badar. A hanya Badar tace su biya ta Shinkafi su siya Chips tace ta ƙoshi amma Badar ta nace se sunje in yaso ta siya ita kaɗai. "Kije can ki zauna kinga akwai layi kafin azo kanmu" ta nuna mata Table ɗin dake kusa dasu, Fatima tayi tsaki, can ƙarshe ta wuce seda ta zauna kafin ta lura da Ahmad ne a gurin. Zabura tayi zata miƙe ya dafe hannunta, karo na farko da hakan ta faru tsakaninsa da wata Mace da ba Muharramarsa ba. Cikin sauri ya saki hannun nata se kuma ya miƙe tsaye ganin tana shirin barin waje yace "Kwana na uku ina yawo cikin makarantar nan, na kasa samunki a waya, idan na canza layi na kira ki da kinji muryata seki kashe daga ƙarshe kindena Amsa duk wata number dana kira da ita why Fatima? So kikeyi zuciyata ta buga na mutu kowa ya huta? Dame kike so naji? Da Matsalarki koda rigimar Jafar? Wlh ko ki tsaya muyi magana yanzu ko kuma ba biki har cikin Hostel, Bet me I'm fuc***g serious zaki sha mamakina yau". Kuka Fatima ta fasashe masa da shi kawai ta zauna tareda kwantar da kanta akan Table ta shiga rera shi. Ahmad ya zauna ya harɗe hannaye yana kallonta ba tareda ya hanata ba. Badar kuwa saya karɓi order ta tafiya tayi Hostel. Seda Fatima tayi kuka me isarta Ahmad na zaune ya na kallonta kafin ta tsagaita ta fara zazzage masa abinda yake ranta wanda Jafar Bechi yaci ace ta gayawa sanda yake zaginta amma ta huce akan Ahmad ɗin. "Kiyi haƙuri dan Allah kuma ki manta duk wani abu daya faɗa shima cikin fushine and he regretted everything he said, zan haɗaku a waya ze baki haƙuri komai ya wuce" Ahmad ya faɗa kamar zeyi mata kuka. "Ni na haƙura sannan kaima na haƙura dakai, Brother ka ya gaya mun what i need to know about your Family, na sani daman ba zasu soni ba saboda ni Talaka ce amma ka sani ka kuma gaya masa tabbas mahaifina Talaka ne amma ba Matsiyaci bane domin yana da wadatar zuciya kuma sana'ar sa da yake zagi Halal yake nema Haram ba sannan ba yawon Maula yake gurin wasu mutane ba balle ya samu damar zaginsa ya Ƙasƙantar dashi. Nasan mutunchin Iyayena dan gaka bazan bari wani ya taka darajarsu ba, ko beyi rantsuwar bazan Aureka ba na rigada na yankewa kaina wannan shawarar sannan ka gaya masa Maita daya dangantamu da ita, nasan ko nayi shari'a dashi a duniya ba za'a bi mun haƙƙina ba saboda shi ɗan masu kuɗi ne amma zamuyi shari'a a Katun da ba'a bada cin hanci" ta faɗa sababbin hawaye na sauko mata. Duk yanda Ahmad ya zata abin ze zo masa da sauƙi ya zarce haka, taurin kaine da ita kamar mutanen farko ta riƙe maganganun Jafar Bechi se maimaitasu takeyi. "Amma Fatima ko Allah daya halicce mu baya kama wani mutum akan laifin da wani daban ya aikata muddin ba sunyi tarayya a cikin aikata laifin ba. In har akan Abinda Jafar yayi miki ne na baki haƙuri kuma in har zakiyi mun Adalci kin san bani na sakashi ba, ki faɗi kanki tsaye cewar bakya sona, ba kya Ƙaunata kawai dan rajin kanki ba saboda abinda Jafar yayi miki ba. Na dade da fahimtar haka, amma na kasa cire rai dake bansan me yasa zuciyata ta kasa haƙura dake ba, ina Addu'a akan Allah ya zaɓa mun mafi Alkhairi a kullum kuma ji nakeyi tamkar ana Ƙaramin sonki, duk yanda nakeji akanki wlh zan jure kuma zan roƙi Allah ya yayemun muddin kika furta da bakinki bakya Sona ba kuma zaki aureni ba nayi miki Alƙawarin daga nan gurin ba zaki sake gani na ba zan kuma fita daga rayuwarki koda Sonki ze zama Ajalina zan haƙura dake Fatima". ************* A YEAR LATER Gudu gudu sauri sauri take tafiya saboda ta kusa makaraz fata takeyi Allah dai ya rufa mun asiri ta samu ta shiga Ajin nan kafin Dr Abolude ya rufe, ba rasa ajinsa ba wannan banzan halin nasa na marking note se kace a primary ko secondary school shine abinda yake bawa kowa haushi dashi balle ita yau da rubutun ya zamar mata biyu, ga nata gana Badar dole taje da wuri ta samu sit a gaba, layin wanka ne ya bata mata lokaci saboda Monday ce kusan kowa na block dinsu nada Ajin safe. Qiris ya rage ta hantsila daidai Basket ball court saboda wani mutum da tun fitowarta daga Amina Hall ya zura mata ido kamar me shirin ganin yayan hanjinta, taja tsaki ta dauki Jakarta data zame ta fadi a ranta tana mitar wannan kallo haka taci gaba da zabga sauri a karo na biyu ta sake yin gaba tana shirin gangarawa daidai Senate building saboda mutumin dazu data gani tsaye gabanta kamar Aljani. Batasan sanda ya biyota ba harya tare mata hanya, zuciya ta harziqomata amma bata tankashi ba ta sake rabeshi ta wuce a kato na biyu se ji tayi daga bayanta ance "Sihh, jimana yammata". Raita ya ninka da baci, a duniya idan akwai abinda ta tsana be wuce irin wannan kiran wulaqancin da maza sukeyiwa yammata ba, se kace wata mota ko Mashin a ringa maka wani Sihh wasu tantiranma har fito suke kamar masu kiran kare. Taci gaba da tafiyarta kamar zata tashi sama ga haushin mutumin ga na bata mata lokaci da yake tayi dan ta tabbata yanzun kam ta makara sedai ta maqale a bakin window idan batayi sa'a ba. Karo na uku ya sako fadowa gabanta, wannan baƙar ɗabi'a ta mutumin da abin takaici take baya ko tunanin zata iya faɗuwa tunda batasan da shi ba ya ringa diro mata kawai kamar wani jifa. "Dan Allah ki saya" ya faɗa yana kallonta se a sannan ita ma ta kalleshi fuskarta babu alamar rahama amma can ƙasan ranta seda ƙirjinta ya buga saboda se yanzu ta kalleshi da kyau. Wani zabgegen mutum me ƙirar ƙarfi jiki a murɗe dan a yanzu da yake tsaye gabanta shigarsa ta nuna motsa jiki yakeyi, rigace Armless jikinsa da wandonta wanda da kaɗan ya zarce guiwa kayan suka qara bayyana surar ƙarfinsa, bata tantance fuskarsa ba dan bata kalleta sau biyu ba, yanda ya kankane mata hanya yasa ta raina kanta da tsahon da take taƙama dashi dan wata yar firit ta ganta a gabansa. "Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faɗa da sautinsa daya sa ta gaza tantance wane yare ne shi, sake daga kanta tayi ta sake kallon fuskarsa, a zubi za'a kirashi Bahaushe ko kuma Hausa Fulani amma a zubin jiki dai yafi kama da Irin zabga zabgan Igbiran nan ko Inyamurai haka fatar jikinsa da take da haske dukda ba fari bane amma a goge take tar yanda kasan ya hada jini da fararan fata. Tsaki ta zabga data kalli sumar kansa da tasha gyara irin na Yan Ball din nan itako yana daga irin abinda ta tsana dan duk girman mutum idan ta ganshi da irin Askunan nan kallon wanda be san kansa take masa ba. Tuna abinda yake gabanta yasa ta kauce ya sake tareta yana cewa "Nayi sallama kin bini da tsaki ki amsa mana Ammata" ya faɗa da wata cukurkudaddiyar hausa yanda kasan wani Yare yake. Tsakin ta sake masa tayi baya a tsiwace tace "Ka matsa Malam ni ina da abinyi" "Zan masa amma se kin mun abu uku, firstly ki amsa sallamata dan wannan dolene a musulunci kinsani then you tell me your name, lastly you give me your digits" ya ƙarasa yana irgawa da yatsunsa. Harara ta galla masa amma yanda ya bake hanyar tasan ko tureshi tace zatayi ko gezau bayi zeyi ba kuma duk inda tayi binta yake wannan yasa ta amsa masa sallamar a ƙufule tana cewa "Se ka matsamun na wuce Malam tunda na amsa maka sallamar ai" "Ai baki cika sauran sharuddan ba" ya sake faɗa se tayi saurin tareshi da cewa "Nayi wanda zan iya" "Baki isa ba, na miki rangwame cikin biyu you choose one, either you tell me ur name or you give me your contact, barshima, bari sunan, bani number kawai" ya faɗa yana miƙa mata wata tsadaddiyar waya da bata taɓa ganin irinta ba. Ta harareshi taa harari wayar tana cewa "Ashema kai zaka zabarmun abinda zanyi? To sunana Afeeya, dan girman Allah ka matsa ka bani hanya dan ka rigada ka makarar dani" "Kince Allah wuce Afeeyah, suna me kyau kamar yanda kike da kyau" ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi ya harɗe hannaye a Ƙirji yana jifanta da wani kallo. Tuni tayi masa nisa, a jikinta taji har sannan yana biye da ita bata waiga ba har ta shiga Department dinsu ta sauke numfashi ganin yan Ajinsu a waje suna hirarraki alamar Malamin bezo ba, ba tareda ta tsaya ba ta shige ciki abunta dan zuciyarta wani bugu take kamar wadda tayi tseren gudu. Ta wutsiyar ido ta kalli window inda taji alamar idanun mutum akainta, yana nan tsaye kuwa ya harɗe hannayensa a Ƙirji damatsansa sun ƙara fitowa kamar an aje duwatsu se tayi sauri maida kainta kan desk tana jin yanda zuciyarta take tsere, bata dade da zama ba Malamin ya ƙaraso, ya ringa zabga dictation suna rubutawa ajin awa biyu ne amma tsabar mugunta ya roqi next Lecturer da ze shigar musu ya ara masa lokacinsa tun takwas da wasu mintina bamu muka samu kanmu a hannun Dr Abolude be barsu ba se sha biyun rana zuwa sannan hannun kowa ya sage nata kam har sun kumbura gefen inda take riƙe da biro sunja ruwa daman haka yake mata duk sanda tayi dogon rubutu tofa se tayi jinyar hannu abinka da Jiki duk Madara inji Qawayenta. Taimakon da Allah yayi musu da yace ba lokacin ze karbi note din ba Class rep ya hada ranar Wednesday ya kai masa kuma shine CA dinsu, tayi hamdala a fili dan rubutun nasu rabi da rabi tayi, idan tayi nata se ta kama na Badar duk a tsoron kar a tashi karɓa ta rasa gara ko yayane dai ta rubuta mata wani abu. A mugun gajiye ta wuce Geography mosque dan Azahar ta kawo kai gara ta tsaya tayi sallah kafin ta koma Hostel ta ɗan kwanta zuwa La'asar suna da wani Ajin. Seda tayi alwala ta shiga cikin masallacin tayi Nafila raka'a biyu kafinta nemi guri saitin fanka ta kishingiɗa tana jin kamar tayi bacci saboda gajiya ga bashin na daren jiya da batayi dakyau ba. Wayarta ta shiga Vibrating ta janyota daga cikin jaka, gaba ɗaya ta sha'afa da ita. Tun gurin ƙarfe Tara an kikkirata dukda bata duba ba tasan baze wuce Ahmad bane me kiran yanzun ma tana cirota kiran nasa na tsinkewa a nan taga missed calls ɗin daya mata guda biyar se Message da yake tambayar lafiya yana ta kiranta bata amsa ba idan tagani ta kirashi. Tayi ƙaramin tsaki da batasan dalilin yinsa ba kafin ta danna kiran layin nasa ringing biyu tayi ya katse se gashi ya biyo baya dukda uban katin wayar da yake loda mata duk satin duniya amma idan ta kirashi baya ɗauka, ire iren halayensa na kyautatawa da suke son tursasa zuciyata sonsa kenan badan ta aminta dashi ba har ƙasan rainta. Cikin muryarsa me sanyi amma ba kamarta mata bafa Aa irin ta Mazajen da hayaniya bata dame su ba yayi mata sallama, ta amsa kafin ta gaishe shi wannan tarbiyyar Ummansu ce gaisuwa ga duk wanda ya girme su ta kuma rigada ta zame mata jiki. "Fatima! Lafiya ina ta kiran wayarki tun da safe baki ɗauka ba?" Ya faɗa bayan daya amsa mata gaisuwar. Taja numfashi saboda Fatiman daya kirata, bata so amma ta rasa ta yanda zata gayawa Ahmad ya dena. Sunan Innar Baffansu ce kuma sunan Kakarsu data haifi Ummansu sannan Babbar Yayar Baffansu wadda ita ta riƙeshi itama sunanta Fatiman. A hannunta ya girma bayan rasuwar Iyayensu, su uku kacal suka haifa daga Ita se shi se ƙaramar ƙanwarsu Umma Halima ita Umma Faɗima wadda ta riƙe Baffa ta girme musu sosai dan shekaru bakwai ta bawa Baffansu shi kuma ya bawa Umma Halima shekaru biyar, wannan tudu ukun da naci na sunana FATIMA yasa kowa yake jin nauyin faɗarsa se AFEEYAH Laƙabin da Baffa ya bata ko a makaranta a rigister kaɗai ake kiranta da Fatima amma kowa da AFEEYA ya santa banda Ahmad da bata tsammanin ma yasan ana Kiranta da Afeeyah. "Kinyi shiru, kina jina kuwa?" Ya sake faɗa abinda ya maidota daga tunanin data tafi ta sauke numfashi kafin tace "Ina jinka, ina Class tun 8 bamu jima da fitowa ba na shigo masallaci kenan daman yanzu nake so na kiraka" tayi masa ƙarya badan tana da niyyar kiran nasa ba. A tausashe ya sake ce mata "Ayya sorry love, gaskiya Malaman nan suna wahalarmun dake da yawa amma kun gama gaba ɗaya yau koh?" "Aa fa ina da wani Ajin 4-6 ma" tabashi amsa, cikin jimami ya sake cewa "Toh Allah ya bada sa'a, in sha Allah kamar yau ne zaki ga kun gama ai sedai ki ringa tuna baya kina kewa. Nima daman ɗazun na shigo Zaria na ɗauki Jafar yanzu haka ma muna hanya zan kaishi Abuja ze koma London. Naso mu haɗu amma babu komai in Allah ya kaimu se Wednesday zan juyo ko Thursday zan tsaya kafin na wuce Kano na ganki. "Allah ya tsare hanya ya maido da kai Lafiya" ta faɗa, cikin tsokana yace "Shifa Jafar, baki yi masa Addu'a ba? Ko na bashi wayar ku gaisa harda ma fa saboda shi naso mu haɗu yau dai Abokanan faɗa suga juna" Cikin sauri tace "Allah ya kiyaye ko Inuwarsa bana fatan Allah ya nunamun ballantana wai mu gaisa dashi, idan so kakeyi na sake faɗa maka na tsaneshi fiye da yanda yake tunanin shi baya sona" cikin tsiwa take maganar tareda fushi tana tuna kalaman Jafar ƙanin Ahmad, shekara guda kenan amma ta kasa manta abinda yayi mata. Murmushi Ahmad yayi haka kuma ta jiyo wani dogon tsaki daga cikin wayar wanda ta tabbatar da Jafar ɗin ne yayi ai ko a fusace ta ɗaga murya tace "Allah ya tsinewa tsaka ma ballan tana kai abin banza" "Fatima" Ahmad ya kira sunanta se tayi shiru amma bata amsa masa ba yaci gaba da cewa "Ni nake Driving, idan na isa zan kiraki Ok?" "Allah ya tsare ka kula mun da kanka kaji" ta fada bawai har ranta ba sedan tabbatarwa da tayi wayar a speaker take kenan tunda yace shi yake tuƙi Jafar yana jin duk maganar ta keyi shi take so ta bawa haushi". "I will, you take care too I love you" Ahmad ya sake faɗa tana jiyo Jafar ɗin cikin fushi yana cewa "Wlh Yah Ahmad either you cut this call ko kayi dropping nawa a nan, da wata muryarta ta Villagers ko Turanci bata iya ba" "Tunda ba karatun fatiha na kasayi ba ai da sauƙi, kaida Turancin yake yaran Babarka ai se kayi tayi" ta faɗa bata jira amsarsu ba ta kashe wayarta tana jan tsaki daidai nan kuma aka fara kiran sallah. Fita tayi ta ɗaurayo bakinta ta dawo ranta na suya, Bata taba haɗuwa da mutumin dayaci mutuncinta yaci na iyayenta irinsa ba ita kuwa bata da babban maƙiyi daya wuce wanda yace ze keta Alfarmar iyayenta a duniyar nan, za'a iya takata ta shanye amma fa kar a taɓa mata Iyaye Jafar kuma ya keta wannan Alfarmar ya zagesu shiyasa bashi da sauran mutunchi a idonta balle ta raga masa. Shi kansa Ahmad ɗin Alfarmar Baffanta yaci da har taci gaba da kulashi dan yace ba laifin Ahmad bane ba ba kuma shi ya saka Jafar yayi abinda yayi ba dan haka ko a gurin Allah laifin wani baya shafar wani ta haƙura taci gaba da saurararsa amma wannan dalili yasa karɓuwar daya fara samu a gurinta a baua ta wargaje kuma har zuwa yanzu tsayin shekara daya da faruwar abun ta kasa mantawa haka zuciyarta ta gagara yarda da Ahmad ɗari bisa ɗari har yanzu. Tana tare dashi ne kawai saboda karamcinsa amma a kullum cikin addu'ar Allah ya fiddo mata da Miji daidai da ita takeyi ba zatayi ɗage ba ta kai kanta inda bata isa ba domin daga abinda Jafar yayi mata ta saka a rant tana tareda babban Ƙalubale idan ta shiga zuri'ar su Ahmad domin ba ƙarya Jafar yayi ba ya faɗi gaskiya ita ɗin dasu akwai banbanci, tazarar dake tsakanin su tamkar ta sama da ƙasa ce ta fito daga gidan Talakawa amma masu wadatar zuciya, Babanta Bakanike ne Ummata kuma Tela ce basu da wani gata sena ubangiji saɓanin su Ahmad da suka fito daga babban Ahali tana nufin gidan da aka tara Arziƙi na Kuɗi dana Zuri'a, Mahaifinsu Babban Attajiri wanda duk mutumin daya kwana ya tashi a Nigeria baki ɗaya yasan sunansa. PAGE 9 Bayan ta idar da sallah tayi addu'a tana shirin tashi Maman Minal ta shigo masallacin, Roommate ɗinta ce dan haka ta dakata ta jirata tayi sallar itama kafin suka rankaya Hostel. Tana hango Senate Building Gayen ɗazu daya tareta ya faɗo mata a rai, taɓe baki a fili tace "Wani sangangan dashi kamar basamude, kai wannan duk yanda akayi ya hada jina ma dasu" "Suwa?" Maman Minal ta tambayeta seta tsuke baki tana cewa "Ai yau gamo nayi da safen nan in gaya miki" ta kwashe da dariya tace "Gamo Afee, na Aljani kona soyayya?" "Mutum Aljan dai, wani fa sangamemen mutum in gaya miki, wlh gani na nayi a gabansa kamar nida Ruth, kofa fuskarsa bana iya gani sosai saboda yanda yayi sama da yawa". Tsabar dariya seda Maman Minal ta kware ta dage Niƙab din fuskarta dan tasha iska sosai idonta cike da hawaye tace "Kinga kin sakani irin dariyar da babu kyau meye kuma Mutum Aljan ana zaune lafiya? Inaga irin yan Basketball ɗin nan kika gani sune zabga zabga ni jiya da daddare da naga wani Yaro seda gabana ya faɗi, kinga tsayi? gashi siriri kamar ze tsinke". "Wannan ba siriri bane gaskiya yana da yar ƙiba badai sosai ba amma fa dogone yanda kika san jinjirin samudawa" ta sake faɗa tana hakaito Jay a zuciyarta. "Allah ya shiryaki dai Afeeyah a ina ke kika taɓa ganin jinjirin samudawan toh da har kike kiran wannan haka?" "To dai yau na ganshi, Allah yasa mu sake haɗuwa zan muku video sa ku gani" ta sake faɗa tana Ƙoƙarin zaro Id card suka shiga hostel. Sururat na maida shinkafar data tace cikin tukunya sukayi sallama, ta amsa tareda watsawa Afeeyah hararar wasa setaa ajiye jakarta akan gadotna tana cewa "Whats up my love?" "My dear, if u like call me Shahrukan but you must wash this plates" muka kwashe da dariya harda ita da tayi maganar Maman Minal tace "Ƙarshen love kenan ba, amma dai a mata haƙuri ta huta yanzu, kinga duk ta rigamu fita da safe" "Wlh Anty Zarah na you dey spoil dis girl, haba yarinya se gaye cinguli work she cannot do" Sururat ta cigaba da Mita, Afee ta rungumeta ta gefe tana dariya tace "Haba sisi na kinsan fa zan wanke yanzun haka wlh kaina ciwo yakeyi, we had a boring class and i still have one more to go" mtsw tayi ƙaramin tsaki danda gaske kan nata ciwo yake mata. Fuskarta Sururat ta nuna tausayawa kafin tace "Eyya, let me finish cooking then you eat and get some sleep you will fell better, sannu kinji". Afee ta wuce gaban gadona ita kuma taci gaba da hada Salad ɗin da takeyi, kayan jikita ta cire ta daura Zani harta zauna kuma kawai ta ɗauki Hijabi da Jakar kayan wankata da Bucket daya ta sauka ƙasa. A bathroom ɗin down floor tayi wanka ta ciko bucket da ruwa ta koma lokacin har Sururat ta gama abincinta zuba musu a babban Try kamar yanda suke ci yawanci idan kowa yana ɗakin yau su uku Badar na Kaduna tasan dai tana hanyar dawowa Ummi kuma se Five zata gama Lecture, Ruth tana kan gadonta duk yanda suke janta a jiki da nuna mata an zama ɗaya takan kama kanta musamman irin lokutan da suke cin abinci sedai ta ɗibi nata a plate daban amma ba zataci dasu ba. Tsaf suka cinye abincin data saka musu suna santi dan Sururat ba daga nan ba gurin iya girki, ta wuce wanka da sauri dan tana da aji ƙarfe biyu ita kuma Afee ta tattare gurin ta haɗe kwanukan dattin duka a bokiti ta sauka dasu ƙasa. Wata Mama da take kai munu ruwa da wanke wanken wasu lokutan n Ta bawa kwanukan na koma ɗaki. Maman Minal tace mata "Afee bari naje dakinsu Nnenna mu Ƙarasa Assignment ɗin nan" "Sannu Eng girls" ta faɗa tana hayewa gado. Tana ganin Ƙoƙarin Maman Minal wato Anty Zahra, Mechanical Engineering take aji biyar. Matar aure ce harda yaranta uku kuma da auran nata ta fara karatun lokacin tana da cikin fari gashi a shekara hudu tayi yaya uku kuma cikin luɗufin ubangiji bata taɓa samun carry over ba Allah ya taimaketa ya bata Miji me fahimta da son tayi karatun duk dashi ba dan boko bane hasalima iyakarsa secondary school amma be tauyeta ba kuma iyayensa sun bata gudummawa Yaranta uku duk a hannun uwar Mijin suke yanzu da sun shekara zata ce ta yaye su taji da karatunta suna can Kaduna ita kuma ya kama mata daki a Off K tun Level one ba kuma ya gajiya da kawo mata ziyara A final year din nan ne ta dawo cikin makaranta gaba daya da zama kuma a nan suka haɗu ɗaki ɗaya da ita sedai idan Mijin zezo ne zata buɗe ɗakinta na Off K ko idan matsalar rashin ruwa ko wuta ta faru a cikin makaranta zasu tafi can duka. Ita ce ta zama Kamar Babbar Yayarsu duk abinda taga zasuyi mara kyau zata tsawatar musu tsakani da Allah take zaune dasu shiyasa suke bata girma sosai. Bata san tayi bacci ba seda Ƙarar Alarm data saita ta manta wayar a saitin kanta ya tayar da ita, a firgice ƙiris ya rage ta faɗo daga gado. Ta ringa tsaki kamar wani ya aje mata wayar, ganin tsakin baze kai ta ba ta miqe. Duk sun fita se ita kaɗai ashe, a gurguje ta sake watsa ruwa saboda yanayin garin da akwai zafi tayi Alwala, Riga mara nauyi me spagetti hannu ta saka ta zame ribbon ɗin kanta, tafi kwana uku bata taje kan ba sedai ta saka hannu ta warwareshi dan bata son jan gashin ta koda kanta ne balle wani yaja mata shiyasa bata kitso ta kwantar sa gaban da bruah kafin ta saka Chantilly cap ta zura Jilbab kalar Maroon me duhu tun wanda Ahmad ya bata haɗuwarsu ta farko, Son Hijabin take kamar rai, dukda ya sake siya mata wasu har Number matar da takeyi wato *UMMU MAHEER 07061838488* Ta karɓa a gurinsa saboda duk wanda ya gani se yace yadin masa kyau a ina ta siya shine kawai Ahmad ya bata shawarar ta fara siyarwaq sosai kuma take cinikin Hijaban a cikin Campus. Ta kalli kanta a Mudubi, gani tayi tayi haske fau da yawa kamar wata Zabiya yau hakan yasa tayi saurin cire Hijabin ta lalubo wani Fari ta saka, Badar ta tsani Hijabin, na Anty Sauda ne da tayi Umarar Azumi dashi ta karbo duk sanda ta saka se Badar tayi tsaki tace "se kace fatalwa" ita kuma son Hijabin takeyi. A gurguje ta fita, tana shirin kulle Ƙofa Badar ta hawo saman da ubannin ledoji tana nishi, ta banka wa Afeeyah Harara ita kuma ta fashe da dariya saboda yanda ta rungumo kaya kamar irin haɗamammun Yaro boys da ba zasu bari wani ya samu ba mayafin tama a Ƙugu tayi ɗamara dashi. "Dole kiyi dariya mana tsabar rashin mutunchi ashe kina nayi kiran wayarki yafi sau nawa baki amsa ba" ta fada tana zube kayan a bakin ƙofar. Ta buɗe mata ƙofa tace "Wlh banji ba ina ta sauri karna makara me yasa baki ƙwalo mun kira daga ƙasa ba to se nazo na tayaki" "Na gama shan wahala tun daga Bakin Hostel se na tsaya wani jiran ki dallah gafara na wuce" ta faɗa tana tureta, Badar rigima, ta matsa mata ta shige ita kuma ta ajiye jakarta ta fara shigar mata da ledojin tana cewa "Sannu da hanya, da naji shiru na zata ma se gobe zaki dawo". Kayanta ta shiga cirewa tana cewa "Neman magana dai, kwana biyun ma kamar Momy zata cinyeni kinsan da yanda ta barni na kawo yau da cewa tayi jiya komai dare se na taho ai" "Allah sa ba tayi fushi ba da banje ba?" Afeeyah ta faɗa tana aje ledar ƙarshe se Badar ta zare ido tace "Ai gara da bakije ba, inaga da muna shiga zata ce mu juyo, ƙarshe ma gori na jawa kaina tana cewa ita so tayi ta haɗa mu dukka ta huta shegen baqin jinina yasa seta sake kashe kuɗin kama gurin biki daban harda fa cewa ƙawayenta wai idan sunji wani na neman mata gani". Afeeya ta dinga kyalkyala dariya har seda taazauna, wato Momyn su Badar character ce me zaman kanta matar nan ga kirki ga zafi babu abinda ya shalleta tas zata maka akan gaskiyarta. Seda ta gama dariyar ta miƙe tana ce mata "Toh na Jira ki ko na tafi?" "Ai ko HOD ne zeyi Aji yanzu dai ba zani ba wlh gara ma ki tafi kya samu ki mana Attendance" ta bata amsa tana zuba ruwa a bokiti Afeeya ta fita a ranta tana mamakin Yau batayi mata Ba'ar Farin Hijab ba ilai huwa se ji tayi tace "In kika mutu a hanya an huta nemo likafani kaiki kawai za'ayi". Minti Arba'in Lecturer yayi ya sallame su saboda duk kusan sunyi covering komai sati biyu ya rage musu su fara Exam. Surayya Mas'ud ta jata Ribadu Hall dan taga Babynta, ta haihu sati uku kenan yau ta fara shigowa Lecture ta bar yaron gurin sister ta acan suka shantake har akayi Magriba kafin suka fito tare Mijinta yazo daukarta ita kuma ta shiga Amina. Tun daga staircase ake jiyo kayaniyarsu Sururat da Badar haka suke kullum basa gajiya da magana kamar Aku ta shiga da sallama ashe video kayan Lefen Anty Yusra Yayar Badar suke kallo, dalilin zuwanta Kaduna kenan ta cire Hijabita ta ninke itama ta shiga kallon, Anty Yusra tasha kaya, ko da yake abu ne irin nasu na kwarya tabi Kwarya, Babansu Badar Ex Senator, zaben da ya gabata ya sauka Baban Angon ya karɓa. Suna kallon suna cin abunda Badar tazo musu dashi da suka gama ta koma kan gadonta ta kira Baffanta. Cikin shaƙuwar dake tsakaninsu suka gaisa, yace mata "Mamana ya makatanta ya karatun? Babu dai wata matsa ko?" Safe da yamma idan sukayi waya seya tambayeta haka, Yanda Baffanta yake sonta yasa take jin zata iya sadaukar da komai sabida shi. "Komai Lafiya Baffa, baka koma gida bane har yanzu naji ƙarar babura?" "Ban koma ba yanzu dai nake shirin tafiyar, kinga Yayanki ya turo miki kuɗi ko? Kiyi haquri da abinda ya samu abinda nake ta jira a biya ni ne har yanzu shiru lamarin ƙasar se Addu'a kuɗi sunyi wuya a hannun mutane ga Yayan naki shima komawarsa Makaranta ya tashi shiyasa nace ya raba wannan ya tura miki idan yaso in Allah ya yarda wasu suka samu se a sake aiko muku" "Babu komai Baffa sefa da nace maka ma ka barshi ina da komai kudin ma akwai canji a hannuna zasu isheni har zuwa sati hudun amma kaƙi yarda da ka barwa Yah Jafar ɗin duka yafini buƙata" ta faɗa cikin muryar shagwaɓa. Baffa yayi murmushi yace "Ba wani nan na sani ko baki da komai ba zaki faɗa ba ni kuma haƙƙi nane dole nayi miki fatana dai kiyi karatu dukda bani da haufi akanki amma ina sake jan kunnenki da ki tsare kanki ki kuma tsaya iya inda Allah ya ajiyeki karki ringa hangen wasu da suka fiki ko kiyi sha'awar abinda suke dashi rayuwa mataki ce wata rana idan da rabo se kiga kin kamo su". Ta haddace wannan kalamanna Baffa, shekara uku ke nan tunda taa shiga Jami'a kullum sukayi waya se yayi mata takararsu. A sanyaye tace "In sha Allahu Baffa ina kiyayewa kuma zanci gaba da kiyayewa" "Yauwa Mamana Allah yayi miki Albarka, ina Badariyya yau ban jiyo karaɗinta ba" Baffan ya sake fada nayi murmushi nace "Gata nan Baffa bata dade da dawowa daga Kaduna bama an kawo Lefen Yayarta jiya ɗazu ta dawo ta kawo mana kayan dadi" "Aiko naji zancen gurin Ummanku tace nan da wata biyu ne auranko? To Allah ya sanya Alkhairi yasa zamu ga lokaci in sha Allahu idan na samu dama nima zanje musu ɗaurin aure saboda kirkin mutanen da yanda suka riƙeki ba wanda zaka yanke zumunchi dasu bane kice ina gaisheta ina mata ya hanya" Kafin ma Afeeya tayi maganar Badar ta wafci wayar dan tunda ta kira sunanta ta miƙe. Ta gaisheshi ta ringa washe baki tana cewa Amin kafin ta miƙa mata wayar har sannan bakinta a buɗe, sukayi sallama yace ta gaida sauran yan ɗakinsu. "Muguwa da zaki mun buƙulun gwalagwalan addu'oin Baffa" ta faɗa bayan data kashe wayar. Zata bata amsa Anty Sauda ta kirata dan haka ta dakata ta ɗaga da sallama kafin ta shiga tsokanarta tana cewa "Amarya uwargidan Alhaji Ali, kin tare gaba kin tare baya" "Faɗi ki ƙara dagani babu wata" ta baya amsa ta tabbata tana can tana fari da ido irin yanda take duk sanda tayi mata kirarin. Dariya sukayi kafin na gaisheta ta amsa tana tambayata makaranta. "Ina Mutumina Mahfuz? Banji Gwarancinsa ba yau?" "Suna gida, nazo Marmara ne, bikin Ƙanwar Baban Aziza za'ayi wannan satin dan wulaƙanci basu kawo mun Anko ba se ɗazu shine na kawowa Umma kuma ranar Laraba za'a saka" "Tofa, seta zarga miki ko Bubu ce ai ina Umman har yanzu ba'a gyara wayarta ta bane?" "Me gyaran yace ya gama kuma Jafar ya koma makaranta ɗazu be karɓo mata ba, ina Badar?" Anty Sauda ta faɗa seta bawa Umma wayar tayi sallama da Hausarta da yau bata saisaita ba, Buzanci ya cinye harshen nata sama da shekaru Talatin da Baffan ya aurota ya kawota Nigeria amma Hausa ta gagara kama harshenta dakyau. Bayan sun gaisa da Umma itama ta sake mata jan kunne akan ta kula da kanta kafin tace na gaida Badar da sauran Roommates ta maidawa da Anty Sauda wayar. "Naji Umma tace kince se kunyi hutu zaki dawo, bikin Zuhran Umma Halima fa saura sati biyu, ba zaki zo ba?" cewar Anty Sauda. Afeeyah ta gyara kwanciya ta ce "Saura sati biyu mu fara Exam kinga satin bikin kenan zan mata addu'a daga nan Allah sanya Alkhairi" "Kedai dan bakwa shiri ne kawai amma nasan da Zainab ce ko jarabawar kike sekin zo ai" "Zainab kikace ai, Yah Zuhra kuwa ko ina Kano be zama lallai naje bikinta ba wlh" "Allah ya shiryeki da ruƙo Afeeya ke abu baya taɓa wucewa a gurinki ne wai?" Cewar Anty Sauda. Afeeya ta tunzura baki kamar tana gabanta tace "Ai wlh duk wanda ya ci mutunchin iyayena ko bayan shekara dubu bazan yafe masa ba balle mu'amalar arziƙi ta haɗani dashi" ta faɗa cikin jin zafin abinda Itama Zuhran tayi mata, faɗe ya haɗo su ta zageta tace mata dangin Sadaka Yallah, kuma ai ba ita ta zaga ba da Ummansu take tunda itace Buzuwa daman kuma kullum idan tsiyar Babarta Umma Halima ta tashi da haka take zagin Umman tasu dan basa shiri, tunda aka aurota bata sonta a yanda sukaji wai da Aminiyarta Baffa yake so tunda ya tafi fatauci Nijar can ya hadu da Ummansu a hannun Mahaifinta ya zauna shikenan daya dawo yace ya fasa auran Ƙawar Umma Halima wannan ya Ƙulla gaba tsakaninta da Ummansu har yau kuma dukda abin yayi sauƙi saboda girma da shekaru amma bata fasa rashin idan rashin mutunchinta ya motsa seta mata gorin cewar tunda aka aurota maimakon Baffa yayi gaba tsiyacewa yake wai yanda take fara tazo musu da farar Ƙafa. Sallama sukayi tana cire wayar daga kunnenta kiran Ahmad ya sake shigowa. Tun tana wayar takejin alamar wani kiran, ta yatsina fuska kafin ta ɗaga ita wlh ta manta ma shaf tace zata kirashi ɗazu. Kamar ko yaushe cikin taushi yayi mata sallama ta amsa tareda gaisheshi sannan tayi shiru. "Baki kirani kinji ya na sauka ba" ya faɗa a sanyaye, ta sauke ajiyar zuciya tana jin babu daɗi a ranta tace "Kayi haquri, bacci nayi, ina tashi kuma kasan na gaya maka ina da class ɗin yamma na dawo kuma ina ta zuci zucin na kiraka na manta wlh" "Kullum dai uzuri Fatima, Allah ya nunamun lokacin da zanyi matsayi a zuciyarki da zaki dena mantawa da al'amurana. To ya makarantar? Ya lecturer? Badar ta dawo?" Kunya ta kamata jin abinda yace kuma beyi fushi ba, tace "Lafiya lau, Badar gata nan ta dawo tun da yamma". "That's great, my regards to her, ki gaya mata idan dawo tare zamuzo da Bukar Babagana, friend ɗina da nake gaya miki surutunsu ɗaya". Ta guntse dariya tana kallon Badar kamar yanda ta tattara hankalinta akanta itama yanda kasan an bata ajiyarta in har auna waya da Ahmad ta ringa matsarta kenan seta tabbatar da batayi wani abun rashin kyautawa ba, ko bata faɗa masa maganar soyayya me daɗi ba dai to ba zata bari ta faɗi wadda zata bata masa rai ba. "Zan gaya mata, kace na tanadi earpiece Aku biyu zasu haɗu ranar bazamuji kunne ba" ta faɗa tana fashewa da dariyar dan ta kasa ruƙuwa. "Nidai babu ruwana bani na faɗa ba" cewar Ahmad shima yana dariya kafin ya sake cewa "Baki tambayeni Jafar ba, jirginsu ya tashi babu jimawa yanzun nan ma na koma Hotel room" "Ayya" ta faɗa a fili a zuciyarta kuwa tace "Da shi kaɗaine a jirgin Addu'a zanji ya kife kowa ya huta da baƙin halinsa ai" Ahmad yace "Ayya kawai zakice? Ba zaki masa fatan sauka lafiya ba jini nane fa Fatima". Kafinna tashi amsa wayar tayi din din alamar shigowar wani kiran, na cire daga kunnenta ta duba sunan Bestie ne yake yawo se ta maida ita kunne tana cewa "Amm, Umma tana kirana bari na amsa idan na gama zan kiraka" "Muyi sallama kawai dan nasan da wuya ki kira, in kuma Allah ya dorani akanki yau kin kira i will be more than happy dan ina so nayi magana dake sosai, i really missed you Fatimaa" yaja sunan nata. Ƙirjinta ya buga, bata so ya ringa wani langwabewa yana mata magana hakan ze saka ta iya narkewa na fara sonsa dan ita ɗin son soyayyane da ita kamar wata India. Yanda take hasaso Mijin da zasu zuba madarar ƙauna ne Sam Ahmad bezo da cikakkiyar suffar ba. Tana lissafin Namiji dogo me ƙirar ƙarfi a matsayin Sharukhan ɗinta, wanda ya iya tarairaya da kalaman soyayya masu saka jinin jiki ya tsaya, irin mazan nan da kallonsu kaɗai ze saka kaji zuciyarka ta motsa ko bashida sisi zata zauna dashi zata masa komai indai ze ringa kasheta da ƙauna yana dagata sama kamar yanda akeyi a India, ya ringa saɓarta kamar jaririya yana goyata Mafarkinta kenan na Abokin rayuwa. Ahmad nada dukka suffofin datake so ta bangaren iya soyayya da tarairaya uwa uba akwai canji a hannunsa burin yammatan zamani Yaro da kuɗi sedai a gurinta ya rasa wani kaso me muhimmanci wanda take nema. Ƙaramin ruwa gareshi, dukda ba gajere bane dan idan suka jera ya kereta dukda tana da tsaho amma rashin ƙibarsa yasa sam bashida kwarjini idan ka ganshi zaka zata befi irin shekara Ashirin da uku zuwa da biyar ba a hakan wai talatin yake. Da ace yana da Dan Jiki koda tsahonsa be kai yanda take so ba zata iya Manaji dashi ko dan tarin kirkinsa. Jinjirin samudawan da tayi gamo dashi yau ya faɗo mata a rai, seta zaro ido a ranta tace "Aa ba kamar wannan ba, ai idan ya samu mace ballata zeyi tas a rasa me ɗorata yayi girma da yawa". "Fatima" Ahmad ya kira sunanta da ƙarfi daya maidota daga duniyar wasiƙar jakin data tafi. "Inata magana kinyi shiru, lafiya kuwa?" Ya tambayeta seta diririce nace "Yi haquri network ɗin ne ya ɗauke banajinka" "To na jiraki ko nayi bacci?" Ya sake faɗa a sanyaye, kiran da Nurain yake ta dokowa kamar Wanda yazo karbar bashi yasa tayi saurin ce masa "Ka kwanta to zan tasheka to idan na gama dan akwai Assignment ɗin ma da zanyi idan na gama wayar" se yayi dan murmushi yace "Shikenan toh, ki gaida Badar" "Zataji" ta bashi amsa tana zare wayar daga kunnenta taji ya jefo mata da I lobiyu harda wani kiss me ƙara daya sa tsigar jikinta zuba, da sauri ta katse kiran tana sauke numfashi wayar Nurain ta sake shigowa ta daga a tsiwace tana cewa "Ni wai Nuraini bashin ko tara da kake faman kirana se kace zan gudu?" Yar banzar dariyarsa me kama data yara yayi kafin yace "Hey hey relax, dawa kike ta waya ma dai da farko na miki over ten missed calls kika ƙi dagawa?" "Toh ubana Hafizu Mu'azu" ta faɗa, ya sakeyin dariyar dake ƙular da ita yace "You are my ward, dole nasan duk wasu whereabouts dinki dan haka just tell me dawa kike waya ko yanzu na kira Baffa na gaya masa kina waya da daddare while ur mates are there in class reading" "Kai ai tutorial kakeyi a nan inda kake ko? Dan Allah barni haka meye kake ta kirana ma?" Ta dakatar da jan maganar sa dan se a kwana anayi. "I'm missing you ne kawai nace bari nazo naga Bestie na, har na shiga Geography na fito na manta yau kince ba zaki fita karatu" Nurain ya faɗa seta duro daga gado tana cewa "Awwn, dagaske kayi missing ɗina?" "Kinsan ba wasa nake ba, saboda ke na shigo school. Ina mutuniyata i missed her also ina white sit ku fito muyi hira mana". Kusada Badar ta zauna ta tureta tana jan tsaki tace "A nan kike rawar kai da ƙafa kan ƙananan yara da ba'a dena basu pocket money ba, saboda Nurain kika kashewa Ahmad waya, ji yanda kike wani lanƙwasa murya kina wani cewa you missed him but you can't talk to ur responsible boyfriend with affection Allah yasa ki gane idan kina da rabo tun kafin lokaci ya ƙure miki". Indai Mitar Badar ce sun haddace akan Ahmad, sonsa take kamar Ƙanin Momy koshi baya jin zafin abinda Fatima take masa kamar yanda Badar takeji. "Bata wayar" Nurain yace mata. Ta san ba zata karɓa ba dan haka ta sakata a speaker "Badar my love" ya faɗa ta harari wayar tana cewa "Don't call me that" "Haba my heart, kin san fa ina sonki kece dai kike mun wulaƙanci ni yanzu ma ke nake son gani nasan na kiraki zagina zakiyi shiyasa na kira wayar Bestie, taimaka ki fito naga chocolate face din nan taki ko na samu karatu ya zauna a kwakwalwata ga saƙonki ma na fito dashi yau". "Hummm, sedai ka yaudari wata badai ni ba marowacin kawai, aron baci ba ka bani abu amma ka hana" "Allah dagaske nake gashi nan yau na kawo miki" ya sake faɗa yana dariya, Badar tayi Ƙwafa kafin tace "Wlh idan ƙarya kake gaban Amina yayi mana kaɗan sedai a kaimu security office dan tsalle zanyi na falla maka mari" "Gara da kikace se kinyi tsalle, my love yi maza kizo zuciyata harta fara narkewa, i can't wait ta see you" ya sake faɗa ze kashewar tace "K dena murna se ka siya mana Mac dee da" "Ko Sambo kike so yanzu zan saka a gasa miki shi ur Highness, ai kinfi ƙarfin haka ya sake faɗa yana dariya itama dariyar tayi kafin ta kashe wayar tana cewa "Wanda besan Nurain ba ya cuceshi, shiyasa yammata suke neman kashe kansu akansa daɗin baki kamar me" Fatima na saka Brassiere dan na rigada tayi shirin kwanciya tace "Ai dan kinƙi ne amma kun dace da Nurain wlh kai da bansan ya zanyi ranar auranku ba my two besties oh my G" "Allah ya isa na, sa'an nawa? amma Afee kin rainani, koda yake baqin jinane ya jamun ta bakin Momy da ba zaki ce na auri Nurain ba" gaba daya suka kwashe da dariya Maman Minal tace "Kefa kike raina Nurain Badar amma ba yaro bane yanda kike tunani he is 28 i think dan naga Birth date dinsa ranar nan da muna cike wata takadda kuma fa ya fara karatu a waje kinsan rashin lafiyarsa tasa ya bari ya dawo gida and he started all over again sannan yanzu kina level 3 yana 5, sanda zaki gama yayi service harya kama aiki saboda kinsan ku Yayan manya aikine yake jiranku ku gama school ba ku zaku nemeshi ba. Kuma haɗinku zeyi daidai, naga kice Babanshi ma Abokin Dadynku ne to dan Allah me kuma kike jira tunda dai ya nuna dagaske yana sonki?Allah da zaki bashi chance he is a good guy zaki ji dadi". "Gaya mata dai Anty" Afeeyah ta faɗa tana mata gwalo ta harareta tace "Munafuka kyama faɗi gaskiya Maman Minal Ƙarya fa yake saboda mu fita ne dan yasan zan hanata shine fa yake mun wannan daɗin bakin ba har zuciyarsa yake faɗa ba". Sururat tace "Haa Mama Minal, that Nurain na good player oo, i know three of his babes a department namu and babu Wanda tasan yana kula wata fa can you Imagine?" "Thank you my sister ke kinsan gaskiya ai" Badar ta sake faɗa tana ficewa bata saurari Maman Minal dake cewa "Amma wlh ni munyi magana yace mun dagaske yana son Badar, kawai dai yasan ta rainashi shiyasa yake mayar da abin wasa". Fatima tabi bayanta tana cewa "Bakiji Anty Zahra na magana ba?" "Zan zageki Afee kuma na koma wlh" "Allah baki haƙuri ta zunnu" Afeeyan ta sake faɗa cikin tsokana. Nurain na ganin su ya taso ya nufi Badar kamar zeyu hugging nata yana cewa"Oyoyo my love" ta galla masa harara ya saka dariya yana cewa "Kai Badar kinci sunanki aradu, yanda aka fafata a yaƙin nan haka kike fata fata da mutane" seda ta murmusa. Suka zauna Abdul shiru shirun Abokinsa yace musu yana waving, sukayi waving back. Badar da take kar a fita se gashi sun shantake suna zuba zance akan movie daya sako mata a flash drive suka bar Afeeya da Abdul da idan ya fadi magana guda se yayi minti takwas be sake cewa komai ba sedai murmushi, irin marasa maganar nan ne har mamakin Abotar su akeyi da Nurain da ko bacci daƙyar idan bakinsa yana shiru, seda goma ta buga Afeeyah tace bacci takeji kafin suka tafi gurin Sambo karbo Macdee. Guda shida Badar ta ce a musu yan 300, Nurain ya buga tsallen albarka yace baze biya ba, ita kadai ze siyawa taya zataci Macdee shida? Sanin za'a kwata hakan yasa Afeeya fita da ATM ɗinta dan tasan hali tsaf se an gama saka musu ze iya guduwa ya barsu a gun gashi kuwa sunzo suna drama yace sedai ta aje huɗu kuɗin biyu ze biya ita dai ta bawa Sambo ya cire kuɗinsa yana dariyar lamarin Badar da Nurain, sedai basuje gurin ba amma kullum se sun siyar da hali. "Wadannan yan uwan naki kullum kukazo se sunyi Drama" Sambo ya faɗa, Afeeyah tayi dariya tace "saurayine me Mammaƙo da Budurwa me kwaɗayi" "Allah ya isa amma kin cucemu" suka haɗa baki gurin faɗa ita dai ta tsallake ta barsu, bata san ya suka ƙare ba dan har ta kwanta Badar ta shigo harda Ƙarin Kaza guda ɗaya da Can Exotic guda shida se L&Z one liter. Suka baje suna ci taji ƙarar text ta duba taga Alert 5k from Usman Bashir Yabo ta nunawa Badar tace "Saurayinki ne, kinsan dadin rantawa Bestie kuɗi harda extra ze biyaka" "Dan rainin hankali,, kawai shi se anyi surutu hankalinsa ze kwanta, da kuɗin fa a jikinsa har cash ya bani bari ma na tura masa kiga karna manta amma shine ze yarfamu akan Macdeen 1800 kuma ki biya ya wani maido miki da kuɗin yaron nan se a hankali". "Sonki yake shiyasa yake neman fitinarki" Maman Minal data dage akan zancen ta ta sake faɗa, Afeeyah tace "Allah ka nunamun wannan rana Nurain da Badar, bangon gidanku Adon Fire extinguisher zan muku saboda tsaro" duk suka saka dariya harda ita da suke tsokana. PAGE 10 Da wata irin kasala ta farka da Asuba sakamakon mafarkin data kwana tana yi. Ta kalli Badar dake masifar tun ɗazu take tashita amma ta mata banza. "Haba Badar ki barta mana" Maman Minal ta faɗa kafin taci gaba da cewa "Kin san dai Afeeya tana riga kowa tashi ko bata sallah se ta farka ta tashemu tunda kikaga yau ta makara se ki mata uzuri". Badar tayi tsaki tace "Idonta biyu fa tsabar iskancine idan ba zatayi sallar ba seta faɗa ai a barta" fuu taci gaba da juye ruwan zafin da take a bokiti. A kasalance Afeeyah ta yunƙura ta tashi zaune tana cewa "Zanyi mana", gabanta ya faɗi saboda yanda tajini a jiƙe, mafarkin da tayi ya shiga dawomata seta kalli Badar data zuba mata ido itama, kamar zatayi kuka amma ta kasa cewa komai. "Kar dai fa Aljanin darene yazo mata? Mutumin data haɗu dashi jiya kwana tayi tana mafarki dashi kuma ta tashi cikin wannan yanayin karfa da gaske Aljanine? kai Innalillahi taga ta kanta ita Afeeya ina ta kwaso Aljanu ta shiga uku" ta raya a zuciyata kafin ta sake yunƙurawa tana tattare rigarta a ranta ta Ƙudurce tana yin sallah zata kira Ummanta ta faɗa mata tun wuri, bata taɓa irin mafarkin ba se yau gara ta faɗa mata koma menene a tareshi tun kafin ya aureta ta shiga uku. Seda na sauka daga gadon ta kalli shimfiɗar stain ɗin jini da ta gani ya sakata sakin ƙaffaffar ajiyar zuciya saboda ganin wani abu daban ba yanda tayi tunani ba. Towel ta ɗauka ta wuce wanka da Ruwan Badar tana jin tana zaginta amma ban tanka ba. Seda ta kintsa kainta kafin ta cire bedsheet din ta kama inda ya baci ta wanke a baza daman yau zasu haɗa wanki, takwas saura suka fita class bayan sun karya har sannan kuma jikinta a sanyaye yake idan na tuna mafarkin jiyan se taji Zuciyarta ta buga kuma wani abun mamaki sukayi waya da Umma da Baffa amma ta kasa faɗa mata kamar yanda tayi niyya, abin ne da nauyi kawai Anty Sauda zata kira to ta faɗa mata. A Ajin ma bata da wani kuzari da kuzari Malamin da kansa seda ya tambayeta lafiya take tace kanta ne yake ciwo. Malamin na fita Class Rep ɗinsu ya tsallaka sit ɗin da suke, ta kwantar da kanta a kan Desk suka gaisa da Badar da Yusuf ta harari Sahid dan basa shiri kafin ya kalleta yace "Whitey (haka yan class ɗin suke kiranta ko Afee whitey saboda haskenta) I have been looking for you since yesterday" Ba tare data ɗago ba tace masa "Ya akayi?" Dan Sahid akwai dan banzan surutu shima da gulmar tsiya "Wani mutumi ne, I mean one guy asked me about you yesterday and i told him every detail i know har layinki na bashi, Afee you don do good catch i swear, from his looks gayen nan is Rich, his face looks familiar to me but i couldn't figure out inda na sanshi" Sahid ya fada. Badar ta harareshi tace "Haka ka iya kai dai ka zama kamar wani kawali kullum cikin haɗa yammata da Samari", hausar bata bawai yana jinta dakyau bane Banufe ne dan haka ya kalli Yusuf da suke tare yace "What is Kalali? Because i know Badariyya, when ever she speak big big Hausa word she is up to no good" dukda yanda nake jina amma seda nayi dariyar maganarsa Yusuf yace "Tana nufin you are a good match maker" "Ehen" Sahid din ya sake fada da alamar be yadda da abinda ya fada ba amma se ya maida hankali kaina yana cewa "He gave 100$" "Kaji daɗi" Afeeya ta faɗa tana miƙewa saboda cikinta daya hautsina, tsallakesu tayi ta fita da sauri can gurin fanfo tana zuwa ta shiga sheƙa Amai masu wucewa suna binta da sannu. Kamar ta kunno ciwo tana gama aman marata ta riƙe ita da bata Mp se gashi ta gagara tashi tsaye daga gurin seda Badar tazo ta ɗagata. "Muje Hostel kawai daman baki da lafiya amma kika fito?" ta faɗa suna tafiya a hankali. Yusuf ne ya kaisu har gaban Amina a motarsa kafin suje ta galabaita juye juye kawai take a cikin motar na azaba dakyar ta iya fita ai kuwa nan gurin Security ta kwanta tana kuka shaɓe shaɓe kamar wadda zata haihu, abinda bata sababa, bata taɓa experiencing ciwon Mara ba se lokacin shiyasa take jinsa wani sabon abu kamar zata maɗe. aka daka saboda ciwo. "Sannu Afeeya me yake damunta?" Anty Amina daya daga cikin matan security da mmsuke mutunchi dasu ta tambayi Badar, "Inaga zazzaɓi ne" Badar ta bata amsa Afeeya ta nuna musu mararta da hannu, cikin tausayawa Anty Aminan tace "Wayyo sannu, daure ku ƙara ciki se kisha ruwan zafi da pain relief, Allah ya kawo Afuwa" "Kuje kuyi aure yara kun zauna kuna fama da ciwo" Ɗaya matar ta ɓaro maganar, Badar ta Anty Amina suka kamata ganin an fara taruwa akana kallonta wasu na cewa Aljanu takeyi. A common room suka ajiyeta ta kasa zama kan kujera se a ƙasa ta kwanta tana cigaba da murƙususu, ashe haka Matan suke ji amma ta ringa cewa Bafar raguwa idan tana ciwon Mara yau gashi Allah ya kamata itama kamar fa an hura mata wuta takeji a gurin wannan abu da akwai Azaba. Ta fi awa a gurin kafin ciwon ya lafa mata lokacin har gashin kanta seda ya hargitse kamar wadda tayi naƙuda. A duddƙe ta ringa tafiya har sukaje ɗaki, duk wanda Badar ta gayawa abinda yake damunta se yayi dariya kafin ya mata sannu dan haka take musu. Sururat ta haɗa mata ruwa me zafi takai mun banɗaki kafin ta fito Badar ta haɗa mata shayi me kauri ta gyara mata gado, kamar wata sarauniya haka suke lelenta suna mata iskanci kuma, tasha Paracetamol ta kwanta bacci ya kwasheta wata Jalalar Mutumin ya sake diro mata a mafarki amma ba irin na daren jiya ba. Na daɗe sosai tana bacci har gurin qarfe biyun rana kafin ta farka ta ji daɗin jikinta se abinda ba'a rasa ba. Kamar me ciki ta seda ta sakeyin Amai kafin tayi tsarki da ruwa me dumi sosai ta canza pad ta koma ɗaki tana tafiya salaf salaf kamar waddata fito daga Labour room. "Abin nema ya samu" Ummi ta faɗa ta harareta kafin ta zauna kan Gadon Maman Minal tana cewa "Tun jiya Ummi daga zuwa Lecture baki kwana a nan ba?" "Bayan na fito daga lectures ne na hadu da Surayya shine kawai na bita City tunda yau banida lecture, yanzu ma motar bati na samu shiyasa na taho da wuri" Ummin ta bata amsa kan tabi Cousin ɗinta city gidan Antynta. Afeeya ta kalleta badan ta yarda Zaria City tasan baze wuce yawonta na banza ta tafi ba. Ummi bataji ko kadan, ta santa tare sue a English da zasu shiga Level 3 ɗin nan ta bari ta koma Library science saboda rashin mayar da hankali ana nema a koreta, party da clubbing a Zaria babu inda bata sani ba yanzun a hakan ma ta rage ne zama dasu suna matseta dole ta rage wasu abubuwan da wuya ta fita ta kwana a waje duk yawonta zata dawo Hostel. "Wlh gidan su Surayya naje idan ma baki yarda na kirata yanzu kiji da kunnenki" ta katsewa Afeeya shirun da tayi dason wanke kanta. Wayar Afeeya ta fara ringing akan gado ta ɗakkota tana cewa "To me kikaji nace Ummi? Duk ma abinda mutum yayi ai dan kansa me kyau ko mara kyau zaka tarar da sakamakonka me sonka ne yake damuwa da abinda kakeyi har yake so ka hau hanyar daidai". Ahmad ne yake kiran kafin ta answer ta ktase se lokacin taga missed call daya mata kafin wannan kiran. Wani kiran ya sake shigowa, ta ɗaga yana narke murya dan bata so wayar tayi nisa. "Fatima kin tashi? Ya jikin?" Ya faɗa cikin kulawa, ta kwanta tana cewa "Da sauƙi, ka kira aka ce ina bacci ne?" "No, dana kira baki ɗaga ba i called Badar ita ta gaya mun bakya jin dadi ta barki kina bacci i hope you are feeling better now? Kodai zakuje hospital ne kira Ilyas ya kaiku?" Ya sake tambayata a tausashe, a maimakon taji daɗin kulawar tasa ma haushi yake bata ya fiya sanyi da yawa ta muskuta tana cewa "Nafa samu sauƙi kuma nasha magani, Ilyas na zata ya bar Zaria ai" "No yana nan be samu sun canza masa din ba so kuma ma saura two months ya gama shiyasa ya haƙura" (cousin ɗinsa ne yaron sister Momy da yake Internship a Shika Asibiti). "Ayya Allah ya bada sa'a, ya kake? Abujan? Yaushe zaka dawo?" "Are you missing me?" Ya faɗa yana sakin murmushi najin daɗi yau Fatima ta tambayeshi wani abu daya shafeshi, kunya ta kamata tayi murmushin ita ma amma bata ce komai ba yaci gaba da cewa "Se Thursday In sha Allah, kina zumuɗin ki ganni ne?" "Uhm" kawai tace, cikin tsokana yace mata "Da gobe fa zan taho, sena haɗu da wata yar farar Yarinya me irin zubinki, ita take so ta riƙeni na kasa tahowa". Ba wani son sa take ba ba amma se da zuciyarta ta sosu da abinda ya faɗa kishi ya taso mata, a ƙufule tace "Kace kayi budurwa yar Abuja yar gidan masu kuɗi" yanda tayi maganar ita kantaseda ta idar ta fahimci muryar da tayi amfani da ita tayi kauri da yawa ta kuma bayyana kishin daya taso mata ƙarara. Dariya sosai Ahmad yayi tayi shiru kunya da takaicin kanta suka rufeta, seda yayi me isarsa kafin yace "Ashe dai Fatima na kishina haka? Gaskiya naji daɗi". Bata sake ce masa komai ba ya gama surutansa tana ji ganin ta ƙi bashi amsa yasa ya canza akalar maganar da cewa "Haka kawai Tuwo nake sha'awar ci da Miyar Kuka, kamar na tafi Kano yau ma nake ji" "Ikon Allah Tuwo kuma ka rasa wacce miya seta kuka?" Ta faɗa cikin mamaki dan zata iya cewa a matasa dai shine mutum na farko data taɓajin yana son Miyar kuka, Yah Malam dinsu cewa yayi ganyen bishiyar Aljanu ne tsaɓar hatsabibanci irin na mata suka mayar dashi abinci shiyasa duk me yawan cinsa kwakwalwarsa toshewa take saboda sharri. "Kuka dai da kika sani, ni ai idan kina so ki burgeni to ki bani abincin gargajiya amma fa with a touch of modernity bawai kuma ayi abu babu sha'awa ba, irinsu dambu, Akubus, Fate, Ɗanwake babu wanda bana ci kuma a kowanne lokaci zan iya ci be it safe, rana dare duk zan iya cinsu musamman idan an shiryashi ya dace da lokacin". Kai ta ɗaga kamar yana ganinta tace "Na gane" "Yawwa idan ma baki iya ba se ki koya dan ni babu ruwana da wasu continental dishes da kika ganni shiyasa ma kikaga nake daidaitan se Umma ta sauke abincin dare nake zuwa gidanku dan ba Ƙaramin daɗin girkinta nake ji ba kuma na ci na Anty Sauda ma naji yayi kalar na Umma Allah yasa kema haka kika iya girki" "Ina koya" ta bashi amsa a taƙaice tana janye wayar daga kunnenta, minti goma sha daya suna magana zan iya cewa basu taɓa kaiwa haka suna waya ba idan ma sunyi to befi sau a ƙirga ba. Kamar ya shiga ranta taji shima yana cewa "This is our longest phone call so far, bari na shigar dashi a Diary yau ɗin ta shiga tarihi". Ta yatsina fuska kamar yana ganinta kafin tayi magana cikin sauri taji yace "Ki huta Fatima, i will call you later Jafar yana kiran ɗaya wayana". Wani tuƙuƙin baƙin ciki ya taso mata dajin sunan wanda ya ambata. Ta tsani Jafar ɗin nan tsana me tsanani da bata san iyakarta ba. Bata ko amsa masa ba ta kashe wayar tqna jan mugun tsaki. Maman Minal da bataji shigowarta ba ta ce "Lafiya kike tsaki haka?" "Babu komai" ta bata amsa tana miƙewa saboda yunwa data faraji. Ta zuba taliyar data gani a tukunya ta hau ci ranta duk a dagule, ta kusan cinyewa Badar ta shigo da alama ta kwaso yunwa dan hannu kawai ta wanke ta dirarwa abincin da Afeeyan take ci seta tsame hannu ta bar mata dan daman ta ƙoshi gudun kar su mata masifar da suka saba idan ta rage abinci yasa take turawa daƙyar. "Jibi tuwo zamuci a ɗakin nan" Maman Minal data idar da sallah ta faɗa, Afeeya ta kalleta, Badar tace "Ai kuwa mun kwana biyu bamuyi tuwo ba. Bari rana ta lafa se muje cefane miyar me za'ayi?" "Kamar Kuka naji kince ko Afee?" Ta jefawa Afeeyah tambayar, zare manyan idonunta tayi tana kallonta da rashin fahimta dan bata gane inda maganarta ta dosa ba, ita yaushe sukayi zancen tuwo? Maman Minal Ta miƙe tana ninke sallaya tace "Zancen tuwo naji sunayi da Ahmad shine naji sha'awarsa nima kinga se ta mana Jibi idan zezo" "Kai Anty Zahra daga jin muna magana bafa cewa yayi yana so ba labari ne kawai ya kawo maganar ba cewa yayi na masa ba" tayi saurin defending kanta kafin su ƙallaba mata abinda bazata iya ba. Badar dake side hannu ta cafe tana cewa "Aiko yin tuwo Lazim idan ba so yake ba meze saka ya miki zancensa kawai dai be fito kai tsaye bane ke kuma in kinada lissafi ai kinsan me yake nufi Allah ya kaimu jibin dama bamu da Lectures kuma na shinkafa zaki mana Aradu ki tuƙeshi da kyau yasa malmala mu kwashi gara abinmu" "Aiko zaki ɗige indai ni zan tuƙa miki tuwo, shima ya nemi inda zeci tun dare be masa ba wlh" Cewar Afeeya, Badar ta hayayyaƙo mata tana cewa "Wlh se kinyi, ko mu ba zaki dafa mana ba se kin wa Ahmad banza wadda bata san Abin kirki ba. Ahmad ɗin nan kwanta miki kaɗai ya rage ya farayi amma hakan be saka yaci darajar mutunchi kema ki ringa mutuntashi ba kici gaba ubangiji ya miki ni'ima amma kina nema ki butulce masa in bakiyi wasa ba kika watsar da damarki ba fata na miki ba gaba se kinyi kuka da dana sanin rasa shi dan wlh a zamanin nan samun kamar Ahmad Namiji kyakykyawa, me kuɗi ga Ilimi da nutsuwa ga hankali kuma ya soki tsakani da Allah bawai da lalataba se an tona ai mazan dai gasu nan ke zaki bada labari dan babu kalar saurayin da bakiyi ba kowa kuma yazo iskanci yake kawoshi koda wanda ya tsaya bayan Ahmad din" Badar ta faɗa a hasale bacin ran ya nuna har kan fuskarta. Kallonta Afeeya tayi bayan data zauna akan gadonta, bata tanka mata ba ta maida kai kan wayarta tana duba number data kirata yanzu kafinkuma ta answer ta katse, ganin ta waje ce yasa ta ajiye wayar ta yuwu Kamfanine ko sacammer. Tana jin Badar na maganganu tayi mata banza dan idan ta tanka se ran kowa ya ɓaci. Badar tana yawan faɗa mata maganganun da bata jin daɗinsu akan Ahmad amma tanayi mata uzuri saboda tasan bada wata manufa take faɗarsu ba a ganinta damuwa da lamarinta nema har yasa take tada jijiyar wuya akan abinda ya shafeta amma kuma idan aka kalli maganar tata ta wata sigar tana nuna kamr Alfarma Ahmad yayi mata da har yake sonta wanda wannan yana daga cikin abubuwan da yasa bata sonsa. Bazata auri Mijin da ya zarce matsayinta ba wanda kowa ze ringa mata kallon cusa kanta tayi ko kuma Alfarma yayi mata daya aureta bata kai Ajinsa ba kamar yanda Ɗan uwansa ya faɗa mata. "Badar na gaya miki ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba idan kina son Ahmad na bar miki shi kuma zanyi duk iyawata gurin ganin kin same shi. Na sani ba tsarana bane, ire irenki ne m daidai dashi, matsayi da Arziqin iyayenku yayi kamanceceniya kinga babu me ganin cewar Alfarma yayi miki idan yayi tarayya dake" Afeeya ta faɗa zafafe tana barin ɗakin saboda gajiya da maganganun Badar dukda yanda Maman Minal da Ummi suke mata magana akan tayi shiru amma taƙi, dagaske neman fitinarta takeyi yau amma ba zata biye mata ba gara ta fita. "Saboda ina sonki na damu dake ina miki burin ki auri Mijin da yake sonki kiji daɗi shine kike gaya mun haka ko Afeeya?" Ta faɗa tana Ƙanƙancr ido. Fes Afeeyan ta kalleta tace "Kinji abinda na faɗa ai, Ahmad ne bana sonsa bazan aure shi ba kuma fatan da kike mun baze kamani ba Allah ze kawo mun Miji Talaka daidaini na aura wanda babu me saka mana ido ballantana a ringa fassara duk wani motsina akan sa da sunan na butulcewa ni'imar ubangiji". "Meye haka Afeeya?" Maman Minal ta dakatar da ita, ta kalleta da idonta da suka fara canza kala tace "To akan me Anty Zahra? Duk sanda magana zata haɗo akan Ahamd se Badar ta yimun gori a fakaice tace yafi ƙarfi na? ni na janyo shi nace ya soni ko yaya? Da yana da zuciya ma ai da bamu kai haka tare ba saboda na nuna masa bana muradinsa ta duk hanyar data dace amma ya nace ya kafe so takeyi na aureshi Alhalin danginsa basa ƙaunata? Ba'a a kunnenta ƙaninsa yayi mun cin mutunchi ya zagi iyayena sannan ta dage sena cusa kaina inda Allah be kaini ba saboda kwadayin abin duniya? Toni kudinsa ko wani matsayi nasa ba zasu rufe mun ido ba su sa na jefa rayuwata cikin ƙunci na rayu da mutanen da basa so na, idan tana sonsa gashi nan na bar mata ta aureshi itace daidaishi" ta ƙarasa tana Ƙoƙarin riƙe kukan daya taho mata amma ta kasa dole ta sakeshi ta doshi Ƙofa zata fita amma mutanen da suka tsatstsaya munafunci yasa ta fasa fitar ta shige bayan Ummi da ke zaune ta kasa cewa komai ta kwanta tana kuka. Maman Minal ta kulle Ƙofar jiki a sanyaye kafin ta zauna tana cewa "Daga zancen tuwo shikenan se tashin hankali? da alama sheɗan ya shigo ya laɓe a ɗakin nan shiya haɗa komai kuma bazeyi nasara ba in sha Allah". Badar da jikinta yayi sanyi laƙwas ta zauna daga tsayuwar da tayi ta kasa cigaba da masifar tata. Har ga Allah ita batayi magana da manufar da Afeeya ta ɗauka ba, ta riƙi Afeeyar a matsayin yar uwa shiyasa har take son cigabanta take kuma son ta da Ahmad ganin cewar mutumin kirkine ya na da duk wasu qualities da mace zata so a gurin Namiji gashi yana sonta baya ga haka wlh ita bata da wata manufa ta daban akan maganar. Dakin ya ɗauki shiru se shasheƙar kukan Afeeya, kowa da tunanin da take a ranta wayarta ta sake ɗaukar ƙara lambar dazun ce bacin ran da take ciki yasa ta kashe wayar gaba ɗaya ba tareda na amsa kiran ba. Ranar har dare dukkansu basu da walwala shiru ɗakin kamar anyi mutuwa, tsakaninta da Badar kuwa se kallo seda Baffa ya kira wayarta akan be samu ta Afeeyan ba sannan nema ta tuna data kashe wayar tata, data miƙa mata bata kar ɓa ba, ta kunna tata ta kirashi. Sururat ce ta saka su shirin dole cikin daren bayan ta dawo Ummi da Maman Minal suka tsara mata abinda ya faru ta ringa masifa ta kuma ɗorawa Afeeya laifi kacokan wannan yasa suma sauran suka buɗe baki tare da nuna cewar ita ce bata kyauta ba su da kyakykyawar niyya suke tare da ita kuma wannan tasa har suke son abinda suke ganin ze zamar mata Alkhairi ba wani abu ba. Bata so aja maganar da tsaho dan haka nace taji ta kuma bawa Badar haƙuri kamar yanda Sururat tayi insisting. "Wlh Afeeya ina jinki kamar Yah Yusra, idan har zan iya aure ko soyayya da Mijinta to zanyi da Ahmad. Son da yake miki da kamalarsa tasa har nake miki sha'awar auransa dan nasan irinsa basu da yawa a duniyar yanzu amma tunda har zuciyarki tana raya miki wani abu daban akan niyyata in sha Allahu zan kama kaina, bazan sake yi miki wata magana data shafeshi ko ma akan saurayi ba gaba ɗaya. Zanci gaba dayi miki Addu'a Allah ya zaɓa miki abinda yafi Alkhairi" Badar din ta faɗa bayan da Afeeya ta bata haƙurin, jikinta yayi sanyi ganin yanda idonta ke zubar kwalla sanda take maganar, ta tabbata har ranta gaskiya take faɗa kuma Badar na sonta kamar yanda ita ma take sonta amma abune yazo da rashin fahimta dukkan su kowa tana da dalilanta na so ko Ƙin tarayyata da Ahmad amma ta haɗiye nata za kuma ta cigaba da addu'a Allah ya fiddo mata da Mijinta daidai ita ya fiye mata sauƙi. Saboda ta tabbatar musu maganar ta wuce yasa washe gari suna gama Lectures tacewa Badar suje kasuwa ayi cefanen, ta kuwa ji daɗi sosai dan da sunta share juna amma daga zuwa kasuwar komai ya wuce aka dawo daidai Harda kayan zoɓo suka siyo, sesaga baya kuma Badar tace su siya Kunun Ayar Shinkafi kawai ba se anyi Zoɓon ba. "Bari na kira Salima Nasir ta zo manada snacks gobe se a hada masa ko?" Badar ta sake faɗa. Dole Afeeya ta amsa gudun karta ƙara laifi a gurin Badar data saki ranta dalilin za'ayiwa Ƙanin Dadynta girki. Sunyi markaɗen stwe a Kasuwa dan haka suna komawa suka ɗora girki suna hira kamar ba abinda ya faru jiya. Washe gari haka Afeeya ta tuƙa tuwon rabin kwano tayi miyar kukar da Ƙamshinta ya karaɗe duka block ɗinsu ya buwayi hancin kowa. A Set din food flask da suka ɗakko da safe a gidan Maman Minal ta saka masa tuwon Miyar aka barta a tukunya akan seya zo se a sake dumamawa a zuba a flask din. Kayan da zan saka ko Badar ta turarasu ya kai sau uku, jikinta har rawa yake idan Ahmad zezo musamman wannan karon, sunyi waya da Afeeya ya gaya mata be taso da wuri na ze kai zuwa uku kafin ya sauka dan haka zuwa biyu ta gama komai tayi wanka suka zauna suna ta labarai. Biyu da rabi ya kirata akan ya shigo zaria. "Na gaji da yawa ni nayi driving zan wuce nayi Lodging hotel idan na huta da Magriba sena shigo kuma bani kaɗai bane tare muke da mutumin Badar" ya faɗa mata. Har zatace masa toh ta tuna da Tuwon data gama shan wahalar tuƙawa hannayenta duk sun sage tafin se radadi yake mata Allah ma yasa kar nayi kanta. Da shagwabar da bata san tayi ba tace masa "Toh Abincin fa? Shima se da magribar zaka ci?" "Wane Abinci?" Ya tambayeta cikin rashin fahimta se sannan ta tuna da bata gaya masa tayi masa tuwon ba dan haka tace "Girki mukayi shine na ɗibar maka ko bazaka ciba?" "Nidin banza, gani nan yanzu kuwa zanzo na karba kamar kinsan yunwa nakeji ko breakfast banyi dakyau ba saboda dokin son ganinki" Guntun murmushi tayi kafin suka aje waya. Miyar aka sake ɗumamawa Maman Minal tayi masa zubi me kyau duk ta kwashe Albarkatun cikin miyar ta bar musu saura. Hijabi ta ɗakko cikin na *UMMU-MAHEER 07061838488)* wankakke gogagge ta ɗora akan doguwar rigar jikinta Badar ta kwaso Ashar ta watsamata ta haɗiye dan daman ta san se sunyi. "Tsabar iskanci in gama shan wahalar turara miki kaya ki wani kwashi Hijabi kamar me takaba ki saka" ta faɗa a fusace tana neman fizge hijabin. Maman Minal tace "Ki barta ai ze dawo anjima se tayi kwalliyar sannan". "Masifaffiyar banza kawai" Afeeya ta faɗa Ƙasa ƙasa. Sururat ce ta tayata ɗaukan Basket da suka zuba abincin. Kallon da bata so ya kafeta dashi tun daga corridor harta fita wajen hakan da yayi yasa hankulan mutane da yawa yayiwo kanta har suka Ƙarasa gabansa yana ta sakin murmushi kamar wani wawa. Kallonsa tayi taga ya sake zama wani dan tsurut musamman daya saka ƙananan kaya se taga ma har tsakiyar kansa tana kallo tsanar sharri, murmushi tayi itama ta shiga gaishe su shida Abokinsa da kana ganinsa kaga Kanuri. Wani Baƙi dashi hausar ma se a hankali se surutu kamar ya ƙone a kai. "Gaskiya Amaryarmu ba kalar rana bace, dan haka kodai ka nemi inuwa ku zauna ko kuma ka barta ta koma ciki an jima idan gari yayi sanyi seka dawo. Ni ganin basket ɗin nan ma gaba ɗaya ya sake tadomun da yunwa" Bukar ya faɗa ga surutu ga saurin baki. Kanta na ƙasa tana wasa da zoben hannunta duk kallon da Ahmda ya kafeta dashi ya takurata, "Bari muje Fatima anjima se na dawo bayan La'asar ko?" Ya faɗa cikin sigar tambaya ta ɗaga masa kai ta ce "Toh". Abokin ne ya karɓi basket ya saka a mota Ahmad ya bishi ya ɗakko wata leda me tambarin super market dinsa BECHI STORES ya miƙa mata ta karɓa ta ɗan rusuna tace "Nagode" "Tsarabarki ce, tukuicin girki kuma se naci naji Ɗanɗanon sa tukunna" Murmushi tayi, ya langwaɓe kai ya jingina da mota yace "Kamar karna tafi, kinyi kyau sosai Fatima Hijab suna miki kyau" Yaƙe kawai takeyi Abokinsa ya leƙo daga mota yace "Kodai na zuba na fara ci ne in ba yanzu zamu tafi ba?" "Kaga kun kwaso gajiya, kodan saboda dashi kuje Anjiman se ku dawo" ta faɗa, seya gyara tsayuwarsa yana cewa "Naga hannunki" Ƙirjinta ya buga, me ze gani a hannunta kuma? Amma haka ta daure ta miƙa masa hannun da daga wrist zuwa fingers ɗin ne a buɗe, "Masha Allah ya faɗa" kafin ya juya yana ɗaga mata hannu da cewar Se ta dawo ita ma ta ɗaga masa. Ta tsallaka ta shige hostel tana ta mamakin dalilin son ganin hannunta da yayi. Tuwo ta tarar suna ci ta wanke hannu ta zauna, tunda ta gama taso taci jarabar Badar ta hanata wai bakinta zeyi warin daddawa se kace idan ta wanke baze fita ba. Seda suka qoshi Ƙat kafin a zazzage ledar tsarabar. Wata Arniyar Turkish gown ce Material me sharashara Amma tana da landing Dark blue ce da flowers Yellow da fari da dan yarfin ja kadan. Irin design da ake sakawa roba a waist ta matse ta sama ƙasan kuma ya buɗe ce se mayafai Medium guda biyu plain da kana ganinsu kasan suma daga Turkey suke saboda samfurin jikinsu, takalmi loafers dark blue qafa daya se Wani kwali ƙarami na turarene babu suna a jiki hakan ya tabbatar mata da sabone basu luncher shi ba testing ya kawo mata kamar yanda ya saba tunda suka haɗu, Ahmad yanayin Designer perfumes kuma duk sanda sukayi sabon Turare kafin a fitar dashi seya kawo mata. Company haɗin guiwa ne da wasu Abokanansa da sukayi karatu tare a Paris Asalin kamfanin yake amma a Dubai suke operating. Tarkacen Chocolate na yan gayu birjik su su Badar suka ɗiba ragowar kayan ta watsa su a kan gado. Ahnad baya gajiyawa kullum cikin hidimta mata yake. Idan ya tashi siya mata kaya tamkar besan zafin kuɗi ba daidai da Slippers yanda yake saka Designer haka yake siya mata tun Baffa da Umma na faɗa har suka haƙura suka zuba masa ido kyautar Kuɗi ce dai Baffa ya dakatar shine yace idan an hanata karɓan kuɗi ai ba za'a hanata kaya ba dukda haka kuma idan zata koma school seya tura mata kuɗi masu nauyi sedai taji dirim. Shida saura Ahmad ya kirata akan sun fito suna hanyar Samaru, bisa takurawar Badar Ummi tayi mata light make up ta cakare cikin Atamfa dinkin fitted straight Bubu, bata kamata tsam ba haka bata yi buhu ba tabi shape dinta ko ina ya fita masha Allah abinka da dogowar Mace na ta juya Anty Zahra tace "Afee kinyi kyau, komai kika saka kyau yake miki". Badar ce tayi mata ɗauri me kyau daya dace da kwalliyarta Seda aka idar da sallar magriba kafin ta fita dan bayan ya isa kirata yace ze shiga central mosque yayi sallah tukunna. Bata cika fita babu Hijabi ba infai ba Abaya ta saka ko irin Bubu plain Gown ba a hakan babu kwalliya gajiya takeyi da idanun mutane balle yau datayi shigar Atamfa harda kwalliya a fuskarta ga ɗaurin gaban goshi wani irin kyau tayi me sanyi da ƙayatarwa ba Maza ba hatta matan dake kaikawo a waje Hostel binta suka ringayi da kallo duk seta jita a takure shoyasa tafi gane ta suturta kanta da Hijabi Ko Abaya. Yanda Ahmad ya saki baki yana yabon kyan da tayi ko har seda abin ya bata kunya ta sunkuyar dakai tana murmushi. Shi kaɗai ya dawo Abokin nasa wai ya shiga City, a nan Basket ball court suka zauna suna hirar duniya dan a itane take sakewa dashi suyi magana ko zancen Business dan tanada sha'awar kasuwanci sosai abinda ma zata ce ya a birgeta da Ahmad kenan Business mind set, a tsaye yake da ƙafafunsa kuma kullum cikin nuna mata amfanin neman na kai yakeyi. Yakan ce mata "Ina so naga matata tana sana'a badan bazan wadata ta da komai na rayuwa ba Aa sedan ni na yarda da ko wani zeyi mun abu ya zamana nima inada abuna wanda zan kalla nace da gumi na na sameshi". Seda aka kira yace ta kira su Badar su fita wannan daman constant ne duk sanda yazo seya fita dams yawo sun sha iska sunyi ciye ciye, tana kiranta minti goma suka fito duk a shirye harda Ruth suka zauna su huɗu a baya ita a gaba banda Maman Minal suka tafi Zaria Suya kamar yanda Badar tace can za'aje sunata hira da Ahmad har suka isa. Sunci kifi sun sha shayi sunyi take away kaza da Suya amma banda Afeeya da idanun da Ahmad ya kafeta dasu suka hanata sakat. Yau se take ganin kamar tasan wani bayan shi me irin idon, amma ta gaza tuna waye. PAGE 11 "Saura sati nawa kuyi hutu?" Ya tambayeta yana sake narkar da idanunsa a kanta. Ta lissafa a zuciyarta kafin tace "Four weeks i think" "Fatima" ya kira sunanta da sautin dake nuna muhimmancin maganar da zasuyi, ta gyara zamanta ta saci kallonsa yaci gaba da cewa "Shekara biyu kenan since i meat you. Banyi zaton zan ƙara wata shida ba daga ranar dana haɗu dake ba tare da kin zama matata ba amma se gashi har an tafi shekaru which kece kika jawo hakan, please Fatima, i will ask you again ki aureni, last week na je na samu Baffa akan ina so na turo magabatana yace na nemi Amincewarki tukunna, idan kin yarda ko yaushe na shirya na tura ayi magana. Bansan me kike jira ba, Fatima Aure baze hanaki ƙarasa karatunki ba tunda shine maganarki kullum ke kinfi so ki gama makaranta ni bazan hanaki karatu ba idan kin gama wannan kina so kici gaba wallahi ko a Nigera ko wata ƙasa ni zan tsaya miki har se ke da kanki kince karatun ya ishe ki tukunna kawai ki Amince mun ki bani dama na tura Iyayena ayi maganar auran mu saboda wlh Haƙuri na ya fara ƙarewa Aure nake so Fatima" Shiru tayi masa kuma kunyar kalamansa na ƙarshe ne ya assasa shirun wai Aure yake so, matso da kujerar sa yayi kusa da tata kamar ze haɗe su yana cewa "Talk to me Fatima bana son shirun nan naki menene matsalarki bayan maganar karatu? Idan da akwai wani abu daban let me know please" Kamar tace masa "shi ɗin ne bata ra'ayin aure se kuma ta canza maganar dan ko babu komai kirkin Ahmad ya wuce tayi masa irin wannan cin fuskar. Kora da hali dai ba wadda bata masa baa baya amma ya ƙifahimta to ya yake so tayi dan Allah? Gyara zama tayi ta dan ja baya saboda kusancin nasu yayi yawa kafin tace. "Nidai Ahmad nafi so na kammala karatuna tukunna in so samu harma nayi NYSC kafin nayi aure, sannan kana cewa muyi aure naci gaba da karatu na tayaya hakan zata faru bayan Matan gidanku bas karatu?" Buɗe ido yayi irin na mamaki ya kalleta kafin yace"Waya gaya miki haka?" "Haka naji a gari" ta bashi amsa tana sauke ido ta saboda yanda ya saka mata nasa, cikin taushi yace "Fatima abin harda sharri? A wane gatin kikaji? Waya ce miki matan gidanmu basa karatu? Matan Yayyena harda me Phd Matar Dr Hassan tana aiki Lecturer ce, inaga a cikin sauran babu wadda batada Degree, idan kuka Ƙannena kike nufi Aslamiyya da Hajiya Ƙarama Level 2 suke kowacce kuma Next two month aka saka ranar Auransu kowacce zata gama Karatun a gidan Mijinta ya za'ayi kice ba'a karatu a gidanmu kodan kinga Alhajin mu ba Ɗan Boko bane?" "Ni bance haka ba, to inaga qadda ta gaya munce bata ji daidai ba" ta faɗa cikin kare kai shaci faɗi kawai tayi seta daki garwa. Ya saki murmushi yace "You know nothing about my family kar kuma kice zakiyi judging da abinda kike ji a bakin mutane. Babu wata mace da aka taɓa aurowa a gidanmu akace ba zatayi karatu ko aiki ba, duk wadda kikaga bata aiki bata da ra'ayi ne, amma dai ni in particular bazan yi miki ƙarya ba tun yanzu ki sani idan har Allah ya sa ka munyi aure babu maganar aiki ba zakiyi ba. Ba zan yarda Matata ta ringa yawo a gari da sunan aiki a Ƙarƙashin wasu ƙatti ba. Business dai wannan idan zakiyi zan baki jari daga naira ɗya har zuwa Miliyan ɗari ya danganta da abinda zaki siyar amma ban miki ƙaryar zakiyi aiki ba" ya faɗa da iyakar gaskiyarsa. Duk yanda yaso ya sha kanta akan ta bashi dama ya tura, ya yarda aje ayi magana idan yaso a saka rana sanda zata gama Makarantar idan haka ne burinta amma ta tubure ita ba haka ba. Cikin yanayin dayake nuna ransa ya ɓaci da rashin samun amincewar tata ya maidasu Makaranta, be tsaya ba yace mata Bukar ze maido mata da Flask gobe be taho dasu ba shi Asubanci zeyi ya wuce Kano. "Idan yazo Badar ce zata karɓo ba keba" ya faɗa da sigar umarni. Cikin wasa Badar ta ɓata fuska tace "Wato ni mara galihu tunda bani da tsayaye ko" "Kika sani ko ya zama tsayayyen?" Ya tsokaneta. Bundle ɗin 1k ya bawa Badar yace "Tukuicin Tuwo, yayi daɗi da alama ke kikayi" "Afeeya ce wlh" ta faɗa bayan data dafe kuɗin, ya juya mota yana cewa "Idan ta amine da muradi ma zan haɗa na bata tukuicin a tare" yaja ya tafi babu wata profer sallama da suka sabayi. "Alamu sun nuna kin kwafsa Afeeyah,wai dan girman Allah se yaushe Ahnad zezo Zaria ya koma da farin cikinki ne?" Badar ta faɗa suna shiga Hostel. "Hmmm" ta bata amsa dan ita da kanta taji rashin daɗin yanayin daya tafi, duk shanye fushinsa yau seda fuskarsa ta nuna, amma ya zatayi toh? A rabon Maman Minal ta yafita mata Kaza taci dan da Badar rantsewa tayi ba zataci ba tunda bata da mutunchi. Harta kwanta wayarta ta fara Ƙara, International number ce, kwana uku kenan ana kiranta da ita kullum kuma ko ta tsinke kafin ta ansa ko kuma taga miss call ita kuma ta san bata da wani a Ƙasar waje da ze kirata shi yasa bata taɓa bin baya ba ta yuwu ma scammers ne. Ta amsa wayar ta saka a kunne ba tareda tayi magana ba, kusan minti guda ita shiru haka wanda ya kira shima beyi magana ba daga can ƙasa dai tana jiyo maganganu alamar yana kusada inda ake hayaniya. Suka ci minti uku, harta yanke shawarar kashe qayar dan ba zata fara magana ba ta yuwu wand aaka ce suna tsotse jinin mutane ta waya ne suna jira tayi magana su gama da ita, harta zareta daga kunne taji wani sauti daya saka zuciyarta tsayaqa na wasu seconds kafin taci gaba da aiki "AFEEEYAAAAHHH!" Yaja sunanta, bata iya amsawa ba se sunayen Allah da take maimaitawa a ranta Ƙirjinta na lugude. "Afeeya!" Me kiran ya sake maimaitawa, bugun Ƙirjinta ya tsananta zufa ta fara tsassafo mata haka numfashinta ya shiga yi kamar ze tsaya tamkar wadda take cikin matsanancin tsoro kuma kamar wadda aka kafe ta kasa cire wayar daga kunnenta se kokawa take da numfashinta dake barazanar tafiya hutu saboda tasirin da muryar wanda batasan ko waye ba yayi a kanta. Bata taɓa katari da Bakin daya iya furta sunanta, ya bawa kowanne harafi haƙƙinsa kamar me waƙa. "Afuwan, Assalamu alaikum" ya sake faɗa cikin wani sauti me haɗe da irin ƙaramar dariyar nan, take ta kware da yawun bakinta ta shiga tari tul tul Ummi data fi kusa da ita ta miƙa mata ruwa tasha tana maida numfashi har sannan kuma be kashe wayar ba, kwakwalwata ta ayyano mata me wannan muryar, sallamar da yanayin da yayinta ya tuna mata da jinjirin Samudawan da tayi gamo dashi ranar Monday. "Sannu, badai loman abinci kikeyi ya Ƙwarar dake ba?" Ya sake tambayeta se kawai taji bakinta ya saki tsaki kafin ta zare wayar ta kasheta tareda ajiwa batama lura da yanda yan ɗakin sukayi shiru tareda zuba mata ido ba se sannan. "Afeeya meya faru? Kinga fuskarki kuwa se kace wadda Fulanin Daji suka kira?" Maman Minal ta faɗa, ta shafa fuskar da hannu, Badar tace "Meya tsorataki? Kin kara waya a kunne kusan minti goma bamuji kince komai ba lafiya ko wani abun ne ya faru?" "Uhm" kawai tace ta miƙe tareda ɗaukar ɗankwalinta ta fita ba tareda ta amsa tambayar ba har sannan kuma zuciyarta bata bar bugawa ba kamar yanda jikinta yake rawa. Last floor ta haye ta tsaya tana kallon 90s mutane nata karaina surutu duk ya cika gurin, tunani takeyi shi ɗin ne ko ba shi ba? Idan shine a ina ya samu number ta sannan kiran me yake mata? Zancen Sahid dayace ya bawa wani number ta ya faɗo mata to ko shi yake nufi a gurinsa ya samu number wayata tunda ta faɗa mata sunanta daman? "Afeee" aka Ƙwala mata kira daga Ƙasa, tayi firgigit daga tunanin da take ta kalli inda taji sautin na tasowa tsabar wulaƙanci Nurain ne yake kwala mata kira daga cikin 90s, bata amsa ba ta harareshi ya ɗago mata Kwalin popcorn yana cewa "Kinyi kyau, zaki ci popcorn?" Still da Ƙarfi yayi maganar abinda ya janyo hankulan waɗanda ke kusa dashi suka kalli gurin dan ganin dawa yake tana ganin haka tayi saurin sauka ta koma Floor ɗinsu dukda haka tana hango su se shegiyar dariyarsa yakeyi tana shiga Badar tace "Cin kan Bestin naki ya motsa yau" "Ke kuma sweetynki ba" tabata amsa tana Ƙoƙarin cire rigar jikinta wayarta ta shiga ringing, data Badar a tare ta ɗaga ganin Ahmad ke kira bayan ta haye kan gado, hira suka shigayi ya saki kamar bashi ya tafi fuska babu walwala ba, Bashi da ruƙo, yana daga cikin kyawawan halayensa se santin kwalliyarta yakeyi har yana cewa saura ƙiris yayi abin kunya next time karta sake saka Red Lipstick idan zata masa kwalliya har se ta zama matarsa. Sedata kashe wayar ta kura Badar ta fita Ruth tace mata sun fita da Ummi Nurain ne ya kirata "Gulma, ana so ana kaiwa kasuwa" ta faɗa,daga nan ta gyara kwanciyarta ta bhau WhatsApp. Lambar Basamude ta gani a farko yayi mata magana "Why did you hang my call and you hissed at me? Not even in your dream you try that again" Ta maimaita saƙonbabu Adadi Mamaki ya kasheta, a fili tace "Ikon Allah, ji wata magana kamar wani uban mutane, wannan yana da lafiya kuwa?" a maimakon ta amsa se ta shiga profile ɗinsa, Hoton Jessy ne akai ta Yan Ball kalar Red da white no 9 an rubuta *JAY* a jiki, batasan ko ta wanne club bace ba abinda ta sani dangane da yan Ball. Tayi tsaki na fita daga chat ɗin tana jinjina Ƙarfin halinsa, status ta fara kallo kira ya shigo video call tayi rejecting wannan mutum ko maye ne ai se haka wannan Naci har ina? Be haƙura ba ya sake kiranta voice call ta sake rejecting, seda ya kira sau uku ana huɗun ta amsa tun kafin tayi magana yace "Wallahi Afeeya, if reject my call again I'm going to deal with you" "Malam kanka guda kuwa? Who are you? Are you suppose to tell me what to do or what?" Ta bashi amsa a haslae jin abin nasa ze zarce ganga da makaɗi. Tana ji yaja numfashi kafin ya sassauta murya yace "Baki san abinda nake ji a zuciyana bane, 3 days i have been calling but you are not answering, na sameki yau and you hanged on me haba Afee bakida tausayi ne?" "Don't call me that again" ta faɗa jinyanda Afee daya kirata ya saka tsikar jikinta zuba, Tanaji yayi wani mayaudarin murmushi yace "*AFEEYAH* God i love the name, gaskiya Dadynki ya kyauta daya saka miki suna me daɗi da Ma'ana, idan munyi aure nima zaki haifarmun tawa Little Cute Afeeya like you ko?" "Qit" takashe wayar,, koda wanda ta sani bata wannan zancen shirmen ballantana da stranger wanda bata san mutum bane ko Aljan. Seda ta kashe Data ta saka wayar a Silent kamar yanda takeyi idan zata kwanta kafin tayi addu'a ta rufe idonta amma bacci yace be san zance ba, dakyar da taimakon Allah ya saceata. Kwana tayi tana mafarkin mutumin wai suna tafiya akan Gajimaren suna tsinkar furen soyayya. Da Asuba ta samu tsarki tayi wanka tana Azkar Ahmad ya kirata suka gaisa ya gaya mata yanzu ze tafi Kano. "Da wurwuri haka?" Ta tambayeshi, tana ji yana warming mota yace "Alhaji ne ya kirani zan takashi Hadeja Ɗaurin Aure kinga dole na tafi da wurwuri karna ɓata masa lokaci" "Haka ne, Allah ya tsare hanya ya kaika lafiya" tayi masa Addu'a ya amsa da "Amin" kafin sukayi sallama ta kashe wayar ta juya da niyyar maida kai taui bacci aka sake kiranta. "Jarabar duniya" ta furta a fili ganin me kiran da farar Asubar nan se kace wanda yake binta bashi ze fara kira wannan wane irin mutum ne mara lissafi ta shiga mita a ranta amma hakan besa taƙi amsa wayar ba dan harga Allah can ƙasan ranta har wani daɗi taji daya kira. Cikin dakakkiyar muryarsa ta Maza irin wadda zakaji kamar har echo tke yi yayi mata sallama ta amsa tana jin wani sabon yanayi yana mamayarta. "Jiya kika kashe waya kuma bayan nace bana so, kuma nayita kira baki amsa ba why?" ya faɗa a tausashe kamar bacci be gama sakin muryarsa ba hakan ya sa muryar tayi wani amo na daban me tsinka jini, numfashi taja ta fesar amma batace komai ba yaci gaba da magana yana cewa "Bana so, don't you ever hang on me again gara ki gayamun ni na kashe wayana da kaina if you don't want to talk to me, raini ne wannan kuma bana so". Ta shagala da sauraron Muryarsa se kuna ta zabura tace "Wai kai a matsayinka nawa ne da zaka ringa kafa mun sharaɗi?" "Ina son tsiwa, amma bana son rashin kunya, idan kika ci gaba sena fasa miki baki, then i will keep kissing it har se ciwon ya warke" ya bata amsa seta hangame baki ta kasa cewa komai, baccin da take tattalawa ya kama gabansa. "Afeeyah, i hate it when someone hisses at me, karki sake" ya sake cewa "Waye kai?" Ta samu kanta da tambaya dan wannan gadarar tasa ta shallake ta masu hankali kuma, "I will call you by 10am, kina free?" Be bata amsar tata tambayar ba ya jefa mata tasa Ta wurga ido kamar yana gabanta kafin tace "No, i have class by that time" "2pm?" Ya sake faɗa se ta karkace tace "That will be my resting time" "In the evening?" Be haƙura ba ya sake tambaya ba kai tsaye tace masa "Kasan me, ina da lokaci amma ba naka bane so you better respect your self and stop calling me talk less of Bossing around kana wani gayawa mutum abunda zeyi da wanda ba zeyi ba" "Idan na kira karki daga kinji" ya faɗa yanda kasan wani Baffanta kafin kuma tace wani abu ya kashe wayarsa ya barta da baki a gantale. "Afee don do new catch" Sururat ta faɗa teasingly, takaicin daya cikata ya sa bata tanka mata ba tana jin Badar na cewa "Tun jiya take wata waya kamar ta munafukai koma wanene yayi ta kansa wlh dan ina gani babu wanda ya isa yayiwa Ahmad over taking". Kwanciya tayi cike da jin haushin kanta da biyewa mutumin har ya samu damar raina mata hankali. "Amma ya haɗu, haka take son tsayayyen namiji, ta tabbayar da Ahmad ne sedai yayita lallaɓata yana cewa tayi haƙuri". AHMAD Ƙrfe Tara da mintina ya isa Kano dalilin Hold up daya samu a Kwanar Ɗangora wata babbar Mota ta faɗi a tsakiyar Titi wannan ya kawo cin koson ababen hawa a titin dan se zagaye suka ringayi suka kaucewa inda hanyar ta rufe ma. A Ƙofar Katafaren Get ɗin gidan Alhaji Audu Bechi ya tsaya yana danna Horn, Issa ya tsallako da gudu daga gidan dake kallon nasu inda suke zaune da sauran masu gadin gidajen layin ciki. girmamawa yake masa sannu da zuwa "Yi sauri Issa, na makara Alhaji yana jirana" ya faɗa ganin Issan ya tsaya ɓata masa lokaci da gaisuwa da sannu da zuwa hakan yasa ya wangale masa Get ya shiga. Cikin Rumfunan da aka tanada domin Ajiye mota yayi parking, motoci ne birjik a gurin yanda kasan kamfanin saidasu, cike da murna ma'aikatan dake kaikawo a Kantamemen compound ɗin suka nufeshi suna masa maraba, duk saurin da yake haka ya tsaya yana basu hannu, babu kyama balle nuna banbancin kasancewar Barorin gidansu ne su yake mu'amalantarsu wannan Ɗabi'a tasa ta karrama Ɗan Adam yasa yake da farin jini matuƙa gurin mutane. Junaidu daya daga cikin masu kula da shara ya ɗaukar masa Ƙaramar Akwatin da kayansa suke ciki, har ya nufi bangarensu na Mazan gidan yayi burki ya juya zuwa ainihin cikin gidan. Da sallama ya shiga tsakar gidan shiru babu kowa kai tsaye ya doshi Falon Momy, ya kai tsakiya ya tsinkayi muryar Hajiya a bayansa tana cewa "Aa, su uban Bilki an dawo kenan?" (Baba Bilki tana kiransa Babanta saboda Tace Asalin sunan Tijjani Amadu ne dan haka da Babangida da Ahmad duk sunan Malam Babansu sukaci shine Hajiya ta samu idan iskancinta ya tashi take ce masa Uban Bilki) Jiya Ɗan uwanka yake cewa kace masa zaka daɗe a Habujan se gaka kuma da Sassafe lafiya dai ko?" Birki yaci yana cije lebensa, ya tsani sunan nan data ke kiransa kuma a duk sanda tayi hakan tana nufin zagin Baba Bilki ne ta yuwu sunyi hatsaniya shine zata fake da haka ta zageta da alama kuma yau da ɓurɓushin mutunchi tunda har ta kira Jafar da Ɗan uwansa Seda ya daidaita fuskarsa kafin ya waiwaya ya kalleta, babu yabo babu fallasa ya durƙusahar ƙasa kamar yanda yake gaida Mahaifiyarsa yace "Hajiya Ina kwana?" Tana ƙara matsowa ta amsa masa da lafiya tana sake maimaita tambayar dalilin dawowarsa da safiyar nan da be bata amsa ba. Ƙatuwar Robar hannunta ya kalla ya girgiza kai, Nama ne shaƙe a ciki yau Juma'a da alama tayi halin, zuwa take ta zaftare naman Abincin sadaka da akeyi duk ranar Juma'ar, tun suna yara haka Hajiyan takeyi ko ran girkinta ko ba nata ba se taje ta kwashe Naman kuma babu wanda ya isa yace dan me hatta kuwa da me bada kuɗin Naman wato Alhajin gidan. Gaba yayi yana ce mata "Wlh Alhaji ne yayi mun kiran gaggawa zan rakashi Hadeja, yanzu ma sauri nakeyi nasan ya shirya ni yake jira". Ya lura da yanda murmushin kan fuskarta ya ɓace ɓat kamar ɗaukewar wutar Nepa hakan kuma nada nasabada jin cewar Alhaji ne ya kirashi. Wucewa yayi ya barta nan a tsaye, Da sallama ya shiga falon Mony wanda ya tarar da Ƙofar a buɗe, Momy na zaune a ƙasa tareda ƙanwarta Anty Maimuna da bata fi minti Goma sha biyar itama da shigowa Kanon ba daga Katsina inda take aure suna karyawa Ahmad ya shiga. Seda ya cire takalminsa sau ciki a baqin wajen kafin ya shiga yana sake nanata sallamarsa Momy da Anty Maimuna suka ɗago a tare kowacce fuskarta washe suna amsa masa ya zube a gabansu yana kallon Antyn nasa dake masa oyoyo kamar wani ɗan yaro yayi dariya yace "Anty saukar yanzu ko nan kika kwana? Koda yake munyi waya da Momy dazun bata ce mun kina nan ba kenan yanzu kika zo". "Zuwana " kenan Amadi ban daɗe ba, kayan lefe nazo haɗawa ƙnin Baban Sayyid nayi waya da shagon da zan siyi kayan basu fito ba shiyasa nayo nan na karya tukunna" ta bashi amsa seya ƙara washe baki yana gaisheta tareda tambayar Yaranta tace duk suna gida suna gaishesu kafin ya juya ya fuskanci Momy da murmushin kan fuskarta ya gagara gushewa saboda farin cikin ganinsa. Cikeda tsantsar ladabi ya gaisheta ta amsa tana tura masa plate din gabanta tace "Nasan baka karya ba" "Kai Momy, so kike Alhaji yamun faɗa kenan ƙarfe tara fa yace zamu tafi gashi yanzu goma ake magana" ya faɗa yana miƙewa tsaye, Momy ta goge hannunta da tissue tana cewa "Dana ji shiru ma na zata har ka shigo kun tafi dan tun ɗazun dana kai masa abin kari naji kuna waya yace ka kusa gida da ai da Takwaran Alƙali zasu je ban san ya akayi tafiyar ta juyo kanka ba" "Haba dai, kina da rai na taho daga wani gari na shigo har cikin gidan nan na fita ba tareda nazo na ganki kin saka mun Albarka ba ai ko bakida rai na shigo na kalli ɗakinki nayi miki Addu'a Momy" Ahmad ya faɗa, wani murmushi me nuna irin Alfaharin da Momyn keyi da kasancewar sa ɗanta tayi kafin ta miƙe tana cewa "Ka hanzarta dan nasan yaji shigowarka karka ja yayi maka suruti" seya rusuna a gabanta yana cewa "Zan fita" "To Ɗan Albarka, Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya Allah kuma ya tsare ku daga sharrin ƙarfe" Momyn ta faɗa tana dafa kansa kamar ƙaramin yaro ya miƙe yana murmushi yacewa Anty Maimunan ya tafi itama tayi masa Addu'a kafin ya zura takalmin sa rabi ya fita da sauri jin agogo yana buga goma. Anty Maimuna ta rakashi da murmushi kafin ta kalli Momy tace "Allah kenan, idan ya baka dubu masu bata maka se ya baka ɗaya da ze wanke maka takaicin duka dubun nan. Yanzu ki gani har qofar dakin nan Salim yazo keda kika haifeshi baki isa ya leƙo yace ya kika tashi ba balleni baƙuwa zuwan yanzu kuma ba kunya ya karɓi abinci yayi tafiyarsa. Momy ta kai zaune tana cewa "Ai Maimuna Al'amarin Salim a kullum maimakon yayi sauƙi ƙara ta'azzara yakeyi. Ba Salim kadai ba ni yanzu Yayansu shi yafi damuna, ace mutum beyi shashanci ba da ƙuruciya se yanzu daya fara tara iyali? Kuma wannan ƙallababbiyar sabgar siyasar da ya shiga ita take neman canza masa alƙibla, daman ni sam abin be kwanta mun ba. Tunda ya fara yake sakani magana, kullum matarsa na hanyar kawo ƙararsa. Yanzu shekaran Jiya seda sukazo sulhu da saboda tsabar wulaƙanci Yaron nan wai wancan satin ya kawo mata wasu ɗirka ɗirkan yayan Ƙabilu gida wai Yawon Campaign suka zo basu da masauki duk Hotel da suke Kano bega inda ze kama musu ba se gidansa yace ahine ta zo nan take gaya mun na kirashi nayi masa tatas ya sallamesu be daddaraba shekaran jiyan sega wata ya sake kaiwa wai sati ma zatayi a gidan shi zasu tafi Abuja dan haka zata zauna a gidan har ya dawo data kira waya ta gaya mun na sanarwa ubansa bece komai ba, se Alƙali na kira na gaya masa shi kuma ya kirashi sukaje can aka kashe maganar to Allah yasa dai yaji, Haba Yanda kika san su kaɗai ne Yaya a gidan nan kullum cikin sakani magana da ɗakko mun zance suke Salim da Babana na rasa yanda zanyi dasu". "Hmmm, Anty Aisha kenan, ai bazangaji da gaya miki ba kin tafka kuskure a baya kuma sakamakon sa kike girba a yanzu. Sufa Yaya kiwo ne Allah ya bamu, ba kuma iyakar wanda ka haifa daga cikinka sune naka ba, Malamai fa suna cewa ranar Lahira hatta akan gidan auranmu da zamantakewar mu se anyi mana Hisabi kinga kenan dole mu yi iyakar iyawarmu gurin ganin mun sauke duk wasu nauyi daya rataya akanmu shine kuma ya haɗa da kula da tarbiyyar yayanmu da duk wand suke zagaye damu. Kinga waɗannan yaran da kika ringa zuba ido ana cutarwa? Rayuwarsu ta ringa gantafalfala alhalin kinada halin taimaka musu ki kwatar musu yancinsu ta yanda koda basu samu dukkan gata ba zasu samu rangwamen halin da suke ciki amma kika naɗe hannu da sunan ba ruwanki baki shiga abinda ba'a sanyaki ba wlh ko kaffara bazanyi ba harda haƙƙinsu cikin abinda ya saka kika gaza ganin daidai a cikin taki zuri'ar. Kuma irin tarbiyyar da kika bari aka ginasu akanta ita naki yayan da suka tashi suka ɗauka, abinda da yawa muke kasa ganewa kenan a duk sanda kaga Ɗan wani musamman na kishiya yana abinda be kamata ba kar kace babu ruwanka ko bazaka tsawatar masa ba domin ze cuɗanya da naki Yayan, duk bakin tarbiyyar da kika haƙiƙance kina yi musu kuwa kina can ba zaki san lokacin da zasu ɗauki halaye marasa kyau ɗin da kika bari suka ci gaba ba. Kinzo gidan nan kin tarar da yara da yawa, da ace ke me dabara ce a sannan jan su zakiyi a jiki kiyi musu irin tarbiyyar da Kike fatan yayanki su tashi akanta, haka mata masu wayo sukeyi suja yayan kishiya a jiki su kula dasu da tarbiyyarsu karki taɓa duba halin uwarsu ko abinda zata miki domin taki gaban kike gyarawa, yanzu wa gari ya waya? Banda Ahmad da Matan da kika samu Allah ya duba miki ya sassauta abin akansu dukda suma ɗin da nasu, gaba ɗaya yayan gidan nan babu wata shaƙuwa ko soyayya a tsakaninsu, kowa kansa ya sani wlh ina jiye muku ranar da mutuwa zata fara ɗauki ɗai ɗai tsakanin Iyaye ko yayayen, kar a wayi gari a ce cikin Rayayyun yan uwa a rasa masu duba bayan abinda Ɗan uwansu ya bari. Wlh ki farka ki dage da Addu'a ki kuma sa a miki Allah ya haɗa miki kan zuri'arki dan wlh cikin waɗannan Yayan naki Ahmad kaɗai nake da tabbacin yau idan wani cikin sauran ya faɗi ya mutu baze bar zuri'arsa tayi kukan maraici ba, amma kinga wannan Uban namu da Salim? Allah ya rufa asiri kawai kawunansu kawai suka sani sedai Allah ya duba ya shiga cikin Lamarin". Jikin Momy yayi laƙwas kamar an zubawa Salak gishiri, maganganin Maimuna sun shigeta kuma ta sani gaskiya ta faɗa a yanzu ne take nadamar rayuwar baya data zama kamar hoto bata taɓuka komai gurin gyaranmakauniyar tafiyar da akeyi a cikin gidan ba, a lissafinta idan taja nata yayan sun isa suyi rayuwarsu sedai kuma ta tafka kuskure gashi kuma yanzu tana girbar abinta saboda wannan hanyar da Yayayen nata suka ɗauka ta kowa kansa ya sani ta samo Asali daga abinda suka tashi suka gani anayi a gidan nasu ne. Maimuna na kurbar shayi tace "Gara dai ki yi ta kanki kina kallo ita Harbutsatstsiyar gidan naku duk da rashin kan gadonta batayi saken da kan yayanta ya rabu ba kuma komai da ita suke shawara bakinsu ɗaya ke kuwa fa? Banda Ahmad wa yake zuwa ya durƙusa gabanki ya faɗa miki halin da yake ciki ko ga wani abu da zeyi?" "Allah ya rufa asiri dai Maimuna, gama cin abincin mu fita rana ta farayi kuma yai Juma'a ki samu ki gama da wuri" da haka suka bar zancen. Ahmad kuwa bayan fitarsa Kusan karo sukaci da Hajiya dake fitowa daga ɗakinta da tabarma a hannunta da alama shimfiɗa zatayi ta zaunasana'ar tata ta sakawa masu shiga da fice idanu. "Aa, Amadu har ka fito kenan" ta faɗa fuska a washe ba kamar ɗazu dayace .ata Zasuyi tafiya tareda Alhaji ba. Cikeda gajiya da tambayoyinta yace "Na fito Hajiya, na gaya miki Alhaji yana jirana tafiya zamuyi" "Ayyo to, da ai da Yakubu zasuje,sedaga baya Yakubun yace yana da aiki nace ma suje da Faisal shi kuma wai tes zeyi a makaranta ashe kai ya kira banda Alhaji seya tattagoka tun daga Abuja base ya ɗauki Direba yayi tafiyarsa ba? Shikenan dai, ya akayi yau naga ka shigo mana gida hannu na dukan cinya babu yar tsarabar daka saba riƙowa ne?" Ahmad yai zuguɗi yana kallonta se kuma ya zabura daya tuna abi da yake gabansa ya tafi yana cewa "Idan mun dawo zan kawo muku" ya wuce da mamakin Hajiyar, tsarabar da kullum ya kawo haka zata amshe tana aibata shi tana masa shaguben Allah sa da kuɗin Halal ya siyo shine yau tambayar bata gani ba?. Hajiya ta bishi da kallon tsana ƙarara tana jan ƙwafa, ta tsani Yaron ya kuma zamar mata ciwon ido dan ta rasa ya zatayi dashi. Yanzu da Alaƙa take ƙara Ƙarfi tsakaninsa da Alhajin ya sake dagula mata lissafi ba kuna zata lamunta ba duk yanda zatayi setabi gurin datseta tun kafin tayi ƙarfi. Ko yanzu da gayya take ta jansa da magana saboda ya ɓata lokaci har Alhajin ya fito yayi masa tijara burinta kenan ba wani abu ba. A gurguje ya shirya, wata dakakkiyar shadda kalar sararin samaniya ya saka ta haska Fatarsa dake da duhu bacan ba ɗinkin babbar riga ne, be sakata ba ya riƙe a hannu da hular da ze saka da Agogo, Takalmi da Azurfa, cikin sauri ya fesa turare ya fita da silifas a Ƙafarsa. Alhaji na tsaye bakin motar da zasu tafi a ciki an kawo masa ita daidai Barabder yana waya da alama Ahmad alamu sun nuna Ahmad kawai yake jira kenan. Cikin tsantsar ladabi jikinsa har rawa yake ya durƙusa yana gaida Alhajin, wata Kafirar Shaddace data sha aiki na Alfarma a jikin Alhajin, yanayin ƙirarsa ga shigar da yayi ta ƙasaita yasa kwarjininsa nunkuwa tamkar wani Basarake. Ba yabi ba fallasa ya amsawa Ahmad gaisuwar kafin yace masa "Ya haka zaka fito kamar wanda aka koro?" "Babu komai Alhaji, daman so nake sena shiga mota sena ida shiryawa". Harara Alhajin ya maka masa, yasan abinda yake nufi dan haka sum sum ya shige falon ya shiga ƙarasa shirinsa. Tsaf ya fito bayan ya kafa hula Babbar rigar ce dai be saka ba saboda karta yamutse kuma takura masa ma zatayi, data son ransa ne ma Normal Kaftan ze saka na yadi ba shadda ba sedai sanin halin Alhajin tsaf idan yayi shigar da bata gamsheshi ba dizgashi zeyi gaban jama'a babu ruwansa. Shi Mamaki yayi ma da Alhajin ya nemi ya rakashi wata unguwa me muhimmanci irin wannan domin be taɓa ba, Yanzu da sabgogi sukawa Su Zakariyya yawa Yakubu ne abokin rakiyarsa ko Faisal, wani Sa'ilin har Lawan ɗauka yakeyi ya rakashi be san dalilin daya saka Alhajin nemansa ba. A kunne motar take dan haka yayi bismillah ya shiga, Alhaji ya gama sallamar Balarabe me ban ruwan Fulawa kafin ya buɗr gidan gaba kusada Ahmad ya zauna yana hailala, wannan kuma haline klda su Naziru ze fita a gaba yake zama. A ɗarare Ahmad daya gama karanto Addu'ar hawa abin hawa ya taka motar suka tafi, a tare suka ringa ɗagawa masu aiki dake musu Allah ya tsare hannu, Alhajin me halin tsiya dana kirki kenan, a ɓangaren mu'amala da mutanen waje bashida matsala. Duk qanqantar mutum in har musulmi ne yazo giftashi zeyi masa sallama har ya bashi hannu suyi musabiha barshi dai da halinsa idan ya motsa wannan kam kowa ma yi masa yakeyi. Tafiya sukeyi babu me cewa komai in banda karatun Alƙur'ani da Ahmad ya kunna can ƙasa yana bi a hankali. Jefi jefi Alhajin yake amsa waya, wata ta kasuwanci wata kuma Abokanansa ne masu tambayar ko ze samu halartar ɗaurin auran bikin ɗan Abokinsa ne da sukayi makarantar sakandire tare. Sun miƙe hanya sosai kamar daga sama Ahmad yaji Alhajin yace PAGE 12 "Rayuwa kenan, duk waɗannan da kaji muna magana dasu a sanda mukayi makaranta ƙyamatarmu sukeyi saboda su lokacin a gaban Iyayensu suke mu kuwa Almajiranci aka kawo mu Kano, naci da dagiya tasa muka Shiga Bokon amma yanzu dubi ka gani kowanne cikinsu so yakeyi yayi alaƙa damu, bakaga roƙon da Alhaji Mustapha ya ringayiwa Babanku Alƙali akan ya ɗaga tafiyarsa Umarah yaje masa ɗaurin aurannan ba, Allah kenan wato shiyasa duk yanda mutum yake karka rainashi dan baka san me ze zama a gaba ba, a lokacin suna ganin su yan gatane se gashi a yanzu da Yan Bokon cikin su da Yan Kasuwar babu wanda ya zarce nida Ɗan uwana" Alhajin ya faɗa cikin Alfaharin abun. Murmushi Ahmad yayi, be tanka ba dan Alhajin yakanyi magana shi kaɗai wani sa'ilin, ya tabbatar idan so yakeyi ya bashi amsa kai tsaye ze ambato sunansa a cikin maganar, to mema zece masa shi? Yana wannan tunani kuwa yaji Alhajin ya sake cewa "Ya aikin Super market ɗin kuwa? Jiya Asiwaju ya kirani yana ta zuzuta gurin yace har yafi na Kano girma da tsari ko?" "Ina ga dai kallon tsoro yayiwa gurin gaskiya amma befi rabin na nan Kano ba, kawai dai yanda aka fitar da taswirar ginin ne yasa ya ɗauki hankalinsa, an kusan kammala komai dan har an fara zuba kaya ma, yace so yakeyi a buɗe ranar Bikin haihuwar Yarsa, daman na bari sena dawo ne se muyi maganar" Ahmad din ya bashi amsa yana shafa kai domin ko Legos ɗin baje baniyyarsa daga Zariya idan ya dawo Kano seya bi jirgi. Ginin sabon Shopping Mall sukeyi wanda wani Aminin Alhajin Asiwaju Bayerabe Attajirine a birnin Ikkoh ganin yanda Bechi Mall ya samu karɓuwa a Kano yasa yace Ahmad yaje ze bada fili suyi haɗin guiwa ya sake gina Bechi Mall a Lagos ɗin gashi har an kusa kammala komai se abinda baza'a rasa bane ya rahe a gurin. "Ai tun daga plan daman da gani kasan ginin ze bada ma'ana, Allah ya sanya Albarka yasa a buɗe a sa'a. Maganar kayayyakin mu kuma idan kuna ka samu Idi kuyi yanda kuka saba". "In sha Allah" Ahmad ya faɗa daga wannan seda suka sake shafe kusan minti talatin suna sharara gudu a titi kafin Alhajin ya sake cewa "Ɗan uwanka fa? ya tafi ne ko yana nan har yanzu?" "Aa ya wuce tun ranar Litinin, be kira waya bane?" ya faɗa yana satar kallon Alhajin. Shiru yayi harya fitar da ran ze amsa masa kafin yaji yace "Kai kafi kowa kusanci dashi ka ringa masa faɗa kana nuna masa rayuwa shi yaro ne har yanzu baze gane abinda ake son nuna masa ba. Saboda nayi masa faɗa nasan uwarsa ce ta zugashi tace ya dena kirana ko? To ka jaddada masa wallahi, muddin na sake samun labari makamancin wanda ya faru sena a nan ze gane ni ba abokin wasansa bane, kuma daga ranar ya bar buga Ball". "In sha Allah zan sanar masa, hakan ba zata sake faruwa ba" Ahmad ya amsa masa dan a yanda Alhajin yake magana ya hasala in kuma yace ze fahimtar da shi ya wanke Jafar daga laifin dayake zargin ya aikata yasan rufta kansa zeyi duk su hadu suyi laifi a gurinsa amma banda haka a bune a buɗe kawai dan shi Alhaji besan me duniya take ciki ba shiyasa ya ɗauki abin da zafi. Rape Allegation ai ya rigada ya zama ruwan dare akan Celebrities, Matan sun maida wannan harkar samun kuɗi a shekara Ɗaiɗaidaikun Manyan Celebrities ne suke tsallake sharrin Mata ba tareda kaji ance anyi ƙararsu akan sunyi Molesting wata ba abinda ya faru da Jafar kenan wata yarinya tayi Ƙoƙarin ɓata masa suna akan yayi Raping nata shi Alhaji har se bayan ma anyi case an gama yarinyar ta Ƙaryata kanta har kotu ta yanke mata hukunci kafin can ya gano tsohon labarin a Jarida. Shine dalilin tattago Jafar yazo gida babu shiri, sunga Tijara daidai gwargwado wanda hakan yayiwa da yawa daga cikin Ahalin gidan daɗi dan Alhaji kulle ido yayi ya wanke Hajiya tass ita da ɗan gaban goshinta. Cewa tayi ita bataga laifi ba idan ma Jafar ya aikata abinda kace yayi, ubanwa ya kai yarinyar gurinsa?/ ko janta yayi ta ƙarfi? Basu suke bibiyarsa kamar jela yana yakice su ba banda ma rainin hankali Maza nawa ta buɗewa ƙafa se shi data raina take bibiya da sharri zatace ya mata Fyaɗe shine fa Alhaji ya zazzage mata tijara a tsakar gida yace ba zata saka yaje ya zubar masa da mutunchi a duniya ba. Abu ɗaya yasaka ya sassauta masa be tsaurara mataki akansa ba saboda sunan Bechi da be jona a sabgar ƙwallonsa ba, ba kowa nema ya san Ɗansa bane banda Close Family and Friends da yawa Muhammad Yayanta sukewa kallon Babansa dan dashi ake ganinsa ko Biography ɗinsa kayi searching it only shows Abdullahi Tijjani As his Father's name Nationality kuma Nigerian from Kano shikenan. Daƙyar Alƙali ya kashe maganar Jafar ya koma ashe Alhajin be haƙura ba. Sun isa Haɗeja Lafiya kai tsaye fadar sarkin Haɗeja sukayiwa tsinke inda a can za'a ɗaura auran. Alhaji Mustapha Babandede yayi matuƙar jin daɗin ganin Alhaji Alhaji Audu Bechi, suka riƙe hannun juna ana gaisawa yanda Alhajin ya sake da tsofaffin Abokanansa ana gaisawa cikin barkwanci ya bawa Ahmad mamaki, koda yake daman hakane, duk girma da wani matsayi da mutum ya kai a rayuqa idan ya shiga cikin waɗanda sukayi gwagwarmayar Karatu tare se kaga duk an koma yara ana tuna baya. To tare akaci daɗi aka sha wuya, lokacin da kowa be gama fahimtar tanadin da ubangiji ya masa a rayuwa ba. Yakubu ya taɓasu labarin daya kai Alhajin taron Tsofaffin ɗalibai a ranar har rawa yayi, wai hana yin video akayi shiyasa be ɗakko musu ba abun ya basu mamaki suka ringa hakaito Alhaji yana rawa wane irin farin ciki ne haka ze sakashi ya taka se gashi yau Ahmad yaga makamancinsa a fuskarsa dan Dariyar da Alhajin yakeyi harda ƙyaƙyatawa abin ya tashin kansa ya kuma sake tabbatar da Abotar makaranta tana da wani ƙarfi da tasiri na daban sama da sauran Abota, an girma shekaru sun taru amma idan aka haɗu se a ringa ji kamar an koma bayane. Se bayan da aka ɗaura auren a gurin Reception ya haɗu da yayayen Abokanan Alhajin waɗanda suka kawo iyayensu. Wasu ya sansu suna hulɗa wasu kuma ranar ya fara ganinsu, Basu bar Haɗeja ba se ƙarfe huɗu bayan sunyi sallar La'asar kafin kowa ya kama gabansa. A hanyar dawowa Alhaji ya ware yana masa labari irinsu "kaga wane? Lokacin da muna makaranta fa kaza da kaza amma yanzu kalli kaza ya faru" Ahmad ya lura Alhajin na cike da shauƙin ganin tsofaffin Abokanai shiyasa yau harya maidashi abokin hira. "Ya kamata ku motsa ku fito da mata kuma tunda ƙannenku mata sun tsaya shiririta. Kasan ban fiya mayar da hankali gurin gayyato tsofaffin Abokanai na na ƙuruciya sabgar auren yayana ba amma ina ganin wannan karon har Gala Nigh zan shirya mana ta yanda zasu zo su kwana musha hira kafin ranar ɗaurin aure" Alhaji ya fada. Ahmad ya shafa ƙeya da hannu ɗaya yana murmushi me kama da dariya, wato su Alhaji har Gala Night za'ayi lallai abin nayi ne, shi kuwa Alhaji yanayin nasa se yasa yayi zaton kunya yaji da yace su fito da Mata tunda yau a giya tara yake yan mutunchin na kusa se yace masa "Toakwai ta a ƙasa kenan irin wannan murmushi da kake bugawa, Yar gidan wacece?" "Ƙuuu" cikin Ahmad ya kaɗa, maganar tazo masa a bazata, ba tanan ya shirya tasota ba. Ya rigada ya gama tsara takan Baba Alƙali zebi shi ze kaiwa maganar auransa kai tsaye tunda dai shima Alhajin idan maganar ta tashi shi ze wakilta amma yanayin nasa neman auran yasa gara ya fara samunsa dan ya tayashi gyarota idanma matsala ta shirya afkuwa yanzu kuma Alhaji na nema ya titsiyeshi, be kuma san ya ze ɗauki maganar ba idan ya sanar masa da wadda yake nema musamman da yaji ya tambayeshi Yar wacece kenan yana tsammanin ze samo yar wani Attajiri ko ƙusar gomnati wanda yana faɗar sunansa ze gano wanenene? "Kayi shiru, ko babu ne?" Alhaji ya sake faɗa yana kallonsa. Harda rage gudu Ahmad yayi kafin ya saci kallon Alhajin yaga shi yake kallo shima sannan ya haɗiye yawu yace "Wata yarinya ce Fatima, a Marmara gidansu yake amma cikin lungune se anyi tafiya kamar za'a shiga Alfindiki, Mahaifinta Bakanikene yana gyaran mota da babur Amma kafin ma na fara zuwa gurinta seda nayi bincike wlh mutumin kirki ne kwarai da gaske haka ma ita yarinyar tana...." "Ban tambayeka halinta kona mahaifinta ba ko kuwa kai ne zaka mun binciken halin waɗanda zan haɗa surukuta dasu?" Alhajin ya dakatar dashi muryarsa dai kadaran kada han babu farin cikin da yake ciki dazu haka babu zafin da kai tsaye Ahmad ze zarce cewa be aminta da abinda yazo dashi ba. Tamkar Ahnad yace "Ai naga kamar su Yaya Naziru su sukayi binciken Matan da zasu aura shiyasa baka hanasu ba" se kuma yayi azamar kwabar zuciyar dake neman kwanto masa ruwa ya shiga taitayinsa, Ya sauke ajiyar zuciya tareda yin shiru Alhajin ya sake jefa masa wata tambayar yace "A ina kuka hadu da ita?" "A Shago, sunzo siyayya tare da Yayarta" ya bashi amsa a sanyaye Alhaji ya sakeyin shiru kafin ya kuma cewa "Ita yayar tata budurwa ce ko matar aure?" Se Ahmad yayi saurin cewa "Matar aurece, Dan gidan Balarabe Faranshi take aure ma yaranta uku yanzu" ya shaidawa Alhajin harda sunan uban Mijin Anty Sauda domin ya sanshi, dukda ya rasu amma har yanzu akwai manyan Yayansa da suke huldar kasuwanci dasu, dabararsa hakan zesa Alhaji ya fahimci ba a gidan banza ya nemo mata ba. Alhaji ya muskuta yace "Marmara? Ina ganin Musbahu ne kamar naje Ɗaurin auransa a nan masallacin sarki idan ban manta ba shekaru bakwai kenan yanzu dan tsiran auran da shekara ɗaya Alhaji Balaraben ya rasu. Amma yarinyar daya aura shi ai kamar Baƙar buzuwa ce dan ban manta ba na halaci Dinner da Alhaji Balaraben ya haɗa musu" Rai fes Ahmad yace "Itace, mahaifiyarsu ce Buzuwa amma mahaifinsu haifaffen nan Marmaran ne duk yan uwansa anan tsukun suke yaran ne dai sukayi kama da Mahaifiyar tasu shi yasa idan aka gansu se a dauka Buzaye ne" "Wato farar fatar ce da dogon gashi suka ruɗeka ko?" Alhajin ya faɗa fuska babu wasa yana tsare Ahmad da ido nan ya diririce murnar da yake ta koma ciki, cikin in ina yace "Aa wlh Alhaji kawai dai.." "Kawai dai me? Da ba Suhaima yar gurin Alhaji Lamin kake nema ba?" Alhajin ya dakatar dashi. Tamkar ze fasa masa kuka yace "Ni daman ita ta ke sona, kuma daga baya tace ita ba zata zauna a Nigeria ba tunda yan gidansu sun koma US sedai na bita can nima abinda ya rabamu kenan" "Eh anyi haka, naji yayyenta biyu ma duk auransu ya mutu da sukace zasu bi uban su koma can da zama, Lamin,Lamin ban san kalar kwayar da yake sha ba. Haka kawai ya tattara wai shi ya bar Nigeria banda shirme waɗanda suke a wajenma idan girma ya riskesu dawowa gida suke su mutu cikin Ahalinsu se shi ze tattara ya koma can, to ita kuma Safiyyah yar wajen Goggonka Salaha fa?" Alhajin yayi kiɗansa ya taka rawarsa lokaci ɗaya. Ahmad da gaba ɗaya ya gama shigewa ruɗani, da fari abu kamar ze zo a sauƙaƙe amma kuma yana neman yayi wahala Alhajin se wani kale kalen magana yakeyi, ta maza yayi dan duk ji yake kamar ya fashe da kuka ko Alhajin ze barshi da zaɓinsa yace "Ai ita Abbanta yace yayi mata Miji, Momy bata gaya maka ba auran ma saura wata biyu yanzun ma Anty Maimuna tazo siyan kayan Lefe Ɗan Mijinta ne wanda Safiyyan zata aura" "Wato sun hanaka zasu bawa Ɗan Mijin Maimuna, kai dashi waya fi kusanci dasu?" Alhaji yayi maganar cikin faɗa Ahmad besan sanda ya ɗage kai da hannu biyu ya saki sitiyari ba yana cewa "Wallahi tallahi ba hanani sukayi ba, gajiya Abban yayi da jiran kuje ayi magana kuma daman ya rigani fara nemanta seda ma Anty Salahan tace a fasa dashi Mony ce tace Aa ba za'ayi haka ba tunda dai ya riga a bashi" "Baka da hankali zaka saki mota?" Alhajin ya buga masa tsawa se ya nemi gefw ya faka, Allah yasa babu mota dake biye dasu gab kuma ba gudu yake sosai ba shiyasa daya sakwta bata watsasu wani gurin ba. To fisabilillahi kamar wanda aka ritsa a Kotu Alhaji se zabga masa tambayoyi yakeyi yana muzurai ba dole ya manta abinda yakeyi ba? Shiru ne ya biyo baya, babu kalar addu'ar da Ahmad beyi a ransa ba akan Allah ya sassauto zuciyar Alhaji ya amince da buƙatarsa babu ja in ja. "Tada motar muje gida, zamu ƙarasa maganar a can" Alhajin ya faɗa bayan daya mula. Jiki ba laka Ahmad yaci gaba da tuƙi, har wani zazzaɓi yake ji yana shirin saukar masa domin yanayin Alhajin ya nuna koda ace ze yarda da batunsa tofa se an kai ruwa rana. Sun shiga Kano anyi magriba, a kusada wata Majalisa yace ya tsaya ganin suna hada jam'i da alama makararru ne nan suka yi alwala suka bisu. Bayan sun idar ganin Alhaji na lazumi Ahmad ya tsallaka inda yaga wani me gasa Nama yayi sa'a akwai wanda sukayi nan da nan yasa aka shiga yanka masa kashi kashi aka gama tsaf ya basu kuɗinsu yara suka kai masa mota ya sake jido fruits ya ƙara daidai nan Alhaji ya shafa Addu'arsa ya taso suka cigaba da tafiya. Har bakin falonsa inda ya ɗauke shi ya tsaya da motar Alhajin ya sauka yana Hamdala, filin gidan tarwai da haske tamkar idan allurarka ta fadi zaka ganta. Sarah ce ta fito da Dogon Hijabi da alama aikenta akayi tana ganin Ahmad ta fasa ihun murna ta ɗaleshi, Alhaji ya zabga mata harara kafin ta sauka da gudu ta koma cikin gida se ga gayyar Maimuna da Yan biyun Anty da Mariya tareda Zayyad ta kirasu suka dabaibayeshi suna sowa da murna ga Yah Ahmad ga Yah Ahmad bakinsa ya gaza rufuwa ya ringa ɗaga wadanda ze iya yana saukewa kafin ya buɗe Boot ya shiga fito da ledojin ciki tun a gurin yasa aka ware dan haka ya danƙawa kowa ta ɗakinsu Hatta su Issa dake nan tsaye yayo musu kashinsu suka karba suna murna dayi masa Addu'a, ya gama rabon tsaf ya rage ledoji biyu a hannunsa, Alhaji na tsaye har sannan be shiga ciki ba yana kallon Ahmad. A cikin Yaransa Ashirin da takwas ya fita daban kyautatawarsa ba kadan bace baga su iyayensa ba ga kowa daya rabeshi se yayi sambarka da halinsa, se yake ganinsa kamar shi a zamanin ƙuruciyarsa. "Ina nawa Naman toh? Tun ɗazu nake haɗiyar yawu a mota" Alhajin ya tambaya fuska a tamke kuma, Ahmad ya ƙarasa gabansa ya rusuna yana miƙa masa Leda yace "Fruits ɗin idan an gyara se a kawo tunda kafi so a matse" "Allah yayi Albarka" Alhajin ya faɗa bayan daya karɓi ledar, cikeda farinciki Ahmad ya amsa da "Amin" domin yasan alfanun Addu'ar iyaye, ita take dabaibaye dashi yake ganin haske a rayuwarsa. Tasowarda yayi kamar hadari yayiwa jama'a da yawa rumfa a matsayinsa na matashin Ɗan kasuwa, buɗe shopping mall ɗinsa ya saka kasuwar wasu da yawa tayi ƙasa badan tasirin addu'ar iyayen ba ai da yanzu maƙiya sun kaishi ƙasa. Da kansa ya kaiwa Momy tata ledar kafin ya wuce ɗaki yayi wanka yayi sallar Isha'a dan an rigada anyi a masallaci. Ya ɗan jima a zaune yana azkar da be samu yayi ba a hanya kafin ya sake shiga cikin gidan yana tafe yana kiran layin Fatima wadda tun suna Haɗeja ya kirata basu wani yi magana me tsayi ba se yanzun yake sake so yaji ya take ya kuma ce ta tura masa da Kwalliyar Juma'ar da duk sati seya roƙa kafin ta bashi. Busy yaji layin nata a ransa yayi tunani ƙila da yan gidansu take waya shi kansa badan tafiyar da yayi ba yau ya kamata ya leƙa ya gaida Baffa dan kusan duk sati indai yana Kano ko Fatima bata nan se yaje ya gaishe su, yanzun babban abinda yake a ransa jiran jin amincewar Alhaji game da maganar auransu wanda kuma a jikinsa yana ji in Allah ya yarda ba za'a samu matsala ba fatansa daya Allah yasa kar Alhajin yayi zancen da Hajiya har ya gaya mata yar wa yake nema ita kaɗaice a cikin gidan yake da tabbacin zatayi Adawa da auransa da Fatima domin ta tsani TALAUCI da TALAKA, ya tabbatar kuwa muddin ta sani se inda ƙarfinta ya ƙare gurin ganin haƙansa be cimma ruwa ba na auran Fatima, ko ba dan komai ba ta samu hanyar rama tsaya mata a maƙwogwaro da yayi ya hanata rawar gaban hantsi, ya tabbatar zata shiga ta fita gurin ganin be samu abin da yake so ba amma Allah ya fita. A haka ya shiga cikin gidan Hajiya Rabi na tsakar gidan tana bawa Baba Mairo sallahun abinda zata taho mata dashi wani satin idan zata zo, Baba Mairo dai me girkin gidan tun zamanin Hajiya na Amarya duk haifarsu akayi suka ganta a gidan bayan sun dawo nan Hotoro GRA kusan shekaru Ashirin kenan, wannan tazarar tasa bata biyo su ba saboda har yanzun Mijinta yana raye yana kwance yana Jinya se ya zama se sati sati take zuwa tana girkin Sadaka ana biyanta dukda girma ya kamata yanzun amma macece me lafiya da kazar kazar sannan aikin na rufa mata asiri shiyasa bata saki duka ta daina ba. "Yaya Ahmad, an dawo" Antyn ta faɗa kamar yanda yaran gidan suke kiransa tana murmushi, ya sunkuyar da kansa shima yana murmushin yace "Tun dazu Anty, har nayi wanka naje sallah ina wuni" ya gaisheta bayan daya idasa kaiwa tsugunne ya sake kallon Baba Mairo da bakinta yaƙi rufuwa da ganinsa yace "Iya, ina wuni? Ya jikin Baba?" "Lafiya lau Alhaji, Malam jiki da sauƙi Alhamdulillahi ko da zan fito seda yace na gaishe ka na kuma ƙarayi maka godiya. Na dai barwa Hajiyar tsakiya sallahu da aka ce baka nan amma naji daɗisosai dana ganka mun gode Alhaji Allah ya saka da Alkhairi yaci gaba da yalwata arziƙi ya kuma rabaka da Alhaji Babba da Hajiya lafiya". Anty ce ta amsa da Amin fuskarta a washe ta tabbata halin nasa yayi musu na Alkhairi, kyautar Ahmad irin wadda Annabi yace ayi ce, ka bayar da hannun dama ba tareda Hagunka ma ta gani ba, ya miƙe yana sake cewa Anty "Ina Aboki? Dana dawo da safe banshi ba ina sauri shiyasa ban shigi na dubashi ba" "Ai bama nan ma da wuri na fita ma kaishi Allura seda muka dawo Momy tace ka shigo amma kun fita da Alhaji, yana ciki rigima yake tayi tunda akayi allurar bari Hasna ta kawo maka shi ko zaka shiga?" "Bari na leƙashi to ance idan anyi allurar ba'aso ana jagwalgwalasu ko ƙila zafi take masa" ya faɗa yana nufar ɗakinta. Tun daga wajen falon kuwa yake jiyo kukan Abdallah Autan gidan a yanzu me watanni uku kuma shine Ɗa na shida da Antyn ta haifa. Babban Ɗanta Musa da suke kira Mu'allim nada shekara goma sha takwas yanzu, se yan biyu mata Husna da Hasna masu shekaru sha biyar sannan Mariya me goma Zayyad me shekaru takwas sai kuma Abdallah data haifa watanni uku baya. Fadar tashin hankalin da akasha da Hajiya akan cikin nan bata baki ne dan tabbas Allah ya hakunta zuwan sa badan haka ba iyakar baƙin cikin da takaicin da Anty ta ringa sha na Hajiya da gori da cin mutunci akan tazo tana ta zuba yaya saboda taci gado yar matsiyata yaci ace cikin ya bare kota haifi yaron da lalura se gashi Allah ya bata lafiyayyan Ɗa kuma Namiji abinda ya sake gigita Hajiyar ta ringa abu kamar wadda ta zauce, Allah kaɗai yasan da yanda tasha kan Alhaji haka ya saka Antyn a gaba taje Asibiti aka juyar mata da mahaifa wai da shekarunsa rututu ga manyan yaya abin kunya ne ace har yanzu ana haihuwa a gidansa yana haifar Ƙannen Jikokinsa badan Manyan Yayan Alhaji Babannan da Babangida duk Mazane ba da yanzu ma ya fara aurar da jikoki itama Antyn tace daman ko bece ba ta gama haihuwar. Karɓan Abdallan yayi daga hannun Mariya dake jijjigashi yana cewa "Ya haka, me yasa yake kuka kuma?" "Wlh Yaya Hasna ce ta ja masa ƙafar da akayi masa allura wai zata fi saurin saki shine fa yake ta kukan nan". Ahmad ya harari wadda aka kira da Hasna ta sunkuyar dakai kafin yace "Banda cin zali ya za'ayi kija masa ƙafa? idan ke kikaji ciwo aka taɓa miki ya kikeji hum?" "Kayi haƙuri Yaya" ta faɗa tana sadda kai ƙasa, yayi tsaki kafin ya juya da yaron ya fita Husna Usainarta tace "Wlh Naso Yah Faisal ne ko Yah Salim da kinji a jikinki banza muguwa kawai. A falon Momy da Ahmad ya shiga ta karɓi Abdallah tana cewa "Meya samu babana tun ɗazu nake jiyo kukansa kuma dai shi baya kukan banza?" "Wai Allura akayi masa" ya bata amsa bayan daya sake gaiaheta. "Wayyo, Babana yau ansha ƙarfe, yi shiru kaji kar suyi mana dariya ace tsohona rago ne, Allah ya taimaka bata saukar masa da zazzabi bama zuwa safiya in sha Allahu ze ware" ta faɗa tana zare masa dogon wandon dake jikinsa ta cire masa Diaper da aka matse masa cinya tana sake cewa "Da gani wannan aikin Hasna ne uwar raino yau kam ai a ɗaga masa ƙafa da wata Diaper a barshi yaji da sagaggiyar cinya" tana cirewa kuwa ya dena kukan ya shiga wulla ƙafa, Ahmad yayi murmushi yace "Babu baki, ƙila ma duk abinda ya takurashi kenan yake ta kukan haka su kuma basu sani ba, ina Anty Muna badai ta wuce ba?" "Ka ganni Amadi sallah nayi kai nake jira ka shigo musha hirar yaushe gamo" Anty Maimunan ta faɗa tana fitowa saga Bedroom ɗin Momy. A nan yaci abincin dare tareda Salim da tunda garin Allah ya waye se sannan ya shiga falon ya zauna da Momyn suka gaisa kuma yana gidan wuni sur sallar Juma'a kawai ya fita ya dawo wai bashida lecture a makaranta shine ya wuni bacci. Har gurin sha daya kafin Ahmad yayi musu sallama ya tafi makwanci ransa cike da mamakin abinda ya samu wayar Fatima yana zaunen ya kira yafi sau goma amma still busy ake gaya masa, abin ya bashi mamaki dan layinta akan tsarin call waiting yake in dai wayace da zasu gaya masa sedai idan a DND ta saka wayar ko kuma a kashe take sharrin Network yake ce masa busy, haka ya kwanta duk yanajin babu daɗi ga kewar muryarta duk ta cikashi danya saba koda ba wata hirar soyayya suke ba amma yana jin daɗin magana da ita a haka bacci yayi awon gaba dashi. FATIMA Ƙarfe ɗaya harda mintuna suka gama Ajin ranar dan Lecturan nacewa yayi akan se yayi covering abinda ya rage mana sannan yayi fixing musu test ranar Monday saboda Next week ake saka ran fara First Semester exam. Sanda suka fita har an fara tafiya Masallaci, tayi murmushi tana kallon yanda Mazan Makarantar suke tafiya a sahu cikin shiga me kyau a fili tace "Allah mun gode maka da kayi mu musulmai, dan Allah Badar kalle su, ina son Juma'a a school ɗin nan ranar ne wanda ma baka taba zaton musulmi bane zaki ganshi da Kaftan ya tafi masallaci". Haka suka ringa hira suna ratsa mutane har suka isa Hostel. A gurguje suka yi Alwala, cikim postgraduate Hostel suka fita zuwa masallacin yau basu samu ciki ba saboda sun makara dan haka a waje sukayi sallar kafin suka koma ɗaki. Ta kira yan gidansu suka gaisa a wayar Baffa dan har sannan ba'a gyara wayar Ummansu ba, yaran Anty Sauda na gidan ta ɓata lokaci sosai suna magana dasu harda Autar Goggonsu Faɗima da taje gidan hutun makaranta. Tana gama wayar kiran JAY ya shiga, tayi ƙaramin tsaki kafin ta sauka daga kan gado saboda hayaniyar mutanen ɗakin sunyi baƙi Jama'ar Sururat kunsan mutanen Yarabawa badai ɗaga murya ba idan suna magana. Guri ta samu me kyau ta zauna kafin ta duba wayar yayi mata two missed calls, kusan Minti goma tana jira ya sake kira dan tace ita ba Asararriya bace da zata kira layin waje da Katin Ahmad, harta fidda ran ze kira se ga wayar ta shiga Ringing bata ko tsaya dubawa ba saboda yanda zuciyarta take azalzalarta da son jin wannan muryar tasa ta kai wayar kunnenta sedai Muryar Ahmad tayi mata sallama ba wadda tayi tsammanin ji ba. A taƙaice sukayi magana dan rabta babu daɗi dalilin ta tsammaci JAY ne, ya gaya mata yana Haɗeja ya kai Alhajinsu Biki dalilin tafiyarsa da sassafe kenan maganar batayi tsaho ba sukayi sallama yana kashewa kiran da take ta zaman jira ya sake shigowa. Ajiyar zuciya ta sauke me ƙarfi har ranta taji daɗin da ta kasa tantance na menene amma dukda haka seda taja aji wayar na dabda katsewa kafin ta daga "Hello Baby" ya faɗa da muryarsa me tsinka daskararren jini kota daskarar da tsinkakken to itama dai daskarar da nata jinin yayi dan hatta bakinta ji tayi ya mata nauyi ta gaza furta komai seda ya sake cewa "I'm sorry, Assalamu alaikum". A hankali taja numfashi kafin ta amsa masa daga nan ta sakeyin shiru. Jay dake tsaye gaban Mirror cikin katafaren Bedroom ɗinsa yana taje Quater Million Sajen dake kan fuskarsa yayi ƙaramin murmushi kafin yace "How are you my love?", zare ido tayi kamar tana gabanshi kafin cikin tsiwa nace "when did i become your love? Don't call me that again" "The first time i set my eyes on you, i know you are my lost but found true love" Jay ya faɗa yana ɗaura agogo, fita zeyi, kiran da ya mata bata ɗauka ba shine ya shiga wanka yanzu ya fito yana shiryawa ya sake kiranta. Baki ta tura amma kalamansa sun mata daɗi, wato da confidence yake komai nasa babu wani ɗari ɗarin irin na Ahmad shi gaba gaɗi yake faɗar abinda yake a zuciyarsa. "Hey sweet, are you there?" "Uhm" ta iya furtawa kawai dan ta rasa bakin magana. Ta kasa gane kanta da wannan stranger ɗin, bala'in jin daɗin magana dashi take kusan zata iyacewa a class hankalinta duk yana kan wayar da sukayi da Asuba, bata sanshi ba bata san waye shiba ba amma har cikin ranta ji take kamar sun shekara dubu tare. "I'm going out, dama na kira ne naji muryarki nayi miki barka da Juma'a, i might be late out though, will you wait for me ba zakiyi bacci ba har na dawo muyi magana?" Jay ya faɗa tamkar me barwa matarsa sallahun ze fita wani guri, mamaki ya sake kasheta amma cikin tsiwa kuma ta miƙe tsaye tana kakkaɓe jikinta tace "To ni meye haɗina dakai kuma da zanƙi bacci na jiraka?" "Abinda nake so muyi magana akai kenan, ina so kisan meya haɗaki dani yau" ya bata amsa a tsume jin zata fara masa rashin kunya, wai kuma se shakkarsa ta shigeta harta gyara harshenta tace "Karma ka kirani dan bacci na zanyi koma zan kashe wayar kawai tunda kai idan ka fara kiran mutane se kace sunci bashinka baka haƙura se an amsa" "Wait for me please" ya faɗa da taushin daya saka ta ɗaukewa na sakanni, yayi miskilin murmushi, ya gama gane lagonta ba ita kaɗai ba yammata da yawa muryarsa na cikin abinda yake saurin kassarasu shiyasa ya laƙanci salo salo da yake amfani dasu gurin ladaftar da masu kunnen Ƙashi irinta. "Will you?" Ya sake faɗa da sautin dayafi na farko taushi, tsikar jikinta ta hau zuba, kai ta ringa ɗagawa kamar Ƙadangaruwa kawai kafin dakyar tace masa "Toh, amma kar yayi dare da yawa" "Till i call, bye, I love you" ya sakar mata maganganun kafin ya kashe wayarsa. Taji I lobiyu tabi kashi Miliyan amma bata taba jin wadda ta gamsar da ita irin wannna da bata da tabbacin da gaske yake ko ƙarya ya sharara ba. Da yamma ta suka fita karatu sai bayan Magriba suka dawo rabi da rabin hankalinta nakan Jay dayace ze kirata, dukda yace se dare amma fata take ya sake kira da yammar. Suna hanya Nurain ya kirata akan ya shigo Makarantar. "Ina my Badar? Wayarta baya shiga?" Ya tambayeta. Ta saci kallon Badar data ƙurawa hanya ido kamar me neman wani abu kafin tace "Gata muna tare, ka jiramu a white sit mun kusa isowa" "Alright Bestie" ya kashe wayar. A nan gurinsa suka lalace suna hira har gurin tara dukda hankalin Afeeya rabi da rabi ne a gurin Badar ce suke kurɓar madarar soyayya da Habibin nata ayi faɗi. Tara da rabi tace ita zata shige ciki yunwa takeji Nurain yace suje su siya abinci a Baescope. "Wlh ba zamuje ka sake yarfamu irin na ranar nan yau ban fito da kuɗi ba" Afeeyah ta faɗa yayi dariya yace "Haba da kenan, yanzu ko wani na gani ze yanƙwana Baby na Badar ai se inda ƙarfi na ya ƙare balle nida kaina. Suka tafi a motarsa, a can sukaci ya siya musu Ice cream suka dawo. "Bestie meya faru ne? Fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa?" Nurain ya tambayi Afeeyah ganin duk walwalarta ta gushe. Tunda suka je gurin yake lura da yanda ta tsume abincinma tsakurarsa tayi bayan ita tace tana jin yunwa jefi jefi kuma tana duba waya tana tsaki. "Babu komai Bestie I'm just too tired, bari na baku guri dan nasan Badar tsuntsun soyayya baze barta ta gaji ba" ta wuce Badar na zaginta. Harta gama shiri ta hau gado badan tana jin bacci ba sedan ranta babu daɗi Jay be kira ba kamar yanda yace. Ta rufe idonta tana jin kamar ta fasa kuka, su Ummi suka tambayeta lafiya tace kanta ne yake ciwo kowa ya mata sannu suka barta. A zabure ta miƙe jin wayarta ta fara ringing, a jikinta taji cewar shine, ta dire daga kan gado tana neman hular da zata saka takalmi ma wari da wari ta zura ta fita har suna karo da Badariyyah. "Wai Afeeya wane salon munafunci kika samu na ba zakiyi waya a ɗaki ba?" Badar ta faɗa tana riƙe Ƙugu, Afeeyan ta harareta tace "Yo aike ke tashen munafunci yanzu, ki gama cika baki Allah ya sawwaƙa me zaki ci da Bestie na ashe mu kika mayar shashashu kuna can kuna tsinke furen ƙauna" "Ya ranki?" Cewar Badar tana fari da ido, Afeeya ta girgiza kai kawai ta fice. Dukda dare ga uban sauro haka ta samu wani saƙo ta lafe ta bi kiran Jay daya katse, be amsa ba ya kashe ya kirata back "Irin Ahmad ta raya a ranta" muryarta na amsa kuwwa a kunnenta ta manta da wani batun Amadi bawan Allah ta fuskanci Jafaru. PAGE 13 "Assalamu alaiki" ya faɗa cikin murya me sauƙi kamar wanda yake cikin nishaɗi sosai. Ta amsa can ƙasa, yayi murmushin daya saka kunnenta fara Ƙaiƙayi kafin yace "Na kiraki morethan ten times baki amsa ba, you are lucky ina cikin farin ciki yau amma da sena hukuntaki" "Toh" tace masa, "Oh toh ma zakice kawai? U are not apologing, Any way how is my sweet baby doing? Ya Juma'a?" Ta karkace ta gyara zama kafin tace "Komi lafiya" "That's great" ya bata amsa se sukayi shiru na kusan minti biyu kafin ya sake cewa "Afeeya, i hope you remeber me?" "Nidai idan zakayi magana ka dena kiran sunana and i don't remember you i don't think we have ever met" ta faɗa da shagwabar da batasan tayi ba saboda yanda yake kiran Afeeyan gaba ɗaya wani yanayi yake sakata. "Babe karki Kashewa Hajiya ni da wannan shagwaɓar taki" ya faɗa, yanda yaja Babe ɗin ya sakata jin wani sanyi yana ratsa mata ɓargo har seda ta haɗe jikinta tanayin kamar kanta na hayaƙin shauƙi. Allah ya sani Ahmad na iyakar yinsa gurin riritata yana faɗa mata kalaman soyayya amma batajinsu kamar na wannan mutumin. "We met on Monday, kina sauri zaki tafi class i followed you to your department a gurin Class Rep naku na samu number ki so you are this popular ina cewa Afeeyah yace ya sanki, i hope you are known for the good not for the other way?". Shiru tayi masa dan idan yana magana bata so ya dena, sautin muryarsa is killing her, "Afeeyah" ya kira sunanta ta amsa da "Uhm". Shiru yayi kafin yaja numfashi yace "Kafin muyi nisa Afeeya let me make this clear to you, ina da saurin fushi like the smallest thing you couldn't imagine can trigger my temper. Na tsani na yiwa mutum magana yayi shiru ko ya amsa mun da uhm ko body language, I prefer kayi mun magana ko zagina zakayi and bana son nuƙu nuƙu da boye boye na tsani ƙarya da munafunci, i love bold and straight forward person in dai kika kiyaye wannan zamu zauna lafiya, lastly I'm a lover boy, i love to be loved and be pampered, kinga idan kina riritani kina shayar dani madarar love na rantse har Ƙafarki zan ringa lasa tsabar biyayya". Bata san sanda ta tuntsure da dariya ba saboda maganarsa ta ƙarshe wai lashe ƙafa kamar wani maye kai wannan mutum da abin dariya yake ma wlh. Tayi dariya sosai shi kuma yayi shiru yana sauraronta seda ta gama dan kanta tace "You are so funny wlh" "Some times" ya bata amsa kafin ya sake cewa "I should make a proper introduction of my self now. Sunana JAFAR but the world knows me as JAY, Bahaushe ne ni haifaffen Kano amma rainon Turai, na bar Nigeria when i was 13 na tafi Manchester nayi joining Football Academy. I'm a professional footballer, shekarana 11 ina taka leda yanzu professionally, I'm currently playing with Arsenal, ina buga number 7 or 9". I'm from a polygamous family, inada siblings da yawa sosai i think that's all that you might want to know now about me for now, may be with time zaki ƙarasa sanin komai a kaina". A duk bayanin nasa babu abinda yayi catching attention ɗinta kamar sunansa da kuma profession dinsa, JAFAR kuma FOOTBALLER? Samun kanta tayi dace masa "Kai kaɗaine Jafar musulmi kuma dan Nigeria da yake buga kwallo a Turai?" "No bani kaɗai bane, akwai Jaybee a Tottenham se Jay Jay a Leinster, but they are all half Nigerians me yasa kika tambaya?" Ya maido mata seta sauke wata ƙarfaffar ajiyar zuciya yanda kasan wadda aka ritsa da bindiga ta samu ceto koda yake da tunanin da yake zuciyarta ai har gara ace bindigar ce, indai ba mantawa tayi ba Jafar ƙanin Ahmad ma ƙwallo yake yi a turai idan ya zama shine Jay da take magana dashi ai sheƙe kanta kawai zatayi ta mutu, zuciyarta ta aminta da cewar Jafar ɗin Ahmad yana cikin ɗayan biyun waɗancan daya faɗa ko Jaybee ko Jay Jay tunda bata san mamanshi ba, ta yuwu halfcast ce kamar yanda yace suɗin half Nigerians ne amma ba wannan JAY ɗin bane ba, babu yanda za'ayi ya zama JAY ma. A yanzun haka suna da aikin da sukayi sharing da Jafar ɗin yasa kaso Arba'in na zumuɗin da takeji akansa ya disashe, zuciyarta har wani harziƙowa tayi da tunanin abokin faɗan nata, Jay da yaji shirunta yayi yawa yayi gyaran murya yace a sanyaye kamar bashi ba yace "Afeeya lafiya kikayi shiru ko da akwai wani abu ne" "Babu komai, kawai sunanka da profession dinka sunyi kama da na wani abokin rigimata" ta bashi amsa, muryarsa har ƙara sauti tayi kamar a fusace yake tambayarta "Wanene shi? Meye ya haɗaki rigima da Namiji?" "Cousin ɗina ne" ta samu kanta da yanko wannan Jibgegiyar ƙarya da seda ta faɗa sannan takaicin kanta ya kamata to saboda me zatayi masa ƙarya? Haka kawai taji bazata iya ce masa ƙanin saurayinta bane ba, daga can Jay ya sauke numfashi yana cewa "Your cousin is a footballer too, wane club yake?" "Nima ban sani ba, amma kamar a Arab countries ɗin nan yake" ta faɗa saboda last tima kamar daga Qatar taji Ahmad yace yazo shiyasa ta bayar kawai tacan Arab countries yake ƙwallon. Bata taɓa ganinsa a fili ko a hoto ba balle ta kwatanta masa shi, a waya suka taɓa magana sau ɗaya wadda yaci mata mutunchi se jefi jefi idan yana gari ta kan jiyoshi tareda Ahmad har ya gasa maganganu itana ta rama. Har sannan murya babu walwala Jay ya sake ce mata "Oh i see, i hope there is nothing between you two? Bama shi ba da farko if you know you are committed to relationship wanda iyayenki suka shiga tell me?" "Babu" ta bashi amsa a sanyaye kamar me tsoron yace ya fasa kulata. "Amma dai Mace kamarki ba zata taɓa rasa suitors ba, ina da kishi beyond your imagination. Bana so nayi sharing abinda nake so da wani, that is why i hate someone saboda the person stole the most precious thing to me" ya faɗa cikin jin haushin Fatiman Yah Ahmad kafin yaci gaba da cewa If you know you are in to any relationship just call it to end saboda me guri yazo kowa ya tafi kawai" "Late comer ya kwace maka budurwa ko?" Ta tambayeshi kishi na neman kamata itama. "Forget it, kawai kiji abinda na gaya miki. Allah i will not accept sharing you with anyone. I love you fisabilillah and i want Marry you Afeeyah. I want to settle down hopely by the end of this year kuma dake nake so nayi aure will you do me the honor and be my beloved wife?" Ji tayi kamar an watsa mata ruwan sanyi, kalamansa sun shigeta har tsajiyar zuciyarta wani yamm takeji a jikinta. Cikin nutsuwa irinta wanda ya san kan soyayya da yanda ze farauci zuciyar mace a karon farko ya ringa tsarata. Tayi shiru tana sauraronsa, tayi nisa cikin hakaito kamanninsa, se ta ringa ji kamar kafin haɗuwarsu a makaranta. Sana'arsa data sani a yanzu ta bata satar amsa tabbas tana ganin fuskarsa a wasu guraren kamar posters, jikin Baburan Adaidaita sahu da sauran gurare. Ta tuna Sani Abokin Yayanta Jay ake masa dalilin son da yakeyiwa Ɗan ƙwallo Jay, amma ya akayi bata ganeshi ba? Koda yake ba wai kallon Ball takeyi ba shima shahararsa ce da kuma yanda su Yah Malam kullum basu da aikinyi se magana akansa tasa ta riƙe sunansa da fuskarsa amma kuma data ganshi a fili ya canza mata. Be rabu da ita ba seda ya tabbatar ya isa duk inda ya kamata a cikin zuciyarta kafin yace taje ta kwanta dare yayi. Be tambayeta komai akanta ba, ta ringa jin wani iri, ta sani surah da kyan fuskar da Allah yayi mata ne ya ruɗi Jay zuwa gareta idan har yasan ainihin ita wacece tabbas ze gujeta, Sanannen mutum a duniya kamarshi bazeyi tarayya da yar Talaka kamarta ba balle har suje ga batun aure. Yanda ya ringa nanata mata Hajiyarsa tana sonsa ya tabbatar mata da Mama's boy ne, yace a gidansu sunfi su Talatin, daga kuma few things daya faɗa mata akan familynsa ta fahimci suma suna da ire iren matsalolin da da yawan Manyan gidajen masu hannu da shuni wanda suka tara Iyalai da yawa suke fuskanta, wasu har a social media zakaga suna raba hali. Yanda ta fahimta suna da matsala irin ta yan ubanci a gidansu, ta tuna Ahmad shima gidansu suna da yawa amma kuma bata taɓajin ya gaya mata wata ɓaraka a tsakaninsa da yan uwansa ba, sudai Allah ya taimakesu toh. Kwana tayi tana juya maganarsa da yake ce mata "Amma kinsan san dana ganki banyi zaton zanji kinyi hausa ba because you look Asian, da akwai wata girlfriend da nayi Zoya she is from Korea amma Dad ɗinta ne Korean mum ɗinta is Arab from Iran so she has that Iranian look and Korean skin, oh my God you need to see her, i have never seen someone as beautiful as she is se ke dana ganinki kunyi kama sosai wlh tsayi kawai zata fiki". "Ikon Allah" ta fada a zuciyata bangare daya kuma haushin wai girlfriend ɗinsa da taji ya ce ya kamata har bata san sanda bakinta ya furta "Oh saboda nayi kama da Ex Girlfriend ɗinka yasa ka kulani kenan?" "Ko ɗaya, sanda nake tare da ita ma she was the one pushing the relationship and i supported her just because she was nice, Zoya was the most beautiful soul i have ever met in my life tana da kirki na ƙarshe ta so ni she really wanted to marry me kuma ko ni i lokacin idan da zanyi aure it will be her but unfortunately she lost her life in a plane crash ta tafi ganin Mamanta a Iran from London bata da lafiya tafiyan da bata dawo na kenan sukayi hatsari shekara biyu kenan and since then i remain single". Ita da kanta ta yarda akwai mutanen da kirkinsu yake sakawa dole kayi mu'amala dasu kamar Ahmad, ta kwatanta a ranta ace shi ya mutu, irin yanda taji yasa tayi saurin kawar da tunanin daga raita Washe gari dakyar ta iya tashi baccin da bata samu isashshe ba, sun daɗe suna magana da Jay a waya sannan data kwanta ta kasa bacci tayita bitar hirar da sukayi. Shida da rabi ta idar da sallah tana Azkar ya sake kiranta ta ɗaga fuskarta da murmushin da batasan ma tanayi ba suka gaisa. "Zan fita ne nace bari na fara kiran Baby na naji ya ta tashi, or you are still in bed?" Ya faɗa salonsa dake kassarata. A shagwaɓe tace "Aa na tashi nayi sallah Azkar nakeyi yanzu". "Kinyi mana addu'a ko?" Ya tambayeta ta ɗaga kai kamar tana gabansa se ya sake cewa "Zan fita Training ki kula da kanki i will call you when I'm back ok?" "Allah ya kaimu" ta bashi amsa a sanyaye dan se taji bata so ya ajiye wayar. Be sake magana ba ya kashe tana ajiyeta kiran Ahmad ya shigo seda ta harari wayar kafin ta ansa. AHMAD Yana zaune a gefen gadonsa, shigowarsa kenan daga masallaci tun Asuba kwana yayi da tunaninta, tunda ya farka da Asubar yaso ya kirata amma ya daure ya bari gari yayi haske. "Fatima, meya samu wayarki jiya taƙi shiga na kira yafi sau goma?" Ya faɗa bayan data ɗaga wayar. Muryarta a kumbure kamar me bacci alhalin haushine ya cikata tace "Bacci nayi da wuri, kuma ban sani ba ta shiga DND se yanzun dana tashi na cire". "Haba nayi mamaki duk hankali na kuma ya tashi amma yanzu na samu nutsuwa tunda lafiya kike, ya school ɗin toh?" Ya faɗa har yana sauke ajiyar zuciya se kuma tausayinsa ya kamata wato So Jarabtace wanda Allah ya dorawa kaɗai yasan wahalarsa gashi itama idan batayi da gaske ba tana neman afkawa komar wanda ze wahalar da ita. Ta miƙe tana ninke sallaya tace masa "Lafiya lau nake, ya hanya? Kun koma Kano ko can kuka kwana?" "A cikin Kano mukayi sallar Magriba ma" ya bata amsa ta haye gadonta tana cewa "Masha Allah kunyi sauri gaskiya toh sannunka" "Yawwa kema sannunki" daga nan suka ɗanyi shiru se ya sake cewa "Bari na barki zaki koma bacci ko yau weekend nima cikin gidan zan shiga na gaida Momy se na dawo na kwanta an jima idan Allah ya kaimu zanje gurin Baffa kina da saƙo ne?" "Aa, babu" ta bashi amsa se yace "Toh shikenan ki kwanta we talk later" "Bye" daga haka ta kashe wayar taja bargo dan bacci be isheta ba Badar ta fincike tana cewa "Gidan uwar wa kika tafi jiya har sha biyu wayarki kuma bata shiga?" "Not this early Badar bacci nakeji" Afeeyah ta faɗa tana sake jan bargon da taga zata takurata ta sakar mata ta janyo Hijabin data cire ta ƙudunduna duk kuma tsiyar Badar bata kula taba dan ita idan taso bacci babu abinda yake hanatayi dan mutum yaga dama ya dakko police band ya kaɗa baccinta zatayi sanin haka itama yasa ta barnta ta koma nata gadon tana cigaba da mita kafin tayi shiru tayi bacci. Se bayan Azahar da tayi wanka tana shiryawa ta lura da aika aikar da sauro yayi mata zaman da tayi a waje jiya jikinta yayi Jaa duk inda ya ciza ya tashi, Maman Minal tace "Yauma cikin flowers kika je yin waya ko? Waini Afeeya wa kika samu da ba zakiyi magana dashi a ɗakin nan ba se kinje cikin sauro?" "Bari na dawo ke kaɗai zan bawa labari Anty Zahra tunda mutane yanzu kowa boye sirrinsa yake" ta faɗa tana hararar Badar ta gefen ido, ta aje turaren hannunta da take fesawa ta kwaɓe fuska tace "Nasan idan kuka sani sena tsani kaina saboda tsokanarku duk na gama cika baki wlh So be kyauta mun ba wlh". Suna class Jay ya kirata lokacin wayar na hannun Badar ta shiga Ig tana duba styles na ɗinkin da zasuyi da bikin Anty Yusra. Ta miƙa mata wayar ta ɗaga ƙasa ƙasa tace masa "I'm in class zan kiraka in mun fita" ta kashe. "Waye kuma Jay kika samu?" Badar ta tambayeta bayan ta maida mata wayar, tayi fari da ido nace "New catch, a big fish" "Yaushe kika zama Money monger Afee?" Ta faɗa tana kallonta, Afeeyah ta zare ido tace "Daga cewa Big Fish? To na janye ni ba abinda nake nufi kenan ba matsayinsa nake kwatanta miki, Professional footballer ne a Arsenal yake wasa ma" Seta kalleta da sauri tace "You mean JAY? No you must be kidding, Afeeyaj a ina ma ze ganki yana UK kina Nigeria? bama wannan ba JAY fa Afee, yes i know you are Beautiful, kin kai a soki but JAY noooo. A yanda nake jin labarinsa he can't date Nigerian girl Hausa for that matter. Shifa ko yammatan da ake ganinsa dasu se kin kallesu kin sake, irin models din nan ne da zakiga kamar su suka yi kansu sedai idan wani ne yake so ya yaudareki da sunansa dan ko a IG kika duba accounts masu sunansa sunfi dubu ma". Kasaƙe tayi tana kallonta, koda ba laifinta bane gaskiya duk wanda tacewa JAY dai na Arsenal take waya dashi kallon batasan me take cewa ba zeyi mata amma dukda haka se tace mata "Toh Badar ina shi Bahaushene me yasa za'ayi mamaki idan yaso Bahaushiya kuma lower class irina?" "Yes Bahaushene Dan Kano nema aka ce amma abinda nake so ki duba shifa babban Celebrity ne, koda yake ke ba sabgar Ball kika sani ba amma da keda kanki idan aka ce miki shine sekin ƙaryata. Kamar fa kice min Messi ya kiraki ne ko Ronaldo". Maganar Badar ɗin ta sakata tunani domin abinda ta faɗi yakan iya zama gaskiya tunda dai ita ba sanin wancan Jay na gaskiya tayi ba haka kuma wannan sau ɗaya ta ganshi sedai tabbas akwai kamanceceniya a tsakaninsu to amma menene ribarsa idan yayi mata ƙarya da sunan wanda ba shine ba? "Dubo mun picture ɗinsa na gani indai shine zan gane" ta faɗawa Badar, seta kalleta kafin tayi dariya da alama cewar da tayi idan ta ganshi zata gane ne ya saka Badar dariyar.i "Ashe kun haɗu face to face ma? ko hoto ya turo miki?" Tayi mata tambayar da sigar rainin hankaki ita kuma Innocently tace mata "A school ɗin nan fa muka haɗu Badar ranar Monday da ace kina nan kema da kin ganshi na fito zan tafi class da safe ya tareni kuma shine wanda Sahid yace ya bawa number ranar da muna tare dake". Data fara dariya har seda hankalin Lecturer ya dawo kansu duk aka juya ana kallonsu babu ɓata lokaci kuwa ya korasu waje kuma har sannan ba wai ta bar dariyar bane guri ma ta samu ta zauna tana ci gaba da abarta dan harga Allah abin na Afeeyah mugun bata dariya yayi, Jay Afeeyah zatace ta gani a cikin ABU Zaria? Jay ne ze shigo Zaria ba tareda garin ya girgiza ba? Da ace Afeeyah na kallon Ball ko ta taɓa nuna ra'ayi akan Jay Footballer da se tace tsabar yanda ta kwallafa rai akansa ne har yasa ya fara mata gizo amma yanzu ta tabbatar wani ne yake so yayi mata wasa da hankali amma ya akayi har Afeeyah tayi falling wa cheap trick kamar wannan da sauri haka? "Bana son iskanci Badar me kika daukeni ne?" Afeeyah ta faɗa a fusace se Badar ta nuna ta tace "Da alama zaman da kikayi a waje kwana biyu kinyi gamo dan wannan maganar da kike batayi kama data me cikakken hankali ba". Ran Afeeyah ya ɓaci ta hayayyaƙo mata tace "Wato kin gama akan Ahmad yanzu kuma kin samu sabo ko? Wani Badar me kika ɗaukeni ne? Alfarma maza sukeyi mun su soni ko kuwa ban kai macen da za'a ce ana so ba?". Kafin ta bata amsa Sahid ya kwaso da gudu kamar wani ƙaramin yaro har yana ture waɗanda suke fitowa daga class ɗin alamar an gama lecture ya tsaya a gabansu yana haki yace "Afeeya i have been looking for you all round the school, na yesterday i remember where i know that Guy's face from, he is JAY Afeeya the great JAY of Gunners was in front of me but i couldn't recognised him God i was so stupid, definetly my village people are behind this misfortune but still I'm lucky and I'm happy that i gave him your number i hope he called? If yes please Afeeya do me this favour of introducing me to him as his ride or die fan wallahi....." "Sahid haba mana ya isa" ta dakatar gashi ganin maganar bata da alamar ƙarewa s zuba yake kamar wanda kanda ya ƙone, a fusace ta sake maida kallonta kan Badar dan ta ƙarasa zazzaga mata abinda ke ranta rungunar da tayi mata tareda fasa ihu kamar zata toshe mata kunne bata ko damu da a waje suke ba ta shiga tsalle tama kasa magana kamar wata wawiya se ihu takeyi. "Innalillahi Badar kinyi haukane ko yaya sakeni dan Allah karki kayar dani" Afeeyah ta faɗa tana Ƙoƙarin yakice Badar amma taƙi sakinta cewa takeyi "Da gaske JAY ne yake son Afeeta innalillahi daɗi kasheni" ta sake fasa wani ihu Sahid na tayata yana mata rantse rantsen wlh shine, yau da safe ya kalli Recap na wasansu kawai ya ganshi shine ya tuna "Amma taya akayi ya shigo harya fita babu wanda ya ganeshi se ku biyu?" Badar data tsagaita da ihub ta tambayeta, Afeetah tayi tsaki tana tafiya tace "Seki nemo shi ai ki tambayesa, ni taya zanyi na sani?" a gurin ta barta saboda haushi ta tafi Hostel tana tafe ranta na suya akan abinda Badar tayi mata so takeyi dagaske ta yarda izgilanci yasa take mata irin waɗannan abubuwan amma zuciyata ta gaza karbar hakan. Da gudu ta bi bayanta dan tayi nisa sosai, ta rungumeta har suna shirin faduwa tace "Haba mana Afee wai fushi kuma kimayi?" wai dan Allah dagaske kin hadu da JAY? Kedai kina da sa'a Afeeyah ga Ahmad yanzu kuma ga Jay kin samu, na daɗe ina crushing akan JAY amma nasan nisan dake tsakanina dashi kamar nisan sama da ƙasa ne shiyasa na sahalewa kaina Afeeya ke me sa'a ce kina zaune yazo har inda kike ya tarar dake na miki murna Allah ya sakamu a danshinku Miji kam se kin zaɓa kin darje" ta faɗa idonta suna kawo hawayen da batasan na menene ba. Wani iri taji, can kuma haushin cewar da tayi Jay crush ɗinta ne shi yasa ta tureta tana cewa "Ni dalla cikani, me kika gama cewa? ban kai kalar matan da yake kulawa ba wani ne yake mun ƙarya dashi" "Afee ki fahimce ni, wlh ruɗewa nayi. Kamar fa nace miki Shahrukhan ya kirani yana sona dan Allah zaki yarda kai tsaye?" ta faɗa da iyakar gaskiyarta, Afeeyah ta fincike hannunta tana cewa "Ai ni ba shahrukhan nace miki ba, Jafar nace Bahaushe kamata dan Kano kinga kuwa ko sarkin ingila ya zama ba abun mamaki bane dan ya so wadda suke da tushe daya. Sannan naji kamar kince crush ɗinki ne ko? Gara da kika faɗamun tunda wuri ba se anyi nisa kizo kina mun ihu da hayaniya a gaban mutane a kansa ba saboda kishi. Zan gaya masa kina sonsa Allah yasa ki masa tunda yanzu na gane ko Nurain da kike mun masifa kina hanani haɗuwa dashi ashe son sa kikeyi". "Karki gaya mun maganar banza Afeeya saboda ma kinga ina lallabaki shine zaki ringa botsarewa bafa ke kadai kika iya tijara ba" Badar ta faɗa tana ja baya yanda fuskarta ta nuna lallai taji zafin abunda Afeeyah ta faɗa mata. Itama seta riƙe ƙugu tana kallonta ta sake cewa "Na faɗa ɗin ko ba haka bane? Duk sanda Nurain ze kirani kin ringa baƙin rai kenan kina bin bini se kinji me muke cewa ba zaki taɓa barina na fita gurinsa ni kaɗai ba haka Ahmad a koda yaushe cikin gasa mun magana kike kina nuna ban kai ba Alfarma yamun daya soni haka kullum cikin yaba kirkinsa kike da nuna da zaki samu kamarsa ba zaki tsaya sokonci iri na ba and now Jafar kai tsaye kin gaya mun he is your crush duk hakan me yake nufi Badariyya?" "Meye haka Afeeyah lafiya kuke taaye kuna hayaniya akan hanya? Abdurrazaƙ course mate ɗinsu daya ƙaraso gurin ya faɗa. Badar data kasa cewa komai tunda Afeeyah ta fara magana ta tsaya kawai tana kallonta ta sauke ajiyar zuciya kafin jiki babu kwari ta fara tafiya ta barsu a tsaye. "Yanzu Afeeya saboda abun kunya keda Badar za'a gani kuna faɗa a kan hanya? Ai koma me ya haɗaku kamata yayi kuje ɗaki ku sasanta amma ba anan ba gaskiya kun bani kunya kuma da alama kece bakida gaskiya dan naji wasu daga cikin maganganun da kikeyi" Abdurrazaƙ ɗin ya sake faɗa. Ajiyar zuciya ita ma ta sauke, bata ce masa komai ba ta juya itama ta tafi, Ribadu Hall ta shiga gurin Islam, ƙawartace tsohuwar Roommate dinsu kuma. Ta kwanta akan gadonta duk tana jin babu daɗ kuma akan abinda ya faru amma ta rasa abinda yasa ta kasa controlling kanta duk abinda ya tunzurata kuma cewar da Badar tayi Jay crush ɗinta ne sosai takejin zafin abin a ranta har sannan akan me zata faɗi haka bayan da tasan suna waya kuma hakan yana nufin maganar So ta shiga tsakaninsu? Islam ta dafa Indomie ta juye a plate kafin ta hau gadon tana cewa "Tashi muci, in Badariyyah na ganki ke kaɗai? Koda yake nasan faɗa kukayi. "Naqoshi, kuma wayace miki faɗa mukayi?" "Ai tunda na ganki ke kaɗai kinzo kin kwanta kamar Manja daman nasan da walakin indai ba bata school ba to faɗa ne kawai zesa ba'a ganku tare ba kuma kece da laifi wato har yanzu dai ba zaku canza hali ba kamar kaji kullum se kun raba hali? Da ana ganin kamar kece abar tausayi Badar ce rigimammiya se wanda ya zauna daku ne ze gane halinki tsaf Afeeyah baki da daɗin sha'ani idan baki so ba" Ƙaramin tsaki tayi tace "You know how Badar can be annoying, rainin wayonta ya fara yawa wlh shiyasa nake kasa yin shiru yanzu" "Yes i know, amma Afeeya kin fita zafin kai maganar ta gaskiya. Na san Badar da faɗa amma da wuya tayi akan rashin gaskiya ke kuwa kina sane kike fitittikewa kiyi abu duk kuma yanda mutum ze nuna miki kuskurenki se kinga dama zaki yarda" Islam ta faɗa calmly. Afeeyah tayi shiru dan tasan gaskiya ta faɗa ko a gida haka Ummansu take cewa tanada rikicin gangan kamar yanzun dai in dai gaskiya ne be kamata maganar Badar ta batamata rai ba amma bata san me yasa take hasala ba duk sanda irin hakan ta hado su dukda cewar koda da gaske tana goranta matan ne batayi ƙrya ba, bata kai matsayin da Maza masu Aji kamar Ahmad da Jafar zasu ringa karakaina akanta ba. Ko a layin ƙawance tsakaninta da Badar ɗin kanta akwai tazara matsayinta na yar Ex Sanetor ita kuma ɗiyar me gyaran mota. "Ke kika takaleta ko?" Islam ta sake tambayarta, a taƙaice ta faɗa mata yanda sukayi da abinda ya haddasa faɗan, "Ke ɗince ai baki iya magana ba Afeeyah ga rashin fahimta kuma da gangan kikeyi" "Yanzu ko wani ne yace miki Badar zata so saurayinki Afeeyah seki yarda balle harke da kanki ki ringa wannan tunanin? Gaskiya kin bani kunya lamarinki kuma ya fara shallake hankali. Tabyaya kina zaune da ita for good three years amma ace babu trust a tsakaninku? kin taɓa kamata da laifin cin Amanarki ko me da zaki ringa wannan tunanin akanta?" Islam ta faɗa cikin fushi kamar wata Mamanta. Ta girgiza mata kai alamar Aa kafin tace "To amma Islam aikin san yanda kullum take mun akan Ahmad, ke kanki shaida ce tasha faɗar da ita ta sameshi da tuni wata maganar akeyi yanzu ba wannan ba" "To ai ko ni zan faɗa miki wlh dani Ahmad yake so Afeeyah da yanzu na haihu ma a gidansa, dan bazamu rufa six months da haɗuwa ba zamuyi aure. Ke kinsan yanda samun Nagartaccen Mijin aure yayi wuya kuwa? Ki ajiye maganar wasata samun me nutsuwa wanda idan ya aureka ze mutuntaka ya mutunta iyayenka ma kaɗai sunyi wuya balle harda Bonus na Tsabar dukiya ga kyau ke kuwa me kike nema a duniyar nna da baki samu ba kike ta bulayi? Let me be prank with you Afeeyah, ki ga wannan Jay kikace ko waye da kika samo yes babban mutum ne world class Celebrity, you can flight with him and get popularity amma zancen aure tsakaninku Afeeyah karki fara saka shi a ranki. Tabbas Allah yakan haɗa soyayya tsakanin duk mutanen da yaso matsayi ko wata nasaba ba zata zama togaciya ba amma kece kike yawan faɗin kin fi so ki auri Miji daidai ke wanda babu me miki kallon kwaɗayi ya saka kika aureshi ko kuma a ringa ganin yafi ƙarfinki, idan ban manta ba kince mun dalilin daya saka baki bawa Ahnad dama ba saboda kina ganin tazarar dake tsakanin Families ɗinku kamar idan maganar aurenku ta tashi za'a iya samun matsala shine yanzu kike so ki saka kanki a soyayyar wanda criticism na fan kaɗai ya isheki kafin aje ga nasa Familyn da baki san waɗanne iri bane ba? Think twice, Afeeyah, kiyiwa kanki Hisabi kafin ki fara abinda zakizo daga baya kina dakin sani. Samun Ahmad da yardar Ahalinsa seya fi miki sauƙi akan wannan sabon mutumin da naga alamun kinyi nisa a cikin soyayyarsa. Kinsan Ahmad kin San duk abinda yakeyi, yana mutuwar sonki idan kika aureshi wlh kin gama dacewa dan kin samu mijin kerewa sa'a amma wannan ɗan ball da kike hasashe kinsan yaya ɗabi'unsa suke? Shin yana da hali me kyau ko kuwa? ace duk kin tabbatar da wannan kin ma kin aureshi wlh yanda kike da bala'in kishin nan iyakar matan da zasu ringa bibiyarsa kaɗai se sunsa kinyi mutuwar tsaye. Soyayyar da kike kwaɗayi ba zaki sameta ba kuma baki isa kiyi ƙorafi ba yana da damar yin duk abinda yaga dama. Ya rage naki kiwa kanki karatun ta nutsu tunda wuri, sannan tun wuri idan kin tabbatar ba auran Ahmad zakiyi ba to ki bar mana filin mu gwada sa'armu tunda ke kanki baya kawo wuta dakyau, lissafinki a gaba a baya kikeyinsa". Ido Afeeya ta zubawa Islam tana auna duk wata magana da take fada amma da kyakykyawan ma'auni bata bari zuciyarta ta kawo mata shirmen data saba ba dan idan haka kawai ne tsaf zata fassarata akan kawai tana so ta rabata da Jafar ne maganar ta ta ƙarshe ta saka ta zabura jin wai ta barsu su gwada sa'arsu akan Ahmad. Tayi rau rau kamar zata saka kuka tace "Duk ku ba zaku gane ba" "Daman ba zamu gane ba mana se ke da kika sakawa kanki abinda yafi ƙarfinki kece zaki gane ai" Islam ta faɗa. Afeeyah tayi shiru me tsayi tana saƙa da warwara. Tabbas auran Ahmad ze fi zama abu me sauƙi fiye dana sabon masoyinta. Amma Jafar take so, ta yarda zuciyarta ta mace akansa Ahmad kuwa koda ta aureshi sedai ta zauna dashi tukuicin kyautatawarsa gareta da iyayenta. Cikin rauni tacewa Islam "Amma yana sona, shifa ya tareni kuma ya nemi number na ya kirani yace yana sona aurena zeyi" "Shi wa?" "Jafar" "Afeeyah kenan, daman zece yana sonki mana, kuma zata yuwu da gaske yakeyi amma kuma ba iyakar son ba kiyi tunanin me soyayyar zata haifar miki? Amma tayaya za'ayi mutumin daga haɗuwa lessthan sati guda ki kamu da soyayyarsa har haka? Ko daman kin sanshi ne?" Islam ta tambayeta. Ta rintse ido fuskar Jafar nayi mata gizo kafin ta buɗe tace PAGE 14 "Ban san shi ba ban kuma taɓa ganinsa ba se ranar. Ni kaina Islam bansan ya akayi ba na kamu da sonsa har haka ba. Ta yuwu kodan yayi daidai da tsari da kuma mafarki na akan Abokin rayuwa shiyasa" "Kiyi addu'a idan da Alkhairi a tsakaninku Allahya tabbatar amma ki cire son rai a yayin da zaki nemi zaɓi a gurin Allah kuma ki dena wannan halin na zargin wata zata kwace miki abinda kike so sannan ki lallaɓa Badar wlh Afeeyah samun mutum da ze soki tsakani da Allah kamar ita a yanzu yana da wahala" "To ni yanzu taya zan bata haƙuri kinsan dai Badar sanda kake lallaɓata sannan zata botsare ta fara rashin mutunchi ni kuma ba zan jure ba sena tanka mata" "Tunda kece baki da gaskiya kuwa haka zaki yi shiru ko zaginki zatayi, yanzu ki kirata tazo nan ku sasanta tun wuri ma ba se kun koma ɗaki ku sake raba hali ba a ringa yawo daku a baki" Islam ta sake faɗa ta kalleta da son jin ƙarin bayani ta yamutsa fuska tace "Eh mana, ce miki akayi duk wanda kake dariya dashi me sonka ne tsakani da Allah? A aji ranar ina jin Ummi na hirar kuna ce mata tana yawo bayan kuma abinda kukeyi kenan ko kuwa samarin da suke kashe muku kuɗi ƙannen babanki ne da zasu ringa muku bauta ba tareda suna benefiting komai a gurinku ba" Take ta sake hasala tace "Ita Ummin take cewa haka?" "Bana faɗa miki bane saboda kije kiyi tashin hankali, ke matsalarki kenan bakya cin ribar zance da an faɗi abu kamar wuta fuu zaki tashi se daga baya kizo kina regretting action naki I'm only telling you so that kusan zaman da kukeyi da kowa kuma ba komai zakuci gaba da sakin baki duk sirrinku kuyi ta faɗa a ɗaki ba, ai dai tun muna tare nake muku wannan faɗan daga ke har Badar kun fiya saurin yarda da mutane baku da sirri". Tilas ta kira Badar dan ta yarda da gaske bata kyauta ba ta ringa bata haƙuri bayan tazo, Badar bata da ruƙo, sha yanzu magani yanzu ce dan haka take ta zazzage mata abinda yaje ranta maganar ta wuce. Ta dai gaya mata wlh koda wasa ta sake maimaita mata abinda tayi zata nuna mata bawai bata da zuciya bane ko kuma ita kaɗaice me baƙin rai, zata fita a harkarta dan bazata cigaba da zama da ita Alhalin zuciyarta bata aminta da ita ba. Gurin Islam suka wuni, Badar bata iya boye abinda yake a ranta tayiwa Afeeyah murna akan Soyayyarta da Jay amma tace "Afee karki sakashi a ranki sosai saboda gudun abinda zeje ya dawo. Muyita addu'a idan shine Alkhairinki Allah ya tabbatar amma magana ta Allah nafi sonki da Ahmad sedai idan kuma za'abi ta suna Jay ɗin nan fa ze ɗaga mana aji, ganinmu za'a ringayi muna cafkewa da world class Celebrities, Allah kenan sega Badar zata haɗu da JAY a ɓagas, kinga su MESSI duk zasu zama Abokanmu wayyo Allah na" suka ringa dariya, Afeeyah jinsu takeyi ta tabbatar gaskiya suke faɗa mata amma kuma zuciyarta ta rigada ta afka ga koginda fitowarta se anyi da gaske. ****************** "Naziru kalleni dakyau nayi kama kama da wawiya da zaka zauna kana tsarawa wannan zancen na kama? Ni ba surutun banza da iska nake so naji ba, kuɗina zaka bani maza ka zuba munsu anan" ta warware ƙaramar Ghana Must Go dataje da ita kafin taci gaba da cewa "Maza maza kana ɓatamun lokaci daga nan janguza zanje an yanka wasu filaye zanje na siye na ajiye abuna tunda lamarin ƙannenku babu Allah yan iskan yaya sun zama ɓarayi, yaron nan Faisal da Jafaru yaƙi bashi kuɗin shine yabi dare yayi mun sata, ni banma san nawa ya ɗauka ba dan lissafi ya kwace mun tunda naga haka nace toh ba yanzu ya saba ba, daman na daɗe ina ganin kuɗin nayin ƙasa se in ɗauka ajiya ce ta saka sikayi laushi. Kuma fa kwana suke cikin sanyi yanda kace, kaji ɗakin kuwa kamar dusar Ƙanƙara zata zubo....." "Haba Hajiya, ki tsahirta mana karki ƙware" Naziru ya dakatar da hajiyar dake ta zuba kamar nunanniyar kanya kafin yaci gaba da cewa "Na gaya miki Hajiya yawan shige da ficen da kuɗi sukeyi a personal account ɗina yana neman ya jawo mun matsala. Kinsan dai yanda EFCC yanzu suke saka idanu kan duk wani motsin manyan kuɗi a ƙasar nan, na gaya miki ba'a account ɗin company suke ba kuma ko a nan ne ke account ɗinki idan aka tura kuɗaɗen nan wlh suna iya rufeshi azo bincike ki saka kanki a matsala. Haƙuri zakiyi kamar yanda nace zan ringa ciresu a hankali ana juyawa se a ringa tura miki da kaɗan ko Miliyan ɗaya ce duk wata". "Ai shiyasa nazo da jaka tashi zakayi mu tafi bankin ka ciremun kuɗina na gaji da wannan ƙarairayin naka kullum bayan Alhaji Zakariyya ya gaya mun ya karɓi nasa ni kake so ka cuta kenan ka cinye mun kuɗi to baka isa ba" Hajiyar ta faɗa cikin ɗaga murya. Naziru ya dafe kai, ya rasa bayanin da zeyiwa Hajiya ta fahimceshi, saboda Allah tayaya ze tura mata Miliyan ɗari uku ko kuma ya cirosu ya zuba mata a Ghana Must Go a wannan halin da EFCC ta matsa ko da account ɗin kamfani cikin takatsan tsan suke abubuwa balle aga kuɗi irin haka suka fita daga personal account ɗinsa ai tona masa asiri zatayi. "Hajiya shima kayan kuɗi ya karɓa ba zallarsu ba kuma kiyi haƙuri ki dena ɗaga murya mutanen gidan sunajinki" ya faɗa a tausashe. Ta zabga masa harara tace "Ni kuɗi na nake so, waima kayan uban wane kuɗi kuke magana akai kamar wasu marasa gaskiya haka yace mun wai kaya ya karɓa su kayan basu da suna ne bayan Mai akwai abinda ka fara siyarwa ban sani bane da ake samun kuɗi saboda mugunta baka gaya mun ba balle na gwada nima?" "Zinare ya karɓa na gaya miki na fara haƙar zinare a Zamfara ai" "Dan ubanka da akace dutse yana ruftowa mutane so kake ka mutu saboda rashin godiyar Allah zaka zurƙuma cikin rami wai haƙar zinare Naziru?" Hajiya ta faɗa tana zare ido kamar ance mata dutsen ya rufta dashi. Ya kalleta, da ace watace daban daya tambayeta a duniya waya kaita son zuciya amma uwarsa ce duk iskancinsa baze kwatanta haka ba se yayi murmushi yace "Bafa da kaina nake shiga ba Hajiya kamfani ne suke haƙan da injina kuma jari kawai na saka ina karɓan ɗanyan gold se na fitar a sarrafashi" "To nima ina so a saka kuɗin, amma ni idan an haƙo gida za'a kawomun abuna in ajiye se yayi tsada sannan na fitar na siyar sarƙoƙina ma zan kwashe su idan zan tafi Umarah Turai tace sunfi daraja yanzu acan zan siyar se in baka kuɗin a ƙara jarin yanda za'a ringa samu da yawa. Wallahi fa ance kuɗi akeyi sosai da harkar nan, kaga yaro bashi da ko taro amma dayaje ya shiga rami ya dawo kaga ya zama Miloniya wannan tubda da Inji nema za'a haƙo sedai muna zaune muyita karɓar kaya toh haka za'ayi, amma bani ko Goma ce yanzu na tafi da ita dan na saka rai zan siyi filayen nan har nace a dubamun na bakin Titi zasu fi daraja idan an kwana biyu". Naziru ya sauke ajiyar zuciya jin ya tsarata kuma ta hau kafin ta sake botsarewa ze san abinyi. Dole ya shirya suka fita Banki ya cire 10M aka saka mata a Ghanarta ko tsoro bataji ta haye Napep wai ta tafi Janguza, dayace ze kaita cewa tayi Aa, a dabararta karyaje yaga inda Filayen suke. Yakubu sau biyu yana sace mata Takardun Manyab Fikaye yaje ya siyar, dake bata mantawa da komai nata har gewaya take zuwa taga lafiyar kadarorinta ɗaya taje taga an yi gini har An saka Amarya ɗayan kuma Plaza akayi tayi masifar tayi bala'in ƙarshe tayi Allah ya isa dan Yakubun taurin kaine dashi kamar me kuma hauragiyarta ba tsorata shi take ba, sa'idar data samu yanzu matsayinsa daya ƙaru a Kamfani, sedai shegen Yaron kamar yanda take faɗa kansa kawai yake Azurtawa. Ko sun so ayi cuwa cuwar da aka saba ya kankane komai ya hana ta tabbatar idan suka matsa kuma kamar yanda yake cewa tsaf ze fasa ƙwai, rabuwa dashi tayi yanzu amma tana nan zatayi maganinsa yanzu maganar auran Hajiya ƙarama data taso ce a gabanta daia Abba Tee har iyayensa sunzo anyi tambaya shima Yakubun Aure zeyi. AFEEYAH Sannu a hankali soyayya da shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakaninta da Jay, wani irin so take masa da bata san iyakarsa ba, kodan ya dace da duk wani mafarki nata akan Mijin da take so t aura ne oho? Ahmad da kansa ya gane cewar akwai wani al'amari a gabanta wanda ya sake karkatar da hankalinta daga kansa saboda yar hirar da yake samun dama sunayi ma yanzu gagara takeyi, duk sanda ze kirata uzuri zata bashi na tana wani abun musamman da suka fara Second semester exam daga tace masa karatu takeyu se ta gaji zata huta alhalin lokacinta karankaf yanzun na Jay ne, karatun kansa ba wani mayar da hankali takeyi kamar da ba da idan akace zasu fara exam da sati ɗaya ma ta dena hawa Social media tattara hankalinta take tsaf har se sun gama sannan to wannan karon kuwa se a hankali, idan tana waya da Jay manta kowa da komai takeyi bata ma son abinda ze katseta se su raba dare suna magana har se da kansa yace ta kwanta tayi bacci dan bata faɗa masa ma mun fara exam ba seda sukayi guda huɗu ya rage uku su gama sannan ranar kuwa tasha fada ta kuma ƙara tabbatar da Jay baya ɗaukar nonsense dagaske kamar yanda yake cewa. Har yajin kiranta yayi na wuni guda aikuwa taji a jikinta dan ya mata mugun sabo da soyayyarsa me tsayawa a rai. Jay ya iya soyayya, ya iya saka mace ta manta kanta duk taurin zuciyar Mace idan ta shiga hannun Jay tilas ta sallama dan yasan duk wani lago na mace da ze karya ta dashi, ita da kanta ta kance salon Jay da Ahmad yana kama. Tabbas da ta bawa Ahmad dama ta buɗe masa zuciyarta ze mallaketa tsaf ta yanda wani baze samu matsuguni ba amma ta rasa abinda ya hanata yin hakan, ta yuwu dalilin zuwan Jay ne, wani lokacin se taji muryoyinsu har kamanceceniya yake mata kawai dai ta Jay tafi ta Ahmad tashi, haka idanunsu iri ɗayane, seda tayiwa hoton Jay kallo na tsanaki ta fahimci haka idanunsu iri ɗayane, shape ɗinsu, kalar kwayar idon da komai Badar tace mata wai Sexy Eyes kenan masu irin idanun sun iya soyayya kuma dasu suke cafke zukatan Yammata ta yarda da hakan dan bata iya haɗa ido da Ahmad se taji gabanta na faɗuwa duk sanda ta kalli idonsa ji take kamar ta sallama masa amma taurin kai irin nata ya sa har aka kawo i yanzu. Saura kwana biyu su gama Exam ranar Ahmad ya kirata, kwana biyu ya bata space tunda tace masa Exam sukeyi idan ya kira bata ɗaga ba kota amsa ta bashi uzuri sosai ransa yake sosuwa shiyasa ya zaɓi daya barta ta gama exam ɗin idan har da gaske itace uzurin daya saka baya samun lokacinta. Tana kwance duk batajin daɗin dalilin yajin kiran wayar da Jay ta daka mata, tunda ya fahimci Exam suke kuma take wasa da karatunta tana biye masa shine yayi fushi. Ya gaya mata baya son mutumin da bashida focus, yana sonta amma baze taɓa haɗa lokacinta da Aikinsa ba me yasa ita zatayi wasa da Karatunta saboda shi? Yace baze sake kiranta ba se sun gama kuma ta tura masa da Time table sannan idan ma ta kirashi baze amsa baz kullum da safe ze mata text haka da rana da dare amma babu phone call saboda magana dashi yasa takeji kamar wata mashashshara ce ta kamata duk ta rasa gane kanta. Tana ganin wayarta na ringing ganin Ahmad ne kamar ba zata amsa ba se kuma ta ɗaga dalilin tunanin da tayi a ranta, tabbas Alhakin Ahmad ne tun ba'a je ko ina ba Allah ya jarabceta da Jay. A sanyaye suka gaisa daga ita harshi babu wani me karsashi, "Yaya Exam ɗin? Saura guda nawa ku gama?" Ya kauda shirun da sukayi bayan gaisuwa ta bashi amsa a taƙaice da "Lafiya lau, saura biyu" "Masha Allah, Allah ya bada sa'a" daga nan suka sakeyin wani shirun. Ya sani idan zasu kwana a haka ba lallai ta sake cewa komai, wlh daze iya da ya rabu da yarinyar nan dan duk wata hanya da mace zata nuna bata ra'ayin mutum ta nuna masa amma zuciyarsa ta kasa haƙura da ita. A kullum cikin Addu'a yake akan idan babu Alkhairi a tarayyarsu Allah ya cire masa ita daga zuciyarsa ya musanya masa da wadda ta fita amma abun kamar ana rura wuta ƙaruwa yakeyi. Idan Jafar yana bashi labarin sabuwar soyayyar daya gamu da ita se yace shi kam bashida sa'a ne a soyayya da Alama. Bega Yarinyar da Jay yake so ba, amma yanda har Jay yake labarinta ya sani ba ƙaramin sonta yakeyi ba itama kuma tana riritashi, ze iya cewa be taɓa ganin Jafar a yanayi na soyayyar gaskiya irin wannan ba, yace masa auran yarinyar zeyi, Bahaushiyace yar Nigeria a Zaria suka haɗu. Yaƙi ko gaya masa sunanta dayace ya tura masa hotonta ya nunawa Fatima ko ta santa nan ya fitittike ya ringa zuba masa Tijara yace kuma baze tura ba se ya dawo zasuje ya ganta face to face ko sunanta baze gaya masa ba balle ya faɗawa Fatiman. "Tana da Friends haɗaɗɗu irinta zan samo maka guda ɗaya ka fita daga sabgar waccen Ajawon Fatiman da take wahalar da kai Yaya Ahmad" abinda Jay ya gaya masa. Ahmad yaja numfashi, kusan minti bakwai daga shi har Fatima babu wanda yace wani abu. A sanyaye yace "Fatima, idan wani laifi nayi miki kiyiwa girman Allah ki sanar mun na baki haƙuri, na gaji da azabatar da zuciyata da kikeyi kusan sati uku kenan kin hanani zaman lafiya nace zanzo kince Aa, idanna kiraki a waya koda yaushe cikin bani Excuse kike me nayi miki? Idan maganar kai gaisuwa da nayi ce kince Aa kuma na haƙura bayan wannan wane laifi nayi miki da kike hukuntani ta hanyar azabtar da zuciyata haka?" A maimakon ta sassauta se maganganunsa suka sake ƙukar da ita, ta tsani Namiji da bashida ra'ayin kansa se abinda mace tace yayi wannan yana daga abinda bata so da Ahmad yanda yake mata wani lako lako kamar ita ce Namijin shine macen, to tun yanzu baya iya taɓuka komai daga abu ya haɗa m Su ya fara kamar zeyi kuka yana lallaɓata idan sunyi auren kenan baze ringa tsawatar mata ba idan tayi masa laifi. Haɗuwarta da Jay tasa ta ƙara fahimtar banbancin Namiji da muna Maza, duk yanda yake nuna So ta yake riritata idan tayi masa abinda be gamshe shi ba murɗewa yakeyi ita ce zatayi ta lallashinsa da ban baki kafin ya sakko kamar dai yanzu daya yi fushi saboda bata maida hankali akan Exam ɗinta ba ta tabbata da Ahmad ne tsayawa zeyi yana lallashinta akan tayi kaza ko kartayi. "Dan Allah Fatima ki tausaya mun. Na sani bakya sona Alfarma kike mun ina roƙon da ki daure kici gaba, ki dubi kalar jarabawar da nake ciki ta Sonki ki tausaya mun. Wlh Fatima da zan iya da tuni na cireki daga raina na rabu dake, koda baki taba buɗe baki kin gaya mun ba nida kaina nasan bakya sona kina kulani ne kawai saboda wulaƙnta ɗan Adam ba tarbiyyarki bace kuma na gode da hakan. Bazan gaji da roƙonki na akan ki bani dama, ki bude mun zuciyarki ko yaya ne in Allah ya yarda ba zakiyi nadamar tarayya dani ba" Ahmad ya sake faɗa a sanyaye. Zuciyarta tayi rauni da jin abinda ya ke cewa, wato shi da kansa yasan bata sonsa amma ya gaza haƙura da ita tashi jarabawar Sonta ita kuma tata Son Jay Allah kenan. Ajiyar zuciya ta sauke na shaking tace "Nifa Ahmad ba haka bane ba, na gaya maka exam mukeyi ina buƙatar isashshen lokaci saboda nayi karatu shiyasa duk wani waya da wani chat na ajiye su amma mun kusa gamawa nan da Three days In sha Allah". Yayi murmushi da jin abinda tace shima yace "Ranar Thursday kenan zaku gama?" Ta yatsina fuska kamar yana kallonta tace eh, se ya sake cewa a sanyaye "To yaushe zaki dawo Kano?" "Paper safe ce, in har na gama komai kafin 12 ma zan taho a ranar in Allah ya yarda" "To nazo na ɗakko ki?" Ya faɗa da sigar roƙo kamar wani me magana da ogarsa a gurin aiki, bata san sanda tsaki ya subuce mata ba tace "Zan dawo da kaina, kasan Baffa ya hana ai ka ringa barin aikinka kana tahowa hidimata". "Dan Allah Fatima karkice Aa kar kuma ki jingina maganar nan da Baffa sedai idan bakya sone kawai sena haƙura" ya sake faɗa gwanin ban haushi kuma ban tausayi kamar ze mata kuka, babu yanda ta iya haka ta yarda akan yazo ya ɗauketa, ita kanta zata ji daɗin hakan saboda hutun Session ne zata tafi da duka kayanta. Ya ringa zabga mata godiya kamar wanda tayiwa kyauta daga ƙarshe sukayi sallama bayan ya sake roƙarta akan dan Allah ko sau ɗaya ne a rana idan ya kirani ta ringa amsawa gaisawa kaiwai zasuyi baze ja mata lokaci ba tace Toh. "Allah sarki Ahmad, wlh yana bani tausayi na daɗe banga soyayya me zafi irin wadda yakeyi miki ba Afeeyah,dan Allah ki tausayawa mutumin nan yaci Albarkacin so wlh na tabbatar ba zaki yi nadamar auransa ba saboda yana sonki" Badar ta faɗa, Afeeyah ta hararaeta tace "Kyaji da fuska biyunki anjima idan Jay ya kira waya jikinki na rawa zakiyita karaɗi kina bashi assurance na ze sameni ke ga campaign coordinator kuma se na gaya masa abinda kike cewa yanzu" "Amma Thruth to be told Afeeya wlh Ahmad yafi sonki, ki gani fa shekara biyu yana binki kina jansa a ƙasa na tabbata Jay baze ɗauki haka ba Mace ta ringa wasa dashi kamar wani Toy, da yanzu ya daɗe da sallama ki" Badar ta sake faɗa. Afeeyah ta tashi zaune daga kwanciyar da take tace "To ai banbancinsu kenan shi yasan mutunchin kansa baze zauna a ringa wulaƙantashi akan abinda yafi ƙarfi ba shi kuwa Ahmad kamar mara zuciya ke nifa ba zan auri Mijin da zan ringa juyawa ba ga yan uwansa basa sona naje ana wulaƙantani baze iya tsayawa ya kwatar mun yanci ba". Badar tayi kasaƙe tana kallonta amma ta haɗiye abinda tayi niyyar cewa ta canza maganar da wata tace "Yawwa, nikam kinsan Familyn Jay ne?" kai ta girgiza mata tana cewa "Aa, me yasa kika tambayeni?" Tayi ajiyar zuciya zata yi magana kenan Ummi tayi sallama ta shigo, ciki ciki ta amsa fuska a ɗaure Badar ce ta tambayeta ya Exam ita kuwa ta zari Bucket ta fita dan tun daga ranar da Islam tace mata tana faɗar maganganu akansu ta washsheta, bata son munafukin mutum, idan ta yarda dakai kayi breaking trust ɗinta shikenan kuma. A gurguje tayi wanka ta shirya dan har Badar ta shirya zata fita Library tace ta jirata suje tare. Maganar da suka fara ɗazu na rantaso take taji dalilin daya saka Badar ta tambayeta ko tasan Familyn Jay dan yanayin da tayi maganar ya nuna akwai wata a ƙasa. A Frizlers sukayi Lunch, tana kallon Badar dake ƙarasa cin abinta tace "Ɗazu kina tambayata akan Familyn Jay?" tasha ruwa ta goge bakinta kafin tace "Oh yah nace kin san wani abu akansu kuwa?" "Nace miki ai ban sani ba, wani abu ne ya faru kuma?" Ta tambayeta tana yatsina fuska, Badar ta gyara zama tace Ranar Monday da naje office din Yah Sani (Abokin Yayantane ta ne da yake Lecturing anan) kinsan na gaya miki na taɓa ganinsa sunyi hoto da Jay sanda yaje Masters Uk hoton na office ɗinsa shine ina zuwa da na gani maganarku ta faɗo mun a rai nave masa two weeks ago Jay yazo school ɗin nan, he was suprised yace mun wai ya akayi na sani, then i told him about your encounter kinga mamakin da yayi kuwa? Ashe Mamansa da Maman Jay cousins ne shima suna bala'in shiri sosai gurinsa ma yazo nan Zaria kwanan sa ɗaya ya wuce babu wanda ya san yazo dan da daddare ya shigo kuma a gidansa ya sauka da safen daya fito ma be san inda yaje ba kuma harya tafi babu wanda yace masa ya ganshi then he asked me wai waye Dad dinki a Nigeria da har Jay yace yana sonki?" "Ban gane ba?" Afeeyah ta katseta fuskar ta na nuna alamar confusion, Badar taci gaba da cewa "Nima abinda nace masa kenan, to cut the story short Afeeyah abinda na fahimta Mamarsa yar Jari hujja ce, Yah Sani ya gaya mun Jay personally bashi da matsala, and tunda yace yana sonki dagaske yake yi amma inda matslar take mawuyacin abune Mahaifiyarsa ta yarda ya aureki saboda a duniya idan da akwai abinda ta tsana be wuce Talaka ba. Yaranta auran Jari take musu kuma babu wanda ta ɗora buri akansa Irin Jay saboda tafi sonsa duk cikinsu matsayin da yakai yasa ta tattara duk wani burinta na duniya akan matar da ze auro, ita a sonta cikin turawa ko larabawa zeyi aure ai kinsan Shahida Anchau ko?" Ta jefo mata tambaya, ruɗu da tashin hankalin da ta shiga yasa dakyar ta ɗaga mata kanta da yayi nauyi Badar taci gaba da cewa "To Mamansu babu yanda batayi akan a haɗa auransu da Shahida ba kinga dai Abbansu kafin ya rasu yayi kuɗi kamar me kuma har yanzu Mamansu kanta tana da kuɗi amma wai Maman Jay taƙi, ba Shahida kaɗai ba yace a Familynsu babu daga gidan da ba'ayi masa tayin aure ba amma taƙi bari ya karɓa. Ki ga dai Familyn ANCHAU duk Kaduna babu wanda be sansu ba saboda tsofaffin kuɗine, arziƙinsu tun duniya na kwance har jikokinsu ba lallai suyi talauchi ba amma Mahaifiyar Jay ta raina su tace bataga yar da ta dace da shi a ciki ba. Ni wlh mantawa nayi ma tunranar ban gaya miki ba se yau abin ya faɗo mun a rai nace masa ma zamuje tare ya faɗa miki da kansa kafin ki ce hassada nake miki ko ƙarya na shirya saboda na rabaki dashi". Ƙasa Afeeyah tayi da kanta tanajin wani abu nayi mata yawo tsakanin ƙirjinta da maƙoshi yaƙi wucewa yayi ƙasa kuma yaƙi haurowa ya fito. Wato kallon yar masu ƙumbar susa Jay yayi mata saboda ya ganta fara ƙal kalar madara ya shaƙi ƙamshin designer turare a jikinta ga Hijabin Crep yard da Ummu-Maheer tayi mata ze tsammaci irin yan Turkey ɗinnan ne ko Egyptian shiyasa yake sonta? Kenan wannan ne dalilin da ya saka yake yawan kawo mata labaran ƙasashen duniya idan ta nuna bata sani ba yace wasa takeyi masa? Bata manta ba ranar nan suna maganar kallon Ball da tace masa Badar na kalla a waya yace me yasa ita bazata kalla ba tace masa kawai, se yace ta roƙi Dadynta wannan Holiday ɗin suje Muje London ta kalli wasan sa Live har take ce masa ita Baffa ne da ita ba Dady ba kuma wace London ita da ko Aiport bata taɓa zuwa ba ya ringa dariya yana cewa ta raina masa hankali kenan kallon yar Masu kuɗi yake mata irin wadda Mahaifiyarsa take da burin ya aura lallai kuwa an yanka ta tashi. "Afeeya your body is shaking, ki nutsu dan Allah ba fa na faɗa miki maganar nan saboda ki saka kanki a damuwa bane ba...." "Na fahimta Badar na gane wlh dama kuma nima ina yawan wannan tunanin a raina, Ahmad da be kaishi matsayi da suna a duniya ba Yan uwansa suna ganin ban dace dashi ba ina ga JAY wanda ba yan uwa ba na tabbata mutanen duniya kansu se sunyi mocking ɗinsa idan suka san yar wa ya aura, damuwata kawai Badar me yasa yasan da wannan tsarin na mahaifiyarsa ze zo gurina? Tun haɗuwata dashi ban boye masa komai a kaina ba, na gaya masa Mahaifina ba kowa bane me neman na kansa ne amma se yayi dariya kawai yaga kamar wasa nakeyi, kuma banyi wani abu na ƙarya da ze saka yayi tunanin na fito daga wani babban Ahali ba ko kawai kenan Surata ce ta rudeshi yayi mun kallon daidai da matsayinsa? Kenan a gidan Masu kudi kadai ake samun Yara masu Kyau da sura irina ba'a haifarsu a gidajen Talakawa?" se tayi shiru tana jin kuka yana taso mata, bata iya riƙe shi ba kuwa ta fara Badar ta miƙe hankali a tashe ta dawo kusada ita ta riƙe hannuna tana cewa "Dan Allah ki dena kuka kinga ana kallonmu" "Badar ina son Jay, idan na rasa shi bansan ya rayuwata zata kaya ba. Na sani ban kai koda matsayin me aikinsa ba amma zuciyata ta yi ɗage ta kai kanta inda be kamata taje ba kuma shine sila, shi ya kwaɗaitamun soyayyarsa irin wadda na daɗe ina nema me yasa be dubi matsayi da tazarar dake tsakani mu ba ya shiga rayuwata da alƙawarurrukan ƙarya da ya san baze cikamun su ba ya san mahaifiyarsa nada zaɓi kullum yake cemun duk abinda yake so shi take so ba zata taɓa hanashi auran wata mace ba muddin yace ita yake da muradi?" "To ai Afeeyah kinga shima Yah Sani ya faɗi abinda ya sani ne kawai akan Mamanshi, zata yuwu ta canza ko kuma kamar yanda ya gaya miki ba zata hanashi auran duk macen da yace yana so ba tunda ta fi sonshi cikin yayanta doke taso farin cikinsa. Ni dalilina na faɗa miki maganar nan saboda karki sake jiki kuma daga ƙarshe ba fata ba ki zama disappointed, amma kamar yanda kika ce shi yasan wacece ke kuma a hakan yace yaji ya gani yana sonki ki kwantar da hankali all shall be well in sha Allah" Badar ta faɗa cikin lallashi. Afeeyah ta kife kai kan Table taci gaba da rera kuka tamkar har ranar rabuwarsu da Jay tazo, she can't imagine loosing Jay, is like loosing her whole life dan bata tsammanin zata sake moruwa, soyayyar sati uku jinta takeyi tamkar ta shekara ɗari uku, daƙyar ta haƙurtar da kanta ta kuma ɗauki shawarar Badar da tace tayi confronting Jay domin tasan makomar relationship ɗinsu tunda wuri tunda dai shi zuciyarta tayi amannan da. Tabbas tana da buƙatar hakan, zata so ya furta mata da bakinsa tunanin da yakeyi akan Ahalin da ta fito sannan zata kawo maaa maganar Mahaifiyarsa taji view ɗinsa akai. PAGE 15 A daddafe suka ƙarasa exams idan kaga Afeeyah se ka ɗauka jinya takeyi saboda yanda ta fita a hayyacin ta. Tun daga ranar da Badar ta bata taƙaitaccen labarin Mahaifiyar Jay ta shiga wani yanayi na tunani da lissafin yanda makomarta zata kasance. Ƙarin tashin hankalinta kwanki huɗu kenan basuyi waya da Jay ba, zeyi mata text safe rana dare ya tambayeta ya take amma a ƙarshe ze sake jaddada mata karta kuskura tace zata kirashi har se ta kammala Exam ta san koda ta kira kuma baze amsa ba ita kuma taso suyi magana, ya warware mata abinda ya addabeta a zuciyarta ko ta samu nutsuwa. Ranar Thursday suka kammala, ƙarfe bakwai da rabi suna shirin fita Ahmad ya kirata wai ya shigo Zaria yana Dogarawa lokacin, tayi kasaƙe da waya tana mamaki dan gaba ɗaya ma ta manta da batun ze zo ɗaukarta yau, ita bata ma shirya kayanta ba dan lissafinta kawai se gobe Juma'a zata wuce gidan amma tunda yazo babu damar tace ya koma hakan dai dole zata shirya ta bishi su tafi dan haka suna fitowa daga Exam basu tsaya komai ba suka wuce Hostel. Ahmad ya sake kiranta akan idan babu damuwa zeje Kd yanzu ya amso wani saƙo kafin ta gama shiryawa ya dawo "Idan ba sauri kakeyi ba ka jira kawai mu tafi tare se mu kai Badar gida" ta faɗa masa, Badar ta ƙwalalo ido tana kallonta tace "Ni nace miki yau zan tafi?" "Nima ai ba yau nayi niyyar tafiyar ba saboda ya rigada yazo yasa dole zan tafi, ki tashi dan Allah karmu tsayar dashi" Afeeyah ta gaya mata. Dole Suka kashi kaya dan shirin da basu ƙarasa ba kaɗan ne, Badar nata mitar batayi sallama da Sweetynta Nurain ba kuma sunyi yau ze kaita yawo yanzu tasakata tafiya gida ita dai ta toshe kunne har suka kama hanya. Badar da Ahmad keta hirar su ba tareda sun damu da Afeeyah ba dan daman sun saba muddin tafiya ztacehaɗa irin haka shiru takeyi tabarsu idan ma daga shi se itane sedai ya gaji da magana ya kunna Radio. A gidan Hajiya Ummu Yayar Hajiya Binta ya karɓi saƙon Laces ne ya siyawa Momy, a mota ya barsu ya shiga shi kaɗai da ze fito Hajiya Ummu da itama zata fita daman shi take jira ta biyo shi suka fito tare. "Au daman tare kake sa baƙi shine ka barsu a Mota Ahmad? Rowar yar tawa kakeyi mun ko kuma baka riƙeni uwa ba shiyasa ka hanasu shigowa?" Hajiya Ummu ta faɗa. Ahmad ya duburburce, sam be kawo zata fito ba kuma shi be ƙiyi musu tayin shiga ba sedan baya so su ɓata lokaci dan yasan Antyn Ummun cewa zatayi se sun zauna sunci abinci dan shi kansa daƙyar ta barshi ya fito shaf shaf ɗin gashi kuma yanzu yayi complicating abun. "Wlh Mama ba haka bane, ita wannan gida zamu sauketa Fatima kuma mu wuce Kano tare. Naga rana tayine bana so mu ɓata lokaci amma kiyi haƙuri bari su shigo". Yanda duk ya rikice yana mata bayani yasa tayi murmushi tace "Karkayi kuka na yarda ba da niyya kayi ba". Ahmad yayi dariya, Badar da Fatima suka fito suka gaisheta ta amsa da fara'a tana tambayarsa wacece Surukar tata a cikinsu. "Ki zaɓa Mama" ya faɗa yana shafa kai, tace "Kowaccece a ciki Allah ya tabbatar da Alkhairi, saura ɗan uwanka ya kamata shima ya bar ruwan ido haka ya fitarda mata" ta koma cikin gida bayan tace su jira tana zuwa. Hijabai ta ɗebo ta basu sukayita godiya. Badar data karɓi ledar bayan sun shiga mota kafin Ahmad ya shiga tacewa Fatima "Ke Hijaban Ummu-Maheer (07061838488) ne, kinga ledarta". "Ai sun zaga duk inda bakya zato Kyau iya kyau, kasha gayunka da kuɗi ƙalilan a ringa zaton tafiyayye kika saka dole ki ganshi a gurin manyan mata irinsu Hajiyar nan". Suna yan hirarrakin Ahmad ya dawo suka kama hanya. Tilas seda sukaci abinci sukayi Azahar kafin Momynsu Badar ta barsu suka tafi. A hanya Ahmad nata mata santin kirkin Maman Badar. "Ai Momy badaga nan ba gurin kirki, ita Badar ta gado" amsar data bashi kenan ta kame baki ya gaji da jan maganar shima ya kunna musu karatun Alƙur'ani ƙasa ƙasa suka cigaba da tafiya. Lokaci lokaci yake kallonta yana ganin yanda ta mayar da hankali kan wayarta kome takeyi se Allah idan ta nisa kuma taja tsaki ita kaɗai tayi tagumi ta kalli window. Yana so ya tambayeta me yake damunta amma ya kanne, so yake ya fara jurewa yana danne sonta ko ze samu ta fara dubansa da kimar da yake so. Bukar ya gaya masa ya bata iska, bawai barta ba tunda yana sonta amma ya koyi kamewa shima ya dena nuna mata cewar idan babu ita baze iya rayuwa ba. Wayarta tayi ƙara, yana ganin yanda ta zabura ta duba in beyi ƙarya ba har sautin ajiyar zuciyar da tayi ya jiyo. Suka haɗa ido sanda ta saci kallonsa kafin ta ɗaga wayar. Zuciyarsa ta harba, daga yanayinta da yanda take magana a wayar dukda bajin me take cewa yakeyi ba tsabar yanda tayi ƙasa da murya ya gane da Namiji take maganar. Kansa ya ɗauki zafi, har wani sara masa yakeyi idanuwansa sukayi jajir lokaci ɗaya saboda wutar kishin data tashi ta fara ci balbal a zuciyarsa. Be san ta gama wayar ba seda yaga tana Ƙoƙarin saka cajin wayar ta ajikin cajar motar. Murya a kausashe da irin sautin da bata taɓa jinsa dashi ba ya kira sunanta kafinyace "Ni ba shashashan Namiji bane da kina zaune tareda ni wani ze kiraki a waya ki ɗauka, this should be the last time da zaki kwatanta wani abu kamar haka. Wlh kika sake sena fasa wayar idan yaso naga da abinda zaki cimun fuska kiyi magana da wani Namiji". Tsabar yanda maganarsa ta shigeta har karkarwa jikinta ya ɗauka, tunani takeyi daman Ahmad ya iya faɗa irin haka? Yanda ya juye mata lokaci ɗaya ya firgitata ga speed daya ƙarawa motar yanda kasan zasu tashi sama. "Kayi haƙuri" ta faɗa bakinta na rawa. Har suka isa Kano kuma be sake ce mata komai ba, a bakin layinsu da suka isa ya faka be kulata ba ya fita ya samu yara ya buɗe booth suka kwashe mata kayanta. Be bata fuskar da zata sake masa wata magana ba, a wajen motar ma ya tsaya har seda ta sauka kafin yaja yayi tafiyarsa ya barta da bin bayansa da kallo. A sanyaye ta isa gida kafin ta shiga dai tayi ƙoƙarin daidaita nutsuwarta saboda gudun tambayar meya sameta. Ta tarar da Anty Sauda da yaranta, ganinsu yasa ta sake sakin ranta musamman kuma da sahibul Ƙalbinta ya kirata ya mata fatan sa'a akan Jarabawar da suka gama yace zasuyi magana idan ta isa gida. Wannan birkicewar ta Ahmad ce ta jirkitata amma tana shiga gida ta manta da babinsa ta shiga sabogogi sedai lokaci lokaci yakan faɗo mata, yanda ya fututtuke se taji kamar Jay yana sababi, daman ance masu haƙuri basu iya fushi ba yau kuwa gashi ta tabbatar. Ahmad kuwa seda yayi dagaske kafin ya danne abinda ya ringa cin zuciyarsa, yana da kishi matuƙa musamman akan abinda yake so kamar Fatima. Koda yake binta yana lallaɓata dan yasan kawai ra'ayinsa ne batayi bawai wani saurayi ne da ita daban da yasa take ƙinsa saboda shi ba. Yasan bata double dating, shiyasa ya nace yake ta roƙon Allah yana kuma ƙara cusa kansa gurinta amma yanzu ya fahinci ta samu wani saurayin da take ra'ayi shiyasa harta iya ci masa fuska ta ringa waya dashi a gabansa shi ga sakarai wato bazeji komai a ransa ba. Seda aka kwana biyu da ɗakkota da yayi be sake kiranta ba, dan ya yanke dole ya koyawa zuciyarsa haƙuri da ita tunda har ya fahimci da wani bayan shi yanzu komai yana iya faruwa kenan. Da safe ranar Asabar kwana biyu kenan da dawowar tata yana kwance a ɗakinsa se gashi ta kirashi. Ya ringa kallon wayar kamar wanda yayi loosing memory saboda ya kasa yarda Fatima ce take kiransa da karan kanta yau. Rejecting yayi kafin yabi bayan kiran duk da zuciyarsa nace masa karya amsa ya bar wayar tayi ringing ta gama harta sake kira dan ya tabbatar da gaske shi take kira ba tuntuɓen number tayi ba. "Ina kwana?" Ta faɗa a sanyaye bayan da yayi mata sallama ta amsa. Ya amsa gaisuwar yana jin tamkar ya taka rawar murna, dahgaske kenan idan mutum yaja aji za'a mutuntashi tunda gashi fushin kwana biyu ya juyo masa da hankalin Fatima. "Kayi haƙuri akan abinda ya faru ranar nan banyi da wata niyya ba" ta sake faɗa a sanyaye. Daɗi ya sake kamashi, har tasan ta kirashi kenan ta bashi haƙuri ai kuwa akwai haske a cikin tafiyar. Ya wani mula yace "Babu komai kawai dai na gaya miki idan kika sake sena fasa wayar tunda bazan iya fasa miki baki ba" "Ai dai nace kayi haƙuri" ta sake nanatawa yace "Na haƙura na kuma yafe miki Alhakina da kika ɗauka kika sa nayi fushi dake". "Uhm" kawai tace, suka ɗan taɓa hira kafin sukayi sallama bayan yace mata zeje da yamma tace tana gidan Anty Sauda ya sameta a can dan kwana zatayi. "Toh ko kefa? Nifa harga Allah zancen wani Ɗan Ball be kwantamun a rai ba. Haka kawai zaki kwasarwa kanki abinda ze saka miki ciwon rai idan ya aureki ɗin ma kenan. A matsayinki nawa Afeeyah zakice zaki auri world class Celebrity? Ai ɗagen yayi yawa, irin waɗannan ai ba kowacce mace ba, kuma duk ma ba wannan ba na tabbatar wlh fuskarki ce kawai ta ruɗeshi, babu tabbacin idan yasan wacece ke ya yarda ya aureki a haka gara miki Ahmad ɗin. Mutumin nan ga Hankali, nutsuwa, mutunchi, karamchi uwa uba yana matuƙar sonki kuma ya sanki ciki da bai yasan Mahaifanki a hakan kuma yace yaji ya gani yana sonki ze aureki na rasa wace masifa ce tasa bakya son Bawan Allahn nan Afeeyah wlh in guje miki kiyi nadanar da ba zata amfana miki komai ba a gaba" Anty Sauda wadda ita ta tursasata kiran Ahmad bayan data shaida mata abinda ya faru tsakaninsu ta faɗa. Afeeyah ta zumɓura baki, kafin tayi magana wayarta ta shiga ƙara, ringing tune data sakawa Jay ne dan haka ta miƙe da sauri da wayar a hannunta ta shige ɗaki Anty Sauda ta rakata da ido tana cewa "Idan kina da rabo Allah ya ganar dake amma wlh nasan wannan Jay yake kowa yaudararki yakeyi ba auranki zeyi ba gara tun kina da sauran dama kiyi amfani da ita amma ba takanki zanbi ba, Baffa zan samu tun wuri asan abinyi baze yuwu shekara biyu ki gama yaudare bawan Allah kizo kice ba zaki aure shi ba" taja wayarta ta shiga kiran Baffansu sedai wayarsa a kashe. Tayi ƙwafa a fili ta sake cewa "Har gidan zanje, gara ko auran dole ne miki tunda baki da hankali" ita dai Afeeyah na kan gado tana malele kuwa Jay na kasheta da kalaman Love, tunda suka shirya ta manta komai. Hatta maganar dake ta azalzalar zuciyarta ta mahaifiyarsa bata tayar ba tama manta da batun ta sake zama daram akan Alƙawarurrukan madarar ƙaunar da yace ze shayar da ita idan sukayi aure. Ya mata Alƙawari nan da watanni shida zezo Nigeria musamman saboda ita, ya kuma ce mata zuwan da zeyi zeje ya gaida Mahaifinta daga nan iyayensa suzo dan ya rigada ma harya gayawa Yayansa maganarta shima shirin Aure yakeyi tare za'a haɗa da nashi dan haka ta fara duk wani shirinta da idan yazo tana iya yuwuwa daga tambaya taji an ɗaura musu aure kawai sedai taji ana fito kibi Mijinki. Ranar tayi dariyar maganarsa yace tasaka wasa zata gani da gaske yakeyi, Alhajinsu bashida wasa ko yau yace masa zeyi aure muddin ya yarda da inda ya nemo auran magana ta ƙare tambaya kawai za'aje ayo. Wannan tasa ta yanke shawarar sanar da maganarsa a gida tunda wuri ba wai se rana tsaka ba, ta fara takan Anty Sauda domin itace tsanin da ze kaita gasu Baffa. Muddin tayi na'am da abin tasan komai ze zo da sauƙi sedai daga yanda ta karɓi maganar tasan ko zata yarda se an yi ƙwaibai da ita dan tamkar Badar itama Ahmad ya lashe mata zuciya sonsa suke nasa son abinda ze taɓa shi. Daga ce mata sunyi faɗa tace seta kirashi ta bashi haƙuri idan ba haka ba ta gayawa Baffa ta samu wani saurayi yana hure mata kunne harta kori Ahmad ta masa wulaƙanci shiyasa ta kirashi. **************** Hajiya Binta zaune kan carpet tana zubawa Alhaji Audu faten Accar da tayi masa saboda tana da buƙatu yau da kanta ta tsaya ta masa girki me kyau ta kashe gayu da wata kamfalarta shadda ta saka daham, lallen bikin da aka mata tun yau litinin yayi raɗau a hannayenta da Ƙafa dukda na Salatif ne me yankan Siga amma da yake fatar da sauran Armashinta ya mata kyau. Humrar da akayiwa Amarya Hafsatu ta bulbula abinta ƙamshin har hawa kai yakeyi dan seda Alhajinya kunna fanka bayan Ac dake falon saboda Atishawar da turaren nata ya saka ya fara jerawa. Hira take masa wadda duk labarin irin tsaruwar gidan Hajiya ƙaramar take zayyana masa. Jiya su Turai suka dawo daga jere, dakyar da roƙon Allah ma ta yarda ta zauna dan cewa tayi da da ita za'aje. "Wannan wane irin abune babu kunya kawai Binta ki bimu se a ganki tsalam ace ga uwar Amarya a ina kima taɓa ganin anyi haka? Ita Aisha data aurar da Yaya biyu gata uku wanne kika gani a ciki tajewa jere baku ne kuke zuwa ba se kece zakice se kinje salon ki zubarwa da yarinya ƙima tun bata kai ga shiga cikinsu ba? Abujar ce baki taɓa zuwa ba ko kuwa ance za'a rufe shigarta ne idan bakije yanzu ba?" Turai ta ringa zazzaga mata bala'i dan lamarin Ƙawar tata ya fara kaita bango. Fafur tace Anty Rabi da Momy ba zasuje mata jere ba, Baba Bilki ma da tace ba za'a da ita ba dake har yau na sanyi tayi ba tace ai uban Binta ma yayi kaɗan balle ita ta hanata zuwa gano gidan Yar Audu. Saboda neman suna tace wai Hajiya Balaraba tazo aje da ita tace Aa saje kai Amarya daga ƙarshe dai bisa tursasawar Turai suka tafi da ita da Momy wadda bata so zuwa ba se Hajiya Zainab da Munirah ƙanwar Binta wadda har yau sama da shekaru hamsin kenan tana zaune bata samu Mijin aure ba bayan rasuwar Mamansu ne ta dawo nan Kano da ta fara zama gidan Binta zama yaƙi daɗi se kawai ta siyi gida take zaune abunta tana kasuwancinta tana cigaba da roƙon Allah daya yanke mata dukda ta san cewar ba komai ya janyo mata shiga halin da take ciki ba se haƙƙin baiwar Allah da bataji ba bata gani ba suka laƙa mata sharrin da harta mutu wasu na kallonta dashi. Suka hanata zaman lafiya a gidan auranta harta koma ga Allah. A can Kaduna suka haɗe da sauran yan uwan Binta akaje akayi jeren wanda babu wani abin arziƙi data siya. Kayan Gado dai a BECHI FURNITURES yace aje a ɗaukar mata duk abinda uba yakeyi saɓanin su Khadija dayake ƙayyade Adadin kuɗi yace a ɗauki kaya na kaza. Su Turai ne sukaje suka zaɓa suka darje kaya na ƙarshen mutunchi a shagon, da Alhaji yaga Invoice ya ringa surfa masifar da bata da Amfani domin dai shiya nada dama kuma sun rigada sun ɗauka har an jera dan a Branch ɗinsa na Abuja suka kwasa ƙarshe abin ya ƙare akan Aslamiyyah yace Gado biyu kujera biyu za'a ɗaukar mata saɓanin Hajiya ƙarama da aka sakawa huɗu, ɗaki biyar ne a gidan da faluka biyu manya se ƙarami ɗaya wanda yake haɗe da Master Bedroom a sama shine na Megidan iyayensa sun gyara masa dan haka hatta ɗakin da me aiki zata zauna Royal aka saka saboda samun guri da nuna akwai. Kayan Kitchen dai daman yace musu a Al'adar Hausawa uwa ce takeyi to yana kan wannan magana har akan Hajiya be saketa ba dan haka ita tayi kayan kitchen tarkacen banza da wofi wasu matsiyatan kuloli da fulasai ta bakin Turai. Yanda ta ringa zuzuta ta gama siyan komai dan ƙin yarda suje siyayyar tare tayi, haka ta nuna mata kayan taƙi se randa zasu tafi Jere da za'a ɗiba aka tattara kaya ko cika buhu biyu basuyi ba amma faɗi take "Kinga kaya ko Turai? Dama na gaya miki sena baki mamaki ai bikin Nazira shammatata akayi amma wannan na shirya" "Billahillazi Binta idan baki fitar da kuɗinki kinci kin morawa kanki ba se kin mutu kina kwance a ƙasa zakiga yayanki na wadaƙa dasu, yanzu wannan kayan kike zuzutu akai? Abinda ko Talaka me zuciya se yayi ninkin abinda kikayi wannan abin kike so akai ace daga gidan Bechi suka fito? Turai ta ringa masifa kamar zata ari baki tana kafa mata hujja da kanta yanda takeyi idan zata aurar da Yayanta da sauran ƙawayensu, ta kawo mata Misalin Momy, auran Khadija da Annah ita da kanta tace har seda suka maido da wasu abubuwan gida dan seda aka kai sukaga an siya an ƙara siya tasan kuma yanzu ma na Aslamiyyah haka zata fitar da kanta kunay. Duk wanda yaga kayan gadonta da kujeru yasan ubanta ne yayi mata ke za'a zaga ace uwarta bata da zuciya dan wlh ko yar riƙo a gidan nanta wuci akaita da wannan tarkacen. Ƙarshe se Alhaji Zakariyya da Alhaji Naziru harda Yakubu Turan ta kira tace kowa yazo ya bada abinda ya samu, ta tattara ta bazama kasuwa tayo mata siyayyar kayan kichen na fita kunya suka kai ta barwa Binta tsiyarta da tace ta ajiyewa Auta Saratu ta huta ita tasan ba zata raina wannan ɗin ba toh fa tunda suka dawo aka kawo mata Video shikenan ta kasa nutsuwa labari data kai aya zata maimaito tun Alhajin yana ji harya gaji yace mata "Binta yanda kike nanata mun labarin gidan nan ko zuwa nayi yanzu bazan ɓata ba danna gama gane kowanne lungu da saƙo na gidan, ki bani abincin naci kafin ya huce dan Allah do nakeyi na fita zamu haɗu da Alƙali mu tattauna yanda taro ze kasance kinga lokaci yana ƙaratowa yau Litinin saura kwana huɗu ɗaurin aure". "Ai toh yi haƙuri wlh santin gidan ne yaƙi ya barni, ai Hajiya dai tayi gida Allah ya tsole idon maƙiya yasa mutu ka raba" ta faɗa tana bashi. Shida ya shiga cin abincin yana jinta dan batayi shiru ba. Ta gyara zama tace "Dama Alhaji zancen gurin Kamu ne an gama magana da mutanen nan yanzu sun dawo sunce wai kuɗi yayi kaɗan se an ƙara kuma ni nayi ƙarƙaf dubu Ashirin yanzu se nayi da gaske zan fito da ita ai bikin nan dai ya talautani da gaske". Ya kalleta ta gefen ido a ransa yana mamakinta, wai ta kashe kuɗi kome ta yi se Allah bayan duk abinda ake ciki yana da labari. Zakariyya ya gaya masa su suka bada kuɗin kayan kitchen bayan ta ɗiora musu Alhakin abinda za'aci a gurin Mother's eve data shirya shi kuma nan be san Buhu nawa da galan na mai nawa da sauran kayan abinci data kwashe masa a Store tace za'ayi abincin biki ba. Kaji ɗari biyu ya saka aka bata ita kaɗai banda Sa da za'a yanka na abincin yini. Tunda aka fara zancen bikin nan Aisha bata ce ma ya bata sisin kobo ba, Bilki ce ta nusashsheshi har ya batan dukda be kai ko kwatan abinda Binta ta Ƙwamusa a hannunsa ba. Kayan gado kansu ya banbanta Hajiya Ƙarama cewa yayi su ɗauki wanda ya musu Aslamiyya kuwa dalilin ɓarnar da su Turai suka masa shiya faɗi kalar wanda za'a ɗaukar masa an gaya masa Ahmad da Sarki ne sukayi cikon Kuɗaɗe masu nauyi suka ɗaukar mata irin na Hafsatun kuma duk abinda ya kamata ace yayi wanda Aisha bata tambayeshi ba su sukayi yana kallo aka ringa sauke ruwa da lemo besan katan nawa bane inji Ahmad Jafar kuma shi ya siya Musu Cinema Tv su biyun nan cikin Yaya bila'adadin daya haifa ne suke da zuciyar bashi gudummawar auran ƙannensu dukda sun san yana dashi ba babu ba amma yaji abinhar cikin zuciyarsa. "Alhaji kayi shiru" Hamshaƙiyar ta girgizashi. Ya aje farantin hannunsa ya miƙe tsaye yana cewa "Ki karɓo kuɗinki kizo kuyi a nan cikin gidan kamar yanda su Aisha zasuyi ni banida wasu kuɗi da zan sake baki kuma a yanzu nayi iya abinda zan iya" "Ai shikenan, kana ji Jafaru wai baze zo bikin bako? Gaskiya ka kirashi kayi masa magana ta yaya za'ayi ace baze halarci ɗaurin auran ba? Ta ya mutane wai zasu san Ɗanka ne yafi so ayi ta kallonsa a ba kowa ba ai idanya fito kowa ya san Ɗanka ne darajar sa seta sake linkuwa a ƙasar nan ko ya kace?" Ta sake soko masa wata maganar, ya miƙe yana shiga ɗaki yace "Duk yanda kika ce Binta, bari na shirya na fita dai na baki guri" ya barta tana cizon yatsa. Daman ba Even centre data kama, tunda taji a gida Momy zatayi Kamunta zata kira masu Decoration taje kakarta ta yanke saƙa bari zatayi ta gama shirya komai se ranar tayi ta kankane ita da mutanenta dan ba zata iya zare Miliyan nawa ta kaiwa masu gurin biki ba, abinci ma da Turai tasa ta kashi kuɗaɗe ta bayar ciwon rai takeyi, so tayi ta bawa masu aikinsu ayi shi nan a cikin gida amma tace gun yan gayu zasu kai, so tayi ya bata kuɗin ta rage asarar wanda tabayar shine yace bashida su yanzu duk kwalliyar nan da tayi ta tashi a banza kenan ai shikenan. Alhaji ya fito a shirye yana waya, bata san da waye ba abinda taji kawai ya fizgi hankalinta shine "Babu damuwa nagode, bari mu gama da hayaniyar wannan bikin zanyi magana dashi. Idan son samune ya haƙura da yarinyar ya nemi wata dan sam banji abin ya kwanta mun a rai ba amma bama so na hanashi abinda yake so saboda yaron nada biyayya nasan muddin nace Aa tilas ze haƙura koda ace hakan ze cutar dashi amma yanzu zan samu Alƙali shima da maganar yanda mukayi zakaji". "Toh fa wane yaro kuma ake magana akai?" Tayi tsalam ta tambaya bayanya kashe wayar. Yana tafiya ze sauka ƙasa tabi bayansa yace "Ahmad ne, ya samu yarinyar da ze aura. Kiyiwa wancan yaron magana shima ya dakata da shashancin da yakeyi ya fitar da mata dan tare zan haɗu bana son Biki a rarraben nan" "Yo naji kana cewa yarinyar bata maka ba? Halan kwashe kwashe yayo ko? Ni daman nasan za'a rina Allah yasa dai ba gidan matsiyata ya kwaso auran ba mu shiga uku su ƙara yawa bamu gama data gidan nan ba ya kwaso mana wata" Hajiya ta faɗa shidai be bata amsa ba ya fice daga falon dan Malam Sadi Driver sa yana tsaye harya kunna mota. Ta wuce ciki inda ta baro ƙawayenta da sukazo ana ta tsara yanda biki ze kasance, Kamu dai rigar na Momy zasu shiga dukda ba haka su Hajiya Zainab suka so ba Turai kuma tace haka ne daidai tunda dai Yaran nan ubansu ɗaya toh ayi Kamun nan a tare idan yaso tunda kowacce gidan Mijinta sun shirya Dinner se suyi abarsu daban ga sauran events da kowacce Amarya zatayi da Ƙawayenta. "Yanzu kawai sedai mu zama yan kallo mun raɓe raɓe kenan?" Hajiya Sha'awa ta faɗa, Binta ta karkace tace "Inji wa? Ai biki namune wahala kawai zasu mana su shirya komai. Da kunji ance ina uwar Amarya ku rufa mun baya mu shige, duk wani kira da za'ayi ku shike kuyi kinini karku basu wata ƙofa a gurin" akayi shewa aka tafa. Se ranar Laraba Ahmad ya kaiwa Fatima Ɗinkakkun kaya, Atamfa me kyau da akayiwa ɗinkin zamani amma Modest ɗinki se wani shegen Lace da Anty Sauda tace ya haura dubu ɗari biyu. Kowanne kaya da mahaɗinsa, Takalmi, mayafi, jaka harda Sarƙa da agogo. Zobunan gold guda biyu ya saka mata a ciki ganinsu ya tuna mata da ranar da yace ta nuna masa hannunta kenan measurement ɗin hannun ya ɗauka. Yace mata Atamfar ta Ankon Kamun ce dan ya gaya mata zasuyi biki har Iv ya tura mata Lace kuma kawai ɗinka mata yayi na Dinner. Tace ba zataje ba Umma ta goya mata baya a cewarta babu tsayayyar magana a tsakaninsu da har zata saka taje musu biki, idan kuma zuwan nata ya janyo wani abu da ba za'a so ba fa? Gara dai da ace anyi magana yan uwansa sun san da zamanta da sauƙi ko cikin yan uwa tana iya samun wata suje tare su dawo. Baffa ma da aka gaya masa cewa yayi Aa. Da kansa ya kira Ahmad yace ba zataje ba, yayi kuma faɗan zobuna har biyu da Umma tace masa zinare ne yace in yazo ya karɓe su ya ajiye idanAllahyasa taje gidansa ya bata ya dai amsa da Toh amma koshi Baffan yasan baze karɓa ba dan yasha ya kawo mata abu yace a mayar yaƙi karɓa sedai ya kalallameshi da magana yace ko babu soyayya tsakaninsu Baffa Babansa ne zeyi mata komai saboda shi. Wannan ya rushe batun zuwanta Biki wanda daman ko da an barta a karan kanta ba zata so taje ba, to wai se taje a matsayinta nawa??? An dai yi biki a gidan Alhajin Bechi lafiya duk kalen bala'in Hajia da yan korarta dole suka kama kansu domin Yan uwan Momy da ƙawayenta wannan karon basu zo da wasa ba. Yanda Hajiyar ta saba musu idan ana biki ba yarta ba amma komai yana hannu ta se abinda tace se yanda ta tsara za'ayi wannan karon basu bari ba. Basu saurari Alhajin ba kansa Ahmad da Sarki sun share mata hawayen komai domin duk halinsa shima wannan karon Ahmad ya shawo kansa sun fitarda mahaifiyarsu kunya ba tareda sunyi jiran kowa ba. Anyi biki lafiya Amare sun tare Hafsatu an tafi Abuja Aslamiyyah na nan Kano se Amaryar Yakubu shima da Allah yayi bana yayi auran tsalle tsalle ya ƙare dukda seda Alhajin yayi masa barazana da ze saukeshi daga Acting Account General dan har yanzu ba'ayi confirming nasa ba kafin ya kawo matar akayi Bikin. Afeeyah kuwa Rikicewa ta ringayi harta fara zaton WhatsApp ɗinta ya samu matsala saboda status ɗin Ahmad da Jay da suka zama iri ɗaya tunda aka fara bikin har aka gama seta yi tunanin repeating sukeyi taga kamar ana Jay dan komai ma gizon sunansa yake mata yanzu. Ko kusa bata kawo cewar Jay ze iya haɗa wata alaƙa da Ahamd ba shiyasa ma bata tsawaita tunani ko bincike ba ganin kuma komai ya koma normal shikenan ta manta. Ada bata fiya wani duba status ba amma haɗuwarta da Jay kusan kullum seta duba update ɗinsa wanda duk akanta yakeyi. Yace mata yaso yazo Nigeria abinda ya hanashi zuwa contract ɗinsa da Arsenal taje ƙarshe, Clubs da yawa suna zawarcinsa har yanzu kuma beyi finalizing inda ze koma ba yana so se yayi sealing deal ɗin kafin yaje wani guri. Ya tura maata da sabon Field name ɗinsa, a maimakon JAY its going to be AJAY. Yace A for AFEEYAH and JAY remain for the JAFAR bata yarda da gaske yake ba har se ranar da yayi sealing deal da PSG sabuwar rigarsa da AJAY aka bugata. Ta ringa murmushi kamar wawiya sanda take kallon Interview ɗinsa, an tambayeshi me yasa ya canza suna kuma me A take nufi yace it remains secret lokacin da ze bayyana yana zuwa. Tana jin Yah Malam ɗinsu da Abokinsa Sani da tsabar yanda yake son Jay sunansa ya koma Jay ranar sunata magana. Ance Initial ɗin budurwarsa ne, wasu sunce Initial ɗin Yayansa ne da yake bala'in so kowa dai da abinda yake faɗi. Kamar taje ta gaya musu gaskiya se kuma ta kama bakinta. Anty Sauda tayiwa Umma zancen itama bata bada goyon baya na cewa ma tayi karsu bari Baffa yaji dan ranta ne ze ɓaci. Ya za'ayi tsayin lokacin nan ta dawo tace wani daban ba Ahmad ba itama tasan wasa takeyi. A ranta ko babu gudu babu ja da baya tasan kuma Baffa baze taɓa bin ta tasu ba ya aura mata abinda bata so. Ai da bakinta bata taɓa cewa wani tana son Ahmad ba ko zata aureshi su suke kiɗansu suna rawarsu dan haka babu wata hujja da za'a kafa da zata rabata da wanda take so, badai yace ya kusa zuwa Nigeria ba yana zuwa zata kaishi gidan ayita ta ƙare da haka suka cinye hutun session daya ritsa da Strike kusan watansu uku a gidan kafin suka koma School First semester Four hundred level. PAGE 16 Rayuwa ta shuɗa, soyayyar Afeeyah da Jay tana ƙara ƙarfi inda al'amarinta tsakaninta da Ahmad yake sake taɓaɓarewa. Zywa yanzu ya gama tabbatarwa Fatima bata ta tashi da gaske wani ya masa shigar sauri kuma ya sure Imaninta. Ya sake tsananta Addu'a akan Al'amarin amma mainakon rangwame se sake jinta yakeyi a zuciyarsa kamar ture. Damuwar da yake ciki da ayyuka da suka masa yawa yasa duk ya sake figewa ya fita a hayyacinsa. Kowa a gidan yaro da babba ya shaida Ahmad yana da damuwa hatta Hajiya kuwa seda ranar ta tsare shi tace "Kai Amadu anya magauta basu danneka ba? Wannan uwar rama haka kamar wanda ake ɗiba ayi miya kullum? Koda yake jarabar neman kuɗi daka saka a ranka ai dole kaƙi abin kirki, ni na rasa ma me kake nema ko kuwa so kake se ka yi gasa da ƙaninka ne? Shidai kasan yan guje guje kawai zeyi a fili ya dirim Miliyoyi sun shiga akawun, shiyasa yake mulla ƙibarsa kai kuwa kana ta fama da dogon wuya kamar tsohon raƙumi takwaran ubanka". A Ƙofar ɗakinta take maganar ga Hajiya bata rage Volume dan haka hatta Momy dake cikin falonta suna magana da Baba Bilki sun jiyota. Baba Bilki ta girgiza kai tace "Yau rashin mutunchin Binta ya motsa kenan, daɗina da ita bata bar kowa ba, kinji Mijinku ne takwaran tsohon raƙumi. Amma fa maganar gaskiya ki matsa Babana ya gaya miki me yake damunsa da gaske wannan ramar tasa tayi yawa, ni dana tambayesa yace wai aiki ne amma kuma wane aiki ne haka damuwarsa zata nuna har a fuskar mutum? Amadi da ko yaushe fuskarsa take a washe ga barkwanci amma yanzu se a wuni baka ga murmushinsa ba gaskiya ya kamata kiji damuwar yaron nan idan kuma naje Bechi daman zan karɓo masa taimako dan dole mahassada suyi masa caaa irin wannan buɗi da ubangiji yayi masa kiga komai yaro ya taɓa se ya zama kuɗi". Tana rufe baki ya shiga falon da sallama ƙasa ƙasa, suka bishi da kallo harya zauna kusada ƙafafun Momyn. Murmushin yaƙe yayi ganin yanda suka zuba masa ido yace "Lafiya dai Innata da Momy kuke kallona haka kamar kunga baƙo?" Inna yake kiran Baba Bilkin Jafar ma ya kama saɓanin sauran da Manyan suce mata Hajiya ragowar Baba. "Ai dole mu kalleka Ahmad, kana duban kanka a Mirror kuwa? Wannan ƙasumbar da gashin daka tara a kanka na magani da menene?" Momy ta tambaya tana dafa kan nasa. Ya shafa gashin shima yace "Lokaci ne ban samu naje aski ba amma yanzu idan na fita zanyi" "Gara dai kayi ko ka koma hayyacinka amma fuska gashi biya biya kuma ba'a kintse ba ai babu kyau" Baba Bilki data miƙe ta sake faɗa yayi murmushi yana tambayarta fita zatayi tace masa Bechi zata tafi kwana biyu bataje ba sati zatayi kafin ta dawo. "Da bana komai ai da na kaiki" "Aa yi zamanka, tare zamu tafi da Yaya Yakubu ai can gidan nasa ma zan tafi yanzu" "Toh Allah ya kiyaye hanya ki gaidasu" sukayi mata bankwana. Bayan fitarta Momy ta fuskance shi dakyau tace "Karka boyemun komai ka faɗamun gaskiyar abinda yake damunka Ahmad". Ya nisa kamar bazeyi magana ba se kuma yace "Momy Fatima ce na kasa gane kanta" "Matsala kuka samu?" Ta tambayeshi tana nazartarsa. Ya karkace kamar zeyi mata kuka yace "Ni dai babu abinda nayi mata Momy itace dai bansan ko na mata wani abu ba. Gaba ɗaya ta canza duk na kasa gane kanta". "Ahmad kama Addu'a kuwa akan lamarin yarinyar nan?" Ta tambayeshi, yaja rantsuwa yace "Wlh ina yi Momy, ko jiya kwana nayi ina sallah ina addu'ar neman zaɓin Allah amma wlh kamar an ƙaramun sonta a maimakon ya ragu a zuciyata" "Kuma ba addu'ar son rai kakeyi ba? Kana cewa kana neman zaɓin Allah amma kuma ranka ba haka bane ka rigada ka zaɓarwa kanka abinda kake so?" Momy ta sake faɗa tana dubansa yace "Momy shekara uku fa kenan, na san ba nacina ko dagiyata ce zata bani abinda nale so ba amma kuma Allah na barwa zaɓina ina ganin da inada wani haske daban bayan ita da yanzu na ganshi amma Momy ita ɗin dai ita na gani nake kuma ji a jikina itace matata". "Toh addu'ar dai ita zamu cigaba dayi akan koma menene Allah ya warware sannan damuwar daka saka a ranka ba zata amfana maka komai ba kayi Ƙoƙari ka cireta, duk abinda Allahya saka cewar rabon bawa ne a duniya seya same shi idan kuma ba rabonka bane duk wuya haka zaka haƙura domin ba zaka sameshi ba. Sannan kuma ni ina ganin cewar harda halinka yasa yarinyar nan take maka koma menene" Ya zabura yace "Halina kuma Momy? Me nakeyi?" Momy tace "Shekara uku kace da bakinka yanzu, wace irin soyayya ce haka har yanzu da za'ace ba za'ayi aure ba? Kaida bakinka kace mun mahaifinta yace maka ko tana cikin makaranta idan ka shirya aurar da ita zeyi to me kake jira har yanzu? Kana tsammanin zata cigaba da zaunawa tana ɓata lokaci dakai ne Alhalin ƙila tana da wasu masoyan da suka fika himma?" Yayi shiru dan besan bayanin da zeyiwa Momy ta fahimta ba. Baya so ya ɓata Fatima a idonta ta hanyar sanar mata cewar itace har yanzu batayi na'am dashi ba kuma ita taƙi bashi damar ya tura ayi maganar auransu idan kuma yayi shiru Momy zata cigaba da bashi laifi na cewa shi yake ɓatawa Fatiman lokaci wannan yasa ta karkata hankalinta ga wani daya fishi himma kamar yanda tace. "To ai Momy yanzu tana Level 4 har sun gama First semester da bari nayi tunda son zo ƙarshe kawai ta ƙarasa daganan se aje ayi magana" "Oh so kakeyi harta gama makarantar tazo ta zauna sa'annan ka gama shiriritarka se aje ayi maganar aure ko? Lallai kuwa kana zaune nan zakaji wani ya aureta. Waima sanyar me kakeyi ne? Ina kace tun tuni ka sanar da Alhaji maganar nan me kake jira da ba zaka sake tayar masa da ita ba tunda ka nace lallai se shi zaka kaiwa maganar auranka?" "Aa Momy ba haka bane ba, naga ai Alhaji ne Ahaƙƙu da na sanarwa da zancen aurena idan yaso shi kuma ya iya saka wakili ya shige mun gaba" ya bata amsa kai a ƙasa. Momy ta harareshi tace "Sannu uban fitar da Ƙoƙon Asali, dama dai yanda kake da ƙulafucin uban nan shima haka yake ta taka amma na tabbata yanzu ya manta ma da kunyi wata magana data shafi zancen auranka dashi. Se kaje ka sake samunsa ai ka tuna masa, idan kuma yace Aa kaga aiseka fara sabon lissafi tunda ga tudun dafawar da duk yanda aka ciza ze tsaya maka kace baka san zance ba ba zakaje ta wurinsa ba". "Ni Momy bana so a sakeyin irinta Yaya Sarki kina kallo dai Alhaji swda yayi ta faɗa akan ya zameshi daga maganar auransa shiyasa amma ba wani abu ba kuma nasan ai dai ko shi na gayawa dole dai Baba Alƙalin ze wakilta" ya sake faɗa Momy tace "Ai shikenan, amma dai mafita guda ce in har da gaske kake son yarinyar nan manya su shiga maganarku, kaje ka samu ubanka ka fayyace masa komai ya tura a nema maka auranta in kuma zaka zauna nuƙu nuƙun ne kuma shikenan" "Toh Momy zanje" daga nan suka bar maganar suka shiga wata. Bayan fitarsa ya ringa shiryawa yana warware ta yanda ze sake tunkarar Alhaji da zancen aurensa da Fatima. Amma ta yaya ma ze taso magana alhalin ita wadda za'a aura ɗin bata yarje masa ba? Ya samu jikin katanga ya lafe ya shiga kiran layinta, yanzu abin ya sake ta'azzara har rejecting take in bata ga damar amsawa ba kuma ya dameta, So hana ganin laifi haka yake jurewa domin ya yarda ƙaddarar sa ce Son Fatima. A kira na biyu ta amsa muryarta ta shaida masa bacci takeyi dan haka yace "Kiyi haƙuri na tasheki a bacci" "Babu komai ina zaune ne nima ban san baccin ya kwasheni ba, ina wuni?" Ta gaidashi. Tana da kirki, tana da tarbiyya, Mahaifanta mutane ne kai tana da duk wani quality da yake nema a gurin matar auransa baya zaton idan ya barta ze damu full option abinda yake nema a gurin mace tamkar nata ya ayyana a ransa. "Kina free yau da dare zanzo?" "Eh" ta bashi amsa a taƙaice, shikenan ya mata sallama akan se bayan Magriba zeje haka kuwa akayi yaje yayi aski ya ɗan shiga saiti ana sallar Magriba ya sha kwalliya ya tafi gidansu. A can yayi sallar Isha a masallacinsu Baffa kafin suka ƙarasa gidan tare. A ƙofar gida Baffa ya dubeshi yace "Malam Ahmad na bawa Mamana Saƙo kusan sati nawa amma banji amsa ba". Da rashin fahimta ya dubi Baffan kafin cikin girmamawa yace "Ina ganin ta sha'afa ne Baffa ko kuma nine na manta da ta gayamun amma wace magana ce?" Baffa yayi murmushi yace "Dama maganar zuwan magabatanka ne nace lokaci yayi daya kamata ace manya sun shiga cikin maganar nan, ni badan ka buye ta tata ba kace a barta ta gama karatun kamar yanda take so ai da tuni kuma ka huta da biyo dare kana maƙalewa jikin katanga" Baffa yayi masa barkwanci. Yayi yar dariya yana sosa Ƙeya, Baffa ya sake cewa "To ina sake maimaita maka tunda da alama ta sha'afa kamar yanda kace, a sanar musu saboda a san abinda ake ciki" "In sha Allahu Baffa zan sanar musu" ya faɗa kai a ƙasa, Baffa ya wuce ciki yana masa Addu'a da fatan Alkhairi. Shiya turo masa Fatima wadda ta manta da batun zuwan Ahmad ɗinma seda Baffa yace mata yana waje. Dogon Hijab ta saka, bata shafa ko hoda ba ta fito tana bulbula ƙamshin designer perfumes ɗin da yake kai mata akai akai. Ta gaishe shi ya ringa kallonta kullum ya ganta ƙara sonta yakeyi, jinta yakeyi har tsakiyar ransa shi be taɓa sanin haka So yake ba seda ya afkawa kogin ƙaunar Fatima. "Yanzu Baffa yake cemun ya baki saƙo amma baki gaya mun ba" ya faɗa yana kallonta. Ta juya ido abinda ya sake kashe shi kafin tace "Wane saƙo kenan?" "Ya wuce ai tunda ya faɗa mun da kansa. Magana ce akan turo magabata na ayi maganar auranmu, na so na gaya masa har yanzu bamu samu fahimtar juna nida ke ba amma kuma na kasa". Ta ringa kallonsa babu ƙyaftawa harya kai aya kafin ta sauke kanta jikinta nayin sanyi kamar wadda rana ta daka, Ahmad ya harɗe hannu a ƙirji yana kallo ta ya sake cewa "Baffa da kansa ya mun magana na turo neman auranki, kar kisa ya ɗaukeni a mutumin banza idan na gaza cika umarninsa. Fatima me kike da buƙata? Ki gaya mun dan Allah me nene dalilin daya saka ba zaki bani dama na shiga rayuwarki ba?" A maimakon tayi masa magana kawai se gani yayi hawaye ya fara mata tsere dan da hasken Nepa tar a ƙofar gidan, ya buɗe baki yana kallonta da mamaki kafin yayi magana ta juya da sauri ta shige gida tana cigaba da kukan. Yayi kasaƙe a gurin, shi ba abin ya bita ciki ba mamakin dalilin kukanta ya rufeshi. Yana tsaye Baffa ya fito be ankate ba seda ya kira sunansa. "Malam Ahmad lafiya kuwa naga ta shiga gida tana kuka ko wani abu ne ya faru?" Baffan ya tambayeshi. To shi me zece masa yanzu? Gaskiya ze faɗa masa ko kuwa yayi shiru Baffan ya zargi wani abun yayiwa yarsa? "Wlh Baffa babu abinda ya faru, tambayarta kawai nayi ta amince na turo iyayena shine ta fara kuka ko magana batayi bama ta wuce ciki" ya faɗa cikin rawar murya. Baffa yayi ajiyar zuciya yace "Kayi tafiyarka kayi abinda nace maka in har da gaske kake son aurenta ka turo magabatanka" "Nagode Baffa in sha Allahu zaka jini bada daɗewa ba" daga nan yayiwa Baffa Sallama ya wuce, farin cikin daya samu dalilin ganinta ya gushe, har wani ciwon kai yaji yana neman kamashi kukan Fatima ya tabbatar masa da gaske bata sonsa tilas ya haƙura da wannan yarinyar muddin ba rabuwa da ita ne Ajalinta ba. A can gidansu Fatima kuwa bayan Baffa ya koma ciki tarar da ita yayi tana sharɓar kuka Umma na tsaye kanta tana faɗa kamar zata rufeta da duka. "Ya isa Zara'u rabu da ita" Baffa ya faɗawa Umman, ta zauna tana tsaki, ji take kamar ta rufe Afeeyar da duka ko zata maidata cikin hayyacinta. "Duk menene dalilin wannan abun? Me ya sakaki kuka daga yace ze turo magabatansa dama bakya sonsa ne ko kuwa ra'ayi kika canza?" Baffa ya tambayeta. Bata amsashi ba se kuka da takeyi ƙasa ƙasa. Umma ta jefeta da takalmi tana cewa "Ba magana ake miki ba kinaji kinyi shiru?" "Nace ki barta Zara'u ko?" Baffa ya faɗa a ɗan fusace. Umma tayi ƙwafa ta wuce ɗakinta. Baffa ya sake duban Afeeyah, yanda taji muryarsa ta tabbata ransa a ɓace yake ta san kuma fushi ba ɗabi'arsa bace tabbas ta kaishi bango ne dan haka yana sake maimaita mata tambayar jiki na rawa taja baya daga kusa dashi kafin tace "Ni daman Baffa ban taɓa cewa ina sonsa ba kawai bazan iya wulaƙantashi bane amma duk wata alama da ya kamata na nuna masa nayi amma yaƙi ya haƙura". Baffa ya ringa kallonta har tayi shiru, yafi minti goma kafin ya iya cewa "Kina nufin tsayin shekara uku da yaron nan yake bibiyarki yana wahalta miki duk ya tashi a banza yanzu zakice ba sonsa kikeyi ba?" "Wlh Baffa ni ban taɓa cewa yayi mun abu ba, kuma ai ko kai kana hanashi amma se ya dage se yayi kuma ni ina gaya masa ya dena kawai shine baya ji" Umma ta leƙo a fusace tace "Dan ubanko dole yanzu kice bakya sonsa mana kuma bake kika saka ya ringa miki wahala ba, Kare ne shi da ze shekara uku saboda rashin zuciya yana tare dake kina nuna masa rashin So kuma yaci gaba da zama dake? Kin gama yaudarar sa kin ɓata masa lokaci saboda baki da mutunchi yanzu zakice bakya Son sa me yasa tun farko baki faɗawa Malam ɗin ba shi da kansa ya kirashi ya sallame shi se yanzu da koɗaɗɗiyar fuskarki zakicewa mutane ke daman bakya son sa to wlh baki isa ba" Umma ta shiga sababi harta manta darene ta muryarta a sama. Baffa daya kasa magana tuntuni ya kalli Fatima yace ta wuce ɗaki, sum sum ta shige tana jin kamar an sauke mata wani nauyi daga kanta tunda har ta iya furtawa Baffa bata ra'ayin Ahmad tasan magana ta ƙare. A ɗaki Umma ta warwarewa Baffa komai game da zancen Yaron da Afeeyah take so wato Jay ɗan Ƙwallo. "A ina suka haɗu?" Ya tambayi Umman, ta watsa hannu kafin tace "Wai acan makarantarsu, Malam ka sanarwa Yaron nan kawai ya turo Iyayensa suzo a ɗaura musu aure kawai idan yaso ta mutu ƙarshen rashin Son Sa". "Ba za'ayi haka ba, za'a bi komai a hankali, magita zata samu da yardar Allah" inji Baffa. Daren raba shi yayi yana sallah da addu'oi, ya kasance me yawan tsayuwar dare amma yau Umma tasan sallar tasa harda ta neman ɗauki gurin Allah kan wannan abin daya tunkaro shi. Baffa na Son Afeeyah, amma abu ɗaya da tayi imani dashi shine baze bi Son rai ya zubar da ƙimar sa ba shiyasa ya maida lamarin ga buwayin sarki gagara Misali wanda duk hukuncin daya yanke babu wanda ya isa yayi inkari akai. Kwanaki uku Baffa ya jera yana Istikara cikin tareda tsananta Addu'a da roƙon ubangiji akan Al'amarin, Afeeyah kuwa rai fes dan Ahmad be sake kiranta ba tunda ya tafi kuma ta furta abinda yake ranta dan tasan Umma ta gayawa Baffa zancen Jay babban abinda ya sakat nishaɗi da farin ciki kuma shaida mata da Jay yayi yana tafe Nigeria nan da sati biyu masu zuwa. Saura kwana biyar su koma makaranta semester ƙarshe ce babu Lectures da yawa se aikin project da abinda baza'a rasa ba dan haka ta yanke ba zata koma bahar se yazo tukunna abinda bata taɓayi ba ƙarin hutu tunda ta fara University. Ta gayawa Badar Jay yana tafe, Badar nason Jay da Afeeyah amma ba kamar yanda take sonta da Ahmad ba kamar yanda take ce mata Ahmad Mijin Aurene Jay kuma na rage lokaci da neman suna domin ita dai bataji a jikinta Jay auran Afeeyah zeyi har yanzu ba duk kuwa da tarin ƙaunar da yake nuna mata akan haka har faɗa suka sakeyi ta dai rabu da ita tana kuma yi mata addu'a a matsayinta na ƙawarta. Takanas taje gidan Anty Sauda tace mata nan zata fara kawo Jay kafin Umma ta sauka daga fushin da takeyi da ita tukunna se ta kaishi gidan. "Yanzu kina ganin abinda kika zaɓawa kanki daidai ne Afeeyah?" Anty Sauda wadda Umma ta gaya mata duk abinda ya faru ta tambayeta. "Haba Anty dan Allah wai ana aure dole ne? Naga kema zaɓi aka baki kika kawo wanda kike so me yasa ni ake nema a tauye mun haƙƙi?" Ta jefawa Anty Saudan tambaya. Seta girgiza kai kawai tace mata Allah ya kawo Jafar ɗin lafiya, bata wani jima ba ta koma gida dukda zaman gidan ba wani daɗi yake mata ba yanzu saboda yanda Umma ta canza mata. Daga ita har Baffa babu wanda ya mata zancen ganinbata koma makaranta bama se Yah Malam daya zo hutu ne yace ya ya ganta a gida tace se wani satin zata koma. Baffabe canza mata kamar Umma ba dan ze amsa gaisuwarta har ya sakata aikace aikace kamar yanda ya saba amma Umma ko gaiseta tayi da harara take amsa mata tti duk yanda zatayi Umman ta sakko amma abu yaci tura tasan dai fushin Umma akan Ahmad ne addu'a takeyi Allahya kawo Jafar wanda yace zuwa ɗaya zeyi kafin yayi na biyu za'a tambaya masa auranta dan ya matsu. "Yah Ahmad ka dena sona wlh, yanzu ace zanzo gida amma babu wani murna ko ɗokin gani na daka sabayi kawai Allah ya kaimu shikenan abinda zaka ce?" Jafar ya dasawa Ahmad mita akan beyi murna daya ce masa zezo gida ba. Ahmad daya kwanta zazzaɓin malaria kamar yanda yayiwa Momy ƙarya amma gaskiyar abinda yake damunsa Love sickness ne. Tun ranar daya baro gidansu Fatiman damuwa ta saukar masa da ciwon kai da zazzaɓi me zafi amma haka yake bankar Anti Malaria da Momy tasa dole yaje asibiti aka rubuto masa. "I told you bani da lafiya Jafar amma kana ta so se ka sakani magana" "Ni ai bazanyi maka sannu ba saboda wannan ciwon kai ka ɗorawa kanka, let me ask you please, is this Fatima made of Gold or some sort of precious stone da tayi deserving wannan soyayyar da kakeyi mata? Yah Ahmad me yake damunka? For heaven sake kana nema ka kashe kanka akan wata banzar mace? Is she the only living woman on earth? Ko dai asiri tayi maka? Oh na manta mayyace believe me ta cinye maka zuciya kuma wlh bata isa ba. Ko waye ubanta she must leave you, seta fita a rayuwanka let me come back first I'm going to deal with her personally, se ta gane bata da hankali wlh" ya ringa sababi kamar ze aro baki daman kuskure Ahmad yayi daya taso masa da maganar gashi yana neman ya sake ƙara masa ciwo. "I love her, kuma banajin zan iya dena sonta idan da abinda zakayi kasa ta soni i will appreciate it more zaginta da kakeyi dan baka san abinda nake ji bane ba nidai idan kana sona da gaske just help me fight na samu Fatima" Ahmad ya faɗa. Jafar yayi shiruj irin wanda takaici ya gama tiƙewa kafin yace "Indai haka ne ze sa ka yarda Ina sonka then I don't love you Yah Ahmad and i will never love you indai se naso wannan yarinyar ne ka cireni a jerin ƙannenka, i hate her, i hate her with all my life kuma ko Allah yasa ka aureta bazan taɓa shiga gidanka ba" yana gama magana ya kashe wayansa yanda Ahmad ya jishi yasan ba ƙaramin zafi ya ɗauka ba. Yayi murmushi, yasan rigimar Jafar na lokaci ne zuwa anjima ze sake kiransa kawai dai wannan ƙiyayyar da yakeyi mata me zafi ce ya rasa dalilinta, saboda shine kuma yanzu so yakeyi ya haƙura da ita ba shikenan ba. **************** "Alhaji, ni tun kwanaki naji kana zancen Amadu ya samu mata ko? Ashe ma ya taɓa kaiwa Ummu ita, se jiya da muke magana Jafaru yace daya zo za'aje masa neman aure shine tace mun zancen ai taga budurwar Amadun ma ya ɗaukota daga makaranta suka biya gidanta wai ya karɓowa Aisha Leshi, wai a Zaria take makaranta, nace Yayan masu kuɗi suna zuwa wannan makarantar kuwa?" Alhaji Audu na kurɓar baƙin shayi daya sha spices, Girkin Hajiya Rabi ne ita ta dafa masa tana kawowa Hajiya Bintan tazo ta kankane gurin dole ta fita ta bata guri dan har ta fara sakar mata maganganu tana ci mata zarafi shi kuma Gwankin na zaune shirim bece komai ba. Ya gama sauraron Hajiyar kafin yace "Oh ya samu mata kenan da yake ke zaki nemo masa auran shiyasa ya fara sanar dake?" "Shi wa? Ummu nace maka ni a suwa Amadu ze faɗamun ya samu Matar Aure Aisha ce ni kowa?" Ta faɗa tana wani taɓe baki. Alhaji ya sake zuba shayinsa yana sha yace "Shi Ɗan naki nake magana" "Wai Jafaru? Dama idan be gaya mun ba toh wa kake so yaje ya fara sanarwa ko yana da wata uwar ne bayan ni a duniya?" "Aa bance ba, shi Ahmad ɗin dake ya ɗaukeni uba ai tun fara neman yarinyar da yakeyi ya sanar dani, kawai inda ya nemo auran ne be gama kwanta mun a rai ba shiyasa ma kika ga an kawo yanzu maganar bata tashi ba amma yafi shekara da sanar dani". Har wani zullo tayi kamar zata kwanta a gabansa tace "Ashe maganar ta daɗe? Daman Ummu tace anfi wata shida da zuwan nasu tun kafin lokacin bikin su Hafsatu to ashema ka sani toh naji kace gidan daya nemo auran ne beyi maka ba, da akwai matsala kenan?" Da zuciya ɗaya yace mata "Yar wani Bakanike ce yarinyar Malam Hafizu akace sunansa a Alfindiki yake, a binciken da na saka akayimun dai Mahaifin yarinyar nace bashi da matsala mutumin kirki ne toh amma ita yarinyarce surutu yayi yawa akan yanda Samari suke zuwa gurinta wannan yazo wannan ya tafi gashi a matsayin mahaifinta irin rayuwar da akace tanayi ta wadata ya zarce ace shi yakeyi mata, kinsan yaran yanzu, zakiga Iyaye suna iyakacin ƙoƙarinsu gurin tarbiyya amma idan sun fita se abinda hali yayi musamman masu tafiya karatu wasu garuruwan ba gaban Iyayen nasu ba to wannan yasa na dakata kuma shima Ahmad ɗin tun maganar farko da mukayi be sake tayar mun da zancen ba dukda dai ina da labarin suna tare haryanzu kuma ita kaɗai yake kulawa ta yuwu yana jira ta kammala makaranta ne tunda ance shekarar ƙarshe take". Tamkar me ɗaukar karatu haka Hajiya ta naba'a tana sauraron Alhaji se gyaɗa kai takeyi har ya kai aya kafin cikin Jimami tace "Ikon Allah, shi kuma Amadu inda ya tafi kenan? Nida nake ta sauraro naji ya samo yar gidan Ɗangwate ko BUA tunda suke abokanan goga kafaɗarka a ƙasar nan seya ɓige da yar gidan Bakanike? Toh Allah ya rufa asiri, ita dai ta Jafaru ance Balarabiya ce dan ya turawa da Munirah hotonta wai irin wanda ake kalla sau ɗaya ne shiyasa bata kwafa ba ta ajiye mana. Todai daya zo koma ya ake ciki zamuji, seka fara shirya wa'inda zasu nemo masa auran inajin dai baze wuce a Saudi Arebia ba ko Dubai" Alhaji yace mata "Toh, Allah ya kawo shi lafiya" "Toh amma Alhaji ina da wata magana idan babu damuwa kuma ka bani dama in faɗa" yanda tayi maganar yasa ya tattara hankalinsa akanta dan yaji me zatace. Hajiya ta gyara zama kamar gaske kai a ƙasa tace "Dama Alhaji akan mu'amalarka da yaran gidan nan ne naga ya kamata a gyara wasu abubuwan, ina nufin su Alhaji Babangida da sauran yaran da basa cikin gidan nan. Bana jin daɗin yanda kowa idan ya tashi yake ɗora mun laifi a ringa cewa ni ce na rabaka da yayanka. Kaga girma ya cin maka, ya kamata ace zuwa yanzu ka fara sakin wasu abubuwan ka bari Manyan yayanka suyi maka". Alhaji yayi tagumi yana kallon Hajiya Binta data sake gyara zama tana cewa "Ba harkar kasuwancinka nake nufi ba, wannan ai kana da magada daka rigada ka koya musu komai kuma suka goge akai ina nufin kamar harkokin aure, kaga daga kai har Yakubu kun manyanta ya kamata ku zauna ku huta ku fara sakarwa Yayanku suna jan ragamar abubuwa". "Wato ba zaki ringa karanta sunan Yakubu ba, Idan beci darajar girmata da yayi kin kirasa da Yaya ba ai kya bashi sunan da kowa yake kiransa dashi Alƙali" Alhajin ya tareta. Ta lanƙwashe kamar yarinya tace "Allah baka haƙuri saboda faɗa ne uffararan Baba Alƙali nake so nace, to da kai dashi duk ku huta ka kirawo Yayanka gaba ɗaya ka zaunar dasu kuyi maganar nan, ka ware wanda zasu ringa zuwa tambayowa Maza aure da kuma wanda zasu ringa karɓan na mata idan an zo. Amma kafin nan ya kamata duk wani abu daya taso ka ringa tarasu kana shawara dasu, ta hakane zaka jasu a jiki suma su sake dakai a hankali se kaga duk sun dawo gida a dena zagina a gari ana cewa na raba yaya da ubansu". Alhaji ya sakeyin shiru yana nazarin maganarta, Alƙali Yakubu ya taɓa yi masa makamanciyar magana irin wannan, yace ya kamata ace ya ringa janyo Yaransa a jiki domin ya gyara kuskurensa na baya. Rayuwarsa ta fara zuwa gangara, be kamatu ace ya mutu ya bar kan iyalansa a rarrabe kamar yanda suke a yanzu ba. Maganar Bintan se ta sakashi Nazari, tabbas abinda ta faɗa gaskiya ne domin Abokanansa masu Manyan Yaya kamar nasa da yawa yanzu a kwance suke suna hutawa komai da masuyi musu, ze gwada shawarar tata koda akan zuwa batun Neman aure ne da karɓar ze saka su yasan babu wanda zece bazeyi ba a cikinsu. "Kamar yanzu da zancen auran Ahmad dana Jafarun nan musamman na Ahmad da kake da kokwanto akan yarda ko akasin haka, ka tarasu, ka nemi shawararsu kaga zasuji daɗi suga ka mutuntasu kuma su sun fika sanin kan duniya yanzu se kaga an samu maslaha ai ko?" Ta sake faɗa. Alhaji ya jijjiga kai da alamar gamsuwa, tayi murmushin cin nasara sannan tace "Toh amma fa karka gayawa matanka ko Yan uwanka shawarata ce dan ka san cewa za'ayi da wata manufa nayi ni kuma Allah yaga zuciyata babu komai face Alkhairi so nakeyi ka shirya da yayanka ka haɗa kan zuri'arka", bata tashi daga gurin ba seda ta gamsar da Alhaji Alfanun abinda tace yayin ya kuma yarda da hakan. Babu ɓata lokaci a daren ya kira Alhaji Babangida, umarni ya bashi akan ya haɗo masa kan Yan uwansa daga Babannan zuwa Mu'allim, banda Matan da kuma Zayyad da Abdallah da basu isa ayi wannan shawarar dasu ba. Alhaji Babangida ya shiga mamakin ko lafiya wannan kira haka da Alhaji yayi musu amma babu damar tambaya. A washe gari ya sanarwa da waɗanda yake da numbers ɗinsu a waya ta hanyar Text message yace su sanar da sauran. Ya sake kiran Alhaji domin ya manta be tambayi ranar da yake da buƙatar ganinsu ba. "Ranar Asabar ɗin nan" Alhaji ya bashi amsa. Alhaji Babangida yace Zan sanar dasu ranar, amma naji Jafar yana tafe ranar Talata, ba za'a iya ɗage taron a jirayi zuwan saba?" "Aa, duk abinda aka tattauna idan ya dawo zaku sanar dashi" da haka sukayi sallama. Ya gayawa Alƙali ze zauna da yaransa duka ya kumayi murna da hakan domin an samu cigaba kenan Alhaji Audun ya shiryi samun daidaito tsakaninsa da Iyalansa. PAGE 17 A bisa dole Iyalan Alhaji Audu suka amsa goron gayyatar daya aika musu dashi. Ba kalar mitar da basuyi ba amma haka suka zo domin koda basa ga maciji da mahaifin nasu sun sanshi sarai baya ɗaukar wargi, farillan rashin mutumchi kuwa sala sala yanadasu wanda yake amfani dasu gurin ladabtar da duk wanda yace zeyi masa giggiwa. A cikin su daman wanda yafi kowa taurin kai Alhaji Hussaini ne, da Dr Hassan ya sanar masa da kiran Mahaifin nasu take yace masa "Bazanzo ba, inada abubuwan da suka fi muhimmaci da sauraron kalaman son rai da wannan tsohon ze faɗa mun in kuma ya fara tafiya gargara ne yake so ya bada wasiyya ka karɓa harda tawa ka riƙe na bar maka in ma mutuwa yayi ni wlh na yafe gadonsa tuni". Seda Hajiya Zubaida Mahaifiyarsu tayi masa kaca kaca bayan da Dr Hassan ya sanar mata da abinda yace tace kuma tilas yaje idan kuma ya isa ya tsallake umarninta daman ita kaɗai take maganin Iya shegensa, yana son mahaifiyarsu yana tausaya mata yana kuma riƙe da abinda aka labarta musu cewar Alhaji Audun yayi mata tun kafin haihuwarsu da bayan zuwansu duniya. Ƙwato su da yayi ya maidasu gidan ya zube su a tsakar gida shine abun daya ƙara ta'azzara tsamar dake tsakaninsu. Yanda Hajiya Binta ta ringa yi musu, kalar azabatarwar da tayi musu har gobe yana addu'ar kafin ta mutu in sha Allahu seta ɗanɗani sama da baƙin cikin data shayar dasu. Matan da akace banda su dalilin irin wannan taro da ba'a taɓa yin irinsa ba suka san lallai da akwai wani babban Al'amari a ƙasa wannan tasa kowacce ta wanko ƙafarta ta taho ranar taron. Momy da Hajiya Rabi basu san wainar da ake toyawa ba har s ana i gobe taron da suka tsinkayi muryar Hajiya Binta na bada umarnin abinda za'a girka gobe da yawan wanda za'ayi. Lokacin Salim na falon Momyn yana cin abinci yayi tsaki yace "Wai me matar nan take shiryawa ne? Dan dai Alhaji bashida wata shawara tasa ta kansa se abinda tace masa" "Wani abu ya faru ne?" Momy ta tambayeshi shine ya faɗa mata kiran da Alhajin yayi musu. Tayi shiru, ita tayi girki jiya yauma itace amma ace Alhajin bega ya kamata ya sanar mata da komai ba ai shikkenan. Bata masa zancen ba har washe gari da Asuba kafin ta baro bangaren nasa taji yana waya da wani abokinsa yana sanar masa baze samu zuwa wani ɗaurin aure ba shine bayan ya gama yake ce mata wai ze gana da Yayansa duka akan maganar aurab Ahmad. Cikin mamaki tace "maganar auran Ahmad kuma? Yaushe zancen ya taso da ni ban sani ba? Sannan naji kace zaka tattauna da Yayanka akan maganar daman haka kakeyi idan auran yayan naka ya tashi ko kuwa wani sabon salo ne ka tsiro dashi da za'a fara akan Ahmad?" "Ya zaki ringa min wasu tambayoyi se kace wani ɗanki? Tsakanin nida ke waye yafi zamarwa dole daya san maganar auran Ahmad ko kuwa ke zakije ki tambayo masa auran?" Alhajin ya faɗa yana wani zare mata ido irin ta zo masa da raini. Zuciyarta ta harzuƙa domin ta tabbatar wata maƙarƙashiyar ce aka shiryota kuma Binta ce idan ba haka ba ita dashi basu taɓa zancen auran Ahmad ba, tabbas Ahmad ya gaya mata iyayen yarinyar sun bashi izinin ya turo magabatansa har yace tayiwa Alhajin magana tace ba zatayi ba ya same shi da kansa bayan nan kuma ya fara rashin lafiya ta tabbatar da ace sunyi magana da Alhajin tilas seya gaya mata yanda sukayi domin a ko ina zata shaideshi baya abu gaban kansa ba tareda yayi shawara da ita ba kuma duk yanda ake ciki seya koma ya gaya mata ta sake bashi haske akan abinda ya kamata yayi. To ace ma Ahmad ya masa magana sun tattauna shiya manta be koma ya gaya mata ba ai shi Alhajin a matsayinta na uwar Ahmad tana da haƙƙin ya sanar mata da zancen auransa ba wai taji a sama yaje ya shawarta da wadda a kullum bata da burin da taga kasawarsu. Ta sani ya fayyacewa Binta inda Ahmad ya nemo aure shine zatayi amfani da hakan dan ta tozarta yarinyar da iyayenta toh kuwa Allah ya fita ba zata taɓa cin galaba ba. "Ai ko riƙon Ahmad nakeyi ba wai ni na haifeshi ba ya kamata a fitar mun da ladan wahalata a sanar mun da zeyi aure, kuma a gidan nan baka taɓa haɗa taro dan wani Ɗa zeyi aure ba akan me za'a farashi akan Ahmad? Saboda shi me biyayya ne duk yanda aka bi dashi zece toh shi yasa kake so ka tauye masa haƙƙi ko yaya?" "Ki fita kuma ƙarfe goma ne taron, umarni ne na baki ba wai shawara ba ki kasance a gurin" ya bata amsa cikin halin ko in kula ba tareda ya bi ta kan maganganunta ba. Hawayen takaici suka zubo mata ta share ta fice daga ɗakin, tana can ƙuryar ɗakinta ta kira Yar uwarta Maimuna ta gaya mata abinda ake ciki. "Kije ki zauna a gurin saura kuma ki zama hoto kiyi shirun da kika saba a zartar da abinda ba haka ba dan nasan munafunci yasa aka shiryi wannan zaman ba wai dan Allah bane" Maimuna ta gaya mata. Tana shirya masa abin kari Hajiya Rabi ta shiga Falonta. Suka gaisa take tambayarta zaman da Alhaji ya kirata a waya yanzu yace mata wai ƙarfe goma. "Nima da Asubar nan ya gaya mun wai akan Ahmad ne, amma ita hamshaƙiyar ai tasan da komai tunda tun jiya naga tana bada umarnin abincin da za'a dafa" Momy ta bata amsa tana murmushin takaici. Hajiya Rabi cikin jimami tace "Ahmad kuma? Nasan dai ba laifi yayi ba koma menene Allah yasa Alkhairi ne, bari naje na shirya toh" daga haka ta wuce tana ta lissafin to wane irin abu kuma Ahmad yayi ko zeyi da har se an masa taron dangi haka? Tun tara Iyalan Alhaji Audu suka fara hallara a gidan. Wasu su kaɗai suka zo wasu tareda yayayensu da matansu dan haka gidan ya cika hayaniyar jikoki kota ina tashi takeyi suna ta guje guje. Ƙarfe goma Mazan suka hallara cikin babban falon da ke bangarensa a ƙasa gaba ɗayansu Jafar ne kawai babu a gurin. Bayan an buɗe taro da Addu'a tareda jawabin maraba daga uban garken, babu ɓata lokaci ya shiga zayyano musu maƙasudin kiransu wannan taro. Shiru falon ya ɗauka banda ƙarar Ac bakajin komai se salallamin da Hajiya Binta takeyi murya a sama tamkar wadda aka aikowa da mutuwar iyayenta dare ɗaya, yanda takeyi seka rantse da Allah yanzu ta fara jin maganar, tamkar bada ita ta tsarawa Alhajin daya tara su ba domin ta ƙaddamar da wani shiri nata. Can kuma ta zabura ta miƙe tsaye idonta akan Ahmad daya sunkuyar da kai ƙasa, abinda yake ji a zuciyarsa baze misaltu ba, wai duk akanme? A ina aka taɓa haka? Shi yaushe ya cewa Alhajin maganar aurensa ta tashi? Auran da yake ƙoƙarin yakicewa ya haƙura da yarinyar shine aka zo ana masa wannan taron dangin akansa? "Amadu ashe baka da hankali ban sani ba? Wayonka da nake gani na banza da wofi ne baka san komai ba se neman kuɗi kamar Ɓarawo?" Hajiya Bintan ta faɗa, Momy ta ɗago a karon farko tun zamanta a falon ta kalleta jin kalmar data jiɓanci gudan jinin nata da ita wai Ɓarawo ita kuwa Hajiya bata dakata ba a fusace taci gaba da cewa "Wallahi tallahi ko sama da ƙasa zata haɗe banga uban daya isa ya ƙulla auran nan ba, yar Bakanike Amadu? Mu zamu haɗa surukuta da Bakanike kuma Sadaka yallah mayu? to idan ita uwarka sallamammiya ce komai aka ce bata musawa ni bazan lamunta ba. Iyakar irin tsiyar da aka ɗakko mana sun isa ba se an haɗo mana da wanda zasu zo suna mana ɗauki ɗaiɗai suna ciyayya ba" Hajiyar ta kai aya tsabar masifa numfashinta har neman sarƙewa yakeyi. Alhaji Audu dake kishingiɗe akan kujera ya nisa yace "Duk wannan a ganina ba wani abun azo ana tayar da jijiyar wuya akai bane, magana ce ta aure kuma shi ma'auri yace yaji ya gani sannan ni da kaina nayi binciken iyayenta kuma ban samu wani abun ƙi da ze saka a hana shi auranta ba, ni kiram da nayi muku na taraku ne dan muyi shawara akan yanda za'abi gurin neman auran, suwa za'a wakilta suje". Momy da Anty Amarya suka kalleshi kamar yanda da yawan yayayensa dake zaune duk suka kalleshin. Harara Hajiya Binta ta maka masa kamar wani ɗanta tace "Lallai Alhaji, ya kake nema ka canza magana koda yake kwanakin nan ka zama me fuska biyu daman" Mamaki kamar ya shaƙesu jin abinda Hajiyar ta faɗa masa, kunne, baki da hanci duk suka zuba suna jiran suga matakin da ze ɗauka amma sukaji muƙus ko tari Alhajin beyi ba sema Hajiya data ci gaba da sababinta tana cewa "Da zakace bakaga wani aibu da ze hanashi auranta ba ai kuwa ita keda babban aibu, Talaka yar talaka jikar talaka kuma Mayya". "Amma Hajiya talauci fa ba fasiƙanci bane, sannan baya cikin sharuɗɗan da suke hana aure. Kuma maita da kike jifanta da ita kin san cewar fa ba ƙaramin abu bane idan sukaji zasu iya yin ƙararki akan hakan tunda baki da wata tartibiyar hujja data tabbatar da abinda kike jifansu dashi" tsautsayi ya saka Hajiya Rabi magana tamkar kuwa Hajiya Binta na jiranta daman tace "Babu shakka Rabi dole kice talauci baya cikin abinda ze hana aure saboda kinji zaki samu ƙarin yar uwa ko Ahalul fuƙara'u za'a ƙara yawaita? Koda yake ma a hakan ita ai ta fiki tunda nata uban ance yana da tsayayyar sa'ar da yake samun abun kaiwa bakin salati ba irin naki tsohon ba da se an bi gidaje anyi yawon maula kafin a tattara a kaiwa Iyali ya isa be isa ba a yayyafa aci shi kansa Alhajin daya kwaso wa kansa ƙaya gashi nan kullum cikin nadama da dana sanin auranki yake, jiya farar safiya gari ko gama haske beyi ba me dattin hula ya buga mana gida wai katangarku ta faɗi, daka fita ka bashi kuɗin ina dawowa kayi kana mitar daka saba duk sanda yazo maka maula irin rayuwar da kake so shima Amadun ka jefa shi a ciki kenan ya ƙare yana nema dangin Sadaka Yalla su dabaibayeshi su cinye sannan subi ɗan naman jikin nasa ma da ba auki ne dashi ba su lashe ni daman kwanakin nan zugewar nan da yakeyi ina ganin har sun fara lasar sane wlh sun zarge kurwa tab" Hajiya Binta ta faɗa tana tsaida idonta akan Alhajin. Baƙin cikin maganganunta suka sanya Anty Amarya barin falon babu shiri saboda kukan daya taso mata, shekaru kusan Ashirin kenan babu ranar Allah da zata fito ta koma ba tareda ta goranta mata talauchin da ba ita ko iyayenta suka siyawa kansu ba, dukda tabbas Mahaifinta shi yake ƙara zubar mata da mutunchi saboda ya kasa wadata da dan Abinda Allah ya hore mata take taimakonsu dashi haka shima Alhajin ta sani iyakar Ƙoƙari yanayi cikin su ukun ita kaɗaice duk watan duniya seya saukewa iyayenta buhunhunan Abinci da kuɗin cefane duk a son Baban nata ya dena banzar ɗabi'arsa ta yawon maula gidajen Masu kuɗi, ya dai rage amma fa kullum yana tafe gidan Alhaji Audu, sabulun wanka omon wanke wanke ko yana da kuɗin da ze siya se yazo ya roqa an bashi. Hajiya ta bita da Harara taja tsaki ganin Mu'allim yabi bayan mahaifiyar tasa bayan daya bi Hajiyar da wani kallon Tsana idanunsa sun tara ƙwallar baƙin ciki "Umma ta gaida Ashsha, dama banga tsegumin daya kawo ku ba Alhalin baku da abin faɗi" Hajiyar ta faɗa tana buga cinya kamar wata yarinya. Alhaji Babangida ne yayi gyaran murya, daga jin yanda yake magana kasan a tunzure yake yace "Amma Hajiya Binta ni banga ta inda zancen Auran Ahmad ko wadda yake son aure ya shafeki ba tun da dai ba ɗanki bane. Ita mahaifiyarsa batayi ƙorafi ko nuna rashin amincewarta akan abun ba se ke meye naki a ciki? Sannan koda ace mahaifin yarinyar nan yafi kowa talauci a duniya wannan ba hujjar ace ba za'a auri yarsa ba tunda talauci ba fasadi bane" "Nima abinda na gani kenan Yaya, duk ma ba wannan ba a gidan wa aka taɓa titsiyewa akan matar da yake son aure? Ina har yar rawar Tiktok aka auro mana gashi nan ta fitini kowa tana koyawa yaranmu shaiɗanci amma waya ɗaga kai yace wani abu kan hakan kodan saboda shi shafaffe ne da mai shiyasa ba'aga aibun abinda yayi ba se Ahmad da an san idan aka ce kar yayi ze haƙ Lura ai biyayya kuma ba hauka bace" Dr Hassan ya faɗa cikin ƙunar rai. Hajiya ta harari Alhaji Babangida, koda ta girme shi amma shakkarsa takeyi ta san ko shi Alhajin yana bashi darajar kasancewarsa Ɗa na fari a gidan, maganar Hassan ce tasa tayi kasaƙe tana kallonsa. Naziru ya zaburo masa yana cewa "Ka kira sunana kai tsaye ka dena wani kwane kwane, kuma na auri yar Tiktok ɗin koda abinda zakayi akai?" "Yi shiru da bakinka Naziru barni dashi" Hajiya ta gyara zamanta taci gaba da cewa "Yanzu kai Hassan tsabar baka da kunya ana maganar matar aure me Asali da tushe daga babban gida har ka saka baki? Koda yake kana da hujjar bin bayan Al'amarin, tunda uwarku ta auru a matsayinta na Tubabbiyar Karuwa ai dole kace wannan ma ba......" Tsawar da Hussaini ya daka mata me kama da saukar Aradu ta saka sauran maganganun bakinta maƙalewa. Cikin yanayin da yake nuna ƙololuwar ɓacin ransa dan hatta da jijiyoyin kansa daya sha askin Skin sun fito ruɗu ruɗu haka idonsa ya rikiɗa yayi jajir ya nuna ta yana cewa "Akul Binta, duk abinda kike ji dashi ya tsaya kan waɗanda kika raina karki yi kuskuren sako mahaifiyarmu a shirginki domin yanzu ba da bace idan kuma ba haka ba...." "Idan ba haka ba me zakayi?" Alhaji Zakariyya ya diro gabansa kamar wanda aka harbo da kwari da baka yana huci, Hajiya da tsoron Hussainin ya cikata jikinta har ɓari yake ta ja hannunsa Zakariyyah tana cewa "Barshi Ubana kasan ɗan hau ne" "Ki ƙyaleni Hajiya ku kuke nuna kuna tsoronsa a gidan nan idan zafin kai da ƙwaya yake ji dasu shi ƙaramin ƙwarone kansa baze ɗauki ko rabin chajin da nakeyi ba an faɗa ance Yayan Tubabbiyar Karuwa kayi abinda zak...." Marin da Hussanin ya ɗaukeshi da shi irin me jirkita ƙwaƙwalwar nan ya sakashi wuntsilawa gefe dafe da fuska yana raba idon, Hajiya Binta ta fasa ihu tayi kansa ganin yanda yake zare ido kamar tunaninsa ya kauce, a fusace shi kuma Naziru ya cakumi kwalar Hussanin ya kai masa naushi a fuska yana cewa "Wlh baka mari banza ba sena rama masa" kafin kace me dambe ya sarƙe a tsakaninsu kowanne ya shiga kaiwa ɗan uwansa mugun hari da yake jikinsu iri ɗaya ne, dukkaninsu sangangan suke irin jikin Audu Bechi wannan ya ƙarawa Damben nasu armashi dan kowa ya gagara kai ɗan uwansa ƙasa amma dai Hussainin yafi kai hari a zuciye. Ahmad, Momy da Dr Hassan ne suka shiga ƙoƙarin raba su sauran jama'ar falon kuwa seka rantse a Tv suke kallon wannan Al'amari babu wanda ma ya motsa balle ya kai agaji sema tattare ƙafafunsu da sukayi dan kar a faɗo musu. Hajiya na gefen Alhaji Zakariyyah dake kururuwa kamar mace sakamakon yanda Marin ya shammaceshi ya shige shi dagaske ga haƙorinsa ɗaya daya turguɗe a ƙasa, ihu Hajiyar take itama tana Zagin Hussaini, jafa'in duniya babu wanda bata janyo masa ba dashi da Hassan ɗinsa harda uwarsu dake can gida bata san wainar da ake toyawa ba ta karɓi rabonta se abi da Hajiyar ta manta ne bata ambata ba. Momy ta kalli Alhaji Audu dake zaune akan kujera tamkar gunki cikin kuka tace "Kana kallo Alhaji, jira kake se ɗaya ya kashe ɗaya kafin ka tsawatar musu? Wannan shine daidaiton da kake fatan samuwarsa cikin zuri'arka? Anya kuwa Alhaji ka shiryi tarar da ubangijinka cikin salama kamar yanda kowanne musulmi yake fata?" Tana gama faɗar haka cikin kuka ta fice daga falon, a bakin ƙofa taci karo da yayansu Mata a tsaitsaye cikin tashin hankali. Hajiya ƙarama datafi kusa da ita tacewa "Kira Babanku Alƙali ki gaya masa yazo babu lafiya a gidan nan" ta shige cikin gida tabar Hajiya ƙarama na ƙoƙarin kiran Baba Alƙali amma sau biyu wayar na suɓuce mata saboda yanda jikinta yake rawa daƙyar ta iya danna kiran. Momy kuwa harta isa ɗakinta hawaye be tsaya mata ba, ba kuma tasan ranar da zata dena zubar dasu ba hawayen baƙin ciki, takaici da dana sanin auran wannan mutumin da sam bata san me zata kirashi ba. Son zuciyane ko kuwa tsabar ƙin Allah ya saka Alhajin yin abubuwan da yakeyi bata sani ba amma koma menene ta tabbata muddin be tuba ya gyara alaƙarsa da Ahalinsa ba ya mutu a haka tabbas baze kwanta cikin salama a Kabarinsa ba. A can falon kuwa Hussaini ya mazge Hassan ɗinsa daya cukumi cikinsa yana ƙoƙarin janyeshi kafin ya kaiwa Ahmad ƙafa amma ya goce ba shiri suka matsa daga rabon damben suka barsu zuwa sannan Hussainin keda nasara dan ya kai Naziru ƙasa ya masa lilis har ya kai baya iya maida martani se Ƙoƙarin kare kansa kawai yake amma Hussaini be haƙura ba yaci gaba da jibgarsa kamar Allah ya aiko shi. Dama ce irin wadda ya daɗe yana fatan samu da ze huce kaɗan daga irin takaicin da Hajiya Binta da Yayanta suka ƙunsa musu a rayuwa. Lokacin yarinta tsoron hukuncin da Alhaji zeyi musu da izayar da zasu sha a hannun Hajiyar tasa yake haƙura idan zuciyarsa ta raya masa daya jibgi yayanta in suka musu abu, yasha ya kwatanta ya dake sun in yaso ya gudu ya bar gidan amma yasan Hassanbaze yarda ya bishi ba, saboda shi ya shanye duk wani wulaƙanci a gidan yanzu kuwa Allah ya bashi damar da duk wanda yace ze shigarwa Nazirun seya haɗa dashi ya zane. Seda Hussani gama yayiwa Nazirun casar gero kafin Allah ya bawa Alhaji Audu ikon yunƙurawa daga zaunen da yake tamkar wanda ya tafi hutu wata duniyar na wucin gadi ya dawo haka ya shiga jan numfashi kamar me Asthma. Ahmad yayi kansa yana cewa "kun gani ko ku bari idan ba kashe shi kuke so kuyi ba". Hussaini daya gama aikin Allah ya tsugunna ya ɗauki Agogon Azurfarsa daya tsinke a garin dambe bayan daya gaji da jibgar Naziru ya kalli Ahmad yace "Toh ya mutu mana, dama wa rayuwarsa ta dama bare idan ya mutu yayi baƙin ciki? Ƙilan ku da su daya ɗauka Yaya ya fifitasu akan kowa sune zasu shiga uku duk ranar da aka ce babu shi" sannan ya kalli Hajiya Binta da idanunsa da suka koma abin tsoro yace "Nan gaba idan wani daga cikin marasa kunyar Yayanki yayi niyyar tsoma baki a sabgata ki gargaɗeshi, idan ba haka ba zanci gaba da nuna muku abun da Ɗan Tubabbiyar karuwa ze iya aikatawa" yana gama faɗar haka ya fice daga falon a fusace fuuuu kamar kububuwa. Maganganun Hussaini sun daki ƙirjin Alhajin kamar shigar bullet, ya yunƙura cikin wani yanayi ya tashi tsaye dan bakinsa kamar an liƙe masa shi da glue yake ji yana tsayuwa akan ƙafafunsa jiri ya kwasheshi ya koma kan kujerar Yaraf kamar wata gingimemiyar giwa ta faɗi. Ahmad da Hassan suka rufu akansa, Hassan ɗin ya kalli Ahmad yace "Riƙeshi, bari na ɗakko Kit ɗina a mota mu gani idan kuma babu hali mu wuce Asibiti dashi kawai" yana gama faɗar haka ya fice da gudu kamar yaro ya nufi motarsa. Da wani irin yanayi Alhajin ya ringa kallon Yayansa Maza da suka fara miƙewa da ɗaɗɗaya suna barin falon harda masu sakin ƙananun tsuka dalilin ɓata musu lokaci da akayi da wannan wasan kwaikwayo da suka rigada suka saba dashi babu Wanda ya nuna damuwar cewa wai Mahaifinsa ne a wani yanayi da ko ba'a faɗa ba sunsan Hawan Jininsa ne ya tashi Allah ma ya taƙaita ba Paralysis ya samu ba irin wannan komawa da yayi ya faɗi akan kujera, wani abu ya tokarewa Alhaji Audu maƙoshi, hawaye ya ziraro a idanunsa abinda ya sake rikita Ahmad kenan a shekarunsa Talatin a Duniya sau ɗaya ya taɓa ganin ƙwalla a idon Mahaifinsa lokacin da aka kawo gawar Brigadier General Baballiya se yanzu kuma hawaye yake dagaske tabbas Al'amarin dake zuciyarsa ba ƙarami bane. Yanda Dr Hassan ya dawo yaga Alhajin yasa yace kawai su kamashi a tafi Asibiti. Seda ya ɗura Ashar kafin su Salim suka saka hannu aka fita da Alhajin dan Manyan daman tun yana wajen yaga suna ta shigewa motocinsu suna jiran Iyalansu su fito su tafi, da alama Abincin da Hajiya tasa akayi zeyi bandaro dan zama beyi daɗin da har za'a jira cin abinci ba. Hajiya ta ringa ihu kamar wadda ta shiga ƙaramin hauka, Ga Zakariyyah fuska harta suntume saboda haƙorin daya fita ba bisa ƙa'ida ba Naziru kuma na kwance numfashi ne kawai ya banbantashi da matacce Hussaini ya sauke masa duk wata giggiwa da yake fama da ita suma ɗin Dr Hassan ne yasa aka watsa su a mota duk suka rankaya a Asibitinsa. A hanya Ahmad ya kira Baba Alƙali yace masa yana tafe ya kusa isowa gidan Hajiya ƙarama ta kirashi se yace masa ai suna hanyar Asibiti be jira jin ba'asi ba yace ze same su acan domin yasan a runa. Haka nan rana tsaka Audu ya tattaro irin wannan haɗuwar ba tareda yabi matakan da suka dace ba, zuri'ar da kowanne yake da wani fushi ko miki a zuciyarsa ta yaya zaka ce a lokaci gida zaka sasanta komai ka samu yanda kake so? Ya tabbatar wani abun akayi ko aka faɗa masa da ze saka jininsa ya hau tilas Allah dai ya taƙaita. Emergency aka karɓi Alhaji Audu su Naziru ma aka watsa su inda ya kamata. Seda akayi stabilizing kowannensu kafin suka samu nutsuwar zuciya. Baba Alƙali ya ringa sababi kamar ya ari baki sanda Dr Hassan ya bashi taƙaitaccen labarin abinda ya faru. "Ka kira Hussainin ka mai komai dare ya sameni a gida yau wane irin abu ne yake damunsa duk me ubanku ya muku ai baze canza masa suna ba ya za'ayi ya faɗa masa irin wannan maganar? Kai bama shi kaɗai ba gaba ɗayanku ku hallara ina son ganinku tunda naga alamar so kukeyi ku janyo mana abinda ze fi ƙarfin mu". " "Nima dai haka na gani Alƙali, ni daga yin abu dan Allah da zuciya ɗaya nace a shirya taron nan ya janyo yayansa a jiki su samu daidaito amma kaga yanda abu ya ƙare dana sani bance ayi ba haka kawai wannan la'anannen yaron ya cutar mun da yaya ya barsu da jinya" Hajiya Binta ta faɗa. Alƙali ya kalleta, cikin tsanin fushi yace "Har akwai wani la'ananne bayan ke ne Binta? Ke ce saboda rashin tsoron Allah zaki ce kin shirya abu da zuciya ɗaya saboda Audu ya samu daidaito da Yayansa ko ki sake farraƙasu? Kinyi ne da niyyar ki tozarta Ahmad da matar da yake son aure tun gabanin ta shigo cikin mu kina so kuma ki lalata kyakykyawar Alaƙar da kikaga ta fara ginuwa tsakaninsa da Mahaifinsa ta hanyar saka Audu ya hanashi abinda yake so daga nan ki saƙa mumummunan zare a zuciyarsa ko? To ba zakiyi nasara ba da yardar Allah duk wani sharri da kike yi bazeyi tasiri ba, duk wani sharri da kika niyyaci ƙullawa akanki ze ƙare. Kin bawa shekaru hamsin baya, ubangiki yayi miki Arziƙin tsahon rai ya baki dama da zaki gyara kurakurenki na baya amma saboda kin rigada kin auri duniya shaiɗan ya gama samun isahshen guri a zuciyarki baze barki ki hango gaba ki tubarwa Allah ki gyara laifukanki na baya ba a kullum zuciyarki sharri ce a ciki shi kike ƙoƙarin aiwatarwa. Ni naji daɗin daya dake su, kuma da kaina zan bashi goyin bayan duk mara tarbiyyar daya sake taɓa martabar Mahaifiyarsa idan ya samu dama ya tsinke masa harshe, abu guda ne bazan lamunta ba rashin Ɗa'a ga ubanku, kome yayi muku tilas yaci arziƙin yin silar zuwanku duniya, in har da gaske yakeyi ya shirya neman sasanci daku ku bashi dama domin ubangiji ma muna saɓa masa kuma mu nemi afuwarsa ya yafe mana wannan shaiɗaniyar ita ce silar faruwar komai a rayuwar Abdulwahabu ku taru ku taimaka masa ku kaita ƙasa ku bata kunya tunda dai ita babu gyara a rayuwarta tamkar dabbar Daji take kullum ƙara nausawa dawa takeyi". Alƙali Yakubu be damu da cewar a Reception ɗin Asibiti suke ba kuma da mutane suna ta kai kawo a gurin duk anyi cirko cirko ana sauraronsa ya wanke Hajiya Binta tas da soson kaba haɗi da klin da hypo, yanda yake maganar murya a sama zaka tabbatar da cewar yau zuciyar Mazan ta harzuƙa dab kuma yake daya kwasa mata mari muddin tace zatayi inkari akan abinda yake faɗa. Hajiya kuwa hannaye biyu ta aza akai tana kuka tana cewa "Daman na sani kaf dangin Audu babu wanda ya tsaneni ya tsani zuri'ata irinka Yakubu, ni kake kira La'ananniya? Nice shaiɗaniya? To bari naje seya tashi ya Zaɓa koni ko kai. Idan kai ya zaɓa daga nan gidanmu zanyi dan babu abinda ze sake zaunar dani a inda ba'a san mutunchina dana Zuri'ata ba idan kuma ya zaɓeni wlh se dai ya rabu dakai ya zareka daga Al'amuransa tsaf babu mu babu kai. Shikenan kawai saboda kai matarka bata da zuciyar haifar Yaya Maza seka ringa baƙin ciki da ɗaukakar da Allah ya bawa nawa dana haifa? Ai nasan duk ba komai bane baƙin cikinka saboda Audu nada Magada kuma Yayana nane akan Dukiyar Audu yau idan ya faɗi ya mutu ko sillin gashi baka da gado a cikin tarin Arziƙinsa. Takaicinka kuma yanda kullum Yaya nane a gaba sunfi duk sauran yayan da aka haifa a gidan Ƙashin Arziƙi". Alƙali Yakubu yayi wata dariya, da alamu ya mance da inda suke shiyasa yake zaro maganganu duk yanda sukayi masa. Kallonta yayi sama da ƙasa yace mata "Ina Alfahari da Yayan da ubangiji ya bani Mata, Namiji gudan daya bani ya fiye mini taron Yuyuyu irin wanda ke kike iƙirarin kin haifa. Ke har kinyi haihuwar da zaki bigi ƙirji kiyi Alfahari da ita Binta? Arziƙin yayan da yake cuɗanye da na sata da na ƙazantacciyar harƙallah? Bari kiji, wlh idan naso jirkita rayuwarki a cikin taƙaitattun sa'oi se kin bazama neman inda zaki boye a cikin ƙasar nan, kije ki fara gyara tarbiyyar Yayan da kike tinƙaho dasu kafin su zama abin Alfaharin, ina mai tabbatar miki Binta da raina ko na mutu akwai ranar da baƙin cikin waɗannan yayan da kika cuta kika gurbata musu rayuwa kika koya musu zalama da rashin wadatar zuci irin naki se sun saukar miki da Ciwon da in bakiyi wasa ba shi zeyi Ajalinki" "Dan girman Allah Baba kayi haƙuri, ba anan ya kamata ayi maganar nan ba, Ahalinmu sanannu ne yanzu se kaji zanje yana tashi a Kafafen sada zumunta daga nan Allura seta tono garma" Dr Hassan daya matsa kusada Baba Alƙali ya faɗa yana kama hannunsa, shiyasan me Alƙalin yake magana akai. PAGE 18 "Gara Allurar ta tono garmar ai ko wannan Mahaukaciyar da ubanku yake zaune da ita shekara da shekaru zata nutsu tasan Annabi ya faku" Alƙali Yakubu ya sake faɗa, Ahnad da Dr Hassan suka rufu suna bashi baki yayinda Binta take kuka tana kiran ita yake cewa mahaukaciya yau tilas Audu ya zaɓa ko ita ko shi. "Hajiya Dan Allah kije waje kina damun marasa lafiya da suke kwance" Wata Nurse ta faɗawa Binta, a maimakon ta fita kamar yanda aka bata umarni seta doshi Amenity ward inda Alhaji Audu yake tana kururuwa da hayagagar zata taso shi ya zaɓa ko ita ko Yakubu securities suka mata burki, Alƙali yace "Ku barta ta shiga, kai Hassan kira ɗan uwanka kace ya maza yazo Asibitin nan ga wani Aikin Allah ya samu". Abin dariya abin takaici sega Hajiya ta taka da gudu ta fice daga reception shi kansa Alƙali Yakubun dukda yanda ransa ya ke a ɓace seda ya dara suka wuce office ɗin Dr Hassan suka cigaba da tattaunawa. Hajiya kuwa Adaidaita ta tara ta koma gida, tana sauka Hajiya Rabi suna fita da Direba bayan ta gama haɗa abubuwan da Alhajin ze iya buƙata a Asibiti dan Momy cewa tayi ba zataje ba. Kamar yanda Baba Alƙali ya bada umarni haka zuri'ar Audu Bechi maza suka sake taruwa a gidansa da daddare banda Naziru wanda yake can kwance gadon Asibiti da Zakariyyah shi an sallameshi bayan da aka bashi magunguna seya wuce gida ya kwanta dan ba wai ya gama komawa hayyacinsa bane ga bakinsa daya suntume an tabbatar dai babu komai a sannu kumburin ze saɓe. Kaca kaca Baba Alƙali yayi musu inda ya fi dora laifi akan Alhaji Babangida da yace shine babba. "Yau idan Abdulwahabu ya faɗi ya mutu kaine madadinsa kuma duk lalacewarsa sunansa baze taɓa canzuwa daga ubanku ba kuma har a gaban Allah baku da wata hujja ta saɓa masa ko muzantashi, idan kuna riƙe da abinda yayi muku ko yayiwa iyayenku a baya tambayarku zanyi ta ina abinda ya faru ya rageku koya tauye rayuwarku? Shin luɗufin da ubangiji yayi muku a yanzu ba sakayyar wahalar da kuka sha a baya bace ba? Waye a tagayyare duk a cikin ku? Kafataninku kuna zaune lafiya kuna rayuwa cikin wadata me kuke nema? Ta ina rashin kulawar da ubanku ya nuna muku ta rage ku a yanzu?" Kallonsa sukayi kowanne da magana a bakinsa, shi ɗin ba wani sakakan mutum ne da zasu iya mayarwa da martani shiyasa sukayi shiru. Ya gama musu faɗa kafin ya koma nasiha yana janyo musu Ayoyi da hadisai da suka tilasta musu yin biyayya ga mahaifansu ba wai ganin dama ba, Umarnin Allah da Manzonsa ne kuma kaucewa hakan babban laifine, yace suyi iyakar iyawarsu su rabu da mahaifinsu lafiya, baya musu fatan daga su harshi su tashi gaban Allah rataye da haƙƙoƙin juna da suka kasa saukewa a duniya. Ya roƙe su da suyiwa Mahaifinsu uzuri, ko babu komai albarkacin silar su duniya da yayi har suka taka matsayin da sukejin sun isa ja dashi a yanzu ya isa yasa su Yafe masa kura kuren da yayi musu. "Kayi haƙuri Baba, amma wata shari'ar se a lahira, banajin zan iya manta abinda Alhaji yayiwa mahaifiyarmu, harta koma ga mahaliccinta da ciwonsa a zuciyarta. Duk sanda na ganshi hotunan yarintarku ne suke yawo a idanuna shi yasa na zaɓi dana zauna a Bechi nayo nesa dashi, idan ka tursasamun kace na yafe masa ko na faɗa iyakar fatar baki ne be zama lallai har zuciyata ina nufin abinda na furta ba" Alhaji Babannan ya faɗi kansa a ƙasa yana direwa Hussain ya cafe cikin ƙunar rai yace "Mufa shegantamu yayi, ƙila da bamuyi kama dashi ba da har yanzu muna watangaririya a duniya baze karɓe mu ba". Se Alƙali Yakubu ya rasa abin sake cewa kuma, a sanyaye yace "Kuyi haƙuri, ku yafewa Ɗan uwana. Na sani yana cike da nadama da dana sanin wani bari na daga rayuwarsa ta baya kuma nasan a shirye yake daya gyara kuskurensa ku bashi damar haka muddin ya nema karkuce zakuyi masa bore". Taro ya tashi jikin wasu ya sanyaya yayin da na wasu ya zama kamar Baba Alƙalin ya tado musu da tsohon tsumi ne. Hussain sarkin ɓarota cewa yayi "Dama duk kaika haife mu bashi ba" "Dani dashi duk abu guda ne, jarabawa ya gamu da ita wadda ba kowanne mutum yake iya tsallaketa ba itace ta rashin dace da Macen ƙwarai, shi yasa a koda yau nake muku nuni da ku ajiye komai idan aka zo gaɓar neman abokiyar zama ku dubi tarbiyya, Addini da nagarta tareda Asali ku bar duk wani ƙyale ƙyale da kwaɗayi domin gujewa maimaita irin kuskuren da mahaifinku ya tafka" Baba Alƙali ya sake tunasar dasu nan ne Faisal yaso ya gwada halin daya tsotso a Nono ya karkace zeyi fitsara yana cewa "Auran mahaifiyarmu ne kuskuren da yayi kenan Baba ko wa?" Kafin ma Baban yace wani abu Yakubu ya bige masa baki har seda leɓensa ya fashe. Haka dai aka tashi taro kowa ya kama gabansa. Kwanan Alhaji Audu uku a gadon Asibiti, jininsa ne ya hau ƙololuwa, yanda bincike ya tabbatar da ace faɗuwar da yayi a ƙasa ne tabbas babu abinda ze hanashi gamuwa da cutar shanyewar rabin jiki. A kwanaki ukun nan da yayi a gadon Asibiti idan kaji sautin muryarsa toh da Alƙali Yakubu yake magana se ko Dr da Hajiya Rabi dake jinyarsa wadda itama jefi jefi yake mata maganar. A ɗan taƙin yayi rama, tsufansa da jindaɗi yayiwa kwaskwarima jinyar kwana uku ta fito masa da ita. Kana kallonsa zaka fahimci cewar yana cikin wani yanayi mara daɗi, yawan shirunsa ya tabbatar sa tunani yakeyi wand kuma hakan yasa jikinsa yaƙiyin yanda ake so. Tun daren da aka kwantar dashi Likitansa me kula da lafiyarsa yaje akan ze maidashi can Asibitinsa kafin ya shirya masa su fita can UK inda ya saba zuwa a duba lafiyar tasa amma yace Aa ze zauna a Asibitin Ɗansa, Asibitin da tun da aka assashi sau ɗaya ya taɓa taka ƙafarsa ranar da aka buɗe se wannan karon da jinyar bagatatan ta kawoshi ya kuma ga gata, shi da kansa ya yarda da Ƙwarewar Dr Hassan tareda ingancin Ma'aikata da kayan aikinsa. Idan Dr Hassan ɗin na Assessing ɗinsa ya ringa binsa da kallo kenan duk inda yayi, a zuciyarsa yanajin wani irin nauyi tareda kunyarsa, wai fa Ɗan Zubaida ne, Ɗan daya kusa shegantawa wanda a silar samuwarsu ya rabu da mahaifiyarsu yau gashi shine yake tsaye akan ganin lafiyarsa ta daidaita. Har wayau shida Ahmad ne tare dashi, su suke kula dashi da jikinsu da dukiyarsu domin dai sile biyar ba'ace ya kawo ba, bayaga Yayansa mata Mazan babu ƙeyar wanda ya gani a Asibitin har ya kwana huɗu aka sallameshi ya koma gida. Tunda Hajiya ta bar Asibitin dama bata koma ba, tana gida tana saƙa da warwarar yanda zatayi, ta dai turawa Turai kuɗaɗe masu nauyi wanda tace zataje mata gurin Malamin da ze mata maganin Yakubu take yanke, baze wulaƙan tata a bainar nasi yaci banza ba, dole su tashi tsaye akansa domin akwai gagaruwar matsala idan akace Alhaji Audu ya riga Yakubu mutuwa, tabbas yanda baya ƙaunarta se yayi duk yanda ya iya ya cuceta ita kuma ba zata lamunchi wannan abu ba. Ta manta ma da wani Alhaji na Asibiti seda taji ance ya dawo. Ta zurma Hijabi a baibai ta fita tana casgaɗa ƙafa yanda kasan wata sabuwar cogal a haka ta isa Falon Alhaji na ƙasa. Yana zaune tareda baƙi, gama sallamar ma'aikatan gidan kenan da suka bishi suna sake masa sannu da zuwa dan duk sunje Asibiti sun dubashi suna fita wasu mutanensa suka zo dubashi sunje can Asibiti aka ce an sallameshi shine suka bishi gida. Manyan mutane ne sosai, suna tsaka da tattaunawa se ganin Hajiya sukayi kamar an jehota tana cangala ƙafa tareda numfarfashi yanda kasan wadda ta tashi daga wani ciwo. "Alhaji ashe ka dawo? Da rabon fuskokinmu zasu gamu ka ganni nima tun ranar nake a kwance, sabili kawai da nace zan shiga na dubaka a Asibiti Alƙali ya koreni na dawo gida duk ba'a hayyacina ba na zame na faɗi a bakin ƙofa tun ranar se yanzu na iya yunƙurawa na fito da naji ance kun dawo nace gara na zo mu haɗu karna mutu a ɗaki har se nayi wari sannan aji a dubani tunda kowa ya tsaneni Matanka babu wadda tako leƙa taga ya nake ace dai kwanaki huɗu ba'a ga giftawata ba ai yaci a tuhumi lafiya dai amma babu wadda tayi" Hajiya Binta ta ringa rattaba zancen da seda ta kai ayarsa kafin ta lura da cewa ba Alhajin ne kaɗai a gurin ba, tayi sak kafin ta shiga rirriƙe hijabi duk ta diririce da gani base an faɗa ba kunya ce tayi mata rubdugu. Alhaji ya nunata da hannu yana kallon wanda yafi sauran kalar jiƙuwa da kuɗi yace "Gata nan, ita ce Surukar Ɗan naka". Wanda aka nunawa Hajita ya kalleta babu yabo babu fallasa kakar yanda sauran baƙin suke kallonta kowanne da yanayin da yake kan fuskarta yace "Sannu Hajiya, ya me jiki? Ya kuma naki jikin?" Babban abun ma shine bata san uban waye cikin surukan nata ba amma dai iyakar zubar da kai yau tayi ta tafka abin kunyar da ita da kanta yau ta gagara naɗe tabarmar kunya da haukan data saba ae jan Hijabi takeyi ita ba abin ta cire ta maidashi daidai ba duk ta rasa abinda zatayi. Momy tayi sallama cikin kyakykyawar shiga ta Abaya ta yafa yalwataccen Mayafi akai bayanta Maimuna ce da me aikinta Amirah kowacce da dogon Hijabi sun ɗauko manyan Trays. Har ta kalli Binta ta wuce ta samu gurin zama kan kujerun da suke daga gefe kaɗan, su Maimuna suka ajiue kayan hannunsu suka gaida baƙin kafin suka fita sa'annan suka shiga gaisawa da Momy cikin dattako da mutuntaka. "Itace Matata ta biyu Mahaifiyar Ahmad" Alhaji ya gabatar da ita. Baban Sirikin Binta yayi murmushi yace "Ga kama nan kuwa har jikin ma irin nata yayi baza'ace ita ta haifesu ba" Alhaji Audu ya ɗanyi murmushi sega Hajiya Rabi nan itama ta shigo a kamalance da sallamarta ta zauna suka gaisa. "Ga kuma Amaryata" Alhaji ya gabatar da ita". Hajiya Binta ta muzanta iya muzanta, wannan abu da Audu ya mata ya kaita wuya amma kamar wadda aka zubawa glue aka liƙe a gurin da take ta kasa gaba ta kasa baya haka ta gagara magana. Momy da Hajiya Rabi suka miƙe a tare suka musu sallama suka fice, tun a hanya da suna dawowa daga Asibiti ya sanar da Hajiya Rabi, Alhaji Tamim Uban Mijin Hajiya Ƙarama yace yana tafe ze shigo dubashi dan yana Kano, ya sanar masa sun wuce gida basa Asibiti ya sameshi a can, shi yace ta gayawa Momy wadda take fushi dashi kan abinda ya faru. Sau ɗaya taje dubashi Asibiti amma kullum zatayi girki safe rana dare akai masa ita kuma Hajiya Rabi can zata wuni da dare ta dawo Ahmad ya Kwana dashi. Abinda yasa yace a gaya mata zuwan baƙin yasab ba zata rasa abinda zata fitar dashi kunyarsu ba dan bata rabo da abubuwan motsa baki tunda yamma ce ba lokacin cin abinci bane ba gashi kuwa data tashi zuwa tazo musu da abubuwan taɓawar da ruwa da Lemo. Shi ya manta ma da Hajjajun seda ta shigo, yanda yaji kunya kuwa dai ba'a cewa komai amma ya godewa Allah da ba ita kaɗai yake aure ba, sedai a tafi da ita kaɗai a baki domin sauran matansa sun fitar dashi kunya. Kamar sun manta da tsayuwar Hajiyar a gurin Alhajin ya musu Bismillah suka ɗan taɓa abinda aka kawo musu. Alhaji Tamim da Abokanan tafiyar tasa wayayyun mutanene suka shiga hirar kasuwanci inda ko wannensu yafi kauri. Hajiya ta gama tsayuwarta kafin ta miƙe ƙafafun da da yake cangalawa ta fice kamar kazar da Ƙwai ua fashewa a ciki. Tana fita ta haɗu da Faisal ta tsareshi da tambayar suwaye a Falon Alhaji. "Baban Abba T ne" ya bata amsa, seta ɗora hannu biyu aka kafin kuma ta sauke da sauri har tana neman harɗewa ta wuce cikin gidan da saurin bala'i. Jikinta har rawa yake ta kira Hajiya Ƙarama, bata bari sun gaisa ba ta shiga surfa mata bala'i harda Allah ya isa akan. "Kin huta yanzu ai se su dawo suyita bada labarin sunzo sun tarar da uwarki kamar mahaukaciya" ta faɗa tana rushewa da kuka kafin tayi cilli da wayar. Audu ya cuceta da be gaya mata su waye zasu zo ba yanzu yaja taje ta zubarda mutunchinta, surukin Hajiya ƙaramar ne kawai ya gaisheta amma tana gani da Aisha da Rabi suka ahiga duka harda sauran Abokanansa suka gaisa a mutunce ba irin tata gaisuqar daya mata ta jeka nayi ka ba. Ta sake zuge tazugen rashin mutunchi ta ayyana yanda zataci kan uban kowa a gidan tunda taga alamar raini ya fara shiga tsakaninta dasu kuma ba zata lamunta ba amma yanzu bari ta fara gamawa da zancen Yakubu tukunna shine Ƙayar da ya tsaya mata a wuya. Ta Alhaji Audu me sauƙi ce saboda tana da maganinsa a hannu, wurudin da Turai ta bata zata cigaba dayi tana banka masa yana sha ya dawo hayyacinsa dan taga alamar yana neman yafi ƙarfinta. FATIMA Ko a jikinta lissafin kwanakin zuwan Jay kawai takeyi wanda ita dashi sukeji kamar su janyo kwanakin su rage musu tsaho. Wani irin so da shaƙuwane a tsakaninsu, yanda suka damu da junansu suke tarairayar juna seya baka mamaki ba zaka ce soyayyar gani ɗaya bace kuma a waya akeyinta. Hatsaniyar da kayi a gidansu Jafar ɗin ce ta kawo tsaiko a zuwan nasa ya ƙara kwanakin zuwansa Nigeria da sati ɗaya akan yanda ya tsara dan abin ya faru yaɓa shi ya kuma ɓata masa rai matuƙa, idan yace zezo a lokacin da abun be idasa lafawa ba rigima zata dawo sabuwa ne domin dukda cewar baya son Fatima baya son auranta da Ahmad amma hakan bashi yake nufin ze zuba ido a Tozarta Ahmad ba, shi laifin Fatiman nema ya sake ninkuwa a zuciyarsa domin ta dalilinta ne aka yiwa Ahmad ɗin haka kuma ta zama silar da take neman sake janyo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu saboda abinda ya faru dole ze sake tsanata gaba tsakanin Yayan Hajiyarsu da Su Hassan sannan a silar auranta Alhajinsu ya kwanta a Asibiti. A ƙa'ida saura kwana uku yazo ranar yace mata an samu matsala se wani satin ze zo. Be gaya mata dalili ba, yanayin muryarsa da taji ta sakata tsurewa kodai wani abu tayi masa saya saka ya ɗaga zuwan? Cikin rawar murya kamar me son fashe masa da kuka ta tambayeshi dalili. Ya sassauto daga tunzurin da zuciyarsa take kai yace mata "Babu komai, gidanmu ne babu lafiya an samu yar hatsaniya shiyasa kawai na ɗaga zuwan nawa saboda ze iya maido da ƙurar data lafa". Bata fahimce shi ba amma tunda dai ba ita ta masa laifi ba ai da sauƙi. Ta ringa masa shagwaɓa da sangarta harda kukanta akan ya fasa zuwa jibi bayan ta fara shirin tarbarsa, wannan ya sanyaya masa zuciya ya shiga rarrashinta da mata Alƙawarurruka idan yazo kafin sukayi sallama ya ajiye waya. 'Ga mata nan irin su Afeeyah birjik a duniya akan Me Yah Ahmad ze nacewa waccen yari yar da babu komai tattare da ita se baƙin talauchi da sharri, daga maganar auranta ji abinda ya faru to inaga kuma ya aurota ya ajiyeta a gidansa ai se abinda Allah yayi kawai. Abin haushi da takaici kuma wai duk badaƙalar nan da akayi yanda Ahmad yace ko gezau beji soyayyarta tayi rawa a zuciyarsa ba tana nan daram dam shi dai yayi Allah wadai da So Ɗaya tak irin na Yah Ahmad' Tunanin Jay. AHMAD Yana tsugunne gaban Alhaji bayan daya gama ɓalla masa magungunansa yasha ya kuma gwada masa Bp da abinda Dr Hassan ya kawo ya kuma koya masa yanda ze ringa masa kullum da safe shi kuma da yamma yake zuwa ya sake dubashi, Sati guda kenan da dawowar Alhajin babu inda yake fita saboda jikin yaƙiyi masa yanda yake so, zuciyarsa a ƙuntace take, duk sanda yayi shiru abinda ya faru waccen ranar ne yake dawo masa dallah dallah. Wani irin abu yakeji a zuciyarsa da baze iya fasaltawa ba, Ɗansa na cikinsa a gabansa ya faɗi cewa mutuwarsa da rayuwarsa bata da banbanci a gurinsa shi kuwa wane irin bigire ya ɗora rayuwarsa akai? Anya idan ya mutu ze ringa samun kyawawan Addu'oi daga zuri'ar daya tara kuwa? "Alhaji da akwai wani abun ne?" Ahmad ya sake tambayarsa karo na uku, yana ta masa magana amma ya zubawa guri guda ido yayi shiru. Yayi firgigit irin na wanda ya farga daga wani tunani kafin ya gyara zama yace "Babu komai, fita zakayi ne?" "Eh Alhaji, yau Jafar ze taso da daddare zasu sauka Abuja, ina tunanin na tafi can na jirashi da safe se mu juyo tare" "Toh Madallah hakan yayi Allah ya kawo shi lafiya, nima dai inaga Abujar zan bika muje can na zauna na lokaci ko na samu jikina ya daidaita dan a nan mutane ba zasu barni da hayaniya na warke yanda ya kamata ba" Alhaji ya faɗa, Ahmad yayi murmushi, yasan da Hajjaju yake dan itace kamfanin hayaniya a gidan. Ba Alhaji ba hatta shi da yake yawan zama tare dashi idan tazo gajiya yake da sauraron maganarta kansa har ciwo yake ɗauka inaga Alhajin da ba lafiya ce ta ishe shi ba? "Ƙarfe nawa zaka tafi?" Ya sake tambayarsa. Ahmad ya duba Agogo yace "Da jirgin shida kona tara nake tunani dan yanzu zanje gidan Baba Alƙali yace yana son ganina". "Akan maganar neman auranka ne, kayi haƙuri da abinda ya faru ban shawarce ka tarko aka kafamun na shiga da kyakykyawar niyya bansan cewar wanda yayi shi da wata manufarsa ta daban ba. Mun tattauna da shi yace ze kiraka ku sake yin magana daga nan ze yanke rana da lokaci da za'aje masa neman Auran. Dama ina so naji zancen Muhalli ka tanada ne ko kuwa baka fara shirin komai ba game da auran?" Ahmad yayi kasaƙe yana sauraron Alhaji, kalmar haƙuri da Alhaji ya fara da ita ta saka jikinsa sanyi laƙwas. Ya ringa tisa maganar Alhajin harya gama kafin ya fara tattaro amsar da ze bashi a zuciyarsa. Shifa Fatiman nan sun kusa sati biyu rabon da suyi magana da ita tun ranar da Baffanta yace ya turo iyayensa be sake komawa ba haka be kirata ba itama bata neme shi ba ya kwanta jinya daga nan kuma wannan lamarin ya faru ya maida hankali ga jinyar Alhajinsu. Daman shi bashi ya tado da zancen aure yanzu ba Alhaji ne gashi yanzu har magana taja ana batun za'aje tambaya dukda cewar Mahaifinta ya bashi dama amma ai itama yana buƙatar amincewarta tunda dai da ita ze zauna idan bata sonsa baze samu farin cikin da yake fata a zamantakewarsu ba. "Kayi shiru baka ce komai ba" Alhaji ya faɗa yana kallonsa, ya shafa kai yace "Dama Jafar nake jira yazo tunda shima da tasa maganar se mu shawarta inda zamuyi gidan" "Toh yayi, da akwai filaye dana siya nan bayan Sufi Mart, kuje kuga gurin idan yayi muku se ku zaɓi biyu a gina" Alhaji ya sake faɗa. "Mungode, Allah ya ƙara girma" Ahmad yayi godiya kafin ya tashi ya fita. Gidan Baba Alƙali yaje, har number Baffansu Fatima Alƙalin ya karɓa a hannunsa da zummar ze kirashi ya basu lokacin da zasuje haka ya bashi dan bakinsa ya kasa buɗuwa ya fayyace wa kowa halin da suke ciki da Fatima. Idan yana da rabon auranta ya sani ze samu, idan ba rabonsa bace in sunje Mahaifinta ze musu bayanin komai, baya so ya faɗi har yanzu basu samu daidaito da ita ba saboda kar daga baya Allah yayi faruwar auransu ya zama yan uwansa su ƙi karɓarta yanda ya kamata. Ya faɗawa Alƙali Yakubu filayen da Alhaji yace suje su gani in ya musu shida Jafar. "Lallai kun gode, toh amma idan akace gini za'a tado zeja lokaci fa ta yuwu sama da shekara kafin ace anyi Auran nan dan nidai kunsan bana son wannan ginin burbur na zamani da akeyi wata shida ace ko ƙasa da haka kaga anyi gini har an tare ruwa be daki bulo da ciko sun zauna da kyau ba, in dai ba kuna so a saka auran da nisa ba shekara zuwa da rabi ba kamata yayi ace an nemi ginannen gida ko kuma cikin waɗanda aka fara ba'a kammala ba in ma tsarin ginin akwai abinda be muku ba kwaskwarima zatafi sauƙi akan ace a tada sabon gini". Ahmad ya jijjiga kai dan yayi na'am da maganar tasa Alƙali Yakubu ya sake cewa "Zan same shi zamuyi maganar" daga nan suka sake tattaunawa har bayan la'asar sannan ya koma gida. Ya zata da wasa Alhaji yake da yace zashi Abuja seda ya koma ya tarar dashi da Hajiya Rabi a shirye wai tare zasu tafi. Jirgin ƙarfe shida suka bi, A katafaren gidan sa na Abuja sukaji zango, gidane da bayyana tsaruwarsa ma ɓata lokacine. Bayan shi yana da gidaje da bazasu irgu ba a Abuja Manya da ƙanana banda Estate da Plazas da sauran Kadarori da iyalansa ma basu san da wanzuwar wasu daga ciki ba. Manya Manyab Mansions ɗin da barin su da akeyi babu kowa ciki se masu aiki da suke kula da gidajen tasa yayi shawarar bayar dasu haya suka zama Masaukan Manyan baƙi tunda da komai na more rayuwa a ciki mutum sedai ya shiga yayi iyakar zamansa ya fita. Wannan gidan kaɗai ya ajiye yake sauka a jiki idan yaje Abujan, duk zalama da son duniyar Hajiya Binta ya rasa yanda akayi bata taɓa nuna sha'awar tana so ta koma Abujan da zama ba, a Shekarun baya dai Aisha ce ma ta ringa nacin daya raba musu gida, kodai ya maida Hajiyar wani guri daban ko su ya fitar dasu amma daya shawarta da Abokanansa akan hakan suka ce masa Aa, a girmansa da shekarunsa be kamata ace ya rarraba kan iyalansa ba, ai duniya ma se tace be isa da gidansa bane shi yasa ya kasa haɗe su a inuwa guda wannan ne ya daƙile maganar. Ahmad yafi gane sauka a Hotel idan yazo Abuja amma yanzu saboda Alhaji tilas ya shiga ɗaki ya kwanta yanajin duk babu daɗi, Sha biyu da rabi na dare su Jafar zasu sauka amma Alhaji yace yayi kwanciyarsa in ya dawo ya kwana a Aiport da safe ya taho gida babu wanda ze fita ɗauko shi a daren nan baze yi masa musu ba ya kwanta yana ta jiran kiran Jay aikuwa Ɗaya saura se gashi ya kirashi ta WhatsApp wai ya fito yana ina? "Alhaji yace ka kwana a Aiport seda safe ka wuto gida" Ahmad ya bashi amsa yana dariya dan ya san abin seya zafafi Jafar aikuwa ya shaƙa yayi tam yace "Amma fa ce mun kayi zaka zo ka jirani a Abuja yanzu kuma kana cewa Alhaji yace menene Allah Yah Ahmad ko" "Toh ai ina Abujan, tare muka zo da Alhajin shima ze tareka" "Ya samu sauƙi kenan? To nidai gaskiya ka saci hanya ka fito ina jiranka" cewar Jafar, Ahmad ya girgiza kai yace "Kayi haƙuri ka zauna zuwa Asuba zan fito kasan yanayin gari yanzu yan one chance fa sun takura shiyasa naso na zauna nan na kama mana ɗaki amma da muka iso yace dole mu wuto gida tare". Saboda Haushi Jafar kashe waya yayi be cewa Ahmad komai ba ya ringa kiransa kuma yaƙi ya ɗauka duk ya damu ya kasa bacci. Can jimawa seji yayi ana buɗe Get, ta window ya leƙa yaga Jafar na fitowa daga mota filin gidan tarwai yake da haske dan haka yana iya hango yanda ya cukule fuska. Masu gadi ne suka biyoshi da Back pack ɗinsa wadda daman ita kaɗai yake ruƙowa idan ze yau kuma ya ganshi da saitin Akwati me biyu da Kit, daga sama yake hangosu kuma dare ne amma a hakan yaga kyansu, bakinsa har kunne dan ya san wannan tsabar Masoyiyar da ake wa kowa rowarta ce, lallai Jafar da gaske yakeyi, a saninsa be taɓa ruƙowa wata Mace tsaraba. Falon ƙasa ya sakko tarbar sa nan ya tarar da Alhaji da alama motsin buɗe ƙofa ne ya fito dashi shima. Jafar ya gaida Alhaji yana hararar Ahmad wanda ya gumtse dariyarsa jin Alhaji na cewa "Ka karya mun dokar gida kana sane ko?" Shiru yayi Alhaji ya juya ya koma ciki se sannan Jafar ya farawa Ahmad mita suka wuce sama tare. "Kai baka san dare bane wai ka bari da safe se kayi surutun naka mana" Ahmad ya faɗa yana zama a gefen gado. Jafar ya shiga cire kayan jikinsa wayarsa daya ajiye kusada Ahmad ya shiga ringing. "Toh fa, ruhi na kira" Ahmad ya faɗa cikin sigar tsokana yana miƙa masa wayar ya karɓa yana wani tura masa baki kamar yaro. A speaker ya saka wayar, muryar Afeeyah dake cakuɗe da bacci ya ziyarci kunnuwansu a lokaci guda. "Love, ka isa gida?" Ta faɗa, Jay ya wani langwaɓe kafin yace mata "Yes Bae na iso gida, waifa Alhaji cewa yayi na kwana a Aiport ba za'azo a ɗauke ba" "Kai! haba dai" ta faɗa" tana ware ido, yace "Wlh fa, but na dawo, na gaji da yawa wanka nake so nayi yanzu, I'm sorry for keeping you late na hana kiyi bacci" "Haba mana, kana zaton zan iya bacci Alhalin kana hanya ban san ka isa gida ko Aa ba?" "Awwwnn I'm blushing" ya faɗa yana shafa kai tareda satar kallon Ahmad dake kallon wayar babu kyaftawa yana auna kalaman me magana a cikin wayar ɗaya da ɗaya. Be sani ba ko kewar Fatima ce tasa yakejin muryar Budurwar Jafar tamkar tata ko kuma irin shauƙi me nuna tsantsar soyayyar da take yiwa wanda take magana dashi wanda ya daɗe yana fatan yaji daga Fatima ne yasa har yake hakaito ita take maganar ko yaya? Besan Jafar ya kashe wayar ba seda ya taɓa shi yana cewa "Da akwai abinci a gidan nan kuma? Yunwa nakeji wlh" "This is past 1 fa Jafar kai kake neman abinci irin wannan lokacin?" "Bazaka gane ba, zumuɗin ganin Afeeyah yasa na kasacin komai, naji haushi sosai da ba zan ganta yau ba, Allah badan Alhaji ze hana ba yanzu zan tafi Kano irin 6 na isa na wuce gidansu kawai" "Ka ɗauka a Turai kake kenan ko Yaya? To a Naija Ƙwamushe mutane akeyi a Abuja-Kaduna Road yanzun da tsakiyan rana ma balle ka kai musu kanka da daren nan, Allah ya tsare hanya kaga Ransom ɗin da zasu saka akanka nasan sedai FIFA ta biya badai Alhaji ba". Da Jafar yayi wanka ya haɗo Tea nan ya hana Ahmad sakat da zancen Afeeyah, idan ya buɗe wayarsa ze nuna masa hotonta se kuma yace "Aa ma, gobe zamuje kawai ka ganta face to face kaga Mace ba muna mata ba irin wadda kake wahalar da kanka akanta bata san kanayi ba" "Uhm, Allah ya nuna mana" Ahmad ya faɗa yana kwanciya, gaskiya Jafar ya faɗa Son maso wani yakeyi da hausawa sukace ƙoshin wahala to amma yaya zeyi? So halittace ce wadda baka iya sanin sanda zata shigeka sannan baka da zaɓin kan wa zata faɗa, masu ganin laifinsa akan yaso Fatima suna bashi mamaki domin jarabtar data same shi tana iya faɗawa akansu suma. Tsananta soyayya tamkar gado ne a gurinsu, abin a jininsu yake, suna da matuƙar zafafawa akan abinda suke so hakan nan in suka ƙi abu toh fa ya shiga uku. Yanzu irin yanda yaga son Afeeyah a idanun Jafar ya tabbatar da ace shima tasa jarabawar ta zamto irin tasa ma'ana yana sonta ita kuma wani daban take so ta yuwu wawancin da zeyi a soyayya se yafi wanda shi Ahmad yakeyi. Bacci be ishe su ba amma saboda yanda Jafar ya azazzaleshi tilas suka tafi Kano a Mota dan sunyi missing Jirgin Safe da already sukayi booking, na rana da probabilityn ayi postponing ɗinsa ya haɗe da na dare kamar yanda wanda ya kira ya sake musu booking ya sanar masa shi kuwa Jafar baya iya jiran har Bayan Magrib kafin ya isa Kano shiyasa yace su tafi a Mota. Sun shiga Kaduna ya kunna layinsa na Nigeria dan ta WhatsApp yake waya da Afeeyah tun jiyan saboda Hajiya kuma yaƙi kunna wayar ilahi kuwa yana kunnata sega kiranta kamar tana jira ta fara masa masifa da bala'in da suka zame mata kalaman barka da zuwa ya ringa bata haƙuri dan faɗan akan meye ze kira Ahmad ya ɗakko shi bayan ta hana? Ita bata ce zata sake haɗa masa taro ba amma ai ta gaya masa muddin ze zo ya sanar da Faisal ko Lawan suje su taro shi daga koma ina ne ba Ahmad ba amma seji tayi ance ya tafi Abujar ƙarin baƙin cikinra tafiyarsu tareda Alhaji harda Hajiya Rabi, ko sallama be mata ba Yakubu daya kawo masa takaddu ya saka hannu kafin suka tafi ne ya gaya mata, kwana tayi tana tijara, ita da taso abinda ya faru ya haifar da Ƙiyayya mai tsanani tsakanin Ahmad da Alhajin amma tun daga Jinyar sa da yakeyi taga alamun shaƙuwa ce take sake shiga tsakaninsu ba wai barakar da tayi fatan a samu ba. Ta ringa kiran layin Jafar kuma a kashe alamar be kunna ba bayan an tabbatar mata daya sauka shine tun farar Asuba take sake gwadawa har Allah yasa yanzu ta shiga ta rusa masa budget ɗinsa na biyawa gidansu Afeeyah tilas suka wuce gida Ahmad na masa dariya domin yasan dama za'a runa ya tabbatar kuma nasa kason yana nan yana jiransa abu guda dai shidai baze bari wani hargagi ko cin mutunchin Hajiya ya shiga tsakanin zumunchinsa da ɗan uwansa ba. Aiko yasa zagi da tijara kamar ko yaushe yayi murmushi ya fice daga gidan, ya rasa me yasa wayar da Jafar yayi da Afeeyah jiya ta tsaya masa a rai ta kuma tado masa da kewar Fatima dan muryarta keyi masa gewaye a ƙwaƙwalwa, da daddare Baba Alƙali ya kirashi yake shaida masa ya kira mahaifin Fatima sunyi magana a waya ya sanar masa da zasuje nema masa auranta yayi murna sedai yace yana neman Alfarma da su bashi lokaci domin akwai shirye shiryen da yake so ya kammala kafin tasowar maganar auran. "Yace daga nan zuwa sati huɗu zamu ji shi duk yanda ake ciki, amma Ahmad anya kuwa iyayen yarinyar nan da kansu suka ce ka turo maganar aure?" Baba Alƙalin ya tambayeshi. Ya sosa kai kamar yana gabansa zuciyarsa na dukan uku uku, Baffa yace a dakata da zuwa nema masa aure bayan shi da kansa yace ya bashi dama daya turo to me hakan yake nufi?? A sanyaye yace masa "Wlh shi da kansa yace mun na turo" "Toh inaga ko wani abun ne ya taso da yake buƙatar ƙarin lokaci, to babu laifi ai sati huɗun daya ambata kamar yauce. Kafin nan shima Jafaru idan inda yake neman sun shirya se aje muku gaba ɗaya a huta" da haka sukayi sallama jikin Ahmad yayi wani laƙwas kamar an zubawa Salak gishiri, ta tabbata dai ya rasa Fatima tunda har Baffa da kansa yace su dakata to tabbas nauyin Baba Alƙali yaji kai tsaye ba ze iya ce musu baze bashi yarsa ba. Amma me yasa Baffa zeyi masa haka? Koda yake ba laufin Baffa bane tunda dai bashi ze aura ba ita kuma Fatiman tace bata ra'ayinsa ai ba za'ayi mata dole ba. Zazzaɓi ne ya dawo masa haɗe da ciwon kai me zafi dan kasa maida kansa gida yayi se Salim ya kira dan Hajiya ta saka Jafar a Ɗaki kamar sabuwar Amarya tunda suka dawo ta hanashi motsawa ko nan da can. PAGE 19 FATIMA Duk irin ɗaure fuskar da Umma take mata tareda maganganu be saka taji ko ɗar a zuciyarta dangane da zaɓinta ba musamman da ta samu lako lako a gurin Baffa, shine me bayar da auranta tasan kuma bazeyi mata dole ba. Idan gidan ya isheta ta gaji da faɗan Umma sta tattara ta tafi gidan Anty Sauda can idan ta nemi ta takura mata da zancen Ahmad buɗe baki take ta mayar mata da martani saɓanin Umma da sedai ta sunkuyar da kai tayi hawaye. "Dan Allah ku barni na auri abinda nake so, yanzu da dole aka miki zaki samu wannan walwakar da kik ciki harki ringa ƙiba kina walwali? Ni ban taɓa cewa ina son Ahmad da aure ba ko shima yasanda haka, to akan me kuma za'a kafa mun ƙahon zuƙa dan nace ga wanda nake so yanzu?" Ta faɗa tana turawa Anty Sauda dake mata mitar zancen Ahmad ƙeya. "Ai shikenan daman mu yan mu baki shawara ne kamar yanda kika ce kece me zaman auren ba wani ba, amma ki sani hausawa sukace Alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, ko Ahmad kika aura na tabbatar se kin haɗa da haƙuri da ɗauke kai saboda matashine da uwar kuɗinsa a hannunsa abinda kika raina ɗin wasu na can suna haƙilon yanda zasuyi su same shi balle kuma kuma wannan da kike So ai wlh faɗuwar gaba da tunanin ina yake su waye tare dashi kaɗai ya isheki, baki kuma isa kice zaki raba shi da mata ba dan dasu kika ganshi. Mutumin dake karakaina cikin masu jajayen kunnuwa Mata masu kyau ba irin wacce be gani ba, Allah kaɗai yasan nawa yake tare dasu a yanzu dan ko be nemi Mace ba su zasu kai masa kansu, to dan Allah meye ribar auran soyayyar da zuciyarka kullum zata zama a tsaye? Ai wlh ka auri Mijin da son sa yafi naka shine ka morewa aure, koda kika ce ina ƙiba saboda Mijina na so na ne, ina juyashi son raina idan nace ina son abu jiki na rawa zeyi mun in ko nace bana so haka ze bari wannan shine burin kowacce me hankali data san me takeyi ba irinki ba da kike nemarwa kanki Jafa'i Mijin da ze ringa ɗaure miki fuska yana fafara miki tsawa" Anty Sauda take sababi. Afeeyah tace "nawa zaɓin kenan, se a tayani da addu'a yanda akeyiwa kowa". Saboda takaici Anty Sauda bata sake ce mata komai ba, daman wai taje ne ta sanar mata Jay ya ɗaga ranar zuwansa. Ita saboda yanda abin yake ɓata mata rai ko Mijinta bata gayawa shegantakar da Afeeyar tazo da ita ba, randa ya tsinci tana mata faɗa ne tayi briefing nasa akan wani ta samo kuma wai yanzu ba Ahmad ba, dake ya iya ɗaurewa ƙarya ƙugu shima yace wai a bita a hankali, Aure da mutuwa babu me tsara su tafe suke da lokacinsu da kuma wanda zasu riska babu kuma wansa ya isa ya canza haka. A ranar bayan Afeeyah ta koma gida da daddare Baffah ya kirata, suna zaune a Baranda saboda garin akwai zafi kuma babu wutar Nepa har Umma tayi masa shimfiɗa a gurin da yace indai ba an maido wuta ba ko kuma ruwan sama ya sauka a nan ze kwana. Ita kanta zafin ya addabeta amma dole ta zauna a ɗaki saboda gujewa maganganun Umma ga Yah Malam ya koma makaranta sun fara Final Exam daman dayana nan ne take samun yancin zaman tsakar gida ko Baffah baya nan tunda yana tare mata faɗan da Umma ta ara ta yafa ya zama halinta yanzu dukda dai shima bawai ya goyi bayan abinda take so tayi bane dan abinda ya gaya mata shima ɗin dai kamar sauran ne "Indai nagarta kike nema a aure to tana gurin Ahmad, idan kuma soyayya da ƙyaleƙyalen rayuwa ce ki auri Jay kuma na tabbatar duk abinda kike hasashen samunsa a gurinsa idan kin bawa Ahmad dama se yayi miki fiye da haka". Ta isa gaban Baffa tana sunkuyar da kai daga gefe ta tsugunna dan tana hangen hararar da Umma ke aika mata ta hasken farin wata da fitilar data kunna musu a tsakar gidan. "Mamana na kiraki ne saboda ina so na ji abinda yake a ranki, dukda kwanaki munyi magana amma yanzu ina so ki sake faɗamun gaskiyar abinda kikeji game da Ahmad" Baffa ya faɗa yana gyara zama. Ta kalli Umma ta sunkuyar da kai, Baffah yace "Ruƙayya ɗan bamu guri mana" "Aiko ina nan Malam bazan shiga cikin zafi saboda maganarku ba" Umma ta bashi amsa, yayi murmushi yace "To ki dena kallonta kar shakkarki tasa ta faɗi ba abinda yake cikin zuciyarta ba" "Uhm" kawai Umma tace ta juya kai. Seda ya sake maimaitawa Fatima tambayar kafin cikin rawar murya tace "Tsakani da Allah ni Baffah ina kallon Ahmad ne kawai a matsayin Yaya, tsayin lokacin nan nayi masa hannunka me sanda saboda kirkinsa ya wuce na buɗe baki nace masa bana sonsa, shi da kansa ya sani tunda yana faɗar haka..." "Tambayarki kawai nayi me kikeji game dashi a zuciyarki ba wai dogon bayani ba" Baffah ya katseta. Ta duƙar da kai cikin ƙaramin sauti tace "Banajin komai game dashi Baffah" "Bakya sonsa so irin na aure kenan?" Baffah ya tambayeta yana tsareta da ido kanta na ƙasa amma taji tasirunsu a jikinta, zuciyarta taki ta tsinke hawaye ya taho mata, daga can ƙasan ranta tana jin tamkar tamkar bata kyauta ba, to amma ya zatayi da muradin tata zuciyar? Idan ta haƙura ta karɓi Ahmad tasan dashi da ita zasu ƙare rayuwarsu ne cikin ƙunci saɓanin haka gara tayi musu gata kowa ya nemi rayuwar da zata dace da muradinsa. "Banajin sonsa a zuciyata Baffah" ta faɗa cikin rawar murya kafin kuka ya ƙwace mata. Umma ta saki ƙwafa tace "Munafuka, ai bakiyi kuka ba tukunna, ranar kuka tana tafe" "Haba Ruƙayya, wannan wace irin magana ce haka? Ya zaki ce mata ranar kuka tana tafe baki fa kikeyi mata?" "To Malam ina kukan daɗi takeyi yanzu ta yaudari bawan Allah ta ɓata masa lokaci shekara uku yana hidima damu da ita sannan rana tsaka tazo tace bata sonsa wani can daban take so? Ai wlh ko ban faɗa ba haƙƙin Ahmad seya bibiyeta, akan me bata sonsa tsayin lokacin nan bata fito ta faɗa ba? Idan da shegiyar ƙaryarta tace nauyinsa takeji mu ta faɗa mana kota faɗawa yan uwanta ko ƙawayenta mana? Ba zata aureshi ba shekara uku ta barshi yana mana bauta har idan ka hana ya zagaye yaje ya kai mata makaranta ta karɓe suturu da manyan wayar da take riƙewa da ya ruɗo mata wanda take Ƙulafucin Son duk waya ke yi mata su ba Ahmad ɗin bane? Sannan yanzu tazo tace bata sonsa to nidai babu hannuna a ciki ba za'ayi wannan abin kunyar dani ba wlh kuma tunda biye mata zakayi kuje can ku ƙarata Allah ya taimaka" Umma ta tattari kayanta ta shige ɗakin da tace da bazata shiga ba saboda zafi. Afeeyah na durƙushe gaban Baffah tana kuka kamar ranta ze fita, yayi shiru ya rasa abin faɗi. A sanyaye yace mata "Kiyi shiru ki saurareni". Ta tsagaita da kukan amma ba gaba ɗaya ba. Baffa yace "A matsayina na Mahaifinki ina da ikon da zanyi miki zaɓin Mijin aure na kuma tursasaki koda bakya so domin Addini ne ya bani damar hakan se dai kuma kema a matsayinki na Ya ba baiwa ba kina da damar da ki kawo naki zaɓin idan har beci karo da Addini ko shari'a ba za'a barki dashi. Auren dole bashi da fa'ida Fatima, yanda na baiwa yar uwarki dama ta kawo zaɓin aurenta kema na baki. Nayi tsammanin lokacin da kika ɗauka tareda Ahmad alamune na cewar kun Aminta da juna, Karatunki da kike da ƙulafuci a tsammatata shine abinda yasa kuka tsahirta tado da zancen aure har se zuwa kin gama. Baki taɓa nuna wata alama ko faɗi da baki cewar bakya sonsa ba dukda Mahaifiyarku da Yayarki suna yawan kawo mun ƙorafin yanda kike mu'amalantarsa basa jin daɗin hakan, nakanyi miki uzurin yanayin halayyarki ta kasancewarki mutum mara sakewa da mutane sosai ban taɓa tsammatar rashin So ko gamsuwa dashi ne yasa kikeyin hakan ba me yasa kikayi ƙwaron baki ki barshi tsayin wannan lokacin se yanzu da Aski yazo gaban goshi zakice kin fasa baki ganin hakana matsayin cutarwa?" Baffah ya ƙarasa yana tsareta da ido. Taja hanci, fuskar nan har tayi Jaa kafin tace "Wlh Baffah nauyi da kunyarsa nakeji shi yasa na kasa faɗa masa da baki amma na nuna masa duk wata alama data kamata ace ya gane" "Da kika ga alamar be gane ba, ko kuma ya gane amma ya cigaba da dagewa domin ya gwada sa'arsa tunda har kika tabbatar bakya ra'ayinsa seki cire wani nauyi ko kunya a gefe ki sanar masa ko ki sanarwa wani ya gaya masa" Baffah ya faɗa a ɗan fusace. Ta sake rushewa da kuka yayi tsaki yace "Yanzu da wace fuska kike so na kalli yaron nan? Ni kike so na gaya masa bakyason sa kenan ko wa?" "Ni Baffah.. Ni wlh ban..." Ta shiga in ina tana kuka ta kasa haɗa maganar. Baffah ya ajiye numfashi, gaba ɗaya ta jefashi a tsaka mai wuya ya rasa abinda zeyi seya nisa yace mata "Shi wanda kike so ɗin wanene? Kuma ɗan gidan wanene?" "Sunansa Jafar, Ɗan ƙwallo ne, Mahaifansa duka yan Kano ne amma shi a Turai yake can yake sana'arsa" ta bashi amsa cikin sauri ya kalleta kafin ya sake tambayar s ina suka haɗu nan ma ta gaya masa. Yayi shiru na tsayin lokaci, zuciyarta ta shiga tsinkewa dalilin shirun nasa. Shidai shine me bayar da auranta, idan be amince da wannan batu ba to fa ko zata mutu tilas ta haƙura da Jafar. Ba kalar Addu'ar da batayi a zuciyarta ba a lokacin can Baffah ya nisa yace "Ahmad yaron kirki ne Afeeyah, babu uban da zeso ya rasa nagartaccen siriki irinsa" batasan sanda santsin bakinta ya jata tace masa "Wlh shima Jafar ɗin yanada nagarta dan baka sanshi bane" takaici ya saka Baffah yin murmushi kafin yace "Ki gaya masa yazo ina son ganinsa gobe". Cikin tsananin murna da zumuɗin hango nasara muraran tace "Bayanan Baffah, ranar Lahadin nan ze dawo kuma daman yace da ya dawo zezo ya gaisheku". "Fatima!" Baffah ya ambaci Asalin sunanta da kakkausar murya, murnar data fara ta datse, tsoro da fargaba suka maye gurbinta dalilin tun tashinta ba zata ce ga rana ɗaya da Baffah ya kirata da Fatima ba kuma da kakkausan sauti irin wannan. Baffan yaci gaba da magana cikin muryar gargaɗi da nuna tabbacin abinda yake magana akai. "Ranar Lahadi kikace ze dawo ƙasar nan, tsakanin Lahadi zuwa Juma'a ki tabbatar ki fitar da ranar daze zo ni dashi mu gana. Ba zan tursasaki ki auri abinda bashi ne muradin zuciyarki ba, zan binciki ko wanene wanda kike so ɗin amma ki sani muddin naci karo da wani abu dangane dashi da beyi mun ba ba zan sake zama dake ko neman shawararki ba, Ahmad shine zaɓin da zuciyata ta aminta dashi kuma shi zanaura miki". Kwana tayi tana juyayin maganar Baffah a zuciyarta. Tana jiyo sababin da Umma ta ringayi bayan tashinta daga gurinsa tana tambayarsa kenan ya goya mata baya? Me ze cewa Ahmad? "Na sani Ahmad yaro ne hankali da nutsuwa, shi rabon aure dana haihuwa basa canzuwa, wani baya auranmatar wani kamar yanda hausawa sukace MATAR MUTUM Kabarinsa, hikimar zancen shine ba'a binne wani mutum cikin kabarin wani kamar yanda wani baze zarga igiyar auransa kan macen dake ɗauke da igiyoyin wani kafin shi ba. Muyi mata addu'a, wannan gaɓar itace gaɓa mafi muhimmanci a rayuwar Mace, idan tayi dacen abokin zama na gari rayuwarta ta inganta haka zalika idan akayi rashin dace rayuwa ta shiga wani hali ina roƙonki da ki tattare duk wani fushi naki ki ajiye shi a gefe kiyi mata addu'a itace abinda tafi buƙata yanzu dama da zagi da hantarar da kikeyi mata. Tun a daren ta sanar da Jay, "Wannan shine first Agenda na, neman auranki is number one on my to do list dana sauka a Nigeria, ina fatan Allah yasa nayiwa Baffanki, karyace baze bawa mutum irina auranki ba kinsan fa akwai mutane da yawa da suka ce Ball ba sana'a bace ba, da akwai Friend ɗina da aka hana aure Baban yarinyar da yake so yace bashida sa'a and haka ya haƙura ya auri wata" inji Jay daga nan suka cigaba da shirye shiryen yanda abubuwa zasu kasance musu. Da sukayi waya da Badar ma ta gaya mata abinda Baffa yace, "Allah ya zaɓa miki mafi Alkhairi Afeeyah" Badar ta faɗata amsa mata da cewar "Amin idan da gaske kikeyi" "Uhm Afeeyah kenan, a bazanji tsoronki in fasa cewa mi dai nafi sonki da Ahmad ba kuma ko Baffan har ransa yafi son Ahmad kawai ya baki damarki ne kuma da kina da tunani seki haƙura kawai ki bi abinda yake so" Badar ta sake faɗi ƙit kuwa ta kashe wayarta dan bata son abinda ze canza mata mood ɗinta na farin cikin dawowar Jay. A gidan Anty Sauda ta shirya tarbarsa, ya sanar mata ya sauka Kano da ranar Litinin zuwa Yamma zeje ya ganta dan baze iya sake kwana guda a Naija ba tare da yaga fuskarta ba. Tsabar takaicin rawar jikin da takeyi Anty Sauda ficewa tayi daga gidan ta barta da masu aiki suna tayata, sanda ta dawo kuwa gani tayi kamar an canza gidan, tana tsammanin har bango Afeeyah ta wanke mata yau ko ina yayi haske ga ƙamshi kamar gidan sabuwar Amaryar Kanuri. Tana idar da Sallar La'asar ta zauna kwalliya dukda ba wani shafe shafe tayi ba powder ce kawai ta lailaye fuskarta da ita se kwalli ta taje gira ta shaf Lip balm me maiƙo da ƙyalli kafin ta taje gashinta da taje tayi steaming tun jiya. Shi kaɗai ne abinda zata iya cewa be gama cika a halittarta ba. Gashi ta nada cika yana kuma da laushi sosai gashi baƙi tsayinsa ne dai da kaɗan ya wuce kafaɗarta ba kamar na Anty Sauda da Ummansu da yake ya wuce tsakiyar baya ba. Jay ya gaya mata yana son gashi, yana son mace me gashi, har hoton gashin nata ta tura masa abinda bata taɓayi ba, yace mata cikarsa yayi masa tsayin ma babu laifi tunda Natural ne idan ta saka Relaxer zefi haka sauka kuma ze taho mata da Mayukan gashi wanda zata gwada amfani dasu dan dagaske fa shi son gashi yake kamar me Iskokan gashi. Ta gyara gashin tsaf ta ɗaure bayan ta shafa White gel kaɗan a gaban yanda ze sake kwanciya dukda daman a kwance yake kamar na jariri sabuwar haihuwa. Ta fesa body spray da body mist kafin ta saka Undies, kaya kala uku ta ajiye a kan Gado, ga Atamfa ga Lace ga Wata Chiffon gown ta rasa wanne zata zaɓa ƙarshe Salaha me aikin Anty Sauda tacewa ta tayata zaɓi. "Ki saka wannan, Abaya na Matuƙar yi miki kyau" Salahar ta nuna Doguwar rigar Kanti. Ta sallameta ta ɗaga rigar tana dubata, wadda Ahmad ya kai mata ce zuwansa Zaria na ƙarshe kafin ranar daya maidota gida hutun First Semester. Se sannan ta tuna da rabonda suyi waya tun ranar da Baffah yace masa ya turo tambaya kusan sati uku kenan. Wani iri taji a ranta, ta saka rigar tayi mata kyau har ya zarce a misalta. Hula ta saka akanta kafi ta yafa medium plain veil daya dace da rigar shima Ahmad ne ya kawo mata ta shafa latest designer oil perfume na kamfanin Ahmad ƙamshin ya ratsata, bata taɓa amfani dashi na se yau. Tayiwa kanta kyau balle kuma Jay ya ganta. Tana tsaka da jujjuyawa a gaban Mirror Anty Sauda ta shiga ɗakin, ga baƙonki can ya iso" ta faɗa tana kallonta. "Nayi kyau" ta tambayeta, ta juya tana cewa "Ban sani ba ina mudubi ne a gabanki ko idanunki basa gani ne da kyau?" Ta rungume Anty Saudan ta baya kamar zatayi kuka tace "Haba yar uwata rabin jikina wai har se yaushe zaku dena fushi dani? Na zata ku masu farin ciki da zaɓi nake tunda ba wani abu na kawo wanda ya take shari'a ba" ta faɗa kamar zatayi kuka. Anty Sauda ta juya ta kalleta ganinhar idonta ya tara kwalla tace "Karki ɓata kwalliyarki kinyi kyau kije anjima in ya tafi zamuyi magana ai yau zanga zaɓin naki". Tamkar wahainiya haka take taku zuciyarta cike da tunani kala biyu, farin cikin ganin rabin ranta da kuma taraddadin yanda makomar soyayyarsu zata kasance yanzu da take kan siratsi. Tayi Sallama, yana zaune akan Three sitter a falon Mijin Anty Sauda, idanuwansa akan hanyar shigowa yanayin zamansa yafi kama dana wanda ya ƙosa da zaman jira dan har zamowa yayi kaɗan daga kan kujerar. JAFAR Toshe kunne kawai yayi yana sauraron hargagin Hajiyar daya zame masa jiki, daƙyar ta barshi ya fita sallar Azahar Masallaci ya gaisa da mutanen da sukayi cincirundo a ƙofar gidansu suna jiransa. Bega Ahmad a masallaci ba seya kirashi a waya yace masa ya fita duba wasu kaya da suka sauka ya huta da yamma idan ya dawo zasu haɗu. "Bayan La'asar fa zanje gidansu Afeeyah dan Allah ka dawo da wuri" ya faɗawa Ahmad. Daga can ɓangaren Ahmad yayi murmushi yace "Na Afeeyah, to ka gaida mun da ƙanwata" "Tare zamuje ai" Jafar ya bashi amsa da sauri Ahmad ya buɗe kamar yana gabansa yace "Kawai goɗai goɗai dani sena rakaka zance? To ba dani za'ayi wannan abun kunyar ba". "Haba Yah Ahmad idan baka rakani ba dawa zanje? You are my only bestfriend fa ka sani. Magana akeyita Jafar zeje hirar gaske bata yaudara ba" Jay ya faɗa yana marairaicewa. Ahmad ya yi datiya yana cewa "Ashe dai kasan kai mayaudari ne" "Ai na tuba, dan Allah ka dawo muje tare" ya sake pleading. "I will come but on one condition, nima zaka rakani gidansu Fatima biko" Ahmad ya faɗa masa. Yayi shiru kafin yace "Deal" ya faɗa ne kawai dan Ahmad ya rakashi nasa uzurin amma ba har zuciyarsa ba. "Idan ka gama shiryawa ka kirani se mu haɗu a hanya saboda bana zaton zan gama abinda nakeyi da wuri na dawo gida ba, ka fito mun da hula" cewar Ahmad daga nan sukayi sallama take kuma ya kashe wayarsa gaba ɗaya, shi kamsa baze ce ga dalilin daya sakashi kashe wayar ba, kawai baya jin daɗin komai kansa ciwo yake masa bama yajin daɗin jikinsa gaba ɗayasan kuma duk bayanin da zeyi masa ba saurara zeyi na gara yayi masa mita da daddare idan sun dawo wani lokacin idan ze koma ya rakashi. Jay ya shirya tsaf ze tafi gurin Afeeyah. Wani Yadi ya saka Dark Ash ɗinkin half Jumper, plain ne yadin haka dinkin babu komai a jiki se links daya saka a hannu shi kansa daya kalli kansa murmushi ya saki. Ya daɗe be saka manyan kaya ba se yaga yau kwalliyar tasa hartafi ta kullum kamar wani sabon Ango in ba idonsa bane ma har ƙyallin goshi yaga yanayi. Ya kafa hula ya ɗaura Agogo sannan ya saka Takalmi. Signature Perfume ɗinsa ya saka wanda Yah Ahmad yakeyi masa, shi kaɗai yake amfani da turaren saboda yakai ya kawo ko suna ba'a yiwa turaren ba amma yanzu Ajay zeyi naming nasa. A safe locker Ahmad yaga wasu kwalabe masu kyau da ko be dubaba yasan Oil ne, ya ɗauki wanda kwalbarsa tafi burgeshi ya shanshana, Ƙamshi me sanyi da kwantar da hankali ya ziyarci hancinsa ya lumshe ido kafinya jefa kwalbar a Aljihu, namatane tunda ya ganshi a gurin kuma ya tabbatar waccen yarinyar da bata san darajarsu ba ze kaiwa gara ma ya bawa Afeeyarsa atleast ta isa tayi amfani da irinsa. Motar da Ahmad ya zuba masa akwatin tsarabar Afeeyah ya fita da ita, Tinted glass ce motar dukda haka ya saka face mask da dark shades yayi badda kamar daya saba. Tun da safe ta tura masa da Address ɗin gidan sisternta, yasan Arean dan haka hankali kwance ya ringa tuƙi yana sake gwada number Ahmad da tunda ya fito daga wanka yake kira amma a kashe. Yaja tsaki sanda ya isa layin data rubuta masa a Address, Yaja da wani Aboki Asharb Bala a arean shiya kira, bayan gaishe gaishen yaushe gamo ya tambayeshi ko yana gida gashi a unguwarsu. "Ina Kaduna Jay, can nake zama yanzu ai baka sani ba? Nasan dai ba takanas gurina kaje ba Wani abu kake nema a unguwar ko wani Address aka baka?" Asharb ya faɗa. Jay ya shafa kai kafin ya gaya masa wani gida yazo shine yake kiransa ya rakashi, daya faɗa masa number gidan kaitsaye ya directing nasa katangarsu ɗaya da gidan ta baya nan sukayi sallama da Alƙawarin zasu haɗu kafin ya koma. Yana faɗawa me gadin gidan sunansa ya buɗe masa Get dan an sanar masa za'ayi Baƙo. Bayan ya ajiye motarsa ya fito ya tsaya a fakaice yana ƙarewa gidan Kallon, gini me kyau na zamani daga gani me gidan Ɗan gayune daga yanda ya ƙalƙale ko ina da kwalliya ta zamani. Mu'az Babban Yaron Anty Sauda ya fito sanue da Jacee me sunan AJAY a jiki da Ball a hannunsa shi ya kira bayan ya gaisheshi yace ya shiga ya sanarwa da Afeeyah yazo yaron ya wuce ciki da gudu se gashi babu daɗewa ya dawo yace masa ya shiga ciki, seda ya rakashi har falon da akace ya kaishi kafin ya juya ze tafi. "Ka sanni?" Jay ya faɗa, se yaron ya tsaya yana kallonsa, fuskarsa rufe da Face mask ta ina ze sanshi? Kamar Jay yasan tunanin da yakeyi ya zare Shade ɗin idonsa tareda face mask. Yaron ya buga tsalle kamar wanda aka baiwa abinda yafi so a rayuwarsa tsabar murna be san sanda ya faɗa jikin Jay ba yana kiran sunansa da ƙarfi. "Shiiii, karka tara mutane mana" Jay ya kwaɓe shi, Mu'az ya riƙe bakinsa da hannu biyu yana dariya kamar sakarai dan ya kasa magana kafin kuma ya falla da gudu ya fice daga falon Jay ya rakasho da kallo yana murmushi. Kacokam ya maida hankalinsa kan ƙofar da yake tunanin tanan ake shiga falon daga cikin gida. Tun kafin ta iso yaji a jikinsa tana tafe, ya zame daga kujerar da yake zaune hannaye da Ƙafafunsa har tsuko suke masa tsabar Zaƙuwar daya ganta se gata kuwa ta shigo falon, kallon da yake mata tamkar ze hango jijiyoyin da suke gudanar da jini a cikin jikinta. Idanunsa suka saka ta sake rage saurin tafiyarta kamar ma ƙafafun sun mata nauyi ne, yanda take tafiyar ne yaga tamkar ɓata masa lokaci takeyi, ya miƙe, taku ɗaya, biyu Afeeyah batayi aune ba se jinta tayi gaba ɗaya a kan ƙirjinta ya zagaye bayanta da hannaye biyu kafin taji kamar ƙafafunta sunbar kan Ƙasa. Cikin Azama ta shiga Ƙoƙarin kwace kanta zuciyarta ma wani irin bugu kamar zata tsaga ƙirjinta ta fito fahimtar abinda take niyyarti yasa ya direta amma be saketa daga jikinsa ba swda tayi yunƙuri da gaske kafin ta janye tayi gefe tana sauke numfashi tareda zare idanu kamar wadda tayiwa sarki ƙarya. "Subhanallahi, I'm sorry, I'm so sorry Afeeyah i don't know what come over me i missed you so badly shiyasa na kasa riƙe kaina. I'm sorry for not seeking your permission before i touched you" Jay ya faɗa yana matsawa kusa da ita, taja da baya da sauri yanda tayi yasa ya fashe da dariya babu shiri. Kamar taga dodo ko wani Aljani. Komawa yayi kan kujerar daya tashi yana kallon yanda take kokawa da numfashinta tana zare ido. "Kizo ki zauna" ya faɗa yana nuna mata kusa dashi, ta maƙale masa kafaɗa. Da wani mayaudarin sauti bayan daya saka idonsa cikin nata yace "Please Afeenah". Yanda kasan ya jata da magnet haka ta fara takawa dukda can ƙasan ranta wani irin tsoro da kokontonsa ne ya shigeta, karo na farko kenan a rayuwarta da makamancin haka ya faru da ita. Namiji Baligi ya runguneta harya ɗaga ta sama tayi tantiran Samari kala kala amma babu Wanda Allah ya bawa sa'ar kwatanta mata irin wannan abun sw Jay. Bawan Allah Ahmad ya faɗo mata a rai, a shekara uku sau ɗaya fatar hannunsa ta taɓa haɗuwa da tata shima bada niyya ba, ko hoto zasuyi basa tsayuwar da jikinsu ze gogi juna... "I said I'm sorry fa, menene kum duk fuskarki ta canza or you are mot happy to see me?" Jay ya sake marairaicewa yana faɗa yatsunta guda goma cikin nasa yana murzawa, bata san sanda harya kama hannun ba seda ya fara magana ta ankare. "Jayyy, babu kyau, don't touch me again" ta faɗa kamar zata rusa masa kuka bayan data zame hannayenta daga nasa. Yayi wani mayaudarin murmushi kafin yaja baya ya zauna dakyau seya tallafe fuskarsa da hannu biyu ya zuba mata iso, irin kallon ƙurillar. Ƙasa tayi da kanta dan bazata jure wannan kallon ba bayan abubuwan daya yi mata, "Kinfi kyau a fili, kinfi kyau a kusa" ya faɗa yana kai hannunsa ya shafa fuskarta, ta tura baki da sauri yace "Don't do that again ki bari ba yanzu ba se kin zama halalina don't make me loose my self Afeeyah you won't like me". Da sauri ta miƙe daga inda take zaune saboda yanda yayi maganar daidai nan Salaha ta turo ƙofa janye da Food Trolley. Akan kantamemen centre table da yake tsakiyar falon ta shiga jere abubuwan data kawo bayan data gaida Jafar. Seda ta gama tas ta fita har sannan Afeeyah na tsaye dan gaba ɗaya Jafar ɗin ya tsoratata. "Ki zauna wlh bazan sake taɓa ki ba" yayi magana yana mata murmushi, gabanta ya yanke ya faɗi, sautin muryarsa da murmushin da yayi taga sun rikiɗe mata ya koma kamar Ahmad. A sanyaye ta zauna kan kujerar da ke can nesa dashi. Yan kallonta yace "Ko gaisawa bamuyi ba duk na tsorataki, anya ma kuwa zaki iya dani yarinyar nan naga alama tsoro ne dake sosai". "Ina wuni" ta faɗa a sanyaye tana ƙoƙarim kauda tunanin Ahmad daya ziyarceta. Seda Jay yayi dagaske kafin ta sake ba duka ba dan salon daya zo mata dashi yasa ta ɗarare ga Ahmad dake ta mata yawo a zuciya. Shiya ringa janta da hira tana amsawa se yayi shiru fuskarsa ta canza nan da nan hankalinta ya tashi ta shiga tambayarsa meya faru. "I said I'm sorry amma from the way you are behaving kamar bakiyi mun uzuri ba. Kasa riƙe kaina nayi nace bazan sake ba in sha Allah amma kalla ko magana ma ni kaɗai nakeyi daman saboda ki ɓata mun rai kika damu nazo" ya wani haɗe fuska kamar gaske aiko ya tayar mata da hankali yanda ya tsammata se gashi ta buɗe baki tana bashi haƙuri yana shan ƙamshi daga nan kuma suka koma normal suka fara hira irin yanda suka saba a waya. Duk abinda tace ita ta girka da kanta ya taɓa kaɗan Chinese rice da tayi da wani Chicken wings yace ta masa packaging zeje gida da shi. Seda aka kira Magriba kafin suka rabu yace zeje masallacin daya gani a farkom dake layin yana fita ya tarar da taron jama'ar da Mu'az ya haɗa a wajen gidan dan megadi ya hanasu shiga. Yaran unguwa Abokanansa ya ringa bi gida gida yana ce musu ga Jay a gidansu suka taho harda manya marasa abinyi za'ace ko kuwa tsabar sonJay yasa suka yarda da maganar Mu'az ɗin shi kuma Malam Sa'idu ya hanasu shiga dan daman ba kirki ya cika ba. A falonya koma yayi sallar dan baze fita ba,bayanya idar ya kirata tace gata nan tareda Anty Sauda zasu gaisa. A mutunce tamkar tanayi dashi Anty Saudan suka gaisa yana jan Amani data liƙe mata suka fito tare bayan sun ƙare gaisuwar ta barshi da Afeeyah suka ƙarasa magana. Jikinsa ya sake janta ya shiga ɗaukansu pictures wanda duk ta kare fuskarta da hannu ba'a ganinta. Tana ƙunƙuni suka fita ta rakashi jikin motarsa ya fitar mata da tsarabar daya kawo mata. "Bangaji da ganinki ba, kamar karna tafi" ya faɗa yana binta da kallo daga sama zuwa ƙasa kamar Maye. Tayi shiru tana wasa da zoben hannunta, yayi murmushi ya sake cewa "Se yaushe, yaushe zanje na gaida su Baffah?" "Yace from today to friday" ta bashi amsa a sanyaye tana tuna kalaman Baffa. Yanzu ace ya san Jafar ya kakkamata haka ai babu ma zancenya bashi auranta tasan cewa zeyi bashi da tarbiyya, ta dai yi masa uzurin kasancewarsa Rainon turai a gurinsu wannan ba wani abu bane su. "Ok, wednesday yayi?" Ya tambaya yana ɗage mata gira, ta gyaɗa kai, ya yashi daga kishingiɗar da yayi jikin mota yace "Gobe anan zan sameki ko gidanku?" "Gobe ma zaka dawo?" Ta tambaya tana ware ido, "Ko kar nazo kin gaji dani?" Ya mayar mata tambayar yana buɗe ido yanda tayi se tayi ƙasa da nata tana murmushi tace "Aa" "Don't worry, I'm not going to touch you again tunda naga raguwa ce ke". Yanda yayi maganar yasa taji kamar ta nitse a gurin da take tsaye, Ƙarara zaka fahimci da biyu yayi maganar musamman murmushin da yakeyi da irin kallon dayake binta dashi seta juya da sauri ta shige gida. Me gadi ya bawa Boxes ɗin ya shigar mata dasu bayan ya masa ihisani ya wuce gida cikin nishaɗi jama'ar da Mu'az ya tara kuwa hannu kawai ya ɗaga musu suka ringa ihu har seda matan cikin gida suka fara zaburowa sunayin waje suga meya faru shidai tuni ma yabar layin ya kama hanyar gida. A traffic ya shafa Aljihunsa yaji kwalbar turaren daya ɗauka a safe ɗin Yah Ahmad, ya zaroshi ya kai hancinsa ya shaƙi ƙamshin, hannunaa na hagu ya shanshana wanda ya fi amfani dashi gurin riƙe Afeeyah ba hannun kaɗai ba duk jikinsa har motar ma ta kama ƙamshin turaren da yake da yaƙinin na jikinta ne dan ya shaƙe shi yanda ya kamata lokacin daya ɗagata sama. Daya kasa gane abinda yake so ya tantance se kawai ya ajiye turaren a gefenshi, ta yuwu yanda ya shaƙeshi a gida da daɗin daya masa yasa yaji kamar shine a jikinta. Da wannan tunanin ya aminta yaci gaba da tuƙi yan tuno ta harya isa gida ganin motar Ahmad yasa ya wuce ɗakinsu ba tareda ya shiga cikin gida ba dukda tun yana gurin Afeeyah yaga kiran Hajiya, yanzu a hanya ma ta sake kira. PAGE 20 Ranar laraba kamar yanda sukayi da Afeeyah tun safe yake shirin zuwa gaida Mahaifita. Ya jawa Ahmad kunne akan kar a maimaita ta wancan ranar, dawowa da yayi ya tarar dashi ba lafiya nema ya rage kaifin Mitar da yayi niyyar dasa masa. "Zaka rakani gidansu Fatima biko nima" Ahmad ya faɗa masa. Jay ya taɓe baki, ya lura kamar sun samu matsala da Fatiman dan beji ya kirata ba kuma sukukun da ya ganshi yasan baya rasa nasaba da rashin shirunsu Allah yasa dai abinda ya faru ya saka ya haƙura da auranta kowa ya huta. BayanSallar Magrib suka shiryi tafiyar dan Jafar baya ditar rana muddinba hayaniya da cunkoso yake so ya haɗa ba. Tsaf suka shirya kamar tagwaye, kaya iri ɗaya suka saka Shadda Cream Color ta karɓi jikin kowanne duk iya hassadar mutum sedai ya kallesu yace Tabarakallah badai ya kushe shigar wani daga ciki ba. Jafar ya sake jefa turaren jiya a Aljihu dan karya manta. Suka jero suna tafiya Ahmad na tsokanarsa har suka zo daidai part ɗin Alhaji. "Ba zaka shiga kayiwa Hajiya Sallama ba?" Ahmad ya tambayeshi se yayi saurin cewa "Kai Aa muje kawai, tun fa dana dawo maganar da take tayi mun kenan wacece nake so a ina nake neman Aure, kasan matsaltsalun Hajiya yanzu setace ba haka ba shiyasa nake so ayi komai a sirrince se an kai kuɗi idan Allah yasa an ɗaura auran kawai se taji labari". Ahmad ya ringa dariya yana cewa "Lallai ka shahara, to wlh na barka da Allah idan ka janyo mun magana dan cewa zatayi ni na zugaka ka ɓoye mata" "Ina zakuje haka?" Muryar Alhaji Audu daya fito da shirin fita masallaci ta dakatar dasu. Ko wanne ya tsume kafin suka shiga gaishe shi. "Se ina haka kuka kafa huluna kamar sababbin Angwaye?" Alhaji ya tambaya. Ahmad ne ya bashi amsa yana shaf kai yace "Gaisuwar surukan Jafar zamuje". Kamar Alhajin zece wani abu daga yanayin kallon daya bisu dashi se kuma ya canza da cewa "Amma da kun jira kunyi sallar Isha'i a Jam'i ba lallai inda zakuje ku tarar basu idar ba" ya wuce is suka bishi a baya. Bayan an idar da sallah suka sake rankayowa tareda Alhajin suka shiga gida. Har Ahmad ya tada mota Balarabe guda daga ma'aikatan yaje da sauri yace masa Alhaji na magana seya bar motar a kunne ya wuce yanajin JafdaƘƙƊƘananun tsaki, har mamakin irin zumuɗin da yakeyi akan yarinyar yake kamar ba Jafar da Mata ne suke zigilli akansa ba se gashi wata ta zargeshi tsaf tana ja a ƙasa. "Yanzu na samu waya Alhaji Munzali yayi hatsarin mota kuma jikin babu daɗi ina so naje na ganshi" Alhaji ya faɗa bayan da Ahmad yaje. Cikin jimami yayiwa Abokin Alhajin jaje da fatan samun lafiya. Alhaji ya sake cewa "Bari na shiryo seka rakani mu duba shi" ya wuce sama ba tareda ya jira amsarsa ba. A waya Ahmad ya kira Jafar ya shaida masa, ya fara balbalin bala'i, "Ai se kazo ka sameshi da kanka ka tuna masa fita zamuyi, nasan ba mantawa yayi ba yana sane tunda ya buƙaci na kaishi kayi haƙuri kawai kaje ma koma tare wani lokacin" Ahmad ya faɗa da Jafar yace wai ya gayawa Alhaji fita fa zasuyi. "Amma ni kaɗai zanje gaida mahaifin nata kamar wani mara galihu?" Ya faɗi kamar ze masa kuka, Ahmad ya sake cewa "Duk ni sanda nake zuwa nawa gaisuwar dawa mukaje? In baka iya zuwa kai kai kaɗai ka kira ko Sadik ko Anwar su rakaka" "Ni dakai nake so muje" "Shikenan seka jira na kai Alhajinmu dawo se mu tafi" "Salon Babanta yace I'm not serious ba? Allah kawai dan ta riga da ta gaya masa ina zuwa da fasawa zanyi kawai naje muyi hira idan yaso daga baya se muje gurin Popsyn nata da kai" Jafar ya dira mita daga ƙarshe ya kama hanya ya tafi shi kaɗai Ahmad kuma ya kai Alhaji AKTH duba Abokinsa. A hanya Alhajin yake cewa Ahmad "Babanku ya gaya mun iyayen yarinyar sun dakatar da zuwa tambaya sunce a basu sati huɗu ko?" "Eh haka yace Alhaji" ya bashi amsa ba dan yaso ya tado masa da maganar ba. Alhaji ya sake cewa "Ka bincika kaji dalilin daya saka suka ce hakan ne?" "Eh, kawunta wanda ze bayar da auran ne baya nan yayi tafiya shine dalili" Ahmad ya yanko ƙarya ya lafta masa. "Uhm kodai basu shirya ba dai kuma suna jin nauyin su gaya maka ka saka musu hannu a cikin shirin nasu?" Alhaji ya sake faɗi yana kallon Ahmad da yanayinsa ya nuna he is not comfortable da maganar da maganar da Alhajin ya tayar. A sanyaye yace kawai yayi shiru be bashi amsa ba hakan tasa shima Alhaji ya kama kansa can kuma ya sake soko wata maganar yace "Wato shi gaban kansa yakeyi babu wanda ya saka cikin lamarin auransa daga kai se Uwarsa ko?" Yasan da Jafar yake dan haka yace "Jiya ya fara zuwa gidansu Alhaji, tsarin Babansu ne kuma se yaga mutum kafinya bashi damar neman auran yarsa shiyasa zeje yau ya gaishe shi amma ba wai maganar auran ce ta taso ba". "Dama aiba zaka taɓa faɗar laifinsa ba, shi kuma yar waye yake nema?" "Nima ban sani ba yanzun zamuje daman kuma ya tafi shi kaɗai" cikin yanayin Ƙosawa da tambayoyin ya bashi amsa se Alhaji ya Ƙaro radion Mota yayi shiru. Jay kuwa be fahimci kwatancen da Afeeyah ta turo masa ba dan haka tace tayi sharing masa live location ɗinta haka kuwa akayi yana biye da Map tiryen tiryen se gashi a cikin gari tsukin unguwar Marmara. A bakin titi yayi parking mota yana ƙarewa gurin daya zo kallo, dukda darene amma Jama'a nata kai kawo yanda kasan kasuwa ga surutu kaya kaya banda ƙarar ababen hawa da suke karakaina akan titi. He couldn't believe it a wannan unguwar suke zaune. Ya ringa zungura kai yana leƙa yan hanyoyin da yake gani, gurin da Map ɗinza yake pointing lungune da babu alamar Mota tana iya shiga. "Ta yuwu Babansu irin mutanen nan ne da basa son canza muhalli shiyasa ya ke zaune a nan ƙila da akwai wata hanya kota can baya da suke bi da mota har ƙofar gida" ya shiga baiwa kansa Ƙwarin guiwa. A waya ya kirata ya gaya mata yana bakin titi besan ta inda ze shigo ba tace masa zata bawa Yayanta wayarta seya zo ya tafi dashi haka kuwa akayi ta bawa Yaya Malam wayar sukayi magana harya gano inda yake. Seda ya rufe fuskarsa da Facemask kafin ya fita daga motar, sukayi musabiha sannan suka tsallaka Titi, suka ringa bin lunguna suna tafiya shidai bin Malam kawai yakeyi a baya a ransa yana mamakin wannan unguwa daya zo yau, a rayuwarsa be taɓa shiga makamancin lungun ba, iyakarsa da nan haka gidan Sarki dan kafin ya tafi Turai yayi nacin son Doki da sallah ko idan an gayyaci Alhajinsu wani taro yakan biyo shi saboda yaga Doki shi be san akwai irin lokunan nan bama a Kano. Tun yana hasashen ganin gida me Gate harya saduda domin dai gidajen jar laka yake tacin karo dasu wanda Hasken Nepa da Sololin da gwamnati ta ƙawata lokunan dasu suka taimaka masa gurin ganinsu tsaf kamar da rana. Seya saki tunanin gidan Gate ya kama na kodai Babansu Basarake ne? Tunda akan samu gidan Sarakai cikin lungu. Bashi da me bashi amsa haka ya ringa jefa ƙafafu har suka isa inda yaga Malam ya dakata da alamu nan ne gidansu Afeeyah. Ya ƙarewa gidan kallo cikin abinda befi sakan biyar ba, da fulasta lulluɓe dan haka bayace ginin ƙasa bane kona sumunti. Filin dai dukansa baze wuce taku Ashirin da biyar a kwance ba idan ma ya kai, be san ya zurfinsa yake ta ciki ba. Zuciya da saƙe saƙe take ta ayyano masa ai Akurkin da Alhaji Audu ya watsasu a gidansa ma yafi wannan gidan girma da yalwa. Muryar Malam ta dawo dashi daga tunanin daya tafi yana cewa "Bari na sanar mata ka iso" ya wuce cikin siririn soron gidan Jay harda tura wuya yana leƙawa. Ya saki ajiyar zuciya me ƙarfi bayan da Malam ya dawo yace masa Baffah yace ya shiga. A baya ya bishi cikin taka tsan tsan dan kar Ƙofar gidan ta rafke masa goshi dan ya lura shima Malam ɗin da yake dogo ne sosai seya ranƙwafa yake shiga. Tilas ya yabawa tsaftar matar gidan domin dukda darene ko ina tsaf yake babu tarkace, a fakaice ya kalli ƙofofi guda huɗu da suke cikin gidan wanda yake tsammanin ɗakuna ne, ya hango kitchen da kuma inda yake zaton makewayine saboda ga famfo nan se siririn lungu ya shiga ciki. A cikin barandar dake gaban ɗakuna biyu suna kuma kallon ragowan biyun ya zauna kan shimfiɗar babbar darduma da akayi. Harda standing fan a ajiye a gurin. Malam ya shige ɗakin Baffah ya sanar masa ga Baƙon wanda tuni Ƙamshin turarensa ya sanar musu da shigowarsa. Dattijon daya tabbatar shine mahaifin Fatima ya fito, fuskarsa a sake yake yiwa Jafar da duk yaji ya rikice kamar wanda yaje gaban Sarki Maraba. Ya zauna daura dashi, Jafar ya duƙe yana gaida shi amma Baffan ya bashi hannu sukayi musabaha. Tattaunawar tasu batayi tsayi ba, ya tambayeshi waye shi sana'arsa data mahaifinsa. Daga yanayi na kamala da kuma tambayoyin da Baffah yayi masa be ga wata matsala a tattare dashi ba. Baffan yace masa "Da akwai wanda yake neman Afeeyah kafin zuwanka sun jima dashi amma ta tabbatar mun da kai take so, ina fatan a shirye kake domin bana so maganar auran taja lokaci, zan baka daga nan zuwa sati biyu ka turo magabatanka domin muyi magana, da zarar ta kammala karatu a ɗaura muku aure" "In sha Allahu Baffah" Jay ya faɗi yana goge zufar data tsatstsafo masa daga goshi. Baffah ya karkato masa da fanka saitinsa yana cewa "Garin da akwai zafi sosai dan ma an samu wuta kasha ruwan ko zaka samu sauƙin zafin" ya nuna masa ruwan pure water da Zoɓon gora wanda Umma take siyarwa Malam ya ajiye masa tun zamansu. Umma ce tace pure water za'a bashi domin su na famfo ma suke sha ai kuwa har kuka Afeeyah tayi akan hakan. Jay ya kalli farantin ruwan yayi murmushi kawai ba tareda ya sha ba, Baffah ya miƙe yana cewa "Bari naje, an gayyaceni Mauludi anan Ƙasanmu zuwan kane ya dakayar dani da tuni naje dan bana so nayi dare a waje" se shima Jay ya miƙe tsaye yana laluba Aljihunsa. Bandir na dubu ɗaya ya zaro ya rage tsayi kafin ya miƙawa Baffan yana cewa "Gashi babu yawa a siyi goro". Baffah ya kalli kuɗin yayi ƙaramin murmushi kafin yace "Nagode Allah yayi Albarka" ya wuce ba tareda ya karɓa ba yana cewa Umma ta leƙo su gaisa. Malam ne ya fito daga falo yace ya shiga can kawai, yayi masa jagora Umma na zaune kan kujera tana kallon Arewa 24 a yar Plasmarta da Baffah ya saka mata kwanannan da Hijabinta har ƙasa Jay ya kai ya gaisheta ta amsa a mutunce tana cewa ya hau kujera sw ya sake kalmashe ƙafa ya zauna sosai akan Centre carpet kansa a ƙasa. "Kira masa ita" Umma ta faɗa tana miƙewa ta fice daga falon sega Malam da Afeeyah, ya baje a gabansa daman Baffa yake jira ya fita dan ta Umma me sauƙi ne. Kamar wanda za'ayi wa Ƙarin karatu haka ya zauna bakin nan har kunne yau gashi ga Jay a gidansu. "Wai meye haka Yah Malam?" Afeeyah ta faɗa tana tura baki. Jay ya kalleta bbau yabo babu fallasa yace "Ina ruwanki? Yayanmu ne kuma Fan" "Loyal Fan ma kuwa, dan Allah ina zuwa be kamata naci amanar Jay ba gara na fara sanar masa ya zo ya ganka inaga har suma zeyi yau saboda Ɗaɗi" Yah Malam ya faɗi kafin ya sake ficewa da sauri kiran Amininsa Sani. Tsabar yanda yake Son Jay ne sunansa ya koma haka, babarsa kanta ta tashi daga Mamansu Sani ta koma Mamansu Jay dako ka zagi Jay a gaban Sani gara ka ambato Babansa Malam Hamza ka zaga. Bayan fitar Malam Afeeyah ta zauna yanda Jay yake binta da kallo kamar me neman wani abu a jikinta ne duk yasa ta tsargu. Atamfa ta saka yau A line gown Dark blue ce da fari se dan jaja kaɗan a jiki kalar ta haska ta sosai ta mata kyau. Cikin sanyin murya ta gaishe shi, ya amsa bataji sautin muryarsa ba laɓɓansa taga sun motsa shine ta fahimci ya amsa mata. Jikinta yayi sanyi, murnar dake ranta ta yau Jafar yazo gurin Baffah alamar maganar auransu na dab da Ƙulluwa ta disashe. Ta tsammaci ganin fuskarsa a washe kamar jiya koma tafi hakan amma se taga saɓanin zatonta, ba yabo ba fallasa, ba wannan Fara'ar da ya ringayi jiya balle zumuɗin taɓata se binta yakeyi da kallon data rasa dalilin sa. Sukayi shiru for almost 10 mins shi yana kallonta ita kuma tana wasa da zoben hannunta zuciyarta na dakan lugude. Meya kawo canji a fuskar Jay? Abinda take tambayar kanta kenan. "Afeeyah" taji ya kira sunanta ta ɗago a hanzarce kamar tana jira, idanunta da suka fara tara saboda tunane tunanen da takeyi ta sauke a cikin nasa daya zuba mata. Tana kallo ya taune Lips ɗinsa na ƙasa kafin ya kalli gefe alamu sun nuna maganganu ne a bakinsa bama magana ba amna ya haɗiye su se ya miƙe yana ƙaƙalo murmushin data tabbatar na yaƙene yace mata "Muje ki rakani, kar Umma tace bani da kunya na shige mata falo nayi zamana". Yanda yayi maganar yasa dole ta murmusa lokaci ɗauke ƙwallar data ziraro mata duk akan idonsa. Ya cire rafar Kuɗin ɗazu ya ajiye a inda ya tashi kafin ya juya ya fara tafiya tabi bayansa tana cewa "Ka ɗauki kuɗinka indai ba faɗa kake so ka janyo mun ba" be amsata ba ya sa kai ya fice. Umma na tsaye gaban ƙatoton Fridge ɗinta tana jera Gororin Zoɓo, dama yanzu take shiri a ranta ta leƙa falon se gasu sun fito. Jafar yayi mata sallama tace ya gaida mutanen gida ta juya taci gaba da aikinta Afeeyah tabi bayansa zalo zalo jiki a saluɓe. A soro ya tsaya bayan ya tura ƙofar gidan ya jingina bayansa da ita ya harɗe hannu a ƙirji yana mata kallon da yake sakata faɗuwar gaba. Ko a mafarki be taɓa hasashen Afeeyan ta fito daga irin wannan gidan ba, ƙirarta, fatar jikinta, kwalliyarta basuyi kama dana wadda take rayuwa cikin wanna lokon ba. Abubuwa da yawa suke masa yawo a rai amma yayi ƙoƙarin furzo wanda yafi tsaya masa a rai da Baffanta yace masa akwai wanda ta daɗe tare dashi amma tace shi take so. Kamar saukar Aradu haka taji tambayar "Wanene wanda Baffa yace kun daɗe tare dashi?". Seda tayi dagaske kafin ta iya danne firgicinta ta saita kanta ta hanyar marairaice fuska, yanayin da tayin ransa a ɓace yake amma abin ya bigeshi se kawai ya ɗage kai sama yana shaƙa tareda furzar da iska me cakuɗe da Ƙamshin turaren da a yanzu ya tabbatar a jikinta yake jinsa. "Kai da kanka kana cewa baze yuwu ace mace kamata na rasa saurayi ba, haka ne amma kuma babu wanda nake so cikinsu" ta faɗa cikin rawar murya Idanunta akan fuskarsa, so takeyi ta fahimci abinda yake zuciyarsa amma yaƙi bayyanar da hakan. Zuciyarta ta sake tsinkewa sanda taji yace "Bana son ƙarya Afeeyah na kuma tsani me yinta. I asked you everything that concerns you me yasa zaki ɓoye mun wannan? Kuma har Baffahnki yasan da zamansa tsakanin ni dashi wa kike shirin ki yaudara?" "Amma kasan babu batun yaudara tunda har na kawoka gaban Mahaifina, idan ƙarya nakeyi maka bazan taɓa bari kaga tushe na ba zamu ƙare soyayyar mune kawai a waya ba zaka taɓa sanin inda zaka saneni ba idan na gama na sallameka" "Shi da k ika fara kawowa shi kika yaudara kenan?" Ya tsareta da idanunsa da suka canza kala saboda abinda shi yaɗai yasan menene. Tayi shiru dan gani tayi kamar ze iya kwasa mata mari idan ta sakw faɗin wani abu. Ya dafa ƙofa yana nunata da yatsa yace "Ki tabbatar da kin sallameshi, karna sake ganinki da duk wani abu daya dangance shi, i mean daga kan sutura, cosmetics har wayar hannunki ki cire Sim yanzu I'm going to send you another one. Ki nemi izini gobe or the next day I'm taking you out to shop, bana so na sake ganin duk wani abu daya siya miki a jikinki har wannan turaren da kike sakawa bana so na sake jinsa a jikinki". Yanda kasan Ya da Uba haka yake nunata yana zazzaga mata maganganu, tunda take a rayuwarta bata tabajin ta tozarta irin na wannan lokacin ba, a tsaye take amma ji tayi inama ƙasa ta buɗe ta shige ciki ko kuma ta rufe idonta ta ɓace ɓat daga gurin. Maganganun Jafar suna nufin ita ko iyayenta basu isa su mallaka mata ire iren suturu da sauran kayayyakin da take ta'ammali dasu ba, yazo yaga gidansu dole ya samu bakin faɗa mata maganganu ai. Yanda yake magana fushin dake cikin muryarsa ya zarta ace iyakar na disappointment ne, ya wuce ace na ƙaryar da yake iƙirarin tayi masa ne tabbas da akwai wani abu daya tunzurashi bayan wannan. Jiki a saluɓe ta shiga gida bayan daya sallameta ya tafi ta shige ɗaki ta faɗa kan katifarta tana sakin kuka me sautin da ta kasayi a gabansa se hawaye. Muryar Umma dake kwarara mata kira da hayaniyarsu Yaya Malam ta sakata dole ta tashi, seda ta wanko fuska a bakin famfo kafin ta shiga falon da suke. "Wannan kuɗin fa na menene?" Umma ta tambayeta tana kallonta kafin ta Amsa Sanin Jay ya zaburo yana cewa "Yana ina Afeeyah? Ni daman nasan ƙarya kakeyi haka kawai ina gurin Babyta ka tasoni yanzu kasa na faɗa mata magana yanzu nayi two zero, ni banyi hira da ita naji daɗi ka yaudareni da sunan Hero". Malam daya sha wahalar nemo Sani ya galla masa harara yace "Minti nawa nayi ina gararanba a lokon nan kowa yace besan inda kake ba? Amma dai ko ƙamshin da gidan nan yakeyi ai ya isa kasan yau anyi babban baƙo" "Ji banza, wane kalar turarene Ahmad be baza mana a Lokon nan ba? Shifa idan yazo tun daga titi ake sanin ya iso gidan nan kuwa a Ƙalla yana kwana uku kafin ƙamshin ya gama bajewa" inji Sani Malam yace "Zubairu" Umma ta daka musu tsawa jin zasu kaure da musun da suka saba tace au fita su bata guri tunda basu san sun girma ba. Afeeyah na tsaye har sannan ta sake nuna mata kuɗin tana tambayar na menene "Shine ya ajiye kuma seda nace masa ya ɗauke zakiyi faɗa amma be jiba" ta bawa Umman amsa. Murmushin takaici Umma tayi tace "Ba laifi ai tunda shi naga harya harbo jirginki da wurwuri ya fahimci mayadariya ce ke kuma makwaɗaiciya. Shi dayake free ne gashi nan ya buɗe miki ai ya nuna miki kar yake kallonki tunda dai yaga ubanki ya san bashi yake miki hidimar da tasa kike jin kanki kina goga kafaɗa da waɗanda suka tsere miki ba kinga ko auransa kikayi yasan ba dan Allah bane kin aureshi ne saboda abin hannunsa. Ko da dai banga wata sufa ta rashin da'a a tattare dashi ba amma ki sani inda kaso dari ya yarda dake daga kalamansa kin rasa kaso hamsin na ƙima da darajar da yake kallonki dasu ada in ma be zarce hakan ba. Ga wanda kika daɗe tare dashi yana bauta miki yanzu da kika hango kazar data fishi maiƙo shine kika tubure akan kw baki taɓa cewa kina sonsa ba ai shikenan ni babu abinda zance miki tunda ubaki ya tsaya miki, Allah ya shige gaba" Umma ta faɗa kafin ta maida hankalinta kan Film ɗin Hausan da aka fara a Arewa. Afeeyah na tsaye tana hawaye, jin Umman tayi shiru ta fahimci ta gama maganarta. Wai dan Allah da wane yare zata fahimtar da Umma? Abinda take tambayar kanta bata da amsa dan haka cikin muryar kuka tace "Kiyi haƙuri Umma" "Da kika mun me ni kuma? Ai ke ya kamata na bawa haƙurin shiga rayuwarki da nakeyi, ni ai babu abinda zan sake cewa kuma Afeeyah ai magana ta ƙare tunda har kin turoshi kenan ba gudu ba jada baya kina kan bakanki shima kuma Malam naji ya bashi sati biyu ya turo, to dai ku tsananta bincike kar azo ayi abinda daga baya za'a ringa wlh tallahi" Umman ta sake magana, yanda tayi seka rantse da wata Ƙawa ko yar uwarta suke shawara akan auran wata, tamkar ba auran yar cikinta ake magana ba wai su tsananta bincike ita da Baffa kenan ta zame hannunta a ciki kai se a bar Umma dai. Kuka Afeeyah ta fashe mata dashi tana zama a gurin "Umma magana kikeyi fa tamkar kin zare hannunki daga cikin sabgata kina nufin nayi gaban kaina?" Ta faɗa cikin kuka, Umma tace "Au wai baki sani ba tuntuni? Ai ni tun daga randa kika nuna mun kin girma, kin isa ki yankewa kanki hukunci na zare hannuna daga sabgarki Afeeya ai yanzu kece uwar kanki, abinda kike so ne kuma na barki da zaɓinki Ke bakiyi ko rabin tashen da nayi a zamanin ƙuruciyata ba, ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba soyayyar da kike iƙirarin kinawa wancan yaron batavkai zafin wadda nayiwa nawa muradin ran ba, da ace na zamo me kafiya da taurin kai irinki da ban auri ubanki ba har nazo na haifeki kika tsaya gabana kina faɗin ke ga wanda ranki yake so. Ban fara son ubanki ba seda na zauna dashi domin daya ganni yace yana sona ya samu Mahaifina uffan ban tofa ba nabi abinda nawa uban ya zaɓar mun gashi naga ribar biyayyar danayi masa saboda shekara talatin da biyar Alhamdulillahi babu abinda zancewa ubangiji se godiya domin matsalolin aure sedai naji su gurin mutane badai a cikin gidana ba, ƙila dana bijire nabi zaɓin raina kamar yanda kike shirin aikatawa Allah kaɗai yasan takaicin da zan kwasa a tsayin shekarun nan" Umma tayi maganar cikin zafin rai. Afeeyah dai se kuka take Umman ta miƙe ta nufi Ƙofa tana cewa "Kukan daɗi kikeyi, Allah ya gani iyakar yi mun kare mutunchinmu, se ki zuba ruwa a ƙasa kisha kin jawo mana abinda za'a yi damu, ba unguwar nan ba na tabbatar duk wanda yaji labarinmu seya zagemu shekara uku kina cinyewa yaro kuɗi yana miki hidima rana tsaka kice baki san zance ba Allah yasa yazo yace a biya shi se ki san ta inda zaki fara tattaro masa kaya da kuɗaɗen daya kashe miki" "Haba Ruƙayya shin wai maganar nan ba zata mutu haka ba?" Baffa da tun daga soro ya tsinkayi mitar Umman ya faɗa bayan dayayi sallama. Ta kalleshi kafin tayi murmushi irin na zallar takaici tace "Malam kenan, ai ba'a ma haifi maganar ba balle ta mutu, yanda mutanen unguwar nan basa raina abin magana idan bamuyi wasa ba ai fita seta gagaremu na wani lokaci saboda yanda za'a ringa zunɗen mu. A haka ma meye ba'a cewa duk akanta balle kuma aji wannan shegantakar Allah dai ya rufa asiri" ta fice daga falon ta barsu shida Afeeyah dake aikin kuka har sannan. "Tashi kije ki kwanta" ya faɗa mata a sanyaye, tabbas Umman batayi ƙarya ba, tarayyar Afeeyah da Ahmad ba abinda mutanen unguwa basa faɗi wasu ma cewa suke lalatarsu kawai sukeyi amma idan ba haka ba Ƙanin uwarta ne kona ubanta ze ringa mata hidima haka?. Jay kuwa da tunani kala kala fal kansa ya bar gidansu Afeeyah, ya ringa bulayi a loko dan ya manta ta inda suka shiga kuma shi kaɗai ya fito, daidai Allah yasa ya ganshi a titi sedai ya banbanta da inda ya ajiye motarsa dakyar da tambaya ya koma kan Titin daya ajiyeta ya figi motar a tsiyace ya bar unguwar. Abu goma da ashirin haka ya ringa saƙa da warwara. Be taɓa koda a hasashe hango Afeeyah ta fito daga irin low class family haka ba. Dukda bata yi masa ƙaryar ita yar masu Arziƙi bace dan ko magana sukeyi takan nuna masa batasan abubuwa da yawa da yake maganarsu ba seya ɗauka wasa takeyi seyau ya tabbatar ya kuma ganewa idanuwansa. Asalinta ko matsayin mahaifinta be girgiza komai daga Son da yakeyi mata ba amma ƙaryar daya kamata dumu tayi masa ita ta hasalashi, seda ya tambayeta idan da wanda yake nemanta har iyayenta sun sani ta gaya masa tace babu. A duniya idan akwai abinda ya tsana be wuci wulaƙanci da ƙarya ba gashi ya kama wadda yake mutuwar so da dukka laifukan saboda shi ta masa ƙarya ta kuma wulaƙanta koma wanene take tare dashi bayan tsayin lokaci daya ɗauka lokaci yana hidima da ita, daga irin suturun da take sakawa kai ko fatarta ka kalla kasanba ƙaramar kulawa take samu ba ta mayuka masu inganci tabbacin koma wanene yana da buruka masu yawa akanta shiyasa baya ƙyashin kashe mata ko nawa ne amma ace lokaci ɗaya ta sutaleshi. Tabbacin da yake dashi shine tana sonsa tunda gashi har mahaifinta ya faɗa shima kuma ya yarda da hakan domin ya gani a idonta ya kuma fahimci hakan daga ayyukanta badan haka ba shima ze ce tana da target akansa idan ta samu wanda ya fishi watsar dashi zatayi. Allah kenan, wato tasu ƙaddarar kenan shida Yah Ahmad soyayya da irin waɗannan yaran. Dalilin abinda yakeji akan Afeeyah yasa yaji ya farayiwa Ahmad uzuri bisa jure cin kashin da Fatima takeyi masa domin yanda yakejin Afeeyah a ransa ya tabbatar shidai baze zama sullutu irin Ahmad ba amma fa ko taƙi Allah ko bata sonsa se ya aureta a hakan sedai ta mutu tunda dai ya samu cikar burinsa amma shi ya zauna yana lallaɓata tana wulaƙantashi bayan yana da makaman da ze iya juya komai dasu se yanda ya tsara za'ayi. PAGE 21 Ya isa gida yana fitowa daga mota ya hango Hajiya daga ƙofar shiga gurinsu tana tsaye kome take a daren se Allah dan goma ta gota tana hangoshi ta nufeshi da sauri. "Hajiya lafiya? Meya fito dake a daren nan?" Ya faɗa sanda suka gamu, tace "Ina fa lafiya, tun Mangariba nake nemanka a gidannan kowa yace besan inda kake ba na kira wayarka yafi sau shurin masaki baka amsawa". Se ya zaro wayar daga Aljihu, tunda ze shiga gidansu Afeeyah ya latseta ta shiga silent shiyasa beji kiran Hajiyar ba. Hajiya data gama ƙare masa kallo daga sama zuwa Ƙasa tace "Daga ina ka fito haka kaci uwar Gizina kamar wanda yaje gaisuwar surukai?" "Sadik na raka" ya bata amsa yana shafa kai lokaci guda zuciyarsa ta shiga tsalle, tabbas da akwai gagarumar matsala domin dai ya sani ko sama da ƙasa zata haɗe idan shi yace yaji ya gani tofa Hajiya ba zata yarda da wannan haɗin ba, a tsarin zubi na halitta Afeeyah ta dace da Matar da Hajiyar take hakaito masa sedai yasan an saɓa lamba, yar talaka jikar talaka yace ze aureta tofa ya taro gagarumin yaƙi ne ta shiga wanda be zamar mata dole bama tayi kane kane inaga maganarsa? Ta yuwu shi ba a gida zatayi masa nasa taron ba fili zata siya a gidan Radio ko Jarida ta wanke shi tas ta Ahalin daya ke shirin jajibo mata a matsayin surukai. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ya faɗa a fili yana dafe kai, Hajiya da tayi magana harta gaji ya zuba mata ido kawai amma alamunsa sun nuna baya tareda ita, cikin hayagaga tace "Da akayi me kake ja mana Innalillahi? Ina maka magana tuntuni ka tsareni da shegun idanunku na gado ko kuwa kana nufi kaima ba zaka shiga maganar bane?" "Wace magana kuma Hajiya?" Ya tambaya yana dafe kansa daya shiga sara masa, hasaso Word War III ya tashi a gidan kwai yake da zarar maganar auransa ta fasu. Sati biyun da mahaifin Afeeyah ya bashi sunyi kaɗan daya shirya harya saita komai bisa tsari ta yanda koda wani abu ze biyo baya ya zamana bayan cikar burinsa. "Muje ciki na gaji, rabona da bacci me daɗi har na manta ni kaɗai kamar wadda ta rabawa masifu goron gayyatar biko da wannan ta fita wannan seta shigo" Inji Hajiya ta juya tana jan ƙafafu. Matsalar Hajiya ƙarama ce take neman zautata, Shegen Mijinta da yayi musu lamɓo akayi aure tunda taje gidan nan a kullum sabon Episode yake haska musu na rashin mutunchi. Yanzu wai bata da lafiya sunje Asibiti an ce ciki ne da ita shine yace sedai a zubar ita kuma taƙi yace ta zaɓa ko aurenta ko cikin wai shekararsa Ashirin da takwas be isa ya fara tara yaya su tsufar dashi ba. Tun wancan satin ake jaraba data kirata ta gaya mata tace ta je ta sanarwa Babarsa matar dake bata da mutunchi a faɗar Hajiya Binta wai tacewa Hafsatun ita babu ruwanta bata shiga rayuwar yayanta yanda kowa ya ga dama haka yakeyi tunda yace baya son haihuwar yanzu seta haƙura idan kuma zaman auren ne bata so ga hanya nan yammata da yawa ze samo wata ya aura. Yau taje gidan Turai suka tattauna shine tace ta samu cikin su Naziru ta saka wani ya kirashi ya masa magana dan tasan Alhaji dai baze shiga wannan batu ba ƙarshe kwancewa kanta zani zatayi a kasuwa kowa yasan halin da ake ciki to ta kira Naziru yace baya Gari, Zakariyyah yace yaron bashida mutunchi baze kirashi ya zageshi a banza ba Yakubu kuwa da tasu a tsakani daman bazata sako shi ba shine take ta neman Jafar wai shi ya shiga ya sasanta dan yanda Hafsatun tace tun jiya ya bar ƙasar ya tafi Dubai bisa rakiyar wata budurwarsa da har gida ta biyo masa suka tafi daman kuma ba baƙon abu bane Ƙawayensa mata sunfi Maza zuwa gidan haka zasu wuni a part ɗinsa idan tayi magana in be dake ta ba se ya gaya mata maganar da zata gwammaci dukan da ita. "Zan kirashi da safe Hajiya" Jay faɗa bayan daya gama sauraronta. Ta muskuta tace "Gara dai ka kira shi, ta yaya za'ayi banda shi ba ɗan Arziƙi bane yace baza'a haihu ba? Dan uwarsa da ba'a haihuwa shi zezo duniyar ne ko kuwa da ba'a haihuwa da yawa layi zezo na haifa masa yar ya aura ya ringa zuga mata rashin mutunchi? Billahillazi se tayi dozen kuma a ƙalla ciki maza takwas koma goma duk wannan jiji da kan da uwar sa takeyi dan ta haifi Namiji ɗaya tal se mun sauke mata shi Hafsatu zata cika gida musu gida da Yaya ta yanda in ubansu ya mutu aka tashi rabon gado za'a haɗa harda su". Cike da mamaki yace "Hajiya, ina kika taɓa ganin jika ya gaki Kakansa?" "Za'a fara akansu" ta faɗi irin ko a jikinta seya miƙe bayan daya ce "Allah ya rufa asiri bari naje na kwanta" 'Kai wai se yaushe zaka nunamun surukar tawa ne? Kuma yar wace ƙasace? Ya kamata fa azo ayi abinda za'ayi tunda wuri dan auranka so nakeyi nayi biki na kece raini Wanda ba'a taɓa kamarsa a faɗin Najeriya ba" Hajiya ta dakatar dashi seya koma ya zauna ya lalubo wayarsa daga Aljihu, cikin hotunan da yayiwa Afeeyah ranar dayaje gidan Anty Sauda ya buɗe kunno mata ɗaya, ta fito sosai a tsaye dukda fuskarta babu fara'a amma tayi kyau kwarjininta ya fito sosai. "Kai kai kai zankaɗi zuƙi, Jafaru a ina ka samo wannan ta Gabas ce ko Yamma?" Hajiya ta faɗa tana zooming hoton kafin tayi gaba tana kallon ragowar da sukayi tare, akan wanda ya rungumeta gaba ɗaya a jikinsa kanta na kafaɗarsa dan haka rabin fuskarta ne ya fito Hajiyar ta tsaya, kamar idanunta zasu faɗo haka take kallon wayar tace "Kyau iya kyau gaskiya kun dace, turamun wannan shi zan nunasu Turai" ya karɓi wayar da take miƙa masa, kunyar kansa ta kamashi da yaga hoton ita kuwa Hajiya kacaniyar nemo wayarta takeyi tana maimaita a tura mata zata aikawa su Turai suga surukarsu "Wayar ba caji zan tura miki da safe" ya miƙe, "Ai shikenan Allah ya kaimu, kai zan iya bacci kuwa? Ganin wannan yarinyar ya wankemun haushin shegen Yaron can ma wlh. Kai Allah dai yayi maka Albarka kai kaɗai ko yaushe baka bani kunya kana biye da tsarina yanda ya kamata. Sanda yaje ɗaki ya tarar Ahmad har yayi bacci, tun daya sahalewa kansa waccen mayyar yake bacci sosai da kuwa seya raba dare yana tsammatar kiranta kuma ba zata kira ba. Ya gama abinda zeyi ya kwanta sedai bacci ya gagara zuwar masa. Tunani kala kala suka addabeshi, laifin da Afeeyah ta masa na boye masa tana da wani bayan shi amma a yanzu damuwar Hajiya ta shafe wannan. Ta yaya ze sanar da saɓanin abinda take hasashe kuma irin abinda yasan zata gwammaci jin komai dashi wato ace shi Jafar data ciwa burin duniya kan matar auransa take zakwaɗin zuwan lokaci se kurum taji akasin abinda take buri wato dai a maimakon taji za'a tafi gidan Tayis Ac sama da ƙasa se a shige Lokon Alfindiki gidan laka shi ya tabbatar yar Bakamiken da Yah Ahmad ya kwaso in ba'ayi wasa ba tafi Afeeyah galihu. Wannan al'amarin kacokan yana ganin ishara ce Allah ya gwada musu daga shi har Hajiyar, dukda shi bece ya tsani Talaka ba kuma be taɓa inkarin cewar baze auri ɗiyar Talaka ba ta yuwu izgilancin daya ke yiwa Ahmad ne kan zuciyarsa bata san abinda ya kamata dashi ba duk matan Kano ya rasa wadda ze so se yar Bakanike se gashi ubangiji ya masa talala ya jefashi a komar wadda yake ga nata uban ko Tartibiyar Sana'a bashi da ita. Ya shafa ƙeya jin a garin lissafi ya sake tafka wata ɓaranɓaramar, ya za'ayi kai tsaye ya yanke Babanta bashida sana'a dame yake ciyar dasu sedai in ɓarawo ne ko ɗan Maula irin Babansu Anty Rabi. "Allah na tuba" ya faɗa a fili jin shaiɗan na sake ingizashi izgilancin nasa na neman tsallakawa kan Baban Hajiya Rabi kuma. "Meya faru?" Ahmad da yayi juyi a bacci ya tambayeshi, bashi da nauyin bacci ko yaya akayi magana yanaji. "Zancen zuci ne ya fito fili, sorry na tasheka" Jay ya faɗa yana gyara kwanciya Ahmad ma baccinsa ya koma ya barshi yana cigaba da saƙa da warwara. Yayi tunanin ya ɓoye wa Hajiya Asalin Afeeyah ayi komai a sirrance tunda dai yasan Baba Alƙali baze kware masa baya ba, shima kuma Alhajin ko ya samu labari baze sake Ƙaiƙayin bakin gayawa Hajiyar ba dan silar na Ahmad har yau be gama komawa daidai maganganun da Yayansa suka sossoka masa ba basu gama sakinsa ba to amma kuma hakan bashida Fa'ida, duk yanda akayi daga baya magana seta fasu kuma abinda Hajiyar zatayi ta yuwu seya zarce wanda zatayi idan tasan komai tun daga mafari. Ko bayan wannan ma shi baze yarda ya gina wata mu'amala tasa da ƙarya ko yaudara ba musamman maganar aure, to shi yaya zeyi yanzu? Yana son Afeeyah so me tsanani cewar ya rabu da ita bama abu ne me yuwuwa ba to ya kuma zeyi da mahaifiyarsa da a duniya babu abinda ta tsana irin Talaka da Talauci?? Bacci ɓarawo ne yayi nasarar sace shi da Asuba kuwa ya farka da ciwon kai dan be daɗe da baccin ba Ahmad ya tashe shi Asuba tayi ga tunani daya raba dare yanayi. Be iya dogon zaman lazumin da Ahmad yake tilasta masa yi ba idan yazo gida ya bi lafiyar gado saboda bacci da ciwon da kansa yake masa, lura da kamar baya jin daɗi dan har idanunsa sun nuna hakan yasaka Ahmad be matsa masa ba shidai yaci gaba da jan carbinsa. Tun jiya yake fama da faɗuwar gaba daya rasa ta mecece ga tunanin Fatima daya masa sauƙi kwana biyu ya juyo dan seda yayi dagaske jiya kafin ya iya dakatar da kansa daga kiranta. Tunda Baba Alƙali ya shaida masa Baffah yace su dakata da zuwa daga nan ya sare daga lamarinta ya tabbata ya rasata kenan tun sannan kuma ya tilasta kansa haƙuri da al'amuranta, ko dar beji sonta ya ragu a ransa ba amma ya taushi zuciyarsa ta karɓi ƙaddarar cewa Fatima ba matarsa bace, yana tsaka da jinyar zuciyarsa kuma sabon abu ya fara bijiro masa daga jiya zuwa yau ɗin tamkar ana masa kiranye haka yakejin so me zafi yana Azalzakar zuciyarsa, kasa dakatar da kansa yayi yabi umarnin zuciyarsa ya cire wayarsa dake jikin chaji ya doka mata kira. FATIMA Tana kwance kan abin sallah wand kusan akansa ta kwana, tun bayan da Umma ta gama soka mata maganganu jiya ta shiga ɗaki ta ringa kuka, Allahn daya jarabci zuciyarta da soyayya shi kaɗai yasan halin da take ciki se Baffah da ya tausaya mata yake ƙoƙarin ganin ta samu cikar muradinta badan haka tasa zuciyar taso ba Umma kuwa ta juya zuciyarta baibai taƙi fahimtarta ta yaya zatace ta zare hannunta daga Al'amuranta? Tana fatan ace barazana takeyi mata saboda ta fasa abinda tayi niyya dan in da gaskene ina zata kama tayaya ma koda ace burinta ya cika na zama matar Jay zata samu farin ciki da nutsuwa alhalin Ummanta tana fushi da ita?? Haka ta raba dare tana koke koke daga ƙarshe taci galaba akan shaiɗanin da yake neman nesantata daga neman ɗauki gurin ubangijinta ta fita tayo Alwala ta ringa jera salloli, a baya koda babu yawa takan tashi tayi sallah ta kaiwa Allah kokenta da buƙatunta amma tun da suka fara raba dare suna zuba sharafin soyayya da Jay shaiɗan yayi kinini ya samu abinda yake so. Sanda ya kamata ta tashi tayi sallolin se baccin da batayi da wuri ba da gajiyar data kwasa a yinin su danneta, sallar Asuba ita da take tashin yan ɗakinsu ya zama yanzu ita ake tashi duk free time da take zama ta jaddada kusancinta da mahaliccinta soyayyar Jay ta cinye yau da duniyar ta mata zafi ta ko ina gashi take karɓa dole ta fuskanci mai duka ta kai amsa kukanta. A baya takan yawaita addu'ar neman zaɓin Allah a cikin lamuran rayuwarta gaba ɗaya, yanda Ahmad ya kasa samun matsuguni a zuciyarta duk kuwa da tarin kyawawan halayensa yasa kawai ta yankewa ranta ba Alkhairinta babe shiyasa ubangiji be haɗa zuciyoyinsu guri guda ba, da Jay ya afko mata yanda ya shiga ranta farat ɗaya nan kuma ta yanke shine cikar burin datake jira Allah ya aiko mata. Bata nemi zaɓin Allah ba kawai ta yanke shiɗinne kamar yanda bata nema akan Ahmad ba ta yanke bashi bane. Ance ba'ayin aure salin alin amma kuma bata tsammaci auran da ze saka ta samu tangarɗa da iyayenta ba ze zamo Alkhairi a rayuwarta ta yaya ma haka zata faru?? Umma tace ta zare hannu a al'amarinta ta ina zata ga haske a gidan Jay?? Toh amma idan ta haƙura dashi yaya rayuwarta zata kasance? Ta tabbatar babu ita babu farin ciki a gidan auran da ba Jay bane ze kasance Mamallakinta, shi take So, shi zuciyarta ta aminta dashi amma kuma Albarkar iyayenta nada muhimmanci da tasiri a cikin rayuwar da zata gabatar tare dashi. Ta ringa jera sallah tana kuka wiwi tareda kwashe mintoci masu yawa a sujjadarta tana kaiwa Allah kokenta da neman agajinsa a wannan siraɗi da take kai, seda taji sallar Asuba kafin bacci ya kwasheta bata jima ba cikin baccin ta ringajin ƙarar wayarta data ajiye dabda kanta bayan ta duba lokaci kafin baccin ya kwasheta. Tayi firgigit ta farka, mafarki take wai Jay yazo a fusace ya ɗaga hannu ze kwasa mata mari be kai ga aiwatar da nufinsa ba ta farka tana zare ido, akan me Jay ze mareta a mafarki? Koda yake da fushinta ya tafi jiya ƙila ya huce ne shine ma yake kiranta yanzu da wannan tunanin ta janyo wayar da azama ta duba. Sunana Ahmad ta gani da manyan baƙi suna yawo a kan wayar, ta ringa maimaita sunan a ranta tamkar ranar ta fara ganin kalmar. "Allah ka haskamun abinda yafi zama Alkhairi a rayuwata, Allah karkasa aurena ya zama silar gamuwata da mahaifana" Addu'ar data ringa nanatawa a sujjadarta tana bin bayanta da sunayen Allah tsarkaka tare da cikakken yaƙinin samun biyan buƙata. Ahmad da ta manta rabon da suyi magana a waya dashi tun kafin dawowar Jay kamar tun ranar da Anty Sauda ta tilasta mata kiransa ta bashi haƙuri shine yake kiranta yau da farar safiyar nan? A maimakon ta amsa wayar se kawai ta kifeta ta fashe da kuka kamar wadda aka mara ta ringayi harda shashsheƙa shi kuwa kamar yasan meke faruwa ya ringa kira har seda ta amsa ba tareda ta bar kukan da takeyi ba. AHMAD A gigice ya miƙe tsaye bayan da Fatima ta amsa wayarz kira uku ya mata kafin ta amsa ana huɗun ya raya a ransa bacci takeyi amma kuma abinda yakeji a ransa game da ita yasa ya kasa haƙura da kiran har seda ta amsa. "Lafiya Fatima, meya sameki? Meya faru kike kuka?" Ya jera mata tambayoyi a rikice, daga can gefen ta sake kecewa da kukan daya fi na farko ba tareda ta bashi amsa ba, ya wuce ya buɗe wardrobe inda Jallabiyyunsa suke yake dubawa da alamu ya manta da wata a jikinsa saboda ruɗewa "Dan girman Allah ki faɗamun meya faru? Me yasa kike irin wannan kukan?" Ya sake faɗi yana zaro riga ya shiga kici kicin sakata akan ta jikinsa. "Bani da lafiya, ƙirjina ciwo yakeyi" ta faɗa tana jan numfashi kamar zata shiɗe, yaja salati ya dire kafin ya saki rigar hannunsa ya nufi ƙofa se kuma ya dawo da sauri ya shiga jijjiga Jay da tun fara wayar daya ambaci sunanta ya kasa kunne yana jinsa dan baccin nasa beyi nisa ba. "Meye kuma?" Ya faɗa yana miƙa kamar sannan ya tashi. Ahmad ya latse wayar ya kashe kafin yace masa "Ka tashi muje, Fatima ce bata da lafiya" "Alhamdulillahi Allah yasa ta mutu kowa ya huta" Jay ya faɗa kafin ya juya abinda ya kwanta harda jan Duvet ya rufe har kansa. Ahmad yayi kasaƙe yana kallonsa kafin kuma ya tuna abinda yake gabansa ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi ya fice. Dake safiya ce ko bakwai batayi kuma ana hutun makaranta dan haka babu cinkoso akan titi nan da nan ya isa unguwarsu Fatima. Ko buɗe ɗe ƙofa basuyi ba ko kuma sakayota akayi oho ya niyyata ze buga kenan ya hango Baffah yana tahowa da carbi a hannunsa da alama sannan ya fito daga masallaci. Mamaki bayyane akan fuskarsa yake kallon Ahmad sanda ya durƙusa yana gaisheshi dan daga nesa be gane shi bane ko kuma be kawo ze ganshi a irin lokacin bane yasa be kawo shiɗin bane. "Fatima ce na kirata tana kuka tace mun bata da lafiya" Ahmad ya bawa Baffah daya tambayeshi ko lafiya ySa ganshi yanzu amsa. Baffah yayi shiru kafin ya tura ƙofar yayi ciki yana ce masa "Bismillah" "Aa Baffah ta fito muje Asibiti kawai kar a ɓata lokaci" ya bashi amsa kai a ƙasa. Baffah ya shige ciki ya tarar da Umma a tsakar gida tana yan kaye kayenta. "Ina Afeeyah?" Ya tambayeta, ta nuna masa ɗakin Afeeyar da hannu dan haushinsa takeji seda suka tafka mahawara jiya kafin sukayi bacci. Wai ya bawa Jafar sati biyu ya turo, data tambayeshi yasan shi ne ko yayi bincike a kansa da zece ya turo maganar aure sati biyu se yace mata "Banji a jikina yaron nan ze aureta ba koda yana sonta shiyasa nayi musu haka kinga daga ita harshi babu wanda zece an tauye masa haƙƙi. Yace sunan mahaifinsa Abdullahi Tijjani Ɗan kasuwane kuma a unguwar Hotoro suke zaune zan sanarwa Malam Saminu seya bincika shine me mutane a shiyyar dan binciken Ahmad ma kinga shi yayi" "Lallai Malam, wato bakaji a jikinka auranta zeyi ba? To idan kuma ya ƙaryata jin naka ya turo magabatansa se ayi yaya?" Umman da mamaki ya cikata fal ta faɗa Malam ya sake tamke mata kai daya ce "Ruƙayya, duk wanda yake shine Alkhairi a gareta Allah ya tabbatar mata, Allah yaga zuciyata, idan son rai na ne Ahmad shi ze zama Mijin Mamana amma tace ba haka ba, bazan mata dole ba zan cigaba da bibiyar lamarinta da addu'a Allah ya zaɓar mata wanda yafi Alkhairi a cikinsu". Tsabar yanda ya kasheta da mamaki yasa ta gagara ce masa komai se kallonsa da ta ringayi, wato baze mata dole ba "Ai shikenan" ta faɗi ta maida kai ta kwanta ranta fal da mamakin Malam Hafizu. Da sanin yau ta masa se tace kwaɗayin matsayin sabon yaron da Afeeyar ta kawo ne ya jashi to amma idan Arziƙine a Nigeria dai ai ba'a gayawa Audu Bechi uban Ahmad ba. Ta yuwu makauniyar soyayyar Uba da Ya ce tasa ze zama sullutu ya biyewa Afeeyar ta mayar dashi Ƙaramin mutum. Ta raya a ranta zata saka musu ido shi da yar tasa ne taga gudun ruwansu ba zata sake cewa komai akai ba, da wannan haushin ta kwana shi yasa da safiyar da yake tambayarta ina Afeeyar ta masa nuni da ɗakinta kawai taci gaba da sabgar gabanta. Baffah ya kada baki ya kira Afeeyah dake kwance wurjajan tana kuka jin daɗi, yo jin daɗi mana babu duka babu zagi mutum ya ƙule a ɗaki yana kuka ai se wanda daɗi yaiwa yawa. Ta amsa tana goge hawayenta kafin ta fito tana kare fuskarta da Hijabi. Saboda karma Umma taji abinda ze hasalata yasa ta shigi kitchen ta basu guri, tana jin Malam na tambayar Afeeyah me yake damunta? "Ahmad na tarar a waje yace kunyi waya yanzu kince masa baki da lafiya meya sameki" inji Baffah. Ta kalleshi da mamaki tana maimaita "Ahmad kuma?" A fili yace "Eh shi, ko bakuyi waya ba" "Munyi, amma ai bace masa nayi yazo ba kuma ni lafiya ta Ƙalau" ta faɗa a sanyaye. "Se kije ai ki sallameshi gashi can duk hankalinsa a tashe, wlh yaron nan tausayi yake bani Jarabta a so babban abu ne me wahalar gaske" Malam ya faɗi yana wucewa ɗakinsa Umma data fito da tukunya zata tari ruwa a famfo ta koma kitchen ba tareda ta kalli inda take bama ita kuma Afeeyah tsoron abinda Umman zatace ya hanata tashi daga inda take har seda Malam ya sake mata magana. Ahmad na jingine da ƙofar gidan, daka ganshi kasan yana cikin damuwa duk yayi wani iri yanajin an taɓa ƙofar ya juya da sauri sukayi ido huɗu. Gabanta ya yanke ya faɗi ba tareda wani dalili ba, kai a ƙasa kamar wata farin shigar munafurci ta gaishe shi, "Muje Asibiti Fatima me yake damunki?" Ya faɗa yana matsawa gabanta. Ta girgiza masa kai idonta na tara Ƙwalla tace "Ciwon kai ne daman kuma ya sauka" "Ciwon kan kikewa kuka haka Fatima? kalli fa yanda fuskarki ta koɗe yanayinki ya nuna ba lafiya ba sannan kice ciwon kaine kuma ya sauka" Ahmad ya faɗa yana ƙare mata kallo. "Dagaske nakeyi maka ciwon kaina yana da zafi sosai har nakan gwammace nayi zazzaɓi akanshi" "Kinga kenan kina buƙatar Dr's attention dan haka muje Asibiti kawai" "Dagaske na warke nasa magananin da aka bani akan duk sanda ya motsa mun nasha Migraine ne" ta sake faɗa cikin tabbatarwa. Se tayi murmushi kallonta yace "Kodai biko na kikeyi shine kika fake da ciwo saboda ki tasoni ko ban shirya ba?" Tamkar tace masa tayi bikonsa a saboda me se kuma tayi shiru tana wasa da yatsunta murmushi ya kwafsa mata ta hanyar sakin kansa ba tareda ta shiryawa hakan ba. Ahmad yayi murmushi yana gyara tsayuwarsa yace "Duk sanda nafara fitar da rai da tsammanin samunki se Allahya kawo silar da zata sake maido ni rayuwarki bakya ganin hakan bayinmu bane yin Allah ne? Ta yuwu akwai wani tanadi da yayi mana amma zukatanmu na nesan tamu da riskar wannan tanadin akan lokaci?" Bata ce komai ba be kuma damu da hakan ba yaci gaba da cewa "A yanzu na rigada na buɗe zuciyata, na sallamawa Ubangiji komai dukda dama a kullum cikin miƙa lamurana a gareshi nake. Tunda kince lafiyarki Ƙalau bari naje gida, se wani lokaci" be jira komai ba ya wuce ya barta a tsaye. Jiki ba laka ta koma ciki ta dasa jiran tsammanin samun kiran Jay amma har Azahar shiru babu shi babu labari. Ahmad kuwa bayan ya koma gida ya tarar da Jay na shiri daya tambayeshi ina zeje yace masa Kaduna daga can ze wuce Abuja gidan Hajiya Ƙarama. A taƙaice yayi masa bayanin da Hajiya ta masa jiya, Ahmad ya jinjina Al'amari, Allah kenan me mutane iri iri. A haifi mutum amma tsabar shahara yace shi baze haifi wasu ba to Allah ya rufa asiri. Be ce ze bishi ba kamar yanda shima be nemi rakiyarsa ba za'a iya cewa wannan shine karo na farko da hakan ta faru ace Jay zashi wani guri ba taredaya nemi rakiyar Ahmad ba. Tareda Manager shi suka tafi shi kuma Ahmad bayan ya shiga gida sun gaisa da Momy da sauran mutane ya tafi Shago duk yanajin babu daɗi. Tabbas akwai abinda yake damun Jafar, amma menene wannan da har ya gagara tattauna matsalarsa dashi? Jiyayaje gidansu wacce yake so basu samu sunyi magana ba balle yaji yaya sukayi tunda kafin ya shigo shi yayi bacci da safe kuma ya fita to kodai shima ya samu matsala irin tasa ance ya dakata ko kuma ma dai iyayenta sun rigada sun mata Miji? Tunanin da Ahmad ya ringayi kenan yana zaune a office ɗinsa. Ya ɗauki wayarsa ze kira Jafar sega kiran Fatima ya sake shigowa wayarsa. Mamaki kamar yayi me, Fatima dai yau meya sameta haka acw a rana da kanta ta kirashi har sau biyu wannan abu kamar Almara. Be sake rushewa da mamaki ba seda ya amsa bayan sun gaisa take tambayar ya yaje gida sannan ta bashi haƙurin tayar masa da hankali da kuma fito dashi da sassafe daga nan sukayi sallama dan ya gagara sakin jiki yayi mata wata Ƙwaƙwarar magana. Allah sarki zuciya da abinda take so, ɗan wannan kiran yasa duk ya rikice ya cigaba da ɗora lissafin gobensa da Fatima, daya tashi daga Shagon daƙyar ya kanne ya wuce gida dan zuciyarsa nata uzzura masa da ya sake zuwa ya ganta ya kumayi mugun Ƙoƙari da be kirata ba. A daren Jay ya dawo, se yaga kamar sanda ya tafi yafi nutsuwa da kwanciyar hankali akan dawowarsa duk ya wani birkice kuma bece masa komai ba still shima ya kama bakinsa be tambayeshi ba. A ɓangaren Afeeyah kuwa abu kamar almara haka aka wuni sur tun tana zaton Jay ze kirata harta fitar da rai ta shiga lalube da lissafin yanda rayuwarta zata kasance idan har da gaske Jay ya barta. Ta kirashi sau biyu wayar ta Ƙaraci ringing ba'a amsa ba kuma be biyo baya ba har dare, A ɗaki ta wuni, sunyi Chat da Badar bata ɓoye mata komai ba akan zuwan Jay na jiya, yanda sukayi da kuman zuwan Ahmad da safe harma da Stand ɗin Umma akansu biyu "Allah na sonki Afeeyah, karki bari ki rasa damar da kike da ita a hannu wlh ba zaki maimaira kamarta ba. Bakoda yaushe abinda muke so a rayuwarmu yake zama Alkhairi ba haka kuma ba duk abinda muke ƙi ne yakan zama sharri tare damu ba. Kiyiwa kanki karatun ta nutsu ki kalli gidajen aurayen da suke a zagaye dake wanda akayisu cikin daɗin rai da sahalewar uwa da uba amma ba'a rabasu da ƙalubale da matsaloli inaga wanda akayi kan doron fushin iyaye? Yanzu ke zaki iya zaman aure da Mijin da mahaifiyarki ta nuna bata sonsa? Bana tsammatar zaki samu cikakkiyar nutsuwa balle kwanciyar hankali nidai irina wlh ko Yan gidanmu ne suka nuna basa son mutum muddin suna da hujja me Ƙarfi zan haƙura dashi saboda su dai dasu zan tattauna duk wata matsala da ka iya tasowa idan babu goyon bayansu ina zan kai kukana? Kina gani dai kina zaune Allah ya sake turo miki Ahmad a lokacin da abinda kike ƙulafuci yake ƙoƙar bari hannunki, idan kika sake kikayi wasa da damarki tana iya zama ta ƙarshe dan haka kiyi tunani kuma ki tattaro ki dawo School ki fuskanci karatunki semester ƙarshe muke karki bari kiyiwa kanki sawarwarar da zaki samu matsala a wannan lokacin tun wuri ki saki komai ki sake kama Allah ki kuma bar komi a hannunsa" abinda Badar ta gaya mata kenan da har yasa ta samu ƙwarin guiwar sake kiran Ahmad. Jay be kirata ba se washe gari, idan kaga yanda ta fita a hayyacinta seka zata ciwo takeyi kwana guda kawai amma ji take kamar ta shekara ba taredashi ba faɗar irin zafin da takeji a zuciyarta kuwa ɓata lokaci ne, ashe haka Ahmad yake ji akanta shima? Tabbas So abune me ciwo da wahalarwa ta yarda yanzu da ta afka masa kuma ta dena ganin baiken masu zaucewa a soyayya domin ita kanta a yini ɗayan nan da takejin kamar tayi bankwana da farin cikin rayuwarta badan tsoron abinda ze je yazo ba ware baki zatayi tayita kwarara ihu a ɗaki harse nauyin da zuciyarta tayi mata ya ragu amma bata isa ba Umma zataci mata uwa da uba ne tabbas a gidan shiyasa sedai ta lafe a ɗaki tayi kuka ta share hawayenta. Tana tsaka da shirya kayanta dan ta himmatu gobe zata koma makaranta kafin baƙin ciki yayi Ajalinta a gidan babu jimawa sun gama magana da Ahmad dukda ba qata magana me tsayi bace ba shiya kirata yaji ya take idan babu damuwa zezo Anjima da anyi Magrib tace masa Toh shikenan sukayi sallama. Tana zuge akwati wayarta tayi ƙara ta zabura jin Ringing tune data sakawa Jay ne. A tare suka sauke ajiyar zuciya bayan data amsa wayar kafin ya kira sunanta a sanyaye bata amsa ba se kawai ta sakar masa siririn kuka daya saka ya miƙe tsaye daga kwancen da yake babu shiri "Kuka kuma? So kike ki ƙaramun damuwa akan wadda nake ciki?" Ya faɗi cikin yanayin daya saka Ahmad dake cin abinci kallonsa. Basu jima da dawowa daga gidan Baba Alƙali ba koda yake Jafar ya ɗakko acan besan ma yaje ba seda ya kirashi yace ya biya dan Alkah su taho tare suna shigowa kuma ya wuce gurin Momy ya karɓo abinci shi Jafar yace Azumi yakeyi seda suka gama magana da Fatima kafin ya fara cin abincin. "To ba kaine ba tun da ka tafi baka waiwayeni ba" ta faɗa cikin kuka. Seya koma ya zauna yana cewa "Kinyi mun laifi, baki kirani kin bani haƙuri ba and you are expecting me to call you kenan baki san girman lafin da kika aikata ba ko?" "Na kiraka jiya sau biyu baka amsa ba" ta bashi amsa tana tsagaita kukanta se yace "Jiya, wato baki damu ba na tafi cikin fushi, baki kirani tun a darenba se jiya shima da rana saboda kin lura ina sonki" "Wlh ba haka bane ba, kai kace na cire layina daga waya na cire se da safe na samu Ƙarama na saka layin a ciki" ta sharfaɗo Ƙaryar da ita kanta se bayan ta dire maganar kunyar kanta ta dabaibayeta. "Kinci darajar Son da nake miki shiyasa na kasa daurewa amma da wlh nayi niyyar bazan sake kiranki ba har se bayan anzo an tambayan mun auranki but i couldn't, my heart is going crazy about you ji nakeyi kamar nayi hauka just a day banji muryaki ba". Ina ruwa Afeeyah ta buga tsalle ta faɗa dajin ba haƙura Jay yayi da ita ba kuma ba fasa auranta yayi ba ashe punishing nata yakeyi da Ƙin kiranta aiko ta ladabtu. "Kayi haƙuri" ta faɗa cikin wata lallausar murya, Jay ya saki murmushi yace "Zan haƙura but let me see ur face first, oh na manta kin cire Sim daga wancan wayan ko? Then zanzo anjima zan taho miki da wani wayan amma ba fa jimawa zanyi ba dan ban gama hucewa ba, zan baki waya ne kawai na tafi" Cike da zumuɗi kamar zata taka rawa tace "Allah ya kawo ka lafiya" "Aiit, take care I love you" ya faɗa, ta mayar masa da "I love you more and i miss you" daga nan suka aje waya. Ya kalli Ahmad dake cin abinci yace "Yau zamuje gurin Afeeyah" "Wacece haka?" Ahmad ya tambaya, Jafar ya ɓata fuska yace "Soyayyata" "Soyayyarka da kake mun boye boye akanta ko? Aje lafiya nima yau gurin Babyta zanje mun shirya". "Kayi haƙuri, i promise you idan muka dawo zan gaya maka komai ba abinda kake tunani bane" "Bana so kuma ba zanje ba na gaya maka gurin Babyta zanje nima" Ahmad ya faɗa shima yana kumbura fuska kamar gaske Jafar yace "How about ka rakani nima na rakaka? Amma gurin Soyayyata za'a fara zuwa" "Then if you mean ita muje amma gurin Fatima zamu fara zuwa nine babba kaga matata tana gaba da taka kuma nasan wayo kake so kayi mu fara zuwa naka daga nan ka zame ka barni" inji Ahmad. Jay ya yamutsa fuska, kamar yasan abinda ya niyyata zeyi kenan, bashida zaɓi tunda yana so Yah Ahmad ya rakashi gurin Afeeyah dole ya yarda da tsarinsa koda yake gara ma yaje face to face ya zazzagewa Wannan Fatiman abubuwan da suke a ransa, wato ta mayar da Ahmad kamar wani Toy tayi wasa dashi sanda taso ta yar sanda taso to yau kuwa ze buɗe mata aiki. Suka shirya bayan da akayi sallar magriba suka kama hanya. Jay ne yake tuƙi, suna fita Ahmad ya kira Fatima danya shaida mata bashi kaɗai bane kuma sun taho. Ita shaf ta manta ma da zuwan Ahmad tunda Jay yace mata zezo ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta zabari mayafi ta tafi kusadasu aka mata baƙin lalle ranar daya fara zuwa yace mata yana so da yake da wuta nan da nan ta wanke kanta ta busar da Dryer ta tayi styling nasa da adon da ze bayyana sanna ta turara kayan da zata saka Two piece Gown and V Hijab data siya a gurin Ummu-Maheer (07061838488), yadi ne me sauƙin kuɗi amma kyakykyawan ɗinkin daya samu yasa idan ta sakasu ake ɗauka tafiyayyen ne daga Egypt haka Hijabanta. Umma nata kallon ikon Allah amma bata ce mata komai ba tasan sunyi waya da Ahmad amma bata zaton zuwansa takewa wannan shirin haka. Tana ganin kiran Ahmad ta tuna da batun zuwansa, ta yi kasaƙe tana tunanin mafita dan Jay ma yace mata yana hanya dukda dai yace ze biya wani guri tukunna. Da sauri ta shiga kiran layin Ahmad bayan data shirya Ƙaryar da zata masa da zata dakatar da zuwansa amma wayar taƙi shiga. Har wani tsirgawa cikinta ya ringayi saboda tashin hankali, ya zatayi idan Jay yazo ya tarar da Ahmad???? PAGE 22 JAY Suna tafe a mota suna hira gwanin sha'awa irin wadda suka sabayi da alamu yardar zeje gurin Fatima tareda Ahmad ta faranta ran Ahmad ɗin matuƙa dan gashi nan a bayyane. Sun hau kan Gadar ƙofar Nasarawa ya tambayi Ahmad ina zasuyi. "Miƙewa zakayi Mandawari zamuje" Ahmad ya bashi amsa. Ya taka mota yana cewa "Ai bansan gurin ba" "Muje masallacin sarki idan mukayi sallar isha se na karɓi tuƙin" Ahmad ya sake bashi amsa. Jay yayi shiru kamar yacewa Ahmad ai nan ne unguwar su Afeeyah se kuma ya ƙyale. Haka kawai yaki jikinsa ya masa wani iri, gudu yake da mota amma se gashi ya rage speed sosai ya koma tafiya a hankali har suka isa Masallacin, yanajin sanda sukayi waya da Fatiman yaja tsaki bayan da Ahmad yake ce masa wai gidan Yayarta zata tafi "Kabarta ta tafi kawai se muje gurin my Afee, naga ta kirani ma bana so na amsa kewarta yasa na gudu na barka kace ban kyauta ba" "Su tsuntsun soyayya, yau dai zanga wannan Afeeyah naga da wane charm ta sace zuciyarka" Ahmad ya faɗa yana dariya. Be manta hanyar daya bi har zuwa bakin titin da ya jira Malam yazo ya tafi dashi ba wannan tasa mamaki ya kamashi sanda yaga bayan sun isa Mandawari Ahmad ya karkata ya shiga titin unguwar su Afeeyah, kasa haƙuri yayi har seda yace masa "Wai nan ne unguwar su Fatiman?" "Nan ne, ko kana zaton wata GRA zamuje? To a nan lungun tawa Babyn data sace zuciyata take kuma wlh karka kuskura muje kace zakayi mata izgilanci domin dai ka sani Arziƙi da Talauci duk na Allah ne kuma a aure Tarbiyyar mace ake dubawa bawai girman gidan data fito ba". Sam bama sauraron Ahmad yake ba illah baza idanu da yayi dakyau yana so ya gane layin da suka shiga da Malam. Akwai wani gida me rumfar langa langa doguwa a daidai kan layin mutane suna zama gurin ya zama kamar masallaci ma dan har butuci ya gani da drum na ruwa a gurin ranar daya zo wannan ya riƙe a ransa matsayin alamar daze ringa gane mashigar lokon nasu dukda idan ya shiga ciki babu tabbacin ya kai kansa saboda zurfin gurin. Zuciyarsa ta buga Dumm sanda Ahmad yayi parking a daidai spot ɗin daya haddace a ransa. Ya ringa kallonsa sanda yake ce masa "Da yar tafiya daga nan zadai ka iya ko?" Se ya ƙaƙalo murmushin dole yace "Nida nake zagaye field sau babu adadi kake cewa zan iya wani ɗan trecking kaɗan". Ya fita yanajin wani sanyi na raysa gaɓɓansa dukda cewar zafi akeyi, ya ringa kallon gurin kamar meson yaga ya canza masa daga abinda zuciyarsa take hasaso ma, suka tsallaka yana biye da Ahmad a baya suka shiga cikin lokon "Ba lallai abinda kake hasashe ya zama gaskiya ba, Ƙaddarah bazatayi muku haka ba, baza ta saka ku Son abu ɗaya wanda baze yuwu ku mallakeshi a tare ba" zuciyarsa ta ringa Ƙarfafa masa guiwa. Ahmad dake masa hira jin baya amsawa ya saka shi kama bakinsa suka ci gaba da tafiya. Jay da yake tunanin idan ya dawo baze iya sake maida kansa gidansu Afeeyah ba se gashi taswirar Lokon na zuwar masa kamar zane a Ƙwaƙwalwarsa, bugun zuciyarsa ya tsananta sanda yaga dagaske sun tasarma layin da gidan Malam Hafizu mahaifin Afeeyah yake ciki, akan kwana yaci burki Ahmad ya kalleshi yace "Ya akayi naga ka tsaya" "Nasan Afeeyah tana can tana jirana, so nakeyi na kirata na gaya mata zanyi latti kartaji shiru kayi gaba zan biyo ka" ya rattabo masa ƙaryar da yake ganin ita zata fitar dashi. Ahmad yace "Ga gidan can ai mu ƙarasa seka kirata ko sarki me Afeeyah" ba tareda ya kalli gidan daya nuna masa ba ya shiga shafa Aljihunsa yana laluben waya amma be jita ba ya saki ajiyar zuciya kafin yace masa "Wayar na mota" Dan Allah muje Jafar na sani daman se munyi haka dakai kuma tunda muka zo nan dai ya kamata ka daure kawai mu ƙarasa yau ɗaya kaga Fatima na tabbatar duk wani grudges dake tsakaninku yau zaku warware shi muje please". "Wannen ne gidan?" Jafar ya tambayeshi a ransa yana fatan ya nuna lungun daya miƙe yace a ciki gidansu Fatiman yake, kai shi da zata yuwu ma Ahmad yace makuwa yayi ba nan unguwar zasu zo ba saboda abubuwan da zuciyarsa take raya masa sunyi muni da yawa baya fatan ace hakan kuma ta zama gaskiya "Wancan me Ash paint da baƙar Ƙofa daidai inda Solar take" Ahmad ya sake nuna masa gidan da kwatancen da duk yanda yaso da kautar da gaskiya dole ya shige shi. Ya zurawa gidan ido kamar me son gano inda aka haƙo Ƙasar da akayi ginin gidan da ita. Ahmad ya cigaba da tafiya yana ce masa "Muje mana" "Zan zo Yah Ahmad Allah bana son rigimar Afeeyah kaga ban gaya mata zan biya wani guri ba kuma na bar wayana a mota kar tayita kira taji shiru kaja mun tayi fushi" ya sake faɗi, yanda yayi maganar da ace Ahmad ya mayar da hankali ze fahimci akwai abinda yake dannewa. Ahmad ya girgiza kai yace "Shikenan, amma wlh idan baka dawo ba Allah ka shirya tarbar rashin mutunchin da zanyi maka" Ahnad ya sake faɗa yana jefa masa key ɗin mota seya cafe yana murmushin da gara ace kuka ya fasa dashi kafin ya juya yana cewa "Zan dawo". Wucewa Ahmad yayi abinsa ya tsaya a Ƙofar gidan kafin ya rangaɗawa Fatima kira a waya, Jay kuwa baya yayi amma be tafi ba, so yakeyi ya tabbatar da gaske wancan gidan Yah Ahmad yake nufi sannan yana so yaga wacece. Fatima a gidan. Indai baya samu makuwar tunani ba wannan shine gidan daya zo shekaran jiya waccen gurin Afeeyah. Irin kallon daya yiwa gidan yasa ko a mafarki baya zaton ze kasa tantance shi balle a zahiri sedai idan kuma gizo idanuwansa sukeyi masa. Bayan fitilar Solar dake kafe a Ƙofar fidan wadda haskenta har tsakar gida yake haska musu da akwai wutar nepa dan haka gurin tarwai yake ta yanda ko abun mutum ne ya faɗi ze iya ganinsa. Yana jingine jikin katangar daya lafe dan bazeyi gigin tsayuwa akan Ƙafafuwansa kaɗai ba, yaga sanda Ahmad ya saka waya a kunne da alamu ita ya kira kafin ya ajiye mintinu kamar huɗu tsakani ƙofar dake rufe ta buɗe cikin Ƙasa da sakanni biyar Fatima ta bayyana. Tarwai yake hango fuskarta daga inda yake tsaye wadda yake ganin zanen fuskar Afeeyarsa akanta. Irin Doguwar riga Omo blue da farin V hijab da Afeeyah ta tura masa da hotonsu ɗazun a matsayin kayan da zata masa kwalliya dasu ne a jikinta. Daga inda yake tsaya yana iya hango fuskarta da take kicin kicin babu ko ɗigon fara'a inda ta Ahmad ke washe kamar yaron daya tsinci haƙorin makkah. Bazece ga lokacin daya ɗauka a gurin ba haka kuma baze iya wassafa tunanin da uake zarya a zuciyarsa ba Ƙafafunsa da sukayi sanyi har suka kusan kayar dashi a ƙasane suka ankarar dashi buƙatar ya bar gurin da yake. Tafiya kawai yakeyi bisa jagorancin Ƙafafuwansa ba tareda linzamin idanu ko zuciyarsa ba har Allah ya fitar dashi bakin titin lafiya. Yayi diri diri domin besan ina ze dosa ba. Daga cikin barandar da mutanen nan ke zaune ya hango wasu mutum biyu sun haɗa sahu suna sallah da alama makararrune, shidai baze ce ga yanda akayi ba ya tsinci kansa tsakiyarsu bayan daya saɓule takalmansa, mutanen sukayi raka'a biyu suka sallame Jay ya miƙe ya cigaba da sallah. Tun suna tsammanin ze sallame bayan rama raka'a biyu da be samu tare dasu ba a zatonsu sallar isha'i ce se gashi suna lissafa masa raka'a takwas a jere, ya tashi ze kai ta tara wani dattijo ya riƙe shi yana cewa "Bawan Allah wace irin sallah ce wannan raka'a goma fa kayi tahiya ɗaya, ai ko sallar Asham ce ba haka akeyinta ba". Be ja ba ya sallame sallar be kuma tanka mutumin ba ya miƙe ya kwashi takalmansa a hannu ya tsallake titi ya tsaya ganin motar Ahmad ya saka ya tuna a mota suka zo harga muƙullin ma a aljihunsa seya zaro shi ya buɗe ya shiga mutanen nan dai suka bishi da idanunu baki harma da hanci wasu na cewa "Da alamu kan ba ƙalau ba". Wani yace "Gaskiya babu alamar hauka a tattare dashi idan dai aka ce damuwace ko firgici ya sakashi aikata hakan bazan musa ba" "Shiko har wace kalar damuwa ko firgici ze sakashi jera raka'a goma har yana shirin ɗorawa ba dan an riƙe shi ba? Wai ba tare suke da yaron nan me zuwa gurin yar gidan Malam Hafizu ba? Su suka tsaya a waccen motar tare kuma suka tsallako yauwa ka gani ma gashi nan ya shiga motar ta yuwu wlh kara zube yake ba ilimin muhammadiyya kasan fa yayan masu kuɗin nan se a hankali da yawansu sallah kawai sukeyi amma basu san me suke yi ba" wani zgudujƙuri ya koro jawabin, oho Jay dai tuni ya bawa mota wuta yai reverse ya fice daga titin ba tare da sanin ina zashi ba. A can ƙofar gidan Malam Hafizu kuwa bayan fitowar Fatima Ahmad ya kalleta cikin shauƙin So, Allah ne ya jarabce shi da ita dan haka masu ganin baikensa su dena. Fuska a washe kamar kullum yana kallonta bayan daya amsa gaisuwar data masa a daƙile kamar an mata dole yace "Kinyi kyau" tace "Uhm" tana wani sake tamke fuska shiko be dameshi ba, ya daɗe da sakawa a ransa Fatima tana cikin jerin mutane marasa yawan fara'a shiyasa haɗe fuskarta ya dena bashi haushi. Ya gyara tsayuwarsa yana ce mata "Yasu Baffah da Umma?" "Lafiya lau suke" ta bashi gajeriyar amaa tana duba wayarta, ya sake mata murmushi yana jingina da bango yace "Da Sabuwar Fatiman nayi magana a waya kwanakin nan, ina ta zumuɗin nazo na tarar da ita se kuma naci sa'ar samun tsohuwar Sarauniya Fatima na nan tana cigaba da zuba mulkinta". Tayi murmushin nan me kama da taɓe baki bata dai ce komai ba shi kuwa yace "Tare muke da Jafar yau dai abokanan faɗa zasu ga junansu". Da sauri ta kalleshi jin sunan daya ambata tace "Ashe ya dawo kenan?" "Gobe satinsa ɗaya da dawowa shima soyayyarsa ce ta azalzaloshi ya taho yanda kuma suke buga wasan da zafi ina tsoron karfa suyi mana over taking" ya bata amsa yana kallon fuskarta kamar yanda itama take kallonsa, ta wani yamutsa baki kafin tace "Allah sarki" "Dan Allah idan yazo kar kiyi abinda ze sa ku raba hali, gaisawa kawai zakuyi ku maida komai daya wuce ba komai ba already na masa magana nasan shidai baze fara takalarki ba" Ahmad ya faɗa cikin sigar lallashi. Ta harareshi a fakaice kafin tace "Wato nice ma zan takale shi na janyo abinda zamu raba hali? Kuma da zaka ce abinda ya wuce ya wuce harda zagin mun uba kana zaton yaci banza kenan? Ni bazan iya pretending naso mutumin daya rigada ya furta da bakinsa baya Ƙaunata ba kaima kawai neman tada zaune tsayene ya saka ka taho dashi, ni wlh dana san shine baƙon da kake nufin zaku zo tare bazan ma jiraka ba tafiyata zanyi dan inada abu me muhimmanci a gabana na aje na zauna jiranka" ta Ƙarasa tana sakin ƙaramin tsaki. Ƙarara fuskarsa ta nuna rashin jin abinda abinda ta faɗa ta gani kuma amma ta ɗauke kai tana cigaba da duba Keypad wayar hannunta tana kallon lokaci kafin ta sake duban hanyar tahowa a ranta tana addu'ar Allah yasa ma yaji haushi ya tafi kafin ya dama mata salalan tsiya. Ahmad kuwa haka ya haɗiye abinda ya taso masa cikin sanyi ya kalli wayar da take ta juyawa a hannunta yace "Meya samu wayarki na ganki da wannan?" "Babu komai chaji ne babu na cire Sim ɗin" ta bashi amsa ba tareda ta kalle shi ba seya zaro wayarsa daga aljihu ya nuna mata yana cewa "Ya kamata ma a canza ta tunda anyi lunching sabuwa tuntuni, IPhone ɗin kike so ko kina son Samsung irin wannan last week nima na canzata?" "Waccen ma ta isheni na gode base ka wahalar da kanka ba" ta bashi amsa cikin yanayin irin kamar ya dameta, ya maida wayarsa yana cewa "Wahala kike kira akan abinda ya shafeki? Idan ban hidimta miki ba neman da nakeyi bashi da amfani kenan. Nifa a rayuwata inajin daɗi kawai na kyautatawa mutum koda baze gode mun ba" Lafazinsa na ƙarshe se taji kamar magana ya faɗa mata ta sake cukulewa bata ce komai ba. Ya waiwaya ya kalli hanya kafin ya ciro wayarsa ya shiga kiran Jay ganin kusan minti nawa shiru babu shi babu labarinsa. A lokacin Jay nata sharara gudu a titi beji kiran ba, sau biyu ya kirashi be amsa ba ya haƙura ya kalleta ganin tana dafe kai ya saka cikin kulawa yace mata "Ya dai, meya faru kike riƙe kai?" "Ciwo yakeyi mun yanzu ina tsayen nan naji ya sara" ta bashi amsa tana yatsina kamar gaske nan nan kuwa yace "Ciwo kuma har yanzu be dena ba amma kika cemun kin warke kin sha magani?" "Nasha kuma ya dena yanzu ne kawai ya dawo kodan na daɗe a tsaye ne ban sani ba" ta faɗa tana wani sake riƙe kan da hannu biyu. Burinta ya cika dan kuwa sannu ya shiga jero mata yana cewa ko zasuje Asibiti, tace "Nafa gaya maka an bani magani daman Dr yace na dena yawan tsayuwa da shiga haske sosai su suke tayar mun da ciwon". Ya kalleta kamar me tantamar abinda ta faɗa amma yace "Shikenan ki shiga ciki, bari na sake trying number Jafar idan yazo se ki leƙo ku gaisa ko yayane dan Allah kinga babu daɗi ace yazo kuma baku haɗu ba" "Tam" ta bashi amsa tana ƙoƙarin juyawa ciki Baffa ya iso gurin, yanda kasan wanda yaga wani da suke wasa ɓuya haka ya sauke ido ƙasa ya kasa kallon Ahmad shi kuma cikin girmamaqar daya saba yi masa ya durƙusa ya shiga gaishe shi ya wuce ciki ya barsu a tsaye. "Kinga yau kuma Baffah surukuta yakeyi dani daga fara maganar auranmu dukda ma yace a bashi sati huɗu zeyi musu magana" Ahmad ya faɗa bayan da Baffah ya shige ciki, batace masa kamai ba se dafe dafenkai da yamutsar data cigaba da yi hakan ya tuna masa da ciwon da tace yana mata yace ta shiga gida ta wuce har sannan dafe da kai yana binta da sannu. Seda ta shige kafin ya sake ciro waya ya shiga kiran Jay a sannan kuma aka ce masa Call waiting tana dab da tsinkewa ya ɗaga muryarsa tamkar wanda yake maye ko cikin wani shauƙi yace "I'm sorry Yah Ahmad kuka ta saka mun ni kuma banma san yanda akayi ba kawai na ganni a ƙofar gidansu". Ahmad ya buɗe baki kamar yana gabansa yace "Tafiya kayi, kuma kake cemun baka san yanda akayi ka ganka a gidansu ba ko saboda ka raina wayo ai shikenan ita kuma motar tana ina toh?" "I'm coming back to pick you" Jay ya sake faɗa da muryar da tafi ta farko zama wata iri, Ahmad yace "Zan hau Napep, and abinda zance maka kaji tsoron Allah kabar koma menene kake aikatawa a inda kake" "Thanks" Jay ya amsa shi kafin ya katse wayar ya bar Ahmad da waya a kunne cikin mamaki. Wato saurin da yakeyi kenan so yake yaje ya taɓa yar mutane, kenan Jafar be bar halayyarsa ba har akan macen da yake iƙirarin yana so ze aureta seya gwada mummunar ɗabi'arsa kenan? Tunanin daya ringa masa yawo akai. Ya aje wayar cikin rashin jin daɗin abin ga ciwon kan daya tasowa Fatima a gefe duk suka dagula masa lissafi suka kore farin cikin daya ke ciki a daren. Titi ya fita ya tare Adaidaita da ze kaishi gida, da ace yasan gidan su Budurwar Jafar ɗin can zeje da ace kuma ya san abinda zeje aikatawa kenan da be barshi ya tafi shi kaɗai ba, dole ma ya kaiwa Baba Alƙali ƙarar Jay akan ire iren abubuwan nan da yake aikatawa, idan aure yake so yayi kawai Ƙila ya shiga hankalinsa ya dena wannan shirmen. A ɓangaren Jay kuwa tafiya ya ringayi a motar ba tareda yasan inda ya nufa ba, seda yayi tafiya me nisa ya bi titin bypass kamar me shirin tafiya Bechi a daren seda ya wuce guraren cunkoson mutane kafin ya samu gefen titi ya gangara ya tsaya ba tareda ya kashe motar ba yayi parking kawai ya kwantar da kansa akan steery. Ya kasa relating abu, Fatiman Yah Ahmad itace Afeeyarsa, Afeeyarsa ita ce Fatiman Yah Ahmad a garin yaya? Ya akayi haka ta faru? Tunani ya shigayi na haɗuwarsa da Afeeyah har zuwa yau, babu wata kafa ko siga da zata saka ya zargi wani abu akanta, babu abinda be sani akanta ba amma koda wasa zuciyarsa bata taɓa kwatanta cewar zata iya zama ita ce Fatiman Yah Ahmad ba, abinda yake so ya fahimta yanzu shin Coincidence ne ko kuma Set up plan? Arashine ko ita ta shirya komai ta haɗa soyayyarsa data Ɗan uwansa mafi soyuwa a gareshi guri ɗaya? Idan shiri ne menene ribarta akanyin haka? Me suka mata data zaɓi hukunta zukatansu da hukunci mafi muni irin wannan? Yana buƙatar sanin amsar waɗannan tambayoyin kafin sanin abin da zeyi a gaba. Wani abu yakeji a zuciyarsa, ya zarce ya ce zafi yakeji ko ciwo koma menene besan me ze kirashi ba. Ta yaya za'ayi suyi tarayya cikin Son abu ɗaya shida Yah Ahmad? Tilas wannan ya kasan ce shiri dukda ya sani Allah babu yanda baya sanya Al'amura su kasance amma yana da yaƙinin ubangiji baze tagayyara zumunchin da yake tsakaninsa da Yah Ahmad. Ya saka hannun akan fuskarsa yana goge danshin dayaji yana bin kuncinsa, shi kansa yayi mamakin kansa Hawaye ne wanda fitarsa ke cakuɗe da dalilai da yawa, Allah ya sani be taɓa jin son wata Mace a duniya irin yanda yakeji akan yarinyar nan ba, zuwansa Kaduna gurin Anty Ummu Yayar Hajiya Binta yaje saboda a kaf dangin mahaifiyarsa ita kaɗaice yake da tabbacin zata iya tarar gaban Hajiyar ta feɗe mata gaskiya komai ɗacinta kuma itace yake da yaƙinin zata bashi goyon baya akan auran Afeeyah. Hajiya Ummu ta goyi bayansa dukda ta jinjina Al'amarin domin burin Hajiya sananne ne ga kowa akan sa. Kowa yasan tanadin da take dashi akan Matar auransa. Ita kanta Hajiya Ummun yarta Samiha ta soshi kuma da ace yana da ra'ayin auran Zumunchi daya auri Samiha kodan Anty Ummun amma haka Hajiya ta shafawa idonta kwalli ta manta cewar Ummu ce ta saki Nono ta kama a gaban kowa tace me uban Samiha yake dashi da zata haɗa surukuta da yarsa? Abinda Anty Ummu ta fara masa bayan daya mata bayanin komai tace "Allah ne ya kama Binta, burin data ci akanka baze zamo gaskiya ba, kanaji ko Jafar idan har kana son wannan yarinyar kar kaji komai kar kuma wani abu ya baka tsoro ka tafi kanka tsaye ka nemi auranta. Karka bi takan Binta ko Mahaifinku domin bakin ganga ne se yanda ta kaɗashi ka tafi kai tsaye ka samu Alƙali nasan in sha Allahu zeyiwa duk wata ɓaraka da ka iya tasowa togaciya tunda wuri, kuskuren da Ahmad yayi kenan amma tunda Alƙali ya karɓi maganar wa ka sake jin yace wani abu akai?" "Amma Mama Ina tsoron Abinda Hajiya zata yi idan taji maganar nan daga baya shiyasa nake tunanin ki fara sanar mata a lallaɓata harta amince da kanta sannan" Jay ya faɗa, Hajiya Ummu tace "Jafar kenan, shawara dai kake nema a gurin kuma na baka, wlh tallahi badai Bintar dana sani ce zata amince da maganar nan da kazo da ita ba, tunda dai ba abune daya saɓawa shari'a kake shirin aikatawa ba magana ce ta aure, idan kuma daman ba son yarinyar kakeyi ba to kaitsaye ka janye kawai karma ka janyo wani abin kace nace ka jawowa yarinya suna zaune lafiya da iyayenta Jarabar Binta ta dirar musu, kaje ka samu Alƙali shi ze san duk ta yanda ze biyowa abun" Abinda Hajiya Ummu ta gaya masa kenan, Daya sake nuna mata hoton Afeeyah data buƙata bayan ta gani tace masa "Niko kamar nasan fuskar nan a wani guri" a lokacin yace mata "Nafa tura miki hotonta kwanaki can Mama" ya faɗa seta jijjiga kai tace "Tabbas na tuna, gata tabarakalla, Allah yasa yanda take da kyaun fuska haka zuciyarta take" nana suka Ƙarƙare daita bayan ta sake jaddada masa yaje ya samu Baba Alƙali kaitsaye kar yabi ta kan Hajiyarsu, daga can ya wuce Abuja gidan Hafsatu kashe tata wutar, maganganun data zayyana masa na kalar zaman da takeyi da Abban se yaji ashe ko rabi Hajiya bata sani ba, ta bashi tausayi matuƙa duk son zuciyar Hajiya nata suka ja mata, samarin Arziƙi tayi su amma ita da uwarta suka raina musu Ajawali, shi shafaffe da mai da yayi daidai da ra'ayinsu gashi nan tun ba'aje ko ina ba tana kuka da data sanin auransa, gara Hajiya raba baƙin cikin akeyi da ita, ita da take zaune dashi take kwasar kashinta a hannu ita take da abin faɗa. Daya tariyo gidan Naziru, da matarsa ta rufin asiri gashi nan ya tattago matar Jaraba irin wadda Hajiyar take so shi kuma tana gasa masa Aya a hannu, Yakubu ma dai sammakal wata yar gidan da Tarbiyya bata wadata ba ya kwaso yar masu kuɗi yan boko ranar nan yana ji suka kwaso rigima wai bata iya sallah ba daga ya mata magana yace a gidan ba'a sakata Islamiyyah ba ta kira Babanta tana kuka tace ya zage shi tas yace musu kafirai uban yazo yayi tijara a tsakar gidan Alhaji Audu akayi sa'a dai baya nan Hajiyar ce ta fita tana bashi haƙuri duk suna ɗaki suka ƙi fita to irin auran da take so yayi shima kenan. Bayan ya dawo ya ciza ya busa yaga dai shawarar Hajiya Ummu wadda kuma daman usulun abinda zuciyarsa ta ayyana masa kenan a matsayin mafita tilas ya aiwatar da hakan shine yaje ya samu Baba Alƙali ɗazun ya zayyane masa komai yace kuma ya kwantar da hankaliynsa ya tambayeshi ina ne gidansu yarinyar yace zeje yau ya karɓo full Address da sunan Mahaifinta akan haka suka rabu. Dalilinsa na ɓoyewa Ahmad komai akanta kuma kawai yana jin nauyin abubuwan daya masa akan Fatima, irin izgilancin daya masa na cewar ya rasa Macen da zeso a duniya se yar bakanike, duk matan da suke sonsa isassu bega matar aure ba se ita abin haushin ma tana wahalar dashi se gashi shima ya Ƙare da faɗawa tarkon yar Talaka liƙis da yake ganin kamar ma Mahaifin Fatiman Yah Ahmad ɗin zefi nata wadata, wannan tasa ya yanke hukuncin su tafi tare, yaga komai da idonsa idan yaso daga baya su tattauna domin yasan Yah Ahmad bazeyi judging nasa ba kamar yanda shi ya masa Ashe shine babban gara a cikin wasan, shi yar bakanike ta ɗanawa mugun tarko ta kamashi kuma yanda ya kamata tayi wasa da hankalinsa. Abubuwa da yawa ne cikin al'amarin, ze tabbatar da Allah ne ya kama Hajiyarsa dashi kansa dumu dumu, rainin arziƙin da yayi musu ubangiji ya tabbatar masa da ba nan take ba, ba rashin wayon Ahmad bane ya saka soyayyarta tayi galaba akansa haka duk izza da jiji da kansa gashi nan ta haushi ta tattakeshi son ranta sannan Tozarcin da Hajiyarsa ta so yiwa Ahmad ne yayi waiwayi ya diro akansa, ina zata tsoma ranta da wannan abin kunyar idan taji labarin yar bakaniken data rainawa Ajawali tayi wasa da Zuciya da Ƙwaƙwalwar Jay da take ganin kaf zuri'ar Audu Bechi babu yashi?. Daga can gefe gaba kaɗan da inda Jay yayi parking Matasa guda uku suna zaune akan Benci suna cin gyaɗa. Gida daga cikinsu yace "Waccen motar tafi minti Ashirin a tsaye anan kuma a kunne", na kusa dashi ya keɓe baki kamar wata mace yace "Kai da ganin motar ai kasan lalatattun Yayan masu kuɗin nan ne baze wuce budurwa ya ɗakko yazo nan yana lalubeta ba, yar iskar saboda ma bata da daraja a gunsa baze iya kama mata hotel ba a mota ze latse ta" yanda yake maganar seka rantse da Allah a idonsa yaga ana abinda yake faɗar, na farko daya fara magana ya cafe yana cewa "Kuma fa haka ne, wlh yanzu haka shegun suke daman indai kaga mota da dare me baƙin gilashi an zuge shi tsaf kuma motar a kunne to wlh Iskanci sukeyi". Na ƙarshen da tunda suka fara maganar saka musu baki ba se sannan yace "Haba Lawan, me yasa ba zaku kyautatawa mutane zato ba? Yanzu idan ranar lahira aka tsayar dakai ta yaya zaka kare kanka akan wannan shaidar daka bayar tamkar ya faru a gabanka? Me yasa a koda yaushe zuciyoyinku suke hasaso sharri a maimakon Alkhairi a kusa? Ba ku tunanin lalura ce ta tsayar da me motar nan? Ta yuwu kiran waya ne ya shigo masa shiyasa ya tsaya dan ya amsa domin yafi Alkhairi akan ya ringa tuƙi yana amsa waya.." Wanda ya kira da Lawan ya katse shi yana cewa "Ji wannan Bashir ɗin wace irin wayace sama da minti ashirin kuma ya bar mota a kunne se kace a gidansu ake siyar da mai?" "Kai kuma me wannan motar ne zaka yi tunanin mai ze zama matsalarsa kalleta fa ni banma san sunanta ba" Wanda ya fara takalo maganar ya bashi amsa, Bashir yayi murmushi yace "To sa ace ba waya yakeyi ba idan kuma lalurace fa wani abu ne ya same shi a cikin motar?" "Kamar yaya?" Lawan da Idris suka haɗa baki gurin tambayarsa, Bashir yace "Kwanaki naji labarin wata mata kamar haka tana tafiya a mota ta gangara gefen titi ta tsaya tun mutane basu damu da tsayuwarta ba har dai suka fara tunanin wani abu ana duba motar aka tarar ashe Allah ya mata rasuwa tana kwance kan sitiyari" Lawan ya zabura ya tashi hannu akai yana cewa "Innalillahi muje mu duba kar gobe mu zama mu zamu bada labarin a radio" ya durfafi motar Jay Idris na take masa baya sannan Bashir. Sau biyu suka Ƙwanƙwasa masa glass, seda ya goge fuskarsa da Tissue idanunsa sun kaɗa sunyi jajir kafin ya zuge glass ɗin gefen da yake gaba ɗaya ta yanda suna iya hangen gefensa zuwa bayan motar. Bashir ya masa sallama kafin yace "Afuwan ranka ya daɗe munga kana tsaye ne tun ɗazu shine mukayi zaton ko ba lafiya ba" Murmushi Jay yayi yace "Lafiya lau, nagode da kulawa" "Kai wannan ai Jay ne" Idris ya faɗa cikin ƙaraji tuni kuma Jay yaja motarsa ya bar gurin Idris da Lawan suka haukace suna cizon yatsa, Jay ne a gurin sama da minti ashirin amma basu sani ba "Kai amma fa naga idonsa sunyi Jaa, kodai shaye shaye yake a motar?" Lawan da be daddaraba ya sake faɗa. Ahmad ya kasa zaune ya kasa tsaye a bakin Gate yana jiran dawowar Jay, baze barshi ba yau se ya masa kaca kaca , yana nan zaune bayan ya kira Fatima tace masa kan da sauƙi sega motar da suka fita da ita ta kunno kai, yanda yake tuƙi ya sake fusata Ahmad dan da gudu ya shiga gidan tamkar me wasan mota. Jay be lura da Ahmad ba dan haka yana kashe motar ya fito yana rangaji ya nufi bangarensu, a daidai barander Alhaji Audu juwa ta kwasheshi kamar wanda iska ta buge se ganinsa sukayi yif ya faɗi a ƙasa Ahmad daya taho a fusace se gashi yayi kansa da gudu cikin tashin hankali, kardai kuma shaye shayen Jay ya fara be sani ba? Tambayar da yakeyiwa kansa. PAGE 23 "I'm fine, i just missed a step" Jafar daya yunƙura ya tashi da taimakon Ahmad ya faɗa. Ko kusa Ahmad be kama zancen wai lafiya yake ba domin idanunsa sun ƙaryata hakan sannan damuwa ta nuna ɓaro ɓaro akan fuskarsa dukda a lokacin be karanci yanayin nasa a matsayin damuwa ba, to wace damuwa ce haka zata samu Jafar. Yana riƙe da hannunsa kamar yaro gudun karya sake faɗuwa su ka kai ɗaki duk yanda Jafar ke ce masa ya barshi ze iya tafiya be saurara ba. Ahmad yayi mamakin da Alhaji be leƙo ba duk salatin da ma'aikatan gidan suka ringayi kuma yana zaune a falo ya tabbatar ma ya hango me yake faruwa dan a buɗe Ƙofar take, Jay ya kwanta akan gado tareda juyawa Ahmad baya, gani yake idan suka cigaba da haɗa ido ze karanto abinda yake ƙoƙarin dannewa ba kuma ya so ya fahimta. "Meya sameka Jafar? What did you take?" Ahmad dake tsaye akansa ya tambayeshi, Jay ya juyo, kafin ya kai ga bashi amsa aka banko ƙofa, tashin muryar da sukajiyo gabanin buɗe ƙofar yasa suka gane wacece "La'ilaha illallahu shikenan magauta sunyi nasara akaina na shiga uku ni Binta na lalace jifa ya tarar da Jafaru" ta faɗa hannaye biyu dafe da kai tana jijjiga. Jay ya tashi zaune Ahmad kuma ya matsa gefe can ya jingina da bango yana kallon Hajiya seta kuma juya a fusace kansa tana cewa "Aniyarka ta bika wallahi tallahi duk wani mugun abu ya ƙare akanka, wato ka ƙunsheshi a ɗaki kana jira ya mutu seka fito dashi ko?" "Haba Hajiya wai meye haka kikeyi? Wace irin magana kike haka dan Allah?" Jafar ya katseta cikin ɗacin rai, ko wane munafuki ne yaje ya gaya mata se Allah, salon tazo ta Ƙara masa damuwa kan wadda yake ciki. Hajiya ta juya kansa tana cewa "Banza sallamamme dabe san ciwon kansa ba, wato ya tattareka ya kaika ta yuwu ma tuni ya sadaukar da kurwarka shine yau ya kai musu kai su lashe, to billahillazi kurwarka ɗaci ne da ita ba zata ciwo ba sedai ya musanya musu data tsohon ubanku da dama yaci yanzu ya matsa ya bar mutane su sarara, taso muje ai inada sauran Tazargade da tsakin kuka yanzu zan turara maka su koma wane shegen maye yayi gigin taɓaka sedai ya cinye kurwarsa wlh" ta matsa ta shiga janyo ƙafafunsa kamar wani yaro ƙarami. Da iyakar ƙarfinta take jansa hakan yasa ya miƙe dan dole yana mata mitar abinda takeyi. Ko a jikinta ta tasashi gaba, ta waiwaya ta gallawa Ahmad dake nan tsaye yana kallon ikon Allah harara kafin tace "Waya sani ma ko kaima har sun lasa maka, to wlh nafi ƙarfin ƙaramin maye irinka manyan ma nan zasu ganni su barni". Dariya ta bashi dan har seda ya murmusa kafin ya zauna akan gado bayan da suka fice ta tasa Jay a gaba. Kwanciya yayi rabin jikinsa na kan gadon Ƙafafuwansa na ƙasa ya tallafe kansa da hannu biyu ya zubawa POP dake ɗakin ido. Meya samu Jay? Wane abu ya fara ko kuma yake aikatawa daman can dabe sani ba? Meya janyo sauyawarsa tun bayan daya dawo yake abubuwa ba tareda ya sakashi a ciki ba? Shi damuwarsa ba rashin including nasa da Jay bayayi a sabgoginsa bane ba Aa yanda yake abubuwan a Ƙudundune ne kamar mara gaskiya. Jay da ko Ƙofar gida muddin yana nan baze fita shi kaɗai ba seya rakashi amma shine ya iya tafiya har Abuja ba tareda rakiyar Ahmad ɗin ba, wannan be bashi mamaki sosai bama akan zuwa gidan Baba Alƙali da yayi nan ma shi kaɗai. Yanzu sun fita lafiya ya dawo cikin wani yanayi daya kasa fassarashi. Babu wata alama a tattare dashi da zata nuna maye ko wani abu makamancin haka sannan daka kalle shi kasan baya cikin hayyacinsa, Fargabarsa da damuwarsa yasan menene yake damun Ɗan uwansa a yanzu. Fatima ta faɗo masa a rai ya zaro wayarsa daga Aljihu ya kirata dan yaji ya anta ciwon kan amma bata amsa ba se ya soka wayar a chaji ya tashi, seda ya cire T shirt ɗin jikinsa ya mayeta da Jallabiyya kafin ya fita dukda goma ta gota ya shiga cikin gida. Momy da Maimuna tareda Sarah autar Hajiya Binta suna zaune a falo, Momyn na kallo su kuma suna aikin filling Samosa. "Manyan yan kasuwa" ya zolayesu bayan daya zauna suka gaishe shi. Sarah tace "Dan ma Yaya kaƙi ka bari mu fara kaiwa Mall ɗinka ai da wlh da yanzu munfi haka" "Wannan jagwalgwalon ze bari ku kai musu?" Momy ta faɗa se yayi saurin cewa "Haba ba jagwalgwalo bane Momy gyare gyare mukeyi shiyasa ma ban amsa musu ba amma da mun gama bayan frozen har soyayye zasu ringa kaiwa ai naci naji da daɗi kuma na yarda da tsaftarsu". Sarah da Maimuna suka tafa cike da jin daɗi kafin suka shiga tattare kayan aikinsu dan daman sun gama suka wuce kitchen. Bayan shigewarsu Momy ta kalli Ahmad tace "Ina kukaje da Jafar ne uwarsa ta shigo ɗazu tana ta hayagaga da faɗar maganganu?" A taƙaice ya bata labarin fitarsu zuwa dawowarsu da kuma abinda ya faru yanzu a waje. Momy tace "Allah ya rufa asiri toh, ta yuwu ko bashida lafiya musamman tunda ya dawo be zauna guri guda ba yana ta stressing kansa ga Ranar kwanakin nan da zafi ba irin wadda ya saba da ita bace, daman ɗazu ina falon Alhaji Babanku ya kirashi yake gaya masa Jafar yaje gurinsa akan maganar zuwa tambayo masa aure ko?" "Eh haka ne" ya bata amsa ta sake cewa "A ina ne?" "Wlh ban sani ba, yau mukayi zamuje kuma ya tafi ya barni" "Au kaima baka sani ba? Koda yake ai na fuskanci kwanakin nan uwarsa ta matsa masa ni tunda ya dawo ma sau biyu ya shigo falon nan "Uhm" kawai yace mata jin haka yasa itama tayi shiru da maganar can ta sake cewa "Toh ya kukayi da ita Fatiman? Babanta yace a bashi sati huɗu me tace maka akan hakan?" "Bamuyi maganar ba Momy amma daman Baban nata yace ai wanda zasu karɓi auran ne basa nan shiyasa yace a basu lokaci amma ko ɗazu ma mun haɗu yace yana gaishe ku" "Toh muna amsawa, ya kamata dai a fara abinda ya kamata dai toh, bari kaga wasu Atamfofi ɗazu *UMMU-MAHEER 07061838488* ta turasu a group ɗinta *BUYERS BATIK/ALIZA BATIK* ne kyau garesu quality kuwa ba'a magana gasu unique designs babban abin da yake burgeni dasu seka gama yayin Atamfar nan baka ci karo da me irinta a gari ba gasu basa koɗewa sedai ka gaji ka bayar kai *BUYERS BATIK* fa ta haɗu" ta ƙarasa tana miƙa masa wayar. Ba wani sanin kan Atamfa yayi ba dan yafi ganin kyan Lace shi a jikin Fatima nema Atamfar take burgeshi amma yana ganin *BUYERS BATIK* ɗin ta tafi da imaninsa. Ya ringa scrolling yana duba designs ɗin da duk babu na banza a ciki, harya hasaso su jikin Fatima dan kalolin duka zasu karɓeta. Ya maida wayar yana cewa "Amma sunyi kyau Momy" "Ƙwarai ma kuwa, guda nawa za'a ɗauka?" Momy ta tambayeshi se yace "Ki zaɓi wanda kike so se ki ɗaukarwa Maimuna ma nawace?" Ya mayar mata cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa. Ta harareshi tace "Tun yaushe muka zaɓi tamu, maganar lefenka nakeyi guda nawa za'a saka ko kuwa seta ƙare sannan?" Se ya hau shafa kai irin na yaji kunya kafin yace "Ai duk sunyi kyau ma" "Se a saka duka design goma ce" daga nan suka cigaba da tattaunawa wanda duk maganar auransa Momyn take sako masa. Jay kuwa bayan sun isa falon Hajiya kwanciya yayi akan kujera tana ta aikin mita ta tafi can kitchen ɗinsu na baya inda suke hura Itacen da ita ta saka dole ake amfani dashi ta samo garwashi a cikin kasko. Tsabar magana tana zuba maganin a wutar seda hayaƙi ya turniƙeta ta fara tuttula tari har bata san sanda ta ture kaskon nata ba gaushin ya zube Allah ya rufa asiri akan Tiles ne carpet ba. Kansa kamar ze tsage masa haka ya tashi ya ɗakko ruwa ya kashe garwashin ya bawa Hajiyar tashi bata daddara ba faɗi tajeyi "Shikenan ashe ba kai kaɗai sukayi galaba akanka ba harda ni" "Dan girman Allah Hajiya ki bari, ni lafiyata ƙalau na gaya miki gajiya nayi kawai bacci bake da buƙatar nayi yanzu" yanda yayi maganar ya saka Hajiya binsa da kallo shi kuma jin bata ce komai ya juya yana tafiya daƙyar saboda yanda zuciyarsa tayi masa nauyi Hajiyar kuma bata dakatar dashi ba. Kan gado ya kwanta ya rufe idonsa, wayarsa ta shiga ƙara a Jikinsa yaji cewar itace. Wani ɓari na zuciyarsa na rasa masa ya amsa ya tambayeta dalilinta na aikata musu abinda tayi inda ɗayan yayi galaba ta hanyar hanshi amsa wayar. Jin muryarta a yanzu babu abinda ze ƙara masa se baƙin ciki da damuwa. Har yanzu gani yakeyi kamar bada gaske bane, dukda a zahiri yaga komai ba gaya masa akayi ba amma so yakeyi ya ƙaryata hakan ya cewa zuciyarsa ba gaskiya bane ko kuma komai be faru ba. Idanunsa suka sauka kan wayar Ahmad da yake chaji ya yunƙura daƙyar ya ɗaukota kansa na sara masa kamar ze tsage biyu. Number wayarta ya shiga dialing yana fatan ya zaman babu ita a wayar sedaj yana saka 0803 numbarta ce ta farko data zo a suggested contacts ga sunan da Ahmad ya mata saving dashi FATIMA da manyan baƙi se Jan Emoji me alamar zuciya a gaba. Ya runtse idonsa da ƙafin ya buɗe WhatsApp a hankali ya ringa bin chats ɗinsu kamar mr bitar karatu yana cike guraben maganganunta da ire iren daɗaɗan kalaman da take amfani dasu gurin magana dashi wanda saɓanin haka chat ɗin nata da Ahmad babu wani armashi balle soyayya a ciki. Ya ga hotunanta da basu da yawa idan aka haɗa da wanda ta tura masa shi daga haɗuwarsu zuwa yau ɗin, wato yarinyar first class maƙaryaciya ce, ma ha'inciya kuma Azzaluma. Ya tuna wayarsu ta farko data tambayeshi ko shikaɗai Jay ɗan Nigeria dayake ƙwallo, me yasa tun a sannan be taɓa hasaso cewar ita ce ba? Maida masa da wayar yayi jikin chaji ya kwanta rubda ciki ya danne kansa da pillow. So be kyauta musu ba daga shi har Yah Ahmad su rasa wadda zasu so se wannan Azzalumar mara tsoron Allah. Shi ya gama tabbatarwa ma da tasan su, tasan gidansu ɗaya shirya komai tayi ya kuma godewa Allah daya saka ya ganota tunda wuri kafin tayi nasarar karya zuciyar ɗan uwansa da babu komai cikinta face tarin Alkhairi da son kyautata mata. Yana jin Ahmad ya shigo lokacin kuma wayarsa ta sake ɗaukan ƙara a karo na babu Adadi amma be amsa ba se Ahmad ne daya shigo ya janyo wayar daga gefen kansa inda ya ajiyeta yana cewa "Na gaya maka ka dena aje waya kusada kanka idan zakayi bacci bakaji kuma duk wannan ƙarar yanzu se kace baka ji ba toh Afeeyah ce kar gobe kazo kana mun kukan ta ƙi amsa wayarka". Da hannu yaja wayar ya latseta gaba ɗaya ta mutu ba tareda ya amsa ba, Ahkad yayi sororo yana kallonsa, da kuma ya tuna ba matsalarsa bace se yaci gaba da abinda yakeyi ya gama yayi shirin kwanciya yabi lafiyar Gado. Zafin jikin Jay daya matseshi ne ya farkar dashi daga bacci dan shi bashida nauyin bacci ko kaɗan, ya taɓa Jay ɗin, zazzaɓi ne rau a jikinsa har numfashinsa hucin zafi yake fitarwa amma bacci yake wanda da gani bana daɗi bane. Ruwa ya samo me madaidaicin sanyi da ƙaramin Towel ya jiƙashi ya fara shafa masa a fusak, Jay ya saki ajiyar zuciya ya buɗe ido daƙyar ya kalli Ahmad ɗin kafin ya lumshe su. Da taimakon ruwan daya shafa masa da Maganin daya saka ya tashi yasha a lokacin zafin jikin ya ragur masa se Azababben ciwon kai da yakeji kamar ƙwayoyin idonsa zasu fito, kafin safiya ya fita hayyacinsa Idonsa yayi Jajir ga jijiyoyi a goshinsa kamar zasu faso su fito, yanda jikinsa ke karkarwar sanyi bayan yayiwo Alwala ya saka Ahmad dakatawa sukayi sallah a ɗakin sannan ya kamashi suka fita a duku dukun suka tafi Asibiti. "Wai me ya same ka? Lafiya kau muka rabu jiya meya sameka a can in da kaje kuma?" Ahmad ya tambayeshi. Cikin dauriya yace masa "Inaga Malaria ce, kwana biyu sauro ya cije ni" "Sedai a gidansu Afeeyan ka kwaso Malaria dan mudai gidanmu babu sauro, kafin kazo seda akayi fumigation kuma still kullum se an saka magani, kuma Malaria ce zata kwantar da mutum haka lokaci ɗaya? Zamuje Asibiti dai koma menene yake damunka da baka so na sani zasu gayamun" Ahmad ya faɗa, shidai Jay be sake ce masa komai ba fama yake da jinyar fili data zuciya, abune goma da Ashirin yayi masa rubdugu lokaci ɗaya. Yarinyar daya ɗora dukkan buri da tanadinsa akanta, Macen da yake So tamkar ransa, da ita yake fatan ƙare rayuwarsa lokaci daya ta rikiɗa ta dawo Macen daya fi tsana a duniya, tun saninsa da ita yake jin ƙinta tun kafin ya ganta yasan wacece ita, abinda tayi musu a yanzu ya sake linka tsana da ƙiyayyarta me tsanani a zuciyarsa. Ya gane dalilin daya saka jininsa da ita a matsayin budurwar Ahmad ya ƙi haɗuwa, Soyayyar da sukayi a rashin sani wannan ya karɓeta a matsayin sakayyar abinda yake gayawa Ahmad dalilin soyayya da ita, Ubangiji ne ya nuna masa isharar cewa shi yake ƙunsa So a zuciyar bayinsa bawai yin kan mutum bane ba amma ya tsinewa dalilin zuwansa Zariya da har yayi silar haɗuwarsa da wannan Annamimiyar yarinyar me suffar salihai. Asibitin Dr Hassan ya kaishi, basu tarar dashi ba se Dr Michel da yayi night duty shine ya dubashi. Ahmad yana waje yana jiransu dan daya shigar dashi fitowa yayi ya basu privacy. A ciki bayan Dr ya gama auna Bp sa saboda ciwon kai da yake shi yake damunsa kuma ido da fuskarsa ma sun nuna hakan. Cikin tsanaki ya kalleshi yace "Bp ka yayi high sosai also rate na heart beat naka ya zarce misali me yake damuka?" "Forget about it Dr, kawai ka bani necessary assistance and please don't tell anyone about it ka cewa Yah Ahmad Malaria ne yake damuna" Jay ya faɗawa Dr Michel, Dr ya zura masa ido ya buɗe baki da niyyar sake masa magana Jay ya haɗa hannaye biyu alamar roƙo yace "Please, do me this favor" "Fine amma dole koma menene ka cireshi daga ranka saboda lafiyarka ta daidaita ka sani this will not be good for your career and..." "I know Dr i will try my best" ya sake katse shi. Dr ya girgiza kai kafin ya danna Ƙararrawar kiran Nurse se gata ta shigo. Paper daya rubuta prescription wa Jay ya bata ta tafi ta haɗa komai ta kai ɗakin da zasuyi admitting nasa zuwa Bp ya daidaita sannan ta koma ta gaya masa. Da kansa ya kamashi suna fita Ahmad ya tayashi har zuwa ɗakin, ruwa ya saka masa wanda ya zuba Allurai a ciki harda ta bacci babu daɗewa kuwa bacci yayi gaba dashi. Cikin damuwa Ahmad ya shiga tambayar Dr me ya samu Ƙaninsa yace masa Malaria ce. Ganin ya samu bacci yasa ya koma gida, Alhaji ya fara sanarwa Jay bashida lafiya yana Asibiti "Toh Allah ya bashi lafiya, se a sanarwa uwarsa ai" Alhajin ya bashi amsa, se yaji abin wani banbara kwai ba yanda Alhajin ya saba ruwa da tsaki a lamarin Yayan Hajiya ba, koda yake daman ko a cikinsu basu fiya jituwa da Jafar ɗinba saboda rikici da taurin kansa sak irin na Alhajin ne dukda yanda Hajiya take so ya zama yafi kowa shiga jikinsa amma abin yaci tura shiyasa take baƙin ciki da shirin da sukeyi da Ahmad a yanzu. Daya gayawa Hajiya kuka ta ringa zundumawa harda tumami a Ƙasa tana kiran ta shiga uku ta lalace shike nan magauta sunci galaba akanta. Ta tattara ta tafi Asibiti can ta tare ita da jama'arta da surukanta data ringa wa waya tana gaya musu suzo an jefe Jay gashi kwnace magashiyyan a gadon Asibiti, Turai ta tafi mata tambaya dan su binciko wanda ya taɓa Jafar ɗin, Momy da Anty sunje sun dubashi da daddare se sannan Ahmad ya koma saboda Hajiya da take a gurin tana ta faɗar maganganu akansa, Alhaji ne yace shi yaje ya kwana da Jafar ita da jama'arsa kowa ya watse ya koma gida. Daze tafi ya tafi masa da wayarsa wadda yaga Missed calls ɗin Afeeyah sunfi Ashirin ga messages nan birjik na ban haƙuri akan laifin da besan me ta masa ba. Ya jefa wayar a Aljihu, besan password ɗinsa ba daya buɗe wayar ya kirata ya sanar mata abinda yake faruwa kodan hankalinta ya kwanta. Yana dabda shiga Asibitin ta sake kira ya amsa cikin nutsuwarsa yayi sallama. FATIMA Tana shiga cikin gida kaitsaye ɗakinta ta shige tana jiyo Umma da Baffah suna magana Baffa yana cewa "Wlh Ruƙayya ban taɓa zaton haka zanji nauyin yaron nan ba, badan fa ya rigada ya ganni ba juyawa nayi niyyaryi amma babu dama" Umma tayi shewa tace "Malam, ai baka ma soma jin kunya ba se ranar daya fahimci yaudarar daka shirya masa kaida yarka, billahillazi in bakayi wasa ba seka gagara fita na wasu kwanaki saboda zancen mutane da nunaka da za'a ringayi". Sama sama take jiyo mahawarar Baffa da Umman, ta zauna kan katifa tana dafe da ƙirjiz seda ta nutsu kafin ta latsa kiran layin Jay tana so taji ina ya tsaya tunda Allah ya taimaka ta sallami Ahmad yanzu se yazo. Wayar ta ƙaraci ringing be amsa ba ta sake kira nan ma dai shiru seta ajiye a zuwan ko yana hanya idan ya iso ze kirata amma shiru shiru har sha ɗaya babu Jay babu dalilinsa kuma be biyo kiranta ba zuwa sannan kuma hankalinta idan yayi dubu ya tashi to me ya faru? Kar dai yazo ya ganta tareda Ahmad shiyasa yayi zuciya ya tafi kuma yaƙi amsa wayarta. Data sake kira tana fara ringing aka katse, cikin sauri ta sake gwada kiran a zatonta ko garin ya amsa ne ya katse ita bama zata iya jira ya kirata ba sedai a karo na biyun aka shaida mata wayar a kashe take. Ta kwanta lamo hawaye na zubowa daga idonta, rejecting yayi kuma ya kashe wayar dan karta dameshi ta tannata yazo ya ganta tareda Ahmad kenan. Tsohuwar wayar dayace ta dena amfani da ita ta ɗauka ta saka sim ta kunna Data, WhatsApp ta shiga dan ta duba ko yana online bata tsaya duba duk saƙonnin da suke ta tuntuɗowa ba ta wuce kan number sa. Mamaki ya kamata ganin Dp sa ya sauka sannan babu about hakan kuma tasan yana nufin yayi blocking nata kenanseta saki wayar a Ƙasa ta rushe da kuka, Umma na tsakar gida tana tattare kaya saboda hadari daya taso har an fara iska ta jiyo kukan nata da sauri ta leƙa ɗakin, "Lafiyarki Afeeyah? Kukan me kikeyi me ya sameki?" Umma ta tambayeta. Cikin kukan tace mata "Jafar ne Umma" Umman taja wani shegen tsaki ta sakar mata labule ta cigaba da abinda takeyi ranta na suya, idan ta buɗe baki zagi zata zunduma mata shiyasa tayi shiru. Afeeyah tasha kuka ta gode Allah a daren kafin safiya ta ɗora da kiran layin Jay da jera masa Texts na ban haƙuri da rantsuwar duk abinda ya gani yake tunani ba gaskiya bane ba amma shiru kamar an shuka dusa be amsa kira ko guda ba haka be bata amsa ba. Zazzaɓi ne da ciwon kan gaske itama ya lafketa haka ta wuni a ɗaki Umma bata bi ta kanta ba seda Allah ya taimaketa Anty Sauda taje ita ta bata abinci da magani tasha harta samu ƙarfin cigaba da kiran Jay ɗin. Kiran ƙarshe da tayi shine Ahmad ya amsa, ta saki ajiyar zuciya me ƙarfi sanda taga sakanni sun fara tafiya. Muryar Ahmad me sanyi ta ratsa kunnenta, ba muryar Jay bace seda ta zare wayar ta duba dan ta tabbatar da wata kirane taga number Jay ce. Cikin muryarta data dashe dalilin kuka ta amsa sallamar kafin tace "Dan Allah Jafar fa? Yana kusa?" "Bashida lafiya yana kwance a Asibiti" Ahmad ya bata amsa, a rikice tace "Yaushe? Meya sameshi? Wane Asibiti yake?" "Relax, malaria ce inaga sauron gidanku ne basu san baƙo ba suka cijeshi, yanzu zan shiga gurinsa zan bashi wayar seya kiraki ok?" Ahmad ya faɗi. Ta sake sauke ajiyar rai, muryar kama take mata da ta Ahmad amma babu dalilin da ze sanya Ahmad ya samu wayar Jay "Nagode toh ina jira" ta faɗi kafin ta sauke wayar ta doka tagumi tana jiran taga an kira kamar yanda yace, tunani take tana ƙarfafawa kanta guiwa dukda hankalinta ya tashi dajin bashida lafiya, ta yuwu ma beje ba jiyan ba ganinta da Ahmad bane ya ɓata masa rai, ƙila ma ko be hau Online bane shi yasa taga kamar yayi blocking nata a WhatsApp amma ba haka bane. Shiru tana ta tunani har minti kusan ashirin ya wuce ba'a kira ba kamar yanda wanda ya amsa wayar ya ce mata ze kai masa yanzu se kawai ta yanke shawarar ta sake kira kodan taji ya jikinsa da kuma abinda yake damunsa. AHMAD Sau biyu kenan da yake jin muryar budurwar Jay tamkar ta Fatima, daya isa ɗakin ya tarar da Manager shi tareda sauran jama'arsa wannan tasa be bashi wayar ba ya ajiye masa ita kawai akan Drawer ya fita zuwa gurin Dr Hassan, Jay kuwa bayan ya sallami baƙinsa ya ɗauki wayarsa da through out yau be riƙe ta ba. Missed calls ɗinta ya fara gani, wani abu ya soki ransa, daga safiyar zuwa yanzu yayi ƙoƙarin ganin ya rage damuwarta a ransa, a maimakon matsantawa kansa da son gano dalilinta na aikata musu wannan abun seya mayar da hankali gurin tunanin ta yanda ze hukuntata dan ba zata ci banza ba tilas ya maida mata da mugun nufinta akansu. Tunaninsa ɗaya yanda Ahmad ze karɓi Al'amarin idan ya sanar masa, baze bari taci gaba da cutar da shi ba daga ƙarshe ta karya masa zuciya tamkar yanda tayi masa. Shi yana da taurin ran da ze shanye damuwarta amma baya tsammanin Yah Ahmad ze iya, he is so much into the girl. "Kaima kana sonta" zuciyarsa ta raya masa, se yayi saurim kawar da tunanin daga ransa domin shine rauninsa. Allah ya sani yana Son ta, so na gaskiya saboda Allah badan wani abu ba amma kuma kash koda ace babu wata manufa game dasu a ranta, ya zama ace abinda ya faru Arashine daga Allah tilas shi ze haƙura da ita domin Ahmad ya rigashi zuwa gurin kai ko ba haka ba ko da ace tasa ce Yah Ahmad yace yana so ze bar masa. Ringing da wayar ta fara ya katse masa tunani, yana kallo harta katse kafin ta sake kira yayi adding nata to blocklist, a fili yake so ya wanke ta, face to face yake so ya warware mata komai ta yanda zata fi ji a jikinta. Haka yayi jinyar kwana biyu aka sallameshi kullum a Asibitin Hajiya da jama'arta suke wuni tamkar wani biki se dare Ahmad kuma yaje ya kwana dashi. A taƙin kwanaki biyun yayi rama fuskarsa kuma ta gagara ɓoye abinda yake ransa amma se yake boyewa da sunan ciwo. Kwanansa biyu da dawowa gida ya fara shirin komawa France. Da niyyar sati huɗu yazo gida, sati huɗun da yake cewa kafin cikarsu za'a ɗaura musu Aure da Afeeyah se gashi komai ya canza ko cikakken sati biyu beyi ba yana cewa ze koma. Hajiya daman cewa tayi gara ya tafi, Turai tace anyi Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya shiyasa ma ya samu sauƙi ya tashi saboda an san ko an bashi magani ko hayaƙi bayi zeyi ba se aka masa aikeb kai tsaye wai Malam ya saka hadimansa sun saka maganin a jikinsa. Ahmad ne kaɗai ya damu da konawar da zeyi domin ya gagara yarda wai Malaria ce take damun Jafar, akwai wani abu daya ɓoye masa kuma ya gagara tambayarsa kamar yanda shima Jay ya kasa furta masa abinda yake ci masa zuciya. Yayi Ƙoƙarin magana da Ahmad tun yana Asibiti, ya tambayeshi kan yanzu ace masa Fatima yaudararsa takeyi bayanshi da akwai wani da take kulawa kuma shi take so yaya zeji? "Already na sani, bayan ni da akwai wani da take tare dashi kuma shi take so bani ba, ya ci ace na haƙura da ita Jafar, amma na kasa. Ni da kaina bansan irin son da nakewa yarinyar nan ba kawai dai ina cigaba da addu'a idan rabo na ce Allah ya bani idan ba tawa bace Allah ya musanya mun da wadda ta fita Alkhairi" amsar da Ahmad ya bashi kenan data sanyaya masa jiki tasa kuma ya fasa faɗa masa gaskiyar abinda ya faru to ta ina ma ze fara? Ya Ahmad zeji? Se kawai ya shanye damuwarsa shi kaɗai ya kuma cigaba da addu'ar Allah ya tarwatsa tarayyar su da Ahmad domin ita ba Alkhairi bace a rayuwarsu. Ranar talata data kama saura kwanaki biyu Jay ya wuce Baba Alƙali ya kirashi akan yaje gida ya same shi yana son magana dashi. Shi kaɗai ya tafi yauma daman Ahmad baya nan ya tafi Jigawa inda yake noman shinkafa dan da tare ma zasuje Hajiya ta hanashi binsa. "Shiru baka sake cewa komai ba dangane da full address da nace ka samo na gidansu yarinyar da kake nema" Baba Alƙali ya faɗa, ya sunkuyar da kansa yace "Amm daman an samu matsala ne Baba so kuma na manta ban dawo na gaya maka ba" "Matsala wace iri kenan?" "Ita yarinyarce da akwai wanda suke tare kafin ni kuma bata gayamun ba se daga baya nayi finding out so i felt thar she betrayed me kuma bata da gaskiya if she could hide such important things to me may be bada gaske take so na ba nima". Baba Alƙali ya ringa kallonsa kafin yace "Kodai uwarka ta shiga tsakani ba?" "Wlh babu ruwanta Baba bata san komai ba har yanzu kawai wannan dalilin yasa nayi blackout saboda ni bana son Ƙarya a rayuwata" Jay yayi saurin defending Hajiya. Alƙali yayi murmushi yace "Amma ko zaka daɗe kana bincike kafin ka samu budurwa da take kula saurayi guda ɗaya, daman ai se anyi takara wanda yafi ƙarfi ya kayar da yan uwansa" cewar Baba Alƙali. Jay yayi murmushi, kamar ya sanarwa da Baban abinda ya faru amma baze so ya zama silar raba Ahmad da abinda yake so ba dan Baban baze bari ya aureta ba ya sani, gara ace ita da kanta taji kunya tace ta fasa tayi biyu babu so that bazeyi blaming kowa da cewar shi ya hanashi auranta ba. "Ai ita Baba har iyaye sun san maganar fa for almost 3 years suke tare yana wahalta mata amma bata gaya mun ba seda naje gurin Babanta and from the way yayi maganar se naji kamar yafi son wancan ma akaina" "Allah ya baka haƙuri ya musanya maka da wadda ta fita Alkhairi, shikenan zamu jira daga gurin mahaifin yarinyar da Ɗan uwanka yake nema shi saura sati Ɗaya wa'adin daya bamu ya cika, idan kuma duk an kasa ku ne se ku ɗauki haƙuri mu tafi Bechi a nema muku mata" ya ƙarasa maganar cikin raha Jay yayi dariya. GIDAN MALAM HAFIZU Kamar yanda na sanar miki sati biyu na bawa wanda kika kawo a matsayin zaɓin ranki, yau kwanaki goma sha biyu kenan tun zuwan da yayi be sake dawowa ba, ina sake tuna sar dake kwana biyu rak ya rage miki idan suka cika ba tareda ya gabatar da kansa ba karkiyi kuka da duk hukuncin da zan yanke domin na baki dama a matsayinki na Ya dan haka nima zan gwada iko na na uba akanki" Baffah dake tsaye akan Fatima ya faɗi. "Kinji me nace ko?" Ya sake jaddada mata seta gyaɗa kai alamar taji ya juya ya fice daga ɗakin. Kwanciya tayi kan katifa ta fashe da kuka amma mara sauti, bata sake samun Jafar a waya ba tun ranar da wani ya amsa yace ze haɗasu. Ta tabbata kuma yayi blocking nata a WhatsApp da sauran social media handles ɗinsa dan duk inda ta masa magana bata tafiya sedai ta gaji da jira ta haƙura. A ɗan lokaci ta fita a hayyacinta, zuciyarta zafi take mata ga ciwon kan da tayi ƙaryarsa ya aureta da gaske me azaba irin wanda ko idanu idan ya tasar mata bata iya buɗewa. Yanda Umma tayi banza da ita tamkar ta manta da wanzuwarta a gidan ne yake sake ta'azzara mata ciwo da damuwa, bata da wanda zata tattauna dashi, Anty Sauda ma ta juya mata baya, Badar Babansu bashida lafiya har an fita dashi India suna can dukansu tunda ta mata sallama basu sake magana ba kusan kwana goma bata san layin da zata sameta acan ba shi kansa Ahmad da take ganin ya zame mata ƙuda ta rasa yanda zata yaki ceshi a yanzu da take buƙatar ɓangaren da zataji sanyi shima ya kaucez tun randa yaje be sake komawa ba haka waya befi sau huɗu sukayi ba saboda ayyuka da yace mata sun masa yawa baya samun lokaci sosai wannan shi ake cewa rana zafi inuwa ƙuna babu inda zata tsoma ranta taji daɗi ga wani sabon batu da Baffah yazo mata dashi ita ya zatayi???? Daga kwancen da take ta janyo wayarta ta buɗe Tiktok, a can ne take zaton be rufeta ba kai tsaye tayi searching account ɗinsa ta shiga profile ɗin. Ƙirjinta ya buga dum da ganin video da yayi pinning a farko, hannunta har yana rawa ta buɗe, videonsa ne da wata yarinya, Jaa ce dan kalar fatarta farace irin me sirkin jini. Ƙirarta irin jikin yayan madarar nan da zaka gansu fatarsu luf kamar an hura musu iska a cikinta, kyakykyawa ce bata cika tsayi ba, tana da cikar ƙirji sosai da mazaunai wanda fitinannen ɗinkin doguwar rigar data saka ya bayyanar dasu. Hannayensu sarƙe da juna tana masa magana yana doka murmushin nan nasa me tsada. Ta ringa maimaita karanta Caption ɗin daya rubuta # FatiyyahJay# PAGE 24 Comment section ta shiga, hawayen da suka lulluɓe mata ido suka saka bata iya ganin abinda aka rubuta. Tana kuka tana typing "Unblock me and answer my calls Jay dan girman Allah I'm going to explain ba abinda kake tunani bane" Tana turawa ta fita ta shiga gurin message nan ma ta fara jera masa maganganganu amma harta haƙura cire tsammani be amsa ba, kuma official account ɗinsa ne babu batun ace be gani ba. Wacece wannan yarinyar? Menene haɗinsa da ita? Ta ringa tambayar kanta. Kuka tasha har seda taji tana neman shiɗewa sannan tayi shiru amma hawaye basu dena zubar mata ba. JAY Abuja yayi zango bayan ya bar Kano, sati huɗu yayi niyyaryi tareda Afeeyarsa kafin ya koma, abinda yake ji a ransa yasa baze iya cigaba da zama a Kano ba kuma baze koma France ba dan ya san kewa ce zatayi masa yawa, damuwar da yake ciki nunkuwa zatayi. Ahmad ne ya rakashi Abuja as usual a Ƙoƙarinsa na son nuna komai lafiya lau sedai Ahmad ɗin ya masa shiru ne kawai yana binsa a yanda yake so amma ya gano tabbas akwai abinda Jafar ya ke ɓoyewa, sanin menene kuma ya barwa Allah yana dai da yaƙinin ko meye idan lokacin daya kamata ya sani yayi base ya tambayeshi ba ze gaya masa. Ya masa magana dai akan Afeeyah saboda sun fita da Alhaji yace masa Baba Alƙali ya masa zancen an fasa zuwarwa Jay tambayar aure kamar yanda aka shirya a farko, daya tambayeshi dalili yace masa "Mayaudariya ce Azzaluma, tana da wanda iyayenta suka fi so yake wahalta mata for ages so tayi ta yaidareni Allah yasa na ganota da wuri" ya bashi sa. Ahmad yace "Kuma da gaske kakeyi ka haƙura da ita? Daman duk kurarin soyayyar nan a bakine ba gaskiya ba? Ai na zata se in har kaji an ɗaura mata aure da wani ne zaka sare ashe ma bada gaske kakeyi ba" "Yah Ahmad kenan" abinda ya sake ce masa kenan daga nan suka bar maganar dan shima be jata ba. Daya kaishi Abuja a ranar ya juyo dan da sassafe suka tafi be kuma zauna ba ya masa sallama ya juyo dan akwai ayyuka a gabansa sosai da yake so yayi. Wannan tasa Jay ya kashe wayarsa dan baya so wani a gida ma yasan be tafi ba, seda ya shafe kwanaki biyu a Hotel room sedai yayi wanka yaci abinci yayi sallah ya kwanta yana tunani. Duk ta yanda ya ke lissafa ze warwarewa Afeeyah se yaga daga ƙarshe abin akan Yah Ahmad ze ƙare. Ranar daya kwana uku ya gaji da kwanciya da dare ya shirya ya fita, mota ya ɗauka a Hotel ɗin ya fita ya ringa yawo a titin Abuja harya gaji, haka nan yaji yana kwaɗayin Shawarma dan haka ya tsaya wani guri dake kan titin daya biyo. Yana tsaye gurin cashier kamar daga sama yaji an kira sunansa "Jayyy" yanda taja sunan ya sanar masa da wacece, ita kaɗai take kiransa haka mamakinsa ya akayi ta ganeshi? Ya juya baya kuma kota gaba ta kalleshi fuskarsa lulluɓe take da facemasks saboda tsaro. Ya juya sosai yana kallonta, FATIYYAH MU'AZ ce, fuskarta ɗauke da murmushi me kyau take kallomsa itama, kafin yayi wani abu ta isa gareshi ta rungumeshi and he couldn't help it but to hug her back. "When did you come back to Naija?" Ya tambayeta bayan daya raba jikinsu, hannunta sarƙe cikin nasa tana binsa da kallo kamar mayya tace "Since last month, mun ma dawo duka nan ai" "Wow, at long last" ya faɗa da wide smile. Ta kai hannu zata zare masa facemask ya riƙe yana girgiza mata kai ta ɓata fuska, "Excuse me sir, your order is ready" muryar wata waiter ta katse shi tana miƙa masa ledar kayansa ya amsa har sannan Fatiyyah na manne rabi a gefensa ya kalleta yace "Let's go". A tare suka fito daga gurin, motar daya zo da ita suka shiga suka zauna Fatiyyah ta shiga ɗaukansu hoto bayan daya zare facemask ɗin. "Ki bari muyi magana mana" ya faɗa yana kwace wayar ta sakar masa tareda maida hankali tana kallonsa harda yin tagumi da hannu biyu. "Idanunta irin na Afeeyah" ya raya a ransa, ya san Fatiyyah tun kafin yasan ze haɗu da wata Afeeyah a duniya. Yarinyar CBN governor ce, a London suka haɗu, friend ɗinta ce Asali budurwarsa Maryam se kuma suka fara Ƙawance da Fatiyyan sosai daga ƙarshe ma Maryam ɗin tayi aure wannan yasa alaƙarsu ta fara canzawa da Fatiyyan saboda tana nuna so takeyi suyi soyayya. Yes tana da komai da ze saka Namiji ya sota amma beji yana ra'ayinta a lokacin ba, abinda ya burgeshi da ita har yasa ya kasa man tata yanda ta kama kanta taja ajinta ta rabu dashi tunda ya nuna baya ra'ayinta saɓanin sauran yammata da suke naci suna binsa yana wulaƙantasu kamar mayu. Kusan three years kenan basu haɗu ba suna dai chat jefi jefi se yau Allah ya sake haɗasu. Sunata labari a mota har seda Maman Fatiyyah ta kirata dan tace zata siyo shawarma ne yanzu ta dawo kuma tajita shiru wannan ya ankarar da ita daɗewan da tayi a wajen sukayi sallama ya rakata motarta, Shawarman daya siya ma bata yayi suka rabu akan zeje gidansu da safe kafin ya wuce saboda yace mata probably ya wuce France zuwa jibi. Bayan ya gama abinda yakeyi ya hau gado ya kunna Wifi ya shiga WhatsApp, status ɗinsa yayi updating da 'found a new love'. Badan yayi blocking Afeeyah ba tun a ranar zata gani, Ahmad ne ya fara buɗewa ya masa replay da "Who is the new catch" "Some one that i deserve, and she deserves me" ya maida masa. Se Ahmad ya kirashi ta WhatsApp ɗin dan tunda ya tafi kamar yanda sukayi zato ta nan suke magana yaƙi kunna wayarsa. "Jay dagaske kake ka haƙura da yarinyar nan wai?" "Dagaske mana Yah Ahmad kasan dai sau ɗaya nake so kuma if i hate something and turned my back against it i never go back to it" ya bashi amsa. Ahmad yayi murmushi yace "Amma ko, da zan baka shawara da nace kayi haƙuri indai abinda ze iya gyaruwa ne tsakaninku ka gyara saboda i can tell you truly love that girl Afeeyah dan ban taɓa ganinka a irin yanayin da soyayyarta ta sakaka ba, kaga koda kake ganin kamar bani da zuciya akan Fatima ba haka bane ba, Ina sonta ne jikina da zuciyata ba zasu taɓa samun nutsuwa da wata mace ba bayan ita shiyasa nake jure komai saboda na sameta" "Yanzu a baka zaɓi ni ko ita wanne zakayi choosing?" Jay ya tambayeshi, yayi murmushi yace "Kai jinina ne ita kuma rayuwata ce" "Ita zaka zaɓa kenan?" Jay ya sake tambaya Ahmad yace "Aa, rayuwa ba zatayuwu ba seda jini yana kwaranya a jikin mutum kaga kenan ku ɗin dafe kuke da rayuwata, rasa ɗaya daga cikinku tamkar rasa nine" "Yanzu kenan ba zaka iya sadaukar mun da soyayyarta ba idan na buƙata?" Jay ya sakeyi masa tambayar da se bayan ta fito yayi nadamar yinta. Ahmad yayi shiru har ya fara zaton ko wayar ta katsene kafin kuma yaji yace "Zan kwanta cikin salama bayan na mutu idan har ka kasance kaine zaka maye gurbina ka tarairayi iyalina, amma fa dukda haka nasan se nayi kishi, amma karka sake faɗar haka Alhalin ina raye amma da gaske kakeyi ko wasa wannan maganar?" Ahmad ya tambayeshi. Kamar wanda ake ingizawa Jay ya sake cewa "Idan da gaske nakeyi zaka iya barmun ita?" "Ta yaya wannan zazzafar Ƙiyayyar zata rikiɗa ta koma soyayya har ta samar da kyakykyawan yanayi na kwanciyar hankali a zaman aure? Kaifa kace ka tsaneta kamar mutuwarka" Ahmad ya sake bauɗewa daga daga barin bashi amsar abinda ya buƙata, cikin yanayi kamar na ƙufula Jay yace "Toh ai baka amsa mun tawa tambayarba" se Ahmad ya saki sanyayyan murmushi yace "Babu abinda bazan iya sadaukar maka ba Ƙanina amma ina son Fatima sedai son da nakeyi mata be kai wanda nake maka ba dan haka indai ita ce burinka zan bar maka ita". Da saurin gaske Jay yace "Wasa nakeyi, kawai so nakeyi na gwada tsakanin nida ita wa kafi so amma Allah ya kiyaye me zanyi da wannan yarinyar? Ya za'ayi ma naso abinda kake so? Ai ko ina sonta na gane tilas na haƙura bazan taɓa takarar wani abu a rayuwar duniya da kai ba ko menene koda rayuwata zata salwanta a dalilinsa zan haƙura na bar maka shi". Sukayi shiru na wani lokaci, a zuciyar Ahmad lissafi yake dalilin daya kawo Jay ya soko wannan maganar? Zancen Afeeyarsa sukeyi me yasa ze kawo maganar ya bar masa Fatima kuma? Shi ya kasa tattara abubuwan ma ya gane me suke nufi. Jay kuwa sake auna nauyin soyayyar da Ahmad yakeyiwa Fatiman yake a zuciyarsa, idan har ya zama silar rabashi da ita beyi masa Adalci ba amma be cancanci Azzalumar mace irinta ba mara tsoron Allah muguwa, Allah kaɗai yasan dalilin wannan haɗi. "Yau na haɗu da matata" Jay ya katse musu shirun, Ahmad yace "Uhm, da wurwuri haka?" "Dama ya kamata ace ita ce, rabon na sja wahala ne yasa na barta kuma yanzu Allah ya sake dawomun da ita cikin rayuwata bazan bari kuma ta kufcemun ba" "Ikon Allah, ita kuma wacece ita?" "Fatiyyah Mu'az" ya bashi amsa, Ahmad ya maimaita sunan da alama so take ya tuna koya santa can kuwa yace "Fatiyyah Fatiyyah dai? Daman kuna tare har yanzu? I thought ma tayi aure itama kamar Maryam?" "Nop batayi ba, we met not so long ago" "Ayyah tana France kenan?" Ahmad ya tambayeshi, se yayi jumm daya tuna ashe ya kusa ya kwafsa kafin yace "Eh, Aa, a Abuja muka haɗu kafin na wuce ai ta koma Nigeria ta gama karatunta" "Allah ya tabbatar da Alkhairi" inji Ahmad da sam be gane kan Jay ba. Washe gari yaje gidansu Fatiyyah kamar yanda yayi mata Alƙawari, Mamanta, Babanta da duka siblings nata sun sanshi sun kuma saba tun a lokacin da suke tare dan haka da yaje normal suka gaisa sukayi hira da Mamanta kafin ta basu guri. Sister ta ce ta ɗaukesu video a wayarsa da Fatiyyan ta karɓa ta bata sanda suka fito rakashi. Fatiyyan da kanta ta shiga tiktok tayi uploading video da Caption ɗin ~FATIYYAHJAY~, shi bema san dashi ba se bayan daya koma Hotel ya kunna router yaga messages ɗin friends ɗinsa da suka sanshi da Fatiyyan a da, kowa tambayar da yake masa "sun dawo tare ne?" Wasu suce they will make a perfect couple. Daman be bi takan comments na tiktok ɗin ba shiyasa ma bega saƙon Afeeyah ba dan normally idan yayi posting turning off comments yakeyi saboda bashida lokacin dubawa, washe gari ya koma France yayi resuming field har sannan kuma zuciyarsa ba'a sake take ba. Mixed feeling yake dashi akan Afeeyah, Soyayyar da yake mata na neman ta hana tsanarta daya fara tun usuli cigaba dayin tasiri a ransa. Sabon babin da suka buɗe na Ƙauna da Fayiyyah ne yake ɗebe masa kewa. Fatiyyah na sonsa, so na gaske, a gefensa zece yana sonta amam ko rabin yanda yakejin Afeeyah har a yanzu cikin zuciyarsa bata kamo ba amma kuma yana jin a ransa ze iya auranta yanzu musamman da yake neman ruwan kashe gobara shiyasa yake iyakar ƙoƙari gurin ganin ya maida mata da kwatankwacin soyayyar da take gwada masa. Abu guda da yake haɗa shi da Fatiyyah rawar kanta kuma tun asali abinda yayiwa tarayyarsu tasgaɗo kenan yar gata ce da bata san komai ba se a tattalata a jiyar da ita daɗi, irin soyayyar da sukayi da Afeeyah wadda da acw a baya ne ko wani ya gani yana kalarta cewa zeyi baƙauye ne a yanzu ita yake muradi a gurin Fatiyyan sedau wayewarta tayi yawa nata salon soyayyar na manyan yara ne masu buɗaɗɗun ido irin wadda take burgeshi a da kenan yanzu kuma soyayya me tafe da sirkin kunya data ɗanɗana a baya ita yake muradin sake samu amma Yah Ahmad ya yi masa tsakani da ita. A ta gefen gidan Alhaji Audun Bechi kuwa rayuwa ce take ta gurgurawa yau fari gobe baƙi, Malam Hafizu ya cika maganarsa kamar yanda yace a bashi sati huɗu shida kansa ya kira Baba Alƙali ya shaida amsa ya shirya suna iya zuwa sannan. Da Alƙalin ya gayawa Alhaji Audu se cewa yayi ba za'aje ba, wai yar ta gwal ce da har se ya bawa mutane lokaci sanda yaga dama sannan za'aje neman auranta? "Kota zubardaji ce ba Gwal ba wannan ba matsalarka vace ba, ma'aurin yace yaji ya gani seka kawo idanu ka zuba yanda ka sabayi a lamarin auran sauran yarorinka, karka cusa bakinka ciki muddin ba Alkhairi zaka saka musu ba" Alƙali ya dakatar dashi. Alhaji Audu yace "Nifa kawai auran yarinyar be kwantamun a zuciya ba, tunda yana jin maganarka ka bashi baki ya nemi wata ga yayan manyan mutane nan yan Asali ko yaushe ne seda Alhaji Madari yamun maganar yarsa yace ko shi ko Jafaru..." "Ai kasan shi Jafaru uwarsa ma ta isheka shiyasa ba zaka somo dashi ba wannan kuma daya zama karkatacciyar kukar kowa me daɗin hawa dole ka nemi hanashi abinda yake so. Ni daman na daɗe da sanin bawai Binta ce kaɗai shaiɗaniya ba, hali ne ya tarar da hali kaida itan shiyasa zamanku yayi tsayi.. To ni duk ba wannan ba, zancen muhalli a ina zauna?" Cewar Baba Alƙali. Alhajin Bechi ya karkace yace "Yanzu Ahmad kake tambayar i FATIMA Kafin cikar wa'adin da Baffah ya yanka ta tattara ta koma makaranta kowa ya ganta seya tambayi me yake damunta se tace musu rashin lafiya tayi saboda yanda ta fita a hayyacinta kana ganinta kasan bata da nutsuwa sam. A bakin Anty Sauda taji cewar Baffah ya kira Kawun Ahmad kamar yanda ya roƙi su bashi sati huɗu lokaci ya cika kuma ya gama uzurin da yake a gabansa yanzu dan haka duk sanda suka shirya suna iya suje. Anty Saudan dai ta sake shaida mata Ranar Juma'a yan gidansu Ahmad zasu zo, Ranar kwana tayi tana kuka har wani zazzaɓine ya sake saukar mata ta ringa sake gwada kiran Jay da tura masa saƙonni ta kowacce kafa da ta san tana samunsa a baya amma a banza kamar me aikawa lahira. Sanda ta samu saƙon sunje har an tsayar da maganar auransu watanni shida masu zuwa kusan suma tayi dan a tsaye take ta sulale ta zauna seda aka jijjigata kafin ta farka daga suman zaunen ta kuma fasa musu kukan da tun suna bata baki da tambayar meya faru har kowa ya gaji ya rabu da ita, Maman Minal ce ta kira Anty Sauda dan taji ko mutuwa akayi a gida akan sanar mata, bata fiya zafi ba amma ranar seda ta warwarwa Afeeyah tayi mata tatas wai dan ma Badar bata nan ta tafi Kd dan har sannan Jikin Babansu se a hankali an dawo dashi dai amma duk weekend a gida takeyi Friday basa komai ranar take tafiya ta dawo Sunday bata ma san da zancen kawo kuɗin ba yanda Afeeyar bata gaya mata ba itama yanzu ta dena damun kanta da matsalarta, ta dai gaya mata yanda suke ciki da Jay ta kuma jimanta mata ta sake nusashsheta abinda ake mata hasashe kenan sanda suke ce mata karta saki jiki dashi shikenan ta kama kanta ta rabu da ita tunda bata ga alamun zata hankalta ta gane Allah guda bane domin har sannan cewa take Ahmad ne ya janyo mata zuwansa ne ranar ya ruguza komai. Sati tsakanin zuwarwa Ahmad tambaya akaje na Jay, a bazata batun ya zowa kowa harda Ahmad da ita kanta Hajiyar seda aka saka ranar zuwa taji labari a bakin Alhaji Zakariyyah, data zabura zatayi bala'i se kuma tayi laƙwas kamar Tarwaɗa taji gishiri ta shiga zare idi dajin Yar wacce za'aje tambayowa Jay auranta. Se gani kawai Alhaji Zakariyyah yayi ta fashe da kuka, a zatonsa kukan bata sani bane kamar yanda ta tasammayin tijara a farko seda yaji tana cewa "Ashe dai burina ze cika, Jafaru ze farantamun ya wanke mun takaicina Allah na gode maka kace dai ya gidan gwaunan bankin Najeriya ce ko ubana?" Zakariyyah murmushi kawai yayi dan yanda Hajiyar ta keyi kamar wata yarinya, daya tana neman ta ishe shi da tambayoyi ya fice ya barta ta shiga bige bigen waya tana sanarwa su Turai abin Arziƙin daya samesu. Ahmad kuwa Baba Alƙali ne ya kirashi yace ya shirya zasuje Abuja neman auran Jay, yayi mamaki, ko awa guda basu cika da gama magana da Jay ba amma beyi mentioning masa zancen auran ba koda yake duk Jay ɗin ya canza ya kuma kasa gane kansa balle abinda yake damunsa. Daya samu labarin shiru yayi be ce masa komai ba, a ransa yayi murna zasuyi aure lokaci ɗaya kamar yanda birinsu yake tun suna yara. Juma'a Baba Alƙalin yace zasu tafi su kwana a can Asabar idan sun gama abinda ya kaisu su juyo a ranar shi kuma yayi niyyar tafiya Zaria gurin Fatima wadda tun bayan Baikonsu Al'amura suka fara sauyawa a tsakaninsu, a yanzu base ya kirata ba takan kirashi da kanta dukda dai babu sakewa ko soyayyar da yake fatan samu daga gareta amma a hakan shi ji yake kamar yafi kowa farin ciki ba kuma shi da wata damuwa dan haka ya kirata ya sanar mata da baze samu damar zuwa ba zasuje Abuja neman ma Jafar Aure, bata nuna taji ba balle ya saka ran zata sakawa lamarin Albarka. Ita kuwa sunan Jafar daya ambata mata tamkar fami ya zamar mata kan nata Jafar ɗin da har yau bata dena kukan rasa shi ba, dangana tayi ta ta kuma buɗe zuciyarta ta fahimci abinda aka daɗe ana nusashsheta amma ta doɗe zuciyarta da idanunta taƙi fahimta a yanzu ne ta ke godewa Allah domin nacin Ahmad ya mata rana domin da ace ya barta tamkar Jafar bata san wa zata kama ba. Ita da kanta ta yarda haɗuwarta da Jafar da soyayyarsu har zuwa rabuwarsu haƙƙin Ahmad ne, ta godewa Allah daya bata damar gane kurenta harya yasa tana da sauran lokacin da zata iya gyarawa, sedai aka ce So ɗayane, har yau har gobe tana son Jay, bata sani ba ko se ranar data tabbatar da ta zama mallakin waninsa sannan zatayi jana'izar soyayyarsa ta binneta badan ta mutu ba. Baba Alƙali, Alhaji Babangida, Alhaji Abdullahi, Zakariyyah Bechi, Naziru Bechi, da Ahmad Bechi da se Aminan Alhaji Audu na ƙut da ƙut Alhaji Mu'azzamu da Alhaji Aliko sukaje neman auran saɓanin na Ahmad da Baba Alƙalin ne tareda Alhaji Abdullahi sukaje, ya sanarwa Alhaji Babangida lokacin ya bashi uzurin ranar ze tafi Umarah dalilin daya saka ba'aje dashi ba. Harka akayita girma, aure ake shirin yi irin wanda ake kira ƙwarya tabi ƙwarya. Shima kamar Ahmad watanni shida aka saka, suka dawo Kano niƙi niƙi da kayan arziƙin da aka haɗo su dashi. Hajiya bata iya bacci ba, tun daren Juma'a take dokawa Naziru kira daya gaji da amsa ma yayi restricting number, yanda kasan zatayi tsuntsuwa ta tafi can haka tayi ta kasa zaune ta kasa tsaye har seda suka dawo abubuwan da suka zo dasu suka gigitata haka ta fita tsakar gida tana taka rawar murna tareda sakin habaici wa Momy da ko biskit ba'a kawo mata daga gidan Surukan Ahmad ba sanda akaje neman aure sun dai kawo tukucin naira dubu hamsin wadda aka cire musu daga dubu ɗari biyar da suka kai kuɗin aure da saka rana. Shima Jay ɗari biyar ɗin aka kai dukda Hajiya tace tayi kaɗan Baba Alƙali dashi ya bada kuɗin daman yace haka yayi niyya kuma baya isa ta saka a ƙara ba ko Zinariya ze auro. Bayan sun dawo Ahmad ya kirashi murya a sake sam be riƙi cewar Jay ya zame shi daga abubuwa da yawa da suka shafi rayuwarsa a yanzu ba ya shiga tsokanarsa da Ango Ango. Seda suka gama barkwanci kafin yace masa "Amma fa na ɗanji babu daɗi, ni ya kamata nayi breaking news na auranka bawai naji labari daga sama ba, amma ya wuce ,I'm happy for you, I'm happy for us, at long last mun kusa mallakar muradan zuciyarmu" "Ka kusa mallakar muradin zuciyoyinmu nida kai dai" Jaya ya raya a ransa a fili kuma ya marairaice yace masa "Kunya nakeji, bansan taya zan gaya maka ba". Dariyar da Ahmad ya ringayi har seda ya sauka daga kan kujerar Momy da yake zaune, seda yayi me isarsa kafin yace "Amma bakaji kunyar kanka ba da kake faɗar wannan maganar? Ni zakace kana jin kunya ba zaka iya gaya mun za'aje neman maka aure ba? Ai shikenan amma ko na ji tausayin Afeeyah ne sunanta ko? Allah kaɗai yasan yanda zataji idan labarin nan ya iske ta". A fusace Jay yace "Allah yasa ya zama silar Ajalinta ma kowa ya huta Annamimiya me fuska biyu munafuka kawai" "Jafar me yake damunka? Me yasa baka da magana seta fatanma wani mutuwa haka kawai san kana da matsala dashi? Babu kyau tsananta Ƙiyayya, ina jiye maka tsoron kar a jarabceka da abinda kafi ƙi a rayuwarka wlh seka gwammaci kida da karatu" Ahmad ya faɗa in a serious tune se Jay yace "Na nawa kuma? Jarabta ai an mun sedai nayi addu'ar Allah ya bani ikon cinyeta kawai amma batun wai wani waye tuni an wuce gurin" "To karkayi saɓo Malam nikam se anjima, daga kira muyi farin ciki kar ka jawo abinda rayukanmu zasu ɓaci, haba, kanka aka fara kasa Namiji a neman aure da zaka ɗauki abu da zafi ka hana rayuwarka sakat? Duk ka canza daga Happy Jay ka koma wani Aggressive person akan me? Ita rayuwa daman ai tilas akwai samu akwai rashi ba kuma dole duk abinda mutum yaso ace ya same shi ba. Nasan zafin So amma idan ka kasance me neman zaɓi da yardar Ubangiji cikin dukkan lamuranka koda zakayi fushi da wani abu daya sameka a rayuwa ya zama na ɗan lokaci, Allah ya fika sanin dalilin daya saka ya hakana samun wannan abun naci da dagiyarka se ta janyo maka abinda zaka zo kana dana sani da nadama mara amfani a rayuwarka se Allah ya barka da abin yaga iyakar gudun ruwanka. Ga rabonka nan ka dace da ita, kayi addu'a Allah yasa ta zamo maka sanyin idaniya macen da kowanne Namiji yake fatan samu" Da "In sha Allah" Jay ya amsa masa shikenan aka gama wayar saboda ya sake goga masa gishiri akan rauni. Tun haɗuwarsa da Afeeyah yake hasaso yanda wannan ranar zata kasance musu, ranar da za'ace yarjejeniyar aure ta Ƙullu tsakaninsu, yaci burin zuwan lokacin har party yace ze shirya se gashi tazo masa da wacce be taɓa koda hasaso zata zama matarsa ba. Gaba ɗaya ma yanda abubuwa suke faruwa shi baze ce ga shi ba kawai dai komai yana faruwa ne tamkar shirin film kamar wasa yanzu an tasarma zuwa No going back stage "Ya rayuwarsa zata kasance da watan Afeeyah???" Tambayar da ke kara kaina cikin zuciyarsa. Shirin biki ya kankama a gidan Alhaji Audu Bechi. Shiri akeyi tamkar a wannan karon ne za'a fara aurar da Ɗa a cikin gidan dukda shirin tsakanin Yayan cikin gida ne na waje dai nasu ido. Hajiya Binta tamkar zata haukacw saboda yanda ta azawa kanta tashin hankali akan wannan aure da Jay zeyi, Turai da Hajiya Zainab ne kan gaba akan shirin Komai, su suke haɗa Lefe, kuɗaɗe masu nauyin gaske ya aika musu na haɗa lefen. Me hali baya fasa abinsa, duk irin zumuɗi da zirgillin da Hajiya takeyi akan shirin Bikin da aka zo batun haɗa lefe taga uban kuɗaɗen da ake narkawa domin Turai tsakani da Allah ta tsaya take abun nan Hajiya ta rikice tace bata san zance ba ta yaya za'aje ana siyan Lesuna na dubu dari biyar zuwa sama ai Almubazzaranci ne. PAGE 25 "Ga Lesunan a Legas nan masu kyau dubu Hamsin dubu sittin duk dai Ƙure gayu ai sun isheta" Hajiyar ta faɗa, saboda takaici Turai bata iya bata amsa ba se Hajiya Zainab ce tace "Haba Binta, a lefen Jafar za'a saka Lagos Lace? Ke kin taɓa ganin yarinyar da Ƙaramar sutura balle ki ringa lissafo mata Lashin dubu hamsin dubu sittin? To ai wlh ko Ahmad da yake shirin auro ɗiyar Talakawa Lefe Hajiya Aisha ta zage tana haɗawa na garari. A gurin *Maryam Hassan 07088361522* fa take siyan Laces matar nan kuma indai Lashi ake magana bata kawo na banza dama kin so gaskiya ne se kice a tafi gurinta a samo Lasuna na fita taro a ci da buguzun dan gasu nan kala kala iyakar kuɗinka iyakar shagalinka" "Kuma suna kaiwa nawa?" Binta ta tambaya tana gyara zama, Hajiya Zainab tace "daga Ƙana dubu goma sha haka har zuwa ɗari da ɗoriya" "To a samu yan Hamsin sittin ɗin a gurinta kawai a mayar da waɗannan wannan Almubazzaranci har ina ai se Allahya kamamu" Hajiyar ta sake faɗi. Data ishi Turai seta dena ma kai mata kayan idan an siya tun randa tace zata kwasa da kanta taje a musanyo tunda ita taƙi mayar da hankali. "Ai gara a rage kuɗin ko Gona ce a siya masa tunda shi baya maida hankali gurin tara kadarori yanzu da zeyi aure ai yaci ya fara" Hajiyar ta faɗa, Turai tace "Dake shi ba irinki bane ai da baki da buri sena ki tara baki ci ba baki bawa wasu sunci ba gara ki ajiye su yi diddiga a share". Ta gefen Momy ma shirin biki suke da yan uwanta babu kama hannun yaro, lefe gangariya suke haɗawa suma Ahmad ya saki bakin Aljihu sosai suna abinda ya dace tun bayan daya tabbatar da Alhaji ze basu gidaje wanda seda akayi Ƙwarbai da Hajiya Binta Alƙali yazo har gida yayi mata cin mutinci kafinaka samu magana ta mutu. Tun bayan daya wa Alhaji Audun zancen ya bawa Ahamd gida lokacinma maganar Jay bata tashi ba bece masa komai ba, ana kai Kuɗin auran Jay Hajiyar ta shiga ta fita akan ai se Alhaji ya bashi gida dukda dai ba zama zeyi ba amma ya zama idan yazo yana da muhallin da ze sauka da iyalansa. Ta kwarkwanceshi tas kamar kuma yanda aka saba yabi ta tatan yace Naziru ya duba masa duk gidan da yayi ya shiga ya zauna labari na isa kunnen Alƙali ya wanko Ƙafa yazk har gida yayiwa Audun tatas yace "Wato ana zatonkura tayi lafiya ashe kama kan bakanka na nuna banbanci a tsakanin Yayan cikinka ko Audu? Shi Ahmad Agolansa Aisha ta kawo maka da tunda mukayi maganar gidansa da kai baka ce komai ba se Ɗan da Binta ta haifa shi ne cikakken Ɗa a gurinka da zakayi masa abinda ya dace uba yayi? To ahir ɗinka, karka kuskura ka lalata tsaftatacciyar Alaƙar da ita kaɗai tayi saura a gidanka, karka janyo abinda ze kawo rabuwar kai tsakanin Ahmad da Jafar, karka yarda Ahmad ya fara tunanin ka faifita Jafar akansa domin muddin ya juya maka baya ba zakaji daɗi ba, duk wata sa'ida da salama da kake ji a cikin gidan nan yanzu dalilin yaron nan ne, shi yakw faɗi tashi gurin ganin gidanka ya saitu to wlh karka bari komai ya lalace". "To ai uwarsa tace ya fara gini har ya kusa kammalawa sun siyi fili shida Ɗan uwan nasa ya fara gina nasa tunda shi wancan ba shiga ciki zeyi yanzu ba" Alhaji Audu ya faɗa tamkar duk beji kashedin da Alƙali yayi masa ba. Cikin takaici Alƙali yace "Ai saboda shi ba me matacciyar zuciya bane kuma be dogara da kowa ba shiyasa ya tsaya da ƙafafunsa yake abubuwansa da guminsa, to a matsayinka na ubansa nace ka kira Ahmad ka bashi damar ya zaɓi duk gidan da yayi masa daga jerin gidajenkana Kano ko duk State ɗin da yayi ra'ayi se ya zaɓa sa'annan ka baiwa Jafar dama shima ya ɗauka dominAhmad na gaba dashi, umarni ne ba shawara ba idan kuma ban isa ba se in sani" yana gama faɗar haka ya tafi abinsa dake da sauran burbuɗin girma da mutunchinsa da yake gani se kuwa gashi yaji maganar. Washe gari ya cewa Ahmad yaje bayan Sufi mart, da akwai gidaje da aka gina an gama komai abinda ya saura ba shida yawa, fentin katangar waje ne se saka kayan wuta wanda komai yana nan a ajiye daman. Gidaje ne gida biyu aka gina masa su, gini badai gini ba, duk sanda ya zagaya yaga gidan nan har wani nishaɗi yake ji a ransa se yaji kamar ya samo wata yar shawalwalar yarinya ya cike ta huɗu da ita ya samu inda ze ringa zuwa yana hutawa da kayaniyar duniya shine fa da Hajiya ta samu labari ta ringa tashin hankali tana tijata akan me za'a bawa Ahmad gida kuma wannan gidan da ita da yayanta duk bin Ƙwaƙwƙwafinsu basu san dasu ba ba'a isa ba ta ringa rashin mutunchi shi kuma Alhajin kamar wanda ta ɗaurewa baki ya gagara cewa komai be dai ce ya fasa kyautar ba kuma bece ba haka ba da abu yaƙi ci yaƙi cinyewa Hajiya Rabi ta kora Hajiya Balaraba a waya ta ce dan Allah ta cewa Alƙali yazo gidansu babu lafiya saboda Hajiyar shiga tayi har falon Momy tana zaginta tana cewa seta warware tsafin da taje tayi daya saka Alhaji yake ɗaukar abubuwansa masu Daraja ba tareda shawara da kowa ba ya mallakawa Ahmad. Abinda be taɓa faruwa ba se gashi Momyn ta biye mata suna faɗi in faɗa Hajiya har tana cewa zata daketa tace da rabon idan batayi kwanan Kabari ba yau zatayi na Asibiti idan kuma tana musu ta gwada kai hannu jikinta. Muryoyinsu har Baban Compound ga Alhaji baya nan babu kuma wani takamaiman tsayayyen Namiji da ze iya tsawatar musu seda Alƙali yazo ya tarasu yaji ba'asi nan ya buɗrwa Binta wuta ya mata kaca kaca yace tunda Ake fifita Yayanta ana musu abubuwa waya taɓa ɗaga ido ya kalla se itace da hassada ta cikawa zuciya bata da burin sedai ita ko Yayanta su mori Audu shine yasa zatazo tana tada masifa akan dukiyar da ba ta ta ba "Amma ubane sila" ta faɗi abinda ta saba duk sanda aka sako zancen dukiyar Audu. Alƙali yace "Allah ne ya bashi ubanki ne sila amma da guminsa ya tattalata harta kai haka ko kuwa taki ya ringa zubawa abinda uban naki ya bashi yayi ta yaɗo yana ƙara yawa? Ke matsalata dake bama mutum ya tsaya yana magana dake ba ba fahimta zakiyi ba dan kin rigada kinci kai inyi miki ta yan zamani, to wlh ko ki bari hankali ya kwanta ko kuma ayi tashin hankalin na gaske. Yakubu, Zakariyyah da Naziru duk se sun fita daga gidajen da suke zaune tunda na Audu ne na sani sarai domin koda sakarai ne amma be manta ni Ɗan uwansa bane baya ɓoye mun komai daya ke ciki, su fita idan yaso ku jira idan ya mutu aka raba gado kowa seya amfana da rabonsa" ya mata fes ta fita tana kuka sannan ya juya kan Momy itama ya mata faɗan biyewa Hajiya. "Ƙureni tayi, amma nayi nadama kuma bazan sake ba in sha Allahu" ta faɗa ya sallameta ya tafi shikenan magana ta mutu amma Binta bata haƙura ba har seda aka bawa Jafar gidan da yake jere dana Ahmad ɗin dan dama guda biyu ne dukda sun rigada sun zaɓar masa wani katafare a cikin Nasarawa GRA wanda ya shallake zaman Matashi me mace ɗaya dai Mansion ne danƙarere har an canza takardu shikenan Jay ya ci tudu biyu abinsa. Da taso mugunta se cewa tayi wai gidajen sun zarce ya basu kyautarsu sedai Aro shida Jafar ɗin duk wanda yake so ya mallaki nasa ya ringa biyansa a hankali dan baze yuwu ya ringa kwashe kadarorinsa yana kyauta dasu ba babu Adalci tunda beyiwa sauran Yayan ba yace mata Toh. Kwanaki na tafiya sati na wucewa a kace duk abinda aka sakawa rana ze zo se gashi anci watanni uku lokaci yayi su Fatima sun kammala makaranta wanda kuma yayi daidai da wata uku kenan saura kwanakin auransu da aka saka. Zuwa sannan za'ace an samu cigaba sosai tsakaninta da Ahmad domin tayi surrender, takanyi iyakar yinta gurin kwatanta bashi kulawar da ya kamata ace ya samu a gurinta. Dukda cewar Ahmad ɗin bana da bane domin shima ya canza, ya rage rawar jiki akanta ya koyi kamewa da jan aji. Wannan lako lakon da maida kansa kamar wani sakarai da yakeyi mata ya dena, a yanzu idan ya kirata ta bashi uzurin tana wani abu ze barta amma fa baze sake kiranta ba har se idan ita da kanta ta kirashi sannan zasu cigaba da abinda suke kai. Sannan yawan zuwa gidansu akai akai da yakeyi a baya shima ya dena, koda ta dawo gida a yayi ƙoƙari jaye sau biyu cikin sati, tun abin baya damunta harya fara ci mata rai ga kwanakin aure suna matsowa tunani takeyi karfa ace lambo lambo Ahmad ya mata a baya, yanzu da ya tabbataemr da zata zama tasa shine ze fara fito mata da true color nasa idan ya zamana bayan sunyi aure yace ze rama irin cin kashin data masa tsayin shekaru uku ai ta shiga uku ta lalace bata hango inda zata tsoma kanta taji sanyi ba. Har Badar tayiwa maganar akan sauyin Ahmad "Badar tsoro nakeji kar ya ƙullaceni jira yakeyi daman ya samu damar da ze rama abinda na masa a baya" "Haba dai ni nasan Ahmad mutum ne me kyakykyawar zuciya baze taɓa kwatanta rama sharri da sharri ba, kawai dai nasan ya fahimci keɗin zuma ce seda wuta saboda idan ya ɗauke miki ai kina shiga taitayinki ki nemoshi kuma gara ya fara shata miki layi karki zata idan kukayi aure haka zakije ki cigaba da masa shirmen da kika saba gara ki sani da da yanzu akwai banbanci Mijinki yake shirin zama na random saurayi da kika sani a baya ba, amma wlh da ace ma da gaske tama ki yakeyi da naji daɗi domin kin azabtar da bawan Allahn nan koda yake Allahnsa ya rama masa kiyi addu'a Allah yasa abin ya tsaya iyakar haka" amsar da Badar ta bata kenan. Biki ya rage sauran sati huɗu aka kai lefe kowanne gefe, na Jafar aka fara kaiwa Akwati iyakar ganinka gasu nan shaƙe da kaya saitin gwal biyar aka zuba wanda tsofaffin na Binta wanda Turai ta yi yaƙi ta bayar dasu aka narka akayo mata sababbin designs ta sake jaɓe su ta ajiye a ciki aka ɗiba aka bata kuɗin rabi kyauta dai haka akayi mata fahin kayanta. Tsabar zirgilli cewa tayi da ita za'aje dukda ba can Abuja aka kai kayan ba Adamawa aka kai can ne Asalin garin mahaifin Fatiyyan dan auran ma acan za'a ɗauro shi daga ƙarshe dai wayo aka mata aka gudu aka barta ai kuwa har kuka tayi, a waya Lawan ya ringa nuna mata videos dake trending dan su Fatiyyah fa bada wasa suke ba ita da Ƙawayenta sun gama gigita Social media da zancen Auran tun ana saura wata biyu aka fara save the date dan ma Angon yaƙi bada haɗin kai yanda ya kamata shiya ragewa abin Armashi dan cewa yayi ma se biki ya rage sati ze dawo da ƙyar ya maida shi sati uku. Kwana biyu da aka kai lefen Jay aka kai na Ahmad, Lefe na mutunchi shima dukda babu tarkacen akwatuna kamar na Jay amma babu wanda ya isa ya raina lefensa ita kanta Hajiyar duk hassadarta da aka buɗe musu suka gani seda tace "Ai daman Amadu badai zuciya ba ita dai yar Bakanike shar da ita toh Allah sa karsu kai kwari su karyar a samu na siyan kayan ɗaki, daman idan tazo kafi diddigi kai ka ɗauki hoton komai yanda ko tsinke ya ɓace zaka gane" kowa ya mata shiru dai ba'a tanka taba. Shima dai da aka tashi kaiwa guduwa akayi aka bar Hajiya, Hajiya Ummu Yayarta da suka zo kai Lefen Jay basu koma ba dasu aka tafi kuma ita tace acewa Binta seda Yamma za'aje tunda kusan duk wanda za'aje dasu a hanya za'a haɗu su da suka tashi fita sukace mata zasu shiga Kasuwa ne shikenan aka barta a gida tana saƙa irin abinda zatayi idan sunje, ta ƙudiri a ranta seta kunyata Aisha, ko za'ayi auran nan ba zata bari tayi shi cikin farin ciki da daɗin rai ba se gashi tana can tana saƙa mugun ƙulli taga ana shigowa da Ruwa da Lemo da Farantan kayan snacks ana kaiwa Ɗakin Momy. Haka taje ta dirawa Alhaji Kuka wai Aisha ta wulaƙantata an kai lefen Ahmad banda ita bayan ita a na Jafar sune kan gaba cewa akayi ita zata wakilceta shi kuma, besan ya akayi ba be kuma bi ba'asi ba ya kira Aishar ya mata tatas akan me zatayi haka ta karya masa doka bayan ya kafa cewar duk sabgar Ɗa ko Yar wanda ta tashi sauran Kishiyoyinta ne zasu wakilceta a gurin ita dai bata tanka ba domin tayi rantsuwar ba zata bati Binta taci galaba akanta ta hanata jin daɗin auran sanyin Idaniyarta ba. Rabon da Afeeyah ta shiga Social Media harda WhatsApp kuwa ta manta, fin watanni uku, kai tun bayan data yarda da gaske Jay ya barta ta cirewa kan lasisin duba Social Media ta sauke komai daga kan wayarta ta zama sedai tayi kira a kirata kawai saboda bata so taci karo da wani abu daya dangance shi, ko me suna Jafar aka kira a kusa da ita a ranar se tayi kuka balle kuma tun mugun ganin da tayi shida wannan yarinyar daya haɗa sunansa da nata har ya iya posting nata a private account ɗinsa ta tabbatar dagaske ne ya barta. Dalilin shirin bikinta Badar ta uzzura mata seta bude WhatsApp da IG, tuntuni ta buɗe musu group acan anan suke ta shiri da sauran ƙawayensu amma babu Amarya a ciki, data rasa uzurin da zata bayar se tace bata da waya. Ita ta fitar da Ankon Yini da Kamu wanda zasuyi na gidansu Ahmad yace zasuyi dinner wannan mutum goma suka ware masu Anko dan karsuyi yawa musamman da bikin biyu ne, bisa uzzurawar Badar da take cewa "You are getting married in to Bechi Family Afeeyah bafa wani karabitin Family bane ya kama muma mu motsa asan da anayi" Tilas ta koma kan Network ta saita komai da dare ranar bayan sun gama waya tana gaya mata mitar da mutane suke tayi ya za'ayi ace ana ta shiri ba'ajin ta bakin Amarya kuma shine ta gaji ya koma. Bayan sun gama maganganunsu a WhatsApp harta kwanta zuciyarta ta ringa Azazzalarta akan ta shiga IG, ta tashi ta kunna Data ta shiga, A jejjere duka bloggers da take bi taga sukayi posting hotonsu, ta ringayin ƙasa idanuwanta kamar zasu cire su diro Ƙasa, jikinta tamkar mazari haka yake rawa gaf gaf wayar ma Ƙoƙarin suɓuce mata takeyi, garin babi zafi sam domin yanayin sanyi ya fara shigowa ita da yake kumamace ma har safa ta saka saboda sanyin data ji bayan tayi Alwalar Isha'i se gashi lokaci gida Zufa ta wanke har kayan jikinta na naso. Ta dinga duba hotunan kamar zararra ta shiga wannan page ta fito ta shoga na Ƙasansa domin kamar da gayya ake posting abun saboda ta gani. Su biyun babu wanda kamanninsa ze ɓace mata duk wuya duk daɗi haka kuma ba zatace gizo bane ko kuma Ƙwaƙwalwarta ce bata fassara mata daidai ba. Dadai taga kallon pictures ɗim baze kaita ba ta shiga duna caption ɗin da yake akan duka pages ɗin, *_"Latest grooms in town, the Bechi brothers"_*. Comment section ta shiga domin har sannan bata gama tantance abinda ta karanta ba, ta ringa scrolling yau idanunta sun zama kamar wasu scanner a seconds take karance abinda aka rubuta, ashe ba ita kaɗai ce cike da mamaki ba, kusan tambayar da kowa yakeyi 'Daman Jay Ɗan Bechi ne?' Su nasu iyakar mamaki ne sedai ita ta shiga gigita, tashin hankali, ɗimuwa kai babu abinda ma bata shiga ba, Jay shine Jafar ɗin Ahmad kuma shine Jay ɗinta? Dishi dishi take ganin screen ɗin ma a zaune take amma juwa ke neman kwantar da ita. Ta shiga call log, she needs to call someone that will wake her and tell her that it was all a dream abinda ya faru a baya ba gaskiya bane ko kuma abinda take gani a yanzu shine mafarki ba gaskiya ba. Rikicewar da tayi ta saka ta kasa fahimtar kira ya shigo wayarta wanda Badar ce take kira, a kusan lokaci ɗaya suka ga hoton, Badar tasan Jay zeyi aure domin dai duk me shiga Social media tuni ya haddace ƙirgen Kwanakin auran Jay da suka rage wanda ze kama rana ɗaya dana Afeeyah, yana daga dalilin daya saka bata damu sosai da barinta hawa social media ba domin tasan sanin abinda yake faruwa ze iya rusa shirin da sukeyi na ganin sunyi bikin farin ciki. Ko yau WhatsApp tace tayi downloading ita kanta bata san sanda ta shiga kiran Afeeyar ba bayan data ga wannan twist ɗin domin a rikice take, Jay Ƙanin Ahmad ne kenan Afeeyah tayi soyayya da Yaya da Ƙani tana sane ko kuwa Arashi aka samu abinda take so ta tambayeta kenan. "Afeeyah Ahmad and Jafar are brithers yanzu na gani a IG" "Badar Ahmad and Jay are brothers tell me this is not true Badar ki cemun hallucination nakeyi" Afeeyah da Badar suka haɗa baki gurin faɗi kana iya tantance tashin hankalin dake cikin muryoyinsu karma ta Afeeyah taji labari. END OF BOOK 2