Posted by UMMU-ABDOUL on NOVEMBER 1, 2016 [3:36pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 1 Babban falo ne wanda aka kawata shi da kayan more rayuwa.captain Sulaiman mamallakin gidan kwance kan doguwar kujera,ya ta faman danna waya,dogo ne,wankan tarwada mai kimanin shekaru 38 a duniya,Allah ya ma sa kyau da farin jini matuka domin kuwa kallo daya za ka masa ka tabbatar da baiwar da Allah ya bashi,ance mutum tara ya ke be kai goma ba,toh shi captain sulaiman abunda ya hana shi cika goma shi ne bin matan banza da karuwai.can gefe guda kuma Captain Aliyu ne aminin Captain sulaiman kwance a kan carpet,ya yi matashi da hannun sa ya na karanta littafi mai suna don’t be sad.Captain Aliyu sabanin captain sulaiman fari ne sol,dogo mai tarin suma irin na larabawa,ya na da kyau ga kyan hali da nutsuwa. Captain Aliyu ya nisa gami da duba agogo,a razane ya tashi zaune tare da fadin oh ma God,oh good God ashe haka lokaci ya ja Sulaiman?Captain sulaiman ba tare da ya kalle shi ba ya ce toh ni ina ruwa na da lokaci officer? Captain Aliyu ya gyada kai haka fa,mu da mu ke da iyali mu muka da mu da lokaci,su tuzurai ko sai dai a tabin yarima a sha kidamtsw Captain Sulaiman ya ja tsaki ka ga kar fa ka takura min,saban shiga kawai,dan ka yi aure kowa sai yayi?an fada ma da ka yi auren fi na jin dadi ka yi?duk abunda ake ma ina samu ni ma,sa ma ni ina da damar zabi,yau inna sami fara,gobe na dau baka,jibi na dau leba..Allah ya sauwake ma,haka dai za ka kare,wlh rabin dadin da na ke ji ba ka samu mu,ko kwata ma,ka yi aure ko ka sake hali pls,Captain suleman ya dubi Captain Aliyu wani hali kenan?Captai Aliyu ya murmusa kwartanci.captain sulaiman ya koma ya kishingida ai Aliyu ko na yi aure ba zan dai na ba,ba ka san tuwo tuwo ne ba,amma na makota ya fi sweet,ya ja tsaki gami da mikewa tsaye,duk randa ka ji ka a kabari ka dai na…ina!captain Sulaiman ya katse shi,ai kafin lokacin na shiryu.ba a yiwa Allah wayo dan ubankaya doki kafadar sa,captain Sulaiman ya na sosa in da ya dake shi ya ce dan Allah ka gaishe min da matar mu,matar ku kai da wa? Captain Sulaiman ya kanne ido ni da kai abokinaAllah ya sauwake,jauda mata ta ce ni kadai…haba ai na zaci abun ka abu na ne,matar ka mata ta ce…ba tare da ya kara sauransa ba ya wuce zai fita,ka ci gaba da fadin haka watarana sai na zubar ma da hakora,ya fita ya doka masa kofa,Captain Sulaiman ya kwashe da dariya,dama abunda ya ke so kenan,dan ya ga Aliyu ya tsani ya kira sunan matar shi da matar mu,shi ko tin da ya gane ya sami mafaka….. [7:03pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2:Jauda sunana,Jauda Mansur Alkasim,Allah ya yi wa Mahaifina marshal Mansur Alkasim rasuwa kusan shekaru goma da su ka shude,Alhamdulillah Allah ya rufawa bayan mahaifin mu asari,sam ba mu wulakanta ba.Mu biyu ne gun iyayen mu,ni da kanwata hauwa wacce mu ke kira jidda.maihaifiyar mu ta ba mu tarbiya sosai da kuma taimakon General Abubakar Wali wanda yake almajirin mahaifiya ta sanda ta na amarya sanadiyyar mutunci da sabo mahaifiyata ta sa mahaifi na ya sa General a makarantar sojoji,hakanan nan har ya kammala karatun sa ya zama cikakken soja. Ni Jauda baka na ke,amma irin wannan bakin mai kyau,ina da manyan idanu dan shi ya fi komai girma a fuskna,ina da gashin idanu zara zara gami da gashin gira.hancina ba wani tsayi gare shi sosai ba,amma dai ba yabo ba fallasa ya na da kyau,haka zalika zagun baki.ban da tsayi sosai amma kuma ba gajera ba ce ni,ba na daga cikin matan da ake kira busty,amma ina da hips matuka da mazauna dan wani sa’in kawaye na kan tsokana ta da cewa da ga sama yar tsut,daga kasa ko kamar wacce za ta kai tusa birni ko ma wasu suce anya ko Jauda wannan kaya na ki be rinjayar ki? Da taimakon General aka daura min aure da captain Aliyu,wanda ya ke aminin kanin matar sa Anty Sa’a,wato Captain Sulaiman. [8:32pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 3:Sanye na ke cikin rigar kakin mijina,bisa da al’adata duk safiyar Allah na kan sa rigar shi ta kaki tare da p-cap din shi yayinda zan shiga kitchen.tin yana mita wai ina ci ma kaki fuska,na rasa inda zan na sawa kaki sai kitchen,har ya zo ya hakura domin kuwa duk da kakin ya min yawa nesa ba kusa ba,ya kan saukar min kasa sosai har ya dan dara gwiwa na,hakan ya sa ban damuwa na sa wando ko zani,gashi hannun rigar ya fi karfi na,haka na ke nadewa abuna.hakan ba karamin kyau na kewa oga ba dan so da yawa da ya ganni cikin shigar sai ya daga ni ya dire wai ina masa kamar yar tsana Dining area na ke,na gama hada komai na brkfast tsaf ina shirin shiga na duba oga sai ga shi ya fito sanye da kakaki,abin ka da farar fata,yamasa kyau ga wani kwarji da Allah ya ba shi.Ya ware hannun shi come hia my baby,na karasa da sauri ya daga ni ya dare,dax my baby,ya mini side hug mu ka karasa dining table,kamar yanda ya saba ya ja kujerar da zan zauna baya ya kame gami da sarawa,ya ce my lady first.Na murmusa gami da zaunawa ya yinda ya sauke hannun shi,shi ma ya ja tashi kujerar ya zauna. Na dube shi cikin jin dadi Wallahi ina san ka ogaya dara har sai da hakoran sa su ka fitoi love you more madam.ka tashi lfy? Ya ce lfy lau,gashi na ma so na makara ba ki tada ni ba,na rangwabar da kai bayan ba in na tada ka da wuri zalina ka ke ci..oh toh na gane in da ki ka dosa yarinya,ni ba babu inda na dosa oga,da na ga zai maida maganar wani abu na yi saurin janyo plate kar ka kara makara sosai,maxa mu ci abunci,ya lakaci hanci na sarkin wayo. Mu na cikin wannan ya na yi kwatsam kamar daga sama mu ka ji sallamar Hajiya babar Aliyu,biye da ita Indija ce yar kanwar hajiya rike da jakar Hajiyar.Hajiya ta shigo a fusace shin ba ki amsa sallama ne?a rikice na mike tsaye ganin Hajiya a kan mu,ina fadin Hajiya sannu da zuwa,yanda na ga ta bini da kallan banza ya sa na tuna kafafuna duk a waje su ke na yi maza na koma na zauna.Aliyu cikin ladabi ya ce Hajiya yi hakuri,ba mu ji ba ne..mstw ta doka tsaki dama ina za ka ji wannan mayyar ta ka sa ta tsare,wai haka ka lalace?aikin ma ba ka fita da wuri Ali?ka na soja?Cikin ladabi ya ce yanzu na ke shirin tafiya,ya durkusa Hajiya ina kwana?lfy,ya kamata a zo a tafi dai.Ni ma na durkusa p-cap dina a hannu na ce Hajiya ina kwana? Ahasale ta ce da ban kwana ba kya ganni? Na dada sun kuyar da kai.cikin yanga Indija ta ce ya Aliyu ina kwana,lfy shine amsar da ya bata ba tare da ya kalli inda ta ke ba,na lura ya kai makura wajan bacin rai.cikin rawar murya na ce Hajiya ku zauna dan Allah na kawo mu ki brk fst..ke da dallah yi ma mutane shiru,har kin kai matsayin da zan zauna na ci jagwalgwalan ki da ki ke barbadewa da magani?cikin nuna rashin jin dadi Aliyu ya ce haba Hajiya ta,me ya yi zafi haka? Hajiya ta kame baki ikon Allah,za ka rama ma ta ne? Ya kau da kai Allah ya ba ki hakuri.ta ce amen,dama hutu na kawo indija,sai a sannan ya dago ya dubi Indija haba Hajiya ta,ya katuwar budurwa kamar indija za ta zo hutu gidan mutane?Indija ai ta wuce wannan stage din…Hajiya ta doka Salati Lailahalillallahu muhammada rasulillahi sallahu alaihi salam,Ali za ta raba ka da yan’uwan ka kenan,Indijan nawa ta ke da za ka dubi tsabar ido na ka ce wai tafi karfin hutu?cikin wayo na dan zunguri Aliyu,Hajiya dan Allah ki yi hakuri,yi min shiru mu na fuka duk ba ke ki ka jawo ba! Aliyu ce Hajiya ta Allah ba ki hakuri..ta ce amen ta ya fito indija ke zo mu je kisa mai gadi ya shigo mi ki da kayan na ki! Ya tashi hajiya ta bara na dan taka miki,yi zaman ka,ba na bukata.ta na tafiya ta ke maganar Indija biye da ita,na ce Hajiya sauka lfy,ta ce in ma ba’a ki ke min garau zan sauka,Atoh.jiki sayaye na bi bayan ta da kallo yayin da kwalla ke kokarin sauka da ga idona,da sauri Aliyu ya zo gabana ya durkusa,pls Jauda,pls i beg of u kar ki min kukan nan na ki mai daga hankali….. [10:10pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 4:kafin ka ce mai tini hawaye ya bude kamar famfo,cikin rudani Aliyu tashi ya ja hannu na ya zauna kan kujera,ya daura ni kan cinyar shi ya na rarrashi,yi hakuri Jauda,ya kamata ace kin saba da halin Hajiya kin dai na zubar da hawayen ki saboda ita,na san bata kyautawa amma ki yi hakuri komai zai wuce kin ji ko? Na gyada kai. Ya ce yauwa goge hawayen toh,ki na yar soja matar soja ki na kuka haka? Na goge hawaye ina murmushi,ya ce yauwa dax my girl bari ki ga brk fast din ma ni zan yi feedn din ki,ya jawo plate ya shiga ba ni abunci a baki. Ito ko hajiya da fitar su ta kira yaron gida ta mika ma sa katuwar jakar Indija ya kai ciki. Ta kalli Indija da fatan dai ba ki manta musabbabin zuwan ki gidan nan ba ko? Indija ta ce Hajiya ban manta ba. Hajiya ta ce toh kar ki ba ni kunya,ki tabbatar hakin mu ya cimma ruwa,in dai ni na haifi Aliyu toh sai ya rabu da yarinyar nan ya aure ki,dan ko zaman kishi ban yarda ku yi ba. Indija ta dara an gama Hajiya,ta budewa Hajiya mota ta shiga,Hajiya a sauka lfy,Hajiya ta ce Allah ya sa,duk yan da ake ciki ki na kira na a waya ki na sanar da ni Indija ta ce toh. Direba ya tada mota mai gadi ya bude mu su gate su ka fice,Indija na daga ma Hajiya hannu har su ka kure,ta kama hanya sai ciki Nan ta taddani kancinyar Aliyu ya na bani abunci ni ma ina bashi,ba ko sallama ta wuce fooo ta shige dakin baki,mu ko ko ajikin mu wai an mintsili kakkausa [11:02pm, 11/9/2014] Khadija Sidi: Matar mu 5:Da yammacin ranar juma’a,na ci ado cikin English wears,riga body hug da wando,ni gwanar sa wando ce dan ganin yanda ya ke karba ta abun ku da mai hipsna taje gashi na na faka shi a tsakiyar kai na irin yanda ake ma yara dan na lura Aliyu ya na so ya ga na yi irin haka dan maganar shi a kullum shi ne Jauda shin za ki tsufa kuwa? Na dubi kai na a madubi na ga na yi yar camas da ni,na janyo humrah na goga a hannu na sa’annan na shiga murzawa a jiki na kamar su bayan kunne,wuya dadai sauran su,haka dai na janyo sauran turaruka na kamar kala biyar na fesa sa su kadan kadan,tuni kamshi mai san yi ya mamaye ni,na sake kallan kai na a madubi,ni kai na nasan na hadu ba tare da na daura dankwali ba na nufi falo taran oga Da shiga ta falon Indija na gani zaune ta na kallo,ta ko bini da kallon da ita kanta ba ta san ta yi ba,na murmusa na ce yan mata kallo ake ne? Ta yi saurin mai da hankalin ta ga TV ta na fadin caf wankan baka asarar ruwa,ko ta yi ma kamar ba ta yi ba..kawai sai ma ta bani dariya.mai aiki na karimatu ta shigo ta durkusa gabana,madam na gama gugan,na ce yauwa Karimatu za ki iya hutawa ba wani aiki,ta ce thank you madam,ta wuce bangaran ta tana dan soshe soshe. Jim kadan na ji ana hoon,ina ji na gane oga ya dawo,ba jimawa sai gashi ya shigo falo,da gudu na je na yi huggn din shi,bisa da al’adar shi ya daga ni ya dire ya yi kissn kumatu na duka biyu,sai goshi sai kuma baki…ya na sunsani kamar mage ta cinci lada mai maiko,ya ce huuuuuum Ni’imatullah sunan kamshin mata ta,ita kuma jannatul na’im ce.. Duk wannan buduri akan idon Indija,ba kin ciki kamar ya kashe ta, Oga ya dada dagani ya dire,ya na juya ni madam anya kuwa wannan nauyi da na ji kin kara,ga wani kyau da sheki da ki ke,anya kuwa? Na dara anya kuwa me? anya kuwa ba baby na ba ne cikin dan cikin nan na kina rangwabar da kai cikin shagwaba shin akwai wani baby da ka ke da shi da ya wuce ni?yayi dariya mai fitar da sauti babu,amma dai ina nufin ko kin sama min karamin soja ne…. Indija ta yi gyaran murya ta ga abun ba na karau ba ne,Y Aliyu sannu da zuwa..gaba daya sai ya tsuke fuska ya sake ni,ni kuwa na sami damar sunkuyawa na cire ma sa takalmi,yauwa kin wuni lfy?baki washe ta ce lfy lau,daganan be sake walwala ba har sai da na gama cire ma sa takalmi yaron gida ya shigo da jakar oga na karba yayi side hugn di na mu ka wuce ciki cikin jin dadi da annashuwa,oga na fada min su Sulaiman sunce su na so su ci abuncin madam,wen za mu gayyace su ne? Na ce duk sanda su ke so.. Indija ta bi mu da kallo ta buga kafa aikin banza kunshi a duwawo,dallah jita baka kirin ta wani lafe cikin miji na,wa ya ga madara da milo!ni ina mamakin test din ya Aliyu da ya ke san wannan bakar matar haka,sai wani riri ta ta ya ke kamar gwal! mtsw ta ja tsaki…. [9:35pm, 11/11/2014] Khadija Sidi: Matar mu 6:kai tsaye C. Sulaiman ya shiga falon gidan Anty sa’a tare da doka sallama,ganin General kwance kan kujera Anty Sa’a na ma kafafuwan sa danna ya sa C. Salaiman dan dakatawa,cikin ransa ya na fadin Babbar yaya miji ya tsufa amma har yanzu lallaba shi ake. Anty Sa’a ta amsa wa’alaikumul salam,Sulaiman yau kuma daga nan za ka tsaya?ta dakata da dannan ta zauna gaban General,C.Sulaiman ya murmusa,ya karasa ciki ya durkusa cikin ladabi,barka da yamma Sir..General ya tashi zaune,barkan ka dai Sule,ka ji sako na ko?C.Sulaiman eh abunda ya kawo ni kenan ma Sir. General ya ce gud.C.Sulaiman ya dubi Anty Sa’a Babbar yaya mun wuni lfy?fuska ba walwala ta ce lfy lau. General ya ce Sule Madan di ta,yayar ka ta kamin korafi akan ka,ta ce ta ga ji da yanda kake gudanar da rayuwar ka,it is time you changed,time for you to settle down nd get yourself a wife..da sauri C.Sulaiman ya kalli Anty Sa’a,ita ko ta sakar ma sa murmushin mugunta domin kuwa ta san yau za a yi ta ta kare.. C.Sulaiman ya fara kame kame,Sir wallahi ai matar ce ban dace da samu ba tukun.General ya tsuke fuska dama ina za ka yi dace da samu tin da ba ka neman na gari?ai sai an nema ake samu,ya kallai Anty Sa’a Madam wani wata mu ke ciki yanzu? ta ce febuary,toh Sule na baka da ga yanzu zuwa karshen shekara wato watan december ka fito da mata a daura ma aure.. Zufa ta fara keto masa dan idan akwai abunda ba ya gaban C.Sulaiman ya bi bayan aure,ya rusunar da kai cikin neman sulhu,dan Allah Sir a dan kara min lokaci saboda..ba wani lokaci da za a kara ma Sule,General ya dakatar da shi,it is an order!C.Sulaiman ya dankame jin sautin muryar da General yayi amfani da,ya ce yes Sir. General ya tashi tsaye good,ina tsimayin ka.Madam bari na yi haramar masallaci ko? Anty Sa’a cikin farin ciki ta ce toh oga,General ya shige ciki,Anty Sa’a ta yi saurin bin bayan shi gudun korafin da C.Sulaiman zai ma ta. C.Sulaiman ya bi ta da kallo,yau dai burin ta ya ciki ta hada shi da General sanin duk duniya ba wanda ya ke jin maganar shi kamar General,bawai dan na matsayin sa na General ba ko na mijin yayar sa kadai ba,har da matsayin marikin shi tin ya na dan karami a sanadiyyar rasuwar mahaifan su a hatsarin mota.C.Sulaiman ya nisa gama da fadin burin ki ai ya cika babbar yaya,kai mata ma dai matsalar su da ban take wlh,ya tashi ya na gunguni ko sallama be damu ya mu su ba ya yi tafiyar shi. [9:06am, 11/12/2014] Khadija Sidi: Matar mu 7;8;9:Yau na wayi gari cikin aiki dan ganin na fitar da oga kunya.tin fitar Oga office na tada Karima da ke ba ta fara min aiki sai ya fita,ba dan girma gida na ba ma da sam ba na bukatar house help dan kusan rabin aiki na ni na ke abuna sai dai dan su wanke wanke da kuma yanke yanke wajan girki da dai abunda ba za a rasa ba. Ita ko Indija yar hutu na ko tsinke ba ta dauke min a gidan,hatta plate idan ta ci abunci in da ta ci nan ta ke bari. Azahar na yi na gama komai,cocoanut rice na dafa tare da cabbage nd chiken soup,sai kuma lemon kankana da madara,da kuma kunun madara da na dama musammam saboda C.Sulaiman,dan ya na balain son kunun.gida ya gauraye da kamshi abin ku da indoor,ina kallan Indija sai kai da komowa ta take sam ta kasa nutsuwa. Bayan na gama tsara komai cikin ma zu bin su na ce da karima ta kwashe ta kai min dining table,na yi maza na shiga wanka. Bayan fitowa ta daga wanka,ina zaune gaban madubi cikin atamfa dinkin bubu,atamfar fa ta karbe ni sosai,na dau jambaki ja ina gogawa a baki na sai ga oga ya shego da sallaman shi,cikin farin cikin na amsa ba tare da na juyo ba ina kallan shi ta madubi,sanye ya ke cikin kaki,hannun shi rike da kugu ya na kallo na ba tare da ya dada motsawa da ga inda ya tsaya ba. Na juyo ina murmushi oga oyoyo..ya girgiza kai ina da sake Jauda wannan jambaki haka?na mike tsaye ina murmushi be min kyau ne oga? Na karasa na yi hugn din shi,ya dago fuskata ya na kallo na,ya mi ki kyau sosai ma shi ya sa dole na yi maganin shi..kafin na yi magana ya fara kissn dina sai da ya tabbatar jambaki ya fita sa’annan ya sake ni ya na fadin haka na ke so. Cikin shagwaba na kalli kai na a madubi na ce ayya mana oga,wallahi ka ga duk ka goge min har da yar kwallata ta kissa.ya juyo da fuska ta mu na duban juna,yace madam kin san yanda na ke kishin ki kuwa? ur beauty is for me,not for the world to behold,idan na bari abokai na su ka ganki da jambakin nan toh na yi asara babba,owk? Na murmusa gami da sarawa yes Sir! Ya ja hanci na good girl,yanzu maza dauko mayafin ki mu je na bar bayin Allah sun kwaso yunwa musammam Suleman.cikin hanzari na ce toh,ina sane na ja wani dan karimin mayafi dan neman tsokana,ya na gani ya ce shi wannan na menene ne? Na yafawa oga,wani kallo da ya min ya sa na aje da sauri na dau mai dan girma ina dariya,shima dariyar ya ke hannun shi cikin nawa mu ka nufi falo. Nan mu ka tadda C.Sulaiman da C.Eze zaune.cikin sakin fuska na ce S.man sannu da zuwa,sunan da mu ke kiran sa da shi kenan ni da jiddah tin kafin na san Aliyu.ya murmusa Matar mu ki na lfy? Kafin na amsa oga ya ce wallahi ka sake kiran ta Matar mu ba za ka ci abuncin gida na ba! mata ta ce,ni kadai in ka yi zuciya ka auro ta ka kai ma Kin gani? Kin ga irin gurin da ya ke min ko kanwata?kawai murmushi na ke musu. Oga ya ce gwara dai ka kira ta kanwar ta ka.C.Eze ya ce go marry your own wife na,haba kin damu aboki ta!C.Sulaiman ya ce shege Eze,duk mu ka yi dariya. Bayan mun gama gaisawa na musu iso zuwa dining table,sai da na tabbatar sun zauna,ko wani mutsi na yi oga na bi na da kallo,na kalle shi cikin girmamawa oga ina daki if you need anything..kafin oga ya amsa C.Sulaiman ya sara min gami da cewa yes ma! Oga ya watsa masa harara,over sabi house boy kawai.na shige daki ina mamakin yanda S.man ya gane lagwan oga haka,ina jiyo shi ya ce masa in ba ka yi da gaske ba sai na hana ka zuwa gida na wallahi,tin ina jiyo dariyar muguntar C.Sulaiman har na dai na ji. Na sami gado na kwanta abu na.ban jima da kwanciya ba na ji oga na kwalla min kiraba shiri na tashi dan daga jin kiran ka san ba lfy Da shiga na falon na ga C.Sulaiman da C.Eze na shirin fita,na bi su da kallo cikin alamar tambaya,har kun yi mai? Ba dai tafiya za ku yi ba?C.Sulaiman ya ce wani dan uzuri gare mu,mun gode kwarai matar mu.C.Eze ya ce yas thank you madam.kawai na bisu da kallo bayan sub fita na mayar da kallo na ga Oga wanda ya ke tsaye hannu cikin aljihun wandan kakin sa.fuskar shi cike da damuwa ya ce zo ki ci abuncin nan ki ji. Na karasa dinin table,na dau spoon gami da diban abuncin da Aliyu ya zuba domin ci,da ga kai loma baki mai zan ji? suger ne cau cikin abuncin!na yi saurin jan lemon kankana domin na kurba ko zan iya hadiyar abuncin,nan ma labari ya sha bambam,shi kuma gishiri ne kamar zai tsinka kunne wayyo Allah kamar zan mutu ganin halin da na shiga oga ya miko min robar ruwa,ban tsaya neman kofi ba na kafa baki na kwalkwali kaya na,ya ja min kujera na zauna. Madam mu ma haka mu ka ji shi ya sa mu ka hakura da abuncin,bari na je suna jira na. Takaici ya hanani iya furta komai har ya fice. Kafin ka ce mai kuka ya kubice min,suger cikin miya? Gishiri cikin lemo na jawo kunun madarar da C.Sulaiman ya zuba na dandana,ina shima gishiri ne fal ciki,wannan zalinci da me ya yi kama? Wa zai min wannan aiki in wuni ina abu amma a min wannan cin fuskar? A fusace na shiga kwallawa karimatu kira…. [11:45am, 11/24/2014] Khadija Sidi: Matar mu 10;11;12:Da gudun ta ta zo,ganin halin da na ke ciki ta rikice ta na fadin Madam lfy? Ba ka da lfy ne?ban kula da damuwar da ta shiga ba na tura mata plate ci abuncin nan.. Hannu na rawa ta dau spoon ta kai loma daya,da kyar ido rufe ta iya hadiya,na tura ma ta lemon kankana sha wannan ma,a rude ta daga ta kurba,ta aje kofin da sauri ta nufi kitchen da gudu sai zink ta kuskure ba kin ta.bayan ta dawo na tura mata kunun madara,tini ta fara kwalla ta na fadin please madam i no fit test tam again abeg. Na yi murmushin then how do you except oga nd his frnds to eat dat? What happend? Me ya faru?haka na yi abunci na? a gaban ki dai na gama komai na kuma ce ki kawo min nan ryt?Karima ta zube gwiwowin ta biyu a kasa I swear Madam ban sani ba,ka tambayi Anty Indija ma,ya san komai,na she even complet d work… what! Na daka ma ta tsawa,na saki aikin ki na fada min wata ce ta karasa min? Dan me ya sa? Me ya kawo Indija cikin aiki na? Zufa ya lullube Karima am sorry Madam,sani ya yi na share mai daki,na ce ya bari na gama aikin da ka sa,ya ce shi zai karasa..na saki ajiyar zuciya,wato Indija da gaske ta ke kenan,wannan aikin ta ne dan ta kuntata min,ta kunya ta ni gaban miji na da abokan sa,wannan karan ta ci nasara,amm babu next time! Cikin fada na dubi karima na ce who am i in this house? Ta ce you are the Madam. Na gyada kai then listen to me good,kar na sake saki aiki wani ya zo da nashi ki bar nawo,idan abunda ya faru yau ya sake faruwa a bakin aikin ki! Sorry madam abeg sorry! A fusace na tashi nd clear d table ryt away! Kafafuna da kyar su ke iya dauka na,wannan ai shi ne an fadi ba nauyi.da kyar na shige ciki,karimatu jiki na bari ta shiga kwashe kwanuka.. Ashe duk abunda ake a kunnan Indija,ta na labe ta na ji. Ta kwashe da dariyar mugunta yayinda ta ke kokarin kiran numbar Hajiya domin ta fada ma ta nasarar da su ka yi. Ranar haka na wuni jiki ba laka,ga wani tashin zuciya da na ke fama da shi. Har aka idar da sallar isha’i ban ji motsin oga ba,wanda tin dawowar shi na masa sannu da zuwa ba mu kara haduwa ba. na duba agogo na ga karfe tara,na saki ajiyar zuciyar gami da yanke hukuncin bin sahun shi. A dakin shi a tadda shi,ya yi kwanciyar rigingine idan shi lumshe.a hankali na kara sallama dan a tunani na bacci ya ke kar na tada shi,na juya zan koma sai na ji ya amsa sallamar .na juyo na kalle shi mu ka hada ido sai na yi maza na maida kallo na kasa ina wasa da kafata kan carpet kamar mara gaskiya. Ya tashi zaune ya na nazarta ta,daga bisani ya ce Madam ya dai?na masa shiru,da ya ji shirun ya yi yawa ya kira sunana JAUDA?na dago na kalle shi,sai na ga ya ware hannun shi ya ce come hia. Na karasa wajan shi,maimakon na shiga cikin hannun na shi yanda ya umarta sai kawai ni ma na zauna gefan gadon,ya aje hannun shi,kin ji ni shiru ko?na zo ki na sallah ai sai na dawo yanzu na ke shirin komowa..a rai na na ce ka na shirin komawa ai shi ya sa na gan ka kwance. Jauda?ya sake kiran sunana,na ce Naam,dama na zo ne na baka hakurin abunda ya faru dazu,wallahi ban san yanda aka yi hakan ya faru ba,na ba ka kunya….shhhh yi shiru..ya katse ni. ba ki ba ni kunya ba,ai daga Suleman din har Eze sun san mata ta is a special cook,samin mace da ta iya girki kamar ki ai sai an binciki,it is a mistake,so kar ki damu kinji? Na gyada kai. Ya cigaba amma to avoid this kind of mistake sai kin rage damuwa,kwanciyar nan da ki ka ga na yi a nan tunani na ke shin wai me ne damuwar mata ta haka? Idan Hajiya ce dan Allah ki cire lamarin ta a ranki,ki na ma na addua,a hankali za ta gane wacece Jauda kuma komai zai wuce.. Ni dai kawai jin sa na ke,amma ba wai gane abunda ya ke fada na ke ba,wani irin tashin zuciya na ke ji,amai ya yunkuro min gadan gadan,da gudu hannuna toshe kan baki na,na shege ban dakin oga,sai amai kamar zan amayo da hanjin ciki na. Oga ya biyo ni ya na fadin sannu,sannu.ya taimaka min na gyara jiki na,ya kama ni mu ka dawo daki sai da ya ga na zauna ya koma ya gyara ban daki. Bayan ya fito ya kalle ni,dama ba ki da lfy shi ne ba ki sanar da ni ba? Na ce ba wani rashin lfy ba ne,dama tin da na dandana wannan abuncin zuciya ta ke tashi.ya ce sau na wa ki ka yi aman? Na ce sau daya ne fa,ya ce cikin ki ya baci ne? Na ce ah ah.ya ce maza tashi ki shirya mu je asibiti,na ce dan Allah ka bari sai gobe,ka ga tin da ma na yi aman na ji sauki. Ya girgiza kai ah ah ban san wasa da lfy Madam.Na ce am owk,pls ka bari sai gobe.ya ce fine,sai a kwanta a yi bacci ko… na ce ba yanzu ba,ban jin bacci,ya tsuke fuska nan kuma ba ki isa ba yarinya,dole ki kwanta,ban an karaba ya gyara min kwanciya ya ja bargo ya rufa min sa’annan ya zauna ya na kallo na,daga bisani ya ce I love you,na murmusa gami da lumshe ido na ce I love you more.daga nan bacci ya kwashe ni da ke dama a gajiye na ke… [10/20, 11:01 PM] aunty jidda: OLD BUT GOLD [11:46am, 11/24/2014] Khadija Sidi: [12:14pm, 11/12/2014] Khadija Sidi: Matar mu 13;14;15:washagari ba mu zame ko ina ba sai asibitin sojoji da ke cikin barrack din su oga. Doc. Usman wanda shi ma kullum ya ke sanye cikin kaki,sai dai ya na dora rigar likitoci wato lap coat a saman kakin na shi,likitan sojoji kuma abokin oga shi ya duba ni,da ga bisani ya ce mu dan bashi lokaci ya na zuwa,ya bar mu cikin office mu na jira. Oga ya ce bara ya duba wani yanzu zai dawo,na ce toh. na rage sai ni kadai cikin office. Na zauna shiru,har na fara kokawa sai ga Oga da Doc.Usman sun shigo suna fara’a,Doc Usman ya ce sorry Madam i kept you waiting. Na murmusa na ce ba komai. Oga ya zauna kujerar da ke kallan tawa,ya kamo hannu na ya rike,shi kuma Doc. Usman ya zauna ta shi kujerar gami da bude wata takarda da ya shigo dauke da ita,cikin farin ciki ya ce wow,wow ya mikawa Oga hannu congratulation officer,inshaAllah mun kusa zama baba..caraf oga ya ruko hannun Doc. Usman dan Allah Doc?ka na nufin….? Ya kasa karasawa,Doc.Usman ya jinjina kai alamar eh. Baki bude Oga ya kalle ni,nan ya zube ya gabatar da sijjadar godiya ga mahaliccin sa,ga dago ya ruko hannu na Jauda? Kina ji fa? Ashe dai babyn nawa ne da gaske,Usman dama fa na ji ta kara nauyi…na yi sauri na rufe fuskata dan gaskiya na ji kunyar maganar oga wanda shi kansa be ma san ya fada ba. Shi ko Doc. Usman dariya ya ke in da sabo ya saba da irin su Oga,saban shiga. Kafin mu tafi Doc. Usman ya sheda ma na cikin wata uku ne,da kuma abubuwan da ba za a rasa ba. mu ka yi sallama mu ka fita,a kaida Oga direba ya ke sawa ya mai da ni gida idan har ba a mota ta na zo ba,ko kuma ya ba ni ta shi motar in direban ba ya nan shi kuma idan sun tashi da ga aiki C. Suaiman ya sauke shi,amma yau da kanshi ya maido ni gida,a hanya ana ta lissafa min hidimawai na dai na aiki,ko girki ma dainawa zan yi,na ce sai mu ci me kuma kai da ba ka iya cin abuncin mai aiki ba? Ya ce sai mu na yin take away,na ce ba wannan maganar girki na zan na yi,ya ja na ja,sai ya hakura wai kar a batawa dan babyn shi rai shi ya sa kawai ya hakura. Haka mu ka isa gida,a gaban mai gadi da yaran gida na Oga ya fito ya bude min kofa,ya sure ni kamar baby ya yi ciki da ni.Nan mu ka ci karo da Indija ta yi sororo ta na kallan mu,da kyar ta ce sannu da zuwa Ya Aliyu,cikin Fara’a da ni kai na ban taba gani ya yiwa Indija ba ya amsa,yauwa Indija,ya wuce daki da ni ya dariya.Indija ta biyo mu ta labe a corridor nan ta ji Oga na kafa min dokoki,har da alalle yanzu kwanciya zan yi babyn shi ya huta.Indija ta dafe kirji baby? Ciki gare ta?cikin bacin rai ta juya da sauri ta nufi dakin kwanan ta ta dau mayafi da jaka,ta fice kamar mahaukaciya. Ba ta zame ko ina ba sai gidan Hajiya,ta na shiga ta fara rusa ihu,wayyo Hajiya,na mutu na lalace! A gigice Hajiya ta fito ta na fadin ke lfy? Rashi aka yi? Indija ta ce Hajiya ba gwara rashi da wannan abun da ya faru ba! Hajiya ta ja ta ciki,zauna ki fada min,duk kin sa hankali na ya tashi.cikin kuka Indija ta zauna dirshen a kasa,ta ce Hajiya matar Aliyu ta na dauke da juna biyu! Hajiya ta dafe kirji ta na salati ta na sallallami,wannan masifa da me ya yi kama? Ke wa ya fada miki? Indija ta ce labewa na yi na ji suna maganar,ba ki ga yanda ya ke lallaba ta ba kamar kwai..ta dada fashewa da kuka. Hajiya ta shiga rarrashin ta,yi hakuri bar kukan,wallahi idan har ni na cika uwar Aliyu cikin nan ba za ta haife ba,toh ta haihu na dau danta na ce na dauki me?jika ko dai jaki? Ishiru yar nan,ai da sake! Indija ta share hawayen ta,dan Allah Hajiya ki yi maganin abun da sauri,Hajiya ta ce sosai kuwa. Indija ta tashi Hajiya bara na koma toh,kila ta na can ta na kulla wani munafunci. Hajiya ta ce aifa,maza ki koma,amma ki kwantar da hankalin ki kin ji ko? Indija ta ce toh.ta tafi ta bar Hajiya ta na ta mita. [2:27pm, 11/12/2014] Khadija Sidi: Matar mu 16;17;18;19: Ina cikin kitchen ina kokarin hada abunda zan ci,dan ni yanzu komai na ci sai na amayar. Kamar da ga sama na ji ana Sallama,da sauri na amsa na fito wa zan gani? Kanwata ce jidda tsaye a falo da sauri na karasa mu ka yi hugn juna ina fadin mutan yola,yaushe a gari? Na ja ta mu ka zauna. Ta ce jiya jiyan nan,na ce da Anty Sa’a kar ta fada mi ki na mi ki suprise.iyye wato ke ba za ki na sauka gida na ba ko? Jiddah ta ce wannan karan rabawa zan yi,gidan kowa zan kwana biyu. Na ce yauwa ko ke fa. Ya hanya ya su Inna ( mahaifiyar mu)Jiddah ta ce lfy lau,ga tsarabar ki can ta ce na kawo miki. Na ce Allah sarki Inna ta,na tashi na dau kayan na kai kitchen na duba su daddawa ne da kuka,da cikwai da fura dadai sauran su. na dawo wajan Jiddah a falo sai na ga fuskar ta daure,ta ce da ni sis yanzu me wannan agwalumar ta ke mi ki a gida? Cikin nuna rashin fahimta na ce wafa? Cousn din Aliyu ta fada cikin tsiwa. Na dara na ce aw wai Indijan ce agwaluma? Auta ban san neman fitana dan Allah,ta ce me ta ke mi ki a gida? Na ce wai hutu ta zo,ni mantawa ma na ke ta na nan..caf amma sis shi ne ki ke korafin ban sauka gidan ki ba? Ai in har ta na nan ba zan iya kwanan gidan nan ba. Na dara auta rigima,toh ya zan yi ita da gidan yayan ta? jiddah ta girgiza kai ba dai ki ga daman yin komai ba,abubuwan yi ko akwai su,yarinyar da ki ka san ba kaunar ki ta ke ba za ki yarda ku zauna gu daya? Na mike tsaye tashi mu shiga ciki auta,zancena ya ishe ni. Na dau yar jakar ta ta na biye da ni ta na fadin ai aishikenan na yi shiru. Kafin Oga ya dawo Jiddah ta koma gidan General. Bayan dawowar sa na ke fada ma sa ina so ziyartar Anty Sa’a. Da fari ma hana ni yayi gaba daya,wai ni da ba ishasshen lfy gare ni ba,da kyar ya yarda amma da sharadin ba zai bari na yi driving ba sai dai na shirya in zai fita barracks ya sauke ni. Haka ko aka yi da sassafe na tashi,na damawa General kunun madara. Mu ka fito da Oga,mun dau hanya kenan C. Sulaiman ya kira Oga wai ya biya ya dauke shi motar shi ta sami matsala. Mu ka biya kafin ya fito na koma baya,da ya fito ya shiga gaba mu ka dau hanya. Bayan mun gaisa Oga ya ce da ni Madam Sulaiman fa ango ne? Na ce kai haba?C. Sulaiman ya daka masa harara,ya ce rabuda shi matar mu,karya ya ke,ina kallo Oga ya zungure shi,ya ce toh sorry matar ka. Oga ya ce wallahi Madam da gaske na ke General ya sa mishi ranar aure da ga wannan wantan zuwa karshen shekara,ya na murmushin mugunta ya ke maganar. Na dara kai Allah ya nuna mana. C. Suleman ya ce ai babu matar ne,ko za ki ba ni Jiddah? Oga ya ce wata Jiddar? Kanwar tawa? Allah ya sauwake! Na ce oga me zai hana? C. Sulaiman ya ja tsaki mstw isar da ba a isa ba,toh dan ka na mijin yayar ta ka isa ka hanani auran ta,har da wani kanwar ta wa,toh ka hana mu gani..Oga ya murmusa haka ka ce? Zan ko yi maganin ka kuwa. C. Suleman ya ce kai ma General na neman ka,Oga ya ce eh an fada min,amma a office din shi ya ce mu hadu. C. Suleman ya ce waya sani ma ko kai cewa zai yi ka karo mata..na zaro ido,Oga har da kwarewa,amma ba ka da mutunci a gaban Jaudar ka ke fadin haka,dan Allah kar ka sa ta yi bari cikin motar nan,hakan yayi daidai da isowar mu gidan General,na ce S.man bakin ka ya sari danyen kashi,duka su ka sa dariya. Na fito hannu na dauke da flask na zagayo ta wajan Oga,ba za ka shigo ka gaida Anty Sa’a ba? Ya ce Madam yanzu ya yi safiya ,amma idan na zo daukan ki zan shiga na ce toh,ya ce tak kia of urslf nd ma little one,na murmusa na ce adowo lfy na wuce ciki, C. Sulaiman ya ce ban fa gane ba,ka na nufin matar mu is carrying our baby? Oga ya dara ya yinda ya ke ko karin juya kan mota,yes mata ta is carrying my Baby. C. Suleman ya ce wow no wonder na ga ka karo takama da wulakanci,Oga ya ce kai ko iyali wasa ne? C. Suleman ya ja tsaki ya kau da kai gefe. Bayan shiga na gidan Anty Sa’a,Anty Sa’a ta min tarba mai kyau kamar yar da ta saba,bayan mun gaisa ta ce ya mai gidan na ki,na ce lfy lau,shi ma ya sauke ni ya ce sai ya dawo dauka na zai shigo yanzu ya yi safiya.Anty Sa’a ta ce haba wani safiya kuma ai ke kin san daga asuba bacci na ke karewa duk da ba yara gare ni ba. na janyo flask na ce ga kunun Oga,Anty Sa’a ta karba,yauwa kunun madarar ne? Kamar kin san ya na kewa kuwa. ni ko Jauda gani na yi kamar kin dab canza min,kin yi wani fresh kamar mai juna biyu,na sa hunnu na rufe fuska. Anty Sa’a ta dara haba ni fa ince,mashaAllahu,amma dai Jiddah ba ta sani ba ne da tuni ta guntsa min ni kuma na guntsawa Inna..kamar da ga sama mu ka ji muryar General,me ake guntsawa haka ni ma a guntsa min mana? Duk mu ka yi dariya,ya ce Jauda ce? Na durkusa Barka da safiya Sir,ya ce ku na lfy? Na ce lfy lau. Ya ce mashaAllahu. Anty Sa’a ta ce ga kunun Madara ma ta kawo ma ka.ya ce toh madallah Jauda,ba ki gajiya,Allah saka da alkhairi. Na ce amin.ya ce jiddah ba tashi ba ko? Anty Sa’a ta ce ina ai sai rana ta fito,a rai na ce zata dai na ne,komai lokaci ne. General ya ce Jauda ni zan wuce office,ba dai matsala ko? Na ce eh ba komai,adawo lfy.ya ce Allah ya sa,Madam sai ki biyo ni da kunun na wa ko? Anty Sa’a ta ce toh,General ya fita Anty Sa’a ta bi bayan shi. na cire mayafi na dan kishin gida ina jira Anty Sa’a ta zo ta min maganar Indija dan na san tini Jiddah ta labarta ma ta. Ile ko ta na dawowa ta fara min maganar. Ni dai sai hakuri kawai na ke cewa… [11:54am, 11/24/2014] Khadija Sidi: [4:41pm, 11/14/2014] Khadija Sidi: Matar mu 20;21;22:General be dade da shiga office ba Oga ya buga masa kofa,General ya ce ya shigo. Bayan shogowar oga ya sarawa General tare da fadin Morning Sir General ya amsa cikin murya mai nuna doka,Morning Captain,ka ji kiran da na ke ma ko? Oga a kame ya ce yes Sir!General ya ce have a seat,cikin girmamawa Oga ya zauna gaban General,ya mi kawa Oga wata farar envelop,Oga ya sa hannu biyu ya karba. General ya ci gaba,Request ne da ga ministry of defance,kamar yanda aka saba bayan every two years ko wani barrack ya na ba da soja daya wanda zai wakilce shi a exclusive course din da ake yi a Sudan na tsahon shekara daya,am very sure u knw abt it. Oga ya ce yes sir. General ya ce wannan karan kai aka zaba a wannan barracks din,za ku tafi nan da wata hudu,so ka shirya ranar Monday za ka je Abuja ka yi reportn a ministry.Oga ya ce yes Sir.General ya ce za ka iya tafiya. Oga ya tashi da sauri ya sarawa General,ya juya zai fita,har ya kai kofa General ya tsaida shi da fadin nd you can go with your wife if you like. Cikin Fara’a Oga ya juyo ya sarawa General yes Sir! Har sai da shi kan sa General ya murmusa,ya gyada masa kai.Oga ya fice cikin zafin nama. Bayan sun tashi da ga aiki Oga ya zo ya dauka na,ya cika alkawari ya shiga ya gaishe da Anty Sa’a shi da C. Sulaiman,nan na fara jin zancen tafiyar shi sudan ya na fadawa Anty Sa’a,ta yi masa murna sosai da ta ji zai tafi da ni.shi ko C. Sulaiman cewa ya yi wato Nigeria ba gaskiya,da ke jauda kanwar General ce sai ya ce za a iya ta tafiya da ita,dan masu gata ne kadai ake bari su tafi da fmly din su. Anty Sa’a ta ce ko kamar ya yi a gaban General sai ta fada masa,C Suleman ya ce dama so ta ke ta hada su ai,ya gama gane lamarin ta. Jiddah ma ta samu su ka gaisa da Oga,kamar kar na bar gidan haka na hakura na koma gida na. Washagari da yamma,na ci adona cikin atamfa orange dinkin styler mai dan karamin hannu,riga da zani,da ke babu abunda ya kai zani fitar da structure,dam ya zauna a kuna. Na kafa dauri na a goshi irin wanda ake kira ture ka ga tsiya na na faka gashi na a kyeya. Na nufi kitchen domin kwaso abincin Oga,ya kusa dawowa. Na zo kofar kitchen kenan Indija ta fito daga kitchen din ta sane ta bangaje ni sai da na kusa faduwa,ciki na ya murda.cikin sauri na tsaida kai na ina fadin Yahayyu ya kayyum! Da ke Indija ba ta da kunya sai ta hau min masifa ta na fadin ke wata irin mahaukaciya ce?ba kya gani ne? Na kalle ta cike da mamaki. Indija ni ce mahaukaciyar? Ki bangaje ni din ki kara min da zagi? Me na tsare mi ki ne dan Allah? Cikin tsiwa ta ce eh ke ce mahaukaciyar! abunda ki ka tsare min ki ki ke tambaya? toh miji na ki ka aure! Na murmusa na ce mijin ki kuma? Ai ni ban san ki na da miji ba,ni dai ni kadai ce gun miji na,daya tamkar da dubu dan kuwa gadan ari sai fanna,wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa har abada,wawiyar banza wawiyar wofi,da za ki gane da iska ta dai na wahalar da mai kayan kara..ta daga hannu za ta mare ni,na ruke hannun na zuba mata mari kwarara guda biyu,ta yi wani ihu za ta riko ni kamar daga sama Oga ya daka mata tsawa kul! Don’t you dare hit my wife! Duk mu ka jiyo mu na kallan shi,tsaye ya ke a bakin kofa,ya cigaba duk abunda ki ka mata a kan ido na,dama rashin kunyar da ki ke ma ta kenan idan ba na nan?toh ki hade kayan ki,ko ki koma gidan ku ko kuma gidan Hajiya amma dai ki bar min gida na!Indija ta sa kuka,ko a jikin Oga sai ma karasowa da ya yi,ya yi hugn dina ya na tambayar ba ta ji mi ki ciwo ba ko?na yi lamo a jikin sa kamar wata yar yaye na ce ma sa ah ah Am fyn.ya kalli Indija me ki ke jira? Da gudu ta shige daki ta na kuka.Oga ya ja ni mu ka shige ciki abun mu. [4:42pm, 11/14/2014] Khadija Sidi: Matar mu 23;24;24: kafin magrib Indija ta hada na ta ya na ta sai gidan Hajiya,ta na shiga ta fara kurma ihu,a falo ta tadda Hajiya ta na sallah,ta zube kasa ta na kuka. Da sauri Hajiya ta sallame ta na fadin lafiya?me kuma ya faru?Indija ta kada baki ta ce Hajiya yau na ga wulaknci iya ganin ido na, Hajiya ta ce wulakanci fa ki ka ce? Wa ya wulakanta ki?cikin kuka ta ce Hajiya ya Aliyu,bayan matar shi ta mammare ni,ta zage ni tas ta uwa ta uba a gaban shi,be hana ta ba sai ma kara min da korar kare ya yi..Hajiya ta fusata! Korar kara? Indija ta ce wallahi Hajiya a gaban ta kuma ya kore ni!Hajiya ta ja waya ta na kokarin kiran Oga,dan be da mutunci ya kore ki daga gidan sa?sakaran banza sakaran wofi mace tafiye ma sa dangi? Bari na kira shi,yau sai ya sake ta..Indija ta yi saurin dakatar da Hajiya tare da fadin Hajiya kar ki kira shi,wlh ko kin sa ya sake ta kin san sai ya ci gaba da bibiyanta yanda ta gama asirce,ai kamata ya yi mu ma ta bi ta da kulle dukan kabarin kishiya. Hajiya ta katse wayar dama ba shiga ta yi ba,ta ce eh nan fa daya,fada min abinda ke ran ki.Indija ta gyara zama,tina ta daina kukan da ke dama na munafunci ne. Ta ce Hajiya sharri ya kamata mu kulla ma ta,sharrin da ba Ya Aliyu kadai ba duniya ma sai ta juya mata baya. Hajiya ta ce wannan ma zai yi,dai na kame kame ki min bayani dalla dalla yarinya. Indija ta yi murmushin mugunta ta ce Hajiya a sannu za ki gane kudiri na,amma idan ya Aliyu ya zo ki ce masa ya turo mi ki mai aikin Jauda. Hajiya ta ce ki na tunanin ba za su zargi wani abu ba? Indija ta ce ko kusa tinda dama ai ke ki ka sama mu su yar aikin ko? Toh ki ce ma sa mahaifiyar ta ce ta zo daga kauye.Hajiya ta ce toh hakan za a yi,bari na idda sallar da ki ka katsemin.ta tashi ta tayar da sallah,Indija ta shige ciki ta na fadin in ta san wata ba ta san wata ba,wallahi sai na sa Aliyu ya wulakanta ta. Ranar lahadi da yamma Oga ya je gidan Hajiya,ba ta masa Tarbar arziki ba,sai ma tatas da ta masa akan korar Indija da yayi bayan na gama zage ta na hada da mari. Cikin ladabi ya ce Hajiya ta ba haka aka yi ba,ta na sane ta buge ta,kin san haka hatsari ne ga mace mai dauke da juna biyu..yi mim shiru mara kunya!ta daka ma sa tsawa,ka manta juna hudu ba biyu ba,ni za ka fadawa maganar banza! Ya sunkuyar da kai,Allah ya huci zuciyar ki Hajiya ta,ayi hakuri.ta ce amin. Oga ya ce Hajiya ta dama ma zo na sanar da ke barikin mu za su tura mu sudan nan da wata hudu. Sudan kuma?in ce dai ba yaki ake ba?oga ya murmusa ba yaki ake ba Hajiya,course aka tura mu,yanzu gobe idan Allah ya kai mu zan je Abuja na yi reportn. Hajiya ta ce toh Allah ya nuna mana ya kai ka lfy ya kuma dawo da kai lfy. Ya ce amen ya Allah,ya fitar da bandir din kudi ya aje gaban Hajiya ya ce Hajiya ga wannan ba yawa. Hajiya ta dauka ba ka dai gajiya da hidima,Allah ya saka da alkhairi. Na ce ina mai aikin gidan ka Karima? Ka turo min ita. Oga ya ce toh,akwai wani abu ne? Hajiya ta ce mahaifiyar ta ce ta zo daga kauyen su take son ganawa da ita. Oga ya ce Allah sarki ina mahaifiyar ta ta ai ya kamata ni ma mu gaisa,Jauda na jin dadin zama da Karima ai,kin ga sai ma na kai ta gida na sa ma gaisa da Jau….rufa min baki da Allah,da anyi magana sai ka ce jauda jauda jauda! Toh ba za ta je gidan na ka ba din,kuma kar ka sake ka kamin matar ka gidan nan,sakarai! Oga ya yi shiru,daga bisani ya ce Hajiya bara na tafi toh.Hajiya ta tsuke fuska a sauka lfy. Oga ya ce Allah ya sa Hajiya,ya tafi ya na tunanin yanda zai yi maganin matsalar da ke tsakani na da Hajiya, Bayan komowar shi gida ya Fadawa Karima sakon Hajiya tare da bata kudin mota,ni ma na hada mata da atamfa tirmi guda da sabulai ta bawa mahaifiyar ta ta. Cikin murna bayan ta gaisa da Hajiya ta ce Oga ta ce mama na ya zo Hajiya ta ce Karima saurare ni da kyau,mahaifiyar ki ba ta zo ba,wani aiki zan saka ki shi ya sa na kira ki. Farin cikin Karima ya koma ciki dan tasa aikin Hajiya ba aikin arziki ba ne,da ke ta saba ba ta kulle kulle da kayan asiri ta na birne wa a gidan Oga. Ta ce Hajiya wani irin aika zan maka? Hajiya ta ce aiki ne babba ba irin wanda ki ka saba yi ba,amma ki sani idan har ki ka min zan baki naira dubu dari..dubu deri Hajiya Karima ta fito da ido cikin mamaki. Hajiya ta ce kwarai da gaske,na kuma hada da zannuwa wanda za ki kaiwa mahaifiyar ki. Cikin zumudi Karima ta ce Hajiya fada min abunda ka ke so,wlh zen yi ma. Hajiya ta murmusa toh ba lefi,ki yi jiran Indija,za ta fada miki ta kuma ta hada ki da abokin aikin na ki. Karima ta ce toh Hajiya,wlh zen yi…. [10/20, 11:01 PM] aunty jidda: OLD BUT GOLD MATAR MU 25,26;27;28:Washagari da safe,na yiwa Oga rakiya har mota,driver ne aka turo da ga barrack zai kai shi Airport. Na dube shi cikin mota zaune na ce Oga ka ki bari na raka ka ko? Ya riko hannu na worry not my baby ni da yau dinnan fa zan dawo. Na ce toh Allah ya kiyaye,ya ce ameen ameen,take kia of your self for Oga. Na sara ma sa na ce yes sir!kar a manta da addua dan Allah,ayatul kursiyu kafin ka shiga jirgi da kuma sanda za ku tashi. Shi ma ya Sara tare da fadin yes ma! Na yi murmushi na rufe motar,ina daga masa hannu yayinda direba ya tada mota. Har sun kai gate sai na ga sun tsaya,Oga ya fito da sauri ya karaso waje na ya yi hugn dina,a cikin rada na ce Oga gate fa a bude ya ke,ga direba da maigadi su na kallo fa… ya ce ba mata ta ba ce?ya dada makale ni,ni kuwa sai raba ido na ke kamar munafuka,na ce matar ka ce amma da kunya ai….da kyar na samu ya sake ni,ya ce i will miss you,na ce i will miss you more.ya juya ya koma mota,har motar ta su ta fita ina daga mu su hannu,na juya na koma ciki ina kewar Oga. Da la’asar sakaliya gaba daya na ji jiki na ba dadi,gaba na sai faduwa ya ke. da kyar na lallaba na shiga kitchen na hadawa Oga abunda ya sauwaka. Tin wajen 12 ya sanar da ni ya gama da ministry,amma sai yamma sosai zai juyo. Na samu na gama komai na shiga na yi wanka,na sanya wata rigata wacce ke tsayawa iya ka gwiwa ta,kai na ya na sarawa saboda haka sai na saki gashi na,ya sauko har kafada ta. na duba waya ta domin jin inda Oga ya ke,na ji shirun ya yi yawa,amma sama ko kasa na nema na rasa,har na gaji na hakura,na haye gado na na dan kishingida. An yi haka ba da dadewa ba na ji ana buga min kofa,daga kwance na ce yes,karima ce? Da ga waje ta ce ita ne. Na ce shigo. Ta shigo dauke da ruwan faro da kofi. Na kalle ta dan ni na san ban ce ta kawo min ruwa ba,ya aka yi Karima? Ta ce Madam ruwa ne na kawo maka. Na ce but Karima I did nt ask for it,did I?ta na dan murtsika ido ta ce Madam na yi tunanin za ka bukata ne. Da kamar zan ce ta tafi dashi sai na sake shawara,owk thank you,mi ko min. Ta miko min na bude na dan kurbi kadan na aje sauran kan bedside,karima ta juya ta fita ta na dan soshe soshe. Banyi cikakken minti goma da shan ruwan ba na na ji kasala ta karu,jikina too weak gaba daya na rasa abunda ke min dadi,a haka bacci mai nauyi ya sace ni. Oga ya kira waya ta tin kafin jirgin su ya tashi amma sai ya ji ta a kashe,haka ya hakura ya taho ba a san ran shi ba. Direban da ya kai shi Airport shi ya dauko su shi.da isha’i Oga ya iso gida,suna ta hon amma mai gadi be bude musu ba,Oga ya fito ya ce da direban may be mai gadin sallah ya ke,bari na sauka a nan kawai. Ya sallame shi ya tafi. Oga ya shigo cike da mamaki,babu mai gadi babu alamar sa. Ciki ya wuce kai tsaye,ga mamakin sa sai ya ga wutar falon a kashe,hankalin sa ya tashi ya na fadin ina Jauda!da gudu ya shige daki ya bankada kofar daki na,me zai gani? Wani katan gardi ne,daga shi sai gajeran wando,ya kwanta dai dai kusa da ni hannu shi zagaye da jiki na yayi hugn di na,ga dogon wandon shi aje kan gado na… [11:59am, 11/24/2014] Khadija Sidi: [1:57pm, 11/15/2014] Khadija Sidi: Matar mu 28;29;30;31:Oga ya tsaya cak,ya kasa fahimtar abunda ke faruwa. Ko da gardin nan ya ga Oga ya tashi a guje,ko wandon shi be iya dauka,ya bangaji Oga da ya tsaya a hanya ya fita a guje. Nan Oga ya dawo cikin hankalin sa ya yi wuf ya bi gardi,ina tini ya tsere ma sa. Da gudu ya dawo ciki,ya tadda ni ina baccina hankali kwance. Kawai saukan mari na ji ban san hawa ba,ban san sauka ba! A gigice na tashi ina fadin Innalillahi wainna ilaihi rajiun! Be bari na gama wartsakewa ba ya ciro belt din jikin shi ya rufe ni da duka,fadi na ke wayyo Allah,Aliyu me na ma ka haka,dan Allah Aliyu za ka kashe! Idon shi ya rufe!ya ce gwara na kashe ki tin da nufin ki ki kashe ni,macuciya,azzaluma,maciya amana. Ashe cikin na ki ma na shege ne! Na sake! Na wuntsilo daga kan godo na fado kasa tsabar zafin duka,na ruke kafar Aliyu ina fadin dan Allah Aliyu,dan Allah dan Allah! Abunda baki na ke iya furtawa kenan! Ya cigaba na tsane ki,na sake ki,na sake saki uku! Na kurma ihu na kamkame kafar shi,ya janye kafar yayi wurgi da ni gefe.Nan na fadi sumammiya. Ya sa kai ya fice ya barni kwance cikin jini. Daga nan ban sake sannin inda na ke ba,sai bude ido na yi na ganni kwance kan gadon asibiti,a hankali na ke bin dakin da kallo,Anty Sa’a da Jiddah na gani zaune sun yi tagumi,daga bakin kofa kuma C. Sulaiman ne tsaye,da shi mu ka hada ido,da sauri ya ce babbar yaya ta farfado. Da sauri su ka zo su ka tsaya kai na. Anty Sa’a ta ce Jiddah kira doctor,Jiddah ta fita a guje,ni ko na kasa magana sai ido kawai. Anty Sa’a sai sannu ta ke min. Jim kadan Jiddah ta shigo tare da Doc. Usman,ya dube ni sannu madam,ya yi dan dube dube,sannan ya ce bayan jiki akwai abun da ke mi ki ciwo? Maimakon na bashi amsa,kawai sai na fashe da kuka mai ban tausayi,hankalin Anty Sa’a da Jiddah ya dada tashi,Jiddah ta sa kuka C. Suleman ne ya ke rarrashin ta,yayinda Doc. Usman ya ce ina bukatar hutu,ya min allura,tini bacci ya sace ni. Bayan fitar doctor Anty Sa’a ta ce da C. Suleman,Sule ka ga halin da jauda ke ciki ko?tin jiya fa da mai gadi ya kira ya sanarda mu ba ta farfado ba sai yanzu,kuma mai gadi ya tabbatar ma na mijin ta ne ya mata wannan dukan kawo wukar a dalilin da shi ma be sani ba. Ku ma Aliyun be zo ba har yanzu. C. Suleman ya nisa babbar yaya tinda ki ka min waya na ke neman Aliyu a waya amma wayar shi a kashe,amma yanzu gidan zan je na same shi.Anty Sa’a ta ce toh,ka fada masa ya yi sa’ar zubdawa yar mutane da jiki,dama be da mutunci haka Sule?wallahi duk na tsane shi,ga shi general baya nan,na ma kasa fada ma sa. C. Suleman ya ce ai gwara kar ki fada ma sa ki bari sai ya dawo.bari na je wajan Aliyun.Anty Sa’a ta ce toh. Haka ya tafi ya barta cikin jimami,ita ko jiddah kuka kawai ta ke. Da fitar shi ya sake kiran numbar Aliyu,ya yi sa’a ta shiga,bugu biyu ya daga,C. Suleman ya ce ka na ina? Ya ce da shi ya na gida,ya ce toh gashinan zuwa. Be zame ko ina ba sai gidan Aliyu. A waje ya tadda shi,ya tsaya gaban shi,Aliyu ya bude mota ya shiga ba tare da ya kalle shi ba ya ce kai ni gidan Hajiya. C. Suleman ya kalle shi ya ga duk ya fita daga hayyacin shi,ba musu ya tada mota sai gidan Hajiya. Sun tadda wata mota na kokarin fitowa daga gidan Hajiya,C. Suleman ya dakata ya na jira motar ta fito su shiga. Gaba daya hankalin Aliyu ya koma kan motar,ya kurawa direban ido har sai da ya gama fitowa,a hankali kamanin shi ke dawowa cikin idon shi sanda ya gan shi kwance da dani..da karfi ya dakatar da C. Suleman ya ce kar ka shiga,shi ne,mu bishi!mu bi waccar mota! Da sauri C. Sulaiman ya juya akalar motar har sai da kora ta tashi ya na fadin shi ne wa? Yayinda ya bi motar. Aliyu ya ce zan ma ka bayani daga baya. trafic lyt ya tsaida su,Aliyu ji ya ke kamar ya zama tsuntsu ya tashi ya caf ko gardin nan. Ko da C. Suleman ya gane,sai ya fita ya barwa Aliyu motar ya ce da Aliyu ya biyo bayan shi. Hankali kwance ya kutsa tsakankanin motoci,ko da ya je motar da suke bi sai ya bude ya shiga. A tsorace mai motar ya ce lfy? Kai malam ba ka hankali za ka shigo min mota? Goshin bindiga ya fara nuna masa ta yanda mutanen da ke waje ba za su gani ba,ya daga masa I.D card tare da fadin sunana Captain Suleman Matazu,ina bukatar ka rage min hanya zuwa gida na. Tini zufa ya rufe mai mota,murya na rawa ya ce toh toh,ba laifi Captain. Aka ba su hannu,da kyar ya ke iya driver,C. Suleman ya sa shi a hanya,Aliyu na biye da su… [1:57pm, 11/15/2014] Khadija Sidi: Matar mu 32;33;34;35:kai tsaye gidan C. Suleman suka nufa,ko da mai gadi ya leko ya ga oga ne da wani sai ya yi sauri ya bude gate su ka shiga,Aliyu ma ya biyo bayan su,ya ja ya yi fakin a gefe. C. Sulaiman ya ce ai sai ka fito mu shiga ko?mai mota ya dibirbirce dan Allah dan annabi officer ka yi hakuri..! C. Suleman ya fito ya daka ma sa tsawa get down!ciki na rawa ya fito, C. Suleman ya karbe mukullin ya tisa kyeyar shi suka shiga ciki.da shigar su falo Aliyu ya biyo su,ko da mai motar ya ga Aliyu sai ya durkusa ya na fadin ashe soja ne,wallahi ba su fada min ba,ni babba tawa ta kare! Cikin mamaki C. Suleman ya tsaya ya na kallan su. A fusace Aliyu ya ci kwalar Babba,ya zuba masa mari har sau hudu sannan ya sake shi ya zube kasa hanci na jini,shi ma ya durkusa gaban shi ya dago fuskar shi ya na fadin tin yaushe ku ke cin amana ta?tin yaushe ka fara kwartanci da mata ta? C. Suleman ya ce what the hell?dan uban ka!dan ba ka da kunya?duk matan da ke garin nan ka rasa wacce za ka na tumurmushewa sai Matar mu?matar soja dan uban ka! Na ga alamar ba a sha ka ba ka na yaro,yau zan maka kaciya da harsashi dan ubanka! Ya fara jan wandan Babba. Babba ya sa ihu,wallahi shiri ne,shirya mu ku aka yi,sharri mu ka mata,babu abunda ya taba hada ni da ita,akasali ma ban taba ganin ta ba…Aliyu ya zube a kasa jiki ba laka,C. Suleman ya dada marin Babba me ka ke nufi? Waya sa ka? Baki fashe ya ce Hajiya Mairo ce,ita da Indija….hawaye na zuba daga idanun Aliyu ya ce da C. Suleman shikenan Hajiya ta ta kashe ni! C. Suleman ya ce da Babba fada min yanda abun ya faru. jiki na rawa ya fara labarta mu su.Indija ce ta yi kirana wai suna da aiki,kuma Hajiya ta yi alkarin mallaka min mota idan har aikin ya yi kyau,ni kuwa yanda na ke san mota zan iya aikata komai,amma wallahi da na san soja ne,da bazan yi ba. Bayan na amince,su ka hada ni da yar aikin gidan ka Karima,wacce aka sa ta sace wayar matar ka,aka kuma va ta maganin bacci ta sa mata a ruwa dan mu samu mu yi aikin mu. Bayan ta ba ta ruwan bacci ya sace ta,ta dauki kudi ta ce da mai gadin gidan ka wai inji matar ka ta ce ya siyo magani hawan jini da ke rubuce a yar takarda ya kai wa Hajiya,da har ya mata musu wai idan ya tafi wa zai yi gadi? Shi fa ba a taba aiken shi ba,ta ce da shi umarnin ka ne,sai ya hakura ya tafi. Bayan fitar shi ne na sami damar shiga gidan,inan cikin farfajiyar gidan na ji hon,daga baya aka sauke ka,kafin ka shigo na je na kwanta tare da matar ka ta na bacci ba ta san abunda ke faruwa ba… In banda hawaye babu abunda ke sauka daga idanun Aliyu. Shikan sa C. Suleman jikin shi ya yi sanyi. Ya dafa kafadar Abokin sa,ka yi hakuri Aliyu,kaddara ta riga fata,ka godewa Allah ba ka yiwa Jauda lahani ba,amma sai dai ka rasa cikin da take dauke da shi. Aliyu ya fashe da kuka kamar karamin yaro ya na fadin ka ce na rasa su duka biyun,Suleman na saki Jauda,na sake ta saki uku! C. Suleman ya dafe kai ya na fadin damn!damn!damn it Aliyu! Aliyu ya ci gaba ya zan yi da rayuwata? Ya zan yi da Hajiya? Ya zan yi da wannan gardin dan Allah? Ka fitar min da shi,ka shanya shi a rana sai jini ya fito daga idon shi,ka dake shi Suleman ka tabbata ka balla min shi,amma ina san shi da rai. Babba ya sa ihu ya na fadin dan Allah,ku yafe min,dan Allah! C. Suleman ya na fadin saboda motar banza motar wofi ka wargaza iyali,motar da ba za ta amfane ka ba dan wallahi sai na kona ta,idan na ga dama na hada da kai na kona!ya tisa kyeyar shi su su ka fita domin aikata abunda Aliyu ya umarta,shi ko Aliyu ya na nan ya hade kai da gwaiwa sai kuka ya ke. Can asibiti kuwa ko da na tashi daga bacci na kalli Anty Sa’a da ke tsaye kai na,na ce Anty Sa’a na gaji,dan Allah ki tada ni daga mafarkin nan. Cikin tausayawa ta ce ki yi hakuri Jauda,ba mafarki ki ke ba. Na lumshe idona in ba mafarki na ke ba da gaske ne kenan,Anty Sa’a dama Aliyu zai iya daga hannu ya dake ni? Dama Aliyu zai iya saki na? Saki kuma? Anty Sa’a ta fada a kidime! Hawaye na zuba daga ido na na ce mata saki uku Anty Sa’a…ta na salati ta na sallallami,me ki ka masa ke kuwa Jauda,na fashe da kuka ina fadin ban sani ba,wallahi bi ban masa komai ba,lfy mu ka rabu kafin ya tafi Abuja.Anty Sa’a ta rungume ni ta na fadin mazan kenan Jauda,mazan kenan,ita ma kukan ta ke…. [12:23pm, 11/24/2014] Khadija Sidi: [1:01am, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 36;37;38:Hajiya zaune a farfajiyar gidan ta tare da Indija. Sun yi dai- dai su na cin kaji na murnar sakin da Aliyu ya min. Baki cike da nama Indija ta ce ai Karima cewa ta yi ya ma ta dukan kawo wuka Hajiya,wata kila ma ta mutu,shi ya sa fa ta gudu garin su. Hajiya ta kada baki ta ce ai dama ya kashe shegiya mun huta,kai wannan mutumin Babba ya burge ni kin ga….tini maganar ta kare a iska ganin Aliyu ya banko gate ya shigo,daga ganin sa ba cikin hayyacin sa ya ke ba,biye da shi C. Suleman ne ya taso Babba a gaba. Ganin yanda suka canzawa Babba halitta ya sa hankalin Hajiya ya dada tashi,gaba daya ya fita daga hayyacin sa,idanun sa sun yi jajur kamar jini,sun hada masa jini da majina tafiya ma da kyar ya ke. Jiki na rawa Indija ta koma kusa da Hajiya. Aliyu ya durkusa gaban Hajiya yayinda C.Suleman shi ma ya durkusar da babban gaban ta,ya juya ya fita dan basu waje. Aliyu ya dubi Hajiya ya ce shin Hajiya ko kin gane wannan? Babba kasa kasa ya ke duban Hajiya,gaba daya ya kasa magana.Hajiya ta yi mirsisi ta ce ina ita ko mai kama da babba ba ta sani ba,ya ma za a yi Aliyu ya ma ta wannan tambayar? Aliyu ya dubi Babba ya ce ka ce Hajiya ce ta turo ka ka kashe ni…..Hajiya ta ce lahailahaillallah kun ga tsinanne,cewa na yi ka kashe shi?yaushe mu ka yi haka da kai Babba? Aliyu ya ce Hajiya kin san shi din kenan? Ta fara kame kame,eh toh ya dai taba min aiki haka,eh wanki da guga ba…cikin ladabi Aliyu ya ce Hajiya shi dai tuwo tuwo ne,ba a sake masa suna,har abada ke mahaifiya ta ce,amma Hajiya ba ki kyauta min ba..hawaye su ka fara zubowa daga idanun shi..Hajiya da hannun ki kin kashe min rayuwata Hajiya,Hajiya ba raba ni da Jauda ki ka yi ba Hajiya kin lahanta min rayuwa,kin dasa min ciwo cikin kirji na,kin sa na kashe dana tin kafin ya zo duniya,shin kin kiyaye kiwon da Allah ya baki?ina hakki na Hajiya? Ya za ki yi da hakkin Jauda….? Kuka ya subuce masa kawai ya tashi ya fice,jikin Hajiya da Indija sai bari ya ke,C. Suleman ya shigo,ganin shigowar shi ya kara mu su kwarjini,a tunanin su ya zo tafiya da Indija ne amma sai su ka ya tunkuda kafadar Babba dan su tafi,nan Babba ya fadi sumamme,ba tare da bata lokaci ba ya suri Babba ya sa a kafada ya yi waje da shi. Indija ta ce Hajiya kashe shi fa za su yi..Hajiya ta ce nasan halin Aliyu ba zai kashe shi ba,kar ki damu zai dawo hankalin sa ya zo ya bani hakuri,ta tashi da sauri ina zuwa bari na shiga bandaki,da sauri ta nufi ban daki sai zawo…. Kwana biyu aka sallame ni daga asibiti,na koma gidan Anty Sa’a. C. Suleman ya zo ma Anty Sa’a da zencen Aliyu ta ce sam ita ba za ta saurare shi ba in dai zancen Aliyu ne,ya jira General ya dawo ya masa bayani. Ni kuwa ban da aiki sai kuka,abinci ma ba na cin na kirki,na rabu da wanda na ke so har abada ga shi kuma dan cikin na sa ma na rasa,kwakwalwata ta kasa daukan abunda ke faruwa,gani na ke tamkar mafarki na ke. Washa gari General ya dawo,ransa in yayi dubu ya baci,ya dubi Anty Sa’a cikin fada ya ce dan me yasa?ga duka ga saki?irin sakin da Allah ba ya so?ni dai ina zaune gaban su kai na a kasa,ko kukan ma ba na iya yi. Anty Sa’a ta ce ni har yanzu ban san dalili ba Oga,dan Suleman ya zo min da zancen na yi watsi da shi,tin da yanzu ka dawo ka neme shi ka ji…A fusace ya ce dan ya rai na ni,ya daki yarinya ya sake ta kuma na neme shi?sakin da za a iya yiwa biko shi ake neman biko,bazan neme shi na ji takaici ba,zan iya masa abunda za a zo ana da sani. Ba dai ya sake ta? Toh idan Allah ya kai mu gobe za a je a kwaso kayan ta,Jauda! Ya kira sunana,na ce naam,ya ce kar ki damu,Allah zai mi ki sakayya kin ji? Na ce toh,amma dan Allah ina neman alfar ma,kar abun nan da ya faru ya taba aikin Aliyu. General ya ce zai yi kokari ya ga hakan ya faru.duka babu wanda be tausaya min ba,ana zancen cin mutunci na da aka yimin amma ni takan aikin shi ma na ke. [8:34am, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 39;40;41: Washagari C. Suleman ya je gidan C. Aliyu,falo ya tadda shi gaba daya ya rame ya lalace ko aiki be zuwa. Sanye da singilet da gajeran wando,ga kwalbar giya ta wisky wanda aka bude amma da alama ba a sha ba tukun aje gaban shi. C. Suleman ya dube shi tare da nuna giyan da dan yatsa aboki na ka dawo ruwa ne? Aliyu ya girgiza kai na so na koma,amma na gagara sha. C. Suleman ya dauke giyar ya sa ta gefe gwara kar ka koma,mu ma da mu ke ciki so mu ke Allah ya yaye mana. Duka su ka yi shiru na tsawon minti goma. Daga bisani Aliyu ya ce ya jikin Jauda? C. Suleman ya ce da sauki,su ka dada wani shirun wanda ya fi na fari,C. Suleman ya rasa ta yanda zai fadawa Aliyu sakon da aka turo shi. Aliyu? Ya kira sunan shi,Aliyu ya kalle shi ba tare da ya amsa ba, C. Suleman ya kau da kai tare da fadin Anty Sa’a da General sun ki su saurare ni. Aliyu ya girgiza kai,banga lefin su ba Suleman. Ya ce ka yi hakuri da abunda zan fada ma,Anty Sa’a ta ce a sheda ma ka yau za a zo a kwashe kayan Jauda…A firgice ya kalle C. Suleman,ya tashi ya ja hannun sa shi ko C. Suleman ya bishi ya na tunanin Aliyu ya sami tabin hankali. Daki na ya shigar da shi,kayan sakawa ta fal kan gadon. Ya nuna gadon kaga gadon nan?ka ga kayan nan?akai na ke kwana na ke wuni,a kudundune da kayan Jauda na ke kwana na ke wuni,ko bazan ganta ba na ji kamshin ta na ga kayan ta,ya na dan sassauta min radadi da ke rai na,Suleman sai kuma a kwashe kayan? C. Suleman ya tausaya masa ka yi hakuri Aliyu,ka yi hakuri. Aliyu ya hau gado ya tattaro kayana wanda hannun shi zai iya runguma,ya rungume ya na fadin na yi hakuri Suleman,na yi hakuri. C. Suleman ya ga ba zai iya cigabawa da ganin Aliyu a halin da ya shiga ba,ya fice da sauri.shi ko Aliyu yayi lamo cikin kaya na,idanu lumshe. A ranar aka kwaso kaya na,ranar sai da Aliyu ya yi karamar hauka. Bayan sati daya na sami sauki sosai,na hada nawa i nawa ni da jiddah sai yola gidan Inna ta. Inna ta yi matukar bakin cikin halin da na shiga,ga shi duk na lalace saboda rashin cin abunci. Ta min nasiha tare da adduar Allah ya zaba min wani mijin mafi alkhairi,ni kuwa a rai na cewa na yi ina ai ni da aure har abada,na gama aure a duniya. Sati na biyu da komawa yalo,wata number ce da ban sani ba take damu na da kira,a kalla ta kan kira ni sau uku a rana,safe,rana da dare,kuma duk sanda na daga ba a magana sai dai na karaci hello di na na kashe,idan kuma na ki dagawa an takira kenan sai dai na gaji na kashe wayar. Da abun ya ishe ni ina mita Jiddah ta ce toh sis ki sake layi ki huta ma na, Inna ta ce da ya fi sauki tin da abu ya ki ci ya ki cinyewa. Na ce ina ga hakan zan yi na huta da wannan maitar,a take na ciro sim din na jefar a shara na ce da Jiddah idan za ta makaranta ta biya ta siyo min wani,amma na fi san Glo pls. Ta ce toh. Aliyu ya daga waya domin kiran numba ta da ya saba kullum sau uku,layi ya siya musamman domin jin murya ta duk da ba ya magana amma ya kan sami nutsuwa idan har ya ji murya ta. Da ya kira ya ji ta a kashe,sai be damu ba da yake ya san idan ya takura min dama kashe wayar na ke. Wasa wasa ya yini ya na tryn amma all in vein sam ba ta shiga,waya a kashe. Jauda muryar ta ki ma kin hanani ji! Ya fada a fili. Ai lalle ba zai iya rayuwa babu ni ba,ya yanke hukuncin neman yanda za a yi a maido auren mu ko da kuwa ta hanyar auren kisan wuta ne,toh amma abunda ya tsaya a ranshi shi ne,shin da wa za a yi auren kisan wutar?dan mutum ne mai bala’in kishi da ya ji na sake wani auren gwara ya mutu ya san ba ya duniyar gaba daya,amma da wata azabar gwara azabar,gwara auren kisan wuta da na dundundun. Ya kwanta da mutum daya cikin ransa wanda yayi imanin zai taimaka ma sa ba tare da an sami matsala ba. [10/20, 11:04 PM] aunty jidda: OLD BUT GOLD [9:34am, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 42;43;44: C. Suleman zaune a office aiki ya masa yawa,ya yi na shi,ya yi na Aliyu. Ya ji an kwankwasa kofa,ya ce yes who geos there?murya Aliya ya ji ya ce friend,ya bude kofar ya na murmushi,sanye ya ke cin kaki da alama ya dawo aiki. Da sauri C. Suleman ya tashi ya tarbo shi ya na fadin officer i would kill to have you back to work..ya rungume shi. Aliyu ya na dariya ya ce ba sai kashe kowa ba gashi na dawo.duka suka yi dariya,su ka zauna cikin farin ciki. C. Suleman ya ce wallahi na ji dadin dawowar ka,Aliyu ya ce godiya na ke aboki na. Ina wannan mutumin kuwa? Wanda mu ka kama akan case din Jauda? C. Suleman ya ce ya na nan a prison din jungum,yau kuma shi ka tuna? Aliyu ya ce eh wlh,ina so a sake shi.. C. Suleman ya ce for what?saboda me ya sa? Aliyu ya murmusa saboda idan muka ci gaba da rike shi mun aika ta zalinci,kar ka manta fa wacce ta sa shi ta na nan tafi karfin dauri saboda mahaifiya ta ce,shi ma kuma ya na da family,so na yanke hukuncin sakin shi haka ko ba komai ya ji hannun maza gobe ba ya kara ba. C. Suleman ya daga kafada ya sauke tare da fadin your wish sir.Aliyu ya ce sai kuma alfarma daya da na ke nema wajan ka aboki na. C. Suleman ya ce haba ai ba wata alfarma tsakaanin mu,komai ka ke da bukata ni mai yi ma ka ne. Aliyu ya murmusa tare da fadin na sani Suleman,ban da haufi kan ka,amma wannan alfarmar ta fi gaban tunanin ka. Ka san yanzu be fi saura watanni uku tafiya ta sudan ko? C. Suleman ya ce yes,amma in har cewa za ka yi ba za ka je ba wallahi ba ruwa na,i can’t cover up for you… Aliyu ya dara ya ce haba ni na isa na ce ban zuwa?C. Suleman ya ce na sani ko ka kara jan wuya? Aliyu ya ce hummm alfarmar da na ke so tafi gaban wannan. C. Suleman ya ce fadi ina jin ka. Aliyu ya gyara murya,Suleman ina so ka fahimci inda na dosa,ka ceto rayuwa ta,ba na so na tafi sudan na bar Jauda kafin na dawo wani ya aure min ita,ka auri jauda bayan ta gama idda…… A firgice C. Suleman ya tashi tsaye,ya koma ya zauna ya kalli Aliyu sai kawai ya kwashe da dariya mai karfi. Aliyu ya kule,ba wasa na ke ba,ther is nothing funny here,ba auren sunnah ba,auren kisan wuta na ke nufi. C. Suleman dariya har da kwalla ya ce shikenan tunani na ya tabbata,Ali da ka zauna a gida babu abunda ka ke sai shaye shaye,gashi har ta fara taba kwakwalwar ka,ya dada bushewa da dariya. Aliyu ya sassautar da murya dan Allah C. Suleman ka taimaka min,wlh lfy lau na ke. C. Suleman shi ma ya tsuke fuska tare da fadin bazan iya ma ka wannan ba,shin wanda ya ba ka shawarar auren kisan wutar be fada ma ka ba auren ba ya hallata a musulunci? Aliyu ya ce shaye- shaye ko bin mata wanne ne daga ciki ya halatta wanne ne ba ka yi? Sai da aka zo wajan taimako na ka ce za ka bada hujja da Allah? C. Suleman ya tashi ya je ya bude kofa ya juyo ya kalli Aliyu ya ce like seriously ba ka cikin hayyacin ka,duk sanda ka fara tunani da kyau let me knw pls. Ka rufo min office idan ka tashi fita. Ya fice abun sa. Aliyu ya buga hannu a table ya na fadin i hate this more dan you dammit!ya tashi ya fita a fusace. Bangaran Hajiya kuwa tin tafiyar Aliyu be kara waiwsyar su ba,har wajen mallam da boka sun je dan a mantar da Aliyu abunda ya faru a jawo hankalin shi gare su amma abu ya gagara,kullum lamari dada lalacewa ya ke. Yau ma daga wajan wani bokan su ke. Hajiya ta ce Allah dai ya sa ba wahalar banza mu ka sake yi ba Indija. Indija ta ce amen dai Hajiya,wlh ni abun har tsoro ya ke ba ni. Hajiya ta ce ba ki ji bokan ya ce taurin kai gare shi ba? Wlh halin uban sa ne ai. Tashi ki dauko turmi ki ga mu fara daka maganin. Indija ta dauko turmi suka fara aikin boka Matar mu 45;46;47:ko da C. Suleman ya koma gida da daddare sai ya nemi bacci ya rasa,taba kuwa ya shanye kusan kwali biyar ya kan na shida,da ya dau tsinke daya zuka biyu ya ke ma ta ta kare. Gaba daya Aliyu ya jagula masa lissafi,mtsw ya ja tsaki yayinda ya tsuki taba ya fuzar da yaki saba. Ya ma za a yi Aliyu ya tinkare shi da zancen nan? Ya za ayi shi Suleman ya auri Jauda? Wai auren kisan wuta?Ai ko na kisan gobara ne da sake! Nan ciyar shi ta shiga sake saken yanda zai kaucewa zancen Aliyu,dan shi mutum ne mai dan karan naci idan ya so abu,tabbas sai ya dawo gare shi… Bangaran Aliyu kowa dama tin rabuwar mu ya yi hannun riga da bacci,in har ya sami bacci toh sai dai sace shi ya yi. Shima zaune ya ke a falo,hannun shi rike da hoto na. Cikin zuciyar sa kuwa saka yanda zai yi ya Sule ya yarda da kudirin shi ya aure ni ya kuma sake ni dan ya samu ya dawo da ni,idon OLD BUT GOLD [9:34am, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 42;43;44: C. Suleman zaune a office aiki ya masa yawa,ya yi na shi,ya yi na Aliyu. Ya ji an kwankwasa kofa,ya ce yes who geos there?murya Aliya ya ji ya ce friend,ya bude kofar ya na murmushi,sanye ya ke cin kaki da alama ya dawo aiki. Da sauri C. Suleman ya tashi ya tarbo shi ya na fadin officer i would kill to have you back to work..ya rungume shi. Aliyu ya na dariya ya ce ba sai kashe kowa ba gashi na dawo.duka suka yi dariya,su ka zauna cikin farin ciki. C. Suleman ya ce wallahi na ji dadin dawowar ka,Aliyu ya ce godiya na ke aboki na. Ina wannan mutumin kuwa? Wanda mu ka kama akan case din Jauda? C. Suleman ya ce ya na nan a prison din jungum,yau kuma shi ka tuna? Aliyu ya ce eh wlh,ina so a sake shi.. C. Suleman ya ce for what?saboda me ya sa? Aliyu ya murmusa saboda idan muka ci gaba da rike shi mun aika ta zalinci,kar ka manta fa wacce ta sa shi ta na nan tafi karfin dauri saboda mahaifiya ta ce,shi ma kuma ya na da family,so na yanke hukuncin sakin shi haka ko ba komai ya ji hannun maza gobe ba ya kara ba. C. Suleman ya daga kafada ya sauke tare da fadin your wish sir.Aliyu ya ce sai kuma alfarma daya da na ke nema wajan ka aboki na. C. Suleman ya ce haba ai ba wata alfarma tsakaanin mu,komai ka ke da bukata ni mai yi ma ka ne. Aliyu ya murmusa tare da fadin na sani Suleman,ban da haufi kan ka,amma wannan alfarmar ta fi gaban tunanin ka. Ka san yanzu be fi saura watanni uku tafiya ta sudan ko? C. Suleman ya ce yes,amma in har cewa za ka yi ba za ka je ba wallahi ba ruwa na,i can’t cover up for you… Aliyu ya dara ya ce haba ni na isa na ce ban zuwa?C. Suleman ya ce na sani ko ka kara jan wuya? Aliyu ya ce hummm alfarmar da na ke so tafi gaban wannan. C. Suleman ya ce fadi ina jin ka. Aliyu ya gyara murya,Suleman ina so ka fahimci inda na dosa,ka ceto rayuwa ta,ba na so na tafi sudan na bar Jauda kafin na dawo wani ya aure min ita,ka auri jauda bayan ta gama idda…… A firgice C. Suleman ya tashi tsaye,ya koma ya zauna ya kalli Aliyu sai kawai ya kwashe da dariya mai karfi. Aliyu ya kule,ba wasa na ke ba,ther is nothing funny here,ba auren sunnah ba,auren kisan wuta na ke nufi. C. Suleman dariya har da kwalla ya ce shikenan tunani na ya tabbata,Ali da ka zauna a gida babu abunda ka ke sai shaye shaye,gashi har ta fara taba kwakwalwar ka,ya dada bushewa da dariya. Aliyu ya sassautar da murya dan Allah C. Suleman ka taimaka min,wlh lfy lau na ke. C. Suleman shi ma ya tsuke fuska tare da fadin bazan iya ma ka wannan ba,shin wanda ya ba ka shawarar auren kisan wutar be fada ma ka ba auren ba ya hallata a musulunci? Aliyu ya ce shaye- shaye ko bin mata wanne ne daga ciki ya halatta wanne ne ba ka yi? Sai da aka zo wajan taimako na ka ce za ka bada hujja da Allah? C. Suleman ya tashi ya je ya bude kofa ya juyo ya kalli Aliyu ya ce like seriously ba ka cikin hayyacin ka,duk sanda ka fara tunani da kyau let me knw pls. Ka rufo min office idan ka tashi fita. Ya fice abun sa. Aliyu ya buga hannu a table ya na fadin i hate this more dan you dammit!ya tashi ya fita a fusace. Bangaran Hajiya kuwa tin tafiyar Aliyu be kara waiwsyar su ba,har wajen mallam da boka sun je dan a mantar da Aliyu abunda ya faru a jawo hankalin shi gare su amma abu ya gagara,kullum lamari dada lalacewa ya ke. Yau ma daga wajan wani bokan su ke. Hajiya ta ce Allah dai ya sa ba wahalar banza mu ka sake yi ba Indija. Indija ta ce amen dai Hajiya,wlh ni abun har tsoro ya ke ba ni. Hajiya ta ce ba ki ji bokan ya ce taurin kai gare shi ba? Wlh halin uban sa ne ai. Tashi ki dauko turmi ki ga mu fara daka maganin. Indija ta dauko turmi suka fara aikin boka Matar mu 45;46;47:ko da C. Suleman ya koma gida da daddare sai ya nemi bacci ya rasa,taba kuwa ya shanye kusan kwali biyar ya kan na shida,da ya dau tsinke daya zuka biyu ya ke ma ta ta kare. Gaba daya Aliyu ya jagula masa lissafi,mtsw ya ja tsaki yayinda ya tsuki taba ya fuzar da yaki saba. Ya ma za a yi Aliyu ya tinkare shi da zancen nan? Ya za ayi shi Suleman ya auri Jauda? Wai auren kisan wuta?Ai ko na kisan gobara ne da sake! Nan ciyar shi ta shiga sake saken yanda zai kaucewa zancen Aliyu,dan shi mutum ne mai dan karan naci idan ya so abu,tabbas sai ya dawo gare shi… Bangaran Aliyu kowa dama tin rabuwar mu ya yi hannun riga da bacci,in har ya sami bacci toh sai dai sace shi ya yi. Shima zaune ya ke a falo,hannun shi rike da hoto na. Cikin zuciyar sa kuwa saka yanda zai yi ya Sule ya yarda da kudirin shi ya aure ni ya kuma sake ni dan ya samu ya dawo da ni,idon shi ya rufe sam baya cikakken tunani,shi dai kawai ya maido ni gidan sa. Birnin yola ni ma hakan take,ba na iya bacci dan da na fara tashi na ke a firgice. Sai da aka dage da addu’a sosai. Cikin zuciya ta na kasa gane mai na kewa Aliyu,tsana ce ko kyewa?da ga baya na yanke hukuncin duka biyun ne,kai ba ma Aliyu ba,duk wani da namiji na tsane shi… Ranar wata lahadi da yammaci C. Suleman na shirin fita sai ga C. Aliyu,da ganin shi sai da gaban shi ya fadi dan rabon shi da Aliyu tin ranar da ya zo ma sa da zencen auren na,ko waya ma sa ba ya dagawa. Kamar mara gaskiya C. Suleman ya rasa makama. C. Aliyu ya karaso gare shi ya ce Suleman,kan ka cemai kawai sai ya durkusa gaban shi,ya sake cewa Suleman na durkusa gaban ka,na zo gare,ka taimaka min ka rufa min asiri. Tini C. Suleman shi ma ya durkusa ya ce ni ma na durkusa ma Aliyu,ka taimake ni ka janye wannan maganar. Aliyu ya ce auren kisan wuta ba wai auren da za ku zauna zaman aure ba. C. Suleman ya ce martaba da kimarta ya fi gaban haka,Aliyu ya ce ba dadewa za ka yi tare da ita ba,idan ka ga dama ko tariya ba za ta yi ba. C. Suleman ya ce ko na sakanni uku ne bazan iya ba,Aliyu ya ce ka duba dangan takar mu da zumunci… C.Suleman ya ce su na dabu shi yasa bazan iya ba….Aliyu ya mi ke a fusace ya na fadin an gaya ma ka ni ma ina jin dadin tambayar ka ne Suleman! Wallahi ji na ke tamkar rai na zai fita duk sanda na maka maganar,amma sai dada kunta ta min ka ke,ka kasa taimaka min,haba dan Allah,idan ba kai ba wazan yarda da shi da wannan maganar,dan na yarda da kai ne Suleman,yarda ce ta kawo na san ba za ka cutar da ni. C. Suleman ya tashi a sanyaye ya ce Aliyu na yarda zan yi abunda kake so na yi maka,amma bazan buye ma ba,ka takura min,ka matsa min ka shiga rayuwata Aliyu. Aliyu ya dafa kafadar shi tare da fadin na sani Suleman ,na kuma gode Allah ya bar zumunci,inshaAllahu ba za ka yi dana sani ba. Ya fice ba tare da bata lokaci ba dan karda ma Suleman ya canza ra a yin sa. C. Suleman rai a bace ya koma dakin ya bude kwabar giya ta konkwada ya yi tatir. [7:07pm, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 47;48;49:Washagari C.Suleman ya je ya sami Anty Sa’a ya sheda mata ya sami matar da zai aura,ta rangwada guda,ta ce ai bari ta yi sauri ta yiwa General albishir. Ko da General ya ji yayi matukar farin ciki,ya kira C. Suleman domin jin maganar da ga bakin shi. General ya kalli C. Suleman da ke durkushe gaban sa ya ce waye mahaifin yarinyar ka ga ya kamata mu je mu gabatar da kan mu ko? Nan fa daya zufa ya shiga ketowa C. Suleman,ya sa hannu ya share ya ce ai Sir dama duk gida ne,Jauda ce wacce na ke so na aura idan ta gama idda…Anty Sa’a ta doka salati,shi kan shi General maganar ta ma sa ba zata,amma sai ya yi sauri ya mai da mamakin shi cikin rai sa. Anty Sa’a ta ce sam da sake,ba za ka ja mana zagi ba,matar tsohon abokin na ka Sule?ko iddar ba ta gama ba kafara kai hari? General ya ce ina Sule,ka na ji na? C. Suleman ya amsa da kasan makogwaro Ina ji Sir. General ya ci gaba a hakika nin gaskiya ba zan iya goya maka baya a wannan magana ta ka ba. Anty Sa’a ta ce ko ni ma ban goyi baya ba. General ya ce sannan kuma ba zan hana ka neman auren Jauda ba, Anty Sa’a ta karbe ni zan hana… Rai a bace General ya ce haba Sa’adatu!ya ina magana ki na katse min haka,wannan ai ba tsari ba ne. Anty Sa’a ta ce Allah ya baka hakuri. General ya koma ga C. Suleman ya ce umarnin da zan baka shi ne bayan Jauda ta gama idda ka je ka sami Mahaifiyar ta ka tambayi Izinin ta,idan ta amince ka nemi auren na ta sai ka zo ka same mu,mu kuma sai mu tinkari dangin mahaifin ta da zancen. C. Suleman ya ce toh madallah,na gode Sir,zan je yolan bayan ta gama idda. General ya ce toh Allah ya zaba abunda ya fi alkhairi. C. Suleman ya ce amen. Ya tashi tare da fadin ni zan tafi,a tashi lfy,General ya ce Allah ya sa,Allah ya kiyaye,ya ce amen ya fita ba tare da Anty Sa’a ta sake ce masa kala ba. Bayan fitar shi General cikin rarrashi ya ce Haba madam,ai irin wannan ba a nunawa kiri kiri ba a so,yanzu ma toh menene lefin auren idan ya nema? Ince ba mu muka dage ya fito da mata mu aura ma sa ba? Yanzu ya ce ga wacce ya ke so sai mu ce ba mu san zance ba?Anty Sa’a ta ce yanzu Oga ya rasa wacce ya ke so sai tsohuwar matara abokin sa? Ai sai jama’a su Zage mu! General ya murmusa ya ce tsohuwar matar abokin na sa dan ya aura haramun ne?yaya fa na saki kani ya aure bare kuma abokai,ba sakin ta yayi ba? Anty Sa’a ta ce amma dai halin suleman ne sai shi,shi Aliyun da mu ke gani nitsastse ga abunda ya aikata,bare kuma Sule wanda ba sai an tona ba ka dai san halin shi.. General ya ce haba madam kamar ba dan uwan ki ba?me zai hana ki masa fatan alheri,ki ka sani ko Jaudar ta zama ita ce hanyar shiriyar shi? Anty Sa’a ta ce Allah ya tabbatar da alkhairi,General ya murmusa yauwa ko ke fa. Ta tashi bari dai na karasa aiki na kar na bar zancen Suleman cikin rai na ya samin hawan jini. Kwanci tashi aka ce asarar mai rai,na kusa gama idda,na fara shirye shiryen komawa makaranta domin yin MBA(Masters in bussness admin) wanda na ke neman admsion anan Federal Uni ta yola,na kuma shiga wata islamiya ta matan aure wanda na ke zuwa weekends.Ina kwance a daki waya ta ta fara kara,na dauka gami da karawa a kunne na na ce Salama’alaikum,na ji shiru,na ce hello,hello,tsit ba amsa. na katse ina fadin na tsani irin haka wlh,Jiddah ta shigo ta ce ke dawa kuma? Na ce wlh wata number ce ta matsamin kwanan,kamar dai waccar,sai a kira a ni amma a ki magana,ina ga zan dai na daga number da ban sani ba kawai,Jiddah ta ce shikenan ya fi sauki ma. [10:19pm, 11/16/2014] Khadija Sidi: Matar mu 50;51;52:Aliyu ya kalli wayar da ke hannun sa ya ce Suleman kullum muryar Jauda dada dadi ta ke min. C. Suleman ya murmusa kawai ba tare da ya ce komai ba. Zaune su ke a Airport,C.Suleman ya rako Aliyu,a ranar jirgin su na zuwa sudan zai keta hazo. Aliyu ya dubi Suleman ya ce Suleman na san ba karamin takura ma ka na yi ba,na gode,Allah ya bar zumunci. C. Suleman ya ce karka gode min tukunna,ka bari na je yola na tattau na da Innar Jauda tukun,ta iya yiyuwa su hana ni. Aliyu ya ce abu ne mawuyaci ta hana ka,ban da haufi akan haka. Kar ka manta ta dalilin ka aka ba ni Jauda,bare kuma kai da kanka ka ke nema. C. Suleman ya ce sai kuma hanzari ba gudu ba,shin me zan ce game da sakin da zan ma ta bayan na aure ta? Aliyu ya ce lokacin za mu fada musu gaskiya,har makasudin mutuwar aure na da Jauda tin da yanzu sun ki su saurare mu. Ka ga ba lefi idan ka ce za ka maido min da mata ta ta hanyar sakin ta na aura. C. Suleman ya saki ajiyar zuciya ya ce Allah ya sa mu dace,Aliyu ya ce amen. Aka fara kiran su Aliyu domin jirgin su ya fara himmar tafiya. Nan su ka yi sallama,da yiwa juna fatan alkhairi,Aliyu ya masa alkawarin kiran sa da ya sauka. Sati biyu da gama idda,sai ga C.Suleman a yola. Ya tadda ina Islamiya,Inna da jiddah kawai ya samu a gida. Bayan sun masa tarba na ban girma ya huta,ya tasowa Inna da maganar neman aure na. Inna ta ji dadin zencen tare da fadin ai zuri’ar Abubakar da ta Sa’a ba abun yarwa ba ne,ba komai sai fatan alkhairi. C. Suleman ya yi godiya sosai,a ran shi fadi ya ke Aliyu ne dai ya turo ni.kafin a tashe mu da ga islamiya har C. Suleman ya koma,so ban dawo na same shi ba. Bayan na ci abunci na huta,sai na haukan wanke wanke,ina cikin yi Inna ta zo ta same ni ta ce Jauda ko sanda ki na islamiya Suleman ya zo ya tafi. Na ce eh haka Jiddah ta fada min,na ce Allah sarki Allah ya yi ba za mu hadu ba. Inna ta ce,gashi kuma musammam dan ke din ya zo ba. Na ce dan ni kuma Inna,ta ce eh,ya zo neman iznin neman aure ne. Na murmusa gami da cewa wato S. man dai da gaske yar jiddar ta mu ya ke so ya dauke. Inna ta ce Jidda kuma?ai ni Jauda ya ce min. A hankali na zame hannu na daga cikin kwanukan wanke wanke na ce Inna ba dai ki fahimce shi ba,Jidda fa ya ke nufi. Ta ce ya azancin ban fahimce shi ba,da bakin shi ya ce da ni Jauda.. na girgiza kai na ce lalle ma mutumin nan ya yi shaye shayen na shi da ya saba ya fada ma sa karya kenan,wallahi Inna be da cikakken hankali….kul!Inna ta kwabe ni,kar in sake ji,dan ya zo neman auren ki sai ya zama kin sami damar cin mutunci Jauda? Na saka kuka,haba Inna,abokin miji na ne fa,abokin Aliyu ne..Inna ta ce abokin tsohon mijin ki dai ba mijin ki ba,wanda ya mi ki dukan kawo wuka ya mi ki sakin keta ba! Na ce wallahi ba na so,ba na san shi bazan aure shi ba Inna Inna ta dafa kafadata tare da fadin na riga na amsa masa Jauda..kuka na ya karu,na ce Inna sai ka ce ba kya so na Inna,inna sati uku fa kacal da gama idda ki ce na auri abokin sa? Inna ta ce ki kasance mai biyayya Jauda,Allah zai kasance tare da ke. Ta fita jiki a sanyaye. Na daura hannu na biyu bisa kai na ina fadin Innalillahi wa’innailaihirrajiun!ya Allah wannan jarabawar ka ce,ya Allah ka sa na gama lfy,Allah kar ka sa hankali na ya gushe……. Mu hadu MATAR MU KASHI NA BIYU…. Ta ku Khadija Sidi. mu 2 by khady sidi Posted by UMMU-ABDOUL on NOVEMBER 1, 2016 [01/11 22:47] Salma Ateeku: [2:30pm, 11/27/2014] Salma Ateeku: [10:57pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 1;2;3: Cikin sauri Jiddah ta shigo ta na fadin haba sis,dan Allah sis ki yi hakuri,kar ki manta ko wani tsananani ya na tare da sauki.. Cikin kuka na ce Jiddah aure fa,aure fa ai aure ba zaman wasa ba ne,bare kuma ace da Suleman zan yi,aminin tsohon miji na. Jiddah ta tausaya min matuka. Ta ja ni mu ka je dadi ki ta ta rarrashi na,har ta samu na dan yi shiru sai shassheka da ajiyar zuciya kawai na ke. A can birnin kano kuwa Suleman ya je gidan Anty Sa’a ya shedawa General yanda su ka yi da Inna,General ya ji dadi dama abunda ya ke so kenan dan shi ya na maraba da kudirin C. Suleman. General ya ce tinda haka ne sai Sa’a ta fadawa su baffa a sa rana mu je mu gabatar da kan mu wajen dangin mahaifin Jaudar ko?Anty Sa’a da ke zaune gefe uhum kawai tace. General ya ce toh kai Sule menene plan din ka? Kamar zuwa yaushe ka ke son auren ya kasance? C. Suleman ya dukar da kai ya ce san samu asa kamar watanni tara,ba dan komai ya zabi wattanni mai tsaho haka ba,sai dan ya samu lokacin ya yi daf da dawowar Aliyu. Nan fa General da C. Suleman su ka raba gari,General ya ce wata tara? Ina ba wannan maganar,wata tara fa? Me ya rasa da har sai ya kai wata tara zai yi aure? C. Suleman ya sosa keya,ya ma rasa karyar da zai yi,kawai sai zancen gida ya fado masa ya ce dama gidan da za mu zauna ne sai an karasa gini dan gidan da na ke ciki yanzu ya mana kadan. General ya dara aw matsalar gida ne? Indai wannan ne kar ka damu ka shiga gidana da yake first gate,ka ga tsakanin mu ma ba nisa sosai,ma ke duba ku ma….gaban C. Suleman ya fadi cikin ran shi fadi ya ke hasbinallahu wani’imal wakilu,dan a tsarin maganar shi da Aliyu ba zancen tariya ma. Be gushe ba General ya ci gaba da fadin saboda haka a wata daya za mu yi komai da komai matar ka ta tare. Kash ya zai yi ba daman musu,dole ya ce toh Allah ya saka da Alkhairi sir. General ya na washe baki a tunanin shi gwanin ta ya yiwa C. Suleman,nan kuwa gaba daya ya ruguza masa lissafi,ya ce ai yiwa kai ne. Ya na komawa gida ya yi kiran Aliyu,Aliyu na dagawa ya ce dashi Aliyu ka kunto min kura!nan ya fada ma sa yanda su ka yi da General. Aliyu ya ce duk yanda za a yi ya yi kar ya yarda a yi auren kwana kusa, C. Suleman ya ce zai jarraba ya gani,shi ma ba zai yarda a sa shi cikin keji ba. Har sun yi sallama zai aje wayar Aliyu ya ce Suleman Jauda fa? Ya ta karbi zancen aure? C. Suleman ya ce be sani ba,amma basan ba za ta so ba. Aliyu ya yi ajiyar zuciya. Su ka ki sallama. Bayan ya aje wayar ya dau taba ya fara sana’a…… [10:58pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: [4:58pm, 11/17/2014] Salmah Ateeku: 4;5;6; Na zama abar tausayi abunci ma ba na ci na kirki,gaba daya na lalace,hatta gashin kai na sai da ya karye dan rashin kula dan Allah ma ya sa ban taba sa relaxer ba.. Ina kwance Jiddah ta shigo ta ke fada min wai General da Anty Sa’a sun zo,kafin ta gama rufe bakin ta Anty Sa’a ta shigo da gudu na tashi na rungume ta ina fadin dan Allah Anty Sa’a ba na so,wallahi ba na san shi,dan Allah ki taimaka min kar a min dole tin da ni ba budurwa ba ce ina da zabi….Da gaskiyar ki Jauda ki na da zabi a musulunce haka ya ke!muryar General mu ka ji kamar daga sama,ashe ya na biye da Anty Sa’a,ta jani kan gado mu ka zauna,General ya ce mun san damar ki ce,amma sai mu ka nemi alfarma,bazan boye mi ki ba da cewa na yi ba zan goyawa Suleman baya ba akan zancen nan,amma ganin alkhairan da ke ciki da kuma yanda Inna ta ke son lamarin a dole na sa baki. Babu mai miki dole,amma mu na neman alfarmar amincewar ki dan mun san ki da biyayya,idan kin amince gobe za mu zo da baffanin Suleman wajan waliyan ki,idan kuma ba ki amince ba,toh hakan ba zai faru ba…na fashe da kuka ina fadin na yi biyayya,na amince. General ya ce Allah ya mi ki albarka. Ya fice. Anty Sa’a har da kwallan ta ta ce Allah ya saka mi ki da alkhairi,gaskiya kin isa ‘ya kin yi biyayya. Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba,aka sa ranar aure na da C.Suleman wata daya dal. Ba ni ba shi kan shi C.Suleman da ya tsokano gobarar hankalin sa a tashe ya ke,sam be yi tunanin General za su ma sa wannan denyan aiki ba. Ya kira layin Aliyu ya ki shiga har ya gaji ya fara tunanin komawa ya ce da General ya fasa auren,amma tsoro ya hana shi,haka ya hakura ya zubawa sarautar Allah ido. Ta bangare na kuwa sunanan sun dage wai su suna shirya amarya,ni ko haushi ma su ke ba ni,duk tsumi,cikwidi ko zumar da Inna da kawayenta ke bani a toilet na ke zubarwa,haka zalika duk abunda aka tambaye ni shawara sai cewa na ke duk abunda su ke so zai yi. Ango kuwa ko kira na be taba yi ba tin da aka fara wannan budirin,haka ya fi min daidai dan daga shi har Aliyun babu wanda na ke kauna. Ni kunyar jama’a na ke ji,dan surutu kan na san sai na sha,wata hudu da mutuwar aure na na auri aminin miji na. [6:30pm, 11/17/2014] Salmah Ateeku: Matar mu 2 7;8;9:Ana sauran sati daya daurin aure aka kawo lefe,lefen ya yi kyau ko na budurwa sai haka. Ni kuwa ko a jika na be ma ishe ni kallo ba. Ranar juma’a aka daura min aure da C. Suleman,rai na kamar zai fita dan kuka,kukan da na yi ya ma fi wanda na yi sanda na ke budurwa. Washagari da safe aka dauki amarya sai kano. Anan gidan da General ya bawa Suleman na tare,gidan ya yi kyau matuka,sama da kasa ne,ni aka bawa kasan C. Suleman a sama. Abokan C. Suleman sun bukaci a musu sword crossing amma ya ce sam ba zai yi ba,bayan daurin aure babu abunda ya kara yi,sai su Anty Sa’a da su ka yi yinin su. Magrib na yi Anty Sa’a ta ce mutan yola kowa ya tattaro nasa ya nasa su bar gidan amarya,ba za su yi wannan al’adar na kwana gidan amarya ba,General ya hana. Nan na shiga birgima ina kuka kamar karamar yarinya,amma ko a jikin su,wata tsohuwa ma cewa ta yi ku barta ai ba farau ba ne da za ta tadawa mutane da fita. Bayan kowa ya watse na sha kuka na na koshi,har sai da muryata ta dashe. Har 12 biyu na dare ido na biyu,ban ji motsin C. Suleman ba,hakan ya min daidai. Na sanya kayan bacci na na yi kwanciya ta. Da misalin karfe uku na dare alarm di na yayi kara,na tashi na kashe.Na shiga toilet na dauro alwala domin yin nafila,na fito ina duba hijab cikin kayana na ji kamar ana bubbuga kofa,na raba kunne ina jiran tsammani..da karfi aka banko kofar daki na,C. Suleman ya shigo ya na tangali,a buge ya ke,saura kiris ya fadi kasa. Na ce Innalillahi wa’innailaihirajiun,ni Jauda irin rayuwar da na koma kenan? Ya daka min tsawa cikin maye ya ce ke! Wacece ke? Tini na sa kuka,ina fadin dan Allah kar ka karaso kusa da ni,wallahi na tsane ka na tsani halin ka S.man! Matsowa ya ke dada yi,warin giya ya bugi hancina,na fara ja da baya,ya na matsowa ya fara kira na da Monika my baby,me nene ki ke gudu na,zo ki ji dadin rayuwa, na ce Suleman Jauda ce,Jauda tsohuwar matar abokin ka ba Monika..ya ware hannu aboki? Monika is my baby aboki na,come here.. Wayyo ni Jauda,na kai bango C. Suleman ya sa ni a lungun ya hada ni da jikin sa yayinda ya ke kokarin kissn dina,tini kai na ya fara juyawa,na yi kokarin tunkudar kafadar shi amma inaaa duk da a buge ya ke karfin shi yayi biyun nawa,tini ya warce ni yayi gado ni ina ihu ina kiran sunan Inna,cizo da yukushi babu wanda ban yiwa C. Suleman ba amma ko a jikin shi,tini ya min yaga yaga da kayan bacci na,ga wani azaba da na ke ji domin ba karamin azabartar da ni C. Suleman ya yi ba,tin ina iya kuka har na kasa sai Inna kawai na ke kira. Be kyale ni ba sai da ya gama biyawa kan sa bukata,nan ya zube a kai na ya fara bacci…. [2:31pm, 11/27/2014] Salma Ateeku: [10:59pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 10;11;12:Na rasa da mai zan ji,da nauyi C. Suleman ko kuwa da ciwan da jiki na ya ke min. A hankali na yi kokari na janye jina da kyar na mirgina gefe,na ja zanin gado na rufe jikina,in banda ajiyar zuciya babu abunda na ke kukan ma ya ki zuwa. Har aka kira sallar asuba ido na biyu ban rintsa ba Sai wajan karfe shida Suleman ya farka,ya bi dakin da kallo a hankali ya na kokarin gane inda ya ke,ko da ya gano ni kudindine cikin zanin gado sai ya runtse ido,gaba daya ya ji ya tsani kan shi dan a sannan abunda ya faru jiya ya zo masa kwakwalwa a zahiri. Ni kuwa ko kallo be ishe ni ba,na kau da kai gefe guda. Cikin zafin nama ba tare da ya ce min komai ba ya tashi ya fita,na bi bayan shi da kallo a rai na na ce katon banza! Kai tsaye dakin sa ya nufa,gaba ji ya ke kamar rashin adalci akan shi ya kare,ya tsani Aliyu ya tsani kan shi,be taba tsanar giya ba kamar ranar. Abunda ke zuwa ran sa shi ne kalmar rape,duk da da sunan aure a tsakanin mu,bandaki ya nufa ya yi wanka ya gabatar da sallar asubah. Ya na idarwa ya fita ba tare da ya sake kallan inda na ke ba. Ni kuwa inan kwance in da na ke,kamar da ga sama na ji sallamar Anty Sa’a ta shigo ta ganni kudunnune nan inda C. Suleman ya bar min,ta ce Jauda? Ta karaso ta tabani sai na sa mata kara dan dukkanin gabobin jikina ciwo suke,ga gajiyar taro da na tafiya,ga shi kuma C. Suleman ya sauke min tashi gajiyar. Anty Sa’a ta ce Jauda lfy? Ta sa hannu ta yaye zanin gadon da na kudunduna ciki. Ko da ta ga yanda rigar bacci na ya yayyage da kuma halin da na ke ciki sai ta sa salati ta na fadin haba no wonder Sule ya zo min da sassafe wai ki na nema na,Jauda ta karfi ya miki haka?shin kin masa gardama ne hana sa hakkin sa ki ka yi har ya aikata mi ki wannan abu haka?kukan da ya tsaya kasan makogaro na tini ya subuce,na kasa ba ta amsa,cikin tausayawa ta ce yi shiru,bari na taimaka miki ki sami sauki kafin baki su fara cika mi ki gida,kya min bayani daga baya. Anty Sa’a ta hada min ruwa mai zafi wanda ta dafa ganyen magarya a ciki,ta zo ta kama ni ta sanya ni cikin ruwan,ta barni ciki zaune ta koma ta yaye zanin gado,ta sake wani. Bayan ta gama ta sake hada wani ruwan zafin ta gasa min jiki da shi har sai da na fara jin dadin jiki na,sanna ta hura garwashi ta dauko itacen farar kaya da ke cikin show glass dina na ruraren wuta,ta ce na zauna bakin gado na matso da kafafu na gaba,ta sa kaskon karkashin kafar tawa yanda hayakin zai na shiga jiki na,ta rufa min zani. Shi icen farar kaya ice ne mai kyau da dinbim tarihi,ance Annabi ya taba mubaya’a karkashin bishiyar. Ammafanin icen shi ne matse mace,matan sudan da shi su ke amfani da sun haihu idan ba a musu din ki ba,akan kuma amfani da shi wajan yiwa amare dukkan. [11:00pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: [8:38am, 11/18/2014] Salmah Ateeku: Matar mu 2 13;14;15 Anty Sa’a ta yi min afmani da farar kayar ne domin yanda C. Suleman ya min sai da farar kayar,amma da sauki tinda ba sai an min din ki ba,haka na ji Anty Sa’a na fadi. Tsaf Anty Sa’a ta gyara ni,ta hada min ruwan tea mai kauri,ina gama sha bacci ne mai nauyi ya sace ni,ba ni na farka ba sai bayan azahar,Anty Sa’a ta tafi gidan cike da mutum yola sun zo min sallama za su koma washagari. Cikin jin dadi na wuni da yan uwana,sau uku Anty Sa’a na kira dan jin lfy ta,in banda Jiddah ko a yan yola babu wanda ya gane ina da damuwa,itama din ce ma ta na yi ba komai,kalau na ke. Da kuka haka na rabu da su Jiddah,magriba na yi na sa mukulli na kulle daki na,ban sake fita ba ban koma ji motsin C. Suleman ba har garin Allah ya waye. Wayar Anty Sa’a ce ta tada ni,wai ta kira ta ji lfy,dan ta kira Sule ya ce am owk ba sai ta zo ba. A zuciya ta na ce eh dole ya ce haka tin da jiya ba a sami damar mugunta ba,wata kila ma wajan karuwan sa ya kwana. Anty Sa’a ta min fada,wai shi ma ta masa ya rinka bi na a hankali,ni ma kuma na daure na dai na masa gardama na ke bashi hakkin sa,toh kawai na ce ba tare da na tonawa C. Suleman asiri ba dan darajar igiyar auren sa da ke kai na. Bayan na yi wanka na fito falo,kan dining table na ga wata yar takar da tare da bandir din kudi,na daga takardar na duba,rubutun C.Suleman ne,incase you need anythng that the house lack…na ja tsaki,na koma daki na nemo biro,bayan takardar ni ma na rubuta I don’t need your money for all the time to come..na ajiye masa na shiga zagaye ina ganin gidan,ba shakka gida ya yi kyau matuka ga shi a wadace. Bangaren C. Suleman ne kawai ban hau ba. Bayan na gama zageye na koma daki na ci kuka na gani na ke rayuwa ta juya min baya. Shi ko C. Suleman ashe gaba daya kwanan gidan ma ba ya yi. Sam be kaunar haduwa da ni. Abun bakin ciki da takaici shi ne ya kasa samun Aliyu,gani ya ke ya cuce shi ya gudu. Ya yi mamaki yanda Anty Sa’a ta ma sa maganar Jauda,hakan ya tabbatar ma sa ban fada ma ta gaskiyar abunda ya faru ba. Da yamma bayan dawowar sa ya tadda kudi da takarda in da ya ajiye,ko da ya karanta abunda na rubuta cikin takardar sai ya ce good for you. Ya dau kudin sa ya mayar aljihu. [10:42am, 11/18/2014] Salmah Ateeku: Matar mu 2 16;17;18: kwanci tashi na kai wata biyu gida C. Suleman,amma maganar arziki ba ta taba hada mu ba,akasali ma da na ji motsin shi guduwa na ke,shi ma kuma C. Suleman din sam ba ya kaunar gani na,akasali ma ya tsani Aliyu gani ya ke ya gama cutar shi ya gudu,gashi har ya yau be sami shi a waya ba,shi kuma be neme shi ba. Anty Sa’a ce mai debe min kyewa,kusan kullum a gidan ta na ke wuni amma ko da wasa ban taba bari ta san halin da na ke ciki ba. Ban rasa komai a gidan C. Suleman ba na dangane da zaman duniya sai dai farin ciki na kawai na rasa. Girki kuwa ba ko da yaushe na ke yi ba dan na iya ciki na na ke girkawa,hatta maigadi Ema cewa ya yi dani Oga ya hana shi karbar abunci,ya na bashi kudin siyan abuncin. Wata sabuwa inji dan caca,period dina ya ki zuwa,tin abun be dame ni ba har ya dame ni,ko Anty Sa’a ban fadawa ba na je asibiti.Bayan an gama gwaje gwaje Doctor ya ba ni result na duba sai na ga ina dauke da ciki wata biyu. Ai tin daga asibiti na fara kuka har na koma gida. Ranar gaba daya cikin kuka na wuni,har na yi bacci ban ji motsin C. Suleman. Da sassafe ya dawo ya yi wanka ya sanya kaki,ya sauko kasa dauke da mukullin motar shi a hannun,ya zauna a falon kasa ya na tunane tunanen da ya saba akan rayuwar takura da ya shiga. Da na ji motsin shi na yi ta maza na zira hijab na fito na same mishi. Ko da mu ka hada ido gabana ya fadi na yi saurin kauda kai. Shi ma ganin nawa ya ma sa bazata. Na mika masa result ba tare da gaisuwa ta shiga tsakanin mu ba. Murya a shake ya ce menene wannan? Na ce ka duba ka gani mana. Sai da yau dauki lokaci har ina tunanin ba zai karba ba sannan ya karba ya karanta. A firgice ya tashi tsaye ya na fadin what! Ciki?ina ki ka samo ciki? Na dallah ma sa harara cikin takaici na ce cikin biyu akwai daya ko a daren yan maye na samo ko kuma a ruwan gidan ka na sha…ya daka min tsawa ke kar ki min rashin kunya,ma za ki shirya mu je a zubar da cikin. Ban san sanda na saki murmushin takaici ba na ce ai ni Suleman ban taba tunanin rashin mutuncin ka ya kai matuka haka ba,an fada ma daya daga cikin karuwan ka da ka saba zubar mu su da ciki ce? Ya ce ni ki ke fadawa haka? Who are you? kin san ko da wa ki ke magana kuwa? Na ce ni ce Jauda yar soja matar soja na ke magana da kai soja,kakin ka da ihun ka be tsorata ni bare kai kan ka captain Suleman Matazu! Yayi kasa da murya ya ce how dere you?ni ma na yi kasa da tawa muryar na ce I dare whenever i like. A fusace yayi sama da gudu ya na fadin yau i wil teach you the right time to dare,sai jikin ki ya gaya miki! A rude na kalli gabas da yamma,kudu da arewa ina nemam wajan tsira,na ga mukullin motar C. Suleman a kasa,ai tini na dauka na yi waje a guje,ban zame ko ina ba sai cikin motar na tada ina yiwa Ema hon ba kakkwatawa. Da sauri ya zo ya na kokarin bude min gate din C. Suleman ya fito dauke da dorinar shi mai baki uku. Cikin tsawa ya ce Ema don’t you dare open dat gate! Ema ya ce yes Sir ya ja gefe,na juya na ga Suleman ya nufo ni gadan gadan,na sa wa motar lock,na daura seat belt,na tada motar na je na daki gate din garam! Ema ya daura hannu biyu a kan sa,shi kan shi Suleman sai da ya runtse idanun shi,na sake komawa da baya da nufi komowa na sake dukan gate din sai na ji muryar C. Suleman ya ce kai Ema ba ta da hankali dan ubanka bude mata,da gudu Ema jiki na rawa ya bude min,na figi motar a guje na fice….. [12:53pm, 11/27/2014] Salma Ateeku: [11:02pm, 11/19/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 19;20;21:Kai tsaye gidan Anty Sa’a na je,na tarar da ita zaune a falo ko da ta ganni na shigo mata a rude tini hankalin ta ya tashi. Ni kuwa ban boye ma ta ba na fada mata komai. Cikin jimami Anty Sa’a ta maimai ta a zubar da ciki?kai ni Sa’adatu ban san na biyun Suleman ba! Kwantar da hankalin ki babu mai raba ki da cikin nan sai Allah,ai zai zo ya same ni ne! Ile ko sai gashi ya iso cikin mota ta,ko ya aka yi ya iya binciko mukullin ma oho. Ku sa da ta shi motar ya faka,ya fito da sauri ya duba gaban motar shi ya ga yanda na lotsa masa gashi na fasa madubin duka biyu,ya girgiza kai,ya shiga ciki rai a bace. Kamar daga sama mu ka ji muryar shi ya na fadin ina mara kunyar nan,iyaka nan gudun na ki ya kare?ina ganin shi da sauri na koma kusa da Anty Sa’a cikin tsoro. A fusace Anty Sa’a ta ce kai kunyar gare ka da ka shigo min gida ba sallama! Kamar tababbe ya ce Salama alaikum,babbar yaya na same ki lfy,toh dan Allah kar ki sa baki ki bar ni na suburbudi yarinyar nan! Anty Sa’a ta ce ka ji hauka,kai da suburbudar ka ake yi dan abubuwan da ka ke ai da ba ka kai ie yanzu ba. Jauda tashi ki shiga ciki abun ki,na tashi simi simi na wuce C. Suleman kamar zai wafco ni. Bayan shiga na ciki ta kalle shi,kar ka tsaya min a kai kamar dogari pls!cikin huci ya sami waje ya zauna. Anty Sa’a ta ce wai kai Sule dan Allah yaushe za ka gane annabi ya faku?ya matar ka ta aure ta na da ciki ka ce ta zubar,kai da zubarwa ake a haife ka?ka na gani haihuwan nan nemanta mu ke ido rufe Allah be nufa ba amma kai tsageri ka samu ka ce kyautar ba ta ma ka ba? Suleman ya ce ba haka ba ne,dama akwai abunda ban sanar da ke ba babbar yaya,amma yau zan sheda mi ki,amma ki yi alkawari ba za ki fadawa General ba dan Allah. Cikin zumudi ta ce ta yi alkawari dan Allah Allah ta ke ta ji abunda Suleman zai fada. Ya fara da aure na da Jauda na yarda zan yi shi ne a matsayin auren kisan wuta…..Auren kisan wuta sule?Anty Sa’a ta maimata. Ya gyada kai ya ce haka,nan ya kwashe lbry komai da komai,be buye ba ya fada mata. Anty Sa’a salati kawai ta ke,amma Hajiya Mairo ta yi asara! Kai ko Sule me ya hana ka neman shawara ta? Dama akwai sirri tsakanin mu?yanzu ai ga irin ta nan,ga kuma rashin amfanin shan giya,ga shi ka sha ka afkawa yar mutane kamar dabba,kai kai kai Jauda abun tausayi ce,wallahi yarinya karama ta sha wahala! C. Suleman ya ce yanzu dai kaddara ta riga fata,dan Allah Anty Sa’a ina mafuta?kin ga gwara dai kawai a zubda da cikin…inaaaa! Anty Sa’a ta katse shi,wallahi nan kuma ba ka isa ba,babu wanda ya isa ya zubarwa yar mutane da ciki,sai ta haife shi,idan kai ba ka so mu muna so,bayan ta haife ka sake ta din abokin na ka ya aura. Anty Sa’a zumunci na ke ji,ban san zumunci na da Aliyu ya lalace ki taimaka min. Anty Sa’a ta ce zumunci ai tin ranar da ka yarda da wannan auren kisan wutan ka sa wuka ka datse zumunci,ai yanzu kuma sai dai gyaran ubangiji kawai. C. Suleman ya dafe kai ya ce na shiga uku. Anty Sa’a ta ce mu ko daya ba mu shiga ba,kuma wallahi ko ciwan kai na ba gaira ba dalili Jauda ta yi toh kai ne,kuma sai na fadawa General. C. Suleman ya dafe kai,ya ce toh dan Allah kar dai ki fadawa General,ta ce indai ka kiyaye sharadai na babu mai ji. Ya yi ajiyar zuciya,kin ga kuwa yanda ta bata min mota? Ka godewa Allah da ba ta kashe kan ta ba,da alhaki a kan ka.Ya ce karbo min mukulli na,kuma dan Allah ki ja mata kunne kan gangacin da ta yi yau,wallahi na tsorata,ga na ta mukullin. Anty Sa’a ta amsa ta ce zan mata sosai ma kuwa,dole ta kula musamman yanzu da ya ke ba ita kadai ba ce.ta shige ciki. A fili ya ce na fuskanci babbar yaya ita burin ta ta matsa min kawai ta ji dadi… Ta karbar ma sa mukullin ta bani nawa. Bayan tafiyar shi ne tamin nasiha mai shiga jiki akan zaman aure da kuma gangacin da na aikata yau. Sai bayan magariba na koma gida. [01/11 22:47] Salma Ateeku: :56am, 11/22/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 37;38;39:Washagari da safe bayan na yi wanka na ji saukin jika na sosai,amma dai ban dai na amai ba. Ina fitowa falo kamshin suyan kwai ya doki hanci na,gaba daya na ji zuciya ta na tashi,da sauri na koma ciki ina karasawa toilet sai amai,kamar hanjin ciki na zai fita. Bayan na gama na daddafa na dawo daki na zauna ina sakar zuci,shin waye ma mai soya kwan?S.Man be ta office ba?bayan wani dan lokaci na sake fita dan zuciya ta ta zaku da ta ga wanda ya ke suyan. Akwai karnin suyan kwan amma ba kamar na da ba. A kitchen na same ta,fara ce kakkaura,ta na da zane guda uku,daga ganin ta ka san ba bahaushiya ba. Ta waigo da sauri da ta ji motsina a bakin kofa,irin kallan da na ke ma ta ya sa ta gane ina bukatar bayani. Ta yi sauri ta ce ina kwana madam? Cikin mamakin ganin ta na ce lfy,yau kuma ke ya turo ki masa girki? Na ki aikin kenan? Ta susa kyeya tare da fadin ni?ni ce sabuwar mai aikin ki,Hajiya Sa’a ta turo ni,Oga ya ce kar a tashe ki bacci ki ke. Na saki numfashin da ya tsaya saman kirji na,na ce ina Ogan ya ke?ta ce tin dazu ya fita. Na kalle ta tin daga sama har kasa na ga ba laifi ta na da tsafta amma bana bukatar mai aiki,da na sami sauki sosai zan sallame ta. Na tambaye ta sunanta ta ce jummai. Na ce wa ya sa ta girki toh? Ta ce Oga ne ya ce ta hada min brkfast,na ce toh bana san kwai ya na sani amai,daga yau ma na hutasshe ta zan na yin girki na da kai na,za dai ta na min wanke wanke da shara. Ta amsa da toh. Na ce wanda ta dafa yanzu za ta iya cinyewa. Na koma falo na zauna ina tunanin me zan ci txt din S.man ya shigo,na karanta….. “I hope kin tashi by now,ya jikin na ki. Ga mai aiki Anty Sa’a ta turo,ba kwana za ta na yi ba,amma in ba ta miki ba pls notify me,tak kia…..” Bayan na gama karantawa,sai na mai reply da…. “All is well,tnx” Ni na ji zaman gidan ma ya ishe ni,na kira Jiddah na ji zancen admsion din mu ta ce ai an tafi strike,na dai yi addua a dawo,shin S. Man zai ma bar ki ki bar kano ki je yola yin MBS da auren shi akan ki,a rai na nace auren ai suna ne. Na ce me zai hana,ki dai da an koma an saki addmision din ki fada min. Ta ce toh InshaAllahu. Sati biyu kenan jummai ta na min aiki,yanda ta ke da tsafta da kuma ladabi ya sa na sami saukin ma amma na kasa sallamar ta. Dangantaka na da S.man ba wani cigaba,amma na lura ya rage kwana a waje in dai ba wai aiki ba. Da yamma ina zaune ina karatun al- qurani,takun takalmi na fara ji tare da wani ni’imantaccen kamshi,daga ido na na yi ido biyu da wata kyakkawar mace wacce ta amsa sunan ta mace,fara ce sol kamar balarabiya,doguwa ga ta a dire ba maza kadai ba ko yan uwanta mata su ka kalle ta sai sun kara,sai na ga na zama mummuna a gaban ta. Sai dai kash shigar da ta yi ba na yan mutunci ba ne,riga ce body fitting gown,gaba ya ya bi jikin ta ya kwanta,kai ba dankwali sai wani dan mayafi karami da ta yana,ta na taunar cingum. Ba sallama bare sannu ta kalle ni ta ce ke Ina Suleman? Na kalleta na watsar na cigaba da karatu,ta kara so ciki sosai ta tsaya tsakiyar falon ta shiga kwalla ma sa kira. Ni ko duk da na kule sai na nuna ban ma san ta na yi ba. Da ta yi kiran ta ji shiru sai ta dawo gare ni,ke wai a masu aikin wata iriyar mara kunya ce?ko ki na nufin dadiro ya ke da ke? Na ma ta banza,ta zo ta rufe min qur’ani ta ce ke ba da ke na ke magana ba? Na dago ido na watsa ma ta harara sai da ta dan ja baya, na aje qur’ani a gefe,ina murmushi na ce ban ga laifin ki ba,shi wanda ki ka zo nema shi ya jawo ko wani kare da biri ya ke iya tinkara ta. Tace what?ni ce kare da birin?ina daga zaune na murmusa sunayen sun miki kadan ko? May b ana kara miki da shasha,mahaukaciya wacce ba ta san darajar kanta ba ko? A fusace ta damko ni yau sai na san waye ubanki,waye mai daure mi ki gindi a garin nan! [10:56am, 11/22/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 40;41;43: let go of my wife!C. Suleman ya daka ma ta tsawa yayinda ya ke saukowa da ga bene,a firgice ta sake ni,a hankali ta maimaita your wife?cikin takama ya karasa saukowa,da muryar umarni ya ce da ni Jauda shiga ciki,na kalle shi da niyar yin musu amma karfin kallan da ya min ya sa na hukara na shige na bar su su kadai. Ta bi ni da kallo ta ce matar ka fa Suleman,aure ka yi dama dan cin amana? Me wannan ta fini in banda namiji ma butulu ne!ya zauna kamar ba da shi ta ke magana ba,ya kunna sigari ya busa hayakin sama. Cikin takaici ta ce da kai na ke magana fa,for your information ina dauke da cikin ka wata uku! Ya saki murmushin mugunta toh ki gaggauta fadawa uban sa ya baki kudin abortion ko na ragon suna…ta fusata wani uban na sa da ya wuce kai! Ya ce na zaci rabona da ke four month kenan? Ta iska na dura mi ki cikin ko yaya? Kin san hali na Ramsy wai dan na tattaka ki ba karamin aiki na bane,maza ki je ki samo mai cikin nan,kar ki sake sa kafa a gidan nan,in kuma ba haka ba sai kin yabawa aya zakin ta,shasha kawai. Ramsy ta fashe da kuka kan wannan baka mummumnar matar ta ka ka wulakanta ni? Wlh sai ka san ka yi da yar halas!ta fita fuuu,C. Suleman ya bi bayan ta ya ce da Ema duk randa ya sake bari ta shigo gidan a bakin aikin sa. Ema ya ce i swear Sir i no go let dat happen,C. Suleman ya ce good for you. Ranar ko da wasa ban sake yarda mun hadu C. Suleman ba,shi ma kuma be zauna a gidan ba. Gashi dai ba san C. Suleman na ke ba amma gaba daya rai na baci ya ke duk sanda na tuna fuskar Ramsy. Sam C. Suleman be sake kawo zancen ta ba,ni ma kuma ban masa ba,na ciki na ciki. Kwanci tashi ciki na ya kai wata biyar,ya fito sosai amma dadinta be min muni ba sai ma dada budewa da hips dina yayi kuma kirgina ya cika sosai ba kamar da ba. Anty Sa’a kance daga ganin yanda cikin yayi tsini baby boy ne,ni ko dariya kawai na ke ma ta. Anan asibitin barrack na ke awo na. C. Suleman kuwa wasa wasa cikin nan ke hada mu magana. Wani yawon dare duk ya sauke,kusan kullum a gida ya ke kwana. Wata rana bacci mai nauyi ya danne ni,alarm di na yayi kara na kasa tashi, ashe shi kuma Oga ya na falo ya na jira na tashi shi ma yau dai mu yi sallan tare,ko da ya ji shiru kawai sai ya shigo dakin da kan shi,ya tadda ni kwance na yi dai-dai ina bacci,da ke ana zafi riga ta da kadan ya dara cinyata mara hannu,na saki gashin kaina ba tare da na daura dankwali ba dan na sami iska,ga shi ciki na da ya dan fito sai ya kara min kyau. Gaba daya yanayin C. Suleman ya canza,ba tare da ya san abunda ya ke ba ya zauna bakin gado kusa dani ya daura hannun sa bisa ciki na,da mamakin sa sai ya ji motsi yayi sauri ya dauke hannun sa,da fari yayi zaton tunanin sa ne kawai,ko da ya mayar karo na biyu ya ji dagaske motsin ne kuma cikin nawa ne ke yi,shi kadai ya ke murmushi har sai da cikin ya dai na. Ya sunkuya ya sunbaci ciki,a hankali ya shafa gashin kai na ya ce my child is growing in your womb Jauda,nd i love the child,thank you for bearing him. Ya bi jiki na da kallo,tin ranar da ya min wanka ya ke yaki da zuciyar shi akan abunda ta ke aiyana masa akai na,saboda haka ne ko matan banza be iya kusanta dan da ya kusance su ni ce ke zuwa ransa,balain sha’awata ya ke amma karfin zumuncin shi da Aliyu ya hana shi kusantata ya na cikin hayyacin shi,ga shi wanda zai dan rage zafi da su a waje gaba daya tawa bukatar ta danne ta su. Ya saki ajiyar zuciya,da da yanda zai yi ya sake zuciyar shi da ya sake,da ya yarda da ita ya huta. Ya sake kissn ciki wanda hakan yayi daidai da farkawata,ko da na bude ido sosai na ganshi zaune kusa da ni sai na yi sauri na ja bargo na rufe jiki na. Ya murmusa irin wannan murmushin na yarinya ai na ga komai,ya ce na ji ki shiru ne na zo na tashe ki mu yi sallah. Ba tare da ya jira amsa ta ba ya tashi,idan kin yi alwala ki same ni a falo sai mu yi nafilan tare. Ya fice. Na yi ajiyar zuciya har ga Allah tsoran C. Suleman na ke,da zai gane da ya dai na shigo min daki,sai da na dau tsahon wasu mintina hankali na ya kwanta sannan na tashi na yi alwala. Shi ko S.man da ya koma falo tuni ya shiga sakar yanda zai yi ya sa na saki jiki da shi na dai na jin tsora. Na fito sanye da hijab,ya bini da kallo mu ka hada ido gaba na ya fadi na yi saurin kau da kai na. Wani abu ya dasu cikin ranshi,wato ba Aliyu ba,babu dalilin da zai sa ya cigaba da cutar da kan shi akan abunda Allah ya halatta masa,abunda ya ke fada cikin ransa kenan yayin da na zo bayan shi na shimfida dadduma ta,ya juyo ya na kallo na cikin ran shi ya na fadin i can’t hold on to this any more,i want her i must have her ko da kuwa shi ne abu na karshe da zai aikata a duniya ba zai iya sake wani jinkirin ba… [10:56am, 11/22/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 44;45;46:Da kyar ya tashi mu ka yi sallah,ni ko cikin zuciya ta fadi na ke ko dai S.Man ba lfy ne? Mu na idar da sallah na yi sauri na koma daki. Ya kishin gida ya na murmushi ya ce ki gama gudun ki Jauda mu na nan tare,zuciya ba ta da kashi hakan ya sa tawa ta kamu da son ki..da sauri ya tashi zaune jin abunda ya fada,wai so fa ya ce,ya sake komawa ya kishingida ya na muhawara da zuciyar shi,shin so ko sha’awa kadai wanne ya ke min ne? Washagari gidan Anty Sa’a na wuni,kullum nasihar ta na bi miji na,na ja shi a jiki na taimaka ya sauya halaye,ni ko gani na ke na yi kadan da na ja S.Man a jiki har ya sauya hali kai na,yanda na ga mata na bin shi tun abun ya na bani haushi har na zo na saba da ganin su suna zuwa neman shi ,gasu duk babu wanda na fi kyau sai dai su fini,amma ko da wasa ban taba fadawa Anty Sa’a ba. Kafin Sallah magrib Anty Sa’a tace na koma gida na kar dare ya min,na ce yanzu korata ki ke Anty Sa’a,ta dara ta ce ba haka ba ne,kin san with your condition be kamata ki na yawo ke kadai ba,da daidai kin haife min yaro na ne sai ma ki kai daya ban damu ba. Ina dariya na ce ashe abun ba dan ni ake ba,san kai ne. Ta ce ya za ta yi da ai yafi kanwa. Duka mu ka yi dariya. Ina shiga gida ana magrib,na sallami Jummai sannan na shiga na yi wanka. Da ke idan dare ya yi cikin daki na nake wuni sai na sanya tight dina iya gwiwa da riga ta body hug mara hannu,ta dame ciki na abun sha’awa. Na shafe jikina da humrah. Na taje kai na ina shirin tifkewa waya ta ta fara kara,na bari na je na dauka,Jidda ce ke kira na cikin farin ciki na daga ina fadin yan mata na,bayan mun gaisa ne take fada min yau fa S.man ya je yola. Na ce ya je yalo? shi ne be fada min ba ko ina da sako?ta ce ai ya ce aiki ne ya kawosu be ma dade ba ya juya kafin magrib ma ya kira Inna ya ce sun iso lfy,Inna ce ta ce ma na yi kiran ki na fada mi ki ki masa godiyan alkhairina da ya ma ta. Toh kawai na ce ba tare da na tambayi abunda ya ma ta. Har mun yi sallama ta yi sauri ta ce dani Sis an koma makaranta fa,an kuma baki admision amma da Inna ta fadawa S.Man yace ba za ki koma ba Saboda..ya ma isa! Kafin ta karasa maganar na katseta,na sake fadin ya ma isa ya hana ni!ban jira ta gama magana ba na aje wayar kan gado ina ji ta na hello hello ido na rufe na nufi bangaran Suleman. A dakin shi na tarar da shi zaune yana rubuce rubuce,ganina ya sa ya aje biron ya tashi tsaye cike da mamaki,amma ko da ya ga yanayin fuska ta ya san bomb ne zai tashi. Na tsaya daga bakin kofa,ya ce shigo mana Jauda,na karaso inda ya ke hannuna bisa kugu na sam na ma manta shigar da ke jiki na masifa ta na ci na ko dan kwali ban daura ba bare mayafi. Ya bini da kallo kamar zai hadiye ni,tin da yake be taba ganin macen da ta bashi sha’awa kamar yanda na bashi a halin da na ke ciki yanzu ba. Sam ban kula da irin kallon da ya ke min ba sai da na je dab dashi na ce dan me ya sa za ka hanani karatu? Yaushe ka fara magana da yawu na? Ya ina neman abu na samu dan rashin adalci ka yanke min hukunci mai tsauri ba tare da ka tambaye ni ba? Sai hawaye su ka shiga gangarowa daga ido na. Maimakon ya min magana sai kawai na ji yayi hugn dina,na shiga kokarin kwacewa amma ya rike ni gam har na gaji ni ma na yi lamo a jikin shi,da ya ji na nutsu ya dago da fuska ta mu ka hada ido,na saukar da nawa idon,ya yi kissin idon nawa sai na buye fuskata a kirjin shi. Ya ja ni muka zauna a bakin gado amma har yanzu be sake ni ba. Ya ce ki yi hakuri Jauda na je yola ban fada mi ki ba,ni ma ban san da tafiyar ba ne. Na ma sa banza. Jauda? Na ji muryar shi ta canza,kuma ni ba yarinya ba ce tuni na gane yanayin da mai irin muryar ke ciki,na yi sauri zan tashi ya dada kamkame ni ya ce ba hanaki karatu na yi ba,amma ba zan iya bari ki tafi har yola ba,za ki min nisa da yawa,ki duba halin da ki ke ciki,hankali na ba zai kwanta ba idan na yi sa da ke. Cikin rai na na ce saban salo kiran sallah husur. Ya dago fuskata na kalle shi na ga idanun sa sun canza,murya na rawa na ce bari na koma daki na toh,ya dada kamkame ni yace Jauda ai yau kin shigo kenan,I can’t let you go. Na fashe da kuka. Ya cikin rarrashi ya na shinshinar gashin kai na ya ce dan Allah kar ki manta akwai igiyar aure na a akan ki,ki taimaka kar ki haramta abunda Allah ya hallata,a matsayi na na mijin ki ina bukatar mata ta a daren yau….be jira na bashi amsa ba ya fara kissing dina kamar babu gobe,ya haye gado dani,ni ko sai kuka kawai na ke. Da ga nan ba sai na tona asirin miji na ba,kuma kun san sauran [01/11 22:47] Salma Ateeku: [8:04pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 47;48;49: Da sassafe na farka,ko sallar asuba ban yi ban. Na duba gefe na ban ga C. Suleman ba sai wata yar takarda na gani nade a gefe. Na dauka na ga rubutun S.Man kamar haka ” You are the best thing that ever happend to me. Na so ace ina nan ki ka tashi,amma aiki ya kamani da safe dole na tafi. Tak kia of yourself for me..” Na aje takardar gefe gami da runtse ido,gani na ke tamkar na ci amanar tsohon miji na duk da kuwa auren aminin na shi na ke,duk da kuma yanayin rabuwar ta mu,amma abun da kunya. Na godewa Allah da yasa S.man ba ya nan dan ban san da wani ido zan kalleshi ba,ban yi shirin fuskantar shi ba. A Hankali na tashi na ga kaya na ninke a gefen gado. Na ja su na sanya. A hankali zuciyata cike da alhini na sauka bangare na. Can bangaren Hajiyar Aliyu kuwa tin da Aliyu ya kai babba gidan ta,har ya tafi sudan be sake waiwayan ta ba. Indija ta sami wani saurayi dan duniya mai suna Bello,ba karamin kashe ma ta kudi ya ke ba,ya nuna ma ta duk duniya babu wacce ya ke so kamar ita,har ta saki jiki da shi. Ana haka ranan ya takura lalle abokin sa ya yi aure ya kamata su je su ga gida. Ta ce toh za ta tambayi hajiya ya ce ah ah,irin wannan ba sai ta tambaya ba,dan kila ta tambaya a hana ta,da safe ma za su tafi ta yi karya ta ce za ta makaranta sai kawai su wuce. Haka ko aka yi,da safe ta ce da Hajiya za ta makaranta,Hajiya ta bata kudin mota da na kashewa. Bayan fitowar ta,ta yiwa bello waya ya zo ya dauke ta sai gidan abokin shi. A waje suka tadda abokin ya shigar da su falo. Ya kawo musu lemo sai tsokanar Bello yake. Shiru Indija ta ga amarya ba ta fito ba,ta kasa shiru ta ce ina amaryar ne,abokin Bello ya sosa kyaya ya ce ta na wanka ne,ki dan sha lemon kafin ta fito. Ta ji sanyi cikin ran ta,Bello ya zuba mata lemon ya bata ta fara sha shi kuma sai hira ya ke da abokin shi. Jim kadan ta ji jiri na kwasan ta,ta ce da Bello dan Allah mu je gida,ba na jin dadi,abokin Bello ya ce ah ah ba ki ga amaryar tawa ba za ki tafi? Indija ta tashi ta ce ma dawo…ba ta karasa magana ba jiri ya debe ta,ta fada kan kujera ta na baccin dole. Bello ya daka tsalle ya bawa abokin shi hannu su ka tafa,abokin ya ce toh sai ka dauke ta ku wuce daki ka ci kudin ka. Bello ya ce tini ma kuwa. Ya yi daki da Indija. Ba ita ta farka ba sai yamma,kanta ya sara ga wani ciwan da ya sassake dukkan gabobin jikin ta,a hankali ta bi dakin da kallo,ta duba jikin ta ta ganta tik,sai a sannan ta gane aika aikan da Bello ya ma ta,ta fashe da kuka mai karfi. Bello ya fito daga toilet yace Indija Indija,Indija babbar budurwa! Ta dada fashewa da kuka ta na fadin ka cuce ni ka gama da ni Bello,dama ba so na kake ba,dama san cuta ka ke min?ya daura kafa daya kan gado ya na kallan ta,ya ce aw ke ki na tunanin zan miki san da ya fi wannan? Hahahahaha toh na soki na ce na so me? Ai dama investing na ke,yau kuma na kwashi kudi na har da riba. Ki godewa Allah da na hana abokina kwasar bati,tin da dai bai sa hannun jari ciki ba! Ta fara zagin shi,tsinan ne,azzalumi Allah sai ya saka min,ko a jikin shi ya ce oho,ki maza ki shirya dallah,masu gidan sun kusa dawowa. Ya fita ya na dariyar mugunta. Bakin ciki kamar Indija za ta hadiyi zuciya,gaba daya ta tsani kanta. A haka ta lallaba ta shirya,Bello ya ce zai sauke ta gida,ta ma sa banza,ta na jiyo dariyar shi ya na fadin in an sami karuwa a gayyace mu suna. [8:13pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 50;51;52:Indija ta kasa fadawa Hajiya abunda ya faru,gaba daya ta canza ko makaranta ba ta iya zuwa,gani ta ke kowa ya san abunda ya faru da ita. Bayan sati biyu ta na zaune,abun duniya ya ishe ta,ta ji Hajiya na kiranta. Ta tashi ta je ta same ta ita ma ta doka tagumi. Ta zauna gaban ta ta ce Hajiya gani. Hajiya ta ce Indija kin ga Aliyu gaba daya ya yada mu,tin da ya sa kafa ya tsallake mu be sake ko da waiwaye ba,ya zan yi dole na yi bikon sa,ina wannan aminin na shi Suleman? Indija ta ce kwana ki ma na ji ance ya yi aure. Hajiya ta murmusa Allah sarki,da lfy kalau ne kin san da na ji ai. Kin san gidan na shi? Indija ta ce eh,Hajiya ta ce toh ki shirya ki je ki ce dashi ni na turoki ki karbar min numbar da Aliyu ya ke amfani da shi a sudan,kya ma ji ma na lbrn yanda Aliyun ya ke dan na san shi dai suna waya. Indija ta ce toh Hajiya. Indija ta shigo gida na ta na sallama,Jummai ce a kitchen ta fito tare da amsa ma ta. Ta sami waje ta zauna tare da gaisawa da Jummai,ta ce da Allah Captain Suleman ko ya na nan? Jummai ta ce ah ah ya fita. Indija ta dan yi jugum,can ta ce amaryar shi fa? Jummai ta ce bacci take,kuma Oga ya hana tashin ta idan ta na bacci. Ta ce toh bara na tafi,pls ki ce da ita kanwar abokin shi Aliyu ce ta zo,ta fada ma sa zan dawo,hakan yayi daidai da fitowa ta,na ce da Jummai bakuwa mu ka yi ne? Mu ka yi ido biyu da Indija a firgice ta tashi ta na nuna ni da dan yatsa. Jummai ta ce dan Allah ki yi hakuri madam kar dai ni na tada ki,sai da na ce ma ta Oga ya hana,na murmusa ina kallan Indija wacce bakin ta ya ke a bude,na ce da Jummai kar ki damu,ban ma ji ku ba,na dai tashi ne. Indija yau kuma ke ce a gida na? Na tambayeta cikin sakin fuska,baki na rawa ta ce wai dama ke ce matar da Suleman ya aura? Na ce eh,zauna mana,ina zama be kamata ba da sauri ta fice ta na simbatu,Jummai ta ce Madam halan wannan ba ta da hankali,na murmusa yayinda na zauna kan kujera na ce ko kusa,lfyn ta lau Jummai. Jummai ta ce toh,Allah ya kyauta,kamar wacce ta ga fatalwa wannan firgici haka,murmushi kawai na ke yi. Da gudu ta shiga gidan Hajiya saura kadan ta afka ma ta akai. Hajiya ta ce ke menene haka!biyo ki aka yi ko me? Indija ta ce Jauda,Hajiya Jauda! Hajiya ta ce Jaudar ce ta haukace ta ke bin mutane? Indija ta ce Hajiya ai sai dai ni na yi hauka amma ba Jauda ba,Hajiya Jauda ce matar da Suleman ya aura! Ke yar nan Jauda fa! Indija ta ce wlh Hajiya har da ciki fa. Hajiya ta sa salati ta na sallallami,ta ce maciya amana,dama tintin cin amanar Aliyun su ke,kin ga gwara ma da mu ka yi silar rabuwar ta su dan ko bajima ko ba dade asirin su sai ya tonu! Indija ta ce Hajiya,ni gaskiya na gaji da irin wannan rayuwa,Jauda kullum dada ci gaba ta ke,hassada ga mai rabo taki,mu kuwa da mu ka shuka sharri gashi sai girba mu ke,wlh ni gida wajan baba ta zan koma. Hajiya ta bude baki kuji yar butan uwa,ni kikewa rashin kunya? Toh kama hanya ki tafi gidan na ku! Indija ta ce yanzu ma kuwa,ta shige ta na fadin rayuwa ba cigaba haka! Hajiya ta doka tagumi duniya ta ma ta zafi,ta rasa inda za ta sa kanta dan bakin ciki,tini hawaye ya cika fuskar ta. [9:33pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 53;54;55:Ciki na ya kai wata takwas,rayuwa ta dawowa S.Man sabuwa,babu hakkin shi da na toye masa,hakan ya sa ya shiryu sosai ya dai na bin mata da shaye- shaye,in banda sigari babu abunda ya ke sha,shi ma din sai lokaci lokaci. Har yau ban fara jin san Suleman cikin rai na ba,sai da akwai wata alaka ta sabo da aminci da ya kullu tsakanin mu,gaba daya zuciya ta ta yarda da shi. Zancen MBS di na kuwa ya min alkawarin bayan na haihu zan sake nema amma a nan jami’ar Bayero. Sam ko da wasa be taba min zancen Aliyu ba,ni kuma ban dai na zargin shi da cin amanar Aliyu ba,amma ban taba furta ma sa ba,na ciki na ciki. Duk dare mu kan fita strolling tare,yau ma tafe mu ke hannu na cikin na shi,hira mu ke sosai,bini bini sai ya tambaye ni kin gaji? Sai na ce masa ah ah,har na gaji da jin tambayar na ce wai menene damuwar ka da gajiya ta ne?yayi kissing hannuna ya ce saboda ba na so ki gaji sosai,na fi so da kin gaji ki fada min na dauke ki dan kar mu je gida na ce mu yi strolling din daki ki ce min kin gaji. Na kwace hannu ina dariya na ce dama nan kafi kauri ai. Yayi saurin mayar da hannu na cikin na sa shi ma dariyar ya ke yace bashakka a wajan ki na fi kauri,you are the best thing that ever happnd to me,ya sankalo da hannun shi kafada ta,na kwantar da kai na jikin shi. Ya ce ranar da ki ka haihu Jauda sai na zabu ruwa a kasa na sha. Na ce Allah dai ya nuna mana,ko ka mance sai na tuna maka,ya ce amen. Haka mu ka ci gaba da tafiya har sai da na gaji din mu ka koma gida,da shigar mu ya dauke cak wai tinda na ki yarda ya dauke ni awaje bari ya min ladan gida yanzu,na ce ai kai za ka sha nauyi,ya tura kofa da kafar shi mu ka shi ga falo ya ce haba Madam Soja na ke fa. Mu ka sa dariya. Gidan Hajiyar Aliyu kuwa gaba daya duniya ta ma ta zafi,ta na zaune ta doka tagumi sai ga mahaifiyar Indija Hajiya Binta tare da Indija sai surfa ma ta zagi ta ke tare da duka,ko da Hajiya ta ga shigowar su da sauri ta je ta ceto Indija ta na fadin baki da hankali ne Binta?Indija ta buya bayan Hajiya ta na kuka. Hajiya Binta ta watsa ma ta harara tare da fadin ya Mairo kin cuce ni,Allah ya isa tsakanina da ke! Hajiya ta ce ni? Ni binta ki ke yiwa Allah ya isa? Ladan rike mi ki ‘yar ki da na yi ko? Hajiya Binta ta ce yo da ki ka ruke min yar mai ya amfana ta da shi? Ga ta nan ta fada mi ki bakin ta abun kunyar da ta janyo ma na. Hajiya ta fito da Indija sarari ta ce Indija wani abun kunya ki ka janyo ke kuwa? Ta kasa magana sai kuka. Hajiya Binta ta daka tsawa za ki yi magana ko kuwa? Murya na rawa ta ce Hajiya amai na ke. Hajiya ta rungumo ta tare da fadin Allah sarki abun ku da annoba,kin san kan ta tafi makota na ta fama da amai da gudawa. Hajiya Binta ta harere ta,amma ban taba tunanin haka ki ke da karamar kwakwalwa ba wlh,toh ciki ta dauko a titi! Hajiya ta kurma ihu CIKI! Innalillahi..wainnailaihirajiun Hajiya Binta ta karasa ma ta,sai da ki ka gama bari ta lalace za ki turo min ita gida,toh ubanta ya ce ba dai a gidan shi ba,ni ko dan ita ba zan bari aure na ya mutu ba,kin ga tafiya. Ta yi tafiyar ta ta bar Indija gaban Hajiya. Hajiya ta fara jibgar Indija ta na fadin shegiya munafuka,me ki ka nema ki ka rasa,waye ya mi ki ciki? Waye uban sa? Indija ta na ihu ta ce Bello ne Hajiya,Bello ne! Hajiya ta ce tashi a daren nan za ki kai ni gidan su! Ta ce Hajiya wlh ban san komai akan shi ba,kawai zuwa gidan nan yake,Hajiya ta ce ba ki san komai a kan shi ba amma ki ka bari har ya mi ki ciki?Ina ki ka san shi?Indija ta ce facebook….Hajiya ta yanki jiki ta fadi baki karkace,Indija ta kurma ihu ta fita a guje ta na neman taimako. [9:44pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 56;57;58:Indija ta samu makota suka taimaka ma ta aka kai Hajiya asibitin barack,nan aka kwantar da ita. Washagari da safe har mota na raka C. Suleman za shi aiki. Ya kalli kafa ta ya ce farce ya taru pls ki tuna min in na dawo na yanke mi ki. Na ce yes Sir. Ya sunkuya yayi hugn ciki na tare da fadin i wil miss you my baby,ina dariya na ce he wil miss his dad too. Ya dago ya yi hugn dina tare da fadin i wil miss his momma more. Ya dago fuska ta yayi kissing goshi na tare da fadin take kia of yourself owk? Na ce owk. Na bude masa kofa ya shiga mota na mayar na rufe. Ema ya bude gate har ya fita ina daga ma sa hannu. Da shigar shi barrack ya yi kacibus da Doctor Usman,ya ke fada ma sa an kwantar da Hajiyar Aliyu rabin jikin ta ya zama paralysed. Be ko shiga office din shi ba wajan Hajiyar ya wuce ya tadda ita kwance wata dattijuwa ce ke jinyar ta. Ganin yanda barin jikin Hajiya ya daina aiki,hatta bakin ta ya karkace ya sa jikin C. Suleman sanyi. Bayan sun gaisa da dattijuwar mai jinyar ta ya je gaban Hajiya ya ja kujera ya zauna. Hajiya na magana da kyar dan sai an kasa kunne ake iya jin ta tace Suleman ina abokin ka Aliyu? Dana Aliyu na cutar da shi,S.man ya ce Hajiya Aliyu be dawo ba,amma sun kusa dawowa,shi ya ke fada,amma gaban sa sai da ya fadi. Ya ce Hajiya ya jiki? Ta ce uhum,jiki gashi dai ka gani,na ce ko ka na da wata numbar da Aliyun ke amfani da shi? Ya ce Hajiya ba sa amfani da waya in ana course din,amma akwai wata numbar da ya ke kira na da shi kafin su fara course din,yanzu ko na kira ba ta shiga. Hajiya ta nisa ta ce toh Matar shi fa Jauda? Nan fa Oga ya tsuke fuska ya ce Hajiya Jauda ki na nufin mata ta kenan? Hajiya ta ce eh haka fa,matar ka,dan Allah ka taimaka ka kawo ta,ina san ganin ta. Ya dan saki ran shi tare da fadin InshaAllahu Hajiya gobe zan kawo ta,Allah ya tashi kafadar ki. Bara na shiga office. Hajiya ta yi godiya,ya tafi gaba daya tunanin shi ya karkata ga waje na,gaban sa sai faduwa ya ke.Gashi ranar wuni yayi yana aiki,ana so a dauki sababbin sojoji amma short service,shi ne mai kula da activities din.ba shi ya gama da office ba sai bayan Isha’i. Tafiya ya ke yana driving,amma gaba daya ni ce a ran sa,cikin kankanin lokaci gaba daya na sauya ma sa rayuwa. He is a better person now. Be taba tsammanin zai so wata ya mace haka ba,shin dama haka aure ya ke? Da ya sani da tin kafin ya kai haka yayi,toh kuma ai da ba zai samu ya aure ni ba,wannan tunanin ya kawo ma sa Aliyu cikin ran shi,a fili ya ce ya zan yi da ke Jauda yar soja matar Soja,yahayyu ya quyyum Aliyu ya kunto min kura…. ya danna hon Ema ya bude gate ya ja gefe ya sara ma sa. Bayan ya faka mota ya shigo sai ya ganni kwance kan doguwar kujera ina bacci. Kai tsaye ya dauke ni ya haura da ni sama dakin shi ya aje ni kan gado ya na nazari na,daga baya shi ma ya hau gadon ya jawo ni jikin shi na dan bude ido mu ka hada ido sai na sakar masa murmushi cikin bacci na sake rufe ido. Jauda ya kira sunana cikin rada,cikin magagin bacci na amsa masa da ummmm. Ya ce kinsan ma’anar sunan ki? Cikin bacci na saki ajiyar zuciya gami da gyara kaina da ke kwance kan kirjin S.Man har sai da ya lumshe ido sannan ya ce yana nufin KYAUTA,indeed ke kyauta ce daga ubangiji gare ni,kin cancanci sunan ki Jauda,ke kyautar Allah ce,bazan taba barin ki ba ko dakuwa zan rasa rai na,ya shafi cikina tare da fadin Allah ne ya bani ke…… Washa gari da safe S.Man ya ce da ni na shirya za mu dubiya. Na tambaya wace ba lfy ya ce wata mahaifiyar shi ce. Na ce toh. Na dau lokaci ina shiri har ya gaji ya shigo daki na ya ganni zaune gaban madubi ya ce da ni dubiya fa na ce za mu ba gidan biki ba,dama dai kin hakura yanda baby na ya kumura ki haka babu abunda za ki sa ki yi kyau. Na zun buro baki tare da fadin ayya mana S.man,ya yi dariya ya ce wasa na ke mi ki,kin san you are always beautiful,amma ki taimaka ki fito mu tafi haka. Na ce toh bani minti biyar, ya ce minti biyar ko? Idan ki ka kara ni da ke ne. Na ce yes Sir. Bakin mota ya je yana jira,ya na nan tsaye ya ga Ema ya shigo da sauri ya bude gate ya ja gefe ya sara yayinda wata mota ke shigowa,C. Suleman ya bi motar da kallo ya na fadin yanda na ga Ema ya na rawan jiki komai aka yi General ne,Toh me zai kawo general da safe haka…..ganin wanda ya fito daga motar gaban C. Suleman ya fadi,hankalin sa ya tashi,ji ya ke kamar ya ruga a guje ya boye Jauda. Cikin farin ciki ya taho da sauri ya rungume C. Suleman ya na fadin amini na long time,ina sauka na ce wlh wajan ka zan fara zuwa,ashe ka dawo gidan nan,cikin zolaya ya ce wlh idan aka dauke Jauda babu wanda na yi missing kamar kai…..kamar daga sama suka ji murya ta ina fadin S.man ko ka yi fushin ne? Zuciya ta daya na fito. Ya na duban fuskar C. Suleman cikin neman amsa ya ce mai Jauda ta ke yi a gidan ka kuma? Ko har an yi auren kisan wutan ne? Gabana yayi mummunar faduwa,duk da ya bani baya amma ko a mafarki na san mai wannan bayan na san muryar nan,ban yi zato ba,ban yi tunanin zan sake dora idona akan shi..bare kuma a yau….. C. Suleman ya kame gaba daya ya kasa magana,ya rasa me zai fada,yawun bakin shi ya kafe. A hankali C.Aliyu ya juyo,fuska ta ya fara kalla,sannan ya mayar da kallan sa ga ciki na,Jauda.. ya kira sunana a hankali,ya waiga ya ce da S.mana dan Allah yi min bayani,shin dama cikin na ta be bare ba? [9:59pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar Mu 2 60;61;62:Da kyar S.man ya ce da ni Jauda shiga ciki,a hankali na juya ina takawa kamar mai koyan tafiya na koma ciki. C. Aliyu ya bini da kallo baki bude,sannan ya gane me ke faruwa, a fusace ya kifawa S.man a mari a kumatun shi har sau hudu,yanda ka san an yiwa dutse ko motsawa be yi. C. Aliyu ya ce Suleman waccar fa mata ta ce,shin dama za ka iya min haka?kasan fa komai Suleman,a gaban ka aka yi komai,ban da aminin da ya wuce kai,dama za ka iya cin amana ta? Auren kisan wuta ashe kai taka wutar ka ke kashewa?SULEMAN ya jijjiga shi,shi ko ya tsaya cak kamar gunki a fusace Aliyu ya na nuna shi da dan yatsa ya na fadin banda makiyi da ya wuce kai wlh sai inda karfi na ya kare! Ya shiga mota,da sauri Ema ya bude masa gate,ya figi motar ya fice. Ya na tafiya da sauri S.man ya shigo ya na kirana,ya taddani kwance na hada kai da gwaiwa ina kuka kamar rai na zai fita. Ya durkusa gaba na tare da fadin ba laifi na bane,ba na ki bane,ba kuma na shi bane,kaddara ce Jauda! Nan take ya bani lbrn da ya dada rudani,gaba daya na ji duniyar ta isheni. Cikin kuka na ce duk wannan lokacin Suleman ba ka fada min ba sai yanzu? Ya taso zai riko hannu na,na daga masa hannu tare da fadin stay away from me,kar ka zo kusa da ni…ya zube gwiwowin sa biyu a kasa ya na fadin Jauda ki taimaka min,ki ceto rayuwata kar da ki juya min baya,da fari a matsayin auren kisan wuta na yarda na aure ki,amma yanzu ke ce rayuwata,ke da dan da ke cikin ki kune rayuwata,billahilazim ba zan iya sakin ki ba ko da kuwa zan rasa rai na,ya kama kafata yana fadin gani durkushe gaban ki Jauda,Allah ba zai ba ni kyau ta ba ace za a kwace min. Wayyo Allah ni Jauda na shiga uku,abunda na fada kenan yayin da na yi sauri na tashi na nufi daki na,S.man ya biyo ni,na yi saurin shiga na ja kofa na rufe,na hau tsakiyar gado ina kuka. Ina ji yana buga kofa na ki budewa har ya gaji ya dai na.ban sake jin motsin shi ba ma,kuma shi ne karo na farko da na kwana a daki na tin da mu ka fara shiri da shi. Washagari da safe na shiryar da wuri na zauna a falo ina jiran Jummai ta zo na sallame ta dan ta ce da ni ta na son tafiya gida. A hankali na ji ana saukowa daga sama,na daga ido sai na ga S.man ne gaba daya ya fita daga hayyacin sa,na ma yi tsammanin ya tafi aiki. A hankali ya karasa saukowa ya zo gabana ya sa hannu ya tayar da ni tsaye,ya yi hugn dina na tsahon wasu yan mitina,har sai da ya ji ciki na ya fara motsi ya sake ni ya dan sukuya gami da dora hannun shi kan cikin nawa ya na murmushi,sai ga hawaye na zuba da ga idanun shi. Na tausaya ma sa,na tausayawa kai na na kuma tausayawa Aliyu. Sai da cikin nawa ya daina motsi ya dago ya kalle ni,yayi kissing dina sosai sannan ya ja ni mu ka zauna kan kujera,ni dai kamar babyn roba,ba um ba um um. Jauda? Ya kira sunana na amsa a hankali,ya dau hannuna ya dara bisa kirjin sa,ya ce kin ji yanda zuciya ta ke bugawa? Na daga masa kai alamar eh,ya ce haka na ke jin motsin dana a cikin ki,Jauda zuciya ta ce ke bugawa a cikin ki,cikin ki shi ya fara haddasa sa min soyayyar ki cikin zuciya ta. Na zame hannu na daga kan kirjin shi. Na ce Suleman ni matar ka ce kuma bazan taba bukatar saki daga gare ka ba,har sai in kai da kan ka ka gaji ka sallame ni. Murna a fuskar S.man har sai da hakoran sa suka fito ya sauko kasa ya durkusa na gode mi ki Kyautar Allah,Allah ya mi ki abunda ki ke min. Na murmusa na ce amma ka daina durkusa min. Ya yi sauri ya tashi tare da fadin na dai na. Na ce wacce za mu duba a asibitin Hajiyar Aliyu ce? Ya ce eh ita ce,na ce toh ka shirya mu je,kaga kafin ka gama na sallami Jummai. Cikin sauri ya rasa min ya ce yes Ma,ya haye sama da sauri. Na saki ajiyar zuciya,ba wai san Suleman na ke ba,amma ina tausayin sa fiye da Aliyu,hakan ya sa na yanke hukuncin kyautata masa ko da kuwa tawa zuciyar za ta na kwana ta wuni cikin kuncin tunanin Aliyu ba zan taba bari maigida ya sani ba,kuma ina ta addua Allah ya cire min Aliyu cikin rai na. [10:24pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 63;64;65:Bayan S.man ya gaisa da Hajiyar Aliyu sai ya fita ya bamu wuri. Tin da na ga halin da Hajiya ta ke ciki na sa kuka,har yanzu kukan na ke. Baki na rawa ta ce Jauda na zalunce ki,ki yafe min,dan Allah. Cikin kuka na ce Hajiya na yafe mi ki duniya da lahira. Hajiya ta nisa tare da fadin Jauda ke mutum ce,da na sani da ban raba da na da mace ta gari ba,jiya Aliyun ya zo waje na,ya zo nan ya na kuka kamar ran shi zai fita,na san daga gidan ki yake gashi kuma ya zo ya tadda ni a halin da na ke ciki,gaba daya sai na kara tsanar kai na. Na ce Hajiya ki dai na fadin haka,kaddara ta riga fata. Hajiya ta murmusa gami da kama hannu na,na gode miki Jauda,dan Allah ki na taya ni addua Allah ya yafe min,bazan tashi ba. Na ce Allah ya yafe mana gaba daya Hajiya. Na fito daga dakin Hajiya ina share hawaye na yi kacibus da Aliyu ya na shirin shiga dakin,ya tsaya cak ya na kallo na,na kalle shi na kau da kai gefe,ya karaso gaba na ya tsaya,na kauce da niyar wuce shi amma sai ya sake shan gaba na,kawai sai na sake sa kuka da ke dama a kusa na ke,ganin haka sai ya kauce ya bani hanya da sauri na yi hanyar fita Aliyu yayi tsaye ya na kallo na,ashe S.man ya ga shigar Aliyu saboda haka ya biyo baya na,ko da ya ganni na fito ina kuka besan sanda yayi hugn dina ya na rarrashi na ba tare da ya lura da Aliyu a wajen ba. Aliyu ya dunkule hannun shi,ji ya ke kamar ya kwalla ihu,da kyar ya ruke kan shi. Captain Suleman ga jani mu ka tafi mota,sai da ya tabbar na yi shiru sannan ya tada mota mu ka dau hanyar gida,ba mu yi nisa da tafiya. Ba wata mota ta zo da gudu ta wuce mu sannan ta sha gaban mu saura kiris mu yi gware S.man ya taka burki. Da Sauri S. Man ya rike hannuna ya ce ina zuwa,fitar shi ta yi daidai da fitowar Aliyu,a fusace ya sharawa Suleman mari gami da fadin ka sakar min mata ta, S.man be yi kokarin rama marin ba,ya ce ba matar ka ba ce Aliyu,mata ta ce,wallahi na rantse da wanda rai na ke hannun sa ba zan sake taba,ni da ita mutu ka raba takalmin ka za…Aliyu ya sake wanke shi da mari,ji ka ke tas! Ko motsi Suleman be yi ba. Aliyu ya nuna shi da dan yatsa wato kenan ka zabi mutuwar ka akan rayuwar ka!ganin S.man ya sa hannu a aljihu ya dauko bindiga hankali na ya dada tashi. Ya dau hannun Aliyu ya damka masa bindigar tare da kama hannun shi ya saita bindigar a goshin sa ya ce Aliyu in dai akan Jauda ne na zabi mutuwa akan rayuwa ta,go head kashe ni ka aure ta dan wallahi ba zan sake ta ba. Aliyu ya fizge hannun shi bindigar ta fadi kasa. Ya na nuna S.man da dan yatsa har ya shige mota,ya juya kan mota ya tafi a guje. S.man ya sunkuya ya dau bindigarsa ya mayar aljihu ya dawo mota,ido na tsumtsumu ya kalle ni gami da shafa gefan fuskata ba tare da ya tanka ba ya tada mota mu ka tafi gida. Ko da Aliyu ya koma asibiti ya tadda jikin Hajiya yayi tsanani,Indija zaune gaban ta sai kuka ta ke. Hajiya ta kalli Aliyu ta ce Aliyu dan Allah ka yafe min ka yafe ni dana,Aliyu ya ruke hannun ta ya ce na yafe miki Hajiya,ni ma ki yafe min na guje ki tsahon shekara daya. Ta murmusa ta ce ba ka yi komai ba Aliyu,da ma na samu ka dawo kafin na bar duniyar,yanda na cutar da kai Aliyu babu uwar da za ta iya yiwa dan ta..ta numfashi ya fara daukewa Hajiya,da gudu ya fita kiran doctor,kafin ya dawo ina rai yayi halin sa. Indija ihu har da birgima. Aliyu ko hawaye ne kawai ke zuba daga idanun sa. Ba mu jima sosai da shiga gida ba Doctor Usman ya yiwa S.Man waya ya fada ma sa rasuwar. A rude ya sauko ko hula be sa ba ya yi hanyar fita,na biyo shi ina fadin lfy? Ba tare da ya tsaya ba ya ce da ni rashi aka yi,bara na je na samu jana’iza. Nan take na gane Hajiya ce ta rasu na sa kuka,a dole ya tsaya ya rarrashe har sai da na nutsu sannan ya tafi. [01/11 22:47] Salma Ateeku: [10:33pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 66:67:68:Bayan an kai Hajiya an dawo,aka zauna rumfar zaman makoki domin karbar gaisuwa. Aliyu zaune cikin yan uwa da abokan arziki sai ga S.man,ya bawa ko hannu suka gaisa ko da ya bawa Aliyu sai ya ki karba,S.man ya aje hannun sa tare da fadin ya hakuri? Fuska a dake yace Alhamdulillah. S.man ya ce Allah ya ji kan Hajiya,jama’a su ka amsa da amen. Ya sami waje zai zauna Aliyu ya dakatar da shi tare da fadin pls bana bukatar ka a wajennan,ka bar ni da zafin rashin mahaifiya ta kadai ya ishe ni ba sai ka kara min ba. S.man ya ce Aliyu…Aliyu ya daga masa hannu ka bar wajannan malam. S.man ya tashi ya ce Allah ya bada hakuri. Jama’a suka ce amin. Ya juya ya tafi. Kowa mamakin al’amarin ya ke musammam abokan aikin su da suka san amintar da ke tsakanin su. Ya same ni zauna kan dadduma,na idar da sallah. Ya zauna gami da jawo ni jikin sa,yayi kissing kumatu na. Cikin mamaki na ce baka zauna wajan makoki ba? Ya na wasa da ‘yan yatsu na yace abokina ya ce baya bukatar gani na awajan. Na yi shiru dai hawaye na fita daga ido na,ya dago fuskata ya ce kukan ya isa haka,pls be kamata ki na daga hankalin ki ba.Ya share min hawayen tare da fadin gobe fa za mu shiga watan haihuwan ki,kin san idan ki ka haifi mace me zan sa ma ta? Na girgiza kai alamar ah ah,ya dada kamkameni sannan ya ce Jauda,Jauda zan kira ta,na murmusa na ce dan san kai? Ya ce san kai laifi ni? Duk mu ka yi shiru muna sakar zuci. Daga bisani na kira sunansa Suleman? Ya amsa da ummm,na ce kar ka damu,komai zai dawo daidai tsakanin ka da Aliyu da yardar ubangiji. Ya murmusa ya ce Allah ya amsa Jauda ta,i miss bn his frnd. Ya tashi ya taimaka min nima na tashi mu ka shiga dakina dan bene yanzu wuyar hawa ya ke min. Gado na ya hau ya jawo ni na kwanta a jikin sa,cikin rada ya ce da ni Jauda kin san me? Na girgiza kai alamar ah ah,ya ce when it comes to you I jst want to hold you,na ji ki a jika kadai ya samin kwanciyar hankali. Na dago na yi kissng din sa sannan na koma na kwanta,a haka bacci mai dadi ya sace ni. Bayan Sati biyu da rasuwar Hajiya General yayi kiran mu gidan sa,mu na falo a zaune sai ga Aliyu shi ma ya zo,tini hankali na ya tashi. Allah ya taimaka zuwan shi yayi daidai da fitowar General da Anty Sa’a. Ba tare da bata lokaci ba ya fara gabatar da abunda ya sa ya tara mu. Kai tsaye ya ce na ji wani mummunar labari dangane da dangantar ku,shin me ke faruwa? Kowa ya yi shiru,ya ce da ku na ke ina neman bayanin abunda ke faruwa. Anty Sa’a tace Sule kai ai sai ka yi bayani. Nan S.man ya kwashe komai da ya faru ya labartawa General,ran General ya yi masifar baci da ya ji batun auren ki san wuta,ya dubi Anty Sa’a ya ce kin san da wannan zancen amma ki ka kasa fada min Sa’adatu? Jiki sanyaye ta ce na yi kuskure,ayi hakuri. Ya ce wannan ai yasheshshen zance ne,auren ki san wuta? Da ki ka sani da kin fada min tin wuri ai da abun be kai haka ba,ai shi ice tin yana danye ake tankwasa shi. Ya dubi Aliyu da Suleman kawai kun tadawa yar mutane da hankali ku dubi halinda ta ke ciki,ba ku tsoran ku ja ma ta matsala?ni dai kai na sun kuye kuka kawai na ke,suma Su ka sunkuyar da kai,yan zu ya kuke so a yi? Kai Ali me ka ke so a maka? Fadi ina jin ka. Aliyu ya ce so na ke ya sakar min mata ta..General ya ce da Suleman kai za ka sakar ma sa matar ta ka? Suleman ya ce Sir wallahi ni ina san mata ta,ba zan iya sakin ta ba. General ya kalli Anty Sa’a kin ga irin ta ko Sa’a?ya nuna Aliyu you are wrong,ya sake nuna Suleman ya ce and you are wrong tooo,nd idan ku ka ci gaba da yanda kuke you wil continue to be wrong,two wrongs can not make a ryt,ina amfanin abun?toh daya dole ya hakura,kai Suleman dau matar ka ka tafi,kai kuma Aliyu ka dau dangana,kaddara ta riga fata,Allah ya baka wacce ta fi Jauda. Rai a bace ba yanda ya iya yace yes Sir,haka kowa ya tafi gida rai babu dadi. [11:20pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 69;70;71;72:Inna ta turo min Jiddah saboda rashin Jummai gashi na kusa haihuwa.yau tin da na tashi da safe na ke fama da ciwo sama sama,amma ban fadawa kowa ba.Mu na zaune a falo mu na hira da Jiddah ta ke fada min sun je sun yiwa Aliyu gaisuwa ita da Anty Sa’a,na ce sun kyauta. Ta ce yanda ta ga ya lalace wlh sai duk ya bata tausayi,na ce rayuwa kenan. Ta ce sis da ki na da zabi wa zaki zaba tsakanin Aliyu da Suleman? Wannan tambayar tata ya yi daidai da shigowar Suleman da ke juma@ ce sanye ya ke cikin manyan kaya,jin tambayar da Jiddah ta min ya tsaya be karasa shigowa ba,mu kuma ba mu lura da shi ba. Na ce Jiddah ya ina da aure na ki na tambaya ta zabi? Zabi ya wuce wanda Allah ya rigaya ya gama rubuta min?zan zauna tare da miji har karshen rayuwa ta. Jin amsar da na bata ya sa shi sakin numfashin da shi kansa be san ya ruke ba,cikin farin ciki ya yi sallama gaba daya mu ka amsa,ya shigo ya na fadin Jiddah ki na dai kular min da Madam ko? Kujerar da ke kallan tawa ya zauna,zaman sa yayi daidai da jin kamar an mintsile ne,wani irin ciwo ya taso min yayinda mara ta ta ruke na fara jin wani abu mai dumi ya na gangaromin kafa ta. Jiddah ta ce masa sosai ma kuwa S.man. kallo daya ya min ya gane halin da na ke ciki,ya dawo kusa da ni da sauri ya ce Madam yaya? Ina cije lebe na ce masa ciwo,sannan na masa nuni da kafata. Da sauri ya dan yaye zanin jiki ba sai ya ga wani brown din ruwa mai din jini jini ya na bin kafa ta,tini ya sure ni ya na fadin Jiddah dauko mayafin ta mu tafi asibiti,yayi waje jiddah ta shiga a guje ta dauko mayafi na,a baya ta zauna tare da ni mu ka dauki hanyar barrack. Abun haushi mu ka tadda wani wawa go slow na ba gyara ba dalili,motoci ko motsawa ba sa yi. S.man ya ja ya tsaya,ya daki sitayari ya juyo ya kalle ni gaba daya na fita daga hayyaci na zufa ke keto min kamar an watsa min ruwa. Cikin zafin nama ya ja dorinar sa mai baki uku ya fita a guje,ya dinga kutsawa cikin motoci har ya kai ga abunda ya haddasa go slow,ashe check point ne,kurtu ne ke abunda su ka ga dama,daya wanda shi ya haddasa go slow din ya sunkuya gaban wata motar kaya,a lalle sai direban ya ba shi kudi,sauran biyun kuma sun tare mai gyada su na ciniki. Cikin zafin nama ya zabgawa wanda ya tsaida motar kayan dorina a gadan bayan sa,a fusace ya juyo ko da yayi ido biyu da C. Suleman sai ya tsorata ya ce identify your self Sir. A fusace ya ce Captain Suleman Matazu dan Uban ka! Tini ya dakawa yan uwan sa tsawa ya ce Behold we are in the presence of a Captain! SALUTE! Gaba daya suka kame gami da sarawa,da saurin kurtun ya janye tayoyi ya saki hanya ya na fadin go,go,go give way! Cikin zafin nama ya dawo mota a guje ya na fadin sannu Jauda,ya ja mota mu ka dauki hanya. Kafin mu karasa asibiti ya yi kiran Doctor Usman,mu na shiga barrack da isar mu asibitin mu ka tadda har sun fito da dan gado,Captain Suleman ya dauko ni ya dora kan gado,Doctor Usman tare da nurses duk sanye da kaki suka shiga tura gadon da gudu,Jiddah da S.man biye da su. Muna isa labour room da kyar Doctor Usman ya dakatar da S.man,ya ma sa alkawari za su yi iya kan kokarin su. Su ka ja kofa su ka rufe. Sai kai kawo suke shi da Jiddah,Doctor ya fito ya ce da shi Captain matar ka haihuwa za ta yi,ai har faya ta fashe,ka taho musu da kaya ne? Captain ya ce ina ana ta kai babu abunda na dauko,Doctor ya ce toh ya kamata,any moment from now za ta iya haihuwa. Ya ce toh bara na je na dauko,ya kalli Jiddah ya ce kira Anty Sa’a ki fada ma ta,bara na je na dauko kayan. Jiddah ta ce toh. Da sauri ya fice jiki na rawa. Tafiyar shi ba dadewa ba na sillibo dana namiji sak kamar Captain Suleman ya yi kaki,ina ji Doctor Usman ya na dariya ya na ce wa Alhamdulillah mun sami twin son din captain,wannan captain ne sak! Ya na hanya Jiddah ta yi kiran sa cikin hanzari ya daga tare da fadin Jiddah ya? Ta ce S.Man an sami karuwa,cikin farin ciki ya ce Alhamdulillah,ya ce ya lafiyar mata ta? Ta ce lfynta lau,ya ce MashaAllahu,me aka samu?ta ce baby boi….be ankara ba ashe wata katuwar mota ta shawo kwana daidai da lokacin da shima ta shi motar ta sha,tini ta gwabji motar S.man motar ta wuntsila gefe guda…! mutane su ka sa ihu aka zo ceton ran Captain Suleman. Shiru shiru na haihu,an gyara ni an kai ni dakin hutu amma banga C. Suleman ba shi da ya ce ranar da na haihu zai zuba ruwa a kasa ya sha. Ina nan kwance Jiddah ruke da baby na Anty Sa’a ta shigo idanun ta sun yi jajur,ta karbi baby a hannun Jiddah ta matso kusa da ni ta min sannu,ko da na kalli fuskar ta sai na ji gabana ya fadi,na ce Anty Sa’a lfy? Ta kau da kai ta ce lfy lau Jauda,sannu. Na ce ban ga Suleman ba,ba a fada ma sa na haihu ba ne? Ta ce eh wayar shi ba ya shiga,ta ce jidda zo ruke shi ina zuwa,ta fita da sauri. Na kalli Jiddah na ce Jidda ba lfy,taimaka min na tashi dan Allah,ta ce ki tashi ki je ina? Na ce ma ta kawai ki taimaka min dan Allah. Ta zo na dafa ta na tashi,na sanya mayafi na,na fito ina taku da kyar saboda dinkin da aka min,Jiddah biye da ni hannun ta dauke da baby. [11:30pm, 11/23/2014] Khadija Sidi: Matar mu 2 73;74;75: Bayan Anty Sa’a mu ka bi,na ga ta shiga office din Doctor Usman,na bi ta zan shiga muryar General ya dakatar da ni ya na fadin yanzu Doctor ina mafita?ko za a fitar da shi ne? Cikin mamaki na ce shi wa? Na ji muryar Doctor Usman ya ce with all respect Sir,amma sorry to say idan Captain Suleman ya dade shi ne ya kai 24hours da rai saboda ribs din sa gaba daya sun lalace Sir. Gaba daya ji na yi kamar an sheka min ruwan sanyi,na daskare a tsaye. Cikin office kuwa Anty Sa’a dake tsaye a bayan General da Captain Aliyu kuka ta sa,yayinda shi kuma Captain Aliyu ya runtse ido. General ya fara ma ta fada ya na fadin Haba Sa’a,idan kuka za kiyi toh ki fita ki ba mu waje. Sai ta yi shiru ta na hawaye kawai. General ya ce toh dan Allah Doctor kar matar shi ta sani ka ga tana cikin danyan jego. Ban san sanda na bude kofa na ce da Doctor Usman kai ni wajan miji na Usman. Ya girgiza kai ya tashi ya fito na bi bayan shi,suma su Anty Sa’a,Jiddah,General da Aliyu su ka biyo mu. Da shiga ta dakin da Suleman ke kwance gaba daya tsigar jiki na ya tashi,ganin shi kwance karafuna sarke a kirjin sa,duk sanda yayi tari ko amai jini ke zuba. Na tsaya ban karasa gaban sa ba ina hawaye,a hankali ya bude ido ya kalli in da nake tsaye,ya murmusa. Anty Sa’a da General suka shigo,biye da su Aliyu ne da Jiddah,ta miko min baby jiki ba laka na karba na karasa gadon S.man,ina kuka na ce Suleman ba ka cika alkawari ba,na haihu ba ka zuba ruwa a kasa ka sha ba. Abun mamaki sai na ji bakin shi radau ya amsa da ki yi hakuri Jauda,Allah be nufa,juyo min dashi na ga fuskar shi. Na juyo da fuskar baby,ya murmusa ya ce da ni an masa hudu ba? Na girgiza kai alamar ah ah. Ya kalli Aliyu ya ce Aliyu ka yiwa dan na ka huduba. Aliyu ya sa hannu ya karbi baby ya masa huduba,ya mikawa Jidda ta karbe she. Captain Suleman ya kalle ni ya ce daya tamkar da dubu,dubu jiran mutum,Jauda kyautar ubangiji. Allah ya saka mi ki da alkhairi,abunda ki ka min Allah ya mi ki. Na ruke hannun shi ina kuka,ya kalli Aliyu ya ce Aliyu ga Matar mu,ga kuma dan ka,dan Allah ka kula da shi tamkar kai ka haife shi,ya sake cewa Aliyu ka yafe min amma ban yi danasanin auren Jauda ba,sai ma alhinin barin ta da zan yi a yau,Jauda ita ce rayuwa ta,ita ta kyautata rayuwata,yau gashi zan koma ga mahillici na a cikakken mutum. Dakin kowa ya yi shiru kamar ba kowa. Captain Suleman ya ja hannu na,na dada matsawa kusa da shi,ya na murmushi ya ce Matar mu ki koma gidan tsohon mijin ki bayan rai na,ya kalli General ya ce dan Allah Sir a mayar da wannan zuri’ar mazau nin….harshe ya karye,maganar S.man a duniya ya kare,ya ruke hannuna gam kamar zai karya yatsuna. General ya sunkuya kunnan shi na dama ya masa kalmar shahada,Aliyu ya rude Anty Sa’a da Jiddah su ka kuka,ni Jauda na nemi kuka na rasa,ina ji ina gani da karfi Suleman ya karbi kalmar Shada yayinda ya damke hannuna,sai kuma shiru,ya saki hannuna! Nan take na fadi Sumammiya. Aliyu ya rungume shi ya na kuka,su Anty Sa’a kuwa kuka har da ihu. General ya sa hannu ya rufe idanun Suleman,Doctor Usman ya ja mayafi ya rufa masa,a tare su ka sarawa gawar. General ya ce da Doctor Usman ayi a hada kayan sa ya na so da anyi sallar juma’a a sallaci Suleman dan ya sami alfarmar Jama’a.Doctor ya sara gami da cewa yes Sir. Tsaye na ke a falo,na kwantar da Suleman da na lallaba da kyar ya yi bacci a kafada ta. Yau shekara biyu da rasuwar S.man,ya rasu ya bar min dan sa mai kama da shi sak kamar yayi kaki ya tofar. Na shafa kan Suleman cikin rai na nace Baban ka mai sunan ka was very special,Allah ya baka halin sa na gari. Ban ji shigowar sa ba sai kawai ji na yi yayi hugn dina ta baya,na lumshe ido tare da fadin ka kusa ba ni tsoro Oga,ya juyo da ni,ya karbi Suleman yayi kissing din shi a goshi tunda ba dana na tsoratar ba ai da sauki. Aliyu wanda aka sake daura mana aure bayan rasuwar Suleman da kusan shekara daya na matukar san dan aminin sa tamkar na shi,hakan ya sa a kullum na ke dada kaunar shi. Ya ja hannu mu ka zauna kan kujera ya zagayo da hannun shi kafada ta,na kwantar da kai na jikin shi,yayinda Suleman ya dada kamkame Captain Aliyu cikin bacci. Alhamdulillah. Ta ku Khadija Sidi. Thanx for readn. For comment or correction txt dis number 07018583783 SHARE THIS: Twitter Facebook Google Advertisements    Loading... RELATED Ina daraja 3d post Diya mace 2nd post Matar mu na khadija sidi PREVIOUS POST Ina daraja final post NEXT POST Matar mu na khadija sidi Notify me of new comments via email. Blog at WordPress.com. RECENT POSTS Kururuwan Shaiɗan 3rd December 11, 2016 KARNINMU 4 November 23, 2016 KARNINMU 3 November 18, 2016 KARNINMU 2 November 16, 2016 KARNINMU 1 November 15, 2016 Matar mu na khadija sidi November 1, 2016 Matarmu 2 by khady sidi November 1, 2016 Ina daraja final post October 18, 2016 TEXT WIDGET This is a text widget. The Text Widget allows you to add text or HTML to your sidebar. You can use a text widget to display text, links, images, HTML, or a combination of these. Edit them in the Widget section of the Customizer . ARCHIVES December 2016 November 2016 October 2016 September 2016 May 2016 ummu -abdoul MENU     