[4/12, 7:00 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page31``* Har misalin ƙarfe ɗaya Anne ta kasa runtsawa saboda yunwa ga kuma bakar zuciya ta ki yiwa kowa magana, har fitowa tayi lokacin basu jima da cin abinci ba ta yi shawagi wai ko Nana zata ganta ta tuna bata kawo mata abinci,ba amma shiru kake ji, dan ita Nana bata ma kawo wannan tunanin a ranta ba sam,aminatu kuwa dauke kai take tana dariya a a fakaice dan sarai ta fahimci shawagin Anne ba akan komai ba ne sai akan adda'am,a ranta cewa take ai tsohuwa tunda kika sake na gane kaunarki da abinci to kuwa kin shiga tara tsohuwar kawai. Haka ta gama shawaginta ta koma daki tana faman zuba ƙwafa cikinta kuwa banda kugin yunwa babu abinda yake, duban agogo Nana ta yi kafin ta dawo da dubanta kan Khalid dake kwance kan cinyar aminatu, sannan ta ce,"aminatu ku je ku kwanta kunga dare yayi kar ki kasa tashin dare",shafa tattausar sumar khalid aminatu ta yi tana cewa ,nana wane dare kuma?ai dare ya riga ya gama yi shi yasa ba zan kwanta ba sai nayi sallolina dan kar na kasa tashi karfe biyu"mikewa Nana tayi tana cewa "to hakan yayi Nima bari na yi amfani da dabarar ki na fara yin sallar kafin na kwanta"to Nana Allah ya tashe mu lafiya yau tare da Khalid zamu kwanta kwana biyu na yi kewarsa saboda tafiyar da yayi gidan adda suhaima",to shike nan Amin"nana ta fad tana taka matakalar step biyar da zai kaita bangaren dakinta. Sai da aminatu ta tabbatar da cewa Nana ta yi balance a dakinta, sannan ta kwantar da Khalid a hankali, tashi ta yi ta nufi kiching, tana shiga ta dauki kayan abincin Anne ta fita da shi ta baya ko tsoro ba ta ji ba ta kaiwa security da yake gadin main kofar da zata sadaka da cikin gidan baki daya,tana dawowa ta kwanta a kujera tana ci gaba da kallon tashar aljazira da suke karanta Alkur'ani me girma,a hankali take bi cikin daddan sautinta tana yi tana kallon gefen hanyar dakin Anne, Dan ta tabbatar sai ta fito neman abinci a yadda dai ta fahimci zaryar da take. Hasashen aminatu ya tabbata dan kuwa Anne ta hango cikin sanda kamar wata ɓarauniya,ta fito daga dakinta,da sauri aminatu ta rufe idonta kamar me bacci,sai dai tana kallon Annen. Hanyar kiching Anne ta yi cikin sanda kamar ɓarauniya dan yasa a ranta ko da zata ci abincin nan to bata son wani ya sani bare idan ta ce bata ci ba a ƙaryata ko kuma idan ta kwanta jinya,sai da aminatu ta tabbatar da shigar anne kiching ɗin sannan ta yi sauri ta miƙe tare da nufar kiching ɗin,bata bari ta yi takun da Anne zata Ankara da shigar ta ba, shi yasa ganin aminatun ya matukar razana ta dan bayan kunyar da ta ke gudu har da tsananin tsoro, take ta diririce, cikin in ina take cewa,"en dama bera ne na gani nake son neman madoki na bigesa dan kin san Ni fa a rayuwata bana son bera, da na ga bera gwara na ga maciji ina matukar jin tsoron bera, shi yasa idan naji motsinsa bana iya zama a wajen"rike kugu aminatu ta yi kafin cikin son boye dariyarta ta ce,"duk tsoron da kike masa shine kuma zaki iya kasheshi?to ma wai ta ina bera ya shigo gidan nan ne?gaskiya dai anne kin iya zubota sai dai idan da abinda ya kawo ki daban amma ba dai batun bera ba",kallonta anne ta yi cike da tsarguwa da masifa taf baki ta ce,"to dan ubanki me nazo nema? idan ma wani abun na zo nema ai gidan dana ne ba na ubanki ba ko?" Tura baki aminatu ta yi cikin gunguni take cewa "uban aminatu bawan Allah ne dan haka a daina zagar munshi",har Anne zata daga murya sai kuma ta tuna hakan yana nufin fallasa halin da take ciki ne,dan haka ta rufe bakinta tare da barin kiching ɗin a fusace cikinta kuma na karar yunwa fadin rai kuma ya hanata ta tambaya. A wannan dare dai haka Anne ta kwana da yunwa,ba dan taso ba karshe akan aminatu ta huce duk da cewa bata san cewa ita ce me shiryawa da bada umarni ba,haka ta kwana tana tsinewa aminatu da ahlinta. Kafin safiya tuni Anne ta jigata,Nana bata tashi sanin halin da ake ciki ba sai da ta je gaida annen ta ganta kwance tamkar wadda ta yi jinyar wata biyu,numfashi kawai take iyawa dan ko sallah asuba a zaune ta yi ta,da sauri Nana ta karasa gaban gadon saitin kanta tana cewa "subhanallahi "anne baki da lafiya ne kuma baki fada ba?"Anne da take jin cikinta kamar zai hade da bayanta ta yi saurin kawar da kanta gefe cike da fushin da yake Kuma taso mata tana danne zuciyarta,jin ta yi shuru karshe ma ta rufe idonta yasa Nana shiga tashin hankali duk a tunaninta zafin ciwon ne,dan haka ta yi saurin juyawa tana cewa bari na kira Abbyn su a kira likita tunda Zahida bata nan",jin haka yasa anne saurin riko hannunta sannan cikin muryar da ke nuna bacin rai ta ce"kar ki kira min kowa tunda ba damuwa yayi dani ba bare ke da bani na haifeki ba,bai san ya na ci ba bai san ya nasha ba,shi dai kawai tunda ya ajiye a dafa a bani gani yake ya fita HAKKINA"matse kwalla ta shiga yi tana ci gaba da cewa, "shi yasa kullum sai nayi kewar ya mace, tabbas na yarda da yan magana da su ke cewa da ka haifi gwamna gwara ka haifi matar gwamna sannan yaya mata rahma ne, duk wanda bai samu rabon mace ba zan iya cewa bai gama more haihuwa ba", zama nana ta yi a gefan gadon tana cewa "dan Allah anne ki yi hakuri ki daina fadin haka Ni ma ai yarki ce,dan haka ki fada min damuwarki?" Matse kwalla Anne ta kuma yi sannan ta ce,"yanzu kamar ni ace an manta da bani abinci a cikin gidan nan sai haka na kwana ciki fayau, ko bacci kasawa nayi saboda azabar yunwa"salati Nana ta sa tana tafa hannuwanta kafin cikin mamaki da damuwar da ta bayyana a kan fuskarta, ta ce,"yanzu Anne kina nufin AMINATU bata kawo miki abincin da na ce ta kawo miki ba"? Cike da fusata Anne ta ce "yo ta kawo min zance banci ba ne ki ji wata banzar tambaya"ganin ta harzuƙa yasa nana ta fara rarrashinta tare da sanar mata yadda sukayi da aminatu akan kawo mata abincin,daga karshe da kanta ta je ta haɗo mata lafiyayyan karin kumallo ta kawo mata, sannan ta sata a gaba kamar karamar yarinya, sai da ta tabbatar ta ci ta koshi sannan ta fita daga dakin dan zuwa ta samu aminatu ta ji dalilin wannan masifa da ta kusan Kunno mata. AMINATU yau ko fita karin kumallo basu yi ba, kiching ɗin sama wanda ke bangaren mus ab ta shiga tana haɗa musu breakfast,hirarsu suke cike da na nishaɗi ita da Khalid, "Khalid wai dama haka Anne take tsoron bera da yawa?"aminatu ta yiwa Khalid tambayar tana juye ruwan shayi a flax,dariya Khalid yasa dan duk sanda ya tuna karon Anne da bera sai yasha dariya,sai da yayi me isarsa sannan ya bawa aminatu amsa da cewa,"wallahi adda aminatu Anne tana tsoron bera kamar ya kashe ta, ita kuma momyna mage take tsoro kamar me dan idan ta ga mage kamar zata shide haka take yi"jinjina kai aminatu ta yi sannan ta ce"shi kuma uncle isma me yake tsoro wanda idan ya gansa zai iya fitsari a wando"?kai tsaye Khalid ya bata amsa da cewa,"kyankyaso"daga nan aminatu bata kuma cewa komai ba sai saka abinda zata fanshe rashin mutuncin waɗannan mutane Uku da take a ranta,Khalid ne ya dinga kai musu kayan ƙaramin falo yana jerewa, daga karshe aminatu ta fito ta dauko kunun kabewa da madara da ayaba da zuma da dabino, da ya zama abincinta, dan tun da ta fara tasawa Nana ta sabar mata dashi har ma da wasu abubuwan da har yanzu aminatun bata fahimci dalilin bata su da Nana take yi ba,tana sha ne kawai dan azabar dadinsu da take ji hatta da ruwayen da take sha daban suke da na gidan watsu tsimi ne na musamman da Nana take yi mata masu dan karen dadi, daukar kofin da ta cika shi da hadin kabewar nan ta yi ta juya zata fita sai hannunta ya bigi cabet din kusa da ita take kunun kabewar yayi tsalle ya fallatsu a fuskarta har zuwa kirjinta kasancewar wata yar bulawus ce me faɗin wuya a jikinta kuma ba bra a jikinta, shi yasa kai tsaye kunun ya tafi zuwa cikin wuyanta ya bata kirjinta sosai, Cak ta tsaya tana kallon kanta ta cikin mirror ɗin kiching ɗin kamar zata fasa ihu, dan fitowarta daga wanka ke nan suka shigo kiching ɗin,ajiye cup din ta yi da niyar ta je daki ta cire rigar, dan kuwa sake wanka ya tabbata a gareta,tana ajiye cup din juyowar da zata yi suka yi ido hudu da mus' ab da shigowarsa ke nan,dan tura bakinta tayi tana cewa "wannan irin shigowa ba tare da neman izini ba ai sai a razana mutum"dan takawa ya fara yi kamar zai karasa inda take sai kuma ya tsaya yana mai ƙure fuskarta da ido zuwa duk inda kunun nan ya fallasa, kafin a hankali ya ɗan ajiye numfashi ta baki tare da cewa "da izinin wa kuka shigo min nan?"shiru ta yi tana kifkifta ido tare da ɗan mici mici da bakinta,ba tare da ta dago ta kallesa ba,sai ma kokarin wucesa da tayi zata fita, tattausar hannunsa taji ya kamo nata hannun ya riƙe tare da dawo da ita baya suna fuskantar juna, hannunsa yasa duka biyu kan ƙafadarta yana kallonta kallon da yake kona mata dukan ruwan jikinta kallon da ke sata jin wani irin nauyi a kirjinta kallon da ke sata ta ji gaba daya ta manta wace ita da matsayinta a wajensa,kasa ta yi da kanta yayin da jikinta ya shiga rawa saboda yadda kallon nasa yayi tsanani tare da tasiri a gareta. Dago da kanta yayi, yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta,kafin cikin wata karyayyar murya ya ce,"me ye wannan?"ya tambaya yana kai harshensa saman idonta da kunun ya ɓata,kasa bashi amsa tayi saboda jin saukar harshensa saman idonnata yana masa wata irin lasa, "uhum ba amsa?"ya kuma tambaya yana yin kasa da bakinsa tare da bin duka inda kunun yake yana lashewa,yayin da sanyin harshensa da kamshin da yake fitarwa ya ci gaba da tasiri wajen kashewa aminatu jiki da zuciya,har bata san lokacin da ta rike kugunsa ba dan ji take ƙafafunta ba za su iya daukarta ba,"har lau dai babu amsa ko da wani damuwa ne?"mus' ab ya kuma yin maganar a daidai lokacin da yake gangaro da harshensa saman wuyanta yana tsotse kayan dadin da ta barar ajikinta, sosai jikin aminatu ya dauki rawar shoki saboda tsanantar yanayin da oga mus ab yake jefata a ciki,ga kuma tsoron kar Khalid ya shigo ya gansu a haka,cikin rawar baki ta yi dauriyar cewa "Hamma MUS'AB Khalid fa zai shigo kuma kuma yasan wannan abun iskanci n...ruf ya rufe bakinnata da nasa ba tare da ya fahimci abinda take cewa ba bare ya bashi muhimmanci,sai da ya shanye bakin maganar tas kana ya gangaro kirjinta inda ragowar kunun suka fallasa, zuba wa wajen ido ya ɗan yi wanda hakan yasa aminatu saurin sa hannu ta kare tare da yin baya tana cewa "Ni wlh bana son kwart.....bata iya karasa fadar kalmar ba saboda yadda numfashinta yayi wani irin daukewa da tsananin mamaki da rudani tare da wanzuwar wani irin yanayi wanda ta kasa tantance sa a cikin dukan rayuwarta,kirjinta sama da kasa kawai yake tsoro ya hanata fahimtar komai saboda yadda mus'ab yake lashe saman kirjinta da fatar ba tare da wani damuwa ko shakkar yin hakan ba,sai da mus ab ya lashe kaf kunun da suka ɓare a jikin aminatu sannan ya dago fuskarsa ya kura mata ido na wasu yan sakanni kafin ya hura mata iskar bakinsa a saman idanunta da ta kasa bude su saboda tsananin takaici da kunyar abinda yake yi matan,bakin nan ya cika taf da iska kamar zata fashe,"hannu yasa ya laka ce lips ɗinta da suka yi wani irin ja saboda shan da suka sha wajen oga mus ab me aiki da cikawa.zata yi magana kenan mus' ab ya kuma haɗe bakinsu dan yasan rashin ta ido zata yi shi yasa yake son yin maganinta ta wannan hanyar amma fa a fadarsa😃. Daidai lokacin kuma Nana ta shigo falon tana tambayar Khalid in da AMINATU take,Shi kuma ya bata amsa da cewa"Nana tana kiching Nima tun dazun nake jiranta bata fito ba shi yasa nayi karyawata dan yunwa nake ji",daga haka Nana ta nufi kiching ɗin kai tsaye batare da tunanin cewa idonta zai yi ganin kunya ba. Ƙarar bude kofar kiching ɗin kawai suka ji take aminatu ta razana tare da kwace kanta daga rikon tsaurin da mus' ab yayi mata, shi ko mus' ab din babu wata alamar razana ko kunya a tare dashi dan ko da da akwai to ba zaka taba ganewa ba,kuka kawai aminatu ta fashe dashi tare da saurin bin bayan nana tana cewa, wallahi nana shine ya zo har inda nake daga kawai yaga kunu ya zube a jikina shine ya ce lallai sai ya lashe sai kace wani maye kuma fa Nana har da kir......tsawar da nana ta daka mata ita ta tsaida ita da ga baranmaramar da take yi,jan hannunta Nana ta yi suka fita daga falon gaba daya,a hankali ya nemi guri ya zauna yana shafa tattausar sumarsa da ta take ta wani irin kyalli baka siɗik da ita,tare da kwantar da kansa jikin kujerar yana lumshe idanunsa da suka yi wata kala daban fuskarsa kamar murmushi zai kwace amma dai babu murmushin wata kila kuma na can kasan zuciya yake yi. Suna zuwa kasa Nana ta saki hannunta tana zabga mata harara kafin ta ce,"ke kam aminatu yaushe zaki hankali?yaushe zaki daina wannan sakarcin da sakin baki haka a gaban kowa eye?"tura baki aminatun ta yi tare da cewa,"to Nana haka kawai sai na barsa ya dinga lalube Ni bayan shi b mijina bane duba fa kiga bakina duk sanda ya samu dama sai ya ci min idan na barsa ai sai dai wata rana na tashi na ga bani da baki,Ni wallahi ki hanasa ko na kai kararsa wajen ab.....bige bakinta nana ta yi tana mai rasa abin cewa ga kunyar da ta lullubeta saboda zantukan aminatun,dan Kore zancan sai Nana ta yi saurin sako mata zancan Anne, "aminatu me yasa jiya baki kaiwa Anne abinci ba?"zaro ido aminatu ta yi tare da cewa "kai kai tab wallahi yau na kuma tabbatar da cewa matar nan bata kaunata kaji wata karya"harara nana ta kuma jefawa aminatun tana cewa "annen ce take karya?"da sauri ta rufe bakinta tare da cewa "a a ba ita ba ce subtar baki nayi amma dai nasan na kai mata abinci ta koro ni wai bani na saba kai mata ba dan haka na mayar ba zata ci ba,kuma da nace mata zan mayar larai ta kawo mata shima cewa ta yi bata so dan yau tunda har na taba abincinta bazata ci ba,bayan ma bata san kusan kullum ma Ni nake girkin ba",dan jim nana ta yi kafin ta ce ai shi kenan amma dai ki kiyaye nan gaba idan hakan ta faru ki fara gaya min",yes ma aminatu ta fada tana mai daga hannunta da kamewa a tsaye irin yadda sojoji suke yi,girgiza kai kawai Nana tayi ta wuce bangarenta a ranta kuwa ta gasgata aminatu dan tasan irin tsanar da anne ta yi mata tsaf zata yi hakan,dan haka take ta share maganar a nan wajen. [4/12, 7:29 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page32``* Dariya aminatu tasa tare da cewa tsohuwa kadan ma kika gani yanzu ne wasan zai fara"daidai nan Khalid ya leƙo ta barenda yana ƙwala mata kira, kallonsa ta yi kana ta samu guri ta zauna ta ce, Khalid dauko min kayan karina na karya anan dan ba zan kuma hawa saman nan ba ato kana zaman zaman ka duk abi a wani sude ka, anya kuwa wannan mutumin bai sa yi maita ba?"adda aminatu waye ya sude ki?"harara ta galla masa tare da cewa ka dauko min abinda na sa ka kawai dan idan kaji me wannan aika aikar to sai kayi kuka anan saboda takaici",Ni dai dan Allah ki fada min Khalid ya fada cikin maganar sa ta yara,zata yi magana kenan ta ji dakakkiyar muryarsa da babu wasa ko kadan a cikinta yana cewa "kar ki sake ki ɓata min tarbiyyar yaro da wannan sakarcin naki, idan kika sake sai na sa kwaɗo na kulle bakin maganar in yaso naga ta kiriniya", ya fada yana fita daga falon gaba daya tare da barin mayen kamshinsa,harara ta bi bayansa dashi kafin cikin yin kasa da murya ta ce,"idan ma ka kulle min bakin ai zan nemi key na bude abina", Khalid ne ya ce adda aminatu me kika yi daddy zai kulle bakinki da kwaɗo?Ni dai babu ruwana daddy baya son magana shi yasa zai kulle bakinki da kwaɗo",rankwashi ta kai masa shi kuma ya goce yayi sama da gudu ta bishi tana cewa zan kama ka ne bari cikina ya dauka, na yi wanka kaga yadda zan yi da kai a gidan nan ehem". Sai da ta yi sabon wanka ta canja doguwar rigar atamfa wadda aka yi mata dinkin Captain ta yi daram a jikinta dirarriyar kiranta ta fita tamkar ita ta zana kanta,fuskarta babu komai sai kwalli da ta zizara da lips glow sai ta yi wani irin sassanyan kyau tamkar ka sace ta ka gudu,saukowa ta yi daga saman dai-dai lokacin Nana ta fito daga dakin Anne cikin shirin fita da alama ma sallama ta je ta yiwa annen,cikin murmushi take duban aminatu da burgewa ta ce,"kai masha Allah ɗiyata tafi ta kowa kyau da burgewa, dama yanzu zan leƙo ku dan tafiya ta kamamu nida Abby dazu ya Kira ni yake sanar dani cewa na shirya kafin ya shigo",ta na rufe bakinta suka ji tsayuwar motar Abby,dan haka aminatu ta yi raurau da ido kana ta ce,yanzu nana bari na zaki yi a tsakiyar maza kalan a shigo a yi min fyade",salati nana tasa kafin ta dora da cewa yanzu aminatu ba zaki dinga yiwa bakinki linzami ba, ina cewa ban jima da yi miki fada ba amma har kin kuma",hawaye aminatu ta fara yi daidai shigowar Abby falon kallonsu yayi sannan ya shige yana cewa "sai ki sauri ki gama rarrashinta kafin na fito dan wannan tafiyar ba ta ku ba ce dole ku zauna a gida,zahida ma tana nan tafe yau din nan". Zama Nana ta yi tana kwalawa Khalid kira, sai gashi ya sauko yana murza ido da a alama bacci ne ya fara kamashi,Nana me kika yiwa adda aminatu take kuka?"Khalid ya tambayi Nana lokacin da yake kallon fuskar aminatu da ta yi jage jage da hawaye kamar wadda aka yiwa duka,kama hannunsa Nana ta yi tana cewa wai dan na yi mata faɗa kuma nace zamu yi tafiya da Abby ba jimawa za mu yi ba, ina ga bai fi mu yi kwana uku ba"hakan da Khalid ya ji sai shima ya kwaɓe fuska zai yi kuka, zaunar da su Nana ta yi tana faman lallashinsu kamar wasu ƙananun yara ko nace kamar wata karamar yarinya,babu jimawa Abby ya fito lokacin tuni sun hakura dan dama ita aminatu kukanta bai kai zuci ba dan dama tana jiran irin wannan ranar ne da babu wanda zai dakatar da ita daga bawa Anne da isma kashi a gidan,har wajen mota suka rakasu, basu shigo gidan ba sai da suka ga fitar su daga gidan. Suna shigowa aminatu ta dubi Khalid ta ce,zaka raka Ni gidan su rahila amma duk abinda ka gani kayi shiru babu ruwan ka da tambaya ka ji ko?"amsawa yayi da to mayafinta ta dauko ta yafa suka fice ba tare da sun sanar da anne ba. Gida ne irin na masu karamin karfi, mace daya ce da yaransu kusan shida ga shi gidan bashi da yalwa shi yasa ko ina zaka samu kaya a jibge,kuma irin wannan gida beraye da sauran kwaruka sun fi takura musu,shi yasa kai tsaye aminatu ta zo nan dan neman bera,mannira ce ta ce "ke ko Amina me zaki yi da bera?"haɗe fuska aminatu ta yi kafin ta ce babu ruwanki idan zaki samo min kawai ki samo min", shike nan kamar nawa kike so?"anzo gun aminatu ta fada tana gyara zamanta akan kujerar tsugunnon da take ,kana ta ce "kamar guda biyu ma sun isa",tom shike nan bari nasa mudan yanzu ya kama miki su dan ba ya.tsoronsu kuma gasu nan ko ina yawo suke baza su yi wuyar kamuwa ba,sai dai kuma ina zaki saka su tunda kince a raye kike sonsu?"mannira ta tambayi aminatu tana mai lekawa dakin su mudan din dan kiransa,tunanin inda za a saka mata su ta shiga sai kuma ga mudan din ya fito yana cewa,"in dai zaki dawo min da dan karamin kejina da na hada zan saka tantabara sai na ara miki",da sauri aminatu ta amsa da cewa zata dawo masa dashi, dan haka kai tsaye mudan ya dauki kejinsa ya shiga dakin tsohuwa inda anan ne beraye suka fi yawa ya kamowa aminatu beraye guda biyu ya saka cikin kejin, cike da farin ciki aminatu ta karba suka bar gidan, jin ranta take yi yau fes ko ba komai zata yi kallon rawar tsoffi. Har za su fita daga gidan aminatu ta ji kukan mage, cikin sauri ta juya sai ko idanunta suka sauka kan wata karamar mage baka idanunta ne kawai suke sheki, bata yi magana ba suka fita mudan yana rike da kejin da ya saka mata berayen, sai da ta ga Khalid yayi gaba yana yin ball da ball dinsa dake hannunsa, sannan ta kalli mudan cikin yin kasa da murya ta ce"mudan magen da na gani a gidanku ta ku ce?"gyada kai mudan yayi tare da cewa ai saboda berayen ake Yaya ya samo mana ita amma kuma gashi bata iya kama beran wata kila sai nan gaba idan ta girma"kuma yin kasa da murya aminatu ta yi Sannan ta ce"za ka bani ita?"shuru mudan ya danyi kafin ya kalli aminatun yana cewa "to ai ba tawa ba ce"kar ka damu ko siya ne sai na yi amma kar ka fadawa kowa ni ka bawa ka barsu kawai a zuwan ta bace kaji"mudan ya ce "to shi kenan,yaushe za a kawo miki ita?"dan daga kanta ta yi sama alamun tunani kafin ta ce "yauwa ka bari sai anjima da dare, amma fa kar ka bari securities din bakin gate su ganta idan kazo kawai ka ce musu sako zaka bani, da ka fada musu haka za su kyaleka ba za suyi maka bincike ba"dai-dai lokacin suka ƙaraso bakin gate ɗin gidan, karbar kejin da ya ke a lulluɓe aminatu ta yi tana cewa to mudan sai anjima da an yi sallar isha ka kawo min sakon kaji"mudan ya amsa da to daga nan ta shige gidan ba tare da ta kula securities din da suke sankame kamar wasu gumaka ba. A falo ta samu Khalid da tuni ya rigata shiga gidan,bata kulasa ba shima ta wuce dakinta ta dauro alwala sannan ta kwalawa Khalid din kira shima yayi alwala suka yi sallar Azhar daga nan suka wuce dinning room suka ci abinci, aminatu tuni ta yiwa berayenta maboya lokaci kawai take jira ta kaddamar da shirinta. Ƙarfe biyar daidai Anita ta je filin jirgi ta dauko Zahida,babu abinda Anita take sai zuzuga kyawun da zahidan ta yi wanda kuma a zahirin gaskiya babu abinda ta kara sai uwar ƙibar da take neman hanata nutsatstsan numfashi,sai dai fatar ta da ta yi kyau wanda dama kowa ya san wannan dole ne ga duk mutumin da ya samu zaman waje ɗaya musamman kasashen turawa,har suka zo gidan zahidan bata tanka mata ba, hasali ma idanunta a rufe suke kamar wadda take bacci,sai da ta tsayar da motar sannan ta dubi zahidan tana cewa to "Ms mus' ab zaki iya bude idanunki domin mun zo gida"sai a lokacin zahida ta bude idanunta tare da dago kanta daga kwanciyar da ta yi jikin kujerar me zaman banzar, a hankali ta tura ƙafafunta waje sai da ta dauki sakonni kafin ta fita gaba daya, kallon gidan ta yi kamar tana tunanin abinda zata shiga tarar a gidan,anita ce ta nuna mata hanya sannan ta fara yin takunta as usual kamar wata sarauniya tana yi tana faman buda hanci da yatsina fuska,a haka suka shiga main falon in da anan aminatu da Khalid suke ta wasan guje gujensu kana kallonsu kasan basu da wata damuwar da ta zauna a ransu. Kasancewar zahida a gajiye take shi yasa bata damu da kulasu ba, kai tsaye hayewa ta yi bangarenta Anita na biye da ita da hand bang da sauran TARKACEnta tamkar dai wata hadimarta. kuma hakan baya damun Anita ko kuma nuna wa ne bata yi Allah masani, Anita na zaune a falon zahida har ta je ta yi wanka ta shirya ta fito, a ƙalla ta dauki sama da mintuna talatin amma hakan ko a ƙwalar rigar Anita,sai ma tararta da ta yi cikin fara a da nuna kulawa,tana zama larai ta shigo dauke da kayan abincin da ta gama haɗa musu bayan ta tabbatar da dawowar zahidan,tana ajiyewa ta fice ta bar su. Anita da kanta ta zubawa zahida abinci da lemo daidai yadda tasan tana bukata daga nan itama ta zuba,fara cinsu ke da wuya Anita ta ɗan dakata da kai lomar da take shirin yi bakinta tare da duban zahidar da take cakular abincin kadan kadan cike da yauki,kana ta ce"wai Ni ko Dr ya labarin majnunin kine har yanzu ba wani important issue with him?"uffan zahida bata ce ba sai da ta mula dan kanta kana ta ce,Anita me ye damuwarki da maganar dan ladi ne kullum baki da tambaya sai nashi?me kike so ki sani bayan na gaya miki cewa ban san ina yake ba ban san ya a kayi ba, hasalima rabona da shi tun wannan daren da aka raba Ni da shi dakyar",ta karasa maganar tana zuƙe ragowar lemon da ke cikin cup din hannunta,Anita ta ce,amma ai kin gaya min cewa ya zo da safe bayan kin fito asibiti har an yi masa dabara an kullesa an hada shi da hotonki?"da karfi zahida ta daki goshinta kafin cikin tsawa ta ce"Anita ya isheki bana bukatar wannan maganar ya daga dawowata baki tare Ni da komai ba sai da batun wani kazamin me wanki"anita ta kwantar da murya tare da cewa haba zahida ni fa kawarki ce kuma aminiyarki abokiyar shawararki ni ce me warware miki matsala duk lokacin da kika shiga damuwa amma akan abu daya sai ki manta ki rufe idanunki ki ta fadar abubuwa marasa dadi"duban ta zahida ta yi fuskar nan a kwabe babu annuri kana ta ce,"anita ba ko mai ne kike da hurumi dashi a cikin rayuwarta ba to dan me zaki dinga min wasu kalar tambayoyi wanda suke sirrina?"cike da mamaki anita take kallon zahida kafin ta buɗe baki ta ce,wai zahida kina nufin har yanzu baki gamsu dani a cikin rayuwarki ba?kina nufin tun tsawon lokacin da muka hadu har zuwa yau baki yadda kin ji cewa zaki iya faɗa min ko wane irin sirrinki ba?"girgiza kai zahida ta yi tana duban Anita ido cikin ido kafin ta ce"Anita har yaushe muka hadun da kike batun na saki jiki dake? Nifa in gaya Miki KO uwata bata isa jin sirrin rayuwata ba,mutum uku ne nayi musu yaddar da za su iya jin wani babi na cikin sirrina bayan su kuwa babu wani mahaluki a duniyar nan, dan haka tun wuri ki cire a ranki cewa dan kina kawata kawar ma da muka hadu a titi Zan iya baki amana ko sirrina, kuma ina gargadinki daga yau kar ki kuma yi min batu akan dan ladi, kar kuma ki kara yi min wata tambaya da ta danganci rayuwata idan ba haka ba zan cireki daga cikin rayuwar tawa gaba daya ba abinda ya dameni ba ne wannan"daga haka ta fice fuuu ta bar falon ta bar Anita da sakin baki tana binta da kallon mamaki. Jiki a sanyaye Anita ta baro bangaren zahida duk da cewa bata ji a ranta zata iya rabuwa da zahidar ba amma dai ta ji ciwon abinda ta yi mata,lokacin da ta sauko tuni an yi Isha dan haka a can bakin gate ta samu aminatu ita da mudan wanda ya cika alkawari ya kawo mata kyliyarta a ɓoye ba tare da ya bari yan gidansu da securities din sun gani ba,Anita tana daga cikin motarta take kallon aminatu wadda sai yau din ne ta ke yi mata kallon tsaf, sosai taga rashin lefin zahida na yadda ta daga hankalinta akan AMINATU, wucewa ta yi bayan an bude mata wangamemeiyar kofar gate ɗin zuciyarta cike da sake sake akan lamarin GIDAN zahida. Yau mus' ab bai samu dawowa da wuri ba saboda kansa ya fara daukar zafi ta ɓangarori da dama,sai karfe goma ya shigo gidan, ko da ya dawo ɗin ma kai tsaye upstairs ɗin bangarensa ya wuce bayan ya shirya kuma ya shige room dinsa na sirri da babu wanda ya san aikin da yake gabatarwa a ciki,yana shiga ya bude na urorinsa yana duba saƙonnin da suka shigo ta email address dinsa na sirri,sako guda da ya ja hankalinsa ya zubawa ido hannunsa tallafe da habarsa, sako ne da aka yi shi a sakaye tare da wasu kalmomin da aka sakaye su cikin HAUSA wanda hakan yaja shi tsawon lokaci dan son gano abinda hausar take nufi amma hakan ya faskara,ya tabbata wannan hausar a wajen cikakkaken bahaushema zata yi wahala bare kuma shi da hausar ba zauna masa ta yi ba, daga karshe dai haka ya hakura sai dai kuma ya kwafe kalaman a cikin kwakwalwarsa domin rubutasu ya ajiye zai iya zama wani abu da zai iya kawo masa matsala cikin aikinsa,fita yayi daga dakin ya koma bedroom ɗinsa, ya dauki karamar wayarsa ya kuma fitowa,kai tsaye dakin su aminatu ya nufa dan duba su. Yau dake aminatu tasan abinda ta shirya sai da tasan yadda ta yi tasa Khalid yayi bacci da wuri, ita kuma ta yi lamfo kamar me bacci,tana jin lokacin da mus' ab din ya shigo,ya jima yana musu addu'a ya shafa sannan ya sumbaci Khalid,har ya juya zai fita sai kuma ya dawo da baya a hankali ya zauna gefan fuskarta ya zuba mata ido kafin ya fara matsowa da fuskarsa daf da tata,zuciyar aminatu kuwa har wani fat far take saboda tsoron abinda zai yi matan dan idan yayi mata irin na dazu to tabbas shirinta zai wargaje dan zai gane cewa bata yi bacci ba,dakyar ta yi yaƙi da zuciyarta da take kokarin tona mata asiri saboda dogon ajiyar zuciyar da taja na ganin ya sumbace ta kamar yadda yayiwa Khalid ya tashi tare da fucewa, yana fita ta saki numfashin da saura kirin ta sake shi tana dafe kirjinta. Ga mamakinsa a dakinsa ya samu zahida, sai dai bai nuna mata ko mai ba kamar yadda itama bata ga komai akan sakarsa ba, kwanciya yayi bai ce mata komai ba, kamar yadda ita ma bata ce masa ba, sai da taga da gaske muskulancinsa ya take nata sannan ta tanka masa da maganar da kullum bata tauna ta kafin tayi masa,"kana kallona na dawo ba zaka tarbeni cikin kauna kayi min maraba ba?" Kai tsaye ya bata amsa da cewa sanda kika tsallake gidanki kika tafi in da ranki yake so kin nemi izini bare sallama?" Jin maganar da ya maida mata yasa ta yin shiru dan yau a bukace take dashi ba zata yadda ta biye masa ba dan taga shi idan zasu shekara a haka ba damuwarsa ba ce. Zahra✍🏽 [4/13, 5:40 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page33``* A can Abuja kuwa bangaren su Abby ke nan,bayan sun sauka a gidajensu, da matansu kamar yadda suka saba,barin su su kayi suka koma hotel inda anan ne zasu yi tattaunawarsu,wadda a wajen matansu tattaunawar kasuwanci ce, to suma a wajensu kasuwancinne .me lasisi ma kuwa,ba ko mai ne yasa suke zuwa da matansu lokaci loci ba sai dan kawai basa so ko kaka su bude kofar zargi tsakaninsu da matannasu shi yasa a ko da yaushe suke ƙoƙarin dai-daita kasuwancinsu da na kowa tare da shigo da matan nasu ta wata fuskar da babu wadda zata kawo zargin wani abu a Cikin harkokinsu. Su uku ne a dakin kamar yadda kowa ya sani ba su taba yadda da wani ba bayan junansu dan haka basu bawa Kowa damar shiga cikin kasuwancin sirrinsu ba baya ga abokan cinikayyarsu,wanda wannan kuma sune duniyarsu,Alhaji Kabir ne ya juya musu laptop din dake gabansa dan su kalli abinda ke ciki,zubawa fuskar ido su kayi duk cikinsu babu wanda yake tunanin ya taba ganin fuskar a rayuwarsa, dan haka su ka maida dubansu kan Alhaji Kabir din sunan masa kallon tambaya,shima bai ja da nisa ba ya shiga yi musu bayani kamar yadda bincikensu ya bayar,ya fara da cewa "wannan da kuke gani shine lauyan da muke nema ido rufe,kamar yadda kuka sani yana amfani da adereshin bogi wanda ta hanyarsa ne duk wasu Click dinsa suke bibiyarsa kuma ta hanyar adresoshinsa na bogi ne yake binciken duk mara sa ar da Allah ya kai hannunsa, to mu dai mun yi nasarar binciko sa ta hanyoyin da baza su misaltu ba kuma mun sha wahala kafin yin wannan nasarar,a yanzu haka na tura masa sakayayyiyar wasika me dauke da sakayayyun ma anoni wanda kafin ya fahimce su sai ya dangana ga cikakken bahaushe,mu kuma ta wannan hanyar ne zamu cimmasa dan zuwa gare mu kamar dai yadda muka tsara"bayan yin shurunsa ne Abby ya kuma kallon hoton kana ya ce"kuna da tabbacin cewa shine wannan?",dukkansu shiru su ka danyi suna mai zubawa hoton ido tamkar dai suna jiran amsar ne daga bakin hoton,can Alhaji Garba ya numfasa tare da cewa ba mu da wannan tabbacin,ci gaba da binciken mu shi zai bamu tabbacin shine ko ba shi ba ne,kuma zata iya kasancewa shine za kuma ta iya kasancewa ba shi ba ne,abinda dai yafi mu kuma maida kai wajen binciken, sannan ya batun wancan asibitin an samu wasu bayanai akansa?"ya tambaya yana duban Alhaji Kabir saboda shine yake da ilmi akan wannan har kar shi yasa komai suke barinsa a hannunsa in dai abinda ya shafi na ura ne,girgiza kai yayi kafin ya ce,a wannan binciken ne dai Gaskiya muke da rauni domin. Kuwa na kasa gano komai ta bangaren binciken na ura sai dai ban hakura ba kullum ina samo sabbin hanyoyin da zasu kara min haske wajen binciken, sai maganar tsohuwar can ita ma mun yi nasara wajen samo videon da yake dauke da matar da muke zargi"macece?" Suka hada baki wajen tambayarsa. Numfashi Alhaji Kabir ya dan ja sannan ya ce,Nima ban san ta ba sai dai ga dukkan alamu mus ab ya San wani abu dan shi mu kaga ta bawa sako, sai dai bamu san sakon meye ba"cike da mamaki da wani irin yanayi na girgiza Abby ya mike tsaye ya dawo kusa da Alh Kabir kana ya ce,nuna min video na gani",girgiza kai Alh Kabir yayi yana cewa ai basu fitar da video ba, dole sai idan mun koma zaku iya gani a can wajensu,sai dai kuma iya daukar wajen kawai ya dauka gaba daya ragowar basu fita ba babu su ma kwata kwata a cikin fotej ɗin ",to me yasa haka cewar Alhaji Garba da shima ya shiga cikin wasiwasi akan mus' ab,bincike ne zai nuna masa komai duk da cewa Ni bana tunanin mus' ab ya san wani abu akan batan innawuro kawai dai ana son yin amfani da shi ne dan a kawar da tunaninmu, kun ga idan muka yi zarginsa to hankalinmu ba zai je kan ainahin wanda yake da alhakin abin ba"wata kakakafar ajiyar zuciya Abby ya sauke har da share wata yar zufa da ta tsatstsafo masa saman goshinsa,dan kuwa ba kara min girgiza yayi da batun sako mus' ab cikin lamarin nan ba,baya taba Fatan abinda zai sa mus ab ya San wani abu daga cikin sirrinsu saboda sanin nasa kan iya jawo sabuwar fitina ta tonewar asirin da dukkansu zai iya sanadin numfashinsu, Alhaji Garba ne ya dubi yadda Abby ya ke ta goge zufa kana ya sheƙe da dariya har da kwanciya shi kansa Alhaji Kabir dariyar yake yi,nunasa Alh Kabir yayi da hannu yana cewa" wai kai me yasa har yanzu kake tado abinda ya jima da faruwa,me yasa tun tasowar mus' ab Baka da kwanciyar hankali akan waccan bannar da muka aikata bayan kuma babu wani mahaluki da yasan abinda ya faru bayan mu ukun nan, dan Allah Alh jamilu ka dinga kyautata mana zaton alkhairi idan kana saka tsoro a ranka tamkar kana tunanin wata rana asirinmu zai tonu ne",numfashi Abby ya ja wanda kafin nan sai da ya dauki sakanni kafin yayi magana. "Ni kaina na rasa me yasa duk na tuna wancan al'amarin sai hankalina ya tashi ban sani ba ko dan nine jagora, shi yasa abin yafi damuna,ko kuma dan saboda tasowar mus' ab ne hakan yake karuwa a raina,tsaki Alhaji Garba yayi tare da cewa wlh ban taba ganin uban da yake tsoron dansa irin kai ba,ace ka haifi da a cikinka amma ya zama dodo a wajenka kullum cikin firgita ka yake"Alh Kabir ya ce a'a fa Garba ka tuna dukan mu nan babu wanda baya shakkar idanun mus' ab,saboda shi wani irin yaro ne da Allah ya bashi kwarjinin da duk mahaluki da ya dubesa sai ya ji hantarsa ta kada musamman mara gaskiya,dan haka kar kaga lefin jamilu,"Abby ya ce "ashe ka fahimceni Kabir idan ba ku manta ba da kaina na hanasa zabinsa na fake da cewa dan yaki zabinna ne na karantar likita shi yasa na hanasa zabinsa na yin lauya, wanda kuma mu ba haka ba ne ta wajenmu,kawai tsananin tsoron yadda yaron ya taso ne yasa naji a raina idan ban canja masa tunani ba to tabbas zai iya zama silar kare rayuwarmu a kurkuku,dan da'a ce dana ya kulle ni gara ace wani ne can a duniya yayi min hakan kamar dai wannan"ya fada yana nuna hoton boyayyan lauya me gaskiya dake kan screen din laptop din Alhaji Kabir har yanzu,"hakan ma bazata faru ba domin tun farko mun riga da mun yi maganin duk wata shaida ko damuwar da zata iya zama mana matsala a cikin duniyar kasuwancinmu"dan haka ku tashi mu koma gida dan hakan ma yana da muhimmanci"ba wanda ya kuma.yin magana a cikinsu illa bin umarnin Alh Kabir da su kayi suka mike tare da ficewa daga dakin dan barin hotel din gaba daya. Tunda Anita ta koma gida ,babu abinda take sai kaiwa da kawowa da tunanin sabuwar hanyar da zata bi domin samun yadda take so a wajen zahida,yanzu ne ta fahimci cewa zahida tana da wayo da hangen nesa akan sirrin da ya shafi rayuwarta,cizon yatsanta ta yi har sai da ta ji zafi ya ratsata sannan ta saurara,kafin cikin kaushin murya ta ce"zahida zan ci gaba da binki a hankali wallahi wallahi duk wayonki sai kin dawo a saman tafin hannuna zan jure har lokacin da haka mu zai cimma ruwa",daga haka ta haye saman gadonta tare da jan bargo ta rufe jikinta har zuwa saman fuskarta. A bangaren isma kuwa yau da ya san cewa Nana da Abby basa nan, abokansa ya dauko su ka siyo kayan mayensu wanda babu nau in da babu a ciki suka shiga kwalbewa,duk da cewa ya fi shakkar mus ab akan iyayennasa hakan bai sa yayi tunanin bari ba,dan acewarsa mus' ab yayi nesa dashi in dai ba fada masa a kayi ba babu yadda za ayi yasan me ya aikata a gidan. A hankali aminatu ta sauko daga kan gadon bayan ta tabbatar da ingancin baccin Khalid, sannan sai da ta tabbatar da cewa kowa iya yanzu duk nacinsa ya yi bacci, bude kofar dakin tayi ta fita, bayan ta dauko safaya key din dakin Anne wanda tun ɗazu ta sato shi a dakin Nana,berayenta ta dauko a maoyarsu, sai da ta duba su ta tabbatar suna nan da ransu sannan ta je bakin kifar Anne,ta bude a hankali cijin sanda tamkar wata ɓarauniya,tana bude kofar kadan sai ta tsuguna ta bude berayen daga cikin kejin suna ganin hanya kuwa suka arce zuwa cikin dakin Anne kamar yadda ta saita,ƙwafa ta yi tana maida kofar tare da rufewa, daukar kejin ta yi ta bar wajen cikin sauri a ranta tana fata a daren nan Anne ta ji bera saman cikinta,daki ta shiga ta fara kada kunne amma shiru tun tana sa rai har ta fidda rai ta kwanta itama bacci ya fara ɗaukarta. Kamar daga sama Anne ta ji wani abu na bin ƙafafunta kamar zai shigeta,ai ko a miliyan ta farka tana yan dube dube da hannunta, jin bata ji komai ba sai ta yi kokarin komawa dan atinaninta ko mafarki ta yi tunda tasan dai abu ne me wuya wani abun cutarwa ya iya shigowa falonsu ma baran tana har dakinta,sai dai kuma kan ta gama gyara kwanciyarta ta kuma jin motsi a saman kanta, dan haka a maimakon ta kwanta sai ta mike zaune tana mai kunna hasken dakin inda idanunta basu sauka akan komai ba sai akan bakikirin din beran da yake ta wasan adabo akan gadon da yake jin kamar aljanna, Anne kuwa bata san sanda ta yi wata yar dungure ba sai gata a akasan gadon tana laluben mafaka bakinta tuni ya dauki kyarma ta kasa janyo wata addu'ar kirki, sai daga can ta fara jan wasu kalamai masu kama da karatun yan bori,allhumma wassikini wa maskini karatun tsoffi marasa kwari"abinda take ta maimaitawa kenan tana tafiya da rarrafe idanunta akan berayen da suke ta sabgoginsu. Kamar ance aminatu ta farka,tana buɗe idanunta ta yi zunbur ta mike tare da fitowa daga dakinta,kai tsaye dakin Anne ta nufa cikin sanda,tana zuwa bakin kofar kuwa ta ji surutan Anne kamar wadda bata cikin hayyacinta,dariya aminatu ta yi tare da sa key din ta bude kofar a hankali wanda motsin kofar yayi daidai da wani irin tsalle da beran yayi kamar an danna remote yayi kan Anne,sai ga Anne ta jika jikinta da fitsari kafin ta ci gaba da Jan gwiwowinta a ƙasan dakin tana rarrafe kamar yarinya, bakinta kuwa tun tana iya karanta karatunsu irin na tsaffin da suka zauna a cikin kauye da duhun jahilci har ta zo tana kasa bude idanunta da ko gani sosai ba sa yi,jin motsin kofar ne ya kuma razana ta ta saki wani mugun ihu tare da sakin ragowar abinda take da tabbacin cewa zawo ne. Isma da yake daf da shigowa falon ne ya ƙara sauri wajen faɗowa falon tare da nufar hanyar dakin Anne, sai kuma mus ab da ihun ya samesa lokacin yana sujjadar karshe ta nafifilunsa, dan haka shima kai tsaye kasan yayo cikin nutsuwarsa da kamewar da suke kuma bayyanar da kwarjininsa, itama aminatu tuni ta karasa fadawa dakin tare da kiran sunan Anne tana yi tana toshe hancinta tare da yatsine fuska kamar zata yi amai,isma yana shigowa kan aminatu yayi cike da fusata yana cewa dan ubanki me kika yi mata?"ya.fada yana ƙoƙarin kai hannunsa jikin aminatu zai bigeta,caraf ya ji an riƙe hannun nasa tare da saukar da shi a hankali,da sauri aminatu ta koma bayan mus' ab Wanda hakan ne ya bawa isma damar fahimtar waye ya dakatar dashi daga samun kyakkyawar damar cin uban aminatu,"haba hamma mus' ab da Ka barni na faffalla mata mari dan na tabbatar maka da cewa ita ce ta yiwa anne wani abun tunda iya su ka daine a wannan sashen" ko kallonsa mus' ab bai yi ba ya nufi wajen anne da take ta son tashi amma ta kasa ya tsuguna gabanta duk da warin da ya cika masa hanci amma hakan baisa ya kasa nutsuwa wajen yi mata magana ba,"me ya faru Anne?"cikin kuka anne ta ce wallahi babban mutum beraye ne a dakin nan fal ganin idona kai ba ma iya su ba ina tunanin har da aljanu yau sun yi nasarar shigowa gidan nan dan wallahi ni naga abinda na gani"isma ne ya shiga duba dakin yana cewa "to uban me ya kawo bera gidan nan wallahi sai dai in shigo da su a kayi dan kuwa babu abinda zai shigo da bera daki"aminatu da ke rabe daga can inda koda isma ya zaburo zata iya buya wajen mus ab,ta ce,"shi bera ina ruwansa duk in da ya gadama ai shiga zai yi koda kuwa gidan shugaban kasa ne"a fusa ce isma ya juyo zai antaya mata ashariya amma sai yayi wani ɗif kamar an dauke nefa,jin yadda yayi shurun kamar ba da shiri ba yasa mus ab kallonsa sai kuma a hankali ya maida idanunsa kan abinda isma din ya zubawa ido baki sake tamkar wani dolo,da karfi mus ab ya rufe idanunsa yana mai kokuwar hadiye katon abinda ya tsaye masa a makoshi,lokaci ɗaya idanunsa suka wani birkice,cike da zafin nama ya mike daga durkuson da yayi a gaban Anne ya nufi aminatu da hankalinta sam ba ya kansu,wata irin rumfa mus' ab yayiwa aminatu ta yadda ko da ƙafafunta ba a hangowa, bakinsa kuwa ya kasa furta komai bare ya samu damar bawa isma umarnin fita ko dauke idanunsa daga kan abinda yake halalinsa mallakinsa duniya da lahira. Wannan abin da mus' ab yayi shi ya dawo da isma hankalinsa sai dai kuma zuciyarsa cike take da kwadayin sake maimaita irin farin ganin da idanunsa su kayi masa,tabbas kira ko ya ce surar aminatu ta tafi dashi, zai iya cewa duk irin yawa ce yawacensa a fadin duniya da mu amalarsa da mata bai taba ganin sura makamanciyar ta Aminatu ba bare wadda ta kaita,ashe ƙadara ce ko ya ce Gara a lulluɓe cikin huhun goro a gidansu bai sani ba,kai anya kuwa ya taba kallon aminatu acikin hayyacinsa kuwa in ba yau ba? tabbas bai taba ba dan da ya taba da tuni ya gano sirrin da yake boye,to shi kuma wannan da yayi baka bakan ya hanashi ganinta me hakan yake nufi, duba fa rungumeta yayi da sunan ya kareta, to idan har shi bai halatta yaga aminatu a wannan yanayin ba shima mus' ab din ai Bai kamata ba dan haka ba zai bar dakin nan ba har sai aminatu ta fita dan hakanne kadai zai bashi damar ganin sauran abinda bai gani ba. Kukan Anne da tsallen da ta yi ta fada kan isma shi ya dawo dashi hayyacinsa,da sauri isma ya angije Anne Yana cewa haba Anne ya za a yi ki taba Ni da wannan zawon a jikinki gaskiya Ni ba ki kyauta min ba,akan bera kawai duk kinzo kin ɗagawa mutane hankali"dan uwanka Ni ka ture to ka tabbata da cewa yau a dakinka zan kwana dan muddin beran nan suna cikin dakin nan to ba Ni babu shi,shi kuma wancan tabararran me yake yiwa yar mutane?"ta faɗa tana jefa idanunta kan mus ab da har yanzu ya kasa motsawa daga rumfar da yayiwa aminatu. ita kuwa aminatu a tunaninta kare ta yayi daga dukan da isma yake shirin kawo mata shi yasa ta yi luf tana zare idon rashin gaskiya ... Fyadam✍🏾 [4/15, 3:25 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page34``* Isma dai ba dan yaso ba sai dan warin zawon Anne da yake shirin kumbura masa ciki,yasa ya tattagi annen ya kaita bayi ya zubar yana toshe hancinsa,da wannan damar mus' ab yayi amfani ya janye aminatu daga dakin, duk da yadda aminatu taso ganin karshen wasan sai dai kuma ta ji dadi da ba a yi batun cire beran ba ko ba komai Film din bai kare ba,isma kuwa duk saurin da yake dan ya fito ya samu aminatu hakan bai samu ba,dan dole ya fita daga dakin yana mugun saka a zuciyarsa,ba tare da ya nemo beran dakin Anne ya fitar dasu ba,Anne kuwa koda ta gama gyara jikinta hankali kwance ta fito dan a tunaninta tuni isma ya dauke berayen da take da tabbacin shigo da su akayi, hakan yasa ta sake shirin bacci ta haye gadon tana la antar wanda ya kawo mata bera dakinta. Kai tsaye mus' ab bangarensa ya wuce da aminatu wadda ke ta zumbure baki tana gunguni akan me zai kaita dakinsa ya barta ta koma dakinsu mana kalan kawai duk ya lallasheta mutum sai kace maye, yana jin duk abinda take fada amma bai kulata ba kuma bai saketa ba har sai da suka dangana ga bakinsa,iska ta shaka tare da yin wani dan karamin juyi wanda hakan yayi sanadiyar dagewar yar rigar bacci me zubin umbrella sama tamkar ana wulwula umbrella shafaffen cikinta ne ya bayyana da dan ramin cibinta, rufe idanunsa yayi yana kokarin saita numfashinsa da ya haɗe guri daya da wani irin yanayi tare da zafin isma da ita kanta aminatu da har yanzu bata yi hankali ba,tsawa ya daka mata wanda hakan yasa lokaci ɗaya ta nutsu tana rarraba manyan idanunta da har sun fara cika da ƙwallar tsoro dan bata taba cin karo da tsawar mus ab ba bare ta san ya kalar kwarjininta yake, sosai shakkarsa ya kuma nunkuwa a ranta dan haka ta samu guri ta maƙure jikinta babu abinda yake sai rawa tamkar wadda aka shekawa ruwan sanyi lokacin hunturu. Ganin yadda ta tsorata sosai ne yasa shi dan sassauta fuskarsa duk da cewa ba wai ya saka mata murmushi ba ne . kana ya tako zuwa gabanta ya tsaya tare da zuba mata ido,yana kallon yadda shigar jikinta ta fidda wani irin sirrin kyawunta. ta bangare guda kuma idanun isma ne suke shawagi a jikin aminatu suke gilma masa,take fuskarsa ta kuma murtukewa makwallonta sakawai da aminatu ta kalla sai da ta kusa shiɗewa saboda yadda taga suna wani irin sama da kasa cikin karfin gudu,wanda ta nan ne kawai makusnacinsa yake gane yanayinsa na tsananin ɓacin rai. Da ƙarfi aminatu ta runtse idanunta tare da hade hannayenta guri guda alamar roko dan bata taɓa tunanin yadda ya kusanto tan ba duka zai kai mata ba,jin shiru yasa a hankali ta bude idonta guda, sai ta gansa har yanzu tsaye gabanta yana mata kallon kurillar da har ta fara sabawa dashi, ajiyar zuciya ta dan sauke tare da dan yin dibi dibin neman hanyar da zata ratse ta gudu, sai dai babu wata hanya dan girmansa da kwarjininsa ya kankane ko ina,dan haka babu wata hanya da ta rage mata,dan haka ta bude idanunta gaba daya ta kallesa ba tare da ta yadda ta kalli cikin idanunsa ba ta ce,"dan Allah dan Allah na tuba ba zan kara ba",ta karasa maganar da zirarowar hawayen tsoronsa da har yanzu bai saketa ba.duk da cewa Kuma bata san lefin da ta yi masa ba,gira daya ya dage mata tare da cewa "me yasa ba ki ji ne amanata?" Yayi maganar tamkar ba shi ba haka kuma zuciyarsa kamar ba cikin barazanar fashewa take ba,"to to me nayi nifa ba Ni ce na kai mata bera ba"ta fada tana kebe baki zata rusa kukan da yake cin zuciyarta,cikin takaicin amsar da ta bashi ya karasa hade jikinsa da nata tare da lalubo bakinta, kana cikin zafin nama ya cafke harshenta yana masa wata irin tsotsa a ransa yana jin yana yin hakanne da sunan punishment, kuka aminatu tasa saboda yadda yake neman cinye duk wani abu da ta mallaka a cikin bakinta,a ranta cewa take shike nan aminatu ta zama bebiya hamma mus' ab ya cinye harshen yin magana,hakan da ta ƙaddara ya gama faruwa yasa ta kuma fashewa da kuka tana dukan ƙirjinsa ko zata samu ya rabu da ita,amma ina shifa dan gwagwarmaya dan Nana Asma'u tuni ya kurmance baya ji baya ganin kowa in ba Nana aminatu yar gidan baffa Yusuf jikar innawuro ba,wata irin azaba yake ji cikin ƙirjinsa wanda yake tunanin abinda yake yiwa aminatun shi zai sa ya samu Salama amma ina tamkar kara rura wutar dake babbaka cikin zuciyarsa yake,ji yake cinye aminatu ko maida ta cikinsa gaba daya ma bai isa kashe masa wannan rurarriyar wutar da bai san iya jimawarta cikin ransa ba,sai dai yayi mata kiyasi da lokacin shigowar aminatu cikin rayuwarsa.sannan bai san zafin na meye ba yanayin da yake tsintar kansa a ciki shima bai san na meye ba,bai san amsar ba, kuma bai san waye zai bashi amsar ba, dan haka dan rage raɗaɗi dole yayi abinda yake jin shi zai ragewa zuciyarsa azaba da raɗaɗin da take ji. Dan kansa da kuma kukan aminatu da ya ji yana kuma zafafa masa zuciya ya hakura, sakinta ya yi tare da janta jikinsa suka kifa saman gadon, jin nauyinsa kanta yasa ta kuma kara karfin kukanta tare da bugun bayansa tana cewa,"aradun Allah ba zan yadda ba tunda ka cinye min harshe yanzu ko magana ba zan iya yi ba,kai mugu ne dan birni na yafi ka kirki duk da cewa shima baya magana kuma ban taba ganin fuskarsa ba,amma dai a hakan ya Fika kirki tunda shi bai taba cin....saukar tattausan lips ɗinsa da ta ji kan nata yasa ta yi shiru tare da datse bakin dan karma ya ce zai kuma cin wani abun,"yanzu da wane harshen kike MAGANA?"ya tambayeta bayan ya kwantar da fuskarsa kan tata fuskar yana dan janye nauyinsa daga gareta, jin ya dan saki jikinsa yasa ta daddage ta turesa daga kanta amma memakon ta samu sararin guduwa kamar yadda take SO sai kawai ta ji ta koma samansa ya zamana shi a kasa ita kuma a samansa wanda hakan ya bata damar jin wani irin tudun abu daga can kasansa, "wayyo hamma mus' ab me ye a jikinka me tauri kamar sand...hannunsa yasa ya rufe bakinta yana dan zare mata idanunsa da suka tuno mata da kwarjininsa, sanin cewa bata da wata hanyar kubuta yasa ta kwantar da kanta a kirjinsa tana mai jiyo bugun zuciyarsa da take harbawa a hankali,a ranta kuma ta kudurta cewa sai taga ciwon da yake jikin Hamma MUS'AB, tunda ta tabbatar da cewa babban ciwo ne dan duk sanda ya rungumeta sai ta ji girman abin ajikinsa,to da alama ma dai kullum karuwa yake dan yau abin ya bata tsoro sosai kuma taji tausayinsa ya kamata,da wannan tunanin bacci me nauyi ya dauketa, shi din ma bacci ne ya suresa ba tare da ya shirya masa ba. Zahida kuwa duk abinda ke faruwa acikin gidan bata sani ba, dan kuwa tana can tana baccin asara baki sake da mafarkan mallakar duniya da mus ab din ta ita kadai, wannan shine kadai burin zahida kuma ga dukkan alamu ta dauko hanyar samun duniyar,mus ab ne kaɗai zai zama wahala a gareta. Isma kuwa ya bar bangaren ne da mugun tunanin ta yadda zai ya samu aminatu ta ko wane hali wala da aure wala ba aure burinsa kawai ya mallaketa a shimfidarsa. Cikin ikon Allah berayen nan basu kuma firgita Anne ba, dan haka tuni Anne ta shanya baki da tunanin an fitar da su ta ci gaba da baccinta hankali kwance duk da cewa da yar ragowar fargabar halin da ta shiga. Sosai baccinsa yayin nauyin da har yaso makara sallah,cikin hanzari ya fito daga bayi, ragowar ruwan hannunsa ya yarfawa aminatu a fuska daga haka yayi fitarsa dan yasan dole zata tashi,aiko dai tashin ta yi bayan addu'ar tashi da ta karanta babu abinda ya biyo baya sai gunguni da haka ita ma ta faɗa bayin ta yi alwala tazo ta tayar da raka'atanil fijri. Duk da baccin da ta ke ji amma haka ta daure ta zauna ta yi karatunta da laziminta lokacin shida ta wuce gari ya fara haske,dan haka ta rufe Kur'anin tayi walha tana idarwa ta maida Kurt anin majiyarsa tare da hayewa saman lafiyayyan gadon mus ab,ba tare da ko hijabin sallar ta cire ba. Koda mus ab ya dawo bai tashe ta ba dan yaga alamun ta yi ibadarta,dan haka kai tsaye ya wuce gemroom, har ya gama ya fito aminatu bata farka ba, again bai tasheta ba ya wuce clothing daga nan ya wuce bayi, nan ma ya jima yana kalkale kalkale kafin ya fito jikinsa daure da karamin towel da karami a hannunsa yana goge bakar sumarsa me sheki, gaban mirror ya je ya fara shafa mayukansa masu ƙamshi da tsada, mikewa yayi tare da yin kasa da towel ɗin jikinsa dan ya samu ya shafa mai a guraren da bai sa ba,da sauri ya yawaiwayo tare da toshe kunnensa da karfi saboda karar aminatu da ta karaɗe ko ina na dakin, lokacin da ya juyo har ta fice daga dakin tana ci gaba da ihunta, girgiza kansa yayi yana mai ci gaba da abinda yake dan tuni ya gano abinda ya sa ta yin wannan ihun, shi bai ma san cewa ta tashi ba da ba zai yi gangancin cire towel ɗinsa ba dan yasan halin abarsa. Dai-dai lokacin da aminatu ta fito daga dakin mus ab da gudu,lokacinne kuma zahida ta shawo kwana cikin shirinta na fita as usual tana wannan takun nata na ƙasaita tamkar ɗiyar sarki,gayu kuwa tamkar zai yi magana a jikinta, dama gashi ta karo uwar kiba, sai ta Kuma zama irin matan alhazawan nan,dan haka kai tsaye suka yi wani irin karo, sai ga zahida zube a kasa daga ita har braekcase ɗinta da jakarta, da sauri aminatu ta ja burki ba kuna dan ta damu da barin makauniyar da tayi da zahida ba ne, a'a sai dan kawai tasan ko ta sauka kasa babu wanda zata sanarwa abin tsoro da mamakin da ta gani,bugu da ƙari tasan bayan Nana zahida ce kawai wadda zata tausayawa mus ab kuma gata likita ta ko ina zata iya taimakonsa, dan haka ba tare da ta jira cewar zahidar ba ta fara magana cikin haki da nuna tashin hankalinta tana mai nuna bangaren mus ab din,"adda zahida dan Allah kije ki taimakawa hamma mus ab jela ne ta fito masa ajikinsa wallahi baki ganshi ba kato ko lankwasuwa ba ta yi, kuma fa girma take yi saboda duk sanda ya rungumeni ina jin tudunta ajikinsa ina taso in san meye sai jiya da ya ke cinye min harshe na kuma jinta, har na tambayesa ya rufe min baki da alama dai baya so hankalin yan gida ya tashi ne shi yasa yaki fada,"dan shuru ta yi tana mai da nunfashi kafin ta kuma fashewa da kuka tana cewa "dan Allah ki taimaka masa wallahi nasan yana jin ciwo sosai ". Zahida fa ina tunanin sumewa ta yi a zaune dan tun da aminatu ta fara maganganun nan ta gano abinda aminatu take kira da jela kuma wai ciwo saboda rainin hankali,shi yasa tun da ta kame bata kuma motsi ba, kunnen ta ne kawai ya ci gaba da jiyo mata maganganun aminatu wanda ita kuma ba haka take so ba, so take in da Hali gaba daya kunnuwanta su toshe, ba gangar jikinta take so ta tsaya da aiki ba kunnenta take so ya daina aiki saboda jin wannan kalaman daidai yake da tashin hankalin jin lokacin mutuwarta. "Adda zahida dan Allah kije ki gani wllh da gaske nake idan aka barsa nan gaba ba zai iya fitowa ba saboda girman abun da ciwon da yake masa, Kum.....bata iya karasawa ba saboda wani mugun naushi da zahida ta kaiwa bakinnata wanda take ya kumbura dan ita kanta zahida bata san lokacin da wannan karfin ya zo mata ba,jinta kawai ta yi a tsaye kan kafafunta, cikin fushi me tsanani ga wani irin bakin ciki mara misaltuwa, cikin fita hayyaci ta ci gaba da kaiwa aminatu duka da mari ta ko ina,bakinta kuwa har yanzu ya gaza furta ko kalma daya ne,aminatu kuwa Cikin kuka da son kare kanta daga dukan da zahida take ta kai mata tace "me yasa kike dukana dan kawai na taimakeki na fada miki halin da mijinki yake ciki haka kawai zaku kashe ni keda mijinki shi ya cinye min harshe ke kuma kin bugeni a labbana"wani irin ihu zahida ta Kuma sawa tana mai zubewa kasa sumammiya saboda kalaman da aminatu ta kuma yi dan kuwa gaba ɗaya abinda aminatu ta ke fada na shirme babu wanda zahida bata fassarashi ta kuma fahimceshi sa ba a matsayinta na wadda ta girmewa aminatu nesa ba kusa ba. Larai ce ta hayo saman da gudu tana fadin "inna lillahi Hajiya zahida me kuma ya sameki?"aminatu zata yi magana kenan idanunta ya sauka akan mus ab da ya dan tokare ajikin kofar sashensa,fitowarsa kenan kuma duk abinda ke faruwa yana saurarensu dan kuwa mus ab Allah yayi masa kunnen ji sosai,fitowa ne kawai bai yi ba har sai da ya gama shirinsa tsaf cikin hadaddiyar cot dinsa Kalar sararin samaniya da nic dinsa baki fuskarsa babu abinda take sai walwali bakin kwantaccen sajensa ya kwanta tun daga gefe da gefen fuskarsa har zuwa karkashin habarsa inda ya tara dan gemun da ya kuma kawata surarsa ta cikakkun maza yan gayu da tsafta ga kuma kyawunsa na Fulani dan haka abin ya kuma hadewa ya bada wani kyawu na musamman me tsayawa a zuciyar yanmata,idanunsa tsaye akan aminatu yana mata wannan kallon nasa na kai tsaye wanda tuni ta fahimci cewa ita ka dai yake yiwa wannan kallon duk da cewa kallon nasa ba iri daya ba ne, a ko da yaushe yana mata kallo ne na daidai da yanayin da suke ciki, amma ta fi sanin ma'anar wannan kallon saboda duk sanda ta yi wani laifi shi yake mata kuma laifinta yafi zamanta lafiya yawa, daga shi kuma sai kallon da yake mata wanda take shiga cikin yanayin jin sanyi da mutuwar jiki kallon da ya fi shigar ta da tsuma ta har da taba zuciyarta,wancan kallon nasa komai yake haifarwa a tare da ita, sai dai kuma kash bata san komai akan yanayin ba kawai dai tasan cewa idan yayi mata wannan kallon to everything is wrong with you, janye idanunta ta yi daga kansa tana kallon larai da har ta ɗebo ruwa tana yayyafawa zahida,cikin natsuwa mus ab ya wuce yana zuwa saitin aminatu yayi kasa da murya sosai kana ya ce"idan kika kuma bude bakin nan kika yi magana makamancin wancan to sai na gutsure harshen gaba daya"yana maganar ya wuce abinsa tamkar bai san da mutane a wajen ba dan ita kanta aminatu badan tana kallonsa ba ba zata ce ya ma kalleta ba bare yakai ga yi mata kashedi,yana gama sauka zahida ta farfado dan haka bayansa kawai ta hango yana fita daga falon hannunsa dauke da yar karamar jakarsa ta laptop,yunkurawa ta yi cikin zafin Nama wanda hakan yasa aminatu ta kwasa da gudu ta sauka kasa tana cewa "wannan fa ina ga ta haukace aradun Allah idan na tsaya kaheni zata yi"aiko aminatu tayi gaskiya dan kuwa zahida bata bi mus ab ba, Dan tasan ba sauraren ta zai yi ba, karshe ma ya yi mata abinda zai sa mutuncinta ya zube gaban yan aiki, shi yasa kawai ta bi aminatun da mugun gudun da bata taba sanin cewa nauyin jikinta zai bari ta yi sa ba. Da sauri aminatu ta banko kofar wanda hakan yayi daidai da zuwan zahida dan haka kofar bata sauka a ko ina ba sai akan goshinta ji kake Kum,da sauri zahida ta dafe gashinta da ta ji yana neman cirewa tare da lailayo wata muguwar ashar ta bankawa aminatu tana mai buga kofar dakin kamar zata karya dakin,goshinta kuwa tuni ya suntume tamkar me bisin kai, ta jima tana buga kofar tare da antayawa aminatun zagi kwando kwando. Aminatu kuwa tana shiga dakin ta sa kuka tana neman maboya, cikin wardrobe ta shige tana cewa Khalid rufe dan wallahi ba zan tsaya wannan lutuwar uwar taka ta kashe Ni ba,dan haka gara na yiwa kaina kamshin mutuwa tun kafin na mutu a hannun iyayenka daga mai cinye min harshe sai mai dukana dan kawai anga ni marainiya ce,"ta karasa maganar da kuka har tana jan majina,"Khalid ya ce "adda aminatu idan fa na rufeki ba zaki shaki nunfashi ba kuma idan mutum baya shakar numfashi mutuwa yake yi"khalid rabu dani kulleni kawai idan Allah yayi zan hadu da dan birni to dole sai na rayu"Khalid bashi da wani dogon tunani dan haka ya rufe aminatu kamar yadda ta bukata ya samu waje ya zauna yana sauraron muryar maminsa da bugun da take yi. Gajiyar da ta yi ne yasa ta hakura da bugun, larai tasa ta dauko mata jakarta da sauran tarkacenta ta fita a fusace ba tare da ta duba yanayin da take ciki ba,dan sam bata san yadda goshinta ya koma ba,ya kumbura yayi suntum fuskarta tayi tsayi gashin yayi tsayi sai kyalli yake yi,tun daga harabar gidan securities duk wanda ya kalleta sai ya sunkuyar da kai yana rike dariyarsa,tana fita kuwa suka samu aikin yi. Kai tsaye hospital ta nufa zuciyarta na wani irin zafi da jin tsanar aminatu kamar ta kasheta tun yanzu ba tare da ta jira umarnin iyayenta ba. Fyadam ✍🏾 [4/15, 5:42 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page35``* Zahida na fitowa daga mota,kowa ya zuba mata ido,mutane yan jinya wanda basu san halinta ba kai tsaye suke mata dariya, wanda suka san halinta kuwa basa iya yi sai sai su sunkuyar da kansu kasa ko su kauce daga wajen suna dariya,tun zahida bata fahimta ba har dai ta fahimci cewa da ita fa suke yi,abin ya bata mamaki shin me ye abin dariya a tare da ita,dube dube ta shiga yi a jikinta sai dai bata samu ko mai ba,har ta isa office ɗinta tana ta faman duba jikinta,dan ko kallon inda masu gaisheta suke bata duba ba bare ta yi musu kallon da ta saba yi musu idan sun gaida tan,tana shiga ofishin kai tsaye ta wuce gaban madubi dan ganin abinda yake tare da ita har wasu banzaye kaskantattun mutane suke yi mata dariya,isheta wajen ke da wuya ta kurma ihu tare da zubewa kasa tana mai sakin wani kakkarfan kuka me tsananin ciwo,wai yau ita zahida mutane suke yiwa dariya akan canjin fuska kawai da ta samu,to idan har mutane za su yi mata dariya dan sauyin kamannin da ta samu to me zasu yi mata idan har ta bari kudi da suka bar hannunta, wannan alamu ne da suke nuna mata na cewa idan har ta bari kudi suka kwace mata to tabbas mutane jifanta zasu dinga yi suna dariya da nuna ta da hannu,da sauri ta share hawayenta tana cewa, zahida kar ki yi kuka, yanzu ba lokacin kuka ba ne lokacin kawo karshen aminatu ne lokacin samun kudi da pawer ne, dole ne aminatu ta biya bashin wannan abun da jininta,ko ta halin kaka sai tayi kudi da wani sashe na jikin AMINATU. Mikewa ta ya da sauti kamar wadda ta tuna da wani abu tare da figar jakarta ta fi ce daga office din ranta a matukar bace,dole masu kallonta suna dariya suka koma sunkuyar da kansu saboda yadda suka ga fuskarta ta koma irin ta bosa bosan nan masu ban tsoro,motarta ta shiga ya kwasheta da wani matsiyacin gudu,ko masu tsaron gate ɗin sai da suka tsorata dan dan sun yi zaton tasu ta kare saboda saura ƙiris ta take su da motar Allah ya taimake su suka janye kofar cikin zafin Nama. Cikin.mintuna ta isa gidan Anita saboda irin gudun da ta dinga fallawa tamkar ita kadai aka yiwa titin,ko murfin motar bata rufe ba ta yi cikin gidan cikin jan kafa tamkar zata kifa,a razane Anita ta sauke labulen dakinta lokacin da ta ga motar zahidan,kokarin saita kanta tayi tare da fitowa falon daidai lokacin da zahida ta fada saman kujerar tare da sakin wani irin nishi tamkar na me haihuwa saboda tsananin takaicin da yake ranta,a hankali Anita ta matso ta zauna kusa da ita tare da dafa kafadarta, kana cikin sanyin murya ta ce"zahida me kuma ya faru na ganki haka a dame?"zahida ta yiwa kanta alkawarin baza ta kuma yin Kuka akan damuwar aminatu ba, dan haka ta hadiye wanda taji ya tsaya mata a maƙoshi kafin cikin dakiya ta sanar da Anita abinda ya faru a cikin wannan safiyar,kafin ta dora da cewa "yanzu anita har nayi lalacewar da wata mace zata zo har gabana tana gaya min irin wannan magana,anita sirrin mijina ne fa wanda ni kadai ce mace daya tal a duniya da ya kamata a ce na san sashen jikin mijina ba wata tsinanniyar bafulatanar daji ba,me Mus ab yake so ya zama bayan nasan shi mutum ne me tsantsani da bin dokokin Allah,tabbas Anita akwai wani abu aboye kuma zan gano ko me ye saboda nasan mus ab farin sani shi ba manemin mata ba ne kuma bana jin zai fara akan wannan yarinyar" shuru tayi tana dan maida numfashi kana taci gaba da cewa "anita me kike tunani akan wannan lamarin?"a hankali Anita ta janye tagumin da ta zabga tana sauraron zahidar kana ta ce "zahida nifa ina tunani akan yarinyar nan ta san wani abu da kuke shiryawa akanta kamar yadda kika sanar dani akwai abinda su Abby suke shiryawa a kanta ko nace suke da dalilin daukota shi yasa take Miki wannan wasan kwaikwayon dan kawai ta juyar miki da tunani dan gaskiya Ni a gani na duk abinda take miki Shiri ne kawai"tunda Anita ta fara magana zahida ta zuba mata ido bata motsa ba har sai da ta kai aya,"anita maganar ki akwai kamshin gaskiya dan kuwa akwai alamomi da yawa da ta nuna mana wanda yasa muke zarginta da sanin wani abu daga cikin sirrinmu, dan haka zan yi bincike sosai akanta muddin kuwa na gane hakan to kashinta ya gama bushewa duk da cewa dama ba kyaleta zanyi ba",tana zuwa nan a zan canta ta mike tsaye ba tare da ta yiwa anita sallama ba ta fice daga falon. Binta da kallo Anita ta yi, kallon da Ni kaina na diga masa ayar tambaya ,dan kuwa kallo ne wanda yake cike da ma anoni ma su tarin yawa,daga karshe kuma ta yi kwafa. Aminatu da kanta ta gaji da zaman cikin wardrobe tasa khalid ya budeta, zama ta yi tana maida numfashi kafin ta mike ta fada bathroom ta yi wanka tana fitowa doguwar rigar atamfa ta saka ta fesa tirarukanta da sauran humrorin da humkum ta hada mata ta fita zuwa falon dan cikinta babu abinda yake sai kugin yunwa. Tana cikin cin abincin Anne ta fito tana dan dingisa kafarta saboda danben da suka sha da bera jiya,aminatu na kallonta ta tuntsire da dariya kamar wata zararra,unbola kawai Anne ta iya yi mata tare da wucewa inda ta nufa,"su Anne an sha danbarwa wasan jiya yayi dadi saura na yau"ta fada tana mikewa daga kan dinning din,kai tsaye daki ta nufa da madarar ruwa a hannunta da Kuma wani dan kwano karami, tana zuwa ta leka karkashin gado ta janyo kwalin da ta boye yar magenta, zarota ta yi ta zuba mata madarar tasha ta koshi daga haka ta saketa a cikin dakin ta fice tare da rufo dakin,daidai lokacin zahida ta shigo falon fuskar nan har yanzu a suntume,da sauri aminatu ta ja baya tana rufe bakinta saboda dariya dake shirin kufce mata,Dan a hakikanin gaskiya wannan abu ba karamin muni yasawa fuskar zahida ba.ko kallonta zahida bata yi ba ta haye upstairs, a ranta tana jin tamkar ta dauki ran aminatu ta huta. Aminatu kuwa ganin khalid yayi bacci yasa itama ta koma sama falon mus ab ta kwanta, ita sam ba ma bociyar yin baccin rana ba ce saboda gani take kamar a sara ce gara ta dauki kur'ani ta karanta ko tayi salatin annbi da sauran tasbihai,sai dai baccin yau ji take kamar an sata shi yasa tana kwanciya baccin ya dauketa. Kamar a cikin bacci kamar ido bude haka take jiyo sautin matar da Kuma kallonta dishi dishi a cikin idanunta,sosai take jin muryar matar a cikin kunnenta kamar haka. Aminatu me kike yi haka?wane irin shirme kike yi, da har yanzu baki fara binciken da zai taimaki Al umma da Kuma daukar fansa ba,haba aminatuwa ya kamata ki ajiye duk wani shirme ki tashi tsaye ki nemi hankali ta Karfi da yaji domin yin abinda ya kamata idan ba haka ba rayuwarki da ta Dan birninki har da ta kakarki duka suna cikin hadari,ban da sauran mutane da fansar rayuwarsu yake karkashin kulawarku, ki nemi dan birni, ki fara saninsa tun kafin su rigaki saninsa, sannan ki tabbatar da cewa kin nemi hanyar shiga dakin da yake bayan dakin Abby,da sauri aminatu ta ce,"wacece ke sannan kuma me zan yi a dakin idan na shiga kalan suce sata zan yi musu"murmushi matar da har yanzu bata ganin fuskarta tartar ta yi sannan,tace "idan kin shiga zaki ga abinda zaki yi kuma zaki samu haske akan babban aikin da yake gabanki"daga haka bat batar ta bace,farkawa aminatu ta yi jikinta duk jike da gumi, kalle kalle ta shiga yi ko zata ga matar dan ajikinta take ji tamkar ba mafarki ta yi ba a zahiri su kayi magana da matar,sai dai babu ita babu dalilinta, sosai aminatu taji zuciyarta ta karkata akan abinda matar take son ta yi da kuma tunanin baffanta da nasa sakon wanda take ganin tamkar duk sako daya ne suke bata, to wai ta ina zata fara neman dan birni ita da ba sanin sa ta yi ba kuma ba fita take yi ba bare ta gano shi?take zuciyarta ta bata amsa da cewa "to kin gwada ne bare ki samu ko kuma kina zaune zaizo ya same ki?. Kamar wadda aka yiwa allura zunbur ta mike tsaye tare da duban agogo taga karfe uku har da arba in. dan haka sai kawai ta wuce dakinta na falon mus ab,wanda ya kaita tun tana yarinya,toilet ta fada ta yi wanka tare da dauro alwala ta zo ta yi sallah daga nan ta canja kaya wanda suke nuna alamun fita zata yi,har da yar bag dinta ta riko a hannu,duk da cewa ba tsayawa ta yi gaban mirro ta tsara kwalliya ba amma tayi masifar kyau babu abinda jikinta ke fitarwa sai sassayan kamshinta da tuni ya gama kama komai nata, ko guri ta zauna idan ta tashi kamshinta zaka ji yana yi. Ba hill ta saka ba, Amma hakan bai hana ka jiyo karar sautin takalminta ba, zahida ce a hakimce a falon gabanta Dan karamin teburin cin abinci ne da kayan abinci akwaieda alama bata jima da gama cin lunch ba,sai hannunda da yake rike da waya ga kuma tv a kunne tana aiki, aminatu bata kulata ba dan tsoro take ji kar ta zauneta, dan haka sai ta wuce gun khalid, zama ta yi a gefansa kafin ta sunkuya daidai kunnensa ta yi masa rada,zai yi magana kenan kofar mai falon ta yi gefe alamun shigowa za a yi,tun kafin yayi sallama tirarensa da takunsa ya fallasa shi,gaba daya suka maida hankali kansa yana shigowa tankar wani saraki fuskar nan fes sai dai a tamke take babu fara a, da sauri khalid da aminatu suka hada ido kafin Kuma su hada hannuyensu ji kake raf karar sautin tafawa du kansu fuskarsu dauke da murmushi,khalid ne yayi saurin mikewa tare da rungume mus ab din daidai tsayinsa yana cewa "daddy na Dan halak barka da dawowa yanzu nake shirin sato wayar momyna na kiraka", da sauri zahida ta maida kallonta kan aminatu dan tabbas tasan abinda ta rada masa kenan,bata ce uffan TA maida kanta kan wayarta tana cu gaba da abinda take yi ba tare da ta dubi inda mus ab yake ba. Aminatu kuwa dake tasan abinda take so yayi mata,karyar da kai tayi kana cikin muryarta yar karama wadda ke dauke da salonta na shawaba ta ce"daddy sannu da zuwa"khalid ne yayi saurin tararta da cewa adda aminatu ba haka ake welcome ba baki ga yadda nayi ba,kema kizo ki rungume daddy" cak zahida ta tsaya da abinda take yi tare da saurin kallon aminatu,bata gama tunanin aminatu zata aikata ko bazata aikata ba sai tsintar aminatun tayi a kirjin mus ab tana wani juyin shawagaba har da dan hawayenta tana cewa, "daddy sannu da zuwa dan Allah ka shirya ka kaimu shan icream kullum muna gida kamar wasu Anne da basu da kafa"khalid ma ya amshe da cewa "ey mana daddy da baka dawo bama kiranka zamu yi kazo ka kaimu yau dai mu bude ido rabonmu da fita da kai fa tun adda na ss1". "Addar uwarka da ubanka shege dan iska asirtacce wallahi Khalid idan baka fita sabgar wannan me kama da Aljanar ba sai na saba maka ko kuma na dauke ka daga gidan naga da uban wa zata yi kiriniyar" Tasowa ta yi ta janye aminatu daga jikin mus ab din tana cewa,"matsa dan ubanki na daji wallahi dole ki rabu da dana dan ba kaki lalata min yaro tun bai san komai ba,shi dai da ban Isa da shu ba yaje yayi amma indai ina da hakki sai Allah ya saka min"daga haka ta wuce sama da sauri tana kokarin maida kwallar kishin da yake neman kasheta,jikin aminatu ne yayi sanyi ganin yadda zahidan ta yi, duk da cewa babu wani abu da tayi dan ran zahidar ya baci Amma taji tausayinta,dakakkiyar muryarsa ta ji yana cewa "give me ten minutes" Khalid da bai damu da abinda uwarsa ta yi ba yasa ihun murna yana cewa ye yau zamu fita da daddy zamu ji dadin mu"anan ne itama aminatu ta saki jiki suka ci agab da murnar zasu fita,sai dai wani bangaren na zuciyar aminatu cike yake da tunanin maganganun matar mafarki da Kuma aiyukan da suka Sara da tunanin ta inda zata fara su,ta Ina zata fahimci abinda suke nufi?sai kin sawa zuciyarki nutsuwa kin ajiye shirme, zuciyarta ta bata amsa daidai da abinda matar mafarki ta fada mata,har mus AB ya sauko am in natu Tana nan cikin zurfin tunani Wanda hakan yayi matukar bashi mamaki sai dai Babu alamun hakan a fuskarsa, let's go"ya fada yana wucewa Khalid da shima tuni ya cake cikin gayunsa ya kamo hannunta yana cewa "zo mu tafi daddy ya fito"wanda hakan ne ya sa ta ankara da kamshinsa da ya hade da nata ya bada wani yanayi me dadi. Har zata shiga baya Khalid ya janyo hannunta ya turata gaba,shi kuma ya shiga baya,duk yana kallonsu bai ce musu uffan ba,a hankali ya Kunna motar tare da yin ribas,tuni security ya bude wawakeken gate din su kawai yake jira su fita,a hankali mus ab ya cigaba da silala motar har suka fice daga gidan ya dauki hanya kan titin anguwar da kamar yau aka gama shi saboda kyansa da laushinsa. Tsawon mintuna goma motar shuru sai daga can Khalid ya fara leka waje yana surutu da aminatu wadda ta kasa tanka masa,hannun mus ab da ya dauka akan nata ne yasa ta Dan waigawa inda yake ta kallesa sai taga hankalinsa na Kan hanya,idanunta ta maida kan hannunsa da ya sarke da nata kafin ta yi magana, ta ji saukar muryarsa a kunnenta cikin tsitstsinka kalamansa kamar me koyan magana,da wata damuwa ne?"girgiza kanta ta yi tare da kwantar da shi jikin makarin kujerar tana lumshe idanunta a natse,can kuma ta bude da sauri kamar wadda aka mintsina tare da zubawa hanya ido tana kallon duk mutumin da yazo wucewa a kafa ko a mota ko mashinan da suke wucewa wai ko Allah yasa ta ganesa ta kamshinsa ko takunsa,Dan karamin bakinta ta tura da tuna cewa kamshinsa iri daya ne da na MUS'AB. dan haka ko ta gansa in dai MUS'AB na kusa da ita bazata gane ba. "Wa kike nema?"ya tambayeta tamkar bashi yayi maganar ba,tura baki ta kuma yi tana kara zura kanta ta window hadi da toshe hancinta dan wai ta daina jin kamshinsa da ya riga ya zauna a hancinta, Amma sai dai tamkar kara feso mata shi ake yi, dole ta koma ta zauna tana gunguni da kebe baki, a haka suka karaso wani hadadden wajen cin abinci. Tunda suka fito aminatu take baza ido tana addu'a Allah yasa na hadu da Dan birni, bata sani ba har maganar ta fito fili, sai ji tayi mus AB ya ce"waye dan birni"dan murguda bakinta ta yi tana farfara idanunta kana ta ce,baka San ni MATAR ƊAN BIRNI ba ce hasali ma saboda shi muka zo BIRNI gashi Kuma har yanzu ban gansa ba, Amma daga yanzu zan fara nemansa ba zan dakata ba har sai na gansa",dauke kai yayi tare da kama hannun khalid ba tare da ya kuma tanka mata ba. Zaman mintuna biyu su kayi aminatu ta fahimci kallon da wani saurayi ya cika ta da shi kamar zai cinyeta,a ranta Babu abinda take yi sai tsaki,sai Kuma ta yi wani tunani idan fa bata kula su ba zata gane Dan birni ba dan haka take ta fara tunanin hanyar da zata samu kusanci da wannan saurayin ta ji kamshin tirarensa kuma hakan ba zata yiwu ba dole sai mus ab baya gun,to yanzu ya zanyi?" Ta tambayi kanta,kafin ta samo amsa an yi Kiran mus ab a waya wanda hakan yasa shi fita daga wajen gaba daya dan da alama wayar tana da matukar muhimmanci.. Zahra✍🏽 500 only Account number 8064537048 Fatima yusha'u Adam opay [4/17, 7:33 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page36``* Kamar jira wannan saurayin yake mus ab ya tashi,sai gashi ya mike ya tashi daga gunsa ya dawo wajen su aminatu,tun daga tafiyarsa aminatu ta tabbatar cewa ba dan birninta ba ne,dan haka take ta hade fuska ko da ya karaso ba tare da ya nemi izininta ba ya zauna, sai wani kokkobarewa yake kallo daya za kayi masa kasan cewa irin yan bana bakwai din nan ne makaryata masu kayan opay da wayar opay,ta kalminsa khalid ya kalla da hularsa ya ji kamar yayi dariya saboda su kansu bai iya sa su ba,yana zama ya fara karya murya cikin salon iyayi yana yi yana wani kashe ido,sai kace wanda ya warke daga makanta,abin ba karamin dariya ya bwa aminatu da khalid ba amma sai suka kanne dan take aminatu ta fara lissafin yadda zata yi maganinsa,"yan mata me kyau me za a kawo muku ne?"take amiantu ta gyara zama sannan ta karbi menu din da aka kawo musu ta fara tuk abubuwa masu yawa da tsada kamar wadda zata bude gidan abinci,ba tare saurayin yasan abinda aminatu tabyi ba ya wani saki murmushu tare da duban Khalid ya ce abokina kai ma ka fada abinda kake so ko nawa ne zan biya"caraf amiantu ta kuma karbar menu din ta dinga tik wasu abinci ma bata taba jun ko sunansu ba,sai da ta gama sannan ta ya fito waeter din ta yi masa rada a kunne, saurayi sai yashe baki yake khalid kuwa dariyarsa neman kasa rikuwa take dan tuni ya ga abinda aminatu take shiryawa saurayi dan karya,aminatu kuwa ta dake sai murmushi takewa saurayi shi kjma.yana ta zuba yana lissafa mata kadarorin mahaifinsa da filaye da gidajen da yake dasu da guraren da ya je a kasashen duniya, kai zance dai barkatai ba sama ba kasa. Dake wajen babban guri ne dai wane da wane ne suke zuwa wajen shi yasa babu yawan mutane,kuma duk wanda suke wurin jikakku ne sun fi karfin a siya musu abinci , shi yasa aminatu ta radawa weter din ya rabawa almajiran da suke bakin wajen abincin da zai ishesu wannan saurayin zai biya. Har lokacin mus ab yana waje yana waya. Cikin kankanin lokaci aka cika gaban aminatu da kala kalan abinci da snacks da drink's,GA Kuma Wanda ake ta fita dashi ana rabawa almajiran dake harabar gun suna jira a fito da na zubarwa ko wani me tausayi ya zo ya basu sadaka ko abinci,tunda aka fara zubewa aminatu abinci a gabanta saurayin nan ya kame, tuni bakinsa ya mutu babu abinda yake sai zare ido cikinsa kuwa tuni ya shiga juyawa saboda tsananin tashin hankali, ba dai wannan abin duk shi zai biya ba?"aminatu da ta karance shi tsaf tuni ta yiwa weter inkiya, sai ko gashi ya taho hannunsa rike da lissafin kudaden da za a biya,yana zuwa ya mikawa saurayin da yake ta sharce gumi yana son tambayar aminatu fafa ta hanasa dan kar ya tambaya ba haka ba ne ta rainsa. Kallon farar takardar da ake mika masa yake ba tare da ya sa hannu ta karba ba,har sai da weter din ya Kuma cewa yallabai GA list din duk abinda aka ci aka sha",karba yayi da suari yana dubawa hannunsa har rawa yake yi, cikin tashin hankali ya yi wurgi da takardar tamkar wanda ya kama kunama, kafin cikin rawar baki ya ce"ku mahaukatan Ina ne yaushe muka ci wannan kudin?"aminatu ta yi zakal ta ce"au sorry ai jin kace babu damuwa shi yasa nace ya rabawa almajiran dake waje suma suci ai ka samu lada"a gidan ubanwa nace miki ina son lada ?" Saurayin ya fada yana mikewa tsaye tare da cire hular kansa da tuni ta jike da gumi kamar wanda aka wanke da ruwa,tsugunawa yayi ya tattare kafar wandansa yana cewa wallahi baki isa ba sai dai ki biya su kudinsu amma ni ab zan biya ba,idan nayi niyar kyautar sanda zan yi sani kika yi,bana son shihsshigi dan haka ba zan biya ba kinga tafiyata",da sauri ami.atu ta ce kai ku rikesa ya biya ku kudinku babu ruw ana"aiko tuni securities din wajen suka cafke saurayi yana shirin artawa, ganin bashi da mafita yasa ya fara rokonsu, dan Allah ku rufa min asiri aradun Allah bani da ko sisi rigar jikina ba ta opay ce kai komai na jikina opay ne dan ku yi hakuri". "Me yake faruwa a nan?" Mus ab da shigowarsa kenan yake tambayar securities din da suka cukuikuiye saurayin aminatu dan karya😃,Daya daga cikinsu ne ya sanar dashi abinda ke faruwa, sai ko saurayin ya juya tare da rike akafr mus ab yana cewa,yallabai kayi min rai wallhi tsautsayi ne ya shigo dani wajen nan dama ba abinda zan siya dan ko kudin ruwan riba bani dashi, tsautsayin zan hadu da aljana sunbuka ne ya kawo ne,dan me wannan aikin aradun Allah se aljana, ku taimaka ku raba ni da ita ku bata hakuri daga yau ba zan kara ba wlh kasuwa ma zan koma na ci gaba da dakona"kallin nan na nu dake ne mus ab yayiwa aminatu kafin ya karbi list din a hannun security ya duba,bai ce komai ba sai atm da ya mika musu, jiki na rawa suka karba suka cire kudin da suka kai kusan dubu dari biyu,daga nan ya sa kai ya fice,duk da halin fargabar hukuncin da zai yi mata sai da ta dungurewa saurayin kai sannan tabisu da gudu. Suna shiga mota Khalid ya fara bawa mus ab labarin saurayin yana yi gana dariya yana kwatanta yadda aminatu ta yi da yadda saurayin yake,shi dai bai tanka ba amma aminatu biyewa Khalid ta yi suka ci gaba da kwatanta maganar saurayin suna sheƙa dariya abinsu, a jikin wani katon store ya tsaya, hakan yasa suka fara murna dan da sun yi tunanin daga nan sai gida,fitowa suka yi a tare kamar gaske, sai dai yanayin takunsa yasha banban da nasu dole suka haƙura ya basu tazara, daidai da zasu shiga wajen Khalid ya ɗan marairaice fuska tare da hade hannunsa waje daya yana cewa"dan Allah adda aminatu kar ki kuma yin lefin da daddy zai tattaramu ya watsa a mota ya maida mu gida"harara ta watsa masa kafin ta ce"oh me ka mai dani ne?kana tunanin zan kuma yin abinda zai batawa daddy rai ne?to ka ma daina wannan tunanin dan har muje gida ba za a kuma jin kaina ba, yau dole na saki raina na ci banza har tsaraba zan yiwa makwabta kuma sai na kwashe rabin kayana na basu tunda yau zamu yi sabbi"ta karasa maganar tana sakin wani lafiyayyan murmushin da ya kara haska fuskarta,hannu suka hada suka tafa sannan suka ƙarasa shiga ciki,wanda shi har ya samu gu ya hakimce tare da kwantar da kansa jikin kujerar idanunsa a lumshe yana sauraron shigowar danjer aminatu da dan korenta Khalid. Kamar abin arziki suka.fara zagayawa suna daukar duk abinda zai musu amfani, daga kan suttura har zuwa kayan amfanin yau da kullum,suna tafiya wajen turaruka Khalid ya shiga diba da yawa kamar ba kudi za a sa a siya ba,zai kuma dauka ta rike hannunsa tana cewa "Khalid mu barsa haka kar mu yi almubazzaranci gwara musa daddy yayi kyauta ga mabukaci"Khalid ya ce"adda aminatu ai daddy yana da wani kudin da zai yi sadaka ba sai mun rage wani abu ba"um um Khalid nace maka babu kyau mu dauki iya abinda muka san zamu bukata daidai misali, a hakan ma idan munje gida sai mun cire zakka mu rabawa makota ko almajirai masu bukata ko?gyada kai Khalid yayi suna ci gaba da zagayawa suna daukar abu daidai da bukata kamar yadda aminatu ta umarcesa. Da gudu aminatu ta fito daga wani bangare tana fadin,inna lillahi wa innahu sulaimanu jama ku yi ta kanku ga dodannin duniyar sama nan"aiko kan kace me jama a sun fara yin takansu har da masu jefar da siyayyar da suka yi da masu karo da juna, kan kace me jama sun taru a bakin kofa wasu ta lipter dukkansu a razane, gashi har yanzu aminatu ba ta daina ihu da kururuwa tana zagaye duk inda tasan da ragowar mutum ba, kuma an kasa samun mutum daya da zai tambaye ta meye ko abinda ta gani,sai da ta fidda kowa daga tafkeken store din nan sannan ta tsaya cak tana makyarkyatar tsoro,hada ido su kayi da mus ab da yake zaune daga can inda suka barsa ya zuba mata ido fuskarsa fayau babu wata alama da zata nuna maka yanayin da yake ciki ko ya dauki lamarin, Khalid kuwa yana gefansa dan tun sanda yaji ihun aminatu ya arta ya dawo wajen daddynsa yana makyarkyatar tsoro. Daya daga cikin security ne ya karaso gaban aminatu yana cewa, a ina kika ga dodon muje ki nuna mana dan ga mutane can a waje duka kowa yana so ya dauki kayansa da ya zubar muje koma meye a fitar dashi"gaba ta yi tana nuna masa hanya kusfa kusfa har suka zo wajen , sannan ta ja ta tsaya, dubanta security yayi tare da cewa yana ina?"cikin rawar hannu ta nuna masa ƙatuwar tedys din da suke zube a wajen saboda bangarensu tazo,wani uban tsaki security yaja yana kallon aminatu a wani irin fusace tamkar zai kai mata duka,kafin ya juya ya koma bakin kofa yace kowa ya dawo yaga abin da take yiwa ihun kar su damu ba abin tsoro ba ne ko na cutarwa, a hankali suka dinga dawowa har sai da suka shigo gaba daya sannan ya tafi da su bangaren toys din ya nuna musu abinda aminatu ta gani ta razana,take mutane suka ayi kan aminatu suna kokarin kai mata duka mus ab ya janye ta suka fito cilli yayi da ita cikin mota Khalid ma fa kansa ya turasa sannan ya shiga ya figi motar tamkar zai tashi sama. A wannan karon gaba ɗayansu dif su kayi suna rarraba ido,aminatu kuwa yau tasan me kwatarta babu shi a duniyar nan, tsayawa suka ji ya kuma yi, suna ji ya fita amma babu wanda yayi gangancin bin bayansa,gani su kayi wata babbar mace ta fito daga katon shagon ɗinkin da yake cike da ma aikata ta ko wane ɓangare, cikin girmamawa ta gaida MUS'AB daga nan ya bude mata but don motar tasa yaranta suka dauki katiwar jakar da take shake da sitturun da basu san lokacin da ya saye su ba,dan ko wanda suka zazzaba basu bi ta kansu ba saboda gayyar da aminatu ta tara musu a store din,sai da a aka gama shiga da kayan sannan suka ga matar ta tsaya suna magana da mus ab, sai dai lokaci lokaci tana kallon aminatu da ta zuba musu ido kamar wanda take tunanin cinikinta ake yi. Amma fa yallabai dole sai ta shigo shago mun aunata saboda bamu taba yi mata ɗinki ba,bare mu san ko mai nata"dan jim MUS'AB ya yi kafin ya dan waiga inda su aminatu suka zura musu ido ita da Khalid sai da yayi musu kallon minti ɗaya sannan ya furzar da huci me zafi ta bakinsa yana duban gefen Hajiyar ya ce"shike nan zaku iya tafiya"karasawa ta yi gaban motar ta bude tare da kamo hannun aminatu da take binta da kallon rashin sani da tambaya,"idan kika kuskura ki ka yi wani abu anan zan hadiye ki ne da ranki kawai oya kuje a aunaki"abinda ya fada kenan ya koma jikin motar ya jingina yana mai sa idanunsa a kan duk motsin aminatun. Burkin da aminatu taja daga bakin shagon shine ya sa Hajiyar saurin kallonta,sai dai kafin ta samu damar tambayar ta dalilin tsayawar tuni aminatu ta yi zaman dirshen a gaban shagon tare da rafka tagumi hannu bibbiyu bakinta dauke da salati da innalillahi kafin kuma ta fashe da kuka tana cewa, "wallahi fitowar nan ta yau babu sa a cikinta dan gashi nan sai cin karo nake da bala u kala kala,idan ba bala I ba me zai kawo sangamemeiyar budurwa ta kafe a waje tsirara haihuwar uwarta, aradun Allah birni ba ta yi ba,kuma ba zan shiga wajen nan ba bare mu hadu mu babbake gaba dayanmu"da sauri Hajiyar ta kalli sassaken gunkin da suke tallan ɗinki da su cike da mamaki dan tunda aminatu ta fara shirmenta ta gane da abinda take,mamaki kuma ba na komai take ba sai na ganin macr har mace yar birni kyakkyawar bugawa a jarida tana magana irinna cikakkun yankauyen da basu taba sanin hanyar birni ba,zata yi magana aminatu ta yi saurin katse ta da cewa wallahi ko zaki haukace ko ki zama irin wannan budurwar ba zan shiga shagon nan ba aradun Allah ba zaku shafa min kashin kajiba,kiri kiri a dinga sabon Allah a......da sauri ta hadiye maganar ta saboda kamshin mus ab da hancinta ya shaƙo a daf da ita, wani irin kakkauran miyau ta hadiye tana raba manyan idanunta tsakanin hajiya da yar tsanonin da suke jere reras a bakin shagon,a hankali ta lallaba ta mike tsaye idanunta sun yi raurau ta mele bakin irin na shagwababbun yara gab take da fashewa da kuka,duban matar yayi a natse ba zaka taba cewa akwai wani abu na bacin rai ko sabaninsa a ransa ba,cikin tsitstsinka maganarsa ya ce"dole sai an yi gwajin nan ne?"yes yallabai dole sai an yi idan kuna son dinki ya fita daidai"jinjina kai yayi tare da dora idanunsa akan aminatu yana watsa mata wani azababban kallon da ya sa cikinta murdawa,babu shiri ta bi bayan matar aka aunata, lokacin da ta fito tuni har an sanyawa yar tsanonin kaya sun yi tsaf kai kace a jikin mutum aka sa kayan ,to sai lokacin aminatu ta fahimci cewa ba mutane bane yar tsanane,sai kuma ta fara murmushi tare da matsawa kusa da su zata shafa su karaf ta ji an figi hannunta da karfi, sanin ko waye yasa bata yi gardama ba ta bisa, sai dai tuni cikinta ya duri ruwan tsoro har wata kara yake yi. Yallabai mus ab a dai yi mana a hankali kar a karya mu 😃 Zahra✍🏽 [4/20, 4:07 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page37``* Da wani irin karfi ya figi motar tamkar zasu tashi sama,sai dai a yanayinsa ba za kaga hakan ba,basu kara tsayawa a ko ina ba sai gida, ita kanta aminatu ta shiga taitayinta dan a wannan karon daga ita har Khalid babu wanda ya kuma yin kwakwkwaran motsi bare yin wani abu me kama da laifi. A darare suka fito daga motar ko wannensu ya kama kansa,"waye zai dauka muku kayan"ya fada muryarsa a dake fuskar nan babu a lamun wasa a cikinta,da sauri suka juyo suka fara daukar kayan da dukkan su yafi karfinsu amma haka suka dinga kinkima suna shiga dasu yana tsaye yana kallonsu, bai matsa daga gun ba har sai da suka gama kwashe gaba daya sannan ya tasasu gaba suka shige ciki,suna kokarin wucewa daki ya buga musu tsawa "ku wuce muje sama"da sauri suka hade jikinsu waje daya kana suka kama hanyar da ya nuna musu aminatu tuni ta fara ruwan hawaye dan yau tasan me kwatarta hannun daddy babu shi tunda nana bata nan duk makiyanta ne a gidan dan haka ko kasheta zai yi babu me ceton ta sai Allah.. Suna shiga falonsa yasa su nil doun yace duka su rufe idanunsu su daga hannunsu sama,tunawa da azabar da ta taɓa sha a wancan karon yasa ta fashewa da kuka,yana ji yayi wucewarsa daki dan yasan babu wanda ya isa matsawa ba da izininsa, sosai aminatu ta fara tausayawa Khalid saboda shi yaro ne sannan kuma duka babu laifinsa a cikin abinda ya faru dan haka ta kallesa taga yadda yake ta tangadi cike da gajiya idanunsa duk sun yi laushi, amma yaron dake jarumi ne bai ko yi hawaye ba,ta ce"Khalid ta shi ka tafi Ni zan hada da nawa da naka nayi duk da cewa kai ba kayi kome ba"da sauri ya girgiza mata kai cike da tsoro yana cewa "a'a daddy zai yi fada kuma zai kara miki punishment"babu komai tashi kaje kawai"sai d ya ɗan yi jim kafin ya lallaɓa ya tashi yana dingisawa da haka ya bar falon ita kuma ta ci gaba da aikin duk da yadda gwiwoyinta suka sage suke neman kasa daukarta. Fitowa yayi tare da bata umarnin taje ta yi sallar magriba ta dawo ta ci gaba,har zai wuce sai kuma ya dakata yana kallon gefanta kafin ya dawo da dubansa kanta,kana ya ce"ina Khalid?"kayi hakuri ba laifinsa ba ne kuma shi yaro ne ba zai jure ba shi yasa nace ya tafi zan yi duka har nasa"a hankali ya lumshe idanunsa yana jin wani abu me kama da tausayi da kuma wani abu na musamman da bai gama tantance ko meye ba,daga nan kuma ya juya ya fita, a hankali ta tashi ta nufi dakinta ta shiga bathroom ta dauro alwala tazo ta tada salla bata tashi ba sai ta dora da karatunta har sai da aka yi Isha ta mike ta yi, bayan ta idar ta shafa addu'a,sai ta tattara sallayar da hijabin ta linke sannan ta fita falo ta ci gaba da aikin da ya sakata,tana yi tana gyangyadi a haka ya dawo ya sameta. A nutsensa ya zauna yana kallonta cikin wani irin yanayin da ya kasa fassarashi, abu daya yq sani shine baya iya jin haushinta baya iya fushi da ita, sannan kuma baya jin cewa laifinta ya kai a hukuntata,nuni yayi mata da ta tashi tsaye,girgiza mai kai ta yi hawaye na gudu akan kuncinta,lumshe idanunsa ya yi tare da kuma maida kansa jikin kujerar ya kwantar yana jin wani abu me kama da zafi akan zubar hawayennata,ganin yayi hakan sai ta yi tsammanin wani laifin ta kuma yi dan haka ta mike a hankali sai dai kuma.kafin ta gama daidaituwa kan kafafunta tuni ta yi luuuu zata fadi,cikin hanzarinsa da zafin namansa ya tarota ta fado jikinsa,ajiyar zuciya ta sauke saboda tuni ta ƙaddara zata sha kasa, kokarin tashi ta fara yi amma sai hakan ya gagara saboda yadda ya shigar da ita jikinsa sosai ya hana mata kwakwkwaran motsi sai na shaƙar numfashin da yake tafiya da kamshinsa tare da bugun zuciyarsa da take harbawa a hankali tamkar wanda ya shiga comer . Shi dinma na ta bugun zuciyar yake saurara da nasa da yake hadewa da natan, sai kuma sakon zuciyarsa da baya fahimtarsa a yanzu. Yanayin sauyin numfashinta da bugun zuciyarta ne ya fahimtar dashi cewa ta yi bacci, hannunsa yasa ya kuma zagayeta da wani irin shaukin da ya kasa tantance dalilinsa. Yau kwanan su abby biyu da zuwa abuja kuma tun da suka zo kullum sai sunyi sittin da sabbin customers dinsu da kusan dalilinsu ne yasa suka zo Abuja,a bangare guda kuma bincike ne zazzafa suke akan asibitin ABM da kuma barister duk da cewa sun gama da bangaren barister tunda sun san shi a fuska abinda kawai ya rage musu ya kawo musu kansa, kuma suna da tabbacin hakan zata faru ta hanyar wasikar da suka tura masa,dan haka basu da ji a wannan bangaren hankalinsu ya fara kwanciya ta bangaren barister dan sun san cewa ba zai taba gudunsu ba saboda tanadin manyan kudaden da suka yi masa idan kuma yaki yadda kai tsaye zasu maida shi ya zama manyan makudan kudade fiye da wanda yaki karba a hannunsu, wannan shine shirinsu akan br. A can asibiti kuwa hankalin halima ya fara tashi saboda yadda taga an fara zafafa bincike akan satar innawuro har ma hoton Hajara da mus'ab ya bayyana acikin c.c camara,sosai ta fara neman hanyar haduwa da mus'ab amma hakan ya faskara, karshe ma tunaninta tsayawa yayi saboda tsoron kar a gano ta acikin case din duk da cewa ta wani bangaren tana samun kwarin gwiwa akan cewa mus ab ba zai bari ba wani abu ya sameta ba. A can gida bangaren su aminatu kuwa,tunda ta tashi yau gaba daya babu nustuwa a tare da ita, saboda tunin da aka sake mata a daren juya akan binciken dakin abby wanda a iya saninta ko Nana bata cika gani tana shiga dakunan abby ba saboda hakan shine abu mafi muni da abby ya tsana shiga duk wani bangare da akasan yana mu'amala dashi a cikin gidan,shi yasa aminatu ta cika da fargaba gashi kuma cikin ranta kamar ana hura mata wuta akan son yin abinda baffanta yake so ta yi da wannan matar da bata san ko wacece ba,aiyanawa ta yi a ranta sai dare zata shiga tunda a lissafinta sai gobe ne zasu dawo dan haka har ta yi abinda zata yi ba tare da kowa ya sani ba. Zahida ce zaune gaban laptop dinta, ta zuba mata ido tana kallon daukar da aka turo mata yanzu ta Hajara da mus ab,wani irin zabura ta yi tare da buga teburin gabanta har sai da takardun da suke kai suka watse, me ya kawo daddyn Khalid nan?me ye hadinsa da wannan matar?tsam ta yi da ranta tana tuna fuskar hajara kamar a ranar ta ga gilmawarta acikin asibitin. Da sauri ta dauki kan waya ta yi wani dan danne danne kafin ta hadata da kunnenta,ba tare da ta jira komai ba ta fara magana,yanzu ina so a turo min ragowar daukar ranar na masu shiga da fita,ake wayar ta yi tana ci gaba da sunturi a cikin makeken office dinnata tana yi tana duba laptop din dake dire ian teburinta, karar shigowar sako ne yasa ta yi saurin komawa ta zauna tare da bude sakon videon da ya shigo. "What?"zahida ta fada tana nuna aminatu da camarar ta dauka suna shigowa harabar asibitin ita da Hajara, hannu tasa ta share zufar da take keto mata,kenan MUS'AB da AMINATU sun san wani abu akan sace innawuro?"ey lallai mana dole taga damuwar AMINATU kadan, me yasa mus ab ya biyewa AMINATU?ko dai ta sanar dashi wani abu akan sirrinsu ne tunda wannan abun da ya faru ya sa ta tabbatar da cewa AMINATU tasan wani abu akansu,ji tayi kanta yana daukar zafi dan haka sai kawai ta saka kiran iyayenta, suna dauka ba tare da ta jira cewarsu ba,ta ce "lallai daddys ku yi saurin baro abuja kome kuke yi ku bari ku dawo akwai ƙurar da ta tashi take neman cinye mu baki daya dan duk lamarin da ya haɗa da mus ab ba lamari ne na wasa ba,lamari ne da ake batun zaki ya bude bakinsa yana zaga daji dan neman me karar kwana"tana zuwa nan ta kashe wayar tare da kida kanta akan teburin tana tunanin ta ina zata fara kafin iyayennata su dawo,neman matar da suke tare ya kamata kisa a fara yi tun kafin wankin hula ya kai ku dare,zuciyarta ta bata amsa hakan yasa ta mike da sauri ta fice tana lalubo wayar danturkyi. Tunda halima taga fitowar zahida jikinta ya hau bari, dan a gabanta zahida ta yi kiran farko dakin cctv din, duk da cewa har yanzu babu video da ya nunata a ciki amma cike take da fargaba da tashin hankali,bata tunanin wannan matar da suka dau innawuro da ita dan tasan ba lallai ne su samota ba(anata tunanin fa)bata iya zama ba itama tatatraw ta yi ta bar asibitin bayan ta sanar dasu cewa bata jin dadi ne. A can Abuja kuwa cikin kankanin lokaci suka gama kome na tahowarsu, dukkansu zuciyarsu cike take da razani na jin cewa ta tabbata da mus ab cikin lamarin,amma sun yi kokarin boyewa saboda matansu kar su fahimci cewa everything is wrong with them,Dan haka suka yi kokarin nemowa kansu nutsuwar dole,a cikin wannan yanayin suka dauko hanyar dawowa Gombe, Zahida ta kasa samun wayar danturkyi duk hankalinta ya kuma tashi,babu abu mafi sata cikin tashin hankali irin idan ta tuna cewa duk musu ab ya gano irin kasuwancin da suke yi babu abinda zai hanasa rabuwa da ita wanda hakan yana daidai da zuwan numfashinta karshe,hakan yasa ta kuma rudewa ta shiga bulayin neman danturkyi a duk inda tasan suna zama,har wajen isha tana yawo, daidai lokacin kuma su abby suka kirata sun sauka,dan haka kai tsaye ta juya da motarta ta nufi filin jirgi dan daukosu. Tana faka motar a harabar wayarta ta shiga kuwa, har zata yi banza da kiran sai kuma idanunta suka hango mata sunan danturkyi yana yawo kan screen din wayar, cikin sauri ta dauka dan kuwa zahida a yani daya ta manta wacece ita saboda tashin hankali akan tunanin abu guda biyu da take matukar so da burin ci gaba da mulkarsu a rayuwarta suna shirin Kubce mata, wato kudi da MUS'AB. "Haba danturkyi ina ka shiga nake neman ka tamkar rai na kasa samunka?bata jira amsar sa ba ta ɗora masa da cewa,"kaje ka shiga WhatsApp ɗinka na turo maka da hoton wata mata ina so duk inda take a daren nan a nemo ta bana son ku kai safiya ba tare da matar nan a hannunku ba",angama ranki shi dade wannan farilla ne agareni cika aikin iyayen gidana ko da zaro hanjin kanin mahaifinane kuwa",ajiyar numfashi ta yi ta re da kashe wayar tana jin zuciyarta tamkar kara hargitsata ake yi, dan bata jin ta sauke koda kwayar zarrar rabin nauyin da yake cunkushe a kirjinta,dakyar ta samu ta danne kadan daga cikin yanayin damuwarta ta fita taro su abby. Hajiya zubaida ta ce ta dinga kallonta cike da son karantar yanayinta,ita ko Nana dama kusan a haka suke rayuwa da ita a gidan babu sakewa a fuskarta a tare da su shi yasa bata kawo cewa zahidar na cikin damuwa ba ne,su kuwa ubayen gayyar kowannensu da tasa zaunanniyar tashin hankalin da suke dannewa, haka suka dauki hanyar gida,duban lokaci Abby yayi yaga karfe tara saura dan haka ya dubi zahida dake ta tsala gudu saman titi cikin yanayin fitar hayyaci, sai da yayi dan gyaran murya sannan ya ce"dougter ina ga ki kaimu babban gida gaba ɗaya zuwa safiya idan muka huta sai mu wuce gida duba da yadda bamu sanar da kowa dawowarmu ba sannan dole yanzu zamu kuma fita office Dan gabatar da gundarin abin da ya dawo damu ba tare da mun shirya hakan ba"har Nana zata yi magana sai kuma ta fasa ta maida kanta gefe tana ci gaba da tunanin ahkinta da kuma abinda ya ke ta nukurkusarta akan gaba daya tafiyar tasu,dan itama tun maganar innawuro ta yi matukar sawa dukkan motsi su ido take kuma jin bata amince da duk wani motsinnasu ba a yanzu. Kasancewar motar babbar mota ce kamar ta family yasa duk ta ccunyesu, daddy yana gaba kusa da zahida yana duba sakonnin da suke ta shigo masa bai samu nutsuwar dubawa ba saboda halin da suke ciki,a cikin sakon har da na br fele Wanda yake sanar da daddyn cewa yazo yana gidansa yana jiran karasowarsu saboda izinin zuwan da suka bashi dan gagarumar matsalar da taso so musu yau din. A can kuma br fele ne zaune a falon da masu aiki suka shigo dashi yana zaman dakon karasowarsu, a daidai lokacin Hajara ta yi sallama hannunta dauke da ruwa da cup kanta a sunkuye tazo ta ajiye wa br fele da har yanzu kansa yake kan wayarsa,Hajara na juyawa wayarsa ta fara ringin daga wayar yayi tare da ficewa daga falon dan amsa wayar. Lokacin da danturkyi ya bude hoton Hajara a cake yake bai ganeta ba,sai da daya daga cikin yaransa suka shigo ya nuna masa tare da sanar musu aikin da zasu yi akanta,yaran me suna bazuka ya ɗan zabura yana murje idanunsa tare da cewa "kai oga wannan ba wannan matar da Alhaji Jamil ya bamu kwangilar bazarwa ba ce?"sai a lokacin suka lura suka kuma dubawa sosai suka ga fa ita dince,dan turƙyi ya ce "tofa an yanka ta tashi asiri dole ya tonu kuma a wannan karon ko zan rasa raina sai na bazar da matar nan ta bar numfashi na rantse da wanda ya busan rai". Suna zuwa gidan sauke su Nana kawai su kayi ba tare da ko fita daga motar sunyi ba suka juya suka bar gidan gaba daya su hudun,hoton Hajara zahida ta kunna musu tare da haska musu ita,bayan sun hau saman kwalta tare da cewa wannan ita ce aka gani tare da AMINATU da mus ab wanda hakan ke nuna i da cewa ta san abinda suke shiryawa shi yasa na bawa su danturkyi damar su nemo mana ita a daren nan"da sauri daddy ya shiga mirza idanunsa kafin cikin tashin hankali ya ce wannan ai sabuwar yar aikin da nake gaya muku na samu ce sabon kasuwanci"wani kallo abby yayi masa kafin cikin tunzura ya ce "amma dai garba kai wawa ne yanzu dan Allah me ye a idonka da ka kasa gane hoton matar da br ya turo maka taje wajensa da hujjoji har muka sa su danturkyi su kasheta". Cikin sauri. Zahida ta kuma duba hoton wanda sai a yanzu itama ta tuna inda ta san fuskar matar,tabbas ita ce matar da taao daga mata hankali da tona mata asiri a cikin asibiti mata me aljanu tabbas ita ce"wani wawan burki zahida ta ci tana mai dafe kanta, kafin ta dago da kanta da idanunta suka yi jawur tana cewa to me yasa bata mutu ba?"wannan tambayar su danturkyi za a yiwa ita"daddy ya fada yana mai daga wayarsa kira daya kuwa, danturkyi ya daga tashin farko da ban hakuri ya fara sannan ya dora da cin alwashin karo na biyu babu kuskure,kai tsaye daddy ya sanar dasu cewa suke tana cikin gidansa amma kar su kasheta a wannan karon dan suna da bukatar jin wani abu daga bakinta......nima a gidan zaki sauke Ni dan ba zan taba bari matar nan tasha ba"cewar daddy da yake jin zuciyarsa kamar zata yi bindiga, "Nima ki ajiye Ni a gidan in yaso sai kai Alhaji Kabir kuje gidan Garba gaba daya,ni kuma zan tsaya domin ankara da motsin AMINATU da MUS'AB" Abby suka fara ajiye wa a kofar gidan sannan suka wuce,ko security a fusace da bindigu suka leko gate din amma ga mamakinsu sai suka ga abby ne shi kadai ba mota ba driver ba Nana,cikin sauri suka fara yi masa barka da zuwa kafin su bude masa karamar kofa ya shige gidan. Amiantu na cikin falon abby tana canke canken dakin da ya kamata ta shiga, zuciyarta babu abinda take sai bugu, duk da cewa kuwa rana da tabbacin ba yau su abby zasu dawo ba,haka.kuma kowa.yayi bacci tunda lokacin karfe goma da sha daya ne na daren hatta da mus ab ya jima da kwanciya zahida ce dai bata tunanin ma tana gidan.ahi yasa kawai ta yi shahada ta shigo a wannan lokacin,daga karshe dai canki zankinta ya tsaya kan dakin da yake daga can lokon corridor din Dan haka cikin sanda ta nufi dakin tare da murdawa, ba tare da ta yi tunanin a bude yake ba kawai ta ji kofar ta bude tamkar wanda aka bude ta a lokacin.ba tare da ta teaya bata lokaci ba ta ahuga bude buden loka da guraren ajiya wanda ita kanta bata san ainihin abinda take nema ko take son daukar ba,idanunta ne suka tdaya kan wani katon littafi me kauri da tudu,cikin sauri ta dauki littafin tana dubawa sai kawai taji wasu takardu sun zubo daga tsakiyar littafin, ta tsugunna tana tattarawa kenan taji alamun taku yana tunkaro dakin, take cikinta yayi wata irin murdawa sai kawai ta tsaya cak tare da zubawa kofar dakin ido........✍🏽 [4/22, 3:05 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page38``* A kofar gidan daddy ya samu su ɗan turƙyi da shirin su na marasa imanin yan daba, ko wannen fuskar nan a shabune suna faman muzurai, daddy Bai tanka musu ba sai da suka shige gidan gaba dayansu, sannan bayan sun fito daga motar daddy ya tsaya da su Alhaji Kabir da zahida kuma cikin falon suna shiga, a nan suka samu br fele ya fito daga falon da yake ciki saboda jin shigowar motar su daddy, "yallabai me yake faruwa ne ?ina nan tun dazu ina jiran ku duk a dame nake saboda ina da tabbacin cewa kiran nan bana lafiya ba ne"br fele yayi maganar yana kallon kofar falon da zuge su daddyn zahida na shigowa shi da su dan turƙyi, Alhaji Kabir ɗinne ya bashu amsa da cewa br kai ma kasan ba lafiya ce zata sa mu dawowa yanzu ba tare da shiri ba,da farko dai ina sin tabbatar maka da cewa wannan matar me suna hajara bata mutu ba hasali ma ta yi badda kama ta. Shigo gidan nan da sunan me aiki"what"br fele ya faɗa yana baza idanunsa a falon tamkar wanda ke neman Hajara a gurin. Cikin ɗacin murya daddyn zahida ya ce"duk wannan bashi muke bukata ba yanzu ɗanturƙyi ku yi hanzarin kewaye gidan nan ta yadda ko kwaro bai isa fita ba sai kun gansa, sannan ku shiga ko ina na cikin gidan nan ku ɗauko min ita ku kai ta can gidan gyaran hali, kar ku kasheta saboda a yanzu rayuwarta muke bukata dan dole sai ta amsa mana tambayoyi,kafin ta tafi inda take gudun zuwa". "An gama oga"ɗan turƙyi ya faɗa yana kallon yaransa da suke jiran umarni sa,kallon da yayi musu yasa gaba daya su ka rabu mutum bibiyu suka ba zama cikin gidan wasu kuma suka yi waje dan tsare hanya saboda kar ta samu damar guduwa. Duk abinda suke fada a kunnen Hajara, hakan yasa ta juya da gudu ta shige dakinta, bata tsaya a nan ba ta kauna fadawa bathroom, tana shiga ta kalli window da tun farkon zuwanta ta fara aikin ciresa saboda shirin zuwan irin wannan rana,dan dama bata saki jiki ba ta tabbatar inda shu umarci da zaluncinsu zahida ya kai inda take zatonsa to tabbas sai sun ganota kuma ba zasu barta ba, shi yasa ta fara neman hanyar matsera,sai dai kuma kasancewar window ba irin karabici ba ne yasa har yau din bata gama ciresa ba,kuma bata da wata hanyar tserewa dole sai ta window sha dinma sai idan ta ciresa,sai dai kuma da alama wankin hula yana neman Kaita dare dan kuwa window zai dauke ta lokaci kafin ta samu nasarar ciresa gaba daya,wata kila kuma kafin hakan ta faru sun riga sun cimmata,tana cikin wannan halin kaikawo da fargabar ta tsunami muryoyinsu zahida na ce musu "ku shiga dakinta ku ɗauko ta,wani irin tsunkewar zuciya ta yi lokacin da ta ji takun sawayensu suna shigowa cikin dakin wanda sam ta manta bata rufe dakin ba saboda tsananin tashin hankali,sai dai ta yi kokarin rufe kofar bathroom din, Dan haka ta ci gaba da kokarin fincike window kafin Allah ya basu ikon karasowa bathroom din. "Bata cikin dakin nan"ta ji wata ƙatuwar murya ta fada da alama daya daga cikin yaran danturkyi ne yayi wannan maganar, Muryar zahida ta ji tana cewa ku duba bathroom tana ciki tunda an duba ko ina a gidan nan bata nan kuma ina da tabbacin cewa bata bar gidan nan ba saboda bata samu abinda take nema ba"hakan da zai da ta fada yasa suka tunkari bathroom din kai tsaye..... ***** Har abby ya dora hannunsa kan hadle ɗin kofar sai kuma ya dakata tare da ɗan sakin karamin tsaki, saboda tunawar da yayi key din dakin yana cikin ɗayan ɗakin nasa, hakan yasa ya juya ya nufi ɗakin dan ɗauko key ɗin. Da sauri AMINATU ta shiga tattare takardun wanda harda hotuna a cikinsu,ba tare da ta tsaya dubawa ba ta cusa su tsakiyar littafin,.kana ta nufi kofar da gudun sauri ta murda tare da fitowa,...daidai lokacin shina Abby ya fito daga dakinsa hannunsa rike da key din dakin da AMINATU ta fito daga ciki,wani irin bugawa ƙirjin AMINATU yayi idanunta tuni sun cika da wani irin yajin tashin hankalin da bata taba tsammatar akwai irinsa a duniya ba.da sauri abby ya dago kansa dake kan key din dake hannunsa tare da zubawa wajen da yaji alamun motsi ido,tabbas yaji motsi hakan yasa ya shiga karewa falon kallo har zuwa yar doguwar corridor da ta raba tsakanin falon da dakin, leƙe_leƙe ya shiga yi har ta kaisa ga daga abubuwa kamar bayan kofa bayan firinji har da su karkashin kujeru yake lekawa,yana fara daddaga labulayen falon aminatu dake boye cikin labulen da ya zagaye bangon da zai ya raba falon da dakin ta ji zuciyarta na neman fitowa waje,yayin da gumi ya jikata sharkaf kai me karatu zaka yi zaton ruwa aka sheka mata,idan kuwa ka saurara Zaka iya jin ƙarfin gudun bugawar zuciyarta. A hankali abby ya kai hannunsa kan labulen da AMINATU take cikinsa,yayin da bugun zuciyar AMINATU ke karuwa, hawaye tuni suka ɓalle mata, fitsarin tsoron da yake makale avmararta tuni ya fara zuba,bakinta kuwa tuni ya shiga karkarwa,ya Allah take fadi kawai a zuciyarta, zuciyar AMINATU na gab da yin bindiga wayar abby ta shiga ruri inda yayi saurin dauke hannunsa akan labulen da yake daf da janyesa,yana mai daga wayar da Muryar ta fita a amsa kuwa, Muryar zahida ce take ce masa "abby me ake ciki a nan din? Kaga daddyn Khalid din?kun yi magana? Abby Ina shegiyar aminatun? dan Allah abby ku hakura da abinda kuke nema wajen aminatu haka mu kawo karshen numfashinta a duniya abby rayuwar AMINATU barazana ce a cikin tamu rayuwar, idan muka kasheta dole musu ab zai hakura da duk wani abu da ya fara dan ita dan Allah Abby "iya abinda qminatu ta samu ji kenan ta fice daga falon da mugun gudu wanda yake tafiya tare da bugun zciyarta da take neman fashewa. Da sauri abby ya dawo da baya yana watsa idanunsa akan kofar falon,yayin da zahida take ta faman surutai baya fahimta saboda yanzu ta kuma tabbatar da cewa wani ya shigo bangarensa"kashe wayar yayi ba tare da ya tankawa zahida ba,kai tsaye ya nufi kofar falon tare da tabawa dan yaji ko a bude take, amma sai ya ji kofar gam babu alamun an bude ta an fita,to amma fa yaji karar taku kamar ma gudu ake yi,ganin yana bata lokaci wajen dogon nazari yasa ya koma dakin ya fara duba abubuwansa masu muhimmanci duk da cewa baya tunanin ko an shigo zaka a iya daukar wani abu a dakin, yana da tabbacin duk abinda aka taba ba zai tabu ba bare ya dauku,idanunsa ne suka tsaya kan littafin da yake tamkar mahaɗin numfashinsa wanda dama yasan ko da yaki da aljanun duniya basu isa iya daukar littafin ba saboda aikin da aka yi akansa,ajiyar zuciya ya sauke tare da jin duk wani kokontonsa ya kau, sai da ya kuma.shafa littafin yana murmushi sannan ya dauki abinda zai dauka a dakin ya fito... ****** Cikin tashin hankali Hajara ta ci gaba da sa duk wani karfinta wajen cire window saboda jin sun fara jijjige kofar bathroom ɗin kuma gab suke da ɓalle kofar saboda dukkan su suka taru akan kofar.hannunta ne ya taba kugunta take ta tuna da yar karamar wayarta da take a kashe sai lokaci lokaci take kunnata idan bukatar hakan ya taso,da sauri ta cirota tare da kunnawa,kai tsaye sunan mus ab ta lalubo duk da cewa bata da tabbacin zai taimaka mata tsakani da Allah, sai dai idan ta tuna abinda yayi akan innawuro sai taji kwarin gwiwa hakan ya sa ta shiga kiransa. ****** Fotowarsa daga bathroom kenan ya dauro alwala ya ga karamar wayarsa na kawo haske,bai yi jinkiri wajen dayawa ba,saboda shi dama baya kashe wayarsa kuma yana yin haka ne saboda masu neman taimakonsa,"nice wadda na baka wasika ranar nan a asibitin JGK a halin yanzu ina cikin masifa dan haka ina bukatar taimakonka,ina gidan surukanka, ka temaka min ta hanyar da ba zasu san kai ne ba saboda bana son jefa rayuwarka cikin hadari"a daidai nan ta samu damar cire window, dan haka ta katse wayar. Zubawa wayar ido MUS'AB yayi kafin kumq ya ɗan fesar da huci ta cikin bakinsa,a nutsensa ya lalubo wata nomber, kira daya aka daga,"ka duba na yi maka test"daga haka ya kashe wayar tare da nufar kebantaccen wajen yin ibadarsa ya tada iƙamar ƙiyamullali. Hajara na samun damar haurawa su kuma suka samu damar ɓalle kofar,ganin window a cire a kasa yasa suka gane cewa ta fice ta nan, dan haka da gudu suka fita dan mara mata baya,Hajara kuwa bata yi kokarin bin tafkekiyar kofar gate din gidan ba dan tasan zasu iya cimmata, kai tsaye ta bi doguwar katangar da ko barawo sai yayi da gaske zai iya haureta,amma dake abin daga Allah ne idan yayi niyar baka kariya ko a bakin kura kake sai ka tsere, sai ga Hajara ta haure doguwar kantanga duk da cewa ta ji ciwo sosai dan kuwa a dirgowar da ta yi sai da taji alamun karaya, bata tabbatar ba sai da ta kasa mikewa alojacin kuwa har sun danturkyi sun fito wajen gidan,"gata can ɗan turƙyi ya faɗa suna nufarta da gudu,sai dai kafin su karasa inda take wata bakar mota ta isa wajen kafin kiftawar ido sun nemi Hajara su ransa ko kyallin motar basa hangowa bare su yi tunanin zasu iya cimmata. Wani irin ihu ɗan turƙyi yayi irin na baƙi cikin anga samu anga rashi,da gudu suka koma gidan dan ɗauko mota su bisu,sai Alhaji Kabir ya hana su yana cewa "baza ku bisu ba kuna da tabbacin waye ya dauketa?ba kuyi tunanin ko MUS'AB ba ne kuke son gin wannan gangancin?"wani irin kuka me hade da ihu zahida ta sa tana cewa "ba zai yuwu ba ba mus ab ba ne,abba kayi min wannan bakin idan hakan ta kasance,zan gwammace mutuwa akan abinda zai biyo bayan rayuwata,daga Ni har ku,babu wanda zai sha,dole ne a nemo Hajara duk inda ta shiga saboda ta wajenta ne kawai za mu samu amsar tambayinmu,dan kun san cewa bibiyar daddyn Khalid ba abu ne me sauki a wajen ko wa nene ba,har gwara waccen yar iskar yar rigar amma itama in dai har bakinsu daya da shi bibiyarta zai zama abu me matukar wuya"ta karasa maganar tana jan wani irin numfashin tashin hankali, idanunta sun kada sun yi jajur kamar garwashin wuta,babu abinda take hangowa sai daukakarta karfinta kudinta da kuma mus ab dinta,yadda take jin tsoron rabuwa da waɗannan abubuwan bata tsoron mutuwa dan ita manta ta ma take a lissafinta. Duban su ɗan turqui daddyn zahida yayi tare da yi musu nuni da su tafi kawai shima br fele umarnin tafiya ya bashi akan cewa idan sun dan samu nustuwa zasu neme su,zama suka yi gaba daya su biyun suna kallon zahida da take yi musu dan karamin hauka,duban juna su kayi suna tuna wani abu shu dadde makamancin wannan wanda basa son yawan tuna shi ma a cikin rayuwarsu.. ****** Abby yana fitowa kai tsaye mota ya nufa ya shiga tare da tayar da ita,ya fice daga gidan bayan security sun bude masa kofar,mus ab dake tsaye can saman barendar dakinsa yana kallon fitar abbyn ya lumshe idanunsa tare da ɗan shafa kwantacciyar sumarsa,yana jin wani abu me nauyi a ransa, ta bangare guda tambayoyi ne suke ta shawagi saman kansa,wai mutanen na suke shiryawa a rayuwarsu?me yake shirin faruwa da gidansu? Ya a kayi AMINATU da innawuro suka shigo cikin labarin?me ye ainihin abinda iyayensu suke dauke dashi tun fil azal,tabbas akwai wani gingimemen al'amari a cikin duka rayuwarsu, lamarin yana bukatar lissafi da nutsuwa ya tabbatarwa da kansa hakan. Numfashi ya fesar ya kuma shaƙar wani , wand yake shakarsa da wani abu me nauyi game da bafulatanar riga matar amana matar katsaham,duk yau baisata a idanunsa ba,yana ji a fansa cewa bata cikin sababben yanayinta, dan ko a safiyar yau din Khalid ne kaɗai yagansa yana sabgoginsa shi da larai,shirin makaranta ma larai ce ta yi masa,barin wajen yayi tare da sanya silifas dinsa a kafafunsa da kamar ba a taka kasa da su,fita yayi cikin yanayinsa na daidaitacciyar nutsuwar da acikinta zaka gane zafin namansa,kai tsaye ya sauka daga upstairs din ,saboda yanayin nisan da bugun zuciyarsa yayi shi ya bashi tabbacin cewar bata dakinta na saman shi yasa kai tsaye ya nufi dakinsu na kasa ita da Khalid.. Tun lokacin da ta shigo dakin ta durƙushe a ƙasa take ta fitar numfashinta da suka rike a jejjere tamkar wadda take shirin shiɗewa,har yanzu a tsorace take kuma a rude take,dan komai na yau din sabo ne a wajenta ji take tamkar yau ne aka fara bude shafin rayuwarta saboda yau ne ta fara shiga wani hali na mutuwa ko rayuwa,yau ne ta fara sanin meye damuwa meye ai nahin tashin hankali,yau ne ta fara sanin kanta da kuma yaƙin da yake gabanta,yau ne ta tabbatar da cewa an bude mata babi na shafin kaddararta wadda ta fuskanta yau da wadda take shirin fuskanta a gaba,shin akwai wani tashin hankalin da yafi wanda ta fuskanta a yau kuwa?,idan akwai anya rayuwarta zata kai labari kuwa?ita kanta bata san tsawon lokacin da ta kai a wannan yanayin ba,domin ta kai ta kawo bata gane komai zuciyarta ta kasa dawowa daidai gana daya a rikice take a tsorace take ji take kamar yau aka haifota duniyar.... Bugun kofar da aka yi ne yasa ta miƙe a wani irin rikice tana kallon ƙofar. yayinda hannunta yake damƙe da littafin da take jinsa tamkar rayuwarta tana baza idonta da take jinsa tamkar ana zuba mata barkono,kara bugun da aka yi cikin nustuwa ne yasa ta yi tunanin boye littafin, hakan yasa ta nufi bayan gadonsu da gudu ta zura littafin tare da komawa gefe ta maƙure tana jiran tsammani,,,, "AMINATU Are U ok?"Muryar mus ab da take fitowa a tausashe ta ratsa kunnenta,. bata san lokacin da ta ganta a bakin kofar ba, tare da sa hannu ta bude ta gaba daya,bata kuma yi wata wata ba ta faɗa jikinsa tana mai sakin wani irin kuka da yake fitowa tun can kasan kasan zuciyarta,cikin wani irin yanayi yasa hannu biyu ta tallafeta tare da yi mata rumfa da fafafdan ƙirjinsa, idan kaga no shi a tsayen nan sai ka dauka shi daya ne saboda yadda aminatu ta lume tsaf cikin jikinsa tamkar zata koma cikinsa. Bai rarasheta ba domin ya tabbata dukkan abinda yasa AMINATU kuka irin haka bashi da misali wajen kwanta tan girmansa,yasan duk abinda ya sauya fuskar AMINATU daga funny face zuwa innocent face ba abu ne na wasa ba,yau aminatu ta zama aminatun da baffanta yake son ta zama,yau aminatu ta fara sanin kalubalen rayuwa daga cikin kaddarorinta da suka fara bayyana,"me yake damun aminatu me yasa aminatu kuka da mabayyaniyar damuwa irin haka?"ya fada a fili cikin deep voice dinsa da a yanzu ta kuma sauyawa saboda abubun da suke zuciyarsa da suka fara bayyana cikin muryarsa da kalaminsa.bata iya bashi amsa ba saboda har yanzu bata dawo cikin nutsuwarta ba,kallon Khalid da yake ta baccinsa hankali kwance yayi sannan ya kuma dawo da kallonsa kan tattausan bakin gashin ta da yake cike taf akan yana wani irin sheƙi,duk tsawon zamansa da ita bai taɓa ganin gashin kanta ba,saboda aminatu tun tana karama ba kasance ma abociyar son bayyana gashin ta ba, lokacin da ta kuma sanin kanta ta san cewa a addinin ma babu kyau barin gashi abude sai hakan ya kuma zama jiki a tare da ita, in dai har ba da kwakkwaran dalili ba haka kawai ba zaka ga gashin aminatu a waje ba ,bare kuma a kai ga batunnbayyana tsirainci wannan kuma tarbiyar innawuro ce kafin Nana ta zo daga baya ta dora tata,kamshin da gashin yake yi ya shaƙa yana kokarin kawar da abinda bai san meye ba daga zuciyarsa da gangar jikinsa. Ɗaukarta yayi cak ya juya ya bar dakin bayan ya rufowa Khalid dakin, kai tsaye upstairs ya nufa da ita, bai kuma tsaya a ko ina ba sai dakinsa inda yayi kokarin kwantar da ita akan gadon, sai dai kuma.yana dagowa yaji ta rikosa gaba daya tana mai kara sautin kukanta,wani irin numfashi ya fusga saboda rikon da AMINATU ta yi masa riko ne da ya ratsa duk wata jojiya da bargo dake cikin jikinsa, saboda yadda hannunta da yake da dumi ya sauka a kan fatarsa gefen cikinsa dake bude saboda budaddiyar pijamas din dake jikinsa,samun kansa yayi da wani irin jan yaji tamkar wani ya ci attarugu kafin ya dawo cikin wani irin slow ya hade fuskarsa da tata da ta yi jage gaje da hawaye ........... Zahra✍🏽 Payment is 500 only Account details 8064537048 Opay Fatima yushau adam [4/24, 8:35 AM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page39``* A hankali ya dora harshensa saman idanunta yana ɗauke hawayen cikin wani irin emotional peeling,kafin ya gangaro zuwa kan dan cutlips ɗinta da ya kuma yin jawur saboda tashin hankali da kuka,cikin yanayi na mutuwar jiki yasa harshensa saman lips dinta yana ɗan goga mata sanyin harshennasa akai,hakan da yayi kuwa ba karamin tasiri yayi wa gimbiya AMINATU ba,dan kuwa har ranta take jin cewa shan yawun mus ab zai kawo mata nutsuwa daga birkicewar da take neman yi daga lafiyayya zuwa juyayya mahaukaciyar mace,dan haka sai kawai ta runtse idanunta ta bude bakinta tare da saurin kama harshen mus ab da yake wasa dashi kan saman tattausan lebenta,shi kansa unexpected abun ya zo masa,a dan sanyaye take shan bakinsa sai dai har yanzu da damuwa acikin idanunta har da ragowar hawayen da basu gama zuba ba,saboda duk ta tuna baffanta da maganganunsa sai taji ta rikici gani take babu abinda zata iya bata da wannan karfin gashi har yanzu bata ga alamun zata ga dan birninta ba,anya kuwa labarin dan birni ba tatsuniya ba ce?ganin yadda ta kuma yin zurfi cikin tunani yasa mus ab fara kissing dinta da zafi_zafi duk a kokarinsa na dawo da ita mood dinta na asali,hanyoyin da ya cigaba da bi ne yasa ta fara juye_juye da kokarin dawowa hayyacinta,hannunta ta sa ta tokare kirjinsa da ya hade da nata tana cewa Ni kam ka daina wannan fa iskan.....cizon lebenta da yayi yasa tayi shiru tare da kwabe fuska leben a gaba tana shirin fashewa da kuka,a hankali ya kuma hade tazararsu fuskarsa na gogar tata sannan cikin deep voice dinsa da kalaman sa da wani lokacin idan ba nutsuwa kayi ba ba ma zaka fahimci abinda yake fada ba,ya ce"waye ya fara iskacin?"rufe idanunta ta yi kafin a hankali ta kuma.budesu akansa sai kuma ta bude baki cikin sanyin murya ta ce"bacci nake ji"bai yi magana ba baya ga turata cikin tsakiyar kirjinsa da ya kuma yi yana shafa bayanta da dogon gashinta dake matukar sha'awarsa saboda kyansa da tsaftarsa ga kuma ƙamshinsa na musamman da duk garin zahida bai tana jin makamancinsa a tare da ita ba. A hankali aminatu ta manna fuskarta kan fatar ƙirjinsa da take a bude, tana mai bude duka kofofin hancinta tana kuma shaƙar kamshinsa da yake kuma.rikita mata lissafi, harma ta fara tunanin anya ba shi ne dan birninta ba?"da wannan tunanin bacci me nauyi ya dauketa. Mus ab bai son tunaninsa yayi tsayi akan damuwar AMINATU dan yasan duk abinda yasa ta wannan damuwar yana da nasaba da iyayensa, wai meye hadin AMINATU da abby ne?tun farkon zuwanta ya fahimci hakan,,fuskarta ya shafa yana jin aransa cewa Akwai wani abu a duhu,da wannan tunanin shima bacci ya daukesa sai dai dukkansu kowa da abinda yake gani a cikin baccinnasa. A bangaren su abby kuwa dukkansu babu wanda ya samu ya runtsa, tunaninsu babu inda bai je ba akan wannan matsalar da suka fara fuskanta,dole suka lallaɓa zahida ta tafi bangarenta na gidan saboda suna son tattauna sirrin da su ukun kadai ya shafa. Dubansu Alhaji Garba yayi idanunsa duk sun zurma a iya wannan awannin da suka yi cikin damuwa,ya ce"Jamil anya kuwa ba bakin mutanen nan ne ya fara bin mu ba?anya kuwa ba tsinuwarsu da la antarsu ce ta fara tasiri akanmu ba?idan ba haka ba ta yaya lokaci daya abubuwa irin waɗannan zasu fara taba mu,na farko dai ga AMINATU duk da cewa mune muka shigo da ita cikin rayuwarmu amma tunda ta waɗo muka Gara ganin ba daidai ba cikin rayuwarmu da kasuwancinmu,sai kuma ga Hajara wadda muke kallonta a karamin alhaki,daga karshe da lalacewar ta yi yawa sai kuma ga mus ab wanda shi kadai gayyane,bana tunanin idan mus ab ya gano kasuwancin mu zai daga mana kafa duk da mun kasance iyayensa"Alhaji Kabir ya karbe da cewa sai yanzu na fahimci dalilin damuwar Jamil akan tunawa da wancan tsohon al amarin,tabbas idan muka bari mus ab ya fara bincike akanmu to allura zata tono garma kuma wallahi kashinmu ya bushe,kunga kenan hanasa cika burinsa na zama br be mana rana ba dan kuwa tsohon mikinsa ne zai motsa ya fanshe takaicinsa akanmu sabodn shi din dan baiwa ne mu sheda ne akan hakan"tunda suka fara magana abby ya kasa tankawa sai fuskarsa da yake ta faman shafawa, sai daga can ya daure ya daga kansa sama tare fara magana da cewa,jikina ya fara bani daya daga cikinsu ya fara bibiyata ko shi ko waccan shu'umar yarinyar me kama da aljanu"zuba masa ido su kayi gaba daya kafin cikin karfin hali Garba ya ce"ya akayi ka gane hakan?"kai tsaye ya bashi amsa da cewa "yau din nan yau naga abubuwan da suka saka Ni cikin kokwanto duk da cewa ban ga alamar shiga ko fitar wani ba, daga kan kofofi zuwa abubuwan da suke ajiye sai kuma na ga alama ta jin motsi da kuma ganin shaidar digon wani abu kamar ruwa kamar kuma fitsari sai da zan fito na taka ban kawo komai ba har sai da na ahiga mota na dau hanyar dawowa nan sannan tunanina da kissafina suka sauya daga kan tunanin babu wamda ya shiga bangarena"tabbas an shiga"cewar Alhaji Kabir yana mikewa tsaye hannayensa goye a bayansa, sannan ya dora da cewa "ke nan wannan shine lokacin da ƙarfan kafa ya bamu na komawa gare sa?". Alhaji Garba ne ya karbe da cewa "tabbas wannan shine lokacin da yayi mana misali dashi kuma tun dazu da zahida take wannan haukan na shiga wannan nazarin kenan tunaninmu yazo daya da kai Kabir?" Hannu abby ya dora sai duka suka dora nasu akan nasa tare da runtse idanuwansu ko wannensu da abinda yake faɗa take kasan wajen ya fara budewa suna yin kasa a hankali a hankali har suka nutse cikin ƙasan gurin, ya koma ya shafe tamkar babu halittar da ta taɓa tsayawa a wajen. Kana kallonsa gaka mahaukaci tuburan,saboda yanayin sutturar dake jikinsa, dattijo ne wanda a ƙalla zai kai shekara sittin da ɗoriya, a zaune yake gefen wani katon kwalbati dan ba dan kayan jikinsa da yanayin dattin da yake tare da shi ba za a iya kiransa da me hankali,baya un baya um'un sai ido da yake bin mutane dashi, AMINATU ce tazo wucewa ta wajen har ta wuce sai ta dawo ta tsaya a kansa tana yi masa magana,sai ga wata mata tsohuwa tukuf har da sanda a hannunta ta tsaya gefen aminatu tana cewa "baya magana tun tsawon lokacin da muka sansa a matsayin mahaukaci"daga haka matar ta tafi ta bar aminatu tsaye tana kallon mutumin da shima kallonta ya ke yi,juyawa ta yi zata tafi ga mamakinta sai ta ji mutumin yana cewa ko da kin tafi ina fata zaki dawo saboda ni, ko da kina nesa da inda nake ina fata ALLAH ya kawo ki inda nake ,duk inda kike ina fata ALLAH yasa miki tunani da son taimakona kizo ki nemeni a duk inda nake a fadin duniyar nan,amma dai yanzu ki tafi domin shirin dawowa gareni domin ki fidda Ni halin da nake ciki dan ina jin cewa kece wadda Allah ya tiro dan ki zama sanadin kubuta,idan kin shirya zuwa temakona kizo garin k........jansa da wasu mutane su kayi shi ne ya hansa karasa mata sunan garin,da gudu aminatu ta busu tana cewa ku barsa ya fada min ku sakesa ku daina dukansa ku barsa ya fada min dena hango ƙurar mutanen da ta yi ne ya sa ta zubewa a wajen tana wani irin kuka tana fadin "ku barsa ya fada min ku dena dukansa dan Allah ku rabu dashi,.ku barsa ya fada min. ku barsa ya fada min.kubarsa ya fada min........ Kamar a cikin mafarki yaji kukan aminatu tana dukansa tana fadin "ku barsa ya fada min ku dena dukansa"abinda take ta fada kenan tana kuka sosai. Riketa yayi sosai yana tofa mata addu'a dan ya tabbatar firgicin mafarki ne,da kyar ya samu ta daina kuka da sambatun ta yi luf ajikinsa tana maida numfashi kamar wadda ta yi gudun ceton rai. Damuwar da ta ga yana ciki ne yasa ta yin shuru amma ba wai dan ta yi baccin ba,saboda mafarkin da ta yi ya tsaya mata tamkar yadda lamarin baffanta ya tsaya mata a rai, sosai fuskar mutumin ya tsaya mata a rai, dan ko yanzu ta gansa tsaf zata ganesa, luf ta kuma yi a jikinsa tana jin saukar bugun zuciyarsa da yake tafiya a nutse,shin da me zata fara ne?bata jin zata iya mantawa da al amarin mutumin nan domin kuwa bata barsa a mazaunin mafarki kawai ba,tana ji a jikinta cewa akwai wannan mutumin kuma tasan yana nan yana jiranta kamar yadda ya fada,ji ta yi zuciyarta ta kuma yin wani irin rauni idanunta suka kuma cika da kwalla tausayin mutumin yana neman hanata sukuni, ji take kamar ba ita ce ta jiyan nan da take ta zuba shaƙiyanci a store da wajen cin abinci ba,ji take kamar ba aminatun da take cikin walwala da farin ciki ba aminatun da bata san meye damuwa ba,aminatun da bata san meye nauyin zuciya ba,ashe bata sani ba aminatu bata gama kammala ba ne,lokacin mafarin shafin kaddararta bai yi ba ne,sai yanzu lokaci yayi, lokaci ɗaya a rana ɗaya dare ɗaya kaddararta ta juya sabanin farinciki wadda bata da tabbacin iya yaushe Ubangiji ya diba mata na kammaluwar babin kaddarar da jarrabawar rayuwarta,iya ƙarshen rayuwarta ne ko kuma Ubangiji zai kawo lokacin yankewarta kafin zuwan numfashinta na ƙarshe?"bata da wannan amsar hakan yasa nauyin kirjinta ya ƙaru,tuni kukanta ya kuma karuwa saboda komai sabo take jinsa gata me kananun shekaru bata jin zata iya dauka,to amma shi fa Ubangiji babu ruwansa da girmanka ko kankantarka idan yaso jarrabarka ze jarrabeka ne duk ta inda yaso a lokacin da yaso ya kuma yanke maka a lokacin da yaso idan be so ba kuma ka kare rayuwarka cikin jarrabawa mafi muni da kalubalen rayuwa iri iri,ko kuma ya jarrabeka ta bangaren da idan ba ka kasance me ilmi ba ba zaka taba cewa rayuwarta ka ma jarrabawa ba ce,domin zai baka lafiya kudi ilmi iyaye mata yaya miji kai gaba daya zaka ga rayuwarka na tafiya daidai tamkar kaine ka tsara abarka,sai dai kuma ita rayuwa me kyau ko akasin haka gaba dayanta jarrabawa ce, Allah ya bamu iko cinye jarrabawar rayuwarmu. Sam babu bacci a cikin idanunta ko da ta rufe idanunta mutanen nan ga da uku take gani ko wannensu na dora a hanyar bukatarsa,baffanta da wannan matar da bata san ko fuskarta ba bare ta gane ta santa ko bata santa ba, sai kuma mutum me suffar mahaukaci,bazata iya bacci ba dan haka a hankali ta zamewa daga jikinsa tare da sauka kasan kafin ta mike nufi bathroom,a ranta tana tuna nasihar malam wadda a lokacin da yake mata hankalinta ma baya kansa saboda bata fahimtar komai akan abinda yake fada din domin bata taɓa ta imanin zata riski kanta acikin makamancin yanayin da yake magana a kai ba. "AMINATU bana so naga kina wasa idan muna karatu saboda ke marainiya ce samun ilimiki shine zai taimakeki duniya da lahira wannan karatun da muke a cikinsa zaki gane yadda zaki fuskanci rayuwarki domin ita rayuwa tana zuwa da kalubale iri iri, idannkika samu ilmin jare kanki to duk a yanayin da rayuwa tazo miki za karbeta hannu bibbiyu saboda kin tanadi makaminki a hannunk"to Ni Malam wace irin rayuwa ce zata zo min nan gaba da har kake irin wannan maganar?"a lokacin malam dariya yayi kafin ya dora da cewa aminatu ai ita rayuwa gaba daya jarrabawa ce sai dai kowa da irin yadda tasa take zuwan masa,ina gaya miki wannan ne saboda gaba duk da cewa bana miki fatan shiga wani hali sai dan ita nasiha da ilmi ba sai ka zo wajen ba ya kamata a dinga tuna maka da su saboda zata yi amfani ko ga waninka ne"to malam me ye jarrabar Nan ne kuma kaine zaka yi min ita?"girgiza kai yayi tare da cewa bani zan miki ba Ubangiji da ya halicci rayuwarki ya halicceki ne tare da jarrabawarki tun kafin kizo duniya Ubangiji ya tsara miki rayuwa tare da kaddarorinki wadda itace jarrabawar da nake fada miki,to ko da zaki kasance cikin rayuwar nan guda biyu wato jarrabawa me kyau ko akasinta,ki kasance me godiya ga Ubangiji ki kasance me kusantarsa ta hanyar ambatonsa sannan ki rike istigfar da talatin Annabi ki yi yakini da duk bukatarki a wajen Ubangiji saboda shi salati maganin komai ne kuma ba a kebance wata bukata ance ita kadai salati yake magani ba, a'a shi salati komai ne haka istigfar neman kusanci ne, idan kin shiga damuwa kinji lissafi ki ya kwace tashi ki gayawa Allah a lokacin da ya fi buƙatar rokon bayinsa yake amsa addu'a ba tare da hijabi ba,nasan wata rana ko a yanayin farinciki kike za ki tunani kuma zakiin addu'a saboda na dora ki a kan hanyar nasara mikakkiya""...... Sosai take kuka tare da tada ikama tana jin wani rin imani na tsarga mata,tana jin kamar daga ita sai Ubangijinta ne a duniyar, take ta kadaice Ubangiji daya ta kuma yi yakini ta fuskance shi da bukatun da ita bata sansu ba amma tasan shi ne mafi sanin komai, saboda shine makaginta masanin gaibu dan haka ta yi imani zai ji kukanta,saboda tsananin miƙa wuya bata jin komai sai kiran Ubangijinta shi yasa har mus AB ya jeru da ita bata sani ba. Shima din ba bacci yayi ba duk abinda aminatu take.yana jinta yana sauraronta,a ransa yaji cewa damuwarsa dan haka shi dinma ba bukatar baccinsa a wannan lokacin.Allah Ubangijia ya bamu ikon cinye dukkan jarrabawar rayuwarmu ka kara mana kusanci da shugaba masoyinka da babu kamarsa a duniya da lahira Annabi Muhammad s.a.w, Allah ka amsa addu'ar bayinsa ka gafarta mana zunubanmu ba dan halinmu ba ***** A daidai wannan lokacin da nagartattun bayi suka mikawa Ubangiji dukkan lamuransu domin sun san idan yayi riko da hannayensu babu wanda ya isa ya kama domin ganin bayansu,a lokacin ne kuma wanda suka juya masa baya suke ganin waninsa zai iya ije musu lamarinsu su kayi gurfane agaban waninsa,(wa iya zubillah). Abby daddy Abba,mutanen da suka nutse cikin kasa tamkar an shafe bakinsu a duniya sune gurfane gaban wani yamutsetstsen tsoho da ko ƙashi babu ajikinsa,tabbas ba dan tsananin ƙarfin iko na Ubangiji ba to da tabbas tsohonnan ba zai iya koda motsi ba saboda yadda yayi yaushi fata ce kawai take buga zamaninta a jikinsa, Yunƙurin tashi yayi daga kwancen da yake tamkar wani jiƙaƙƙen tsumma yasa suka kuma ƙankan da kansu,ga tsananin mamaki na yana tashi wata irin guguwa ta shiga kadawa a cikin kogon har wajen kogon,yayin da bishiyu suka shiga rangaji tamkar wanda zasu fado daga jikin reshinansu namun daji da tsuntsaye kuwa tuni suka fara yin takansu iblisan aljanu kuwa take suka fara haniniyar farinciki saboda sun san lokacinsu yazo, gaba daya kogon ya turnuke da wani rin ɓakin hayaki ko tafin hannunka baka isa gani ba,take wani irin gurnanin zaki ya fara tashi a cikin kogon da haniniyarsa, kafin kuma lokaci daya hayakin ya washe sai wani rin jan haske wanda a cikinsa na gano wani turmushshen zaki bakiƙirin idanunsa kuwa sune suke bada wannan hasken jan, abinda zai baka tsananin mamaki babu ɗaya daga cikin mutanen nan uku da ya razana, har yanzu suna nan durƙushe agaban wannan yamusheshshen tsohon arnen bokan wanda a yanzu ya rikiɗe ya koma baƙin zaki me jajayen idanuwan da yake bawa kogon haske.......... Zahra... [4/25, 6:45 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page40``* Bude bakinsa yayi zai yi magana sai ga wani irin ɓakin hayaki yana fitowa daga bakin me shege wari, amma duk da haka babu wanda ya damu a cikinsu, Karar sautin maganarsa kadai abin razanarwa ne da ace da me imani a gun tabbas zai iya sumewa saboda jin sautin maganarsa. "Kunzo akan lokaci da ace kun bari se bayan wani lokaci to da babu abinda zan iya yi muku,jamilu ka yi sake tabbas ka yi sake kaima Garba kayi sake,dukkan ku masu kuskure ne Kabiru ne kawai bai yi wani abu ba a cikinku,amma ku da kanku kune kuka jawo matsala cikin tafiyarku,me yasa kuka haka?"ya tambaye su yana kallonsu da siffarsa ta zaki da idanunsa masu hasken ja,"abby ne yayi Magana cikin ƙankan da kai"ayi mana afuwa hakan ya faru ne ta sanadin sharaxin da ka bamu na nisantarka tsawon wannan lokacin"cikin wata irin gigitacciyar tsawa tamkar saukar aradu ya ce"to yanzu me ya dawo daku?"gaba dayan su suka.hada baki wajen cewa,saboda lokacin yayi daidai da lokacin da ka kwatanta mana na dawowarmu gareka"girgiza kai yayi ransa a matukar ɓace ya ce Kum yi kuskure ba wannan lokacin na misalta muku na dawowa ba,lokacin tuni ya riga ya shude,sai dai hakan ba yana nufin zan ƙi taimaka muku ba ne tunda kuna da sauran dama" Daga haka ya yi wata girgiza ya koma suffarsa ta ya musheshshen tsoho sannan ya shige wani waje dake can ƙuryar kogon, ya jima kafin ya fito hannunsa rike da wani jan ƙoko yana zuwa ya miƙa musu ƙoƙon yana cewa da farko dai dole sai mun fara dauko wancan littafin da AMINATU ta dauke a dakinka idan ba haka ba babu wani abu da zan iya yi muku saboda ruhinku da ruhin mutanen da kuka sha jininsu da duk wani tarihi na baya da ya shafi rayuwarku yana cikin wancan littafin kuma karanta shi shine makullin bude masifun rayuwarku da mu ka sa a ciki muka kulle"a razane suke kallon juna kafin cikin madaukakin mamaki ,abby ya ce idan aminatu ta dauki littafi shi kuma wanda na gani a dakin fa meye?ya akayi ta shiga bangarena da yake da matukar tsaro?babban abin mamakin ya aka yi ta iya daukar littafin a hannunta bayan kai da kanka ka sanar damu cewa idan ba daya daga cikinmu ba babu me iya daga littafin nan a duniya?"wata irin muguwar dariya sunduƙi ya shiga ɓaɓɓakawa babu ji babu gani kai baka yi tunanin zai dakata da dariyar ba sai kuma lokaci daya tamkar an dauke nefa yayi ɗif idanunsa sun koma na zaki sai wani rin duhu da ya mamayesu,cikin tsawa ya ce "ku kalli idanuna"take duk suka zuba masa ido tsawon sakanni hamsin sannan ya basu umarnin janyewa, ya dora da cewa me kuka gani a cikin idona?" Babu ko mai sai duhu"suka hada baki wajen bashi amsa,dariya ya kuma sheƙewa da ita kana ya ce,to Nima abinda na gani kenan dan haka bani da amsar tambayarka,lokacin da na baku littafin nan Ni nasan cewa babu abinda ya isa taba shi ko ɗaga shi, sai kuma yanzu ga shi an samu wadda ta daga shi daga jinsin mata, sannan littafin da ka gani shima bashi ba ne an sauya shi ne domin janye hankalinka Ni kaina sai da nayi da gaske wajen fahimtar bashi din ba ne, wannan dalilinne yasa na shiga kogon duba amma abinda kuka gani a idona nima shi na gani wato banga dalilin da yasa ta iya dauka ba ban kuma ga ta yadda ta shiga dakin ba,banga kuma ta yadda kayi aka sauya littafin da irinsa ba,abu daya ne ya bayyana a cikin duhun shine fuskarta, dan haka zaku zauna anan na tsawon kwana uku zan yi aiki tare da ku dan dawo da littafin amma muddin hakan bata yiwu ba to sai dai kaje kayi mata ta karfi ka karɓa littafin sannan ka tabbatar bata fara karanta ko wane shafi ba duk da cewa duk shafin da ta karanta zata dakata akansa ne har sai ta warware matsalar shafin Farko sannan zata kuma bude wani shafin dan haka sai ku daura damara"daga haka ya ɓace ɓat a cikin kogon ya barsu cikin tashin hankali da rabuwar tunani,duk da cewa sun yadda da sunduƙi amma suna cikin tashin hankalin abinda ya fada,tabbas aminatu ta karanta littafin nan shike nan ta bude makullin masifun rayuwarsu, komai da suka aikata akan mahaifinta se ta gani a ciki ,kai hatta da sirrin da suka binne a junansu sai aminatu ta karanto shi..... ****** Washe gari da safe zahida da ta farka bata ga iyayenta ba,sai kawai ta shirya ta wuce gidan Anita,duk cewa har yanzu bata ji zata iya bude mata cikinta ba,amma dai tasan idan ta je ɗin zata samu nutsuwa da wasu shawarwarin daga gare ta. .... Aminatu kuwa lafiya kalau ta tashi duk da cewa ba wani bacci ta yi me yawa ba,dan basu kwanta ba har sai da su kayi sallar asuba daga ita har mus ab din,tana zaune a falonsa ya fito cikin shirinsa na office, kallo daya ta yi masa ta dauke kanta,shima kallonnata yake saboda ganin har yanzu jikinta a sanyaye yake gaba daya aminatu ta sauya lokaci daya abinda bai taba tunani ba ke nan anan kusa,so yake kawai yaga mood dinta ya dawo , a nutse ya zauna gefenta har kafadarsu na gugar juna,matsawa ta yi tana dan tura bakinta sai dai bata ce komai ba,a hankali ya kai yatsunsa saitin idonta kamar zai tsokane idon,aiko da sauri ta zabura tare da juyowa ta fuskanceshi fuskarta a kwaɓe alamun kiris take jita ta fashe da kuka,dage girarsa daya yayi tare da yi mata maganar bebaye wai meye na kukan, kawar da fuskarta ta yi tana tuna fuskar mahaukacin nan wanda duk wani motsinta tunaninsa ke karuwa a ranta, sosai ya fahimci yanayinta, yana so ya rarrasheta yasa ta ta yi farinciki sai dai bai san ta ina zai fara ba, a hankali ya lumshe idanunsa tare da kamo hannunta daya ya ɗora a kan ƙirjinsa, sai kawai ta bude idanuna sosai tana kallon fuskarsa da gashin idanunsa da su kayiwa idanun rumfar saboda lumshesu da yayi ta bangare guda kuma tana sauraron bugun zuciyarsa da yake bugawa akan tafin hannunta. "Daddy"ta kirasa cikin wata irin raunanniyar murya da har sai da ta sa ya bude idanunsa akanta,"me yake damuna wai?wacece ni?me ye a cikin rayuwata?me yasa girmana ya fara da haka?me yasa nake jin na samu sauyin rayuwa tun daga jiya?me ya sa nake jin cewa farincikina da walwalata ba zasu dawo ba?me yasa nake jin kamar an rataya min igiya me dauke da girman dala da gauran dutse, ji nake tamkar ina dauke da wani babban nauyin da in ban sauke saba zan iya mutuwa"ta karasa maganar wasu hawaye na gudu saman kumatunta.hannunta ya janyo tare da mannata a jikinsa yana jin yanayin yadda tempuriture dinta ke sauyawa kamar wadda zazzaɓi zai rufe,dago fuskarta yayi yana kallon idonta da suke ta hawaye kafin a hankali ya sanya harshensa da yayi sanyi ga wani kamshin da bakinsa ke fitarwa ya shiga lashe hawayen da suke kwanciya a tattausan kumatunta, sai da ya shanye su tas sannan ya hade fuskarsa da tata yana kallon cikin idanuna da ta kasa bude su ta kalli nasa idanun,magana ya fara yi cikin tsinkakkun kalamansa da basa fita dai-dai, ya ce"ba ko wani irin nauyi ne kike ji ba sai nauyin igiyar aure"yadda yake maganar labbansa na taba nata labban haka furicin nasa yake dukan zuciyarta,ci gaba yayi da cewa "AMINATU MATAR ƊAN BIRNI Aminatun baffanta Yusuf Aminatun innawuro Aminatu kawar bintalo da halimatu Aminatu rigimammiyar dadda ,Aminatu me leƙen dan birni a cikin bukka duk da taurkun nata kuma gashi har ya tafi bata taɓa ganinsa ba"shuru yayi da alama dai yayi abinda bai saba da yi ba,hakan yasa ya yi shiru yana maida numfashi tare da ci gaba da lalubo abinda ya kamata ya fada mata dan samar mata da nutsuwa wanda kuma zai sa ta fahimci abinda yake son fahimtar da ita....zai yi magana kenan wayarsa ta fara kawo haske da wani silet kida me taken momyna wanda hakan dole yasa ya yi shuru tare da daga wayar Nana. Aminatu kuwa babu abinda zuciyarta take yi sai bugu,duk ina daddy ya San mutanen nan ko dai innawuro ce ta fada masa?anya kuwa daddy zai zauna innawuro ta bashi wannan labarin wanda duk yawancinsu shirmenta ne da ta tafka na kuruciya,zuba masa ido ta ci gaba da yi yana waya da Nana da take sanar dashi ta dawo gidan,"Nana ta dawo" ya fada mata yana kashe wayar,ganin yana kokarin janyeta daga jikinsa ya muke yasa ta yi saurin kanƙamesa tana girgiza kanta a kirjinsa sai dai ta kasa cewa komai,duk da cewa tambayoyine makil a bakinta wanda take son yi masa,ya gane dimuwar da ta shiga dan haka bai saurareta ba ya mike gaba daya da ita a jikinsa, sai da taga sun nufi hanyar fita ta dawo.hayyacinta tare da saurin sauka daga jikinsa tana mai girgiza masa kai alamun dai bazata fita ba,zuba mata ido yayi yana kallon tsoro karara a cikin idanunta,wato ke nan akwai abinda ya hanata zuwa wajen Khalid tun tashinta?ey no wonder yaga Aminatu taki sauka ashe da abinda take tsoro,cikin nutsuwa da komawa ainihin mus abb dinsa ya kama hannunta tare da kallon tsakiyar idanunta fuskarsa babu wasa kana cikin deep voice dinsa ya ce"gaya min wa ye kike tsoro?me ya same ki jiya?ko zahida ce?da sauri ta girgiza kanta fuskarta tuni ta koma kalar tausayi,to gaya min Anne ce?nan ma girgiza masa kai tayi,cikin yanayin fushi da yar tsawa yace "to waye ne kike tsoro fada min ko na saba miki anan". Ganin kamar zai kai mata duka ne yasa ta dora hannunta saman kanta tana kare fuskarta tare da kokarin shanye kukan da yake son kwace mata fuskarta tana bayyana firgici da tsoron da take ciki,ganin yadda ta tsorata yasa ya ɗan sassauta, ba tare da ya ce komai ba kuma ya juya ya fice, tsugunawa ta yi a gun tare da sakin kuka me dauke da ma'anonin da ita kanta bazata iya fassarasu ko fahimtarsu ba,sai da ta yi me isarta sannan ta miƙe ta koma ɗakinsa dan bata jin zata iya sauka kasa ta haɗa ido da abby,saboda gani take kamar yana kallonta zai gane ita ce ta shigar masa daki,fadawa ta yi saman gadon tana yamutsa shimfidar dake kai tamkar ita ce ta yi mata laifi,wani ɗan ƙaramin littafi ta ji ta kama da hannunta, shuru ta yi tana rike da littafin ba tare da ta dago ta ga wane iri ba ne. A hankali ta dago kanta da ke cikin shimfidar gadon da ta cusashi tare da dawo da hannunta dake dauke da dan littafin saitin fuskarta ta yadda zata iya ganinsa sosai,zubawa littafin ido wanda yake dauke da kwalliyar zaiba, kamar zata ajiye sai kuma ta fasa tana daga kwancen rugingine ta bude littafin tare da fara karanta shafin Farko da aka rubuta da manyan baƙi. KOMAI YANA DA SANADI KUMA DUK ABINDA UBANGIJI YAYI YANA DA MANUFARSA, ALLAH YA KADDARA ZAN AURI AMINATU YUSUF SHI YASA YAYI SANADIN ZUWA NA RUGAR MALAM YUSUF........... MAFARIN AL AMARIN......Tafiya ce ta samesa zuwa rugagen Fulani dan yin wani obxabation da ya danganci aikinsa,Nana kawai ya sanarwa inda ya tafi amma daga zahida har abby basu san ina mus ab ya je ba,dake su ma harkar neman kudinsu ita ce a gabansu shi yasa sam basu damu da sanin ba,shi kadai ya ɗauki hanyar rugagen cikin hilux dinsa bayan ya tanadi duk abinda ya san zai bukata duk da cewa ba wani jimawa zai yi ba. Sai da ya ziyarci rugage uku kafin ya isa rigar malam YUSUF wadda ita kuma ta karshe daga nan gida zai juya,tabbas musu ab zai iya cewa duk rugagen da yaje babu rigar da ya samu karɓuwa aka gwada masa karamci sama da rigar malam YUSUF,sosai yayi mamakin karancin mutumin duk da cewa kuwa akwance yake magashiyan cikin cutar da kullum ba a sa ran zai farka da rai,amma a haka bawan Allah nan ya dinga nan nan da mus ab yasa aka kaisa bukka ta musamman wadda mus ab yayi mamakinta saboda babu abinda babu a ciki na zamani har da fanka da sauran abubuwa na bukatun yau da kullum,shi yasa mus ab yaji dadin zama a garin fiye da duk wata riga da ya zauna,sun yi sabo da malam YUSUF sosai duk da cewa mus ab ba ma abocin hira ba ne amma haka nan yake zama da malam YUSUF sabida ya fahimci Malam Yusuf din yana jin dadin hakan dan har dan zama ya kanyi sabanin kafin zuwan mus ab din da ko ruwa sai an tayar dashi an bashi. Yawancin hirarsu da malam Yusuf din hirar tilon yarshi ce me suna AMINATU,ta haka ne mus ab ya fahimci tsananin son da malam YUSUF ke yiwa Aminatu,bayan sin kuma har da tausayi wanda a lokacin mus ab yana tunanin ko dan malam YUSUF din yaga yana gargarar mutuwa ne,sai daga baya kuma ya fahimci cewa ba haka bane akwai wani boyayyan dalilinsa,mus ab bai tana ganin Aminatu ba amma kaf halin Aminatu ya gama saninsa a bakin baffanta a lokacin yana tunanin Aminatu bazata wuce shekara shida zuwa bakwai ba,kaf rashin jin Aminatu sai da ya sanshi a bakin baffanta. Wata ranar Alhamis ne ya kammala abinda ya kawo shi, dan haka yake sanarwa da baffan cewa zai koma gida washe gari juma kenan,baffan ya danyi tari sannan ya ce "idan ka tashi tafiya zamu yi wata magana da kai"daga haka baffan bai kuma cewa komai ba ,to shi din ma ba gwanin magana ba ne dan haka ya tafi nakwancinsa ba tare da zuciyarsa ta raya masa abinda baffan ke shirin aikatawa ba. Washe gari mus ab bai fito da wuri ba sai wajen karfe sha biyu na rana,dan haka a dan gaggauce ya karasa bukkar malam YUSUF,inda ya samesa tare da mahaifiyarsa me suna innawuro,ganin suna magana da innawuro yasa mus ab ya fasa shiga bukkar ya koma da baya ba tare da ya bari sun Gandhi ba,shi din na bai ga fuskar innawuro ba,bai. Koma bukkar ba har sai da ya tabbatar sun kammala maganar da suke saboda ya fahimci maganar tana da muhimmanci tunda har yazo bakin bukkar amma basu ankara dashi ba,yana shiga baffa Yusuf ya saki dan murmushin dake nuni da jin dadin ganin mus ab da yayi,dan da farko jin shuru mus ab din bai zo ba har ya karaya a tunaninsa ko ya yi tafiyarsa ne ba tare da yazo sun yi sallama ba, Abinda ya biyo bayan gaisuwar da mus ab yayiwa baffa ne ya matukar girgiza shi da dimuwar da tunda yake bai taba shigar makamanciyar ta ba,duk yadda mus ab ya kai ga iya boye labarin fuskarsa a cikin zuciyarsa a wannan ranar abun faskara yayi ,domin malam YUSUF yazo masa da bukatar da bai taba zaton zaizo masa da ita ba sannan ya kuma haɗawa da dora masa nauyin da baya jin zai samu salama a rayuwarsa sai ranar da ya sauke shi idan ma ya karba din ke nan,matukar karamci da kauna da yadda da Malam Yusuf yayiwa mus ab yasa yaji ba zai iya sarayar da bujatarsa ba, mu a ab ji ya di ga yi jamar mahaufinsa ne a gabansa yake rokinsa akan ya taimakeshi ya amsa bujatrsa domin ta hakanne kadai zai kubutar da aminatu da ga sharrin azzaluman mutanan can. Malam Yusuf ya ci gaba da cewa mus abu ka daure ka yi min wannan alfarmar ka auri Aminatu saboda aurenka da Aminatu shi kadai ne hanyar kariya gareta, wallahi mus abu na yarda muddin ka zama kariya ga Aminatu na amince ka sake ta ka zama uba a gareta, amma dai yanzu aurenta nake so kayi dan Allah yarona,amana ce zan baka kan amana ga yata nan aminatu marainiyar Allah bata uwa sannan uban bashi da tabbas din kasancewa da ita, amana ta biyu kuma mahaifiyata innawuro sai kuma nauyin dukiyar aminatu da girmanta da zan rataya a wuyanka, sai dai ina rokon yafiyarka domin na dora maka nauyin da muddin wasu mutane suka gane hakan to rayuwarka na cikin hatsari,shin musu abu ka yarda wannan nauyin da nake shirin dora maka?"kai tsaye mus ab ya samu aknsa da amsawa domin sai yanzu ya san cewa AMINATU marainiya ce sai yanzu ne kuma ya gaskata hasashen da yake na cewa akwai dalilin da yasa baffanta yake mata wannan tsananin son da tausayin. Mus abu yaga tsananin farin ciki a tare da baffa wanda har sai da mus ab ya dinga jin wani iri a ransa da yadda yake sa masa albarka tana masa godiya da addu'a masu matukar dadi, Ana idar da sallar juma a aka daura auren mus ab da aminatu baffa sani Kani ga innawuro shine wakilin aminatu baffa Yusuf kuwa shine ya zama wakilin mus ab,mus ab da kansa ya bada sadakin aminatu, daga nan baffa Yusuf ya nemi da a kira aminatu su tafi, sai anan mus ba ya kuma yin magana ya nemi da baffa yayi hakuri yaje gida ya sanar da iyayensa idan yaso sai su taho baki daya su tafi da aminatun,baffa ya amince da wannan sai dai kuma kullin silallan gold din da ya haɗe su da wasu takardu na kadarori ya ce mus ab din ya fara tafiya dasu domin zamansu anan kusa dashi hadari ne, babu yadda muka AB ya iya bai so ba amma ba zai iya musu da baffa ba dan haka ya tattara ya tafi dasu ba tare da sun hadu ko sau daya da aminatu ba, Baffa wuro ma sai da mus ab ya tafi. Sannan ya dawo shi yasa bai sanshi ba a fuska. **** Ɗora littafin ta yi a saman fuskarta hawayen tuni suka jika littafin sharkaf,take ta ji komai ya na dawo mata tamkar wanda aka saita memoriin kanta....... [4/26, 6:13 PM] yushauadamfatima: Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page41``* Sosai abubuwan da suka faru a dai-dai wannan lokacin suka dinga dawo mata. Duk lokacin da ta shiga wajen baffa sai taji wani irin kamshi wanda yawan shakarsa da take yi yasa har ta haddace kamshin a hancinta,a iya tunaninta a lokacin babu irin wannan kamshin a duniya dan haka ta sa masa ƙamshin ƴan aljanna,haka kuma so daya ta taɓa jin takunsa lokacin da take shanya a bayan bukkar baffa, shi yasa ta rike sautin takunsa wanda take ganin sun isheta makami wajen nemansa da ganesa.kamar yadda baffan bashi da abun fada a wajen mus ab sai ita,haka a wajenta bashi da abun fada sai ɗan birni dan alokacin baya fadin sunansa shine yasa masa dan birni,baffanta ne ya sa mata soyayyar dan birni da sha'awar zuwa birni amma ba tare da kowa ba sai ɗan birni. Bayan an daura aurenta da mus ab ne kenan baffan yake kiranta da matar dan birni, runtse idanunta ta yi tana kallon lokacin a cikin idanunta tamkar a talabijin, Tana kallon lokacin da baffanta ya kirasu ita da innawuro yana gargarar mutuwa babu abinda yake nanata musu illa su ci gaba da zama a nan saboda yasan tabbas wata rana dan birni zaizo nemansu, a cikin dare baffa Yusuf ya ce ga garinku nan, duk da kuruciya dale samun aminatu amma taji zafi da ciwon mutuwar baffanta dan har sai da innawuro ta fara hada mata da tofi sannan ta dangana. Tun daga lokacin ne kuma rayuwarsu ta fara yawo basa wannan ruga basa wannan ruga basa wannan ruga,saboda hari da ake kawo musu a duk RUGAR da suka zauna, baffa wuro shine ya zama komai nasu, daga karshe dai zamansu ya mika a rigar ardon gari, daga nan ne kuma ya tattara su ya kawo nan. Kenan mus ab yasan ita ce AMINATUnsa?No wonder yake mata abubuwa irin na mata da miji,ashe shi yasa itama bata iya dakatar dashi akan wasu abubuwa da yake mata?me yasa bai koma nemansu ba kamar yadda baffanta ya fada musu?ta yaya akai ya ganeta? Ko dai shine yasa baffa wuro ya kawo su nan?to amma ai lokacin da suka zo alamu sun nuna cewa mus ab bai san komai akan zuwansu gidan ba,wai me yake faruwa ne ? Wannan wace irin hargitsatstsiyar rayuwace mara kai meye baffanta yake boye mata?me ye asalinta ? Su waye suka kashe baffanta ? Menene baffanta yake so ta gano? Zunbur ta mike tsaye tana yan dube dube,bafa a nan kika ajiye littafin ba"zuciyarta ta fada mata,domin ta ji a ranta duk abinda take son sani yana cikin wannan littafin,da wani irin sauri ta fita daga dakin kai tsaye ta sauko kasan, ko mai yinsa take a.hanzarce kamar wata zauntacciya,kacibus suka yi da Nana wanda hakan yasa ta mugun razana tare da hade jikinta waje daya,zuba mata ido Nana ta yi cike da mamakin sauyin da ta gani a tare da aminatun dan kuwa koda aminatu bata nuna mata ba kallo daya ya isheta fahimtar cewa wannan aminatun dake gabanta ba aminatun ta ce ta kwanakin baya ba. "AMINATU lafiyarki kuwa?me ya same ki?Nana ta fada tana janyo ta jikinta,ajiyar zuciya aminatu ta sauke tana jinta tamkar ajikin mus ab,kasa cewa Nana komai ta yi, dan ita kanta bata san me yasa take boye abinda yake faruwa da ita ba,haka nan take ji a ranta ya zama tamkar sirrin da ya kamata ta boyesa a yanzu,kama hannunta Nana ta yi suka zauna a kan kujera, sannan ta dago da kan aminatun tana kallon idanunta da su ka yi haske alamun dai sunci kuka, "aminatu baki bani amsar tambayata ba,shin wani abu ya same ki ne ko wani ya miki wani abu?girgiza kai aminatu tayi tare da cewa Nana innawuro nake son gani dan Allah ki kaini gunta na ganta"shine abinda ya saki kuka da damuwa?"nana ta tambayeta zuciyarta cike ds wani wasi akan aminatun,jinjina kai kawai aminatun tayi tana mai kawar da fuskarta dan gujewa kallon rashin gamsuwar amsar da ta bawa nanan a idanunta,ba dan nanan ta gamsu ba ta rabu da ita sai dai ta gaya mata dole ganin innawuro sai ta bari mus'ab ya dawo, saboda ita bata da ikon kira mata innawuro dan itama shi da kansa yake kira mata ita, saboda baya son ana yawan kiran innawuro saboda dalilin da ya barwa kansa sani, aminatu bata ce komai ba tunda dama ba wai damuwar rashin innawuron ce ke damunta ba, tunda tasan innawuro tana cikin aminci da kulawa ta musamman. Duk a ranar aminatu ta kasa sakewa duk taji motsin fita ko shiga sai hankalinta ya tashi,saboda ji tayi bata da wani abu da take gudun gani a yanzu sama da Abby. A bangaren Nana kuwa ita ma din hakuri take da juriya na danne damuwarta a matsayinta Na uwa ,amma rashin jin wayar abby da rashin sanin ina suka je me suke ciki?ya hanata sukuni,saboda wayar da suka yi da hajiya zubaida ya tabbatar mata da cewa suma yadda abby bai waiwayeta ba suma gare su haka ne,ita damuwarta ba ta kome ba ce sai ta fahimtar da ta yi cewa su abby din akwai abinda suke boyewa ko suke aikatawa,baran ma idan ta haɗa da batun abinda suka so yiwa innawuro da abinda ya faru daga jiya zuwa yau ,duk sai ta ji ta cikin shakka da zargin su abby din da aikata wani mummunan abu, ga kuma rashin zahida wanda hakan yake nufin suna tare da iyayennata kenan, dan haka p cikin rashin sukuni ta wuni a gidan. Ko da aka tashi su Khalid daga makaranta kai tsaye suhaimance ta zo ta daukesa kamar yadda mus ab ya bata umarni,dan baya son yaran ya fahimci damuwar da aminatu take ciki,yasan dole shima zai damu daga karshe ya cikata da tambayoyi, wanda a ransa.yake.jin cewa tsaf aminatun zata iya sanarwa da Khalid abinda su bazata iya sanar dasu ba, dan haka ya zabi nesanta su da juna na wasu yan kwanaki. ****** Ba tare da sallama ba zahida ta fada dakin Anita wadda take kwance tunda ciki tana duba wasu takardu ga kuma waya a kunnenta tana yi,cikin sauri Anita ta tashi zaune tare da saurin tura wasu daga cikin takardun da take dubawa can bayan gadon, jikinta.da yanayinta yana nuna rashin gaskiya da kuma tashin hankalin da zuwan bazatan zahidar ya haifar mata,tsayawa zahida ta yi tana kallonta na yan sakonni kafin kuma ta nufi kujerar hutu ta dakin ta kwanta tana maida numfashi ba tare da ta kuma kallon anitar ba,dan taga alamun anitar ta tsorata da shigowarta,sai da ta samu wasu yan mintuna kafin ta kauda shirin nasu da cewa,Anita meye haka kike yi nazo wajenki dan ki taimakawa zuciyata ta samu salama amma kin wani firgita kina kallo na,da kin san kina jin tsoron kike zaune a gida ke daya?wata boyayyar ajiyar zuciya Anita ta sauke tana mai kokarin dawo da hayyacinta, cikin dabara kuma tana hade kan takardun da ta baza dama tuni wayar da take yi ta mutu. ******* Fada sosai ake da wani dattijon bafulatani wajen bin layin ganin likita,acewarsa ya riga wanda aka kira ya shiga dan haka dole shi ne zai shiga idan ba haka ba kuwa babu uban wanda zai kara wucewa ta gabansa ba tare da ya sauke masa sandar dake hannunsa ba,ganin abu ya ki ci yaƙi cinyewa yasa dole security ɗin gurin suka yi kokarin fitar da wannan dattijon,ganin abinda suke kokarin yi masa yasa ya shammacrsu ya fada dakin ganin likita da gudu yana cewa, "aradun Allah yau sai naga likita ya duba yaga abinda yake damuna acikina ko da zaku kasheni kuwa"har securitys din sun sa hannu zasu daukesa sai likitan ya dakatar dasu tare da basu umarnin fita daga office ɗin. Suna fita likitan ya nunawa dattijon waje ya zauna,zama yayi yana cewa na gode likita"ya sunanka?likitan ya tambayesa yana karbar Katin dake hannunsa,sunana baffa wuro?me yake damunka?likita ya kuma tambayar mutumin da sai yanzu na gane shi saboda tsomalewa da ramar da yayi kamar ba tsoka a jikinsa,baffa wuro ya gyara zamansa yana cewa,"likita yau tsawon shekaru ina fama da lalurar da na kasa gane kanta,duk abinda na mallaka,ya kare akan neman lafiya a wajen likitocin gargajiya,sai da komai ya kare sannan na yi tunanin zuwa asibiti,asibitin da naje na farko ban yadda da abinda suka fada min ba shi yasa na taho wannan saboda tabbacin da na samu akansa kuma nasan zaku fada min tsakani da Allah tunda ku ba dan kudi kuke aikinku ba"jinjina kai likitan yayi tare da cewa "asibitin da kaje na farko me suka ce maka?takardar scanning din da aka bashi ya zato yana cewa "cewa su kayi wai ƙodar da aka cire min ce ban tsaya an yi treatment din wajen ba shi yasa ciwon da yake wajen ya harbi daya ƙodar"kai me yasa baka yarda ba?likitan ya kuma jefa masa tambaya,baffa wuro ya ce,saboda Ni ban san akan me suke magana ba,Ni ban taba kwanciya a asibiti ba ma balle har a cire min koda,ko koda zata yi tsalle ne ta fita ba tare da na sani ba?"girgiza kai likitan yayi tare da yin rubutu a jikin katin baffa wuron sannan ya muka masa yana cewa kaje lab a sake maka wani scanning din Dan mu tabbatar da abinda yake damunka"karba baffan wuri yayi ya fita yana surutu da tsinwa wancan asibitin wai har da cewa sai anyi masa aiki gagarumi idan ba ayi nasara ba sai dai a sake masa wata ƙodar,kaji shegu ku gani a kanku". "Anita so nake ki raka ni gun boko me maganin idonka idona"cewar zahida tana kallon Anita wadda jin abinda zahidar ta faɗa yasa ta yi wata irin zabura har da dage kirjinta,cikin mamaki zahidar ta ce"meye hakan meye damuwarki da zuwana wajen ko da kwai wata matsala ne?"girgiza kai Anitan ta yi tana ɗan share gumin da ya you a kan goshinta,kafin dakyar ta samu ta daidai ta kanta tana cewa"ba haka ba ne zahida gani nai ga abinda ya faru wancan zuwan bai zama alheri ba kuma ban taba zaton zaki ce mu kuma komawa ba ,shi yasa kika ga na zabura"to idan kin dauka ki ajiye dan kuwa zan koma kuma a yau cikin wannan rana kuma tare da ke" zahida ta fada tana komawa cikin kujerar da kwanciya fuskar nan Tata tamkar an yaba kashi saboda cushewa da rashin fara a,cikin rashin kuzari Anita ta ce"to yanzu akan me zaki je?"kai tsaye zahida ta bata amsa da cewa "akan musu ab zanje, dan ba zan taba bari mus ab ya gano wani abu akaina ba tare da na samu gurbin da ba zai taba iya rabuwa dani ba a zuciyarsa,Anita dole ne na mallake musu ab kafin ya san sirrina dan ina da tabbacin idan ya san ko Ni wacece bayan sakina da zai yi har kasheni zai iya yi". "Saboda me kike fadar haka?meye dake da har kike wannan tunanin?Anita ta tambayeta cike da zumudin samun damar jin wani abu daga cikin sirrin zahidar,sai dai kuma bata samu amsar zahida yadda take so ba,dan kuwa mikewa zahidar ta yi tana cewa muke kar dare yayi mana saboda bani da lokaci "hankalin Anita ne ya dawo jikinta cikin sauri ta dauki wayarta jikinta na rawa ta ce muje waje gani nan zuwa bari na dan yi fresh up"daga haka ta fada bathroom hannunta rike da wayarta,fita waje zahidar ta yi tana cewa ki yi sauri karki ɓata min lokaci bana cikin mood din da zan iya daukar wata damuwar yanzu wadda nake ciki ma ta isheni". Anita na shiga bathroom ta danna kiran wata nomber,jim kadan aka daga,bata tsaya sauraron abinda yake fada ba,ta dora da cewa "yallabai na shiga Uku zahida na shirin gano komai akaina,yanzu ya zamu yi a ina zamu sake nemo bokan karya"shuru ta yi tana sauraronsa kafin ta kuma cewa,"ok shike nan na nutsu oga,yanzu zamu tafi wajen dan haka kayi kokarin ganin ya riga mu zuwa ayi duk shirin da ya kamata Ni kuma zan dinga jan lokaci tunda Ni zan yi driving ɗinta"cikin tsawa ta ji zahida na kwala mata kira tana masifarta cikin isgili da nuna cewa anitar ce a kasanta,cikin sauri Anita ta kashe wayar tare da boyeta sannan ta wanke fuskarta ta fito tana cewa sorry cikina ne ya ɗan murda kinga bai kamata mu fita a haka ba tunda doguwar tafiya zamu yi"bata ce komai ba zahidar sai harara da tabi anitar da ita, a haka dai Anita ta lallaba zahidar ta gama shiryawa sannan suka tafi. ****** Abinda aka fadawa baffa wuro a wancan asibitin da yake ta zaginsu shine ya kuma fitowa a wannan asibitin na ABM,Wanda mutane suka shaida nagartarsa da ingancin likitocin cikinsa. Kuka baffa wuro yasa yana fadin,"yaushe aka cire min koda ban sani ba?Ni wane irin mutum ne da za a taba cikina ba tare da danina ba?"likita ya ce tabbas an cire maka koda ka dai je kayi nazari sosai ka tuna inda hakannta faru" daga haka ya sallame shi akan cewa zai je ya dawo dan ayi shirin yi masa aiki. ***** Isma il bai san cewa Nana ta dawo ba,saboda tun ranar da ya fito daga dakin Anne Bai Kuma shiga gidan ba,saboda gari yana wayewa ya bar gidan, sai yau ya dawo da mummunan shirinsa akan aminatu. Mus ab yana fitowa daga mittin dinsu na kai da kai,kai tsaye hanyar komawa gida ya dauka,tun fitowar sa da ga Company ya lura da wata bakar mota tana binsa a baya, da bai yi tunanin shi take bi ba har sai da ya tsaya sai yaga motar ta yi slow daga baya kuma yaga an finciketa da gudu an wuceshi,bai zurfafawa kansa tunani ba ya wuce gida. Tun karfe tara aminatu ta kulle kanta a daki da shirin karanta littafin da ta dauko a dakin abby,duk da cewa tana son ganin daddy a Karo na farko a matsayinsa na ƊAN BIRNIn ta,amma haka ta hakura, sai dai kuma ta wani bangaren zuciyarta cike take da tsoron bude littafin da tunanin abinda zata ci karo dashi a ciki. A can bangaren isma kuma ya gama shirinsa tsaf na kaiwa aminatu ziyara,domin saida yasha yayi tatul ta shiga fada masa karya,sai dai bai fita daga hankalinsa ba saboda me aji da tsada yake sha, [4/28, 7:18 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page42``* Tunda mus ab ya shigo yake zuba idanun ganinta inda aminatu zata bullo amma shuru kake ji,har ya ɗan ci wani abu yayi wasu ayyukansa na cikinsa sannan yayi shirin bacci amma har lokacin bai ganta ba,haka nan yaji abun ya taba shi, dan yasan ya barta cikin damuwa duk da cewa yanar mata abinda zai ɗebe mata kewa,yasan aminatu zata so ganinsa sai dai ina bata karanta sakon da ya bar mata ba,sai da yayi Sallah misalin sha biyu sannan ya zura silifas ɗinsa ya fita kasan, dan sam ya kasa samun nutsuwar kwanciyar ba tare da yaga halin da aminatu take ciki ba. A can bangaren su zahida kuwa sai da tafiya ta miƙa sai mota ta tsaya cak a tsakiyar daji,wanda duk cikin shirin Anita ne,hankalin zahida ya fara tashi ganin dare yayi sosai bata son ta kwana daji ga azalzala da zuciyarta take ciki,burita kawai ta ganta gaban boka domin kuwa tana da tabbacin zai bata maganin damuwarta saboda wancan aikin ma na idonka ina da yayi mata yaci kuskure kawai a kayi ta hadu da ɗan ladi abin ya Wada kansa,shi yasa yanzun take jin kwadaituwar komawar,Anita kuwa bata tayar da motar nan ba har sai da ta tabbatar sun gama saita komai , sannan ta yi 'yantabe tabenta a cikinmotar azuwan cewa itata gyara motar sannan ta tashe ta ,tana jin ajiyar zuciyar da zahida tasauke har da sakin dan karamin murmushin da ba a cika ganinsa akan fuskarta ba in dai ba a cikin tagwar manyan mutanen da suke da kudi da fawer ba. ***** Kasancewa cikin dogon nazari da zuzzurfan tunani yasa baffa wuro kamo bakin zaren inda matsalarsa ta samo asali,tashi yayi tsaye yana ɗan dafe gefan cikinsa,cikin cije baki da karfin hali,sakatar gidan ya zare yana shirin fita, matarsa da motsinsa ya farkar da ita, ta yi saurin miƙewa tana riƙosa da fadin "ina zaka je cikin daren nan malam?"cikin kuka da rashin hankali ya ce"ki sake ni zanje wajen waɗan can azzaluman mutanen ne na tambaye su dalilin da yasa suka ci amanata a matsayina na mutumin da ya kasance yana tare da su yana musu duk yadda suke so,duk abinda suka saka ni sai nayi koda kuwa ya haɗa da kisan kai ne,amma ba su dubi girman amanar dake tsakaninmu ba suka rufe idanunsu suka zalunceni ta hanyar kwakulemun ƙoda ba tare da na sani ba,kuma suka haɗa ni da kudin da ko rabin fansar lafiya ta basu kai ba bare na ƙodar da suka cire,gashi sanadin haka dayar itama ta kamu, kuma idan har ban samu kuɗin siyan wata ƙodar ba to sai dai ina ji ina gani na mutu,kai wallahi zalunci bai yi ba,gashi nan tun kan aje ko ina na fara ganin sakamakon hakkinsu aminatu da hakkin amanar ubanta da naci"ya karasa maganar tare da rushewa da kuka,cikin karfin hali matar ta kamo shi ta mai dashi ciki tana cewa "kayi hakuri ka rabu dasu muji da matsalar dake gabanmu idan kuma har kaje ka samesu to kasan kasheka zasu yi ko?dan haka kawai ka barwa Allah hanya daya ce da kai ta gyara lefukanka a yanzu ita ce neman yafiyar wanda ka cuta ka kuma yi ƙoƙarin ganin ka ciresu daga halakar da ka kaisu"wannan shine burina a yanzu koda zan mutu ina fatan Ubangiji ya a ra min lokaci domin ganin bayansu Alhaji Garba". """""Motsin da ta danji daga bayan window ta ne yasa ta, ta yi saurin maida littafin inda yake,tuni jikinta ya fara rawar tsoro,dan ita fa gani take Abby ya ganta rabuwa kawai yayi da ita domin ganin abinda take shirinyi masa da ajiyar da ta dauko wadda ita kanta bata ce ga abinda yake ciki ba,kuma bata san dalilin da yasa take son budewa ba,jin anata taba kofar yasa ta kuma rikicewa tare da saurin hade bayanta da bango tana kallon kofar da idanunta da suka fara zubar da hawaye,ji ta yi kamar Muryar mus ab yana cewa pls ki bude nine mus ab"Jim ta yi tana juya muruar da yaddaya ambaci mus ab din a ranta,girgiza kanta ta yi don kuwa ko a mafarki taji muryar mus ab sai ta ganeta bare kuma a zahiri,cikin kasa da murya aka kuma cewa ki bude mana aminatu nine fa"kamar yana kallonta haka ta ci gaba da girgiza kanta tana kuma jin cewa a ranta wannan ba mus ab ba ne wata ƙila ma abby ne ya canja murya zai yi mata wayo, wannan tunanin da ta yi yasa ta jin wani sabon tashin hankalin yayin da zuciyarta ta farabugawa da karfi tamkar zata faso kirjinta ta fito,cikin hanzari ta koma ta sakewa littafin waje dan tasan ko da zai shigo shine farkon abinda zai fara tabayarta,ita kuma koda kasheta zai yi bazata taba bashi littafin nan ba har sai ta ga abinda ya kunsa. A gefen isma kuwa abin yazo masa a bazata domin bai taba tsammanin zai sha wahala wajen shiga dakin aminatu ba,da yasan haka ne da da wuri zai ta naji safaya key,sai dai kuma ba ko wanne key ne yake yiwa kofofin gidan ba saboda tsananin security dinsu,ya san cewa yau dai ta wuceshi amma ji yake kamar kar ya bar wajen saboda shi kadai yasan abinda yake ji,to amma fa bari wajen ya zama dole saboda ko da yaushe wani zai iya ganinsa, wannan tunanin ya sashi barin wajen zuciyarsa baki kirin da jin haushin rashin biyan bukatarsa. Yana barin wajen MUS'AB din gaske ya karaso tare da yin knocked din ƙofar,cikin nutsuwa wanda tashin farko aminatu ta dauke wuta daga sheshshekan kukan da ta fara saboda yadda lokaci daya bugun zuciyarta ya sauya a karo na biyu da ya kuma yin bugun tare da yin magana sai gaba daya gaɓoɓin jikinta suka yi sanyi take ta fara jin sauyi a gaba daya yanayinta muryarsa da ta ji ya kuma tabbatar mata da cewa shi din ne yanzu da gaske,to amma shi din wancan waye? Abby din ne ko kuma wani daban?sautin takunsa da ta ji yana juyawa da barin wajen shi ya dawo da ita hayyacinta ta nufi kofar cikin wani irin zafin naman da bata taba sanin tana dashi ba,bude kofar ta yi lokaci daya tana bin bayansa da ɗan karamin gudu da bai wuce taku daya da rabi ba ta kamo shi,cak ya tsaya tare da sauke boyayyar ajiyar zuciya yana mai sanya hannunsa saman hannunta da ya zagaye cikinsa yayi masa zobe, a gadon bayansa ta kwantar da kanta tana maida numfashi tamkar wadda ta yi gudun ceton rai,cikin nutsuwarsa da yanayinsa na kamewa da BASARWA ya juyo da ita gabansa suna fuskantar juna,dago kanta ta yi tana kallonsa da idanunta da suka kuma girma saboda kasancewa cikin kuka da damuwa,zata yi magana yayi saurin girgiza kai tare da jan hannnunta, da sauri ta kwace hannunta tare da komawa ta rufe dakin har da cire key din sannan ta matso kusa dashi tana kallonsa kallon farko a matsayinsa na dan birninta,bacin rai sosai ya hango a cikin idanunta hakan yasa bai tsaya ba ya kuma jan hannnunta ta suka bar wajen gaba daya. ***** Lokacin da su zahida suka ƙarasa bukkar bokan ba karamin farin ciki tayi ba,domin sai da hakan ya bayyana akan fuskarta, ji take tamkar ta samu mus ab ta gama,ko da suka shiga ciki sai Anita ta fito acewarta zahidar na bukatar sirri,binta da kallo zahidar ta yi tana jin wani abu me kama da aminci akan anitar a karo na farko saboda wannan abun da ta yi mata,bokan ne ya katse ta da cewa "kema kinga abinda na gani kenan a tare da kawar ki?"da sauri zahida ta dawo da kallonta kan bokan tana cewa kamar yaya?"wani kyalle ya dauko ya mikawa zahidar yana cewa euba nan ki ga Ni" cikin sauri zahidar ta girgiza kanta tana cewa "pls boka duk abinda za ka yi kayi zan baka duk kudin da kake bukata amma dan Allah kar ka nemi na taba wani abu a wajen nan saboda shi kansa zaman da nayi a kyankame nake shi yasa ban saki jikina ba,ba dan ina son mu ab ba da babu abinda zai kawo Ni wajen nan dan Ni sam bana yarda da irinku ,a wannan karon ne kawai naji na yarda kuma na gamsu cewa kai zaka bani mafita,saboda abinda ya faru a wancan karon,dan haka kayi min komai saboda kudina kuma ka sani cewa banzo wajen nan akan ko wace irin bujata ba sai buƙatar mijina da nake ya dawo hannunna karkashin iko na ya zama nice masarrafin rayuwarsa"shuru ta yi tana gyara tsuguno da ta yi a wajen, baki da matsala kuma nada duk abinda ya kawo ki dama wannan kyallen na baki shi ne domin ance gani ya kori ji,to amma tunda kin bani wuka da nama zan yi komai yadda kike so sai dai sharadin biyan bukatarki yana tare da majanuninki wato dan ladi me wanki"kallon mamaki da tashin hankali zahida ta yi masa, kafin ta ce "mene amfanin sako dan ladi a cikin wannan batun kuma?"dariya boka ya sheƙe da ita sannan ya buga kasa yana wasu surutai kafin ya gama ya dago kansa yana wani hade rai da muzurai ya ce"dole ne sai kin nemo dan ladi kafin burinki ya cika saboda asirin jikinsa yana daf da karyewa kuma muddin kika bari yakarye yana nesa dake to aikin da muke yi akan mus ab ba zai taba yuwu ba,dan haka kije ki fara naki aikin kamar yadda nima zan fara nawa yanzu, sannan abinda kike gudu ba zai faru ba saboda zamu toshe duk wata hanya da asirinki zai iya tonuwa a wajan mus ab,har zuwa lokacin da zamu kammala aukinmu AKANSA ". Sai alokacin zahida ta numfasa tsoron dake dankare a kirjinta ya ragu,duk da cewa tana cike da tunanin hanyar da zata bi dan fahimtar da su Abby dan su yarda su saki dan ladi da kuma tsoron abin da zai biyo baya,sai dai kuma kwarin gwiwarta yana ga tabbacin samun biyan buƙatarta,dan haka ta cake masa kudi duk da ya ce da ita ta bar kudinta har sai an kammala aiki result ya fito,sai dai ba ta sauraresa ba ta fito daga bukkar ta samu Anita tana ta zabga gyangyadi a mota,bata tashi anitar ba da kanta ta shiga ta ja motar suka dauki hanyar barin kauyen. **** Kai tsaye bedroom dinsa suka shiga,suna shiga ta fincike hannunta daga nasa tana kallonsa cikin jin haushi da takaici,shafa fuskarsa yayi yana ɗan basarwa, bai ce mata komai ba ya wuce ya shiga bathroom Jim kadan ya fito ya sameta a inda ya barta sai dai a yanzu kuka take yi sosai fuskar ta duk ta yi ja,matsawa yayi daf da ita har jikinsu na gogar juna, kasa magana yayi sai daga can ya kokarta ya ce"ar U ok?"wani irin haushu ne ya kuma turnuketa har bata san lokacin da ta shiga kai masa duka akan mayalwacin kirjinsa ba. Tsayawa yayi cak ba tare da ya yi kokarin dakatar da ita ba, har sai da ta yi ta gaji dan kanta daga karshe ta yi masa wata irin runguma rungumar da ke nuna abubuwa da dama,babu abinda take yi sai cakuda jikinsa da murza fuskarta a kirjinsa ji take tamkar ta shige cikinsa ko ta samu sassaucin abinda take ji akansa da damuwarta,dago muskrata yayi ya hade da tasa yana kallon hasken idanunta da suka haskeshi, kafin cikin tashin murya ya ce"an sorry MATAR ƊAN BIRNI"da sauri ta sanya hannunta a gadon bayansa tana rike shi cikin wani irin yanayin da ita kanta bata ce mene shi ba, sannan cikin wata irin murya me sanyi ga kuma kukan da ta yi ya kuma dusar da Muryar ta ce,"me yasa baka zo ka nemeni ba kamar yadda baffa ya faɗa yasa ina ta jiranka?ko kuma dan baka Sanni ba ne yasa ka gudu baka dawo ba?tana fadar haka ta fara kokarin barin jikinsa sai dai bai bata damar hakan ba,tuni ya kuma hadeta da kirjinsa muryarta na saukar masa da wata irin kasala,ya kasa cewa komai sai shafa gadon bayanta da yake yi a hankali kafin cikin deep voice dinsa ,ya kuma cewa duk ba haka ba ne ban san ina zan nemo ku ba ne,canja maganar yayi da cewa me ya same ki yau kafin zuwana akwai abinda ya faru ne?saboda akwai alamar wani yazo dakin kafin ni ko da bai shiga ba,kai tsaye ta samu kanta da bashi amsa da cewa anne ce"duk da cewa bai gamsu ba amma bai kuma tambayarta ba,sai kwantar da kanta da yayi a jikinsa ya ja jiki tare da ita ya kwanta saman lallausar shimfidar gadonsa,tana samansa tamkar jaririyar da ake son rarrashi, hannunta ta janye daga kan cikinsa tare da dan bude idonta tana kallonsa sai kuma ta maida hannun kan cikin tana tabawa saboda bata taba sanin mus ab shima yana da tunbi ba sai yau duk da cewa ba me yawa ba ne kawai na alamta hutu da jin dadi ne,"daddy kaima kana da cikin haihuwa irin na uncle j .....cizon labbanta da yayi yasa ta yin shuru tare da tura bakinta gaba, sai kuma ta kuma cewa daddy har yanzu baka ji sauki ba? wannan ciwon fa har yanzu yana nan kuma girma yake kara yi kaje asibiti karya fara hanaka baka fita. Kuma fa yana maka zaf...... kyakkyawan cafkar da ya kaiwa bakinnata yasa ta hadiye sauran maganar ta ba tare da ta shirya hakan ba,cikin kankanin lokaci ya shiga bata wasu sabbin darussan da yasa ta ji kanta kamar ba a cikinta ba ,yayin da taji ta tamkar ba aduniyar da shedanu irin su Abby suke ba,samun kanta ta yi da yiwa mus ba din wata irin runguma ta tundaga zuciya da ruhi da gangar jiki, duk da cewa bata san me hakan yake nufi ba,amma tana jin cewa yanzu ne ta kammala da ta tabbatar da mus ab shune dan birninta yake take jin wasu abubuwa da ya jamata a ce ta ji su akansa a matsayinta na budurwar matashiya me ingantacciyar lfy,yadda yake sumbatar ta da zafi zafi shi zai nuna maka cewa akwai wani abu me nauyi akasan zuciyarsa da ya rasa yadda zai yi dashi yake kuma neman hanyar bayyannashi ta wata siga da salon taba zuciya.... Ita ɗinma samun kanta ta yi da shigewa jikinsa tana bin duk wasu bangare tana shinsunawa da kokarin kara tabbatarwa da zuciyarta shine fa wannan dan birnin da babu kamarsa a birni da kewayen kauyen su..... [4/29, 7:34 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page43``* ....a hankali ya shiga zame rigar dake jikinta saboda ganin kamar tana takurata dan ba rigar bacci ba ce,tashin hankalin da take ciki san bai barta ta tuna kayan da yake jikinta ba,da sauri ta rike hannunsa tana mutsu mutsu dan hanasa abinda yake shirin yin,dan dakatawa yayi yana kallon fararen cinyoyinta da suka baiyana sakamakon janye rigar da ya fara yi,a hankali ya maida hannunsa kan kafafunta inda suke a bude wanda hakan yasa ta dan zabura duka tsigogin jikinta na tashi saboda saukar fatar tafin hannunsa me sanyi a jikinnata,janye kafafunta ta fara yi tana kuni_kuni da son cewa wani abu amma ta kasa,saboda yadda jikinta yake wani irin tsuma,numfashin da yaja ya kuma fesar a wuyanta yasa ta yin wata irin sheshsheka kamar me shirin rushewa da kuka sai kuma cikin muryarda take sanya mus ab cikin sassarfar ƙwaƙwalwa da juyewar tunani daga kan kome zuwa wata duniyar da yake hangosa daga shi sai aminatun,ta ce"daddy plsssss...katseta yayi ta hanyar hura mata iska saman idanunta wanda har sai da gashin idanunta suka kada daga nan ya dora yatsansa saman jajayen lips ɗinta yana watsa mata kallon da yake shiga can kololuwar ruhinta yake bin duk wani jini da yake gudana a sassan jikinta yana narkar da wani gingimemen abu da ya tokare a kahon zuciyarta,sai kawai ta rufe bakin har da idanunta tana saukar da numfashin da yake sauka saman kirjinsa da yake a bude, saukar numfashinnata yayi daidai da tashin duk wata tsiga ta jikinsa wanda bai san yana da ita ba,bai kuma san tana tashi irin haka ba,sosai ya samu kansa cikin feelings din da bai taba sanin cewa yana da su ba,kai shi bai ma san yana da lafiyar jiki da zuciyar jin wanna abun da mace ba,macen ma yarinyar da yake kallo a matsayin yar amana wadda yake da burin bata damar yin rayuwar yanci da duk mijin da take so. in dai har ya yaba da nagartarsa ya kuma tabbatar da cewa zai bata kariya fiye da yadda shi zai bata. Samun kansa yayi da kai mata wata yar sumba wadda ta zowa aminatu a bazata,hakan yasa ta kankamesa tana rasa inda zata saka karamar ƙwaƙwalwarta da har yanzu take bulayin nemo mata dalilin da yasa take tsintar kanta a cikin irin wannan yanayin a duk lokacin da take tare da daddy mus ab ɗin,shammatar ta yayi bata yi tsammani ba sai ji tayi ya zame rigar gaba daya yayi gefe da ita,yana cewa "meye kike tsoron na gani bayan ke din amanata ce,ki saki jikinki ki daina min irin haka saboda Ni a matsayin kanwa na dauke ki uhm kin gane?"ya faɗa yana zura hannunsa ta bayanta bata ankara ba a karo na biyu ta ji saukar br dinta daga jikinta,da wani irin hanzari ta hade kirjinta da nasa tare da fashewa da kuka,tana cewa"dama yaya yana ganin jikin ƙanwarsa ne ko mutum yana taba amanar da aka bashi ne?wani dan makalallen hadadden murmushi ne ya subce saman fuskarsa wanda ya kara masa wani rin haiba da kwarni dan da aminatu tana kallon fuskarsa a wannan lokacin tsaf zata iya sumewa dan bata taɓa ganin murmushinsa ba ,sai dai fuskarsa ta kasance ba yabo ba fallasa,abinka da abinda mutum bai saba ba ,to duk sanda yayi sai kaga yafi karbarsa fiye da wanda ya saba yinsa.hannunsa yasa yana kokarin raba ƙirjinsa da nata amma ina tuni ta kuma mannesa wai dan kar yaga abinta,bayan ga abin tana manna masa shi,shi kuma so yake ta rabu dashi saboda hakan yana saka shi cikin damuwa sosai,yana jinta tana ta magamganun shirmenta wanda daga karshe ya ji ta yi ɗif sai saukar numfashinta da yake sauka a kan ƙirjinsa a hankali da alamu dai yau ta samu nutsuwar bacci,gashinta ya shiga shafawa kafin ya dora kansa akan gashin yana shaƙar kamshinsa ,shi ma a haka ya baccin ya rinjaye sa bayan yayi musu addu'a. ***** Sai cikin dare zahida ta ta sauke Anita ita kuma kai tsaye ta yo gida dan bata jin zata iya kwana gidan Anita, saboda bata yiwa anitar kallon me darajar da har zata iya kwana a gidanta. Ita kuwa Anita zahida na barin gidan ta kulle gidanta tare da fadawa dakinta shima sai da ta tabbatar ta kulle, sannan ta fara kokarin kiran nomber da ta kira dazu,ringin daya kuwa aka daga,ban san me aka ce mata daga can bangaren ba amma dai da alama lambar yabo aka bata dan sai da ta murmusa sosai,kana ta ce"yallabai in sha Allah komai zai tafi yadda muka tsara dan na tabbata yadda zahida ke son mijinta babu abinda ba zata yi akansa ba, so kar ka damu nasan zata nemo mana dan ladi kuma bazata taba bari wani abu ya samesa ba yanzu fatanmu daya Allah yasa basu kashe shi ba"daga nan ta ɗan yi shiru zuwa sakanni kafin ta kuma cewa "Yes sir"daga nan ta kashe wayar ta ta fada bathroom ta yi wanka sannan ta fito ta yi kwanciyar ta zuciyarta cike da kwarin gwiwar cewa ta kusa samun nasara akan zahida. *** Sosai Nana ta shiga cikin damuwa da ɗorawa kanta tunani kala kala saboda rashin samun Abby a waya da kuma tunanin inda suka je ba tare da sun sanar da su ba,a cikin wannan hali ta ji motsin shigowar zahida,dan haka ta yi saurin fitowa daga sashenta zuwa babban falon, inda suka ci karo da zahidar tana shirin hadewa upstairs,"zahida Ina kika je tun jiya da kika dauko mu daga ke har iyayen naki babu wanda muka kuma sawa a idanun mu?"dakatawa zahida ta yi ba tare da ta juyo ba ta ce"nana ni ban san inda su Abby suke ba, Ni kuma ina tare da Anita"daga haka ta cigaba da wayewa saman ba tare da ta kalli nanan ba,binta da ido nanan ta yi cikin mamakin halin zahidar da baya zama abin sabo a wajenta, numfashi ta ajiye sannan ta juya ta koma bangarenta a ranta tana jin cewa itama zahidar akwai abinda take kullubewa amma babu kome suke zuwa dan babu wani abu me dorewa a duniya bare kuma zalunci,a maimakon ta kwanta sai kawai ta yi alwala ta fara sallar dan rokon Allah ya warware musu duk wani al'amari ya kuma kawo haske cikin abinda ya shige musu duhu daga ita har ahlinta. Zahida na shiga dakin ta ta yi cilli da kome da yake hannunta kafin ta fara zarya a dakin, cikin sauri kuma ta nemo inda ta jefar da wayoyinta ta dauki daya tare da sanya kiran su Abby,sai dai kuma har yanzu babu wani kabari duka wayoyinsu a kashe suke,anya kuwa zata iya hakura har sai sun dawo akan maganar dan ladi,kai ita fa bata ki a wannan daren a fito mata da dan ladi ba,domin ji take tamkar shine mahaɗin rayuwarta tun da ya zama makullin warware al'amuran ta da mus ab,da kyar ta iya runtsawa shima din dan bacci ya kasance barawo ne. **** A can kuma duniyar su Abby,suna can suna fafatawa da boka sunduki, tsananin iya tsafi da aiki da aljanu yasa sunduƙi bai yi kwanakin da ya ambata ba tuni har ya kammala aikin,sai dai kuma kash ya kasa ganin komai akan al'amarin bare har ya ga inda littafin yake ,aljanun da ya tura ma a kone suka dawo masa cikin azabar kuna ba tare da sun iya tunkarar inda aminatu take ba ma balle har su sa ta dauko littafin su kuma su samu damar kwacewa saboda su sun kasa ganin inda yake,haka ne yasa ran sunduƙi yayi matukar ɓaci wanda take kogon ya shiga girgiza tamkar wanda ake girgizar kasa ,dajin kuwa da kogon tuni ya dauki wani irin sauti mara dadin amo, dan acikin sautin babu kalar kukan jinnun da babu aciki,yayin da wani irin bakin hayaki me tsananin wari da yaji ya turnuke su Abby yana zagayesu da wani irin gudu,wanda hakan ya kuma tabbatar musu da cewa ba karamin fushi sunduki yayi ba domin wannan hayakin ba kowa ba ne sai shi, tsananin fushi da fusatar da yayi ne yasa yake jin tamkar ya cinye su Abby shi yasa yake musu wannan zagayen idan yayi niyar hadiyesu sai kuma ya fasa, gane hakan da su Abby su kayi ne yasa suka fara neman gafara tamkar wani ubanginsu. Sun jima suna kasan da kansu ta hanyar wasu surutai da nuna girmamawa da tuba a garesa wanda hakan ya sanyaya sunduƙi har ya fara saukowa,a hankali komai ya dinga dawowa daidai, daga nan shima ya rikida ya dawo suffarsa ta tsohon sunduƙi, dukkansu kawunansu a duƙe suke babu wanda ya iya ɗago kansa ya kalli sunduƙi saboda tsananin biyayya,sai da shi da kansa ya basu umarnin kallonsa sannan suka ɗago gaba dayansu a tare suna masa kallo me cike da ladabi,bude baki yayi cikin amon muryarsa mara daɗi tamkar Juan jaki ya ce dasu "gobe zaku koma gida amma ba ta hanyar da kuka zo ba,zaku tafi a mota saboda duka iyalanku sun dawo gida kuma dukansu babu wadda zuciyarta take da kyakkyawan zato a kanku,dan haka ku yi tafiya irin ta mutane sai dai zamu gajarta tafiyar taku ta zama kun isa cikin sauri, abu na gaba shine Ni da aljanuna gaba ɗaya mun gagara dauko wannan littafin wannan shine abinda ya bata mana rai har muka kusa yin ajalinku anan,saboda a iya tsawon rayuwarmu babu wani abu da ya taba gagararmu sai a kan wannan yarinyar,dan haka idan kun yi naku muma ba zamu kyale ta ba domin irinsu ne suke kawo karshen mu a doron duniya,ku tashi kuje ku karbi littafi ta ko wacce hanya idan kunso zaku iya saceta ku boyeta ku yi gadinta saboda kar ta samu damar karanta littafin nan,ina mai kuma jaddada muku cewa kar ku bari ta karanta littafin nan idan hakan ta faru Ni babu sauran amfanina a wajenku da sauran mutanena ma baki daya dan haka wannan yaƙin banki kadai ya shafa ba muma ya shafe mu, dan dai abin ya gagaremu ne shi yasa muka barku domin ku din zaku iya dan naga wannan acijin bincike na shine ma ya bani kwarin gwiwar sanar daku,ku tashi ku tafi"daga haka wajen ya bace ɓat ya shafe gaba daya wajen ya koma fili fetal tamkar sahara. ********* Tunda suka yi salla aminatu ta koma baccinta,dan ko sallar da jallabiyarsa ta yi ta, tana idarwa kuma ta zame ta ta koma ta kwanta ta ƙudundune cikin bargo saboda bazata iya barin jallabiyar a jikinta ba, dan ta yi mata yawa da tsaho sosai tamkar wadda za a naɗeta a ciki,nata kuma ta nemesu ta rasa da alama ya fita dasu daga dakin gaba daya,dole yasa ta kwanta ba tare da tasaka wani abu ba,shi kuma yana can dakin geaming,bashi ya fito ba sai wajen takwas, hannunsa rike da karamin towel yana goge fuskarsa ya shiga dakin,ganin har lokacin bata tashi ba yasa ya shige bathroom dan yin wanka. A bangaren zahida kuwa ko da ta gama duk wani shirinta na fita dan neman su Abby bata yi niyyar shiga ko ina ba,dan har ta fara kokarin sauka sai kuma wata zuciyar ta bata shawarar zuwa duba mus ab ki dan ta ga wani irin kallo zai yi mata ,tunda boka ya ce zai yi aikin da zai rufe hanyar da mus ab zai iya gane wani abu akanta,kai tsaye ta shige falon ta nufi ɗakinsa da tasan anan yafi Zama ,ba tare da sallama ko knocked ba ta faɗa dakin kai tsaye,idanunta kuma basu tashi sauka akan kowa ba sai kan aminatu da take baccinta hankali kwance jikinta gaba ɗaya cikin bargo fuskarta ce kawai a waje ta yi fes da ita zara_zaran gashin idon sun yi luf kai kace na kanti ta saka,wani irin jiri zahida taji yana neman yarda.ita amma tuni ta yi karfin halin tsayawa akan kafafunta zuciyarta kuwa ta kasa dakatar da ita daga tsananin bugun da take yi,kafin ta shiga takawa har zuwa gaban gadon ta tsaya akan aminatu tana yi mata kallon kin mutu yarinya,cikin wani irin zafin nama ta sanya hannu ta warce bargon da aminatu ta ke ciki,lokavi daya taji nunfashunta na neman daukewa sabida yadda taga aminatu babu kome ajikinta daga ita sai dan fant,wata irin fincika ta kaiwa aminatu tare da yin wurgi da ita tamkar wata kaza,tuni aminatu ta farka tare da dafe goshinta da tuni ya fashe ya fara zubar da jini saboda gwara kanta da zahida ta yi a jikin katakon gadon,kuka ta saka me karfi wanda hakan ya fito da mus ab daga bathroom ba tare da ya gama tsane fuskarsa da towel din da yake hannunsa ba,cikin hanzari da rashin nutsuwar da ya fara bayyana a tare dashi ya janyo aminatu jikinsa tare da yi mata rumfa yana kareta daga kallon baƙin ciki da hassada da kuma tsana me ƙarfi da zahida take yi mata. Wani irin zafi ne ya dinga tasowa daga maƙogaransa yana bayyana saman haibarsa da tuni ta rikiɗe ta koma wata kala,zahida kallonsa ta koma yi cikin tsananta al'amarin da yayi matukar muni a gareta ,wai yau mus ab ɗinta ne rungume da wata mace babu kaya a jikin ta, yau mus'ab ɗinta ne take kallon tsananin damuwa da tashin hankali akan an taba wata mace acikin idanunsa da saman fuskarsa,mus ab din da duk abinda za kayi ba zaka fahimci damuwarsa ko rashin nutsuwarsa ba,amma yau shine ya ke kokarin birkicewa akan ta fasawa kucaka ballagazar yar kauye talaka goshinta,wani rin miyau me kauri ta hadiye tare da kawar da fuskarta daga kansu saboda ganin mus ab din ya juya bayansa yana daurawa aminatu towel din da ya riƙosa a hannunsa. Cikin kakkausar murya zahida ta kuma figo amiantu daga hannunsa tana cewa "zo ki fita daga dakin nan yar kunama tun kafin na kashe ki na kashe banza, raunanniyar ballagazar karuwa sheda iya ta karu......."ke"wata irin raunanniyar tsawa mus ab ya mata wadda hatta aminatu da take jikinsa sai da jikin ta ya hau kakkarwa yana ɓarin tsoro,"wallahi muddin kika kuma kiran aminatu da karuwa sai na miki abinda har a cikin kabarinki sai kin tuna dani"mus ab ni matarka kake kora akan wannan abun?musu ab ka dawo hankalinka mana kasan wannan din ita wacece kuwa?"hannunsa yasa yana tare jinin da yake zuba daga goshin aminatu kafin ya bata amsa da kalmar da ta kashe ta a tsaye cikin wani irin razani da tashin hankalin da bata taba tunanin akwai makamancinsa a duniya ba.. "Ni nan na fi kowa sanin wacece aminatu MATAR ƊAN BIRNI kuma nine namijin da ya kamata na kare hakkin ta da martabarta saboda ita din ta kasance ɓangare biyu matsayi biyu ruwa biyu a wajena,ita din AMANATA ce kuma MATATA"""""" Zahra✍🏽 [4/30, 3:05 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page44*`` Ba tare da ya kuma sauraren ta zahida ba ya dauki aminatu cak ya fice da ita daga dakin ya maida ta dayan dakin ya rufe kofar,zuciyarsa na jin ɗacin kallon tsiraicin Aminatu da zahida ta yi, tabbas ba dan ya kasance mutum me tsananin danne fushi ba to da tabbas yau yadda zahida ta bata masa rai zai iya karyata baras, Da sauri zahida ta dafe ƙirjinta da take jinsa kamar zai fado, zuciyarta kuwa zafin da take bata ga da abinda zata iya misalta shi ba,gaba daya ta kasa sarrafa hankalinta ji take ma kamar ta zauce, dan haka sai kawai ta shiga wani irin ihu tana yi tana jifa da duk abinda ta ci karo dashi,gaba daya ta shiga hargitsa dakin tana yi tana kuka me haɗe da ihu,hatta da madubi sai da ta fasashi gaba daya ta fita hayyacinta banna take kawai tana jiwa kanta ciwo, da gudu Nana da Anne da larai suka hayo saman ,cikin tashin hankali suka fara kokarin dakatar da ita ta hanyar kokarin kamata, sai hakan ya gagara,hatta Anne da ba shiga sabgarta take ba yau ta tsorata da yanayin zahidar,gaba daya sun kasa dakatar da zahidar hakan yasa Nana ta shiga kokarin kiran mus ab dan a tunaninta ko ya fita ne,zahida kuwa har falo bata saurara masa duk abinda bai fashe ba sai dai idn ta kasa fasashi ne ko kuma ba na fashewar ba ne, hannunta ba abinda suke sai zubda jini kamar wadda aka yanka. Nana tana cikin kiran mus ab din, sai kawai ganin fitowar sa daga dayan daki tayi jikinsa sanye da kananun kaya wanda suka amshi jikinsa yayi wani irin kyau duk da cewa kana kallon fuskarsa a wannan karon zaka fahimci cewa yana cikin mood mara daɗi,sai kuma aminatu da take riƙe da hannunsa tana raɓewa a gefansa saboda tsoron zahida da yashigeta Farad daya,itama sanye take da bakar abaya wadda ya bata ta saka ba tare da ta san ina ya samota ba Kallonsa kawai Nana take sake da baki dan bata taba tsammanin cewa yana ciki yana jin zahida ba,sai kuma yanzu ta fahimci dalilin wannan haukan ta zahida,Anne kuwa taɓe baki ta yi tare da cewa "gayyar tsiyar ashe duka suna ciki"babu wanda ya kulata dan zahida tuni hankalinta ya koma kan mus ab da aminatu da yake.kokarin fita da ita ba tare da ya tsaya ko Nana ya saurara ba kai tsaye mota ya saka aminatu Sannan shima ya shiga,ba su ankara ba sai ganin zahida suka yi ta fito da gudu hannunta rike da ƙatuwar wuka tana cewa"wallahi da naga wannan mummunar ranar gwara mu yi mutiwar kasko gaba dayanmu"Nana da ta biyo bayanta ce ta tayi saurin shan gabanta tana cewa "haba zahida idan hankali ya bata ai tunani shi yake nemoshi me yasa da hankalin ki amma zaki mayar da kanki mahaukaciyar dole?"wani mugun kallo zahida ta yiwa Nana kafin cikin kunar zuciya da tafasar ruhi ta ce"yi min shuru munafuka ai duk abinda ya faru ke kika jawo dan me zaki rabu dashi ya auri wannan tsinananniyar bakauyiya, to wallahi da ace Ni zahida na yi kishi da wannan abar gwara muyi mutuwar kasko gaba daya dani da ku". Kafin ta karasa inda suke tuni mus ab ya figiotar dan da bata yi saurin matsawa ba tsaf sai ya takata,suna ficewa ta juyo kan Nana,cikin bakar zuciya ta nuna Nana da wukar hannunta ta ce"wallahi wallahi wallahi Nana ba zan hakura ba dole aminatu ta biya farashin zunubinta da abu mafi tsada a cikin rayuwarta"tana fadin haka ta yi cikin falon da gudu tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, tana can tana yaƙin neman soyayyar mus ab ashe yana nan yana yana cin amanar ta,kai ita wallahi da zata ga bokan da yayiwa innawuro aiki akan mus ab da ita ma sai.ta je ya mata dan a yanzu babu wani abunda take buri a rayuwarta sama da samun soyayyar mus ab,sai dai kuma kash hakan ba zata samu ba,wankin hula ne yake neman Kaita dare, wani irin zafi ta ji zuciyarta na yi yayin da duhu ya mamaye ganinta su Nana basu ankara ba sai ganinta suka yi hif a kasa ta zube babu alamun numfashi a tare da ita. ***** Saboda tsananin tsoratar da aminatu ta yi tuni ta sumewa mus ab ,jikinta kuwa ya yi zafi saboda zazzaɓin da ya rufe ta a dalilin jinin da goshinta yake zubarwa,tana jikinsa yake tukyin a haka tsaf fuskarsa take kuma sosai yayi kokarin daidaita nutsuwarsa domin a wannan lokacin nutsuwarsa ta fi komai muhimmanci,a haka suka ƙarasa ABM hospital,inda a take aka shiga bawa aminatu temakon gaggawa,cikin kankanin lokaci aka yi mata dressing a goshinta sai magani da aka bata saboda zazzaɓin jikinta,kanta yana saman cinyarsa a haka a ka gama yi mata komai ba tare da ya bari wani namiji ya taba ta ba,komai macece ta yi mata duk da cewar ba wai wani abu ne da ya danganci taba jiki sosai ba,bacci ne ya dauke ta amma kana kallonta kasan bana jin dadi ba ne,dan har firgita take yi lokaci zuwa lokaci,wayarsa ce ta fara kawo haske alamun kira na shigowa,daga wayar yayi tare da karawa a kunnensa ba tare da ya ce komai ba,shuru na tsawon minti daya kafin ya ce" ba zan iya barin inda nake ba yanzu amma zuwa anjima zan kiraka sai kazo ka sameni"daga haka ya dauke wayar yana gyarawa aminatu gashinta da ya leko ta cikin hular kanta. **** Zubewar zahida yayi daidai da shigowar su Abby da gudu suka yo kanta, ba tare kuma da bata lokaci ba suka tarairayeta zuwa cikin mota,Nana ta bude zata shiga Abby ya dakatar da ita da cewa _ki koma kawai itama da an duba ta zamu dawo gidan ba zama zamu yi a asibitin ba in dai har babu wata babbar matsala",yana gama fadin haka ya shuge motar Alh Kabiru yaja abby kuma yana gefensa, sai daddy da yake tare da zahidar a baya,har suka isa gjk hospital basu tankawa junansu ba,suna zuwa likitoci suka yi kan oga kwata kwata Dr zahida me duniya,basu suka samu mutawa ba har sai da suka samu daidaitowar numfashin Dr zahida da yake tsakanin ƙirjinta shi bai fita ba shi bai koma ba,sosai suka kula da ita har ta farfaɗo. Tana buɗe idanunta da fuskar Abby ta fara cin karo, rufe idamunta tayi ta kuma budewa dan ta tabbatar da cewa su din ne ba mafarki tayi ba,tabbatar da su din ne yasa ta fashewa da kuka tare da kama hannun daddyn ta tana cewa"daddy Abby mutuwa zanyi ku temaki rayuwa ta kada na mutu a sanadin mus ab da aminatu,Abby ku hakura da burinku na kan aminatu ku sadaukar da ita gare ni ma ana ku barni na kasheta da hannuna a kuma wannan lokacin ba na bukatar kara ganinta acikin rayuwata wannan alfarmar nake so ku yi min dan Allah daddy"Abby ne ya ce"wai zahida me yake faruwa ne dawowarmu kenan fa muka sameki cikin wannan yanayin?"take fuskarta ta kuma sauyawa har wani ja take yi saboda tsananin damuwa da kuka,cikin tsananin kukauryarta har ta fara dashewa ta ce"Abby mus ab ya cutar da rayuwata ashe duk halin da ake ciki a gidan nan auren aminatu yayi"what"suka hada baki wajen faɗa yayin da gumin fuska ya fara tsatstsafo musu sai kallon juna da suke yi tamkar wanda basu taba ganin junannsu ba sai.yau,cikin kakkarwar harshe Abby ya jefa mata tambaya da cewa"zahida me kike fada ne ko dai kwakwalwarki ta tabu ne bamu sani ba?"kanta kawai take girgizawa tana cewa wallahi daddy dama nasan baku sani ba tunda ku an san kuna so na ba zaku yarda da wannan auren ba,shi yasa bai gaya muku ba amma tabbas nasan da hadin bakin NANA munafukar mata kawai"ta karasa fada tana dafe kirjinta da take jin zai fashe saboda babbakar da yake yi tamkar ana rura wutar itace a cikinsa. Juyawa Abby yayi a matukar rude da fusatar da basu taba ganinsa aciki ba,gaba dayansu jikinsu sanyi yayi,saboda sun san cewa watan cin kaniyarsu yayi, in dai har AMINATU tasan wani abu da ga cikin sirrinsu to tabbas mus ab ma zai sani,idan haka ne kenan littafin ma zata iya bashi, wannan tunanin da suka yi ne ya kuma tashin hankalinsu domin sun san muddin mus ab ya karbi littafin nan babin babbakar rayuwarsu ya fara dole su fara lissafin ragowar kwanakinsu a duniya ko cikin farin ciki,to wane farinciki ma ake batu, bayan tuni aminatu ta yi musu shinge dashi yanzu kuma jaruminta zai karasa rusa ragowar kwarin gwiwar da suke dashi na ci gaba da rayuwa kamar baya,jiri daddy ya ji zai yar dashi hakan yasa yayi saurin kama karfen gadon da zahida take kai tare da yin zaman dirshen a wajen,Muryar zahida yaji tana cewa "daddy Ina kuka kai ɗan ladi?ku fito dashi duk ma inda kuka kaisa domin ina bukatarsa hatta da ku zai muku amfani dan muddin mus'ab ya dawo ƙarƙashin ikona to babu abinda zai iya yi mana ko da agabansa zamu ci gaba da aikata duk abinda muke yi"gaba daya su biyun suka juya suna kallonta da alamar neman karin bayani,jinjina kai ta yi bayan ta basu labarin abinda boka ya faɗa mata. ***** "Innalillahi wa inna lillahi raji'un"aminatu ta faɗa tana yunƙurawa a kiɗime, cikin mutuwarsa da baya rabi da ita a ko yaushe ya kamata ya maidata jikinsa yana tifa mata addu'a saboda fahimtar yayi mafarki tayi,"calm down"ya faɗa yana riƙe fuskarta domin samar mata da nutsuwa,kawar da kanta ta shiga yi tana kokarin tashi ,dan yanzu babu abinda take bukata illa ta ganta a dakinta tare da wannan littafin,ganin ya hanata tashi gashi babu wani karfi a jikinta saboda jinin da ta dan zubar,cikin haki ta bude baki tana cewa "daddy ka barni danjer gida na dauka littafin nan wallahi yanzu na kuma ganinsa yana jaddada min akan temakonsa da na yi alkawarin zan yi, kuma.yace ba zan iya taimakonsa ba har sai na bude littafin nan, to to kuma littafin yana can naga Abby ya dawo,,,,dan Allah daddy ka ɗauke littafin ka boye idan ya san Ni na dauka kasheni zai yi Abby mugu ne bashi da imani dan Allah dan Allah daddy ""ta fada tana fadawa jikinsa tare da kara karfin kukanta. Shafa bayanta ya shiga yi kafin ya tausasa muryarsa da ta kuma yin laushi da zurfi irin ta mazan da suke a tsaye cak,ya ce"ki nutsu babu abinda zai faru yanzu zamu tafi gidan amma sai kin kwantar da hankalinki"rungumesa ta yi tana shigar da fuskarta cikin wuyansa tare da cewa daddy Ina jin tsoron Abby zai kashe Ni ne kamar yadda baba mahaukaci ya ce ya kashe shi"wani irin dum kirjin mus ab yayi cikin wani irin faduwar gaba ya dagata tare da daidaita mata rayuwa ya sanya mata mayafinta, sannan ya kama hannunta suka fita daga dakin da asibitin gaba daya. ***** Tamkar wanda aka jefo daga sama haka su Nana suka ga Abby ya faɗo falon tamkar wanda baya cikin hayyacinsa,kafin Nana ta yi wani batu tuni ta ji saukar mari hagu da dama Abby yana mata marin makauniya,yana yi yana wani irin huci tamkar ɓakin kumurci,"jamilu lafiyarka ƙalau kuwa?me Nana Asma'u tayi maka kake mata wannan marin na rashin imani ka zaɓe karfinka,tamkar ba mace kake duka ba?"Anne ce take magana tamkar zata kai masa duka saboda mamaki da taikaici,Nana kuwa tunda ta dafe kuncinta da hannayenta duka biyu bata kuma yin motsi ba bare ta dago ta tambayesa ba'asin marin da yake sharara mata,nuna ta yayi da yatsa tana cewa wallahi yadda kika sa ya auri wannan Aljanar yarinyar to sai kinsa ya saketa ko kuma ke na sake ki ki tafi ki bar min gidana"daga haka ya wuce sashen aminatu bagazan bagazan tamkar zai tashi sama,yana shiga dajin ya shiga birkita komai na dakin kayanta kuwa kaf sai da ya fito da su ya daga kujera da katifar gado, lokaci daya ya futarvda dakin daga hayyacinsa shima ya futa daga hayyacinsa dan ji yake a ransa da ya rasa wannan littafin gwara ace ya bayyana halinsa in yaso sai karfinsa da littafin su kwace shi,ganin bai samu komai ba yasa shi fitowa a fusace kai kace idan ya samu naman mutum zai cinyesa danye.daidai lokacin aminatu da mus ab suka shigo yana rike da hannunta goshinta zagaye da bandeji,cak ta tsaya ba tare da ta kuma daga kafarta ba, sai ƙirjinta da yake wani irin duka gangar jikinta babu abinda take sai rawa,da sauri mus ab ya juya ya kalleta saboda yadda yaji gana dyaa ƙirjinta ya dau karkarwa,waje daya yaga ta zubawa ido hakan yasa ya bi wajen da kallo inda ya zubawa Abby ido na yan sakonni sannan ya dawo da dubansa kan Nana wadda har yanzu hannunta yana biyu suna saman kuncinta,ji yayi an fizge hannun aminatu daga nasa kafin yayi wani yunkuri tuni Abby har ya kai kofar dakinta da ita inda bai yi wata wata ba ya jefata dakin shima ya shiga,kafin mus ab ya karaso tuni ya rufe ƙofar da key. Da sauri mus ab ya juyo yana kallon Nana dan yana bukatar karin bayani akan abinda Abby yake yi duk da cewa aminatu ta yi masa wata maganar da ya kasa fahimta ,to wane littafi ne aminatu take magana akai?waye kuma mahaukacin mutumin nan da take mafarki dashi akan yana son ta taimakesa?me ye hadin mutumin da su Abby da kuma wannan littafin?tabbas shima yana bukatar littafin nan a hannunsa dan haka ba zai taba bari AMINATU ta bawa Abby littafin ba,gama wannan tunanin nasa ke da wuya ya juya cikin hanzarinsa da zafin nama ya tunkari kofar cikin shirin bude ta ko ta wace irin hanya. A can cikin dakin kuma, kai tsaye Abby ya tunkari aminatu da idanunsa da suka juye suka koma wata kala tamkar idanun mage,cikin tsoro aminatu ta kuma ja da baya tana girgiza masa kai tare da magiyar kar ya tabata,amma ina Abby bai da wannan imanin dan haka cafka ya kaiwa wuyanta tare da shaƙeta a jikin bango yana cewa"Dan ubanki Yusuf ki dauko min wannan littafin tun kafin na zama ajalinku"kuma ki gata min ta yadda aka yi ki ka auri mus ab ba tare da sanina ba?"kakarin amai ta AMINATU take yi tana jin tamkar ranta zai fita,buga kanta yayi a bangon yana cewa dan ubanki ki fada min yaushe mus ab ya zama mijinki sannan ku fada min ta yadda aka yi jika dauko littagin da kuma inda yake yanzu idan ba haka ba ba zan kuma barinki ki shaƙi numfashi a duniya ba yanzu zan kasheki kamar yadda na kashe U....sai kuma yayi shuru yana kuma matse wuyanta a bango,hannu tasa tana son banbare hannunsa da take da tabbacin ya kuma yin mintuna a wuyanta to zai kasheta ne kamar yadda ta faɗa,gashi kuma ya hanata damar yin magana, dakyar ta samu ya sassauta rikon azabar da yayi mata yana cewa maza fada min yadda komai ya kasance ba tare da sanina ba"cikin azaba aminatu ta ce"Ni Ni Nima ban sani ba sai daga baya ban san shine ɗan birnin da baffa ya bawa aure na ba sai jiya, dan haka ban san komai ba kuma ba laifina ba ne"wani azababban mari ya sharara mata wanda har sai da taga giftin wuta ta fuskarta, sai dai Abby yana jin cewa a wannan duniya a kuma a wannan rana da wannan lokaci babu wani abun halitta da ya fishi shiga tashin hankali,wani irin watsi yayi da ita yana mai jin zuciyarsa zata fito,wai musu abunsa shine mutumin da suke nema ruwa a jallo?shine mutumin da ba da shi ba da yanzu sunnjima da shanye roman aminatu sanadinsa ne aminatuntake raye a dunya har zuwa wannan rana,ke nan duk abinda suke nema na dukiyar aminatu tana wajen mus ab?to ta yaya haka ta faru?" Tambayoyin da bashi da mai bashi amsa yake ta yiwa kansa,ji yayi zai zauce abu goma da ashirin sun taru lokaci daya sun zo masa a matukar bazata,da wani irin huci da fusata tare da niyar kisa ya juyo kan aminatu dan atunajinsa yadda ta bashi amsar baya haka ta gaba ma zata bashi abinda ya bukata,danƙar gashin kanta yayi yana figarsa tamkar zai cizgoshi da ga ƙwaƙwalwarta tare da cewa"sanar da Ni inda kika kai min littafi idan ba haka ba zan kashe kakarki innawuro dan a halin yanzu tana hannuna"wallahi wallahi wallahi Abby ba zan baka littafin nan ba har sai na karanceshi na ga abinda yake cikinsa koda kuwa zaka kashe ni ko ka binneni da raina"hannu yasa ya kuma kifa mata marin da take jinin habo ya ɓalle mata gefen idamunta shima jini ya taru saboda tsananin maruwar da ta yi,hannu yasa zai kuma kara mata fiye da na baya yaji an yi wurgi dashi da hannun nasa gaba ɗaya, Yana dago kansa suka yi ido hudu da mus ab tsaye ƙyam yana yi masa wani irin mugun kallo kallon ƙyama da bakin cikin kasancewarsa ubansa, hannu yasa ya ɗago aminatu tare da sata a jikinsa duk da yadda jini yake zuba ta hancinta da bakinta amma hakan baisa yaji cewa zata iya bata shi ba,janta yayi suka shige bathroom ya wanke mata fuska tare da tsayar mata da jinin,dago kanta ta yi a wahalce ta kallesa tana cewa"dan fiyayyan halitta daddy ka ɗauke ni daga gidan nan idan ba haka ba Abby da mukarrabansa zasu kasheni ba tare da na cimma burina na gano sirrinsu da sauke alƙawarin da na dauka ba,dan Allah daddy na rokeka"ta fada cikin wata irin raunanniyar muryar da ta sake karyarwa da mus ab zuciya, rungumeta kawai yayi yana kasa cewa komai kansa kuwa har wani harbawa yake yi saboda tsananin ciwon da yake yi [5/1, 3:33 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page45``* Abby kuwa tsananin mamakin mus ab ne ya hanasa miƙewa dan bai taba zaton cewa zai iya yi masa haka ba,wai yau shi ɗansa na cikinsa yake.turewa saboda mace,lallai da dake,ya.fada yana yunƙurawa dan tashi amma sai.yaji wani mugun zafi ya.ziyarci hannunsa wanda hakan ya tabbatar masa xewa ya samu targane ne ko karaya,dakyar ya iya tashi, daidai lokacin mu ab ya fito da aminatu da take ta azabar kuka, da sauri ta koma bayan mus ab din tana cewa'daddy kasheni zai yi fa"wani mugun kallo mus ab din ya sakarwa Abby,yayin da shi Abby din ya dauke kansa ba tare da ya furta komai ba ya fice daga dakin zuciyarsa cike da mugun nufi akan aminatu. Mus ab kuwa dole sai barin gidan yayi da aminatu dan fafur ta ce bata iya zama,amma fa sai da ta dauki book dinta wanda shi kansa mus ab din bai San sanda ta dauka ba,Nana ma sosai ta bashi goyan bayan ya bar gidan da aminatu dan abinda Abby yayi tun akanta ba karamin tsorata ta yi ba,dan ta dauka itama kashentan zaiyi,sam bata yi tunanin gayawa mus ab din marin da Abby yayi mata ba dan hajann bala I kawai zai tayar dan haka ta rabu dasu suka bar gidan. Kai tsaye gidan sa na miyatti Allah gra ya nufa, ko da suka zo gidan sai da aminatu ta juyo ta kallesa ta ce"daddy Dan Allah kar ka kaini gidan da Abby zai iya ganoni"hannunta da yake cikin nasa kawai ya ɗan murza cikin sigar lallashi ba tare da ya iya cewa komai ba,gidan ba wani girma ne da shi ba cancan amma yana da tsari da burgewa,dan da abaya ne lokacin tana aminatunta da sai ta tsaya yawan magana kan ta shiga gidan,yana riƙe da hannunta suka shiga har cikin bedroom,kafin ya saketa yana dubanta cikin kulawa ya ce"babu wanda zai san kina nan ki Kwantar da hankalinki yanzu kije ki yi alwala ki yi sallah dan ko azhar bana jinkinyi,Ni kuma zan samo miki wani abu kici,kina jin yunwa ko"?ya karasa maganar da tambayarta yana shafa dan shafaffen cikinta,girgiza masa kai ta yi idanunta suna cika da hawaye,ɗauke hawayen yayi tare da nuna mata hanyar bathroom shi kuma ya juya ya fice tare da rufeta ta waje. **** Kai tsaye Abby asibiti ya koma,gaba daya binsa da kallo su kayi saboda tashin hankali da damuwar da suka ganina tare dashi ,zama yayi tare da sanar dasu abinda ya faru bai boye musu komai ba,suma a take hankalinsu ya ya nunku cikinsu babu abinda yake sai kartawa,sun shiga cikin tunanin yadda zasu yi da mu ab tunda yanzu sun gano shine wanda yake rike da dukiyar aminatu kuma dama ita ce dalili na barin aminatu da rai da suka yi,dan haka yanzu kai tsaye zasu iya kashe aminatu in yaso sai su ji da mus ab ɗin,Abby da bai san batun fito da dan lardi ba suka sanar dashi kamar yadda. Zahida ta sanar dashi,shima ya gamsu amma ba kamar su ba dan acikin ransa akwai wani lissafi da yake yi. Zahida sun yi waya da Anita ta sanar da ita cewa daga yanzu zuwa ko wane lokaci za a iya ganin dan ladi,Anita bata nuna mata maganar dan lardi ya sameta ba sai tashin hankalinta da ta nuna akan rashin lafiyar zahidar duk da ta ce mata da sauki ciwon bakin ciki da na zuciya ne kawai wanda kuma shi maganinsa samun mus ab a hannu da kuma ganin karshen Aminatu,kai tsaye Anita asibitin ta yo. Abby da daddyn zahida da Abba sun fito daga dakin bayan sun yi waya da su danturkyi akan cewa ya saki ɗan ladi amma ya tabbatar ya rufe masa ido kafin su fito dashi,amsawa danturkyi yayi tare da cika umarnin oganninsa,sai da suka fito cikin gari sannan suka watsar da dan ladi a gefen titin, dan ladi fa yasha wahala sosai a zaman da yayi tare da wannan mutanen da bai san ko su waye ba, sai dai yana gab da sanin ko su waye din tunda idan shi sun rufe masa ido ai camararsa da ya dana ajikinsa basu isa rufe mata ido ba,cikin jin nauyin jikinsa ya shafa gefen cikinsa ya tabbatar dan dunkulen camararsa tana nan sannan ya mike dakyar yana numfarfashinn wahala, wajen wani mutum da ya gani a tsaye yayi tare da rokonsa alfarmar Aron waya,bai musa ba mutumin ya bashi, sai da ɗan ladi ya ɗan matsa daga can gefe sannan ya sanya nomber da yake bukatar kiran da ita,jim kadan aka daga wayar ba tare da an yi magana ba,cikin saurin baki da haki ɗan ladi ya ce"ina magana da yallabai Musa tanko ne?"daga can mutumin ya miƙe zaune daga kashingiden da yake saboda daukar me muryar da yayi amma dan ya kuma tabbatarwa sai ya amsa masa da cewa shune dawa nake magana?"ajiyar zuciya ɗan ladi yayi sannan ya ce"yallabai ahmad ne ke magana". Cikin sauri mutumin da ake kira da yallabai ya miƙe tsaye yana cewa"Ahmad kana ina yanzu ina fata dai kana cikin tsaro?"ey yallaɓai Amma yanzu zan karaso jikina ne babu ɗaɗi saboda ciwon da yake na zama waje daya"Ahmad amma dai basu yi maka komai ba kuma ka tabbatar ka dauko camarar nan dan ta hanyarta ka dai ne zamu samu shaidar wanda muke zargi"dan ladi ya ce duk na yi yallabai yanzu kasanar da anita abunda ake ciki"mutumin ya ce kar ka damu Ahmad ka ƙaraso kawai a yanzu Anita itama ta tafi dauko ragowar shaidun dan ta sanar min da cewa ta samu damar yin hakan ina fatan Allah ya bamu sa a baki ɗaya"Amin Amin daga haka ya kashe wayar tare da goge nomber daga kan wayar sannan ya juyo ya dawo inda mutumin yake ya miƙa masa wayarsa yana godiya,karɓar wayar mutumin yayi yana masa wani mugun kallo har sai da ɗan ladi ya ji ya tsargu, hakan yasa ya ɗan yi dumi dumi cikin rashin yarda da mutumin,taku daya ɗan ladi yayi dan barin wajen yaji an cafke sa tare da watsawa fuskarsa wata hoda take anan ya sume, su kuma suka ciccibesa suka saka shi a mota. Lokacin da Anita ta karaso asibitin a maimakon ta nufi dakin da aka kwantar da zahidar sai kawai ta canja ta miki hanyar office ɗin zahidar cikin nutsuwa da BASARWA dan kar wanda yayi zarginta,hakan yasa har ta shiga office din bata samu matsala ba, dama ta jima da tanadarwa kanta key din office ɗin zahida saboda zuwan irin wannan ranar,koda acikin likitocin wani ya ganta gaisar da ita kawai suke su bata hanya saboda sun santa da zahida, da haka ta samu ta faɗa office din tare da rufewa, cikin sauri kuma ta fara neman abinda ya kawota abinda yasa take bibiyar zahida kuma shine sanadin shigarta rayuwar zahida,tana gama wannan aikin shike nan ta kammala abinda ya akawota babu ita babu zahidan sai idan sun haɗu a inda zahidan bata taba zato ba. ******** Akan idanun isma mus ab ya fito daga gidan,hakan yasa shi sakin murmushi tare da daga key din da yake hannunsa yana dage girarsa daya, sannan ya ce"Abby wannan aikin ba naka ba ne nawa ne,kai temakona kayi da ka bani umarnin na biyo maka bayansu maga inda zasu je,zan jefi tsuntsaye da dutse daya wato na biya maka buƙatarka Nima na biya tawa,dan yau babu abinda zai hanani jin daɗi da yarinyar nan"dariya ya sheƙe da ita yana buga sitiyarin motar tare da cewa wai matarsa"kai amma fa bayan nan ya rainawa mutane hankali ko a yaushe ta zama matar tasa oho?"Ni dai yau sai na ji abinda kake ji ato dan wallahi ba san bari a barni a baya ba,ina kallo ayi min ta leko ta koma ga dadi a gida ba zan je dawa ina nema ba"yana karasa zansa ya fito daga motar kai tsaye ya nufi gidan kasancewar da yar tazara daga inda yake biye dashi da motarsa dan ma ba motar gidan ya dauko ba, saboda lokacin da Abby ya kira shi ya sanar dashi abinda ke faruwa da abinda yake son yayi masa baya gidan, shi yasa ya dauki motar abokinsa ya fito da ita. Cikin sa a yana saka key din ya bude kofar, shiga cikin gidan yayi ya ɗan kalli farfajiyar gidan ya tabbatar babu me gadi sannan ya sa kai cikin falon da yake madaidaici me kyau da tsari,daga nan ya fara bin dakunan yana gwada keys din hannunsa, sai dai ko alamun budewa dakunan basu yi ba,lokacin aminatu ta yi sallar azhar da la'asar tana zaune saman sallayar ta zubawa littafin dake hannunta ido, a hankali tasa hannu zata bude sai kawai ta ji alamun bude kofa hakan yasa ta yi saurin maida littafin ta ajiye a tunaninta mus ab ne ya dawo,to amma sai ta ji kamar ya kasa bude kofar, hakan yasa ta miƙe ta nufi kofar dan bude masa. ****** Tsayawar da Abby yayi daidai wani tsohon gida da su ma su daddy basu taba sanin da shi ba yasa su dubansa,dariya suka ga yayi tare da cewa ku fito kuga wani abin mamaki"cikin hanzari suka fito suka bi bayansa, har zuwa cikin gidan da yake da dan zurfi,a nan suka ga su ɗan turqui da yaransa sai faman muzurai suke yi,dakin da suke tsaye tsaye ajikin kifar suka budewa su Abby,dakin duhu sosai sai da aka kunna haske sannan suka ga abinda ke ciki,da sauri Abba Kabir ya dubi Abby ya ce"haba jamilu ya mu kayi da kai ai na dauka tuni kasa an saki yaron nan kamar yadda mu kayi da kai?"daddyn zahida ma kallon Abby yake yana jiran amsar da zai basu dan a halin yanzu da asirin jikin dan lardi suke takama da shi ne suke jin kwarin gwiwar samun abinda suke so ta wajen mus ab da zarar zahida ta mallakeshi,kujerar da dan turqui ya ajiye musu Abby ya ja ya zauna,yana cewa lissafinku da nawa ba daya ba ne,amma bari kuga wanu abyn mamakin"ya fada yana daga wayarsa tare da sanya kiran zahida,tana dagawa ya ce"maza ji ta shi ki bi ƙawarki Anita zuwa office dinki akwai abinda zaki gani,daga karshe zan turo su danturkyi yanzu zasu taho da ita nan amma ki yi iya yin ki na ganin bata kufce miki ba"ƙit ya kashe wayar yana kallin su daddy da suka yi suman tsaye,dakyar abba ya bude baki ya ce me hakan yake nufi kenan"?. Abby ya ce"wannan tambayar na kiraku mu hadu mu yi musu idan an kawota, abu daya na fahimta shine ɗan ladi da Anita sun shigo rayuwarmu ne da wani dalili daban,shi yazo a matsayin me wanki ita kuma taxo a matsayin kawar zahida dole da wani abu a kasa kuma a yau nake son sanin komai idan ba haka ba na kashe su na kashe banza,da fari dai ka fara bani camarar da kake maganarta a waya sannan ka kira wanda kuke wayar dashi yanzu ka sanar dashi inda zaku hadu, ba kuma tare da ka nuna masa kana hannun kowa ba idan ba haka ba na fasa kanka da bindigar nan"Abby ya fada yana zaro bindiga daga kugunsa tare da saitata akan ɗanladi wanda har yanzu fuskarsa take rufe da bakin ƙyalle. ***** Anita gaba daya ta haɗa uban gumi saboda har yanzu bata ga abinda take nema ba,hankalinta ba karamin tashi yayi ba dan har ta fara hawaye,tare da sambatu kamar wadda zata yi hauka,gaba daya ta firgita office ɗin, ta ma kasa nutsuwar tsayawa ta duba a hankali ko ta dace,babu abinda take hangowa sai karamin kaninta nuraddin cikin jini zuciyarsa a bude babu kyan gani,babu abinda zaka hango a idanunta sai wani irin fushi da azababbiyar wutar fansa da ke ta da ɗa ruruwa,muddin bata ga fayal ɗin nan ba to ta tabbata babu wata shari a da zata iya kwatar musu hakkinsu, babu wani lauya da zai iya tsaya musu, tunda shima wanda Shari'ar tasu take hannunsa ba sanin fuskarsa su kayi ba bare har idan ya gudu su iya nemosa, tabbas idan ba su hadu sun kawo karshen su zahida ba rayuwar mutane tana cikin hadari dan barin irinsu a duniya babban zunubi ne,a nan idanunta suna hango mata wata durowa sai dai kuma da pin take amfani, duk da haka Anita bata karaya ba da sauri ta karasa jikin durowar tare da fara gwada lambobi daga cikin nombobin zahida da ta sani na sirri wanda suma din ta sansu ne ba tare da zahidar ta sani ba. ****** Da gudu zahida ta fita daga ɗakin da aka kwantar da ita,sai bayan ta fito ne ta yi kokarin saita kanta,zuciyarta kuwa babu abinda bata raya mata akan abinda zata tarar Anita ta na yi a office dinta ba,ita dama taji a jikinta cewa Anita akwai abinda take nema a wajenta,daidai lokacin ta karaso office dinta inda ta na dora hannu a jikin kofar ta ji ta bude, bata tsaya wata wata ba ta faɗa office din, cak ta tsaya tana kallon..... ****** Waya Abby ya mikawa dan ladi yana cewa,karba nan ka yiwa ogannaka magana ,maza saka nomber ka kirashi,ya fada cikin tsawa,cikin kakkarwar jiki dan ladi ya karba wayar amma saboda babu kwari a jikinsa sai ta subce ta faɗi taki zama a hannun,mari daddy zahida kai masa tare da naushi yana cewa "ɗan tsinanniya mu zaka rainawa hankali ba zaka karba ka kira shi ba,cikin jan numfashi ɗan ladi ya kuma karɓar wayar nan ma dai zamewa ta kuma yi,sai Abba ne ya dakatar da su da cewa"tunda ya kasa rikewa me zai hana ya fada mana nomber mu shigar da kanmu ba idan yaso sai yayi magana da kansa kamar yadda muka tsara masa"sun gamsu da shawarar da Abba Kabir ya bayar dan haka Abby ya karbi wayar daga hannun daddyn zahida yana cewa fada mana nomber idan kuma shima ka kasa wallahi ba zan yi jinkiri wajen harbeka ba,amma sai na tabbatar da ka bani wannan camarar da ka dauka lokacin kana wancan gidan,butulu maci amana kawai"(hhhh su butulci manya). Cikin wahala ɗan ladi ya fara faɗo musu nomber yana sakawa,tunda abby ya fara saka nomber ya ji zuciyarsa na wani irin tsalle, nomber na kammala ya ƙwalla wata sheigiyar kara tare da yin jifa da wayar sannan yayi kan ɗanladi ya maƙure shi a bango...... ******** Wani irin daukewa numfashin aminatu yayi bayan ta bude kofar, saboda fuskar wanda ta ci karo dashi, murmushi ya sakar mata tare da jan hannunta zuwa cikin dakin.......✍🏽 Hohoho jama a akwai ƙura fa. Waye yaja hannun aminatu ne? Mus ab ko isma?" Wacece Anita da ɗan ladi?" Shin me Abby ya gani akan wayar sa ya shiga irin wannan kiɗima da tashin hankali haka?" Meye alakar ɗan kadi da Anita?" Shin Anita ta samu damar bude durowar nan ta tsere kafin zuwan zahida? Me zahida ta gani acikin officer ɗin?" Allah yasa dai ba Anita ta gani ba😂. Akwai ƙura fa abubuwan mamaki da al'ajabi wanda baku taba zato ba, Akwai boyayyen ƙulli ta fuskar da babu zatonta ko tunaninta a cikin kwakwalwa ku dai ku karkato ku biyo NI mu ji ya shirin zai kaya..... Idan kina son jin karshen labarin nan ki sanya 500 dinki acikin wannan opay din 8061537048 Fatima yusha'u Adam opay Ba zan yi Allah ya isa ba amma dai aji tsoron Allah munyi na Allah mun yi na annabi na fara ganin pgs Dina na yawo wasu a maimakon su tambayeni na 14 sai kaji ana dan Allah idan kina da pg 35 tati kazai.20 kaza ki bani🤔 Ni dai Zahra ban da abin cewa amma dai a kiyaye, Zan yi Free book da na gana ina sha Allah amma ga wanda su kayi payment din matar dan birni aha muje zuwa yan amana😂 [5/2, 7:31 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page46``* A hankali ta tsuguna ta dauki ID din da ta ci karo dashi zuciyarta na tafiya da sauri da sauri,zuba masa ido ta yi tana duba shaidar da take tabbatar mata da cewa Anita yar sandar sirri ce,bude idanunta ta yi tana kuma kare masa kallo ki zata ga abunda ta yi kuskure gani aciki ,sai dai ina abu ɗaya yake nuna mata,maida idanhnta ta yi cikin office ɗin tana kare masa kallo, komai a watse a wargaje tamkar wnada akayi dambe a cikinsa,cikin wata irin murya me cike da fushi ta ce"Anita ki fito salin alin daga inda kika boye,dan wallahi muddin kun ka bari na kamaki da kaina zaki gane baki da wayo zaki gane cewa acikin yansandar ma ke banza ce baki cancanci aikin ba, dan haka kafin na kirga uku ki fito",shirun da zahida ta ji ne yasa ta dafe ƙirjinta cikin tashin hankali take cewa,na shiga uku kar dai Anita ta gudu"?tana gama faɗin haka ta juya da baya ta bar office din tana yi tana waya da su dan turqui,gaba daya ta rikice tamkar zata zauntacciya haka take yiwa su dan turqui ihu akan kada su bari Anita ta Kubce musu. Anita dake can ƙuryar dakin hutun zahidar inda ta boye kanta cikin sif din dake jikin bangon office din, tun bayan da ta ji takun zahidar ta bar jikin durowar nan ta gudu cikin dakin ,jikinta babu inda baya rawa zuciyarta kuwa kiris ta rage ta faɗo ƙasa saboda tsananin tsoratar da ta yi dan tasan in dai zahida ta kamata to sai dai wata ta haifo me sunanta dan ita tata ta ƙare,acikin sif din ta ga wata yar kofa inda bata yi wata wata ba ta fara gwada pin, cikin ikon Allah da kudurar sa ta yi da ce kofar ta bude inda anan ta ci karo da fayal fayal irin wanda take nema,da sauri ta kwashe su gaba daya ba tare da ta bar ko takarda daya ba,tana jin ihun zahida da kiran da take mata akan idan bata fito ba, dan haka tana jin fitar zahidar itama ta fito da mugun gudu ta fice daga office ɗin,zahida na jiyowa taga gilmawar anita duk da cewa bata tabbatar ita din ba ce ba,Amma haka ta sa aka bi bayanta, Anita kuwa tana fita daga hospital din ta faɗa wata adaidaita sahu tana ce masa su je kar ya tsaya ko ina"jan a daidaitan yayi ba tare da ya ce mata ƙala ba. ***** Wai Jamilu me ye haka?me ka gani a wayar kake neman yin hauka?"bai iya amsa musu ba har sai da ya gaji da dukan ɗan ladi dan kansa sannan ya zube kasa tare da fashewa da kuka,bai san wani irin tsoron mus ab zuciyarsa take yi ba,ko da yayi niyar dakewa ji yake ya kasa, shi har mamakin abun yake ji yake inama yadda yake tsoron mus ab haka yake jin tsoron ganawarsa da Allah, sai dai ina baya ma tuna lahirar bare yaji tsoron me ita,duniyar kawai yake so yake tunani shi yasa ya fi tsoron mus ab idan har ya gano ta adin da yake shiryawa,to ma me ya haɗa dan ladi da MUS'AB ne?wayar kawai ya miƙa musu saboda ya rasa bakin magana,Abba ne ya karba ya duba screen din wayar shima a razane ya kalli dan ladi kana ya kalli daddyn zahida da tuni shima ya firgice,ya ce"me hakan yake nufi kenan?dole fa mu nutsu mu binciki yaron nan dan duk yadda aka yi mus ab ne ya bashi aiki akanmu idan har ban yi kuskuren tunani ba"daddyn zahida ne ya matsara da kujerarsa gaban ɗan ladi da yake ta layi sai dai duk yana jun abinda syke cewa, shi kansa mamakin yadda aka yi nomber da ya bayar ta kasance ta mus ab ya ke yi,duk da cewa yasan ba nomber da suka nema ya basu ba, a iya saninsa shi dai yasna ya hanasu lambar oga musa ne sabida yana tunanin ba zai iya kwatar su a wajensu abby ba,shi yasa zuciyarsa ta karkata akan lambar wani mutumi na musamman da yasan cewa ya fi karfin su Abby, duk kuwa da cewa bai taba ganinsa ba bai taba jin muryarsa ba,amma yana da muhimmanci cikin rayuwarsa domin shine mutum daya tal da suka amince su dankawa amanar kwatar musu hakkin kaninsu shida yayarsa Anita,duk Kuma tsawon lokacin da suka dauka tare basu taba waya murya da murya ba sai dai yayi masa text, tunda ya haɗa su da oga musa bai kuma waiwayarsu ba,sai dai sun san cewa duk nasarar da suka samu a cikin bincike da shiga jikinsu zahida duk shine ya shirya ne hakan, su dai kawai aiki suke domin kasarsu da kuma tilon ƙaninsu haidar,amma basirar ba ta su ba ce,shi yasa kai tsaye ya bada nomber sa dan yana da tabbaci akansa,marin da Abba Kabir ya kai masa ne ya dawo dashi hayyacinsa. "Malam mu zaka maida mahaukata muna maka tambaya amma kallon mu kake kamar tsohon maye,shin me ye alakarku da MUS'AB?"wane mus ab din?" ya dawo musu da tambayar su cikin mamakin da ya rufe shi,shaka daddyn zahida ya kai masa yana cewa "dan uwarka ka gaya mana alaƙarka da wannan me nomber da ka bamu idan baka fahimci mus ab din da muke nufi ba kuma to shine me wannan nomber da ka bamu dan haka muna jiran amsar ka?"take kan ɗan lardi ya shiga juyawa saboda tunda yake babu wani abu da ya taba sashi cikin tsananin firgita da al'ajabi sama da wannan lamarin me suke nufi kenan,suna nufin mus ab me gidansa kuma ɗa ga daya daga cikin mutanen da bashi da buri a duniya da ya wuce ganin karshensu,to me hakan yake nufi?wata iriyar zuwa ce ta shiga tsatstsaga goshinsa tana keto naman ciki tana fitowa,shi kam bashi da amsar da zai iya basu har sai shima ya fita daga cikin rudanin da ya shiga. ***** Da karfi ta fizge hannunta jikinta na karkarwa fuskarta kuwa tuni ta dame da ruwan hawaye,"me ya kawo ka nan me ka zo yi?"dariya yayi irin ta rainin wayon nan, sannan ya kuma kai hannu zai taba ta ,tayi saurin ja da baya tana girgiza kanta zuciyarta sai bugawa take da ƙarfi,kuma matsawa yayi gabanta tare da cewa "ko me zaki yi sai na yi abinda ya kawo ni ke ko da mutuwa kika yi wallahi sai nayi dagawarki kinji karewar zance dan haka ki gyara min nayi cikin salama tun kafin wancan mijin ƙaryar taki ya dawo"hannunta ta haɗe biyu tana nuna alamun roko dan bakinta ya mutu idan ta bude ta yi magana ma zata iya yin aman zuciyarta,jin jina kai yayi fuskarsa dauke da murmushin mugunta ya tunkarota gadan gadan tare da kai hannunsa zai cafkota,ita kuwa runtse idanunta ta yi tare da makurewa guri daya jira kawai ta ke ta ji me faruwa ta faru,amma a maimakon haka sai karar wani abu taji kamar ta karyewar katako ko itace har sau uku,ƙas ƙas ƙassss,sai kuma ihun isma me haɗe da karaji wanda yake fitowa tun daga kasan zuciya yake nuna tsananin azabar da mutum yake ji, da sauri ta bude idanunta guda daya kafin cikin wani irin yunkuri me karfi ta yunkura ta yi kan mus ab da yake rike da hannun isma har yanzu bai sakeshi ba,isma kuwa fitsari ya sake a wando saboda tsananin azaba kafin ya sume daga tsayen, sai a sannan mus ab ya sake hannun nasa suka tafi kasa tare da hannun da tuni ya rabe gida biyu fata ce kawai ta basu damar yin reto ba tare da sun rabu da juna ba. AMINATU kuwa tunda ta rungumesa ta baya ta kasa motsawa kukan ma yau ya gagagreta yi,a hankali ya juyo da ita gabansa yana kallon fuskarta da idanunta da suka yi wani haske da girma saboda tashin hankali,wani irin tausayinta ne ya tsarga masa tare da wani abu me girma kuma na musamman da yake ji akanta tun lokaci me tsayin da ba zai iya tantance shi ba, ta ngumeta yayi sosai a jikinsa yana kuma shigar da ita tamkar zai maida ta ciki,cikin kukan da ta samu damar yinsa ta dago fsukarta tare da cewa"daddy ya zan yi nan ma sun biyo NI?dan Allah ka nesanta Ni da Garin nan bana son zama a cikinsa na tsanesu bana sonsu"ta karasa fada tana mainda kanta ƙirjinsa, bai ce komai ba sai wayarsa da ya dauka ya danna jim kadan ya ajiye,daga nan ya dauketa cak suka bar dakin,a tunaninta fita zasu yi daga gidan amma sai taga ashe daki ya canja mata. Sosai ta saka masa rigima akan ita fa ba zata kuma zama a garin ba bare kuma gidan gaba daya,duk.ya birkice ya rasa ta inda zai fara rarrashinta ga kukanta da yake matukar sosa masa zuciya ji yake tamkar ana kartar naman zuciyarsa,cikin mutuwar jiki da azabar da yake ji na damuwarta da kuma azabar kishin isma da yake ji tamkar zai masa illa,ya kuma janyota jikinsa da take ta zamewa tana kukan ita ya barta ta tafi inda duk zata ba zata zauna a garin ba,riketa yayi sosai yana kokarin ce mata wani abu ko zata sauraresa amma ina ,sai ma duka da ta shiga kai masa tana CEWA "Ni ka rabu dani tunda kaima baka sona so kake su kasheni shi yasa ka bari wancan kwartan ya biyo NI zai ci min mutunci, dan haka wallahi ba zan zauna......da wani irin zafi zafi ya haɗe bakinsa da nata ya shiga aika mata da wani irin hot kisses, wanda tun da yake bai taba yiwa wata mace shi ba,hatta da ita aminatun bai taba kwatanta mata makamancinsa ba,sai dai yau din komai ya zama na musamman,domin da dukkan zuciya da ruhi yake yinsa,,tun aminatu na turesa har dai abin ya fi karfin tunaninta ,dan haka ta fara yin laƙwas wanda hakan ya kuma juya ƙwaƙwalwar mus ab ya shiga nuna mata kala kalan zafafan salo na musamman da aka tanadesu dan abincin zuciya,a hankali ya shiga zame rigar da ta yi masa shinge daga duk wani abu da ya zama halalinsa,a wannan karon aminatu kasa hanasahi ta yi saboda bata da wannan zarrar,damshin miyansa da sanyin harshensa ta fara ji tun daga kasan tafin kafarta yana tahowa har zuwa saman cikinta inda yayi birki akan dan ramin cibinta,wani irin yunƙuri aminatu ta yi tare da riƙe kansa tana fitar da wani irin numfashi me zafi wanda har tsatstsayawa yake tamkar wadda ake shirin zarewa rai,yadda yake tsotse ramin cibinta kai kace alewar madara ya samu,gaba daya mua ab ya kwance tamjar ba wannan miskilin mara fara a da kamewa ba, dan hatta da numfashinsa sai da ya sauya salon fita,kiran sallahr magriba da aka kwalla a cikin wayarsa ne ya yi masa burki,kuma.ahi kadai ne ya dawo dashi hankalinsa,sama yayi da.kansa tare da kifawa kan kirjinta yana maida numfashinsa. A can kuma dayan dakin tuni mutanen da yayiwa waya suka shigo suka janye isma suka tafi dashi inda ya basu umarni. ****** Anita tana rungume da takardunta tamkar rayuwa, tana yi kuma.tana duba bayanta tare da leƙawa waje,idan ta leka sai ta kuma bawa me nafef din damar kara gudu,a haka har suka zo wani raod da babu yawan mutane sai jefi jefi saboda kamar hanyar barun gari ce,su dai basu ankara ba sai ganin mota suka yi ta yo kansu gadan gadan,duk yadda me nafef din yaso kaucewa motar abin ya gagara take motar ta tunkudasu cikin ramin da yake gefen titin,kara Anita tasaka tana ambatan innalillahi wanda daga karshe nafef din ya kai karshen ramin tare da kamawa da wuta tamkar wadda aka kunna, Zahida da take tsaye bakin ramin tana kallon wutar da take ci daga jikin nafef din ta yi wani irin murmushin mugunta duk da cewa har yanzu bata cikin kwanciyar hankali dan kowa zata kashe idan har ba aminatu ta kashe ba, to tabbas bazata taba yin farin ciki ba,juyawa ta yi ta koma cikin motar tare da barin gurin da mugun gudu, tana jin cewa ta dan rage aiki amma babban aiki na gaba. Kai tsaye gidan da su Abby suke ta nufa tana zuwa ta tarar suna fama da ɗan ladi akan ya gaya musu meye alaƙarsa da mus ab,dakatar da su ta yi tana zama dirshen a gaban ɗan ladi har da tankwashe kafafunta, sannan ta dago habarsa da yatsanta manuniya tana masa wani irin kallon kaskanci,kafin cikin Marmara idanunta ta ce masa"kai waye?"shima kallonta yayi kadan kafin ya kawar da kansa daga gare ta yana cewa,da alama kin fi iyayenki kaifin ƙwaƙwalwa dan tun tuni wannan tambayar ya kamata su fara yi min kafin ko wacce tambaya ta biyo ba"hannu abby ya kai zai shaƙeshi zahida ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu, sannan ta ci gaba da cewa "ina jinka bani amsar tambayata"murmushi dan ladi ya yi tare da cewa tabbas ke ce jika biyo ta hanyar da zan baki abinda suka kasa sawa na basu sabida kin fisu dabarun aiki irin na jami an da suka samu kyakkyawan horo,su kuma aiki suke yi irin na jahilai kuma yan alfarmar jami'ai,dan haka kunci jarajarta yanzu zan baku amsa da iya abinda na sani,amma da fari ku fara gaya min inda yayata Anita take?". Kallon juna su kayi mamakinsu da kaɗuwarsu na kuma nunkuwa,zahida ce ta ce "ka bani amsa kawai saboda yayarka ta kufce min a halin yanzu ban san inda take ba,amma fa hakan ba yana nufin ba zan nemeta dan ta karɓi hukuncinta ba ne"murmushi ahmad yayi tare da fadin "Allah duk inda yayata take ka kareta ka zama gatanta ka shiga tsakaninta da azzalumai,daga haka ya fara da cewa....Ni sunana Ahmad wanda kuka fi sani da ɗan ladi amma ɗan ladi ba shine ainihin sunana ba, Ahmad shine sunana da yanka,dan lardi kuma sunan da aka sauya min ne yayin shigowa cikin rayuwarku.... ****** Wanka ya fara yi kafin ta dauro alwala, sannan ya tashe ta itama ta je tayi wa ka ta yi alwala,yasan bazata barsa ya fita Masallaci ba gashi dama masallacin da yar tafiya dan sai ya tafi a mota, shi yasa kawai ya shimfida musu abin sallar ya bata hijabi acikin kayan da ya kawo mata ta saka, sannan ya tada musu sallah,koda suka sallame karatu yasa ta suka yi batare da Alkur'ani ba,dan so yake zuciyarta ta samu salama daga rikicewar da ta yi,sosai kuwa taji sauki har tana iya motsa idanunta da suka kumbura, ana kiran sallah isha suka dora bayan sun idar suka kuma ɗorawa da nafila daga nan suka dire da shafa i da wutir,a hankali ya matsa jikinta yana zame mata hijabin tare da kwantota saman jikinsa,a hankali ya raɗa mata a kunnenta har iskar bakinsa na shiga cikin kunnenta ya ce"ar U feeling hungry?"dago kanta ta yi tana kallonsa a maimakon ta bashi amsa sai hawaye,dafe kansa yayi yana kallonta kafin ya janyo madara da naman da yake kan Centre table ,ba tare da yayi magana ba ya shiga dura mata naman dake tana jin yunwar sai ta fara karba,daga karshe ta kawar da kanta tana dauka a hannunta tare da yi masa alamar ya bude bakinsa shima ta bashi,bai musa mata ba ya bude ɗan karamin bakinsa ta saka masa, sai da ya ɗan ci da yawa sannan ya dakatar da ita yana ɗan ya tsine fuskarsa tare da nuna mata cikinsa yana girgiza mata kai alamun ya koshi kar ta yi masa dura, yadda yayi din abin ya bata dariya, batasan Lokacin da ta fara kyakkyawa da dariya ba,dariyar da rabota da yinta tun tana aminatu MATAR dan BIRNI, tsayawa kawai yayi yana kallonta kafin yasa hannu a saitin kumatunta inda suka loba can ciki kamar zaka zuba wani abu ya zauna,tsayawa ta yi da dariyar tare da dan kawar da fuskarta,ji ta yi ya juyo da fuskartata yana dora mata glass cup ɗib madarar da ya cika dashi a bakinta,bude bakin ta yi ya zuba mata sai dai kafin ta haɗiye yayi saurin hade bakinsu waje daya ya zuke madarar tas har yana lashe wadda ta ɗan zuba a gefen bakinta,tura bakin ta yi tana ƙunkuni kafin ta dauki madarar ta dora abakinta ta kwankwade tana kallonsa tana dariya wai ita ta yi masa mugunta ta shanye. Wata taga ya ɗago a cikin roba tare da kaiwa bakinsa,sai da ya cika bakinsa taf, sannan ya ɗago da kanta daga jikinsa ya hade fuskarsa da tata ya shiga ɗure mata madarar a bakinta...... Kar kice ban fada miki ba na kudi ne, 500 kacal 8064537048 Opay Fatima yusha'u Adam Shaidar biya 08064537048 Sai naji ku [5/3, 6:16 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page47``* Da sauri ta runtse idanunta saboda bazatar da yayi mata ga kuma sanyin madarar da ya gauraye bakinsu gaba daya,take ta dinga jin wani irin yanayi na tsarga duk wani kafa ko jini da bargon da suke yawo a cikin jikinta,ji ta yi yi sama da ita wanda yasa ta yi saurin bude idanunta, sai taga ashe saman gadon ya dora ta sannan ya bi jikinta ya kwanta yana murza fuskarsa a cikinta,kamƙame kansa ta yi jikinta na daukar wani karkarwa tare da zafin da take da tabbacin cewa na zazzaɓi ne,yadda mus' ab yake anutse haka kome nasa yake a nutse soyayyar sa ma nutsatstsiya ce me kashe gabbai da karya zuciya,ji yake kamar ba zai iya jurewa ba ji yake kamar zai maida aminatu cikakkiyar mace,sai dai tunanin ya aminatu zata daukesa yake karya masa gwiwa,baya son ya zama me son kansa,yasan cewa AMINATU tana karama aka bashi ita, bai san me ye burinta ba,dan hake yake ji idan yayi mata shigar sauri tamkar ya zalunceta ne, Jinsa shuru yasa aminatu dago kansa daga kifuwar da yayi a cikinta, tana kallonsa kamar zata yi kuka saboda gaba daya jikinta a mace yake,wani irin abu take ji me nauyi a ƙirjinta, shi be gaba baya be yi baya ba,lumshe idanunsa ya yi tare da maida kansa kan cikinta yana ɗan fidda numfashi a hankali, tunaninsu ne yake ta rarrabuwa sai dai mafi rinjayen sashe shine wanda yake gaya masa cewa kar ya zalunci aminatu ya tsaya ya fara fuskantar damuwarta tukunna kafin ya kai kansa gareta,tunaninsa ne ya katse saboda jin Muryar amunatu cikin wani irin sauti tana cewa, daddy baka da lafiya ne?ko wani abun yana damunka"?ta tambayesa tana yowa kasa da ianta tare da daidai tsayinsu duk da cewa ko da gwaji ba ta isa kai tsawonsa ba,hannunta biyu ta sa ta tallafe fuskarsa tana kallon bakinsa da idanunsa da suke a lumshe, ji ta yi a ranta bari itama ta gwada abinda yake mata taji me yake ji a cikin cin bakinnata da yake yi,hakan yasa ta ɗora lips ɗinta akan bakinsa wanda hakan yasa shi bude idanunsa yana kallon fuskarta da ta hade da tasa,ji yayi tana cusa harshenta cikin dan bakinsa da yake rufe gam,rage mata wahala yayi ta hanyar bude bakin gaba daya yana taimaka mata wajen karbar sakonta da yake jinsa har kolokuwarsa,saukar nunfashunta kawai yaji a saman fuskarsa wanda haka ya tabbatar masa cewa ta yi bacci,gyara mata kwanciya yayi a jikinsa tare da shigar da fuskarsa cikin wuyanta yana shaƙar kamshinta da yake jinsa sosai a ransa. ******** Dare yayi sosai kowa yana makwancinsa a daidai wannan lokaci ne kuma Anita take ta kokarin fitowa daga bayan ramin da nafef yayi wurgi da ita,dakyar ta iya miƙewa tana laluben hanya, saboda bata iya ganin kome a gabanta dan duhu yayi sosai,kuka tasa sosai tana son leka ramin dan ganin halin da me nafef yake ciki,don kuwa a halin yanzu shi tafi tausayawa akanta,saboda an hukuntashi da lefin da bai aikata ba,ko da ta leka ramin babu abinda take hangowa saboda tsananin duhu,hakan yasa ta kuma fashewa da kuka tare da dingisawa tana kokarin barin gurin,tuntube tayi da wani abu kamar hannun mutum duk da cewa taji tsoro amma hakan baisa ta dawowa da baya ba,tsugunawa tayi a daidai wajen da ta yi tuntuben bata yi kokarin laluba gurin ba,saboda bata san me zata ci karo da shi ba,da ta rasa yadda zata yi sai kawai ta yi niyar mikewa ta tsira da tata rayuwar kodan rayukan al umma,har yanzu hannunta yana dauke da takardun da suke lullube cikin bakar jaka,kamar daga sama taji ana magana cikin numfashin wahala"ku ku temaka min"ai da gudu ta juyo ta dawo inda take jin sautin maganar sai taga ashe inda ta yi tuntube ne,babu makawa wannan me nafef din daya dauko ta ne, Allah ya tsallake dashi bai mutu ba,cikin sauri ta kama shi ta dagoshi ga alamun ciwuka nan a jikinsa sosai dan taji jini ajikinsa, dakyar ta iya jansa suka karasa fita daga wajen tana mai fatan Allah ya kawo mai taimakonsu, Suna fita kuwa suka ga wata nafef din tana tahowa daga dan nesa dasu, cikin sauri ta fara sa hannu tana tsayar da nafef ɗin,Anita bata tdaya mamakin ganin macece me nafef din ba tunda tasan yanzu sun fara yi daidaiku a gari,mamakinta daya ne na kasancewar mace a wannan lokacin tana aiki to wa zata dauka in ba aljanu ba ko irinsu da suke hannun makiya"figar nafef din da matar ta yi ne yasa ta dawowa hankalinta sai kuma alokacin tsoro ya ɗan fara shigarta kai dai ace ma zahida ce ta turo a gani ko ta mutu,dan haka ta fara tsaida ita tana cewa"zamu sauka anan"amma matar ko waige bata yi ba bare anita ta sa ran zata kulasu,hankalin Anita ya fara tashi ga me nafef din nan da yake fitar da nunfashi dakyar tasan in dai basu isa asibiti a wannan lokacin ba to komai zai iya faruwa,Anita tana dagowa daga da kanta daga kan me nafef din da yake kan cinyarta sai kawai ta gansu a cikin asibitin ABM ,juyowa ta yi dan ta yiwa matar magana amma sai taga wayam babu ita ba dalilinta,gaban Anita ne ya kuma faduwa innalillahi me hakan ke nufi?aljana ce ta taimakesu kenan?"Allah kadiran Allah manyashau tabbas duk wanda ya tsaya ga Allah hakika zai taimake shi, Allah yasan suna kan gaskiya yasan kyakkyawan nufin su shi yasa ya kawo me temakonsu wanda bata kasance jinsinsu ba,ta ko ina Allah me iyawa ne da isar da sakonsa, shi yasa idan har kana musulmi kar ka karaya da san Allah zai taimake ka ya kawo maka dauki ta inda baka taba zato ba, Allah mun gode maka da ka yi mu musulmi akarkashin dan aikenka masoyinka annabin karshen zamani Annabi Muhammad s.a.w" Bata tsaya wata wata ba ta kira noses da gudu suka fito dauke da gadon daukar marasa lafiya, kana ganinsu kasan dama a shirye suke da ceton rai a duk sanda hakan ta bijiro musu,haka suka taitayi me nafef babu kyara babu tsanantawa akan sai an kawo dan sanda tukunna zasu taba shi tunda sunga yana bukatar taimakon gaggawa,amma fa sun sanar da Anita cewa lallai zuwa safiya ta yi kokarin kiran jam'i an tsaro. ****** Dukkansu sun bada hankalinsu wajen ji da sauraron Ahmad dan ladi,shi kuwa sai da ya ɗan ja numfashi sannan ya ci gaba da cewa,mu mun kasace yan cikin garin Basrah ne wani kauye dake cikin yankin jahar gombe. mahaifin mu da mahaifin mu da mahaufiyarmu duka basu da kowa sai mu yaransu guda uku ,yayata zainab wadda kuka sani da Anita sai kuma Ni Ahmad sai kaninmu me suna haidar,mun taso cikin kulawa da tarbiyya gami da kwanciyar hankali,dan rayuwarmu muke yi simple babu zafafawa duk da cewa mahaifin mu babu lefi yana da rufin asiri na gonaki manya guda biyu da yake matukar ji dasu saboda gadon mahaifinsa ne,kuma da su yake amfanuwa ta bangaren noma da fidda hatsin da zai siyar kuma muci, so dayawa mutane suna kawowa gonayennan hari ta hanyar yi masa tayi da manyan kudade masu yawa amma duk da haka mahaifin mu yaƙi rabuwa da ko guda daya daga cikinsu,a haka muka ci gaba da rayuwa muna karatu dai dai wadatar mahaifin mu,kuma hankalinmu a kwance babu me wata damuwa a cikinmu,kwatsam muna tsaka da gudanar da rayuwar mu cikin kwanciyar hankali ba tare da wata mummunan ƙaddara ta ratsa mana ba,sai wasu mutane su uku suka shigo cikinta da wata fuska da bamu taba zaton zata juye ta zama abin tsana da ƙyama a wajen mu ba, da fari sun zo ne daniyar bawa manoma tallafi,wanda mahaifinmu shine jagoran tafiyar,sun bada tallafin musamman ga masu karamin ƙarfi,hakan yasa duk kauyenmu da kewansa babu abinda ake magana sai maganar karamcinsu, su kuma da wannan damar su kayi amfani suka ci gaba da zuwa suna yaudarar mutanenmu a hankali a hankali suka dinga karbe gonakin mutane da sunan za a yi musu birji tare da fadada ta dan kawar da annobar fari da suka fara cin ye mana gona, Ana cikin haka ne layi yazo kan maiahina inda ya nuna sam bai yarda da batun su ba,duka ta dabara da aikata sun yi masa amma basu samu kan mahaifina ba,da suka ga taurin kansa yayi yawa sai kawai suka fito masa a mutum suka nuna masa asalin fuskokinsu na azzaluman da suke tara dukiya ta hanyar kwace da mallakar abinda ba nasu ba ta karfi, anan fa suka shiga fafatawa da mahainmu inda daga karshe suka dauke mahaufiyarmu sannan suka yi masa barazana da rayuwarta akan indai bai sa hannu a takardun gonakin nan ba zasu kasheta daga ita har yayansa,duk da cewa alokacin ba mu da wani wayo sosai ma.hakan bai hanamu fahimtar tsananin tashin hankali da damuwar da mahaifinmu ya shiga ba,daga karshe dole yana ji yana gani yasa musu hannu a duka takardun ya basu amma memakin su sakar mana innarmu sai kawai ganin gawarta muka yi a kofar gidan mu inda a take shima mahaifinmu ya fadi kasa a sume,tun daga nan ne kuma bai kara yin lafiya ba ciwon zuciya me karfi ya kamashi daga nan shima yace ga garinku nan,sai ya zama daga ji sai yayata da kanina haidar dan shekara uku a duniya,tsananin tashin hankalin da muka shiga ba zai fadu ba, gashi ba mu da kowa bare mu koma wajen yan uwa,dan haka sai kawai muka rungume rayuwarmu a haka muka ci gaba da gurgurawa, mun sha wahala matukar wahala mun sha gwagwarmaya ga yunwa ga talauci ga kuma rashin ilmi dan gaba dayanmu karatun mu ya tsaya cak saboda rashin kuɗi to cikinmu ma dakyar muke samu mu bashi,a haka har muka ja shekaru biyar da rashin iyayenmu zuciyarsu kuwa kullum ya fasa take wutar daukar fansa na ruruwa a cikinta,a haka ne Allah ya kawo wani bawan Allah me suna Musa cikin rayuwarmu da sunan yana son aunty zee, da farko bata yarda ba sai kuma da ma baya ta amince saboda yadda ya nuna kulawarsa a kanmu ya nuna mana kauna da daukar alkawarin zai inganta rayuwarmu tamkar ta ya'yan da ya haifa a cikinsa,a lokacin aunty zee ba wani kaiwa budurwa tayi can ba dan bata wuce shekara sha huɗu ba a lokacin amma haka ta amince wa Musa su kayi aure duk saboda mu,sai daga baya da muka dawo cikin birnin Gombe ne muka fuskanci cewa su din babban dan sanda ne wanda muna tare ya dinga samun karin girma har ya kai matakin cp,a inda ya samarwa anty zee gurbi na yin karatun jami'ar sirri kamar yadda ta bukata Ni kuma na ci gaba da karatu inda na ke karantar low,shi kuma haidar aka saka shi a primary 2,mun ji dadin zama da uncle Musa sosai dan mutum ne da yasan hakkin dan Adam,shi yasa muke matukar sonsa da girmamashi. Rana ta biyu da ba zamu manta ba,mun tashi da rashin lafiyar haidar,.inda duka hankalinmu ya tashi muka dauke shi sai asibitin gjk,inda likitoci suka karbe shi cikin gaggawa aka shiga dashi dakin da ake duba marasa lafiya,fuskar ki tana daga cikin wadanda suka tarbemu duk da cewa baki da fara a da son mutane amma kin tsaya kin kula da haidar har ya fara samun samun sauki kuma shirin sallamarmu ne, haidar ya kuma birkicewa da wani irin ciwon ciki, a nan ma kin tsaya tsayin daga gurin kulawa dashi inda daga karshe kika tabbatar mana da cewa haidar yana bukatar koda saboda kodarsa duka biyun sun samu matsala idan har muna son rayuwarsa sai dai mu siya ko mu nemo wanda zai bada koda a saka masa,hankalinmu ya tashi inda anan ne uncle Musa ya bada shawarar a nema kawai a saka masa saboda dukanmu yara ne bai kamata ace an tabawa wani koda ba,da farko ban amince ba sai daga baya ya fahimtar dani abinda yake nufi sannan na amince" Ɗan shuru ɗan ladi yayi yana jan numfashinsa zuwa cikinsa inda ya ci gaba da cewa,ranar da aka shiga da haidar tiyata a ranar ne na shiga office ɗin zahida Dan amsa kiran da ta sa ayi min bana nan sai bayan nazo ne zainab take gaya min shi yasa na tafi ba tare da na yi tunanin bata office din ba ko kuma ta shiga wani aikin,ina zuwa da hotunan mutum uku nan na ci karo wanda sam ban taba kula dasu ba,sai ranar cikin firgici na juya zan fita dan ba zan taba manta fuskokinsu ba,duk da cewa ina yaro ne abin ya faru,na juya kenan zan fita sai naji alamun motsi a bathroom din office din hakan yasa na dan karasa bakin kofar tare da kai kunnena dan jin abinda ake fada,sai kawai naji Muryar zahida tana cewa kar ka damu daddy tuni mun yi yadda muka saba yanzu haka har mun cire lafiyayyun mun dasa matacciyar fito dashi kawai ya rage a yi"cak na nemi numfashi na na rasa take kaina ya fara juyawa, jin kamar za a fito yasa Ni saurin fita daga office din, kafin na cewa aunty na komai an fito da haidar a sankame a kamun babu rai"zubewa kawai nayi na kasa cewa komai na kasa kuka na kasa hawaye sai zuciyarsa da take wani irin tafasa, ban tsaya na saurari kukan da zainab take yi mijinta na rarrashinta ba na sunkuci gawar nayi waje da ita,da gudu suka biyo ni suna kirana amma babu wanda na saurara, dole sai hakura suka yi suka biyoni gidan inda a nan muka yi masa wanka muka kaisa makwancinsa,to tun daga nan ne nasha alwashin daukar fansa daga karshe na sanar da zainab da mijinta abinda na sani da kuma abinda nake zargi,mun jima muna neman lauyan da zai tsaya mana amma hakan ya gagara daga kasrje dai muka samu wani bawan Allah,bamu taba ganinsa ba sai dai ya yi mana magana ta email address dinsa shine ya tsara mana hanyiyin da zamu bi don nemo shaidar da zai iya kwatar mana yanci, baku taba ganinsa ba kuma bamu taba jin muryarsa ba amma baya bamu gudunmawa me tarin yawa ya dora mu akan hanyar kaiwa ga gaci duk abinda zamu yi ko mu kayi shine yake tsara mana ta hanyar sakonsa da shi kadai muke gani yake nuna mana alamar cewa yana tare damu" Cikin mamaki zahida ta fesar da iska daga bakinta tare da cewa,"me yasa ban gane Anita ba lokacin da ta waɗo rayuwata da niyar yaudara?"dariya Ahmad yayi tare da cewa,ai ba zakintaba ganeta ba sabida girmankanki da jin cewa ke isashshiya ce yasa baki tsayawa kiwa talaka kallo daya ma bare a kai ga batun ganewa,duk sanda zaku hadu da Anita bakya duban fuskarta haka Nima bakya kallona,na sani ikon Allah kadai yasa ko kallon rainin da kikewa talaka mu baki tsaya kin yi mana shi ba kinga kuwa baki taba kallonmu ba,kuma wannan ne ya bamu damar shigowa rayuwarku ba tare da kun gane mu din su waye ba,yau har gashi rayuwarku ta fara tangal tangal"ya fada yana tuntsurewa da dariya!mari daddy ya sharara masa kafin cikin tsawa ya ce"dan ubanka ka fada mana waye mus ab me Kuma ya sani game damu?"dan ladi ya ɗago kansa tare da watsawa daddy wani banzan kallo kana ya ce"ku matsiyata masu ci da gumin wasu wanda komai nasu ya kasance haramun wallahi kunyi karya a wannan lokaci baku isa ba karshenku yazo, kuma karamar ƙwaƙwalwarku bata gano muku waye mus ab ba a cikin labarin da na baku,tunda bata gano muku ba to bari nayi muku Gwari wari yadda zaku fi fahimta,wato MUS'AB dan Alhaji jamilu shine lauyan da muke tare dashu ba tare da mun sani ba,kuma shima bai san mu su waye ba saboda bai taɓa ganin daya daga cikinmu ba, sannan bai san wane gida ya turo mu ba,kar ku damu har yanzu danka bai gane komai a cikin wannan wasan ba amma fa ku fara gudu dan hakan na gab da faruwa wallahi dukkanninku sai kashinku ya bushe". Wata irin zufa ce take jika su ba tare da su kansu sun sani ba,zahida ce ta kuma yi masa tambaya cikin karfin hali,"waye boka ko shima fake dinne?"dariya dan ladi ya kuma sheƙewa da ita har yana buga ƙafarsa da kasan gurin kafin ya dan tsagaita ya dubi zahida yana cewa,"komai da kika sani ƙarya ne,kwallin bita zaizai duk karya ne ,kuma duk yana daga cikin shirin mu,tabbas da ace kun kasance irin ko wace mace da miji to da mus ab ya fahimci labarin tun lokacin da a kayi dramar kwallin bita zaizai"wani marin Abba Kabir ya kuma sheka masa har sai da yaga tartsatsin wuta,shi ko Abby har yanzu ya kasa motsawa saboda tsananin tashin hankali,to amma samun saukin su daya ne na jin cewa har yanzu mus ab bai gane komai akansu ba,dan haka dole su yi hanzarin samun littafin nan dan shine matakinsu na karshe na samun tabbacin ci gaba da rayuwarsu kamar baya.... Da sauri ya mike tare da yin Ball da Ahmad yana cewa,ku tashi mu tafi yaki zama bai ganmu ba,da fari dai bari na fara neman wayar isma saboda na bashi aikin bi min bayan mus'. Ab ɗin "gaba daya suka fita ba tare da sun damu da dare ba dan dama su namun dajin dawa ne basa fara farautarsu sai tsakiyar dare,sai da suka tabbatar sun bar dan ladi cikin tsaro sannan suka shig mota suka bar dajin..... Zahra✍🏽 Kin san dai na kudi ne ko? 8064537048 Opay Fatima yusha'u Adam [5/4, 7:22 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page48``* ......kai tsaye Anita gida ta koma ta fara adana takardun hannunta sannan ta kira mijinta ta sanar masa duk abinda ke faruwa,hankalin cp Musa ya tashi ainun, yanzu kina ina kuma ina Ahmad?"cikin jan ajiyar zuciya irinta wanda yasha kuka ya koshi ta ce ban sani ba tun da ya fito da kai kawai yayi waya bai kira Ni ba,bare nayi tracking nomber da ya kira"ya isa haka ki bari zanzo kawai sai musan abin yi"a'a kar kazo yanzu ka bari a kira sallah sai ka fito ka ji"shike nan karki damu amma ina dai kin san zamanki a gidan nan akwai damuwa kawai na zo na dauke ki yanzu"?a'a babu wata damuwa ai ba tasan ban mutu ba shi yasa yanzu hankalinta ba zai kawo kaina ba ko zuwa gida ba dan haka ka nutsu idan an yi sallar sai kazo mu tafi"ok ki kula sosai zainab kinji"in sha Allah babu abinda zai faru" ok by"suna yin sallama ta yi saurin rufe gidan tare da adana takardun daga nan ta fada bathroom dan tsaftace jikinta daga dattin wahala. Washe gari kowa ya farka ne da abinda ya kwana dashi a ransa,su Abby gaba dayansu babu wanda yayi bacci ko da gyangyadi ne,ko wannensu kullawa yake yana kwancewa ,Abby ya dora hope dinsa akan isma gashi isma kuma.ya bace masa bat, Babu irin kiran wayarsa da bai yi ba amma a kashe,dole ya koma neman wata mafitar atunaninsa ko isma ya tafi sharholiyarsa ne. Zahida kuwa itama tana daka tana saka da warwara ta rasa abin kamawa itama so take ta iya sarrafa harshenta akan mus ab ta kirasa ko zai fahimceta ya dawo inda take, wannan nisan da yake da ita shi yake sanya ta cikin kaduwa da tashin hankali, ta dauki waya dan jarraba kiransa ya kai sau dari amma ta kasa,kwarjininsa da haibarsa take ganowa wanda yake cika mata ido ta ji sam ba zata iya tunkararsa da wata magana ba. Tunda amunatu taga mus'ab yana shiryawa ta fara rau rau da ido, duk inda ya bi binsa take da kallo, zuciyarta cike da tsoron kar ya ce zai fita ya kuma barinta ita kadai a gidan,har ya gama shiryawa tsaf bata daina kallonsa ba saima hawaye da ta fara saukarwa, gabanta ya karaso ya tsugunna tare da kama hannunta yana kallon cikin idonta da ya cika da hawaye,hannu yasa yana share mata su kafin cikin taushin murya ya ce " babu abinda zai faru in sha Allah,babu wanda yasan ina da gidan nan bare yazo shima biyo bayanmu yayi dan haka ki dena damuwa kinji,kuma yanzu nake kadai bace akwai masu gadi mutum uku da tun jiya na kirasu.gyada kanta ta yi tana kokarin maida kukan da yake son kwace mata,"kin koshi dai ko?ya fada yana shafa shafaffen cikinta da kamar ba a sa masa abinci,nan ma gyada kanta tayi,daga haka bai kuma magana ba ya miƙe ya fita daga dakin ya barta da shaƙar kamshinsa,tana jiyo sautin motarsa da fitarsa da kulle gidan har da Muryar mutane daga haka kuma bata kuma jin motsin kowa ba, a hankali ta miƙe kamar wata barauniya cikin sanɗa ta bude dakin ta fita, sai da ta yi dan diri_diri kafin ta gane dakin,zuciyarta na bugawa ta bude dakin tana fatan Allah yasa isma baya ciki, babu kowa a dakin hakan yasa cikin sauri ta fara duba inda ta ajiye littafin zuciyarta na aiyana mata cewa yau in sha Allah sai ta bude littafin nan taga abinda yake ciki,bata fatan wani abu ya kuma katseta kamar yadda yake faruwa duk sanda tazo budeshi,can karkashin gadon ta gano shi abinda ya so bata mamaki tunda Ita dai tasan a kan gadon ta barsa,bata zurfafawa kanta tunani ba ,ta yi saurin dauka ta fita daga dakin. **** Gaba daya lissafinsu Abby ya gama kwancewa hakan yasa suka nemawa kansu mafita akan gwara su koma ga sunduƙi ya taimaka musu da neman inda aminatu take idan yaso su sai su karasa aikin karbar littafin, wannan tunanin da su kayi yasa suka hadu guri daya sannan suka yi siddabarunsu na zuwa wajen sunduƙi. A maimakon haske sai duhu da ya mamaye dajin da kuma cikin kogon, duk da cewa safiya ce amma a wannan waje zaka yi tunanin sulusin dare ne,ko tafin hannunsu basa iya gani,haka suka yi gurfane a inda suka san sunduƙi yana wajen,babu motsin komai a wajen sai duhun da kuma kukan tsuntsayen da ke shawagi a cikin dajin,sun jima a durƙushe a wajen kafin su ji saukar Muryar sunduƙi me kama da kukan jaki yana cewa, na rantse da abin bauta idan har kuka ci gaba da yin sake a cikin wannan aikin har yaran nan suka ci galaba akanku to ba zan kyaleku ba domin Nima kunja min babban tashin hankalin da zai iya sanadiyyar raina,dan haka ku kalli nan"ya fada yana kunna wata wuta da take ci tamkar ana kona taya,ga tsananin mamakinsu aminatu ce zaune a saman gado ta kurawa bangon littafin, a zabure Abby ya yunkura tare da kai hannunsa zai kama wutar dan shi gaba daya ya sha afa gani yake kamar iminatunce a gabansa,bige hannunsa da daddyn zahida yayi ne ya ankarar dashi halin da yake ciki dan haka sai ya koma ya su sunkuyar da kansa wata irin zufa na shekowa tun daga saman kansa har zuwa kirjinsa da yake wani irin bugu fat fat,dariya sunduƙi ya sheƙe da ita kafin ya maida wutar ya kashe ɗif suka daina kallon aminatu,muryarsa ce ta kuma garwaye kogon yana cewa,ku yi sauri ku je gidan ku hanata karanta littafin nan duk da cewa zan yi nawa kokarin daga nan amma bana ganin cewa hakan ya wadatar, ku karba wannan ku dinga dannawa duk bayan sakon biyar shine zai kaiku har gidan da kuma dakin da take, cikin hanzari da rawar jiki Abby ya kai hannu zai karba amma sai sunduƙi ya ya hanashi yana cewa "baka da sa a a wannan karon dan haka ka bari yan uwanka su gwada tasu sa ar"dole Abby ya janye hannunsa Abba Kabir ya mika masa ya karba yar guntuwar layar,daga haka sunduƙi ya sallamesu, shi kuma ya shige baƙin Kogonsa dan fara nasa aikin. *************** Anita tuni ta dankawa cp Musa duk wasu takardu da ta dauko a office ɗin zahida,daga nan ya dauketa suka bar gidan, kai tsaye lauyansu ya turawa da bayanan halin da ake ciki. Mus ab na zaune a office yaji shigowar sakon imail ta wayarsa hakan yasa ya ajiye abinda yake ya shiga duba sakon, murmushinsa me tsada yayi kafin ya ajiye wayar yana mai jingina bayansa da kujerarsa, ya tabbatar da cewa ko yanzu yana shedar kama su zahida sai dai ba zai yi hakan ba har sai ya bude littafin wajen aminatu yaga meye a cikinsa domin yana tunanin akwai wani babban zunubin acikin wannan littafin,yana jin nauyin zuciya a duk lokacin da ya tuna waye mahaifinsa, ba zai iya irga casa casan da suke hannunsa ba wanda duk wanda aka bashi idan ya duba sai yana kaso mafi yawa akan asibitinsu ne,ya jima yana cikin zargi da taraddadi,sai bayan karbar case din su Anita ne ya kuma tabbatar masa da abinda yake zargi da kuma abinda ya faru da innawuro,a baya baisan Anita da ɗan ladi sune ya karba case dinsu ba,har sai da Anita ta kawo labarin yarinya me suna aminatu da take cikin rayuwar zahida ita kuma take.son ganin bayanta saboda ta fuskanci akwai wata alaƙa me girma tsakaninta da mijinta,ba kome ne yasa ya kawo musu shirin boka batun boka ba sai ɗan yana so ya tabbatar da su dinne,sai kuma hakan ta tabbata,aka samu akasi kuma ɗan ladi ya shiga hannunsu, alokacin dan ladi yana tare da camarar da yake amfani da ita a cikin gidan,to yanzu kuma gashi ya kuma samun tabbaci ta hanyar decomment din da Anita ta dauko, numfashi yayi tare da mikewa tsaye zuciyarsa cike da son ganin ya aminatu take,key ya dauka ya fice daga office din cikin hanzarin da zuciyarsa kesa shi yi. Aminatu na zaune saman gado ta zubawa littafin ido, budewa take son yi amma zuciyarta na fargabar abinda zata ci karo da shi,ita dai ana bangaren bata ga abin tashin hankali akan littafi ba,to amma yadda masu littafin suka daga hankalinsu akansa shine yake bata kwarin gwiwa akan son bude LITTAFIN, a hankali ya kai hannu ta bude littafin take jikinta ya fara rawa,hannu ta kuma kaiwa zata bude shafin littafin inda take hango shatin rubutu amma sai taji hannunta na wani irin rawa kafin shima dakin ya fara girgiza, cikin kankanin lokaci kayan dakin suka fara barewa shi kansa dakin ya shiga juyawa kamar katantanwa,amma duk da haka aminatu na kankame da littafin nan,haka kuma zuciyarta cike take da dakiya da jin cewa duk runtsi fa yau sai ta bude littafin,to wai shi littafin nan wace irin masifa ce a cikinsa da haka take faruwa a duk lokacin da ta zo budesa,juyi aka ci gaba da yi da ita acikin dakin tare da Neman kifar da dakin da ita kanta da take kwaƙume da littafin,tun qminatu na dauriya har dai ta nemi gazawa saboda yadda ake wulwulata tamkar fanka,daga can kuma ta fara jin muryoyi suna magana tamkar a cikin kunnenta,ta wani bangaren kuma tana jin hayaniya da karar fashe tashen abubuwa kamar dai kokuwa ake yi,hakan ya kuma ruɗar da ita da saka ta cikin firgici. A can kuma ɓangaren su Abby suna biye da duk inda turakarsu ta tsafi take nuna musu, fatansu daya shine su samu shiga gidan kafin mus ab ya koma gidan ,dan duk cikinsu babu wanda yake da kwarin gwiwar tunkarar mus ab din,dafe kai Abby yayi cike da takaici ya ce"ashsha batun mus ab ya mantar damu bamu karɓi camarar hannun dan ladi ba"Abba Kabir ya ce"kar ka damu bamu da matsala ta wannan bangaren tunda shi yana hannunmu da haka suka bar batun dan lardi suka koma kan ci gaba da tunkarar gidan. Mus ab yana kan hanyarsa ta dawowa wayarsa ta yi haske alamun kira, kamar ba zai dauka ba sai kuma ya ɗan yi tsaki gami da kai hannunsa kan wayar ya daga,ba tare da ya yi magana ba,"shike nan ki dakata daga inda kike saboda fitowarki a kwai hadari ki tabbatar dai kin adana Flash din shi kuma Ahmad babu abinda zai sameshi zan karbo shi daga hannunsu insha Allah"shike nan amma dan Allah yallabai ka yi sauri gani nake kafin kazo ka karɓa wani abu zai iya faruwa"ya ce kar ki damu mama na tabbata yanzu hankalinsu baya kanki duk da cewa sun san kin tsira"ajiyar zuciya Hajara ta yi sannan ta kashe wayar tana kallon Flash din da dan ladi yasa ta daukowa daga gun da aka sace shi. Yana tunkarar gidan yana jin wani irin bugun zuciya da har idan kai matukar kusantarsa zaka iya jin sautin da kuma yadda take harbawa da ƙarfi,so yayi ya fara zuwa wajen Hajara to amma ba zai iya ba saboda yana ji ajikinsa cewa aminatu tana bukatarsa a daidai wannan lokaci, hakan yasa ya karawa motar gudu sosai ta yadda zai iya zuwa cikin kankanin lokaci. ******* Tunda suka tafi suka bar ɗan ladi da masu gadinsa yake kuka da hawayensa, ba kukan kome yake ba sai kukan farin ciki dan ya tabbata i yanzu Hajara ta bawa mus ab sakon da ya bar mata,(abinda ya faru shine lokacin da dan ladi yake waya tuni ya fuskanci cewa wannan me wayar ya biyo shi saboda yaji takunsa ta bayan sa,haka ne ya sa shi tsarguwa the cewa da wata a kasa,sauri yayi ya fara danna nomber hajara wadda itama ya riketa akansa, ya tura mata sako tare da saurin gogewa Sannan ya ci gaba da yin wayar ,ko mai yayi shi cikin kwarewa da dabara ne shi yasa har yayi ya gama mutumin bai fahimta ba,lokacin da ya mika masa wayarsa a lokacin ne yayi saurin dukawa ya ajiye camarar cikin ciyayin wajen tare da yin shedar da ya fadawa Hajara zata gane wajen,daga nan ne suka cafke sa suka dawo dashi nan)hakan yasa yake ji a ransa koda bai kubuta ba in sha Allah mus ab ba zai kyale mutanen nan ba duk da cewa da mahaifinsa a cikinsu,yana tsaka da tunanin ne kuma yaga alamun cewa babu kowa a kusa da inda yake,kasancewar sun manta basu kullesa ba yasa yayi saurin miƙewa tare da leƙawa wajen,sai kawai ya gansu kwance tamkar gawarwaki ga kwalaben giya nan a baje a kusa dasu ko wanne da zamankansa yake zaune,bai tsaya wani tunani ba ya tsallake su ya bi hanya ya fice da gudu duk da cewa babu kwari a tare da shi saboda uban dukan da ya ci kamar wani jaki,amma a haka ya lallaɓa ya fito daga gidan bayan ya dauke key din gidan daga cikin aljihun daya daga cikin masu gadin. Duk Irin gudun da mus ab yake amma gani yake kamar ana dawo dashi baya abin ba karamin mamaki ya bashi ba,to gidan ne ya kara nisa ko me hakan yake nufi,take motar yayi ya kara mana gudu amma dai again sai ya kuma ganinsa a baya,take ya shiga tsananin damuwar da har ta bayyana akan fuskarsa abinda bai saba faruwa da shi ba,a nan ya kuma tabbatar da cewa akwai wani abu me kama da sihir da yake gudana a cikin lamarin gidansu. Su Abby kuwa a dai-dai lokacin da suke tunkaro gidan zuciyarsu tuni ta cika da doki da hanzarin karasawa gidan dan sun tabbatar da nan ne inda sunduƙi ya nuna musu,sai dai suna gab da karasawa jikin karamin gate din gidan suka ga wata irin guguwa ta taso ta rufe gidan tamkar wanda aka sakaye shi cikin yana. At tha sametime Kuma aminatu ce ta yi wata irin kabbara tana mai jan la ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minaxxalimin tare da bude shafin littafin wanda bude shafin yazo da wasu abubuwa masu tarin yawa na ban al'ajabi daga ciki kuma har da hoton mahaukacin mutumin da bazata manta fuskarsa ba da ta yi tozali da ita a cikin bangon littafin an rubuta ( SULAIMAN JA'AFAR LAMIƊO)da manyan baƙi...... Zahra...✍🏽 Na kudi ne 8064537048 Opay Fatima yusha'u Adam [5/5, 5:03 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page49``* Take jikin AMINATU ya shiga wani irin bari hannunta kuwa tamkar wanda ake girgizashi saboda tsananin rawar da yake yi,fuskar mutumin kuwa tamkar zata yi magana a cikin bangon littafin,cikin kankanin lokaci komai da yake faruwa a dakin ya tsaya cak komai kuma.ya koma mazauninsa tamkar ba anan aka yi yakin ba,shafa fuskar mutumin tayi da hannunta tana kokarin bude wani shafin inda ta hangi rubutu kananu kamar ba hannu ne ya rubuta ba,zaman sa kawai ta ji a gefanta yana mai sanya hannunsa ya janyota jikinsa ya rungume yana sauke boyayyar ajiyar zuciya tare da yiwa Allah godiya da ya bashi ikon karasowa gidan da kuma ganin aminatu lafiya,a hankali ta dora hannunta kan nasa hannun da yake kan cikinta kafin cikin rawar murya ta ce"daddy kasan wannan?" ta faɗa tana maida kallonta kan littafin,zubawa fuskar mutumin ido yayi yana jin wani irin nauyin zuciya, tsawon sakonni kana ya kauda fuskarsa yana jan numfashinsa zuwa cikinsa sannan ya furta cewa "ban san shi ba,ke kin sanshi ne kuma meye a cikin littafin ne da duk wannan abun suke faruwa saboda kawai kin dauko littafin?"da sauri ta amsa masa da cewa Ni ma ban sani ba shi yasa nake so na karanta littafin, wannan mutumin nasan shi shine mutumin da nace maka yana zuwa min a mafarki wai na temaka masa, duk sanda yake kokarin fada min inda zan samesa sai wani abu ya gifta na farka bana samun bayanansa"Nima ina son karanta littafin" ya fada yana taya ta bude shafin gaba na littafin. A bangaren su Abby kuwa tunda suka ga gidan ya rufe da wata irin bakar yana shike nan suka gigice, gashi sun kasa ci gaba da tunkarar gidan,bude shafin littafin da karanta sunan da yake kai tare da hoto shine farkon wargatsewar lissafinsu, dan kuwa take motar da suke ciki ta fara wata irin haniniya tana juyi da daga hancinta kai kace wata muguwar dabba ce,cikin gigita suka rike junansu cikinsu na wani irin hargitsawa,Abby ne ya toshe kunnensa saboda wata irin kara da ta cika motar karar mutanen da akalla zasu kai hamsin,ko wanne da kalar tasa karar, su din ma abinda suke ji kenan, da sauri daddyn zahida ya bude idanunsa da suke rufe saboda tashin hankali da tsoron da ya kamasu wanda basu taba zaton zasu tsinci kansu cikinsa ba,kokarin fita daga motar suka fara yi amma hakan ya gagara dan ko motsi ta ki yi bare su saran zara budu,da wani irin gudu motar ta kwashesu suka bar wajen, babu abinda suke sai ihu babu wanda ya iya jan addu'a ko salati a cikinsu sai ihu da neman ɗauki a wajen bokansu, A can bangaren sunduƙi shima ba a barshi a baya ba,dan lokaci daya kogonsa ya dauki wani irin tururi na tsananin zafin da zai iya kona fatar jiki,cikin gigita ya miƙe daga kan buzun tsafinsa da yake ta gwagwarmaya da aminatu da mus ab, da farko ya fara cin galaba akansu amma lokaci daya yaji komai ya tsaya cak, yana kokarin sake wasu dabarunne, wannan masifar ta rufto , miƙewa tsaye yayi tare da ɗaukar sandar tsafinsa ya haska wani bangare daga cikin kogon inda a take anan su Abby da tashin hankalin da suke ciki suka bayyana,wani irin kara da kururuwa sunduƙi wani irin hayakinna fita wa daga bakinsa tare da wani shegen wari da ya cika gurin, ya ce "kun kashe mu me yasa kuka bari su ka bude littafin nan,to yanzu fa sai yadda rayuwa ta yi damu domin masifun da muka fara shiga ba zasu tsaya ba har sai sun gama karanta shafukan SULAIMAN JA'AFAR LAMIƊO,daga nan ne zamu samu damar kuma wani kokari akansu amma muddin muka barsu suka bude wani shafin to ku tabbatar da cewa bala un da zaku gani sunfi wanda kuka fara gani da wanda zaku gani nan gaba" Yadda sunduƙi yake kallonsu ta cikin madubin tsafinsa yake musu magana haka suma suke kallonsa da sauraron abinda yake cewa, Abba Kabir cikin tsananin tashin hankali ya ce"yanzu sunduƙi me ye abinyi ya zamu yi mu fita daga wannan masifar da muke ciki?wai ka duk me ya janyo mana wannan tabarbarewar al amuran lokaci daya ?anya kuwa babu sa hannun maƙiya?"ya karasa fada kamar zai rushe da kuka, "babu abinda zan iya yi muku ayanzu ai na fada muku tun ba yau ba,idan bala in ya tashi har dani zai hada dan haka ku nemo hanyar fidda kanku"da sauri Abby ya tari numfashinsa da cewa "sunduƙi kataimaka mana mu gida daga cikin motar nan wallahi masifun da yake cikin motar nan bai kai wanda zamu tarrar a waje ba,har yanzu fa kukan mutane da ihunsu muke ji tamkar dodon kunnenmu zai mutu sunduƙi ka taimaka mana kayi mana rai ba dan halinmu ba"Abby ya karasa da hade hannunsa guri daya alamun roko,sunduƙi ya ce"shike nan zan taimaka muku duk da cewa nima ban kashe tawa masifarba",daga haka suka daina ganinsa, alokacinne kuma suka ji motar ta yi wani irin jan burki,hade da watso su waje kamar wasu kayan wanki, aiko suka ce kafa me naci ban baki ba, kai kace yan tseran gudu ne basu tsaya a ko ina ba sai a dakunansu ko wanne yana tunanin abinda zai kuma biyowa baya. ***** Zahida kuwa tana tsaka da tunanin hanyar dawo da mus ab hannunta wani irin bacci ya fizgeta me karfi,wanda hakan yasa ta bingire a kasan dakinta tana yinsa babu ji babu gani,kamar a mafarji kamar kuma a gaske ganin kanta kawai ta yi a cikin wasu irin kayoyi suna tsikarinta,daga gefe kuma mutane ne yara da manya suke ya kudi fatar jikinta suna ci tare da cewa sai kin biya mu hakkinku azzaluma me fuska biyu ba za mu taba barin ki ki huta ba saboda kin kashe mu ta hanyar da bai dace ba,kin zama sanadin mutuwarmu ta hanyar da bai dace ba,wasunmu marayu ne wasunmu talakawa ne masu neman cin na yau,wasunmu muskinaine da masu raunin zuciya, amma duk baki duba haka ba kika kashe mu ta hanyar cire mana abinda Allah ya haliccemu dashi saboda neman duniya,to yanzu ga duniyar nan kin sameta kuma kina kan samu se ki zauna zaman jiran duniya tunda ku babu lissafin mutuwa a Yarenku"a matukar firgice ta tashi ta haɗa wata uwar zufa, tsananin zafin da ya ratsa ta ne yasa ta yi saurin duban jikinta,ga tsananin mamakinta sai taga gaba daya fatar jikinta ta kuje wani wajen ya kwashe ga shatin farce Nan ga kuma na kayoyin da suka dinga tsikarinta nan,da gudu ta mike ta shige bathroom tana kuka tana taba fuskarta da lokaci daya ta sauya kama. **** Sosai suka maida hankalinsu kan rubutun da yake cikin shafin kafin su fara karanta tare da kallon abinda yake kunshe dashi wanda suke ganinsa tamkar a gabansu a kayi. TSANGAYAR DAMATURU.. Yaro ne ɗan kimanin shekara goma sha biyu yake tafiya hannunsa rike da roba irin ta almajirai,shidinma kana duban kayan jikinsa zaka tabbatar da cewa almajiri ne,kacibus suka yi da wani yaro da bai fi sa an sa ba yana zaune daga gefen kwalbatin babbar hanyar da zata aidakai TSANGAYAR malam auwal yana ta kuka har da tumurmusar kafafunsa,cikin sauri almajirin ya karasa inda yaron yake tare da dora hannunsa akan kafadarsa yana cewa,"waye ya dakeka kake kuka"?ture hannunsa yaron yayi daga kan kafadarsa yana mai hadiye kukansa,rambayarsa almajirin ya kuma yi yana kokarin zama a kusa da yaron,amma ga mamakinsa sai yaga yaron yayi saurin miƙewa yana toshe hancinsa tare da yatsina fuska har da kokarin yin amai,cike da mamaki almajirin ya ke kallon yaron, can kuma ya tsinkayi Muryar yaron yana cewa "kai fa almajiri ne dan me yasa zaka taba Ni har ma ka dinga kokarin zama a kusa dani bayan hakan yana nufin kana son daidaita kanka dani ne"da sauri almajirin ya dubi jikinsa kafin cikin sakin fuska ya ce,"ka yi hakuri na manta ganin kana kuka ne yasa na manta cewa Ni almajirin gidanku ne"yaron gyada kai yayi yana wani hura hanci kafin ya kuma cewa da almajirin, Anne ce ta aikeni na zubda kudin shi yasa nake kuka ko kana da maganin kukan nawa ne talakan almajiri?"girgiza kai almajirin yayi tare da cewa "yau ban samu kudi ba saboda bana jin dadi ban je dako ba"wucewa yaron yayi gaba yana cewa "babu ruwana kai zaka biya Anne kudinta tunda kaine ka jawo aka aikeni har na yar da kudin"almajirin bai ce komaiba sai bin bayansa da yayi ba tare da yayi kokarin jerawa dashi ba. Suna shiga zauren gidan suka ci karo da Kabiru dan makotansu Jamil yana ta irga kudi yan ashirin ashirin, birki jamilu yayi yana cewa"Kabiru a ina ka samo kudi haka da yawa?"dariya Kabir yayi yana cewa ai na innarmu ne da take sawa a banki na dauko zan je Nima na ji yadda ya'yan masu kuɗi suke ji"tsaki Kabir yayi tare da warce kudin yana cewa"aikin banza wadan nan yan kudadenne zasu yi maka maganin damuwarka to ka ma sake lissafi"daga haka ya cusa kudin a aljihunsa yayi gaba, tura baki Kabiru yayi tare da har SULAIMAN almajiri kamar shine yayi masa lefin,girgiza kai kawai suleman yayi kana ya shige gidan shima.yana shiga ya samu anne na yiwa Jamil fadan dadewar aiken da yaje yayi kuma bai samo abinda aka aikeshin ba,saboda yana shigowa kudin da ya karba a hannun kabiru ya mika mata,tana ganin sule ta washe baki tana cewa a'a sule ka dawo daga dakin ne yaro dan albarka ke nan babu ruwansa da kayan kowa sai dai ya nemi halalinsa"take jamilu ya hade fuska yana cin magani dan yasan da shi anne take wannan habaicin,feee ya fi ce daga gidan yana maganganu ƙasa ƙasa. Sule kuwa cikin ladabi ya ce "anne ai yau banje dakon ba saboda bana jin dadi"da sauri Anne ta kamo hannunsa tana cewa sannu dan albarka me ya sameka? bari na kawo maka magani kasha kaji,ta karasa fada tana shiga dakinta,binta da kallo sule yayi yana jin daɗin irin kulawar da iyayen gidansa suke bashi, gashi dai babu abinda ya haɗa su aike kawai yake yi musu suka jawo shi a jiki suka mai dashi tamkar dansu,shi yasa yake sonsu yake kuma kayuatta musu,yaron su daya tal shine Jamil,sai dai Jamil baya jin magana ko kadan kullum fama suke dashi ko makaranta yaki zuwa, samun sule da suka yi yasasuka rabu dashi tare da yi masa addu'ar fatan shiriya, Sule dan asalin garin Gombe ne cikin wani kauyen Fulani me suna bingel,tun yana shekara uku iyayensa suka mutu sai ya koma wajen baffansa da zama,saboda tsana da tsangwama da matar baffansa take nuna masa yasa baffansa ya tattara shi ya kaisa DAMATURU karatun almajiranci,sule yaro ne me nutsuwa da hankali babu ruwan shi da rawar kai irin ta almajirai shi yasa yake da shiga rai da kuma farin jini,ko a wajen malaminsu yana da alfarma, yaro ne me hazaka da neman nakansa dan shi ko bara bai yarda yayi a bashi ba sai dai ya fita yayi aikin karfi ya samu abinda zai sawa bakinsa na salati,a halin yanzu har makarantar boko yake zuwa saboda abin yana burgeshi da bashi sha,awa gashi abin nasa yayi albarka dan yanzu yana ajin daga ke se secondry, shi kuma Jamil yaki karatun babu abinda ya iya sai janyo magana da yan sace sace saboda shi yana da babban buri a zuciyarsa , sosai ya tsani sule da dabi'unsa,shi yasa basa shiri. Gidansu Kabir yana jikin gidansu Jamil ta hagu shi kuma gidan su Garba yana ta dama,gaba dayansu ukun abokaine da hali da rayuwa suka zo daya shi yasa suke jone suke matukar son junansu. Sannu sannu kwanaki na shuɗewa su zama watanni watanni na shuɗewa su zama shekaru ,gashi yau matasan samarin har sun cika shekara sha biyar biyar, ko wanne kuma burinsa bai sauya ba,sai abinda yayi gaba,ta bangaren sule yanayin rayuwarsa na rashin girman kai da neman hakan da rashin raina samu duk kankantarsa ya fara kaisa matakin nasara,bai damu da irin hantarar da su Jamil suke masa da gori ba dan duk abinda ya samu sai ya basu nasu kason kuma su sa hannu su karbe ba godiya sai dai su bishi da harara da gorin rashin iyaye da takaicin almajiranci duk da cewa su din ma talakawa ne bambancin su dashi shine su suna gaban iyayensu ne,kamar yau ne sule ya dawo daga kasuwa wajen da yake yan buga bugarsa ya samu, ya kuma samo me albarka har yayi musu guzurin hatsi, Jamil na gefe da wayarsa da ya samu ta hanyar kwace yana faman latsata,duk albarkar da iyayensa suke sakawa sule yana ji sai dai bai tanka ba, da abin ya ishesa ne ya mike yana buga uban tsaki tare da fucwa daga gidan,baby abinda zyciyartsa take aiyanawa sai kudi karfi mulki duk inda ya kamata ya samesu sai ya samesu, acewarsa karamin samu ma an martaba mutum bare kuma akaiga babban samu. A kofar gida ya tarar da Garba da Kabir suna lido,zama yayi yana huci wanda hakan yasa suka bar abinda suke suka fuskanceshi tare da tambayarsa abinda yake damunsa,a.maimakon ya basu amsa sai shine ya juya musu da tambay,abokaina kuma son muyi kudi cikin kankanin lokaci?"gaba daya suka daga masa kai kamar wasu kaɗangaru,hannunsa ya dora akasa su kuma suka dora nasu a bayan nasa,daga haka ya ce da su ,"daga yanzu duk wani abu da muka san zai kawo mana kudi kawai zamu yi shi babu tunanin abinda zai je ya zo"dariya suka sa tare da daga hannun su sama da yake a hade....... Zahra..✍🏽 8064537048 Opay Fatima yusha'u Adam 500 only [5/6, 11:21 AM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page50``* Tun daga wannan lokaci su jamilu suka sauya dama can suna da dabi arsu ta kwacen waya kudi da yan abubuwan da ba a rasa ba,amma a wannan lokacin da zuciyarsu ta kuma tsunduma akan lallai sai sunyi kudi ta ko wane hali sai abin nasu ya fara yawa,har ta kai da sun fara haurawa gidajen mutane,abun nasu dai babu imani ko kadan,ana cikin haka zance ya fara baza anguwa, har magana ta dawo kunnen mahaifin Jamil,a lokacin Garba da Kabir su iyayensu maza sun rasu a hannun iyayensu mata suke,su kuma tun da ya zamana zasu nemo musu suci shike nan suka daina fada musu gaskiya sai albarka da take biyowa baya,shi ko mahaifin Jamil faduwa yayi tun da yaji labarin, da kyar aka samu kansa, ko da ya tashi nan ma gorin mutane ya sashi a gaba wanda dole yasa ya fara hada kan iyalansa dan su bar garin DAMATURU. Alokacin shi kuma SULAIMAN ya jima da komawa garinsu Gombe ,inda ya tarar da baffansa ba lafiya anan ya shiga jinyarsa da yi masa hidima ta kudi, har Allah ya karbi abinsa,SULAIMAN bai karaya da rashin dangi ba sai ya sawa zuciyarsa hakuri ya kuma tabbatarwa da mutane cewa babu Maraya sai rago,dan cikin ikon Allah neman na kai da jajaircewa ya fara kai SULAIMAN wasu matakan nasara inda ya tashi gonarsa ta gado ya habbakata tare da yi mata yan uwa,a gefe daya kuma yana ci gaba da neman ilminsa na boko da na addini, Kai tsaye malam ilya maihaifin Jamil Gombe ya taho,ƙafarsa kafar Jamil dan bai yarda ya barshi a wajen abokansa da yake tunanin su suke lalata Jamil din ba,kasancewar SULAIMAN ya bashi cikakken kwatancen kauyensu da kuma gidansu yasa basu sha wahalar ganewa ba,SULAIMAN yayi farin ciki iya farin ciki da ganin iyayensa na riko mutanen da ba zai taba mantawa da su ba,a nan fa ciwon hassada ya fara motsawa Jamil saboda yadda yaga Jamil fes baya cikin wata damuwa komai nasa cikin rufin asiri da wadatar zuci,ga kyau da cikar kamala irin ta matasan da suka san kansu, dakin da yake ciki ya bawa Jamil suka ci gaba da zama a tare, yayin da ya fara son jawo Jamil din a jiki yana nuna masa wasu kananun harkokinnasa da kawai ya cire masa tunanin wancan banzar dabi ar da ta sasu suka baro garinsu. To abin dai na Jamil ya yi sauki dan sosai ya kwantar da kai ya fara cin arzikin SULAIMAN duk da cewa ta ciki na ciki, to amma yanzu babu yadda zai yi saboda albarkacin sulen yake ci,duk da cewa a ransa yana jin cewa kome sule ya zama iyayensa ne suka zama sila shi yasa yake ji a ransa kamar duk abinda sule ya samu shima yana da hakki a cikinsa. Sannu sannu har gashi sun zama cikakkun samari, arzikin sule shine abinda ya fara sanyawa zuciyar Jamil ciwo,daga nan burinsa na baya ya tashi daga baccin da yayi,hakan yasa rana tsaka ya tashi ta kanas ya tafi har DAMATURU ba tare da sanin kowa ba ya janyo abokansa,a lokacin mahaifiyar Garba ta rasu,ko da suka zo sai suka kwantar da kai suka nunawa malam ilya cewa suma fa tuni sun shiryu har da neman gafararsa,hakan yasa suka ji dadi, sule shi ya rungumesu ya ci gaba da tallafawa rayuwarsu har da ta iyayensu, dan shima Kabir har mahaifiyarsa sule yasa shi ya dauko daga damaturu, sun hadu sun zama family daya jajirtaccen cikinsu shine sule,duk wani abu da za a ci a sha a hannun dan sule ne,yadda iyayen su su Jamil suke nunawa sule so yasa suka kuma tsanarsa a ransa,a cikin haka ne suke ya kammala dgree dinsa kasancewarsa me sa a yasa bai sha wahalar samun aiki ba,damar da ya samu yasa shi wargaje gidansu ya zama na zamani, sam. Aransa bai ji yana sin komawa birni ba dan acewarsa mutanen garinsu yake gani yake jin dadi a matsayinsa na maraya wanda bai da kowa a duniya. A yawan shige shigensu ne Jamil ya hadu da wani mutum me suna don, don karen masu kudi ne duk wani me ji da arziki yasanshi,tun da Jamil ya kula da irin kudaden da donnyake kashewa ahike nan ya zama cingim dinsa har dai daga karshe ya nuna masa hanyar da yake bi yake samun kuɗi,Jamil bai wani girgiza ba ya nuna masa ba matsala yana da abokan da zasu dinga yin aikin tare,ko da ya samu abokansa da maganar duka babu wanda yayi musu, duk da dai suna tunanin ta inda zasu fara ciro koda ko zuciyar mutum suna kaiwa iyayen gidan da don ya haɗa su da su to amma dake sun sawa zuciyarsu dakiya akan cewa zasu nemi kudi ta ko wace hanya sai basu ga wahalar abin ba,cikin kankanin lokaci suka fara wasa da kudade, daga nan likkafa ta ci gaba su ka fara kwacen gidaje da gonayen mutane a boye,kai tsaye suke sace mutum su kaishi tsakiyar daji su bashi biro yasa hannu a cikin takardun gonarsa bayan sun yi masa barazana da kisa,amma memakin idan mutum ya sa hannu su barsa sai kawai susa a farke ka a dauko musu zuciyarsa da kodarsa daga nan su tsallekeka su Barka cikin jini a mace. A cikin sati daya kawai sai a tsinci gawa sama da biyar, gaba daya kauyen ya rikice har wasu sun fara yin balaguro daga kauyen,take malam ilya ya fara dora zarginsa a kan yaransu, wanda sanadiyar ganowar ya rasa ransa ta hanyar bugawar ZUCIYA, Nana Asma'u kyakkyawar bafulatana ce me hankali da ilmin addini, sun dade suna soyayya da sule ba tare da kowa ya sani ba,sule yana gab da bayyana kansa wajen iyayen nana, shi kuma jamil ya hadu da Nana lokaci daya.ya nuna mata yana sonta amma sai ta nuna masa tana da wanda take so,bai yi niyar rabuwa da ita ba,ya ci gaba da bibiyarta ba tare da yasan wanda take so din ba,ana cikin haka kuma SULAIMAN ya samu karin girma wajen aikinsa tare da gida da mota,a bangare daya kuma harkar gunakinsa suna habbaka tare da companin taki da ya bude, hakan yasa kai tsaye ya tunkari mahaifin Nana da maganar son auren Nana da yake,nagartar suke da sanin halayensa na gari da kuma nutswarsa yasa a take a wajen mahaifin Nana ya bashi aurenta tare da sanar dashi juma a me zuwa za a daura auren,sun yi farin ciki da murna hatta da Anne sai da ta raba goron murna, alokacin kuma Jamil ba sanan sun yi tafiya. Jamil da Kabir da kuma Garba, sun yi tafiya me tsayi domin haduwa da wani iblishin matsafi, wanda wani abokin harkallarsu ya haɗa su dashi, acewarsa duk mutanen da suka hada hannu da sunduƙi to basu da sauran takaici domin duk abinda suka sa a gaba sai sun cimmasa, tsarin tsafin sunduƙi ya banbanta dana sauran matsafa saboda shi tsafinsa a littafi yake,wani littafi ne wanda idan zai baka shi sai ya rubutu kundinka na duk abinda ka aikata a baya da wanda zaka yi a gaba,da kuma sunaye da tarihin duk wanda suka taba cuta ko su ka zauna tare dashi, daga haka zai tsaface littafin ya baka shi ka je ka ajiye shi a waje na musamman kana bauta masa, sai dai sharadin sa ba me sauki ba ne,dan duk ranar da wani ya samu nasarar daukarsa ko budesa har ta kaisa ga karanta shafin da yake cikin littafin to tabbas rayuwar me littafin da shi kansa tana cikin matsala, tunda sunduki yake tsafinsa har izuwa lokacinnsu jamil ba a taba samun akasi ga sauran mabiyansa ba,shi yasa yake jin kamar tsafinsane yayi karfin da har ba a taba samun wanda ya taba littafin ko ya budeshi ba,tun daga wannan lokacin suka karbo littafin suka yi masa waje a dankareren gidan da suka siya a cikin babban birnin Gombe, Ko da suka dawo lokacin saura kwana uku auren SULAIMAN,a nan ne ya ɗebe su gaba dayansu ya kaisu gidansa da aka bashi a cikin wata unguwa me kyau da tsari sai dai anguwar akwai kananun talakawa masu rangwamen ƙarfi,tunda suka ga gidan sule sai suka tabbatar ashe duk buda hancin da suke masa wai su sunyi arziki aikin banza suke yi sai ranar suka gane cewa sule fa yayi musu nisan da tarar dashi sun tashi tsaye,saboda a ranar ne suka gano boyayyayun kadarorinsa da bankunan da yake amfani da su,sun dawo kauye cikin tashin hankali da tunanin yadda zasu yi su mallaki abinda yake hannun sule,kwatsam kuma sai wani abun baki cikin ya kuma faruwa, wato daurin auren sule da Nana Asma'u,ai Jamil saboda bakin ciki har sai da yayi kwanan asibiti,tunda ya fito kuma suka fara kulla wadda zata fishshesu, MAFARIN arzikinsu ke nan handama kwace fili gonaye gidaje , cire zuciya da koda, shine abinda suka mayar halattacciyar sana ar su,daga nan kuma suka samu mata suka aura daidai da rayuwarsu wato yan gayu masu budedden ido,suma sai suka tare a cikin wannan anguwar da sule yake shi da matarsa da su Anne,duk da cewa akwai layi biyu tsakaninsu da layin da sule yake, A hankali a hankali kauyen su sule ya koma kufai dan sun gaji duk sun gudu sun bar dukiyoyinsu dan kawai su tsira da rayuwarsu,hakan ba karamin farin ciki ya sanya aminan guda uku ba,take suka fara saka gwanjonsu suna sayarwa, a cikin haka ne kuma sule yayi bincike ya gano duk abinda suke aikatawa, ransa ya yi matukar ɓaci tare da yin Allah wadai da su har yana da nasanin barinsu zama a cikin kauyen,daga karshe yayi musu nasiha da tuna musu lahira,a lokacin nuna masa su kayi sun ji kuma sun yi nadama sannan da kansu zasu nemo ragowar mutanen da suka bar kauyen,musamman iyayen Nana da su ne wanda aka fara nema aka rasa, ya amsa musu ne kawai amma ba wai dan ya yarda da su ba,shi yasa ya ci gaba da bibiyarsu tare da sanya musu ido, dan yasha alwashin muddin ya kuma kamasu da lefi sai ya maka su a kotu,a wannan tsukinne kuma mahaifiyar Kabir itama ta koma ga mahaliccin ta, sai ya zama saura Anne kawai a manyan da suka rage musu. Nana ta samu ciki, kar ka so kaga farin cikin da sule yayi har da su Jamil ma,daga nan aka shiga tattalin Nana har Allah ya sauketa lafiya ta haifi zakin santalelen yaronta me kama da mahaifinsa kamar an tsaga kara,ba karamin murna suke yayi ba dan alokacin sai da ya raba kujerar Makka kusan ashirin saboda murna da jin dadi,talakawan da suke kewaye da shi kuwa ai kaf dinsu babu wanda bai juyawa talauci baya ba, wannan halin sule ne ba sai lokacin Zakka yake fitar da dukiyarsa ba,ajininsa ne san kyautatawa, shi fa bai ki ya baka ya rasa ba, wannan ita ce zuciyar imani,sai da mus ab ya kusa shekara biyu a duniya sannan matansu jamil suka samu ciki,sai dai banda zubaida matar Garba,lokacin da Garba yake sanar dasu irin damuwar da zubaida ta yi , sai kawai Jamil ya bude baki ya ce" ka ce mata itama ta fito a matsayin me ciki kuma ta tabbata duk sanda zata fito cikin mutane ta sanya kwarya a cikinta,a lokacin Garba ya amsa ne kawai ba tare da ya gane manufar Jamil ta yin haka ba, sai dai sun ƙaddara cewa duk abinda Jamil zaiyi yana da manufa kuma ta karuwa a gare su shi yasa duk abinda ya ce suke yinsa kai tsaye, Kwanci tashi asarar me rai, matar Kabir ce ta fara haihuwa bayan kwana goma matar Jamil ta sauka tana haihuwa ta ce ga garinku nan,cikin jini Abby ya dauki jaririyar ya dankawa Garba yana cewa"maza ka kaiwa zubaida daga yau wannan jaririyar yar zubaida ce da kai halak malak"cikin tsananin mamaki da rudewa Garba ya ce"me kake nufi Jamil?matarka fa ta mutu baka da tabbacin zaka kuma samun wasu yaran,ina ma lefin kace ta shayar da ita zuwa lokacin da za ka samu wata matar"dariya Jamil yayi tare da cewa kar ka damu abokina ai Ni ina da yaro mus ab shine Dana na kuma nasan Nana zata kuma haifa min wasu yaran dan haka kai kaje da wannan bamu da lokaci bana son kowa ya san wannan bayan mu ukun nan har matarka hudu kenan"sake da baki Garba ya bi jamil da kallo zuciyarsa cike da sake sake akan maganganunsa,to ya za ai matar sule ta haifa masa wasu yaran? sannan ya za a yi dan wani ya zama nasa ?" Dafa kafadarsa da aka yi ne yasa shi dawowa hayyacinsa, Kabir ne yayi masa murmushi tare da nuna masa cewa ya yi abinda Jamil ya sashi babu kome a ciki sai karuwa,jinjina kai yayi sannan yaja kafafunsa da suka yi masa nauyi ya fita daga dakin. Kowa ya gama dauka cewa adawiya matar Abby ta mutu tare da jaririnta,anyi baki cikin rashi kuma an yi farin cikin samu,ran kwana bakwai Abby da kansa ya radawa yarinya suna zahida,sosai Abby yake jin matukar son zahida a ransa sai dai ya riga ya sawa ransa cewa dole sai ka sadaukar da wani abun kake samun wani,dan haka ya dauki hakurin rashin matarsa da yarsa na zuwa lokacin da ya kayyade wa kansa. Jamil shi kadai yake ta shirinsa na ganin bayan sule,haka ta bangaren sule yana ta ci gaba da cigiyar iyayen nana da kuma bincike me kyau akan su Abby,Jamil bai sanar da su Garba shirinsa ba har sai da ya gama tsara plan dinsa daidai ta yadda ba zai samu wata matsala ba,kamar yadda suka saba sun bashi goyan baya tare da saka hannu wajen cika muradansu, Jamil ya kullaci sule akan abubuwa da dama,tun na yarinta har zuwa girma,musamman yadda ya kwace masa iyaye da kuma arzikin da ya samu, wanda shi a ganinsa suke bai dace da samun wannan daukakar ba saboda shidin almajiri ne mara gata, amma sai gashi sule ne ya samu abinda shi ya kamata ace yana dashi,kudi ta hanya me kyau matar aure me kyau, sannan ga iyaye daga sama, kai ina ai gatan yayi masa yawa dan haka dole ya kwace komai dole komai ya dawo hannunsa mata kudi da iyayensa dole su dawo hannunsa,amma yasan hakan ba zata faru ba har sai idan sule baya raye, shi yasa ya yanke hukuncin turasa lahira,kafin shi ya turashi magarkamar da yake shirin kaisa,saboda yana sane da duk wani bincike da sulen yake yi akansu saboda ya samu damar maka su a kotu,shi Jamil yasan shirin sule akansu amma shi sule bai san abinda suke shirya masa ba, A wata ranar alhamis ne,sule ya tashi da rashin kuzari inda ya dauki Nana suka fita ba tare da sanin kowa ba,sai bayan a wa daya suka dawo, itama nanan gaba daya jikinta a sanyaye yake,saboda abinda sulen ya gabatar mata dashi,dukkansu ranar basu wuni da kuzari ba,washe gari kuma ya shirya tsaf suka fito tare da nanan da take ta faman sauke hawaye, ji take kamar ta hanashi tafiyar da yake kokarin yi amma ba hali,gabanta faduwa yake sosai baran idan ta tuna maganarsa ta jiya me kama da wasiyya duk sai jikinta ya kuma mutuwa,da kuka da tashin hankali suka rabu da Nana da mus ab ɗansa daya tilo da yake matukar so. Tun da ya tafi Nana ta kasa nutsuwa duk mintuna biyar sai ta kirasa taji ya yake,shi fa kansa ya fara yi mata dariya yana tsokanarta da cewa,ko dai takaba kike tsoro ne nanata naga duk kin daga hankalinki,kuka ta saka masa tana cewa "bana son wannan kalmar da take fitowa daga bakinka in dai akan kiran da nake maka ne ba zan kuma kira ba har sai kai da kanka ka kirani"daga haka ta katse kiran taa share hawayenda suka bata mata fuska, sannan ta fara kokarin kawo walwala saman fuskarta saboda kawar da hankalin mus ab. A firgice nana tafarka tana laluben makunnin dakin, bakinta dauke da salati saboda mummunan mafarkin da ta yi,wayarta da ke kan bedsite drower ce ta fara kawo haske tare da ɗan ƙaramin sauti,cikin sauri ta dauki wayar ba tare da ta duba me kiran ba,dan a ranta yasan cewa sule ne kawai zai yi mata wannan kiran na cikin dare,sai dai a maimakon ta ji muryarsa sai kawai ta ji Muryar wani daban yana cewa,ke ce Nana Asma'u?"cikin rawar baki ta amsa da ey nice Ina me wayar me ya sameshi?"Hajiya kwantar da hankalinki dama cewa yayi ki yi hakuri kar kijisa shuru zuwa da safe zai yi kiranki"haka nan dan sandan ya ji ya kasa sanarwa da Nana halin da mijinta yake ciki saboda yadda yaji ta ba anutsewa kuma da alama ita kadai ce a inda take idan ya gaya mata komai na iya faruwa,zubawa wayar ido Nana ta yi zuciyarta na bugawa da saur da sauri kamar zata bullo ta fito,kasa komawa bacci ta yi , sai sallar da ta kwana tana yi akan Allah ya tsare mata mijinta a duk inda yake.......... [5/7, 7:09 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page51``* Juya wayar dan sandan ya dinga yi a hannunsa na tsawon wasu sakanni kafin ya maida kiran kan sunan Abby da ya gani kafin kiran Nana,wanda yake nuna cewa shine mutum na biyun karshe da suka yi waya da sule,dama Abby a shirye yake tsaf jiran kiran kawai yake yi,hakan yasa ana kiransa suka dunguma suka yo wajen gawar da shi da mukarrabansa, suna zuwa suka samu har an rufe sule da likkafani saboda gaba daya fuskarsa ta yi damege duk sanin da kayi masa baka isa gane shi a wannan yanayin ba,haka suka kwashi gawarsa suka.tafi da ita,driver kuwa shi gaba daya ya kone ko makamashinsa ba a samu ba sai toka. Basu yarda sun kai sule gida ba sai bayan sallar asuba sannan suka taho dashi, cikin yanayin tashin hankali da alhini,Abby ne ya ce a barshi da kansa zai fadawa Nana halin da ake ciki,babu wanda ya Musa masa, dan haka kai tsaye dakin Nana ya nufa inda ya tarar da ita saman dadduma tana ta shararo addu'a wa mijinta,kallonsa take cike da mamaki da kuma takaici na yadda ya shigo har dakin mijinta kai tsaye,Abby Sarai ya fahimci mugun kallon da Nana take masa amma sai ya basar tare da, sanar da ita abinda ya kawo shi kai tsaye babu lallashi babu kwana kwana ko kame kame,wani irin duhu ne ya mamaye ganin Nana,wanda a take annan ta zube babu alamun numfashi,cikin sauri Abby ya zaro tsumman tsafin da sunduƙi ya bashi ya sanya mata akan fuskarta,daga haka ya daga karkashin gadonta ya saka wata karamar kwalba ya mayar ya rufe,dariya ya sanya yana cewa shike nan na gama da babinki har abada ke da kara tuna wani sule a matsayin mijinki na baya a ranar da kika kammala takarbarki a ranar zaki zama matar Jamil burina ya cika saura kuma na bi na tattara kadarorin mijinki da duk wani abu da ya mallaka ya zama nawa"dag haka ya bar dakin yana sauya yanayinsa har da matsar kwalla,karo suka ci da mus ab da yake kokarin shiga dakin Nana,cikin sauri Abby ya kama hannunsa tare da shafa masa wani turare a saman kansa, cikin sauri mus ab ya rufe idanunsa saboda yadda warin turaren ya bugi kansa har ya shiga juyawa kamar wata fanka,a lokaci daya kuma ya bude idon, tozalin da ya fara yi da Abby shine yasa har rana irin ta yau yake kallon Abby a matsayin babansa sule kamar yadda nana take yi masa kallon mijinta sule. Kwana bakwai aka share makoki daga nan Abby ya nufi inda yake da tabbacin cewa kadarorin sule suna nan,sai dai me wayam yaga gurin ko biro bai samu ba bare wata takarda da zata nuna masa shaidar kadara,sosai hankalinsa ya tashi, to shin ina sule ya kai arzikinsa ko dai sun kare garin yiwa talakawa hidima,ya jima cikin zuzzurfan tunani,kafin ya bar wajen yana cewa in dai matarka ka bawa ko yaronka ai babu wata matsala tunda Dukansu a karkashina suke",wasa wasa fa abu yana nema zama gaske dan duk inda suke zaton sule ya wuce nan,kuma sun tabbatar da cewa sule boye kadarorinsa yayi,to a ina kuma yaushe?"kwafa su kayi tare da samun kwarin gwiwar cewa matar da dan duka yanzu suna karkashin ikon mus ab. ****** Suna zuwa nan a karatun suka dakata tare da dago kansu suna kallon juna, fuskar aminatu jiƙe da hawaye,mus'ab kuwa makwallatonsa zaku gani kawai ku gane yanayin da yake ciki,idan tunaninsu yayi daidai kenan Abby ba shine mahaifinsa ba?"aminatu ta ce ta kuma maida hankalinta kan littafin inda ta dawo kan shafin da hoton sule yake,zuba masa ido ta yi sai kuma ta yi saurin kallon mus ab tana cewa'daddy wallahi bai mutu ba shine yake kirana nazo na taimaka masa yana nan a raye shine babanka ba wannan azzalumin ba"ta karasa fada tana fadawa jikinsa tare da kankamesa kamar za a kwace mata shi,shi kansa mus ab jikinsa ne ya yi murus idanun babu abinda suke sai yaji tamkar an zuba barkono a cikinsu,zuciyarsa wani irin gudu take tana bugawa da ƙarfi. """"Zunbur Nana ta farka da ga dan baccin da ya fara saceta,ji ta yi tamkar ta tashi daga wani mummunan mafarki,tashi tsaye ta yi tana gyara daurin kallabinta da sauri ta dafe kanta da yake matukar sara mata,kafin cikin wani irin sauti me karfi ta fara ambaton sunan sule, dakin ta fara zagayawa cikin fitar hayyaci,ko mai ya dawo mata sabo amma dai tana da tabbacin mafarki ne ba gaske ba,da gudu ta fito daga bangarenta ta nufi dakin Anne tana shiga ta rike Anne tana cewa,"Anne da gaske sule na ya mutu, da gaske yayi hadari ya mutu ko gane fuskarsa ba ayi?"cikin tsananin mamaki Anne take duban nana, ganin dai nanan bata hayyacinta yasa ta rikota ta zaunar da ita a kusa da ita tana cewa,"haba nana me zai sa ki birkice akan mutuwar sule yanzu bayan sule tuni ya manta da zama turbaya saboda shekarun da a ka yi da mutuwarsa,tun fa mus ab yana shekara biyu a duniya sule ya mutu,to me zai sa ki dawo da hannun a gigi baya a lokacin da ake kan jimami ma kika hakura kika dangana dake da danki bare kuma yanzu da aka dau kusan shekara talatin da biyar"tunda Anne ta fara magana Nana ta zuba wa bakinta ido, a take kuma komai ya dinga dawo mata tun daga kan abinda Jamil ya shaka mata har zuwa aurenta da ya sake yi da rayuwar da suka yi da ya'yan da suka haifa dashi,to me yasa a lokacin ta ke kallon abby a matsayin sule?tabbas akwai wani abu da ba daidai ba, tabbas akwai wani biyayyan al'amari game da kome da ya shafi rayuwarsu ita da danta, sannan mutuwar mijinta ma lallai akwai sa hannu a ciki,kallon da Anne take mata ne yasa ta miƙewa cikin sanyin jiki tare da cewa,ki yi hakuri Anne wani mafarki nayi mara daɗi shi yasa kika ga duk na birkice"daga haka ta fice daga dakin tana share hawayen da suka kasa tsayawa. Ganin kukan aminatu yawa yake kuma yi dan har ya fara saukar mata zazzaɓi yasa mus ab ya nuna jarumtar nan tasa da dakiya na kokarin ɓoye firgicinsa ko tashin hankalinsa,ya juyo da ita tana fuskantarsa,hade fuskar sa yayi da tata, sannan cikin muryarsa da a yau ta bayyana halin da yake ciki ya ce"princess me yasa kike kuka haka da yawa?"bata san sanda ta antaya masa wata irin harara tamkar idanunta zasu fado ba, kana ta tura karamin bakinta tare da kokarin kawar da fuskarta daga kallonsa,amma sai ya sanya hannunsa ya rike fuskar yadda bata isa juyawa ba,a hankali ya sanya harshensa ya ɗan lashi labbanta da ya ga alamun bushewa a tare da su,lumshe idanunta ta yi tana jin wani irin yam a jikinta kafin ta yi saurin shigewa cikin jikinsa ta naɗe sai kace wata yar mage,hannunta ta dora a kan fuskarsa tana shafawa a hankali,rike hannun yayi yana cewa"ke eee so kike karatun ya tashi daga nan wata matsalar da zata hanamu karasawa ta bullo"?kallonsa ta yi idanunta suna wani shigewa ciki kamar wadda ta sha abin maye,wanda hakan ya kuma birkita lissafin mus ab,jikinsa har wani tsuma yake wajen kokarinsa na haɗe bakinsa da nata,sai dai bata bashi damar hakan ba saboda sautin zamewa da tayi daga jikinsa tana wani rangwadar da kai tare da cunno jajayen lips ɗinta gaba tana wani kif_ƙifta ido cikin kallonsa,sumarsa ya ɗan shafa yana lumshe idanunsa alokaci daya kuma yana cewa,kin tada wutar da kasheta cikin sauki ba mai yuwuwa ba ne,kuma kin gudu?"shafa cikinta ya yi ba tare da ta tankawa maganarsa ba ta ce"daddy yunwa nake ji abinci zanci,amma bana so ka.sake fita ka barni Ni daya ba zan iya ba kashe Ni za suyi, Dan kaine baka sani ba yau a dakin nan yaƙin duniya na farko a ka yi a ciki?"yanayin da fuskarsa ta nuna kadai zaka fahimci cewa murmushin ciki yayi wanda bai bayyana akan fuskarsa ba. Matsawa ta yi da dashi tare da sanya hannunta akan fuskarsa ta ce, daddy me yasa baka son yin dariya ko murmushi nasan zai yi maka kyau tunda kai me kyau ne,WLh daddy Ina son murmushinka Ina son muryarka bare kuma ƙamshinka da yake sani cikin wani yanayi, dan Allah daddy ka fada min meye ne abinda nake ji a raina game da kai,uhm ji nake fa kamar zan mutu idan....sai kuma ta yi shuru tare da kwanciya a kan kafafunsa, sannan ta janyo littafin zata bude,yayi saurin rkiewa ya dakatar da ita,kana cikin rarraba kalmar da zai fada ya ce"me zaki fada kika fasa?"maimakon ta bashi amsa sai kawai ta yi wani irin juyi a jikinsa take mus ab ya ɗauke numfashi saboda juyin da aminatu ta yi sai da ya tabo masa sirrinsa,ita ko bata san hakin da ta jefa ɗan gidan nana ba, dan haka cikin kwanciyar hankali ta bude shafun gaba ta dora daga inda suka tsaya,shima din zubawa shafin da ta bude idanun yayi. *********** Tunda abby ya juyar da hankalin Nana da mus ab,shike nan ya ci gaba da cin kare masa babu babbaka harkoki kuwa sabbi aka buɗe, ko da yaushe da irin sabon kasuwancin da zai bullo musu,duk da irin manyan kudaden da suke samu amma hakan bai wadatar da su ba,dan sun ce har yanzu burin su na yin kafada kafada da manya kuma kusoshin gwamnati da masu mulki bai cika ba,dan haka suka kara bude kofar zaluncinsu,lokaci daya suka.gina wasu irin manyan gidaje masu kyawun tashin hankali,a cikin anguwar da ta kasance ta talakawa masu karamin ƙarfi,wanda sun yi haka ne da manufar su ta kara samun abinda yake kawo musu Kudi,cikin boyayyiyar fuskarsu su ka fara janyo talakawan da suke kewaye da su jikinsu,inda suka samu galaba suke yi musu dauki dai-dai. A haka har aka ja shekaru Nana ta samu karuwar yara har uku bayan mus' ab,isma shine me bin mus' ab,sai suleman wanda aka sanya masa sunan marigayi sule, sai suhaima autarsu,matar Kabir ma ta kuma haifar da namiji,tunda ga sannan kuma babu wadda ta kuma yin ko batan wata,zubaida dama tuni ta cire rai da haihuwa shima Garba be sa abin akansa ba,a haka rayuwa ta dinga tafiya da abubuwa masu tarin yawa. Duka yaransu su suka zaba musu abinda suke son su karanta, dama ita zahida burinsu da ya shi yasa basu sha wahala akanta ba,akan musu ab ne suka dan sha wuya kafin ya hakura ya bar burinsa ya karbi nasu ya je ya karanci kasuwanci. Har zuwa yau din nan su Abby ba su daina tunani da binciken neman inda suke ya kai kadarorinsa ya biye ba, kullum kansu da da kullewa yake akan dukiyar sule,sai dai sun kasa karaya da hakan . Babban asibiti suka gida suka fara da taimakon mutane da basu magani kyauta, kai duk wata hanyar yaudara sai da suka yi ta akan asibitin nan, inda kuma suka samu nasarar kama.kutame a hannunsu,da wannan damar su kayi amfani suka yaye kansu daga hannun ubangidansu, suka suka gina kansu ta hanyar zama masu gidan kansu,lokacin da zahida ta dawo da nata halin da kuma burinta sai abin yayi musu dadi, sai da suka dan yadda su kayi suka hada aure tsakaninta da mus' ab, sannan ta fara aiki a asibitin gjk,babu wanda suka.yadda dashi akan kasuwanci su shi yasa basu sake jiki ma aikatan asibitin sun san me suke aikatawa ba,likitoci biyun da suka san me ake yi suma siyansu su kayi da kudinsu kuma suka basu ilimin da kudinsu,dan haka basu taba kokarin tona musu asiri ba. Sunduƙi da kansa ya basu hutu ya kuma yin musu misalin lokacin da ya kamata su dawo gareshi, wannan shine ka idar aikinsa baya so ka kuma waiwayarsa sai masifa ta tunkaroka. Nana da mus' ab kuwa tamkar an goge musu tarihin rayuwarsu a cikin kwakwalwarsu ne,dan kuwa basa tuna kowa a matsayin uba da miji idan ba Abby ba. Cikin nutsuwa aminatu ta dago da kanta ta kalli mus ab da idanunta suka yi ja sai dai tas ya shanye baki cikinsa da damuwarsa,hannunta ta kai saman dogon hancinsa ta ɗan ja tare da cewa, wannan shine tarihin abbanka daddy,a yanzu na riga da nasan yadda zuciyarka take zafi, sai dai kuma Ni nayi farin ciki saboda na tabbata Abba bai mutu ba kuma in sha Allah sai nayi addu'a akan Allah ya bashi ikon sanar da Ni inda zan samesa kamar yadda take son sanar dani"jinjina kansa kawai yayi tare da maida bayansa jikin makarin gadon yana rufe idanunsa da suke masa wani irin yaji......... Itama kwantar da kanta ta yi a jikinsa tana jin wani irin mugun tausayinsa da shi da babansa har ma da Nana. ******* Su Abby kuwa tunda su aminatu suka.fara karanta shafin nan suke ganin Bala U kala kala,daga inda zasu ji ana kiran sunansu, sai inda zasu dinga ganin inuwa tana gifta musu,kai har da kukan jarirai,ga wani irin azababban ƙaikayi da jikinsu yake yi babu abinda suke sai soshe soshe,gaba dayan su suna tare dan basu yarda sun rabu ba dan a halin yanzu dukkansu sun fara shiga cikin tsoro da firgici na halin da suka tsinci kansu,basu suka dawo hayyacinsu ba har sai da su aminatu suka gama karanta labarin sule,wanda hakan yasa su hanzarin komawa wajen sunduƙi dan nemo mafitar da ya ce musu zai yi idan shafin sule ya kare. Tunda Ahmad ya samu ya subce daga wannan gidan yake gudu ba tare da waiwaye ba,duk da cewa babu kuzari a jikinsa amma haka yayi ta maza ya ci gaba da gudu,bashi ya tsinci kansa a titin ba sai da gari ya fara duhu, daga nan ya samu me nafef ya kwatanta masa gidan cp Musa. A bangaren kasuwancinsu fa komai ya tsaya dan tunda suka fara shiga wannan matsalar harkallar da ake a cikin asibitin ta tsaya cak, to dama ba mutum ne yake kawo kansa ba sune suke kawo mutum cikin sigar yaudara, shi yasa yanzu da basa cikin hayyacinsu asibitin ya zama kamar makabarta saboda shurunsa. Halin da suka tarar da sunduƙi shine abin da ya fara girgizasu tun tsawon rayuwarsu,tabbas idan suka ce basu taba ganin abin tsoro da al'ajabi irin wannan ba ba suyi karya ba,ja da baya suka dinga yi cike da tsananin tsoron da basu taba jinsa acikin zuciyarsu ba...... 500 only 8061537048 Fatima yusha'u Adam Opay [5/9, 3:55 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page52``* Ba kome ne yasa su wannan razanar ba, sai ganin sunduƙi da suka yi cikin yanayin ban tsoro da tsananin wahala,gaba daya rabin jikinsa ci yake da wata irin bakar wuta me tsananin zafi,rabin kuma gaba daya wasu irin bakaken kunamu ne suka baibaye shi,kansa kuwa yayi wani irin girma kunnensa wasu irin kananun kwari ne suka cika kunnen suna shigewa har can cikin tsakiyar kansa,idanunsa kuwa wasu irin hawayen jini ne suke fitowa saboda tsananin azaba, dadin karin tsoro shi ne yana nan da ransa,dan har baki ya bude yana son yi musu magana amma sai ya kasa, babu abinda yake sai juya kansa saboda jikin ma ya kasa motsashi,a hankali a hankali suka dinga ja da baya saboda shi kansa kogon ba zai shigu ba saboda tsananin zafin da ya dauka,Abba Kabir ne ya bude baki cikin tsananin firgita da tashin hankali ya ce"me yake shirin faruwa ne me ya samu sunduƙi?"daga can suka ji wata murya na magana cikin zafi da takaici tana cewa,"haba jaruman duniya ya haka da saurin tsorata, to wannan ai kadan ne da ga cikin irin ikon Ubangiji wannan fa ba kome ba ne iya duniya ne fa ba aje can ba,dan haka kar ku wani damu ku ci gaba da yin kome ba kome ba ne kunji yan samari"daga haka Muryar ta dauke ɗif, cikin tashin hankali Abby ya kama hannunsu dan komawa inda suka fito sai dai kuma sihirin nasu ya ƙi sunyi sunyi amma hakan ya gagara,haka dole suka fara tafiya suna ratsa baƙin dajin da babu kome a cikinsa sai tashin hankali da ababan ban tsoro. Yau zahida tunda ta tashi take jin wani irin firgici da tsoro a ranta ga shi jikinta har yanzu bai daina radadin ciwon ya yakushin da tasha jiya ba,dan gaba ɗaya jikinta yayi ruɗu ruɗu,zaman falo ta sauko saboda tsoron zama ita kadai da take, gashi asibitin ma ta kasa fita saboda tsoron abinda zata je ta tarar,kowa na gidan sai da yayi mamakin ganin zahida a falo, babu wanda ya tanka mata kamar yadda babu wanda ta tankawa,sai dai kowa ya fahimci tana cikin tashin hankali,daga ƙarshe kuma tunanin zuwa gidansu ta yi ko ta samu sassaucin abinda take ji idan tana kusa da mamanta,dan haka ta dauki key mota ta fita ta bawa m jauro driver akan ya Kaita,bai musa ba dan dama ba su isa musawar ba. ****** Baccin da ya daukesu ba wani me nauyi ba ne,dan shi mus ab ma ba baccin yi ba yana ganinnta samu baccin ya mike ya hau saman kujera ya bude laptop din da ya shiga rage aikin da ya cunkushe masa, daga ɓangaren aminatu kuwa farkawa ta yi cikin mamakin mafarkin da ta yi,duk da cewa ta wani bangaren ba abin mamaki a ne idan tayi la'akari da yadda ta sanya abin a ranta, Addu'a ta yi kafin ta sanya idanunta akan mus ab da yake ta shigar da wasu muhimman aiyuka ta cikin laptop din, dafe kanta ta yi tana ɗan yatsina fuska alamun dai kan yayi mata nauyi,duk da cewa idanunsa na kan abinda yake yi amma hankalin sa tuni ya koma kan aminatu tun bude idanunta, "what happened?"Ya tambayeta idanunsa na kan wayarsa,tashi zaune ta yi tanà dan cije lips ɗinta, bata ce masa kome ba,rufe laptop din yayi kana ya miƙe a hankali ya dawo kusa da ita tàre da kama hannunta yana ɗan matsa shi ta yadda zata ji daɗi,bude idanunta da suka yi wani luuuu dasu ta yi tana kallon kyakkyawar fuskarsa me cike da kwarjini da haiba."mafarki"?ya fada yana kallon fuskarta da kyau,kwantar da kanta ta yi à kafadarsa tana ji wani irin rauni à ranta, babu abinda take bukata a yanzu sai zuwa ga abban mus' ab,duk da cewa a afarkin da ta yi ba wai ya sanar dà ita kai tsaye inda yake ba ne,to amma tana jin yadda da zuwa inda matar mafarkinta ta gaya mata da ta je,in sha Allah zata je Kuma zata dawo dashi duk da cewa bata san garin ba kuma bata taɓa zuwa ba,amma tunda garin sananne ne tasa ba zata sha wahala ba tunda Allah ne ya nufeta da zama sanadi tasan ba zai barta ta wahala ba zai dafa mata wajen cimma burinta,shafa fuskar ta da ƴayi ne yasa ta jan dogon numfashi tana dora hannunta akan nasa hannun da yake saman fuskarta,shafa cikinta ta yi tare da dan tura karamin bakinta ta ce"daddy yunwa nake ji?"bai ce komai ba yajanyeta daga jikinsa yana miƙewa tare da barin dakin gaba daya,yana fita ta janyo littafin ta ajiyesa gefe guda da niyar ko cikin dare ne zata farka ta ci gaba da karantawa ko Allah zai sa ta ci karo da abinda ya shafi babin nata rayuwar. ****** Su Abby sun sha matukar wahala kafin su fito daga cikin ƙungurmin dajin nan,zuciƴarsu ta wahala matukar wahala kuma sun ji jiki iyakar jin jiki,sai da suka gansu a cikin motar da zata kaisu cikin garin gwambe Sannan hankulansu suka fara dawowa jikkunansu,duba daya zaka yi musu kasan cewa sun ji jiki,babu wanda ya tanka ko da da karamin tari ne sai dai maganar zuci, ko wannensu da abinda yake saƙawa wanda yake ganin zai zama mafita a gare su baki ɗaya, a cikin wannan yanayin suka karasa garin inda suka umarci me motar da ya kaisu gidan gonar su,kasancewar daukosa suka yi drop.yana ajiyesu suka shige ciki daddy n zahida ne ya dawo hànnunsa dauke da bondle kudi yà mikawa me motar sannan ya koma ciki,haka mé mota yàja ya tafi yana murna yau kakarsa ta yanke saƙa,sai da su kayi wanka suka ɗan ci abinci sama sama sannan suka zauna mittin ɗin yadda zasu ɓullowa a al'amarin tunda komai ya riga ya kwaɓe dole sai dai su sake sabon shiri. Daddy Garba ne yayi gyaran murya tare da fara magana kamar haka,"Ni dai a nawa nazarin gani nake mu nemi wani matsafin tunda sunduki ya gaza ƙarshe dai tasa ta ƙare ko ya kuka gani?"ya fada yana dubansu dan jin amsoshinsu da kuma yadda zasu karbi shawarar tasa,girgiza kai abba Kabir yayi kana yace"gaskiya ku hakura da batun mutanen nan dan Ni gaskiya abinda ya faru da sunduƙi yasa naji rashin yadda akansu, dan ƴadda àbín ya kasance ya bani tsoro matuka , kun dai ina dai kura zàta yi maganin zawo to kantà ya kamata ta fara yiwa kuna ganin yadda sunduƙi ya ƙasance ya kasa yiwa kansa taimakon kome aƙan halin da yake ciki kun ga kuwa taƴaya mu zai iya taimaka mana,shi yasa na dawo daga rakiyarsu idan zamu nemawa ƙanmu mafita mu nema idan kuma muka nace sai matsafa ne zasu taya mu to wallàhi muna cikin matsala babba,dan wallahi ni yanzu ma nake jin cewa kamar duk abinda ya ke fada mana karya ne"sai a nan Abby ya numfasa tare da amsar maganar da abba Kabir yake yi da cewa,"tabbas ƙabir maganarka na kan hanya amma fa duk a binda ßunduki ya fada gaskiya ne,ƙawai dwi wannan abin da ya faru dashi ne yasa muka gane cewa ba zai iya taimakonmu akan wannan bala in da muke ciki ba,kunga kenan dole mu sanja salo da taku muyi da karfin mu da dabararmu domin ceton dukiyarmu dà rayuwarmu da kuma gujewa fadawa babbar masifàr TALAUCI wadda shine asalin fadawarmu wannan hanyar"daddyn zahida ya ce "haka ne maganarku amma ni nasan duk abinda ya faru mu muka jawa kanmu dan kuwa da ace mun yi koyi da sule mun tashi mun nema kuma mun yi haƙuri da kaɗan da yanzu mun zama kamarshi,àlókacin nan nasha faɗa muku cewa muma mu dinga gwada yan dabarun da yake yana samun na kashewa ko dako ko aikin leburanci ko wanki da guga ko garuwa, amma ku sài kuka nuna mun fi karfin yin irin wannan sana o in,sabodà alokacin tuni zuciyarmu ta riga ta mutu kuma mun sawa ranmu cewa wannan kananun sana o in ba zasu kawo mana arziki dare daya kamar yadda muke so ba,to kuma abin mamaki sai gashi da sana o in da muka raina din da su sule yayi arziki har ya kere mu dan na tabbata da cewa idan sule bai fi mu ba to muma ba za mu fishi ba, yanzu dai ga abinda girman kai da rainuwa suka jawo mana"yw kare maganar cikin rauni kamar wamda ya fara yin nadamar ABUBUWAN da ya aikata.duk shuru su kayi ba tàre da sun ji haushin maganar Garba ba saboda sun san gàskiya yà fada to amma ya su kayi dole sai ta wannan hànyar ne zasu yi àrzikin amma yanzu tundà sun samu abinda suka samu zasu iya ajiye komai àmma fà sai bayan sun ga bayan makotansu dan kuwa duk wanda yake son sanya shi cikin bala i da wahalar TALAUCI wallahi sai sun kawar da shi a duniya koda ya haɗa da mus ab dinne,tunaninsu daya ne dan haka suka ɗago suka kalli juna a tare tare da jinjina kaii. Abby ne ya gyara zama tare da cewa,"yanzu dai duk ba wannan ba, me ye mafita?"Kabir ya ce "ai kai muke sauraro tunda kai ne uban tafiya kasan tun muna yara kai ne me kawo shawara mu kuma mu bi"cikin jin dadin maganar abby ya ɗan murmusa kana ya dora da cewa "idan har muna son dakatar da duk abinda yake faruwa to fa lallai sai mun samu kan mus ab ma ana dole sai mun karbe duk wata sheda dake hannunsa na farko dai littafi sai kuma camara da kuma takardun da anita ta debo,duk da nasan cewa ba su kadai ba ne amma wann6sune masu muhimmanci a wajen mu bamu da matsala ta bangaren shedun mutane tunda dan ladi yana hannun mu,waccan matar kuma har yanzu baku san inda take amma fa ji a raina tana tare da wancan tsinannan yaron,kun ga kenan idan har muka yi garkuwa da abu mafi soyuwa a gareshi duk zamu fanshi kanmu"abba kabir ne yayiwa Abby wata junjinar ban girma kafin ya ce "wannan shawara ta yi sosai ma kuwa sai dai kuma kasan waccan aljanar yarinyar ce kadsi zamu sace mus ab ya gigice gashi kuma bamu da zarrar dauke aminatu na farko dai itama aljanar kanta ce sannan kuma tana tare da mus ab wanda shima wata babbar kariya ce a gare ta"wata banzar dariya Abby yayi tare da jingina da kujerar da yake kai, yana cewa"idan har kun amince da shawara ta to ku zuba min ido ku bi ni kuga yadda wasan zai kasance"ya fada yana dora hannunsa akan table din da yake gabansa,babu mata lokaci daddy Garba ya dora nasa a saman na abby sannan shina Abba Kabir ya dora nasa.daga nan suka mike kowa ya dauki mota daya daga cikin motocinsu da suke zube a gidan kowa ya nufi hanyar gida. Tana ajiye littafin ta muke ta shiga bathroom ta dauro alwala tana cikin sanya hijab ya shigo hannunsa dauke da leda me tambarin zababs restorent, kowane fuska ta yi tana kallonsa cikin tuhuma,sarai ya gane me take nufi amma sai ya basar ya wuce ya ajiye ledar shima ya fada bathroom din Dan dauro alwalar magriba,tsayawa ta yi tana jiransa fuskarta kuwa har yanzu a shagwabe take,yana fitowa ya ja musu sallar bayan sun idar suka yi addu'ar su da karatun shafi Daya na alkur ani,daga nan ya janyo ledar ya bude ya dauko mata abincin da yake ciki tare da budewa, spoon ya dauka ya shiga bata abaki bai kyaleta ba har sai da yaga ta kawar da kai daga nan ya bata madara tasha, sannan shima ya dan ci kadan dan baya jin text din bakinsa ko kaɗan, yana ajiyewa yaga ta maida hannunta cikin abincin ta kuma debowa bakinsa ta kai tana yi masa alamun haaa irin yadda ake wa yara dai,kafada ya makale alamun ya a'a,turbune fuska ta yi ta kuma dauke hannunnata, dole haka ya bude bakin ta zuba masa abincin,loma daya biyu a ta uku ya rike hannun tare da lashewa, karkatar da kanta ta yi kafin cikin sanyin murya ta ce"Daddy ina son ganin Nana"jan ta yayi suka miƙe tsaye bai yi magana ba sai hannunta da ya kama suka shige bathroom,yana ƙoƙarin cire mata kaya dan ta samu ta yi wanka ya fara amsa mata dan janye hankalinta,Nana tana lafiya Bamu jima da yin waya ba itama innswuro suna lafiya babu wata damuwa"ta gansu da abinda ya fada amma a bangaren Nana sai take jin faɗuwar gaba haka nan take ji kamar akwai abinda yake shirin faruwa,sanyin ruwan da ta ji a jikinta ne yasa ta jan ajiyar zuciya me sanyi,ware manyan idanunta ta yi kafin kuma ta yi wani irin tsalle ta rungumesa tana girgiza kanta tare da dukan kirjinsa, kana ta ce"Daddy mintinanka nawa kana kallo na wannan ina da ina ka kalla?"uhum ya fada yana son rabata daga jikinsa,ganin taki yarda yasa shi cewa"dago na nuna miki abinda na gani"rashin wayo irin na aminatu tuni ta dago kanta tana baza ido taga abinds ya gani ɗin,da wannan damar yayi amfani ya hade bakinsa da nata, ya kuma zura hannunsa daya ya kewaye kugunta,daya hannun kuma ya dauki sabulu ya shiga murza mata ajikin... Kai tsaye Abby bangaren Nana ya wuce,yana daf da shiga dakin sai ya ji kamar ana magana hakan yasa ya ɗan dakata,"kayi hakuri ba wai na ki waiwayar dukiyar mus ab Dan ina sane ba ne sai dan bana hayyacina kai na ma manta da Ni wace ce,amma yanzu in sha Allah kome ya zo karshe me abu ya kawo girma da hankalin da zai iya rike dukiyarsa dan haka zan sanar dashi kome, tunda shi kansa bai san komai ba,"bum ta ji an bankado kofar an shigo,tana daga ido ta ga abby tsaye yana sheka mata wani irin kallo,karasowa ya fara yi gabanta hakan yasa ta yi saurin goge nomber da ta yi kira, tana mai ja da baya dan gani ta yi abby ya dawo mata asalin jamilun da ta sani......... 8064537048 0pay Fatima yushau adam 500 only Zahra✍️ [5/10, 12:14 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page53``* Tun tana ja da baya har ta kai ƙarshen bango wanda hakan yasa dole ta tsaya tana kallonsa, yana ƙarasowa inda take ya sa hannu ya shaƙe wuyanta yana cewa "tsawon lokaci ina ta bulayin neman inda sule ya kai dukiyarsa ashe ina tare da me dukiyar hannu ban sani ba,ashe tana wajenki munafuka macuciya ,wato kin gwammace ki bawa wani can a duniya ya adana miki dukiyar akan ki bani na juya har zuwa lokacin da mus ab zai buƙaci kayansa,yadda ya shakure wuyanta yasa ta dinga kici_kicin ƙwacewa numfashi ta na fizga tamkar zata mace,magana ta ke son yi amma ta gagara,sai da yaga tana neman mutuwa sannan ya yi wani irin watsi da ita tamkar yayi watsi da shara,sai da goshinta ya fashe amma duk da haka bai raga mata ba ya kuma binta zai taka ta ƙafarsa da take sanye cikin wani arnen coversue, sai kuma ya dakata kamar wanda ya tuna wani abu,hannu yasa ya dagota ta mike tsaye jikinta har bari yake saboda tsoronsa,hijabin Sallah ya dauka ya zura mata sannan ya nuna mata hanya ba tare da ya damu da jinin da yake zuba daga goshinta ba,a hankali take takawa kamar wadda kwai ya fashewa a ciki,bai fita da ita ta asalin kofar falon ba,sai ta can wata kofa da basu taba sanin da ita a cikin gidan ba,a bin mamaki baya karewa dan wata kofar ce Jamil ya kuma budewa wadda zata kaisu har waje ba tare da kowa y gansu ba,kai tsaye ya je fata cikin motar da ya ajiye a wajen tunda babu wanda yasan y dawo gidan saboda tanan ya shiga gidan kuma suka fito tanan,a hankali yaja motar suka bar anguwar gaba ɗaya,Nana bata san me Jamil yake nufi da ita ba, dan bata taɓa tsammanin duk iskancin Jamil zai iya sace ta dan cimma burin sa ba. Sai da ya tsaya ya sanya kyalle ya rufe idanunta ya daure hannunta sannan ya ci gaba da tafiya,ji ta yi kawai sun tsaya daga nan sai ji ta yi ya janyo ta kamar wata dabbar da za a yanka,bata fahimci komai ba baya ga ƙuntataccen dakin da ya watsata a ciki, alamun tsugunnawarsa ta ji a gabanta sai Kuma sautin Muryarsa da ta ji yana cewa,"zaki zauna anan har zuwa tsawon lokacin da zaki fanshi kanki ta hanya guda biyu,na farko zaki sa danki ya bani duka hujjojin da suke hannunsa kama da daga kan takardu mutane camaras dan nadan ba za a rasa wata a wajen sa ba bayan ta hannun ɗan ladi ba, ina so duk kankantar sheda ta dawo hannunna, sannan ke kuma ki bani duka abinda sule ya baki wanda ya danganci manyan gidaje gonaye da filaye da kuma tsabar kuɗin da ya bari duk ki bani su a hannuna,ni kuma zan barki keda danki, surukarki kuma zai bani ita ta zauna a hannuna har zuwa lokacin da wanda ubanta ya dankawa dukiyarta a hannunsa ya bayyana sai na dawo muku da ita dan ni babu ruwana aurensa da ita,bukatata kawai dukiya daga nan zan fita daga rayuwarku gaba daya,amma muddin kuka ce zaku wulaƙanta ni ta hanyar hanani arziki wallahi sai na kashe ku gaba dayanku yankan rago zan yi muku ba tare da tausayi ko imani ba"daga haka ya miƙe ya cire mata daurin da yayiwa fuskanta da bakinta da hannunta ya juya zai fita amma sai yaji Nana ta kyalkyale da dariya irin ta tura haushin nan,dakatawa yayi tare da juyawa yana kallonta ta cikin dan hasken da ya taso ta wajen dakin,sosai yake mamakin dariyartata kafin kuma ya tsinkayi muryarta tana cewa"jamilu ai kayi sake wallahi ka yi sake,sai yanzu na gane nufinka na kawo mana aminatu cikin gidan ashe kai da mummunan nufinka akansu ita da kakarta wato saboda kakar bata da amfani a wajenku shi yasa ku ka fara kokarin kasheta ta hanyar cire mata zuciya sai kuma Allah ya tsareta domin bai nufi mutuwarta a wannan lokacin ba"wani makirin murmushi ta yi sannan ta dora da cewa, "jamilu ba kanka ka kawowa aminatu ba ,mus ab ka kawowa aminatu, shin baka yi tunanin ta yadda aka yi aminatu ta zama matar mus ab ba?ko lokacin da ka ji baka yi tunanin mus ab zai iya kasancewa shi ne dan birnin aminatu da ta yadda ta shigo birni saboda ta neme shi ba?girgiza kai ta yi tana cewa "Wallahi jamilu kai sakarai ne kwakwalwar ka sam bata ja, to idan baka sani ba daga yau ka sani mus ab shine mijin da uban aminatu ya daura mata aure da shi a can riga tun tana yar shekara bakwai zuwa takwas, kuma shine wanda ya damkawa ragamar dukiyar aminatu idan......marin da ya dalla mata hagu da dama shine ya katse maganarta, rike fuskarta ta yi tana kallonsa ba tare da tsoro ko nadama ba,kafin ta ce "wallahi jamilu idan ka bari ka mutu da wannan babban zunubin akanka ka shiga uku, jamilu ka tuba tun kafin lokaci ya ƙure maka Allah gafururrahim ne zai yafe maka nasa lefin da ka yi masa,daga nan sai ka ji da hakkin rai da ka dauka wannan zai sa ka samu rangwame daga azabar Ubangiji domin shi tuba nasuhan yana da ladansa na musamman da Ubangiji ya tanadarwa me yinsa,shi kadai ya isa ya rage maka zunubin hakkin ran da ka ɗauka,ka ga ko a lahira sun ji kanka sun yafe maka,.amma in dai har baka tuba ba Wallahi ina tausaya maka daga nan duniya har zuwa lahira...."dan ubanki idan ke ki ke bada aljanna sai ki hanani"ya fada yana kai mata hari da ƙafa saboda hankalinsa ya kuma tashi babu abinda yake sai zufa bai taba zaton ko a mafarki zai kasance mus ab shine wanda suke neman dukiyar aminatu a hannunsa ba. Nana ce ta katse masa tunaninsa ta hanyar cewa "jamilu bani da wuta kuma bani da aljanna sannan Ubangijin da ya halicci samaniya da kasa ya halicci duniya da abinda yake cikinta shi kaɗai yasan ɗan wuta da dan aljanna, Ni dai kawai nasiha nake maka kamar yadda Ubangiji ya umarce mu da yi idan kuma abin ya fi karfinmu sai mu kawar da idanunmu muyi addu'a"cikin wani irin zafin da yake taso masa tun daga kasan zuciyarsa ya ce"tunda kin san da haka ki min shiru,dan baki sani ba sai ki ga ni na shiga aljannar ke kina can kasan wuta "wa'iya zubillah ta fada tana runtse idanunta kafin ta budesu cikin yanayin jarumta ta ce "dama ku yan adam kuna amfani da fadar Allah wajen saɓa masa, kar fa kayi amfani da wannan hadisin da yake cewa (saura taƙi kaɗan ka shiga wuta sai ka kasance kayi aiki irin na yan aljanna sai ka shigeta,kuma saura taƙi kaɗan ka shiga aljanna sai ka kasance ka yi aiki irin na yan wuta sai ka shigeta Allah ya yi mana tsari da ita)kar ka yi duba da haka ka ce zaka sabawa Ubangiji saboda kana taƙamar zai yafe maka, to idan ya kasance mutuwar ta yi maka hanzari fa? kasan fa mutuwa baazata ce babu wanda yasan lokacin da zata daukesa"wani uban tsaki yayi sannan ya fice daga dakin tare da rufe ta, take ta daina ganin haske ko ƙanƙani ko tafin hannunta bata gani,saka kanta ta yi cikin gwiwoyinta tana addu'ar fita daga tsananin musiba,innalillahi wa inna ilaihi raji un, la ila ha illahuwar azimul halim,sai kuma ta ci gaba da karanta Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan wa anta taj'alal huzna Iza ma shi'ita sahlahu.duk tsananin masifar da mutum ya shiga ya karanta wannan addu'o in in Sha Allah Allah zai kawo masa mafita da sauki cikin lamarinsa. Tunda ya bar dakin ya shiga Mota yayi shuru ya kasa jan motar,saboda maganar Nana ta shigesa kai shi fa ko maganar sanin mus ab ne br unknown bai daga masa hankali irin sanin da yayi cewa shine mutumin da ya jima yana nema ba,dafe kansa yayi kafin yaja motar da gudu kai tsaye gidan ya koma, ko securitys din barka da zuwa kawai suka dinga yi masa, duk atunaninsu lokacin ya dawo gidan,babu wanda ya tankawa haka ya shige gidan zuciyarsa babu dad'i,dakyar ya samu ya ya kice damuwar kan fuskarsa ya duba anne har take masa maganar halin da Nana take da bashi izinin ya duba ta ko asibiti ne suje dan taga kamar bata jin dadi"amsa mata kawai yayi sannan ya fice daga dakin, sai a lokacin ya tuna da isma da halin da yake ciki,dama shi sule karami bai damu dashi ba saboda sunan sule babba aka sa masa,dan haka tunda ya kaisa kasar Dubai karatu bai kara waiwayarsa ba,sai dai yasan mus ab yana kula dashi ta hanyar tarbiyya da abin bukata duk da cewa yanzu ya kama aiki a can dan shima bai damu da dawowar ba, shi da suhaima ne kaɗai Allah ya shirya masa su dan gaba daya halin nana ne dasu basu dauko son zuciyarsa ba,hakan yasa yafi damuwa da zahida da isma, da wannan tunanin ya haura bangarensa yana kuma laluben nomber isma ko zai dace. ******** Yau watan baffa wuro daya a ABM Hospital,idan ka gansa kamar ba shi ba ya warware yayi tsaf da shi saboda tsananin kulawar da ake yi dashi ,an gaya masa kullum akwai wanda yake zuwa yana duba lafiyarsa sai dai bai taba ganinsa ba bai san ko waye ba,amma duk da haka yana shan addu'a a bakin baffa wuro matarsa da yayansa suma suna cikin kula da gata,yau saura kwana biyu a sallame shi amma fata yake mutumin nan yazo ya ganshi ya yi masa addu'a da godiya, likitan da yake kula dashi ya sanarwa yana son ganin bawan Allah da yake kula dashi,likitan ya sanar masa zaizo amma sai a ranar da aka sallameshi. ****** A falo daddyn zahida ya samesu zaune,Hajiya zubaida tana ta lallashin zahida da bata baki, duk da cewa bata san me yake damun zahidar ba,dan ko da ta tambayeta shiru ta yi mata,to amma ita mom zubaida ta dauka duk akan mus ab ne dan tasan matsalar zahiri ta zahiri bata wuce mus ab, shigowar Garba ne yasa zahida tashi zaune tana kallonsa dan a yanzu babu abinda take bukata irin taji ci gaba a kan harkokinsu da kuma batu akan mus ab dinta,duk da cewa tana ji a ranta idan taga zata rasa mus ab din zata iya hakura da komai ta zauna dashi,zahida bata taɓa sanin son da take yiwa mus ab ya kai inda ya kai ba sai yanzu da take ganin zai kufce mata,kai tsaye daddy ya wuce can wajen hutawarsa yana cewa da zahida ta biyosa,tashi ta yi ta bisa mom zubaida ta bisu da kallo. Suna shiga wajen zahida ta fashe masa da kuka tana cewa daddy me kuke yi ne haka kun tsaya kuna ji kuna gani zan rasa mus ab?wallahi dad idan har na rasa mus ab to nima zaku rasani"kama hannunta yayi ya zaunar da ita kan kujerar hutu ta wajen, sannan shima ya zauna, kafin cikin rarrashi da tausasawa ya fara sanar da ita duk shirinsu,a fusace ta kwace hannunta da yake cikin nasa tana cewa "dad wannan shirin da kuke ba nawa ba ne bana dawo min da farin ciki na ba ne,ko hanya ma basu hada ba dan haka ni zan yi duk yadda zan yi na tsira da soyayyar mus ab,ko da kuwa naku shirin zai War gaje"hana zahida me yasa kike abu kamar wadda kika fita daga hankalinki? shin kun manta tonan asirinmu naki ne?shin kin manta cewa idan mus ab ya haɗa hujjojin maka mu a koto ke zaki tsira ne bare a kai batun auren ki da shi?ki maida hankalinki jikinki ki nutsu mu hada kai mu kwace hujjar da take hannunsa idan har mu kayi haka ke zamu iya fitar dake akan cewa baki san komai ba kema a rufe muke baki komai ba tare da kin san abinda muke yi ba"ajiyar zuciya ta dan sauke sannan ta ce na fahimceka dad, Amma ko a cikin hujja babu anita da abinda yake hannunta a ciki dan tun a ranar na turata garin da ba a dawowa,shi kuma ɗan ladi da camararsa yana hannunsu ka ga kenan mune da mafi rinjayen hujja bamu da matsala idan har ya maka mu a kotu zaku fita akan rashin hujja nima zan fita akan ban san komai ba"da kyau shi yasa nake sonki yata,bari ma na kira ɗanturqui na gaya masa suƙara tsaro akan Yaron nan kafin mu zo mu karbi camarar wajensa sannan shima mu turashi ya tafi inda yayarsa ta ta tafi"ya fada yana latsa wayar , wayar bata shiga kin san wajen da akwai matsalar network,gibe na sake kira saboda a yanzu komawa wajen ba zai yiwu ba saboda idanun mus ab gaba daya yana kan duk wani motsinmu wata kila ma har da yan sanda kinga dole ne mu yi kaffa kaffa". A can bangaren Abba Kabir shima ba a barshi a baya ba,daya daga cikin yayaransa me suna Kashim ya kira suka zauna,Kashim ya jima tare da Kabir kuma duk wasu aiki da ya gagari ɗanturqui shi yake sawa yayi musu,dubansa ya yi tare da yin gyaran murya sannan ya ce"Kashim aiki nake son sa ka amma bana bukatar kuskure komai kankantarsa"kai tsaye kashim ya ce ina jinka oga kar ka samu damuwa"jinjina kai Kabir yayi sannan ya mikawa Kashim din taswirar gidan mus ab kana ya dora da cewa "duk yadda za kayi ka shiga gidan nan ban ce ka taba kowa ba,kaga abinda nake so ka dauko min"ya fada yana nuna masa zanen littafin, sannan ya ce littafin kawai nake bukata zaka iya bari ma sai sun fito daga gidan sai ka shiga sabida bana son ka taba yarinyar nan domin tabata zai iya kawo mana matsala wajen dauke littafin, iya abinda na saka shi kawai za kayi"daga nan ya mika masa wasu mukullai ya ce idan ka je ka bude gidan da su,amma fa ka yi hattara gidan da zaka shiga da mutanen da suke ciki ba gama garin mutane ba ne shi yasa nake jaddada maka da ka kiyaye"karba yayi yana cewa an gama oga zan zo maka da littafin kamar yadda ka buƙata"daga haka ya sallame shi ya tafi. ****** Wankan mus ab da aminatu dai ya juye ya koma wani irin wanka na musamman,inda daga karshe ya dauke ta cak daga cikin ruwan suka fito daga bathroom din,a hankali ya shimfideta saman tattausan gadon da ya ji lafiyyyar shimfida ta alfarma tare da bin duk jikinta yana mata wata irin massage da lokaci daya ta rikita tunanin aminatu, babu shiri ta shiga kakkame jikinta tana fidda wani dan makirin numfashin da yake sauka a kan fatar kunnen mus ab yana zaga jini da kwakwarsa yana saculatin bargonsa tare da tafiya da duk wata jarumtarsa da kwarin gwiwarsa da yake jin zai iya hakura da aminatu,a hankali yake bin jikinta da wasu irin zafafan kisses masu ɗauke hankalin wanda ya yi zurfi cikin shaƙin ƙaunar da bai tantance ta ba,dukkansu farin shiga ne sabbin yan koyo ne sai dai zuciyoyinsu tsaffine feelings dinsu ma tsoho ne gangar jikinsu ne kawai sabbi, hakan yasa tsohuwar kauna da feeling dinsu ya rinjaye gangar jikinsu da take sabuwa akan baƙon al'amarin da ya ziyarceta......... Zahra✍️ 8064537048 0pay Fatima yusha u Adam Amount 500 [5/11, 2:51 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page54``* Jin inda ya kama yasa Aminatu sakin wani dan jinjirin kuka wanda bata san shine ya karawa mus ab karfin gwiwar ci gaba da abinda yake yi ba,babu inda mus ab bai bi ya aikace ajikinta ba,cikin salon da bashi yake yinsa ba zuciyarsa da ta yi zurfi da kuma feelings din da yake gangar jikinsa da kuma zuciyarsa sune suke fidda tsohon mikin da baisan dadewarsa a tare dashi ba,ji yake kawai zuciyarsa na sarrafa gangar jikinsa wani irin mayen romance mai tsayawa a kwanya yake yiwa Aminatun da karamar ƙwaƙwalwarta take neman juyewa, sai dai itama ana ta bangaren bata san cewa zuciyarta na sarrafa gangar jikinta ba,saboda yadda hannunta da jikinta yake kai komo a duk inda ya ci karo da shi a tare da mus ab ɗin, wani baƙon al'amari da ta fara ji shi ya yi kokarin dawo da ita cikin hayyacinta,a take ta fara kokarin ture mus ab da yayi nisa ba ya jin kira,a hankali ya dinga karanto addu'ar kasancewa da iyali yana yi yana kokarin daidaita jikinsa a jikin aminatu, duk da yadda mus ab ya ke jin kansa kamar ba shi ba hakan bai hanashi janyowa kansa natsuwa ba ko dan gudun cutar da aminatu,kukan da ta fara yi ne yasa shi saurin haɗe bakinsa da nata yana masa shan daga ke ba kari,duka da yakushi babu irin wanda mus ab baisha ba,yana samun natsuwa ya kankameta ajikinsa tamkar zai karya mata kasusuwan jiki,sai a lokacin ya saki bakinta ta samu damar fasa kukanta ta yi sa yadda ranta keso tana yi tana mintsinansa da ture shi amma dan gidan nana ko gezau bai yi ba,(yo ke ko aminatu wa ya gaya miki ana fada da jarumi kamar Mus ab)ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi tare da ɗago fuskarta da ta yi share share da hawaye da majina yana kallonta,lumshe idanunsa yayi tare da ɗan kai mata kiss a goshi hannunsa guda yana gyara mata dogon gashinta da ya burkice kamar na mahaukata sai azabar ƙamshi kamar wadda ta yi barin turaren gashi,"am sorry ya faɗa yana kai kansa cikin wuyanta yana sunsuna, "me kikeso na a wajena faɗa min ko meye shi ina ji"banza ta masa tana faman jan ajiyar zuciya. Shi kansa wani irin zazzaɓi ne ya rufe sa amma duk da haka sai da ya tashi ya shiga bathroom ya haɗa mata ruwa me zafi, sannan y adawo ji tayi kawai ya sunkuceta kamar wata jaririya,bai direta a ko ina ba sai cikin ruwan ,tare ta sanya kuka me karfi tare da sin rashi , sai dai ina karfin ba daya ba dan mus,ab sosai.ya danneta yadda ba zata iya tashi ba,haka takaraci kukanta da dukansa har ta dawo tana jan ajiyar zuciya har da su gyanggadi,cireta yayi ya sauya wani ruwan shima sai da ya barta ta ɗan yi mintuna sannan ya tsaya akanta ya ce ta yi wankan tsarki, dai da yaga ta fara sannan ya juya ya fita,wankan ta yi tana faman lumshe ido saboda baccin da take ji,tana gamawa ta langaɓe kanta a jikin bahon sai bacci,yana shigowa yaga tana bacci hankalinta kwance ,hancinta ya ɗan ja sannan ya dauke ta bayan ya naɗeta cikin towel,akan gadon da ya gyara ya canja bedsheet ya sauketa tare da lullbeta sannan ya koma yayi nasa wankan,yana fitowa ya kwanta kusa da ita yana kallon fuskarta da take ta sheƙi. Wani abu me sanyi ya ke ji yana kwaranya a ransa, sannan nauyin da yake ji a kirjinsa ya ragu,hannu yasa yana shafa fuskarta da tayi masa wani irin kyau,"AMINATU"ya ambata a saman labbansa kafin ya lumshe idanunsa yana jin damuwarsa na raguwa, Allah ka dai yasan irin farin cikin da aminatu ta bashi a wannan dare tun daga kan bangaren sauya rayuwarsa ta hanyar bayyana masa wani haske, yasan shi waye ta bangaren nasaba, sannan y San shi waye ta bangaren auratayya, bai taba sanin dadin aure ba bai nisan yaya yake ba,amma yau aminatu ta dandana masa zumar alfarmar da suke cikin aure ta mai dashi mutum cikakke ko yanzu zai iya bugar ƙirjinsa ya ambaci kansa da magidanci,aminatu ta inganta rayuwarsa, ji yake yi da ana maida mutum cikin zuciya da tabbas ya maida aminatu ya huta da nauyin sonta da yake neman tafiya da nunfashinsa. ******* Lallashin da da daddy yayiwa zahida yayi tasiri dan har gashi ta shirya fita office,duk da cewa zuriyarta tana ta yi mata raye raye akan shiga asibitin saboda tun baya kafin wannan abubuwan su fara faruwa da su ta fahimci cewa ABM hospital ya riga da yayi shuran da ta tarar dasu zai yi wuya,wani lokacin har mamakin karbuwar asibitin take saboda ko su lokacin da suka yi shura basu yi sauran da ABM yayi ba, take zuciyarta ta raya mata wani abu akan asibitin,tabbas akwai wani kasuwanci makamancin nasu da asibitin take yi, sai dai ga dukkan alamu sun fi su iya taku dan basu taba jin ance an mutu bisa ganganci a cikin asibitin ba,dole ta nemi me asibitin nan ko mace ko namiji dole ne suna bukatar temakon irin wannan mutanen a cikin tafiyarsu ta bangaren asibiti, anan ta yadda cewa muddin tana son daga darajar asibitinsu to dole sai ta kama hannun director na ABM hospital,da wannan tunanin ta gama shirinta ta bar gidan. Tunanin zahida da Abbas dinta yazo daya dan lokacin da ta isa asibiti waya ta yi da Abby tana neman shawararsa akan tunanin da ta yi, sosai ya bata goyon baya kuma yaji dadin wannan mafitar da ta samo musu yasan muddin suka yi nasara akan su mus ab asibitinsu zata tsira har su samu damar ci gaba da harkallarsu cikin kwanciyar hankali kamar baya.suna gama waya da abby zahida ta fara binciken ABM hospital da mamallakin asibitin, a yau dai bata samu wani impomation ba amma tasan idan tasa naci zata da ce. Lokacin da su ɗanturque suka fahimci cewa dan ladi ya gudu ba karamin tashin hankali suka shiga ba ,dan sun san lefinsu ne,hakan yasa suka nadama nemansa ba tare da sun sanar da iyayen gidansu ba,dan sun kudiri niyar ba zasu bari su sani ba tunda suna da kwarin gwiwar samo dan ladi a duk inda yake. ****** Hankalin dan ladi ya tashi lokacin da me nafef ya saukesa a gidan cp ya samu ba sa nan sai saƙo da me gadi ya bashi,karɓa yayi ya duba sai yaga adireshi ne na inda zai samesu,ajiyar zuciya ya ɗan sauke, kafin cikin sauri ya haye nafef ɗin yana cewa"dan Allah ka kaini tasha"lokacin da yaje tasha babu motar da ta cika dole sai zama yayi yana jiran su gama lodi,daga ƙarshe dai dole sai safiya suka tashi,har a lokacin ɗan ladi hankalinsa bai kwanta ba,sun ɗau hanyar barin gari ke nan sai ga wata bak'ar mota tasha gabansu,sosai ɗan ladi ya firgita dan ganin wanda suka fito daga motar, babu hanyar da zai ɓuya hakan yasa ya miƙa kansa dan kar yajawa na cikin motar,tunda ya fito daga motar suka tasa ƙeyarsa har cikin motar su suka ja bai ƙara sanin inda kansa yake ba,lokacin da ya farka mamaki ne ya kamashi ganin wasu sabbin fuska daban sannan su danturqui a ɗaure ta mau da alama dai sun shiga sabon hannu ne daga shi har su,to waɗan nan su waye haka?"bashi da mai bashi amsa,dan haka ya gum da bakinsa,bai iya cewa komai ba saboda kwarjinin mutanen yafi gaban a kallesu,bayan girmansu hatta da fuskarsu babu sukunin annuri bare har ya iya yi musu tambayar da take kewaye a cikin kansa,hakan yasa ya maida kansa ƙasa tare da dan motsa hannunsa da yake tunanin a daure yake kamar yadda nasu ɗanturqui yake a daure,amma ga mamakinsa sai yaji hannunsa a sake,sai kawai ya gyara zamansa ya jingina kansa yana ci gaba da kallon su,abinci yaga ɗaya daga cikinsu ya garo masa a cikin robar take away,bai yi ƙasa a gwiwa ba ya ja gabansa ya buɗe dan yunwa yake ji sosai,abinci ne me rai da motsi ga danƙwaleliyar kaza a kai ga kuma ruwa da lemo, ɗaga kansa yayi ya kalli mutanen, sannan ya mayar kan abincin tare da yin Bismillah ya fara ci. **** Tunda suka yi salla suka koma,bacci suka yi wanda yasa zazzabin jikinsu ya sauka,kananun kukanta ne ya farkar da shi,dago fuskarta yayi yana ɗan zubawa cikin idanunta idanunsa da suke yi masa wani sakayau,kawar da kanta ta yi tana ɗan turesa daga jikinta,matsawa yayi daga jikinnata, sai dai kuma tana kallon yanayin da suke ciki daga shi har ita ta kwalla ƙara tare da mannewa a ƙirjinsa, sosai fuskarsa ta nuna murmushi me sanyi wanda ya fito tun daga ƙarƙashin zuciyarsa,tare da sanya hannunsa a wuyanta yana shafawa a hankali,ɗora hannunta ta yi akan nasa tana son cirewa, sai dai kuma bata wani kuzari hakan yasa ta tura fuskarta a ƙirjinsa tana cewa"daddy dama kai mugu ne ban sani ba?dama duk girman ciwon nan naka Ni zaka sany.......gum ta yi da bakinta saboda jin abinda take korafi akansa yana kokarin maida mata shi,hannu tasa ta turesa tana fashewa da kuka dan bata manta azabar da ta ci yan awowi da suka wuce ba,janye jikinsa yayi ba tare da ya tanka mata ba,doguwar farar jallabiya ya saka sannan ya shiga bathroom brush yayi ya sake fitowa ya fice daga ɗakin,tana jin alamun fitarsa ta miƙe a hankali tare da ɗaura towel, sannan a hankali kamar wata me jin tsoron taka ƙasa ta shige bathroom din, ruwa ta kuma shiga kamar yadda yayi mata ɗazun, aiko sosai ta kuma jin daɗin jikinta daga nan ta yi brush ta fito.tana fitowa ta samu ya kawo mata wasu dogayen riguna masu kyau, bata saka kayan ba har sai da ta gyara jikinta da ƙamshi duk wani loko da daƙo da tasan yana bukatar ƙamshi sai da ta bazaza masa,kana ta ɗan goga lips glow da kwarri a idanunta take idanunta suka ƙara yin wani haske abinka da fara,simple makeup ɗin da ta yi ba karamin fito da ita yayi ba,kayannta dauka zata saka sai kuma.ta dakata tana kallonsu,basu da nauyi dan gaba dayansu siririn hannu ne da su gasu kuma shara shara idan ta sa babu abinda ba za a gani a jikinta ba,ajiye kayan ta yi tare da riƙe ƙugunta kamar me shirin yin dambe, ƙamshinsa ne ya fara yi mata sallama kafin takunsa me cike da nutsuwa da izza irin ta sarakai,sai kuma kwanciyarsa da ta ji a gadon bayanta, janye jikinta ta yi tana tura ƙaramin bakinta da yasha lipstick yana ta shiening kamar zai ɗiga a ƙasa,cikin iananun shagwaba ta kallesa da idanunta masu haske da ƙyalli kamar an ɗiga musu maiƙo, ta ce"hana daddy wannan ai kalan iskanci ne ya za ayi na saka wa annan kayan knduba fa kaga“ta faɗa tana daga rigunan tare da cilli da su a saman gadon kana ta ɗora da cewa kalli fa kai kayi shiga ta mutunci amma Ni sai ka kawo min kayan ƴan iska to ai gara ma na zauna da towel ɗina aradun Allah"ta yi maganar tana ƙosƙarin gyara guntun towel ɗinnata da yake gab da yin ƙasa. Duk abinda yake fada yana tsaye yana bin ko ina nata da mayen kallonsa da yake ratsata,shi yasa duk maganar da take ta kasa kallon idonsa,hannunta yayi saurin rikewa wanda hakan yasa ta tsorata har ta saki towel din yayi ƙasa,zata rungumesa yayi saurin zaunar da ita a gefen gadon yana ci gaba da kare mata kallo abinda bata so ɗin,rufe idanunta ya yi ta ana mis mis da bakinta dan maganar ma ta ki fitowa saboda tsananin kunya da ya rufeta,da kyar kalmomin bakinta, cikin in ina,dan Allah da daddy kayi hakuri since idan mutum yana kallon tsiraicin wani makancewa yake ni kuma bana so ka makance ka baka abbanmu ba a zahiri ba,Ni kaga na taba ganinsa a mafarki"tunda ta fara suritunta ya zubawa bakinta zuwa ƙirjinta ido kafin a hankali ya zauna kusa da ita yana mai sakata cikin jikinsa dan ji yayi yana neman kasa sarrafa kansa,itama shiru ta yi jinta a kirjinsa,daƙyar ya iya haɗiye abinda yake ji akanta ya daure ya sanya mata rigar dan yasan tana jin yinwa sannan suna da abubuwan da zasu yi daga kan ci gaba da karatu zuwa kan binciken da yake kan duk wani abu da ya shafi su Abby ɗin,yana gama sa mata ya mikar da ita tsaye tare da kan hannunta zuwa falo,dole tasa ta bude idonta babu shiri ta kuma mayarwa ta rufe saboda kayan da ta ci karo da su a jikinta,wai dama haka daddy yake bai da kunya?"ta tambayi kanta tana ci gaba da maida kafarta duk inda ya cire tasa. "Bude idanunki"ya fada yana zaunar da ita a wata kujerar me taushi wadda aka yi mata kwalliya da wasu irin furanni masu kamshi da burgewa,bude idanunta ta yi tare da ba zasu a ko ina na wajen, karamin falo ne me dauke da set din kujeru ɗaya,,sai wani irin ado da aka yiwa falon da kalolin balums da suke dauke da tambarin i love You,ga teburin gabanta cike da kayan dadi dai dai cikinsu babu banna bare almubazzaranci gefe daya kuma sautin qira'ar sheik Muhammad sudais ce take tashi abin gwanin tada tsigar jiki,wani irin farin ciki ne ya lullbe aminatu,bata san lokacin da ta mike ta rungume mus ab ba tana dariyar farin ciki,shina mrmushi ne dauke a kan fatar bakinsa,wanda yayi sanadin janye War numfashin aminatu na yan sakanni,bai yi zato ba ya ji daukar tattausan lips din aminatu akan nasa lips din ta bashi wata irin kyautar sumba kyau mafi soyuwa da ya taba samu daga mace macen ma matarsa ta sunna abinda bai tana tunanin zai same sa ba rayuwarsa,dan haka ya tarbeta cikin farin ciki da bata abinda ya fuskanci tana matukar so a garesa wato murmushinsa,zaunar da ita yayi a kan cinyarsa ya shiga ciyar da ita daga cimar da ya tana da mata wanda duk abinda take so ne. A wannan lokaci ne kuma yaron Abba Kabir ya samu damar shigowa gidan har cikin falon farko da zaka tarar a gidan,yana cikin canki in canka din dakin da yake da tabbacin zai samu littafin idanunsa suka yi masa kyakkyawan gani,take ya yi dariya me bayyana haƙora kana ya tunkari wajen tare da sanya hannu ya dauki littafin, sai da ya duba litattafin a kan wayar da ya tabbatar da shine sannan ya fice ta hanyar da ya shigo salin alin ba tare da kowa ya gansa ba, ****** Wani irin ihu farin ciki zahida ta saki tana duba sakon email din da ya dawo mata bayan tsawon lokacin da ta ke ta jiran amsarsu, glass ta sanya tana kuma duba sakon dan dai ta tabbatar ba gizo yake mata ba,wai yau ita me wannan sa'ar?to idan hala ne lallai sa'ar kasuwancinsu tana gab da dawowa tunda har ta samu rana da time na haduwarsu da ABM hospital director,har ta daga waya zata gayawa Abby sai kuma ta fasa tana cewa bari mu fara haduwa mu tattauna idan yaso sai nayi musu surprise din da zai tashi kansu"... Zahra✍️ 8064537048 opay Fatima yushau Adam [5/12, 8:10 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page55``* Tunda suka gama cin abincin ya koma gefe yana shigar da wasu muhimman sakonni ta cikin computer dinsa,a hankali aminatu ta matsa kusa dashi tana lekawa,"rufe computer yayi tare da matsar da ita daga kusa da shi, fuskarta ya shafa kafin ya ɗan sumbaci kumatunta yana cewa "yaya jikin hope dai yayi sauƙi?"rufe idonta ta yi tana ɗan mulmula bakinta, murmushin gefen baki yayi, kana ya ce"muje mu ci gaba da karatun ko?"dan jim ta yi kafin ta janye daga jikinsa tana shirin tashi,daga ta yayi cak ya dora a kafardarsa yana cewa nasan abinda kike jira kenan"tura baki tayi tana kwantar da kanta a ƙafadarsa,suna shiga dakin ya direta akan kujerar hutawa sannan ya dauko littafin ya dawo ya zauna kasan kafafunta, itama zamowa ta yi kasan tare da dora kanta a kafaɗarsa tana kallon shafin da mus ab ya bude, wanda hoton baffanta ya bayyana akai kamar yadda hoton abban mus ab ya bayyana,zuba masa ido mus ab yayi dan ba zai taba mantawa da fuskar da ta nuna masa kauna ba, a nutse ya bude musu shafin da rubutun ya ke. ******* YUSUF LAMIDO....... Yusuf lamido dan asalin garin Gombe ne,wanda yake rayuwa tare da mahaifiyarsa da matarsa a cikin rugar da suke kira da rigar malam Yusuf,malam Yusuf mutum ne me mutunci da son kyautatawa na kusa da shi,yana da ilmin addini matuka gaya dan shine yake koyar da duk dattinjan rigar da yara matasa,baffa Yusuf yana da tarin arzikin dabbobi da na gonaki da shanaye wanda shi kansa bai san kimarsu ba,dan wani lokacin ko satar dabbobi aka yi masa baya fahimta sai dai idan ya gansu saboda shedar da yake gane dabbobinsa da su,duk wata dabbarsa tana da shedar sunan aminatu da Hausa ajami, shi yasa da wuya ko za a yi sata a saci dabbar baffa Yusuf saboda ko ka sata idan ka kai cikin gari sayarwa to fa suma sun san kayan baffa Yusuf sai dai kaji an yi ram da kai,daga karshe ma sai satar ta yi sauki saboda yadda baffan ya dauki nauyin matasa a kan duk wata sabgarsu, sana a zaka yi aure zaka yi karatu ne duk abinda yake da amfani baffa Yusuf ya dau nauyinsa,shi yasa mutanen rugarsu suke kallonsa kamar wani waliyi,baffa wuro makocin baffa Yusuf ne wanda aminci ya shiga tsakaninsu,duk wata ɗawainiyar gidan baffa wuro baffa Yusuf ne yake yinta. Mahaifiyar sa me suna zainabu amma suna kiranta da innawuro ta dauki baffa wuro tamkar da,ita kuma matar baffa wuro me suna fatsima ta dauke shi yaya, dan haka baffa wuro yana da babban matsayi a cikin ahalin Yusuf , duk wata yardarsa ya dorata akan wuro,shi yasa wuro yasan yawan arzikin da Allah yayi wa Yusuf. Matarsa Fatsima ta jima bata haihu ba,sai kuma lokaci daya Allah ya kawo mata karuwa,haihuwar aminatu ta zo da abubuwa masu tarin yawa wanda suka shafi arziki,baffa Yusuf a duniya babu abinda yake so sama da aminatu, bai sani ba ko dan bai taɓa haihuwa ba ne, amma shi kansa ya san yana kaunar aminatu,kai ko ga sauran mutanen rugarsu, aminatu me farin jini ce,duk da cewa ta taso da yawan tsokana a cikin kuruciyarta,inna wuro ita ce kome na aminatu tun tana karama,shekarar aminatu uku a duniya, a wata ranar Laraba baffa Yusuf ya kwashe iyalansa gaba daya suka fita birnin Gombe dan siyayyar abubuwan amfani,kafin dawowarsu ne cikin yammacin ranar,wasu mugayen mutane da aka rasa suwa ye suka shigo rigar su kayi sata me tarin yawa kama da kan kwace takardun gonaye da filaye har zuwa kan dabbobi,daga nan suka kama wasu daga cikin yaran garin suka tafi da su lokacin da baffa Yusuf ya dawo ya shiga tsananin tashin hankali,take yan uwa suka bashi shawarar ya saida kome ya tattara ya bar rigar dan a ko da yaushe mutane zasu iya dawowa saboda duk wata gona me girma idan suka bukaci takardunta sai baffa wuro yayi tsagal ya ce ta yusufa ce,duk yadda mutanen garin suka so boyewa hakan bai samu ba sai da mutanen sun san waye Yusuf ta hanyar baffa wuro wanda shi acewarsa ya fada ne saboda tsoron kar su yi musu wani abu. Baffa wuro ya dauki shawarar mutanensa amma ya tabbatar musu da cewa ko zai canja ruga dole sai idan zasu bishi,to dake a tsorace suke kuma baffa kamar shine shugabansu a komai,Dan haka suka amince, washe gari baffa ya tattara dukiyarsa wadda zata tattaru suka tasa shanayen baffa suka kuma nausawa cikin jeji, basu suka tsaya ba sai da suka tabbatar sun yi nisa da rugarsu ta baya, sannan suka yada zango a cikin jejin, inda cikin lokaci kankani suka sauya shi ya koma cikakkiyar riga dan hatta da makaranta da masallaci sai da suka yi,daga nan suka fara rayuwarsu cikin kwanciyar hankali a karkashin arzikin baffa Yusuf,saboda kowa sai da ya bashi sana ar da zai yi saboda temakon kansu,ko sarin kaya za a fita cikin gari mutum biyu suke wakiltawa suma ta boyayyiyar hanya suke fita haka ta wajen dawowa suna taka tsantsan da duk wani bakon fuska. Sun dauki shekara guda cir a cikin sabuwar rigar su,suna rayuwa cikin farin ciki,dan har sun fara farfadowa daga tashin hankalin rashin kadarorinsu,dabbobin su sun fara yalwanta dan Allah ya sa musu albarka acikin wannan riga,kwatsam rana tsaka suka kuma samun sumamen wadan nan mutane wanda hakan ba karamin mamaki ya basu ba,dan su sun tabbatar da cewa suna matukar taka tsantsan da fita da shigarsu,haka suka kuma kwasar dukiya da wasu daga cikin mata suka fice dasu,ba tare da kowa yaga fuskarsu ba bare ya shaida ko su waye. Amma abin mamaki duk abinda mutanen nan suka kwasa bai girgiza dukiyar baffa wuro ba,wanda har mamakin hakan shi kansa yake yi,dan wani lokacin ma sai yaga kamar ba Adauki kome ba,ko kuma yaga an dawo masa da wani abu daga cikin abinda suka karba,a wannan lokacin ba su canja riga ba har sai da hakan ta kuma faruwa sannan suka kuma yin hijira zuwa gaba,daga nan ne kuma suka fara bincikar junansu dan sun tabbatar akwai me fitar da sirrinsu zuwa ga wannan mutanen,sai dai duk yadda suka so ganowa basu gano ba, wannan karon yalwal arzikinsu yafi na waccan rugagen da suka baro, baran ma arzikin baffa Yusuf da ya kuma nunka na baya. Acikin haka ne wasu baki suka yi musu tsinke,da farko sun tsorata a tunaninsu ko wadancan mutanen ne da suka addebesu,sai da suka yi musu bayani akan cewa su masu binciken dajika ne,sun zo ne dan daukar yanayin wannan dajin saboda da farko bai nuna musu da mutane a ciki ba, wannan bayanin yasa suka amince da mutanen har da yi musu sauka ta mutunci babu abinda baffa Yusuf bai ajiye musu na jin dadin rayuwa ba. Kwanansu goma suna binciken yanayi a cikin rugar babu wani abu da ya faru, sai a cikin kwanansu na sha daya ne, aka fara tashi babu wasu daga cikin mutanensu,tun suna ganin abin kamar me wucewa ne har abun ya fara isarsu,saboda rashin da suke yi ya yi yawa,a cikin rashin da suka yi har da na mahaifiyar aminatu,wanda hakan ya kuma tashin hankalin baffa Yusuf take ya fara binciken wadannan bakin mutanen ba tare da sanin kowa ba, har Allah ya sa ya gano cewa sune mutanen da suka dinga kawo musu hari, yanzu sun canja salo ne shi yasa suka zo musu da wata fuska,kuma sune suke dauke mutanensu suna kaisu can cikin gari suna amfani da wani sashe na jikinsu,kama daga kan zuciya zuwa ƙoda ko dai wani abu da ake bukata daga jikin ɗan adam,lokacin da baffa Yusuf ya gane hakan ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, cikin hikima da sirri ya fara janye mutanensa yana fitar da su daga rugar,tashi kawai mutanen su kayi suka ga babu kowa cikin rigar,a lokacin daga baffa Yusuf sai baffa wuro dan hatta da iyalan baffa wuro ya fitar da su,ajikinsa ya ji bai yadda da baffa wuro ba,amma dan ya tabbatar da abinda yake zargi sai bai nuna masa komai ba,cikin dare suka sulale suka bar rugar shida wuron. Sabuwar rayuwa suka bude a sabon wajensu,sai dai basu saki jiki kamar yadda suka saba ba,kowa a darare yake dan sun tabbatar akwai munafikin da yake tare da wadancan mutanen a cikinsu,baffa Yusuf bai baza dukiyarsa yadda ya saba ba,dan haka kowa cikin kaffkaffa suke da junansu,dukiyar baffa Yusuf kuwa a tsare take dan ko sun kwace in sha Allah washe gari zai ga abinsa ya dawo kuma gaba daya gonakinsa babu abinda yake taba su,ba ko mai ne yasa hakan ba,sai wata bafulatanar aljana da take tare da shi tun yana cikin tsumma, tun baffa Yusuf bai san da ita ba har dai ta bayyana a gareshi yasan ta da kuma irin temakonta a garesa,ana cikin haka ne baffa Yusuf ya kwanta matsanancin ciwo wanda ya debesa watanni, gashi kuma ya hana a kaisa asibiti,daga karshe dai baffa wuro ya lallaɓasa akan ya yarda ya kawo likitan da zai duba sa amma baffa Yusuf yaƙi dole baffa wuro ya rabu dashi. A cikin wannan yanayinne Allah ya kawo MUS'AB garin,wanda da farko mutane sun nuna rashin yardar su akansa,amma sai aka samu sabanin hakan daga wajen me gayya me aiki wato baffa Yusuf,tunda baffa Yusuf ya karɓi mus ab hannu bibbiyu dole suma suka bi sahunsa,iya ƙauna baffa ya nunawa dan birni kamar yadda kuka ji a cikin labarin mus ab da ya rubuta a cikin jota, wannan shine abinda ya faru kafin zuwan mus ab. Bayan tafiyar mus ab da kwanaki baffa wuro ya sake dawowa da baffa Yusuf magana akan zuwan likita, a lokacin baffa Yusuf ya amince, wanda hakan ba karamin murna wuro yayi ba, baƙon likita ya shigo cikin garin, an kuma ga ya shiga dakin baffa da kayan aiki da wata bakar akwatu,babu wanda yasan me ya faru da baffa sai wayar gari aka yi ya ce ga garinku nan, wannan shine dalilin da yasa baffa wuro ya samu damar kuma jonewa da mutanensa Garba Jamil da kuma Kabir,daga nan suka zaba masa inda zasu ci gaba da rayuwa domin ya dinga yi musu gadin aminatu da innawuro,dan sun sha alwashin sai sun yi ruf da ciki akan dukiyar da baffa yake ta wahalar da su akanta dan duk abinda suke yi suna yi ne saboda dukiyar Yusuf din ga kuma irin bakar azabar da suke sha a duk lokacin da suka taba wani abu na Yusuf din,dan ko lokacin da suka tafi da matarsa mahaifiyar aminatu sun gane kurensu, lokacin da suka yi aiki suka cire zuciyarta kuwa anan suka gane cewa shayi ruwa ne dan da Allah yasosu da shirya da alokacin zasu shiryu dan ko bacci sai da ya ya gare su,amma dake sun yi nisa bada jin kira suna samun kansu suka dora fiye da yadda suke a baya, wannan dalilinne yasa suka bar aminatu a raye saboda suna son dukiyar ubanta kuma dole sai wanda aka bawa dukiyar ya dawo ga Aminatun ne zasu samu abinda suke so,daga nan zasu cire zuciyar inna wuro da tuni suka yi cinikin ta da kuma ta aminatun bayan sun samu yadda suke so wanda aka bawa amanar dukiyarta ya bayyana, wannan shine lissafinsu sai dai kuma hakan bata samu ba,dan lissafinsu ya fara kwancewa ne tun bayan da suka dauko aminatu suka dawo da ita kusa da su. Su kansu ba su isa su ce ga abinda yake cikin rayuwar Aminatu ba,saboda sun sha wahala akanta da mahaifinta da suka zama sanadin mutuwarsa dan wannan likitan da suka turo likitansu ne yayi aiki ya cire zuciyar baffa Yusuf ya kawo musu,sun sha wahala ta jiki da zuciya amma duk da haka basu karaya ba suka ci gaba da gadinta amatsayin kadararsu,amma su kansu sun shaida akwai wani abu a acikin rayuwar Yusuf da iyalansa ko kuma dai su din yan baiwane. ****** Kuka sosai Aminatu take yi, mus ab kuwa tunda ya dauke kansa daga kan rubutun ya maida kansa jikin kujerar da yake jikinta tare da rufe su yana jin sautin kukan aminatu da yake diga a ransa kamar ana diga dalma... Jin kukannata yawa yake kuma yi yasa shi dora hannunsa akan ta yana yamutsa gashin kanta me santsi,kafin cikin taushin murya ya ce "sorry nurr"lafazin da yayi amfani da shi wajen bata kalma daya ta rarrashi shine ya ja hankalinta har kukanta ya tsaya ɗif,saidai jan ajiyar zuciya da take yi,sai da ta dauki minti ɗaya kafin cikin Muryar ta da ta yi kasa sosai ta ce"daddy nima su suka kashe iyayena kuma da sa hannun amintaccen mahaifina mutumin da bashi da na biyunsa,baffa wuro ya ci amanar baffa na da baffa zai dawo duniya yau da ban san wane irin tashin hankali zai shiga na jin cewa baffa wuro ne sanadi tare da shi aka kashe rayukan mutane da basu ji ba basu gani ba, akan kuɗi abin banza da zaka mutu kabarsu,shi yasa nai bana don asibitinsu ashe abinda ake aikatawa me karshen muni ne"kukane ya kuma kwace mata saboda tuna baffanta da ta ke yi dan tafi sha kuwa dashi fiye da innarta kuma lokacin da ta mutu mata da wayo shi kuwa baffa ko yanzu tana tuno lokacin mutuwarsa. Dago kanta yayi a hankali yana mai haɗe bakinsa da nata, ai ko take ta hadiye kukanta,yadda yake sumbatar bakinta da zafi ,zafi yasa ta tuna halin da take ciki, tsoro ne ya kamata, hakan yasa ta shiga kokarin kwacewa, sai dai ina yan mazan Nana sun yi ram da Nijar innawuro,dole ta hakura sai dai kanfanin hawaye da take yi tana jin ciwo a duk inda ya kai hannunsa musamman kirjinta da har yanzu bata ji ya dawo daidai ba,a hankali ya zame rigar da ya daka mata ta yi kasa, rike da ta yi sosai tana juya kanta hawaye duk ya bata mata fuska saboda babu damar kwallawa dan ya rike bakin kam kamar ba zai rabu da shi ba,ganin ba sarki sai Allah yasa ta ɗan sassauta tare da bude bakinta sosai tana taya sa cikin enjoying,Wanda hakan yasa shi sakin jikinsa,ita kuma hakan ya bata damar kwacewa ,da gudu ta mike tana yi masa Gwalo,wai ita fa tayi masa wayo,lumshe idanunsa yayi tare da yin balance a wajen dan a hakika nin gaskiya aminatu ta yi masa dabaibayi ta sarkakfe shi tare da mugun kullin da fitarsa daga ciki abu ne da ba zai taba yiwuwa ba. A hankali cikin rashin kuzarin da ta haifar masa ya daga hannunsa yana yi mata alama da ta dawo gareshi,makale kafada ta yi tana kuma turo masa harshe har da kada masa dararan idanunta masu maiko...... Zahra✍️ [5/13, 6:32 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page56``* Numfashi yaja me nauyi tare da shafa kansa,daya daga cikin wayoyinsa ne ta yi haske alamun kira ya shigo,zubawa wayar ido yayi saboda nomber da ya gani tana yawo akan screen dinta,bako wace nomber ba ce sai ta abby,ji yayi hannunsa yayi nauyi ya kasa ko motsa shi bare ya daga wayar,dan shi yanzu ko Muryar abby baya son ji,ji yayi kawai Aminatu ta daga kiran, ba tare kuma da anjira cewarsa ba, aka fara tun tsira dariya, dariya irin ta naci dubu se ceto, saida yayi me isarsa sannan ya fara magana da cewa,"mus ab ina fata dai ka ga ne babanka ne a kan layi ko?bai jira amsarsa ba ya ci gaba da cewa,"i zuwa wannan lokaci na san wannan tsinanniyar yarinyar da take tare da kai ta bude maka abinda yake cikin littafin nan ka gani,dan haka ba bukatar na kuma yi maka dogon bayani,yanzu dai kasan ko ni waye a gare ka da matsayina da komai nawa,dan haka zan tafi kai tsaye zuwa kan dalilin kiranka"wayar ya kai saitin bakin Nana sannan ya daddage ya tsinka mata marin da yasa ta yin baya tare da sakin kukan dole,dan sam bata yi niyar yin magana ba saboda kar ta daga musu hankali musamman aminatu, aiko tunaninta yayi daidai dan Muryar aminatu ta ji yo tana cewa "daddy kukan Nana ne fa wannan,wayyo Nana kina ina me ya same ki ke da waye"?cikin dauriya Nana ta ce"boddo ki kwantar da hankalinki ina lafiya baki ji Ni da Abby ku ba ne?" "Cikin tsawa Abby ya katseta da cewa "ƙarya kike baki isa ki kwantar musu da hankali da sunan kina lafiya ba,kai bari ma na fito na bayyana maka abinda nake nufi,na dauke uwarka yanzu haka tana hannuna kuma azaba zan ta gana mata, kullum da kalar wuyar da zan bata,dan haka idan har kana son mahaifiyarka a raye to duk wani abu da kasan shaida ne tun daga kan mutanen da ka haɗa har zuwa kan wasu takardu da camarory duk ka haɗa ka bani, sannan da uwa uba littafin sirrina,dan wannan da Kabir yasa aka dauko ba shi ba ne,kai Ni fa duk yadda kuke zatona na wuce saninku wallahi,shegiyar yarinya ba ke kina takama da aljana ba,to nima aljanin kaina ne,ai tun wancan na farkon da kika sa aljanarki ta ajiye min a daki to tun daga kansa na gane irin naku na aljanu,dan haka ku bani ko mai nima na baku uwarku, kuma duk abinda na duba naga fake ne to wallahi sai na kashe ta idan yaso nima a kashe Ni"daga haka ya ajiye wayar yana dariyar mugunta dan ya tabbatar da cewa tarkonsa ya danu daidai da yadda ya saitashi. Tunda ya kashe wayar aminatu ta ke kuka tana cewa"dan Allah daddy mu bashi komai ya bamu Nana, Daddy muna fa da babbar shaida wato Allah dan haka ba zai sa mu ji kunya ba"tana zuwa nan a maganar ta ta saki hannunsa da ta rike ta dauko littafin tana cewa kawai ka tashi mu kai masa ai mun gama karanta duk abinda muke da bukata ba wani abu ba ne dan mun bashi kaji daddy"rikota yayi jikinsa yana sauke numfashi a hankali,shiru ta yi tana jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya wanda anan kawai zaka gane r8kitaccen yanayin da mus ab din take ciki,take aminatu ta yi wani tunani, hakan yasa ta dago kanta daga kan saitin zuciyarsa tare da maida hannunta ta cikin rigarsa tana shafa kirjinsa a hankali,sai kuma ta yi saurin balle botiran rigar ta cusa kanta a kan kirjin tana sumbatar ko ina da ta ci karo dashi,cikin ikon Allah taji yanayin bugun zuciyarsa na sauyawa yana dawowa daidai, hannu ta sa ta zagaye shi duk da cewa bata rutsa shi ba,bakinta ta sanya ta sunbaci idanunsa wanda shima take ya marmarasu suka dawo aiki daga suman quick gadin da suka tafi,sosai aminatu ta yi kokarin fitar da mus ab daga cikin shock din da ta fahimci ya shiga,amma in dai ba mutum me tsananin kusanci ko fahimtarsa ba babu me gane hakan, wannan dalilinne yasa mus ab ya tabbatar da cewa ya samu mace mace ma zai iya bata suna da tafisu,yanzu kuma kallon mamaki yake mata, gata dai yarinya ba wata babba ba amma ta iya cire mijinta daga cikin bad condition,hannu ta kai kamar zata tsokal3 masa ido, wani dan guntun murmushi ya saki yana ji a ransa cewa da babu aminatu a tare da shi ya riski kansa cikin wannan tashin hankulan da tabbas duk karfin imaninsa sai ya shiga mummunan yanayin da sakamakonsa ba zai yi kyauba,tabbas mace ta gari i ta ce rabin addini karshen nutsuwa, ita kadai ta isa samar da i gantacciyar rayuwa me dauke da farincikin da yake tattare da sanin Allah wato yarda da jarabawa da kuma karfin imani,duk halin da ya shiga tun daga kan sanin waye shi har zuwa yau da mahaifiyarsa ta ke hannun da yasan tabbas zai aikata mata duk abinda ya faɗa,bai taba rikicewa ko shiga yanayi irin na raunin imani ba,idan har ilminsa ya bashi kwarin gwiwa to tabbas kadancewar aminatu a tare da shi ma ya bashi kwarin gwiwa. Jin da yayi ana jansa ana nishi shi ya dawo dashi duniyar da aminatu da azzalumai irin su Abby suke,ware manyan idanunsa yayi a kanta, sannan ya kalli dogon hannunsa da take ja duk a kokarinta na son daga shi ya tashi,murmushine me taushi ya kuma subce masa a bazata,dan kuwa aminatun ta bashi dariya saboda ganin yadda ta hakikance bilhakki tana don dagashi,tana kuma jansa ya rinjaye ta ta dawo jikinsa gaba daya. take towel din da ta daura yayi takansa,da sauri ta sanya hannu ta kare kirjinta tana tura lips dinta da suka sha tsotsa wajen mus ab,janye hannun yayi yana kafe ta da lumsassun idanunsa a ransa yana fatan ko mai ya shige domin ya samu nutsuwar rayuwa da aminatu, rayuwa me inganci wadda take ciki da farin ciki da shauki da kuma mutunta juna, yana son yayi koyi da ma aiki wajen shimfida rayuwar aurensa bisa tsari da koyarwar ma aiki,"Muryar ta da ta kuma yin sanyi ya ji tana cewa " dan Allah daddy ka kirasa ka gaya masa zamu bashi kome duk abinda yake so amma kar ya taba Nana dan Allah"wayar kawai ya dauka tare da danna kiran Abby, wayar bata shiga ba, dan haka sai suka yi masa test suka tura masa, take kuwa ya dawo musu da adireshin wajen da zasu kai kayan sannan ya tabbatar musu da cewa sai ya duba ya samu komai lafiya Sannan zai saki Nana,sun amince da hakan.dan haka aminatu da kanta ta tattara duk wata shaida daga wajen mus ab sannan ta haɗa da littafin, tana gamawa ta kallesa ta ce"ka tashi mu je yanzu kar dare yayi"mus ab ya zama kamar wani soko duk abinda aminatu ta ce yayi yi kawai yake dan yana ji a ransa akwai wani abu da take boye masa shi yasa lokaci daya ta amince da sharadin Abby da kuma karfafa masa gwuiwa akan cewa in sha Allah sune da nasara. A ranar sai da suka tabbatar duk abinda Abby ya nema sun bashi,abinda ya kuma bawa mus ab mamaki da aminatu shine,kai tsaye ta sanarwa da Abby cewa sun janye kara tunda yanzu babu wani amfaninta ba tare da shaidu ba,mus ab, ba ma abocin magana ba ne hakan yasa ya yi shiru sai dai yana cike da dokin ganin abinda da aminatu take shirya wa su Abby dan yasan ba zata taba kyale su ba,ko lefinsu bai kai wannan ba aminatu sai ta hukunta su, dan yasanta fiye da sanin da yayiwa kansa. ***** Su Abby fa duniya ta dawo sabuwa,a yanzu jin kansu suke yi kamar wasu waliyay saboda tsananin sa a da da yadda kwallon duniya ya dawo hannunsu suke garashi duk inda suka so. A bangaren dan ladi kuwa, Film kawai yake kallo a wannan gida,Gashi dai suna daure shida su ɗanturqui amma duk lokacin da su abby zasu bugo musu waya ko video Call dan su tabbatar dan ladi yana nan,sai abin ya juya, duk lokacin da hakan zata faru to zai ga su danturqui akan matsayinsu na baya,abin yana matukar bashi mamaki sai dai bashi da bakin tambaya. Anita ma tunda suka bar garin suka dawo Kano, basu kuma waiwayar Gombe ba. Zahida hankalinta fa har yanzu bai dawo jikintaba,saboda bata samu mus ab dinta ba,gashi dan nata ma anrab ta dashi ,saboda ita ko inda yake ma bata sani ba bare kuma gidan suhaima da yake can yana rayuwarsa cikin kwanciyar hankali, dan babu wanda baya waya dashi tun daga kan Nana har zuwa kan innawuro,daddyn sa ne ma da aminatu suke daukar lokaci basu yi magana ba. Zahida ta bar batun Mus ab ne har zuwa lokacin da zata hadu da me ABM,ta tabbata idan kome nata ya dawo to mus ab ma dole ya dawo gare ta,dan kudi da power sune komai a wannan zamanin shi yasa bazata yi wasa da nemansu ba, kullum cikin irga kwanakin haduwar tasu take saboda yadda take jin labarin su ta tabbatar da cewa ita din me sa a ce. ...duk da cewa mus ab da aminatu sun tattarawa su Abby komai amma sai yaki sakin Nana , acewarsa ai nana matarsa ce dan haka yana da iko akanta,a karo na hudu aminatu ta kuma nemansa a waya,yana dagawa ya dura wani uban ashar yana cewa"wai ku yaran nan wane irin Mayu ne?karfa ku manta matar nan ina da yara da ita dan haka na fiku bukatarta, lamuni daya zan yi muku shine duk sanda kuke son magana da ita ku kirani ni kuma zan hadaku sannan duk abinda zaku fada a gabana zaku fadeshi idan ma so kuke ku ganta sai na baku dama, amma fa ku sani baku isa gano inda nake ba duk iskancinku da dabarunku wallahi nawa ya ci uwar naku,dan karku dauka bani da wayo na barku da nombata muna waya ku dauka cewa ban yi wani shiri akan hakan ba"dariya ya yi sannan ya dage girarsa daya tare da yi musu irin kiss din nan me sauti, runtse ido aminatu ta yi maganganun na dukan ranta,shi yasa duk sanda zata kirashi sai ta bari mus ab ya fita daga gidan dan tasan shi ba zai jure wannan iskacin na Abby ba, gyaran murya ta yi bayan ta yatsine fuska da dakin wani uban tsaki,kana ta ce"wai kai tsohon dan iska nan ka dauka duk abinda mu kayi maka tsironka ne ya sa mu kayi?ta wani girgiza kai tare da cewa lala lala,kawai dai akwai wani abu Nana kuma ka ci gaba da rike ta har nan da lokacin da zaka bayyana wa duniya kankan, wallahi Abby na dauki alkawarin sai ka tonawa kanku asiri da kanku tsofaffin banza da wofi kawai"daga haka ta katse wayar tana jiyar da kiranta ka wata nonber da ita da kanta ta tafa ta sannan ya fara magana cikin fillanci, to ango gun Ni dai kunsan ba iyawa nayi ba,dan haka ba san da waye aminatu ta yi waya ba,dan bata bamu wannan damar ba. Kasancewar mus ab ya yi alkawarin ba zai kuma neman aminatu ba har sai bayan da suka samu nutsuwa, duk da bai san yaushe ba ne wane lokaci ne,a kusa ne ko a nesa ne? duka bai sani ba,abinda ya sani shine ba zai iya rayuwar aure da aminatu cikin rashin kwanciyar hankali ba,dan haka yasawa kansa hakuri dan ita kanta aminatun ya fuskancin wani abu a tare da ita,shi dai ya zuba mata ido ya kuma sakar mata da wuka da nama. Sosai su Abby suke shirye shirye wajen hada kan costomominsu don harka zasu koma ka in da na in,yayin da a ta gefe kuma suke shirin kashe mus ab da aminatu ba tare da zahida ta sani ba,don sun tabbata sune kadai matsalarsu,baran ma da suka fara tunanin isma yana hannun mus ab din ,amma dai basu tabbatar ba,suna dai kan bincike ne kawai. ***** Suna juya baya sunduki yayi bindiga ya fashe tamkar wani bom haka kogon ya tashi da wuta,wutar na gama ci wajen ya shafe ko alamun wutar babu bare tokar sunduki,(Allah ya shirya mu ya bar mu kan tafarkinsa Allah yatsaremu gogayya da makusantan irin wannan mutanen , Allah yaranmu masu tasowa ka kare mana su ka shirya mana su ka basu halak komai kankantarta ka kuma basu hakuri da kankantarta ka saka musu wadatar zuci, wallahi duniya ba bakin kome take ba,duk wanda yayi hakuri wata rana sai labari, wani ma arzikin da dako ya fara ya sameshi wani kuma da jan kurarruwa, idan fa za mu tsaya mu nutsu mu yi nazari zamu ga cewa duk wanda su kayi arzikin nan ba haka suka samesa ba, tabbas sai da suka sha wuya kuma su kayi hakuri idan ka lissafasu ko a cikin dangi ko a wani gurin da kuka san asalin me kudi zaku ga duk yawancinsu yan kauye ne wanda basu sakawa kansu girman kai ba,ko kuma wadanda suka yiwa iyayensu hidima cikin rashi ko samu wanda basa kyashi ko jin kunyar tallafawa na kasa dasu masu kyakyarwa niya da son aikata alkairi,idan kuma kuka ci karo da akasin haka to lallai ishara ce daga Ubangiji zuwa garemu, domin hausawa sunce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah,mu yi kokari mu cire son ya'ya mu tsaya akan tarbiyarsu tare da addu'a akan Ubangiji ya taya mu ya shirya mana su kan hanya madaidaiciya,rayuwa ta lalace musamman a wannan zamanin dan haka kar mu zauna mu saki baki muce wai Allah ya shirya, ey dama ke kike shiryawa Allah ne me kome amma komai akwai sanadi dan haka ki tashi tsaye da addu'a da kwanji da kuma nasiha ki ceci rayuwar iyalanki, Allah ya shirya mana dan alfarmar shugabanmu Annabi Muhammad s.a.w). **** Yau ne kwanakin da ABM suka bawa zahida na haduwa da su,dan haka tun safe bata je ko ina ba,hatta da larai da anne sai da suka gane cewa zahida na cikin farinciki,ban da kaiwa da kawowa babu abinda take yi,ta yi shiri ta sauya ya kai dau goma,duk dan kar taje su rainata, saboda a kwanakin da take zaman juransu sosai ta yi musu kutse cikin al'amuransu dan bayan asibitin ta kuma.gano wasu boyayyayyun asibitocin kusan uku da kuma gidajen mai masu irin sunansu wanda bincike ya tabbatar mata da nasu ne,ga kuma companies da suka tashi kanta lokaci daya arzikin ABMs ya tashi kanta ya nemi kusan zarar da ita,tabbas ABMs sune irin mutanen da ta jima tana nema domin ta yi mu amala dasu ta bussiness sai gashi ta da ce cikin laluben da bata tsammaci haka daga cikinsa ba. Karfe biyar saura mintina a sharin ce ta yi mata cikin hamshaqin asibitin da duk zagayenta na yawon duniya bata taɓa cin karo da me kyau da tsarinsa ba,tun daga harabar asibitin zaka san cewa an kashe mata kudi bana wasa ba,kuma wai ace duk domin talakawa kuma ɗan Allah,kai dole akwai wani abu a kasa makamancin nasu,abinda zahida take sakawa ranta ke nan tana faman bin ko ina na asibitin da kallo,tana nuna shedar da aka turo mata a waya, taga wani babban mutumin yaiso gare ta tare da nuna mata hanya bayan sun gaisa,yana gaba taba binsa a baya ,tana kuma da da shan mamakin asibitin ko ina ja a ne ,masu jinya da masu lafiya suna hadagadarsu cikin tsari da kwanciya hankali, likitoci kawai take cin karo da su jar fata da bakar fata suna faman zagaye suna duba marasa lafiya cikin kula da tarairaya,a ranta ta ce dama nima tun farko na saki raina na nuna musu kauna da yanzu asibiti mu ce akan wannan matsayin,amma yanzu ma lokaci bai kure ba zan gyara kasuwanci ne ta yadda sai na rufe babin abms a duniya,daidai lipter ta sake su a hawa ba bakwai,inda mutumin ya bude mata wata hadaddiyar kofa ta shiga,take jikinta ya kuma mutuwa zuciyarta kuwa cike take da zumuɗin ganin wannan mutumin da ya bawa raywarta wahala. Nuna mata wajen zama mutumin yayi tare da dan russunar da kai sannan ya koma daga wajen kofar ya kame kamar wani gunki, Takun da zahida ta ji tare da kamshin da yake kusanto ta ne yasa ta maida hankalinta saitin wajen da ya raba inda take da wasu shegun labulaye ido, yayin da zuciyarta ta shiga wani irin bugawa da karfi, duk takun da za a yi yana tafiya da bugun zuciyarta ne,wai waye ABMs din nanne?ta tambayi kanta daidai lokacin da aka dage dogon labulen da yayi shinge da tsakaninta da ABMs............. Zahra✍️✍️ Opay Fatima yushau Adam 8064537048 Decommen is coming Payment is 1k [5/14, 3:31 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page57``* Cikin wani irin azabar bugun zuciya da hanzarin da ya wuce hankali ta miƙe tsaye bakinta sake,idanunta a buɗe ƙofofin hancinta gaba dayansu a bude, numfashinta kuwa take ya fara barazanar barin ƙirjinta,cikin fitar da numfashi sama sama kamar me asma ta bude bakinta da yake wani irin karkarwa cikin in ina ta ce"ke ce"?a hankali kuma cikin nutsuwa da takun birgewa ta ƙaraso ta zauna cikin kujerarta da take juyi kamar fanka,a hankali ta ɗauki ƙafarta ɗaya ta ɗora akan ɗaya tare da zare glass ɗin da yayiwa kyakkyawar fuskantarta kawanya, sannan cikin sanyin muryar ta ta ce"nice mana kin yi mamaki ne?"wani irin kallon tashin hankali da fitar hayyaci zahida ta yiwa AMINATU tana cewa "Wallahi ƙarya ne ni za a mayar 'yar iska? maza ki kira min ABMs din ko yanzu na ɓaɓɓallaki a wajen nan dan wallahi sai na huce fushina na tsawon rayuwar da muka yi da ke,shegiya me kwacen miji,yanzu kuma kin bar ƙwacen miji kin koma kwacen dukiya ko?"aminatu ta ce "eh mana da ke kin san abin gado ne daga uba"sharaf zahida ta yi a dandagaryar kasan wajen tana kallon aminatu cikin sarewa kana ta ce"wai da gaske kike ke ce ABMs?" Muryar da ta ji yana bata amsa da cewa "tabbas" ne ya sa ta suman zaune, Bala i kan Bala i kenan wane irin mafarki ne wannan,ya Allah ka gaggauta farkar da Ni daga wannan mummunan mafarki"ta fada tana kallon MUS'AB da yake takawa a hankali cikin kamewarsa da wannan asalin fuskar tasa da ta sani mara fara a da rashin daukar raini ga kamshinsa da ya cakude da kamshin aminatu da tun shigowarta office din take jin kamshin yana ratsa kofofin hancinta, bayan aminatu ya tsaya tare da zura hannunsa ta cikin wuyanta yana gyara mata zaman sarkarta,aminatu kuwa bulhakki ta sanya masa kukan tabara wai dan me zai fito,cikin kananun hawaye ta sanya karamin hannunta ta janye nasa da yake wuyanta yana shafa zaunannen wuyanta da yayi dabas babu rama bare kuma wajen da kashi zai zauna,ta ce "cewa nayi fa karka fito daddy har ka bari ta tafi"a hankali ya ɗan sunkuyo da kansa saitin wuyanta ya sumbata kana cikin dakakiiyar muryarsa wadda ya tausasata ingantata wajen rarrashin gimbiyarsa ya ce"Ni bana tsoro akan duk abinda zai same Ni, amma ina tsoro akan duk abinda ya shafeki duk abinda zai kusance ki indai na cutarwa ne to na yi alkawarin shiga tsakani nayi alkawarin kare rayuwarki d dukkan karfina da zuciyata da kuma numfashina, addu'a ta kullum ita ce Allah ya bani dama ya bani ikon kula dake fiye da zinaren da aka hako cikin tsananin yunwa da ishi,ya bani ikon riritaki fiye da jaririyar da ake da tabbacin cewa daga ita ba kari ita ce ta farko kuma ta karshe,to ta yaya kike tunanin zan barki tare da kurar da ta jima ta na farautar namanki eh?"kalamansa ba karamin sanyin jiki da na zuciya suka saka mata ba,idanunta tuni suka fara zubar da kwalla,cikin sauri ta mike ta rungumesa tana wani sakin marayan kuka kafin cikin wani 4iin shaukin da ya bayyana tun daga kasan zuciya ta ce"daddy i love....shiiiii ya katseta bayan ya dago kanta da ido yayi mata alamar cewa ba anan ba ta adana kalamanta domin suna da tsadar da ba zai iya sharing din junsu da wani ba,da karfi ta kuma rungumesa tana sakin wata yar sassanyar dariya, och ya fada yana dan yatsuna fuska cikin sauri ta sakesa tan tambayarka lafiya cikin rushewa da bayyana tsananin damuwa,kanta ya nuna sannan ya nuna saitin zuciyarsa da wuyansa sai kuma alamar mutuwa,dukan kirjinsa ta yi tare da shigewa cikinsa tana fidda wani irin murmushin da ya kusa sumar da dan gidan Nana. Kukan da zahida ta fashe dashi ne ya sasu kallon in da take,hango ta su kayi har ta kai bakin kofa cikin rarrafe, numfashinta da kyar ya ke fita kamar zata mace musu anan,zamewa aminatu ta yi zata nufeta ya yi saurin riketa yana girgiza mata kai,waya ya dauko yayi yan danne dannesa sannan ya janyo aminatu suka fice daga office din,wani uban ihu zahida ta kurma tare da zubewa wajen a sume,cikin sauri Dr ele ya kira mus ab ya sanar da shi,kai tsaye ya ce su kai ta can Asibitinsu gjk kar su sake su kwantar da ita a nan,cikin bin umarni Dr ele yasa aka ɗauki zahida kamar wata gawa aka saka ta a mota ,kai tsaye asibitinsu aka nufa da ita. Mus ab suna fita daga ɓangaren nan, kai tsaye Dr Idris ya kira, yana zuwa ya ce "yallabai wannan mutumin yau ne za a sallamesa kuma yana nan yace ba zai tafi ba har sai ya ganka ido da ido yayi maka Godiya"dan jim mus ab yayi sannan kuma ya jinjina kai tare da wucewa hannunsa cikin na aminatu da duk mamaki ya ishe ta akan abinda ya faru tsakaninsu da zahida,tunaninta ne ya katse lokacin da suka shiga wani daki me dauke da gadon majinyaci daya sai kujera doguwa guda daya da cafet da fringi, kana kallon dakin dai kasan cewa v I p ne,duk da cewa su nan basu da wani v i p sun dauki me kudi da talaka duk daya ne ba wani banbanci dan haka inda za a kwantar da me karamin karfi nan za a kwantar da me babban ƙarfi,kallonta ta mayar kan majinyacin da tun shigowarsu miyan bakinsa ya dauke, yunkurin da yake dan tashi tuni ya fasa, fuskarsa tuni ta nuna wata irin firgita da dimauta,aminatu ma zuba masa ido ta yi kafin cikin sauri ta dauke ta maida kan mus ab da bai kalli kowa a cikinsu ba,kafin ta yi magana ta ji muryar Dr idris yana cewa "to malam baffa wuro ga mutanen da kake ta son gani nan kuma sune masu wannan asibitin da duk wani abu da ya danganci sunan abm gaba daya, sai kayi musu godiya duk da cewa su ba ita suke bukata ba "daga haka ya juya ya fice daga dakin tare da rufo kofar ...... ******** Alhaji Jamil Alhaji Garba da Alhaji Kabir, suna zaune a falonsu na gidan gona suna ta haɗa haɗar hada sabbin customer,baka Jin komai sai a falon sai dariyarsu cikin farin ciki da nishadi,Abba Kabir ne ya fara tsagaita wa da dariyar da suke akan tsoron da su mus ab suka ji suka janye karar da suke shirin shigarwa ya ce"amma fa ina dan jin shakka akan yaran nan wallahi gani nake kamar da wani abu da suka taka"Garba ya ce "kai ba wani abu da suka taka mun riga mun karɓe komai daga garesu, bakinsu kuma ba zai wadatar da su a ko tun ba kunga kuwa dole su janye,Abby ya ce "bari ma ku gani yanzu na sa su ɗanturqui su kashe yaron nan dan yanzu shi kadai ya rage mana gara mu aika shi tun kafin ya samu dama ya kufce ya dawo mana da aiki baya"cike da gamsuwa suka hada hannu ji kake fas fas sun tafa, daga nan abby ya sanya kiran danturqui,kira daya kuwa ya daga yana masa irin gaisuwarsu ta yan shaye shaye, dakatar dashi Abby yayi da cewa "ku kashe yaron nan kawai ku dauki gawarsa ku jefa ta can rami,idan kun kashe shi ku ɗauki vidon ka turo mana dan mu tabbatar"an gama oga kabar wayar ka a kusa da kai yanzu zaka ji sako"daga haka Abby ya kashe wayar suna ci gaba da kyalkyala dariyarsu. Kwace wayar dake hannun danturqui wani basamude yayi, kana ya dubi na kusa da shi ba tare da ya ce masa komai ba, amma tuni ya gane me yake nufi cikin sauri ya fita jim kadan sai gashi dauke da kaza a hannunsa, mikawa danturqui yayi yana cewa "maza saka kanta gabas ka yankata akan wuyan Ahmad"zaro ido dan ladi yayi a tunaninsa shi za a yanka, to su su waye wadan nan ɗin?tambayar da yayiwa kansa kenan bai samu amsa ba yaji daya daga cikin mutanen yana cewa "yi sauri ka kwanta bamu da lokaci"kwanciya dan ladi yayi yana salati da fatan Allah ya kawo masa ɗauki,yanka kazar yayi wanda take ta fara tsartar da jini me uban yawa, saitata yayi saurin yi a wuyan dan ladi jinin na zuba a wuyansa yana gangarawa kasa kai idan ka ga dan ladi sai ka yi zaton yankashin a kayi da gaske,wanda ya fuskanci shine ogansu ne yayi magana ya ce"ka rufe idanunka ka yi kamar ka mutu za a yi maka video"kafin ya rufe bakinsa ma tuni dan ladi ya rufe idonsa tare da mirginar da kansa kamar matacce, video suka yi masa har da wukar da suka yanka kazar sannan suka turawa su Abby daga nan suka kwance dan ladi, tare da bashi wasu kayan ya saka,su kuma su danturqui suka tasa keyarsu bayan sun nuna musu ID din su,take jikinsu ya shiga rawa hankalinsu ya tashi ashe duk zaman nan da suke yi da jam'i an tsaro suke yinsa, ankwa suka sanya musu suka tasa keyarsu,dan ladi kuwa kai tsaye babbansu ya bada umarnin inda za a kai shi daga haka suka rufe gidan suka bar wajen. Lokacin da videon ya shigo musu ba karamin farin ciki su kayi ba,dan haka take su ka hada shagali a daren ranar wanda suka dinga kiran abokan hulɗar su suna basu goron gayyatar,abunka da masu iko tuni suka saka oder duk abin da suke bukata kama daga kan abun sha da ci har zuwa kan kayan maye nau nau'i,har da mata saboda bakinsu masu bukata, to anan dai shima garba ya ce dole dai dan tuna kuruciya ko da na ranar ne. Tunda aka kai zahida aka kwantar babu likitan da ya bi ta kanta saboda dama yawancin likitocin duk sun gudu saboda matsalolin da ake fuskanta a asibitin,dama ta bari ne idan sun hadu da abm sai su dauki sabbin ma aikata gigaggu kuma akan aikinsu,dan haka bata samu wata kulawa ba a matsayinta na wadda take tafiyar da asibitin, dan kanta ta farfaɗo daga doguwar sumar da ta tafi. ******* Da sauri aminatu ta juya zata fita daga dakin,mus ab yayi sautin rikota yana kallon idanunta da suka sauya kala babu abinda suke fitarwa sai wani irin ruwan bakinciki da takaici wutar daukar fansa na ci a cikinsu,da ido ya shiga yi mata magana wanda hakan yasa ta tsayawa sai dai bata kuma kallon inda baffa wuro da iyalansa suke ba,kukansa ne ya karade dakin yi yake tamkar ba zai daina ba,kafin cikin kukan da ya ɗan rage sautinsa yake cewa"kaicona kaicona kaicon rayuwata wallahi nayi nadama na yi da na sani ba sai yanzu da na ganki a gabana na yi nadama ba,wallahi tun lokacin da na fahimci yaudarar da su jamilu su kayi min, Aminatu ki yafe min a madadin mahaifinki da mahaifiyar ki duk da nasan cewa hakkin ragowar jama'ar rigarmu ba zai barni ba,dan shine ya fara kamani tun yanzu, kallon yaransa da matarsa yayi kana ya ce"ko ba yan raina ina so ku guji taba mutum hakkin mutum ko da na dabbane da kuke gani ba karamin bala I ba ne dan hakki tun a duniya yake fara taba ka wala dukiyarka ko lafiyarka, wato hakki da kuke gani wani abu ne da baya taba barin mutum yayi gaba,ko bashi da kuke gani idan har mutum yana sane ma ana saboda mugunta ya hanaka to wallahi hakkinsa zai iya taba arzikinka duk abinda ka taba zai iya lalacewa, wannan nasiha nake muku a karo na farko a kuma matsayina na mahaifinku, kuma ina rokon yafiyarku dan Allah d....ya kasa karasawa saboda kukan da ya ci karfinsa,take zuciyar aminatu ta yi rauni nadamarsa da ta ganu tun daga zuciyarsa yasa ta ji ta yafe masa,kadan kenan daga cikin sakamakon Ubangiji akan tubatun nasuha,tuban da da kayi sa domin Allah daniyar ba zaka sake sikatashi ba, dan haka ta kallesa duba na Rahma ta ce "baffa wuro Allah gafururrahim ne me gafara, domin kullum kofofinsa na karbar masu tuba a gareshi a bude su ke,dan haka nima na yafe maka sai ka ci gaba da istigfar ga Ubangiji Allah ya baka lafiya ya kiyaye gaba"bata tsaya sauraron godiyar da yake mata tare da shi da iyalansa ba ta fice tana goge kwallar idanunta,shima Mus ab kallonsa yayi tare da cewa daga nan nasa a maida kai gidan ka saboda yanzu ya dawo hannunka daga wancan hannun da ka siyar kaga kenan yanzu zaka ci gaba da zama cikin gidanka hankali kwance saboda babu haram a cikinsa dan karar da haram din, yanzu kuma sai ka yi kokarin gina halak dinka dan haka idan ka yi tunanin sanar da zaka yi ka kira Ni kai tsaye"ya fada yana mika masa katinsa me ruwan gold, babban dansa ne yayi saurin karba yana zuba godiya, anan mus ab ya kuma yi musu albishir da cewa za su ci gaba da karatunsu dan ya dauke nauyin wannan bangaren. A bangaren zahida kuwa tana farkawa ficewa ta yi daga dakin, ba tare da ta damu da kallon da mutane suke Binta da shi ba,kai har ta kai ga an fara nunata da yatsa, kallon kanta ta yi a jikin wata mota me bakin glass dake fake a harabar asibitin, sai da ta rufe idanunta ganin yadda lokaci daya ta koma kamar wata mabaraciya me neman na abinci,bude idanunta ta yi tana kokarin sauke ajiyar numfashi,kit numfashin ya tsaya kwayar idanunta kuwa tamkar zasu fado kasa, kafin ta fara ja da baya da baya tana nuna saitin glass din motar da hannu, ihu ta saka tana durkushewa a wajen tare da cusa kanta cikin cinyoyinta,take mutane suka taru akanta ana tambayarta lafiya wasu ma saboda tsegumi suka zo dan kowa mamakin ganin zahidar cikin wannan yanayin yake yi.duk wanda ya taba ta turesa take yi tana nuna motar gami da cewa,"fatalwa ku taimakeni fatalwa nake gani"tsaki wani dattijo yayi yana cewa "fatalwa ba ai yanzu kuka fara ganin fatalwa tun da ku jurinku kashe mutum"dakyar wasu daga cikin likitoci da suka yi ragowa suka tayar da zahida tare da tambayarta abinda ta gani,bude idanunta da tun dasu suke a rufe ta yi tana kallon inda motar take,motar na nan kuma a rufe glass dinta yake kamar yadda ta gansa tun farko, sabanin ganin da ta yi a karo na biyu,waige ta fara yi tana cewa "Wallahi na ga anita tana kallona ta cikin motar nan"tuni aka nemo me motar ya zo ya bude aka duba cikin motar amma babu wani me kama da Anita ma bare kuma ita da kanta,dan haka sai suka dauki zahidar suka saka a mota aka nufi gida da ita, sai dai wani abin mamakin shine suna zuwa kofar gidan taga wata nefef ta faka a kofar gidan wata makociyarsu tana sauka tare da mikawa me nafef kudinsa, sai dai kuma matar na juyowa su ka yi ido hudu da anita fuskarta duk jini tana kallon zahidar cikin kunar rai,wani irin ihu zahidar ta saka tana nuna musu cikin nafef din da Anita take ciki, sai dai hallau basu ga komai ba, sauri suka yi suka kaita cikin gida suka barota ita da anne da larai suna rarashinta,larai ta ce "wai dama anita ta mutu ne kuma akan me zata dinga zuwan miki a fatalwa tunda bake kika kasheta ba?"har zahida ta bude baki zata yi magana sai kuma ta fasa tana mai girgiza kanta saboda jinsa take kamar zai rabu da kwakwalwarta. ****** Suna zuwa gida aminatu tun daga falo ta tsare mus ab da tambaya,fuskantar sa ta yi bayan ta tare kofar shiga bedroom dinsa, tana cewa dan Allah daddy ka fada min wai me yasa kasa na jewa zahida a haka, kuma me yasa ka ce musu nice me ABM ?to ma abm din na waye?"naki ne"ya bata amsa kai tsaye tare da shigar da idanunsa cikin nata,dafe kirjinta ta yi, tare da cewa"daddy ta yaya ya zama nawa naji fa ance Abm din nan suna da yawa Ni ina na ga kudin da zan iya mallakar su?"dage kansa yayi tare da nuna mata alamun ya gaji tabarsa ya huta da magana,make kafada ta yi tana mai kuma tare hanyar ta hanyar riƙe ƙugunta tana yin fadi, sannan ta ce "aradun Allah daddy banni barinka hutawa sai ka fede min buri har wutsiya"cikin rarraba kalmomin da zai fada ya ce "dukiyarki da baffa ya bani ita ce ta zama abms"ware manyan idanunta ta yi kafin ta kai masa wata dimautacciyar runguma tana cewa "wayyo ni Aminatu MATAR ƊAN BIRNI Allah ka barni da hamma mus ab dina,namiji guda a cikin miliyoyin maza,nagartaccen namiji me amana jarumi kuma gwarzon BODDO rayuwa babu kai gawa ina sonka da dukkan zuciyata ina sonka da dukkan rayuwata kai din kayi kuma na musammanne kamar yadda komai naka yake na musamman, wallahi mus ab din aminatu ba duk kai ba,daddy mus ab ya zama ƘADDARA SANADIN HASKE NA bayan KUDURAR ALLAH da ta riga ta haɗa mu,wani irin juyi ta yi ajikinsa tare da sumbatar labbansa ta na ci gaba da cewa MUS'AB dina me kyau ne jarumi ne domin jarumtarsa ta wuce ta BOYAYYIYAR RAIHAN kuma kyawunsa ya fi na hamma wazeer , shi yasa nake da yakinin cewa insha Allah zan haifa masa yarinya me kyau kamar ZAHRA YAR GIDAN YARBAWA"jan dogon hancinta yayi tare da girgiza kansa kana cikin karamin sauti me dauke da wasu irin zafafan sinadaran karya lagon jarumar mace ya ce" a'a na fiso ki haifa min me kama da AMINATU MATAR ƊAN BIRNI"daga haka ya daga ta cak bai direta a ko ina ba sai a bathroom..... **** Gidan gona da ya fara daukar haramin manyan kusoshin masu kudi masu fada a ji da kuma yan mata hadaddu da kayan shaye shanye na musamman,duk wanda ka kalla zaka ga fuskarsa cikin farin ciki da walwala hira kawai ke tashi ta ko ina , ga kuma tattausan kida da yake tashi a hankali. Karfe takwas na daren guri ya kuma dinkewa da jama a, babu abinda ake sai shagali,iyayen biki kam ba zan iya ce muku komai akan su ba, dan su din sun fita da ban cikin dubban mutanen da suke makare a wajen,su daddy harba tuni an shiga harka da mata abin nema ya samu,Abba Kabir kuwa kwalaben giya ne a gabansa yake ta durawa cikinsa,shi kuwa dama Abby kudi ne butinsa dan haka baya ko daya daga cikin wadannan dabi un,idan ka cire zallar rashin imani,ana tsaka da shagali wuta ta dauke gaba daya gidan take komai ya tsaya....... Wanda bai karanta wannan littafan nawa ba zai iya tuntubata dan bayarwa akan farashi me sauki✍️ Zahra..... 8064537048 opay Fatima yusha u Adam De comment is 1k only [5/15, 4:54 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page58``* "Kai me ye haka? maza kuje ku tada jen"Abby ya fada yana kokarin kunna wayarsa,duk wanda ka gani da haske a gun to wayarsa ya kunna,Garba kuwa yana can yana sharholiyarsa da mata har uku, a cewarsa yau fa sai yayi kara i,zagawa baya abby yayi da wayarsa yana mita,"me za a yi da harka da talaka daga an dauko ku kuyi aiki amma gaba daya kun lalata mana sabga, me za a yi da rashin haske" daidai lokacin da ya zo inda jen din yake yana haske wajen, cikin zafin rai ya ke cewa "au guduwa kuka yi kuna ina ne wai?"ya fada yana kara haske wajen da wayarsa amma bai ga kowa ba, tsaki yayi tare da juyowa wajen da jen din yake dan ya duba da kansa ya ga me yake damun injin, abinda ya gani ne ya haifar masa da rawar kafa hannunsa kuwa tuni ya saki wayar dake hannunsa yana haskawa mararsa kuwa wani irin daurewa ta yi, bakinsa banda karkarwa babu abinda yake yi, a hankali ya dinga juyawa har sai da ya bawa abinda ya gani zaune akan injin baya,rayawa yayi a ransa cewa shine fa me shiga daji duk duhunsa me hawa tsauni duk tsayinsa shine fa me mu amala da sunduki me sauyawa zuwa duk suffar da ya gadama kuma hakan bai taba girgiza shi ko tsorata shi ba,sai yanzu dan kawai wani mutum da ya jima da mutuwa ya zo masa a fatalwa shine zai sauya masa nishadinsa,hakan yasa shi juyawa dan kuma fuskantar sulaiman idan ma wata mutuwar yake bukata shi mai iya kara kashe shi ne a yanzu ba da bata lokaci ba,sai dai yana jiyowa yaga wayam, dan haka sai yayi dariya yana cewa da na tsorata da shike nan na bashi hanyar da zai ci gaba da bibiyata"injin ya kuma sunkuyawa zai tayar,sai kuma ya fasa ya dago kansa dan neman ma aikatan da suke da wannan alhakin,juyawa yayi daniyar barin wajen amma sai yaji kamar an rike ƙafarsa daya ta cikin kasa,kallon kasan kafafunsa yayi, bai san sanda ya kurma wani uban ihu ba, sakamakon ganin dan ladi da yayi kwance a gabansa cikin yanayin da aka turo masa shi a waya, da gudu ya fita daga wajen yana tsalle tsalle da taba kafafunsa da suka ɓaci da jini. Yana shigowa wajen taron kowa ya fara yin ta kansa saboda ihun da ya ci gaba da yi dan duk ya taba ƙafarsa yaji wannan jinin sai ya zabura,cikin kankanin lokaci kowa ya watse hatta da ma aikatan da suka dauko sun yi ta kansu, sai yasu yasu da suke ta faman rike abby saboda yadda yake ihu kuma duk inda ya juya sai yaga dan ladi cikin jini ko kuma sule da yake ta zuwa masa cikin kamanni kala kala,take dai Abby ya zama tamkar wani mahaukaci,Garba da Kabir har yanzu basu ga komai ba shi yasa suke zaton ko dai gamo Jamil yayi,dan haka suka yanke shawarar tafiya gida cikin iyalansu ko zai dai na gani tunda ita kanta gonar daji ce,saidai me suna tunkarar kofar fita suka ci karo da wani tashin hankalin dan kuwa kofa ta rufe kanta ga wani rubutu da aka yi a jikin kofar da jini, take suma hankalinsu ya fara tashi, duk kofar da suka nufa dan barin gidan sai su ji ta a kulle ga duhun da ya mamaye ko ina na cikin gidan,Garba ne ya koma da baya yana laluben wayarsa akan kujera amma a maimakon ya dauki waya sai kawai ya ji ya damki gashin mace cikin hannunsa,take ya zabga wani uban ihu yana mai komawa da baya,da sauri Kabir shima ya fara neman yin takansa sai dai kuma ina hakan bata samu ba,ji kake tim yaci tuntube da abinda ya tabbatar da cewa gawace sai ga goshinsa na fitar da jini,cikin rawar baki abby ya ce"kun ga abinda na ke gani ko kuna gani matatun da muka kashe ne suke ta dawowa,hatta da sule fa ya dawo dan ladi ya dawo sai kuma wasu da ban san su ba amma suma inaga duk suna daga cikin wanda muka kashe sai.....tsawar da suka ji an yi ne yasa suka hade guri daya suka cure kamar wasu kudaje,jikinsu rawa kawai yake idanunsu kuwa sai walwala sule saboda karshen budewar kwayar idon,jira suke kawai ko ji daga ina tsawar take, a maimakon haka sai kuka da suka ji ya biyo baya daga haka kuma sai dariya,wayyo fans zan so kuga yadda jarumai marasa imani suka koma cikin lokaci kankani, gaba daya sun fita daga kamanninsu,Kabir ne ya fara sakin fitsarin da ya rike masa mara kafin na abby ya biyo baya,wata siririyar murya suka ji daga can saman benen tana cewa, "sannunku da kokari aikin ku yayi kyau sai dai sakamakonsa ba me kyau ba ne ku a naku jahilcin kun dauka idan kuka kwace duk wata shaidar zama a kotu kun tsira kenan?"wata irin dariya Muryar ta kuma shekewa da ita kana ta ce"muje zuwa dan iska ka fasa muddin baku tonawa kanku asiri ba ba zaku taba daina ganin tashin hankali kala kala ba,daga haka suka ji dif tare da kawowar haske a lokaci daya. Da mugun gudu suka nufi kofa suna ture junansu kamar wasu akuyoyi,ga mamaki su suna zuwa suka ga kofar ta bude gaba ɗaya,ai take suka ranta a na kare, duk cikinsu babu wanda ya nufi hanya daidai saboda tsananin tashin hankali. Aminatu da mus ab kuwa tun bayan fitowar su daga wanka ya bata abinci ta ci sannan ya kwantar da ita kamar jariryya haka ya dinga jijjigata har ta samu ta yi bacci, cikin dare ya ji aminatu ta farka, sai da ta leka fuskarsa ta taɓa idonsa ta tabbatar bacci yake sannan ta zaro wayar ta ta sauka daga kan gadon tare da ficewa daga dakin cikin sanda,bude idonsa yayi kafin ya gyara kwanciyarsa ba tare da zuciyarsa ta raya masa bin bayanta ba. Zama ta yi a kan kujera kafin ta fara magana kasa kasa tana cewa "Allah kuwa aunty zainab ban taba tunanin shirin zai kawatar irin haka ba,yanzu dai dukkansu sun fara karbar zunubinsu na duniya a hannu, ai yanzu ma aka fara wasan fata na dai su yi abinda muke son su yi, tunda dai bafulata ta tabbatar mana ba zata cutar da su ba kawai dai za a jijjga su ta yadda zasu tonawa kansu asiri da kansu wa duniya"dan jim ta yi da alama tana sauraren dayan bangaren ne, kana ta fesar da numfashi ta ce wallahi aunty zainab bana don ganin daddy cikin damuwa tausayinsa nake ji saboda halin da ya shiga na jin yadda komai ya faru na bangaren rayuwarsa"daga can bangaren anita ta ce,ai yanzu ke ce abin tausayi sminstu saboda ke duka uwa da uba babu kinga kuwa kece marainiya"aminatu ta ɗan turbude fuska kamar yana ganinta sannan ta ce"aunty ni ba marauniya ba ce saboda ina da daddy shine komai na a yanzu kumanna tabbata idan ina tare dashi ba zai taba barina cikin damuwa ba sai dai abinda ya fi karfin iyawarsa da kuma kaddarar da bai isa kawar da ita ba "murmushi anita ya yi sannan ta ce kije ki kwanta kar yarinman naki ya juya yaga bakya kusa dashi"daga haka ta katse wayar ta bar aminatu da sakin murmushi,ko da ta koma yana na a kwance idanunsa a rufe, bacci ya ke son komawa amma bai koma ba sai da ya jita ta rungumesa ta baya sannan ya saki boyayyiyar ajiyar zuciya tare da kuma janta cikin jikinsa. ********* Har wayewar gari su Abby basu fahimci inda suke jefa kafafunsu ba, dan haka basu suka koma gidajensu ba sai wajen karfe tara na safiya,yadda yake abirkice haka ya je ya samu zahida abirkice saboda jiya itama vata yi bacci ba kwana ta yi iface iface saboda duk sanda ta rufe idanunta bata ganin komai a cikin su face ƙananan yara wanda ta dinga fedewa tana cire kodar ko zuciyarsu suna yi mata kuka a kunne,dan haka lokaci daya ta yi wani irin baki ta fige idanun nan sun firfito waje kana ganinta kasan cewa a tsira e take cikin ko wane lokaci,tana ganin abby ta nufosa sai dai kafin ta karasa inda yake yayi wata irin zabura ya janye saman bene yana cewa karki zo kusa dani dan Allah ki gafarce ni ki yi min rai kinga dai bani na kashe ki ba"mamaki ne ya kama zahida to ko dai shima ya fara ganin abinda take ganin?"zahida fa ba dayawa ta yi ba tsananin tsira ta ne yasa Abby ya ga zahida ta juye masa anita,da wannan sautan ya fada dakinsa. Suma dai su Garba cikin tashin hankalin suka koma gida sai, shima Garba yana zuwa ya ci karo da dan ladi a bakin kofar dakinsa tsaye cikin fararen kaya,take Daddy Garba ya saki gudawa tare da kokarin komawa baya,sai dai kuma yana juyawa yaci karo da wani tashin hankalin dan kuwa Abba sule ya gani cikin irin shigar dan ladi wanda hakan yasa daddy Garba faduwa kasa sumamme bayan karar da ya saki.cikin sauri zubaids ta zo tana kokarin daga shi da zuba masa ruwa amma babu alamar zai farfaɗo dan haka suka ciccibesa suka yi cikin mota dashi, Shi ma dai Abba Kabir ba a barda a baya ba dan bafulata ce ta dinga sauya kamannin su Abba sule da dan ladi tana firgita shi tare da sanar dashi cewa lallai fa idan basu tunawa kansu asiri ba, basu fara ganin komai ba,wanda hakan yasa shi fitowa da mugun gudu kamar mahaukaci sabon kamu, yaransa biyu da matarsa su ne suka rikesa amma kokarin kwacewa kawai yake yi. A can bangaren asibiti kuwa, ganin halin da zahida ta shiga yasa kowa ya tattara inasa inasa suka bar asibitin hatta da ma aikata ba abarsu a baya ba,masu gadi ne kawai suka tsaya sai wasu likitoci biyu da suma suka tsaya dan gadin asibitin.dan haka koda su Hajiya zubaida suka kai daddy babu wanda suka samu da zai tsaya a kansa, dakyar dai suka lallaba wannan likitoci guda biyu suka shiga bashi taimakon gaggawa. A cikin kwana biyu kawai su abby suka zare ko ina ganinsu za aka yi suna gudun ceton rai shida kabir ,shi kuwa dadin zahida duk sanda ya farfaɗo ko mintina biyar ba a yi zasu ga ya koma suma shi kadai yasan abinda yake gani,bzahida kuwa gaba daya kunnen ta ya daina jin komai idan ba kukan mutane da na jarirai ba,abin na su Abby ya fara tsoratar da mutane dan gaskiya ba iya abinda aminatu suka shirya akansu ne yake faruwa da su ba, akwai ikon Ubangiji da ya fara tabbatuwa akansu tun a duniya, sai ya zamana basu da wani wajen zama su ji dadi kan kace me an fara haskasu a gidan talabijin da takardun jaridai da gidan rediyo,akan cewa gjk sun haukace rana tsaka. Nana tana can tana kallon duk abinda yake faruwa hankalinta kwance, dan tun a ranar da suka yi shagalin ganin fatalwu mus ab ya dauke ta daga gidan ya maida su babban gidansa da ya yi da guminsa dan zama tare da iyalinsa, gidan kamar etatet yake dan unguwa ce guda ya gineta saboda baya son yin nisa da ahlinsa so yake su gade waje guda gaba dayansu,musamman da yake binciken inda abbansa yake, a yanzu haka inna wuro da Nana da kuma Hajara da ƴaƴanta duka suna cikin gidan su ne kaɗai suka rage basu dawo ba, wato shi da aminatu da kuma abbansa. ****** A cikin kwana na uku da faruwar al'amarin ne Aminatu ta tashi da niyar yin wani abu guda da ya rage mata cika shi a duk cikin wasiyun da aka bata,dan haka tunda ta shi ta fada kichin tana hada kayan ciye ciye tun daga kan abinci har zuwa kan abin sha,mus ab tashin kanshi kawai ya jiyo,bai wani damu ba saboda tun da suka zama daya da aminatu bata wasa da duk abinda ya shafe shi, dan haka bashi da damuwa ta bangaren abinci dan kullum da salon girkin da yake ci a gidan, a hakan ma ɗan hankalinsu bai gama kwanciya ba ne,jinta yayi a ruwan cikinsa tana cewa daddy ka tashi ka shirya mun yi baki"cikin biyayyayyan yanayinsa ya kalleta wanda ita kuma tuni ta karbi jirginsa wato dai yana mamaki ne ammahakan bai bayyana akan fuskarsa ba bare kuma ya furtawarsa,yadda ta damesan har hakan na son SA masa danuwarta yasa ya muke tare da ita a jikinsa suka shige bathroom din,suna shuga ya hade bakinsa da nata yana mata shan yunwa dan hakika ya jigata da rashinta a tare shi, dauriya kawai yake ta yadda babu wanda zai fahimci feeling dinsa akan rashin aminatun,dakayr aminatu ta samu ta kwafi kanta ba dan komai ba sai dan muhimmancin bakin a tare da su,cikin rashin kuzarin da ya bayyana a yanayin rashin hanzarinsa suka gama shiryawa,aminatu rike kugu ta yi tana kallonsa kafin ta kai masa kyakkyawar sumba da ta zo masa a bazata tana cewa kayi kyau yariman aminatu"daga haka ta kama hannunsa suka fice daga dakin. Suna fitowa falon yaja ya tsaya cak yana kallon mutumin da hotonsa ba zai taba dacewa a cikin kwakwalwarsa ba,mahaifinsa farincikinsa Alhaji sulaiman,zaune cikin kyakkyawar shiga ta kamala da lafiya me kyau duk da cewa kana kallonsa zaka ga tsananin ramar da ta bayyana a jikinsa,a hankali ya maida kallonsa kan aminatu da take ta zabga murmushi me dauke da wani irin zallar farinciki, dage masa gira ta yi kana ta hade hannuwanta waje daya tana cewa sorry yariman aminatu kaina bisa wuya na so yin bazata da kyauta Mafi daraja ne a cikin rayuwarka,hannunsa ta kama ta karasa dashi gaban Abba sule sannan taja gefe tana kallon yanayinsu da ba zai iya fasaltuwa ba,mus ab ksa cewa komai yayi baya ga wata irin hadamammiyar runguma wadda ke cike da zumudi da ya kaiwa abban nasa, mus ab jarumi ne da wiya kaga abinda zai shi kuka dan haka yanzu ma bai bari ya zubda hawayensa gaban yara ba, tunda har bai zubda hawaye ba lokacin da yake karanta labarinsu me cike da rudani ba to tabbas ganin mahaifinsa a gabansa ba zai sa ya zubdq hawaye ba,duk da cewa koda yayi to ba komai ba ne sai na zallar farinciki, hankali anita da Ahmad suka sulale suka bar falon aminatu na shirin ficewa taji Abba ya kira sunanta, wamda hakan yasa ta tako a hankali ta dawo gabansu,kallonta mus ab kawai yake yi ya rasa ta inda zai fara nuna mata godiyarsa da kaunarsa a gare ta,ga kuma.tambayiyin da suke cunkushe a kansa na yadda a kayi duk haka ta faru ba tare da saninsa ba,tsaf aminatu ta karanci zuciyar jaruminta dan haka sai ta kuma.hade hannunta tana mai karya kanta kafin cikin taushin muryarta da ya ji kamar an kara mata zaki ta ce. "Dan Allah Daddy kayi hakuri wallahi tausayinka nake ji shi yasa na yi hakan ba tare da saninka ba,bana son damuwarka saboda halin da ka tsinci rayuwarka a ciki"shiru bai ce komai ba yasa ta ci gaba da cewa,tun ranar da muka gama karanta littafin nan na kuma yin mafarki da Abba, kuma acikin mafarkin ya sanar dani garin da yake wato garin Kano,na fara tunanin sanar da kai kenan sai bafulatanar baffana ta bayyana a gareni cikin kyakkyawan yanayi da suffa irin ta dattijan mutane,ban razana da ganinta ba kuma hakan baya rasa na saba da yanayin da tazo min acikinsa, a lokacin ta kwantar min da hankali ta ce mun kar na fada maka kuma duk abinda su Abby suka umarce mu da yi mu yi musu kai tsaye ita zata taimaka mana kuma in sha Allah sai su Abby sun girbi abinda suka shuka,ta gaya min cewa da kanta zata dauko Abba ba tare da wata cutarwa ba,na gamsu da abinda ta gaya min dan haka na bata kwarin gwiwa ta hanyar saka yarda ta a kanta, washe gari ta dawo min da kyakkyawan labari akan ta dauko Abba ta kuma kaisa inda ya dace wato ta barsa a hannun a nita saboda ya samu kyakkyawar kulawa, daga nan ne kuma ta shirya mana duk abinda take son mu yi akansu Abby da zahida,Abba sule da Ahmad da kuma Anita duk a matsayin matattu suke a idon su Abby dan haka da su za mu yi amfani wajen sa su Abby su gayawa duniya abinda suke aikatawa, ni ban san komai akan Anita da dan ladi ba kuma ban san alakarka da su ba,bafulata ce ta haɗani da su tarw da sanar da ni komai akansu da labarinsu,kuma a wajen su na san kai br ne,wannan dalilin shine yasa zaka ga ina yawan yin waya a boye,kuma ina yin video call da Abba,duk abinda mu ka yi mun yisa ne domin sauran rayukan da basu ji ba basu gani ba,amma a yanzu haka tuni muka daina razanasu saboda mu fahimci cewa hakkin mutanen da suka dauka da kuma hakkin ran da suka dauka ya fara bibiyar rayuwarsu dan gaba dayansu babu wanda yake cikin natsuwa",shiru ta yi tana kallon fuskar mus ab da yake yi mata wani irin kallo me kumshe da sakonni iri daban daban,Abba ne yayi gyaran murya tare da cewa "Allah yayi muku albarka mus ab kaima naji duk irin gwagwarmayar da kayi da rayuwar aminatu Allah ya shirya mu ya gyara mana bayanmu,yasa al umma su amfana da darasin da yake cikin rayuwarmu"Amin suka amsa. Daidai lokacin Anita da Ahmad suka dawo falon,addu'a Abba yayi musu doguwa Sannan suka shafa,dubansu yayi yana cewa to a taimaka a karasa lada akaini wajen zinariyata,dariya su kayi gana daya har mus ab sai da ya murmusa,kanne masa ido aminatu ta yi tare da yin solut dinsa kana ta yiwa hannunta kiss ta hura masa,tashi Abba yayi yana cewa mu wuce kar a samu tsaiko kuma kun samu ku huta gaba daya dan naga kuna neman mantawa dani a wajen".dariya suka kuma yi daga haka kuma suna rankaya a mota suka nufi estate din mus ab..... Zahra✍🏽 [5/16, 2:32 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page59``* Anne na zaune ita kadai abin duniya ya isheta saboda gaba daya gidan ya hargitse, na farko dai halin da danta ya shiga ga kuma na zahida da suke kamanceceniya,sai kuma Nana da har yanzu bata san inda take ba,ga isma shima da baya nan ko wayarsa ta kira baya shiga,a wajen suhaima kawai take samun sauki, itama suhaiman bata san me yake faruwa ba, dan mus ab tuni yayi mata biza ita da Khalid suka bi mijinta Faransa inda yake aiki, shi kuma Khalid aka nema masa makaranta a kasar Dubai, kwanansu biyu a Faransa Khalid din ya wuce makaranta bayan ya samu yayi waya da masoyansa baddonsa da kuma nanansa,Mahaifiyarsa kuwa ko tunaninta baya yi,sai lokaci lokaci abinka da uwa ko wace irin ce akwai soyayyarta a cikin zuciyar danta,mus ab yayi haka ne saboda baya son Suhaima da Khalid su san abinda yake faruwa, Khalid kuwa cikin farin ciki uncle sule ya taresa a Dubai daga nan kai tsaye makarantar su ya wuce da shi, inda anan zai yi karatunsa tun daga kan haddarsa ta alkur ani har zuwa bokonsa,karatun addini kuwa sai inda Allah yayi zai tsaya domin wannan shine burin mus ab yaransa su tashi da ilmin sanin Allah da duk wani hukunci da Ubangiji ya tanadarwa mai barinsa,wanda hakan shi kadai ne zai taimaki mutum wajen kare kansa daga sabawa ubangiji. Wannan dalilin yasa anne ta zama wata iri dan ma akwai larai tana taimaka mata wajen kwantar mata da hankali amma da abin yayi mata yawa,kamar yau din da suke cika kwana uku da fara shiga wannan tashin hankalin, Anne na zaune a falon ita da larai saboda yanzu gaba daya sun daina zaman daki, dan muddin suka matsa daga Falon Abby ko zahida zasu iya ficewa daga gidan,su fita waje har ragowar securities din bakin gate su san halin da ubayen gidansu suke ciki,shi yasa basa matsawa daga falon, suna zaune cikin jimami suka jiyo karar fashe fashe hashen glasses da sauran abubuwa na karau ga kuma karar zahida a waje daya tana yi tana surutai da magiyawa kananun yaran da suke mata kuka acikin kai,da gudu suka haura saman, kai tsaye bangaren zahifar suka nufa inda tun daga kira suka fara cin karo da abubuwan da ta farfasa kama daga kan showglas tauraruka da dai duk wani abu me amfani ko da ba mai fasuwa ba ne,turus su kayi daga bakin kofar a tsorace suna kallon zahidar da hannayenta da duk ta ji musu ciwo,tana kallon anne ta nufi ta da gudu ta riketa tana wani irin gunjin kuka,kama ta larai da anne su kayi cikin tsananin tausayawa anne ta ce "me yake damunku ne zahida me yake faruwa da ku ku hudun nan? tabbas akwai wani abu da ku ne kaɗai kuka sani, shin haukacewa kuka yi ko kuma cikin hankalinku kuke yin duk abinda kuke dan wannan abinnaku ya fi kama da masu hauka sabbin shiga?"girgiza kai kawai zahida take kafin dakyar bakinta ya samu ya buɗe,cikin haki da rawar murya ta ce"Anne da ace zan yi hauka na fita daga hayyacina na daina jin Abinda nake ji na daina ganin abinda nake gani da na fi kowa farin ciki domin nasan sassauci ne Allah ya kawo min, amma wannan halin da nake ciki ba hauka ba ne tsananin masifa ce ji nake komai ma zan iya yi in dai zai sa na daina jin abinda nake ji, wallahi anne baki dacen ɗa ba, tabbas ba dan rashin iyaye na gari da nayi ba da wata ƙila halin da nake ciki bai kai haka ba,duk abinda nake aikatawa ban taba nadama ba ban taba dana sani ba ban kuma taba tunanin wannan rana zata iya zuwa min ba, sannan ban taba tunanin mutuwa a cikin rayuwata ba,anne ina cikin masifa da bala inda ba zasu iya faduwa ba, ya zan yi ku gaya min ya zanyi?"ta karasa fada tana mai ƙanƙame anne da kuma sakin wani irin kuka me ƙarfi. ****** Suna karasowa estate din aminatu ta yi saurin fita, bata jira kowa ba ta isa har dakin Nana,cikin farinciki Nana ta daga kanta tana kallon aminatu da take rahowa gareta da gudu,bude mata hannunta ta yi ta shige ciki, tana cewa my love I miss you "cikin dariya Nana ta amsa mata da cewa "me too yar gidan Nana,dagowa ta yi daga kafadar nana tana cewa ina innawuro?mikewa su kayi a tare Nana na bata amsa da cewa "tana kichin wallahi wai yau biski da miyar kubewa zata yi mana shi yasa tun dazu suka shige kichin ita da kaka sabuwar me aikinmu nima yanzu nake kokarin bin bayansu"aminatu ta ce "ai gara da baki bisu ba da yanzu kina kauri, amma dai Nana ya kamata a dauko Anne da larai daga wancan gidan ko?"nima abinda yake raina kenan dan barin nasu zai iya zama haɗari"Nana ta fada tana kama hannun aminatu,binta aminatu ta yi tana cewa,"babu wani hadari dan wanda zasu sasu a hadarin suma gudun ceton ransu suke yi"dan duban aminatun Nana ta yi, daidai suna karasowa falon, bude baki Nana ta yi dan tambayar aminatu dalilinta na fadar hakan, amma sai bakin ya tsaya a tsaka tsaki, ma ana shi ba a bude ba kuma shi ba a rufe ba,idanunta kuwa tsaye kyam akan Abba sule,tsawon minti ɗaya kuma sai ta juyo ta kalli aminatu kafin ta kumamjiyawa ta bi taguwar da suke zaune a falo da kallo,da karfi ta kuma damke hannun aminatu da yake cikin nata,kara aminatu ta saka tana cewa "wayyo daddy Nana zata karya maka hannun shalelenka duk dan taga nata masoyin"da karfi Nana ta kuma rike hannun Aminatun tana cewa "nima razananin zaku yi saboda baku da kirki to zan karya hannun gaba daya idan ya so a kulle ni ko ya rama miki"kuka aminatu tasa tana tsalle da son kwace hannunta daga cikin na Nana tana cewa wallahi nana da gaske ba fatalwa abba yake miki ba shine da gaske bai mutu ba ki tafi kawai ki rungume abinki ki yi kukan farinciki idan yaso daga baya sai ya fada mana yadda a kayi ya tsira daga mutuwa a wancan lokacin"sakin hannun aminatu Nana ta yi tare da fara takawa a hankali tana isa gabansa ta sanya hannu ta taɓa shi sai taga yayi dariya hawaye na zuba daga kurmin idanunsa,take Nana ta durkushe a gabansa tare da sakin wani irin kukan farinciki dan kuwa a yanzu ta gama tabbatarwa da shi din ne,hannu yasa ya dagota, wanda hakan yasa gaba daya suka watse daga falon. Aminatu na shirin fadawa kichin inda su innawuro suke mus ab yayi sautin kama hannunta ya hanyeta zuwa lokon corridon da zai maida kai kichin zuwa falon,dan ware idanunta tayi dan bata yi tsammanin ya biyota ba,"kai n.....bata kara ba ya hade bakinsu ya shiga aika mata sakonninsa da suke dauke da wutar zalama, ji yake kamar kamar akan aminatun,yar yarinya me barkwanci da shiga rai ta sanya shi farin ciki ta sanya iyayensa,ko yadda ta yiwa Nana abun ya kayatar dashi, dan tabbas da bata yi mata haka ba da zata iya shiga cikin tsananin shock din da zai iya haifar mata da wata cuta, a hankali ya kai bakinsa kunnenta kana cikin muryarsa da ta bayyana mata faruncikinsa ya ce"ke ta musamman musamman din musamman ce,kin cika yar gidan kara yar gidan baffa Yusuf, Allah yasa na ajiye me kama dake anan"ya fada yana shafa cikinta, runtsue ido aminatu tayi saboda yanayin da ta tsinci kanta a ciki, muryarsa ta kuma ji ta daki kumennta ta wuce ta daki zuciyarta kai tsaye ta kuma.yi balancing cikin jini da gangar jikinta,da ƙwaƙwalwarta"ina sonki matata ina kaunar ki ina miki sonso, kauna kololuwar kauna,kin zama mahadina farincikina,ki yi hakuri dani cikin ko wane yanayi ki kasance tare dani cikin ko wane hali ba zan iya rayuwa babu ke ba,dan Allah aminatu ki soni ko da kwatankwatan son da nake miki ne alfarma Please"ya fada cikin jan kalmar, sannan ya dauke numfashi yana mamakin daga inda wadannan maganganun suka fito dan bai ma yi zaton shine ysl3 fadar su ba,har sai da yaji aminatu ta sanya fatar labbanta akan kirjinsa tare da bashi wata zazzafar sumba sannan ta ce,"daddy ina sonka fiye da kaina da rayuwata, bani da kowa bani da wanda zan so sai kai shi yasa ka zama kololuwa kuma makura a nan"ta fada tare da dora hannunsa akan kirjinta,bakinta ya sumbata da goshinta da hancinta har zuwa idanunta kana ya kalleta tare da dage mata gira daya sannan ya furta "na gode"juyawa ta yi tana murmushi, da saurin ta juyo da kallon ta kansa tana dan rufe ido alamun jin kunya, shima kallon inda ta kalla yayi kana ya ɗan saki wani miskilin murmushi me sanyi da burgewa abinka da basabanba,rada masa ta yi a kunnensa "mu gudu daga gidan nan tun kafin Abba da Nana su yi abinda zasu hanamu hada ido da su"kunnenta yaja ba tare da ya ce komai ba,wucewa su kayi wajen innawuro ,inda suka samu su anita har sun kwashe komai sun fada mata, kuka innawuro ta ke yi lokacin da su amintu suka shigowa dan haka sai kawai ta hada su ita da mus ab ta rungume tana sa musu albarka tare da yiwa iyayen aminatu addu'ar neman gafara da samun aljanna. Anan dai suka baje suka ci biskin innawuro ga kuma girkin aminatu da suka taho dashi, kowa ka kalla fuskarsa wasai,aminatu kuwa sai zuba shagwaba take tsakaninsu,tana sakin bakinta cikin yarinta da tabara,wani ayi dariya wani kuma a yi shiru saboda kunyar barambaramar da ta yi. ******* Zaunar da zahida anne ta yi sannan suma suka zauna fuskokinsu dauke da tausayi,Anne ta ce "me kuka aikata me girma irin haka da har zunubinsa ya kai yasa sanya ku cikin wannan halin?"girgiza kai zahida ta yi tana cewa Anne ba zan iya fada anan ba, dole sai dai naje gidan jaridu da talabijin nasanar da su abinda muka aikata ko da hakan zai zama izna ga masu irin halinmu,da masu tasowa domin su guji aikata mummunan hali irin namu"larai ta ce"zahida abinda kika gani fa kadanne ko na ce so min tabi ne akan azabar lahira, wannan a duniya ne domin Allah ya nuna misali akanku da kuma tsoratarwa ga masu mummunan hali ko wane iri ne,nasan dai ba zai wuce akan dabi arki ta wulakanta dan adam ba wanda kuma dama can kuskure babba kike aikatawa domin kuwa ko wane mutum da kika gani akwai irin darajar da yake da ita wadda ke baki da ita, Allah subhanahu wata a ala yana cewa wa lakad karramna bani adama......kinga Ubangiji da kansa ya karrama dan Adam bare kuma mu yan adam ɗin,shi mulki ko kudi da kike gani ba wai zaba Ubangiji yayi ya bawa masu su ba, sannan talaka ba wai dan Ubangiji baya sonsu ya barsu cikin talauci ba,kowa ya bashi ne dan jarraraba karfin imaninsa,arziki da talauci duka abu daya ne domin Ubangiji yayi su ne dan jarrabawa,game arziki ya gwadasa ne yaga shin zai yi amfani da arzikin ta hanya me kyau kamar taimako sadaka zakka tausayawaq da dai sauransu,shi kuwa talaka ya jarabasa da talauci ne dan ganin imaninsa akan juriya, ma ana shin zai iya hakuri da babunsa , sannan bai biyewa zuciya akan jefa rayuwarsa cikin neman haram ba, wannan kadan ne daga cikin ikon Ubangiji akan bawansa,amma wasu daga cikin masu kuɗi sai su dinga ganin kamar su din na daban ne a wajen Ubangiji,to zahida ki sani cewa babu wanda yafi wani wajen Ubangiji face me tsoron Allah da gudun saba masa". Kuka sosai zahida take yi, kafin ta ce"larai tabbas na tafka babban kuskure a rayuwata wanda kuma har da rashin ilmin sanin Allah da yadda zan bauta masa,da ace ina da ilmi da nasan zan dinga gudun aikata wasu abubuwan ko kuma idan na tuna da lahira nadama ta dinga zuwarmin,nifa gaba daya bana tunawa da mutuwa saboda ban san irin azabar da Allah ya tanadawa masu irin halinmu ba, wallahi rashin ilmin addini masifa ce, rashin iyaye na gari ma masifa,larai nifa abinda na aikata har da kisan kawuna ba daya ba ba biyu ba duk dan saboda neman duniya da arzikin da sai yanzu nasan cewa bani ce zan yiwa kaina ba,dan duk inda nakai ga nemana idan Allah bai sako ni cikin jerin hamshakan masu kudi ba ban isa na zama ba,yanzu gashi ina ganin sakamakon abinda na aikata wai ma a hakan a duniya ne,wayyo me zan gani kenan a lahira ?"anne da jikinta yayi mugun sanyi ta dafa zahida tare da cewa Allah gafururrahim ne ki tuba ki koma makaranta ki nemi ilmin addini ki ci gaba da istigfar Allah zai dubeki"cikin kuka saboda ta kuma.cewa wayyo ann3 lokaci yakure min baku ga nasarar da nake ciki ba ne,a rediyo fa lokacin ina zaman hostel wata calasmate dina naji tana jin wa azi a wayarta, akan cewa Ubangiji baya yafe hakkin wani akan wani,a lokacin har fada sai da mu kayi da ita akan ta saka min wa azi,to anne ta yaya kuke ganin Allah zai yafe min hakkin dubban ran mutanen da na dauka ,bayan a yanzu ma hakkin nasu ne yake neman kasheni"?shiru su kayi gaba dayansu suna jimamin wannan rayuwa. Sallama suka ji daga can kasa,laraice ta mike ta sauka dan dubawa,larai ta yi farin cikin ganin bakin sai dai kuma razana da ganin ubangidanta Alhaji sulaiman Ja'afar, da gudu ta koma sama ta janyo Anne har zahida da take cikin tashin hankali,dan ita yanzu ko zama ita kadai bata son yi. Da sauri Abba sule ya rike anne da take neman faduwa,idamunta gaba daya a waje,ganin ya rike ta yasa ta fara nustuwa duk da cewa tana cikin matukar firgici na ganinsa,"sule baka mutu ba kenan ko dai nima na fara yin gane ganen da su zahida ke yi?"zaunar da ita yayi akan kujera yana cewa nine Anne ban mutu ba Allah yayi da sauran kwanaki a gaba". "Ƙarya ne ka mutu kai fatalwa ne, kuma ko da kake fatalwa ba zan kyale ka ba sai na kasheka,kai bari na fada maka sule ko da zan kashe ka sau dari ka dawo sau dari to sai na kuma kashe ka sau dari,ba kai ba har sauran fatalwun da suke binmu duk sai mun kara kashe su ko Kabiru "Abby ya fada tana kallon abba Kabir da jikinsa ya shiga wata irin tsuma, dama gaba daya a firgice suke dan ga sunan ne dai su ba masu hankali ba su kuma ba masu Lafiya. Gaba daya duka mutanen da suke cikin falon suka juya suna kallonsa,daidai nan kuma suka ji murya daga cikin television din da take kunne tana hasko shirye shiryenta,ta hasko Daddy Garba dake kan gadon asibitinsu na gjk a jigace a kuma firgice yana cewa,dole ce tasa na nemeku domin sanar da duniya halin da muke ciki, saboda ba mu sani ba ko yin hakan zaisa mu samu sassaucin halin da muke ciki sannan mu samu wasu daga cikin mutanen da muka cuta da suke raye su gafarta mana.....rairai ya fara bada tarihinsu kamar dai yadda ku ka ji daga bakin aminatu da mus ab lokacin da suke karanta littafin sirrin su Abby..... Zahra✍️ Ar u ready to payment 8064537048 opay Fatima yusha u Adam Decomment is 1k [5/17, 4:33 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page60``* Lokaci daya aka shiga kallon kallo a falon,kafin kuma su tsinkayi Muryar zahida tana cewa"wallahi Jamil da ka kasance ubana gwara mutuwata, wallahi tur da halinka,yanzu dama saboda abin duniya zaka iya sallama jininka?kaico kaico, ban dace ba, wallahi gwara nazo a shegiya mara uba da na zo a yarka"ta fada tana rushewa da wani azababben kukan da ya firgita aminatu itama ta rushe da kukan, cikin zafin nama mus ab ya kamata tare da sanyata a jikinsa yana jijjigata da yi mata busa a kunne. Cikin kuka anne ta ce"tabbas zahida kin yi gaskiya baki dacen uba ba Ni kuma ban yi dacen ƊA ba,tun yana yaro yake sanya mu magana haka mahaifinsa ya mutu da bakincikinsa,ban sani ba wannan ko lefinmu ne ko kuma jarabawa ce?Ni dai nasan cewa munyi iya kokarin mu wajen nunawa jamilu daidai sai dai kuma hakan bata samu ba saboda Ubangiji ya sanya mana shi a matsayin jarrabawarmu, Allah mun gode maka Allah ka bamu ikon cinye jarrabawowinmu na duniya"rungumeta Nana ta yi tana bata baki yayin da kowa yayi jugum jugum yana kallon su Abby da har yanzu idanunsu suke kan tv suna ganin yadda mutane suka yanyame asibitin daga masu jifa sai masu kokarin bankawa asibitin wuta,jin kowa yayi shuru sai kukan anne da na zahida da ya karade falon yasa abby ya juyo yana fuskantar su,kana ya bude baki ya fara magana,kamar haka, "kun gama ?nace kun gama?"ya kuma tambaya cikin tsawa yana zazzare idonsa, babu wanda ya tanka masa, dan haka ya ci gaba da cewa "sule wai ma ya a kayi ka kubuta daga mutuwa dan yadda fuskarka ta koma awannan lukacin ko ka rayu sai dai canja maka fuska dan dai wannan ta tashi daga aiki,ka fara fada min abinda ya faru kafin na fara tunanin ta yadda zan ɓullo da al'amarin dan wallahi ba zan taba barin dukiyata ta salwanta ba akan wani banzan shirmenku ko da zan yi yawo tsirara sai na tabbatar da na kare dukiyata "Abba Kabir ne ya tari nunfashinsa da cewa "A'a Jamil ya isa haka mu bari haka iya ishara mun ganta zuwa yanzu ya kamata mu nemi yafiyar wanda muka zalunta ta bakin Garba, Ni dama tun da al'amuran mu suka fara rikicewa na fara shiga babin nadama dan dai na rasa goyon baya daga gare ka ne dan na tabbata idan na ce maka na yi nadama zaka iya kasheni" Mus ab ne ya dubi Abba sule ya ce"Abba ko zamu bar gidan nan ne kaina ya fara ciwo ga Aminatu tana cikin kidima saboda hatsaniya?"cikin sauri anne ta ce "a'a mus ab ya kamata ya fara fada mana abinda ya faru anan daga nan sai ku tafi tunda nima zan so na ji"ta fada cikin karaya dan tasan tafiya za su yi su barta a gidan daga ita sai zahida,gyaran murya Abba yayi sannan ya fara magana cikin nutsuwa. **** Lokacin da accident din ya faru Allah yafitar da Ni daga cikin motar saboda tsallan da katantanwar da motar ta din ga yi damu, ema driverna shine ya mutu ba Ni ba kuma shi kuka yiwa wanka,kuma na tabbata da Asma'u ta ga gawar zata shaida ba Ni ba ne.lokacin da motar ta yi watsi da Ni ban fada ko ina ba sai cikin wani rami, kaina ne ya bugu jikin dutsen ramin wanda hakan yayi sanadin bacewar tunanina ma ana dai na zama tuburarran mahaukaci,ba zan iya fada muku rayuwar da na yi cikin rayuwar hauka ba saboda bana cikin hankali na amma kowa yasan cewa rayuwar mahaukaci ba rayuwa ce me kyau ba,saboda rayuwa ce ta babu ruwana da sanin wane irin abinci ya kamata naci?da abinda Yakamata nasha ,babu ruwan mahaukaci da wanka, wajen kwana ba'a batunsa dan duk inda ya samu bacci yake koda kuwa a cikin kwatami ne,duka mahaukaci babu ruwansa da wannan, ni dai ban tashi tsintar kaina ba sai a cikin garin Kano kuma tun daga lokacin da na fuskanci halin da nake ciki na fara mafarki da wata yarinya da kamar ana min nuni da cewa ita ce zata taimakeni,bana jin a raina zan koma gida da kaina sabida ban san ta ina zan fara ba, domin tun dawowata cikin hankalina na fuskanci irin rayuwar da na yi da mutane dan haka nasan ko da na nuna na dawo hankalin babu wanda zai yarda Saboda na riga na zama a bin kyama cikin mutanen da na yi shekaru sama da talatin a cikinsu,dan haka sai kawai na ci gaba da rayuwata a haka har zuwa lokacin da bafulatar aminatu ta bayyana a gareni da siffar aminatu,ko da zuwanta gare ni ban firgita ba saboda ban yi zaton ba mutum ba ce. Bamu baro Kano ba har sai da ta tabbatar ta Kaini asibiti anyi min texts na kwayoyin cututtukan zamani wanda kuma cikin kiyayewar Ubangiji ba'a samu wasu cututtuka masu daga hankali ba,baya ga maleria olsa da kuma matsalar fata wadda kazanta ta haifar min,daga nan na karbi magani da kulawa ta kwana ɗaya, sannan mu ka bar Kano,to a nan dinma ta sanar da ni duk abinda yake faruwa dan haka ta umarce ni da na zauna na huta na kuma samun lafiya da qarfi in yaso sai mu koma gida dan tafi son ahlina su ganni cikin kyakkyawar kama(ya boye musu tsotar da su abby da suka yi a gidan gona da sauran gurare). Kamar jira Abby yake Abba sule ya rufe bakinsa ya yi wata irin zaburowa cikin wata irin shammata da basu taba zato ba ya janye aminatu tare da hankadata cikin dakin da suke kusa dashi ya rufe yana cewa "idan har kun isa ku kwace ta daga mutuwarta a yau dan sai na yanka makogaronta"ya fada yana saita kakkaifar wukarsa da baya rabo da ita a jikinsa a wuyan aminatu ,babu wanda a cikinsu ya kawo Abby zai iya tunkarar wani a cikinsu da niyar cutarwa duba da halin da suka tsinci kansu, shi yasa har ya samu dama akan aminatu,idanun mus ab kawai zaka kalla ka tabbatar da cewa a wannan karon ya kai kololuwar fusata da bakin ciki kuma zai iya aikata komai a cikin wannan yanayin da yake ciki,innawuro da Nana har da su anita da Hajara kuka suka sanya dan dukkansu sun shaida rashin imanin Abby sun san in dai ba ayi hanzarin balle kofar nan ba to tabbas sai ya yanka aminatu.abba Kabir kuwa ganin abinda yake faruwa a cikin asibiti yasa shi fita da gudu ya nufi a sibitin dan taimakawa Garba da suke neman cinna masa wuta ,tunda asibitin suketa zazzagawa fetur ciki da bai dinsa dan sun sha alwashin sai sun kona duk wata kadara da suka san ta gjk ce tunda da jinin iyayensu da yan uwansu a ka siyeta,Hajiya zahida kuwa ganin idan ta tsaya ta ce lallai sai ta ceci Garba za su hada da ita yasa ta su lale ta gudu abinta,daidai Abba kabir yana karasowa suna cinnawa asibitin wuta,da gudu ya shiga ya tattago Garba da ko tafiya me kwari baya iya yi suka fara kokarin fitowa , sai dai ina tuni wuta ta fara shanye fiye da rabin asibitin har ta fara taba inda suke,kasancewar kofar da zasu bi itama ci take ganga yasa suna ketota wani bangare na jikin kofar ya fado a bayan Garba,shi kuma Kabir barin jikinsa, lokacin da suka samu fita ta bayan asibitin wannan kofar da mus ab yasa aka fitar da innawuro, tuni wuta ta gama cinye gaba faya asibitin,su kansu basu yi zaton zasu tsira ba,suna fita yan sanda suka kwashe su,ko da suka isa devition din tuni likitan da zai duba su ya kara so,dan haka ana dan yi musu dressing aka watsa su cikin su danturqui da idan ba farin sani ka yi musu ba ba zaka iya gane su ba. *** Sai da abby ya gama tabbatar da cewa sun rasa hanyar ceton Aminatu sannan yakyalkyale da dariya yana cewa, ba zan taba mutuwa ba tare da na bar muku tarihi ba,na san cewa a yanzu wannan yarinyar kawai zan kashe na jijjiga duniyarku dan na tabbata wasu daga cikinku sai sun bita, dan haka basu sakon karshe yarinya dan ina ga ma rai biyu zan kashe wata kila kina dauke da ɗan so"daga haka ya fallawa aminatu mari sai da bakinta ya fashe da hancinta daga nan yasa wukar akan wuyanta yana wata shegiyar dariya irin ta rikakkun azzalumai wanda suka yi hannun riga da imani,ya fara tamkar fatarta kadan yaji an yi wani irin yin sama da shi kamar wanda mala ika ya daga,ji kake hif ya fado daman kofar da mus ab ya ƙaryata da karfin kaunar aminatu, dan shi kansa Abby saboda yasan irin kofar da yayiwa gidan ne yasa ya yi wannan lissafin. Kafa ya daga zai take kan Abby Abba sule ya dakatar dashi da cewa,"mus ab kar ka yi kisa, kabarsa da Ubangiji zaka ga sakamakon da zai yi masa"wannan furucin yasa mus ab ya rabu da Abby tare da ɗaukar Aminatu ya fice da ita,a bakin kofar suka hadu da zahida, wuceta zai yi ta tare hanyar tana cewa mus ab ka yi hakuri na yi nadama ka tafi da Ni duk inda zaka zan zauna da kai a ko wane irin hali kuma koda mata dari za aura zan zauna da s......wata irin hambara aminatu ta kaiwa bakin zahida da kafarta tana cewa Wallahi ba zamu zauna dake ba ahlin mugaye kije can kiji da masifar da bakin zunubinki ya jawo miki"kallon mus ab ta yi tare da sa kuka har tana kokarin sauka da ga jikinsa,ganin haka yasa shi saurin barin wajen bayan ya zaro wata farar takarda a aljuhunsa ya cusawa zahida a hannunta,babu wanda ya kula da abinda ya bawa zahidar sai ita, zubawa takardar ido ta yi, kafin ta warware ta a hankali, rubutun mus ab ne me kyau da tsari yana sanar da ita cewa ya sake ta saki biyu daga yau kar ta kuma bari ya hadu ko da da inuwarta ne,hannu ta ɗora aka ta zunduma ihu kafin ta fadi a wajen, lokaci daya bakinta ya karkace barin jikinta ya shanye.anna ce kawai ta yi kanta yayin da su nana suka bi bayan mus ab gaba dayansu hatta da larai bata tsaya ba, sai ya zamana daga Abby da yake kwance ya kasa matsi sai zahida da ke shimfide cikin rai kwakwa,sai kuma Anne dake kanta tana kokarin taimaka mata amma ta kasa saboda itama bata da wani karfi girma ya zo,shigowar isma ce ta sanya Anne farin ciki duk da cewa shi din ma hannunsa daya daure yake da ƙafarsa daya da duk suka sha bandeji da ga dukkan alamu ma dai kawo shi a kayi,da dan din gishiri ya karaso yana cewa Anne,"Ina Abby yake wallahi duk halin da muka shuga shine sanadi ashe dama zahida yarsa ce ashe dsma mus ab ba dansa ba ne?nima fa mus ab dinne ya sa wasu karti suka biyeni kuma dan rashin mutunci duk abinda ake ciki sai ya tiro musu sun sanar dani,yanzu ma su suka kunna waya suka nuna labaran da daddy Garba ya bayar akanmu Kum....hayaniyar da suka biyo daga waje da kuma karar jifa shine ya hana isma karasa maganarsa,cikin sauri ya kama hannun anne yana cewa"maza mu bar gidan nan dan nima yanzu da kyar nasha a hanya da tuni mutane sun kasheni da jifa" Anne ta ce babanku fa da zahida yana ciki kwance da alama mus ab ya karya kashin bayansa"haba anne da kanki kike janyo mana masifa kin san cewa kubutar da mutanen nan daidai yake da jefa tamu rayuwar cikin Bala i,mu ji ma da wanda suka jawo mana"yana gama fadin haka ya janyo hannun Anne suka yi waje da gudu. Shima abby kokartawa yayi ya mirgina daga kwancen da yake tare da jan ciki dan fa da alama mus ab ya karya kashin bayan abby kamar yadda anne ta fada ɗin.yana fitowa da jan ciki ya samu zahida a yadda su isma suka barta,kuka ya saka a karon farko yana kallon kansa da zahida babu yadda zai yi ya taimake su,yana cikin wannan halin ne mutane suka samu damar shigowa cikin gidan baka jin komai sai iface iface da karar duwatsu,sun balle kofar falon kenan suka ji jiniyar yan sanda wanda hakan ya taimaki su Abby daga kisan wulakancin da mutane suka shirya yi musu,dauke zahida da abby su kayi aka nufi asibitin da yake karkashin hukuma, a take bincike ya nuna zahida ta samu matsalar shanyewar barin jiki sauki kuma sai Allah ya kawo,shi kuma Abby ya samu karaya a kashin bayansa, shi da zama sai dai yaga ana yi in dai ba aiki aka yi masa ba,babu abinda yake sai ihu da zage zage dan yana kallon tv da ke cikin dakin tana haska irin barnar da mutane su kayi musu, dan sun bi duk wani Company ko asibiti sun banka masa wuta, yayin da a gefe daya wasu daga cikin matasan da suka far musu suka dauke wayoyinsu tare da kutsawa cikin account din su suka kwashe miliyoyin kudaden da suke ciki kai tsaye suka mika ga gidajen marayu wasu aka rabawa talakawa musamman wanda duk ya kawo kokensa akan shima an taba cire masa koda a cikin asibitin ko kuma wani nasa,lokaci daya komai na su Abby ya zama tarihi, kallon wannan yasa abby ya zare babu abinda yake sai zagi da tsinuwa da tonawa kansa asiri har dq abinda mutane basu san ya aikata ba,daga karshe dai da kyar aka samu allurar da tasa shi baccin awa ɗaya. ***** Suhaima da sule karami babu abinda ba su gani ba, tunda gaba daya duniya aka haska barnar su Abby,sun sha kuka iya kuka daga nan suka godewa Allah da ya tsamesu daga sharrin halin ubansu,sun yi masa addu'a saboda shine yayi sanadin da suka samu uwa kamar nana da kuma dan uwa kamar mus ab,ko iya haka sun yiwa Allah godiya, Khalid dai bai san komai ba saboda makarantar su cike take da matakan tsaro ta ko ina dan babu abinda suke sai karatu basu da wani lokacin kallo ko amfani da waya,tun da hakan doka ne,duk wanda zai yi waya daga gida a ofishin directer zaka yi wayar ka ka gama ta cikin katon laptop kuma video kana magana da mutum tamkar kuna a waje daya ne. Mijin suhaima yayi kokari sosai wajen kwantar mata da hankali saboda yaron cikin da take dauke da shi, wanda Allah ya basu a yanzu bayan shekarun da suka dauka basu samu ba,da yaso kiran mus ab to kuma sai ya bari hankali ya gama kwanciya dan yasan su kansu suna cikin damuwa. ******* A bangaren gwarazan namu kuwa, kai tsaye estate suka wuce,inda Nana ta rike aminatu a cewar ta sai an yi biki sannan zata kaita gidanta dake cikin estate din da kanta,kallon mus ab aminatu ta yi kafin ta maida kallonta kan Nana kana ta ce"haba Nana daddy ba zai iya miki wannan karar ba, dan wallahi ba zai iya yin bacci ba tare da n.....hannun Nana saman bakinta shi ya dakatar da maganarta,sai kuma taga kowa na sulalewa yana barin wajen ba tare da sun iya kallon inda mus ab ke zaune kamar baya wajen ba,tura baki ta yi tana cewa "nana me kuma nayi gaskiya fa na fada kuma tun ranar farko ba mu kuma yin...."dalla Malama ta shi ki bi mijinki ku je can ku karata,kuma kar na sake ganin kafafunki a gidan nan"daga haka ta mike tare da dauko mata wasu manyan jarkoki guda hudu tana cewa "kije ki sa a frige ki dinga sha"na gode Nana amma da kin fada min amfanin wadannan kayan dadin da kike ta banka min tun ina yarinya?"wucewa ta yi tana cewa kije mijin naki ya fada miki"dariya aminatu ta yi tare da wucewa wajen mus ab da tuni ya kai kofa a ransa godewa Allah yake da yasa aminatu ba ta zama me kauran baki ba da tabbas yau an gama dashi, jawo shi baya tayi tana cewa shine zaka rigani fita bayan ina can ina maka faiting"shiru yayi saboda larai da ta dauko musu jarkokin ita da kaka,shiga motar su kayi bayan sun yi salama da larai,kwantawa aminatu ta yi a kafadarsa tana cewa ba zamu dawo gidan nan ba sai ranar da muka dawo daga honny moon"....... Zahra✍️ [5/17, 7:33 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page61``* Suna zuwa gidan,bayan yayi fakin ya fito sannan ya bude kofar bangarenta ya mika mata hannu alamar ta fito,amma sai ta makale kafada tana kallonsa,"me ya faru" ya fada yana kallon idanunnata da har ta tara masa kwallah,cuna baki ta yi tana barin hawayen suna zuba kana ta ce goya ni za kayi ba zan iya tafiya ba"bai musa mata ba ya juya tare da durkusawa ta haye bayansa tana dariya,a haka suka shiga dakinsa,amma a maimakon ya ajiye ta sai kawai ta wuce bathroom da ita,a cikin ruwan da ya taru a cikin kwamin wankan ya sakata, kokarin fitowa ta ke ya bi bayanta, daga kashe sai acikin ruwan ya zame musu duka kayansu,bayan sun yi wanka sun fito, ya kuma.futa ya karbo abincin da Nana ta aiko musu tare da dauko jarkokin aminatu,yana shigowa ya sa Meta gaban mirror tana faman lailaye jikinta da wasu shegun humras da aka hada su da alims kasancewar muna cikin yanayin zafi ne,Nana kuwa duk wani abu da zai ingata jiki dan hana zaman wari ta san sirrin, shi yasa tun aminatu na karama ta koya mata amfani da alim, babu ruwan ta da kayan da zamani ya kawo a madadin ko da zata yi amfani da na zamani to fa dole sai ta haɗa da alim dan alim duniya ne,duk tsananin zafi in dai kina amfani da alim kafin ko wane irin turare a jikinki to wallahi ko da zaki kwana dari baki wanka ba yanayinki ba zai sauyawq ba,bare kuma ace kina dorawa da shu'umar humra irin ta humcom ai kin gama tashin kan mai gida baby. A hankali ya matso kusa da ita tare da dora kansa a kafadarta yana wani lumshe ido saboda yadda kamshin jikinta da na gashin ta suke ratsa kofofin hancinsa, take duka tsigogin jikinsa suka mike,(uwar gida wallahi kamshi duniya ne shi kuma kanshi ba ya samuwa sai da tsafta kar ki bari matan bariki ko matan mazan wasu shine burinmu su kwace miki miji,ta hanyar janye su da abinda bakya yi, babu abinda ya fi saurin raba mace da mijinta sama da kazanta dan ko da shi ma kazaminne wallahi yana son mace me tsafta dan haka mu kiyaye rijalun yanzu ka tsaya ka dage ma ya a aka cika bare kin bar damarki wasu sun dama)hannunta tasa ta shafo tattausar sumarsa tana cewa daddy zanci abinci"janyewa yayi daga gare ta,kana ya kama hannunta ya Kaita har gaban abincin da shi da kansa ya jere komai a kan tabarmar cin abincin da ya shimfida,zama ta yi yayin da gaba daya towel din jikinta yayi sama fararen cinyoyinta da suke ta daukar ido suka bayyana dan hatta da da farin fant dinta ana gani,a hankali mus ab ya ɗan dauke numfashin da yake jinsa a wuya jikinsa duka yayi sanyi, aminatun tsumashi take ta ko ina, jin sa yake tamkar ba namiji ba saboda juriyar da take neman gagararsa,da kansa ya shiga ciyar da ita, sai da ta ji babu wajen saka wani abincin in ba kayan ruwa ba sannan ta janye kanta,tare da janyo jarkokin da Nana ta bata ta bude ta tsiyaya a cup, kana ta kafa kai sai da kowanne ta yi masa shan gamsuwa sannan ta mike ta boye kayanta a frij,har lokacin bata ga mus ab ya ci wani abu me yawa ba,dan haka sai ta koma ta zauna daf da shi tare da sanya hannunta ta shiga bashi a baki,sai da ya rike hannunnata ya lashe duka yatsun sannan ta bashi ruwa da madara yasha,daidai lokacin aka kiran sallar magriba dan haka aminatu na fita da kayan ta sanya hijab su kayi salla,tare da nafilolin basu suka tashi akan sallayar ba har sai bayan da suka yi Isha suka dora da nafila ra aka goma, daga nan Mus ab ya shiga kwararo musu addu'ar zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman shiriya wa zuriar musulmi baki daya, tare da neman tsari da azzalumai irinsu Abby, da fatan shugabanni na gari da zaman lafiyar kasarmu baki daya,da neman sassauci a cikin halin da talaka ta tsinci kansa,(abinda yawancin masu kuɗi ba sa yi kenan wato yiwa talaka addu'a,) Daga nan suka rufe da salatil Ibrahima, da kansa ya zare mata hijab din jikinta, daga nan bai wuce da ita ko ina ba sai saman lafiyayyar shimfidarsa. Anya kuwa idan na misalta muku zaku gane?kai ba zaku gane ba, na ce Ba zaku gane ba dan ba kowace mace3zata fahimci irin wannan yanayin ba sai wadda mijinta ke mata so kololuwar sonso,mus ab ya tashi kan aminatu aminatu ta tashi kan mus ab,da salo me rikita lissafi wanda a tari bai taba jinsa ko ganinsa ba,idan nace zan fede muku irin wannan salon to tabbas zaku ga rashin kunyata 😊,kukan aminatu ba komai yake karawa mus ab illa wani irin shauki da kaimi, (kar ki kasance me yiwa miji shiru a shimfida Yes ai kin gane😃)shiru aminatu ta yi saboda jin kamar daddyn nata kuka yake abinda a tsawon rayuwarta da shi bata taba gani ba kenan,duk irin halin da suka shiga mus ab bai taba zubda hawaye ba, to yanzu me yasa shi kuka ?me ta yiwa daddy haka me girma da ya sashi zubda hawayensa masu tsananin tsada,hannunta har rawa yake wajen shafa fuskarsa tana cewa"daddy me nayi?me yasa ka kuka ?ko nayi maka wani abun?"sai kawai itama ta fashe da kukan, cikin zafin nama ya hade bakinsa da nata yana mata wani irin zazzafan kisses da yasa ta hadiye kukanta ba tare da ta shirya ba,sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa sannan a hankali ya bude baki da muryarsa da ta yi can kasa dan ba dan dare ba ne da ita kanta ba zata ji abinda yake fada ba,a cikin kunnenta ya shiga fada mata, a duniya ban san da cewa akwai abinda zai sani rag2anta ba, sai yau da na tsinci kaina a duniyar aminatu boddon innawuro shalalen Nana rayuwar mus ab,aminatu le makura ce,isasshiya me yalwar Ni ima, hawayena ba na kome ba ne sai na godiya ga Allah da yasa na zama zaɓaɓɓe a cikin mazan da ya mallakawa mata irinki, i love You with all my heart my friend my love my wife my wold my my my my everything m.....karasawa yayi da bin ko ina dake fuskarta da wani irin kiss tamkar zai hadiyeta ya maida ita ciki,hannu bibbiyu ta sanya ta rungumesa tana jin wani irin farin ciki da takasance mace daya tilo da mijinta ke matukar alfahari da ita,tana jin a ranta zata iya yin kome dan mijinta fatanta daya Allah ya sa ya ci gaba ya koma dore da bata wannan farin cikin,ya ci gaba da kasancewa miji adali a gare ta farincikinta garkuwar ta,daga nan ya kuma dora Mata da wata irin ginanniyar soyayyar da saboda kwarinta ko katangar karfe da sai dai ta ganta ta kyale.a wannan daren sai da mus ab ya shafe duk wani babin bakin ciki da ke zuciyarsu, babu abinda suke tunawa sai farkon hafuwarsu rayuwarsu har zuwa wannan dare me cike da tarihin ni'imar Ubangiji dake cikinsa. A bangaren Nana da Abba sule ma ,ba abarsu a baya ba, dan inganta wannan dare sun yi kokari sun shafe bakincikin rayuwar da su Abby suka guma musu,cikin tawakkali da nunawa junansu kauna ta asali, Innawuro da Hajara da duk wanda ya danganci wannan ahli wannan daren ya zame masa daren farinciki,wanda suka yi sa cikin baccin kwanciyar hankali da godiya da ubangi da ya basu nasara kan makiya,sai dai fatan Ubangiji ya kuma kare mu da zurar mu baki daya,wadanda suka riga mu gidan gaskiya ya ji kansu da Rahma mu kuma yasa mu cika da kalmar la ila ha illallah Muhammadurrasulullah Sallallahu alaihi Wasallama 🙏. Isma kuwa rasa inda zasu nufa yayi dan duk gidan da yasan na abby ne idan suka je sai suka ga ansa masa kwado ko da da yan haya a ciki kuwa,saboda dukiyarsu gaba daya ta zama ta Baitul Mali dan gaba dayanta sun sameta ne ta hanyar kwace da fashin gidajen talakawa da gonayen Fulani da shanyen su da dabbobinsu,hakan yasa isma ya damu wani mutum ya a ra masa waya ya kira daya daga cikin abokansa amma yana jin Muryar isma ya kashe wayar baki daya,haka ya dinga bin abokansa yana kira suna kin taimaka masa, duk da irin bushashar da yayi musu lokacin yana isma dinsa,tun yanzu ya fara nadamar biyewa abokan banza da ya tsaya yayi karatunsa yadda ya kamata da yanzu shima yana rike da wani muƙamin cikin rufin asirin Allah kuma, amma Gashi yanzu sun gujesa haram din da yake takama da ita itama ta gujesa lafiyar da yake takama da ita babu,kai duniya zan can banza ce wallahi idan ba mu yiwa kanmu fada ba zamu yi asarar rayuwa,hannu yasa yana goge tawayen da suke zuba kan fuskarsa, kallon anne yayi sai yaji wani irin tausayinta barin yadda yaga tana takawa dakyar kafafunta har sun kumbura,dare yayi sosai dan haka bai san wa zai kuma kira ya saurareshi ba,dan haka ya nemi gefen hanya ya zaunar da anne da ta har yanzu ta kasa yin magana daboda yadda zuciyarta k3 ci da wutar bakinciki duk ta tuna halayyar jamil sai ta ji hawaye cikin idanunsa3da kunar zuciyar da bata san yaushe ne zata daina ba, mota suka gani a gabansu har sun tsorata sai kuma su kaji Muryar malam jauro driver yana cewa anne tun dazu Alhaji babba da Hajiya Nana suka ce na koma gidan can na daukoki,amma banganki ba,gashi bana son komawa gida dan ban san me zance dasu ba,sai yanzu Allah ya sa na ganki ku tashi mu tafi "cikin farin ciki da godiyar Allah isma ya kama hannun Anne suka saka ta amota shi kuma ya shuga gefen m jauro suka tafi. Lokacin da suka isa gidan larai da Hajara suka samu suna dakon jiransu kamar yadda masu gidan suka roke su da su yi,daki Hajara ta kai anne tare da shiga bathroom ta hada mata ruwa me zafi, kana ta fito ta kamata ta ta kaita banɗakin,tana fitowa ta samu larai ta shirya mata abincin da take so wato dan wake,ko da anne ta fito kasa cin komai ta yi har sai da larai ta ce zata sanrwa da Alhaji babba saboda wannan umarninsa ne akan cewa kar su bari anne ta kwana da yunwa bare wata damuwa, wannan kalamin shi ya sanya Anne jin wasu hawaye suna gangaro mata, bata taɓa tsammanin cewa bayan abinda Jamil yayi sule zai kuma kallon ta a matsayin uwa ba,sai gashi ya fara da bata gatan da ko a baya bai bata shi ba. A bangaren isma shima ya samu kulawa daga wajen m jauro,shima m jauro yana gidan saboda tun mutuwar matarsa bai kuma wani auren ba,,kuma dama bashi da ya'ya. A bangaren zaunab (Anita)ma sun koma ainihin gidansu na nan ita da mijinta da kaninta. ********BAYAN KWANA UKU...... hankula sun kwanta, mus ab tuni y adauke matarsa suka wuce kasa me tsarki yayi da sai daga baya su Nana gaba daya dai gidan zasu bi bayansu su je gaban ka a ba dan kara yiwa Allah godiya daga nan su kaiwa suhaima da sule karami ziyara,isma kuwa yana asibitin aminatu yana karbar magani bayan an yi masa dori me kyau dan a kwana biyun ya fara tafiya de de sabanin da da yake dingisawa. A cikin kwanaki ukunne dai gwamnati ta shiga binciken asibitoci ka in da na in Dan tsafatace su daga baragurbi, dan yanzu mutanen Gombe sun kiyaya da sauran asibitoci,yayin da kuma mus ab ya kuma sanya hannu wajen bada tallafi ga talakawa da wanda suke daga cikin wanda aka taba kwacewa wata kadara, Baffa wuro takanas ya je har estate Dan ganin innawuro ya bata hakuri da neman gafararta,itama dai bata ja da nisa ba tunda wanda suka yi abin ma gamsu nan suna karbar hukunci tun a duniya, to shi kuma wanda ya gane gaskiya ai ba lefi ba ne dan an yafe masa. Gaba daya abokan kasuwancin su Abby sun razana da abinda ya faru dasu,dan hak da yawansu suka.dinga ajiye wannan mummunan dabi ar suna komawa ga Allah yayin da suke ta fito da dukiyarsu suna yin sadaka da nema Allah ya yafe musu,dan babu wanda zai so rayuwarsa ta yi karshe irin na su Abby. Matar Alhaji Kabir tuni ta tattara ƴaƴanta maza suka bar kasar dan dama ita ba yar kasar Najeriya ba ce,acewarta gwara ta yi nisa da in da suke ko Allah yasa rayuwar ƴaƴanta ta inganta, Itama Hajiya Zubaida garinsu ta gudu gidan iyayenta da fatan bude sabuwar rayuwa me inganci dan so take ta yi aure ko Allah yasa rabon yana tare da wani. Garba da Kabir dai da alama ba zasu kai ba, dan treating din da aka yi musu na konar da su kayi ba wata me inganci ba ce,shi yasa ta dinga cin jikinsu ga kuma tururi da suka shaka,daga karshe dai a cikin wannan ranar suka amsa kiran Ubangijinsu a tare sai dai banbancin lokaci,shi Kabir da safe shi kuma Garba da sha biyun rana, Allah ya sa hutunsu kenan Allah ya sassauta musu alfar shugaba da kuma tuban da suka yi har ransu. Zahida kuwa gaba daya sai yadda a kayi da ita,idanunsa ne kawai a bude babu abinda kake gani a cikinsu sai hawaye saboda babu wanda yake lekota, dan ba ta samu tana karkashin kulawar jami'ai ai da ko kashi ta yi babu me wanke mata,shi kuwa Abby gaba daya idan ba da allura ba baya barin mutane su ji gari dan har an fara tunanin da ya ɗan warware za a mikasa asibitin mahaukata. ***** Yau satin su aminatu daya a saudiya,tun da suka je ibada kawai suke, har zuwa yau da su Nana suka karaso,hatta da kaka da larai masu aiki sai da aka taho da su,m jauro Hajara da su zainab Anita da Ahmad Anne da isma, securities kawai aka bari a gidan,zuciyar kowa cike take da farin ciki, sai kuma ga suhaima da sule karami suma sun iso,kai wannan ahli fa ya cika da farin ciki, ririta juna kawai suke ,yayin da suka a dukufa wajen yiwa Ubangiji godiya tare da mika masa bukatun al ummar Annabi Muhammad s.a.w da nema musu sauki da shiriya,sai da suka yi sati biyu sannan suka rankaya suka tafi Dubai wajen Khalid. ***** Khalid yana karasowa cikin gestroom dinsu sai kawai ya tsaya yana karewa kowa kallo, zuciyarsa cike da farinciki duk fuskar da ya kalla sai yaga murmushi akanta,tsaida kallonsa yayi akan fuskar Abba sule wanda a cikin mutanen da suke zagaye da shi shi kadai ne bai sani ba,Muryar aminatu ce ta bashi amsar tambayar da yake yiwa kansa da cewa,he is grand father ur name is Alhaji sulaiman Ja'afar"kafun6ta rufe bakinta ya nufo waje ta da gudu ya rungumeta,dama tunanin wajen wanda zai fara zuwa yake yi, kunnensa ta yi masa rada, hakan yasa ya sake ta ya nufi Abba sule da gudu ya rungume sa yana cewa idan kaine baban daddy na shi kuma Abby daddyn waye?"kai tsaye aminatu ta yi poiting yatsanta kan isma tana cewa daddyn uncle isma ne sannan grand fa dinka again"daga nan bai kuma yin wata tambayarba ya dinga binsu yana basu hug har yazo kan daddynsa, inda ya shige jikinsa yana cewa "daddy I miss You kai da adda aminatu"Nana ta ce mu da ba ayi missing namu ba sai a koremu,gaba daya suka sa dariya,sun jima tare da Khalid inda ya dinga karbar kyaututtuka daga ɓangaren iyayen sa zuwa kan kakanninsa,sai da suka zo yin sallama ne ya dubi daddynsa ya ce "daddy ina mommy ita bata zo ba har yanzu bata sona ko?"tale jikin kowa yayi sanyi babu wanda ya iya magana sai aminatu ta data ja shi gefe ta yi masa wasu maganganun da babu wamda yasan me ta ce masa,sun dai ga ya ware sun yi sallama cikin dadin rai, sai kewa da ta cika kowanensu. Daga nan kuma su amintu suka wuce Faransa tare da suhaima da mijinta suke karami ya wuce gidansa tunda shi dama a Dubai din yake,amma yanzu ganin ahkinsa yasa shi jin kwadayin komawa gida,yayin da su kuma su abba sule suka.rankayo sai gida Najeriya. Sun dawowa Abba sule ya karbi dukiyarsa da ya barwa Nana ita kuma ta dankata a hannun lauyansa,dan haka cikin aminci ya bude Companys dinsa da gidajen gona sai gidajen mai da aka dena amfani da su,isma ya jawo da shi da Ahmad ya danka musu wasu abubuwa da fatan zasu rike amana dan duniya yanzu ba tasa ba ce ta mus ab,yayi wannan ne kafin ya gama hutunsa ya dawo su ci gaba da tsare tsaren da ya kamata.to isma dai yayi hankali da karatun ta nutsu shi yasa ya sawa ransa rike amana ba zai taba yadda yayi rayuwa irin ta mahaifinsa ba,Abba sule da kansa ya je asibiti yasa hannu aka bashi zahida dan tuni aka gama shirye shiryen fita da ita US dan yi mata magani akan lalurarta,shi kuwa Abby hauka ta tabbata dan yana samu aka yi masa aiki ya fara tafiya shike nan ya ɓalle suka nemesa suka rasa,dan yadda ya fita babu kyan gani kusan tsirara yake dan duk ya yage fiye da rabin kayan jikinsa,surutansa na haukan duka ne da rashin imani, Allah yasa mu yi kyakkyawan karshe Amin. *****BAYAN WATA BIYAR.... wata kyakkyawar bafulatanar matashiyar yarinya ce,gefenta wani dangayun kyakkyawan bafulatanin da ya juye ya koma helf case ne,sanye suke cikin kayan sanyi da huluna irin na turawa masu taushi,tana gefen jikinsa suna saukowa daga matakalar jirgi, cikin kankanin lokaci idanun suka koma kansu,take fuskar mus ab ta koma ta ainihin mus ab mara dariya wanda hakan da yayi ne yasa na gane su,boyeta yayi cikin rigar sanyinsa me girma sai ya zamar mata dan jagora dan bata ganin gabanta sai inda ya sanya kafafunsa, a haka suka karasa gaba motar da aka zo daukar su da ita, wannan abin ba karamin burge mutane yayi ba,har wanda suke tare da mazajensu suka shiga wani kumbure kumbure wai ala dole suna so a yi musu irin na aminatu matar dan birni😃 [5/18, 8:52 PM] yushauadamfatima: Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page62``* Da gudu motocin suka bar harabar filin jirgin, aminatu dakyar ta iya ciro kanta daga cikin rigar mus ab,tana samun kanta ta tura baki cikin shagwabar da sake sabuwa tun bayan samun juna biyunta,ta ce"daddy yanzu tsakani da Allah kana sane zaka kashe yar so?"Ni kuma yayi saurin magantuwa dan idan bai yi maganar ba wani sabon tashin hankalin ne,hawaye ta saki tana kuma cewa su tambayata ma kake yi bayan ka kulle mana fuska yar so na so ta kalli mutanen najeriya amma ka hana tsakani da Allah wannan aldaci ne?yadda fa kake jinka cikakken mutum haka itama yar so take jin kanta ato wallahi ama daina raina mata hankali?hannunsa ya dora kan cikin da ya ɗan fara tasawa kana ya ce "to yar so ku yi hakuri keda matar so"hannunta ta dora akan nasa ta janye tana cewa "haba daddy ya zaka dora Mata nauyin hannunka gashi nan kasa ta kuka"duk sai Mus ab ya rikice dan shi duk ya dauka gaske ne abinda aminatu take fada dan bai taba zama da me ciki ba ko cikin Khalid duk yadda yaso ya bawa Dauda kulawa sai ya hakura dan bai ga fuska ba,am sorry babyn so"ya fada yana dan shafa kan aminatu cikin kulawa da taka tsantsan,a haka suka karaso estate din, m jauro dai guguwa yayi kamar yana jin tutu ya tafi baya yana sheka wariyar da da baiyita ba tabbas sai ta zamar masa allura ashe dai har yanzu aminatun ce dai MATAR DAN BIRNI bata sauya ba. Gaba daya mutanen gidan na waje kowa na cike da dokin ganin aminatu da kuma yar so din da kullum ba a da wani batu sai nata hatta da Khalid idan suna waya maganar yar so kawai ake yi,rungumeta Nana ta yi tana mata Barka da zuwa haka innawuro har zuwa kan su Hajara da anita da tazo itama da nata katon cikin dan tarbar aminatu,mus ab dai yana ta kallonsu har dai da suka gama da matarso sannan suka juyo kansa, ɗan karyar da kai wa Nana yayi lokacin da ta rungumosa gefenta, dariya ta yi tana cewa "kai fa ka girma dole sai kayi hakuri da ganin banbanci "alhaji babba da fitowarsa kenan shima dafa kan aminatu yayi yana mata barka daga nan ya rike hannunta suka karaso gun nana da innawuro,shima rungume mus ab yayi yana cewa "yaro na dai ya kusa zama baba in Sha ALLAH"wannan miskilin murmushin gefen bakin nasa yayi idanunsa akan aminatu da ta wani sunne kai kamar gasken kunyar take ji,gaba daya suka juya dan shiga cikin gidan,anan ne mus ab da aminatu suka yi ido hudu da zahida dake zaune kan kujerar guragu tana kallonsu idanunta cike taf da kwallar tausayin kanta,take aminatu ta turbude fuska tana kallon Mus ab da ya dauke kansa kamar bai ganta ba,ganin hakan yasa aminatun ta ɗan murmusawa zahida tare da cewa "adda zahida ya karfin jikin?"d sauki aminatu" zahida ta bata amsa cikin maganar ta da har yanzu bata daidaita ba,daga nan ta bi bayan mus ab,tana ji Nana na ce mata"me yasa kika fito ke da ba wadatarciyar lafiya gareki ba?"daga haka Nana ta turata suka shigo falon a tare,take wasu zafafan kwalla suka zubowa zahida,da ace bata kasance me son zuciya ba da yanzu ita ma tana gefen MUS AB a matsayin matarsa, ina ma zata samu alfarmar zama matar mus ab a Karo na biyu da ta fi kowa farin ciki a duniya kuwa. ***** Lokacin da aka hadu a dinning room Dan cin abincin da aka yi musamman dan aminatu da mus Ab,kuwa zahida kasa sakewa ta yi dan duk sai taji ta mozanta,isma kuwa shima tunda suka gaisa ya wuce bangarensa dan shima kunyar hada ido da mus ab din yake. Kowa ya fara cin abin da yake bukata sai dai aminatu bata taɓa komai ba,duk da cewa ba ita yake kallo ba amma hankalinsa kaf yana kanta kuma yasan abinda ya hanata cin abincin,to rayuwar da suka yi kaf aminatu bata cin abinci da hannunta tun kafin su bar gida ma,shi yasa yanzu ta koma kalar marayun da suka rasa me tallafinsu,Nana ce ta ajiye spoon dinta tana kallon aminatu da cewa,boddo yaya dai naga kin kasa cin komai,ko da wani abu da kike bukata wanda babu shi anan?"girgiza kai aminatu ta yi ba tare da ta ce komai ba,take kuma kowa sai ya bar abinda yake hankalinsu ya koma kan shalele matar so,alhaji babba ya ce aa diyata akwai damuwa dai ko?"da fadar haka aminatu ta rushe da kuka tana fadin Ni yunwa nake?"anne ta ce ki ji min wani sakarci duk abincin dake gabanki ko dai saboda da shakiyanci?"harara aminatu ta watsawa Anne tare da cewa Wallahi ki min shiru ko yau ki kwana da bera a dakin ki"ai ko take Anne ta yi gum da bakinta, dariya su anita da Hajara suka saka saboda dramar Anne da aminatu sababbiya ce da ba zasu iya dena wa ba, duk da cewa yanzu anne bata kallon aminatu da fuskar baya,kallon masoyiyar jika take mata, shi yasa fadansu ya koma na jika da kaka. Nana ce ta dubi mus ab tana cewa"ka yi shiru kabarmu da shagwababbiyar matarka bayan nasan sarai kasan abinda ya hanata cin abincin?"kallon Aminatun yayi yayinda da ta kashe masa ido ɗaya tare da keɓe baki tana masa nuni da yar so fa yunwa take ji,kawar da kansa yayi yana kasa cewa komai,Muryar aminatu ya ji tana cewa "Abba ya sani fa yar so bata iya jure yunwa kuma ya sani dole sai ya bata a baki zata ci amma shine yayi shuru yana fiki fiƙi da idanu kamar bai san komai ba"da sauri Hajara ta miƙe ta shiga tattara duk abinda zasu bukata tana zubawa a cikin basken,sai da ta haɗa musu kayan abincin sannan ta kalli aminatu ta ce "taso matar so kuje dakinki na bangaren Nana ya baki abincin kar yar so ta samu matsala dan yunwa zata iya jigatata"kamar walkiya haka suka ga Mus ab ya bar wajen saboda maganar matsala da hajara ta yi,take suka sanya dariya, zahida kuwa wani irin kuka ta ji ya taho mata wanda hakan yasa ta Gara kujerar ta da hannunta da yafi lafiya ta bar wajen,gaba daya da kallo suka bita sai dai babu wanda ya tanka suka ci gaba da cin abincin su. Hajara na ajiye basket din ta fita tana dariyar mus ab da duk ya wani birkice akan aminatun,shigewa jikinsa ta yi tana tura fuskarta cikin kirjinsa tana shaƙo ƙamshinsa da cikin ya kuma saka mata nacinsa,hannu yasa ya zagaye ta a hankali cikin takatdatdan dan yanzu sai ta ce ya matse yar so na kuka,amma idan ita ta so babu dabdalar da bata yi a jikinsa ba tare da ta yi korafin yarso ba,dago kanta yayi yana mata kallon cikin ido kafin a hankali ya motsa bakinsa yana cewa muje ki ci abincin ko?"girgiza kai ta yi tana wani shigar da idanunta cikin nasa,kawar da kansa yayi tare da janta suka zauna bakin gadon,shafa fuskarta yayi kana ya zura hannunsa cikin rugarta yana shafa cikinta zuwa samanta,kana ya hade bakinsu waje daya,ganin abinda yake kokarin yi yasa ta a kwacewa tana cewa daddy in gaya maka tsakani da Allah "?gyada mata kai yayi yana dan ajiye numfashi, ta ci gaba da cewa "wallahi daddy tsoro nake ji kar wasu ya'yan so din su karu akan yar so kaga zasu danneta amma wallahi ko Ni ina son jinka a tare da Ni wannan tunanin ne Yasa kaga ina ki"dafe kansa yayi yana jin takaicin sakarcin aminatu wani lokacin, wai a nufinta wani cikin zai kuma shigar ta ne bayan wanda take dashi,ta shi yayi zaune tare da janyo abinda yasa zata iya ci ya shiga bata, bai kyale ta ba har sai da ya tabbatar ta koshi sannan ya fice daga dakin,duk sai kuma taji damuwa dan tunda taga ya yi mata haka fushi yayi,to ita da baya mata fushi ko dan yaga zahida ne? Saurin da wannan tunanin ta yi tare da shigewa bathroom ta yi wanka da ruwa masu kamshi, tana fitowa ta shafa humras da sauran turarukanta sannan ta zura doguwar riga me santsi wadda ta bi jikinta ta kwanta, daga nan ta ɗora abaya baka akai ta lulluba dan kwalinta aka ta fito fuskanta ta yi wani fes kana kallonta kaga me juna biyu. Falon Alhaji babba ta nufa inda tana daf da shiga ta ji Muryar Alhaji babba yana cewa,"mus ab tun lokacin da aka fitar da zahida US cikin ikon Allah ta samu taimakon gaggawa daga manya kuma kwararrun likitoci shine dalilin da yasa aka samu wannan ci gaban,yanzu haka tafiya ce kawai bata yi kuma kullum ana samun ci gaba dan bakinta ma yana fitowa kuma dayan hannun shima tana iya amfani da shi tafiyar ce dai sai a hankali,shi yasa na zauna na yi nazari da tunani akan maganar ka da ita,na ce me zai hana tunda ta yi nadama kuma akwai rabon da a tsakaninku ka mayar da ita dakinta ka bata dama ta karsh....faduwar Aminatu da suka ji ya hana Abba karasa maganarsa,da gudu duka fito dan ganin abinda ke faruwa,aminatu suka gani kwance babu alamar nunfashi yayin da har jini ya fara bin kafafunta,cikin kidima da ficewar hayyacin da ba a taba ganin mus ab a ciki ba ya sunkuceta yayi waje,da gudu m jauro ya karaso ya shiga ya tayar da motar tare da fugarta suka bar gidan,shima Abba da nana mota suka shiga suka bi bayansu, lokaci daya hankalin jama ar gidan ya tashi da ganin jinin dake bin jikin aminatu. Kai tsaye ABM hospital m jauro ya wuce da su,mus ab gaba daya ya rude fuskarta kawai yake mari yana kallon jinin da ke zuba a jikinta wanda tuni shima ya bata shi,suna shiga aka matso da gadon marasa lafiya dan a dorata a kai amma mus ab tuni ya sunkuceta yayi ciki da ita ba tare da ya tsaya sauraren gadon ba,da gudu likitoci kusan biyar suka bi bayansa, dama su kullum a shirye su ke bare kuma an zo kan me kankat ai basu ga ta bata lokaci ba,dakyar suka lallaba mus ab ya fita daga dakin,daidai lokacin su Nana suka karaso da sauran yan gidan da duk suka biyo su daga baya,kowa ka kallesa hankalinsa a tashe,mus ab kuwa tun da ya kifa kansa jikin kofar dakin bai dago ba, bare a fahimci halin da yake ciki,Abba kuwa gab daya ji yayi kamar shine ya zama sanadi dan ya tabbata maganar da yayi aminatu ta ji har hakan ya zama sanadin faduwarta. Tunda zahida ta ga an yaye an tafi asibiti ta kuma jin wani irin karaya, tale ta sawa zuciyarta hakuri da mus ab Dan yansu ta kuma tabbatar da cewa ta rasa shi rasawa ta har abada,har yanzu kishin nan nata yana nan dan haka koda ta koma auren mus ab ba zata taba zama lafiya da zuciyarta ba ko da ace bata cutar da aminatu ,kuma yasan bazata taba samun farin ciki faga ko wanne bangare ba saboda ita tana da babban tabo na uba da kuma ita kanta,kuka ta ci ta koshi ta bawa kanta hakuri da niyar ta bar mus ab har abada. ****** Fitowar Dr ema shi ya sa mus ab dago kansa, dan ba dan a hankali ya bude kofar ba da mus ab zai iya faduwa saboda yadda ya hada kansa da kofar,zubawa Dr ema din ido yayi ba tare da ya iya bude bakinsa ba, jan hannunsa Dr ema yayi suka wuce office dinsa,zama yayi akan kujera yana kallon mus ab da ya yi masa tsaye hannayensa goye a bayansa idanunsa kyam akan ema ɗin ko kiftawa ba yayi,duk sai ya dabarbartar da ema din da tsananin kwarjininsa ya rasa ta ina zai fara maganarsa ma,gane hakan da mus ab din yayi ne yasa shi dauke idanunsa da kansa yana fesar da numfashi me zafi, cikin sauri ema ya fara masa bayani"firgitar da ta yi ne yasa ta fadi, mun yi ƙoƙarin tsaida cikin dake jikinta,duk da hakan yana da nasaba da saurin kawota da aka yi,in sha Allah zata farka lafiya, sai magungunan da za a bata wanda zasu taimakawa cikinta wajen inganta lafiyarsa"shi kansa Dr ema sai da ya sauke tasa a jiyar zuciyar bayan yaji saukar ta mus ab,hannu ya mika masa ssu kayi masabaha yana cewa,"zan iya ganinta"?yes zaka iya ganinta amma ba a bukatar hayaniya "fita mus ab yayi,gaba daya suka yo kansa, kasa ce musu komai yayi dan ba shi da bakin da zai iya zaman yi musu dogon bayanin da Dr ema yayi masa,ganin ya shige dakin qminatun yasa Abba ya tafi wajen eka din ya jiyo bayanin da kansa,yana sanar da su kuwa suka shiga hamdala fuskarsu na bayyana irin farincikin da yake kasan zuciyarsu. A hankali ya zauna daf da kanta yana kallon fuskarta da ta yi fayau kamar wadda ta yi jinyar kwanaki,shi kansa bai san tsawon jimarwa a wajen ba, ji yayi kawai ta ɗora hannunta saman nasa da yake kan goshinta, a hankali ya bude idanunsa da suke a lumshe,tare da sunkoyowa ya sumbaci labbanta da suka dan bushe yana fadin me kike ji ina yake miki ciwo?"maimakon amsa sai hawaye da suka shiga zarya akan fuskarta,lumshe idanunsa yayi yana jin zafin zubar hawayennata a cikin zuciyarsa da gangar jikinsa,hannunsa dake kanta ta ture tana ƙoƙarin tashi, kamata yayi ya taimaka mata ta tashi zaune hannu yasa yana share mata hawayen da suka ki tsayawa,yana cewa pls abinda kika ji ba zai yiwu ba, sminatu ba zan iya rayuwa da wata mace bayan ke ba,saboda Annabi umartarmu yayi da cewa mu yi aure idan har mun san zamu yi adalci, to Ni mus ab sulaiman jaafar ba zan taba iya adalci tsakanin Aminatu da wata mace a duniya ba ko a aljanna kin isheni a matsayin mata, saboda nasan zaki bani farin cikin da mata dari ba zasu iya bani shi ba,ki yarda dani dan Allah kar ki mana asarar yar so"daddy ba kai ne da kanka ba kana da iyaye kuma ba kai ne ka nemi wannan auren ba abba fa da kansa yake baka umarni, abba kuma mutum ne mafi kololuwar daraja a wajenmu matsayinsa ya wuce yayi umarni mu ki bi, wallahi daddy mutuwa zan yi ba zan hana ba ba kuma zan bijire ba sai dai nasan daga wannan rana ba zan kara lafiya ba wata kila wannan batun shine sanadin mutuwat....."ba zaki mutu ba qminatu in sha Allah Ni ba zan zama sanadin mutuwar ki ba, ko da bake CE kika zama sanadin dawowata cikin farin ciki na ba,kuma ba umarni na bawa mus ab ba shawara ce, dan haka daga nan mun kulle maganar nan har abada ba zata kuma tashi ba,dan haka ki kwantar da hankalinki kar ki min sanadin tawa matar son"ya karasa maganar da mayalwacin murmushi akan fuskarsa, maganarsa ta bawa wanda suke bayansa dariya ta kuma bawa qlinatu kunya sai gata cikin kirjin mijinta,da sauri abba ya juya yana cewa su Nana "ku muje gida kawai zasu taho daga baya "hakan yasa suka koma basu karasa shiga dakin ba duk da cewa sun so ganin aminatun sosai. Suna fita mus ab ya kuma yi mata shinfida a cikin jikinsa yana cewa ashe matar so haka take da kishi ban sani ba"mintsininsa ta yi a ciki wanda yasa shi sakin faffadan murmushin da yanzu ya daina yiwa aminatu wuyar gani inndai suna a tare daga ita sai shi,idan kuwa acikin mutanene sai dai ya dinga binta da mayen kallon da yake huda tsokar jikinta yana shigewa jinin jikinta.anan suka zauna har sai da ta cika awa biyu cif sannan aka sallame su ,suka tafi gida. A nan zahida ta kuma ganin tsagwaron son da mus ab da ahlinsa suke yiwa aminatu, abinci ma a baki Nana ta bata tana wani lallaiyata kamar kwai innawuro na sannu Hajara na kaiwa da kawowa wajen ganin ta wadatata da komai,Anne ma har da ja mata yatsun kafa saboda kwanciyar da tasha,ita kan sai komawa ɗaki ta yi tana faman ciwon rai da nadamar da har ta mutu ba zata daina yinta ba. Sai wajen karfe tara sannan Anne ta ce aminatu ta tashi su rakata dakinta, kallon annen ta yi sannan ta leka mus ab da yake daga can karamin falon Abba, sannan ta kuma dawo da dubanta kan Anne tana cewa "kiji min mata mijina yana nan zaman jirana amma ki bude baki kice wai zaki rakani"tabe baki Anne ta yi tare da cewa to yar Sarkin miji a umma ta gaida ashsha"dariya aminatu ta yi sannan su kayi sallama. Suna fitowa waje aminatu ta coge tare da rike kugu tana yatsina fuska, kallon ta yayi da alamar tambaya?tura baki ta yi kama cikin Muryar ta ta sangarta da in ta yi take sanya musu ab cikin wani hali na tsananin shaukin ta ta ce"to ba yar so ce ta ce ita bazata iya tafiya ba sai dai daddy ya goyata "juyawa kawai yayi ya kurkusa ta haye gadon bayansa tana dariya har da cewa kuma ka yi a hankali kar ka yi sauri saboda kar ta gaji"cikin sauri zahida ta yi baya daga jikin windown ɗakinta tana maida numfashin ta da taji kamar za a zareshi. Bai dauke ta a ko ina ba sai dakin su dan babu abinda suka raba komai nasu a tare yake, mus ab ya ce aminatu ta zama rayuwarsa rabuwa da rayuwa kuwa sai lokaci yayi.duk da cewa ta sha wanka a bangaren Nana amma sai da ta kuma yi tare da yarimanta inda tun daga bayin lissafinsu ya fara kwancewa,a haka har suka fito kai tsaye masaukin da zasu amayar da zazzafar kaunar da suka tara suka nufa,cikin bargo suka shige aminatu na cewa daddy kashe mana wuta fyadams duk ta kwashe mana sirrinmu tana ta barbadawa fans dinta na yar gudan yarbawa da matar dan birni, b azamu bata sirrin yau ba saboda me tsada ne "daga haka kuwa naji dif sun kashe fitila da lalube na samu na baro dakin ina cizon yatsa dan nasan yau da dakyar idan oga mus ab bai kuma yin kuka ba. ***** Anita ta dauka lafiya,duhaima ma ta sauka lafiya, saura Amina tun mu, da kullum ba a rasa sabon salon masu ciki a tare da ita,mus ab dai ya dauka kuma ya jura,a cikin haka ne mus ab ya budewa aminatu babban Foundation din da ta bukata dan tallafawa marayu da gajiyayyu da marasa lafiya, sannan tasa aka gina masallaci da bohol da makarantar islamiyya domin ladan ya dinga kaiwa ga iyayenta,mus ab ya fada kasuwancin mahaifinsa tsundun, yayin da sule karami ya tattara ya dawo kasarsa shima suka hadu suna juya dukiyar mus ab cikin amana. An yanke wa su danturqui daurin rai da rai, zahida kuma zaman shekara ashirin ko kuma diya ta makudan kudade, Abba dai ya kuma yiwa zahida gata dan ya biya mata diyyar shekara goma sha biyar shekara biyar kawai zata yi a gidan kaso. ***** Bayan gumurzu da aka sha lebur room daga karshe Allah ya dauki aminatu lafiya da santalelen babynta me kama da mus ab tamkar yayi kaki ya dire,zo kuga murna mara misaltawa a wannan family dan haƙora mus ab da ba a taba gani ba a yayin dariya a wannan rana yayi barinsu abin ba acewa komai,Ammaru kuwa da ya rike ta ya fara zuba mata kisess har sai da sule karami ya janyesa sannan ya hakura. An yi suna yaro ya ci sunan baffan aminatu wato Yusuf,daga nan rayuwa ta ci gaba da garawa cikin kwanciyar hankali, a bangare guda kuma aminatu na ci gaba da habbaka Foundation dinta,cikin lokaci kankani sunansu yayi shura wajen taimako da tausayin talaka,ba iya asibiti su suke ziyara ba har sauran asibiticin gwamnati kai ziyara suke da bawa marasa karfi tallafi kullum basa gajiya da karbar kukan talakawa, aminatu bata aikin komai duk da cewa ita cikakkiyar likita ce,sai dai ta tsaya a iya Foundation dinta a gida da kuma bawa mijinta da dansu cikakkiyar kulawa irin ta cikakkiyar macen hausawa, wannan shine burin Nana wanda kullum bata gajiyawa wajen rokon Allah, gashi kuma ya biya mata ya nuna mata fiye ma da yadda ta roka, Hajara dai an daura musu aure da m jauro, isma da sule karami da Ahmad Dan ladi suma duk sun samu mata an yi aure an cika estate da family wanda albarka ta sauka a cikinsa suke ta hayayyafa,Khalid kuwa duk wata sai sunje gaba dayansu sun dubasa bayan sun je je Makka sun yi addu'a,wa musulmi da musulunci.zahida ma suna zuwa duba ta akai akai kuma cikin ikon Allah ta samu lafiya har ta fara tafiya kamar ba ita ce ta yi wannan mummunan faduwar ba. Soyayya kauna ririta juna shine abinda yake wanzuwa tsakanin aminatu da ƊAN BIRNIN ta,ba zan ce muku ba sa fada ba domin rayuwa zo mu zauna zo mu saba ce kuma duk dan adam ajizi ne sannan bai cika goma ba,sai dai ko da sabanin suka samu aminatu bata bari mus ab ya kwana da fishinta duk da cewa har ransa baya iya fushi da aminati sai dai ya nuna masa a fuska saboda gyaran tarbiyya,mus ab yana alfahari da aminatu domin ta cika mace da ake kira mace ta gari duk shirmenta ta san girmansa ta Kuma san darajar aurenta domin da ilimin ta na addini daidai gwargwado,bata musu da shi sannan bata fadi in fada da shi, wannan shine abin da yqke kara mata daraja da kima a wajensa domin kuwa duk iskancin namiji idan kina masa biyayya da bin umarninsa to ko ke bai nuna miki ba wata rana sai kin ji yana yabon halinki a waje ko cikin abokansa. ****** Bayan shekara biyar zahida ta fito daga gidan yari daga nan Abba sule ya daura mata aure da wani ma aikacinsa me mata biyu ta zama ta uku,a hakan ma Godiya ta yi da tuni ta fidda rai da aure saboda tasan ta yiwa kanta tabon da ba lallai ta kuma samun mijin aure ba,da haka ta yi hakuri ta zauna gidan mijinta tare da ci gaba neman gafarar Ubangiji. Aminatu ta kuma haifar Asma'u da Fatima,suhaima ma yanzu yaranta uku kenan haka anita tana da biyu,matan su isma ma kowacce da nata yaran biyu, Hajara ma ta haifa wa jauro yara biyu. BAYAN SHEKARA UKU. Zahida ta samu yaro guda, aminatu kuwa yanzu yaranta hudu cif, Yusuf Asma'u Nana karama kenan,sai kuma Fatima suna kiranta zuhra,da karamin danta mus ab wanda ita da kanta ta sanya masa sunan,shi yasa ya zama ɗan lale,To shima dai mus ab ya dage sai ya kuma jefa kwallonsa a raga ya samo aminatu,to bayan mus ab karami ya yi shera uku ,mus ab babba yayi sa ar samo aminatunsa daga nan aminatu tabce a dakata haka,ya ce bai san wannan ba dole a samo masa sule,daga karshe dai sai da aminatu ta dire shida sannan mus ab ya hakura maza uku mata uku ko ya ce huɗu har Khalid da ya zama ɗan saurayi, kuma har yana can yana shan karatu sai dai kuma baya cikin kewa dan iyayen nasa sun maida Dubai kamar falo da daki. Can cikin shara a ka tsinto gawar Abby tsutsotsi sun cinyeta Daga karshe dai sai a haka aka dan tona rami aka saka shi ba tare da an samu damar yi masa sallama ba,dan sai bayan da abin ya faru su Abba suke jin labari har da hoton da yan jarida suka buga lokacin suka tsinceshin. Allah yasa mu yi kyakkyawan karshe Amin Duka duka anan na kawo karshen wannan labari nawa me suna AMINATU MATAR ƊAN BIRNI, Kuskuren da nayi cikin rashin sani Allah ya yafe min, abinda ya zama na darasi Allah yasa al umma ta amfana da shi,ina fata duk abinda na rubuta ya zama izna ga al umma Allah kasa mu da ce love U all my fans🥰🥰