[4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: Typing* 💕 **MATAR ƊAN BIRNI* 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page1``* Tun daga nesa zaka hango ƙurar dake tashi kamar yaƙi, wadda sai ta kusantoka ta baɗeka da ƙura har idanunka sannan zaka fahimci cewa ba mota ba ce ko yaƙi mutum ne. mutum din ma yarinya ƙarama ta mace ita ke wannan aikin. Duk wanda ya samu rabonsa kuwa sai kaga ya tattara kayan sana'arsa ya bar shiyar, dan muddin ya cigaba da zama to kuwa zai yi asarar da sai ya kwana uku bai maida ita ba. Ita kuwa wannan yarinya bata tsaya da gudunta ba, takalmi a hannu ƙugu ya ci damara da siririn gyalen da ya murɗu kamar hanjin kaza, dai-dai lokacin da tazo gifta bafulatana hajar me nono kanta ɗauke da ƙwaryar nononta zata nufi kasuwa, amma sai me? ji kake kif yarinyar dake ta tada ƙura a garin kamar ana yaƙi ta kifar mata da nonon ba tare kuma da ta juyo ba ta ci gaba da gudunta babu alamun tasan ta yiwa wani abin halitta barna. Ihu, hajar ta yi kafin cikin azama tabi bayan yarinyar tana cewa "wallahi yau bazan yadda da asara ba dole a biyani ko ubanki zai dawo daga lahira kuwa"bata rufe bakinta ba ta hango yaronta da take jira su tafi kasuwar kwance a kasa yana "ihu da murza idanunsa kamar zai shiɗe! da gudu ta karasa inda yake ta ɗagosa tana tambayarsa abinda ya samesa? duk da cewa bata raba ɗayan biyu waccen shedaniyar yarinyar ce,nuna mata ƙurar yarinyar ya yi yana cewa "matar ɗan birni ce ta zuba min ƙasa a ido"zabura ta yi ta kama hannunsa suka ci gaba da bin yarinyar da basa hangota sai dai ƙurar da take tayarwa. Ita ko yarinyar sam bata damu da binta da hajar ke yi ba sai ma nufar rijiyar da yara ke diban ruwa ta yi, cikin zafin nama ta fara zubda ruwan tana watsa ƙananun botikan dake wajen cikin rijiyar, babu wanda ya iya tanka mata a yaran sai ma takansu da suka yi dan sun san idan suka tsaya su din ma ba ƙyale su zata yi ba. Tana gamawa da nan ta kuma yin gaba, su kuwa yara tuni sun kaiwa iyayensu ƙara dan haka cikin ƙanƙanin lokaci sai ga gungun iyayensu mata sun fito sun bi sahun hajar dan bin matar ɗan birni dan a biya su asarar da ta yi musu. Dariya bafulatanar yarinyar da suke kira matar ɗan birni ta yi! tana cewa "wahala ce bata isheku ba ku yi ta bina muna zagaye anguwa dan Ni bani da abin yi sai na tsokana"dai-dai lokacin ta zo wucewa ta fadar Arɗon gari, tana zuwa ta yi turus, kafin ta sunkuya a hankali ta kwashi ƙasar wajen tana cewa "arɗon gari da fadawansa kuma bari a baku naku rabon idan yaso sai kuyi sulhu da kyau dan nasan ƙarshe dai wancan zugar a fada zasu tsaya, dan ni kam na riga na tsere ba mai iya kamani sai dai a kai kara fadar arɗon gari shi kuma arɗon gari, yau bashi da ido bare kuma ƴan korensa" tana gama faɗin haka ta daddage ta watsawa arɗon gari da mutanensa ƙasar da ta deba, aiko bata samesu ko ina ba sai cikin bakunansu da suka buɗe suna ta zubawa me gari gulma shi kuma ya bude baki da ido yana saurare dan jin ta ina zai fara hukuncinsa na zalunci,tana zuba musu ta kuma kwasa da gudu tana cewa "hooo Ni matar ɗan birni babu me ja dani ka ja dani mijina na birni ya kaika bayan kanta wooooo" tuni ta ɓace ta bar dattijai da murza idanu, baki kuwa ya cika taf da ƙasa bakajin komai sai sautin furzar da kasar da ta cika musu baki. Dai-dai lokacin dandazon mata da yaran da suka biyo Aminatu matar ɗan birni suka ƙaraso fadar bakin kowa ɗauke da ƙorafinsa akan Aminatu, jiki a sanyaye suka zube gaban arɗon gari suna kallon yadda suke ta fama da babbar riga dan goge idanunsu da suke jin tamkar zasu faɗo saboda ƙasar da take cikinsu,hajar ce ta fara buɗe baki dan faɗin korafinta amma sai Arɗo da ya ƙyallara ido guda ya yi saurin katseta ta hanyar daka mata tsawa tare da nuna mata hanya da hannu yana cewa "maza ku tashi ku bar Wajennan tun kafin nasa a watsa min ku yanzu, wannan ma ai rashin hankali ne kuna kallo Nima dai yarinyar nan bata barni ba a gaban idanunku ta buɗemu da ƙasa amma saboda rashin hankali irin naku kun zube zaku fara ƙorafi to ku tashi koma me yake tafe daku daga baya na saurareku idan kuma akan Boɗɗon innawuro ne sai dai nace daku ku yi hakuri kawai". Jiki a saluɓe suka tashi daga fadar ko waccensu gida ta koma dan babu wadda zata iya tunkarar gidansu Aminatu da sunan kai ƙara, dan tsaf zaka fito da rotse a kanka, ko da suka biyota dama sun yi tunanin zasu iya kamata ne su bigeta kafin ta shiga gida. Da gudu ta shiga gidan ji kake, kakaf kaf kaf ƙarar ture butocin da a kayi alwala da su,bata tsaya ko ina ba sai dakin innawuro ta banko ƙofar ta rufe tana cewa "innawuro idan kin gama cika aiki se ki min magana na buɗe ɗakin"jin jina kai innawuro ta yi! tana mai ci gaba da kaɗinta sai daga can ta buɗe baki ta ce "oho yau ma kin jawo maganar ko?" Daga haka ta mike daga zaunen da take ta janyo wata sanda irin ta Fulanin nan me shegen zafi ta aje kusa da ita tana cewa shige ɗaki ki ɓoye naga ɗan buhun uban da zai shigo gidan nemanki"ta taga Aminatu boddo ta kuma lekowa ta ce "innawuro ki ɗauko wannan turaren me yaji ki saka a zauren duk wadda ta shigo ta fita da tari da majina"innawuro bata ce komai ba ta ci gaba da kaɗinta tana yi tana kallon hanyar zaurenta dan ganin uban wamda zai shigo, sai dai kuma shuru kake ji ko sauro basu gani ba hakanne ya nunawa innawuro cewa matakin da ta ɗauka akansu yayi aiki dan haka ta kwalawa Aminatu kira ta fito ta ci abinci. Fitowa ta yi tana yatsina ƴar kyakkyawar fuskarta me cike da zallar KURUCIYA,zama ta yi kusa da innawuro tare da jawo akushin dake gefen innawuron a rufe, buɗewa ta yi tana cewa "me kika yi minne yau kike ta so na ci? Allah dai yasa baki samun maganin mallaka irin wanda matar tsalha ke sawa didiya ba" rike baki innawuro ta yi kafin ta magantu da cewa "yanzu boɗɗo ni zan kaheki duk kaunar da nake Miki kike tunanin zan kaheki?"tura baki Aminatu ta yi tana cewa yo innawuro a wannan zamanin ai ba abin mamaki ba ne dan kaka ta sawa jikarta maganin mallaka kuma ni ba cewa nayi zaki kahe ni ba ehe kar ma kice zaki min ƙage" ta ƙarasa faɗa tana tura danbun da ta debo a bakinta. Kafin innawuro ta buɗe baki tayi magana,an kwana sallama daga wajen bukkarsu.da sauri boɗɗo ta ƙarasa hadiye lomar da ta zuba a bakinta tana miƙewa tsaye,dan tasan zugar Arɗo ce suka biyota har gida,wuri_wuri innawuro ta shiga yi dan neman abinda zata tare su daga shigowa,sai dai boɗɗo tuni ta rigata dauko kalkashin da suke miya da wanke kai dashi ta zuba ruwa a ciki, kai tsaye ta nufi hanyar fita daga bukkar su inda yake a sumulce mulmul kamar ka kwanta, cikin sanɗa ta ta karasa kana ta labe tare da tsugunawa ta zuba ruwan kalkashinnan gaba dayansa kana ta komawarta ta zauna ta ci gaba da cin danbunta hankali kwance.innnawuro bata ce mata komai ba sai ma ci gaba da ta yi da nata aikin har da ƴan waƙe_waƙenta, dai-dai lokacin aka kuma kwalla sallama cikin fullaci kamar maƙogaran me sallamar zai tsage,amsawa innawuro ta yi tare da bada izinin a shigo. Tsurawa hanyar ido Aminatu ta yi tana shirin ganin waye me rabon karaya ko targade yau a gidansu.aiko bata kai karshen tunaninta ba suka ji ihun dan aiken yana fadin "wayyo Allah kuguna wayyo bayana jama'a kuzo ku tsinto min jikina da suka tarwatse"boɗɗo da ta karaso inda yake kwance yana babatu ta ce "ai babu wani abinka da ya bar jikinka ruwan zafi da dori kawai zaka je a yi maka gaba ka kuma dawowa tsegumi Aminatu ce dai babu yadda zaku yi da ita matar ɗan birni kenan"juyawa ta yi ta bar wajen tana juya mazaunanta daga karshe ta fashe da dariya tana kwaikwayon dan aiken arɗon gari..... Daƙyar aka ɗaga dan aiken arɗo babu abinda yake sai ihu da kiran a duba masa Kwankwasonsa ya cire,bi bayansa Aminatu ta yi tana tillaƙar dariya tare da cewa "na fa gaya maka bayanka yana tare da kai amma ka kusa rasasa in dai zaka dinga zuwa bukkarsu boɗɗo" "Ke Boɗɗo ke Boɗɗo amma anyi lalatacciyar yarinya in sha Allah nan kusa zaki bar garinnan ko ma ɗan huta da jarabarki yarinya sekace iblishiya tana girma tana Dada cin ƙasa kuma alƙur an ba zan ƙyaleki ba ba dai Ni ka yada a ƙasa ba?to muddin na rasa kwankwasona wallahi se kin biya aradun Allah"Aminatu me zata yi ba dariya ba dama abinda take nema kenan gashi kuma yanzu ya samu dan haka yi take har dasu faduwa kasa, duk cikin wanda suka dauki dan aiken arɗo babu wanda ya tanka mata bare shima iskancin Aminatu matar dan birni boɗɗon innawuro ya biyo ta kansa, a haka suka lallaɓa suka kaisa gida matarsa banda zagi da wuta balbal babu abinda take yiwa aminatu dan tasan ko ta ce zata rama to ita ce a ruwa.. Gyada ce a gabanta tana ci tana duba littafin da ake koya musu a ƴar karamar makaranta dake cikin rugar tasu, ta dage dole sai ta karanta abinda aka rubuta alhalin ko sannu bazata iya fada da turancin ba ba bare akai ga dogayen kalmomi,amma a haka din ita ce ster a cikin rugar kuma ita ce me iyawa dan idan kaga yadda aminatu take taƙarklƙarewa tana koyawa yara turanci se abin ya baka mamaki da dariya,to yanzu ma dubawa take yi dan anjima kaɗan zasu shiga lesson ɗin da take yi musu duk ranar Friday. Innawuro dake fitowa daga ƙurya ce ta fara mita da cewa,"ke kam boɗɗo naga ranar hankalinki yanzu karatunne ba zaki yisa a zuciyarki ba sai kin bi kincika min kunne gashi Ni ba sanin abinda kike fada na yi ba".dariya aminatu ta yi daidai tana cinye gyaɗarta ta ƙarshe sannan ta ce, "innawuro dole ki yi hakuri dan sai na ƙware da turanci saboda auren ɗan birni sai da turanci"zama innawuro ta yi tana cewa "ey kuma fa haka ne maza yi karatun ko zamu samu dan birnin a kusa kafin yazo kin iya sosai" yauwa innawurona amma fa gaskiya dole kema ki tsaya na koya miki turanci saboda shigar gidana se me turanci saboda yan birni basa son hulɗa da wanda basu da turanci" to shike nan daga yau Nima zan fara koya in yaso sai mu dinga yi a gida hakan shi zaisa mu kuma kwarewa har mu fi ɗan birni iyawa" cewar innawuro kenan tana gyara zama ɗan koyan turancin aminatu boɗɗo ....... Muje nets pg muji ya turancin aminatu yake😂😂😂 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page 2``* Kallonta aminatu ta yi cikin ɗage gira kafin ta ce,"haba innawuro yu do don't spikelalizin conturalizin abarbayalizin ya za a yi na koya miki turanci ke kaɗai?ai dole sai kin waitanin franck ka naina sunzo" babu abinda innawuro take sai Gwale ido da buɗe kunnuwa so take kawai ta fahimci abinda boɗɗon ke fada amma da alama hakan ba zai samu ba,dan haka ta kuma gyara zama tare da ɓantaro farin goronta ta ce "haba boɗɗodo jikar innawuro matar ɗan birni ɗan daure ki faɗa min abinda kika ce ko da hillacinne ko Allah yasa na rike wasu kalmomin da zan iya tsayawa gaban ɗan birni dasu".miƙewa aminatu ta yi tare da cewa ko na fassara miki ma ba ganewa za ki yi baki bari kawai na dinga koya miki a hankali saboda kanki yayi girma da ɗaukar irin wannan dogon turancin" ta fada tana shura takalmanta na roba da alama fita za ta yi,ganin haka yasa innawuro saurin cewa "a'a fa Boɗɗo ki haƙura da fitar nan dan yau na gaji da yawan magana idan kuma baki ji ba to duk maganar da kika ɗauko zan barki da ita ato". Bubbuga ƙafafu aminatu ta shiga yi kafin ta zube a wajen tana shurasu tare da yarfa hannu ta kasa cewa komai sai burgima cikin ƙasa da take yi kamar wata katantanwa, riƙe baki innawuro ta yi cikin jin haushin tabarar aminatu ta ce, "wallahi idan baki tashi a cikin ƙasar nan ba yanzu zansa a kira min baba wuro daga can tsangayar Fulani tunda a duniya shi kaɗai kika jin shakka yanzu ya hayo amalanke ya iso mu ya zane min jikinki" kamar an tsikareta haka ta miƙe tana tura ƙaramin bakinta ba dan taso ba ta shige bukkarsu tana gunguni. Daf da magriba bukkarsu boɗɗon ta fara cika da yaran Fulani har da wanda suka girme mata duk da cewa suna tsoron boɗɗon, amma saboda kulafucin turancin da take koya musu haka suke mata biyayya kamar yaro da ubangidansa,cikin takun fadi ta fito daga bukkarsu ta nufi dan filin da suke zaman karatun tana wani haɗe rai ita a dole ga teacher,suna ganunta suka shiga gyara zama da kara sanya nutsuwa a kansu dan yanzu idan ta ga dama sai ta kori mutum babu gaira babu sabar. Zama ta yi akan dan damalin da ta saba zama tana kare musu kallo kafin ta bude baki ta fara magana,ban koya muku gaisuwa da turanci ba dan wulaƙanci shine zaku min dunkuskus babu me gaida Ni" ai sai gaba dayansu suka mike tare da maƙale hannayensu a goshi suna mai ƙamewa guri daya yadda dai ake sarawa yansanda da sojoji kafin su hada baki wajen fadin "gudu gudu mama" wani murmushin jin dadi aminatu ta saki kana cikin karamar muryarta me zaƙi ta ce "gudu_gudu fafas hau iz your timeme? Gaba ɗaya suka kuma haɗa baki wajen cewa "Yesa mama" tanakayu Mayu boyas sitidawun"gaba daya suka zauna suna ta yashe baki sun iya gaisuwa da turanci,daga nan kai tsaye aminatu ta shiga koya musu karatu, tana hango innawuro daga gefe ta yi zukuɗi ita ba ta yarda ba tana ɗaukar karatu. Idan kaga yadda aminatu ke diling ya'yan mutane sai ka rike baki tsallan kwaɗo da gudu kuwa har sai da kafafun falmata suka kasa miƙewa tana ganin haka kuwa ta sallamesu bayan ta karɓe kudin makarantar da kullum sai an kawo su babu fashi. Har sun kwanta bacci suka jiyo Muryar dadan falmata tana kwada sallama daga kofar bukkarsu kamar zata ari murya,murtsuke idanunsu su kayi tare da tashi suna laluben fitila. Karo innawuro suka yi ita da aminatu take innawuro ta sa ihu dan ita bata san aminatu ta farka ba, dama cike take da tsoron wanda ke kwaɗa musu sallama da wannan daren ko dan su suna bacci da wuri ne oho. Jin haka yasa boɗɗon saurin buya dan take basira ta zo mata dan yasan ƙararta aka kawo dan kullum su kayi karatu sai an samu uwar da zata zo cin ƙaniyarta to yanzun ma ta shaida Muryar dadan falmata, innawuro kuwa sosai take sambatu da ihun aljanun dawa yau ya shigo ruga tsine masa kawai take tana fadin "duk yadda muke rayuwa tare da ku amma hakan bai hana ku zaluncemu ba, kun turo wata na sallama me makon ku tsaya iya haka a'a sai kun haɗa da fasa min goshi to muddin wani abu ya samu goshina Alkur'ani ba zan yadda ba kafurawan banza da wofi" tana fadan tana fita waje inda ta samu dadan falmata tsaye ta rike ƙugu da shirin ko ta kwana. "Au jikinki ya shiga me dawan?"innawuro ta faɗa tana kallon dadan falmata cikin takaici,"ey Kya fadi haka mana tunda kin san halin jikarki kuma kin san ɓannar da ta yi min na kusan karya min ɗiya" ashshha ashe bata karye ba?" Cewar innawuro tana watsawa dadan falmata harara cikin hasken farin watan da ya haske filin rugar,cije yatsa dadan falmata ta yi bakinta har kunfa yake wajen masifa nema take ta ture innawuro ta shige bukkar dan janyo aminatu ta ci na jaki a faɗarta. Aminatu kuwa tun bayan fitar innawuro ta yi saurin shammatarsu itama ta fice, ta can bayan bukkarsu ta yi cikin sanda ta janyo wani dan tsani da suke hawa suna yin shanya a saman bukkokinsu, takawa ta yi a hankali ta haye can saman bukkar tare da kwanciya ruf da ciki, sai ta zuro da iya kanta ta saitin dadan falmata bayan ta nade fuskarta da baƙin mayafi baka ganin komai sai fararen idanunta manya masu maiko.dadan falmata nata kumfar baki sai kawai jin wani irin huci ta yi a saman kanta daga kan da zata yi ta kuwa yi ido hudu da fararen idanun aminatu wanda ta kuma zaresu suka ƙara girma. Wani irin baya dadan falmata ta yi jikinta na wani irin karkarwa, tunda take rayuwa a daji bata taba tunanin zata yi ido hudu da aljan ba shi yasa abin yazo mata a bazata kuma ya kada yan hanjinta,juyawa ta yi da wani irin asabar gudu kankace me tuni zaninta na saki ya kama gabansa,kira take "ekuwa jama a yau nayi gamo wa innawu yau ga ranar islamiyya jama a ku koyan addu'ar korar shaidanu". Aminatu kuwa cikin sanda ta sauko daga saman bukkar, kana ta nufi kofar bukkar inda ta samu innawuro tsaye kamar gunkiya ta kafe guri daya da ido jikinta da hannunta da bakinta ko ina karkarwa suke maƙogaranta babu abinda yake sai kaiwa da kawowa.zungurinta boɗɗo ta yi bakinta cike da dariya!kana ta ce "innawuro na me yake faruwa ne? Tunda ɗazu nake jin hayaniya cikin barcina kamar a mafarki"da sauri innawuro ta cafki hannun aminatu kafin ta rungumeta a lokaci daya tana mai sakin kukan tashin hankali,cikin rike dariyarya aminatu ta ce "innawuro ba dai gamo kika yi ba da farkon daren nan?" Cikin kuka innawuro ta ce "yar nan Ni Ko na yi gamo yau naga abinda na gani wanda tunda aka haife Ni a daji nake rayuwar daji ban taba cin karo da aljani ido da ido ba sai yau, yau jinnu sunci amanar fillo dole sai na kaiwa ta baleri ziyara da sassafe dan ta bincika min taga daga wane nahiyar yake kuma dame yazo?" Dariya aminatu ta saka dan ta kasa riƙeta, duka innawuro ta shiga kai mata a haka suka shige bukkar, innawuro ko rufe ido ta kasa yi saboda tsoro,aminatu kuwa baccinta ta koma har da su munshari. A bangaren dadan falmata ma haka ta tafi bukkarsu daga ita sai dan funjima dan tuni ta yada zaninta,ranar itama bata yi bacci ba Allah Allah take gari ya waye ta tafi wajen boka ta baleri. Aminatu na ganin asuba ta yi ta yi saurin tashi ta saka kayan sakinta baƙake ta fice ko sallah babu batunta burinta ta isa bukkar ta baleri kafin innawuro ta isa,tana zuwa ta samu ta baleri na aikin hura wutar bokancinta, dan dakatawa ta yi tana kallon aminatu da ta yi mata tsaye aka rike da ƙugu,"ke me ye kika shigo min bukka haka tsidim ba tare da bin ƙa ida ba?" Aminatu bata tanka mata ba sai janyo kujerarta da ta yi ta zauna ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tana ci gaba da watsawa ta baleri kallon uku a'hu,ganin kallon da boɗɗon ke mata yasa ta fara wasu yan surutai irin na yan tsubbu ita ala dole zata kira masu yi mata maganin boɗɗon. Ganin hakan da boɗɗon ta yi yasa ta kuma tsuke fuska kana cikin yatsina fuska ta ce "ke ta baleri ki dakata da wannan sakarcinnaki ko kuma na tona Miki asiri an gaya Miki ban san kan harkar ba?" Dakatawa tabaleri ta yi daga surkullenta tana kallon aminatu cike da mamaki! kafin ta samu damar magantuwa aminatu ta ci gaba da cewa "ki daina kallona haka in dai nice kin san zan aikata fiye da haka kuma na san komai yaudarar mutane kike kina fada musu ƙarya kina basu maganin karya ko ba haka ba ne?" Ta karasa da tambayarta tana wani zaro ido kamar ta samu karamar yarinya sa arta. Guri ta baleri ta samu ta zauna ba tare da ta ce komai ba,domin sarai ta san halin aminatu dan ita kanta ba barinta ta yi ba kuma muddin ta bari aminatu ta yi mata tonon bankada ta shiga uku a gurinta da kuma mutanen garin dan haka cikin lalama ta dubi aminatu ta ce,"me kike bukata boɗɗo?"dariya boɗɗo ta yi tana gyara zamanta har da karkata kallabi, sannan tace,"yauwa ƴar gari yanzu kika hau kan hanya, gyara zamanta ta yi sannan ta ɗan leka bayanta dan tabbatar da tsaro kafin ta dubi tabaleri ta na cewa "so nake yi ki dinga aiki da umarnina Ni ba kudinki nake so ba yanzu haka innawuro tana hanya da dadar falmata zasu zo saboda gamon da suka yi jiya da dare,dan haka idan sunzo kice musu aljanuna ne muddin basu yi min biyayya ba to kullum sai sunzo sun tsoratasu kuma kema sunfi karfinki dan haka dole su yi min biyayya, ina fata kin fahimceni?" Ta karasa maganar tana wani turo karamin bakinta,jinjina kai tabaleri ta yi tunda dai babu batun raba kudi ai duk wannan me sauki ne,dan haka ta bude baki ta ce,t"o boɗɗo dan wannan ai ba wani abu bane kar ki ji komai har da abinda baki ce ba duk zan kara dan haka baki da matsala tashi kije kar su zo su sameki ko kuma ki shige cikin bukka"da sauri Boɗɗo ta yi cikin bukkar dan bata so tabaleri ta yaudareta Gara komai a yi a kunnen ta. ******** JGK international hospital. Babban asibiti ne wanda ya amsa sunansa asibitin kudi,kaf garin gombe babu asibitin da ake ji da ita ta kuma yi suna kamar wannan asibiti,asibitin takasance ta hadakar mutum uku Aminan juna kuma manyan mutane kusoshi masu fada aji a kasarmu,duk yadda zan baku misalin wannan asibiti ba kamar yadda zaku ganta ba, tana da matukar kyau a ido dan idan ka shiga zaka yi zaton a kasar waje kake, sai dai duk da haka bai hana samunta da sauki ba, ma ana dai asibitin tana da saukakawa talakawa, wannan kenan. Dari uku kafin na gama free PG Ga account nomber 👇🏽 8064537048 opay Fatima Yusha'u adam ...........✍🏼 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page 3``* Cikin takun isa take saukowa daga mata kalar benen dake cikin falon,kallo daya zaka yi mata kasan cewa akwai gayu da ji da kai, sannan kana kallonta zaka bata shekaru sama da talatin,tana da jiki sosai wanda shi yake nuna shekarunta ƙarara a fili. ba wata kyakkyawa ba ce amma ba zaka sa ta a layin munana ba domin yar gayu ce ta ajin ƙarshe,Hajiya zahida kenan mata gurin MUS'AB JAMIL babban da ga wannan ahli.. Tana saukowa wata mata dake dakon saukowarta ta yi saurin tashi tare da miƙa mata farar labcort ɗin da take hannunta cikin tsantsar biyayya da taka tsantsan ɗin yin kuskuren da zai sa tasha zagi ta uwa ta uba.ba tare da ta yiwa matar kallo ɗaya ba ta karɓa tana wani ƙara tsuke fuska wadda tasha sun glass baƙi,daga haka ta ci gaba da takun isa idanunta akan hadaddiyar wayarta, sai da taje bakin ƙatuwar kofar galass din da ta raba tsakanin valconin gidan da falon kana ta ɗan dakata, sannan cikin fuzgo maganar kamar ana mata dole ta ce "larai har yanzu ba a samu me ci gaba da kula da khalid ba?" Cikin ladabi larai ta ce"ki yi hakuri ranki shi daɗe ana nan muna cikitawa saboda har yanzu ba a samu wadda ta cike sharadanki ba" ci gaba ta yi da tafiya ba tare da ta tanka ba,sai da larai taga fitarta sannan taja ajiyar zuciya tare da hamdala sun rabu lafiya da uwar dakinta ba tare da anzagi iyayenta na kabari ba,wucewa ta yi dan ci gaba da haɗawa mutanen gidan karin kumallo kafin su fito. Tana gamawa kuwa sai ga uwar gida sarautar mata Hajiya Nana,daga nan sai Khalid yaro dan shekara biyar cikin shigar makaranta shida auta suhaima wadda ita ce ta shiryasa,daga nan sai bukar me bin mijin Hajiya zahida sai karaminsu suleman,daga nan sai kan gidan wato kakarsu wadda suke kira da anne. Tunda suka zauna babu me surutu har suka gama suka tashi da daddaya kowa na wucewa sabgarsa me makaranta me aiki duka kafin wani lokaci sun watse,sai iya anne da Hajiya Nana wanda sune kawai basa fita aiki. Kai tsaye zahida JGK hospital ta wuce inda a nan ne take aiki a matsayin likitar mata, sannan kuma tasan sirrin fida dan haka ake ji da ita a asibitin duk da ta kasance ɗaya daga cikin ya'yan masu asibitin. Duk yadda take da girman kai da raina talaka hakan baisa ta hana ko ta gaza wajen basu taimako ba a duk sanda hakan ta bullo, wanda hakan yake matuƙar bawa yawancin mutanen da suka santa mamaki da bincike da bin kokofin cewa lallai da wani abu a ƙasa dan abin da matuƙar mamaki ace zahida Garba da bata da tausayi da imani ace tana taimakon talaka da bada gudummawarta a duk sanda hakan ta taso,da yawan mutane suna zargin cewa akwai manufa akan hakan wasu kuma suna ganin ai dama ɗan adam tara yake a komai bai cika goma ba,to koma dai me ye zahida Garba na ɗaya daga cikin amintattun wannan asibitin wanda suke bada gudummawa ta temako akan talaka me ƙaramin ƙarfi wannan kenan. ****** Alhaji Garba da Alhaji Kabir da Alhaji Jamil, Aminan junane tun zamanin KURUCIYA tare suka taso babu wanda yasan sirrinsu daga su sai su,tare suka yi arziki suka yi aure suka kuma gina rayuwar ahlinsu a tare ba tare da wani yaji kansu ba,dukansu marayu ne babu me uwa ko uba a cikinsu sai Alhaji Jamil, banbancin su suna da yan uwa na jini amma shi shi kadai iyayensa suka haifa, shi yasa mahaifiyarsa anne ke ji dashi kamar tsoka daya amiya,tare su kayi aure suka fara haihuwa. Alhaji Garba 'yarsa ɗaya zahida daga kanta bai kuma samun haihuwa ba,shi kuma Alh kabir yaransa biyu duka maza,sai Alh Jamil wanda yafi su yawan ya'ya, nasa guda hudu ne maza uku mace ɗaya,Dukansu sun fito daga daga asali daya wato Fulanin gombe.matansu duka yan Gombe ne komai nasu yana cikin gida arzikinsu ne kawai yayi shura ha fita kasashen duniya. JGK hospital idan ka haɗa farkon sunansu zata bayar asibitinsu ce guminsu ce babu wanda yasan yadda suka yi suka samu tarin arzikinsu sai su tsakaninsu,basu yi karatu suna yara ba sai da suka fara samun duniya sannan suka yi yaƙi da jahilci wanda idan baka sani ba bazaka taba cewa basu yi karatun tun farkon kuruciyarsu ba,amma fa sun tsayawa yaransu sun yi ilmi na boko da Arabia sosai dan haka rayuwar ahlinsu ta ginu da wadataccen ilmin duniya da na lahira,sun yi kokari sun haɗa zahida da MUS'AB aure a matsayinsu na masu iko da ya'yansu ba wai dan shi mus ab yana so ba,sai dai ita zahida tana balain sonsa duk da cewa ba wani mugun girmanta ya yi ba dan shekara ɗaya ne tsakaninsu. Abu na farko da ilimin addinin da suka basu ya fara tasiri kenan akan mus ab dan bai yi jayayya ba dan shi baya musu da iyayensa duk da cewa wani lokacin tsananin muskilanci ne yake sawa ya haƙura da son ransa, zahida dai a bayyane tayi makarantar addini amma a badini babu komai a kanta dan bata da basira ta fannin ilimin addini sai wajen boko a nan tafi kauri. Zahida takasance mace me shegen son kudi ko nace son duniya, hakan ya sami asali ne daga yadda take da girman kai da son ace kowa tafi shi kuma kowa a kasanta yake wannan ne yasa ta dage ta yi ilmin boko dan cimma burinta na zama sananniya a bangaren dukiya da ilmi a duniya,dalinlinta ne aka kirkiri JGK hospital,kuma duk cikin ya'yansu ita kadai ce likita kowa da abinda yakaranta, dan haka duk cikin ya'yansu babu wadda suke alfahari da ita kamar zahida sabida ita ce makullin wani bangare kuma jigo na sirrinsu. ****** Aminatu na daga cikin bukkar tana hangen ko mai, akan idanunta innawuro ta bada sadaka aka bata magani haka dadar falmata kuma abinda ta umarci tabaleri shi ta yi, aiko idanun dadar falmata har cikowa su kayi da kwallar tashin hankali,cikin sauri tabar wajen tana cewa zata je ta bawa Boɗɗo hakuri dan ita tasan bala'in da ta gani jiya,ita ko innawuro bata ce komai ba amma dai tasan babu abinda zai sameta tunda aljanun jikarta ne tana da tabbaci baza su yi mata kome ba. Aminatu na ganin sun tafi ta yi sauri ta fito ko kula ta baleri ba ta yi ba ta ruga da gudu dan ta riga innawuro zuwa gida. Ardon gari na kwance a fadarsa yau babu kowa a fadar duka sun tafi kiwo sai shi kadai, dan haka ya saki jiki da baki yayi kwanciyar rigingine yana ta sharar baccinsa kana gani kasan hankalinsa kwance yake bai da wata matsala. Aminatu na tafe hannunta rike da ɗan karanta tana rera wakenta tana yi tana juyi cikin farin cikin dake duniyar KURUCIYA, har ta gifta ta fadar sai kuma ta dawo da baya tana kallon arɗon da yake ta zuba munshari kamar me baccin dare,rike baki ta yi cikin kaɗa harshe ta ce "au bacci ma kake saboda lalacewa da wannan hantsin sai kace wanda baiyi kwanan dare ba?" Tana gama faɗin haka ta yi kwafa tare da matsawa kusa dashi dai-dai wajen kansa. tsinke ta ɗauka ta fara yi masa waiwayi a hanci, ji kake fas arɗo ya bawa kansa wani kyakkyawan duka a hanci bai damu ba saboda shauƙin bacci ya juya ya cigaba da baccinsa,ganin haka yasa aminatu sake matsowa ta zura masa a kunne tana masa susar ganin kamar dadi yake ji sai ta sauya salo,a hankali ta janyo butar da ta gani a wajen ta lallaɓa ta zuba masa ruwan dake ciki a hancin. Cikin sambatu arɗo yayi dungure har rawaninsa na zamewa ya mike yana cewa "kan ubannann yaƙin basasa ne yau ya biyo ta hancina dan zalunci a rasa a ina za'a yi yaƙin sai cikin hancina a radu ban yadda da wannan zaluncin". Aminatu me zata yi ba dariya ba har da su kwanciya, jin sautin dariyarta ne ya dawo da arɗo hayyacinsa,fahimtar da yayi sharrinta ne yasa ya zubura zai yi kanta, aiko aminatu ta ce kafa me naci ban baki ba,ardo bai fasa Binta ba ita kuma bata fasa wahalar dashi ba, acikin gudunne suka haɗe da yar arɗon ta ɗauko niƙan gari, tana ganin aminatu kuwa ta kauce amma saboda salon tsakano aminatu sai da ta yi yadda ta yi ta bangajeta garin ya ɓare gaba daya a fuskar arɗo da ya kawo kai dan tare barnar da boɗɗon ke shirin yi masa. "Aradun Allah se kin biya garin nan ko na koreki daga ruga shegiyar fitinanniyar yarinya, anya ko wannan yarinyar ba aljana bace?" Ya fada yana sunkuyawa gaban garinsa da 'yarsa da take ƙoƙarin tattare abinda ya samu sai dai hakan ya faskara dan ya haɗe da ƙasa idan aka matsa kuma sai dai a ci ƙasa,juyowa Boɗɗo da ta ɗan yi musu nisa ta yi tana musu gwalo har da rawar koroso wanda ke nuna cewa ta ci dubu sai ceto. Daga can nesa dadar falmata ta hango Boɗɗo tana tahowa, har zata canja hanya sai kuma ta fasa ta taho suka hade da Boɗɗo da ta ci kunu tana faman gatsina fuska kamar taga kashi,washe baki Dada ta yi tana cewa "kaga aminatun Boɗɗon innawuro wa ya tabaki haka yanzu yasha sanda aradun Allah" wani kallo aminatun ta watsa mata kafin ta bude baki ta fara mata magana cikin turancinta da ko ita bata san me take cewa ba, "dadan falmata hayatu stopiyan a will colonyu daga idanuna if dont stop by the door" cikin rawar jiki dada ta ce "to Allah ya baki hakuri amma Ni ban fahimci me kike nufi ba ko zaki min da fillo" wucewa aminatu ta yi tana cewa "shike nan jeki kawai amma lallai falmata ta dawo makaranta"shike nan zata dawo se kin auri ɗan birni in sha Allah ke din matar ɗan birni ce Boɗɗon innawuro" wannan kalamai su suke kwatar mutum daga tsiyar aminatu dan haka take ta washe baki tana cewa yau ba zansa falmata aiki ba kuma na ɗauke mata kuɗin makarantar yau" aiko Dada ta ji dadi haka ta tafi tana murna kamar an biya mata hajji. ******** "Malam jibo ka je ka dauko MUS'AB daga filin jirgi kasan kasan baya son jira" cewar dattijuwa anne kenan dake zaune kan kujera tana bawa mutumin dake gurfane gabanta umarni,cikin hanzari Malam jibo ya amsa tare da tashi da fita a lokaci daya dan cika umarnin anne. Mintuna ashirin ne suka kaisa filin jirgin wanda kuma yazo a daidai lokacin da jirgin yake sauka. A hankali cikin wata irin nutsuwa da kamala ya sanyo ginannan jikinsa wanda kana kallonsa kasan cewa yana shan gym, a hankali yake taku amma sautin takun fita yake da wani irin zafin nama na nuna cewa namiji ne ke tafe,dogo ne sambal babu rankwafawa haka kuma jikinsa a gine yake babu rama, fuskarsa a hade take tsaf sai wakiliya da shekin hutu da take yi kasumbarsa kuwa babu abinda take sai sheki tayi luf abinta da gani kasan tana samun kula na musamman, fararen idanunsa masu walkiya suna sanye cikin farin glass wanda bai boye komai daga baiwar idanunsa ba kyawunsa me hade da haiba ya gama bayyana ta ko ina, duk in da ya gifta idanune ke binsa babu maza babu mata a haka ya karasa jikin motar ya shige bayan malam jibo ya bude masa kofar [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ **Pg4* A hankali ya maida idanunsa ya lumshe bayan ya kwantar da kansa jikin kujerar tare da furzar da huci daga bakinsa, kamar kuma an mintsinesa haka ya buɗe idanun yana bin hanya da idanun kamar yana neman wani abu.shafa fuskarsa ya ɗanyi yana jin amsar kuwar muryar bafulatanin dattijon a kunnensa,da ƙarfi ya maida idanun ya runtse yana mai cije labbansa kamar zai fincikesu daga muhallinsu, har yau har gobe ba zai daina tunawa da al amarin ba wanda ya zamar masa tamkar mafarki a rayuwarsa ya kuma zamar masa dafin da shi kadai ne yake tagayyara rayuwarsa duk minti duk sakon. Da wannan tunanin yaji Malam jibo na ce masa "yallabai mun karaso" shanye komai ya yi kamar yadda ya saba ya fito cikin takunsa na nutsuwa,cikin sauri mlm jibo ya ɗauko jakarsa ya biyo bayansa. Sam mlm jibo bai kula da kowa ba sai ji yayi an ɗaukesa da mari hagu da dama,dafe kuncinsa yayi tare da sunkuyar da kansa bayan ya fahimci wadda ta yi masa wannan cin mutuncin, wadda yake ganin a haife ya haifi irinta biyu amma bata duba wannan ba ta ɗaga hannu ta maresa kamar ta mari ƙaramin ƙaninta,muryarta ce ta dawo dashi duniyar mutane,"kai sakaran inane baka kallon hanya ne kake ƙoƙarin taka ni wallahi da ka takani da kaga kaskancin da baka taba gani ba a rayuwarka, dan sai na kulleka na tsawon ragowar numfashinka, fita ka bani guri kafin na ƙara maka" zahida ta faɗa tana nuna masa hanyar waje,ɗif falon ya yi kowa ya kasa tankawa dan babu wanda ya isa ya fara hatta anne ko nana basu isa hana zahida abunda ta yi niya ba,mutum ɗaya ne ƙwara daya rak shi kaɗai yake iya hukuntata, shi kuma bai iya dogon surutu ba shi yasa a mafi yawan lokuta yake rabuwa da ita. Ɗan dafe kansa ya yi kafin ya juyo ya kasheta da wani irin kallon bala'i ,kana ba tare da ya ce mata komai ba ya ɗau jakarsa da malam jibo ya ajiye a nan ya bi ta wani dogon corridor wanda zai kaisa bangarensa ya barsu da shaƙar ƙamshinsa da ya bari a wajen. Dan tsaki ta saki tare da gunguni "ka dawo fa zaka fara takurawa rayuwata"barin falon ta yi ita ma tana ɗan jin shakkar kallon da ya yi mata a ranta, to amma tasan ba wani tasiri zai yi ba tunda ga abbi a tsakiya. Ko da ya shiga ɗakinsa kai tsaye bathroom ya shige ya kimtsa kansa kana ya fito ya sanya farar jallabiya me asalin kyau da tsada ya ɗan gyara kwantacciyar sumarsa ta asalin Fulani tare da turarukansa masu ɓadda kama sannan ya fita dan shiga Masallaci yin sallar magriba. Ko da ya dawo bai saurari kowa ba ya wuce domin yana buƙatar hutawa ko zai samu damar tuna abin da ya kamata yayi a kan makomar auren bafulatar ruga da kuma rayuwarta da amanarta da dukiyarta da aka Danƙa masa. ****** Zahida ce take ta faɗa da masifa kamar zata ari baki, duk son fitarta da sassafe yau haƙura ta yi saboda kawai larai ta fito ta ci mata mutunci akan taƙi samo me kula da Khalid ,suhaima da ke jan hannun Khalid dan kaisa makaranta ta yi tsagal ta ce, "aunty ai ba laifinsu ba ne sun kasa samo wadda ta yi daidai da ƙa'idojinki ne kawai"a fusace zahida ta kalli suhaima kafin cikin fushi ta ce "wai suhaima nasa dake ne? Me yasa a kullum kike son shiga sabgar da bata ki ba? Me yasa duk gidan nan kika fi rainani?" Saboda kema baki girmama na gaba dake ba" suka ji dakakkiyar muryarsa me cike da nutsuwa ta ratsa kunnuwansu,durƙusawa yayi gaban Khalid da ya rugo ya rungumesa ya sumbacesa tare da shafa sumar kansa kwantacciya irinta ubansa daga nan bai kalli inda zahida ta daskare ba saboda kunya, ta wannan hanyar kawai MUS'AB yake cin galaba akanta har ta saurara da wasu abubuwan saboda ta tsani a dizga ta gaban ƙannensa bare kuma 'yan aiki, hakan na matukar tunzura rayuwarta. A fusace ta juya zata fita abbi da yake karyawa tun ɗazun bai ce komai ba yasa murya ya kirata,bayan ya gama yin wani dan nazari akan buƙatar zahidan,dawowa ta yi tana cin magani kamar zata haɗiye ranta,dubanta abbi yayi sannan ya yi dan gyaran murya tare da goge bakinsa da tisue ya ce "zahidan abbi karki damu da batun me aiki Ni da kaina zan kawo Miki su har biyu da yarinya da dattijuwa dan haka ki kwantar da hankalinki kinji" jinjina kai kawai tayi tare da barin falon cikin sauri saboda yau din ta makara sosai. Dubansa ya sauke kan MUS'AB kana ya ce "ya kamata ka dinga binta a hankali kasan ita mace kullum tamkar yarinya karama haka rayuwarta take" tak MUS'AB bai tanka ba ya ci gaba da lodawa cikinsa kayan aiki dan shi din ba ya wasa wajen bawa cikinsa haƙƙinsa, suhaima kuwa tuni taja Khalid suka fita yaya bukar kuwa baya kasar sule kuwa yana da jarrabawa da wuri ya bar gidan dan haka daga abbi sai anne da Nana da su kayi kamar basa wajen saboda tsananin takaicin halayyar zahidan wadda basu da damar saitata ko yi mata fadan dai-dai duk da fadan anne kuma ita ba wai tsoron zahidan ko abbi take ba kawai dai bata son shiga sabgar ne dan haka nan take jin ƙin zahidan a ranta shi yasa bata shiga shirginta. Abbi kai tsaye comfanin shinkafa ya wuce inda anan ne suke haduwa da aminansa dan aikinsu yafi karfi a nan ɗin,bayan haɗuwar tasu sai kuma suka wuce wajen mitting ɗinsu keɓaɓɓan wajen sirri inda duk abinda zasu tattauna da ya shafi sirrin kasuwancinsu anan suke yi ba tare da wata damuwa ba. Bayan shiru na wasu mintuna ne abbi ya yi gyaran murya tare da gyatta zamansa ta yadda zai ji dadin maganarsa kana ya ce "ina ga fa lokaci yayi da ya kamata mu shigo da yarinyar nan cikin rayuwarmu tsaronta a wani waje ba zai haifar mana da me ido ba, kar kuga cewa mun sa musu tsaron da ko wajen rugar basu isa su shiga ba ba tare da mun sani ba to duk da haka sai mun kiyaye idan ba haka ba abinda muka diba tsawon shekaru muna nema zai garemu samu". Duban juna su kayi kafin Alh Garba ya ce "tabbas maganarka jamilu na kan gaskiya dole mu dawo da mutanennan kusa damu" to tayaya?" cewar Alh kabir kenan,yauwa tambayar da nake jira kuyi min kenan cewar abbi kana ya ci gaba da cewa zamu kawo su gida a matsayin masu aiki saboda zahida tana neman me ci gaba da kula da khalid saboda waccen tunda ta gudu har yau bata dawo ba" dariya suka yi gaba daya tare da tafawa, abbi ya ce Ni zan shirya yadda za a dauko su ba tare da sun ji tsoro ko sunyi zargin wani abu ba" daga nan suka ci gaba da tattauna muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarsu. ****** AMINATU na shiga rigarsu ta samu innawuro ita da wanda take kira da baba wuro aminatu kuma ta ce mishi baffa wuro shi kadai aminatu ke dan ragawa saboda kullum innawuro na sanar da ita cewa bata da kowa sai shi. kuma shine ka dai zai sada ta da dan birninta, hakan yasa take daga masa ƙafa ba wai dan tana tsoronsa ba sai dan kawai kar yaƙi kaita birni wajen ɗan birni. Zama tayi gefen baffan tana washe baki ba tare da ta iya furta kome ba, saboda duk randa yazo rugarsu murna kan hanata sukuni, dan bashi da magana sai na ɗan birninta wanda ita kuma hakanne kaɗai ke sanyaya mata rai.innawuro ce ta buge bakin tana cewa"ke kam boddo me yasa kullum nutsuwa nisa take kuma yi dake me ye hakan kika sashi gaba babu gaisuwa bare sannu da zuwa"tura baki aminatu ta yi kafin cikin fillo ta ce"baffa sannu da zuwa kazo lafiya ya kabaro mutanen rigarku?"bata bari ya bata amsa ba ta cigaba da cewa "baffa wai ya batun ɗan birni har yanzu baka nemo shi ba, nifa na fara gajiya da karyar da kake ta shuka min tsakani da Allah baffa manya fa basa karya?"salati innawuro tasa tana mai tafa hannayenta cikin fusata ta janyo muficin dake gefenta ta wurga mata tana cewa "wannan yarinya kwai yar nema baffan naki ne yake karya?"tare numfashin innawuro baffa yayi yana cewa rabu da ita innawuro kin san dai KURUCIYA ke damun aminatu amma duk da haka nasan irin hukuncin da zan yi mata" ya fada yana karya hularsa irin tasu ta fillo,jinjina kai innawuro ta yi ba tare da ta kuma cewa komai ba sai harara da take ta zabgawa aminatu da tayi kicin kicin da rai. Fuskantar aminatu baffa yayi kana cikin lallashi ya fara magana "aminatu ki kwantar da hankalinki in Sha Allah a wannan lokaci zan cika Miki burinki Kar ki damu kinji diyar kirki"turza kafafu aminatu ta shiga yi yayin da ta saka kuka me karfi tana cewa "Ni dai na gaji da wannan alkawarin yan birnin da kake min idan ba zaka kaini ba Ni zan je da kaina na nemo abina aradu na gaji da zuki ta mallenka"hannu innawuro ta kai zata bugeta karar karamar wayar baffa dake cikin aljihun yar shararsa ta dakatar da innawuro daka kaiwa aminatu duka,zaro wayar yayi yana mai kallon fuskar wayar dan karanta sunan da ke saman wayar,kasancewar baffa yana yawan shiga cikin birnin Gombe yana cudanya da mutane sosai shi yasa ya ke dan gane sunayen mutane,yana ganin sunan me kiran ya mike cikin rawar jikin da yasa suka bishi da idanu daga wuron har aminatun dake turje turjen sangarta. Bai daga wayar ba sai da ya bata tazara sosai tsakaninsa da bukkar innawuro, cikin girmamawa da ƙanƙan da kai ya gaida mutumin dake can bangaren wanda daga jin muryarsa zaka tabbatar da cewa babban mutum ne me rike da duniya a hannunsa,shiru baffa yayi yana sauraron abinda mutumin yake fada masa bai motsa ba har sai da mutumin ya kai aya a zancan ko na ce umarnin da yake basa, sannan baffa ya sheke da wata shegiyar dariya yana cewa kar ka damu Alhaji wannan damar dama kawai nake jira dan yanzu ma kar su fahimci a kawai wani abu shi yasa baza ka ganmu a yau ba,amma ina mai tabbatar maka da cewa gobe iwar haka suna cikin gidan ka " daga haka suka katse wayar. Ko kallon bukkar innawuro baffa baiyi ba ya sa kansa yamma ya nufi rigarsa fakan fakan yana mai jin duniyarsa ta zama sabuwa,saboda ya tabbata ya kai su ya gama aikinsa da yake yi na tsawon shekaru goma,yanzu zai fara cin gashin kansa da uwar dukiyar da aka alkawarta masa muddin ya gama aikinsa lafiya ba tare da an samu wata matsala ba. "Innawuro kinga ya kuma guduwa ko saboda yasan karya yake bai san inda ɗan birni yake ba" fuskantarta innawuro ta yi kana ta ce"boddo ko mu ba mu nemi ɗan birni ba tabbas shi zai nememu nasan dole zai nememu,ki yi hakuri ki bar batun muje birni nemansa saboda mu bamu san inda zamu gansa ba kuma bamu san fuskarsa ba amma shi yasan inda zai ganmu, duk da cewa bai sanki ba amma ina da tabbaci a kansa"jan majina boddo ta yi sannan ta ce "innawuro kullum haka kike cewa zezo gashi kuma har yanzu baizo ba" zezo ki kara hakuri kinji aminatuwa hakurin da zamu yi shi zai kai mu ga cin nasarar rayuwa" da haka ta samu ta rarrashi boddo har ta samu ta yi bacci kamar wata jaririya. ********* Duk da cewa mafarkin da yayi ya dan girgiza shi amma ba zaka taba fuskantar hakan ba domin komai yana yinsa ne cikin wata irin kamala da nutsuwa sam ba ya bari ya rikice rikicewar da har zata bayyana a kan fuskarsa.tashi yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala ya tada sallah yana mai ƙudurta buƙatunsa cikin zuciyarsa da fatan Allah ya kawo masa mafitar da zai sauke nauyin da yake kansa. A can bangaren Aminan guda uku kuwa hadakar waya suka hada dan tattaunawar sirri a tsakaninsu idan bukatar hakan ta taso musu cikin dare,a maimakon su fita sai kawai su rufe kansu a kebantatun dakunansu su yi hadakar waya a tsakaninsu,kamar yadda ya kasance a wannan daren kenan. Alhaji Kabir ne ya fara magana da cewa "dalilin da yasa nace muku ina da maganar gaggawa daku shine, zama nayi na yi tunani akan shawarar da muka yanzu a jiya sai na gano cewa kamar hakan ba mafita ba ce,kar ku manta fa ba su ka dai muke bukata ba har da shi wancan da ya zamana komai na hannunsa kunga kenan dole can zai je ya neme su tunda yasan ba yan cikin birni ba ne"Abbi ya karbi maganar da cewa to kai kana da tabbacin zaije nemansu?kana da tabbacin zai rike amanar da aka bashi? Ko ku so ko ki kawo su gidan nan shine kadai mafita a garemu tunda su dinma akwai da dadden burinmu akansu"wannan maganar taka haka take dan haka Ni a ganina mu bar waccen shawarar ta farko tunda har an riga an yi magana da shi me gadin kifayen" cewar Alhaji Garba kenan,shike nan na amince na kuma gamsu inji Alh Kabir,daga haka suka rufe maganar. ZAHRA [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: chat.whatsapp.com/LolAB9n5hMEKVScwJDYIj9 ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ Pg5 A hankali yake baza idanunsa a loko da sakon Fulanin da suke zube kowacce da kwaryar nono a gabanta babu abinda yake kiyastawa a ransa sai ace yaga yarinyar.tayaya zaka ganta bayan baka santa ba baka taba ganinta ba yarinyar da a lokacin da ake kiran an aura maka ita bata fi shekara bakwai ba? wani sashe na zuciya yake masa wannan tambayar, ajiyar numfashi yaja tare da lumshe gajiyayyun idanunsa, tunda ya tashi yau din ko office bai shiga ba yake zagaye gari wai ko Allah zai sa ya gane waccen hanyar amma ina tamkar an shafe kwakwalwarsa da taɓo dan ya kasa tuna kome da ya danganci rigar Fulanin.cikin yanayin da yake boyewa a ransa ya juya kan motar a hankali kamar wanda baya son yin tukyin ya bar gefen titin da ya zama wajen zaman masu fitowa daga rigagage siyar da nono. ********* "Aminatu aminatu boddo dan Allah dan annabijo ki shaya ki shaurareni" cewar wani bafulatanin saurayi da yake ta gudu dan cimma aminatun,a karo na uku ya kuma danƙara mata kira,aiko a wani sukwane aminatu ta juyo hannayenta rike a kugunta tana aunawa saurayin wani mugun kallo,amma da ta tuna yau babu wanda ta cola kuma gashi ita idan bata ja magana ba bata jin dadi dan wani lokacin har zazzaɓi take yi, tuna hakan yasa ta dan saki fuskarta har da dan karamin murmushin da koya ta motsa sai kumatunta sun lotsa gaba daya,ganin yadda aminatu ta saki fuska yasa saurayin ya kuma gyara yar shararsa yana wani banƙare baya kai kace raƙumin da ya fara tashen samartaka ne, shi a la dole sai ya yi kama da dan birnin da aminatu take so. Sai da yazo daf da ita sannan ya kuma kobarewa tare da ƙara janyo yar shararsa gaba,dubansa AMINATU ta yi tare da saurin toshe hancinta harda kakarin amai kafin dakyar cikin fidda numfashi sama_sama hannunta akan hancinta ta ce "gaddafi me ye haka yau kwananka nawa baka yi wanka ba kuwa?zai yi magana ta katse shi da cewa "dan Allah gaddafi ka fadan gaskiya ba cewa zanyi bazan kulaka ba" sosa ƙeya gaddafi yayi yana ɗan nuku nuƙu irinna rashin gaskiya duk da yasan cewa ba warin yake yi ba dan kuwa ko be wanka ba in dai zai fito sai ya jiƙa jikinsa da turarensa dan ɗuri me shegen karfi kamar turaren aljanu dan yasan zai iya haduwa da aminatu, yau dinne ma bai sa ba amma tabbas baya wari. Tafa hannu aminatu ta yi tare da cewa "a hakan kake so na gaddafi bayan kasan cewa Ni ɗan birni nake so? To gaskiya idan har kana so na dinga kulaka sai munje yanzu kayi gayu" gaddafi ya ce in dai har zaki kulani yanzu zanje na fesa wanka har da turaren bulbule me ɗan banzan ƙamshi zan sako miki" taɓe baki ta yi sannan ta nuna masa hanya tana cewa muje" cikin murna gaddafi ya bi bayanta murna kamar ta kashe shi yau aminatu ta saurareshi. ****** JGK hospital. Wata mata ce zaune a cikin reseption ɗin hospital din ta haɗa uban tagumi cike da tsananin damuwa,kana kallonta zaka san cewa zaman jiran tsammani take yi daga likitoci,daga can nesa da ita ma wasu ne mace da namiji a raɓe daga ganinsu kaga mata da miji sai dai suma cike suke da fargabar abinda sakamakon yarinyarsu guda ɗaya tilo zai bayar,su dinma dai zaman jiran tsammanin suke yi. Dukkansu kallo daya zaka yi musu kasan cewa talakawa ne tikis masu neman taimako daga masu shi. Lokaci daya suka miƙe idanunsu akan ƙofar da suka ji alamun za a fito, wato kofar dakin da suke kyautata zaton nan ne dogon dakin da babu me shigarsa sai zahida da wasu daga cikin amintattun likitocinsu. Zahida ce ta fito daga ɗakin wanda da alamu dai ba daki guda ne a ciki ba dan kuwa kofofine kusan takwas wata na kallon wata, saboda kofar da zahida ta fito daga ciki dogon coridow ne kamar dakunan hotel shi ne aka sakaya a kayi masa wata kofar ta musamman kana gani dai kasan wajen yana cike da tsaro, yadda zahida ta bude kofar sosai ne ya basu damar kallon wajen ba wai dan suna gane tsari da kyau ko dokar wajen ba ne a'a sai dan kawai majinyatansu kuma majibantansu suna cikin wajen. Yadda suka zubawa zahida idanunsu masu cike da fargaba yasa ta jin wani irin takaicin su a maimakon tausayinsu, da kyar ta hadiye yawun masifar dake cinta tare da sassautawa ta hanyar yi musu nuni da su biyota,cikin kosawa da shan kamshi da jan ran da take musu suka bita, a ransu kuwa babu abinda suke sai zagin talauci dan badan sun kasance talakawa masu neman taimako a karkashin asibiti nata ba da tabbas ba zasu juri izgilancin zahida ba. Sai da ta bisu da kallo daidai da matsayinsu sannan ta bude baki kamar ana mata dole ta ce, "an kammala aiki kuma anyi nasara zuwa anjima za a fito da su ga wannan magungunan kuje permacy ku karba" daga haka ta maida kanta ta jinginar jikin kujerarta tana mai jan ajiyar zuciya me ƙarfi ta alamun gajiya.godiya su kayi suka fita gaba daya dan karbo magungunan,. Sai dai a bangaren ɗayar matar nan ta farko sam bata ji gamsuwa da kalaman Dr zahida ba, saboda har yanzu bata ji zuciyarta ta daina bugun da take yi akan halin da mijinta yake ciki ba, to amma tunda har ta ce lafiya zata daure ta jira sakamakon aikin wanda fitowarsa lafiya shi kadai zai bata nutsuwa. Suna fita zahida ta daga wayar office tayi kira,mintuna biyar da kiran aka yi knocked din kofar,izinin shigowa ta bayar sannan wani mutum da bai wuce shekara arba in ba ya shigo, wajen zama ta nuna masa, bayan ya zauna ne ta kuma fuskantarsa kana ta ce, ce "Dr Rayyan aje a fito da yarinyar ina so a samu tazara tsakaninsu da mataccen, sannan kar ku kuskura ku sanar da ita ya mutu ku barta ta gani da kanta saboda mu result dinmu yana dauke da bayanin mun fito da shi lafiya daga dakin tiyata ne ina fata ka gane?"na gane Dr in Sha Allah ba za a samu wata matsala ba" daga haka ya fice daga dakin ita kuma ta maida kai hankali kwance kamar ba rai ne ya mutu da gangan a hannunta ba. Lokacin da aka fito da yarinyar wannan matar ta tabbatar yarinyar tana lafiya sai ta ji hankalinta ya dan fara kwanciya har wata da ke nuna alamun kanwarta ce take cewa kin gani ko yaya dama na gaya Miki baban Sadik yana lafiya" in Sha Allah wasu mata da suma dai suke tare suka fada. Sai bayan an fito da waccan yarinyar da kusan mintuna talatin sannan suka gargaro gadon mijin wannan matar da take a ƙage da son ganin lafiyar mijinnata, da sauri suka bi gadon har zuwa dakin da aka tanada musu dan hutun mara lafiyar. "Bacci yake kar ku yi dogon Surutu saboda ana buƙatar hutawarsa sosai" cewar Dr Rayyan kenan bayan ya gyarawa mutumin kwanciyarsa wanda tuni ya jima da rigamu isa gidan gaskiya."tom shike nan zamu kiyaye in Sha Allah likita mun gode fa Allah ya saka da alheri" cewar matar mutumin, "Amin ya Allah Dr Rayyan ya amsa fuska cike da fara a,kasancewarsa me yawan fara a da kyakkyawan mu'amala da majinyatansa. Yana fita matar ta isa bakin gadon tana ɗan kallon fuskar mijinnata da take ta sheƙi kamar me baccin gaske, " Inna kinga dai da alamu baban Sadik baccin nutsuwa yake zo kiga yadda fuskarsa take ta annuri" matsowa wadda aka kira da Inna ta yi tana mai kallon fuskar baban Sadik din kafin kuma cikin dan firgici ta kama hannunsa tare da kai kunnenta kan kirjinsa take kuwa ta saki kuka hadi da salati tana cewa "shike nan lawandi rai yayi halinsa Allah yasa can yafi maka nan" take matar nan ta saka kururuwa tana faduwa ana rikota cewa take "wallahi bazan yarda ba sai kun biya ni mijina, ba haka mu kayi da ku ba baku ce min zaku kashe shi ba" daidai nan likitocin da suke kusa suka shigo ɗakin wata likita ce ta ɗan yi 'yan aune aunenta ta kuma tabbatar musu da cewa ya mutu amma bata ce musu ya jima da rasuwa ba, hasali ma cewa tayi ko minti ɗaya bai yi da cikawa ba,shaƙeta matar mamacin ta yi tana cewa "ƙarya kuke yi macuta kun daɗe da kashe min mijina wallahi ko zan yi yawo tsirara sai nayi Shari'a daku" Daga ƙarshe dai da suka rasa yadda zasu yi da matar da 'yan uwanta dole sai sawa suka yi a ka fita dasu ita kuma gawar aka ɗauke ta amota suka bisu da ita. Amma har suka kaisu gida tare da gawar matar nan bata daina kiran sai ta ga bayansu ba mata kamar me aljanu cewar driver da ya kawosu har sai da hakan yaso ya dan taba zahida daga karshe dai ta yakice tunanin matar ta cigaba da sabgoginta dan ko iyayenta bata gaya musu ba acewarta wannan ba wata babbar matsalar da zasu sani ba ce. ************& Gaddafi ganin inda AMINATU ta nufa dashi yasa ya dan dakata tare da kwantar da murya ya ce " boddo shin wai ina zamu je ne na aika gida kika rakani nayi gayu?" Kallon banza ta watsa masa kana ta ce, "lallai ma gaddafi ya za ayi na kaika gida na na barka ka shiga kewayen bukka kayi buja bujarka ka fito kace min kayi wanka, ai aradun Allah kaika zanyi gurin lamido me wankin shanu ya wanke min kai tas babu cuwa cuwa, idan kuma ba zaka je ba kayi gabas na yi yamma karka ƙara shiga gonata ehe" ta faɗa tana wani juya fararen ƙwayar idanunta tare da murguɗa dan tsukakken bakinta wanda a take jikin gaddafi ya shiga rawa yana cewa " muje aminatu MATAR ƊAN BIRNI dole idan ina son damunki sai na zama ɗan birni kuma ɗan gayu" ashe dai ka gane" aminatu ta faɗa suna karasawa wajen lamido me wankin shanu. "Yauwa lamido na kawo wanki ne" cikin fara a lamido ya ajiye tafkeken sosan kaba dake hannunsa yana dirzar jikin wani ƙaton sa, yana cewa "a'a wa zan gani kamar boddon innawuro" nice lamido aiki na kawo maka" aikin meye boddo kin san Ni fa ban iya wani aiki ba sai na wanki da durzar dabbobi" Nima ai wankin na kawo maka" cewar aminatu tana kallon gaddafi da yake ta washe baki kamar ance an aura masa boddon. "Atoto na gane ina shanun suke ban ganku tare ba?" Lamido ya fada yana duban bayan aminatu,"Gashi nan wanda zaka wanke min" ta faɗa tana nuna masa gaddafi,"ikon Allah gaddafin za a wanke Miki?" Cikin tunzura baki aminatu ta ce "shi zaka wanke min kuma wallahi ya fita tas kuma ba da sosan laushi zaka wankesa ba da irin wannan da kake wanke shanu dan yafi fita". Take gaddafi ya zaro idanu tare da kai hannunsa kan fatar jikinsa fara tas irin ta fararen fillo yana shawa tare da hango jini na tsartuwa a kan fatar. "Wayyo Allah yadikkona" gaddafi ya fada cikin firgici bayan gama tunaninsa dan ji yayi kamar an fara durza masa wanna sosan me kama da zaren ɗaurin itace. Aminatu ta ce" wallahi gaddafi idan baka tsaya an wanke min kai ba to babu Ni babu kai" jin haka yasa jikin gaddafi na rawa ya matsa kusa da lamido da tuni ya haɗa uban ruwan kumfarsa da sosansa a hannu yana jiran gaddafi dan shima ran nasa taf yake da son mugunta kamar aminatu. Gaddafi na matsawa aminatu ta ce "ka cire wannan yar sharar me shegen wari dan ko an gama maka wankan to ba zaka kuma maida ita ba a haka zamu tafi har ka bushe" cirewa yayi gaba daya gaddafi ya zama wani kalar tausayi kamar wanda uwarsa ke tsaye akansa tana bashi umarni da cewar idan bai yi ba zata tsine masa........ (Gaddafi kana ruwa😂) ZAHRA ✍🏼 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg6* Cikin yanayin ƙasaitarta da ke nuni da tsantsan gajiyar da ta kwaso a yau ta danna madannin da zai bata damar tura kofar glass ɗin falon wadda ke da duhu take kuma nuna hoton mutumin dake tsaye a wajen.babu wata sallama dake bakinta sai faman yatsuna bakin da fuskar take kamar taga kashi,babu wanda ta kalla a cikin mutum ukun dake zaune a falon sai Khalid da suke assignment shida suhaima, ta ɗan shafa wa kai daga nan ta ɗan kalli gefan da Anne ke Hakimce akan kujerar zamanta fuskarta akan karamin littafin addu'o'in dake hannunta idanunta kuma sanye da farin glas dinta na Karin gani. "Hi Anne" daga haka ta wuce sama cikin sassarfa ko kula da Nana dake cikin kiching ita da laure suna aikin girkin dare ba ta yi ba,nana dake daf da kofar corridon kiching ɗin ta dan bita da kallo tana mai yiwa danta fata da dacewa akaro na biyu, dan kuwa bata masa fatan zama da zahida tilo a matsayin matar aure ta har abada,tana masa kwaɗayin zama irin magidancin da ya samu kulawar aure daga iyalinsa kamar dai ita da mahaifinsa ko kuma fiye da haka. Tana masa fatan samun macen ƙwarai me addini wadda zata kula da tarbiyyar 'ya'yansa da su kansu ahlinsa,"in sha Allah zan ga wannan rana kafin ƙasa ta rufe idanuna"tayi furucin a fili har sai da laure ta ɗan kalleta da tunanin ko da ita take? Girgiza kai nana ta yi suna mai ci gaba da aikinsu dan kuwa Nana duk rintsi in dai ba wani muhimmin abu ba bata barin ƴan aiki akan sabgar gidanta da me gidanta su kaɗai, dole sai tayi joining da su dan acewarta matar da bata bauta a gidan mijinta ba matar aure bace ,ita kuwa tana kwaɗayin ladan da macen ƙwarai take samu a ƙarƙashin igiyar aurenta,shi yasa take wa ya'yanta wannan kwaɗayin da fata ako da yaushe. Ita kuwa Anne da aka ce mata hi ko kallo bata ishetaba, dan Anne irin mutanen nanne da in suka tsani abu to shara ma ta fisa daraja a wajensu,shi yasa bata shiga shirgin zahida dan ita bata daukar raini da iskanci duk yadda take da mutum ya rainata yanzu zasu fara takun saka shi yasa ko wasan jika da kaka bata yi da jikokinta, kowa yasan cewa Anne acting din uwa take dauka. ********** Cikin mugunta lamiɗo ya zage ƙwanji ya fara dirzar fatar gaɗɗafi kamar zai cireta gaba ɗaya,tun gaɗɗafi na dauriya yana taune leɓe har dai ya gaji ya rushe da wani ƙaƙarfan kuka me haɗe da ihun neman ɗauki.cike da mamaki aminatu ta dubesa tare da cewa "kai ko gaɗɗa me ye haka ƙato da kai ka saki baki kana kuka?"juya kai gaɗɗa kawai yake yi irin fa aminatu baza ta gane ɗin nan ba,shi ko lamiɗo bai fasa durza jikin gaɗɗa ba ,hakan da gaɗɗa ya gani ya san cewa lamido ba zai kyaleshi ba har sai ya fara ganin fatarsa a hannunsa dan haka ya dage ya kwasa da wani mugun gudu yana mai jin azabar da fatarsa ke yi. Dariya aminatu da lamiɗo suka kwashe da ita aminatu har da bajewa cikin ƙasar wajen ,sai da ta ci dariyarta ta ƙoshi sannan ta miƙe ba tare da ta kakkaɓe ƙurar da ta yi mata butu_butu ba, hanya ta ɗauka dan barin wajen amma sai lamiɗo ya tare hanyar yana mata duban kin ma raina min hankali,itama kallonsa ta yi da idanunta masu haske tana farfara su dan jin ba'asin tare mata hanya da yayi,jinjina kai yayi yana cewa "tafiya naga kina shirin yi baki biyani kuɗin ba" ey mana tafiya zan yi ko hanani zaka yi?"wallahi aminatu babu inda zaki ba tare da kin biyani ba" tabɗijan lallai ma lamiɗo nan aradun Allah ba zan gidda maka ko sile ba bayan ma ba wanka ka yi masa ba mugunta ka yi masa bawan Allah bai ji ba bai gani ba duk an dirje masa fata" ta karasa maganar da alamun tausayawa gaɗɗafi,lamiɗo ya ce" aradun Allah ko arɗon gari kika yiwa wannan abun duk son matansa bai barinki dan haka nima ban barinki" . Zaro manyan idanunta ta yi cike da mamaki sannan ta zaro harshe tana karkadashi lalala lamiɗo arɗon ka zaga arɗon ne me son Mata arɗon ne dan iska? To aradun Allah daga nan sai fada dan sai na gaya masa iskwalamtuyu wallahi is bendiriyu" ta ƙarasa zancenta da fitaccen turancinta da ake ji da shi a rigarsu. Take lamiɗo ya shiga bata hakuri amma sam bata sauraresa ba, sai ma ɗiba da tayi da wani azaɓaɓɓen gudu tamkar filfiluwa wanda take ya daina hango sawayenta sai dai ƙurar da ta tayar. Komawa bukkarsa inda ya tarar da matarsa na kaɗi,dubansa ta yi kana ta yi dariya tare da cewa "ai tunda na ji Muryar boddo tare da kai nasan cewa ba za ku rabu lau ba,ta shuka maka tsiyartata ko?" lamiɗo bai iya bata amsa ba sai buta da ya zara ya fada makewayi dan fidda zawon tsoron da ya matsoshi. Innono matar arɗon gari ta biyu ce tafe akan hanya sai sauri take kanta ɗauke da ƙwaryar nono sabuwar tatsa wadda zasu dama su yi Karin Azhar da ita, sosai innono tasha wahala wajen tatsar nonon saboda rana ta ɗaga bata tatsa tun safe ba.bata Ankara ba sai ji tayi kwaf an bangajeta gaba ɗaya nonon ya sheƙe a kanta da kan aminatu da tayi ɓannar, amma aminatu ko dubawa bata tsaya yi ba ta ci gaba da sheƙa gudunta tana yi tana laso nonon da yake kwaranyowa kan leɓenta da na gefan bakinta,duk wanda ya ganta ba zai ganeta kai tsaye ba saboda yadda nonon ya bata duka fuskarta har jikin wuyanta. Innono duk da bata ga fuskar wadda ta yi mata ta adin ba , amma tana da tabbacin ba wanda zai aikata hakan sai aminatu, dan haka ta miƙe daga zaman daɓaron da aminatu ta sata ta yi tana jin takaicin rasa nono da tunanin an dawo mata da sabon aiki dan ko ba nono ba dole ta sarrafa wani abun da za su ci. Tun daga nesa arɗo da yan fadarsa suka fara hango tashin ƙura kamar doki na kilisa, basu gama tantance waye ba suka hango aminatu da basu gane ita din ce ba ta tunkarosu da azabar gudu fuska fari fat kamar aljana sunbuƙa.ai da ganin haka take kowa ya watse daga gurin aka bar arɗo yana ƙoƙarin tashi daga wuntsulawar da yayi a ƙoƙarinsa na guduwa,bai iya barin wajen ba har sai da aminatu ta karaso ta zube a gabansa tana hakin gudun da tasha. Rufe idanunsa arɗo ya yi yana mis mis da bakinsa da alama addu'a yake son yi, dan bude idon yayi dan yaga ko addu'ar sa ta yi aiki amma sai karaf ya kara cin karo da fuskar Aminu da manyan idanunta suka fito tarwai ga maikon cikinsu da shep dinsu da suka Kuma razana arɗo ya tabbatar fa wannan din ba mutum ba ce,ganin addu'ar sa bata yi ba sai kawai ya kama kuka yana sharbar majina da babbar rigarsa yana cewa "yau ga illar rashin addini da na je makarantar malam buba da yanzu na samu dalasiman korar sheɗanu" dariya aminatu ta sa tana yi tana wanke fuskarta da ruwan butar arɗo,arɗo na ganin fuskar aminatu ya janyo sandarsa yana cewa "kaga ƴar ƙaniya wato rashin mutuncin naki kullum ci gaba yake yi kuma a kaina ko?". Rike sandar ta yi tana ci gaba da ƙyalƙyala dariya tana maimaita kalaman arɗo a ranta wato da ya je makarantar malam buba da yanzu ya samu dalasiman korar sheɗanu, idan ta fadi hakan a ranta bat san sanda wata dariyar ke kuma cinta ba, daƙyar dai ta samu ta dakatar da dariyar tana cewa nifa arɗo duk wannan abun da ya faru y faru ne saboda zaginka da aka yi na kasa jurewa shine fa na garzayo dan na sanar da kai amma shine kake dukana da sanda" ta karasa maganar cikin keɓe baki zata sa kuka,cikin sauri arɗo ya dakatar da ita yana cewa "a'a boddo yi shuru shalele faɗa min waye da wannan aikin?" Sai ga sauran da suka gudu suna dawowa cikin borin kunya, amma dake yanzu ba wannan ne a gaban arɗo ba sai bai yi musu korafi ba. Kowa ya zubawa aminatu ido yana son jin wane me ƙarar kwanane ya zagi arɗo. Gyara zama aminatu ta yi har da gyaran murya sannan ta fara suburbudo lafiyayyen turancinta da ba dukkai ba ko a can birnin. Matan cikin bukka da yara ƙananu da ma daidaita kamar su aminatu duk sai da suka fito saboda jiyo zazzaƙar Muryar amunatu ta na ragargazo Turanci, take aka zagaye aminatu duk da cewa ba jin abinda take fada suke yi ba amma dai suna jin dadin tirancin da jin alfahari suma suna da yar boko cikin rigarsu. Ganin haka da aminatu tayi yasa ta kuma lanƙwashe murya tana ci gaba da cewa" aradun Allah ardo shegotihappi is kankanatiyu an suflashiyu we lamiɗo cewa kai ɗan iskayu me kallon matayu is lemmon pregnant toyu wallahi lamiɗo na rantsetayu" ta karasa maganar tana ɗan share hawaye irin bata ji dadin nan ba. Ajiyar numfashi arɗo yayi kana ya ce " sannu aminatu sam ke baki gajiya da wannan yaren Ni ko iyawa nayi ai ba zan iya doguwar magana irin wadda kike yi ba gaskiya kina kokari,amma dai yanzu ki daure ki fassara mana da fillanci dan bamu fahimci duka Yaren ba" . "To ardo shegotihappi yanzu zan fassara muku,abinda nake nufi shine lamiɗo ne ya ce, babu wanda ya isa ya riƙe masa kudi kaf rigar nan ko da kuwa ardo ne da ya fisa son kudi da mata ba zai yadda mace ta rike masa kudi ba dan haka shi ba ɗaya yake da shegen arɗo ardo dan iskan riga ba,shi yasa na garzayo na sanar da kai wagga cin mutuncin arɗo da zaginsa ba a gaban idanun aminatu ba ato" Take arɗo yasa aka je ka taho da lamiɗo, aka gurfanar da shi gaban jama a, duk hakurin da yake bayarwa ba a sauraresa ba sai da aka yi masa hukuncin bukatar shaɗi guda goma tare da tarar zabbi da kaji guda goma sannan kuma ya bawa arɗo haƙuri,take aka kuma tasa ƙeyarsa har bukkarsa ya bada tarar zabbi da kaji , ana kawowa arɗo ya bawa aminatu zabbi biyu kaji biyu,aiko bakin aminatu har baka haka ta ɗauki kayanta ta nufi bukkarsu cike da farin ciki yau za a ragargaji daɗi. A can ƙofar bukkarsu ta hango ƙawayenta su bikisa suna ƴanta, da sauri ta ƙarasa tare da jingine kajinta jikin bukkar innawuro ta ratsa cikinsu aka ci gaba da gwabza wasa da ita,cikin ƙanƙanin lokaci da zuwan aminatu tuni har ta fara hargitsa wurin wasa tuni ya dawo hannunta ta wuce kowa saboda shegen runto, saura bai fi fita daya ta fita ba salame ta tanka Mata da cewa ita fa gaskiya bata yadda da wasan aminatu ba dan kuwa da runto ta ke shirin fita a wasa, kan ka ce me faɗa ya kaure. Aminatu ta dungure kan salame tare da cewa ,ke salame daga yau kika kuma zuwa makarantata sai na sa an tare miki hanya shegiya wadda bukkarsu take wari ƙazamai masu kashi a bukka" aiko aminatu ta tabo salame dan take salame ta yi tsalle ta dire tare da cakumo wuyan rigar aminatu tana kunduma mata zagi,cikin kuri aminatu ta ce" wai ke dan kina ganinki katuwa a cikinmu kin ɗauka zaki iya dukana bayan girman naki ma mun san dalilinsa duk wannan kibar ta cin kayan Allah ya isa ne tunda baffanku kowa yasan yana sato kayan gona da nonon shanun mutane, banza masu kaya ɗaya" kafin aminatu ta gama rufe bakinta tuni salame ta kau mata wata mahangurɓa kafin wasu sakonni tuni faɗa ya harƙe. Sai ga aminatu kwance shame shame a ƙasa tana fidda numfashi ɗaya daya. [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ **Pg7* Da gudu innawuro ta fito daga kewayensu saboda jin ihun shalelenta,aiko tana zuwa tayi arba da salame saman ruwan cikin aminatu tana jibgarta kamar ta samu baiwa,da sauri innawuro ta zo ta hankaɗe salame tare da ɗago aminatu da take ta danbarwa a ƙasa gaba ɗaya ta tumurmushe jikinta faɗi take aradun Allah bazata yadda ba sai ta rama, salame kuwa ƙugu ta riƙe tana wani cin magani kamar wata bos,"ke kuwa salame me aminatu ta yi miki zaki kashe min ita?" Cewar innawuro tana mai ɗaga aminatu tare da kaɗe mata jiki,cikin rashin kunya salame ta ce ai bani zaki tambaya ba ki tambaye ta mana ko ma baki tambaya ba ai kin san halin kayarki ko ma meye ai tsokanarta ne ya jawo mat......kafin salame ta kai aya sai ji tayi an rufe bakinta har da idanunta da uwar ƙasa ksanceqar tana cikin maganar aka zuba mata kasar sai da wata ta tafi cikinta idanunta kuwa tuni suka rufe,bata gaba dawowa daga wannan raɗaɗin ba aminatu ta tsugunna ta ja ƙafafunta ji kake tim sai ga salame a ƙasa ta kasa ko motsi, innawuro ta ce "da kyau boɗɗo na Ni nasan ban haifi rago ba dan haka shima ba zai haufa min jika raguwa ba rama dukanki ragowar ki barwa Allah" Aminatu bata sauka akan ruwan cikin salame ba har sai da t tabbatar ta daku sannan ta miƙe tana cewa dan dai innawuro ta ce na barwa Allah ragowar ya saka min ne da wallahi sai na rama duka(kaji fa dan Allah ta zage ta yi dukan da ko rabin sa ba salame bata yi mata ba amma suke kiran sun barwa Allah). Da ƙyar salame ta iya tashi gashi duka kawayensu aminatu ta janyesu da cewar su zo su tafi innawuro ta yi musu Farfesu su ci, dan haka bata samu taimakon kowa ba haka ta tafi bukkarsu da ke da dan tazara da bukkarsu aminatu. Aminatu ce zaune tare da ƙawayenta sun kewaye Farfesun da aka sauke shi yanzu da zafinsa kowa sai haɗiyar yawu yake,kawayen nan Allah Allah suke Aminatu ta basu umarnin sa hannu su ci kamar yadda ita take ta zaƙula tsoka tana cika baki,ko zafin bata ji , tun suna ganin tururin naman nan har suka daina ganin wani alamun zafi, har ta kai da cewa sun fara daina ganin tsoka a jikin naman sai ƙashi da Aminatu ke ajiyewa da zarar ta zare tsokar jiki. Laure ce cikin karfin hali da hadiye yawun da yake shirin zuba ta ce "boɗɗo naga ya huce muna iya fara ci?" Wani kallon uku ahu aminatu ta yiwa laure tare da cewa ey dole kisa hannu mana tunda ke kika yi haƙilon samun zabbin, Ni bana son hadama da kwadayi idan kuka yi hakuri ai ci zan yi na rage muku" safina ta yi caraf ta ce "to ai kin cinye sai ƙashi kawai a ciki" dalla malama rufe mana baki iyayen kwaɗayi dama ai ƙashin zan baku tunda ba wahalar ku ba ce". Innawuro na jin haka ta ta miƙe ta je ta ɗaukowa ko wannensu cinya ta zo ta basu,tana cewa karba ku tashi ku tafi ai kuma kun san halin ƙawar taku sarai sai abinda ta yi niya yau da alama ƴan kyautar basa kusa sun yi nisa" da sauri kuwa suka karba jiki na rawa suka miƙe dan sun kaɗan da aikin aminatu ta bisu ta ƙwace,ƙafa aminatu tasa ta shure ƙwaryar dake gabanta cikin rigima irintata ta ce "innawuro ya haka nama na ne fa ba naki ba kin san wahalar da nasha da turance su arɗo da nayi ya bani aradu sai sun bani kayana kashi zasu tsotsa" aiko suna jin haka suka ranta ana kare suna gudu suna cin naman dan koda Aminu ta cimma su bazata samu abin karɓa ba. Kuka Aminatu tasa har da su birgima tana cewa innawuro sai ta biya ta namanta ko kuma duk ta je bukkarsu ta ɗauko kaji day daya. Da ƙyar innawuro ta lallaɓa boɗɗo da lagonta wato ƊAN BIRNI. Baffa wuro kuwa ko Baccin kirki bai samu ba a ranar saboda lissafi da tunanin irin sabuwar rayuwar da ke can birnin Gombe tana jiransa,ya gama lissafa cewa sai ya je ya gama shirya kome sannan zai dawo ya tafi da iyalinsa, dan haka ranar Bacci sai barawo. Da sassafe ya tashi ya kammala duk shirinsa sannan ya saba yar jakarsa ya fice bayan ya yiwa iyalinsa sallama ba tare da ya sanar da su kome ba, basu damu ba tunda dama sun san yana shiga birni. Daga nan babu inda ya tsaya sai rigarsu aminatu, kai tsaye ya yi sallama cikin bukkar innawuro, cikin mamaki innawuro ke dubansa dan alokacin boɗɗo ko tashi bata yi ba.kin yi mamakin ganina ko?" Ya faɗa yana neman gurin zama, innawuro bata ce komai ba sai binsa da ido da take yi,shima bai nemi cewarta ba ya dora mata da cewa,yadda naga hankalin boɗɗo ya kasa kwanciya da maganata ne yasa ina fita jiya na shiga fafutukar neman mafita don cika mata burinta,cikin ikon Allah ina cikin tunanin mafita sai wani ubangidana a can birnin Gombe dake cikin anguwar.......ya kirani akan na temaka na samo musu me renon yaron ɗansa kuma babba da yarinya me shekara sha uku suke bukata,to jin haka yasa na ce masa faduwa ta zo daidai da zama ina da wandazan kawo masa kuma yau ɗin nan zan kaiku,ban nemi shawarar ku ba saboda dama abinda muke buƙata kenan dan haka ku tashi ku haɗa abinda kuke buƙata". A hankali innawuro ta cire tagumin da ta yi tana sauraron baffa wuro tare da ajiyar numfashi,kana ta ce anya kuwa hakan zata yuwu wuro Kasan fa ƴan birnin nan ba kowa ne abin yadda ba" haba innawuro zan kaiku inda zaku cutu ne shekara nawa nake rike da amanarku ban cutar da ku ba sai yanzu, duk amincin dake tsakanina da mahaifinta kuma danki haba innawuro banji dadin rashin yardar da kika nuna min ba" shi kenan wuro zamu tafi amma ai ka bari mu ɗan yi sallama da jama a da maƙota ko"? A'a innawuro wannan fita a sirri zamu yi ta Babu wanda zai sani ke dai tashi boɗɗo ku shirya" innawuro kasa Musa masa ta yi dan kar ya kuma fusata haka ta tashi aminatu wadda tana jin inda zasu ta hau murna cikin tsanaki ta bari innawuro ta yi mata wanka me kyau ba irin nata buja buja ba. Ba tare da kowa ya sani ba suka hau amalanke ya fita da su bakin hanya daga nan suka hau a kori kura suka ɗau hanya. ************ Abby ko fita bai yi ba saboda zaman jiran karasowar wuro, ko da ya fito tun karfe takwas suna can gardin tare da abokansa suna tattaunawa,Abby ne ya ɗan yi gyaran murya tare da ɗan muskutawa kana ya ce " na gama tsara kome game da wuro dan haka da ya kawo su tsarin zai fara aiki, kamar yadda kuka sani mun kulla kasuwancin mu da Alhaji macciɗo dan a halin yanzu Dr zahida ta gama shirin tiyata wuro kawai muke jiran karasowarsa dan yau ta riga kowa fita daga gidan nan". Gaskiya zahida na kokari sai dai muyi ta mata addu'a amma tabbas tana bada taimako ga marasa lafiya yadda ya kamata da kuma mu kanmu dan asibitinmu na samun lambar yabo ta ko wanne bangare tunda duk a sanadin ta ne gwamna ke son mu shigo cikin tafiyarsu ta siyasa"cewar Abby ke nan yana mai kallon fuskokinsu, Alh Garba ya numfasa tare da cewa ai mu bar batun siyasar nan rayuwarmu tafi mana daɗi a haka ko ya kuka gani"? Ya karasa maganar da tambayar su,jinjina kai su kayi cike da gamsuwa daga haka suka ci gaba da tattauna abinda ya shafesu. Shigowar su cikin ƙwaryar birni, duk sai aminatu ta ruɗe dan wannan shine karonta na farko a shigowa birni, duk abinda ta gani sai ta taɓa ko ta yi tambaya akai dan ma innawuro na tsawatar mata da abin sai ya fi haka,lokacin da suka shigo unguwar ji tayi ta gama mutuwa saboda manyan gine_ginen da ta fara cin karo da su amma kuma ga mamakinta sai ta dinga cin karo da gidajen madaidaita masu karamin karfi a cikinsu, dan haka.ta dubi baffa wuro ta ce,baffa amma dan Allah su kuwa masu kananan gidajennan me ya kaisu yin gini tsakiyar manyan gidaje basa tsoron su rikito su dannesu?"washe baki baffa wuro ya yi tare da ƙara karfin rikon da yayi mata ji yake idan ya sake ta kamar ya saki arzikinsa,kana ya ce"ai wato boɗɗo ita wannan anguwar ta mutum uku ce sune suka siyeta to amma a dalci irin nasu sai basu tashi ainahin mutanen da suka samu a cikinta ba saboda ainahi anguwar ta marasa ƙarfi ce duk yhaɗuwar da kika ga ta yi yanzu duk sune suka maida ita haka da kuma manyan masu kuɗin da suke saidawa gidajen da suka gina,shi yasa zaki ta cin karo da munanan gida amma ai duk da haka sunfi bukka nesa ba kusa ba ko"? Jinjina kai kawai ta iya yi ba tare da iya ranka masa ba, innawuro wuro kuwa bata cewa kome sai idan taga aminatu zata yi shirme da jan magana,zasu wuce ta kofar wani gida aminatu taga yara yan mata kamarta a kofar gidan yan wasanni kasancewar yau weekend,kama baki ta yi tana cewa "to Allah ma yaso zan samu yan wasa amma naji daɗi Allah yasa ɗan birni zai barni na dinga fitowa wasa",buge bakinta innawuro ta yi tana cewa karba kuma jin bakinki anan shirmammiya kawai" tura bakin ta yi ba tare da kuma cewar ba. A haka suka karaso jikin wani katon gida kamar gari dan duk layin babu me kwatankwacin girmansa,kai tsaye suka tunkari ƙatuwar kofar gidan wanda masu tsaronta suka kai wajen biyar duk da uniform ajikinsu,a wannan karon aminatu ta kasa magana sai zare manyan idanunta take tana basu abinci,sai da aka yi waya ta mintina biyu sannan aka buɗe musu wawakekiyar ƙaramar ƙofar gidan security guda daya shi ya ja gorancesu zuwa cikin ainahin gidan. A bakin kofar shiga falon ma wani security ne a tsaye kamar gunki, shi dai bai ce dasu komai ba saboda yaga amintaccen security gidan kuma ogansu ne ya rakosu,tsayawa aminatu ta yi tana kallon kanta a jikin mirror ɗin kofar glass ɗin har dai ta kasa daurawa ta kai hannu tana shafa kanta tana washe fararen hakoranta wanda da ace na yi musu wankin da ya kamata da sai mutum yaga fuskarsa a cikinsu,wayyo Allah innawuro kina kallona kuwa na zama biyu amma dai wannan ba mudubi ne irin na riga ba ko?" Security ne ya daka mata tsawa "You Are very stupid, wuce muje village girl" tura baki aminatu ta yi tana cewa "Allah dai yasa ba za a yi min ƙaryar turanci ba kai da na ka ma turancin na kafuraine Ni ko nawa na musulmai ne ehe" ta fada cikin gwamutsa fillanci da Hausa kasancewar sun iya hausa saboda zaman rigage da su kayi,harara security ya zabga mata yana jin kamar ya sa ta tsallen kwado yaga ƙaryar sakarci to matsalar bai san matsayinsu wajen masu gidan ba dan haka yayi kwafa tare da ci gaba da ƙamewarsa oganne ya basu umarnin su shiga su zauna yanzu me gidan zai fito. Suna shiga falon aminatu ta tsandara ihu tare da maƙalkale innawuro jikinta na karkarwa kana ganinta zaka san cewa tayi matukar tsorata, larai ce ta fara fitowa da gudu daga kiching tana salati su Anne da Nana kuwa duk suna sashensu amma duk da haka sai da suka jiyo ihun aminatu da har zuwa yanzu ta ƙi yin shuru kuma ta ƙi sauke ƙafarta ƙasa sosai ta maƙale innawuro har tana neman kayar da ita. Larai da take musu kallon mamaki da rashin sani ta ce "lafiya bayin Allah daga ina ita kuma wannan me yasa Meta a ƙafar?" Ta jera musu tambayoyin duk a lokaci guda,kafin su samu damar bata amsa suka jiyo Muryar Abby Yana cewa "baƙin gidan nan ne larai" oho ai banshina ba Alhaji" ta fada cikin nuna biyayyarta,Muryar amunatu ce ta karaɗe falon da kororotarta,dan Allah innawuro ki taimakeni zan faɗa cikin ruwa dan Allah bana so na mutu ban ga ɗan birni ba dan Allah baffa ku kawo agaji" dariya ce ta kufcewa nana da itama ihun aminatu ya fito da ita Abby ma dariya ya shiga yi ita kanta larai aminatu ta bata dariya,larai ce ta matsa kusa da aminatu cikin rarrashi ta shiga ce mata ,"kwantar da hankalinki ɗiyata ba ruwa ba ne wannan baki ga duk mun taka bamu nitse ba" sai alokacin amunatu ta kula suma duk suna wajen ba su hau saman katifar dake shimfiɗe tsakiyar kogin ba,ajiyar zuciya ta sauke kana ta ɗira a hankali cikin sanda kamar ɓarauniya sai da ta tsaya sosai taji bata nitse ba sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya tana cewa aradun Allah kuwa ba kogi ba ne,to bari na yi sauri na hau kan wannan katifar dan da gani zata yi laushi" dariya suka kuma yi gaba ɗaya sannan suka zazzauna innawuro da baba wuro suma zama su kayi a kan katifar, nana ce ta ce a'a "ku ai da kun zauna saman kujera ko?" Da sauri amunatu ta ce a'a ki rabu da su suma su ɗata katifar birni kafin ɗan birni ya dawo ya siya kana irinta saboda shima dan gayu ne sosai sannan kuma ai saman innawuro zata iya faɗowa ko innawuro?" Innawuro ta ce haka ne boɗɗo nima ina son ɗana wannan katifar gata ko da dan banzan laushi" murmushi nana da Abby su kayi saboda dramar innawuro da jikarta [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ **Pg8* Larai ma wucewa kiching ta yi tana dariya tare da mamakin daga ina aka samo waɗannan yan ƙauyen fitik da ala ma ma basu taba shigowa birni ba. Cikin girmamawa innawuro ta gaida Abby da nana,ita ko aminatu babu abinda take sai kalle kalle da taba abinda taga zata iya daga inda take dan gaba daya hankalinta ba akansu yake ba,Abby dai sannu da zuwa yayi musu tare da bawa larai umarnin da ta kaisu ɗakin da tun jiya ya ce ta gyara,larai bata taba tunanin cewa yan aiki za asaka a wannan dakin ba sai yanzu da yake bata umarni, amsawa ta yi tana mai jin jina girman zahida a ranta dan tasan duk wannan karramarwar da a ka yiwa su aminatu sabida ita ne da kuma danta tilo zasu raina,dan haka itama sai ta karbesu da girmamawa. Da kyar larai ta kama hannun aminatu suka bar falon saboda gaba daya ta ƙi kallon hanya tsabar rikicewar da ta yi wajen kallon kayan alatun da bata taba gani ba a rayuwarta. Baffa wuro kuwa nutsuwa ya kuma yi burinsa kawai yaji dumus,amma sai yaji Abby Yana kiran wannan security din a waya,cikin sakan kuwa sai gashi ya shigo. Abby ya nuna masa baffa wuro yana cewa "kaishi masauki ya huta" daga haka ya miƙe ya bi bayan Nana da ta bar falon itama,ran baffa wuro bai so ba ya bi bayan security din dan a so samunsa ne a cika masa jakarsa kawai ya ware. Tunda suka shiga ƙaton ɗakin aminatu ta gama rikicewa, cewa take innawuro wai ko aljanna baffa wuro ya kawo mu ne? Kai Allah ka kwararawa baffa wuro albarka" ita kanta innawuro baza ido kawai take tana bawa idonta abinci,wani abun ya birgesu wani ya basu tsoro da mamaki. Ita dai larai dariya kawai take yi, sai da taga abin nasu bana kare ba ne, sannan ta ce to" aminatu ga banɗaki makewayi shiga ki yi wanka kafin nan na kawo muku abinci idan kin fito sai innar taki ta shiga"a'a ba sunanta Inna ba sunanta innawuro" aminatu ta fada tana shafa bangon dakin da take kallon kanta a ciki,girgiza kai larai kawai ta yi tare da barin dakin. Daƙyar aminatu ta bar SHIRMEN da take yi ta shiga wurin da aka nuna mata matsayin makewayi. Larai na daga can kiching nana kuwa tana saman Abby,sai Anne da ke Hakimce a falo ita da suhaima da bata jima da shigowa ba,ko wannensu a firgice ya baro inda yake zuciyoyinsu na bugun tara tara sakamakon aminatu da innawuro da suka fito daga dakin da aka kaisu da mugun gudu aminatu ajiƙe sharkaf da ruwa tana diga kamar an tsamota daga kogi. Larai ce ta rike ta tana tambayarta me ya sameta,amma ta kasa magana sai tsalle take tana nuna hanyar dakinsu,tsawa Anne ta daka mata kana ciki rashin daukar raininta ta ce "wannan wane irin sakarci ne ana tambayarki kin kasa bawa mutane amsa?" Kuka Aminatu ta kuma ɓarkewa da shi dan sam ita a tsawon rayuwarta bata san me ye tsawa ba shi yasa take tsoratata,Nana ce ta dubi innawuro cikin nutsuwa tace,"me yake faruwa ne?" Sai a sannan innawuro ta iya magantuwa da cewa "ey kam Nima bana ce ga abinda ya faru kai tsaye ba sai dai nasan ina zaune ina jiran boɗɗo ta fito daga makewayi sai kawai na ji tana kwala min kira kafin naje inda take sai gata ta fito a yadda take dinnan, sai kuma ƙarar tafiyar kogi da naji a cikin makewayin" suhaima ce ta yi saurin shiga dakin jim kadan sai gata ta fito tana ƙyalƙyala dariya," ke kuma lafiya kike dariya sai kace sabon kamu?"cewar Anne dake fusace da wa ɗannan ƴan ƙauyen da aka kawo musu,suhaima ta ce "wallahi Anne ko ke ki kaga abinda ya korosu sai kin yi dariya ruwan shayar sama ne fa ta kunna"annen dai ba tai dariya ba sai nana da lralai da suka murmusa,cikin tura ƙaramin bakinta aminatu ta ce, "ina shiga makewayin banga ruwan wanka ba daga ina dan taba wasu ƙulalai da na gani a jikin madubin makewayin(tana nufin bangon tiyals din bandakin da suke masu sheki kamar zaka ga fuskar ka aciki)sai kawai naji an barke da ruwan sama,da na dauka ruwan Allah ne sai da na ɗaga kaina naga ta inda ruwan yake zubowa a rufe sannan na gane wani siddabarunne shi yasa na gudo" . Kama hannunta larai ta yi tana cewa "laifina ne da ban tsaya na nuna muku yadda kome yake ba zo muje na nuna muku"nokewa aminatu ta yi tana cewa Ni ba zan yi wanka ba na fasa aradun Allah ba zan je ruwa ta tafi dani ba" wa ya ce Miki kogi ne?" Inji suhaima da dramar innawuro da jikarta ta fara burgeta,Anne tsaki ta yi tabar wajen dan bazata iya jure ganin kayan haushi ba,Nana ce ta kama hannun aminatu da kanta, aiko aminatu bata yi mata musu ba ta bita suka koma cikin dakin ganin zasu kuma komawa bandakin yasa aminatu ta ɗan fara nokewa, lallaɓata Nana ta yi ta jata har cikin bathroom din abin mamaki sai ga Nana ta zage da kanta ta cude aminatu tayi mata wankin babban bargo tun daga kanta har zuwa ƙafafunta da duk wani guri da yake bukatar tsafta, aminatu har kuka ta yi saboda wankin da tasha cewa take "wayyo Allah gaɗɗafi yau an rama maka muguntar da nasa aka yi maka Allah yasa ka huta gaɗɗafi",Nana dai bata kulata ba sai da ta gama wanke ta tsaf ta daura mata towel sannan ta yi mata brosh wanda shima daƙyar ta bari aka yi shi, suna fitowa Nana ta bawa innawuro umarnin da ta je itama ta yi wankan,dan ita ma ta haɗa mata ruwan wankan Tsaf Nana ta gyara aminatu tamkar yarta, sai ga aminatun innawuro ta fara komawa kalar birni a cikin mintinan da basu gaza na awa daya ba, sai da Nana ta tabbatar ta gyarasu sun koma kalar da duk iyayin Dr zahida bazata kushesu ba a dai yanayi na yan aiki, sannan ta fito daga dakin,larai kuma ta kai musu abinci. Cike da jindadin mutuntawar da Nana da mutanen gidan suka yi musu innawuro ke saka lomar daddan abincin da aka kawo musu,ita ko aminatu bata ji wani abu dabanba tunda a ganinta kowa ma yana da kirki kamar ƴan rigarsu da suke tamkar ƴan uwan juna. Sai da suka ƙoshi sannan aminatu ta fara tunanin ta inda zata fita daga wannan ƙaton gidan dan taje ta zaga gari kamar yadda ta saba a riga ta tsokani na tsokana ta lakaci na lakata,mikewa ta yi tare da kallon innawuro kana ta ce "innawuro "ki zauna a nan bari na dubo ko baffa wuro ya tafi"innawuro ta ce "a'a boɗɗo ki hakuri da wannan shegen yawon naki ba ganin wuro zaki yi a gidan nan ba, dan wannan gidan yafi rigarmu da dajin dake kewaye damu girma idan kuma kika bata kinwa kanki babu ke babu ganin dan birni". Ɗan jim aminatu ta yi tana nazari kafin ta ce "to amma zan dan fita iya wajen nan me kyau da muka fara tararwa "innawuro ta ce idan katifar kikewa ba ga wata anan ba" kallon ƙaton gadon da innawuro ke nuna mata ta yi sannan ta yatsuna fuska ta ce "innawuro wannan yayi tudu da yawa kuma bai kai taushin wancan ba" daga haka ta fita daga dakin ba tare da ta saurari kiran da innawuro ke yi mata ba. Duk irin bajakolin kayan dadin dake gabansa ji yayi yafi bukatar a sallame shi da dukiyarsa idan yaso duk ya siya wannan daga baya,yana cikin tunanin za a bashi ko ba za bashi ba taraddadin ƙila wa ƙala dake sawa zuciyarsa na harbawa fiye da yadda ta saba harbawa,motsin shigowar da ya ji yasa shi maida hankalinsa ga me shigowar. Abby ne ya shigo hannunsa dauke da wata leda me kyau, zama yayi kan daya daga cikin kujerun dakin kana ya ce da baffa wuro,"wuri ka kwantar da hankalinka zuwa gobe zamu sallameka ka tafi duk inda kake so ga wannan" ya fada yana mika masa ledar da ya shigo da ita,duban ledar baffa wuro yayi cike da nekan ƙarin bayani, jinjina kai Abby yayi har da dan murmusawa kana ya ce "wannan maganin wartsake gajiya ne anjima idan kazo kwanciya sai ka sha zaka ji ka tashi garau da kai" karba baffa wuro yayi amma ba dan yana jin zai sha ba dan shi ba mahaukaci ba ne babu wanda ya isa ya yaudareshi,duk da Abby ya fahimci baffa wuro bai yarda dashi ba amma bai nuna masa ba baya ga sallama da yayi masa ya fice. Tunda aminatu ta samu ta fito daga dakinsu Allah ya taimaketa ta samu wata hanya ta bi ta can take ta zagaye gidan kamar gidan ubanta duk abinda ta gani sai ta taɓa ta kuma yi sharhi a kansa, har wajen daf da sallar magriba tana abu daya, a kokarin ta na komawa cikin gidanne ta bace sai ganinta ta yi a wani kayataccen gardin wanda ita ta kiransa da aljanna, murtsuke idanunta ta yi tana kuma ƙarewa lambun kallo tana cewa "ikon Allah yau ga aminatu a aljanna ashe ma aljannar ba sai an mutu a ke zuwa ba dama innawuro Sharota kawai take yi idan ta samu sanyin waje aiko innawuro tunda kika yi min ƙar ......au ance manya basa ƙarya ta fada tana mai saurin rufe bakinta,. Ci gaba da shigewa ciki ta yi har dai ta karaso wani kebantaccen wuri har da ruwa ke zuba kamar ƙorama,daga can ɗan nesa da ita ta jiyo Muryar Abby Yana cewa KARKU damu ku kwantar da hankulanku ko me zai tafi daidai da tsarinmu" . Juyawa ta yi da sauri ta ta bar gurin tana cewa bari na yi sauri na je na gayawa innawuro itama ta zo ta ga aljannar har da mutanen aljannar". Daƙyar aminatu ta fiddo kanta daga inda ta kai kanta, a filin ƙaton gidan ta ganta wanda shima sai da ta tsaya ta yi nazari sannan ta fahimci ƙofar da aka shiga dasu ɗazun. A dai-dai lokacin Dr zahida ta sako hancin motarta da wani matsiyacin gudu wanda in da sabo kowa ya saba da halinta a cikin gidan,fitowa ta yi kamar yadda ta saba tana famana shan ƙamshi da yagutsa fuska kamar taga kashi, kai tsaye ta nufi hanyar da aminatu take tsaye a bakin wajen ta rasa ta yadda zata yi ta bude kofar saboda yanzu ba security a wajen,wani irin burki Dr zahida taja lokacin da tayi kacibis da aminatu a bakin kofar, "hou are you" zahida ta fadawa aminatu cikin tsawa, toshe kunne aminatu ta yi hade da runtse ido duk a lokaci daya, cak zahida ta tsaya tana ƙare mata kallo cike da ƙyama da wata irin haddasa, a rayuwar zahida ta tsani taga wamda ya fi ta kyau ilmi ko ƙwarewar aiki yanzu zata ji ta tsani mutum. Shi yasa take taji tsanar ƙaramar yarinya me shekarun da ba za su haura sha hudu ba wadda bata taba gani ba kuma bata san daga ina tazo ba.jin shuru ya ratsa wajen yasa aminatu ta buɗe manyan idanunta da suka kuma firgita kwanyar zahida, ganin matar har yanzu tana mata kallon da ita bata san wane kala ba ne yasa ta tura ƙaramin bakinta tana cewa "yo Allah yasa dai aminatu ba jahila ba ce itama ta iya turancin nan bare ayi mata burgar banza dashi"cikin mamaki zahida ta kuma ƙure Aminatu da kallo kafin cikin wata irin ƙufula ta ce " ke dan ubanki wa ya kawo ki gidan nan me kika zo yi ke ƴar gidan uban waye ne?" Kai_kai_kai kika zage Ni malam buba fa ya ce babu kyau zagi shi yasa ya hanamu amma ba dan haka ba da na ce miki sai dai ubanki ba dai ubana ba" wani irin kukan kura zahida ta yi zata yi kan aminatu amma sai oga mus ab ya tari gabanta ya zamana yana tsakiyarsu ya juyawa aminatu baya yana fuskantar zahida. "Ai ban zageki ba se ki bari na zageki sai ki buge Ni" aminatu ta faɗa tsakaninta da Allah,gadan-gadan zahida ta kuma yin kanta mus'ab ya riƙeta yana watsa mata kallonsa da shi kadai ya isa hukunta mutum. Riƙe baki aminatu ta yi cike da mamaki ta ce" tab wannan ai iskanci ne namiji ya riƙe mace ko da yake babu ruwana dadin taedai walakiri ba gajiya da jibga yake yi ba". Daga haka taga larai ta bude kofar dan haka ta fada ciki a guje ranta fes ba tare da wata damuwa ba. Na kusa gama free Pg a yi kokari a yi payment 8064537048 opay Fatima yushau adam Shaidar biya. 08064537048 Sai naji ku🙏🏻 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: MATAR ƊAN BIRNI ❤️ **Pg9* "Ka rabu dani naje na taka wuyan wannan banzar yar ƙauyen kuma wallahi ko wacece yau sai ta bar gidan nan mara kunya har ta isa ta zage Ni ta zauna lafiya a cikin gidan nan"sakin ta yayi ba tare da ya ce mata ko mai ba ya wuce dama masallaci zai tafi yaga tana shirin haiƙewa yar mutane duk da cewa bai kalli ko wacece ba amma yasan yarinya ce ƙarama ko ya ce matashiya,sai dai wani abu guda da yatsaya masa a rai shine Muryar ta, Muryarta tayi masa kama da wata murya,amma dan kar tunanin hakan ya bijiro masa da tsohuwar damuwarsa sai kawai ya ya kiceta ya shiga bautawa Ubangijinsa da ƙadaiceshi a lokacin da yake gabansa. Zahida kuwa duk da cewa kallon gargaɗin mus'ab ya shigeta hakan bai hanata shiga falon a fusace ba. Ita ko aminatu ba tare da tsaya tantance wanda ya kawo mata dauki ba ta fella da gudu cikin falon, anan ta samu innawuro idanunta sun yi luhu luhu alamun dai kuka tasha,Nana ce ta ce " ke ko aminatu ina kika shiga duk kika tayarwa da mutane hankali dubi kakarki tun dazu take kukan rashin ganinki?" Dan gunguni aminatu ta yi kafin ta ce "to bana gaya mata zanje ganin gida ba, wa zai iya bacci a wannan ƙaton gidan ba tare da yasan kansa ba"shigowar Dr zahida ne ya dau hankalinsu saboda yadda ta shigo a mugun fusace, "nana wannan ƴar ƙauyen wa ya kawota cikin gidan nan har take da bakin zagina?" Zagi kuma?" Nana ta fada tana maida dubanta kan Aminatu da ta kafe bakin zahida da ido tana kallon yadda take magana kamar ana mata dole. Tura baki ta yi tare da kawar da idanunta daga kallon zahidar sannan ta ce "Nifa Dada ba zaginta nayi ba ita ta zage Ni shine nace badan malam buba ya hanamu zagi ba da sai na rama"sai kuma kika yi zagin ba ke wallahi yau ko yar gidan uban waye ke sai kin bar gidan nan" zahida ta fada tana tunkaro aminatun gadan gadan. "A'a dakata zahida" Abby dake shigowa falon ya fada yana shigewa cikin wani ƙawataccen falon bayan wanda suke ciki, sai da ya kai tsakiyar falon sannan yayiwa zahida alamun da ta karaso,ba dan ranta yaso ba ta hakura da fitar da aminatu daga falon ta wuce kiransa,gaba dayansu ajiyar zuciya suka sauke nana ta ce su wuce su koma daki su kwanta su huta sai gobe zasu fara aikinsu sannan sun dan huta. Larai kuwa a ranta cewa ta yi Allah ya taimake mu yau da mune muka kawo bakin da ba zasu kwana cikin gidan nan ba. Duk abinda ke faruwa Anne na jinsu Amma ta tafasa ba tace ba kai ka dauka bata gurinne. Ko Ni ban san me Abby ya ce da zahida akansu aminatu ba, amma dai tabbas bayan cewar su din masu raino ne akwai wani sirri da ya tattauna da ita wanda haka ne kaɗai zai sa zahida ta yi hakuri da zaman su aminatu a gidan ba tare da ta tada rigimar a canja mata su ba. Oga kwata kwata kuwa bai san duk wannan rigimar da ake yi ba hasalima bai tsaya sauraren batun da muhimmanci ba. Tunda aminatu ta baje saman gadon bacci ya kwasheta ba ita farka ba sai da gari yayi tangararan, hamma aminatu ta yi tana cewa innawuro dake zaune kasa kasan sallaya tana lazimi, aradun Allah Baccin yau yafi na kullum daɗi Ni da nake tashin asubahi amma yau sai da gari yayi tangaran yan birni suna jin dadinsu"harara innawuro ta watsa mata kana ta ce "da baki tashi kin yi sallah ba ruwan sanyi zan watsa Miki se ki tashi da hujja"a hankali aminatu ta zura yan tausasan ƙafafunta farare tas da suka sha wankin Nana ƙasa ta miƙe maimakon ta wuce bayi kai tsaye sai kawai.ta nufi wajen kwanukan abin karin da larai ta kawo musu ta fara bubbuɗewa tare da buɗe kofofin hancinta tana shaƙar ƙamshin soyayyun kayan dadin da aka kawo musu. Sai da innawuro ta korata da carbi sannan ta shige bayin tana ƙunƙuni "wai ita sallar nan kullum sai anyi ta ne ba a hutawa?" Innawuro ta ce boɗɗo idan na barki kina hutawa da Sallah gaba ko ta hau kanki baƙar wahala zan sha Gara ki saba tun yanzu duk da yanzun ma ina shan wahala". Ƴar faki ba yawa se lada sunan sallar aminatu kenan ana farawa aka idar,kai tsaye wajen kayan karin da suka hanata sakat ta nufa ta baje a gabansu, tana ci tana shafa kunne tare da lumshe idanunta kai kana kallonta kasan cewa dadin yana kai mata can inda ya kamata. Innawuro babu shiri ta katse laziminta dan taga alamun aminatu kwanuka take shirin bar mata, sai da suka ci suka ƙoshi sannan suka bar saura dan duk haɗamar aminatu sai da ta hakura, dai-dai nan larai ta shigo suka gaisa da innawuro dan ɗazu da ta kawo musu karin kumallo innawuro tana sallah.duban aminatu ta yi ta ce to aminatu sai ki shiga kiyi wanka ki fito ga kaya nan na kawo muku idan kun gama sai muje a gabatar da ku wajen iyayen yaron da zaku kula dashi",zaro ido aminatu ta yi kafin ta ce "a'a nifa wankan da Dada ta yi min jiya na sati biyu ne, yo i dan ma nayi wankan yanzu me zan wanke?" Ta fada tana cino karamin bakinta, rike haɓa larai ta yi kafin ta ce to ai shike nan idan kika tara daudar ta kuma yi miki amma ki sani gidan nan basa shiri da ƙazami" daga haka ta fice daga ɗakin, innawuro ta ce ki daure boɗɗo ki ɗan yi ko yaya ne kin dai ji abinda ta ce" wallahi innawuro ba zan yi ba har yanzu fa fatata zafi take yi jikina tas yake bari kawai na canja kayan sai suga kamar nayi wankan" haka kuwa akayi kaya ta canja innawuro ma ta canja sannan suka fito,suna ci gaba da ƙarewa loko da saƙon gidan kallon da basu yi masa ba jiya. Duka mata da mijin a matse suke da su bar gidan amma Abby ya tsaidasu akan sai sun tsaya 'yan aikin sun san su waye uwayen gidansu,zahida dai sai ƴan gunguni take yi shi ko gogan ko a fuska bazaka gane yanayin takurar da yake ciki ba, fuskar nan a haɗe na ba yabo ba fallasa idanunsa dake sanye da farin glas suna kan tap din dake hannunsa yana taɓata kamar yana taɓa kwai. Aminatu na doso falon ta fara raba idanunta dan son ta gano wanda yasa irin ƙamshin ɗan birnininta, sai dai bata ga kowa ba sai mutanen gidan da kuma wani da ban da bata gansa a jiya ba, duk da cewa yanzu kansa a sunkuye yake ba a ganin fuskarsa sai kwantacciyar sumarsa baƙa siɗik me tsananin sheƙi,idanunta ta tsayar akansa tana kallon sumarsa da kuma tuna waccan ranar da innawuro ta yi mata bukulun ganin fuskar ɗan birninta, zaunar da ita innawuro ta yi ganin taƙi zama kuma ta kafe bawan Allah da ido, duk da cewa ita kanta innawuro sai da taji wani abu game da ganin wannan kamammen mutum. Muryar zahida ce ta dawo da aminatu cikin hayyacinta, Abby ni dai Allah yasa ba Mayu ka kawo min su reni dana ba ina tsoron kar su cinyesa" mu ba Mayu ba ne sai dai in ke ce mayya" aminatu ta faɗa kanta tsaye ba tare da tsoro ko shakka ba,zahida zata yi magana Abby ya hanata,ba dan taso ba ta yi ƙwafa tare da kwantar da kanta jikin kujerar da take kai. "MUS'AB" Abby ya Kira sunansa ganin bai da alamar bashi hankalinsa,ba tare da ya amsa ba ya ɗago lumsassun idanunsa ya zuba su saman fuskar Abby wanda hakan ke nuna alamun amsawarsa a bayyane,sanin halinsa yasa Abby bai damu da rashin furtawar tasa ba dan haka ya ci gaba da cewa, "wannan sune zasu ci gaba da kula da Khalid shi yasa nace ku tsaya na gabatar muku dasu a matsayinsu na wanda zasu ci gaba da kula da ɗanku" .a hankali mus ab ya maida idanunsa ya lumshe ba tare da ya ce ko mai ba, muryar aminatu ce ta sashi buɗe idanunsa ya zuba su a saman kananan lip ɗinta da take zuraro zance dasu. "Taɓ Nima fa har yanzu innawuro rainona take yi bare kuma Ni na raini wani ɗan da dai cewa kayi innawuro ita kadai Ni kuma na samu abokin wasa" ta faɗa tana washe haƙoranta da suka zama farare a jiya ranta fes ta samu abokin wasa, murmushi Abby ya yi tare da cewa "haka ne ɗiyata mantawa nayi na sa dake"tsaki zahida ta yi tare da miƙewa tana cewa "Abby zan wuce kasan yau ina da important tiyata babu amfani zaman sauraren wannan rubish girl ɗin" , harara aminatu ta watsa mata tare da cewa muma dai muna jin turancin barantana a zage mu ba mu sani ba, I wish wisss fan to be fairrys" itaka tayi mata nata turancin tana farfara manyan idanunta,dariya Abby da suhaima da ke shigowa ita da Khalid suka saka shima kansa Khalid sai da ya yi dariya, a nitse ya kalli aminatu ya ce,"ba haka ake yin turanci ba ki bari zan koya miki se kema ki dinga yi ko?" Da sauri aminatu ta miƙe ta koma kusa da Khalid ta ce ina so kai ne wanda innawuro zata ci gaba da renonmu tare"?jin jina kai yayi duk da bai fahimci inda zancen nata ya nufa.. Duk wannan bidirin da ake yi yana nan zaune yana ƙarewa duk wani motsin aminatu kallo ba tare da kowa ya fahimci hakan ba,a take wasu abubuwa da take yi suka fara bayyana masa wacece aminatu, jin innawuro ta kuma ambaceta da boɗɗo yasa shi fesar da wani zazzafan huci yana mai jin wata ƴar nutsuwa na sauko masa duk da dai bai gama tabbatarwa ba ,amma in sha Allah yana fata ace ƙarshen wahaarsa ne yazo Allah ya karbi addu'arsa a lokaci ɗaya, ya kawo masa su har inda yake tabbas Allah buwayi ne gagara iko da misali shi kaɗai ne ya isa yin abinda zato bai taba zato ba, miƙewa yayi tare da yiwa Abby sallama ya fice ba tare da tankawa kowa ba,aminatu kuwa da ƙyar aka rabata da Khalid ta barsa ya tafi makaranta, amma tunda ya faɗa mata lokacin da zai dawo shi kenan ta dami mutanen gidan da lissafi da tambayar agogo. Baffa wuro kuwa tunda ya kwanta Baccin dare bashi ya farka ba sai misalin ƙarfe uku na rana, daƙyar ya iya motsawa yana cike da mamakin dalilin Baccin nasa me tsawon da ya wuce tunani haka,gashi duk tunaninsa ya kasa tuna kome, sai jikinsa da yake jinsa kamar ba nasa ba kai gaba ɗaya ma ji yake kamar bashi ne ba,dan runtse idanunsa ya yi yana jin cikinsa fayau wanda yake da tabbacin cewa yunwa ce,tashi yayi kamar iska zata huresa ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito ya rama sallolinda suke kansa daga nan yaja kular da ya gani ya hau bawa cikinsa hakkinsa,sai da ya gama tsaf sannan ya jingina yana son tuna abinda ya faru dashi. Bai iya tuna komai ba sai mafarkin da yayi ya gansa a cikin asibiti ana farke cikinsa kamar dai tiyata ake masa ko a mafarkin iya abinda ya tuna kenan, ganin zai saka kansa cikin damuwa sai kawai ya share. Shigowar Abby ta kuma katse masa tunanin. Suna gaisawa Abby ya tura masa wata baƙar jaka me madaidaicin girma kana ya ce "ga kudinka nan yanzu ka bar gidan nan amma kafin nan ka fara zuwa kayi sallama da su dan fita daga zargi" washe baki baffa wuro yayi yana leƙe jakar da take cike da kuɗade daloli,ransa fes ya shiga yiwa Abby godiya daga haka babu abinda ya tdaya dauka ya saɓa jakarsa suka fito tare da Abby,ya rakasa har wajen innawuro suka yi sallama tare da yi mata alƙawarin zai dinga zuwa dubasu lokaci lokaci. Daga nan ya bar gidan yana jin farin cikin ya samu arzikin da yayi bankwana da talauci. Tunda Khalid ya dawo daga makaranta suke tare da aminatu har lokacin da malaminsu na islamiyya ya zo, suhaima tuni ta tafi amma Khalid ya kasa tafiya saboda yadda yake cin dariyar labaran rigarsu da su arɗo da take bashi, da suhaima ta takura masa sai kawai yaja aminatu suka ɓoye a wajen da dadynsa ne kawai yake hutawa a wajen,hankalinsu kwance suka kama wasan yar ɓuya,wasa ya juya kan aminatu dan haka ita aka rufewa ido, tana ta faman lalubensa duk runton aminatu ta kasa yiwa Khalid shi yasa ta rufe fuskarta bata ganin kome sai duhu. "Yeeeee na kamaka na kamaka dama kaine kake ƙamshin turaren ɗan birninako?""""""" Free Pg Account number 8064537048 Opay Fatima yushau adam [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg10* Jin kaurin mutumin da ta rungume ya fi kaurin ɗan talili Khalid yasa ta shiga shafa shi dan ta tabbatar Khalid ɗinne ko ba shi ba ne ,amma sai taji wannan fa da ta rungume ba Khalid ba ne dan haka cikin sauri ta janye tare da buɗe idanunta fes suka sauka akan mus'ab da tun da ta riƙesa yaji wani irin dum,saboda jin kalmar da ya fi riƙeta a wancan lokacin(baffanaa ya ce Ni matar wannan ɗan birnin ce ya ce kar na kula kowa in ba ɗan birnina ba dan haka duk wanda ya ce muku yana so na kuce masa Ni matar dan birni ce). "Yeee bata kamani ba daddy ta kama, daddy tunda an kama ka kaine zaka nemo mu yanzu" cewar Khalid da ya fito daga maɓoyarsa ya hango aminatu riƙe da daddynsa, harara MUS'AB ya watsawa Khalid kafin cikin muryarsa me ɗan kauri da amo ya ce " me ya hanaka zuwa daukar karatu?". Rufe fuskarsa yayi yana ɗan raɓe_raɓe na marasa gaskiya,aminatu kuwa tamkar an dasata a gurin ko motsawa ta kasa yi, tunda take babu wani mutum da ta taɓa jin shakkarsa sai wannan santalelen mutum dake gabanta, gaba ɗaya ya cika wajen da wani irin kwarjininsa ,duk hayaniyar aminatu sai gata tsaf a nutse a gabansa tana faman farfara idanunta da take jin suna ƙoƙarin rufewa. "Ke kika hanasa zuwa karatu ko?" Muryar mus'ab ta katse mata yar ruɗewar da ta shiga, abinda ya zame mata al'ada tayi wato TURO bakinta amma bata iya cewa kome ba sai haɗiye zancanta da ta yi a can makoshinta,muryarsa ta kuma ratsawa ta cikin kunnuwanta, "ki wuce kuje tare daga yau tare zaku dinga ɗaukar karatu"daga haka yayi gaba cikin natsatstsen takunsa,binsa ta yi da kallo a ranta tana cewa da ace na taba ganin fuskar ɗan birnina da tabbas zan iya cewa wannan shine, Khalid ne ya kama hannunta yana cewa muje kin san daddyna bai yarda da ƙin zuwa islamiyya ba,idan bamuje ba zamu fuskanci kalar hukuncinsa"kamar kanwarsa haka yajata suka nufi wajen karatun. Dama malam sani tuni an sanar dashi ya samu ƙarin daliba, dan haka cike da ƙwarin gwiwa ya shiga maimaita musu ƙarin dan suhaima tuni ya gama da ita ta wuce gida tunda ba waje ɗaya suke da Khalid ba,kasancewar yanzu ƙarin Khalid yake yi sai bai damu da wasan da aminatu take yi ba,bai juyo kanta ba har sai da ya gama da Khalid sannan ya ɗauko mata ƙarinta tun daga qulhuwallahu wato suratul iklas. Malam sani ya maimaita wa aminatu ƙarin yafi sau dubu amma ita ba ta shi take yi ba, dan abu daya bata tsaya ta fuskanta ba bare ta iya,tsumagiyarsa ya ɗauka ya ɗan kai mata bugu yana cewa "maza biya min ko na zane ki a wajennan"cikin mamaki aminatu ta ke dubansa kafin ta buɗe baki ta ce "me zan biya maka kuma?"shima cikin mamakinta ya ce "karatun da nayi miki yanzu shi zaki biya dan na ga gaba ɗaya hankalinki baya kaina yana wajen wasanki"cikin ƙunƙuni aminatu ta ce "aradun Allah ban iya wannan karatun naka Ni ba haka Malam buba yake mana ba,ya za a yi na iya bayan ka haɗe murya ka tsuketa kamar zaka yi amai ni gaskiya ba zan iya ba idan kana so na iya sai kayi min irin na malam buba", tana gama fadin haka ta miƙe zata gudu aiko malam sani ya ce bai san wannan zance ba dan haka ya ɗauki tsumagiyarsa yabi aminatu da tayi hanyar gida da gudu. A hankali cikin yanayinta na izza ta fito daga motar bayan malam jauro ya buɗe mata,kallon ƙasƙanci ta watsa masa kafin ta ƙarbe takardun da ya ɗauko zai bita dasu ta yi gaba ba tare da ta nemi rakiyarsa ba yau,tana tafe tana duba fayals ɗin dan akwai aiki me muhimmanci da zata yi da su a gida, takaddu ne na manyan kudaɗe, kun san dai mutuniyar taku bata wasa da duk a binda ya danganci shigowar kuɗi.babu zato su kayi wani mugun karo da aminatu da malam sani ya biyo da tsumagiya, gaba ɗaya takardun suka tarwatse wasu ma sun yage saboda yadda aminatu ta gabjeta da ƙarfi kamar ma harda hannu Aminu ta ƙara tana sane, "kan bura ubannan Ni zaki yiwa akuyanci irin naku na ƴan riga, wallahi yau dai ba zan ɗauki asarar nan ta bangaren mahaukaciya dabba kamarki ba dole sai kin biya asarar nan da kika yi min da farashi me girma". Malam sani na ganin haka yayi sun sum ya koma da baya dan duk wanda yake mu amala da gidan yasan wacece zahida da irin rashin mutuncinta da yadda ta maida talaka tamkar kashi,aminatu kuwa bin takardun da ake kira sai ta biya da farashi me girma ta yi da kallo kafin ta ɗauke kanta daga kansu, ta maida gun zahida ,ta ce "wai takardun zan biya tab Allah ya kiyaye takardar da muke kaiwa me ƙosai ta bamu ƙosai shine yau ake nuna min tana da muhimmanci?" Cikin fushi da harzuƙa me haɗe da wani irin tsana me tsanani Dr zahida ta nufi aminatu dan yau bata jin akwai abinda zai dakatar da ita daga sabawa yarinyar nan kamanni,da gudu aminatu ta shige falon zahida ta mara mata baya tana zaginta ta uwa ta uba tamkar yar gidan maguzawa. Dai dai mus'ab yana fitowa daga sashen Abby, ji yayi kawai an cukumeshi ta baya. Da ƙarfi aminatu ta kuma ruƙunƙumesa tana cewa ɗan birni temakeni zata ƙwada min rodi kasheni zata yi" wata irin kara zahida ta saka saboda ganin yadda aminatu ta riƙe mijinta da take so take kishi kamar rai da rayuwa, a rayuwar zahida ko Nana bata so taga ta dafa kan mus'ab bare kuma wata banza kucaka yar ƙauye,take taji numfashi ta na sama da ƙasa yana fizga kamar za a zare shi. Ihun ta yasa duka mutanen gidan fitowa kowa ya yi curko curko yana kallonta tana jan numfashi kamar zata mutu,Nana ce dubi mus ab da yake tsaye kamar an dasashi da aminatu da har yansu take rike dashi tana ta faman cusa fuskarta a mararshi da neman ɗauki matarsa zata kasheta. A hankali ya fesar da iskar da ta cika bakinsa sannan ya fara kokarin raba aminatu da jikinsa, amma da zarar aminatu ta ɗago kanta taga zahida a wajen tan nuna ta da yatsa bakinta na rawa sai kuma maida kanta jikinsa tana kuma maƙalƙesa tamkar mayan ƙarfe. Abby ne ka ɗai ya fuskanci abinda ke rikita zahida dan haka cikin nutsuwa ya kama hannunta tare da zaunar da ita ya bata ruwa tasha, sannan ya shiga tambayarta me ke faruwa?" Cikin wani irin gunjin kuka ta nuna aminatu da mus'ab da ya gaji da tsayuwar ya jingina jikin bango sai hakan ya kuma bawa aminatu damar kwanciya ajikinsa kamar ta samu gadon bononon innawuro."kalli fa Abby idan waccen matsiyaciyar yarinyar bata rabu da jikin daddyn Khalid ba to tabbas zan mutu amma ba zan mutu Ni kadai ba sai dai mu tafi tare da ita shegiya matsiyaciya me idanun Mayu",jin abinda ta ce yasa aminatu ta saki mus'ab wanda sai a lokacin ta fahimci abinda ta aikata, cike da tsoro ta kallesa ta ce" nifa ba ƴar iska ba ce matarka ta ke son kasheni Shi yasa na rike ka" ,daga haka ta yi gaba abinta, shi ɗin ma wucewarsa yayi dan ba zai iya ci gaba da sauraren shirmen zahida ba. Kuka zahida ta Kuma fashewa dashi ganin sun maidata mahaukaciya, cikin kukan ta ce "wallahi Abby na tsani yarinyar nan ji nake kamar na kasheta bana son ganinta dan dai zama da ita ya zame min dole ne amma da tuni na kaɗata rigarsu"lallashinta Abby ya ci gaba da yi har dai ya samu ta daina kukan ta kuma yi haƙuri da dukan aminatu da tasha alwashin yi. Aminatu kai tsaye kiching ta nufa wajen larai,"Inna larai bari na zo nayi miki tabin gihiri", ta fada tana buɗe tukunyar da taga larai ta sauke,larai ta ce "a'a boɗɗo se dai kizo ki koya,shi girkin nana ba sai an ɗanɗana ba da ɗanɗanonsa yazo, da wannan jan maganar da kike ma ai gwara kizo kiching ɗin ki dinga koyar girkin da zaki yiwa ɗan birnin naki tun dai kin san su gayu ba zai barsu su ci abincin ƙauye ba",to zan dinga koya cewar aminatu tana fakar idanun larai ta kamfaci gishirin da ta gani a roba ta zuba, larai na juyowa ta fake da juya mata miyar tana cewa "kai gaskiya larai miyar nan ta zuba daɗi yau su oh oh za a sha daɗi dan ga dukkan alamu bata wasa da ciki dan ga tanan a dunƙule kamar kayan wanki", Dariya larai ta yi tana zuba miyar a cikin kuloli,aminatu ce ta tayata suka jera komai a kan dinnin daga nan ta taya ta suka gyara kiching din.larai ta ce to sai ki daure kije kiyi wanka tunda ɗazu baki yi ba" wai larai in ruwanki da wanka na ne na ce miki wannan dadar wankan sati biyu ta yi min jiya dan haka ba zan ƙara yi ba sai na yi dauɗa", riƙe baki larai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba sai bin aminatu da kallo har ta bar kiching ɗin. Ƙa idar gidan ce in dai mutum yana gidan sai ya fito anci abinci dashi, shi yasa babba da yaro zaka gansa a dinning room ko da mutum ba zai ci ba sai ya zauna a cewar Anne Shi yake kara sawa a fahimci juna idan wani yana da wata damuwa a lokacin za a gano shi a taimaka masa da abinda ya kamata,shi yasa duk iyayin zahida dole take aje jin kanta ta fito zaman cin abinci ,yanzu ma duk yadda take cikin damuwa sai da ta fito cin abincin, dake ita ba ta wasa wajen zubi. Kowa ya hallara sai oga me gayya mai aiki ake jira. A hankali yake saukowa daga upstairs ɗin jikinsa sanye da ash ɗin jallabiya me asalin kyau da tsada, sumar nan tasa a kwance a luf luf fuskarsa ta yi fayau kana kallonsa zaka san cewa ya samu nutsuwar zuciya saboda Allah ya kawo masa abinda yake hanasa nutsuwar har gida, Ba tare da yasha wata wahala ba. Yana zama suhaima ta fara yin saven ɗinsu kamar yadda suka saba. Aminatu na laɓe daga can corridon da zai maida kai ɗakinsu tana leƙensu, babu lomar wand take so tagani sai ta zahida, muguwa yau albarkacinki kowa sai ya ci gishiri". Kamar haɗin baki a tare suka fara kai lomar abincin bakinsu,sai gashi daga wanda yake yin kakarin amai sai wanda yake furzarwa,zahida kuwa har da su amai ta je ta yi a sink din dinning room,mus'ab kuwa runtse idanunsa yayi bayan ya zuba abincin bakin nasa a tissue, gaba daya abincin suka zubawa idanu baran ma Nana da ita tayi girkin Kuma tasan lafiya ƙalau ta baro kiching ɗin, koma dai meye to sai dai in bayn barowarta kiching din ya faru,a tare suka shiga ƙwalawa larai kira, karma zahida ta taji labari da dama jiran ƙiris take yi,da gudu larai ta karaso jikinta na rawa saboda yadda tag zahida na watsa mata kallon rashin mutunci. "Me ya kawo gishiri cikin abincinmu yau kuma?"Anne ta tambayi larai cikin tsarewar gira,bakin larai har rawa yake wajen rantsuwa da fadin cewa bata san ya a kayi ba dan babu kowa a kiching ɗin daga ita sai aminatu ne suka shirya abincin,salati Anne ta saka zahida ta ce" kanbala'i ashe tsuguno bata ƙare ba yau mun ɗebowa kanmu annoba ai da jin wannan batu ma kun san wace ce ke son kashe mu a gidan nan", Kai tsaye zahida ta nufi dakin su aminatu tana kunfar baki kamar zata aro wani bakin,daga dukkan alamu dai yau me ƙwatar aminatu hannun zahida sai ya shirya.dan yadda ta ke a fusacen nan babu wanda ya isa ya iya dakatar da ita daga sumar da aminatu. Free Pg 10 A gaggauta a yi payment 8064537048. Fatima yushau adam Opay [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg11* Aminatu na ganin tahowar zahida tamkar soja a fagen fama ta fara kokarin guduwa, sai dai kafin ta daga ƙafarta tuni zahida ta cafkota,kici_kicin ƙwacewa take amma zahida ta yi ram da ita dan yau ji take sai ta sauke haushin aminatu na kwanaki biyun da ta yi a gidan. A hankali ya dauki tissue ya goge hannunsa da bakinsa kana ya miƙe dan barin falon. Tsayinsa kawai aminatu ta gano ta shiga ƙwala masa kira,"ɗan birni ka zo kar a yi kisan kai a gidanku wallahi wannan ƙatuwar idan ta zauneni bazan ƙara numfashin rayuwa ba"bugu zahida ta kaiwa bakin aminatu sai dai kafin ta cire hannun aminatu ta yi masa kyakkyawan riƙo da siraran haƙoranta masu kaifi,ihu zahida ta saka tana son ƙwace hannunta daga bakin aminatu amma hakan ya gagara dan aminatu bata saketa ba sai da taga ɗan birni na tunkarosu kamar namijin zaki. Da sauri ta sake hannun zahida tana faman rarraba baƙar ƙwayar idanunta akan kyakkyawar fuskarsa da babu ko ɗigon annuri bare ka sa ran samun sassauci daga garesa,kuka zahida take yi kamar ranta zai fita dan kuwa ba ƙaramin zafin cizon nan taji ba dan har shedar haƙoran aminatu sai da suka fito,wanda take da tabbacin cewa da bata saketa ba tabbas sai jini ya ɓullo. Aminatu kuwa ganin yadda ɗan birni ya tunkarota a fusace, sai kawai ta rushe itama da kukan tana kiran innawuro da ke can ɗaki tana laziminta hankali kwance,kafin ta samu damar guduwa ya damƙi hannunta tare da janta. Ɗif zahida ta yi daga kukan da take yi tabi hannunsa da yake riƙe da na aminatu da kallo ƙirjinta na bugun goma goma,"na shiga uku mus ab me kake shirin yi ne?" Bai bata amsa ba sai tafiya da ya cigaba da yi da aminatun riƙe a hannunsa,shan gabansa ta yi idanuta cike da Bala in wutar kishi ta ce"mus'ab sake ƴarinyar nan idan ba so kake zuciyata ta kama da wuta ba kasan dai sarai halin zuciyata sam bata da sassauci indai akan kishinka ne,mus ab bazan lamunci ganin hannunka akan wata ƴa mace ba in dai ta wuce suhaima dan haka ka sake yarinyar nan tun kafin na illatata". "Mus ab sake aminatu ta koma ɗakinsu kowa yayi hakuri nasan hukunci zaka yi mata amma kayi hakuri" wani kallo yayiwa Abby dake maganar,kafin cikin muryarsa me amo da kwarjini ya ce, "Abby aminatu amanata ce dan haka daga yau bana bukatar hannun kowa akanta",daga haka ya figi aminatu suka yi sama ba tare da ya kuma duban kowa ba,wani irin kallon da ba kowa zai fahimta ba Abby ya bi mus ab da shi yana mai nanata kalamansa akan harshensa tare da wasu irin tunani yana mai son fassarasu sai dai abin ya ci tura domin bai fuskanci komai ba daga kalaman ɗan nasa. Ihun kukan zahida ne ya dawo dashi hankalinsa kokarin bin su take yi Abby ya riƙeta, cikin fitar hayyaci take nunawa Abby hanyar da suka bi tana cewa, "Abby duba fa Ka gani tafiya yayi da ita me zai yi da ita ina zai kaita? wayyo na shiga uku wallahi sai na kashe yarinyar nan rayuwata zata huta,kamar Ni ace mus ab ya riƙe hannun wata mace a gabana",suhaima da ta gaji da hayaniyar ta ce "wai aunty Zahida me yaya mus ab zai yi da aminatu ƴarinyar da sai yanzu ta fara ƙirgar dangi gaskiya kin raina mana yaya wallahi"..buge bakinta Anne ta yi tana mai kwarara mata harara daga nan ta bar teburin tana bawa larai izinin ta kawo mata fruet, Nana ma tashi ta yi ta nufi bedroom ɗinta tana yiwa ɗanta addu'ar samun mafita. Ganin kowa ya watse ya barsu yasa Abby zaunar da Zahida kana ya fara rarrashinta, wanda shi kansa da zai samu me rarrashin nasa da zai so haka, matarsa da take da damar rarrashinsa bata san komai akan sirrinsa ba bare ta fahimci damuwar da yake ciki.da ƙyar ya samu kan zahida ta tafi ɗakinta, amma fa zuciyarta cike taf da burin ɗaukar fansa akan ƙaramar yarinya me Shekaru sha hudu zuwa biyar. Son fuzge hannunta take amma hakan ya gagara, bai tsaya da ita a ko ina ba sai wani ƙaramin ɗaki me kyau kome da akwai a cikinsa, hatta da gadonsa ɗan ƙarami ne gwanin sha awa, sai wasu tarin littafai irin na ƴan aljanunnan masu rubutu manya manya,da ƙarfi aminatu ta fincike hannunta ta nufi tsakiyar ɗakin cike da maɗaukakin farin ciki tana wani irin juyi da yake nuna tsananin jin dadinta, littafi ɗaya ta ɗauka ta buɗe kai kace wata professor ce, manyan rubutun da ta ci karo da shi farkon littafin tare da ƴaƴan teddy yasa ta ƙyalƙyale da dariyar farinciki tare da zama bakin gadon ta ɗauki ƙafa daya ta ɗora kan ɗaya,ta fara zuba karatunta na professor's. Lokacin da aminatu ta fizge daga hannunsa,sai kawai ya jingina da kofar dakin ya harɗe hannunsa a ƙirji yana bin duk wani motsinta da ido,ware manyan idanunsa da yau bai sakayasu cikin glas ba yayi lokacin da ya ci karo da zazzaƙar Muryarta tana zazzago turancinta na ƙwararru Wanda a yanzu take ji ta kuma kere sa'a tunda ta kuma tsintar kalmomin turanci a bakin masu gidan da kuma Khalid da yake son yi mata magana da turancin tun da ya ji tana kwamacalar nan. Aminatu kuwa hankali kwance cikin bayyanannan nishaɗin da yake shimfiɗe saman kyakkyawar fuskarta ,ta ke karanta littafinta."soptiwe don't worry is berry and ginger and shuger banana my tanks we me and you" ta kuma karkatar da kai irin fa tana jin dadin yadda take suburbuɗa turanci ba tare da ta yi kuskure ko ɓatan wasali ba,ganin abinnata ba na ƙare ba ne yasa shi juyawa zai bar ɗakin sai dai kafin ya saka ƙafarsa a wajen yaji aminatu a bayansa cikin karkarwa da tsoro ta runƙumesa tana cewa,"na tuba karka barni a nan tsoro nake ji ka mai dani wajen innawuro"kasa motsawa yayi saboda riƙon mutuncin da ta yi masa, numfashi ya ɗan fesar kana cikin nutsuwa ya dinga juyowa har suka fuskanci juna duk da haka bata yi gangacin sakinsa ba" daɗinta ma walakiri ba gajiya yake yi ba"ya faɗa cikin taushin muryarsa me haɗe da wani salon hausa, wani abu aminatu taji ya tsira mata kamar tashin tsigar jiki amma bazata iya cewa ga ma'nar hakan ba,ya ci gaba da cewa "ba haka kika ce ba ran nan da na kama matata to ke kuma me za a ce miki tunda kin riƙe mijin da ba naki ba?" Ya yi maganar kamar bashi yayi furucin ba,tura ƙaramin bakinta ta yi kana ta ce Ni ai yarinya ce" shi yasa zaki riƙe babba mijin wata kina tumurmusheshi a garinku hakan dede ne ko kuma a can ma haka kike riƙe kowa idan kina neman tsira?" Ya watsa mata tambayar yana mai jin fargaban amsar da zata bashi ba tare da yaji yana da dalilin yin tambayarba,a maimakon ta sake shi saboda abinda ya fada a'a sai ma ƙarfin riƙon da ta kara tana cewa "ai su basa ƙamshi kuma basa gayu dan haka jikin innawuro na kawai na ke maƙalewa idan anbiyoni" ta yi maganarta hankalinta kwance,mirza goshinsa ya yi a ransa yana cewa ina da babban aiki a gabana fa,hannunta ya kama ya cireta daga jikinsa yana cewa daga yau anan zaki dinga zama komai naki yana cikin nan kayan sawa da kome duk zaki samu, idan kuma kika kuma takalar waccan matar duk abinda ta yi miki babu ruwana" ƙwalƙwal ta yi da idanunta za ta fara kuka yayi saurin ɗora yatsansa saman tausasan lip dinta yayi mata zeepin ɗinsu,dole ta haɗiye kukanta dan kuwa a hakikanin gaskiya wannan ɗan birnin ba ƙaramin kwarjini da tsoro yake bata ba,tana ji tana gani ya fita ya barta ita kadai a ɗakin tana ta rarraba idanu cike da ƙwallar da tsoron hukuncin dan birni ya hanasu zubowa. A tsorace ta kwanta saboda ta gwada guduwa amma taji ƙofar a rufe,saboda tsoro ko bayin ta kasa shiga duk fitsarin da take ji haka ta fiske tayi kwanciyarta. A shirye ya fito tsaf gwanin kyau da burgewa kai ka ɗauka wani ɗawisune saboda tsabagen iya wanka da yadda yake yiwa kaya kyau sajennan ya kwanta yayi luf baƙi siɗik dashi sai sheƙi yake yi,kamshinsa gaba ɗaya ya riga shi bayyana a wajajen da ba ma nan ya nufa ba,kai tsaye ɗakin amimatu ya nufa ya buɗe ya shiga, cak ya tsaya yana binta da kallo tare da tsantsar mamaki da takaici tabbas idan har ba ruwa ta zubar ba to kuwa fitsarin kwance ta yi,da ƙarfi ya kama goshinsa yana matsawa yana jin lallai da aiki a gabansa dan kuwa aminatu sabon reno zai yi mata dama ya nemota tun da wuri yasan da aikin bai girmama zuwa haka ba,rasa ta yadda zai tasheta yayi kawai sai ya tattare hannun rigarsa ya je ya fara buɗe ƙofar banɗaki ya shiga ya tara ruwa masu yawa a baf sannan ya dawo ya sunkuceta gaba ɗaya ita da kayanta. Aminatu bata tashi jinta ba sai cikin ruwa luntsum tana iyo kamar an sata a kogi,temakonta ɗaya da ruwan bai kasance masu sanyi cancan ba, amma dai ba za a kiransu da na ɗumi ba dan kuwa punishment dinta ya shirya yi da gaske kuma gyaran yake son yo da gaske da zuciya daya kamar yadda ya ɗauki amana. "Wayyo innawuro ki kawo ɗauki an kowani ɗakin kogin aljanu ruwa zai tafi dani wallahi Ni bazan mutu yanzu ba sai na ga ɗanbirni dama kun shirya kasheni dan kawai nasa muku gishiri cikin miya" ,duk wannan surutan da take yi idanuta a rife suke dan ita duk ɗakinne ya zama kogi,cikin sheshshekar kuka ta ci gana da cewa baffa wuro wutabalbal babu yafiya tsakaninmu ka kawomu inda zamu mutu lokacinmu baiyi ba, to aradun Allah k asheda ko da na mutu sai na dawo maka a fatalwa kai da waɗanna mugayen mutanen masu yankankai". Tana cikin surutan tana ana ƙokarin cire mata kaya, aiko ta daddage ta kuma kurma wani uban ihun tana cewa innawuro kina ina kizo ki taimakeni za a ......"shut up ya fada cikin tsawa wanda sai a lokacin ta buɗe idanunta fes ta kuma fahimci a inda take da kuma wanda yake son cire mata kayan,duk da yadda take shakkarsa amma hakan bai hanata harsashi tare da gunguni tana cewa dama saboda ka min iskanci shi yasa ka kawoni nan Ni kadai yadda babu wanda zai iya cetona to wallahi aniyar bi aniya Ni nafi ƙarfin kaf ƴan birni ma bare kuma k.... Ganin irin kallon da yake watsa mata yasa ta kasa karasa maganarta sai kawai ta karasa da gunguni tana mai ƙokarin suturta wajen da ya fara banƙada mata,sunkuyowar da yayi yana ci gaba da cire rigar da take ta kokarin mayarwa tare da yin magana cikin deep voice ɗinsa yasa ta ɗan nutsu dan mus ab ɗin nan fa ba duk kai ba. "Ke kazamiya me fitsarin kwance ki min quait da karamin bakinki ko yanzu na saɓa miki kama, dan sakarci banza kawai ki saki jiki ki ƙwalalawa mutane fitsarin kwance". Sai ga aminatu na ƙif_ƙifta idanun irin na marasa gaskiya, sai kuma ta marairace fuska ta ce" ba Ni nayi ba fa ƙalan sharri aka yi"nine na ƙala miki sharrin kenan?"ya faɗa yana tsare ta da shu uman idanunsa masu sakata ladabin dole,sunkuyar da kanta ta yi tana girgiza kan tare da cewa ba kai ba ne mafarki nayi na shiga bayi ina fitsari shine nayi ashe ba a bayin ba ne", bai ko tanka mata ba ya zare rigar jikinta da tun zuwanta da Nana tayi mata wanka bata kuma ganin ruwa ba me kayan ma bata ga ruwa ba bare kuma kayan. Aminatu tana ji tana gani wannan santalelen dogon ɗan birnin yayi mata wanka tas, kallonsa kawai take ɗan yi sai ta kuma kalli ƴan matasan breaz dinta taga ko yana kallonta sai ta ga hankalinsa ba anan yake ba,jimawa kadan ta kuma leƙen fuskarsa a haka har ya gama mata wankan, duk abinda take yi yana kallonta ita ce dai bazata gane yana kallon ba dan ba kowa ne yake fahimtar yanayin kallon mus ab ba in dai ba kallon kai tsaye yayi maka ba wanda shi kuma wuya yake a gurinsa. A towel ya naɗota kamar ƴar jaririya aminatu babu abinda take sai zunbure baki kamar me shirin tabo hancinta da bakin. A can bangaren cikin gidan kuwa kowa hankalinsa a kwance yake amma banda zahida da jin kai ya hanata zuwa ta duba shin tare da aminatu ya kwana ko kuwa dai wani punishment din yayi mata kamar yadda Abby ya fada dan ya kwantar mata da hankali,babu abinda take sai kaiwa da kawowa, hankalinta bai tashi ba sai lokacin da taga kowa ya hallara da yin kalaci duk da kuwa yau ba a fito da wuri ba saboda weekend ne. Dubanta Abby yayi a tsanake kana ya ce "Dr zahida ki nutsu mana" kallonsa ta yi idanunta na son zubda hawaye ta ce "wane irin nutsuwa zan yi Abby bayan mijina yana can tare da wata tsinanniya a cikin gidan nan kuma kowa yana kallo amma babu wanda yayi masa magana ko ba danni ba ai a tsawatar masa saboda rashin dacewar hakan, me ye tsakaninsa da yarinyar ƴar aiki ce fa ƴar aikin ma ƙasƙantacciya talaka mara galihu ai wallahi yau na gama raina ajin mus ab" miƙewa ta yi ta haura sama da gudu tana tare hawayenta dan bazata taba yadda aga hawayenta akan namiji ba. Ƙamshinsa ne kawai ya tabbatar musu da cewa ya na kusa dasu, dan haka gaba ɗaya suka juya suna kallonsa daga shi har aminatun da take ta wani ciccin magani dan karma a yi mata maganar fitsarin kwance dan tasan tuni kowa ya sani. Free Pg remaining 2 Pg. A ci gaba da payment 300 only idan na gama free Pg 500 ne. Payment account 8064537048 Opay Fatima yushau adam. Yan nijer kuma su sa a nan👇🏽 80416252 amanata [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg12* Khalid yana hango aminatu ya miƙe ya nufota yana dariya ,ya ce" shine kika gudu na nemeki na rasa ko?" Da sauri aminatu ta kalli mus ab sai kuma ta marairace fuska kafin cikin raɗa ta ce "dan Allah karka fada musu nayi fitsarin kwance waccan lutuwar matar taka dariya zata yi min",banza yayi da ita sai ma wucewarsa da yayi wajen yana gaida Nana da Anne, cikin rashin fara arta na ko da yaushe ta dubesa ta ce, "mus Abu ina ka kai wannan yarinyar jiya a ina ta kwana"? Ba tare da ya dubi annen ba ya bata amsa da cewa "ɗakin da na jima da tanadar mata na kaita",kallon mamaki annen ke masa da kuma wasu tarin tambayoyin sai dai tasan ko da ta yi su ba zata samu amsa ba wannan ɗin ma da ta samu bata zata ba, dan haka taja bakinta ta tsuke, Nana kuwa babu wani alamun damuwa ko tuhuma a tare da ita hankali kwance ta ci gaba da breakfast ɗinta,suhaima ma bata damu da wannan sa idon ba. Su ko su sule dama baya nan ake kome dan yayi kaura zuwa hostel acewarsa yafi ganewa hakan sai dai yazo gida da ziyara ko nishaɗi. A bangaren Abby shima bai nuna komai ba ba kuma dan babu ko mai din ba ne, haka suka fara karyawa kowa na saka abinda ke damunsa a ransa. Aminatu kuwa tunda su ka haɗu da Khalid suka shiga sabgar gabansu , sai dai mus ab ya ga basu da niyar zuwa su karya sannan ya zare musu ido akan su zo su karya. Aminatu hanya ta ɗauka zata koma ɗakin innawuro yasa hannu ya janyota,sai ga aminatu dabas saman cinyar mus ab tamkar abun shiri kuma akan idon zahida da ta sake fitowa dan ganin ya fito ko har yanzu yana can tare da figaggagiyar yarinyar rigar,sai kuma idanuta su kayi mata mugun gani,wani irin kakkauran miyau ta fara haɗiyewa me shegen ɗaci kana ta shiga saukowa daga upstairs ɗin cikin sassarfa da zafin kishi mara sarrafuwa. Babu wanda ya kula da ita sai kawai ihun aminatu da suka tsinkaya zahida ta zabga mata wani mahaukacin Mari wanda take aminatu ta fara haɓo,runtse idanunsa yayi yana son Saita kansa saboda shi mus ab mutum ne da baya son yin hukunci cikin fushi ,aminatu kuwa banda turza da katantanwa babu abinda take a jikinsa wanda hakan yake kuma karawa zahida wutar bala'i a ranta hannu tasa tana shirin finciko aminatu amma sai ta ci karo da birkitattun idanunsa akanta wanda hakan ya dakatar da ita daga abinda take shirin yi,kawar da kanta ta yi tare da saurin barin falon dan bata so yaga hawayenta akansa,kukan da aminatu ke yi har hawa kansa yake "shut up idan na kuma jin sautin ki a nan zan saɓa miki" ɗif aminatu ta yi kamar dama kukan na ƙarya ne, kallonsa kawai ta ke yi da idanunta da suke cike da hawaye wanda suka haɗe da maiƙon cikin idanun suka bata wata kala me kyau ,shi ɗin ma kallon cikin idanun nata yake ba tare da ya san abin yi a daidai wannan lokaci ba. Hannunsa ta kama ta ɗora a gefen fuskarta inda zahida ta mareta sannan cikin sheshsheƙar kukan da take son haɗiyewa ta ce "wallahi da zafi hannunta kamar rodi"suhaima ta ce "ki yi hakuri aminatu Allah ya saka miki" Nana ma cewa ta yi kiyi hakuri kin ji boɗɗo", Anne kuwa ko kallonsu ba ta yi ba baya ga taɓe baki da take ta yi kamar taga abin tsantsani, shima Abby bai ce ko me ba sai ma shi da yayi ya bar wajen. Nana ta dubi suhaima ta ce "suhaima ja Khalid ku tafi islamiya ita wannan idan ta gama ya rakata dan naga sai an yi mata da gaske akan karatu, suhaima ta ce "wallahi kam Nana Gara ta fara zuwa har bokon a daina yi mana ƙaryar turanci" daga haka suka fice ita da Khalid, Nana ma tashi ta yi ta shige bedroom ɗinta. Aminatu kuwa har yanzu kuka take hannunta akan hannunsa da yake gefan fuskarta tana ta murzawa,janye hannunsa ya yi ba tare da ya janye ta daga jikinsa ba ya shiga zuba mata tea a cup,da kansa ya shiga bata a baki kamar wata baby haka take sha tana zuba shagwaɓa, sai da ya tabbatar ta ƙoshi sannan ya sauketa daga jikinsa yana tsareta da mahukuntan idanunsa, share mata hawayen da ya fara bushewa a kan kumatunta da ɗan guntun jinin da yake gefan hancinta ya yi yana mai ci gaba da tsareta da idanunsa da suke matukar ladabtar da ita,kawar da fuskarta ta yi tare da sauke kanta ƙasa tana jin girmansa na cika ko ina na gurin,"oya muje ya faɗa yana mai yin gaba abinsa. Sai da ya tabbatar ta zauna a gun malam sannan ya bar wajen bayan ya zuba mata kashedi da idanunsa. Zama ta yi tana guna guni tare da hararar Khalid da yake mata dariya suhaima kuwa hankalinta na kan ƙarin da ake yi mata. ******* Tunda baffa wuro ya ji kudaɗensa a hannu ya baza babbar rigar da ya siyo musamman dan irin wannan ranar ya ɗau hanyar cikin gari, sai da yayi nisa sosai sannan ya yi cikiyar dillalai masu sayar da gida a ka gama komai ya sayi kyakkyawan gidansa de de misali amma shi a matsayinsa na wanda ya fito daga riga ji yake kamar ya sayi wani ubangida na nuna Sa'a,kai tsaye ya dau hanyar komawa riga, ko da ya je ya samu ana ta cikiyarsu aminatu da innawuro abin har mamaki ya bashi saboda yadda yaga kowa yayi jugum jugum kamar wanda aka yiwa rasuwa,duk yadda aminatu ta addabesu amma wai hakan bai hana su yin jimamin rashinta ba,shima bin yarima yayi aka sha kiɗa, dan sam nuna musu yayi bai san inda suke ba har kuka sai da yayi suka dinga bashi baki da kyar ya wuce rigarsu da ba dan dole sai ya wuce ta rigar su aminatu ba da babu wanda zai san dawowarsa da fitarsa. A rigar tasu ma haka ya sa matarsa da yaronsa guda daya suka shirya bai bari ya kuma wayar gari a riga ba dan baya jin zai yi saken da za a zo a sutaleshi, duk kuwa da yadda yake jin yanayinsa kamar na mara lafiya dan wani lokacin har yi yake kamar zai faɗi amma duk bai bawa hakan muhimmanci ba. Ko da suka taho hanya matarsa take tambayarsa,"ya dai wuro naga kamar zaka faɗi ko dai da gaske ne akwai giyar kuɗi? To idan haka ne kuwa malam Ni ban bari ta kadani dan aradun Allah ban amsar kudin nan bare ta fara katantanwa dani"wannan magana da hamziya ta yi take ta sawa baffa wuro ƙwarin gwiwa dan kuwa ta ganar da shi abinda ya kasa ganewa tunda aka bashi kudadennan,dan haka ya kalleta da ɗan ƙwarin gwiwar da ya samu na maganarta ya ce" to hamziya in dai wannan giya ba kasheni zata yi ba ai ko da za a kirani da ɗan marisa aradun Allah ina son kudi kuma zan zauna dasu". ******* Yau ɗin ma dai haka aka yi uwar watsi da aminatu da malaminta,babu abinda ta ɗauka shi kuma ya ƙi ya rabu da ita saboda wannan umarnin me gidansa ne oga mus ab,Shi kafiya ita taurin kai dan haka aka dinga ɗauki ba daɗi daga ƙarshe dai yau ɗin ma guduwarta wajen innawuronta ta yi ta barshi da fadin "Allah ya kaimu yamma. Kuka take yi sosai kamar wadda aka ce uwarta da ubanta sun mutu, dan yau tunda ta je officeta gagara yin ko mai dan ma yau babu wata tiyata da take da ita da dole matsalar damuwar zahida ta taɓa musu mutuncin kasuwancinsu abinda basa fata ke nan. Ita dai Anita Debora kallon ta kawai take tunda tayi iya yinta akan zahidar ta yi shiru ta sanar da ita damuwarta ko dalilin da yasa tana wajen nata aikin ta kirata amma hakan ya faskara,sai da ta yi me isarta sannan ta share hawayenta dan dama neman damar kukan ta ke a inda babu wanda zai san ta yi, sannan ta zaiyanewa Anita Debora abinda yake faruwa,tsaki Anita ta yi kana cikin takaici ta ce "yanzu akan ƴar ƙauye yarinya ƙarama jahila kike wannan kukan gaskiya zahida da na raina ajinki a yau tunda har wannan dalilin zai iya sa ki zubda uban hawaye irin haka"?shuru zahidar ta yi sai kuma ta ɗan numfasa tare da cewa Anita ba zaki gane ba Ni nasan me nake hangowa a tare da yarinyar nan su Abby ma tun bata kai haka ba ta tsayar da duk wani lamarinsu na ci gaba ta zame musu ciwon ido me kwantsa da hana ganin haske, bare kuma ace na barta ta girma tare da mijina mijin da nake yi masa son mutuwa",wani kallo Anita ta bita dashi sannan ta ce me ye tsakaninsu Abby da kuma yarinyar?" Itama zahidar kallon baki da hankali ta yiwa anitar sannan tace "wannan ba hurumin ki ba ne kuma ba abinda na kira ki ki ji ba kenan" ,miƙewa Anita ta yi tana cewa "shike nan ni zankoma office amma dai zanzo gidan nima na ganewa idona ƙwailar jahilan yar kauyen da ta saka rich zahida kuka" daga haka ta fice daga office din ta bar zahida da mugun kishin da ya ke neman zazzago mata da zuciya. Yau Abby da wuri ya dawo dan tun a waya ya sanar da Nana zasu yi baki aminansa yau tare zasu yi dinner Shi yasa ya dawo da wuri,haka yasa zahida ta dawo da wuri saboda ya ce mata a wajen dinner akwai magana me muhimmanci da zasu yi , ba dan taso ba ta dawo gidan dan da aniyarta sai kowa yayi bacci zata koma. Har malam ya gama da su Khalid da suhaima babu aminatu ba dalilinta dan dole ya kwashi littafinsa ya tafi yana fatan ina ma zai samu damar jibgar aminatu da kuwa ta gane shayi ruwa ne. Mus ab bai shigo gidan ba sai da aka idar da sallar Isha kamar yadda ya saba a mafi yawan lokuta,tare suka shigo gidan dasu Abby, Wanda sai a nan Abby yake sanar dashi zasu yi dinner ne gaba dayansu dan haka ya fito da wuri, jinjina kai kawai yayi sannan ya wuce upstairs. "Boɗɗo wai yau me ake yi a gidan nan ne naga jama a na ta shige da fice?" Innawuro ce take tambayar aminatu lokacin da aminatun ta fito daga bayi ta yi alwala,ɗan jim aminatun ta yi kafin kuma cikin sauri ta yayimi hijabin sallah tana cewa bari nayi sauri na yi yar faki ba waya se lada se na leƙa na gano mana bidirin da ake yi, Allah yasa wannan lutuwar ce ta karye",riƙe baki innawuro ta yi tana bin sallar aminatun da kallo daga ƙarshe ta jinjina kai da cewa "ey lallai kuwa yar faki ba yawa se wurgowa, yo wane lada a wannan sallar taki boɗɗo ai kafin ta je kan fankar nan an wulwulo miki kayarki"daidai nan aminatu ta sallame sallar ciki sauri ta zare hijabin ta jefar tana cewa "bana son mugun baki innawuro ke kullum ba zaki fadi alheri ba, wallahi sallata tuni ta riga ta ƙi zuwa kaji wani batu dan Allah sai kace ita ce me karbar sallar", daga haka ta fice da gudu zuwa falon. Cak ta tsaya tana raba idon inda zata gano mutanen gidan dan ga dukkan alamu yau ba a wannan falon suke cin abinci ba,gashi har yau bata gama gane kan hanya dan ba duk uban yawon da ta ci yau kuwa,tana cikin tunanin sai ga Khalid ya fito nemanta ,aiko cikin washe baki ta kama hannunsa suka nufi hanyar da ya fito. Suna shiga kallo ya dawo kan aminatu,wata ZABURA zahida ta yi tana nuna mata hanya, "bagidajiyar banza da wofi fita kibar wajen nan saboda babu ahlinki a nan" rau rau aminatu ta yi da ido tana satar kallon MUS'AB da yake ta cin abincinsa hankali kwance kai baka isa ka ce yasan abinda ake yi ba,dadyn zahida ne ya kama hannunta yana cewa "meye haka zahida ki zauna mana?"dady barni wannan yarinyar so take ta sani ciwon zuciya kawai kuma in dai zata zauna a nan to wallahi ni ba zan zauna ba dan nasan dole sai t yi karuwancin da dole sai jikinta ya taɓa na Abban Khalid"ta faɗa tana kokarin fizge hannunta daga riƙon da dady yayi mata,suhaima ta yi tsagal ta ce to ke aunty zahida tayaya aminatu zata fiki iya karuwancin zama da mijinki wannan ma ai ji ne kawai"? Malama ba dake nake ba KARKI kuma sa min baki,ai gaskiya ce" suhaima ta kuma fada tana murguda baki. Dadyn zahida da kansa ya bawa aminatu umarnin shigowa dan duk abin nan da ake mus ab bai ce kome ba Abby ma da nana basu tanka ba anne kuwa dama bata fito ba. Aminatu kanta tsaye ta shigo kuma bata tunkari kowa ba sai ɗan birni, wata uwar ashar zahida ta kunduma mata tana cewa dan ubanki shi ya kira ki da zaki nufi gunsa shegiya karuwar ƙauye" a nan ne fa mus ab ya ɗago shanyayyun idanunsa wanda suka yi laushi saboda gajiya da hayaniyar ya zuba su kan zahida yana watsa mata dafin cikinsu, atake ta yi ladab har ta koma ta zauna sai dai bata bar watsawa aminatu kallon gargaɗi ba,ita ko aminatu tsaf ta gama shirya tsiyarta,dan haka cikin sum sum da Kai ta zo ta zauna kujerar da dadyn zahida ya nuna mata wadda take gefansa, tana zama ta ɗago kanta sai ko idanunta caraf cikin nasa yana mata kallon da bata fahimtarsa,ɗauke kanta ta yi ta dawo dashi kan abincin da daddyn zahida ya zuba mata sannan shima ta kallesa dan ta fara mamakin kulawar da yake ta bata tun shigowarta falon duk da cewa bata san matsayinsa a gidan ba shima kuma bai san nata ba a tunaninta.gyaɗa mata kai yayi da murmushi dauke kan fuskarsa, dan haka sai ta maida hankali kan abincinta. Kamar daga sama Aminatu taji ana gogan mata kafafu zuwa gwiwarta da ƙafa, a hankali da kuma nutsuwar da bata san tana da ita ba ta ɗago kanta tana kallon saitin daga inda take jin al'amarin,sai ko idanunta cikin na daddyn zahida yana mata wani irin kallo da duk rashin wayewarta sai da tayi zargin kallon. Janye ƙafafunta ta yi jikinta na yin wani irin sanyi, dan ta tabbata wannan abun shi ake kira alamun iskanci da innawuro kullum take mata gargaɗi akai,wata zuciyar ta ce da ita shi kuma ɗan birni meye ke nan tunda shi har wanka ya yi miki idan haka ne ai shine ɗan iskan ba wannan babban mutumin me cike da kamala ba. Ƙara jin ƙafafunsa da ta yi har cikin zaninta shi ya dawo da ita hayyacinta ta yi wata irin ZABURA cike da tsoron da ya bayyana akan saman kyakkyawar fuskarta,saboda zaburar da tayi har kujerarta ta yi baya tana shirin wuntsulawa,babu wanda yasan yaushe ya miƙe bare a san isowarsa sai kawai gani su kayi ya tareta ta faɗo jikinsa....✍🏾 Muje nets Pg kuma na karshe a free Pg in sha Allah Account number [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg13* Jinta a jikinsa yasa ta ƙankamesa tana sakin kuka me ƙarfi, gaba ɗaya ya zareta daga cikin kujerar ya zamana tana jikinsa, bai ce komai ba ya ɗau hanyar barin falon da ita. "Dady kaga Ni ko ban san yaushe Abban Khalid ya koma haka ba, yau ma tafiya zai yi ya kwana da ita a gaban kowa yana kallo babu me tsawatar masa na shiga ukuna"Nana ta ɗago kanta ta kalli zahida ido cikin ido kana ta ce " yarona ba lalatacce ba ne ba sai dai idan ke kika lalatashi kuma har abada ina da kyakkyawan zato akan mus Abu ba zai taba bani kunya ba a fili ko a boye" daga haka ta miƙe tabi bayan mus ab da aminatu, suhaima ma bar musu falon ta yi ita da Khalid, sai ya zamana sai su isu. Zama Abby ya gyara yana kallon zahida kafin ya buɗe baki ya ce,"zahida ina so ki dinga Saita kalamanki kuma ki dinga tunawa a ko da yaushe aminatu ba zamanmu take ba mune muke zamanta idan har wannan zafin kishin naki yasa kika lalata mana shiri ko hakan yayi sanadiyar barin aminatu da kakarta gidan nan uhmm" amma Abby me kuke shiryawa akanta da ina tunanin kamar wancan dalilin ne kawai amma yanzu lamarin ya fara bani tsoro tabbas akwai wani abu da kuke boye min, baran ma idan na kuma yin duba da yadda daddy ya ke bata kulawa a rana ta farko" Alhaji garba da bai cika magana ba ko zama ne yahadasu ya danyi gyaran murya kana ya ce "zahida wannan ba huruminki ba ne ki tsaya a iya huruminki tone tone ba zai har far miki da ɗa me ido ba" binsu Abby ta yi da kallo dan taga shin sun karɓi maganar da daddy Garba ya yi mata ko zata ga rashin jin daɗin hakan a tare da su,amma ga mamakinta ko gezau basu yi ba sai ma jinjina mata kai da su kayi alaman dai wannan maganar haka take,zata sake yin magana dadyn ta ya dakatar da ita ta hanyar bata umarnin tafiya, ba dan taso ba haka ta miƙe jiki babu laka ta bar falon da tashin hankali biyu ga na iyayenta ga kuma na mijinta. Bai dore ta a ko ina ba sai ɗakinta na jiya,duban ɗakin ta yi kafin cikin tura baki ta ce,Ni dai ba zan kwana a nan ba tsoro nake ji"ba zaki bar dakin nan ba sai ranar da kika yi hankali kika fara son karatu, kuma ki wuce yanzu ki yi wanka kazamiyar kawai tun kayan da na barki dashi ne ajikinki baki wanka kin sauya ba", dan Allah ka barni kaima ɗazu ai ka dirjeni da kyau harfa yanzu jikina zafi yake saboda dirzar da nasha"kije ki yi ko yanzu ma nazo na dirje kin" ya faɗa yana zama gefan gadon tare da fara latsa wayarsa,a jima a tsaye a wajen kafin cikin jin haushin matsamatan da ya fara yi ta wuce bayin tana ƙunƙuni se ka ce wani baffana sai wani takura min ake yi, sarai ya ji ta sai dai bai tanka ba dan yanzu uzuri ya ke yi mata har zuwa lokacin da zata yi hankali. Ko minti biyar ba a yi ba sai ganinta yayi a gabansa daure da towel ɗin da taga ya daura mata ɗazu kanta kuwa babu abinda yake sai ɗigar ruwa,zuba mata ido yayi yana tunanin ta ina zai fara sai kuma ya ɗan ja numfashi tare da lumshe idanunsa da buɗesu a lokaci ɗaya, sannan cikin yanayin muryarsa da ke nuna gajiyar da yayi ya ce,ina wankan?" Kawai sai ta zame towel ɗin tana cewa gashi wallahi na fita sosai"maida idanunsa ya yi ya rufe yana jan numfashi,shifa ko ɗazu da yayi mata wankan nan bai tsaya ya kalleta ba,amma saboda rashin wayo yanzu tazo ta tsaya masa tik,ɗaukar towel ɗin yayi ya daura mata yana mai kauda kansa daga kallon kyakkyawar surarta me tsananin ɗaukar hankali, dan aminatu ba dai ƙira ba tun yanzu ma bare kuma idan maƙerin budurci ya gama kerata, wayyo me rabo kam sai dai ya godewa Allah. Da kansa ya dauko mata kayan bacci ya bata ta saka, ya bata turare ta shafa komai sai da ya koya mata sannan ya ce ta kwanta, zata yi masa gardama ya kuma tsuke fuskar ai babu shiri ta kwanta,tana satar kallonsa,ajiyar zuciya ta sauke ganin ya nemi waje gefen gadon ya zauna yana ci gaba da latsa wayarsa wanda da alama wani aikin yake yi. Sai da ya tabbatar ta yi bacci sosai sannan ya yi mata addu'a ya rufeta da duvet me taushi, sannan ya fita daga ɗakin. ********** Kaiwa yake yana kawowa hannayensa goye a bayansa, babu abinda yake hangowa sai yarinyar duk motsin da zai yi sai yaji ta a ransa,wai me yake shirin faruwa dani?" Ya faɗa yana zama gefan gadonsa,ya jima da ajiye wannan dabi'ar ta sa tun kafin auren zahida da mus ab,sai yau katsaham yake jin wani abu me girma akan bafulatanar rigar da suke da bururruka akanta yau ga wani burin ya kuma karuwa dan kuwa tunda ya ƙyalla ya gani sai ya cimma burinsa ,kai shi fa idan ba dama zai iya aurenta ko kuma su dawo gidansa da zama amma yana son yarinyar nan kuma yana son ɗanɗana zumarta,a ranar kam Baccin dadyn zahida kaɗan ne duk rabin daren ya ƙarar dashi ne a tunanin yadda zai yi ya mallaki aminatu. ******* A lalace yau satin aminatu daya a gidan Alhaji jamilu,kuma a yau ne aminatu ta fito tsaf cikin uniform ɗinta na makaranta,da kansa ya kaita ita da Khalid a ka bata ajin da yayi daidai da ita, sannan ya dawo gida ya shirya. Washe gari kuma school Bus ta fara ɗaukarsu ita da Khalid,kai idan ka kalli bakin aminatu abin sai ya baka dariya,suna tafe an gama daukar daliban mota ta dauki hanyar makaranta direct,sai kawai ganin aminatu su kayi ta zuro kanta ta window motar tana kaɗa hannu tana cewa "ina zaku je Kano ko makaranta muna kaiwa duk inda kuke so"gaba ɗaya sai ta zamarwa yaran abin kallo, sosai aminatu ta maida kanta kwandasta, driver yayi mata magana amma ko kallo bai isheta ba,to abin ka da lamarin ya'yan masu kuɗi ganin aminatu ta ƙi saurarensa sai kawai ya rabu da ita,aiko yaga kayan takaici dan kuwa yara ƴan makaranta masu karancin hankali irinnata tsayar da su suka dinga yi, idan yayi niyar kin tsayawa sai dai yaga aminatu tana ƙoƙarin kama giya wai zata tsayar da shi,haka driver ya tsaya yana sharce gumin tashin hankali, sai da ya cika motar har babu wajen tsayawa, kuma kowanne dalibi sai da ya kaisa makarantarsa aminatu ta karbe kudin mota tana cewa "gobe ma kutsaya zamu yo ta nan mu daukeku"gashi duk cikin motar tafi su girma duk yara ne dan haka tsoronta suke ji sosai,. Sai karfe tara suka isa makarantar,koda dercter ya fara yiwa driver faɗa nan ya shiga bada hakuri yana faɗar abinda ya faru, directer bai ɗauki abin da muhimmanci ba yayi wa aminatu uzuri na sabuwar zuwa. Ashe wasa farin girki. Aminatu na ta raba ido a cikin sabon aji kuma sabbin mutanen da bata taba sani ba,lokaci ɗaya kuma taga kowa ya miƙe sun ruɗe da fadin "good morning uncle" kallon bakunansu kawai take yi har uncle John ya basu umarnin zama aminatu na zaune tana ware manyan idanunta akansu da kuma uncle John ɗin. "Hey standup" uncle John ya faɗa yana nuna aminatu da makar hannunsa,aminatu bata fahimci abinda John ya ke nufi ba kuma har yanzu bata yadda bata iya turanci ba,kawai dai ta fuskanci cewa da ita yake magana dan haka ta gyara zama tare da gyaran murya ta ce" we went Spiderman and suck and gate game cartoon or play and car" hankali kwance ta yi maganarta saboda duk abinda take ji Khalid yana fada ta rike kuma yau turancinta akansu ya kare,ji ta yi ƴan ajin sun ƙyalƙyale da dariyar shewa, shima uncle din dariyar yayi ba tare da ya kuma ce mata komai ba ya fara yin abinda ya kawosa. Aminatu kuwa tuni ta cika ta yi fam da dariyar da su kayi mata dan haka cike take da su. Gab da za a tashi ta fita daga ajin, jim kaɗan ta dawo hannunta a ɓoye babu wanda ya lura da ita ko abinda take ɓoyewa,kai tsaye yaron da yafi kowa yi mata shaƙiyanci da kwatanta turancinta shi ta fara nufa yana cikin yara Yarennata sai jin bakinsa yayi ya cika fal da kasa kafin ya dawo hayyacinsa ta watsa masa ragowar a duka jikinsa da fuskarsa kasa har cikin idanun kunle,tsit a jin yayi kowa yana kallon aminatu da mamakin ƙarfin halinta,juyowa ta yi tana nuna su kafin cikin kakkausar murya ta ce "aradun Allah kowa sai ya san aminatu boɗɗo yayiwa dariya ba dai kun yi min dariyar turanci ba to duk zan dau fansa da mabanbanta hukunci a tsakaninku arnan banza da wofi kawai"dai-dai nan aka kaɗa ƙararrawar tashi, da gudu kowa ya ɗauki jakarsa ya bar ajin aka bar kunle da murje ido da furzar da ƙasa gashi gaba ɗaya kayansa sun ɓaci da kasa, aminatu ma ficewa ta yi daga ajin ta kulleshi ta waje ta yi tafiyarta. A can cikin mota kuwa duk sun shiga ita kawai ake jira, ko ba dan Khalid ba shi kansa driver Yana tsoron tafiya ya bar aminatu yar balaja'u dan yau kadai ya shaida halin boɗɗo. Adekunle kuwa sai da aka zo nemansa daga gida sannan aka fahimci abinda ke faruwa, take directer ya baza malamai nemansa a ji aji anan aka samo shi cikin ajinsu ya ci uban kuka ya ƙoshi ga idanunsa sai ruwa yake yi ko bude shi ba ya iya yi sosai, kayansa kuwa kasancewar farine uniform din KO gane kalar ba a yi,daƙyar ya yi musu bayanin abinda ya faru take yayansa da yazo ya ce bazasu yadda ba dole a hukunta yarinyar,dole directer ya kira wayar MUS'AB ya sanar dashi abinda ke fatuwa dan haka gibe suna nemansa a makaranta dan yin case ɗin. Yana sauke wayar daga kunnesa ya dafe kansa yana mai shafa goshinsa, ba dai zaka fahimci yanayinsa ba shi ka dai yake barwa zuciyarsa baya bari abinda ke cikin zuciyar ya bayyana kan fuska sai dai fa fuskar nan ta yi murtuk kai kace ba a taɓa halittar dariya akan fuskarsa ba. A dawowar ma haka aminatu ta dinga ɗibar fasinja dan haka basu suka dawo gida ba sai kusan karfe huɗu saura dan duk sai da aka kai fasinjojin da ta sa aka ɗiba,da suka zo sauka ita da Khalid sai ta mikawa driver kudin tana cewa "sai kaje ka shawo mai tunda dama amfanin kasuwancin ke nan" aiko driver ya karɓe kudin yana washe baki shi idan haka ne ai gaba ta kaisa kullum ma aminatu ta yi kwandasta shi kuma yayi tuƙyi. Haka kawai yau take jin tsoron dawowarsa ya sameta ido biyu, dan haka tunda taga magriba ta yi ta gudu wajen innawuronta ko abinci a can suka ci daga nan ta garkame kofa suka kwanta tana addu'a Allah yasa gobe kar su hadu dashi har ta tafi makaranta,ita dai tasan bata yi masa laifi ba to amma haka nan ta wani sashen take ji kamar tayi laifin. Babu irin mitar da innawuro ba ta yiwa aminatu akan ta tashi ba , amma hakan ya gagara sai ma juyi da take kuma yi alamun dai bacci ya yi daɗi, Yana dawowa daga masallaci kai tsaye ya nufi bangaren innawuro yasa hannu ya ɗan yi buga, kasancewar asuba ce ya sa innawuro bata ji tsoro ba ta miƙe ta nufi kofar tana tambayar waye"? Cikin deep voice ɗinsa ya bata amsa da cewa nine mus ab"da sauri innawuro ta buɗe tana cewa to mus Abu Allah ya sa dai lafiya ?" Lafiya aminatu fa" ya bata amsa hade da tambayarta aminatu,nuna masa ita ta yi tana ta sharar bacci hankali kwance,ta ɗora da cewa "tun ɗazu nake fama da ita amma ta yi biris da ni Gara da Allah ya kawo ka" ta fada tana bashi hanya,shigowa yayi har inda take ta juyi ba tare da yayi dubi da innawuro da ke tsaye ba ya kwashi aminatu kamar wata yar jaririya ya yi waje da ita, daidai zahida na kokarin giftawa daga corridon ta zuwa nasa ta can upstairs ɗinsu. Murza idanunta ta shiga yi dan son tabbatar da abinda take gani, kai wannan wane irin Bala i su daddy suka kawo mata har cikin gida? me yake shirin faruwa da ita ne ?wai wacece aminatu me su daddy suke nema a wajenta? Me ye hadinta da mus ab tabbas akwai abubuwan da take buƙatar sani kafin tasa a yi mata maganin tsinanniyar yarinyar dole ma aminatu ta mutu ko ba ta waccan hanyar ba ita ce da kanta zata yi sanadin mutuwarta. Last free Pg Account number 8064537048 A maunt 500 Shedar biya 08064537048 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg14* Yadda mus ab ɗin yayi kamar bai ganta ba yasa ta kuma jin wani irin baƙin ciki mara misali, duk da tasan cewa shariyar halinsa ne,da ƙyar taja ƙafafunta ta koma ɗaki tana saƙa abinda zai fissheta da tunanin hanyar da zata bi ta gano ko me da yake faruwa . Aminatu bata tashi tsintar kanta ba sai a cikin bahon wankan da yake cike taf da ruwan kumfa,babu shiri ta buɗe idanunta tana ware su akansa, fuskar nan a tamke babu annurin murmushi ko kaɗan a cikinta,"na baki minti ashirin da biyar kiyi wanka idan kika fito ƙasa da haka ko kika haura hakan zaki fuskanci ɓacin rai"daga haka ya fice daga bayin,ya bar aminatu da tura baki ba dan taso ba yau ɗin ta tsaya ta yi wankan kirki ta goge baki da alwala sannan ta fito ,yana zaune bakin gadon yana jiranta, da ido yayi mata nuni da ta shafa mai, saboda tsabar sakarci irin na aminatu duk abinda ya ce ta yi da ta gama zata tsaya tana kallonsa sai ya kuma bata wani umarnin sannan zata ci gaba a haka ta gama shiryawa sannan suka fita tare, shi bai zauna zaman karyawar ba saboda shirin aminatu bai barsa yayi nasa shirin ba,dan haka cikin dan gaggawa da zafin nama ya haye upstairs. KO da school bus ta zo bata samu ɗaukarsu ba dan tuni sun wuce da mus ab ɗin a motarsa,kuma har lokacin bai cewa aminatu ko me game da laifin ta ba,ko da suka isa school din tuni iyayen kunle suma sunzo dan haka aka shiga dogon turanci sai anan aminatu ta fahimci dalilin da yasa hamma mus ab ɗin yau ya kawosu school da kansa,tana jin lokacin da yaron ya faɗi son ransa akan case din a tunanunsa tunda a gaban directer ne da kuma iyayensa aminatu zata ji tsoro, amma sai yaga saɓanin haka, dan kuwa aminatu kuka ta fashe da shi tana fadar yadda aka yi ta ƙara da cewa "kuma wallahi suma ragowar ba haƙura nayi ba duk sai na rama gobe ma sa kuma yi min dariyar turanci",duk da yadda mus ab ya tsareta da rikitattun idanunsa hakan bai hanata ƙarasa zancenta ba,sai da ta dire zancan sannan ta yi ƙasa da kanta dan kaucewa dafin da kallonnasa yake sakar mata a duk wata gaɓa da jini ke gudana a cikin jikinta. Anan directer ya bawa Kowa lefinsa aka jawa yaron kunne akan kar ya ƙara, ita kuma aminatu aka bata hakuri akan ta yafewa ragowar ,amma sai ta wani maƙale kafaɗa tana farfara manyan ƙwayar idanunta da suke wani maiƙo, take directer ya shiga wani rawar jiki yana cewa," ai in dai turanci ne sai kinzo kin fara koya musu ke dai kawai ki bada himma kar ki wasa in dai turanci ne kamar kin iya kin gama a makarantar nan kum....kallon da mus ab ya yarfa masa ne yasa shi kasa karasa maganarsa sai ya fuske da sosa ƙeyarsa yana yaƙen tashin hankalin bala in da ya hango a cikin ƙwayar idanun mj (mus ab Jamil)kasancewar mutane daga waje ƴan kasuwa da abokan ciniki da na aiki kowa da mj yake kiransa. Miƙewa yayi yana kallon aminatu na ƴan sakonni kafin cikin muryarsa me zurfi da ƙamewarsa ya ce," idan aka kuma kawon kararki ba zaki kuma zuwa makarantar ba sai ki zauna a gida a ci gaba da yi miki dariyar banzar turancin naki oya go back to class" ta Shi ta yi sum sum ta bisa tana cewa a ranta "ba dole ma na iya turanci ba ko dan na rama abinda aka yi min da kuma waccan lutuwar matar da ba a da halin yin magana sai ta maƙe murya tana wani tirancin ƙarya daddy you see dis rubbish girl,wayyo ashe na fara iyawa ta fada da ƙarfi tana ƙyalƙyala dariya ganin ya juyo ya watsa mata kallon nasa ya sa ta rufe bakin tana cewa "sorry daddy I think Ni kadai ce" da sauri ta kuma dukan kanta tana washe fararen haƙoranta da suke ƙananu jere reras kamar wanda aka zauna aka shirya mata su,saboda yau dai ta ji a ranta ta ɗan yi abin arziƙi ko da gyara tasan bashi da yawa,sai da ya tabbatar da ta shiga class ɗinsu sannan ya fesar da iskar bakinsa yaja motar ya bar harabar makarantar. Da misalin ƙarfe sha biyu aka sake zuwa kiran aminatu, ba dai daddy ne ya dawo ba? "To Allah yasa ba wani sharrin aka kuma yi min ba tsinannu ƴaƴan arna wallahi dai aminatu dashen Allah ce babu yadda za ai da ita ehe"ta faɗa daidai da shigarta office din directer,wanda ta gani a hakimce a kan kujera yasa ta yi turus cike da mamaki, duk da cewa aminatu bata da wani hankalin girma sai tarin kuruciyar rayuwar riga da ya cika kanta,amma hakan baisa ta kasance ballagaza ko shashasha ba dan komai innawuronta na gaya mata ko da bata fahimta ba idan abin yazo tana tunawa da maganar innawuro kuma alokacin zata san ma anar abin, da dalilin nusar da ita da innawuro take yi,ƙaraso mana aminatu directer ya faɗa yana ƙoƙarin fita daga office ɗin,a hankali a kuma tsorace ta karaso tana kallonsa da tsoron da ya bayyana akan fuskarta dan bazata manta abinda ya faru ranar ba sarai abin yana zaune a kwakwalwarta. "Zo mana aminatu ga waje zauna ki saki jikinki mana nifa uba ne a gunki ko ba kya yin uban dani?" Ya faɗa yana ƙoƙarin kama hannunta amma sai ta yi sauri ƙwacewa ba ta bari ya kamata ba, sannan cikin rawar murya ta ce" Ni bani da Baba dan haka kai ba baffana ba ne"to to naji amma ai kya sake dani ko tunda na girmi mahafinki dan haka na samu girmamawa ta girman da nake dashi"ya faɗa yana kara kusanta kansa da ita. Ja da baya ta fara yi tana kallon tsakiyar idanunsa da shima yake mata kallon maita kallon kwaɗayi kallon ya zanyi idan ban samu ko rungumarki na yi ba,da dai taga ba zai daina kokarin taɓa ta ba kawai sai ta tsaya cak bata ƙara matsawa, ita dai bata san me ya faru ba sai gano dadyn zahida ta yi ana wani irin juyi da shi kamar katantanwa ba a direshi a ko ina ba sai can ƙarshen office din ji kake tim an watsar da shi kamar an yi wurgi da kaza,juyawa ta yi ta bar office din ba tare da ta tsaya mamakin yadda hakan ta faru ba. "Ƙara yasa yana mai riƙe bayansa da yake jinsa kamar ba ajikinsa ba,sai alokacin ya tuna baya da wancan tsohon al marin da yakasance kusan shekaru goma,dafe kansa yayi yana cewa "wai meye a tare da yarinyar nan ne haka? Me yasa duk lokacin da muke son taɓata wani abun al'ajabi yake faruwa damu?" Jinjina kai yayi tare da daddafawa ya mike yana cije bakinsa, tabbas taɓa aminatu abu ne me wahala amma kamar yadda bamu haƙura akan wancan ƙudurin ba to Nima ba zan taɓa haƙura akan nawa ƙudurin ba mu zuba mu gani idan ma aljanune ai duk muna tare dole musan abin yi tun kafin wankin hula ya kaimu dare. Yau har aka tashi aminatu bata kuma yiwa kowa magana ba, ko a school Bus din yadda kasan bata ciki babu hayaniya bare ɗaukar fasinja. Ko a gidan ma shuru kake jinta duk janta da innawuro ta ke yi sai da ta shiga damuwar rashin walwalar aminatu, sai da ta zuba mata ido sannan ta gano akwai wani abu dan haka sai ta rabu da ita,malam kansa yau yasha mamaki dan tsaf aminatu ta kafance masa surorin da kullum take haƙilon ta biya ta ƙiya hatta karatun fiƙihun da yake da hadisai duk sai da ta biya masa,washe baki yayi yana cewa "yau aminatu babu faɗa an yi abin kai ashe haka kike da ƙwaƙwalwar yan baiwa shi yasa kike abinda kika ga dama"tana jinsa bata tanka masa ba dan kansa ya gaji da sambatun ya yi shuru. Nana ma da kanta sai da ta tambayi aminatu lafiya saboda yau taga bata cokali kowa ba tayi wani shuru da ita kamar ba ita ba,babu kome Nana abinda ta cewa Nana kenan,Anne dake wajen kuwa tsaki taja kana cikin gwasala ta ce " Ni banga abin damuwa akan haka ba ai ko ba ko mai yau kunnenmu ya huta yarinya sai kace shedadiya kinzo ke kadai kin hargitsa gida dubi yaro duk hankalinsa ya koma kanki sai ka ce wata mutum,ko dai menene Allah zai yi mana maganinsa dan bana tunanin haka kuka shigo gidan nan ance reno to gashi ku ake raina shi kansa yaron da ake cewa zaku kula dashi din babu wani abu da kuke masa sai shi da yake kula da ku wannan kuwa ai babbar masifa ce Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu gida duk sai taron tsuntsiya ba shara" tunda Anne ta fara magana aminatu ta zuba mata ido ko kiftawa bata yi wanda sai da annen ta gama surutun sannan ta ji a jikinta,gani su kayi kawai ta miƙe jikinta na rawa tana faman sharce gumin da suka kasa gane na meye,binta su kayi da kallo har ta bar falon sai a sannan aminatu ta janye idanunta daga kallon da take yiwa annen tare da sauke ajiyar zuciya. Innawuro ce ta fito ta janye aminatun saboda ta fahimci abinda ke damun aminatun, suna shiga daki innawuro ta dubeta tana cewa boɗɗo yau me yake faruwa ko baki faɗa min ba tabbas akwai abinda ya faru kuma yake da jibi da wancan al'amarin da ta dalilinsa ka ɗai kike wannan ɗabi un, gaya min aminatu kin haɗu da wani daga cikin waɗan can azzaluman ne"? Girgiza kai aminatu ta yi sannan ta ce Ni ban sani ba innawuro kin san dai ban san ko mai ba ko kuma ban san su ba to tayaya zan gane hakan"?amiantu abinda yake tare da ke dole ya bayyana in dai har kin kusanci mutanencan Ni na sani zuwanmu birni babu abinda zai haifar sai damuwa dashin hankali dan haka dole ne mu bar gidan nan tun kafin komai ya lalace". "A'a innawuro babu inda zamu je dan Allah ki barni a wannan karon na cika alƙawarin baffa ki bari a wannan lokaci mu yi gaba da gaba da maƙiyanmu wannan guje gujen babu abinda zai kara mana, karfa ki manta baffa da kansa ya ce min aminatu da taimakonki Allah zai kawo ƙarshen mutanennan saboda dubban mutane sun mutu a hannunsu ba tare da sunji ko sun gani ba dan haka ko ba dan ɗaukar fansar rayuwata da su kayi ba ina so ki jagoranci zuwan karshensu"ajiyar zuciya innawuro ta sauke a hankali ta koma ta zauna sannan ta ce "shike nan boɗɗo Allah ya bamu sa a Allah kuma ya bayyana mana ɗan birni" sai alokacin amiantu ta yi dariya tare da amsawa da Amin",fuskar daddy zahida na yi mata gizo a cikin idanunta. Misalin daya na dare amiantu fitsari ya matsata,ta tashi innawuro da ta rakata innawuro bacci na cin idanunta ta juya ta ce " amiantu bayi gaki ga shi sai na raka ki je kiyi ki dawo" saboda matsatan da yayi ta mike ta sauka daga kan gadon amma a maimakon ta nufi bayin sai nufi kofa ta bude ta fice, cikin magagi ta shiga ratsa falukan gidan,dab da zata haye upstairs ta ji kamar magana da ga can wani loko da bata fiye ganin a na shiga ba,kawai sai ta nufi wajen, duk da cewa aminatu magagi take amma muryar da ta ji da kuma batun da ake taunawa a wayar da ake yi duk sun zauna a ƙwaƙwalwarta. Juyawa ta yi a maimakon ta koma ɗakinsu sai ta rasa hanya dan haka ta haye upstairs da nufin ta koma ɗakinta da daddyn Khalid ya kaita,tana zuwa ta buɗe ƙofar da bata gama tantance ina ne ba ta shige abinta,kai tsaye ta faɗa saman haɗadden gadon da yaji lafiyayyun shimfiɗun alfarma,a hankali ta lumshe idanunta tana shaƙar ƙamshin da a wajen mutum ɗaya ta taɓa jinsa sai kuma yanzu da take jinsa a wajen hamma mus ab daddyn Khalid, shigewa ta yi cikin duvet ɗin tana ƙara shaƙar ƙamshin tare da cusa fuskarta inda take da tabbacin daga nan ƙamshin yake kai tsaye...... Zahra✍🏾 PAID 8064537048 Opay Fatima yushau adam Amount 500 Shaidar biya 08064537048 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ **Pg15* A hankali yake bude shanyayyun idanunsa da baccin dake cikinsu ya kuma sauya musu launi,juyi zai yi amma sai ya ji ta ko ina an kadandaneshi saukar numfashinta kawai yake ji saman ƙirjinsa tamkar zata tsaga ta shige,mamakin yadda aka yi ta zo yake yi, fuskarta ya buɗe yana kallo, hankalinta kwance take ta baccinta tana saukar da numfashi a hankali tamkar yar baby,Shi bai ma San ya zai yi da ita ba, idan yayi ƙokarin janyeta ya miƙe sai ta kuma riƙeshi, a haka har aka kira sallah fwn haka yayi ta zama ya janyeta da ƙarfi sannan ya tashi ya shige bayi dan daura alwala. Har ya fito bata farka ba, dan haka bai saurareta ba ya fice zuwa Masallaci. Cikin tashin hankali innawuro ta shiga neman amiantu sai dai babu aminatu babu dalilinta, har gari ya fara haske bata ga aminatu ba dan dole ta fasa ihun kukan da ya jawo hankalin mutanen GIDAN,a lokacin Dr zahida har ta fito cikin shirinta tsaf dan duk ranar da take da aikin zuciya karfe shida ma bata fita yi mata a cikin gidan ba, tana fitowa taga kowa yayi cirko cirko ana neman amiantu dan Nana babu inda bata duba ba babu ita, Nana ta ɗan kalla ta ce "amma kun duba ɗakin dadyn Khalid kuwa kun san dai yanzu nanne wajen zuwanta?"harara Anne ta manna mata kana ta ce"me zai haɗa jikana da wannan ƙwailar duk ganinsun da kike yi kin dai inda yake kaita" tabe baki ta yi tare da yin taku daya zuwa biyu sannan tankuma juyowa tana watsawa innawuro wani banzan kallo kamar ita ce tayi maganar,sannan ta ce "to shi dakin da kuka san yana kaitan kun duba?" . Suhaima ce ta bata amsa da cewa "ko ina fa an duba aunty zahida dan Allah ki tafiyarki tunda ba jimami zaki taya mu ba" ,dariya zahida ta yi tana cewa "to maras kunya Allah yasa idan kun tashi ganinta ku ga gawarta", daidai Nana Abby da must ab suka dawo daga masallaci,gaba daya kallon mamaki Abby ya bisu dashi, shiko oga kwata_kwata ko tsayawa bai da niyaryi har sai da ya kusan hayewa upstairs ɗin sannan ba tare da ya juyo ba ya ɗan dakata cikin deep voice dinsa da yanayinsa na fuskewa ya ce"tana bedroom lafiya ƙalau", "what ban gane ba wane bedroom?" Zahida ta yi maganar numfashinta na kokarin fuskewa, ko kallo bata ishesa ba bare ta samu amsar tambayarta ya karasa hayewa ya barsu tsaye cirko cirko babu me iya cewa komai. Cikin hauka zahida ta bishi saman, duk kiran da Abby yake mata amma ta kasa dakatawa,wasu irin zufa ne suka shiga tsatstsafowa saman goshinsa ya daƙyar ya iya kai hannu ya goge su yana shiga wani irin tashin hankali, me ya kawo wannan matsalar a dai-dai wannan lokacin da suke buƙatar nutsuwar zahida?tabbas rashin nutsuwar zahida zai iya haifar musu da babbar asara me tarin yawa wanda zata iya durƙusar da su ƙasa wanwar,me yasa matsalar bata taso ba sai yau da suke shirin biyan bashin tsawon shekaru? Ina da sake ba zan taba bari haka ta faru ba" ,shi kadai yake wannan sambatun a ransa, kafin cikin sauri da zafin nama yabi bayan zahidar. Anne ta shiga tafa hannunwa baki ɗauke da salati, na shiga uku Ni Sallamatu me yake shirin faruwa a gidan nan ne haka anya kuwa ta bakin zahidar ba Mayun aka kawo mana ba dan dai Ni jiya na ga abin mamaki daga yiwa yarinya magana aka shiga azabtar dani ta ciki da waje, dole sai na fara turaren Mayu da na aljanu a gidan nan idan Allah ya taimake mu sai su gudu da kansu"Nana bata ce ko mai ba sai suhaima da ta duba ta ce "kuje ku yi shirin school kar ku makara" innawuro ma wucewa ta yi zuciyarta fal tsoron da har yanzu bai saketa ba,itama nana kiching ta koma wajen larai suka ci gaba da haɗa karin kumallo.ganin sun watse sun barta yasa ta ja wani kafirin tsaki sannan itama ta koma ɗakinta tana mitar ita kaɗai. Yana shigowa gun amiantu ya nufa yana tashinta,amma sai ta tashi a firgice tana wasu irin sambatun da dole ya sa shi kamata ya riƙe yana mata addu'a,sai ko ta yi lum a ƙirjinsa tana sakin ajiyar zuciya, a nan ne zahida ta faɗo dakin kamar mahaukaciya hannunta riƙe da wuƙa tana cewa wallahi yau ko ku bar gidan nan ko kuma na kasheki na kashe kaina kowa yayi asara tsinanniyar karuwa yarinya ƙarama da ke amma duk wani salon iskanci kin iya shi har kin san ki zo ɗakin mijina ki kwana saboda tsabagen iya taaddanci saboda kinga bashi da mafaɗi bare a gaya masa abinda yake yi ba daidai ba ne", zahida ya faɗa ransa idan yayi dubu duka sun ɓaci duk da cewa baka ganin hakan akan saman fuskarsa amma kana kallon ƙasan maƙogaransa da idanunsa zaka fahimci yanayinsa babu daɗi, amiantu kuwa ganin waƙa na sheƙi muraran yasa ta jin wani mugun fitsarin tsoro ya matsata,ga maganganun jiya da ta ji sun shiga dawo mata kamar ana tuna mata,hannunta tasa ta toshe kunneta tana runtsue idanunta, tana cewa wayyo kunnena zai fashe dan Allah dadyn Khalid ka ce ta fita ta je ta yi aikin da yake gabanta idan ba haka ba ko mai zai lalace" daidai daddy na shigowa ɗakin kalaman aminatu caraf a kunnensa,ke nan dai har yanzu babu abinda ya sauya har yanzu tana nan a yadda muka santa shekara goma baya anya wannan yarinyar mutumce kuwa ya a kayi tasan aikin da zahida zata yi?" Saurin kawar da tunanin yayi da cafkar hannun zahida da ƙarfi yaja ta suka bar ɗakin bai yadda ya rabu da ita ba sai da ya kaita har cikin asibitin da kansa sannan ya tsaya yayi mata maganganun da zasu dawo da ita hayyacinta daga nan bar asibitin, kai tsaye inda suka saba yin mittin ya nufa yana tafe yana kiransu a waya cikin kankanin lokaci suka haɗe a gidan kamar dama duka suna hanya. Amiantu kuwa tana ganin sun fita ta saki ajiyar zuciya,mus ab bai ce da ita ko mai ba bai tambayeta ba, wanka kawai ya bata umarnin ta yi ya kwaso mata kayan makaranta, anan ta shirya tsaf sannan suka fito a tare suka karya. Yau ma shi ya kaisu school ɗin ya kuma yi mata kashedi da idanunsa masu sanya ta ladabin dole. Har yanzu amiantu ba kowane malamai ta sani ba kasancewarta sabuwar ɗaliba,a period ɗin karshe wani malami ya shiga tunda aminatu tazo makarantar bata taɓa ganinsa ba sai yau, shi yasa tunda ya shigo ta saki hanci da baki tana kallonsa har ƴan ajin suka miƙe suka gaisheshi suka zauna aminatu tana can ta shanya hanci da baki tana kallon tulelen cikin da a iya saninta mata ne suke dashi su din ma idan suka kusa haihuwa amma yau ga mamakinta sai taga namiji da ƙaton cikin haihuwa yau ko gobe,har ya fara yi musu aiki aminatu na kallon cikin mutumin nan ita so take ta gano ko da kafar jaririnne saboda da ta kai gaba da kyau,tun tana toshe bakinta dan kar dariyar da take boyewa ta bayyana har dai ta kai ga ta kasa hakan. Dariyar da ta saka ne ya janyo hankalin ƴan ajin har dashi kansa malamin, gani su kayi ta yi point hannunta kan cikin malamin tana ci gaba da ƙyalƙyala dariya har da su waɗowa ƙasa tana "cewa dan Allah kuyi wallahi ba zan iya jurewa ba saboda naga abinda ban taɓa gani ba arayuwata namiji da cikin haihuwa, to malam Allah dai ya raba lafiya" ta faɗa tana mai ƙara kwashewa da dariya,duk yadda yaran nan suke tsoron uncle muda sai da aminatu ta sanya suka kwashe da dariyar da ta kuma harzuƙa uncle muda,nuna ta yayi da yatsa kafin cikin wata irin ƙwafa ya fita daga ajin, nan fa aminatu da yan ajin suka ci bana da kwasar dariya. Shigowar uncle muda yasa duk suka nutsu amma aminatu ko ta yi shuru da zarar ta kalli tulelen cikinnan sai dai kaji ta kwashe da dariya,babu zato babu tsammani ta ji an ɗaga ta sama cak an yi waje da ita,bai dire ta a ko ina ba sai tsakiyar filin da suke yiwa ɗaribai punishment,ganin ƙatuwar bulalar da ke hannunsa gashi kuma yana naɗe hannun riga yasa amimatu ta ce kafa me naci banbaki ba, ko kunya haka ya shiga bin amimatu suna zagaye filin amimatu bata bar dariya ba saboda duk takun da uncle muda yayi sai cikinsa yayi halara yayi girgiza gashi kuma ya dage gudu yake sai ya cimma amimatu ita kuma hakan ba ƙaramin sakata nishaɗi yake ba dan dariyarta take ci tana cewa, dan Allah uncle idan ka haihu ka faɗa mana muzo mu tayaka murna ka rabu da halara ta yi girgiza Allah yasa dai babyn kar ya ɗauko halinka". A cikin wannan yanayin aka tashi, tuni hankalin dalibai ya yo Kan uncle muda da yaƙi gajiya da bin amimatu kamar abin asiri duk inda ta yi tana masa dariya da gwalo haka zai bita idan yayi kamar zai kamata sai ta kuma kufcewa tana ƙyalƙyala dariya, ƙarshe dai sai ga uncle ya ci tuntuɓe da takalmin amimatu da tasa masa tana sane, ruf da ciki ya faɗa aiko amimatu tasa ihu tana kiran taimako" wayyo a temaka cikin uncle muda zai zube uncle muda yana naƙuda kuzo a kaisa a asibiti"dagowar nan da amimatu zata yi sai ko idanunta cikin na bos mus ab da yake tsaye a gun tun kusan mintuna biyu dan dawowa yayi ɗaukarsu saboda shima gida zai koma akwai aikin da zai yi a can. Sum sum ta mike ta bar wajen da uncle muda yake ta ƙoƙarin tashi yana faman antayawa amimatu zagi kamar dan maguzawa,kallonsa mus ab yayi yana jin wani abu can kasan ransa akan zagin da yake yiwa amimatu, to amma ya ya iya ita taja kuma bata da gaskiyar da zai ɗau matakin zagin da ake mata,sai dai bai ji a ransa zai bada hakuri ba dan haka ya wuce gaɓa ta bishi kamar munafuka,sauran malaman ne suka kori daliban da suka ƙi tafiya suna kallon uncle muda suna tuntsura dariya,baran ma ƴan ss, cike da borin kunya uncle muda ya bar makarantar yana tsinewa amimatu. Khalid tuni yana mota yana jiransu,ko kallonta bai yi ba ta buɗe bayan ta shiga tana muzurai duk da tasan cewa ba zai daketa ba, Khalid ne ka dai yake ta surutunsa bakin amimatu ya mutu tunda tasan ta yi laifi amma fa duk da haka idan ta tuna cikin uncle muda sai ta buya ta yi dariyarta. Suna shigowa ta yi saurin fita daga motar, dakin innawuro ta wuce ta cire uniform sannan ta ci abincinta a dakin,daga nan Khalid yazo kiranta malam yazo dan haka ta bishi suka tafi, sai magriba suke tashi daga makarantar shi yasa har ta manta da laifin ta na ɗazu ta fara harar wani leke kawai take tana neman abinda zata janyo magana amma ta rasa,sai da malam ya tafi sannan suka nufo gida ita da Khalid dan suhaima tana rigasu gamawa,a nan take bawa Khalid labarin uncle muda suna yi suna tuntsura dariya harsuka shigo falon,dakin innawuro ta kuma wucewa ta yi yar fakinta daga nan ta kuma fitowa. Idanunta akan mutane ukun da suke shigowa ya sauka ko ta ce huɗu har oga mus ab,tsohon najadu kamar yadda ta sawa dadyn zahida sai kuma dayan da bata san sunansa ba da kuma Abby, gani tayi sun nufi kujerun dining kai tsaye hakan yasa tayi saurin bin bango ta riga su isa,surutu kawai suke cike da farinciki da alama sun yi nasara akan aikin da zahida ta yi dan duk ka kalli fuskokinsu zaka gane hakan,zama suke shirin yi akan kujerun dining din sai kawai ganin daddy zahida a kasa dabar dan sai da yazo yana shirin zama da ƙarfinsa sannan amimatu ta zare kuejrar daga wajen ta matsara da ita can gefe ita kuma ta boye bayan labule tana toshe bakinta dan ƙiris ya rage ta tonawa kanta asiri ta hanyar dariyar da take shirin saki. Sai dai kuma bata san cewa ta yi shuka a idanun makwarwa ba ne dan akan idanun mus ab ta tafka tsiyartata, sosai dadyn zahida yaji zafin faɗuwar da yayi , sannu suke ta yi masa da tambayarsa ya aka yi hakan ta faru ,bai ce musu komai ba dan yana tunanin aljanun aminatu ne zasu yi masa irin ta office ɗin directer tunda shi ya bada shawarar azo nan a yi celebration dan kawai ya samu yaga aminatun, dan haka ya samu ya mike daƙyar yana cije baki ya janyo kujerar ya zauna a ransa yana cewa wallahi duk abinda zaku yi min sai naga aminatu. Amimatu da taga dai dole zaman zasu yi sai ta kuma saɗadawa ta fita ta waɗa kiching, ɗan jim ta yi saboda ko mai an riga an jera babu wani abu da ya rage da za a akai musu, mus ab kuwa ganin ta bar wajen yasa ya ɗan girgiza kansa tare da hayewa sama yana fadin Allah ya shiryaki ange...sai kuma ya kasa karasa faɗin kalmar tare da ɗan lumshe idanunsa da buɗe su a lokaci ɗaya . Amimatu na cikin tunanin abin yi ta ji Muryar Abby na ƙwalawa larai kira bai tsaya ta amsa ba ya dora da cewa ki kawowa daddy zahida Jinja drinks ɗinsa na fama" tsalle aminatu ta yi har da rawa da juyi sannan ta shiga haɗa Jinja kamar yadda taga nana nayi sai da ta gama tsaf Jinja fa ta ji citta da barkono abin ba'a magana dan ita kanta da ta ɗanɗana saida ta yi ta fifita harshenta tana zaroshi waje saboda azabar yaji, anan larai ta shigo ta kofar baya, dan haka aminatu ta miƙa mata tana cewa "gashi ki kai musu nana ce ta haɗawa dadyn zahida,dama ji nayi tana cewa kizo ki dauko ni kuma na shigo kiching ɗin zansha ruwa shi yasa zan tafi musu dashi amma tunda kinzo karbi aikinki ba zan karasa ba" oh Ni larai da waya saki ki yi na farkon yar nema kawai" larai na fita aminatu ta fara ɗebo shoki da skelewo, yau fa tsohon najadu za a leka a dawo", Larai tana kawowa ya cika kofi ya ɗaga yayi masa zuka ɗaya dan ba yayiwa Jinja Shan wasa, sai da yayi kofi biyu kyawawa sannan ya fara gumi da fifita da hannu kamar tsohon kuturu,kafin ka ce me ya fara fita hayyacinta dan take ya fara dukan kansa yana wani irin kakari kamar zai mayar da hanjin cikinsa. Da gudu su Anne da Nana da suhaima suka fito jin gidan ya ruɗe da hayaniya lokaci ɗaya,aminatu dake kiching da gudu ta fito itama kai tsaye ta nufi inda dadyn zahida yake maƙure da maƙogaransa yana shirin margayawa, ta ce" buɗe bakinka na zuba maka maganin kauda zugi haka ake yi a rigarmu yanzu zaka ji baka jin komai amma da na zuba maka ka fara gauraye bakinka dashi sai kayi saurin haɗiyewa" a wannan lokaci baya fahimtar ko mai dan haka aminatu ta samu ya buɗe bakin ta afka masa abinda yake hannunta, wayyo Allah ta kasheni mutuwa zanyi" abinda suka ji daddin zahida na faɗa ke nan kafin ya faɗo daga kan saman kujerar dining yana wani irin furje furje kamar wanda ake zarar ransa....... Jama a me kuma aminatu ta kuma ɗirkawa tsohon najadunnata🤣🤣🤣 Yanzu aka fara wasan in dai aminatu ce baku ga komai ba aradun Allah 🤣🤣🤣🤣 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg16* Dai-dai lokacin zahida ta shigo falon,ganin daddynta a cikin wani yanayin yasa ta jefar da Jakarta tayo kansa tare da ture aminatu da ta maƙure hannunta akan bakinsa ala dole sai ya shanye gishirin da take kira maganin Kore yaji,dan ubanki matsa zaki kashe shi ne da surkullenki? daddy me ya faru wannan ai gishiri ne zai illataka wa ya ce a ka gishiri?"cikin sauri suka maida kallonsu kan aminatu jin zahida ta ambaci gishiri,tura ƙaramin bakinta ta yi tana wani mis mis da baki ba tare da abinda take fada ya fito fili ba,Nana ce ta ce aminatu da gaske gishiri kika bashi?"ɗaga kai ta yi dan tabbatarwa sai karaf suka haɗa ido da mus ba,kallon yau zaki gane kurenki yayi mata, hakan yasa ta fara kokarin guduwa dakin innawuro sai dai ina tamakaro dan taku daya zuwa biyu ya cafkota. Anne ta ce "ke dai wannan yarinya kin zama annoba ke kadai duk kin rikita gida" ƙasa ƙasa aminatu ta watsawa annen kallon kema zanzo kanki, jan hannunta mus ab yayi suka fice daga falon,yayin da har yanzu daddy yake cikin mawuyacin hali duk muguntarka idan ka kallesa sai ka tausaya masa, Abby da alahji garba ne suka ƙamashi suka fita da shi dan kaisa gida. Kowa ya watse ya bar falon sai zahida da take tattara jakarta,har zata wuce sai kuma ta dawo ta ɗauki jog ɗin jinjar da daddy yasha ta kafa kai ta kwankwada ba tare da tasan cewa wannan jinjar ce musabbabin rikicewar daddyn ba,daki ta wuce kai tsaye tun tana jin abin wasa_wasa tana ƴan mita da cewa "tsabar iskanci yau lemon yaji ma aka yi musu ba dole daddyna ya shiɗe ba yanzu haka ma ana sane aka yi masa tunda an san shine yake sonta sosai aiki.....kasa karasawa ta yi saboda wani irin gumin azaba da ya fara keto mata bakin kuwa ta kasa rufe shi saboda tsananin azabar yaji da ɗaci da ko mai ba na kwamacalar aminatu. Binsa kawai take kamar raƙumi da akala hankali kwance dan tasan ba wani abin kirki zai yi mata ba, yadda yake kamar beban nan babu wani hukunci da zai iya yi mata, wannan gardin ɗin da suka taba zuwa da Khalid shi ya kawosu, zama yayi a kan kujerar simintin da take gun, ita kuma ya nuna mata da ta tsugunna,tsugunnawar ta yi a gabansa tana jiran umarni na gaba dan har yanzu bata kawowa ranta wani hukunci zai yi mata ba. "Me yasa kike son Jan magana me yasa kika yiwa daddy abinda kika yi? Ina kallonki fa ke kika janye masa kujera shine again kika kuma hada masa Jinja me yaji ko?"Marmara manyan idanunta ta shiga tana ɗan sosa dogon hancinta, shike nan samun gwiwowinki a ƙasa ki daga hannunki sama ki rufe idanunki", kai tsaye ba tare da wata gardama ba tayi yadda ya ce dan a tunani ta abin na wasa ne. Tofa gwiwowin aminatu sun fara amshin shata tun amintunan farko, kasancewar wajen dutsunan wutane ƙananu, take ta fara ƴan muskuce muskuce na alamun gajiya, jin yayi banza da ita yasa ta fara buɗe ido daya sai taga hankalinsa yana kan laptop ɗinsa yana ta aiki cikin nutsuwa da kamalarsa da yake da ɗa bayyana kwarjininsa da kyawunsa a fili, buɗe ɗayan tayi tana satar kallon fuskarsa da hasken farin watan da ya haske gun ya kuma haskashi, cikin wata irin shagwababɓiyar murya wadda ke bayyana tsantsar yarintarta ta ce "ayya Hamma MUS'AB aradun Allah jikar innawuro ta gaji ayi mata afuwa ba zata kara ba daga yau" . Bai ko motsa ba bare tasan yaji abinda take faɗa, bata daddara ba ta ci gaba da yi masa magiya amma ko ajikinsa,daga ƙarshe ma sabon aiki ya sata dan kuwa cewa yayi ta kama kunneta saboda wannan nishaɗi yake sata ga dukkan alamu,shima kamun kunnen a cikin mintina biyar ta fara haɗa zufa dan ya fi na baya wahala sai ga aminatu na kuka wiwiwi amma Hamma MUS'AB bai tausayawa boɗɗo jikar innawuro ba. A can bangaren zahida kuwa zan iya cewa tafi aminatu shan wahala dan sai da ta yi tik a daki duk dan ta samu Salama amma ina ji take kamar ana kara azabar yajin a maimakon ya ragu maƙogaranta kuwa kamar zai yage,har kusan sha biyu ne dare zahida na abu guda cikin azaba da raɗaɗi. A dai-dai lokacin aminatu ta zame kasan gurin tana ci gaba da gursheken kuka harda su majina a ranta kuwa babu irin Allah ya isar da ba ta zabgawa mus ab Dan bata taɓa tunanin cewa mugu ne har haka ba,dubanta yayi cikin nutsuwa fuskar nan babu annurin murmushi ya ce" cewa nayi ki zauna? Ai kwana zamu yi a wajen nan a haka oya tashi ki ci gaba" kasa motsawa aminatu ta yi dan kuwa da gaske duka ƙafafunta sun rike har da cinyoyinta,zai yi magana wayarsa ta yi haske alamun kira, daga wayar yayi ganin sunan Nana ya fito akan screen din wayar, Assalamu alaikum Nana Barka da war haka?" Barka dai mus ab, ta ɗora da cewa ina aminatu?". Dan duban aminatun yayi sannan ya bawa Nana amsa da cewa "gata nan punishment dinta nake yi"ajiyar zuciya Nana ta sauke sannan ta ce "a'a mus'ab kabarta haka nan kasan aminatu har yanzu yarinya ce ko shekara sha biyar bata cika ba,ba ta haka ya kamata ka gyarata ba" wani zazzafan huci ya fesar yana ɗan kallon aminatun da ta ke zaune dirshen tana kuka,kana ya ce."Nana bata ji yau din baki ga abinda ta yiwa wani uncle dinsu ba a school " murmushi me sauti Nana ta yi tare da cewa duk da haka dai a yi haƙuri, karfa ka manta ita din matarka ce dole duk abinda zaka yi ka dinga tunawa da hakan"ok in sha Allah" ya fada yana sauke wayar daga kunnesa. "Oya tashi muje gobe idan kin koma school ki kuma jan magana" ya faɗa yana miƙewa tsaye,maƙale kafaɗa ta yi sannan cikin kuka ta ce " waye zaije school ɗin bayan babu ƙafar zuwa wallahi anci zalina kuma sai Allah ya saka...haɗa idon da suka yi ya sa ta waske da cewa ya sakawa wanda aka zalinta kamar dai irinsu gaɗɗafi da garzali ya ci zali da irin su arɗo da suke dukan jama ar gari da dai saura makamantan hakan", mus ab bai san sanda wani dan ƙaramin murmushi ya kufce masa ba sai dai bai bari hakima mandiyar ta gani ba ya shanye abinsa, dan sarai ya gane da shi take. Gaba yayi abinsa,ganin yana shirin barinta ita kadai yasa ta kuma tsala wani kukan da har saida ya runtse idanunsa saboda yadda ya shigar masa kai, "Ni ba zan iya tashi ba innawuro ki taimakeni za a kasheni banji bangani ba Ni wallahi da zaman garin nan gwara zaman riga",cak ya ɗagata Yana kallon fuskarta da ta yi caba caɓa da hawaye,tana sane ta cusa fuskarta a jikinsa duk ta goge masa hawaye da majinar da ta tara, shima yasan tana sanen amma bai ce ko mai ba a haka ya wuce da ita har bedroom ɗinta ya kwantar da ita akan gadonta. Bayi ya shiga ya haɗa mata ruwa me zafi sannan ya dawo ya ce da ita taje ta gasa jikinta,banza ta yi dashi ba tare da ta motsa ba,a hankali ya zauna a kusa da ita sannan ya kama hannunta ya nutsar dashi cikinnasa take hakan ya bada wani yanayi me sanyi,"aminatu" ya furta tamkar wanda yake lallaba sunan,ɗago idanunta da har yanzu basu bar tsiyayar hawaye ba ta yi tana kallon cikin idanunsa kai tsaye da shima yake saka nasa cikinnata,da sauri ya janye nata tare da son janye hannunta da yake cikinnasa,amma sai taji ya janyota jikinsa gaba daya tare da cusa fuskarsa cikin wuyanta yana busa mata wuyan zuwa cikin kunnenta,.kafin a hankali cikin wata irin murya da nata sanshi da ita ba ya ce "ba zaki gasa jikinnaki ba?" Kuka ta fashe da shi tana cewa Ni bazan iya tafiya ba cinyata kafata duka ciwo",kafin ta dire zancanta ya ɗaga ta cak ya nufi bayin da ita,cikin ruwan ya sakata sannan ya zame rigar dake jikinta,da sauri ta rufe ƙirjinta da suka fara tasawa irin na matashiyar budurwa tana cewa "wallahi ka rufe idanunka idan ka kalleni zan gayawa innawuro tunda ta ce babu kyau"kin san da hakan ki ke so kullum nayi miki wankan da kaina ai kina sane kike ƙin yin wankan dan nayi miki" ya karasa maganar da ɗage mata gira,take ta shiga watsa masa ruwan tana cewa shike nan innawuro wayyo innawuro ya gane miki jikin aminatunki" bai saurareta ba ya shiga gasa mata jikinta bai rabuda ita ba har sai da ya tabbatar taji dadi dan yana kallo har wani gyangyadawa take yi saboda yadda taji dadin jikinta. Ashe shi bai sani ba har ta yi bacci saboda yadda taji dadin jikinta, dan haka ya gyarata ya kwantar da ita kamar wata jaririya, janyo abin rufa yayi ya rufa mata iya wuyanta sannan ya yi mata addu'a ya shafa mata,dan sunkuyowa yayi ya sumbaci jajayen labbanta masu taushi yana kuma kallon fuskarta da take tuna masa da fuskar mahaifinta da kuma al'amarin aurenta da ya zamo wani al'amari me ban mamaki ga dukkansu, Allah ne kaɗai yasan dalilinsa na hada wannan aure ba tare da kowannensu ya ankara baz tabbas akwai abinda Ubangiji ya ɓoye wanda shine dalilin da ya kaisa rigar a wancan lokaci, shi yasa yake jin aminatu a ransa matsayin ƙanwa ta jini, zai kula da ita kamar yadda zai kula da Khalid da suhaima zai bata ilimi da tarbiya zai bata ilimin addini wanda shine ja gaba kuma shine zai zama abin haska mata hanyar da take lulluɓe da gagarumin duhu, zai tsaya mata zai ci gaba da riketa amana da ta dukiyarta har zuwa lokacin da ko kai zai warware, in sha Allah da kansa zai zaɓa mata mijin da zai kula da ita da rayuwarta, da wannan tunanin ya fita ya bar ɗakin tare da rufota. Zahida dai baccin wahala ya kwasheta bayan ta gama rawar sabada a ɗakinta ita kadai ba tare da taimakon kowa ba. "Daga wannan matakin saura mataki na gaba wanda shine na karshe da zamu samu ƴancin kanmu daga biyan bashin da ya rataya akanmu dan haka mu dage mu kuma tsayawa zahida domin ta samu nasarar cire mana wannan zuciyar domin rasa ta daidai yake da rasa ko kai namu, saboda idan bamu yi kokarin biyan Alhaji Laminu da wannan zuciyar ba to kuwa da zuciya mafi tsada da daraja zamu biya shi a gaba, ka dai san yadda zuciya irin wannan ke wahala kuma kasan adadin mutanen da suka mutu duk a dalilin neman zuciyar nan sun mutu ba mu dace ba su basu da ce ba,kaga kuwa dole mu kasance cikin farinciki da kasancewar samun zuciyar a da ta yi daidai a wannan gabar tunda waɗan can zuciyoyin killatattune wanda dama can mun riga da mun san cewa a daidai suke......a matukar firgice aminatu ta farka tana mai share zufar da ta jika mata jiki. Tun ranar da ta ji wannan maganganun shike nan suka zamar mata abin bita sun zauna a ƙwaƙwalwarta sun yi daram ba tare da tasan ma'anar hakan ba,gashi kuma ta kasa gayawa kowa bare a fassara mata kalaman, a hankali ta koma ta kwanta tana cewa zuciyar waye? me za a yi da ita? dama ana cire zuciya? Abby da Shi da wa yake wayar nan? Me yasa kalaman suka zauna a kaina kamar karatu? Ni meye nawa a ciki? Rufe idanunta ta yi tana hada kalaman Abby da na baffanta,(aminatu duk da cewa ke yarinya ce amma nasan kina da baiwar da idan na fadi abu zaki riƙeshi koda baki san ma'anar sa ba,aminatu ke yar baiwa ce Allah ya halicceki domin ki zama sanadin tsirar wasu rayuka da ke cikin al ummar musulmi, Allah ya halicceki da baiwar ki ne domin ki zama silar kifar da zalunci, aminatu zuciya wata aba ce da mutum idan babu ita ba zai taba rayuwa ba,dan haka Ni ba zan yi rayuwa ba tunda bani da zuciya kuma a yanzu ba zaki iya cetona ba, amma nasan watarana zaki ceto dubban mutane zaki ƙwatar musu da ƙarfin ikon Allah,shi yasa na bawa wannan yaron ke dan ina so ki samu ilimin addini me zurfi kinji aminatu na"a lokacin aminatu bata fahimci komai ba hasalima ta manta da duk maganganunsa sai kuma yanzu suke dawo mata filla filla tamkar yanzu yake karanta mata su....idan haka ne kenan akwai alaƙa da wancan maganar baffanta da kuma ta Abby to meye alakar tasu? .. Kamar yadda ya saba yana dawowa daga masallaci ya nufi dakinta, daidai lokacin da ya buɗe daidai nan aminatu ta ji ta cikin abu ke danshi dan haka da sauri ta buɗe idanunta tana kallon gadon,ware manyan idanunta ta yi kafin ta kurma wani uban ihu ta faɗi a sume.........✍🏾 Tofa ana wata ga wata akwai fa badakala na ce muku akwai badaƙala wanda bai biya ya karanta cikin nutsuwa ba wallahi dadi da karuwa sun barshi, dan shifa wannan labarin komai ya haɗa, ku shirya ku kimtsa dan suburbuɗe salon da nazo muku da shi a wannan karon. Wannan Pg ɗin na yi kyautarsa ga Mammana yusra. Ragowar ma Pg dinku na gaba ina Allah ya bar kauna✍🏾 8064537048 Opay Fatima yushau adam [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg17* Da wani irin zafin nama ya ƙarasa buɗe ƙofar, kai tsaye ya haye gadon yana kiran sunanta dan fa aminatu da gaske ta sume,dagotan da zai yi sai ya ga jini a kan shimfidar da kuma jikinta duk ya ɓaci,zubawa jinin ido yayi wanda a take ya gane ko jinin me ye,samun kansa yayi da sakin wani ƙawataccen murmushi sha anin aminatu Abin takaici da dariya ne yanzu jinin al'adar take sumewa ko da yake ba abin mamaki ba ne tunda duk wata mace da yanayin yadda take karbar nata a farkon zuwa bare kuma irin su aminatu iyayen sakarci. Ruwa ya ɗebo ya zuba mata, ajiyar zuciya taja tare da buɗe idanunta, kallon jikinta ta kuma yi, aiko da gudu ta miƙe kafin mus ab yayi wani yunƙuri har ta kai ƙofa ta fice tana ihun kuka da kiran innawuro, "innawuro kizo an yanka Ni wallahi gidannan ƴan ya kan kaine kizo mu gudu kar kema su yanka ki" da gudu kuwa sai ga innawuro da mayafinta tana cewa 'muje boɗɗo,a ina aka yankaki? Ey tabbas kuwa ga jini a jikinki"cikin zafin nama mus ab ya fito daga ɗakin yana ƙoƙarin riƙe aminatun dan kar ta tonawa kanta asiri, amma ina tuni kowa ya fito Anne banda masifar an hanata bacci babu abinda take yi,suhaima da Nana kuwa tuni suka fahimci abinda aminatu kewa ihun an yankata,duk inda ta yi musu ab yayi niyar kamata sai ta sa ihu tana cewa "dan Allah kuyi mana rai ku barmu mu koma riga Ni na fasa auren ɗan birnin KARKU kashemu kar ku cire mana zuciya dan Allah ku yi hakuri"....karaf sai a kunnen zahida wanda kalmar aminatun ta yi matukar girgizawa, KARKU cire mana ZUCIYA"zahida ta maimaita kalmar akan harshenta. Karasa saukowa ta yi tana mai kafe aminatun da ido so take su haɗa ido ko zata fahimci wani abun daga aminatun, to a ina aminatu ta ji kalmar nan?maganar nana ce ta katse mata tunaninta in da take cewa da amina tazo gareta babu abinda za a yi mata,kallonta aminatu ta yi cike da tsoro da shakka,a hankali nana ta matsa kusa d ita ta ci sa a bata gudu ba,dan haka ta kama hannunta tana cewa yi hakuri kinji aminatu babu wanda ya yankaki muje nayi miki bayani",sai da ta kalli innawuro wadda ita sai a lokacin kunya ta rufeta dan ta gane jinin al'adane ta fara, ganin innawuro bata nuna damuwa ko tsoro na sai ta bi Nana ba tare da ta kalli inda mus Abu yake tsaye yayi foldin hannayensa yana kallon ikon Allah, ajiyar numfashi ya sauke a can ƙasan maƙogaransa Sannan shima ya wuce upstairs yana ɗan dafe kansa da yake sara masa. Cikin nutsuwa da dabara irin ta wayayyun mata masu ilimin addini Nana ta fahimtar da aminatu ko menene ajikinta,ta ƙare da cewa ina fata kin gane?" Jinjina kai aminatu ta yi sannan ta ce"dama wannan shine jinin da innawuro take faɗa min to amma ya naganshi da yawa kuma yaushe zai ɗauke?"murmushi nana ta yi sannan ta ce muje na nuna miki yadda zaki gyara jikinki daga baya zan yi miki bayanin komai".sannu sannu Nana ta gyara aminatu tana yi tana mata bayanin ko mai cikin nutsuwa yadda zata fahimta, hatta da wanka sai da ta koya mata dama ta san ba ayin salla idan yazo. Ranar dai kusan yini suka yi aminatu da Nana suna karatun fiqhu, Nana tasha mamakin brain din aminatu dan kuwa a yini guda ta bata mamaki saboda ko makaranta bataje,ita kuma Nana ta tsaya tsayin daka domin ta gyarawa aminatu ibadarta dan idan bata san yadda zata tsarkake jikinta daga najasa ba to babu amfanin ibadar,a ranar Nana ta yi iya yinta ragowar kuma ta barwa suhaima da malam. Tun daga wannan ranar aminatu bata kuma kara kula mus ab KO haduwa su kayi ɗauke kai take ta canja hanya,kwananta biyu ya ɗauke saboda dama duk kusan na farko haka yake baya jimawa ko kuma yayi miki wasa kafin ya zama normal. Misalin ƙarfe takwas na dare,aminatu zaune a falo ita da Khalid suna yin assignment Khalid Yana da kokari sosai shi yasa yake taimakawa aminatu da wasu abubuwan da ya sani tunda tafi shi aji,a yanzu dai aminatu babu laifi dan tunda yan aji su kayi mata dariya bata kuma yin kalar nata turancin ba sai dai ta yi irin nasu wanda idan ta yi Sai dai ka samu ƴan gyararrakin da sai a hankali zata goge,tunda a halin yanzu tana ajin masu zana jarabawar ss,ƙamshinsa kawai tashaƙa ta haɗe rai har da gunguni,cikin yanayinsa na kullum ya karasa shigowa idanunsa akanta, sai yaga ta kuma yi masa girma ko dan girman ya kamata ne ko kuma ɗan ya kwana biyu bai ganta ba ne oho,fuskarsa babu yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar Khalid yana ɗan shafa kansa cike da kulawa da kauna, Khalid ya ce "daddyna zanje wajen adda suhaima ta yi min nawa assignment din"jinjina masa kai kawai yayi, da gudu Khalid ya kwashi littatafansa ya bi dogon corridon da zai kaisa dakinsa da na suhaima. Itama kwasar littafanta ta yi ta yunƙura ta miƙe tana faman harhaɗe fuska tare da yin magana ƙasa ƙasa,"dole dai sai mutum yayi abinda za a ci zalinsa sannan za a sami abin cin zalin"bakinnata kawai yake kallon yadda take ta faɗe fadenta ba tare da tasan yana jinta ba, dan shi kan mus ab ba dai ji ba,kafin ta bar wajen ya rigata, bata yi zato ba sai jinta ta yi ajikinsa, shi kansa mus ab din bai sai yadda hakannta faru ba shi dai kawai yaji ya kasa sarrsafa kansa da jure wannan shan kamshin da yajin aikin da take masa, tamkar wani mayen karfe haka ya ji zuciyarsa da gangar jikinsa suna mannuwa izuwa gareta, kokarin ƙwacewa take yi tana tura ƙaramin bakinta cikin yanayin jin haushinsa da ta tsinci kanta tun daga waccan ranar, "Ni ka rabu dani babu ruwan da kai"cusa kansa yayi a wuyanta yana shaƙar kamshin da ya fara kama jikinta wanda wannan aikin duk na Nana da suhaima ne,cikin wata irin murya da ya ce."kin yi wankane?"wane irin kwanka kuma? wai ku gidan nan baku da aiki sai wanka ɗazun nan fa Nana ta sani nayi wankan amma har an fara tambayata na yi wanka aradun Allah saboda wankan nan zan gudu haka kawai a yi ta takurawa mutum"tunda ta fara maganar yake karewa jajayen lip dinta da kallo daya zaka yi musu kasan cewa zasu yi taushi ido, yana kuma jin wani abu yana zagaye jikinsa da duk wani ruwa ko jini da suke aiki a jikinsa,shi sam bai san wani abu wai shi feeling ba dan yanzun ma bai abinda yake kokarin aikatawa ba,a hankali yake matso da lip ɗinsa kusa bayan ya dago fuskarta da tafin hannunsa yana kallon cikin idanunta, kallon kai tsayen da yake haifarwa da aminatu zazzabin cikin ƙashi,sai da ya haɗe fuskarsa da tata hancinsu na gogar juna bakinsu na gogar juna, buɗe baki ta yi tana cewa "dan Allah ka rabu dani wallahi nana ta ce idan na bari namiji ya taba ni ciki zanyi irin na uncle muda"ta ƙarasa maganar hawaye na taruwa cikin oily eyes ɗinta,yadda take maganar laɓɓanta na gogar nasa duk sai ya nemi duk wani kuzarinsa ya rasashi wanda baisan ya a kayi ba sai tsintar kansa yayi yana tsotse bakin aminatu tamkar ya samu alewar madara. Idanun aminatu budewa su kayi sosai tana jin wani sabon al'amarin da bata taba Kasancewa cikinsa ba ko a TV bata taɓa gani ba ko a labari bata taɓa ji ba, sai yau da ya faru akanta tare da mutumin da bata taba tunanin ko a hanya zata iya haɗuwa dashi ba,slowly yake bin duk wani loko da sako na cikin bakinta yana lashewa, aminatu kuwa tsananin shock ya hanata ƙwatar kanta daga hannun ɗan gidan Nana. Ƙarar fashewar abu shi ne ya dawo da mj hankalinsa sai dai duk da hakan bai saki aminatu ta bar jikinsa ba,aminatu ma zahida take kallo hannunta yana jini saboda glas cup din da ta matse a hannunta ya fashe bayan wanda ta watsar a wajen, hakan yasa hannunta yake jini sosai kamar ansa wuƙa an yanka, dukkansu an kasa samun wanda zai ce wani abu,zahida dai tsananin tururi da bakin ciki su suka hanata yin wani hargagi,wai yau mus ab ne yake shan bakin wata ba ita ba , shan da bata tunanin a tsawon rayuwarsu ya taba yi mata shi, shaukin da ta hango a tare dashu bai taba shigar kwatankwacinsa idan suna tare ba,sai akan wannan afiruwar da ko makerin budurci bai gama ƙerata ba, shin yaya zata yi da wannan bala'l da ya tunkaro rayuwarta?" Tana can tana tunani bata sani ba mus ab ya janye aminatu ya kaita dakinta har yayi mata shirin bacci ya fito ya haye upstairs,sai da ta ji takunsa sannan ta dawo hayyacinta a firgice tamkar wadda ta farka da ga mummunan mafarki,sai kawai ta dinga ƙoƙarin ta maida al'amarin mafarkin dan kawai ta samu sa adar zuciyarta. A hankali ta tura kofar dakinnasa zuciyarta na harbawa,dan ji take yi tamkar hakan babbar faduwa ce bin miji, a zuciyarta babu abinda take sai tsinewa aminatu da kaf ahlinta,yana zaune tsakiyar gadonsa aikinsa yake a laptop cikin nutsuwa da kamewa kamar kullum,yana jinta amma bai ɗago ba har sai da tazo ta zauna a gefansa tana kallon screen ɗin laptop din, "mj magana nake so mu yi da kai amma naga baka da niyar saurarona"banza ya yi da ita wanda hakan ya kuma tunzura zuciyarta halin na motsawa, "yanzu mus ab kamar ni na ya da ego ɗina nazo gareka Amma ka kasa bani hankalinka wai me yake damunka anya kuwa babu wani abu da ake yi dan a rabamu?". "Abinda kika zo faɗa kenan?"ya tambayeta fuskarsa na kan laptop ɗinsa,shuru ta yi tana jin zuciyarta na kasa jura, mikewa ta yi tana kallonsa a wani irin fusace kana ta ce " shike nan muje zuwa tunda abinda ka zaɓa kenan, amma ka sani wallahi wallahi wallahi baku ci bulus ba kaida karuwar dajintaka ina nan tafe kanku daga kai har ita ba zan ƙyaleku ba" daga haka ta fice daga dakin tare da buga kofar kamar zata tsige ta daga muhallinta,sai dai shi wanda take dominsan babu abinda ya girgizasa dan idan ka dubesa sai kayi zaton tun ɗazun shi kaɗai yake babu wanda yazo inda yake. ******** Yau ake hada haɗar ɗaukar azumi, idan ka kalli aminatu sai ka dauka bata da lafiya, duk inda ta samu kwanciya take yi, taki kula kowa, sai dai duk mintuna zaka sameta a kiching tana yiwa cikinta dura,ita ko aminatu babu abinda yake sata fargaba illa wannan karon dole ta yi azumi full babu gauraye. Koda innawuro ta tasheta yin sahur, haka ta zage ta dibi abinci acewarta bata son ta ji yunwa, innawuro ta ce haba boɗɗo ki yiwa cikinki adalci mana ke kullum bakyason abinda zai rabaki da cin abinci shi yasa kullum kike hawa kamar kazar gona",sai da ta daga harkar ruwa ta kwankwada sannan ta ce."innawuro ba zaki gane ba wannan karon ba babu batun konturola dole mankuli zuryan zanyi kinga kuwa dole na bawa cikina hakkinsa har na ranar goben",jinjina kai innawuro ta yi tare da cewa to Allah ya kawo sauki da hankali, Allah ya sa dai manƙulin za a yi ba konturolar ba",haba innawuro idan fa nasha sai na rama sittin da daya to ko kinga yi dole". Kasancewar yau asabar ne aka dau azumi babu makaranta,tun karfe sha biyu aminatu ta fara bin bango tana riƙe ciki,kowa ya mata banza, da taga babu wanda zai tanka mata sai ta tafi wajen Nana ta kwanta a jikinta tana ci gaba da rike cikinta har da guntun hawaye,dafa kanta Nana ta yi tana cewa aminatu girma fa ya kamaki dole ki koyi juriyar yin azumi acici "Nana idan ku ka bari na kai magriba banci komai ba wallahi mutuwa zanyi"ta faɗa tare da yin wani irin juyin yunwa tana riƙe cikinta [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: ❤️MATAR ƊAN BIRNI ❤️ *Pg18* "Ba zaki mutu ba aminatu dan babu wanda azumi ya taba kashewa", shiru dai kawai ta yi amma ba wai dan tana jin zata ita ɗin ba. Sosai aminatu ta jigata da wannan azumi, dan Nana sai da ta yiwa innawuro faɗa akan yadda ta sangarta aminatu ta barta bata azumi,yanzu gashi nan abin yana son zama matsala,"ta ce innawuro shi yasa fa kika ga tun yara suna ƙanana iyaye masu dabara suke barin su su yi azumi ko da guda ɗaya ne, saboda da haka yaro yake sabawa, yanzu gashi ita tun azumin farko ana fama da ita tana neman kasa jurewa". Innawuro girgiza kai ta yi tare da cewa "uhm Nana baki San wacece aminatu ba ne har yanzu,Ni kadai nasan irin wahala da faman da nake akan aminatu tun tana kucilarta har ta fara girma ina kan yi, Ni da aminatu fa zamu tashi sahur rumi rumi amma wallahi bana tashi ganin aminatu sai da kayan ciye ciye, duk nasiha da banbamin da zan yi aminatu ba zata yi azumi irin na kowa ba sai rabi da rabi,ina ji dai kina jin tana cewa yanzu mankuli zata yi ba konturola ba?" Dariya Nana ta yi tare da cewa "Allah dai ya shirya mana amma aminatu sai mun dage da addu'a, amma fa zata daina kuruciya ce", jinjina kai kawai innawuro ta yi amma ba dan ta yadda aminatu zata daina halinta ba. A daddafe dai aminatu ta kai azumin farko,haka aka kuma tashi da shi, an tafi kan na biyu,to shima dai na biyun salonsa daban dana farko. Tun misalin ƙarfe ɗaya suka ga aminatu na sunturi tana kaiwa da kawowa, idan aka ɗan jima sai ta huta, bayan mintuna kaɗan sai ta kuma tashi tana zaga gidan, har lokacin shiga kiching yayi Nana ta kirasu ita da suhaima dan dama wannan shine ka'idar Nana sam bata yadda da barin ya'yanta su tashi a sangarce ba,shi yasa suhaima ta yi bala in iya girki kuma take kan karantarsa domin yana daga cikin hubby nata,to an saka aminatu cikin sahu(wa yaga aminatu da girkin yan birni😃). Tunda suka fara Nana taga aminatu sai share zufa take tana faman yatsina fuska wani lokacin har da ɗan durƙusawa take yi, ɗan dakatawa Nana ta yi daga abinda take tana kallonta kafin ta ce "boddo wai lafiyarki kuwa ko dai azuminne?"zata yi magana kenan taji abinda take rikewa yana shirin zubowa ai da gudu ta watsar da abinda yake hannunta ta yi hanyar fita daga kiching ɗin, dai-dai lokacin mus ab ya shigo dan yanzu da la asar yake dawowa gida saboda azumi,wasu ayyukan a gida yake yinsu,fitowarta ya gani da gudu ta wada dakin innawuro, innawuro sai da ta tsorata har ta kai ƙarshen gado tana zare idanunta sai kuma ta ga ashe aminatu ce ta shiga bayi,ajiyar zuciya ta sauke tana cewa "Allah ya nuna min ranar hankalin boɗɗo". A can falo kuwa gaba dayansu fitowa su kayi daga kiching ɗin suka yi cirko cirko suna jiran ganin ta inda aminatu zata bullo,shi kansa mj waje ya samu ya zauna yana mai kallon ƙofar dakin innawuro ta ƙasan idanunsa yadda babu wanda zai iya fuskantar cewa yana kallon gurin ma bare ayi tunanin shima zaman jiran aminatun yake yi. Can jimawa kaɗan sai ga aminatu ta fito tana kuka wiwiwi, innawuro na binta tana tambayarta lafiya,Nana da suhaima ma gaba ɗaya suka yo kanta suna tambayarta lafiya?amma ina aminatu ta kasa magana sai kuka har da su sheshsheƙa tana yi tana bin bango tana kallon oga mus ab da yayi tamkar baya wajen,tana son ta faɗa amma tana shakkar fada saboda Hamma MUS'AB na wajen,janyo hannunta Nana ta yi tana cewa "aminatu meye ne ana tambayarki kina kuka me ya sameki?" Sai da ta saci kallon MUS'AB sannan a hankali ta ce "Nana azumin ya karye"subhanallahi jinin ne ya kuma zuwa" girgiza kai ta yi ba tare da ta ce komai ba, innawuro ta zaburo kamar zata buge ta tana cewa ai nasan muddin kika shiga bayi sai ji sha ruwa ai ba yau kika fara ba to ki sani tunda kika karya azumin nan sai kin yi sittin da ɗaya idan ba haka ba walakirin da kike cewa ba gajiya yake ba to kema zai biyo ta kanki dan ba gajiya zai yi da fallarki ba". Cikin kuka ta ce wallahi innawuro ba laifina ba ne na kasa jurewa shi yasa"rufe min baki sakarya wadda bata sanin ta girma dubeki gotai_gotai dake amma kin kasa azumi kin fi so kullum ki yi ta ci baki ba zai huta da tauna ba" innawuro ta fada kamar ta jibgi aminatun saboda takaici,Nana ta ce a'a innawuro wannan fadan bashi ne mafita ba, aminatu me yasa kika karya azumin?" Mutsu ta take tayi saboda yadda kallon mus ab yake sukarta babu wanda ya san cewa yana ma sauraronsu bare kallonsu, sai dai ita da abin yake taɓawa ita kaɗai take jin kallon nasa a jikinta da duk wata tsoka da jini da suke gudana a jikinta,da kyar ta iya buɗe baki ta ce "wallahi nana matsata yayi tun asuba naso yi, amma na kasa shine baizo ba sai da yaga an kusa shan ruwa, dan mugunta dan yasa ayi min mugunta banji ba ban gani ba, wallahi duk wanda ya zalunceni Allah ba zai bari ba tunda yasan bana sane na karya" innawuro ta ce "yanzu ba zaki fada abinda ya matsakin ba ko surutun banzan shi yafi Miki?"tura bakinta ta fara yi sannan ta kuma matsawa can nesa da inda mus ab yake ,kana ta ce."kashi ne fa innawuro kin san dai idan mutum ya ci abinci dole ya yi kashi to yau ban da suba ba kuma ya ki ruƙuwa." Gaba ɗaya suka ƙyalƙyale da dariya hatta da larai dake kiching ba a barta a baya ba,zama Nana ta yi a kujera cikin dariya tana cewa suhaima je ki wajen larai ku ci gaba kar muyi dare,ke kuma aminatu zo nan". A nutse cikin kamewarsa ya miƙe ya tattara kayansa ya ɗau hanyar barin falon,babu wanda ya fahimci yanayinsa sai shi da ya barwa kansa sani. Da kyar Nana ta samu aminatu ta zo ta zauna a gefanta, kana cikin tausasa murya ta ce."aminatu wa ya ce dake ba a kashi idan ana azumi"? To Nana ai dama haka ne ko ba a fadawa mutum ba ai yasan cewa ba a kashi ko tusa idan ana azumi"murmushi Nana ta kuma yi kana ta ce."to ba haka bane daga yau KARKI kuma ƙin yin kashi ko tusa ko fitsari abinci ne kawai ba a ci da duk wani abu da zai iya shiga ciki sai wasu dabi'u da ake so mutum ya daina idan yana azumi, kamar gulma shaye_shaye alfasha, da dai sauransu, in sha Allah a hankali duk zaki fahimta tunda ana koya miki, Ni dai fatana ki dage da karatu wajen Malam wanda shine zai Kore Miki duk wani jahilci da duhun kai, aminatu duk wanda bai nemi sanin Allah ba yana sane da ransa da lafiyarsa to tabbas yana cikin fushin Ubangiji kuma ba zai shiga aljanna ba,dan haka yanzu ki dage da karatun Alkur'ani da kyautatawa iyayenki kiyi duk abinda kika san zasu sa Miki albarka" idanun aminatu ne suka kawo ruwa hannu tasa ta goge sannan ta ce "Nana Ni bani da iyaye su wa zan kyautatawa a matsayinsu su ji dadi Allah ya bani lada?" Cikin sauri Nana ta goge hawayen tausayin aminatu da taji suna ƙoƙarin zubo mata, sannan ta shafa kan aminatun tana cewa,"ki yi musu addu'a ki yi duk abinda kika san suna so kiyi lokacin da suna da rai,amma ki sani aminatu kina da iyaye Ni nan nice mahaifiyarki ga kuma innawuro kakarki dan haka ki dai na cewa baki da iyaye kinji", jinjina kai ta yi ba tare da ta iya furta ko kai ba. "Yauwa aminatu MATAR ƊAN BIRNI, sannan idan kina so Allah ya dinga biya miki bukatunki akan duk abinda kika roka to ki dinga salla me kyau kuma ki daina tashi da kin yi sallah ki dinga tsayawa kina addu'a, domin Allah yana fushi da wanda baya rokonsa, kinji aminatu",aminatu ta ce to Nana zan dinga yi kuma dama ina addu'a,tunda innawuro tana tashina muna yin sallar tsakar dare duk ranar da bacci bai ci karfina sabida baffana ya ce min tsakiyar dare shine lokacin amsa addu'a saboda a lokacin kofofin amsar addu'a a bude suke haka baffa ya ke faɗa min ina tunawa a yanzu ko mai yana dawo min kaina",cikin farinciki Nana ta rungume aminatu tana cewa alhamdulillahi da samun uba irin baffa naji dadi ina da tabbacin Allah ya amshi addu'ata ya bani irin surukar da nake rokonsa ya bani", aminatu bata fahimci maganar Nana ba sai dai kalmar ta zauna a ranta. Kwanci tashi yau azumi har anci kwana ashirin, alhmadll aminatu dai an fara sabawa da azumi, har yanzu bata ƙara shiga sabgar zahida ba ko da yake ma ba haduwa suke yi ba, dan haka nan zahidar ta kauracewa duk abinda zai hadata zama da aminatun ko shan ruwa bata yi a gidan sai a gidansu kwanciyar bacci kawai ke dawo da ita gidan,babu wnada yayi mata magana ko neman sanin dalilin yin hakan. Yau dai aminatu bata azumi, dan haka sharholiyarta kawai take ita da Khalid, girki ta yi musu ita da Khalid sun yi dama dama da kiching ɗin kamar ana girkin bikin mutum biyar,laraice ta shigo kiching ɗin tana binsa da kallo kafin ta dubi aminatu da take ta sakin ɗan wake Khalid na gefanta yana miko mata ruwa tana dangwala,abin dan wake kuwa har kan hancinta,larai ta ce ikon Allah yau fa mata na girki, to idan kin gama dan waken ki sawa Anne a flet Khalid ya Kai mata dan itama yau bata jin dadi bata yi azumin ba dama nazo samar mata wani abinne kinga na huta", tsayawa aminatu ta yi da sakin tana kallon larai cike da mamaki sannan ta buɗe baki ta ce,"yanzu larai kina nufin har yanzu Anne ba ta daina yoyon jinin ba?"yar nan ki rufa min asiri ce Miki nayi fa bata da lafiya cikinta ne yake dan murɗawa kuma ai ita ta tsufa zata iya dinga hutawa ko da lafiyar ta ƙalau",taɓe baki aminatu ta yi sannan ta ce "to zamu bata ba dan halinta ba masifaffiyar mata kawai". Larai na fita amiantu ta kalli Khalid ta ce."Khalid bani fulawar can daban za ayi mata nata yadda komai zai ji daidai da tsufanta ", da sauri Khalid ya dauko fulawar ya bata, nan ta kwaɓa bayan ta zabga uwar jarkanwa a maimakon tasa ungurnu kamar yadda ta kwaɓa nasu,wani gari ta nemo wanda ake ce masa garin fulasko saboda innawuro na da basir shi yasa larai take dan jika mata ƙadan tana bata idan ta sha sai cikinta ya saki ta yi tsuguno,ita da ta dauko sai da ta zuba baban cokali guda da rabi ta haɗa ta kwaɓa cikin ɗanwaken, adda aminatu mu baki zuba mana wannan abin ba"cewar Khalid yana daga ledar fulaskon, ƙwacewa ta yi ta mayar tana cewa kai dalla ba ce maka nayi haɗin tsoffi na musamman za a yi Anne ba"? Oh na tuna nata sai yafi daɗi kenan?" Kwarai ma kuwa amiantu ta faɗa dai-dai tana fara sakin ɗanwaken Anne,kafin ya dahu aminatu ta haɗa musu nasu suka baje a kiching ɗin suka ci suka ƙoshi har da su kwai haka su kayi fatinsu suka gama. Miƙawa Khalid ta yi bayan ta zuba a plet ta haɗa mata mai da yaji da dunƙule,ta ce,"je ka kai mata ka zauna a gabanka ka tabbatar ta ci da yawa, sannan kar ka ce mata Ni nayi kasan ba ƙaunata take yi ba sai ta gwammace zama da yunwa akan ta ci",karba yayi ya fita daga kiching ɗin, kai tsaye dakin anne ya nufa . Tana zaune a kan kujerarta ta hutawa da alama dai daga bayi ta fito take dan hutawa tana maida numfashi,"Anne ga ɗanwaken larai ta ce na kawo miki", karɓa ta yi fuskarta na dan nuna jin dadi , ta ce," kai masha Allah larai ta kyauta kuwa" (Anne nason ɗanwake sosai ) shi yasa ta ji dadin ganinsa, dan haka ba tare da bata lokaci ba ta buɗe ta fara kai loma bakinta, duk da taji yadda kanwar ta kama mata baki hakan baisa ta daina ci ba. Khalid da yaga tana son ajiyewa sai ya kama yi mata hira har yana saka mafa a baki da haka ta ciye fiye da rabin ɗan waken,gashi dai babu dadi a baki a idona ma yayi bakikirin,amma dake idan mutum yana da rabo to baya tsallake rabon nasa haka ta cinye ɗanwaken ba tare da ta damu ba. Khalid na fitowa da kwanon aminatu ta taresa tana cewa "yauwa kanina dan albarka mu gani ta cinye?" Aminatu na yin arba da plet din ta saka dariya tana cewa masha Allah yau akwai bidiri fatana dai kar ta hana su nana shan ruwa lafiya"Khalid ya ce Adda aminatu me za ta yi?" Janyesa ta yi tana cewa muje wajen Malam yau da ƙarfinmu zamu yi karatu waccan tambayar taka kuma sai anjima result zai fito".daga haka suka wuce suka dauki littafansu suka tafi karatu. Anne na zaune ta kafe TV da ido sai ji ta yi cikinta yayi wata irin karta, dafe cikin ta yi kafin ta yunƙura da gudu ta faɗa bayi, ji kake zuuu fattttt kurrrr,,,,tamkar an kunna injin nika.. Aminatu gaba ɗaya ba anitse take ba Allah Allah take malam ya gama da ita ta je ta ji ya batun Anne yake,kamar ya sani kuwa bai sallmesu ba sai gab da shan ruwa, haka aminatu ta tafi tana gunguni. Tuni Nana da su larai sun gama jera komai a muhallinsa, idan ka kalli saman teburin nan dole sai ya burgeka ya baka sha'awa dashi da kayan maƙulashen da ke kai na buda baki,(Allah ka yassarewa kowa Allah dan girmanka ka budawa musulmi kasa su fi karfi duk wata cimma me kyau da ake yinta cikin wannan wata me albarka da yake kusanto mu Amin ya Allah) Ana kiran sallah aminatu ta hallara kan teburin saboda duk abinda za a ci tare da su za a ci, dan kuma ta samu damar leƙen hajjaju Anne da kyau. Takunsa da ƙamshinsa shi ya fara yi mata sallama, samun kanta ta yi da lumshe kyawawan idanunta tana kara bude kofafinin hancinta dan shaƙar ƙamshinsa da take bala'in so a rayuwarta, ƙamshin da babu na biyunsw a gurinta.... Fyadam✍🏾 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page19``* Ashe bata sani ba kallonsa take yi har sai da ta ji muryarsa daf da kunneta dan har labbansa suna taba fatar kunnenta,kana cikin deep voice ɗinsa ya ce"ya da kallo haka kar ki cinyewa Nana yaro dai"ba tasan sanda ta watsa masa harara ba har da murguda baki tana cewa "Allah ya kyauta Ni ba mayya ba ce, ko da Ni mayyace ba zan ci ka ba dan babu abinda zanci ,sai dai na ci wannan lutuwar matar taka"zama yayi a hankali kana ba tare da ya dubeta ba ya ce."me ye matsalarki da lutuwar matata ne jewel?"banza ta yi da shi amma kalmar matartasa da ya ambata sai sukarta take yi, dan haka ta yi kicin_kicin tana ta zuba duk abinda ta gani, ta haɗa komai a plet guda ba tare da ta kula da hakan ba,sai da ta ji tattausan hannunsa kannata sannan ta ɗago da oily eyes dinta ta watsasu saman kyakkyawar fuskarsa me tsananin kwarjini da annuri,da ido ya nuna mata plet ɗinta. A hankali ta maida idanunta kan plet ɗin, zare idanun ta kuma yi kafin ta juya tana kallon Nana da sauran mutanen da duk suka zuba mata ido wanda ita sam bata san lokacin da suka shigo dinning din ba,Nana ta ce "kuma haka zaki haɗa duk ki cinye abinda kika zuba"juyawa ta yi ta kallesa sai taga ya yi mata alamun tabbacin abinda Nana ta faɗa,haɗiye yawun bakinta ta yi,.kana cikin fuskewa da nuna rashin damuwa,ta ce Nana kin dai san halina wanda baya cin abinci ne zai ji tsoron cin abinci me yawa kuma Ni bana shakkar cin kwamacala in dai da dadi". Dariya Khalid ya yi tare da cewa EY mana adda aminatu kamar dai irin haɗin da kika yiwa Anne ɗazunnan na ɗanwake, yanzu gashi can ko zama ta kasa yi saboda zawon da take ta yi tun da ta ci ɗanwaken"duk taka kafar Khalid da aminatu take amma bai dakata ba har sai da ya dire zancansa Yana dariya abinsa. Gaba daya kallo ya kuma dawowa kanta, yayinda ta shiga sosa dogon hancinta tana faman ƙif_ƙifta idanunta wanda da haka mus ab yake gane rashin gaskiyarta,salati Nana tasa kafin ta ce."dama halin da Anne ta shiga aikinkine aminatu?"da sauri ta girgiza kanta tana cewa nifa Nana babu ruwana larai ce ta ce mu yi ɗanwaken da Anne kuma ai muma munci me yasa ba muyi zawon ba"?caraf Khalid ya kuma karɓe zancan da cewa kai adda aminatu mu namu me daɗi ne har siɗe kwanon mu kayi, na Anne kuwa har garin nan da larai take haɗawa innawuro idan tana son tsuguno ta saka a cikin na Anne". Ji kake muƙut amiantu ta haɗiye yawun bakinta da ya wuce daƙyar, sannan ta ce "kai Khalid kaji tsoron Allah Ni za ka yiwa sharri yaushe aka yi hakan?"Abby da tunda ake maganar bai tanka ba sai yanzu ya dago ya kalli aminatu da ta yi wiƙi_wiƙi ya ce."aminatu kashe min uwa zaki yi?"kallon Abby ɗin ta yi haka kawai ta samu kanta da ƙuresa da idanu ta na mai nanata kalmarsa ta tsakiya (uwa) ganin kallon da take masa ya sashi saurin waskewa da cewa gaskiya aminatu baki kyauta ba kin san su tsoffi hakuri ake yi da su dole ki yi hakuri da Anne"janye idanunta ta yi tana jin wani irin bugun zuciya, samun kanta ta yi da jin wani irin shakka da wani irin zargi akan Abby da duk wani abu da ya shafesa, kalmar uwa da ya jingina kansa da anne sai take ji kamar da wani abu a kasan kalmar a lulluɓe. Muryar Khalid ce ta dawo da ita hayyacinta, tana can duniyar tunani ashe Khalid ya tafi dauko ragowar ɗanwaken da Anne ta rage, diresa yayi a tsakiyar teburin yana cewa daddy Ka ga ma sauran ɗanwaken",gaba daya suka bi ɗanwaken da ido, zuwa yanzu tuni ya narke saboda kanwa da ta tsumashi,harara aminatu ta watsa masa ba dai ta ce ko mai ba ta maida hankalinta kan abincin gabanta ta fara ci,mus ab ya ce da Khalid ya dauke ɗanwaken kar ya sa mutane amai. Tun aminatu na cin abinci cikin kwanciyar hankali har dai ta fara haɗa zufa,ajiye Spoon din ta yi tana kallon mj, sai dai shi bai ko nuna yasan me take nufi ba, jira kawai yake yaga emtyn plet a gabanta tunda shi tun ɗazu ya gama shan ruwansa, idanunsa akan wayarsa ya ce"Malama ki sauri ki cinye kafin a tayar da Sallah"rangwadar da kai ta yi sannan ta kalli Abby da yake shirin barin wajen ta ce. "Wallahi Abby na koshi babu wajen saka ragowar" Abby ya ce "to aminatu ai ba Ni zaki fadawa ba ga wanda ya kasa ya tsare nan shi zai yi hakuri ko?" Daga haka ya wuce ya barsu, Nana ma miƙewa ta yi tana cewa "mus ab zaka yi latti fa idan ka dakata aminatu ka rabu da ita kawai", itama barin wajen ta yi tana jan hannun Khalid da ta san cewa aminatu na nan juyowa kansa,suhaima dama ta jima da barin wajen sai ya kasance saura su biyu. A hankali ta fara kokarin sulalewa ta gudu saboda taga kamar hankalinsa baya kanta dan bata ji wannan yanayin da take ji na kaifin idanunsa akanta ba,amma kafin ta yunƙura taji dakakkiyar muryasa yana cewa kika kuskura kika bar gurin nan sai kin yi tuƙyin mota ko zamu kwana zaune kuwa"daɓas ta koma ta zauna tana yi masa hararar gefan ido, fakar idanunsa ta yi ta janyo yajin da nana ta ci doya dashi dan ita bata ci sos,ta afka shi akan abincin ta juya, take abinci ya koma jawur kamar an cika miya. Cikin sanyaya murya ta dubesa tana cewa "hamma mus'ab kaga fa abincin da yaji ba zan iya ci ba" bai ce mata komai ba sai miƙewa da yayi ya ɗauki abincin ita kuma ya nuna mata hanyar upstairs da ido yana mata alamun da su je,yadda ya tsare gira yasa ta kasa musawa haka ta bisa har can kololuwar ɗakinsa, suna shiga ya ajiye plet ɗin a kasa itama ya ce ta zauna, dole ta zauna kamar yadda ya umarce ta,"ki tabbatar da kin cinye su kafin na dawo" daga haka ya shge bayi ya dauro alwala, har ya fito tana zaune ta tasa abincin a gaba ta kasa taba ko loma,fita yayi bai tanka mata ba sai kashedi da ya zuba mata da ido. Yana fita ta mike zata gudu, sai dai gam taji ƙofar alamun ya rufe daga waje,komawa ta yi ta zauna tana cewa yau na shiga komar mugu reshe ya juya da mujiya, wallahi idan na sake naci abincinnan tabbas yau sai na kwana ina zawo Allah sarki Anne yanzu haka alhakinta ne". Zamanne taga ba zai yi mata ba, gashi duk ta tuna da punishment ɗinsa sai taji gabanta ya fadi, dan haka sai kawai ta yi shahada ta duma hannu ko cokalin ba ta kalla ba ta runtse idanunta ta fara kai loma da sauri_sauri,cikin ƙanƙanin lokaci ta fara haɗa zufa duk sanyin fanka da ac da ke dakin ji ta yi tamkar an sakata a cikin oven,tuni bakinta da harshenta suka ɗau zafin yaji da raɗaɗi, kwanciya ta yi a wajen tana juyi kamar macijiya. Ya jima sosai kafin ya shigo saboda sai da su kayi tarawi sannan yayi wasu nafilolin, kai tsaye dakinsa ya nufa,yana shigowa ya sameta kwance tana juyi harshe a waje hannu akan cikinta sai kuka take yi,da sauri ya ƙarasa inda take yana faɗin "subhanallahi jewel me ya sameki?" Kaji wata tambayar rainin hankali aminatu ta faɗa a ranta, shi kuma har ga Allah ya manta komai da ya faru na ɗazun,ture plet ɗin da tayi da ƙarfi shi yasa shi kallon plet ɗin a lokaci ɗaya kuma yana tuna abinda ya faru,dafe kansa yayi yana fadin "subhanallah me yasa kika ci jewel?"bata san lokacin da ta sa ƙafarta ta hanƙadashi baya ba saboda tsanani takaicin tambayoyinsa gareta, wannan ai tsabar rainin hankali ne, yasa ta abin sannan yazo yana mata wasu watsatstsun tambayoyi,dan ya kasance namiji tsayayye me cikar zati da ƙarfi da babu abinda zai hanashi faduwa wanwar, a maimakon hakan sai kamota da yayi ya mannata a ƙirjinsa yana ƙoƙarin calming ɗinta , sai dai tamkar zugata yake yi dan kuwa duka take kai masa ta ko ina babu sauƙi. A hankali ya birkito da fuskarta saitin tasa bai yi wata_wata ba ya cafke harshen da ta kasa sarrafashi a cikin bakinta saboda zafi da raɗaɗi, take sanyin bakinsa ya gauraye da bakinta da yake ɗau da yaji, wani irin sanyi ne da zaƙi_zaƙi suka gauraye bakinta, take duk wata azaba da take ji ta ɗauke,sai ga aminatu na zagaya hannunta ta bayan ƙeyar mj tana ƙara manne bakinta da nasa yayin da a gefe guda kuma jikkunansu suke amsawa da kowanne saƙo da bakunansu suke aikawa gangar jikinnasu,yadda yake aika mata sakonnin zafafan kisess yasa ta mance kowa da komai a cikin wannan duniya, sosai yake tsotse duk wani yawun dake cikin bakinta, aminatu kuwa bata san lokacin da bacci yayi awan gaba da ita ba,shi ma baisan baccin ta yi ba har sai da ya samu ya dawo daga nishaɗantacciyar duniyar da bai taɓa sanin akwai makamanciyarta ba. Gyara mata kwanciya yayi ajikinsa kafin shima ya lumshe idanunsa, wanda a take bacci me daɗi ya kwashesa,asuba tagari muj'am. ********* A hankali rayuwa take garawa, sakanni su zama mintuna,mintuna su zama a wanni,awanni su zama kwanaki,kwanaki su zama sati,sati su zama watanni watanni su zama shekaru,wasu na rayuwa bisa yadda suka tsarawa kansu, wasu na rayuwa da yadda Ubangiji ya tsara musu tasu, wasu na yinta cike da godiyar Allah wasu kam yinta suke cikin saɓa masa da ganin sunfi kowa da komai na duniya basa tuna wanda yayi su dama ya a'ra musu na cin karensu babu babbaka,sun sake sun baje kolin kayansu basa tuna wata rana zasu tafi su bar komai, zasu tafi kamar yadda suka zo, basa jin wa azi bare su dinga tunawa akwai kiyama,kai abin dai babu daɗi sai dai fatan cikawarmu da imani. Suma ahlin wannan gida uku, haka suke tafiyar da rayuwarsu cike da nasara da damar da Ubangiji ya basu,wanda suke gani tamkar su suka bawa kansu, gani suke bazasu taɓa yin nadama ba saboda suna ganin kamar su suke tsarawa kansu rayuwa ganin duk abinda suka sa a gaba sai sun cimmasa har fiye da yadda suke zato. A bangaren su aminatu kuwa zamu iya cewa nasarorin rayuwa sun sameta, saboda ta fita daga rayuwar jahilci, idnaunta sun buɗe da rayuwar birni daidai misali ba irin budewar da sheɗan yake muradi ba,a halin yanzu aminatu sauke Alkur'ani mai girma tare da manyan littafan addini wanda bata taɓa zaton zata sansu a rayuwarta ba,ta gama secondary school ɗinta cike da himma da kwazo ta samu ilmin nasarar da take ƙawazucinsa tun tana kucaka,sai dai fa halinta ba dainawa ta yi ba, canjin da aka samu kawai na hankali da ta yi a yanzu duk abinda tayi a yanzu baza'a kirashi da kuruciya ba sai dai shaƙiyanci da sakalci. Lafiya suka zauna a gidan da zahida saboda wanda ake bala'in akansa shima yayi balaguro zuwa wani cost a can ƙasar Saudiya wanda ya shafi aikinsa na lauyoyi,duk gidan babu wanda yasan cewa mus ab Yana wani cost da ban bayan na kasuwancin da yake yi, Nana ce kawai TASAN cewa mus ab babban lauyane wanda ƙasa ko nace duniya ke ji dashi, mutane da yawa sunansa suka sani basu san fuskarsa ba,shi yasa duk inda zai shiga sai shiga hankali kwance ba tare da yan jarida sun yi masa mamaya ba. Suhaima kuwa tana gidan mijinta Mustafa, shekara daya kenan da yin auren, Khalid ma a yanzu yana frimary 4, ga wata irin shakuwa dake tsakaninsa da aminatu tamkar wanda suka fito ciki daya,Anne na nan da halinta sai dai tuni ta kiyayi aminatu ta daina shiga sabgarta tunda ta nuna mata asalin kalarta. A bangaren daddyn zahida shima yana nan akan bakansa na son samun biyan bukatarsa akan aminatu, sun bar komai ne a ranar har zuwa lokacin da suka tanada suka tsara dan fara yaƙin. Yau tsawon shekara biyu kenan aminatu bata saka mus ab a cikin idnaunta ba, shi yasa yau da ake shirin tarbarsa take jin wani irin ɗoki da farinciki na jin cewa zata gansa, ko ya ya zama ko wane iri. Kyau ya kara ko yaya sajensa ya koma? "Wannan tunanin shine yake ta zarya a ranta. A bangaren zahida ma duk girman kanta da son kamewa wajen mus ab, ta kasa daure dokin dawowarsa, dan tun sassafe ta fita zuwa gyaran jiki. Nana da kanta ta ɗauki aminatu ta kaita gidan wata yar aniyarta,me suna humkon gidan kamshi dan a gyara mata ita a fito mata da kuruciyarta da budurcin ta da ya fara haskawa yake tashe a kan ganiyarsa. A can nana ta baro aminatu ta dawo gida, ta da aminatun idan an kusa gamawa ta kirata sai ta tura mata malam jauro ya ɗaukota. Misalin ƙarfe biyar na yamma jirgin su mus ab ya dira a ƙayataccen filin jirgin saman Ahmad gidaɗo,a dai-dai lokacinne aminatu ta kira Nana ta ke sanar da ita an gama malam jauro yazo ya ɗauketa,"kash Nana ta faɗa tana dan dafe kanta kafin ta ce."kinga yanzu ya tafi dauko hammanki a filin jirgi "amma bari na kirasa idan ya ɗaukosa ya biyo ya daukeki tunda kina kan hanya" kafin aminatu ta ce wani abu Nana ta kashe wayar,minti biyu ta kuma kiran aminatun ta ce ta jira kaɗan gashi nan ya dauko mus ab ɗin zasu tsaya su dauketa... Fyadam✍🏾 8064537048 Opay Fatima yushau adam Amount 500 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page20``* "Yallabai a yi min afuwa zamu ɗan tsaya a nan kan hanyar byfas mu ɗauki boɗɗo umarnin Hajiya Nana ne" cewar malam jauro kenan,as usual bai ce komai ba sai ɗan kaɗa kansa da yayi, yana mai ci gaba da duba saƙonnin dake shigo masa ta email address dinsa,kamar an ce ya dago kansa saiko idanunsa suka sauka kan wata kyakkyawar bafulatanar da ta wani bangare ta yi zubi da yan ƙasar Itofiya saboda kalarta da ta koma ta 'yan can,doguwa ce matsakaiciya me wani irin diri da zubin halittar da duk namijin da ya ci karo da ita sai yayi fatan ace ta zama mallakinsa,sanye take cikin doguwar bakar riga me tsananin kyau da tsada wadda ta dace da yanayin tsarin halittarta,fuskata fayau babu abinda take sai sheƙi, babu ɗigon kwalliya akan fuskarta sai kwallin da ko bata saka shi ba ba za ka fahimta ba saboda dashi aka halicceta da kuma dogayen gashin idanunta da suma tamkar ta saka na kanti haka suke. Duk inda ta motsa kamshin turarukan humkum duniyar kamshi take yi, me sanyi da kwantar da hankali, hon din da ta ji yasa ta dan waigowa tana duban motar da ta tabbatar da cewa ba ta irin samari da manyan dattawan da suke ta faman tsaya mata ba ne,lekowa da malam jauro yayi shi ya kuma bata tabbacin hakan dan haka ta tako cikin takunta me tsari zuwa jikin motar,kai tsaye bayan motar ta buɗe ta shiga ba tare da ta kula da wanda ke hakimce cikin motar ba,"malam jauro nayi tunanin kana kusa shi yasa na fito tun sama da mintuna goma kasa tsamaye da shara da bola sai kare min kallo suke dan wallahi sai da na kusa rotsawa wani dattijo kai dashi da gilashin motarsa",dariya malam jauro yayi yana cewa "to alhamdulillahi da baki rotsa din ba boddon nana da innawuro nasan zaki aikata"ƙwafa ta yi kana ta kuma cewa "malam jauro ina ji dai ka ɗauko mutumin nan me baƙin nunƙufurci ka kaisa gida dan naji gaba daya motar ta ɗume da munafukin ƙamshinsa da aka kasa gane wane iri ne?",gyaran murya malam jauro yayi sannan ya ce.da kin kwantar da hankalinki kin duba gefanki to da zaki ga me ƙamshin"ɗif aminatu ta yi, sai kuma a lokacin ta fara jin wannan yanayin da ta yi kusan shekaru biyu rabon da ta tsinci kanta cikinsa,EY lallai me idanun magic ya dawo kuma yana cikin motar nan. A hankali ta fara juyo da fuskanta inda take tsammanin yana wajen, "ah ta faɗa cikin ruɗewa tana zaro idnunta da suke wani irin maiƙo tamkar an diga musu man zaitun,kafin kuma ta fara sosa dogon hancinta da shafa kwantacciyar sumar ƙeyarta, cikin in ina ta ce,uhm sann...sannu da dawowa",bai ce mata komai ba kuma bai daina yi mata kallon kai tsayen da yake yi mata shi a yanzu ba,tura dan karamin bakinta ta yi kafin ta kawar da kanta tana kunƙunin an takura mata da kallon maita,kamar daga sama ta ji dakakkiyar muryasa da ta jima bata ji ba, yana magana as usual kamar baya so ko wane harafi daban yake fitar dashi cikin wani irin salo,"baki canja ba ko?"ya fada yana ta son shigar da idanunsa cikinnata da ita kuma ta ƙi yadda da hakan.bata Ankara ba taji hannunsa cikin nata yana murza yatsunta cikin wani irin yanayi me kashe jiki, cikin daburcewa da rawar muryar da kwarjininsa da kyauwunsa da ya karu suka saka ta,ta ce,"Ni Ni bana so"meye baki so?" Ya faɗa yana shafa fatar bayan hannunta da su kayi wani laushi tamkar fatar tarwaɗa. Kai tsaye ta ta ce,"to dai yanzu na girma kuma nasan babu kyau taɓa jikin da mutum bai da hurumin taɓawa", dai-dai nan malam jauro ya faka motar a cikin makekiyar harabar gidan na Alhaji Jamil, fita yayi yana ciro kayan dake cikin but din motar, da sauri aminatu ta fizge hannunta dake cikin na mus'ab ta fito daga motar ilahirin jikinta na rawa. Shima fitowar yayi yana sakin wani ɗan taƙaitaccen murmushin da shi kansa bai san dalilin yinsa ba,zahida da tun shigowarsu ta fito da gudu dan tarbar me gidan nata, bayan ta yi yaƙi da girman kanta tsayawa ta yi turus zuciyarta na wani irin bugu kanta na juyawa tamkar katantanwa,ta gabanta aminatu ta zo ta wuce ba tare da ta lura da zahidar ba,shima har zai wuce amma ganin zahidar sai yayi slow yana ƙoƙarin kawar da komai dan ya yi mata magana a matsayinta Na matarsa da yasan akwai dubban hakkinta a kansa,sai dai kafin ya ce komai ta riga shi bude baki cikin kakkausar lafazi ta ce."wallahi mus ab dawowarka bata nufin komai a gareni fa ce masifa da bala'i, dawowarka asara ce a gareni, bana farinciki da dawowarka a yanzu tunda har na fuskanci kana nan baka sauya ba, kana nan a matsayin bunsurun yar ƙauye wallahi wallahi wallahi mus ab muddin ka ce zaka ci gaba da ƙuntata min ta hanyar waccan mayyar yar kauyen to tabbas za ayi ɗa kwance uwa kwance dan wallahi babu wanda zan bari yayi numfashin arziki a cikin gidan nan kai dama duniyar baki ɗaya dan haka mu zuba Ni daku dan iska ka fasa", daga haka fuuuu ta wuce kamar kububuwar da ke shirin haɗiye mutum,ajiyar numfashi yayi kawai kana ya tura kofar da Turota da ƙarfi kamar zata fasa galas ɗin. Tarbar Nana da yasa mu ita ta ɗan sanya shi farinciki da kawar masa da damuwar kalaman zahida, ita ko Nana duk abinda zahida ta yi ta kuma faɗa akan kunnen ta ne,shi yasa ta ninka kulawarta akansa tare cin alwashin tabbatar da farinciki da nutsuwa a rayuwarsa.. Duk wani abu da tayi ya rushe son mus ab da kiahinsa ba zai bari ta rayu cikin salama ba,dan haka dole ta yi wani abun tun kafin abin ya girmama ta yadda bata iya komai akai ba,key din motarta ta dauka ta fice daga gidan a fusacen da duk wanda ya ci karo da ita sai ya bata hanya,gidan Anita ta nufa, Tunda zahida ta shiga dakin, Anita take mata magana amma ta kasa tanka mata ruwa kawai take sha tana ƙarawa,ko zata samu zuciyarta ta yi sanyi, sai da ta ɗauki kusan mintuna talatin sannan ta fara magana cikin baƙincikin da yake dan ƙare aranta,"Anita ya zan yi ki bani shawara akan tsinanniyar yarinyar nan, bani da halin kasheta a yanzu sabida burinsu daddy a kanta amma wallahi da tuni an shafe labarinta a duniya",nisawa anita ta yi kafin ta dafa kafadar zahida ta ce,"zahida tuntuni na baki shawarar zuwa wajen shu umin boka a kan al'amarinki da mus ab amma kika nuna baki so,kuma ni dai ita ce shawara kawai a wajena dan ko ni ma da bazar shu umin boka nake taka rawata, numfasawa zahida ta yi kana ta ce,"Anita Ni fa waɗannan mutamen basu damenu ba,dan gani nake kudin mutum kawai suke cu a banza".wani kallo anita tayiwa zahida kafin ta ce,"ke kuma duk kuɗin da kike samu amma wanda zaki bayar a biya miki buƙatarki shine suka tsole Miki ido ko?to wallahi zahida idan baki bi wannan shawarar ba ina mai tabbatar miki da cewa sai aminatu ta saki gudu gudu kuma irin na ceton rai"cikin tsawa zahida ta dakatar da anita sannan kamar wadda ta yi gudun tun yanzu ta fara cewa Anita bana son iskanci wannan wane irin mugun fata ne? to ahir dinki ba zaki ga wannan bala'in a kaina ba sai dai a kanki, ta ɗora da cewa ki tashi muje yanzu, kuma duk abinda ya biyo baya ki tabbar da cewa akanki zan ɗora lefin", daga haka ta miƙe ta rataya jakarta da ɗan figigin mayafin da dashi da babu duk daya, babu ɓata lokaci suka ɗau hanyar dajin da zai kaisu wajen shu umin boka. ******** "Wai ke matar nan meye sa kike da naci kamar tsohuwar maiyane, tun shekaran jiya kike zuwa gidan nan baki samu ganin barrister ba amma kin ƙi haƙura"? A hankali matar da yamutsatstsan me gadin yake yiwa wannan banbamin ta samu gefan kofar gidan ta zauna tana cewa, "wallahi bawan Allah ko dame zaka kira Ni ba zan bar wajen nan ba har sai naga barrister fele" jinjina kai me gadin yayi har da shekewa da dariya yana mamakin ƙarfin halin matar,sannan ya ce "ey lallai kam zaki dauwama har mutuwar ki a ƙofar gidan nan, dan muddin ba abani umarnin barinki ki shiga ba to ba zan barki ki shiga ba wallahi dan ba zaki min asarar akina ba". Bata wuce zaman mintina goma ba sai ga wata baƙar mota zata shiga gidan, hakan yasa ta yi azamar ta shi ta bi motar da gudu,kafin me gadi ya samu damar hanata har ta shige gidan, da sauri me gadin ya maida kofar ya rufe ya nufi wajen matar da gudu yana cewa "wallahi sai kin fita kaji min da mayyar mata alk....Muryar me gidan kuma barrister fele ita tashi yin shiru daga abinda yake son fada, meye haka ne dan ladi, bana ce duk wanda yake son ganina ogent ka kira ni k sanar da Ni ba,tunda kaga taki tafiya kasan dame ta zo ne?". "Sorry yallabai ba za a kuma ba dama dan naji ka ce kar abar kowa ya shigo ne in dai bakai appointment da Shi ba amma zan kiyaye", baiwar Allah mu shiga daga ciki kamar ma naso gane fuskar ki ko?"br ya tambayeta yana yin gaba,da sauri matar ta jinjina kai tana mai jin sanyi a ranta. ******* Tsohon awa biyu suna fama da tafiya sai daga ƙarshe Allah ya basu ikon isa wajen shu'umin boka,sun taki sa a kuwa basu samu layi ba, dan mutum daya suka samu, itama suna zuwa aka sallameta,ba tare da sun yi masa wani dogon bayani ba ya kwashe Abinda ya kawosu ya sanar da su,zahida dubansa ta dinga yi da mamaki wanda take a gurin ta yi amanna dashi dari bisa ɗari,wani kwalli ya bata wai shi bita zai zai, ya ƙara da cewa,abinda yasa na baki wannan kwallin saboda dole masu halin ko in kula irin na mijinki sai an fara yi musu irin wannan sihirin da zai janyo hankalinsu inba haka ba za a sha baƙar wahala akansu,dan haka da jinje gida ki tabbatar da cewa kin saka shi a idanunki kun yi ido hudu dashi, kina yin haka shike nan sai yadda kika yi dashi zai zamar Miki kafarkinkafarsa in yaso daga baya sai mu dora aiki na gaba, amma fa ki tabbatar da cewa da shi kika.hada ido idan kika yi kuskuren kallon wani ba shi ba to babu ruwana kin ɓata aiki kuma bashi da makari a nan kusa", Anita ta ce shike nan shu'umi zamu kiyaye ga wannan ko", ta faɗa tana zube damin kuɗaɗe a gabansa,ita dai zahida har suka baro wajen bata ce ko mai ba ,amma har cikin ranta tana ɗokin ganin ranar da mus ab zai dinga binta tana yarfashi cikin dubban mutane, tuna hakan yasa ta saki murmushi, "lokacin ramuwar gayya ya zo mus'ab gani nan tafe bisanka". ******** "Yauwa baiwar Allah tun da mun nutsu da ga Ni har ke, sai ki yi min bayanin abinda ke tafe dake duk da cewa naso na shaida fuskarki" cewar br fele kenan. Gyara zamanta ta yi a kasa sannan ta fara magana da cewa,Ni sunana Hajara Abubakar kamar yadda na taba sanar da kai shekaru baya da suka wuce,a wancan lokacin na sanar da kai cewa kara nazo shigarwa akan mutuwar mijina da ban yadda da ita ba, ƙarar kuma ba akan kowa ba ne sai akan asibitin JGK hospital, a lokacin ka tambayeni ina da hujjojin shigar da kara na ce maka bani da su dan haka ka ce min naje na samo hujja kai kuma in sha Allah zaka taimaka min", ta yi dan shiru tana jiran cewarsa,ajiyar zuciya br fele ya sauke yana kallon matar da mamaki,kana ya ce," to yanzu kin samo hujjar ke nan?"... Da sauri ta daga kai jikinta har rawa yake ta na cewa "EY na samo yallaɓai dan Allah ka taimaka min wallahi tsawon shekara biyu ban samu nutuwa ba ban samu aiwatar da komai ba sai wannan aikin saboda bana ji idan har ban kwatarwa mijina hakkinsa ba zan iya rayuwa Cikin salama,dan Allah ka taimaka min kaji" ta ƙare maganar da sakin wani ɗan Marayan kuka, har yanzu tana hango lokacin da aka fito da gawar mijinta a matsayin rayayye bayan ya riga da ya mutu, har yanzu tana hango cin mutuncin da zahida ta yi musu tana kuma hango rashin gaskiya ƙarara a fuskarta da furucinta. "Ya isa haka bani decomment din hujjojin na gani" da sauri ta miƙa masa zuciyarta ɗaya,a hankali ya fara buɗe decomment din, da result din mutuwar mijinnata ya fara cin karo daga nan sai wasu result na mabanbanta mutane kusan biyar da manyan hujjojin da ko ba a ƙarkare Shari'a a ranar ba dole za a rufe a asibitin dan gudanar da bincike akansa,cikin dabara yasa hannu ya share zufar da ta keto daga cikin sumarsa zuwa kan goshinsa kana ya dubeta ya ce,"shike nan kije gida ki kwantar da hankalinki daga yau zan shigar da ƙara kuma nima zan fara gudanar da bincike akan al 'amarin in sha Allah zan taimakeki,amma fa ki sani dole sai kin kiyaye kin rufe wannan sirrin kar ki kuma zuwa wajen wani br da maganar idan ba haka ba kuma duk abinda ya faru da ke babu ruwana", Hajara ta ce yallaɓai wuyar da nasha kafin nazo matakin ganinka tana da yawa, kafin na zo kanka sai da na nemi lauyoyi ɗay_ɗay har guda goma amma duk wanda naje masa da buƙatata ƙarshe ya kore ni har da wanda suke sakar min karnuka, da har na karaya saboda na fuskanci babu ragowar masu gaskiya a cikin wannan duniya tamu, sai kuma Allah ya haɗani da kai a lokacin,jin ka saurareni har ka nemi da na sami hujja yasa na sakankance na daina yi muku kuɗin goro,kuma na san cewa ashe na Allah basa ƙarewa, sai kuma yanzu na kuma tabbatar da hakan, dan haka na miƙa amanata da duk wata yarda ta a gareka ina sa ran kaine zaka ceto ragowar da suke shirin shiga hannun azzalumai irinsu", kar ki damu wahakarki tazo karshe da kaina zan neme ki ki rubuta min adereshin ki da nomber waya anan", ya fada yana mika mata takarda da biro, a nutse da cikakken yaƙini ta rubuta ta bashi daga nan suka yi sallama har kudin mota ya bata dubu biyar tayi ta masa godiya a haka suka rabu. Cikin tashin hankali br fele ya dauki wayarsa, ya shiga kiran nomber me gidansa Alhaji Garba,sai da tayi ring kusan biyar sannan ya daga,br fele bai tsaya gaisuwa ba ya shiga rattaba masa duk abinda ke faruwa bai boye ko alif ba, wata irin zufa ce ta shiga karyo musu su duka kasancewar suna tare kuma yasa wayar a amsa kuwa,Alhaji Jamil ne ya ce "br ina fata ka karbi hujjojin nata ka kuma riƙeta anan?" Br fele ya ce,"a'a yallaɓai ban riƙe ta ba amma nasan komai nata hatta da idan take nasa ta rubuta min", dadyn zahida ya ce,"maza turo mana da bayanan" cikin mintuna biyu br fele ya tura musu da bayanan Hajara....... Fyadam✍🏾 [4/8, 8:21 AM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page21``* Da sauri Hajara ta bar jikin ƙofar falon br,wani irin gumi na karyo mata, to ke nan wa zata yadda dashi a cikin duniyar nan? Tunda gashi wanda ta sa ran me gaskiya ne kuma zai taimaketa shima ya watsa mata kasa a ido, ashe br yaudararta ya yi?yanzu da ace bata manta da gaya masa cewa zata koma ƙauyensu saboda kudin hayarsu na nan ya ƙare ba da shi ke nan itama kasheta zasu yi banza ba tare da ta cika burinta na tona musu asiri ba? tabbas zata haƙura da maganar a yanzu amma fa ba dan ta haƙura gaba daya ba, ba dan tana jin ta yafe ba, kawai zata koma ne tayi sabuwar ɗamara tunda ta fuskanci yaki ne babba a gabanta, bata fidda rai cewa akwai wanda zai zo dan taimakonta ba,bata fidda ran akwai na gari masu gaskiya ba sai dai tasan cewa sun yi matuƙar karanci a cikin duniya,jin kamar motsin fitowarsa yasa ta yi saurin ɓuya a bayan fulawowi,bata bar gurin ba sai da ta tabbatar Br fele ya bar gidan sannan ta fito itama cikin sauri ta fita ko sauraran me gadi da yake mata a sauka lafiya ba ta yi ba. Tana zuwa gida cikin azama ta haɗa kan yaranta suka fito ta tare a dai-daita, har cikin tasha, hankalinta bai kwanta ba sai da motarsu ta tashi sannan ta saki ajiyar zuciya tana fatan sauka lafiya ba tare da an samu wata matsala ba. "Hello ɗantunƙyi kuyi sauri ku ɗau mota na turo maka da bayanan wata mata, ina so yanzu na ji labarin mutuwarta idan kun sameta a hanya ku bi ta kanta da mota idan a gida kuka sameta ku sakawa gidan fetur ku kunna masa wuta maza maza bana son naji labari saɓanin na mutuwarta", an gama ya haj baka da damuwa da wannan sa ranka a inuwa forever ya hajj",ɗantunkyi ya fada cikin muryarsa ta mashaya kuma cikakkun 'yan daba ma ɗauka rayukan al umma. Daidai lokacin br fele ya karaso gidan gonar ta su,cikin fusata Abby ya ce "br me yasa tun farko baka sanar damu labarin wannan matar ba? Yanzu da ta barka ta tafi wajen wani br fa?" Cikin ƙanƙar da kai fele ya ce "Alhaji ba zata samu wanda zai karɓi wannan shari'ar ba dan kafin Ni sai da ta je wajen mutum goma, nine na sha ɗaya kuma duka wajen mutanenmu ne dan har na yi waya da mutum biyar daga ciki kuma sun bani tabbacin taje ɗin ", alhaji Garba ya ce,"a'a Br wannan ba hujja ba ce da ace kuma ta je wajen wanda ba namun ba fa me kake tunani zai faru?" Ayi hakuri Alhaji in sha Allah zan kiyaye gaba", Alh Kabir ya ce,yanzu ma kayi kokari sosai tunda ka karbe hujjar ko da barinta mu kayi babu abinda zata iya kayi kyan kai Br", a take suka kunnawa fayal din wuta ya ƙone ƙurmus, Abby ya ce "yadda hujjar nan ta ƙone to haka maganar nan ta mutu har abada babu me ɗagota". ******* Lokacin da zahida ta shigo gidan gaba dayansu suna dinning room, Abby ne kawai da Anne da innawuro basa nan, duk hadewarsa yau haka ya dan saki ransa cikinsu saboda ganin yadda nana take ta ina ka saka ka ɗauka dashi. Burum ta shiga falon ba tare da ko sallama ta yi ba,bata kalli kowa ba ta fara kokarin hayewa upstairs,nana ce ta dakatar da ita ta hanyar cewa ,zahida ina kika je ke da na dauka zaki zauna ki tari mijinki?"ba tare da ta kalli Nana ba ta ce,"to ai Nana ya samu wadda zata tarbesa kinga kuwa Ni bani da wani amfani a wannan bangaren,shi yasa na tafi aiwatar da abinda yafi min zaman",daga haka ta haura saman da sauri har tana haɗa step biyu. girgiza kai kawai Nana ta yi ta ci gaba da cin abincinta, shi ko dama ogan ko a jikinsa dan yayi alwashin in dai har zahida bata gyara halinta ba to babu shi babu ita har abada,kamar an ce da aminatu ta miƙe, sai gata zunbur a tsaye,bata ce da kowa komai ba ta nufi hanyar ɗakinta, ta kasan ido ya bi ta da kallo kafin ya dawo da kallonsa kan nana yana mai goge bakinsa da hannayensa da tissue ya ce,"nana zan je na huta zuwa anjima",to masha Allah a huta lafiya", Akan idanun zahida mus ab ya hauro ya shiga bangarensa, dan haka cikin sauri ta juya ta koma ɗakinta tana lakuben kwallinta. Tunda aminatu ta shiga dakinta take sintiri tana tuna abinda ta hango a cikin idanun zahida, me hakan ke nufi kenan?" Ta tambayi kanta tana mai kara murza idanunta tabbas idnunta basu yi mata ƙarya ba zahida ta hango zaune a tsakiyar wata bukka ana bata wani kwalli tare da cewar tasa a cikin idanunta kuma ta tabbatar ta haɗa ido da mus ab,to na meye kwallin? Kai Anya ma kuwa abinda na gani gaskiya ne me zai sa idanuna su hango min abinda zahida ta aikata a wane dalili,to ko dai da gaske Ni mayyarce?" Da sauri ta toshe bakinta tana girgiza kanta no amiantu ke ba mayya ba ce ke ƴar baiwa ce kamar yadda baffanki yake faɗa miki,aminatu ki yi sauri kar ki bari zahida ta haɗu da mus ab ki yi wani abu dan cetonsa daga tarkon zahida,tana gama wannan tunanin ta yi wuf ta fito jikinta har karkarwa yake yi,babu kowa a falon hakan yasa ta dan tsaya tana tunanin abin yi,door beel ɗin falon da aka taba ne yasa ta duban wajen, kafin ta karasa ta buɗe a natse,ɗan ladi me wanki ne tsaye rungume da kayan zahida. Ajiyar zuciya aminatu ta sauke kana ta ce "ya a kayi dan ladi?"yauwa dama kayan likita ne na kawo ko zaki ɗan miƙa mata?"girgiza kai aminatu ta yi tana mai bashi hanya sannan ta ce,"wace ni da wannan gangancin kai dai je ka kai mata tana ɗaki yanzu ta shigo", shima ɗan jim yayi aminatu ta yi saurin yanke masa tunani da shakkun zuwan da yake ta hanyar ƙara bashi hanya tana cewa kaje knocking kawai zaka yi mata zata fito ta karɓa idan bata fito ba kar ka bar wajen har sai ta karba da hannuta in ba haka ba kai ma kasan shauran ba zai maka dadi ba", wannan maganar ce ta ɗan bashi kwarin gwiwa dan haka ya wuce ɗin kamar yadda aminatu ta bashi dama. Binsa ta yi da kallo a ranta tana tunanin ko ma dai meye zata yiwa hamma mus ab ba zai yi ba zai koma kanta, dan haka ya koma kan kujera ta naɗe tana jiran Sakamako. Knocking ɗin da ɗan ladi yayi shi yayi daidai da kokarin fitowar da zahida take yi wadda ta rangaɗa kwallinta tana shirin zuwa turakar me gida. Tana dora hannunta akan handle ɗin kofar ta murza ta buɗe ba tare da tunanin komai ba ta sawo kai da niyar fita,caraf idanunta suka shige cikin na ɗan ladi abin kamar shirin Film tsarin aminatu ya tafi daidai da yadda take muradi,wani irin ƙara zahida ta saki tana mai komawa cikin ɗakin da gudu, shi ko dan ladi take ya ji wani abu mai kama da magnet ya fizgesa, jikinsa ne ya shiga karkarwa saboda tsananin ɗoki da kaunar ganin zahida da ya soke shi alokaci ɗaya, samun kansa yayi da binta har cikin ɗakin fuskarsa a washe da murmushi yana cewa "abar ƙauna ga shi na kawo miki kayanki ko na tsaya na jera miki su a cikin sip?" Cikin gigitacciyar tsawa zahida ta ce "fita daga ɗakinnan tun kafin na yi maka Lahani",ajiye mata kayan yayi a tunaninta fitar zai yi amma sai taga yana ƙoƙarin zama akan resting chair idanunsa akanta kamar zai haɗiyeta,zahida ta ware idanunta akansa bakinta har rawa yake ta ce,"na shiga uku me na jawowa kaina?"aminatu da ta ke shigowa dakin akaronta na farko tun zamanta cikin gidan ta ce,"bala in da kika so jefa ɗan birni a ciki shine ya dawo kanki ƙaiƙayi koma kan masheƙiya kenan, zahida likita 'yar birni matar dan birni ta zama masoyiyar ɗan ladi me wanki" ta karasa maganar da shekewa da dariya tana nuna ɗan ladi da yake ta murmushi yana kallon zahidar cikin tsananin ƙauna,aminatu ta kuma duban dan ladi kana ta ce,"to dan ladi kaga dai illar rashin addu'a da yin azkar safe da yamma ko,dan haka sai wannan ya zama darasi a gareka da sauran masu hali irin na ka na rashin son tsayawa a bawa addu'a muhimmanci. Har zata fita sai kuma ta ɗan dakata tare da juyowa kan zahida da take rakuɓe a saman gadonta idanun nan sun yi waƙi_wiƙi kamar an tsamo kaza daga ruwan sanyi,dariya aminatu ta kuma yi kana ta ce,"kai wallahi aunty zahida kin bani dariya, wai ke a tunaninki asirinki zai yi tasiri akan hamma mus ab? Aiko kin yi kuskure dan wallahi duk wanda ya tsaya ga Allah ya kuma yi yakinin cewa babu halittar da ta isa cutata masa face abinda Allah ya tsaro masa da wuya kiga irinku sunci galaba akansu,shifa me karatun Alkur'ani da yin azkar da salatin Annabi da hailala,na musamman ne ko a wajen mutane bare kuma me kowa me komai, dan haka sai ki sauya ɗamara ki canja salo hamma mus ab a tsaye yake wajen neman kariya da kusanci ga Ubangiji, Ni nayi gaba Allah ya bar kauna ɗan ladi." Har aminatu ta fice zahida ta kasa motsi saboda tsananin firgici da tashin hankalin yadda zata yi da wannan al'amarin,da ƙyar ta motsa jikinta ta miƙe zaune tana kallon ɗan ladi da bashi da niyar fita daga ɗakin daga yadda taga alamunsa,cikin masifa ta kuma nuna masa hanyar waje tana cewa "ka tashi ka bar dakin nan tun kafin na tara maka jama a dan ladi", tashi yayi kamar zai tafin amma sai taga ya tunkarota gadan-gadan ,hakan yasa ta kurma wani uban ihu da duk gidan sai da ya amsa. Kamar a mafarki yaji karar zahida a cikin kunnensa, cikin nutsuwa ya buɗe idanunsa da suke cike da bacci da gajiyar hanya, sai da ya ɗan dauki sakanni a zaune yana addu'a kana a hankali ya zuro ƙafafunsa da kamar baya taka ƙasa da su ya zurasu cikin silipas ɗinsa masu taushi,kana ya miƙe tare da ɗan yin miƙa ya nufi hanyar fita, yayin da duk takun da zai yi sai yaji ihun zahida na ƙaruwa a cikin kunnensa haka ne yasa shi ƙara sauri wajen barin ɗakin. Aminatu na jin ihun zahida ta fasa sauka ta tsaya daga bakin barendar da ya raba tsakanin dakin zahida da bangaren mus ab,da gudu Nana da innawuro suma suka fito suna tambayar lafiya suke jin kamar ihu,taɓe baki aminatu ta yi tare da basu hanya tana cewa "Nima abinda na ji kenan na fito", dai-dai lokacin mus ab ya fito daga bagarensa yana duban aminatu kafin ya kaida jallinsa kan nana da innawuro da suke hayowa upstairs ɗin,cikin muryarsa dake nuna tsantsar takurar da yake ciki akan yawan magana ya ce,Nana lafiya dai?"Nana da ta wucewa ta gefan aminatu ta ce to ni ma dai ban san abinda kefaruwa ba hawowata kenan",ihun zahida da suka kuma ji ne yasa duk suka zabura suka nufi ɗakinta, turus duk suka yi suna kallon ɗan ladi da yake ta yiwa zahida magiya cikin kuka akan ta tausaya masa ta soshi ta kaunace shi idan ba haka ba mutuwa zai yi". Nana da mamaki ya isheta ta ce,"kai dan ladi dama baka da hankali yaushe ka fara shaye_shaye matar auren kake cewa taso ka zaka mutu?to ka mutun mana fita daga ɗakinnan ko yanzu nasa security su fiddaka", innawuro ta ce to Ni wannan wace irin masifa ce kai yanzu har ka yi tsaurin idon biyo uwar dakinka har cikin daki saboda hauka"?caraf aminatu ta yi ta ce,"aa fa innawuro ku daina ganin laifinsa ita da kanta ta jawowa kanta masifa dan haka ku rabu da ita ta je can ta ƙarata mu dai zamu sha kallon show a wagga gida", ta fada tana mai ƙyalƙyalewa da dariya,haɗa idon da su kayi da oga mus ab yasa ta haɗiye ragowar dariyarta tana faman kif_kifta manyan idanunta. Tsare aminatu yayi da lumsassun idanunsa kafin cikin kamewarsa ya ce."me yake faruwa a nan?" Tura ƙaramin bakinta ta yi kafin cikin ƙunkuni ta ce," kawai ku lallabasa ya fita tunda ba yin kansa ba ne idan kuma kuka ce ta karfi zaku fiddashi to wallahi sai dai ku rufesu shi da ita a dakin dan ba zai taɓa fita ba", shotup tambayar ki fa nayi amma kike ce min a bar matata tare da wani ƙato a ɗaki aminatu Are U out of sense?"ba ƙaramin tsorata aminatu ta yi da tsawar mus ab ba hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka,Nana kuwa shawarar aminatu suka bi ita da innawuro dan dukkansu sun san wacece aminatu, da kyar suka lallaba dan ladi ya tafi amma da sharaɗin zai dawo da sassafe,ta gaban mus ab yazo ya wuce, yana yi yana waigen zagida da ta yi tsuru_,tsuru har ta rame a cikin ƙanƙanin lokaci. Nana ficewa ta yi tana hararar mus ab saboda tsawar da yayiwa aminatu akan wata banzar matarsa da bata san muhimmancinsa ba,har suka fita aminatu bata bar kuka ba har dasu sheshsheƙa kamar wadda ake yankar naman jikinta,a hankali zahida ta ƙarasa inda yake tsaye jikinta a matukar sanyaye sannan ta wani ɓangaren abinda mus ab yayiwa aminatu akanta yasa ta fara zaton ko dai ragowar kwallin yayi aiki akansa, shi yasa ta matso tare dasa hannu ta rungumeshi,tana sakin kukan munafurci,take kukan aminatu ya ƙaru sai ga aminatu na neman shiɗewa, cikin wani irin zafin nama mus ab ya hankaɗe zahida daga jikinsa yayi kan aminatu da take shirin yin kasa ya tarota zuwa jikinsa,kafin yayi wani abu tuni aminatu ta sume a jikinsa, daukarta yayi cancakaras ya fita daga ɗakin zahida kai tsaye ya nufi ɗakinsa da ita,yayin da ya bar zahida tana wani irin kukan neman ɗauki, zuciyarta kuwa kamar zata hudo ta fito, tabbas dole ta ɗauki mummunan mataki a akan aminatu, dole zata fuskanci su daddy idan ba zasu yi aikin da zasu yi akan aminatu ba to ita ta gaji da jira dan wallahi ba zata bari ta kashe ta a banza ba. A hankali ya kwantar da ita saman lafiyayyan gadonsa, kana ya dauko ruwa a dispenser ya zuba mata kadan akan fuskarta, a hankali taja wata doguwar ajiyar zuciya tare da buɗe idanunta tana bin dakin da kallo, kafin kuma cikin sauri ta miƙe zata fice daga ɗakin zuciyarta na yi mata ƙuna da zafin da ta rasa akan meye?riƙo hannunta yayi yana cewa "common ina zaki baki bani labarin abinda yake faruwa da matata ba?"wani shaƙurarran kuka ta saki tana son fizgar hannunta da ya riƙe kam,amma ta kasa ƙarshe ma janyota yayi ya zaunar bisa cinyoyinsa yana mai kamo fuskarta dan kallon cikin idanunta, so yake kawai ya tabbatar da abinda yake zato kuma yake gani a cikin idanunnata shi yasa yake kuma tunzurata da kalaman da ya fuskanci sune damuwarta......kasa ƙwatar kanta da ta yi yasa ta yi sarunder tare da shigewa cikin jikinsa tana ci gaba da kukan da bata san dalilinsa ba,",nifa yanzu na girma nasan hukuncin taɓa jikin da ba halalina ba dan haka ki daina tumurmushewa zahida jikin mijinta" ya fada dan guntun murmushi na subcewa daga kan kyakkyawar fuskarsa...... Fyadam✍🏾 8064537048 opay Fatima yushau adam. Yan nijer 80416252 Amanata [4/11, 7:53 AM] yushauadamfatima: https://chat.whatsapp.com/KjZ4tAsifjTHdEEUdPWRXD *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page 22``* Ƙananun Duka ta shiga kai masa wanda da ƙyar ya samu ya riƙe hannunta, kana a hankali ya haɗe tazarar dake tsakanin fuskarsa da tata,cikin kuka aminatu ta buɗe bakinta zata yi magana sai dai kafin ta furta abinda ke ranta, sanyi da kamshin harshen mus ab yayiwa bakinta tsinke,wani abu me kamar mayan ƙarfe ya shiga jansa duk da yadda yake son rinjayar zuciyarsa na barin aikata abinda yake aikatawar,hannunsa ya zura ta cikin rigarta yana shafa shafaffen cikinta da kamar ba a zuba masa abinci har zuwa cikin ramin cibinta,wani irin sheshsheƙa aminatu tayi tamkar zata shiɗe saboda yadda tsigar jikinta suka mimmiƙe, yawo yake da hannunsa a jikinta cikin wani irin salo me tafiya da imanin ma'aboci bege, bakinsa kuwa a hankali yake sauko dashi har zuwa wuyanta yana shaƙar sassanyan ƙamshinta da ya ke neman ruguza masa duk wani tunani yana mai goga gemunsa a duk inda ya samu,hannunsa da ya kai kan brz ɗinta yasa ta ja wani ƙaƙƙarfan numfashi tamkar zata sume duk da cewa ba wai ya taɓa fatar jikinta ba ne.cikin sauri ta zame daga jikinsa ta haye saman gadon ta dukunkune kanta tana maida numfashin tashin hankali da wani irin yanayi da ta tsinci kanta a ciki wanda ita kanta bata san na meye ba. Shima noƙewa yayi cikin fuskewa da shanye yanayin da yake ciki ya wuce bayi,bai jima ba ya fito ya samu har ta yi bacci dan haka sai kawai ya kwanta a gefenta wanda da a baya ba haka yake yi ba,amma yau sai yaji ba zai iya nesa da ƙamshin da aminatu take yi ba,can gefe ya kwnata bayan ya tofa musu addu'a,a hankali ya lumshe idanunsa yana son ya manta da abinda ya faru yanzun, sai dai ina duk juyin da zai yi taushin fatar jikin aminatu yake ji a cijin hannunsa,haka kuma duk numfashin da zai yi tare da ƙamshinta yake maidashi, a nutse ya bude idanunsa da suka sauya launi ya watsasu kan fuskarta da ta ke ta sheƙi tana baccinta cikin nutsuwa, kallonta yake yana jin abinda yake ji yana ƙaruwa a tare dashi, kasa jurewa da yayi ne yasa shi matsawa kusa da ita tare da janyota jikinsa, cusa fuskarsa yayi a cikin wuyanta yana mai shaƙar ƙamshinta me sanyi, wanda hakan ya samu baccin da yake nema ya daukesa ba tare da ya shirya ba. Da misalin ƙarfe biyu mus ab ya tashi aminatu,yasha mamakin ganin aminatu ta tashi ba tare da ta yi ƙunƙuni ba kamar yadda ta ke yi a baya, lafiya ƙalau tayo alwala suka fara sallah (kar ku manta a yadda aminatu take rayuwarta a yanzu bata san komai a cikin rayuwarba,bata san cewa akwai wani kalubale da yake lulluɓe a cikin duniyarta ba,bata da wata damuwa da zata sa tayi tunanin neman taimako gurin Allah ko yin addu'a dan Allah ya kareta ba,to amma duk da tasan da wannan hakan bai hanata bin tafarkin da nana da innawuro da kuma hamma mus ab dinta suka dorata ba,kar kice sai kina da damuwa ko bukata zaki nemi taimakon Allah tashin dare da yawanta addu'ar neman tsari, baki da matsala a yanzu bashi yake nufin iya kaddararki kenan ba baki da damuwa bashi yake nufin bazaki miƙa kukanki wajen Allah ba,karki manta da cewa kina da babbar damuwa damuwar da tafi kowace damuwa a duniya damuwar kuwa ita ce mutuwa, tashin alƙima, me zaki tarar, me kika aikata, wuta, aljanna,duk wannan sune babbar damuwar muminin kwarai,dan haka ba sai Allah ya jarrabeki da kalubalen rayuwa ba ne zaki fuskancesa,a'a neman lahirarki shine babban kalubalenki, wannan shine abinda magabatan aminatu suka koyar da ita suka nuna mata lallai ba sai tana da damuwar duniya ne zata tashi ta nemi lahirarta ba, wallahi mu farka duniya bata da tabbas mu nemi lahirarmu kafin lokaci ya ƙure mana, koda zaki yi sharholiyarki karki bari kimanta da Allah da kuma mutuwa domin tuna sune kadai yake dawo damu kan hanya, Allah ya shirya mu yasa mu cika da imani) A yayin da waɗannan bayin Allah suke tsaye gaban Ubangijinsu suna raya daren da kyakkyawar dabi a, a daidai lokacinne kuma zahida take dakinta tana Safa da marwa, tunani iri da kala ta kasa samowa kanta mafitar rabuwa da ɗan ladi da kuma samun ƙaunar mus ab,a maimakon hakan ba sai damuwa da tashin hankali ne da suke nunnunkuwa a ranta duk ta tuna cewa ɗan ladi ya zamar mata maƙale mata kuma ƙarfan kafa,ƙarshe ma zama ta yi dirshen ta fasa kukan da bashi da magani ko nace bata san hanya me saukin da zata bi ta magance matsalarta ba. Baccin awa daya suka kuma yi aka kira sallah,yanzun ma bai sha wahalar tashinta ba dan duk yanzu aminatun ta saba da wannan rayuwar. Sai da gari ya ɗan yi haske kana ya shigo gidan kamar yadda ya saba,Nana ya samu a falo a tsaye da alama dai jiran wani abun take yi,ile kuwa hannunsa ta kama suka nufi ɓangarenta tana cewa "magana nake so mu yi da kai shi yasa na tsaya jiranka dan wannan lokacin shine ya dace da yin maganar sirri kuma me matukar Muhimmanci", bata tsaya iya falonta ba sai da suka dangana har uwar makeken lafiyayyan dakinta, zama ta yi tana nuna masa kujerar hutawa ta dakin dan ya zauna,a maimakon ya zauna sai ya zauna a kasa gaban ƙafafunta kana ya fara da gaisheta cikin wata irin biyayyar da ƙauna, itama amsawa ta yi cike da alfahari. Kana ta ɗanyi gyaran murya kafin cikin taushin murya irin ta dattawan mutanen da suka san rayuwa ta ce," mus ba,me kake shiryawa a gaba? A halin yanzu dai ka sauke nauyin amanar da aka baka na abubuwa guda biyu masu muhimmanci,ka sauke wancan alkawarin da ka yi ya tabbata har gashi yana shirin haifar da abinda ake nema wato nasarar da al'amarin yake ta samu a daidai wannan lokaci,na biyu ka inganta rayuwar aminatu da ingantaccen ilmimmuka masu tarin yawa ta hanyoyi masu ban mamaki, acikin shekara biyun nan ka samarwa da aminatu ilimi wanda ita kanta idan aka ce ta faɗi iya abinda take karantawa bazata iya ba,ban taba ganin kwaƙwalwar da aka zubawa ilimin shekara bakwai acikin shekara biyu ba sai ƙwaƙwalwar aminatu tabbas wannan ba ƙaramin yaki ba ne kuma babbar nasara akan amana da alkawarin da ka ɗauka, su kansu malaman aminatu wanda suka koyar da ita cosess ɗin mamaki suke yi, dan dr helen cewa ta yi inama zaka iya bata aminatu ta koma da ita Istanbul da taji daɗi kuma kasarsu ta ci gaba", a nan ne ya dago rikitattun idanunsa ya kalli nana kafin ya ɗan fesar da numfashi kana ya ce,mu ce mata aka yi bama bukatar cigaban, batasan son ci gaban namu ne yasa ban tsallaka da aminatu can inda suke ba na daukosu gida?".jinjina kai Nana ta yi kana ta ci gaba da cewa. Mus ab aminatu ta samu kyakkyawar rayuwar da kake buri domin a halin yanzu aminatu tasan rayuwa daidai irin wadda ka nuna min kana so aminatu ta kasance a cikinta,aminatu bata san mene girman kai ba,bata san raini ba bata san dizgi ba,abu daya ne ba zai canji a wajen aminatu ba shine gabunta na yar fari sai dai wasu abubun sun ragu tunda yanzu ta yi hankali,"duk da irin gidan da aminatu ta tsinci kanta a halin yanzu hakan baisa ta manta nasabarta ba, sam aminatu bata san meye rayuwar karya ba, duk da cewa ko mai mun wada tata dashi hatta suhaima kafin ta bar gidan nan sai da rayuwar aminatu ta canja ta, wannan halayyar ba mu muka koyar da aminatu ba da binta tazo duniya,kaf cikin anguwar nan babu da wnada aminagu take hulda sai talakawan cikinta har da na makwabtan anguwa, idan Khalid ya tambayeta me yasa bata yin kawaye masu kuɗi irin na mom ɗinsa takance masa,khalid ai nima talakace kuma dan duk ɗan halak baya manta mafari, sa misali ma nice Kai na tashi cikin daula rayuwar jin daɗi, bana hulda da masu ƙaramin ƙarfi, to dan Allah Khalid ta yaya zan yi na gane al'umma suna cikin wani hali ta yaya zan tausayawa na kasa dani? ta yaya idan Allah ya buɗa min zan taimaki talakawa,?khalid ba zan yi ba in dai har ban zauna dasu na san yaya rayuwarsu take ciki ba,Khalid idan kana so ka taimaki marashi to dole sai ka sauke girman kai ka manta da kai waye ka daidaita matsayinka da nasu ka shiga cikinsu kayi rayuwa matsakaiciya kuma ka yadda cewa da kai dasu duk ɗaya ne ta hanya ɗaya kuka zo duniya ta hanya daya kuma zaku koma ga Allah, kasa a ranka kuma ba dan Allah baya son su ba ne yasa suke shan wahalar rayuwa sai dan kawai ya gwada imaninsu yaga shin zasu yi hakuri su riƙe jarrabawarsu ba tare da sun faɗa wata mummunar hanya ba,kaima ba ya baka ba ne dan yafi sonka sai dan ya gwada imaninka ya ga ta ina zaka sarayar da arzikin da ya baka, dan haka kasa a ranka baka da wani arziki a duniya sai na kasancewarka musulmi wanda ya taso a tutar Muhammadur Rasulullah s.a.w). Mus ab kaji fa wasu kalamai daga bakin ƴan baiwa wanda suke keɓabbu acikin al umma masu zuciyar zinare, wallahi mus ab Ni kaina na ƙaru ƙaruwa mafi girma a cikin rayuwata da su aminatu, na koyi abubuwa da yawa wanda tun kafin ƙwakwarwarta ta cika da ilmummuka na zamani da na addini na samesu,shi yasa na kiraka domin na shaida maka irin nasarar da muka samu a mataki na farko dana biyu na alkawari da amanar da aka bamu dan haka kai tsaye ka tafi kan mataki na gaba wanda yafi ko wanne hadari kuma me sauki idan an nemi taimakon Ubangiji,mus ab lokaci yayi da zaka fara bincike akan wadannan azzaluman mutane da suka kashe iyayen aminatu dan tabbas ina ji a jikina har yanzu suna nan a duniya suna ci gaba da yin ta adi da rashin imani dan irinsu basu cika mutuwa da wuri ba, Allah yana ara musu dama ko zasu yi hankali su koma gareshi, mus ab ka fara yakinka ni kuma zan ci gaba da taimaka maka da dukkan karfina da kuma na kasancewata uwa kuma musulma da zan iya yi maka addua a kan dukkan wani al'amari da naka", a hankali cike da samun kwarin gwiwa da wani irin alfahari ya bude baki zai yi magana,amma sai ta yi saurin taresa da cewa mus ab Allah yayiwa rayuwarku albarka Allah ya doraku akan makiya tashi kaje bana bukatar jin komai daga gareka, abinda zaka yake cikin zuciyarka na bayyana maka tunda nasan kai ba zaka iya baiyanashi ba, bayan kuma bayyanawar ita ce za ta zama silar shiryuwar wani, domin halayyar aminatu halayyar da ya kamata a bayyanawa duniya ce,ta shi kaje Allah ya fushshemu alkhairi ",cikin natsuwa da kamewarsa ya miƙe tare da bawa Nana sumba a saman goshinta dan karrama kalamanta da babu wanda ta yi kuskure ko son zuciya a cikinsa. Yana fita ta daga hannunta sama ta yi addu'a me tsayi wadda babu wnada ya ji ko yasan me ta fadawa Ubangijinta daga ita sai shi. A firgice zahida ta farka daga dan baccin da ya sace ta ba tare da ta sani ba,babu salati babu hailala haka ta miƙe a zabure ta faɗa bayi, duk dadewar da zahida ta saba yi a bayi ana kalkale kalkale yau bata samu dama ba dan bata son ta yi jinkirin barin gidan har ɗan ladi yazo ya sameta, a ranta babu wadda take tsinewa sama da anita da aminatu dan duk sune sila, a gurguje ta gama shirinta ta fito, kana kallonta zaka fahimci a firgice take saboda gayun da ta saba yi yau duk babushi,tana saukowa suka yi kicibus da mus ab ya fito daga sashen Nana,ɗan jim ta yi tana kallonsa bakinta na motsi kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa ta fita a sukwane kamar wadda ta samu kwancewar kai,girgiza kansa kawai yayi ya haye upstairs,bai samu aminatu ba dan tuni ta sulale ta koma ɗakin innawuro ta ci gaba da baccinta. Zahida bata jima da fita ba sai ga ɗan ladi yazo ana rigima dashi wajen shiga,saboda kafin ta fita sai da ta bawa securitys din umarnin karsu sake su bar ɗan ladi ya shiga gidan duk haukan da zai yi musu kar su barsa,hakan yasa suka hanasa shiga, shi kuma ya dage sai ya shiga dan har ya fara tara musu jama a a kofar tangamemen gate ɗin, yanuyar da ake yi yasa gaba daya mutanen gidan suka fito, Abby ne ya fito ya sa aka bar dan ladi ya shigo, to da ya shigo din ma basu tsira ba dan ihu ya sa musu akan saiya shiga dakin zahida ko ta fito ya ganta,da suka kasa shawo kansa sai aminatu ce ta kawo dabarar bashi hoton zahida tare da kaisa wani daki daban,da wannan dabarar suka samu Salama akan tashin hankalin da zahida ta ballowa kanta. Duk abinda ake mus ab naji kuma yana kallo amma da tanki bai tanka ba,har ya bar gidan babu wanda yaji ko tarinsa ne. Shima Abby barin gidan yayi inda kai tsaye ya wuce gidan gonarsu inda suka saba haduwa da duk wani criminal Wanda yadanganci sirrinsu. A nan ya samu Alhaji Kabir da Alhaji garba, sai kuma wani cusmer ɗinsu me suna danial,suna zaman jiran Abby ɗin, Abby Yana zuwa sai kuma ga ɗantunƙyi nan yana tafe yana layi sai kace tsinke kwakwa shaye shaye duk ya cinyesa, Abby Yana zama ki gaisawa basu yi ba ya fara tambayar dantunkyi sakamakon aikin da suka sashi na kashe Hajara,cikin maganar su ta cikakkun mashaya ya ce,"ya haj ai bamu samu kowa a gidan ba tun jiya bamu zauna ba saboda neman matar nan amma ɓat ta ɓata bamu sameta ba,sai dai na yi alƙawari da babata sai na kawo muku gawarta gabanku in dai hakan shine farin cikinku ya haj", da farko hankalinsu ya so ya tashi to amma da suka.tuna sun kwace duk wata sheda dake hannunta sai kuma hankalinsu ya kwanta,da ɗjn da ɗawa kusan kaf lauyoyin da zata iya tunkara sun sayesu dan haka basu da fargaba akan rashin mutuwar Hajara,kuma suna da tabbacin cewa in dai ta ji Br fele bai neme ba to ba shakka ita zata nemeshi tunda bata san komai akan abinda suke shirya mata wannan shine tunaninsu,dan haka Abby yagyara Zama tare da cewa "rabu da ita tunkyi muna zaune zata kawo mana kanta dan haka mu ci gaba da aikin binciken masu wancan asibitin ina ga shine abu mafi muhimmanci a halin yanzu". Alhaji Garba zai yi magana kenan,Muryar wata yar jarida dake ta zango labarai a tashar tnn ta fara kawo kanun labaran da yayi matukar jan hankulansu da da sam baya kan tv. Fyadam✍🏾 8064537048 opay Fatima yusha'u adam Amount 500 Shaidar biya 08064537048 [4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page 23``* A yau ne asibitin ABM suke gudanar da shagalin murnar cikarsa shekara biyu da fara aiki,wanda gashi nan dai kuna ganin yadda jama suke dafifi wajen zuwa dan taya wannan asibiti da ta samu nasarori masu tarin yawa a cikin shekara biyu murna, ga shi zaku ji kadan daga irin taimakon da wannan asibiti take yiwa talakawa a bakin daya daga cikin wanda suka samu tallafin aikin ido kyauta da suka saba yi duk watanni uku". Daga nan ta aka.hasko wani bafulatanin dattijo yana feso bayanai na aikin warai da taimakawa matasa ƙarfi da tun kafa asibitin take yi,wanda ya zarta na asibitin GJK da suke yi wanda da yawan mutane suke zargin ba dan Allah suke yi ba akwai wata boyayyiyar manufa da yasa suke hakan dan janyo hankalin al umma,ya dora da cewa, "mun san cewa mutuwa dole ce da sanadi ko babu, amma mutuwar da ake yawan yi a asibitin GJK muna zargin bata Allah da Annabi ba ce,saboda a kullum idan ba a fidda gawa uku ba za a fidda ko da guda daya ko biyu ce,mun san cewa Allah ne me rayawa da kashewa kuma mun yadda da ingancin asibitin ABM,taimako kawai yake ba tare da ya bari munsan ko waye shi ba macece namiji ne Allahu a'alamu, muna samun magani kyauta, mjna samun kulawa ba tare da mun biya maƙudan kudade ba, kulawar da ko masu biyan maƙudan kudade basu sameta ba, babu kyara babu tsangwama, duk ƙankantar kudinka idan baka da lafiya kai tsaye zaka tafi wannan asibiti domin kasan ba za a koreka ba za a tsaya a duba lalurarka da kalilan din kuɗi cikin mutuntawa", yar jaridar ta watso masa tambaya da cewa, malam Bashir baka tsoron ace wannan mutanen kuɗi suka baka dan kawai kazo ka bayyana nasararsu ko ka tallata musu asibitinsu?"dariya yayi yana cewa wallahi ko kadan bana tsoro tunda nasan me gaskiya yana tare da Allah abinda na sani ne wallahi ban taba kebewa da ko nas din wannan asibiti da sunan makamanciyar wannan maganar ba bare masu asibitin da har yau babu wanda yasan ko da inuwarsu ne,Ni dai babu abinda zance sai Allah ya saka musu da alkhairi ya biya musu dukkan bukatunsu ya karesu daga sharrin magauta, Allah yasa masu tasowa su yi hali irin nasu", daga nan aka yanke magana dashi. Babu abinda su Abby suke sai zufa suna mai kasa cewa komai,a haka aka ci gaba da nuno irin mutanen da asibitin ta taimaka da irin gudummawar da take bayarwa wajen marasa lafiya, Alhaji Garba ne ya kashe tv tare da kutuntuma wani uban ashar yana cewa,"tun farkon fara aikin asibitin nan na baku shawarar mu binciko me asibitin kuka ki acewarku babu wata asibiti ko me ikon da zai iya yin abinda asibitinmu ke iya yi,to yanzu ga irinta nan bamu yi maganin matsalar ba har sai da ta girmama", Abby ne ya sharce gumin da yake ta tsartuwa a goshinsa kana ya ce,tabbas ka fi mu gaskiya Garba mun yi sakaci da yawa,amma yanzu ba zamu kara barin kofar da hakan zata faru ba", juyawa yayi gun ɗan tunkyi da yake ta layi a zaunen ba faduwa yake neman yi,tsawa ya daka masa firgigit ya zabura yana cewa sorry ya haj na leka sama ta hamsinne na gano aljanna", Alhaji kabir ya ce,"a gidan uwarka zaka gano aljannar dalla ka bar shirme Ka nutsu kayi mana abinda ya dace", "To ya haj ina saurare wa kuke so a sheƙe yanzu na sa ya shaƙi ƙamshin lahira?" Alhaji Kabir ya ce "wannan mutumin zaka nemo ka kawo mana shi nan", ya faɗa yana nuna masa hoton mutumin da ya gama magana yanzu a labarai akan asibitin ABM,wanda suka dauka a waya alokacin da yake ta zuba da zuzuta asibitin,kana ya ɗora da cewa, ba kashe shi zaka yi ba da ransa muke buƙatarsa dan dole sai mun fara bincikarsa ya gaya mana su waye masu wannan asibitin da kowa ya kasa ganosu"baka da matsala ya haj daga yanzu zuwa anjima ku zuba idon ganinmu dashi",daga nan suka sallami ɗantunƙyi da kudade masu yawa, sannan suka ci gaba da magana akan ainahin abinda ya tarasu. Alhaji Garba daddyn zahida shi ya fara yin magana saboda duk ya fi su zakuwa da son ganin sun cimma manufarsu akan su aminatu dan kawai shima ya cimma tasa boyayyiyar manufar da su basu san yana da ita ba,numfashi yaja kafin cikin nuna muhimmancin maganar da zai yi ya ce,"ga danial nan shine yaron da Alfa Romeo ya aiko akan kasuwancin zuciyar kakar aminatu, saboda yanzu ne daidai lokacin da ya bamu akan samo masa irin zuciyar da tayi daidai da wadda yake nema, to kun san dai bature da rashin saba lokaci baran ma akan biyan buƙatarsa dan haka dole mu san abin yi akan ita kakar kafin mu cimma namu ƙudurin akan aminatu tunda ita dole sai mun samu wancan tsinannan da ubanta ya danƙawa ragamar komai nata sannan zamu samu yancin kasuwancinta",ya aje maganar yana binsu da kallo da sauraron abinda zasu ce,a hankali Abby ya janye tagumin da ya rafka hannu bibbiyu kana ya fesar da wani zazzafan huci ta bakinsa da hanci, sannan ya dubi danial da duk abinda suke fada ba ji yake ba dan da hausa suke maganar suna yi suna jefa fillanci shi yasa ya maida hankalinsa kan wayarsa tunda shi dan aike ne babu ruwansa da abinda suke fada abu daya ya sani shine su bashi amsar aikensa ya juyawa inda ya fito. Sai da Abby ya yiwa danial kallon sakonni sannan ya juya gare su yana cewa,"Garba duk abinda aka fada shine a raina bullowar wannan asibiti da kuma damuwar da zahida ta saka kanta a ciki shine duk ya jagula min lissafi,abinda yasa suka fi damuna kuwa shine wannan asibiti da ta ɓullo shahararta da ƙaruwarta wajen gwamnati da talakawa shine babban ƙalubalenmu dan kuwa ta dauko hanyar rushe gobenmu dan kuwa asibiti ita ce gobenmu ita ce gatanmu kusan fiye da rabin abinda muka samu da wanda muke samu duk ta hanyar wannan asibiti ce,to idan har ta rushe ta yaya zamu ci gaba da samun irin makudan kudaden da muke samu?abu na biyu kuma damuwar zahida, zahida ita ce ƙashin bayan asibiti, duk duniyar nan babu amintanccen likitar da zamu samu mu bata amanarmu ta riƙe mana sirri sama da zahida,to idan zahida bata cikin natsuwa ta yaya zata iya ci gaba da aiki ba tare da wata matsala ba?sanin kanku ne wannan kasuwancin namu yana bukatar jajirtacce kuma na gida me amana me irin zuciyarmu,shi yasa har muka yi dabarar gina rayuwar zahida da irin burinmu, to idan babu zahida wa muka sani ciki da bai me irin zuciyarmu da rikon amanarmu da rufe sirrin mu?"ya ƙare maganar yana kallonsu da dukkan zuciyarsa, fan zamowa Alhaji Kabir yayi kana shima ya fara magana cike da nuna gamsuwa akan maganganu da abinda Alhaji Jamil yake tunani,"babu kuskure a maganganunka gaba daya sai gaskiya dan haka Ni a ganina mu hada taura biyu a bakinmu duk zamu iya tunda muna da mataimaka ta ko wacce fuska,ma ana muji da lamarin zahida mu hadu mu samo mafitar damuwarta sannan mu ji da matsalar Mr alfa Romeo mu yi aikin da ya dace akan kakar aminatu, amma abu mafi muhimmanci dole mu fara da zahida tunda ita ce zata yi wannan aikin kaga dai-dai lokacin da zamu samar da zahida tuni mun gama tsare-tsaren hanyar kai kakar aminatu asibiti cikin dabarunmu da muka saba na kai duk wanda muke da bukata asibiti ba dan raɗin kansa ba", tafi suka saka gaba dayansu suna mai yin amanna da wannan shawarar dan haka daddyn zahida ya kuma gyara zama yana mai jin cewa shima wannan shawarar zata taimakesa wajen cimma manufarsa akan aminatu ko da kafin su cimma wancan babban burin ne tunda ba kasheta zai yi ma baiwar jikinta kawai yake so ya ɗanɗana,dan haka cikin farin cikin da ya fara bayyana saman fuskarsa ya ce,"to me zai hana aminatu ta dawo gidana na dan lokaci shi kuma yaron sai mu sa dantunkyi ya boye mana shi babu wanda zai kuma jin duriyarsa bare ya addabi rayuwar zahida ina ga wannan ce mafita kunga mun warware matsalar zahida cikin ƙanƙanin lokaci daga nan sai mu tafi kan wancan matakin",cike da farinciki suka amince da wannan shawarar farin cikinsu na mai bayyana suna ji kamar komai ya gama tafiya dai-dai,da wannan shawarar suka watse bayan sun sallami danial ya koma masaukinsa. Da zafi zafi akan bugi karfe cewar Abby dan haka yana dawowa gida yamma liƙis yasa securityn da yake dan amanarsa ya buɗe ɗan ladi daga ɗakin da aka rufe sa aka hadashi da hoton zahida, Allah sarki bawan Allah duk ya rame a cikin kwana ɗaya da yini ɗaya,haka Abby yasa aka fitar dashi da yaudararsa kan zahida na can asibiti ya je ya sameta a can, duk gidan babu wanda yasan Abby yasa an fidda dan ladi sai aminatu da duk abinda ya faru akan idanunta ne, sai dai kuma bata kawo komai a ranta ba, bata san cewa Abby ya fitar da dan ladi ne dan su ɗantunƙyi su samu damar ɗaukesa ba,dan haka ta juya ta koma falo tana cewa haka kawai kin yi abinda zai cutar da bawan Allah wallahi Allah sai ya saka masa", Sai da Abby ya haye bangarensa sannan ya kira wayar ɗantunƙyi ya sanar da shi ko mai tare da tura masa hoton dan ladi,an gama ya haj baka da damuwa shima wancan tsohon tuni mun cafke shi yana hannu",dariya Abby yasa tare da jinjinawa dantunkyi da yi masa kirarin da ya kuma tunzurashi da fasa masa kai. Ɗan ladi yana kan hanyarsa ta zuwa asibitin a ƙafa ba tare da yayi tunanin abin hawa ba, dan gaba daya hankalinsa baya tare dashi burinsa kawai ya sanya zahida a cikin idanunsa dan haka tafiya kawai yake ba tare da jin wata gajiya ba,bai yi wani nisa sosai ba ya ga baƙar mota me baƙin galashi ta tsaya a gabansa kafin kuma wata matashiyar budurwa ta leƙo daga cikin motar tana kiran sunansa,bai ko yi alamar tsayawa ba har sai da yaji tana cewa zahida ce fa take maka magana", ai da gudu ɗan ladi ya juyo zuwa gaban motar yana fadin "masoyiya zahida kina ina?"budurwar ce ta kuma bude masa bayan mota tana cewa "ka shigo tana cikin mota", ba tare da hayyaci ba dan ladi ya shige mota, yana shiga suka fesa masa wata hoda shi kenan aikinsu ya kammala suka figi mota suka wuce inda Nima ban sani ba. Ajiyar zuciya Abby ya sauke bayan da ya gama jin cewa an gama da batun ɗan ladi, waya ya daga ya kira zahida, sai da ya kira sau uku bata daga ba kafin ana hudun ta daga, ba ta yi magana ba sai sheshsheƙar kukanta da ya ji, cikin nutuswa da kamalar da suke yaudarar mutane da ita ya ce".calm down my zahida wai meye matsalarki ne?" Cikin kuka zahida ta ce haba Abby yanzu dama baka san damuwata baka san me yake samun zuciyata ba?"sorry zahida ki kwantar da hankalinki ai mun riga mun gama yi Miki maganin damuwarki karfa ki manta zahida ke ce rayuwarmu idan har muka barki da samuwar da zata rusa farinciki ki muma ta rusamu to meye amfanin so da muhimmancin da kike dashi a gunmu,ki dawo gida haka tuni mun yi maganin matsalarki da dan ladi bazaki sake ganinsa ba a rayuwarki bare ya tayar Miki da hankali ya hanaki nutsuwa itama aminatun ki cireta daga lissafin mutanen da zasu hanaki walwala gobe zuwa jibi zata koma gidanku bazata dawo gidan nan ba har abada bare ta raɓi mijinki mus ab naki ne ke kadai ɗiyar arziki", wani irin ihun murna zahida ta saki ji take kamar ta shiga ta cikin wayar ta rungume Abby saboda tsananin farinciki,dakatar da ita Abby yayi da cewa amma ina so ki yi min alkawari daya zaki nutsu ki kwnatar da hankalinki ki mana duk abind amuke so dan akwai aikin da zaki yi shi a cikin kwannakin nan kuma ba akan kowa ba ne sai innawuro kakar aminatu", good Abby aiki ya biyo ta kan mayu kenan in dai wannan ne KAR ku ji komai dan kuwa rayuta fansa ce akan duk abinda kuke so", cikin farinciki Abby ya sauke wayar bayan ya tabbatar mata gobe zasu haɗu a gidan gona dan shirye shiryen aikin. Kowa yayi mamakin yadda zahida ta shigo gidan cikin farinciki da walwala wanda ko a baya da bata da wata damuwa bata kasancewa cikin wannan yanayin,sai dai babu wanda ya tanka mata akan hakan hatta da Khalid yau yaga canji a gun maminsa dan har fara'a ta yi masa wanda hakan ya yi masa wani banbarakwai ya kasa tanka mata sai kallo da ya bita dashi har ta haye upstairs,sai a lokacinne ma nana ta tuna da ɗan ladi dan haka ta dubi aminatu da take ta ɗurawa cikin ta wani hadin kankana da kabewa da madara da zuma da kwakwa da nana ta hada mata wanda kusan yanzu duk ire_iren kayan nan ne suka zama cimar aminatu, shi yasa kullum zaka ga kamar gana cnja maka kamar wata tarwada sabida sheki da kyau ciki da waje,ta ce."aminatu in kin gama je ki samar da faf security ya foto da dan ladi haka nan a lallɓashi ya tafi gida"aminatu da ta cika bakinta da wannan hadin ta ce ,"kai Nana wane dan ladin?ai tuni Abby yasa an fito dashi ya tafi gida abinsa", hamdala Nana ta yi tana mai ci gaba da kallon labaran da aka wuni yau ana haskowa na asibitin ABM. Fyadam✍🏾 Amount 500 8064537048 Fatima yushau adam opay [4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page24``* Ɗif nana da ta maida hankalinta kacokam kan saurare da kallon haɗaɗɗen asibitin taji ankashe tvn,da sauri ta ɗago dan ganin waye me wannan wulaƙancin, haɗa ido su kayi da Abby wanda yayi saurin sauya yanayin ɓacin ran da yake ciki akan ganin asibitin ya waske da dage mata gira yana cewa "gaba ɗaya kin maida hankalinki kan TV yau bakya ta ni ba dole na kashe ba tunda yau na samu kishiya"dan murmushi nana tayi tana mai gyara zamanta da matsawa saboda kokarin zaman da Abby yake yi, kana ta ce,nima da ka dawo ai baka neme ni ba kaga kuwa dole na kama kaina",yar dariya yayi sannan ya ce,kuma fa kin fini gaskiya to kaina bisa wuya wani dan aiki na karasa shigarwa a computer shi yasa ban miki magana ba",juyawa yayi inda aminatu da Khalid suke zaune sun maida hankalinsu kan wasan yar tsun da suke yi,dariya Abby yayi yana kiram sunansu,tare da cewa aminatu ke sam bakya girma yanzu dan Allah ina ke ina wannan wasan wannan ai wasan yara ne", dan tura bakin ta yi kafin ta ce", Allah kuwa abby har yanzu ban girma ba gaba daya shekarata fa sha takwas dan haka sai sanda khalid ya girma nima zan girma", rike baki nana ta yi ta ce ah lallai ba girman za ki yi ba", khalid ya ce,to nima nana ai banaso adda aminatu ta girma ta barni dan kar na rasa dan wasa shi yasa na fido mu girma tare", dariya suka sa gaba daya suna jinjina shirmen Khalid da aminatu wamda har ma Gara Khalid din tunda akan kuruciyarsa yake. Dai dai lokacin ƙayataccen ƙamshinsa ya turnuke falon wanda ashi ya basu tabbacin cewa yana kusa, zubawa kofar shigowar ido aminatu ta yi tana jin wani irin sanyi da bugun zuciya wanda take kasancewa a cikinsa duk lokacin da yake kusa da inda take, ba tare da ta gama daidaita kanta ba ta tsinkayi dakakkiyar muryarsa yana sallama, bai shigo falon ba har sai da nana da Abby suka amsa masa, kana ya ƙaraso cikin falon a kamensa fuskar nan babu yabo babu fallasa, ya so wucewa upstairs bayan sun gaisa to amma sai Abby ya dakatar dashi da bashi umarnin zama,zaman yayi yana kallon aminatu ta kasa kasa yanda ko ita ba dan tana jin kallon har cikin ƙashinta ba to da bazata taba sanin yana kallonnata ba, Abby ya ce",gobe in Allah ya kaimu isma zai dawo ina tunanin ma yasanar da kai ko?"jinjina kai kawai mus ab yayi idanunsa a lumshe kansa a jikin bayan kujerar da yake kai,Abby bai damu da shurun nasa ba ya ci gaba da cewa sai abu na gaba zamu yi magana dakai kafin ka fita da safe maganar tana da muhimmanci kar ka fita bam tare da kazo mun yi ba", nan ma gyada kansa ya yi ba tare da ya motsa ba, Abby dinne ya fara miƙewa ya wuce zuwa bangarensa. Khalid ne ya matsa jikin mus ab din Yana masa surutun school,aminatu kuwa tana zaune tana tura baki ta yi funfurus ta ƙi koda kallonsa ne bare a kai ga batun gaisuwa,juyawa Nana ta yi tana duban aminatun kafin ta ce."aminatu yaushe kika koyi ƙin gaida mutane ne ban sani ba?"ƙifi_ƙifi ta yi da idanunta tana kalmashe ƙaramin bakinta ta hanyar maidashi gefe kafin cikin sakalci ta ce." to nana ya za ayi na dinga asarar gaisuwata inda ba amsawa za a yi ba",to boddo da ki ƙi yin gaisuwar ai gara ki yi a ƙi amsawa", tura bakin ta tayi ba tare da ta ce komai ba kuma ta ƙi duban inda yake bare ta yi abinda Nana ke son ta yin,gashi har yanzu tana jin kaifin idanunsa a jikinta,a hankali ya zame khalid da tuni ya fara bacci ajikinsa ya kwantar dashi,kana ya miƙe yana dubanta ƙasa_ƙasa daga bisani kuma ya buɗe baki kamar ana masa dole cikin tsintsinka kalmomin ya ce "nana I need coffee",daga haka ya wuce cikin takunsa na cikakkun mazan da suka amsa sunansu maza,Nana ta ce "yanzu zan TURO aminatu ta kawo maka", da sauri aminatu ta zaro idanunta da suke wani irin maiƙo ba tare da ta ce ko mai ba ta ɗan bisa da hararar ƙasan ido kafin cikin ƙunkuni ta ce,"dama so yake a ce na kai masa ya kamani ya tsotse min ruwan jiki mutum ba abinda ya iya sai iskanc......kallon da ya watsa mata bayan ya taka step biyu ne yasa ta datse maganarta ba tare da ta ƙarasa ba kuma ta ankara da cewa a fili ta yi maganar,muryar nana ta ji tana cewa "Allah ya shiryamin ke boɗɗo",ba kunya kuma ta amsa da amin tana ci gaba da mitarta a ranta. Har nana zata shiga kiching ɗin sai kuma ta dawo da baya tare da ya fito aminatu, tashi ta yi ta bi Nana kiching ɗin tana shiga ta sameta a tsaye gaban Caved din kiching ɗin, ƙarsowar Aminatun yasa nana bata waje tana cewa "maza haɗa ki kai masa"ta buɗe baki zata yi magana nana ta watsa mata hararar da yasa ba shiri ta ja bakinta ta tsuke,tana kallo nana ta bar kiching ɗin wanda hakan ke nuni da cewa lallaifa sai ta haɗa coffee ta kai masa, hada coffee ɗin tayi yadda ta gadama, ta zabga masa uban shuga da zuma bayan kuma tasan baya son zaki da yawa,tana gamawa ta fita tana dariyar mugunta tasan ko hanashi sha ta yi zata ji daɗi. Da murmushi a fuskarta ta fara taka step ɗin ba tare da ta kalli me yake gabanta ba,karon da suka yi da zahida da ke ƙoƙarin saukowa yasa ta farga, wanda kuma kafin ta fargan har coffeen ya watse a jikin zahida, take zafinsa ya ratsa fata zuwa ƙashin zahidar wanda hakan yasa ta yi wata irin fusata tare da dagewa iya karfinta ta hankaɗa Aminatu baya,ƙara aminatu ta ƙwalla wanda hakan yayi sanadin fitowar gaba daya mutanen gidan dai-dai aminatu na gangarowa tun daga kan step na bakwai da suka ci karo da zahida har zuwa na ƙarshe wanda a take a gun hannunta ya yi wata yar bazawarar ƙarar da bayyana cewa ta karye ko ta samu gocewar ƙashi, da sauri innawuro da Nana suka yi kanta cikin ruɗewa da tashin hankali suke ƙoƙarin kamota amma ina aminatu azaba tuni tasa ta suma,mus ab kuwa ture su yayi ya dagota jikinsa yana dan marin fuskarta cikin yanayin dakiyarsa da ba kowa yake gane yanayin da yake ciki ba. "Larai maza kawo ruwa a zuba mata",cewar Abby ke nan da yake kallon zahida cike da tuhuma,da sauri larai ta cika umarnin da aka bata,nana ce ta karɓi ruwan ta buɗe tare da zubawa mus ab a hannunsa da ya miƙa mata, a hankali ya shafawa aminatun a fuska yana kuma dan marin fuskarta a nutse, da azabar kuka ta buɗe idanunta tana mai kasa motsa hannunta ,"wayyo Nana ta karya ni wallahi ta karya ni muguwa azzaluma kalan tasa dan birni ya ce ba zai zauna da nakasasshiya ba, wallahi idan ya ce baya sona sai dai ki hakura da na ki ɗan birnin ki barmin zalumu kawai me zuwa wajen boka mashrikiya",duk abinda ake zahida na tsaye babu wani alamu da zai nuna maka cewa ta ji ciwon abinda ta aikata, a ranta ma fata ta yi aminatun ta samu gagarumar matsala ta yadda bazata kuma moruwa ba,Nana ta ce,"zahida me ya haɗa ki da aminatu kike neman kasheta?Aminatu fa har yanzu da kuruciya a tare da ita ko ma me ta yi miki bai kamata ki nemi makasarta ba",kuka zahida ta fashe da shi tana cewa amma ni baki duba cewa ta nemi kashe nin ba ruwan zafi ta fasasshe fa ta kwara min tana sane", aminatu da mus ab ya ke ƙoƙarin ɗagata cikin kuka ta bude baki duk da azabar da take ji ta ce."wallahi nana ƙarya take yi karo mu kayi shine ta tunkuɗe ni", Abby ya katse muhawarar da cewa"mus ab me ka tsaya yi maza ku tafi asibiti mana", da sauri aminatu ta kalli mus ab ta ce wane asibitin za a mu?"anne da haushi ya isheta ta ce to wane asibitin kika san muna dashi a gidan nan banda wanda kika ƙi jini na me gidan da yayi muku alfarmar zama a karkashin inuwarsa, in banda butulci da Rasha na hankali ma ya za ayi yarinya ta dinga juya mutane duk sanda za a kaita asibiti sai ta zaba wanda take so yarinya sai kace ta shanue ku",kiciniyar sauka daga jikin mus'ab aminatu ta fara yi tana cewa "wallahi ba zani asibitin nan ba in dai shi za a kaini to a barni na mutu",gaba daya zuba mata ido su kayi baran ma zahida da Abby da suke cike da zargin aminatu akan sanin wani abu na sirrin asibitinsu wanda suke tunanin shine makasudin tsanar asibitin da ta yi,a take dukkansu suka sha alwashin bincikar aminatun ta ko wane hali dan tabbatar da zargin su ko akasin hakan. "Mus ab kuje Ka kaita ABM tun kafin hannun ya kumbura dan da alama dai gocewar ƙashi ta yi",cewar nana tana mai kawar da tunanin da suka tsunduma da kuma banbamin da Anne take ta faman yi akan sun sangarta aminatun bayan kuma babu dangin iya babu na baba,zahida ta yi caraf ta ce,"haba nana ya ga asibitin gida amma za a kaita na duniya bayan asibitin da ta raina shine best asibiti da muke da shi a jihar nan", aminatu da take kwance jikin mus ab tana faman raki ta kuma yin tsagal ta ce,"ina ruwanki da asibitin za a kaini naku ne dai ba zanje ba bare ku samu abinda kuke so me warin baki kawai",kut ni kike cewa me warin baki dan ubanki to in gaya miki tun kafin a haifi ubanki balbela take da farinta tsinanna sadakar yalla", suna gab da fita falon aminatu ta mayar mata da cewa hamma mus ab ashe tsohuwar guzuma ka aura bamu sani ba tunda a yadda take nuna mana ma ta haifeka",tun da ake fade faden bai ce ko mai ba sai yanzu da yayiwa aminati duban kai tdaye tare da cewa "idan baki rufe min baki ba zan sake ki anan ki ƙarasa dagargajewa",rufe bakinta ta yi tare da karyar da kanta akan kafaɗarsa tana cewa "zafi zafi wayyo zan mutu hannuna zai cire",Anne da ta bisu sa harara tana cewa, ai zafin ciwon bai hanaki yiwa mutane rashin kunya ba", zahida kuwa gaba ɗaya ji take kamar ta cire zuciyar aminatun tun yanzu kowa ya huta da bala'inta. Nana ta dubi innawuro da gaba daya jikinta ya kuma gama yin sanyi saboda cin kashin da Anne da zagida suke musu wanda ita aminatu sam basa damunta,da fata nana tayi tare da cewa innawuro je ki kwanta ki huta aminatu zata kasance cikin kulawa in sha Allah", cikin gamsuwa innawuro ta jinjina mata kai tare da shigewa corridon da zai kaita zuwa dakinta. Sai da nana ta tabbatar da innawuro ta shige ɗakinta sannan ta dawo da dubanta kan zahida tare da cewa "dan Allah zahida ki dinga kama girmanki kinga gashi nan ta yi miki rainin da bata yiwa wani a gidan nan ba",zama Abby ya yi cike da tunanin kalaman aminatu na yanzun, gaba daya ta kulle shi ta saka shi cikin sarkakiya, me take nufi da kar su yi mata abinda suke yi me ye abinda suke yi din? Zahida ma wucewa ta yi tana juya kalaman a ranta tare da son fassarasu da gano ma'anarsu amma hakan ya ci tura,Anne ma cikin mitarta da ta ƙi dainawa ta koma dakinta, Nana kuwa tana tsaye akan Abby tana kallon yadda ya lula duniyar tunani duk maganar da take yi masa bai san tana yi ba,da dan sauti me amo ta ta kuma kiran sunansa har da dan buga kujerar da yake zaune akai, firgigit yayi kamar wanda ya farka daga bacci ke nauyi, zuma masa ido Nana tayi cike da tuhuma wanda hakan yasa shi ƴan kame_kamen da ya kuma jefa zuciyar nana cikin zargi,bata ce masa komai ba ta juya ta barsa da kame_kamensa,cike da fargaba da tashin hankalin da aminatu ta haifar masa shima ya koma bangarensa. Kai tsaye ABM hospital mus ab ya wuce da aminatu, suna zuwa aka karbeta cike da kulawa,bangaren kashi aka kaita take likitoci kusan uku suka hadu akanta dan gyara targaden da ta samu a hannu,ana farawa aminatu ta cika wod din da ihu, idan ta yi salatin sai kuma ta koma jawa zahida Allah ya isa daga karshe dai ta yiwa kanta fada ta hanyar ci gaba da kiran sunan Allah a haka har aka samu aka gama kafa gyaran,amma su kansu likitocin sun ji a jikinsu dan babu wanda aminatu bata ciza ba duk fuskarsu shatin hannun aminatu ne na yakushi,lokacin da suka fito mus ab ya kalle su takaici ya sa shi harararta kafin kuma ya basu hakuri, duk cikinau babu wanda ya damu sai ma dariya da nishaɗin da aminatun ta sakasu duk kuwa da cewa sun ji a jikinsu,daga nan ya kamata suka tafi gida tana ci gaba da rakinta. Lokacin da suka karasa gidan tuni aminatu ta yi bacci, basu samu kowa a falon ba,ko ina yayi tsit kamar babu wani abu me numfashi a gidan,ko daga can wajen babu motsin kowa sai na securities din da suke on duty da suke ta kai komo tsakanin harabar gidan zuwa wajen gidan,kai tsaye bangarensa ya wuce da ita dan ita ya kwantar da ita yana kallon fuskarta da duk ta ɓaci da da shatin hawayen rigima,samun kansa yayi da dan jan dogon hancinta a saman labbansa yana fadin rigimammiya a ko wane hali take sai take bakinta baya rissina,bayi ya wuce ya haɗa mata ruwa me dumi, kana ya dawo daukarta yayi kamar yadda ya saba ya kaita har cikin bathtub ɗin,ajiyar zuciya ta saki tare da far da idanunta,da sauri ta maida ta kulle ta kuma budewa sai sannan ta yadda da inda take,turbune fuska ta yi kamar zata sa kuka,ɗan yatsansa ya ɗora kan jajayen labbanta yayi mata alamar ta yi shuru,hakan yasa ta haɗiye kukanta sai dai ba ta daina kwaɓe fuskar ba,janye rigarta yake kokarin yi ta yi saurin dafewa tana kallonsa da odnaunta sa suka cika da ƙwalla ga kuma maiƙon cikinsu da yake wani irin sheki hakan yasa kallonnata ya bada wani irin yanayi, wanda ya saukarwa da mus ab wata irin kasala da mutuwar jiki tsigogin jikinsa suka dinga mikewa tare da wani irin sanyi na musamman da ya dinga ratsa duk.wata tsoka da ɓargon jikinsa,lumshe idanunsa yayi yana son saita kansa da kuma tuhumar kansa a kan yanayin da yake shiga a duk sanda ya kasance da aminatu, yanayin da baya jinsa akan ko wace irin mace duk kyanta da ajinta kuwa,aminatu kuwa takaicin kanta da haushin kanta ne ya kamata, saboda tasan cewa abinda take bari yana faruwa tsakaninta da mus ab ba daidai ba ne, to amma ta rasa dalilin da yasa take kasa sarrafa kanta da yaƙar sheɗan a duk sanda kusancinsu ya wuce na alaƙar uban gida da da hadimarsa,ta kan rasa masarrafin a ko wace kafa ta jiki ta da zuciyarta, to me yasa hakan ke faruwa bayan kuma idan wanin mus'ab dinne bata yadda ko yatsanta ya riƙe?saukar tattausan labbansa me wani irjn ƙamshin da bata iya tantance na wani abin ƙamshi ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi,buɗe bakin ta yi zata yi tsiwar tata da ta saba, amma hakan bata samu ba sai ma amfani da yayi da wannan damar ya ƙarasa zura gaba ɗayan harshensa cikin bakinta...... Fyadam✍🏾 [4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page25``* A dai-dai wannan lokacin ne kuma innawuro a can dakinta ta kasa zaune da tsaye, dan kuwa sosai lamarin gidan ya dameta baran ma mu'amalar boɗɗon ta da MUS'AB, damuwarta ta kai maƙura mafita kawai take nema domin tana ji tana gani ba zata bari a lalata mata rayuwar jika ba,EY lalatawa mana tunda in dai har suna ci gaba da kusantar juna irin haka da mus ab dole wani abu ya faru,ko da kuwa shi mus'ab din bashi da niyar keta mutuncinta ai shi sheɗan yana da kwarin gwiwar sarrafa zuciyoyinsu, wannan tunanin da ta yi yasa ta fita daga dakin zuwa bangaren Nana da tun zamanta a gidan shigar ta ɗaya,tana zuwa ta ƙwanƙwasa ƙofar, jim kaɗan taji muryar Nana na tambayar waye?nice" innawuro ta amsa da muryar damuwa, buɗe kofar Nana tayi tana kallon innawuro da lokaci daya ta karanci damuwar da take ciki, hanya ta bata ta shigo, bayan innawuro ta shigo ta nuna mata kujera da ta zauna,zaman ta yi ba tare da musu ba, itama nanan zama tayi tana fuskantar innawuro da kuma sauraron abinda ya kawota a dai-dai wannan lokaci. Jin innawuro ta yi shiru tana ƴan kame_kame wanda ke nuni da cewa nauyin maganar da zata yiwa nanan take ji yasa Nana cewa. "karki damu innawuro ki faɗa min damuwarki ki dauke ni matsayin 'yarki da zaki iya faɗawa duk abinda kike son fada", wannan maganar ta nana sosai ta bawa innawuro kwarin gwiwa, hakan yasa innawuro gyara zamanta tana mai fuskantar Nana da dukkan zuciyarta, kana ta fara magana da cewa,ki gafarce ni akan abinda nake son faɗa miki,ki fahimceni fahimta irin ta uwar da ta ke son inganta tarbiyyar ƴarta ta hanyar da ya dace,na kasa barin abin a raina saboda yanzu damun da yake min har ya kai ya hanani runtsawa gashi kuma a matsayin mu na yan aiki wanda aka inganta rayuwarsu ba tare da nuna banbanci ba bani da zarrar yin fito na fito ta hanyar da bata dace ba,shi yasa na dangana na kuma samu kwarin gwiwar fuskantarki ta dalilin halayenki da suke nuni da cewa ke uwa ce ta gari kuma mace me adalci ga wanda yake ƙarƙashinta, numfashi innawuro ta dan ja sannan ta ci gaba da cewa, Nana kin san dai cewa MUS'AB ba muharramin AMINATU ba ne ko? Kuma kin san cewa kusancinsu a addinance harma da al'ada haramunne,to me yasa mun san haka, amma a matsayin mu na iyaye mata wanda tarbiyyar yaranmu suka ta allaka a hannun mu zamu yi saken da zasu lalace ta hanyar basu gudummawarmu?ban yi mamakin yadda duk tarbiya da hankalin mus ab yake yin hakan ba tare da shakka ba, saboda nasan mafi akasarin masu kuɗi ko yan boko basu maida hakan wani babban al'amari ba,ke kanki ina mamakin yadda baki iya tsawatar da shi babu me magana akan hakan sai Anne wadda sam bana jin haushinta akan abinda take yiwa AMINATU",a hankali innawuro ta zamo kasa ta sa gwiwarta akasa tare da hade hannunta biyu idanunta na zubda ƙwalla ta ce",dan Allah ku rufa min asiri idan har ba zaku iya tsawatar da yaronku akan irin rayuwar da yake kokarin nunawa aminatu ba to ku bari mu tafi mu yi nesa da ku, AMINATU amana ce a wajena duk da cewa na kasance kakarta wadda ta haifi ubanta amma hakan bashi yake nuna cewa zan yi sake da amana da kuma tarbiyarta ba". Da sauri Nana ta kama innawuro ta maida ta kan kujerar da take kai, sannan ta fara magana cikin tsananin tausayin innawuro da ganin wani irin kimarta da darajar ta da suka karu a idanunta, ta ce, innawuro dama wannan ranar nake jira ranar da zaki magntu akan abinda ke faruwa, to alhamdulillahi anzo gabar kuma naji dadi matuka da ya kasance na haɗa wata babbar alaka da ku saboda ku din mutane da kowa zai so ace ya haɗa alaka dasu idan fa har yasan me ye mutunci da karamci, innawuro ki kwantar da hankalinki kisa a ranki cewa AMINATU tana rayuwa tare da mijinta ne," da sauri innawuro ta kalli Nana kafin cikin rawar baki ta ce,a'a kar muyi haka dake AMINATU tun tana kankanuwarta ubanta ya daura mata igiyar aure wannan ita ce ƙaddarar AMINATU saboda Allah ya jarrabeta da son abinda bata taɓa gani ba abinda jinsa kawai tayi a bakin baffanta, wanda tun daga nan sunan MATAR ƊAN BIRNI ya bita kuma shine silar shigowarmu birni dan kwai mu nemesa, har zuwa yau aminatu bata manta da dan birnin da bata sanshi ba yana nan a ranta duk da cewa yanzu bata yawan yi min maganar nemosa kamar yadda take yi a baya", murmushi Nana saki kana tajefowa innawuro tambayar da ta dan jefa ta Cikin dogon tunani,shin kin san dalilin da yasa ta daina tambayar wancan dan birnin ta kuma daina shiga damuwa a duk lokacin da ta tuna shi?Nana bata saurari amsar innawuro ba tunda tasan bata da amsar ta ɗora da cewa,saboda ta sameshi ne, yana kusa da ita idanun ta ne basu sanshi ba amma zuciyarta ta sanshi kuruciya ce ta hanata ganoshi amma da sannu zata ganesa da kanga ba tare da wami ya nuna mata shi ba, innawuro ina mainsanar dake cewa shi wancan dan birnin da kuka bawa auren aminati sabida yadda da kauna wadda bata da iyaka SHINE MUS'AB dina yaro daya tamkar da dubu, yadda da amincin da danki yayi hasashe a tare da shi ina mai tabbatar Miki da cewa dan ki dan baiwame kamar yadda jikar ki ta zama yar baiwa dan kuwa hasshensa daidai yake ya bada AMINATU a hannun da ya dace, ko ke baki ga haka ba?". Wata irin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya innawuro ta sauke kafin ta ce," bani wata shaida da zai tabbatar min da abinda kika faɗa ", murmushi Nana tayi kana ba tare da bata lokaci ba ta bawa innawuro labarin abinda tasan cewa babu wanda ya sani daga ita sai baffan AMINATU da kuma uban gayya dan birni mijin AMINATU,a take innawuro ta yi sujud shukur har da kukanta,anan Nana ta kuma sanar da ita dalilin da yasa baizo nemansu ba da kuma niyar neman a daidai ganar da Allah ya sauƙaƙe masa wahala ya kawosu har inda yake ta wani sanadi daban da su dukansu basu sanshi ba. Hankalin innawuro kwance ta koma dakinta ta yi alwala ta fara sallolin nafila dan godewa Ubangiji me iko da aiwatarwa a duk sanda yaso. ******* Kuka AMINATU tasa saboda ta kasa ƙwatar kanta ji take kamar zai cire mata fatar baki,ga hannunsa da yake ta kokarin kaiwa ga inda take ganin idan ta bari ya taba shi ke nan ta gama taɓewa babu ita babu samun Rahma,kukan da ta saka me ƙarfi shi ya dakatar dashi daga abinda yake yi, zame bakinsa yayi daga nata, ba tare da ya kula da kukan da take ta masa ba ya kama hannunta ya gasa mata,yana ji tana ta maganganunta da ba wani fahimtarsu yake ba,da haka ya gama ya naɗota cikin towel kamar wata jaririya ya kaita har saman gadon, sannan ya kawo kayan bacci masu taushi ya saka mata, wanda dakyar ta bari ya saka matan dan turasa ta dinga yi tana kare ƙirjinta da bata san cewa ya fi ta son kiyaye kallon wannan guraren ba,bai barta ta yi bacci ba sai da ya tabbatar ta sha furar da ya ɗauko mata dan yasan da yunwa a tare da ita, ita kuma ba wani jure yunwa take yi ba, dan kuwa kafin kaga abinda zai hana aminatu cin abinci zaka jima. Tun daga wannan ranar innawuro ta samu nutsuwa,sai dai ta bangaren zahida da Abby babu wannan nutsuwar Allah Allah suke aminatu ta warke su tattarata ta koma gidan daddyn zahidan kamar yadda suka tsara,sun san cewa ko ma meye aminatu ta sani game dasu basu nada wani amfani tunda gaba daya rayuwarta su suke juyata bata da wani karfi ko wayan yin wani abu akan duk ma me ta sani ɗin wannan tunanin yasa suka watsar da shakkun da suke da fargabarsu akan aminatun. Ta bangaren aminatu kuwa tun daga wannan ranar bata kuma bari ta kusanci inda mus ab yake ba,saboda ita kanta duk da rashin hankalin ta tasan cewa abinda yake faruwa tsakaninsu haramunne, dan haka ta dauki damarar yin yaki da zuciyarta,a haka har ta samu sauki tayi garau da ita,wanda dama burin Abby da zahida kenan. Yau suna gama karyawa ,Abby ya umarci Nana da ta kira innawuro yana so zasu yi magana da ita,Nana ba ta kawo komai a ranta ba ta kira innawuro, ko da innawuro ta zo shi ya fara gaidata kamar yadda ya saba a duk sanda suka haɗu wannan halayyar tasa tana daya da daga cikin abinda ya kuma siya masa girma da yarda a wajen innawuro, dan gyaran murya ya yi kafin cikin nutsuwa ya fuskanci innawuro ya fara da cewa, "innawuro wata alfarma nake nema a wajenki ina kuma fatan zan samu?"ya karasa maganar ta sigar tambaya idanunsa kuma akan innawuro,cikin nuna girman da yake dashi a gunta ta ce,"in sha Allah in dai har bata fi ƙarfina ba zan iya yi maka", jinjina kai yayi cike da gansuwa kana ya ɗora da cewa, so nake ki amince aminatu ta koma gidan daddyn zahida wajen mahaifiyar zahida kenan, na dan wani lokaci ne kawai zata dawo nan daga baya", kamar ya ban fajimceka ba akan me aminatu zata koma gidansu zahida? a wane dalilin?"Nana ta faɗa cike da nuna rashin yarda da kuma mamakin bijurowar wannan sabon al'amarin lokaci ɗaya?"ɗaga mata hannu Abby yayi fuskarsa a haɗe tare da cewa "babu ruwanki ba da ke nake magana ba kuma ba umarninki nake nema ba,"dubansa ya maida kan innawuro yana cewa innawuro wannan ce alfarmar da nake nema a wajenki ina har zan samu",gaba ɗayansu innawuro suka zubawa ido har aminatun da tunda suka fara magana take bin bakunansu da ido kamar wadda ta tashi a makanta,a hankali innawuro ta sunkuyar da kanta ƙasa kana cikin ladabi irin na hadimi ga ubangidansa ta ce,"Ni yanzu bani da iko da aminatu dan haka ka yi magana da wanda yake iko da ita idan har ya amince Nima na amince". "Waye me iko da AMINATU a gidan nan sama da ni da na kawo ku gidan?"Abby ya tambaya idanunsa akan innawuro yana jiran jin amsarta,kafin wani daga cikinsu ya ƙara yunƙurin yin magana,dakakkiyar muryarsa me cike da ginshira da wani salo na musamman ta karaɗe kunnuwansu, "Abby nine nake da iko da AMINATU dan haka sai da izinina za a zartar da hukunci a kanta",cike da wani irin mamaki Abby yake kallon MUS'AB da yake neman wajen zama fuskar nan babu annuri ko kaɗan,da ƙyar Abby ya iya haɗiye kakkauran miyan da ya tokare maƙoshinsa kana ya iya cewa,"mus ab me ye haɗinka da aminatu da har ikon ta zai koma hannunka?"nana ta ce,"ni a ganina shine magajin gidan kuma tun ranar da ka kawo aminatu gidan nan ka saki hannunta mus ab ya kama dan haka dole shine me iko da ita",wani mugun kallo ya watsa mata kafin cikin tsananin fusata ya ce," Nana ni kike faɗawa wannan maganar? to bari ki ji na gaya miki ko kun so ko kun ƙi sai na yi iko da AMINATU tunda shima me ikon da ita nine ubansa me iko da shi idan kuma ban isa ba ku fada min?" Shiru suka yi babu wanda ya tanka masa, juyawa yayi ya fuskanci aminatu tare da cewa aminatu kin amince zaki je inda na buƙaci kije?"kai tsaye ta ɗaga kanta kana ta amsa masa da cewa "zanje",yauwa yar albarka"Abby ya faɗa fuskarsa cike da fara,a,da sauri ta kawar da kanta dan kaucewa mugun kallon da mus ab yake auna mata, duk da cewa koda bata kallesa ba tana jin kaifin idanun nasa a jikinta,a ranta tana jin cewa mafita ce Allah ya kawo mata ta kaucewa daga saɓcon Allah,to amma can ɗin ma ai baki tsira ba,kai tsaye ta bawa zuciyar da take mata wannan tambayar amsa da cewa, shi wancan tsohon najadun zan iya dakatar dashi koda ace bai sauya ba, shi kuma wannan bana iya sarrafa kaina a duk lokacin da ya kusanceni dan haka can ɗin yafi min, zanje na ɗan lokaci tun da ba zama zan yi na har abada ba, wannan tunanin da ta yi tun fara muhawarar tasu ne yasa da Abby ya tambayeta ta amince ba tare da wani ja in ja ba. Tana jin karfin takunsa lokacin da ya mike ya nufi upstairs,ta kasan idanunta take kallon ƙafafunsa da yake takasu akan mables din falon a haka kamar ba takun yake yi ba, amma kuma duk takun da yayi sai kaji sautinsa har cikin ranka,da haka ta daina hango shi, Muryar Abby ta ji yana cewa tashi kije ki shiya kizo mu tafi",sai da aminatu ta bar falon sannan ya dawo da dubansa kan innawuro cikin rarrashi da son kwantar mata da hankali ya ce,"innawuro aminatu ba nisa za tai da ke ba,tunda duk a cikin Layin nan muke,nisan mu da gidan Alhaji Garba bashi da yawa dan haka duk sanda kika so ganin AMINATU zaki ganta,"jikin innawuro a sanyaye ta amsa kana ta mike ta bi bayan aminatu. Saboda takaici Nana barin wajen ta yi zuciyarta cike da wasi_wasi da zargi akan wannan sabon al'amarin,zuciyarta babu abinda ta raya illa cewa yayi haka ne kawai saboda farin cikin zahida, tunda yanzu duk wanda yake tare da su yasan abinda zahida ta ƙi jini a rayuwarta aminatu ce,shi yasa ranta ya ɓaci matuka da irin wannan hukunci. Innawuro kuwa nasiha ta yiwa aminatu akan a ta ajiye wannan sakarcinnata dan kar ta dauko rigimar da zata sa a kulle so ko a koresu da ga gidan,dan ba kowa ne Zidane zasu iya hakurin da su Nana suke da ita aminatun ba,da haka suka rabu ba tare da aminatu ta wani nuna mata taji nasihartar ta ba. Aminatu na so ta yiwa nana da Khalid da Shi kadai take jin kewarsa sallama amma Abby ya hana, haka ya tasata gaba suka fice daga gidan..... Fyadam✍🏾 8064537048 Fatima yushau adam opay [4/12, 5:04 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page26``* Har motarsu ta fice daga gidan mus'ab da yake ta can saman barendarsa idanunsa yana kansu,wani zazzafan huci ya fesar yana mai ƙara buɗe idanunsa da kuma lumshesu a lokaci guda, ba zai iya cewa ga yanayin da yake ciki ba shi kansa bare kuma wani ya fahimta, komai nasa a nutse yake dan haka babu me gane ainahinsa ta ciki da waje,motsin da ya ji ne yasa shi buɗe idanunsa da suke a lumshe, Nana ce a tsaye bakin ƙofar tana yi masa kallon jin ƙai da tausayi, ba dan ko mai ba sai dan tasan ɗanta ba mai son hayaniya da magana ba ne, shi komai ma in dai har akan yayi doguwar magana ne to gara ya haƙura dashi, tasan cewa yana da abin cewa akan tafiyar aminatu amma tsananin miskilanci ba zai barsa ba, ya gwammace ya rabu da Abbyn na shi yayi duk yadda yake so da abinda yake ikonsa, duk da tasan cewa har da biyayyar da kuma yasan cewa abinda Abby ya faɗa gaskiya ne na cewa koda ikonsa ce amimatu shi kuma shi yake iko da me iko da AMINATU dan haka dukansu ikonsa ne,a hankali ta karasa tare da dafa kwantacciyar sumarsa baka siɗik, kana ta fara magana cikin kwantar da murya da cewa,"mus ab na san cewa ba da son ranka haka ta faru ba kuma dole idan muka tsananta da son dakatar da shi, sai fa idan mun fada masa matsayin aminatu a wajensa wanda kuma hakan ba mai yiwuwa ba ne a yanzu,ko ba dan ko ba dan waccan binciken naka ba dole mu rufe maganar saboda zahida,dan kuwa muddin zahida tasan matdayin aminati a wajenka zata iya aikata komai akan aminatu,amma kayi hakuri na san aminatu ba zata dore a gidan nan ba muna zaune zaka ganta da sawayenta ta dawo",ta karasa maganar da ɗan bubbuga kafaɗarsa,a hankali ya bude idanunsa da suka dan sauya launi akan nana kana cikin taushin muryar da tsintsinka kalmomin ya ce,"kar ki damu Nana bani da damuwa da hakan ko mai lafiya daga gareni", murmushi ta yi ba tare da ta kuma cewa komai ba ta fita daga barendar.shima ta shi yayi ya koma can wani kebantaccen ɗakinsa da yake gudanar da ayyukansa na sirri dan yana da wata shari'a da zai gudanar abcikin kwanakin wanda hakanne yasa a kwanakin bashi da lokacin kansa. Gidan sak irin na Abby Dan haka aminatu ba ta damu da kalle gidan ba kamar yadda ta saba bawa idanunta abinci akan duk abinda yake sabo a wajenta,yadda securities suke zagaye da gidan Abby haka nan ma suke ta faman sunturi tamkar sojan da suke fareti,kai tsaye suka shiga falon gidan wanda ba da ban canjin launin kayan falon da kujerun dakin ba da tabbas cewa zata yi a gidan su ƊAN BIRNI take, daddyn zahida da Shi da macen da take tdamannin mahaifiyar zahida ce suna zaune a falon kujera ɗaya, kallo daya zaka.yi mata kasanbcewa wayayyiyar macece ta nunawa sa a ko daga yanayin zaman da su kayi zaka tabbatar da hakan,hannu su kayi da shi da Abby suna gaisawa amma idanunsa suna kan aminatu tamkar zai cinyeta ɗanya, "ko kunya baya ji tsohon banza" aminatu ta faɗa cikin mulmula bakinta,matar da ta ji Abby ya kirata da hajiya zubaida ce ta kamo hannunta tana cewa,"zo ki zauna ɗiyata ai ni ba 'yar tayin zama kuka kawo min ba ɗiya kukawo min, aminatu saki jikinki ki dauka nan ma gida ne kin ji",aminatu dai binsu da kallo kawai take yi amma ko ihum bata ce ba bare su sa ran zata gaidasu,to su ɗin ma basu damu da gaisuwarta ba abinda ya damesu shine a gabansu, Bayan ɗan tattaunawa na wasu mintinan da basu gaza ashirin ba, Abby ya yi musu sallama ya tafi yana mai haddadawa aminatu ta saki jikinta na zuwa lokacin da zata koma can gidan,shima bata tanka masa ba dan gaba daya cike take da kallon iskancin da daddy yake yi mata, Abby Yana tafiya ta mike zunbur tana me tura ɗan karamin bakinta kana ta dubi Hajiya zubaida ta ce,",yunwa nake ji",dariya dadyn zahida yayi yana cewa to hajiya aiki fa ya sameki dan ɗiyar taki bata wasa da cikinta"ƙwafa aminatu ta yi a ranta tana cewa ba dai kasa an kawo ni gidanka ba ai.ka shiga uku da kai da wanda babu tsakinsa ma dan wallahi sai na gallabeku sai na hanaku baccin kirki daga kai har watsatsiyar matar taka kafin na koma. Me aikinta me suna azumi hajiya zubaida ta kwalawa kira,cikin minti ɗaya sai ga azumi ta zube gaban Hajiya zubaida tana cewa "gani ranki shi daɗe"kallon AMINATU ta yi tare da cewa me zaki ci baby?",kut kaji wani iskanci gandamemiyar budurwa dani za a cewa baby,aradun Allah baby na bayan uwarta",azumi bata san lokacin da ta ɗago kanta ba saboda tsananin mamakin ƙarfin halin wannan yarinya,ita ma Hajiya zubaida kasa motsi ta yi da jin wannan katobarar ta Aminatu me kama da zagi zagi,shi kuwa oga Alhaji bai shiga wani shock ba saboda yasan kadan daga cikin halin aminatu fiye da wannan ma zata iya faɗa,kuma hakan ba damuwarsa ba ne in dai har zai samu biyan buƙatarsa,azumi ce ta kasa jurewa ta ce,"ke kuwa ɗiyata wannan kalaman naki ai daidai suke da zagi ko ba komai ai sun haifeki",Ni ki bani abinci yunwa nake ji",aminatu ta faɗa ba tare da ta bi ta kan maganar azumi ba bare ta nuna cewa ta damu da abinda ta faa din,Hajiya zubaida ta maida dubanta kan azumi tare da cewa tashi ki kawo mata abinci kar ki damu kuruciya ce bata san manufar abinda ta faɗa ba", Alhaji Garba ya ce to zauna zata kawo miki abincin,zaman ta yi ba tare da ta tanka ba,ba a dau dogon lokaci ba azumi ta kawo mata abijcine rai da motsi, nan ta zauna ta vi ta koshi ta ruwa da lemo daga nan hajiya zubaida da kanta ta kaita dakin da alhaji garba ya ce a kaita,duk da cewa dakin yayi kusa da nata da nasa amma bata kawo ko kai a ranta ba sai manl daɗi da hakan yayi mata. A can gidan su mus ab kuwa, lokaci ɗaya kewaye aminatu ta fara tasiri a wajensu baran ma Khalid da bai san cewa aminatu ta yi nisa ba ne, duk shigar da zai yi sai ya tambayi Nana ko larai ina aminatu,daga karshe dai nana ta fada masa gaskiya aminatu sai ta yi kwanaki zata dawo,aiko kuka Khalid yasa rarrashi duniya yaki yin shiru, daidai lokacin kuma Abby suka dawo dashi da isma da ya biya ya dauko daga filin jirgi,to dawowar isma ce ta kwnatar da rigimar Khalid tunda dama isma mutuminsa. A daddafe dai yau aminatu ta kwana uku a gidan su zahida ba tare da wata matsala ba, sai dai ita da ta kasa sabawa, gashi duk abinda tasan zai bata musu rai shi take yi, amma mutanen kamar mayu basu nuna wata damuwa saima tarayrayarta da suke kuma yi,ita fa aminatu ji take kamar ana saka mata shakkun akan wadannan mutane,ji take kamar ana nuna mata su da wasu abubuwa da suka dangance su a cikin duhu,bata san me yasa ake cusa mata al'amarin waɗannan mutanen cikin tunaninta da ranta ba? sam bata yarda dasu ba hatta da mom zahidar bata yadda da ita ba, haka nan take ji dole akwai wani abu da suke buƙata a gunta, sosai ake nuna mata cewa ta bibiye su wanda ta kasa fahimtar daga ina take jin hakan kuma me yasa take jin hakan? Yau da ta samu kwana hudu cif a gidan ta farka da wata irin kewar su Nana Khalid da innawuro kai harda Anne abokiyar faɗanta,da dukan mutanen gidan,sai dai a tan gefe guda akwai wanda take ji kewarsa ce ta lulluɓe ta kowa kuma da za ace zata gansa da bazata damu da kewar su ba,so take ta ya kicesa ta manta dashi amma tana ji kamar wannan kewar da take ji ta sa ce,tura bakinta ta yi tamkar yana kallonta kana ta ce,"me zai sai na yi kewarsa? mutum bayan iskanci babu abinda ya iya, Ni kewar su nana kawai nake da innawuro na",a tunaninta maganar da ta yi zata iya sawa ta ji tabbacin hakan a ranta amma sai ta ji tamkar tsokano ciwo ta yi,hakan yasa ta zura tattausan silifas tare da yana mayafin bayar da yake kanta ta fice daga daga dakin,harabar gidan ta fito sai taga nan ma kamar yayi mata kadan hakan yasa kai tsaye ta yi mikakkiyar tafiya har zuwa gate ɗin gidan. Tun daga dan nesa da gate ɗin ta hango biyu daga cikin securities din gidan suna tura wata mata waje,daga dukkan alamu dai son shigowa take suna hanata ita kuma taƙi hanuwa,da ɗan gudu aminatu ta karasa wajen tana cewa "kai laifiya kuke tura babbar mace haka?shegu arnan da basu san meye daidai ba",su kansu securities ɗin babu wanda bai san matsayin aminatu a wajen me gidan ba shi yasa suke girmamata kamar wadda ta yi zaman shekara a gidan,hannu tasa ta lakucewa lutin cikinsu hanci tana cewa "ƙaton banza da bai san aikinsa ba,idan ba kuyi wasa ba duk sai nasa an koreku daga aikin, ɗayan ne ya buɗe baki zai yi magana, kan ya fadi abinda ke bakinsa aminatu tuni ta tattare duk miyan bakinta waje ɗaya yana buɗe bakin ta daddage ta tofa masa su acikin bakinsa maganar da zai yi kuwa sai haɗiyeta yayi tare da miyan AMINATU, ba aminatu da ta yi aikin ba hatta da matar da aka hanata shiga sai da ta samu kanta da ke cewa da dariya, baran ma yadda suka ga securityn na ta zura hannunsa can cikin maƙogaransa yana so yayi aman miyan AMINATU gaba daya ya rikice sai kokowa yake da numfashinsa yana kakarin amai wai ki zai samu ya mayar da miyan, amma babu alamar amai zai zo,cikin dariyar ƙeta aminatu take nunasa da yatsa tana cewa "dama ka ɗauki dangana ka kora miyan MATAR ƊAN BIRNI da ruwa dan yau babu kai ba cin abincin dare tunda ka ƙoshi da shayin miyan MATAR ƊAN BIRNI me garɗi", aminatu na juyowa sai ganin dayan security din tayi ya kama tsallen kwaɗo babu ji babu gani,shi kuwa ba komai ne yasashi yin tsallen kwaɗo ba sai dan yasan shima nasa hukuncin na nan zuwa wata ƙila ma shi kashi zata yi masa a bakin shi yasa ya gwammace yin tsallen kwaɗon ko ya samu ta tausaya masa,matar nan kuwa na tsaye tana kallon dramar aminatu da abin yayi matukar tafiya da ita, tsawon shekaru uku rabonta da yin murmushi in Ka cire yake bare akai ga dariya amma yau daya da ta haɗu da aminatu ta sata taya dariyar da ta jima rabon da ta yi irinta,kama hannunta ta ji aminatu ta yi wanda shine dalilin da ya katse mata tunaninta, jan matar aminatu ta yi tana cewa muje ciki ki fadi abinda ya kawoki kai kuma idan baku kiyayi aminatu ba aradun Allah gobe gashinta zaku ci kafirai banza da wofi kawai",zaman dirshen security nan yayi yana ci gaba da kuskure bakinsa da har yanzu bai dena jin yauƙin majinar miyan AMINATU ba,shima lutin zama yayi bayan ya tabbatar da bacewar aminatu a idanunsa,numfashi kawai yake ja yana aiyana cewa da zai samu dama sai ya karya aminatu biyu. Suna shiga falon aminatu ta nuna mata wajen zama tana cewa zauna bari na kira matar gidan", jinjina kai matar ta yi tana mai bin falon da kallon kauyanci. Dole sai ka.wuce dakinta dana Alhaji Garba sannan zaka isa ga dakin Hajiya zubaida,daidai lokacin da aminatu ta zo giftawa ta dakin daddy wayarsa ta yi kara wanda ke nuna cewa kiransa a kayi, har aminatu zata wuce amma ta rasa dalilin da yasa ƙafafunta suka ƙi yin gaba wanda har yasa ta fara sauraren wayar da daddyn zahida yake yi,Alhaji Alhaji ribado kana nufin kace min anyi nasara a kanku?yanzu daure yaronka za ayi kenan?sai da ya dan yi shiru na saianni wanda ke nuna cewa yana sauraron me magana ne,kana ya ce,"a'a ba zai yiwu ba dole sai mun nemo wannan shu'umin lauyan ai babu wani lauya me GASKIYA da ya isa yayi tasiri a cikin wannan jaha tamu in dai muna numfashi,kara yin jim.yayi kafin ya dora da cewa,yo ribado in dai da kudi ai ƙaryar me gaskiya ta kare kuma ina tabbatar maka da cewa duk boyon da yake da hana yan jarida magana dashi da kin nuna fuskarsa da yake to wallahi in dai muka sa shi gaba ko bai so ba sai ya bayyana mana kansa idan yaƙi ya saida mana da gaskiyar ta sa mu sai mu siyeta ta ƙarfin tuwo",dariya yayi wadda ke cike da ƙeta kafin ya ce,"ina haba ribado kai ma baka sakar masa kudi ba ne amma da kasa kar masa kudi da tuni kune da nasara,to Allah na tuba yaronka fyade nawa yayiwa yara kana siye lauyoyi sai wannan ne zai gagareka,ko yaƙi yarda ku haɗu ido da ido ai akwai hanyoyin da dole idan ka bisu zai kawo maka kansa cikin sauƙi,amma dai mu ka tsaya kayi kallon yadda wasan zai kasance,dan ina tabbatar maka da cewa kamar yadda muka yi wayar nan da kai nasha maka alwashi akansa, to haka zan kuma yi maka waya nasanar maka da cewa ya sayar mana da gaskiyartasa ko kuma mun siyeta ta ƙarfin tuwo",daga nan ya kuma sheƙewa da dariya, daga haka aminatu ta samu ƙwarin gwiwar wucewa daga bakin kofar tasa,zuciyarta cike da tambayoyi akan waɗan nan mutane, ta wani ɓangaren kuma yanzu so take kawai TASAN ko su ɗin su waye. Koda Hajiya zubaida ta fito, zama ta yi tana yiwa matar kallon rashin, gaisheta matar ta yi sannan ba tare da bata lokaci ba, ta faɗa mata bukatarsa na cewa ta taimaka mata da aiki ko na bawa fulawa ruwa ne saboda suna cikin matsin rayuwa ga shi tana da marayu a gabanta yanzu haka ma biyu basu da lafiya suna can ƙauye wajen mahaifiyarta tana kyale dasu, shine ita ta fito neman kudin aikin da za ayi wa yaro guda ɗaya,kafin Hajiya zubaida ta yi magana suna tsinkayi Muryar daddy Yana cewa, Hajiya ki bata dakin zama ko da dai bama bukatar aiki amma zamu taimaka mata, yarin naki dan shekara nawa ne za ayiwa aikin?"ya tambayi matar yana samun wajen zama,"matar ta bashi amsa da cewa shekarar goma",jinjina kai kai yayi tare da ɗan yin jim, zuba masa ido mayar da aminatu su kayi dukkansu zuciyoyinsu sai da suka.masa kuma suka tabbatar da cewa akwai lissafin da Alhaji garba yake yi wanda shine dalilin saurin amincewarsa. Azumi ce ta kai matar dakin da zata zauna,tana fita Hajara ta sa hannu ta share hawayen da suka cika idanunta,kafin cikin kaushin murya ta ce, wallahi in dai Ni yar halak ce ba zaku sake min na biyu sai na tona muku asiri,azzaluman da basa aikin Allah sai idan sun san zasu samu amfani(wannan mata ba kowa bace face Hajara Abubakar da ta yi basaja ta dawo cikin rayuwar zahida dan kawai ta cimma burinta na ɗaukar fansar ran mijinta) To fa ana wata ga wata shin dama Hajara baki hakura? ba duk da cewa kina jin kamar ba zaki samu lauya me GASKIYA da adalcin da kike nema ba,?muje dai mu ga ya lamarin zai kaya. Su kansu GJK din su waye? me ye alakarsu da AMINATU? Zaki yi dariya iya dariya zaki yi farinciki da annashuwa koda kina cikin damuwa. Akwai cakwakiya da abubuwa masu ɗaure kai wanda zasu zo ba tare da zato ko tsammani ba,akwai rikita rikita me tashin kai. Da kuma Sirrika boyayyu masu ban mamaki ku yi hakuri kar ku gaza ku biyo NI a sannu dan warware muku kulli da haska muku haske cikin duhun da ya mamaye labarin, Ku siya ku karanta yan amana ,domin gyara gobenku da tsarkake zukata da kuma karin ilmi cikin ilmin ttarbiyar yaranku mata, da kuma karin ilmi akan yadda zaku gyara zaman auren ku da yin tsaftataccen kishi wanda zai sa me gida yaji kamar ya fasa, da yadda zaki fahimci me sonki dan Allah da kuma samun annashuwa tare da sabunta soyayyar me gida cikin tsaftatacciyar kauna me taɓa zuciya, Kauna iya kauna sadaukarwa iya sadaukarwa nishadiniya nishadi kishi iya kishi,son zuciya iya son zuciya,neman kudi ta kowa ce hanya ido a rufe,da kuma rayuwar lauyoyinmu a yau,ku dai ku biyo niiiiiiiiiiiii✍🏾 Da kudinki anan 8064537048 Fatima yushau adam opay Amount 500 only ✍🏾 Na gode daga gimbiyarku me kaunar ku Fyadam ✍🏾 [4/12, 5:28 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page27``* A can gidan kuma zahida ce take buga sharafinta, dan sai yanzu ne hankalinta ya dawo jikinta, ta kuma sabunta halayyarta da ta yi sanyi,se yanzu ne ta kuma sanin muhimmancin mus ab da fahimtar ita din fa ba ƙaramin dace ta yi da samunsa ba, dan haka take matuƙar ɗagawa da kasancewarta matar mus ab,yadda take taku cikin ƙawayenta da hura hancin ita matar mus ab ce kadai ya isheka kallo,su kansu ƙawayenta ba wai da kudinta take tashin Kansu ba, sai dan kasancewarta matar young biloniya me ji da tsantsan kwarjini da sassanyan kyawun da ya haɗe da tsananin kwarjini da kamala,kar fa kuce wai mus ab irin mazan indiyawa ne ko larabawa da ba a samun irinsu cikin nahiyar africa,a a bafulatanin mutum ne irin ko wanne bafulatani, banbancin sa da sauran maza shine tsananin tsafta da iya gayu da son ƙamshi sai tsananin kwarjini da hasken addini da miskilancin da yake a juninsa tamkar wani saraki(uwar gida koke kika zauna kika fuskanci mijinki kika gyarashi tsaf zai iya zama kamar mijin Novel irin su mus ab, din aminatu da kuma al'amin din fahrin,sai yaya abdalla na bintu da kuma hamma wazeer na raihan sai kuma gwara zan ku na shekara zahlanku ta gidan YARBAWA sorry na manta sunan gwarzan zahla🤣ato dan babu ruwan Zahra Kar kije kinawa mijinki wani gani gani ya tambaye ki dalili kice masa littafin aunty Zahra kika karanta to bance ba babu ruwana 🤣). Wannan dalilin ne yasa suke girmamata da sanyatq a cikin matan da suka yi da ce, dan haka zahida take tsula tsiyarta a cikinsu, ga shi babu wadda ta isa ta yi mata hirar mus ab KO da ambatar sunansa ne,to kuwa yanzu zata fita hayyacinta ta yi ta faɗe faɗe marasa kan gado da maganganun da suke nuni da kamar tana musu izgili, haka rayuwar zahida take sam bata yin abu ta fuskar addini tunda bata dashi ɗan wanda take dashi kuma tuni ta yi watsi dashi,a halin yanzu jinta take bata da wata damuwa tunda an kawar da damuwarta daga inda take kuma bata jin mus ab zai taba zuwa inda aminatu take ko da a mafarki ne kuwa,dan shekarun da ta yi da aminatu jinta take duk a daure zuciyarta a kuntace take da zafin kishi da wutar bala in tsanar aminatu da hassadarta da take hanata sukuni cikin rayuwarta, ko a can asibitinsu ji suke yi inama ta koma zahidar baya me cike da damuwar da idan tazo asibitin bayan aiki babu abinda take iya taɓukawa bare har ta samu damar cin kashin na ƙasanta. Cike da takunta na ƙasaita take kokarin shiga bangaren mus ab,sai hura hanci take jinta take tamkar wata sarauniya a duk sa ilin da ta tuna ita din wacece da kuma matsayinta da take amsawa na babbar likitar mata da kuma ɓangaren fiɗa da babu kamarta acikin jaharsu,gata yar me kudi ita me kudi mijinta me kudi surukinta me kuɗi,wani irin murmushi ne ya kufce saman fuskarta lokacin da ta hango gwarzan maza mus ab Jamil zaune ƙasan tattausan cafet din da yayiwa falon ƙawanya,sai da ta dan yi jim tana kallon kyawu da tsarinsa da ko a wane hali yake sai ka gansa cikin wannan yanayin na nutsuwa da kamewa irin ta mutanen da suka san kansu, wanda ilimin addini da na zamani suka cika kansu da rayuwarsu ma ana irin mutanen da suke amfani da ilimin su acikin zamantakewar rayuwarsu, yaji a jikinsa ana kallonsa yanayin kamshin turarenta da ya ɗan hautsine da nasa da ya kama komai nasa yasa shi fahimtar ita ɗince,bai dago ba bai kuma motsa ba yana nan cikin zamansa na kalmashe ƙafa daya karkashin dayar da take a miƙe laptop ɗinsa a gabansa, ga dukkan alamu dai aikin da yake yana da dan muhimmancin da yake bukatar nutsuwa. Wannan halin na mus ab shine babban kalubalenta acikin rayuwar aurensu,dan zahida bata son Shariya da wulakaci, Shi kuma mus ab wannan ce babbar ɗabi arsa a ganinta shima girman kai ne da shi da ɗagawa saboda yana ganin yana da duk qualities ɗin da ya kamata a ce yayi hakan,ita a kan kanta tana jin da ita ce da baiwar da yake da ita da sai ta yi fiye da haka,to amma ai ita matarsa ce a ganinta ita ce ta cancanta ya saukarwa da kai ba wasu ba,don idan tayi duba ta wani ɓangaren sai taga cewa kamar ma ya fi mata wannan wulakancin akan jama ar da suke tare da shi, wanda ako da yaushe bata jin suna kusheshi kamar yadda ake kushe nata halin da yi mata Allah wadai,to amma ta danganta wannan da kwadayin mutane, suna yabonsa ne kawai dan kyautatawar da yake musu da rashin ƙyamar da yake nuna musu,ita ko wannan bai dameta ba in dai har sai ta basu ne ko kuma ta kulasu ne zasu yabeta to su bar yabonsu bata bukata. Da wannan tunanin ta daure ta ƙaraso inda yake, zama tayi tana ci gaba da kallonsa kamar zata haɗiyesa dan so, amma idan ta sake ta nuna masa shike nan ta kashe kanta, a hakan ma ya ta cika da wulakancinsa bare ta sakar masa jiki da zuciyarta,yatsina fuska ta yi kafin ta ce, "mus'ab kana ji na fa amma babu wani reaction a tare da Kai da zai nuna cewa kasan nazo", sai da ta fidda ran tankawarsa. kana kuma kamar ana matsa shi dole ta tsinkayi dakakkiyar muryasa can ƙasan maƙoshi yana cewa, "taya zan tanka Miki zahida?bayan baki cika sharaɗin musulunci ba,da kika zo kin yi sallama ne?"ya tambayeta tare da ɗagowa yana watsa mata rikitattun idanunsa da take matuƙar shakkar kallarsu a duk lokacin da tasan ta yi masa ba daidai ba,kawar da fuskarta ta yi, cikin takaici ta ce", to Ni da dakin mijina har sai nayi wata sallama zan shigo?kai babu dama a zauna zaman mutunci na mintuna da kai ba tare da ka kawo batun musulunci ya ce addini ya ce Allah ya ce annabi ya ce an rawaito daga abu kaza ba,haba dan Allah mus ab ni fa matarka ce, yanzu ba zaka iya bani lokacinka ka tarairayeni ka lallaɓa Ni ba sai dai kullum faɗa dan dai Ni ce na kawo rashin daidai duniya",cikin motsa laɓansa ya karanci auziya dan jin kalamanta yake tamkar saɓo saboda rashin dadinsu, daga haka ya tattare komai nasa ya tashi ya barta a wajen sake da baki da ta kaicinsa,ƙwafa ta yi tare da ficewa daga falon a fusace. Alhaji Kabir Alhaji Garba Alhaji Jamil,zaune a gidan gonarsu in da suka haɗu dan tattauna batun innawuro, wani ruwan magani a cikin kwalba daddy zahida ya miƙawa Abby tare da cewa, karɓi wannan shi za a zuba mata cikin ruwan da zata sha, Dr Shazam ya ce bashi da banbanci da ruwa dan haka babu wanda zai gane an sa wani abu a cikin ruwan shanta,wannan maganin shi zai tayar mata da ciwon cikin da dole sai an dangana ga asibiti,kuma dai kun san cewa tunda yar balaja'un ta ta bata kusa da ita dole GJK za a kaita,shike nan daga nan aiki ya kammala dan mu din masu nasara ne ako da yaushe shi yasa bama kawo rashin nasara cikin lissafinmu",ya kammala maganar da sakin wani shu'umin murmushi. Su ɗin ma dariya su kayi,yayinda da Abby yake juya ruwan maganin a hannunsa zuciyarsa fes, saboda nasarar da suke hawa mataki mataki ba tare da ta taɓa kwaɓe musu ba,to ko da ta kwaɓe ɗin ma nasararsu ce take sawa su yi saurin Ankara su yi maganin matsalar, Alhaji Garba ya dube su daya bayan daya fuskarsa cike da annashuwa kana ya ce,"na samo mana wani sabon kasuwancin",gaba daya suka zuba masa ido suna jiran karashen zancan,muskutawa ya ɗan yi sannan ya basu labarin sabuwar me aikin da suka samu har gida tare matsalarta,dariya suka.sheke da ita Alhaji Kabir cikin nuna daddyn zahida da hannu yake cewa "gaskiya garba da kai da jamil ban san wanda yafi wani iya salon neman kudi ba,kaji fa wata dabara", murmushin bosawa Abby yayi kana ya ɗauki laptop dinsa ya fara ƴan danne danne, cikin sakanni sai gashi ya yi hadakar kira da shi da duk wani customers dinsu na nan gida da na can kasashen waje,ko wanne da fuskarsa wajen su hamsin, take Abby ya sanar da su sabon kasuwancin da suke dashi a yanzu koda ko zuciya ta yaro dan shekara goma, dan haka me so a yi ciniki yanzu tare da yin buking,take kowannensu ya fara saka farashi kamar dai yadda ake saka farashin hannun jari ko siyan Company,daga karshe dai mutum biyu sun yi nasara me koda da me zuciya sun saka farashin da babu wanda ya kuma sakawa dan haka ciniki ya fada, take su kayi rubutu da saka rabin kudi aka tsaida date din karba, kamar yadda suka saba.tafawa su kayi suna mai shiga tsananin farinciki dan bayan zuciyar innawuro da ta aminatu wannan yaron ne mafi tsadar farashi da suka samu,tabbas dole Mutanen nan su riki kasuwancinsu da muhimmanci dan ba karamin kudi suke samu ba, kai me karatu idan kaji farashin zuciya ƙwaya daya sai numfashinka ya kusa ɗaukewa, dan talaka futuk idan ya samesu to babu shi babu talauci har zuwa kan tattaba kunnensa.da wannan suka rufe zamansu na yau. Daddyn zahida ba shi ya shigo gidan ba sai misalin ƙarfe ɗaya, dan sai da ya biya yayi sharholiyarsa da ya daina ta a baya, amma zuwan aminatu cikin rayuwarsa sai da ta tada masa da tsohon miki,duk da cewa ba wai yana samun gamsuwa ba ne,dan duk macen da zai kusanta sai ya fara aiyana aminatu a ransa tukuna yake jin dama dama,jin gidan shiru yasa ya wuce ɗakinsa kai tsaye,wanka ya yi kafin ya zura kayan baccinsa ya haye saman gadonsa yana maida numfashi,sai kuma ya kasa baccin ya fada duniyar tunanin aminatu kamar yadda ya zame masa jiki tun ranar da ya fara sata cikin idanunsa,dan acikin wannan shekaru babu ranar da baya mafarkinta,yau ma atepting din shiga dakinta ya fara yi kamar kullum sai dai Yana tsoron tijarar yarinyar shi kuma baya son yayi mu amala da mace ba acikin hayyacinta ba,har zuwa karfe biyu na dare ya kasa bacci kuma ya kasa tsaida matsaya dan da yayi kamar zai je sai kuma ya tuna wacece aminatu, daga karshe dai shi ya rinjayi zuciyar da take sagar masa da gwiwa ya zura silafas dinsa ya fice daga dakin yana aiyanawa ransa cewa babu abinda zai faru, wannan ne ya bashi kwarin gwiwar shiga dakin aminatu idanunsa rufe da son biyan buƙatar kansa. Cikin bacci aminatu ta dinga jin numfashin mutum a kusa da ita,kafin ta tantance abinda ke shirin faruwa ta ji an fara shafa jikinta wanda hakan yasa ta zabura tana kiran sunan Allah,kasancewar fitila a kashe hakan ya bawa Alhaji Garba damar bin aminatu yana ƙoƙarin kamata, kuka.tasa tana taresa da fadin waye wannan na shiga uku kashe Ni za kayi? Aminatu bata samu amsa ba take suka fara kokowa da mutumin da har yanzu bata tantance waye ba kuma tunaninta bai harsasho mata cewa daddy zai iya biyota a cikin gidansa ba.ihu ta fara yi sosai da neman ɗauki, jin ta fara ihun da zai sa a jita ne yasa daddy ya fara kokarin guduwa sai dai cikin wani irin al'ajabi suka.ga wutar dakin ta kawo hatta da karar kunnawar sai da duk suka jisa a cikin kunnuwansu,take wannan hasken ya bawa aminatu damar ganin fuskar Alhaji Garba a daidai lokacin da yake ta kokarin ficewa daga dakin ya kasa, tamkar wanda aka riƙesa, EY Shi Kam zai iya cewa rike san a kayi dan sosai yaji an riƙe ƙafafunsa wanda ba a bashi damar fita ba har sai da AMINATU ta ga fuskarsa fes a cikin idanunta,yana fita suka ci karo da Hajiya zubaida tare da azumi kai har da Hajara me zuwan yau,cikin tashin hankali Hajiya zubaida ta taresa tana tambayarsa me ya faru?kafin ya bude bakinsa aminatu ta fito daga dakin da gudu tana kuka da faɗin wayyo kwarto ne ya shigo wallahi kwarto ne fyade zai yi min ya cuce ni ya cuci dan birni",cikin in ina da daddyn ya ce ,"na rasa shi na bisa amma ban gansa ba,ku koma ku kwanta zan je na bincika",azumi ta ce ",garin yaya kwarto zai Iya shigowa ko dai a cikin securities ne?" Hajiya zubaida ta ce,"ko securities ba za su iya shigowa cikin falon nan ba bare dakin aminatu gaskiya abin da mamaki,aminatu ko zaki gane wanda ya shigo Miki a cikin securities din gidannan?"Hajiya zubaida ta juyo tana tabayar aminatu,aminatu ta bude baki zata yi magana daddy ya tare ta cikin kame kame dan ya hanata magana,amma ina aminatun ba zata hanu ba,dan kuwa baki ta bude cikin daga murya ta ce,"hajiya wallahi ni dad......."ke ke Aminatu baki da lafiya kin manta je ki kwanta,"daddy ya katseta cikin tashin hankali goshinsa babu abinda yake sai zubar da zufa kamar wanda aka saka cikin tandun gurasa,da zarar aminatu ta dauko magana sai ya katseta cikin rawar baki da karkarwar jiki,da aminatu taga haka sai abin ya zamar mata abin tsokana dan kuwa cikin kara rudashi ta kuma.daga baki ta ce shine ya sh......caraf ta ji hannun daddy saman fatar bakinta ya rufe mata baki cikin tashin hankali yana cewa ",yanzu haka ma jemage ne baki lura ba",take azumi da Hajara da ta canja sunanta zuwa karema suka kalli juna cike da mamaki dan tuni sun dago jirgin aminatu na son tonawa daddy asiri dan babu kokonto sun fahimci shine kwarton. Hajiya zahida kuwa cike ds fusata ta ce "a'a uban jemage,haba daddyn zahida ya za a yi ka hana yarinya magana kiri kiri bayan ta san wanda ya shigo mata daki",janyewa ya yi daga kusa da aminatu yana cewa "to to to ba jemage ba ne karan gidan busert ne kin san shi da jaraba idan bai samu karya ba yaran mutane yake nema",caraf aminatu ta ce au daddy kai ne karen?"take azumi da karema(Hajara)suka tuntsure da dariya dan kuwa sun kasa jurewa hajara a rayuwarta bata taba tunanin zata iya yin irin wannan dariya ba tare da ta samu aldalci ba, amma sai gashi yau daya da ta zo gidan nan aminatu ta girgiza 'yan hanjinta da dariya, ƙarar ƙugin cikin daddy da ƙarar zawon da ya saki ne yasa gaba daya suka fara karon barin wajen dan kuwa ba zasu iya rike dariyar su ba kuma hakan na iya jawo musu kora ta har abada, Hajiya zubaida kuwa wani mugun kallo ta watsa masa tare da barin wajen tana toshe hancinta da warin zawonsa ya game wajen,aminatu dariya tasa tana nuna jallabiyarsa da ƙafarsa da zawon ya zuraro tana cewa "subhanallah kwarto ya bige da zawo azumi ku kawo dauki",jin ta kira su azumi ai baisan sanda ya taka da wani uban gudu ba, ya fada ɗakinsa cike da borin kunya da mozanta da yayi a gaban ma aikatansa.aminatu kuwa ƙin komawa ɗakinta tayi, sai Hajara tabi zuwa dakinta. Azumi ita ka dai ta dinga babbaka dariya, ko da ta yi shiru da zarar ta tuna,karkarwar me gidan da batun jemage da kare da zawo sai ta ji ba zata iya jurewa ba, haka a can bangaren aminatu da hajara suma dariyar suka dinga yi karma hajara ta ji labari, dan ita dariya biyu take yi har lokacin bata manta da miyan AMINATU da security yasha ba wannan ne ya ke karawa dariyarta armashi..... [4/12, 5:30 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` Page28``* Alhaji Garba yana shiga ɗaki kai tsaye bayi ya nufa ya wanke jikinsa, ko wanka bai tsaya yi ba ya fito cikin gaggawa ya dauki waya ya dannawa Abby kira, sai da ya kira sau wajen biyar sannan Abby ya daga bayan ya lallaɓa ya baro dakin da suke tare da Nana,dayan dakin ya shiga tare da rufowa sannan ya fara magana, "haba Garba me ya faru kake min irin wannan kiran cikin dare bayan kasan ina tare da Nana tun da ba mu yi da kai zamu yi waya ba bare na shirya?",cikin azalzala alhaji garba ya tafi kan maganarsa ba tare da ya biyewa tuhumar Abby din ba,"ina fata dai ka bawa innawuro wannan maganin?" Na bata me ya faru?"Abby ya tambaya cike da kaguwa,ba tare da ya bawa Abby amsa ba ya ci gaba da cewa to ya sakamako ya fito?"a takaice Abby ya kuma bashi amsa da cewa ina nan ina jira dai nasan zuwa asuba zata kasa jurewa ta kira nana shi yasa nake tare da nanan",Alhaji Garba ya kuma cewa "to Jamil ka tabbatar da cewa kun fita tare da zahida dan ina mai tabbatar maka da cewa aminatu zata iya dawowa gidan nan cikin ko wane irin lokaci kuma kasan cewa muddin zahida taga aminatu ta dawo gidan nan bazata samu nutsuwar yin aikin nan ba zata iya jawo mana asarar biliyoyin kudaden da muka ci fiye da rabi idan aka ce zamu biya ba ƙaramin jinjga zamu yi ba,dan haka ka yi yadda zaka yi ka tabbatar bata haɗu da aminatu ba", Abby ya ce. "to me kuka yiwa aminatu da har zata iya dawowa gidan nan bayan kuma da amincewarta na kawota?"hannu yasa ya goge zufar da ta ke ta tsatstsafowa a goshinsa kana ya ce."jamilu kasan halin wannan sheɗaniyar yarinyar me kama da aljanu dai ba sai na yi maka karin bayani ba, dan haka kayi abinda na ce maka ka ceci nasararmu daga faduwa,"shike nan ko mai zai tafi daidai gashi can ma naji motsin Nana yanzu haka ciwon innawuron ne ya fito da ita", daga haka suka.kashe wayar Abby kuwa yana fita ya tarar da Nana cikin tashin hankali tana sanar dashi innawuro ce bata da lafiya sosai,wucewa yayi suka nufi dakin innawuro a ransa yana cewa "anzo wajen". A cikin daren suka fita da innawuro zuwa asibiti,hatta da mus ab bai zauna ba sai da ya bisu,ko a can asibitin shi ya dinga kaiwa yana kawowa dan ganin innawuro ta samu kulawar likitoci,sai da aka kira sallah sannan Abby ya jashi suka tafi masallaci wanda dama wannan damar kawai yake jira saboda hankalin sa ya ɗan tashi ganin mus ab din ya ki matsawa daga dakin da aka kai innawuron. Lissafin Alhaji Garba yayi daidai, dan kuwa aminatu na idar da Sallah asuba ta dauki abin da ta zo dashi ta fito dan barin gidan,da Hajiya Amina suka ci karo, bata tambayi aminatun dalilin ganinta da haka ba dan tasan dama hakan zata faru,waya kawai ta mikawa aminatun tare da cewa "Nana ce take son magana da ke",cikin sauri aminatu ta karbi wayar lokaci daya tqna sakawa nana kukan taɓara, sai da nanan ta rarrasheta sannan ta snaar da ita cewa suna asibiti innawuro ce tq kwana da ciwon ciki daga karshe da takwantar mata da hankali da cewa amma ta ju sauki har tana magana dan haka aminatun ta taho a nutse. Tana mikawa Hajiya zubaida wayar ta ja akwatin ta tana shirin fita,kasa dakatar da ita mom zahida ta yi sai kalli da ta bita dashi dan har yanzu shock ɗin da ta shiga jiya bai saketa ba, duk da cewa tasan halin mijin nata,to amma bata yi zaton akuyancin nasa ya kai ya farma yarinya ƙarama marainiya ba. A harabar gidan suka hadu da hajar tana share farfajiyar wajen,kallon aminatun ta yi cikin damuwar tafiyar da zata yi dan ɗan zaman da suka yi har sun saba,"yanzu tafiya zaki yi kenan"?hajar ta tambayi aminatu cikin damuwar da ta bayyana kan saman fuskarta,kama hannunta aminatu ta yi tare da cewa ,"hajar ai yanzu tafiya ta zamar min dole tunda kakata na asibiti ba lafiya ƙarin damuwata ma shine an kaita asibitin da bana so, asibitin da na yiwa tsanar da ban san dalilinta ba,shi yasa yanzu dole can zan tafi kai tsaye ", wane asibiti ne"?hajar tayi tambayar zuciyarta cike da fargaba,jan akwatin aminatu ta yi kana cikin rashin bawa tambayar hajar din muhimmanci ta ce,"GJK hospital",da gudu hajar ta bi bayan aminatu tana cewa zan iya rakaki na duba kakar taki dan Allah idan ban takura ki ba", zuba mata ido aminatu ta yi tana kallon cikin idanunta wanda har sai da hajar ta ji tsoron hakan ya shigeta dan sai taga idanun aminatun sun yi wata kala da ban kamar ba nata ba,a hankali kuma sai taga sun koma daidai har aminatun ta buɗe baki ta ce, "babu wata damuwa na gode da kulawa", dai-dai nan suka ƙaraso tsakiyar tafkeken filin gidan da yake barazanar cinye unguwa guda,malam tanko driver su ka gani ya ƙaraso da mota gabansu tare da cewa "Hajiya ku shigo Alhaji ya ce na kaiku asibitin", wani kallon rainin hankali aminatu ta yiwa daddy da yake tsaye daga dan gefansu cikin yanayin rashin gaskiya,kafin ta ce, "bama buƙatar shiga motar jemagu, idan mun fita da sawayen mu su tare mana hanya a ja mu lungu a yi mana fy.....wata irin ƙatuwar atshawa me haɗe da tari Alhaji garba ya saki sarai aminatu ta gansa kuma idanunta akansa take yin maganarta ba tare da shakka ko tsoro ba, da sauri malam tanko ya fita daga motar ya je yana masa sannu tare da bashi ruwan robar da ya ɗauko masa a motar, karɓar ruwan yayi ya kafa kai bai sauke robar ba sai da ruwan suka ƙare tas, sannan ya dire yana maida numfashi tamkar wanda yayi tseren gudu,sosai hajar ta yi dauriyar riƙe dariyar dake cinta tana jinjina wa aminatu da mamakin halinta na rashin tsoro da rashin barin ko ta kwana,jan hannunta da aminatun ta yi shi ya dawo da ita hankalinta, fita suka yi daga gidan sai da suka yi tafiya me ɗan nisa sannan suka samu adedeta sahu suka hau. Aminatu bata taɓa tunanin haka jikin innawuro yayi ba, dan lokacin da suka ƙarasa asibitin har an fito da ita za a shiga da ita dakin tiyata, riƙe gadon aminatu ta yi tana wani irin kukan da tunda tayi wayo bata taɓa yinsa ba,saboda innawuro ita ce komai nata bata san kowa ba sai ita shi yasa bata son ko ciwo innawuro ta ji ajikinta, cikin kuka take cewa "yanzu da tafiya zaku yi da innawuro na ban ganta ba?me za kuyi mata?ina zaku kaita me ye ya sameta da har za a yi mata aiki?Nana da sauran likitocinne suke ta ƙoƙarin kamata,amma ta riƙe gadon katamau tamkar wadda ake ƙarawa ƙarfi,da karfi ta doke hannun wata likita da ta kama ƙafadarta tana cewa, "ni ku rabu da ni bana bukatar wannan asibitin ban sonsa ku bani ita na kaita wani asibitin bana so na rasa innawuro ita ka dai ce da Ni a duniya, ita ce kawai me sona",da sauri Abby ya ɗan matsa gefe tare da sa kiran mus ab, dan kuwa tabbas idan suka ƙyale aminatu ta ci gaba da wannan zantukan zata jawo musu babbar asarar da suke gudu,mus ab din Yana ɗagawa ya ce,maza mus ab ka dawo idan ka gama sa hannun dan ga amimatu nan duk ta birkice mana kowa ya kasa control ɗinta ta hana a shiga da innawuro dakin tiyata kuma hakan kan iya jawo babbar matsala",ko rufe bakinsa bai yi ba ya hango mus ab din cikin nutsuwa yana tunkarosu,sauke wayar yayi daga kunnesa yana sakin ajiyar zuciya,tare da goge gumin fuskarsa,a ransa yana cewa "wannan wace irin yarinya ce haka? Me yasa take son bamu matsala cikin rayuwarmu?me yasa muke tsoronta duk da mun san cewa babu wani abu da zata iya ko da kuwa tasan wani abu daga cikin sorrinmu?"bai da wannan amsar dan haka yayi kokarin saita kansa,a hankali cikin makewarsa ya karasa inda aminatun take ƙankame da gadon innawuro ta hana kowa taɓawa bare aja ta zuwa dakin tiyatar, dogayen hannayensa yasa ya ɗagota daga durƙusan da tayi gaban gadon tare da ɓanɓare hannunta daga jikin gadon,kafin cikin taushin muryarsa da ko wane harafi yake fita daddaya ya ce,aminaaaaaatu," da sauri ta buɗe idanunta da su kayi wani irin ja saboda kuka tana cin karo da fuskarsa kuwa ta wani irin rungumesa irin rungumar nan dake tabbatar da cewa ta samu inda za a share mata kukanta, dogayen hannayensa yasa yayi mata zobe yana mai tafa bayanta cikin wata irin lallaɓa da kulawar da duk wata mace zata so ace ita ake yiwa, goga fuskarta ta shuga yi a kirjinta tana ɗan bugunsa cikin kuka tana cewa "ƊAN BIRNI kar ka bari su tafi min da innawuro na ita kadai gareni idan na rasata bani da kowa tinda har yanzu Ban samu ƊAN BIRNI na ba bani da me kulawa dani bani da me jure shiriritata, idan na tsokano faɗa babu me tsayawa gabana na boye a bayansa dan Allah su dawo min da innawuro na kaji Ɗan BIRNI". Duk wanda yake sauraron aminatu gurin nan sai da kalamanta suka soke shi, dan ita Nana ma kuka take yi haka hajar da sauran mutane masu taguwar zuciyar dake reception ɗin,cikin wannan halin likitocin suka samu suka janye gadon da innawuro take kai suka wuce ɗakin tiyata. Abby dai ya samu wancan baragabar ta sake shi yanzu kuma fargabar da yake shine na kar zahida ta fito taga mus ab da aminatu a cikin wannan halin,dan muddin zahida ta gansu a haka zata iya birkice musu rasa kanta, wanda shima hakan babbar matsala ce, tunda saboda buƙatar nutsuwar ta ta ne ma har suka nesan ta ta da aminatun, wannan tunanin da yayi ne yasa shi zabura ya nufi ofishin zahidar dan ya dan dauke mata hankali har mus ab yabar wajen da AMINATU. Har yanzu aminatu kuka take, wanda haka yasa mus ab ya yi kasa da murya dai-dai saitin kunnenta ya fara mata magana cikin lallashi, so sorry angel innawuro zata fito lafiya, ga Nana tana sonki ga suhaima da Khalid duk suna sonki ki daina cewa baki da kowa",dago kanta tayi da kan ƙirjinsa tana mai kallon idanunsa da bata iya kallar cikin su ta ce,kai baka so na?"sosai tambayar ta buge da amma dake jarumi ne ba komai zaka fuskanta daga garesa ba, sai ya ɗan furzar da hucin bakinsa kafin cikin wani irin yanayi me sanyi da lumshe kwayar idanunsa da suke tamkar na mai jin bacci ya ce,"SONSO me zurfeen da bashi da iyaka da ƘAUNA irin wadda babu irinta a duniya",shi kansa mus ab baya ce ga da ga inda kalaman nan suka fito ba shi dai kawai ya tsinci zuciyarsa da bakinsa suna rera kalaman tamkar wani waƙe,aminatu kuwa wani irin zazzaɓi ta ji yana shirin kamata saboda yadda kalaman suka shigeta shigar bazata, duk da cewa bata cikin hayyacin da zata iya fahimtar kalaman nasa dalla,jin yanayin jikinnata yasa shi duban Nana ba tare da ya ce komai ba,jinjina kai Nana tayi dan ita tuni ta gama laƙantar gane yaren kuramen dannata,shi yasa ko motsi yayi tana iya fuskantar abinda yake nufi,kamar dai yanzu da ta gane yana mata nuni da zasu tafi gida da aminatun ne dan ta samu nutsuwa,da kansa yasa ta amota sannan ya shiga yaja suka bar harabar asibitin. A can bangaren zahida da Abby kuwa, tare ta yayi da wasu bayanan da bata wani ganesu,wanda bai kyaleta ba har sai da ya fito ya tabbatar da cewa mus ba ya tafi da aminatu,yana shirin komawa ta fito sanye cikin kayan aiki hannunta sanye da hand gloves da wata nas a gefanta rike da wasu TARKACE acikin faranti,ajiyar zuciya Abby ya sauke wadda ke nuni da fara dan samun nutsuwar da yayi tunda bayajin mutuwarsa zata kammala har sai an fito da zuciyar innawuro da ƙodarta lafiya. Zahida na dora hannunta saman saman hadle din kofar da zata sasanta da dogon corridon da dakunan tiyatar suke a jere reras kamar dakin hotel,taji an riga ta buɗewa ta ciki ba kuma buɗewa ce da ke nuna lafiya ba,dan hatta da farantan karkace kayan operation din dake hannun nas ɗin nan sai da suka tarwatse, kasa, securities din dake gadin kofar tuni suka yi kan likitan da yayi wannan barnar dan kuwa su kullum a shirye suke cikin shrin ko a mutu ko ayi rai. Sai da suka tabbatar likita ne sannan suka janye daga dabaibayin da suka yi masa da bindigun su hagu da dama,cikin tashin hankali Abby da ya kasa fita da ga wajen ya matso yana cewa kai lafiya me ya faru?" Zahida ma kallon Dr Salomon take cike da fusata da tambaya,cikin rawar baki da na hannu yake nuna musu hanyar dakin tiyatar ba tare da ya iya cewa komai ba,cikin tsawa zahida ta ce "dalla malam ka bude baki ka gata mana me ye yake faruwa?"dakyar Dr Salomon ya iya bude bakinsa dake matukar rawa cike da rashin hankali ya ce,babu shi babu majinyaci ya bace bamu gane sa ba", da sauri Abby ya shaƙi wuyan Salomon Yana cewa me kake nufi wane majinyacin kake fada yi mana bayani mu fahimta,?"cikin tsananin walahalar shaƙar da salonmon ya ji yake cewa Hajiya innuwurr shine baya nan ya bace", da wani irin gudu zahida da Abby Kai har ma da securities din suka bangaje Salomon suka shige dakin dan ganewa idanunsu abinda take shirin faruwa..... Tofa wai ya haka ne? Me ke shirin faruwa? Da gaske innawuro aka sace? Idan ita ce wa ye ya sace ta? Ta yaya kuma hakan ta faru bayan duk likitocin da zasu yi aikin sun kasance a dakin? Uhhhhhh bana cewa komai yanzu.... Fyadam ✍🏾 ,8064537048 Opay Fatima yushau adam Amount 500 [4/12, 5:49 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page29``* Turus su kayi gaba dayansu suna kallon gadon wayam,babu innawuro babu alamunta,cikin daga murya da hargowa zahida ta ke tambayar likitocin da suke kula da innawuro,"me ye hakan tayaya duk kuna dakin za a sace mutum guda ba tare da kun sani ba?"cikin in ina nas halima ta ce", wallahi Dr bamu san komai ba, saboda nas ahlam ne ya shigo ya ce in jiki kin ce ya maida ita dayan dakin me kallon wannan,shine mu ka bari yaja gadon ya fita har da ce mana mu tsaya mu haɗo kayan aikin sai mu biyosa,to a garin tsayuwar ne har haka ta faru ba tare da mun Ankara ba sai daga baya ne ma muka fuskanci cewa ba nas ahlam din ba ne ya shigo yaudararsa aka yi aka sumar dashi aka yi amfani da kayansa dan ancimma a manufa",wata irin zufa ce ta shiga ketowa Abby da ya kasa cewa komai bayan zare idanunsa da yake zuwa loko da saƙon ɗakin kamar zai ga innawuro anan,cikin tsawa da hargowar da ke nuna tsananin tashin hankali zahida ta ce "ina nas ahlam din yake?"Dr yana cikin dakin canja kaya a sume",cewar dr salomon da ya fi kowa tsorota dan shi gani yake yi aljanu ne kawai suka yi wannan aikin ba mutum ba, domin kuwa lissafin ya kai lissafi,tabbas wanda yayi wannan aikin ba ƙaramin me lissafi da wayo ba ne", Da gudu Zahida ta da Abby tare da sauran nas din suka fice zuwa ɗakin canjin kaya, a ƙasan ɗakin suka samu nas ahlam kwance daga shi sai gajeren wando wanda hakan ya kuma tabbatarwa da Zahida da Abby cewa amfani a kayi da kayansa na aikin tiyata aka ɗauki innawuro,Dr zahida ce ta durƙusa a gabansa tasa hannunta a kofofin hancinsa sannan ta dago kanta tana kallon ragowar likitocin kafin ta ce "ku ɗaukesa zuwa emagency ku tabbatar da cewa ya farfaɗo cikin mintinan da basu gaza talatin ba"Sannan ta maida kallonta kan securities da likitocin da suke dakin, kafin cikin kaushin muryar da take nuna tsantsar gargaɗi ta ce ", daga iya mu dun nan bama bukatar kowa ya san wannan bangare idan ma wani yaji to a tabbatar an toshe maganar ta tdaya iya nan,domin kuwa fitar wannan maganar daidai take da rusa wannan asibitin, kun san dai cewa mutane suna jiran kiris ne akanmu dan haka mu bar maganar ,mu kuma zamu yi duk abinda ya dace dan ganin mun binciko wanda yayi wannan aikin,cikin ruwa fun asiri ba tare da kowa ya ji ya gani ba,muddin na samu maganar nan ta fita to wallahi dukkanku nan baku tsira daga karbar mummunan hukucin mu ba",daga karshe ta nuna musu hanya tare da ceqa kuje ku yi abinda na umarce ku", gaba daya fita suka yi daga dakin suka bar zahidan da Abby da yake ji tamkar zai yi hauka. Suna fita Abby ya zabura yana cewa Zahida ya zamu yi me ye abinyi ta ina zamu fara?"ɗan jim Zahida ta yi kafin ta kalli Abby ɗin da lokaci daya duk ya wani firgice,kana ta ce"Abby yanzu Bama da wani abinyi baya ga mu nemo wata zuciyar da tayi daidai da waccan mu yi aiki kanta idan ba haka ba muna cikin matsala kun dai fini sanin halin Mr alfa Romeo bashi da daga kafa akan harkar kudi komai kankantarta, in yaso idan muka gaba da matsalarsa sai mu fara binciken wannan shu umin me aiki tamkad da jinnun, tabbas Abby wannan kwamushen yana da alaƙa da wanda yasan sirrinmu ko kuma yake zarginmu",jinjina kai Abby yayi kafin ya ɗan dafe kansa na sakanni can kuma ya ɗan zaburo tare da cewa",anya kywa babu sa hannun AMINATU?"girgiza kai zahida ta yi kafin ta ce, "a'a Abby aminatu ba zata iya ba, ka manta aminatu ko zuwa asibitin nan ba ta yi ba kai bana tunanin ma tasan ankwao innawuro nan kaga kenan babu ita a cikin zarginmu ",ey haka ne fa amma duk da haka ba zamu kasa bincikarta ba kin san yarinyar nan tamkar aljana take komai aka ce miki zata yi kar ki musa", Abby muje kar shurun mu ya kuma dasa zargin da mitane zasu yi mana binciken kwakwaf akan wannan al'amarin". Fita su kayi daga dakin suna mai tunanin ta yadda zasu fuskanci aminatu Nana Mus ab da wannan maganar me girma wadda tafi ace mutuwa suka bayyana. Da sauri Nana ta ƙaraso gaban Abby idanunta cike da ƙwalla tana cewa,me yake faruwa shin da haskene an rasa innawuro?"jan hannunta Abby yayi amma sai ta dinga kokarin fincikewa tana ci gaba da yi masa tambayoyin da wasu ma bata san tana yin su ba, a haka ya saka ta amota ya figi motar suka bar harabar asibitin. Abin ya faru akan idanun wasu tsirarun mutane, to amma lokaci ɗaya maganar ta mutu saboda yadda aka nuna cewa innawuro bayi ta shiga ta faɗi a ciki bayi bayan farfadowarta saboda ba ayi mata allurar bacci ba,da wannan maganar suka samu suka rufe batun ɓatan innawuro. Suna zuwa gidan ya kashe motar ya zagayo da kansa ya kuma buɗe mata tare da kamo hannunta suka wuce cikin gidan, ba tare da ya kula da ƴan ƙananun kukan da ta ci gaba da yi ba,sai da ya kaita har dakinta sannan ya fita zuwa Masallaci bayan ya bawa larai umarnin kula da ita, Yana fita itama mikewa tayi ta shiga bayi ta dauro alwala tazo ta tada sallah,sai da ta fara yin nafila kafin ta maida farilla, ko da ta idar ta jima a zaune tana karatun Alkur'ani idanunta a lumshe baka jin ko mai sai sassanyan Muryarta da take tashi cikin kamewa da fitar da haruffa tare da tajwidi,a hankali ta dinga jin zuciyarta na sanyaya duk wani datti na korewa,ba ita ta dakata ba har sai da taji shigowarsa dakin kana ta shafa tare da mikeqa tana dan kallonsa kasa kasa. Cikin dakakkiyar muryasa ta ji yana cewa "innawuro tana lafiya,yaushe zaki koma wancan gidan?"girgiza kanta tayi tare da cewa "a'a Ni ba zan koma ba na dawo gida kusa da innawuro na",me yasa ai na ga ke kika ce za ki je ba wani ya miki dole ba",tura ƙaramin bakinta tayi tana kokarin fita daga dakin ta ce,"to yanzu kuma na canja ra ayi ina nan"daga haka ta fice daga dakin tana mitar sa a ranta,shima fita yayi har zai haye upstairs sai kuma ya dakata tare da canja hanya zuwa falon saboda jiyo muryar nana da yayi.zuba mata ido yayi saboda yanayin da ya ganta a ciki, aminatu na gefenta tana ta zuba mata tambayar yaya jikin innawuro ta farfaɗo? me yasa basu dawo da ita gida ba?"amma Nana ta kasa amsa mata ko tambaya daya,shima mus ab din kasa haɗa ido ta yi da shi saboda ta fahimci irin tambayar AMINATU yake mata ta yanayin kallon da yake mata,da kyar ta iya bude baki ta ce"tana nan lafiya bari na je na yi sallar zuhur na dan huta kafin mu koma hospital ɗin",, daga haka ta zame hannun ta daga na aminatu ta wuce zuwa bangarenta,shi kuwa da ma Abby yana ajiyeta juyawa yayi yabar gidan dan bai ga zama ba a cikin irin wannan lokaci,yana tafe yana kiran su Alhaji Garba akan su haɗu a can gidan gonarsu. Ganin yadda jikin Nana yake a sanyaye yasa aminatu ta yi kwaƙwal da idanunta zata yi kuka,kama hannunta mus ab yayi yaja ta suka bi bayan Nanan, saidai suna.gab da shiga dakin suka ji yo Muryarta cikin kuka tana waya da suhaima tana sanar da ita halin da suke ciki na batan innawuro,wani irin bugawa zuciyar aminatu ta yi,har mus ab na jin bugun zuciyar saboda kusancin da suka yi,baki ta bude zata yi magana yayi saurin tarar numfashinta ta hanyar sa hannunsa ya rufe bakinnata tare da janta suka koma da baya,kuka take son yi da magana amma ya hanata wannan damar. Bashi ya saki bakinta ba har sai da suka shiga ɗakinsa ya zaunar da ita saman gadonsa tare da janyo laptop dinsa gabanta ya kunna,aminatu tana so ta yi kuka kuma tana son ganin abinda mus ab yake kokarin yi, dan haka ta dake zuciyarta da take ji tamkar zata faso kirjinta ta fito ta zubawa laptop din ido tana kallon abinda zai bayyana a ciki,ware manyan idanunta tayi cike da mamakin abinda take gani tar saman screen ɗin laptop,bakinta har rawa yake wajen ambatar sunan innawuro kafin wasu zafafan hawaye su sauko mata sai kawai ta rungume laptop ɗin tana wani irin kuka da yake fitowa tare da dariyar farinciki, ajiye laptop din tayi tana kallon innawuro kafin ta buɗe baki ta ce, "innawuro na aka ce an sa ce ki?yanzu kina ina?a ina kike? murmushin dariya innawuro ta yi saboda ganin farincikin aminatunta kafin ta ce ", boɗɗo na ki kwantar da hankalinki ina cikin aminci tare da mutane masu karamci, amma hakan bata samu ba sai da taimakon wata mata da ta ce sunanta Hajara tare da mus abu wanda shine yayi komai, amma ba zaki fahimci ko mai ba a yanzu sai nan gaba, kuma muma har yanzu bamu fahimta ba sai nan gaban idan bincike ya tabbatar, aminatu gaba dayan mu nan muna cikin duhu saboda matar har muka rabu da ita bata bayyana mana komai game da dalilinta na bada gudummawa wajen sace Ni ba",dafe kirji aminatu ta yi tana cewa , innawuro da gaske dai sace kin aka yi ko?"jinjina kai innawuro ta yi kana ta ce,a wajen wasu sata ce amma a wajen mu taimako ne kamar yadda ta fada mana kuma ta ce in dai har muna son sanin gaskiyar abinda yake faruwa to kar na bayyana a idanun duniya,kema saboda kina da hakkin sani ne bana so kuma hankalinki ya tashi shi yasa muka sanar da ke,ita ta shirya abin amma mus ab shi ya gabatar da shirin,gashi nan a gabanki amma bana so ki tambaye shi dan shima a duhun yake lokaci ne zai nuna komai,"to innawuro tunda dai kina nan lafiya alhamdl da zan ga wannan matar da na rungumeta na mata godiya,amma dan Allah innawuro shi na rungumesa runguma daya da sumbata ɗaya ta nuna godiyata innawuro na Miki alkawari ba zan wuce haka ba",kasa magana innawuro ta yi saboda kunya sai kawai ta rufe laptop din gabanta tana yiwa boddonta addu'ar shiriya. Aminatu kuwa bata saurari amincewar innawuro ba dan bata ma san ta rufe laptop din ba, saboda tana gama magana ta rungume mus ab tare da Kai bakinta saitin nasa ta sumbaci labbansa tana shirin dauke bakinta taji ya sa hannunsa gaba daya biyun ya tallafi bayanta tare da manne ƙirjinsa da nata bata yi aune ba taji tattausan harshensa yana ratsa ko wace kusfa da kofa da loko da ke cikin bakinta, shan bakinta yake tamkar ya samu alewar lollipop, hankalinsa kwance, runtse idanunta ta yi tana dan mutsu_mutsu da jikinta dan son kwacewa, idanunsa a lumshe ya dan dauke bakinsa da ga kan nata kana cikin wata irin murya me ratsa kashi da jijiya yace,"tunda kika fara sai kin ƙarasa,da kin sani ma baki yiwa innawuro alkawarin cewa daga haka babu kari ba",daga haka ya birkitata zuwa kan gadon tare da kwanciya saman cikinta ya ɗan sakar mata nauyinsa kadan yana kallon cikin idanun ta da take ta ƙif_kifta su kamar munafuka,jin nauyinsa yasa ta ɗan yi kara tare da tura ƙaramin bakinta tana cewa "wannan fa iskanci ne ka daina babu kyau Allah yayi....bata samu karasawa ba saboda ruf ya rufe bakinta da nasa ya ci gaba da bata wani irin fashionally Kisess masu taɓa zuciya da war gaza tunanin lafiyayyar mace,juya ta kawai yake yana shanye miyan bakinta,sai dai bai yarda ya taba ko inan ta ba dan ba wannan ne a ransa ba duk da cewa ba ƙaramin juriya yake yi ba, yana jin wani irin feelings akan aminatu me ƙarfi sai dai hakan ba shi yake nuna zai so kansa ya tauyeta ba, dan ya yiwa kansa alkwarin cewa idan komai ya kammala zai bawa aminatu yancinta na zabar mijin da take so,shi yasa duk abinda zai yi yake kokarin kawo adalci cikin lamarin, wannan din ma wasu lokuta da dama baya sanin hakan tana faruwa,some times yana kasa riƙe kansa ne da fita hayyacin da har take kaishi ga aikata hakan. Aminatu dai bata san lokacin da bacci ya dauke ta ba,mus ab ya jima a zaune yana kallon fuskar aminatu tare da tuna batun mata me suna Hajara. Abinda ya faru bayan gama wayarsa da Abby akan yazo ga aminatu ta hana a shiga da innawuro dakin tiyata,sai kawai yaga mata a gabansa ba kuma tare da ta ce masa komai ba ta mika masa wata doguwar takarda ta bar wajen,buɗe takardar yayi yana karantawa cike da daurewar kai,idan kana son farincikin aminatu to tabbas sai ka kubutar da kakarta daga shirin barin duniya idan kana bukatar taimakona ka kira Ni a wannan layin, kar kuma ka yi min ko wace irin tambaya saboda ba zan sanar da kai komai ba, dan kuwa babu yardar farad daya tsakanina da duk wani kwayar halitta a cikin duniyar nan,yana gama karantawa ya dago kansa yana laluben inda matar ta yi sai dai kuma bat babu ita babu dalilinta,har zai share batun sai kuma yaji ya kasa yin hakan baran ma da ya haɗa da ta riyo lafuzan aminatu na baya da na yanzu,to idan haka ne kenan akwai kamshin gaskiya akan zargin da mutane suke yiwa wannan asibitin? sannan kuma hakan na nufin aminatu ta san wani abu akan wannan asibitin tunda har take gudunsa,dole fa sai nabi maganar wannan baiwar Allah sannan duk zan samu amshoshina daga baya. ya bawa kansa amsa yana mai yaga takardar kuci kuci,kafin ya shiga inda su Aminatu suke sai da ya fara kiran daya daga cikin likitocin da zasu yiwa innawuro aiki me suna Dr halima,kudi kawai ya cikata da shi ta amince zata fito masa da innawuro,cike da yakinin cewa Allah zai kubutar da me gaskiya ya shiga wajen aminatu yana rarrashi,ya bar Dr halima da matar me suna Hajara, Dr halima ita ce ta shigar da Hajara ta wata kofa da ba kowa ne ya san da ita ba idan ba isu isu amintattun likitocin ba,ko su fa basu san cewa duk wata zuciya ko koda da ake cirewa ba ana cireta ne dan lalura ko dasheba, saboda lokuta da dama ana kawo matacciyar zuciya ko kodar da bata da amfani a ce dashe za a yi wa mara lafiya, dan haka suma duk a duhu suke amfani kawai ake dasu dan su masu sanin basu wuce mutum biyu ba. Dan haka da wannan damar Dr halima da Hajara suka samu suka fidda innawuro, wajen fita da ita daga asibitin ma mus ab Shi ya kwatanta musu hanyar da zasu fita ba tare da securities sun gansu ba,hanyar da ko ita hakima bata sani ba,hara na fita ta samu motar da mus ab ya aiko suka shiga suka bar asibitin ba tare da kowa ya kula dasu ba bare a yi zarginsu,halima kuma dama bata fita ba bare yan uwansa su yi zarginta dan suna tare take aiwatar da shirinta cikin taka tsantsan. Koda suka kai innawuro gidan da mus'ab ya bawa driver umarni Hajara bata shiga ba, fita ta yi ta koma gidan Alhaji Garba saboda kar ta bashi kofar da tunaninsa zai juyo kanta.wannan shine dalilin kubutar innawuro daga hannun su Abby. Numfashi yaja me huci tare da kwanciya kusa da ita yana fuskantarta idanunsa akan fuskarta,zuciyarsa cike da bincike da zargin da ya fara darsuwa akan asibitin iyayen nasa wanda a halin yanzu yake hatta da mahaifinsa ba zai tsira daga binciken da zai fara dan nemo gaskiya ba,duk da cewa yana kan binciken nemo mutanen can na baffan AMINATU to amma hakan ba zai hanasa haɗawa da binciken asibitinnasu ba,don shima abu me me matukar muhimmanci. [4/12, 6:23 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page30``* A can bangaren zahida kuwa itama can gidan gonar ta su ta bisu kamar yadda suka bukaci da tazo,idan na ce muku tashin hankali to na rage muku armashin tashin hankalin da su Abby ɗin suke ciki, domin kuwa har Mr alfa ya fara danno musu kira jin su shiru babu su babu sako babu dan aike,daga karshe dai su ɗan turƙyi suka sa ya nemo musu wadda zasu yi amfani da ita a matsayin innawuro,basu bar gidan gonar ba har sai da dan turkyi ya tabbatar musu da cewa aiki ya kammala dan a halin yanzu matar tana cikin asibitin tana jiran zuwan dr Zahida,hakan yasa kai tsaye Zahida ta koma asibiti su kuma kowa ya nufi gida da fatan kar ta kuma kwaɓe musu kwabar da tunda suka fara kasuwancinsu ba su taba yin makamanciyarta ba. Zahida tana zuwa ta buƙaci ganin matar a office ɗinta,Mata me shekaru sittin da yan kai ta zauna ta zaiyanewa Zahida abinda yake damunta ta ɗora da cewa, "wannan yaron ne ya ga halin da nake ciki a titi da lalura Shi yasa ya ce zai kawo Ni inda za a taimaka min a bani magani kyauta ba tare da ko sisina ba,da na dauka ma wancan dayan asibitin da ake ce masa ko ABM Shi zai kai Ni sai kuma naga ashe nan ne,yar nan da tafiya zan yi wlh saboda na fi gamsuwa da wancan asibitin fiye ds nan ɗin,sai dai kuma yadda wanda ya barni tare da su suka dinga koɗa min irin tsaimakonku da tabbatar min da cewa duk abinda ake fada a kanku karya ne,yasa na hakura na zauna har kika zo kika sameni",da kyar zahida ta kai zuciyarta nesa ba ta sheƙe matar nan da mari ba, amma fuskarta babu wata fara a acunkushe take. kana kallonta kasan cewa dole take zaune da matar nan a gabanta,wani ruwan magani ta mikawa matar tare da cewa "karbi nan kisha taimakon farko ne da wannan asibitin ta fara baki",babu wani tunani matar nan ta karba maganin ta sha kamar yadda zahida ta umarce ta,tana sha ko minti daya ba a yi ba ta bingire da bacci, da sauri zahida ta mike tare da kiran Dr Samir a waya,cikin kankanin lokaci yazo a ka taitayi matar zuwa dakin tiyata. Sosai mus ab yayi kokarin yiwa Nana bayani ta yadda zata fahimta,to dake ita ma a nutsen take ta fahimceshi sosai. sai dai kuma abin ya matukar bata mamaki ya kuma tsaya mata kamar yadda ya tsaya musu shida innawuro dan ba zai sa waccan shargallen a ciki ba dan ita baka taba gane damuwarta kullum cikin yanayinta na calikanci take aminatu kenan matar dan birni, jin shigowar Abby yasa shi mikewa ya baro dakin ya fice ta can baya ba tare da ya bari sun hadu da Abby din ba. Hankalinsu ya kwanta saboda sun samu nasarar cire zuciyar wannan matar,sai dai kuma sun lulluɓe Mr alfa ba su sanar dashi an samu canji ba kuma basu gwada wannan zuciyar ba cireta kawai su kayi,ko gawar matar can suka jefar a juji kamar yadda suka saba duk sanda suka gabatar da irin wannan aikin. Kwana biyu hankula sun kwanta a wajen su Abby suna daukar cewa duk acikin nasarar sune suka samu kan aminatu ta yi hakuri da rashin innawuro.mus ab kuwa bai ce komai ba bayan addu'ar Allah ya baiyanata cikin aminci. Anne Kam tunda ake wannan turka turkan cikanku ba ta ce ba,wanda hakan ya matukar harzuƙa aminatu, duk abinda za a yi da abinda za a ce tana daki idan ma tana kusa ko kallo baku isheta ba,bare ta tofa tata, shi yasa aminatu ta ci alwashin sai tasa ta tayi magana dan dole shegiyar tsohuwa me kan kwakwa da baƙin rai. A can bangaren gidan Alhaji Garba kuwa Hajara ta kama aiki gadan gadan ,wanda hakan yake yiwa Hajiya zubaida dadi gashi ta samu abokiyar debe kewa,saboda ta fi azumi kwari da wayewa,shi ko Alhaji Garba gaba daya ya maida hankalinsa kanta saboda yasan tana dauke da kadarar da zasu iya samun manyan kudaɗe da ita,dan haka shima lallaɓata yake yana kyautata mata duk dan ta kara yarda da su ta yadda zata kawo ɗanta gidan ba tare da wata tantama ba. Yau Litinin da wuri Abby ya fita, dan har ya riga Zahida barin gidan,dan yanzu kuma gaba daya hankalinsu ya koma kan binciken asibitin ABM da kuma Br, a baya daukar al'amarin suke yi karami sai kuma yanzu da suka samu kansu cikin kasa nemo shaida daya da zata sa su gano waye br,haka a bangaren asibitin duk da cewa suna bi suna kama wasu mutane da suke ganin suna da dangantaka da asibitin dan tuhumarsu da yi musu barazanar mutuwa,sai dai babu wani labari maganar daya ce basu sani ba ko da kuwa zasu kashe su ne, wannan abu ba ƙaramin tayar musu da hankali yake ba, dan kasuwancin ma a yanzu sun dan lafa masa saboda sun fuskanci mutane sun yi matuƙar sa musu ido musamman da yawan mace_mace ya ƙaru a sibitin nasu. Ta fannin Zahida da kuwa ganin aminatu ta dawo gidan sai kawai ta kirkiri tafiya dan kawai ba zata iya jurar ganin aminatun a garin kuma tana numfashi daidai da nata ba,aminatu kuwa ko ajikinta bata ma san tana yi ba walwalar ta take yi ta yadda duk wanda ya ganta zai shaida cewa bata da wata damuwa. Khalid ne zaune shida aminatu tana koya masa assignment, isma ne ya shigo falon wanda tun dawowarsa gida basu taba haduwa da aminatu ba saboda shi din ba wani zama yake ba, sannan isma dan sharholiya ne na bugawa a jarida shi yasa yawanci ya fi kwana a waje,Dan can wajen yafi sakewa yayi shaye shayensa ba tare da sa idon mus ab ba.duk da cewa har yanzu mus ab bai san boyayyun halaiyar isma ta shaye shaye da Neman mata ba, wannan dalilin ne yasa yake Dan zaman gidan dan kar wata rana mus ab ya fahimci banzar dabi'ars.,zama yayi a kujera yana ƙure aminatu da ido yana tunanin wannan hurul inin kuma daga ina? Khalid ne ya katse masa tunani ta hanyar gaidasa ,firgigit yayi yana dan shafa ƙeyarsa kafin yace ,"Khalid wannan wacece,?", dariya Khalid yayi tare da cewa "kai uncle isma adda aminatu ce baka sani ba?" Sai a sannan ya tuna yaji Nana tana yawan ambatar sunan,oh na tuna ya fada yana kannewa aminatu ido cike da nuna duniyanci,harararsa aminatu ta yi har da jan siririn tsaki kafin ta fara tattare littafan da suke a baje a gabansu dan barin wajen,sai da ta hade su tsaf ta mike zata bar wajen, ganin haka da isma yayi sai kawai ya yi saurin sa ƙafarsa a hanya, ba tare da ta yi aune ba kuwa ta ci wani mugun tuntunɓe da kafar isma, sai gata kif ta wadi kasa, ta ji zafi kuwa sosai dan take ta fashe da kuka kamar wata karamar yarinya,Anne ce ta fito tana cewa "to yar fama yar mai, yau dai masu sangarta kin basa nan idan kika kuskura kika min taɓara zaneki zan sa ila yayi",khalid ne ya jawo hannunta yana kokarin dagata idanunsa cike da hawayen damuwar kukan da aminatu take yi,isma ya ce "rabu da ita Anne Ni ne nan na yarbar da ita,dan iskanci ni da gidanmu amma na shigo yarinyar nan ko kallo ban isheta ba sai kace wata yar karuna, to ko shi karunan ba zai nuna mana girman kai da iya shegantaka ba",Anne ta ce "yauwa dan albarka sai yanzu na samu me goya min baya dan ita zahidar da basa mutuncin itama ba ɗaɗa ni ta yi da kasa ba bare na dinga sata tana ci min ubanta,amma yanzu tunda Allah ya kawo min kai takaicina ya ƙare", ta karasa maganar da zabgawa aminatu harara,isma kuwa gyara kwanciyarsa yayi saman doguwar kujera yana cewa,"ke me idon mage maza je ki kawo min abinci nan ko yanzu na kwakule idanun,"da sauri aminatu ta yi gaba sai da ta je dab da upstairs din mus' ab,sannan ta juyo ta ce,"naki ba zan kawo ba ,kuma Allah ya isa na ban yafe ba mugu dan shaye shaye", wata mahaukaciyar ashar isma ya yiwa aminatu wadda tasa ta haura sama da gudu tana masa gwalo,shi kuwa gaba dayaa kansa ne ya daure ta yaya yarinyar da yau din nan ya fara ganinta ta san halinsa da ko uwarsa da ubansa basu san yana yi ba,tashi yayi ya fita daga falon yana fadin lallai yarinyar nan watan mutuwar ki ne ya kama dan idan ba ki iya bakinki a gidan nan ba sai na illataki.anne kuwa zagin aminatu ta shiga yi wai ta yiwa jikanta sharri. Isma ya jima ya na mamaki da son gano ta yadda akayi wannan yarinyar me kama da aljanu ta san yana shaye shaye, sai da yaga yana neman zautuwa saboda tunani sannan ya hakura da zama akan cewa hasashe aminatu ta yi, dan haka ya ci burin gallazawa rayuwarta tunda har ta shiga gonarsa. Da misalin ƙarfe shida na yamma aminatu ce ita da Nana da larai a kiching suna karasa hada dinner, nana ce ta dubi aminatu ta ce,maza aminatu ku karasa jera kayan bisa dinbin Ni kuma bari na je na yi alwala tunda nasan ke bayi za ki yi ba,idan yaso sai ki ɗauki na Anne ki Kai Mata,ke kuma larai ki kaiwa isma nasa can bangarensu", da sauri aminatu ta ce,bari na kai musu larai kuma ta karasa jerawa a dinning",nana ta ce to kin san dakin nasa ne"?kai tsaye qminatu ta amsa da ",EY duk kuwa da cewa bata sani din ba,amma ba zata bar wannan damar ta ramakon abinda yayi mata ya wuce ba, daukar kular abincin ta yi ta fara kaiwa Anne nata ta fito ba tare da ta kula da harara da habaicin da ta saba yi mata ba,komawa kiching ɗin ta yi,.bata samu kowa a kiching ɗin ba dan haka ta dauki kayan abincin isma din, juyowar da zata yi kuwa sai goshinta ya bigi kirjin isma da tun fitowarta daga ɓangaren Anne ya biyota zuwa kiching ɗin,a razane ta dago kanta tana kallon isma din da yake watsa mata wani banzan kallo da bata san da wane abu zata fassarashi ba, zube kayan da ta dauka.ta yi tana ja da baya cike da tsoron da ya bayyana saman fusmarta,Binta ya fara yana cewa wa na kama?" Kwaɓe fuska ta yi zata fasa kuka yayi saurin sa hannunsa saman labbansa yayi mata alamun ta yi shiru,hadiye kukan ta yi tana kuma ja da baya saboda kusanto tan da yake kuma yi,ƙafarsa da ke sanye da wani shegen takalmin ball yasa ya take yatsun ƙafaarta da karfi take aminatu ta kurma ihun da.yake.tafr dw wani irin kukan azaba,wanda haka. Yasa isma saurin ficewa daga kiching ɗin ta kofar baya,zubewa ta yi a gun tana kuka me taɓa zuciya, Da sauri mus' ab dake shigowa falon ya ɗan lumshe idanunsa tare da fitar da huci ta bakinsa,dan kuwa karar aminatu tamkar a cikin kunnensa haka ya ji ta,kai tsaye ya nufi inda yake da tabbacin daga nan yake jigo sautin kukanta, Sautinsa ne kawai ya fi na sallamar da yayi shima ba dan tsananin laƙantar motsinsa da aminatu ta yi ba da ba zata ji ko tasan cewa yayi sallama ba,duk da ta ji shi a jikinta ta kuma ji shi a motsinsa hakan baisa ta dago kanta daga durkushen da tayi tana faman murza ƙafarta hade da kukanta da ya yi kasa sosai ba.a hankali ya tako gabanta haɗi da dukawa daf da ita har tana iya shaƙar numfashinsa tare da ƙayataccen ƙamshinsa da yake matukar tafiya da ita tun bata san kanta ba,hannun sa me taushi ya sa ya kama yatsun kafar yana ɗan murzawa kadan kafin cikin deep voice ɗinsa da ba kowa ne ya cika jinta ba,ya ce",baby crayin me ne ya samu kafar kuma?"dago kanta ta yi ta zuba masa oily eyes dinta tana kara kebe bakinta irin na jikakkun yara kana ta ce,"wani mugune wai shi isma ya take min kafa ya wuce kamar ya taka dabba wallahi kuma ba zan yafe ba duniya da lahira wutabalbalin acibalbal din innawuro ta ruga aradun Allah sai na rama",zuba mata ido yayi cike da mamakin sakarcinta duba fa tayi Allah ya isa kuma tana cewa sai ta rama,duk da cewa Allah ya isar ma tata ce ta daban dan bai taba jin irinta ba.bakinsa ya bude a hankali, kana kallonsa kasan ba karamin takura kansa yake yi wajen yin magana ba,ya ce, "to ba kin yi Allah ya isa ba ki bari Allah ya isar Miki idan kuma baya sane sai ki yafe masa",murguɗa karamin bakinta tayi tana mai farfara fararen kwayar idonta kana ta ce, "aradun Allah yana sane,dan kawai saboda dan uwanka ne shine zaka ce na yafe?to bani yafewa mugu me sh....karar faduwar abu ne yasa ta hadiye maganarta tare da juyawa dan ganin abinda ya fadi,ido hudu su kayi da isma yana watsa mata kallon gargaɗi a fakaice ba tare da ya bari mus ab ya gani ba.kana cikin sauri ya tsugunna yana daukar cup din da ya fadi tare da cewa "oh sorry Hamman mu mantuwa nayi na shigo ba tare da sallama ba"ya dauki cup din yana duban aminatu cikin tausayawa kana ya ce, sorry sis har yanzu bai da na ciwo ba ko? ki yi hakuri ban kula ba ne", daga haka ya fice daga kiching din yana aiyana irin cin uban aminatu da zai yi muddin ba ta daina kokarin tona masa a siri ba. "Kin gani ko ya kuma baki hakuri",ya fada yana dan dage girarshi guda tare da ɗan matsa yatsan da karfi har sai da ta dan yi karamin ihu tana mai rike tsintsiyar hannunsa da wasu gashi suke a kwance tamkar sun kwanta a ƙorama,dan dakatawa yayi tare da kallon hannun nata da yake rike da nasa,wanda hakan ya sa ta yi saurin janye nata hannun tana dan yar far dashi kamar ta taɓa garwashin wuta,buɗe idanunsa yayi tare da lumshe su a lokaci guda kafin kuma ya mike tsaye da hannunta da ya janyo, babu shiri ta ganta a tsaye, kafin ta fara mitar tayar da Itan da yayi, ya kuma jan hannuta da karfi wanda yasa dole ta fara takawa tana binsa cikin yanayin tafiyarsa me ƙarfi wanda nutsuwa tasa ba a fahimtar karfinta da saurinsa a lokaci guda, sai dai ka gane hakan ta nisan kilomitarsa. A can bangaren Anne kuwa ta saba kullum da an gama abinci za a kai mata ko mai a hada mata a ƙaramin dinning dinta, amma yau tun tana zuba ido har dai ta zo ta fara ji yunwa shiru kake ji babu abinci babu me kawo abinci, ga shi ita kuma Anne irin dattijann nan ne da girma bai hanasu cin abinci ba, dan kuwa Anne Masha Allah tana yiwa cikinta zubi shi yasa gata nan kullum kamar ana hurata dan irin matan nan ne masu jiki, sosai Anne ta yi fushi har ta sawa ranta yau bazata ci abinci ba idan ya so idan yunwan ta kasheta sa fidda gawarta,dan ma rashin mutunci ita da gidan ɗanta amma ace abincin da zata ci ma ya gagareta,(dan adan me manta baya duk yadda ka kai ga kyautata masa rana daya idan aka samu akasi to fa duk ya manta da wanda ka yi masa a baya),dan haka ta yi shirin kwanciyarta haka duk kuwa da yunwar da ke sakadar yan hanjinta. Har su Nana suka fito su kayi dinner tare da zaman hirarsu da duk wanda ya samu ,bata shiga kiching taga halin da yake ciki ba. bare ta ga kulolin abincin Anne,ita ma larai Allah bai sa ta lura ba har ta kammala gyaranta ta wanke ko mai ta fice daga kiching din,aminatu kuma tana sane amma ta yi biris dan a cewarta daga rana irin ta yau Anne ta shiga komarta bazata rabu da ita ba har sai randa ta koma ga Allah. [4/12, 7:00 PM] yushauadamfatima: *Typing* 💕 *MATAR ƊAN BIRNI ** 💕 *NA* *FATIMA Y. ADAM* _____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *_____________________________________* ``` *Page31``* Har misalin ƙarfe ɗaya Anne ta kasa runtsawa saboda yunwa ga kuma bakar zuciya ta ki yiwa kowa magana, har fitowa tayi lokacin basu jima da cin abinci ba ta yi shawagi wai ko Nana zata ganta ta tuna bata kawo mata abinci,ba amma shiru kake ji, dan ita Nana bata ma kawo wannan tunanin a ranta ba sam,aminatu kuwa dauke kai take tana dariya a a fakaice dan sarai ta fahimci shawagin Anne ba akan komai ba ne sai akan adda'am,a ranta cewa take ai tsohuwa tunda kika sake na gane kaunarki da abinci to kuwa kin shiga tara tsohuwar kawai. Haka ta gama shawaginta ta koma daki tana faman zuba ƙwafa cikinta kuwa banda kugin yunwa babu abinda yake, duban agogo Nana ta yi kafin ta dawo da dubanta kan Khalid dake kwance kan cinyar aminatu, sannan ta ce,"aminatu ku je ku kwanta kunga dare yayi kar ki kasa tashin dare",shafa tattausar sumar khalid aminatu ta yi tana cewa ,nana wane dare kuma?ai dare ya riga ya gama yi shi yasa ba zan kwanta ba sai nayi sallolina dan kar na kasa tashi karfe biyu"mikewa Nana tayi tana cewa "to hakan yayi Nima bari na yi amfani da dabarar ki na fara yin sallar kafin na kwanta"to Nana Allah ya tashe mu lafiya yau tare da Khalid zamu kwanta kwana biyu na yi kewarsa saboda tafiyar da yayi gidan adda suhaima",to shike nan Amin"nana ta fad tana taka matakalar step biyar da zai kaita bangaren dakinta. Sai da aminatu ta tabbatar da cewa Nana ta yi balance a dakinta, sannan ta kwantar da Khalid a hankali, tashi ta yi ta nufi kiching, tana shiga ta dauki kayan abincin Anne ta fita da shi ta baya ko tsoro ba ta ji ba ta kaiwa security da yake gadin main kofar da zata sadaka da cikin gidan baki daya,tana dawowa ta kwanta a kujera tana ci gaba da kallon tashar aljazira da suke karanta Alkur'ani me girma,a hankali take bi cikin daddan sautinta tana yi tana kallon gefen hanyar dakin Anne, Dan ta tabbatar sai ta fito neman abinci a yadda dai ta fahimci zaryar da take. Hasashen aminatu ya tabbata dan kuwa Anne ta hango cikin sanda kamar wata ɓarauniya,ta fito daga dakinta,da sauri aminatu ta rufe idonta kamar me bacci,sai dai tana kallon Annen. Hanyar kiching Anne ta yi cikin sanda kamar ɓarauniya dan yasa a ranta ko da zata ci abincin nan to bata son wani ya sani bare idan ta ce bata ci ba a ƙaryata ko kuma idan ta kwanta jinya,sai da aminatu ta tabbatar da shigar anne kiching ɗin sannan ta yi sauri ta miƙe tare da nufar kiching ɗin,bata bari ta yi takun da Anne zata Ankara da shigar ta ba, shi yasa ganin aminatun ya matukar razana ta dan bayan kunyar da ta ke gudu har da tsananin tsoro, take ta diririce, cikin in ina take cewa,"en dama bera ne na gani nake son neman madoki na bigesa dan kin san Ni fa a rayuwata bana son bera, da na ga bera gwara na ga maciji ina matukar jin tsoron bera, shi yasa idan naji motsinsa bana iya zama a wajen"rike kugu aminatu ta yi kafin cikin son boye dariyarta ta ce,"duk tsoron da kike masa shine kuma zaki iya kasheshi?to ma wai ta ina bera ya shigo gidan nan ne?gaskiya dai anne kin iya zubota sai dai idan da abinda ya kawo ki daban amma ba dai batun bera ba",kallonta anne ta yi cike da tsarguwa da masifa taf baki ta ce,"to dan ubanki me nazo nema? idan ma wani abun na zo nema ai gidan dana ne ba na ubanki ba ko?" Tura baki aminatu ta yi cikin gunguni take cewa "uban aminatu bawan Allah ne dan haka a daina zagar munshi",har Anne zata daga murya sai kuma ta tuna hakan yana nufin fallasa halin da take ciki ne,dan haka ta rufe bakinta tare da barin kiching ɗin a fusace cikinta kuma na karar yunwa fadin rai kuma ya hanata ta tambaya. A wannan dare dai haka Anne ta kwana da yunwa,ba dan taso ba karshe akan aminatu ta huce duk da cewa bata san cewa ita ce me shiryawa da bada umarni ba,haka ta kwana tana tsinewa aminatu da ahlinta. Kafin safiya tuni Anne ta jigata,Nana bata tashi sanin halin da ake ciki ba sai da ta je gaida annen ta ganta kwance tamkar wadda ta yi jinyar wata biyu,numfashi kawai take iyawa dan ko sallah asuba a zaune ta yi ta,da sauri Nana ta karasa gaban gadon saitin kanta tana cewa "subhanallahi "anne baki da lafiya ne kuma baki fada ba?"Anne da take jin cikinta kamar zai hade da bayanta ta yi saurin kawar da kanta gefe cike da fushin da yake Kuma taso mata tana danne zuciyarta,jin ta yi shuru karshe ma ta rufe idonta yasa Nana shiga tashin hankali duk a tunaninta zafin ciwon ne,dan haka ta yi saurin juyawa tana cewa bari na kira Abbyn su a kira likita tunda Zahida bata nan",jin haka yasa anne saurin riko hannunta sannan cikin muryar da ke nuna bacin rai ta ce"kar ki kira min kowa tunda ba damuwa yayi dani ba bare ke da bani na haifeki ba,bai san ya na ci ba bai san ya nasha ba,shi dai kawai tunda ya ajiye a dafa a bani gani yake ya fita HAKKINA"matse kwalla ta shiga yi tana ci gaba da cewa, "shi yasa kullum sai nayi kewar ya mace, tabbas na yarda da yan magana da su ke cewa da ka haifi gwamna gwara ka haifi matar gwamna sannan yaya mata rahma ne, duk wanda bai samu rabon mace ba zan iya cewa bai gama more haihuwa ba", zama nana ta yi a gefan gadon tana cewa "dan Allah anne ki yi hakuri ki daina fadin haka Ni ma ai yarki ce,dan haka ki fada min damuwarki?" Matse kwalla Anne ta kuma yi sannan ta ce,"yanzu kamar ni ace an manta da bani abinci a cikin gidan nan sai haka na kwana ciki fayau, ko bacci kasawa nayi saboda azabar yunwa"salati Nana ta sa tana tafa hannuwanta kafin cikin mamaki da damuwar da ta bayyana a kan fuskarta, ta ce,"yanzu Anne kina nufin AMINATU bata kawo miki abincin da na ce ta kawo miki ba"? Cike da fusata Anne ta ce "yo ta kawo min zance banci ba ne ki ji wata banzar tambaya"ganin ta harzuƙa yasa nana ta fara rarrashinta tare da sanar mata yadda sukayi da aminatu akan kawo mata abincin,daga karshe da kanta ta je ta haɗo mata lafiyayyan karin kumallo ta kawo mata, sannan ta sata a gaba kamar karamar yarinya, sai da ta tabbatar ta ci ta koshi sannan ta fita daga dakin dan zuwa ta samu aminatu ta ji dalilin wannan masifa da ta kusan Kunno mata. AMINATU yau ko fita karin kumallo basu yi ba, kiching ɗin sama wanda ke bangaren mus ab ta shiga tana haɗa musu breakfast,hirarsu suke cike da na nishaɗi ita da Khalid, "Khalid wai dama haka Anne take tsoron bera da yawa?"aminatu ta yiwa Khalid tambayar tana juye ruwan shayi a flax,dariya Khalid yasa dan duk sanda ya tuna karon Anne da bera sai yasha dariya,sai da yayi me isarsa sannan ya bawa aminatu amsa da cewa,"wallahi adda aminatu Anne tana tsoron bera kamar ya kashe ta, ita kuma momyna mage take tsoro kamar me dan idan ta ga mage kamar zata shide haka take yi"jinjina kai aminatu ta yi sannan ta ce"shi kuma uncle isma me yake tsoro wanda idan ya gansa zai iya fitsari a wando"?kai tsaye Khalid ya bata amsa da cewa,"kyankyaso"daga nan aminatu bata kuma cewa komai ba sai saka abinda zata fanshe rashin mutuncin waɗannan mutane Uku da take a ranta,Khalid ne ya dinga kai musu kayan ƙaramin falo yana jerewa, daga karshe aminatu ta fito ta dauko kunun kabewa da madara da ayaba da zuma da dabino, da ya zama abincinta, dan tun da ta fara tasawa Nana ta sabar mata dashi har ma da wasu abubuwan da har yanzu aminatun bata fahimci dalilin bata su da Nana take yi ba,tana sha ne kawai dan azabar dadinsu da take ji hatta da ruwayen da take sha daban suke da na gidan watsu tsimi ne na musamman da Nana take yi mata masu dan karen dadi, daukar kofin da ta cika shi da hadin kabewar nan ta yi ta juya zata fita sai hannunta ya bigi cabet din kusa da ita take kunun kabewar yayi tsalle ya fallatsu a fuskarta har zuwa kirjinta kasancewar wata yar bulawus ce me faɗin wuya a jikinta kuma ba bra a jikinta, shi yasa kai tsaye kunun ya tafi zuwa cikin wuyanta ya bata kirjinta sosai, Cak ta tsaya tana kallon kanta ta cikin mirror ɗin kiching ɗin kamar zata fasa ihu, dan fitowarta daga wanka ke nan suka shigo kiching ɗin,ajiye cup din ta yi da niyar ta je daki ta cire rigar, dan kuwa sake wanka ya tabbata a gareta,tana ajiye cup din juyowar da zata yi suka yi ido hudu da mus' ab da shigowarsa ke nan,dan tura bakinta tayi tana cewa "wannan irin shigowa ba tare da neman izini ba ai sai a razana mutum"dan takawa ya fara yi kamar zai karasa inda take sai kuma ya tsaya yana mai ƙure fuskarta da ido zuwa duk inda kunun nan ya fallasa, kafin a hankali ya ɗan ajiye numfashi ta baki tare da cewa "da izinin wa kuka shigo min nan?"shiru ta yi tana kifkifta ido tare da ɗan mici mici da bakinta,ba tare da ta dago ta kallesa ba,sai ma kokarin wucesa da tayi zata fita, tattausar hannunsa taji ya kamo nata hannun ya riƙe tare da dawo da ita baya suna fuskantar juna, hannunsa yasa duka biyu kan ƙafadarta yana kallonta kallon da yake kona mata dukan ruwan jikinta kallon da ke sata jin wani irin nauyi a kirjinta kallon da ke sata ta ji gaba daya ta manta wace ita da matsayinta a wajensa,kasa ta yi da kanta yayin da jikinta ya shiga rawa saboda yadda kallon nasa yayi tsanani tare da tasiri a gareta. Dago da kanta yayi, yana kallon tsakiyar ƙwayar idanunta,kafin cikin wata karyayyar murya ya ce,"me ye wannan?"ya tambaya yana kai harshensa saman idonta da kunun ya ɓata,kasa bashi amsa tayi saboda jin saukar harshensa saman idonnata yana masa wata irin lasa, "uhum ba amsa?"ya kuma tambaya yana yin kasa da bakinsa tare da bin duka inda kunun yake yana lashewa,yayin da sanyin harshensa da kamshin da yake fitarwa ya ci gaba da tasiri wajen kashewa aminatu jiki da zuciya,har bata san lokacin da ta rike kugunsa ba dan ji take ƙafafunta ba za su iya daukarta ba,"har lau dai babu amsa ko da wani damuwa ne?"mus' ab ya kuma yin maganar a daidai lokacin da yake gangaro da harshensa saman wuyanta yana tsotse kayan dadin da ta barar ajikinta, sosai jikin aminatu ya dauki rawar shoki saboda tsanantar yanayin da oga mus ab yake jefata a ciki,ga kuma tsoron kar Khalid ya shigo ya gansu a haka,cikin rawar baki ta yi dauriyar cewa "Hamma MUS'AB Khalid fa zai shigo kuma kuma yasan wannan abun iskanci n...ruf ya rufe bakinnata da nasa ba tare da ya fahimci abinda take cewa ba bare ya bashi muhimmanci,sai da ya shanye bakin maganar tas kana ya gangaro kirjinta inda ragowar kunun suka fallasa, zuba wa wajen ido ya ɗan yi wanda hakan yasa aminatu saurin sa hannu ta kare tare da yin baya tana cewa "Ni wlh bana son kwart.....bata iya karasa fadar kalmar ba saboda yadda numfashinta yayi wani irin daukewa da tsananin mamaki da rudani tare da wanzuwar wani irin yanayi wanda ta kasa tantance sa a cikin dukan rayuwarta,kirjinta sama da kasa kawai yake tsoro ya hanata fahimtar komai saboda yadda mus'ab yake lashe saman kirjinta da fatar ba tare da wani damuwa ko shakkar yin hakan ba,sai da mus ab ya lashe kaf kunun da suka ɓare a jikin aminatu sannan ya dago fuskarsa ya kura mata ido na wasu yan sakanni kafin ya hura mata iskar bakinsa a saman idanunta da ta kasa bude su saboda tsananin takaici da kunyar abinda yake yi matan,bakin nan ya cika taf da iska kamar zata fashe,"hannu yasa ya laka ce lips ɗinta da suka yi wani irin ja saboda shan da suka sha wajen oga mus ab me aiki da cikawa.zata yi magana kenan mus' ab ya kuma haɗe bakinsu dan yasan rashin ta ido zata yi shi yasa yake son yin maganinta ta wannan hanyar amma fa a fadarsa😃. Daidai lokacin kuma Nana ta shigo falon tana tambayar Khalid in da AMINATU take,Shi kuma ya bata amsa da cewa"Nana tana kiching Nima tun dazun nake jiranta bata fito ba shi yasa nayi karyawata dan yunwa nake ji",daga haka Nana ta nufi kiching ɗin kai tsaye batare da tunanin cewa idonta zai yi ganin kunya ba. Ƙarar bude kofar kiching ɗin kawai suka ji take aminatu ta razana tare da kwace kanta daga rikon tsaurin da mus' ab yayi mata, shi ko mus' ab din babu wata alamar razana ko kunya a tare dashi dan ko da da akwai to ba zaka taba ganewa ba,kuka kawai aminatu ta fashe dashi tare da saurin bin bayan nana tana cewa, wallahi nana shine ya zo har inda nake daga kawai yaga kunu ya zube a jikina shine ya ce lallai sai ya lashe sai kace wani maye kuma fa Nana har da kir......tsawar da nana ta daka mata ita ta tsaida ita da ga baranmaramar da take yi,jan hannunta Nana ta yi suka fita daga falon gaba daya,a hankali ya nemi guri ya zauna yana shafa tattausar sumarsa da ta take ta wani irin kyalli baka siɗik da ita,tare da kwantar da kansa jikin kujerar yana lumshe idanunsa da suka yi wata kala daban fuskarsa kamar murmushi zai kwace amma dai babu murmushin wata kila kuma na can kasan zuciya yake yi. Suna zuwa kasa Nana ta saki hannunta tana zabga mata harara kafin ta ce,"ke kam aminatu yaushe zaki hankali?yaushe zaki daina wannan sakarcin da sakin baki haka a gaban kowa eye?"tura baki aminatun ta yi tare da cewa,"to Nana haka kawai sai na barsa ya dinga lalube Ni bayan shi b mijina bane duba fa kiga bakina duk sanda ya samu dama sai ya ci min idan na barsa ai sai dai wata rana na tashi na ga bani da baki,Ni wallahi ki hanasa ko na kai kararsa wajen ab.....bige bakinta nana ta yi tana mai rasa abin cewa ga kunyar da ta lullubeta saboda zantukan aminatun,dan Kore zancan sai Nana ta yi saurin sako mata zancan Anne, "aminatu me yasa jiya baki kaiwa Anne abinci ba?"zaro ido aminatu ta yi tare da cewa "kai kai tab wallahi yau na kuma tabbatar da cewa matar nan bata kaunata kaji wata karya"harara nana ta kuma jefawa aminatun tana cewa "annen ce take karya?"da sauri ta rufe bakinta tare da cewa "a a ba ita ba ce subtar baki nayi amma dai nasan na kai mata abinci ta koro ni wai bani na saba kai mata ba dan haka na mayar ba zata ci ba,kuma da nace mata zan mayar larai ta kawo mata shima cewa ta yi bata so dan yau tunda har na taba abincinta bazata ci ba,bayan ma bata san kusan kullum ma Ni nake girkin ba",dan jim nana ta yi kafin ta ce ai shi kenan amma dai ki kiyaye nan gaba idan hakan ta faru ki fara gaya min",yes ma aminatu ta fada tana mai daga hannunta da kamewa a tsaye irin yadda sojoji suke yi,girgiza kai kawai Nana tayi ta wuce bangarenta a ranta kuwa ta gasgata aminatu dan tasan irin tsanar da anne ta yi mata tsaf zata yi hakan,dan haka take ta share maganar a nan wajen.