MASARAUTAR MU! 2 Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com SADAUKARWA Ga Bilkisu Askira, (Billie Askira), Maiduguri, sabida gudummuwar ki yayin rubuta wannan littafi. JINJINA Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. MASARAUTAR MU 2 Ya kara tattaro dan sauran karfin gwiwar da ya rage masa, yace cikin kwantar da murya, kodayake kodayaushe muryarsa a kwance take. "Baturiyar Asia ce, Jew (bayahudiya), ta yarda zata karbi addinin muslunci in dai zan aure ta". Daga sarki har Ya Gumsu a razane suka dube shi. Mai martaba ya kasa cewa komai kamar an dinke masa baki. Ya mutu a zaune cikin kujerar sa. Ya Gumsu ta mike tsaye tana nuna shi da dan yatsa "....ka yi kadan Yarima, karya kake ka tozarta ni a idon duniya da idon kishiyoyi na masu son ganin faduwa ta!. Ko mata sun kare ban yarje maka auren nan ba, da yawun baki na bazan taba saka albarka ta ba!!!". Sarki Yusufu ya ce "kana iya tafiya Yareema zamu yi shawara, duk abinda muka yanke Waziri zai kira ka". Ya Gumsu ta zaro ido tana kallon Mai Askira tamkar idanun ta zasu fado. Tunda har ya amince zai tattauna zancen nan da Waziri ta san karshen alewa kasa.....ba ya kai zance ga Waziri sai ya fara yin na'am da shi a karan - kansa. Ta fashe da kuka ta tashi ta bar falon. Yarima ya mike zai bi bayan ta. Sarki ya ce ya kyaleta sai ta huce yanzu bazata taba sauraron sa ba. Ya koma ya zauna jikin sa a sanyaye, da wannan damar Sarki Yusufu yayi amfani ya dinga tambayarsa abubuwa akan Rose din, da yadda suka hadu, shi kuma ya gaya masa duk abinda ya kamata ya sani banda wanda bai kamata ba. Ya kare zancen sa da cewa yana mata kwadayin musulunci ta hannun sa don jihadi, sabida kyawawan halayen ta, sannan ita din ma tana sha'awar addinin muslunci a karan - kanta. Ta zabi ta bar kowa nata in dai za'a bar shi ya aure ta. Alanguburo ya fahimce shi sabida saukin kansa, a lokaci guda yana kokawar ture nasa BURIN akan Yarima Sageer can gefe daga zuciyar sa, yana fadawa zuciyar sa ya bar shi yayi jihadin; wani ya shiryu ta hannun ka yafi a baka jajayen Rakuma tunda Allah bai haramta ba. Ba duk abinda muka yi burin tabbatuwar sa ne yake tabbata ba. Wasu mafarkan a mafarkai kawai suke tsayawa, ba sa zama REALITY yadda muke burin su. Wasu kuma Allah kan jinkirtawa bawa zuwa lokaci mafi dacewa. Ya sallame shi da cewa ya saurari kiran Waziri idan sun tattauna gobe. **** Sarki Yusufu da Wazirin sa Ibrahim suna tattaunawa akan al'amarin Yarima bayan sun kadaice a falon ganawar sirrin su, Waziri yace su bar Yarima yayi auren su samu ladan muslunci, amma bisa sharuddan cewa zata biyo shi gida su zauna tare dasu cikin MASARAUTA a matsayin sa na Yarima mai jiran gado. Dole ya dawo gida gabadaya ya zauna cikin ahalin sa. Lokacin da Waziri ya kira Yarima ya gaya masa hukuncin da suka yanke, Yarima Sageer yayi dan jim! Domin nan kusa bai shirya dawowa gida ba, ba zai iya rayuwar karamin gari kamar Askira ba, zai takura, ba zai shana yadda ya saba ba, sannan Rose ma zata takura, ga zafin Maiduguri, bata taba zuwa Africa ba haifaffiyar South - Korea ce. Aiki ya kai iyayenta Amsterdam. Ba abinda ya tsana irin ace shine 'mai jiran gado', bayan ba shikadai ne namiji ba, shi sarauta sam bata cikin tsarin sa, Yarima Sageer bakin bature ne kawai wanda ya rungumi affluent western lifestyle ya manta da asalin sa tsayin shekaru masu yawa, wannan kuma ya faru ne da laifin su iyayen sa da suke ganin yin nisa da gida fintinkau shine abinda zai nutsar musu da shi; don nutsuwa ya nutsu irin wanda tarin shekaru ke haifarwa da namiji, amma ba nutsuwa irin wadda su suke zato ba. Karewa ma, ya goge ne yayi mastering akan harkar neman mata, har wadanda ba addinin su daya ba. Amma in ka gan shi a fuska tsammani zakayi wani saint ne shi din (waliyyi) sabida tsabar iya badda-kama a gaban iyaye. Abu daya Allah ya tserar da Yarima akan sa shine shan giya, ko sha'awar ta bai taba yi ba. Yana matukar kyamar ta. A cewar sa ai sai da hankali ake sallah dai-dai, kuma a yi ta akan lokaci. Hatta sigari tun lokacin tashen samartakar sa ya bar ta. Amma da ya duba wannan alfarma da iyayen sa suka yi masa wadda bai taba zaton zata zo masa da sauki haka ba, sun bar shi ya auri zabin sa dai-dai da ra'ayin sa, sannan sun toshe kunnuwan su daga duk abinda zasu ji akan auren nasa, auren da a tarihin masarautar su ba'a taba yin irin sa ba, sai ya ga cewa ya zama dole shima ya amince da tasu bukatar na dawowa Askira tare da matar sa. Kafin nan zai roke su su bashi lokaci, ya kammala phd din sa, ya tattaro kasuwancin sa zuwa Nigeria ya kuma nemi aikin da zai rike shi in ya dawo, ba zai zo ya dogara da mahaifin sa ba kamar yadda akasarin 'ya'yan sarauta ke yi. Koda ya yiwa Waziri wannan bayanin take ya amince, ya kuma ce sun bashi shekaru biyu ya kammala komai, ya dawo tare da matar a musuluntar da ita a daura auren su. Awaisu was shocked lokacin da yaji labarin nan domin bai taba zaton iyayen su zasu amince da zancen Rose ba, haka bai taba zaton Yarima is serious akan maganar Rose ba, ya dauka yana fada ne kawai for fun irin nasa. Shikam tuni Ba'ana ta zaba masa mata 'yar kanwar ta mai suna Asiya suna dawowa za'a hada auren nasu lokaci guda shi da Yarima, don yarinyar bata kare sakandire ba ma. Kwanan su bakwai suka koma Amsterdam with nostalgia (cike da begen gida) a yadda suka tsammaci masarautar ta su sai suka tarar akwai cigaba na zamani sosai fiye da yadda suka tafi suka bar ta. Suka kuma fara tunanin hanyoyin da zasu kara kawo mata daukaka da cigaba na zamani ta kara zama zakaran gwajin dafi a masarautun jihar Borno tsararrakin ta. Tuni Yarima ya tsara sababbin gine-gine da za'a kara cikin masarautar, da yadda za'ayi renovating din ta daga kamfanin gine-gine da tsare-tsaren gidaje na COSIMCO na kasar Amsterdam (Neitherlands). Yana komawa abinda ya maida hankali akai kenan, wato project da cosimco akan masarautar su. Daga can suka taho suka fara ayyukan su a masarautar Askira. Gininnika na zamani masu tsayi da nagarta suka kara fiddo da martabar masarautar Askira. "Lallai dan zaki an girma" Sarki ya fadawa Waziri cikin murmushi a lokacin da suke zagaye cikin masarautar da wajen ta, suna kallon renovation din da Yarima ya tsara da kansa ya kuma turo COSIMCO construction company suka yi. Waziri da sauran 'king-makers' sai albarka suke sanyawa Yarima, fatan su bada jimawa ba ya dawo ya karbi sarautar mahaifin sa tun yana raye. Wanda basu sani ba wannan baya cikin tsarin Yarima Sageer ko kadan. Bar shi dai a gogaggen dan bokon sa. Awaisu ne kawai ya san hakan. **** Hutun su Sa'ade na karewa suka koma makaranta, ashe wani abin alhini ke can yana jiran ta, shiru-shiru tana zuba idon ganin dawowar Raheema amma har ta share sati biyu da komawa Raheema bata dawo ba. Sa'ade ta kasa sukuni, ta kasa walwala ta kuma kasa cigaba da harkokin karatun ta yadda ta saba a dalilin babu Rahima, ta kuma rasa wanda zata tambaya ko ya san abinda ya hana Rahima dowowa don kowa ita yake tambaya. Ga wani kuskure data yi bata taba karbar adireshin Raheema ba, sabida tana ganin ko ta karba babu wanda zai kaita, Fulani bazata taba barin ta ta je ba. Da abin ya isheta sai ta tafi ofishin principal, tayi gaisuwa ga principal sannan ta soma share hawaye. Principal tace "what's wrong Sa'adatu Hashim?" Sa'ade ta idasa fashewa da kuka a gabanta sannan ta gaya mata yau sati uku kenan Raheema Kyari bata dawo ba. Principal tasa aka yi bincike akan rashin dawowar Raheema, nan malamin dake kula da dawowar dalibai ya sanar da ita sakon da mahaifin Raheema ya aiko na cewa sun bar kasar Najeriya. Wanda ke nufin Raheema ta bar makarantar gabadaya. Damuwar Sa'ade sai ta nunku akan ta da, me ya sa Raheema za ta bar kasar ba tare da ta yi mata sallama ba? Laifin me ta yi mata? Amincin dake tsakanin su ya fi gaban haka. Bata san ta yi mugun shaquwa da Raheema ba sai yau data wayi gari babu ita cikin kwalejin El-Kanemi. Rayuwar Sa'ade gabadaya sai ta sauya a makaranta ta zama ba umh ba umh-umh. Haka ta dukufa yi wa Raheema addu'a ba dare ba rana kan Allah yasa tana lafiya, tana kuma rokon Allah ya sake hada su cikin gaggawa. Sannan a fannin karatu ta kara dagewa, don yanzun shi kadai ne abinda ke debe mata kewa. Tana yawan tunanin Zarah da Fulani, amma kullum tana sawa a ranta Fulani bata son ta don haka is a waste of time yawan tunanin ta data ke yi, har addu'a take yi a kowacce sallahr farillarta Allah ya rage mata son da ta ke yi wa mahaifiyar ta Fulani Bilkisu! **** BAYAN SHEKARA BIYU! Abubuwa da yawa sun faru cikin shekaru biyun nan, wadanda yawanci rigingimu ne na kishi a cikin gida tsakanin Ya Gumsu da Fulani Bilkisu. Sun ki zama lafiya da juna, amma kashi 80% na rigingimun in ka bincika zaka tarar laifin Ya Gumsu ne, tana kishi da Fulani Bilkisu ba dan kadan ba, a bisa abubuwa da dama; muhimmi shine son da Askirama ke mata wanda ya zarce na kowacce cikin matan auren sa, kuma ba ya iya boyewa. Yayin da ita Ya Gumsu a wurin ta ita ta cancanci wannan fifitawar a matsayin ta na uwar Yarima kuma uwar manyan 'ya'yan sa. A haka dai ake rayuwar, da dadi ba dadi a gidan sarkin Askira, kamar kowanne gidan sarauta, duk wani babban gida ko ba na sarauta ba ya gaji haka, girma na kara kama kowaccen su, kamar kuma suna girma ana kara rura wutar kishi a tsakanin su. A yau Litinin, gidan sarautar Askira an tashi da hidimar shirin tarbar Yarima Sageer wanda zai sauka a yammacin yau tareda matar da zai aura, 'Rose Hathaway'. Labari ya gama baza cikin gida na inda Yarima ya nemo aure. Surutu ba irin wanda ba'ayi a sassan kowacce daga cikin matan gidan in ka dauke unguwar Fulani Bilkisu, ita kadaice ta goyawa Yarima baya akan auren da yake so kuma bata yi Allah wadai da zabin nasa ba, ko dama kusan koyaushe ra'ayinta na zuwa daidai dana maimartaba ne. Yamma lis Yarima Sageer da dan uwansa Awaisu da Rose wadda ta sha doguwar riga har kasa da mayafinta kamar balarabiya suka iso masarautar Askira karkashin rakiyar dogarawan fada masu yawa, wadanda suka dauko su daga filin jirgi daga Maiduguri a mota civilian ta Askira Emirate. A wannan lokacin Sa'ade na makaranta tana zana jarrabawar shiga aji biyar SS 2. Ya Gumsu ta yi tsalle ta dire tace ba dai baturiyar Yarima a sassanta ba, babu ita babu wannan auren koda za'a sa mata wuka a makoshi. Don haka Mai Askira ya ce a kaita unguwar Fulani Bilkisu ta zauna karkashin kulawar ta. Dakin Sa'ade ta sa Fanna ta gyarawa matar Yareema, duk abinda zata bukata Fulani ta tanadar mata, to saidai hira ta gagara tsakanin su don Fulani bata iya turanci ba, saidai ta yi magana da Yarima a waya shikuma ya kira Fulani ya gaya mata abinda ta ce. Kwanan su biyu da dawowa aka musuluntar da Rose a masauratar Askira aka daura auren ta da Yarima Sagir, babu wata gayya ta kunya da sarki yayi iya jama'ar gari ne kawai da king-makers suka shaida auren Yarima Sagir, bai gayyato 'yan uwan sa sarakuna ba, shi kansa bai san meyasa a can kasan ran sa baya farin ciki ko kadan da auren ba, duk da cewa bisa amincewar sa da yardar sa ne. Ya dauka Rose zata zo tare da wani nata, sai ya ganta zikau daga ita sai jakar kayan ta... sai ya soma tambayar kansa ranar da 'ya'yan Yarima suka tambayi dangin mahaifiyar su me zai ce musu??? Ko dai uwar Yareema, Ya Gumsu, ta fi shi gaskiya ne??? **** Babu wani shagalin biki kamar ba auren Yarima guda ba, haka aka dauki amaryar aka kaita gidan da Maimartaba ya ginawa Yarima wanda ke gefen masarauta. Gida ne tankarere ginin sarauta kuma ginin zamani, wanda ya lashe miliyoyin kudi har ya zarta ginin masarauta tsari sabida an yi amfani da hikimar kamfanin cosimco. In ka ji ana aljannar duniya to gidan Yareema Sageer ne. Auren Awaisu sai bayan shekara biyu don matar da aka bashi bata gama makarantar sakandire ba. Rayuwar Yareema da amaryar sa Rose wadda ta karbi suna (Aisha - Sultana), sun dora ta ne daga inda suka tsaya a Amsterdam, wato rayuwar nasara zallah, don su kan manta cikin masarautar Askira su ke, Yareema na matukar son Sultana yayin da ita kuma ta karbi muslunci ne don son data ke wa Yareema ba don tana ra'ayi ba, don ya ce mata shine kadai hanyar da iyayen sa zasu yarje mishi auren ta. Don haka kusan zamu iya cewa addinin ta karbe shi ne kawai a baka, amma daga sanda suka bar cikin gida zuwa nasu gidan ta jinginar da sallahr data fara a sassan Fulani Bilkisu, ta gayawa Yareema ita bazata iya kullum ba, akwai wahala sai ta saba tukunna, yayin da Yareema ya nuna ba zai lamunci hakan ba sai take yi a gaban sa, in baya nan kuwa a hadu a gaba. Sati hudu ana barzar amarci, an cika musu gida da bayi da hadimai, Sultana sai a lokacin take lakantar ko wanene Yareema Sageer Yusuf Askira? Ashe a baya bata san komai a kan shi ba? Banda kasancewar shi abokin shashancin ta, ta fahimci a yanzun tana sahun gaba na mata masu sa'a a rayuwa, domin Sageer daya ne cikin dubu, wanda irin sa ta fannin nunawa matan su soyayya tsiraru ne a cikin al'umma. He's genius a halayya da dabi'a, superb a rayuwar auratayya, splendid a tafiyar da matar sa.... Ko don ta cigaba da rayuwa da Yareema zata cigaba da zama cikin rigar addinin sa mai wahala, amma ba don ya dadata da kasa ba. Watanni ukku Yareema ba ya komai sai neman aiki ta yanar gizo ba da sanin maimartaba ba, sai amarci da mai jan kunnen sa, Fulani Bilkisu ta zama uwar dakin Sultana ita ke kula da komai da ya shafe ta don Ya Gumsu ko gaisheta tayi bata amsawa, haka Ya Maira bata taba takowa gidan ta ba sai Humaira da Naja'atu, mazan kam suna zuwa sosai wajen Yareema musamman Ashgar wanda ya maida gidan wajen hirar sa sabida yadda Yarima ke jan sa a jiki, don yana tsananin tausaya masa, kuma yana samun sauki sosai daga rehabilitation din da Yarima yasa shi ya samu a kasar Amsterdam. Ayyuka har biyu Yareema ya samu a lokaci daya, NTNU (Nigerian Turkish Nile University) dake Abuja sun bashi aikin koyarwa (lecturing) kamar yadda ya zaba a tsangayar (Pure and Applied Chemistry), haka OAU (Obafemi Awolawo University, Ile-Ife) suma sun dauke shi da gaggawa, tun kafin dawowar sa ya yanke shawarar komawa academia wani professsion da 'ya'yan sarauta basu fiya karba ba. Kamar yadda komai nasa yake daban da na sauran mutane, haka tunanin sa ma ya ke. Ba ya danganta kansa da sarauta ko kadan kamar yadda mahaifin sa ke so, a ganin sa tana hana 'yanci, sannan takura ce. Gashi shikuma mutum ne mai tsananin son rayuwar da babu takura, kuma babu matsantawa a cikin ta. Mutum ne mai (tsinkaye) da tsantseni a cikin dukkan mu'amalolin rayuwar sa, mai son dogaro da kai, mai zafin nema, mai zafin nama, sannan mai nasara a kan duk abinda yasa a gaba. Bar shi dai da son matan sa (his only shortcoming) abinda zamu iya kira nature a jikin maza jinin sarauta, wanda zamu iya cewa tun bayan auren nan wata irin nutsuwa ta saukarwa Yareema Sageer Askira; Mata suka rage burge shi banda matarsa Aisha-Sultana. Haka ya zauna yana deleting numbobin mata kala-kala yare daban daban dake kan wayar sa, ya na fadawa kansa da kansa; yadda ya bar Amsterdam gabadaya, haka ya baro ta tareda dukkan matan da ya baro cikin ta. Kasuwancin automobile din sa ma ya maido shi gida Nigeria ya dora Awaisu akan komai. Yanzu kuma da ya dawo sai ya hada da biyu daga cikin kannen sa wadanda suke gab da kammala karatun digiri akan kasuwanci, Suhail dan wajen Ya Kirjinoma da Ahmad kanin sa a dakin su. An kai ruwa rana kafin Maimartaba ya yarjewa Yarima komawa Abuja da iyalin sa, don a tunanin sa da farko ya dawo Askira kenan don har ya fara shirin yi masa nadin sarautar Chiroma, amma sai Yarima ya zo da batun samun aikin sa da NTNU yana rokon Maimartaba alfarmar ya bar shi ya tafi, sai da Fulani Bilkisu ta sa baki sannan maimartaba ya amince don baya iya hanata kowacce alfarma ta nema, kuma Yarima ya zama dan gidan ta yanzu tun lokacin da Maimartaba ya damka mata amanar Sultana. Ya bar shi ya tafi da alkawarin duk bayan wata uku a gida zasu yi hutun kowanne karshen zangon karatu na jami'a. Ranar wata Lahadi Yarima Sagir da maidakinsa Aisha-Sultana suka tattara suka koma Birnin tarayyah. Humaira da Naja'atu da sauran kannen sa maza ne suka yi masu rakiya, basu dawo ba sai da suka taya su suka shirya gidan su tsaf wanda Jami'ar NTNU ta baiwa Yareema Sagir cikin jerin gidajen malaman Jami'ar. Jami'ar NTNU mallakar Turkawa ce (Turkish University) da suka bude a kasar Nigeria, suna biyan malamansu sosai a matsayin ta na (private international university) ko kusa ba daya take da jami'o'in Arewacin Nigeria ba wajen biyan malamai. Haka gidajen malaman jami'ar dole tsarin su ya burge ka. Flat ne hawa daya mara girma sosai, dakuna ciki hudu, kitchen da bandaki a kowanne dakin barci, tafkeken falo da bangaren cin abinci (dining) sannan akwai garden daga bayan kowanne gida, daga gaban gidajen kuma balcony ne domin shan iska da yamma, akwai rumfar gargajiya (hut) a cikin gate din kowanne gida wadda aka zuba kujerun roba da gadon shan iska na Turkawa, gabadaya ginin daga na jami'ar har na gidajen malaman an dauko tsarinsa da sample dinsa daga Istanbul ne, duka gidajen iri daya ne sun kai guda 100 a cikin jami'ar. Su Humaira suka dawo gida suna ta santin gidan Yayan su Yarima (Dr. Sagir Yusuf Askira) sunan da Jami'ar ta mayar masa, da alwashin zuwa hutu duk sanda suka samu hutu domin ba laifi Aisha - Sultana tana da kirki ga kowa nasa, daga auren zuwa yanzu ta saba da daukacin kannen Yarima na sauran dakunan matan sarki, banda 'yan dakin Ya Gumsu. Tun bata fahimta ba sabida rashin jin yaren hausa dana kanuri har zuwa yanzu ta fahimci Ya Gumsu bata yi na'am da ita a matsayin surukarta ba. Da suka je mata sallama ma zasu taho abuja ko kallon ta bata yi ba, haka tace da Yarima cikin fushi "tattara wannan danyen naman ku bar min sassa tun ranka bai baci ba". Ba wai ta ji me Ya Gumsu ta ce bane amma ta fahimci ba maganar arziki bace duk da Yarima bai nuna komai akan kyakkyawar fuskarsa a lokacin da ta yi maganar ba, baya ga cewa da yayi da ita ta tashi su koma gida dare yayi. Satin su guda itama ta fara neman aiki da (Insurance Brokers) kasancewar tattalin arziki ta karanta, Yarima ya samar masu kuku da mai gyaran gida duka kabilu, ba'a jima ba kuwa suka dauke ta, sai ya zamo daga shi har ita ba mazaunin gida, a lokacin ne Yarima yayi wani aboki dan kasar Turkey wanda yana cikin masu ruwa da tsaki na jami'ar sunan sa Dr. Ziyad, zasu yi shekaru daya kuma a tsangaya daya suke koyarwa. Tun haduwar Sageer da Dr. Ziyad abubuwa suka kara canzawa Yarima, domin Dr. Ziyad fitinanne ne na karshe kuma shi ba shi da mata, gidan sa babu nisa da gidan Yarima don haka lokuta da dama suna tare, suyi yawo cikin gari ko su debo 'yammata gidan Dr. Ziyad, A haka suke rayuwar shi da Sultana kowa yana sha'anin gaban sa, don so suna son juna har gobe amma rashin albarkar uwa ya hana auren gamsar da kowannen su ba tareda sun san hakan ba. Itama tunda ta waye da rayuwar Abuja shikenan ta koma harkokin ta na baya, bata kara tuna wani abu wai shi musuluncin data karba ba, shaye-shaye take na fitar hankali, data gane inda ake sayar da giya a Abuja kuwa shikenan kakarta ta yanke saka. Ta san halin Yarima akan 'giya' don haka bata taba gigin shigowa da ita gidan ba, kullum ta taso aiki sai ta tsaya a Bar ta sha mai isar ta, ta yo guzurin kayan mayen ta kala-kala sannan zata dawo gida, tana riga shi dawowa sau tari domin Dr. Sagir yafi fixing laccar yamma ga daliban sa, tana shigowa kai tsaye dakin barcin ta take nufa ta zube a kasa ko a gado tayi ta barci, har sai ya dawo ya tasheta da kan sa ya ce ta yi sallah. Wannan itace kalar rayuwar Yarima da matarsa Aisha Sultana a birnin tarayyah, Abuja. Rayuwar da kowanne ya zabawa kansa. A haka lokaci ya cigaba da mikawa. Abinda Yarima bai sani ba tun dawowarsu Abuja da sati daya, Aisha-Sultana ta je an juya mata mahaifa. ***** BAYAN SHEKARA BIYU! Yau ne daliban El-Kanemi College of Islamic Theology suka kammala rubuta final paper din su ta barin makarantar sakandire wato SSCE wadda ta kasance darasin addinin muslunci (islamic studies). Farin cikin dake zukatan su ba zai bayyanu ba, fuskar Sa'adatu Hashim tafi ta kowa yalwar far'a, ta yi dakacen wannan rana inama da Rahima Kyari! Sun yi hotuna na tarihi kala-kala da kawayen ta da abokan arziki da suka yi zaman aminci tare. Babban farin cikin SA'ADE shine Alanguburo yayi mata alkawarin karatu a jami'ar Turkawa dake Najeriya (Nigerian Turkish Nile University) muddin ta fiddo da 9 credits, kuma daga yadda ta rubuta kowacce paper tana da kyakkyawan zato akan kokarin ta. Humaira ta gama makaranta shekaru biyu baya, yanzu haka tana jami'ar Maiduguri. Da suka iso gida yau ta yi abinda bata taba yi ba a tsayin rayuwar ta (without minding the consequence); a guje ta shiga sassan su tana kwalawa Fulani kira, Fulani bata san hawa ba bata san sauka ba tana tsaye tana yi wa little Zarah fada taji anyi wuf! Da ita an kankameta a tsakar dakin. Dama ga ta babu kiba ko kadan. Saura kadan ta sha kasa "I have finally graduated Fulani, i've really -really made it!". Kokarin banbare Sa'ade take daga jikin ta kada wani ya shigo ya gansu a haka, yayin da Little Zarah ke ta kyalkyala dariya cike da murnan ganin Sa'aden, ta tafi itama ta rungume su, Sa'ade ta saki Fulani da ke ta banbamin fadan so take ta karya ta? Ta russuna ta dauki Zarah tana rada mata cikin kunnen ta "na taho miki da choculates mai dadi" Zarah ta ce "bazamu san wa Fulani ba tunda tana yi miki fada" a haka suka shige dakin Sa'aden wanda Fanna ta gyare tsaf. Ta sanya turaren wuta irin nasu. Don tana da masaniyar yau ne graduation din Sa'adatun. Sa'adatu Hashim dalibar El-Kenemi, doguwa ce sosai, mai kirar jiki na bare-barin usli, wadanda suka hadu da shuwa suka haifeta, suka bata colour din fata mai kyau da daukar ido. Doguwa sambaleliya tamkar kirar matan Saliyon, a yanzu ne take cikin shekaru goma sha takwas komai nata ya kai ya kawo, cikakkiyar budurwa mai wani irin class na daukar hankali. Duka wadannan Fulani Bilkisu ta nazarce su ne a lokacin da Sa'ade ta dauki Zarah suka bata baya zuwa dakin Sa'aden, ta bisu da kallo cike da kauna tana jin wata irin soyayyarsu su a zuciyar ta, a yanzu kam ta saduda, ta tabbata ta kuma haqqaqe tana son 'yar ta, kwatankwacin ko ma fiyecda yadda ta ke son Fatima-Zarah. Ta koma cikin hamshakiyar kujerar falon ta ta zauna, ta lumshe idon ta a hankali, yayin da tunanin shekaru goma sha tara a baya na yadda ta samu 'yar, ya soma rewinding filla-filla a cikin kanta..... **** SHEKARU GOMA SHA TARA A BAYA! Mu 'yan kabilar "Baggara" ne wadanda aka fi sani da "Shuwa-Arabs", asalin mu makiyaya ne masu yawo da dabbobin su a kasashen Africa, mun fito daga kasar Chadi wadda take daga yammacin Ifriqiyyah, yawanci zaki samu yan kabilar Baggara sun watsu a kasashe irin Sudan, Cameroon, Niger, Chad, Nigeria, da kuma Central African Republic. Baggara musulmi ne na haqiqa masu rikon addini tun karni na goma sha uku, harshen mu shine "Chadian Arabic" wanda muke yin shi da shuwa-dialect, Allah ya zubawa Baggara kyawun surah na kirar jiki data fuska, da wata irin kalar fata mai sheki da kyau, wanda ya samo asali daga cakuduwar su da larabawan Sudan. Mahaifina Malam Soumana ya baro kasar Chadi tare da mahaifiyata a lokacin tana da cikina tare da 'yan uwan su Baggara zuwa Nigeria inda suka yada zango a yankin Borno, daga baya suka koma Damaturu bayan an haifeni da shekaru hudu, inda mahaifina yake sana'ar kiwo, shanu yake kiwo da tumaki ya sayar a karshen kowacce shekara ya sayi wasu ya sake sabon kiwo. Mahaifiyata Roumana tunda ta haife ni bata sake haihuwa ba, inada shekaru biyar Allah yayi mata rasuwa. Babana shi ya cigaba da raino na, yasa ni a makarantar firamare, daga baya jarin kiwon nasa duk ya balbalce, wani abokin sa ya yaudare shi ya saye su da zummar washegari zai kawo masa kudin gabadaya, cikin dare ya bar Damaturu da dabbobin gabadaya, wanda hakan yayi silar talaucewar mahaifi na, muka koma rayuwa cikin kaka-ni-kayi, abinda zamu ci kansa ba kullum muke samu ba, mahaifina ya koma yin dako a kasuwa duk don mu samu abinci baya ko zancen aure don tsoron matan borno wadanda ba kabilar sa ba. A haka na rayu hannun mahaifina cikin kwanciyar hankali don talaucin mu bai hana mana kwanciyar hankali ba, duk wata buga-buga da dan adam zai yi don ya samu abinci mahaifi na yayi ta har na gama makarantar firamare, inada shekaru goma sha uku watarana mahaifina ya zo da dabbobi masu yawa, ya dinga yi musu turke yana daure su daya bayan daya, na tambayeshi inda ya samo su sai ya ce ya karbe su ne yayiwa wani kiwon su zai dinga bashi ladan kiwo duk karshen wata. Sabida zai yi tafiya Kano ci-rani bashi da wanda zai dinga kula masa da su. Watarana muka wayi gari dabbobinnan babu ko daya, an biyo dare an sace su. Mahaifina ya shiga tsananin tashin hankali, domin mai dabbobi ya kusa zuwa gida, duk bayan wata uku yake zuwa, sabida tashin hankali mahaifina har kwanciya yayi ciwo don bai san bayanin da zai yiwa mai dabbobi ba. Bansan yaya suka kare ba, illa a wani dare mahaifina yana kuka ya gayamin gobe zai daura min aure, bashi da abinda zai biya mai dabbobi, shikuma ya ce sai ya biya shi, ko ya bashi aure na madadin dabbobin sa. Na rasa a wane yanayi na karbi wannan zance na mahaifina. "Auren biyan bashi" zai yi dani, sai kace ni din ba mutum bace mai darajah. Ban taba yiwa mahaifina musu ba amma wannan karon na ce a'ah, bazan auri mutumin da ban sani ba ban taba gani ba, sannan kuma tafiya zai yi dani can wajen ci-ranin sa ya rabani da mahaifina wanda shi kadai nake da shi a duniya. Amma rashin yardar tawa bata kara komai ba, washegari mahaifina ya daura min aure. Bayan gama daurin auren yana kokarin shiga gida ya fadi, faduwar da ta zamo numfashin sa na karshe. Kwana uku da rasuwar mahaifina makota sun tayani zaman makoki, kowa ya tausaya mun, na zama abun tausayi, hankalina ba ya kara tashi sai na tuna auren da mahaifina ya daura min. Na tsani auren na tsani mai dabbobin tunda bashi da zuciyar musulunci da ba zai iya yafewa mahaifina asarar data same shi ba, zai ce ayi masa biyan bashi dani sabida rashin sanin darajar dan adam. Washegari sai ga mata uku sun zo wai sun zo tafiya da ni, daya tace sunan ta Yagana matar Yayan mijin nawa ce, sai matan abokinsa guda biyu. Ina kuka ina komai haka suka fidda ni daga gidan mu ko wanka babu, a gidan Yayan sa Malam Kyari aka bamu daki wai zuwa sati mai zuwa zamu wuce Kano inda yake ci-ranin sa. Ban ga mijin ba sai da daddare. Ya manyanta sosai, ga shi bakikkirin ga rashin kyawun gani, ni duk ba wannan ne damuwata ba yadda zan zauna daki daya da shi. Ga dakin ciki daya falle daya. Ya cire babbar rigar sa ya rataye ya jawo ledar da ya shigo da ita yana ta far'a yace "Amarya Bilkisu taho ki ci, ki kwantar da hankalin ki ni mai kaunar ki ne, na dade ina son ki, kuma na gayawa Babanki yace shi bazai aurawa kowa ke ba sabida baki da kowa a kasar nan, burin sa shine ku koma Chadi cikin dangin ku. Nayi duk iya kokari na ba abinda ban bashi ba amma ya ki karba. Sabida haka ne na bashi ajiyar dabbobi na kuma biyo dare na kwashe abina don in samu hanyar mallakar ki. Gashi dabara ta tayi min amfani, saidai ban ji dadi ba da ya rasu ban nemi gafarar sa ba. Na so bayan auren mu in gaya masa cewa ni na kwashe dabbobin". Na daga rinannun idanuna ina kallon mutumin nan da wata irin tsana...tsanar da ban taba yiwa wani dan adam a duniya ba, kawai sai na sa kuka mai cin rai. Ya kawo hannu wai zai lallashe ni na kai masa mahangurbar data sa dole ya ja da baya. Ya sake kokarin kamo ni na buga tsalle na bar dakin da gudu. A ranar a dakin Yagana na kwana. A gabadaya kwana bakwai din da aka ce zamu yi a garin Damaturu ban kara yarda na shiga wancan dakin ba, nasiha da lallashin duniya matar Kyari ta yi da shi kanshi Yaya Kyarin, amma bana ce musu komai sai kuka. Tunanin makomar rayuwata nake da ba uwa, ba uba, babu dangi sannan bansan asali na ba, abinda na sani kawai shine daga Western Chad muke. Bayan wannan bansan komai akan iyayena da asalin su ba. Sannan ga auren wannan azzalumin mutumin! Yo azzalumi mana! Wanda ya sanya mahaifina cikin kaka-ni-kayi don biyan bukatar zuciyar sa. Ya raba mu, rabuwa ta har abada. Don na tabbatar bakin cikin irin auren da yayi min ne ya sa ya fadi, faduwar da ta zamo ajalin sa. Kwana bakwai ta cika, Yaya Kyari ya sameni shi da matarsa, ya fara da yimin nasiha da nuna min girman hakkin aure a wurin Ubangiji, sannan ya kuma tabbatar min kanin sa mutumin kirki ne zai kula dani, in kwantar da hankali na in bi shi, duk abinda yayi min wanda bai kwanta min ba yayi alkawarin tsaya mini, yace daga yau shi uba ne a gare ni ba suruki ba, in na yarda da hakan to in bi Hashimu mu tafi garin Kano. Haka ina kuka ina komai muka shiga motar da zata kai mu Kano, ko fuskarsa ban yarda na kalla ba, don yadda na tsani Hashimu da za'a bani wuka ace kisa halal ne da na caka masa na huta. Duk wata kulawa da tarairaya yayi min a mota, komai ya gani sai ya saya mani duk da bana yarda in karba balle in ci. A haka muka iso Kano, daganan muka hau motar unguwar da yake zaune. Gidan karami ne sosai, sana'ar kayan gwari yake yi (kayan miya) a kasuwar 'yan Kaba, idan ya fita tun goma na safe sai magariba yake dawowa, kafin ya dawo kuwa na gama duka abinda zanyi na dau abinci na na shige daki na sanya sakata. Bana kara budewa sai washegari inna tabbata ya fita kasuwa. Mun dauki watanni a haka, a wani dare da bazan iya tantancewa ba, cikin barci na ji kamar ana kokarin balla kofar daki na, kafin a yi haka na ganshi a kaina. Na soma kurma ihu ya toshe min baki ya sa igiya ba tausayi ba imani ya daure ni jikin karfen gado. A wannan bakin daren ne na samu cikin SA'ADATU. Kuma daga ranar bai kara kusantata ba, domin ya tausaya min azabar da ya gana mini. Washegari ba irin kyautatawar da Hashimu bai yi min ba, amma ba abinda hakan ya kara min banda tsanar sa. Ban taba sanin alamun shigar ciki ba, sabida ban tashi tare da mace ba, koda naga cikin ma yana turowa ban taba kawowa a raina cikin bane, don bansan me ake a samu cikin ba. Balle in yi tunanin na samu. A haka ciki na yayi ta girma, sai da na soma jin motsi da wutsilniya na tabbatar cikin Hashimu ne a jiki na. To dama haka ake samun cikin kamar kiftawar ido? Kamar azal? Fadin tashin hankalin da na samu kaina abu ne da bazai fadu ba, nayi kuka nayi kuka har na ji babu dadi. A karshe dole na dangana, ina ji ina gani na haifewa Hashimu 'ya. Tunda na samu kaina na ce saidai ya sake ni ko in kai karar sa. Shikuma a lokacin ba abinda yake so a duniya irin rayuwar jaririyar sa, na fice mai a ka, sabida duk iya kyautatawar da namiji zai yiwa mace a duniya domin ta so shi yayimin, amma na kasa kallon shi da kauna komai kankantar ta. Ba don komai ba sai don abinda yayi wa mahaifi na, da hanyar da ya bi ya samu aure na. Sai yace "mu yi jinga, na yarda zan sake ki, amma bayan kin shayar min da yarinyar nan na tsayin shekara daya kacal, ni kuma zan sawwaka miki kije duk inda kike son zuwa". Da wannan yarjejeniyar na yarda na shayar da Sa'adatu na tsayin shekara daya. A ranar da ta cika shekara daya ya cika alkawarin sa ya sake ni saki daya. Yace ga gida nan ya mallaka mini albarkacin haihuwar Sa'adatu, ya san bani da kowa, ya san bani da inda zani, amma tunda haka na zabawa kaina shi ya bar min gidan, ya dauki 'yar sa yace kauye zai koma ya raine ta. Wannan ba damuwa ta bace tunda na samu 'yancin kaina. Ba wadda zata san zafin kiyayyar namiji sai wadda aka yiwa irin auren da aka yi min. Auren dole is a challenge da ba duka mata ne zasu iya jure shi ba. Kwana bakwai a tsakani na sayarwa da makocinmu gidan, na kulle kudi na sai tasha, na hau motar Maiduguri, don na kudurce a raina ni da Damaturu har duniya ta nade. **** Aka sauke mu a tashar Bama, daga nan na rasa ina zan nufa. Ga yunwa ga gajiya. Haka na hau tafiya a gefen titi dauke da kullin kaya na. Tunani yayi min yawa har bansan na hau bisa titi ba, a yayin da zungureriyar motar ta shararo a guje, duk kokarin da direban yayi bai yi nasarar kauce min ba sai da ya kwashe ni ya watsar bisa titi. Jini kuwa ya balle ko ta ina, baka jin komai sai salatin mutane. Sauran motocin dake biye dasu in convoy duk suka dakata a gefen titi. Fadawa suka fito bisa umarni suka ciccibe ni suka saka a mota sai asibiti. Ban samu kai na ba sai bayan awanni uku. Na farka na ganni a wani hamshakin asibiti. Likitoci farar fata fal a kaina, ga karin ruwa ga karin jini, juyawar nan da zan yi sai na yi tozali da wani babarbaren mutum ma'abocin zati da kamala, mai yawan murmushi, yasha nadin rawanin da ya tabbatar min yana da alaqa da babbar sarauta. Baza'a kira shi tsoho ba, amma kuma ba yaro bane ko kusa. A bayan sa Fadawa ne guda biyu a tsaye sai muzurai suke. Ya fara da bani hakuri, sannan ya gaya min an dauko shi ne daga Airport zasu wuce garin su direbansa yayi duk kokarin da zai yi ya kauce min Allah ya rubuta sai sun kade ni. Ya tambaye ni sunana na gaya masa. Ya ce in bada kwatancen gidan mu aje azo dasu sabida na samu karaya a kafa da hannu bazai yiwu a sallame ni a yau ba. "Bani da uwa bani da uba, bani da 'yan uwa, nikadai ce. Ban da kowa, kuma bani da inda zani". Na bashi amsa cikin kuka na zafin ciwo. Maimartaba Sarki Yusufu mai Askira, ya dade yana kallo na kafin ya ce "Kin yarda ki bini masarautar Askira cikin amana in zame miki uwa da uba sannan MIJI abokin rayuwa?" Haka naji furucin sa tamkar cikin mafarki, na kasa yarda da abinda kunnuwa na suka jiye min, na kasa amincewa ido na biyu it was just in a dream..... (and that was how I became a QUEEN) wannan ne silar zamowata Sarauniyar amaryar sarkin Askira, wanda daga kallo na farko na ji ya kwantamin a rai, da wani irin exceptional feelings..., wata irin kwantacciyar soyayya da kauna, da ban taba ji a rayuwa ta ba. Komai ka ga ya faru da bawa to dama can rubutacce ne a lauhul-mahfuz, na yarda rabon Sa'adatu ne ya sabbaba aure na da mahaifin ta, ban taba jin son sa ba, domin soyayya ta Allah ce. Shi yake kimsa ta a zuciyar bayin sa. Haka itama kiyayya. Amma a ganina da ba ta hanyar da Hashimu ya bi ya aure ni ba kenan zan iya hakurin cigaba da zama da shi ko don maraici na dacrashin gata na. Bayan na gama iddah a gidan Liman inda aka yi min masauki, Limamin Askira shi ya zama waliyyi na, Wazirin gari Ibrahim ya zama waliyyin Sarki Yusufu suka daura mana aure, auren da ya jawo cece-kuce mai yawa a masarautar Askira domin Sarki Yusufu bai taba auren diyar talaka ba balle mara asali mara dangi. Duka matansa 'ya'yan sarakuna ne daga masarautu daban-daban na jihar Borno. Gorin kishiyoyi da damuwar rashin dangi dana shiga shi yasa maimartaba maida hankali ya binciko min dangin mahaifana, wadanda suka zo kasar Nigeria tare, ta hanyar su ne aka bi aka cimma sauran a Chadi duk da cewa da yawa sun watsu cikin duniya wasu kuma sun murmutu. Kusan mutum biyar aka samu masu alaqar jini da iyaye na a kasar Chadi. Sannan ne na samu kaina daga gorin rashin asali dana dangi daga wajen kishiyoyi na. Aka maida gorin kan ('yar talakawa). Rayuwar gidan sarauta rayuwa ce mai wahala, musamman ga ni da ban ta so cikin sarauta ba, na sha wahala ba 'yar kadan ba a hannun Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma bata da matsala sosai, ita kuwa Hibbani sai munafurci da tsugudidi da daukar zance. Sa'a ta guda daya ce; matsanancin son da miji na ke yi mun, wanda yayi maganin kowacce damuwa da kowanne kalubale dake cikin babban gidan sarautar Askira. Sarki Yusufu bai kyale ni haka ba cikakken ilmin addini dana boko ba, malama ya dauka mai digiri take zuwa har gida tana koyar dani karatu da rubutu na zamani, sannan ya daukar min malamar karatun addini, don haka daidai gwargwado inada sani a duka fannonin har fiye da kishiyoyi na wadanda girman kai ya hana su zama daukar karatu wurin kowa. A cewar su wanda suka yo a gidan iyayen su ya ishe su. A haka nayi haihuwa har biyar 'ya'yan basa sati a duniya suke komawa. A cewar maimartaba alhakin SA'ADEN dana baro a lokacin da tafi bukatata ne, ko hakan ne ko ba hakan bane a halin yanzu na yarda na amince akwai hakkin Sa'ade a kaina, wanda ya zama dole in nemi yafiyar ta, ban taba ganin yarinya mai hakuri da son mahaifiya irin Sa'adatu ba. Mahaifiyar da ko sau daya bata taba kyautata mata ba!!! Amma kullum ta zo gaba na sai annurin fuskarta ya canza. Walwalar ta ta karu. Sai ta nuna kaunar da ta ke mun cikin fararen kwayan idanun ta. Meye laifin ta akan tsakanina da mahaifin ta? Bata san komai ba, bata san an yi ba. Don haka cikin mu'amalar mu ta Uwa da Da na amince akwai daukar hakki...... A hankali Fulani Bilkisu ta sake lumshe idanun ta. Ta bi kofar dakin Sa'ade da kallo, inda take jiyo karadin su ita da Zarah. Ko in ta baiwa Sa'adatu labarin nan zata yi mata uzuri ta yafe mata?? Domin hakika ta cuzguna mata ba dan kadan ba. Wannan tunanin ne ya sa ta mikewa tsaye, ta doshi dakin Sa'ade cikin sanyin jiki da mutuwar zuciya...... **** "Bude bakin.....haa...in sa miki choculate" ta ji Sa'ade na fadi a lokacin ta tura kofar dakin, ta same su bisa gado itada Zarah, har sun sake wanka sun sake kayan jikin su kasancewar akwai wasu kayan Zarah a dakin Sa'ade sabida yawan yi mata wanka data ke yi idan tazo hutu. Murmushi Fulani tayi ta karasa gare su ta zauna a gefen gadon. Sa'ade ta saki baki tana kallon ta don abu ne da bata taba gani ba; Fulani a zaune gefen gadonta tana mata murmushi irin na UWA....murmushin Fulani, da zama akan gadon ta ya dugunzuma zuciyar Sa'ade. Kullum ta shigo tana tsayawa ne daga bakin kofa ta fadi sakon da ya kawo ta ta juya. Yau kuwa kyakkyawar fuskarta a sake, dauke da murmushi mai taushi. Ta lura da kallon tsoron da Sa'ade ke mata sai ta kara kashe ta da lallausar murmushi. "Ki daina dura mata chocolate baki ga hakobranta duk sun cinye da zuma ba?" "Tana so ne Fulani, kuma da ta fara fanfara duk ficewa zasuyi masu kyau su fito". Ta sake yin murmushi, "an gama makaranta sai aure ko? Ko baki da saurayi ne?" Nan da nan Sa'ade tayi kicin-kicin da fuska kamar Fulani ta aiko mata da sakon mutuwa. Kamar zata yi kuka tace a shagwabe "to ni ina nake zuwa balle inyi saurayin? Daga makaranta sai daki na, ko tsakar gidannnan ba bari na kike in je ba, sabida bakya so a gane ni 'yar ki ce. Kuma Alanguburo yayi min alkawarin tafiya Jami'a a Abuja idan na ci SSCE dina, ke kuma kina zancen aure". Fulani ta dora hannayenta biyu akan kafadun Sa'ade duka biyun tana murmushi tace "karatu ai ba ya hana aure Sa'adatu. Sanda ina kamar ki haihuwata uku don dai basu rayu bane, kuma shi Alanguburo ai ra'ayin ki yake bi amma ni da shi duka mun fi so mu yi muki aure....." da sauri ta tare Fulani "to sai ku bari sai Allah ya kawo mijin, ni 'yar mitsitsiyata dani....." ta fada tana zumburo baki. Fulani tayi dariya ta dalle mata siririyar fatar bakin nata "zaki je makaranta kamar yadda kike so, amma bazamu bari ki zauna a hostel ba, saidai gidan Yarima, tunda shi malami ne a makarantar zai taimaka miki, sannan gidan sa cikin jami'ar yake, zaki samu saukin zirga-zirga". Fuskar Sa'ade ta nuna ba haka ta so ba, campus life take sha'awa, ta ganta a jami'a tana rayuwa a cikin dalibai 'yan uwan ta, rayuwa ta 'yanci ba irin ta EL-KANEMI ba. Sa'ade ta ga cewa zuwa jami'ar ma da aka barta dama ce, domin babu wadda ta samu irin wannan alfarmar a 'ya'yan gidan, da sun gama sakandire Askirama ke aurar dasu, itama ya duba maraicin ta ne da kuma tunanin karatun shine gatan da zai yi mata a rayuwa ranar da baya doron kasa. Ta tambayi Fulani ko wanene Yarima? Da ta ce a gidan sa zata zauna a Abuja? Fulani tayi mata bayani yadda zata gane cewa babban dan maimartaba ne a maza, shine Yarima mai jiran gado, Chiroman Askira, wanda ya dawo daga kasar Amsterdam shekarun baya yayi aure. Sa'ade ta kwantar da ido tana kallon Fulani, ganin yau akwai rahma tattare da ita, watakila in tayi sa'a ta gaya mata abinda ta dade tana son ji daga gareta....an ce Dama tana zuwar wa dan adam sau dayane a rayuwa....watakila daga yau din bazata sake ganin murmushin mahaifiyar ta ba, bazata sake ganin ta cikin wannan maternal mood din ba...don haka ta tambayeta abinda ta dade yana cin ta a zucci.... "Don Allah Fulani me yasa ba kya so na? Me babana yayi miki kika tsane shi? Meyasa kike bakin cikin kasancewata diyar ki? Fulani ko don ni babana talaka ne shine dalilin da......." ta kasa karasawa sai kuka ya kufce mata, tana tuno bad memories na tun zuwanta hannun mahaifiyar ta..... Ga dukkan madaukakin mamakin ta, sai jin hannun Fulani tayi ya zagayeta cikin runguma kyakkyawa, ".....Ban taba kin sa don yana talaka ba, hasalima ni a mai arzikin sa na san shi. Ban taba neman komai a hannun sa na rasa ba, ya ciyar da ni ya tufatar da ni a tsayin zamana da shi. Laifin sa gare ni daya ne....hanyar da ya bi ya aure ni.....". Tiryan-tiryan ta soma bata labarin ta, labarin da ya dauki hankalin Sa'ade har bata san lokacin da tace. "Lallai Baba bai kyauta ba. Amma ki dubi Allah Fulani ki yafe masa albarkacin ni da nake tsakanin ku, da kuma kasancewar a halin yanzu ba ya duniyar". Ta fada tana share hawaye. Fulani ta kara jawota jikin ta, ta sanya fuskarta cikin tafukanta "daga yau kin daina zargi na akan babanki? Kin daina ganin beke na a kan sa?" A hanakali Sa'ade ta gyada kai. Ta ce "to na yafe masa duniya da lahira, kema ki yafe mini deprivation dina a gareki da yadda na tafiyar da ke a zaman mu tare. Nayi kokari in tanqwara zuciyata na kasa....amma alhamdulillahi yanzu na samu sauki daga duk wani duhu da kullaci dake cikin raina". Ranar sai ta zama ranar reunion ta soyayyar uwa da 'yar ta. Kusan kwanan zaune suka yi a dakin Sa'ade, tana bata labarin rayuwar data yi tare da mahaifin ta a garin Tsanyawa tun tana karama har girmanta, da rayuwar wahalar data yi a hannun inna Laure da kuma yadda mutuwar mahaifinta ta kasance, har zuwa yadda suka yi suka zo Askira ita da Baba Saleh. Sai ga Fulani Bilkisu tana share hawaye, "nikuma na zo na yi shekaru shidda ina cuzguna miki, a matsayi na na mahaifiyar data haife ki. Bayan a lokacin ne ya kamata ki ji dadi kamar kowanne da a hannun uwarsa...don Allah Sa'adatu ki yafe mini". "Na yafe miki Fulani ban taba rike ki ba, kullum ina gayawa raina ne kina da hujjar ki, haka kawai uwa bazata ki dan ta ba, Allah ya yafe mana bakidaya". Tun daga ranar, mu'amalar Fulani Bilkisu da diyar ta Sa'ade ya canza, ta cire mata takunkumin fita, ta bata damar shiga ko'ina take so cikin masarauta, bata ki ba don gaskiya ta fito gaban kishiyoyin ta a yanzu cewa Sa'ade 'yar ta ce, tunda ta san ba shegiya bace da uban ta. Ta ja ta a jiki har fiye da kima, idan zata shirya abincin mai Askira kasancewar da kansu suke masa abinci sai ta kirata sun shiga kicin tare, tana yi tana mata bayanin yadda ake komai, anan Sa'ade ta koyi girkin sarauta iri-iri dana zamani, kasancewar Fulani Bilkisu kwararriyar kuku. Ta kuma dinga koyawa Sa'adatu tsaftar jiki data muhalli da amfani da turarukan Borno a jiki da tufafin ta. Duk da ta bawa Sa'ade damar shiga koina cikin masarauta Sa'ade bata yawon, kullum tana sassan su ko dakin Fulani, ko kuma suna kicin suna girkin Askirama idan ita ce da girki. Hatta gashin kan Sa'ade Fulani da kanta ke zama ta gyara mata yanzu, gyara na masu kwarewa akan kula da gashi, wata irin shaquwa suke yi cikin 'yan watannin nan wadda basu taba yin ta a shekara shidda da suka yi tare ba, ta yadda har Fulani ta soma zullumin zuwan ranar tafiyar Sa'ade makaranta Abuja. Maimartaba ya fi kowa jin dadin wannan sauyi da ya ke gani a tattare da Bilkisu da 'yar ta Sa'adatu, 'yar da yake jin kamar shi ya haifeta saboda son da yake wa mahaifiyar ta. Jin dadin hakan yasa ya hada musu tafiya umrah karshen wannan watan don dai su kara shaquwa da juna ba idon kowa tare dasu, amma dole tareda Fanna zasu tafi sabida kula da hidimar Fulani. A saudiyyah ba abinda Fulani Bilkisu ke roko a wurin Ubangiji sai miji nagari ga Sa'adatun ta, wanda zai rike mata ita amana ya rike maraicin ta, wanda ba zai taba duban asalin ta ya wulakantata a kan sa ba. Wanda zai zame mata miji kuma uba sannan Yayan da bata da shi a kafatanin rayuwarta. Ta kuma sakankance cewa an amshi rokon ta, don wannan shine ladabin addu'a. Ba son tafiyar Sa'ade jamia'ar Turkawa take ba, amma ta yarda da hujjojin Maimartaba, na cewa gara Sa'ade tayi karatu kafin Allah ya zaba mata mijin aure. Karatun zai zamo gata kuma majingina a agareta ranar da babu su. Suna dawowa suka tarar da sakamakon su Sa'ade ya fito, Mai Askira da kansa ya kira Yarima ya gaya masa kowacece Sa'ade, gaskiyar ya gaya masa cewa 'yar Bilkisu ce. Ya damka masa komai na alhakin nemo mata makaranta da daura masa dukkan nauyin hidimar karatun ta. Ya kuma gaya masa a gidansa zata zauna ba a hostel ba. Wata irin zufa ce ta soma ketowa Yarima ko mu ce Chiroman Askira. A tsarin rayuwar su shi da matar sa, ko kuda basa so ya gifta a tsakanin su balle dan mutum ya zauna a cikin su. An tarbiyyance su da rashin yin musu ga magabatan su, an raine su a bisa bin umarnin na gaba, balle Mai Askira gabadaya. Don haka amsar sa ita ce kawai "toh" amma a ransa ya ce kora da hali kawai zai sa yarinyar ta bar masa gidan sa. To amma kuma Maimartaba ya ce 'yar Fulani Bilkisu ce ta cikin ta, matar da duk fadin gidan su in ka dauke mahaifiyarsa ba wadda yake gani da mutunci kamar ta, ba wadda ke kula da al'amarin sa dana matar sa kamar ta. Anya zai iya wulakanta jinin ta? Babbar damuwarsa Sultana bazata taba amincewa ba musamman sabida yadda take shaye-shayen ta babu takura, ta dauka bai sani ba, amma kallon ta kawai yake, duk abinda take ciki ya sani, baya magana ne don ya san shima da nasa guntun kashin a katara. Aka ce wai in ka ji ma'aurata masu ha'intar juna suna zaman lafiya to tabbata daya na ha'intar daya, babu yadda dayan zai yi ya hana, kada nashi asirin ya tonu. Wannan shine tsakanin Yarima Sageer da matar sa Aisha-Sultana. **** Babu yadda zai yi, haka yasa neman admission din Sa'ade a gaba a washegari a matsayin first thing da ya shiga ofis ya zauna, takardun ta duk sun yi kyau. Ya tsurawa sunan ido.... SA'ADATU HASHIM ASKIRA. Hatta course din ma nasa ta dauka......Pure and Applied Chemistry. "Does she know me?" Ya tambayi kansa cikin mamaki. Salon karatun ma mai Askira ya ce ni zan koya mata??? Tsaki yayi ya ture takardun gefe ya janyo na wasu, a lokacin da Dr. Ziyad ya turo kofar ya shigo dauke da sallama a bakin sa. "Wata hot baby na samo yanzunnan daga zuwa na Millenium Park, akwai abubuwa, kayi maza ka gama mu bar ofis dinnan". Tsaki yayi ya ce "kai baka san halin da nake ciki ba, wata yarinya za'a kawomin riko daga gida, Allah ya sa ba spy mai martaba zai kawo min ba, ko wani ya kai gulmata ban sani ba, ka san a ko'ina yana da jama'a musamman nan Abuja" ya fada kyakkyawar fuskarsa dauke da damuwa tsantsa. Dr. Ziyad yace "i don't think so. How old is she?" "JAMBITE ce fa" "whao!" Inji Dr. Ziyad. Kace sweet 16 za'a kawo mana kawai, yo meye abin damuwa banda mu dinga kwasar rabon mu kawai muna saya mata pizza muna cika mata aljihu? Gida na is very quite and secret ko Sultana bazata san muna kwasar gara ba". Wata muguwar harara Yarima Sageer ya zabga masa, ya tsartar da miyau da sauri. "Allah ya sawwake Allah ya tsare ni, ni ba dan akuya bane, ina dai neman matan bisa titi amma ban da na mutunci balle wadda ta fito daga gidan mu, daga gidan mun ma daga hannun mahaifi na, 'yar matar mahaifi na mai yawan karamci a gareni. Allah ya kiyaye! Iskancin nawa mai limit ne, and i'm hoping watarana in bari gabadaya". Dr. Ziyad ya kyabe baki tareda mikewa tsaye yana dariya yace "kai din? Na yarda bazaka iya neman ta gidan ku ba, ko don kada asirin ka ya tonu, amma bazaka iya barin mata ba i swear ...." Yarima ya dauki mukullan dake bisa teburin sa ya jefe shi dasu, Dr. Ziyad ya dafe keya ya fice da gudu yana masa dariyar data kara masa takaici kan wanda yake ciki, na yarinyar da za'a turo masa babu gaira babu dalili. Cikin sati daya ya gamawa Sa'ade duk shirye-shiryen ta, an dauke ta a NTNU a tsangayar da yake koyarwa (B. Sc Pure and Applied Chemistry). Ya aikawa Askirama admission letter din ta ta email. Abinda ke gabansa yanzu shine ta yadda zai tunkari Sulatana da maganar. Amma abin mamaki da ya koma gida da yamma, ya tarar ta riga shi dawowa, ta shawo ta yi mankas tana kwance dai-dai a tsakiyar falo. Haka ya tsallake ta yana tsaki ya wuce dakin sa ya sunce ya shiga wanka. Yana fitowa ya shiga kitchen don neman abinda zai ci, ya bude firji, abin takaici babu komai sai Giya nau'i nau'i, yanzu Sultana ta daina shakkar ya san shaye-shayen ta, kai tsaye take komai don ta ga baya daga ido balle ya nuna ya san tana yi. Wani mugun tsaki ya saki ya rufe firinjin da karfi, yanzu in yarinyar nan ta zo ta gani fa? Mai Askira yace rana ita yau za'a kawo ta tare da kayan ta su gyara mata daki. Ji yayi yunwar da yake ji ta kama gaban ta, da sauri ya fito ya sa kafa ya shuri Sultana da karfi. Ta bude idanu jazur dasu, ta sauke su a kan shi, dama gasu tun asali kamar na mage (brown eyes). A fusace yace "ki tashi ki kwashe abubuwan da kika cika min firji dasu, we're having a guest from Askira, and she's going to stay with us for years, so mind yourself else.....duk abinda ya biyo baya ba ruwa na". Sultana tayi mici-mici da ido "bakuwa? A gidannan? Daga Askira? To ban yarda ba" ya galla mata harara yana hango wani irin muni a tare da ita da bai taba gani ba wanda yake bayyana in ta sha giya "sai ki kira maimartaba ki gaya masa" ya jefa mata wayar hannun sa. Har dare suna fafatawa, ta dage sai ya kira Babansa ya ce bata yarda ba, shi kuma yace ba tarbiyyar da aka yi musu kenan ba but she's free to call him herself. "To ko dai aure suka yi maka shine za'a fake da karatu don nasan mamanka bata so na!" Sultana ta fada cikin kuka. Shi don mamakin kalamanta ma dariya yayi, wai aure! Wa ya isa yayi masa aure ba da yardarsa ba? Besides, su gidan su ba'a auren dole. Sannan ya gama aure a rayuwar sa ba zai taba yin mata biyu ba duk da kasancewarsa basarake. Tashi yayi ya dau motar sa ya bar gidan zuwa inda ya tabbatar za'a faranta masa rai, yau ranar kwata-kwata a birkice ta zo masa. He's upset, sannan wannan mahaukaciyar Sultanar ta kara masa bacin rai. Ai kuwa ya samu Dr. Ziyad ya dauko musu baby din da ya gaya masa sun hadu a millenium park, nan ya manta da zancen Sa'ade da Maimartaba ya shantake acan har karfe daya na dare. Sanda ya shigo gida ya tadda Sultana ta baje kwalabe sun fi biyar duk tayi emptying din su. Ta koma zukar marijiuana cikin tsumma, gashin kanta a birkice, gabadaya sai ta zame masa kamar motsatsiyar tsohuwa, ya dinga tambayar kansa tun farko me ya gani a tare da ita ya yarda ya daukota har kasar sa ya aureta??? Tsaki yayi ya tsallake ta ya wuce dakin sa. Wanka ya fara yi ya tsaftace kansa, yana jin wani abu na tsirga masa a zuci da gangar jiki, wanda yafi kama da jin kunyar Ubangiji. Wankan janabar da bata aure ba alhalin ga matar sunnar ya tsallake tana nata sabon Allahn. Wannan wace irin rayuwa ce??? Idanun sa a rufe ya hau gadon sa ya kwanta. Addu'a yake cikin ransa in yana da rabon dainawa kafin ya mutu, Allah yasa ya daina......!!! **** Tunda Askirama da kansa ya shigo ya ce da Fulani gobe ne tafiyar Sa'ade gidan Yarima jikin ta yake a sanyaye, don bata san wane irin riko da karba Sultana zata yi mata ba, tunda ita ba jinin gidan bace, duk da su Humaira suna fadin bata da matsala. Amma ga Sa'aden sai murna take, very enthusiastic ga tafiya makaranta, bata tunanin komai da ya danganci abinda zata ta tarar banda kasancewa dalibar Turkish University. Don a daren Fulani ta zaunar da ita a gabanta. Don ta ga murnar tata har ta so ta yi yawa, tun azahar ta kammala daure kayanta tsaf. Kadan ta bari wadanda bata cika amfani dasu ba. Allah-Allah take garin Allah ya waye ta kama hanyar birnin tarayyah. "Sa'adatu bani hankalin ki nan" inji Fulani. Ta dago fararen idanun ta ta dubeta, wadanda a lokuta da dama suke wani irin sheki da walainiya (sparkling eyes) wanda shine babban sirrin kyawun Sa'adatun. Fulani tace. "Na ga sai rawar kai kike, ki kama kan ki, gidan Yarima zaki je, sannan matarsa asali ba musulma bace, sannan ba bahaushiya bace, don haka dole ki kula da tarbiyyar kan ki da kan ki, ki maida hankali akan abinda ya kai ki kawai, ba ruwan ki da rayuwar su, ban da sa-ido, banda daukar zance, banda shiga shirgin da ba'a sanya ki ba. Tsakanin ki da su yi na yi bari na bari. Ki dinga taimaka mata da girki da ayyukan gida tunda ita ma'aikaciya ce. Na hore ki da kama mutuncin kanki, ko ya kike da namiji kada ki yarda ki kebe da shi, Ko hannun ki namiji ya taba cikin shege zaki yi, kin ji na gaya miki?" Sa'ade ta gyada kai cikin fahimta, sannan ta dan zaro ido ta ce "to ai gidan ba maza ko?" Fulani ta hana kan ta yin dariya sabida yadda muryar Sa'ade ta koma razana zallah. Tace "shi mai gidan ma ai namiji ne, kuma ba muharramin ki bane ba, don haka matsayin uba yake a gare ki, ki kama kan ki, ki rike mutuncin ki. Allah yayi miki albarka ya saka albarka a neman ilmin ki. Ga waya karama na saya miki duk halin da kike ciki ni zaki kira ki gaya min, ban yarda ki bawa kowa lambar ki ba". Sa'ade ta gyada kai cikin murna a lokaci guda tana mika hannu don karbar karamar wayar siemens da Fulani ke mika mata. Kawai sai ta ji Fulani ta hada da hannun ta ta janyota jikin ta ta rungumeta... "Ki yafe min Sa'adatu don Allah ki yafe mini..." "ni baki yi min komai ba Fulani, na yafe miki abinda na sani da wanda ban sani ba. Nima ki yafe mini!" Sallamar tasu is very emotional da ta fiddo hawaye daga idanun kowaccen su. Washegari daya daga cikin direbobin gidan karkashin rakiyar kuyangin Fulani Bilkisu mata guda biyu maimartaba yasa suka dauki Sa'ade zuwa Abuja a daya daga cikin motocin 'Askira Emirate'. Tun asussuba suka kama hanya basu isa Abuja ba sai karfe takwas na dare. Inda Allah ya taimake su shine sun yo guzurin abinci da abin sha wadatacce wanda har suka iso Abuja sallah ce kawai take tsayar dasu a gidajen mai na gefen hanya. Suna fitowa daga mota Sa'ade tayi mika....ta ware ido tana kallon kyawawan gidajen estate din malamai na NTNU kamar kana kasar Istanbul. Ashe ba ginin masarauta kadai ne gini mai kyau ba, ginin Turkawa ma abu ne mai matukar kyau da daukar hankali. Ita dai tunda take bata taba ganin kananan gidaje masu tsari da kyawun zubin wadannan ba, ko ya mutanen cikin gidan suke? Koda yake Fulani ta ce turawa ne, ai sai turawan.... "wannan gida wanke hannu ka taba". Sa'ade ta ce cikin ranta. Daidai lokacin da daya daga cikin kuyangin da suka zo tare ta yi mata magana ganin ta shagala a kallon gidan "ranki ya dade mu karasa daga ciki ko?" Suka isa ga entrance na gidan suka hau danna kararrawa, suka yi har suka gaji ba'a bude ba, a lokacin Sultana na kwance a falo ta sha ta kai mata karo, tun misalin karfe 6 na yamma take kwance har a lokacin bata san inda kanta yake ba. Allah ya kawo Uche (kukun gidan) zai shiga da cefane, kasancewar yana da mukullin gidan ta kofar kicin ta baya. "Hey! What do you want here?" Ya tambaye su. Aka rasa mai amsawa don 'yan rakiyar Sa'aden basa jin turanci, sai itace ta gayamasa daga Askira suke, sun zo wajen masu gidan ne. Ya tambayeta ko Dr. Sageer ya san da zuwan su? Ta ce "ya sani" a takaice, domin bata da tabbacin hakan, Allah-Allah take ta sanya hakarkarinta akan shimfida sabida gajiyar zaman mota data kwaso. Wayar sa ya dauko ya kira wata lamba yayi magana cikin harshen turanci, ya kalle su, sannan ya maida wayar aljihun sa ya ce su biyo shi. Ta baya suka shiga ta kofar kitchen suka kurda zuwa falon gidan. Nan Sa'ade taga mace jajawur kwance magashiyyan a dandaryar tayals, gashin kanta ya baje ya rufe fuskarta, Uche bai ko dubi inda take ba ya bude wani daki yace su shiga nan ne dakin bakuwar. Sannan ya ce su bashi minti 15 zai kawo musu abinci. Kafinnan ga ruwa da lemo su sha. Tsaruwar dakin ya burge Sa'ade, duk da bai kai dakin ta na Askira ba amma daki ne mai tsari irin na turawa babu tarkace sam a cikin sa. Gado ta fada tana ce da Fariha daya daga cikin 'yan rakiyar ta in an kawo abincin ta tashe ta tunda ita tana fashin sallah, in taci abinci sannan tayi wanka. Uche ya kawo musu abinci mai rai da motsi suka ci suka koshi, sannan Sa'ade ta fara yin wanka, ta shirya cikin kayan barci tabi lafiyar gado bayan ta kure iyakwandishan, sukuma kuyangin suka kwanta daga kasa. Ba wanda ya nemesu har washegari. Da asubah suka kama hanyar Maiduguri lokacin Sa'ade tayi sallah ta koma barci. **** Sai karfe takwas na safe Sa'ade ta tashi, ta duba babu 'yan rakiyarta, sai ta tuna sun ce da asubah zasu kama hanya, tsaki tayi tana mitar shine ko su tashe ta su yi sallama. Wanka ta fara yi, kafin ta ji cikin ta yana kiran chiroma, a gurguje ta shirya tana fadin bari in bi su kitchen din tunda sun manta da mutum a gidan. Tana kokarin fita bayan ta murda kofar dakin taji ta yi karo da mutum....Wani irin sassanyar kamshi mai huda zuciya, coupled with his gait and geniusness, beautiful elegant face wadda babu far'a sam a cikin ta. A kiyasce yadda ta kimanta shekarunsa zasu kai talatin da biyar zuwa da shidda. Alamu sun gama nuna ya gama samun duk wasu achievements na rayuwar dan adam. Kama daga ilmi na addini dana zamani, sannan ya zauna da kafafun sa ya gama kama kasa. Da farko ta dauka Askirama ne a gabanta (mai martaba) sabida tsabar kamannin su, saidai data lura sosai sai ta fahimci wannan akwai tarin kuruciya da hasken boko a tare da shi, bi ma'ana yaro ne mai jini a jika, babu ko tsillin furfura a kwantaccen sajensa zuwa gashin kansa, wanda ya kwanta luf a gefen fuskarsa. A duniya bata taba katari da mutum mai cikar kamala da kyawun suffa kamar sa ba, ga wani irin kwarjini da ya banbanta shi da sauran maza. Sarauta ta gama bayyana kanta a komai nasa. His lips are so luscious kamar ana basu extra kulawa, fatar jikin sa fresh kamar haifafen kasar Morocco. Sai ta ga kamar ta taba ganin sa, somewhere else da bazata iya tunawa ba. Yadda ta saki ido, hanci da baki tana kallonsa shi ya fi komai bashi haushi, amma da yayi kokarin yin magana sai ya samu halshen sa da kasa motsawa. Suka dubi juna directly cikin ido yayin da wani gravity mai karfi ya fizgi ido da zuciyar kowannen su. Alal hakikah a rayuwar Dr. Sageer Yusuf Askira, bai taba ganin macen da ta tabo wani sashe na kololuwar zuciyar sa irin wannan da ke gaban sa ba. As professional as he is akan sha'anin mata, ya fada a zuciyar sa cikin 'yan dakikan da suke tsaye..... "ta mallaki komai da yake mafarki a diya mace". Amma kuma nan da nan mulkin sa da izzarsa ta Yariman Askira ta zo ta shafe komai, daga ganin yarinya baka san komai akan ta ba, sannan wadda ta fito daga gidan ku? Tuni ya mallaki kansa, fuska a daure ya ce da ita "come for breakfast". Ya juya ya fita, ba tareda ya kara wata kalma ba. Komawa ta yi ta dauko mayafin ta ta yane kanta akan doguwar abayar dake jikinta ruwan hanta, da sallama ta shigo falon, can bisa dining ta hange su shida matar sa. Gaskiyar Fulani ashe...baturiya tsantsa. Ai kuwa sun dace duk da shi baki ne kamar Askirama. Sa'ade ta fada a zuciyar ta. Sultana ta daga ido tana kallon Sa'ade, kallo daya Yarima yayi mata ya maida kai ga cin abincin sa. A take ta ji wani irin kishi ya soke ta, wannan kyakkyawar yarinyar za'a dauko a ajiye mata a gida? Ai da sake wai an bawa mai kaza kai. Ta dauke kai daga kallon Sa'ade ta mayar kan abincin ta. Har kasa ta tsugunnan tana gaishe su, daga matar har mijin babu wanda ya amsa mata. Wannan abu ya sosa mata rai. Daga bisani Yarima ya mike yana goge bakinsa da tissue. "If you finish meet me outside" ya ce da Sa'ade. Matar ta tambayeshi inda zai kai ta? Yace tare zasu dinga shiga makaranta. Har zata yi magana, sai kuma ta ja bakin ta tayi shiru, itama ta mike ta bi bayan sa. Haka jiki ba kwari ta ja jiki zuwa tebir din cin abincin, ta zuba abinda zata iya ci, duk yunwar data ke ji sai taji ta rasa appetite din ta, sabida irin tarbar da masu gidan suka yi mata. A can kofar gida rigima ake tsakanin Sultana da Yarima, ta ce ita sam bata yarda su dinga tafiya tare ba, ko dai ya daukar mata direba ko ta dinga tafiya da kanta tunda babu nisa zuwa cikin makaranta. Ya san halin nacin Sultana in bai yi mata abinda take so ba bazata barshi ya fita ba, don haka yace zai daukar mata direba amma for the mean time zasu dinga tafiya tare kafin a samu direban kuma ta gama registration dinta. Daga bisani ya sassauta murya "you want to me into trouble with my father? Do you know how much he loves this girl?" Sultana tayi narai - narai da ido, sai ya sunkuya ya sumbaci bakin ta cikin lallashi. "Ki kwantar da hankalin ki ni babu wata bakar mace a gabana, look at you me zan nema a wurin sauran mata? I just want to live in peace with my father shiyasa na karbi yarinyar kuma da an yi hutu zan maida ita Askira sai an koma makaranta". Dai-dai lokacin da Sa'ade ta fito ta gansu a haka kamar zasu manne cikin jikin juna, sai ta samu kanta da jin kunya tayi maza ta juya don bata taba ganin namiji da mace so close hakan ba. Sultana ta harareta sannan ta ja da baya ta budewa Yarima kofa shikuma ya budewa Sa'ade kofar gefensa ya ce ta shigo. Don haushi bata iya ta tsaya ta ga fitar su ba ta juya ta dauki tata motar don tafiya nata wajen aikin. Tana tafe tana tunanin irin takurawar da zaman Sa'ade zai yi mata don tun shekaranjiya Yarima ya kwashe duk wata kwalbar giya dake cikin gidan ya zubar. Jiya sai Bar ta je ta sha abinda ta dade rabon ta da yi. Suna shiga cikin makaranta Sa'ade ta bude ido tana shan kallon NTNU (Nigerian Turkish Nile University). Its various faculties and administrative offices...the equisite lecture halls and different departments. Wani shauki na diban ta idan ta tuna ta zama cikakkiyar dalibar NTNU yanzu. Haduwar ofis din YARIMA Sageer Yusuf Askira ya tafi da ita, ko'ina sai raba da sanyi da kamshi mai sanyi. Sai da ta jira ya gama abinda zaiyi sannan ya hadata da assistant dinsa ya taimaka mata ta fara registration. Cikin kwana na uku ta gama, ta zama cikakkiyar dalibar tsangayar (Pure and Appplied Chemistry). Ranar litinin zata fara daukar lacca. **** Yau asabar, daga matar har mijin duk suna gida, Sa'ade in ta gansu a falo bata fitowa tayi ta zama a dakin ta kenan, ko abinci bata yarda ta zauna ci tare dasu sai ta jira sun gama sun tashi, sannan zata zo ta zuba ta ci ta kwashe kayan ta kai kicin, Uche ya karba ya wanke ya dora wani. Saidai ita sam ba jin dadin abincin gidan take ba sabida abincin turawa ne ake yi kullum, wani ma bata san da me aka sarrafashi ba ko sunan sa, ga kaguwa (shrimps) da ake zubawa a kowanne girki, don haka yau da bazasu je cikin makaranta ba kasancewar hutun karshen mako ne sai tace da Uche kada ya sanya abincin su da ita, she want to cook for herself (tana so ta dafa da kanta). Uche ya bata duk abinda zata bukata don ta ce tuwon acca zata yi miyar egusi. Nan da nan ta hau girkin ta cikin kula da takatsan-tsan da kuma kwarewa. A can falo Sultana ke tambayar Yarima yaya zacen direvan da ya ce zai daukarwa Sa'adatu? "Ana nan ana bincikawa", yace da ita, a lokaci guda yana cigaba da marking takardun dalibansa ba tareda ya bata hankalin sa ba. Ya rasa me yarinyar ta tare mata, bata da zance sai na Sa'adatu a tsayin satinnan bakidaya. Shikuma a yadda ya lura sam yarinyar bata da matsala, sannan bata takura musu, bata sa musu ido kamar yadda suka yi tsammani, tana da tsananin kamun kai da gudun zuciya. Sannan rayuwar ta is very simple. Wani unique kamshin girki da bai saba ji ba ya bakunci hancin sa, dama kuma yunwa yake ji, ya kwalawa Uche kira. Ya fito da sauri har yana tuntube. Daidai lokacin da Sa'ade ta zo ta wuce su da food flask biyu a hannun ta na tuwo da miya da plate da cokali tayi dakin ta. Ya dan kalle ta ta gefen ido yadda bazaka taba zaton ya kalletan ba yace "Uche, me kake girkawa haka?" "Ba ni bane Oga, Sa'adu ne" yayi murmushi jin sunan da ya kira Sa'ade dashi yace "me ta girka?" "Tuwo ne Oga, with egusi soup" "ok idan da saura debo ka kawo min" "ya kwashe duka ya tafi daki" "saboda rowa ko saboda me?" Uche yayi dariya, "Oga akwai wanda ta diba min, lemme bring it" "thank you Uche". Uche yaje ya kawo abincin a kyakkyawan flasks a rufe ya aza bisa dining. Sultana na daga kwance tana kallon Yarima yana cin tuwon nan zuciyarta na tafasa, bata isa kuma tayi magana ba yace zai bar gidan, don yace duk renakun weekends baya son korafi, in ta yi masa complain ko guda daya ne zai bar mata gidan ya tafi gun Dr. Ziyad. Ita kuma sam bata son alaqarsa da Ziyad don bashi da aure kuma kullum tana ganin shi yana kwashe-kwashen mata a motar sa zuwa gidan sa. Shiyasa take making sure bata yi abinda baya so ba a kowanne weekend don dai su zauna tare. Bai san yayi missing cimar gida ba sai yau, sosai ya ji dadin tuwon, da izzar shi zata barshi ai da yace da daddare ma ta kara yi masa, musamman mai miyar ganyen Ugu, yana son ganyen sosai. Shikuma Uche tunda ya lura Ogan sa na son tuwo sai yake kokarin yi masa, amma sam baya kyau da dandano kamar na Sa'ade don bai kware ba, a wurin Sa'ade ya koya don ya ce mata ta koya masa ya dinga yiwa Ogansa. To amma kullum yayi haka yake dauko shi Oga ya yi loma daya ya ajiye, ko yace ya dafa masa wani abun. Don haka Uche yake mata wayo, kullum zata dora girki sai ya ce ta dora da dan yawa, shima yana so, tana bada baya zai shirya abincin ya kaiwa Yarima, ya gaya masa Sa'adu ne ya girka, ya rasa ya aka yi Uche ya dago shi kan yana son cin girkin Sa'adatu. Duk ranar da bata yi girkin ba ta wuni a makaranta ne yake cin na Uche. Sultana ta shigo gida yau da sabon bed-side fridge wanda babu a dakin ta. Washegari kuma data dawo aiki ta dawo da manya-manyan kwalaye. Tana kokarin fito dasu daga mota direban da Yarima ya dauka ya sauke Sa'ade. Ganin tana kiciniyar ciccibar kwalayen Sa'ade ta karasa da sauri ta ce. "Can i help you aunty?" "No, thank you" In ji Sultana. Ta ciccibi manyan kwalayen ta daya kan daya tayi cikin gida. **** Tun daga ranar Sultana ta daina zuwa Bar ta koma shaye-shayen ta a dakin ta, a zuciyar ta tana tsinewa Sa'adatu, ita da gidanta an zo an takura ta. Bata sha a weekend sabida Yarima yana gida, da yamma kuma sanda ta dawo shima ya dawo, don haka sai ta tsiri kulle kanta da zarar ta dawo aiki bata kara fitowa sai lokacin barcin su. Dr. Sageer yana lura da sabon sauyin nata, ya rasa me take kulle kanta tayi a daki, bugun duniya in zai yi bazata bude ba sai ta ga damar fitowa wajen sha biyun dare. Tuni ya harbo jirgin ta. Rannan ya faki idon ta ya dauke safayan mukullin. Tana tsaka da shan whisky ya bude kofar dakin ya shigo ya mayar ya rufe. Kayan barci ne na RALPH LAUREN farare sol a jikin sa. He never looked so handsome in her eyes like today. Ya tsaya a kanta ya harde hannayensa a kirji yana kallon ta with furious eyes... "Sultana why? Ba na hana ki shan giya ba? Ko syrup ban hana ki sha ba? Ban gaya miki haramun ne a muslunci ba? Idan da kin yi na kyale ki yanzu kin sani ba mu kadai bane a gidannan, a slight mistake will probably go to my father, har yanzu jiki na na bani spy ce ya sanya mun. Ki yi a hankali idan ba kina son janyo min bala'i ba". Ta daga rinannun idanun ta ta dube shi, cikin maye tace "I....i cannot live without beer, a haka ka ganni ka aure ni, kai ma ka sani bazan taba iya barin giya ba". "Sai ki zaba ko aure na ko giya, tunda na sanar dake addinina ya haramta kika ce kin amince zaki daina, tunda kika fara aiki na san kin koma shan beer, sallah kin dade da daina ta, na sa miki ido ne don in ga iya gudun ruwan ki, and now na lura duk musluncin ki ba na gaskiya bane kin dade da daina sallah. Ni kuma bazan zauna da kafira ba". Ya fadi yana watso kwalaben dake jere cikin firji, ya hada su da bango ji kake taratsatsa! "Kika sake shigo min da wannan kazantar gida, zaki ga yadda zamu kwashe, i'm not that fool and i respect my religion......". Wani wulakantaccen kallo Sultana tayi masa....tace "addini! Kai nan har kana da bakin cewa ka san addini? Addinin naka ne ya baka damar yin adultery? Tunda na san ka na san you are an adultrer wanda baya iya rayuwa sai da mata. Na dauka in mun yi aure shikenan zaka bari, gara ni giya da kayan maye kawai nake sha amma bana zina, balle da aure na". Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka fuskarsa ta koma, bai taba sanin ta san wannan side din nashi ba, abinda bai sani ba shine tana bibiyar wayar sa. Sultana ta lura da efffect din kalamanta akan sa, sai ta yi wani miskilin murmushi "tunda na barka kana zina, ban taba takura maka ba, sai ka bar ni in sha giya, ko wannan yarinyar ta bar min gida......" ta mike tana layi tayi toilet ta bar shi a wajen. **** Kwana biyu basa magana da juna, abinda basu taba yi ba a rayuwar auren su, wani abu da Sultana ta tsiro da shi don ta baiwa Yarima haushi shine ta daina boye shan giyar da kayan mayen ta, nan falo take zama ta baje tana abin ta. A ranta ta kudure duk ranar da ya gayawa iyayensa tana shan giya itama tace musu yana neman mata. Gara ma yayi hakuri su ci gaba da zaman su yadda suke yin sa, wata figigiyar yarinya bakauyiya bata isa ta canza mata rayuwa ba. Sa'ade ta shigo falon da sallama, misalin karfe shidda na yamma, direbanta Salis ya riko mata manyan littafan chemistry har zuwa kofar shiga falo, ya mika mata tayi masa godiya. Tana kokarin shiga Yarima na parking. Ta juya suka hada ido ta cikin gilashin motar sa, sai ya yafito ta, yace "Sa'adatu help me with these files" ta karasa cikin nutsuwa ta karba, shi kuma ya dauko daurin answer sheets na daliban sa ya bi bayan ta suka shiga falon tare. Nan idanun sa suka yi kyakkyawan gani. Kamewa yayi a inda yake tsaye, a lokacin ta kai bottle na whisky bakin ta, ta gefen idon sa ya saci kallon Sa'ade don ganin reaction din ta, sai ya ga babu wani sauyi a tare da ita, ga dukkan alamu bata san menene a hannun Sultana ba, ta dauka just lemo ne. Sannu da gida kawai ta yiwa Sultana ta ajiye masa takardunsa bisa centre table, daga nan bata kara kallon su ba tayi shigewar ta daki. Yayi catching breadth din sa da karfi tana bada baya ya wankawa Sultana mari, ya sake wanka mata, sai da ta nemi jin ta da ganin ta na wucin gadi ta rasa. Tana farfadowa ta kai hannu zata rama ya kama hannun ya murde shi. Ta saki karar data kai kunnen Sa'ade. Har zata fito da gudu ta tuna hudubar Fulani (ba ruwan ki da shiga shirgin da ba'a sanya ki ba) tunda dai ta san su biyu ta bar su. Kwanan tashin hankali aka yi tsakanin ma'auratan, irin wanda bai taba faruwa tsakanin su ba, zagi ta uwa ta uba babu irin wanda Sultana bata yi wa Dr. Sageer ba, har tace duk da kasancewarta kafira kamar yadda yake kiranta bata taba zina ba shi ya koya mata, shi yayi disvirgining din ta, musluncin sa bai kare shi da komai ba, fasiqi mara tsoron Allah. Gara ita giya kawai take sha. Duka wannan a kunnen Sa'ade, wadda hayaniyar su ta hanata barci, ta tsaya jikin kofar dakin ta sai shivering take (karkarwa). Bata taba jin abinda ya kada ta ya gigitata irin wannan ba, gidan masu zina da shan giya aka kawo ta! Uncle Yarima da take gani da matukar girma da kima shine mai yin zinar? Ko dai Sultana karya take yi? Abinda ta gani tana sha dazu shine giyar kenan kuma shi ya hada fadan? Tana jiyo kukan Sultana da alama marin ta ya kara yi, jikin ta na rawa ta dauki waya ta kira Fulani, hawayena zuba mata tace "Fulani! Ni dai gobe a zo a dauke ni bazan iya zama a gidannan ba, zan koma hostel" cikin muryar kwantar da hankali Fulani tace "take it easy....gaya min me ya faru? Ana miki wani abu da ba kya so ne?" Cikin kuka tace "no, Uncle Yarima is very nice to me....amma yana dukan matar sa....gata can sai ihu take.....kuma ta ce shi mazinaci ne...." ba shiri Fulani ta dauke wayar daga kunnen ta ta juya, sai idon ta cikin na Askirama da ke gefen ta da alama shima sauraron wayar yake yi don ta manta a (hands-free) take. Yanayin da ta ga fuskar sa a ciki yasa ta jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaqe Sa'ade har sai ta daina numfashi. "Wallahi maganar Sa'ade shirme ce ni na tabbata....". Fulani ta fada muryar ta na rawa, kwalla cike da idon ta. Daga taimako Sa'ade zata baro musu tashin hankali da yake ita butulu ce, ina ruwan ta da abinda ke faruwa tsakanin Yarima da matar sa? Bayan ta gargadeta? Sai ta tuna Sa'aden bata san tana turakar Askirama ba, kuma ita ta bata damar duk halin da take ciki ko karfe nawa ne ta kira ta ta gaya mata. "Ba shirme bace Bilkisu..... he has this taboo since childhoood". Ya fada muryar sa abin tausayi. Har yaran bayi yake raping...na dauka ya bari, na dauka girma ya sa ya nutsu, na dauka aure ya canza shi...ashe i'm mistaken. To aikin zai bari ya dawo gida kusa da ni kawai ya karbi sarautar gidan su, in cika masa gida da mata da kwarkwara tunda hakan yake so.....da raina da lafiya ta bazan bar shi ya karasa rayuwar sa a haka ba........". The way Mai Askira ke magana ya taba zuciyar Bilkisu, bata taba ganin sa cikin wannan sad mood din ba. A muryarsa da fuskarsa bakin ciki ne zallah. Ya kare zancen sa da cewa "zan raba Sa'adatu da gidan sa, tsoro na Allah yanzu tsoro na kada itama ya taba ta......" "Haba-haba Askirama! Kada bacin rai ya kai ku ga yi masa mugun fata, ni na tabbata ko Yarima na neman mata bazai nemi na cikin gida ba balle Sa'adatu kanwar sa, don Allah a kyautata masa zato, kada a raba shi da aikin sa he is very young da karbar sarauta yanzu, sannan kaima in ka zauna a gida me zaka yi? Da cikar lafiyar ka da shekarun da basu kai 70 ba. A yi masa hakuri ayi masa addu'a, ita ce kawai mafita. Kuma daga Sa'ade ta fadi abu ai bai kamata mu yarda ba tunda bamu gani da idon mu ba". Mai Askira yayi murmushi mai ciwo "baki san Yarima ba!" Da kyar, da lallashi da ban baki Fulani ta ciwo fushin maimartaba ya fasa cewa Yarima Sageer ya dawo gida, amma ya ce dole zai dauki mataki. Shi ya gama amincewa Sa'ade ba karya take ba, ta fadi abinda ta gani ne da abinda ta ji tabbas. Koda ya tura Sa'ade gidan Yarima yana da dalilin sa, gashi tun ba'a je koina ba zuwan ta ya sa yanzu ya san halin da Yarima yake ciki. **** Da asubah Fulani ta koma daki ta kira Sa'ade, wadda ta kwana zungurgur a bakin kofa, ta dade bata ji ma'auratan sun gama fadan nasu ba, ta ji abubuwa da yawa da suka razanata, Sultana ta dage in ya takura mata akan shan giya to zata koma addinin ta na Jew (ridda). Shikuma ya ce ta koma din, amma ta sani muddin ta bar muslunci a bakin auren ta. Zina kuma yanzu ya fara in ita uwarsa ce ta hana shi. Sa'ade bata taba fadawa tashin hankali irin na yau ba, ta ji ta tsani Yarima da matar sa bata ko marmarin sake ganin munanan fuskokin su. Kuma sai gwada wayar Fulani take ta tubure mata azo a dauketa ta kasa samun ta, sai goshin asubahi sannan ta samu kiranta. Jiki na rawa ta amsa wayar, cikin kuka tace "Don Allah Fulani....don Annabi ki aiko a dauke ni, bazan kuma kwana a gidan nan ba, ko na minti daya ban yi barci ba, they are fighting....." Fulani tace "Ki nutsu Sa'adatu ki saurareni, babu inda zaki, ba ruwanki da fadan su tunda basu sanya ki a ciki ba, kiyi kamar baki ji komai ba ki cigaba da harkokin karatun ki. You are not there for Yarima or matar sa, you are here to study. Kada ki kara sauraron maganganun su kin ji na gaya miki. Yanzu baki san abinda wayar ki ta jawo ba. Askirama ya ji duk abinda kika fada kuma ya ce sai ya dau mataki akan dan sa, duk akan surutun ki, ina ruwan ki?" Cikin kuka Sa'ade tace "wallahi ba sauraron su nake ba, ba labe nake musu ba, da karfi suke magana, ni ina daki na ma" Fulani tace "na fahimta, amma ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kiyi pretending as if baki ji komai ba, fadan mata da miji sai Allah, kwana biyu zaki ga sun shirya. Tunda dai ba takura miki suke ba to ba ruwan ki dasu" da haka Fulani ta samu ta lallasheta ta daina kukan, tace tayi alwallah tayi sallah tayi azkar tayi shirin tafiya makaranta. Yadda Fulani tace ta yi haka ta yi, da misalin karfe 8:30 ta fito rataye da jakarta, tayi shirinta tsaf. Hannun ta rungume da manyan littafan ta na chemistry. Da Yarima ta fara tozali yana sipping shayi akan dining, gabadaya ya birkice kamar bashi ba smart guy mai tafiya da imanin mai kallon sa, gashin kansa ya cukurkude kuma ga dukkan alamu ko wanka bai yi ba. Ta gefen idon ta ta saci kallon sa, a ranta tana fadin how comes this perfect and handsome gentleman is adulterer? Ga goshin sa har da tabon sujjadah. Watakila matar sa ta dai fada ne don ta bata masa rai tunda shima ya ce tana shan giya. Ta dan russuna daga bakin kofar dakin ta ta ce ciki-ciki "barka da asubah". Ya dago lumsassun idanun shi ya dube ta wadanda suka canza kala zuwa brownish sabida rashin barci. Ta ki yarda su hada ido ta sunkuyar da kanta wanda hakan ya bashi damar ganin yadda idanun ta suka tasa, kada dai kuka tayi? Kada dai ta ji fadan su shi da Sultana? Tabbas da ya shiga uku ya lalace. Murya a cunkushe ya ce "come take your tea" cikin rawar murya ta ce "i'm ok" tasa kai zata wuce ya daka mata tsawar data firgitata "kina nufin haka za ki fita baki ci komai ba? Me ya samu idanun ki haka? Have you slept yesterday night?" Jikin Sa'ade ya soma rawa sabida bai taba yi mata magana cikin tsawa ba. Ta tuna Fulani ta gargadeta akan ta nuna bata ji komai ba. Sai tayi narai-narai da ido gab take da sakin kuka ta ce "na tashi da ciwon ciki ne" Yarima ya ji wani irin relief ya sauko masa, ya nuna mata kujerar dake gefen sa "zauna ki sha tea ko kadan ne, bai kamata ki fita haka ba, sai in baki magani" ta bi umarnin sa kan ba yadda zata yi, amma kwarai take so ta bar gidan ko ta samu sa'ida. Da kansa ya hada mata tea din, wanda shi ya dafa shi da kansa. Uche ya masa waya cewa ya tafi garin su Ogun mahaifiyar shi ta rasu a safiyar yau. Ta karbi tea din da yake mika mata ba don ranta ya so ba, amma kaifin idanun sa da ya tsare ta dasu ya sa ta kasa kurbar shayin. Yarima ya mike ya bar dining din zuwa dakin sa don ya bata dama ta sha shayin, ya lura yau wani tsoro-tsoron shi take ji, jiya kuwa har labarin karatunsu ta bashi. Yana tashi tayi maza ta kurbe shayin, saura kadan ta kware, ya fito a daidai lokacin da ta mike tana daukar handbag dinta, hannunsa rike da kwalbar gestid. Ya jijjiga ya zuba a murfin ya mika mata. Hannu na rawa ta karba daidai lokacin da Sultana ta fito daga daki cikin nata shirin na tafiya ofis. Wani kallon banza tayi musu sannan ta dauke kai ta wuce su fuuuu! Sa'ade na fadin "good morning aunty" ko kula ta bata yi ba. Salis ya soma horn don ta gane ya iso yana jiranta. Kallon Yarima tayi ta kasa-kasan ido tana jiran ya bata umarnin tafiya sai ta samu idanun sa a kanta suke. Da sauri ta kara sadda kanta. Ya ce "in kin dawo kin yi abinci ki sa da ni, Uche ya tafi garin su Maman sa ta rasu" kai kawai ta gyada tana mamaki a cikin ranta. Ita wacece da zata yi abincin da Uncle Yarima zai iya ci? Har suka isa makaranta tana kakabin abin cikin ranta, in matarsa ta ce ta yi mata shishshigi fa? In Uche baya nan meye amfanin matar sa? Koda yake wannan mai jan kunnen bata taba ganin ta tana dafa ko da ruwan zafi ba. Gara dai ta fara tambayar Fulani, kada ta yi abinda ba dai-dai ba. Data gama lectures din yau zata fito ne ta tadda Salis a parking lot ta kira Fulani tana cigaba da tafiya a gefen hanya, bayan sun gaisa tace "Fulani wai uncle Yarima ne yace yau in zan yi abinci na in sa da shi, sabida Uche yayi tafiya, ina tsoron kada in yi abinda ba shikenan ba" Fulani ta yi dan jimm! Kafin ta ce "meye gamin ki da Yariman da har kuke hira?" "Ba hira muke ba, dazu ne da safe da zan fito ya gaya mini" Fulani ta yi ajiyar zuciya ta ce "Sa'adatu! Ki kula da kan ki kin ji? Ba zan hana ki bashi abinci ba tunda Yayanki ne, amma bana son wata mu'amala mai zurfi a tsakanin ku bayan kasancewar shi guardian din ki. Maza duka ba abin yarda bane you have to be careful!" "To Fulani in ce bazan bayar ba mana? Wani abu ne?" "A'ah kar ki ce hakan, just cook and keep it on dining ki shige dakin ki, ban yarda da hira mai tsayi tsakanin ku ba" da haka suka yi sallama. Tana shiga gida ta ajiye littafanta tasa apron ta shiga kicin. Girki na nutsuwa ta yi, wanda ta inganta da kayan kamshi na gargajiya, lallausan tuwon semovita miyar danyar kubewa data ji ganda da busashshen kifi. Sannan ta markada abarba ta hada da zobo da pinapple flavour. Sai tayi farfesun kayan ciki mai rai da motsi. Sugar kadan ta sanya. Tana gamawa ta shirya masa a dining ta shige dakin ta ta kulle ta hau yin assignment din da aka bata yau daga laptop dinta. Yarima ya riga Sultana dawowa domin data tashi aiki Bar ta wuce ko don ta sauke bacin ran data kwana ta kuma wuni da shi, domin hakika tana shakkar sake shan giyar a gaban sa don yadda ta ga ya rikide mata jiya ta san komai zai iya faruwa da auren ta, one thing shine tana son Yarima bazata iya rabuwa da shi ba. Yana shigowa falon, falmaran din black Italian suit din jikin sa ya fara cirewa, yayi loosen tie din wuyan sa, kai tsaye dining ya nufa, a yunwace yake sosai, rabonsa da abinci tun tea din safe. Yana budewa ya ja kujera ya zauna ya soma ci cikin nutsuwa irin tasa, kunnen sa har wani irin motsi yake yi. "She's blessed in cooking!" Ya fada a hankali. Yana so ya kira ta, bai san in ta zo mai zai ce mata ba, he just want to check she is well, don haka yasa murya a tausashe ya kira ta. "Sa'adah!" Ta ji kiran nasa amma sai ta kasa yarda kiran nata yake yi, it sound so weird, don bai taba kiranta da wannan sunan ba, sannan amon muryar ya taimaka wajen sawa taji kiran kamar ba nata bane, don haka ta cigaba da aikin ta, hankalin ta ya rabu biyu, ya kan kirata Sa'adatu ne in full. Da ya ji shiru kai tsaye ya mike zuwa dakin nata, bayan ya wanke hannun sa a sink din dake manne a gefen dining din, ya tsane da karamin tawul. Kanta a sunkuye tana sarrafa na'ura mai kwakwalwar ta, riga da wando ne na pakistan a jikin ta ruwan goro turarre, ta yane mayafin su a kanta. Bata ji karar bude kofar sa ba sabida yadda hankalin ta yayi nisa kan abinda take yi. Sai sassanyan kamshin INVICTUS (By Paco Rabbanne) ya ziyarci hancin ta, ya kuma sauya atmosphere na dakin bakidaya wanda ke cakude da rabar iya kwandishan. Har gabanta Yarima ya zo ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu, a hankali Sa'ade ta dago ido sai idon ta cikin na Yarima.....wani abu mai karfi tamkar magnet ya manne idanun su wuri guda. Yarima Sageer ya tuna wannan kanwar sa ce a gaban sa (step-sister) kuma amanar mahaifin sa.... amma akwai wasu abubuwa cikin idanun yarinyar da ke da matukar tasiri akan sa, wadanda yake kasa controlling din su, wadanda bai san yadda zai fassara su ba. Watakila kyawun idanun ta ne ko hasken da ke cikin su? Juyawa ya yi ya bata baya don kaucewa kaifin idanun ta. Murya cunkushe ya ce "I just want to check on you. Have you eaten?" Kai ta gyada duk da ba kallon ta yake ba "zan ci in na gama" ta fada da sassanyan sauti. Taku daya, biyu yayi kamar zai fita, sai kuma ya juyo gabadayan sa. "Sa'adatu will you help me with your food har Uche ya dawo?" Ba tare da ta dago ba tana cigaba da typing din ta ta motsa dan bakin ta a hankali "sai na tambayi Fulani" yadda tayi maganar innocently ya burgeshi, ta nuna bata da wani ra'ayi kai tsaye sai na uwar ta. "Fulani bazata hana ki sammin abinci ba, nima uwata ce har fiye da ke" murmushi tayi wanda ya kara fiddo kyawun karan hancin ta. "Har fiye da ni? Ai daga ni sai Zarah ta haifa. Ka ga kuwa bata da kamar mu" ya dubeta straight cikin idon ta duk da ba shi take kallo ba "ni ta fara haifa kafin ta haife ku" murmushin ta ya zarce zuwa dariya "ai watakila ma ka girmeta Uncle Yarima" "sabida kin ganni da furfura?" "Ni ban gani ba, amma ko baka girme ta ba zakuyi age mates" ya juya ya fita yana murmushi cikin fadin "i look forward to my dinner Sa'adah. Na bar ki lafiya". Bin sa ta yi da kallo har ya fice, amma dakin ta bai bar INVICTUS perfume ba. Abinda ta ji jiya ya fado mata a rai. A fili ta ce "ba kama....". Sannan tayi ajiyar zuciya ta cigaba da aikin ta. Wannan baturiyar ta yi sa'ar zankadeden miji wanke hannu ka taba, amma don asara ko abinci bata bashi... tadin Sa'ade kenan ita da zuciyar ta. Ta kira Fulani ta gaya mata yadda sukai da Yarima, Fulani ta shiga dan rudani, ta ce "Sa'adatu ya ce da ke wani abu bayn wannan?" "Wallahi iya abinda ya fada kawai kenan, sai cewa kema uwar sa ce har fiye da ni" Fulani ta yi murmushi ta ce "bakomai ki dinga dafa masan in har kina gida, kinsan turawa basu daukarwa kansu irin wannan wahalar, shikuma watakila yana marmarin abincin mace ne". Da wannan Sa'ade ta cigaba da dafawa Yarima Sageer abinci har tsayin kwana uku, wanda ya haifar da wata 'yar kwarya-kwaryar shakuwa a tsakanin su, duk da Yarima ba sakar mata fuska yake ba itama kuma hakan, amma yana nuna concern akan al'amarin karatun ta. Da tabbatar da ta ci abinci akan lokaci don in tasa kwamfuta a gaba mantawa take da cikin ta. Aisha Sultana bata san me suke ciki ba, ta dai lura yanzu tana bashi abincin ta tun tafiyar Uche, hakan kuma bai dadata da kasa ba don ta san ita bazata iya ba. Ga yarinyar da shegen zafin nama cikin 'yan mintuna ta sarrafa abinci mai wahala. Ko suna shiri a tsakanin su ko basa yi ita dai Sa'ade bata sani ba. Yau da Sultana ta dawo hatta firjin kicin sai da ta cika shi taf da kwalaben giya bana dakin ta kadai ba. Sabida za'a shiga weekend bazata samu zuwa bar ba ta san Yarima bai barin ta fita koina a karshen mako. Yarima ya fito falo misalin karfe na goma na safe yayi wanka yayi fresh da shi cikin kananan kaya DKNY ash colour, tsammani zakayi saurayi ne dan shekaru ashirin da biyar ba magidancin dake neman talatin da biyar ba. Maganar da maimartaba yayi masa a daren jiya a waya da ita ya wayi gari tana cin zuciyar sa, ya kuma yanke tunkarar Sultana da maganar. "Kai da matar ka sai yaushe zaku kawo min jika? Ko sai na mutu ban ga kwan ka a duniya ba? Aure shekara biyar ana neman ta shidda babu ko labarin bari a gidan ka Yarima? A matsayin ka na mai jiran gado?" Wannan magana ce da maimartaba bai taba yi masa ba sai wannan lokacin, don haka sai yaji tamkar an yi masa tuni ne akan abinda ya manta. Sultana ta fito sanye cikin wando 3 quater da yar karamar rigar shan iska armless ta nemi waje ta zauna a nesa da shi duk don ta nuna masa har yanzu fushi take. Ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a makogaro sakamakon kallon zara-zaran kafafun ta da suka sha adon jan farce purple abinda ya hanata sawa sabida ya gaya mata baya sallah amma ta ki daina shafawa. "Ki shirya mu tafi asibiti yanzu, a bincika a ga shin ni da ke waye baya haihuwa?" Ba karamin duka maganarsa ta yiwa Aisha -Sultana ba, amma bata bari fuskarta ta nuna ba. Mikewa yayi tareda daukar mukullin mota yayi waje yace yana jiran ta a mota. Ta bata lokaci kafin ta fito cikin shigar atampa hiterget, suka tafi zuwa Nizamiye Hospital inda suke da file. Da tana da yadda zata hana zuwa asibitinnan da ta yi, amma yadda ta ga fuskar Yarima ta san babu wani excuse da zai karba, fargabar dake ranta kadai ta isheta don bata taba zaton watarana Yarima zai taba sha'awar haihuwa ba. Ita kuma duk son da take masa bata shirya haihuwa da bakar fata ba, ta aure shi ne domin ya dinga satisfying soyayyar da take masa ba don su tara 'ya 'ya ba. A gaban sa likita ya duba ta, tayi fuska kamar bata san abinda ta aikata ba, ya kuma tabbatarwa Yarima Sageer babu mahaifa ma a jikin matar sa, an cire ta gabadaya. Yarima ya daga kai yana kallon Sultana wadda ta sunkuyar da kai, girar idon sa har wani irin tattarewa take yi sabida bacin rai, har suka zo gida bai iya ya ce mata komai ba. Suna shigowa gida kowa ya nufi dakin sa rai a bace. Har zai wuce daki yayi tozali da abincin da Sa'ade ta shirya masa akan dining, ya kuma jiyo kamar jan majina irin na kuka da sheshsheka daga dakin nata. Sai ya ji bazai iya wucewa ba tareda ya dubata ba, haka yau bacin rai bazai bar shi ya iya cin abincin ta ba. Knocking yayi mata har sau biyu, daga ciki ta amsa cikin dusashshiyar muryar data ci kuka. "Waye anan?" "Sunana Sagir" Murmushi tayi sabida yadda ya fadi sunan cikin lallashi? Ta taso ta bude kofar, tareda dan ja da baya don ta bashi damar shigowa. Cikin idanunta ya kalla, wadanda suka kada zuwa brown, "kukan me kike yi?" Akwai alamun hankalin sa ya tashi da ganin halin da take ciki, ai kamar jira take ya tambaya sai ta idasa rushewa da kuka. Da kyar Yarima ya samu tayi shiru, sannan ta rufe ido ta gaya masa ta fadi kwas din Physiology shine dalilin kukan ta. Ajiyar zuciya ta kwacewa Yarima, ya dauka wani abu ne terrible. Kai Sa'adatu 'yar maman ta. "Do you have issue with some of your courses baki taba gaya mun ba?" "Ai Fulani ce ta ce kada mu dinga hira" dariya ta kama shi sabida wautar ta data fito fili a yayin maganar. Ya tako zuwa gaban ta, gab da ita ya tsaya duk invictus ya mamaye ta. She can feels him breathing softly.... "gaya min abinda yasa Fulani ta ce kada mu dinga hira" gabadaya ta daburce ta kuma ga wautar kanta data fada masa hakan. Sannan bai bada space a tsakanin su wanda zata yi masa musu ba. Da sauri ta ja baya, amma sai taji bayan ta ya hadu da kofar dakin "umh...umh nima ban sani ba Uncle Sageer" "ni na sani, in kin amince in gaya miki....." da sauri Sa'ade ta girgiza kai "don Allah kada ka gaya min ni ba son sani nake ba" ta fada, her voice trembling. Kai gabadaya tsokar zuciyar ta ma rawa take sabida closeness din dake tsakanin su da kamshin Paco Rabbanne da yake hargitsa ta. A hankali ya ja da baya yana murmushi yace "ki ce ma Fulani, ai mutum baya cutar da abinda yake so ya zama nasa gabadaya. Ta bar ki kiyi hira da Yayanki. Fi-amanallah, har zuwa lokacin da zai dau ajiyar da ya bata". Bata gane zaurancen sa ba amma ta ce "toh" da sauri don ta samu ya bar ta haka, tayi jinyar sababbin abubuwan da ke ziyartar ta, a zuciya, ruhi da gangar jiki gabadaya. "Gobe zamu fara karatu ni da ke, physiology will never fail you again. Na bar ki lafiya". Har ya fita bata san meyasa ta kasa dauke ido akan sa ba, al'amuran sa na yau masu ban mamaki ne data kasa gane inda yasa gaba. A hankali tabi lafiyar gadon ta, ta lumshe ido tana tariyo maganganun Yarima Sageer daya bayan daya. In wani yace mata yana magana haka zata karyata. To me ya canza shi haka? Me ya kawo canjin? Sai dai kuma ga mamakin ta ta kasa kiran Fulani ta gaya mata abinda yace din duk da bata iya boye mata komai. Amma wannan karon sai ta ji ta kasa. Kamar tana jin kunya.... Kamar yadda barci ma ya gagare ta. Sai scenes din Uncle Yareema ke mata gifcin gizon makauniya. **** Washegari da safe basu hadu ba, kowa ya kama gaban sa, cikin daren an tafka rigima tsakanin Yarima da maidakin sa Aisha-Sultana, yace tunda ta yaudareshi ta cire mahaifarta ba da sanin sa ba tasa a ranta ta bashi lasisin auren wadda zata haifa masa 'ya'ya. Sultana ta dauki kalaman nasa a matsayin abinda ake kira 'shifcin gizo', watakila ya fada ne out of frustration na ta cire mahaifa, amma in ma mafarki yake na zai hada ta da wata diya mace a duniya su yi sharing din sa ya dade bai farka ba. Lokuta da dama in a buge take bata mayar masa da magana, tana bin shi da ido ne kawai. Wadanda basa ko buduwa sosai. To yau ma hakan ta bishi da rinannun idanun ta har ya shige turakar sa. Zaune take akan irin kujerun sumintin nan na cikin makaranta karkashin wata bishiyar lemon tsami mai duhun ganyayyaki, fitowarta kenan daga lacca ta zauna tana kara nazarin abinda tayi jotting cikin littafinta. Sallama ta ji a kanta da wata lallausar murya kamar ba ta namiji ba, da sauri ta dago ta kalli wanda ke tsaye a kanta, kallo daya tayi masa ta gane shi, coursemate dinta ne amma bata san sunan shi ba. Ta amsa sallamar sa tare da maida kanta kan littafin ta, yaron ya cika kyau kamar aljani, da ganin sa ruwa biyu ne ko kuma bafillace. Cikin lallausar turancin sa ya ce "Ma'am, ki taimaka min da laccar da kika rubuta inyi photocopying, i missed alot from it" Sa'ade ta zumburo baki "bana bada aron littafi na" murmushi yayi ba tareda ya ji haushin abinda tace ba, kawai sai ya sa hannu ya dau littafin daga cinyarta ya juya ya soma tafiya. Sa'ade ta mike da sauri ta bi bayan shi tana fadin "Malam...malam" "sunana Mr. Sa'id ba malam ba" "to ni ina ruwa na da sunan ka? Ka bani littafi na" yayi kamar bai ji ta ba, ya nufi wani shago da suke photocopying, Sa'ade bata yi kasa a gwiwa ba wajen binsa tana ta mita "haka kawai sai ka daukar mun abu ba izni babu yardata? Don baka san wanene Yayana a jami'ar nan ba wallahi sai na sa an baka carry-over" bai san sanda dariya ta kubuce masa ba data fiddo fararen hakoransa, yarinyar akwai wauta kamar diyar fari ga magana cikin shagwaba. Ya hadiye dariyarsa ya mika wa mai hoton takarda littafin ya fada masa yayi masa photocopy sannan ya juyo ya dubeta da wani irin kallo. "A'a spill-over zaki sa a bani ba carry-over ba. Sa'adatu Hashim I loved to be your friend" zaro ido tayi na mamakin inda ya san sunan ta, sai ta tuna a jikin littafin ya gani, ta kyabe baki tace. "Allah ya sawake in yi abota da namiji, matan ma sun ishe ni kallo ne balle kai sungumemen kato?" Yayi dariya yace "ko sai na yi kamun kafa da Yayanki mai jami'a?" Wani kallo tayi masa na sannu sarkin tsautsayi, sannan ta juya tana cewa. "In ka so ka kwada littafin ka cinye na bar maka". Ta kama hanyar komawa hall. Tana zama laccara na shigowa suka fara karatu, sai ga wanda ya kira kansa Mr. Sa'idu ya zo ya zauna a gefenta, a hankali ya ajiye mata littafin ta yana murmushi, a ranta tace sai shegen murmushi kamar gonar auduga, jan aji da class sai Uncle Yariman Askira, kafin yayi murmushi ma za'a dade. Amma shi wannan sai faman murmushi yake kamar mace. Wata zuciyar tace Sa'ade! Me kike cewa? Da sauri ta ce "ba abinda nace kenan ba, nufi na Uncle Yarima yafi kowa jan aji a duniya" ta kara ankara da kalar tunanin da take yi tayi saurin toshe bakin ta tare da dafe kanta tana fadin "Yaa Ilaahy! Na tuba ya Allah!" Bata san cewa a fili ta fada ba. Kowa a ajin sai da ya juyo ya dube ta, kasancewar an yi tsit ne ana sauraron malamin. Tayi maza ta sunkuyar da kanta tana fadin meke damu na ne? Ni Sa'aden Tsanyawa? Ba komai bane sai tunanin Yarima Sageer Yusuf Askira. Wanda ya dusar da hasken sauran maza daga idanun ta, ya dasa wani dan kankanin tsiro a zuciyarta daga lokacin da bazata iya tantancewa ba. Sa'id bai bar Sa'ade ba, tun daga ranar ya like mata, inda duk tasa kafa cikin NTNU nan yake mayar da tasa. Ba da sanin ta ba ma ya bi bayansu a mota itada Salis bayan sun tashi karatun ranar ya ga gidansu cikin quaters ne, nan ya tabbatar 'yar wani babban Dr. Din ce kamar yadda tayi masa barazana. Kodayake ta ce Yayanta. Tun tana basar da shi amma yawan hakurin sa da yawan murmushin sa yasa dole ta soma kula shi suke harkar karatun su tare. Dama tana neman abokin karatu kuma ajin nasu maza sunfi yawa, tsirarun matan dake ajin kabilu ne. Tun ranar da Yarima yace zai fara koya mata karatu kuma tafiya ta kama shi zuwa Lagos (Lagos State University) zai halarci annual conference. Basu kara haduwa ba sai yau da ya dawo, kuma Uche ma ya dawo daga Osun, tayi masa ta'aziyar mahaifiyar sa ta shige dakin ta a ranta tana fadin "shikenan na huta da girkau, wahalar da ba'a ce min an gode". Uche yana tsaye yana girki ta shigo kitchen din, ruwa take so ta sha, na firjin dakin ta duk sun kare. Ta bude firij din kitchen din tana fadin "Uche what are you cooking for your Oga?" Uche ya ce "Basmati Rice and salad nake yi masa, ban sani ba ko zai so" tace "kada kasa spices din can da kake using, kayi amfani da rosemary, coriander da oregano, basu da karfi, he really likes their aroma". Uche yayi godiya da gyaran data yi masa. Ta bude firji babu ruwan gora sai wasu manyan kwalabe, an cire takardun jiki babu rubutun komai, Uche ya bata baya yana yankan albasa bai lura da abinda take ba, ta dauka tana juyawa a hannun ta sannan ta bincire murfin zata kai bakin ta. Sai ji tayi an yi wurgi da kwalbar daga hannun ta, ita kanta saura kadan ta fadi sabida yadda Yarima ya angije hannun ta da karfi. Kwalbar ta fashe, ruwan ciki ya malala a kasa, wani ruwa mai wani irin tsami da hamami, Yarima bai tsaya ba ya finciki hannun ta suka bar kitchen din yana ce da Uche ya gyara wurin ya fitarda duka whisky daga firinjin ya zuba a bola. Bai tsaya da ita koina ba sai a falo ya jefata jikin Aisha-Sultana, wadda ke zaune tana danna ipad din ta. Ta dago a fusace sai idon ta cikin na Yarima, yadda ta ga idanun sa kamar na mayunwacin zaki ya kada mata 'ya'yan hanji. Muryarsa har sarkewa take ya ce "Sultana! Ban hanaki shigomin da giya gida ba? Ko kin san saura kadan yarinyar nan ta sha giyar ki? Me kike so in cewa iyayenta da ace ta sha da suka damka min amanar ta? Kuma har a firinjin kichin sabida kin raina ni?" Sultana tayi mici-mici da brownish idanunta, "cewa nake mun yi da kai sai ka daina shiga gidan Ziyad yin zina nima zan daina shan beer?" Da sauri Yarima ya nunawa Sa'ade hanya yace ta bace a wurin kafin ya kifta idon sa. Ai kuwa kafin ya kifta din ta kai kofar dakin ta tana jin karar marin da ya kaiwa Sultana. Ta dafe kunci ta ce "you slapped me?" Bai tsaya a wurin ba ya danna kai dakin ta ya watso su duk daga firinjin ta, ya kwalawa Uche wani mahaukacin kira, ya fito da gudu daga kitchen yana amsawa, ya nuna masa dakin Sultana yace ya kwashe whisky ya je ya zubar gabadaya. Yau Sa'ade ta ga tashin hankali don har dare ya tsala tana jiyo fadan Yarima da matar sa har tissue tasa ta toshe kunnuwan ta tana kuka, marin da ya yiwa Sultana ya daga mata hankali ba kadan ba, ita bata san giya bace kuma ba sha zata yi ba sunsunawa zata yi taji menene? Sai Allah ya kawo shi. Tana so ta kira Fulani ta gaya mata ta tuna abinda Fulani ta gaya mata wancan karon cewa maimartaba ya ji wayar su, har yace zai dau mataki akan Yarima. Ina ga in ya ji ana shan giya kamar ruwa a gidan sa? Wa'iyazu billah. Ko isashshen barci bata samu ba yau, don haka washegari ko karin kumallo bata tsaya yi ba ta riga kowa ficewa a gidan ko Salis bata jira ba, duk nisan dake tsakanin gidan su da cikin makaranta ta gwammace ta taka a kasa data kara ganin fuskar Yarima mai zuwa yin zina ko matarsa mai shan giya kamar yadda suke cewa. Sa'idu ya ganta duk a birkice, ya bata wuri ta zauna, "hi friendy, me ya sameki haka?" Kawai sai ta saka kuka tace "don Allah ka san inda ake shiga motar Askira?" Ya ce "ni ko sunan garin ban taba ji ba" ta sake rushewa da kuka, yayi-yayi ta gaya masa abinda aka yi mata ta ki, har malamin su ya shigo suka fara darasi, dole ta tsagaita da kukan ta bashi hankalin ta, don inda abinda ta ki jini a duniya to carryover ne. Da wuri suka gama lacca yau, tace da Sa'idu gida zata koma, da in sun gama lacca da wuri maimakon su tafi gida lab suke zuwa suyi research da ya shafi karatun su, yace ina direban ta tace ba shi ya kawo ta ba da kafarta ta taho, kuma ta baro wayarta gida balle ta kira shi ta gaya masa inda take. Sa'idu yace "do me a favour to drop you at home, tunda naji kina zancen zuwa Askira bazan barki ki tafi ke kadai ba". Ya dage da nacin sai ya kaita, ta san Sa'idu zuwa yanzu yaron kirki ne mai kokari da son taimakon ta, don haka ta amince ta shiga motar sa kirar civic suka karasa gida. Sa'idu na yin parking daidai Yarima ya zura mukulli jikin motar sa zai bude, yayi mugun hadewa cikin danyar shaddah ruwan madara samfurin excelcior (London). Wadda ta sha aiki da zare ruwan kasa irin na sarauta. Gilashin idonsa ya zare a hankali don tabbatar da Sa'ade ce yake gani a motar wani ko wacece? Fasa bude motar yayi ya kafa musu manyan lumsassun idon sa har Sa'idu ya kashe motar Sa'ade ta bude ta fito tana masa godiya. Sa'idu ya so ya fito ya gaida Yayan Sa'ade amma yadda yaga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas dole ya kama kansa, ya ja motar sa da gudu ya bar harabar gidan don kwarjinin Yarima da haibar sa da cikar kamalar sa kadai ya tabbatar masa ba karamin mutum bane, kada yaje ya gane shi ma wani abu ya samu karatun sa, duk da ya so ya fito ya gaisheshi ya gaya masa taimaka mata kawai yayi shi dan ajin su ne, amma ina! Tsoro ya hana shi. Makarantar ma bai koma ba ya gudu gidan su a unguwar Maitama. Ta gaban sa Sa'ade ta zo ta wuce amma ga mamakin sa ko kallon sa bata yi ba ta wuce ciki. Mamaki ya kusan kayar da shi, bin bayan ta yayi cikin takunsa na kasaita. Tana saka kafa a dakinta ta turo kofar yasa hannu ya dafe kofar. Sai ta sakar masa, ta juya ciki ta na kokarin sauke jakar dake goye a bayan ta wadda ta lamushe dukkan komatsanta harda laptop. Muryar Yarima har tsakar kanta, babu alamun wasa ko kadan a tattare da shi. Zata iya rantsewa bata taba jin sa yayi magana da irin wannan muryar ba. So furious, angry and jeolous.....! "Sa'adatu who is this boy?" Bata san yaya aka yi ba, bata san wa ya kitsa mata ba, kawai sai ta samu bakin ta da cewa "saurayi na ne" bayan ita kanta bata gama sanin ma'anar kalmar saurayin ba. Kawai ta san ta tsani Uncle Yarima ne yanzu, tunda dukan matar sa yake yi, in ta sha giya ai shi ya bata dama. Idanunsa sun rikide sun juye zuwa wani yanayi da bazata iya fassarawa ba. "Look into my eyes...and tell me he's your boy friend" kokarin ja da baya take. Data rasa mafita, ga zuciyarta na wani irin azalzala da mixed feelings; haushi, tsana, da zazzafar soyayyah duka a lokaci daya, kawai sai ta saka kuka. "Ni dai a maida ni Askira, wallahi na gama zaman gidan ku" Yarima ya ja da baya sabida da karfi ta fasa kukan. "Da mu kayi miki mene?" Ya fada yana hararar ta, in wani yaji irin kukan da ta fasa tsammani zai yi wani abun yayi mata. Ba ta ce komai ba sai cigaba da kukanta. Da zata iya da ta ce dashi sabida dukkanku fasikai ne marasa tsoron Allah. Amma ta san ko giyar wake tasha bazata iya dubar tsabar idon Dr. Sageer ta gaya masa haka ba. Apart from all these she respects him so much. Yana da wata irin kima a idanun ta da bata san yaushe ta samu matsugunni a zuciyarta ba. Tafi danganta hakan da kulawar sa da kyautatawar sa gareta. Yarima ya dubeta a fusace, ya rasa yanayin da yake ciki yau, amma ya tabbata bai taba ganin abinda ya bata masa rai a duniya irin Sa'adatu da saurayin ta a mota ba, yaga yadda hawaye ke gudu akan kundukukinta kai ka ce wani mugun abin aka yi mata. Ya nunata da dan yatsa ba tare da ya bari hawayen da take zubarwa sun yi tasiri akan sa ba "Yau ta zama rana ta karshe da zai kuma tako min gida, ba shi kadai ba kowanne rubabben saurayin ki ma, in ba haka ba in gayawa Fulani da maimartaba su cireki a makarantar su yi miki aure tunda hakan kike so". Sa'ade ta zaro ido abin dariya abin tausayi "Uncle Yarima wasa nake ba saurayi na bane ba, wallahi, dan ajin mu ne" ya juya ya fice bai saurareta ba, damuwar duniya Sa'adatu ta shigeta, ba abinda take tsoro, taki jini take kuma gudu a rayuwar ta irin AURE! Saida yayi kwana uku bai kara kula ta ba, bai kara nemanta ba, he's really suffering a ruhi da zuciyar sa akan ganin Sa'ade da saurayi akan dalilin da bai sani ba. A haka su Sa'ade suka fara jarrabawar karshen zango babu shiri ko kankani tsakanin ta da Yayan nata Yarima. Ranar da sukayi takardar karshe ta kira Fulani ta gaya mata, Fulani ta gayawa maimartaba, shikuma ya kira Yarima yace yasa direba ya kawo Sa'ade gida tayi hutu. Yarima yace dama shima zai shigo Askiran jibi, zai taho da ita da kansa. Sa'adatu na kwance a gadon ta tana karanta mujallar turanci ta 'Thrills and Boom' taji knocking a kofar ta. Ta gyara kwanciyarta da dankwalin ta daya cire sannan tace "yes". Yarima ya sanyo kai a dakin, t/shirt ce a jikin sa fara kal an rubuta Marks&Spencer da bakin rubutu, sai bakin wandon jeans mai kauri. Hararar ta Yarima yayi sannan ya jingina da kofar, a hankali ya ce. "Sabida na hanaki kula samari, shine kika daina gaishe ni ko?" Sa'ade ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, amma sosai taji kunya, wai wa yace ma Uncle Yarima Sa'idu saurayin ta ne? Bata cika son magana tayi tsayi a tsakanin su ba, karatun ma da yace zai koya mata bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi saida ta san yadda tayi ta kaucewa hakan ta roki Sa'idu ya koya mata lokacin jarrabawar kwas din, yana da effect mai karfi kanta wanda shi bai sani ba itama bata sani ba, abinda ta sani kawai shine bata son mu'amala mai zurfi a tsakanin su. "Ki shirya gobe da asubah zamu kama hanyar Askira, maimartaba yace a kai ki kiyi hutu" bata san lokacin da ta dago zaune ba tana ta faman blushing, bai tsaya kallon ta ba yasa kai ya fita. Tun a daren ta hada duk abinda take bukatar tafiya da shi. Baccin ta ma ragagge ne sabida doki. Tayi kewar Fulani da Zarah.....Shi kansa Askirama ta yi kewarsa. Washegari data yi sallahr asubah bata koma barci ba, wanka tayi, tayi ssaukar shiga ta bakar abaya mai santsi da adon stones sosai a jikin ta. Bata shafa komai a fuskarta ba sai wet-lips ta kuma fesa sassanyan turare. Ta zauna bakin gadonta da trolley dinta a gaba tana jiran Yarima. Bai fito ba sai wajen karfe shidda na safe, kallo daya tayi masa da ya murda kofar dakin ya shigo bayan tayi masa izni, taji bazata iya jure kallon ba, kwayar idanunta ta zamo mai rauni sabida yau ya fito Prince dinsa. Ta taba ganin maimartaba da irin kayan jikin sa, yakan saka kayan in zai zauna cikin iyalinsa, kaya ne kufta da wando na sarautar Askira wadanda basu cika nauyi ba. Amma kuma sun sha aikin zare na silver da hula zanna bukar a kansa. Kasancewar kusan kullum cikin shigar suit take ganin sa yau sai ya zamo mata wani daban, classique and elegant kai kace Askirama ne ya zama yaro. "Lets go!" Inji Yarima, ganin ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bayan a badini kirjinta ne ke wani irin harbawa da sabbabin emotions da bata san daga ina suke fitowa daga karkashin zuciyarta ba. Hannu yasa ya ja trolley dinta. Ya fita ta bishi a baya bayan ta dau handbag dinta tana mamaki a cikin ranta; Yarima ya dau kayanta da kansa. Sai taji har tsigar jikin ta na tashi da wani irin feelings mai sanyi a zuciyar ta. Hakan kuma bai janye bakin fentin data ke kallon shi dashi ba. A falo suka ci karo da Aisha - Sultana, kayan barci ne a jikin ta, ta tsaya jingine da kofar dakin ta tana kallon su, ta gabanta Yarima ya wuce dauke da jakar Sa'ade, Sa'aden na gaisheta da safiya, wata harara ta zabga mata ba tareda ta amsa ba. "Mun tafi Askira Aunty, sai na dawo" jin bata amsa mata ba ta wuce ta, ta tadda Yarima a mota, Salis ne ya ja su. Ta dauka a motar zasu tafi har Askira amma sai ta gansu a filin jirgin saman Abuja. For the first time Sa'ade a jirgi, in ka gansu itada Yarima tsammani zakayi sababbin couples ne sabon aure duk da babu hira a tsakanin su. A cikin jirgin Azman ne mai zuwa Maiduguri a first-class seats, ga kujerar ta ga ta Yarima, Lokacin da waitress ta kawo abin motsa baki kasa cin komai tayi sabida uneasiness din da take ciki na zama a gefen Yarima. Ga kamshin Paco Rabbanne dinsa dake kara hargitsa ta. Shikuwa yayi amfani da wannan damar wajen kare mata kallo, kallon da bai taba yi mata ba, har ya zarta ka'idar muslunci domin kallo ne na kurullah. A zuciyar sa ba abinda bai fada ba, wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani, a zahirin sa kamar ba ita yake kallo ba. Bai fi minti goma ya rage suyi landing ba Sa'adatu ta soma jin amai na taso mata sakamakon wani Igbo da ya gifta ta gabanta yana warin qashi irin na maza, ai kuwa tana yunkurawa domin ta tashi sai amai ya kelayo a jikin Yarima Sageer, basu da yawa a first class seats din don haka hankalin sauran mutanen ya dawo gare su, Sa'ade ta hau zazzare ido cike da tsoro bakin ta na rawa tana son furta ban hakuri kalaman sun ki fitowa. Amma ga mamakin ta ko a fuska bai nuna kyama ba, wani irin kallo yayi mata yace "sai kin goge min shi tas!" Tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka don damuwar abinda tayi masa "...don Allah kayi hakuri Uncle Yarima....ban yi da sani ba" a ginshire ya ce "na ce kin yi da sani ne?" "To kayi hakuri don Allah bazan iya goge maka ba" suna wannan jayayyar sai ga waitress tazo don ta gyara wajen tana ta yiwa Sa'ade sannu don a zaton ta ciki gareta. Kasancewar kayan rubi biyu ne ta saman kamar jabba take mara nauyi akwai jamfa daga ciki yasa ya cire ta saman. Sa'ade tayi maza ta dauko turarenta a jakarta ta mika masa. Karba yayi yana jujjuya shi a hannun sa 'sapphire' itama Fulani ce ta bata, a tunanin ta zai bukaci turare tunda tayi masa kayan karni. "Me zan yi da turaren mata?" "Ka fesa saboda karni" Ta fada kamar zata saki kuka don damuwa, ta rasa da bakin da zata bashi hakuri. Mika mata turarenta yayi yana dubanta ta kasan ido yace a hankali "idan matata taji kamshin turaren ki a jiki na what do you expect?" Sa'ade ta runtse ido tace "ni fa ban bayar da wata manufa ba, don ya kashe smell din aman ne" "idan kuma ni son smell din aman nake fa?" Kallon sa tayi da budaddun idanuwa.... mamakin ta ya bayyana karara cikin idanun ta Ba jimawa jirgin su yayi landing a Maiduguri. Motocin ASKIRA EMIRATE har guda biyar manya da kanana suka zo tafiya dasu, da fadawa da dogarai cikin uniform din su na bayin masarautar. Mota guda suka yi amfani amma da yake babba ce sosai kirar (4matic) mai kujeru takwas ba kujera daya suka zauna ba, Sa'ade na daga kujerar baya Yarima na owner side. Suka dauki hanya. Ji take kamar tayi fiffike ta ganta a dakin mahaifiyar ta. Har suka zo Askira barci take wanda a jirgi takuruwar zama kusa da Yarima bai barta ta yi ba. Ana bude musu motar ta fice da azama bata jira fitowar Yarima ba, wanda tun shigowar su Askira taga kamar komai nasa ya canza, simplicity din da annurin ya tafi, ya juye ya rikide ya zama cikakken Prince din sa. Da gudu ta karasa unguwar Fulani Bilkisu ko jakarta bata dauko ba sai biyota aka yi da ita. Da Zarah ta fara tozali, suka ruga da gudu suka makalkale juna. Zarah na tambayar me ta taho mata dashi daga Abuja? Tace "everything, sweetheart". Fulani ta fito daga shigifarta cikin wata irin kyakkyawar shiga ta alfarma, ta tsaya daga bakin kofa tana kallon su da murmushi, kamshin ta ne yasa Sa'ade ta lura da ita, ta ajiye Zarah ta kwasa da gudu ta rungume Fulani, kawai kuma sai ta fara hawaye. Fulani tace "yau nake ganin sakarci, me aka yi na kuka? Ko suna miki wani abu ne?" Ta girgiza kai "babu komai, kukan farin cikin sake ganin ki nake yi, watanni shidda ba kwana shidda ba". Fulani ta hau tureta daga jikin ta jin takun ana shigowa, Fanna ce ta taho dauke da abinci a makeken tray ta ajiye a dining. Tana murmushi tace da Fulani "Allah ya taimakeki yau tare na hada muku abinci da uwar daki na, don Allah ku ci tare" Sa'ade ta sa dariya cikin dadi tana kallon uwartata. Fulani ta gimtse fuska tace "Fanna yaushe na koma abokiyar wasan ki?" Fanna tayi nara-narai da ido tana murmushi tace "Allah ya ja da ranki Alfarma ce muke nema, wata shidda cif bamu ganki ba". Babu wanda ya gayawa Fanna Sa'ade 'yar Fulani ce ta cikin ta amma ta dade da fahimtar hakan. Yadda aka yi ta samu 'yar ne bata sani ba. Tana gama fadin hakan ta juya ta fita, Sa'ade tayi wata irin super ta dane jikin Fulani saura kadan ta kada ita, Zarah sai dariya take yi. A haka suka ci abincin cike da begen juna su uku. Tana gamawa tayi wanka ta sauya kayan jikin ta zuwa marasa nauyi ta dauko waya ta kira Sa'id. Yace "Sa'adatu, yaya kwana biyu kuma ya hutu? Ina fatan kina bitar Physiology textbook dinnan?" Sa'ade tace "ni yanzu ina garin mu bana Abuja ka kyale ni in huta da wani karatu, ina tare da uwata rabin raina" Sa'id yayi murmushi yace "sai na zo Askira kawo gaisuwar neman iri" Sa'ade tayi tsaki tace "Allah ya sawwake inyi saurayi da classmate dina, wani dan yaro da kai, ni dinnan da kake gani matar manya ce inji Fanna" dariya sosai Sa'id yayi, ya ce "me yafi ka auri yaro sabon jini kamar ka? Ya sa ka dariya kaima ka saka shi? In yaga dama ya goyaki ya yi ta zagaye gida dake?" Sai ganin Fulani tayi tsaye a kanta. Ba karamin firgita tayi ba ganin expression na fuskarta. Tayi maza ta kashe wayar ba tareda ta yiwa Sa'idu sallama ba. Tana zazzare ido na rashin gaskiya. "Keda wa kike waya?" Fulani ta tambaya fuskarta babu annuri. A tsorace tace "dan ajin mu ne kawai" Fulani ta juya bata ce komai ba. Saidai kwarai ta so ta magantu din, but she don't want to be too strict har Sa'ade ta koyi boye mata sirrikan ta. Saida ta kai bakin kofa sannan tace mata ta tafi wajen Askirama kada ta nemeta..... **** Rami ne mai tsananin zurfi, wanda har baya iya hango karshen sa sabida zurfin sa, ya leka ciki sabida ya ji kamar muryar Yarima yana kuka yana neman taimako. Bai ga ta inda ta bullo ba kawai ya ganta ne a bakin ramin, tana rike da igiya mai tsayi, tana zuwa bakin ramin ta jefa masa igiyar tace "Kama ka fito da iznin Ubangiji". Bai ga fuskarta ba sabida ta sunkuya ne akan ramin, gashin kanta ya sakko ya rufe fuskar tata gabadaya, saida tayi magana sannan ya shaida muryar ta. Ba jimawa ya ga ta kama igiyar nan tana janyo wanda ke ciki har ta fiddo shi tsaf, yana fitowa suka rungume juna suna hawaye. A lokacin ne ya samu damar ganin fuskokin su gabadaya; Sa'adatu ce da dan lelen sa YARIMA SAGEER. Tamkar an warware masa dukkan baccin da ke kansa ya farka firgigit misalin karfe biyu na sulusin dare, lokaci ne da aka tabbatar mafarki yana iya zama reality. To ko me wannan mafarkin da yayi yake nufi? Sa'adatu as saviour of Sageer? Ba don babu kyau bayyana mafarki ga wani ba, da ya nemi Limamin Askira ya gaya masa mafarkin da yayi. Duk da haka a nasa hankalin, ya fahimci tamkar wani hannun ka mai sanda ne Ubangiji yayi masa, mai nufin akwai wani babban al'amari tsakanin Sageer da Sa'adatu kamar yadda ya so hakan ta kasance a baya. Bai san sanda ya sa hannu ya soma tashin Fulani Bilkisu wadda ke barci sadidan a gefen sa. Ta tashi tana yamutsa fuska tana mutstsikar ido. Ya ce "Bilkisu bude idon ki ki dube ni". A yanayin da Askirama yayi maganar cikin rauni yasa ta dole watstsakewa. "Lafiya Askirama? Lafiya gatan mara gata? Lafiya giwan ASKIRA?" Ta fada cikin tausasa murya, mai Askira ya kama hannayenta duka biyu ya rike cikin nasa. "Alfarma nake nema wajen ki irin wadda ban taba nema ba...... ki bani Sa'adatu in aurawa Yarima a gobe". Fulani Bilkisu ta ji maganar ne tamkar saukar aradu a kunnen ta, kwakwalwarta ta kasa digesting maganar yadda ya kamata sabida wani abu ne da bata tsammani ba a rayuwar ta. Bata kin Yarima don tamkar dan cikin ta ta dauke shi. To amma neman matan da ake cewa yana yi fa tun bai san kansa ba har girman sa har ita Sa'adatun ma ta shaida da bakin ta? Shin Sa'ade ta cancanci hada rayuwa da wayayyen mutum irin Yarima? Ina Sa'aden ta ina hada kishi da Aisha-Sultana? Don haka Fulani ta rasa amsar da zata baiwa mijinta mai Askira, sai bin shi da ido, a zaton ta makuwa yayi cikin barcin sa. Amma da ya girgiza kafadun ta ya sake maimaitawa sai ta tabbatarwa kanta mai Askira yana nufin abinda yake fada ne. "Kin amince ko Bilkisu? Hankalina bazai kara kwanciya ba batare da na tabbatar da sunnah tsakanin Sageer da Sa'adatu ba, jikina na bani itace zata zamo maganin dukkan matsalolin sa, don ban taba yin mafarkin da bai zama gaskiya ba". Ya kwashe mafarkin da yayi duka yanzun nan ya fada mata. Fulani Bilkisu ta rasa abinda zata ce, she's mute for some minutes, tana mai tariyo tarin alkhairin Sarki Yusufu ga Sa'ade tun zuwanta Askira, shin bazata manta da komi ba ta bisu da addu'a ta zama mai rama khairan da khairan? Ta lumshe idon ta cikin na Askirama, wanda ke tabbatar masa da ta karbi alfarmar sa, bata da abin cewa. Itada Sa'adatu duka abin ikon sa ne sai abinda ya hukunta a gare su. **** Koda ta koma dakin ta a washegari bata ce da Sa'adatu komai ba, cikin dimuwa da zullumi take, sabida Mai Askira ya ce kafin su koma hutun nan da suka zo sai da igiyar aure a tsakanin su. Sa'ade ta lura a wunin ranar bakidaya Fulani ta zama sukuku! Bata umh bata umh umh. Abinci wannan a wunin yau bata ci shi ba kuma tace ba azumi take ba. Ta lura tunda ta dawo daga turakar maigidanta take cikin wannan halin, to ko ita da Mai Askira ne suka samu sabani? Saidai hakan mawuyaci ne don bata taba ganin ma'aurata masu fahimtar juna kamar su ba. Sai itama ta shiga damuwa, damuwar uwarka ai yana nufin taka damuwar. Damuwar Fulani shine bata san ta ina zata farawa Sa'ade zancen aure ba, she's too young and innocent, auren ma kuma da Yarima Sageer, wanda ta riga ta gama sanin sirrin su shi da matar sa, ta kuma dauke shi matsayin guardian dinta. Sama da komai bata taba tunanin yiwa Sa'ade aure nan kusa ba, ta so sai ta gama karatun ta, to kana naka Allah na nasa kuma nasan shine gaskiya. Sa'ade sai zarya take tsakanin dakin ta dana Fulani very disturbed, ko Fulani zata kira ta tace zo kiji damuwata, amma Fulani ko kallon ta ta kasa yi, ji take kamar ta yi ba daidai ba ta kuma yi mata laifi data karba mata zancen aure bada sanin ta ba. Ba jimawa jikin ta ya dau dumi, data tuno me ake yi a gidan Yarima Sageer "Zina da Shan giya". Ba ga matar ba ba ga mijin ba kowanne shegen kansa ne, ta dauki innocent 'yar ta ta kai musu, matar ta sha giya ta rotsa mata kai, ko mijin yayo zinarsa ya goga mata cuta? Amma kuma wanene Yarima? Dan Askirama mafi soyuwa a gare shi. Askiraman da ya maida Sa'aden mutum a lokacin da ita ta kasa karbar ta. Wannan damuwa a take ta kwantar da Fulani Bilkisu, amma sai ta mike tana rangaji ta sawa kofar ta mukulli kada Sa'ade ko Fanna su zo su dameta. **** Ya Gumsu na tareda mai Askira a washegari, itace tayi turaka kuma itace zata wuni tare da shi a wunin yau da baya fita fada, duk ranar Jumaah daga ya dawo masallaci sallahr jumaah baya kara fita, yana zama ne ya ribaci yammacin da ibada musamman karatun Suratul-Kahfi da suratul Mulk, Yaasin da Waqi'ah. Sannan yana karanta Suratul Nouh kafa 41 a kowanne yammacin Juma'ah. Tana hada masa shayi a cikin kofi (mug) ya dubeta da murmushi. Ya ce "Gumsun Askira, Uwargidan mai Askira....inada wani kyakkyawan albishir dauke a bakin nan nawa". Ya Gumsu ta karkace ta gyara zama bisa tattausar dardumar da maimartaba ke zaune har da tattara dukkan nutsuwar ta ta bashi, a zaton ta albishir zai mata da tafiyar su wata kasar su huta. Amma abinda mai Askira ya fada bata taba jin abinda ya girgiza zuciyarta da rayuwarta bakidaya irin sa ba. Ya jirkita kwanyarta, ya gusar da annurin fuskarta nan take ya mayeshi da wani mummunan bacin rai da Askirama ko wani mahaluki bai taba gani a kan fuskarta ba. "Kwanaki uku masu zuwa zan daura auren Yarima da Sa'adatu!" Amma Ya Gumsu sai ran ta ya bata gara ta tambayeshi don ya tantance mata wace Sa'adatun yake nufi? Don haka ta hadiye komai cikin laluma ta tambayeshi. "Allah ya taimaki Giwan Askira, ko zan iya sanin wacece Sa'adatun?" "'Yar ku Sa'adatu wadda yake riko a gidan sa ta wajen Fulani Bilkisu......". Ai bai karasa ba sai ganin Ya Gumsu yayi tsaye a kansa, idanun ta a warwaje tana huci, yau da ba shi ne sarkin Askira ba, da ba shine uban 'ya'yan ta ba, furfurarsa ko wannan himilin rawanin nasa bai hanawa ta kwashe shi da mari. "Idan wasa kuke..... Allah ya taimake ku ku bari, bana son irin wannan wasan....." cikin mamaki Askirama ke kallon ta baki a bude, ya dauka wannan karon farin ciki zata yi da zabin da yayiwa Yarima, shi da take fushin ya auri mai jajayen kunnuwa mara addini, ga wadda suka san asalin ta suka san addinin ta suka bata tarbiyya cikin gidan amma tana neman kawo masa zancen banza. "Ni ne nake miki wasan? Zaki ga wasa kuwa ganin idon ki". Mikewa yayi zai bar wajen Ya Gumsu ta sha gabansa idanunta tamkar an gumbuda musu barkono "Allah ya taimake ka ashe kuwa zaka bani takardar saki na.......kafin ranar da zaka aurawa Da na aure da tsintacciyar magen da har yau bamu san asalin ta ba, da 'yar data fito daga hannun makiyiyata don su hada kai su cuce ni su ga baya na nida zuri'ata a gidannan.....na tabbata ita ta kitsa maka wannan sharrin to insha Allahu a kanta zai kare! Ba dai Yarima ba! Ba irin tsiya irin talauci ba, irin da babu cikakken asali don ni ban yarda ma BAGGARA ne su ba sun fi kama da bororon daji......". Mai Askira ya hadiye tsananin bacin ransa bai nuna ba ko a fuska, babu wata mace data taba yi masa irin wannan tsaurin idon a rayuwar sa....amma Gumsun Askira zata ci albarka da yawa....albarkar 'ya'yan ta...albarkar kasancewar ta uwar 'ya'yan sa. Da albarkacin kasancewarta UWA ga duk wani mahaluki dake cikin Askira. Kawai sai ya zagayeta zai wuce, bai taba sa'in sa da kowa ba, tsakanin sa da kowa dake karkashin sa biyayya ne ana so ko ba'a so. Shiyasa ba karamin yaki yayi da zuciyar sa yau akan Ya Gumsu ba, sabida babu saki a tarihin sarautar su, babu kaskanci ga uwar iyali. Ya Gumsu bata daddara ba ta sake jawo Alkyabbar sa..."wallahi sai ka bani amsar inda kuka samo yarinyar nan....ba tun yanzu ba nasan watarana sai ta zame min jidali, na san sai an kakabawa 'ya'yana, yadda naga uwarta ta ci buri a kanta, dama dalilin kawota gidan kenan don ta samu ta auri dan sarki.....kamar yadda ta samu tsuntsu daga sama gasashshe....to ai ba ni kadai na haifi maza ba......don haka in har inada hakki akan Yarima na haihuwa da shayarwa to ban yarda ba ban amince ba.....". Mai Askira yayi murmushi yace "sai kace dan wani na arziki ne da kike tada haqarqari akan sa ke mai da! Dan da tun yana karamin sa ya san dadin zina......girma da aure da martabar gidan su bata sa ya daina ya kama kansa ba. Zan rufa masa asiri da 'yar mutunci don ta taimaka mana ya kintsu shine kike wannan zubar da kimar? Gumsu ina jiye miki ranar jin kunyar ki.....ranar da duniya zata san dan da kike tinkahon dashi har yanzu bai bar zina ba, matar sa shan giya take, rayuwa suke kamar ta dabbobi, musuluncin nasu duka ba maraba.....gara ita nata babu tushe amma wanda bai ji tsoron Ubangiji ba kuma girman aure bai hana shi yin zina ba ba abun tutiya da shi a matsayin Da bane.... A da, na sanya kwanaki uku auren Yarima da Sa'adatu, don in samu inyi gayyata, to na fasa yanzu, nida Waziri zamu daura auren yau Juma'ah bayan sakkowa masallaci. Don in nuna miki ni ke da iko daku daga ke har dan naki. Gara ke na baki hakkin ki na uwa na sanar miki... shikuwa saidai ya ji labari......". Yana gama fadin haka yasa kai ya fice fadar da bai yi niyyar fita yau ba. Waziri sai ganin maimartaba yayi yana shigowa fada a matukar fusace, shikadai yake iya gane fushin mai Askira. Kyawun fuskarsa da kamalarsa kan boye fushin sa a yawancin lokuta. Yana zama fadawa suka yi kirari suka kuma basu wuri, don sun lura ya shigo fada ne kawai sabida Wazirin sa Ibrahim. "Ka fadawa 'King-makers' akwai daurin auren Yarima bayan sakkowa daga masallaci yau". Waziri yayi kabbara a fili, don ya dade yana jiran ranar da Askirama zai zo masa da zancen karin auren Yarima, yana daga wasu daga cikin labaran halin da rayuwar auren Yarima ke ciki daga abakin Awaisu, hatta zancen cire mahaifa da Aisha -Sultana ta yi ya sani, bai gayawa mai Askira bane don ya san in rashin jikoki ya ishe shi da kan shi zai magantu. "Amma Allah ya taimakeka baka ganin gara a hada masa guda uku a wanke su rana daya a kai masa? Hakan taimako ne babba gare shi a bisa nazari na na halin da yake ciki, kamar guda daya ta yi masa kadan". Askirama yayi murmushi ya dubi Waziri Ibrahim, "wannan daya ce tamkar da goma! Kuma itace maganin matsalolin Yarima insha Allahu. Tun farko ita naso ya aura ya kawo min zancen baturiyar nan, idan har ta fito daga cikin Bilkisu ina tabbatar maka karamar Bilkisu ce.....da ace Bilkisu na fara aure a rayuwata babu macen da zan kara aure". Waziri Ibrahim bai san sanda yayi dariya ba, yau mai Askira ya saki layi sabida soyayyar Fulani Bilkisu, ya manta ko da wa yake magana.... A take ya dau waya ya fara aiwatar da umarnin sarki. Kafin karfe 2 na rana duk wani da ya kwana ya tashi a garin Askira mace ko namiji ya samu gayyatar daurin auren Yarima Sageer da Sa'adatu, banda Sa'aden da uwarta dake kule kowacce a dakin ta zuciya babu dadi, ita Sa'ade halin da ta ga Fulani a ciki ne ya hanata kwanciyar hankali, tun jiya data shige daki ta rufe bata kara fitowa ba, sannnan daga ita har Fanna da Zarah tace bata bukatar ganin kowa. Abinci ma tace bata bukata tanada cake da friuts a firjin gefen gadon ta. Duk tunanin Sa'ade yafi bata matsala suka samu tsakanin ta da Askirama. Wajejen karfe daya Fanna ta shigo ta samu Sa'ade dake kwance a gado tun safe, waya take da Sa'id yana gaya mata yadda garin Abuja ya zame masa boring saboda rashin ta, maimakon tayi dariya ta bashi amsa cikin raha yadda suka saba sai tace "Sa'id, ina cikin damuwa, mamana ta shige daki ta kulle tun jiya tace kada wani daga cikinmu ya je inda take" Sa'id yace "manya kanyi irin wannan a lokacin da suke so su kebe don su samu suyi tunani ko neman mafita kan wani mhimmin al'amari da ya shafe su, so karki damu tunda kinsan lafiyar ta kalau, ita da kanta in ta samu saukin al'amuranta zata neme ku......." Fanna ta ce "ranki ya dade....ranki ya dade!" Ta cire wayar daga kunnen ta ta dubi Fanna, Fanna ta ce "lokacin sallah ya yi, ga kuma abincin ki". Sa'ade ta yamutsa fuska ta ce "maida abincin nan" "me yasa bazaki ci ba?" Inji Fanna cikin damuwa, uwa ta ki ci, 'yar ma tun safe ta ki cin komai duk sun sa ta a damuwa....Lokacin yayi daidai da bugawar dakikar agogo karfe biyu da rabi na rana, ya tafi tare da bugun zuciyar SA'ADE.... ba tareda ta sani ba, ta zama karkashin igiyoyin Yareema Sageer har guda uku. "An daura auren Yarima Sageer Yusuf Askira da Sa'adatu Hashim Askira akan sadaki lakadan ba ajalan ba.....". Abinda Fanna ta ji kenan data sako kafarta a kitchen don dawo da kayan abincin da Sa'ade ta ki ci, amma bata yarda tasu Sa'adatun bace don wani abu makamancin wannan bai taba zuwa mata a rai ba, Yarima mijin baturiya wacece zata yi gigin shiga gidan sa? Ai sai mai tsautsayi, matar da aka ce har kwalba take dagawa. Don haka ta tausayawa koma wacece wannan Sa'adatun da aka aurawa Yarima. Don daula zata samu zata shigeta iya shiga....amma tabbas ta hadu da gamon ta. Abinda Fanna ke ta fada a ranta kenan tana cigaba da ayyukan ta a kicin. Yarima yana dakin Awaisu na gidan Waziri a wannan lokacin, shima Awaisun ya zo sakamakon kiran gaggawa da Waziri yayi masa. Ya kuma gaya masa ko me kenan amma yace kada ya bari Yarima ya sani har sai an gama daurin aure, mai martaba zai gaya masa da kansa. Awaisu, kamar zai suma don dadi da farin cikin jin wadda aka zabawa Yarima, once or twice, Yarima ya taba yi masa maganar Sa'ade, yace ta iya girki sannan ga ta da hankali. Daga wannan bai kara cewa komai akan ta ba. Ya tabbata ko baya son ta zai karbeta tunda har yana yabon ta, sannan uwarta mutuniyar sa ce (Fulani Bilkisu). Bazai bada mata kasa a ido ya ce baya son 'yar data fito daga hannun ta ba. Yarinyar kawai yake tausayawa zama da Sultana amma zai nemi Yarima da ya raba musu gida don a zauna lafiya. Shi dai Yarima ya ga Awaisu sai shiri yake cikin farar shadda excelcior, yana yi yana bin waka a radio da alama cikin nishadi yake, ya ce Asiya tana jirana a cikin gida don haka na sallameka inada daurin aure a fada inna gama da ita". Yarima ya kulu da wannan kora da Awaisu yayi masa yace "ni kake kora? Daurin auren wa?" ALLAH ya taimaki Yarima wane ni in kore ku! Amma don Allah ka kara gaba ko in bar maka mukullin dakin in ka gama hirar ka rufe, inada daurin aure muhimmi". Daga haka ya sanya hularsa da takalmi ya fesa turare, ya dubi Yarima yana murmushi ganin kallon takaicin da yake masa.... dariya yayi a rans yace ka kuma zama namiji malam, a da muna maza ne tunda mai jan kunne kake aure, yanzu ne zaka san ka yi aure da matan usli da suka amsa sunan mata.... Yayi ficewar sa ya barshi kwance a gadon sa da baki sake, yana mamakin Awaisu ne yau yayi masa wannan wulakancin? Daurin auren da zai je ya fi shi Sageer muhimmanci??? **** Bayan daurin aure aka zarce da bushe-bushen algaita da kalankuwa, masu goge da masu ganguna kowa na baje kolin nasa. Gabadaya garin ya rude da hayaniya anata labarin Yarima ne aka daurawa aure da 'yar da kishiyar mahaifiyar sa ke riko, wasu na fadin 'yar ta ce data yi shegen ta kafin tayi aure (wa'iyazu billah) Allah ka kare harshenmu daga fadin gaibu, da abinda bamu da tabbas a kan shi. Wannan zance ya kai kunnen Ya Gumsu ta hanyar 'yan kanzagin ta da 'yan hana ruwa gudu, cewa ashe Sa'aden 'yar Bilkisu ce data yi shegenta kafin tayi aure aka kuma biyota da ita har gidan auren ta. Saura kadan Ya Gumsu ta haukace, ga Askirama yana fada bazai shigo ba sai bayan isha balle taje ta huce akansa. Me ya dace ta yi? Ban da ta je su yi wacce zasu yi itada Fulani Bilkisu? Shegiya a cikin iyalinta! Ai gara mata mara addinin! Yau babu ko mayafi haka ta ratsa ta tafi unguwar Fulani Bilkisu, ta wuce bayin ta da hadimai fuuuuuu! Ko gaisuwar da suke mata bata karba ba.... yau ko ita ko Bilkisu, koda hakan shine zaiyi sanadin igiyar aurenta. Fanna na kokarin fitowa da tsintsiya a hannun ta Ya Gumsu tayi ciki da ita, saura kadan ta fadi, sai wara ido take tana neman Fulani amma bata ganta ba, ta daga murya kamar zata tsaga gidan tace. "Bilkisu! Fito wajen ki na zo!" Wannan kira har cikin kwanyar Fulani Bilkisu, gabanta ya fadi ta dafe kirjin ta, Ya Gumsu ta soma dukan kofar dakin ta tun karfin ta, tana cewa "Da na ya fi karfin auren SHEGIYA kurwar mu kurr. Yadda kika lashe mai Askira shine kika kawo shegiya ta lashe Yarima? Wallahi sai bayan raina wannan auren zai tabbata...." dukan kofar take kamar zata ballata. Bilkisu jikin ta sai rawa yake hawaye na zubo mata, tana so ta fito ta fuskanci Gumsu ta fada mata 'yar ta ba shegiya bace da ubanta kuma itama bada son ranta bane amma ta san halin Ya Gumsu, zata tara mata mutanene aka, ta wulakantata gaban bayin ta, su taru su zubar da mutuncin mai Askira don ta tabbata Gumsu dambe take so su yi ba wani abu ba, ta samu hanyar lalata maganar auren, to ko za'a lalata zancen auren nan ba daga gareta ba, da Gumsu ta san halin da ta ke ciki akan auren da ta tausaya mata, itama bata so, ko kadan bata so. Saidai ta zabi farin cikin Askirama akan nata da na Sa'ade. Don haka ta daure ta cije bata fito ba, ta bar Ya Gumsu ita kadai tana ta zage-zage, bakaken maganganu ba irin wadanda bata fada akan Bilkisu ba, har da cewa da ganin ta dama an ga tsohuwar karuwa ta zo ta hargitsa musu miji bakidaya ya daina ganin kowa da gashi sai ita, duk wannan bai isheta ba ta zo ta hada auren masifa da bala'i a cikin zuri'arta, to ko zata yi yawo tsirara sai Yarima ya sakar mata 'yar ta. Kuyangi da bayin Fulani duk sun sunkuyar da kai ko motsi sun kasa, sai yanzu suka fahimci dawa aka daurawa Yarima aure, jikin su yayi matukar sanyi musamman Fanna, hawaye ta soma na tausayin Sa'ade don bata cancanci aure na rashin kwanciyar hankali irin wannan ba ko shekaru ashirin bata yi ba. Saida Ya Gumsu ta tabbatar ta gayawa Bilkisu maganganun da har ta mutu bazata manta ba, in kuma tana da zuciya to zata karbi 'yar ta daga auren Yarima sannan ta bar falon, duk wannan bai isheta ba ta so ne Bilkisu ta fito tayi mata dukan da Askirama zai kasa ganeta. Ita kuwa Sa'ade tana daki a kwance, tun shigowar Ya Gumsu data soma dukan kofar Fulani ta taka aguje ta shige toilet ta rufe kanta, a zaton ta Ya Gumsu ta samu tabin hankali ne, so yawancin duk abubuwan da take fada bata ji su ba kasancewar kofar sound proof ce. Bayan fitar Ya Gumsu data ji shirun yayi yawa sai ta fito, a guje ta nufi kofar Fulani tana kuka tana rokon ta ta bude. Kome Fulani tayi tunani? Sai kawai ta taso ta bude kofar. Halin da Sa'ade ta ganta a ciki ya matukar tada hankalinta, fuskarta ta kumbura tayi jazur idanun ta sun yi luhu-luhu. Sa'ade ta fada jikin Fulani ta wani irin rungumeta tana tambayarta "dukan ki ta yi? Is she lunatic?" Duk da halin da Fulani ke ciki sai da Sa'ade ta sanyata murmushi. Ta ja ta suka shige ciki bayan tasa mukulli ta rufe kofar. Suka zauna a tare a gefen gadon ta. "Ba duka na tayi ba, zagi na dai kawai tayi saboda an aurawa dan ta 'ya ta". Innocently Sa'ade tace "to ke ina ruwanki don an yiwa dan ta aure? Ko ke kika ce ayi masa?" Fulani tayi murmushi ta murza tausasan hannun Sa'ade cikin nata sannan tace. "Laifi na gareta shine ni na haifi 'yar da Askirama ya aurawa dan nata, bayan wannan bani da hannu a ciki". Sa'ade ta yamutse fuska tace "ban gane ba? Zarah ta isa aure ne?" Kwatakwata ta manta itama 'yar Fulani ce tsabar rudun da kalaman Fulani suka jefa ta". "Zarah kadai na haifa? Kafun in samu Zarah wa na fara samu?" Sa'ade ta luluka a duniyar a tunani, ita lallai so take ta canko wa Fulani ta haifa wanda ya isa aure amma tunanin ta ya kasa bata, domin bata ga marabarta da Zarah ba. Murmushi Fulani ta sake yi sannan ta rungume Sa'ade, "ki yi hakuri Sa'adatu kin ji? Mun yi miki laifi daga ni har Askirama, ya nemi alfarmar in bashi ke ya aurawa Yarima nikuma kinsan bazan iya juya masa baya ba. Tunda daga ni har ke zamansa muke yi cikin gidannan mu abin ikon sa ne, sannan in da halarci ko mahaukaci Askirama ya kawo yace ki aura daga ni har ke mun isa mu ce a'ah? Balle dan cikin sa mafi soyuwa a gareshi?" Sa'ade sauraron ta take absent-mindedly tana hada daya da biyu domin ya bata ma'ana. Aure.... ita da Yarima......Yarima wanne? YARIMA! Yarima!! Yarima!!! Shikadai ne mai wannan sunan duk masarautar Askira. "Don Allah Fulani ki fiddani duhun da kalamanki suka sanya ni.." ta fada cikin karkarwar jiki data murya. Ta kama hannuwan Fulani biyu ta rike tamau a cikin nata. Fulani ta ga wannan shine lokaci mafi dacewa da zata gayawa Sa'adatu komai, tunda bakin alkalami ya riga ya bushe. Tiryan- tiryan ta gaya mata mafarkin da Askirama yayi akan ta da yadda ya roketa ta bashi aurenta....da kuma auren da aka daura dazu....."Shine fa Ya Gumsu ta zo tana wannan jidalin". Ita dai Fulani ta san Sa'ade na sauraron ta amma bata san lokacin da ta fado jikin ta yarab! Cikin hali na unconsciousness......kamar suma, kamar fita hayyaci, cikin biyun bata san wanne Sa'aden ta ke ciki ba. Sai ta rungumeta tana kuka abin tausayi ta rasa wane irin taimako ya kamata ta bata.... MASARAUTARMU! Ba ta taba jin tausayin Saade da soyayyarta ba irin yau, yau din da ta tabbatar sun kusa rabuwa, rabuwa ba ta aje a dawo ba, aah rabuwa irin ta kowacce diya mace da iyayenta idan munzalin aure ya riske ta. Fulani ta rasa taimakon da za ta bai wa Saade da ke kwance a jikinta numfashinta na shirin barin gangar jikinta. Ta san Saade za ta razana in ta ji zancen nan, amma ba ta zaci har haka ba. Abin da ba ta sani ba shi ne, Saade ta san sirrin Yarima, ta san na matarsa Aisha-Sultana, tana kyamar dabiunsu na sabon Allah fiye da yadda ba a zato. Hakan kuma bai hana ta ganin wani irin girman Yareema Sageer ba, da kimarsa cikin idanunta, saboda iyakar kyautatawa a zamanta tare da su Yareemah ya yi mata. Amma kalmar AURE a tsakaninsu, ai is underestimated. Wani abu ne da hankalinta da tunaninta ba zai dauka ba. Kullum kallon kanta ta ke yarinya karama tamkar Zarah. A aura mata Uncle Yareema ta kai shi ina? Matarshi ta sha giya ta yi mata shegen duka ko kuwa za ta iya manta kalmar zina' da Sultana ta ce yana yi? Duk da ba ta gama sanin mene ne ainihin maanar kalmar zina ba, amma ta fahimci wani abu ne mummuna, abin kyamata a addini da alada, kuma da shi za ta ke kallon Uncle Yareema in har ba ta samu tabbacin ya tuba ya bi Allah ba daga bakinsa. Ba ta taba kawo wa ranta aure a nan kusa ba, karatu ta ke so, shi ne kuma burinta, sannan tana matukar jin dadin abunta, yau da ba Askirama ne da kansa ya yi mata wannan yankan kaunar ba, cewa za ta yi ba ya kaunarta don ba shi ya haife ta ba. Amma ta sani, ta kuma amince kaunar da Mai Askira ke mata daga Allah ne. ba zai taba yin wani abu da niyyar cutar da ita ba, amma har abada zuciyarta ba za ta yi amanna da auren Uncle Yareema ba. Kamar yadda ba za ta iya karbarsa a matsayin miji ba. Ba gara mata auren Saidu ba in ma auren ya zama dole? Shi ne tsaran aurenta. Fulani robar ruwan faro ta dauka ta yi ta shafa mata a fuska, wuya zuwa kirjinta. Ba ta fasa ba sai da ta ji Saade ta saki nannauyar ajiyar zuciya. Ta kara langwabewa a kafadar Fulani ba ta kara dagowa ba. Duk suka yi shiru cikin wannan yanayin, kowanne da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Zuwa can Saade ta yi magana a hankali. Ni bana son Uncle Yareema Fulani, kamar yadda Mamanshi ba ta sonki. Ki ba wa Maimartaba hakuri, ba zan iya ba. Ta soma wani irin kuka a hankali mai girgiza zuciyar mai sauraro, balle kuma zuciyar UWA! Sosai kukan na Saade yake motsa zuciyarta. Ta shafa kwantaccen gashin kan Saade da hannun damanta ta ce. Saadatu, me zan yi in faranta miki? Ki fadi ko mene ne, amma ban da cewa ba za ki yi auren nan ba. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Laifi kan laifi mun yi miki ni da Askirama, ina rokonki ki dubi Allah da darajar da Allah ya bai wa iyaye a kan yayansu, ki dubi karamcin mai Askira gare ki ki yi hakuri ki yi hakuri ki yi hakuri ki bar wa Allah komai. Saade ta ce, Ta ya ya zan zauna da shi mahaifiyarshi ba ta sonki? Ni ma bana sonshi, matarsa ba ta sona. Komai na rayuwarsu daban yake da tawa. Fulani yadda ake shan ruwa a firji haka ake shan giya a gidan nan kuma kuma Ta kasa cewa ZINA don sai ta ji kalmar ta yi gundumemiya a bakinta ta alakanta ta da Uncle Yareema, saboda cikar kamalarsa da cikar zatinsa kadai yana hanawa ka alakanta shi da kowanne irin aibi Kin taba jin kishiya ta so kishiya ne Saade? Don haka ki cire wa kanki damuwar wai Gumsu ba ta sona. Yanzu matsayin uwar miji ta ke a gare ki, ki yi duk iya yadda za ki iya wajen kyautata mata. Sauran lamarin sai ki bar wa Allah. “But I dont love him Fulani, ina da saurayi na dan ajinmu da na ke so, sunansa Saidu Ki san abin da za ki dinga fada, don ke matar aure ce yanzu. Mace kuma addini bai bata damar ta so kowa ba ko da kuwa da fatar baki ne sai mijin aurenta. Ki gaya min me ki ke so in yi miki in faranta miki ki saki ranki ki manta da komai? Ki sa a ranki babu wani bambanci tsakanin rayuwarki ta da da ta yanzu. As if normally makaranta za ki koma ki ci gaba da karatu, ni kuma zan tsaya in ga cewa Yareema bai hada ki gida daya da Aisha-Sultana ba, kin san yana jin maganata. Sannan zan roke shi ya daga miki kafa har ki kare karatu, in ba zai iya hakan ba ya kara mata ta uku. Saade kamar ta fashe da kuka saboda ita yanzu ko sunan Yareema ba ta son ji. Ya shigo rayuwarta unexpectedly ya rusa ta. Duk burinta na yin karatu mai zurfi ba a yi shawara da ita ba an kakaba mata aurensa. Yariman da ta tabbata yana neman mata. Laifin me ta yi wa Fulani da Askirama da zasu rasa wanda zasu aura mata sai Yarima Sageer? Ta mike za ta bar dakin idon ta fal hawaye Fulani ta sake riko ta tana murmushi. Ba ki gaya min me zan yi miki ba a matsayin gift dina na aurenki. Saade ta ce, Fulani ni me ye nawa a ciki da har sai an ba ni gift? Ai ba'a nemi yardata ba kafin a daura don haka bana bukatar kowanne gift din ki Fulani ta danne dariyarta duk wani tension da ta ke ciki shirmen Saade ya sa ya tafi, ta ce, matsayinki na babbar kanwar ango. Saade ta kyabe baki ta ce, Yana da kannensa su Humaira yan gayu, ni in kina so ki faranta min kawai ki sa a kai ni Tsanyawa in ga Hanne da Innarta, Baba Saleh da Inna Laure. Ta yi ficewarta zuwa nata dakin, ta bar Fulani cikin tunani. Hakika ta yi kuskure da ba ta kara kai Saade Tsanyawa ba, wajen bayin Allahn da suka sada ta da ita. Da kuma matar babanta, duk da Saade ta ce ba zaman dadi suka yi ba, amma dai ai ta rike ta komai lalacewar riko a lokacin da ita ta yasar da ita. Ta kudire a ranta za ta faranta wa Saade da wannan kuma za ta nemo mata wan mahaifinta Kyari da yarsa Rahima kawarta duk da ba ta da tabbacin da gaske Rahima yar Kyari ce ko ko kamanni ne kawai da suna ya zo daya. A take ta kira Askirama a waya kasancewar ba girkinta ba ne. Ta gaya masa tunanin da ta yi, ya ce shi kuma ba zai kai Saade gidan Yarima ba sai ya nemo Babagana Kyari, sai ya aika an dauko Baba Saleh da iyalinsa don ya tabbatar wa Ya Gumsu cewa, Saade da asalinta. Ba don ya sassauta kiyayyarta ga auren ko ga Saade ba, sai don ya cika farin cikin Bilkisu da yarta. A koina Mai Askira yana da mutane, daga bayanin unguwar da Kyari ya zauna a Damaturu daga bakin Fulani ya bi ya dinga tracing labarin Babagana Kyari. Mutanen unguwar suka tabbatar masa Kyari da iyalinsa sun dade da barin Damaturu zuwa garin Maiduguri inda Babagana Kyari ke kasuwancinsa na fata, har gidansa na Maiduguri sai da aka binciko, inda makwabtansa suka tabbatar da cewa Kyari da iyalinsa suna kasar Italy kwata-kwata inda yake sanaar kai fatu. Mai Askira bai gushe da ci gaba da tracing Kyari ba har sai da wani abokinsa ya bada lambar wayarsa ta kasar Italy, kuma a daren shi da fulani suka yi zaman kiran Kyari Babagana inda suka yi magana a handsfree baki da baki shi da Bilkisu. Ta cikin wayar Kyari yake kuka da ya ji mutuwar dan uwansa Hashimu, ya ce Ba yadda ban yi da shi ba ya dawo gida ya ki, wai tunda kin guje shi ba shi ba Damaturu. Na ce ya ba ni yar in rika, Hashimu ya ce mai raba shi da yarki sai mutuwa. Ashe kuwa ita din ce za ta raba su, daga baya na bi bayansa har Kano inda ku ka zauna ban tadda shi ba, aka ce bayan kun rabu ya koma wani kauye da yarshi, kauyen da har yau nake bincike Allah bai ba ni ikon sani ba. Ina fatan yar tawa tana lafiya, kuma ya ya sunanta? Fulani ta gaya masa sunanta Saadatu, sannan cikin jin kunya ta ce, Mai Askira ya daura mata aure jiya, da Dan wajensa Yareema Sageer. Askirama ya karbi maganar da cewa, Ka yi hakuri na yi maka shisshigi, ya kamata a ce ni na fara nemo ka kafin daurin auren hikimar hakan ba ta zo min ba har sai da Fulani ta ankarar da ni. Ka yi hakuri, ka yi hakuri, na yi gaggawa ga sadakinta nan na damka wa Bilkisu na warawaran danyar gwal guda shida. Alhaji Kyari Babagana ya yi murmushi, ya ce, Its a pleasure meeting you your Royal Highness the Emir of Askira. A yi min alfarmar kara sati daya kafin a yi bikin yata Saadatu, don ni da uwarta da yan uwanta mu samu halarta. Da sauri Askirama ya ce, An yi wannan alfarmar, na sanya har sati biyu biki da tarewa, don bikin da ban yi a auren Yarima na farko ba shi zan yi a yanzu, tunda yanzu ne na san Yarima ya yi aure irin wanda hankalina ya kwanta da shi, kuma na yarda da shi. Matarshi ta farko daga Asia ya kawo ta. Sun dade suna tsara abubuwa na yadda bikin Saadatu da Yarima Sageer zai kasance kafin su yi sallama. Maimartaba ya dubi Fulani tana hamma, ya ce, me ya hada ki da Gumsun gari? An gaya min wasu maganganu marasa dadi wadanda ban yi zato daga gare ku ba. Fulani ta tabbatar ba wanda zai kawo wannan gulmar sai Fulani Hibbani uwar tsugudidi, Allah kadai ya san iya abin da ta gaya masa. Ta yi kwafa sannan ta ce, Ni da idanuna ban ga Ya Gumsu ba, kusan watanni shidda kenan. Amma na ji an ce ta zo nemana ina barci. Bayan wannan ban san wani ba kuma. Maimartaba ya jinjina kai, amma bai ce komai ba. Ya san Bilkisu ba za ta yi masa karya ba, amma maganganun da Hibbani ta gaya masa sun tayar masa da hankali. Cewa ta yi, Ya Gumsu da Bilkisu sun yi dambe a gaban bayinsu da kuyangi. Bai yi wa Gumsu maganar ba don tun artabunsu akan maganar auren rabonta da sake tako kafarta turakarsa. Yanzu abin da ya sa a gaba shi ne, ta yadda zai fuskanci Yarima da maganar, ya hana Awaisu gaya masa, ya ce shi da bakinsa zai gaya masa ta hanyar da za ya fahimta. Yarima bai san wainar da ake toyawa ba, domin bayan rabuwarsu da Awaisu a ranar Maiduguri ya tafi, akwai wani project da yake rubutawa zai yi bincike a UNIMAID, wanda zai dauke shi har tsayin kwanaki uku. Bincike ne da yake bukatar nutsuwa (applied research) a fanninsa don haka ya kashe wayarsa. A daren ranar aka yi ta tura masa text na taya murna da fatan alkhairi ba tare da ya sani ba, don duk wayoyinsa ya kashe su. Ya tattara hankalinsa kan abin da yake yi, yana gidan saukar baki na jamiar Maiduguri. Awaisu ne kadai ya san inda yake. Kwanansa biyu kawai sai ga Awaisu. Har masaukinsa ya je, Yarima zaune cikin tattausar kujerar leather ta falon masaukinsa yana kurbar lemun Don Simon a cikin tambulan, ya dubi Awaisu wanda bakinsa ke ta motsi yana yan mutsu-mutsu wadanda Yarima ya riga ya gama gane su. Akwai abin da ke faruwa wanda ba ya son gaya masa idan yana irin wannan mutsu-mutsun. “You better be comfortable, wannan mutsu-mutsun naka da magana Dariya Awaisu ya yi ya ce, Me ya samu wayoyinka na kasa samunka? Shi ya sa fa na zo da kaina. Tunda na zo ban kunna su ba, ina da muhimmin project a gabana, amma dama yanzu zan dan kunna in ji lafiyar Saadatu. Tunda muka zo ba mu kara haduwa ba, kuma ni nan da kwana uku zan koma Abuja, ina so in ji yaushe za ta koma sai in dawo in dauke ta. Awaisu ya tsura masa ido yana son karantar wani abu game da shi a kan Saaden, bai fahimci komai ba, ban da seriousness irin na Sageer da wuya ka iya karantar abin da ke zuciyarshi. Maimartaba ya ce, in zo mu taho ni da kai yanzun nan. Cikin mamaki Yarima ya ce, Lafiya? Sai dumbin alkhairi. In ji Awaisu, Amma a yammacin nan mu kama hanyar Askira is too late, ka yi hakuri ka kwana zuwa gobe, sai in tattara hankalina waje daya in kammala aikina a daren nan da safe mu kama hanya. Awaisu ya ce, Zan bi shawararka ne only in ka amince za ka jinkirta kiran Saadatu har sai ka fara ganawa da Maimartaba ko in ce ka yi hakuri da kunna wayar zuwa goben after encounter dinku da Maimartaba Kokari yake ya fahimci me Awaisu ke son boye masa ta hanyar kura masa ido, kuma sai kawai ya ji gabansa ya fadi. Wani abu ne ya faru da ita? Ya tambaya in subdued (cikin karayar murya). Awaisu ya gyara kwalar rigarshi yana murmushi, ya ce, Ita wa ke nan? Ita Saadatun da ka ce kada in kira. Ya fada cikin daure fuska don ya kasa gane inda Awaisu ya dosa. Awaisu ya sake sakin murmushi, in dai wannan damuwar da ya gani kwance a kan fuskar Yarima a kan Saadatu ne, to insha Allahu komai zai zo wa Maimartaba da sauki, Yarima ba ya taba damuwa da lamarin wanda ba ya so, ko da kuwa ba so ne na soyayya ba, to akwai alamun shakuwa da aminci. Babu abin da ya faru da ita, tana dakin uwarta. You better call your wife not Saadatu, bana tunanin tunda ka zo ka kira ta. A hakan ake mana ikirarin duk duniya ba wadda ake so sai ita. Ita ma ko za ka kira ta, to fa sai gobe, in ka fito daga turakar Maimartaba Ya fada yana dariya, tare da kwashe wayoyin Yarima guda uku da ke bisa center table din gabansa, ya zuba a aljihun jamfarsa. Ya zabi daki daya cikin 3 bedrooms din da ke falon ya shige yana ce da Yarima, Lemme take a shower, ko na samu saukin gajiya ta. Yarima ya bi shi da kallo, ya kasa cewa komai, lamarin Awaisu sai shi. Sai ya dauki kan telephone ya yi dialling lambobin da yake bada umarnin a kawo masa abinci, ya yi wa Awaisu odar abin da zai ci. Daga haka ya maida hankalinsa kan macbook dinsa yana ci gaba da abin da ke gabansa. Sai dai kuma duk hankalinsa ya rabu biyu, jikinsa ya ba shi akwai muhimmin abin da ke faruwa a cikin gida da Awaisu ba ya son gaya masa, ya fi so ya ji kai tsaye daga bakin Maimartaba. Kuma da kyar in alamarin bai shafi Saadah ba, in ba haka ba don me Awaisu zai ce kada ya kira ta? Yana aiki yana ta tunane-tunane, duk a kan Saadatu da alamarinta da ya yi wa zuciyarsa karan tsaye, ya hana shi sukuni ya kuma hana shi enjoying komai da yake yi sabida rashin ganinta cikin kwanakin nan, sai dai ya kudire a ransa suna isa Askira da ya ga Maimartaba zai je har unguwar Fulani Bilkisu don kawai ya ga Saadatu. ****** Suna kwance a bayan mota 4-matic mai dauke da rubutun ASKIRA EMIRATE, direba na ta sharara gudu don su isa Askira cikin lokaci, ta garin Damaturu suka bi, duk da ta fi nisa amma ta fi lafiya sabida insurgency da ya fara kafuwa a daidai lokacin a jihar Borno. Zuwa Askira ta Chibok bai yiwuwa dole sai an bi ta Damaturu. Duk hirarrakin da Awaisu yake masa don ya dauke masa tunani ya ki kulawa, jikinsa ke ba shi kawai, theres something fishy going on akan Saadatu da har ya sa Maimartaba ya yi masa kiran gaggawa. Ana kiran sallar magriba suka shiga Askira. Inda Awaisu ya ji dadi shi ne kafatanin fadawa da dogarai da duk wanda ke wajen ya shiga masallaci sallah lokacin da suka iso, ba don haka ba da tun fitowarsu mota za a fara tarar Yarima da Allah ya sanya alkhairi. Yan tsirarun da suka hadu da su a hanya mata ne bayi suke wucewa. Gaishe su kawai suka yi suka wuce. Suna shiga sassan Yarima da ke cikin gidan alwallah suka yi suka tada sallah, kafin su idar hadiman Yarima sun gama jera musu abinci. Awaisu ne kawai ya zauna yana ci, Yarima sai magiya yake masa ya ba shi wayoyinsa yana cewa, sai ya fito daga ganawa da Maimartaba. Kawai sai jin sallamar Ya Gumsu suka yi a kansu, karkashin rakiyar kuyanginta. Daga bakin kofa suka tsaya ita kadai ta shigo sai huci ta ke kamar mesa. Yarima da Awaisu suka mike tsaye a tare har suna hada baki a tare wajen cewa, Ya Gumsu lafiya?? Kawai sai ta zauna a kujera ta sa fuska cikin tafuka ta fashe da kuka. Yarima da Awaisu suka tsugunna a gabanta suka kasa magana, suna nan durkushe gaban Ya Gumsu tana kuka suka jiyo takun tafiyar Askirama. Daga kirarin da ake masa daga waje suka gane shi ne yake tahowa. Ya karaso har dakin Yarima bakinsa dauke da sallama. Idonsa ya sauka a kan Ya Gumsu, ransa ya yi mummunan baci, da kyar in ba ta lalata komai ba. Biyo ni Yarima. Abin da ya ce kawai kenan ya juya ya fita. Yarima ya kasa tashi daga gurin ya bar Ya Gumsu da ke kuka har sai da ta dago idanunta jage-jage da hawaye, ta ce, In ka karbi auren nan da ya yi maka sai na dauke maka albarka. A razane Yarima ya cira kai ya dubi mahaifiyarsa, kafin ya samu zarafin ce mata komai ta tashi ta fice kamar kububuwa. Yarima ya shiga cikin halin rudu mara misaltuwa. Kawai sai ya bi bayan maimartaba ya bar Awaisu a wajen. Awaisu ya jinjina kai cike da taraddadin wannan alamari, bai yi zaton ya Gumsu ba za ta so auren nan ba in ya yi laakari da yadda ta ke adawa da auren Yarima na farko. Da ya tuna kishin da ke tsakanin matan gidan sai mamakinsa ya ragu, don Saadatu ta fito daga dakin Bilkisu ne wadda suke kishi da ita fiye da kowacce matar sarki. Yarima bai zauna ba sai da Askirama ya fara zama a kujerar mulkinsa. Ransa a tsananin bace don a zatonsa Ya Gumsu ta riga ta yi masa riga-malam-masallaci. Ya yi kokarin boye bacin ransa sabida ba ya taba bari a gane fushinsa, ya dubi Yareema Sageer da ya samu wuri ya zauna daga kasan kafafunsa. Kafin in ce komai Yareema idan na yi maka umarni, uwarka ma ta yi maka, na wa za ka bi a cikinmu? Yarima ya kara rudewa, gabadaya sun rikita shi, ya kasa gane komai. Kawai sai ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Mai Askira ya yi murmushi ya ce, Aure na yi maka shi ne ta ke adawa, aure na mutunci da rufin asiri, auren da na tabbatar zai dauke dukkan kwadayi da shaawarka daga kan sauran mata kamar yadda ya dauke nawa daga kan Bilkisu ko kwarkwarorina na hakura da su daga ranar da na mallaki Bilkisu, domin matan BAGGARA daban ne. Don haka ne nake da kyakkyawan zaton cewa abin da ta haifa ma zai zamo irinta ga Sarki mai jiran gadon Askira. Na aura maka diyar Bilkisu, wato SAADATU don in raba ka da kusantar zina da matan haramun. Ya rage naka ka bi umarnina ko na mahaifiyarka. Ka tashi na sallame ka, ka je ka yi tunani kan abin da ya fi dacewa da kai. Rana ita yau za a fara biki, biki irin wanda ba a yi a aurenka na fari ba, bikin aladar gargajiya na masarautar Askira. Na kai shi zuwa rana ita yau ne don kawunta da ke kasar Italiya ya samu halarta shi da iyalinsa. A nan Maimartaba ya gaya wa Yarima labarin asalin Saade, tun daga auren mahaifiyarta da Malam Hashimu zuwa rabuwarsu. Rayuwar Saade a kauye da ranar da abokin Babanta Malam Saleh ya kawo ta Askira ya karbe ta, wahalar da ta sha a hannun fulani kafin ta amshe ta matsayin ya, da nagartattun halayen Saade da ya dade yana fahimta. A karshe ya gaya masa tun farko ya yi niyyar aura masa Saade a matsayin matarsa ta farko sai ya kawo zancen Aisha-Sultana, shi kuma ya ba shi dama don ya fita hakkinsa. Yanzu ne yake so ya yi masa biyayya da auren Saade, duk abin da suke ciki shi da matarsa ya sani, kuma wannan shi ne matakin da zai iya dauka. Ga mamakin Mai Askira tunda Yareema ya dukar da kai bai dago ba sai da ya kai aya, da ya dago idanunsa sun kada sun yi jazur kamar an gumbuda musu borkono, labarin Saade da ya ji daga bakin mahaifinsa ya gama kashe zuciyarsa, ya luguiguitata. Tun asali kuma ya dade da wani irin feelings a kan Saadatu wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani. Feelings din da shi kansa bai san ma'anar sa ba, bai san a muhallin da ya sanya shi ba. Yau da ya samu wannan labarin na zamowar Saadatu halalinsa, matar auren sa ta sunnah daga bakin da ba zai taba yi masa karya ba, zuciyarsa ta ki tsugunnuwa a waje daya, sai dawurwura ta ke a cikin kirjinsa kamar za ta fito ta bakinsa tsabar contentment din da ya cika zuciyar sa da wani sabon yanayi da ya samu kansa a ciki irin wanda biro ko yawun baki ba zai iya bayyanawa ba. Lokacin da Yarima ya dago ido don ya baiwa mahaifinsa Askirama amsa, Askirama couldn't believe cewa hawaye ya gani a idon Yarima...... Hawayen da bai san na menene ba, tsakanin.... bakin cikin abin da ya yi masa, tausayin labarin Sa'ade, ko ko na farin - ciki ne kai tsaye? Ba zai iya cewa ba!!! Mu karasa a littafi na 3. Na yi muku alkawarin cigaban ba zai jima ba, insha Allahu. Taku har abada; Sumayyah Abdulkadir Takori. 27th August, 2021