*MARUBUCIYA*✍️ Na Autar Marubuta _________________________________________ Bismillahir rahmanir Rahim. Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, Zan fara wannan labari mai suna MARUBUCIYA✍️ Wanda na sadaukar da wannan labarin ga marubuta....👇 Gageren labari ne , kuma kagaggene daga alkalamin Fatima Abdallah kano (Autar marubuta ✍️) Bayan dogon lokacin dana dauka banyi typing ba yanzu na dawo, sai dai inajin alkalamin nawa yana da'kirewa🤭 Tooo Allah ya bamu sa'ar duniya da lahira ✌️☺️ *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<> Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g Page 1&2 "A hankali yake shafa jikinta yana wani irin murmushi, lokaci guda ya fara cewa gaskiya baby...". Salma ce ta mike zuwa gaban 'yan aji ta fisge littafin a hannun wata budurwa dake karanta littafin a gaban yan ajin . Kowa ido ya zuba mata ganin yadda take huci , amma babu wanda ya iya cewa komai , sai wata budurwa sa'arta wacce ita ce marubuciyar labarin. "Ke Salma dallah bama san hauka mene haka wai."? Cikin fusata tai maganar Wacce aka kira da Salma ba tare da annuri ba ta kalli mai maganar tana cewa . "Haba dan Allah Hadiza, wannan wanne irin littafi ne , to wallahi abin ya isa haka , wannan ai iskanci ne da rashin mutunci, kuma a cikin islamiyya, to wallahi zan sanarwa da malam Auwal ." Cikin fuskar rashin mutunci Hadiza ta mike ta Sha gaban Salma ta fisge littafin tana cewa . "Aikin banza , ai ni na dade da sanin bakin cikin da kike mini , saboda kinga ba a karanta littattafan ki ." Murmushi Salma tayi ba tare da taso ba , kana ta ce . "Allah sarki ." Kawai ta koma gurin zamanta kusa da wata aminiyarta zainab ta zauna. "Aikin banza aikin wofi , hassada ta yi wa mutum yawa." Hadiza ta karasa maganar tana neman gurin zama . Zainab ce ta kalli Salma tana cewa. "Salma shi yasa baba yake hanaki rubutu saboda marubutan batsa da sukai yawa, suke bata muku suna , tunaninsa abin da kike yi ke nan." Ajiyar zuciya Salma tai tana cewa. "Wallahi haka ne Zainab, ni kuma gaskiya ina da buri a cikin duniyar marubuta, sai dai baba yana bani matsala." Tana karasa maganar sukaji karar kararrawa alamar an tashi , hakan yasa kowa ya mike tare da jakarshi a hannu wasu a kafad'a. "Zainab ki sauri dan Allah muje ki bani hadisin nan , kin san malam Naziru idan ban masa aikin nan ba , bazai barni ba ." Salma tai maganar yayin da suke fita daga get din makaranta. "Haka ne wlh ai ba shi da kirki ,mi sauri kan a kira magari ba ." Suka fara tafiya cikin sauri , kamar yadda Zainab ta bukata. "Allah ya kawo mu lokacin da zaki waya Salma, kodan ki zo online ki ga irin littattafan da Hadiza take yi na marasa mutunci, ni wlh bama na iya karantawa." Salma ta ce . "Hmm!." "Ai ki bari kawai Yaya Umar yana son sai min waya kwanan nan ." Ta karasa maganar tana tuntu'be da wani dutse kamar zata fadi . Dariya Zainab tai tana cewa. "Ai kodan soyayyar shi yasai miki." Salma ta ta'be baki tana cewa. "Wacce soyayya kuma bayan muna gida daya." Ta karasa tare da jefa mata harara . Hadiza cikin fushi sosai tabar islamiyya suka nufi gida ita da kawarta Ruma . "Ai wallahi Ruma na tsani Salma,bana san ta wlh , munafuka ce ta karshe bana kaunarta ." Ruma tai murmushi tare da cewa . "Haka ne , ammma ki dena damuwa da ita mudai a cigaba da rubuta mana littattafai muna more duniya, idan badan haka ba ai wani abin ba sani zami ba , tunda dai ko a islamiyya ba a Mana filla filla 'baro 'baro yadda zamu gane , sai dai aita damun mu da wani wankan wajibi wankan tsarki ." "Kuma ke mene naki na damuwa Hadiza, ke fa Hadiza RM sunanki , ita kuma Salma Aminu, a suna ma naki yafi dadi bare littafi." Sannan Hadiza ta samu tai murmushi Har yanzu Salma bata samu ta isa gida ba , sakamakon tana tsaye kofar gidansu Zainab tana jiran fitowarta ta kawo mata Littafin Hadisi A lokacin wani farin gaye kirar yaran hutu ya tsaya gaban Salma yana cewa . " 'yan mata adon gari , kwana biyu." Wani takaici Salma taji ya rike mata zuciya, ta kalleshi tana cewa. "Lfy lau. Ammma dan Allah bakajin kiran sallah ake ka tafi inda ya dace ." Farin saurayin me suna Kalifa ya ce . "Haba Salma, bafa na samun damar ganiinki , kuma kinsan irin san da nake miki." Lokacin Zainab ta fito rike da wannan littafin ta mikawa Salma, kana Salma tai godiya Zainab ta ce mata "Saida safe." Sannan ta shige ba tare da ta ce da wannan gayen komai ba . Salma ma ta juya ta nufi hanyar gida. Baban Salma ne da yayanshi Yusuf, dawowarsu daga masallaci ke nan Yayan nashi yake cewa. "Har yanzu Salma wai bata dawo ba ." Yake tambayar Yaya Umar da shima shigowarshi ke nan. Ansa ya ba shi tare da cewa . "Eh baba ammma nasan tana hanya ." Sallama Salma tai tana shigowa cikin gidan ta na hada ido da yayan babanta taji gabanta ya fadi..... Bayan Hadiza ta isa kofar gidansu ta hangi wata vabbar mota cike da kaya a ciki , hakan yasa ta karasa da sauri cikin mamaki , mahaifiyarta dake ganawa da mai motar ta fara tambaya. "Mama me yake faruwa ne Ina zamu haka ."? "Shiga mota kawai Hadiza, babu lokaci yau sai kwanan sokkoto mun bar kano domin bamu da kowa ." "Mama wannan wanne irin tashi ne haka fisabidillahi, sai ka ce ana korarmu na shiga uku." Mahaifiyarta kawai ta shige gaban motar , yayin da shima driver ya shige , ganin babu yadda Hadiza zata yi , ta kama motar ta shiga kusa da mahaifiyarta cikin bakin ciki. Sannan driver yaja mota cike da kaya suka tafi . Tunda Salma ta shigo ta durkusa gabansu tana ta kuka , sakamakon irin maganganu da Alaji Yusuf yake yi . Malam Aminu ba shi da kowa sai wannan yayan nashi Alaji Yusuf, suna zaune lfy sosai , sai dai Alaji Yusuf yafi mlm Aminu rufin asiri domin har yaje ya zama Alaji. Irin girmamawa da malam Aminu yake da ita , hakan yasa yake daukar duk maganar yayan nashi Alaji Yusuf, hakan yasa ma Umar ya zo ya zauna gurin malam Aminu har ya kammala karatunsa , yadda yaji dadin zama da kuma yadda yake son Salma yasa har yau bai koma gida ba . Kuma Salma take sharba sosai , sai dai mahaifiyarta babu yadda zata yi ne , ammma bata san wannan hali na Alaji Yusuf. "Tom ai ba lefinki ba ne , domin tuntuni nake cewa ka bani yarinyar nan ta dawo gidana da zama, duk ga sa anninta nan su Karima da Husna , ammma kaki ." Cikin fusata da fada Alaji Yusuf ya cigaba da cewa "To in Sha Allah komai ya kare , gobe ki shirya kayanki tsaf Umar ya kawo ki." Kuka Salma ta sake rushewa dashi tana kallon mahaifiyarta. Babanta malam Aminu shi ne ya ce . "To mene abin kuka kuma, kin san cewa bama san wannan rubutun da kike yi , karya da gaskiya da shedanci , ammma bakya ji ." Umar ne da ransa ba ya masa dadi ya kallah kanin babanshi yana fad'in . "Baba wallahi wannan abin da Salma take bafa abin sabo bane ko ...". Kafin ya karasa maganar babanshi ya dakatar dashi da cewa . "Baki daya Umar nawa kake da har kasan duniya, mu muka ga ga jiya muka ga yau , duk iskancin da ake a fim kala kala su waye ke rubutawa in ba marubuta ba , to bazai yiyu yarinya ta zo tana jaa mana zagi ba ." "Wanne irin iskanci ne basa yi duk aita lalata tarbiya." Ya sake kallon malam Aminu yana cewa."Wai har da marubutan matan aure, tsabar isgili to rubutu dai Salma ba a wannan zuri'ar tamu ba ." Ya mike tsaye tare da sake kallon Salma yana cewa "Gobe babu fashi Ina sauran ku ." Ya nad'e malum malum ya fice , mahaifiyarta na cewa "A sauka lfy Allah yasa haka ne yafi alheri." Salma ta sake bushewa da kuka . 07040805269 WhatsApp only Autar marubuta ✍️ MARUBUCIYA Na Autar marubuta ________________________________________ *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<> Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g Page 3&4 Bayan Alaji Yusuf ya tafi Salma ta mike ta shige daki ta cigaba da kuka , duk yadda Umar yayi domin ya rarrasheta taki , domin tasan idan ta koma gidan Alaji Yusuf burinta na zama marubuciya tabbas sai dai mafarki. Haka tai ta kuka tana sunbatu kala-kala har akai kiran sallar isha'i Ko abinci bata iya ci ba ta shige daki ta rufe , mahaifiyarta abin yana damunta sai dai babu yadda zata yi , domin komai wuya tafi son Salma a kusa da ita . Anan cikin gidan Alaji Yusuf kuwa . Karima ce zaune sai had'a gumi take rike da waya a hannu , da gudu Husna ta shigo tana cewa. "Wallahi Aunty Karima ga babana ." A firgice ta aje wayar tare da tula mata kaya tana dariya 😂 "Kaiiiiiiiiiiii Husna wallahi littafin nan abin tausayi, gaskiya marubuta suna kokari, ai wallahi komai nacin baba yau saina gama karanta shi ." Dariya suka sake fashewa da ita , sannan suka fita tare domin yi wa baban nasu sannu da zuwa. Salma kamar hankalinta ya fita ta yanke wannan d'anyen hukunci na barin gida , kayanta ta tattara ta zuba a wata karamar bakko , sannan ta fara sanya ido, mahaifiyarta harta kwanta , shima Umar haka sai dai duk basi bacci ba , kuma ba a rufe gida ba sakamakon malam Aminu bai shigo ba . A hankali ta dauko wannan bakko ta jawo dakin , daidai sanda ta hangi mahaifiyarta na kwance ta ji kuka ya sake rufeta , haka tai sauri ta wuce ta kofar dakin Umar ta fita waje tana kuka , tana kuka zuciyarta na sa'ka mata tana shirin yin babban kuskure, wannan ba shi ne hanyar cikin burinta ba , ammma wata zuciyar na fad'a mata aka sin haka , hakan yasa kawai tai gaba ta nufi tasha tana kuka . Babu jimawa mlm Aminu ya dawo , aiko babu wata -wata ya rufe gida . Cikin tasha take tafiya tana kuka tana waige -waige "Salma Ina zuwa lafiya kuwa."? Da firgice ta juya don ganin me magana Kalifa ne saurayinta "Ina zaki , ke da bakya fitowa da dare." Salma ta share hawaye tana cewa. "Kalifa ka rantan dubu biyar in sha Allah zan biyaka ." Dariya Kalifa ya yi yana cewa. "Haba sweetheart, ai kinfi karfin rance a guri na , kina da kyau da hankali." "Zan baki dubu 10 Salma, amma idan kina so ." "Ina so mana." Ta fada cikin kuka "Tom ki dena kuka ki zo muje dakina minti biyar zaki a can zan baki dubu 10." Wani abu Salma taji ya tokare mata zuciya dajin wannan batu daga bakin Kalifa , ashe tabbas gaskiya ake fada a kanshi ya lalata yan mata da yawa . Abin da yazo kanta ke nan. Ba tare da ta ce Komai ba kawai ta juya zata tafi. Jawo mata hijabi ya yi yana cewa. "Haba Salma karki wasa da damarki ." Juyowa tai cikin sabon bakin ciki da takaici ta falla masa mari , bata san lokacin data d'uro wata ashar ba tare da cewa. "Wallahi zan maka ihu anan gurin banza jahili mahaukaci wawa dabba ." Kawai ta dauki kayanta tai gaba Koda taje tasha bata san inda zata ba , kuka ta tsaya kawai tana yi , zuciyar ta na saka mata ta koma gida "Sister ina zaki ."? Wata yarinya da bata wuce sa'ar ta ba ta tsaya gaban ta tare da wani saurayi tana tambaya, Salma tai shiru kafin ta ce . "Unguwa zani ." Ta fada kamar tanajin tsoro . "Ki dena kuka komai tsanani yana tare da sauki ki yi hakuri." "Ki zo ga mota yanzu zata tashi zaria zamu ." Salma ta bi bayansu ta shige motar , ba tare da tunanin babu Wanda ta sani a zaria ba . Bayan sun zazzauna mota ta cika ta fara tafiya Salma ta cigaba da kuka tana shashsheka . Hakan yasa wannan matashiyar ta kalli wannan kyakykyawan saurayi da suke matukar kama da juna , murmushi ya yi mata kawai , hakan yasa ta dora hannu jikin Salma tana cewa "Sister." Salma ta d'ago cikin hawaye "Ki yi hakuri dan Allah." Murmushi Salma tai tare da share hawaye tana cewa. "Na gode mene sunanki ." Ita ma tai murmushi tare da fad'in ."Suna na Salma, ga yanana can Yaya Umar." Salma bata san lokacin da tai dariya ba tana cewa. "Abin mamaki, nima suna na Salma kuma ina da Yaya Umar." Ta karasa maganar tana kallon wancen Umar din . Murmushi d'ayar Salman tai tana cewa. "Masha Allah, mu zamu tafi zaria ne , saboda munzo ziyara nan kuma ga shi mun yi dare." Salma ta ce . "Uhmm Allah ya sauke mu lafiya ." Sauran mutanen motar sun yi shiru kowa da abin da yake sakawa a ransa, babu gida gaba babu baya , sawu na motoci da mutane duk ya dauke a wannan hanya . Lokacin driver yaji mutum ya fado gaban motarsa , wanda kowa Saida ya firgita , yana shirin tsayawa, wani mutum ya ce . "Karka tsaya wallahi hanyar nan bata da kyau." Driver ya ce . "Innalillahi mutum ne fa na kad'e ." Yayi sauri ya fito , kowa hankalinshi ya tashi , mutumin da ya kade jikinsa duk jini yana cewa. "Kai sauri kaja motarka ku tafi , yan bindiga dadi ne suka biyo ni , kai sauri kaja motar ku bar nan ." Cikin rudewa driver ya ce . "Taso mu tafi bama barka anan ba ." Yana zuwa kusa dashi sai karar bindiga suka ji ta koina Sai ihu da salati , mutane suka fito daga motar sai gudu Sun yi wa driver da wannan mutumin kaca-kaca da harbi Salma da gudu suka nufi wata hanya su biyar cikin tashin hankali suna gudu . Sai ji sukai a bude wuta a ta wajen su juyawar da Salma zatai taga duk an zubar da su kasa , sai ita kadai a tsaye Ta fashe da kuka ganin yadda wannan Salman take rike da gawar yayanta Umar an fasa masa kai . Yan bindigar ne suka sake biyosu suna harbi , da kyar Salma Aminu ta rarrashi Salma ta taso tabar gawar yayanta Umar agun suka cigaba da gudu suna faduwa suna kuka Gudu suke sosai basu san inda suke sa kafarsu ba , daji ne ga duhu Haka har asuba tai musu a wannan gurin ,jikin dayar Salma duk yayi rauni haka ta fadi a wannan wajen . Babu gida gaba babu gida baya , kurgurmin daji ne sai bishiyu , hakan yasa Salma ta tsaya gurin dayar Salman tana kokarin tashinta zaune . Bayan ta tasheta ta jingina ta jikin wata bishiya tana wani irin nishi tana cewa. "Mun yi tafiya Sosai sister, daga nan babu inda zan kara , sai dai nasan mun tserewa wannan yan bindigar mun yi musu nisa." Tana yi tana wani irin nishi idanunta sun yi jaaa Salma kawai ta fashe da kuka mai matukar gwanin ban tausayi. 'Dayar Salman ta cigaba da cewa . "Sister Allah yana tare da ke , ammma ni mutuwa zan yi a wannan gurin , sun kashe Yaya Umar a gabana , sun kashe mutane da yawa, Allah ya hada mu a aljanna." Cikin tashin hankali da sabon kuka Salma Aminu ta fara cewa. "A'a Salma, ba mutuwa zaki ba , bazan barki anan gurin ba , mu karasa gaba ko zamu samu wani rafi mai ruwa , zaki dawo daidai."😭 Kawai shiru Salman tai domin irin jigatar da tai da irin abin da take ji yasa bata iya magana sai kokarin magana da hannu tana nuna tabar ta a gurin ta tafi. "Salma bazan barki anan gurin ba , ki karfafa gwiwarki Allah zai taimaka mana." Tai maganar tare da kokarin cicci'bata a bayanta . "Timm." Salma taji ta fado kasa , da sauri ta juyo ta durkusa gabanta Tana juyota ta ga ko motsi bata yi "Salmaaa."😭 Ta fada cikin murya mai kara da kuka "Salma."😭 "Haba dan Allah, innalillahi wa innailaihir rajiun." Salma ta fad'a tana jijjigata Kuka ta kifa tana yi sosai ita ma kamar ranta zai fita a wannan lokacin Ba karamin tashin hankali Salma ta shiga ba ganinta a wannan yanayi , haka rana ta fara fitowa mai zafi ta fara dukanta . Yadda taji matukar yunwa da kasala yasa ta mike tsaye domin tafiya gaba ko Allah zai had'a ta da wata halittar Ta juyo ta kalli Salma dake kwance matsayin gawa ta rushe da kuka tana cewa. "Innalillahi wa innailaihir rajiun, ki yafe mini Salma, wallahi kafafuna basa daukata nima , da saina dauke gawarki a wannan wajen." 😭 "Ki yafe mini , ki yi hakuri."😭 Ta juya cikin tashin hankali na kuka tana d'ingishi ta fara tafiya tana juyowa tana kallon gawarta . Autar marubuta 07040805269 WhatsApp only *MARUBUCIYA* ✍️ Na Autar marubuta ____________________________________________ Page 5&6 Haka Salma ta cigaba da tafiya cikin matukar wahala da tsoron wannan dajin , tana tafiya tana duban hanya tana juyo bayanta, har tai nisa sosai ta dena ganin gawar Salma, lokacin da taji matukar yunwa ne yasa ta sake fad'a wa cikin wani dajin, sai dai babu wata itaciya da ta gani wacce ake ci , sai wata bishiyar goruba , d'anya shakaf , ganin ta yi mata tsayi yasa ta zauna kasan bishiyar tana tunanin daga nan ina zata je , babu zato taji abu yana bin bayanta, da sauri tasa hannu ta kamoshi cikin tsoro tana yar'bar dashi . A million ta mike tasa gudu ganin koren mucijin data kamo da hannunta, ta sake danna kanta cikin dajin . Anan kuwa tunda garin Allah ya waye Umman Salma bata fito ba , sakamakon yadda kanta yake mata ciwo tun daren jiya. Sai dai har yanzu bata ji motsin Salma ba, saboda Salma ta saba kullum tana fitowa tayi shara, koda kuwa zata koma bacci. Wannan tunanin yasa Umman nata dauriya tana fitowa waje , ta tura dakin Salma yana budewa ta ga babu alamun motsinta , ban daki ta leka nan ma babu labarinta. "To ina Salma ta shiga ne ."? Take tambayar kanta A lokacin Umma taji gabanta ya fadi tare da tunanin tabbas sam bata ji motsin Salma ba , hakan yasa ta nufi dakin malam Aminu, karo taci da Umar Ya durkusa har kasa yana gashsheta. "Ko ka aiki Salma ne ." Jin Umma ta ce dashi haka ya sa shi fad'in. "A'a yanzu ma na bude gidan , don yau da asuba duk bamu je masallaci ba." Ya karasa maganar yana nuna mata mukullin da kwad'o Ajiyar zuciya tai tana cewa."To ina ta shiga haka ." Jin wannan kananun maganganu ne ya sa Malam Aminu fitowa, "Wai me ake yi ne ? Me ke faruwa."? Umma ta maida masa da cewa. "Salma ce ba a gani bafa Malam." "Kamar ya ba a ga Salma ba , ku sake dubawa dai ." Ya fad'a cikin mamaki Umma ta sake sauke ajiyar zuciya tana cewa."To babu dai inda ban duba ba ." Malam Aminu yasa kai cikin gidan ya nufi dakin Salma, suma suka bi bayanshi . Ido suka tsurawa dakin kamar suna duban wani abu Wani akwati dake kasa malam yasa hannu yana bude cikinsa, ganin hijabai a ninke guda uku yasa shi cewa. "Ina sauran kayan nata ? Ko daman su ke nan."? Umma da Umar suka leko suna duban kayan . "Haba dai kayan Salma ai duk basa nan." Cewar Umma Malam Aminu ya ce . "To tabbas kuwa Salma ba a gida ta kwana ba ." "Kira babanka muji ko taje can ." Umar dajin haka ya zaro wayar a aljihunansa yana danna kira ga Alaji Yusuf, kira guda ya yi, mamansu Karima ta miko masa wayar . "Salamu alaikum Umar." Bayan Alaji ya d'aga wayar "Baba ina kwana, an tashi lafiya."? Alaji ya ce ."Lafiya alhamdulillah har kun taho ne ."? Jin wannan maganar yasa Umar ya fara yin jimm kafin ya ce . "Baba bata zo bane ."? Alaji ya ce ."kamar ya ta taho ne ." Umar ya mikawa malam Aminu wayar yana cewa."Baba kai masa bayani." "Wanne irin bayani mene ke faruwa ne." Alaji Yusuf ya fad'a yayin da baban Salma ya kara wayar a kunne . "Dama Salma ce ba a gani ba , kuma ga dukkan alamu bama ta kwana a gida ba ." Ya fad'a masa haka kai tsaye "Wannan wacce irin magana ce, to ina taje ku sake dubawa dai." Alaji yana gama magana ya kashe wayar "Alaji meke faruwa kuma." Cewar matarshi "Wai Salma ce , ba a gani ba tun jiya." Ya karasa maganar yana mikewa tsaye Cikin mamaki mamansu Karima ta ce ."Innalillahi garin ya kuma." Alaji ya ce . "Ai yanzu zanje taraunin wannan wanne irin magana ne." Jingum-jingum su Umma sukai, domin duk inda suke tunanin samun Salma babu labari. Lokacin da dabara ta zo wa Umar ya kira number zainab A spiker yasa wayar tana ta shiga amma ba a dauka ba , tana katsewa ya sake kira . A bacci Zainab kiran ya tasheta , ta jawo wayar tana dauka . "Su Salma an sami wayar Yaya Umar ke nan." Jin haka yasa Umar murmushi yana kallon su Baba. "A'a Zainab ni ne ba Salma ba ce ." "Ahu Yaya Ina kwana." Ya amsa da fad'in."lafiya lau Zainab ko Salma tazo nan ." Taji gabanta ya ce rasss Sai da tai shiru kana ta ce ."Salma kuma bata zo ba , lafiya kuwa."? Umar ya ce ."Lafiya lau, dama tun jiya ne ba a ganta ba ." Cikin tashin hankali Zainab ta ce ."Innalillahi amma jiya da dare ta zo gidanmu ta kawon Littafin Hadisina , harda jaka a hannunta na ce ina zata ta ce gidan Aunty Murja." Malam Aminu da Umma suka kalli juna. Sannan Umar ya ce . "Tom shi ke nan bari na kira Aunty Murjan." Ya gintse wayar . Duk Zainab taji ta nemi wannan baccin ta rasa , cikin matukar mamaki ta mike ta zauna, kallon Littafin da Salma ta kawo mata a daren jiya tai, cikin mamaki tasa hannu tana dauko Littafin Sun sake shiga matukar tashin hankali sosai yayin da suka kira Aunty Murjan wato kanwar umman Salma, domin ta tabbatar musu rabonta da Salma za ai wata biyu zuwa uku, hankalin su ya sake matukar tashi tsaye a wannan yanayi Da sauri Husna ta shigo daki tana tashin Karima "Aunty Karima ki tashi , ga baba can ya fita , Salma ce ta bata tun jiya ." Zumbur Karima ta mike tana cewa."Mee wacce Salma." Husna ta ce ."Nima yanzu mommy take sanar mini." Sukai jugum- jugum. Sokkoto birnin shehu 😍 Su Hadiza sun sauka lafiya lau, yanzu da Adam ya shirya fita aiki yake cewa."Mama yaushe zaku tafi ne , kinsan an kusa kawo kaya, ya kamata ace kuna Kano." Umman Hadiza ta kalli dan nata tana fad'in."Adam ka jini da kunnen Basira, baka ganin mun debo duk kayanmu ne , tom mun dawo nan , mun dawo nan , idan kuma baza ka iya rike mu bane sai naji ." Adam ya ce ."A'a Umma shi ke nan, ni zan tafi wajen aiki." Ya musu sallama ya tafi ransa babu dadi . Haka Umman Hadiza ta samu daki ta zuba kayanta, sakamakon gidan 'dan ta ne Adam da suke zaune da mahaifiyar baban Adam, lokacin da Allah yayiwa baban Adam rasuwa ta koma Kano tai aure, bayan mahaifin Hadiza shima ya rasu shi ne ta dawo sokkoto, ta ce bazata kuma aure ba , tunda dai duk wanda ta aura sai Allah yayi masa rasuwa. Salma kuwa anan ba a cewa komai, domin ta matukar jigata da gajiya da tafiya saidai har yanzu bata iya hangen komai a inda take . Komai nata ta zubar kafafunta kuwa sun kunbura tsabar gudu da irin abubuwan da take takawa a hanya Wani rami ta hango cike da ruwa, sai dai gurin ya cika da ciyayi da kananun ramuka da kayoyi, yadda taji tana bukatar amfanuwa da wannan ruwan yasa ta fara takawa a hankali tana shiga cikin ramin . Kafin ta karasa ciki, ta fara jin wani kuka mai karfi yana ziyara a kumnenta , amma ta duba koina da ina babu abin data iya gani , dawo da kanta da zatai zuwa cikin wannna ramin ta ga wani bakin abu a cikin ruwan idanu jajaye yana dilalo yawu yana kallon ta . Firgita tai da ganin wannan halitta da bata ta'ba gani ba , hakan yasa ta fito da gudu tana canza hanya , shima binta yayi a guje yana kuka tana neman cizanta . "Innalillahi wa innailaihir rajiun, la ila ha illallahu , innalillahi, Allah ya Allah." Abin da Salma ke nan ta ringa fad'a tana gudu kamar zata fadi Tsalle ya yi. Ya kamo mata riga , ta fincike ta sake sa giya tana ihu . Ya dade yana binta suna cin wannan uban gudun , duk abin ya yazo bakinta fada take tana addu'a, Kamar irin yadda mutum yake yin gudu yana duban bayanshi haka Salma take, sai wannan halittaar ganinta yake kara bata tsoro. Shiru Salma taji babu kukun wannan dabba , tana juyawa kuwa babu ita babu alamun ta, nan take jikinta ya fara rawa yana 'bari , domin tabbas a tunanin ta wannan ba komai bane bace àljani koda kuwa wacce irin dabba ce , cikin wannna yanayi ta cigaba da tafiya, tafiyar na harde mata kamar zata fadi, tari ne ya biyota tana kokarin amai , ta kai kasa tana zubar da wani irin koren ruwa daga bakinta , lokaci guda kuma tsoron wannan abin yana ranta , ta mike tana d'ingishi domin barin gurin kafin wannan abin ya dawo . Sai da ta jigata sosai ba kadan ba, ta fara tafiya tana jan kafa . Autar marubuta *MARUBUCIYA* ✍️ Na Autar marubuta ____________________________________________ Page 7&8 Lokacin da Alaji Yusuf ya karaso, babu wani labari dai na Salma, nan suka zauna suna tunanin mafita da yadda za a bullowa lamarin. "Da dai an sanar da 'yan sanda ko."? Inji Umma Alaji Yusuf ya ce ."Yanzu yarinyar nan bana tunanin 'bata tayi ko sace ta akai , to mu sanar da yan sanda mu ce musu me ." Malam Aminu ya ce ."Haka ne ." Umma ta sake fad'in."Sanin gaibu ai sai Allah duk bamu da tabbacin meke faruwa da Salma ko ." A lokacin Zainab ta rado sallama tana turo kai , ganinsu jigum wasu a tsaye yasa taji duk ta sake shiga yanayi, haka ta gashshesu, suka amsa Sannan Zainab ta kalli Umar tana miki masa wannan Littafi na hadisi tana cewa. "Yaya Umar naga wani rubutu a ciki Salma ce tayi ." Jin haka yasa duk suka 'kagu dajin abin dake faruwa "Mene a ciki karanto shi." Inji Alaji Yusuf Yayin da Umar ke kokarin budewa , page din karshe da yake da rarar gun rubutu ya nufa kamar yadda Zainab tai masa nuni. Yana bude gurin ya kallesu sannan ya fara karanta rubutun a zuciyarshi Alaji Yusuf ne ya sake fad'in."Karanto mana Umar." Umar cikin rashin jin dadi ya sake sa ido kan rubutun da akai da pencil. "Zainab idan kin ga wannan rubutun ki kaiwa Yaya Umar, domin ni daga nan bansan inda zan nufa ba , saboda babansu Karima zai mai dani gidanshi, saboda baya so na cigaba da rubutu." "Ina mai basu hakuri, na yanke wannan hukuncin ne domin cikar burina na zama marubuciya, Ina son rubutu kamar raina, kuma Ina San iyayena fiye da komai, amma zama gidansu Karima zai zama tarnaki ga burina, a yi hakuri a yafeni, kar kuma a neme ni domin nayi nisa daku ." Daga karshe aka zana wata fuska tana kuka Umar ya d'ago yana kallonsu "Habawa habaawa, wannan shi ne abin da Salma zatai mana, mene ne mutane zasu ce innalillahi wa innailaihir rajiun." Inji Alaji Yusuf cikin matukar mamaki Umma kawai kai ta durkusar ta fara kuka Malam Aminu Kam yayi shiru yana mamakin ikon Allah. Alaji Yusuf ne ya kuma fad'in."Wannan yarinyar ta lalata tarihin gidanmu , yanzu dai ta rantse sai ta yi wannan rubutun." Malam Aminu ya ce . "Tom yanzu me ne abin yi ."? Umar ya yi shiru yana sake kallon wannan rubutun. Cikin kuka Umma ta ce ."Ga shi nan yanzu Salma tabar gida mene aibun abin da take yi , Allah ne yasan sanda zanga Salma." "Allah ya bayyana ki Salma, Allah ya kareki a duk inda kike." Ta sake fashewa da kuka Alaji Yusuf ya ce ."Allah ya kyauta amma wannan yarinyar tayi rashin hankali ke taya kika samu wannan rubutun nata ." Ya nuna Zainab Zainab ta ce . "Jiya da muka taso daga islamiyya na bata, saboda zatai Assignment, kuma a jiyan ta dawon dashi, saida Yaya Umar ya kirani dana duba na gani ." Alaji ya girgiza kai , haka duk jikinsu yayi sanyi babu wanda yaji dadin wannan abin, Alaji Yusuf ya koma gida. Aiko yana isa gida duk suna zaune a falo suna jiranshi domin ya dawo suji inda aka kwana. Jiki a sanyaye Alaji ya shiga gidan, domin yana tunanin silarsa ne Salma tai wannan aika aika . "Alaji an ganta kuwa."? Tambayar da mamansu Karima ta fara masa ke nan, zama yayi kan kujera yana cewa."Allah ya kyauta." "Ta ya za a ganta ta gudu harda wasika ta ajiye." Husna da Karima suka kalli juna "Wai Alaji meke faruwa, sai kace za ai mata auren dole." Cewar ummansu Karima Alaji Yusuf ya jingina jikin kujera yana cewa."Saboda mun hanata rubutu, mun hanata rubutun banza dana wofi shi yasa." Sannan Alaji ya kalli Karima yana cewa. "Ke Karima karki kuskure wannan zancen ya fita dangin mijin da zaki aura . Saboda Salma ta gama zubar mana da mutunci, idan kuwa kika sake kika saki baki zancen ya fita, to ina tabbatar miki kin samu abin Gori wajen dangin miji." Karima ta sauke kai kasa Umma ta ce ."To ubangiji Allah ya bayyana ta." Alaji ya tashi ya shige ciki Husna da lamarin ke dukanta ta ce ."Amma Aunty Salma ta yi rashin hankali wallahi." Karima tai ajiyar zuciya tana girgiza kai . Umman Salma ta matukar shiga wani yanayi, sai dai kawai Allah ya bayyana mana Salma Salma tafiya tayi tafiya, tamkar Mahaukaciya ta koma , lokacin data fara hango bakin titi da giftawar abin hawa yasa ta dau damarar kaiwa wajen , tafiya ta fara yi sosai, abin da ya bata mamaki tana tafiya amma kamar bata yi , domin akwai gonaki sosai kafin ta kai ga bakin titi. Haka har yamma ta kawo kai rana ta kusa faduwa, sannan ta isa wata gona ,daga wannan gonar sai titi. Saidai babu kowa gurin banda wani tsoho da ya tula Kara kan kekensa. Ganin yana shirin hawa ya tafi Salma ta nufi gunshi da sauri tana d'ingishi tana cewa."Baba. Baba." Jin haka yasa tsohon dakatawa bayan yana shirin hawa. Kallon Salma ya yi yana cewa."Ke yarinya yanzu ai babu aikin gona sai kuma gobe ." "Gobe ki zo ." Salma ta sake matsawa kusa da shi tana cewa."Baba ba aiki na zo ba , wai dan Allah nan wanne gari ne ."? Dattijon ya sake kallon Salma da fad'in. "Yarinyar baki san inda kike bane , ai nan Gombe ke nan ." Wani dasss taji a ranta dajin irin amsar da ya bata . "Gombe kuma ." Ta maimaita cikin mamaki tana duban garin. Autar marubuta *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<> MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 9&10 Haka wannan tsohon yaja kekensa ya tafi, tun Salma na hango shi , har ta dena ganinshi. Ga magariba ta kawo kai, lokacin da ya tabbatar mata tana Jahar Gombe ta sake shi ga tashin hankali, kafadunta sun kunbura duk ciwuka a jikinsu . Kuka ta fashe dashi ta kara matsawa bakin titi tana tare abin hawa , amma babu wanda yake tsayawa, domin wasu ma suna mata kallon Mahaukaciya ne . A daidai wannan lokacin ne wata farar mota ta tsaya gaban Salma, sai dai bata iya ganin waye ciki , saboda bakin gilashi dake rufe . A hankali akai kasa da gilas din motar Salma cikin hawaye take kallon mai motar . Wata farar matashiya ce mai kimanin shekaru 28 Sanye da abaya da rolling din mayafi, sai wani card dake sa'kale a wuyanta . "Ke lafiya kike tsaye anan kina kuka ."? Tambayar data fara jefawa Salma ke nan "Wallahi ina bukatar taimako, tun daga Kano nake , yan fashi suka tare mu , sun kashe koya , muna ta gudu cikin Daji yanzu wani tsoho yake tabbatar mini a Gombe nake yanzu, babu wanda na sani ." Ta karasa maganar da kuka Matashiyar ta kalli Salma sama da kasa , ta kuma gamsu da jawabinta , hakan yasa tai jimm na wani lokaci kafin ta ce . "Allah sarki. Ki yi hakuri." "Shigo ciki ." Ba tare da Salma tai tunanin wanne irin hannu zata fad'a ba kawai ta shige cikin motar Matar ta rufe glass din , suka tafi . Ganin halin da Salma take ciki yasa matar murmushi tare da kara gudun na'urar sanyaya motar. "Nagode Allah ya saka da alheri." Salma ta kalli matashiyar ta fad'a cikin girmamawa "Mene ne sunanki ."? Matashiyar ta tambaya tare da karyawa da shiga zuwa wani titi da ya rabu biyu . "Suna na Salma." Matashiyar bata kuma cewa komai ba , kawai ta cigaba da tuki . Wani titi ta sake shiga wanda kana iya gano wasu manya-manyan gidaje na masu kudi . Nan tai tare da shiga wani lungu ta nufi wani babban gida launin toka . Tana karasawa mai gadi ya bude mata babban bakin get din , kana ta shige . Sannan tai burgi , ta fito ta budewa Salma kofa . Salma ta fito tana kallon wannan katafaren gida tun kafin ta shiga ciki . "Taho." Matashiyar ta fad'a tare dasa kai ciki Suna shiga falon , wata farar mata ce mai kimanin shekaru 47 Zaune tana cin abinci. "Assalamualaikum." Tai sallama Matar bata amsa ba , hakan bai hana matashiyar zama a daya daga cikin kujerun alfarmar ba Salma kamar mai jin tsoro ta karaso ta zauna a kasa "Ina wuni hajjiya."? Ta gaida wannan matar A lokacin ta d'ago cikin isa tana cewa. "Lfy lau, wannan kuma daga ina."? Matashiyar kawai tai ajiyar zuciya tare da warware rolling din dake kanta . Bayan Umman Salma ta idar da sallah, tai addu'a kamar yadda ta saba , sai dai kwana biyun nan tana yawan kuka , shima haka malam Aminu yana cikin damuwa Sosai, sai dai suna ta addu'a. Hadiza ce ta ke sauraran voice din da Ruma ta aiko mata bayan ta gama saurara ta maida mata da cewa . "Allah sarki kawata, wallahi nima bansan zamu tashi ba ,kawai abin ne ya zo ." Sannan ta tura mata ,Ruma da kamar jira take a aiko tai saurin budewa tare da maido da amsa . "To ai shikenan kawata, Allah ya sa haka ne yafi alheri, sai dai gaskiya ina kewarki sosai , sannan kuma in baki labari mutuniyarki Salma an nemeta an rasa wlh , ta gudu saboda kanin babanta ya hanata rubutu." Bayan Hadiza ta gama saurara, ita ma ta maida mata da fad'in. "Waii Ruma gaske ko karya , tab , dama ina ita ina had'a kanta dani to Allah ya kyauta." Tana tura mata , ta bude group dinta domin yin reply Wani sako ta gani wata mai irin sunata tana cewa. "Muna godiya Aunty Hadiza, gaskiya wannan labarin akwai citta." Ba tare data bata amsa ba ta sake karanta wani sako dake kasanshi . "Mun gode, muna jiran update na yau dan Allah ,gaskiya Najif ba shi da hankali gaban kowa ya fad'a wa matarshi daga aure." Ita ma bata bata amsa ba , ta fito daga group din kana ta bude wani sako wanda number babu suna . "Wallahi kiji tsoron Allah, kina koyawa yara iskancin banza da sunan novels, Allah yana ganinki , ko mutuwa kikai wannan abin bazai goge ba , kin rubuta wallahi ki tuba ." Bayan Hadiza ta gama karantawa kawai tai blocking din ta . Salma ce kwance kan kujera , bayan ta yi wanka da ruwan zafi , aka bata wani riga mara nauyi ta Sanya Sannan likitan da aka kira ya sanya mata ruwa , tare da rubuta mata magunguna , kana ya tafi . "Har yanzu bansan sunanki ba ." Salma tai maganar tare da kallon ta Murmushi tai tare da rike hannun Salma tana cewa. "Suna na Hauwa'u, kuma ni yar jarida ce , sannan 'yar gata ce ni kafin iyayena da mijina su rasu , yau watanni 4 da kwanaki da rasuwarsu , sakamakon hadarin mota ." Hawaye suka gangaro mata Salma ta share mata hawayen tare da fad'in. "Ki yi hakuri Aunty, Allah ya musu rahma." Aunty Hauwa tai murmushi tare da cewa. "To salmana ki kwantar da hankali nan gidanku ne , na samu kawa, sannan waccen matar da kika ganta . Sunan ta hajjiya Aisha matar mahaifina ." Kafin ta karasa maganar wani saurayi ya bankado labulai kana yasa ido yana kallonta . "A'a Aunty Hauwa wannan babyn fa ." Ya nufo da nufin ta'ba Salma Tsawa Aunty Hauwa tasa masa tare da cewa. "Baka da hankali ne Anas, mene haka ."? Jin haka yasa shi cewa . "Ai shi ke nan." Ya wuce sama yana tafiyar yan shaye-shaye. Hankalin Salma ya matukar tashi ganin wannan yanayi , hakan ya sa ta kalli aunty Hauwa tana cewa. "Aunty wa ye wannan kuma ."? "Ki kwantar da hankalinki , wannan yaron hajjiya Aisha ne , amma ba babanmu daya ba , kusan anan gidan ya girma." Salma tai ajiyar zuciya Lokacin Aunty Hauwa ta mike da cewa . "Ina Suwaiba ne , ko har ta tafi." Salma ta bata amsa da cewa. "Ai tunda ta gama girki ta tafi." Ta ce . "Okay.".... Umar ne cikin daki har ya kwanta, rike yake da wayarshi yana kallon hoton Salma, baisan lokacin da hawaye suka zubo masa ba Ya share su tare da sake sa ido cikin hoton yana cewa. "Haba Salma, yaushe zaki dawo? Kin barni cikin kunar zuciya da kewar ki, rayuwa bata mini dadi Salma." Ya aje maganar yana rumgume wayar yana kuka . Wayyyo masu karatu a jona da wannan page 😫 Sai mun had'u a wani. 07040805269 WhatsApp only Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<> Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 11&12 Misalin karfe 11 na safe , Adam har ya iso Kano, domin a halin da ake ciki yanzu yana zaune a falo, sun gaisa da Alaji da kowa da kowa . Sai dai abincin da Karima ta aji ye masa , bai fara ci ba , kawai ruwa ya iya sha . "Assalamualaikum." Karima ta shigo da sallama, harara ta jefa masa tana cewa. "Wai dan Allah ka ci abinci." Murmushi Adam ya yi yana cewa. "To ta ya zanci abinci, kin kawo mini kuma kin fita , tare zaki zo mu ci ." Murmushi ita ma Karima tai masa tana cewa. "Haba , sai ka ce a novel." "Hhhhh ." Adam ya yi dariya , sannan ya ce . "Novels ko, ki ce kina karantawa ke ma ko kina rubutawa." "A'a, wane ni , rubuta novels ai sai 'yan baiwa , fasihai marubuta." Adam ya ce . "Tom kema ai 'yar baiwa ce Sosai, kuma a gurare da dama ." "Kin ga kanwata Hadiza ma marubuciya ce ." Zunburo baki Karima ta yi kana ta ce . "Ammma baka ta'ba fad'a min ba ." "Tom ni dai gaskiya ka bani number ta." Adam ya bude baki cikin mamaki yana cewa. "To mene na sauri , naga dai kin kusa komawa kusa da ita , kuma bake za a ba number ta ba , ita za a ba taki ." Ya gyara zama yana cigaba da cewa. "Wato naji haushin dawowarsu Umma, naso sun yi zamansu a nan ." Karima ta sake murmushi tare da fad'in. "Nifa ka fara cin abinci sai sanyi yake yi.".. Ya ce . "To masoyiya." Tai murmushi a karo na ba adadi Aunty Hauwa ce tai saurin fitowa harabar gida Kana ta doshi kusa da wani mutum dogo yasha malum-malum "Haba Baba ai daka iso ciki , amma ka tsaya anan." Babban mutum din ya yi murmushi yana cewa. "Haba Hauwa'u, ai ba saina shigo ba , sauri nake yi ma , saboda mun zo daurin aure garin naku ne , na ce bari na shigo naga 'yata." Aunty Hauwa tai murmushi tare da fad'in. "Allah sarki Baba ,yasu momy dasu Khalid."? Ya maida mata da cewa. "Suna nan alhamdulillah Hauwa'u, ya kuma hakuri da zama da hajjiya Aisha."? Murmushi Aunty Hauwa ta fara yi , sannan ta ce . "Baba ke nan." Hakan yasa ya sake cewa. "Tomm Hauwa'u , hajjiya Aisha ta gama takaba, kuma kema kin fita harkin cigaba da aiki ." "To maganar gaskiya a matsayina na mahaifinki , bazan sa ido wannan muguwar matar ku cigaba da zama ba , duk abin da Alaji ya bari naki ne ,kuma zaman ta ya kare anan , tunda ba mutunci ta sani ba ." Aunty Hauwa ta durkusar da kai kasa ta ce . "Haka ne Baba ,sai dai akwai kadarorin Daddyna da yawa a gunta , ammma bana son a tayar da wannan maganar , sai na dawo daidai, domin har yanzu wannan mutuwar tana dawo mini sabuwa." Ganin yadda kulla ke kokarin zubo mata ya sa shi cewa . "Shi ke nan Hauwa'u, babu komai a cigaba da hakuri." "Ni zan koma yanzu, domin an kusa daura auren .Ina abokiyar taki Salma."? Aunty Hauwa ta ce . "Tana ciki , ai har gida zamu zo ne ." Ya ce . "Tom shi ke nan, Allah ya kawo ku Hauwa." Sannan ya fita , Aunty Hauwa tai ajiyar zuciya sannan ta koma ciki Allah sarki Umma duk tabi ta rame, rashin Salma yana matukar dukanta Tana zaune tsakar gida malam Aminu ya fito daga daki. "Malam sannu da fitowa." Ya ce ."yawwa sannu da gida , sai dai ya kamata ki cire damuwa a ranki , domin da ikon Allah Salma zata dawo ." Umma ta ce. "Tom malam idan zata dawo sai yaushe, wa ne yasan a wanne hali take yanzu, ai dole abin ya dame ni ." Ta sake kallon mlm Aminu tana cewa. "Tom malam ko zamu koma wajen malam Sharif mai almajirai ne ." Malam Aminu ya yi ajiyar zuciya tare da fad'in. "Karki manta , malamai suna ta addu'a, in Sha Allah Salma zata bayyana kawai ki cigaba da addu'a ke ma ." "Sannan ya kamata kije gidansu Umar, an kawo kayan Karima." Yana rufe baki Murja kanwar umman Salma ta rado sallama Aunty Hauwa ce zaune cikin dakinta tana yin waya . Salma ce ta shigo da sallama, kana ta zauna a kasa Aunty Hauwa ta cigaba da wayarta tana cewa. "To director in sha Allah ma London zasu tura mu , domin zamu fi jin dadi." "Tom shi ke nan sai na jika ." Sannan ta aje wayar tana murmushi da kallon Salma. "Ina kwana Aunty."? "Lafiya lau Salma ya jikin naki."? Salma ta ce . "Alhamdulillah naji sauki Aunty." Sannan Aunty Hauwa ta ce "Kina bacci dazu yayan babana ya zo yana tambayar ki ya zo daga Akko local government daurin aure." Salma ta ce . "Allah sarki har ya sanni ."? Aunty Hauwa tai dariya ta ce . "Eh mana , mahaifiyarsu daya da babana ." Salma tai murmushi Hakan yasa cewa da Aunty Hauwa. "Salma kin bani labarin ki, a gaskiya yayan babanki bai kyauta ba , ta ya zai kore ki a gidansa kawai dan kin zama marainiya." Wani dassss Salma taji a ranta , domin batason Aunty Hauwa tana tuno labarin data bata na karya da gaskiya. Cikin yanayin tsoro Salma ta ce . "Aunty wallahi ma irin yadda 'yan fashi suka tare mu , suka ringa kashe mutane shi ne yake cina ." Ta fashe da kuka tana cewa. "Allah sarki Salma, cann nabar gawarta aunty babu yadda na iya ." Aunty Hauwa tasa hannunta kan kafadar Salma tana cewa. "Ki yi hakuri Salma, in sha Allah komai ya wuce , sai dai yayan babanki duk sanda na samu lokaci zamu je gurin shi a Kano." Salma tai murmushi mai yake kana ta sunkuyar da kai. "Ammm Salma mene ne burinki , kin gama makaranta ne ."? Salma taji tambayar a kunnuwanta "Aunty na gama makaranta." "Sai dai bani da burin da ya wuce na zama marubuciya." Murmushi Aunty Hauwa tai tare da cewa . "Masha Allah, buri mai kyau ke nan Salma, kina da baiwar rubutun ko zaki shiga makaranta ne ."? Cikin jin dadin maganar Salma ta ce . "Aunty basai nayi makaranta ba , domin lokuta da yawa nakan kirkiro labari." ."Ina son zama MARUBUCIYAR online, mai ilmantarwa Sosai." Aunty Hauwa ta ce . "Allah sarki Salmana karki damu." Hadiza tana zaune rike da wayarta, kashe datar ta ke nan ta fito daga Facebook Kana ta shiga app din da take rubutu, ba tare da bata lokaci ba ta fara rubutu kamar haka . "Aure dadi By Hadiza RM Paid book." Ba tare da tasa kudin littafin ba ta cigaba da rubutu kamar haka. "Page 67." Mahaifiyarta ce ta katse ta da cewa . "Hadiza ina bayi kina ta kirana lafiya."? Hadiza ta ce . "Muna waya ne da amaryar Yaya Adam, na ce ki zo mu gaisa baki zo ba ." Umman nata ta ce . "Tom ni dai bari naje gidan wannan kawar tawa Saude, domin biki kwana kadan ya rage ." Hadiza ta maida mata da cewa. "Tom a dawo lafiya." Ta maida kanta kasa ta cigaba da rubutun . Autar marubuta *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<> Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 13 & 14 Ga kayan lefe nan kota ina birjik Dactor Adam ya yi kokari sosai . Amarya Karima abin da ya bata mata rai kuwa , irin littattafan da ta ga Hadiza take rubutawa. Sakamakon tana yawan ganin littafinta ana sharing din shi , sai dai sai yau tasan kanwar Adam ce . Wato Hadiza RM , ta tara masoya sosai da tarin mabiya , an santa sosai tayi kaurin suna a rubuta littattafan batsa Washe gari Bayan Aunty Hawwa ta shirya tsaf domin tafiya gurin aiki , sai sukai sallama da Salma sanna ta wuce , Salma harda rakota falo Anas dake zaune tare da mahaifiyarshi yake cewa. "Aunty Hauwa a dawo lafiya, Allah ya tsare." Ta maida masa da cewa. "Ameen Anas." Tana murmushi sannan ta wuce, tana farin cikin yadda ta ga Anas kwana biyu yana girmamata . Haka Salma ta koma dakinta Anas yana binta da kallo Hannu hajjiya Aisha ta sa ta makeshi tana cewa. "Kai wanne sabon hauka ne ke damunka kwana biyu, sai shishshigewa Hauwa kake , karka ce mini waccen tsintacciyar yarinyar kake so." Ta aje maganar tana nuna hanyar da Salma tabi Dariya Anas ya yi yana cewa. "Haba mommy, me zan yi da waccen yarinyar ." "Kawai abin da nake so ki gane , Aunty Hauwa da kuma ke , ku zauna lafiya, saboda naji Aunty Hauwa tana cewa. Zasu je Dubai su yi wata biyu ." Sannan ya sake fuskaantar hajjiya Aisha yana cigaba da fad'in. "Kin san wannan yayan baban nata , yana gaf da cewa mu tashi, to wallahi mommy mu yi biyayya mu ci abin da zamu ci , in ba haka ba mun zama sorry, mu zauna lafiya har lokacin da zata tafi Dubai ." Hajjiya Aisha tai shiru tare da tunanin gagarumin shawarar da Anas ya kawo mata . Salma kam tana kwance kan gado , domin kuwa babu aikin fari bare na baki , sai zama da kwanciya. "Allah sarki Umma, dan Allah ki yafe mini ." Salma tai maganar tare da tunanin gida . Mikewa tai sakamakon yunwar da taji tana ji , ta fita zuwa kichin domin samo wani abu. Sai dai gashi har yanzu Suwaiba yar aiki baza zo ba , ga rana tana yi sosai. Hakan yasa Salma tai tunanin yin taliya jollop Tukunya ta dauko tare maimakon ta dora sai ta tsaya cak Tana kallon electric din. Tunanin da take , ta ya ne zata kunnata , tana ganin irinta ne kawai a cikin films. Ba zato taji an rike mata hannu tare da damke rigarta ta baya . "Innalillahi." Ta fad'a cikin tashin hankali da juyawa baya "Kaii ne ."? Ta cewa Anas Wata shegiyar dariya ya yi yana cewa. "Tom wa kike tunani ni ne ." "Sake ni ." Yaki sakinta "Wallahi zan maka ihu ." Ta sake fad'a Wata dariya ya sheke da ita tare da cewa. "Tom ai nan gidanmu ne , daga ni sai ke sai mommy." "Kawai malama ki cire wannan rigar." Ya fad'a yana dora hannunsa a bayanta. Bige hannunsa tai da nata tana jin tsoro jikinta na rawa "Dan Allah ka yi hakuri." Jin hakan yasa ya fincike hannun rigar Salma sai ji take Feshhh Rigar ta yage Daidai karfinta ta wurgar dashi tasa gudu , ya mike da gudu ya bi bayanta . Da sauri Salma Allah ya bata sa a ta shige dakinta ta kulle , Ta dafe kirjinta dake bugun dubu dubu , jikinta na rawa da durkusa kasa . "Innalillahi wa innailaihir rajiun. Wannan wacce irin masifa ce."? Ta tambaya kanta cikin tashin hankali. "Ki bude kofar nan , ki bude kofar nan ." Taji muryarshi yana magana a kofar dakin , wani tsoron ne ya sake rufeta Shiru tai masa kawai tana ta kakkarwa "Shi ke nan, kere na yawo zabo na yawo ai ." Jin hakan ya tambatar mata da ya tafi , sakamakon taji sautin takunsa . Kuka Salma ta fashe dashi tana cewa. "Innalillahi wa innailaihir rajiun."😭 Haka ta zauna a dakin nan ko bacci bata iya yi ba , ga yunwa tana ji har saida Aunty Hauwa ta dawo . Koda Aunty Hauwa ta dawo bata fita falo ba , kawai dai ta bude kofar dakinta sannan ta cire wannan rigar." "Assalamualaikum Salma." Ta shigo rike da jakar aikinta a hannu Murmushi Salma tai mata mai cike da matukar kewa kafin ta ce . "Sannu da zuwa Aunty." Aunty Hauwa ta zauna gefen gado tana cewa. "Ya baki da lafiya ne Salma,na ga idonki ya yi ja ." Murmushi na yake Salma ta kuma yi kana ta ce . "Lafiya lau Aunty babu abin dake damuna." Aunty Hauwa tai ajiyar zuciya tare da zuge wannan jaka tana cewa. "Tom ai shi ke nan." Waya ta zaro Hot 30i sabuwa a cikin gidanta tare da SMS din Glo da MTN Sannan ta mikawa Salma Wani dassss Salma taji a zuciyarta tasa hannun ta karba kamar mai jin tsoro. Kafin ta ce komai Aunty Hauwa ta sake zaro wata bakar laptop karama ta sake mika mata "Salma wannan naki ne ki yi amfani dasu saboda rubutun ki ." Wasu hawaye ne suka zubowa Salma lokaci guda Domin bata taba tsammanin irin wannan ba . Cikin kuka ta ce . "Bansan ta ya zan gode miki ba Aunty, Allah ya saka da gidan aljanna, Allah ya jikan iyaye , Allah yasa baki abin da kike nema , wallahi Aunty..." Aunty Hauwa ta dakatar da ita da cewa. "Na gode Salma, ki gode Allah, ammma ki yi shiru ki dena wannan kukan ." Salma ta share hawaye tana sake kallon irin wannan kaya da suke hannunta . Sannan Aunty Hauwa ta sake fad'in. "In Sha Allah zuwa dare zan nuna miki yadda zaki rubutu a laptop din , ki yi saving, ki yi share." "Sannan anjuma zamu je ai miki register na SMS." Salma ta girgiza kai alamun tom domin ta kasa magana Tana gama magana ta mike , ta sake kallon Salma tana cewa. "Salma ki maida hankali kinji, sannan akwai wani marubuci Sir Abubakar Sadiq, shugaban kungiyar Lafazi writer's Association, zan had'a ki dashi , domin shiga kungiyar zai taimaka miki." "Too Aunty." Abin da ta iya fad'a ke nan, sai Aunty Hauwa ta fita . Allah sarki Umman Salma addu'a ta rike gashi ta fara dangana da rashin Salma, domin a yanzu haka tana zaune tana sauraran redio Hadiza ce kwance a tsakar gida tana danna waya . Umman ta ce ta fito daga daki cikin masifa tana cewa. "Wai ke babu inda zaki iya zuwa ne , kullum kina gida yau juma'a ma babu inda zaki." Hadiza ta ce . "Haba umma to ina zani , islamiyya dai yau babu ai." Tana rufe baki wani yaro ya shigo yana cewa. "Assalamualaikum, wai Hadiza ta zo in ji wani a cikin mota ." Hadiza suka had'a ido da mahaifiyarta Bayan korafin rashin ganin page 5 &6 da page 7&8 tom zan sashi a channel kadai.🥴 Autar marubuta 07040805269 *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<> Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g MARUBUCIYA ✍️ Na Autar Marubuta _______________________________________ Page 15&16 "Tom ka ce tana zuwa." Ummanta ta bawa yaron amsa , sannan ya fice "Tashi ki je ." Cewar Ummanta Hadiza babu musu ta tashi da sauri ta fara shiryawa, wata abayarta tasa ruwan toka , sannan ta baza turare aka fita . Cikin taku mai kyau ta fita waje ta hangi wani dogon saurayi fari kalar hutu, ya jingina jikin bakar motarshi yana danna waya . Kamar kamshin turaren Hadiza ne ya dakeshi, ya juyo yana kallonta tare da cire gilashi. Ganin taki karasowa inda yake , hakan yasa ya taka cikin taku na girma ya tsaya a gabanta . "Assalamualaiki ma 'a bociyar kyau da kasaita." Ya fad'a yana murmushi Murmushi tai kamar baza ta amsa ba, sannan ta amsa . Kana ya cigaba da cewa. "Suna na Sultan yaron gidan Alaji Babawo." Da sauri Hadiza ta sake kallo hadadden saurayin cikin mamaki ..... "Tom sannu da zuwa." Cikin kunya da durkusar da kai ta fad'a. "Wato Hadiza ina yawan ganinki zaki tafi islamiyya, da nai tambaya ake sanar mini ai baku dad'e da dawowa nan ba ." Hadiza ta ce . "Haka ne , amma dan Allah mene ya kawoka saboda Umma ta sani aiki a ciki." Murmushi ya yi yana rausaya kai , kana ya ce . "Tom babu damuwa Hadiza, idan kin amince zan dawo wani lokacin." Ta ce . "Babu damuwa." Da gudu ta shige gida tana tsalle , ita ma Umma dake jiran shigowarta ta fara tambaya. "Ya akai mene ya faru ."?.... Tun asuba da Salma ta tashi bata koma ba , saboda irin tarin shauki da farin cikin da take ciki . Wayarta ta dauka tare da yiwa Sir Sadiq Abubakar magana. Nan suka gaisa ta gabatar masa da kanta, nan take ya fahimci wacce Aunty Hauwa tai masa magana akan ta ne . Ta yi matukar farin cikin yadda shima ya karfafa mata gwiwa da yabon kokarinta sosai. Haka ta cike form din shiga wannan kungiyar ta Lafazi writer's Association, kana ya sata cikin muhimman group na marubuta, ciki kuwa harda Bakandamiya reading club. Ta samu kanta cikin matukar farin ciki sosai a wannan yanayi Hakan yasa babu 'bata lokaci ta fara rubuta littafin ta na farko mai suna "FATIMA DA ZARAH." Lokacin da take tunanin sunanta Salma Aminu Waziri , tai tunanin kawowa kanta matsala, hakan yasa ta canza sunanta zuwa Autar marubuta 💚 Haka har gari ya fara wayewa , Aunty Hauwa ta fara shirin fita , sai hankalin Salma ya tashi kuma , ganin cewa Anas yana nan kuma baza ta iya sanarwa da Aunty Hauwa wannan lamarin ba . Hakan yasa bayan ta tafi , Salma ta rufe dakinta ta cigaba da abin dake gabanta . Bayan wasu kwanaki...... Anan kuwa Masha Allah biki ya yi biki , Amarya Karima saidai mu ce Allah san ya alheri ya kawo na yan baya , lokacin da aka zo tafiya da Amarya su Husna an sha kuka , hatta shima Umar ya yi wannan kuka sakamakon yadda yake yawan tunanin Salma babu labarinta . Bayan wani lokaci. Hadiza ce kwance kamar kullm , sai dai a wannan lokacin tana bangaren Karima. Datarta a kunne ta ga sako ya shigo daga cikin group dinta . "Dan Allah Fatima da zarah daga page 5 zuwa inda aka tsaya." Bayan ta karanta sakon tai shiru tare da tunanin ina tasan wannan Littafin Fatima da zarah. Karima ce ta shigo ta katse ta da fad'in. "Hadiza kin bar karamar wayarki dakin Mama ana ta kira ." Hakan yasa ta tashi ta nufi cann , ita ma Karima wayarta ta dauka kai tsaye ta nufi WhatsApp, sakon kanwar ta Husna ta bude kana ta kunna voice din. "Haba Aunty, to a gaida Yaya Adam din, kar dai garin karanta novels aje a kona masa girki. Kuma Aunty har yau ina ta jira baki turan Littafin kanwar Yaya Adam din ba ." Iya kar voice din ke nan . Karima tai murmushi tare da maida mata da cewa. "Ke yarinyar nan wallahi ki kiyaye ni ,wato wayar mommy kike dauka,kinga idan baba ya gano ki babu ruwana, sannan kuma rabu da littattafan Hadiza duk ba dadi na fita a channel da group din ta ma, akwai wata sabuwar marubuciya Autar marubuta zan turo miki link din group din ta." Tana gama voice din ta tura mata, ganin Husna bata online yasa Karima kashe data Duk su Aunty Hauwa suna falo, ana ta hira , Salma indai ba Aunty Hauwa bace ta dawo samm bata sakin jiki kamar haka . "Gaskiya Salma kina kokari sosai wannan Littafin da kike rubuta wa Allah ya kara Basira." Hajjiya Aisha ta ce . "Amin summa Amin." Anas yayi murmushi, Salma ta kauda kai ko kallonshi batai ba "Aunty Hauwa gobe shekarar Umma 5 da rasuwa." Cewar Anas Aunty Hauwa ta ce . "Haka ne ,ya akai baka manta ba , ai na zata ni ka dai nake lissafin." Kafin ya kuma cewa komai Salma ta ce . "Wa ce Umman."? Anas ya bata amsa da fad'in. "Mahaifiyar Aunty Hauwa ke nan , mutuniyar kirki." Jin hakan yasa ta kalli hajjiya Aisha "Dama ba tare suka rasu da su Daddy ba ."? Salma ta tambayi Aunty Hauwa "A'a ba tare bane Salma, su Baba da mijina ko shekara basi ba , sun yi accident ne ."😭 Ta karasa maganar tana kuka "Haba Hauwa'u ki yi hakuri mana , ai addu'a ita ce komai." Cewar hajjiya Aisha Salma ta ce . "Haka ne, dan Allah Aunty ki yi hakuri Allah ya kara haske a kabarinsu .".. Umman Salma ce zaune tana sauraran redio, kwana biyu kamar yadda take jin wata tasha da Salma ke saurara ita take saurara tunda Salma tabar gida. Domin ana karanta littattafan Hausa kala kala na marubuta da dama , har akan gayyato wasu daga cikin marubutan, a dai dai wannan lokacin Malam Aminu ya shigo yana daddafa bango Umar ya rikeshi . Da sauri ta tashi tana fad'in. "Innalillahi Umar lafiya."? Umar ya maida mata da fad'in. "Wallahi Umma faduwa ya yi." Ta sake fad'in. "Subahanallahi." Ta fara kokarin kawo tabarma "Mun gode Autar marubuta Allah ya kara Basira da daukaka." "Gaskiya Fatima da zarah wannan Littafin ya yi Allah yasa a gama lafiya." "Ikon Allah Fatima da zarah muna jiran cigaba, Allah ya sa afi haka." Irin yadda Salma take karanta comments ke nan abin yana faranta mata sosai . "Gaskiya Umma na samu kudi a wannan Littafin." Cewar Hadiza "Dubu 29 fa yanxu haka,kuma ba a gama siye ba nasan." Karima dake yankan alaiyahu tai murmushi "Tom ai ina miki addu'a Hadiza." Cewar Ummanta Ajiyar zuciya dai Karima tai cikin zuciyarta tana cewa. "Allah ya shirya." Wani dassss Salma taji a ranta ganin update din wani Littafi mai suna "Aure dadi ." A cikin group din ta Na Hadiza RM Abin data gani ke nan , zuciyarta taji tana mata zafi ganin irin yadda Hadiza ta sake kwarewa a shashanci da rubuta batsa babu ko kunya ko tsoron Allah. Goge posting din tai tare da rubuta, "duk wacce ta sake turo irin wannan zan cire ta." Kana ta fito daga group din tana mamaki. Cikin ikon Allah ta kammala Fatima da zarah harta fara wani Littafi mai suna . "HIJIRA." Anan kuwa gama cirewa Malam Aminu karin jini ke nan. Matarshi dake zaune cikin damuwa ya kallah yana cewa. "Yau baki kunna redion taki ba ." Murmushi tai kafin ta ce . "Hmm Malam ke nan, ai bana takura ma ba kana bacci ma Alaji Yusuf ya zo , ya ce zai dawo ." Umar ne ya shigo yana dariya yana bude hakora gaban baban nashi ya zauna yana cewa. "Baba yanzu aka aikon da sako a waya , wannan aikin na company da nake nema an dauke ni ." Ya koma ya kalli Umma cikin farin ciki. "Alhamdulillah , Alhamdulillah Umar Allah mun gode maka." Umman Salma ta fad'a Cikin karfin hali Malam Aminu ya nuna farin cikin sa matukar gaske , tare da yiwa Umar tarin nasihohi da fatan alheri, sannan Umar ya shirya domin tafiya gidansu Dawaki, da wannan babban zance mai dadi . Autar marubuta https://chat.whatsapp.com/G3YMYAHnKG4DiU7ZeuwDGk *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 *AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻 🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹 _Faduwar wani tashin wani_ _Yau ake yi, gobe sai labarin_ _Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_ _Cikawa da imani fatana_🤲🏼 <><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<> Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 17&18 Salma sai dai mu ce Alhamdulillah, domin tana da tarin mabiya da suke karanta Littafin ta, wani abin farin cikin da ya sake samunta shi ne , yadda masu YouTube suka sai Littafin nata akai audio dinsa, nan ne sunanta ya sake bunkasa domin ba karamin hikima da tunani aka zuwa a wannan Littafin mai suna Fatima da zarah ba , duk da cewa ta fara rubuta wani Littafin. Aunty Hauwa tana tsaye cikin falo tana amsa waya, domin tana waya ne da yayan babanta, tana sanar dashi tafiyar da zatai zuwa Dubai . Bayan ta gama ta dawo cikinsu hajjiya Aisha ta zauna, ta kalli Anas da fad'in. "Tom tafiya ta zo ." Salma da sam batasan da tafiyar ba ta kalleta tare da tambaya. "Aunty wacce irin tafiya."? Cikin damuwa ta tambaya Da annuri a tare da ita ta ce. "Daga wajen aiki ne Salma, zamu je Dubai wata biyu kawai zami ." Ajiyar zuciya Salma tai kafin ta sake fad'in. "Yaushe Aunty har wata biyu."? "Eh Salma wata biyu zami , sauran sati daya mu tafi , amma ai ga mommy karki damu." Ta nuna hajjiya Aisha Hajjiya Aisha tai wa Salma murmushi tare da fad'in. "Karki damu Salma, ai an zama daya , sai dai mi mata fatan Allah ya dawo da ita lafiya." Ajiyar zuciya mai zafi Salma ta sake saukewa tana kallon Anas. "Tab Aunty ni zaki bari a wannan gidan, wallahi akwai matsala." Tai maganar cikin zuciyarta Aunty Hauwa ce ta sake fad'in. "Kuma ina dawowa zamu je Kano, wajen yayan baban naki.". Salma tai murmushi mai cike da damuwa tare da cewa. "Tom Aunty." Tunani Salma ta sake lulukawa ciki tana hango irin damuwar da zata shiga a wannan gidan idan babu Aunty Hauwa. Jikin Malam Aminu ya yi tsanani sosai, domin jiya ma a asubiti suka kwana, sai dai mu ce Allah ya bada lafiya Su Aunty Hauwa suna cikin cigaba da hirarsu, aka fara kiran wayarta . Ganin kanin babanta ne yasa ta tashi ta shige dakinta. "Assalamualaikum Baba." Abin da Aunty Hauwa ta ce ke nan bayan d'aga wayar Daga can bangaren yayan baban nata ya ce . "Wa'alaikumus salam Hauwa'u, muna waya na tafi wani uzurin ." Da girmamawa ta ce . "A'a babu komai Baba." Jin hakan yasa ya cigaba da cewa. "Tom wannan shi ne , da hajjiya Aisha zata bayar da kadarorin mahaifinki tuni ta bayar, to amma babu niyyar haka, dan haka kotu zamu kaita ." Ajiyar zuciya Aunty Hauwa tai tare da cewa. "Baba bawai bana so a tayar da maganar bane, ammma hajjiya Aisha duk ta canza wallahi kwana biyu, a yi hakuri idan na dawo daga Dubai sai a yi maganar, yi hakuri Baba." Kamar bai ji dadin maganar ba ya ce . "To ai shi ke nan Salma, ina yin wannan ne kawai a matsayinki na amana a guri na , tunda haka kika ce Allah ya dawo dake lafiya." Ta amsa masa da"Amin babana." Sannan sukai sallama ta kashe wayar Yayan baban nata yana kashe wayar ya kalli matarshi dake gefe ya ce . "Allah sa mu dace , Allah raba mu da sharrin hajjiya Aisha." Matar tashi ta amsa da "Amin dai wallahi, ai ni tunda ta d'aga hannu zata mareka na tsani matar nan , banda ma ta'be wa irin tata , mene na zama a gidan babu d'a babu jika." Ya ce . "Allah dai ya kyauta." Fitowarta daga bandaki ke nan Hadiza, ta ajiye buta kana tayi mika Karima ta kallah dake gefen mahaifiyarta tana cewa. "Aunty Karima naga fa yau duk sai a hankali ke , kodai kodai an samu karuwa ne ." Cikin yanayin mutuwar jiki Karima ta ta'be baki tana cewa. "Hmmm." Umman ta ta ce . "Kyaji dai da rashin kunyarki." Hadiza ta ta'be baki tana cewa. "Kai Mama kwana nawa ne na bar miki gidan , kinga dai Sultan ya turo, yana dawowa zaku sha biki ." Da gudu Hadiza ta fad'a daki jin wayarta na ruri. Karima kam ta tashi ta shige lungunta domin sam yau bata jin dadi , ta dauki wayarta da nufin zuwa tirkot tai kalloh . Bayan Hadiza ta dauki wayar cikin raha ta fara cewa. " 'Kawata Ruma kwana biyu ya garin ko online bana ganinki." Daga can bangaren Ruma ta amsa mata da cewa . "Ai baki da mutunci wallahi, sati biyu ke nan da sace min waya." Hadiza ta ce . "Ohh Allah sarki Allah maida alheri, ke yarinya an sa mini rana fa ." Dariya Ruma tai tana cewa. "Kai haba dan Allah ki ce lokacin zuwana sokkoto ya yi , da Sultan din aka sa ."? Hadiza ta ce . "Kwarai kuwa yaron hutu ba , ai yana dawowa daga Jemani zaku sha biki." Ruma ta ce . "Tom Allah ya kaimu kawata gaskiya ina missing dinki da novels dinki ." "Yawwa kin ga wata marubuciya Autar marubuta, Littafin ta na Fatima da zarah, kin tuna Littafin da Salma ta taba yi, shegiya ashe satar ilmi take ." Dariya Hadiza ta kwashe da ita tana cewa. "Aiko na gani , na rasa inda nasan Littafin to Allah ya kyauta ko ta dawo garin ne ." Ruma ta ce . "A'a wallahi , an yi nisan kiyo ai waya sani ma ko karuwanci ta tafi kuma dazu babansu ya rasu ." Hadiza ta ce . "Tab to Allah ya kyauta." Tunda Karima ta bude data ta ci karo da rasuwar kanin babanta wato Malam Aminu, nan ta shiga cikin firgici da tashin hankali, Allah sarki Malam Aminu Allah jikan wanda muka rasa , Allah yasa mu yi kyakykyawan karshe isar annabi Muhammad. Anan kuwa umman Salma an sha kuka an more , gashi har dare ya rufa , yau dai Malam Aminu Allah ya yi , yabar mana duniya, shima Umar ya shiga yanayi mai matukar girma domin lamarin babu wanda bai girgiza ba . Haka Alaji Yusuf abin dai ba a cewa komai. Allah ka jikan wanda suka rigamu gidan gaskiya. Karfe 10:02 Salma na zaune kan gado tasa laptop a gabanta , typing din ma yaki yiyuwa, samm ta rasa inda yake mata ciwo, komai bata jin dadinsa , domin hatta abincin dare bata iya ci ba "A gaskiya ya kamata na koma gida, nasan na yi rashin hankali ku gafarce ni Umma." Ta fashe da kuka yayin da take maganar a cikin zuciyarta "Allah ne yasan halin da suke ciki, tabbas ni Mahaukaciya ce." Ta sake fashewa da sabon kuka, tunanin gida Salma ta ringayi a daren yau, ta kasa aikata komai domin tana tunanin ya kamata ta koma gida, ko dan tafiyar da Aunty Hauwa zatai ta barta, haka har bacci ya dauketa a wannan wajen. Yau da asubar fari Karima da mijinta suka tafi Kano, Umman Hadiza ta ce idan sun isa sai a kira ta tai musu gaisuwa. Gida ya cika da maza da mata masu shigowa suna yin gaisuwa, idan Umma ta tuna babu Malam Aminu babu Salma sai ta sake shiga cikin tashin hankali da matukar rauni. Allah ya horewa Salma saurin typing da hikima cikin rubutu, hakan yasa marubuta da yawa suke zuwa domin su yi Littafi tare .Tana daukar wayarta Facebook ta shiga kai tsaye , bayan ta ga yadda akai mata comments sosai yasa ta fito domin gamawa da na WhatsApp. Wata number ce mai 56 karshe ta fara bude sakonta. "Ke Mahaukaciya karuwa kawai, kina tunanin ban gane ki ba ne , wawiya mara hankali." Abin da Salma ta gani a rubuce ke nan, mamaki ne ya rufe ta tare da tunanin tabbas wrong number ake nema akai mata magana. Autar marubuta ce . https://whatsapp.com/channel/0029VasuzYr6rsR0bxO94J1I *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Kaggagen labari ne ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ Autar marubuta ce MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 19&20 Salma jimm ta yi tana tunanin wannan sako, ba tare data fice daga ciki ba , hakan yasa ta sake ganin shigowar wani sakon . "Kina magana da Hadiza RM, kin gudu daga gidanku to asirinki ya tonu." Salma ta sake karantawa Hadiza kuwa Shahada kawai tai ta tura wannan sako ga Autar marubuta, domin bata da tabbacin Salma ce , sai dai wannan Littafin na Fatima da zarah yake bata yakinin wannan Salma ce , idan kuma ba ita bace hakuri Hadiza zata bata kawai. Murmushi Salma tai kafin tai mata reply ta ce . "Lallai yarinyar nan ta ya ta gano ni , tabbas Hadiza bata kaunata, ai ba komai bane danta gano ni , daman gida zan koma ." Typing Salma ta fara mata tana rubuta . "Hmmm." Abin data tura mata ke nan Ran Hadiza ya baci da ganin wannan reply, hakan yasa ta sake tura mata da cewa. "Karki damu, ni bazan tona miki asiri ba, amma ki sani nayi miki nisa nayi miki rata, alkalamin ki bazai ta'ba taddo nawa ba ." Ta tura mata, sannan ta shiga channel din Salma wanda ta ga an yi sharing dinsa a group dinta,abin da ya fara d'aga wa Hadiza hankali ganin tarin followers dake wannan channels sun ninka nata sun kuma ninkawa , tsaki tai ta fito daga ciki ,kana ta goge Link din a cikin group dinta sannan tai remove din wacce ta turo . Salma kam kawai sakon ta bude tai shiru ba tare da amsa ba , hakan yasa Hadiza ta gamsu Salma ce . Wata wutar kiyayyar Salma ta sake ji tana ruruwa a zuciyarta, ganin yadda Salma take matukar samun masoya da yadda ake son Littafin ta . "Na tsaneki Salma, bana kaunarki wallahi, ni ce ajalinki duk inda kike anan zaki mutu, dani kike zancen." Sannan ta rafka wani uban tagumi tana tunani Umman ta ce ta shigo dakin tana cewa. "Lafiya Hadiza." Hadiza ta d'ago kai cikin rashin jin dadi tana cewa. "Dazu Inna ta kira waya , ta ce ba yanzu zata dawo ba tana gidan Baba Musa , Yayan baban yayaUmar ." Umman Hadiza tai dariya da cewa. "Allah sarki Inna masu yaya da yawa." Hadiza ta sake zabga tagumi, ganin halin da take ciki yasa Umman ta cewa. "Wai lafiya Hadiza na ." Hadiza tai nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce ."Umma burina zai lalace, kinga kudin da nake samu zan dena samu , sannan shaharar da zan yi ita ma lalata min ita za tai." Ta'be baki Ummanta ta yi , kana ta ce . "Wa ce ce kuma ,me yasa zata miki haka." Hadiza ta ce . "Hmm Mama akwai matsala dai kawai , shi ke nan tawa ta kare , kudin da muke dan samu ma yanzu ba zasu zami ba ." Umman nata ta rike kugu tare da fad'in. "Tab aiko ta yi kadan, batasan dawa take yi ba , shirya yanzu muje wajen Malam Zarto, kafin ta hanaki ke kin hanata." Hadiza tai jimm kana ta kara da cewa. "Allah ko Umma, amma zaki gane gun Malam din."? "Ayyuririri." Umma tai bud'a sannan ta kuma cewa. "Ke Hadiza nifa haifaffiyar sokkoto ce , kina gani nan nayi aure, har na haifi Adam , abin da ya kaini zaman Kano auren babanki ne , kuma bayan babu shi ,gani na dawo sokkoto, mu muka san koina shirya kawai." Tana gama magana ta fad'a daki Kafin Hadiza ta motsa daga inda take sai ga sallamar Karima Murmushi Hadiza tai tana cewa. "Ahh mutanen Kano an yi 7 an dawo sannu da zuwa Aunty." Karima cikin gajiya ta aje jakar dake hannunta tana cewa. "Yawwa sannu Karima ina Umman."? Hadiza ta kalli kofar dakin Umma kana ta ce . "Yanzu ta shiga daki, shima Yaya Adam bai dade da fita ba , yau ba shi da aiki ." Tana gama magana Umma ta fito da fad'in. "Sannu da hanya Karima ya aka ji da karin hakuri."? Karima ta ce . "Mun gode Allah Umma wani gun zaki ne ."? Ta tambaya ganin ta sako takalmi da hijabi Hakan yasa Hadiza ita ma ta dauko nata hijabin... Gombawa d'ibar fari , ba a kwana daku ba an tashi daku 💪 Ta shirya tsaf Aunty Hauwa, domin har tasa akwatin ta a mota ,sun fito harabar gidan ana bankwana jikin Salma a matukar mace da kasala "Aunty har wata biyu."? Abin da take ta fad'a ke nan tun jiya da take tayata shirya kaya Anas ne ya ce . "Ni fa Aunty har airport zan kai ki , saina dawo da motar ." Aunty Hauwa ta ce . "A'a rufa mini asiri inà ka iya wata mota , acan gun aiki zan barta kayi zaman ka ." "Ni fa gaskiya Aunty zan raka ki ." Ta sake fad'in. "Anas muna da yawa fa ka barshi." Ya shige gaban motar yana cewa. "Ni dai sai naje har sai naga tashin ku." Aunty Hauwa tai dariya da cewa . "Tom ai shi ke nan." "Tom ni zan koma ciki, Allah ya tsare Hauwa aje lafiya a dawo lafiya sai mun yi waya ." Cewar hajjiya Aisha Ta maida mata da cewa. "Tom mommy nagode zan yi kewarku." Kana tana murmushi da d'ago hannu hajjiya Aisha ta koma ciki Falll hawaye idanun Salma ta kalli Aunty Hauwa. "Haba Salma kuka zaki kuma , kar ki yi dan Allah." Ta fara rarrasheta, Salma cikin kukan ta ce ."wallahi Aunty baza ki gane ba amma Allah ya dawo dake lafiya." Kafin ta bata amsa Saida ta duba agogon hannunta kana ta ce . "Yawwa Salma sai mun dawo, idan akwai wani abin ki kirani, idan mun je zan kiraki , sannan na tura miki dubu 30 a opay din ki." Salma ta ce . "Tom shi ke nan na gode Aunty." Ta shige motar suka tafi tare da Anas tana musu bye-bye. Su Hadiza suna tafiya suna hira har suka isa suna zuwa suka shiga ciki , kamar yadda ya bukaci su zauna kan wata tabarmar kaba ,nan suka zauna kana ya saka hularshi ya dauki carbi, sannan kasar dake gabanshi yasa hannu ya share samanta , sannan ya d'ago ya kalli Umma. "Kwana biyu Mero, shekara da shekaru." Umman Hadiza tai murmushi da cewa. "Lafiya lau ai kasan mijina ya mutu, tom sai muka koma Kano." Ya ce . "Allah sarki mijinta ce baban Adam ." Umma ta ce . "Yawwa akwai abin da ke tafe damu." Tasa hannu ta dunguri Hadiza alamun tai magana "Ita ma wannan yarki ce , naga Kun yi gama wajen idanun." Ya fad'a yana dariya Umma cikin raha ta ce . "Ehhhh." "Tom yanzu me kuke so a yi ."? Ya tambaya Hadiza ta ce . "Akwai wata da nake so a tabbar min tana raye kota mutu . Kuma a wanne hali take ciki." Ya shafa saman kasar tashi yana cewa. "Ya sunanta dana babanta , awanne gari take." "Sunanta Salma Aminu, tana garin Kano karamar hukumar tarauni." Ya rubuta Salma Aminu kan kasar tare da wani jagwalgwalon rubutu. Jimm ya yi yana kallon kasar , daga bisani ya d'ago yana cewa. "Sunanta Salma Aminu Waziri, wacce ake kira da Autar marubuta, kuma yanzu haka tana cikin garin Gombe." "Cikin daula da wadata." Da sauri Hadiza ta kalli Umma jin ya bayyana Salma, domin tabbas tuaninta , ya zama gaskiya "Me kuke so a yi mata yanzu, ko kuna so ta dawo inda kuke ."? "Ahhhhhh." Cewar Hadiza "Kawai dai ina so a hanata sukuni , kuma wannan rubutun ta dena yi , a makantar da ita kuma a kuturtar da ita ." "Makanta da kuturta ko."? Ya fad'a Hadiza ta ce. "Eh." Ya shafa kan kasar tashi , sannan ya ce . "Zaku kawo kofaton jaki guda daya , da kuma idonsa guda daya." Hadiza ta kalli Umma Ina cigiyar book dina na DAJIN MUTUWA 😭😭 Autar marubuta 07040805269 WhatsApp only https://whatsapp.com/channel/0029VasuzYr6rsR0bxO94J1I *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Kaggagen labari ne ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ Autar marubuta ce MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 21&22 Tunda Salma tai alwalar magariba ta shiga daki ta kulle, duk da cewa tunda Anas ya tafi raka Aunty Hauwa bata sake jin motsinsa ba Wajen karfe 8 taji ana kwankwasa mata kofa . "Waye ."? Suwaiba dake tsaye kofar dakin ta ce . "Ni ce nan hajjiya ce take kiranki a falo." Salma ta ce . "Tom gani nan ." Ta tashi tasa hijabiinta kana ta fita zuwa falon , tana zaune ta harde a kujera, ganin wannan yanayi yasa Salma ta durkusa a kasa tana cewa. "Gani hajjiya." D'ago kai ta yi , sannan ta ce . "Ki tattare kayanki a wannan daren kibar gidan nan ." Dasssss Zuciyar Salma ta bayar "Mommy ina zani kuma."? Cikin tashin hankali Salma tai maganar "Ki tafi duk inda zaki je mana, wannan gidan daga ni sai my son dan kuwa na sashi a kasuwa , gobe da safe muma zamu tashi ." Jin hakan ya sake sa Salma cikin tashin hankali "Assalamualaikum." Anas ya shigo rike da wayoyi guda biyu a hannunsa, guri ya samu ya zauna yana cewa. "Mommy kin ganni sai yanzu ko, ai yanzu ma sun je, har airport naje ." Hajjiya Aisha da duk hankalinta ke kan hannun Anas ta ce . "Ya nake ganin kamar wayar Hauwa kuma." Salma ta kalli hannunsa "Eh mommy wayar ta ce wallahi, sam'bad'ota nayi , wannan wayar ta kai dubu dari biyu da hamsin , nasan tun a jirgi zata neme ta, sai sun sauka ta ga babu ita ." "Innalillahi." Salma ta fad'a a fili ba tare da tasan sautinta ya fito ba "Wannan yarinyar me take yi anan ne."? Anas ya tambayi hajjiya Aisha "Na ce ta kwaso kayanta tabar gidan nan , shi ne take mini gaddama da futsara."Mommy ta ba shi amsa Cikin hassala ya mike tsaye tare da fad'in. "Zaki tashi ko kuwa yar mutumarrr..." Da sauri Salma ta nufi daki ta fara had'a kaya tana zu ba wa a cikin jaka , tasa laptop da wayarta , hijabi kala biyu kawai tasa sai wasu dogayen riguna guda biyu, sai ga Anas ya shigo , firgita ta yi da gudu ta dauki jakar ta fice , haka ya biyo bayanta har waje . "Ke garin nan ma zaki bari yau din nan kuwa, muje bakin titi." Cikin tsoro 🥺 ta bishi , bakin titi yaje ya tsaya tare da ita , ammma babu wata mota da take tsayawa ,ganin ya gaji yasa ya tsayar da irin babbar motar nan wacce take cike da shanu . "Yaa mai gida dan Allah kara mini wanna yarinyar mana ka sauketa duk inda ka tsaya." Ya mika masa wasu kudade . "Ni fa Bauchi na nufa kai tsaye."Cewar mai tuka babbar motar "Ehh ba matsala ga wannan kasa mai." Ya karba Salma ta fashe da kuka , haka ta hau gaban wannan mota daga ita sai mai tuki sai shanu ga dare yayi, kana ya tuka motar suka tafi Kuka Salma ta ringa fasawa a wannan lokacin, sai dai bai ce da ita komai ba kawai taba yake sha abinsa . Haka suka tafi kwana tafiya, wajejen karfe 5 na asuba wannan mutum ya karasa Jahar Bauchi, sauke ta kawai ya yi yanufi cikin kasuwa. Cikin tashin hankali Salma tana kuka ta rasa meke mata dadi, ta fara tafiya har ta fara gano gidaje Wani kofar gida kawai ta samu ta zauna, babu abin da take so illar a halin yanzu ta koma gida, sai dai rashin kudi, samm ta manta da kudin da Aunty Hauwa ta ce ta tura mata . Kiran sallar asuba aka fara , sai dai sai kuka take Salma domin babu inda ta sani , ana cikin haka sai ga wani saurayi ya fito daga kofar gidn da take zaune, bai ce da ita komai ba , kawai ya wuce masallaci yana tafiya yana waigenta , dawowa ya yi saboda yana tunanin zata shiga gida tai masa sata. "Ke me kike yi anan ne tashi ki bar mini kofar gida." Ya fad'a cikin masifa Mikewa tai Salma cikin kuka tana magana tana hardewa . "Dan Allah ka taimaka mini wallahi nasha bakar wahala, babu wanda na sani anan , daga Gombe nake , tun daga Kano nake haduwa da jarabawa babu yadda zan yi ka taimaka mini." Ta kai kasa tana kuka, tausayin ta yaji ya rufe ta sosai , hakan yasa ya ce . "Tom shi ke nan, zan taimaka miki da kyakykyawan zuciya, amma indai kika cutar dani ko matata bazan yafe miki." Ya nufi ciki Salma ta bishi suna shiga matarshi tana alwala "Baby lafiya." Abin da matar tashi ta ce ke nan tana kallon Salma. "Fatima ga wannan, ki bata daki idan na dawo zan miki bayani ." Kana yayi sauri ya juya , kamar yadda ya ce , ta bawa Salma daki, ta fito ta yi alwala tana yin sallah bacci ya dauketa a gurin . Wajen karfe 11 na safe Hadiza tana zaune falon Karima tana daura dan kwali ga dukkan alamu fita zatai domin ga Jakarta nan a gefe . "Hmm amaryar sultan." Karima ta fad'a tana kalloonta . "Aunty Karima da Allah ki bani jan, janbaki nasa." Inji Hadiza Karima ta ce . "Ki je ki dauko mana yana ciki, ki zo ki turan WhatsApp." Hadiza ta mike da nufin dauko janbaki tana cewa. "Wayar na jakata ai ki dauka ki tura Aunty." Karima ta jawo jakar tare da zugeta, kana tasa hannu a ciki Dasssss dauuu Abin da Karima taji a zuciyarta, sakamakon cin karo da abu aleda "Ido da kofato." Cewar Karima tsoro ya kamata sosai , domin duk a tunanin ta idon mutum ne Da gudu ta fad'a uwar daki tana cewa. "Idon mutum a jakarki àljanu Hadiza." Cikin matukar tsoro Dariya Hadiza ta sheke da ita tana cewa "Kai Aunty, wanne irin idon mutum, idon jaki ne fa." "Me zaki dashi."? Ba tare da kwanciyar hankali ba ta sake tambaya Ajiyar zuciya Hadiza tai tare da aje janbakin tana cewa. "Gaskiya Aunty bana so na fad'a miki, saboda karki fadawa Yaya Adam ya kashe ni." Karima ta ce . "Babu abin da zan fad'a masa." Sannan Hadiza ta fara cewa. "Tom Aunty kinga akwai wata marubuciya Autar marubuta tom tana son kawon matsala da rashin cigaba hatta novels dina tana cewa babu kyau wai haram ne , tom shi ne muka je gun wani malami ni da Umma, za a kuturtar da ita harda makancewa, dan Allah karki fadawa Yaya Adam." Ai baki daya Karima mutuwar tsaye tai da jin wannan batu, haka Hadiza tasa mayafi ta fi ce "Innalillahi wa innailaihir rajiun, wannan wacce irin zuciya ce da Umma da Hadiza, yanzu mene laifin wannan marubuciya, innalillahi wa innailaihir rajiun." Cikin tashin hankali Karima ta zauna a bakin gado tana maganar Jimm ta yi sosai domin wannan maganar ta girgiza ta matukar gaske , yanzu bata san mene abin yi ba . Autar marubuta. *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Kaggagen labari ne ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ Autar marubuta ce MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 23&24 Bauchi Karfe 11:20 Salma ta farka a bacci , sannan ta karewa dakin da take ciki kallo, kana ta mike ta fita tsakar gida, koda ta fita mai gidan da matarshi suna zaune suna ta hira Salma ta durkusa gabansu tana cewa. "Ina kwanan ku , kuyi hakuri ." Murmushi mijin ya yi , kana ya ce. "Aa karki damu, Fatima ki dauko mata abinci ta karya ." Ta mike kamar yadda ya ce . Ta kawowa Salma doya da kwai sai kunu a cikin kofi "Na gode ." Salma ta fad'a bayan ta aje mata a gabanta "Ammma baiwar Allah kinga jikin ki babu wahala, taya zaki tsinci kanki a haka." Cewar matar tashi Fatima "My sweetheart ki bari ta huta mana kina mata wannan maganar ko abinci bata ci ba ." Ya fad'a wa matarshi Murmushi Salma tai tana cewa. "A'a babu damuwa ai , daga Gombe nake , Aunty na ta tafi Dubai jiya , tom shi ne matar gidan ta koreni , suka ma siyar da gidan , sannan yaronta ya sacewa auntyna waya bayan ya rakata airport, ya zo ya sani a mota tun dare jiya , ya ce duk inda zani naje ." "Gashi sai nan da wata biyu zata dawo ,babu inda na sani ." "Allah sarki." Ya fad'a yana kallon matarshi "Tom ni suna na Aliyuu ga matata Fatima." Salma ta ce . "Ni suna na Salma." Fatima ta ta'be baki tana kauda kai "Zaki zauna damu tsawon wata biyun , idan Allah yasa ta dawo sai ki koma." Aliyuu ya fad'a , da sauri matarshi Fatima ta kalleshi tana cewa. "Baby kamar ya wata biyu, daga baka labari baka san gaske take ko karya ba , kawai sai ta zauna damu." "Haba Fatima, duk da ba a gane macuci wannan yarinyar ai da gaskiyarta , ki dubeta fa mene wata biyu, taimako ne kawai ." Salma kasa tai da kai kawai tai shiru , matar tashi ta mike ta shiga daki. "Karki damu Salma ki zauna anan ki yi hakuri, kije ki ci abinci." Ya shige yabi matar tashi, kana Salma tai ajiyar zuciya tare da daukar abincin tai daki ita ma . Kano Allah sarki baiwar Allah umman Salma tana zaune ta yi shiru. Tana rike da wata takarda a hannunta, jin Shigowar Umar yasa ta muskuta tana amsa sallamar da ya yi , tare da tura wannan takardar karkashinta ,gabanta ya zo ya tsuguna . "Umma babu wata matsala ko, ko akwai abin da babu."? Ta murmusa tare da fad'in. "Allah ya maka albarka Umar, sai dai akwai komai , sai dai kuma Umar tunda Allah yasa kana aiki , ka yi aure mana, rufin asiri ya samu ai ." Jin hakan yasa shi jin kunya . "A'a Umma, ina nan ina jiran Salma inajin tabbas zata dawo." Umma ta ce . "A'a Umar, ni yanzu na cire rai da Salma, ka manta da ita kawai, haka ta zabarwa kanta ." Umar ya ce . "Tom Umma kinga wannan gidan, zan gyara miki shi asa tayill a gyara dakuna koina in Sha Allah." Umma tai murmushi tare da fad'in. "Tom Umar nagode." Washe gari Sokkoto ❤️ Tun jiya da Adam ya dawo daga aiki ya gaza gane kan Karima, sai dai Karima tunda taji zancen Hadiza duk ta rasa nutsuwa, duk da cewa batasan wannan marubuciya ba , amma abin da taji za ai mata ya matukar d'aga mata hankali, sai dai aduk tunanin ta babu hanyar da zata iya hana wannan aika_aika. Misalin karfe 8 na safiya, Salma harta samu ta karya ta yi wanka , kana shi Aliyuu ma har ya tafi wajen sana'arshi ta shayi da burodi . Jimmm ta yi sakamakon yadda taji kanta yana mata ciwo sosai . "Allah sarki Aunty Hauwa, kona kira bana samu ." Tai maganar tare da tuna cewa ta ce ."Ta tura mata dubu 30." Murmushi Salma tai tare da ciro wayarta a caji da nufin shiga opay . Diffffff Salma duhu kawai ta gani , tasan da cewa waya ce a hannunta, amma bata iya ganin komai sai duhu . "Innalillahi wa innailaihir rajiun meke faruwa."? Ta fad'a cikin tashin hankali tare da wurgar da wayar hannunta. "Aunty." "Aunty Fatima." "Auntyyyy." Salma tana kira cikin tashin hankali, yadda matar aliyuu taji tana kiranta , dah kamar baza ta fito ba , amma ta fito ta shiga dakin Ganin idanun Salma a bude yasa tai tsaki tana fad'in. "Kina ta kirana kamar makauniya lafiya."? Salma ta daddafa ta mike tsaye tare da fad'in. "Wallahi Aunty bana ganin komai sai duhu, bana ganin komai wallahi." Ta fashe da kuka. "Okay wata yaudarar kika zo msna da ita ke nan, to wallahi kiji tsoron Allah mijina ba kudi gareshi ba , shayi da burodi ne yake siyarwa." Fatima ke nan Cikin sabon tashin hankali Salma ta ce . "Innalillahi wa innailaihir rajiun."😭 Ta ke ce da wani kuka sai ga wasu hawaye zirrrr Sai a lokacin fatima ta matsa kusa da ita , kana tasa hannu a fuskar ta , don tabbatar da bata gani . "Innalillahi tom garin ya kika dena gani Salma, dama kina irin wannan ne , ko kina da àljanu."? Da mamaki Fatima tai maganar tana jahh da baya , Fi ce wa tai tare da daukar wayarta, kai tsaye ta kira mijinta, dake shima dan albarka ne ko minti 10 bai bata ba , sai gashi ya zo Tsakar gida ya samesu dake Fatima ta riko hannunta sun fito "Me ke faruwa haka ne ? Da gaske bata gani."? Da rudewa ya ke maganar "Wallahi kuwa, ina daki take kirana." Fatima ta ba shi amsa Aliyuu ya juya ya juyo da matukar mamaki . "To ai gara mu tafi asubiti, tun kafin lamarin ya yi tsamari ." Haka suka wu ce suka tafi asubiti, aiko suna isa likitan ido ya zo ya duba Salma. "Dactor ya ake ciki to ."? Likitan ya kalli Aliyuu yana ba shi amsa da fad'in. "A'a karka damu ba babbar matsala ba ce , muna warware irin wannan da dama , dan haka in sha Allah zata sami lafiya, sai dai akwai kudade sosai da zaku cire , domin magunguna idan ta kama harda aiki ma ." Ajiyar zuciya Aliyuu ya yi yana kallon Salma "Tom shi ke nan likita." "Yaya Aliyuu akwai dubu 30 cikin account dina , sannan a gida ina da laptop, a siyar tare da wayata ." Matukar tausayin Salma ne ya sake rufe Aliyuu, sai da wasu hawaye su ga gangaro masa , yasa hannu ya share . "Tabb sannu wai kuka kake yi nan , idan bani da lafiya ko irin wannan baka mini." Cewar Fatima Da fuskar tausayi ya kalleta " Haba Fatima ki dubi halin da take ciki ." Ya koma ya kalli Salma dake cikin damuwa da hawaye ya ce . "Ki yi hakuri Salma, ni ba mutum ba ne mai kudi, banda haka bazan siyar da laptop da wayarki ba , sai na siyar na hada da nawa zan samu damar ....." Bai kai aya ba Salma ta katse shi . "Na sani , ko baka ce ba , babu yadda zan da wannan kaddarar ."😭 Ta cigaba da kuka ,da sauri Aliyuu ya fice cikin wani yanayi . Fatima ce ta zauna wajen Salma har wajen magariba , tunda Aliyuu ya fita bai dawo ba sai a wannan lokacin "Wai sai yanzu zaka dawo haba , ka barmu da yunwa babu kudi ." Abin da Fatima ta fara tarar shi dashi ke nan Wani bacin rai yaji ya turnike masa zuciya, kawai shiru ya yi , ya kalli Salma da fad'in. "Ya jikin naki Salma."? "Da sauki ." Ta bashi amsa "Tom kin ga yanzu haka na hado dubu dari biyu Salma, sannan SMS dinki suna kasa ." "Dan haka bari naje gun likita ." "Wai dan Allah mene ne na wannan barin jikin, na ce maka yunwa nake ji , ammma sai ta wannan yarinyar kake yi ." Yaji wani abu ya tokare masa makogaronsa, ya fita babu cewa komai "Wallahi bari Baba ta dawo daga katsina ,zaku had'u." Abin da Fatima ta fad'a ke nan tana kallon Salma da harara Autar marubuta 07040805269 *SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️ Kaggagen labari ne ✍️ A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌ ~Ba labari ba ne mai tsayi~ Autar marubuta ce MARUBUCIYAR ..... Gubar rayuwata Kawar karuwai Dajin mutuwa Fatima da zarah Mahaukacin so Dangin dalas...🥂👇 https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 25&26 Bayan Aliyuu ya kai wannan kudin , likita ya rubuta musu wani magani suka siyo , ya ce a diga cikin idon nata , haka dai har kwana uku babu wani canji duk da irin magunguna da Salma take sha , hakan yasa likitan ya musu transfer zuwa babban asubitin da ake duba marasa lafiyar ido , domin yi wa Salma aiki . Aliyuu ya matukar rame sosai , ko dan irin abin da matarshi ke yi masa , domin tana tunanin a karshe tabbas zai ce yana son Salma, har yakai ya aureta, wannan lamarin take gudu yasa take yin abin da take Kimanin kwana 3 Aunty Hauwa tana jaraba kiran wayar Salma, amma shiru ,domin ta samu ta maida komai nata bayan tasai waya a Dubai, Allah yasa komai tana aje shi a email kamar yadda ta koyawa Salma. Bayan yayan baban ta ya tabbatar mata hajjiya Aisha ta tashi ta siyar da gida , kana ta kori Salma kamar yadda Suwaiba take sanar dashi. Hankalin Aunty Hauwa ya matukar tashi sosai, har shugaban kungiyar Lafazi tai wa magana amma ya ce shima number Salma bata tafiya, online ma babu labarinta. Washe gari da safe jigum Aliyuu ya yi , domin an shigar da Salma ana mata aiki yaso ya sanar da mahaifiyarshi wannan lamarin , sai dai tana cann wani kyauye a katsina nertwork ma babu , idan taje ta yi wata biyu ko 4 kafin ta dawo . Allah dai ya baki lafiya Salma Yana zaune sai ga Dactor din ya fito, shigarsa da fitowarshi bai ci ace ya yi wannan aiki ba , hakan yasa da tsoro Aliyuu ya mike tsaye. "Dactor meke faruwa."? "Biyoni office." Abin da ya ce ke nan, bayan Aliyuu yabi bayanshi suka shiga office suka zauna. "Likita me yake faruwa dan Allah."? Kafin ya fara bashi amsa , ya yi ajiyar zuciya tare da fad'in. "Ammm Malam Aliyuu, zan maido maka da kudadenka ,saboda wannan yarinyar ciwonta bana asubiti bane , hakan yasa ban yi mata aiki ba ma." "Likita kamar ya kuma." Da damuwa Aliyuu ya tambaya "Eh kamar dai shafar àljanu ne , saboda a halin da ake ciki yanzu, hannayenta duk biyun, sun tsaya cak , basa aiki ." "Tom ashawarce a koma gida a yi magani saboda duk asubitin da zaku je , Tom zasu ci kudin ku ne kawai." Durkusar da kai Aliyuu ya yi , bayan likitan ya karfafa masa gwiwa ya tashi ya koma wajen Salma. Yana shiga tana zaune hawaye sai kwarara suke a idonta , ya dubi hannayenta Yatsunta duk guda goman wasu sun lankwashe kamar zasu karye, wasu kuma suna tsaye cakk , baki ya rike sakamakon wani kuka da ya ke ce masa , jin hakan ya tabbatar wa da Salma ya shigo inda take . "Allah yana jaraftar bayinsa ta duk inda ya so , ki yi hakuri Salma irin taki kaddarrar ke nan, gida zamu koma zamu nemi mai magani ." Cikin kuka kamar mace Aliyuu yake mata wannan maganar Bayan su karasa gida, Fatima tana zaune ta kara wayarta a kunne tana sauraran wani Littafi Sallama Aliyuu ya yi , amma bata ko kulasu ba , yarinyar data rako Salma ya nuna mata dakin Salma ta shige da ita , kana ta fito ta tafi , Aliyuu yana ciro naira 50 yana bata . "Yanzu rashin mutuncin ki yakai haka Fatima, mu shigo ko kallo bamu isheki ba." Duk da ya yi wannan maganar ko a jikinta, volume din Littafin ta karo . "Fatima da zarah kashi na 57 , mai sauraro mun tsaya daidai gunn." Hannu yasa ya zaro wayar ya wurgar da ita saida ta rabe gida biyu . Wani gigitaccen kuka Salma ta fashe dashi sakamakon yadda taji Fatima tana sauraran Littafin ta , amma gata cikin gidanta ba tare da tasan ita ba ce . Irin rayuwar da Salma suka ringa yi ke nan cikin wannna gidan har kimanin wata biyu, sai Fatima ta gadama zata taimaka wa Salma da wulakanci, Aliyuu yasha danko mata masu aiki domin su kula da Salma, amma basa zama , saboda Aliyuu ba ya iya biyansu Karfe 11 na dare Aliyuu ya rufe shago ya dawo, bayan ya yi wanka ta kawo masa abinci. Ba tare da ya bude abincin ba ya kalli Fatima da cewa. "Ina kika je dazu , na aike ki gidan Baba ne." Ajiyar zuciya tai kana ta ce . "Tom naga dai Baba ta dawo jiya,lefi ne dan naje ña gashsheta , ta ce kuma karka fita koina ka jirata da safe tana zuwa." Ya mike ya shige daki yana cewa."Dauke abincin ki." Gombe state Akko local government Yayan baban Aunty Hauwa ne shida matarshi har wajen 11:29 sai hira suke matar tashi ce take cewa. "Tom ni ai ban yi mamaki ba , dan hajjiya Aisha ta yi haka ." Mijin na ta ya ce "Hmm tom ai ke abin da baki sani ba ,duk wannan baya damun Hauwa'u, wannan yarinyar Salma da ba a san ina take ba , shi ne babban tashin hankalin Hauwa'u, ta ce mini kullum saita kira number ta ko Allah zaisa a samu , wani karin abin ma ta ce ba yanzu zata dawo ba , sai nan da wata 4, wani aikin ya kuma bullo musu ." Matar tashi ta ce "Allah sarki Hauwa, Allah dai ya bayyana yarinyar ko hankalinta ya kwanta." Ya ce . "Amin ." Washe gari da safe misalin karfe 8, bayan Aliyuu ya yi wanka ya tsaya jiran mahaifiyarshi. Ba zato yaji sallamar ta a kunnuwansa , da firgice ya mike ya fice yana amsa sallamar yana cewa. "Sannu da zuwa Baba." Baba da idanunta taji kwalli , irin mutanen nan ne da suka ga yau suka ga jiya , idanunta a bude . "Ki shigo ciki baba.". Aliyuu ya fad'a yayin da Fatima ke fitowa "Ba zama nazo ba Aliyuu, ina son yanzu ka kori yarinyar daka kawo gidanka take tsiyata ka , kake ramewa , dube ka ." Ta nunashi da hannunta jajir yasha kunshin tsofaffi Dogon numfashi Aliyuu yaja yana cewa. "Baba ki yi hakuri mana , wallahi duk abin da Fatima ta zo ta fad'a miki ba gaskiya bane ." "To mene ne gaskiya, me yasa kai baka zo ba , tun shekaran jiya na dawo , ammma babu kafar ka cikin gidan me yake faruwa."? Saida Aliyuu ya yi nannauyar ajiyar zuciya yana kallon matarshi, sannan ya ce . "Baba , dan Allah ki zauna mi magana zaki fahimce ni ." Tsawa ta daka masa da cewa. "Ina wasa da kai Ali, wa ce ce wannan yarinyar kuma tana ina."? Murmushi Fatima tai tare da nuna farin ciki. "Abin da yake faruwa Baba, wannan yarinyar bata da lafiya tsawon watanni 3 yanzu ke nan." Aliyuu suna tsaye kemm ya gama bawa mahaifiyarshi labarin Salma tun a ranar da ya ganta kofar gidansa, har zuwa wannan ranar." Salma dai tana daki tana kuka tare da tunanin idan tabar nan ina zata nufa a wannan mawuyacin yanayin . "Ina yarinyar take ." Baba ta tambaya bayan ta gama sauraran labarin ta . Da hannunsa Aliyuu ya nuna mata dakin Salma, kana Baba ta taka ta shiga dakin, suka bita a baya . MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 27&28 "Assalamualaikum." Baba ta fad'a tana shiga cikin dakin Idanun Salma kamar mai gani cike da hawaye ta amsa sallamar Baba ta dubi hannunta ta dawo ta dubi idanunta "Innalillahi wa innailaihir rajiun." Abin da ta fad'a ke nan ganin yadda Aliyuu yake bata labari lamarin duk ya wuce nan . "Ba kwa gyara mata daki , dubi sai zarni, barinta kuke tai Kashi da fitsari anan ."? Tai tambayar tana kallon Fatima murmushin farin ciki ne ya rufe Aliyuu ganin yadda mahaifiyarshi ta fahimta, domin a kullum ita ke fad'a masa ya yi adalci ya yi taimako tabbas zai ga cigaba a rayuwar shi .Gashi kuwa bata ba shi kunya ba Kusa da Salma ta matsa tare da d'ago ta suka fito waje, kai tsaye ta wuce ban daki da ita , ruwan zafi ta samu ta wanke Salma tass har kanta saida ta wanke , sannan ta debo kayanta nan ma ta wanke su, bayan ta gama ta share dakin nata , ta yayyafa ruwa ta goge shi, sannan ta shiga dakin Fatima ta dauko turaren wuta ta kunna cikin dakin Salma. Duk Aliyuu yana tsaye yana bin mahaifiyarshi da kallo ta gama wannan aikin, domin ta matukar faranta masa rai sosai ba kadan ba . Bayan duk ta gama wannan ta maida Salma daki, ita kanta taji dadin jikinta sai murna take tana godiya. Hatta wajen sana'arshi Aliyuu bai iya fita ba , saboda wannan yanayi Baba ta zauna dakin Salma, Aliyuu ma ya shigo tare da Fatima tana ta fishi . "Bazan iya dena godiya ba , na gode sosai Baba." Salma ke nan Murmushi Baba tai tana cewa. "Babu komai yarinya, ai duk wanda ya taimaki wani , to shima Allah bazai barshi ba , sannan ni suna na Baba Laure wato mahaifiyar Aliyuu, saboda haka ina nan zan kula dake harki samu lafiya." Jin hakan yasa Salma ta fashe da kuka Aliyuu ne ya rarrasheta ya kwantar mata da hankali Jimmm Baba Laure tai tana kallon Salma "Baba ko akwai wani abin ne."? Inji Aliyuu Baba Laure ta d'ago kai tana cewa. "Dama kin ta'ba yin irin wannan abin ne ko yaya."? Salma tana share hawaye ta ce . "A'a Baba, lokaci guda abin ya sameni ." Jin amsar salma yasa ta kalli Aliyuu. "Yanzu wanne maganin ake yi."? Cikin karfin gwiwa ya ce . "Baba wani magani ne , saboda munje asubiti har guda biyu , amma sun ce ba ciwon asubiti ba ne ." Baba ta girgiza kai tana cewa. "To babu ko shakka wannan sihiri ne akai wa wannan yarinyar." Gaban Aliyuu faduwa ya yi . "Sihiri kuma Baba, me wannan yarinyar ta tsarewa wani ." Baba ta ce . "Aliyuu mu muka san duniya babu inda bamu shiga ba , saboda haka ina tabbatar ma wannan sihiri ne aike ne akai mata." Wani iri Salma taji a ranta , to waye zai mata wannan abin, babu wanda yasan da zaman ta, tunanin da take yi ke nan "To mene abin yi yanzu."? Aliyuu ya tambayi Baba Laure Girgiza kai Baba tai kafin ta ce . "Akwai wani babban malami a Katsina naga irin yadda yake aiki sosai kan irin wannan matsalar, indai ya yi maka magani baka warke ba , to tabbas cutar ajali ce ." Rassss Salma taji a zuciyarta "To mu kaita mana Baba." Da sauri Baba ta kalleshi. "Kai baka da hankali ina muka ga kudi , yana karbar kudade sosai." Salma ta sauke ajiyar zuciya yayin da shima Aliyuu ya zube tashi "To haka zamu barta yanzu ke nan Baba."? Ya tambaya cikin damuwa Kafin Baba Laure ta ce komai Fatima ta ce . "To ai naga cewa tai Auntinta wata biyu zatai ta dawo, yanzu gashi har wata uku sai ta koma garinsu ." Aliyuu ya jefawa matarshi wani kallo Baba ce tai magana da fad'in. "Tom babu inda zata , mu zamu nemi kudin gurin yan uwa da abokan arziki ai mata magani, yaushe kika zama mara tausayi Fatima, ke yanzu ace ke ce cikin wannna halin a dauke ki akaiwa yan uwanki dadi zasu ji , bari wannan yarinyar da bata da gata sai Allah." Salma tai kasa da kai tare da hawaye Aliyuu ya yi murmushi ya ce . "Allah yaja da ranki uwata , Allah sa aljanna makoma ." Baba Laure ta ce . "Amin dan albarka ta shi ka tafi wajen nemanka , nima zan fara samo wani abin." Aliyuu ya ce ."To Baba nima akwai wasu sittiru na masu kyau, zan kaiwa Salisu mai dinki ya siyar dasu , a yi a had'a kudin nan ." Baba tai murmushi tare da fad'in. "Yaron kirki ka gado mahaifinka, Allah ya jikanshi da rahma, Allah ya yi wa nemanka albarka." Ya amsa da."Amin babata saina dawo." Sannan ya wuce ya tafi Sokkoto ❤️ Karima ce zaune cikin falonta, yau kimanin wata uku da kwanaki bata ganin posting Littafin wannan marubuciya, har number ta ta dauka ta ce ."Aslm." Ammma har yau babu alamun hawanta, sau da yawa tana gwada kiran number ta, amma bata samu, tana tunanin ko a wanne irin hali take ciki Allah masani . "Salamu alaikum Aunty." Hadiza ta shigo ta zauna a kujerar kusa da ita , da sauri da firgita Karima ta tashi , sannan tai ajiyar zuciya "Wai Aunty tsoro na baki ne haba ." Murmushi Karima tai tana cewa. "Eh mana bansan kin shigo ba ." Dariya Hadiza tai , sannan Karima ta zame ta zauna a kasa tana dafa kirjinta, domin ita Karima yanzu tana matukar jin tsoron Umma da Hadiza, hatta hira bata sakewa su yi kamar daah. Wayarta Hadiza ta cigaba da dannawa Sai dariya take ganin irin yadda ake tambayar cigaban Littafin HIJIRA na Autar marubuta, mutane ba adadi "Aunty Karima sauran wata 4 fa biki, dazu sultan yake cewa na gashsheki, kin ga yadda ya kara kyauu kuwa, gaskiya Germany ta yi, ya ce sai mun yi aure zamu koma tare ." Murmushin yake Karima tai tana cewa. "Tom Allah ya kaimu musha biki." Kano State Tarauni Anan kuwa umman Salma ana zaune ana hutawa, an gyara gida , gida yayi matukar kyau sosai , an sha kyau an gyara koina an yi fenti an sa tayil, har babbar waya Umar ya saiwa Umma, suturu kuwa kala kala alhamdulillah. Umma ganin karfe 4 ta yi yasa ta mike ta dauko redionta , kana ta kamo daya daga cikin tashar da take yawon sauran. "Assalamualaikum masu saurare yau zamu fara kawo muku sabon Littafi, duk da cewa ba sabon Littafi bane a gurin mutanen da sukai following YouTube channel din mu , aje ayi subscribe a danna mata kararrawa mun gode." Kana aka saki wani sauti mai taushi Umma tana zaune tana kasa kunne domin jin an fara wannan labarin, tsabar kewar Salma yasa Umma ta koyi sauraran novel, saboda Salma kullum sai tasa wannan redio ta saurara, daga lokacin tafiyar Salma zuwa yanzu taji su da dama , kuma taji tabbas akwai Basira da tarin nasihohi da tarbiya harda zaman ta kewa da ake dauka , ba kamar yadda Alaji Yusuf yayan baban Salma ya fahimci marubuta ba . "Fatima da zarah. Mallakar Autar marubuta." "Kashi na daya ." Kan Umma ne ya sara mata, har saida tasa hannu ta rike , cikin wannna yanayin Umma ta cigaba da saurarar labarin da aka fara shi da kasar saudiya. "SAUDIYA." "Dawowarsu ke nan daga asubiti , Najib da Ahmad tare da mahaifiyar su da bata da lafiya, eh tabbas wannan iyalin kana iya ganin tsantsar soyyayar mahaifiyarsu..." Umma ta kasa kasa kunne don jin yadda wannan labarin zai kasance.... Autar marubuta 🥰 MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 29&30 Baba Laure ce zaune tsakar gida tana yi wa Salma kitso, zanen hausa take rangada mata a kanta mai matukar kyau, gefe guda kuma ga Fatima can tana iza wuta Aliyuu ne ya shigo yana yin sallama, murmushi ya jefawa mahaifiyarshi da cewa. "Babata ta kaina." Kana idanunsa suka kai kan Salma idanunta sama kamar shi take kallo, sai dai bata iya ganin komai. Shagala ya yi da kallon Salma irin yadda wannan kitso yayi matukar fito da kyawunta "Allah ya yi halitta, kodai kyan wannan yarinyar ne yasa akai mata wannan sihiri." Abin da Aliyuu yake fad'a ke nan a zuciyarshi, ganin yadda ya shagala da kallon Salma yasa Fatima ta taso ta bangaje shi ta wuce tana harararshi. A wannan lokacin ya dawo hayyacinsa yana murmushin ya'ke "Tom mene ne ya dawo da kai ne ."? Cewar Baba Laure, saida ya sosa 'keya sannan ya iya cewa. "Baba daman kawu Tanimu ne ya kirani , ya ce ya turo dubu 20 a had'a ai wa Salma magani ." Baba Laure ta ce . "To Masha Allah, Allah ya saka muna godiya, amma banda abinka basai ka bari saika dawo ba , sai kawai ka kamo kafa ka taho ." Ya murmusa yana sunkuyar da kai "Da Allah kama hanya ka tafi mana, kasan muna neman kudi gashi yanzu har an sake wata guda wannan kudin basu hadu ba ." Wayar Aliyuu ce ta fara ringin , yasa hannu ya cirota a aljihunansa Dariya ya yi yana cewa. "Baba mutuminki ne Sa'adu yake kira." Ya d'aga wayar yana sata a spiker Baba tana dariya "Salamu alaikum." Sa'adu ya yi sallama, Baba ce ta amsa masa tana cewa. "Sa'adu ya gidan ya katsina." "Sa'adu ya ce lafiya lau babarmu ya mutanen gidan." Ta ce . "Alhamdulillahi Sa'adu ya manyan naku." Ya mayar mata da fad'in. "Lafiya lau, daman na kira na fad'a miki ne gobe Malam Shafi'u zai tafi Niger, to naji kuma kina cewa zaku kawo yarinya ai mata magani, nace bari na sanar dake." Da sauri Baba Laure ta saki kan Salma ta mike tsaye tare da cewa. "Niger zai tafi gobe kuma ."? Ya ce . "Eh wallahi Baba Laure." Ta ce ."To shi ke nan Allah ya kaimu goben." sannan sukai sallama ya kashe , cikin tashin jin dadi Aliyuu ya ce . "Tom Baba mene abin yi ."? Ta kalleshi da cewa. "Mene abin yi kuwa Ali , yanzu yanzu sai Allah zamu tafi katsinan , kaje tasha ka samo mana mota ." Zaro ido ya yi yana cewa."Yanzu kuma baba kudin fa basu hadu ba ." "Babu wannan zancen Ali , tashi Salma." Ta d'ago Salma tsaye "Kaje ka samo mota , kudin ko a can zasu hado." Aliyuu ya juya da sauri yana cewa. "Tom bari na samo mai motar." Masha Allah Hadiza an yi kiba bulbul, sai shirin aure ake , irin yadda take son Sultan ba a cewa komai , mu dai sai dai mu ce Allah sa a yi damu wannan gagarumin biki . Washe gari Katsinawan dikko, kunya gareku badai tsoro ba 😌 A daren jiya su Baba Laure suka isa garin Katsina, aiko gari yana wayewa tun asubar farko suka nufi gurin Malam Shafi'u, sun tarar da layi sosai kafin a zo kansu . Bayan Malam Shafi'u ya ga Salma ya tabbatar musu sihiri ne gami da aiken àljanu akai wa Salma. Sai dai Salma abin yana matukar bata mamaki, wane zai mata sihiri a wannan duniya me take dashi Malam Shafi'u ya debo ruwa cikin wani 'ko'ko , kana ya zuba ganyen magarya ciki, ya kaishi gaban Salma tare da fad'in. "Karanta ayatur kursiyu ki tofa a ciki ." Kamar yadda ya bukata haka Salma tai kana bayan ta gama ya ce tasa hannayenta a ciki, bayan ta zasu ya dauki carbi yana ta ja , ko mene yake cewa Allah masani "Rufe idanunki." Ya fad'a Ta rufe , cigaba ya yi da jan wannan carbin wajen minti talatin, daga bisani ya fara karanto wasu ayoyi da surori cikin Littafin Allah mai girma. Kuka Salma ta fara yi , sakamakon irin zafin da take ji a duk jikinta, jinta take kamar ba ita fa , wajen awa daya da rabi sukai a haka , sannan ya ce ta cire hannunta ciki, ta cire aka dauke 'ko'kon daga gun Hannu Malam Shafi'u ya d'aga sama yana addu'a yana kuka Shi dai Aliyuu yau yana ganin abin mamaki, ita ko Baba Laure ta saba ganin wannan lamarin tun tana karama Bayan ya gama wannan addu'a ya aje carbin a gefe ya kalli Baba Laure yana cewa. "Wallahi aike ne , sai dai mu munfi karfin duk wani àljani , da ikon Allah da manzonmu Muhammadur...." Baba ta girgiza kai Mikewa ya yi ya debo wani kullin magani guda biyu, ya mikawa Baba. "Ku karbi wannan, saboda tsarin jikinta ga duk wani shedani, sannan a ja mata kunne ta dage da addu'a." Tasa Hannu biyu ta amsa tana cewa. "To malam." "Sannan kuma zatai cuta mai tsanani sosai, daso samu ne yau ku koma Bachin, sai dai in baku koma ba babu matsala, amma idan aka koma zai fi." Baba ta ce . "In Sha Allahu kuwa daga nan sai gida." Ya kallesu yana cewa ku je waje ku jira ta Su baba suna fita minti biyu, me yayiwa Salma Allah masani , ta mike ta fito idanunta a bude hannayenta sun dawo daidai. Kuka ta fashe dashi yayin da suka had'a ido da baba Laure, Salma ta zube kasa ta sume . Bayan kwana biyu Bauchi Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah, sai dai godiyar Allah, Salma a halin yanzu tana shan jinya Sosai da sosai, domin yanzu haka jini ake kara mata Irin yadda Fatima take ganin ana kulawa da Salma sai duk tsantsar kishi yake damunta, domin tana ganin karshen wannan lamarin to Aliyuu auren Salma zai . Bayan an cire mata wannan Karin jini bacci ne ya kwashe ta , ba ita ta farka ba sai karfe 9 na dare, abin yana matukar bawa Salma mamaki, wai idanunta sun dawo daidai, hannunta ma babu abin da bata yi dashi , duk da cewa tana cikin jinya Sosai amma idan ta dubi yadda take tana jin dadi ta gode Allah. Bayan ta tashi tashi aka bata ruwan zafi tasha, kana aka soya mata kwai kamar yadda ta nuna tana bukatar ci . Har kowa na gidan ya yi bacci, amma bata iya baccin nan ba , farin ciki da mamaki, bata ta'ba zaton zata tsinci kanta cikin wannna yanayi ba . Washe gari da safe , Baba Laure kamar wacce ake kora, tai wanka ta hado kayanta , tana gama karyawa ta ce yau sai gida , tsakar gida ta fito rike da jakar kayanta, hakan yasa duk suka fito "Baba yanzu fa karfe 8:45. Dan Allah ki bari rana tayi , ina nan ina gidanki." Cewar Aliyuu Baba ta ce . "Tom ai kaji mene ka ce , ina nan ina gidana, daman jinyar wannan yarinya ce ta zaunar dani." Ta nuna Salma "Yanzu kuma jiki Alhamdulillah zan koma zuwa gobe ko jibi nazo naga jikin nata ." Salma durkusa wa tai gabansu tana cewa."Baba hakika kun yi mini abin da bazan ta'ba mancewa ba , kuma kun yi mini sanadin farin cikin da bazan ta'ba gushewa ba , bani da abin da zan gode muku , Allah yabar zumunci ya bani ikon saka muku ." Murmushi Baba Laure tai tana cewa."Karki damu Salma, ki ci gaba da kula da kanki, idan kinji sauki kuma sai Ali ya kawoki gidana." Salma ta kalli Aliyuu tana murmushi da fad'in. "In sha Allah kuwa zan zo Baba." Baba ta ce . "Masha Allah, yarinya mai hankali da tarbiya, kowa zai so kizo a sirikarshi ko yarsa." Salma ta sunkuyar da kai. Wani mashi Fatima taji ya sokar mata zuciya, sabuwar kiyayyar Salma taji ta sake samun guri a zuciyarta Nan Baba tai sallama dasu kana ta wuce gidanta Salma shigewa daki ta yi ta samu guri ta zauna "Idan har sihiri akai mini wannan abin ya faru dani , to wane ne ? Na baro gida , kan karamin dalili,kamar dai mara hankali." Maganar da take cikin ranta ke nan sai ga Aliyuu ya shigo , matarshi Fatima dake biye dashi ta tsaya kofar dakin "Salma ya jikin."? Salma cikin girmamawa ta kalleshi da cewa. "Da sauki Yaya Aliyuu." Ya zura hannu a aljihunansa yana cewa."Allah ya kara lafiya." Wata kifat din Tecno ya zaro ya mika mata, kana ya mika mata sauran SMS dinta guda biyu da ya shigo dasu . "Ga wannan wayar second ce , ki yi hakuri da ita sai kisa layukanki ciki ." Hannu biyu tasa ta karba tai godiya tana cewa. "Na gode Yaya, Allah ya saka da gidan aljanna." Sannan ya fice ya tafi Cikin farin ciki Salma ta bude wayar tana saka layukanta ciki Cikin yanayin fusata Fatima ta shiga kichin ta dauko wuka , kai tsaye ta fad'a dakin Salma. MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 31&32 Salma tana d'ago kai ta ganta , da sauri ta mike tsaye tana jaa da baya . Idanun Fatima jajir tamkar wacce ta fita a hayyacinta . "Wato kin zo gidana , ki hanani farin ciki, kin yi cuta an miki magana, an sa miki jinin mijina, mahaifiyarshi tana yabonki a gabana, ya sai miki waya , abin da ya rage ki aure shi kooh." Salma da matukar tashin hankali take ja da baya tana cewa. "Wallahi Aunty Fatima ba haka bane , babu komai tsakaninmu saii.." Dakatar da ita tai tana d'aga wukar kamar zata caka mata "Kafin na yarga biyar , ki kwashe kayanki ki bar wannan gidan , idan baki fita ba wallahi saina kasheki Salma." Jikin Salma na rawa tai sauri ta zura hijabi, kawai tai waje babu ko takalmi sai wannan wayar a hannunta. Tana nishi da ajiyar zuciya ta fito ta tsaya "innalillahi wa innailaihir rajiun. Wannan matar kodai tana da àljanu, ko takalmi bata bari nasa ba ." Salma tai maganar tana haki, bakin titi ta nufa , duk ta rame tayi wani irin tsayi, tunanin ta kawai yanzu ta je ta hau motar Kano Ringin din waya take ta ji tare da ita , amma ta kasa sanin daga ina ne , sai daga baya ta lura ashe akwai waya a hannunta, ta dubi fuskar wayar yayin da akai kira biyu babu amsa . Kafin ta cire fuskar ta kan wayar sai ga wani kiran yana shigowa Kara wayar tai a kunne kamar mai jin tsoro "Hello." Muryar mace taji tana cewa. "Salma Salma." Salma ta ce ."Eh ni ce waye." Babu zato ba tsammani ta ji an ce ."Aunty Hauwa ce Salma kina ina ne ."? Wani rasss taji a ranta da faduwar gaba "Aunty Hauwa ke ce ." Kawai ta fashe da kuka Wani farin ciki Aunty Hauwa taji ya rufeta, ko tsayawa rarrasheta batai ba ta cigaba da cewa. "Kina ina duk inda kike ki taho Salma na , na dawo ." Cikin kuka da matukar shauki Salma ta fara mata magana."Ina Bauchi Aunty amma gani nan yanzu zan taho , sai dai hajjiya Aisha ta siyar da gidan."😭 Murmushin farin ciki Aunty Hauwa ta sake yi tana cewa. "Na sani Salma ki hawo mota ki taho idan kin zo zan miki kwatancen sabon gidanmu." Salma ta share hawaye tana cewa" To Aunty amma babu komai a gurina babu kudi wallahi yanzu ma daga wani gida aka koroni bani da lafiya." Ajiyar zuciya Aunty Hauwa tai kana ta ce . "Tom ki samu wani ya kawoki idan kun zo sai na bashi kudin, idan bai yarda ba kice za a ninka masa ." Da sauri Salma ta nufi tasha kamar zata fad'i, sam ta mance ma babu takalmi a kafarta, mutane kuwa sai kallonta suke , daga taje gurin wannan mai motar sai taje gun wannan, haka ta samu wani ta ce Gombe zai kaita ita kadai , da kyar ya yadda sai da ta hadashi da Allah da annabi sannan ya ce ta hau , suka tafi. Matukar shauki da farin ciki take ji kamar tai fiffike ta sauka a Gombe, sam ta mance ma bata da lafiya, haka suka ringa tafiya har suka fara shiga birnin Gombe Wajen karfe biyu Aliyuu ya shigo gida , ganin takalmin Salma zube a kofar dakinta, yasa shi mamakin me yasa bata fito ta ce masa sannu da zuwa ba kamar yadda ta saba "To ko dai jikin ne."? Ya tambayi kanshi "Salma." Yaji shiru "Salma." Fatima ta fito a daki fuskaantar babu annuri "Na koreta ta tafi inda ta baro, tunda nan dai ba gidan ubanta bane ." Wani yammm Aliyuu yaji maganar kamar da wasa, ya leka takin nata . Sai dai ga komai nata nan , hakan yasa bai yarda ba Ganin bai yarda ba ya sake fusata Fatima tana cewa. "To wallahi na koreta babu ko takalmi, shegiya matsiyaciya , harda wani sai mata waya , daga nan kuma ka ce zaka aureta ko." Da sauri Aliyuu ya juyo tare da mamaki sosai. "Wai dan Allah da gaske kin koreta, baki da hankali ne Fatima, mene ta tsare miki." Yayo kanta da jajayen idanu kamar zai daketa "Saboda ba gidan ubanta bane, ba kuma na mijinta ba ." Jin zancen shirmen dake fitowa daga bakin Fatima ya sake bakanta masa rai . Ganin karya 'bata lokaci yasa ya fice da gudu, neman Salma ya shiga yi lungu da sako ko Allah zaisa ya ganta , haka har yaje tasha yana ta tambaya, nan ya samu wasu suke tabbatar masa ta hau mota zuwa Gombe kuma tun dazu ne, yanzu baza ta gaza zuwa ba . Bakin ciki da takaici ne ya turnike masa zuciya, cikin kasala ya nufi gidan mahaifiyarshi Baba Laure tana zaune gama cin abincinta ke nan ya samu guri ya zauna bayan sun gaisa . "To ko jikin Salman ne , mene yake faruwa."? Ta tambaya domin ta ganshi a wannan yanayi. Sai da ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara cewa. "Wallahi Baba shigata gida ke nan yanzu, wai Fatima ta kori Salma tsabar rashin mutunci." "Aliyuu ban gane me kake magana ba , dazu fa na baro gidan , kamar ya ta koreta me tai mata ."? Cewar Baba Laure da ita ma labarin bai mata dadin ji ba Aliyuu cikin yanayin rashin walwala ya ce ."Baba gaske nake miki, yanzu ma daga Tasha nake , an ce mini ta hau motar Gombe, yanzu ma taje." Baba ta rike haba tana cewa."Innalillahi wa innailaihir rajiun meke damun Fatima, wannan wanne irin rashin hankali ne , yanzu ya za ai."? Aliyuu ya maida mata da cewa. "Babu yadda za ai kuwa Baba , domin ni ko number Salma bani dashi ." Baba ta girgiza kai. "Wannan matar taka ko 'yar banza wallahi, an yi shasha sha." Aliyuu ya zame ya kwanta bisa wannan tabarma Anan kuwa Salma da driver suna tsaye suna jiran ganin ta inda Aunty Hauwa zata bullo Wata mota Salma ta ga ta nufosu blue mai bakaken murfi . "Motar Aunty Hauwa ba blue ba ce ." Cewar Salma tana sake hangawa Bayan motar ta tsaya ko gilashi ba a bude ba , kawai aka bude kofar motar . Da gudu Salma ta nufi Aunty Hauwa ta rumgumeta da matukar kewa da farin cikin yadda ta ganta , amma tun da farin Aunty Hauwa abin data fara lura dashi Salma ta rame sosai babu ko takalmi kuma a kafarta. Driver da ya kawo Salma ya yi murmushi yana cewa. "Kai ai dah raina wannan yarinyar nake , ashe yar masu kudi ce . Bari naje a sallame ni ." Ya matsa kusa yana wata far'a Hawaye har sun kawowa Salma, ta kalli wannan driver tana cewa."Aunty ga wanda ya kawoni , duk cewa suke baza su zo wata Gombe ba , shi ne ya taimaka mini . " Jin haka yasa ya yake hakora "Allah sarki, mun gode bawan Allah." Cewar Aunty Hauwa tana zura kai a mota , kudi ta ciro kimanin dubu 30 ta mika masa, cikin murna yasa hannu ya karba ya gamsu shimm ya yi godiya. Hakan yasa Salma suka shige mota suka fara tafiya. Rufe idanu tai tana wata nannauyar ajiyar zuciya, yadda tai kewar sanyin motar Aunty Hauwa yasa ta tuna farkon haduwarsu, har lumshe ido take tana jin cewa tabbas duk kan wahalar ta ta kare . Aunty Hauwa kamar tasan tunanin da take , ta kalleta tana murmushi kafin ta ce .. "Salma wayata aka sace mini sam ban kula ba , har saida muka je Dubai , ki gafarta mini." Jin hakan yasa Salma ta bude idanunta. "Aunty na sani , domin kuwa Anas shi ne wanda ya sace miki waya bayan ya rakoki, har gida ya zo da ita , sannan suka koreni suka siyar da gidan ." Aunty Hauwa ta sha kwana , sannan ta kalli Salma tare da maida hankali zuwa tukinta tana cewa. "Daman Anas ne ya sace mini waya , lallai yaron nan , ai yanzu zancen da nake miki hajjiya Aisha tana cann an kulleta, domin tunda na dawo na shigar da ita kara, dukkan duniyar mahaifina ta dawo gurina ." Jin hakan ya sa ran Salma sanyi , ta sake furzar da iska Wani gida Aunty Hauwa tai parking motarta bai kai wancen girma ba , amma yafi wancen kyau sosai da kayan more rayuwa, gidan a bude yake suka sa kafa suka shiga . MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 33&34 Suna shiga ciki , sabuwar yar aikin Aunty Hauwa dake zaune falo tana kallo, ta sake rissinawa tana cewa. "Sannu da zuwa Aunty." Aunty Hauwa ta kalleta tare da zama a kujera tana cewa."yawwa sannu Farida, fatan kin dorawa Salma ruwan wankan da nace ." Cikin girmamawa Faridan ta ce ."Na dora Aunty, har abinci ma an gama ." Ta ce "yawwa." Salma tai murmushi sannan ta nemi guri ta zauna , yayin da Farida take shigewa ciki . Ajiyar zuciya mai zafi Salma ta sauke ."Aunty wannan gidan ya yi kyau sosai." Ta fad'a tana duban koina Aunty Hauwa ita ma ta murmusa tare da fad'in."Tom Salma kije ki fara wanka , ki ci abinci sai kiyi sallah." "Tom Aunty." Salma ta fad'a tana bin hanyar da Farida tabi , ba tare da tasan ina ne a cikin gidan ba , bayan Salma tai wanka , ta saka wata atamfar Aunty Hauwa, sannan ta fito falo ta saka sallaya ta fara sallah, daidai lokacin data idar da wannan sallar, ita kuma Aunty ta gama cin abinci Shiru Salma tai tayi zuruu , hakan yasa Aunty cewa. "Salma ga abinci nan." Ta nuna mata kular dake gefe tare da ruwa da lemo "Gaskiya kin rame sosai Salma." Saida Salma tai murmushi ta ce . "Ai Aunty nayi kiba ma , nasan yanzu Yaya Aliyuu hankalinshi yana tashe shi da Baba Laure." "Su waye su , baki fad'a musu zaki dawo bane , sannan ina babbar wayarki , kullum ina kiranki Salma, ammma shiru , kuma ke baki neme ni ba ." Aunty Hauwa tai magana cikin damuwa, zama Salma ta gyara kana ta ce ."Hmmm Aunty ke nan, na yi zatan mutuwa zan wallahi, ashe zamu sake haduwa." Aunty Hauwa tai dariya tana cewa. "Salma wai mene ya kai ki Bauchi to."? Jin wannan tambayar yasa Salma ta fara bata labari , tun daga ranar data sa kafa ta tafi Dubai, har zuwa wannan ranar "Innalillahi wa innailaihir rajiun, Salma makancewa fa kika ce." Aunty Hauwa bayan ta saurari duk labarin abin da ta ce ke nan. "Hmmm Aunty ke nan, harda kuturta ma kuwa." Girgiza kai Aunty tai kafin ta ce . "Abin mamaki tom wane ne zai miki sihiri Salma, gaskiya su Baba Laure sun yi kokari, in sha Allah zamu kai musu ziyara da zarar aiki ya ragarmin." Ta sake muskutawa tana cewa. "Ikon Allah Salma, gaskiya kina shan wahalar rayuwa, amma in sha Allah yanzu ta kare , ko yaushe na kira wayarki a kashe , Allah sarki." Salma ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi "Tom ki ci abinci Salma ni yanzu zan fita wani aiki, duk abin da kike bukata ki yi wa Farida magana." Ta karasa maganar tana mikewa tsaye Salma ta ce . "To Aunty a dawo lafiya." Har ta kai kofar falon sai ta juyo tana cewa. "Idan na dawo kuma da dare ,zamu je shopping daga nan sai ki siyo waya da laptop din ki ." Jin dadin hakan yasa Salma ta washe baki tana cewa. "Na gode Aunty a dawo lafiya." Sannan ta fice ta tafi Ajiyar zuciya Salma tai mai matukar girma, sannan ta jawo wannan abincin ta fara ci . Bayan kwana biyu Alhamdulillah Salma dai sai farin ciki, a halin yanzu tana zaune dakinta tana danna laptop, har an yi kiba an yi kyau . Aunty Hauwa ce ta shigo ta zauna, hakan yasa ta aje duk abin da take yi tana fuskantar Aunty da cewa. "Aunty lafiya. Naga jikin ki duk a mace ." Aunty Hauwa tai murmushi tana fad'in. "Kai Salma baki ga daidai ba , daman ina so na sanar dake akwai wani babban shago dana siya, tom akwai abaya a ciki , atamfofi da sauran duk kayan mata , to Salma babban shago ne , akwai ma'aikata , ina so gobe ki shirya muje , domin zan mallaka miki shi ." "Me kika ce Aunty."? Cewar Salma Aunty Hauwa tai murmushi tare da mikewa tsaye tana cewa. "Ai kinji duk me na fad'a, kuma bana son godiya." Tana gama maganar ta fi ce Ai Salma ji take kamar ba ita ba ce , irin wannan babban magana, tom sai dai mu ce Allah ya tabbatar da alheri, aiko washe gari da safe , suka shirya suka tafi wannan babban shago , aka nunawa Salma komai , sannan Aunty ta wuce office Anan kuwa Hadiza ce a online. Bude datarta ke nan ta ga sabon update na cigaban Littafin HIJIRA na Autar marubuta Yadda ta ga ana posting dinshi a koina take mamakin yadda wannan abin ya faru . Kai tsaye ta nufi Facebook shafin Autar marubuta "Alhamdulillah masoyana na dawo , cikin ikon ubangiji bayan doguwar jinya , na yi kewar ku sosai." Abin da ta gani ke nan, kwana daya da rubutawa Hankalin ta ne ya tashi ganin wannan lamarin, like dubu biyar akai wa wannan Post na Salma, banda comments marasa adadi , zazzafar ajiyar zuciya tai , tana cewa."Kutumar u..."🤭 Cikin mamaki take sanar da mahaifiyarta, yayin da Umma take tambayar ya za ai , Hadiza ta ce abar mata komai a hannunta Karima kuwa kullum tana sauraran Littafin Fatima da zarah da ake yi a gidan redio, Littafi ne mai yawan gaske , domin kuwa har yau ba a kammala ba , wayarta ta lalace hakan yasa Karima bata WhatsApp, sai idan an karbo daga wajen gyara Sunan Autar marubuta ya yi shura sosai, hatta a masana'antar kannywood saboda irin fina finai da take rubutawa, sai dai ana kawo mata gayyata sosai daga gidajen television domin hira da ita , sai dai Salma bata amsar wannan bukata, ta ce akwai lokaci Sir Sadiq Abubakar yana matukar farin cikin yadda Salma take tare dasu har yanzu, ita ma Aunty Hauwa ba karamin alfahari take da Salma ba, sai dai duk yadda zatai alfahari da ita, to Salma tana ninka wannan adadin tana alfahari da Aunty Hauwa Tana cikin falonta, gefe aje da shayi, tana rubuta wani fim , Aunty Hauwa ce ta kwala mata kira tana daga falo , hakan yasa Salma tashi ta nufi falon, zama ta yi tana cewa. "Aunty meke faruwa." Aunty Hauwa ta ce . "Gaskiya Salma na yi mamaki sosai, ki dubi adadin ribar da kika samu 2 millionaire Salma, cikin kankanin lokaci, Allah yayi wa rayuwar ki albarka, sai dai daga yau duk abin da aka samu kar naji labarin, domin sirrin ki ne ." Dariya Salma tai tana cewa. "Kai Aunty." Ita ma dariya ta yi tana cewa. "Sannan kuma an kirani daga gidan redion Kano Salma, akwai abokin aikina a can , ya ce kuma sun nemi hira dake , amma baki amince ba , tom dan Allah Salma ki amince ." Saida tai ajiyar zuciya mai zafi, sannan ta ce . "To Aunty, ai duk abin da kika ce mini wajibi na aikata, kinfi karfin wannan, su ne mutanen farko dazan fara hira dasu ." Aunty Hauwa ta ce . "Yawwa kanwata , Allah ya kara Basira da lafiya da nisan kwana, sannan kuma tare zamu je kanon , daga nan zamu biya gidan yayan baban nan naki ." "Saboda nima zan yi kwana uku bana aiki a lokacin." "Tom Aunty." "Amma Aunty ina so daga nan zamu je Bauchi, domin ganin su Inna, ina so na saiwa Yaya Aliyuu mota." Murmushi Aunty Hauwa tai tana cewa. "To Salma rigima, banda abinki ai ni Baba Laure ya kama ki yiwa wani abin. Ammma tunda haka ne , akwai tsohuwar motata, sai a bashi , ita kuwa Baba Laure zuwa hajjin bana ki shirya zuwa da ita ." Ta karasa maganar tana dariya Ita ma dariya sosai Salma tai , kafin ta ce ."Tom shi ke nan Auntyna. Allah ya saka da alheri na gode ." Aunty Hauwa ta ce ."Babu komai ai Salma, mahaifina yabar mini dukiya mai yawa, zan yi amfani da ita domin gina lahirarsu da tawa. Sannan kuma yau zan bada akai motar Kano, idan munje sai a dauka danke baki iya mota ba ." Tai dariya tana cewa."Aunty banda gori ." bayan Salma ta koma daki , ta tsaya ta yi jimmm Cikin zuciyarta take cewa. "Tabbas lokaci ya yi dazan fadawa Aunty Hauwa gaskiya koni wace ce, domin na gaji da yaudarar ta, Allah yasa ta fahimce ni ." Taji wasu hawaye Karima da Adam ne suke karyawa, farin ciki ya ishi Karima, domin kuwa jiya da dare bayan ya dawo ya taho mata da wayarta, sannan yake tabbatar mata yanzu idan ya fita zai sa a sako mata data "Wai kuwa kin karbo dinkin ki Karima, bukin nan fa sauran kwana biyu." Cikin shagwababbabbiyar murya Karima ta ce da mijin nata "Ni ban karbo ba , kai ne zaka anso mini." Ya kalleta da cewa. "Ni kuma , ina ni ina shiga gidan mata ." "Ni dai ba ruwana." Cewar Karima Mikewa Adam ya yi ya dauki jakar shi ."Tom ni dai zan tafi my love ki kula da kanki ." Nan ta mike sukai sallama sannan ya wuce gun aikinshi na asubiti MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 35&36 "Jama'a anan muka kawo karshen wannan Littafin namu mai suna Fatima da zarah." "Na wannan shahararriyar marubuciya Autar marubuta." Umman Salma ke nan dake sauraran redio. Nan ita ma Karima tana zaune tana bude WhatsApp take sauraran wannan gidan redio, daidai lokacin da yake cewa. "In sha Allahu gobe misalin karfe 4 na yamma zamu kasance tare da wannan marubuciya a wannan gidan mai albarka." "Ga duk masu son turo sako zasu iya fara turowa tun yanzu a wannan number kamar haka."... Sai ga Hadiza ta shigo Firgita Karima ta yi ganin Shigowar Hadiza, domin kullum Karima bata barin Hadiza taji tana sauraran Littafin Autar , "Gaskiya ne Aunty ki ce kema kina yin wannan marubuciya." Cewar Hadiza Hade rai Karima tai sannan ta ce ."Ina fa , kawai ina kamo tashar naji ana fad'a, to amma naji ya ce za a gayyato ta , taji sauki ke nan."? Ajiyar zuciya mai zafi Hadiza tai , sannan ta fara cewa. "Shegiya ba , ai Aunty Karima ki bari kawai, gobe ranar aure na , kuma gobe sai na yi ajalin wannan yarinyar, farin ciki biyu, ki duba fa wannan fim din da ake mai suna Zumunci ita ce writer fa ." Murmushin yake Karima tai sannan ta kashe redion. Hannun Hadiza ta ja wo tana zaunar da ita ."Haba Hadiza, me ne wai wannan marubuciya tai miki, kisa fa ba abin wasa bane ." Hadiza ta janye hannunta tana cewa. "Wannan yarinyar sunanta Salma Aminu kuma 'yar tarauni ce a Kano, shekara wajen biyu ke nan da guduwa daga gidansu , dan kawai tana so tai gasa dani a duniyar marubuta, na tsaneta wallahi Aunty." Wani faduwar gaba Karima taji da tashin hankali. "Salma kuma ." Ta maimaita sunan cikin tashin hankali "Eh sunanta Salma a tarauni take . Ko kin santa yar Kano ce ." Sai da Karima ta fara mutuwar zaune, kana ta jingina da kujera."A'a bansan ta ba Hadiza, amma yanzu ta ya zaki kasheta kanon zaki je ke nan."? Jin hakan yasa Hadiza dariya ta ce . "Haba Aunty, nima fa yar kano ce , kuma ita yanzu tana Gombe, amma gobe zata zo gidan redio, kuma nasan wanne gidan redion ne , shi yasa tun jiya na kira wani domin a gama da ita ." Karima jin kanta tayi ya kuma mata nauyi sosai . "Kamar ya to."? Ta tambayi Hadiza "Zai tsaya da babbar mota, nasan da cewa a mota zata zo Kano , kafin ta karasa gidan redion ta mutu , shi kuma ya fito ya gudu , zan kasheta tun kafin iyayenta su san tana raye , domin har yau bata koma Kano ba ."Tana gama fade ta mike tsaye "Aunty zanje salun ne fa , zuwa anjuma zan dawo ." Karima ta ce . "Tom Allah ya kaimu." Kana ta fice Karima na binta da kallo Kanta taji ya sara mata kamar zai fashe "Daman Salma ce wannan, innalillahi wa innailaihir rajiun, meke shirin faruwa ne."? Karima tai maganar cikin sabon tashin hankali "Tabbas Hadiza bazan bari ki kashe yar uwata ba , ke azzaluma ce Hadiza jahila mara ilmi, to wallahi ko hakan zai sanadin rabuwata da Adam sai na tona asirinki." Karima ta dafe kai tana tunanin yanzu me ya kamata ta yi , wayarta ta dauka tai sauri ta bude WhatsApp, kafin ta nemo number wayar Salma nertwork ya dauke baki daya .haka Karima ta ringa sintiri cikin tashin hankali, babu wanda ta iya fad'a wa wannan maganar Nertwork bai dawo ba duk irin zaman da Karima ta zauna jira har karfe 12 bacci ya kwashe ta Washe gari da safe kuwa, Karima harta zuge ta rame , anjuma za a daura auren Hadiza da a karfe biyu, domin kuwa har baki sun fara zuwa. Tun asuba ta fara yiwa Salma magana a WhatsApp, amma Salma ta hau bata duba ba , hakan yasa ta ringa mata flashing na company, amma Salma bata biyoba , da sassafen nan Karima ta fita ta siyo Kati . Ita kuwa Salma tun da ta tashi da asuba hankalinta yake tashe , shi yasa ko damar duba waya bata dashi , sam ta kasa samun sukuni, hakan yasa ta nufi dakin Aunty Hauwa Tana zaune tana jan carbi , tasan sam bata ganin Salma a dakinta a irin wannan safiyar. "Salma lafiya meke faruwa, kar dai ki ce mini Kano ne baki son zuwa." Cewar Aunty Hauwa dake kan sallaya , yake Salma tai ta zauna cikin mutuwar jiki. "A'a Aunty ba haka ba ne , ina son fad'a miki wani abu." "A'a mene haka kuma Salma fad'a mini da sauri mene ne ."? In ji Aunty Idanunta Salma kamar zatai kuma ta ce . "Amma ki mini alkawari, baza ki juya mini baya ba , ko ki kasa fahimta ta ." Jin hakan ya sa hankalin Aunty Hauwa ya tashi. "Haba Salma mene haka, fad'a mini mene ne."? Salma ta sunkuyar da kai kasa duk ta tada hankalin Aunty Hauwa "Ina jin ki ." Cewar Aunty Hauwa da matukar 'kaguwa taji wannan maganar D'ago kai ta yi tana cewa. "Da farko ki yi hakuri, na shirya karbar duk kan hukuncin da zaki mini Aunty." Taja numfashi sannan ta cigaba da cewa. "Aunty Hauwa mahaifiyata da mahaifina suna raye a wannan duniyar." "Kamar ya."? In jita Salma ta ce . "Kwarai kuwa na yi miki karyar cewa kanin babana ne ya koreni a gidansa, maganar gaskiya babu wanda ya mini hakan, nabar gida ne saboda kanin babana baya son na zama marubuciya, hakan yasa yake zuga banana." Cikin sabon mamaki Aunty Hauwa ta ce . "Ni fa ban fahimta ba Salma." Nan Salma ta zage ta warware mata komai da ya baro da ita daga gidansu har da yin kuka Shiru Aunty Hauwa tai ranta babu dadi , cikin wata irin murya ta ce . "Kina nufin karya kika mini a komai, har zuwa Bauchi ke nan da cewa kin makance ."? Da sauri Salma ta girgiza kai tana cewa. "A'a wallahi Aunty, wannan gaskiya ne , har zuwa Gombe da nayi a kafa , nasan nayi kuskure dan Allah ki yi hakuri." Cikin kuka tai magana Yadda ta ga fuskar aunty Hauwa yasa Salma sake rudewa da kuka . "Salma wannan ai yarinta ne da rashin hankali, tsawon lokaci da duk irin wahalar da kika sha, amma baki koma gida ba , wannan wacce irin zuciya ce dake , baki tunanin halin da iyayenki zasu shigaba Salma, shekara biyu harda watanni , ko dan kina da iyayen ne kike haka , ." Cikin zafi Salma ta ga Aunty Hauwa tana maganar Da sauri Salma ta sake matsawa kusa da ita tana sake rushewa da kuka , ta rike hannunta. "Wallahi ba haka bane Aunty, wallahi ba haka bane , ina kaunar iyayena, babana yana jin duk maganar da yayanshi ya fad'a masa, yana girmamashi sosai ." Cikin sake turo sabon kuka Salma ta cigaba da fad'in. "Hakan yasa ya ce zan koma gidanshi, wallahi idan na koma gidanshi burina bazai taba cika ba , yana da zafi yana da tsauri." Ta aje ajiyar zuciya ta cigaba da damke hannun Aunty Hauwa tana cewa. "Sannan ina son tabbatar wa mutanen da suke tunanin marubuta ne ke lalata tarbiya, ba haka bane,mutane da yawa suna mana wannan kallon , cikin burina harda tarwatsa alkalamin marubutan batsa, shin ba babban abu bane Aunty, ko kuwa ya dace su hanani."? Cikin jajayen idanu Salma ta gigice da kuka tana kwanciya a kafarta. Jinkin Aunty Hauwa taji ya mata sanyi , ta sa hannu ta d'ago Salma dake sharar kuka tana cewa. "Haka ne Salma, amma tuntuni da kin fad'a mini , sai naje na same su , da duk haka basu faruwa." Salma da shashshekar kuka ta ce . "Wallahi baza su amince ba , domin ya canza musu tunani, amma Aunty gani , ki hukunta ni dan Allah kafin mu je Kano si mini nasu, ki hukunta ni Aunty." Jin wani kuka mai gwanin ban tausayi yasa Aunty Hauwa ta rumgumeta. Sunyi wajen minti guda a haka, tana sauraran kukan Salma Daga bisani ta d'ago Salma tana murmushi da cewa. "Shi ke nan, ya isa , ta faru kuma ta kare Salma, sai dai kin yi kuskure amma ni na yafe miki." "Ta shi kije ki yi wanka , gashi har 7 ta yi ." Salma ta share hawaye da cewa. "Bazan ta'ba mancewa dake ba Aunty, ke ce nasarata kuma rayuwa ta." Aunty harara ta jefa mata kana ta ce ."Tom gwana sarkin barin gidansu ai mini shiru." Dariya Salma tai hakan yasa itama tai dariya tana cewa. "Ki tashi fa zuwa 12 nake son muje gidan redion nan mu gama komai ." Salma da jajayen idanu ta ce . "Ke nan hirar ba kai tsaye ba ce ."? Aunty ta bata amsa da fad'in. "Eh sai karfe 4 zasu sake ta ." Aunty Hauwa ta mike tsaye tare da cire hijabi tana cewa. "Okay yanzu na gane abin da yasa ba kya hira da kafafen sada tsumunta , Allah ya shirya ki ." Salma tai dariya gami da hawaye. MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 37&38 Karfe 8 suka shirya tsaf domin tafiya, tun a wannan lokacin Salma bata duba wayar taba , tana gama shiryawa ta jefata a cikin jaka , falon suka fito da akwati sun sha abaya ruwan toka iri daya . Aunty Hauwa ta kalli Salma tana cewa. "A'a har Yanzu Farida bata fito ba , kota tafi ne ."? Dariya Salma tai tana cewa. "Ta tafi fa tun dazu." Sannan suka fito , Aunty Hauwa ta tsaya rufe kofa , ita kuma Salma take sanya akwati a cikin Booth, suna gamawa suka shiga , sai aka dau hanya , ni ko nace Allah ya tsare . Karima kamar hawan jini zai kamata , ta yi harta gaji, amma Salma bata dauki waya ba, bata duba maganar ta a WhatsApp ba , ta yi mata text amma Salma shiru, hakan yasa Karima take tunanin to ko dai har an kashe Salma ne, ta yi tunanin sanar da Yaya Umar amma ta ce babu abin da zai iya akai. Matukar tashin hankali Karima ke ciki, hakan yasa ta cigaba da kiran Salma voice call ko Allah zaisa hankalinta ya yo wajen . Gidan biki kam ya fara cika, sai hayaniya ake . Anan kam tafiya ta mika musu sosai, domin Aunty Hauwa sun kusa Kano, iskar da Salma take ji yasa ta take jin bacci , amma batai wannan bacci ba , kamar an tsikareta tasa hannu a jaka ta zaro wayar ta. Tsaki taja ganin wata number 21 missed call, kawai ta bude data, nan ma karo ta ci da wannan number an yi sako ta WhatsApp sau 13 Kawai Salma taji gabanta ya fadi, tasa hannu ta bude wannan sakon . "Aslm." "Salma babu lafiya wallahi." "Kina magana da yayarki Karima daga kano" "Karki mamakin ta yadda akai na gano ki." "Rayuwar ki na cikin hatsari karki shigo Kano, domin an sa a kashe ki ." "Dan Allah yar uwata karki shigo Kano." Abin da Salma ta gani ke nan gutsutstsuran sakonni harda voice call Gabanta taji ya Fadi, ta sake komawa tana kara karanta wa. "Tsaya tsaya Aunty Hauwa." Cikin tashin hankali Salma ta fad'a, babu musu suna gaf da shiga Kano Aunty Hauwa taja gefe ta tsaya "Mene ya faru Salma."? Ta tambaya yayin da take cire facemask, har Salma ta had'a gumi "Dubi dubi dubi Karima." Aunty Hauwa ta aje numfashi tana cewa. "Kimin yadda zan gane Salma." Cikin sarawar ciwon kai ta mika mata wayar tana karantawa sannan ta Dora mata da cewa. "Tun asuba take kirana Karima ce ita ce 'yar yayar babanmu." "Wannan zancen kuwa Salma gaskiya ne,? amma kirata kiji." Ta mika mata wayar Karima ganin Shigowar kiran Salma yasa zuciyarta wani irin bugun tsoro da fargaba, ganin koina ya tara mutane yasa ta shige lungunta ta shiga bandaki ta rufe, kafin ta d'aga kiran ya katse, yana sake shigowa tai saurin d'aga wayar tsabar farin ciki yayin da Karima taji muryar yar uwarta sai ga hawaye "Salma ni ce , ni ce nan Karima." Cewar Karima yayin da Salma tasa wayar a spiker "Karima ya kike , ina kika samo ni da har kika san wannan zancen."? Cikin kasa kasa da murya Karima ta ce . "Duk ba lokacin wannan maganar bane yanzu Salma, kina ina ."? Salma ta ce "Gamu mun kusa shiga Kano ." Ajiyar zuciya Karima tai kafin ta ce . "Tom ina cikin tashin hankali Salma, kinsan Hadiza ko."? Salma ta ce. "Wacce Hadiza Karima."? "Hadiza RM marubuciya." Dasss Salma taji a ranta , bayan Karima ta bata amsa. "Eh Karima." Ta bata amsa jiki a sanyaye. "Tom ita ta shirya yadda za a kasheki Salma da zarar kin shiga Kano daidai titin da ya shiga gidan wannan redion, akwai wani da babbar mota ta shirya kasheki Salma." Salma ta kalli Aunty Hauwa cikin matukar rauni da tashin hankali, Karima ta cigaba da cewa. "Ba wasa nake miki ba Salma akwai hatsari a Shigowar ki Kano , akwai maganganu sosai." Jin hakan yasa Salma cewa. "Tom ke Karima duk ina kika san wannan."? "Ina auren yayanta Adam na yi aure Salma, gidanmu daya dasu , sun dawo sokkoto." Inji Karima Girgiza kai Salma tai tana cewa. "Gaskiya Karima hankali na ya tashi , me nai mata haka ."? Da saurin baki Karima ta ce . "Salma ina ce kin yi cuta, kika makance kika kuturce , to wallahi duk ita ce , duk ita ce ta aikata miki wannan bata kaunarki Salma." Girgiza kai Salma ta sake yi cikin tsananin mamaki tana kallon Aunty Hauwa, duk sun kasa cewa komai tsabar mamaki da rudanin da suka shiga , hakan yasa Karima sake fad'in."hello Salma." Salma tai ajiyar zuciya tana cewa. "Ina jinki Karima, abin ne ya bani mamaki, nasan cewa Hadiza bata sona , amma ban yi zatan abin yakai haka ba , karki damu Karima, na gode sosai yar uwata, zami waya ." Karima ta ce ."Tom shi ke nan." Sai a lokacin Karima taji sanyi a zuciyarta da walwala Salma ta kalli Aunty Hauwa da ta yi jimm tana cewa. "Aunty mene abin yi ."? Kawai Aunty Hauwa ta ja motar suka cigaba da tafiya Karima ba karamin farin ciki ta tsinci kanta ciki ba ,duk ta saki jiki sai annushuwa take , su Hadiza an sha kunshi an yi kyau, har wasu kawayen ta marubuta sun zo domin ta ya ta murnar aure, su Ruma ma an zo tun jiya aka yo Shigowar dare . Gaban Salma matukar faduwa yake sosai ,haka suna cikin tafiya har suka hau kan wannan titin da zai kaisu gidan wannan redionqq,ql1qadi , hakan yasa Aunty Hauwa ta tsaya domin karta take shi, babu wanda ya fita cikinsu har wannan tsohon ya mike da sanda da robarshi ya matso kusa da murfin kofar tasu yana fad'in. "A taimaka mana da na Allah da annabi, a taimaka mana." MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 39&40 Wani iri Salma taji irin yadda wannan tsohon yake kallonta, juyawar da zatai ta ga wata babbar mota ta yo kansu gadan gadan Ihu Salma tasa tana cewa. "Wayyo Aunty Hauwa gata nan." Sai ji suke "Tau tau tau 'dau ." Karar bindiga ana harbata 'yan sanda ne da farin kaya . Jin hakan yasa wannan mai shigar tsofaffi ya ke ce da gudu yana cillar da sandar, shima mai tuka wannan babbar mota ya diro , Allah ya bawa wani dan sanda damar cafke shi , ya kaishi kasa yana bangare shi tare da sa maka ankwa. Salma matukar rudewa ta yi jin wannan karar ta bindiga, karo na biyu ke nan data ta'ba jin irin wannan, sai da Aunty Hauwa ta nutsar da ita sannan ta dawo hayyacinta, domin tana ganin kamar za a kuma irin lokacin da zata je Zaria, haka wannan 'yan sanda suka tafi da shi , duk da cewa wasu sunbi dayan amma basu samu damar kamashi ba . Haka su Aunty Hauwa suka isa gidan wannan redion, sai dai Salma duk ba a daidai take ba , har saida aka zubo musu shayi ,kana ta ga fuskoki kala kala suna kawo mata gaisuwa sannan ta fara nutsuwa Bayan wannan driver ya ci duka sosai , ya fara basu hakuri. Sun yi masa jina- jina yaji jiki. "Zaka fad'a mini me ne ne yasa zaka kashe mutane har guda biyu ko kuwa , daman ka saba kashewa ko." Cewar wani kofur din yan sanda dake rike da kulki . "Wallahi yalla6ai ba haka bane , motar ma ba tawa ba ce dan Allah ku yi mini rai." Jin haka yasa wannan kofur cigaba da lafka masa sanda ta koina. Dpo ne ya tsaya daidai bakin kantar yana cewa' "Kai kofur sani , sashi a bakin daki ." "Okaysir ." Cewar kofur Ihu wannan matashi ya saka yana cewa."wallahi yalla6ai zan fadi gaskiya, ku yi mini rai karku rufe ni ." Dpo ya ce . "Muna sauraran ka ." Yana haki kamar zai shid'e ya ke cewa. "Wallahi dubu dari biyu aka bamu, aka bamu hoton yarinyar da zamu kashe, motar ba tawa ba ce yalla6ai, mun dade a gurin muna jiransu, hakan yasa dayan yayi shigar tsofaffi domin samun damar lekawa kowanne mota , idan yaga akwai wacce aka bamu hotonta sai ya mini a lama na taho na danne motar , daga nan sai mu gudu." Cikin jigata ya karasa maganar "Wa ne ne ya saku aikin ."? Cewar DPO " Wallahi yalla6ai Daga sokkoto ne , sunanta Hadiza." Inji shi Dpo ya kalli kofur sani yana cewa. "Ka dauki bayanansa yanzu a kawo mini officer." Dpo ya wuce ciki, yayin da wannan yake ihu yana fad'in. "Yalla6ai dan Allah ka ce su dena dukana, wallahi ban taba kashe rai ba ." Kofur sani ya ce ."Yi mini shiru ." DPO yana shiga office, babu dadewa kofur sani ya Kai masa wannan bayanai , ganin hakan yasa DPO yin waya ga abokan aikinsu zuwa Sokkoto birnin shehu . Misalin karfe 1 mai tattaunawar mai suna Muhammad Ayuba ya fara hira da Salma, babu boyeboye Salma ta bayyana cikakken sunanta da tarihinta Tattaunawar ta yi nisa har ta zo gangara, kallon Salma ya yi yana cewa. "To hajjiya Salma, akwai maganar da take yawo cewa. Kina daga cikin sahun marubuta matasa masu shahara da kuma arziki, alhalin baki dade cikin duniyar marubuta ba ." Murmushi Salma tai sannan ta ce . "To ai ita shahara ko daukaka daga Allah ce, ba boka babu Malam, kuma arziki na kasuwanci ne , duk da cewa ina samun wani abu daga rubutu, to amma bai kai kasuwanci na ba ." Ta aje maganar tana kallon shi, hakan ya tabbatar masa ta gama bashi amsa , ya dubi takardar dake hannunshi , kana ya d'ago yana cewa. "To autar marubuta mun saurari, kalubalenki kafin ki kawo wannan matsayi, mun ji kuma tarin nasarori da jeren littattafan ki ." "Wacce shawara zaki bawa marubuta masu tasowa da kuma wanda suke cikin rubutu ka'in dana 'in." Ajiyar zuciya Salma tai tana gyara zaman gyalen abayarta Sannan ta fara cewa."Tom har ila lau dai shawarar guda daya ce zuwa biyu." "Marubuta su ji tsoron Allah, su rubuta abin da zai amfani al'umma, kar si hassada a junansu , su jayo kananun marubuta a jika , tabbas yin hakan zai kawo babban cigaba." Muhammad Ayuba ya ce . "Tom ko mu dakata ne , anjuma sai mu cigaba, domin ba kai tsaye bane ." "A'a haba dai a cigaba ai kadan ya rage ." Cewar Salma Dariya Muhammad Ayuba ya yi , sannan ya ce ."Okay wa ne ya ce miki sauran kadan , ki gaji ke nan." Salma tai dariya Hankalin shi ya mayar ga aikin yana cewa." Tom yanzu zamu amsa sakonni masoyanki." "Wannan take cewa , gaskiya Autar marubuta Allah ya kara daukaka da nisan kwana muna tare da ke . Daga Basira Hudu Salma ta ce . "Amin summa Amin ina godiya." Sannan ya kuma karanto wani sakon yana cewa. "Aslm, nima marubuciya ce , dan Allah Autar mu, ki bamu shawarar yadda zamu magance marubutan batsa da masu tura mana abin banza a cikin group, saboda sai mun sakankance ake tura mana abin da bai dace ba na gode." Da sauri Salma ta ce . "Wannan abu ne da kullum nake bawa marubuta shawara, da farko dole ya zama kanmu yana hade ne , duk marubuciyar batsa ku hana ake sako muku novels dinta cikin group,duk wanda ya sako ku cireshi koda ita ce , sannan zancen masu tura abin batsa cikin group." "Gaskiya wannan ruwan dare ne cikin group din marubuta, Allah ya shirya masu yi, abin da zaku yi anan shi ne , ba wai iya marubuta ba , duk inda kuka ga an tura irin wannan, sai ku yi saving number wannan wanda ya tura din, Tom da zarar ka ganshi cikin group kai maza kayi reporting admin su cire shi, su ma marubuta idan sun yi saving number irin wannan mutanen, to da zarar ya turo request a group zai shigo,sai ai cancel din shi kar a yi approval nashi ." "Idan ta kama su ringa saving numbar tasu irin daya , kamar kawai si yi saving da A, ko Y koma mene, to duk inda ka gansu zaka ganesu. Domin masu wannan halin kullum yawa suke karawa." "To Ina tabbatar muku idan kun dauki wannan shawarar wannan matsalar ta kau sai dai wata ." Sokkoto Yanzu misalin karfe 1:47, an taru sosai a cikin masallaci, wakilin Hadiza ake jira domin a daura aure, Nan gidansu Amarya kuwa, sai farin ciki ake ana ta hidima da Kai kawo, su Umman Hadiza an sha kyau sosai uwar Amarya, ana ta yin hotuna da 'yan uwa , motar yan sanda ce ta tsaya a kofar gidan, kana yan sanda uku suka fito, macen cikinsu ce tasa kai, Kai tsaye cikin gidan , hakan yasa 'yan uwa aka fara binta da kallo. "Ina Hadiza."? Cewar 'yar sandar da hausa bata wadaci bakinta ba "Gata can amaryar ." Cewar wata mata , ganin wannan 'yar sandar yasa Karima isowa wajejen gurin da sauri . Bayan ta ishe Hadiza da ta ci kwalliya ta ce . "Ki wu ce muje zuwa office akwai tambayoyi da zaki amsa ." 'yar sandar ta sake magana Hankalin kowa ya yo wajen caaaa ana mamakin meke faruwa "Kamar ya na wuce , bikina fa ake babu inda zani mene nai muku , ." Inji Hadiza Umman Hadiza ce dake dakinta ta fito da sauri tana cewa. "Ina zata je , ranar auren nata ma sai an yi mata bakin ciki da hassada , to wallahi Allah yafi karfinku ." Jin hakan yasa wannan 'yar sandar daba bahaushiya ba fad'in. "Babu ruwanmu da biki, zami aikinmu ne , idan baza ki taho ba zami sa miki karfi , muna da yawa a waje ." Hankalin Hadiza taji ya tashi sosai MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 41&42 Bayan Salma sun gama wannan tattaunawar, har abinci suka samu suka ci, sukai sallah, sannan suka hau mota. Ganin Aunty Hauwa ta murza kan mota sun jiya yasa Salma cewa. "Aunty wannan titin ai bazai kai mu Tarauni ba ." Aunty Hauwa ta kalleta tana cewa. "Eh zamu je station ne , sun kira mu , domin an taho da Hadiza daga sokkoto." Salma ta aje numfashi mai nauyi , Aunty Hauwa ta cigaba da tafiya. Nan kuwa hankalin mutane duk ya tashi, ko aure ba a daura ba an tafi da Amarya har Jahar Kano, hakan yasa ango da zugarshi suka bisu , jingum-jingum kowa ya yi a cikin gida , saboda labari ya zo musu cewa ana tuhumar Hadiza da kisan kai ne .. Sai da wajen misalin karfe 4:30 su Aunty Hauwa suka samu suka taho, bayan Hadiza ta amsa laifinta tare da nadama, sai dai babban abin da ya Sanya Hadiza amsa laifinta babu bata lokaci, ganin Sultan da Alaji Babawo a wannan gurin, domin a tunanin ta tabbas za ai mata uzuri da alfarma, domin babban mutum ne Alaji Babawo. Sai dai aka sin haka ne ya faru , domin kuwa yana jin hakan ya yi Allah Wadai yaja zugarshi suka koma sokkoto .domin ya ce yarinyar da zata iya wannan, to tabbas zata iya kashe masa sultan. Anan kuwa umman Salma tana cikin matukar tashin hankali, domin tunda ta fara sauraran hirar da aka saki cikin gidan wannan redion ta kasa sukuni Hakan yasa ta kira Umar yana cann kallon Ball Da sauri ya iso gida, domin ya ga irin Kiran da take masa, yana shiga a tsaye ya sameta "Umma lafiya, me yake faruwa ne."? Umman Salma ta nuna masa redion tana cewa. "Wallahi Umar yanzu naji anan gidan redion, wannan Autar marubutar Salma ce , Salma ta ce ." Jin wannan batu yasa Umar rike haba tana cewa. "Salma kuma Umma? Ko dai mai irin sunanta."? Umma ta ce . "Ka tsaya ka sauraran Umar wallahi wannan yata ce Salma, muryar ta ma bata canza ba har irin dariyar ta." Shi dai Umar lamarin ya daure masa kai , baisan ta Ina zai fara ba Da kyar Salma ta iya gane gidansu, saboda gyaran da yaji da kuma tarin sabbin gine- gine . "Assalamualaikum." Salma ta fara shiga cikin falon tare da tashin hankali, Umar da Umma suna tsaye Babu Wanda ya amsa sallamar duk a cikinsu, har ita ma Aunty Hauwa ta shigo . "Salma." Cewar Umar, murmushi mai ciwo Salma tai sannan ta ce . "Na am Yaya Umar." Yayin da idanunta suka kawo ruwa , Umma take kallo cikin matukar tashin hankali da tsananin kewa da kauna har hawaye suka fara zubo mata, ita ma Umma hawaye ne suka zubo mata , amma ta share su cikin kwarin gwiwa. Da sauri Salma tai yunkurin sunkuyawa gaban Umma Amma Umma cikin izza ta dakatar da ita tana cewa. "Dakata anan." Jin hakan yasa su duk mamaki "Dakata anan ." Ta sake fad'a, sannan ta cigaba da cewa. "Ya kamata ki nemi izini yayin shigowa gidan mutane, domin kina daya daga cikin Wanda ba muharraman wannan gida ba ." Cikin wani sabon tashin hankali Salma ta zaro idanu tana cewa. "Umma me kike fad'a ne , baki gane ni ba ne? Salma ce fa yarki." Jin wannan maganar ya sake fusata Umma. "Bani da wata 'ya a wannan duniyar, Ina so ki fitar mini a gida yanzu." Kuka Salma ta rushe dashi mai matukar gwanin ban tausayi, aunty Hauwa babu abin da ta iya fad'a a wannan yanayi "Ba haka Ummana take ba wallahi, Ummana nasan tana kewar gani na kuma tana kaunata " Cewar Salma cikin kuka Babu annuri ko kadan a fuskar Umma ta ce. "Salma burinki ya cika ,kin samu daukaka kin samu kudi, babu abin da ya rage fa ce ki canja iyaye da zasi daidai da kudi da daukakarki." Umma taja numfashi na bacin rai sannan ta cigaba da cewa. "Kin tafi kin bar gida babu tunanin wanne hali muke ciki , babu neman mu har Saida burinki ya cika , ki fitar mini a gida Kona miki abin da baki tunanin shi ba ." Kuka ta sake kecewa dashi tana faduwa kasa tana cewa."Haba Umma, Haba Umma." Zazzafar ajiyar zuciya Umar ya sauke sannan ya ce . "Haba Umma, idan rai ya baci hankali ba ya gushewa." "Kayi mini shiru Umar tun kafin na bata maka rai ." Inji Umma Umar ya sake ajiyar zuciya tare da fad'in."Ki gafarce ni Umma, amma bazan iya shiru ki cigaba da cutar da kanki ba, domin kullum kina addu'a Allah ya kare Salma ya kuma dawo da ita zuwa gareki " "Ki yi hakuri Umma ga Salma ta dawo, tabbas kina da damar hukunta Salma, sai dai karki hukunta kanki , domin har yanzu kina kaunar Salma fiye da komai, har sauraran gidan redion novels kike saboda kewarta." Umma ta sunkuyar da Kai kasa, yayin da Salma take mikewa tsaye tana ci gaba da kuka "Yanzu da zarar Salma ta juya , kuncin da zaki kuma shiga Allah ne masani Umma, Dan Allah ki yi hakuri, yanzun nan fa kika kirani cewa kinji Salma gidan redio, kin kasa samun sukuni, to me yasa ta zo gabanki zaki mata haka ."? Jin wannan zan tuka na Umar yasa jikin Umma sanyi ta fara kuka Da sauri Salma ta fara fad'in. "Dan Allah Umma ki dena kuka, wallahi Umma ina kaunar ki, rayuwar masifar dana shiga ta hanani zuwa gareku shekara biyu da watanni kuna zuciya ta, dan Allah Umma ku yafe mini dan Allah Umma." Da sauri Salma ta fad'a jikin Umma tana kuka, jin Salma a jikinta yasa Umma ta rumgumeta ita ma tana kuka Aunty Hauwa tai murmushi tare da kallon Umar Kuka mai gwanin ban tausayi Salma take yi tana cewa."Ki yafe mini Umma, ki yi hakuri, tabbas nayi ba daidai ba wallahi, amma badan kudi ko daukaka ba Umma, ki yi hakuri Umma ki yi hakuri." Umma jin Salma tana wannan maganar cikin kuka ya sake karya mata zuciya tana sake rumgumeta "Na ga rayuwa mara adadi Umma, banyi zaton sake ganinki ba da Baba, amma cikin ikon Allah Aunty Hauwa ta zame mini gata , wallahi Umma na yi kewarku ki furta kin yafe mini dan Allah." Cewar Salma ke nan cikin kukanta "Na yafe miki Salma, wallahi na yafe miki." Jin hakan yasa Aunty Hauwa da Umar wani murmushi suna ta ya Salma farin ciki Sakin Umman nata tayi , tana kallonta cikin idanunta da har sun kunbura tsabar kuka ."Umma ina Baba nasan zai yi fishi dani sosai fi ye da ke , ku hukunta ni Umma amma karku mance ni 'yar ku ce , da ta yi kuskure ." Taja numfashi tana kallon Umar, "Yaya Umar ina baba yake ."? Umar ya kalli Umma yayin da suke had'a idanu, ganinsu kamar marasa gaskiya yasa Salma rudewa "Umma ina Baba ya ke ." ? Cikin tashin hankali ta sake tambaya Babu wanda ya bata amsa cikinsu, hakan yasa take jin tabbas wani abin ya same shi "Ko ya mutu ne ."? Cikin tashin hankali ta fad'a tana rike baki, da sauri Umma ta matsa ta bude wata dirowa tana dauko wata takarda, ta mikawa Salma Da sauri ta karbe jikinta da hannayenta na rawa ta bude takardar Autar marubuta MARUBUCIYA ✍️ Na Autar marubuta ________________________________________ Page 43&44. End. Allah - Allah Salma take ta fara karantawa cikin zuciyarta ba tare da nutsuwa ba ta fara karanta rubutun mai blue biro . "Assalamualaikum 'yata Salma, nasan komai dadewa zaki dawo wannan gidan, ni kuma wata kila kafin wannan lokacin bana raye, hakan yasa nake son sanar dake cewa, ban ta'ba kyamar rubutun da kike yi ba , na biyewa yayana ne matsayinsa na babba da yake da wahalar fahimta, amma sai gashi matsalar ta kai ga har kin bar gida ." Salma ganin wata fuska da aka zana tana kuka ne yasa hankalin ta sake tashi tana rudewa da kuka, a wannan yanayi ta cigaba da karanta wannan takardar "Duk inda kike Allah ya kare ki , ki girmama yayana domin shima mahaifinki ne , na yafe miki Salma duk abin da kikai mini , Bissalam." Karshen rubutun ke nan , kudundune takardar tai cikin hannunta tare da shiga wani sabon yanayi, hakan yasa Umma jin tausayin Salma "Baba ya rasu ke nan Umma, ya rasu ke nan Umma, innalillahi wa innailaihir rajiun, innalillahi wa innailaihir rajiun."😭 Maganar Salma ke nan cikin sabon yanayi mara dadi Aunty Hauwa hawaye taji sun zubo mata, saboda irin yadda Salma tai matukar bata tausayi "Allah ya yi masa rasuwa Salma, yanzu shekara 1 ke nan, yana sauran kwana biyu zai rasu ya bani wannan takardar." Inji Umma cikin damuwa Sunkuya Salma tai bisa jirin da take ji , ta zauna a kasa tana dafa kanta tana cewa. "Allah ya jikanka Baba, babu rabon mu sake ganin juna , Allah sarki babana." Ta mike tsaye kamar an tsireta tana kallon Umar da cewa. "Yaya Umar ina son zan je kabarinsa, ka rakani dan Allah." Umar ya ce . "Tom shi ke nan." Umma ce ta kalli Aunty Hauwa tana cewa. "Baiwar Allah ki karaso ki zauna mana". Hakan yasa Aunty Hauwa zama tare da gashshe da Umma tana mata ta'aziyya tare da rarrashi . "Umma wannan ita ce Aunty Hauwa." Cewar Salma Nan shima Umar ya zauna Salma tana basu labarin irin rayuwar data shiga tunda ta fice a wannan daren , Umma ta tausaya mata sosai, sannan ta jinjinawa aunty Hauwa tare da mata godiya sosai, Wajen karfe 6 Yaya Umar yake kiran Alaji Yusuf yake sanar dashi dawowar Salma, a cikin dare kuwa sai ga zainab ta zo , bayan an sanar da ita Aunty Hauwa ita ma a wannan gida ta kwana da sassafe Umma ta tashi ta dora musu doya da kwai , Umar ya siyo breadi A social media kuwa babu abin dake yawo kamar irin yadda marubuciya Hadiza RM ta yi yunkurin kashe Autar marubuta, abin da yake yawo ke nan a duk inda ka shiga , sai dai a halin yanzu an tura Hadiza zuwa kotu, Umman Hadiza tana cikin matukar damuwa, domin Karima babu tsoro ta bayyana cewa wannan Autar marubuta da Hadiza tai yunkurin kashe wa , to 'yar uwarta ce , shi kanshi Adam ya yi mamakin irin yadda bata ta'ba bashi labarinta ba. Umman Hadiza kuwa tsanar Karima ta yi sosai, domin yanzu bata son jinin wannan Autar marubutar , Da safe Karima ta shirya tsaf domin tafiya Kano, nan Umma babu abin da ta iya cewa da ita , domin asan samun Umma, Adam ya saki Karima, sai dai bazai iya hakan ba , wai a hakan ma Umma tana yin haka ne ba tare da tasan Karima ce ta yi sanadin tonon asirin Hadiza ba , da abin yafi haka kam. Da safe suna gama karyawa sai ga Alaji Yusuf nan, nan ya zo gurin Salma suka gaisa harda bata hakuri, domin tun daga rasuwar kanin shi yayi sanyi sosai, har albarka ya sa mata sannan ya koma . "Salma yau zamu je Bauchi fa , domin babu lokaci." Cewar Aunty Hauwa Umma ta ce . "Yau kuma daga zuwa ." Salma tai murmushi ta ce . "Eh Umma ai Aunty Hauwa bata da lokaci sosai, wannan ma sa'a aka ci ya zo kan ga'ba ." Salma ta kalli Yaya Umar. "Tare da kai fa zamu tafi." Zaro idanu ya yi yana cewa. "Tare dani kuma , yau ina da aiki fa ." Harararshi Salma tai tana cewa ."To wallahi sai kaje babu ruwanmu da aikinka." "To ko dai an samu wani ne acan, sai a fadan na nemi daidai ni." Inji Umar Dariya Umma da Aunty Hauwa suka yi , nan sukai ta wasa da dariyar su, har lokaci ya ja , sannan suka tashi sukai wanka , Aunty Hauwa da Salma suka hau mota daya , sannan Umar yaja motar da za a kai wa Aliyuu Sun isa Bauchi cikin farin ciki da walwala, nan suka sauka gidan Aliyuu, aiko Baba Laure ma tana wannan gida, sakamakon Fatima ta haifi na miji kwana biyu yau ke nan, Salma tai matukar farin ciki, haka ita ma Baba Laure sai murna take da ganin Salma, aikawa akai aka kira Aliyuu can gurin shayi da burodi, mamaki ne ya ishe shi da ganin Salma a wannan lokacin, nan Aunty Hauwa tai ta koda Salma gabansu tana tabbatar musu wannan makauniyar tasu ita ce Autar marubuta fa, farin ciki da mamaki ya kama kowanne a cikinsu, haka aka sha wasa da dariya har sukai canjan numbobinsu, haka Fatima ta roki alfarmar Salma ta yafe mata saboda irin abubuwa data aikata mata , Salma ta ce babu komai. Da suka tashi tafiya Aunty Hauwa ta bawa Fatima dubu 50 asai wa jariri fanfas, sannan ta sake bawa Baba Laure dubu 50 ta ce ta yi hakuri a haka . Sannan suka rankaya suka fito waje domin rakasu, nan ne Salma ta mikawa Aliyuu mukullin wannan mota , sannan take tabbatar wa da Baba Laure hajjin bana tare da ita za ai, murna kam ba a cewa komai, duk sun kasa zaune sun kasa tsaye ganin wannan arziki a gidansu, bari Baba Laure da taji zata hau jirgi a je ga .... Haka sukai musu addu'a suka hau mota suka juyo Kano Anan kuwa umman Hadiza ta samu ta kawowa Hadiza ziyara Tana zaune tana ta jira domin ganin an fito da ita . Da gudu Hadiza ta nufi Umma tana kuka kafin ka ce komai ita ma Umma ta dau kuka "Innalillahi wa innailaihir rajiun, Umma kinga yadda duniya take yi dani, sultan ba ya nan , kotu yanke mini hukuncin zama a gidan yari za tai , shi ke nan rayuwa ta ta lalace Umma, innalillahi wa innailaihir rajiun." Haka Hadiza tai ta sunbatu Umma tana kuka , Allah yasa mu dace , Allah ka raba mu da sharrin zuciya. Karima harta iso Kano da dare , aiko tana zuwa gidansu, ta taho tarauni gidansu Salma Nan su Salma suna dawowa suka tarar da Karima, aiko aka sha hira sosai , irin yadda Karima ta gano Salma duk ta sanar da ita , farin ciki dai yau cikinsa aka kwana Har Salma take cewa da Umar tana son za ai rijiya ko masallaci domin mahaifinta, ya ce mata ai shi ke nan Da safe suna karyawa Aunty Hauwa tai wanka ta shirya "Tom Salma ni zan koma ." Cewar Aunty Hauwa Murmushi Salma tai tana cewa."Babu dadewa zan biyoki kuwa Auntyna , gaskiya zan yi kewarki ." Aunty Hauwa ita ma tai murmushi tare da fad'in."Tom ina nan Ina jira , amma da Allah ki amsa tambayar da akai miki zuwa BBC." Salma ta ce . "In sha Allahu Aunty duk zanje har ma da gidan TV da suka gayyace ni ." Aunty ta ce . "Tom shi ke nan sai na jiki ." Nan ta shige mota, suna tai mata addu'a, Salma harda kuka sannan Aunty Hauwa ta wuce Gombe. Bayan kwana biyu Salma tana zaune tana rubutu , sai ga Umar ya shigo Salma ta kalleshi tana murmushi "Ni fa na zo na hanaki rubutu, domin soyayya nake so mu yi ." Cewar Umar Ajiyar zuciya Salma tai tana cewa. "Tom zaka ga soyayya ni Gombe ma zan tafi gobe , domin shagona da Auntyna." Inji Salma Umar ya jefa mata wani kallo yana cewa."To yaushe ne auren namu."? Salma ta kifa laptop cikin kunya tana durkusar da kai . Alhamdulillah masu sauraro, nan na kawo karshen Littafina mai suna MARUBUCIYA ✍️ Wanda ni Autar marubuta na rubuta , Allah ya bamu ikon ganin kuskureen mu , abin da ba daidai ba Allah ya ganar damu, godiya ga d'imbin masoyana a duk inda suke , sai Allah ya sake had'a mu cikin wani sabon labarin ✍️. Bissalam.