hausa novel blog ‹ › Home View web version Friday, 6 January 2017 aisha ummi at 08:34 MARTABA TA 1-50 5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA Pg 1-5 DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI!! A gaggauce take fitowa daga cikin bathroom din tana daure da towel wanda ya rufe iya gwiwarta, da sauri ta nufi room 4 dakinsu, tana shiga ta isa gaban mudubi ta fara shiryawa cikin sauri nikaina Ummi A'isha sai da nashiga mamaki saboda ganin tsaruwar dakin wanda sam baiyi kama da na yan makaranta ba, komai a jimulle yake acikin dakin tamkar dakin gida, bayan ta gama shiryawa ne ta isa gaban makeken akwatinta ta bude ta ciro wata hadaddiyar doguwar riga kalarta blue mai duwatsu tayi mutukar tsaruwa, da sauri ta saka doguwar rigar bayan ta feshe jikinta da daddadan turaren Mazda, dan siririn mayafi blue kalar rigarta ta yafa tayi rolling tare da daukar wayarta wadda ta kasance kalarta blue kirar galaxy s7, dogon takalmi ta sa baki ta jiyo da zummar ficewa daga cikin dakin, cubus suka yi da wasu yan mata guda biyu. Kallon kallon suka fara, cikeda fada daya daga cikin yanmatan ta kalleta "wai yau ma haka zaki fita ba kiyi mana girkin ba? To wallahi yau a dakin nan sai dai kowa ya zauna da yunwa dan wallahi nidai ba zanyi girkiba" Kallonta budurwar tayi "haba Sadiya kinga fa nakusa makara tun jimawa aka shiga lecture, dan Allah kuyi mana girkin ko taliya ce ku dafa mana" ta karashe maganar kamar zata fashe da kuka "Tab wallahi yau kowa tashi ta fissheshi fati amma wallahi ba zanyi girki ba, ke kullum babu abinda zakiyi da zarar anyi magana sai kice lecture kamar ke kika fi kowa karatu" Sai a lokacin daya budurwar tayi magana wadda tun lokacin da suka fara mahawarar take tsaye tana kallonsu "ya isa haka ku da kullum baku da aiki sai na fada, in dai girki ne ni zanyi, shikenan period magana ta kare" Harararta Sadiya tayi "sai kiyita yi ai, dama ai dan kina yine shiyasa bata son yi" "Eh din ina ruwanki sai tayi din" fati ta fada tana hararta, "ya isheki haka malama" Sadiya ta fada cikeda masifa "Maza dai kar ki tafi har afito daga lecture din kin tsaya neman fadan da kika saba" A'isha ta fada lokacin da take shiga cikin dakin murmushi fati tayi tareda yiwa sadiya gwalo ta fice daga cikin dakin da sauri, tana fita A'isha ta kalli Sadiya tana dariya "Allah ya barni daku yaran nan kuna bani dariya wallahi" Dariya Sadiya tayi "ai nasan zanyi missing din fati idan muka gama makarantar nan" dariya A'isha tayi ba tareda tace komai ba. Koda fati ta fita a hankali take takunta har ta fita daga harabar hostel din, jin karar wayarta ne ya sata rage takun da take tare sakin wani murmushi "hello yayana yakake?" Tafada tana murmushi shima murmushin yake daga inda yake zaune akan luntsumemiyar kujerarsa ta office sai juyawa yake, office din nashi ya tsaru mutuka, farine bufulatani na asali,dogo marar kiba yana da dogon hanci mai tsini tareda manyan idanuwa farare kakal, sumarsa kawai zaka kalla kasan cewa ruwa biyune,yana sanye da blue din riga mai dogon hannu da bakin wando, wuyansa daure da necktie baki,a yanda na kiyasto muku shekarunsa ba zasu haura 34 ba, "yanmata yakike?" Yafada yana murmushi mai kayatarwa "Yaya Aadil kaga ka hana Sadiya, kullum kullum sai ta jani da fada" takarasa maganar cikeda shagwaba Tsam ya mike daga kan kujerar da yake ya nufi window din office din, ahankali ya sauke glass din ya fara hango mutanen daketa kaiwa da komowa a kasan benen nasu wanda ya kasance hawa bakwai kuma shi office dinshi a last floor yake. "How comes?" Ya fada yana dariya "common baby,haba yanmata yau ma sai da kuka yi fadan? Ke tsokana gareki ita kuma Sadiya saurin fushi, amma duk me ya kawo fadan? Fada min kinji sha lele" ya fada cikin sigar lallashi Rausayar da kansa yayi tareda kurawa wani dan kayataccen lambu dake girke a can kasan office dinsu ido, "kin san bana son bacin ranki ki fada min menene" Shiru tayi bata bashi amsa ba tana nazarinsa a hankali "Kina so ki tayar min da hankali ko? Kina so hankalina ya tashi na kasa samun nutsuwa?" Dan murmushi tayi hakan ya sake rudashi dan duk a zatonshi kuka take "Kuka kike?,uhm?" Sai a lokacin tayi murmushi "Kai yaya Aadil nifa ba kuka nake ba, kawai dai ina tunanin irin son da kake yimin ne, domin na kasa banbance tsakanin nida anty Salima wadda kafi so" Murmushi ya saki mai kayatarwa ya saki dan zaren labulen dake hannunsa ya fara takawa a hankali ya nufi kayataccen falonsa. Murmushi kawai yakeyi "kema kin san nafi sonki ai, shiyasa ma nabar Salima a gombe saboda ke idan na aureki nan zan kawoki kusa dani yanda zan samu damar kulawa dake" "Hmmm yaya aadil kenan to kuma idan anty salima taki fa?" Fridge ya bude ya dauko madara mai sanyi ya zauna ya fara kurba kafin ya fara bata amsa "Ai itama antyn naki tasan irin son da nake miki saboda kin san ance amarya bata laifi" Bata rai tayi kamar yana ganinta "ni baka sona dayawa, idan kana sona kayi min waka" Dariya ya fara harda kwarewa "waka kadai kike so yanmata?" "Ehh" tafada cikeda shagwaba "To zanyi miki kar kiyi kuka pls, karkade kunnenki kiji zan fara" "Ina jinka" ta fada a hankali "Fatima, fatima yar auta, fatima tauraruwar mata Dafari da farko, fatima gunki nataso da kidan jita fatima daure leko Yau ga mai sonki fatima dauke da sako Nidai fatana fatima kice dani miko, Ki amince min fatima nayo roko zan sa kuka in bakya sona yanmata"! Dariya fatima tafara kyalkyalawa "ayya yaya aadil basai kayi kuka ba, ina sonka kar kayi kuka" Dariyar shima yayi "to tunda kin hanani shikenan bazan yi ba amma da baki hanani ba da kuka zanyi" Murmushi tayi "wakar tayi dadi yaya aadil, dama ka iya waka shine baka taba yimin ba? Tunda ka iya yanzu kullum sai kayi min". Murmushi ya saki mai hadeda farin ciki dan bashida buri illa yaga fatinsa tana cikin fara'a da annashuwa "Zan rinka yi miki, amma yanzu me kike?" "Lecture zan je" "Kinyi laifi, dama lecture zakije shine baki fada min ba, kika biyeni na rike ki da hira? Idan nazo gombe sai nayi punishing dinki" "Am sorry yayana" "Na hakura amma kiyi sauri ki shiga lecture" "Yes sir" tafada tana dariya tareda saurin zare wayar daga kunnenta dan tasan bazai kara cewa wani abuba tunda tace mishi lecture zatayi. Sai alokacin da ta gama wayar sannan ta fara daga kafarta da niyyar taje ta iske lecture din amma sai me? Tana bullowa ta wurin hall din ta hangoshi tsaye jikin motarsa kirar BMW ash colour, shikuma yana sanye cikin dark red din t shirt da black din trouser, sumar kansa tamkar ta larabawa domin a kanannade take akalla shekarunsa ba zasu wuce 30 ba a duniya, yana da kyau mai mutukar daukar hankali, nidai Ummi A'isha nakasa tantance tsakanin saurayin farko da wannan na biyu wanda yafi wani kyau da aji. Take ta murtuke fuska domin a rayuwarta idan da wanda ta tsana to JAWAD ne, nan fa ta fara harare harare marassa dalili, a hankali ya taso yazo yasha gabanta, "Fatima Xarah" ya fada yana kallon fuskarta Dauke kanta tayi tamkar bata san da mutum a Gabanta ba, Ahankali ya fara yi mata magana tamkar wani me yin rada,cikin hausarsa marar fita me kamada ta yan koyo ya soma yi mata magana amma abisa dukkan alamu hausar bata samu gurbin zama ba a bakinsa saboda fillanci da turanci su yafi iyawa sai wasu lokatan yakan dan hada da larabci domin asali ma shi hausa wahala take bashi saboda bai iyata ba shiyasa bai fiya yawaita yinta ba, ganin zai wahala da yawa yasa ya fara yi mata magana cikin harshen turanci, "Queen why all this hateness? Meyasa kika tsaneni yanzu?" Wata harara ta wurga masa kafin tayi magana cikeda gatsali "Kaga Malam ni dama can ban sanka ba, balle har na soka, so stay away from..." Cikin sauri ya katseta idonsa har ya sauya launi daga fari zuwa ja "Karya kike fatima kin sanni, kuma kin soni, kuma har yanzu kina sona, kuma wallahi dole kici gaba da sona har abada"! Wani dan malalacin murmushi ta saki kafin ta kalleshi fuskarta cikeda masifa "Kai zan so? Hmm har abada bazan taba sonka ba, kasa a ranka fatima makiyiyarka ce ta har abada, dan haka ina mai shawartar ka da ka cire Fati daga sahun masoyanka domin bata kaunarka ko kadan" Kallonta yayi ido cikin ido "Karya kike, ke masoyiya ce agareni ba makiyiya ba, kuma sunanki da matsayinki bazai taba gogewa daga masoyiya ba, zanci gaba da tattalin sonki acikin zuciyata kamar yadda kema nasan kullum da sona kike kwana kike tashi" Sausauta muryarsa yayi tareda ci gaba "Queen ki sausautawa ranki, ki taimakawa zuciyata da taki mu ci ribar soyayyar da mukewa junanmu" "Dawa zaka rayu?" Ta tambayeshi cikeda bacin rai "Kar ka kuskura kayi gangancin rayuwa dani, domin tsanar da nayi maka tana iya sawa na kasheka" Cikin bacin rai ya kalleta idanuwansa sunyi jajur "Sai na rayu dake in yaso ki kashenin domin na shiryawa mutuwata in dai ta sanadinki ne, amma ki sani da sonki zan koma ga mahalicci na" Yana kaiwa nan ya juya ya nufi motarsa cikeda bacin rai kafin wani lokaci har ya bar cikin makarantar cikin wani mahaukacin tuki, itama fatin cikeda damuwa hadeda bacin rai ta ta juya tabar wurin, lecture din da bata shiga ba kenan. Ummi A'isha🏻 [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA Pg 6-10 ~~~Cike da bacin rai pherty ta juya tabar wurin ta nufi hanyar hostel tana tafe zucyarta na yi mata tukuiki kamar wuta, A daidai wata baranda ta zauna ta fara kuka "nikam me zan yiwa jawad ya kyale rayuwata na huta? Na tsaneka jawad bana sonka bana kaunarka, bana kaunar duk wani me kaunarka, i hate u!" Haka take ta furtawa tamkar wata zautacciya. Ta dade a zaune tana faman kuka sannan ta tashi taja kafarta dakyar ta nufi hostel fuskarta cikeda damuwa, Tana zuwa daki ta samu Sadiya tana yiwa A'isha kitso, ko kallonsu bata yi ba tafada kan gadonta ta fara wani sabon kukan, dukkaninsu tsayawa suka yi suna kallonta domin a yan kwanakin nan kusan kullum sai tayi kuka wanda su basu san dalilinsa ba. Cikin damuwa A'isha tayi magana "pherty menene? Me ya ke damunki?" Shiru bata bata amsa ba kafin ta sake wata maganar tuni wayar phetyn ta soma ruri, cikin kuka ta daga wayar "yayana" tafada tana share hawayen fuskarta, "yanmata na me yake faruwa?" Cikin kuka tace"yunwa nake ji kuma ina jin ba suyi mana girki ba" da sauri ya katseta "suna ina?" "Gasu nan" tafada tana kuka "oya bani A'isha" Mikawa A'isha wayar tayi takoma ta kwanta "Hello yaya aadil" cikin sauri yace "haba A'isha ya zaki bar pherty na da yunwa har tana kuka?" Cikin murmushi A'isha tace "yaya aadil wallahi girkinta ne yau kuma bata yi ba nikuma nace zanyi to yanzu kitso Sadiya take yimin shine nake son da zarar ta gama min sai na dora mana girkin, muma wallahi bamu ci komai ba, amma ga cornflakes nan tasha kafin ayi girkin" Murmushi yayi "naji wannan to amma me ya hadasu fada da Sadiya dazu kafin ta tafi lecture?" "Yaya aadil fati bata son aiki duk ranar girkinta sai sunyi fada da Sadiya saboda batayi ita kuma Sadiya itama sai tace bazata dafa ba" "To shikenan daga yau ku daina girki ku rinka zuwa captaria kuna cin abincin in yaso duk end of month zan rinka biyan abincin, shikenan? Girgiza kai A'isha tayi "a'a yaya aadil kabari kawai ni nayi maka alkawarin kullum zan rinka yin girkin in yaso fati sai ta rinka wanke wanke ko cefane" "Phertyn nawace yar wanke wanke? No gaskiya ki sake mata duty" Murmushi Aisha tayi "to yaya aadil zan sake mata, sai anjima" Mikawa Sadiya wayar tayi "ungo yaya aadil zakuyi magana" Karbar wayar tayi tana dariya "yaya aadil ina wuni?" "Bazan amsa ba saboda kin yi mana laifi nida pherty na" "Tuba nake yayanmu" Murmushi ya saki a hankali "to na yafe miki amma kar na sake ji" "baza a sake ba" "To sai anjima" Mikawa pherty wayar tayi tana yi mata dariya,cikin haushi pherty ta fusgi wayar tareda karata a kunnenta "Hello yayana" tafada a hankali "Yanmata kiyi hakuri komai ya wuce kinji? Ki daina kuka kinji pherty na, ina nan zuwa ganinki" Cikin doki tace "dagaske? Yaushe zaka zo?" "Sai kin daina kuka sannan zan fada miki", "nadaina yayana fada min" murmushi yayi mai dan sauti "to yi dariya naji" dariya ta fara harda kyakyacewa ahankali yace "zanzo upper week, me kike so na taho miki dashi?" Cikin farin ciki tace "ni kai kadai nake son gani" "Ki fadi abunda kike so pherty na", "wallahi bana bukatar komai yayana" murmushin jin dadi yayi "to shikenan yanzu ki zauna ki huta sannan anjima zan turo miki 20 thousands ta account dinki, saboda nasan akwai abubuwan da budurwa irinki take da bukatarsu amma kunya ba zai barki ki tambayeni ba" "Yaya aadil inada kudi fa, kabarshi kawai" "Nidai anjima zan turo miki" "Tom, nagode Allah ya saka da alkairi, Allah ya kara budi, Allah ya...!" Katseta yayi ta hanyar dora dan yatsanshi akan lebenshi "shiiiiiii godiyan ya isa haka pherty na, nasha fada miki duk abunda nayi miki cancantar kice ta sani yi miki, nidai kawai addu'ar da zaki yimin kwaya daya ce, cewar Allah ya bani ke" Cikin murmushi tace "amin" "Bari na kyaleki zan kira antynki bata jin dadi tana fama da mura, kema ki kirata kiyi mata sannu kinji, and expect my call later" "Zan kirata, sai najika yayana, bye bye" tafada tareda zare wayar daga kunnenta, cikin sauri ta danna number Salima ta fara kiranta, ringing uku ta daga, "Hello kanwata" aka fada daga can bangaren "Anty yajiki? Yanzu yayana yake fada min bakida lafiya" Murmushi Salima tayi "Ai yayan nan naki ya cika surutu, bafa wani ciwo bane mai yawa ba, just mura ce fa, kuma naji sauki ma" "Ayya, Allah ya baki lafiya, gasu Sadiya da A'isha zasu gaisheki" Wayar ta mika musu kowaccensu ta gaisheta sannan suka yi sallama, A'isha ce ta mike ta janyo risho ta kunna ta fara kokarin dora musu girki, kallon pherty tayi, "oh da haka mata suke da an zauna lafiya aduniya, wallahi nikam anty saliman nan tayi min, tana burgeni babu ruwanta" Sadiya ce ta karbi zancen ta hanyar cewa "ai shiyasa shi kansa yaya aadil din yake darajata saboda bata nuna irin wannan kishin haukan ba, domin daga lokacin da mace ta zubar da kimarta wai dan mijinta yana neman aure to wallahi daga ranar ta rasata har abada" Baki A'isha ta tabe "ai kuwa yawancin matan yanzu haka suke, basu san Kansu suke ragewa daraja ba,wata ma dan tsabar rashin aji har budurwar take yiwa waya ta zaga dan tsabar bada kai" Sai a lokacin pherty tayi magana "ni wallahi dan mijina yana neman aure banda time din kiran budurwar, aure ai hajace tazo kowa ya baje tasa mai rabo sai ya siyar" "Banda matan yanzu, matan yanzu mugunta da son kai sunyi musu yawa kowa sai tace ita kadai zata zauna a gidanta, alhalin kuma tana da kanne, idan kannenta ne tana son su auri mijin wata amma ita bata son a auri mijinta" A'isha tafada lokacin da take dora tukunya akan rishon data kunna "Allah dai ya rabamu da sharrin zuciya" inji Sadiya "Amin" suka amsa dukansu, pherty kuwa hoton aadil ta kurawa ido, yana tsaye yasha bakaken suit wanda suka yi tsananin yi masa kyau, yanata murmushi ya dafa wani karfe a bakin wani tafkeken kogi da alama hotonma a kasar waje yayi shi, murmushi ta fara yi ita kadai saboda tunowa da tayi yace zai zo nan da sati biyu masu zuwa. ********************** A bangaren jawad kuwa koda ya fita daga makarantar su pherty gidansu ya nufa cikeda kunar zuciya saboda kiyayyar da pherty take nuna masa yanzu tayi yawa alhalin shi kuma yanzu a duniya idan da wacce yake so to itace. Cikin tsananin gudu ya isa gidan nasu yana zuwa bai jiraba ya kutsa kan motarsa zuwa harabar gidan wanda yake katoton gaske, a fusace ya kashe motar ya zare key din ya nufi side dinsa,yana shiga bedroom dinsa ya shige yaje ya fada kan gado take zuciyarsa ta fara tafarfasa, idanuwansa kuwa tamkar gauta dan ja, Zaraf ya tashi zaune kamar wanda aka tsikara "Xarah, Xarah wallahi sai na aureki, mutukar ina numfashi bakida mijin da ya fini, nine mijinki ko kinki ko kin so, wallahi babu mai aurenki sai ni, haba Xarah!" Ya fada tamkar wani zautacce, "Kai jawad kai da waye?" Wata mata fara tamkar balarabiya ta fada cikin harshen fillanci kana kallonta zakaga tsananin kamarsu da dan nata jawad, kamar kara aka tsaga, shekarunta zasu kai 45 a duniya, Cikin damuwa ya jiyo ya kalleta "Ummi babu komai" yabata amsa cikin harshen fillanci shima, "Kowa ya kalli fuskarka yasan kana cikin damuwa jawad, ka fada min abunda yake damunka", Tamkar zaiyi kuka yace "Ummi wata budurwa ce bata sona, ta tsaneni nikuma ita nake so ummi, wallahi bazan iya rayuwa da wata mace ba idan ba itaba, she's the part and parcels of my life, i can't do without her, my life without her is just like a car without fuel, i can't survive without her" Ya karashe maganar cikin rawar murya Cikeda tausayawa mahaifiyar tashi ta karaso gabansa ta zauna kusa dashi tareda dafa kafadarsa, kayi hakuri jawad hakika kai ba kayi kamada irin mazan da mata suke tsana ba domin ka mallaki komai, wannan kar ya daga hankalinka zaka aureta zata soka fiye da yanda kake sonta". Ummi A'isha🏻 [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha: [4/25, 6:23 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA Pg 11-15 ~~~Fuskarsa da damuwa ya kalli ummin tasa yace "Ummi Xarah daban take acikin mata, sannan kuma duk abunda ta aikata a gareni daidai ne saboda....!" Kasa karasa maganar yayi, yai shiru da bakinsa, "Saboda me jawad?" Mahaifiyar tasa ta bukata, "jawad anya kuwa babu wani abu wanda kake boye min?" Kallonta yayi da jajayen idanuwansa "Ummi babu abinda nake boye miki, nidai ki tayani da addu'a kan Allah ya saukaka min al'amura na musamman ma dangane da pherty saboda idan har ban aureta ba to bazan taba gafartawa kaina ba" "Saboda me?" Ta tambayeshi tana kallonsa "Ummi saboda zuciyata tana sonta" Hannunsa ta kama "ka tashi kazo muje kaci abinci, dan uwanka ma yana nan zuwa nan da wani dan takaitaccen lokaci", Sai da gabansa ya fadi jin an anbaci cewar dan uwansa zai zo, shidai a halin yanzu idan da wanda yake jin haushi a rayuwarsa ta duniya to bai wuce dan uwan nasa ba domin ya fahimci yana yi masa shisshigi a gonarsa, "Katashi muje jawad" Muryar Mahaifiyar tasa ta dawo dashi cikin hayyacinsa, dan haka dole ya mike ya bita ba dan yaso ba. Part din mahaifiyarsa suka shiga an kawata komai akan table, abinci ne iri iri daban daban na alfarma, sai kamshin kanumfari da tafarnuwa ne ke tashi, idan da sabo to ya saba domin ko farar shinkafa aka dafa a gidan sai an sa mata kanumfari wannan yana daya daga cikin al'adar mahaifiyar tasu kasancewarta balarabiya usul, Kadan ya zuba abincin ya fara ci yana ci yana tunanin hanyar da zai magance matsalar da ta kunno kai gareshi, daga karshe ya yanke shawarar ci gaba da farautar zuciyar pherty har Allah yasa ya dace. **************** Yau ta kama ranar weekend dan haka gaba daya hostel din cike yake da hayaniya, pherty da A'isha kowacce tana kan gadonta a kwance, Sadiya ce ta shigo cikin dakin "To yan hutu sai ku tashi aje ayi wanki" Juyi A'isha tayi tareda dago kanta ta kalli Sadiya "Dan Allah ki bari ajima sai ayi" Harararsu tayi su duka "Wallahi ko ku tashi ko kuma na debi iya kayan da nasa na wanke na bar muku naku" Juyi pherty tayi sannan ta tashi zaune "Meye" ta fada tana hararar Sadiya "Ba asani ba" Sadiya ta fada tana hararar ta itama, "Wanki za ayi wai yanzu da sanyin safiyar nan" A'isha ta fada tana kallon pherty "Tab babu wankin da zanyi wallahi, daga tashina ko muryar yayana banji ba", wayarta ta dauka ta fara kokarin kiran yayan nata, "Kun san halina ai, kowaccenku tayi duk abinda take so yanzu" Sadiya ta fada lokacin da take kokarin ficewa daga cikin dakin, "Yayana ko baka tashi ba?" Pherty ta fada a hankali, ita kam A'isha kwanciya tayi tafara sauraron hirar pherty da aadil, ita dai a duniya bata taba ganin masoyan da suke burgeta ba kamar pherty da Aadil, Yana daga kwance akan makeken gadonsa yayi murmushi tareda yin juyi "natashi tun dazu antynki ce ta tasheni ma, badon haka ba sai 11 zan tashi" Murmushi tayi "ai kuwa dai ta kyauta dan da bata tasheka ba da bazan ji muryarka ba yau sai nan da 11?" "Eh mana" ya fada yana kokarin bude laptop dinshi wacce ke ajiye a kan bed side drawer dinshi, Yana budewa hoton pherty ne ya mamaye kan screen din, hoton ya tsaya yana kallo, "Kinyi kyau pherty na" ya fada lokacin da yake shafa hoton, "Kaima ai kullum kana yin kyau yayana" "To yaushe kika tashi?" "Yanzun nan Sadiya ta tada mu wai zamu yi wanki, nikuma wallahi yaya na tsani wanki bata min rai yake yi" "Shine baki taba fada min ba? Ina sadiyan?" "Tafita" "A'isha fa?" "Gata" "To bani ita" A'isha ta mikawa wayar, "ungo yayana zai yi magana dake" karbar wayar A'isha tayi ta kara a kunnenta "Hello yaya aadil" "A'isha daga yau na soke yin wanki, babu ku babu wanki, ku rinka kaiwa shago ana wanke muku kinji? Wadanda zaku iya wankewa kawai na yarda Ku wanke" "To yaya aadil zamu kiyaye" A'isha ta fada tana kallon pherty tareda mika mata wayar Karba tayi ta juya suka ci gaba da hirarsu da aadil har Sadiya ta shigo ta fara aika musu da harara, "Albishirinki?" Inji A'isha "Goro" Sadiya ta mayar mata da amsa "To yayan pherty ya hanamu wanki yace sai dai muna kaiwa shago inners wears kawai ya yarda mu wanke, zama Sadiya tayi "ai yaya aadil dinnan yana shagwaba yarinyar nan ina jin idan sunyi aure babu abinda zata rinka yi" Dariya A'isha tayi "ai kuwa ya kyauta danni wallahi hakan burgeni yake" Mikewa Sadiya tayi ta nufi risho tana fadin "eh ai keda ita duk halinku daya na rashin son yin aiki". Ranar Monday da wuri dukkaninsu suka shirya domin zuwa lecture kowaccensu taci kwalliya ajin karshe, atare suka fito suka nufi area classes, a ta gaban wani babban hall pherty ta hangoshi zaune acikin motarsa kirar KIA kalarta ja yana sanye da bakin face a fuskarsa, "Jawad ko kai maye ne sai haka" tafada acikin zuciyarta, yana hangosu ya fito ya nufo inda suke, kasancewar basu sanshi ba sai suka tsaya kallon gun wacce zai zo, Agaban pherty ya tsaya yana mayaudarin murmushinsa dake sace zuciya wanda pherty ke ganinsa tamkar hayaki dan baki, "morning my queen" ya fada a hankali, Kanta ta juyar, yayinda A'isha taja hannun Sadiya dan su dan basu waje, suna matsawa ya dubi fuskarta wadda tasha kunu murtuk a hankali ya furta "ki saki fuskarki, wannan bata ran da kikayi bai kamaci kyakkyawar fuskarki ba pherty na" Dam,dam gabanta ya fadi, saboda wannan sunan yayanta ne kadai ke kiranta dashi, Gabanta ya dan sake matsowa "don't break d heart that love you pherty, love can neva being hate, and you know..!" Hannu ta daga masa, "kai jawad, kai macuci ne, kai azzalumi ne, kai marar imani ne, wai me na tare maka a rayuwar duniya da kaketa burin sai ka ga bayana? Jawad har yau ina tareda bakin cikin da kunsa min koda wannan ka barni kayi wa MARTABA TA babbar illa, kayi hakuri ka kyaleni ka barni da abinda nake ji, kai maha'inci ne nasan duk maganganunka na yaudara ne, yanzu nasamu mai kare MARTABA TA dan haka kayi nesa dani" "Impossible" ya fada cikin daga murya "Ni jawad nine mutumin da zan dawo miki da MARTABAR KI nine zan aureki zan nuna miki soyayya sannan na kare miki MARTABAR ki, wallahi kinji na rantse mutukar ina rayuwa to sai na aureki pherty, indai kika ga ban aureki ba to mutuwa nayi" yana kaiwa nan ya juya ya nufi motarsa, sai a lokacin tabi bayanshi da kallo yana sanye cikin dark blue din jeans da yellow din t shirt mai gajeren hannu. Kamar ta fashe da kuka take ji saboda ta rasa yadda za tayi da jawad ya fita daga cikin rayuwarta, Su A'isha da Sadiya ne suka karaso inda take "yau yaya aadil ya samu abokin takara kenan" A'isha ta fada tana dariya, "Kuma fa kinga shima ya hadu" Sadiya ta bata amsa, ai pherty na jin haka hawaye ya fara sulalowa daga cikin idonta dama kamar jira take, Cikin mamaki dukkaninsu suka fara magana "Allah ya baki hakuri daga wasa?" Wasu hawayen ne suka gangaro mata ba tareda ta basu amsa ba, "Kiyi hakuri pherty mun san yaya aadil kike so, to amma shi masoyi bai taba zama makiyi ba dan haka shima wannan din ki lallabashi ku rabu lafiya" Sadiya ta fada tana kallonta, jan hannunta A'isha tayi "muje mu shiga lecture pherty zamu tattauna daga baya" inji A'isha. Koda suka fito daga lecture ma bata sauya zani ba in banda kuka babu abunda pherty take yi lallashin duniya suka yi mata amma taki yin shiru ganin haka yasa Sadiya Kiran aadil a waya ta sanar dashi, cikin rudu yace "Bani ita" bata wayar Sadiya tayi "ga yayanki zaku yi magana" Karbar wayar tayi cikin kuka ta fara magana. Ummi A'isha🏻 [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [4/27, 6:12 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA Pg 16-25 *** Cikin kuka hadeda shagwaba pherty ta fara magana "Yayana" Arude ya amsa mata "Pherty na me ya sameki? Ki fada min pls" Hawayen fuskarta ta goge "Yaya Aadil kaina ke ciwo amma yanzu ya daina" "Um um fa phertyma ki fadi gaskiya" Murmushi tayi itama "Wai yaya Aadil baka kunyar fadin sunana bayan kuma sunan umminka ne" Yar dariya yayi mai dan sauti "To ai ba sunan Ummi na fada ba sunan matata na fada kuma sunan first born dina" "Anty saliman mace zata haifa?" Ta tambayeshi cikeda zolaya "Ke dai, kece zaki haifi mai sunanki insha Allah" Shiru tayi, can kuma tayi zakal tace "To ai babba shine ya kamata ya fara haihuwa,in dai ba tsari ake yi ba" "Babu wani tsari ita kanta antyn naki tana son haihuwa nima kuma ina mutukar kokarina kawai dai Allah ne bai kawo ba" "Wanne kokari kake? Babu wani kokari" "Haka kikace? To bari muyi aure zaki ga rashin kokarin nawa" "Allah ya baka hakuri wasa nake ai nasan kai mai kokari ne ako ina" Murmushi yayi "matsoraciya, har kin tsorata? To albishirinki?" Cikin doki da murna tace "goro" "Nafasa zuwa next week, this week zanzo naganki, so ki daina kuka kinji?" Cikin murna tace "ranar yaushe?" "Ranar juma'a zaki ganni domin wurinki ma zan fara zuwa" "Woooh" ta fada cikeda murna "yeeeeh" ta sake sakin yar kara "zanga yayana" Dariya ya soma yi mata daga karshe yace "tunda naga kinata murna to bari na barki anjima zan kiraki" "To yayana, bye" Tsalle ta daka ta dale jikin Sadiya da A'isha "yaya Aadil zaizo this Friday, me zan dafa masa? Yeeeh fried rice zanyi in hada masa coconut juice" Sadiya da A'isha dai kawai dariya suke suna kallonta kamar ba itace take kuka dazu ba amma yanzu gashi tanata dariya, haka suka rankaya suka nufi hostel. Tun daga ranar pherty kullum cikin lissafi take na zuwan yayan nata, yau ta kama ranar laraba a lissafinta saura kwana biyu yayanta yazo, ko kwalliya ta daina yi sai ranar da zai zo zatayi. Shiryawa tayi ita da A'isha suka nufi class yayinda suka bar Sadiya kwance tana bacci saboda ita bata da lecture, yau ma kamar kullum yana tsaye inda ya saba tsayawa, wani kululun bakin ciki taji ya tokare makogaronta amma yau tayi niyyar yi masa abinda indai yana da zuciya ba zai sake zuwa gareta ba. Kanta ta dauke tareda kama hannun A'isha suka wuce,shima bai yi kasa a gwiwa ba ya bi bayansu yana kiran pherty, Juyowa tayi ta dubeshi fuskarta a daure ga dalibai fal kowa yana harkar gabansa, "Tsaya ki saurareni queen" "Me zan saurara? Karya ko yaudara? Aciki wanne kake son na saurara? Jawad ka fita daga harkata rayuwar data faru can abaya tsakanina da kai ka barshi a matsayin mummunar kaddara kuma jarrabawa a gareni" Kallonta yayi a raunane, "tayaya zan barki bayan zuciyata tana sonki?" Ya fada cikin harshen turanci Dan murmushin takaici tayi "sanin kanka ne bazan taba aurenka ba har abada" Cikin daga murya ya mayar mata da amsa "dole sai kin aureni kuwa, kuma wallahi bazan hakura dake ba" Hankulan jama'a tuni suka daddawo Kansu saboda yanda jawad yayi maganar da karfi, "You kid your self jawad, pherty will not marry you,idan mafarki kake to ka farka, dan bazan aureka ba ko ka zata na manta waye jawad? To har yau ina sane da kai, kai macuci ne, mayaudari, maha'inci sannan babban mazinaci" Da sauri A'isha ta jiyo ta kalleta, yayinda daliban wurin suka shiga mamakin wannan wulakanci da ake yiwa wannan kyakkyawan saurayi dan ya hadu tako wanne bangare, Shi kuwa jawad wata kunya yaji ta rufeshi a wurin saboda yanda mata da maza suke turarreniyar kallonsa, wani bacin rai yaji ya ziyarci zuciyarsa, "Marar tsoron Allah mai raba "yayan mutane da MARTABAR su..!" Bata karasa maganar ba sakamakon janyeta da A'isha tayi suka nufi bayan wani hall shima jawad juyawa yayi ya shige motarsa ya fizgeta da karfi yabar wurin, "Haba pherty wannan wulakancin da kike yiwa gayen nan yayi yawa,idan wani abu yayi miki ai ya kamata ace kin yafe masa, idan kuma ramawa kike son yi to bai kamata ki rama ta wannan hanyar ba domin kin ci mutuncinsa mutuka" Cikin masifa pherty ta kalleta,"naci mituncin nasa idan yanada zuciya daga yau kar ya sake zuwa wurina" tana gama fadin haka ta juya ta nufi hostel ba tareda ta jira Aishan ba. Bin bayanta A'isha tayi tana yi mata magana "ai so baya zama ki, wulakanci bai kamata ba" juyowa pherty tayi "sai kiyi tayi kuma" Haka dai suka ci gaba da tafiya suna fada har sukaje hostel, suna shiga daki suka samu Sadiya zaune tana shirya musu kayan sawarsu cikin akwatinansu Nan suka ci gaba da fada har Sadiya tasa baki "indai gayen nan na rannan kika yiwa rashin mutunci gaskiya baki kyauta ba" nan pherty ta sake harzuka,kawai sai ganinta suka yi tasa kuka, harararta Sadiya tayi "ace mutum bashida wani aiki sai na kuka?" "Um ai kin san gaskiya wuya ne da ita" A'isha ta fada lokacin da take kokarin tashi domin rage kayan jikinta, jin maganganunsu yaki karewa yasa pherty ta tashi tabar musu dakin ta tafi wani dakin. Tun daga lokacin ta fita harkarsu har ana igobe zuwan yayanta, shi kansa bata fada masa ba, ganin tanata fushi yasa A'isha da Sadiya lallashinta har ta sauko suka koma harkokinsu kamar da amma basu sake tayar mata da batun jawad ba. ****** A bangaren jawad kuwa yaji bakin cikin wulakancin da pherty tayi masa acikin mutane domin har kwalla ya zubar amma yayi alqawarin jure duk wani wulakancinta har sai ya cika burinsa na mallakarsa a matsayin mata, daren ranar bai iya bacci ba saboda bacin rai. Yau itace ranar da Aadil zaizo daga Abuja, tunda sassafe su pherty suka je kasuwa suka iyo cefanen da zasu yiwa Aadil kayan sauka, Fried rice da hanta suka yi masa wadda tasha cabbage da su carrots da sauran tarkacen kayan lambu, ga lemon kwakwa da aka hada masa. Karfe 12 daidai ya iso cikin makarantar, pherty ansha kwalliya cikin brown din doguwar riga mai tsananin kyau ga make up data tsarawa fuskarta tasha turarruka kala kala, kallonta suka yi kawayen nata "kinyi kyau yanmata" murmushi tayi "nagode, bari naje in yaso kwa kawo abincin ko?" Dariya Sadiya tayi "irin wannan kwalliyar kam bai kamata ki dauki kwanukan abinci ba" dariya suka yi su duka ita dai pherty juyawa tayi ta fita yayinda su kuma suka fara kokarin shisshiryawa. A karkashin wata bishiya ta hangoshi ya shimfida katuwar darduma yana zaune cikin manyan kaya farar shadda goggagiya mai tsada yasha hula mai adon fari da baki hannunsa daure da agogon azurfa yana yin waya da alama da matarsa yake wayar, Da murmushi a fuskarta ta karasa, shima murmushin yake yi, a hankali ta zauna can dan nesa dashi kadan tana jiran ya gama wayar, "yau ko zaki ganni sai dare dan daga nanma gidan Ummi zanje" haka taji ya fada lokacin da yake ajiye wayar. Yana ajiyewa ya juyo ya fara aika mata da tsadadden murmushi, "pherty na" ya fada yana murmushi "Yaya na sannu da zuwa, ya hanya? Yaka sauka?" "Alhamdulillah pherty na, antynki tana gaisheki tace kuma karki cika mun cikina da daddadan abincinta gudun kar nakasa cin nata abincin idan nakoma gida" Murmushi tayi ta kalleshi "ai kuwa sai dai tayi hakuri dan yau cikinka iya abincina zai dauka, gobe sai ya dau nata" Kallonta yayi cikin farin ciki "kinyi kyau pherty na" hannunta tasa ta rufe fuskarta tana murmushi "Haka ma agida zaki rinka yimin wannan kunyar?" Dakyar ta iya kallonsa, "ya aiki? Ina fata yanmatan abuja basa kallon yayana?" "Yayanki nakine keda antynki kawai, ki kwantar da hankalinki" "A'a ka fada ne fa kawai" tafada kamar zatayi kuka "Haba pherty na, yau bakya son wakar?" "Ina so" tafada tana dariya Daidai lokacin Sadiya da A'isha suka karaso dauke da kwanukan abinci a hannunsu "Sannu da zuwa yaya Aadil" suka fada dukkaninsu atare tareda ajiye abincin a gabansa, bayan sun gaisa suka juya suka tafi, Abincin ta zuzzuba masa ta tura masa gabansa,kallonta yayi "duk wannan abincin a cikina zan sa?" "Eh mana yayana" Murmushi yayi "pherty na kenan" Kallonsa ta tsaya lokacin da yake cin abincin ita dai bata taba tunanin zata auri namiji mai mata ba sai gashi ashe mai mata ne mijinta, taso ta more rayuwarta da saurayi ashe da bazawari zata yi, "Ya akayi ne kika tsaya kinata kallona" Murmushi tayi babu komai kawai kayi min kyau ne shiyasa" "Fadi gaskiya dai" Hira suka yita yi har ya gama cin abinci yayi alwala ya tafi sallar juma'a ita kuma ta koma hostel ta sake wani sabon wankan ta sake shiga cikin wata atamfa kalar ruwan kwai tasha dauri su A'isha da Sadiya sai tsokanarta suke, gurin Aadil ta sake komawa bayan ya dawo daga masallaci, "Yau dai zaki barni natafi kuwa?" Ya fada yana kallonta "naga sai kyau kiketa zubawa" "Yaya banda zolaya dai" "Babu wani zolaya" ya fada yana yi mata murmushi. Har yamma suna tare sai wurin 5 sannan ya tafi bayan ya firfito mata da shopping din da ya siyo musu, kaya kamar a shago kama tun daga kayan makulashe har zuwa turarruka da hadaddun mayuka, yana fita daga school dinsu pherty gidansu ya wuce wato gidan iyayensa. Lokacin da ya shiga gidan nasu mahaifiyarsa da kaninsa suna zaune a tsararren falon ummin tasu, cikeda fara'a ummin ta fara yi masa sannu da zuwa amma shi dan uwan nasa kau da kai yayi tamkar bai ganshi ba, Kusa da ummin yaje ya zauna "sannu da hutawa Ummi". "Yawwa Aadil barka da sauka" da sauri ta tashi ta nufi kitchen domin hado masa kayan motsa baki,tashi yayi ya nufi inda kanin nasa yake ya mika masa hannu "Assalamu Alaikum ya Aki" "wassalam" jawad ya fada tareda dauke kansa ya tashi ya fice daga cikin falon ba tareda ya bashi hannu sunyi musabaha ba, bin bayansa da kallo Aadil yayi wannan wacce irin kaddara ce take kokarin kutso kai tsakaninsa da dan uwansa, yana nan zaune Ummi ta dawo dauke da faranti wanda ta doro kayan motsa baki a kai, akan dan table din gabansa ta ajiye, nan ta zauna ta fara hira da dan nata har tsawon wani lokaci daga bisani yayi sallama da ita ya nufi sashen mahaifin nasa. Lokacin da yafito ya shiga part din abbunsu a lokacin shi kuma jawad yana kokarin fitowa, wata harara jawad ya aika masa da ita ya dauke kansa ya wuce, wucewa ciki Aadil yayi yanata jajanta wannan lamarin acikin zuciyarsa, a babban falon mahaifin nasa yayi ya tarar dashi yana kishingide yana wuridi da casbaha a hannunsa, Da sauri yaje ya duka a gaban mahaifin nasa bayan sun gaisa ne yake sanar masa da cewa yana so zai kara aure,kallonsa mahaifin nasa yayi "aure Aadil? Lafiya zaka kara aure?" "Lfy lau abbu, kawai dai akwai dalili ne, ina son taimakon yarinyar ne abbu, domin inada halin iya rike mata hudu tunda Allah ya bani arzikin da zan iya yin haka shiyasa nake son yin amfani da wannan damar wurin taimakon yarinyar" kada kai mahaifin nashi yayi "Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya albarkaci rayuwarka, dama nayi tunanin ko dan saboda matarka bata haihu bane shiyasa zaka kara aure to amma tunda ba haka bane to Allah ya tabbatar da alkairi" "Amin abbu" "Nan da yaushe zaka kara auren?" "Abbu nan da watanni hudu" "To Allah ya kaimu" "Amin abbu,a huta lfy" Tashi yayi ya fita ya koma yayiwa mahaifiyarsa sallama ya fito ya nufi gidansa inda matarsa ke zaman jiransa. Koda yaje ya samu Salima cikin kyakkyawar shiga tasha kwalliya tayi kyau sosai, nan ta tarbeshi cikeda kisisina, wanka ta kaishi yayi ta shiryashi cikin kayan shan iska. Bayan wani dogon lokacine Aadil ya shafo gashin kanta yace "Salima kiyi hakuri da abinda zakiji daga gareni" Dam gabanta taji ya fadi amma sai ta daure tace ina jinka "Salima bikina da phertyma nan da watanni hudu masu zuwa za ayishi, dazun nan muka gama maganar da abbu" Duk da hankalinta ya tashi amma sai ta dake tayi murmushi ta riko hannunsa "Allah ya nuna mana lokacin, Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu" Hannunta ya damke "amin baby, hakika ina jin dadin yanda kuke mu'amula keda pherty tun kafin tashigo gidan" "Babu komai dear ita kishiya ai yar uwace" "Allah yayi miki albarka, nikuma nayi alaawarin kulawa dake har karshen rayuwata". Washe gari da misalin karfe 3 yaje wurin pherty bayan sunsha hirane yake sanar mata da batun bikinsu nan taji jikinta yayi sanyi amma ta nuna masa farin cikinta a fili, koda ya tafi ta shiga hostel nan ta fadawa su Sadiya da A'isha sai kuma ta fara kuka, nan suka shiga tsokanarta wai kukan farin ciki take. *** Jawad yana zaune a falo daga shi sai three quarter da yar body hug yana tv game ajikin computer kamar wani yaro, Ummi tana zaune tana waya kamar daga sama ya jiyo ta tana cewa "bikin Aadil ne ya taso nan da 4 months zai auri wata yarinya phertyma shine nake son ki hado min kayan lefe....!" Zunbur ya mike kamar an tsikareshi, da sauri ya wuce side dinshi ya dauko key din motarsa ya nufi gidan yayan nasa Aadil, lokacin da ya shiga gidan iya Aadil ne zaune a falo yana kallo yayinda Salima take kitchen tana aiki, A can ciki yayi sallama,shi dinma Aadil din a dakile ya amsa domin ba don ta zama wajibi ba ma to da bazai amsa ba, Kallonsa jawad yayi idonsa kamar gauta dan ja, "nazo ne nayi maka kashedi, pherty ba taka bace tawace, ta sanadiyyata ka ganta har ka kamu da sonta saboda tsabar abin kunya" Kallonsa Aadil yayi "Kai wanne irin shasha ne? Kana tsammanin pherty zata aureka ne? To idan mafarki kake gara ka farka, bayan ka gama rusa mata MARTABAR TA shine yanzu zaka dawo kace wai kana sonta? To babu abinda pherty zata yi dakai gara ma ka daina batawa kanka lokaci" "Ba batawa kaina lokaci nake ba kuma kai kanka zaka tabbatar da haka domin indai ina rayuwa to nine mijin pherty, kuma nine zan dawo mata da MARTABAR TA" "Ahakan? You are very stupid, idiot" Har ya juya zai tafi ya sake dawowa, "kar ka kuskura ka sake zagina dan zan iya daukar mataki" "An zageka din, idiot ko zaka rama ne?" Idonsa jawur ya kalleshi "kai kanka kasan a doke ba iya duka na zakayi ba dan ko fafatawa muka yi ba zakayi nasara ba akaina so be very careful" ya nunashi da yatsa sannan ya juya ya fice daga falon yabar Aadil a tsaye. Ummi A'isha🏻 [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [4/28, 8:49 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 26-30 ~~~ Jawad yana fita Aadil ya dunkule hannunsa ya naushi iska "oh! My God", ya fada da karfi tareda fadawa kan kujera dabas ya zauna daidai lokacin Salima ta fito daga cikin kitchen ta zauna kusa dashi, "Sahibi meke faruwa ne?" Cikin kunar rai yace "Babu komai" "Da kuma sai naji kamar muryar jawad" Shiru yayi bai bata amsa ba sakamakon tafarfasar da zuciyarsa keyi, aransa fadi yake "yaron nan jawad na fuskanci ya gama rainani amma zanyi maganinsa dan ni ba sa'ansa bane, a haifi yaron akan idona amma yazo yana kawo min raini?" Dafashi Salima tayi tareda fara rarrashinsa tamkar karamin yaro duk kuwa da cewar bata da masaniyar abunda ya faru amma dai taga ransa a bace don haka ta fara kokarin mantar dashi bacin ran dake tare dashi. ****** Lokacin da jawad yabar gidan Aadil gudu kawai yake shekawa ya nufi sch din su Xarah wato state university gombe, yana zuwa babu jira ya shiga cikin makarantar a gaban auditorium yayi parking yana daga cikin motarsa a zaune, wani irin zugi yaji zuciyarsa nayi masa tabbas ko shakka babu yasan yana daf da kamuwa da ciwon zuciya. Yana nan zaune cikin motar tasa kamar daga sama ya hangosu itada Sadiya sun fito karatu, da sauri ya bude motar ya fita ya nufesu, sai da gaban pherty yayi mummunar faduwa lokacin data ganshi, cikin dashewar murya yace da ita "Zo ina son magana dake" Yana gama fadin haka ya juya ya yi gaba, kamar wacce take tsoronsa ta kalli Sadiya tace "ina zuwa, bari nadawo" Binsa tayi har wurin motarsa ta tsaya ta waje tana kallonsa cikeda alamun tsoro karara akan fuskarta, "Gani" ta fada tana kallon wani wuri, "Pherty" Yakira sunanta cikin damuwa, "Kina son ki hadani da dan uwana ko? Kina son hada yaki acikin familynmu ko? Aadil is my brother and i love him more than how you are think, so kar ki jawo abun da zaisa na tsani dan uwana, kar kisa nafara gaba dashi, tabbas idan kika auri Aadil kin gama da rayuwa ta kuma babu abinda yayi saura acikin rayuwata" Kallonsa ta danyi ta gefen ido ga mamakinta sai taga yar kwalla acan lungun idonsa,idanuwansa sun kada sunyi jajur, "Sai dai kayi hakuri jawad amma a gaskiya ni ahalin yanzu banida miji in ba yaya Aadil ba...!" Cikin sauri ya balle murfin motar ya fito wata damka ya kai mata "ke me kike takama dashine? Am asking you dame kike ji? You are not serious pherty, ke kin isa ki auri wani namijin da ba niba? Kinyi kadan wallahi ni zaki aura" Yana kaiwa nan ya sassauta rikon da yayi mata "pherty kar kiyiwa rayuwata haka, bai kamata ki rama abinda nayi miki ba ta hanyar auren dan uwana, haba pherty so kike ki kasheni ne? Wallahi indai baki aureni ba mutuwa zanyi i will die if you didn't marry me, pls save my life, pls pherty,pls, pls" kansa ya kifa akan kafadarta kwalla tana kokarin zubowa daga idonsa, ita kanta phertyn hawaye ne yake kwaranya daga idonta domin tasan tana son jawad so nagaskiya to amma bazata taba iya aurensa ba, dole ta auri aadil saboda wani dalili mai karfi, Yakai mintuna biyu ajikinta yana shakar kamshin jikinta sannan ya dago kansa yana kallonta, "idan har na mutu ko kuma na fada cikin wani hali to ki zargi kanki" Yana kaiwa nan ya matsa daga kusa da ita ya shiga motarsa yaja ya fita yana driving yana hawaye Wanda shi kansa bai san ko na menene ba, yana isa gidansu part dinsa ya shiga ya kwanta akan tangamemen gadonsa ya fara tunani "hakika pherty nasan na cutar dake, amma ki yafe min ki bani dama domin gyara kuskurena,pls and pls pherty" haka ya fada a hankali, Juyi kawai yake ga wani irin ciwo da yaji kansa yana yi masa gashi yayi nauyi kamar an dora masa katoton dutse akan nasa, daren wannan rana yayishi ne cikin bakin ciki da tashin hankali. A bangaren aadil ma haka abun yake domin shima hankalinsa a tashe yake kwata kwata bashida walwala sai sakar zuci yake, dan haka koda Salima tayi bacci falo ya koma ya zauna yayi tagumi, yayinda bacci yayi kaura daga idonsa. Wannan dare darene mai cikeda fargaba, kunci, takaici, bacin rai ga mutane guda uku wato jawad, aadil da pherty, domin itama tun lokacin da jawad ya tafi ya barta take kuka dakyar su Sadiya suka sata tayi shiru, amma idonta kyamas babu alamun bacci. Washe gari da safe bayan aadil yayi wanka yayi breakfast ya shirya domin fita zaije yaga pherty sannan yaje gidansu, lokacin da yaje makarantar yana ganin pherty yasan akwai matsala saboda fuskarta duk ta kunkunbura alamun tayi kuka ta more amma tambayar duniya yayi mata taki fada masa gaskiya, Kallonta yayi cikeda damuwa "pherty na ban sanki da haka ba, ada bakya boye min komai amma yau kin canza daga yanda nasanki" Murmushi ta dan kakaro "yayana yau ma ba canjawa nayi ba, gaskiya na fada maka babu abinda ke damuna" Kallo kawai ya bita dashi amma bai yarda da abunda ta fada ba sam, daga karshe dole ya hakura ya tafi. Yana zuwa gidansu yayi parking din motarsa a gurinda aka tanada ya tasamma cikin gidan yana shiga ya hango jawad akan dinning yana yin breakfast shida Ummi, kamar kazar da kwai ya fashewa aciki haka ya karasa inda suke, durkusawa yayi ya gaida Ummi sannan ya mike yana kallon jawad wanda yayi kicin kicin ya hade rai, shi dinma aadil din ta ciki na ciki yake kallon jawad cikeda jin haushi, falo ya koma ya zauna yana jiran Ummi tagama tazo, shi kam jawad sai hararar aadil yake kasa kasa gudun kar Ummi ta ganesu. ****** Tun tafiyar Aadil pherty take faman kuka kamar ranta zai fita, cikeda damuwa pherty da Sadiya suka sakata a tsakiya, "Pherty dan Allah kiyi hakuri, shifa auren nan ba mutuwa bace" A'isha tafada tana dafa kafadarta, "Ni nafasa ma auren, shima yaya aadil din nafasa aurensa tunda abin hakane" tafada cikin kuka, "Kinada hankali kuwa?" Sadiya tafada cikin razani, "Wallahi da hankalina Sadiya, da hankalina,idan na auri yaya aadil zan haifar masa da matsala tsakaninsa da dan uwansa, zan jawo rikici a tsakaninsu wanda har sai duniya tayi ala wadai dani, haka auren jawad ma bazai haifar min da kwanciyar hankali ba domin idan na aureshi banyi wa yaya aadil halacci ba sannan nazama butulu wadda take mance alkairi hakan zaisa nan gaba mutane suji tsoron yiwa wani taimako domin idan sunji labarina zasu dauka kowa mai irin halina ne" Cikeda mamaki dukkaninsu suka kalleta "Bamu ganeba kin bamu abu a dunkule" Aisha tafada, "Dan Allah ki daure ki warware mana ko mafi fuskantarki" Sadiya ta fada tana kallonta, "Tabbas nasan zamanmu daku ban taba sanar daku labarina da matsayin yaya aadil agareni ba, to amma yau ya zama dole nasanar daku labarina wanda babu komai acikinsa face, gargadi, bacin rai, tausayi, ban mamaki hadeda ban haushi, labarina cike yake da sarkakiya da abun mamaki nagaske, ina so ku nutsu ku saurareni domin jin wannan labari nawa domin ina so ya zamo izina ga yanmata da iyayenmu mata" Nutsuwa suka yi cikin mamaki sukace "muna sauraronki, amma kafin ki fara meye alakar aadil da jawad?" "Aadil yayan jawad ne uwa daya uba daya, zaku fahinci hakan idan kuka biyo labarina" "Muna sauraronki" suka fada a tare. Masu karatu kun shirya jin labarin pherty?? Nidai Ummi Shatu na shirya, dani daku mubi pherty Xarah dan jin labarinta, gaisuwa gareku masoya masu bibiyar labarin. Ummi A'isha🏻 [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [5/1, 7:32 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 31-35 ~~~ Kowaccensu gyara zama tayi ta nutsu ta fara sauraron labarin pherty wacce ta fara da cewa "phertyma maitama Umar shine cikakken sunana asalin mahaifina dan gombe ne acikin wata local government da ake kira da kumo, muna zaune acikin unguwar tudun wada, mahaifina Malam Umar sunyi aure da mahaifiyata tun auren saurayi da budurwa kuma suna zaune lfy basuda wata matsala sai ta rashin haihuwa, duk zamansu shekara da shekaru basu samu haihuwa ba amma hakan bai Sa mahaifina kara aure ba, Mahaifiyata malama Adama yar asalin gombe ce acikin karamar hukumar funakaye,sana'ar mahaifina itace kasuwanci kuma a unguwa shine na'ibin limamin unguwarmu kasancewar mahaifina mutum ne mai addini, Tun lokacin da aka haifeni na taso cikin gata da kulawa domin rayuwar gidanmu rayuwace ta babu yabo babu fallasa iyayena suna gudanar da rayuwarsu cikin godiyar ubangiji. Nayi karatuna na primary har nakai ga secondary gashi babu laifi nayi karatun addini daidai gwargwado. Tun daga makaranta har gida banida kawaye, kawata kwaya daya ce hawwa wacce muka taso tare sannan hatta makaranta tare muke zuwa. Lokacin da nashiga aji hudu a makarantar secondary a lokacin ne samari suka fara yimin caa gashi dai ba wani girma gareni ba sai dai kyawuna wanda ya fara bayyana a lokacin domin nafara zama cikakkiyar budurwa. A zahirin gaskiya nikaina nasan inada kyau daidai misali kuma inada kirar jiki mai daukar hankali wannan dalilinne ma yasa samarin fara bayyana min soyayyar su adai dai wannan lokaci. Kamar kullum yau ma nadawo daga makarantar boko jikina sanye da uniform riga da wando jajaye da farin dankwali da farin hijabi, kafata sanye da takalmi sandal in banda yunwa babu abinda ke damuna domin da safe banyi kyakkyawan breakfast ba natafi kasancewar na makara, A gaggauce nashige gida duk kuwa da cewar naga wani saurayi sai bina yake amma ban saurare shi ba domin nagama gajiya, ko sallama ban iya yiba nashige cikin gidan "phertyma ya ko sallama babu" muryar mama najiyo daga cikin kitchen "Mama nagaji ne ga yunwa wlhi" "To ai maganinki kenan tunda kullum bacci kikeyi bakya tashi da wuri kinga kuwa ai dole ki rinka makara" Daki nashige naje na tube uniform dina na dauro zani kawai na fito na nufi kitchen wurin mama, Ina zuwa na tarar ta tana jifan dan wake, "sannu mama" nafada ina kokarin jawo filet "Sannu phertyma, an dawo, amma kin shanyo rana" mama tafada cikeda tausayina "Wallahi mama yau ana kwalla rana ga zafi" Dan waken na zuba na saka mai da yaji nan na zauna nafara durashi acikina,ina ci muna hira da mama acikin hirar tamu har korafin samarin dake yawan damuna nayi mata, amma sai tace babu komai Allah ya zaba min abinda yafi Alheri agareni, daf da zan gama cin abincin naji sallamar hawwa kawata, Dan waken na zuba mata muka shige daki muka kule "hawy nikam ina fama da jarabar samari, kema suna damunki haka?" Murmushi tayi tafara gauraya dan waken dake gabanta tace "pherty ai kin san dama su samari haka suke da zarar sunga ka kusa gama makaranta sai subi su addabeka" Baki na tabe na dubeta "Hawy nidai gaskiya ko zanyi aure to sai nagama university saboda ni kinga ni kadaice a gidan nan banida yaya banida kani dole nice mai taimakawa su mama, gara ke kinada yayyu" "A'a pherty nima fa ina son yin karatu saboda gaskiya karatu yanzu shine babban gata" "Yawwa to kin gani, dan haka kuwa in dai zamuyi karatu to dole mu share samarin nan na zamani" Yar dariya hawy tayi tace "Ai dama hakan shine mafita" Hirarmu muka ci gaba dayi har tsawon wani lokacin kafin hawy tayi min sallama ta tafi gida, gun mama nakoma na zauna muka fara hira. Haka rayuwata taci gaba da tafiya cikin farin ciki da kwanciyar hankali domin banida wata damuwa da haka muka shiga s s 2 komanmu nida hawy muke yi, ajinmu daya bencinmu daya, kuma koda yaushe agida muna tare. Lokacin da bazan taba mantawa ba shine lokacin da muka shiga s s2 second term har a wannan lokacin banida saurayi kuma ban taba son wani saurayi ba,bayan mun taso daga makaranta nake cewa hawy zata rakani kasuwa da yamma sai tace itama dama tana son zuwa akwai abunda zata siyowa mamansu, bayan nadawo gida nayi wanka naci abinci na huta wurin misalin karfe 3 na yamma na biyawa hawy gidansu anan nasamu yayanta nan ya fara tsokanata "Kaga phertyn mama me kukan kitso" Dariya nayi nace "kukan kitso sai kace hawwa" "Ke me kike nufi, nice me kukan kitson?" Hawy ta fada daidai lokacin da take saka hijabinta "Oho miki" nafada ina dariya, fitowa tayi muka kama hanyar kasuwa, cefane na iyowa mama sannan na siyo mana kayan amfanin gida, ganin kayan sun yimana yawa yasa na ce wa hawy mu ajiyesu in yaso idan mun karasa siyayyar sai muzo mu dauka mu tafi gida, wata sabuwar plaza muka je a bakin kasuwa, kuma da alama ma ko fara amfani da shagunan ba ayiba, "kinga mu bayar ajiyar anan" hawy ta fada tana nuna min plaza din,wurin mai gadin dake zaune awurin muka je muka bashi ajiyar sai yace mu saka daga dan ciki gudun kar tashi ya kamashi ga kayan awurin, daga ciki din muka saka muka koma cikin kasuwa. Bayan mun kammala siyayyarmu ne na dubi Hawwa nace "gaskiya sai dai mu nemi keke napep saboda kayan nan namu da yawa" "Nima haka zan fada kika rigani phertyn mama" tabani amsa cikeda zolaya "Kya karata dai hawwan mama" nafada ina dariya amma dariyata sai ta tsaya saboda ganin kayanmu a warwatse agaban wannan plaza din, wani matashin saurayi muka gani tsaye sai yatsina fuska yake yanata nuni da hannunsa sai kace wani bebe, sai alokacin na iya daga kaina na duba sunan plaza din JAWAD PLAZA haka aka rubuta da manyan harrufa, "Kut, kan bala'i" nafada cikin jin haushi "Wannan rashin mutuncin fa" Hawy ta fada itama cikin bacin rai, "Kuyi hakuri kunji me wurinne yazo, kuyi hakuri yayana" mai gadin wurin ya fada yana kallonmu Nanfa naji na kulu saboda hango always din da nasiyo ayashe ana gani, "waye me wurin? Shi ba acin arzikinsa?" Na tambayi mai gadin "Kuyi hakuri kawai yara" Bakin cikine ya rufe mu dukkanmu nida hawy saboda tsakanin nida ita babu mai iya zuwa ya dauki always dinnan dan kunya, "wallahi bazan hakura ba na fada cikeda masifa" Wannan saurayin na gani ya nufo inda muke sai a lokacin na yi masa kallon kurulla farine jawur kamar kana taba fatarsa jini zai fito, yana sanye da doguwar riga jallabiya baka da wando jeans aciki, da hannu yake tambayar mu wai me ya faru yaga muna fada, "rainin hankali" nafada da karfi "Ba yajin hausane yanmata daga turanci sai larabci, eh ai balarabe ne kuma bature" mai gadin ya fada yana washe baki "Kar yaji din" nafada da karfi "Yana ma ji, wulakancine kawai tsaba" inji hawy Ganin munki kulashi yasa ya fara tambayar me gadin wai me ya faru nan yayi masa nuni da kayanmu da ya zubar mana, hannuwansa ya hada guda biyu ya dan risina a gabanmu alamun muyi hakuri, kayan yaje ya fara tattara mana, sai da yazo kan pad din sai ya jiyo yana kallonmu,dauke kaina nayi acikin raina ina cewa "dan iska kawai meye zaka wani kallemu" ina juyowa sai naganshi tsaye a gabana yana miko min ledar pad din "take, and am sorry queen" fuska na hade na bata rai na karbi ledar naja hannun hawy muka je muka deddebi kayan muka karasa bakin titi muna zuwa muka yi sa'a muka samu mai keke napep muka hau,har lokacin wannan saurayin yana tsaye yana kallonmu har sai da ya daina hangomu. Hannuna hawy ta dafa "yauma da alama kinyi sabon saurayi" "Tab, wannan ya zama saurayina ai fada zamu rinka yi saboda naga kamar ya fiya iyayi" "Irinsu ai sunfi, sune first class" tafada cikin zolaya, haka muka rinka hirarsa har muka isa gida. Tun daga wannan lokacin ba mu sake zuwa kasuwa ba har wurin sati biyu sai acikin sati na ukune sannan muka shirya muka tafi, kamar yadda muka saba kowacce tasha hijabinta dogo har kasa "phertyn mama wai mu meyasa ba zamu rinka irin wannan kwalliyar ba kullum mu kenan acikin hijabai" hawwa ta tambayeni daidai lokacin da zamu tsallaka titi, "Kin San dai ko ana bidi'a bai kamata a yita agidan na'ibin liman ba ko?" Nafada ina murmushi caraf muka hada ido da wannan saurayin na rannan yana zaune akan farar kujera a bakin plaza dinnan, "Kinga gayen nan na rannan amma karki kalleshi sosai kar ya gane maganarsa muke yi" na radawa hawy a hankali, Ganinsa kawai muka yi tsaye a gabanmu yana murmushi, "barkanku da fitowa yanmata" ya fada cikin harshen turanci, Mamaki nafara araina wai dagaske wannan bai iya hausa ba? Na tambayi kaina, lallai kam dan gashinan dan gayu dashi nafada acikin zuciyata, "Yau idan kun yi siyayyar ku kawo na ajiye muku kunji?" Ya sake magana da turanci, "Mun gode kuma zamu kawo" Hawy ta bashi amsa, fuuuu najata muka shige cikin kasuwa muna tafe muna fada sai faman masifa nake mata na kulashi da tayi, daga nan nace mata "Wallahi idan dan yankan kaine babu ruwana iyakaci idan ya yanke kanki na kaiwa su mama labari" Dariya ta fara shekawa sannan ta bani amsa "Dadinta ma dai bani yake so ba balle har ya yanke kaina" "Eh sai kifadi wanda yace yana so" Muna siyayya muna fada nida ita har muka gama dama fada sabon mu ne amma da yake kowa yasan kowa shiyasa baya zama na gaske da zarar munyi fadanmu kuma zamu ci gaba da hira, "Dan Allah hawwan mama ko ya sake tasowa karki kulashi" nafada ina rikeda hannunta "Haba ta mama, wulakanci fa babu kyau, gayen nan wallahi sonki yake" Ban bata amsa ba saboda ganinsa da nayi ya taho inda muke "Kun gama ne?" Ya tambayemu yana kallona, nikam dauke kaina nayi, yayinda Hawy ta bashi amsa da "ehh" "Nazo na kaiku gida?" Nanma bashi amsa tayi da "ehh" Yana tafiya dauko motarsa na harareta amma banyi magana ba ita kuma ta mayar min martani da murmushi Wata mota hadaddiya new end of discussion ya dauko baka mai kyau, gidan baya nabude zan shiga, hawy ta rikeni "karki bada mu mana, ki shiga gaba pls" "Ke meya hanaki shiga gaban" nafada cikeda masifa nashigewata gidan baya, itama bayan ta shigo, muna tafiya suna hirarsu da hawy ni bana saka musu baki da haka har muka karasa unguwar mu, kasancewar ga gida ga gida tsakanin gidanmu da nasu hawwa yasa muka sauka a kofar gidansu ban tsaya jiranta ba na dauki kayan na shige gida, nan nabarta suna magana dashi. Ta dade awaje kafin ta shigo tana dariya "yau dai kin samu matsala a kwakwalwarki ko?" Na fada ina hararta "wlhi ras nake kawai keda saurayinki ne kuke bani dariya" ta fada lokacin da take zama kusa dani "Saurayinki dai malama" na fada ina kallonta Zama tayi kusa dani ta fara yimin bayanin maganganun da suka yi dashi wai yana sona kuma zai zo gobe, "Ke nifa na fada miki ba yanzu zanyi aure ba" "Eh nasani phertyn mama to amma at least dai ace kanada wanda zaka aura a hannu ai da dadi, saboda kinga yanzu idan kika rike wannan kuna soyayya har ki gama karatunki, lokacin da kika gama sai ayi maganar biki kinga lokacin kun gama sanin halin juna basai an tsaya binciken halayen juna ba" "Eh maganarki gaskiya ce ta mama amma nifa kin san natsani fita zance gaskiya" "Duk wannan mai sauki ne ku zaku tsara kayanku" "Shikenan tunda kince haka sai dai naga kamar baya jin hausa fa" "Eh ai daidai kenan" tafada tana dariya nan muka shantake har bayan magrib sannan ta rakani gida. ****** Washe gari bayan na dawo daga sch da yamma sai ga hawy ta shigo, adaki ta sameni ina kwalliya, "ke bakonki fa har yazo" "Dan jaraba ko dan me?" Nafada ina dariya "Dan Allah yi sauri muje" "Sai kiyi kuma" Kaya natashi nasa wani material ash colour nasa farin hijab, muna fita hawy tace gani nan ta kawoni bari ta shiga gida, tana tafiya naji na takura kasancewar wannan shine karo na farko da na fito zance "Pherty my queen" ya fada cikin daddadar muryarsa Kallonsa nayi ta gefen ido yana sanye da bakar t shirt da bakin wando na jeans, gaskiya ya hadu ba kadan ba, hira yayi tamin duk kuwa da cewar maganar tasa a hankali yake yinta dan da alama bashida yawan surutu kuma bai da hayaniya, Ya dan jima sannan ya tafi, yana tafiya nashiga gidansu Hawy nafara bata labarin hirar da salim yayi min domin yace min sunansa salim dariya kawai take yi har nagama bata labarin "Bana son wulakanci fa" "Allah ya baki hakuri" ta fada tana dariya. Tun daga lokacin soyayya mai karfi ta kullu tsakanina da salim, yanzu yana zuwa wurina duk bayan kwana biyu sai dai wani abu da yake daure min kai dashi shine yawan son taba jikina da yake yi, Yauma kamar yadda ya saba zuwa yazo bayan sallar magrib, hijabi nasa nafita na sameshi zaune cikin motarsa, gaban motar na shiga na zauna, "Queen" ya fada yana kashe min ido Dan murmushi nasaki "King" nafada nima ina kallonsa Hannu ya miko zai shafi fuskata amma sai na dauke kaina, "Wai queen bakya sona ne? Kullum idan muna hira sai ki rinka kyamata" "Ni ban kyamaceka ba salim, lokacine dai bai yiba wanda zaka rinka taba min jiki" "Yaushe ne lokacin?" "Idan munyi aure" "To ai kafin aure ma akwai taste before marriage" Kallonsa nayi cikeda kuruciya a tare dani "To ai ni ban saniba" Hannunsa yasa wanda yake baibaye da gashi ya kamo nawa hannun "Ki kwantar da hankalinki queen bazan taba cutar dake ba, aurenki zanyi" Hannun yakai kan fuskarsa ya fara shafar fuskarsa dashi in banda shock babu abinda jikina keyi wurin kamar mintuna biyar nace mishi zan shiga gida saboda abbana ya kusa dawowa daga masallaci kuma idan yazo ya sameni anan fada zai yi. Yana tafiya nashiga gidansu hawy na sameta, hannunta na janyo muka fito waje "hawy mutumin nan fa gaskiya dan iska ne" nafada ina kallonta "Meya cemiki, maganar iskanci yayi miki?" "Hawy nidai gaskiya zance ya daina zuwa saboda kullum fa sai ya rinka wani shasshafa ni yana kokarin sai ya rike hannuna ko ya taba jikina" Kallo na tayi kafin tayi magana muka hango abbana yana tahowa ganin haka yasa kowacce shigewa gida batare da mun karasa maganar ba. Ummi A'isha [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [5/3, 5:52 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 36-40 ~~~ Koda nashiga gida naci abinci nayi sallah shirin kwanciya nayi amma koda na kwanta sai nafara tunani acikin raina shin me salim yake nufi dani? Nafarko dai ni agaskiya nafara tsorata dashi saboda yadda yake shafata idan muna hira gashi kullum bashida zance sai na ni kyakkyawa ce yasan yanda nake da kyau awaje aciki ma haka nake, abunku da kuruciya sai dai nayi murmushi nace nagode, da yake yarinta na damuna tuni na watsar da zancen nayi baccina. Da safe kamar kullum nayi shirin tafiya sch, ta gidansu Hawy na biya lokacin tana kokarin shiryawa, bayan mun gaisa da mamansu ne nafara yiwa Hawy masifa "kullum ke kike makarar damu, gaskiya sai kin taho" nafada lokacin da nake kokarin fita daga cikin dakin, "yi hakuri phertyn mama" Juyowa nayi na kalleta "wannan sunan bazai fita daga mouth dinki ba ko?" Murmushi tayi "ai sunanne ya shiga bakina sosai" Dariya nayi saboda tun ina karama aka lakaba min wannan sunan yan unguwa ko kwatance za ayi da gidanmu sai dai ace gidansu phertyn mama, Bayan ta gama shiryawa ne tafito muka dauki hanyar makaranta muna tafe muna hira, "Yawwa phertyn mama maganar jiya tsakaninki da salim meke faruwa ne?" "Um hawyn mama ai salim dinnan dai dan iska ne, abubuwan da yake min sun fara yawa gaskiya" "Meya ce miki?" "Ai ba wani abu yake cemin ba ni kawai taba min jikin da yake ne bana so" "To idan ya sake kokarin tabaki ki hade rai ki bata fuska kice ke bakya son haka" "Na fada masa fa amma dai zanyi hakan" "Yawwa kiyi masa haka, kin san su irinsu sunada jarabar son taba mace gashi dai yace a mecca yayi rayuwarsa, amma baya tsoron Allah" "Wallahi kam, Allah dai ya kyauta" Haka muka karasa makaranta muna tafe muna hirar salim. Yau ma da daddare salim yazo dan haka na shirya na fita, acikin motarsa yake zaune sai kamshi turare ne ke tashi yayi kyau sosai cikin farar t shirt da red din wando ya gyara sumarsa da sajensa, ahankali na shiga na zauna kaina akasa na gaida shi, Wani mayaudarin murmushi yayi min sannan ya fara kokarin matsowa jikina da sauri na dakatar dashi raina abace "salim meye wannan?" Nafada cikin fada, "Sorry my queen wannan ai itace soyayyar kece baki sani ba" "Nidai ka bari gaskiya bana so" nafada kamar zanyi kuka "Ashe bakya sona?" Yafada cikin fillanci "Ina sonka mana" nafada ahankali "To tunda kina sona ai dan na tabaki babu damuwa, wannan abunfa shine son" Shiru nayi bance komai ba,hannuna ya kama na kwace, "Nidai ka daina gaskiya" "Allah ya baki hakuri phertyma, amma daga yau bazan sake dawowa gidanku ba tunda abun hakane" Hankalina naji ya tashi domin gaskiya ina son salim sosai, "Kayi hakuri, wallahi ina sonka sannan kasan babu kyau mutum ya rinka taba mace in dai ba aure suka yi ba" Dan murmushi yayi "sai yanzu nagane abunda kike nufi, wato gani kikeyi kamar ba aurenki zanyi ba ko, tunda hakane ina komawa gida yau maganarki zan yiwa dad dina za azo a nema min aurenki a kawo komai gidanku in yaso kina gama karatu sai ayi bikinmu" Wani dadi naji ya shigeni yanzu kam nasan da gaske salim yana kaunata, "Yawwa kaga haka yafi" nafada cikeda jin kunya, yan yatsuna naji ya kama "Jarababbe ai bazai hakura ba" nafada cikin zuciyata. Sai da yagama mammatsa min yan yatsuna sannan ya tafi amma ni duk sai ban kawo komai ba araina tunda aure za muyi. Lokacin da nashiga gida abba na yana biye dani a baya yana shiga falonsa naji yana kwalla min kira, da sauri na tafi wurinsa, "Waye wanda naga yanzu?" Tambayar da abba ya jefo min kenan "Abba sunansa salim" nabashi amsa "Meye alakarki dashi?" Shiru nayi banyi magana ba, "To daga yau kar nasake ganinsa a kofar gidana idan ya sake zuwa ki fada masa kar nakara ganinsa, idan aurenki zaiyi ya bari idan kika gama karatu sai ya fara zuwa, idan kuma bazai iya jiranki ba to Allah ya hada kowa da rabonsa" "Haba Malam ya za ai kace haka? Yaron nan dan arziki ne be kamata ka hanashi zuwa ba, kabarshi yaci gaba da zuwa har lokacin da zata kammala karatunta in yaso sai ayi bikinsu" mama ta fada tana tsaye a kofar daki "To me amfanin tarayyarsu tunda ba yanzu za ayi bikin ba? Akan me zai rinka zuwa wurinta mutukar ba yanzu za ayi bikin ba?" "Malam dan Allah ka kyale maganar nan haka" inji mama "To tunda yanzu na fuskanci kin fasa yin karatun idan ya dawo kice masa ya turo magabatansa muyi magana dasu in yaso kina kammala secondary sai ayi miki auren tunda haka kike so" "Sai tayi karatu zata yi aure amma dai ya turo manyan nasa" inji mama "Dama yace yau zai fada agidansu kan azo a nemar masa aurena" nafada cikin tsoro kamar wata marar gaskiya, "Tashi kije" abba ya fada amma da alamu ransa ya baci. Tunda nafito nake jiyo musayar yawu tsakanin abba da mama abunda ya zame min sabon al'amari domin ban taba jin sunyi musu ba sai yau akaina, shi abba yana cewa yaron nan yadaina zuwa gurina har sai na kammala karatu ita kuma mama tana cewa a'a yaci gaba da zuwa, nidai kawai sai taintar kaina nayi cikin hawaye saboda sai naji hankalina ya tashi. Bayan faruwar haka da kwana biyu sai ga yan gidansu salim da akwatuna guda uku masu kyau da tsada da kudi dubu dari biyu wai kayan angani ana so da kudin aure,mama ba karamin murna tayiba, yan unguwa sai shisshigowa suke suna kallon kayan, nikuwa ina can gidansu Hawy muna hira da ita, "phertyn mama kin fasa karatu kenan sai aure?" Ta tambayeni "Waya fada miki? Zan yi karatu na mana" "Tayaya?" Tasake tambaya ta "Ta yanda zakiyi" na mayar mata da amsa "To Allah ya kaimu lokacin" "Amin"na amsa mata Tun daga lokacin da salim ya kawo wadannan kayan gidanmu tun daga nan salon zancenmu ya sauya ada idan ya nemi taba min jiki idan nace babu kyau yana yarda amma yanzu ko nace masa babu kyau sai yace ai yanzu ni matarsa ce aure za muyi, dan haka in kyaleshi, kullum sai munyi fada dashi akan wannan, yauma tunda yazo muke fada akan wai lallai dole sai nayi masa kiss nikuma naki, "Hmm wlhi yarinyar nan bakya sona kuma nagode" "Meya faru" nafada ina kallonshi "Wlhi indai baki yimin kiss dinnan ba na hakura bazan sake zuwa ba" Shiru nayi nafara tunani, "yanzu pherty ashe ba zaki rinka yimin abinda zuciyata keso ba?" "Kayi hakuri" "Indai kina so in hakura to kiyi min ko ki barni nayi" Ban bashi amsa ba nayi shiru ganin haka yasashi matsowa jikina, ban ankaraba naji lebensa kan nawa, ahankali ya fara kissing dina, akaron farko, abunku da abun shaidan sai naji na samu kaina cikin nishadi nan ya fara yi min wasu abubuwa wanda ban taba sanin su ba, mun jima sosai cikin wannan halin sannan ya matsa daga jikina yakoma kujerarsa ya zauna idanuwansa sun sauya launi, kafin mu rabu sai da ya gargadeni cewar kar na kuskura na fadawa hawwa kawata domin wannan sirrin mune wato sirrin mata da miji, nikuma a lokacin ina fama da kuruciya kawai sai na rinka yarda da abubuwan da yake fada min koda wasa ban taba fadawa hawwa abunda yake faruwa ba. Haka muka ci gaba da gudanar da soyayyarmu nida salim cikin wannan yanayi na tasting dan yace duk wadandan abubuwan acikin taste suke wai, da haka muka kwashe lokaci mai tsawo yanzu har takai nagama sabawa da salim bana jin komai dan ya taba jikina,a lokacin ya fara nuna kwadayinsa na son kebewa dani anan ne nikuma nayi turjiya nace sam bazan yarda, lallashi na ya fara yi wai ni kadaice fa gatanshi ni kuwa nace ga iyayenshi nan haka tun yana nacin har ya hakura. Wata rana da yamma kwatsam sai ga salim wai yana son muje na gaida umminsu, da dafarko nace ba zanje ba amma koda ya yi min dadin baki sai na yarda naje nafadawa mama cewar za muje na gaida ummin salim, mama bata kiba tace amma kar na dade gudun kar abbana ya dawo bai sameni agida ba. Ko Hawy ban fadawa ba dan salim yace kar na fada mata baya son mu tafi da ita kuma ma wai ai ba komai zan rinka fada mata ba, haka na shirya naci kwalliya nasha shadda ja mai kyau dinkin doguwar riga nayi kyau das dani sai dai kallo daya zaka yimin kaga kuruciya karara akan fuskata. Komai ja nasa, haka kawai sai na samu kaina cikin faduwar gaba ga wani irin sanyi da naji jikina yayi, haka na fito daga gida nashiga motar salim mai mutukar kyau, shima yayi kyau sosai cikin ash colour din riga da jan wando jeans sai kamshin turaren midnight ne ke tashi daga jikinsa, wata faduwar gaba naji lokacin da muka hada ido dashi. Ummi A'isha🏻 [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [5/4, 3:41 PM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 41-45 ~~~ Wata faduwar gaba naji lokacin da muka hada ido dashi, gashi zuciyata sai harbawa take da sauri da sauri haka na daure na kakaro murmushin dole na aika masa, "My Queen ki saki jikinki naga kamar a tsorace kike" maganar da ya fada min kenan lokacin da ya fara driving, daidai lokacin da muka hau titi ya kamo hannuna ya rike ya fara driving da hannu daya, "Ina sonki sosai queen, saboda kina da kyau, nadade banga Hausa/Fulani kyakkyawa kamarki ba" Murmushin jin dadi nayi saboda yabona da naji salim yana yi, "Kefa kina sona?" Ya tambayeni lokacin da yake kallon gefensa zai karya kwana, "Uhm" nafada cikeda jin kunya Hannuna yasake damkewa ya matsa tafin hannuna "Banga alamun hakan ba atare dake, amma idan dagaske kike zan gani" Shiru nayi bance komai ba,sai da muka danyi tafiya mai nisa sannan muka shiga cikin garin gombe kasancewar ban san cikin gombe sosai ba bazan iya tantance unguwar ba amma dai shiru unguwar take sai hadaddun gina gine masu kyau daga ganin unguwar ta masu hannu da shuni ce. Wani dankararren gida muka dosa, da kansa ya fita ya bude get din gidan sannan muka shiga gidan bayan yayi packing ne ya koma ya rufe gidan yazo ya kama hannuna zuwa cikin gidan. Da farko wani babban falo muka shiga hannuna rike cikin nashi, bamu tsaya anan ba yaja ni zuwa wani hadadden bedroom wanda yaji kaya na alfarma komai ja, abakin gado ya zaunar dani shima ya zauna, "Ina ummin?" Na tambayeshi cikin tsoro "Meyasa baki yarda dani ne wai? Nifa mijinki ne, wlhi queen nakasa daurewa har sai munyi aure, pls aid me" Cikin tsoro da rashin fahintar inda zancensa ya nufa nace "salim meya faru?" "Queen pls help me just one pls and pls" Kallonsa nayi idonsa tuni har ya zama ja kamar wanda yasha abin maye "Salim me zanyi maka?" Nafada a tsorace "Pls pherty" Hannuna ya kama yajani zuwa jikinsa take jikina ya fara rawa, "karki tsorata queen u are my wife, don't reject my..." Bai iya karasawa ba saboda yadda ya shide,nan ya fara shinshinata tamkar wani zararre, nayi iya kokarina ganin na hanashi amma nakasa, ina ji ina gani ya rabani da kayan dake jikina amma har lokacin jikina rawa yake tamkar mazari. Idanuwana na kulle saboda ganin salim yana tube kayan jikinsa, ban taba ganin namiji babba ahaka ba sai lokacin, "innalillahi" itace kalmar da bakina yake fada lokacin da naji salim ya fara yimin wani salo yana juya ni son ransa. Tun ina daurewa har nafara kuka saboda zafin dake shigata, "Daure queen" haka salim yake ta fada har ya samu ya cimma burinsa, shafata ya fara yana yimin kalamai masu mutukar dadi tareda kwantar da hankali. "Queen wannan abun da yafaru tsakaninmu ina so kibarshi a matsayin sirri don't tell to any body, tsakanina dake ne kin gane, kiyi hakuri sannan har yanzu ina nan akan burina na sai na aureki" Cikin kuka na daga kaina na kalleshi "yanzu nasan shikenan ka daina sona salim" Dasauri ya rufe min bakina da nashi ya fara kissing din lips dina sannan a hankali ya rada min "wannan abun kara min sonki yayi, yanzu nema nasan ina sonki, ashe da ba so nake miki ba" Shasshafa min jikina ya ci gaba dayi har ya sake samun damar yin maimaici, "Haba salim kaji tausayi na mana, da wahala fa" nafada ina hawaye "Sorry nadaina" Tashi yayi ya nufi toilet bai jima ba ya fito daure da towel ajikinsa, "queen muje nayi miki wanka" "Kabarshi zanyi" nafada a hankali, daukata yayi ya kaini toilet, sai da ya fita sannan nasamu nayi wanka, duk jikina sai ciwo yake yimin hatta tafiyata ta sauya ganin haka kawai sai na fashe da kuka, da sauri ya shigo cikin toilet din, "Queen what happened?" Yafada arude, "Salim wlh idan abbana ya gane ina jin kasheni zaiyi, kaga fa tafiyata ma duk ta sauya" "Sorry zakisha magani yanzu, sannan ki daure ki shiga cikin ruwan zafi, bari na taimaka miki" Karasa shigowa ciki yayi ya tayani nashiga ruwan zafi na fito, daukata yayi ya maida ni cikin daki nashirya nasa kayana, juice ya dauko min da magani yace indai nasha zanji dadi, karba nayi nasha nan take naji dan dama dama, agogon dakin na kalla karfe 6 daidai, kallon salim nayi "Katashi muje wurin ummin sai ka mayar dani gida" "Basai munje wurin ummiba saboda kinga dare ya fara yi kar abba yazo ya tarar bakya nan yayi fada tunda bai san mun fito tare ba" Kai nadaga "to shikenan" Tashi nayi nafara tafiya a hankali yana biye dani har muka karasa motarsa. Bayan mun fita daga cikin gidan ne ya kama hannuna yana yimin murmushi "Queen yau kin gama biyana, yanzu abinda ya rage kawai kina gama karatu sai ayi bikinmu" Dadi naji ban ce komai ba, kasuwa muka shiga yayi min siyayyar kayan make up masu kyau da tsada sannan ya sai min waya mai kyau kirar Samsung yace gashi nan na boyeta kar nabari mama tagani ko Hawy zamu rinka yin waya a boye, kayan kuma nacewa mama Ummi ce tabani. Ana kokarin yin sallar isha'i muka isa gidanmu muna zuwa ya kalleni cikeda so yace "zanyi traveling amma dai za muyi waya, ki boyeta kinji?" "To shikenan sai ka dawo" nafada tareda dibar kayan nayi cikin gida ina tafiya ahankali. Lokacin da nashiga Ummi tana salla dan haka na ajiye kayan a falo nashige daki naje nayi alwala sannan na boye wayar da yabani acikin akwatina nadawo falo nayi salla. Bayan na idar ne na fara nunawa mama kayan, murna mama tafara 'ta karbeki hannu bibbiyu kuwa?". "Eh mama, ta karbeni sosai ma" Dariya mama tayi "to ai gashi nan ta hadoki da kayan kwalliya yadda zaki tayiwa danta kwalliya" dariya nayi bance da mama komai ba muna nan zaune abba ya dawo, nan mama ta nuna masa kayan amma abba baiyi murna ba sai fada ma da yayi wai danme zan bi salim gidansu shi baya son wannan sakarcin kar nasake zuwa nan gaba koda wasa saboda wasu samarin suna amfani da wannan damar suna bata yara, ajiyar zuciya nayi jikina yayi sanyi sai a lokacin hankalina ya tashi. Ina komawa daki nafara kuka nadade ina kuka sannan nayi shiru na dauko wayar da salim ya bani na kunnata, massages dinsa ne suka yita shigowa rututu na kalaman soyayya daga karshe ya kirani mu kayi hira ya kwantar min da hankali cewar maganar aurenmu fa ta na nan kar na daga hankalina. Tun daga wannan lokaci muke waya da shi a boye tuni har na warke daga abinda yayi min, kuma ko Hawwa kawata ban bari ta saniba. Bayan wasu lokuta masu tsawo kamar watanni biyu har lokacin salim bai sake zuwa gidanmu ba a cewarsa tafiyar da yayi har yanzu bai dawo ba mama ma tasha tambayarsa sai nace mata yayi tafiya ne. Kiba na danyi sannan sai nake jin kasala ga kwadayi da nake fama dashi, shinkafa kuwa a duniya ji nayi na tsaneta daga na ganta sai naji hankalina ya tashi. Yau da safe bayan nayi shirin sch mama tace min ga tea nan da wainar kwai, "mama bana son wainar kwan nan, idan naje sch zan siyi awara naci" "Yau bakya son wainar kwan? To Allah ya kiyaye hanya sai kin dawo" Fita nayi nabiyawa hawy muka tafi makaranta muna tafiya ina fada mata yau awara nake sha'awa gashi yanzu bana son ganin shinkafa, daga ni har ita bamu zargi komai ba da haka muka karasa sch. After first period second period na shiga malamin mathematics dinmu ya shigo, ina jin kamshin turarensa take naji cikina ya fara juyawa numfashina ya fara yin sama, da gudu na fita gaban class na fara sheka amai kamar wacce zata amayar da hanjin cikinta, hawy ce ta biyoni ta rikeni, sai kwara amai nake kafin nagama har na fita hayyacina hakan yasa hawy ta kira yan bencinmu suka taimaka mata suka kaini clinic din makarantar, nan aka kwantar dani aka fara kara min ruwa. Nadade ina bacci kafin nafarka duk bakina babu dadi, hawy tana zaune kusa dani lokacin an kusa tashi daga makaranta, antyn clinic dince ta shigo ta kalleni "sannu kin tashi? Kinada aure ne?" Ta bambayeni "A'a" nabata amsa "Yaushe rabonki da al'ada?" Ta sake tambayata Tunani nafara yi rabona da period tun kafin salim yayi min wannan abun dan lokacin ma kwanana biyu da gamawa hakan ta faru "Za akai 2 months" nafada ina kallonta Kallona tayi sosai "akwai matsala kenan" tafada tareda juyawa har takai bakin kofa tasake juyowa tace "zaku iya tafiya tunda kinji sauki" Tashi muka yi nida hawy muka fita lokacin an fito second break nan na hango mai wainar fulawa da sauri na kalli Hawy "Hawwa dauko min kudin break dina a aljihun jakata, ga mai wainar fulawa can, yunwa nakeji" Tafiya tayi ta dauko nikuma nakara wurin mai wainar fulawar ina zuwa nafara ci ban jira hawy ba,sai da naci ta naira dari. Bayan an tashi daga sch ne nafara yiwa Hawy korafin rashin zuwan salim, kallona tayi "idan bai dawoba Allah ya kawo miki wanda yafishi" Cikin razani na kalleta "hawy anya zan iya rayuwa da wani namiji idan ba salim ba? Ya rigada ya dandana min zumarsa a bakina hawy" Hawaye nafara na dafa hawy "Hawy ina son salim kuma bana fatan rabuwa dashi domin muddin idan na rabu dashi to kamar na rabuda MARTABA TA ne" "Ban ganeba" ta fada cikin razani Hannunta naja muka nufi karkashin wata bishiya nafara bata labarin abinda salim yayi min saboda bazan iya boye mata ba nakare labarin da cewa "da yana yimin waya akai akai amma yanzu sai dai ni na kirashi kuma kwata kwata yanzu ma wayar tasa ta daina shiga" Kuka hawy ta yi sosai sannan tafara magana cikin hawaye "pherty meyasa kika yarda da zancen salim, meyasa baki fada min ba, meyasa kika bari ya cimma mummunan kudirinsa akanki, meyasa kika yarda yayi nasarar rabaki da MARTABAR KI?" Ta jero min wadannan tambayoyin tana kuka, "Hawy kidaina kuka aikin gama ya gama" "Tashi muje gida da yamma sai muje wannan plaza din tasu ta kasuwa ko zamu sameshi acan" tafada tareda jan hannuna muka tafi amma har lokacin bata daina kuka ba. Da yamma hawy tazo tacewa mama mamansu ta aiketa kasuwa shine tazo na rakata, mama bata hanaba tabari muka tafi, muna tafiya take yimin magana "samarin nan fa basuda tabbas pherty" "Hakane hawy amma lokacin da abun ya faru baki ga yadda ya rinka makalkale mun ba yana min wasu surutai ni banma san ko wanne irin yare yake yiba daga karshe yace zancen aurenmu yana nan bai fasaba" "Ai mayaudari ne yasan yana son naki meyasa bazai bari har sai kunyi aure sannan zai karbi wannan abun ba, Allah yasa ma ba guduwa yayi ba" gabana ne naji yanata faduwa. Lokacin da muka je plaza din babu kowa sai wannan mai gadin da muka taba bashi ajiyar kaya, bayan mun gaisa ne sai hawy ta tambaye ina salim "Wanne salim fa?" Ya tambayeta itama "Wanda ya yi mana watsi da kaya" "Auho jawad zakice ai, jawad ya dade bai zo nan ba dan akalla zai kai watanni biyu rabonsa da nan kuma yana kasar dan ko jiya da naje gidan nasu na ganshi" Kallona hawy tayi muka hada ido tace "um baba inane gidan nasu?" "Gidansu yana nan a new g.r.a acikin gombe" "Amma baba ai ance yakusa aure ko?" Tasake tambayarsa "Anya kuwa? Shi jawad bana zaton zaiyi aure nan da shekaru 4 ma saboda naga shi bature ne" "Baba ko zamu iya sanin waye jawad?" "Me zai hana yayan nan" zama ya gyara ya fara da cewa. "Alhaji Habibu mai goro shine mahaifinsu, sana'ar mahaifinsu itace sayar da goro tun yana sayarwa acikin kasar nan har takai yana fita kasashen larabawa yana sayarwa acikin yawonsa ne ya auro mahaifiyarsu a kasar saudiyya, babarsu balarabiya ce, su biyune awurin mahaifan nasa daga shi sai yayansa Aadil mahaifinsu dan asalin cikin garin gombe ne, Allah ya bashi arziki mai tarin yawa ta sanadiyyar sayar da goro, tun lokacin da aka haifi jawad aka yayeshi ya tafi saudiyya acan yayi rayuwarsa baya zuwa sai lokaci lokaci, nikuwa nadade ina tare da mahaifinsu tun da kuruciyata muke tare, amma maganar gaskiya jawad bashida niyyar yin aure yanzu" Hankalina ne naji ya tashi mutuka, tabbas salim mayaudarine kuma marar gaskiya tunda gashi harda boye sunansa na gaskiya, "Mun gode baba" Hawy ta fada tareda jan hannuna muka fara tafiya, "kinji dai da kunnenki sunansa jawad ba salim ba,muje gida kafin musan abin yi gobe" nidai kasa magana nayi binta kawai nake har muka je gida, gidansu ta shiga bayan tayi min gargadin na kwantar da hankalina gudun kar mama ta gane. Ina shiga gida na iske wani tashin hankalin domin ashe bayan tafiyarmu kasuwa principal din sch dinmu yazo ya samu abba ya sanar dashi cewa ina dauke da juna biyu na wata biyu dan haka sun dakatar dani zuwa makaranta. A falo nasamu mama tayi jugum fuskarta sharkaf da hawaye abba kuwa sai fada yake ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, "Dama ni tunda naga yaron nan naji ban yarda dashi ba, gashi nan kin zuba musu ido yaje yayi mata cikin shege, to wallahi bari kiji, ni bazan zama mutumin banza ba, bazai yiyu ina na'ibin limami aga wannan danyen aiki agida ba, dan haka dole ne phertyma tabar min gidana ayau, kuma wallahi ban yarda taje gidan wani nawa ba, ke ko wurin wanda nasani taje ya taimaketa Allah ya isa ban yafeba" Kalaman dake fita daga bakin abba kenan, da sauri na juya na nufi dakina na dauko wayar da jawad ya bani nafice daga gidan, tashar mota na nufa ko gidansu Hawy ban shiga ba, lokacin da na shiga tasha karfe 8 na dare, ina zuwa nabayar da wayar aka bani dubu uku alhalin kudinta yafi haka kawai dan sunga a matse nake ne amma ni nasan mai tsada ce, dakyar na samu motar da zata je gombe saboda babu passenger da yawa, saboda tsabar tashin hankali ko kukan ma yaki zuwa. Karfe Tara da wani abu lokacin da muka je cikin gombe ana saukemu nasamu mai keke napep nace ya kaini sabuwar g.r.a koda naje unguwar shiru take baka jin motsin kowa, sauka nayi na biya mai keke napep kudinsa sannan nafara tunanin yadda zan lalubo gidansu jawad, a karkashin wasu fulawoyi dake shuke akofar wani gida na makale, sai a lokacin naji kuka ya subuce min take nafara kukan bakin ciki. Kwana nayi ina kuka har gari ya waye lokacin mutane suna wucewa jifa jifa masu zuwa office da masu kai yara makaranta dakyar nasamu ruwa nayi alwala nayi sallar asuba sai lokacin na tuna da cewar ko sallar magrib da isha jiya ban yiba,tashi nayi na fara neman gidansu jawad,sai wurin karfe 10 sannan na samu gidan, gidane mai mutukar girma da tsari kwankwasa gate din na fara yi ahankali mai gadin yazo ya bude min, "Nan ne gidansu jawad ko?" Na tambayi mai gadin "Eh nanne" hanya ya bani na wuce ciki, bin gidan kawai nake da kallo saboda tsaruwarsa ta isa, wani babban falo na shiga, ina bude kofar na hango jawad zaune daga shi sai three quarter baki da farar body hug yana yin tv game, daga can kuma wata matace tamkar balarabiya zaune tasha jan kunshi taci ado cikin koren lace tasha dauri tana lallatsa wata fankaceciyar waya, "Assalamu alaikum" Nafada lokacin da nake karasawa cikin falon "Wa alaikis salam" Matar ta amsa min, wacce kallo daya nayi mata na fahinci itace mahaifiyar jawad domin babu ta inda jawad ya barta, kamar su daya, Ina shiga nasamu wuri na zauna, gaba ne yayi masifar faduwa saboda ganin irin kallon da jawad ya jiyo ya watso min, kallone mai nuna alamun ban sanki ba, ban taba ganinki ba sai yau, Ahankali na gaishe da matar cikin sanyin jiki, na dan kalli jawad ta gefen ido wanda yafi mayar da hankalinsa akan game din da yake yi, nan na fayyacewa matar komai duk abinda ya faru tsakanina da jawad sai da na fada mata har kayan auren da ya kaimin da zancen cikin jikina, "Jawad kasan wannan?" Ta jefa masa tambaya "Ummi ni ban taba ganin wannan yarinyar ba sai yanzu" ya fada hankalinsa yana kan tv "To kinji bai sanki ba, kila wanda ya kwatanta miki gidan bai kwatanta miki daidai ba, idan kuma wani ne ya turo ki dan ki bata mana suna agari to ki koma ki fada masa yakoma yabi wata hanyar" Wasu zafafan hawaye masu dumi naji sun fara zarya akan kumatuna kamar an bude fanfo "Jawad kaji tsoron Allah, ka tuna zaka mutu ka tarar da Allah, abinda kayi min nabarka da Allah shi kadai ne zai yi min sakayya" Kofa aka bude aka shigo, wani matashi nagani mai kamada jawad amma daga gani ya girmi jawad din, Cigaba nayi da fadin "jawad ka cuceni ka rabani da MARTABA TA, ka rabani da iyayena ka rabani da mahaifata, to insha Allahu sai Allah ya saka min...!" "Ke maza tashi ki fice min daga cikin gidana, ya zaki zo har gidana kina yiwa dana mummunan baki?" Murmushi takaici nayi nace "danki ya aikata fin haka shi yasan duk abinda nafada babu karya aciki amma ki binciki danki saboda Allah ne kadai yasan yawan yanmatan da ya yaudara yayiwa ciki" Kallon jawad din nasake yi bayan na mike "jawad zan shiga duniya da cikinka ajikina kuma zan haifeshi zan reneshi har sai yayi girman da zai nemoka ya kasheka" ina kaiwa nan najuya na fita ina zubar da hawaye zuciyata tana tafarfasa, shi dai wannan yayan jawad din yana tsaye cikin mamaki yana kallonmu, ina fita nabi lungun gidan nafara tafiya ga azababbiyar yunwar da nake ji, ko kadan bana ganin abinda ke gabana, ban ankara ba sai ji nayi na fada kan wani dutse take dutsin ya bugi gefen marata ta dama, wani azababben zafi nafara ji yayinda marata da cikina suka gauraye suka fara ciwo babu kakkautawa, wata kara nasaka daidai lokacin da naji marata ta murda jini ya fara bin jikina. Ummi A'isha🏻 [5/5, 7:16 PM] Ummi A'isha🏻: [5/5, 5:36 PM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 46-50 ~~~Wata kara nasaka daidai lokacin da naji marata ta murda jini ya fara bin jikina, juyowa tayi ta kalli Sadiya da A'isha wadda ko wacce acikinsu hawayene kawai ke bin kumatunta sun rafka uban tagumi, "Kun san meya faru?" Ta tambayesu tana murmushin takaici "Tayaya zamu sani alhalin baki fada mana ba" suka fada atare "Amma meya biyo baya? Ni na kagu naji karshen labarin" Sadiya ta fada tana goge hawayen fuskarta, "Zakuji ai amma ba yanzu ba saboda ko sallar azahar ba muyi ba gashi har lokacin la'asar yayi,kuma ni yunwa ma nake ji" "Ai ni yau labarinki ya kosar dani dan ko yunwar ma bana ji" A'isha ta fada a hankali "Hmmm duniya kenan kaji abubuwa iri iri, ku tashi kuyi salla ni tunda bayi zanyi ba sai na dafa mana indomie" Sadiya ta fada daidai lokacin da take tashi daga kan gadon, wurin da suke girki ta nufa domin dora musu abinci yayinda A'isha da pherty suka fita yin alwala. Bayan sun idar da sallar ne suka fara cin abinci, wayar pherty ce ta fara ringing tana neman agaji, dauka tayi ta duba, yaya aadil ne da kamar ba zata dauka ba sai kuma ta daga tafara magana a hankali "Yayana" "Pherty na yau shine bakya nema na?" "Ayya yaya aadil bana son shiga hakkin anty nane shiyasa" Murmushi ya danyi sannan yace da ita "kinaji da antyn nan naki kila ma idan kikazo gidan hade min kai zakuyi" "A'a yaya" tafada tana dariya,"kaga zaka sani in kware gashi abinci nake ci" "Zaki ci dani?" "Why not?" "To aci dadi lafiya" yafada yana murmushi. Kashe wayar tayi tana dariya "kuji yaya aadil da tsokana ko a ina dadin yake, shi dan makaranta ai baya wani samun dadi" "Mudai kici gaba da bamu labari kawai malama" Sadiya ta fada "Gaskiya kam" A'isha ta sake fada, "Hmmm to,tunda kun matsa bari nakarasa yanzu, tunda na fadi ban sake sanin a inda nake ba sai bayan wani lokaci sannan na dawo hayyacina, ahankali na bude idona,acikin wani daki naganni wanda abisa dukkan alamu dakin asibiti ne, gefena na kalla wannan saurayin nagani yana zaune yana jiran farkawa ta, koda muka hada ido dashi sai naji nafara hawaye, da sauri ya karaso gaban gadon da nake kwance "sannu pherty, kin tashi?" Ya fada da sauri, ban bashi amsa ba illa kukan da yaki tsayawa wanda nake yi ganin haka yasa shi juyawa ya fita da sauri. Jim kadan sai gashi shida wani doctor sun shigo tare, da sauri doctor din ya karaso inda nake "sannu, inane yake miki ciwo?" Muryata a dashe nace "gefen marata ne yake min ciwo sosai gashi ina ji kamar an anjiye min wani katon dutsi a wurin" Kallon yayan jawad likitan yayi ya girgiza kai, "Aadil am sorry to say gaskiya yarinyar nan ta samu matsala sosai a mararta wanda ina tunanin idan ba wani iko na Allah ba bazata kara iya daukar ciki ba balle har ta haihu, ina jin gaba daya wurin yayi damage dan ko lokacin da na dauki hoton wurin naga yadda buguwar da tayi ya haddasa mata matsalar zubewar cikin jikinta, gashi kaga she's still bleeding, jini take fitarwa kamar zata karar da jinin jikinta" "Pls doctor help me, pls and pls try your best pls..!" Wanda aka kira da suna aadil ya fada a rude "Aadil am so sorry because i hv trying my best but abunne yafi karfina, duk wanda yace maka yarinyar nan zata sake iya daukar ciki to ya yaudareka ne kawai, saboda gefen mararta gaba daya ya tashi daga aiki, kai harta rayuwar aure ma dakyar idan zata iya saboda za arinka fama mata wannan ciwon da take tare dashine, but ga shawara guda daya ka fitar da ita kasar India kawai, ina jin idan Allah ya taimaka zata iya samun lafiya but is under probability" yana kaiwa nan ya juya ya fita daga cikin dakin, Juyowa aadil yayi ya nufo inda nake kwance ina kuka mai tsuma zuciyata "yanzu shikenan ni ba mace bace?" Tambayar da naketa yiwa kaina kenan acikin zuciyata, "Pherty" ya fada idonsa cikeda hawaye "Kiyi hakuri kinji, nayi miki alqawarin zan taimaki rayuwarki har sai inda karfina ya tsaya, sannan ina son ki manta da duk wani abu wanda ya faru dake a baya, ki fuskanci rayuwar da zata zo miki nan gaba, kuma ki yarda da qaddarar data hau kanki, ki dauka hakan wata jarrabawa ce daga Allah subhanahu wata ala" Daga kaina nayi na kalleshi abin mamaki sai na ganshi yana kuka, hawaye suna bin kumatunsa, "Nagode yaya Aadil amma karka wahalar da kanka wurin taimako na saboda mutuwa zanyi, ni yanzu ba mace bace, babu namijin da zai yi sha'awar aurena, jawad ya cuceni ya rabani da MARTABA TA, mutuwa yanzu itace tafi dacewa dani" "Karki sake fadin haka pherty domin zakiyi sabo, babu kyau bawa yana nemarwa kansa mutuwa, kidaina yiwa kanki fatan mutuwa kinji, ki dauki kaddarar da Allah ya aiko miki da ita, nikuma da taimakon Allah zan yi duk iya bakin kokarina na ganin kin samu lafiya sannan zan dawo miki da martabar ki" Idanuwa na narufe naci gaba da hawaye yayinda shi kuma ya fice daga cikin dakin da sauri, hannu nasa na shafo marata wadda ke radadi da zugi ga wani bleeding da naji ina yi kamar an bude fanfo. Ban sake ganin yaya Aadil ba sai dare, yana shigowa ya hada min tea ya taimaka min nasha, doctor yazo ya bani magani nasha ba tareda bata lokaciba bacci ya dauke ni. Kwanana uku a asibitin ina fama da ciwo kullum babu sauki, a kwana na hudu ne yaya aadil yazo da driver suka daukeni muka tafi airport lokacin ko tafiya bana iyawa, acikin jirgi ma ajikinsa ya jinginani nayi barci har muka je kasar India. Wani hadadden hospital aka kaini aka kwantarni nan manyan doctors suka taru akaina suna yimin aiki. Nasha wahala mutuka domin bayan sun gama min aiki harda wankin ciki suka yimin da wasu karafa, bayan an gama aikin ne yaya aadil ya shigo cikin dakin nake, sannu yayi tayi min nan ya samo min abinci naci nasha magani, duk wata kulawa wacce marar lafiya yake bukata to ina samunta wurin yaya aadil shine ya rinka kulawa dani har na tsawon sati biyu amma har a lokacin zan iya cemuku har yanzun nan da nake baku labarin ina jin wannan ciwon a marata domin ba karamar buguwa nayi ba. Satinmu uku acan aka sallame mu babu laifi sunyi kokari domin nadan ji sauki da taimakon Allah amma sun bawa yaya aadil tabbacin cewa kila idan anci sa'a zan iya daukar ciki idan kuma aka yi rashin sa'a to ko rayuwar auratayyar ma bazan iya ba, haka dai muka tarkato muka nufo Nigeria tunda na dan ji sauki domin bleeding din da nake yi yanzu ya tsaya sannan ciwon marar ya dan lafa sai dai yana dan damuna daga lokaci zuwa lokaci. Kafin mu baro kasar sai da yaya aadil yayi min siyayya mai tarin yawa sannan muka taho, tun acikin jirgi yake jana da hira yana son jin meya faru tsakanina da kaninsa jawad, dakyar na iya fada masa duk abinda ya faru daga farko har karshe, "Kiyi hakuri phertyma, jawad bai kyauta ba sannan kuma wallahi agida ba asan cewar ya na neman aurenki ba, wannan kawai wani salon yaudara ne ya bullo dashi yaje ya nemo wasu suka kai kaya gidanku, amma kiyi hakuri insha Allah hakan zai zame miki alkairi" "Allah yasa yaya aadil" nafada ina share kwallar data cika min ido "Bana son ki rinka kukan nan kinji?" Kaina na daga ba tare da nace komai ba. Wurin karfe 3 na yamma muka sauka nan driver yazo ya dauke mu ya nufi unguwar riyal damu, wani madaidaicin gida muka shiga yafito yace mushiga ciki, wata yar dattijuwa muka samu zaune a falo tana kallo, "dada kin ganmu sai yanzu" ya fada yana murmushi, "Ayya sannunku da zuwa, lale lale" tafada cikeda fara'a, wuri nasamu na zauna aka kawo mana abinci muka ci sai hirarsu suke da wannan matar, bayan yayi sallar la'sar ne yayiwa Dada sallama yace zai tafi nikuma ya kirani nabi bayanshi, Adaidai bakin gate din gidan ya tsaya yana kallona "pherty zanje gida ke anan zaki zauna wurin dada amma insha Allah kullum zan rinka zuwa ganinki kafin nakoma abuja wurin aikina, yanzu zan tafi saboda naga antynki sai damuna take da waya kamar wanda na bata" Kallonsa nayi "kanada mata ne?" "Yes, shekarata biyu da aure haihuwa ce dai ban samu ba har yanzu, may be uwar yayan nawa ta kusa zuwa" "Ayya Allah ya baka masu albarka yaya aadil, Allah yabaka masu jin kanka" "Amin pherty na, nagode" Sai da naga tafiyarsa sannan nakoma wurin dada, haka zamana ya ci gaba da tafiya a wannan gida, kullum yaya aadil na zuwa safe da yamma hakanne ma yasa nayi mutukar sabo dashi muka shaku mutuka, bayan kamar dawowar mu da sati biyu ranar da yamma sai gashi yazo yana sanye da t shirt ja da bakin wando yasha turare, ina zaune a falo ina kallon wani Indian film a tashar zee aflam ya shigo film din ya tafi dani sosai musammam ma saurayin cikin film din (Luv story 2015) shine sunan film din, "Sannu mai kallo" haka ya fada yana dariya, "Lah yaya aadil sannu da zuwa" nafada nima ina dariya" Zama yayi a kan kujerar dake kusa dani "ina dadan?" "Tana kitchen tana yimana tuwo" nabashi amsa, sai ga dadanma ta shigo bayan sun gaisa ne ta koma kitchen,kallona yayi "Dada fa kanwar babar dady ce uwa daya uba daya dan haka ki saki jikinki da ita kinji?" Kai nadaga wlhi dama nagama sakin jiki da ita saboda bata da matsala ko kadan "Yawwa to ni sallama nazo muyi saboda gobe abuja zan tafi, amma ya jikinki babu wata matsala ko? Kin daina bleeding din ko kinayi?" Shiru nayi ban bashi amsa ba saima rufe fuskata da nayi da dan kwalina, "Bazaki bani amsa ba? Shikenan Allah ya sawwake" Haka muka fara hira tsilla tsilla har magrib tayi lokacinne yayi mana sallama ya tafi. Washe gari kawai sai nasamu kaina cikin damuwa saboda rashin ganin yaya aadil sai kawai nafara kuka, dada tayi rarrashin duniya naki daina kuka, da haka har yayi sati daya da tafiya kullum cikin kuka nake ganin haka yasa dada yi masa waya ta fada masa, aranar sai gashi da yamma. Ina daki bayan naci kuka na koshi ko ruwa bansha ba bare abinci ya shigo ya sameni "haba pherty na" Haka ya fada lokacin da yake shigowa cikin dakin, Tashi zaune nayi nafara murmushi "sannu da zuwa yaya" "Bazan amsa ba, tashi ki shirya nakaiki gurin antynki yau kuga juna" Zumbur na mike na shiga wanka shi kuma ya koma falo, kwalliya nayi sosai nafito na sameshi shida dada zaune a falo, "ja'ira mai kuka kawai" dada ta fada tana dariya, muma dariyar muka yi yayi mata sallama muka tafi. A unguwar Federal low cost gidan yaya aadil yake, gidane tsararre wanda kana ganinsa kasan naira tayi kuka, lokacin da muka shiga cikin tamfatsetsen falon nasu daidai lokacin wata kyakkyawar mata ta fito daga cikin wani daki, "Ko kanwar tawa ce yau tazo?" Matar ta fada tana fara'a "Kamar kuwa kin sani itace, yau zakiga pherty na" Murmushi tayi tazo ta kama hannuna shikuma yaya aadil ya shige dakinsa, zaunar ni tayi ta cikani da kayan cima kala kala, "Kinga amaryarki yau ko?" Yaya aadil ya fada daidai lokacin da yake fitowa daga cikin dakin, "Naganta kuma gaskiya ka iya zabe, she's very beautiful, cute, pretty and amazing" ta fada tana dariya, filitanci ya fara yi mata, itama tana mayar masa suna dariya har naji na tsargu, "Ko zaki zauna da ita Gida daya pherty na? Nace ke abuja zan tafi dake tace wai a'a tafi son ku zauna tare" Murmushi nayi a zuciyata nace au dama filatancin da kayi mata ce mata kake dani zakaje abuja, "Ai muna nan tare da ita sai dai kai ka nemi ta tafiya abujanka" ta fada tana dariya, "Ai kuwa wasa kike dan kafata kafar pherty na" Abunsu gwanin sha'awa har dare nakai a gidan sai wurin 8 sannan yaya aadil ya daukeni muka koma wurin dada, washe gari sai gashi da kaya niki niki ya kawo min ciki harda wayar hannu mai tsada wai gashi nan sai mu rinka yin waya idan baya nan basai nayi kuka ba, haka yayi kwana biyu ya tafi tunda ya tafi na sake shiga damuwa danma dai muna waya. Haka naci gaba da zama da dada duk karshen sati yaya aadil yana zuwa ganina, da haka yaci gaba da yi min hidima acikin rayuwata har yayi min cuku cukun karatu ya sama min admission a wannan university din bayan nasake paper, idan baku mantaba, ranar farko da nafara zuwa makarantar nan yaya aadil ne ya kawo ni karewa ma shine ya hadani daku lokacin da kuka fito daga hostel, yaya aadil yayi min komai na rayuwa yanzu kuma daidai lokacin da zai aureni sai ga jawad kaninsa kwatsam ya dawo da soyayyata wai shi zai aureni saboda shine first love dina" Hmm tayi murmushin takaici ta dubi Sadiya da A'isha tace "yanzu ya dace naki aurar yaya aadil na auri kaninsa jawad? Ko kuwa ya dace na auri aadil nabar jawad fitina ta kunno kai cikin zuri'arsu? Ni pherty naga wani abu wai shi rayuwa" Ajiyar zuciya Sadiya da A'isha suka yi atare "ina labarin gida,ina su mama da hawy kawarki?" Sadiya ta tambayeta "Tun lokacin da na baro gida har yanzun nan da nake yi muku magana ban sake jin labarin gida ba" "Hakane amma ni ina ganin auren jawad agareki shine alkairi" A'isha ta fada tana kallonsu "Hmm A'isha kenan, Allah dai ya bamu mafita" pherty ta fada a hankali.. MARTABA TA 51-End 🏻: 👑 MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 51-52 ~~~Hmmm A'isha kenan Allah dai ya bamu mafita pherty ta fada ahankali, "Amma ni sai nake ganin yaya aadil yafi cancanta da aurenki pherty, duk da cewar nasan ke jawad kike so acikin ranki" Sadiya ta fada tana kallonta, "Tabbas idan nace muku bana son jawad nayi karya, amma ahalin yanzu son da nake yiwa yaya aadil ya danne wanda nake yiwa jawad" "Pherty nikuma idan nice ke jawad zan aura, saboda shi saurayi ne bashida mata, matashi mai karancin shekaru, zaku rayu sosai zaku ci soyayya, sannan kuma zaku more rayuwar aurenku fiyeda ace kin auri yaya aadil domin shi ko babu komai shekarunsa sunyi wa naki nisa, sannan kuma kinga yana da mata dole matarsa zata rinka kawo miki cikas fa" A'isha ta fada kamar zata saka kuka, "A'a A'isha yaya aadil yayiwa pherty alkairi mai yawa kinga bai kamata tayi masa butulci ba, kuduba zancen nan nawa fa" Sadiya ta fada, "Ya isa haka, time for prayer" pherty ta fada tana kokarin mikewa. Daren ranar babu wacce tayi bacci acikinsu haka suka kwana suna hirar jawad da aadil har gari ya waye, kowaccensu shiryawa tayi suka fita lectures bayan sun yi breakfast, Karfe 11 daidai pherty ta fito daga lecture din da tayi amma kallo daya zaka yi mata ka fahimci cewar tana cikin damuwa. Hango jawad tayi tsaye jikin motarsa yana yi mata kallon kurulla, kallonsa ta danyi ta fara kokarin barin wurin da sauri yabi bayanta "My queen" ya fada cikin tausashasshiyar murya, Juyowa tayi ta kalleshi "jawad kayiwa Allah ka rabu dani dan Allah" "Pherty kin san kuwa abinda kike fada? Taya zan iya rabuwa dake? Rabuwa dake tamkar rabuwa da numfashi nane pherty, kece rayuwata, wlhi bazan iya rabuwa dake ba" Kallonsa ta tsaya yi ba tare da tace komai ba, yana sanye da riga da wando bakake abinku da farar fata sai kayan suka yi mutukar karbarsa, Karasowa gabanta yayi ya tsaya, "Pherty karki manta soyayyar mu, karki manta da jawad dinki pherty" "Dama ta yaya zan iya mantawa da kai jawad? Ai bazan manta dakai ba tunda kayi sanadiyyar rabuwata da iyayena, kayi sanadiyyar rashin lafiya agareni, kayi sanadiyyar rushewar MARTABA TA, sannan kayi sanadiyyar....!" "Ya isa haka pherty, ya isa dan Allah, wai pherty so kike na mutu ne? Eye? Nace so kike na mutu?" Gabanta ya karasa "Ki kasheni pherty, nace ki kasheni tunda bakya sona" "Ni bazan kasheka ba amma dai abinda nasani shine bazan taba aurenka ba, ko maza sun kare a duniya jawad bazan taba aurenka ba" "Kika ce ba zaki aure ni ba?". Murmushi yayi mai kunshe da damuwa, "Wallahi kuma ni zaki aura saboda nine nake sonki, aadil ba sonki yake ba domin nafiki sanin ko waye shi, pherty wallahi ni zan aureki mutukar ina numfashi" ya karasa maganar daidai lokacin da hawaye yake bin kumatunsa, "Kaga malam idan kai baka da abinyi to ni ina dashi dan haka sai anjima" juyawa tayi da niyyar tafiya, cikin sauri ya janyo gefen mayafinta, tana jiyowa ta daga hannu da niyyar kai masa mari amma sai ta fasa, "Meyasa kika fasa? Ki mare ni mana pherty, ki mareni amma wata rana zakiji kunya saboda kin mari mijinki,sannan ki ajiye acikin ranki wlhi ni jawad nine mijinki, ki saka wannan acikin zuciyarki" Juyawa tayi tabar masa wurin cikin tashin hankali, juyawa jawad yayi ya koma ya dauki motarsa ya nufi hanyar ficewa daga cikin makarantar, daidai bakin gate din fita yaga motar aadil tana kokarin shigowa, glass din motarsa ya sauke ya dallawa aadil harara ya wuce, shima aadil din bin motar jawad din yayi da harara ya wuce ciki. A inda ya saba tsayawa yau ma anan ya tsayawa yana jiran gimbiyar tasa, yana zaune ya hangota tana tahowa cikin tafiyarta ta nutsuwa, tana sanye da jar atamfa ta yafa jan mayafi,tausayinta yaji acikin zuciyarta saboda tunowa da yayi da lalurar da take tare da ita, "Assalamu alaikum yayana" ta fada tana murmushi "Wa alaikissalam pherty na, amarya bakya laifi ko kin kashe dan masu gida" ya fada cikeda zolaya "A'a yaya bazan ma kashe muku da ba" "To ai kin isa ne pherty na" Murmushi ta dan yi bata yi magana ba, "Kin San dalilin zuwana yanzu?" Ya fada yana kallonta "A'a sai ka fada yayana" "Zuwa nayi naji wanne irin gado kike so? Royal bed kikeso ko Italian bed, ko kuma dubai bed?" Gabanta taji ya fadi tab yanzu zan kwana gado daya da yaya aadil watarana? Tambayar da tayiwa kanta kenan acikin zuciyarta "Baki fada min ba, wanne kike so? Ina son zan bayar ne a siyo miki kayan dakin" "Yaya ni duk wanda ya samu ina so" ta fada cikeda kunya "To shikenan duk guda ukun zan siyo miki, ke ai yar gatace" "Yaya sunyi yawa, dayanma ya isa" "No,guda uku zan yi miki pherty na" Murmushi ta kakaro dakyar tayi , "nagode yayana" ta fada idonta cikeda kwalla "Kar kiyi kuka pherty na, kinfi haka a wurina" "Nagode yaya". Bayan sun dan taba hira ne ya yi mata sallama ya tafi ita kuma ta koma hostel. ****** Gudu aosai jawad yayi daga makarantar su pherty zuwa gidansu, kai tsaye side dinshi ya wuce, kansa ya dafe tare da fadawa saman kujera domin jin kan nasa yake kamar zai rabe gida biyu dan tsabar zugin da yake masa, zunbur kuma ya tashi zaune "What? Impossible, Xarah hakan ba zai taba faruwa ba" ya fada shi kadai kamar wani zautacce, tashi yayi ya fito ya nufi side din Ummi, yana zuwa ya tarar da ummin zaune ga tulin akwatuna masu kyau da tsada a gabanta, kallon akwatunan yayi cikin faduwar gaba, guda bakwai ne kalarsu pink colour, Zama yayi dabas a gaban Ummi, "Ummi wannan kayan fa?" Ya fada cikin dar dar "Kayan auren aadil ne da aka hado masa, kasan bikin nashi ya taho saura lokuta kadan ya rage" Kafin yayi wata magana aadil ya bude kofa ya shigo, tashi jawad yayi ya tunkareshi yana zuwa yafara kokarin cin kwalarsa "Sai yau na yarda kai ba dan uwana bane, ayau nagane cewa kai ba jinina bane, ko kadan bamu hada jini dakai ba aadil, kai ba dan uwana bane domin shi dan uwa yana taimakon dan uwansa ne a duk lokacin da ya bukaci taimako, ba irinka ba mai son zuciya da son kansa ba, ba irinka ba mai kokarin raba naka dan uwan da tashi rayuwar ba" Wani mugun kallo aadil ya watsa masa sannan ya fara kokarin banbare hannun jawad din daga rikon da yayiwa rigarsa "gaka nan mai son zuciya mai son kansa, yarinyar da kagama wulakantawa a baya sai yanzu zaka dawo kace ita kake so saboda kaga yanzu ta zama cikakkiyar mutum, to wlhi baka isaba ko bazan auri pherty ba bazan taba barinta ta aureka ba, gara nabawa bare aurenta akan nabaka, banza mayaudari kawai" Ai jawad najin haka ya sake tunzura tare da fara wujijjiga wiyan rigar dake jikin aadil, da sauri Ummi ta taso ta fara kokarin rabasu, "Kai jawad sa'anka ne? Cikashi, ka cikashi nace" ta fada cikin harshen fullanci "Ki kyaleshi Ummi na koya masa hankali yau" jawad ya fada cikin karaji "Idan kai baka koya min ba to ni zan koya maka, dama can kawai saurara maka nake yi" aadil ya fada shima a harzuke Nan suka kaure da fada Ummi tayi tayi ta rabasu ta kasa, tun suna yi a falo har suka karasa dining area,sai naushi suke kaiwa junansu, wani wawan naushi aadil ya kaiwa jawad cikin sa'a ya sameshi a fuska, take jini ya fara fita daga hancin jawad "Haba aadil kashe kanku zakuyi? Akan me?" Kuka Ummi ta fara, da sauri ya saki jawad ya nufi Ummi shikuwa jawad durkusawa yayi agun hancinsa yana ta zubar da jini. Ummi A'isha [5/10, 9:04 PM] Ummi A'isha🏻: [5/10, 9:02 PM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA 👑 Na UMMI A'ISHA 53-55 ~~~Da sauri aadil ya saki jawad ya nufi wurin Ummi, "aadil kashe kanku za kuyi? Ko lokacin da kuke yara kanana ba kuyi kuruciyar fada ba kai da dan uwanka, sai yanzu da kuka girma kowa ya mallaki hankalin kansa" Ummi tafada tana kuka, "Yi hakuri Ummi mun daina ba zamu sake ba" aadil ya fada kamar zaisa kukan shima, Mikewa ummi tayi ta nufi wurin jawad wanda duk ya babbata wurin da jini jini ne yake fita a hancinsa sosai, hannunsa ummi taja ta nufi dakinta da shi daidai lokacin mahaifinsu ya shigo, ganin abinda ya faru ya sashi fara tambayar meke faruwa, ko kadan aadil bai iya bude bakinsa ba yana nan tsaye gaban dining area din yana ganin yadda jinin jawad ya zuba da yawa, Jim kadan sai ga ummi tafito itada jawad din ta wanko masa fuskarsa amma har a lokacin jinin yana fita kadan kadan, "Hajiya Fatima wai me ya faru ne?" Mahaifinsu ya tambaya cikeda mamaki "Kagansu nan fada sukayi sai kace kananan yara gashi nan harda zubar da jini" Ummi tafada fuskarta cikeda hawaye, Cikin mamaki mahaifin nasu ya dubi aadil "aadil fada? Kai da kaninka? Duk duniya kanada wanda yafi shi ne? To yanzu da ace ka haihu yaronka ya girma da agabansa zaka yi haka? Aadil kai fa ba yaro bane, shekarunka talatin da wani abu, ace har yanzu ba kayi hankalin da zaka rike dan uwanka ba? Meya hadaku? Tambayarka nake meya hadaku fada?" Shiru sukayi daga aadil din har jawad babu wanda yayi magana, "Ba zaku fada min abunda ya hadaku fadan ba sai na sassaba muku?" Mahaifin nasu ya sake fada cikin fada, "Daddy babu komai" aadil ya fada kansa a sunkuye "Kai jawad me ya hadaku" "Dady babu komai" jawad ya fada shima "Kaji zancen banza, babu komai kawai zaku kama fada harda fasa jikin juna?" "Alhaji akwai abinda ya hada su dan daga jin musayar yawun da suka yi nasan fadan nasu akan yarinyar da aadil din zai aura ne" ummi ta fada tana kallonsu "Meya samu yarinyar? Akanta suke fadan? To in babu dama ahakura da auren indai zai jawo fitina a tsakaninsu" yana kaiwa nan ya juya ya fice daga cikin falon, Yana fita ummi ta kallesu "ban taba ganin sakarkaru irinku ba, fada akan mace? Cikinku daya fa ko kun manta? Kai aadil yanzu ko wani kagani zai cuci dan uwanka ai bai kamata ka barshi ba balle kai da kanka, sanin kanka ne tun jawad yana karami ba a dukansa a fuska dan ko marinsa akayi hancinsa ya rinka jini kenan amma shine dan rashin tausayi yanzu kazo ka dake shi a hancinsa" Dukar da kai aadil yayi sannan yace "ummi kiyi hakuri,hakan ba zai sake faruwa ba" "Shikenan kaje maganar ta wuce" ummi tafada tareda ficewa daga cikin falon itama, Tana fita jawad ya fara harararsa "wlhi har yanzu ban hakura da pherty ba kuma yanzune ma nasake jin sonta acikin raina" Kallo aadil ya bishi dashi "kaje ka aureta ga wurin nan" yana gama fadin haka ya juya ya fice daga falon. ******* Bayan faruwar haka da kwana biyu aadil ya shirya yaje makarantar su pherty, ita sam bata san abinda ya faruba, bayan ya fito sun gaisa ne dai take ganin kamar yana cikin damuwa, "Pherty na wani wuri za muje, kije ki debo kayanki kamar kala biyar dan sai kinyi 2 weeks sannan zaki dawo dan haka sai kiyiwa su Sadiya da Aisha sallama" "To yaya" haka kawai tace ta juya ta koma hostel, tana zuwa ta dauki trolley ta fara hada kayanta aciki tana fadawa su Sadiya zasuyi tafiya da yaya aadil, Bayan ta gama shirya kayanta ne suka rakata har wurin motar aadil suka yi musu Allah ya kiyaye hanya, kallonsa ta juya tayi lokacin da suka fara tafiya "Yayana meke damunka ne?" Tafada tana kallonsa "Pherty na lfy lau nake kawai dai bana jin dadin jikina ne" Murmushi tayi sannan ta sake kallonsa "to yanzu dai ina zaka kaini?" Murmushi shima yayi "gidan sayar da mutane" "Ah yaya yaushe ka fara yanka kai?" "Ai nadade ina yanke kan raguna pherty nace bata saniba" Dariya ta fara harda buga kafa amma sai dariyarta ta tsaya ganin sun nufi hanyar kauyensu, "Yaya aadil wai ina muka nufa?" "Gidanku" ya fada agajarce Shiru tayi bata iya cemasa komai ba illa tunani da tafara yi, yau shekararta hudu rabonta da garinsu, komai ya canja na tsarin garin tun daga kan tituna har zuwa kan gine ginen dake cikin garin. Juyawa tayi ta kalli aadil saura kadan tasaka kuka, girgiza mata kai yayi, "Kar kiyi kuka pherty na, na tabbata su mama suna nan suna addu'a Allah ya dawo dake garesu, domin duk abinda ya faru sun san kaddara ne" "Nagode yaya, hakika kai nadabanne acikin mutane sannan kana da abubuwan da ba kowanne mutum ne yake dashi ba" "Nagode pherty na wannan Kalmar taki tayi min zaki kamar sugar, oh no ba sugar ba kamar Zuma zakinta yake agareni,kin san zuma tafi sugar zaki" Dariya tasa amma gabanta sai faduwa yake, saboda bata san yadda zata samu gidan nasu ba ko su mama na nan ko sun tashi oho. Tafiya kadan suka shiga cikin garin kumo nan ta fara bin ko ina da kallo har suka isa unguwarsu, komai ya canja amma gidajen suna nan yanda suke in banda yan sauye sauye da aka samu "Allah sarki hawyn mama kawata ko tana nan ko bata nan" haka ta fada acikin zuciyarta daidai lokacin da suka zo kofar gidansu hawyn, Akofar gidansu yayi packing ta fito, unguwar shiru kamar babu kowa, tsayawa tayi ta kasa shiga gidan sai aadil ne ya wuce gaba tana biye dashi a baya, lokacin da suka shiga gidan abbanta yana kishingide a tsakar gida akan tabarma yana jin radio ita kuma mama tana kitchen tana girki, sallama aadil ya rangada, tashi abbanta yayi daidai lokacin da yake amsa sallamar, zumbur ya mike, "Hajiya Adama, Adama, Adama kina ina? Maza fito kigani yau Allah ya amshi addu'armu ya dawo mana da yarmu" abbanta ya fada cikin farin ciki Da gudu mama ta bazamo ta fito, tana fadin "malam me naji kunnuwana suna fada min? Me nakeji malam?" Idanuwanta ne suka kai kan pherty ai da sauri ta karasa wajenta ta rungumeta. Kuka suka fara yi ita da maman nata "Assha meye kuma na kukan? Tunda ta dawo ai bukatarmu ta biya" abbanta ya fada Wuri aadil ya samu ya zauna kusa da abbanta, bayan sun nutsune aka gaggaisa nan aadil ya fara yiwa iyayenta bayani "baba ba tone tone za ayiba, ga pherty nan dai yau ta dawo sai dai ayi addu'ar Allah ya kiyaye gaba" "Amin dannan, amin amin, wallahi ko lokacin da ta tafi nayi bakin ciki mutuka domin abinda ya faru kaddara ce kuma shima yaron da yayi mata cikin yazo ya nemi afuwarmu" juyawa yayi ga pherty "phertyma kiyi hakuri kinji nasan nabaki tarbiyya iya iyawata kuma kinyi aiki da ita kawai wata kaddara ce da jarrabawa ta samu rayuwarki" Ita dai pherty itada mamanta basu ce komai ba in banda kukan da suke yi, "Ba kuka za ayi ba mama godewa Allah za ayi" aadil ya fada yana kallonsu "Abba bayan tafiyata daga gida wannan shine ya dauki dawainiyata yayi min komai na rayuwa ya kula dani har zuwa yanzu" "Allah yayi masa albarka, Allah ya yi masa albarka, mun gode, mun gode madalla" Nan aka barke da hirar yaushe gamo duk abubuwan da suka faru sai da pherty ta fadawa iyayenta abu dayane basu fada ba itada aadil maganar rashin lafiyar da take tareda ita domin bata son su tayarwa da iyayen nata hankali. Aadil ya dade agidan Kafin yayi musu sallama ya fita, bin bayansa pherty tayi suka tsaya a soron gidan, "Pherty na sai munyi waya, gobe zan koma abuja" "Allah ya kiyaye hanya yayana,sannan banda kallon yanmata, gashi zaka tafi baka ga kawata hawwa ba" Murmushi yayi "idan nazo next time zan ganta, ki gaishe min da ita" "Zata ji" "Yawwa amarya ta" ya fada yana dariya "Kaima ai ango ne" itama tafada tana dariyar "Idan na biya ta taki zan kwana anan, sai munyi waya pherty na, bye bye" "Bye bye yayana". Tafada lokacin da yake shiga cikin motarsa, Hannu ta fara daga masa har ya fice daga cikin layin nasu ta juya ta koma gidan nanfa suka cigaba da hira ita dasu mama ananne ma taji cewar yan unguwar basu san abinda ya faru ba kawai dai ance ta b'ata ne amma basu sanar da kowa abun kunyar da tayi ba, dad'i taji ya rufeta lallai naka sai naka, "Mama ina hawwa?" Ta tambayi mama "Hawwa dazun nan ma ta shigo, tana nan, ta kusa kammala karatunta itama a jami'ar tarayya dake garin katsina" "Mama bari naje naganta, nayi missing dinta over" Zuruf ta mike ta fice daga gidan ta nufi gidansu hawy, tana shiga ta hangota tsugunne tana wanke wanke, "Sannu da aiki yanmatan mama" Dasauri hawyn ta jiyo wa zata gani? Dagudu ta tashi taje suka rungume juna, "Phertyn mama kece? Muje daki" hannunta taja ko ta kan mama basu biba domin tana daki, wanke wanke kuwa tuni anmanta dashi, zama sukayi suka fara bawa juna labarin duk abun da ya faru bayan rabuwarsu, nan pherty ta bata labarin aadil, "Phertyn mama ko kin san cewar jawad yazo rannan kuwa? Har kirani yasa akayi na rakashi wurinsu mama, sannan yace shi yanzu aurenki zaiyi domin yana son gyara kuskuren da yayi a baya" "Hmm hawy kenan ai jawad bashida aikin yi ne, domin nafada masa ni yanzu bazan aure shi ba yayansa zan aura" Ido hawy ta zaro "wai dama shi aadil din yayansa ne?" "Uwarsu daya ubansu daya" "Tofa wannan abu akwai mamaki amma" Hannun hawy ta kama ta dora akan mararta "hawy taba kiji fa, kiji yanda gefen marata yayi tauri kamar dutse, gashi doctor yace ba lallai ne na haihu ba, ko sex dinma dakyar idan zan iya, taya zan auri jawad? Aadil zan aura domin ko babu komai shi dama ba jikina yake so ba sannan kuma zai iya hakura ya zauna dani koda kuwa bazai samu wani abu awurina ba" "Pherty kaddarar da kika hadu da ita kenan?" Hawy tafada idonta taf da kwalla, "Kar kiyi kuka pls, ai ko jiya ma saura kiris na mari jawad wlhi" Girgiza kai hawy tayi "Gara da baki mareshi ba, jawad yayi nadama pherty kuma wlhi yanzu dagaske yake sonki, kamar yadda nasan kema kina sonsa, kawai kyautatawar da aadil yayi miki ne take hanaki nuna soyayyar jawad, amma ni nasan kina sonshi, to ga shawara ki daina bacci ki yawaita tsayuwar dare kina kai kukanki wurin ubangiji kan ya zaba miki abinda yafi alkairi, nima kuma zan tayaki da addu'a" "Nagode hawy dama nasan ke ta dabance a gareni" Murmushi tayi ta goge hawayen kan fuskarta "Sannan magana ta gaba itace kar kisake yiwa jawad wulakanci pherty saboda kinga baki san abinda Allah zaiyi ba ta yiyu shine mujinki idan kuma ba mijinki bane sai a rabu salin alin, nasan abunda yayi miki da ciwo to amma kaddara ce babu yadda za ayi" "Shikenan hawy nagode zan kiyaye insha Allah" Mikewa tayi "zan koma wurin mama domin ban gama ganinta ba" "To muje nima ina nan shigowa" Ummi A'isha🏻 [5/11, 12:36 PM] Ummi A'isha🏻: [5/11, 7:59 AM] Ummi A'isha🏻: 👑 MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 55-60 ~~~ Dakin maman hawy suka je, itama kamar a mafarki ta ganta nan aka gaggaisa sannan ta koma gidansu. Tana zuwa ta dale jikin mama suka fara hira irinta d'a da uwa, daren ranar sun dade a zaune suna hira har sai wurin 2 sannan suka hakura, wayarta ta jawo saboda jin mama tayi bacci, tana budeta taga kiran yaya aadil babu adadi, agogo ta kalla anya kuwa ya kamata ta kirashi yanzu, kiransa ta fara yi ringing biyu ya dauka yana murmushi "Pherty na yau nayi fushi, wato dan kin samu mama shine zaki manta da yayan ki ko?" "Ni na isa yaya aadil? Na isa mantawa dakai, ban isa ba gaskiya hirace tayi yawa shiyasa ina fata kaje gida lfy" "Lfy lau amarya" Dariya tayi "Yaya aadil kana son kirana da sunan nan alhalin kuma kaima angone" Murmushi shima yayi, bayan sun dan taba hirane sukayi mata sallama domin gobe jirgin asuba zai bi zuwa abuja. Washe gari da safe bayan ta tashi tayi wanka ta shirya tana zaune a tsakiyarsu mama da abba tana yin breakfast suna hira sai ga hawy ta shigo, kallonta tayi tana murmushi "Ta mama har antashi?" "Eh Allah ya nufa" hawyn ta fada tana dariya Daki suka shige bayan hawy sun gaisa dasu mama, "Hawy ina labari?" "Labari ai yana wurinki kawata, ina aadil?" "Yau banyi waya dashi ba amma dai nasan ya koma abuja yabar gombe" "Oh Allah ya taimaka, inasu Sadiya da A'isha?" "Ai ina tashi da asuba bayan nayi salla dasu na fara waya" "Allah sarki, Allah dai yabar zumunci" "Amin" hira suka fara har suka gangaro ta kan hirar jawad amma ita pherty yanzu sam bata son taji an ambaci koda sunansa ma haka dai suka dade adaki suna hirar. ****** Satin pherty biyu a kumo sannan ta koma gombe, taji dadin wannan zama sosai domin bata fuskanci wata matsala daga iyayenta ba ko kadan, tana shiga hostel su sadiya da A'isha sukaje suka rungumeta nan aka shiga hira har tsawon wani lokaci. Soyayyarta da aadil kuwa sai karuwa take domin kullum suna nan makale a waya, bayan sati uku da tafiyarsa aka harhada komai aka kai gidansu pherty, harda Salima matarsa a yan kaiwa kayan,nan aka bar rana kamar yadda yasa afarko, komai yaji a kayan jama'a sai yabawa suke yi. Nacin jawad kuwa bai hakura ba saboda yanzu kullum sai yazo makarantar wurinta duk da cewa ba wani sauraronsa take ba, da haka akwana a tashi har biki ya rage saura sati biyu nanfa su Sadiya da A'isha suka fara shirye shiryen biki, hawy tayiwa waya tazo sch dinsu dama aadil ya turo musu da kudade dan haka kasuwa suka shiga su hudun suka iyo siyayyar kayan biki harda kayan da amaryar zata saka. Ana biki saura kwana tara suka tattara suka koma kumo, shikuma angon sai saura sati daya biki zai zo daga abuja, ranar da sukaje aranar sai ga jawad kamar mahaukaci yazo gidansu, tana fitowa taga shine, "Pherty bakida imani ashe? Bakida hankaline pherty? Wannan abun da kike shirin aikatawa wlhi mugunta ce tsantsarta, danme zaki auri aadil? Saboda kina son kasheni?" Kallonsa tayi ya dan rame kadan kamar wani marar lafiya "Kaine marar imani marar tausayi jawad, kaine kake shirin kisan kai sai kuma Allah ya juya maka al'amarinka da mummunan kudurinka kanka, na dade da fada maka bana sonka yanzu na tsaneka, ni bakai nake so ba yayanka nake so kuma shi zan aura, da shi zan rayu" Tsugunnawa yayi ya dafe kirjinsa, kanta ta dauke amma koda ta jiyo sai taga jini yana fita daga bakinsa, da sauri ta kalleshi amma ba tayi magana ba, da kyar ya mike bakinsa duk jini ya kalleta "Nagode pherty, tabbas kinyi min sakayya kuma nagani sannan nagode, zan tafi da sonki kuma zan mutu dashi, ina muku fatan alkairi keda mijinki masoyinki sannan Allah ya baku zuri'a dayyaba" yana kaiwa nan ya juya yana dingisawa idonsa cikeda kwalla bakinsa duk jini ya shiga motarsa, sai da yayi kamar minti biyar yana zaune yana kuka sannan ya iya fara tuka motar yana tafe yana aman jini yana kuka, ita kanta phertyn ta dade a tsaye kafin ta shiga gida tana zuwa daki kuma ta zauna ta fara kuka wanda ita kanta bata san ko na menene ba, matsowa kawayen nata suka yi suka fara tambayarta meya faru amma bata iya basu amsa ba. ****** Allah ne kadai yakai jawad gida lfy domin yayi mutukar galabaita wani irin harbawa zuciyarsa take yi masa kamar zata faso kirjinsa ta fito waje gashi aman jinin da yake sai karuwa yake, yana shiga gida yayi packing ya fito yana dafe da kirjinsa, tafiya kadan kuma ya fara wani irin tari mai sarke kirji nan ya fara aman jini sosai, ahaka ya mike jiri yana daukarsa ya nufi side dinsa, sharafff ya fadi akasa sumamme daidai lokacin maigadi ya nufo wurinsa yana ganinsa kwance cikin jini ya nufi part din Ummi da gudu "hajiya, hajiya fito jawad ba lafiya" haka mai gadin ya fada daidai lokacin da ya shiga falon ummin, zuruf ta mike "Yana ina?" "Yana waje" Dagudu Ummi ta fita ta nufi tsakar gidan, tana zuwa ta ganshi kwance bakinsa duk jini gashi ko alamun numfashi babu a tattare dashi, salati ta fara daidai lokacin motar dad dinsu ta shigo gidan, da sauri ya fito yana tambayar meke faruwa ganin jawad acikin wannan hali yasa yabawa driver da maigadi umarni su saka jawad a mota, dagudu Ummi taje ta dauko mayafinta ta shiga motar suka nufi asibiti. Wani private hospital suka kaishi, nan likitoci suka nufi wani daki dashi, kuka Ummi kawai takeyi dad yana bata hakuri. Kimanin awanni uku doctors din suka shafe suna kokarin ceto ran jawad amma abun yaci tura har lokacin bai farfado ba sai daf da sallar magrib sannan ya fara motsi nan kuma yafara tari yana aman jini, dakin Ummi ta fada ganin halin da yake ciki yasata sake fashewa da kuka. Wani babban doctor ne ya shigo hannunsa rikeda fayil ja, "ba kuka za kuyi ba, addu'a za kuyi masa, agaskiya abun nasa yayi worst, yana dauke da ciwon hawan jini, jininsa ya hau sosai irin hawan da ba aso, sannan kuma a halin yanzu yana fama da ciwon zuciya" Wani kuka Ummi ta fasa mai ban tausayi tana fadin "jawad wacce damuwa kasa aranka haka? Haba jawad? Tashi dad yayi yabi bayan likitan zuwa office dinsa bayan sun zauna ne likitan ya fara yi masa bayani "Am Alhaji yaron nan naka yana cikin wani hali gaskiya, yanzu babbar matsalar itace idan yatashi farkawa kila zai tashi da ciwon shanyewar rabin jiki saboda irin wannan faduwar dama itace ke haddasa wannan matsalar, amma za muyi iya bakin kokarinmu sai dai idan hakan bai samu ba sai a fitar dashi kasar waje" Wani gumine yaketa tsattsafowa dad din baice komai ba ya tashi ya fita ya koma dakin da jawad yake. Kwanansu uku a asibitin amma jawad ko motsi bai yi ba yana nan kwance kamar gawa, aranar aadil yazo garin koda yaje gidan bai samu kowa ba sai maigadin ne yayi masa bayani, wayar dad ya fara kira ya tambayeshi sunan asibitin yana fada masa yakarawa motarsa wuta ya isa asibitin, har a lokacin jawad bai motsa kai idan ka ganshi ba zaka taba tsammanin zai kara awa daya a raye ba saboda gaba dayansa acikin wasu karafa yake gashi ansaka masa abun numfashi wato oxygen tube, gefe kuma ana yi masa karin ruwa, Ummi na zaune fuskarta ta gama kumburewa saboda kuka, tayi jawur abunku da farar mace, Ahankali ya karasa kusa da Ummi, "sannu Ummi, ya mai jiki?" Cikin hawaye Ummi ta juyo tana ganin aadil sai ta sake fashewa da kuka mai ban tausayi Riketa aadil yaje yayi nan shima ya fara hawayen, doctor dinne ya bude kofa ya shigo ya kallesu "kuyi hakuri kudaina kukan nan domin patient dinku baya son hayaniya asali ma isolating din masu irin lalurar su ake yi asauran hospitals nan dinma saboda kune shiyasa muka barku kuke tare dashi" kallon dad yayi "Alhaji muna da bukatar jini domin akara masa" Mikewa aadil yayi fuskarsa cikeda kwalla yace "muje a dibi nawa a kara masa" Fita sukayi da doctor din suka nufi lab anan aadil din yake tambayarsa me yake damun dan uwan nasa, hawan jini da ciwon zuciya itace amsar da doctor din ya bashi, nan hankalin aadil ya tashi domin yasan yana dab da rasa dan uwan nasa gashi su biyu kacal iyayensu suka haifa, haka aka dibi jinin nasa leda biyu aka tafi domin karawa jawad, ba komai ne yafi daga masa hankali ba illa cewar da akayi kila jawad zai kamu da ciwon shanyewar barin jiki, dakin da jawad din yake ya koma ya samu Ummi "Ummi wai duk mai ya haddasa masa wannan lalurar?" "Wlhi aadil nima ban sani ba saboda jawad yanzu ya sauya hali dama can kasan shi ba mai yawan magana bane baya son hayaniya tun kuna yara kafishi magana shi sai ya wuni baiyi magana da kowa ba to yanzun kuma abinda ya tsira sai ya wuni a daki bai fito ba, nidai kawai ina zaune sai ga watchman wai nazo ga jawad can yafadi yanata aman jini, yanzu gashi doctor yace ciwon zuciya da hawan jini ne ke damunsa, ban san abunda yake damunsa ba har ya kamu da wannan lalurar" ta karasa maganar cikin kuka tareda rungume dan nata aadil "Kidaina kuka Ummi insha Allahu zai samu lafiya, Ummi gara ke kinada wani dan kuma kina da yan uwa nikuwa fa? Iya jawad ne dan uwana banida wani dan uwan sai shi idan na rasashi shikenan narasa wani bangare na rayuwata" aadil ya fada yana kuka hawaye suna bin kumatunsa "To yanzu meye amfanin wannan kukan, haba aadil kamar ba namiji ba?" Dad ya fada yana kallonsu duk kuwa da cewar shima dauriya kawai yake yi. Sai wurin karfe 9 na dare sannan aadil yaje gida yayi wanka anan yake sanar da Salima abunda yake faruwa, komawa asibitin yayi, daga Ummi har dad duk tausayinsa suke ji saboda sun san akwai soyayya mai tsanani tsakaninsa da dan uwansa, ko abinci ya kasa ci. Kwanansu biyar acikin asibitin sannan jawad ya fara bude idonsa amma baya gane komai ga wata kumbura da fuskarsa tayi sai kuma ya fara tari mai wahala nan jini ya fara fita daga bakinsa da sauri aadil ya karasa gaban gadon ya rike hannunsa "sannu jawad" Ko jinsa jawad bayayi, nan Ummi ta fara kuka sai janyeta dad yayi ya fitar da ita daga dakin, doctor ne ya shigo ya fara wasu rubuce rubuce ajikin fayil sannan ya yiwa jawad wata allura, nan yaja hannun aadil yana cewa yafi dacewa da adauki jawad akaishi kasar chairo zai fi samun lafiya fiyeda nan. Wajensu Ummi aadil ya koma yayi musu bayani yace yanzu zaije yayi musu cuku cukun visa su hudun "A'a aadil ban da kai, kaga yau kai saura 5 daurin aurenka, kayi mana mu uku kawai dani da mahaifiyar ka dashi jawad din" "To dad" ya fada ba dan yaso ba, kallon Salima yayi amma baiyi magana ba ya juya ya fita. Cikin kankanin lokaci aka samu visa nan suka tattara duk wani abu da zasu bukata aadil ya kaisu airport suka nufi kasar chairo, daga nan kumo ya wuce gidansu pherty. Lokacin da ta fito ta ganshi sai taji gabanta ya fadi "yayana baka da lafiya ne? Naga ka rame?" "Pherty na jawad ne bashida lafiya, yanzun nan ma aka tafi chairo dashi, aman jini yake tayi" "Allah yabashi lafiya" ta fada kamar zata yi kuka. "Amin, Abba yana nan?" "Eh" tafada a hankali "To muje naganshi" Rakiya tayi masa wurin abban ta fita ta basu wuri, ya dade awurin Abba sannan ya fito, ita da A'isha da Sadiya da hawy suka fito wurinsa "Yaya aadil ango" suka fada su duka Dan murmushi yayi "Bakuda bukatar komai ko?" "Muna son kudi wanda za ayiwa amarya gyaran jiki da kunshi" inji Sadiya da hawy "Nawane?" "20 thousand" "To bari na bakubaku 50 thousand saboda ina son pherty na tayi kyau" Motarsa yaje ya dauko kudin ya basu yayi musu sallama ya tafi ba tareda sun sake wata magana da pherty ba. Ranar juma'a da misalin karfe 2 jama'a suka taru domin shaida daurin auren pherty, bayan karfe biyu da rabi suna zazzaune agida adakin mama amarya tasha kyau saboda gyaran jikin da kunshin da akayi mata, wayar yaya aadil ce tashigo tana dauka yace tazo yana soron gidan, tashi tayi ta fita ta sameshi yasha farar shadda da jar hula wato kwankwasiyya sai kamshi yake "Sannu yaya aadil" "Yawwa pherty sannunki ya hidima?" Murmushi tayi bata amsa ba, "Pherty ayau ina mai farin cikin sanar dake cewa na cika miki burinki na aura miki wanda kike so" Kallonsa tayi "ban ganeba yaya aadil" "Ina nufin yau kin zama matar jawad" Kwalalo ido tayi "haba yaya gaskiya ni bana sonsa kai nake so ni gaskiya bazan zauna dashi ba, awarware auren nan cikin gaggawa" "Ni ina sonsa saboda dan uwana ne, pherty kenan nasan jawad kike so ni kawai kina yimin alkunya ne saboda abunda nayi miki na taimako, ina so kiyiwa jawad biyayya ki kulashi kamar yadda zaki kulani sannan ki sani jawad yana tsananin sonki fiyeda tunanin mai tunani, yanzu jirgi zanje nabi nida Salima domin gano halin da yake ciki sannan kuma nayi masa albishir da kin zama mallakinsa, pherty jawad dan uwana ne uwa daya uba daya duk duniya banida kamarsa tun Muna yara mun taso da son junanmu nasan abunda yake so nasan wanda baya so, kayan dakinki suna nan zuwa anjima nabar komai a hannun baba maigadi shine zaiyi muku jagora zuwa gidanki, sannan ina so kici gaba da kallona a matsayin yayanki ba yayan mijinki ba kamar yadda kike kallona ada, ko wani abu jawad yayi miki kar ki kunyar sanar dani, ban yarda ki kai kararsa wurin kowa ba sai wurina, ni nayi masa walinci nabada sadakinki Dubu Dari biyu da hamsin, Allah ya sanya albarka acikin aurenku, Allah ya baku zuri'a dayyaba" Wasu hawaye ne suka fara bin kumatunta "Nagode yaya aadil, hakika kai wani mutum ne mai mutukar muhimmanci a rayuwata nagode yaya aadil Allah ya saka maka da mafificin alkairi" "Pherty tun farko nasan jawad kike so, kamar yadda shima ke yake so, Allah ya barku tare" Yana fadin haka ya juya ya fita ya nufi airport inda Salima ke jiransa domin jirginsu ya kusa tashi. Gida ta juya ta koma tana ta kuka "zaki fara sana'ar taki ne?" Sadiya ta fada tana kallonta "Kibarta kukan farin ciki ne" hawy ta fada tana dariya "An auri jawad ai dole ayi kukan farin ciki" inji A'isha domin dama su sun san da jawad aka daura mata aure itace bata sani ba nan suka shiga tsokanarta ita dai sai kuka take. ****** Misalin karfe 4 na yamma su aadil suka sauka akasar chairo, asibitin da su jawad suke suka nufa shida salima, lokacin da suka shiga dakin da jawad din yake yana kwance idanuwansa a rufe, inda yake aadil ya karasa ya kama hannunsa "Jawad bude idonka kaji, ka bude idonka, pherty ta zama matarka, wlhi dama ban taba sonta ba kamar yadda itama bata sona kai take so, ni kawai taimakon da nayi mata ne yasa take girmama ni, haba dan uwana taya zan so abunda kake so, wlhi duk abinda ya faru nayi shine domin na kubutar dakai daga rasa abunda kakeso domin ba dan na rike maka pherty ba da tuni ta shiga uwa duniya kuma ba lallai ka iya gano inda take ba gashi kana fama da ciwon sonta, sannan ba don na nuna ina sonta ba da tuni yanzu wani ya gama siye zuciyarta kuma koda ka koma ba zata saurareka ba, duk taimakon da nayi mata nayi shine saboda kai dan uwana, ka saki ranka wlhi ban taba son abunda kake so ba" Bude ido jawad yayi, idanuwansa cikeda kwalla, sake damke hannun aadil yayi, "Meyasa baka aureta ba? Kai kafi cancanta da aurenta saboda kaine ka taimaketa a lokacin da take bukatar taimako,Kaine ka zaba gatanta a lokacin da bata da gata, nikuwa ban yi mata komai ba a rayuwarta face zalunci shiyasa Allah ya kamani" "Kayi shiru dan uwana kar su Ummi suji, kayi hakuri ka rigada ka zama ango amma wani hanzari ba gudu ba, tanada matsala a mararta, buguwar da tayi lokacin da tasamu miscarriage dinnan taji ciwo a gefen mararta" Daga kai jawad yayi yana hawaye "Allah ya saka maka da alkairi dan uwana, nagode nagode, banida bakin yi maka godiya" Cikin kankanin lokaci jawad har ya fara samun sauki, jikinsa ya danyi kyau gashi kumburin nan na fuskarsa ya sabe domin jininsa ya sauka ya koma normal, ciwon zuciyar ma tuni ya lafa sai dai har yau baiji muryar amarya ba. ****** A Gida Nigeria kuwa an gama gabatar da shagulgulan biki lafiya, anyi yini anyi walima sannan kawayen amarya sun shirya sisters night, mama kuwa ta dage ta gyara yarta tsaf ciki da waje, yau ake sa ran kaiwa amarya gidanta. Misalin karfe takwas na dare aka dauketa akayi cikin gombe da ita bayan iyayenta sunyi mata nasiha daidai gwargwado, wani tamfatsetsen gida aka kaita wanda indai bata manta ba to nanne gidan da jawad ya kaita, amma an sake gyara gidan an zuba masa sababbin funitures komai blue, hatta gadajen blue ne, dakuna uku da faluka biyu ga dining area da kitchen da store aciki, anan kawayen nata zasu kwana tunda ango baya nan. "Masha Allah gida yayi kyau Allah ya kawo yan uku" inji hawy "Yan Hudu dai ya kamata ki rokar musu" Sadiya ta fada tana dariya "Kai duk ba wannan ba gaskiya ba zaku kwana akan gadon ma'aurata ba kuzo mu koma falo mu kwanta acan" A'isha ta fada tana kifta musu ido Ita dai pherty tashi tayi ta shige toilet ba tare da tace musu uffan ba. Ummi A'isha🏻 [5/12, 11:48 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 61-63 ~~~ Kwana suka yi suna hira sai tsokanarta su A'isha suke, sai da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta bacci. Kwanansu biyu sannan suka koma sch suka barta da iya hawy kawai, tana kuka suna kuka haka suka rabu dasu Sadiya, ranar da suka tafi da yamma suna zaune ita da hawy a falo jawad ya kirata a waya kamar ba zata dauka ba sai ta dauka "My queen" ya fada a hankali "Ina jinka" tafada cikin gatsali "Kinji yadda al'amari ya sauya ko?" "Eh naji amma ai ni dole aka yi min domin ba sonka nake ba" Harara hawy ta wurga mata itama ta rama, Shiru yayi ya rasa abin da zai ce mata can ya daure yace "Ko jikin nawa ba zaki tambaya ba Queen?" "Banida alaka da shine shiyasa kaji ban tambaya ba" "Ok to nagode sai munyi waya" Kashe wayar tayi sai kuma taja tsaki "mtsww" "Mijin naki kike yiwa tsaki pherty? Wlhi kiyi ahankali tom" hawy ta fada tana hararta, "Anki ayi ahankalin kuma anyi masa tsakin sai me?" "Sai ya gyara miki zama idan ya dawo" "Ya gyara din" "Yarinya kenan, round biyu zai yi miki kwarara zaki shiga hankalinki" "Yayi round goma ba biyu ba" ta fada tare da ficewa daga bedroom din ta nufi dayan. Kwanansu biyar tareda hawy agidan amma kullum sai sunyi fada akan jawad da haka har pherty ta fara shirin komawa sch aranar itama hawy ta koma gombe. Kayanta ta harhada cikin trolley ta nufi sch nan kawayen nata suka fara yimata oyoyo,tunda ta koma kuma ta watsar da jawad duk da cewar tasan tana sonsa amma haka take basarwa watarana ma da saninta zata kashe wayarta dan kar ya kirata ya sameta, sai dai har lokacin basu yi waya da aadil ba amma takanyi masa text ta gaida shi lokaci lokaci. ****** Acan kasar chairo kuwa tuni jikin jawad yayi sauki garau kamar bai taba jinya ba har an bashi sallama nan suka fara shirye shiryen dawowa gida Nigeria amma shi aadil da Salima zasu wuce kasar London domin hutawa to sai muce adawo lafiya. Ranar asabar da yamma ranar su jawad suka sauka a Nigeria yayi fresh yayi kyau saboda yanzu bashida wata damuwa gashi yana samun kulawa sosai wurin ummi sai dai har yau su Ummi basu san dalilin aadil nakin auren pherty ba sun rasa dalilinsa na aurawa jawad phertyn. Washe garin ranar da suka dawo Sadiya da A'isha suka matsawa pherty kan lallai dole sai ta shirya sunje duba jawad, fada sukayi sosai kafin ta yarda ta shirya cikin lace blue ta yafa mayafinta kashka shima blue,sarka ta saka silver mai kyau tasa farin takalmi flat,fita suka yi suka nufi unguwarsu jawad din domin yana gidan ummi, keke napep suka hau har unguwar. Kallon gidan take tayi tana tuna ranar da tazo lokacin da jawad yayi mata ciki, Part din ummi suka shiga suka sameta zaune tana duba wani littafi idonta sanye da medical glass, pherty tana baya Sadiya agaba, sai A'isha, sallama sukayi ta dago ta amsa musu, "A'a pherty sannunku da zuwa" tafada cikin hausarta wadda bata fita sosai, Zama suka yi ita kuma tafita taje da kanta ta hado musu kayan marmari ta kawo musu, pherty dai bata iya hada ido da ita ba kanta yana sunkuye suka gaisa, "Jiya ai munje gidan naku munyi godiya, angama biki lafiya ko?" "Lafiya lau" tafada cikeda kunya Zama suka yi shiru har na yan mintuna sai daga baya su sadiya suka tambayi jawad tace yana side dinsa tun dazu yafita, tashi suka yi suka nufi side din nasa. Lokacin da suka shiga yana cikin daki yana kwance akan gadonsa, jin sallamarsu tasa shi tashi yasa riga, shiga suka yi suka sameshi zaune, "Sannu ango ya jikin naka?" Suka fada a tare banda pherty "Alhamdulillah, am cued" ya fada yana kallon pherty wadda ta bata rai, Tashi Sadiya da A'isha suka yi suka koma falo suka basu wuri, kallonta yake tayi a hankali, sai hannunta yake bi da kallo saboda har yanzu kunshin da tayi bai gama fita ba, gashi tayi kyau fatarta tayi lukwi lukwi tayi kyau sai kyalli take saboda gyaran da tasha, "Ba zaki gaisheni ba?" Shiru tayi masa bata bashi amsa ba, Hannu ya mika mata alamun ta matsa gareshi amma ta dauke kanta, tashi yayi ya shiga toilet sai a sannan ta fara bin dakin da kallo, ya tsaru sosai komai akan tsari, yana fitowa ya nufo inda take, cikin sauri ta mike, hannunta ya riko da niyyar janyota jikinsa, k'i tayi ta koma jikin bango binta yayi ya fara kokarin shinshina ta, "queen kinyi kyau" yafada acan cikin makoshinsa,bakinsa yakai kan fuskarta, nan ta fara kiciniyar hanashi kissing din bakinta bai damuba duk inda ya samu akan fuskar tata anan yake sakar mata kiss din,tana makure ajikin bango shi kuma ya matseta sai kai mata kiss take yana fitar da numfashi a hankali, janta yayi zai rungumeta ta kuwa kankame jikinta dole ya hakura ya saketa ya koma gefen gado ya zauna, a inda take ta zauna, har lokacin numfashi yake fitarwa, tsam ta mike ta fice bata yi masa magana ba, a falo ta tarar da sadiya da A'isha suna hirarsu, "Sai ku tashi mu tafi ai" Tashi sukayi suka fice sai da suka koma suka yiwa Ummi sallama sannan suka wuce makarantar tasu. Tun akan hanya suke tsokanarta "kinsha kiss ko?" "Oho" tafada tana zaro wayarta ajaka saboda ta jiyota tana ringing "Hawyn mama" "Um ya sch din?" "Kin ganni ma a hanya nadawo daga dubiya" "Jawad kika dubo?" "Shi dai" "Ya bayani, amma dai ba haka kika taho ba ko?" "Oho miki" ta fada tareda kashe wayar. Tun lokacin bata kara zuwa dubashi ba har ya karasa warkewa ya koma gidansu yabar gidan Ummi, ranar da daddare ya shirya yaje makarantar koda yayi mata wayama sai tace ita bacci zatayi, marairaice mata yayi yace ganinta kawai zai yi sai ta koma, daga ita sai kayan bacci ta fito amma ta zira dogon hijabi lokacin wurin karfe 9 nadare. Yana cikin motarsa taje ta tsaya a waje sai shine ya fito ya zagayo ta inda take tsaye, "Queen bacci tun yanzu?" "To me zanyi maka idan banyi bacci ba?" "Allah ya baki hakuri abun bana fada bane" Dauke kanta tayi hakan ya bashi damar karewa jikinta kallo, hijabin jikinta ya daga da niyyar ganin kayan dake jikinta Kamar wacce take jira ta fara masifa, "Meye hadinka da kayana da zaka daga min hijab? Bana son haka" tana gama fadin haka ta juya zata tafi, ta bayanta yaje ya rungumeta, yafara laluben kirjinta, ta bude baki kenan da niyyar yi masa masifa yayi saurin rufe mata bakin da hannunsa, Kasa kwakkwaran motsi tayi saboda yanda ya kankameta gashi ya rufe mata baki da hannunsa, kamshin turaren da yasaka ne ya fara cika mata hanci, "Pherty na kin koyi masifa ko? Da dai Queen dina mai hakuri ce ba mai fada ba" Hannunta tasa ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata, sakinta yayi ya tsaya ta bayanta, ko jiyowa bata yi ba tayi gaba abinta ta wuce hostel shi dinma juyawa yayi ya shiga motarsa ya tafi. Koda yaje gida yayi shirin kwanciya amma sai ya kasa baccin juyi kawai yake gashi yasan koda ya kirata ba lallai ne ta dauka ba, haka ya karaci juyinsa daga karshe ya rungume filo bacci ya daukeshi. Itama phertyn kasa bacci tayi sai juyi kawai take yau jawad ya baro mata aiki, juyawa ta sake yi ta kalli Sadiya da A'isha wacce ko waccensu take baccinta hankalinta kwance, dakyar ta samu baccin ya dauketa. Washe gari ta kama Friday su Sadiya duk sun tashi da shirin tafiya weekend kallonsu ta fara cikin jin haushi "Wai dagaske tafiyar zakuyi? Nikuma ni kadai zaku bari?" "Kema kina iya shiryawa ki je naki gidan ranar Sunday sai ki dawo" Sadiya ta fada lokacin da take zuge zif din Jakarta, "Tab ai ni ko zan dawo ma wlhi sai Tuesday" A'isha ta basu amsa "To nima Tuesdays din zan dawo ko Wednesday" Sadiya ta sake bata amsa, nan suka shirya kayayyakinsu ganin zasu tafi su barta yasa itama tashi ta shirya suka fita gaba daya. Keke napep ta hau har gidanta, lokacin da ta shiga taga alamar jawad yana nan saboda ga motarsa nan a ajiye agidan, gaisawa suka yi da maigadin ta wuce ciki, a falo ta sameshi kwance akan 3 sitter daga shi sai three quarter, wayoyinsa da laptop dinsa kuma ajiye akan center table, kallo tabishi dashi duk jikinsa ko ina gashine a kwance, jin tsikar jikinta ta fara tashi yasata shigewa cikin dakinta, Kayan jikinta ta cire tasa wando iya cinya da yar riga milk colour yar karama iya cibiyarta, kitchen ta shiga ta dora abinci, tana cikin girkin sai gashi ya shigo ganin itace acikin kitchen din ya sashi yin murmushi "Queen kece ashe?" "Um" tafada a gajarce Juyawa yayi ya fita ita kuma taci gaba da girkinta, indomie ta dafa da kwai ta zubo a filet tazo zata wuce daki, "queen ina nawa abincin?" "Banyi dakaiba" tafada cikeda rashin kunya Tashi yayi yabi bayanta, tana zama sai gashi ya shigo, abincin ta fara boyewa shikuma ya hau kan gadon nan suka fara kokawa, tsoro yaji kar ta kone yasa ya barta yatashi zai fita har yaje bakin kofa yaji tace "da saura a tukunya idan zaka ci" Kitchen din yaje ya dibo sauran data bari ya koma falo. Tana gama cin abincin ta ta ture filet din ta cire rigar jikinta ta kwanta daga ita sai bra da dan gajeren wandonta, wayarta ce ta fara ringing sai kuma ta katse wayar ta mutu, ta manta ashe bata da charge gashi ta manto charger din a sch, daukar wayar tayi ta nufi falo domin neman charger,jawad yana zaune yana cin abincin sai kawai ganinta yayi ta fito a haka, baice mata komai ba yaci gaba da cin abinsa amma sai kallonta yake yana mamakin yadda ta kara cika sosai, dube dube ta fara a falon ganin bata samu abinda take nema ba ya sata nufar daya dakin wato na jawad, tashi yayi ya bita tana sunkuye tana kokarin jona wayar a charge, tana dagowa ta ganshi tsaye yana kallonta "Wayasa ki fito a haka? Ko baki san ma'aikatan gidan nan duk maza bane?" "Nida gidana sai anfada min yadda zan fito? Nafita duk yadda nagadama mana ina ruwan wani dani" Matsowa yayi kusa da ita "kin koyi rashin kunya ko?" Kawar da kai tayi ta kyaleshi, cikinta ya kalla "ke cikinki baya girma ne idan kinji abinci?" Nanma shirun tayi, matsawa yayi yabata hanya alamar tazo ta wuce, tana zuwa saitinsa yasa mata kafa tafiya tayi zata kifa yayi saurin rungumeta kafin tayi wani yunkuri yayi kan gado da ita, Jagulata ya fara yi tako ina ita kuma sai kokarin kwacewa take riko daya yayi mata takasa motsi kiss ya fara kaiwa kirjinta, ganin yana neman wuce gona da iri yasa ta yi masa dabara "ka daga ni kaga ni bana daukar abu mai nauyi saboda marata" juyawa yayi tana ganin haka ta mike "kadaina taba min jiki" Ficewa tayi daga dakin ta koma nata ta kwanta dama bacci take son yi. Ta jima tana bacci kafin ta tashi tayi wanka tayi salla tana gaban mudubi daure da towel tana shiryawa ya shigo,towel dinne ya zame nan taci gaba da kwalliyarta ba tare da ta gyarashi ba, kallon kirjinta ya fara ta cikin mudubin, "Am, um queen zan fita" ya fada muryarsa a shake, "Umhum" tafada tana shafa powder Juyawa yayi yana tafiya yana waiwayenta har yaci karo da bango, dawowa yayi "queen bakya bukatar komai ko?" "Bana bukata" Ficewa yayi ya nufi tsakar gida,ita kuma ta tashi tasaka kaya, riga da wando masu santsi ta fesa turare mai kamshi a jikinta ta fita falo. Ummi A'isha🏻 [5/13, 7:58 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 64-66 ~~~ Motarsa ya shiga ya fita ya nufi cikin gari amma yana tafe yana tunanin pherty gaba daya yau ta sauya masa tunani nan yaji hankalinsa ya fara tashi haka ya daure ya karasa gidan ummi. Ita kam pherty koda ta gama shirinta falo ta fito ta nemi wuri ta zauna nan kuma zaman ya fara gundurarta saboda gidan shiru babu motsin kowa, dakin jawad ta tashi ta shiga ta zauna agefen gadonsa ta dauki laptop dinsa ta bude, password din ta fara gwadawa farko tasa sunansa yaki budewa, sunan umminsa tasa nanma bai budeba, tana saka pherty taga ta bude wani hadadden hotansa ne akan screen din yayi kyau sosai cikin jar riga da blue din wando, game ta gani kala kala dan haka ta zabi daya ta fara, ta dade adakin nasa tana game kafin ta kashe masa ta fice daga dakin. Dakinta ta koma tayi sallar magrib ta dawo falo hannunta rikeda cazbaha tana ja, tana nan zaune har aka kira isha, bayan ta idar da sallar ne ta shiga kitchen ta dora ruwan zafi tareda tsayawa ta fara tunanin abinda zata dafa, jalop din taliya da kifi tayi ta sauke ta koma daki ta shiga wanka tana cikin wankan jawad ya dawo, dakinta ya fara shiga bai ganta ba, kofar toilet din ya bude sai ya ganta tana wanka, "Meye" tafada cikin masifa "Nadawo ne ban ganki ba shiyasa ashe wanka kike" "Malam ka fice daga bathroom dinnan" Ciki ya shiga "ki tsaya in yi miki wankan" "Allah ya sawwake" ta fada cikin fad'a Soson hannunta ya mika hannu zai karba, "kawo inyi miki" "Nace banaso, bana so, bana so,a'a ko dole ne....!" Shiru tayi sakamakon jinta da tayi acikin kirjinshi, Hannunshi yakai jikinta nan suka fara kokawa "bana so, nace bana so" haka ta fara fada a hargitse, "Yi hakuri queen, na fita" Sakinta yayi ya juya ya fice, sauri tayi ta sawa kofar toilet din key taci gaba da wankanta yanzu ta fuskanci kamar baya son bacin ranta duk abinda ta nuna bata so hakura yake. Tana fitowa daga wankan ta shafa body spray tasaka wasu kayan bacci pink colour riga da wando, rigar da kadan ta rufe cibiyarta wandon kuma bai karasa gwiwa ba, fita tayi ta shiga kitchen lokacin jawad yana kwance akan doguwar kujera, abinci ta zubo ta wuce dakinta, tana gamawa sai gashi ya shigo idonsa kamar ya tashi daga bacci, "Queen zaki zo dakina?" Kallonsa tayi duk jikinsa a wani sanyaye idonsa kuma kamar yasha wani abu, "Me zanzo nayi a dakinka?" Langabar da kai yayi "To ni nazo?" "Bana nemanka" tafada gamida zamewa tayi kwanciyarta, "To shikenan sai da safe" yafada cikin kalar tausayi, bata amsa ba ganin haka ya sashi juyawa ya fita bayan ya kashe mata light din dakin. Dakinsa yaje ya kwanta akan gado nan yaji kwanciyar bata yi masa ba, kan doguwar kujera ya koma ya kwanta, mintuna kadan ya sake tashi ya dauki pillow ya koma kan carpet ya kwanta nan dinma bai wani dade ba ya tashi ya koma kan gadon, haka yayi ta sauye sauyen wurin kwanciya kafin asuba ya sauya wuri yafi sau goma. Karfe tara daidai ya fito da saurinsa ya tsaya a falo daga shi sai gajeren wando lokacin masu aikin gidan har sunzo sun fara aikinsu, tsayawa yayi yana kallonsu suna gyara falon yasan ba karamin aikinta bane ta fito a yanda ta fito jiya tunda ya fuskanci yanzu wata sangarta take ji da ita, ko minti biyar baiyi ba da tsayawa ta bude kofa ta tsaya tana mika da saurinsa ya karasa kofar dakin ya turata ciki daga ita sai dan kayan baccinta wanda basu da maraba da abin tace koko, "Queen karki fito a haka pls kinga da mutane a falo suna aiki" Mikar da ta fara ta karasa tareda yin wata yalwatacciyar hamma, hakan ya bashi damar ganin har cibiyarta, "To nikuma ina ruwana da masu aiki? Ko akaina zasu yi aikin?" Tafada tana yatsina fuska, Cikinta ya kalla ya lashi lebenshi "kiyi hakuri yanzu zasu gama, mopping suke yi sun gama sharar" Juyawa tayi ta koma cikin dakin ta fada kan gado taja bargo tareda janyo wayarta ta kunna data, fita yayi yaja mata kofar, Chtn tafara dasu Sadiya da A'isha da hawy dadi taji saboda ganin duk suna online "amare an shigo?" Hawy ta turo mata "um sai yanzu" ta tura mata amsa "komai ya wakana ko?" Sadiya ta turo,dariya tayi ta mayar mata da amsa "abinda ya fishi muka yi" "kun takurawa pherty fa, Ku kyaleta ma da ciwon jikin da jawad ya sa mata" A'isha ta turo harda gwalo, dariya tayi ta mayar musu da amsa "kuna wasa yara, wlhi bama daki daya muka kwana ba" ,"ehhh amma ai a takure kuke" hawy ta tura, "Allah ya shiryeku" ta tura musu tana dariya "phertyn jawad sai yaushe zaki dawo?" Sadiya ta tambayeta "sai sun gama soyewa" A'isha ta bata amsa " "sai ta samu ciki zata dawo kun san jawad bana wasa bane shi a karon farko yake bada tukwici" hawy ta tura musu amsa,"sai anjimanku zanje na dora breakfast" ta tura tana murmushi, "bawani kawai dai kice zakije dakin jawad" Aisha ta mayar mata da amsa, sauka tayi ta kashe data dinta tana murmushi, daidai lokacin jawad ya shigo, "Ki fito sun gama sun tafi" Bata bashi amsa ba ta taso tazo ta wuce ta gabansa ta fice, bayanta yabi yaje ya sawa kofar falon key ya rufe sannan ya koma dakinsa, kitchen ta shiga ta fara dan soye soyenta, plantain ta soya da dan dankali sannan ta soya kwai, kan dining takai kayan ta koma daki tayi wanka tayi brush ta fito, vest tasa ja da wani dan guntun wandonta wanda da kadan ya fi pant, komawa falon tayi ta zauna ta fara breakfast, tana gamawa shikuma yana fitowa, falo ta koma shikuma ya hau kan dining din, dan guntun wanda ta bari ya fara ci yana ci yana kallonta aransa yana kissima yanda zai yi da ita duk ranar da ta shiga hannunshi, Tv ta kunna ta fara dube duben channels, a zee aflam ta tsaya saboda ganin suna wani hadadden film mai suna kites duk da badaga farko ta fara ganin film din ba amma ya burgeta, wata irin soyayya taga jarumin film din yana nunawa yarinyar, take jikinta ya fara shock saboda yanda taga suna romancing junansu, idonta ta rufe,da sauri ta bude idonta saboda jin tafiyar tsutsa a wuyanta, jawad ta gani kusa da ita, take ta fara kokarin hade rai, hannunta ya kama ya fara mammatsa shi, shi dai a duniya yana kaunar hannun nan nata saboda yanada mutukar laushi lum lum, kiss yayi mata a goshi ta dauke kanta tareda fara kokarin fusgewa daga hannunsa, riketa yayi gam ya dauketa cancak ya dorata akan cinyarsa, kokawa sosai suka shiga yi daga karshe ya dorata akan kujerar ya matseta sosai, bakinsa ya sa a wuyanta ya fara kissing dinta, "Jawad...!" Bai barta ta karasa ba ya hade bakinsa da nata ya fara tsotsa, hannunta ya damke yaketa mammatsawa, dagowa yayi ya kalleta "Bakida karfi sai kuri" akule ta fara kallonsa "nafada maka bana so" rungumeta yayi tsam tsam ajikinsa tareda cusa kansa a tsakiyar kirjinta, dakyar ta iya tureshi ta tashi, anan ya kwanta inda ta barshi, daya kujerar ta koma ta zauna amma itama tana cikeda bukatarsa, Kofa taje ta bude ta fita ta nufi bayan dakunan da sauri ya tashi ya bita yana fita ya hangota tana tsino kananan duwatsu, tsayawa yayi tazo ta wuce ta koma falon ta zauna ta fara yar carafke, bayanta yabi ya koma ya kwanta acikin kujera, yana daga kwance yana kallonta tana ta carafke kamar wata karamar yarinya da haka bacci ya kwashe shi. Sai da tayi yar carafken ta tagaji sannan ta tashi taje kitchen ta dora abincin rana, macaroni da wake, tana fitowa ta ganshi tsaye yana waya da alama har ya tashi daga baccin dan gashi nan sanye da three quarter, kallo ta bishi dashi, "Dan Allah a daure ayi aski" ta fada tana yatsina fuska, binta yayi ya janyota ya matseta ajikin bango tareda fara kokarin zame three quarter din jikinsa, runtse idonta tayi, "Ki bude idonki kigani idan banyi askin ba" "Bana son gani" "Sai kin gani kuwa" kiss ya kaiwa bakinta ta goce ta shige daki da gudu.Ba ita ta fito ba sai da ta jiyo abincinta ya fara kamawa, da sauri ta fito ta shiga kitchen ta sauke abincin, dan kadan ta zubo ta zauna a falo ta fara ci, ganin jawad yana fitowa daga dakinsa ya sata kawar da kanta. Ummi A'isha🏻 [5/14, 9:18 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 67-68 ~~~ Kusa da ita ya zo ya tsugunna ya kamo hannunta a hankali yayi mata magana cikin fillanci "sammun abincin queen" Sam ita bata fahimtar fillanci sosai amma ta dan fahimci nufinsa, "Menene?" Ta fada fuskarta a murtuke "Cewa nayi ki sammin" ya fada da turanci, "Je ka zubo naka" ta fada tana kallon wani wuri, kiss ya kaiwa kan fuskarta yayi mata akan kumatunta, tashi yayi ya wuce kitchen din ita kuma ta jiyo taci gaba da cin abincinta aranta tana tunanin ko yare nawa dansu zai ji idan yazo duniya. Bayan ta gama cin abincin daki ta koma ta kwanta aikin kenan daga kwanciya sai zaman falo, bacci ta dan fara yi sama sama amma sai taji alamun mutum a kusa da ita, bude idonta tayi cikin magagin bacci ganin jawad a kusa da ita ya sata saurin tashi, "Meye haka?" "Yi hakuri queen, dan Allah ki barni naji dumin jikinki dan Allah" ya fada cikin fuskar tausayi "Tab wlhi bazan kwanta akusa da kai ba, idan baccin za kayi ka koma dakinka, idan kuma sai anan zaka kwanta to ka matsa can karshen gado" ta nuna masa da yatsanta, Matsawa yayi ya koma karshen gadon ya kwanta, itama komawa tayi ta kwanta taci gaba da baccinta, kasa hakuri yayi ya sake matsawa jikinta ta bayanta ya rungume ta, tana jinsa tayi zumbur ta tashi tana kallonsa, "Gaskiya ka tashi ka koma dakinka" Idonsa ya lumshe sannan ya budesu sunyi dan ja "Haba queen dan Allah ki barni, pls pls" Komawa tayi ta kwanta ya rungumeta ta baya yana dan shafarta a hankali, baccin da bata yi ba kenan amma shi mintuna kadan taji ya fara numfashi a hankali alamar yayi bacci kenan. Sai misalin karfe hudu sannan ya farka lokacin ita harma ta shiga wanka, fita yayi ya nufi dakinsa yayi wanka ya shirya yayi salla ya fito, a falo ya ganta kwance tana game a wayarta tana sanye da wata bakar riga mai siririn hannu, rigar bata da nauyi domin har yana iya hango farar bra da farin pant din da ta sa ajikinta, tsayinta kuwa bazai wuce cinyarta ba dan ko gwiwarta bai karasa ba, tsayawa yayi yana kallonta yana lasar lebe kamar wani sabon maye, "Zan fita" ya fada yana kallonta, "Sai kadawo" ta fada cikeda rashin kulawa, juyawa yayi ya nufi kofa yana tafe yana waiwayenta har ya fice. Bai dawo gidan ba sai wurin karfe 8,a dakinta ya sameta kwance ta kure ac tana shan iska tasa kayan baccinta milk colour yar karamar riga da yar top dinta, "Queen kinci abinci ne?" "Banci ba" "To kizo na taho miki da abinci" "Kawo min shi nan" tafada tana yatsina fuska, fita yayi ya debo mata tarkacen da ya shigo mata dashi ya ajiye mata a gabanta ya fita, tashi tayi ta fara bude ledojin, gasasshiyar kaza da shawarma, da tarin kayan zaki su chocolate da ice cream, shawarmar taci tasha ice cream ta dauki chocolate ta fara sha, tasha chocolate sunfi goma sannan ta hakura ta shiga toilet ta wanke bakinta ta dawo ta kwanta, shigowa yayi yana sanye da kayan bacci "Lafiya?" Ta tambayeshi "Lafiya lau, anan zan kwana saboda jiya kasa bacci nayi" ya fada yana kokarin hawa gadon, "To karshen gado nanne wurin kwanciyar ka sannan ba za akashe light ba" Fuskarta ya kalla "Ban iya bacci da light ba queen, ni komai kankantar haske hanani bacci yake" "To sai ka koma dakinka, saboda nima ban iya bacci a duhu ba" tana gama fadin haka ta koma ta kwanta, karshen gadon ya koma ya kwanta ya juya mata baya kamar yadda itama tayi, wurin minti goma da kwanciyar su ta juya ta kalleshi sai taji ya bata tausayi saboda yadda ya takure ya cusa kansa cikin hannuwansa dan kar hasken ya dameshi, tashi tayi taje ta kashe wutar ta dawo ta kwanta. Asubar fari ya tashi ya fice bayan ya tasheta tayi sallah, komawa tayi ta kwanta bayan ta idar da sallar, bata fita ba sai wurin 9 lokacin masu aiki har sun gyare gidan tsaf, kazar da ya kawo mata jiya ta dumama ta dafa ruwan zafi ta ajiye akan dining, daki ta koma tayi wanka tayi kwalliya sosai ta shiryo cikin riga da wando na Pakistan kalar ruwan kwai, kan dining ta hau ta fara karyawa, shima jawad fitowar yayi ya hau kan dining din, "Queen dan Allah ki tausaya min, kiji tausayina pherty" ya fada yana kallonta "Me nayi maka?" "Haba queen kullum sai tsokanoni kike yi kuma ki hanani kanki, wannan abun sam bai dace ba queen, kinki saurarata bayan kin san inada bukatarki" "Au shiyasa ka kawo kayan zaki ashe dama saboda in baka jikina ne?" Ta fada tana tabe baki "Ni ba saboda haka bane, amma dai kin san ina da bukatar ki ko?" "Ni ban sani ba" tashi tayi ta shige dakinta, Tana nan kwance tana chtn da mutanen nata ya shigo, hayeta yayi ya fara kissing dinta, "Jawad bana so, meye haka?" Bakinta ya tsotsa yaci gaba da sarrafata baji ba gani, tutture shi ta shiga yi amma ta kasa, bai barta ba sai da ya gama tara mata gajiya, duk tsikar jikinshi ta gama tashi har wani jiri yake ji, haka ya tashi zai fita ya dan kalleta, "Dama fa kyaleki nake bana son nayi miki ta karfi ke kuma kinki ganewa" "Malam ka fice min acikin daki sannan kar ka sake shigo min daki" ta fada cikeda masifa, fita yayi yana murmushi ya koma dakinsa ya fada akan gado ya kwanta. Haka ta gama weekend din nata babu wani abu da ya gudana a tsakaninsu jawad yayi nacin yayi nacin amma taki bashi hadin kai dole sai hakura yayi ya kyaleta. Kayanta ta shirya domin komawa sch, su Sadiya sun koma tun safe ita kuma tace sai da yamma zata koma, kafin yammar babu yadda jawad bai yi ba akan taji tausayinsa amma taki fur da ya matsa mata ma sai tasa kuka, hakura yayi ya kyleta. Wanka tayi ta shirya cikin atamfa pink ta yafa mayafi pink ta dauki jakarta ta sameshi a mota, duk baya jin dadi baya son ta tafi saboda yasan zai yi missing dinta duk da ba wani zaman arziki suka yi ba, duk da haka sun dan shaku a yan kwanaki ukun da tayi agidan, itama a tata zuciyar tunanin yanda zata yi missing dinshi take duk da bata wani jiyar dashi farin ciki ba dan ko taba jikinta zai yi sai dai ya faki idonta ya tabata ko kuma yayi mata bazata ya matseta ba tare da ta sani ba amma duk da haka sai tayi masa masifa. Tunda ta shiga motar babu wanda yayi magana acikinsu shi dama sam bashida yawan magana sai kuma abin ya hadu da jimamin rabuwa da pherty, radio ya kunna minti kadan ya kashe ya kunna wata wakar larabawa mai dadi, babu wanda yayi maganar har suka shiga cikin makarantar, "Queen dan Allah karki rinka yawo da kananan kaya kamar yadda kike yi agida" ya fada yana kokarin kamo hannunta, "To ba mata bane yan uwana, ko da maza aciki?" Tafada tana zumburo baki "Duk da matane bana so kiyi yawo haka" "Naji" tafada tana basarwa aranta kuwa cewa take "yaushe zanyi yawo ahaka a hostel agidan ma saboda daga ni sai kai ne shiyasa" Hannunta ya murza "sai nazo hira" "Um" tafada ahankali, kiss yayiwa hannun nata ya saki, fita tayi ta nufi hostel shi kuma ya juya ya koma gida. Ummi A'isha🏻 [5/15, 8:39 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 69-70 ~~~ Hostel ta shiga amma tana ta jin tausayin jawad aranta na yanda ya rinka rokonta dazu amma tayi mirsisi tayi biris dashi har kuka ya kusa yi mata amma taki yarda, tana shiga dakinsu ta samu kawayen nata sunata shisshirya kayansu, kan gadonta kawai ta haye ko takalmin kafarta bata cireba, "Malama ya haka? Idan jawad dinne baki gaji dashi ba gara tun wuri ki dauki kayanki ki koma" Sadiya ta fada cikin tsokana, "Gaskiya kam dan na fahimci yanzu jawad ya zama rabin ranta" A'isha ta fada itama cikin zolaya "Sai kuyi kuma" ta basu amsa, nan suka ci gaba da tsokanarta tana mayar musu da amsa amma tunanin jawad yana nan makale acikin zuciyarta. Shima jawad hakan take dan ko gida bai koma ba gidan Ummi ya tafi can ya shantake sai bayan sallar magrib sannan ya koma gida nan dinma bai tsira ba saboda sai a lokacin yaji hankalinsa ya tashi da rashin pherty,wanka yaje yayi ya shirya cikin kananan kaya yasha turare masu kamshi ya nufi makarantar tasu, daf da zai shiga makarantar yaga sakonta ta rubuto masa text "kana ina yanzu?" Reply ya tura mata "ina wani wuri" "Ok kazo to" ta dawo masa da reply "Ki fito gani nan zuwa" ya mayar mata da amsa,tana daga kwance akan gadonta sanye da kayan bacci riga da wando, mikewa tayi taje ta dauki turarruka ta feffesa daga ita sai Sadiya a dakin domin A'isha ta tafi wani dakin hira, hannun Sadiya ta kama "Zo ki rakani" babu musu Sadiya ta dauki hijab dinta tabita, itama babban hijabi ta zira, lokacin da suka je inda yayi packing yana cikin motarsa yana waya, gaban motar ta bude ta shiga ita kuma sadiya ta shiga baya, mintuna kadan ya gama wayar, "Queen" yafada a hankali saboda har kamshinta ya fara rudashi, hannunta ya lalubo ya rike cikin nasa daga karshe ya janyo ta cinyarsa, wutar motar ya kunna ya fara kokarin cire hijab din jikinta domin yana son ya tabbatar da ko taji maganar da yayi mata dazu ko kuma bata jiba, "Baku gaisa da Sadiya ba" tafada tana rike hannunsa, shi sam bai ma san su biyu suka shigo ba, juyawa yayi suka gaisa da sadiya, suna gaisawa Sadiya ta fita tace tana jiranta a waje, hijabin nata ya daga kayan nata ba masu sharara bane sannan ba kanana bane dan rigar ma ba mai siririn hannu bace. Fuska ta bata ta hade rai "nifa bana son haka" "Oh dama saboda Sadiya tana nanne shiyasa baki yimin gardama ba ko" Baki ta zumbura ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata, cikinta ya shafa "kinci abinci kuwa?" "Naci" tafada a takaice, bakinta ya kaiwa kiss ya manna mata, "Bacci nake ji sai da safe" tafada tana kokarin tashi daga jikinsa, "To queen sai da safe kiyi mafarkina" bata bashi amsa ba ta bude motar ta fice, tun a hanya sadiya take tsokanarta har suka shiga daki suna zuwa sadiya ta fara bawa A'isha labari nan suka hadu sukai ta tsokanarta. Kullum sai jawad ya kirata awaya amma taki zuwa weekend yayi yayi da ita kan tazo gida amma taki zuwa bayan kuma itama tana cikin damuwar rashinsa, wannan week din dai ta shirya zuwa gida dan haka ana idar da sallar juma'a ta yiwa A'isha da sadiya sallama ta tafi gidanta. Lokacin da taje gidan jawad baya nan dan haka daki ta shige tayi kwanciyarta, bata wani dade sosai da zuwa ba sai gashi ya dawo, yana ganinta ya fara murna ya karasa kusa da ita ya zauna tana kwance daga ita sai bra da pant tana shan iska,hannunta ya riko, "Queenkin mayar dani gwauron karfi da yaji, kinga fa ko abinci sai naje gidan Ummi nake samu" Kallonsa tayi ta gefen ido,"to yanzu me kake son ayi kenan?" "Queen ki hakura da zaman hostel dinnan ki dawo gida pls, nayi miki alkawari zan rinka kaiki kullum" Zumbur ta tashi zaune,"nadawo gida fa kace, tab wlhi a'a indai kaga na bar hostel to wlhi gama karatuna nayi" ta karasa maganar tana zumbura baki, dafata yayi "Shikenan ya isa maganar ta wuce, kinyi girki?" "Nifa kaga hutawa nazo yi babu girkin da zan iya yi yanzu saboda gaba daya a gajiye nake" "Ok to me zaki ci?" "Zanci komai amma banda shinkafa" "To bari na aiki mai gadi ya siyo mana abincin, nima yunwa nake ji" bata bashi amsa ba har ya tashi ya fice. Amala da miyar dage dage ya kawo mata gefe kuma sakwara da miya sai fresh milk roba biyu, tashi tayi ta fito falo daga ita sai pant ta bra, kofar yaje ya kulle gudun kar wani ya shigo sannan ya dawo ya zauna yana tambayarta wanne zata ci amala ko sakwara, amalar ta dauka dan rabonta da amala har ta manta gara gara ma sakwarar lokacin da tana gidan dada tana yawan yi. "Bakida kunya yanzu ko queen? Ki rinka zama tsirara?" Ya fada yana kallonta "To meya shafeka?" Ta fada tana harararsa "Ya shafeni mana tunda property nane" "Nice property din?" Ta fada cikeda jin haushi, "Yes you are my property queen" Rabuwa tayi dashi bata sake magana ba har ta gama cin abincinta ta tashi ta koma daki. Koda lokacin bacci yayi ya shigo dakin hanashi kwanciya tayi nan ya shiga magiya amma fafur taki dolensa yabar dakin ya koma nasa ya kwanta. Da safe da fushi ya tashi akan fuskarta dan gaskiya yana shiga wani hali a yan kwanakin nan kawai daurewa yake gashi abun yana neman fin karfinsa, yana kwance acikin falo yana wasa da wayarsa sai ya kamo wani tune din mage,zuruf pherty ta fito da sauri daga cikin daki, "Jawad me nake ji a gidan nan kamar kukan mage?" Ta tambayeshi a tsorace "Eh mage ce amma ta fita ai na dade da kawota gidan nan, bata zama ne yawo take fita sai dare take dawowa" Idanuwanta mayalwata ta zaro "tab ai kuwa ka fitar da ita saboda ni bana shiri da kuliya tsoronta nake" kofar falon taje ta sadada ta leka amma bata hangota ba dan haka tayi gaggawar rufe kofar ta dawo ciki tana ta yi masa masifar danme zai kawo mata mage gidanta, wunin ranar tayi shine acikin daki ko falon kin fitowa tayi saboda tsoron mage, shidai yana jinta duk fadan da take amma bai cemata uffan ba. Bayan sallar isha ta shiga wanka, sadadowa jawad yayi yazo ya tura wayar karkashin gadonta ya fice, tana gama wankan ta fito ta shirya ta shafa humra da turarruka bayan ta shafa man ambar musk, wata light blue din rigar bacci ta saka wacce da ita da babu ba bambanci ta haye gadonta ta kashe wuta ta kwanta. Can ta dan fara bacci ta jiyo kukan mage a karkashin gadonta, ai da gudu ta sauko daga kan gadon ta nufi kofa ta fara lalube, ita kuwa mage sai kuka take miyau miyau, dakyar ta samo kofar jikinta sai rawa yake, dakin jawad ta nufa da gudu tana shiga taga dakin duhu dim bata yi tunanin kunna haske ba ta fara neman gadonshi acikin duhun, gadon ta hau jikinta sai rawa yake tana laluben jawad amma bata jishi ba, yau nashiga uku tafada acikin zuciyarta, can tsakiyar gado ta jiyo shi yana kwance ya rungume pillow, pillow din ta zare ta shige jikinsa ta kankameshi har lokacin jikinta rawa yake, "Queen menene?" Ya tambayeta yana sake rungumeta, "Jawad magen nan ta dawo,tana dakina, tana karkashin gadona" "Gobe zan fitar miki da ita tunda kinga yanzu dare yayi" kankameshi tayi saboda duk a tsorace take gani take magen na iya biyota nan dinma. Ahaka suka yi bacci tana kankame dashi har asuba tayi, ahankali ya zare jikinshi yaje dakinta ya dauko wayarsa daga karkashin gado yazo yayi alwala ya tasheta. Sam kin komawa dakinta tayi sai da gari yayi haske sosai tare suka je ya rakata a gabanta ya dudduba ko ina amma babu mage babu dalilinta, ce mata yayi har ta fice yawonta dan haka ta saki jikinta, haka ta zauna a dakin amma har lokacin a tsorace take, shima jawad din ta hanashi fita ko ina tace sai dai su zauna tare. Daren ranar dama ko tunanin kwanan dakinta bata yiba dakin jawad taje, yau kam yazo mata da sabon salo amma fur taki aminta, lallashin duniyar nan babu wanda bai yi mata ba amma taki, magana ya fara yi mata cikin rawar murya kamar wanda yake kuka "Haba Xarah wannan wanne irin rashin imani ne, meyasa wai bakya tausayi nane? Yanzu idan baki kwantar min da hankali ba ina kike so naje abani kwanciyar hankalin, ki tausaya min Xarah, wlhi ina cikin wani hali ko so kike na mutu?" Ya fada muryarsa tana rawa sosai, banza tayi masa bata bashi amsa ba, "Xarah, pherty, pherty" ya kira sunanta yana girgiza ta amma taki bude idonta, tana jinsa jikinshi har wani dan zafi yayi kamar me zazzabi, sakinta yayi ya juya mata baya ya kwanta, ta bayanshi ta rungumeshi saboda har yanzu tana tsoron mage hakan da tayi ya sake rikitashi, take ya fara hawaye amma bai bari taji ba, juyawa yayi ya kwanta ruf da ciki, hayewa bayansa tayi ta sake kwanciyarta, shikuma abin duniya yayi masa yawa gashi ya kasa bacci da haka har asuba tayi, tashi yayi yai alwala ya tasheta shi kuma ya fice daga cikin dakin. Tunda gari ya waye ta fara harhada shirginta saboda yau zata koma sch gobe tana da test sassafe, jawad kuwa ko magana baya yi yayi shiru yana kwance akan kujera, kitchen ta shiga ta dafa farar shinkafa ta hada salad ta yi yar sos ta fito, zama tayi taci ta koshi ta bar masa nashi a flask, tana gamawa taje tayi wanka ta shirya ta dauko dan kit dinta ta fito lokacin karfe 3 daidai, a inda ta barshi anan ta sameshi, "Nafito" tafada tana kallonshi duk ya bata tausayi saboda bashida maraba da marar lfy, jikinshi duk ya saki idonsa ya dan yi ja, bai ce da ita komai ba ya tashi ya dauko key din motarsa ya fice tana biye dashi a baya. Sai da suka hau titi sannan ya kalleta tasha atamfarta yellow da farin mayafi "Ke bakida tausayi ko? Kin kwammata na mutu akan ki bani abinda nake so ko? Saboda bakya kaunata, nagode" Kallonsa tayi duk tausayinsa ya cikata amma ba tace komai ba, shi dinma bai kara magana ba har suka je makarantar ya ajiyeta ya juya ya tafi, sukuku ta shiga hostel duk zuciyarta babu dadi. Tunda ta koma bata da wani farin ciki ko karatun test dinma ba tayiba haka ta rubutata, tunanin halin da jawad kawai yake ciki take yi, wayarta ta dauka ta tafi gaban dakinsu ta zauna ta fara neman layin hawy, ringing biyu ana ukun ta dauka, "Ta mama ya kike?" Fuskarta ta dan yamutsa "Ba kalau ba, hawy jawad yana cikin wani hali amma duk laifina ne, jiya babu rokon da bai yi min ba amma nayi kememe na hanashi kaina" Masifa hawy ta fara yi mata "ai bakida wayo, tun yaushe kukayi auren? Yaufa wurin 2 months da bakinku haba phertyn mama shifa namiji ne mai jini ajika taya ba zai bukaci mace ba, gaskiya banji dadiba, yanzu bakya tsoron ya samu wata lalurar ta dalilin wannan ko kuma bakya tsoron yaje ya nemi matan banza a waje? Gaskiya nidai kin bani mamaki, kin bani kunya, koda zaki rama abunda yayi miki a baya ai bai kamata ki rama ta hanyar hanashi kanki ba kuma ma har ya fito fili ya nuna miki yana bukatarki amma kika hanashi" Wasu hawaye ne suka sauko akan kumatun pherty "hawy bazan sake ba in Allah ya yarda, wlhi bazan sake ba wannan dinma kuskure ne" "Yawwa phertyn mama dan Allah kar ki sake yiwa jawad rowar kanki kinga ba dan kin hanashi ba da tuni kila kinada juna biyu yanzun" Murmushi tayi, "yaushe zaki zo min?" "Sai komai ya daidaita zaki ganni" Daga nan sallama suka yi ta tashi ta shiga daki ta kwanta tafara tunanin jawad. Tun daga nan bata sake jin jawad ba amma ta daura niyar zuwa koda shi bai zo ba. A ranar da daddare sai gashi yayi mata text wai tazo yana jiranta gashi ya shigo sch dinsu, hijabinta kawai ta dauka ta dauki phone dinta tacewa su Sadiya zata je wurin jawad, nan A'isha ta shiga tsokanarta wai yau bata neman yar rakiya, murmushi kawai tayi ta fita. Acikin motarsa ta sameshi ya kifa kansa jikin sitayarin motar, zama tayi jikinta a sanyaye, takai minti biyu da zama amma bai dago kansa ba, "Jawad baka da lafiya ne?" Sai a lokacin ya dago kansa idonsa a lumshe, "Xarah koma baya gida zamuje, dan Allah Kar ki k'i zuwa, wallahi banida lafiya, ko driving dinma dakyar na iya yi nakawo kaina nan" Kujerar baya ta koma ta zauna shikuma ya koma dayan sit din ya zauna ya zaro wayarsa dakyar ya kira driver din dad yace yazo ya sameshi anan ya mai dashi gida saboda shi bazai iya mayar da kanshi gida ba, hannunsa ya mika baya ya kamo nata, "Queen banida lafiya sosai, banida lafiya" ita dai bata iya cewa komai ba, mammatsa hannunta yaci gaba dayi jikinshi duk yayi kuna ya danyi zafi, da haka driver yazo ya samesu ya daukesu amma shi driver din bai ma san su biyu bane saboda bai ga phertyn ba, sai da ya kaisu gida yayi packing ya tafi sannan suka fito suka shiga ciki suna zuwa falo jawad ya yanke jiki ya fadi sharaffff!. Ummi A'isha🏻 [5/19, 5:23 PM] Ummi A'isha🏻: [5/19, 3:38 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 71-72 ~~~ Da sauri pherty ta k'arasa inda yake ta tsugunna a gabanshi tareda fara jijjigashi, "Jawad, jawad" tafada bakinta yana rawa, idonshi ya dan bude kadan wanda suka yi jajur, dakyar ya iya bude bakinsa yayi mata magana, "Xarah bani ruwa nasha pls" ya fada yana sake lumshe idonsa, da sauri ta tashi taje ta dauko masa ruwan ta kawo masa, adaidai kanshi ta zauna ta dauki kansa ta dora akan cinyarta a hankali, robar ruwan ta saka masa akan bakinshi, "Jawad karbi ruwan kasha kaji" Ahankali ya bude bakinsa ta bashi ruwan yasha, bayan yasha da kamar minti uku ya fara yi mata magana a hankali, "Queen ciro min phone dina a aljihuna ki kira min doctor" Bata jira ya karasa ba ta fara laluben aljihunsa, wayar ta ciro ta fara kiran doctor Ansar kamar yadda taga ya rubuta ajiki. Mintuna kadan dr din yazo, hannunta yana makale cikin nashi jikinshi kuwa kamar wuta don kuna, yayi zafi rum, agabansu dr din ya tsugunna lokacin da ya shigo ya fara tattaba jikin jawad tareda tambayarsa abinda ke damunsa amma ita bata san me suke fada ba saboda da fulatanci suke magana ita kuma ba wani ji take yi sosai ba. Mintuna kadan dr din ya jiyo yana kallonta, "ke ba wife dinshi bace?" Ya tambayeta "Itace" ta bashi amsa a tsorace, "Amma kika barshi ya shiga cikin wannan halin?" Kwalla ce ta ciko idonta batare da tayi magana ba, "Mijinki bashida lafiya sosai, gashinan ma yanzu may be sai na kara masa ruwa amma tunda fever ya rufeshi yanzu allura zanyi masa sai natafi, tomorrow in the morning i will be back in yaso sai naga yanda jikin nashi yayi" Kwallar idonta ce ta gangaro kan kumatunta, dr dinne ya daga jawad ya nufi cikin bedroom dinta dashi, tashi tayi tabi bayansu, a kan gadonta ya kwantar dashi yazo ya dauki first aid box dinshi ya koma dakin lokacin tana tsaye a gaban gadon sai hawaye take, juya jawad Dr din yayi tareda zaro sirinji zaiyi masa allura, idanuwanta ta kulle har sai da ya gama sannan ta bude, juyashi ya sake yi ya rufe first aid box dinshi ya yi mata sallama ya tafi. Yana fita ta karasa kan gadon ta hau jikinshi ta taba taji har yanzu da akwai zafi rau, kallonsa tayi cikeda tausayawa sai kuma ta fara kuka "Dan Allah jawad kar ka mutu, karka mutu ka barni, yanzu idan ka mutu me zan cewa su Ummi? Me zan fadawa yaya aadil idan har nayi sanadiyyar mutuwar dan uwansa?" Haka tayi ta fada acikin zuciyarta,tun tana kukan zuci har ta fara na fili, a hankali jawad ya bude idonsa, hannunsa ya mika ya jawota ya kwantar da ita a gefen jikinshi, kukan ta daina tayi shiru tana ajiyar zuciya, zuwa can taji yayi bacci, agogo ta kalla karfe 1 daidai,a hankali ta tashi taje ta rufo kofar falo ta dawo ta rufe ta dakin ta koma kan gadon ta zauna tareda tsurawa jawad ido. Tana nan zaune yanda taga rana haka taga dare har asuba tayi, bayan ta idar da salla taga ya fara motsawa a hankali, da sauri ta tashi taje inda yake, "Sannu jawad'muje kayi alwala" dakyar ya mike jiri yana daukarsa luuuuuuh, saurin rikeshi tayi ta rakashi toilet yayi alwala ya fito, daga zaune yayi sallahr yana idarwa ta taimaka masa ya koma ya kwanta akan gadon, minti kadan ya sake komawa bacci,kusa dashi taje ta kwanta tareda rungumeshi ajikinta,bacci ne itama yayi awon gaba da ita. Wurin karfe 8 na safe ta farka, jikin jawad ta taba yanzu babu zafin da alama zazzabin ya sauka daga jikinsa, tashi tayi taje ta shiga kitchen ta hada musu breakfast ta kawo ta ajiye akan dan karamin stool din dake ajiye agaban gadon,toilet ta shiga tayi wanka ta fito daure da towel ajikinta ta zauna tayi simple make up ta tashi tasa wata farar riga yar kanti mai siririn hannu da wandonta jeans fari iya gwiwarta,jawad ta kalla wanda har yanzu yake kwance yana ta sharar bacci amma fuskarsa ta dan rame kadan, tausayinsa taji yana shigarsa, bugun da taji ana yiwa kofar falon ne ya sata daukar katon hijabi ta fita, dr ansar ta gani lokacin data bude kofar, tare da dr din suka shiga dakin har inda jawad yake kwance, "Har yanzu bai tashi ba?" Dr din ya tambayeta "A'a yatashi yayi salla da asubha" ta fada cikin rawar murya Jikinsa yaje ya fara bincikawa yana tabawa, magunguna ya fito dasu ya mika mata, "Gashi idan ya tashi yasha wadannan magungunan bayan yayi breakfast, amma karki tasheshi har sai ya tashi da kansa, idan da wani problem sai yayi calling dina" dr ya fada daidai lokacin da yake kokarin barin dakin, "Ok dr mun gode" ta fada ahankali, yana fita taje ta zauna a gefen gadon ta kamo hannun jawad ta rike cikin nata. Ta dade azaune tana wasa da hannunshi tana kissing dinshi ganin bai tashi ba ya sata komawa falo sai a lokacin ta tuna da wayarta, wayar ta dauka taga missed called bila adadin nasu Sadiya, Aisha da hawy, su Sadiya ta fara kira tana dauka ta fara yi mata tsiya "Kaga phertyn jawad mai komai dozin, shine tafiya babu sallama?" Myrmushin karfin hali tayi tace "wlhi Sadiya jawad ma kin ganshi can kwance bashida lafiya, shiyasa jiyan ban dawo ba" Ayya to Allah ya bashi lfy, idan ya tashi ki gaisheshi" "Zai ji, ina A'isha?" "A'isha taje lecture amma idan tadawo zan fada mata" "To shikenan ki gaisheta" kashe wayar tayi ta fara neman layin hawy, "Ta mama ina kika shigane najiki shiru" "Hmm kibari kawai yanmatan mama jawad ne bashida lfy tun daren jiya" "Kai, meya sameshi? Hala dai kece sanadi ko?" Hawy ta jero mata wadannan tamvayoyin lokaci daya, "Um haka dr yace wai laifinane" tafada kamar zata yi kuka, "Hmm shima jawad ya bani haushi ai, wlhi da ace nice shi da tuni nadade da tara miki gajiya,amma shi ya wani tsaya lallaminki kamar wadda yake tsoronki" "To muguwa sai kuma Allah yayi ba ke din bace balle kiyi mugunta" "Ai wlhi bari ya warke sai kin dandana kudarki" "Malama sai anjima, lokacin da kika gyara kalmominki za muyi waya amma yanzu ki barni da abinda ke damuna" tana gama fadin haka ta kashe wayar ta tashi ta nufi dakinta. Lokacin da ta shiga dakin daidai lokacin jawad ya bude idonsa, zaune ya tashi fuskarsa a murtuke babu fara'a, kokarin saukowa daga kan gadon ya fara, da sauri pherty taje kusa da shi da niyyar rikeshi saboda tana tsoron kar ya sake faduwa irinta jiya, dakatar da ita yayi da hannunsa, cikin sauri ta kalleshi, "Jawad menene?" Ta tambayeshi a jagule "Babu komai, karki tabani, ai nagane bakya sona bakya kaunata tun tuni, idanma na mutu ke bakida damuwa, da raina kina neman sai kin halakani,saboda kin san koda na mutu ke bakida asara" Manyan idanuwanta ta sauke akan fuskarsa, "Haba jawad ya zaka rinka furta irin wadannan maganganun? " Bai sake magana ba yayi gaba ya nufi kofar fita, dakinsa ya shiga bata yi kasa a gwiwa ba ta juya ta bishi, lokacin data shiga yana kokarin cire rigar jikinsa, toilet ta shiga ta hada masa ruwan wanka ta fito, baiyi mata magana ba ya shiga toilet din, Ajiyar zuciya tayi tace "wata sabuwa,kaima ramawa zaka yi kenan" dakinta ta koma ta kinkimo kayan breakfast din data hada ta kawo dakinsa lokacin har ya fito daga wankan yana daure da towel, kayan ta ajiye ta koma ta dauko magungunansa ta kawo ta ajiye, tana zaune tana kallonsa ya tsane jikinsa da dan karamin towel ya fesa turare ya dauki kananan kaya yasa, short nicker da t shirt baka, "Ga breakfast din, dr yace kar kasha magani sai kayi breakfast" tafada kamar wata marar gaskiya, "Ba wani magani da zan sha, amfanin me maganin zaiyi min? Dan bansha maganin ba ai ba mutuwa zanyi ba, kuma kema ki rike abunda kike takama dashi idan kin hanani hakan ba zai zama sanadiyyar karewar rayuwata ba" ya fada yana gyara belt din wandonshi, Kallonsa ta tsaya yi tana tunanin amsar da zata bashi saboda kalamasa sunyi mata zafi sosai ba kadan ba, "Dama dan na hanaka kaina ai ba zaka mutu ba sai dai kawai kayi rashin lafiya tunda na fuskanci wannan din shine mahadin rayuwarka,kuma ai mutuwar ma zaka iya yi idan baka samu ba" Kallonta yayi ya dauki cumb ya fara gyara sumar kansa, "Kin San dai duk abinda yake agidan sarki akwai shi a kasuwa ko?" "Ehh da akwai amma na kasuwa ai jagwalgwalo ne" tafada tana hararsa, "Jagwalgwalo? Meye jagwalgwalon?" Ya tambayeta yana kallonta, "Oho maka, kabari ka iya hausa tukunna kafin ka gayawa mutane magana" tana kaiwa nan ta juya ta fice daga dakin ta koma falo ta zauna. Tea ya hada yasha ya dauki magungunan ya tura cikin drawer gadonsa yana tsaki domin shi a duniya idan da abunda ya tsana to maganine, sam baya kaunar magani, falon shima ya fita ya sameta tana kwance a doguwar kujera ta cire rigar jikinta daga ita sai bra da dan short trouser dinta iya gwiwa,kujerar nesa da ita yaje ya zauna yana satar kallon cikinta, ita kam kanta ta dauke daga kallonsa daga karshe ma ta juya masa baya ta mayar da kanta daya barin. Ummi A'isha🏻 [5/21, 9:30 AM] Ummi A'isha🏻: 👑👑👑MARTABA TA👑👑👑 Na UMMI A'ISHA 73-75 ~~~ Zaman kurame suka ci gaba dayi kowa yana ta faman fushi, tashi pherty tayi taje kitchen ta hado tea empty ta dawo ta zauna ta fara juya tea din da spoon, juyowa jawad yayi ya kalleta sai kuma ya dauke kansa yayi tsaki, hararsa tayi ta fara shan tea din aranta tana cewa "kayi tsakinka ka gama ehe" Tana gama shanyewa ta tashi ta koma kitchen ta ajiye cup din ta dawo, cikinsa taga ya rike yana kokarin saukowa daga kan kujerar da yake zaune, cikin sauri ta tashi taje wajensa, "Jawad menene? Baka sha maganin ba ne?" Ta tambayeshi a rude, bai iya bata amsa ba saboda aman da ya fara yunkurin yi, cikin sauri ta rungume shi a kirjinta nan ya fara sheka amai tea din da yasha duk sai da ya amayar dashi ajikinta gashi ko riga babu daga ita sai bra, dandanan zazzabi ya sake rufeshi, rungumeshi ta sake yi "Sannu" tafada cikeda tausayawa, akan carpet ta kwantarshi ta tashi taje ta dauko karamin towel ta dawo ta fara goge masa aman jikinsa, rigar ta cire masa ta goggoge masa wuyansa sannan ta fara kokarin gyara nata jikin, bra din ta balle ta cire ta goge jikinta, bude idonsa yayi a hankali ya kalleta, suna hada ido taji kunya ta kamata saboda yanda ya kurawa kirjinta ido da sauri ta mike ta nufi dakinta ta sako riga ta ta debo ruwa acikin dan karamin kwano ta dauko wani towel din ta dawo inda jawad yake, towel din ta tsoma acikin ruwa ta fara goge masa jikinsa a hankali, fatarsa luwai luwai ga gashi kwance tako ina ajikinsa, daidai kasan cibiyarsa taga wani digon baki mai kyau nan ta tsaya kallo ganin idonsa a lumshe yasata kai bakinta wurin, harshenta tasa ta fara lasar digon bakin, shi dai jawad yana kwance yana jinta amma jikinsa sai kace wuta dan zafi. Hannunta ya kamo "Xarah kashe fankar nan har ac din sanyi nake ji" Da sauri ta tashi taje ta karkashe ta dawo wurinsa, "shine kika rufe min bayan ban gama gani ba" ya fada idonshi a lumshe, hannunsa ta matsa, "Nakira dr ansar yazo ya dubaka?" Kai ya daga mata alamun ehh, cikin sauri ta tashi taje dakinsa ta dauko wayarsa ta fara kiran dr din amma wayar tasa a kashe, "Wayarsa akashe dan Allah ka daure kasha maganin" Kamar wani karamin yaro ya yamutse fuska "bana son magani wlhi" Kusa dashi tazo ta zauna ta kamo hannunsa ta rike, "kayi hakuri kasha kaga ai baka da lfy sosai" Idanuwansa ya lumshe,sumar kansa ta shafa "na dauko maka kasha?" Kai ya daga mata, tashi tayi taje ta dauko maganin ta kawo masa, "To tashi kasha" "Ki dauko min cock" kallonsa tayi"da cock zaka sha?" "Uhm" yafada lokacin da yake kokarin tashi, cock din ta dauko masa ta ciro magungunan ta bashi ya karba yasha, yana gama shanyewa ya koma kan doguwar kujera ya mike sai bacci. Ajiyar zuciya tayi ta kalleshi, "jawad case ace shan magani sai da dabara?" Kujerar da yake kwance ta karasa ta tsugunna agabansa gamida hada fuskarta da tashi, ta dade tana jujjuya fuskarta akan tasa sannan ta tashi taje kitchen ta dora musu abinci, jalop din zallar wake da kifi ta dafa. Lokacin da ta fito ya farka, da sauri ta karasa gabansa "sannu" Hannunta ya kamo ya tashi zaune "hada min ruwa nayi wanka zafi nakeji" "To zo muje" hannunta ya rike yabita har cikin dakinsa ta shiga toilet ta hada masa ruwan ta fito, "Kashiga kayi wankan" Kai ya langabar "muje kiyi min" ido ta zaro "Yi hakuri kayi kaji" shigewa cikin toilet din ya yi batare da yace komai ba. Falo ta koma ta je ta shirya masa abinci ta zauna tana jiran fitowarsa, daga shi sai farin gajeren wando da farar t shirt mahadin wandon ya fito, "Sannu na kawo maka abincin ko?" Zama yayi yana kallonta "Kunna min ac,kadan zaki zubo min" tashi tayi taje ta kunna ta zubo masa faten waken a filet ta kawo masa, janta jikinsa yayi "kibani a baki queen" Batayi musu ba ta fara bashi,hannunta ya kama "nakoshi bani ruwa nasha" "Ayya jawad dan kara kadan kaji, dan kara pls" cigaba da bashi tayi har sai da ya cinye tas, tsakiyar falon ya koma ya kwanta akan carpet, "Queen zo kiji" ya fada yana mika mata hannu,bata yi musu ba ta tashi ta koma kusa dashi ta zauna, janta yayi jikinsa ya kwantar da ita ya fara lalubarta, bata yi masa gardama ba balle tayi kokarin hanashi yau dai ta tayi abun kai wacce rana ya tabata bata yi masa masifa ba. Yar guntuwar rigarta ya zame, ya kankameta ya fara wasanni ajikinta, idanuwanta kawai ta lumshe tana jin yanda yake bidirinsa a jikinta son ranshi, hannunsa ta rike, "Kamanta abinda ka fada dazu? Dazun nan ka gama cewa na rike abinda nake takama dashi" Dan murmushi yayi wanda ya kawata fuskarsa "ai kawai fada nayi amma ba har zuciyata ba, tayaya zan iya fushi da ke?" Bakinta ya tsotsa ya ja hancinta, "ni yanzu ma babu abinda zan iya yi saboda jikina ba lafiya" sai a lokacin taji hankalinta ya dan kwanta,jagulata ya fara yi ta kowanne bangare yana wasa da kirjinta wanda shine yafi komai daukar hankalinsa. Sun jima acikin wannan yanayi kafin ya iya hakura ya kyaleta yana maida numfashi a hankali, rungumeta yayi tsam ajikinsa ya fara sinsina gashin kanta, tana kwance akan kirjinsa a haka bacci ya dauketa, amma shi bai yi baccinba sai ma cigaba da yayi da mammatsa jikinta har lokacin salla yayi. Zameta yayi ya tashi ya shiga dakinsa dama jira take ya tashi dan haka yana tashi itama tayi gaggawar shigewa dakinta tasa key, toilet ta shiga tayi wanka ta fito tayi salla bayan ta idar ne ta fara kokarin shiryawa, kwalliya ta tsara a fuskarta jikinta kuma ya dauki daddadan kamshi mai tausasa zuciya, wata pink din riga tasa mai zanen lips ajiki, an rubuta KISS ME da manyan harrufa, rigar roba ce sannan bata da nauyi yar shafal take yar karama da ita, bakin wando jeans tasaka iya gwiwarta ta gyara gashin kanta ta daureshi da ribom pink colour. A hankali ta bude kofar dakin nata ta dan leka, jawad ta gani kwance akan kujera yana waya, fitowa tayi ta shige kitchen daga tsaye ta tsaya ta zuba faten waken dan kadan taci ta dauki juice ta fita, "Zo kiji pherty na" ya fada yana yi mata murmushi,kusa da kujerar da yake taje ta zauna, "Yaya aadil sun dawo dazu, yaushe za muje muyi musu sannu da zuwa?" Dan murmushi tayi ta kurbi lemon dake hannunta, "Sai ka samu saukin jikinka sai muje" Gaban rigarta ya kalla, a hankali ya tashi ya matsa kusa da ita, "Ya akayi?" Tafada tana kallonsa, "Umarni zan cika na abinda kika nema, gashi nan rubuce jikin rigarki" ya fada yana nuna mata da dan yatsansa, ja da baya tayi "Nidai gaskiya ba zaka bata min kwalliyata ba, tashi tayi zata gudu yayi saurin riketa ya jawota, kokawa suka fara,akan kujerar ya shimfidar da ita ya matseta, "Gaskiya jawad nidai ka bari kar ka bata min kwalliya ta" ta fada a shagwabance, "Idan na bata miki zan sake miki wata kinji my queen" "A'a nidai ban yarda ba gaskiya" bai barta ta karasa ba ya hade bakinsa da nata, lips dinta na sama ya kama, "In ciza?" Ya rada mata a kunnenta, "Ka ciza mana nima in rama" ta fada tana lumshe idonta,dan cizar lip dinta yayi, nan suka fara kokawa ita a dole sai ta rama, kanshi ya cusa a wuyanta, gefen kunnenshi ta samu ta ciza, "Ahh sai na rama ai ba haka nayi miki ba" "Kaima da zafi kayi min" a tsakiyar kirjinta ya sake cizonta, yana dagowa ta rike lip dinsa na kasa da hakoranta, kwankwasa kofar da aka fara yine ya katse musu wasannin da suke yi cikin nishadi,dagata yayi yaje ya bude kofar, Sadiya da A'isha ne suka shigo, tana nan kwance inda ya barta ganinsu ya sata daka tsalle taje ta rungumesu, "Nayi missing dinku yan dakinmu, sannunku da zuwa" akan kujera suka zauna ta shige tsakiyarsu, "Sai yanzu zaku zo maimakon kuzo tun safe mu wuni" "We are sorry amarya" suka fada atare suna dariya, "Yaya jawad ina wuni? Ya jiki?" Suka fada suna kallon jawad "Lfy lau jiki yayi sauki" ya fada cikin hausarsa ta yan koyo, "Kun ganshi nan har yau ya kasa iya hausa, ya iya kowanne yare hausa ne bai iyaba dan rashin kara" pherty ta fada daidai lokacin da ta tashi ta nufi kitchen, "To ai kece baki koya min ba" ya fada tareda tashi yabi bayanta, a kitchen ya tarar da ita tana yanyanka lemo dasu abarba da sauran fruit akan filet, ta bayanta ya turata ya matseta ajikin lokokin dake jere cikin kitchen din, "Wash jawad marata, dan Allah kabari" Matsawa yayi,"kawayenki sunzo shiyasa zaki kyaleni ko? Wannan ranar ta yau ranace mai mutukar muhimmanci agareni, ranar da pherty ta barni ta sakar min fuska, ta kyaleni nayi wasa da ita" Murmushi tayi ta dauki katon farantin data zuzzuba kayan zata fita, jawo rigarta yayi "bakiyi comment ba, let me go and write this moment in my diary" Sakinta yayi ta fita yabi bayanta ya wuce dakinsa, Sadiya da A'isha suka hada ido suka kwashe da dariya, "A'a bangane bafa, ya zaku tasani gaba kuna dariya? Yanzu zanyi muku rashin mutunci" "Mu bake muke yiwa dariya ba" A'isha ta fada tana wata dariyar, "Ai dama har angane yan dakinmu shiyasa mutane bazasa son zuwa saboda duk wanda yazo sai kunyi masa dariya keda Sadiya" "Yoh mutum da bakinsa, ai dole muyi dariya" inji Sadiya "Sai kuyi tayi ai" inji pherty Kayan da ta hado musu ta gabar musu nan suka shiga hira suna motsa baki sai daf da mangaruba sannan suka tafi. Dakin jawad ta shiga yana kwance akan gadonshi, a gefenshi ta kwanta, "jawad kayi salla?" Kai ya daga mata, "to me zaka ci?" "Fura da nono zansha" Tashi tayi taje ta damo masa a kofi ta kawo masa, ta koma dakinta ta shiga wanka ta fito tasa sleeping dress kamar tayi kwanciyarta a dakinta sai kuma ta tuna da batun magen rannan, zuruf ta tashi ta nufi dakin jawad, tana shiga taganshi ya fito daga wanka, kan gadon taje ta haye taja blanket ta rufe jikinta ta rufe idanuwanta. Ummi A'isha🏻 [5/22, 8:28 AM] Ummi A'isha🏻: [5/21, 9:06 PM] Ummi A'isha🏻: 👑👑MARTABA TA👑👑 Na UMMI A'ISHA 76-78 ~~~ Kwanciya tayi ta juya bayanta tana jiran hawowarsa gadon, sai da ya feshe jikinsa da turarruka masu dadin kamshi sannan yasa kayan baccinsa ya kashe wuta ya hau kan gadon, jikinsa ya matso da ita ya rungumeta yana shafa gashin kanta nan da nan bacci ya dauketa, shi dai sai da ya kwashe lokaci mai tsawo kafin yayi baccin. Koda safiya tayi makara suka yi basu tashi ba sai wurin 6 harda yan mintuna, pherty ce tafara bude idonta ta kalli jawad wanda ke kanannade da ita kamar za a kwace masa ita, bakinshi akan tsakiyar gashin kanta ya makalkaleta sosai, murmushi tayi, tayi kissing din kirjinsa sannan ta fara kokarin tashinsa, bayansa ta shafo ta kirashi a hankali, "Jawad, jawad tashi" Ahankali ya bude idonsa ya sauke su akan kyakkyawar fuskarta wadda kamar ba daga bacci ta tashi ba, murmushi ya sakar mata ta mayar masa da martani, tashi yayi ba tare da yayi magana ba, ya shiga toilet kafin ya fito har ta gudu dakinta, bayan ta idar da salla ta sake kwanciya har sai wurin 9 sannan ta tashi tayi wanka taci gayunta cikin bakar t shirt da jan wando, kitchen ta shiga lokacin har masu aiki sun gama kimtsa ko ina, dankali ta dauka ta fara ferewa tareda kunna karatun alqur'ani kira'ar sudais acikin wayarta tana aikinta tana bin karatun, shigowar jawad cikin kitchen dinne ya sata kashe karatun ta jiyo ta kalleshi da alama ya warke domin yayi kyau sosai ya sha riga ja da blue din wando sai kamshin turare mai dadi yake gashi ya gyara sajensa da sumarsa sun kara fito da kyawunsa. "Morning my queen, Xarah, my wife, my luvly one and only" ya fada yana murmushi, "Morning" ta fada ta cigaba da aikinta,gas ta kunna ta dora mai ta zuba dankalin, lekawa jawad yaje yayi tsall mai ya fantsalo masa a hannu cikin sauri ya matsa yana yarfe hannunsa, matsowa tayi kusa dashi "mu gani, ka kone?" "Na kone mana, queen kalli kigani" hannun nashi ta kamo tana dubawa shi kuma yana duban rigarta wadda ta dameta kamar zata yage, kirjinta ya shafa da sauri ta matsa, "Koma falo ka jirani" "Queen tayaki fa zanyi kike korata" "Nidai nace ka koma falo" juyawa yayi ya fita ya koma falon ya zauna yana jiranta, murmushi tayi taci gaba da aikinta har ta kammala ta harhado ta kawo falo ta shiryasu akan table. Bayan sun kammala break dinne yace ta shirya su tafi gidan yaya aadil, tashi tayi taje ta shiryo cikin wani leshi maroon ta yafo bakin mayafi da bakin takalmi ta dauki bakar jaka, tana tunanin ta yadda zata iya hada ido da yaya aadil yau,Allah sarki gashi duk kayan da take sawa kayan lefen da ya hada mata ne ashe da rabon ba shine zai ga kwalliyar ba. A mota ta samu jawad suka tafi, yana ta yi mata hira a hanya har suka isa gidan aadil kamar wata marar gaskiya haka ta zama, jawad yana gaba tana biye dashi a baya, a babban falo suka tarar dasu Salima na zaune kusa dashi suna karanta magazine,yayi kyau yayi kiba abinsa gashi ya sake haske, caraf suka hada ido lokacin da ya dago domin amsa sallamar su, saurin sunkuyar da kanta tayi har suka karasa cikin falon kanta yana kasa, a kasan kujera ta zauna shikuma jawad ya hau kujera ya zauna,sannu da zuwa anty Salima ta fara yi musu wacce kallo daya zaka yi mata ka fahimci tana dauke da juna biyu domin alamu duk sun gama bayyana, a kunyace ta gaishe su amma bata bari sun hada ido da yaya aadil ba, sam ta kasa sakewa wata irin kunya taji tana ji. Basu fi minti 20 ba jawad yace ta tashi su tafi dan ya fahimci ta kasa sakewa nan suka yi musu sallama suka tafi gidan Ummi, nanma taga karamci domin ummi ta karbeta hannu bibbiyu anan ne suka dade dan har jawad ficewa yayi ya barta sai la'asar lis sannan ya dawo ya dauketa suka koma gida. Suna shiga falo ta fada jikin jawad, "Nagaji yimin tausa, amma bari na cire kayan nan nasha iska" riga da skirt din ta cire ta zauna daga ita sai underwear da bra, jikinta ya fara mammatsa mata tana lumshe idanu can taji ya canja salo dan haka tayi saurin rike hannunsa, "Pls queen" ya fada idonsa a lumshe, zuruf ta tashi ta kwasa a guje tayi dakinta binta yayi tana kokarin rufo kofar ya hanata ya shiga, bathroom ta sake kwasa zata shige yayi saurin damkota ya dorata kan bed anan aka fara dambatawa har dai ta fahimci yau jawad da gaske yake dan haka ta kyaleshi ya shiga nuna mata zallar soyayya amma kuma acan kasan ranta tunani take ko zata iya bashi abinda yake so? Tunanin ta ne ya tsaya daidai lokacin da taji mararta ta yi wani irin murdawa, nan ta fara jin ciwo kamar zata mutu, kankame jawad tayi ta rirrikeshi tana numfarfashi, "Wayyo zan mutu, wayyo Allah, jawad marata, wayyo marata" haka ta yi ta fada a gigice, Da sauri ya katse abinda yake yi ya tallafota ya rungumeta "Xarah menene?" Ya fada a rude, "Marata jawad" ta fada tana cije lebenta, wata kara tasa sakamakon wani irin azababben ciwo da taji sai kuma ta fara bleeding jini guda guda ya fara fita daga jikinta, cikin tsoro gamida rudu jawad ya sake rungumeta, "Pherty wannan jinin fa? Jinin meye wannan?" Bata iya bashi amsa ba sai hawaye data fara zubarwa, nan jawad ya sake rudewa yama rasa me zaiyi saboda har yanzu jinin ne yake fita bai daina ba, kwantarta yayi ya saka kayansa, yaje falo ya dauki wayarsa ya kira dr ansar, da sauri ya dawo wurinta ya dauko kayanta ya fara saka mata, ita kuwa pherty in banda kuka babu abinda take amma ba kukan ciwo take ba kukan kaddarar da take tare da ita take saboda tasan dole jawad ya sake aure nan gaba tunda ita ba zata iya biya mishi bukatarsa ba,yama za ace zai iya zama da ita a haka? Sai dai kawai ya kalleta amma babu wani abu da zai samu daga gareta. Nan hankalin jawad ya sake tashi kololuwa, mintuna kadan sai ga dr ya iso nan jawad ya shiga yi masa bayanin abinda ya faru, "To shi wannan jinin na mensuration ne ko me?" Dr ansar ya fada cikeda al'ajabi, "No ba period bane dama ta taba samun problem ne ta bugu a mararta" jawad ya fada kamar me shirin yin kuka, nan dr ya fara kokarin bata taimakon gaggawa, bayan ya rurrubuta mata magunguna ya bawa jawad shawarar lallai suje asibiti suga likitan mata domin shi ba likitan mata bane, ita dai pherty tana kwance tana jinsu. Bayan dr ya tafi ne jawad ya tashi da niyyar zuwa ya siyo mata magungunan, hannunsa ta riko, "Ina zakaje? Ka zauna kar katafi" kai ya gyada mata, "To bari na bawa mai gadi ya siyo miki maganin" hannunsa ta saki yaje ya dawo ya kwanta akusa da ita ya rungumeta shi kansa tunani yake wannan wacce irin kaddara ce? Ga mace har mace amma ace ba zata iya rayuwar aure ba, hakika wannan wata jarrabawa ce acikin rayuwar aurensu shida pherty. Jin ana kwankwasa kofar falon ya sashi sakinta yaje ya bude maigadin ne ya kawo maganin da aka aike shi ya siyo, karbowa yayi ya dawo ciki ya dauko mata ruwa ya tayar da ita zaune ya bata tasha maganin ya sake kwantar da ita, gumi ta fara hadawa duk da sanyin ac din dake ratsa dakin, babu shiri ya cire mata kayan dake jikinta ya barta haka, babu bata lokaci ta fara aikin bacci. Ummi Shatu🏻 [5/23, 7:57 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 79-80 ~~~Ta jima tana baccin wahala kafin ta iya bude idonta lokacin har gefen marar tata ya kumbura kadan, juyi tayi ta kalli jawad wanda ke kwance a gefenta fuskarsa cikeda tausayinta gami da alhinin halin da suka tsinci kansu. "Sannu queen, ya jikin naki" ya tambayeta cikin rada "Da sauki, hada min ruwan zafi zanyi wanka" ta fada tana kwalla, girgiza mata kai yayi, "Don't cry my queen,karki sawa kanki damuwa pls insha Allahu zaki samu lafiya" Hawayen fuskarta ta goge ta fara kokarin tashi zaune, jawad dinne ya taimaka mata ta zauna ya jawo mata towel ta daura ya shiga toilet ya hada mata ruwan zafi ya fito, dakyar ta iya tashi ta shiga toilet din saboda zugin ciwon da gefen marar ta yake yi mata. Acikin toilet dinma ta dade tana kuka kafin tayi wankan, jin shiru shiru bata fito ba yasa jawad binta cikin toilet din nan ya sameta zaune sai faman kuka take, agabanta ya durkusa ya kamo hannuwanta ya rike ya fara yi mata magana a hankali, "My dear menene abin kuka? Kowacce cuta tana da maganinta kar ki sawa ranki damuwa har wani ciwon ya kama min ke kinji? Oya tashi nayi miki wankan" mikar da ita yayi, shine yayi mata wankan yana yi yana yimata wasu yan wasanni da haka har yayi nasarar mantar da ita bacin ran da take ciki. Acikin towel ya nadota tamkar yar jaririya yazo ya ajiyeta akan gado, mayuka ya debo zai shafa mata, nan ya shafeta da mai yayi mata kwalliya ita dai tana zaune tana kallonsa saboda yace ba zata kalli mudubi ba har sai ya gama, powder ya shafa mata ya shafa mata jan baki, wasu abubuwan ma bata san a inda yake shafa mata ba ko goshi ko kumatunta da haka har ya gama yi mata kwalliyar ya zabo mata kayan da zata saka, wata jar riga doguwa mai hannun shimi ya dauko mata, tun daga wurin cinya har kasa a yanke yake saboda haka ana ganin cinyarta guda daya gashi daga kirjin rigar anyi wata tattara kuma kirjin a bude yake dan haka ana iya hango albarkatun kirjinta, jan siririn mayafi ya dauko mata ya daura mata ya tsaya yana kallonta, "Ya akayi?" Tafada tana kallonsa "Kinyi kyau queen, taso ki gani" hannunta ya ja suka karasa gaban mirror, kallon kanta ta tsaya yi saboda yadda jawad ya rangada mata kwalliyar kai ka rantse wata shahararriyar mai kwalliyar amare ce tayi mata, abubuwan da bata taba saka su a fuskarta ba ma yau ya saka mata, rungume shi tayi tace, "To sai muyi picx din tarihi ko dan wannan kwalliyar tayi kyau" hotuna suka shiga yi ita dashi tun suna dauka a daki har suka dawo falo suka ci gaba da dauka, kan kujera ya fada ta kuwa bishi tafada kan kirjinsa tana kallonsa kyatt ya dauka karbar wayar tayi ta kurawa hoton ido yayi kyau sosai duk cikin hotunan ma wannan na karshen yafi burgeta. Tana kwance a kan kirjinsa yana shafa kanta yana yi mata dadadan kalamai kasa kasa har magrib tayi sai a lokacin suka tashi dan gabatar da salla. Bayan sun idar da salla ta shiga kitchen, binta yayi ya tayata suka dafa indomie da kwai suka fito, a baki ya rinka bata har ta koshi. Koda lokacin bacci yayi dakinta yazo bayan yayi shirin bacci ya rungumeta tsam ajikinsa har bacci ya daukeshi amma ita pherty duniyar tunani ta shiga har bacci barawo yayi nasarar dauketa. Tunda wannan abun ya faru jawad bai sake kokarin kulata ba amma yana bata dukkan kulawar data dace domin kullum akoda wanne lokaci yana manne da ita yana yi mata soyayyarshi mai tsada, ko girki zata yi sai ya bita ya tayata, suna aiki suna taba soyayya. Ta dan samu sauki babu laifi sai dai kumburin da mararta keyi yanzu shine tashin hankalinsu, gefen mararta ya kumbura kamar an hura tattali amma kuma bleeding din ya tsaya. Tana kwance agefen gadonta daga ita sai wata yar ficiciyar riga fara mai shara shara da gajeren wando baki jawad ya shigo, a kusa da ita ya kwanta ya dauketa ya dorata a samansa ya fara yi mata cakulkuli nan ta shiga zillewa tana dariya, shima dariyar yake, "Dan Allah ka daina" ta fada tana dariya, "To nadaina queen, kin san wani abu? Ya kamata muje asibiti kiga Ganny doctor akan matsalar nan taki" ya kare maganar yana shafa kanta, "Jawad ba sai munje ba saboda tun lokacin da abun ya faru doctor din yace ba zan sake daukar ciki ba kuma dakyar idan zan iya rayuwar aure" wasu hawaye suka silalo daga idonta lokacin data gama maganar, "Kar ki sake fadin haka queen domin babu wanda yasan gobe in banda Allah" "Kaga jawad kawai mubar maganar nan zancen zuwa asibiti ma bai taso ba ahakura kawai" Kallonta yayi "kina nufin haka zamu zauna da wannan lalurar ba zamu nemi mafuta ba?" Sauka tayi daga jikinsa "to wacce irin mafuta? Ai mai faruwa ta faru sai dai hakuri" "Dole muje asibiti pherty saboda fadar likita ai ba fadar Allah bace" "Ehh amma ai aikinsa ne dan haka abinda ya fada dole ayi aiki dashi" ta fada cikin tsiwa, "To yanzu me kike nufi? Zamu ci gaba da zama a haka ne?" Ya fada a kule, "Eh haka zamu zauna sai dai tunda kai ba zaka iya jurewa ba sai ka nemi solution" ta fada cikin bacin rai, "Pherty, ke pherty wai meyasa ku mata kuke da karancin tunani ne?" "Malam nidai inada tunani na, kawai ka fito fili ka cemin kai dai ba zaka iya zama dani ba tare da kana samun biyan bukatar ka ba, tunda yanzu ni ba mace bace shiyasa ba zaka zauna haka ba, dole ka nemo mai daukar dawainiyarka" "Ta yaya da zan zauna ahaka? Ni dutse ne ko kuma ni ba mutum bane? Idanma kika yi tunanin zan iya zama a haka kin yaudari kanki, taya zan zauna kullum daga kiss sai hugging? Kinga ki maida hankalinki ki shirya muje muga likita" "Eh ai sai yanzu na gano inda ka dosa, dadinta ma dai ansan ba haka nake ba tun asali kuma babu wurin likitan da zanje" Bai sake tanka mata ba ya tashi ya fice daga cikin dakin, yana fita ta fashe da kuka saboda dama wannan ranar take gudu ranar da jawad zai bukaci mace tunda ita ba zata iya yi masa komai ba. Tun daga wannan rana ta dauki fushi kamar yadda shima yaketa faman fushi, ganin zaman gidan yayi mata zafi ya sata tunanin komawa sch, a falo ta sameshi kwance kan kujera yasha kananan kaya kusan ita bata ma taba ganinshi da manyan kaya ba. "Ina son zan koma sch gobe sannan kuma provision dina ya kare" tana gama fadin haka ta juya ta koma dakinta ba tare da ta kalleshi ba, bin bayanta yayi da kallo yayi kwafa ya tashi ya fita, wani provision store yaje ya iyo mata siyayyar komai da komai na duk abinda zata bukata ya kawo ya jibge mata a falo yayi ficewarsa ya tafi gidan aadil bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha. Koda ta fito taga kayan barinsu tayi a wurin sai washe gari wurin karfe 11 ta shirya tasa mai gadi ya nemo mata mai keke napep ta kwashe kayan tayi tafiyarta sch lokacin ko tashi daga bacci ma jawad din bai yi ba sai tashi yayi yaga bata nan hakan ba karamin sake kular dashi yayi ba ya fuskanci yanzu yarinyar nan wata rashin kunya take ji da ita amma zai bata mamaki. Tunda pherty ta koma sch tayi watsi da tunanin jawad duk da cewa tasan hakan ba mai yiyuwa bane, yau ma kamar kullum tana kwance akan gadonta a dakinsu hannunta rike da waya tana kallon hotunan da suka yi ita da jawad ranar da yayi mata kwalliya suna tsaka da soyewa hotunan sukan sata nishadi duk lokacin da ta kallesu, murmushi kawai take yi ita kadai domin hotunan sun burgeta musamman ma wadanda suka dauka a falo, wani yana kissing din wuyanta, wani kuma bakinsa kan kumatunta amma wanda take kwance kan kirjinsa duk yafi burgeta, "Baiwar Allah lafiyarki kuwa?" Sadiya ta fada tana yiwa A'isha signa, "Tambaye ni dai" ta bata amsa tana sake kallon hoton, sai kuma ta tashi zaune ta ajiye wayar ta fita da sauri, shaf ta manta da lecture note dinta a room 1 da taje hira can dazu dan haka ta tafi daukowa da sauri. Tana fita sadiya ta dauki wayar ita da A'isha suka fara ganin hotunan, "Kai wato yarinyar nan kawai sha'aninsu taje suka yi babu wata rashin lfy da jawad yayi" inji A'isha, "Ai mu suka mayar garori amma luv dinsu kawai suka sha" Sadiya ta fada tana budo wani hoton, shigowar pherty ce ta katse musu hirar, "Kut kuban wayata malamai, waye yasa ku kallar min sirrina nida mijina?" Hanata wayar suka yi suka gudu nan ta hakura ta kyalesu har sai da suka gama ganin picx din sannan suka dawo mata da wayar. Ranar tana zaune yaya aadil ya kirata yayi mata fada saboda jawad ya fada masa ya sata abu taki yi kuma sai faman fushi take yi dashi, nasiha yayi mata sosai sannan suka yi sallama aranar da daddare sai ga jawad din yazo wurinta. "Shine zaka wani je ka hadani da yaya aadil ko?" Ta fada a shagwabance tana kallonsa, "Eh ai naga kinfi jin maganarsa ne fiyeda tawa saboda har yanzu nasan shi zuciyarki take so" Kallonsa tayi sai kuma tayi murmushi, "Ni wlh ba sonsa nake ba kawai ina girmama irin halaccin da yayi min ne kamar yadda nake girmama irin son da zuciyata take yi maka" Murmushi yayi yakai ma goshinta kiss, "to yanzu yaushe za muje asibiti? Koda yake nasamu wani likitan mata nayi masa bayanin matsalar ki to sai yake nuna min kawai gara muje kasar saudiyya sai aduba ki acan tunda abin yayi worst amma ya kika gani?" Cikin jikinshi ta shige domin tayi missing dinshi sosai, "To amma abari nagama exams dina tunda kaga next week zan fara" "Ok to babu damuwa, i wish u all d best my queen" kwantar da kanta tayi acikin kirjinsa tana shakar daddadan kamshin da yake futarwa. Akwana atashi yau har pherty ta kammala exams dinta tanata shirin tafiya gida duk jinta take babu dadi saboda zasu rabu da mutanen nata sai bayan dogon hutu sannan zasu dawo sch, rungumesu tayi tana kuka suna kuka ta tafi gida. Tunda ta koma gida jawad ya fara yi musu shirin fita kasa mai tsarki, kwananta biyar da dawowa suka daga ko kumo bata je ba sai waya tayi ma su mamanta tace zasu tafi umara, haka hawy ma tayi mata wayar ta fada mata. Karfe 4 na yamma suka sauka a kasa mai tsarki a wani hotel mai suna ALAM TOWA acikin unguwar markaziya, aranar suka halacci asibiti suka ga likita, an dorata akan magani sannan zasu yi mata aiki, dan haka tunda suka zo kasar ta dage da ibada tana addu'ar Allah yasa ta samu lfy, cikin ikon Allah akayi aiki a sa'a kwananta biyu a asibiti aka sallameta da tulin magunguna. Daga nan yawo jawad yajata zuwa gidajen danginsu da sauran wurare, har sch din da yayi duk sai da ya kaita ta gaggani, yanayin kasar ya karbi jikin pherty nan tayi lukwikwi da ita tayi fes saboda in banda shakatawa babu abinda suke yi acikin wannan kasa duk da cewar suna ibada sosai. Yau satinsu biyu da zuwa kuma ahalin yanzu tana jin jikinta normal babu wani ciwo,toilet ta shiga tayi wanka da sabulu mai kamshi ta fito, bayan tagama kwalliya ne tana tsaka da fesa turare jawad ya shigo, ta bayanta yaje ya rungumeta,ya fara shafata, "Jawad ya haka?" Ta fada a sabule, "Queen gwaji zanyi, so nake naga ko kin samu lfy" kokarin kwacewa ta fara amma ta kasa, cak ya dauketa bai direta ako ina ba sai akan gadonsu. Ranar dai pherty tasha wuya a hannun jawad saboda ji tayi kamar wannan ne karon farko harma yaso yafi karon farkon, shi kuwa jawad kasa banbance waccan ranar da wannan yayi domin queen dinsa dai ta juye ta zama cikakkiyar budurwa tun anan ya gane shi dinne dai yanzun ma dama kuma baya zargin gwanar tasa. Sai da komai ya lafa sannan ya shiga rarrashinta yana yi mata wasu kalamai wanda nidai ummi A'isha bana jin ko me yake fada, ajikinsa ya dorata ya kwantar da ita nan ta fara baccin gajiya. Sai da tayi baccinta ta more sannan ta tashi duk jikinta ciwo yake mata amma mararta lfy lau ko alamun ciwo babu, lokacin data farka jawad baya cikin dakin dan haka ta lallaba ta shiga toilet tayi wanka da zazzafan ruwa ta fito, mai kawai ta shafa tasa turare ta zira wata yar guntuwar riga iya gwiwa tayi kwanciyarta, jawad ya shigo hannunsa dauke da wata babbar leda mai kyalkyali, "My queen kin tashi?" Tana ganinsa ta fashe da kukan shagwaba, da sauri ya karaso inda take ya dauketa ya goyata yayi falo da ita yana jijjigata tareda yi mata albishir din kayan sawar da ya siyo mata harda sarkar gold da awarwaro da zobuna, a bayansa tayi bacci sai da ya daina jin motsinta sannan yaje ya kwantar ta. Koda ta tashi wani rikicin ta sa masa nan ya shirya itama ta shirya cikin bakar doguwar riga ta nade kanta da jan gyale suka fita yawon zaga gari, ko ina jama'a ce anata hada hadar kasuwanci kai ba zaka ce dare yayi ba, sai wurin karfe 2 nadare sannan suka koma masaukinsu. Hakika sunyi rayuwa mai dadi acikin wannan kasa sunsha soyayya sosai sannan sun jiyar da junansu farin ciki, satinsu biyar acan suka fara shirin dawowa Nigeria. Ummi Shatu [5/29, 1:56 PM] Ummi A'isha🏻: [5/27, 9:32 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 81 ~~~ Satinsu biyar a kasa mai tsarki sannan suka fara shirye shiryen dawowa kasar mu Nigeria bayan sun jibgo tsaraba mai tarin yawa. Ranar talata suka baro kasar saudiya suka nufo Nigeria, kwanciya pherty tayi ajikin jawad ta rungumeshi acikin jirgi tana tuna daddadar rayuwar da suka yi ita dashi akasar saudiyya amma samun lafiyarta yafi mata komai dadi. Karfe 4 na yamma suka sauka acikin garin gombe yaya aadil ne yaje dauko su sai faman fara'a da murmushi yake hakan yasa pherty tsarguwa gashi ko hada ido dashi ta kasa domin a halin yanzu kunyarsa take ji. Gidansu ya kaisu ya ajiyesu sannan yayi musu sallama ya tafi, gidan tsaf tsaf an gyara musu ko ina kamar suna nan, wanka suka yi sukai salla suka ci abinci jawad ya fita ya tafi gidan Ummi ita kuma pherty ta kwanta domin hutawa. Kwanansu biyu da dawowa suka je gidan ummi suka wuni acan da daddare suka biya ta gidan yaya aadil suka kai musu tsarabarsu kasa kasa pherty take kallon aadil da salima wadda cikinta ya dan fito yayi das ajikinta, hannunta salima ta kama zuwa cikin bedroom dinta suka zauna, ta debo mata kayayyaki na amare ta bata ita dai pherty duk kunya ta rufeta, sun dan jima sosai sannan jawad yace ta fito su tafi. Tun a hanya yake damunta da tambayoyi wai me ta samo, kanta ta dauke taki bashi amsa, "Queen tambayar ki fa nake, menene wannan?" "Maganin ciwon cikine anty salima ta bani" Juyowa yayi ya kalleta "kamar kuwa kin san nima cikina ciwo yake ,muje gida sai ki sammin nasha" Shiru tayi bata bashi amsa ba har suka je gida, dakinta ta wuce ta zuba kayan acikin drawer din mirror dinta ta wuce bathroom tayi wanka, lokacin da ta fito ta iske jawad zaune kan dan stool din mirror da jarkar tsumin da anty salima ta bata dazu, da sauri taje ta zata kwace saboda har yasha rabi, "Haba jawad danme zaka dauka min kasan ko meye?" Idanuwansa ya lumshe ya budesu a hankali, "menene? Naji da zaki kuma da kamshi" "Kai kasani wayasa ka shamin?" Gaban mudubin ta karasa ta karbe robar ta rufe ta ajiye ta tsaya ta fara kokarin shiryawa, hannunta ya riko, "Ni ki bari haka ba sai kinyi kwalliya ba haka kinfi kyau natural beauty" harararsa tayi ba tare da tayi magana ba, tashi yayi ya rungumeta ta baya, ta cikin mudubi ta kalleshi idonshi yayi dan ja kamar me jin bacci, "Yau nashiga uku,da ya muka kare ma balle yanzu kasha wani abu" kokarin kunce towel din jikinta ya fara tayi saurin dakatar dashi, "Meye haka" malam nifa agajiye nake ka rabuda ni in huta ka gane?" Idanuwansa a lumshe ya sake matseta ajikinsa, "Kiyi hakuri pherty na, kinga fa nayi hakuri sosai tunda a saudiyya ma sau daya kika barni" Abubuwan da ya fara yi matane suka hanata magana dolenta ta rabuda shi ta bada kai bori ya hau. Washe gari suka shirya domin zuwa kumo wannan shine karon farko da pherty zataje gida tun bayan bikinta wurin wata hudu kenan, duk zumudi da doki ya cika mata rai saboda har ta kasa boyewa ko jawad sai da ya gane murnar da take ciki. "Bafa kwana zakiyi ba" ya fada da niyyar zolayarta, "Wlhi kwana biyu zanyi dan har kayana ma na debo" "Ba kun koma sch ba?" "Mun koma amma ni bazan koma ba sai upper week,yaushe rabona dasu mama ai dole ma na kwana" Murmushi yayi ba tare da yace komai ba, suna shiga cikin garin kumo kasuwa jawad ya wuce dasu, a sabuwar plaza dinnan tasu ya tsaya wadda yanzu an budeta shaguna shake da kaya babu abinda ba a sayarwa,fita yayi ya barta cikin motar yaje ya debo kaya Wanda ita dai bata san ko na menene ba kawai dai taji an bude but ana zuba kayan, bayan an gama loda kayanne ya koma cikin motar suka nufi cikin gari. Lokacin da suka shiga unguwar su pherty pherty ji take kamar tayi tsalle ta fada gidan ai kuwa yana tsayawa ta bude kofa tayi cikin gida, tana shiga ta fara kwallawa mamanta kira, "Mama, mama, mama kina ina?" Da sauri maman ta fito daga cikin daki tana cewa, "wa nake ji haka? Yan tafiya har an iso mana?" Tsalle pherty tayi ta dane jikin mamanta tana dariya daidai lokacin jawad ya shigo ya harareta, itama harararsa tayi ta saki mama ta wuce ciki. Har cikin falo mama ta shigar jawad tayi masa shimfida ya zauna ita kuwa pherty ana can cikin daki sai bincike take yiwa mama, "Mama ina abba na?" Tafada tana daga can cikin daki, "Yafita kasuwa sai anjima zaki ganshi ya dawo" mama ta fada lokacin da take ajiyewa jawad ruwa da lemo a kusa dashi, cikin hausarsa dai wacce bata gama isarshi ba ya samu suka gaisa da mama. Ya dan jima agidan kafin ya yiwa mama sallama ya fita, "Sai ki fito ki rakashi ai ja'ira kawai" mama ta fada lokacin da ta shiga dakin da pherty take ciki tana bincike, "To mama bari naje" mayafinta ta dauka tayi hanyar kofar gida ita kuma mama tana ta fadan binciken da pherty take yi. Lokacin data fita ya samu yara sun fara debo kayan suna kokarin shigar dasu cikin gidan, tsayawa tayi tana kallonsa kamar yadda shima ya tsaya jikin motarsa ya zuba mata manyan fararen idanuwansa, sai da yaran suka gama shigar da kayan ya sallamesu suka tafi sannan ya dubeta ta wani rike kugu tana kallonsa, "Zaki cinyeni ne ko yaya?" Ya fada da zummar tsokanarta, "Babu mamaki" ta fada tana dubansa,Murmushi yayi ya nufota, ciki da koma ta buya a bayan kofar zauren gidan yana shiga ya ganta, binta jikin bango yayi ya matseta yasa dan yatsansa a saman idonta, "Yau bazan iya bacci ba, yau zan kasa bacci queen" Bata yi magana ba taji lips dinsa kan nata, ahankali ya fara tsotar bakinta har na tsawon wani lokaci,ita kanta tasan zata yi missing din shi, hannunta yaja zuwa inda motarsa take, Kashe mata ido yayi, sunkuyar da kanta tayi saboda duk ya saukar mata da kasala, murmushi yayi yace, "To ni kinga tafiyata yau da daddare sai ki nemi abokin bacci" motarsa ya bude ya shiga ya fara daga mata hannu ya tafi, murmushi tayi ta koma cikin gida tana tunanin hali irin na jawad komai nashi simple ne. Tunda ta koma ta saka mama agaba sunata hira sai wurin la'asar sannan ta samu ta leka gidansu hawy cikin sa'a kuwa ta samu tana nan itama tazo weekend, kallonta hawy tayi cikeda tsokana, "Kawata cikin naki wata nawa ne?" "Ke zaki fada tunda ke kika san ina dashi" dariya hawy tayi "kema kin san kina dashi kawai fada min ne ba zaki yiba" hirarsu suka sha har lokacin sallar magrib tayi sannan suka rankaya suka koma gidansu pherty. Suna zuwa pherty ta cicciro mata tsarabar da ta iyo mata ta takalmi da yar jaka sai atamfa mai dan karen kyau, har dare suna tare da hawy, sai lokacin da fita rakata ne sannan jawad ya kirata a waya, wata kunya taji saboda sam ta manta bata kirashi taji yaya ya sauka ba. Ummi Shatu🏻 [6/2, 10:11 AM] Ummi A'isha🏻: [5/31, 9:07 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 82 ~~~ Kara wayar tayi ajikin kunnenta ta soma yin magana a hankali, "Jawad ya kaje gida?" "Bayan kin manta dani" ya fada a shagwabance, "Kayi hakuri yanzu nake son kiranka dama" "Haka dai kikace, yau kin manta dani saboda kin samu su mama ko?" Girgiza kai tayi kamar yana kallonta, "A'a kana raina kaima ban manta da kai ba" Sun dan taba hira kadan sannan suka yi sallama ta kashe wayar, ta karasa raka hawy, "Um soyayya, yanzu kina sonshi kenan?" Inji Hawy, "Da ance miki bana sonshi ne?" Pherty ta fada tana hararar hawy, "Ato idan ke kin manta to ni ban manta ba" hawy tafada tana murmushi, "Kinga malama sai da safe wanka nake son zuwa inyi yanzu yanzu" tana fadin haka ta juya ta nufi gida tana yiwa hawy dariya. Wanka tayi bayan ta koma gida, shiryawa tayi ta dawo falo wurinsu mama nan suka bude sabon babin hira har karfe 10 tayi sai a lokacin kowa ya tashi ya nufi makwancinsa, kan gadon mama taje ta dale tana fadin, "Mama yaushe rabona da hawa gadonki? Yau akai zan kwana" "Kema ai kin samu naki gadon ja'ira" mama ta fada daidai lokacin da take fita daga cikin dakin, murmushi pherty tayi ta lumshe idonta. Tunda pherty taje gida kullum suna tareda hawy suna hira, jawad kuwa kyaleta yayi har sai da tayi kwana biyar sannan yazo ya dauketa suka tafi bayan su mama sun hada musu goma ta arziki. Dawowarsu gida sunyi rayuwa mai dadi kuma jawad ya nuna mata yayi missing dinta over, kwananta 6 ya hado mata provision ta koma sch bayan su Sadiya sunce mata suma sun koma, tsarabarsu ta saudiyya ta fiddo musu ta basu kowaccensu riga da wando na pakistan da takalmi flat mai tsada ta siyo musu, sunyi murna mutuka tareda addu'ar Allah yasa sun kusa shan suna ai kuwa kamar sun fada a bakin "yan amin domin ko sati daya ba ayi ba pherty tafara jin wani irin yanayi a tattare da ita. Babu rashin lfy babu amai babu komai sai dai tana jin tashin zuciya ga yawu da yake taruwa a bakinta, tana zaune agefen gadonta da zani daurin kirji tana tsifar kai, sadiya kuma tana rubutu akan gadonta itama yayinda A'isha take kwalliya wani man shafawa A'isha ta ciro da niyyar shafawa tashi pherty tayi ta fita waje taje ta zubar da yawun bakinta ta dawo gefen gadonta ta zauna, "A'isha man nan naki tayar min da zuciya yake wlhi" pherty tafada tana yamutsa fuska, "Ke kuma naki cikin haka yake?" Sadiya tafada tana dariya, "Ni ba cikine dani ba kawai son ganin man nata ne banayi" pherty ta mayar mata da amsa, "To idanma cikin ne menene? Dama ai tunda akayi aure ai an san za ayi haihuwa" A'isha tafada tana dariya, tsaki pherty tayi, "Ku kuka sani dai" Tashi tayi ta dauki cumb da kibiyarta ta fice tabar dakin ta nufi wani dakin ba ita ta dawo ba sai wurin bayan awa hudu, tana shiga ta samu sun kunna risho sun dora musu abinci,ji tayi zuciyarta ta tashi sakamakon warin rishon da taji ta shaka, "Dan Allah ku rinka kunna rishon nan awaje" kallonta suka yi, "Saboda?" A'isha ta tambayeta, "Saboda bana son warin risho" Dariya sadiya tayi harda kwalla sannan tace "sai ance kinada ciki kice ke bakida ciki to meye warin risho? Ba wani wari da rishon nan keyi kece kike ji" "Sai kiyi kuma" pherty ta fada tareda saka kayanta ta fita ta nufi captaria domin samowa cikinta abinda zata saka masa domin yanzu bata sha'awar abinci totally, abinci ta gani da kayan ciye ciye kala kala lokacin da taje captaria amma duk basu yi mata ba sai ma tashin zuciya da take ji, a wurin wata mata mai siyar da abinci ta hango awara acikin farin bokiti, awarar taje ta siyo ta dari biyu ta sai coke mai sanyi ta koma hostel. A inda ta tafi ta barsu ta dawo ta samesu suna zaune suna cin abinci, kan gadonta taje ta zauna ta kalli abincin da suke ci, taliya da wake jallop, idonta ta dauke saboda yanzu duk abubuwan da take so da ta tsanesu, "Zo kici abinci ga naki nan a flask" Sadiya ta fada, "Ba zan ciba ku cinye" tafada cikin sanyin murya, "Meyasa?" A'isha ta tambayeta, "Awara zanci gata na siyo" "Ashe zamuci awara yau" inji Sadiya "Dai dai zan san muku wlhi wannan shine abincina har dare" ta fada tareda mika musu awarar guda biyu, yaji ta dauko ta fara dandana tana cin awarar har ta ci rabi sannan ta daure sauran ta ajiye ta dauki coke ta kora ta sauka kasa ta zauna tana jiran Sadiya tayi mata kitso, koda aka zo kitson ma wai ba za asa man kitso ba bata son kamshin man haka akayi kitson suna yi suna fada da sadiya har suka gama. Yau rabonta da jawad sati uku kenan saboda tun dawowarta sau 1 yazo mata hira shiyasa ta shirya tafiya weekend acikin wannan satin, tana zaune tayi zugum tana tunanin abin yi saboda kwadon kanzo take son ci yau domin yanzu ta tsani awarar da ta zama abincinta da, tun ranar da tayi aman awarar taji ta fita daga cikin ranta, "Pherty me zan dafa mana?" A'isha ta tambayeta lokacin da take kokarin fitar da rishon da zatayi girkin waje, "A'isha wallahi kanzo nake son ci, nidai jawad ya hadani da lalura" takarasa maganar acikin zuciyarta, "Kanzo?" Sadiya ta fada cikin mamaki, "Yanzu a ina za asamu kanzo? Indai ba son wahalar da kai ba kin san dai duk hostel dinnan ba za asamu kanzo ba" A'isha ta bata amsa, Kallonsu tayi daya bayan daya kawai sai ganinta suka yi ta fara hawaye, "Yi hakuri zamu samo miki, ai dole mu samowa dan baba kanzo" Sadiya ta fada tana dariya tareda tashi ta fita, itama A'isha fitar tayi suka tafi yawon neman kanzo duk kuwa da cewar sun san abune mai wahala samun kanzo acikin hostel. Ita kam pherty suna fita ta shafa cikinta tana goge kwallar idonta, "yanzu jawad shi babu abinda ya dameshi yana can yana zamansa lfy ni kuma nan ya barni da laulayi" haka ta fada acikin ranta, tana nan zaune suka dawo basu samo kanzon ba nanfa taji hankalinta ya tashi wani kukan tafara kokarin yi amma shigowar Ummi Hambali yar department dinsu yasa ta hadiye kukan, "Pherty ga wainar fulawa na kawo miki" ummin tafada tana mika mata wani flask karba tayi fuskarta dauke da murmushi, "Nagode ummi kamar kuwa kin san yau babu abinda naci" da sauri ta dauko yaji ta fara ci ko sadiya da A'isha bata barwa ba sai da taji tayi dam sannan hankalinta ya dawo jikinta. Harararta Sadiya tayi "malama ki kira mijinki ya kawo miki kanzo saboda kar kizo kina tashinmu cikin dare kina cewa ke kanzo kike so" Dariya A'isha ta saka "wlhi kar kisa yau naki kwanan dakin nan" Murmushi pherty tayi "idan kunyi hakuri ma gobe zan tafi gidana wurin mijina" "Dakyau dan Allah idan kinje kar ki dawo sai kin samo kanzon" Sadiya ta mayar mata da amsa, murmushi kawai tayi ta dauki wayarta ta soma kiran mamanta suna gaisawa ta fara yi mata zancen kanzo take so akawo mata, "Kanzo kuma pherty?" "Eh mama dan Allah ki kawo min dama kinga fa baki taba zuwa gidana ba mama, dan Allah kizo" ta fada cikin shagwaba "To shikenan bari mahaifinki yazo zan sanar masa idan ya yarda zanzo ranar asabar idan kuma bai yarda ba to zan taso hawwa kawarki ta kawo miki" "Mama dan Allah Ku taho tare dan Allah" "To shikenan phertyma sai ranar asabar din" Kashe wayar tayi tana murna nan ta tsiri shirin tafiya gida. Washe gari da yamma kuwa jawad yazo ya dauketa, sai kallonshi take cikin burgewa komanshi tsaf tsaf amma ita ya hadata da aiki bata da aiki sai tara yawu ta zubar, shi kam jawad bai ma san tana da cikin ba. Suna zuwa gida ta fita daga motar taje ta zubar da yawun bakinta, "Jawad murhun karfe da itace zaka siyo min kasa min acan baya dan bazan iya girki a gas ba" ta fada tana yatsina fuska, hannunta ya kama suka shiga cikin falo ya zaunar da ita akan cinyarsa, zumbur ta tashi saboda kamshin turarensa da ta shaka nan taji cikinta ya soma juyawa zuciyarta ta fara tashi. Ummi A'isha🏻 [6/3, 7:27 AM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 83 ~~~ Zumbur ta tashi saboda kamshin turarensa da ta shaka nan taji cikinta ya soma juyawa zuciyarta tafara tashi, yawune ya cika mata baki da sauri ta shiga dakinta nan dinma babu dadi domin kamshin da dakin yake yi shima baiyi mata ba, toilet ta shiga ta zubar da yawun bakinta ta koma falo wurin jawad, "Queen wai meke faruwa ne?" Ya tambayeta "A inafa?" Itama ta tambayeshi "To naji kince na siyo miki murhu, me zai hana ki rinka girkin a electric stove tunda kince baki son yin girki a gas" Zama tayi nesa dashi ta yatsina fuska, "Nifa gaba daya warin girkin ma da warin rishonne bana so har warin gas din duk bana so murhu nake son ka samo min da fire wood" "Angama ranki ya dade" mikewa yayi ya fita dan siyo mata murhun, tashi itama tayi ta shiga dakinta tana tottoshe hanci nan ta tattara kayan da zata bukata ta koma daya dakin kuma cikin sa'a sai taji nan din babu kamshin da bata so din. Kamar yadda tace haka jawad ya siyo mata murhu guda biyu da itace ya kawo mata, acan bayan kitchen dinta ta ajiye murhun ta kunna wuta ta dora abinci, tuwon shinkafa miyar wake da busasshen kifi tayi, lokacin data gama jawad yana kishingide a falo,gabansa ta kawo abincin ta jere tashiga dakinta taje tayi wanka ko mai bata shafa ba saboda shi kansa man tayar mata da zuciya yake, yar doguwar riga ta shan iska ta zira tafito falo inda jawad yake zaune yana cin abinci. Dan gutsiren tuwo tasa a plate ta zuba yar miya ta fara ci, sam bata jin dadin tuwon kawai ci take domin rabonta da abinci har ta manta shiyasa duk ta dashe sai uban fari kauu da tayi, kallon jawad tayi sai zira lauma yake kamar zai hadiye kwanon, tana kallonsa ya cinye ya sake karawa ganin haka sai kawai ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ya kalleta tareda matsowa kusa da ita, "Queen menene?" "Jawad bana jin dadin abinci gashi bakina babu dadi, komai naci bana jin dadinsa sam yanzu bakina babu taste" ta fada tana share hawayen idonta, "Am sorry dear, tun yaushe?" "Tunda na koma sch fa, wlhi rabona da abinci har namanta" Hannunta ya kama ya rike cikin nasa fuskarsa cikeda tausayinta, "Sorry queen, ko na kaiki kiga dr?" Girgiza kai tayi "Why?" "Nidai basai naje asibiti ba" tafada cikin shagwaba "Ayya sorry, to na kira miki dr ansar?" Nanma kai ta girgiza, hadata yayi da jikinsa yaci gaba da bata abincin a baki amma dakyar ta yarda ta ci rabin wanda ta zuba, "my pherty sarkin daru" yafada tareda jan hancinta. Daren ranar kuwa bata yarda ta hada daki da jawad ba saboda wai bata son kamshin turaren da yake yi, juyin duniyar nan yayi taki yarda ya kwanar mata adaki yayi rarrashin har yagaji yayi fushi ya fita daga dakin. Washe gari da safe kuwa kowa harkar gabansa yake ita fushi jawad fushi, shi jawad fushin da yake na ta hanashi kanta ne alhalin rabonshi da ita anfi sati uku, ita kuma pherty nata fushin na tana fama da lalura ne gashi kuma jawad bai nuna tausayinsa akanta bane, Wanka tayi ta tsuke cikin riga blue body hug mai kyan gaske an rubuta IT'S YOUR TIME! Ajiki, da bakin wando mai laushi amma kuma tied ne, bakar hula tasa ta fita baya taje ta soya dankali da kwai tayi yar sos tana yi tana zuwa zubar da yawu da haka har ta gama ta hado kayan ta kawo masa kan dining sannan ta koma ta juyo ruwan zafin data dafa ta kawo masa, yana kallonta babu abinda taci sai aikin zuwa zubar da yawu minti kadan sai ta tashi haka ta kwanta akan doguwar kujera, ganin haka ya sashi sassauto da nashi fushin yazo ya sameta, "Xarah me kike son ci naje na siyo miki?" Bude idonta tayi ta kalleshi, "Jawad babu abinda zan iya ci sai abu me k'uli k'uli" "Zaki ci indai mai k'uli k'uli ne?" Kai ta daga alamun ehh, key din motarshi ya dauka ya fita, wayarta ta dauka ta kira su A'isha tana fada musu to yanzu gashi nan mijinta ya tafi samo mata abinda take so tunda su basa nemo mata. Kasuwa jawad ya shiga nan ya fara neman abinda zai siyo mata, zogale da kuli kuli ya siyo mata sannan yaga gurasa da kuli kuli nanma ya siyo daf da zai fita daga kasuwar yaga agwaluma itama ya tsaya ya siyo. Lokacin da ya koma tana kwance inda ya barta tana bacci dan haka bai tasheta ba ya ajiye mata kayan ya fita ya nufi gidan ummi, bai dade da fita ba ta tashi, ai tana ganin kayan da ya siyo mata taji yawunta ya tsinke nan ta sauka ta zauna a kasa ta dauki zogalen da guraza ta fara zurawa, ita kuwa agwalumar da ya siyo mata koda yaushe tana tareda ita tana sha. Ranar asabar da wurwuri ta tashi ta fara shiryawa su mama delicious, fried rice tayi musu mai dadin gaske ta soya musu kaji sannan tayi musu kunun shinkafa duk bata jin kasala yau saboda dokin zuwansu mama, bayan ta gama shirya komai ne taje ta tsalo wanka tasa wata koriyar atamfa dinkin riga da skirt mai tattara rigar ma tasha tattara, bata yi kwalliya ba saboda ko mai bata shafa ba, falo ta fito ta duba agogo lokacin karfe 11 da minti 15, "Oh nikam mama anya zasu zo?" Ta tambayi kanta, tana nan zaune har 11:30 duk ta kosa da zaman jiran da take, kamar daga sama taji shigowar mota gidan da saurinta taje ta leka window, maman hawy ta hango da mamanta da kuma hawyn, da sauri ta nufi kofa taje ta taro su,dakinta ta kaisu bakinta yaki rufuwa sai murna take, bayan ta gabatar musu da kayan saukar da tayi musu ne suka gaggaisa sannan ta jawo hawy suka koma daya dakin. "Phertyn mama kinyi fari gashi kin dan rame" Hawy tafada cikeda tausayi akan fuskarta, "Um hawy ai dole na rame saboda bana cin abinci kwata kwata" "To ai ga kanzon da kike so can an taho miki dashi" Tashi pherty tayi taje ta dauki kanzon cikin leda viva ga kuli kuli dakakke, kitchen takai kayan ta debi wani acikin kwano ta jika tun anan taji yawunta ya guda saboda yanda kanzon yake fari tas daga gani na masara ne da shinkafa a hade, kyakkyawan hadi tayi masa tasa man gyada ta yanka kayan miya ta dauki maggi ta nufi wurin hawy,kallonta hawy tayi tana dan murmushi, "Allah ya bada lfy amma agaskiya ki rinka cin abinci pherty" Yamutsa fuska pherty tayi "wlh ba laifina bane, bakina ne babu taste in banda bakin shayi babu abinda nake iya sha" "To Allah ya rabaku lfy dai" "Amin" nan kuma suka shiga hirarsu har tsawon wani lokaci,suna nan zaune jawad ya leko bayan yaje sun gaisa dasu mama, "Xarah kawo min abincina daki" zaraf hawy tayi tafara tsokanarsa "kaga ango" murmushi kawai yayi mata suka gaisa ya wuce, Tiren abinci pherty ta dauka ta nufi dakin jawad kanta tsaye ta wuce cikin dakin ta dora abincin akan dan karamin stool din dake girke gefen gadonsa, ta bayanta taji yazo ya rungumeta, "Sannu da kokari my queen" "Yawwa sannu" tafada tana kokarin kwacewa, sakinta yayi ya bata hanya ta wuce ta koma wurin hawy, yinin ranar nan tayi shine cikin farin ciki sai yamma likis sannan su mama suka tafi nan kuma taji hankalinta ya tashi sosai, suna tafiya tasa kuka, rungumeta jawad yayi ya maida ita cikin dakinta. Ummi Shatu🏻 [6/5, 7:43 PM] Ummi A'isha🏻: [6/2, 6:40 PM] Ummi A'isha🏻: 👑MARTABA TA👑 Na UMMI A'ISHA 84-85 ~~~ Dakyar jawad ya iya shawo kan pherty ta daina kukan tafiyar su mama, hannunta ya kama "Oya taso ki rakani unguwa" Babu musu ta saka after dress ta gyara fuskarta tabishi, wakar p square ya kunna musu lokacin da suka hau titi, gidan yaya aadil taga ya nufa, dan murmushi tayi mai kayatarwa ta kalleshi shima kallonta yayi yana murmushin har suka isa gidan. Hannunta rike cikin nashi har tsakiyar falon su yaya aadil, anty Salima na zaune tasaka katon cikinta gaba tana kallo shi kuma yaya aadil yana kitchen yana yi musu girki, pherty ji tayi sun burgeta domin dama can shi yaya aadil tasan mutumne shi mai saukin kai, zama tayi kusa da anty Salima yayinda shi kuma jawad yabi aadil kitchen. Dakyar yauma ta iya gaida yaya aadil amma tasaki jiki da Salima sosai suna hirarsu, har dare suka kai agidan kafin suka yi musu sallama suka tafi, ahanya saida jawad ya tsaya yayi musu siyayyar kayan makulashe gasasshen kifi dasu ice cream da chocolate sannan suka karasa gida, bayan pherty ta zauna ta tande kayan dadin da jawad ya kawo matane kuma ta mike da niyyar tafiya dakinta, kallonta jawad yayi da kalar tausayi amma ta maze tayi tafiyarta saboda ita yanzu wannan abun duk ya fita aranta. Washe gari ranar sunday ta shirya zata koma sch jawad dai sai cika yake yana batsewa ya murtuke fuska haka ya kaita ya dawo amma kawai kyaleta yayi saboda yasan idan ya nuna mata karfi dan karamin cikin dake jikinta yana iya zubewa, ko kallonta baiyi ba lokacin da ta fita daga motar ya figi motarsa yayi gaba. Tun daga wannan ranar ya shareta ba waya ba zuwa haka ya rabu da ita, ita kam pherty hakan yafi mata domin yanzu tana bukatar hutu, satinta biyar cif a sch tsakaninta da jawad babu wani communicating ko ta ganshi online baya kulata itama haka, bayan sallar magrib ta fara kiran wayarsa saboda yau kwadayin kifin da ya taba siyo mata take,wayar tajima tana ringing sannan ya daga a hankali, "Hello Xarah" ya fada kamar me yin rada, "Jawad kana inane?" "Naje hirane wurin kanwarki, lfy?" Dam taji gabanta ya harba, "hira jawad? Wacce kanwar tawa? Wacece?" Ta jero masa wadannan tambayoyin ajere, "Gata zaku gaisa" Kafin tayi wata maganar sai jin muryar mace tayi tana yi mata sallama, tabbas wannan koma wacece tayi sa'a da samun zazzakar murya domin muryarta carkwai take nanfa kishi ya motsa pherty ko amsa sallamar da yarinyar tayi mata bata yiba balle ta tsaya amsa mata gaisuwar da take yi yanzu, kit ta kashe wayarta ta tura masa text massage kamar haka... "Idan ka gama hira da budurwar taka ka siyo min gasasshen kifi ka kawo min" Tura masa text din tayi duk ranta abace, lallai jawad wato ita yabarta da fama shikuma can yatafi neman aurensa ko? Haka tayi ta fada cikin zuciyarta, Bayan sallar isha sai ga text dinsa wai ta fito ta karbi kifin gashi ya kawo mata, ranta a hade ta fice daga cikin dakin su dai su aisha da Sadiya basu san ko me ya bata mata rai ba, tana zuwa inda jawad yake ta tsaya daga waje ta rike kugu, lekowa yayi ya kalleta, "Ki shigo mana queen" Cikin bacin rai ta bude kofar motar ta shiga ta zauna fuskarta a daure, "Malam bani sakon danni ba zama nazo yi ba, kuma wlhi gidanmu ni zan tafi inyaso kai sai ka zauna da amaryarka" tafada hawaye yana sauka akan kumatunta, light din cikin motar ya kunna ya tsura mata ido yanzu kam alamun masu ciki sun gama bayyana a tareda ita ta danyi kumatu fatarta tayi subul gashi cikin nata yadan fito kadan amma ba kowane zai gane ba, "Queen koda nayi aure ke ta dabance a rayuwata, bazan taba mantawa dake ba, kece first lady" Kallonsa tayi "dagaske auren zakayi kenan?" Kai ya daga mata, "aure zanyi amma ba wai dan nadaina sonki ba, kuma kin san wani abu? Yarinyar da zan aura itama sunanta pherty" Wayar hannunsa ta warce tafara kuka mai tsuma zuciya, "Queen ba laifina bane laifinki ne saboda yanzu kin daina bani kulawa kinga kuwa dole na kara aure gudun kar nafada sabon Allah" Ledar kifinta ta dauka tafice daga motar ta tafi tana kuka tana ji jawad na kiranta amma taki ko juyowa, kafin ta shiga hostel tayi kokarin tsayar da kukan ta shiga daki duk kifin ma jitake ta tsaneshi, agefen gado ta zauna ta bawa su Sadiya kifin ta fara binciken wayar jawad, ga text din budurwar tasa nan burjik, morning massages, good night, juma'at massages duk gasu nan amma shi bata ga nashi ba sai guda daya wanda ya tura mata shima thanks kawai ya rubuta, ta inda taji dadi number yarinyar yayi saving da pherty amma ita kuma tata ya rubuta my queen ko anan tasan yafi bata matsayi fiyeda waccan amma duk da haka dai haushinsa take ji, wayar tasa ta ajiye agefen pillow dinta ta dauki wayarta tafara chtn da hawy tana fada mata jawad yana neman aure, ido hawy ta zaro tareda fara bata hakuri, nan ta zayyanewa Hawy abubuwan da suka faffaru, shawara Hawy tabata sosai ta yanda zata sake siye zuciyar mijinta, taji dadin shawarwarin hawy kuma ta daura aniyar yin aiki dasu, Karar shigowar text cikin wayar jawad ne yasata yin sallama da hawy ta kashe wayarta, ta dauki wayar ta bude sakon nan taga daga budurwarsa ne ta rubuto masa "sleeping is a thing line btw life and death......" Da sauri ta goge text din ta lalubo picx din jawad tafara kallo daya bayan daya ita kanta tasan mijinta ya hadu kuma babu dama ne a fagen soyayya dan haka ya zama dole tayi duk iya iyarwata dan ganin ta mantar dashi kowacce mace acikin zuciyarsa face ita guda daya tilo. Daren ranar sai bacci barawo ne yayi gaba da ita amma kasa bacci tayi, gari yana wayewa dama ya kama ranar friday duk su ukun basuda lectures, dan haka tace yau ranar aikinta ce,da A'isha tafara, "A'isha yau ki kure basirarki ki tsara min jan lalle,Sadiya ke kuma kiyi min kitson da baki taba yiwa wata maceba agashinta" Shewa suka saka su duka "tafiya zakiyi haka" A'isha ta tambayeta "Babu inda zanje kawai zan yiwa mijina kwalliya ne" Dariya Sadiya tasa tace "yau soyayyar jawad ta tashi kenan?" "Kudai kawai kuzo kuyi min pls". Hadadden jan lalle A'isha ta tsattsarawa pherty wanda ya kama yayi dau yazama maroon, ita kuma Sadiya tayi mata kitso mai tsananin kyau wanda ni kaina ummi aisha sai da naso ace kainane, yamma tanayi ta shirya ta nufi gidanta. Lokacin da taje gidan jawad baya nan dan haka ta shiga tayi wanka ta sake sabuwar kwalliya cikin riga da skirt bakake marassa nauyi bata daura dankwali ba haka ta fito falo, tana zama jawad yana shigowa shima ya hade cikin kananan kaya, cikin mamaki yake kallonta kamar ba itaba tasha kwalliya cikinta ya dan fito kadan, "Queen saukar yaushe, kai queen yau ke baturiya ce ko balarabiya" karasowa kusa da ita yayi ya fara kallon kunshin da aka rangada mata da kitson kanta, "Queen dan Allah kar kiyi min irin na rannan, kar ki hanani kanki pls" yafada a sululuce, Murmushi tayi ta kama hannunsa tana fara masa fararen idanuwanta tuni ya sunkuceta yayi bedroom dinsa da ita. Washe gari da safe bayan tasha kwalliya cikin shadda kalar shanshanbale riga da zani tafito tanata faman kamshi, kitchen ta shiga ta hada lafiyayyen breakfast ta zo ta shiryashi bisa dining table, kitchen ta koma tana duba guntun kanzonta da ta tafi tabari agidan amma bata gani ba, fitowa tayi fuskarta a turbune daidai lokacin shima jawad ya fito cikin kananan kaya wanda suka yi mutukar yi masa kyau shagwaba tafara yi masa harda buga kafafu a kasa, "Wlhi ka nemomin kanzona duk inda ka kaimin" "Kanzo queen" da sauri ya shiga kitchen din a cikin store ya samo ya kawo Mata yana tsokanarta. Bayan sun kammala breakfast yaya aadil ya iyo waya anty salima ta haihu yan biyu suna asibiti, nanfa pherty aka shiga murna suka garzaya sai asibiti, yara kyawawa masu tsananin kama da aadil farare tas dasu, nan asibiti ya cika da yan uwan salima dasu ummin jawad kafin daga bisani aka sallamesu suka rankaya suka koma gida gaba daya pherty ta dadume jariran ta rikesu bama kamar namijin har saida jawad ya tsokaneta yace itama ta kusa samun nata. Tunda akayi haihuwar kullum suna gidan maijego har ranar suna inda yara sukaci suna jawad da phertyma, murna wurin pherty ba a magana nan sukaje supermarket suka jibgowa jarirai kaya kamar bada kudi suka siyo ba, satin anty salima biyu da haihuwa suka bar garin gombe suka nufi kasa mai tsarki. Irin kulawar da pherty ke bawa jawad a halin yanzu tasashi mantawa da kowacce mace sai ita kadai, cikinta ya girma ya shiga wata na takwas a lokacin bikin kawarta hawy ya taso ahaka ta kokarta taje kumo bikin, itace babbar kawar amarya haka ta zage tayi dukkanin abubuwan da babbar kawa keyi, kwanta biyar har saida takai hawy dakinta sannan ta jirgo nata ya nata ta dawo gida, damma yanzu bata zuwa sch hutu suke nan jawad yaci gaba da kulawa da ita da babynsu har ta shiga watan haihuwa nan ta haifo santalelen danta namiji lokacin yaran yaya aadil sun girma Xarah da jawad,murna wurin jawad kamar ya taka dan shege, nan aka shiga bidiri yayiwa maijego da baby kaya na garari, tun ana igobe suna Sadiya da A'isha da hawy suka zo, ranar suna yaro yaci suna aadil suna kiransa da junior, hhh nasan masu karatu har natuno muku da junior din kuluwa ko, washe garin suna su hawy da A'isha da Sadiya da Anty Salima ne suka yi mata aikin komai. Aranar kowa ya baje aka barta da babynta sai wata yar tsohuwa da mamanta ta kawo mata mai suna iya ladi, nan suka shiga ganin gata ita da junior awurin jawad da dukkanin dangi har sukayi arba'in lokacin ansa date din bikin Sadiya da A'isha, shi kam jawad yanzu bashida damuwa dan haka ya cire kowacce mace cikin ransa sai iya queen dinsa. Awatan may su pherty suka sha bikin Sadiya da A'isha kwaccensu an kaita gidanta anan cikin gombe, yanzu junior har yayi wayo domin watansa 11 yana gudunsa ko ina pherty kuwa sun kammala karatunsu. Yau tana kwance cikin kujera tasha wani lafiyayyen leshi orange colour hannunta da kafarta kuma sunsha jan lalle ta gyara gashin kanta yayi yalo yalo ta kafa dauri tana waya da mama jawad ya shigo hannunsa rikeda junior wanda yake mutukar kama da jawad yana sanye cikin blue din riga da jan wando kafarsa sanye da combos fari yana yi mata albishir da cewar anty salima tasake haihuwa, da sauri ta ajiye wayar tana murmushi, "Allah ya raya wancan karon sunyi min takwara nida mijina yanzu kuma kila su Ummi zasu yiwa" "Kece zakiyiwa Ummi takwara" jawad ya fada yana kallonta rai ta bata "A'a ni salim dina zan yiwa takwara tsohon saurayina" tafada cikeda zolaya Hancinta ya lakuce yace "that salim is not your true lover,i jawad am your true lover here and for the hereafter" Murmushi sukayi gaba dayansu shima junior da bai san abinda suke fada ba sai da ya dan dara Kadan, to nima dai Ummi Aisha murmushin nayi domin Allah ya nufeni da kammala wannan story. ALHAMDULILLAH! Anan na kammala wannan labari ina fata ya fadakar, ya nishadantar kuma ya wa'azantar, inda nayi kuskure agafurceni kuma ina addu'a Allah ya yafe mana gaba dayanmu dani daku masu karatu. Na sadaukar da wannan littafi gareku kawayena PHERTYMA XARAH (d writer of Xarah) SADIYA LAWAL BALA (d writer of Ballagaza) MISS A'ISHA HAWWA SULAIMAN(HAWY) Ina muku fatan alkairi akoda yaushe, Allah ya sanya albarka acikin rayuwarku. Kin cancanci yabo babbar kawata, aminiya sahiba CWT KAUSAR LUV,mai bani shawarwari akoda yaushe, Allah ya barmu tare, ina alfahari dake kawata. Jinjina gareki uwar dakina HAWWA M JABO nagode da kulawarki agareni,Allah ya kara miki kaifin basira. Kina raina ADDA BENAXIR nagode miki much Na yaba miki kawata KHADIJA SIDI Allah yabar zumunci. Ban manta dakeba ta hannun damana MIEMIE BEE Fatan alkairi agareki ANTY BEBEELO Allah ya raya mana iman. Dominku ne kawayena HUMAIRA (yarjejeniya) A'ISHA (Maman Shakur) FIDDAUSI SODANGI A'ISHA (chuchun gaye) A'ISHA DANSABO LEMU UMMI HAMBALI Na gaisheki SA'ADATU DANTIYE babu shakka kinfi kowa son martabata Masoya nagode sosai hakika kun kaunaci martabata, ina kaunarku fiyeda yadda kuka kaunaceni, yan groups dina da sauran groups duk Allah yabar zumunci,wanda na ambaci sunansu dama wanda ban ambata ba duk kuna cikin raina idan hali yayi zaku jini cikin littafi nagaba, Allah yabar soyayya,masoyan Ummi A'isha aduk inda kuke Ummi A'isha tana sonku sosai, nagode Recommend this on Google Comment as: Publish Preview No comments: Post a Comment aisha ummi a teenager who loves to read and writes. here are some of my writeups I will like to share with you people enjoy!! View my complete profile About Me ▼ 2017 (24) ▼ January (24) RUWAN KASHE GOBARA..64 RUWAN KASHE GOBARA.. 61-63 RUWAN KASHE GOBARA.. 51-60 RUWAN KASHE GOBARA.. 41-50 RUWAN KASHE GOBARA.. 31-40 RUWAN KASHE GOBARA..21-30 RUWAN KASHE GOBARA..! 11-20 RUWAN KASHE GOBARA..! 11-20 RUWAN KASHE GOBARA..,! 6-10 RUWAN KASHE GOBARA..,! 6-10 RUWAN KASHE GOBARA..! 1 RUWAN KASHE GOBARA..4-5 RUWAN KASHE GOBARA.. 2 RUWAN KASHE GOBARA.. 3 WANI HASKE...! 62-END RUWAN DARE.. WANI HASKE...! 62-END MARTABA TA 1-50 MARTABA TA 51-End MARTABA TA 1-50 MACE GUDA DAYA TILO SANADIN GATA 1-End SANADIN GATA 1-End KWARYA TABI KWARYA 1-End ► 2016 (6) Blog Archive Watermark template. Powered by Blogger . 0 More Next Blog» Create Blog Sign In