Bismillahirrahmanirrahim *MANNUBIYA* *Book 2* *page 01* Sai da aka fara kiraye kirayen assalatu tukunna da taimakon shed’an Yassir ya samu wani bacci mai d’an karen dad’i ya kwashesa. Ba dan ya saka alarm d’in 7:30am ba to da ba zai ga fitar Yashjub d’in da ya shiryawa gani ba. Alarm d’in yana fara k’ara, ya farka, dan bashi da wani nauyin bacci dama. Da sauri ya d’auki wayarsa ya kalla sannan ya kashe alarm d’in kafin ya ajjiye ta tukunna ya fad’a toilet… Fitsari ya fara yi, tukunna yayi brush sannan ya fito ya k’arasa jikin windown d’akin ya tsaya. Sai da ya yi kusan mintuna biyu a tsaye a wajen tukunna Yashjub ya fito.. Tabbas Yassir ya ji babu daɗi a lokacin da ya ga Yashjub ya kira driver ya bashi makullin motar ya ce “ya tuk’asa su je”, da alamun aiki ne a gabanshi birjik! Dan suna shiga cikin motar ya ga ya baza takardu da computer ya duk’ufa aiki a nan doguwar kujerar bayan, inda ya shiga ya zauna. D’aga kafad’u Yassir ya yi ya d’an tab’e Baki a ransa ya ce ’’Atleast ka samu Abokin mutuwa’’ Sai da ya ga fitar su tukunna ya koma cikin d’akin ya d’auki airpod d’insa ya mak’ala a kunne ya kunna kid’a a wayarshi. Wani d’an labule ya d’aga ata gefe guda chan kusurwar d’akin kayan motsa jikinsa suka baiyyana, tsaki yayi a ranshi ya ce ‘’Wajen motsa jiki sai kace d’akin b’era! Wallahi na ƙagu a-yi-ayi a gama min ginin chan in tartara in koma gidana nima… Gaba ɗaya a masifar takure nake a nan ɗin!’’. Daga haka ya fara motsa jikin nasa….. Ya d’an jima, dan a k’alla ya yi 30 minutes yana abu d’aya, tukunna ya fad’a toilet domin ya samu ya watsa ruwa ko wacce b’ular gashi dake a jikinshi tana mai tsatstsafo da zufa. A band’akin ma sai da ya kwashe sama da mintuna ashirin, tukunna ya fito ya shiga goge-goge da shafe-shafe da feshe-feshe, tukunna ya d’auki wasu had’ad’d’u kuma tsadaddun suite masu masifar kyau ya sanyawa jikinsa. Tsaff ya shirya ya fito tas da shi, ya kuwa yi kyau, longsleeve d’insa ce kawai fara amma hatta takalminsa da belt da links duk komai bak’ak’e ne. A gaban madubi ya tsaya yana taje sumarsa wacce takenan tsaf da ita sannan a cike taff bak’ak’irin, gaba ɗaya ilahirin kan nasa kuma babu ko da alamar sank’o ne…. ga wani had’ad’den gyaran fuska da ya sha wanda ya tafi dai-dai da tsararren sajensa da kuma gashin Baki had’i da d’an guntun gemunshi…. Kallo ɗaya za a yi wa sumar tasa a fahimci ta asalin Bahaushe ce, amman tsabar kud’i da gyaran da take sha ya sanya har wani shek’i sumar take yi, mai tsananin kyau da d’aukar hankali. Kallon kansa ya yi a gaban madubi ya sake, tabbas ya san yana da kyau! Son kowa k’in wadda ta rasa….a yadda yake da kyan nan Wallahi mace ko da kud’inta sai da rabon ta, amman wai dukda haka kalli yadda Kausar take gara shi itama wachchar shegiyar Munirat d’in sai wani kakkaucewa takeyi ta k’i ta bada had’in kai a yi a wuce gurin!Wallahi ba dan ya kwallafa rai a kanta ba da tuni ya watsar da lamarin ta…. Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo hayaniya a nan saman, bai gama fahimtar su waye ba ya jiyo muryar Yasmeen tana kuka tana cewa “Mommy! Ya Yash ne sukayi accident shine doctor d’in ya kirani, wai yanzun nan aka kai masa su.’’ Wani kalar murmushi Yassir ya saki daga jin zancen Yasmeen, A take wani farin ciki marar misaltuwa ya lullub’e sa. Sai da yayi da gaske tukunna dakyar ya samu ya iya kawar da farin cikin da ya baiyyana ƙarara akan kyakkyawar fuskarshi sannan ya fita a gigice…. Yana fitowa ya tarar da su gaba d’aya, kowacce tun a kallon farko ake iya fahimtar hankalinta a tashe ne har su Ummi……. Tuntuni Daddy ya riga ya tafi office shi da Yasira, dan haka suka tura musu message kawai, daganan gaba d’ayansu suka d’unguma zuwa asibitin da Yasmeen ta gaya musu an kai yash ɗin, dan a yadda hankalinsu yake a tashe babu wadda za ta yarda a tafi a barta. Baba Larai ce kawai ta tsaya a cewar Mommy in wani ya dawo sai ita ta je. Sai da suka kusan Isa asibitin ma tukunna su Yasmeen suka lura babu Kausar. Kasancewar kowacce hankalinta ba a jikinta yake ba a wannan lokacin ya sanya basu neme ta ba. A b’angaren Kausar d’in kuwa, duk wannan ife-ifen da akayi aka gama sam ba ta sani ba, har suka fita Jiya yadda ta ga rana haka ta ga dare, ko rintsawa bata yi ba. Shiyasa daff da asuba da taga ciwon Kai yana shirin halaka ta ta sha maganin bacci mai tsananin k’arfi. Suna isa Asibitin direct su ka wuce cikin ward na emergency dai-dai lokacin Likitan ya fito kenan daga inda aka shiga da drivern domin bashi taimakon gaggawa. Gaba d’ayansu rufar masa suka yi, Yasmeen kuwa bata ma tsaya bi ta kansa ba ta fad’a cikin d’akin da ta ga ya fito. Girgiza Kai likitan yayi fuska cike da alhini ya ce ’’sai dai fa haƙuri! we couldn’t save him(ba mu yi nasarar ceto rayuwarsa ba)!’’ Diff numfashi kowa ya d’auke a wajen, suka ma kasa cewa komai Wani mahaukacin bugawa zuciyarta ta yi, jin Likitan yana ci gaba da cewa ‘’amma Yashjub is fine! Da ikon Allah da taimakon seat belt sannan kuma kasancewarshi a seat d’in baya…ya samu iyaka gocewar k’ashi a hannunshi na hagu. Amman motar da suka daka itama gaba d’aya mutanen ciki duk sun rasu! Haka shima driver d’insa ya rasu sakamokon buguwar da yayi da kuma glass d’in da ya chakesa a ciki, mun yi dukkan iyaka bakin ƙoƙarinmu amma Allah ya karɓi abunsa.” A hankali Yassir, wanda ya fara ganin dishi-dishi, ya matsa kusa da Likitan ya dafa kafad’arshi tukunnan ya ce ‘’Doctor, Yashjub yana nan lafiya am man s h i ko??’’ Ya yi masa tambayar a rarrabe. Jinjina Kai Likitan ya yi kafin ya d’aura da cewa “yana wanchan d’akin, a nan muka ajjiye shi domin ya samu ya huta, an gama gyara Hannun nasa da duk wasu abubuwan da suka kamata a yi masa.’’ ‘’Alhamdulillah!” gada d’ayansu suka furta, cikin tsananin jin dad’i banda Yassir wanda wata kalar zufa ta shiga tsatstsafo masa kafin a hankali wani hawaye ya biyo ta idonshi guda d’aya, da sauri ya sunkuyar da kansa k’asa ya sa Hannu ya goge ya fara murmushi mai kamar dariya kafin a fili ya ce ‘’Alhamdulillah!’’ sai kuma ya d’ago ya kalli Likitan tukunna ya ce ’’za mu iya ganin shi??’’ ‘’Yes,sure!’’ Likitan ya sake bashi damar ganinsa a karo na biyu kafin ya kira wata nurse ya ce ‘’ta musu iso zuwa inda Yashjub ya ke’’. Daganan ya juya ya koma wajen Yasmeen zuciyarsa taff cike da mamakin yadda gaba d’ayansu suka nuna halin ko in kula game da rasuwar drivern Yashjub. Yana shiga ya tarar da Yasmeen ta na waya, da alama da familyn drivern take waya. Tana gamawa ta kallesa ta ce ‘’Sir! Wallahi na tsorata sosai, ashe ma ba abunda ya samu Ya Yash, Alhamdulillah bara in je in ganshi.’’ Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace “am sir….familyn deceased ɗin (iyalan marigayin) suna hanya, dan na ji yadda hankalinsu ya tashi a wayar na san daga yanzu zuwa ko wanne lokaci za mu iya ganinsu anan’’. Daga haka ta wuce ta fita. A d’akin da Yashjub ya ke suka tarar da Daddy da Yassira, dan office d’insu ya fi kusa da asibitin shiyasa suka riga su zuwa. Suna shiga Yahanasu ta tafi da gudu ta fad’a jikin Yash ta fashe da wani Irin kuka. Tun d’azu sai yanzu ya samu murmushi ya d’an sub’uce masa, a hankali ya d’an bubbuga bayanta alamun rarrashi. Cikin kuka ta d’ago ta shiga duddubashi tana kallon Hannun a hankali tace ‘’Allah ya ci gaba da kare ka a duk inda kake’’ Murmushi ya yi, ya ce ‘’Ameen, Allah ya kare mu gaba d’aya’’ Daga haka ya d’aga Kai ya fara bin su da kallo d’aya bayan d’aya. Duk matsowa suka yi suka yanyamesa suna yi mishi sannu. Yayi mamakin rashin ganin Kausar amman kawai sai ya basar a d’ayan b’angare na zuciyarsa kuma yana mai sake tabbatar da zarginshi akanta. Guri kowannensu ya samu ya zauna, aka shiga jimami kafin Daddy ya kalli Yahanasu ya ce ’’Likitocin sun fito daga wajen drivern??’’ Shiruu ta ɗan yi, sai daga baya tukunna ahankali ta girgiza Kai ta ce ’’ya rasu’’ ‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’ Yashjub da Daddy suka shiga maimaitawa. Daga haka d’akin ya yi shiruuu. Dan rasuwar drivern ta girgiza Yashjub ba kad’an ba. Kasa zama ma suka yi shi da Daddy har sai da suka je suka ganshi, a lokacin har nurses d’in sun rufesshi an toshe kunnuwa da hanci… Duk dauriya kalar ta Yash sai da ya yi hawaye, rai ba daɗi yayi masa addu’a tukunna suka koma d’akin da Yash d’in yake bayan sun ce “in iyalin nasa sun zo a yi musu magana.” Ko da suka koma d’akin ma, haka aka ci gaba da zaman jigum, kafin Yahanasu da Ummi suka ci gaba da jajanta al’amarin. Gyaran murya Daddy yayi kafin Ya ce ‘’Tsautsayi irin haka daman ya kan faru a irin wannan lokutan na shiga sabon fagen rayuwa’’ Duk nutsuwa suka yi suna sauraron shi yayinda shi kuma ya ci gaba da cewa “Na so dama yau in gaya muku, amman tunda gamu duk anan Alhamdulillah. InshaaAllah nan da sati biyu idan komai ya tafi dai-dai babu wata matsala to Za’a d’aura auren Yashjub! Hajiya Mama ma ta riga ta sani dan haka daga yanzu zuwa ko wanne lokaci in ta gayawa su Abhi za ku iya ganinsu, har da su Imam. Khadija ke da Saddik’a idan akwai walima da taron da kuke buk’ata za ku yi sai ku yi min magana in samu in sallameku da wuri.’’ Daddy yana dasa aya cikin tsananin murna Munirat ta ce ’’Allah ya sanya alkhairi’’ Ta fad’i hakan fuskarta d’auke da faffad’an murmushi Sai kuma ta yi shiruu da sauri ganin babu wanda ya ce komai sai ita sannan tsabar yadda da fad’a cikin murna da kuma yadda duk aka yi tsit sai muryar tata ta fita da ƙarfi sosai ta cika d’akin. A b’angaren su Yassira kuwa, tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wadda a take a lokacin bata shiga cikin maɗaukakin tashin hankali ba…sun san da maganar ba wai basu sani ba amman kuma fad’a musu d’in da Daddy ya yi a yanzun ya sanya suka sake tabbatar da dahir d’in maganar wanda hakan ya sanya damuwar da suke a ciki tun farkon lokacin da suka ji zancen auren ta sake hauhawa. Murmushi Ummi ta yi tukunna ta ce “MashaaAllah Yashjub, na yi matuk’ar farin ciki….dukda bamu da isashshen lokaci amman in sha Allah za mu zage dantse a yi hidima sosai. Na ji dad’i kwarai Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya ya sa Matarka ce har abada har a gidan aljannah’’ Murmushi ya yi, a hankali kuma sai ya ce ‘’Ameen Ummi, na gode.’’ Kafin ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zubasu a kan Mommy dai-dai itama shi ɗin take kallo tana nazartar fara’ar da yake ta zubawa. Diriricewa ta yi, dan haka sai ta hau kame-kame kafin ta ce ’’ni na ma rasa Bakin magana’’ Shiru Daddy, Ummi, Munirat da Yashjub sukayi suna tsammanin su ji ta d’aura da wani abun amman sai suka ji ta yi shiru, dan haka duk sai aka zuba mata idanu. So take ta yi magana amman da ikon Allah sai ta kasa, gashi dama kuma tama rasa me za ta ce ne shiyasa kawai sai ta hau wasa da bakin mayafinta kamar wata Yarinya. Girgiza Kai kawai Daddy ya yi tukunna a hankali ya ce ‘’Hmm’’ Cikin son kawar da yanayin, Ummi ta ce ‘’na san yanzun ba lokacin da ya dace bane duba da kasancewarka a gadon jinya amman kuma duba da yanayi na lokaci na ga yakamata ko zuwa anjima ne idan ka d’an huta sai mu fara maganar had’a lefe… dan na san Maza ba ku iya zab’ar test d’in da mu Mata muke so ba. Ka yi mana magana, sai in taya Mominka tunda bamu da isheshshen lokaci.’’ Murmushi Yashjub ya yi kafin finally ya d’auke idanuwanshi daga kan Mommy ya mayar kan Ummi tukunna ya ce ’’am..actually Ummi Yahanasu ce za ta had’a, na ma tambayeta tun-tuni…’’ Cikin katse shi Yasmeen ta ce’’ au,wato Yahanasu ta riga ta san maganar auren naka ahead of us(tun kafin mu mu sani) kenan, ko Yaha??’’ Ta k’arashe maganar tata tana mai kallon Yahanasu da alamun tambaya. Wani kallo Yash ya d’ago ya watsawa Yasmeen ɗin wanda hakan yasanyata ta kawar da kanta gefe. Yahanasu tana shirin yin magana Ya’isha ta sake cewa ‘’Yaha ba ki amsa tambayar Yasmeen ba’’ Sai kuma ta kalli Yash ta ce ‘’I mean no disrespect(ba wai da nufin raina ba) amma a ganina Allah fa ya baka ƙanne Mata very classy! Kuma wayayyu har kusan mu shidda, dan haka mai yasa za ka zaɓi Yahanasu wadda ba ta san komai ba a matsayin wadda za ta haɗa maka lefe?? No offense (kada ku ji haushi) Amma duk nan ai mun san bata da wayewar mu, gashi bata son shiga mutane tunda ita haka nan yanayi da ɗabiarta suke. Wannan fa shine biki na farko da za a yi a family d’in nan so inaga bai kamata mu bawa kanmu kunya ta ko wacce hanya ba. Sam bai kamata a bar Yaha ta je ta ta had’o abunda bai kamata ba gudun kar ta ja mana jin kunya, tunda na san itama Yarinyar da za ka auran dole ƴar manya ce. Anyways, raina ya riga ya ɓaci tun farko da na fahimci ’sai da ka fara gaya mata har kuka fara had’a lefe tukunna mu muka sani’ Dan haka a gaskiya ba zan iya ci gaba da zama a ɗakin nan ba! bara kawai in wuce saboda kar raina ya ci gaba da ɓaci in je in fad’i wata maganar da za ace na yi rashin kunya!!’’ Shiruu kawai Yashjub ya yi ya zubawa Ya’isha ido…ranar da Najeeb ya fito mishi a Mutum ya ce masa ’’Ya’isha bata da kunya, kullum rashin kunyarta k’aruwa take yi’’ dukda ya san tsiwa nature d’inta ne dama amma sai da ya ɗin ji zafin Najeeb ɗin! Yau kam tabbas ya tabbatar, dan gashi shi a karon kanshi Kansa ya kasa ɗaukar yadda take magana da kuma attitude d’inta, sam babu shayi ko alamun girmamawa a tare da ita. Muryar Ummi ce ta katse mishi tunani jin cikin kwantar da murya tana cewa “Ya’isha wa ya ce miki ta san maganar kafin ki sani? Ai cewa ya yi ita yakeso ta had’a kawai, bai riga ya ce ya bata ba, bayaga hakan ma ko ta sani ɗin ai itace Babba kuma naga kamar ya fi shak’uwa da ita’’. Cikin katseta Ya’ishan ta d’aga mata Hannu ta ce “Ummi Plss’’ Sannan ta juya ta kalli Yashjub ta ce ’’Allah ya sanya alkhairi Allah ya baku zaman lafiya Allah ya baka lafiya’’ Daga haka ta juya ta fita fuuu kamar zata tashi sama. Tsayawa kawai Yashjub ya yi yana kallon inda ta bi ta fita a ransa ya raya’wato dai yanzu ita bata tsoro ko shakkar kowa’ Yassir dama neman hanyar fecewa yake yi, dan haka da sauri ya samu ya juya shima ya fice hankalinsa a mugun tashe. Ajiyar zuciya Yasmeen ta sauk’e kafin itama ta mik’e ta ce ’’nima bara in bi bayan Ya’isha mu tafi tare.’’ Har ta yi gaba sai kuma ta juyo ta ce “Ummi dan Allah nan gaba kar ki sake cewa wani wai Yash ya fi shak’uwa da Yahanasu ko kuma wani abun makamancin hakan! Saboda ba haka family d’in nan yake ba…babu banbanci a tsakanin sibling d’in gidan Daddy, duk ɗinmu ɗaya ne kuma iri ɗaya ne, duk kanmu munnshaƙu da juna equally….. Iyakar faɗin hakan ma da kikayi ya soosa min rai’’ A hankali ta kalli Yashjub sannan ta ce ’’ina fatan za ki yi hasashen kalar zafin da zan ji idan aka yi treating d’ina hakan sannan aka nuna bani da wani muhimmanci.” Daga haka ta ce masa “Allah ya ƙara sauƙi Allah ya baka lafiya” Tana gama fad’in haka ta juya ta fita. Dafe Kai Ummi ta yi tana dana sanin kula su Yasmeen da ta yi a yau ɗin bayan ta yi wa kanta alk’awarin fita a harkar su har abada, Wataƙilan kawai dan tana cikin farin ciki ne shiyasa ta manta ta biye su..dan har ga Allah ta ji dad’in maganar auren Yashjub, ta san ko wacece Yarinyar to tabbbas tana da hankali da tarbiyya dan a yadda Yashjub yake tana sa yaƙinin ba zai d’auko musu ballagaza ba da izinin Allah, tun a bakin Daddy take jin labarin Yashjub lokacin shi yana uku, da kuma ya dawo ya fara aiki da su nan ta tabbatar tabbas Yash Mutum ne asalin jajirtacce me hankali wayo nutsuwa neman na kanshi me mutunci kamala da sanin ya kamata…………. …..ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya ce ’’Yash! Da gaske su ke Yahanasu ta san maganar auren nan kafin su??’’ Lumshe idanu yayi ya bud’e kafin ya ce ’’Daddy plss mana….’’ Cikin d’an fushi Daddy ya ce ‘’tambayar ka nake yi, ka bani amsata kawai!’’ A hankali Yashjub ya jinjina Kai kafin ya ce ’’eh’’ Shiruuu Daddy yayi kafin chan ya kawar da kanshi gefe kawai. A hankali Mommy ta matsa inda Yash d’in yake ta dafa kanshi tukunna ta ce ’’Allah ya ci gaba da kare ka a duk inda kake, Allah ya baka sauk’i’’ Tana gama fad’in haka ta juya ta fice… Hatta Yadira bata ci gaba da zama a d’akin ba dan Mommy tana fita suma duk suka bi bayanta suka fice. Yassira ce kawai ta tsaya sai Ummi da Munirat da Daddy da Yahanasu. Cikin sanyin jiki, Yassira ta matso kusa da su ta ce ’’Ya Yash,aure zaka yi, new member zaka kawo mana! Shin tayaya kake tunanin za ta yi respecting d’in mu a matsayinmu na ƙannenka idan kai da kanka ka nuna mata akwai banbanci a tsakaninmu?. Aƙalla idan mu Mata baka gaya mana ba ai ya kamata ka gayawa Yassir tunda shima Namiji ne kamar kai, ya kamata ka fara jan shi a jikinka. Mata, surukan gida fa…idan aka auro su, su ne suke tarwatsa kan family musamman idan suka ga akwai hanya mafi sauk’i da za su bi su yi hakan….. Na san za ka ce wannan k’aramin abu ne amma mu a wajen mu da kuma yadda yanayin rayuwa yake sam wannan ba k’aramin abu baneba. Kamata yayi idan aka fara auratayya to mu had’e kawununamu mu yi sticking together kar mu bawa kowa damar shiga tsakaninmu….. Amman a yadda ka fara nunawa ɗinnan tun yanzu ta fahimci Yahanasu ce favorite d’inka ita ka fi so kaf cikimu To fa idan(matar taka) ta zo Yahanasun kad’ai za ta ja a jikinta, mu kuma ba za ta bamu muhimmanci ba wanda hakan ba k’aramin matsala zai janyo ba. Dan Allah ka yi la’akari sannan ka duba maganata, idan kuma na b’ata maka rai to ka yi hak’uri amma dan Allah ko ba komai ka yi k’ok’ari ka gyara tsakaninka da Mommy da kuma Yassir kafin Matar nan ta zo ta fahimci wani abun. Ka duba fa ka ga duk kowa ya ji haushi ya fice, Mommy fa ko Allah ya sanya alkhairi bata ce ba, ka san maanar hakan kuwa? wallahi duk lalacewa dole sai da albarkar ta. Dan Allah kar ka bari Matarka ta fahimci kana da issue da su, na ji na yarda mu ci albarkacinta ka jawo Yassir Jikinka sannan ka dinga nunawa duniya Mommy itace ta haifeka Plss Ya Yash dan Allah.’’ A hankali ta juya ta kalli Daddy ta ce ’’Daddy ka sa Baki’’. Daga haka ta juya ta fita itama. Ganin duk sun fita kuma kamar Daddyn yanaso ya yi magana da su Yash d’in ne yasanya Ummi ta mik’e ta ce ’’akwai abunda kake sha’awar ci? Ko in dafa maka komai ma??’’ Murmushi yayi ya ce “ ‘’Anything Ummi, tnx’’ Allah ya k’ara sauk’i suka yi mishi daga haka suka juya suka fita ita da Munirat. Suna fita Daddy ya mik’e daga inda yake ya k’araso ya zauna akan kujerar da ta ke kusa da gadon, inda Yash yake kishingid’e Yahanasu kuma a zaune. Shiruu duk suka yi kafin Daddy ya kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa “Yashjub, abunda Yassira ta fad’a gaskiya ne’’ Lumshe idanu Yash ya yi kafin ya bud’e a hankali ya ce ’’haba Daddy, kana jin maganar tasu fa ka san kawai shirmen Mata ne’’ ‘’Koma akwai shirmen Matan to gaskiya ta fi yawa a ciki’’ Daddy ya bashi amsa cikin katseshi kafin ya d’aura da cewa “ba ka kyauta ba! From today onwards(daga yau har abada) bana son ka bada ƙofar da wata zata gane akwai banbanci tsakanin y’an uwanka, inaso ka nuna mata duk d’aya suke a wajen ka sanann ka nuna mata mahimmancin su da mu kanmu a wajenka!!! Hakan shine dai-dai, kuma kamar yadda Yassira ta fad’a hakan ne zai sa ba zata samu damar shiga tsakanin ku ba’’ Kamar Yashjub zai yi kuka dan takaici cikin b’ata fuska ya ce ‘’Haba Daddy, you sound exactly like them(ya kaima ka ke magana kamar su), yanzu ta Ina Manubiya…’’ Cikin katseshi ya ce ‘’Bana son musu’’ A hankali Yahanasu ma ta ce ‘’Yashjub, ka yi abunda sukeso a samu a zauna lafiya’’ Cikin jin dad’in abunda ta ce ɗin Daddy ya ce ’’yauwwa y’ar albarka, kishi a tsakanin y’an uwa bashida dad’i sam kuma ba zan lamuntaba, dan haka kar ka bada ƙofar da za a soma shi!!! Dan kar ka sha mamaki idan hakan da ka yi ya sanyawa ita Yahanasun bak’in jini. Meyasa ka ji ana cewa iyaye kar su ke nuna wanda suka fi so a tsakanin y’ay’an su?’’ Bai jira jin amsar su ba ya cigaba da cewa ‘’saboda irin haka!. Kuma aure ya zo a k’urarren lokaci mahaifiyarka kanta bata sani ba ni kaina ina tunanin ta yadda za su d’auki abun ba tare da sun ji wani iri ba sannan kuma kwatsam ka zo da wannan al’amari!? Haba, dole a ji haushi mana Yashjub. Umarni nake baka, daga yau bana so in sake jin komai, kana ji Ummi har ta fara cewa kun fi shak’uwa kai da Yahanasu Ita da ta zo jiya jiya har ta fahimta, dan haka kamar yadda suka buk’ata ka gyara tun kafin itama ta zo ta fahimci wani abun azo ana samun matsala. Sannan whatever it is (ko ma menene) da yake going on a tsakaninka Kai da Mahaifiyarka inaso ka gyara shi da wur wuri ku shirya, in dai har kana son albarka kuma kanaso nima mu shirya ni da kai!!! uwa ba abar wasa bace ba! sabuwar rayuwa za ka shiga! Ka je ku shirya ka nemi albarkarta’’ A hankali Yashjub ya ce ‘’Tam, in sha Allah Daddy’’ Shiruu d’akin ya kuma yi kafin chan Daddy ya furzar da numfashi ya ce ’’sai maganar Yassir, his company…wallahi har bana so in yi tunanin abun, ban san Ina ya kai kuɗaɗen ba komai ya tsaya chak! Sannan contract d’in ma da ya d’an samu shima abun ya ƙi ya yiu kuma laifinsa ne dan sam bai d’auki abun da mahimmanci ba. Da farko da nace zan zuba masa ido ne kawai in kyale shi amma duk yadda na so yin hakan na gagara, he is still my son(Saboda shi ɗin ɗana ne)’’ Daddy ya k’arashe maganar tasa a hankali yana mai fesar da iska kafin ya cigaba da cewa’’ni dai na riga na gama sakawa araina ba zan sake bashi jari ba, tunda bai san ciwon kanshi ba, amman kai za ka iya idan ka ga dama ba wai tilasss nakeyi maka ba sai In ka ga dama.’’ Ajiyar zuciya Yashjub ya sauk’e kafin ya ce ’’akwai abunda nake shirya mishi, aikin da nake yi d’azu da safe ma kenan shiyasa na zauna a doguwar kujerar baya…..’’ BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 02* Shiruu ya yi kafin chan ya fesar da iska ya ce ’’sabon company ne na bud’e masa, na riga na gama registerring da CAC tun-tuni, na biya komai na karb’a har certificate. Dama wani d’an information suka bid’a kuma shima na tura a d’azun. Na bud’e masa company d’in ne domin ya samu ya dinga shigo da k’ofofi windows bulbs da duk wasu kayan gine-gine dai nake ganin dacewar ya fara karɓar kwangilar su, naga abun it’s easier (yafi sauƙi) kuma in a fancy way tunda za’a dinga yawan tafiye-tafiye wanda na san abunda ya fi so ɗin kenan, gashi kuma babu wahala… In sha Allah ni da Uncle ɗin Najeeb za mu harhaɗa shi da Mutane da zarar ya fara, zai samu alkairi a ciki sosai in sha Allah kuma kaga yanada ilimin architect so in yanada wayo zai iya cin moriyar hakan ya dinga samun riba biyu, tunda wannan aikin dai ba zai dinga cinye masa lokaci da strength ɗinsa ba, kuma dama na san wahalar ce baya so. Already yanada building d’inshi, dan haka sai ya fara anan ginin ɗin dan adress na wajen ma na saka. Tunda yanzu ya fara na san wajen zai ishe sa kafin mu ga abunda gaba za ta haifar. Amman Daddy ka yi hak’uri ka yi mishi magana, ka ja mishi Kunne. Ka ga dai yadda ya mayar da wanchan campany d’in zane-zanen nasa, na san wannan babu wani wahala kowa ma zai iya But it’s Yassir that we are talking about here (amma magana ce mu ke yi akan Yassir) dan haka sai an ja masa kunne akan ya maida hankali.’’ A hankali Daddy yana jin tsananin k’aunar Yash d’in tana sake ratsa shi ya ce ‘’inshaaAllah Yash, zan ja masa Kunne sosai’’ kasa hak’ura ya yi sai da ya ce ‘’na ji dad’i sosai da ka damu da d’an uwanka har haka.. Allah ya yi maka albarka, Allah ya sake had’a min kanku. Amman naga kamar har yanzu bakwa shiri da shi tun abun nan da ya faru ranar chan a gida’’ Murmushi Yashjub ya yi kafin ya ce ’’eh!baya min magana, he’s still mad at me (har yanzu yana fushi da ni) shiyasa dama na bari akan sai na gama komai sai in had’a a lokaci guda in basa takardun tare da sabuwar motar da na siya masa ta neman sulhu. Murmushi Daddy yayi kafin yace’’Allah ya muku albarka’’ Yana mai jin wani irin farin ciki yana ratsashi. A tare duk suka had’a Baki suka ce ‘’Ameen’’ Daganan suka shiga tattaunawa akan yadda auren Yashjub d’in zai kasance…da farko Daddy cewa ya yi ko za a d’an k’ara lokaci tunda bashi da lafiya amma kalar zaburar da Yash d’in ya yi saida ya sakasu dariya shikuma ya sa kanshi a kunya dan haka ya ja Bakinshi ya yi gum! bai sake cewa komai ba, a ransa kuma yana mamakin yadda Manubiya ta maida shi. Daddy dama ya san maganar gida ba shi ne zai yi ba tunda abun na masu yi ne, aikuwa ilai yana yin maganar Yashjub ya ce “ya gama da wannan ma.” Sun tattauna sosai tukunna Daddy ya tafi bayan Yashjub ya yi mishi alk’awarin shiryawa da Mommy da zarar ya koma gida InshaaAllah, dan tuni dama ya ji ya d’an fara hucewa akan abunda ta yi masa, ga kuma maganar da suka yi da Manubiya kuma yanzu kam tunda har Daddy ma ya sa Baki inshaaAllah zai je su shirya ya bata hak’uri dukda kuwa itace mai laifi. Sai da Daddy ya fita tukunna Yashjub ya sanar da Yahanasu cewa ’kunce masa tayoyin mota fa akayi’ Dan sam baya so kowa ya sani ba tare da ya gama sanin abun yi ba. Hankalin Yahanasu ba k’aramin tashi ya yi ba gashi ya ce mata ‘’ta yi shiru ta tsaya tukunna kar a fara bincike har sai ya gama deciding akan ‘zai d’au mataki ko ba zai d’auka ba’ tukunna ’’. Sai da yayi da gaske tukunna ya kawar da batun yana dana sanin gaya mata dan in da ace ya san haka zata d’aga hankalinta to da shiru zai yi….. Cikin son kawar mata da tunanin ya sake sako maganar auren nasa, ta fahimci abunda yake son yi shiyasa kawai itama ta d’an sake ta biye masa ba wai dan fargaba, tashin hankali tare da tunanin abun sun barta ba. Cikin sanyin jiki Yashjub ya fesar da numfashi ya shiga tunani… ‘abu ya kankama sai shirye-shirye ake yi amma shi damuwarsa d’aya bai san ya za su kaya da shi da amaryar tashi ba dan a cikin kwana biyun nan ya lura gaba d’aya a k’ule take da shi jiya kamar za ta yi masa kuka wai kaff su Ya Musbah da Inna gani akeyi kamar auren takeso da wuri shiyasa ta ce a kira Ya Musbah da wurwuri ita dai gaskiya in b….!.’ ‘’Inaga gara mu ci gaba da had’a kayan ni da su Ummi ko?’’ Muryar Yahanasu ta katsewa Yashjub tunani. Girgiza Kai kawai Yashjub ya yi kafin ya ce ‘’kar ki damu, suma za su yi wani abun important, had’a lefe aikinki ne ke kad’ai…’’ har ya d’an lumshe idanunsa ya sake kishingid’ewa sai kuma ya bud’e ya kalleta ya ce ’’Yaha! A tunaninki Kausar za ta iya kasheni??’’ Shiruuu ta yi, ta dad’e tana nazari kafin ta sauk’e ajiyar zuciya ta ce ’’gaskiya a’a!. Amma mai yasa ka yi tunanin hakan?” Ta basa amsa tare da jeho masa tata tambayar. Ajiyar a zuciya ya sauk’e kafin yace “kawai dai…kin san na fad’a miki maganar da na ji itada Mommy suna yi a wachchar ranar da kuma abubuwa da yadda ta ke ta yi min. Da suka had’u da Manubiya kuma na ga tashin hankali a Idanunta ba kad’an ba…a ganina a nawa tunanin da nake yi shine ‘Ta ga ba za ta iya karawa ko ta kada Manubiya ba shiyasa ta yanke shawarar ta kasheni kenan kowa ya rasa’ ko ya abun yake?? I’m confused…’’ Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin ta ce ’’ka tabbatar tayoyin kunce su akayi ko?’’ Jin jina Kai yayi kafin ya ce ’’na tabbatar Yaha” ‘’To ka bari a yi bincike mana Yash’’ Ya jima yana nazari kafin ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an furzar da iska tukunna a hankali ya ce ’’i don’t want to dig up more dirt….ba na so garin bincike in je in bincikowa kaina abunda zai tarwatsa min farin ciki saboda kin ji da Kunnenki yanzun nan Daddy ya gama cewa yana buk’atar zaman lafiya a tsakanina da Mommy..A ganina indai har Mommy za ta iya rufe ido ta goyawa Kausar baya su ci amanar Yassir sannan kuma ta so ta k’ulla aurenta da ni to ba na jin akwai abunda ba za ta iya goya mata baya ido rufe akai ba.’’ Da sauri Yahansu ta ce ’’no no no no Yash! Mommy ba za ta tab’a supporting Kausar ta kashe ka ba’’ Cikin tarar numfashi ta yace’’Yeah, na san da wannan, ba wai hakan na ke nufi ba amma na san idan aka fara bincike, to shakka babu mommy za ta rufe ido ne ta bi bayan Kausar, kuma na san ba zata tab’a bari ayi interrogating d’inta ba!! Ni kuma in dai har hakan ta faru to daga ranar ni da Mommy mun raba gari kenan har abada saboda Zuciya da Kaina ba za su iya jurar ganin ta na goyon bayan wanda ya so ya kasheni ba! Kinga kuwa babu zaman lafiya kenan kuma ni kaina na san daga hakan na janyowa kaina bala’i ne saboda fushin uwa ma kad’ai fitina ne ballantana kuma ince zan raba gari da ita.” Wata zazzaafar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ci gaba da cewa “Kamar yadda na gaya miki da farko, gara kawai a barshi dan ba na so in bincikowa kaina abunda zai zamto silar damuna ko ma ya tarwatsani…. Kawai daga yanzu zan dinga kiyayewa ina kula in kuma yi takatsantsan, sannan in sha Allah zan zauna da ita lafiya… Inaga kawai gara in haƙura in yarda sannan in rungumi cewa ‘mahaifiyar da ta haifeni bata wani damu da ni ba!’…sam ban yi sa’a ta wannan fannin ba.’’ A hankali Yahanasu ta sunkuyar da kanta k’asa muryarta na d’an rawa cikin son kwantar mishi da hankali da kawar mishi da tunanin ta ce ‘’Komai zai yi dai dai, komai zai gyaru…..it will be okay, we all will be okay.’’ ‘‘InshaaAllah’’ya ce Daganan duk suka yi shiru …. Sunanan zaune, familyn drivern nasa suka iso, dan haka ya mik’e ya fita… Shi bai samu zuwa har k’auyen ba, Daddy da wasu daga cikin drebobinsu waenda su ka zo asibitinne suka bi Mutanen har chan kauyen da baifi tafiyar mintuna talatin ba, inda za’a yi masa sutura a binne sa. Bai dad’e da dawowa d’akin ba Likita ya shigo ya sake duba shi, daga nan ya yi masa allurar bacci. Ba shi ya tashi ba sai da su Ummi suka dawo ita da Munirat da abinci nik’i-nik’i. Ya ji zafin rashin ganin su Ya’isha amman kamar yadda su Daddy suka ce dukda ya san ba su fi sa gaskiya ba amma shima kawai sai ya bar abun akan ‘sun ji haushin fifita Yahanasu da yayi akan su ne’ shiyasa suka yi fushi da shi, idan ba dan hakan ba da wallahi wannan attitude d’in da suka bashi shikuma sai ya nuna musu origin d’in attitude tunda basu da kunya. Sallah ya fara yi tukunna ya ci abinci kad’an da taimakon d’uren Yahanasu….. Ranar Yashjub ya bawa su Ummi mamaki dan ba su yi tunanin yana magana har haka ba, abu d’aya da suka fahimta tashi d’aya shine ‘In dai kana buk’atar ya yi maka hira sosai da fara’a to ka sako maganar Manubiya’, dan haka suka samu abunyi kuwa, haka nan suka dinga hirarta, dama kuma suma ɗin abunda suke so kenan. Ya kuwa ji dad’in yadda su ke k’aunar Manubiyan tun kafin su ganta Babban burinshi a yanzu shine su Mommy ma su k’aunaci Manubiya kamar yadda su Ummi suke k’aunar ta. Tabbas ya na son y’an uwanshi ko ba komai jininshi ne su ɗin, Bai san wanne kalar shed’an da sabon iskanci ne ya shiga kwakwalwarsu suka fito da wannan shirmen ba amma it definitely has to end(dole ma su daina), bai damu da wacce hanya zai bi ba ta rarrashi ko ta k’arfi iyakar abunda ya sani shine ‘it has to end’!. …. Dakyar Munirat ta rabu da shi ta hak’ura, dan da itama cewa ta yi sai an kira Manu ta gaishe ta. Shi kuma Yash baya so ya kira ta, sai zuwa gobe, gudun kar ta ji muryarsa wani iri ta fahimci ba shi da lafiya, dan baya so ma ta sani balle hankalinta ya tashi. Yahanasu ta so ta kwana da shi amman ya tubure akan ‘shi ba Yaro bane, kuma ai ciwon nashi ba mai tsanani bane’ Ba yadda suka iya haka suka hak’ura suka shirya suka tafi. Suna zuwa gida, Yahanasu ta tura masa wani a cikin masu gadin su, shi ya zo ya kwana da shi. •••••• A b’angaren su Manubiya kuwa, ganin abun ya fi k’arfinsu kuma ba yadda za su yi ne ya sanya su Ya Nafi’u suka samu dattawan layin akan maganar su Uncle. Dakyar kuwa aka samu aka shawo kan su Baba Habu da Uncle da kaka mallan wanda ya fi kowa zak’ewa akan sai su Baba sun tashi a gidan…..da kyar suka hak’ura bayan an yanke an kuma ja layi akan ‘Babu ruwan kowa da kowa! Kuma ko kallon banza in su Manubiya suka sake yi wa wani a cikin Ƴaƴan gidan to sai sun fuskanci shariah.’ Dayawa daga cikin dattawan tun a kallo ɗaya Baba ya ke basu tausayi, dan duk wani mai imani in ya ganshi a wannan lokacin to dole ya tausaya masa saboda duk ya yi wani iri gashi ya zama so silent, ko a wajen meeting d’in ma ‘’To’’ kawai ya dinga cewa. Kuma ko bai fito ya faɗa ba, ana ganinshi kai tsaye za a fahimci Abunda su Uncle sukayi masa ya girgizashi matuk’a…….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 03* Yassir yana fita daga asibitin, direct gida ya nufa dan yana buk’atar ya ganewa idanunsa wanne hali Kausar take ciki…. Wanda dole ya san zai kasance ɗaya daga cikin biyu ‘Ko dai tana chan ta b’oye kanta tanata kuka' ko kuma dai ‘bata damu da Yashjub d’in ba shiyasa bai ganta a asibitin ba….’ A b’angaren Kausar kuwa, sai a wannan lokacin ne ta samu maganin baccin da ta sha ya sake ta. Dan haka ta mik’e ta nufi toilet, tana cikin wanke fuskarta ta fara jiyo muryar Baaba Larai a cikin d’akin nata tana cewa “Kausar wai baccin uban me kike yi ne haka tun d’azu…’’ Dan haka ta yi maza ta k’arasa wanke fuskar tata ta fito. ‘’Lafiyarki kuwa??’’ Muryar Baba Larai ta katse mata tunanin da ta fito tana yi. A hankali ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ’’na d’an sha maganin bacci over dose ne, shiyasa har yanzu kaina yake juyawa’’ Girgiza Kai Baba Larai ta yi kafin tace “Ni dai fa ince, na ga ban ga kin fito an tafi da ke ba’’ ‘’ina?’’ Kausar ta yi mata tambayar cikin katseta. ‘’Yashjub ne yayi hatsari, shine aka tafi asibiti tun d…..’’ Da k’arfi Kausar d’in tace “what!!!’’ Cikin katseta, sai kuma ta tafi luuu za ta fad’i. Da sauri Baba Larai ta tarota a rikice ta ce “relax, ba abunda ya same shi sai gocewar k’ashi kawai a Hannu, amma Baba Iliya kam an amsa kira’’ Ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e, da kyar ta k’arasa bakin gadonta ta zauna kafin tana haki da kyar ta samu ta iya cewa ‘’ba shi yake driving d’in ba kenan?’’ sai kuma ta sake mik’ewa, ganin tana shirin zubewa yasa ta ce ’’Baaaba, d’an rik’e ni, jiri nakeyi,bari in je asibitin, ki zo ki taya ni sauk’a’’. Matsowa Baba Larai ta yi ta rik’eta sannan ta ce ‘’ki nutsu, su Mommy sun kirani yanzu suma suna hanya, ki nutsu sosai mu jira ta dawo tukunna..’’ Cikin fushi ta hankad’e ta tukunna ta ce ’’Baaba kin san me kike fad’a kuwa? In nutsu kamar yaya? Yashjub ne fa ba lafiya yana kwance ya yi hatsari shine kike ce min wani in nutsu??’’. ‘’Shikenan.Bismillah’’ Baaba Larai tace da ita daga haka ta juya ta fita. Yassira Kausar d’in ta kira, domin ta tambayeta sunan asibitin amma kamar yadda Baaba Larai ta ce mata itama Yasirar haka ta ce “ta yi hak’uri ba sai ta je ba, suna hanya suma, akwai d’an case ne dan haka in aka ga ita ta je abun zai rinchab’e. Kuma don ta sani, yanzunnan suma Yasmeen take ce musu ta ji a bakin likitan yana cewa wa’enda suka kawo su Yash d’in sun ce wai kamar kunce tayoyin motar tasa akayi.’’ Tashi d’aya hankalinta ya sake tashi, ko sallamar da Yassira ta yi mata ma ba ta ji ba! Ji ta yi kawai ta kashe wayar…. Zato zunubi amma tunani da zarginta tashi d’aya akan Yassir ya dira!! Dan a lissafinta in ba shi ɗin ba ta san kaf gidan babu wanda zai yi wannan aika-aikar tunda dai su babu wanda ya ke shigo musu gida, bayaga haka kuma in ba black snake wanda suka tab’a yin fad’a da Yash d’in ba ta san Yash bashi da wani Abokin fad’a, yo yaushe ma ya dawo k’asar dududu. To amman mai yasa Yassir zai yi haka saboda kishi ko me? Tabbas dama ta san yana zargin ta, ta san bai gama yarda da ita ba, amma sam ba ta yi tunanin abun nasa ya kai har haka ba. Tabɗijam!! Ai kuwa in dai har hakan ne to aiki ya ganta! Dan dole ta tashi ta d’au mataki saboda al’amarin na Yassir ya fara zama wani abun daban…ba ta riga ta tabbatar ba amma muddin ta gama tabbatarwa shi ne to fa ba za ta zauna ta zuba masa ido tana gani yake wasa da rayuwar Yashjub ba, shirmen nasa ya yi yawa…… A hankali tana Jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa ta nemi guri ta kwanta, ta lumshe idanunta, a take hawaye suka shiga sintiri akan farar fuskarta… Har ga Allah ba ta san yadda za ta yi da Yassir wanda ya zame mata k’adangaren bakin tulu ba, gashi ba ta Isa ta yi wani abun ko ta tunkare shi da maganar ba tunda ta lura abunda ya ke expecting daga gareta kenan. Tashi d’aya ciwon Kan nata ya sake hauhawa, in banda sarawa ba abunda kanta yake yi, shiyasa ta yi shiruu ta kwanta kawai ta lumshe idanuwanta………. Ba ta dad’e da gama waya da su ba suka dawo gaba d’ayansu, kafin kowa ya shiga inda take Yassir ya shiga shiyasa su Yasira suka wuce d’akunansu kawai. Ya yi mamakin ganinta a kwance, hankalinta kwance! Amman dai fuskarta ta kumbura ta yi jaa wanda hakan ya ke nuni da kuka ta yi. Ƙarasawa ya yi inda take ya d’an zauna a gefen gadon a hankali ya ce ‘’Kausar’’ Da kyar ta samu ta danne Zuciyarta wadda ta ke yunk’uro mata…….. …A da, da farko ta san tana son Yassir, da Yashjub ya dawo gaba d’aya sai ta ji Yassir ya fita a ranta, dan tashi daya k’aunar Yashjub ta ci k’arfin komai a zuciyarta! A yanzu kuwa a halinda ake ciki tabbas ta tsani Yassir, tsana ba ta wasa ba! Dan ya yi mata kane-kane ya tare gaba ya tare baya ya hana ta sakat sannan wannan zargin da ta fara akansa yasanya ta sake jin tsanar sa ta nunku a zuciyarta, kuma indai har zargin ya tabbata to ba ta jin akwai wanda za ta tsana sama da Yassir a kaff fad’in duniyar nan… Da kyar! Ta taushi zuciyarta, ta d’an bud’e idanunta kad’an. Suna had’a ido da shi ta yi murmushi, a hankali ta d’an miƙe daga kwancen ta jingina a bakin gadon ta ce “Baby!’’. Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Yassir, har sai da ta kai shi ga sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciyar, kafin ya sake matsawa kusa da ita ya ruk’o Hannunta ahankali yana kallon cikin idanunta saboda ƙoƙarin ya fahimci yanayin da za ta shiga ya ce “ban gan ki a asibiti ba, maiyasa??’’ K’ura masa idanu itama ta yi, kafin da kyar ta samu ta iya cewa “I’ve better things to do(ina da abubuwan da su ka fiye mini zuwa asibitin mahimmanci), bayaga hakan ai ba kai ne ka yi hatsarin ba, Bare har in damu kai na.’’ Wani kalar murmushi ta ga ya yi kafin ya ce ’’kalamanki suna nufin kin san Yashjub ya yi accident, amma ba ki damu ma ki je ki duba shi ba, ko??’’ Wani k’ululun bak’in ciki Kausar ta had’iye, tana jin wani kalar takaici yana sake lullub’e ta…ji take kamar ta yi tsalle ta damk’i wuyansa har sai ta ga ya daina numfashi tukunna ta cikashi. Zuwa yanzu ta gama tabbatarwa Yassir ne ya kwance tayoyin motar Yashjub musamman ma da ta tuna yadda a jiyan ya ƙi barinta ta kwana a d’akinshi, dama tun jiyan taketa sak’e-sak’e a ranta game da hakan tana so ta fahimci what he is up to(me ya ke shiryawa)…. ‘’Don’t you care about him (Shin Ba ki damu da shi bane)??’’ Ya sake jeho mata tambayar still yana kallon cikin idanunta. ‘Wato saboda ya na so ya fahimci ko tana son Yashjub shiyasa ya yi wannan haukar kenan??’ Kausar ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba, kafin da kyar ta ce ’’kamar yadda na gama gaya maka yanzunnan Yassir ‘Ina da abubuwan da su ka fiye mini zuwa asibitin mahimmanci’ Misali; bacci, hutawa… Duk sun fiye mini in kwashi jiki in tafi dubashi” Ta fad’a mishi hakan tana mai kawar da kanta gefe, a ranta ta na aiyyana ’dole ta yi k’ok’ari ta danne kanta, ta yi tunani mai kyau, da taku mai kyau, dan in dai ta bari Yassir ya fahimci wani abun tou daga ita har Yashjub rayuwar su tana cikin hatsari, dan ta lura Yassir ya haukace’ Matsowa kusa da ita ya yi sosai ya sa Hannu ya kamo fuskarta ya juyo da ita saitin tasa daff da shi tukunna ya ce ‘’Mai yasa to ki ka yi kuka? Yadda idanunki da fuskanki su ka yi ɗinnan ya tabbatar min da kuka kika yi.’’ Lumshe idanun nata ta yi ta bud’e tukunna ta ce ’’ba ni da lafiya’’ Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘’Kausar! Allah dai ya sa ba ƙarya ki ke yi min ba, umm???…… ‘’ A hankali tace ‘’na ce maka bani da lafiya, shiyasa ka ganni haka, me ye ne yake damunka haka wai? Akwai matsala ne?’’ ta yi mishi tambayar idanunta suna ciccikowa da hawaye. Zuciya da abinda take so, dan tashi d’aya sai tausayinta ya lullub’e shi, dan haka duk sai jikinsa yayi sanyi, a take yahau inda-inda. A hankali ta lumshe idanunta ta bawa siraran hawayen nata damar zubowa, suka shiga sintiri, wanda hakan ya sake yin tasiri ba kad’an ba a zuciyar Yassir….dama tunda ya shigo ya ganta hankali kwance ya d’an sak’k’o, da kuma ta ce ba ta damu ba sai ya kawar da zarginsa a kanta, dama kawai ya yi mata tambayoyin ne saboda yanaso ya tabbatar ta yanda zai kawar da duk wasu zarginsa a kanta, kuma inshaaAllah daga yau ya kawar ɗin, inshaaAllah ba zai sake d’aura ayar tambaya a kanta ba….. Yana wannan tunanin ya jawota zuwa jikinsu a hankali, ya shiga rarrashinta, a chan k’asan ransa ya ce ’’Alhamdulillah’’ dan ba k’aramin dad’i ya ji ba da ya fahimta kuma ya tabbatar da ‘Kausar d’insa ba ta son wanin sa’.. Amman fa dukda haka ba wai zai bar Yashjub bane, dan ko ba komai ya san in dai Yash ya na da rai to babu shi babu walwala, saboda har ga Allah jin sa yake yi kamar a tsakiyar kansa, ko yanzun ma da kyar ya ke ta rarrashin kansa yake tausar zuciyarsa wadda take ta faman tunzura shi akan ya je ya ce ‘zai kwana ya kula dashi’ daganan ya samu ya k’arasa abunda ya soma….. Kawai dai ya san indai hakan ta faru tou kamar ya baiyyana kanshi ne, saboda shi zai fara zama suspect tunda shi ya kwana da shi….shi kuma ya riga ya san ba zai iya danne zuciyarshi daga yi masa kwab d’aya ba dan indai suka kad’ance daga shi sai Yashjub tou tsaf zai iya danna masa pillow a cikin baccin sa……….. Shiyasa ya taushi zuciyarsa ya hak’ura ya bari akan gara ya sake sabon plan ta yadda ba za’a kama shi dumu-dumu ba.. •••••• Tun kwana biyu da suka wuce Baba ya fara tantama akan ‘anya kuwa Baraka tana gidan Musbahu’ duba da yadda kullum yake tare da mai sunan Baba tun safe har dare, shiyasa yau yana zuwa shi kuma ya tambayesa… Cikin nutsuwa da fahimtarwa suka yi wa Baba bayanin abunda ya faru akan batun Baraka dalla-dalla, sannan suka ce ‘ya yi hak’uri akan k’in gaya masan da suka yi, dama suna so ya d’an huta sanann abubuwa su d’an yi sanyi ne tukunna, dan ba sa so hankalinsa ya tashi sosai a lokaci guda.’ Shiruu kawai ya yi da farko kafin daga baya ya ce ‘Allah ya rufa asiri’’ daga haka ya ja Bakinsa ya yi shiru yana kallon su Muhsin suna koya wa Inna rik’e abu dan jikin nata Alhamdulillah anata samun ci gaba a cikin kwanakin da ba su kai sati d’aya ba. Suna nan zaune gaba d’ayansu,Ya Nafi’u ya kira Ya Musbah ya ce masa “yanzu sir Najeeb ya kira shi yake sanar masa’Yashjub ya yi accident, yana asibiti, driver d’insa ma har ya rasu.’’ Tunda suka ji Ya Musbah ya yi salati dama gaba d’ayan su suka juyo suna kallonsa, ai kuwa yana ajjiye wayar suka hau tambayar sa ’’me ya faru?” Abunda Ya Nafi’un ya gaya masa shima ya fad’a musu idanunsa a kan Manubiya, ai kuwa hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba a take!! Sanna ga mamakin su kawai sai suka ga ta fashe musu da kuka….. Murmushi kawai Baba ya yi yana mai jin wani kalar kwanciyar hankali da nutsuwa su na ratsashi dama yanayin yanda suke waya akai-akai ya fahimci kamar itama tana son Yash d’in yau kam ya tabbatar, shiyasa ya ji zuciyarsa ta yi k’al! Ko ba komai ya san zai kai Manu gidan wanda itama take tsananin so. .. Cikin d’an k’ankanin lokaci suka yanke akan ‘Manubiya, Ya Musbah, Muhsin da Jidda! Su fara yin gaba, su je su dubo shi, su yi masa ya jiki’ Dan haka aka fara shiri domin su samu su je ɗin da wuri, shi kuma Baba ya ce ‘’idan Aisha ta zo kamar yadda Nafi’u ya ce, sai ta zauna da Inna, shi kuma sai ya taho da mai sunan baba idan ya farka dan tun d’azu da suka shigo ya fara bacci. Dan haka in ya tashi sai su taho su uku har da Ya Nafi’un wanda yace yana gama abunda yake yi za su zo. In ya so sai su dawo gaba d’ayansu a tare’.” Ya ƙarashe faiyyace musu hakan, yana mai zaro kud’i daga aljihunsa ya mik’awa Jidda ya ce ’’gashi su siyawa Yashjub d’in su ayaba da lemo a hanya’’. Jikin Manubiya har karkarwa yakeyi, tun kafin kowa ya shirya ita har ta shirya ta karb’i address da room number da sir Najeeb ya turo a wajen Ya Musbah, ta zura hijabinta, ta d’au jakarta da wayarta ta tsaya musu a bakin k’ofa. Girgiza Kai kawai Ya Musbah ya yi, wanda hakan ya sanya ta d’an lura da zumud’in nata dan haka ta fara kame-kame..ta hau wasa da bakin hannun hijab d’inta. Jidda ma dariya ta yi kafin ta kalli Baba ta ce “Baba dan Allah bara in kira Siyama sai mu je tare” Kamar Baban zai hanata, sai kuma ya kawar da wannan tunanin, dan a ganinshi ai babu mahaifiyar Siyama a cikin case din.. iyakar da aka yi ‘ tsakanin shi da su Uncle da Baba Habu ne’ shiyasa ya ce mata ‘’to’’ kawai. … Sai da suka tabbatar su Innar basa buk’atar komai tukunna suka yi musu sallama suka fice. Suna fita kuwa Baba ya matsa kusa da Inna saboda dama akwai maganar da yake so ya d’an tattauna da ita akan auren Manubiya kafin su ya Nafi’u su k’araso, suma su tafi…. Da kyar Manubiya ta rarrashi kanta, ta hana kanta kuka a cikin adaidaita sahu… A ranta ta shiga aiyyanawa ‘kullum shi yake kiranta, da ta ga bai kira ta ba jiyan kamata ya yi ace ita ta nemesa… Allah dai yasa bai karyeba, Allah yasa bai ji wani mummunan rauni ba! Allah yasa babu abunda ya samu Yashjub…’ In kuma ta tuno ance ‘driver d’in shi har ya rasu ma’ sai ta ji gaba daya hankalinta ya sake tashi. Tsararren private hospital ne mai kyau sosai da had’uwa, sai da suka fad’i sunan shi da number d’akin da yake a ciki a reception d’in tukunna aka raka su har bakin k’ofar d’akin. Suna tsayawa a bakin k’ofar d’akin, su Jidda suka tuna ba su siyo kayan dubiyar da Baba ya ce a siya ba, dan haka suka juya da sauri ba tare da sun cewa kowa komai ba! saboda a yadda Ya Musbah yake a fusace kwana biyun nan sun san in suka ce ‘sun manta!’ sam ba zai yi la’akari da ‘har da shi aka yi mantuwar ba’ zai rufe ido ne ya ci k’aniyar su. Suna juyawa ya lura dan haka ya juya shima ya bi su da sauri bayan ya cewa Manubiya “ta shiga suna zuwa’’. Muhsin ma bin bayan Ya Musbah ya yi dan a yadda ya ga duk sun fita da sauri ya d’auka wani abun ne ya faru… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 04* Ji ta yi kamar itama ta juya, dan tashi d’aya ta ji k’irjinta ya fara bugawa.. Da kyar ta samu ta d’aga Hannunta ta d’an yi knocking a hankali. Sam bai kawo itace ba dukda kuwa yadda ya ji yanayinsa ya ɗan chanza saboda shi dai ya san bai gaya mata ba. Jin an sake yin knocking a karo na biyu ne ya sanya shi cewa “Yea, come in..’’ Ya fad’i hakan, a ransa kuma yana tunanin wataƙila ko sir Najeeb ne ya dawo ko kuma finally Likitan ne ya zo domin ya sallameshi daga wannan kurkukun… A hankali ta murd’a handle d’in, ta shiga. Yana kwance a gefen Hannun damansa mara ciwon, ya d’an d’ago Hannun, ya na amfani da shi ta hanyar daddana computer da ke akan bedside d’in jikin gadon. Tana shigowa ya d’ago ya kalle ta, bai san lokacin da ya tashi ya zauna ba, sai kuma ya mik’e tsaye gaba d’ayansa, ya nufe ta. Da farko ya d’auka gizo take yi masa, sai da ya je daff da ita tukunna ya tabbatar ita d’in ce. A hankali ya sa Hannu ya tura k’ofar da ta bari a bud’e tukunna ya ce ’’ya aka yi ki ka sani?’’ Sai a lokacin ta samu ta d’an daidaita numfashi ta, kamar za ta fashe masa da kuka ta ce ’’Mai yasa ba ka gaya min ba??’’ Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘’Sorry’’ A hankali ta kalli Hannun, kafin ta d’ago tace masa ’’ mai ya sami Hannun?’’ Dukda yadda ta ji dad’in ganinsa garau a kan k’afafunsa, amma sai da ta shiga tashin hankali daga ganin yadda aka d’aure Hannun nasa. Yashjub kuwa yadda ta nuna damuwarta garesa abun ba k’aramin dad’i ya yi masa ba, Shiyasa ma ya gagara bata amsa hakanan kawai ya tsaya ya kafeta da idanu yanata zuba mata wani kalar sihirtaccen murmushi. Kallon sa ta yi taga yadda yake kallonta yana murmushi shiyasa gaba d’aya sai ta jita a takure dan haka sai ta hau wasa da y’an yatsun Hannunta. Y’ar siririyar dariya Yashjub ya yi kafin ya ce ‘’mu je ki zauna mana’’ daga haka ya d’an matsa ya bata hanya yana mai jin wani farin cikin da ya dad’e bai tsinci kansa a ciki ba. Ji ta yi kamar ta ce masa ‘a’a bara su Jidda su shigo tukunna’ ko kuma ma kawai su yi sallama ta juya tunda ai ta ga jikin nasa, ita sai yanzu ma lissafinta yake bata yadda ta burkice da kuma yadda ta shigo tsulum ba tare da ta yi kawaicin jiran su Ya Musbah su dawo ba, dan kamata ya yi ace ta jira su ko kuma a d’azun kafin duk su tafi da ko Hannun Muhsin ne ta dan rik’e ta hana shi bin Ya Musbah sun shigo tare…. shikenan yanzu ta san za su ga rashin kararta, in ba da kyar ba ma sun riga sun gano sirrin da ke cikin zuciyarta, shikenan ta tonawa kanta asiri da kanta… Wallahi ita gaba d’aya hankalinta gaba yayi ne d’azun, shiyasa kwata-kwata bata yi waennan tunanin ba…. So take ta juya kawai ta tafi, amman kuma still tana so ta ga yanayin jikin nasa, sannan ta ji ya akayi hakan ta faru…tana so ta duba shi sosai. Shiyasa duk yadda ta so sam sai ta kasa tafiya. D’agowa ta yi ta d’an saci kallonsa…still itan yake kallo yana murmushi, shiyasa ta d’an d’auke idanunta kafin ta wuce ciki ta isa kan kujerar mai jinya ta zauna. Dariya ya yi kafin ya juya shima ya k’arasa bakin gadon ya zauna, sannan ya ce ‘’Tabbas Likita ya na shigowa zai sallameni, dan yadda kika zauna anan kujerar za ki yi jinya ta! na san ko mintuna uku ba zan k’ara ba zan warke.’’ Sake yin k’asa ta yi da kanta kawai, tana sauraronsa…ita ba abun ta tashi ta koma chan gefe kan sofa d’in da ke cikin d’akin ba dan tunaninta a lokacin da ta kalli sofar ‘kar ta je ta zauna tunda guda d’aya ce shima Yash d’in yace zai zauna akai’ shiyasa ta yo nan tou gashi nan d’in ma ba ta tsira ba, ba ta tab’a jinta un comfortable (ba a sake ba) sosai dashi kamar yau ba! Dan a kusa da ita sosai ya zauna. A b’angaren Yash kuwa, so yake ma ta d’an d’ago amma ta k’i, k’arshema gani ya yi ta d’an muskuta ta ja baya ita da kujerar tata sannan ta sake sunkuyar da kanta. ‘’Inaa Yarinya ba za mu yi haka dake ba wallahi’’ Yash ya fad’i hakan a cikin zuciyarshi, a fili kuma sai yace “Auch’’ Da d’an k’arfi. Da sauri ta mik’e tsaye ta d’an matsa inda yake, kafin ta ce “menene, me ya faru? Hannun dai?’’ Ta jero masa tambayoyin a gigice saboda yadda ta ga yana yi kamar irin azabar nan yake sha. Kamar zai yi kuka ya ce ’’zafi sosai, har cikin zuciyata’’. Ai kuwa babu shiri ta yunk’ura ta ce ’’Bara in kira Doctor’’ Ta fad’i hakan tana shirin juyawa. Da sauri ya mik’e ya tare ta ta hanyar tsayawa a gabanta, tukunna ya ce ’’in kikayi murmushi ma kad’ai ya wadatar, zai daina, dama kyaliyar da kika yi min ne ya sanya Hannun ya fara wani irin azababben zugi’’ Shiruu ta yi da farko, sai kuma ta d’ago ta kalleshi, murmushi ta ga yana yi mata, suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya…. Ɓata rai ta yi, sai kuma ta maida kanta ƙasa a ranta ta ce ‘’lalle wannan Mutumin, da alama garau yake, kawai tab’ara ce yake ji da ita’’. Murmushi ya yi, kafin ya d’an matso kusa da ita a hankali ya d’an lek’a fuskarta, ya langab’ar da Kai sannan ya ce ’’kuma wai a haka an ƙi ace mun ana sona’’ Ji ta yi kamar ta nitse cikin k’asa, dan haka ta juya da sauri ta bashi baya tana jin yadda yanayin bugun zuciyarta ya sauya lokaci guda. A hankali ya d’an sake taku d’aya izuwa gareta ya tsaya a dai-dai bayanta tukunna ya ce ’’Manu plsss, jan ajin nan ya fara cutar da ni, ki fad’a min wani abun mai dad’i mana, ko so kike in yi miki kuka tukunna???’’ Shiru ta yi kawai ta kasa cewa komai, dan zuwa wannan lokacin bugun da k’irjinta yake yi ba na wasa bane ba, ba ta jin kalmar ‘A’ za ta iya fitowa daga gareta. Jin da ya yi ta yi shiru yasa ya ɗan sake matsawa kad’an a hankali dai-dai saitin kunnenta ya ce ‘’dan Allah ki ce kina so na…plss Baby!….’’ Inaa….she can’t take this anymore (Ba za ta iya ci gaba da jurar wannan abun ba)! Dan haka da sauri ta d’an yi gaba kad’an, kafin ta juyo da niyyar fita.. wanda ta yi hakan ne gudun karma ta juyo tashi d’aya ta je ta afka jikinsa. Amman ta na juyowa sai ta ga ba hanya dan gefenta fridge ne, d’ayan gefen gado, bayanta kujera, gabanta kuma shi… Da sauri ta sunkuyar da kanta dan wani irin kallo ta ga yana yi mata, ba ta gama dawowa dai-dai ba ta ga kamar ma tunkarota yakeyi, dan haka ta yi sauri ta d’ago ta ce ’’Allah ya k’ara sauk’i, Allah ya ji k’an driver d’in ka ya sa ya huta, z z an wuce ggi d a….’’ta fad’i hakan cikin in inaa Tsayawa ya yi chak, kafin ya ce ’’Saboda na ce ki ce kina sona shine za ki gudu?? Haba mana Baby, aure fa za mu yi amman har yanzu ban san matsayi na ba, kuma daga na yi magana sai a fara gudu na…’’ Juyar da kanta ta yi gefe, tukunna ta girgiza masa kai alamun ‘’A’a’’ kawai. ‘’Good! Saboda gaskiya yau ba za ki fita daga d’akin nan ba sai na san matsayina a cikin zuciyarki. Inaso mu wuce wannan stage ɗin mai ƙunshe da su kauda kai! Kasa kallona! Jin kunyata da kike yi, mu shiga next stage (mataki na gaba) saboda in samu in dinga faiyyace miki yadda na ke ji game da ke!! Saboda feelings ɗin sun cika mini zuciya da gangar jikina dayawa. Dan haka, ina sauraronki” Shiruu ta yi, shima haka. duk suna anan tsaye ba wanda ya sake cewa komai… Manubiya ji ta yi inama ace ba ta zo ba, gashi kwata-kwata ya k’i ya daina kallonta dede da na second d’aya, gashi ya titsiyeta, shiyasa ta ji kamar ta fashe masa da kuka……. Sun fi mintuna goma a haka, sam tama k’i ta yarda ta kalli direction d’in shi ballantana ta fad’i masa abunda yake son ji d’in. A hankali ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya, kawai! Sai kuma ya koma ya nemi waje ya zauna akan gadon jinyar nasa. “Na gode, ki gaida su Inna. InshaaAllah zan zo in gaida ita da zarar na fita a nan.” Ya fad’i hakan cikin kumbura fuska. Duk kuma sai ta ji ba dad’i. Har za ta wuce ta fita, sai kuma ta tsaya kamar wadda ba ta son yin magana ta ce ’’Tun d’azu nake ta tambayar ka ya jiki baka ce komai ba, ya aka yi hakan ta faru? Ya kuma hak’urin driver d’in ka’’ Numfashi ya fesar kafin ya ce ’’Jikina Alhamdulillah da sauk’i kafin ki zo! Amman yanzu kam na san idan kika tafi kika barni a haka akwai matsala. Hak’uri da godiya, sannan tsautsayi da k’addara ne ya janyo hakan, sai mu yi adduar Allah ya kare gaba’’ Ya k’arashe maganar tasa yana mai zaro wayarshi daga cikin aljihu, ya fara daddanawa… shi ala dole ya yi fushi da ita, watakil in ta ga hakan ya san za ta yi masa yadda yake so. Yana addua Allah yasa maganarta ta zama positive, dukda bashi da tantama akan itama tana sonshi, amma yana so ya ji ya tabbatar. ‘’Allah ya ji k’an musulmi, Allah ya baka lafiya, Allah ya kare gaba’’ tace da shi kamar yadda shima ya jero mata, kafin ahankali ta fara tafiya zuwaga k’ofar, zata fita. D’an d’agowa ya ke yi yana satar kallonta yana kallon wayar tashi, ganin tana shirin ficewa ne ya sanya ya yi sauri ya mik’e ya ce ’’au, ba za ki tambayeni me zai dawo min da ciwon nawa bayan kin tafi ba ko??” Duk yadda ta so daurewa sai da murmushi mai had’e da y’ar siririyar dariya ya sub’uce mata, a ranta tace “Mutumin da ya had’e rai shi ala dole ya yi fushi yayi zuciya amma kalli shine ya mik’e yanzu yake wannan batu.” Sarai ya ji sautin murmushin nata, dan haka ya k’araso ya tsaya a gabanta ya ce ‘’Dariya ma kike yi min ko??’’ Ya fad’i hakan cikin b’ata fuska kamar wani k’aramin Yaro. Wani d’an siririn murmushi wanda ya sanya Yash ya ji kamar zai suma ta saki kafin a hankali ta ce ’’na san mecece amsar da za ka ba ni, shiyasa ban tambaya ba’’ Cikin tarar numfashinta yace ‘’Mecece amsar??’’ Sai da ta d’an kalleshi kad’an tukunna ta sunkuyar da kanta ta ce ‘’Cewa za ka yi saboda ban fad’i abunda kake son ji ba, kuma ai na ga ma fushi ka yi da ni yanzun.’’ A hankali cikin yin k’asa da murya ya ce ‘’ni, na yi fushi dake??’’ bai jira jin amsartaba yace ‘’Never!’’ kafin ya d’aura da cewa “Kin san rashin amsar taki ce za ta k’aramin rashin lafiya, amma shine kika zab’i ki tafi ki barni a haka?? Saboda kin tsane ni, ko?. Wannan sarkin nacin.’’ Yayi maganar yana nuna kanshi Da sauri ta d’ago ta kalle sa tashi d’aya ta ce ‘’A’a’’ Dukda yadda ya ji sanyi a ranshi amma sai ya dake ya sake had’e fuska ya ce “to yaya ne?’’ ‘’Ba sai na fad’a ba na san ka sani’’ Ta bashi amsar tana mamakin yadda sam ba ya gajiya da kallonta, tunda ta shigo cikin d’akin ba ta jin ya d’auke idanunsa a kanta in ba lokacin da ya yi fushi ya d’auko waya ba, ita har tsarguwa da wannan kallon nashi takeyi….kullum in suka had’u kamar ranar ya fara ganinta… Muryarshi ce ta katseta jin yana cewa ‘’i’ll love to hear it (zan so in ji), ba ki san taimakon da za ki yi min ba idan kika fad’a Manu’’ Kamar zai yi kuka yace “so plssssss’’ ya ja plss d’in sosai har cikin ranta sai da ta ji,tukunna ya ce “Idan amsarki ‘Yes’ ne ina da buƙatar in ji kin faɗa min yanzu, ji kawai nake so in yi. Na garu dayawa, a tausaya min haka mana…….’’ A hankali cikin tarar numfashinsa ya ji ta ce “Yes!’’ ‘’Yes what?(eh me?)” Ya yi mata tambayar yana kallonta yana murmushi sosai. Turo Baki ta yi, ta saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta da su tukunna ta yi ƙasa da kanta, dan kunya take ji sosai, sannan ta yi tunanin da ta basa amsar zai kyaleta ne amma ta ga alama wannan so yake su kai dare anan ana abu d’aya. Yashjub kuwa tsabar murna ji yake kamar ya zare Hannun sanna ya janyota jikinsa ya rungume.…..ahankali ya ce ’’ pls mana, kin ce min yess kawai kin barni,elaborate mana(ki min ƙarin bayai mana), sannan na ce fa bana son wannan sunkuyar da kan, a d’an rage wannan kunyar ta yi yawa fa…’’ Knocking ya ji an d’an yi dan haka da sauri ya juya ya murza key sannan ya juyo gareta ya ce ’’um..” alamun ita yake sauraro. Zaro idanu ta yi waje, kafin a rikice ta ce ‘’Dan Allah ka bud’e, wataƙilan su Jidda ne suka dawo, har da Ya Musbah muke tafe, dan Allah ka bud’e kar su yi tunanin wani abun’’ Ta fad’i hakan ahankali k’asa-k’asa kamar wani zai jiyo ta sanann duk a rikice. Ba k’aramin dariya ta basa ba ganin yadda duk ta tsure tashi d’aya, a ransa yace ‘’perfect(dai-dai kenan)” Amman sai ya dake, ya wani mak’e kafad’a sannan ya ce ’’um um, ni kam ba zan bud’e ba’’ sai kuma ya d’an sake matsawa kusa da ita kafin ya ci gaba da cewa ’’har sai kin fad’a min komai yau, tukunna, babu ruwana ko waye ya zo to ya jira Queen ce take zuba mulki da jan aji dan haka shima ta shafe sa.’’ Dai-dai nan aka sake yin wani knocking d’in, sai da ta d’an zabura kafin ta kalli k’ofar sannan ta kalleshi a gigice ta ce ‘’to me kake so in ce?? ko waye fa a bakin k’ofar nan na san ya ji lokacin da ka saka key, kuma yanzu kana bud’ewa sai a ganmu tsulum mu biyu kawai ka ga ai hakan babu dad’i, na riga na ce maka ‘yes’ ai, dan Allah ka bud’e k’ofar nan’’ Cikin tarar numfashi ta yace ‘’waye zai bud’e k’ofar?? Ai in gaya miki muna nan ni da ke har abada muddin ba ki bani amsata ba, bari ma kiga in zare key d’in in cilla shi ta window’’ Ya fad’i hakan yana mai juyawa Da sauri tace ‘’ɗan tsaya to!’’ Sai da ya d’an yi y’ar guntuwar dariya tukunna ya juyo. Kamar za ta fashe da kuka ta ce ‘’to me zan ce?’’ ‘’Abinda yake a cikin zuciyarki game da ni’’ Ya ba ta amsar kanshi tsaye. Kallon shi ta yi ahankali ta d’aga Kai ta ce ’’Yes….’’ sai kuma ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ce ’’na ce maka yes tun d’azu…’’ ta fad’i hakan kamar za ta fashe da kuka, dan ita har ga Allah wallahi kunyar gaya masa complete abun kuma kai tsaye ido da ido take ji. Juyawa kawai ta ga ya yi, ya zare key d’in. Still kuma har yanzu anata faman knocking k’ofar Da sauri ta ce ’’me kuma na sake yi?’’ Kallo ta ya yi kafin ya ce ’’Yess’’ Da d’an mamaki ta ce’’yes kuma?me kenan?’’ ‘’Yauwa exactly my point, kinga kema ai ba ki gane ba ko? Dan haka ya kamata ki fahimci nima ban gane me ‘yes’ d’in ki take nufi ba. if you want to express yourself, all you have to say is (Idan kina so ki gaya min abunda ya ke a cikin Zuciyarki game dani a dunƙule, iyakar abunda za ki ce shine) ‘i love you Yashjub’, ni har ga Allah banga abun wahala a y’an waennan kalmomin ba…’’ Knocking aka yi da k’arfi sosai wannan karon, Manubiya ba ta san lokacin da ta fara bubbuga k’afafunta ba kamar wata y’ar Yarinya tana cewa ‘’ni kam Allah A’a, dan Allah kawai ka bud’e’’. Shagala yayi kawai yana kallonta, sai da suka suka had’a ido sai kuma ta tsaya chak! Tsabar kunya kasa ma cigaba da fuskantar sa ta yi dan haka sai ta yi saurin juyawa. Murmushi ya yi da sauri ya ce ‘’a’a pls, kar ki daina, you look cute’’ Bugun da akayi da mugun k’arfi wannan karon ne yasanya ta juyo ta ce ’’dan Allah’’ Ta fad’i hakan hawaye suna taruwa a kyawawan idanunta ai kuwa a take idanun nata suka fara kyalli wanda hakan ya sake d’imauta Yash. A hankali ya ce ’’Manu! Ba zan tab’a bud’e k’ofar nan ba idan har ba ki gaya min abunda nake son ji ba, in ma bakya sona ne to ki fad’a min!. Ni a ganina ke kika bari har aketa bugun nan, sannan ina so ki san cewa in har Doctor ne yake knocking d’innan to Mutane zai koma ya je ya tattaro a zo a b’alle k’ofar, tunda marar lafiya ne a cikin ɗakin dan haka in su ka ji shiru yayi yawa za su yi tunanin ko wani abun ne ya sameni, gashi jiya na sanya sun zare cctv d’in d’akin nan, kinga ana zuwa ba ma Mutum d’aya ba mutum dayawa ne za su ganmu tsulum ɗin! kuma Allah kad’ai ya san tunanin da kwakwalwar kowa za ta basa. Dan haka komai yana a hannunki, ki yanke hukunci da wuri tun kafin a zo a b’alla k’ofar nan saboda idan akwai abunda ya ke tabbatacce to shine ‘ni dai ba zan tab’a bud’ewa ba yau har sai na ji ishashshiya kuma gamsashshiyar kalma daga gareki’.’’ Ya k’arashe maganar yana murmushi k’asa k’asa yana kallonta Dole ta ajjiye kunya a gefe tun kafin ya janyo mata magana a cikin asibiti.. Dan haka ta runtse idanunta da k’arfi tukunna ta ce ’’i love you(ina son ka)” A hankali Yash wanda tashi d’aya kasala ta rufar masa ya d’an matsa kusa da ita kad’an yana mai bin fuskanta da kallo, ahankali kamar wanda baya so kowa ya ji ya ce ’’how much?(kamar adadin yawan yaya?)’’ Direct daga zuciyarta ta ce ’’so very much(marar adadi)’’ Wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yance’’za mu yi auren mu nan kusa ko?’’ Jinjina kai ta yi still idanunta a runtse tace ’’inshaaAllah’’ ‘’Ki haifamin ya’ya masu kama da ke?’’ ahankali ta sake cewa ’’inshaaAllah’’ Wani bugun aka sake yi wanda ya sanya Manubiya ta bud’e idanunta da suke ta kyalli dan a cike su ke taff da kwallah! Ta kalli k’ofar da sauri… tabbas yau kam ta san babu yadda za’ayi ta iya had’a idanu da Yashjub dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa tukunna ta ce ’’plss ka bud’e, dan Allah’’ Lumshe idanunsa ya yi ya bud’e, yana mai sauƙe wata nannauya kuma zazzafar ajiyar zuciya, a ransa kuma yana mai ji kamar ya fita wajen ya je ya shak’e koma wanene a bakin k’ofar da yake ta yi musu wannan uban knocking haka, me shegen naci!!!! Tashi d’aya ya ji ya tsani knocking! Dole zai rubuta a cikin diary d’inshi shikam ‘ya tsani knocking, har abada!!’ This is the best moment of his life!, yana da buƙatar ya kaɗaice da ita sannan ya samu yayi expressing kansa more and deep amman kawai an kama an zo an dame su, gashi ba ya so ya karya alk’awarin da yayi mata ta hanyar k’in bud’e k’ofar. Da k’arfi aka sake yi dan haka Manu ta sake cewa ‘’dan Allah’’ A hankali ya juya ya zura makullin ya murd’a ya bud’e k’ofar yanajin kamar yana bud’ewa kawai ya fellawa wanda yake knocking d’in mari………….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 05* Yana bud’ewa suka yi ido biyu da Yasmeen, a hankali ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin ya ce ’’ban yi tsammanin ganinki a nan ba” Babu Mommy da Daddy a wajen ballantana ta yi rashin kunya, shiyasa ta yi shiruu ta d’an sunkuyar da kanta k’asa, kafin kuma ta d’an d’ago ta kallesa tukunna ta ce ’’Yau ce ranar da na ke shigowa aiki nan asibitin, shine na ce bari in lek’o in duba ka’’ ‘’Nagode’’ kawai yace da ita, daga haka ya fara k’ok’arin maida k’ofar. Manubiya tana jin muryar Yasmeen zuciyarta ta fara wani irin tuk’uk’i….yanayin conversation d’in su ba kad’an ba ya d’aure mata kai, gashi ta ji Yarinyar sai wani kashe murya takeyi tana wani lallaɓasa…… Da sauri Yasmeen ta sa Hannu ta d’an tare k’ofar kafin ta ce ‘’Those are for you(waennan naka ne)” Ta fad’i hakan tana mai nuna masa allurar Hannunta. Wannan karon ɓata rai Yashjub ya yi, cikin d’an fushi ya ce ‘’i’m fine, na warke. Idan kuma allurar mai mahimmanci ce to ki ji ki nemo Likita ya zo ya min.” A ranshi yace ‘’lalle ma Yaran nan, rainin hankalin nasu ya yi yawa, su gama basa raini da attitude a gaban Mutane, shine yanzu kuma dan ta maida shi d’an cikinta za ta zo mishi, kuma ko bada hak’urin rashin kunyar da ta yi masa ma bata da shirin yi. Kamar ma bata yi komai bama’’ Ta ji zafi sosai amman sai ta dake, ta d’an yi murmushi, kafin a hankali ta ce ’’nima ai Likita ce, kuma shi ya shiga surgery, just let me (kawai ka bari in shigo) in i…..’’ Cikin fushi sosai ya ce ‘’Ke! Ina miki wasa??’’ Bai jira jin amsar ta ba ya ce ‘’b’ace min a gani, kafin in karya ki a wajen nan’’. Dai-dai nan Jidda da Siyama suka k’araso wajen, dan basu samu lemo da ayaban a kusa ba shine Ya Musbah ya karb’a suka tafi nema shi da Muhsin bayan ya balbalesu a titi kamar zai rufesu da duka. A hankali Yasmeen ta d’an sunkuyar da Kanta ta fara k’ok’arin maida kwallar takaicin da take shirin yin nasarar zubo mata. Sai da Jidda ta d’an rissinar da kanta tukunna ta ce ’’Ya Yashjub, Ina wuni’’ Haka ma Siyama Jinjina Kai ya yi kafin a hankali ya ce ‘’Alhamdulillah’’ Daganan ya juya ya shige, bayan ya bar musu k’ofar a bud’e. Kamar ba za su kula Yasmeen ba, sai kuma jidda ta ce mata ‘’Sannu, Ina wuni’’ tunda ko da ace dai Likitarsa ce(dan sun ganta sanye da lap coat) amma tare suka gansu suna magana de. Da kyar ta iya d’agowa ta kallesu….kyawawan Mata ajin farko, masu ji da asalin kyau da k’uruciya, gashi sai wani kalar k’amshi sukeyi, su duka biyun. Sai dai tashi d’aya yanayin kayan jikinsu zai sanya a fahimci suna cikin yanayi na rayuwa…..sanye suke da dogayen rigunan Abaya bak’ak’e, amma tsabar yadda kayan suka ji ruwa har bak’in ya d’an fara komawa kamar kalar dark ash! Sannan rabin stones d’in jiki duk sun zube, tashi d’aya ta ji gabanta ya yanke ya fad’i!!! Kallon da taga suma sunayi mata ne ya sanya kawai da kyar ta ce “fine’’a cikin zuciyarta tana tunanin ‘to wacece budurwar Yash d’in a cikinsu’……….. Sai da suka tura k’ofar suka shige, tukunna ta samu damar yin ido biyu da Manubiya wadda itanma Allah Allah dama takeyi a d’an bud’a k’ofar ta samu ta ga wacece take magana da Yash d’inta haka yake disga ta. A bud’e su Jidda suka bar k’ofar dan a tunanin su shigowa za ta yi. Har Manubiya ta d’auke idanunta daga kanta amma ita Yasmeen din ta kasa, kallonta kawai take yi tana sakewa….sanye take da dark army green ɗin jilbab har k’asa, yanayin yadda ta yi parking gashinta ta d’aure igiyoyin jilbab d’in ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba….…’’Hi Yasmeen’’ d’in da sir Najeeb ya ce mata ne ya dawo da ita daga duniyar k’arewa Manubiya kallo, da sauri ta kawar da kanta ta mayar gareshi kafin dakyar ta samu ta d’an k’ak’alo murmushi ta ce ’’Najeeb, Ina wuni!’’ Ta fad’i hakan tana d’an murmushi. D’an lek’awa ya yi, ya hango Yash suna gaisawa da su Jidda, bai ga fuskokinsu ba dan sun bashi baya ne iyakar gefen fuskar Manubiya ya samu ya gani. Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya ce ‘’ya na ganki a bakin k’ofa?’’ ya yi mata tambayar yana tsare ta da idanuwa. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce ‘’ko da na zo ma na kusan 20 minutes, tukunna da kyar aka bud’e min, ashe Madam ce a ciki shiyasa, Itace yayar tamu ko?’’ ta yi mishi tambayar tana kallon Manu. Direction d’in inda ya ga tana kallo ya kalla shima, tukunna ya d’anyi murmushi ya juya ya kalli Yasmeen d’in sannan ya ce ’’Yeah itace! Ba ku gaisa ba ne? Mu je cikin mana..’’ Girgiza Kai kawai ta yi kafin ta ce ‘’Yace ma in ban bar nan ba sai ya karya ni, ma gaisa wata rana, bara in wuce’’ Ta fad’i hakan tana d’an yin gaba, sai kuma ta juyo ta ce ‘’am… d’azu, na ga miss calls d’inka, sorry ina driving ne, shine na saka wayar a silent’’ Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce ‘’akan Ya’isha ne! Kin dai san halinta….. Anyways (mu bar zancen yanzu kawai), na ga kamar kina sauri, ki je za mu yi magana anjima’’ ‘’Ok’’ kawai tace, kafin ta juya ta yi gaba…. Shiruu Najeeb ya yi ya ɗan bita da kallo har ta b’ace ma ganinsa, a ransa yana tunanin ‘menene yake damun Yash haka ne?’ Shi, shi kad’ai iyayenshi suka haifa, Yana yawan fatan inama ace yanada siblings (ƴan uwa), shiyasa har gobe yake mamakin Yash, ya rasa dalilin da yasa baya appreciating kyautar da Ubangiji ya basa ta ‘siblings..’ Girgiza Kai kawai ya yi, kafin ya shige cikin d’akin Bakinshi d’auke da sallama. A hankali duk suka amsa, kafin Manubiya ta d’ago cikin girmamawa ta gaidashi Murmushi ya yi, ya ce ‘’Lafiya, ya gida, ya mai jiki?’’ ‘’Alhamdulillah’’ ta ce, daganan ta sunkuyar da kanta. Kusa da Yash ya d’an matsa tukunna ya ce masa “Ya jiki?’’ Kamar ba zai amsa shi ba, sai kuma ya ce ‘’Alhamdulillah, ai na d’auka ba za ka shigo ba’’ Murmushi Najeeb d’in ya yi kawai ya girgiza Kai kafin ya mayar da idanunsa a kan su Jidda waenda suka ce masa ‘’ina kwana’’ A tare. Sai da numfashinsa ya yi sama! sakamakon ido biyu da sukayi shi da Siyama. Dakyar ya samu ya iya ce musu ‘’lafiya, Alhamdulillah’’ sannan ya yi sauri ya d’auke Idanunsa daga kan Siyama wadda ita bama ta san yana yi ba, dan suna had’a ido ta sunkuyar da kanta. Manubiya ya kalla kafin ya ce ’’ya na ganku duk a tsaye? Ku zauna mana. Itanma sistern ki ce?’’ Ta san sun had’u da Jidda ranar a asibiti, shiyasa ta fahimci Siyama yake nufi, dan haka ta ce ’’Eh,k’anwata ce, cousin sister’’ A hankali ya ce ’’MashaaAllah’’, Sai kuna ya sake cewa “ku zauna mana’’ ‘’Tam’’ Jidda ta ce, daganan suka juya suka nufi sofa ita da Siyama suka zauna. Shi kuma ya zauna a gefen Yash kan gadon. Manubiya ya sake kalla ya ce ‘’Amaryarmu ba za ki zauna ba ke??’’ Da sauri Yashjub ya juya ya na mishi wani irin kallo! Dan haka Najeeb ɗin yayi dariya, kafin ya ce masa ‘’Sorry!’’ sai kuma ya kalli Manu ya ce ‘’Amaryar Yashjub shi kad’ai! Ki taimaka ki zauna’’ A hankali ta juya da niyyar zuwa inda su Jidda suke, amman sai ya sa Ƙafa a daidai inda za ta bi ta wuce…. Dukda k’afar ba ta wani kafeta sosai ba amma ta fahimci sarai abunda yake nufi! Zuwa yanzu ta riga ta san halin Yash, ta san ba k’aramin abu bane a wajensa yanzunnan sai ya ja mata ta ji kunya a gaban su Jidda muddin ta k’i yin abunda yake so, shiyasa kawai sai ta nemi waje ta zauna a kujerar mai jinya, tana mamakin shi a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma tana mamakin Sir Najeeb shima! Mutumin da a da ko kallon kirki baya yi mata, daga ɓaɓɓata fuska sai ciccin magani kullum, amman yanzu wai shine haka kamar zai goyata. D’an zungurin Yash Sir Najeeb d’in ya yi ganin yadda yake ta kallon Manu, ƙasa-k’asa yace masa’’kar ka cinye ta da ido mana..’’ Dariya Yash d’in ya yi shima k’asa-k’asa, kafin kawai ya d’auke kansa daga kan Manubiya ya maida kan Najeeb ɗin sannan ya ce ’’wanne munafurcin Yasmeen ta shirga maka ɗazu?” Shiruu Najeeb ya yi yana kallonshi, kafin ya mik’e tsaye sannan ya ce ‘’za mu yi magana da kai anjima” sai kuma ya kalli Manu ya ce ’’bari in bawa bak’inmu ruwa’’… …tun lokacin da su Siyama suka koma chan gefe suka zauna, yake ta so ta juyo ya sake kallonta amman ta ƙi!… Suna zaune abunsu hankalinsu na ga wayar Siyaman……ya san hakan bai dace ba, bai kamata ba! Sannan ko a ta b’angaren sa shima sam two-timing (soyayya da Mata biyu a lokaci guda) baya a tsarinsa, daɗin-daɗawa kuma ga Yashjub a wajen, dan haka abun zai yi kamar cin fuska sannan ya san yana yin wani abun Yash d’in zai gano sa!!! Shiyasa tun d’azu yake ta tausar kansa amman duk yadda ya so sam ya gagara hak’ura, a yanzu so yake ko ƙaƙa ya ɗan sake kallon Fuskarta….dan haka ya yanke shawarar kai musu ruwa….. bai damu ba dan ya zama waiter (hadiminsu), in dai har hakan zai bashi damar ya kalli fuskarta a karo na biyu. Muryar Manubiya ce ta katseshi jin tana cewa ‘’Laa,a’a fa, yanzu ma za mu tafi, su Baba kawai muke jira’’ Da sauri Yash ya kalleta ya ce ‘’Nooo! Dan Allah ki kirasa ki ce ya zauna a gida, ba sai ya zo ba, ai na warke.’’ Sai kuma ya juya ya kalli Najeeb ya ce ’’ka ga abunda ka janyo ko??’’ Murmushi Najeeb ya yi kafin yace ‘’Sorry’ tukunna ya kalli Manubiya ya ce ‘’ki kirasa ki ce ba sai ya zo ba’’. Da sauri ta d’ago ta kalli Sir Najeeb d’in ta ce ’’Allah in ma nace kar ya zo fad’a zai yi min, ya riga ya gama shiryawa akan zai zo d’in.’’ Dafe Kai Najeeb ya yi, yad’an fesar da iska, kafin ya zaro waya ya ce ’’okay, bari ni in gwada yi masa magana’’ Yana gama fad’in haka ya koma chan gefe kare da waya a kunne. Shiruu suka yi kafin chan Yashjub ya ce ’’yanzu duk za ku saka ni jin kunya wallahi. Allah yasa ya hak’ura da zuwan’’ Shiruu Manu ta yi kawai ta sunkuyar da kanta k’asa. A take kuwa ya turo Baki, ya b’ata rai tukunna ya ce ’’yanzunnan a gaban idona kika gama kallon ido da fuskar Najeeb, ni kuma kin wani sunkuyar da Kai k’asa’’. Tana shirin yin magana Sir Najeeb ya dawo ya ce ‘’ai suna bakin gate ma’’ ‘’Innalillahi! Najeeb ka kashe ni’’ Yash ya fad’a, kafin ya mik’e tsaye kawai ya na zabgawa Najeeb d’in wata uwar harara. Bai dad’e da mik’ewan ba, su Baba suka k’araso…. Shi da mai sunan baba da Ya Nafi’u da Ya Musbah da Muhsin waenda suka had’u da su a hanya… Ba k’aramin dad’i Manubiya ta ji ba ganin yadda Yash ya gaida Baba cikin tsananin girmamawa. Da kulawa Baba ya amsa yana mai tambayarsa ‘ya jiki, daganan ya yi mishi jaje da adduar Allah ya kare gaba kafin ya masa gaisuwa.’ Daga haka, suka gaisa da su Musbah suma suka yi masa kamar yadda Baba ya masa. Yash ya dad’e bai had’u da Yaron da ya shiga ransa tashi d’aya kamar Muhsin ba.. ɗan sukuti da shi so chubby, gashi fari tass kalar ajebo no 1 Dan sam babu wanda zai kalli Muhsin ya yi zaton ya taso a wahala. Yanayin round face d’in shi irin na Manubiya, ga Yaron da ladabi dan sai da ya d’an durk’usa tukunna ya gaida shi.. tashi d’aya Yash ya fara addu’ar Allah yasa Manu ta Haifa masa irin wannan, wai!! Ranar bai san ya zai ji ba, zai iya bada komai nasa dan ya samu ya ga wannan rana…… Har kanshi Yash ya d’an shafa yana tsokanarshi da d’an auta, aka yi dariya, mai sunan Baba shima yanata tsalle tsallen shi… Sosai Yaran suka burge Yashjub kwarai, dan yana matuk’ar son Yara. Manubiya ce ta bawa Baba kujera, ya zauna, ita kuma ta ja su Muhsin suka koma wajen su Jidda, su ya Musbah suka tsaya a tsaye. Sun d’an jima suna alhini kafin Baba ya sanar da Yashjub d’in ‘ai Daddy ma ya kirasa…. Daddyn ya ce yana so za su zo ayi tambaya da abubuwan al’ada, sannan ya ce d’aurin auren nan da kwana goma za ayi inshaaAllah…in an gama daidaita komai. Hallau Daddyn ya ce d’an uwanshi kawai yake jira, za su taho daga uk yau Gobe inshaaAllah idan sun ƙaraso za su zo tare’’. Tsananin murna da kunya ne suka sanya Yash kasa cewa komai, ya sunkuyar da kanshi kawai, ya kasa had’a ido da Baba. Sir Najeeb ne ya ce “Allah ya nuna mana, Allah ya tabbatar da alkhairi yasa za ‘ayi da mu’’. A tare gaba d’ayansu suka ce ‘’Ameen’’ har Yashjub, daganan Baba yace “Allah ya ci gaba da kareka, Allah ya k’ara sauk’i, na ji dad’in ganin jikin naka haka, da aka ce ka yi hatsari na firgita sosai, amma ganin ka haka ya kwantar min da hankali. Allah ya k’ara lafiya, Allah ya ji k’an driver d’inka Ya ci gaba da tsare ka a duk inda kake’’. Cikin tsananin jin dad’i Yash ya ce ’’Ameen ya rabbi, na gode sosai Baba’’ Daga haka suka mik’e suka yi masa sallama, suka tafi, Yash yana ji kamar ya janyo Manubiya ya rik’eta ta ci gaba da zama tare da shi….. Ba su dad’e da tafiya ba Likita ya shigo, yana shigowa kuwa Yash ya fara masa mita yana cewa ‘shi dai a sallameshi’, dariya likitan ya yi kafin yace “ai na riga na sallameka, Yasmeen har ta kira su Daddy ma. allura na zo in yi maka, ga kuma takardun sallama nan (discharge papers) ka yi signing, sai ka dinga zuwa follow up kuma akai-akai’’ Sai a sannan Yash ya yi murmushi a ranshi ya ce ‘Alhamdulillah’’ Dan kamar a k’an k’aya haka yake jinsa. Sai da aka yi masa allura, Likita ya sake duba Hannun tukunna Yash ya yi signing papers ya yi wa likitan godiya daga haka Likitan ya fita. Likitan, bai jima da fita ba ya sake aiko wata nurse da sabbin magunguna… Karɓa kawai Yash d’in ya yi, ya d’an dudduba, kafin ya ajjiye a gefe ya ci gaba da zaman jiran su Daddy. Yana nan zaune boredom(zaman shiru) ya ishe sa, dan haka ya mik’e ya fita domin ya shak’i fresh air, kafin a zo d’aukar sa. Yana fita wajen, motar Yassir ta danno kai, dama Yashjub ya san wataƙila Daddy Yassir d’in zai turo dan yanzu a kaff gidan kusan shine kad’ai yake zaman banza, a yanzu. A take tausayin k’anin nasa ya lullub’e shi, sam ba shi da wani abun yi, gashi shekarunshi sun kusan kaiwa talatin amma ba shi da wata hanyar samu mai k’arfi, shares d’in shi (kasonsa) na companyn Daddy kawai garesa, wanda a ko da yaushe yake adduar Allah ya taushi zuciyar Daddy ya sa ya k’arawa Yassir wani abun…. Dan a ganinshi ya kamata a k’ara mishi, saboda ko ba komai ma bai kamata ace yana Naamiji wanda daga yanzu zuwa ko wanne lokaci zai fara tara iyali amman ace shares d’insa ya kasance dai-dai da na mata ba, kuma kullum yana zaman banza. Ya san komai da ya ke faruwa da Yassir ɗin laifin shi Yassir ɗinne tunda ko company d’insa ma da hannunsa ya lalata…..baya san zuwa aiki wani lokacin sai 11 zai ci uban kwalliya ya je, kuma ko cikakkun awanni biyu ba zai yi a cikin building ɗin ba, haka nan zai fita ya shiga gari…. Amman koma dai yaya ne, haka za su dage, su ci gaba da taimakon sa dan Hannunka ba ya tab’a rub’ewa, ka yanke ka yar. Yana cikin wannan tunanin Yassir ya yi parking a gaban shi, ya fito ya zagayo a ranshi ya ce ’’Mutumin da ya kamata in je kai ziyara kabarinsa, shine na zo d’auka daga asibitin zan maidashi gida garau! Anyways, na riga na tanadar maka babban shirin da ya fi na baya..” Dakyar ya k’ak’alo wani d’an guntun murmushin yaƙe Ya ce ’’hi’’ Murmushi shima Yash d’in yayi, ya ce ‘’Follow me(biyo ni)’’ daganan ya juya. Binsa Yassir ya yi kamar yadda ya buk’ata, suna zuwa cikin d’akin, Yashjub ya k’arasa ya d’auko takardun da suke cikin jakar computer d’in shi, da wani a cikin k’aramin envelope, ya dawo nan kan sofa inda Yassir yake wanda ya nemi waje ya zauna kawai yana binshi da ido . A tsaye ya tsaya ya mik’a masa takardun, sai da yace “ungo mana’’ Tukunna Yassir ya janye idanuwanshi a cikin na Yashjub, ya maida kan takardun kafin ya sa Hannu ya karb’a, sannan ya fara duddubawa. Tashi d’aya ya fahimci na mene ne, sai kuma d’ayan takardun mota ne, motar da ya dad’e yana ta yi wa Yash d’in nacin ya siya masa… Ajiyar zuciya ya sauk’e bayan ya gama duddubawa, kafin ya ajjiye takardun a gefenshi ya d’ago ya kalleshi ya ce ‘’What’s the catch?(ina gizo ke saƙar?)” Dukda dama Yashjub bai yi tsammanin Yassir ya huce da wuri ba amman sam bai ji dad’in yadda ya yi ɗin ba, dan ko d’igon murna bai gani a fuskar Yassir ba. Kud’in da ya kashe ya siyi motar ba wani abu bane a wajenshi, amma wahalar da yasha wajen registering da had’a mishi company d’in nan ba kad’an bace. Ganin ransa yana shirin b’aci ne ya sanya yayi saurin cewa ‘’Auzubillahi’’a cikin ranshi, sannan ya fesar da iska ya mayar da hankalinshi ga Yassir wanda ya tsareshi da dara-daran idanuwanshi tun d’azu, cikin sigar rarrashi ya ce ‘’Na yi kuskure Yassir, sorry, amman fa dukda haka ka nisanci Yarinyar nan (Munirat), saboda ka ga ko ta fannin Daddy in muka ɗauka yanzu haka ya na zargin ita take kai kanta gareka ne, kar ka shiga tsakaninsu dan in ka yi hakan abun ba zai yi musu kyau ba. Idan kuma ka san son ta kakeyi tsakani da Allah to ka yi magana a aura maka ita. Yassir, muna da Yarinya mai shekaru 17 a gida, inda ace ita ta ga abunda ni na gani ranar a kai da Munirat mai kake tunani?.. Anyways, ya riga ya wuce, ka yi laifi dan Allah ka gyara, nima kuma na yi laifi I’m sorry. Company d’in na yi maka ne saboda inaso inga kaima ka tsaya da k’afafunka…dan dukda kana b’oyewa amma na riga na san abunda yake faruwa a building d’inka..pls Yassir!! Put all your hard work into this new one (Ka sanya dukkan ƙoƙari da jajircewarki a wannan sabon). Ya kamata ka farka, ka fara abunda zai fishsheka. Sannan motar na siya maka ne As Peace offering (a matsayin kyautar neman sulhu)..Ka yi hak’uri akan abunda na yi maka that very day(a wachchar ranar), ya kamata ace naa fahimci ka riga ka girma.’’ Ya k’arashe maganar yana murmushi. Da kyar Yassir ya samu ya k’ak’alo murmushi ya yafawa fuskarshi tukunna shima ya mike tsaye, Rungume Yashjub ɗin ya yi kafin ya ce ’’na gode’’ Bubbuga kafaɗan Yassir Yashjub ya yi a hankali, tukunna ya ce ’’We’re good right?(mun shirya ko?)” ‘’Of course we are, (e mna, mun shirya)” Yassir d’in ya ce daganan ya cika shi ya sake cewa ‘’na gode’’ Murmushi duk sukayi, daga haka suka had’a y’an kayan Yashjub…. Yassir ne ya kira wata cleaner ta tayashi kaiwa mota, Yashjub kuma ya je ya rufe duk wasu bills daganan suka kama hanyar gida. A motar ma Yashjub hira yayi ta jan Yassir da shi, yana basa ideas da yadda zai janyo Mutane da yadda abubuwa suke da yadda zai fi mishi sauk’in samun shigowar kuɗaɗe. A fuska kam ba laifi, Yassir yayi iyakar bakin k’ok’arin shi dan sam bai bari Yashjub ya yi tunanin komai daga gareshi ba, amman fa a zuciyarsa ji yake kamar ya mutu…..saboda bashi da shi!! Saboda shi talaka ne wato ta kai har Yashjub ya ci mishi mutunci kuma yake k’ok’arin ci mishi hanci da mota mai tsada. Sannan shine ma zai nuna mishi yadda zai yi business da ragowar abubuwa wato kenan shi an maida shi ma bai san komai ba!!!!. Shi ne ya kamata ya zama shi yake rabon kud’i da abubuwan alfarma amman kullum akasin haka ake samu, kullum sai dai Yashjub ya basa ya bawa wasu…. Shakka babu lokaci ya yi da zai kawo ƙarshen hakan!! Dukda Daddy shine sila, amman ya fi jin haushin Yash tunda shike da kud’in yanzu… Ya tabbatar inda ace Daddy bai ci mishi fuska ya fifita Yash tun farko sama da shi ba to da tuni haka ba ta faru ba! Da tuni shima yanzu yanada company wanda ya yi nasara har ma da estates kamar Yash……… …. Yasmeen tana isa gida, direct wajen Mommy ta nufa, tsabar rashin tunani da tsananin son Kai su fa ala dole sai dai a tarwatsa maganar auren gaba d’ayanta kuma a yi musu farrak’u(Yash da Manu). Tana zuwa ta zayyanewa Mommy yadda Yash ya shanyata a bakin k’ofa tanata uban bugu! Bayan ya bud’e kuma ya disga ta, ya hanata shiga inda yake, bayan ya san Manubiya tana ciki kuma tana ji sannan tana ganin komai, sannan da k’annen Manubiyan suka zo ya mutunta su ya amsa gaisuwar su da kulawa, ita kuma aka barta a tsaye a bakin k’ofa, su suka shige ciki. Kamar za ta fashe da kuka ta d’aura da cewa ‘’Mommy kinga yadda Yarinyar take kallon mutane kuwa, ‘akan hanci’ mun had’a ido da ita amma ko gaishe ni bata yi ba…… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 06* Kamar za ta fashe da kuka ta d’aura da cewa ‘’Mommy kinga yadda Yarinyar take kallon mutane kuwa, ‘akan hanci’, mun had’a ido da ita amma ko gaishe ni bata yi ba, k’annenta ne kawai suka gaishe ni, amman ita d’auke Kai ta yi ta sake tamke fuska’’ Yusra da suke tunanin Yarinya ce itanma yau kam ta bi bayansu….dan a lokacin da Yasmeen ɗin ta shigo itama Yusran tana d’akin Mommyn, a tare ta gansu tana taya ta gyaran wardrobe…sosai itama Yusra ta taya Yasmeen zuga Mommy.. Dama chan ba son auren suke yi ba, yanzu kuwa ganin Manubiya da kuma abunda Yasmeen d’in take ik’irarin an yi mata shi ya sake tunzura su Yasmeen d’in, a cewarsu ’sam ba zai yiu su bari Yash ya auro wata chan daban ba, gashi tun yanzu k’annenta sun fi su daraja da mutunci a idanun Yash, ba ma ita ba. Dama irin abunda suke gujewa kenan, ga shi kuwa an fara tun yanzu,…’ Dan in ba hakan ba fisabilillahi ta ya zai shanya Yasmeen a waje ya hanata shiga, sannan ya dinga wani ririta k’annen wata chan daban wai ita budurwarsa!. Sam bai ma nuna musu wacece Yasmeen d’in ba ballantana su girmamata. Dan haka a gaskiya ba zai yiu su bari Manubiya ta rayu da Yash ba, tunda ya fara haka to akwai babbar matsala a gaba, gara kawai a tarwatsa wannan auren a had’a shi da Kausar tunda itace tasu, ta hakan ne kuma za su zama d’aya kansu ya had’u da d’an uwansu.’ Ita Yasmeen wani sabon abunda ya sake d’aga mata hankalin ma shine ‘Yarinyar y’ar gidan talakawa ce’ Saboda yanayin abayoyin Jidda da Siyama da hijabin jikin Manubiyan kad’ai sun isa su sanya mutum ya fahimci talakawa ne… Shiyasa in dai suka barsu tare to fa Shikenan ta san akanta zai k’are ita da dangin ta! Dan yadda yake ta uban rawar k’afar nan ta san bud’e musu bakin aljihu zai yi! ya yi ta b’arin kud’i, su tatike komai, komai ya koma wajenta!! ita kuma ita da su Mommy a ajjiyesu a gefe, dan ta lura Yarinyar bata da kunya sam kuma bata da mutunci, dan haka tashi d’aya za ta raba shi da su. Haka nan dai kamar za su haɗiyi harshe Yusra da Yasmeen suka yi ta mita su biyu, dan sam Mommy ta ma kasa magana saboda ita duk ba wannan ne abunda ya fi d’aga mata hankalin ba! Dan ta san ta riga ta gama tsarawa ‘indai ta haifu cikin uwarta da ubanta! to Manubiya ba ta isa ta auri Yash ta shigo mata cikin family d’inta ba wallahi,’ dan ko hauka take yi ba zata tab’a bari Yash ya auri Yarinyar da take tafe da downfall d’in ta ba, saboda Baaba Larai ta ce ‘’indai har Manubiya ta kasance a tare da Yash to ba za ta (mommyn) taɓa cimma burinta ba sannan duk wasu sirrinkanta na sama da shekaru talatin ma da y’an kai sai sun bankad’a a fili kowa ya ji ya gani, kuma sai ta shiga masifar da bata tab’a tunani ba’’. sannan bayaga haka indai tana raye to Yashjub bai Isa ya auri wata mace idan ba Kausar ba, saboda ta san duk fad’in duniyar nan Kausar d’in ce kawai za ta iya yi mata yadda take so. Shiyasa ta tsaya tsayin daka take ta fafutukar ganin ta yi ko ma menene ya kamata muddin za ta samu ta hana auren Yash da Yarinyar nan, dan ba ta da guri a cikin family d’inta. Sai dai kuma idanunta da suka rufe akan hana auren shi kaɗai sai ya kaita ga kasa yin tunani mai zurfi, dan kamata ya yi ace ta raba shi da ita har abada, tun a karon farko, ba wai iyaka auren ba tunda ko babu aure indai har suna tare to akwai matsala… gashi kuwa yanzu Yasmeen ta zo mata da wani zance na sabon tashin hankali wanda zancen ne ya sanya ta fahimci tabbas ta yi tuya ta manta da albasa… dan ba k’aramin tashi Hankalinta ya yi ba da ta ji Yasmeen ta ce ’Yash ya shanyata a waje sama da mintuna talatin, tana ta knocking, sun ƙi su bud’e mata da shi da Yarinyar’…. A yadda Yash yake da kud’in nan, ta san ba ko wacce irin Mace ba ce zai nuna yana buk’ata ta k’i amincewa da shi, ballantana Yarinyar da ta riga ta san ita zai aura nan da kwanakin da ba su fi goma ba. Karfa ta je tanata k’ok’arin hana d’aurin Aure aje Yarinya ta samu ciki kafin ma ta shigo cikin gidan, dan indai ta riga ta samu ciki to komai ya zo musu k’arshe kenan, dan ta zamewa Yash k’arfen k’afa kenan. ‘’Mommy!’’ Ɗin da Yasmeen ta ce mata ne ya katse mata tunani, fir-gi-git! Ta yi, sai kuma ta kallesu, ta ga gaba d’aya su biyun ransu a b’ace, hankalinsu a tashe!! Yasmeen ta bud’e Baki za ta yi magana kenan Mommy ta katseta ta hanyar ce mata ‘’Tashi ki je ki kira min Baaba Larai, Yusra kema bita ku turo min ita’’ Wani sanyi Yasmeen ta ji a ranta, dan haka ta mik’e ta fice da sauri, Yusra ma ta bi bayanta. Kamar bayan mintuna sha biyar da fitar su Yasmeen Baaba Larai ta shigo…. A yadda su Yasmeen suka fita suka barta a haka ta shigo ta sameta. Kusa da ita ta nemi waje ta zauna kafin ta ce “yi haƙuri, sun sameni ina girki ne…Ummi na tarar za ta yi masa girki wai an sallameshi Yassir ya tafi d’auko shi, shine na samu na k’arba, da kyar kuwa ta barmun kin san halinta’’. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce ‘’Kin kammala abunda kika fara ne?’’ ‘’Eh! Ai shiyasa ma na karb’i girkin’’ Baba Larai ta bata amsa a cikin ranta tana addu’ar ‘’Allah ya taimakesu, su samu nasara a kan Yashjub, dan abun nasa kamar gado ya yi, saboda shima ɗin ko me aka yi masa to fa ko an ci sa’a ya kamasa ba ya yin wani tasiri kuma baya dad’ewa ya ke karyewa.’’ Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce “Sannu y’ar uwata’’ Sai da Baaba Larai ta gama nazartarta tukunna ta ce “mai ya faru kuma?’’ Ta yi mata tambayar tana gyara zama. Sai da Mommy ta sake sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce ’’Gobe za’a kai kaya, ayi tambaya a yi komai. Daddy sai shirye-shirye yake, har yanzu banga alamun fasawa ba, anya Baaba ana yin komai yadda ya kamata kuwa? Dan ni naga har yanzu kamar ma rura wutar ake yi.’’ Ahankali Baaba Larai ta ce ’’da izinin Allah za mu yi nasara. inshaaAllah ba za’a d’aura ba, ke dai kawai ki zuba min ido kamar yadda na gaya miki’’ Numfashi Mommy ta fesar kafin ta ce ‘’sai maganata ta biyu… Mun yi tunanin Yara fa Baaba, mun gaza mu yi lissafi mai kyau, ba mu auna cewa tsaf shaid’an zai iya tunzura Yashjub aje Yarinyar ta samu ciki ba ko da kuwa ba ayi auren ba! Kinga kuwa idan akwai ciki to bamu isa hana aure ba ko da ace ma mun hana d’in to munyi ta banza ne. Na san Yashjub ba shi da neman mata amma akwai shed’an, ita kuma Yarinyar a nata b’angaren na san a yadda Yashjub yake da kud’i kyau da kwarjini ba ko wacce Mace bace za ta k’i amincewa da shi dan in akayi rashin sa’a akaje ba nutsatstsiya bace sannan gashi tana ganin an kusan auren su kinga ai komai mai iya wakana ne. yanzun fa Yasmeen ce min ta yi ta fi mintuna talatin a bakin k’ofar d’akin da yake d’azu tana knocking amman basu bud’e mata ba, Me kike tunani??? Ina amfanin tarwatsa aure in ta riga ta samu ciki?? Dan na san kafin mu samu mu raba su ko mu san abunyi akan cikin asiri na ya gama tonuwa…..’’ ‘’Tabbas ba mu yi wannan tunanin ba’’ Baaba Larai ta fad’a tana mai sake gyara zamanta, kafin ta d’aura da cewa ‘’zan san abunyi, matsalar shine sunan Yarinyar da har yanzu bamu gama sani ba, Yassira ta ce kamar Manubiya ko Maryam ta ji Yahanasu tace ko?’’ sai kuma ta yi shiru kamar mai tunani, kafin ta fesar da iska tukunna ta ce “inshaaAllah komai zai yi dai-dai’’. Ruk’o hannunta Mommy ta yi kafin ta ce ‘’Baaba na gaji, zuciyata ba za ta iya sake nad’ar wani sabon bak’in cikin ba..’’ Cikin son kwantar mata da hankali Baaba Larai tace “kar ki damu, komai zai tafi cikin tsari.. InshaaAllah ba zan zuba ido Ina ganinki cikin damuwa ba…’’ Daga haka ta shiga lallab’ata tana bata Baki tare da bata tabbaci….. Tukunna da kyar Mommy ta samu ta d’an nutsu, dan ba kad’an ba ta tsorata matuk’a kuma hankalinta ya tashi kwarai. …. A bakin k’ofar shiga side d’in Yashjub Yassir ya yi parking, shi da kanshi ya taya shi shigar da jakar computersa da kayan dubiyar da aka kawo mishi tukunna ya yi mishi sallama ya tafi. Gwaggo da Ummi ne suka kai mishi abinci, daganan suka tambayeshi ko akwai abunda yake buk’ata ya ce ‘’ba komai’’ dan haka suka mishi Allah ya kare gaba ya k’ara sauk’i, suka tafi domin ya samu ya huta… Ai kuwa bai huta d’in ba, dan duk sai yau masu gadi suka samu zuwa dubiya saboda ta’aziyya da suka tafi na driver kuma dama shima ya ce kar a gayawa waenda ba su saninba asibitin da ya ke. Wannan ya shigo wannan ya fita haka masu gadi da drebobi har ma da na mak’ofta da maƙoftan da kansu aka dinga sintiri, har dare! dan haka ciwon Kai sai ya sake turnik’e shi. Ya na sane da su Mommy, kaff cikinsu Yadira ce kawai ta shigo ta duba shi, itanma ya lura kamar fushi take dashi amman kana ganinta ka san ta damu sosai! Da yake Yarinyace itan shiyasa ya yi saurin b’aro jirginta. Hakanan ta yi mishi ya jiki harda d’an dessert d’inta ta had’o ta kawo masa. Sam fuskarshi babu annuri haka ta yi ta tafi dukda kuwa ya ji dad’in zuwan da ta yin amma ya kamata ya koya wa Yaran nan hankali, shiyasa d’azu ma ya ƙi sakarwa Yasmeen! Ba zai yiu su yi fushi da shi a sanda sukaso ba tare da wani kwakkwaran daliliba sannan in sunga dama su kulashi a lokacin da suke so, ba. Sam ba zai d’auki wannan iskancin ba…in the first place ma (ai tun farko ma) ba su Isa yin fushi da shi ba ko ma me ya yi ai shine Babba shine a matsayin ubansu, ko da ace shine bashi da gaskiya ba zai basu damar yi mishi wannan rashin ɗa’ar ba! Ballantana kuma shike da gaskiya….. ..wannan tunanin ne ya sanya ciwon kan nasa ya sake hauhauwa, dan abun ya b’ata masa rai sosai musamman ma ta b’angaren Mommy, ya ji zafi kwarai, a ganinsa bai kamata ta biyewa Yara ta k’i zuwa duba shi ba, ya riga ya san halinta da mugun tirjiya shiyasa kawai ya share ya yi k’ok’ari ya rarrashi kansa da niyyar zuwa wajen ta anjima inshaaAllah ya bata hak’uri kamar yadda ya shiryawa yi tun a asibiti….Daddy ya yi masa magana, haka ma Manubiya, sannan shima a karan kansa baya son irin zaman da suke yi da ita har cikin zuciyarsa amma ita take janyo komai, Mommy tanada wani halin da sai wanda ya zauna da ita ne kad’ai zai iya sani, tanada shiru shiru tanada hak’uri amman kuma ba ta da dad’in zama kwata-kwata, shiyasa duk wanda ya ga irin zaman da sukeyi ita da shi sai ake ganin kamar shi ne ba ya kyauta mata bayan ita take tab’o sa. A hankali ya fesar da iska ya lumshe idanuwansa tashi d’aya tunanin dayake ta yi da rashin sanin abunda ya kamata ya yi game da rasuwar drivernsa ya taso masa…dan haka ya d’au waya ya kira Manubiya akaro na uku daga dawowarshi zuwa yanzu, dan tabbas yana buk’atar shawara. Bayan sun gaisa ne ya nemi ta bashi shawara akan ‘ya yi bincike akan rasuwar driver d’insa, ko kuma ya barshi’ saboda ya san ba accident bane, dukda ya yi alk’awarin d’aukar d’awainiyar iyalin Mutumin daga nan har abada inshaaAllah,,to amma kuma yana gani kamar bai kyauta ba idan ya bari mutuwar sa ta tafi a banza saboda ya kare kanshi daga sakamakon da binciken zai bayar, wanda ka iya tarwatsa shi gaba d’aya. Bata tsananta bincike ba, ta daure ta cije sosai tukunna ta bashi amsa iyaka ta dai dai abinda ya tambayeta…. Cikin son fahimtar da shi ta yi masa nuni da yadda idan ya yi binciken kuma ya je sakamakon ya tarwatsa kamar yadda ya ke zato shin waye zai ci gaba da kula da Iyalan mutumin??. abu mafi dacewa da zai yi wa mutumin shine ya kular masa da iyalansa, shari’ah kuma a barwa Allah subahanahu wata’ala, shi zai bi masa hakkinsa. Ya ji dad’i kwarai kuma, ya samu relief dan dama so yake a hanashi yin binciken. Sun d’an tab’a hira, yau ɗin ya ji dad’i dan babu mita babu complain haka suka sha soyayyarsu kafin su yi sallama ya katse kiran suna jin kamar kar su kashe wayar. Suna gama waya, ya mik’e ya nufi cikin gida. Yana shiga side d’in Daddy ya wuce, suka hau shirye-shiryen gobe, ya dad’e sosai a wajen Daddy kafin su yi sallama ya tafi… Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ya ga hatta cokali Yashjub ya riga yayi order, ya sayi komai! kuma gidan ma ya tsara komai, ya had’a komai, ga lefe shima Yahanasu tana kan had’awa… Ya san inda ace Yassir ne to da zuba ido zai yi ya naɗe Hannu a yi masa komai…. Yashjub yana fita side d’in Mommy ya wuce, sai dai yana zuwa k’ofar d’akinta ya ji a rufe…. Ya so su tattauna ya bata hak’uri su fahimci juna, amman yadda ya yi ta faman bugu ya ji shiru ne ya tabbatar masa da ta yi bacci.. Haka nan ba dan ya so ba ya juya ya tafi ya barwa gobe. A b’angaren Mommy kuwa, a lokacin da ya zo tana parlournta, ta fara jiyo muryarshi yana magana da Yadira wadda take masa sai da safe.. dan haka ta yi sauri ta afka d’akinta ta rufe da wuri saboda ba za ta iya fuskantar Yashjub a halinda take ciki ba! Dan ta san tsaf zata iya shak’e sa!!!!! Haka kurum, tashi d’aya! Yaro ya tsund’umata a cikin bal’ai da tashin hankali, rabonta da ta yi bacci fiye da na awa biyu har ta manta…haka kurum ya je ya d’auko musu mayya!Yo mayya mana, idan ba mayya ba wacce iriyar Yarinyace haka da za’a yi ta yin aiki a kanta amman a banza?. Ba abunda ya fi sake d’aga mata hankali kamar d’azu da ta lab’e ta ji Daddy yana waya da Abhi wai yana hanya ya taho, ta tabbata kenan gobe za a kai kaya a saka rana, dukda Baaba Larai ta ce ‘’ta jira ta ga goben tukunna in an kai to shine sun yi failing(sun faɗi)’’ Amman ita a yadda ta ga anata shirye-shirye gadan-gadan ta san an riga an kai ma an gama, saidai su nema wani alternative d’in(wata hanyar)… Daɗin daɗawa kuma ga maganar da Yasmeen ta gaya mata d’azun, shiyasa duk take a gigice ta rasa inda za ta tsoma kanta ta d’an ji sa’ida. •••• Tun lokacin da Manubiya ta gama waya da Yash hankalinta yake a tashe, bata nuna masa bane dan bata so ta sake assassa masa abun gashi ta ga bashi da lafiya, amma ba k’aramin firgita ta yi ba da ta ji yace “ba accident (hatsari)bane wani ne ya so kashesa‘’. Ganin ta a zaune tanata tunani ne ya sanya Jidda matsowa ta shiga tambayarta….ai kuwa ita kanta Jiddan ba k’aramin firgita ta yi daga jin zancen ba amman sai ta daure itama ta shiga kwantarwa da Manubiyan hankali, sannan ta d’aura da cewa’’kawai ta dage masa da addu’a Allah ya kare sa daga sharrin masharranta, dama mutum kamar Yashjub dole yanada mak’iya.’’ Suna zaune suna d’an tattaunawa Baba ya shigo, dan yau ya shiga busy shi da su Ya Musbah so suke su samu su gama shirye-shiryen tarbar su Daddy wanda za su yi a gobe idan Allah ya kaimu. Sai da ya ci abinci ya d’an huta, tukunna ya kira Manubiya ya zaunar da ita….nutsatstsiyar nasiha mai ratsa jiki ya yi mata, wanda sai da ta kai Manubiya ga yin kuka. Murmushi kawai ya yi ya dafa kanta yace ‘’Allah ya miki albarka da ke da y’an uwanki, Allah ya sa ki shiga gidan aurenki a sa’a.’’ Ahankali duk suka ce‘’Ameen.’’ Daganan Baba ya mik’e ya sake fita, dan ba su gama ba ya shigo. Murna a wajen su Jidda abun ba’a cewa komai, dan yanzun kam maganar biki ta kankama tunda har suka ga Baba ya fara yi wa Manubiya nasiha. Shiyasa suka yi ta murna suna cewa “Allah ya sanya alkhairi” kamar daga sama suka ji muryar inna ta ce ’’Ameen’’ cikin muryarta da suka jima suna begen jin. Aikuwa duk d’insu rufar mata suka yi, saida ta sake maimaitawa suka tabbatar tukunna Muhsin ya fita da gudu ya je ya kira su Baba a masallaci inda suke ta shirye-shirye….. A ranar murna wajen Manubiya da ahalinta ba’a magana, dan har kuka sai da Baba ya yi..kukan farinciki da ya ji muryar Inna a zahiri, haka suma su Manu suka dinga kuka suna godewa Ubangiji subahanahu wa ta ala. Sun jima suna murna, suna godewa Ubangiji, har da Ya Nafi’u. kafin su Baban suka fita domin zuwa su sanar da su Kaka Mallan maganar kawo kud’i da saka ranar Manubiya wanda za’ayi a gobe idan Allah ya kaimu…… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 07* Su Baba suna fita daga d’akin ba da jimawa ba, su Jidda har ma da Manubiyan duk sai suka kaure da hawaye, dan tashi d’aya suka sake fahimtar ‘nan fa da kwanaki goma Manubiya za ta tafi gidanta ta barsu.’ Da kyar ta samu ta share nata hawayen kafin ta samu ta shiga rarrashinsu, tukunna suma suka yi shiru, Muhsin ya yi bacci, ita da Jidda kuma suka cigaba da tattaunawa…y’ar uwar Inna d’aya ce tak a duniya kuma Baba ya ce “ya riga ya gaya mata d’azu’’ dan haka sun san inshaaAllah nan da kwana biyu za ta taho idan an ci sa’a mugun Mijinta jatau ya barta kenan….Gwaggwo Furaira tana da son zumunci, amman sai ta yi rashin sa ar Miijin aure ‘Jatau sarkin yak’i’, a chan k’auyen su Inna take har yau, Mijinta irin bokayen soron nan ne, ya kafeta a gidan, ko kara idan ya ajjiye ba ta isa ta tsallake ta ba, dan tun lokacin da ya fahimci ta fara shiryen-shiryen guduwa sakamokon ganowa da ta yi ba ya haihuwa ga kuma mugayen halayen shi da su ka yi yawa, shikenan ya kafeta a gidan. Tun daga ranar ko waya sai ya so tukunna za ta yi da Inna….. Gwaggo Furairah sai Mama ta gidan Ammi, su kad’ai ne waenda Manubiya za ta nuna ta ce za su yi mata uwa tunda Inna tana kwance… Dukda ta so ace Inna ta ga aurenta akan k’afafunta amman bata isa jayayya da abunda Ubangiji ya riga ya tsara ba. Ta san su Umma Kuluwa ba lalle su kulasu ba, amma dukda haka suma za’a gaiyyace su, watak’ilan in sunga dama su yarda Mazajensu ma su yarda idan aka zo d’aukarta su rakata d’akin Mijinta kamar yanda akeyi wa ko wacce ƴa mace…. Siyama kam sun san batada matsala, za ta tsaya mata a y’ar uwa, haka ma Aisha matar ya Nafi’u .. Su kenan jama’ar Manubiya, bata da wani dandazon Jama a sai ko mak’ofta, dan haka suka yanke akan ko Gwaggwo Furairah ta zo tace a yi taro su kam ba za su yi ba, iyakacin abunda suke buk’ata suke kuma adduar samu shine a yi auren a gama lafiya, ta samu Matan da za su rakata d’akinta.. Dama kuma ita Manubiya tun ba yau ba bata da buk’atar hayaniya a biki, sam ba ta so. Maganar kayan d’aki kuwa Jidda tana sako zancen Manubiya ta ce ’’Jidda babu wani kayan d’aki da za’ayi, Idan ma ya ce a yi jere nikam zan fito mishi k’iri-k’iri ince ya yi hak’uri, dan ba zan ma fara d’agawa su Baba hankali da wannan batu ba, an samu da taimakon Allah da na ya Nafi’u da ya Musbah muna ci muna sha to hakan ma ya ishemu Alhamdulillah. Ke kanki kin san yanzu ana fara maganar jere Baba zai fara tunani… k’arshe na san bashi zai ci dan cewa zai yi sai ya yi, kuma na san k’arshen abun ba zai yi kyauba.’’ A take Jidda itama ta goya mata baya d’ari bisa d’ari akan hakan, dan haka suka yanke shawarar ana fara maganar jere ma za ta yi kicin kicin ta ce ‘’bataso!’’. Sun jima sosai da Jidda, kafin daga k’arshe Jidda ta yi barci ta bar Manubiya tana ta tunani, sai da ta ga shigowar Baba tukunna ta samu ta yi barci bayan kowa a d’akin ya yi. …. Washegari.. A jiyan, dare ya yi kafin suka gama tabbatarwa shiyasa sai a yau ɗin da safe su Jidda suka tura Muhsin ya je ya gayawa Mama ‘za a kawo kud’in auren Manu’. Ba k’aramin dad’i Matar ta ji ba kuwa, dan haka bayan zuwan Muhsin da kamar mintuna biyar sai ga ta, duk da ta san Inna ba za ta iya bata amsa ba amma haka ta zauna ta shiga yi mata ‘’Allah ya sanya alkhairi’’ tana ta murna aikuwa ga mamakinta ta ji Inna ta ce mata’’Ameen’’ itama… Ba k’aramin dad’i hakan shima ya sake yi wa Mama ba, sosai ta yi murna kamar za ta yi kuka dan farin ciki, haka nan ta yi ta maimaita ‘’Alhamdulilla’’ su Manubiya suna ta murmushi, suna jin tsananin dad’i da annashuwa. Mama ba ta jima da zuwa ba Sofia ta zo, suka fara aikin su, su kuma su Mama suka koma gefe itada su Manubiya, daga nan ta shiga tsokanar Manubiya wai ‘dama ashe tana da saurayinta amma shine bata tab’a ba ta labarinsa ba…..’ Bayan wasu ƴan lokuta, Sofia ta yi ta gama ta ce musu ‘sai zuwa anjima da magrib, za ta sake dawowa’ daga nan ta yi musu sallama ta tafi. ita kanta tana mai mamakin ci gaban da ake ta samu na lafiyar Innar. Da Mama da Siyama sai Aisha, su hud’u ne har Jidda suka zauna har rana lokacin da aka kawo kud’in auren Manubiya daga b’angaren Yashjub. Maama ta yi matuk’ar mamaki da ta ji sati biyu kacal aka saka haka itama Aisha da kuma Siyama…Haka su ma su Baba Habu da Kaka Mallan wanda da da farko ya cewa Baba ‘’Ba zai je ba, ai an ja musu layi a tsakaninsu’’ amma tunda ya lek’a ya ga zunduma zunduman motoci a bakin masallacin a take hankalinsa ya tashi! Haka nan ya je ga Baba Habu akan ya zo su je, har da zaginsa akan ya ce “shi fa ba zai je ba’’. Cikin gaggawa ya dinga azalzalarsa yana ce masa ’’ai shine Babba, ya yi hak’uri, ya turawa Baba aniyar sa, ya je ko dan zumunci’’ Da fad’a da rarrashi haka nan ya jijjib’oshi, suka nufi masallacin yanata sauri dan karsu makara….. Ai kuwa jama’ar wajen sun ga ikon Allah a wajen Kaka Mallan. Daddy da K’anninsa(Abhi) wanda ya iso daga uk jiya around 3:00am(wajajen ƙarfe ukun dare), sai Yassir da wani babban Abokin Daddy ne suka zo suka kawo kud’in(naira miliyan biyu) aka saka rana nan da sati biyu inshaaAllah…kaff cikinsu babu wanda Kaka Mallan bai bi ya karb’i numbersa ba, duk kalar disgin da Yassir ya yi masa da b’ata ran da yake ta yi sai da ya hak’ura ya kula shi ya bashi wrong number…dan ya tsani tsohon, ya tsani layin gaba d’aya, shi tunda yake a rayuwarsa ma bai tab’a tunanin akwai tsukukun layi irin wannan ba, gashi karakakaf layin gida uku ne manya sai masallacin da yake da kyau shima amma gaba d’aya ragowar gidajen kamar kango a ransa ya ce “me Yashjub ya gani da ya zo nan??’’ ya yi wa kansa tambayar, ba tare da ya san wa zai ba shi amsa ba, Kafin ya d’an tab’e Baki a ransa ya ce ‘’koma dai yaya, shi ya sani, atleast zai k’ask’anta kafin ya mutu, dama nan ne ya fi dacewa da shi, shiyasa gashi ya zo nan d’in zai d’and’an k’ask’ancin daganan ya mutu’’ Ko gama tattaunawa ba a yi ba Yassir ya mik’e ya fita daga cikin masallacin…. Kallonshi kawai Daddy da Abokinsa suka yi, kafin suka d’auke Kai aka ci gaba da tattaunawa. Dakyar Baba ya yarda da buk’atar da Daddy ya zo da ita ta inda yake cewa’’Dan Allah kar su zo da komai, Yarinyar kawai ake so, basa buk’atar kayan d’aki’’ Daganan suka tsayar ‘nan da kwanaki goma za su dawo a d’aura aure inshaaAllah’ bayan Baba ya nemi a d’aura a nan masallacin, sun amince. Su Yaa Musbah ne suka tartare Pepper chicken da su cake da doughnuts da lemukan da ya Nafi’u ya kashe uban kuɗaɗe ya yi order, dan a cewarshi bai kamata a ji kunya ta ko wanne b’angare ba, ya san ba za su yi abunda ya kamata ace sun yi wa mutane masu uban arzik’i kamar su Daddy ba amma koma yaya dai ya kamata su kamanta. Har mota suka kai musu suka jibge, Daddy ya na ta faman saka musu albarka da shi da Abokin shi, daga nan suka yi musu sallama suka shiga motocin su suka wuce, suka bar su Baba suna mamamakin Yassir! Ko da ya shigo fa sune suka gaida shi, tunda ya zauna a cikin masallacin bai ce komai ba hakanan ya had’e fuska yana kallon mutane akan hanci, ko irin murmushin nan bai yi ba lokacin da Daddy ya gabatar da shi a matsayin d’an uwan Yashjub wanda yake bi masa, daga k’arshe ma tashi ya yi ya fice gaba d’aya, yanzun ma da suke yi masa sallama bai ko kalli inda suke ba ballanta su sa ran zai amsa, Har Hannu Kaka Mallan ya mik’a masa amman ya wuce da sauri ya shige motarshi…..addu’arsu d’aya itace ‘Allah dai ya sa ragowar y’an uwan Yashjub ba haka suke ba’ dan yanayin Yassir da yadda sam Daddy ya kasa tsawatar mishi ko da da ido ne ya ba su mamaki ya tab’asu matuk’a. Daddy dai shi ba shi da matsala, amma sun lura hatta k’aninsa (Abhi) bai yi wani farin ciki da wannan hadi’in ba… Gudun kar ma su kawo wani tunanin su je su janyo wani mugun abun da Bakinsu ne ya sanya gaba d’ayansu su ukun sukayi shiru kawai, ba wanda ya kawo zancen rashin da’ar Yassir, kowa ya rik’e abun a cikin ranshi kawai. Su biyu suka tartare masallacin, suka kunna turare, daganan Ya Nafi’u ya d’auki jakar kud’in dama shi su Baba suka cewa ya k’arba tun lokacin da Abokin Daddy ya mik’o. Da sauri Kaka Mallan ya ce ‘’yanzu menene abun yi?’’ bai jira an bashi amsa ba ya d’aura da cewa “ku kawo kud’in, akwai wani Abokina da d’ansa yake kayan d’aki na gani na fad’a, kunga sai a basa ya had’a mata komai, mu samu mu fita kunya, itama Yarinya ta fi k’arfin gori, kar ku biyewa Mahifinsa wai dan ya ce kar a kawo komai, ya zama dole mu yi mata ko dan mu fita kunya.’’ Da mamaki Ya Nafi’u yake kallonsa, daman tun d’azu ya k’ule da shi sabida yanayin yadda ya dinga abubuwa a gaban su Daddy, gaba d’aya ya basu kunya sai wani zumud’i yake yi… shiyasa yana shirin ci gaba da magana yanzun Ya Nafi’un ya ce ’’dakata Kaka Mallan, da kai da wa za ku fita kunya??’’ bai jira jin amsar shi ba ya d’aura da cewa’’Bayaga haka ma me ka ke yi anan ne?’’ Ya faɗa mishi hakan kanshi tsaye, dan wasu mutanen in ba a ajjiye kunya da kara a gefe an yi musu wuta wuta ba! Tabbas sai su kassara mutum cikin sauƙi. Da sauri Baba Habu ya juya ya fice gaba d’aya daga cikin masallacin Cikin takaici Ya Nafi’u ya ɗaura da cewa ‘’Ba Kai ne ka ce ba zaka zo ba jiya?ina har hantarar mu ka yi da muka je gaya maka?’’ Cikin fushi Kaka Mallan ya ce ‘’Ka ci ubanka Nafi’u! Ashe baka da hankali ban sani ba? Banza d’an karere kawai’’ Da sauri ya Musbah ya ce ‘’A’a kaka Mallan Nafi’u kam ba d’an karere bane a wannan lamari, a ko wanne lamari ma na rayuwarmu Nafi’u ba d’an karere bane, dan ya yi mana uwa ya yi mana uba’’ Salati Kaka Mallan ya rafka kafin ya ce ‘’Musa kana ji abunda suke yi min ba za ka ce komai ba?’’ Sai kuma ya fashe da kuka daga nan kawai ya juya ya fita yana cewa ‘’Dama amana nakeso in rik’e, amman tunda bakwaso shikenan, kai Musa ubanka yana chan kabari amman na san an haska mishi wanna son datse zumuncin da kake k’ok’arin yi’’. Numfashi Baba ya fesar ya girgiza kai yana msmakin yadda sam kaka mallan ba shi da lissafi, baya jin shakkar ya ji kunya ko ya zubar da kanshi indai ta b’angaren abun duniya ne. Kuma ya tabbata inda gari banza ne Nafi’u ya yi masa haka ya san da sai ya tara musu jama’a ya yi musu tijira, amma da yake ya ga da akwai abu a wajen su shine ya kwantar da Kai har da kuka… a hankali a fili ya ce ’’Allah ya kyauta’’ yana aiyyanawa a ranshi ‘inshaaAllah zuwa anjima zai je ya yi musu godiya da shi da Baba Habu, Allah ya sa su k’are lafiya. … Suna zuwa suka mik’awa Manubiya kud’inta…kasa karb’a ta yi dan tashi d’aya fargaba da kunya suka rufe ta ,daga k’arshe ma sai ta saka musu kuka Murmushi kawai duk aka yi ana kallonsu ita da Jidda da Siyama da Muhsin da suka shiga taya ta yin kukan. …. Ƴar tattaunawa aka yi, ta inda ya Nafi’u ya soma da ‘Daddy yace kar azo da komai… amma dukda haka tunda ga kud’i nan ta samu sai a siya mata gado mai kyau da tsada da shi. Shi kuma da Ya Musbah da Baba za su siya mata y’an kayan kitchen, dangin su flask sannan za su yi y’ar walima.’ Kowa yayi amannah da hakan banda Manubiya, dan tashi ɗaya sam ta k’i yarda a yi hidima ko wani kayan daki, saboda ko da su Ya Nafi’u ma suka fita cewa ta yi ’’kud’in a barshi kar a siya mata komai, za ta bawa Baba ya Nafi’u da Ya Musbah jari bayan auren da shi. ‘Dama ta shirya za ta gayawa Yashjub ba za ta zo da komai ba, to kuma yanzu tunda iyayenshi sun buk’aci hakan ai Alhamdulillah’”. Murmushi Mama ta yi kafin ta matso ta dafa kanta tana jin tsananin k’aunar Manubiyan a ranta, za ta iya cewa bata tab’a had’uwa da Yarinyar da ta shiga ranta lokaci d’aya ba kamar Manubiya tanada hankali da hangen nesa….. A hankali Mama ta sauk’e ajiyar zuciya bayan ta dafa kanta nata tukunna ta ce ’’Ba za ayi haka ba Manu, ba zai yiu Mutanen nan su kawo har naira miliyan biyu sannan ga sadaki a gaba da zasu kawo amma ki ce ba za’a kai ki da komai ba, ni sai naga rashin dacewar hakan’’ ta fad’i hakan tana mai juyawa ta kalli Inna kafin tace ‘’ko ya ki ka ce??’’ Lumshe ido innar ta yi ta bud’e alamun eh sannan a hankali ta d’an yi murmushi, murmushi suma duk suka yi kafin Aisha tace ‘’Nima na bi bayan su Inna! Dan Gaskiya Manubiya kamar yadda baban khairat ya ce ya kamata ko gado ne wanda za ki saka a d’akinki d’an waje mai kyau a samu a siya miki, ki je da shi, ba dan komai ba ko dan kema ki dinga gani kina jin dad’i sannan ko ba komai muma za mu ji dad’i bamu kai ki haka ba komai ba, kuma ke kanki kin wuce gori, dukda dai na san a yadda suke da kud’in nan ba lalle su yi k’arancin tunani irin na k’ananun Mutane ba amman fa y’an uwanshi Mata har su shida ya ce miki ko? kinga kuwa ai Mata ba‘a rabamu da k’ananun maganganu ba. Dan haka gara kawai ki bari ayi miki wani abun, su Baba Allah zai duba su suma’’. Da sauri Siyama ta ce ‘’Na san ma zai bawa Ya Musbah aiki shi Mijin naki inshaaAllah’’ Murmushi Aisha ta yi kafin ta ce ‘’Ban d’au wannan akai ba, amman dai in ya bayar Alhamdulillah’’ Ba yadda Manubiya ta iya, haka nan ta yarda ba dan ta so ba amma dukda haka sai da aka ware duba d’ari d’ari akan zata bawa Ya Musbah d’ari Ya Nafi’u d’ari Baba d’ari, sannan ta ware kud’in saka Muhsin a makaranta. Ba dan Mama da Aisha sunso ba, haka nan suka yarda suka mutunta tata shawarar itama. Still, Manubiya ba ta so ba amma sai da su Siyama suka fitar da anko, ba yadda ta iya haka ta yarda ta biye musu ta barsu akan za su yi ankon atamfa wadda za su saka ranar da za a kaita, dan walimar ma tace “dan girman Allah su hak’ura, tunda za ayi wuni in an d’aura aure, kar su d’aurawa kansu hidima da yawa.” .. Siyama dama tanada ƴan kuɗaɗenta, dan haka ita da Aisha da Manubiya da Mama suka cikawa Jidda.. A take a lokacin Aisha ta fitar musu da atamfar da za su yi aka turawa Siyama a wayarta akan za ta nunawa anty umma sai kuma sukace zuwa anjima za su lek’a ita da Jidda har side d’in su Uncle duk su nunawa kowa dukda dai an ja layi an musu tsakani amman za su gwada sun san ko ba komai za su samu lada. Bayan kamar awa biyu su Aisha suka tafi kasuwa itada Siyama da Jidda, suna fita Mama ma ta yi musu sallama ta tafi dan tanaso ta karb’i number wata mata a wajen Ammi mai sayar da magungunan gyara na mata, InshaaAllah ita za ta yi wa Manubiya uwa, tana tsananin k’aunar Yarinyar sannan ba ta samu sa’a da damar aurar da tata y’ar ba wadda a yanzu tana kyautata zaton ta riga ta yi aure ta ma hayayyafa, dan haka inshaaAllah za ta zamewa Manubiya uwa, ta yi mata duk wani gata,ta aurar da ita. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 08* In da rabo…idan Allah ya k’addara za ta ga y’ar tata sannan ta ga jikokin ta Alhamdulillah! Idan kuma Allah ya riga ya k’addara sun rabu kenan har abada to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi… Ita dai fatan ta shine ‘Allah ya sa itama y’artata ta samu wadda za ta tsaya mata kamar yadda itama za ta tsayawa Manu da zuciya d’aya!’ Tunda ita kam ba ta da ikon zuwa ko da kusa da ita ne, ballantana ta kula da ita. Ba za ta yi tsammani ko ta dogara akan cewa ‘kishiyarta wadda ta bari a wanchan gidan! Za ta yi wa ƴartata uwa ta ko wanne fanni na rayuwarta ba!’ Dukda kuwa ba ta tab’a kama kishiyar tata da wani mugun hali ba amma kishiya a duk inda take kishiya ce. Ta san dai ba za ta cutar da y’ar tata tunda ta san tanada hali mai kyau daɗin daɗawa kuma mijinsu ba zai taɓa bari ba dan yana tsananin son ƴaƴansa, amma kuma ta san ba za ta tsaya mata ta kula da ita ba kamar yadda ko waccce uwa take yi wa y’arta tsakaninta da Allah! Sannan ba gajiyawa..Dan duk girman ƴa Mace to tana buk’atar uwa ko wadda za ta zame mata tamkar uwa a rayuwarta a kullum da ko da yaushe . Da yamma lik’is Likitar Inna ta dawo…kamar ko yaushe yanzun ma ba kyama ba komai haka take kula da duba Inna da wasu ingina, sannan ta d’an yi mata exercise. Sai da duhu yayi tukunna ta tafi… Wani abun mamakin kafin dare kusan kaff mak’oftansu Manubiya sai da suka shigo, har k’awayenta waenda sukayi islamiyya tare ita tama manta da wasu dan ba harka suke yi tare ba tun rabuwar makarantar amma haka suka dinga shigowa suna yi mata Allah sanya alkairi sannan suna tambayar ta anko da event nawa ne. Ita kam sai dai ta ce musu “ba komai, babu event’’ kawai. Haka dai suke tafiya suna masu nanata mata akan ‘idan an fitar ko an chanza ra’ayi za’ayi event d’in, kar ta manta da su ta sanar musu da wuri dan Allah’’ Gaba d’aya ita kam ta shiga damuwa, duk ta yi jigum ta zama so silent. Sai da hayaniyar ta ragu, tukunna ta samu ta aika Muhsin ya je ya karb’o mata wayarta daga charji dan kwana biyu Nepa suna gwada musu hali. Dama ta san sai ta ga misscalls d’insa, dan haka ko tsayawa k’irgawa ma ba ta yi ba ta shiga kiransa dan itama ta yi missing d’insa, iya wunin yau da ba ta ji muryarsa ba duk wani iri ta ke jinta!! Tana tsananin son Yashjub amma kuma ba ta so ta yi aure a d’auke ta a rabata da ahalinta…. ‘’Assalam alaiki Matar Yashjub!!’’ Muryarsa ta katse mata tunani, ba ta san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba, dan wani sanyi ta ji yana ratsata daga jin sunan da ya kira ta da shi… Cikin sanyin muryar a hankali ta ce “ameen wa alaikaAssalam’’ Murmushi ya yi kafin ya ce ’’ba ki ce mijin Manubiya ba’’ Shiruu ta yi tana murmushi k’asa-k’asa dan haka ya ce ’’ashe wata za ta ganni na zo yanzunnan, tunda na san hanya, kuma wallahi idan na zo sai k…. “ “ameen wa alaikaAssalam Mijin Manubiya’’ Ta fad’i hakan cikin tarar numfashinsa, dan tana tuna abunda taurin kanta ya janyo mata ranar chan a asibiti. Aikuwa murmushi da dariyar da ya shiga yi sai da ta yi mamaki da dariya itama, kafin chan ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace “bana jin akwai sunan da aka tab’a kirana da shi na ji dad’i kamar wannan, da farko da na kira ki fushi nakeyi dake akan cillar da wayarki da kika yi tun d’azu na kasa samunki, amman yanzu kam na daina dan kin yi bribing d’ina (kin bani cin hanci na) da wannan daddad’an sunan… Ɗan sake fad’a in ji….’’ Sai da ya sake cewa ’’plsssss mana’’ kamar zai yi kuka tukunna ta ce ’’Mijin Manubiya’’ Cikin tsananin nishad’i ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin yace “Allah ya barmu tare, Allah ya tabbatar mana da alkhairi’’ Ahankali tace “Ameen’’ Daganan suka shiga hira…. Manubiya in banda mamaki ba abunda take yi dan murna da zumud’in da Yash yake yi har tsoro ya fara bata, kamar a kanshi za’a fara aure a duniyar nan.. wani abun ya bata dariya wani abun ya sata jin kunya, har sunan y’arsu ta farko sai da ya tsayar dan shi yace ‘’ya fi son ta haifa masa baby girl a farko mai kama da ita sak! sak!!InshaaAllah, amman in Namiji Allah ya fara basu shima zai yi tsananin murna muddin daga gareta ne, babu abunda zai gani yanzu a gaba bayan auren su wanda zai sanya shi matuk’ar farincikin da sai ya kusan suma kamar ya ga jninsa shi da ita, ranar bai san wani kalar farin ciki zai yi ba, yana masifar son Yara dama yana kuma masifar sonta dan haka ta ƙiyasta ta ga kalar dad’in da zai ji idan ya samu babies daga wajenta…..’’ Ita kam Manubiya gaba d’aya hirar tasa sai ta fara zame mata uncomfortable, dan yadda yake batun soyayyar da zai nuna mata!ciki!da haihuwa!….. kanshi tsaye ba kara abun ya girmewa tunaninta, gaba d’aya ji take yi kamar ta nutse, shiyasa ta samu ta yi masa wayo ta ce ’’bacci take ji sosai’’ dan ta samu ya barta, da kyar kuwa ya barta bayan ya ce mata’’ta shirya gobe inshaaAllah zai zo su d’an fita, su sayi abubuwan buk’ata da za ta yi amfani da su a biki’’. Kafin ya d’aura mata da zazzafan ‘i love you’ ɗin da sai da ta ji sa har tafin k’afafunta da tsakiyar kanta, tukunna suka kashe wayar. Tana ajjiye wayar ta shak’i numfashi sannan ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi gasar rik’e numfashi. •••••• Sai dare bayan sun kammala dinner tukunna Abokin Daddy ya yi musu sallama ya tafi, ko cikin gida Abhi bai bari sun shiga ba, anan garden d’in inda suka zauna da Abokin Daddyn, ya cewa Daddy “ya tsaya, yana so za su yi magana’’. Murmushi kawai Daddy ya yi, saboda dama ya lura da yanayin Abhi ɗin tun d’azu, shiyasa a hankali tun kafin Abhi ya ce wani abun shi ya dafa kafad’arsa ya ce ‘’Abhi, da mai kud’i da talaka duk Ubangiji ne ya haliccesu.. Yashjub Yarinyar ya nuna yana so itace zab’insa, namu kawai mu goya mishi baya, mu aura masa ita, ko da kuwa a bukka take’’ Cikin katse shi Abhi yace “seriously??? Talaucin nasu is too much, Yashjub is way too rich Ya je wajen ta’’ Numfashi Daddy ya fesar kafin ya ce ‘’and yet he did(gashi kuma ya je ɗin), so dan Allah Abhi kawai mu yi supporting d’insa…mu goyi bayansa pls.” ya fad’i hakan a gajiye. Shiruu Abhi ya yi yana tunani a cikin ransa…. ‘wallahi in da ace ya san irin wannan Yash zai kwaso to da ya gwammaci ya yi masa auren dole da y’arsa Naeema, Yarinyar tana son shi(yash) shiyasa ma ta ce ita zata zauna a gida har a yi bikin a k’are dan ba zata iya ganin auren sa ba. baya so ya yi masa dole shiyasa bai tada maganar ba, amma yanzu kam yana dana sani dan gwara auren dole akan wannan auren da yake shirin yi…..’’ Cikin son fahimtar da shi Daddy ya ce ’’na san kaine a matsayin uba, tunda a wajen ka yake… Kar ka ga kamar na yi maka shishshigi, dan Allah ka fahimceni brother. Sannan kar ka nuna kamar ba ka so dan za ka bawa Hajiya Mama k’ofa ne itama ta fara. Dukda na san ita ba zata k’i auren saboda talaucin Yarinyar ba amma indai ta ga kana kakkaucewa to tashi d’aya za ta saka ayar tambaya akan lamarin sannan ta fara cewa itama bata so….ka san kuma na riga na yi musu (su Yashjub) alk’awari tun ba yau ba kuma nima hankalina sai ya fi kwanciya idan ya auri wadda yakeso…. Sannan Yash is very obidient(yana da hankali da biyayya), baya biye-biyen mata, dan haka a ganina tunda har ya nuna wannan ɗin ya ce yana so to the best thing(abu mafi kyautuwa) da za mu yi shine mu aura masa ita. A yadda yake son Manubiya hana shi aurenta shine abu na ƙarshe da za mu iya aikata masa a wannan halin da da yake ciki..idan ka lura ba ya shiri da kowa! Kullum yana cikin yanayi na rashin walwala, ga kuma Khadijah wadda har gobe ta k’i ta gyara halinta ballantana a samu ya sake da ita…..Abhi farin cikin ƴaƴana nakeso Ingani, idan ni bana cikin farin ciki bai kamata ace suma ba za su yi ba”. Shiruu kawai Abhi ya yi, dan a take ya ji tausayin d’an uwan nashi ya lullub’e shi… Ya lura tabbas idan suka zubawa Khadijah da Kausar harma da Baaba Larai ido to tsaf za su kashe mishi d’an uwa da bak’in ciki! Tunda ya san ba zai iya yin magana ba, kuma ba zai iya aikata komai ba… Haka kurum Mata ta tattaro gaba d’aya danginta ta tare a gidan ta ƙi gaba ta ƙi baya?! Suna sane da yadda ta hanashi k’ara aure bayan kowa ya san yanaso ya yi, sai yanzu da Allah yayi. D’an bubbuga kafaɗanshi Daddy ya yi a hankali, kafin ya ce ’’yanzu mu je ciki, tunda ka zo ba ka shiga ba, ba ka ga amarya ba ma’’. Girgiza Kai kawai Abhi ya yi kafin ya ce ‘’idan Hajiya Mama ta zo ma gaisa da ita a tare’’ Yana shirin shigewa Yashjub ya k’araso wajen, tun d’azu da safe da suka fita shi da Najeeb sai yanzu ya dawo… Har k’asa ya durk’usa ya yi musu godiya bayan sun gaisa, daga nan suka wuce tare shi da Abhi dan a side d’insa dama Abhin ya sauk’a… Hakanan da Abhi da Daddy suka yi ta mamakin tsananin murna da walwalar Yashjub d’in ta yau, abunda ba su saba gani ba. Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e bayan ya ga shigewar tasu, kafin ya furzar da iska a hankali ya lumshe idanuwansa. ….. Washegari da Asubah, misalin 4:00am, Daddy da Abhi suka nufi airport domin d’auko su Hajiya Mama. 5:00am dai-dai jirginsu ya yi landing (ya sauƙa) a garin Kano… Suna tsaye suna jiransu, Daddy ya hango Junior ya karyo kwana.. Murmushi Daddyn ya yi kafin ya ce ’’Wai!!Tubarkallah! Ai ban ga chanjin a hotuna da video calls ba kamar yanzu a fili’’. Da sauri Abhi ya d’ago shima ya kalli direction d’in da ya ga Daddy ya na kallo yana tsananin murmushi….. Dogon saurayine wanda a k’alla zai kai kimanin shekaru 27 a duniy, kalar fatarsa bak’i ne, irin mai shek’i da kyau d’in nan. Ba shi da muni kuma ba za a kirashi da kyakkyawa ba. Yana da fad’in k’ashi sannan jikinshi a murd’e yake wanda tun a kallo ɗaya ake iya fahimtar ya saba da ziyartar gym. Sanye yake da dogon wando pencil bak’i irin na maza, sai bak’in takalmi sauciki, da farar riga mai gajeran Hannu me kama jiki an rubuta ‘lucky trip’ a jikin gaban rigar, yayinda Kanshi yake sanye cikin hula irin ta sanyi bak’a itama ya d’an tura ta baya kad’an, sai jakarsa bag pack da ya goya da trolly… Daddy yana cikin k’are mishi kallo ya k’araso daff dashi, Yana zuwa ya sa Hannu ya rungume Daddyn sannan ya ce ’’I miss u Daddy.” Murmushi Daddy ya yi ya d’agosa yana mai sake k’are masa kallo kafin yace “Imam ya gida, ya uk, ya aiki??’’ Murmushi yayi ya ce ’’Alhamdulillah, Ina wuni’’ Cikin katsesu Abhi ya ce ‘‘Ina Hajiya Mama?’’ Dariya Junior ya yi kafin ya ce ‘’Suna chan tana karb’ar number wata Mata… wai Matar ta ce mata tana Maganin mayu da asiri, shine ta tsaya karb’ar numberta saboda tana so za ta yi inviting nata gidan a yi maka feshi da ruwan addu’a.’’ Ya ƙarasa faɗin hakan yana kallon Daddy yana dariya. Shiruuu duk su ka yi kafin Daddy ya ce ‘’Allah ya kyauta’’ Dai-dai nan wasu Mata guda biyu suka tunkaro su, d’ayar ba za ta kai shekaru hamsin ba..bak’a doguwa, sanye cikin doguwar rigar abaya ta rufa mayafinta. Sai d’ayar Matar kuma wacce a k’alla za ta kai shekaru 70 a duniya…fara ce k’all sannan doguwa ce sosai amman bata da jiki, kyakkyawace sosai dukda ta tsufa amma hakan bai b’oye kyawunta ba, tana sanye da laffaya blue black Idanunta kuma sanye cikin farin glashi. Magana suke yi k’asa-k’asa itada d’ayar Matar wanda kana gani ka san sirri ne akeyi shiyasa har ba su ma lura da su Daddy waenda suka nufesu ba, dan sai da suka k’arasa daff da su tukunna suka lura da su. Har k’asa su Daddy suka durk’usa suka gaida ita, da kyar ta iya cewa ’’lafiya Alhamdulillah’’ Idanunta suna masu ciccikowa da hawaye tun lokacin da ta kalli Daddy, kafin a hankali ta d’an rissina ta d’agosa tsaye. A hankali take kallon shi tana me shafa gefen fuskarshi kamar wani Yaro tana jin tsananin tausayin sa yana sake ratsata. Murmushi yayi yana mai kallon Mahaifiyar tasa kafin ya kama Hannunta wanda ke a gefen fuskarshi ya rik’e a hankali ya ce ‘’ya hanya?’’ ‘’Lafiya’’ kawai tace still idanunta suna a kansa kafin daga bisani da kyar ta kauda idanunta ta maida kan Abhi ta ce ‘’Hankalina bai kwanta ba sam, shiyasa nake ta jera addu’o’i tunda muka taho. Yanzu haka ma a jirgi yi nake ta yi, da ikon Allah kuwa sai na ji Matar bayana suna magana da ta gefenta, daga yanayin conversation d’insu (hirar tasu) na fahimci maganar tasu, shiyasa da aka fito na tsaida ita, shine take ce min ‘Dad d’inta babban malamine, kuma da ya zo rasuwa ita ya barwa malintar’ shine fa na tsaya na karb’i numberta, to cut it short dai (a taƙaice dai) na bata adress za ta zo ta yi feshi gaba d’aya gidan da ruwan addu’o’i’’ Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e Abhi kuma ya sunkuya da kanshi k’asa saboda a da yana ganin rashin kyautawa da rashin gaskiyar Hajiya Mama amman shima yanzu gaskiya ya d’an fara bin bayanta… A hankali Daddy ya ce ’’Mama pls mana, Matar da ba ki gama saniba itac……’’ Wani kallo Hajiya Mama ta yi mishi wanda yasanya shi had’iye ragowar maganganun nashi, ba ta sake bi ta kansa ba ta juya ta kalli Abhi ta ce ’’take me to the car”. ‘’Right away’’Abhi ya ce da sauri, daganan suka nufi inda Junior yake tsaye gaba d’ayansu har wad’anda suka turo akwatunan su Hajiya Mama. Suna zuwa Junior shima ya bisu duk suka d’unguma zuwa wajen motocin da aka taho da su. Ana kiran sallah suka isa gidan, dai-dai Yashjub ya fito kenan zai tafi masallaci, sai da aka yiyyi murna da oyoyo tukunna su Hajiya Mama suka shige ciki bayan Daddy ya kira gwaggwo ya ce mata “ta nuna musu inda aka gyara musu’’ Junior ma da wucewa zai yi, sai da Daddy yayi mishi da gaske tukunna ya yarda ya bi su masallacin a cewarshi wai ’’ya gaji bacci yake ji.’’ Ana idarwa kuwa ya ce a nuna mishi inda Yassir ba ya nan, dan ya san indai suka had’u to ba zai yi baccin ba. Side d’in Yashjub suka nuna mishi, daganan Daddy suka nufi sama side d’insa dan akwai maganar da suke so su yi both akan business da kuma family issue. Sai around 7:00am, Tukunna y’an gidan suka shirya kowa ya fara shirin sauk’a k’asa domin yin breakfast. Sai da numfashin Mommy ya yi sama! A lokacin da ta fito, dan ta na fitowa suka yi ido biyu da mom, ta san kuma indai ta ga mom tou kamar ta ga Hajiya Mama ne. Murmushi ta k’ak’alo da kyar, tukunna ta k’arasa inda mom din take tsaye jikin k’ofa. A hankali tace’’Sameeha, sauk’ar yaushe?’’ Murmushi mom ta yi bayan ta juyo tukunna ta ce ’’Khadija ykk, ya gida? Ba mu dad’e da zuwa ba’’ Dai-dai nan Hajiya Mama ta fito daga d’akin inda mom ta rik’e mata k’ofa, tana fitowa suka yi ido biyu da Mommy dan haka ahankali a fili ta ce “A’uxubillahi Bismillah’’ Sunkuyar da Kai Mommy ta yi kafin ta ce ‘’ina kwana Mama, sannu da zuwa’’ Banza Hajiya Mama ta yi da ita dan haka Mommy ta sauk’e numfashi kafin ta durk’usa sosai har k’asa tukunna ta ce ‘’Ina kwana mama’’ ‘’Ashe dai kinada tarbiyya kad’an’’ cewar Hajiya Mama ba tare da ta kalle ta ko ta amsa gaisuwar tata ba. Dai-dai nan Yassira ta fito, sanye cikin skirt da suite, sai d’an mini hijab iya kafad’arta, yanayin tsayuwar tasu kawai ta gani ta fahimci har an fara, da farko ba ta yi niyyar zuwa inda suke ba sai kuma suka had’a ido da Hajiya Mama dan haka kawai sai ta dake ta k’arasa inda suke, tana zuwa rungume Hajiya Maman kafin a hankali ta ce ’’welcome, we are glad u make it(sannu da zuwa? Mun yi farin cikin isowarki lafiya)” D’an guntun murmushi tsohuwar ta yi kafin ta ce ’’ya aiki?’’ ‘’Alhamdulillah’’ Yassira tace, Sannan ta cika Hajiya Mama ta kalli mom tace ‘’Sannan ku da zuwa, i’m late muna da baƙi kuma, bari in yi sauri in wuce, we’ll catch up later(za mu haɗu anjima)” Tana gama fad’in haka ta wuce . Ganin suna shirin wucewa suma kamar ma sun manta da ita ne ya sanya Mommyn ta ce ’’bara in yi sauri in d’an had’a muku special, ba ku ce za ku zo yau ba ai da an had’a muku special ɗin tun wuri’’ ‘’Eh ni na cewa d’an albarkar kar ya gaya miki ai, gudun kar ki hana, ki bar abincinki zan ci na masu aiki’’. Cewar Hajiya Mama. Baki Mommy ta bud’e, za ta yi magana su Abhi waenda suka fito yanzu suka k’araso, Abhi ya ce ‘’Mommy mu je gaba d’aya mana’’ Sai da ta juya za ta yi mishi magana tukunna ta lura da su Yasmeen….shi kanshi Abhi d’in ta san ya zo amman bata ganshi ba sai yau dan haka ta ce ’’duk sannun ku da zuwa” daganan ta miƙe ta juya ta nufi d’akinta dan ba ta jin za ta iya had’iyar ko da ruwa ne a yau kam. Sai da Daddy ya yi wa su Yasmeen wani irin kallo, tukunna suka matsa kusa da Hajiya Mama suka gaida ita Itada Ya’isha, dan Yusra da Yadira ba su tashi ba tunda ba fita za su yi ba! Yusra ta gama finals d’in ta, Yadira kuma sun fara hutu. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 09* Ba yabo ba fallasa ta amsa musu, daga nan aka sauk’a aka nufi dining table. Ko zama Daddy bai yi ba ya shiga kitchen dan ya san Ummi tana ciki, ai kuwa yana shiga da ita ya fara yin tozali ita da Munirat da masu aiki…a gaban mutane ne shiyasa Ummi ta d’an gaida Daddy da kulawa ba yabo ba fallasa amma fa dukda hakan a baɗini ji takeyi kamar ta je ta shak’e sa! Dan ita kanta tana mamakin yadda haka kurum tsanarsa ta nunku ta ke sake yin ninƙaya a cikin zuciyarta kwana biyun nan, wani irin mugun haushinshi takeji. Amsawa ya yi yana mai binta da kallo, dan ba kad’an ba ta yi masa kyau yau d’in sosai, dad’in dad’awa yana son Matarshi kuma ya yi missing d’inta ‘’Daddy Ina kwana’’ d’in da Munirat ta ce masa ne ya dawo da shi cikin kitchen d’in. A hankali ya juya ya kalleta tukunna ya amsa da kulawa, kafin ya maida dubanshi ga Ummi ya ce ’’Hajiya Mama sun zo, tare da d’an uwana da Matarsa, ki fito ku gaisa’’ Tukunna ya shiga amsa gaisuwar masu aikin. Murmushi ta yi tana mai jin wani tsananin farin ciki yana lullub’eta dan suna waya da hajiya mama, kuma suna shiri sosai, shiyasa ko gama abunda take yi ba tai ba haka ta cika ta kira gwaggwo ta bata ta ce ta ƙarasa daga nan ita ta fita, ita da Munirat, da murna kwance akan fuskarta. Daddy ya ji dad’in yadda Ummin ta yi farin ciki da zuwan Mahaifiyar tasa, ya san Hajiya Mama ba sa shiri kwata-kwata da Mommy kamar ba y’ar aminiyarta a farko ba haka take rufe ido ta tsigale ta tass!sannan ya ji abunda ta yi mata yanzu amma dukda haka yadda Mommy ta nuna tashin hankalinta wanda gashi har ya kai ta gagara sauk’owa a yi breakfast da ita hakan ba kad’an ba ya sosa masa rai, dan ya san daga ita har su Yasmeen da suka k’i zama duk saboda Hajiya maman ne, amma zai ci ubansu in ya samu lokacinsu dan uwa ba ta fi uwa ba. Faram faram kamar su Ummi da Hajiya Mama za su cinye juna haka aka shiga gaisawa ana murnar had’uwa, har ma da Sameeha dan Itanma suna waya suna chatting da Ummin. kamar yadda suka yi wa Ummi haka suka yi wa Munirat Itama, ta ji dad’i kuwa matuk’a, dan ko ba komai ta fahimci ba duka aka taru aka zama d’aya ba, kuma yanzu ta tabbatar Ummin ta za ta d’an rage zafi tunda ga oga kwata kwata ta gani da idanunta ba wai a waya ba, ta na sonta kuma tana ji da ita. Su kad’ai sai Daddy da Abhi ne aka yi break fast d’in yau, dan ko Ya’isha ma k’in zama ta yi tace musu in ta tsaya za ta makara wani aiki da ya shafi masters ɗinta da take yi. Tana fita Hajiya Mama ta kalli Daddy tace ‘’Saboda shegiya! da kai da matarka kun janyowa y’ay’anku karatu a Nigeria’’ Kallon Ummi ta yi, sai kuma ta kalli Daddy kafin ta ci gaba da cewa “ai ni ban san irin power da wannan shegiyar Yarinyar take da ita a cikin gidan nan ba, Saddik’a saboda fa ni da Daddy mun ce ‘idan kausar ta fita k’asar waje karatu za ta sake lalacewa, dan haka a barta ta yi karatu anan gida Nigeria’ shine ita uwar Yaran tace ’tunda Kausar ba ta fita waje ba to babu wanda zai sake yin karatu a waje’. Duk dan kar ran y’ar gwal d’in ya b’aci! Akan ranta ya b’aci gara na ya’yanta ya b’aci, kuma shima Imam din ya zuba mata ido ya k’i tab’uka komai akai, shiyasa ka kaf cikinsu Yassira ce kawai ta zo ta yi karatunta Itanma dan ta riga Kausar d’in farawa ne da wata d’aya shiyasa aka barta ta kammala Oxford, sai Yash da Yassir da Yahanasu tunda su sun riga ta yi’’ Hajiya Mama ta faiyyace hakan cikin d’an b’acin rai. Shiruu Ummi ta yi ta rasa abin cewa, dan haka kawai sai ta sunkuyar da kanta. Cikin b’acin rai still Hajiya Mama tace ‘’Kuma ai gaskiya aka fad’a, tun kafin fa ta tafi makarantar k’asar wajen ta yi ciki ta haihu d’an ba rai,lokacin tana gama secondary school. Me kike tunanin zai faru inda an barta ta je wata k’asar..?’’ Ahankali Abhi ya ce ’’Maaamaaa’’ Ya d’an jaaa maganar. Sai a lokacin Hajiya Mama ta lura da yadda gaba d’aya ita kanta Ummin she’s not comfortable( ta kasa sakewa) da zancen, dan haka ta yi shiruu kawai tana mai sake tabbatar da innocence ɗin Ummin, a ranta ta ce ’’tabbas ban ga ta zama ba, dan matar nan ba ta san komai ba, sannan ba ta san wacece Khadija(mommy) ba, ya kamata a yi wani abun tun kafin ta cutar da ita that is if(matuƙar kuwa) ta kasa cireta a gidan kenan…’’ Shiruu dining d’in ya yi, ba a jin k’arar komai sai cokula sai kuma albarkar da Hajiya Mama taketa sakawa Ummi, dan ta ji dad’in girkin da ta tarar Ummin ta yi da kanta kuma ya yi mata dad’i sosai. Ummi kuwa Baki har kunne, dan ba kad’an ba take jin dad’in addu’o’in da Hajiya Mama take ta zuba mata. Sosai Daddy ya ji dad’in yadda Ummi da Hajiya Mama suka fahimci juna suke shiri da kuma yadda Ummin take girmama Hajiya Mama shiyasa ya yanke shawarar zai sake tuntub’ar ta wataƙilan zuwa yanzu ya san ta huce..shi dai ba zai bata hak’uri ba duk rintsi! dukda zuwa yanzu shi kansa ya san ya garu!Ummi ba yaji ta yi ba tana cikin gidan shi amman fushin ta gareshi ya fara illata shi matuk’a….. Ganinta a tsakiyar manya yasanya gaba d’aya ta ke ta jinta unconfortable (a takure), shiyasa ta yi sauri ta kammala, daga haka ta mik’e tace musu’’ta k’oshi’’ ta yi musu sai anjima kafin ta nufi sama. Kusan karo da juna suka yi da Yassir wanda yake sauk’owa k’asan, sanye da suite har da brieficase, ya yi masifar yin kyau! Ana ganinsa an san office zai tafi. Sarai ya lura da ita amman sai ya d’auke kai kawai ya wuce, wanda hakan kuwa ba k’aramin gigita Munirat yayi ba! Dan ba ta yi tunanin zai iya yi mata haka ba..tun jiya take jiran kiranshi bai kira ta ba sannan yanzu kalli abunda ya yi mata duk dan shekaran jiya ya ce ‘’su had’u a gidan Abokinsa’’ ita kuma ta k’i yarda, ta ma yi fushi tace ‘’ita ya ma daina yi mata irin maganar nan bata so’’ dga haka ta kashe wayar, to ashe shima ya d’au zafi da gaske tunda gashi ya d’auke mata d’iff…anya kuwa ba za ta sauk’ar da kai tun wuri ba su shirya ta nuna masa komai ba komai ba, dan tana jin tsoro kar ta je ta taro match d’in da ba za ta iya ba, saboda ita dai wllahi a yadda ta ke ji ta san ba za ta iya rayuwa babu Yassir ba…. Ya yi mamakin ganin Hajiya Mama dan haka ya yi saurin k’arasawa suka gaisa ba yabo ba fallasa kafin ya tambayesu Junior. Ya kuwa ji dad’i kwarai da ya ji Junior ya zo, bai wani damu ba da aka ce mishi Na’ima ba za ta zo ba dan bai damu da Yarinyar ba saboda muguwar gidahumace, kamar ba a uk aka haifeta ta girma ba, ga ta da shegiyar rowa bata taɓa bari a amfana da Jikinta, sannan tun ranar da ta fito mishi a mutum ta gaya mishi Yash take so ya fita sabgarta, ko chatting d’in kirki ba sa yi! shi mantawa ma yakeyi da ita in ba a family group ya ga ta yi magana ba. Kad’an ya d’an chakali abinchin, kafin ya mik’e ya yi musu sallama ya ce ‘’bara ya je office’’ Duk jama’ar wajen sai da su ka fahimvi asalin farin cikin da Daddy ya shiga a take! Dan sai murmushi yake ta zubawa sakamokon ganin Yassir da ya yi a shirye caff! Zai tafi office kuma da wurwuri haka, a ranshi ya godewa Allah ya shiga addu’a ‘Allah ya sa fad’an da aka yiwa Yassir ya shige sa kenan, Allah ya sa ya shiryu kenan har abada’. Kasa hak’ura Daddy ya yi sai da ya mik’e har bakin k’ofa ya je ya shafa kansa ya yi masa addu’o’i tare da fatan nasara tukunna ya koma ya zauna yana ta zuba murmushi. Tunda Yassir yake a rayuwar sa bai tab’a jin guilty conscious(jin laifin abunda ya aikata) irin na yau ba, ya san saboda Daddy ya ga zai je aiki ne ya sa yaketa wannan murnar alhalin a asalin gaskiya shi ba aiki ne zai kaisa ba..wani Abokinsa ne ya had’a shi da wata Yarinya! yarinyar ta had’u matuk’a mahaifinsu ya rasu kuma itace babba shine take neman aiki, shiyasa aka had’ata da shi, shi kuma yace su had’u yau ya ga ko za su daidaita…… ‘’Tunanin mai kake yi??’’muryar Daddy ta katse masa tunani, wandaya juyo daga inda ya ke zaune yana kallonshi… murmushi kawai ya yi bayan ya kallesa daga haka ya yi waving d’insu ya sa kai ya fice. Dukda uwar suite d’in da ya ci kuwa, yana fara magana Yarinyar ta fahimci inda ya dosa ta kuma fahimci ba aiki ake son ba ta ba, dan haka ta mik’e tsulum ta fice ta bar sa cikin tsananin mamakin ta. Dan ko irin sallamar nan ba ta yi masa ba hakanan kawai ta mik’e ba um ba um um ta fice ta bar masa office d’insa….. Ko mintuna uku bai k’ara ba shima ya fice daga company d’in ransa a mugun b’ace, yana mmakin yadda sam ya daina cin galaba a kan y’an mata anyhow, kamar wani wanda aka yiwa asiri…. duk wani abu mai kyau na gidan Daddy Yashjub ya d’auke harma da farin jinin y’an mata…… Ko da ya dawo gida, direct side d’in Yash ya nufa wajen Junior, aikuwa kafin awa d’aya ya ware war suka yi ta hira abunsu dan kusan Junior shine best friend d’in Yassir, saboda halin su kusan d’aya ne dan indai aka zo batun Mata to kowannen su sai a hankali kawai sai dai unlike Yassir (saɓanin Yassir) shi Junior ya san class d’insa sannan shi Mutum ne mai himma da kwazo sosai, dan yanzu haka Doctor ne shi wanda ya yi fice saboda tarin nasarorin da ya samu a aikinsa dukda kuwa bai jima da farawa ba, sannan yana gab da zama consultant..dan bai fi wata biyu zuwa uku ya zama ba. Junior ya yi mamaki da ya cewa Yassir ‘’ya zo su je su gaida antynsu (matar Yashjub)” dan kai tsaye ya ji Yassir ya ce ‘’shi bai ma tab’a ganinta ba’’ amma kumada Junior d’in da ya tuna waye Yashjub sai ya ga hakan a wajenshi ba komai bane, dan haka ya kawar da zancen su ka fad’a wata hirar. …. Mommy tana shiga cikin d’akinta ta fashe da wani irin kuka mai hawaye wiwi kamar wata Yarinya. Ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai faman safa da marwa take yi tana hawaye tunda ta shigo cikin d’akin. A haka Baaba Larai ta turo k’ofar d’akin ta shigo dan d’azu tana parlourn Kausar wadda itama damuwa ta sauk’arwa da zazzab’i ta fara jiyo Hajiya Mama da Mommyn shiyasa ta bari sai da suka wuce tukunna ta biyo ta ga halin da y’ar uwartata take a ciki. Da mugun sauri ta rufe k’ofar ta k’arasa kusa da ita ta rik’eta tace’’subhanallah Mommy….’’ Ingijetan da Mommy ta yi ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana, cikin tsananin fushi Mommy ta fara magana…tana hawaye take cewa’’kar ki soma tab’ani, ki bar ni kawai in mutu Larai tunda kin kasa yi min maganin matsalata. Abu d’aya tak! Zuwa biyu amma ya gagareki wanda hakan ya sanya na fara tunanin ‘anya ma kuwa kina yi min aikin nan tsakani da Allah?.’ In ba ki ci! In ba ki sha! In baki sutura da wajen zama amma ace wai ki kasa mi……’’ Yadda Mommyn ta ga Baaba Larai ta kafeta da manyan idanunwanta waenda suka yi jazir suka cicciko da kwallah ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana, dan haka kawai sai ta juya mata baya ta sake rushewa da wani irin kuka. Baaba Larai ta so yin fushi da Mommy itama, ta so mayar mata da martani daga nan in yaso su yi kacha kacha ma amman kuma sai ta kasa, saboda ta san zafin rashin nasarar da suke ta fuskanta ne ya tunzura ta ga furta mata hakan, dan ko ita kanta daurewa kawai takeyi amman abun ya fara bata tsoro kuma ta fara gajiya….ba wai iyaka kai kud’in Yash da suka kasa hanawa ba, hatta su Hajiya Mama sai da suka so su hana su zuwa amma kalli tsulum kawai sai ganin su sukayi….. Tana cikin wannan tunanin Mommy ta juyo tana kallonta tana goge hawayenta kafin ahankali cikin sheshshek’a ta ce ’’yi hak’uri dan Allah’’ sai kuma ta sake rushewa da wani kukan. Wani irin tausayin Mommy ne ya lullub’e Baaba Larai tashi guda..tun suna Yara ita kanta ta san abunda yake saka Mommy kuka ba k’arami bane, shiyasa yanzun da ta ga tana kuka ta sake tausaya mata ta tausaya musu ta kuma yi wa kanta alk’awarin ‘inshaaAllah ba za su kwashi kashin su a hannun ba….’ Ahankali ta sa Hannu ta janyota zuwa jikinta ta rungume sannan ta shiga bubbuga bayanta alamun rarrashi. Kamar zuga Mommy ake haka ta shiga rera kuka kamar jira takeyi, cikin kukan ta fara magana tana cewa ’’Larai na gaji, kuma na sadaƙar, dan na san tunda har aka kai kud’i aka saka rana kuma Matar nan (Hajiya Mama) ta riga ta zo, to kamar an yi auren Yash ne an gama…shikenan mun yi failling, mun faɗi, mun ci tura, mun faɗi warwas a ƙasa Larai. Sannan ga zuwan Matar nan, bana son ta a cikin gidana, mutuwa zan yi Larai, bana son ganinsu a cikin gidana! Zuciyata za ta buga… Ban san da wanne zan ji ba, abun ya yi yawa, duka ta ko’ina ban san wanne zan tare ba…..’’ Ganin yadda take magana saboda zafin zuciya da baƙin ciki ne ya sanya Baaba Larai ta zaro ta daga jikinta cikin sigar rarrashi ta ce ’’ban san mai zan ce miki ki sake yarda da ni wannan karon ba, amma inaso ki yarda da ni sannan ki ɗora dukkan amincewa da hope ɗinki a kaina! inshaaAllah ba zan sake baki kunya ba, ni na san mai zan yi wannan karon, ba za mu faɗi ba inshaaAllah, ba za ayi auren ba, ba nan da kwanaki tara masu zuwa ba, ba kuma a har abada ba!. Ba za a taɓa yin auren nan ba. Sannan itama Hajiya Mama inshaaAllah sai sun koma inda suka fito, da yardar Allah, dan ba zan zuba miki ido in barki a hakaba, ba zan iya ba y’ar uwata…..sannan ba zan zuba ido ina gani ake ci miki kashi a cikin gidan ki ba! sanann ga shi daga zuwanta na lura so take ta yi wa mutane handsfree a gaban idon kowa’’… ••••••• Gyara sosai Manubiya take sha, dan a cikin kwana d’aya da aka yi mata sau biyu safe da rana kawai har ta fara chanzawa….in banda ƙamshi ba abunda yake tashi daga jikinta, fatarta har ta fara sumul sumul da yellow ta na d’aukar ido. Yanzun ma na uku aka yi aka gama, dan Mama ta ce ba su da lokaci dan haka a dinga yi akai-akai tunda ba su fara da wuri ba… Ana gama gyaran jikin ta fad’a wanka tana fitowa kuma ta sake zama a kan kujerar tsugunno ba dan ta so ba sai dan yadda ta ga Mama ta dage akan sai fa ta sake zaman, a cewarta ‘’d’azu tana sane da ita ba ta zauna sosai ba ta fake da cin abinci’’… dariya duk suka yi, har Manubiyan wadda take Allah Allah ta yi ta shirya dan ta san daga yanzun zuwa ko wanne lokaci zai iya zuwa saboda ce mata yayi da yamma…dama Jidda ta tambaya mata su Baba sun bata go ahead, amma sun ce ta tafi da d’an rakiya shiyasa tun d’azu ta cewa Muhsin ya shirya. Sai da ta kusan sakawa Mama kuka tukunna ta yarda ta ce shikenan ta tashi tana ta yi mata tsiya tana ce mata’’raguwa’’daga haka Maman ta yi musu sallama ta tafi dan tana so ta je itama ta d’an huta. Manubiya ta na tashi ta nufi wardrobe, ta zaro kayan da za ta zata saka tukunna ta zauna ta shiga shiri…mai gyaran jikin tana gama shirin tafiya dai-dai itama ta gama shirin ta kenan, kiran Yashjub kuma ya shigo wayarta, duk a lokaci guda. Dama wayar tana Hannunta yau kam babu wani maganar jan aji dan ita kanta kawai gani ta yi ta d’auka ta kara a kunnenta…..shiruuu ta ji ya yi da farko kafin chan ta ji ya ce ‘’Ina k’ofar gida.’’ Da kyar ta iya cewa ‘’tam’’ daga haka ta kashe ta k’arasa wajen Inna ta d’an durk’usa ta gaya mata, kafin ta mik’e ta d’auki mayafi me kyau da girma da kauri sosai ta d’aura akan doguwar riga y’ar kantin dake a jikinta. Har za ta fita, sai kuma ta dawo ta k’ara turare har da d’an lipstick pink ta d’an goga sannan ta gyara zaman hularta….ta na juyawa suka had’a ido da inna dan haka gaba d’aya duk sai kunya ta rufeta, da sauri ta juya da niyyar cewa Jidda Ina Muhsin yayi amma sai suka had’a ido da shi ya d’ago labule, dan haka ta yi gaba bayan ta ce musu ‘’sai sun dawo‘’ suka fita ita da Muhsin da mai gyaran jikin…. Suna fita ta yi mata sallama, Matar ta wuce, ita kuma ita da Muhsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 10* Suna fita ta yi mata sallama ta wuce, ita kuma ita da Muhsin suka tsaya kallon dalleliyar motar da ke fake a gaban su. Dukda ba ta riga ta ga na cikin ba dan motar tinted glass gareta amma tashi d’aya Jikinta ya bata shine. A b’angaren Yash kuwa tunda ya zo ya yi parking a k’ofar gidan yake sake k’arewa gidan kallo yana sak’e-sak’e a ranshi…tun ranar farko da suka zo shi da Najeeb yake tunanin ta yadda zai siya musu gida su yarda su karb’a dan ya san tabbas da wuya su amince da hakan, amman dai zai gwada ya gani saboda har ga Allah daga arean har gidan basu kwanta mishi ba.. A take tashi d’aya tausayinta da k’imarta suka mamaye shi, a ranshi yace “yanzu a nan ta girma ta yi wayo amma kalli yadda abun duniya da kwad’ayi sam ba su rufe mata idanu ba.’’ Yana wannan tunanin ya ganta sun fito su uku, sun yi wa d’ayar Matar sallama ta wuce, ita kuma sun tsaya ita da Muhsin. Murmushi ya yi, kafin ya d’ago wayarsa ya shiga kiranta, so yake ya ga yadda za ta yi shiyasa ya k’i fitowa balle ma taga inda yake… Tana d’auka kamar d’azu ya ce ’’ki shigo mana” kawai. Shiruu ta d’an yi sai da ta ji ya sake cewa ’’Come in pls’’ tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta kashe wayar suka nufi motar ita da Muhsin. Su na zuwa ta bud’ewa Muhsin gidan gaba, sai da ya shige ya zauna ta rufe masa tukunna ta nufi baya ta sa Hannu a kan handle d’in…. Dariya ce sosai ta ke tasowa Yash wanda yake zaune a gidan baya, dama ya san hakan za ta yi tun lokacin da ya ga sun fito ita da Muhsin… A take ya hau Ɗoki da zullumin son ganin yadda za ta yi idan ta shigo gidan bayan suka yi ido biyu da shi, yana cikin wannan tunanin ya ga ta d’aura Hannunta a kan handle d’in dan haka ya yi saurin matsawa ya bud’e mata tun kafin ta murd’a. Ta d’an yi mamakin ganin yadda k’ofar ta bud’u tun kafin ta murd’a, amma sai ta yi tunanin maybe Yash d’in ne ya bud’e mata ta gaba inda yake zaune. K’amshin mayatacccen turarenshi da sanyin ac ne suka fara yi mata sallama, har ga Allah sam ba ta lura da shi a ciki a zaune ba, dan motar da d’an duhu, sai da ta d’an sunkuya ta shiga ta zauna ta mayar da k’ofar ta rufe tukunna ta d’an zabura ta d’ago ta kalleshi sakamokon kamshinsa wanda ta ji ya k’aru sosai a cikin hancinta da kuma alamun mutum da ta ji a zaune a gefen ta. Suna had’a ido ya yi mata gwalo, yana mai jin ƙamshin da take yi yana shirin zautar da shi, da kyar k’asa-k’asa ta yadda ya tabbatar ita kad’ai ce za ta ji ya ce ’’an guje min kuma anzo an taddani… A clear reminder to you wifey ‘destiny will forever bring us together,’ (Ki ɗauki hakan a matsayin tunatarwa Matas, a ko da yaushe ƙaddara za ta ci gaba da haɗa mu, har abada).. Har abada muna manne da juna, InshaaAllah’.’’ Shiruu Manubiya ta yi dan ita ta ma kasa magana, sam tunaninta bai sa ta tuna da hannunshi ba sai da suka yi ido biyu da shi ta kalli hannun tukunna ta tuna ‘ba fa zai iya tuk’in ba.’ A hankali ta d’ago ta d’an kalleshi kafin ta ce ’’Ina wuni’’ Cike da kasala ya ce “ lafiya “ idanunsa a kanta yana mamakin mai ya same ta haka da ta k’ara wannan azabb’en kyan cikin k’ank’ani lokaci, a gefe guda kuma na zuciyarsa yana jin takaicin kasancewar drivern da ke gaba na cikin motar, dan ya san shima tabbas ya shak’i wannan sumamman k’amshin da take ta zubawa, addu’ar sa d’aya kar drivern ya zo gaisheta yace zai juyo, haka kurum ya k’are mata kallo, dan shi a rayuwarsa baya son abunda zai sa ake kalle masa ita balle yanzu da shi kansa yake jin numfashinsa yana shirin d’aukewa…..yana cikin wannan tunanin ya ji ta cewa drivern’’ina wuni’’ Cikin girmamawa da yin k’asa da kai drivern ya gaisheta ba tare da ya juyo ba, daganan ya kunna motar bayan Yash ya fad’amasa Ina suka nufa, suka d’au hanya….. Dukda drivern ne ya kamata ya gaidasu amman sai Yash ya ji dad’in yadda Manu da Muhsin suka girmama dattijon Mutumin dan ko Muhsin shima bayan sun gaisa sai da ya gaida drivern…wanda hakan ya nuna sun san girman d’an Adam da farin gemu saɓanin su Yasmeen. A k’ofar shagon wata shahararriyar mai d’inki suka yi parking, tukunna drivern ya kashe motar ya fita haka ma Muhsin… bai yi gigin bud’e musu ba dan bai san ko za su tattauna ba kafin su fito, dan haka ya koma gefe ya ja ya tsaya haka shima Muhsin. A hankali cikin wata murya kamar ta wanda ba ya son yin magana ya ce ’’mu je ko?’’ Jin jina Kai ta yi tukunna ta sa Hannu da niyyar bud’ewa amma sai ta gagara, ta juyo da niyyar yin magana ta ga ya bud’e side d’insa ya fita ya zagaya. Da kansa ya bud’e mata, dan ko da drivern ya matso ma d’aga masa hannu kawai ya yi ya tsaidashi. Ahankali duk tana jin kunya da nauyi sun lullub’eta haka ta sa k’afa ta fito, sai da ta gama fitowa tukunna ya rufe marfin motar ya ja ya gyara mata mayafinta wanda ya d’an zame yana shirin sauk’a daga kanta tukunna suka nufi k’atoton shagon, suka bar driver cikin tsananin mamakin yau Oga ya zama driver! Amma kuma har ga Allah ya ji dad’i kuma sun matuk’ar burgesa, hatta Muhsin ma da yake Yaro sai da suka burgesa, bai bisu har ciki ba ya tsaya a wajen driver suka shiga hirar su. Suna shiga wajen ta ga ashe har ya bayar da kaya wajen kala ashirin majorments d’inta kawai ake buk’ata…dan haka suka shiga wani d’aki Matar ta aunata aunin kwakwaf dan ba abunda ba ta gwada ba saboda wai za’ayi d’inkin nikkah wanda zai yi fitting ragowar ma duk ana so su yi fittng tunda a lefe ya ce mata za’a saka dan haka dole kayan su fito rasss!!! Hakanan ta yi ta janta da hira dan matar professional tailor ce, mai kirki kanta a waye shiyasa kamar za ta goya ta. Manu ta ji dad’in yadda Yash ya yi respecting decision d’inta (ya mutunta shawararta), dan tunda ta ji matar tace ‘’iyaka d’inkin nikkah, ragowar kuma na lefe” to ta san ya yarda shi da y’an gidansu akan ‘babu wani event d’in da za su yi kenan.’ Babu maganar deposite dan Yash complete ya juyewa Matar kud’in d’inkunan kaff a account, har suka fito suka shiga mota suka fara tafiya kan Manubiya bai daina juyawa ba…sai da aka tura kud’in tukunna ta ji dan wallahi ba dan hakan ba to da ba za ta yarda a yi wannan uban b’arnar kud’in a iyaka d’inkuna ba…. Ba gida suka koma ba wajen jewelries da shoe and bag d’in da za ta yi amfani da su sukaje suka sissiya, daganan suka biya mudassir… Ya riga ya sayi komai amma akwai d’akin dama da ya ware akan itace za ta zab’a da kanta sai kuma deco (kayan ado na gida) da kayan kitchen da yake da bukatar ta k’ara da zaɓinta akan waenda ya sissiya, shiyasa ya kaita ya ce ta tayashi zab’e dan ya kasa.. Siyayya sosai kuwa suka yi dan har sai da ta fara tunanin wataƙila ko harda iyayenshi zai chanjawa kayan kyale-kyale da na kitchen saboda bikin, dan uban kayan da suka d’iba wasu aka yi order abun ba ‘a cewa komai. Tabbas ta yi mamaki matuk’a amman da ta tuna yawan estates d’in shi da business d’in da yake yi, sai taga kud’in da suka bata tsoro waenda suka kashe a iyaka yau ɗin kad’ai ba komai bane a wajensa. Ta san Yash yana sonta kuma ta san so gaskiya ne, amma yadda taga yake rawar k’afa da waensu abubuwan duk akanta wasu lokutan har tsoro da mamaki takeyi…duk wani kud’i! dukiya!class! ajjiyewa yakeyi a gefe ya sauk’ar da kanshi k’asa sannan ya kawar ya goge gaskiyar cewa ‘shi ɗin sam ba ajinta bane ba, ba class ɗinsu ɗaya ba’. Yadda yake ɗaukarta yake yi mata a gaban kowa da koina kamar wata sarauniya tabbas hakan yana bata alajabi, gashi dai ya san itan ma tana sonshi ballantana tace ko campaign yake yi…. Ita kam tabbas ta yarda ta amince she’s fortunate, infact she’s morethan fortunate… (ta yi sa’a! A zahirin gaskiya ma kalmar ‘mai sa’a’ ta yi kaɗan wajen baiyyana kalar sa’ar da ta yi ba). …. Sai chaan dare tukunna suka d’auki hanyar gida, bayan ya loda na lodawa ya kira wani driver d’insa ya naɗa shi a matsayin mai jagora, sun tafi kai kayan da za a kai gidan amarya… Ta gaji lik’is, dan haka ta na gishingid’ewa bacci ya kwasheta. Ahankali ya d’an tab’o Muhsin wanda suke ta hira da drivern dan har sun saba sosai kamar wasu sa’anni, sai da ya juyo tukunna Yash ya d’aura yatsarshi akan bakinsa alamun su yi shiru kar su tasheta… jinjina kai Muhsin yayi ya juya yana murmushi, bai gama sanin meye so ba amman yana jin dad’in yadda ya Yash ya damu da Addar su, shima drivern ya gani kuma ya fahimci mai Yash yake nufi shiyasa ya yi shiruu ya bada himma a tuk’in da yake yi. A hankali kamar mai shirin d’aukar cracked egg haka Yash ya d’auki wata suite d’insa dake a cikin jakar kujerar driver ta baya, ya d’an matsa kusa da ita kad’an ya lullub’a mata dan ya lura ba ta son sanyin. Manu bata da nauyin bacci shiyasa yana rufa mata ta farka, amma ba ta bud’e idanunta ba…ta ji dad’i a ranta, duba da yadda yanzun suka gama fad’a kuma yayi fushi da ita amma kalli yadda yake kula da ita, ba ta son yin fad’a da shi amma ta lura idan ba hakan ta yi masa ba to ba zai hak’ura ba, ba kuma zai bar maganar ba!. Saboda Allah ta ya dan su Baba sun aura masa ita sai kuma kawai aga sun kwashe kaya su koma gidan da ya ce ya basu, a ganinta hakan ba dacewa bane ba, ta san sun zama family amman kuma idan suka yi haka ai sun sake da yawa, idan ma zai basu gida gaskiya ba yanzu ba besides ta san ma Baba ba zai tab’a yarda ba… Tana wannan tunanin ta ji an yi parking an kashe motar, ta na ji Muhsin ya yi musu sai da safe da godiya ya jidi laidojin gabansh ya fita, dan haka ta yi saurin bud’e idanunta dan ta lura ba shi da niyyar tashinta,dai-dai nan drivern ma ya fita kenan..da sauri tace’’mun gode, sai da safe” daga haka ta fara kokawa da shegiyar handle d’in da ta rasa dalilinta na k’in bud’uwa a koda yaushe idan ta ja. Murmushi ya yi kafin ya ce ’’kar mu rabu muna fad’a mana, ai tunda kin nuna bakyaso ba zan sake yin maganar ba, amma ki yi tunani akai pls’’ Jinjina kai kawai ta yi, ta ci gaba da k’ok’arin bud’ewa… Murmushi ya yi ya ce ’’ba fa za a bud’e k’ofar nan ba sai kin yi min murmushi.’’ Jin tayi shiru ya sanya cikin wata kalar kasalalliyar murya ya ce ’’kin san Allah zan yi miki cakulkuli’’ Sai da ta zabura sosai kamar ya riga ya yi mata cakulkulin ne, tukunna ta juyo kamar za ta fashe da kuka ta ce ’’dan Allah ka yi hak’uri, dare fa ya yi, ka bud’e min’’ Ganin yadda ta fara fita a haiyyacintane ya sanya ya fahimci kad’aicewar tasu ce ba ta so, dan haka tashi d’aya ya sa Hannu ta gaba ya bud’e mata sannan ya bud’e tashi k’ofar ya fice da niyyar zagayawa domin ya bud’e mata amman tuni ta yi wuff ta fice dai-dai shikuma ya zagayo, tashi d’aya ya ji ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kamar wadda ta yi y’ar tsere…. murmushi kawai ya yi, yana mamakin yadda daga sun zauna a mota iya su biyu duk ta bi ta gigice, a ranshi ya ce ’’Yarinya za ki yi bayani ne’’. Duk taurin kanta kuwa sai da ta yi masa murmushin nan tukunna ya kyaleta. Da shi da ita da driver suka yi jidon ragowar siyayyar da ya yi mata har soro, ya ajjiye mata, yana sake mamakin gidan tukunna ya bata wata jaka mai d’an karen kyau ya ce ”invitation ne a ciki ta bawa su Baba, zai turo mata na waya ma sai ta tuttura, shi kam ba wanda bai riga ya turama a cikin friends d’insa ba” Karb’a ta yi, ita dai har i yau ta kasa daima mamakin zumud’i irin na Yash, kafin yayi mata sallama suka rabu yana jin kamar ya d’auke ta su koma. Tabbas inda ace irin wata d’aya d’in nan aka saka aurensa da Manubiya tou da bai san ya zai yi ba kafin ta zo….wata kalar zazzafar k’aunace ta ke d’awainiya da shi…the more yana sake saninta yana sake shaƙuwa da ita the more k’aunar tata take sake dagargaza mishi lisaafi! tunani! da zuciya….. Sai da ta zo shiga tukunna kuma sai ta fara kame-kame… Ba k’aramin dad’i ta ji ba da bata ga Baba a d’akin ba, amma dukda haka sai da ta d’an ji nauyi dan kasa had’a Ido ta yi da Inna, illa kawai sai ta je ta durk’usa ta gaida ita daganan ta cewa Jidda ta zo ta tayata d’aukar kaya dan Muhsin yana shigowa ya fad’a toilet. A hanya take tambayar Jidda ‘ko su Baba sun yi fad’an daren da ta yi?’ amman sai ta ji Jiddan ta ce mata a’a, besides ai ba ta yi dare sosai ba ma…. Sai a sannan ta sake, su ka kwashi kayan suka kai ciki. Sai da Jidda ta je ta kira Siyama tukunna hankalinta ya kwanta, tare suka ware ledojin da komai,ita Manubiya sai da suka ware ma tukunna ta ga gift d’in Muhsin(agogo mai tsananin kyau na maza)da wayar da ya saka mata ba tare da saninta ba iPhone mai kyau k’irar wadda ake yayi, shiyasa a take ta kirasa domin ta yi masa godiya…. har ga Allah gaba d’aya Yash ya sa ta fara jin wani iri dan gaskiya ita dai hidimar ta yi yawa..tana fara masa godiya kuwa ya chanza topic d’in dan dama yace mata ta daina yi masa godiya ba ya so!ba k’aramin dariya ya bata ba da ta ji ya ce ’’ta je aiki,ta na da report’’ da farko ta d’auka da wasa yake yi sai da taga ya dage tukunna ta tabbatar da gaske yake yi. Aikuwa sai da ta yi da gaske ta ce ’’ga skul da za su koma soon” dan ba’a ba su wani hutu mai tsayi ba, ‘ga kuma hidimar biki, dan Allah ya yi hak’uri ya bari ta tura masa kawai’’ tukunna da kyar ta samu ta shawo kansa ta lallab’asa ya d’aga mata k’afa amman da cewa ya yi sai ta je. Daga nan ta ji ya yi shiruu kamar mai tunanin wani abun, dan haka ta shiga tambayar sa menene, sai da k’irjinta ya buga da ta ji ya ce ‘’Abbakar ya tab’a cewa yana son ki ne??’’ Sai da ya sake cewa’’umm???’’ Tukunna da iyaka gaskiyarta ta ce masa ’’A’a” Numfashi ya fesar kafin yace “can I ask you a favor???” Ahankali ta samu da kyar ta ce ’’E mana! anything’’ saboda yadda ta ji tashi d’aya muryarshi ta chanja sannan ranshi ya b’aci. Cikin katse mata tunani ta ji Ya ce ’’ko gaisawa ba na so ki sake yi da shi” Sai da ya sake cewa “am I asking for too much?(ko hakan ya miki tsauri da yawa?)” tukunna ahankali ta ce ”A’a” sai kuma tace “ba ma ya yi min magana fa,ya daina kulani” cikin tarar numfashinta yace”saboda kishi ne ai yasa ya daina yi miki magana, saboda ya ji an fara maganar aurenmu, yanzu kuma ya ga za’a koma skul shine ya je ya karb’i transfer, yanzunnan Najeeb yake gayamin ya samu transfer, bakiga kalar wahala da kud’in da ya kashe ba amman haka ya bi a gaggauce ya yi transfer” Shiruuu Manubiya ta yi, tana jin wani takaicin Abbakar yana taso mata…a tunaninta da kuma ganinta sam alk’awari bai ce haka ba, wato ma gudun ta yake yi, a ranta tace”idan ma wani abun na yi mishi ai kamata ya yi ya neme ni da zancen mu sasanta ba wai ya yi irin wannan abu haka ba’’ dan ita kwata kwata ba ta yarda da maganar Yash da ya ce ‘saboda kishi ne ya sanya shi ya yi transfer ba….’ Ta fi yarda da ko dI wani abunsa sgi Abbakar ɗin ne ya sa ya yi hakan, ko kuma mahaifiyarsa…. Cikin son kawar da zancen Abbakar d’in Manubiya ta sako wata hirar, dan ya b’ata mata rai ba kad’an ba, da kyar kuwa ta samu mood d’in Yash ya chanja, har yake bata labarin “ai Najeeb ma ya samu wani zazzafan appointment, dan haka zai bar skul d’in”. Ta kuwa yi murna sosai dan ko ba komai sir Najeeb ya taka muhimmiyar rawa a rayuwarta….. Sai da Manu ta tabbatar Yash ya huce sosai tukunna suka yiwa juna sallama, kamar za su cinye juna don so haka nan su ka yi sallama ko wannen su cikin tsananin so da shauk’in d’an uwansa. Tana gamawa su Siyama suka tisa ta a gaba da tsokana, abun mamaki har da Muhsin, ita sai a lokacin ma ta fara da na sanin yin wayar a gaban su. Sai da Baba ya zo ta nuna mishi komai ya sanya albarka bayan ya gama fad’an hidimar ta yi yawa tukunna suka b’are wayar aka jonata a chargi Dan jidda tace”tayi maza ta kwashe important abubuwanta ta cire layinta a tshohuwar wayar ta bata dan ta ma riga ta zama tata…… Har k’ofar side d’in su Siyama suka rakata dan lokacin da ta zo tafiya dare yayi sosai, tukunna suka koma nasu d’akin.. •• Yashjub yana gama waya da Manu dai-dai ya shiga bedroom d’inshi kenan kiran Daddy ya shigo wayarsa, yana d’auka ya ji muryar Daddy yana cewa”ka zo parlour na,Hajiya Maama na son magana da kai” Yadda Yashjub ya ji muryar Daddy dama sai da gabansa ya yanke ya fad’i, shiyasa ko wanka ya gagara yi tashi d’aya ya juya ya nufi side d’in Daddyn yana jin yadda k’irjinsa ya ke bugawa akai-akai. A zaune ya same ta, ita da Daddy da Ummi da mom da Abhi. Sai da ya gaishesu one by one suka amsa tukunna ya nemi guri ya zauna. Yana zama Hajiya Mama ta yi gyaran murya tukunna cikin rarrashi tace”Yash! da ni da iyayenka gasunan mun yanke shawarar za’a d’aga aurenka, za’a k’ara wata uku a kai. sakamokon matsalar gocewar k’ashi da ka samu. kar ka yi gaggawa, ka bi komai a hankali, a je a samu a duba ka sosai dan a gaskiya ban gama yarda da gyaran da suka yi maka a nan ɗin ba, ka yi hak’uri ka bari a d’aga bikin, lafiyarka ta fi komai. ka warke garau tukunna sai a yi komai cikin nutsuwa da kwanciyan hankali, ka ji d’an albarka” Hajiya Mama ta k’arashe maganar cikin tsananin lallami. Tunda ta fara magana idanun Yash suka cicciko da hawaye. Kamar wani d’an Yaro haka ya d’aga kai ya kalli Abhi da Daddy Irin ‘ku sa baki mana’ d’innan.. ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace‘’Yash it’s for your own good (domin lafiyarka ne). in banda kai da abunka ma ina kai ina yin aure a haka saboda Allah fa, tunda har mukazo aka yi tambaya aka yi komai aka baka Yarinyar nan to a ganina dan an k’ara wata uku ba komai bane, kamar yau ne. ka yi hak’uri ka bi Junior da mom d’inku, ku je a duba maka hannun sosai ka warke garau! In yaso sai ayi auren… I promise you, zan tsaya maka ka auri Manubiya under any circumstances (ko da ta halin ƙaƙa) Ina nan har 3 months da ni da Hajiya Mama inshaaAllah sai an yi auren an kai maka amaryarka tukunna za mu koma.” Cikin bashi assurance (tabbaci) Daddy da Hajiya Mama ma suka mishi alk’awarin duk rintsi inshaaAllah za su tsaya masa ya auri Manu, haka ma su Ummi. Zuwa yanzu Yash har wani dishi-dishi yake gani tsabar tsaka mai wuyar da ya shiga…. manya sun sakashi a tsakiya suna so a d’aga for his own good sannan sun yi masa alk’awarin tsaya masa duk rintsi a yi auren,on the other hand kuma (a wani ɓangarem kuma ) gani yakeyi kamar idan aka d’aga wani abun ka iya faruwa, bayaga hakan ma kwata kwata baya k’aunar abunda zai janyo a d’aga auren nan. Ahankali Hajiya Mama tace’’ka yi hak’uri, ka kwantar da hankalinka, ka samu lafiya tukunna. fiancé d’inka (matar da zaka auran) tananan tana jiranka babu inda za ta je, kana dawowa za’ayi auren, ka ji ko?” Cikin son jin amsar da za ta fito daga bakinsa Abhi yace”kai muke jira Yash,a matsayinmu na iyayenka ga abunda muka ga ya dace,na yi magana da friend d’ina tuni, za a yi maka booking appointment dan haka ya kamata ku tafi da wuri a je a dubaka da wuri, ko?’’ Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa…. da kyar muryarsa har wani karkarwa take yi yace”…….” BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 11* Da kyar Yash ya d’ago rinannun idanunsa… da kyar muryarsa har wani karkarwa take yi ya iya cewa ”duk yadda kuka ce Abhi Allah ya sa hakanne ya fi alkhairi.” Ba k’aramin dad’i suka ji ba kuwa, dan haka suka shiga saka masa albarka tare da fatan alkhairi. Ganin yana shirin fashewa da kuka a gabansu ne yasanya ya mik’e har wani jiri-jiri yake ji ya ce musu”sai da safe” daga haka ya sa Kai ya fice, yana mai ji kamar ya kurma uban ihu!! So yake ma ya yi kuka amma sam ya kasa, shiyasa ya nufi side d’insa ya na zuwa ya shige d’aki ko bi ta kan Junior bai yi ba ya shige ya rufe kanshi ya kashe wayoyinsa……. Sai washegari da safe tukunna Manubiya ta ji labari, duk yadda take ta cewa ita dai 2weeks ya yi kad’an a d’aga amman sai ta ji ba dad’i, musamman ma da Yash ya kira ta ta ji kamar kuka ma yake shirin yi mata…gaba d’aya sai ta sake gigicewa. Suna kashe wayar itama ta nemi fashewa da kuka, sai da Jidda ta d’an kwantar mata da hankali ta had’a da tsokanarta tana cewa “au dan an d’aga aurenta shine za ta yi kuka?” Tukunna ta wayance ta fake da borin kunya. Dukda su Mommy sun ji, kuma sun san d’agawa kawai aka yi ba wai fasawa gaba d’aya ba, amman hakan bai hanasu shiga cikin tsananin farin ciki ba, ji suke yi kamar su zuba ruwa a k’asa su sha dan Baba Larai ta ce ’’d’agawan da aka yi hakan ma nasara ne, kuma za su samu isashshen lokacin da za su tarwatsa maganar inshaaAllah. dan watanni uku kam is more than enough for them (ya ishesu) su yi abunda ya dace,” Shiyasa murna a wajen su har kasa b’oyuwa ta yi, tun daga kan Baba Larai har izuwa kan Yadira, kowaccensu idan aka kalla tashi d’aya za a san tana cikin tsananin farin ciki wanda hakan ba k’aramin sake ingiza Hajiya Mama ya yi ba, dan tabbas ta sake tabbatar da cewa ‘dukkansu ba son auren suke yi ba.’ A b’angaren su Manubiya kuma kaka mallan ne yaketa b’ab’atun sa shi kad’ai, duk inda ya zauna ya tashi sai ya sanar ‘ai an fasa auren Manubiya!!’….a cewarsa ‘’babu wani d’agawa da akayi, Yaron ne ya fasa, saboda ya gama lalubeta, dan kusan kullum sai ya zo ya d’auketa sun fita kuma basa dawowa sai dare…tun Mutanen layi basa biyeshi har aka fara ƙus-ƙus dan in ya zauna har rantsuwa yake yi yana cewa “Yaron nan fa ba zai auri Manu ba, tunda ta kasa rik’e kanta ta bi kud’i ta bashi abunda dama ya kawo sa wajenta, dan wallahi akwai ranar da a gaban idanunsa suka dawo da daddare har da Muhsin amman sai aka cewa Muhsin d’in ya fita, shi da driver, su kuma suka zauna a bayan mota wallahi wallahi sun fi awa uku a cikin motar kuma motar har motsi yaga tanayi…shikam daga k’arshe ma hak’ura ya yi ya shige ciki bai san lokacin da suka gama ta shigo gida ba.” Duk wannan gulmace-gulmacen da gutsiri tsoman da yake yi, hakan ba ta ishe sa ba sai da ya sa aka kira masa Ya Musbah takanas yace masa”ai ga irinta nan, ranar a masallaci sune har da yi masa rashin mutunci saboda yaga y’ar uwarsa ta shiga daula, to ga irinta nan ai tun kafin a je koina saboda abunda suka yi masa ne ya sa aka fasa auren, waye waye..” Hakanan dai ya yi ta b’ab’atun sa, uffan! Ya Musbah bai ce da shi ba har ya yi ya gama, sai da ya dasa aya tukunna Ya Musbah ya mik’e ya ce ”Allah bamu alkhairi” daga haka ya sa kai ya fice. … Bayan sati d’aya da d’aga bikin Yashjub ya zo yi mata sallama. A cikin sati d’ayan nan zazzab’i sosai yake yi, shiyasa ko iya fita ma bayayi balle ya je wajenta, sai dai kullum suna waya. Ko da ya zo a waje ya tsaya ta fito, tashi d’aya hankalinta ya yi tsananin tashi dan ba kad’an ba ya rame sosai, ashe shiyasa kullum take jin muryarsa wani iri idan kuma ta tambayesa sai yace mata”ba komai.” Cikin tsananin mutuwar jiki ta k’arasa ta gaida shi, da kyar ya iya amsawa har da d’an k’ak’alo murmushi duk dan kar ta gane. Cikin rashin jin dad’i ta ce ”ba ka da lafiya ne?” Murmushi ya yi kafin ya girgiza mata kai kawai, ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ”gobe da asuba za mu tafi,” Sai da ya sake fesar da numfashi tukunna ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce ”ni kam har ga Allah na fara da na sanin amince musu da na yi, kawai inaga gara a d’aura mu wuce tare, na so in same su da maganar amman sai na ga gara in fara yi miki maganar in ji ta Bakinki, amma duk da haka dan Allah baby kar kice A’a, kawai kema ki amince a d’aura a yau dan hakan nake so” Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka. Da kyar Manu ta iya danne kukan da ya taho mata, ta d’ago idanunta waeda suka cika taff da kwallah ta ce ”na san ba za ka ji dad’in abinda zan fad’a maka ba amma hakan shine daidai….ana barin halak ko dan kunya, kai fa da kanka ka ce min kawaici da alkunya ne suka sanya ka amince da buk’atar su, yanzu kuma kawai sai ka zubar ka je ka samesu ka ce ka chanja shawara? Kuma kowa gani zai yi saboda ka zo ka yi magana da ni ne” Cikin sanyin murya ya ce ”baby gani nake yi kamar idan aka d’aga wani abun zai iya…” Cikin katsesa ta ce ”duk abunda ka ga ya faru to muk’addari ne daga Ubangiji, wayonmu ko saurin mu bai Isa ya k’ara ko ya rage lokacin da Ubangiji ya riga ya tsara za’ayi ba….dan Allah inaso kamar yadda ka ji kunyar su ka yi kawaici a farko to yanzun ma ka zauna akan bakarka, ka yi musu biyayya, baka san dad’in da hakan zai sanya su ji ba. amman yanzu idan ka bijire, to kowa rashin hak’uri da karar mu zai gani,kuma hakan ne. Dan haka gara kawai mu yi musu biyayya, mu yi hak’uri mu mik’awa Ubangiji komai, inshaaAllah za mu dace” Ganin yadda ya yi shiruu ya kasa cewa komai sannan idanunsa suka yi jajir yasanya manubiya ta kawar da kunya direct daga cikin zuciyarta tace masa ”inshaaAllah, i’ll forever be yours, no matter what(duk rintsi, ni taka ce, har abada)” Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, dan ba kad’an ba kalamanta sun yi tasiri a kansa. Cikin tsareta da lumsassun idanunsa waenda suka k’ank’ance suka yi jaa ya ce ”promise??( kin yi alƙawari?) Ahankali tace”I promise(na yi alƙawari)” Lumshe idanunsa ya yi wanda hakan ya bawa kwallar da yake ta k’ok’arin rik’ewa damar zubowa, da sauri Manubiya ta kauda kanta ta sunkuyar k’asa dan tashi d’aya itama ta ji tata kwallar tana shirin zubowa. A hankali ya share idanunsa, ya d’an ja hanci kafin ya ce ”3 weeks (sati uku) zan yi in dawo, na san kuma zan koma follow up kamar sau biyu haka kafin auren namu” Cikin yin k’asa da murya ya ce ”zan yi missing ɗinki sosai, take care of yourself ( ki kula da kanki), ki dinga rik’e wayarki a ko da yaushe pls” Ahankali ta d’ago ta kallesa tace “inshaaAllah” Cikin wata kalar kasalalliyar murya ta ji ya ce ”I love you, always and forever” Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa duk yadda ta so ci gaba da rik’e kwallar kasawa ta yi dan tashi d’aya suka zubo mata, gudun kar ya gane yasanya ta sa hannu ta goge a hankali tukunna itama ta ce ”I love you too” Murmushi ya yi, daga haka yace”see you in three weeks time..” Ahankali ta d’ago ta ce”bye” Kamar baya so haka ya yi Waving nata, tukunna shima ya ce ”bye” Daganan ta yi sauri ta juya ta shige cikin gidan dan tabbas Idan ta ci gaba da tsayawa a gabansa tou za ta yi kukan ne mai yawa ba d’an kad’an ba ma. Ai kuwa tana shiga, ta nemi waje ta zauna a kan d’an dakalin hanyar d’akinsu ta saki kukan ta…..ta yi k’ok’ari ta kwantarwa da Yash hankali bayan ta san tabbas ta fisa shiga damuwa dauriya ce kawai take yi…ta jima ta na kuka mara sauti mai cin rai kafin daga bisani ta goge fuskarta ta tashi ta shige cikin d’akin, a da ba ta ganin nisan watanni dan nan da nan indai aka saka rana sai ta ga lokaci har ya yi, amman tabbas a yanzu watanni ukunnan da aka k’ara jin su take yi kamar shekaru d’ari uku….. *Bayan Wata Uku* Kwanci tashi…..cikin hukuncin ubangiji watanni ukun da aka k’ara a kan bikin su Manubiya har sun cike cif cif….wasu suna cikin tsananin murna wasu kuma suna bak’in ciki yayinda waensu suka ji kunya…. Cikin nasara Yash ya je aka duba masa Hannusa, aka yi masa duk wasu abubuwan da suka kamata. kafin wata biyu ya ware sosai shiyasa a lokacin har Hajiya Mama ta ce ko za’a d’aura kawai, amman sai su Daddy suka ce kar ma ta bari ya ji, kawai a jira dan dai wata d’aya da kwana 7 ai kamar yau ne…. yadda auren ya sake tahowa ne ya sanya su Mommy suka fara d’aga hankalinsu, sai da kowa a cikin gidan ya lura. Shiyasa Hajiya mama da dage ta tsaya tsayin daka a kan al’amuran gidan, dan Matar nan da ta kira ta yi musu feshi kwanakin baya yanzu kusan kullum sai ta zo, haka aka dage da addu’o’i a cikin gidan ba kama Hannun Yaro. Idan kuwa anayi Baaba Larai ji take kamar ta mutu, dan har ga Allah ba k’adan ba Hajiya Mama take b’ata mata aiki gashi ta kasa korar ta a gidan. Kamar yadda Yash ya fad’a sau biyu ya je follow up a UK..a ranar daya gama da ganin Likita suka tarkota har da mom suka nufo Nigeria. Suna zuwa aka shiga murna da oyoyo, Hajiya Mama tana ta tsokanar Yash tana cewa “ba ga shi lokaci har ya yi ba, amman da har da kwallar sa da aka ce za’a d’aga auren, Itafa gaskiya tana kishin wannan kishiyar tata tun kafin ta zo, dan yadda yake wannan rawar k’afar ta san tana zuwa zai manta da ita” Dariya duk akayi banda Mommy wadda take jin kamar zata mutu, cikin tafiyar tsofaffi Hajiya Mama ta nufi kitchen..yau dan rigima da kanta ta dafawa Yash jalof d’in taliya dan ta san yanaso, ba yadda Ummi ba ta yi da ita akan ta kawo ta yi ba amma ta ce “ta yanka mata albasa kawai”(shima saboda matsalar idon ta ne), daganan ta girka abunta tsaf kuma ya yi dad’i sosai. Mom da Ummi ne suka bi bayan Hajiya Mama yayinda Daddy da Abhi suka nufi waje dan suna da wajen zuwa, junior kuma ya bi bayan Yadira da ya ga ta nufi garden alamun waya take yi. Yash yana zaune yana murmushi ya ji kawai an damk’i hannunsa yana d’agowa suka yi ido biyu da Mommy dan haka ya sauk’e ajiyar zuciya kawai yana kallonta…dan tun d’azu da ya shigo bayan ya je sun gaisa ko ‘ya hanya’ ba ta ce masa ba, kamar ma fushi ta ke yi da zuwan nasa,kuma a cikin watanni ukun nan ya lura kamar ma gudun sa take yi dan idan ya je k’ofar ta kullum a kulle. Yana cikin wannan tunanin ya ji tace “biyo ni, Inada magana da kai” Daga haka ta juya ta nufi parlourn bak’i. Sai da ya fesar da numfashi tukunna ya mik’e ya bi bayanta, yana wucewa su Yasira da Baaba larai suka yi sama dan kar ma a zo a tambayesu yana ina. Yash ba k’aramin shock ya shiga ba dan yana shiga parlourn Mommy ta rufesa da fad’a, kamar za ta had’iyi harshe! Abunda ba ta tab’a kwatantawa ba kenan, babu abunda ya fi b’atawa Yash rai kamar akan abunda take yin fad’an, in da ma wani abunne ya faru recently har ta kai ta ga yin fad’an to da dasauk’i amman fa tana fad’an ne akan wai ‘lokacin da za’a d’aga auren sa ba a yi mata magnar ba, ba’a tuntub’eta ba, sai ji ta yi kawai an d’aga. Kuma wai Manubiya ba ta kiranta ta gaida ita amma tana ji suna yawan yin waya da Yahanasu har ma da Ummi…idan so yake ta yafesa a cikin y’ay’anta ne to kawai ya fito ya fad’a, dan abunda ya ke yi mata ya isheta,in ba rashin sanin ciwon kai da wulak’anci ba ta ya zai dinga fifita kishiyarta da y’ar kishiyarta sama da ita a rayuwarsa???….” Yash ya so ya yi mata bayani ta fahimta, sannan ya bata hak’uri amma yadda ta k’i sauraronsa da kuma yadda ya fahimci kamar ma Baki take shirin yi masa ne ya sanya shi kawai ya fice ta k’ofar baya ya bar mata parlourn, zuciyarsa tana wani irin tafarfasa. Sam ya rasa dalilin da ya sanya Mommy take bak’in ciki da farin cikinsa. Bai nufi side d’insa ba direct mota ya nufa ya shiga ya kunna ya fice daga mansion d’in gaba d’aya, ya nufi gidansu Manubiya. Yana yin parking a k’ofar gidan ya ji zuciyarsa tana yin sanyi ahankali ahankali, rabonsa da ita tun last month dan wannan karon da yaje uk ya dad’e sosai shiyasa yake ji kamar ya yi shekara uku bai ganta ba, suna waya da chatting har ma da video call kullum amman yayi mugun mugun missing d’inta…… Tana zaune suna hira, ita da mai gyaran jikinta da su Siyama a parlourn su Siyama ta ga kiran sa, murmushi ta yi tana wani Irin blushing kafin ta yi picking, a hankali ta ji ya ce ”surprise!ina waje” Kad’an ya rage ba ta tsala Ihun murna ba, da kyar ta iya cewa “ok” tukunna ta katse kiran ta kalli Siyama ta cw ”yana waje” ta fad’i hakan fuskarta tana baiyyana tsananin farin cikin da take a ciki. Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ”Allah adda idan aka zo kaiki kika yi mana kuka kowa ya san kukan murna ne,” Dariya duk suka saka wanda hakan ya sa Manubiya ta d’an nutsu ta bar zumud’in rufa mayafin da take yi, kafin ta kalli Jidda ta galla mata harara tukunna ta kalli mai gyaran jikin ta ce ”an gama?” Murmushi matar ta yi kafin ta mik’e ta shiga harhad’a kayayyakin ta tace “ai ko ba’a gama ba jeki kawai” Dariya sosai suka yi kafin Siyama ta ce ”ki shigo da shi nan, bari mu tartare” “To” kawai tace, daga haka ta sa kai ta fice. Tunda ta taho ya kafeta da idanu, har sai da yasa ta ji kamar ta nutse dan yau kalar kallon nasa na daban ne….a b’angaren Yash kuwa har wani jiri-jiri ya fara ji tsab’ar kasalar da ta rufar masa tashi guda! Ya san yana son Manubiya so mai tsanani na tsanakani da Allah amma tunda yake bai tab’a jin kalar sha’awar ta da yake ji a yanzu ba, ya na ji from time to time ba wai ba ya ji ba amman abun na yau ya girmama, dan har wani ciwon ciki ne ya ziyarcesa tashi d’aya…..ta yi wani kyau ta yi fresh kamar wata y’ar baby, har wani murmurewa ya ga ta sake yi gwanin ban sha’awa. Cikin d’an turo Baki ta ce ”ni dai ka daina kallona” Murmushi ya yi ya bi Bakin da ake turo masa da kallo wanda yakenan kamar na y’ar jinjira ma’abociyar tsotso, kafin da kyar ya d’an k’ura wa fuskarta ido tukunna ya ce ”gani na yi kin sake zama baby, y’ar babyn Yashjub” A hankali ta sunkuyar da kanta tana murmushi k’asa-k’asa kafin ta ce” kaima ka k’ara kyau sosai” dan Itanma tunda ta fito ta lura da haske da kyan da ya k’ara….wani irin blushing Yash ya shiga zubawa kamar mai tallar makilin, kafin da kyar ya samu ya tsayar da murmushin tukunna ya amsa gaisuwa da ya hanyar da take yi masa. Daga nan ta yi masa iso zuwa parlourn su Siyama wanda har sun gyara tsaf sun kunna turaren wuta…..Tabbas Yash da Manu sun yi missing juna dan sai da suka kashe sama da awa uku ba tare da sun ma sani ba, dukda kuwa Yash dauriya ce kawai yake yi dan yau kam shi kanshi mamakin kansa yake yi saboda bai tab’a jin desire irin wannan ba, ga kuma ciwon ciki, amman kuma ba ya so ya tafi so yake kawai ya yi ta kallonta… Da kyar dai, yana jin kamar kar ya tafi, ya yi mata sallama dan Najeeb yana chan yana ta jiransa. Har mota ta raka sa, yana ta zuzuta yadda ta yi kyau dan ba kad’an ba ta tafi da imaninsa…..itan ma santin kyan da ya k’ara take ta yi a cikin zuciyarta, a haka suka rabu kowa yana muradin d’an uwansa. Bai yi tunanin za su yi dare shi da Najeeb ba, dan har sha biyu na dare ba su samu sun kammala abubuwan da suka tisa a gaba ba. Sai da yaje mota domin d’aukar wasu abubuwa tukunna ya ga wayarsa tana haske dan haka ya yi saurin d’auka ya k’ara a kunnensa… Yana d’agawa ya ji muryar Daddy ya ce ”come home yanzu, Hajiya mama tana nemanka ta d’agawa kowa hankali”. “Okay tam” Kawai yace, daganan Daddy ya katse kiran, sai a sannan Yash d’in ya lura da uban jerin misscalls d’in da aka jera masa….. ajjiye wayar ya yi, ya je ya cewa Najeeb zai tafi sukayi sallama, tukunna ya nufi gida. Yana zuwa, bai tsaya ma yin tunani ba saboda kar ya ji ba zai iya shiga ba dan har ga Allah ba ya son had’uwar sa da Mommy gudun kar ta kuma yi masa abunda ta yi d’azu…wayoyinsa kawai ya d’auka ya zuba su a aljihu, daga haka ya rufe motar ya nufi cikin gidan. Tun kafin ya shiga cikin main parlourn ya fara jiyo hayaniyar Hajiya Mama, tashi d’aya ya fahimci ita da Mommy ne sakamakon yadda ya ji tana magana cikin fad’a da rashin kara sannan tone d’inta very rude!. “Ai dama ba ki gaji arzik’i da ɗa’a ba, wallahi yadda na ga ba ki wani damu ba na san kece kika b’ata masa rai ya bar gidan nan bani da tantama. Dama ta ya za ki so ya yi aure ya tara iyali ba tare da kin riga kin mallakesa ba! Ƴaƴa dai Allah ya baki amma wallahi ko Akuya ta fi ki sanin ciwon ƴaƴanta! ke kuwa kanki kawai kika sani, burinki kawai ke kanki kad’ai sam baki damu da farin cikin su ba. To bari ki ji, wallahi tun wuri ki san yadda kika yi ya dawo gida idan ba haka ba kema sai kin bar gidan nan!Yau zan nuna miki cewa ba fa surk’ullenki da munafurce munafurcenki ne suka sanya na barki cikin gidan ɗana ba” A hankali ya ji Daddy yace “Mama ba fa inda Yash ya je, maybe aiki ne ya rik’e shi..” Cikin tsawa Hajiya Maaman ta ce ”shiyasa sometimes (wasu lokutan) nake jin kamar in rufeka da duka! Ai ko ba’a fad’a ba na riga na sani, jikina ya bani, gashi kuma ba ya d’aukar waya, amman sai wani ce min kake yi aiki ne ya rik’esa, wanne irin aiki ne zai hanasa d’aukar waya??” Ba ta jira jin amsar sa ba ta ce ”kuma Yadira ta ce min fita yayi ranshi a mugun b’ace” cikin fushi ta juya ta nuna Mommy tace “Kuma na san wanann makirar ita ta janyo fad’a da shi, ba ni da tantama!! Ita ta b’ata mishi rai, ita za ta yi abunda zai fasa auren. dama tun farko ita ta hanashi yin budurwa. Wallahi Khadijah ki ji tsoron had’uwar ki da Ubangiji! son zuciyarki yayi yawa, kwata-kwata ba ki da tunani da lissafi mai kyau!” Wani irin kuka Mommy ta fashe da shi wanda ya sa su Yassira suka k’arasa inda take itada Yasmeen suka rufar mata, suka shiga bata hak’uri, fuskokinsu tamau! Alamun sun ji haushin abunda Hajiya maman take yi. Itakam ko a kwalar rigar ta, haka nan ta ci gaba da tsigale Mommy tass. A haka Yashjub ya yi sallama ya shigo ya samesu, da da farko so yayi ya juya dan wallahi kansa har ya fara ciwo amman kawai sai ya dake ya shigo. Dasauri kowa ya d’ago ya na kallonshi, Hajiya mama kuma ta nufeshi cikin takun ta na tsoffi da d’an sauri tana zuwa ta rungumeshi, sai kuma ta d’ago tana kallonshi kafin ta ce “Karka b’oye min komai, mai ta yi maka? Me ta ce maka? matsala take shirin kunnowa ko? So take ka fasa auren na sani.” Ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace “idan akwai wanda zai kunno matsala a aurena ai ke ce, tunda gashi yanzu ma abunda kike yi na san duk kishi ne ya rufe miki ido kike k’ok’arin ki tada husuma tun kafin kishiyar taki ta zo” Dariya Yadira da Munirat suka yi, kafin Ummi ta d’an matsa kusa da su ahankali cikin ladabi ta ce “Hajiya mama mun gaya miki tun d’azu, babu komai InshaaAllah. Yadira kuma zolayar ki kawai take yi wataƙilan kawai so take ta ja ki da magana” “Umm um fa Ummi, ba ki san halin matar chan ba, kuma na san duk zolayar Yadira ba za ta fad’i abunda zan yi wa uwarta fad’a ba ai. Anyways tunda kowa b’oyemin yake yi ba komai.” Tana gama fad’in haka ta cika Yashjub ta Isa gaban Mommy ta tsaya ta ce ”ko za ki mutu! Sai Yashjub yayi aure da yardar Ubangiji, kuma idan kin haifu ki je ki yi wani abun da zai jawo tangard’a, ko a makirce ko a asirance ko a Isa da mallaka na matsayinki na uwa! A nan ne za ki gane shayi ruwa ne!”. Tana gama fad’in haka ta wuce sama ta bar ta anan ita da su Yasmeen waenda suka kawo iya wuya! Mom da Ummi ne suka bi bayanta, daga haka aka fara watsewa daga parlourn. Sai da Yash ya k’arasa wajen su Daddy da Abhi suka d’an gaisa tukunna ya juya ya nufi side d’insa… Har ga Allah yadda Mommy ta durk’ushe tana kuka duk sai ya ji bai ji dad’in abun ba. Da ruwa mai zafi sosai ya yi wanka, ya d’an gwada kiran Manu, jin shiru bata d’auka ba ne yasa ya fahimci ta yi barci, dan haka ya ajjiye wayoyinsa ya fito ya nufi wajen Mommy bayan ya rufe side d’in nasa dan tuni Junior ya tartare kayansa ya koma side d’in Yassir tun lokacin da aka gama yi masa gininsa. Allah ya so shi kuwa basu rufe ba, dan haka ya shige ya haye sama yana mai sake jaddadawa da tirsasawa kansa “dole ya sasanta tsakaninsa da Mommy, dole ya nemi albarkar ta! dole ya lallab’ata! uwa uwa ce!” Ya yi mamakin samun su da ya yi a d’akin Mommyn su dukansu har Baaba Larai da Yadira kamar wasu masu yin meeting. Sake gaidashi suka yi gaba d’ayansu, daga haka suka fara mik’ewa suna yi wa Mommyn sai da safe suna ficewa one by one, dan yana gama amsa gaisuwar ta su ya koma gefe ya chake ya tsuke fuska… Sai da Baaba Larai ta zo fita tukunna ya kamo Hannunta ya ce “Banda ke Baaba” Kallonshi ta yi ta kalli Mommy kafin tace “to d’an albarka” daga haka ta koma kusa da Mommyn ta zauna anan gefen gado. Shiruu d’akin yayi kafin ahankali Yashjub ya fara takawa zuwa inda suke zaune, yana zuwa ya durk’usa a gaban Mommy. Ba k’aramin shock suka shiga ba dan ko da wasa ba su tab’a kawo hakan ba, yaushe ne ma Yash ya durk’usa mata irin haka ba lalle ta iya tunawa ba… Suna wannan tunanin suka ji a hankali ya fara magana yana cewa “Mommy akwai abubuwa da yawa da kuma misunderstandings (saɓanin fahimta) a tsakanin mu. Ke mahaifiyata ce, shiyasa duk yadda na so in rik’e ki a raina hakan ba zai yiu ba dan ya zame min dole in yafe miki sannan kuma in nemi gafarar ki… Amman pls Baaba ki zama shaida sannan ki nuna mata mahimmancin mu musamman ma ni a wajenta. Akwai abubuwan da kikayi min da yawa shiyasa idan na tuno raina yake b’aci, idan nine wani abun ya faru da ke hankalina a tashe har sai na ga an yi miki adalci amman ke sam bakya dubani a ko da yaushe.. Anyways komai ya wuce yanzu albarkarki da yafiyarki nake nema. Sannan akan abunda kika yimin magana d’azu shima ki yi hak’uri, zan yi k’ok’ari in gyara kema kuma dan Allah ki gyara Mommy.” Ahankali ta sa Hannunta duka biyu ta d’ago shi ta zaunar dashi a gefen ta. Shiruu ne ya biyo baya kafin ta sauk’e numfashi tukunna ta fara magana “Yashjub ba wai ban damu da kai bane A ‘a Ina duba ɗabi’ar al’amura ne… Sannan na san kana jin haushina akan Yassir. Yashjub! Ba ka riga ka haihu ba, shiyasa ba za ka tab’a sanin yadda na ji a lokacin da naga Yassir kamar gawa ba….inaso ka fahimceni ka fahimci ba wai dan na fi son shi akan ka bane ya sanya na fad’i maka abubuwan da na fad’a ba a wachchar ranar… na fad’a na sake fad’a gaba d’ayanku ya’yana daidai kuke a cikin zuciyata, na san ko kai ne ka tarar da d’anka a halin da na ga Yassir a wachchar ranar na tabbatar sai ka yi kuma ka fad’i abubuwan da su ka fi waenda ni na yi na kuma fad’a. Amman duk da haka ka yi hak’uri, ba zan sake ba, inshaaAllah, b’acin rai ne” A hankali Yash ya rik’o Hannunta, ya girgiza mata Kai sannan ya ce “ba komai Mommy, ba sai kin bani hak’uri ba” Murmushi ta yi ta d’an shafa fuskarshi kafin ta ce ”I love all of you amman kuma in ka lura mahaifinku ya fi fifita ka sama da kowa, idan nima na yi hakan to tabbas mu da kanmu zamu taru mu lalata tsakanin ku ne musamman ma tsakaninka kai da Yassir wanda yake ganin kamata ya yi ace kunada equal right (haƙƙi dai dai wa dai da) da kai da shi, shiyasa dole wani abun zan ke kauda kai ba wai dan ban damu da kai ba sai dan son ganin an zauna lafiya. Sannan maganar Kausar dan itama na san kana ganin kmar Ina fifitatata sama da ku ko?” Bata jira jin amsar sa ba ta d’aura da cewa “Kamar yadda ka kauda duk wani abun da kake tunanin na yi maka ka zo ka bani hak’uri sannan kake neman yafiya da albarka ta a matsayina na mahaifiyarka To nima albarkar tawa mahaifiyar nake nema dukda kuwa ba ta raye, saboda inaso inga na cika mata burinta dan kafin mahifiyarmu ta rasu sai da ta damk’a min amanar maman Kausar tana kuka tana rok’ona in zame mata uwa da uba mu had’e kawunanmu, to haka itama maman Kausar a lokacin da ta zo rasuwa tana kuka haka ta bani amanar Kausar, ta yaya kake tunanin zan zubar da wannan amanar?? Kuma bayaga haka ma Allah ya d’aura min tausayi da k’aunar Kausar sannan ka duba kaga Yarinyar nan ko uban da ya haifeta bata saniba wasu lokutan a gaban idonta Mama da Daddynku suke kiranta da ‘shegiya!’ Na san ba mu Isa chanza wannan fact d’in ba amma kara ai tana da dad’i, kuma abun yana damunta sosai sannan gashi ba uwa ba uba, ka gaya min idan ban ja ta a jiki na sa ta ji itama tana da family sannan na bata mahimmanci ba wa zai yi? ina za ta saka kanta? Ba wai na fi son Kausar a kanka ba ne, kai kanka ka san hakan ba zai tab’a yiwuwa ba tunda kai a cikina ka fito kawai dai Ina k’ok’arin inga ban biyewa son zuciyata na cutar da kowanne a cikin ku ba, kuma kamar yanda kake fushi da ni akan na fi son wasu akanka ko kuma kake ganin kamar ban damu da kai ba to haka nima nake fushi da kai, shiyasa ka ga kawai Ina rabuwa da kai wasu lokutan dan sai inga kamar baka damu da ni sosai ba, d’azun ma k’ureni ka yi kuma ai kai kanka ka san gaskiya na fad’a Yash baka shawara da ni, ban gama jin d’uminka ba aka d’auke min kai kuma ban Isa in ce wani abun ba sannan kai d’in da nake saka ran za ka share min hawaye gaba d’aya ka k’i ka sake da ni da y’an uwanka gashi har za ka yi aure ka sake yin nesa da mu shikenan na san burina na ganin mun had’e kai Ni da Kai da y’an uwanka ba zai tab’a yiwuwa ba kenan??” Kasa ci gaba da magana ta yi sakamokon kukan da ya taho mata… Ahankali ya janyota ya saka ta a jikinshi ya shiga rarrashinta, kafin cikin kwantar da murya ya ce “Mommy sam ba haka bane ata b’angare na, su Yassira Mata ne Yassir kuma kinga yanayinshi, Idan ban tsaya na yi haka akansu ba akwai matsala sannan Mommy ba wai ban saki jiki dake bane kasa fahimtata kikayi…amman inshaaAllah zan gyara. Ina da fatan za ki daina fushi da ni sannan ki saka min albarkarki.” Ahankali Baba Larai ta ce ”Ku dai gyara tsakanin ku, jini ya fi ƙarfin komai, kuma sabuwar member za ka kawo Yashjub, duk abunda ta ga kana yi wa family d’inka to itanma haka za ta yi musu”…Cikin son fahimtar da shi su biyun suka shiga nuna mishi mahimmancin family kama daga y’an uwanshi har iyayensa. Tabbas kuwa maganganun nasu sun ratsa Jikinshi matuk’a… Daganan suka fara maganar auren nashi…ya saki jiki da su sosai bai b’oye musu komai ba, ya ji dad’in yadda Mommy ta ce”komai komai ya wuce” sannan ta nuna farin cikin ta a auren ta kuma gaggaya mishi abubuwan da shi ba su ma shirya ba daga shi har Yahanasun. Tabbas duk lalacewar uwa Uwa ce kuma tanada matuk’ar amfani ata ko wanne b’agare na rayuwar y’ay’anta, dan shi sai yanzun ne ma da suke maganar tukunna yake jin wasu aladun da kuma abubuwan da ya kamata a yi waenda da duk ba za ayi su ba. Bai bar wajen ba har number Manubiya sai da ya bawa mommy, hakanan suka rabu ran Yashjub fess…Mommy ta sake sosai sannan ta amince kuma ta sanya albarka a auren d’ari bisa d’ari. Yana murmushi haka ya fito daga d’akin, da fari ko sanda ya shigo cikin gidan ko kallonta baya son yi amman gashi da ya danne zuciyarshi ya zo suka fuskanci juna ya ji sanyi a ranshi. Addu’ar sa itace”Allah ubangiji ya bashi ikon had’a kan Manubiya da su gaba d’aya, Allah ya sa komai ya zo mishi da sauk’i dan no matter yadda mutum yake jinshi jajirtacce indai lamari ya had’a da Mata dayawa kuma ya zamana shine a tsakiya to fa abun babu sauk’i. Yashjub yana fita Mommy ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta kalli Baba Larai ta ce “yanzu menene abun yi na gaba???” Shiruu Baba Larai ta yi, kafin ta furzar da ajjiyar zuciya tukunna ta ce ”ki yi hak’uri, mu ajjiye komai, mu hak’ura a yi auren”. A mugun furgice sannan da k’arfi Mommy ta ce “watt!!” Jinjina Kai Baba Larai ta yi kafin ta ce “Khadijah! Ba ki kaini tsanar Yarinyar nan ba inaga, sannan baki kaini k’in auren nan ba amman ya zama dole mu hak’ura, dan ba zan b’oye miki ba bamu da yadda za mu yi, babu yadda zan yi dan babu abunda zan iya sake yi! Kuma ko ba ni d’in ba ko ina za ki je Wallahi sai dai a ci kud’inki…ƙarshen basirata na k’arar amman ki duba ki ga jinkiri kawai aka samu. Ki yi hak’uri tunda ta nace akan sai ta shigo gidan mu barta ta zo ɗin, inshaaAllah sai ta fita da k’afarta… barin ma yadda muka samu Yash d’in ya fara jan mu a jiki ai an samu riba kuma komai zai zo mana da sauƙi!!… Ki duba fa ki ga yau har durk’usa miki ya yi, sannan ya nuna miki girmanki da matsayinki a wajensa, kinga kuwa wannan ai babban nasara ne, dama garin ƙoƙarin buɗe wata ƙofar wata take buɗuwa lura ne kawai da ba a yi… Dan haka daga yau, inaso tun daga kanki har izuwa kan Yadira kowaccenku kawai ta nuna tana son auren, bama so amma mu nuna masa muna so d’in, idan aka yi aka gama sai a san abunyi..” Da sauri Mommy ta ce “Ta ya zan bari a yi auren bayan kin ce in har su ka kasance tare har hakan ya janyo ta rayu da mu to nakasata ta zo kenan” Cikin tarar numfashinta Baaba Larai ta ce “Kinga da farko dai ba za mu bata damar yin dogon zangon zama a cikin namu ba ta hanyar hanasu kasancewa a tare ballantana har nakasar taki to tabbata, zaman da za ta zo ta yi kamar na baƙunta haka nan za ta zo ta yi shi ta tafi. Ki kwantar da hankalinki, kin ji ko, in sha Allahu ba za a bata damar kasancewa a tare da shi ba, ballantana wata matsala ta taso ko kuma har su yi shaƙuwar da za su kasa rabuwa ko kuma ta samu abunda zai iya janyowa ta yi dogon zangon…” Cikin tarar numfashinta Mommy ta ce “in aka riga aka shafa fatiha Larai ta zama matarsa fa a idanun duniya da koina kenan, kinga kuwa ai sun gama kasance tare ko” Wani ɗan guntun murmushi Baaba Larai ta saki, kafin ta ce “Mommy, dan an yi aure tsakanin Mace da Namiji ba shi yake nufin Mata da Mijin sun kasance tare ba..Yash dama chan shi ga yadda ya ke, kuma akwai abunda zan ƙara akai, dan haka ba za a bari su kasance taren ba!” Ta ƙarashe maganar tana mai ƙurawa Mommy wadda itanma ta ƙura mata idanu…. Sun ɗan jima a hakan kafin Mommy ta ɗauki haske, dan haka ta sauƙe wata nannauyar ajiyar Zuciya tukunna ta ce “na fahimta” “Madalla” Shine abunda Baaba Larai ta ce kafin ta ɗaura da cewa “dan haka mu bari a ɗaura Khadeejah, sannan daga yau, inaso duk ku daina fushi da shi, sannan ko goya su Yahanasu zai yi wannan ma babu ruwanku, a tak’aice dai duk wani abun da zai janyo saɓanin fahimta ko fushi a tsakanin ku da shi ku gujeshi, A iyaka maganarsa ta yanzu na lura kuma na fahimci Idan har muka yi hakan to za mu samu kanshi cikin sauk’i, kinga kuwa idan muka samu kanshi komai zai zo mana da sauk’i kenan, dan inshaaAllahu kafin ma amaryartasa ta gano steering da za ta kama ta tuk’a rayuwar gidan nan da shi kansa Yash d’in tuni sai dai ta ji ta a waje.” … Sosai hud’ubar Baaba Larai ta ratsa Mommy, dan haka washegari da safe suka tara su Kausar suka yi musu bayani, kowa ya yarda ya amince amma banda Kausar… babu yadda ba a so a fahimtar da ita ba amman furr ta birkice musu k’arshema barin d’akin ta yi ta banko musu k’ofa bayan ta cewa Mommy “ai dan ba ita ta haifeta ba shiyasa ta k’i bawa abun mahimmanci, gashi yanzu har za a yi aure, kuma a haka suke so ta kwantar da hankalinta, tana ji tana gani Yash ya auri wata su tare kenan ko ya su ke nufi???…..” Ganin duk sunyi mata shiru ne ya sa kawai ta fitan, ta bar musu d’akin. •••• Abun har mamaki yake bawa Mutane, yadda jikin Inna ya ware, dan tun watanni biyu baya da suka wuce take tashi ta zauna da kanta, wanka ma Manubiya za ta kama ta ta kaita band’aki ta sanya mata kujera ta fito ta barta ta yi abunta, dukda ba fita take yi ba amma a wannan lokacin likitar tace “a barta ta dinga gwadawa, shima wani exercise d’in ne” Sannan magana d’aya biyu tana kwatantawa cikin ikon Allah, har waya ta karb’a dukda maganar tata bata fita sosai haka ta yi wa Yashjub godiya dan ba kad’an ba ta jinjina masa akan yadda ya tsaya tsayin daka, dan ba kowa zai Iya abunda ya yi ba… har wasu magunguna likitan ta rubuta shi kuma ya siyo mata masu mugun tsada, wanda akace ta dinga sha safe rana da dare. aikuwa ba ta sha na kwana hud’u ba ta k’ara jin dad’in jikin nata matuk’a, kafin wata d’aya kuwa tsaff Inna ta ware gar kamar wadda ba ta tab’a samun stroke a rayuwarta ba, sai dai y’an abunda ba’a rasa ba. Haka nan ƴan gidansu Manu su ka kasance cikin farin ciki, abinci suna samu jikin Inna kam Alhamdulillah. Jidda ma har ta fara first semester exams d’inta na level one a northwest yayinda Manubiya kuma ta gama first semester level 3 a buk. A yau ne za su karb’i lefen Manubiya wanda yayi dai-dai da sauran kwanaki 7 d’aurin auren kenan, shiyasa gaba d’aya suketa hada hada isu isu tun shekaran jiya….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252. *MANNUBIYA* *Book 2* *page 12* Ya Musbah ma ya samu aiki a wani company wanda Yash ya nema masa, har makaranta ya koma (ta manya) dan inda Yash d’in ya nema masa dole sai da karatu, dukda yana gane aikin ba wai ba ya ganewa ba amma yana buk’atar k’ari. Har ya murmure kuwa, dan wajen ana samun alkhairi sosai…. A cikin watannin da basu kai uku ba har d’aki da band’aki ya gina musu, a filin da ke jikin d’akin nasu wanda yake mallakinsu, da shi da Muhsin suka koma ciki da zama dan mai sunan baba ya koma wajen mahaifiyarsa. ……….. Watanni uku da suka wuce su Mommy sun fi kowa farin ciki, amma a yanzu kam sun fi kowa shiga cikin tsananin tashin hankali dan abun bai zo musu da sauk’i kamar yadda suka yi tunani ba. A b’angaren Kausar kuwa, gani takeyi kamar ta fi kowa shiga matsala da tashin hankali, shiyasa take jin haushin kowa da komai musamman ma su Mommy, dan a ganinta inda ace sun bar ta ta kashe Manubiya tun farko da ba’a zo nan ba…k’iri-k’iri suka hanata ko da tab’a Manubiyan ne, hakanan ta amince ta yi yadda suke so bayan sun yi mata alk’awarin mara mata baya akan Yashjub, amma kalli yadda yanzu tashi d’aya suka chanja tunani suke so ta bari a yi auren sannan tsabar cin fuska ita gani take ma kamar farin ciki suke yi da auren, dan da su taga ake yin komai, ita kuma sun manna mata hauka sun tattara sun ajjiye gefe! Bayan da farko plan d’insu shine ‘Duk runtsi ba za su bari Manubiya ta shigo cikin gidan ba’, amman kalli yadda suka sauya shawara tashi d’aya, babu wanda ya damu da ra’ayi ballantana mahangar ta. Shiyasa gaba d’aya ta shiga cikin bak’in ciki! Takaici da haushi, tana jin kamar ta had’iye Zuciya ta mutu, ta rasa Ina za ta saka Kanta ta ji sanyi. A b’angaren su Yassira kuwa, ba k’aramin k’ok’ari suke yi ba wajen danne kansu da nuna farincikin da take tunanin na gaskiya ne. Yau kam duk yadda suka so danne kansu abun na neman ya gagara, sakamokon akwatunan lefen Manubiya da su Hajiya Mama suka jere a parlourn k’asa tun safe, shiyasa duk suka gaza sukuni. Sun shirya tsaf tun d’azu amman kuma sun kasa sauk’a k’asan. A karo na biyu Ummi ta yi knocking k’ofar d’akin Mommy, bata shiga ba ta tsaya a wajen ta ce ”Hajiya Mama fa tun d’azu ku take jira, an kawo sark’ar, ku fito mu tafi.” Tana gama fad’in haka ta juya ta koma k’asa zuciyarta fal cike da sak’e-sak’e. Bata dad’e da sauk’a ƙasan ba su Mommyn ma suka sauk’o, gaba d’ayansu a shirye tsaf! Suna yak’e. Tashi d’aya idanun Ya’isha suka sauk’a akan sir Najeeb, yana tsaye shi da wani driver suna gyara d’aurin carpet…..ya yi kyau ya yi fresh abunshi kud’i sun sake zama daram..har ga Allah dama chan ita tana son Ya Najeeb, kawai dai tana ja mishi aji ne saboda ita ta san tana da mutunci da daraja dan haka duk wanda zai sameta to sai ta wana shi! Saboda ba za ta taɓa bari a same ta a b’agas ba.…amma tunda ta lura kamar Najeeb d’in yana shirin sub’uce mata ta yi sauri ta gyara ta daina duk wasu halaye da ta san tana masa marasa kyau, sai dai kuma gani take kamar ta makaro dan ta fahimci sam sam kamar ba ta gabansa kamar ya daina sonta, ko dan ya ga yanzu ya yi kud’i sosai ne maybe shiyasa yake ganin kamar ya fi k’arfinta….amma inshaaAllah za ta sake gyara komai, za ta zage dantse za ta yi duk abunda yake so dan ita kanta ba ta san tana mahaukacin son shi kamar haka ba sai yanzu da ta ga yana shirin sub’uce mata…. Tana cikin wannan tunanin ya matso suka gaisa da Mommy, da su Yasmeen kafin ya juya ya cewa Hajiya Mama “zai jira su a mota” daganan ya sa Kai ya fice daga cikin parlourn ba tare da ya kalli ko da inda take ne ba. Yasmeen ji ta yi kamar ta rufeta da duka, idan shi bai kulata ba ai ita kamata ya yi ta gaidashi, shiyasa ta juya da niyyar ce mata “ta bishi motar” amman sai mom ta katsesu ta hanyar matsowa ta fara nuna musu zabgegiyar sark’ar gold da bangles d’in da aka kawo yanzu…sark’ar Hajiya Mama ce ta bada as gift daga b’angarenta ita kuma mom d’in bangles d’in ne ta bada. Shiyasa Yasmeen ta ja Bakinta ta yi shiru da niyyar in sun keb’ance za ta yi wa Ya’ishar magana, dan ya kamata ta kama Najeeb da kyau tun kafin ya sub’uce mata. Saida suka yi da gaske tukunna Yasira ta d’anyi murmushi ta karb’a ta shiga yabawa, yayinda Hajiya Mama ta yi shiruu kawai ta zuba musu ido ita da Ummi……… Tun safe yau Kausar bata lek’o ba, ko breakfast ba ta yi ba, jira take ta ga ko wani a cikin su Yassira zai lek’ota amman gashi har kusan yamma babu wanda ya lek’ota. Bak’in ciki, tashin hankali, fargaba, k’unci da yunwa ne suka tuso ta a gaba, ganin tana shirin sumewa a d’akin ne yasanya kawai ta mik’e ta fita dan kanta. Hankalinta bai sake tashi ba sai da ta sauk’a k’asan, ta ga uban lefen da aka had’a sannan ta ci karo da sark’ar da ta gani a Hannnu Yassira da bangles wanda tun kafin ta k’arasa sauk’k’owa ta fahimci d’anyen gold ne. Babu wanda ta kula, babu wanda ya kula ta. Haka nan ta wuce kitchen tana ganin dishi-dishi, ta d’auki abunda za ta d’auka ta zo ta wuce da sauri ta haye sama. Tab’e Baki kawai Hajiya Mama ta yi, ta d’auke Kai dan kai tsaye ta hango baƙin ciki da tashin hankali a idanun Kausar, kamar yadda tun ɗazun ta ke hangowa a Idanun Mommy da su Baba Larai! Ita fa wani lokacin har tsoro bayan mamaki Mommy take bata, anya kuwa Mutum ce wannan Matar? wacce iriyar muguwar zuciya gareta haka? Ta ya k’iri-k’iri za ta k’i auren d’anta? Kalli yanzu Allah kad’ai ya san mai da mai ta rad’awa su Yasira dan suma kaff d’insu da ganinsu an san yak’e ne kawai sukeyi amman babu mai son wannan auren. Kausar tana shiga d’akinta ta fashe da wani irin kuka…. Wato dai auren Yashjub za’ayi a cikin gidan nan, sannan a gaban idanunta kuma no body is willing to do anything about it(babu wanda ya ke ƙoƙarin yin wani abu game da hakan)…. Shin wai Mommy bata san idan ta bari aka d’aura auren nan tsaf za ta iya mutuwa bane ko yaya?! Tabbas zuwa yanzu ta yarda ta amince cewa ‘ita kaɗai ce kawai, bata da kowa!’. Inda ace Yasira ce ko d’aya a cikin ya’ya’n Mommy ta san da tuni an nemi mafita amman da yake itace yau an fi sama da watanni nawa kullum ce mata akeyi ta yi hak’uri za’a san abun yi, yau gashi har za akai lefe bata ga alamar tab’arb’arewar komai ba k’arshema sun b’ige da bin bayan d’an uwansu, sannan shima Yashjub d’in ta lura kamar ma rura wutar tsanar ta aka kuma yi a cikin zuciyarsa, ga kuma d’an kad’afe ‘Yassir’ wanda gaba d’aya ya hanata sakat, ko numfashi in yananan da kyar take shak’a, dan ma ta samu ta yi masa wayo yanzu yana zuwa office yana d’an aiki ba laifi a cewarta “ya dage saboda shima aga ya zama serious, kuma sai ya na da isassun kuɗaɗe ne tukunna zai iya yin destroying sannan ya yi galaba akan duk wani maƙiyinsa, tunda yanzu komai na kud’i ne” To dai an ci sa’a yana zuwa office d’in yanzu, ba dan haka ba ta san da tuni kullum yana nanik’e da ita. Kuma ta lura kamar su Yassirar sun d’an fara jin haushinta akan Yassir d’in saboda suna gani kamar tana yi wa ɗan uwansu wasa da hankali tunda duk sunsan ba ta son shi amma kuma gashi ta ƙi rabuwa da shi, wataƙila ma shiyasa suka k’i taimakon ta suka barta ita kad’ai kowa ya kyaleta take ta fama da tashin hankali dare da rana…… Wani sabon kukan ne ya kuma kufce mata, bayan ta gama waennan saƙe-saƙen, tashi d’aya ta fara ganin duhu-duhu kafin daga k’arshe ganinta jinta da k’arfin jikinta ya tsaya chak, komai ya d’auke, daga haka ta tafi luuu ta zube a wajen kamar matacciya…. Duk yadda Mommy ta so ta d’an rabu da Kausar ko da na kwana biyu ne sam sai ta ji ta kasa, dan tunda taga yanayinta ta gaza hak’uri, kuma a yadda ta ga fuskar Kausar d’in ta kumbura ta yi jaa ta san akwai matsala, dan haka ta mik’e ta bi bayanta domin ta je ta rarrasheta ta kuma sake bata hope…. Wata razananniyar k’ara Mommy ta saka daga shiga d’akin Kausar d’in, sakamakon hangota da tayi wanwar a k’asa a zube. A gigice ta fita ta tsaya a dai-dai k’afar bene ta shiga rambad’awa su Yassira kira, dama suna hanya dan tunda suka jiyo ihunta Yassirar ta mik’awa mom sark’ar Hannunta suka nufi saman gaba d’ayansu. Har Ummi za ta bisu dan bata san menene ba, sai kuma kawai ta rabu da su dan ta lura kwana biyun nan wuyar ta su ga babu idon Hajiya mama kiri k’iri suke sauk’e mata maganganu!harare harare!da tsuka kamar masu jiran ta biyesu su dambatu. Suna shiga d’akin suma duk suka gigice, suka rufu akan Kausar… Sai da Yasmeen ta tabbatar musu da ‘tana da rai’ tukunna hankulansu suka ɗan kwanta. Sai dai kuma babu kalar dabarun da Yasmeen d’in ba ta yi mata ba amman ta ƙi yin koda motsi ne, dan haka suka kinkimeta suka sauk’o k’asa domin kaita asibiti. A nan k’asan suka tarar da kusan kaff masu aiki da masu gadin gidan suna ta jidar akwatunan suna kaiwa cikin motocin da suke nan jere a compound d’in gidan. A kan doguwar kujera suka shimfid’e Kausar kafin Yassira ta k’arasa kusa da main driver d’in gidan ta ce ”Baba Sani, yi maza ka fito da babbar mota, za mu fita gaba d’ayanmu, Kausar ba lafiya”. Shiruu ya yi, dan tuni babbar motar a cike take! Dan a cikinta ne ma aka jiide gaba ɗaya kayan su shinkafa carpet da tabarma da su randa…. Yana cikin tunanin mai zai ce mata ta daka masa wata uwar tsawa ta hanyar cewa “Ina maka magana ka yi shiru, ba ka ganin Kausar a kwance kamar gawa ne??..” Cikin tarar numfashinta Hajiya mama tace “and so what?? (To sai me??) idan Kausar tana kwance kamar gawa?. Ai ita dama haka take, indai aka zo abun farin ciki na ni da d’ana har ku kanku ma tou sai ta b’ata. Maganar auren Yashjub kuwa, idan a rami ake dannata wallahi sai an yi kuma sai mun yi farin ciki!. Ita ta sani, ta yi ta kwanciya karta tashi daga nan har abada”. Ahankali Ummi ta matso ta ce ”. Maama…...” Cikin katseta Hajiya Mama ta ce ”Saddik’a kar ki wani damu, makirci ne, so sukeyi a fasa auren Yashjub!. ni na gaya maki muna fita Kausar za ta mik’e, dan lafiyarta k’alau! Na riga na san duk acting ne takeyi” Tana gama fad’in haka ta kalli mom da Yahanasu da Ummin ta ce musu “let’s go( mu tafi)” Tunda iya su ne yanzu za su tafi, Munirat ba ta nan yayarta ta yi kira yau ta tashi bata da lafiya sosai shine ta d’an je ta dubota ta dawo. Basu bar muusu driver ko d’aya ba, gashi Hajiya Mama ta sanya su Yassira sun rarraba makullayen motocinsu a drebobin da za su kaisu tun d’azu. Dan tashi d’aya ta fahimci basa san zuwa da motocin su shiyasa ta karb’e tun da wuri dan so take ayi convoy. Haka su Hajiya mama suka jera convoy d’in nan kuwa dan kaff motocin gidan sai da suka kwashe iya na Daddy Yassir Yashjub ne kawai babu suma kuma dan sun fita a ciki ne. Motar Ya’isha kuma ta samu matsala balle su Mommyn su fita a ciki,gasu da uban yawa….. Suna fita Mommy ta fashe da kuka tace “Baba Larai na ce miki dama ba zan iya tolerating (jurar) matar nan ba, kalli wulakanci da rashin tausayi da isa da mallaka a cikin gidana?!!” Shiruu duk sukayi zuciyar kowa a wuya, da kyar Yassira ta share kwallar da ta zubo mata, ta wuce ta nufi dak’in Kausar…da kyar kuwa ta ga makullin motar Kausar d’in dan haka ta d’auko ta fito aka samu aka tafi kaita Asibiti daga Mommy sai Yassira da Yasmeen wadda ta zauna da Kausar d’in a baya dan motar ba za ta ishe su su duka ba….. Kaff layin su Manubiya har ma da makwaftan layin sai da aka san yau an kawo lefe, dan convoy d’insu Hajiya Mama sai da ya cika layin taff. Suna zuwa Yahanasu ta kira Manubiya ta ce mata “ga su sunzo” ita kuma Manubiya ta sanar da Ya Musbah, dama sun ji zuwan nasu. Aisha da Jidda, aka tura suka yi musu iso zuwa parlourn su Siyama inda yake nan a gyare tsaf sai tashin k’amshi yake yi. Manubiya tana zaune a d’akinsu, ta ji anata wucewa da kaya ana hada-hada shiyasa tashi d’aya jikinta ya yi sanyii, hakanan ta koma gefe ta rakub’e ta yi shiruuu, tana jin yadda gabanta yake ta fad’uwa. Sai da suka gama shigewa tsaff, tukunna anty Umma ta zo kiran su inna da mama domin su je su gaisa da surukan nasu, inna ce ta samu ta je yayinda mama ta ce “sa had’u next time(a gaba), bari ta zauna da amaryar” Su anty umma sun so ta je amma tace “ba komai,”dan haka suka fita suka barta ita da Manubiya wadda ta fara hawaye kad’an-kad’an…cikin rarrashi mama ta shiga lallab’ata had’e da nasihar zamantakewar aure mai ratsa jiki. Ba mom ba hatta Ummi ta sha mamakin gidansu Manu, dan a tunaninsu Yarinyar y’ar manya ce, ba wai reni ko wani abun ba, kawai dai sun yi tunanin Yash ba zai zo nan ba, amman tunda nan d’in ya zab’a to Allah ya basu zaman lafiya, inshaaAllah su kuma za su so ta su rik’eta amana. Hajiya Mama ma ba ta ji komai ba, sai ma sake ganin hankalin Yash da ta yi dan ta san tabbas tunda ya zo nan tou tarbiyya da hankali ya bi ba wai kyalkyalin duniya ba!, Ai kuwa Inna tana zuwa ta tabbatar da hakan, dan ba kad’an ba kawaici da nutsuwar Matar suka sake tabbatar mata da hankalin Amaryar tasu. Cikin mutunta juna da barkwanci suka bada lefe akwatuna goma sha biyu da su taburmi, carpets…da dai kayan al’ada. Su kuma su inna suka basu tukuicin naira dubu d’ari da hamsin suna ta jin kunya amman yadda Yahanasu ta sa Hannu ta karb’a cikin mutunci da karamci da kamala ne ya sanya suka d’an ji sanyi, dan su kansu sun san d’ari da hamsin ya yi kad’an a wannan uban kayan da suka cika musu gida da shi. Hajiya Mama ta so a kira mata Manu su d’an gaisa, amman kuma yadda parlourn ya cika taff da jama’a ake jan numfashi da kyar ne ya sanya ta hak’ura, dan makwafta har sun fara shigowa….shiyasa suka yi musu sallama tare da fatan alkhairi bayan sun ce ”rana ita yau by this time ( i war hakan) inshaaAllah za su dawo su d’auki amaryarsu. Hakanan aka rabu cikin mutunta juna, yayinda su Siyama Jidda da Aisha da Muhsin su ka yi musu rakiya da tray tray na pepper chicken, daughnuts, chin chin, meatpie, cakes da drinks… Tunda suka zo ya yi parking ya kashe motar ya fara addu’a ‘Allah Ubangiji ya sa yau ma ya ganta….’ Indai ya samu suka had’u yau ɗin kuwa to sai ya karb’i numberta, shi kad’ai ya san wahalar da ya sha a cikin watannni ukun nan, da tunanin ta yake kwana yake tashi. Kunyar Yashjub ya ke ji shiyasa ya gagara ce masa ya karb’a masa numberta a wajen Manubiya…… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 13* Tunda suka zo ya yi parking ya kashe motar ya fara addu’a ‘Allah Ubangiji ya sa yau ma ya ganta….’ Indai ya samu suka had’u yau ɗin kuwa to sai ya karb’i numberta, shi kad’ai ya san wahalar da ya sha a cikin watannni ukun nan, da tunanin ta yake kwana yake tashi. Kunyar Yashjub ya ke ji shiyasa ya gagara ce masa ya karb’a masa numberta a wajen Manubiya…… Yana cikin wannan tunanin ya ga sun fito ita da Jidda rirriƙe da trays na gifts, da sauri ya yi wuff ya fice gudun kar ma su nufi wata motar da ba ta shi ba. Yana fita suka hangoshi kuma sun gane sa Abokin Yash ne shiyasa suka nefesa da niyyar gaidashi sannan su saka gifts d’in a cikin motarsa. Kafin su k’arasa su Hajiya Mama suka fito kare da waya a kunnenta, wadda tun a kallo d’aya in aka yi mata za a fahimci tana cikin tsananin tashin hankali… Da sauri duk d’insu suka nufi Najeeb ɗin dai-dai suma su Siyama sun iso kenan. Da sauri mom ta ce ”Najeeb! Hurry up and call Yash, ku fara nema mana flight za mu wuce, Na’ima ta yi accident!” Ta fad’i hakan a lokaci guda tana dialing number Abhi, kafin ta kara wayar a kunnenta. Da sauri su kuma duk suka ce”subahanallah!” A gigice. Tukunna ba tare da ɓata lokaci ba Najeeb ɗin ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran Yash, tukunna ya juya ya bud’ewa su Siyama gidan baya suka ajjiye gifts d’in…. Cikin rashin jin dad’i su Aisha suka shiga yi musu jaje, dukda ba su san wacecen Na’iman ba, tare da add’uar Allah ya kare gaba. Sai da suka ga tashin motocin nasu tukunna suka juya suka nufi cikin gidan. Already su Hajiya Mama suna da visa d’insu a Hannu shiyasa suka ci sa’ar samun flight dan a ranar suka samu na dare. K’arfe 3:00am daidai jirginsu ya d’aga gaba d’ayansu har da Abhi suka wuce uk. Su Yasira ba k’aramin dad’i suka ji ba dan ko ba komai sun san sun rage zafi, Ummi kuwa kamar za ta yi kuka…ta so ta bi su amman kuma in aka ce itama sai an nema mata visa tukunna za su tafi to za ta b’ata musu lokaci, shiyasa ta hak’ura akan inshaaAllah za ta je ta ga jikin Na’iman in an shirya mata komai. … Mommy ce ta zauna a asibiti tare da Kausar, dan suna zuwa aka basu gado sakamokon jininta da suka ga ya yi mahaukacin hawa. 12:00am daidai Kausar d’in ta farka lokacin duk su Yassira sun tafi, tunda ta farka kuwa sam ta k’i yarda ko da had’a idanu ne ta yi da Mommyn,babu kalar rarrashin da Mommy ba ta yi mata ba amma ta k’i kulata, hakanan ta hak’ura ta mik’e ta fita ta je ta kira Dr aka zo aka shiga dubata. Ko bayan fitar Dr d’in ma Mommy ci gaba da rarrashin Kausar ɗin ta yi amman ko arzik’in kallo ba ta samu daga gareta ba. Suna zaune a haka kira ya shigo wayar Mommy, ganin sunan me kiran nata ne ya sanya ta saurin d’auka cike da mamaki dan lokacin 2:00 ya wuce ma, a hankali ta ce ”Yasira, har yanzu ba ku yi bacci ba?” Cike da farin ciki Yasirar tace mata”Hajiya Mama sun wuce, yanzun Yash ya tafi kai su airport gaba d’ayansu”. Sai da Mommy ta tashi tsaye dan ba kad’an ba ta ji dad’in zancen Yassirar, tukunna tace”haka kurum suka tafi,Ina Larai?bata wayar….” Sun jima sosai suna magana da Baba Larai….tukunna suka yi sallama, ta kashe wayar tana jin wani sanyi yana ratsata a ranta ta ce ”inshaaAllah daga yanzu mun fara samun nasara akan duk wani mak’iyinmu kenan, da izinin Allah.” Ajiyar zuciya ta sauk’e tukunna ta koma kusa da Kausar ta zauna akan kujerar da ke kallonta, cikin kamo Hannunta ta fara magana “Kausar, a cikin kwana biyun nan da suka wuce kin b’ata min rai matuk’a, dan ban tab’a tunanin za ki gaya min abunda kika fad’a ba…duba da yadda na rufe idanuna na ke bin bayanki a ko Ina sannan akan komai. Wallahi Allah Kausar yadda nake jin su Yassira haka nake jin ki a cikin zuciyata, kuma ko da ace su d’in ne a cikin situation d’in (halin) da kike ciki dole haka zan zuba idanu in hak’ura saboda babu yadda za mu yi. Baba Larai ta yi iyakar bakin k’ok’arinta nima na yi amman abunda muke so d’in bai faru ba kuma tace ba ta da yadda zata yi, no way out(babu mafita), shin ya kike so mu yi?” Ba ta jira jin amsarta ba ta d’aura da cewa”na fad’a miki zan kuma sake fad’a miki cewa ki yi hak’uri a yi auren nan! Bayan auren inshaAllah da ni da ke da su Yassira da Baaba Larai za mu taru mu kwatar miki Yash, kuma na yi miki alk’awarin ba zan bari ki zauna da kishiya ba dan kafin ma ki shiga gidan na san ta dad’e da fita. Amman fa idan kina so hakan ta faru dole sai kin kwantar da hankalinki kin nutsu kin yarda da mu an taru an yi abu d’aya tukunnan za mu taru mu taimaki juna. Ban san me kike ji ba amman na san na fiki k’in auren nan, saboda ba ki san abunda auren ka iya janyomin ba shiyasa nake so ki yarda da ni saboda ko dan kai na ba zan tab’a barin Yarinyar nan ta yi lasting (ta daɗe) a gidan Yashjub ba dan zaman ta a tare da mu barazana ne ga duk wani farin ciki na da gata na. Ahankali Kausar ta share hawayen ta tukunna tace”inshaaAllah Mommy zan yi yadda kike so.Sannan ki yi hak’uri da abunda na fad’a miki b’acin raine ya janyo hakan, ba zan sake ba.” Wani sanyi ne ya lullub’e Mommy tashi d’aya ta mik’e ta koma kan gadon ta yi hugging Kausar tace”that’s my girl….” Daga nan ta ci gaba da kwantar mata da hankali tana yi mata nuni da yadda suka fara samun galaba a kan Yash gashi Hajiya mama itama ta tafi, ta yi hak’uri ta bi komai a hankali za su yi nasara bi’izinillahi. Jinjina Kai kawai Kausar d’in take ta yi alamun fahimta,amma a ranta ta riga ta gama tsara ‘za ta bawa su Mommy second chance (dama ta biyu), za ta basu one month dukda tana jin kamar ba za ta iya bari a gaban idanunta Yash ya tare da wata ba amman za ta kwatanta fatanta shine Allah ya sa ta iya d’in. In har wata ɗayan nan ya cika Manubiya ba ta bar gidan Yash ba to za ta bi ta ko wacce hanya ta fitar da ita, ko dai ta fitar da ita da ranta ko kuma a fitar da gawar ta….. Kwanan Abhi shida a Uk ya dawo Nigeria…..jikin Na’ima da sauk’i Alhamdulillah ba ta samu buguwa ko wani serious internal injury ba ta dai karye a k’afa ta kurje a hannu. Kuma shima Alhamdulillah abun ya zo da sauk’i ga kuma kwararrun likitoci a kanta….Ummi ta so zuwa kafin biki ko da kwana d’aya ne ta yi ta juyo, Daddy ma da farko tashi d’aya ya amince yanata murna ya cewa Yash ya biya musu kud’in jirgi ita da Mommy su tafi su je su yi kwana d’aya su dawo, cikin murna Ummi ta ci gaba da shirye-shiryenta amman washegari da safe Daddy yana tashi ya ce babu inda za su je, da ta bishi d’aki domin ta sake rok’onshi ma sai ya rufeta da fad’a dan haka dolenta ta hak’ura ta fito ta kyaleshi, da daddare ta sanarwa mom sun fasa zuwa, wanda mom ɗin da hajiya maman ne ma suka d’an kwantar mata da hankali dan ba kad’an ba ranta ya b’aci. Sosai Manubiya take karb’ar gyara dan mama da anty umma sun dage sosai, inna da Baba har ma da su Manubiyan sun ji dad’i kwarai akan yadda anty umma ta shigo jikinsu itama dan da ita ake yin komai na bikin, ta tsaya tsayin daka! Ko ba komak sunsan an samu nasara sab’anin da da kowa ta kansa kawai yake yi, kuma suna addu’ar Allah Ubangiji ya wayar da kan ragowar suma a samu a had’a kai a yi zumunci, dukda kuwa ba su hango alamar hakan daga garesu ba amman Allah suka ce! dan duk yadda ake ta tururuwar shigowa ganin lefen Manu kaff cikin matan uncle da baba habu babu guda d’aya da ta lek’o, ko su ko y’ay’ansu. Aisha da su Mama so sukayi sai washegari da safe idan aka d’aura aure tukunna su had’a da gadon da aka siya da su flask da kayan lefe su kai gidan amarya, duk a lokaci d’aya. Amma yadda unguwar ta d’auka aketa zancen lefen da tsadar kayan da gwalagwalan ciki ne ya sanya suka yanke shawara…..Aisha ta kira Yahanasu ta zo a take suka kwashe lefen kaff da ragowar kayayyakin da za’a tafi da su suka kai gidan amarya dan ya fi security….gadon ma dan sun samu matsala ne amma da tuni ankai, 3 months ago suka je suka zab’a sai suka barshi a wajen, to shekaran jiya suna zuwa d’auka me wajen ya hau kame kame, wai su yi hak’uri an yi order wasu yau da daddare za su k’araso shiyasa last month da ya samu mai siya ya siyar tunda su sun ce ba yanzu za su ɗauka ba, amma kar su damu exactly irinsu d’aya kuma yau cikin dare kayan za su iso, su yi hak’uri su jira dan Allah…….. ……Aisha tana dawowa daga gidan amarya ta haukacewa su Siyama…labarin gidan take basu tana maimaitawa amman gani take yi kamar ba za su tab’a fahimtar kyan gidan ba har sai sun gani a idanunsu, shiyasa daga k’arshe ta hak’ura ta yi musu iyaka bayanin da za ta iya ta mik’e ta fita ta barsu ta tafi gurin su anty umma waenda suke ta rabon abincin sadaka na walima dan basu yi taro ba iyaka girki aka yi mai uban yawa aka kai asibiti da gidan marayu yanzun kuma ake rabawa almajirai… …Suna zaune su uku a d’aki jidda Siyama da Manubiya lokacin k’arfe biyar daidai na yamma kowa ya gaji da hada hada, Muhsin ya shigo ya cewa Manubiya “wai ta je kaka mallan yana kiranta.” Dariya Siyama ta yi kafin tace”tsohon nan fa neman shiri yake yi, jiya Ina jinsa yana cewa Ya Musbah wai ‘yanayin tsarin bikin ya burgesa ai dama ba a so a yi ta kid’e kid’e a biki, albarkar ake kwashewa.’ Ko wa ya tambayesa oho.” Murmushi Manubiya ta yi hakama Jidda daga haka Manubiyan ta mik’e ta gyara zaman 3D vail d’in da ta rufa akan tsaddaden lace d’in da ke a jikinta tace musu ”bara in je in dawo” Tana fita Jidda ta kalli Siyama ta ce ”har yau kema ba ki ganshi ba?” Jinjina Kai Siyama ta yi kafin ta ce ”kema kin cika damuwa wallahi, da kyar ma idan Muhsin d’in ba tsokanar ki yake yi ba, dan ni Wallahi ko kyallin Ya Yusuf ban gani a cikin gidan nan ba. Baya ga hakan idan ma ya dawo ɗin ai shi ya sani, ke ina ruwanki?” Wata nannauyar ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin ta ce ”ba wasa Muhsin yake yi ba, d’azunnan na ji inna tana gayawa Baba wai ya bita har d’akin ummanku yayi mata murnar warkewarta da Allah ya sanya alkhairi.” Ahankali ta sauk’e numfashi kafin ta ci gaba da cewa “Siyama Ya Yusuf ba alkhairi bane ba, Ina tuna yadda ya tsundumamu a bala’i kwanakin baya, shiyasa kika ga duk na tsure, kuma inajin tsoro kar Baba ya aura masa ni…” Da sauri Siyama ta katse ta ta hanyar cewa ”a’uzubillahi, Jidda dan Allah kar ma ki fad’a wani ya ji, inshaaAllah Ya Yusuf ba shine Mijinki ba, sannan ki kwantar da hankalinki da yardar Allah ba abunda ya Isa ya yi muku”. Shiruu kawai Jidda ta yi, dan ita gaba d’aya kwana biyun nan sai a hankali, tunda Muhsin ya ce mata ya ga Ya Yusuf shikenan gaba d’aya hankalinta ya yi masifar tashi, jiya kuma tsautsayi ya sanya ta ta shigo d’akin lokacin mama tana ciki suna waya da Al’ameen, kuma wayar maman irin me muryar nan ce shiyasa ta jiyo dadd’ad’ar muryarsa rad’au…after abunda Ammi ta yi musu da kuma yadda shi kansa Al’ameen d’in ya yi watsi da ita sam bata yi tunanin za ta ji haka dangane da shi ba! Dan tun a jiyan da ta ji muryarsa suna waya da Mama shikenan komai nata ya tsaya chak! Llissafinta, wayonta fushin da tayi da shi da komai tashi d’aya duk ya tsaya chak, ta ji ita kawai all she needs and want is him!him alone nothing more(abin da take buƙata kuma ta ke so shine ‘shi’, shi kaɗai kawai, ba wani abun ba) Tun jiya take k’okarin ta yi controlling kanta ta b’intike tunanin Al’ameen a ranta amma ta gagara, shiyasa tashi d’aya tausayi da haushin kanta suka lullub’eta, ga kuma fargabar had’uwarta da ya Yusuf…. Tunanin nan da take yi ne ya janyo har ba ta san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba. Da sauri Siyama ta matso ta dafa ta ta ce ”subahanallah, Jidda lafiya kuwa,wai duk akan Yusuf d’in dai??” Girgiza Kai Jidda ta yi, cikin son ragewa kanta damuwa ta ce ”Siyama Ya Al’ameen bai kyauta min ba, ki duba ki ga yadda ya watsar da al’amurana, da ya san ya daina sona ai kamata ya yi ya fito fili ya gaya min ba wai ya share ni ba, ba abunda ya fi b’ata min rai irin yadda ya san ya bani waya kuma na san ya kira ya ji shiru a kwanakin baya, amma bai damu ya nemi sanin mai ya faru ko ya bincikoni ta wata hanyar ba sannan kuma har yau bayan na yi welcome back kusan watanni biyar bai damu ya sake kira ya ji ko na kunna layin ba, bai damu ya san me ya faru ba…bama ya nema na tunda ga layin ai a kunne yanzu amma ko alamun kiransa ban taɓa gani ba…bai damu ya san shin Ina raye ko bana raye ba sam shi ba damuwarsa bane..” Kukan da ya taho mata ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana, shiruu Siyama ta yi tana jiyo tsananin k’auna da son Al’ameen k’arara a cikin zantukan Jidda, dan haka a hankali ta shiga rarrashinta dan ta ma rasa ta Ina za ta fara nuna mata ‘hakan fa ba daidai bane ba!”. Sun jima Siyama tana aikin rarraashi kafin dakyar tukunna aka samu Jidda ta yi shiru. Siyama tanaso Jidda ta d’an huce kafin su yi maganar Al’ameen, shiyasa ba ta sake yin maganar ba,instead sai ce mata ta yi”am…ni kam Jidda ko kin san abunda yake damun Ya Musbah? Naga gaba d’aya ya chanza tun watanni uku ko ma ince hud’u baya, gaba d’aya na lura a fusace yake kuma kamar haushin kowa yake ji,ko dai matarsa yak….” Cikin katseta Jidda ta ce ”tab! Allah ya kiyaye” Dariya Siyama ta yi kafin ta ce ”kar dai ki yi halin dangin Miji, indai har yanzu yana son abarsa a ganina gara kawai ku bashi shawara ya dawo da itan…” “Hmm” kawai Jidda tace, daga nan bata sake cewa komai ba, dan ta san inda ace ita kanta Siyama ta san me Baraka ta yi da ko zancen ta ba za ta sake yi ba…. Manubiya tana zuwa wajen Kaka Mallan ya karb’eta Hannu bibbiyu, abunda bai tab’a yi ba, tunda Manubiya take bata tab’a sanin cewa kaka mallam yana da wannan hankalin kuma ya san me yake yi ba sai yau! Dan nasiha yayi mata mai ma’ana da tsananin ratsa jiki har sai da ya sakata kuka….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 14* Manubiya tana zuwa wajen Kaka Mallan ya karb’eta Hannu bibbiyu, abunda bai tab’a yi ba, tunda Manubiya take bata tab’a sanin cewa kaka mallam yana da wannan hankalin kuma ya san me yake yi ba sau yau Dan nasiha yayi mata mai ma’ana da tsananin ratsa jiki har sai da ya sakata kuka….. kafin ya sallameta yanata saka mata albarka. Kamar yadda ta fita ta bar su Jidda a zaune haka ta shigo ta same su, sallama kawai ta yi suka amsa daga haka ta nemi guri ta zauna, suna ganin idanunta suka fahimci kuka ta yi….sun san idan suka fara bata hak’uri sake b’arkewa za ta yi da wani kukan shiyasa suka ja bakunansu suka yi shiru, amma dukda haka ba su tsira ba dan kamar wadda aka daka hakanan ta fashe musu da kuka tashi d’aya. Wanda hakan ya yi dai-dai da shigowar su Aisha da anty umma da Mama da inna cikin d’akin…. A hankali Aisha ta zauna a kusa da ita, ta kamo Hannayenta tukunna ta ce ”haba mana Manu, kanki fa zai yi ciwo, ki yi hak’uri haka nan mana, ke ki godewa Allah ma a garin za ‘a ajjiyeki waenda ake d’aukar su a kai su wani garin daban su kuma su ce me??” Cikin karb’ar zancen anty umma ta ce ”wasu ma k’asar gaba d’aya ake bari da su, kuma haka suke zuwa su zauna su rayu, ke kam gidanki ko da k’afa idan Mutum ya zage tsaf zai je, ki yi hak’uri ki yi shiru karki ja wa kanki zazzab’i. dama indai sunan ki Mace to wannan rana tana jiranki…… mu kanmu sai hankalinmu ya fi kwanciya idan muka kai ki d’akinki gobe inshaaAllah, fatanmu shine ki yi biyayya ki nuna cewa mun baki tarbiyya mai kyau.” Kamar zuga Manubiya sukeyi haka ta sake fashewa da kuka, shiyasa suka hak’ura suka kyaleta… anty umma suka fita ita da inna dan su ci gaba da shirye-shiryen gobe, Mama kuma Ammi ta kirata tace “ta zo ta taya ta girki tana da bak’on cikin dare, yau.” Suna fita d’akin ya rage daga Manubiya sai Aisha Siyama da Jidda… Sai da Aisha ta lallab’a Manu aka samu ta yi shiru da kyar, tukunnan ta bud’e mata abunda ta shigo mata da shi a flask ta bata ta ce “ta ci.” Har ga Allah kayan nan sun fara Isar Manu dan wani irin ciwon mara take yi amma ta san ba ta Isa ta cewa Aishar A’a ba shiyasa ta hak’ura da kyar ta danna tana ji kamar za ta yi amai, marar ta kamar za ta fashe. Ahankali ahanakali Aisha ta samu ta d’an kwantar mata da hankali tukunna Manubiya ta d’an sake…..ana fara kiraye-kirayen sallar magrib kiran wayar Yash ya shigo wayarta, ta yi mamakin ganin kiransa a dai-dai lokacin sallah amma sai ta d’auka cikin sanyin murya ta gaidashi, Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ”lafiya Alhamdulillah” Kafin ya d’aura da cewa “yau na shiga busy ban samu na dame ki da kira ba,” Murmushi kawai ya ji ta yi a hankali Shiruu ya yi kamar mai nazartar wani abun kafin ya ce “wa ya saka min ke kuka??. Fad’a aka ta yi miki ko?” A hankali ta sake yin murmushi kawai. Numfashi ya sauk’e kafin ya ce ”Aikuwa yanzun za’a sake yi mana wani, dan na san nasiha Baba zai yi mana, ya kirani akan yana buk’atar ganin mu a tare. Ina ma unguwar ya ce bayan magrib zai ganmu.” Maganar sa ce ta katse jin ana shirin shiga sallah, shiyasa ya yi mata sallama ya ce ta zama ready suna idar da sallah Baba zai gansu. Sallah ta fara yi, tukunna su Aisha suka taimaka mata ta chanza kaya zuwa super(exclusive)black colour d’inkin riga da zani, da ash chantily vail mai kyau, kauri da tsada!. D’aurin gaba ta yi irin kalar wanda ake yayi, ta rufa mayafin nata har ka, kana ganinta ka ga amarya dan ta fito rass da ita kamar ka sace ta ka gudu saboda tsabar tsananin kyau da haiba. Tana cikin gyara sakun d’an kunnen ta Ya Musbah ya lek’o ya ce ta zo su je ita ake jira. Sai da ya kaita k’ofar parlourn su Siyama tukunna ya juya…ya so ya shiga ciki shima amma sai ya zab’i ya koma masallaci domin ya samu su rik’e Kaka Mallan a chan, dan tunda ya ga Yash ya zo gaba d’aya hankalinsa ya tashi!!! Dan haka sun san indai ya shigo cikin gidan to sai ya je inda yake, su kuma ba sa so ya je gudun kar ya kwafsa, shiyasa da shi da ya Nafi’u suke ta jan sa da zance tunda yanzu yana kula su yana ji da su….dan su samu su yi buying time ma (su jaa lokaci saboda) su Baba.. A zaune suke akan carpet su biyu suna magana, Yashjub sai wani sussunkuyar da Kai yake yi, amman ta na yin sallama bai san lokacin da ya d’ago ya kafeta da idanuwa ba… Har ta k’araso ta zauna bai daina kallonta ba sai da ta ce ”ina wuni tukunna ya yi snapping out (ya ɗan dawo dai-dai) da kyar ya ce “lafiya” daga haka ya sunkuyar da kan nashi k’asa yana mai jin wani yalwataccen farin ciki yana ratsasa ta koina….. …Nutsatsiyar nasiha Baba ya yi wa Yashjub da Manubiya tare da fatan alkhairi da sanya Albarka, Daga nan ya bawa Yash d’in amanar Manubiya…… Hatta Yash jikinsa sai da ya yi wani irin sanyi, Manubiya kam tun lokacin da Baba ya fara magana ta fara kuka. Sosai kukan nata da nasihar Baba suka taru suka kashewa Yash jiki, shiyasa ya gagara d’agowa yana jin kamar shima ya fashe da kukan. Sai da aka kiran sallar isha tukunna Baba ya sallameta shi kuma suka wuce masallaci shi da Yash. Tana shiga d’akin nasu Aisha ta dafe Kai ta ce “shikenan an dawo mana da aiki sabo” Murmushi su Inna da Siyama suka yi, daga haka suka ci gaba da had’a jakar takeaway d’in da za a raba gobe inshaaAllah a wajen d’aurin aure. Kamar d’azu, yanzun ma Aisha ce ta yi ta aikin rarrashi, musamman ma da ta tab’a jikin Manu d’in ta ji zafi rad’au, nan take hankalinta ya sake tashi…… Da kyar kuwa Manubiya ta samu ta yi sallah, dan tashi d’aya zazzab’i da ciwon Kai suka yi mata rufdugu, shiyasa Aisha ta ja ta zuwa d’akin su Ya Musbah, ta bata magani ta sha tukunna ta ce “ta kwanta anan”dan d’akin nasu ya cika da makwaftan da suka lek’o taya su aiki. Ba ta dad’e da kwanciya ba, bacci ya yi awon gaba da ita dan har da maganin bacci Aisha ta had’a mata da shi, ai kuwa kasancewarta a gajiye kwana biyu ya sanya nan da nan baccin ya d’auke ta. Ko da Yash ya kira Aisha ce ta d’auka, yana ji Aishar tace ta yi bacci ya ce “Alhamdulillah” dama aikin rarrashi ya so ya yi kafin ya wuce amma tunda har an lallab’ata ta yi bacci shikenan, dan haka ya yi wa Aishar sallama da godiya, daga haka ya kashe wayar ya wuce bayan yayi sallama da su Baba da Kaka Mallan……… *Washegari* A d’akin Ya Musbah Aisha Manubiya da khairat suka kwana, dan tunda Manu ta kwanta sai kiran sallar asubah ne ya farkar da ita, Aisha bata so ta tasheta shiyasa ta cewa su Ya Nafi’u su tafi da shi da su Muhsin da Ya Musbah kawai dan yau d’akin nasu is occupied. Tana farkawa ta hango Aisha a kan darduma tana nafila, dan haka itama ta mik’e ta fad’a toilet…ta kama ruwa ta yo alwallah bayan ta d’auraye Bakinta da iyaka makilin d’in da yake available a cikin banɗakin tukunna ta fito tana jin yadda Jikinta yake yi mata ciwo, dan ba ta saba kwana da manyan kaya ba. Har ta fito Aisha ba ta Ida ba… darduma itama ta nema ta shimfid’a a gefen Aishar, sannan ta tada ik’ama domin gabatar da nafila….ta na idarwa aka kira assalatu dan haka ta mik’e ta gabatar da sallar asubah…. Sai da suka kammala Azkar tukunna suka gaisa ita da Aisha, ta bata wayarta..miscalls d’in Yash ta gani na jiya kafin Aisha ta d’auka sai wanda ya kirata around sha biyu na dare da kuma yanzu da asubah. Sai da ta fara cire wayar a silent tukunna ta kira sa…ringing uku ta yi ta kashe dan ta san ko ta bari ya kai k’arshe ba d’auka zai yi ba. Ko gama haske wayar ba ta yi ba ya biyo kiran, sai da ta d’an d’auki lokaci dai-dai wayar tana shirin tsinkewa tukunna ta amsa. Murmushi ya yi kafin ya ce ”sai an ja min aji tukunna za’a d’auka? Kar ki damu gobe by this time (iwar haka) na san babu maganar jan aji ko kunya a tsakanin mu dan tuni zan yi fata-fata da su.” Da sauri cikin san kawar da zancen tace”Ina kwana” Ta fad’i hakan a ranta tana mamakin Yash! Wanda a da kamar ba ya magana amma ta lura tun lokacin da aurensu ya matso ya zama mai surutu, kuma ko wacce iriyar magana in ta zo Bakinsa juye mata ita yake yi, gaba d’aya ya daina jin kunyar ta.” Ta na cikin wannan tunanin ta ji ya ce ”lafiya Alhamdulillah, matar Yash in the next (nan da) 5 hours!7 minutes!37seconds inshaaAllah.” A take ta ji gabanta ya yanke ya fad’i, tana son Yash amman ta rasa dalilin wannan fargaba da tsoron da suka lullub’eta tun shekran jiya suka k’i barinta, tun shekaran jiya hankalinta yake a tashe…. A hankali ta ji ya ce “Baby! Kin yi shiruu, ko ba a yau zan cire kunyar b…” Cikin katseshi ta ce”na’aam!” Kamar irim ta amsa kiran da ake mata a gefe ɗinnan, Sai kuma tace”inna tana kirana, bari in je?” Dariya sosai ya yi dan ya fahimci zillewa take son yi, tukunna ya kylaleta kawai ba dan wayonta ba….cikin sanyin murya ya ce ”ki gaida ita….” Ahankali tace “sai anjima” Yana wani irin blushing yace”Allah ya kaimu” Daga haka Manubiya ta yi saurin kashe wayar ta d’aura a kan k’irjinta tana haki akai akai, dariyar da Aisha ta kwashe da ita ne ya dawo da hankalinta cikin d’akin, sam ita ta ma manta da Aisha a d’akin wallahi…. Sosai Aisha take dariya kafin ta mik’e tsaye ta je ta ta tofawa y’arta wadda take ta bacci add’ua tukunna ta juyo ta kalli Manubiya cike da zolaya ta ce ”Yarinya ba ki ga komai, kuma ba ki ji komai ba.” Tana gama fad’in haka ta sa Kai ta fice abinta… Da sauri Manubiya ta cusa kanta a cikin cinyoyinta tana mai jin kunya!fargaba! da wani irin yanayin da ba ta tab’a tsintar kanta a ciki ba. Har Yash ya kashe wayar ya ajjiye a gefe bai daina blushing ba, ya jima a zaune yanata tunane-tunane da zumud’i kafin ya mik’e ya fad’a bathroom. A side d’in Yashjub daga shi sai Abokansa biyu da suka zo jiya..…Gidan kamar ba biki ake yi ba!bakowa, dan side d’in su Mommy ma ba kowa hatta y’ay’an uncle d’inta ma ba su zo ba sakamokon fad’an da suka yi da ita kacha kacha recently(ba da jimawa ba). Yayar Munirat ma ta so zuwa amman sai ta had’u da laulayi mai tsanani shiyasa ta hak’ura akan bayan bikin in ta samu sai ta zo ta ga amarya ta yi Allah ya sanya alkhairi. K’arfe 7:25am Yashjub ya fito daga wanka, k’arfe 8:00dai-dai ya shirya tsaf ya kafa hula ya d’auki makullin mota da wayoyinsa ya zuba a aljihu rik’e da babbar rigarsa ya nufi k’asa sai tashin k’amshi yake yi. A zaune ya tarar da Abokansa suna breakfast akan dining table ko wanka ma ba su yi ba, tsadadden agogon da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa ya kalla kafin ya ce ”ku yi sauri fa kar ku sa mu makara.” Dariya d’ayan yayi kafin yace “ango ka sha k’amshi” “Bai sha ba tukun!. Wai Yash da gaske yanzu kake so mu tafi? 8:00fa yanzun, ba sai 11:00 ne d’aurin auren naka ba?”cewar d’ayan Cikin takunsa ya k’araso ya zo ya chake musu ya ce ”na san 11:00 ne mana, amman ai ya kamata mu tafi da wuri, pls ku taso in ba haka ba Wallahi zan yi gaba in barku” Dariya suka yi daga nan suka fara tsokanarshi da’mai zumud’i’suna yi suna ƙoƙarin fahimtar da shi akan ya d’an jira amma inaa! Sam Yash ya k’i hak’ura, hakanan suna ji suna gani ya azalzalesu suka yi wanka suka shirya 8:30am suka fice daga sid’e d’insa, suka je suka gaida Daddy ya yi masa addu’a ya sa masa albarka haka itama Mommy da Ummi…daga haka suka fice daga gidan shi kam ko breakfast d’in ma bai yi ba. Tun k’arfe 8:00am unguwar su Manubiya ta san yau akwai gagarumin d’aurin aure sakamokon motocin polisawa da sojoji da suka fara yi musu sallama, kafin 10:00am kuwa taff layin ya cika da jama’a, duk saurin Yash sai 10:00 am d’in tukunna shima ya samu ya k’arasa unguwar dan suna fita suka had’u da Najeeb da electrician d’in da zai yi wani wiring a gidan dan haka suka d’unguma gaba d’ayansu, da farko Yash so ya yi yace musu ‘su su je su tsaya a kan electrician d’in!shi kuma ya wuce’, sai kuma ya ga idan ya yi haka kamar yayi rashin kara ne ga kuma su Najeeb d’in da suke ta cewa “wallahi idan ya je tun yanzu dariya za’a yi masa,” shiyasa kawai ya hak’ura ya bi su ba dan ya so ba. 10:30am dai-dai Daddy da Abhi suka k’araso tare da tawagar manyan mutane (Abokanansu,) ba iyaka layin ba hatta titin sai da ya cika da manya manyan motoci na alfarma……. 11:00am dai-dai dubban mutane suka shaida d’aurin auren Yashjub Iman kura Da Amaryarsa Manubiya Musa, akan sadaki naira dubu d’ari uku, lakadan ba ajalan ba. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 15* Mai kwalliyar da Aisha ta d’auko tana kammala pinning mayafin Manubiya a jikin d’ankwalinta, suka ji loudspeaker tana ƙarar sanar da d’aurin auren Yashjub Imam Kura da Manubiya Musa wanda aka gama d’aurawa yanzun akan sadaki dubu d’ari uku, lakadan ba ajalan ba…sai kuma hayaniyar Maza ta fara tashi….. Kukan da ya zame mata sana’a, shi ta saki kafin ta zube anan kan katifar, yayinda su Aisha kuma suka shiga jero hamdala, Matan da suke shigowa cikin gidan yanzun kuma suka shiga rangad’a gud’a…..nan da nan a cikin mintunan da ba su kai ashirin ba d’akin nasu har ma da gidan gaba d’ayansa ya cika taff da jama’a, ba masaka tsinke!… Masu hoto da amarya na yi, masu Allah sanya alkhairi da hayaniya suna yi,…..itakam Manubiya gaba d’aya fuskarta ta kumbura, kwalliyar ma har ta fara d’an gogewa. Suna cikin haka gwaggo Suwaiba ta kira waya, da Inna suka fara gaisawa ta yi mata Allah ya sanya alkhairi sannan ta sake bata hak’urin rashin zuwanta (dan k’iri k’iri jatau ya hanata zuwa) tukunna ta nemi magana ta Manu…..fad’a da nasiha ta yi mata, sannan ta sanya mata albarka daga haka suka yi sallama. Duk yadda Manu ta so daurewa sam sai ta kasa, dan haka ta sake sakin hawayen da take ta rik’ewa tun ɗazun, tana yi tana sheshshek’a da jan hanci…..su kansu su Aisha zuwa wannan lokacin jikinsu ya fara yin sanyi, dan sai yanzu suka sake tabbatarwa da cewa “Manubiya tafiya za ta yi ta barsu” ga kuma fargaba da sanyin jikin da kan lullub’e kowa kama daga kan Amarya zuwa kam y’an uwanta tashi d’aya a lokaci irin wannan ɗin duk suma sai ya bi ya lullub’esu gaba d’ayansu. Jidda ce ta fara sakin kuka, ganin haka yasa itama Siyama ta saki nata kukan da take ta k’ok’arin dannewa…. murmushi kawai inna da mama suka yi, suka ci gaba da harhad’a abubuwan da sukeyi, ba tare da sun yi yunk’urin rarrashinsu ba, dan sun san muddin suka doshi inda suke tau tabbas suma kukan za su yi. Musamman ma Mama wadda hankalinta yake a matuk’ar tashe! sannan kanta ya d’aure katamau tun lokacin da ta ji an ambaci ‘imam kura’ da kuma sunan angon, ta san wataƙila tsananin coincidence ne, amman dukda haka sai da ta shiga cikin tsananin fargaba. Dakyar Aisha ta daure ta k’arasa inda Manubiyan take da niyyar rarrashinta amman tana zuwa itama kawai sai ta fara hawaye. Dai-dai nan anty umma ta shigo tana cewa ”Siyama ku zo ku tayani fara zuba abinci kuna mimmik’awa jama’a, ga mutane chan suna ta shigowa har a b’angaren su Uncle, sannan ku kira su Musbahu a samu a fitar da takeaway d’innan kafin jama’a su watse…...” Salati ta saka ganin yadda suke shirin mayar da d’akin kamar na zaman makoki, k’arasa shigowa cikin d’akin ta yi ta ajjiye k’atuwar kular hannunta tukunna ta k’arasa inda suke suka shiga rarrashin Manu ita da ragowar Matan da ke a cikin d’akin. Da kyar aka samu suka yi shiru kuwa, tukunna ahankali cikin mutuwar jiki Aishar ta ce “Bari in je mu fara mik’a abincin” Mik’ewa su Jidda suka yi suma, suka bi bayan Aisha…… Duk wannan girkin da hayaniyar d’aurin auren da ake ta yi babu wanda ya lek’a ya taya su inna girki sai anty umma sannan kaff gidan ya Yusuf ne kawai ya lek’a wajen d’aurin auren sai kaka mallan wanda ya daddannawa Baba Habu zagi da ya so ya hanashi zuwa….sune ba sa kula Baba kuma fa ya bisu ya basu hak’uri ya fi sau nawa, shekaran jiya ya bi su ya basu invitation amman sunce”wai sau d’aya ya gaiyyace su kuma bai sako su a cikin al’amarin sosai ba, sannan lokacin da aka kawo kud’i a gaban sa Nafi’u ya so yiwa Baba Habu rashin kunya amman bai ce komai ba sai daga baya ya biyosa zai basa hak’uri tsabar ya raina musu wayo.” Shiyasa yanzun ma ba su je ba kuma ba su turo matayensu hidimar mata ba,kaka mallan ma sun so su hanasa zuwa amman ya k’i hanuwa dan shi tun sassafe ma ya shirya ya sanya farar shaddarsa ta sallah ya nufi masallacin bayan ya yiwa baba habu kaca-kaca…da shi kuwa aka dinga tarar bak’i…..babu wanda ya lura da su ba wanda ya san da su ma a wajen amman haka suka dinga faman shishshigi a gurin, da shi da Yusuf! Shi Yusuf connection yake nema, Kaka mallan kuwa maula tuk’uru ya dinga yi a wajen..dan ko marok’in wajen bai kai ya shi a iya maula da tara abun duniya a wannan rana ba. Ba wanda ya fi tsanar sa a kaff wajen kamar Yassir, dan ji yake yi kamar ya d’auke shi ya je ya jefa a rami kowa ya huta, ya tsani tsohon nan haka kurum bai mishi ba tun farkon had’uwar su. Ya tsani layin…gaba d’aya kunyar Abokansa guda biyu da suka zo d’aurin auren tare yake yi, shiyasa fa dama shi bai gaiyyaci kowa ba! waennan d’inma dan Yashjub d’in ya sansu ne shiyasa ya gaiyyacesu da kansa su kuma suka zo,tunda suka shigo layin suke ta jero masa tambayoyi “me ya kawo Yashjub nan? a nan kuma matar tashi take? waye waye…..” Tou kuma yanzu ga kakanta wanda idanunsa suka rufe har Yashjub d’in ya je ya cewa “ya bashi kud’in da za a rabawa almajirai anjima, ayi musu sauk’a”…… Anan cikin gida kuwa…. Su anty amarya suna nan a d’aki har yanzu ba wanda ya lek’o ko murna ko taya aiki, sun so su d’an lek’a su yi murna amma sai mazajensu suka sake hanasu,hatta su Salaha rufe su a d’aki maman su ta yi hakanan Yaran suka hak’ura ba dan sun so ba….sai dai kuma ko mintuna talatin ba ta yi da rufe k’ofar ba aka zo aka fara bubbuga mata tana bud’ewa ta ga mak’oftan da take shiri da su ne suka shigo wunin biki hakanan suka shige suka zazzauna mata, kafin minti d’aya parlourn nata ya cika har ma da na su Baba Habu suma duk sai da aka shiga, ba yadda suka iya dan duk wanda ya fi shiri da su a neighbors idan ya zo wajen su ya ke zuwa ya zauna bayan ya je ya ga amarya…. Su Siyama ma haka suka dinga kai abincin suna ajjiyewa da fara’a a fuskokinsu kamar ba su san me ma suka yi ba, shiyasa gaba d’aya kunya ta kama su dan gashi dai ko Allah sanya alkhairi ba su je sunyi ba amman wunin biki ya kankama a parlukansu. ….. Anan waje kuwa, sun sha hotuna abunsu…haka aka yi komai aka kammala da ikon Allah cikin kwanciyar hankali da tsananin farin ciki. Sai da su Daddy suka wuce, Abokan Yash suma duk suka wuwwuce dan bai cewa kowa zai shiga ya ga amarya ba saboda tsabar kishi, tukunna shi da Najeeb suka k’arasa wajen Ya Musbah wanda suke tsaye da shi da Ya Nafi’u suka mik’a musu Hannu aka yi musabaha suka yi wa juna Allah ya sanya alkhairi kafin Najeeb yace”Am, muna so za mu ga Amaryar, za a d’an yi hoto, sannan za mu gaida su Inna” Ahankali Ya Musbah wanda gaba d’aya yake jinsa upsidedown (a wani irin juye) ya jinjina musu Kai, kafin ya ce ”Bara in sanar da su Innar” Daga haka ya wuce ciki…. Su Siyama suna gamawa, suka yi sauri suka shiga wanka, dan Aisha su take jira..za su je su kwashi kaya su kai gidan Amarya. Suna fitowa suka ha shiri da hanzari… Ba komai a fuskokinsu sai Vaseline, sannam ankon su da suka yi na atamfa shi suka saka dan har Aisha Itama shi ta saka da Mama, A shape aka yi wa Siyama, Jidda kuma riga da skirt… Kalar Atamfar, kalar light blue ne da fari, shiyasa ta karb’i jikinsu ta sake fito da ainihin kyawun hasken fatar su…Tsayin su kusan d’aya ne, sai dai Jidda ta d’an fi Siyama jiki kad’an. Farin mayafi Siyama ta rufa ta yi d’aurin ta mai kyau, Yayinda Jidda ta rufa blue vail itanma sosai d’aurin ta ya yi kyau. Suna fitowa daga side d’in su Siyaman, suka had’u da Ya Musbah…sak’on Yashjub ya gaya musu saboda d’akin su Innar ya cika taff shiyasa bai samu ya iya shiga ba. Yana gama gaya musu sak’on ya juya ya koma d’akinshi ko waje wajen Nafi’un ma bai koma ba, dan kansa wani kalar azababban ciwo yake yi masa..ba dan bai gama yarda da tsubb’ace-taubb’ace ba to da babu abunda zai sa ya k’i yarda da cewa ‘Baraka tsafi ta yi masa!’ Idan fa ya rufe ido har ganinta yakeyi, sannan ji yake kamar ya je ya d’auko ta kawai ya dawo da ita, bai tab’a missing (kewar) Mutum kalar yadda yake missing (kewar) Baraka ba!!! Sannan a iyaka kwana biyu kawai, ya ji soyayyarta da k’aunarta sun dawo mishi sun zauna daram sun mamaye koina, sab’anin kwanankin baya da ya tsani ya ji ko da sunanta ne. Dama tun sati biyu bayan da ya sake ta ya fara jin hakan, amman abun bai yi tsanani kamar yanzu ba. A shagub’e ya ɗan gwada tuntuɓar Nafi’u ba wai kai tsaye ba, wanda amsar da Nafi’un ya basa ya sanya ya fahimci tabbas indai har ya dawo da Baraka gidansa to Abotarsu shi da Nafiu za ta iya tarwatsewa, shi kuwa a yadda yake jin Nafi’u yanzu ya ma fi k’arfin Aboki a wajen sa sai dai d’an uwa shiyasa sam ba ya son abunda zai shiga tsakanin su…..To! Nafi’u ma ya nuna baya so ina kuma ga Inna wadda aka yi wa abun! Shiyasa gaba d’aya yake a burkice, bai ma san ta ina zai fara kallon family d’inshi ya ce musu ‘zai dawo da Baraka’ ba! Shi kuma tabbas a yanda yake jin Baraka a halin yanzu in dai har bai dawo da ita ba tou akwai matsala……. …. Jidda ce ta wuce d’akin dan sanar da su Inna yayinda Siyama ta nufi parlournsu, ta shiga tattarewa bayan ta cewa bak’in ciki “dan Allah angwaye za su shigo”, su kuma sun fita. Tana cikin tattarewa Jidda ta kirata ta ce “su inna da anty umma sun ce a bari su Yashjub d’in su gaida su a d’akin kawai…… saboda akwai Matar Mai Unguwa kuma gurguwa ce, so idan akace sai ta sake jan kujerarta zuwa parlourn su Siyaman wani sabon aiki ne…. Amma dukda haka gata nan zuwa ita da Adda Manu, su Innar sun ce ta je parlourn su zauna su yi hotunan a ciki” Mata wajen biyar ne a d’akin, ga kuma matan uncle da su anty umma suka cewa su Jidda su je su kira, tafe! shiyasa anty umma da mama suka nemi waje a bayan gidan suka zauna, wanda dama abunda maman take so kenan shiyasa ta san yadda ta yi ta ja anty Umma, dan har ga Allah bata so ta had’u da Angon!!! saboda bata san wanne hali za ta shiga ba idan zarginta ya tabbata, ko kuma akasin hakan…tsabar yadda ta rud’e..ita ba ma ta san me zata ce tana so ba a halin yanzu…ya tabbata ko kuma kar ya tabbata. Sai da aka d’an tartare d’akin aka saka turaren wuta tukunna aka cewa su Jidda su je su shigo dasu…. matan su Uncle ɗin da aka tsammata, ko da aka gaya musu ma basu tashi zuwan ba, dan yaddda suke ganin ran mazajen nasu a mugun b’ace, kuma sun san akan auren ne aka b’ata musu rai yasanya bama su gwada tambayar su zuwa su gaisa da Angwayen ba gudun b’acin rai…… Yashjub yana tsaye suna waya da Yassira, ya hango Yassir yana sallama da Abokansa, suna wucewa ya ga shima ya bud’e mota yana shirin shiga ya wuce, dan haka ya yi saurin cewa Yasira “ina zuwa” daga haka ya kashe wayar ya d’an d’aga murya ya kira sunan Yassir. Sai da ya yi tsaki, tukunna ya rufe motar ya juya ya na kallonshi… yaffito shi Yashjub d’in ya yi da Hannu, daga haka ya d’auke Kai ya ci gaba da magana da Najeeb. Kamar zai kama da wuta! Haka Yassir yakeji tsabar takaici..sai da ya taushi zuciyarsa da kyar tukunna ya fara k’ok’arin takawa zuwa inda Yashjub d’in yake, dan dama a kumbure ya ke saboda sai da suka yi shi da Daddy da Abhi suma kafin su wuce! Akan yadda yake ta faman ciccin magani yake kuma k’in shiga a yi abu dashi, sune har da zaginshi Abhi yana ce mishi mai bak’in hali, tukunna suka wuce. shiyasa tun d’azun yake a wuya, yanzu kuma ga Yash shima yana shirin k’arasa kaishi bango…sam sun kasa la’akari da yadda ya danne kanshi ya shigo cikin wannan mugun layin dukdan saboda su amma still babu godiya babu jinjinawa kalli abubuwan da akeyi ta masa…..da kyar dai ya dan danne kansa dan wani mugun takaici yake ji, tukunna cikin takunshi fuskar nan tamau ya fara takawa izuwa inda suke, a ranshi yana aiyyana “tabbas ya san sai ya sha maganin allergy dan he’s allergic to (yana da rashin jituwa da) warin kwata, kuma kwatocin layin kusan duk a bud’e suke, gaba d’aya koina wari yake yi…dole ne ma ya je ya ga Likita” Yana cikin tunanin asibitin da ya kamata ya je ɗin ne ya k’arasa inda suke tsaye, ya tsaya kawai ba tare da ya ce komai ba. Kallonsa Yashjub d’in yayi kafin da mamaki ya ce “ya na ga kana shirin tafiya? Ba za ka shigo mu gaishe da su ba?. Ka tsaya idan muka gaida su muma duk wucewa za mu yi, sai mu tafi tare.” Yassir ji ya yi kamar ya d’aura Hannu aka ya kurma uban ihu tsabar takaici….yanzu dan rainin hankali wannan mugun gidan yake so ya shigar da shi cikinsa saboda tsabar son wulakanci?! iyaka layin da ya shigo da su bai ishe sa ba shine sai ya danna shi a cikin gidan nan kenan! A ranshi yace “Tabbas na ga alama sai na yi wa Mutumin nan da gaske tukunna zai d’aga min ƙafa” A fili kuma cikin tsananin tsageranci da wulak’anci ya kalli idon Yash d’in tukunna ya ce”ka san dai Allah d’aya ne ko?! To wallahi Allah idan na shiga gidan nan sai an yi deworming d’ina!(sai an bani maganin tsutsotsi da ƙananun kwari)…. Yanzu haka I’ve fallen sick(har na fara rashin lafiya). Na san ka san Ina reacting to ƙazanta da ababen ƙyama amma dukda hakan sai faman k’ok’arin forcing d’ina kake yi, haba mana!…” Sakar Baki kawai sir Najeeb yayi yana kallonshi shi Yashjub kuwa ya zo iya wuya jira kawai yake Yassir ɗin ya kai aya shi kuma ya fara cin ubanshi, tunda ya lura bashi da hankali… Manubiya da family d’in nata ne ƙazantar ko me? tabbas yau kam Yassir ya kuma kaishi bango zai kuma sha mamaki….. Yassir ya lura da yadda Yashjub yake kallonsa amma sam bai damu ba! A ransa ya aiyyyana “to ai gwara ma ya kaishi bangon, ya k’ular da shi ta yadda zai yi shirme a k’ofar gidan surukan nasa! Oho! Shi kam dad’i ma zai ji” Ya aiyyana hakan a ransa, sai kuma cikin son sake fusata shi a fili Yassir d’in ya ci gaba da cewa “Har ga Allah ka fara kaini bango kark……” Maganar tasa ce ta mak’ale sakamokon hango Siyama da ya yi tsaye a bakin k’auren gidan, tana magana da alamar akwai wani a ciki wanda take magana da, ‘Anya ba gamo na yi ba kuwa?’ Ya yi wa kansa tambayar a cikin ransa, yana mai jin wani sanyi yana ratsashi, bai gama dawowa dai-dai ba Jidda ta fito, tana hararar Siyaman wadda ta tare hanya ta hanata fitowa har sai da ta sauk’e mayafinta daga Kai tukunna ta bata hanya ta fito daga gidan, ahankali Yassir ya motsa Bakinshi ya ce “woow” ba tare da sautin woow d’in ya fito ba. Girgiza Kai sir Najeeb ya yi kawai, ya juya, dan ya san tabbas Maata Yassir ya gani…. Wani tashin hankalin takaici ne ya lullube sir Najeeb ɗin a sanda ya juya sakamokon had’a ido da sukayi da Siyama dan yana juyowa kamar ance ta d’ago, suka had’a ido… Wato ita Yassir yake k’arewa kallo shine ya k’ame haka…. Dakyar ita kanta ta sunkuyar da kanta k’asa ta ci gaba da takawa inda suke tana jin yadda k’irjinta yake bugawa ahankali ahankali….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 16* Sai yanzu Jidda ta hangesu, dan haka itama ta bi Siyaman suka jera suka nufesu. Duk yadda Sir Najeeb ya so sam sai ya gagara d’auke Idanunsa daga kan Siyama….ya so yin hakan amman sam sai ya kasa…babu kwalliya a fuskarta dan ko kwalli ba su samu sun saka ba sakamakon saurin da suke ta yi, amman ba k’aramin kyau ta yi masa ba, shiyasa ya shagala da kallonta yana mai zuba wani Irin murmushin da shi kanshi bai san yana yi ba. Hatta Yashjub wanda juyowar sa kenan sai da ya lura ya kuma fahimci kalar kallon da Najeeb d’in ya ke yi wa Siyama, shiyasa kawai ya tsaya yana kallon shi da d’an mamaki kwance a kan fuskarshi. Jidda ce ta samu ta ce mishi “ina wuni” Dan gaba d’aya Siyama ta d’an rikice sakamokon yadda take jin idanuwanshi suna yawo a Jikinta…. Da kyar ya d’an kalli Jidda yace mata “Alhamdulillah”sannan ya juya ya amsa gaisuwar Siyama wadda ta Isa har cikin zuciya, ruhi da kwakwalwarsa. Ahankali sukace “Ya Yash ina wuni” Wanda shi Kuma sai da ya d’an yi murmushi tukunna ya ce “Alhamdulillah” Daga haka suka yi masa Allah ya sanya alkhairi, ya amsa cike da fara’a kafin ya sake duban Najeeb wanda still yake ta satar kallon Siyama yana murmushi. Dakyar jidda ta iya cewa Yassir “Ina wuni” Siyama kuwa ko kallonsa ba ta yi ba dan kwata-kwata gayen bai mata ba. Cike da fara’a Yassir d’in ya amsa kafin ya d’aura da ”ya taro?” Girgiza Kai kawai Yashjub ya yi, kafin ya kalli Siyama wadda take cewa ”Ya Musbah yace mu shiga da ku wajen su inna, Manu ma ku take jira” Sai a sannan Yashjub ya yi murmushi ya ce ”Lead the way” Ya fad’i hakan yana nuna mata hanya. Juyawa ta yi hakama Jidda daga haka suka yi gaba su kuma suka mara musu baya. Najeeb ji yake kamar ya janyota ya sakata a bayansu shi kuma ya shige gaban Yassir, Ya san yadda shi kansa ta d’au hankalinsa bashi da tantama Yassir ma k’are mata kallo yake ta yi, shiyasa kwata-kwata ya ƙi yarda ya kalli Yassir d’in dan ya san idan har ya ga yana kalle masa ita to tsaf zai iya bige masa ido… ba wai iyaka Yassir kad’ai ba hatta Yashjub wanda shi danna wayarsa ma yake yi sai da Najeeb ya ji kishin shi, yana mai jin takaicin dalilinta na rufa mayafi bayan ta san yau maza za su taru!…’ Yassir kuwa gaba d’aya lissafinshi ya kunce…yana ganin Munirat mai shape da kyau to ga iyayenta a shape da kyau da komai ma Yara kamar aljanu!!. Tabbas yanzu ya fahimci dalilin Yashjub na zuwa nan ɗin ya mak’ale…. A bakin k’ofar gidan me hoton da yaransu suka zauna dama, dan haka suna zuwa suka kutsa suka shige a tare gaba d’ayansu. Har d’akin su Manubiya suka shiga,dukda d’akin yana da girma sosai amma da kyar su kansu angwayen suka samu wajen zama, masu video coverage da hotuna kuwa a waje suka tsaya suka yi y’ar dabara suka d’auki abunda ya sauwwak’a.….Yadda al’ada ta tanadar haka suka gaida iyaye Matan, su kuma suka sanya musu albarka, daga nan sukayi musu y’ar guntuwar nasiha suka basu amana…. Dubu d’ari huɗu su Yash suka ajjiyewa ko wacce uwa, daganan suka mik’e suka yi musu sallama suka fita, suka barsu cikin shock. inna ta ji ba dad’i da ta ga su mama ba su samu shigowaba har aka gama…ba wai dan kud’in ba sai dan ita a ganinta a hidimar bikin nan ai mama da anty umma sune iyaye..matan d’akin kuwa suma sun yi kara dan sun lura da yadda su maman suke ta hada hada shiyasa aka had’a kud’in guri guda aka raba daidai har da su. Sai da suka fito tukunna Yashjub ya lura da Yassir, dama kamar ya ji muryarsa a bayansa yanata ‘Ameen Ameen’, “Hmm” kawai yace daga haka suka mik’a, su Siyama suka kaisu har parlournsu inda Manubiya take. Parlourn tas da shi sai tashin k’amshi yakeyi, ba kowa daga Manubiyan sai Aisha wadda ta gama gyarawa Manubiya kwalliyarta, dan duk ta chab’e saboda kuka…. Jidda ce ta gabatar musu da Aisha a matsayin sister d’insu itama. Da kulawa suka gaisa da ita, ta yi musu Allah ya sanya alkhairi suka amsa da fara’a… Ba a daɗe ba, da wani brother d’inta zai wuce ta basa ƴarta(Khairat), tace masa ya kaita wajen mamanta anjima idan za su taho sai su zo da ita, kuma dama Aishar bata yi kama da Matar aure ba dan duk wanda kalleta ma ba zai yi tunanin ta ma yi auren fari ba, shiyasa har ita(Aishar) bata tsira daga kallo da mugayen tunanin Yassir ba… Kan Manubiya a lullub’e yake, yana cikin mayafinta har zuwa wannan lokacin amma yana iya ganin yanayinta kad’an-kad’an…shiyasa gaba d’aya Yassir ya sake gigicewa,hatta k’afafuwansa karkarwa suka fara yi…. ya san ba zai yiu ya had’e su su duka hud’un ba amman wallahi shi dukkansu yake so… Dan haka ya shiga lissafi…. ……dukda bai ga fuskar Manubiya sosai ba amman itama ta yi mishi. Ya san ba shi da damuwa a case d’inta, he’ll find his way (zai nemawa kansa mafita) ko ta halin k’ak’a ne, tunda Matar yayansa ce dan haka kamar ma a gidansu take ai. Aisha kuma bata kai su Jidda kyau ba, dan haka zai yi hak’uri ya cire ta a lissafi ba dan yana so ba… A yanzun matsalarsa itace ta yadda zai samu both Jidda da Siyama dan har ga Allah bai ga ta yarwa a cikinsu ba…… Dariyar Najeeb ce ta katse masa tunani….cikin sigar tsokana Najeeb d’in ya cewa Yash “ya dai? Ko kawai mu ce a bamu Amaryar mu tafi da ita tun yanzu mu da kanmu?” Sai a sannan hankalin Yashjub ya ɗan dawo Jikinsa, a hankali ya yi murmushi yana mai jin wani farin ciki mara misaltuwa yana sake lulub’esa, tukunna cikin nutsuwa ya taka ya k’arasa inda take zaune, ya yi bismillah sannan ya zauna a daff da ita kamar zai shige cikin jikinta! A tare daga shi har itan suka sauk’e b’oyayyiyar ajiyar zuciya, kafin ya sunkuyar da kanshi yana wani irin murmushi….. Su Jidda har ma da masu hoto, suna nan tsaye suna jira ya bud’e mata fuska a yiyyi hotuna amman sai suka ga ya d’ago ya kallesu ya ce ”Bismillah, ku zo a yi hoton. Jidda bismillah” Ya ƙarasa faɗin hakan yana mai nuna mata gefen Manubiya alamun ta zo ta zauna. Mai hoton ne ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce ”Am… ranka ya dad’e, ai sai ka yaye mayafin nata tukunna za’a fara ɗaɗɗauka…haka na ga ana yi a duk lokacin da na je d’aukar hoto” “Haka ka yi wa taka kenan??” Yashjub ya yi masa tambayar ba tare da ya kalle shi ba dan zuwa wannan lokacin hanakalinsa ya tafi zuwa ga y’an yatsun Hannunta waenda take wasa da vail d’inta da su…. tun ranar da ya rik’e mata Hannu a office d’insa yake muradin ranar da zai sake samu ya rik’e, shiyasa without thinking twice (ba tare da ɗaukar lokaci ba) ya ruk’o Hannun nata cikin nasa duka biyu. A tare duk su biyun suka sauk’e ajiyar zuciya wanda duk sai da sukaji, sai kuma ta yi sauri ta sunkuyar da kanta k’asa….jin shiru ba a fara d’aukar hotunan bane yasanya Yash ya d’ago da kyar, ya zubawa me hoton lumsassun idanuwansa. Najeeb mai hoton ya kalla wanda ya ce masa “ka d’auke su a hakan mana” tukunna ya matsa ya fara saita camera….. wajen kalar biyar zuwa shida aka yi musu, me hoton yanata mamaki dan shi kam yau ya ga amarya mai lullub’i. Sai da aka gama yi musu su biyu, tukunna su Jidda ma suka shiga, Yassir kuwa har da zama kusa da ita, aka yi musu su uku…wanda zaman da yayi a kusa da itan saida ya sanya Yashjub ya ji kamar ana zare masa numfashi. Najeeb kam ya san halin kayansa shiyasa ya tsaya a tsaye a gefenshi akayi musu. Zuwa yanzu hatta masu hoton sun lura da yadda Najeeb yake ta kallon Siyama wadda gaba d’aya ita kuma take a takure da shi, shi kuwa sai wani nan nan yake da ita abun har mamaki ma yake bata…shiyasa ita da Jidda harma da Aisha suka d’an fara fahimtar inda Mutumin ya dosa . Masu hoto suna fita Aisha tace “Yauwa mu zamu wuce, muna d’an sauri saboda akwai kayan jere da za mu kai gidan nata” Da mamaki Yashjub ya d’an d’ago ya kalle ta kafin ya ce ”ai all the rooms are full(ai koina a cike ne)” Sai kuma ya kalli Manubiya ya d’an matsa Hannunta wanda ke a cikin hannayensa har yanzu kafin ya ce”Baby ba mun riga mun gama shirya komai da ke ba? me ya kawo zancen kaya kuma??” Ya yi mata tambayar yana murza Hannun nata dake a cikin nashi. Ita kam Manubiya kasa ma cewa komai ta yi, dan yadda yake yi mata da Hannu gaba d’aya ya burkita mata lissafi, shiyasa duk yadda ta so sai ta gagara cewa komai. Wani shu’umin murmushi Yashjub ya yi mai had’e da dariya kafin ya sake cewa” Babyn Yashjub, kin yi shiru….” Dariya Sir Najeeb ya yi tukunna ya ce ”Keys d’in suna Hannuna, za mu iya barinka anan ko??” “Yeah,” kawai yace, ba tare da ya kalleshiba, dan har yanzu idanunsa suna kan Manu yana murmushi sannan ya ƙi ya daina murza hannun nata. Sai da Najeeb ya sake sakin murmushi tukunna ya kalli Siyama ya ce “mu je, za a san inda za a saka kayan” “Dagaske Najeeb ba waje ka sani kuma” Yashjub d’in ya fad’a still ba tare da ya kallesa ba. Cikin sigar zolaya Aisha ta ce “kai dai ka ji da Amarya ka barmu da jere” “Yauwa abunda nima zan fad’a kenan” Siyama tace hakan tana d’an dariya. Murmushi Najeeb yayi kafin yace “Ashe kin iya magana” Ya fad’i hakan yana kallonta wanda ya sa ta d’an ji kunya. Yashjub ya yi tunanin Yassir zai zauna da shi, amman sai ya ga shima ya mik’e yana cewa”bari mu je gidan, sai anjima” “Okay”kawai Yashjub ya ce, a ranshi yana aiyyana “In dai har Yassir ya nuna yana son d’aya a cikin Yaran nan to InshaaAllah shi kuma zai tsaya mishi har sai ya ga ya aura” dan ya lura da yadda suka nutsar da shi a cikin awa d’aya kacal. Ya san tunda har so ya chanja shi ya maida shi mutum mai walwala raha da dariya to ya yi imanin inshaaAllah so zai iya chanja Yassir shima ya nutsar da shi ya shiryar da shi. Yash bai ma san sun fita ba sai da ya ga d’akin ya k’ara haske tukunna. A hankali ya d’an cika hannun nata tukunna ya kamo k’asan vail din ya yi sama da shi…ko a kan kafad’unta bai bar sa ba sai da ya kai chan k’asa tukunna ya ajjiye shi akan kujerar kawai, ya shiga kallonta. Ahankali tana mai jinta duk a takure ta d’an juyo ta kallesa kad’an…..d’inkin babbar riga ne a jikinshi na wani irin yadin da bata tab’a ganin irin sa ba tunda take a rayuwarta. Yanayin kwalliyar d’inkin anyi sa ne da bak’in zare mix with white (mai haɗe da fari), da d’inkin da yad’in da kwalliyar d’inkin sunyi mugun tafiya da imanin ta…..ba ta san yanayin d’inkin maza da kyawunshiba asalima ba burgeta yakeyiba amman wannan kam ta yi declaring nashi as the best!!! Dan ya matukar yi masa kyau, wankan nasa ya bi jiki. Ya murza bak’ar hula kamar zanna bukar ita dai bata san ko akwai hula zanna bukar kuma bak’a ba amma yau ga ta anan, sannan hatta cuff links da agogonsa ma duk bak’ake ne ga kamshin mayataccen turarenshi wanda tun lokacin da ya shigo cikin parlourn shi ya fara yi mata sallama….kallonshi take yi sam ta gagara d’auke idanunta a kansa(ba wai cikin idanunsa ba dan ta ƙi yarda su sake haɗa ido, amma shi ɗin kawai take kallo), wani irin kyau kwarjini da haiba ta ga ya k’ara…..ahankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata moments d’insu tun daga farkon had’uwarsu a office d’in sir Najeeb, har kawo yanzu da yake zaune a kusa da ita a matsayin mijin aurenta…ahankali ta lumshe idanunta a cikin zuciyarta ta shiga godewa ubangiji dan tabbas idan akwai Mace mafi sa’a a duniya to ita kuma ta naɗa kanta a matsayin wadda ta fi ta sa’a, dan ba kowa bace take samun dama ta auri wanda ya ke sonta so na haƙiƙa sannan kuma first love ɗinta, amma itakam gashi ta samu…har ila yau, kalli kyan Yash, kud’i, aji, ilimi da komai ma nashi duk marar aibu, amma ita ya zab’a, ita ya so, ita yakeso ya yi rayuwa da……….da kyar ta ɗan buɗe idanuwan nata ta ci gaba da kallon abunta. “Na yi kyau har haka ne???” Muryar Yashjub ta dirarwa dodon kunnuwanta… Wanda shima ɗin dakyar ya nemo numfashi da nutsuwarshi ya sakawa gangar jikinsa dan tun lokacin da ya bud’e fuskar tata ya neme su ya rasa…..ta yi wani irin kyau wanda tsayawa fad’a ma b’ata baki ne,tabbas Manubiya itace rayuwarsa, shiyasa ya kasa daina tasbihi hamdala da hailala ma Allah subahanahu wata’ala da ya mallaka masa ita a yau. “Yahayyu ya Kayyum ka bamu tsawon rai mai amfani ka sa mu tsufa tare kasa kar Manubiya ta riga ni mutuwa dan ban san ya zan yi rayuwa idan babu ita a duniyar nan ba” Ya yi adduar a cikin ransa yana mai ci gaba da k’are mata kallo!. Ahankali ya ji tace”Ina wuni…” Bata samu damar d’aura komai ba sakamokon sallama da shigowar Muhsin a tare hannunsa d’auke da lemuka. Kunya ce ta kama Yashjub…shi da yake Ango amma ya zo ya shantake gashi har an kawo masa lemo!shiyasa ya cewa Muhsin d’in “ya maida, shi kam tafiya ma zai yi.” Muhsin yana fita, ya janyota jikinshi ya rungumeta wanda hakan yasa duk sukayi shiru…… Sai da ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya tukunn a hankali dai dai cikin kunnenta yace”Allah ya bamu zaman lafiya” Wanda hakan ya sanya ta ji numfashinta ya yi sama kamar zai ɗauke, Cikin tsantsar kulawa da bege ya ɗago ya yi kissing forehead d’inta sannan ya ce ”thankyou” tukunna da kyar ya daddage ya yi kokawa da zuciyarsa ya cikata ya mik’e da sauri, dan ya san idan ba da saurin ya mik’e ba tou tabbas sai ya k’ara jan lokaci…….Ahankali yace mata “sai Allah ya kaimu anjima” Daga haka ya sa kai ya fice. Allah ya so shi babu mutane sosai dan sai da ya fito ɗin tukunna wata sabuwar kunya ta lullub’e shi, ya ji kamar ya nutse a wajen. Earlier (awannin baya da shuɗe) (11:45am) Tun k’arfe goma lokacin da aka sallamo Kausar, suka dawo gida gabad’ayansu! suka gaza sukuni, kamar wasu masu zaman makoki haka suka koma, Kausar kam k’arshema d’aki ta mik’e ta shige ta rufe kanta. Hankalin Mommy bai sake tashi ba sai da ta kira Daddy ya tabbatar mata da an d’aura auren….tashi d’aya ta gaza nutsuwa k’arshe ma kawai sai ta kama hawaye, ba ta yi tunanin za ta shiga damuwa kamar hakan ba, duba da yadda suka hak’ura suka tsara dakatar da komai har sai Manubiyan ta shigo tukunna su d’aura daga inda suka tsaya. Suna zaune a d’akinta itada Baba larai Yassira ta shigo ta same su… Numfashi Yassirar ta fesar kafin ta k’araso ta zauna a kusa da ita tukunna tace “Mommy, idan Ina ganin ki a haka za ki sa in je in yi shirme a wajen d’auko Yarinyar nan, ku ne kuka ce mu kwantar da hankalinmu amman ganinki a haka gaba d’aya yana nema ya dawo min da komai sabo. “Ta ya kuke so mu tarbeta Hannu bibbiyu mu yi maraba da ita bayan gashi muna ganin yadda ta zama silar kukan ki!” Ajiyar zuciya Baaba Larai ta sauk’e, kafin ta kalli Yassira ta ce ”dan Allah kar ku dawo mana da Hannun agogo baya, mun riga mun gama magana, yanzu ki bar jan lokaci mu samu mu je mu yi abunda za mu yi a cikin gidan kafin ta tare….na riga na gaya muku idan har ta tare ba’ayi ba to gaskiya akwai matsala! Ki yi sauri ki je ki cewa Yahanasu ta baki makullai da frames d’in da suka siyo ita da Ummi a kasuwa za ku had’a ku kai gidan tare da flasks d’in da kuka siya kuma…..na ji d’azu Ummin tana ce mata ya kamata a kai a kafa kafin zuwan Amaryar, dan haka ki yi sauri ki karɓo mana komai.” Sai da Yasirar ta fesar da wani bahagon numfashi tukunna tace”okay Baaba” daga haka ta sa kai ta fice. Sai a sannan Mommy tace “ni kam da kun yi abun nan tun a jiya…” “Ai dole sai a ranar da za ta tare tukunna za’ayi, kar ki damu ba za a samu matsala ba…..” Baaba Larai ta bata amsa. Shiruu Mommy ta yi, tana tunani, kafin a hankali cikin mutuwar jiki ta ce ”kin tabbatar zuwan nata ba zai taɓa surrukana ba dai ko?” Sai da Baaba Larai ta sauk’e numfashi tukunna ta ce ”na gaya miki ai…ita Manubiya tana tafe ne da fad’uwar ki a bayanta, muddin ta zo ta zauna ta daɗe da shi kuma ta zauna a cikinmu to komai naki sai ya tab’arb’are, a hankali a hankali za ki yi ta shiga bala’i kala-kala kuma babu ranar farin ciki….amma inshaaAllah, da izinin Allah mu kuma ba zamu bata ikon dad’ewa a cikin gidan nan ba! Ba za mu bari ta samu kwanciyar hankalin son zama da mu ba! Sannan ba zamu bata damar kasancewa a tare da shi ba! Ballantana har ta samu gindin zama da shi idan ciki ya samu ko shaƙuwar da ta fi ta yanzu ta wanzu a tsakaninsu….. Ballantana har matsala ta fara tasowa…kuma dukda haka still Ina ta add’ua inshaaAllah babu abunda zai taso har ta zo ta yi ɗan zaman da za ta yi ta tafi ɗin. Zuwan nata ma dan bamu da yadda za mu yi ne tunda akwai rabon zaman a tsakaninsu..kinga ai yadda akayi ta shan fama amman duk ya tafi a banza,but inshaaAllah na yi miki alk’awari ba za ta yi dogon zango a cikin gidan nan ba. Ina fatan kin fahimceni???” Jinjina Kai Mommy ta yi kafin ta ce”na fahimceki,” Sai kuma ta share kwallarta ta d’ago ta kalle ta kafin ta ce ”ki yi min alfarma guda d’aya ‘ku je ku d’auko ta banda ni, sannan duk runtsi kar ki bari a wani kawota nan a ce ta gaida ni’ dan muddin na yi ido biyu da Yarinyar nan yau tou tabbas zan iya mutuwa….” Shiruu ta yi kafin ta fashe da wani irin kuka ta ce ”Larai na tsani Yarinyar nan!! Ban tab’a tsanar Mutum kamar yadda na tsane ta ba! A cikin watanni da basu wuce hud’u ba gaba d’aya ta ɗaga min hankali ta raba ni peace of mind d’ina(kwanciyar hankalina)……” Cikin share hawayen da suka wanke mata fuska sosai ta ce “dan Allah Larai wannan karon ki dage sosai!!! Sannan a yi duk abunda ya kamata, dan ba zan karb’i wani uzurin daga gareki ba kuma du! zuciyata ba zata iya jurar Yarinyar nan na tsawon lokaci ba. Baya ga haka ma idan har ta dad’e na san kin fi kowa sanin abunda zai faru da mu….” Murmushi Baba larai ta yi kafin tace “ki kwantar da hankalinki, inshaaAllah ba za ta yi dogon zango ba…sannan ina sake yi miki albishir ɗin ba za mu bari ta gauraya da zuriar gidan nan ba ta hanyar hana komai shiga tsakaninta da Yash! Ba abunda zai shiga tsakaninsu ballantana har ta samu gindin zama a gidan, ko ta sake shiga ransa…ni na san me daa me na ke shirya mata, ki kwantar da hankalinki kawai..” Dai-dai nan Ya’isha, Yadira da Yusra suka shigo suka nemi guri suka zazzauna suma suna jiran dawowar Yasira da Yasmeen a samu a kama hanya da wuri, dan yanzun suka had’u da ita tace makullai za ta karb’o a wajen Yahanasu sai su wuce, shine Yasmeen ta bita su kuma suka yo nan. Suna zuwa suka tarar da Yahanasu tana waya tana shiryawa da sauri da sauri…tana ganinsu dama ta san ba alkhairi ne ya kawo su ba, dan haka ta yi sallama da wanda suke wayar ta ajjiye wayar ta kalli Yasira ta ce “Yassira har kun shirya? Ai sai yamma tukunna za’a d’auko Amaryar” Sai da Yasirar ta nemi waje ta zauna tukunna ta ce ”Am, Ina buk’atar keys ne, za mu kai gifts d’in da muka siyawa Ango da amarya gidan, idan kinada abunda za’a tafi da shi kuma sai ki kawo mu yi miki gaba da shi, dan mu yanzunan za mu tafi.” Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin ta ce ”keys ba sa Hannuna….inada sak’o, amma na bawa friends d’insa yanzunnan suka wuce da shi suma wai za su kai gifts ne, daga nan su biya su yi masa sallama saboda flight d’insu ya kusan d’agawa….” Cikin tarar numfashinta Yasmeen tace “no wahala…ki bamu adress d’in gidan kawai sai mu wuce.” Ta fad’i hakan tana mai k’arasa shigowa cikin d’akin, dan ita a bakin k’ofa ta chake ta tsaya tun d’azu. Murmushi Yahanasu ta yi tukunna ta ce “Yasmeen nima ba sanin address d’in gidan na yi ba, shiyasa ma kika ji nace miki na bawa friends d’insa sak’ona sun tafi min da shi dan na ji sun ce su sunsan gidan wai sunje d’azu da safe….” Tana gama fad’in haka ta d’auki makullin motarta sannan ta k’arasa inda Yasira take ta damk’a mata key d’in d’akin nata ta ce ”idan kun fita ki rufemin pls, Ina sauri ne.” Daga haka ta sa Kai ta fice da sauri dan ko hauka takeyi ba za ta bari su Isa gidan nan ba tare da an riga an kai Manubiya ba…. Tana fita Yasmeen ta ce ”idan nace muku ku barni in ci uwar Matar nan ku ce ba haka ba, yanzu kalli! Gaba d’aya ta raina Mutane, gani take yi itama ta kai Mutum…” Shiruuu Yassira ta yi tana lissafi kafin ta mik’e da sauri tana shirin bin bayanta ta jiyo tashin mota, sannan ta ji an wangale gate an fice da gudu. Ko ba’a fad’a mata ba ta san tashin motar Yahanasun ne shiyasa cikin b’acin rai ta yi wulli da makullin da ta bata akan gadon ta fice, ranta a b’ace. A yadda suka fita suka bar su Mommy a haka suka dawo suka tarar da su…suna shiga ko zama ba su yi ba Baaba Larai ta ce ”ya aka yi? Ta baku?” Ajiyar zuciya Yassira ta sauk’e tukunna ta matsa kusa da ita ta ce “ta fice, da sauri! Bayan ta ce mana keys ba sa Hannunta, sannan wai bata san kwatancen gidan Yash ba saboda tsabar ta raina uwarta!” Sai da ta sake sauk’e numfashi tukunna ta ce ”Inaga ta zargi wani abun ne……a ganina gara kawai mu hak’ura, kin san halinta mahaukaciya ce! Ina tsoron kar ta je ta gayawa Yashjub ko Daddy wani abun mu je ta taso mana da case. “Ta fad’a d’in” Mommy ta fad’i hakan tana mai k’arasowa inda suke, sannan ta sake cewa “dan Allah ta fad’a! Sai me?. Ki kira Yashjub d’in yanzu ya yi miki kwatance, ku bi bayanta na san gidan ta nufa..idan kukaje ko a gaban ta ne ku yi abunda kukaje yi, ita ta sani, ta dad’e ba ta fad’a ba.” Shiruuu Baaba Larai ta yi, sai da ta gama lissafi sannan ta kalli Yassira tace “ki kira Yashjub d’in… Saboda wannan shine kad’ai damar da za mu iya samu dan haka ba za mu yi da sanyi sanyi ba! saboda in dai har muka bari Manubiya ta shiga gidan a haka sakayau ba komai to munada gagarumar matsala.” Shiruuu Yassira ta yi ta k’i cewa ko yin komai sai da Yasmeen ta ce mata “ko ni in kira shi ne?” tukunna ta fita waje domin yin wayar…. mintuna biyu ta d’auka a waje kafin ta dawo….tana shigowa duk suka tsura mata idanu suna jiran amsa….. Sai da ta zauna akan gado ta dan dafe kanta tukunna ta d’ago tace”Mommy dan Allah mu bar wannan idea d’in” Sai kuma ta kallesu duka kafin tace “ba zan b’oye muku ba gaskiya ni tsoro nakeji….na san babu yadda za ayi Ya Yash ya bar gidansa babu cctv…haka kurum a hangomu muna yayyafe yayyafe da hayak’i da abubuwa….. Inda ace cewa akayi idan mukayi ba za ta tare ba tou da zan biye muku ayi komai ta fanjama fanjam, amman ba zan d’au wannan kasadar kawai saboda wani tushe ko ginshiƙin korartata da mukeso mu gina ba, haka kurum muna zaman zaman mu kar ku janyo mu saka kanmu a case gaba d’aya. Ni kam count me out (ku cire ni daga wannan) gaskiya!. Yanzun da na fita na kira shi har sau uku bai d’auka ba, a na hud’un kuma da ya ɗauka ya ce ‘mu bari kawai ba sai mun kai flasks d’in yanzu ba, mu saka a motocin mu, idan muka d’aukota anjima sai mu yi zuwa d’aya….k’arshe ma kashe wayar ya yi bayan yace min yana zuwa.’ Na san kuma wataƙila zai yi wa Yahanasu maganar, ita kuma Allah kad’ai ya san me za ta ce masa ta yadda na san tashi d’aya zai fahimci gidan kawai muke so mu je.” Cikin fushi da fad’a Ya’isha ta ce “ya fahimta mana sai me? Gidan d’an uwanmu ne fa!…kina wasa!! Idan ban kwashe kayana na koma chan da zama ba ki chanja mini suna!” Cikin sako wani sabon issue ɗin Yasmeen ta kalli Mommy ta ce “Ya’isha ta yi magana anan fa Mommy, mu muna nan su suna chan abun fa ba zai yiu ba, ya kamata ace ko Yadira ta je gidan ta zauna da su.“ Mikewa tsaye Yassira ta yi a fusace kafin ta ce ”wai ba ki da lisssafi ne?me yasa bakwason bin komai a hankali? Ya ana neman toshe wannan ke kuma kina neman b’ullo da sabon abunda zai d’agawa kowa hankali??….Ki yi shiru da wannan zancen dan Allah ki bari ayi komai at once (ɗaya bayan ɗaya).” Cikin son su fahimce ta Yasirar ta ci gaba da cewa ”idan har zan bada shawara a bi, to kar wanda ya janyo fad’a ko case da Yash..dan haka yanzu kawai mu hak’ura….dan Allah a bar batun zuwa gidan yanzu a nemi wani madadin. Haba mana!!! Ku ko ta Kausar ma bakwayi? Sannan idan fa muka bi komai a sannu muka samu Kausar ta shiga gidan na tabbatar Manubiya ba ta Isa ta k’ara ko da sati a cikin gidan ba, ai kunsan wacece Kausar! Kunsan ita kad’ai ta ishi Yarinyar riga da wando wallahi! Ba zata barta ba, kunga wannan ma ai wani madadin, gara shi akan zuwan da mu ke son yi yanzu dan ya fi sauƙi…amman gaba d’aya kun k’i ku nutsu ku bi komai a sannu kun dage sai kun bankad’a komai a idanun kowa an gani…..” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga cikin d’akin.” Tana fita Baaba Larai ta sauk’e ajiyar zuciya…..tabbas ta san Yassira tana da gaskiya..gaskiya ta faɗa!! Sai dai kuma indai ba abunda ta shirya akayi kafin Manubiya ta shiga cikin gidan nan ba to kwata kwata bata hango rabuwa tsakaninta da Yashjub ba!. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce ”Larai, manta da zancen Yassira ba zata fahimta ba, Yarinyar nan ba alkairi bace ba, rayuwarta a matsayin Matar Yash hatsari ne garemu, dan haka kar ki biyewa Yasira, kar mu ɗauki duk wani abu da ya shafi Yarinyar nan lightly(da wasa)…”. Ajiyar zuciya Yusra ta sauk’e kafin ta ce ”Mommy bana son Yarinyar nan tun farko.” Cikin tarar numfashinta Yadira ta ce “tunda aka fara zancenta babu zaman lafiya a cikin gidan nan, gashi sai sake raba kanmu takeyi mu da Ya Yash..” “Bata Isa ba kuwa, Allah ya fi ta” Cewar Baaba Larai, kafin ta kalli Ya’isha ta ce ”ki kira Najeeb, ki tambayeshi location d’in gidan, idan zai yiu kar ki bari ya san zuwa za mu yi. …………… Tuni, an sallami masu hotuna, shiyasa suna fita suka kama gabansu. … Su Jidda su kuma, Aisha suka tsaya jira wadda ta shiga gida domin ta sanar da su Inna sun wuce. A gefen Jidda Yassir ya d’an tsaya kafin ya ce “Bismillah, ku jira ta a mota mana, akwai rana”. Kasa bashi amsa ta yi sakamokon tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki yanzunnan, da kyar ta d’an juya ta kalleshi, a hankali ta ce “to, gamu nan zuwa”. Bakinta kawai ya bi da kallo, kafin da kyar ya ce ”ok” daga haka ya wuce ya nufi motarshi ya shiga ya zauna. Ita dai Siyama za ta iya cewa tunda take a rayuwarta bata tab’a had’uwa da wanda tashi d’aya ta tsaneshi kamar Yassir ba, gashi dai kyakkyawa kuma d’an gayu amman sam bai mata ba! Ta lura da yanayin kallon da yake yi wa mutane wanda duk wanda ya gani kai tsaye zai san ba na Allah da Annabi bane sab’anin na sir Najeeb…wanda ana ganinsa dama an san ya fi sa hankali. Shiyasa yana wucewa Siyaman ta kalli Jidda ta ce ”sai dai fa ke ki shiga motarsa, dan na san idan na shiga ni to kafin mu k’arasa tsaf zan iya tsinka masa mari in gaggaya mishi magana! Na tsani Namiji mai kallon iskanci….” Jin Jiddan ba ta ce mata komai bane yasanya ta kalleta sosai kafin ta ce ”Jidda!” Firgigit ta ga Jiddan ta yi, kafin ta d’an juyo ta kalleta sai kuma taga ta sake juyawa ta maida idanunta ga balcony d’in gidansu Al’ameen, a ranta tana mamakin “anya shi ta gani kuwa! ko dai gizo ya ke yi mata..yaushe ya dawo…ko nemanta bai yi ba” da sauri kuma sai ta kawar da tunanin…amma dukda a zuciyarta sai da ta sake cewa ”ko ma ya nemeni ni kam dama ba kulasa zan yi ba” Da mamaki Siyama take kallonta kafin ta kalli inda ta ga ta tsurawa ido tukunna ta ce ”Jidda! Ki shafawa kanki lafiya, ki rufawa kanki asiri…” Kasa cewa komai Jidda ta yi tana mai jin yadda kwallah take k’ok’arin zubo mata dan haka ta yi sauri ta ce ”ki zo mu je kawai, Aisha in ta fito sa tafi da wanchan” Ta yi maganar tana mai yin gaba abunta….Tabbas ta san ko da ace tanason ta b’oye sannan ta share al’amarin to ba lalle ta iya ba! Dan ba kad’an ba ta ji tsananin ciwon abunda Al’ameen yayi mata, har fa aiki yayarta ta yi a gidansu duk ata sanadiyyarsu amman shine ko sak’on ‘hi’ bata samu daga garesa ba bayan ya dawo kuma ta san ya ji komai. Tana k’arasawa ta bud’e gaban motar ta shiga ta zauna ta runtse idanunta…k’ok’ari kawai takeyi ta ga ta hana kanta kuka. Tun d’azu ta lura da yanayinshi da yadda yaketa faman shishige mata, shiyasa yanzun ma ta ƙi yarda ta tsaya opposite d’inshi ko kuma kusa da shi, ba ta son shiga motar Yassir har ga Allah to amma d’ayar motar kuma ta sir Najeeb d’in ce, shiyasa ta tsaya tana wasu-wasi akan ta bi bayan Jidda ne ko kuma ta tsaya Aisha ta zo su wuce tare a motar Najeeb d’in…..ba ta gama tunani ba ta ga ya tunkaro ta. Tashi d’aya ta diririce ta kuma fara da na sanin k’in bin Jidda da ta yi….har ga Allah fargaba ta ke ji idan ya matso kusan ta. Yana k’arasowa dai-dai Aisha tana fitowa rik’e da robar capulas wadda ke d’auke da turaren wuta, coal har da kasko da ashanarta. A hankali Siyama ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya wadda har sai da duk su biyun sukaji, dariya ya d’an yi kafin ya ce da Aishar “kin barmu a rana” Kallonshi kawai Aisha ta yi a ranta tace “ikon Allah” ita yake yi wa magana amman idanunshi na akan Siyama, shiyasa kawai sai ta yi murmushi tukunna ta ce ”ku yi hak’uri”. Siyama ce ta ce mata “ga Jidda chan, bari in je mu tafi tare, ke kwa taho”. Da sauri Aisha ta ce ”a’a, bari ni in je mu tafi tare da su, ku kwa taho ku biyu.” Tana gama fad’in haka ta yi gaba, dan ita har ga Allah had’in nasu ya burgeta, gashi Najeeb d’in nutsattse dashi daga gani…..ko bai fad’a ba ta san yana ciki ne da Siyama shiyasa ta basu sarari ta barsu su biyu, ita kuma ta nufi motar da akace mata Jidda tana ciki mai uban tint! Ita kanta Jiddan sai da ta shiga ma tukunna ta lura da tint d’in tsabar b’acin ran da take a ciki. Ko minti uku batayi da zama ba Aisha ta bud’e gidan baya ta shiga, dan haka Yassir ya kunna motar bayan sun gaya mishi inda za su je su kwashi kayan daganan su wuce gidan amaryar… sam Yassir bai so Aisha ta shigo ba, so yayi a bashi chance da guda d’aya kawai musamman ma Jiddan dan shi a rayuwarsa dama yana matuk’ar son mace fara fat! Ga ta wannan ga shape ga kyau ga ta da Yarintarta… Kuma zuwa yanzu ya lura tana da hankali da nutsuwa gata very innocent dan ba ya jin ta yi magana sau uku tun daga farkon ganinta da yayi har izuwa yanzu.. Ba dan yaso ba ya kunna Motar yayi gaba yana tuk’in yana satar kallon Jidda yana mamakin abunda yake shirin sakata kuka. Aisha tana wucewa, Najeeb ya lura da yanayin Siyama…dariya ya yi ganin yadda ta yi da fuska kafin ya ce “Savior d’in taki ta tafi ko?” Shiruu ta d’an yi kafin ta d’an girgiza kai kawai. Murmushi yayi yace “ki fad’i abunda ke ranki fa”. Shirun da ta yi ne yasa ya sake cewa “to tunda ba za ki fad’a ba, bari ni in bada hak’uri dan ni kaina na san na takuraki, ki yi haƙuri nima na kasa hana kaina ne, shiyasa, ayi min afuwa…um..?” Ya fad’i hakan yana had’e hannuwanshi alamun rok’o. Kamar ba zata yi magana ba sai kuma tace”ba komai fa”. “Really?to ya naga sai faman had’e rai kike yi, musamman ma a wajen hoto?” Ya fad’i hakan cikin tarar numfashinta. Kamar za ta ce masa Yassir ne bataso, sai kuma ta yi shiru dan sun fahimci Yassir k’anin Yashjub ne, kar ta je ko shima sunada dangantaka da Najeeb d’in sosai apart from Abota ta je ta kwafsa.. Wucewar motar su Yassir ɗin ne ya sanya shi cewa ”mu bi bayansu kar mu b’ata, kin d’auke hankalina Like seriously banma san lokacin da ya kunna motar ba.” Ya fad’i hakan yana kallonta sannan ya d’an matsa ya nuna mata hanya da Hannunshi. Wucewa ta yi, shi kuma ya bi ta a baya yana mai jin wani shauk’i da annashuwa suna ratsashi….tun a asibiti ya kamu yau kam ya sake kamuwa katamau ya fad’a tsundum! Adduar shi d’aya ‘Allah ya sa babu wani, sannan Allah ya sa ta amince da shi,’ dan shi kam ya ga mata, kuma inshaaAllah sai ya samu, da izinin Allah. Ba kad’an ba ta ji kunya da nauyinsa da ya bud’e mata marfin motar, dan ta san wannan ya fi sa’an su Ya Yusuf ma a shekaru, sosai….. Sai da yace “bismillah” tukunna ta d’an d’aga kafarta dakyar ta haye motar dan irin ƙirar jeep d’innan ce mai tudu da fad’i sosai amma ba ta cika tsayi ba. Sai da ya rufe mata murfin motar tukunna ya juya ya koma side d’inshi, ya bud’e ya shiga ya kunna da sauri da sauri dan ya daina hango Yassir, kuma ya san ba gidan amarya a ka nufa direct ba. Da kyar kuwa ya hango shi bayan sun fita titin, dan haka ya shiga binsa har ya samu ya tadda shi, suka jeru… Sai da ya jeru da Yassir d’in tukunna ya d’an kalli Siyama wadda take ta faman danna wayarta ya ce “ku dai Mata bakwa gajiya da chatting!”. Kashewa ta yi, ta d’an sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ”ba chatting nake yi ba, pictures d’in d’azu da na yi da wayar nake dubawa”. Kallon hawaii d’in tata ya yi kafin ya ce ”ai mai hotunan zai turomin clear ones…” ganin ya samu opportunity yasa ya yi sauri ya mik’a mata wayarshi tukunna ya d’aura da cewa”ki saka min numberki, sai in yi miki sendin ta watsapp idan ya turo”. Kamar ba zata karb’a ba sai kuma ta karb’a ta rik’e wayar a hannunta ta shiga jujjuyawa…..da kyar ta gano inane gaba sakamokon hasken da screen ɗin ya yi, sai kuma ta rasa ta yadda za ta yi sliding dan babu alamun touch ko hanyar dake nuna mata ta inda zatayi sliding keyboard d’in ya fito, kuma ita har ga Allah bata shirya basa number ta ba! Bata dad’e da fita daga bak’in cikin ex boyfriend d’inta (tsohon saurayinta) ba, wanda har ya gama cin amarcinshi ya dawo sai faman naci yake yi mata tsabar ya raina mata wayo. ko me yake nufi da ita oho. Bata shirya samun wani sabon baƙin cikin namiji ba bayan wanda ta riga ta samu…. had’in su Manubiya aya ne izina ce! Allah ne yayi had’insa, ita kuwa ba za ta d’aukowa kanta dala babu gammo ba….. Shirun da ya ga tayi ne ya sanya ya d’an sosa k’eyarsa kafin ya ce ”okay fine! Ko zan iya samun numberki? Saboda ina matuƙar buƙata,..ba wai saboda sending pictures ba” Ya fad’i hakan yana mai yin kalar tausayi da fuskarshi. Murmushi kawai ta d’an yi..ba tare da ta san ya za ta yi ba ta d’an shafa kan wayar, da ikon Allah kuwa sai taga ta bud’u, tashi d’aya ta hango Phone dan haka ta shiga ta juye masa digits d’in nata daga haka ta mik’a masa wayar tana da ta sanin bashi. “Tnx” yace. Sai da ya kira ya ji ya shiga wayarta tukunna ya yi saving ya ajjiye wayar ya ci gaba da janta da hira. Sama-sama ta ke d’an biye shi..ya lura Siyama irin y’an matan nan ne masu jan aji shiyasa tashi d’aya ya fahimci zai sha wahala..sam bai damu ba dan shi indai za ta kulasa to ba ruwansa..tabbas ya san sai yanzu zai fara soyayya! Dan a lokacin da Ya’isha take ja mishi rai k’ulewa yakeyi ya ji haushi amma da ikon Allah ko fushi ya kasa yi anan, duk kalar basarwa da cin maganin da Siyama take ta yi sam ya kasa yin ko da fushi sau d’aya d’an kad’an ne. A b’angaren Siyama kuwa ba wai jan aji bane kawai ita bata so ta zak’e da shi dayawa ne, har ga Allah ba ta so ta saki jiki dashi gudun kar ta je ta fara sonshi A samu matsala. Suna tafe kuwa Ya’isha ta kira shi, sarai ta lura da yadda ya yi da farko kamar irin baya so ya amsa a gabanta d’in nan. Sai da Ya’ishan ta sake kira tukunna ya d’auka ko tsayawa jin me zata ce bai yi ba ya ce ”ina driving, zan kiraki” Ba ta ji me akace daga d’ayan b’angaren ba sai ji ta yi shi ya ce ”Nndc quarters! Da sunan layi da number gida…..” Yana gama fad’in haka yayi sauri ya kashe. Ba ta san wacece ta kirasa ba amman tabbas ta sake yin dana sanin basa numberta da ta yi. Ba ta yi mamakin yadda ya ci gaba da flirting yana mata hira ba dan ta riga ta san halin maza, shiyasa kawai ta dinga binsa da “um,um um…” A haka suka tsaya suka d’auki gado da ragowar kayan kitchen aka had’a su da manyan motocin d’aukar kaya da masu kafi suka wuce. Sun d’anyi tafiya mai nisa kafin suka k’arasa gidan Yashjub dake a unguwar sharad’a nndc quarters..dank’areren gida mai hawa biyu! Tun daga waje suka fara kallon aljannar duniya,tun kafin a shiga ciki kuwa suka fara ganin ikon Allah dan gate d’in gidan ma…… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 17* Da remote aka bud’e musu. Gaba d’aya motocin harda na kaya ciki suka shige dan atleast compound d’in gidan zai ci motoci sama da bakwai ma. Sai da suka gama shiga tukunna gate man d’in ya rufe musu daga nan inda yake sannan ya ajjiye abun ban ruwan da yake yi wa flowers, ya tunkarosu dan tuni daman ya san da zuwan nasu… Basu kai ga fara fitowa ba suka ga ya koma da sauri ya d’an lek’a tukunna ya d’anna wani abu a jikin gate d’in ya bud’u. A tunanin su ma Yash ne, shiyasa basu juya dubawa ba. Aisha ce kawai ta fito dan Yassir yana ganin Jidda tana shirin fita ya ce mata”please wait”. Ganin masu kaya sun fara k’ok’arin sauk’ewa sannan motoci har uku sun shigo ne ya sanya Najeeb ya ce ‘bara suma su fita,’ sam bai lura da motocin da kalar su ba, kawai shi dai ya san an shigo. Bai bud’e side d’in Siyama ba….kamar d’azu yanzu ma sai da ya zagayo sannan ya bud’e mata da kansa. Cikin rashin jin dad’i dan ita har ga Allah bata so ta ce ”ka daina, ba na jin dad’i” Murfin motar ya rik’e yana kallonta kafin ya ce ”dan ma ban nemo red carpet na shimfid’a miki daga nan har bakin k’ofar entrance d’in ba?!…” Ya fad’i hakan yana kallon ta yana murmushi, a ransa yana mamakin yadda ya koma…dan gaba d’aya ya nemi jan aji!muzurai!da duk wani class d’insa ya rasa.” Ba ta sake tanka shi ba, sai matan da suka fara fitowa daga motocin ta d’an kalla…ta gane Yasmeen dan sun had’u a asibiti shiyasa tashi d’aya ta fahimci dangin Yash ne. Ganin inda take kallo ne yasanya Najeeb d’in shima ya d’an juya…. …Ya san dama ko ba yau ba dole za ta ta sani, amman dukda haka sai da ya d’an ji wani iri, kuma yana juyawa da Ya’ishar suka fara had’a ido…. D’auke Kai ya yi, ya juyo ya kalli Siyama ya ce “Bismillah” ya yi maganar fuskarsa ba yabo ba fallasa. Fitowa ta yi, shi kuma ya maida k’ofar ya rufe mata. Zuwa wannan lokacin Siyama ta fahimci wani abun tsakanin sa da Ya’isha sakamokon kalar kallon da ta ga Ya’ishan tana ta yi mata har ana yi mata magana ma bata sani ba. Sai da Yassira ta ce mata “keee!”da d’an k’arfi, tukunna Ya’isha ta samu ta d’auke dubanta daga kan su sir Najeeb idanunta suna masu ciccikowa da hawaye. Da sauri Yasmeen ta matso ta tsaya a gabanta ta d’an kareta daga Najeeb d’in tukunna ta ce ”ba ce miki mukayi karma ki kallesu ba?amma kalli yadda kike..….” Shiruu Yasmeen d’in ta yi sakamokon hawayen da ta gani taff a idanun Ya’ishan suna shirin zubawa…ta san in har tace wani abun ko kuma tace za ta rarrasheta to fa hawayen nan da suka cika suka yi mak’il sai sun fito duba da yadda idanunta suka cika taff sannan sukayi jaaa!hatta farar fuskarta ta yi jaa itama… Hakan ya sa Yasmeen d’in ta yi shiru, kafin kuma kawai ta jaa hannunta da sauri suka nufi k’ofar parlourn. Suna zuwa suka tura k’ofar…… Allah ya so su akwai masu goge goge a ciki so k’ofar already a bud’e take. Ba ta tsaya da ita a parlourn, ko sama ba dan hanyar saman shima akwai masu guga har biyu haka ma cikin parlourn, kuma ta san kafin su Isa kukan zai iya kufcewa Ya’isha shiyasa ta nufi d’akin da ta gani anan k’asan da ita. Suna shiga suka rufo k’ofar tukunna Yasmeen ta cika mata Hannu….ko magana Yasmeen ba ta yi ba Ya’isha ta fashe da kuka, da sauri Yasmeen ta toshe mata Baki, tana yi tana dan kallon k’ofa cikin yin k’asa da murya tace”so kike a jiyo ki? wanne Irin rashin lissafi ne wannan? ce miki akayi wani abun ne a tsakanin su? ki tsaya ki tabbatr mana!.” Ingije Hannun Yasmeen Ya’isha ta yi kafin ta ce ”Haba Yasmeen! Yanzu ke ba ki fahimci komai ba? ba ki ga yadda yake murmushi yana kallon ta ba? da kansshi fa ya bud’e mata mota ta fito kuma ya mayar ya rufe, abunda bai tab’a gigin yi mini ba kenan. Sannan ki duba ki ga ya ganni fa mun had’a ido da shi amman bai zo inda nake ba, ko sake kallon inda nake ma fa bai yi ba…..” Kukan da ya taho mata ne ya sa ta kasa ci gaba da magana dan haka ta yi shiru da magaar ta ci gaba da kukanta. Cikin d’an fad’a fad’a Yasmeen tace “Yanzu kuka za ki tsaya kinayi ko tunani mai kyau??kalle ki yadda kika koma a cikin y’an sakannni saboda shi!! wanda hakan yana nuni ne da tsananin son da kike yi masa, dan haka sai ki tashi ki nemi mafita tun kafin dare yai miki, ba wai ki tsaya kina kuka ba. Sannan kar ki bari su ga kukan ki! ballantana su rainaki. Tun farko kuma ai ke kika yi wasa da damarki, abunda naketa gayawa Yadira akan Junior kenan amman sam ta k’i fahimtata.. Haka kuke! Sai kun shure abu da k’afa kuma sai ku dawo kuna rarumowa da Hannu.! Kuma Ya’isha har yanzu fa ba kya lallab’a Najeeb ba kya yi masa yadda ya kamata…a yanzu duba da yadda Najeeb ya yi kud’i haka sosai dole fa sai da tarairaiya kwantar da kai lallami da rarrashi, dole sai kin bi ta koina kin mamaye kin rik’esa da kyau! kin ajjiye kishi da girmankai a gefe dan wallahi one mistake (kuskure ɗaya) idan kikayi to tashi d’aya zai cika wandonsa da iska sai dai labarin wani ba shi ba. A da ma ya aka k’are y’an mata sun yi masa chaaa! ballantana yanzu.” Cikin kuka kamar za ta shid’e Ya’ishan ta ce ”Yasmeen shekaran jiya fa da kuka ce idan ya zo in je in basa hak’uri wallahi da na je har k’asa na durk’usa na bashi hak’urin! Shin, Har ya ya kamata in lallaɓa shi bayaga hakan? Wacce kalar biyayya da kwantar da kai ne a sama da hakan??? How much more good can i possibly be?” Ya’isha ta yi mata tambayar tana kuka sosai.” Tausayinta ne ya rufe Yasmeen, shiyasa ta ma kasa ci gaba da magana, ahankali ta sa Hannu ta rungomota…ita kanta ta jijjiga da lamarin, babu abunda ya fi d’aga mata hankali kamar yarinyar. Itama Ya’ishan haka dan dukda ta san tana da kyau amman fa ta san ba ta Isa ta tsaya ta ce za ta kara da Yarinyar da ta gani yanzu a fannin kyau ba. (Ba za a kira Siyama doguwa chan ba sannan ba gajeriya ba ce, tanada haske sosai itama sai dai yanayin hasken ta ba kalar na Jidda bane dan ita ba fara bace fat! Ta fi kama da kalar ruwa biyu, waenda su ka yi haɗin nasu da turawa. Kamar yadda fuskarta take round haka idanuwanta suke suma, ba manya chan bane ba kuma ba k’anana ba y’an madaidaita sannan farare k’al waenda sukayi daidai da yanayin tsarin fuskarta mai ɗauke da cikar gashin gira Pointed nose, da ƴan madaidaitan lips ɗinta masu tudu waenda suka haɗa ɗan ƙaramin Bakinta. Bata da jiki sosai amman kamar su Jidda itama tanada structure (ƙira) mai kyau tubarkallah………) ….. Su Ya’isha suna wucewa, Jidda ta fito daga motar Yassir ranta a b’ace. Inda Aisha take ta k’arasa ta tsaya, bayan ta karb’i d’ayan flask d’in da aka mik’o mata daga motar kayan, dama flask biyu ne kawai a cikin kayan sai robar turare. Dan haka Aisha ta d’au k’aramin flask da robar ita kuma Jidda ta d’auki babban mai d’an girma. Ganin su Yassira ma duk sun fito ne yasa Aisha ta ce ”inaga dangin angon ne, dan ga wata mai kama da Yashjub d’in, ku taho mu je a gaisa sai mu wuce ciki gaba d’aya a tare.” Dai-dai nan Siyama wadda ta samu ta zillewa sir Najeeb da kyar ta k’araso wajen. Tana shirin yin magana ta ji shi a bayanta ashe tare suke tafe ita bama ta sani sani ba, cikin nutsuwa ta ji yana cewa Aisha “ga sisters d’in Yash da aunty d’insu, mu je ku gaisa dasu” “Ok”Aisha ta ce daga haka ya wuce gaba suka bi sa a baya. Kamar Siyama za ta tambayi Jidda mai ya b’ata mata rai har haka sai kuma kawai ta kyaleta tana mamakin abunda ya sake fusatata daga shigowarsu cikin gidan. Yassira, Baba larai sai Yadira da Yusra ne suka tsaya a bakin motar, suna jiran fitowar Yahanasu dan wallahi yau ba za su raga mata ba, rainin wayon nata ya yi yawa! Matar da ta ce musu ba ta san kwatancen gidan ba shine suna zuwa suka tarar da ita a bakin gate tana jira a bud’e mata…. Yahanasu kuwa ba k’aramin dad’i ta ji ba da taga su Aisha, dama tunda su Yasira suka je suka tambayeta ta san su da naci shiyasa hankalinta bai kwanta ba tace bari dai ta zo ta tabbatar da ba su zo d’in ba…..da farko da ta ga motocin su Yasirar a bayanta hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba ta shiga lissafin yadda za ta yi ta taka musu burki amman da suka shigo ta ga su Aisha sai ta ji wata nutsuwa da kwanciyar hankali sun rufar mata ga shi har da sir Najeeb! Ta san duk bala’in su ko ma menene suka zo yi ba su isa su yi a gaban sir Najeeb ba, ga kuma Ummi a hanya itama wadda ta tsaya yin waya da ita ne ma shiyasa ba ta fito daga cikin motar ba har yanzu… ….d’azu da Ummin ta ga su Yassira sun fito ne ta fahimci gidan za su zo, shiyasa ta ce su jira ta ta d’auko mayafi itama tana so ta zo gidan amman tana fitowa sai wayam ta gani! Sun ta fi sun barta, shine a take ta kira Yahanasu ita kuma ta yi mata kwatance, yanzu kam da suka yi wayar ma tana bayan layi…. Su Baaba Larai suna tsaye suna jiran fitowar Yahanasu suka ga su Aisha sun tunkarasu. Baba Larai ji ta yi kamar ta koma cikin motar dan ta tsani Yaran dama tun kafin ta gansu, sam ba ta k’aunar Manubiya da duk wani ahalinta…. Ba yadda ta iya haka ta tsaya dan ga Najeeb ya tunkarosu ta san shima gaida ita zai yi ba dan hakan ba wallahi da tuni ta koma cikin motar. Aisha ce ta fara gaida Baaba Larai kafin su Siyama. “Alhamdulillah” kawai tace, daga haka ta d’auke Kai, Yasira kuma ta yi sauri ta kara waya a kunneta ta matsa gefe gudun kar ma su yi gigin kulata. Still Aisha ce ta cewa su Yadira “sannunku” Kamar ba su ji ta ba haka suka yi mata. Still Aishan ce ta kuma cewa Baba larai”ya taro?Allah ya sanya alkhairi” Sai da ta juyo ta kalleta kafin tace“Ameen”daga haka ta zubawa Jidda da Siyama jajayen idanuwanta. Ita Jidda har ga Allah tsoro matar ta bata, ga kuma Al’ameen da shege Yassir da suka kunno ta, ga shi taga ana amsa musu dakyar, su Yusra kam ko kallo ma ba su ishesu ba. Shiyasa kawai sai ta juya ta ce “Siyama, ku taho mu wuce ciki” Kamar dama jira Yusra take, sai cewa tayi ”Atleast ai kya tsaya ki yi kyakkyawar gaisuwa da y’an uwan wanda kike k’ok’arin shigewa cikin gidan nasa” Ta fad’i hakan tana murmushin da Mutum zai kasa gane rashin iya magana ne koko dai rainin hankali ne. Cike da mamaki Najeeb ya ce “Yusra! Languagee!” Ya d’an ja k’arshen yana mai d’age gira sannan yad’an motse Baki. Juya ido kawai ta yi ta kalli sama dan haushinsa dama gaba d’ayansu suke ji. Ganin abunda ta yi ne yasa kawai ya d’auke kansa ya kalli Baaba Larai ya ce ”Ina wuni Baaba ya hidima? Murmushin yak’e ta yi kafin ta ce ”Alhamdulillah, Ya gajiyarku?” “Mun gode Allah” yace, kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta gama wayar k’aryar ta zo tana gaida shi, da kulawa ya amsa mata daga haka ya juya ya nufi cikin gidan yana mamakin yadda Yadira da Yusra suka yi masa..wato ko kallo ma bai ishe su ba! Tabbas Yara sun girma kam…. Sir Najeeb yana shiga motar Ummi ta k’araso. Already su Siyama ko gama gaisawa basu bari sir Najeeb ya yi da su Yassira ba suka matsa da niyyar shiga ciki….Yahanasu ta fito da fara a ta tarbe su kamar za ta goyasu, wanda hakan ba k’aramin sake tunzura su Baba Larai ya yi ba…ita Baba larai Babban tashin hankalinta ma shine ta yaya za ta aiwatar da mission d’inta da waennan jama’un a cikin gidan?.. Lissafin da takeyi kenan suka ga gate ya zuge motar Ummi ta danno kai. Cikin b’acin rai Yassira ta ce “Innalillahi! Tabbas Matar nan ta ci a bata sarauniyar y’an naci, Mace ace ba zuciya kwata-kwata, a taho a barki amman sai da kika zo? Ko waye ma ya yi mata kwatance oho?!” “Ba zai wuce angon da kika kira yace ‘mu jira mu taho da y’an d’aukar amarya’ba, kinga ita da ta fiki ai gashi yayi mata tashi d’aya!” Yusra ta bata amsa tana mai wucewa ciki ranta a mugun b’ace… …..ta so su Jidda sun biyeta yau da sun ji maganganu wallahi! Ta san ba class d’inta bane su ɗin sannan ta san idan ta yi hakan zatayi acting childish (za a ga Yarinta a lamarin nata) amman wallahi sai dai a kirata da jinjirar k’auye! Ba ta damu ba. Dan tunda ta d’aura idanunta a kansu ta ji ta rasa duk wani haƙuri kawaici da hankalinta tashi d’aya. Tunda take a rayuwarta bata tab’a jin tsana irin wadda take yi musu ba…gashi ta san dole ta dinga ganinsu tunda sun riga sun had’a y’ar uwarsu da yayanta, watak’il ma a haifo musu mai kama da su Innalillahi!!! wallahi za ta iya mutuwa idan hakan ta faru!….. Ya zama dole a san na yi da Manubiya dan ba ta da guri da muhalli a rayuwar d’an uwanta! Ashe dama akan wannan y’ar talakawan Ya Yash ya d’agawa kowa hankali! Dan ganin da ta yi wa su Jidda ya nuna mata cewa Manubiya talakan tukuff ce!… Babu abunda ya fi sake b’ata mata rai kamar ankon atamfar 6500 d’in da suka yi a bikin d’an uwanta! Kamar Yash ace wai an yi ankon 6500 a bikinsa wannan lalacewa haka har ina?….. Tana tafe tana waennan saƙe-saƙen Kamar za ta fashe! Haka ta afka cikin parlourn, ko bi ta kan masu goge-goge bata yi ba ta wuce sama… Wucewa su Yassira suma suka yi suka nufi cikin parlourn dan haka da sauri Yahanasu ta ce”mu je ciki muma, idan muka je kowa sai ta kama floor a samu a sassaka turaren wuta ya ratsa ko Ina dan ba lokaci.” Ko ishashshiyar gaisuwa da introduction (gabatarwa) Yahanasu bata bari Ummi da Munirat sun yi da su Siyama ba, haka nan ta azalzalesu suka shige ciki. Aisha ta d’an fahimci wani abun, ga kuma yadda y’an uwan Yashjub d’in suka rabu gida biyu da masu hankali da jahilai, shiyasa suna shiga itama ta cewa Siyama ta tsaya ita da Munirat da Jidda su saka turare a k’asan su yi ta gyaygyarawa. Ita da Ummi kuma suka yi sama da masu gado, Yahanasu kuma ta yi chan sama turakar mai gida…inda d’aki d’aya ne tak a floor d’in sai tafkeken roof top open terrace. Saman farko kuma d’akuna biyu ne da parlour d’aya, sai wani parlour mai kamar d’aki wanda Yash ya zuba kayan gym a ciki dan haka suka tattara kayayyakin gym d’in Najeeb ya kira wasu a cikin masu gyara gidan suka kwasa aka kai d’akin Yashjub dan akwai wani guri a cikin glass inda za a iya zuba kayan, su kuma suka fara kafa gadon su a nan, Najeeb yana cewa “idan Yashjub ya zo Aisha zai nuna” Itama tace “Shi za ta ce ya chanza masa tsarin gida!” Hakanan suna raha suka shiga had’a gidan. A tunanin su Aisha sun yi zab’en gado mai kyau da tsada amman sai da suka b’ige da d’an jin kunyar gadon nasu da suka ga kayan gidan, dan hatta d’akin chan k’asa guda daya na bak’i Turkish ne a ciki wanda a k’alla sai an zuba miliyan goma tukunna za a sayi gadon. Kaff gidan Turkish ne, Main parlourn k’asa ne kawai royal, white da royal blue, colour din mai masifar kyau. shima kuma saboda ansan Turkish zai ɗan yi wa parlourn kad’an kasancewarsa tafkeken gaske shiyasa aka zuba royal complete set ɗinsa d’urma d’urman gaske mai tafe da set d’in dining table da madubin sa da komai ma…. Kitchen d’inta ma royal blue ne da white, wanda had’uwa girma da tsaruwar kitchen d’in yasanya Siyama da Munirat suka tsaya a ciki suna ta zancen kitchen d’in da k’auyanci suna yi wa kansu dariya Dan tashi d’aya tasu ta zo daya gashi har sun saba…… Gidan ya had’u k’arshen had’uwa… Duk inda aka ware domin deco da saka tv an yi decorating nashi da wani had’add’en painting wanda ya ke nan jikinshi kamar marbles, kuma duk iri d’aya grey da white wanda hakan kalar marbles d’in gidan yake gaba ɗaya mai masifar kyau, Pop da chandelier kam ba a magana ga toilets da closets suma abun kallo,gida dai ya had’u iya had’uwa babu makusa sai dai ta fannin masu Hassada …. Shiyasa su Siyama suka dinga jinjina izza da kud’urar ubangiji dan tabbas idan ba Allah ba to babu wanda zai yi hakan, ‘wai nan ne gidan Manubiya!’ Allah mai girma da iko!. Murna da farin ciki kam sun yi mata bila adadin dan ta samu duniya sai dai ta tashi ta nemi lahira, sannan ta samu Miji mai tsananin sonta da k’aunarta, ga hutu Allah ya bata matsalar d’aya ce ‘dangin miji’ amman baya ga wannan Manubiya kam ta samu komai…a ce a d’aukota daga gidansu tashi d’aya a kawota wannan gidan haka mara makusa ko d’aya! dan tun daga waje!gate!har compound d’in gidan wanda ya ji interlocking concrete da grass carpet, da garden a haka ma basu zagaya baya sunga swimming pool ba, Duk koina babu makusa. Duk iya kushewar mutum sai dai ya hak’ura in ya shigo wannan gida na Manubiya da Yashjub. ……. …D’akin bak’i Jidda ta bud’e ta shiga,ita sam ba ta yi tunanin akwai mutum bama sai da ta yi ido biyu dasu Yasmeen tukunna tashi d’aya ta ce ”Sorry” daga haka ta juya. Tsaki Ya’isha tayi,dai dai Jidda ta kama handle d’in k’ofar ta bud’e da niyyar fita ita kuma Yasmeen tace “Nikam ace wai mutane ko darajar privacy basu saniba saboda Allah, kamar wasu dabbobi!”Daga haka suma suka nufo k’ofar da niyyar fita da kuma bi ta kan Jiddan idan ba ta ba su hanya da wuri ba. Duk ba su lura da Najeeb a bakin k’ofar ba, sai da Ya’isha ta zo zata wuce tukunna suka yi ido biyu da shi. Kallon ta yayi sosai kafin ya maida dubansa ga Jidda yace “Anata nemanki! ki je sama wajensu Ummi, za ki taya su da wani abun” Jinjina kai kawai ta iya yi dan ita kam ta gama shiga shock bayan b’acin rai da kuma mamaki…su da suke a matsayin surukan juna amma kalli yadda suke musu magana kamar masu shirin shiga filin dambe!. A tunaninta wayayyun mutane masu kud’i da illimi kamar su ba za su yi wannan tumasancin ba. Shi kansa Sir Najeeb tunanin da yake yi kenan….ya san Ya’isha ba ta da kunya kuma tana da tsiwa amman sam bai yi zaton hakan daga garesu gaba d’ayansu ba. Ya ma rasa me zai ce shine matsalarsu ko yana damunsu! shin kishi ne! ko haushi! ko bak’in ciki! ko rashin sanin ya kamata?. Shiyasa Jidda tana wucewa shima ya juya zai wuce ko second look bai yi tunanin sake yi musu ba. Ahankali ya ji Ya’isha tace “Ya Najeeb!” Kamar ba zai juyo ba sai kuma ya juya ya ce ”Naam Ya’isha!” Wuceshi Yasmeen ta zo ta yi, ta basu sarari shi da Ya’ishan. Ganin ta yi shiru ta ƙi yin magana kuma sai wani irin kallo take yi masa ne ya sa yace “Inada abubuwan yi fa Ya’isha, akwai matsala ne??” Ya yi mata tambayar yana d’an juyawa yana kallon masu aiki dake a cikin parlourn dan har sun kusan kammalawa. Ba k’aramin b’aci kuwa ranta ya sake yi ba, shiyasa itama ta fito bakin k’ofar ta tsaya daff da shi sannan ta ce ”A ganinka bai kamata mu yi magana anan ba ko? shiyasa kake k’ok’arin zillewa, gudun kar ta ganmu tare??” Dama ya san sai ta yi maganar Siyama, shi kuwa har ga Allah bai shiryawa maganar yanzu ba dan ya san tsaf zai iya kawo ƙarshen alaƙar da ke tsakanin shi da ita nan take!!! shi kuma ba ya so su rabun ta hanyar da bata dace ba, ya fi so a rabu cikin lumana… Sai da ta sake cewa”Bakace komaiba” tukunna ya juyo yace “Tou me kike so in ce miki?? Ya’isha Meyene matsalarku da Mutanen nan? Daga ke har su Yasmeen! Har ga Allah kun bani kunya wallahi! Kuma na tabbatar kin san me zai faru idan Yash ya ji haukar da kukeyi ko? Dama ashe kishi tsakanin Matar wa da siblings d’inshi gaskiya ne?? Dan ni dai ban tab’a gani ba sai a kanku, gaskiya!. sannan kishin naku ma is way too local(ya yi zubin rashin wayewa da yawa) haba mana!. Ki gayawa su Yasmeen, kar su sake yin wani shirmen, kema kuma ki nutsu! Amarya za a kawo, idan kuma ba haka ba to wallahi zan fad’a ma Yash.” Yana gama fad’in haka ya fara k’ok’arin juyawa sakamokon hango Munirat da Siyama da yayi sun tunkarosu da kaskon turaren wuta…..ya san abunda yakeyi is so selfish (ya yi son kai da yawa) amman Yaisha ita ta janyo komai tun farko! Dan in da ace tana bashi lokacinta to da wataƙila a lokacin da ya ga Siyama months ago (watannin baya da su ka shuɗe), da ba lalle ya saka ran samunta ba, zai iya rarrashin zuciyarshi ya hak’ura da ita duk da ya san zai sha wahala. Amman Ya’isha ita ta banzatar da shi, shi kuma ya kamu ya fad’a yayi dakon soyayyar Siyama har na tsawon kusan 4 months, sannan yanzu da ya sake ganinta a yadda yakeji wallahi ko goya sa Ya’isha takeyi ba za ta samu gurbi a zuciyarsa ba dan Siyama ta mamaye ko Ina shiyasa shi kansa ya ke d’an jin tausayin Ya’ishan dan har ga Allah ba ta da matsayin da zata hana shi zama selfish(yin son kai), bata da matsayin da zata sa yak’i rabuwa da ita, kuma bata da matsayin da zata hanasa bin zab’in zuciyarsa…… Ba k’aramin mamaki ya shiga ba da ya ji Ya’ishan ta ruk’o hannunshi, dan haka ya juyo a mugun firgice Ita kanta su Siyaman ta hango shiyasa ta yin hakan, Hannun ya kalla kafin ya d’ago! Ranshi a mugun b’ace yana shirin fara magana ya ga fuskarta shab’e-shab’e da hawaye. Da mamaki ya ce ”Ke!lafiyarki kuwa?” Cikin kuka tace”na san saboda sister d’inta kake ta wahalar da ni, haba Ya Najeeb! Ta ya kake tunanin ba zan ji haushinsu in kuma tsanesu gaba d’aya ba? kalli fa yadda ka ganni a halin da ka ganni amman sam baka damu ba maimakon hakan ma barazana ka ke yi min akan za ka gayawa Yash mun tab’a dangin matarsa. Shekara nawa muna tare tashi d’aya ka juya min baya ya kake so in yi? Shin ba ka tsoron hakki? Idan ka yaudareni fa Allah ba zai barka ba. A tunanina a matsayin k’anwa nake a wajen ka bayan masoyiya, ta yaya za ka min haka tashi d’aya sannan kuma kace ni da y’an uwana ba za mu ji haushin su ba?” Tausayinta ne ya d’an kama shi ganin yadda take kuka wiwi…tabbas ya kamata ya rabu da Ya’isha da wurwuri ya yi setting nata free tun kafin a samu lahani da ɓarnar da ta fi hakan….” Yana cikin wannan tunanin ya ji kansa ya wani irin sarawa sakamokon rungumar da ta yi masa. Cikin kuka tace “Allah ban shirya barwa kowa kai ba”. Bai tsaya wata wata ba ya zarota da dukkan k’arfinsa cikin fushi ya ce ”ba ki da hankali ne? wanne irin shirme ne wannan?..” Ya fad’i hakan yana juyawa domin ya ga ko Siyama ta gansu, bai ga kowa ba amman tabbas ya san ta gansu….ji ya yi kamar ya rufe Ya’isha da duka! Ko hannunshi bata tab’a rik’ewa ba sai yau! kuma yau d’in ma har da runguma tsabar iskanci….. Ganin idan ya ci gaba da tsayuwa a gaban ta zai iya mammaketa ne ya sa kawai ya juya da sauri, ko a parlourn bai yarda ya ci gaba da zama ba tashi d’aya ya fice, ya na fita ya nufi motarsa ya shige ya zauna ya kunna ac….. Bashi da tantama Siyama ta gansu tabbas shiyasa ta yi sauri ta gudu, shikenan ya san tun kafin aje ko Ina har ta fara yi masa kallon d’an iska kuma mayaudari. Suna shiga kitchen Siyama ta cika Hannun Munirat tukunna ta dafe k’irjinta ta na mamakin zafin kishin Najeeb da ta ji! Yau ne fa kawai suka d’an samu momment amman kalli yadda zuciyarta take tafarfasa na ganin shi da wata da tayi. Dariya Munirat ta yi kafin ta ce ”Tab! Amman ba ki riga kin shiga university ba ko? Kina ina couple suke yin abunda ya fi wannan ma in public! Dan kinga d’an wannan shine duk kika koma haka sai kace wadda taga wani abu babba….” Cikin katseta Siyama tace”couple?Mijinta ne?” “A’a, amman saurayinta ne kuma shi za ta aura, na ji Mommyn su tana fada rannan Kamar sun kai kusan 7 years tare, tun tana secondary school…amma gaskiya ni kaina ta bani mamaki saboda ban tab’a ganin wani d’an gidan da bad behavior haka ba bayaga Kausar sai Kuma Yassir, ban yi tunanin suna irin hakan ba suma, shi kansa Ya Najeeb d’in he looks decent(kamar nutsatstse).. Anyways sha…su ta shafa!. Kina gayamin Manubiya a buk take? maybe ma mun taba haɗuwa fa” Sai yanzu Munirat ta lura da yadda sam hankalin Siyaman baya a kanta. Dan haka ta d’an kyasta ƴan yatsunta ta ce ”Hey!” Firgigit Siyama ta yi, dakyar ta d’an daidaita b’acin ranta tukunna ta kalleta ta ce ”Yassir! wanda suka kawo mu shi da Ya Najeeb ko?,dama daga ganinshi wanann d’an iska ne” sai kuma ta yi sauri ta ce ”Au, yi haƙuri, brother dinki ne ko?” Shiruuu Munirat ta yi daga jin zancen Yassir…wanda zuwa wannan lokacin ta gama tsara yadda za ta yi su shirya dan tana mugun son Yassir gaskiya….. “Munirat kin yi shiru” Muryar Siyama ta katse mata tunani. Numfashi Munirat ta fesar kafin tace”A’a ba brother d’ina bane, mu bar maganarsa kawai” “Ok”Siyama ta ce kafin ta d’aura da cewa “dama na ga kamar yana ɗan ciki da ƴar uwata ne shiyasa na ke so in d’an yi confirming halinsa kafin komai.” Dasauri Munirat tace”da gaske? wanann farar ko?” “Eh” kawai Siyama tace daga haka ta chanja hirar ba tare da ta tsaya ta lura da fuska da kuma yanayin Munirat ɗin ba.. A parlour Su Baba Larai suka zauna Yassira kuma ta wuce sama wajen Yahanasu, ba abunda ya basu mamaki ya kuma basu takaici kamar yadda su Aisha suka rarrabu Kamar irin sun fahimci wani abun kuma sun lura Yahanasu ce ta nace akan ayi hakan……. Tana zaune akan couch d’in private balcony na d’akin, tana tunani ta ji an bud’e k’ofa, shiyasa ta mik’e da sauri ta shigo cikin dakin. Ido biyu sukayi da Yassira dan haka tace “Ashe kece” “Ko akwai wani da ki ke tsammanin zai shigo bayan ni ɗin? Kema ki ka shigo ballantana kuma ni? A tunanina da lissafina na san na fi ki iko da d’akin nan da gidan nan ma gaba daya” Yassira ta fad’i hakan tana mai k’arewa d’akin kallo. Numfashi Yahanasu ta fesar kafin ta matsa kusa da ita ta tsaya tukunna ta ce ”daga ƙarshe dai! Gashi kin fito da fuskarki ta asali kenan ko? Hakan yafi ai! Dan kin san ni I hate pretence(na tsani riya), sannan FYI (ina so ki san cewa) da ni da ke duk iko d’aya muke dashi da d’akin nan, Kawai ke kina rayuwa ne cikin ruɗi!” Shiruuu Yassira ta d’an yi sai kuma ta kawar da ƙoƙarin fahimtar maganar da Yahanasun ta gama gaya mata yanzun, kafin ta matsa kusa da ita ta ce “Mecece matsalar ki? me kikeso ki yi proving? A tunaninki ni da Hannuna zan cutar da d’an uwana ne ko me kike zato? Dan tsaf na fahimceki, na kuma gano abunda kikeyi wanda har ya kai ga kina k’ok’arin saka zarginmu a idanun waennan k’azaman Mutanen! So kike ki nuna musu wani abu akan mu ko me?. Na san ba uwa d’aya ce ta haifemu ba amman dukda hakan ke ɗin y’ar uwata ce kuma na san matsayinki a wajenna shiyasa kika ga Ina binki a sannu… amman fa Yahansu karki kuskura ki kai ni bango!! Kar ki bari mu fara yaƙi da ni da ke a cikin gidan Imam kura dan wallahi in kika ja hakan ta faru to ba za ki ji dad’i ba!… Dan na lura kwana biyun nan wani gigi kike ji, kina ƙetare iyakar ki!!!. Tsabar rainin hankali ɗazu in tanbayeki kwatancen gida ki ce baki sani ba sannan kuma ko kunya ma bakiji ba mun had’u da ke kinsan mun gane k’arya kika yi mana amman shine zaki zo da wani sabon shirme? Amma, daga wannan ba za ki sake ba! Saboda lokaci ya yi da za ki koma matsayarki! Dan na lura ƴanci bai kamace ki ba..” Murmushin takaici Yahanasu ta yi kafin tace”Madallah! Da kyau, hakan ya yi kyau!…. Gara da kika fito k’iri-k’iri kika gaya min komai, na ji dad’i. Sai dai inaso ki san cewa nima fa na san kaina, kuma zan iya tsare jikina da ayoyin Ubangiji, dan haka ko me kike tunanin yi a banza ne” Da fushi sosai Yassira ta ce “me kike nufi? wa ma ya damu da wata ke ballantana ya miki wani abun, bayaga hakan ma me kika maida Mutane?” Dariya sosai Yahanasun ta yi sannan ta ce “dad’ina da ke Yassira har gobe ba ki iya magana ba….kina nan da rashin iya sakaya maganar nan naki har gobe bai chanza ba. Na san kin san me nake nufi dan haka mu rufe chapter kawai. Inaso kawai ki san cewa ‘ba zan tab’a bari ku zalinci Manubiya ba..’ and kamar yadda kika tuhume ni ba zan ɓoye miki ba! eh, hakan ne, saboda maganar gaskiya ban yarda da ku bane shiyasa na yi duk abunda nayi, kuma kar ki sha mamaki idan aka kawo Manubiya in zaunar da ita in zaiyyane mata su waye ku! Saboda gudun kar ku yi mata shigo shigo ba zurfi, dan an yi min ban ji dad’i ba shiyasa ba zan bada k’ofa ayiwa wata ba! Hatta su Ummi lokaci kawai nake jira, sannan akwai abunda nake dubawa shiyasa kawai nake ɗaga muku ƙafa amma dukda hakan akwai ranar da zan yi wa kowaccenku zazzagar kwanyo, har a gaban Daddy, dan wallahi ba wai ke kad’ai ba hatta Mommy ba tsoron ta nakeji ba yanzu! Kuma za ki tabbatar da hakan soon” Cikin fushi Yassira ta d’aga Hannu za ta kifa mata mari, da sauri Yahanasun ta rik’e Hannun tukunna tace “Wannan zamanin ya riga ya wuce Yassira, na wuce haka daga gareki har abada wallahi, sannan Ina so ki san kun yi kuskure! Tara abokanan adawa da yawa shi yake janyo Mutum k’asa wanwar, kinga ga ni ga Ummi sannan ga Manubiya kuma dukkan mu babu yadda kuka isa ku yi damu wallahi, ban san wanne dukan za ku fara karewa ba dan tabbas kun d’aukarwa kanku dala babu ganmo…. Kin d’aukarwa kanki aiki mai tsananin wahala, kin jefa kanki a masifa, sannan kin biyewa son zuciyar da ba inda zai kaiki sai garin dana sani” Cikin sauk’e ajiyar zuciya ta ci gaba da cewa “Inama ace za ki san kuma za ki ga abunda na sani, to da kin gane wacece Mommy, da kin daina biye mata. Gaba dayanmu mu ukun ba abun tsana bane a wajen ki, ni y’ar uwarki ce! Manubiya matar wanki! Ummi kuma Matar Daddy ce, masoyiyar mahaifinki ba abar gaba bace a gareki. Zan so ki gane sannan ki fahimci cewa Mommy amfani kawai take yi da ku domin cimma manufarta..using d’inku kawai takeyi amman na san ba za ku fahimci hakan ba!. Kamar yadda na faɗa miki tun farko ‘kina rayuwa ne cikin ruɗi!, akwai abubuwa da yawa da ya kamata ace kin sani.” “Mommyn tawa ce take using d’ina? Tabbas yau na sake tabbatar da ke ɗin mahaukaciya ce, bari ki ji!!! Mahaifiyar da ta tsugunna ta haifeni idan tana da dama ko mosquito ba za ta tab’a bari ya cijeni ba. Ni ba mahaukaciya ce Irin ki ba, na san menene dai dai nasan menene ba dai dai ba, babu wanda yake using ɗina ko tunzurani, komai in kinga na yi to na san me nake yi kuma gaban kaina ne…” Shiruu kawai Yahanasu ta yi tana la’akari da yadda maganganunta suka tab’a Yasirar……tashi d’aya mood d’in Yahanasun sai ya chanza, da kyar ta iya hana kanta kuka, ahankali ta kalli Yasira sosai kafin ta ce “ki yarda da ni in na ce miki ‘Mommy za ta iya aikata abinda ya fi using d’inki ma Yasira’.” Wani irin yanayi Yassira ta ji ta shiga daga kallon idanuwan Yahanasu, da sauri tq kauda kanta gefe ta yi shiruu, na y’an sakanni…da kyar ta fatattaki tausayin Yahanasu tare da mugun tunanin da take k’ok’arin dasa mata a rai! Ta juya fuuu ta fita da sauri. Tabbas sun yi sake kam d’an hakkin da ka raina…. gashi har tana yi mata barazana…. Yahanasunda a da idan ta saka mata kara bata Isa ta tsallaka ba amman wai yau itace take fad’a mata maganganu har haka! Ba laifin kowa bane laifin Mommy ne wadda ta fara taka musu burki a kan Yahanasun, a tunanin Mommy Yahanasu ba ta Isa yin komai ba, to gashi yanzu ta zame musu problem. … Babu yadda ba su yi ba, amman duk ta inda suka zaga gidan a cike yake taff. Baaba Larai kamar ta d’aura Hannu aka ta fashe da ihu!!! Haka nan tanaji tana gani ta hak’ura da abubuwan da suka zo da su za su yi, ko d’aya cikin kwalayen flask d’in da suka shirya a kan za su saka turaren a ciki su je su jere ya gama su tafi da shi fasawa sukayi dan zuwa wannan lokacin ba damar yin wannan basajar, saboda Yasira ta yi mata signal d’in Yahanasu sannan ga dangin amarya sun kunna nasu ba zai yiu su suna dangin ango su zo su hau kunne kunne ba suma, bayaga hakan ma ko mahaukaci Idan ya ji warin ya san ba turare bane suka kunna…….Yayyafe yayyafen da suka shirya yi shima ko Ina mutane…… Dakyar Yassira ta lallab’a Baaba Larai had’e da d’an fad’a tukunna ta hak’ura amman da cewa ta yi ”sai ta yi a gabansu bata damuba” Ita dai yassira tsoro takeji da kyar dama ta yarda ta biyo su gidan tun farko…. bata nuna bane amman maganganun Yahanasu sun ratsata, ga kuma abunda Ya’isha tace mata sir Najeeb yace kuma ta san tsaf zai iya bada sheda in Yahanasu ta je ta fad’i wani abun akansu….ita tsoronta kar su je su sake lalata relationship d’insu da d’an uwansu shiyasa ta yi dagaske suka tarkata suka yi gaba bayan sun gama kushe gadon Manubiya a gaban su Jidda….. Yasmeen harda cewa “Irin gadon matar mai gadin su ne exactly. Itakam dan Allah anjima a rufe d’akin in an kawo amarya, dan wanann abun kunya ne ba kad’an ba” Yadira ma y’ar k’arama da ita amman harda ita a masu cewa “Ita Wallahi da ta ji anata jeere jere ta d’auka za ta zo ta ga wani abun kirki, ita wallahi gadon ma tsoro yake bata…” Ba wanda yace musu uffan, amman Ummi ta gama shirya gayawa Daddy idan ta koma dukda basa magana amman zata kulashi saboda Manubiyan ko da ace zai ji haushin tane, saboda ba za ta zuba ido su tisa y’ar mutane a gaba ba, dan a yadda taga take taken su indai aka barsu to akwai kallo. A b’angaren Jidda kuwa, zuwa wannan lokacin wallahi ji take kamar ta hana Manubiya tarewa da wannan Mutumin, kamar ta wargaza auren ma gabad’aya haka ta ke ji, saboda waenan mutanen. ta san yanzu ta makaro shiyasa kawai ta yi shiru ta dinga ajiyar zuciya tanaji kamar za ta fashe. Haka ma Siyama, ga takaicin Najeeb ga kuma takaicin dangin mijin Manubiya…anya akwai haske a lamarin nan kuwa! dan ita ko a wasa bata tab’a jin labarin jahilan dangin miji Irin waennan ba….. K’iri k’iri suke yin abunsu babu b’oye b’oye ko kauda kai, babu kissa ballantan kawaici…. A yadda suka dinga gaya musu zafafan maganganu babu control wallahi da waensu aka samu da sai an dambatu! kawai dai sun samu masu kauda kai ne da gudun magana shiyasa suka kyalesu. A haka ma basu ga matsugunnin su ba kenan, shiyasa daga Jidda har Siyaman suke ta addu’ar ’Allah yasa banda su za a zo d’aukar amarya.’ Bawai dan suna jin kunyar gidan nasu bane ‘A’a’! Kawai dai ba sa so su zo su yi musu shirme a gaban Mutane ne. Suna wucewa Ummi ta yi musu sallama bayan ta ajjiye ragowar frames d’in da ta zo da su tace “za ta je ta d’auki k’awarta, sai sun had’u a wajen d’aukar amarya.” Munirat dama tashi d’aya ta ce mata ”ta tafi kawai, sa had’u a wajen d’aukar amaryar” Ummi tana wucewa suma suka fara shirin tafiya… Aisha da Yahanasu za su zauna a gidan har a kawo amarya, Siyama kuma za su wuce gida wajen Manubiya dan an santa ba k’awaye gareta ba so tana buk’atar su. Jidda ba ta son shiga motar Yassir Siyama ma ta nace itama ba zata shiga motar Najeeb ba. Allah ya so Siyama Najeeb ya tafi gida yin wanka dan an kusa tafiya d’auko amarya, Yassir ma ya d’an fita shiyasa suka yi wayo suka ce “ba za su iya jira har su dawo ba babu time za a b’ata lokaci, gashi akwai vail d’in manubiya a wajen Siyama kuma yanzu ta kirata tace tanaa buk’ata zata chanja kaya…” Ba dan Yahanasu ta so ba ta barsu suka tafi su kad’ai amman da har ta d’auki waya za ta kira musu Najeeb. Sallama suka yi musu daga haka suka fita suka yi tafiyarsu a adaidaita sahu. Ba kad’an ba Munirat ta girgiza da ganin gidansu Manubiya, hatta su Jiddan sai da suka d’an fahimta. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 18* Manubiya tana chan d’akin su Siyama, dan Inna kara ta yi ta ce “a tafi da ita chan ɗin, idan an zo d’aukarta a d’auke ta a chan.” Haka nan aka wuce da ita d’akin Anty Umma bayan Innar, Baba, Ya Nafi’u da Ya Musbah sun gama yi mata fad’a, sun yi mata sallama had’e da saka albarka..da kyar aka b’anb’are Manubiya daga jikin su Baba tana wani Irin kuka kamar za ta shid’e! Ba k’aramin mamaki Inna ta ji ba da ta ga maman Abbakar da maman Baraka sun zo mata, dan ana fita da Manubiya sai ga su sun zo suna ta washe Baki kamar ba su ba, sai da suka zauna a d’akin suka shiga yi mata Allah ya sanya alkhairi tukunna ta tabbatar da gaske wajen nata suka zo dan sam ita bata yi tsammanin ko iskar su ba…kasancewarta Mace mai kawaici ya sanya kawai ta karb’esu ba yabo ba fallasa, daga haka ta gaya musu inda Amaryar take. Kan Manubiya har juyawa ya soma yi saboda tsabar turaren wuta, a nan makwaftan dama akwai wata mai siyar da kayayyakin gyara, haka aka had’a da wanda Inna ta basu kafin su fito da na matar da na wajen su mama ake ta banka mata, saboda dama ita Inna kunyar fulani ba lalle ta barta ta cewa Manubiyan ta yi ba. Haka suka d’aura ta akan kujerar tsugunno itakam kanta in banda ciwo ma ba abunda yake yi mata. Har zuwa wannan lokacin ba matar Baba Habu ba matan Uncle babu y’ay’ansu, kamar ba biki akeyi ba. Adaidaita sahun su Siyama tana yin parking, motocin Abokan Ango suka k’araso suma wajen guda goma. Ba k’aramin dad’i Siyama ta ji ba da taga babu motar Najeeb a ciki, wanda abunda ba ta sani ba ashe mota ya chanza…d’azu da Yahanasu ta yi shirin kiransa ashe ya shiga ita bata sani ba, daga jin yadda Siyaman take bada uzurin ƙin jiran nasa da aka ce su yi! tashi d’aya ya fahimci dodging d’insa (guje masa) take yi, shiyasa ya chanjo mota mai tint yana tunani da addu’ar shigarta motar, dan yana buk’atar su fahimci juna a yau, ya samu ya wanke bak’in fentin da ta yi masa. Ana ajjiyesu ya hange ta kuwa, murmushi ya yi dan a take wani irin sanyi ya shiga ratsashi….. ya san ya yi mata laifi, kuma Ya’isha ta b’ata mishi sunanshi a idon Siyaman amman kuma abunda ta yi ɗin wanda yake nuni da kamar kishinsa ne takeyi, hakan ba k’aramin dad’i ya yi masa ba…. Ba kad’an ba Munirat ta girgiza da ganin gidansu Manubiya hatta su Jidda sai da suka d’an fahimta, gudun kar su ji ba dad’i ne ya sanya ta yi sauri ta ware dan ita kawai mamaki ta d’an yi ba wai kyama ko wani abun ba saboda ta san da talaka da mai kud’i duk Allah ɗaya ne ya yi su. Kudin yana cikin jakar Jidda shiyasa ta tsaya sallamar mai napep d’in su Siyama kuma suka ce bari suyi sauri suje su sanar da su Anty Umma, a fara shirye-shirye. Tana gama bada kud’in, ta juyo kenan, kawai ta ga Mutum a tsaye a daff da ita….. Ba ta d’ago ta kalli fuskarsa ba amman tabbas ta fahimci shine, sannan ga k’amshin turarensa wanda ta sanshi da shi shekara da shekaru!.... She’s not suppose to be feeling this way(bai kamata ace ta na jin hakan a kansa ba!) Dan kamata ya yi ace babu wani sauran son shi da k’aunar sa da ya rage dede da kwayar zarrah a cikin zuciyarta, sai dai kuma tashi d’aya ta ji komai ya dawo mata sabo! kamar ma bai tab’a yi mata laifi a rayuwa ba ballantana har son nashi ya ragu!!! haka takeji a halin yanzu ba ta da wani burin da ya wuce ta d’ago ta kalli kyakkyawar fuskarsa ma’abociyar murmushi wadda ta bada gudunmawa kwarai da gaske wajen sace zuciyarta! Ta yi misssing d’insa sosai, sannan ta tabbatarwa da kanta har yanzu tana son abunta, amman kuma ba zata iya fatali da abunda ya yi da kuma wahalar da y’an uwanta suka sha duk a ta dalilinsa ba.! Dan haka da sauri ta yunk’ura za ta matsa shi ma ya yi sauri ya sake shiga gabanta ya tsaya har sai da goshinta ya ɗan bugi k’irjinsa!. Sosai ta ke iyaka bakin ƙoƙarinta amman tabbas ta ga alamun Al’ameen ya rantse sai ya karya lagonta ya kawo ƙarshen juriyarta….ba ta san lokacin da hawaye suka fara sintiri a kan kyakkyawar fuskarta ba, tana mai jin wani irin yanayin shauk’i k’auna tausayi mai tafe da rashin jin dad’in hakan da ta ke ji game da shi. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya sauk’e kafin ya ce “Ba ki ma yi missing d’ina ba ko?Takura miki ma na yi ko? Jidda kin tsaneni har haka ko kalllona ma bakya son yi?” Ya k’arashe maganar tasa a hankali, sannan kamar mai shirin fashewa da kuka!. Sai da ta yi kokawa da Zuciyarta tukunna ta samu ta d’aga mishi kanta alamar ‘EH’. Shiruuu yayi kamar baya wajen shiyasa ta d’an d’ago ta kalle sa…. ba ta yi zaton ganin hawaye a idonshi guda d’aya ba amman sai ta yi sauri ta saka a ranta crocodile tears (hawayen ƙarya) ne, sannan ta yi saurin mayar da kanta k’asa…. So take ta ce ya matsa ta wuce amman ta kasa saboda a asalin gaskiya sam bata k’aunar matsawar tashi daga inda take. Ajiyar zuciya ya sauk’e tare da fesar da numfashin da har sai da ta ji calm scent d’in numfashinsa kafin ya ce ”Na san dole za ki ji haushina, dole za ki yi fushi da ni amman ba ki san yadda na ji da kika ce ko ganina bakya son yi ba, a tunani na mun wuce haka!. Amman ba komai, laifina ne, na d’auki alhakin saboda Jidda bakya laifi a wajena kin riga kin sani. Alfarma d’aya nake nema a wajen ki, dan Allah dan Annabi ki yi min adalci ki taimaka ki bani lokaci In yi miki bayani sannan in faiyyace miki komai, dan Allah pls” Ya k’arashe maganar tasa yana mai had’e hannayensa biyu waje d’aya alamun rok’o, ba tare da ya damu da a waje su ke ba. D’agowa ta yi ta kallesa da idanuwanta waenda suka cicciko da hawaye kafin tace ”Ya Al Ameen! ni da kai ba zai yiu ba!. Baka san halin da ahalina suka shiga ba duk a ta dalilin biyewa son zuciya da nacin mu, idan akwai alfarmar da zan rok’a a duniya a halin yanzu daga gareka itace ka fita a harka ta! ka hak’ura dani! ka rabu dani har abada dan girman Allah” Da sauri ya ce ”Jidda kin san ba zan iya ba” D’an matsawa gareta ya yi wanda hakan yasanya ta ja baya da sauri, kamar zai fashe da kuka ya share fuskarsa da duk hannunwansa biyu sannan ya d’an ja hanci kafin ya ce ”Pls just one more chance! Zan gyara komai in saita komai, na yi miki alƙawari… sannan zan yi miki clearifying komai dan na san kina jin haushi na ne akan rashin nemanki da na yi tun bayan tafiya ta, Inada dalili Jidda kuma na san idan kika ji za ki yi mini uzuri” Sunkuyar da Kanta ta yi sosai ta share hawayenta, daga haka ta zagayesa dan ba ta ga amfanin tsayuwar tasu ba, ita kunya ma takeji wani a cikin y’an gidan su ya ganta da Ya Al’ameen. Tana wuce sa ta ji ya rik’o vail d’inta, da sauri ta juyo da niyyar ce masa ya cikata amman sai ta gagara sakamakon ido biyu da suka yi da Ya Musbah. Tashi d’aya ta rikice wanda hakan yasa Al’ameen d’in waigawa shima, shi kansa sai da ya d’an ji kunyar Musbahu dan haka ya d’an lumshe ido ya bud’e kafin ya k’arasa juyawa gaba d’ayanshi. Ganin yadda Ya Musbahn ya k’i kallon either of them instead kawai ya tsurawa hannun Al’ameen wanda ke rik’e da mayafin Jiddan ne ya sanya Al Ameen d’in cikata a hankali, daga haka ya d’an fesar da numfashi ya kallesa sosai tukunna ya mik’a masa Hannu alamun su yi musabaha. Ba tare da ya kallesa ko hannun nasa ba ya cewa Jidda “Wuce ki shiga gida!” Kamar jira takeyi kuwa hakanan ta wuce wuff har tana d’an tuntub’e. Bata san ya sukayi ba amman ko da ta je gaff da shiga gidan ta juyo sai ta tsinci Ya Musbah yana magana da Al’ameen d’in kuma daga gani ba maganar dad’i bace, dan ran Ya Musbah a mugun b’ace yake yi masa maganar, har yatsa taga yana nunawa Al’ameen d’in. Tana shiga d’akin su ta fara nufa, ba kowa daga Inna sai Mama sai wata y’ar tsohuwa(iya ramma). Inna tana had’a y’an ragowar kayayyakin Manubiya waenda suka yi saura tana hawaye, Mama tana zauna a gefenta suna rarrashinta ita da iya ramma. Anan ta zauna ta shiga taya Innar, suna yi suna hawaye duk su biyun, sun k’i ma su ji rarrrashin da ake ta yi musu. Jidda ba ta yi mintina uku da zama ba…suna gama zuge akwatin wayar Mama ta hau k’ara, cikin mutuwar jiki ta k’arasa ta d’auki wayar a hankali ta kara a kunnenta, dan duk su Inna sun gama kashe mata jiki… “Subahanallah” Suka ji Mama ta ambata kafin tace”ki yi hak’uri ki daina kuka, gani nan zuwa.” Tana ajjiye wayar Inna ta mik’e ta na share hawayenta kafin ta shiga tambayar ta “mai ya faru?” A gaggauce tace mata ”Ammi ce ta kirani, wai in zo mu kai Al’ameen asibiti, yanzunna haka kurum yana shiga gida ya yanke jiki ya fad’i… Dama fa ni tunda ya dawo wallahi na lura kamar ba shi da lafiya kullum wani iri nake ganin sa.” Cikin rashin jin dad’i ta k’arasa ta rike Hannun Inna kafin ta ce ”ki yi hak’uri inna, na so in zauna na raka Manubiya d’akinta, amman Alhaji baya nan, dole suna buk’atata!” Da sauri Inna ta ce ”kar ki damu, ki je ba komai, hakan ma wallahi na gode kwarai Mama, Allah ya basa lafiya” A hankali ta jinjina Kai tukunnan ta yi musu sallama ta wuce….. sai da ta fita tukunna Inna ta lura da yadda Jidda ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta jikinta har wani irin vibration yake yi tana wani irin silent kuka kamar ranta zai fita, ajiyar zuciya ta sauk’e saboda dama sai da ta saka hakan a ranta daga jin bayanin Mama….a hankali ta k’arasa kusa da ita ta zauna tukunna ta sa Hannu ta d’ago fuskarta wadda ta yi dagaje-dagaje da hawaye da gumi har ma da majina, sai da ta share mata fuskartata tukunna ahankali sosai ta ce ”kin had’u da shi ne yanzu?” Cikin kuka Jidda take kallonta tana so ta yi magana amman sam sai ta gagara, shiyasa kawai sai ta afka jikin Inna ta sake fashewa da wani Irin kuka abun tausayi. Ajiyar zuciya wannan tsohuwar ta sauk’e kafin ta k’araso kusa da su ta ci gaba da rarrashinsu dan ita ba ta ji abunda innar ta ce da Jiddan yanzu ba……Sun jima sosai matar tana rarrashinsu kafin da kyar aka samu Jidda yi shiru ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere. A haka Siyama ta shigo ta same su itama idanunta sun yi jaa alamun ta taya Manubiya kuka, sai da ta k’arasa kusa da su ta zauna jikinta duk a sanyaye tukunna ta ce ”Ummaa tace wai ace miki iyayen ango sun zo, a je a ce musu su shigo ne? Dum!! Haka duk su biyun suka ji k’irjinsu ya buga. A hankali Inna ta kalli Jidda tace mata “su je ita da Siyama su shiga da su parlourn su Siyaman. “ Ba su dad’e da fita ba itama suka fita ita da wannan Iya ramma wadda ta tilasta mata dole suka wuce parlourn su Siyaman tare….. Su Jidda suna fita da Baaba Larai suka fara cin karo tsaye a bakin motar Yassira tana zazzare ido tana k’arewa gidan kallo fuskar nan a yatsine. “Ya salam” Jidda ta ambata a cikin zuciyarta, kafin ta d’auke Kai ta k’arasa wajen Yahanasu wadda ta gani suna fitowa daga mota itada wata, kusa da motar Yahanasu motar Ummi ce itama su biyu dan haka Jidda ta d’an saki fuskarta….Su Ummi dama tun ranar farko ba su raina gidansu Manubiya ba, to haka yau suma k’awayensu da suka zo tare da su haka….. talaka da mai kud’i duk Allah ne yake yinsu,kuma Ubangiji yana iya maida talaka mai kud’i cikin dare d’aya vice versa(haka ma ɗaya ɓangaren), sannan kowa da kalar tasa baiwar, kuma babu wanda ya fi wani a wajen ubangiji sai wanda ya fi bauta masa ya fi tsoronsa, shiyasa su kam basuga kuma basuji komai ba, iyakar abunda ya ke da mahimmanci shine Yash yana son Matarshi kuma tana da tarbiyya, hankali da nutsuwa. Sab’anin su Yassira waenda hankalinsu ya sake tashi, ransu ya sake b’aci….”tabbas dama a yadda Yash yake nuna halin ko in kula a garesu da Mommy kanta! Ta san cewa yanada matsala kuma bai san ciwon kansa ba amman bata tab’a sanin cewa shi mahaukaci har haka bane ba sai yau. Yanzu nan ya zo? Ashe dama akan wadda ta fito a wannan gidan Ya Yash ya ke abubuwan da yake yi da uban rawar k’afar da yake ta faman yi kamar wanda zai auro y’ar gwal!?. Sannan su kansu k’annenta ashe daga nan suka fito amman har suke da ƙarfin hali da kwarin guiwar wani ciccin magani a gabansu? Ba laifin kowa bane laifin Yash ne da ya had’asu da su..tabbas Yash ya janyo musu babban insult da abun kunya a rayuwa….wallahi ko gidan su gwaggwo mai aikin su ya fi wannan kyan gani…….” Yasira ta zaiyyane hakan a cikin ranta. Iri ɗaya da su Ya’isha suma, dan duk lissafin da suke yi kenan. Yasmeen kam ji takeyi kamar ta fashe da kuka, dan ba kad’an ba a ganinta wannan abun insult ne, ta ya Yash zai had’asu family da Irin waennan mutanen, “mai ya shiga kansa har hakan?” ta yi kanta da kanta tambayar sannan cikin bawa kanta amsa tace “tabbas wannan aikin asiri ne, babu tantama, amman za ta gane inda ta zo ne!……dan ba ta jin za su iya jurar Yarinyar nan na wata ɗaya ma wallahi. Gara da Allah yasa ba su yi gaiyyata ba, yau da sun kwashi abun kunya!….. Yassira bata iya fitowa a mota ba sai da ta kira Mommy a video call ta shiga nuna mata gidan. Mommy ta san Yash ya wulak’antasu, kuma ya k’ask’antar da su da shi kansa, amman kuma ta d’an ji dad’i, dan a yadda Manubiya take bata da gatan nan tabbas ta tabbata k’aramin alhaki a hannunta….. shiyasa har Kausar wadda take ta faman rarrashi tun d’azu ta nunawa video call d’in da Yassira takeyi sannan ta sake tabbatar mata da cewa ‘Ba su da wata matsala, dan Yarinyar da ta fito daga wannan gidan ba za ta zame musu jidali ba InshaaAllah’. Har waje Yassira ta fito, tana video call d’in tana nunawa Mommy gidan da layin ba tare da damuwa ba, wanda hakan ba k’aramin d’aurewa Mutanen da suke kai kawo Kai ya yi ba, saboda a ganinsu saboda me ya sa za ta yi hakan!? Akan wanne dalili za ta fito tana yin video d’in da kowa ya fahimci layin da gidan kawai take d’auka, dan in da ace videos d’in d’aukar Amarya za ta yi ai kowa ya san sai an shiga ciki tukunna ake farawa Bayaga hakan ma yanayin yadda take yin video d’in nata kana gani za ka san gidan kawai take d’auka cike da raini ba komai ba. Waenda suke kusa da ita sosai ne suka fahimci video call ne, ragowar kuwa sam ba su fahimta ba….. Girgiza Kai kawai Ummi ta yi ta fito da ga cikin motarta, kafin ta k’arasa inda su Yahanasu suke tsaye ita da su Jidda… Da farko Siyama da taga abunda Yassira takeyi har za ta kula ta su yi, amman kawai sai ta basar da ita gudun kar su yi abun kallo ta ja wa Manubiya abun fad’e, kuma tana juyawa suka had’a ido da Ya’isha, ta san idan ta biye su to tsaf za a yi ta ba dad’i dan ta lura kamar Yarinyar fad’a take nema da ita dan yanzun ma tana juyawa ta zabga mata harara shiyasa kawai ta rabu da su amman wallahi ba dan yau ranar Manubiya bace da sai ta koya musu hankali gaba d’ayansu. Kallon duk su biyun Ummi ta yi kamar ta san me ke a cikin zuciyarsu, ta ce ”ku yi hak’uri, ku yi komai saboda yar uwarku, kar ku bari ayi abun fad’e a ranar aurenta, ku danne zuciyoyinku kunji y’an albarka” Murmushin k’arfin hali Jidda ta yi, dan ba k’adan ba itama zuwa yanzu ta hau saboda har wata dariya take jiyo su Yusran sunayi Irin dariyar rainin hankali da k’ask’anci d’innan, a hankali tace”inshaaAllah Ummi” Daga haka suka sake gaisawa suka gaida k’awayensu kafin su ce musu “bismillah” Su Jidda a gaba su Ummin kuma a baya, haka suka nufi gidan. Dai-dai su Siyama sun zo wucewa kenan Yusra ta ce ”Am Yasmeen ni kam anya ba kejin kaji da tumaki aka mana kwatance ba kuwa?inaga gara fa mu kira mu sake tabbatarwa….” Wani irin tafarfasa zuciyar Siyama ta shiga yi, inda ace iyakar i su iskancin nasu ya tsaya to da da sauk’i amman kejin kaji da tumaki da Yusra ta ambata it means tana nufin har da iyayen su kennan, shiyasa duk yadda Siyama ta yi alk’awari ta kuma so ta kyale su sam sai ta kasa, ta san tana juyawa za ta iya kifawa Yusra mari shiyasa still sai da ta kuma tausar zuciyarta tukunna ta juyo ta ce “Group leader d’in ‘rashin sanin yakamata‘ kuna iya shigowa kuma idan kun so, ku d’auki Amarya kamar yadda aka umarceku ku yi daga gida” Tayi maganar tana kallon Baaba Larai dan Babba bai fi Babba ba. Tana gama fad’in haka ta wuce ciki. Shiruu duk suka yi, saboda ba su yi tunanin za ta kulasu ba! Dan sun lura kamar Yaran sunada d’an tsoro, amman fa sun ji dad’in kulasun da ta yi hakan ya nuna ta ji zafin maganar tasu kuma wallahi sai sun nuna mata ba su san ya kamatan ba kuwa!. Yasmeen ce ta ce “mu je ciki mu d’auki Amaryar” daga haka duk suka yi ciki suma…… Sam Ummi ba ta so Siyama ta tanka musu ba, dan ta san za su yi mata shirme ne a gaban dangi da y’an uwa, kamar ta san hakan kuwa suka shirya d’in!…. Siyama ta yi zaton za su tanka mata amma sai ta ga ba su ce komai ba, kusan tare ma suka shiga parlourn nasu kafad’a da kafad’a ita da su Ya’isha ba wadda ta kalle ta a cikinsu. Parlourn cike yake taff da Mutane…Dukda k’amshin turraren wutan da yake tashi tundaga k’ofar gidan hakan bai hana su yatsine fuska ba sannan suna tafiya kamar kar su taka k’asa sai kace masu tsallake kwata….Lace ne a jikin Yassira wanda a k’alla ya kai naira miliyan ɗaya, haka itama Ya’isha dan nata da na Yassira kala ce kawai ta bambanta na Yassira blue na Ya’isha kuma brown, mayafi 3D suka rufa a kansu y’an k’ananu suka zagaye wuyan su da shi, Yassira bubu ne a jikinta Ya’isha kuwa fitted gown. Iyaka zobuna da awarwarayen gold d’in dake a Hannayensu kad’ai sun isa su gigita Mutum. Su Yasmeen kuma super ce a jikinsu ita da Yusra(super babba!), su kam har d’auri suka yi suka rufa mayafansu a kafaɗa.. amman suma dank’ara dank’aran gold d’in jikinsu Hannu wuya kunne da y’an yatsu kad’ai abun kallo ne. Yadira ce kawai mai material d’inkin fitted gown amma itama kana gani kasan yadin yaji kud’i, A kunneta kawai ta saka gold sai agogon ta na gold, ko zobe ba ta saka ba ita. Maganar gaskiya kaff gurin kayansu ne ya haskaka ko Ina!, dan tun a waje kafin su shigo babu mai kyallin su! Duk wanda ya shigo cikin layin kuwa idan ya kalli kowa a lokaci guda kai tsaye zai fahimci su ɗin ne dai suka zama pronounce, ga wayoyin Hannayensu kalar wadda ake yayi ta shekarar. Shiyasa suka zama abun kallo sannan behaviour d’insu (ɗabi’arsu) itama ta zamana kowa ya gani saboda idanun kowa a kansu ya ke dama…. Suna shiga parlourn wata mata tace “Allahu Akbar! Ga dangin ango!” Dakyar Yassira ta d’an yi murmushi sannan ta ce ”na jini ma kuwa” Ta yi maganar tana kallon Munirat wadda ta fito daga d’akin da Manubiya take ciki d’auke da kaskon turaren wuta a Hannunta”. Murmushi Munirat d’in ta yi kafin tace mata ”ina wuni, har kun iso?” K’ura mata ido kawai ta d’an yi kafin ta d’auke Kai ta maida dubanta ga Matan da su ke karkad’e kan kujeru duk sun rikice sun ga gwalagwalai da sutura, dan tashin Mutane ma akayi akan kujerun aka shiga karkad’e musu inda za su zauna. Ba wani datti a wajen amman dukda haka sai da Matar da ta karkad’e wajen tukunna ta ce musu “bismillah” ya fi sau biyar sannan dakyar Yassira ta d’an zauna ita da Yasmeen da Baaba Larai, su Yusra kuwa a tsaye suka tsaya akan kafet da takalman su!Sam ba su damu da yadda su ke tattaka abincin da aka ci aka zuzzubar akan kafet d’in yana mammannewa ba, wayoyinsu kawai su ke daddannawa. Ita Yassira abunda ya fi damunta ma shine kar ta je ta kwashi infection a jikin kujerun dan har wani danshi danshi ta ji bayan ta d’an d’osana mazaunanta akai ta zauna…jin yadda danshin yake sake ratsata ne ya sanya ta ga inaa! Ba za ta iya ba! Dan haka tashi d’aya ta mik’e ta zare d’an kwalinta dama a ka ta rufa mayafin shiyasa ta zaro shi ta shimfid’e akan kujerar tukunna ta koma ta zauna, wanda hakan da ta yi sam bai yi wa rabin Matan parlourn da suka san ciwon kansu dad’i ba. Dariya k’asa-k’asa Yasmeen ta yi wanda hakan ya sake k’ular da su Siyama waenda suka dawo daga d’aukowa su Ummi fararen kujerun zama suka shigo yanzun. Ba tare da sun kalli su Yasmeen d’in ba suka wuce suka ajjiyewa su Ummi kujerun fuskokinsu tamau. Suna ajjiyewa Ummi ta ce ”Siyama ki barshi ba sai kun yi wahala ba ai,” Murmushi kawai Siyama ta yi tace”ba komai Ummi, bismillah” Dai-dai nan Inna, Iya ramma da Maman Siyama suka fito daga cikin d’aki. Su Inna basu damu ba suka zauna a chan gefen carpet yayinda su Yasira suka hahharɗe k’afafu akan kujera, Su Ummi ma inda su Innar su ke suka k’arasa su ka zazzauna aka shiga gaisawa cikin mutunta juna ana gabatarwa. Yahanasu ce ta gabatar musu da tun daga kan Baba Larai har izuwa kan Yadira, su kuma suka nuna Inna farar bafulatana mai k’aramin jiki kkyakkaywar gaske a matsayin mahaifiyar Manubiya Maman Siyama kuma a matsayin gwaggon ta. Ummi ce ta ce musu “Ita Ummin sa ce step mom, Mahifiyarsa tana gida bata samu zuwa ba”. Kamar jira Yasmeen take ta tari numfashinta tace “Eh! Tanada allergy.. (rashin jituwar jiki..) shiyasa duba da yanayin arean nan yasa ba ta zo ba”. Rabin Matan ba su gane me take nufi bama sai y’an kad’an ne suka fahimceta. Shiruu Ummi ta yi haka ma kowa kafin Yahanasu ta ɗan yi murmushi ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa “ko za’a fito mana da Amaryar tamu wuce!Na ga magariba har ta gabato” Sai a sannan maman Siyama tace”da ikon Allah, bari in je in kawo muku ita” Daga haka suka mik’e su biyu ita da Iya ramma sannan sukace Ummi ta biyo su. Ba wai Yaro kaɗai ko Babba idan ya kalli fuskar Baaba Larai a wannan lokacin to sai ta bashi tsoro!!! Ta had’e rai ta yi tamau da fuska ta kumbura, gashi Idanunta sun yi jaa!!! Ita a nata lissafin.. ..wai tsabar an rainasu shiyasa ko saka su ma ba a yi itada su Yassira a cikin karɓan Amarya da bayarwan ba! Sai Ummi da Yahanasu kawai suke komai, sam su ba a d’aukesu da mahimmanci ba. Ga kuma takaici da tsanar Manubiya da ahalinta baki d’aya, Gashi ba su samu sun yi abunda suka yi niyya d’azu za su yi a gidan Amaryar ba..Shiyasa gaba d’aya ranta ya b’aci ta kumbura ta yi suntum! Tana mai jin kamar ta d’aura Hannu a ka ta yi ya zabga uban ihu…. Ba a yi mintuna shida ba suka fito da Manubiya, sanye cikin fara k’al d’in alkayabba sai kyalli da tashin k’amshi takeyi. A gefen Ummi suka ajjiyeta, tana zama Ummi ta rungomo ta izuwa jikinta sannan ta ce ”Allah ya yi miki albarka, Allah ya sa ki zame mana sanyin idaniya” “Ameen” gaba d’aya kowa ya ce ana raha daga nan aka bawa Ummi amanarta, suka karb’a Hannu bibbiyu ita da Yahanasu, aka yi addu’a aka shafa kafin a fara shirin mik’ewa…..Yassira ta ce “Yauwa Inada magana, saboda akwai al’adar da muka saba da ita mu y’an gidanmu!” Runtse idanu Yahanasu ta yi, kafin ta buɗe ta kalli Yassirar ta ce “Yassira inaga gara mu wuce kawai, yamma ta yi” Murmushin rainin hankali Yasirar ta yi mata kafin tace “Nop!ba zai ɗauki lokaci mai tsayi ba ai.” Sannan ta kalli Inna ta ce ”and da farko kafin komai, inaga ya kamata in d’an buɗe sannan in faiyyace muku wani abu” Ta yi maganar idanunta cikin idon Inna, kafin ta ci gaba da cewa “Ita wannan wadda kika bata amanar y’arki! Matar Babanmu ce, itama kamar uwa take a wajen mu amman ba ta san cikakkiyar Al’adar gidanmu ba! Dan ko shekara d’aya ba ta yi a gidan ba. Wannan itace yayar Mahaifiyarmu wadda aka turo ta wakilceta” ta yi maganar tana nuna Baba Larai kafin ta ci gaba da cewa “A haƙiƙanin gaskiya, yadda al’adar mu take.. ..Mu da muka zo d’aukar amarya, to tun daga kan Baaba Larai har izuwa kan Yadira dole ne sai Manubiya ta bi mu ɗaya bayan ɗaya ta durk’usa a gabanmu, sannan ta gaishe mu! A matsayinmu na dangin Mijinta, daga nan ne idan mun ga muna so za mu karb’e ta mu yarda da ita tukunna mu d’auke ta mu tafi da ita’.” Cikin tarar numfashinta Ummi tace “Yassira wanne irin shirme ne wannan???” Da d’an murmushi kwance a kan fuskar Yasmeen ta ce ‘’Ai gaskiya ce Ummi, kuma ai ba abun zafi bane ba, kamar dai wasa haka game ɗin ya ke! Ke dai kawai ki Kalla…it will be fun.” Ta k’arashe maganar tana murmushi. Yusra ce ta d’aura da cewa “ai ya kamata ta san mu sannan ta san matsayin mu na siblings d’in Mijinta(kannen mijinta) tun yanzu! Ta san cewa idan ta shigo za ta girmama mu ne ta bamu girman mu! A garinmu hakan shine ma main purpose (babban maƙasudi) na b’ullo da wannan al’adar…. Wanda a yadda ake ɗinnan banga alamun hakan daga gareta ko wani a cikin parlourn nan ba, dan na lura kamar ba ma a san da mu ba! Ko irin y’ar amanar ta ma ɗinnan ba a bamu ba Ummi kad’ai aka bawa. So ya kamata ta yi gaisuwa ta yi durk’uso kafin mu d’auke ta mu kaita gidan Ya Yashjub d’inmu mai tsada… Ku duba fa ku ga yadda za mu d’auke ta daga nan!” Yusran ta fad’i hakan tana kallon parlourn tana nunawa da Hannunta kafin ta ci gaba da cewa “mu kaita chan aljannar duniya, gidan Ya Yash!… A ganina ko cewa muka yi ta kwanta ta gaida mu bai kamata ace kun yi jayayya ba. Bayaga hakan ma ba wai mu muka tsara ba Al’Ada ce ta Mahaifiyarmu sannan Mahaifiyar Ya Yash, mune wakilanta, dan haka a gaskiya babu inda Amarya za ta je ba tare da an gwada kuma anyi abu guda ɗayan da zai yi nuni da an darajata an daraja mu sannan an karrama Al adarmu ba……” Ganin kowa yayi tsit an kasa magana ne yasa Siyama cewa “Tou inaga za ku iya kwasar motocinku ku koma, saboda an samu gagarumar rashin fahimta! Ta inda mu muke ganin mun yi muku alfarma na baku one in town ɗin ƴar uwarmu da mukayi, kuma kuma naga kuna ganin kamar kun yi mana alfarma ne…” Da sauri iya ramma ta ce ”Siyama ya Isa haka!” Ba dan Siyama ta so ba ta yi shiru tana mai rama hararar da taga Baba larai tana yi mata. Bayan Ya’isha Baba larai ce second halittar da Siyama ta fi tsana a cikin su, Ita wallahi tunda take bata tab’a ganin babbar kwabo babbar banza irin wannan matar ba… Matsawa Iya ramma ta d’an yi tukunna ta kalli Ummi tace “y’an uwansa ne kika ce ko?” Jinjina kai Ummi tayi tana shirin yin magana Yassira ta ce ”Daga Yashjub! sai ni da d’an uwana twin brother d’ina Yassir! sai wannan Yasmeen! sai wachchar Ya’isha! sai Yusra sai y’ar autarmu Yadira!” Tana dasa aya ta d’aura da cewa”ku ne fa kuke ganin kamar cin fuska ne yin hakan ko wani abun na daban, alhalin mu al’ada kawai muke so mu raya, kuma munaso dangantakarmu da Amaryar ta samu kyakkyawan tushe!! Shine fa kawai!. Ku ne kuke ta dagula abubuwa, you guys should just let her bow down!(kawai ku barta ta durƙusa mana), a yi a wuce wajen.” Jinjina kai tsohuwar ta yi kafin tace “na ji, na fahimceki!” Sai kuma ta kamo Hannun Manubiya ta mik’ar da ita tsaye dakyar tukunna ta ce ”y’ar albarka!mu je ki gaidasu”. D’iff! Haka parlourn ya yi tsit, ba wanda ya iya cewa uffan! Ummi tana so ta yi magana amma ta san idan ta yi magana abun sai ya fi haka zafi dan tanada tabbacin maganar da Siyama ta yi musu tun farko ne ya sanya su yin wannan haukar.. Ahankali Ahankali sheshek’ar kukan Manubiya yake tashi a cikin parlourn…cikin rarrashi Iya ramma ta ce ”ki yi shiru, ki yi hak’uri ki je ki gaidasu, ki tafi d’akin ki. Aure fa ibada ne, dama haka abun yake sai kin yi hak’uri da duk wasu k’alubale da za ki fuskanta… ki yi hak’uri, ki yi ta hak’uri, ki rungumi hak’uri dan yanzu kika fara hak’uri…Indai har zaman auren kike son yi kuma aljannah kike nema…” Kamar Siyama za ta fashe da kuka tace”Iya ramma,ta Ina gaida su ya zama ibada??”. Cikin fushi da d’an fad’a fad’a Iya ramma tace “za kiyi shiru ko sai na hamb’are ki?” Cikin kuka Manubiya ta cewa iya ramma “ba zan fa gaidasu ba, ku maida ni d’aki ka…” Cikin katseta Iya ramma ta girgiza kai kafin tace “Manu ki yi hak’uri, kar ki ce haka, dangin mijinki ne su..ki kauda kai kawai kar ki biyesu”. Dariya Ya’isha ta yi kafin ta matso tace “Au wai itanma cewa ta yi A’a?. Wow! This is gonna be fun(al’amarin nan zai ƙayatar)…dan mu kam yau sai an yi Al’ada. Bari ki ga ta kaina ma za ki fara” Ta fad’i hakan tana mai matsawa kusa da Manubiyan ta tsaya a daff da ita…. Kowa shiruu yayi kawai yana kallon ikon Allah…tabbas waennan sun tabbata dabbobi! Wanne irin cin mutunci da cin fuska ne wannan haka a gaban mak’ofta da y’an unguwa saboda Allah… Kuka ne ya tahowa Jidda, dama a high take, shiyasa ta yi sauri ta juya ta shige d’aki. K’ok’arin juyawa itama Manubiyan ta fara yi…a hankali cikin tsananin mutuwar jiki Inna ta mik’e ta k’arasa inda take tace………….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 19* K’ok’arin juyawa itama Manubiyan ta fara yi…a hankali cikin tsananin mutuwar jiki Inna ta mik’e, ta k’arasa inda take dai-dai ita kuma ta gama juyawa, sai da ta juyar da ita tukunna a hankali murya cike da rauni ta ce ”durk’usa!” Shiruu Manubiya ta yi ta k’i motsi sai da Innaa ta sake cewa “durk’usa!” Tukunna a hankali ta durk’usa a gaban Ya’isha tana wani irin kuka. Jinjina kai Inna ta yi kafin tace “Allah ya yi miki albarka” Gaba d’aya parlourn a tare aka amsa da “Ameen” har su Yahanasu. A hankali Innaa ta cika ta ta kalli Iya ramma ta ce ”ki kaita ta gaida ragowar.” Mik’ar da ita Iya ramma ta yi suka nufi Baba larai, suna wucewa Inna ta yi sauri ta fice daga parlourn. Tana fita ta saki hawayen da take ta k’ok’arin rik’ewa…. Hatta Yadira sai da Manubiya ta je ta durk’usa a gabanta. Tukunna Yassira tace “Alhamdulillah, muna iya wucewa da Amarya yanzu tunda ta nuna zatayi biyayya. Once again, sorry fa! Idan na b’atawa wasunku rai, Al’ada ce ta zo da hakan.” Daga haka ta mik’e ta kalli Ummi tace “za ku iya fitowa da ita, ni na gama nawa.” Tana gama fad’in haka ta d’auke d’ankwalinta wanda ta shimfid’a ta zauna a kai ta yi gaba, a take Yasmeen da Baaba Larai suka mik’e suma suka bi bayanta. Suna fita su Yadira ma suka fice. Za’a fara maganganu da gulmace gulmace Iya ramma ta yi sauri ta mik’ar da Manubiya ta nufi k’ofa da ita, ganin haka yasa Umman su Siyama ma ta mik’e haka ma su Yahanasu. Su Maman Baraka sun shiga wajen Amaryar uncle basanan akayi show d’in, labari kuma yana zuwa musu da suka fito lokacin suka tarrar har an fito da Manubiya, sun so sun tarar sun ganewa idanunsu….. sallama suka yi wa Amaryar uncle suka bi bayan y’an kai Amarya, gudun kar a yi shima babu su. Babu yadda Manubiya bata yi ba amman haka tanaji tana gani suka hanata shiga wurin Inna wadda tun d’azu ta lura ta fita daga parlourn, ba tare da sun barta ta shiga d’akin nasu ba aka yi waje da ita aka saka ta a mota tanata kuka kamar ranta zai fita, Mata kuma sunata rangad’a gud’a!. Yahanasu tana fitowa daga gidan su Manubiya ta d’au waya ta kira Yashjub….duk abunda su Yassira suka yi sai da ta kwashe kaff ta gaya masa komai har abubuwan da suka faffad’a akan gadon Manubiyan d’azu da rana duk sai da ta fad’a masa. Ran Yashjub idan yayi dubu tou yau ya b’aci, shiyasa ko gama sauraronta ma bai iya yi ba ya kashe ya kira Yasira ransa a masifar b’ace yace mata ”kar ta kuskura ko da wasa ta k’arasa masa gida!Tunda mahaukaciya ce ita to ta kad’a kan ragowar mahaukatan su wuce gida! Idan kuma suka kuskura suka je masa gida to wallahi sai ya ba su mamaki. Iyakar b’arnar da suka yi masa ya Isa haka, kuma hakan ma su jira zuwansa gobe zai samesu, they will answer to him…” Tabbas yau mai rabata da Yahanasu sai Allah, dan tashi d’aya ta san itace ta gaya ma Yash! Abunda basa so ɗin kenan gashi kuwa tun yanzu ya fara korarsu yana cewa ‘kar aje masa gida’. Sun kusan Isa gidan lokacin da ya kirata, haka nan tana ji tana gani ta kira Yasmeen da Ya’isha ta zaiyyane musu tukunna ta ce ”su juya akalar motocinsu su nufi gida, Idan suka isa gidan sai a tattauna” Sai da kuwa suka yi wa Ya’isha da gaske tukunna ta yarda ta juya ɗin dan da farko cewa ta yi ‘wallahi sai ta je,’. Haka nan dai ta hak’ura, ta nufi gida tana jin kamar ta kama da wuta dan bala’i….. Guiwa a mugun sace sannan Zuciyoyinsu fal takaici da bak’in ciki suka k’arasa gida, Yasira tana ji tana gani matakinsu da su ka shirya na gaba ya tafi a banza, dan akwai abunda ta kuma shiryawa za su yi a gidan Amaryar…… ……. Maman Siyama da Iya ramma ne a gefe da gefen Manubiya, sai Maman Aisha a gaba. Kukan da takeyi sai da ta bawa kowa tausayi, Yassir kam wanda shine ya d’auki Amaryar ba k’aramin mamakinta yake ta yi ba, dan shi bai yi tunanin Amare suna kuka har haka ba bayaga hakan ma ita da za ayi mata gata!…Ita da za a d’auketa daga wannan garbage d’in a kaita aljannar duniya, ga kuma mijinta miji kamar Yashjub ta samu amma shine take wannan kukan!….. shiyasa gaba d’aya mamakinta ya rufe sa ya shiga tunani da kuma san ya nemo ‘ko dai akwai wani dalilin da ya sanyata kukan….’ “Mu je” Muryar Iya ramma ta katse masa tunani. Jinjina kai kawai ya yi daga haka ya kunna motar ya danna double signal, ragowar na gabansa da bayansa suna ganin haka suma suka tashi motocinsu da suka cika taff da jama’a, suka sanya double signal, suka fara k’ok’arin barin layin….. Komawa ciki Siyama ta yi domin ta je ta taho da su Jidda dan ta lura ba su fito ba. Sir Najeeb sam bai yadda ya bud’e motarsa a kowa ba, ba ya so Siyama ta hango shi ta k’i shiga kuma ba ya so a cika motar dan bai shirya d’aukar kowa ba sai su d’in, shiyasa ya ji dad’i sosai da ya ga har an fara tafiya su basu riga sun tafi ba. Dan haka ya gyara zaman motar tasa a dai-dai k’ofar gidan. Babu irin neman da Ya’isha ba ta yi masa ba….shi kam ya ganta sarai amma ya manna mata!.. Dan tana d’aya daga cikin dalilan ma da ya d’auko mota mai tint, kuma da ya zo d’in ya sake jin takaicinta dan tun daga farkon zuwan su har kawo yanzu da aka fito duk yana kallonsu, ba k’aramin haushi ta sake basa ba da yaga kalar shigarta! Kayan Jikinta da kuma yadda ta rufa mayafinta a iyaka Kai ba kaɗan ba ya bashi takaici….dan gaba d’aya jikinta a bud’e, gashi ta yi wa lace mai mugun tsada d’inkin fitted gown matsattse sosai kuma har da tsaga a baya! A rayuwarsa ko bai san Mace ba sam ba ya so ya ga ta yi irin wannan shigar…. Yana cikin wannan tunanin ya ga su Siyama sun fito ita da Jidda har da Munirat. Tsayawa kawai ya yi yana kallon yanayin shigar ta simple and cute, so breathtaking!. Yana kallonsu suka bud’e har motoci biyu amma babu guri. Haka kawai dama Siyama ta ji motar datake fake a k’ofar gidan bata burgeta ba, ganin ana shirin wucewa a barsu yasa ta ja hannun Jidda suka nufi motar…. Sai a lokacin ya sauk’e ajiyar zuciya. Bai ji dad’i ba da Munirat ta bud’e gaba ta shiga, ya so Siyaman ce ta zauna a gaba…tana shiga tace “laa!Ya Najeeb Ina wuni.” “Alhamdulillah” kawai ya ce a hankali ba tare da ya kalleta ba dan baya so Siyama wadda take shigowa yanzun ta fahimci shi d’in ne. Tana shiga ta rufe ta juya ta kalli Jidda ta ce “Da ikon Allah motar kuma empty ma” Yana jin ta rufe k’ofar ya sa lock ya kunna motar dai-dai itama ta fahimci ashe shi d’in ne dan gefen fuskarshi kawai ta kalla ta gane shi. Da sauri ya kunna motar ya bi bayan convoy d’in. Yana ganin ta tana ta k’ok’arin bud’e k’ofar amman ta kasa, dariya ta basa dan yadda ya ga ta had’e rai ba kad’an ba ta burgesa, abunda ya kasa fahimta guda d’aya shine ‘idan ta samu ta bud’e k’ofar motar shin fita za ta yi kenan a haka yana cikin tafiyar ko yaya?’….. Murmushi ne ya sub’uce masa wanda duk saida suka ji, daga nan ba wanda ya yi magana haka suka d’au hanya motar shiruu a haka har suka k’arasa gidan amarya Manubiya, dan tuni Yassira ta sa Yassir ya gayawa ragowar ‘ba sai an je gidan Mommy an gaida ita ba, direct kawai a wuce gidan amarya.’ …. Ko da su Yasira suka fito daga motocinsu babu wadda ta iya cewa k’ala har Baaba Larai, hakanan suka nufi cikin gidan kowa da abunda take sak’awa a cikin ranta…..ba k’aramin dad’i suka ji ba da suka hango Daddy zaune a main parlourn k’asa yana kallo, tashi d’aya Ya’isha ta k’ak’alo hawaye ta k’arfi da yaji, ganin haka ya sa su Yusra yin kalar tausayi suma. Yanayin su kawai Daddy ya kalla ya fahimci akwai matsala, shiyasa ya kafe su da idanuwa har suka k’araso suka shiga gaishe sa! Bai amsa gaisuwar tasu ba sai tambayarsu da ya shiga yi akan “mai ya faru?”. nan kuwa suka zauna suka shirya masa k’arya da gaskiya… A haka Mommy ta sauk’o ta samesu, ba k’aramin dad’i ta ji ba da ganin yadda Daddyn ya fusata matuk’a….ya na jinjina maganar tana kuma yi masa zafi…ta ya ana bikinka zakace ‘k’annenka kar su kai Amarya’ har da wani ‘kar suje masa gida’!. Tabbas da sake dan ba zai yiu ba,dole ya san abunyi!, bai aurowa d’ansa wadda zata raba masa kan ya’ya ba wallahi…! Hatta Baaba Larai zagewa ta yi suka yi ta shirya labarai ba kunya ba tsoron Allah dan ta san Daddy ba zai yi titsiye ya ce zai bi diddigi ba shiyasa suka shirga k’arya kala kala, kuma duk a bayanin nasu suna yi ne akan wai rashin fahimta suka samu su da k’annen Amaryar shine Yashjub ya bi bayan k’annen Matarsa har ta kai sa ga hanasu zuwa kai amaryar. Sai da suka tabbatar Daddy ya hau ya zauna daram! Tukunna kowacce ta zame ta wuce ciki. Dukda bak’in cikin dake k’unshe a cikin zuk’atansu game da auran da Manubiya da Yashjub d’in kansa sai da suka ji kamar su taka rawa, dan a yadda suka ga yanayin mood d’in Daddy sun san gobe akwai case!!!! Direct d’akin Mommy Baaba Larai ta wuce, a tsaye ta same ta kamar yadda ta yi zato, dan ɗazu suna tsaka da magana ta yi excusing kanta ta hawo sama… Baba Larai tana shigowa Mommyn ta k’arasa inda take tace”Ya ake ciki?” Tiryan-tiryan Baba larai ta zaiyyano mata yadda suka yi na ƙoƙarin ganin sun yi ammman Yahanasu ta kafa ta tsare ta hana a yi komai…. Dab’ass!!! Haka Mommy ta zauna akan gado ta yi shiru kawai dan ta ma rasa me zata ce. Ajiyar zuciya Baaba Larai ta sauk’e kafin tace “Ki yi hak’uri, wallahi d’azu shiyasa da suka zo chanja kaya na k’i yarda in shigo saboda banaso in baki mugun labari….so na yi idan aka tafi kaita ko da ace ta riga ta shiga gidan ne in samu in yi dan da babu gara ba dad’i to sai kuma Yash d’in ya hanamu kai Amarya. Amman kar ki damu, na hango mana wata hanyar da za mu iya bi cikin sauk’i mu yi nasara a kanta, shiyasa ma kika ga na hawo da kwarin guiwa ta.” Ba ta jira jin me zata ce ba ta d’aura da cewa “Yanzunnan yanayi da mood d’in da Daddy ya shiga daga jin bayanin su Yassira ya sanya na fahimci idan akace Yashjub da Matarsa su dawo cikin gidannan da gudu zai yarda…Daddy yana son Yash matuk’a na san dan babu yadda zai yi ne shiyasa tun farko ya barsa ya je ya tare a wani waje daban, amman in ta shine bai k’i su zauna a nan a bangaren Yashjub d’in ba kusa da shi tunda akwai space……yanzu a yadda na lura da shi ya fusata sosai ɗinnan iyakar abunda kawai ya kamata mu yi shine mu kuma d’aura sa akan ‘idan ya yi sake to Manubiya da y’an uwanta za su kwace masa d’a!’, ke kuma sai ki tado da maganar dawowar ta su nan, daganan inshaaAllah za ki ga yadda al’amari zai chanja, ni kuma daga nan zan karb’i aikin kuma muddin ta dawo nan d’in wannan karon kam InshaaAllah bazamu samu failure ba. Dan zaman ta a kusa da mu kamar k’arshen ta ne, tunda kinga ga ni! sannan ga Yaran nan waenda na san ko ba komai takurawa da baƙin cikinsu kaɗai ya isa ya korata… Sannan kinga duk wani abun da ba mu samu mun yi na yau ɗin a chan gidan nashi ba sai mu yi a nan inda zata zaunan, kafin ta taren. dukda dai na yau ɗin ya fi tunda shi aka fi buƙata a yi a yau(ranar shigowarta gidansa ta farko) amma da babu gara ba daɗi, sai a jarraba a gani..” Ita dai Momy da “to” kawai ta bi Baaba larai da , dan ba kad’an ba ta ji haushi kuma ta tsorata da ta ji tace “ba su yi komai ba” a ganinta tunda har basu yi d’in ba kuma ga abunda ita kanta baba larai d’in ta fad’a da farko akan abun to fa babu wani abu da zasu yi daga baya wanda zai yi tasirin da za su samu nasarar cire Manubiya a gidan….da sauri ta kawar da tunanin gudun ma kar tunaninta ya tabbata dan idan ya tabbata bata san kuma ya zata yi ba….cikin son bawa kanta kwarin guiwa ta d’aura gaba d’aya hope d’inta akan zancen dawowar Manubiya da Yash ɗin kusa da su. Sannan tana addu’ar Allah ya sa abunda su ka yi ya zauna a jikin Yash, Allah kuma ya sa ya riƙesa har su dawo gidan nata da zama dan yadda ake ɗokin amarcin nan dukda Baaba Larai ta tabbatar mata amma tana tsoron kar su je Manubiya ta samu ciki kafin ta dawo cikin gidan da zama...dan muddin suka dawo kusa da su ɗin to kamar yadda Baba Larai ta ce komai zai zo musu da sauƙi ne, shiyasa damuwarta ta fi ta’allaƙa akan kafin su zo kusan, dan zamansu su biyu a chan ango da Amarya abun da kamar wuya ace ba za su yi komai ba!….. Tana cikin wannan tunanin ta ji Baaba larai tace”sai kuma maganar Yahanasu itama ya kamata asake..” Dasauri Mommy ta katseta ta hanyar cewa “Larai mu bar maganar Yahanasu tukunna” Cikin tarar numfashi ta Baba larai tace”She is out of control… Yahanasun da na sani ko shegen duka su Yassira suka yi wa Manubiya bai kamata ace ta yi magana ba, kar fa Yarinyar nan ta zo ta yi b’aramb’atama wata rana.!” Kallon da taga Mommy tana yi mata ne yasa ta had’iye maganar ta ta kasa ci gaba da cewa komai. Ahankali Mommy tace “Dan girman Allah ki yi min uzuri akan case d’in Yahanasu Larai, ko me za ta yi kiyi min alk’awarin za ki tsaya akai mu gyara b’arnar da ta yi kawai, dan abunda kike tunani bazan iya sake bada goyon baya akai ba…na ga illar hakan!. A ganina Yahanasu k’aramin alhaki ce a halin yanzu da ke kanki kin san idan ba mu tsayawa kanmu ba komai mai iya faruwa ne, dan haka mu ajjiye batun Yahanasu a gefe mu maida hankali akan abubuwa da su ka fi mahimmanci….” Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin ta mike tsaye tukunna ahankali tace “inshaaAllah, duk yadda ki ka ce…sai da safe.”……… ….. Motar Najeeb ce ta k’arshe shiyasa basu samu damar yin parking a cikin gidan ba, sai a waje a bakin titi. Yana sane ya k’i bud’e side d’in Siyama, ita kanta ta fahimci shine ya k’i bud’e mata dan tare suka fara kokawar bud’ewa ita da su Jidda amman duk na su ya bud’u nata kuma shiru. Ganin tana ta bawa kanta wahala ne ya sa ta hak’ura da niyyar Jidda na fita itama za ta bi bayanta ta fice. Munira ce ta fara fita ta ce ”mun gode” Da murmushi ya amsata dan ba k’aramin farin ciki yake ciki ba..dramar Siyama burgesa takeyi..yadda ta had’e rai ta chuno Baki abun ba k’aramin dad’i yake yi masa ba. Jidda tana sauk’e k’afafunta k’asa ta juyo ahankali cikin nutsuwar ta tace masa”Mun gode” daga haka ta sauk’a a motar. Ganin Siyama har ta matso tsakiya yasa ya yi sauri ya juya ya sa Hannunsa ya janyo murfin motar yana me cewa “Ba komai Jidda” Yana dariya k’asa-k’asa yana kallon Siyaman, bayan ya tabbatar ya sake saka lock a duk k’ofofin. B’ata rai ta yi sosai kafin tace “Zan fita”. Murmushi ya yi tukunna yace “Ashe Inada aiki a gabana sosai ni ban saniba, dan handling Mace mai kishi Is not an easy task(ba ƙaramin aiki bane ba)”. Da sauri ta d’ago ta kalle shi, sai kuma ta kau da kanta kawai. Ganin ta ƙi cewa komai ne ya sanya ya ce “Amman naki kishin yayi tsauri sosai, ya yi yawa, dan Allah a d’an rage, atleast a bani dama in yi bayanin da zai wanke ni”. Cikin tarar numfashinsa tace “Ni fa ba kishi nake yi ba, bayaga hakan ma yaushe har na sanka….yau kad’ai fa na sanka ta ya zan yi kishi?? Infact babu wani abu a tsakanin mu ai! Kuma na riga na sani Ya’isha girlfrnd d’inka ce Ita za ka aura kowa ya sani…bai shafe ni ba sannan ba komai dan ka yi hugging d’inta saboda ba hurumina bane ba tsakanin ku ne ku da Ubangijinku. dan haka pls dan Allah ka daina cewa ina kishi saboda babu komai tsakanina da Kai sai mutuncin da muka yi a iyaka yau!. Babu ruwana da alaƙar ku Kai da Ya’isha!. Bud’e mini k’ofa in fita Pls.” Ta fad’i hakan tana mai sake matsawa kusa da jikin k’ofar dan ta samu ya d’auke Hannunsa yanzu. Ya d’an ji zafin yadda ta ce”ba ta kishinsa, amman sai ya kawar yace “Okay!In yi miki tambaya guda d’aya, za ki amsamin?” Kamar ba za ta ce wani abun ba sai kuma ta d’aga masa kanta alamun ‘yes’ ba tare da ta kalleshi ba. Sai da ya sake juyowa ya fuskanceta sosai kafin yace “D’azu, you were nice to me(kin yi min kirki),amman tunda kika ganni da Ya isha ki kalleni ma aiki ne a wajenki, kuma it’s obvious haushina kike ji, shin ta ya zaki yi min bayanin hakan ba a matsayin kishi ba?.” Wannan karon murmushi ya ga ta d’an yi…tabbas idan ba ta yi da gaske ba to mutumin nan ba barinta zai yi ba gashi kuma akwai wani abun game da shi wanda ta san idan har ba ta yak’i ta kuma fatattaki tunaninsa da shi kansa daga rayuwarta ba tou tabbas akwai matsala…tana tsoron kar ta je ta jangwalowa kanta abunda ba za ta iya ba, dan haka ta d’ago ta kallesa kafin tace”Bana kishinka! Kamar yadda na faɗa make ban ma sanka ba ballantana har in shak’u da kai wanda shak’uwar ce za ta janyo abunda zai sanya in yi kishin naka, kawai dalilin da ya sanya ka ga Ina guje maka yanzun shine har ga Allah...ka yi haƙuri da zan gaya maka hakan ƙiri ƙiri...amma sam ba na shiri da Abota, ni ko kirki ma ba na yarda in yi da Namiji irinka.” Shiruu ya d’an yi kafin yace “Namiji irina?,menene ni d’in??”. Itan ma sai da ta d’an yi shiru tukunna tace”Masu two timing! (Soyayya da mutum biyu a lokaci ɗaya), waenda a fuskar duniya ake yi musu kallon mayaudara!”. Kamar zai fashe da kuka yace “Siyama ni ba mayaudari bane ba, can you pls allow me to explain myself(dan Allah ki bani dama in yi miki bayani mana)”. Cikin katse shi kanta tsaye tace “A yadda ka karb’i numberna, da kuma yadda kake treating d’ina yau tun safe har daren nan, da ni da kai duk mun san inda zancenka zai sauk’a, bayan kuma ka riga ka san kana da wadda za ka aura, wadda kake so itama take sonka. Menene hakan kake shirin yi mini idan ba yaudara ba? Ko mata biyu za ka aura a lokaci daya? besides na san ma itan za ka aura tunda itace dai dai da kai, ni kawai a side kake da shirin ajjiyeni ka b’ata mini lokaci” Da sauri ya ce “idan za a bani zab’i ke zan zab’a, ke kad’ai!” Da sauri ta d’aga masa hannu tace “Plss…dan Allah, banaso in ci gaba da gaya maka maganganu masu zafi saboda dukda abunda ka yi min still Ina ganin girmanka sosai…. Na cire kunya na cire komai na gaya maka abunda yake raina da abunda na fahimta a kanka Wanda na tabbata hakan shine gaskiyar lamarin, dan haka dan Allah inaso ka fita hanya ta kwata-kwata. Bana son case da su Ya’isha, ba wai tsoron ta nakeji ba amman duk inda na kai ga iya fad’a ba zan had’a kaina fad’a da Mutanen da basusan darajar d’an Adam daidai da kwayar zarra ba. Dan haka dan Allah For the last time… Ka fita a hanya ta, sannan ka bud’e min k’ofa in fita.” Shiruu kawai ya yi ya tsura mata ido…bai ma san me zai ce ba! Dan bai san ta Ina zai fara fita a hanyar tata ba, shi da yake son shiga cikin rayuwarta amma gashi tashi d’aya ita kuma ta ce masa ya fita a hanyarta ma gaba d’aya!! Wanda hakan shine abu na ƙarshe da zai iya yi arayuwarsa, dan shi kansa ya san ba zai iya rabuwa da ita ba, ya tabbatar da hakan… Ba ta san yadda ya dinga fama da soyayyar ta sama da wata uku ba ne shiyasa har ta ke iya gaya masa hakan… Ba zai iya yi mata ma alk’awarin fita a hanyarta ko rabuwa da ita ba dan ya san ko ya yi alk’awarin to ba za ya cika ba. Ahankali cikin son ta fahimce sa yace “Siyama ba zan iya rabuwa da ke ba, ki yi hak’uri ki fahimce ni ki bani dama, ba zan tab’a yaudararki ko in cutar da ke ta ko wacce hanya ba, na yi alƙawari!” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “me ye tsakanin ka da ita, Ya’isha? Ka gaya min gaskiya kawai! dan Allah” Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce “She s my girlfriend(budurwata ce)”. Yadda kalmar ‘She’s my girlfriend’ ta daki k’irjinta Ita kanta sai da ta yi mamaki. Da kyar ta iya cewa “kuma har yanzu kuna tare ko?” Still sai da ya d’an runtse idanunsa na y’an sakanni tukunna ya bud’e yace “Eh! Amma Siyama wallahi ke nakeso, kuma ba wai haɗa ku biyun nake shirin yi ba, very soon ita ɗin zan yi mata bayani ta yadda za ta fahimce ni cikin sauk’i, zan rabu da ita InshaaAllah… Ni da ke haɗi ne daga Allah, ki d’an ba ni lokaci, zan yi mata bayanin komai….” Da mamaki Siyama ta tsaya kawai tana kallonsa kafin da kyar tace “Ka na ji da fahimtar abunda ka ke faɗa min kuwa?” Bata jira ta ji abunda zai ce ba ta d’aura da cewa”za ka rabu da ita saboda ni??” Da sauri yace”Yeah” sai kuma ya sake cewa”tun ba yau ba Ina…” Girgiza kai kawai ta yi cikin katse sa tace”pls………”sai kuma ta runtse idanunta kafin ta kama handle d’in k’ofar tace “zan fita!” Da sauri yace “You ask for the truth(ke kika nemi jin gaskiya) shiyas…” Bud’e idanunta ta yi kamar zata fashe da kuka tace “Ka bud’e min k’ofa in fita! Wai ta ya kake tunanin zan iya yarda da kai..in yi trusting d’inka? ka bar wata saboda ni! Ka ga kenan in ka had’u da wata a gaba nima ka rabu da ni saboda ita ban Isa in ce zan ji haushi ba!” “Ba haka bane, abun namu akwai sarƙaƙiya a cikinsa ne, its complicated, ki fahimceni dan Allah” Cikin takaici ta kallesa sosai tace “Ta yaya ya ke da Sarƙaƙiyar?? Complicated how?” Tashi d’aya zuwa yanzu Najeeb ya fahimci ya riga da ya jagula komai da hannunsa, ga shi ya lura Siyaman ta zuciya sosai dan idanunta da kan hancinta sun d’an yi jaa! shiyasa kawai ahankali ya sa hannu a gefen seat d’inshi ya bud’e mata motar, yana shirin ce mata ‘ya bud’e’ kawai ya ga ta bud’e ta fice da sauri dan yana dannawa ta gane ya bud’e ne. A ranta tace “baka da abun fad’a ai dole ka bud’e min. Mayaudari kawai…….” Juyawa kawai ya yi ya jingina a jikin kujerar da yake zaune a kai ya yi shiruuu….idan akwai abu ɗaya wanda ya ke da tabbaci akai to shine ‘ba zai tab’a iya hak’ura da Siyama ba’ Ko menene zai faru sai dai ya faru amman Siyama tashi ce da izinin Allah. Kawai dai kamar yadda ta fad’a anya ba zai zalinci Ya’isha ba idan ya yi hakan? Ga shi shi harga Allah ba zai tab’a iya auren mata biyu ba, tsarinsa na mace d’aya ne tun farko, bayaga haka a yadda yakejin soyayya da k’aunar Siyama 95% da kuma yadda yakejin na Ya’isha da bai wuce 5% ba ya san idan ya had’asu su biyu a matsayin matansa to tabbas akwai matsala dan ya san ba zai tab’a kwatanta adalci ba. Ko a lokacin da yake tare da Ya’isha shi dai ya san yana sonta amman bai san zafin so da asalin mene shi so d’in ba ma sai a kan Siyama….. Kaff y’an kawo amarya babu wanda bai shiga shock ba! Dan tun daga gate da compound suka fara ganin ikon Allah….an san dama Mijin yana da kud’i duba da yanayin kud’in da aka bayar lokacin da aka zo saka rana da kuma lefe amman sam ba su yi tunanin ya kai har ba, dan a kaff cikin su 5% ne kawai suka tab’a sanin akwai Irin gine ginen nan ma a Nigeria, ga furnitures kamar ba za a mutu ba!Tabbas Manubiya ta dandalo arzik’in, dan a kaff area d’insu babu y’ar da ta tab’a dandalo kalarsa….Ah lalle kam dole dangin miji su ce ta durk’usa uwarta kuma ta amince, yo idan sune ko kwanciya akace y’arsu ta yi ai sai ta yi wallahi, Irin wannan aljannar duniya haka gida kamar ba a Africa ba….. Haka nan dai suka dinga mamaki da zancen zuci waenda kuma ba za su iya dannewa ba suka koma gefe aka shiga tattaunawa…….. Tun case d’in Baraka da Ya Musbah su Maman Abbakar ba kula su Manubiya sukeyi ba sai yau! Yadda Maman Baraka ta ga Manubiya ta samu duniya ne ya sa hankalinta ya sake tashi ta kuma bada goyon baya akan y’arta ta koma gidan Ya Musbah dan ko banza yanzu kam Musbahu ba shi da nauyi a kansa dan ta san duk Manubiya za ta d’ebe komai, wataƙila suma su samu su dandala…… Ba a fara barin gidan Manubiya ba sai wajajen 11 na dare…shima kuma sai da Yash ya kira Najeeb yace “Idan bai zo sun fara kwasar jama’a suna maidawa gida ba to wallahi zai shiga gidan da kansa ya ce musu ‘dare yayi”’ Najeeb ya san tsaff Yash ɗin zai iya aikata hakan, shiyasa ya mik’e ya dauk’i makullin motarsa ya fice, gaba d’aya gab’ob’in jikinsa na masa ciwo, ga tension da tunanin ta Ina zai fara da Siyama da Ya’isha dan gaba d’aya kansa ya d’aure…. …. Zuwa yanzu gidan ba kowa daga Manubiya, Jidda, Yahanasu sai Aisha, Siyama da Munirat….Su Najeeb sun tafi kai wasu a cikin Mutanen su dawo. A tunanin su su ne za su d’auki su Siyama ma su maida su gida, nan kuwa ba su san tuni su Siyaman sun cewa su ya Nafi’u idan sun gama za su yi musu magana, ba. Suna zaune gaba d’ayansu sukaji kamar an shigo parlourn bedroom d’inta, dan haka da sauri Yahanasu ta lek’a.. dariya ta yi kafin ta ce ”Au Yassir!Asahe kai ne, ai na yi tunani angon ne” Bai damu da yadda ta tsaya ta tare k’ofar d’akin ba, haka ya kutsa ya fara k’ok’arin shigewa, ganin kamar zai shige jikinta ne yasa ta d’an matsa tana cewa ”babu kyau fa shiga d’akin Amarya”. Sai da idanunsa suka sauk’a akan Jidda wadda yake ta faman nema tun d’azu ya samu ya d’an nutsu tukunna ya juyo ya d’anyi mata murmushi kafin ya ce ”Really! In ji wa?” Ya fad’i hakan yana me maida kwayar idanunsa ga Jidda wadda ta had’e rai ta tamke fuska amman fa a chan k’asan ranta tsorone ya lullub’eta…dan tun d’azu ita kuma take ta k’ok’arin b’uya gudun kar su had’u, yanzu kam tana ganinsa gaba d’aya hankalinta ya tashi! Sam bata son Yassir, dan idan akwai mutanen da bataso ta gani yanzu to Yassir ne sai su Yassira. Muryarshi ta tsinkaya kawai yana cewa”Jidda mu je Ko” Ya fad’i hakan yana kallonta. ‘Dum!!!’ Haka k’irjinta ya bada kafin a ranta tace “Lalle wannan mutumin bashi da hankali…yanzu shi har yana tunanin zan iya tsayuwa a k’ark’ashin inuwa d’aya ma dashi bayan abunda yayi min ballantana har in bisa… In bisa ya k’arasa rungumar da d’azu bai samu damar yi ba kenan…” Yahanasu ce tace”Ai sun kira brother d’insu, zai zo ya d’auke su” Sai da ya d’anyi shiruu kafin yace”Am..siyan baki za su yi, Yash yana k’asa, a yadda na gansa d’innan na san idan ba su yi sauri sun sauk’a k’asan ba to za su yi loosing (rasa) kud’in siyan bakin…dan da kyar muka tsaida shi da ni da Najeeb, kema ku yi sauri ku wuce, ku basa space, dan na lura a matse yake..” Da sauri Yahanasu ta ce “A’uzubillahi” Sai kuma ta kai masa duka. Kaucewa yayi yana dariya Idanunsa suna akan Jidda wadda ta runtse idonta da k’arfi tana mamakin rashin kunya da tsaurin ido irin na wannan bawan Allah. A hankali Munirat ta sunkuyar da kanta k’asa…a ranta tana aiyyana shin shawarar da ta yanke anya kuwa ta yiwa kanta da rayuwarta adalci kuwa. So take yi kawai wani ya bata go ahead yace ta yiwa Yassir duk abunda yakeso amman daga Ummi har sister d’inta sun kora mata zazzafan warning akan Yassir sun ce ta rabu da shi, sun k’i ma su tsaya su saurareta kuma tun ganinsu tare da Ummi ta yi gaba d’aya sun k’i su sake da ita balle su ji cikinta sosai ta yadda za su fahimce ta…ita kuma gaskiya ba za ta iya rayuwa babu Yassir ba, ga shi ta lura ko ta kanta ma ya daina bi, ta san kuma yana samun guri a wajen Jidda shikenan tata ta zo k’arshee…. Ba ta Ankara ba kawai ta ji hawaye sun zubo mata, da sauri ta yi firgigit ta sake yin k’asa da kanta tukunna ta sa hannun ta goge, sai a sannan ta ji muryar Yahanasu tana cewa”Munirat ko bacci kika fara ne daga sunkuyar da kan da kika yi yanzun nan?” Sai da ta d’an gyara fuskarta da style tukunna ta d’ago tana murmushi tace “A’a” Daga haka ta mik’e tsaye tana gyara mayafinta. Shi Yassir harga Allah sai yanzu ma ya ganeta, shi fa idan ba ganinta ya yi ba wallahi mantawa yakeyi da ita. Ya san sun had’a ido lokacin da ya shigo amman sam hankalinsa ba ya wajen shiyasa ma bai wani fahimci ita d’in ce ba….. .. Aisha cewa ta yi ba zata je ba, haka itama Yahanasu.. sai da Yahanasun ta saka baki tukunna da kyar Jidda ta mik’e ta yarda za ta je….. ba kad’an ba k’irjin Munirat ya dinga bugawa dan ba ita kad’ai ba Hatta su Aisha sai da suka lura da yadda Yasir ya ke bin Jidda da ido….. Babu Yadda Yassir ɗin bai yi ba akan a barsa ya ga fuskar amarya a cewarsa “ai shima zai iya yaye lullub’in tunda k’anin ango ai ango ne”amman k’iri k’iri Yahanasu ta hanasa….haka nan yana ji yana gani ya hak’ura suka fita,ya so ya ga fuskarta sosai wallahi dama yanzu ne chance d’insa na yau dan ya san Yash ba zai tab’a yarda ya rakosa ba. Yassir ya so ya d’an wanke kansa a wajen Jidda amma sam ta k’i ta basa damar ya yi mata magana ma, haka nan ta mak’ale a tsakiyar su Siyama har suka sauk’a. A k’ofar parlourn chan k’asa dama Najeeb ya tsayar da Yashjub k’iri k’iri ya hanasa shigowa ko cikin parlourn ya ce “wallahi yau sai yayi al’ada” gashi ya tusa shi a gaba da tsiya da zolaya…tun Yashjub yana fushi wai ko Najeeb d’in zai hak’ura har ya hak’ura ya d’an fara dariya kad’an-kad’an. A haka su Siyama suka sauk’o suka samesu, sai da ya hangesu tukunna ya bar Yashjub ya shigo ya zauna… Shiruuu parlourn ya d’auka bayan duk sun zauna, su Siyama basu tab’a sanin ma yadda ake siyan baki ba, Munirat kuma tana d’an shakkar Yashjub sannann ga tunanin Yassir shiyasa ta yi shiru. Tashi d’aya suka fahimci bama su iya siyan bakin ba shiyasa kawai Yassir ya fara dariya k’asa-k’asa Ganin za a rainasu ya sa Siyama ta yi k’arfin halin cewa “Siyan baki za mu yi” Murmushi duk sukayi kafin Najeeb yace “Ai ba ku za ku yi siyan bakin ba mu ne za mu yi,ko??” Yayi mata tambayar yana murmushi Nan ma duk shiru sukayi dan dama itace me d’an bakin to kuma Najeeb ya sako Baki shiyasa itanma sai ta ja tayi gumm! Ganin suna b’ata masa lokaci ne ya sanya Yashjub dag’owa ya kalli Munirat yace”Munira bani acc number d’inki” Dariya sosai Najeeb da Yassir sukayi. Cikin nutsuwa ta karanto account number Yashjub yana shirin turawa Najeeb ya ce masa “wait mana!ba kaara?bari inyi ai wannan aikin mu ne ba naka ba..” Dama Munirat ta yi expecting kud’i masu nauyi amman bata yi tunanin har 1.5M ba. Murmushi tayi tace sun gode daganan ta mik’e tace “bara muje mu sauk’o da amaryar, da sauri Yashjub yace “Wacce amaryar kenan?” ya fad’i hakan yana gyara zama sannan ya d’an had’e fuska. Nan ma dariya suka yi hadda Siyama kafin Najeeb yace “Kwantar da hankalinka muma mun gaji, tafiya zamu yi, muje mu huta” sai kuma ya kallesu yace “ku saukk’o mu tafi.” “To”kawai Munirat tace daganan suka nufi sama gaba d’ayansu. …… Nasiha sosai Aisha da Yahanasu sukayi mata, bayan fitar su Munirat, har sai da suka taso mata da tsumin kukanta, sannan Yahanasu ta yi welcoming d’inta warmly into their family. Dare ya yi sosai, sun san idan aka tsaya sallama shima wani b’ata lokacin ne, shiyasa iya su biyun suka yi mata sallama, suka d’aukarwa su Jidda jakankunan su… Da kyar kuwa ta saki Hannun Yahanasu dan sai yanzu wani tsoro da fargaba suka rufeta, gashi haka kurum sam sai ta ji bata so a tafi a barta ita kad’ai….. Aisha ma har da y’ar kwallar ta, haka nan tana hawaye tana waving d’inta har suka fice suka rufe mata k’ofar d’akin nata, dai-dai su Jidda sun k’arasa hawowa dan haka suka yi sauri suka basu jakankunan su, suka ce su wuce gudun kar ma ta ji muryoyinsu ta ce za ta fito…….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 20* Tun lokacin da aka faara siyan baki dama Siyama ta turawa Ya Musbah message, shiyasa dai dai sun hau sama kenan Ya Nafi’u ya kira Aisha ya ce “su sauk’kk’o sun zo” Sun so yi wa Manubiya sallama amman Aisha ta hanasu ta damk’a musu jakunkunan su tace su tafi…hakanan suka je suka yiwa Yash sallama tare da fatan alkhairi suka wuce. Yahanasu ce ta d’auki Munirat a motarta dan ita bata fito da tata ba,suma suka wuce….Yassir ma sallama kawai ya yi masa ya wuce. Najeeb ne sai da ya d’an tsaya ya yi masa y’ar guntuwar nasihar rik’e alkawari da amana kafin shima ya yi masa sallama ya wuce Yash d’in yana ta godiya. Sai da ya ga fitar Najeeb d’in tukunna ya k’arasa cikin motarsa ya dauki duk abubuwan da ya sissiya ya wuce cikin gidan, yana shiga ya maida main door d’in ya rufe yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya…kamar a mafarki haka yake ji wai yau shine Angon Manubiya! Alhamdulillah Alhamdulillah ya yi ta maimaitawa, kafin ya saita gabas ya durk’usa ya sanya goshinsa a k’asa ya yi godiya ma Ubangiji Subahanahu wata a la!. Kitchen ya nufa, ya harhad’a komai, da decorations d’in, tukunna ya fito ya nufi sama. Sai da ya fara duba d’ayan d’akin tukunna ya lek’a d’akin gym d’insa, dan dama ya san wataƙila anan su Aisha za su ce za su jera kayan gadon da suka nace sai sun yi…ai kuwa yana bud’ewa ya hango ta zaune a kan gadon wanda aka shimfid’awa wani had’add’en bedsheet mai tafe da wani k’ayataccen quilt da pillows farare tas tas, masu tsananin kyau da d’aukar hankali. Ba kad’an ba ya ga d’akin ya yi masa wani irin masifaffen kyau, sannan tashi d’aya ya ji wani irin sanyi da annashuwa sun lullub’esa. gadon tun a kallo ɗaya ake fahimtar ba mai tsada bane ba amman kasancewarta a ciki ya sanya ya ga gaba d’aya kaff gidan babu wajen da ya kai ya wannan a kyau da bashi peace of mind(kwanciyar hankali)… Sallama ya yi mata, kafin ahankali ya fara takawa zuwa inda take… Tun kafin ya kaiga k’arasawa gareta ya fara jiyo sheshshek’ar kukan ta….. Ba ita ba, hatta shi zuwa wannan lokacin yanayi na bugun zuciyarsa ya tsananta…itakam dama tun lokacin da ya rufe k’ofar falon ta fara jin inama akwai inda za ta je ta b’uya!…. Yadda yake takawa zuwa inda take haka take jin takun nasa kamar a kan k’irjinta yakeyinsa…. Sai da ya ƙarasa dai dai kanta tukunna ya ja ya tsaya kafin a hankali ya durk’usa a gabanta, sannan ya saka hannu ya yaye hular alkyabbar. Shiruu kawai ta yi ta lumshe idanunta tare da damk’e hannuwanta guri d’aya wanda hakan ya sake bawa hawayenta damar sauk’a akan kumatunta… ajiyar zuciya ya sauk’e yana mai jin takaicin su Yassira yana sake lullub’esa, dan ya tabbata har da bak’in cikin abunda sukayi mata ne yasanya tsadadden hawayenta k’in daina zuba. ba zai yi mata maganar ba, dan ba zai sako ta a ciki ba amman idonsa idon su Yassira gobe tabbas sai ya ci uban su!. A hankali ya mik’e ya zauna akan gadon gefenta, kusa da ita sosai!! Har cinyarsa tana gogar tata, kafin a hankali ya ɗan gyara ya fuskanceta sosai sannan ya sa hannayenshi biyu ya yi cupping fuskarta a cikin tafukan Hannayensa tukunna ya shiga share hawayen nata da babban ɗan yatsanshi still yana rik’e da fuskar tata bai cika ba, yana kallonta yanajin wani sanyi yana ratsasa. Maimakon kukan ya ragu sai yaga hawayen nata ma k’aruwa sukeyi dan haka kawai sai ya janyota zuwa jikinsa ya rungumeta da kyau! Ta yadda hatta yanayin yadda zuciyarsa take bugawa tana iya ji. Kamar zai fashe mata da kuka ya ce “Dan Allah ki daina! bana k’aunar ganin hawayenki, inshaaAllah babu kuka a gidana, ba zan baki dalilin yin kukan ba da yardar Allah, na dad’e da yi wa kaina alk’awarin ba za ki yi kuka a gidana ba! Zan baki dukkan farin ciki da jin dad’i!…. Dan haka kar ki fara karya min alk’awarina tun yau, pls, dan Allah ki daina kuka..” Jin yadda yake ta had’ata da Allah itakuma ta gagara tsaida hawayen nata ne ya sanya ta d’ago a hankali ta d’aura Hannunta a kan Bakinsa, kafin ta shiga girgiza masa Kai, alamun ya yi shiru ya daina rok’onta, a lokaci guda kuma ta samu ta tsaida hawayen nata. Shirun kuwa ya yi, ya shagala da kallonta yana mai shak’ar kamshin da itakanta ta ke yi da kuma d’umi da kamshin da hannun nata sukeyi..wanda tashi d’aya ya ji yanayinsa ya fara chanzawa. Itanma dakyar ta iya d’auke idanunta a fuskarsa ta sunkuyar da kanta k’asa tukunna Ahankali tace “Ina wuni!” tana mai jinta kamar ta fi kowa zama safe a duniyarnan kasancewarta rungume a k’irjinsa. Murmushi ya yi mai had’e da dariya, kafin ya lumshe idanunsa cike da shauk’i yayi kissing tafin hannunta wanda ke a kan bakinsa. A hankali ta fara k’okarin zamiye hannun nata dan tashi d’aya sak’onsa ya dirar mata ya shiga ratsata ta ko Ina. Ruk’o hannun ya yi da sauri, kafin ya samu ya bud’e idanunsa da suka fara chanja launi, tukunna yace”Lafiya Alhamdulillah amarya ta kuma uwargidana” Sunkuyar da kanta kawai ta sake yi tana murmushi k’asa k’asa….dai dai kunnenta ta ji ya ce”Tunanin me kikeyi ne haka bayan gani a gabanki?” Ya fad’i hakan cikin d’an turo baki sannan yana mai sake ruk’umk’umeta… Yanayin yadda ta ji k’irjinsa ya shiga bugawa fiyeda da ne ya sanya ta d’an d’ago a hankali tace”zan sha ruwa” Dariya sosai ta basa amman sai ya dake, wata nannuyar ajiyar zuciya ya sauk’e tukunna ya cikata da kyar dan wani irin shauk’i ne yake jansa….mik’ewa ya yi ya d’an daidaita kansa tukunna yace”muje!na had’a mana dinner a k’asa”kafin ya juya ya cire hularsa ya ajjiyeta a gefe tukunna ya mik’a mata hannunsa yace”Bismillah” Ba kayan d’azu bane a jikinsa amman shima wannan d’in fari ne k’al, jamfa, yanayin d’inkin mai masifar kyau. Ahankali ta mik’e tsaye ta shiga gyara zaman alkyabbar ta harda sake rufa hular… Murmushi kawai ta ga yayi kafin ya matso ta sosai tukunna ya sa hannu a gaban rigar ya shiga b’alle bottons d’in alkyabbar, sai da yakai har ciki inda bottons d’in suka tsaya tukunna ya sa hannunsa a bayanta yad’an turota jikinsa kafin ya ja alkyabbar k’asa ta tafi ta fad’i a wajen. D’inkin lace ne a jikinta…..ba k’aramin tafiya kuwa ta yi da imaninshi ba dan lace d’in da d’inkin da ita kanta gaba d’aya sunyi masifar yin kyau! Dama ita Allah ya yi mata sura mai kyau gashi d’inkin an yi sa ne style d’in fitted gown, yayinda d’ankwalinta ya d’an yi baya gashin gaban goshinta da rabin na kanta duk sun baiyyana a waje, sai shek’i suke yi…..Shiyasa Yash ya ma kasa magana dan shi kam an tashi kansa, bai tab’a ganinta a irin yanayin nan ba, bai tab’a samu ya k’are mata kallo kamar hakan ba, gashi rigar kusan rabin k’irjin duk a net yake… Ganin kallon yak’i k’arewa ne yasa ahankali tace”Muje” tana mai jinta gaba d’aya a takure ga wani kunya da fargaba da suka lulub’eta. Hannayensa ya sark’e around her waist, cikin lumshe idanu da bud’esu ya ce”Anya dinner d’innan za ta yiu kuwa?? Na fara ganin dishi-dishi wallahi…” Da sauri ta d’an ja baya, sai kuma ta yi gaba ta wuce ta gefen sa da hanzari tana mai jin yadda k’irjinta yake dukan uku-uku. Murmushi kawai yayi kafin ya juyo yana wani Irin kallonta, tukunna da kyar ya d’aga k’afa ya fara takawa nan inda take tsaye ta juya baya tana wasa da y’an yatsun hannunta…….. Ya zagaya k’asashen duniya daban daban amman zai iya cewa bai tab’a ganin mace mai kyawun structure kamar Manubiya ba har ma fuska bai tab’a ganin mace mai yanayin irin kalar kyawunta ba….ya san kuma soul d’insu ne ya had’u saboda yanada tabbacin ko da ace ba hakan take ba looks ɗinta ba haka duke ba, dole dai zai kamu da sonta…bai san ya zai yi ba da ace bai sameta ba, shiyasa ya ke ta daɗa godiya ga Allah s w t da ya amsa Addu’o’insa ya bashi ita, kuma in sha Allahu sauƙa da sadaƙar da ya rarraba aka dinga yi tun lokacin da auren ya matso har kawo yau akan ‘Allah ya tabbatar masa da alkhairi, ya kuma kaɗe duk wata fitina!’ ba za a daina ba, zai yi ƙoƙari a ci gaba da yi, na ‘godiya ga Allah’, har zuwa wani lokaci, dan shi kam Ubangiji ya yi masa babbar kyautar da bai ma san yaddda zai fara godiya ba… Tana tsayen, ta ji shi a bayanta, kafin ta matsa ko ta yi yunƙurin yin wani abun ma ta ji ya yi sauri ya d’aura hannunsa akan flat tommy d’inta (shafaffen cikinta), kafin ahankali ya ce ”da gaske fa na daina jin yunwar” Dasauri tace”Cikina har ciwo yake min tsabar yunwa”. Dariya ta ji yayi wadda har sai da d’umin numfashinsa ya addabi wuyanta, kafin a hankali ya yi kissing wuyan dan yadda d’ankwalin nata ya tunkushe ya zame both daga saman goshinta da kuma k’eyarta ya had’e da ribbon d’inta hakan ba k’aramin kyau yayi masa ba….a yadda yake tsaye a bayanta ba k’aramin kyau sajen k’eyartata da bak’ak’irin d’in sumarta suka yi masa ba shiyasa ya kasa hana kansa appreciating moment ɗin, cikin sake shigewa cikin jikinta ya sake sakar mata wani passionate peck a wajen, ya san zata matsa dan haka ya yi saurin sake ruk’ota da kyau da dukkan hannuwansa biyu. Yadda jikinta ya fara karkarwa shi kansa sai da yayi mamaki… dan ba kaɗan ba ta taɓu sakamokon abunda ta ji a jikinta wanda abubuwan da ya yi mata suka haifar, da kuma abubuwan da ta ji daga gareshi wanda ya janyo tsoron da ya bada gudummawa wajen kiɗimata. A hankali ya durk’usa, ya d’ago k’afafunta ya tallafota, kai tsaye ya d’auke ta gabad’yanta in a bridal style..wanda hakan ya sanya ta runtse idanunta sannan ta yi saurin zagaye hannayenta a wuyansa, a haka ya nufi k’ofar ya fita da ita daga cikin ɗakin, gwanin ban sha’awa. Har suka nufi stairs bai ajjiye ta ba kuma bashi da niyyar ajjiyetan, dan haka tace “Inada nauyi fa” Kallon d’an mitsitsin bakin nata yayi da idanunta waenda suke a lumshe har yanzun kafin Ya yi murmushi ya ce “Ni kuma Inada k’arfi..” Bai ajjiyetaba sai da suka shiga cikin kitchen tukunna ya ajjiyeta a hankali. Da kyar ta d’an zame hannayenta da ta sak’ale wuyansa da su, suna masu shak’ar numfashin juna… sai da ta daidaita tsayuwar ta, tukunna ta fara k’ok’arin bud’e idanunta. Facing juna sukeyi itada shi, shiyasa tana bud’e idanun nata suka had’a ido yana yi mata murmushi kafin ya ce ”I made it for you(na haɗa ne domin ki)” A hankali ta fara juyawa…tun kafin ta gama juyawa ta fuskanci mini dining table d’in ta fara murmushi.. Ba wani uban decoration yayi mai yawa ba, just simple amma mai kyau gwanin burgewa sannan a take ya yi masifar tafiya da imaninta…….flower bouquet ne mai asalin kyau a ajjiye a kan dining d’in da card a ciki, sai ballon guda d’aya babba da aka sak’ale ta sak’k’o kan dining d’in da rose’s masu kyau zub’e a k’asa, da kuma kan dining d’in sai abincn da ya jera a kai ‘drinks da chicken’ sai candles da ya kunna y’an kad’an a kan dining tabble d’in. A hankali ta ji ya rungumeta ta baya kafin yace “da fatan ya burge ki” Murmushi tayi ahankali ta jinjina masa kanta alamun ‘yes!’ Ajiyar zuciya ya fesar yace “Alhamdulillah” Kafin ya sake kwarin ruk’on da yayi mata yana mai sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere. A hakan suka tsaya kowannen su yayi shiruu kawai. Ita ta fara kawo k’arshen shirun sakomakon yadda ta ji yanayin tsayuwar tasu da komai ma yana shirin chanjawa, shiyasa ta d’an muskuta. numfashi ya fesar , kafin yace”Oh sorry.. Mu je ki ci abincin ko?”. .. Ahankali ta sa Hannu ta fara d’aukar note d’in jikin flower ta shiga karantawa, ai kuwa har da y’ar kwallarta dan ba kad’an ba kalaman soyayyar da ya rurrubuta suka shige ta suka ratsata…cikin jan hanci ta juyo ta ce ”Thankyou, I love it and I love you more..” Wani irin blushing (murmushin) ya shiga yi tukunna suka rungume juna a wajen suna ji kamar su cinye juna dan so, sun jima a hakan kafin ya ruk’o hannunta suka k’arasa kan kujerar dining table ɗin suka zauna…Sam Manu ba ta ji dad’in cin abincin ba kuwa dan a kan cinyarsa ya d’aura ta kuma shi ya dinga bata a baki, tana ci yana bata labarai kala kala Childhood d’insa da schools d’in da ya yi, sai da ya ga ta d’an sake kuma ta ci sosai tukunna yace “suje su yi sallah”…..Loma d’aya kawai ya iya yi shikam kuma hakan ma dan ta tilasta masa ne saboda sam shi kam ba zai iya wani cin abinci ba, ba wai baya jin yunwa bane kawai dai ya riga ya san bakinsa ba zai iya d’aukar taste d’in komai ba a halin yanzu. Ganin kamar zai yi mata kuka ne yasa ta hak’ura ta tsaya kallon ikon Allah Babba yana shagwab’a! Sai da ta rurrufe ragowar abincin ta saka a dank’areren fridge d’in da ke a kitchen d’in tukunna ta yarda su fita d’in dan har ga Allah bata so su fitan, gashi gaba d’aya kunyar shi ita takeji ma, shiyasa taketa k’ak’alo aiki. Shi kam kallonta kawai yakeyi yana rik’e da hannunta har ta yi ta gama. Ganin yana shirin d’aukarta kamar d’azu ne ya sanya ta fincike hannunta ta fice da sauri tana murmushi…murmushi shima yayi ya fito a kitchen d’in yana y’ar dariya yace”First position fa nakeyi a race lokacin Ina skul! Are you sure za ki iya tsere min??” Yayi mata tambayar yana nufota da d’an sauri Sai da ta d’an rik’e k’asan gown d’in jikinta tukunna ta d’iba a guje ta yi sama wanda hakan yasa ya fashe da dariya sosai dan bai yi zaton za ta iya gudu kamar haka ba, shiyasa kamar jira yakeyi ya bita shima a guje. Batasan lokacin da ta yi ihu ba! Sanda ta juya ta ga har ya kusan kamota saboda ba kad’an ba ta ji tsoron yadda ta ga har ya kusa kamotan, dan haka ta k’ara k’arfin gudun nata….saida suka kai cikin bedroom d’inta tukunna ya samu nasarar cafkota!da sauri ta ce ”Yi hakuri dan Allah”. Dariya yayi sosai kafin ya d’auketa d’in da bataso….direct ya nufi toilet da ita…. Sai da suka shiga cikin shower glass tukunna ya ajjiyeta ya kunna gaba daya shower d’in da suke cikin wajen ya daidaita d’umin ruwan. Nervousness (fargaba), ne yasanya ta kasa cewa komai, ta sunkuyar da kanta k’asa, tana jira ya fita ta samu ta yi wanka, dan tana buk’atar yin wankan….Ahankali ta ji ya matso wanda hakan ya sanya fargabarta ƙaruwa, cikin kasala ya sa Hannu ya zare d’ankwalin kanta za ta yi magana yace mata “shhh…” Daga nan ya fara rabata da su ƴan kunnaye ribbon agogo har sark’a da zobune sai da ya cire mata su duka. Sai da ta ga yana shirin cire gown d’in tukunna ta san da gaske fa yake…..ba ta gama shiga mamaki da al’ajabi ba sai da ta ji ashe shi wankan ma tare yake so su yi….. Da kuka da lallami ta samu ya kyaleta ya fita da kyar, sai da ta fito har closet ta zuge glass d’in wajen ta mayar ta rufe, tukunna hankalinta ya d’an kwanta ta koma cikin massive bathroom d’in ta rufo k’ofar…. brush ta fara yi da sabon toothbrush d’in da su Aisha suka jera mata tukunna ta yi wanka da ruwa mai ɗumi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sannan ta d’auro alwalla ta fito. Ta san Yashjub zai yi fushi amman idan ta fito sakawa k’ofarta key zata yi sa k’arata da safe, dan wallahi wani irin fargaba kunya da tsoro ne suke adddabarta sannan sai hauhawa sukeyi, ita sai yanzun ne ma ta ga wautarta da bata yi sauri ta bisa ta rufe k’ofar tata ba d’azu sanda ya fita…… Tana wannan tunanin ta fito daga cikin bathroom d’in d’aure ta d’an guntun towel gashin kanta na d’igar ruwa dan ya riga ya jik’a mata shi tun d’azu, tana k’arasawa tsakiyar closet d’in suka had’a idanu da shi ta cikin glass d’in sanye cikin jallabiya fara k’all! Dan lokacin da ta tashi fitowar yana durkushe yana bubbud’e akwatunan ta yana neman abu, motsin ta ya ji shiyasa ya d’ago ya kalli wajen ai kuwa suka had’a ido. Ja ta yi ta tsaya chak ta kasa gaba ta kasa baya. Murmushi kawai ya yi, ya d’auki hijabin nata da yake nema ya mayar da akwatunan ya rufe ya mik’e ya nufi inda take….yadda yaga duk ta diririce sai da ta basa dariya da tausayi, shiyasa yana zuge glass d’in ya k’arasa inda take ba tare da b’ata lokaci ba ya ware hijabin nata ya nemo wuyan ya zura mata. Ai kuwa har ajiyar zuciyar da ta sauk’e sai da ya ji kafin ahankali yaji tace “thankyou” Murmushi kawai yayi yana kallonta yana mamaki da tunanin ta yadda zai sa ta d’an saki jiki da shi ta cire wannan tsoron….kafin ya jinjina mata kai kawai sannan yace” welcome,mu je ki yi alwallah mu yi nafila” Ji ta yi kamar tace masa’ita bama ta sallar’sai kuma kawai tace “Nayi” Kamar ɗazu yanzun ma Jinjina kai yayi daga haka ya kama hannunta suka fita waje, cikin d’akin. …. Akan kafet d’in ya shimfid’a musu darduma ya tada ikama suka gabatar da sallar nafila raka’a biyu….ya jima yana addu’o’i kafin ya juyo gareta ya d’aura Hannunsa a kan goshinta nan ma ya yi addu’a tukunna ya gyara zama sosai yana fuskantar yace ‘Ta yi mishi karatu, yana son jin k’ira’arata….’ Suratul Mulk ta karanto masa tun daga farkonta har k’arshe…kamar kuwa kar ta daina haka ya ji, kafin shima yace ta zab’i inda takeso ya karanta mata..ganin ba zata iya magana ba yasa ya yi bismillah ya fara karanto mata Suratul Ibraheem… Shiruu ta yi tana sauraron yadda yake karantun nasa bisa ka’ida, kamar wani shahararren malamin ne yake karatun haka ta ji. ita har ga Allah duba da yadda ya girma a Uk sam ba ta yi tunanin yana da ilimi har haka ba. Tambayoyin da suka shafi addini ne suka biyo baya… Ai kuwa ba kad’an ba shima ya yaba da ilimin addininta sannan ya jinjina mata, kuma ya sake godiya ga Ubangiji…. Dan ya ji matuƙar dad’i, sosai, game da yadda matarsa ta kasance mace mai ilimin addini, saboda hakan yana da fa’idodi da yawa. Ganin tana hamma ne yasa yace mata “Ta tashi ta shirya ta kwanta.” dan ya lura a gajiye take Yadda ta mik’e zumbur!lokaci guda, sai da ta basa dariya yanzun ma….. Yana kallonta ta d’auki manyan manyan kayan bacci ta shige closet d’inta…busar da gashin kanta ta fara yi da hair dryer da su Aisha suka fitar mata daga cikinnkaya suka jere mata a closet ɗin, tukunna ta saka kaya… har ta fito bai yunk’ura ba, kuma bai ce mata uffan ba!! instead sai kawai ya girgiza kai yana mamakin kayan baccin da ta saka masa! abun takaicin ma har da hula kuma wai a hakan ma sai wani kakkare jikinta take ta faman yi….. yana zaune a nan kan dardumar ta zo ta wuce ta haye gado ahankali tace masa”sai da safe” “Za ki yi bayani ne” Ya fad’i hakan a cikin ransa, A fili kuma yace”Allah ya bamu Alkhairi”. Wani sanyi ta ji a ranta ganin bashi da niyyar yi mata komai, cikin nutsuwa ta ja quilt d’in dake shimfid’e a kan gadon ta lullub’e duk jikinta da shi, har kanta. Tsorone ya kamata jin ya mik’e ya je ya kashe wuta kuma bai fita ba, tana cikin tunani da zullumin son jin fitartasa ta ji ya yaye fuskarta dake cikin bargon kafin yace”Kar ki rufe har fuskarki” Sai kuma ya durk’usa yayi kissing forehead d’inta yace “good Nyt” Har da d’an murmushi ta yi mishi wannan karon, kafin ahankali tace”nyt” tana kallonsa ya koma kan dardumar, ya ci gaba da karatu. K’are masa kallo kawai takeyi tanajin yadda sonshi yake sake shigar ta…ita ala dole tana b’oyewa ne a bargon kar ya gane kallonshi takeyi ba ta san gaba d’aya hankalinsa yana a kanta ba duk abunda tayi yana kallon ta. Gashi a gabanta tana kallonsa, ga sanyin A c, ga shauk’i ga kuma farin cikin an rabu da ita ta huta…shiyasa sam ba ta ma san lokacin da barci ya kwasheta ba!. Ba ita ta tashi farkawa ba sai wajajen k’arfe 3 na dare, lokacin da ta ji bak’on al’amari a tare da ita a ranta tace “kenan Yashjub wayo yayi min….sai da ya bari na sakankance.” Shi kuwa Yash ba zai iya jurar ganin kukanta ba ne, kuma tun d’azu a closet ya fahimci kukan zata yi masa muddin yayi yunk’urin yin wani abun. Kamar kuwa ya san abunda ke a ranta kenan ɗazun. …Tun tana magiya da rarraashi har ta fara kuka, hankalinta bai gama tashi ba sai da ta ji shima ya saka mata kukan yana rarrashinta, amma kuma bashi da niyyar kyaleta. Babu abunda ya fi bata tsoro irin yadda ta ji yana yamutsa ta kamar ba ya haiyyacinsa, kamar wani mahaukaci…. Da tafiya ta yi tafiya kuwa had’iyar zuciya kawai ya rage Manubiya ba ta yi ba, gashi a yadda ya koma mata ta san ko aljanace ita ba lalle ta iya kwatar kanta a hannunsa ba. bata tab’a sanin Yashjub mugu bane ba sai da ta ji yana shirin kasheta…duka cizo yakushi amman duk a banza, sam bai ji ko d’aya ba dan a wannan gab’ar inda ace za’a saita masa bindiga to ko sunansa ba lalle ya kawowa ba!…. Tun Manubiya tana tunanin kalar jinyar da zata yi idan Allah ya bata ikon tashi har ta zo ta cire rai ta fara bashi wasiyya had’e da shirme da surutai, shi kam ya san dai tana magana amman bai gane ko d’aya ba…. Yana so ya tausaya mata amman sam ya kasa. Sai da kyar da mugun kyar tukunna Manubiya ta samu ya sarara mata lokacin har an fara kiran sallah a masallaci……. … Shi kansa ya san yayi laifi, amman kuma ba laifin sa bane ba! kasancewarta Macen da ta fi ko wacce mace a duniya ne silar janyo mata wannan b’arna da aika aikar da yayi…..sam bai yi zaton hakan ba, dan tabbas komai ya wuce zatonsa, an tashi kansa ta koina shiyasa ya gagara controlling kansa. Ahankali yanajin yadda take numfashi da sheshshek’ar kuka da kyar, ya samu ya janye daga gareta wanda hakan da ya yi ya sanya ta ji kamar ana zare mata rai ne. Cike da kasala yana jin yadda kansa yake wani irin mahaukacin sarawa ya koma gefe ya kwanta, cikin lumshe ido da sauk’e numfashi yace”Alhamdulillah”a fili. Manubiya kuwa wadda ke kwance a gefensa ji tayi inama ace tanada k’arfi da lafiyar da za ta samu ta juyo ta rufesa da duka. ….. Earlier Tare motar Yahanasu wadda suke tare da Munirat suka shiga cikin mansion d’in da ta Yassir… lokacin twelve har ta d’an gota. Gidan shiruu baka jin komai sai kukan tsuntsaye. Ita Yahanasu sai a wannan lokacin ne ma ta tuna cewa makullin d’akinta yana hannun Yassira! Tashi d’aya ta san za su yi case idan ta shiga dan itama yadda take jin zuciyarta a yanzu kam wallahi kaff cikinsu babu wadda zata iya ragawa. Tana yin parking Yassir ma yana fitowa daga cikin tasa motar. Tun lokacin da suka taho dama Munirat ta riga ta gama shawarar abunda za ta yi a cikin ranta, dan haka ta juya ta kalli Yahanasu tace”Bara in karb’i sak’o na, sai na shigo”. Yahanasu ba ta kawo komai a ranta ba tace mata “to” daga haka ta bud’e musu motar suka fito a tare, ita ta nufi main door Munirat kuma ta bi bayan Yassir wanda ya nufi b’angaren sa….tana ganin Yahanasu ta shige ta k’ara sauri.. Sarai ya ga lokacin da ta biyosa, amman ya yi banza da ita, yayi wucewarsa kamar bai ganta ba. sai da ya zo shiga har ya zaro key ya ji tace “Na san ka lura da ni” Shiruu yayi kamr mai tunanin wani abun, kafin ya zura key d’in ya bud’e k’ofar tukunna ya juyo yace “Munirat a gajiye nake sosai!Make it fast pls..me ki ke sot?” Matsowa kusa da shi tayi tace “har haka muka zama? Make it fast?baka ma da lokacin saurarona? Okay ba komai shikenan!” Ta fad’i hakan tana k’ok’arin juyawa… rik’o hannunta ya yi, ya janyota garesa har sai da fad’a jikinsa kafin ya tallafe k’ugunta da hannunsa d’aya yace”Ke fa kika tura ni nesa da ke….wallahi har gobe Ina sonki Ina k’aunarki, amman duk rintsi ba zan taɓa yi miki dolen ƙulla alaƙa da ni ba…..” Gaba d’aya Munirat ɗin is uncomfortable, dan tunda take wani Namiji bai tab’a yi mata irin wannan ruk’on ba idan ba shi d’in ba amman kuma so take su shirya,kar ta turesa ko kuma ta hanashi rik’eta ya zama ya fusata, sannan ga maganganunsa na ‘yana sonta’ Da suka k’ara narkar mata da zuciya, shiyasa ta k’i motsi sam tak’i cewa komai. Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Yassir ba, dan haka ya sake rungumeta da kyau kafin yaci gaba da gaya mata k’arya da k’arairayi har da cewa”har zazzab’i da rashin lafiya yayi kwanaki duk a ta dalilint,idan ya ganta kamar zai mutu haka yake ji gashi ba ta kulasa shiyaaasa za ta ga kamar gudun ta yake yi!”.. sannan ya fito k’iri k’iri ya ce mata ‘shi fa ba zai iya yin soyayyar y’an k’auyen da take so su yi ba, in dai har tana sonshi to ta sake da shi..ko ma me suka yi ai shi ɗin ne dai zai aureta a ƙarshe, dan haka ta daina wahalar da kanta tana wahalar da shi, indai har ta yarda da shi kuma shi takeson aura to a ganinsa ya kamata ta sake jiki da shi.!’ Ko da ta yi masa maganar Kausar ma, kanshi tsaye sannan ba kunya ba tsoron Allah yace mata “shi ba komai tsakanin sa da Kausar, ba sonta yake yi ba, kawai dai sun shak’u ne tun Yarinta”….. Sai da Yassir ya tabbata ya gama zurma ta ta kamu tukunna ya d’aura da cewa”I love you so so much,ke kaɗai nake so Munirat” Har cikin zuciya da jininta kuwa ta ji wannan kalmar tana yawo…… sai da ta lumshe ido ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace”I love you too”ta fad’i hakan tana k’ok’arin zamewa jin yadda ya sake mannata a jikinsa,kallon fuskarta ya yi kamar bai fahimci son zamewa take yi ba yace “mun shirya ko?” Jinjina masa kai ta yi tana murmushi,ahankali yace”bari in tabbatar to”bata ankara ba ta ji ya fara kissing lips d’inta. Bata biye sa ba saboda shock da tsoro gashi kuma bata saba ba. Ya kai 1 minute tukunna ya rabu da ita yana mayar da numfashi tukunna ahankali yace”haka na ke so…” Ya fad’i hakan yana murmushi yana shafa kumatunta. Ya lura da yadda jikinta ya d’au karkarwa tun d’azun har yanzu,sannan sam ta k’i magana ta ƙi ma ta yarda su haɗa idanu. Ahankali yace “Munirat,ko na b’ata miki rai ne?” Ya fad’i hakan yana lek’en fuskarta. Dakyar ta iya cewa “A ‘a” Murmushi yayi…. Ya na buƙatar hutu kuma ya lura ba abunda za ta iya yi masa yanzu dan ya ga yadda ta shiga shock daga iya ka kiss kawai. shiyasa cikin son sallamar ta yace “Muje in raka ki,kema ki samu ki huta ko?” Ahankali tace “Okay” Gaba d’aya jikinta a sanyaye…..rik’e hannunta yayi, daganan ya d’an janyo k’ofar entrance na side d’innasa suka fara takawa yana d’an janta da hira amman ita daga ‘um’sai ‘um um’. Sai da ya kaita kan kwanar da za ta sadata da main door d’insu tukunna ya d’ago hannunta yayi kissing yace mata”good nyt, zan kiraki” Ahankali ta d’anyi murmushi tace “Sweet dreams” daga haka ya yi waving d’inta suka rabu. Sai da ya b’acewa ganinta tukunna ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya….ta san yin hakan babu kyau sam bai dace ba! amman ba ta jin zata iya hak’ura da Yassir gaskiya! Dan haka za ta biye masa, kuma inshaaAllah zata nuna masa rashin dacewar hakan a hankali a hankali in tafiya ta yi nisa, ta san Yassir yana sonta dan haka idan ta sake ɗaukar hankalinsa ta samu ya sake dulmiyawa a cikin kogin sonta to ta san za ta iya hana sa abubuwan da yake yi mata kuma ya hanu! Inyaso daga nan sai su yi tsaftataccen relationship d’insu, su yi aurensu in ya so sai ta sallama masa komai ta kula da shi yadda ya kamata su samu happy ending. A ganinta hakan shine mafita akan dai ace ta rabu da shi bayan suna son juna, ba za ta iya zuba ido tana kallonsa ba, dan yadda ta ga ya fara nuna intrest akan Jidda ta san in ta bari aka tafi a haka shikenan sunanta sorry. Ba ta da mai bata shawara su Ummi tun kwanaki da ta ganta da Yassir sam suka daina sake mata, ko hira Ummi da Yayarta sun daina yi da ita sun nace akan ta fito da miji kawai faka faka ta yi aure, ba dan haka ba da ko yayarta ta tuntub’a da maganar amman ta san sam ba za ta fahimceta ba wani sabon case d’in ne ma zai taso,shiyasa ta yanke decision d’in ta da kanta,ta yi abunda ta ga shine dai dai… A gaba, In lokacin yayi kuma aka samu suka ɗan huce sannan su ka ga Yassir ɗin da gasken gaske ya shiryama aurenta, to ta san dole za su haƙura su yarda da shi suma. Da wannan tunanin ta k’arasa bakin main door na mansion d’in ta danna, ganin a bud’e ne ma yasa ta tura zundumemiyar bullet proof door d’in ta shiga…. A tsattsaye ta samu kowa, Mommy da Kausar ne kawai babu sai Daddy, amman har Ummi tana k’asan, amsa sallamar ta Ummi tayi kafin tace”Daga ina kike??” Cikin tarrar numfashin Ummin Munirat ɗin tace”Waya na tsaya yi ne” Kallonta Yahanasu ta yi ta d’an yi shiru sai kuma tace “Mu je d’akinki, in kwana achan”. Daga haka ta juya ta kalli Yassira tace “Ki dafa key d’in ki cinye dan Allah!” Ta fad’i hakan tana k’ok’arin wuce ta. Fincikota Yassirar ta yi ta dawo da ita gabanta ta tsayar tukunna tace “Inaga baki fahimceni ba Yahanasu! bacci ne kwata-kwata yau baki Isa yi a cikin gidan nan ba! Dan wallahi yadda kika shiga tsakanin mu da d’an uwanmu ki ka d’aga mana hankali to kuwa kema ba ki isa kin runtsa ba!.” Cikin fushi Ummi tace “baki da hankali ashe Yassira?” Kafin Yassira wadda ta juyo a fusace ta yi magana tuni Ya’isha ta amshe cikin tsiwa ta fara cewa “Haba ke kuwa! Wai ashe kwata kwata kwakwalwarki bata d’aukar lissafi ke!. Magana ake ta y’an uwa! Tun d’azu sai ce miki ake yi ki wuce ki tafi d’akinki amman kin nace sai da kika ji komai, kuma hakan ma bai ishe ki ba, tsabbar shishigi kin wani tsomowa mutane Baki.. Ina ce Daddy dakansa yace ‘ki fita harkar kowa, kuma idan family suna magana ki daina saka Baki’.?” Cike da kwarin guiwa sannan ba tare da shayin komai ba Munirat ta taho tace “Ya’isha! Tou ai ni a ganina idan aka bar family d’in za su yi b’arna da shirme ne, tunda basu san abunda ya dace ba, shiyasa Ummin take saka muku baki dan idan aka barki Allah kad’ai ya san kalar dak’ik’ancin da za ku yi” Da sauri Ummi ta damk’o Hannun Munirat ta tura ta tace “wuce ki tafi d’akinki kafin na makeki” Dan yadda ta ga Yusra da Ya’isha sun yo kan Munirat ɗin a harzuƙe ta san idan bata yi wani abun ba to tsaf za su rufeta da duka. Za ta yi magana Ummin ta daka mata tsawa tace “wuce!! Nace ki wuce!” Da sauri Yasmeen tace “ai sai ta wuce d’in mu gani idan saman ubanta ne ya gina!.Kun je kun gama yi wa Mutane shishshigi kun k’ulla k’ullalliya shine yanzu zaku ce za ku kwana lafiya? Ai ba ku taki zaman lafiya ba, dan haka bacci bai ganku ba, masifa da tashin hankali ne suka ganku!” Cikin fushi Munirat tace “Okay!…. Sai yanzu na gane matsalar ku, ko kuma ince matsalolinku!… Na farko baku samu yadda kuke so ba! Na biyu kuma Ya Yash ya fatatttake ku, shine kuka zo zaku d’aga mana hankali zaku hana mutane bacci! saboda tsabar bak’in ciki da k’unci… kun rasa Ina zaku sa ranku shine kuke so ku huce a kanmu, ko?. Ai ba mu muka ce ku zama bad people ba….kuma da ace kuna da kirkin sannan kuna yi wa Mutane kirki to da duk hakan bata faru da ku ba. Kuma abunda ban gane ba, shin idan mun tsaya d’in mai hakan zai k’are ku da? kawai kar mu yi bacci shine burinku ko me?? kuna jin abunda kukeyi kuwa? kowa fa ya na jin hakan ya san kawai kuna neman inda za ku sauƙe fushi da ɓacin ranku ne, haba mana! Ku gyara abun naku ta hanyar yin wani abun mai ma’ana wanda hankali zai ɗan ɗauka ba wai wannan ba!” Fincikota Yusra ta yi da dukkan k’arfinta daga gaban Ummi, Ummi ta yi mamakin yadda Munirat ta zabgawa Yusran mari dan ba ta yi tunanin wannan ƙarfin halin daga Munirat d’inba….. .. A chan sama kuwa, tun d’azu da Baba larai ta cewa Mommy “ba su yi komai a gidan Yash ba suka dawo”shikenan Mommyn ta koma kamar robot, dukda Baba Laran ta kawo sabon plan amman sam ita gani take tunda basu yi wanchan na farkon ba shikenan ta shiga uku!da farko ta ɗan nutsu hankalinta ya kwanta kamar kuma wata wadda aka kunno tashi ɗaya sai ta sake burkicewa! Bayan ta yi dogon nazari…. Har ila yau, ganin hakan ya sanya Baba Larai ta zaunar da ita, bayan abubuwan da aka yi wa Yash ɗin itama Manu ba a barta hakan ba, dan a take Baba Laran ta yiyyi abunta ta gama tukunna ta bawa Mommyn tabbacin ta kunce mata jini…amma ko gezau! tashin hankalin da mommy ta ke a ciki bai ragu ba! Ta dai ce mata to ne kawai amma masifar da take a ciki ba kaɗan bace ba….ji take kamar za ta mutu dan so take ma ta yi kuka amman sam hawayen sun gagara fitowa daga cikin idanunta. Tana a wannan halin ne kuma ta je ta yi wa Kausar bayanin dawowar Manubiya da Yash cikin gidan tukunna a samu a yi komai, aikuwa a take sai kausar ɗin ta ƙarasa hautsina ta!!…dan a tunanin Mommy Kausar za ta yi murna da hakan amman sai ta ga sab’anin hakan, dan tashi d’aya Kausar d’in ta birkice ta shiga ce mata ”Ashe ma bata da burin raba auren Yash da Manu kenan, tunda har ba za ta iya korarta a wanchan gidan ba har sai an kuma d’aukar lokaci an barta ta dawo nan, kafin nan ma wataƙila ta dawo da ciki!! shikenan komai ya lalace mata, dan ta san indai Manu ta samu ciki to ta gama cin riba a kansu……ita kawai ta lura ja mata rai suke yi suna yi mata wayo, dan haka yanzu kawai abunda Mommy za ta yi mata shine ta kira Yash a yanzu ta ce masa ya saki Manubiya idan kuma yaƙi sakinta to ta ce masa za ta tsine masa!!! Indai har Mommy ta yi hakan to ta yarda ba raina mata hankali suke yi ba, idan kuma bata kira Yash ba wallahi sai ta bar gidan a yau kuma ba zata sake ganinta ba!” Hankalin Mommy idan ya yi dubu tou ya tashi, ta san idan ta yi hakan tabbas Yash zai saki Manubiya amman ko hauka takeyi ba za ta tab’a yin hakan ba saboda ta san yin hakan kamar ta kashe relationship d’inta da Yashjub da Daddy ne, dan kowa bak’in ta zai gani kuma ita kanta Kausar d’in muddin hakan ta faru to Yash ba zai tab’a yarda ya aureta ba har abada, hatta su Yasira ta san sai bak’in jininta ya shafesu, watak’il ma ya tartara kayansa ya tafi ya koma uk ya zauna a chan shikenan ba za a sake ganinsa ba har abada, kuma wataƙilan suna nan su basu sani ba shi kuma ya lallaɓa ya maida manubiyan…. Shiyasa ta fara k’ok’arin fahimtar da Kausar d’in cikin lallami. Ganin hakan ya sanya Kausar ta wuceta da sauri tana wani Irin kuka ta d’auki wayarta da makullin mota ta fice da gudu, gudun ma kar Mommyn ta yi yunk’urin tsaida ita, a ranta ta gama yanke decision ‘wallahi sai ta bar gidan, a yau!.’ Dai-dai nan ne kuma Munirat ta zabgawa Yusra mari, suna shirin rufar mata suka ga Kausar ta sauk’o da mugun gudu tana kuka Mommy ma wadda ta biyo ta tana kiran sunanta tana hawaye sharr kamar an kunna famfo. Da sauri Yassira ta k’arasa bakin main door ta tsaya dan taga nan Kausar d’in ta nufa. durk’ushewa Kausar ta yi a daidai gaban Yasira tace”Yasira dan girman Allah ki matsa in fita, idan na ci gaba da zama a cikin gidan nan mutuwa zan yi, ba zan tab’a iya zama a gida d’aya da Yash da Manubiya suna tare ni kuma ina kallonsu a gefe ba…..yanzu haka ma baki san ya nake ji ba, na san suna chan tare! Duk da haka na yi k’ok’ari na danne kaina amman naga Mommy so take yi sai na mutu tukunna za ta kyaleni”…. muryarta ce ta sark’e sakamokon numfashinta da ya d’auke, dan haka ta kasa ci gaba da magana ta shiga kokawar janyo numfashinnata . A hankali Yassira ta durk’usa a wajen k’asa k’asa tace “Kausar kar ki yi disgracing kanki(kar ki kunyatakanki), kalli yadda su Ummi su ke kallon….” Cikin tsananin fushi tace “Disgrace my foot!(ina ruwan abun kunya) Su kalla mana!ina ruwana? so kike in yi ƙarya da munafuncin ban damu ba bayan kowa idan ya ganni ya san Ina cikin tashin hankali, kuma na kasa, kuma kun kasa yi min maganin matsalata?…akwai disgrace (abun kunya) da rashin gatan da ya fi wanda nake a ciki??” Ahankali Yasira ta janyota ta shiga rarrashinta. Kamar Kausar d’in zata mutu tace “Ina ta k’ok’arin ganin na yi picking pieces of myself na yi haƙuri na daure amman shine kuma duk da haka wai Mommy saboda ba ita ta haifeni ba ta zo tana ce min wai Manubiya za ta dawo nan! Wanne irin rashin adalci ne wannan?.Ba ku ma da shirin korarta kwana kusa kenan sannan ta ya zan iya zama ta dawo nan Ina kallonsu tare a waje d’aya a d’aki d’aya da Yash!?” Ganin yadda su Yahanasu suka zuba musu ido ne yasa Yasira tace”calm down mana Kausar(ki huce haka mana Kausar ki kwantar da hankalinki), ki zo mu je….” Fincikewa Kausar d’in ta yi cikin tsananin fushi tace “Stop telling me to calm down! (Ku daina ce min in kwantar da hankalina) tun yaushe kuke cemin in kwantar da hankslinnnawa in yi shiru za ku san abunyi amman har yau shiru???inda ace ke ce ko su Yusra na san da tuni Mommy ta uzzurawa Baba larai an yi an wuce wajen…….” Da sauri Mommy da Baba larai suka k’arasa inda take k’asa k’asa suka shiga yi mata magana amman inaa kamar zuga Kausar ake yi, gashi sai d’aga murya take yi tana ta yi musu b’aramb’atama. Takaici ne ya rufe Yassira ga Munirat Ummi da Yahanasu sun tsura musu ido, shiyasa ba ta san lokacin da tace “Useless munafukai kawai!kun wani tsaya kun tsurawa mutane ido” Yahanasu ta ji zafin zagin amman sai ta danne ta saki dariya kafin tace”Ku fa kuka ce kar mu yi bacci yau,ko ba kune kukace kar wadda ta bar parlourn nan tsakanin mu nida Munirat ba!?” Cikin fushi Yassira ta k’arasa inda take ta tsaya a daff da ita tace” Yahanasu ki kiyayeni! Wallahi ki kiyayeni!. Mara Imani mara tausayi kawai!na tabbatar baƙin cikin da ki ka ga Kausar a ciki ne yasanya ki farin ciki da dariya haka, muguwa azzaluma!” Murmushi Yahanasu ta yi kafin tace”Sam ba abunda ya saka ni dariya ba kennan, farin cikin ganin yadda kuka fara tonawa kanku asiri ne yasanya ni dariya Yassira, ramin k’arya ai dama k’urarre ne!” Cikin fushi Yasmeen ta matso ta ce “I have said enough Yaha” kafin tace “Da ke da Ummi da Munirat ku wuce ku bawa mutane waje. Tun zagin da Yasira ta yi musu dama Munirat ta zo k’arshen wuya, Ummi kuwa ji ta yi da ta sani da tuni ta yi sama abunta…cikin b’acin rai Munirat ta ce”Saboda kar mu ji more of your dirty secret?(ƙarin munanan surranku?) Wai ni Yasmeen wa kuka haifa a cikin mu ne? ni ko Yahanasu ko Ummi? dan naga yadda kuke yi mana magana kamar irin kun samu ya’yan cikin ku d’innan” Ta fad’i hakan tana matsowa daff da su. Yassira a k’ufule take shiyasa tashi d’aya ta rufe Munirat da wani irin mahaukacin duka, kamar jira Yasmeen take itama ta sa hannu dama ta tsani Yarinyar, haka Yusra itama dama a wuya take tun marin da ta yi mata!… Hatta Ya’isha da Yadira shiga sukayi sukai mata rubdugu. Yahanasu da Ummi ne suka fara k’ok’arin kwatar Munirat, ba tare da tantama ba su Yasmeen suka fincikosu dama haushin Yahanasu suke ji, shiyasa suka fi rufar mata suka fi laftarta, itama Ummi sai da suka kai mata duka a Kai suka kaita har k’asa. Dai dai nan Daddy ya fara sauk’owa k’asan sakamokon hayaniyar da ya jiyo. Wata mahaukaciyar tsawa ya daka musu wadda ta sa suka d’an tsaya, sai da suka d’ago suka had’a idanu da shi tukunna suka ja da baya suna huciii, har Mommy wadda ta matso kwatar Yahanasu. Duk yadda Ummi ta so kasa daurewa ta yi, ba ta san lokacin da hawaye suka fara sintiri akan kumatunta ba…..wajen Ummin Daddy ya fara zuwa, ya d’an shafa inda ya ga Yassira ta kai mata duka akai, wajen har ya d’an yi jaaa. Tashi d’aya idanuwansa suka yi jazir ya juya ga Yassira tana shirin yin magana ya fara kimarta, hatta Yasmeen da Yusra saida suka karb’i rabon su amman su sun samu sun zille dan Yassirar ya rik’e, ita ta fi fusatashi. dama Ummi ba ta dad’e da gama faiyyace masa abunda suka aikata a gidan Yash da gidansu Manubiya ba…tashi d’aya daga jin zancenta ya fahimci ashe k’arya suka shirga masa d’azun da suka dawo, shiyasa dama yana jin haushin su akan hakan yanzu kuma ya ga wannan shirme da aika aikar da suka yi, shiyasa ya fusata ba kad’an ba. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 21* Abunda bai tab’a yi ba kenan Wato ‘dukan y’ayansa’. Shi da kansa yana jin zafin dukan nasu da yake yi a halin yanzu amman kuma ya zama dole a taka musu burki, dan tabbas abun nasu ya zarce misali….. Waya Mommy ta karb’a a Hannun Yadira wadda ta b’uya a bayanta, tashi d’aya Mommyn ta danna kiran Yassir, dan sun gagara kwatar Yassira a hannun Daddy. Yana d’auka tace “dan Allah Yassir ka yi maza ka zo yanzunna.” Sai da kyar tukunna daidai Yassir d’in yana shigowa cikin parlourn Ummi ta samu ta janye Daddyn yana huci….babu abunda ya fi d’aga masa hankali kamar Yahanasu da ya gani a kwance shame-shame kamar gawa dan ko numfashi ma yaga kamar ba ta yi…idan sun daki Munirat saboda Allah Yahanasu da Ummi ai ba sa’anninsu baneba.! Cikin kuka Mommy ta matso tace “a kanta ka dakar mini ƴaƴaana mata ba maza ba?? yanzu kai a ganinka ya dace ace ka yi musu wannan dukan?? Dan ni a ganina ko Yadira ta wuce duka ballantana Yassira! Yassira fa ka daka! Ka bud’e idanunka da kyau ka gani” Cikin rashin jin dad’i Ummi tace “Tabbas Mommy kin tabbata wadda ba ta san abunda ya kamata ba, dan an daki Yassira? Kalli Yahanasu fa ko motsi ba ta yi, kalli goshin Munirat duk jini, sannan ni kaina Yaran nan ba su kyaleni ba amman shine……” Cikin tsananin b’acin rai Mommy ta yi kan Ummi kamar za ta daketa ne ta ce ”Saddik’a! zan yi miki gargaɗi na farko kuma na ƙarshe! Daga yau duk wani abunda ya shafe ni! Ni ko ƴaƴana kar ki sake shiga! Babu ruwanki da mu, ba ruwanki da rayuwarmu, ba ruwanki da damuwarmu! Ban san wanne Irin naci, maita, jaraba da shishshigi Allah ya yi miki ba…duk inda ake case d’in da bai shafeki ba a cikin gidan nan to sai an ganki a wajen. Har ga Allah kin takurani ko tari ki ka jiyo na yi sai kin zo, wanne irin jaraba ne wannan??” Sakar Baki kawai Ummi ta yi tana kallon ta…Baaba Larai kuwa ji ta yi kamar ta rufe Mommy da duka, dan yanzu kam ta san Mommyn ta riga ta gama nunawa Ummin wacece ita, ta ganta tsirararta. Ummi tana shirin yin magana Daddy yace mata “wuce ki tafi sama, ki jirani a d’akina” Har za ta yi musu, sai kuma kawai ta juya ta wuce saman zuciyarta fall cike da mamakin Mommy, tashi d’aya itama Munirat ta mik’e ta nufi saman tana mamakin yadda ko kallon inda take Yassir bai yi ba amman ya nufi Kausar ya je ya durk’usa a inda take yana ta faman rarrashinta kamar shima zai fashe da kukan ne. Sai da Ummi ta biya da Munirat d’akinta ta bata paracetamol ta goge mata ciwon da ta ji da spirit ta saka mata plasta tukunna ta nufi chan sama ta shige bedroom d’in Daddy ta zauna zaman jiran nasa kamar yadda ya ce. Suna wucewa Daddy ya dakawa Yassir tsawa “Tashi a wajen ka kyaleta! Ban san mai ya faru ba, amman na san itace ummulabaisin abun nan da ya faru!” Cikin rashin jin dad’i Yassir ya mik’e ya ce ”Haba Daddy…” Wata uwar tsawa Daddy ya kuma daka masa cikin cewa “na ce ka kyaleta! Ka zo ka tayani kai Yarinyar nan asibiti ko?” Kamar Yassir zai fashe dan takaici, haka nan ya na ji yana gani ya baro Kausar ya zo ya durk’usa ya kinkimi Yahanasu suka fice tare da Daddy ko kallon Yassira wadda take durk’ushe a wajen Daddy bai kuma yi ba…. Ita ta ma rasa ta yi kuka ne, ko ta yi ihu! Ba ma ta san ta Ina za ta fara ba, yau ita ce Daddy ya daka haka anya ba mafarki takeyi ba kuwa? Me ya faru? Me ya shiga jikin Daddyn nasu tashi d’aya yau haka…… Su Yassir suna fita Baaba Larai ta matsa inda take ta mik’ar da ita ta zaunar da ita tukunna ta shiga rarrashinta, sai a lokacin ne ta samu ta fashe da wani irin kuka kamar za ta mutu tace “Nima fa na ji ciwo, kalli goshina! Sannan cheeks d’ina gaba d’aya ciwo suke yi min, amman ki duba ki ga yadda aka tafi kai Yahanasu asibiti ni aka barni anan.” Gaba d’ayansu kanta suka nufa banda Kausar wadda ta yi suman wucin gadi. A hankali Mommy ma ta k’arasa wajen Yassirar zuciyarta tana wani irin tafarfasa..ta san ta tsani Ummi tsana ba ta wasa ba ta tsani the sight of her ko labarinta bata son ji amman bata tab’a jin tsanarta ta masifa kamar ta yau ba!..a kanta aka dakar mata ƴaƴa! Inaa ba zai yiu ba da sake..a tunaninta Ummi k’aramin alhaki ce ashe abun ba haka yake ba dan gashi da idanunta ta gani kuma ta fahimci abunda ta yi ta ke kuma kan yi akanta sam ba ya aiki!..Babu abunda ya fi bata takaici irin yadda Daddy yace “ta je ta jirasa a d’akinsa” Ita kuma ta yi masa biyayya ta wuce d’ingui-d’ingui ta tafi. A b’angaren Yassira kuwa ta riga ta gama kai wa wuya! Wallahi Daddy ya kunna wuta a cikin gidansa da Hannunsa, dan wallahi sai dai in ya koreta a gidan amman da Manubiya da Munirat da Yahanasu da Ummi sun shiga uku a Hannunta…ita kanta tana jin tsoron abubuwan da zuciyarta take aiyyana mata ta aikatawa su Ummin! wallahi duk sai sun ci ubansu….. Babu yadda Baba Larai bata so ta fahimtar mata da amfanin kissa da siyasa ba amman tashi d’aya tace “wallahi ita ta gama kissa da siyasa, dan bata ga anfani da ribar yin su ba! Sai ta nunawa Ummi da Munirat nan fa gidan ubanta ne, wallahi hatta Yahanasu sai ta gane kuranta, sai ta sake fahimtar cewa ‘ba ta fa da uwa! ba ta da gata! sun fi ta power a cikin gidan’.” Cikin takaici Baba larai tace “Yasira wai ya Ina baki kina k’in karb’a ne? duk fa inda mata suke mata ne kuma dole kowacce da tata kalar power, ku daina ganinsu kamar k’ananun alhaki za su baku mamaki! yanzu kalli abunda aka aikata muku duk a ta dalilinsu, kuma ina mai tabbatar muku muddin kuka ci gaba da wannan shirmen wallahi wallahi abunda ya faru a yanzu a parlourn nan somin taɓi kenan….dan haka daga yau tunda har ga abunda ya fara faruwa to indai zan baku shawara ku d’auka hatta Manubiya dan Allah inaso daga yau ku nemi zaman lafiya da ita a gaban idanunsu Daddy, inyaso daganan sai mu san abunyi ta kark’ashin k’asa…” Cikin katseta Ya’isha tace “Baba larai munfa gama siyasa, mu da gidan ubanmu!? amman ki ce sai mun yi musu siyasa? sun shigo sun mak’ale ta k’arfi da yaji and still ace ba mu isa mu fad’a a yi ba kenan?so kike a taka mu a maida mu gefe kenan? ko ya kike nufi?” Cikin fushi Baba larai tace “wai ta ya zan yi muku bayani ne ku fahimceni?…ai ba su Ummi na ce ku yiwa siyasa ba! Daddy ne ba na so ya lura ko su fahimci kune masu takalo fad’a sannan suma kuma su Ummin ba wai b’aro b’aro za ku yi musu ba dole a sakaya wani abun idan ba hakan aka yi ba wallahi ina mai tabbatar muku shi Daddyn naku sai ya maidaku gefe su Ummin kuma su taka ku, idan bai zab’a muku mazaje ko kuna so ko bakwa so ya yi muku aure kun bar masa gida ba kenan! kuna abu kamar wasu marasa lissafi! Ki duba fa ki ga yadda muka gaya masa abunda ya faru a gidan su Manubiya, d’azu da muka dawo amman ya ajjiye namu ya ɗauki na Ummi saboda ita ta fi ki iya kissa!, dan ba ni da tantama itace ta zuga shi saboda tunda ta dawo ta haye b’angarensa ban sake ganinta ba sai yanzu da ta ji hayaniya tukunna ta sauk’k’o.” Cikin tarar numfashinta Yadira tace”tunda suka dawo take samanshi.” Da sauri Baba larai tace”kin ji ko?ai na sani dama tunda na ji yana dukanki yana cewa ‘kina Babba amma ke ce mai janyo magana, ba za ki b’ata masa sunan family ba’to na san cewa Ummi ta fad’a masa wani abun. Dan Allah ku tsaya ku nutsu, mu taru mu rufawa juna asiri, ina danne ku kuna biyewa dokin zuciya wallahi za ku kwashi kashinku a hannayenku fa! kuma idan har hakan ta faru kar wadda ta kalle ni dan babu abunda zan iya yi infact yanzu ba kamar da baceba saboda a da da Mutane masu sauk’in sha’ani muke karawa sab’anin yanzu! Ki duba fa ki ga Manubiya a yadda ta shigo cikin gidannnan ta k’arfi da yaji, gashi abubuwanta har gobe ba komai ake iya gani ba, sannan ita kanta Ummin yanayin aurenta da Daddyn naku komai a lullub’e yake, dan haka ya zama dole ku yi accepting fact ku daina ganinsu a matsayin k’anananun alhaki, mu had’a k’arfi da k’arfe da wayo da dabara da komai ma tukunna fa shine za mu ci riba. Ya kamata ace mun dad’e da wuce wajen nan wallahi ku kuke dawo da mu baya, last time duk kun sauk’k’o kun yi yadda ya kamata ammman yanzu kun sake burkicewa, dan Allah ku gyara.” Shiruu duk suka yi kafin chan Mommy tace”Allah ya sa mu dace” Sai kuma ta kalli Yassira tace “Yasira, ba na son fad’a tsakanin ki da Yahanasu, bana so ki yi mata komai…” K’ura mata ido Yasira ta yi ba tare da tace komai ba, wanda hakan ya sa Mommy ta matso kusa da ita ta dafa ta tukunna ta ce ”Kamar yadda Baba larai ta fad’a ’Ummi!Munirat!Mannubiya!Yahanasu duk kar ki bari hayaniya ta tashin hankali ta shiga tsakanin ki da su wanda har zai janyo idanun Mahaifinku har ma Yash, ban ce dole sai kin yi zaman lafiya da su ba amman kar ki bari su Daddy su fahimci kune masu jangolo rigimar, mu yi abunda Baba larai ta ce har zuwa lokacin da Allah zai k’addara rabuwar mu da su a samu su kama gabansu.…sannan yanzu ‘abunda ya kamata mu saka gabanmu mu maida mafi mahimmanci shine Daddy! A yadda ya zuciya d’innan komai ka iya faruwa, dan haka inaso da ni da ku mu yi sauri mu gyara mu dawo da hankalinsa garemu, idan ba haka ba akwai babbar matsala dan indai har baya bayanmu to komai ya d’auko hanayar lalacewa kenan.” Jinjina kai Baba larai ta yi kafin ta ce”Yauwa, ko ke fa! hakan ne ya kamata and InshaaAllah nan ba da jimawa ba Daddy zai dawo saiti na san abunda zan yi, amman fa ku ma sai kun taimaka!…” daga nan ta ci gaba da yi musu lecture…. Shiruu kuwa duk suka yi suna sauraron ta….Yadira ce ta fara lura da yadda Kausar take nan sheme a bakin k’ofa dan haka ta kwala kiran Kausar d’in sai kuma ta nufi inda take suma duk suka rufar mata…..yau ma sai da Yasmeen ta sha wahala tukunna da ikon Allah aka samu Kausar ta farfad’o. Babu wanda ba ta bawa tausayi ba dan tana farfad’owa da sunan Yashjub ta fara sai kuma ta fashe da kuka. Dan tun d’azu idan ta rufe idanunta Yash ɗin kawai take hangowa tare da Manubiya dan ko ta k’i Allah ta riga ta san a dai dai wannan lokacin kam suna manne da juna, wallahi wallahi inda ace za ta iya d’aga k’afafuwanta da sai ta nemi gidan ta je a yau idan ba ta kashe Manubiya ba to ba sunanta Kausar ba. Baba larai da Yasmeen ne suka d’auketa suka yi sama da ita dan jikinta in banda karkarwa ba abunda yake yi ta ma kasa tsayuwa…Mommy da cewa ta yi a kaita asibiti amman sai Yasmeen tace”ba komai stress ne da tashin hankali idan ta samu hutu ta d’an nutsu za ta dawo daidai, ko sun je asibitin ma abunda za’a ce musu kenan.!” A d’akin Kausar d’in suka ya da zango tukunna Yasmeen ta fita ta je ta had’o allura mai mugun nauyi su Mommy suka danne ta aka yi mata, aikuwa ko gama tsiyaye ruwan allurar Yasmeen ba ta yi ba Kausar ta fara lumlumshe ido nan da nan kuwa ta yi bacci. Sai a sannan tukunna suka samu kunnuwansu suka huta dan kuka sosai Kausar d’in take yi tana cewa”ita fa ba zata kwana a cikin gidan nan ba,ba ta da k’arfi a jikinta dan Allah Yassira ta taimaka mata ta fitar da ita daga cikin gidan nan,a nemo mata Manubiya, yau sai ta kasheta……”waye waye..harda shirme hakanan ta dinga had’awa tana yi kafin aka samu ruwan allura ya saka ta a silent. Su Mommy kuwa a tsaye suka kwana, dan tashi d’aya bacci ya k’auracewa idanunsu tsabar tashin hankalin da suke a ciki. Yadira ce kawai ta d’an runtsa Mommy kuwa ko zama bata iya yi ba, dan abu biyu ne suka had’ar mata, na farko ba wai iya Kausar bace take cikin tashin hankali a wannan rana har ita dan wallahi babban abunda zai k’arasa kasheta bai wuce ace Manubiya ta samu ciki ba, dukda Baba larai ɗazu ta yi kuma tace mata “ta kwantar da hankalinta ta kunce mata jini, har zuwa lokacin da za su dawo cikin gida kusa da su da zama a san abunyi” amman sam hankalinta ya gagara kwanciya . Abu na biyu kuma ‘Ummi da Daddy’!dan tun d’azu take safa da marwa a bakin stairs d’in Daddy amma ba ta ga sauk’k’owar Ummi ba.Tana ganin Daddyn ya zo ya wuce lokacin da suka dawo daga asibiti, a tunaninta magana kawai za su yi da Ummin ta saukk’o amman har yanzu an fi awa uku da hawan sa babu Ummi babu motsinta. …… A kwance cikin sofa Daddy ya sami Ummi, a cikin d’akin nasa, har ta d’an fara bacci saboda sun d’an dad’e a asibiti tukunna suka dawo. A kusa da ita ya nemi waje ya zauna, ya d’an ruk’o hannunta ya na kallon saman goshinta inda Yasira ta daketa, still wajen har ya d’an yi jaa….farkawarta kenan ta ji ya mik’e dan haka ta shiga bud’e idanunta dai dai ta ga ya nufi fridge da towel a hannunsa, yana zuwa ya bud’e ya d’auko ice ya saka a cikin towel d’in ya juyo ya nufota. mik’ewa ta yi ta zauna dai dai ya k’araso, ta ce ”ya jikin Yaha?”a hankali ya ce”Alhamdulillah,she’s fine, tana d’akinta” tukunna cikin kulawa ya zauna kusa da ita sosai ya fara daddana mata k’ank’arar a inda ya yi jaa ɗin yana mai jera mata sannu a d’an rikice…. Ummi ba ta san lokacin da ta saki wani sassanyan murmushi ba, wanda hakan ya sanya ya tsayar da abunda yakeyi, ya shiga kallonta. ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya sunkuyar da kansa k’asa, yana tunano ire iren abubuwan da aka yi mata a cikin gidan, amman ta yi hak’uri ta zauna…. bada hak’uri baya daga cikin tsarinsa amman tashi d’aya a yanzu ya yanke shawarar chanja tsari, dan tabbas Ummi ta chanchanci ya bata hak’uri, ya jinjina mata… A hankali ya d’auke hannunsa daga kan goshinnata, ya runtse k’ank’arar dake a cikin towel d’in a hannunsa duk biyu, kafin ya kalleta cikin rashin sanin ta Ina ma zai fara ya ce ”am..Ummi,ki yi hak’u…!” Da sauri ta sa hannunta ta toshe masa baki, ta shiga girgiza masa kai alamun kar ya bata hak’uri, sannan tace”ba komai, ka d’auka a ranka kamar baka tab’a yi min komai ba, kamar su Yasira ma ba su tab’a yi min komaiba…” cikin tarar numfashinta yace “taya zan iya?” Yanzun ma katsesa ta kuma yi tace “dan Allah, dan Annabi, komai ya wuce,pls ka manta da komai, kawai mu faro daga farko.” Ta fad’i hakan tana murmushi sannan ta sake cewa”plssssss” ta had’e hannuwanta waje guda. Kallonta kawai ya tsaya ya na yi, yana mamakin kyakkyawar zuciya irin tata…yana mai jin k’aunarta tana sake shigarsa. A hankali ya ajjiye k’ank’arar a gefe ya sa hannuwansa duk biyu ya rungumota izuwa jikinsa, daidai saitin kunnenta yace”thankyou Saddik’a!you are right!let’s just start a fresh ta yadda zan nuna miki da gaske i’m sorryy and I love you so much!” Murmushi tayi itama tace”i love you”tana mai jin son mijinta yana sake shigarta. …… Sai da gari ya fara haske tukunna Yashjub ya farka daga wahalallen baccin da ya yi awon gaba da shi sakamokon zazzab’in da ya rufar masa lokaci guda! Juyawa ya yi, ya kalli Manu wadda ke kwance lamoo a gefensa, idanunta a lumshe. wani kalar farin ciki da annashuwa ne suka lulub’esa…yana kallonta yana jin kamar ya had’iye ta gaba d’ayanta ya huta, watak’il in ya yi hakan zai samu sauk’in abunda yake ji game da ita. Yadda fuskarta ta kumbura, saman idanunta sukayi luhu luhu ne ya sanya ya d’an ji wani iri, dan ya san ya yi laifi!… Sam, baya so ya zama silar kukanta amman kuma wani ikon Allah ji yake kamar ya k’ara! Wallahi ba ya jin zata taɓa isar, he can’t get enough of her..Manubiya ita ce Mace ta farko kuma inshaaAllah ta k’arshe da ya fara sani amman tabbas ya san ita ɗin ta daban ce, ta musamman ce, dan ba lalle a kuma samun irinta a cikin mata ba, idan kuma an samu to ba su fi kaso ɗaya a cikin ɗari ba! shakka babu, wallahi..shi kad’ai ya san me ya ji. Ahankali ya matsa gareta yana mai jin yadda gaba d’aya gab’ob’in jikinsa sukeyi masa ciwo, sosai ya shige jikinta yana addu’ar Allah ya basa ikon rarrashintan ɗin da yake da niyyar yi ba tare da ya sake yin wani laifin ba…. wani sassanyen murmushi ne ya sub’uce masa wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili, kafin a hankali ya sa Hannu ya rungumeta da kyar sannan ya lumshe idanunsa yana mai sauk’e wata nutsatsiyar ajiyar zuciya,…. tashi d’aya ya shiga koro kirari ma Ubangiji a cikin zuciyarsa, kafin ya d’aura da addua da sanya albarka a Manubiyamatarsa, farin cikin sa, cikar burinsa…. Sun jima ahaka kafin ya bud’e idanunsa, yana mai kallon fuskarta yace”Baby!”a hankali. Tun d’azu idanunta biyu, dan bacci ba nata baneba! Sai dai kuma ba ta jin za ta iya bud’e daidai da kwayar idanunta a halinda ake ciki… Sau uku yana cewa “baby” Jin shiru ya sa ya sake zubawa fuskarta idanu sosai k’irjinsa yana dukan uku uku, ganin tana d’an motsi ne yasanya sa fesar da numfashi a hankali yace “Alhamdulillah”. Sai kuma ya sake hugging d’inta ya ruk’umk’umeta kamar wanda akace za’a kwace masa ita……da godiya ya fara yi mata maganar, kafin ya d’aura da sanya albarka, sai kuma alk’awarurruka iri iri… har da hawaye sai da Yashjub ya yi yana mai yi mata godiya cike da shauk’i da k’auna bayan wanda ya yi a daren jiya. Itakam wasu kalaman nasa ta fahimta, wasu kuma bata fahimta ba saboda tsabar azabar da take a ciki….ta san ruwan ɗumi zai taimaka mata shiyasa ya zamana bata da burin da ya wuci da ta jita a cikin ruwan ɗumin a halin yanzu, dukda ta san za ta sha sabuwar azaba amman ta san hakan kad’ai ne zai taimaka mata. Kamar ya ji abunda yake a ranta kuwa, dan shima tashi d’aya tunanin had’a mata ruwan zafi ya zo masa….anan kuwa ake yinta!Dan duk k’okarin sa na ganin ya ya tashin sam sai ya ji kasa, ya ma kasa matsawa daga gareta, yadda ya yi hugging d’in nata ya sanya ya sake jinsa a sama! ya ji bashi da wani burin da ya wuce ya sake jinsa a cikin duniyar da ya tsinci kansa a cikinta jiya. tsabar fitina shi kansa gab’ob’insa da cinyoyinsa ciwo suke yi masa, ga kuma zazzab’in da ya rufar masa amman a haka ya fara k’ok’arin maida su ruwa…. Manubiya ba ta san tanada ragowar k’arfin da har sautin muryar ta zata iya fita ba, sai da ta ji ta rushe masa da wani irin gigitaccen kuka, mai k’ara!. Shiruu ya yi, ya tsaya yana maida numfashi, kafin ya samu da kyar ya cika ta, ya mik’e ya nufi bathroom kai tsaye ya na tangad’i, dan ya san idan ba tashi ya yi ba to bazata tab’a daina yi masa wannan kukan nata wanda yake jinsa har cikin ransa ba. Sai da ya shiga bathroom d’in tukunna ya nemi towel ya d’aura, sannnan ya soma had’a mata ruwa a cikin makeken bathtub d’in. Ko da ya fito, a yadda ya barta a haka ya sameta, sai dai ta d’an sassauta sautin kukan nata… Ko bargon da ya sauk’a ya bar mata a iyaka guiwarta saboda saurin ganin ya bar cikin d’akin ba ta samu ikon ja ta rufe jikinta da shi ba. Shiyasa ya samu dama ya yi tsaye a kanta ya ya shagala kwarai wajen kallota kawai.. yana kallon nata a ransa yace “Allah mai halitta! How can some one be this beautiful! and this perfect!!. So awesome. (Komai nata dai-dai kuma mai kyawu, abun mamaki..”) Ta san yana kanta a tsaye, kuma yana k’are mata kallo, gashi ta kasa motsi, shiyasa kawai ta k’ara sautin kukan nata. Shi kam yana chan, zuwa wannn lokacin idanunsa sun sauk’a akan d’an jinin da ya biyo ta gefen cinyoyinta d’an kad’an ba mai wani yawa ba!…(haɗe sannan gauraye da wani abu mai kauri, yawa kuma garai-garai) Dama ko da ace bai ga hakan ba, ya riga ya sani..ya san a yadda ya sameta! Amman ganin da ya yi sai ya sake sanya shi cikin wani irin farin ciki, yana mai jin sa a saman gajimare yana yawo, ga kuma tsananin nutsuwa da nishad’in da ya samu, shiyasa kawai ya fara jinsa kamar wani sabuwar halitta!. Ya ma rasa wanne irin gift zai bawa Manubiya as token of appreciation (a matsayin ƙaramar kyautar godiya) dan tabbas bai isa ya ce zai bata gift dai dai da abunda ta basa ba…. Ba kad’an ba, ganinta a hakan ya sauya shi! Amman sai ya daure… yana mai jin tausayi da begenta suna ratsashi,ahankali ya lumshe idanunsa waenda suka d’an fara chanja launi ya bud’e su, kafin ya k’arasa inda take ya d’urkusa ya shiga share mata hawayenta yana cewa “ni kaina haushin kaina nakeji,kar ki damu anjima zan baki bulala ki zaneni!”yana gama fad’in haka ya d’auketa suka nufi bathroom d’in.. bai ajjiyeta a koina ba sai cikin ruwan d’umin da ya gama had’a mata. .. Ita kanta batasan ta na da raki ba sai yau, amman kuma ba za ta kira hakan da raki ba dan wallahi ko macen soja ce ta ji kalar azabar da take kwasa to ta tabbata itama sai ta koka. Da kyar ta tsaya ya yi mata ruwa biyu, ya taya ta tai wankan tsarki, yai mata wankan sabulu, daga haka ya sake sakar mata warm water ya juya ya fita domin ya samu ya chanja zanin gado. Yaye mara kyan ya yi, ya shimfid’a sabo, tukunna ya d’auki mara kyan ya nufi toilet d’in da shi..yana sshiga ya saka a washing machine, bayan ya wanku an busar ya saka a closet domin ya d’an sha iska.. tukunna ya koma cikin bathroom d’in wajenta. A kwance cikin ruwan ya sameta kamar d’azu ta lumshe idanunta,ita kanta tana jin dad’in yadda ruwan zafin yayi mata, tana jin yadda jikinta yake d’an sakewa ciwon yana raguwa…. kamar d’azu yanzun ma d’aukarta ya yi, bayan ya d’aura mata towel sai faman shagwab’a takeyi shi kam kamar ya maida ita ciki haka yake ji sai wani lallab’a ta yake famin yi kamar ya samu kwai.. A haka suka fito, sai da ya sanya mata babban hijabi ya kwantar da ita a kan gadon tukunna ya koma ciki domin yin nasa wankan bayan ya ce mata “ta yi sallah anan inda take babu, damuwa.” Sai da ta d’an zauna da kyar tukunna ta samu ta yi sallar, ta na idarwa ta kwanta atake bacci mai masifar nauyi ya yi awon gaba da ita…. ko da ya fito ya ga tana baccin bai tasheta ba, Sallah shima yayi daganan ya je ya soyo musu omelet, ya had’o da ruwan zafi, kayan shayi da dambun nama… Sai da ya faranajjiyewa a ɗakin tukunna ya wuce sama d’akin shi ya shirya tsaf cikin wata dakakkiyar sky blue d’in shadda da farar hula!… Ya yi kyau matuk’a, kyawunsa ya sake fitowa gashi har wani glowing yakeyi, ya fito ango abunsa ras…duk inda aka gansa dole a sake waigawa a kalla. Tana cikin baccin ta ji ana shafa fuskarta, turo Baki ta yi kad’an kafin ta d’an bud’e idanunta….kyakkaywar fuskarsa ce ta fara yi mata sallama, yana kallonta yana murmushi, A hankali ta mayar ta rufe idanunta ta d’an kauda kai gefe. Murmushi ya yi ya kama kunnensa kafin yace”sorry!” Ganin ta k’i ta bud’e idanun nata ne ya sanya ya d’an rissina dai-dai saitin kunneta ya shiga rad’a mata wasu kalamai waenda suka sanya ta ta fara k’ok’arin tashi a gigice amman kuma ta gagara tashin…. ganin k’iri k’iri ta kasa tashin ne yasanya kawai ta fashe da kuka…. Cikin rashin jin dad’i yace “Wasa fa nake yi miki…so kike hawayenki su k’afe a yau ne??” Ya fad’i hakan yana mai taimaka mata ta zauna kafin a hankali ya sakata a jikinsa, ya shiga rarrashinta har sai da ya ga ta yi shiru tukunna ya mik’e zuwaga gaban dressing mirrow ya d’auko abincin. Kamar jiya yau ma shi ya bata a baki yana ci yana bata tana ci yana gaya mata cewa”likita za ta zo ta yi mata allura, ta bata magani” Tana gama cin abincin kuwa lokacin dai dai 8:00am ko gama saka kaya da shiryawa ma ba ta yi ba wayarsa ta hau k’ara, dan haka ya fita ya sauk’a cikin mintunan da ba su gaza biyu ba ya dawo d’akin ya kama hannunta suka fita wajen Dr d’in…….sosai ta ji dad’in allura da maganin ga wani bacci mai d’an karen dad’i da yake ta faman fusgar ta. Akwai abubuwan tafiyar su da zai karb’a sannan ya kamata ya je ya ga su Mommy, dan haka yace mata “ta basa 30 minutes inshaaAllah zai je ya dawo yanzu… “ Sai da ya rufe koina, ya tabbatar bata buk’atar komai tukunna ya fita bayan yaga bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita….. shi kad’ai sai faman murmushi yake ta zubawa yanta saƙe saƙe a ransa… ….ya san dama zai iya yin komai akan Manubiya amman yanzu ya sake tabbatar da hakan! Mata rahama ne shakka babu…shi a lokacin da bai fara soyayya ba mamaki yake idan ya ga wasu mazan suna nan nan da matan su da kuma mutanen da idan suka fara zina ba sa iya dainawa sai waenda Allah ya kubutar…sai yanzu ya fahimci bayan zazzafan so da k’auna ashe wannan rahamar ce dalili…. Yana wannan tunanin ya tsaya ya karb’i sak’on nasu daga nan ya wuce gida. … Ba kowa shiruu parlourn, dama ba ya son hayaniya balle a rik’esa. Zai samu lokacin su Yassira amman ba yau ba, dan a halin yanzu fuskar Manubiya kawai yake son gani! Allah Allah yake ya koma gidan kawai!!!….. Bayaga hakan kuma ba zai tab’a yarda ya ɓatawa kansa wannan moment ɗin (yanayin) da yake a ciki na asalin farin ciki na haƙiƙa ba, ta hanyar tunkurar su Yasira…. Maganar gaskiya, wallahi jikinsa har ya fara karkarwa….ya san za su fafata da ita kam tabbas, idan ya je! Dan shi kansa bai yi zaton jinsa a hakan, kurkusa ba, amman he can’t help it. D’akin Mommy ya shiga, ga mamakinsa sai ya tarar ba ta nan, dan haka ya d’auki waya ya kirata….har wannan lokacin suna d’akin Kausar, ta samu wani bacci mai dad’i ya kwasheta kenan anan kan sofa, wayartata ta fara ƙara…. Baba larai ta kalla bayan ta ɗaukko wayar taa kalli screen d’in, kafin tace “Yashjub!” Da sauri Baba larai ta matso tace”Ki d’auka. duk yadda na gaya miki ki yi, dan Allah ki yi k’ok’ari ki danne zuciyarki…” Sai da ta tsinke ya sake kira tukunna Mommy ta iya d’auka, dakyar, ahankali tace”Yashjub!” Numfashi ya fesar kafin yace “Na zo bakya nan” “Ganinan zuwa”tace, daga haka ta kashe wayar ta rik’e a hannunta tana huci. Ba k’aramar lecture Baba larai ta yi mata ba, itada Yassira wadda aka samu da mugun mugun kyar karatun Baba larai ya shiga kunnenta ya samu mazauni a kanta, kafin ta mik’e ta nufi side d’in nata fuskarta a murtuke….sai da ta yi da gaske tukunna ta samu fuskar nan ta d’an sake, dan ba kad’an ba hankalinta ya ke a tashe, ji take kamar ta yi hauka!…..abubuwan sun yi mata yawa, jiya haka ta dinga zirya har asuba tana lek’e ko za da ga sauk’k’owar Ummi daga side d’in Daddy amma shiru babu Ummi babu alamarta, kuma har bacci ya d’auketa lokacin 8:49 ba ta ji ta sauk’o ba, shiyasa ta kuma shiga cikin tashin hankali tana mai jin kamar ta je ta barbard’a musu fetur ta kyasta ashana! Tsabar rashin mutunci ko sallar asubah fa ba ta ga Daddyn ya fito yi ba….. Ko da ta zo shiga side d’in nata ma, sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta tura k’ofar ta shiga dan wallahi sam ba ta k’aunar ganin fuskar Yashjub!. A parlournta ta samesshi yana ta faman safa da marwa, dan ya k’agu ta zo su gaisa ya biya ya gaida Daddy ya wuce. Sai da gabanta ya yanke ya fad’i sakamokon wani kalar fresh da ta ga ya yi. Su na had’a idanu ya ɗan daidaita kansa, kafin ya taka zuwa inda take ya d’an rissina yana kallon k’asa yace”Mommy Ina kwana!” ya fad’i hakan yana sosa k’eya. Murmushi ta yi kafin tace”Da ikon Allah yau kunyata Yashjub yake ji. Ina ita surukar tawa? ya ba ku zo tare ba??”. Yanzun ma sosa k’eya yayi kafin yace”Am..tana bacci. sai zuwa jibi InshaaAllah za mu zo tare” . Dum!!! Haka k’irjin Mommy ya buga, da kyar ta lalumo nutsuwa ta sakawa kanta kafin ta yi yak’e cikin son fahimtar wani abun ta ce ”Ai dama da gajiya!” Cike da son b’oye sirrinsu da kuma kar ya bawa kansa kunya Yash d’in yace”Ni kaina kam gajiyar bikin nan tambaya ta take yi, balle ita da ta ke mace” Ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Yashjub ya ji, dan haka ya d’an kalleta. Da sauri tace”Inata fama da Kausar ma shiyasa ban yi muku ko breakfast ba, ku yi hak’uri!” Tashi d’aya Mommyn ta lura da yadda yanayin fuskarsa ta chanja daga jin an ambaci sunan Kausar, a ranta ta ce”Tabbas akwai aiki jaa a gabanmu” A ɓangaren Yashjub ɗinnkam hakan take dan sunan Kausar da Mommy ta kirawo ne ya b’ata masa rai matuk’a a take, ya san matsananciyar tsana ba ta da kyau a musulunci shiyasa yake so ya d’an rage tsanar Kausar a ransa amman sam ya gagara, cikin son kawar da ita a kansa yace”Ba komai Mommy. Bara in je in gaida Daddy sai na wuce, na barta ita kad’ai.” “To”kawai ta samu damar cewa kafin ya fice fitt!. Binsa kawai ta yi da kallo Baki a sake ganin yadda yake ta uban rawar k’afa, ko zama fa bai iya yi su gaisa da kyau ba, “wanne irin abu ne haka?” ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba. Baba larai ta ce mata ta kuncewa Manu jini sannan shima yanzu a yanayin maganarsa ta d’an fahimci babu abunda ya shiga tsakaninsu amman kalli yadda yake ta rawar k’afa wannan Allah ya rufa asiri duk ranar da ya san Manubiya a Mace ai ta su ta k’are! Ya zama dole fa su yi sauri su san na yi da Manubiya tun wuri, a samu ta kama gabanta dan tabbas idan har suka bari Yashjub ya santa a matsayinta na Ƴa Mace to abun zai yi musu dank’o kafin su iya fitar da ita a gidan. Daga side d’in Mommy direct side d’in Daddy ya wuce ya gaida shi….sai da yayi da ya sanin zuwa kuwa saboda yadda Daddyn ya tusa shi a gaba da tsokana, har da cewa ya ƙara yin fari overnight (a dare ɗaya) sai wani kyalli yakeyi….har hajiya mama wadda ya shiga ya tarar suna video call itama sai da ta tofa albarkacin bakinta. Ganin Yashjub yana shirin shigewa cikin k’asa ne ya sa suka d’aga masa k’afa… Daga nan, Daddy Hajiya Mama da Ummi wadda ta shigo da breakfast suka saka sa a gaba suka sake yi masa nasiha sannan Daddy ya nuna masa muhimmanci y’an uwansa, ya ɗaura da cewa “dan Allah kar ya yi fad’a da su saboda Matarsa, kuma kar ya yi musu wani abunda bai dace ba a gabanta”wanda Daddy ya yi hakan ne saboda idan akwai abunda ba zai so gani ba to shine ‘rabuwar kan y’ay’ansa!’ kuma ya san abunda su Yassira suka yi ba su kyauta ba, shiyasa yake so ya yi saurin yi wa tufkar hanci tun kafin abu ya fara tab’arb’arewa tun yanzu. Jinjina kai Yashjub ya yi bayan ya kammala sauraron Daddyn kafin yace”inshaaAllah Daddy zan kiyaye” A ranshi yana lissafin …maybe Daddy ma ya ji tab’argazar da su Yassira suka yi a gidan su Manu, shiyasa ya yi hakan! Daddy yau da kansa ya rok’esa abu while he’s in a good mood (yayinda ya ke cikin yanayi na farin ciki) kuma tunda har Daddy yace’saboda Manubiya’ to ya san yanzu yana yin wani abun bak’in jini zai janyo mata a wajen Daddyn, shiyasa kawai ya saka a ransa zai bar maganar ta wuce inshaaAllah, ba zai yi musu komai ba, amman still zai yi wa Yassira warning!….. Maganar Ummi ce ta katse masa tunani jin tana cewa “ga breakfast d’inku chan, da har na cewa driver ya yi maza ya shirya ya mik’a muku ashe ma kazo, idan kun gama ka yi min magana sai mu je in nuna maka, idan kuma ya riga ya shirya gwaggo ta basa ya wuce da shi shikenan.” Murmushi ya yi yace”Thankyou Ummi” Tsaf Daddy ya lura Yashjub so yake ya tafi shiyasa ya tsaida Ummi wadda ta ke shirin fita ta basu guri ya had’ata da Yash d’in ya sallamesa suka fita shi da Ummin shi kuma suka ci gaba da video call d’insu shi da Hajiya mama. Ko da ya biya d’akin Yahanasu ya ga kamar bata jin dad’i a take ya shiga tambayarta “me ya faru?” A mugun dame!! Dan ko fitala ɗaya bai tarar a kunne a ɗakin ba gashi ta duƙunƙune a bargo wai ta na jin sanyi sannan ba ta son haske…. Kai tsaye ta ce masa “babu komai”dan ta san idan ya ji to yanzun case zai tashi a cikin gidan hankalin kowa sai ya tashi,ita kuma ba ta son ta ɓata masa ranakunsa na musamman dan yadda ta gansa cike da annuri da annashuwa hakan ba k’aramin dad’i ya yi mata ba. Shiyasa ta yi iyaka bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta saka shi ya yarda da cewar ‘ba komai’ ɗin. Da taimakon Ummi wadda ta shigo d’akin basa basket d’in abinci aka samu Yash ya yarda ‘ba komai, kawai gajiya ce ta saukar mata da zazzab’i’ Daga haka yayi musu sallama bayan ya karb’a basket d’in abinci, ya wuce nndc quaters. … A tsaye ya sameta tana d’aura d’ankwali, ta chanza kaya zuwa wani red lace mai d’ankaren kyau shima d’inkin fitted gown, ya zauna a jikinta d’ass!! Kamar A saceta a gudu. K’arasowa ya yi, ya ya tsaya a bayanta ya rungumota yana mai sauk’e ajiyar zuciya. Tunda ta ji shigowarsa dama ta ji gabanta ya fad’i amman sai ta dake….cikin sunkuyar da kanta ta yi masa sannu da zuwa…. bai iya amsata ba sai juyo da ita da yayi ya zuba mata ido, ya shiga yi mata wannan kallon k’urillar nasa.. “Ya su Mommy??” Ta yi masa tambayar cikin son kawo k’arshen kallon. Ahankali ya ce “Um..l-afiya s una gaida k e” Sai kuma yace “K inyi k yau s osai” Ya yi maganar kamar Yaro mai koyon magana “Thankyou”ta ce, ta d’an kallesa tanaso ta tambayesa ko ba shi da lafiya ne ta ji muryarsa a rarrabe kuma yana d’an shivering(karkarwa.) bai bata damar tambayar tasa ba sakamokon kissing d’inta da ya fara yi cike da so da ƙauna… Tun yana yi a hankali a hankali har abun nasa ya soma zarta misali… sai da tafiya ta yi nisa tukunna Manubiya ta fahimci dalilin yanayin maganar tasa, ai kuwa tace ba zai yiu ba shi kuma ya ce ba ta Isa ba!. Tou dai wannan karon su Manubiya har da cewa “Allah sai ya yi musu hisabi!”. … Tayi kuka kamar ranta zai fita! jiya ta fi jin zafi amman wahala da azaba kuwa sai yanzu ne ta san menene ma’anar su, dan ashe jiya bata ga komai ba somin taɓi ne akayi mata….. shi kansa Yash sai da yayi mamakin yadda kwata kwata ya kasa Sarrafa kansa, fahimtar da ya yi komai fa ba a hannunsa yake ba ya sa ya daina ƙoƙarin sarrafa kan nasa kawai ya ci gaba da nemawa kansa nutsuwa yana mai godiya ga Allah, ba tare da ya san lokacin da Allah zai ba sa ikon tsayawa ba…… After 3 days….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 22* After 3 days Ramar da Kausar ta yi a cikin kwana biyun kacal da su ka shige sai da ya bawa kowa mamaki, har duhu sai da ta yi, gaba d’aya ta fita a haiyyacinta, wanda hakan ne ya sake tasowa da Yassir tsumin zargin ta da ya yi a kwanakin baya. A kaff cikin sisters d’insa babu wadda bai tambaya “mai yake damun Kausar?” ba, amman duk suka b’oye masa… Kuma Mommy ce ma ta sake bada goyon bayan a b’oye masa d’in, dan ta san ba k’aramin aikin sa bane ya d’agawa kowa hankali ya hautsina komai ba tare da sun samu yadda suke so ba. Shi kam zuwa yanzu ya san tabbas akwai abunda ake b’oye masa….ya na zargin Kausar tana son Yash tunda sai da ya yi aure tukunna ta zama haka, kuma ko a baya chan ma sai wata maganar aurensa ta taso tukunna take burkicewa, shiysa ya kullaci su Mommy yana mamakin ta yadda suka iya goyawa Kausar baya shi kuma su ka ci amanarsa….tabbas ba zai barsu ba kuwa musamman ma Kausar d’in wadda a kwana biyun nan ko wajenta ya je sai ta ke yi kamar ma irin takurata d’innan yakeyi. Munirat kuwa idanunta sun rufe ba ta ji ba ta gani har side d’in Yassir zuwa takeyi su sha hira su sha soyayaya, hakan kuwa ba k’aramin dad’i yayiwa Yassir d’in ba dan Munirat ta sakar masa ragamar rayuwarta….kamar yadda ta yi zato kuwa tabbas ta taimaka wajen yaye masa tunani da muradin Jidda amman fa ko kad’an ba ta samu gurbi a cikin zuciyarsa ba, dan tsantsar so da kishin Kausar ne cike taff a zuciyarsa…a halin yanzu yanzu bayan san ganin bayan Yashjub babu abunda ya fi sakawa a gaba kamar ya samu ya gano gaskiyar lamari ta fannin Kausar. Sir Najeeb ma yana cikin damuwa, dan kusan kullum sai ya kira Siyama, amman sam ba ta d’auka, jiya kam ya san saboda shi ne ma ta kashe wayartata gaba d’aya…zai ba ta sarari ta huta daga gajiyar biki ,sannan ta d’an yi tunani, shima kuma ya samu ya rabu da Ya’isha cikin lumana kafin ya fara yi mata nacin da shi kansa ya san sai ya takurawa kansa. Jidda kam itama tana cikin matsala, gashi ita tata matsalar ma bata isa ta tattauna ta da kowa ba dan kunya takeji..dukda ta ji Mama tana cewa Inna”jikin Al’ameen d’in Alhamdulillah, ulcer da hawan jini su ke damunsa but yanzu ya ji sauk’i anma sallamosa” Amma hakan bai hanata shiga cikin matsananciyar damuwa ba, iyakar abunda take so, ta kuma san zai kwantar mata da hankali uwa uba ta ke da buƙata a wannan lokacin shine ta samu ta ga ya jikinsa, su shirya sannan su yi aurensu….ta san babu wanda zai fahimceta shiyasa ta rik’e damuwarta iya ita d’aya take ta fama….har ramewa ta yi tashi d’aya duk ta yi zuru zuru. ••• A b’angaren Manubiya kuwa Yashjub ya zame mata abun mamaki….tun tana fushi tana jin haushi har ta daina, dan ita gani takeyi ma kamar he’s possessed….shiyasa ta zubawa sarautar Allah ido amman fa a cikin kwana ukun da suka wuce ta gane Allah d’aya ne! Ga wahala ga azaba shi kuma Yashjub bai san maganar kauda kai ko kawaici a wanga harka ba….ita kam gaba d’aya komai ya fita kanta gashi sun ƙi su yi bak’o ko guda d’aya, ballantana ta samu ta huta. kullum sai ta kira su Jidda amma an hanasu zuwa har y’ar rama ta yi shi kuwa Yash sai kace wanda yayi watanni da yin auren dan ya murmure abunsa ya yi haske sosai ya k’ara kyau. Yau dai Allah ya d’aura Manubiya akan Inna ta yarda akan su Jidda su zo su kawo mata ragowar takardunta da aka manta ba a had’o da su ba. Har da su Ya Musbah za a zo amman Manubiya bata saniba…Ya Musbah da Baba har ma da Ya Nafi’u ne suka harhad’a kud’i suka yi mata gara, kuma sunyi k’ok’ari sosai. Shine za su zo su kawowa a yau. Tun safe taketa faman zumud’i dan ma Yash ya ce “kar ta damu ya riga ya yo order” ne, amma da tuni ta shiga kitchen….bata ma riga ta fara shiga kitchen ɗin ba saboda ya ce “sai sun dawo daga honey moon ɗinsu tukunna sai ta fara girki”, Ummi ce take ta faman yi musu aike breakfast lunch har dinner. Suna zaune ta ji k’arar doorbell, dan haka ta mik’e da sauri ta nufi k’ofa, da mayafinta a Hannu. murmushi yayi ya bi ta da kallo, yana mamakin zumud’in da takeyi, ya san kuma har da murnar freedom d’in da zata d’an samu na wunin yau takeyi. Tana bud’ewa ta ja ta tsaya, ta yi turuss! sakamokon ido biyu da sukayi da Yassira ita da muk’arrabanta a bayanta, har da Kausar. Kallo d’aya Kausar ta yi wa Manubiya ta d’auke kai da sauri, sakamokon bugawa da ta ji k’irjinta ya yi! Tun ba ma da ta yi tunanin ‘Yanzu fa a haka taketa yawo a gaban Yashjub, kwalliyar ma gaba ɗayanta saboda shi ta yi.’. A b’angaren Manubiya kuwa, ba wata kwalliya ta yi ba sakamokon gajiya da ciwon jikin da take fama da shi..ita batama da energy d’in yin kwalliyar. Sanye take da red lace mai adon duwatsun silver, d’inkin riga da skirt wanda ya d’an kamata ba laifi kuma ya fito da asalin surar jikinta…dan mayafin ma a Hannu ta riƙesa dama ganin kuma ba su Ya Nafi’un bane ya sa bata yi yunƙurin rufawan ba ma… babu komai a fuskarta sai d’an ragowar jan jambakin da ana gani an san sid’ewa akayi, jewelries kuwa iyaka y’an kunne ne kawai a kunnenta sai agogo a Hannunta.. Kayan ba k’aramin karb’ar ta ya yi ba kuma ya haskata sosai, sannan yanayin simple d’aurin da ta yi shima sai ya sake fito da asalin kyawun fuskarta, ga kuma kyallin amarci, shiyasa ta sake fitowa ta yi wani irin azababben kyau…. Da kyar ta iya danne takaicin abunda sukayi mata ranar da aka je d’aukota, dan tana ganinsu komai ya dawo mata sabo, a take ta shiga k’ok’arin yakice abun a cikin ranta…dan a ganinta fad’a da gaba da su bashi da amfani tunda su dolen ta ne itan ma kuma dolen su ce!sannan in dai har tana son Yash ya zama dole ta so su. Ta ji zafi kwarai amman tunda shine na farko, gara kawai ta manta ta yafe, but zatayi k’ok’ari wajen ganin ba su maimaita cin kashin su a kanta a karo na biyu. Murmushi ta yi a hankali da niyyar welcoming d’insu warmly ta ji Ya’isha tace “Yassira ki bangaje ta mana ki wuce!” Dariya Yusra ta yi kafin tace ‘’ki yi mata uzuri, kin san a gidan tsoho dogon soro ake antayawa…sannan kin san babu k’ofa ba door bell shiyasa take tunanin shin ya kamata ta barmu mu shige musu parlour kai tsaye ko kuwa?…tunda ba ta san ya ake shiga gida mara soro ba.” Lumshe idanu kawai Manubiya ta yi, tama kasa magana, ta tsaya kawai waje d’aya nan rike da k’ofar. Tsaki Ya’isha ta yi kafin ta taho gadan-gadan zata bangajetan ta shige, daidai Yash ya k’araso wajen yana cewa”Baby ya kuka tsaya a waje, su shigo man.. “ Da sauri Ya’isha ta ja ta tsaya, sai kuma ta koma gefe ta had’e rai ta tamke fuska. Kallon su ya yi d’aya bayan d’aya kafin yace “Ina Yahanasu?”. Sai da Yassira ta d’an fesar da iska tukunna tace”May be tana hanya” Shiruu ya yi kamar zai ce wani abun, sai kuma kawai ya yi shiru. Sam bai yi tunanin suna da audacity d’in (ƙarfin halin) da za su zo inda yake kwana kusa ba bayan abunda su ka aikata,sannan har da wata Kausar,ba ya so ya yi musu wani abun a gaban Manubiya..kamar yadda Daddy ya fad’a, shiyasa yake k’ok’ari wajen ganin bai bada k’ofar da Manubiya za ta ga wani abu na sab’ani tsakaninsa da y’an uwansa ba. Dakyar ya danne zuciyar da ya ke ji tana taso masa, dan yana ganin fuskokinsu komai ya dawo masa sabo. A hankali yace “baby mu je” yayi maganar yana rik’o Hannun Manu, kafin ya kalli Yassira yace mata “bismillah” Daga haka ya ja hannun Manu… kamar wata Yarinya haka ta juya ta bisa suka nufi cikin parlourn wanda hakan yasa Kausar ta ji kamar ta kurma uban ihu!..dama sai da ta cewa Yasira “ba za ta zo ba!kar ta zo ta ga tashin hankali” amman suka tilasta mata a cewarsu “ba za su bar Manu ta sake ta shak’i iska a cikin gidan dai dai da na kwana d’aya ba, sun dinga zuwa kenan daga yau har zuwa lokacin da zata koma mansion d’insu da zama su samu su fitar da ita daga rayuwarsu gaba d’aya.” A kan one seater Manubiya ta zauna, dan taga suna da yawa sannan bata buk’atar zama kusa da d’aya daga cikinsu. Tana jira taga shima ya zauna a d’ayar one seater d’in kawai taga ya nemi guri ya zauna a kusa da ita kamar zai shige cikin jikinta dan kujerar ta yi musu kad’an sosai. Ahankali su Kausar suka k’araso cikin parlourn duk suka nemi guri suka zazzauna, Kausar ta sunkuyar da kanta k’asa sosai kamar zai karye. Tun d’azu Yash ya lura da yanayin Manubiya kuma bashi da tantama a zuwan su ne kafin ya k’arasa k’ofar akayi mata wani abun, Wataƙilan Kausar ce ta harare ta ko ta fad’i wani abun…. Yana wannan tunanin ya ji sun fara gaida shi cike da mutuntawa, jimullah ya yi musu yace “lafiya” Daganan ya koma ya fara kallonsu one by one yana jira ya ji sun gaida Manubiya amman sai ya ji shiru… Minti d’aya ya ware musu, yana cika kuwa ya gyara zama ya ce “ba za ku gaisa da matar gidan ba?”. Ba iyaka su ba ita kanta Manubiya sai da ta ji wani iri, dan ba ta yi tunanin zai iya ce musu hakan ba. Ganin yadda ya tamke fuska kamar bai tab’a dariya bane ya sanya Yusra cewa “Ina wuni” Ta fad’i hakan ba tare da ta kalli Manubiyan ba, dakyar Yadira ma ta gaida ita. Ahankali Manubiya tace “Lafiya Alhamdulillah” kanta a k’asa ba tare da ta d’ago ba… daga haka parlourn ya d’auki shiruuu kamar babu halittar mutane a ciki, kafin Yashjub ya mik’e tsaye kawai ya wuce sama bayan ya cewa Yassira “ta biyosa”. Suna hawa, a nan parlourn saman ya ja burki ya tsaya ya juyo ya ce “Kun zo Gidana! kuma na gode, amma ba zan d’auki iskanci ba! dan haka na baku 3 minutes ku tattara ku tafi, duk lokacin da kuka san abunda ya kamata u guys are free to come back (za ku iya dawowa)”. Kamar za ta fashe da kuka tace”Ya Yash ni ce zan gaida ita??” ta yi masa tambayar tana mai nuna kanta da yatsa. Cikin takaici yace “Yassira gidanta fa kuka zo! A gaban ta kuka gaida ni, a matsayinta na matata ya kamata ace kun gaida ita ko da kuwa kun girmeta, idan ma kuma kuna ganin kun girmeta ɗin ai ko ‘Hi’ da ‘ya gida’ ya kamata ace kun ce mata. Na ga take taken ku na lura fitina kuke nema da ita wanda ban san ribar ku a kan hakan ba, sarai na san abunda kukayi a gidansu, Daddy ne ya ja min burki shiyasa na d’aga muku k’afa ba dan haka ba Wallahi da sai kun gane kuranku! Na yi masa alk’awarin ba zan yi muku komai ba akan wanchan abunda kuka yi ɗin amma hakan ba wai yana nufin zan zuba ido ku taka min Mata ba, dan haka be warned!…kin riga kin san wat i’m capable of ( me na kan iya aitawa,) but for now! (amma yanzun dai) kar ki bari in sauk’o in same ku a cikin gidan nan.” Yana gama fad’in haka ya wuce ya barta anan a tsaye zuciyarta tana wani irin tafarfasa. Ta so ta shiga d’akin Manubiya wanda yake a nan saman ta samu ko da ɗan style ne yadda dai ba za a gane me ta yi a camera ba, ta ɗan zuba abunda Baba larai ta bata ta ce ‘ta zuba’, amman sai akayi rashin sa a ko taku biyu ba ta iya ta yi ba Manubiya ta hawo saman, dan Yashjub yana tashi su Ya’isha suka fara yada mata da maganganu marasa dad’i! Saboda dama a wuya suke da ita! Ji sukeyi kamar su rufeta da duka. Tana d’aga kanta, dayake dama ana iya hango parlourn saman daga nan k’asan ta ga Yashjub ya wuce ya sake hawa bene ya nufi d’akinsa Itakuma Yassira tana tsaye a nan parlourn, shiyasa ta mik’e da sauri ta wuce su ta nufi saman ba tare da ta ce musu uffan ko ta tsaya ɗaukar mayafinta ba ma, tsabar sauri. Takaici da bak’in ciki da rashin jin dad’i duk sun kanainayeta a lokaci guda, zuwa yanzu ta riga ta gama sanin Allah ya had’ata da dangin mijin da ba su san darajar d’an Adam ba sam, kuma ba sa k’aunarta. Ita ko a labari bata tab’a jin labarin jahilan dangin miijin Irin nata ba. Tana wannan tunanin ta hayo sama idanunta taff da kwallah, Yassira ta ji motsinta tun daga stairs shiyasa ta juyo…….ta na juyowa kuwa dai dai ta gama hayowa ita kuma dan haka su ka yi ido biyu!! Da sauri Manubiya ta d’auke kanta, dan sam bataso Yassirar ta ga idanunta, shiyasa tashi d’aya ta kauce ta nufi d’akinta ba tare da ta nuna ta ma ga Yasirar a wajen ba… dai dai ta zo wucewa kenan kawai Yasira ta sha gabanta ta ja ta tsaya, lumshe idanu kawai Manubiya ta yi kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tana mai k’ok’arin rik’e kanta dan tabbas in ta d’ago a yanzu da wannan temper da take ji ta na taso mata to ba Yaseera ba ko wacece sai ta d’auke ta da mari. Sun kusan second ashirin a haka kafin Manubiya ta kauce ta chanja hanya amma sai Yasira ta sake shan gabanta ta tare mata hanya…a hankali Manubiya ta d’an d’ago still tana mai k’ok’arin danne zuciyarta tace”Anya ba daga gidan mahaukata kuka gudo ba kuwa?”. Murmushi mai had’e da dariya Yassira ta yi kafin tace “eh to! amma tare da tsohon da ya d’aura miki aure muka gudo! Anyways Dama idanunki kawai na ke so in gani, saboda ina so in ga gwargwadon ƙarfin jarumtarki, kuma na riga naa gani..dan yadda idanuwanki suka cicciko ɗinnan ya tabbatar mini da cewa ‘u are weak!’(‘ke mai rauni ce’)!! Hakan ya sanya a take a yanzu wallahi har kin bani tausayi, saboda bakiga komai ba! there is a lot coming your way(dan abubuwa masu yawa su na nan tafe zuwa gareki)…” Sai kuma ta kalleta sama da k’asa tukunna tace “Da ni da y’an uwana ba ma yin ki!ba ma sonki, ba ma k’aunarki! Kausar ita mukeso ta auri d’an uwanmu amma kika shiga kika fita, amma dukda haka kar ki yi zaton kin ci riba, dan wallahi idan sama da k’asa za su had’e sai Kausar ta auri Yashjub!!!. Mark my words (Ki rubuta ki ajjiye).” Tana gama fad’in haka ta wuce fuuu cikin tsananin takaici da bak’in ciki….dukda maganganun da ta gayawa Manubiya sun d’an rage mata takaici, amma ji takeyi kamar ta mutu…wai ace yau itace ta zo gidan Yayanta a karo na farko amman ya koreta!!! Saboda ba ta gaida matarsa ba. Gashi ba ta zuba maganin da ta ci burin zubawan ba, kuma Yash yace su tafi! Sannan ta tabbatar ko da ace su Mommy sun shiga maganar an samu an sasanta ta zo gidan gobe to ko dai ya ƙi sake musu, ko kuma ma ya sake ce musu su tafi gaba d’aya!. Ga kuma takaici da tsantsar tsanar Manubiya da ta ke ji tana ratsa ta…ta ya ma Yashjub zai kalle ta ya ce ta gaida wannan Yarinyar, saboda Allah idan shi ya zubar da kansa ya watsar da ajinsa ya aureta ya zubar da mutuncinsa, ai bai kamata ya yi tsammanin hakan daga garesu suma..bai kamata ya sa ran za su zubar da class ɗinsu a wajenta ba suma… Duk lalacewa dole ita Manubiyan ce ya kamata ta gaida su after all ta auri Yayansu!!! an rufa mata asiri!! ta shigo cikin family dinsu y’ar talakawa da ita.!! Amman ace ba ta san na gaba da ita ba!! Haba, -abun sam ba tsari….wato daman zaman da ta yi da kuma tare k’ofar da ta yi tun farkon zuwan nasu jira takeyi su gaishe ta kennan!! shi kuma Yash ya biye mata da ya ke bai san darajar su ba…saboda giyar amarci tana d’ibaar sa shine zai ci musu tuwo aka a gabanta ya wulakanta su saboda ita….. Waennan tunane tunanen ne suka sa duk dauriyar Yassira ta kasa daurewa, dama har yau akwai takaicin dukan da Daddy yayi mata saboda su, shiysa ta na sauk’a k’asan da suka had’a ido da su Yasmeen kawai sai ta fara sakin hawaye….. Gabad’ayansu kanta suka nufa suka shiga tambayar ta “mai ya faru?” Dakyar ta iya controlling kanta tace musu “Ku d’auko handbags d’inku mu tafi” K’asa k’asa da murya Yasmeen tayi kafin tace “Kin zuba, har kin gama?” Girgiza kai kawai ta yi kafin ta sake ce musu “ku taho mu tafi!” Cikin rashin jin dad’i Yasmeen tace “Kamar ya mu tafi? Ba tare da mun yi abunda ya kawo mu ba?” Ahankali Kausar wadda ta fi kowa nad’ar takaici ta d’an dafa Yasmeen d’in tukunna tace “mu je kawai, ma dawo wata rana” Saida Yasmeen ta kalli Yassira tuukunna Yassirar tace mata “ku taho mu tafi kafin ya sak’k’o” Cikin fushi Ya’isha tace “Ba dai shi ya ce mu tafi ba??” Bata rai Yassira ta yi kafin tace “Shikenan! Ni dai kunga tafiya ta…idan ya sak’k’o ya same ku babu ruwana” Ta fad’i hakan tana mai yin gaba ta nufi k’ofa. Cikin tarar numfashinta Ya’isha ta ce”Ai kuwa yau sai dai ya kashe ni wallahi amma babu dalilin da zai sanya in fita a cikin gidan nan!aikin banza ku kuke jin tsoronsa…za a ga ikon Allah yau a cikin gidan nan!” A hankali Yasmeen wadda itama jikinta yayi sanyi ta matsa ta shiga bawa Ya’isha baki. Itakam Kausar juyawa kawai ta yi, ta bi bayan Yassira suka nufi k’ofa, dan tunda uwarta ta kawota duniya ba ‘a tab’a yi mata disgi irin wannan ba! Yashjub bai aureta ba! sannan tunda ta shigo ko kallonta baiyi ba! kuma saboda ba ta gaida matarsa ba yace su fitar masa daga gida.!… Dakyar da mugun kyar Yasmeen ta lallab’a Ya’isha, tukunna ta yarda za ta tafi. Su Yassira suna bakin k’ofar dan a yadda sukaga Ya’isha ta burkice sun san idan har Yashjub ya sak’k’o ya tadda ita to fa ba za su k’are ta sauk’i ba. Tana zuwa ta wucesu, ita ta bud’e k’ofar da k’arfi dan a wuya take, tana bud’ewa suka yi ido biyu da Siyama wadda ta d’aga hannun ta da niyyar yin knocking…tun jiya take kiran Najeeb a waya amman ya’ki ya d’aga kuma bata da tantama saboda wannan shegiyar Yarinyar ne. Hannun Siyaman wanda ta dunk’ule da niyyar yin knocking d’in Yaisha ta bi da kallo, tukunna ta kalli fuskarta tace “Er mallan Shehu bell ake dannawa ba kwankwasawa ake yi ba!” Murmushi kawai Siyama tayi, kafin ta matsa gefe ta tsaya ta hard’e hannuwanta akan kirjinta, kawai. Zuwa yanzu Ya’isha ta fara bawa Yassira haushi, dan ta ga alamun ta rantse sai ta janyo abunda ransu zai kuma b’aci! dan haka ta yi gaba kawai ta fice ta barta a wajen, hakama su Yasmeen suka wuce aka barta daga ita sai Yadira. Ya’isha so tayi ta hana su Siyama shiga, dan ba zai yiu ita ta gidan yayanta amma ace bata samu zama ba wasu kuma su zo su shige a gaban idanunta! amma kuma ganin da ta yi su Yasmeen duk sun watse sun barta ne ya sanya kawai sai itama ta watsawa Siyama tsaki ta wuce tana jin tsanar Yarinyar tana ratsata!ji takeyi kamqr ta koma ta yi mata illa. A harabar gidan suka tarar da Aisha ita da su Ya Musbah da ya Nafi’u sunata faman sauk’e kayan gara daga motar ya Nafi’u da d’ayar y’ar k’urk’urar da suka zo da ita. Takaicine ya sa tunda su Yassira suka yi musu kallo d’aya ba su yarda sun maimaita na biyu ba….tsabar tsiya kalli kayan garar da aka kawo gidan d’an uwansu kamar an rok’o! A haka wai amma har wani so yake a gaida ita! Inaa da sake wallahi… dama sunsan ba za su barta ta rayu a cikin gidan ba, amman dukda haka dole ta gane kuranta ta san matsayinta kafin ta fita a gidan, dan ruwa ba sa’an kwando bane ba. Dama tunda suka tunkarosu Aisha tacewa su Ya Nafi’u ‘kar ma su kula su, kar su ce musu komai, basu da mutunci.’ Haka kuwa suka zo suka wuce bayan sun sake tamke fuska tamau kamar ba su tab’a dariya ba. Ba k’aramin tashi hankalin Ya Musbah ya yi ba, tashi d’aya ya shiga tunanin shin ‘tayaya k’anwarsa za ta yi rayuwa a tsakanin waennan Yaran….’ Tashin motocinsu ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, a hankali ya Nafi’u ya matso kusa da shi ya d’an dafa shi dan shi dama tun ranar da aka kaita Aisha ta basa labarin iskancin da su Yassirar suka yi… Sai da ya fesar da iska tukunna yace “InshaaAllah komai zai yi dai dai, ka kwantar da hankalinka” Cikin rashin jin dad’i Ya Musbah yace “Nafi’u kaga d’aya daga cikin illolin yin aure ba tare da anyi kwakkwaran bincike ba ko? Abunda na ke gudu kenan shi kuma Baba….” Da sauri ya Nafi’u ya katse shi ta hanyar cewa “Karka ce haka! babu ruwan bincike da abunda Ubangiji ya riga ya tsara, kaidai kawai mu taya ta da addu’a”. Lumshe idanuwa ya yi ya bud’e, daganan suka fara jidar kayan suna kaiwa bakin k’ofa,Siyama kuma ta fara kiran Manubiya a waya, dan ya Musbah yana zuwa yace “kar su shiga kai tsaye, su jira Yashjub ɗin ya zo ya shigar da su tukunna.” .. Tun lokacin da Yassira ta wuce ita kuma ta shige d’akinta ta zauna ta fashe da wani irin kuka.. Zuwa yanzu ta riga ta gama amincewa ‘babu ta yadda za ayi su zauna lafiya ita da sisters d’in Yashjub, banda Yahanasu.’. Wanann wacce irin k’addara ce!! Ace wai k’annen mijinka ne za su fito k’iri k’iri su ce maka “ba sa sonka!! Kuma sai sun aura masa y’ar uwar su!” Shin tayaya za ta yi rayuwa a cikin su, taya y’ay’anta za su rayu a tsakanin su?…… Tana cikin wannan tunanin ta ji an bud’e k’ofar an shigo, dan haka ta yi saurin juyar da kanta gefe ta fara k’ok’arin share hawayenta. Murmushi ya k’ak’alo shima dakyar, tukunna ya k’arasa inda take ya tsaya ya shiga k’are mata kallo.. kafin chan ya fesar da iska, ya zauna a gefen ta yana mai ruk’o ta izuwa jikinsa, cikin sigar rarraashi yace “Wanne d’an gangancin ne ya tab’a mini matata? Ko Inna kike missing?” Shiruu ta yi ba ta ce k’ala ba kuma bata daina sauk’e ajiyar zuciya akai akai ba. Murmushi ya sake yi ya d’ago da fuskarta yana kallonta kafin ya ɗan girgiza mata kai alamun ‘ki daina kuka’ tukunna ya ce “i’m not suppose to make you cry…babu kuka ta silata, ki daina pls Baby ki yi hak’uri” Girgiza kai kawai ta yi ta fara k’ok’arin mik’ewa…a hankali ya ruk’o ta yace “Ki yi hak’uri!ko..na baki hak’uri ai,next time idan sukazo za su yi miki magana,it’s only a matter of time (ba da daɗewa ba) za ku fahimci juna da su inshaaAllah… Yanzun akwai abunda ya d’an faru ne….” Ba tare da ta kalle sa ba kanta a k’asa tace “saboda ka ƙi yarda ka auri Kausar?” Sai da gaban Yashjub ya yanke ya fad’i ba na wasa ba! Dan sam bai yi tsammanin jin hakan daga gareta ba, bai so ace ta ji wannan maganar ba!Maganar da yake rok’on Allah Ubangiji kar ya tab’a nuna masa ranar tabbatuwar ta, ko da a cikin mafarki ne. Besides waye ma ya gaya mata?, sannan ai shi ba saboda ya ƙi yarda ya auri Kausar bane ya sa su ke rikicin nan da su! yaushe ma aka tab’a maganar auren sa shi da Kausar?? Ya yi tambayar a cikin ransa. Shiruu yayi ya sake fad’awaduniyar tunani…. sai yanzu kansa ya d’au chaji! wato hatta su Yasira sun san zancen maganar Kausar tana son shi kenan , kuma sun so ya aureta ne, abunda shi da kansa bai sani ba….shiyasa kenan suke fushi suke wannan haukar. To amma Mommy ma a bayansu take itama ba ta son aurensa da Manu! Ba ta son farin cikin sa kenan?! Ita da y’an uwansa duk so suka yi su manna masa Kausar saboda basu damu da farin cikinsa ba ko ya abun yake ne???…. Tashi d’aya ya ji kansa ya d’aure…… Ajiyar zuciya ta sauk’e ganin yadda yayi shiruu ya sha jinin jikinsa, a hankali tace “Ba ka tab’a ce min Kausar family d’inka sukeso ka aura ba. ko a ranar da muka fara had’uwa da ita cemin ka yi she’s just a sister” Ahankali ya fesar da numfashi, ya kamo hannayenta tukunna yace”Wallahi Allah nima yau na fara jin zancen nan Wai ‘Kausar family d’ina suke so na aura!’ ban san maganar ba, In da na sani kin san da zan fad’a miki,but a Ina kika ji zancen?” Girgiza kai tayi tace “Shikenan” daga haka ta fara k’ok’arin barin wajen! A ranta kuma tana mamakin yadda still yake k’ok’arin b’oye mata zancen bayan ga mamaki nan k’arara a kwance a kan fuskarsa wanda hakan yake tabbatar mata da ya san da maganar. A b’angaren Yashjub kuwa mamaki yakeyi…shi dai ya san ya ji lokacin da Kausar tace tana son shi, ya san kuma dama Mommy za ta iya goya mata baya, amma bai san abun ya kai har haka ba, kuma harda su Yassira ma sun san maganar kuma suna so ya aureta ne bayan sun san ita d’in budurwar Yassir ce…. To me yake faruwa ne a cikin gidan nasu wanda shi bai sani ba?, dan ko Manubiya bata gaya masa ba ya fahimci a zuwan su na yau ne aka samu wata ta gaya mata wannan maganar domin a shiga tsakanin ta da shi! Me yasa su Yassira za su zama haka ne! Wannan wacce iriyar halayya ce suka k’irk’iro da ita sabuwa….. Ji yayi kawai ta bud’e k’ofar ta fita, har ga Allah har ta miƙe ta isa ga ƙofa ta fice duk bai san lokacin ba…tana fita wayarta ta d’auki k’ara, dan haka ta d’auka ta kara a kunnenta… Bama ta iya ganin sunan mai kiranba sai da Siyama ta fara magana tukunna ta fahimci ita ce me kiran, shiyasa ta yi iyakar bakin k’ok’arinta ta tsayar da hawayen ta d’an share, tukunna ta sauk’a k’asan da sauri dan ta ji kamar Yashjub d’in zai fito ita kuma har ga Allah a yanzu dai ko fuskarsa bata k’aunar gani! Zuciyarta ta gama aminta da cewa ‘ya san da zancen Kausar amman ya k’i gaya mata’ dan haka tashi d’aya ta yi concluding akan shima yana son Kausar d’in wataƙila dai akawai wani abu da yake b’oyewa amman dai yanada niyyar auren Kausar duba da yadda ya yi shiruu ya gagara cewa komai. Wani irin mahaukacin tafarfasa zuciyarta takeyi, ita kanta ba ta san ta na son Yashjub kuma tana kishin sa irin haka ba sai yanzu da ta ji maganar aure na shi da wata sannan kuma yanayin martanin da ya bata na maganar da kame kamen da ya hau yi mata duk bayan ya ji maganar sun tabbatr mata akwai zancen b’oye mata kawai yayi. Kafin ta k’arasa k’asan har ta fara haki, tsabar yadda k’irjinta da zuciyarta suke lugude ga kuma sauk’an stairs. A bud’e ta hango k’ofar dan haka ta tsaya ta ɗauki mayafinta wanda ta bari akan kujerar ɗazu, ta rufa, tukunna ta ƙarasa da d’an sauri sakamokon fara hango ahalinta da ta yi..dan chan ta hango Muhsin yana fama da roba sai k’ok’arin d’auka yake yi. Da sauri ta k’arasa, ta na fita sukayi karo da su jidda dan haka ta fad’a jikinsu cikin murna da kewar su. Sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta hana kanta kuka, dan ganin su ɗin da tayi ba kad’an ba yasa ta sake zama emotional(sake jin zuciyarta ta yi rauni). Murmushi kawai suke ta zubawa suna kallon ta tana faman bin su ɗaya bayan ɗaya tana rungume su har Ya Musbah, Ya Nafi’u ne kawai batayi hugging ba.. Daga nan ta fara jan hannun Jidda tana cewa”su shigo” ba tare da ta kalli kowa ba, dan sai yanzu ta tuna yadda ta sauk’o ba tare da ta wanke fuskar ta ba…ta san tabbas idan suka yi mata kyakkyawan kallon kurilla to tsaf za su fahimci kuka takeyi, sai dai kuma abunda ba ta sani ba shine tana fitowa duk suka lura da hakan. Ya Musbah ne ya tsaida ita ta hanyar cewa”ki bari ya zo ya shigar damu mana” Dariya Siyama tayi kafin tace “Allah ya Musbah ka iya abun dariya,” Sai kuma ta kalli Manu tace “Tun d’azu fa shi ya tsayar da mu, akan wai ala dole sai Ya Yash ya ce masa ya shiga tukunna zai shiga.” Ahankali ta juyo tace “Dan Allah ku shigo mana”. Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah, amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”. Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalin sa ya tashi da ganin yanayin Manubiya, dan ya tabbatar da kuka ta yi, kukan ma bana wasa ba dan gashi hatta kan hancinta yayi ja!…… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 23* Ahankali ta juyo tace “Dan Allah ku shigo mana”. Yana shirin yin magana Yashjub d’in ya k’araso shima yana d’an murmushi yace “bismillah, amma dai next time ba sai na ce ka shigo ba gaskiya”. Duk murmushi sukayi banda Ya Musbah wanda hankalinsa ya tashi da ganin yanayin Manubiya, dan ya tabbatar da kuka ta yi, kukan ma ba na wasa ba tunda gashi hatta kan hancinta yayi ja!…… Anan parlourn k’asan suka nemi guri suka zazzauna, tukunna su Jidda suka shiga gaida Yashjub cikin girmamawa da mutuntawa. Da kulawa ya amsa yana tsokanar Muhsin da d’an lukuti, kafin ya amsa gaisuwar Aisha da y’arta daganan suka gaisa cikin mutunta juna shi da su Ya Musbah. Yunk’urawa Manubiya ta yi tace “bara na kawo muku ruwa” da sauri Ya Musbah yace “A’a sauri fa mukeyi” Aisha ce ta kalli Yashjub tace “ga gara nan mun kawo, da kayan zak’i. Allah ya sanya alkhairi, ya baku zaman lafiya.” Murmushi Yashjub yayi kafin yace”kun dage dai Aisha, har da wannan wahalar itama?. Wannan fa duk bidi’a ne” Sai kuma ya ce “An gode! Haka ake cewa ko?” Ya yi musu tambayar yana kallonsu. Duk dariya sukayi, kafin su fara mik’ewa da niyyar tafiya… da sauri yace”Au wai dama da gaske kuke? tafiya haka da wurwuri kamar ana korar ku?” Wayarsa ce ta d’auki k’ara, dan haka ya yi excusing kansa ya matsa gefe domin amsa kiran Mommy… Yana wucewa Manubiya ta d’ago Kai ta kalli Aisha wadda har yanzu bata zauna sosai ba ta ce ”Wai da gaske tafiya zakuyi haba mana” Ta fad’i hakan kamar zata fashe da kuka. Murmushi Aisha ta yi tana shirin yin magana muryar Ya Musbah tq katseta ta inda ya ke cewa”Manu, kuka kikayi ne?” Saida ta sunkuyar ta kanta k’asa na d’an lokaci, tukunna ta d’ago ta kalle sa tace “A’a” Sai kuma hawaye sharr suka b’alle mata a take kamar an kunna famfoo. Cikin rashin jin dad’i Aisha tace “Kinga dalilin da ya sa mukeson tafiya da wurin kenan!.. Yanzu dan Allah idan ya dawo ai sai yayi tunanin mu muka ce wani abun ko. Taya zaki sa kuka haka? So kike ki janyo mana bak’in jini?”. Zuwa yanzu Ya Musbah ya tamke fuska tamau tsabar takaici!… Duk rashin hak’urin Baraka sai da ta yi wata goma sha d’aya a gidansa tukunna ta fara kuka a ranar sunan mai sunan baba, saboda ba’a yanka mata rago da tunkiya ba instead an yanka iyaka rago. Amman shi kalli k’anwarsa ko sati d’aya ba ta yi a gidan miji ba amma har ta fara kuka! Ba ma hawaye ba… A hankali ya mik’e ya k’arasa inda take ya zauna a gefenta, yana jin tsananin tausayin ta yana ratsashi, cikin nutsuwa ya bud’e Bakinsa ya fara magana “Manu ko ma menene ya faru ki yi hak’uri kinji ko? ki daina kuka, haka auren yake sai hak’uri..” Ajiyar zuciya Ya Nafi’u wanda ya ke shirin tsaida Ya Musbahn ya sauk’e, dan a tunanninsa tambayar ta Ya Musbahn zai kuma yi akan ‘mai akayi mata’ amman sai yaga yayi lissafin manya, dan haka ya d’an ji sanyi aranshi saboda shima ba kad’an ba ya ji ba dad’i game da yanayin da suka tadda Manu d’in a ciki.” Dakyar Ya Musbah ya sake cewa”Mun so mu d’an zauna amman kukan nan naki ya koremu” Da sauri ta dag’o kanta ta shiga goge hawayen nata tana cewa “Allah na daina” Murmushi yayi yana mai jin inama ace yanada ikon da zai iya goge mata koma wanne irin takaici ne yake addabar zuciyarta haka. Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ”nan gaba idan mun zo, sai ki yi k’ok’arin k’in yin kuka ko?idan har ba ki yin ba sai mu zauna,kin ji?” Ya fad’i hakan cikin d’aga mata gira d’aya. Dai dai nan Yashjub ya k’araso wajen, tun d’azu ya gama waya da Mommy amman ya kasa komawa wajen su..tunda yake bai tab’a jin kunya da nauyi irin wannan ba, dan tun d’azu tunda ya d’ago ya ga Manubiya tana kuka ya ji wata kalar kunyar ta da nauyin su Ya Musbah sun yi masa kawanya. Sam bai kamata ace ya bari hawayenta su zuba ta silarshi ba, ever!. Yana k’arasowa Ya Musbah ya mik’e ya k’arasa inda yake ya mik’a masa Hannu, da kyar duk su biyun suka k’ak’alo murmushi kafin Ya Musbah yace “Kayan suna varender anan muka jere su ,mun so mu shishshigo da su har kitchen mu d’an zauna to amman wannan shagwab’abb’iyar matar taka ta kore mu…daga ganin mu ta hau kuka. Bara mu wuce Allah ya sanya alkahairi.” Wani abune ya tokare k’irjin Manubiya ganin yadda duk cikinsu babu wanda ya damu ma ya tambaye ta me akayi mata, sannan kuma bama za su tsaya ma ta gansu sosai su yi hira ta d’an ji sanyi ba, har zasu tafi..ga kuma kishin Kausar wanda zuwa yanzu haka kurum ta ji ya sake turnik’e ta, dan haka kawai sai ta mik’e da kyar ta je ta yi hugging su Siyama tace “na gode” daga haka ta wuce sama da sauri mai kamar d’an gudu dan bataso ta sake sakin wani kukan a gaban su kar su ce sun fasa dawowa next time d’in ma gaba d’aya. Tun kafin ta kai ga k’arasawa d’akin nata ta saki kuka. Yashjub ne ya rakasu har mota yana ta musu sannu da godiya da basu sak’on gaisuwa a Baba da Inna, dauriya ce kawai yake yi dan gaba d’aya jin sa yake wani iri duk ba da’di. Sai da ya ga fitarsu tukunna ya kira masu gadi yace su shigar da komai ciki. Kasa tsayawa ya yi har su gama, hakanan ya barsu anan k’asan ya nufi d’akin Manubiya ransa duk a jagule…ya lura bayan cin fuskar da su Yassira suka yi wa Manubiya da kuma zancen Kausar tabbas akwai shagwab’a da tab’ara a lamarin nata, ya san sai ya yi rarrashin da gaske tukunna za ta sak’k’o…gashi Mommy ta kira shi tace “ya zo shi da Manubiya yanzun nan!…..” Kamar d’azu yanzun ma a zaune ya same ta a bakin gado, tana kuka. A hankali ya k’arasa inda take ya durk’usa a gaban ta….shi fa bai iya rarrashi ba wallahi bai ma san ta Ina zai fara ba!. Tun lokacin da ya durk’usa a gaban ta gaba d’aya sai ta ji ba dad’i! Dan duk lalacewa, komin takaicin da take ji bai kamata ta bar shi ya d’urkusa haka da sunan bata hak’uri ba, dan ta san hak’urin zai bayar. A hankali cikin sharar hawaye tace”Ka tashi,ba kuka nake yi ba” Murmushi yayi kafin ya ruk’o k’afafunta ahankali yace “Dan Allah ki yi hak’uri…” Da sauri ta zamo daga kan gadon, ta fara k’okarin kwace k’afafun nata tana cewa”Ni dai dan Allah ka daina!babu kyau.” Y’ar guntuwar dariya ya yi yana kallonta yace ‘’babu kyau miji ya bawa matarsa hak’uri?’’ Cikin tarar numfashinsa tace ‘’A’a, babu kyau ka durk’usa kamar haka, dan Allah ka daina, kana sakawa Ina jin ba dad’i” Ta fad’i hakan tana mai goge ragowar hawayen da sukayi saura a fuskar tata. Cikin kwabe fuska tare da kwaikwayar muryar ta yace “To ke ba ki san babu kyau ki yi ta kuka kina d’aga min hankali ba?” Sannan ya ɗaura da cewa “sannan kalli fa a yadda su Siyama suka tafi, na san duk hankalin su a tashe yake, za ayi tunanin ko har na fara cutar da ke ne tunda daga ni sai ke a gidan. Ni addua ta d’aya ma kar su gayawa su Baba”. Shiruu ta yi tana sauraron sa, ganin hakan yasa ya matso kusa da ita sosai ya tallafo fuskarta a tafin hannunsa yace “Hawayen ki tsada gare su, dan Allah dan Allah Baby ki daina saurin zubar min da su. kalla idanunki gaba d’aya kin wahalar min da kanki ba tare da kin tsaya kin ji kan zancen ba ma.” Shiruu ta yi kawai ta kasa cewa komai, haka shima yayi shiru ya zubawa kyakkyawar fuskarta ido…kad’an kad’an ta ji yana matso da fuskarta garesa yana d’an murza gefen kumatunta, ta san inda ya nufa shiysa ta yi saurin mik’ewa ta juya masa baya tana kallon gadon tana mai gyara d’aurin dankwalinta. Lumshe ido ya yi, ya bud’e kafin ya mik’e tsaye ya na kallonta, lokaci d’aya ya saka hannu ya yi hugging nata tsantsan ta baya, a hankali ya d’aura kansa a kan dokin wuyanta yana mai shak’ar k’amshin jikinta mai sanyaya zuciya had’i da ɗimauta shi a ko da yaushe. Cikin tsananin mutuwar jiki ya ce “ki yi hak’uri ban gaya miki asalin maganata da Kausar ba, dalili kuwa shine a lokacin da na ji maganar sam ban dauk’i abun serious ba, shiyasa kikaga ban saka shi a fannin da yake da mahimmanci na rayuwata ba. Dukkannin abunda na gaya miki kika sani game da ni tou shine mai mahimmanci duk abunda kika ga ban gaya miki ba tou bashi da mahimmanci da amfani shiyasa, amma naga kamar rashin gaya miki maganar Kausar d’in yana neman janyo wani labule a tsakanin mu wanda ba zan bada k’ofar hakan ba.” A hankali ya juyo da ita yana facing d’inta rik’e da k’ugunta ya fara zaiyyano mata yadda ranar ya ji Kausar tana gayawa Mommy ‘tana sonshi’ sannan ya d’aura da cewa”Wallahi Wallahi apart from Kausar d’in da Mommy sai kuma Yahanasu da ya gayawa sam shi bai ma san wani a ciikin su Yassira ya san da zancen ba, bai san maganar ta je kunnuwansu ba ta yadda har suke tunanin zai aureta, shi a mazaunin shirme da rashin tunani ma ya d’auki maganar tata shiyasa bai bawa abun mahimmanci ba. Amman yana so ta yi masa alfarma d’aya!’ta manta da komai da kowa ta yarda da shi akan abunda zai fad’a mata yanzu ‘Tun yana Yaro shi tsarin mace d’aya garesa, kuma Kausar ita ce Mace ta ƙarshe da zai iya aura, saboda kwata kwata jininsa bai d’auke ta ba tun yarinta, ko da ace su biyu ne kad’ai suka rage a duniya ba ya jin zai iya rayuwa da Kausar a matsayin matarsa’….’’ A hankali Manu ta sunkuyar da kanta tana jin wani sanyi da nutsuwa yana lullub’eta, dan tabbas maganganunsa sun rufe kusan kaso arba’in na damuwarta, zuwa yanzu ta fahimci ba b’oye mata yayi ba. Dukda tana fargaba da kuma kishin yadda Kausar d’in take son Mijinta amman still ta d’an ji sauk’i da ya fito ya gaya mata komai, sannan daga yanzu ta zaɓi ta yarda da shi akan lamarin,kamar yadda ya buk’ata. Cikin son sake kwantar mata da hankali ya d’ago da fuskarta yana mai kallon kwayar idanunta yace “Mannubiya ce kad’ai a cikin zuciyar Yashjub! Ba ki san yadda kika tare gaba da baya ba shiyasa kike wannan tunanin, amma inda ace kinsan yadda kikayi bake bake a cikin zuciyata to da ko ni da kaina idan nace miki zan k’ara aure ko zan kula wata na san ba za ki tab’a yarda ba… I love you, only you, no one else!.. So idan ma akwai wani tunanin zan auri wata ko zan kula wata daban a ranki gara ma tun wuri ki cire saboda wahalar min da zuciyarki kawai kike yi, Iyaka abunda na sani shine ‘ke kaɗai ce tawa’ kuma na san su Daddy ba za su tab’a yi min auren dole ba. Dan haka..pls Baby! ki daina b’ata ranki…um?!..” Ya k’arashe maganar tasa cikin sa hannu ya janyo ta jikinsa sosai, kafin ya d’aura da cewa “ko amarci na ma ban fara ci ba har Amarya ta fara shiga damuwa ta fara fushi da ni, Pls ki daina, Plssssss” ya fad’i hakan kamar zai fashe da kuka yana sake sakata a jikinsa. Shiruu Manubiya ta yi, a ranta tace “au bai ma fara cin amarcinba a hakan…” Tana wannan tunanin ta ji yanayin nasa yana shirin sauyawa dan haka ta d’an yi y’ar dabara ta goce dakyar tukunna tace”Ya wuce fa! Ni ba fushi na yi ba, kuma na daina kukan ai” Cikin sake ruk’ota yana dariya dan ya fahimci zillewa ta ke son yi yace “ba wani nan!fushi kikayi mana bayan k’iri-k’iri d’azu aka yi denying d’ina kiss, yanzu kuma hug anjima kuma Allah kad’ai ya san mai za a hanani…” Daga haka ya janyota ya fara aika mata da sak’onninsa ma su zafi da tsada…… Addua ta fara yi ‘Allah ya kawo mata ceto’ dan a yadda ta ji ya fara sakin layikan nan ta san k’aniyarta za ta ci. Allah kuwa ya amsa adduar tata dan tashi d’aya wayarsa ta fara k’ara…sai da aka kira har sau biyu bai kula ba, jin kiran ya ƙi k’arewa ne ya sa yace”Ohh God!” kafin dakyar ya samu ya sa hannu ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kasheta gaba ɗaya amman sai idanuwansa suka hango masa sunan Mommy b’aro-b’aro…shi fa sai yanzu ma ya tuna da neman nasu da takeyi, wallahi shaf ya manta…sai da ta tsinke ta sake kira tukunna dakyar cikin k’ok’arin daidaita muryarsa ya d’auka ya ce”Mommy ga mu nan zuwa” daga haka ya kashe wayar ya kalli Manu ya ce ”Bamu je ba, gashi Mommy har ta fara neman mu. kece kika k’i ki warke da wuri shiyasa mukayi letti” ya fad’i hakan yana dariya k’asa k’asa yana mai sake kissing d’inta tukunna ya mik’e da kyar…. Yasan idan suka zauna a d’aki d’aya suka ce za su shirya to ba za su yi sauri ba, gashi ya d’an jiyo fushi a muryar Mommy, hakan ya sanya ya ce mata”ta shirya da wuri, bari shima ya je ya shirya” Daga nan ya koma ya sake kissing nata kafin ya fice da sauri dan ji yakeyi kamar akwai wani magnet d’in da yake jansa zuwa gareta. Yana fita ta sauk’e ajiyar zuciya, had’i da ta’a’uzi dan tashi d’aya ta ji wani tsananin kishi ya lullub’e ta sakamokon tunowa da ta yi ‘zata had’u da Kausar idan ta je gidan.’ .. Cikin nutsuwa tana ta korar shed’an a hankali ta shiga shiryawa…wanka ta fara yi tukunna ta fara d’auko kayan da za ta saka. A ganinta gidan surukai za ta je, shiyasa ta yanke shawarar saka kayan da suka yi mata a cikin lefe dan ta san in suka ga ta saka za su ji dad’i kwarai. Wata dandatsetsiyar atamfar exclusive ta saka, kalar royal blue da ratsi ratsin silver da red, an zuba mata d’inkin riga da skirt na zamani waenda sukayi asalin amsarta…ita kanta ta san d’inkin ya fito da ita ras , matsalar ta d’aya yadda d’inkin ya matseta gashi kusan rabin k’irjinta duk a waje, sannan skirt d’inma ya kamata, ga waist d’in ya fito sosai shima…d’inkin ya fito da surar jikinta gaba d’aya. dama tun jiya da ta zo zab’ar kaya ta lura da yanayin d’unkunan..gaba d’aya sun yi fitting dayawa, dan haka ta yanke akan gaskiya idan ta samu lokaci zata ce su mayar musu a dan bud’a mata dan ba zai yiu a kashe uban kud’i ba kuma a yi mata d’inkunan da ranta bai so ba…. Dama tanada abun d’auri na ture kaga tsiya, dan haka ta d’auko ta saka a cikin dankwalin nata ta ajjiye, kafin ta koma gaban madubin ta d’auka powder ta shafa ta saka eye liner ta d’auko lipstick ta shafawa labb’anta. Ita kanta ta san tayi kyau, irin sosai d’innan..murmushi ne ya sub’uce mata ta san Ya Yash yana shigowa zai hau mita yace ‘mugunta ta had’a masa, saboda ta san ba zama za su yi a gidan ba shiyasa ta chab’a wannan uwar kwalliyar.’ A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya tana jin tsantsar k’aunar mijin nata tana sake shiga jikinta tana ratsa ko’ina. Tana tunanin shi tana murmushi a haka ta shiga tufke gashin kanta a ta baya chan k’asa ta kanainaye sa ta saka d’an siririn ribbom black gudun kar ya sunce, daga nan ta d’auko dannkwalin da ta saka abun daurin a cikin ta d’aura sa perfectly. Saida ta san yadda ta yi ta b’oye uban tulin gashin nata da ya fito ta k’asan d’aurin, tukunna ta tafi closet ta bud’e wardrobe ta zaro mayafi, jaka da takalmi, kafin ta d’auko iyaka y’an kunne zobe da agogo kawai dan ba ta cika son sark’a da awarwaraye ba.Y’an kunnenta,zobe agogo da Mayafinta silver yayinda jaka da takalminta suka kasance red colour. Tana shirin yafa mayafi ya turo k’ofar ya shigo..dama k’ofar take facing dan a kan gadon nata ta jere jaka da mayafin nata. Saida numfashin Yashjub yayi sama ya dawo bai san lokacin da a fili yace”MashaaAllah,Ubangiji mai halitta.”ba. Kamar had’in baki shima sanye yake da kaftan blue nasa da farar hula da farin takalmin da agogo,wanda hakan ya yi kamar anko sukayi. Ahankali ya taka ya shigo cikin d’akin idanunsa a kanta. Gaba da’ya Manubiya sai ta diririce sakamokon kallon da ta ga yana yi mata…so take ta ware mayafin ma ta rufa amman sai ta kasa. Murmushi yayi kafin ya maida k’ofar ya rufe ahankali ya k’arasa inda take, still idanunsa suna a kanta. Saida ya gama k’are mata kallo tukunna ya sa hannu ya karb’i mayafin sannan ya zagaya ta bayanta ya tsaya tukunna ya ware mayafin gaba d’aya ya rufa mata shi a saman kanta, gefe da gefen kuma ya zagaya dashi ya rufe mata gaba d’aya jikinta dashi wanda hakan ya basa damar yin hugging d’in ta! A tare shi da ita suka sauk’e ajiyar zuciya kamar ta saani dama aikuwa ta ji yace “Wannan dai tsokanata akayi, amman kar ki damu, zan fanshe idan muka dawo”. Daga haka ya manna mata wani dogon peck a kumatunta, kafin yayi saurin cikata dakyar, yana mai sauk’e ajiyar zuciya. Jakarta ya d’auka, daganan ya ruk’o hannunta suka fita tare gwanin ban sha’awa. Wani Irin shauk’i da so ne suke jan Yashjub game da ita, ji yakeyi kamar ya had’iye ta ya kora da ruwa ko ya samu sauk’in abunda yake ji. Gaba d’aya robobin kayan zak’in garar Manubiya tace su tafi da shi a su Mommy, ita za ta raba har su sai ta basu nasu haka akeyi. Sai da ya bud’e mata mota ya sakata a ciki tukunna ya kira masu gadi suka kwasa suka sanya a boot da seat d’in baya sannan ya shiga motar ya ajjiye Jakarta da yake rik’e da ita, ya zauna tukunna ya kunna mai gadi ya bud’e musu suka fice. Har suka k’arasa gidan Daddy yana rik’e da hannunta..da hannu d’aya yayi tuk’in sai dai in zai chanja gear ne ya ke d’an cikata yana chanjawa kuwa ya ke sake ruk’ota kamar wani zai kwace masa ita ne. Haka kurum suna zuwa bakin gate d’in gidan da taga ya danna horn ta ji gabanta ya yanke ya fad’i sosai..da kuma ta tuna su Yassira da Kausar sai ta ji ranta ya b’aci…..salati ta shiga yi a cikin zuciyarta, da ikon Allah sai ta ji fad’uwar gaban da b’acin ran suna raguwa. Tunda suka shigo gidan ta shiga alajabi da mamakin tsantsar girman gidan, ita tana ganin gidanta Babba ashe ga mansion anan! MashaaAllah masu kud’i suna hutawa..tashi d’aya ta fara addu’ar ‘Allah itama ya bata ikon fara aiki, ya bata kud’i, ta samu ta siyawa su Baba gida ko d’an flat ne suma su ji dad’in rayuwa.’ A parking space sukayi parking, kafin ya kashe motar ya d’auki jakarta ya fita da niyyar zagayawa ya bud’e mata… da sauri ta juya ta bud’e ta fito da kanta kafin ma ya zagayo. B’ata rai ya yi sosai kafin yace”Why?!” Murmushi kawai ta yi tace “yi hkr”…. Da kyar ya d’an saki fuska ganin ta masa kalar tausayi tukunna suka wuce suka nufi main parlour. A bakin k’ofar shiga suka ci karo da Yassir wanda ya zo shiga shima..bai dad’e da dawowa daga office bama jakarsa kawai ya ajjiye a side d’insa ya zo da niyyar ganin Kausar dan kwana biyu karantarta kawai yake yi…ya fi minti d’aya tunda ya hangosu har suka k’araso suka tsaya yana k’are musu kallo yanajin yadda zuciyarsa take wani irin tafarfasa! A ransa yana aiyyana”how can Yashjub be this lucky….ta ya zai fi sa sa’a ata ko wanne b’angare ata ko wanne fanni na rayuwa!….” Da mamaki Yashjub yake kallosa yana la’akari da yadda idanuwansa suke sauya kala dan lokaci guda yaga sun fara rinewa suna chanzaa kala zuwa jajajaja… Babban abunda ya b’ata masa rai game da Yassir d’in shine yadda ya kafe Manubiya da idanuwa ko kiftawa ba ya yi. Ashe haka take!wacce iriyar kyakkyawar halitta ce wannan mai tafiya da imanin d’an Adam…tabbas ya zama dole Yashjub ya mutu kwanan nan ta yadda cikin sauk’i zai had’a Kausar da Manubiya a matsayin matansa ya yi rayuwa mai dad’i.Dan bayan Kausar ba ya jin akwai wata da ya ji yana so ya yi rayuwar aure da ita bayan wannan baiwar Allahn. “Yasir’’ d’in da Yashjub yace maasa a d’an zafafe ne ya dawo dashi daga duniyar da ya lula. Wani lumshe idanuwa yayi wanda hakan ya kuma k’ular da Yashjub, kafin ya bud’e ya ce “Welcome” Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya wadda tashi d’aya ta ji kamar ta rufe sa da duka ganin irin kallon da ya shiga yi mata…. Murmushi ya d’an yi yace “antynmu, barka da zuwa, bismillah” Ya fad’i hakan yana nuna mata k’ofa, kafin ya d’aura da cewa ‘’Yau dai Ya Yash ya bari anga fuskarki” Da kyar da mugun kyar Manubiya ta k’ak’alo wani d’an guntun murmushi wanda ya tsaya a iyaka labb’anta ne tukunna ta bi bayan Yash wanda ta ga ya juya kawai ya ruk’o hannunta suka nufi cikin parlourn. Bayan su kawai Yassir ya bi da kallo yanajin yadda k’irjinsa yake wani irin bugawa…yadda ya kafe Manubiya da ido yana k’are mata kallo hatta yanayin kwalliyar stones d’in jikin rigar ta sai da ya gani ya haddace ta cikin mayafin ta. Suna shigewa ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya jinjina kansa kafin yace “da sake!” daga haka ya sa kai shima ya nufi cikin parlourn… A main parlourn gidan suka samu Mommy, Baba larai, Ya’isha da Kausar a zaune suna magana da alama mai mahimmanci ce, sallamarsu ce ta sanya sukayi sauri duk suka d’ago suka zuba musu idanu…. tashi d’aya yanayin fuskar Ya’isha ya sauya ganin Yashjub d’in ne ma ya ruk’o wa Manubiya jaka. Da sauri ita kuma Kausar ta mik’e ta wuce sama Yayinda Baaba larai ta mik’e ta fara cewa “Lale marhababiki Amarya surukar mu… Yashjub bismillah mana, k’araso! Ku shigo ciki, ya ka barta nan bakin k’ofa a tsaye..” Ta fad’i hakan tana nufar su tana Isa ta kamo Hannun Manubiya ta zare a cikin na Yashjub ta ja ta suka nufi cikin parlourn. Dakyar Manubiya ta iya janye idanuwanta a kan Baba larai, sarai ta shaida ta..itace suka ce sai ta durk’usa sannan duk wani mai hankali yana kallon fuskarta tashi d’aya zai shaida ba farin ciki takeyi da auren ba, amma kalli yau itace kamar zata cinye ta! Tabbas waennan shaid’anu ne!!! wato idan a gaban Yashjub ne ba za su nuna mata k’iyayya ba kenan! dan ta lura da Yasira ma d’azu saida ta bari babu Yashjub a wajen tukunna ta gaggaya mata maganganu….. A gefen Mommy daff da ita Baaba Larai ta zaunar da Manubiya kafin ta ce ”bari in je in kawo muku ruwa, sannu Amarya, lalle marhaba” Ta fad’i hakan tana mai wucewa da sauri har da d’an yin tuntub’e. Yashjub ne ya d’an tsayar da ita ya sanar da ita batun kayan zak’’i, dan haka ta karb’i makullin motar tasa tace ‘bari ta nunawa su gwaggo su kwasa su saka a kitchen.’ A hankali Ya’isha ta mik’e kamar ba itace ta baro gidan d’azu tana fushi ba ta k’arasa wajen Yash tace “kawo jakar ni in rik’e mata” Ta fad’i hakan tana mai amsar jakar. Tashi d’aya kawai sai ya ji kunyar Mommy ta kama shi, dan haka ya cika mata jakar ya k’arasa inda Mommyn take ya zauna a gefen ta dai-dai nan su Yassira ma suka fara sauk’owa, da alamar Kausar ce ta gaya musu Yash d’in ya zo….. tare suka sauk’o gaba d’ayansu har da Daddy, da alamun tare suke da shi a saman, shi Yashjub ma bai yi tunanin Daddyn yana nan ba, ya d’auka yana office duba da yadda shi baya nan Yasira ma ya ga yau ba ta je ba. A hankali Manubiya wadda tun d’azu ta ke jin nauyin zama a kusa da Mommy ta d’an sullub’o daga kan kujerar tace “Mommy Ina wuni” Saida Mommy ta yi namijin k’ok’ari dagasken gaske tukunna ta iya dafa kanta a hankali tace “lafiya y’ar albarka, ya bak’unta” “Alhamdulillah”tace, a ranta tanajin wani sanyi dan yadda Mommyn ta yi mata ya sanya ta ji dad’i sosai, ta kuma fahimci itan tana sonta ba kamar su Yassira ba..ta san dama zuwa d’auko ta da kai lefe ba hurumin Mommy bane amma da aka d’aukota tace “a wuce da ita ba sai ta zo ta gaida ita ba!” da kuma yadda take kiranta a waya amma ba ta amsawa ya sa ta d’an ji tsoro ta shiga damuwa da tunani….. Muryar Daddy ce ta katseta jin yana cewa”Manubiya mik’e ki zauna a kan kujera mana, tashi kinji” Murmushi ta yi sai da Yashjub wanda shima yaketa zuba murmushi dan ba kad’an ba ya ji dad’in yadda iyayen nasa suka nuna kulawar su ga matar tasa, ya d’an sunkuya ya kalleta a hankali yace “mik’e ki zauna mana.. Daddy yana magana” Tukunna ta mik’e ta zauna a kusa da Mommy inda take tun farko tanajin wani nauyi da girmanta yana ratsa ta, dai dai nan su Daddy suka k’araso suka zazzauna, shima saida ta durk’usa har k’asa tukunna ta gaidashi ya amsa da kulawa. Da sauri yace”Ummi bata sauk’o ba Yassira je ki ki kirata” sai kuma ya zaro waya yace “Bari in kirata” ya fad’i hakan yana dialing number Ummi, ba ta dad’e tana ringing ba ta d’auka. Tana d’auka yace “ki zo munyi bak’i” daga haka ya katse kiran yana mai tambayar Manubiya “ya bak’un ta” Cike da girmamawa da kunya suke amsa shi. Suna a haka Munirat suka sauk’o ita da Ummi. Da sauri Munirat ta k’arasa ta je ta zauna a kusa da Manubiya tana “oyoyo antynmu, ashe kune Ina wuni” sai kuma ta kalli Yash ta gaidashi. Kamar yadda Manubiya ta yi wa Mommy da Daddy haka ta zamo ta gaida Ummi itama..ta kuwa ji dad’i, dan haka ta shiga tambayar ta ya sabon waje ya su Innarta…. mik’ewa Yash ya yi yace”Bara mu lek’a Yahanasu,ya jikin nata?.” Da sauri Mommy tace”da sauk’i!.Munirat ta kai Manubiya wajen Yahanasu, kai kuma ka zauna munada magana da kai!” Shiruu ya d’an yi, da sam bai ji dad’i ba , ya san Manubiya zataga kamar an ware ta ne… Yana cikin wannan tunanin suka mik’e ita da Munirat suka nufi d’akin Yahansun jiki ba kwari. Lumshe ido Yashjub ya yi har su ka shige bai bud’e ba.. Muryar Daddy ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula jin yana cewa “Yash, mai ya faru yau ka koro k’annenka daga zuwan su na farko gidanka?” Da sauri ya bud’e idanuwansa ya kallesa, sai kuma yayi kan Yassira a zuciye…. Da sauri Mommy ta mik’e ta tsaya a gaban Yasirar tace”ai ni za ka daka ba ita ba! tunda nice nan na gayawa Daddyn naku, ba ita ba!” Ummi ba ta san kan labarin ba, ba kuma ta san abunda ya faru ba amman tashi d’aya ta fahimci laifin su Yassirar ne…baya ga haka saboda Allah ta ya Daddy zai biyewa Mommy a zuwan Yashjub da Manubiya na farko gida a fara da case! Su da ya kamata ace sun saka su a gaba sun yi musu fad’a da nasiha , sannan sun yi k’ok’ari wajen basu chance su fahimci juna, amman kalli yadda tun farko aka sallami Manubiya akace a rakata d’akin Yahanasu, saboda Allah wanne irin rashin lissafi ne wannan?,ya suke tunanin Yarinyar za ta ji saboda Allah….. Ta san inhar ta zauna to tabbas za a yi fad’a da ita ne, shiyasa kawai sai ta mik’e tace ‘’Am Daddy bara in d’an baku guri dan Allah”tana gama fad’in haka ta wuce sama, bata yarda ta kuma had’a ido da Daddyn ba….sai da ta had’a da sauk’ar AlK’urani da addu’o’i tukunna ta daina jin matsananciyar tsanar sa, haka kurum ta samu sun shirya shima ya daina fushi da ita da kyar ! ba ta ga dalilin da zai sa ta zauna a wajen da zata fad’i abunda zai ji haushi su yi fad’a su sake komawa ruwa ba. “Ta fi Nono fari” Mommy tace a cikin zuciyarta, kafin ta maida hankalin ta ga Yashjub wanda ya ke cewa Yassira da ta b’oye a bayanta “k’ara ta kika kawo? ke ba ki fad’i abunda kuka yi ba?” Cikin tarar numfashin sa Daddy yace ‘’Mai sukayi?’’ Tun kafin Yash yayi magana Ya’isha tace ‘’Wallahi Daddy bamuyi komai ba, dama tunda mukaje ta tare hanya ta hanamu wucewa, sai da ya zo tukunna ta matsa. Ina ga yanayin fuskar ta ya kalla dan tanata faman kumbure kumbure shine ya kira Yasira ya ce ta kwashemu mu tafi’’ Wani irin takaici ne ya lullub’e Yashjub wanda ya sa ya ji kamar ya finciko Ya’isha daga kusa da Daddy ya feffella mata mari…ya godewa Allah da ba a kusa da shi take ba dan ya san yau da sai ya illatata! Ganin Yaran suna neman haukatasa ne yasa ya koma ya zauna, ya dafe kansa wanda ya fara sara masa. Gyaran murya Daddy ya yi kafin yace”Yashjub!! tun wanchan ranar a asibiti na fad’a maka kar ka bada k’ofar da matarka za ta raina y’an uwanka! And again a washegarin ranar da ka yi aure ma sai da na rok’ek’a da kaina akan kar ka bada k’ofar da kawunan ku zai rabu a ta dalilinta, amman naga abunda ka dage, ka durfafa sannan kuma ka ke ta ƙoƙarin yi kenan…. Sam!ban ga dalilin da zai sanya dan ka yi aure ka tsame y’an uwanka a jikinka ba, ba zai yiu ba!! ba zan zauna in zuba ido zumuncin ku ya tarwatse ba saboda rashin tunanin ka da kuma gigin giyar soyayyar da ka kurb’a.” Yashjub ji yayi kamar ya d’aura hannu aka yayi ta faman zunduma ihu…ta ya Daddy zai biyewa waennan Yaran, ya hau kan maganganunsu ya zauna daram, sannan ji fa tone d’insa sai kace na mace, yana magana kamar ta mata… yanzu wannan d’an k’ank’anin abun har ya kai a titsiyesa a gaban su haka……. Muryar Daddy ce ta katsesa jin yana cewa”ina sauraron ka, ka fad’amin exactly abunda ya faru. Ku kuma” yayi maganar yana nufin a su Yassira yace”kar in ji bakinku, har ya gama magana.” Wato dai a gaban Yaran nan za a yi masa haka! alk’alanci kenan Daddy zai yi musu shi da k’annensa…. “Ina jin ka mana!” Ya ji muryar Daddyn a d’an zafafe. A hankali ya d’ago ya kalli Daddyn yace”Ba su kula ta ba. Kaff cikin su, saida na yi magana tukunna Yadira ta gaida ita‘’ Da takaici Mommy tace “Saboda ba su gaida matarka ba shine ka koro su daga gidanka??’’ Cikin son fahimtar da ita yace ‘’Mommy saboda sun rainani, kuma sun ki su yi abunda nace a gabanta sun nuna min ban Isa ba, shiyasa na koro su.. Bayaga haka Mommy ta ya za su je har gidanta su k’i su kulata? sannan kuma ni da kaina in ce su yi su k’i yi! Maatata ce fa!’’ Ai ko da ace ba za su gaida ita ba da ko ‘Hi’ ya kamata su ce mata…..” Cikin tarar numfashin sa Ya’isha tace ‘’Daddy cewa ya yi duk sai mun gaida ita, har Yasira da Kausar. kuma fa ita ma bata kula mu ba, how yake tsammanin mu mu gaida ita?.” Throw pillow Daddy ya jefawa Ya’isha, cikin fad’a yace “Ba na ce bana son jin bakin kowa ba?” Da b’acin rai sosai ya juya ga Yashjub ya ce “Yashjub’’ Ahankali Yash ya kalle sa ya ce ‘’Na’am Daddy’’ Cikin bada umarni da fahimtarwa Daddy ya fara magana ‘’kamar yadda na fad’a d’azu.. ba zan bari giyar soyayyar da ka sha ta lalatamin zumuncin dake a tsakanin ku ba! Ba zan bari wata mace ta shiga tsakanin ku ba, dan baka san yadda muka sha fama ni da mahaifiyarku wajen ganin mun daidaita kanku ba!” Ahankali Yash ya lumshe ido yana mamakin yadda su Daddy suka d’auki laifi gaba d’aya suka d’aurawa Manubiya…ta yaya Manubiya za ta shiga tsakanin sa da su Yasira, shi kuma ya yarda.. Dan mai ya sa tun farko idan irin haka ta faru a tsakanin su ba’a d’abbak’a abun sai yanzu da yayi aure? Kuma shi rainin da suka yi masa a gabanta ne ma ya sake harzuk’a shi har ya koro su!! a tunanin sa ya Isa da su. Inda ace ci musu fuska ya so yi ai da a gaban Manubiyan zai fatattake su…Ita Manubiyan ma da suke ta cewa ‘za ta shiga tsakanin su’ bama ta san da case d’in korar sun da yayi ba. Ahankali tunanin sa ya dawo cikin parlourn jin Daddy yana cewa “Inaso ka sanar da Manubiya, idan kuma ba za ka iya ba to ni zan sanar mata cewa ‘Yadira da Yusra za su gaida ita wannan dole ne! Amma tun daga kan Ya’isha har zuwa kan Yassir har Kausar ita ce zata gaida su tunda duk sun girme ta.’” Da mugun sauri Yashjub ya d’ago sosai ya zubawa Daddy idanuwansa. “Kwarai kuwa”Daddy yace shima yana kallonsa, kafin ya d’aura da cewa “Ba wai nace dole idan sun had’u sai ta gaida su ba, ruwanta ne idan taga dama ta kula su in bata ga dama ba karta kula su, amman kasancewarsu yayyu a gareta ya sanya ba zai yiu ace su su fara gaida ita ba. Idan ta kula su ta gaida su su amsa Idan kuma bata kula su ba to wannan alhakin yana a kanka na ganin ka daidaita alak’ar dake a tsakaninta da su! Kai ne za ka nuna mata cewa yayun ta ne su ɗin kuma ta dinga gaida su saboda a samu a zauna lafiya, a raya zumunci…. Sai kuma magana ta biyu ‘Daga yau har gaban abada idan su Yasira za su je gidanka a rana sau goma to baka da iko sannan baka Isa ka kore su ba! Na san gidanka ne, na san kai ne ka siya ka zuba furnitures ka yi komai da kanka amman ni kuma nine ubanka! dan haka in dai ni na haife ka, to Yassira,Yahanasu,Ya’isha,Yadira,Yasmeen,Yusra,Yassir kai har ma da Kausar duk za su je gidanka a duk lokacin da suke so! Idan ma hutu suke so su yi to za su je su yi har sai sun gaji dan kansu tukunna su dawo amma kai dai baka da ikon koro su…in har kuma kace za ka yi taurin kai to zan sa ka had’omin spare key na kaff gidan naka in rabawa ko wanne a cikinsu…. Ban d’aura auren da zai tarwatsamin kan ƴaƴana ba wallahi.!” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce ‘’a kiyaye” daga nan ya wuce sama.” Shiruu Yashjub yayi, ya ma kasa cewa komai… Har sai da Mommy tace “Sai magana ta uku! Yadira ta had’a kayanta tun d’azu. Idan kun zo tafiya ku wuce da ita, za ta zauna a gidan naka for sometimes.” Saida ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya ce “To Mommy ba damuwa, amma jiya na gaya miki za mu tafi Cyprus..mai zai hana a bari sai mun dawo t….” Cikin tarar numfashinsa tace “Ka wuce da ita,idan kun zo tafiya sai ka dawo da ita, in kuka dawo sai ku koma tare da ita” Ahankali yace”Mommy, jibi ne ai…” Cikin fushi tace “Ka san Allah Yashjub idan ka gwada min taurin kai idan bance ku tafi honeymoon d’in tare da ita ba ka chanja mini suna..” Shiruu ya yi kafin ahankali ya ce “Shikenan Mommy..ki yi hak’uri”kafin ya kalli Yadira ya ce “Ki d’auko jakar taki yanzu zamu wuce. Bari in yi wa Daddy sallama” Ya fad’i hakan yana mai hayewa sama. Murna a wajen Yadira ba a magana…tashi d’aya itama ta yi wuff ta haye ta je d’auko kayanta. Ko da Yashjub ya je wajen Daddy basa hak’uri yayi sosai tukunna dakyar ya samu ya d’an sauk’k’o bayan zazzafan warning d’in da Daddyn ya zuba masa akan “indai har yanaso su zauna lafiya da shi tou ya ja k’annensa a jiki…duk ranar da aka ce ya mutu shi ne Uba!…kar ya biyewa Mace ta rabasu tun yanzu.” “InshaaAllah”kawai Yashjub d’in ya ce daganan yayi masa sallama suka rabu lafiya, A ranshi yana mamakin yadda Daddyn yayi masa sannan yadda suka d’auki laifi kachokam suka d’aura akan Manubiya wadda bata ji ba bata gani ba! It’s like kamar ma Daddyn har ya fara jin haushinta ne tun kafin a je koina, kawai dai bai nuna masa bane, amma ya fahimta, dan tunda har Daddy ya ce “har Kausar sai Manubiya ta gaida ita” To fa abun babu sauk’i sam! dan duk mutumin da Daddy zai yi favoring (zai fifita) Kausar akan sa to yakamata ayi gaggawar gyara tsakanin su.. Shiyasa kawai ya hak’ura yake ta basu hak’uri…ya san su iyaye ne fushin su garesa masifa ne, sannan kuma yasan yanzu yana yin taurin kai ko ya yi wata maganar to Manubiya zai sake janyowa bak’in jini a wajensu. A d’akin Yahanasu Yadira ta samesu dan haka suka fara shirin tafiya. Manubiya ce tace “tana so ta je ta yi wa su Mommy da Ummi sallama”dan haka Yadira da Munirat suka tafi rakata. Suna fita Yahanasu tace ‘Ayi hak’uri Yash, ayita hak’uri…d’azu Ina kitchen na ji mommy tana waya da su Yassira, suna ajjiyewa kuma na ji ta kiraka, dama tun daga nan na san akwai matsala, aikuwa da suka tashi shigowa kusan dukkansu da kuka suka shigo! wai ‘ka kore su, k’annenta kuma suna gidan yanzu haka.’ Dama yadda na ji Mommy da su suna yi wa Daddy bayani, shi kuma yana fad’a na san kawai ya riga ya hau shiyasa ban saka Baki ba. Na yanzu ya faru sai a kiyaye gaba, dan Allah Yash karka basu k’ofar da za ka janyowa baiwar Allah n nan bak’in jini a wajen Daddy…” Ajiyar zuciya ya sauk’e daganan yace “InshaaAllah’’ Ba a wani dad’e ba su Manubiya suka dawo… Sark’ar gold Ummi ta bata y’ar k’arama wadda ba za ta wuce 600K ba, a cewarta ‘ta ajjiye ne a tunaninta za’ayi bud’ar kai, to kuma sai ta ga ashe su basa bud’ar kai…’ daga nan ta d’an yi mata nasiha. Mommy kuwa sallama kawai sukayi daganna suka fito Manubiya tana mamakin yadda yanayin fuskarta ya chanja, dan d’azu sam ba haka ta yi mata ba a gaban Yash. Yash ya ji dad’in gift d’in Ummi matuk’a kuma bai ji dad’in rashin ganin gift daga wajen Mommy ba, yana sane ko a lefe ma ba ta basa komai ba Mom da Hajiya mama sai Yahanasu ne kawai suka bada…dukda ya san yau d’in ranta a b’ace yake amman ai dama Uwa tana tanadan gift d’in Amarya a irin wannan ranar ko da ace ta bayar da na lefe, ya san maybe za suce ai ya yi komai ya saka komai amman ai Ana bada gift ne saboda karramawa ba wai dan babu ba. Har mota Yahansu da Munirat da Yassir suka rakasu su da Yadira da akwatunanta har biyu. Sai da suka ga ficewarsu tukunna suka nufi main door, signal kawai Yassir ya yi wa Munirat daga nan Yahanasu bata san inda sukayi ba ita dai ta ganta ta shiga parlourn ita kad’ai. Kausar tana ganin ficewarsu ta windown d’akinta ta koma ta kwanta ta fashe da wani irin kuka, babu abunda ya fi b’ata mata rai irin yadda yake wani rik’e mata jaka yake bud’e mata murfin mota. Tana kwance tana ta faman kuka a haka ta ji an bud’e k’ofar d’akin an shigo. Ta san Mommy ce dan haka tace ‘’I’m fine” Murmushi Mommy ta yi, ta nemi guri ta zauna a kusa da ita kafin tace”Ki yi hak’uri Kausar, saura d’an k’an’kanin lokaci.. Na san da ciwo, amman ki k’ara hak’uri… Ki duba kiga yanzu da ikon Allah Daddy ya fara karkatowa side d’inmu, duk abunda muke so shi yakeyi. Shima Yashjub d’in ki duba kigani ko b’acin raina ba ya son gani wanda da sam ba haka yake ba. Ki kwantar da hankalinki, na yi miki alƙawari indai kina da ni to bazakiyi kuka ba…” Ahankali ta tashi ta zauna tana kallon ta ta ce ”thanks for everything Mommy, amma na ga suntafi da Yadira, kenan ba ranar dawowarta nan gidan kwana kusa kenan? Idan fa ba ta dawo ba babu ta yadda za ayi mu…” Cikin katse mata magana Mommy tace “Kar ki damu za ta dawo, komai a hankali a keyi, ki kwantar da hankalinki, kinji” Ahankali Kausar ta jinjina Kai daganan ta matsa ta kwanta a jikin Mommy tana mai sauk’e wata nannnauyar ajiyar zuciya. Mommy tana so ta fad’a mata zancen tafiyar su Yash honeymoon amma kuma bata san ta Ina za ta fara rarrashinta ba! Dan da kyar aka samu aka iya ruƙo sannan aka saita Kausar ɗin ta yarda ta ɗan nutsu sannan ta yi haƙuri da al’amarin a yadda ya zo da kuma batun ‘sai su Manu sun dawo mansion ɗin tukunna za a raba aurenta da Yash ɗin’, shiyasa ta ke tsoron gaya mata gudun kar ta sake burkice musu.. Gashi ita kanta Mommyn, tun jiya da ya gaya mata ta rasa Ina za ta sa kanta…fatanta shine Yadira ta yi abunda ta tura ta yi a gidan…inshaaAllah in dai har ta yi to ita Manubiyan ce da kanta za ta tarwatsa batun tafiyar tasu. …. Suna fita Daddy ya sauk’e ajiyar zuciya, dan shima yana tsaye ta window yana kallonsu har suka fice….ya san he’s a little bit hard akan Yashjub (ya san ya ɗan tsaurarawa Yashjub) amman kuma idan bai yi wa tufkar hanci da wuri ba tou tabbas akwai matsala.. duba da yadda Yash ya kori k’annensa ranar da aka je d’auko amarya dukda ya san laifin su Yasira ne amma a yadda shi da kansa ya rok’esa sannan ya ce su had’a kawunansu sam bai yi tunanin Yash zai sake korar su daga gidansa ba kuma du, baya ga haka kalli yadda yake nan nan da Manubiya! Ya san zafin soyayya! Ya san yaya mutum yake ji! shiysa ya fahimci indai har bai tashi ya tsaya a kan Yash ya yi masa wuta-wuta ba to a yadda ya rikice a kan Yarinyar tsaf zai yi fatali da zumunci ya zab’i soyayya…… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 24* Tunda su Manubiya suka kamo hanya babu wanda yace ‘k’ala’ a cikin motar…Abu d’aya ta lura da shi shine yanayin Yash gaba d’aya ya chanja, kamar yana fushi. Sam ba ta yi mamaki ko ta ji haushi akan tahowa da Yadira da suka yi ba, kawai dai ta saka a ranta wataƙila hutu za ta yi musu, ko kuma zaman d’aki ko kuma ma wataƙila za ta zauna a wajen su ne har abada, tunda a saninta dai Yash shine Babba a gidansu, kuma dole dama yadda yake da rufin asiri ya kamata ace yana ragewa Daddy waensu abubuwan. Addu’arta d’aya itace ‘Allah Ubangiji ya sa Yadira kar ta zame mata matsala’… dukda ta lura ko d’azu da suka zo ita da Yusra ne suka gaida ita, sannan yanzu ma bataga alamun rashin kunya ko rashin mutunci a tartare da Yarinyar ba, sai dai kuma ta fahimci ba sa yi mata rashin mutuncinsu idan a gaban Yash ne but yanayin Yarinyar na yanzu ta ga kamar ba irinsu bace ita, dan haka kawai sai ta saka kyakkyawan zato a ranta, ta yi ta addu’ar ‘Allah Ubangiji ya sa su zauna lafiya ita da Yadira…’ dan tabbas ta san tafiyar Yadira ba kwana kusa bane, idan ma za ta tafin d’in kenan! Duba da yadda ta ganta da akwatunanta d’urma d’urma har guda biyu da jaka. Ta san ko tafiyar ma da za su yi honeymoon definitely sai dai su barta a gidan a turo wata babba ko mai aiki ta zauna da ita kafin su dawo…. tanata wannan tunane tunanen ta ga Yash ya d’auki hanyar gidansu, ba ta san lokacin da ta fara zuba murmushi ba wanda har sai da Yashjub d’in ya ji ya d’an juyo ya kalleta, suna had’a ido ya d’aga mata gira d’aya kafin yayi wani d’an guntun murmushi ya maida hankalinsa ga tuk’in da ya ke yi. Tun lokacin da su Ya Musbah suka bar gidan Manubiya yake k’unci!. Gaba d’ayansu sun ji haushi, kuma sun ji babu dad’i game da halin da suka je suka tarar da y’ar uwar tasu a ciki amman kuma dama Ya Nafi’u ya san akwai abunda yake damun Ya Musbahn kwana biyun nan, gashi yau ɗin tun kafin su je gidan Manubiyan ya ke la’akari da shi, ya kuma lura da damuwar tasa ta yau ma ta fi ta kullum….shiru kawai ya yi masa ya na mamakin yadda k’iri k’iri wai shine Ya Musbah yake b’oyewa damuwarsa, dan ya lura sam baya so ma ya fahimci yana da damuwar…. Shiyasa yau kam ya na yin parking a k’ofar gidan, ya cewa su Aisha “su shiga wajen inna, za su taho nan ba da jimawa ba da shi da ya Musbah. Sai da Ya Musbah ya bud’ewa Muhsin wanda suke zaune a gaban Motar tare da shi ya fita, tukunna ya juya ya kalli ya Nafi’u ba tare da ya rufo murfin motar ba yace ‘’Jiya ma ka tambayeni, kuma amsa d’aya zan baka, ‘babu abunda yake damuna’ Saboda dagaske babu abunda yake damun nawa‘’. Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace ‘’Ko kuma dai ba za ka gaya min ba, saboda ka san ba zan tab’a goya maka baya ba ko?, Haba Musbahu, na fa san a kan Baraka ne ka shiga wannan damuwar.” kafin ya gyara zama ya fuskance sa da kyau tukunna ya d’aura da cewa “har wanne dad’i ku ka yi da Baraka da har zai sanya kake missing d’inta har haka?. Baraka fa Musbahu!” Ya k’arashe maganar tasa cikin rashin jin dad’i. Shiruuu Ya Musbah ya yi kafin yace “ba fa a kan Baraka na shiga damuwa ba! Shin ba ka ga halin da muka tadda Manubiya sannan muka baro ta a ciki ba ne?” Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace“Jiya waye ya je wajen Baraka bayan sallar Magrib???” Da sauri Ya Musbah ya d’ago ya kalle sa, sai kuma cikin fushi yace “Bibiyata kake yi?”. “Babu zancen bibiya a nan! amsa kawai nakeso ka bani”. Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba, sai kuma ya kallesa yace ‘’Wajen mai sunan baba na je, ko ban Isa na je naga d’ana ba??” Cikin katsesshi sannan cikin tsananin fushi Ya Nafi’u yace ‘’ba za ka tsaya ka gaya min gaskiya ba? Yau nine na zama wanda za ka yi wa wannan k’umbiya k’umbiyar??? Shikenan ka je ka yi ta yi, dama shawara ce zan baka amma tunda na ga bakaso fine! In dai Baraka ce bismillah, ga ka ga ita, amma inaso ka san cewa ba za ta tab’a chanza zani ba.” Ya fad’i hakan yana mai k’ok’arin zare makullin motar ya fita. A hankali Ya Musbah ya ce ‘’d’an tsaya Nafi’u.” Shiruu Ya Naif’un ya yi kamar ba zai kula sa ba, sai kuma ya juya yana kallon sa tare da basa dukkannin hankalinsa. Ahankali Ya Musbah ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Ina son ta, har yanzu’’ Wani irin kululun takaicin Baraka da tsantsar tausayin Ya Musbah ne suka lullub’e Ya Nafi’u a lokaci guda. Da kyar ya had’iye abunda ya ji ya tokare masa mak’oshi, yana shirin yin magana ya ji Ya Musbah ya ci gaba da cewa “Har gobe inason Baraka, har abada!. Kai Abokina ne, kana fahimta ta akan komai, dan Allah ka fahimceni ka bani goyon baya akan wannan ma. Itama ta shiryu, ta ce min za ta gyara halayyarta sannan tana so ta zo ta bawa su Inna ma hak’uri, kuma tace za ta rik’e Muhsin, idan ta dawo… Har yanzu ba ta riga ta fita a idda ba, shiyasa da ni da ita muke so a had’u a gyara abun nan kafin ta fita idda kaga ba sai an yi sabon d’aurin aure ba. Wannan shine abunda yaketa damu na, na rasa wa zan gayawa, kuma ni a ganina Baraka za ta zauna lafiya da ni da kowa ma tunda yanzu Ina aiki kuma Inada rufin asiri.” Cikin tarar numfashinsa Ya Nafi’u yace ‘’Musbahu duk Matar da ba ta zauna ta ci talaucinka ba to bata yi deserving arzik’inka da kai kanka ba. Musbahu Baraka bata da kirki, ta raina ka, ta raina iyayenka…..” Shiruuu Ya Nafi’un ya d’an yi, ya tsagaita da magana sannan ya dafe kansa saboda ciwon da ya ji ya fara yi masa a sakamokon b’acin rai da takaicin Ya Musbah shi da Baraka. Ya d’an jima bai ce komai ba kafin ya cika Kan nasa tukunna ya kalli Ya Musbah ya ci gaba da cewa “shikenan, tunda ka nace…sai ka je ka samu Inna ka ce mata kanaso za ka dawo da Baraka.” Da d’an zafi Ya Musbah yace ‘’Ya za ka ce in je in samu Innaa?Bayan abunda Baraka ta yi mata taya kake zaton zan je in ce mata zan dawo da ita? Ai wannan aikin ka ne! Kai ka san ta inda za ka b’ullowa al’amarin, Kai ne za ka taimaka mini, shiyasa na ke gaya maka, saboda ka taimakeni‘’ Shiruu kawai Ya Nafi’u ya yi yana nazartar sa…bayaso ya zargi Baraka amma kuma kana ganin Ya Musbah da zantukansa tashi d’aya zaka fahimci tabbas aikin asiri ne, ko shakka babu ba haka ta bar sa ba. Ya taso masa da maganar Innar ne saboda yanaso ya tuno masa da abunda Baraka ta yi wa Mahaifiyarsa ya ji zafin abun ya daina tunanin dawo da ita amman it’s like kamar ma an goge wannan takaicin da wannan ranar ta k’unsa dan kwata-kwata bai hango haushi ko takaicin Baraka a idanunsa ba bayaga zazzafar soyayyarta da tausayinta da ya ke hangowa a tattare da shi. “Ba laifinta bane itama, sharrin shaid’an ne, amma ta yi mini alk’awarin ba za ta sake ba, har hak’uri tace za ta zo ta bayar. ka yarda da ni Nafi’u Baraka ta shiryu tun ba yau ba” Ya sake jin muryar Ya Musbah. Kallonsa ya yi da kyau kafin yace “Tun ba yau ba? Kenan tun ba yau ba kuke waya kake zuwa???” Bai basa damar cewa komai ba yace “Am Musbahu… ba zan baka goyon baya ba, sannan ba zan hanaka ba. Gwargwadon shaƙuwarmu da kuma sanin da na yi maka ni dai na san kanada hankali da sanin abunda ya kamata, dan haka ka yi duk abunda ka ga dama.” Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice kai tsaye ya wuce cikin gida, ya bar Ya Musbah a nan zaune shi kad’ai. Ya jima sosai a cikin motar, tukunna ya zare makullin ya rufe motar shima ya nufi cikin gidan. A zaune ya same shi suna raha wasa da dariya shi da su Inna, yana shigowa Ya Nafi’u ya mik’e ya yi wa su Inna sallama suka wuce shi da iyalinsa…ko ba a fad’a ba tashi d’aya za a fahimci Ya Nafi’u haushin Ya Musbah yakeji, shiyasa dukkan su suka shiga al’ajabi dan abu ne wanda bai tab’a faruwa ba. Su Ya Nafiun suna fita Baba ya kalli Ya Musbah yace “Tashi ka bi sa ku sasanta.” Zai yi magana yace “Jeka” Saboda dama shi tunda aka ce masa suna waje suna magana ya san akwai wani abun, yanzu kuma da ya ga hakan sai ya fahimci tabbas sab’ani suka samu…wataƙila ma shiyasa kwana biyu yake ta ganin Musbahun a cikin damuwa… Ba su jima da fita ba Baba ma ya mik’e ya fita bayan an tabbatar masa da cewa ‘su Manubiya suna lafiya’ daganan Muhsin yace “bara ya je d’akin su” Jidda kuma ta tafi raka Siyama… Suna fita Siyama tace “ni kam ina ma ace Ammi za ta hak’ura wallahi…kinga d’azu fa dakyar ya iya jan motarsa ya shiga gida! Ko ba ki lura da shi a time d’in da muke shirin shigowa gida ba?, lokacin shima yana k’okarin shiga gida. Kinga yadda ya rame kuwa a cikin kwana hud’u gask…..” Kukan da Jidda ta fashe mata da shi ne yasanya Siyaman yin shiru, kafin da sauri tace “Innalillahi, yi hak’uri Jidda, mai ya yi zafi??” Cikin kuka tace ‘’Siyama dan Allah ki daina min maganar Ya Al‘Ameen, dan Allah! Kin san Amminsa ba za ta tab’a amincewa ba, ko ta amince ma su Ya Musbah suma yadda suka zuciya na san ba za su bada goyon baya ba. Ki daina yi min zancen sa ki taimaka min in samu in fitar da shi a raina dan Allah.” Shiruu Siyama ta yi tana mai jin tausayinta yana sake rufeta… rana d’aya tak ta d’an samu moment da Najeeb ta kuma fahimci k’udirin sa a kanta amman ba k’aramin Namijin k’ok’ari take yi wajen dannawa calls d’insa reject ba. Shiyasa ta ke ganin k’ok’arin Jidda na hak’ura da Al’ameen da ta yi bayan shekaru wajen hud’u da suka yi a tare suna soyayya kawai yanzu tashi d’aya an raba su, tabbas abun da ciwo. Rarrashin ta ta shiga yi tare da bata baki….dakyar Jiddan ta d’an dawo dai dai dan a kwana biyun nan ita kad’ai tasan halin da take ciki..kwanakin baya ta ji haushi ta ji takaici amman kuma tunda ta gansa gaba d’aya sai ta ji ta yafe masa. Kuma tabbas a yadda ta ga ya yi ta san yana da uzuri sannan uzurin nasa mai k’arfi ne…so take kawai ta ji ta Bakin nasa, bayan nan ta yafe masa sannan ta mantar da komai daga nan ta kasance a tare da shi!!!…. Tana wannan tunanin suka fara takawa towards wajen su Siyama, kowa ta yi shiru da abunda yake damunta a haka suka k’arasa…Siyama ta zaro makulli daga jakarta ta bud’e Parlourn, dan maman nata bata nan ta tafi gidan suna. Suna shiga ko gama zama ba su yi ba Siyama tace “Kina ganin mu kira Manu mu yi magana, ko mu je gidanta bayan kwana biyu?” Shiruu Jidda ta yi kafin tace “Sai dai zuwa anjima mu kirata, dan kinsan tafiya za su yi tace jibi ne da asuba. Amman zakice na gaya miki dangin mijin nan nata ne suka sakata kuka babu ruwan Ya Yash, kinga yadda jikinsa yayi sanyi ai, ba laifin sa bane.” A hankali Siyama ta nemi guri ta zauna sannan tace “Ina fatan ya zamana su ɗin ne, dan ba na so su fara samun matsala da shi. Allah dai ya sa ta gaya mana.” Cike da tabbatarwa Jidda tace “za ta fad’a inshaaAllah..idan na bayar da shawara ne sai mu bata, idan kuma munga ya fi k’arfin mu sai mu sanar da su Innaa, dan ba zai yiu mu zuba ido ba…kwata-kwata fa yau ne ta yi 4 days a gidan.” Ahankali Siyama tace “InshaaAllah ma k’aramin abu ne, Allah ya sa ba wani babban issue bane ba.” .. Ya Musbah yana fita daidai motar su Nafi’u tana tashi, sarai ya san ya gan sa amman haka nan ya murza giya ya ja sukayi gaba. Shiruu ya yi kawai ya fad’a duniyar tunani a hankali ya nemi guri ya zauna akan d’an dakalin k’ofar gidan, ya buga uban tagumi…Bai tab’a samun matsala da Nafi’u ba tunda yake sai a kan Baraka, shiyasa ya ke jin tsoron tunkarar su Baba ma da maganar dan ya san suma akwai matsala, shi kuma a yadda yake jin Baraka in har aka hana shi ya maida ita to tabbas akwai matsala Babba….. Ya jima sosai yana tunani a wajen, ya ga motar Yashjub ta yi parking a daidai k’ofar gidan. Dama tunda suka nufo sa ya gane su dan haka ya d’an k’urawa motar ido kafin ya mik’e tsaye bayan sun gama parking d’in. Murmushi ya yi ganin yadda Manubiya ta fito har tana d’an tuntub’e, shi kuma Yash d’in yana cewa ‘ta yi a hankalin’ yana mai zagayawa da sauri inda take. Yana gani Yadira ta bud’e k’ofa ta fito, dan haka ya d’auke Kai ya maida hankalinsa ga Yashjub yana mai ce masa “Ashe kuna tafe, barka da zuwa, mu shiga daga ciki mana” murmushi Yashjub ya yi yana mai jin dad’in yadda Ya Musbah ya amshesa sam bai rik’e kukan da ya baro Manubiya tanayi a rai ba. Cikin jin dad’i ya cewa Ya Musbah “ya gajiyar ku” “Alhamdulillah” yace, kafin cikin yanayin sigar zolaya ya cewa Yash ɗin ”A k’aida fa sai Mace ta yi watanni uku tukunna take zuwa ganin gida, daganan kuma ita da ta dawo sai ta haihu” Wani kallo Manubiya ta yi masa kamar za ta yi kuka, sai kuma ta fara bubbuga k’afa tana cewa “dan Allah kar ka fad’a ya ji, Allah ba zai d’auka da wasa kake ba” Da sauri ya tsare gida yace “Au ke a naki tunanin wasa ne?” Sai kuma ya kalli Yash yace “Dagaske Yash ba a zuwa sai bayan watanni uku” Jinjina Kai Yashjub ya yi, sannan shima cikin tsare gida yace ‘’ai ban sani ba, yanzu kam mun riga mun zo dama kuma shima saboda za mu yi tafiya ne shine muka zo yi muku sallama, amman daga wannan zuwan kam inaga sai in ta haihu d’in kenan’’ Kan Ya Musbah Manubiya ta yi ta na cewa”Allah bana so ka daina” Ganin ta na shirin fara kuka ne yasa duk suka saka dariya wanda hakan ne ya sanya ta fahimci zolayar ce dan haka ta koma gefe ta chuno Baki gaba. Murmushi Ya Musbah ya yi yace”yi hkr mana”ya fad’i hakan kamar yana rarrashin wata y’ar Yarinya. Yadda ya yi d’in ne ya sanya murmushi sub’uce mata ba tare da ta shirya ba. Daganan ita da Yadira wadda ko kallo Ya Musbah bai isheta ba balle ta gaida shi sukayi cikin gidan, Ya Musbah da Yashjub kuma suka nufi masallaci…ba ya son case ko ta kawo masa raini a gaban mutane shiyasa kawai ya rabu da Yadira, yana addu’a a cikin ransa Allah ya sa in sun shiga ta gaida su Inna, a d’ayan b’angare na zuciyarsa kuma yana mamakin ta yadda Daddy ya kasa gani da fahimtar how wrong and rude behavior d’insu Yadira yake. A fanfon masallacin sukayi alwallah duk da masallacin yanada matuk’ar kyau amma yana alwallar yana aiyyana yadda zai sake gyara masallacin duk da inshaaAllah ya san su Baba sun kusan tashi dan ya gama siya masu gida amman yanaso kawai ya gyara masallacin saboda yana daga cikin tarihin rayuwarsa. Ba su dad’e da shiga ba Baba ya shigo kusan a tare shi da su Baba Habu…. Da mutuntawa Yashjub ya gaida su, ba yabo ba fallasa suka amsa shi, daga haka suka koma gefe shi kuma da shi da Baba suka d’an gaisa sama sama suma dan ba su wani tsananta magana ba sakamokon a masallaci suke kuma Allah ya taimakesu babu Kaka Mallan wanda kwana biyu yake fama da zazzab’i da sai gaisuwar ta fi haka. Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar Magrib d’in Ko da aka idar bayan an gama gaishe gaishe. Yashjub a masallacin ya zauna dan yana son ya yiwa Ya Musbah magana….. Sam bai ji dad’in yadda Ya Musbah shima ya k’i amincewa da maganar tashin nasu ba, dan kamar yadda Manubiya ta ƙi yarda ya chanja musu gida hakanan shima Ya Musbahn ya ƙi amincewa bayan Yash ɗin ya gaya masa, amman dai ya ce zai sanar da su Innaa su saka masa albarka but ya san suma bazasu tab’a yarda ba. Sun jima suna kai ruwa rana kafin daga baya Yashjub ya hak’ura kawai, ya rabu da shi, ba wai dan ya hak’ura ba sai dan ya basa lokaci ne ya yi nazari kafin ya sake zuwa masa da zancen. Sai da aka yi sallar isha tukunna Yashjub ya shiga ya gaida Inna. Tsaraba ya so ya siya musu amman babu lokaci kuma ya lura kamar C I D aka turo Yadira dama shi kuma ba ya son case a halin yanzu, shiyasa sai da ya bari su Manubiya sun dawo daga wajen Aisha dai dai sun zo tafiya kenan tukunna ya damk’awa Muhsin kud’i yace da shi da Siyama da Jidda naira dubu hamsin hamsin…. Ya so ya basu wanda ya fi haka amman ya lura ba lalle su karb’a ba idan ya fi hakan Dan dubu hamsin hamsin d’in ma sai da ya yi dagaske tukunna Muhsin ya k’arba musu…saboda shi Yaron kud’in ma tsoro suka basa gashi saida Yashjub d’in ya ga su Jiddan sun yi gaba su da Manubiya tukunna ya basa. Har mota suka rakasu kuwa, Manubiya ta so ta shiga ta ga Mama amman sai Yashjub yace mata “ta bari taa ganta next time yanzu dare yayi, ya na so su yi sauri su je su had’a kayayyakin su saboda gobe siyayya za su yi na tafiya, jibi kuma 6 za su bar k’asar…” Ba dan ta so ba ta bari akan za ta kira ta ta yi mata sallama, cikin share kwallarta ta shiga motar ta zauna dan tunda aka zo tafiya ta k’ank’ame Inna da kyar ta cika ta, su Jidda suka rakata har mota suka wuce. Su Jidda sunso su yi maganar da suke son yi da Manu d’in..su samu su tambayeta menene matsalar ta, amman Yadira ta kafa ta tsare….da kyar aka ci sa’a ta gaida Inna, k’iri k’iri da aka zo yin alwallah ta k’i shiga toilet tace wa inna “idan suka k’arasa gida za ta yi” Babu bak’ar magana babu rashin kunya amma yadda ta dinga wani d’ari d’ari tsaf kana gani ka san kyankyamin gidan take yi, kuma kamar gadin Manubiyan take yi tana nad’ar zance, dan idanuwanta kyar a kan kowa… A b’angaren Yadira kuwa, tsoron Yash ne kawai ya hanata yi wa su Yasira videon d’akin…ashe daman a inda suka d’auki Manubiya ba nan ne asalin d’akin su ba ma,ashe dama Babanta gurgu ne??.. Shiyasa ta na zama ta zaro waya ta hau watsapp hatta kalar k’ofar band’akin su Manubiya da komai sai da ta zaiyyanewa su Yasira a group….. …. Washegari da sassafe Ya Musbah ya gagara gane kansa, ko aiki ma ya kasa zuwa, ganin yana neman mutuwa ne ya sa ya mik’e ya fad’a toilet ya yi wanka dama Muhsin ya dad’e da tafiya makaranta. Da kyar ya samu ya kimtsa dan kamar muryar Baraka ya ke ji a duk wata kusurwa ta d’akin…a daddafe ya fito ya sakawa d’akin nasu key ya nufi d’akin su Inna.. ya san Inna za ta ga kamar ya yi mata tsaurin ido, amma kuma hakan shine kad’ai zaɓinsa, bashi da wani zaɓin da ya wuce yin hakan… A zaune ya sameta tana nad’e kayanta da na Baba, tana gyara musu wajen kayan.. dan Jidda ma bata nan ta tafi makaranta dan har sun koma, gaba d’aya tashi d’aya duk sai ya ji kunyar Innar ta rufe sa amman kuma sai ya kasa hana kansa abunda zuciyarsa ta ke so……. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 25* Ganin ya koma ya zauna ya yi shiru bayan sun gaisa ne ya sanya Inna ta ajjiye kayan dake hannunta, ta mik’e ta k’arasa inda yake ta zauna. A hankali tace”Da! Na ce ba zan yi maka magana ba nima, amma kuma na ga abun naka kullum k’aruwa yake yi. Jiya dai Baba ya ce mini yana tunanin matsala kuka samu kai da Nafi’u kwana biyu, duba da yadda kukayi jiya kai da shi a gabanmu, sai dai kuma ni ina kokwanto. Dan haka inaso Musbahu ya gaya mini meye ne yake damunsa kwana biyun nan? Ko ya fara b’oyewa Innarsa abu ne bata sani ba?”. A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa kafin yace ‘’Inna kunyar ki nake ji, shiyasa kika ga na kasa gaya miki,” da sauri ta kamo fuskar tasa da hannu biyu ta d’ago da shi kafin tace”kunya ta kuma Musbahu? Ni ce ma kenan silar damuwar taka?. Gaya mini kar ka d’auki lokaci, Ina sauraron ka, ka gayamin ko ma menene yanzunnan.’’ Ahankali ya Musbah ya kama hannayen nata duka biyu, yana jin wani nauyinta da kunyar ta, tukunna da kyar kamar wanda dama chan jira yakeyi a tambayesa yace “Idan na ce inaso in dawo da Baraka Inna za ki iya yafe mini?’’ Ya fad’i hakan kwayar idanunsa suna kallon k’asa. Ahankali ta zame Hannunta daga fuskarsa ta kawar da kanta gefe. Da sauri yace ‘’ki yi hak’uri, inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba‘’ A hankali ba tare da ta kallesa ba tace ‘’Musbahu mai ka d’auke ni?” Da sauri ya sake cewa ‘’Ki yi hak’uri Inna, inshaaAllah ba zan sake yin maganar ba har abada, dan Allah ki yi hak’uri’’ Ya fad’i hakan yana mai k’ok’orin mik’ewa. A hankali ta ruk’o hannunsa ta juyo da fuskarta, ta kalle shi kafin tace‘’Ba ka bani amsata ba!. Mai ka d’auke ni?” Ganin ya yi shiru ya sunkuyar da kansa k’asa ne ya sa tace”A tunanin ka idan uwar Mijin Jidda ko Manubiya ta bayar da gudunmawa wajen kashe musu aure murus zan ji dad’i?. Sannan kana tunanin dama chan Ina farin ciki ne saboda ka hukunta Baraka a ta dalilina? Bari kaji..Baraka ta yi mini k’ololuwar rashin mutunci, amman a ko da yaushe idan na tuna da mai sunan baba na tuna cewa a ta dalilina iyayensa suka rabu gaba d’aya sai in ji babu dad’i. Dukda na ji dad’i kuma ka zame mini abun alfahari Musbahu saboda yadda ka nuna b’acin ranka a lokacin da aka wulak’anta ni, na ji dad’i! Na ji dad’i matuk’a! kuma har gobe Ina sanya maka albarka amma kuma idan ka ce za ka dawo da matarka ba zan ji haushi ba, dan Babban burina a yanzu shine in ga kai da k’annenka zaune lafiya a gidajenku..” Hawayen farin ciki da k’aunar mahaifiyar tasa ne suka shiga sintiri a kan fuskarsa, bai san lokacin da ya rungumeta ba ya ce ”Amman Innaa sai nake gani kamar ban kyauta miki ba…” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta saki murmushi ta d’ago ta kallesa tace ‘’ka dawo da ita, na san yanzu ta kusan fita daga idda ma ko?” Ba ta jira jin amsar tasa ba ta d’aura da cewa”ni kaina ba son zaman nan naka nake yi a d’aki gabjeje da kai ba. Ka dawo da ita, ku koma gidanku ku ci gaba da rayuwar ku, Allah ya yi maka albarka.” Tana gama fad’in haka ta mik’e ta fice daga d’akin ta nufi kitchen bayan ta d’auki mayafinta. Ya Musbah bai tashi a wajen ba sai da ya maida Baraka, Cikin tsananin jin dad’i ya mik’e ya fice…wajenta ya fara zuwa ya sanar mata ta yi masa iso cikin gidansu ya sanar da Mamanta, aka kira kawunta a waya dake ba a garin yake ba shima aka sanar masa…tukunna ya wuce aiki daga baya, suna ta murna shi da Baraka. Sai dare tukunna Innaa ta samu Baba ta gaya masa yadda sukayi da Ya Musbah. Dama ta san zai yi fad’a shiyasa ta bari sai daren..ai kuwa ta sha fad’a, dan rabon da Baba ya yi mata irin haka har ta manta. Jidda kanta ba ta ji dad’i ba dan ita har ga Allah a tunanin ta Baraka ta tafi kenan..wacce iriyar zuciya ce da Inna haka? Ta ya za ki bayar da goyon baya d’anki ya dawo da matar da ta yi miki wannaann kalar wulak’ancin…. Kuma ta san Innar ta san Baba ba zai yarda ba shiyasa ta k’i tsayawa a yi shawara da shi ta yanke hukuncin ita kad’ai. A b’angaren Baba kuwa….ya san idan har zama bai k’are ba to ko yankasu Baraka take yi a da! sai ta dawo. Dan haka dama shi basa da ma burin raba aurenta da Musbahu murus! rabuwa ta har abada, kuma shi ba wai yanaso ta dawo baneba, kawai dai a nasa b’angaren duk abunda Allah ya tsara tou zai yi maraba da shi…Kawai shi babban abunda ya b’ata masa rai shine yadda aka dawo da ita da wurwuri ba tare da ta gama gane mutuncin iyayensa ba, dan yanzu ba ta horu ba, ya tabbatar ko da gidan gyaran Hali aka kaita bai ci ace ta yi hankali a cikin wata uku da y’an kwanaki ba. Saboda Allah tsabar rashin lissafi ace wai duk kalar tujarar da Baraka ta yi amman Musbah ya maido da ita ko idda ba ta fita ba sai kace ƴar gwal!. Ba kalar fad’an da Baba bai yi ba, daga k’arshe ma kawai ya mik’e zai fita dan takaici yasa yake ji ba zai iya ci gaba da zama a cikin d’akin ba. Yana Isa bakin k’ofa ya ci karo da Ya Musbah da mai sunan baba. Bai gama k’are musu kallo ba ya ga Baraka a bayan su…da farko so ya yi kawai ya zagayeta ya wuce amman kuma sai ya koma ya nemi guri ya zauna.. To dai Allah kad’ai ya san kalar turare da rubutun da Baraka ta yi sannan ta sha kafin ta zo ɗin dan tashi d’aya zuciyar Baba, Inna da Jidda har ma da Muhsin wanda shigowarsa kenan daga d’akinsu ta yi sanyi. Har k’asa da durk’usa ta bawa Inna hak’uri tana kuka tana cewa sharrrin shaid’an ne haka shima ma Baba ta basa hak’uri. Har Jidda sai da ta bawa hak’uri Akan abubuwan da ta yiyyi. Daganan d’akin ya d’auki shiru kafin Baba ya kalli Ya Musbahu yace “ka riga ka maida ita ko?” Jinjina Kai ya yi alamun ‘eh’ ya na mai jin kunya da nauyin Baba. Ajiyar zuciya Baba ya sauk’e kafin ya ce”Sai ku tare da wuri, Allah ya so naga gidan naka babu kowa a ciki” Daga haka ya fara k’ok’arin fita. Kamar Ya Musbah ba zai ce komai ba sai kuma ya d’an yi gyaran murya yace “Wai da sai nan da sati biyu tukunna, dan itama ta samu ta bayar da kayayyakinta gyara nima kuma akwai y’an gyare gyaren da zan yi a gidan.” Jinjina kai kawai Baba yayi daga haka ya mik’e ya ce “Allah ya yi albarka.” Yana gama fad’in haka ya sa kai ya fice. Sai chan dare tukunna Baraka ta tafi ta barsu da abubuwan mamaki…ko magana za ta yi da Inna sai ta sunkuyar da kai k’asa, Hatta Jidda yadda take janta a jiki abun sai da ya basu matuk’ar mamaki… Gashi tace za su tare ne tare da Muhsin! Shi dai Muhsin ya bita da to ne amman har ga Allah in ya tuno halayenta sai ya ji baya son bin su, matar da ada kwata kwata ko dariya ba ta yi masa bata jansa a jiki yanzu kuwa tashi d’aya ta dawo kamar za ta goya sa! dukda Yarone amma ya saka a ransa watakil dan ta ga Innaa ne kuma dan taga Gidansu ta zo shiyasa take ta faman lallab’asa, dan haka ya san yana zuwa gidanta zata fara cin k’aniyar sa. Dukda yadda yanzun yake jinta har cikin ransa amman still yana iya tuno halayen Baraka a gidanta…. Jidda kuwa Allah Allah takeyi Baraka ta tafi ta samu ta kira Manubiya, dan kanta ya rabu biyu, ta inda take tunanin Ko dai Fad’a akayi mata a gida da kuma yanayin duniya da ta gani ta gane gaskiya ta yi dana sani ta shiryu da gaske Ko kuma dai Wani abun ne a cikin zuciyarta, dan Barakar da ta sani ba zata nutsu irin haka a lokaci guda ba tare da kwakkwaran dalili ba…… Sai chan dare su Manubiya suka isa Gida, dan sai da suka biya suka ci abinci suka d’an zagaya suka fara rage siyayyar su tukunna suka nufi gida kowa a gajiye.Suna zuwa Yashjub ya cewa Yadira “ta zab’a d’aki” Na nan saman opposite d’akin Manubiya ta ce tana so, dan haka ya cewa drivern gidan “ya tayasu hawowa da kayayyaki, ya saka mata kayan ta a ciki”. Wanka kawai ta yi ko sallah ba ta nutsu ta yi ba ta d’auki abunda su Mommy suka bata ta fito. A zaune ta sami Manubiya tana waya da Jidda tana bata labarin Baraka…… Kamar Manubiya za ta had’iyi zuciya kuwa haka taji..ashe dama shiyasa ta ga yanata tunani a cikin makonnin da suka gabata, d’azu kuma ita a tunaninta ma ko kukan da ta yi ne ya b’ata masa mood d’insa ya saka shi a damuwa ashe shi tunanin shegiya Baraka yakeyi. Taya Ya Musbah zai so Baraka ta dawo, wanne irin abu ne haka!…a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e kafin ta d’ago ta kalli Yadira tace “zauna mana” Sai kuma ta sake sunkuyar da kanta tace “zan yi kiranku Jidda” daga haka ta katse wayar, tana mai jin kanta yana wani irin juyawa tsabar takaicin Baraka da Ya Musbah. Tsaki Yadira ta yi kafin tace “Ai ko ba ki fad’a ba!” Sai kuma ta zauna tace”duk fushin da Mutum zai yi nan gani nan bari..zama daram babu inda zanje” Ahankali Manubiya ta d’ago ta kalle ta, har za ta bata amsa sai kuma kawai ta mayar da kanta k’asa. Ba tare da b’ata lokaci ba kawai ta ga Yadira ta mik’e tafad’a toilet d’inta wuff! A shirye da shirin ta na bacci tsaff ta ganta shiyasa abun ya bata mamaki ta shiga tunanin ‘to mai ta shige za ta yi…’ A b’angaren Yadira kuwa, babu kalar barbad’en da batayi ba a banɗakin, gashi ta ji daɗi dama toile babu camera dan haka ta zage ta dinga zubawa… dukda ta ji ba dad’i kuma tana ganin abun wani iri amman hakanan ta rufe ido ta yi ta bankawa tana yi tana jin wani iri, dan kusan kullum a makaranta ita da k’awayenta basu da aiki sai zagin masu asiri da uwar da take koyawa ƴaƴaanta asiri amma sai gata yau tsulum a cikin harkar dumu-dumu… Tunda ta shige Manubiya ta saki Baki dan Yarinyar ta bata mamaki sosai… Ita ba ma wai batun zargi ko wani abun ba ƙarfin halin Yarinyar ne ya fi bata concern. Tashi d’aya kuma sai ta ji gabanta ya yanke ya fad’i! tsigar jikinta tana tashi, dan haka Yadiran tana fitowa ta mik’e tace ‘’Dakata Yadira’’. Ko kallon ta Yadira bata yi ba haka ta juya ta kama hanyar fita…tsabar takaici Manubiya bata san lokacin da ta matsa da sauri ta ruk’ota ba, dan a ganinta wannan k’arshen rainin wayo ma kenan!! Ta shigo ta gaya mata magana, ta mik’e ta shige mata toilet, kuma ta fito ko sallama ba ta yi mata ba zata fice… Shiyasa ta na ruk’ota ta juyo da ita cikin fushi tace ‘’akwai band’aki a k’asa na bak’i, akwai a dakinki akwai a corridor d’in saman nan sannan akwai a d’akin bak’in dake a k’asa, duk wani uzurin ki ki je ki yi a chan ko da wasa kar in sake ganin kin shige mini band’aki, bamuyi wannan sabon ni da ku ba dan a iyaka sani na da kuma yadda kuke nunawa ‘kun tsaneni!’.’’ Cikin fushi Yadira ta fincike hannunta sannan tace ‘’Eh lalle Manubiya kin auri mai kud’i, Allah sarki d’an Adam mai manta gobe, yanzu ke har kin manta yadda ke da uwarki da ubanki kuke sharing band’aki shine yanzu har ke kike da Bakin ce mini wannan personal toilet d’inki ne…..” Mahaukacin marin da Manubiya ta d’auke ta da shi ne yasa ta gagara ci gaba da magana, dai-dai nan ne kuma Yashjub ya shigo cikin d’akin. Da sauri ya k’arasa inda suke a tsaye yana cewa “lafiya??!Baby mai ya faru har kika mareta haka?..” Ihun kukan da Yadira ta fasa ne yasa ya kasa cigaba da magana, da sauri ya juya ya kalleta ya shiga duddubata yana kallon yadda shatin y’an yatsun Manubiya suka fito rad’au a fuskarta..cikin kid’ima da tashin hankalin ya shiga addu’a a cikin ransa’Allah ya sa kar Yadira ta gayawa su Mommy an daketa’, dan idan akwai abunda Daddy ya tsana to shine ka tab’a masa Yaro” Cikin d’an fushi ya juya ga Manubiya yace “nan gaba idan ta yi miki laifi, u report to me! (Ki kawo min ƙararta), kar ki sake marin ta.” Daga haka ya ja Hannun Yadira suka fice tanata uban kuka tana kiran sunan Mommy. Suna fita Manubiya ta share zafafan hawayen da suka zubo mata, ta durk’ushe a wajen….anya auren Yashjub ba mistake bane ba kuwa! anya zata tab’a samu farin ciki a cikin gidan nan kuwa! Gashi tun ba a je ko ina ba ta fahimci kamar so yake ya hanata karatu!… dan da farko yace mata ‘ba ya son chud’anyar ta da maza’, yanzu kuma ya zo yace ‘ya riga ya yi wa Najeeb magana shi kuma Najeeb ɗin zai sanar da ex colleagues d’insa su yi mata chuku-chukun deferring zuwa nan da har zuwa lokacin da za su dawo. Shi kuma Zai yi tunani kafin nan…’ Ta jima a tsugunne a wajen, kafin ta mik’e ta fad’a toilet domin ta wanke fuskarta… Tana shiga cikin band’akin lokaci guda ta ji duk duniya babu wanda ta tsana sannan ba ta son kallon ko da fuskarsa ne kamar Yashjub! Ita tunani ma ta fara yi wanne dalilin ne ya sa ta aure shi in the first place, dan ta nemi soyayyar da take yi masa tashi d’aya ta rasata…. … Suna shiga d’aki Yadira ta juyo tana kuka tace “Wallahi Ya Yash ban yi mata komai ba!” Cikin katseta Yashjub yace”ban tambayeki ba!. Yadira kin bani mamaki…ashe haka kika zama, haka kika koyi k’arya?Manubiya mahaukaciya ce da za ta dake ki ba tare da kin yi mata komai ba? Dama zuwa kika yi ki kashe mini aure? Ashe bakya sona a matsayina na d’an uwanki ni ban sani ba..” Tashi d’aya ya fahimci yadda jikinta yayi sanyi k’alau, dan haka ya sake tabbatarwa tabbas akwai abunda ta yi wa Manubiya….a tunaninsa su Mommy sun turota cid ne, amman yanzu ya fahimci an turota ne ta kashe masa aure! mai ya yi wa su Mommy ne da har suke son rabasa da Manubiya su had’a sa da Kausar, dan ko shi Yarone tou ya kamata ace zuwa yanzu ya fahimci manufarsu kenan!! Mai yayi musu da zafi har haka, mai yasa duk yadda yake k’ok’ari wajen ganin ya shafe laifukan Mommy dole ita kuma sai ta san yadda ta yi ta nuna masa bafa ta son shi….. Kasa ci gaba da tsayuwa a d’akin ya yi, dan haka kawai ya juya ya fita zuciyarsa tanata faman tafarfasa…. Kitchen ya fara zuwa ya zauna a kan dining table d’in ya yi shiruu, kafin chan ya nufi fridge ya d’auki ruwan sanyi ya b’alle murfin ya kafa a Baki ya hau shaa.. sai da ya shanye tukunna ya ajjiye robar yana mayar da numfashi….ya jima kafin ya fito, ya nufi sama d’akin Manubiya. Yana shiga dai-dai ita kuma tana fitowa daga band’aki…d’auke Kai ta yi ta turo Baki gaba ta yi kamar bata gan sa ba. Murmushi yayi ya k’arasa inda take anan gaban madubin ya rungomata ta baya. Yadda Manubiya ta ji ita kanta saida abun ya bata mamaki dan ji ta yi kamar wani k’aton arne ne ya rungumeta.. saida ta yi da gaske tukunna ta rarrashi zuciyarta da take azalzalarta akan ta hankad’e sa. Ahankali ya d’an sunkuyar da kansa ya yi kissing wuyanta kafin yace “ki yi hak’uri, Yadira Yarinya ce,um…” ya fad’i hakan ya na sake rungumarta sosai izuwa jikinsa . …Inaa!! Ba za ta iya jurar hakan daga garesa ba!!! dan haka ta juya da sauri ta hankad’esa! Kalar hankaɗewar da ba dan Yashjub yana da k’arfinsa ba to da sai ya zube a wajen. K’ura mata ido ya yi, sai kuma ahankali ya d’an matsa ya kamo hannunta yana kallon fuskarta da serious face yace “are u okay??” dan har wani jaa yaga idanuwanta da kan hancinta sun yi, irin mutum yana cikin tsananin tashin hankali da b’acin ran nan. Ba ta kulasa ba kuma ya ga alamun bazata kula shin ba, dan haka ya sake matso ta a hankali da kyar kamar wanda yake jin tsoro yace”mai ta ce miki? Mayene ya faru dear, tell me, menene matsalar??” Tashi d’aya ta fashe da wani irin gigitaccen kuka wanda ya gigita Yashjub, yana shirin sake matsowa tace “Kar ka tab’ani, ka fita kawai, bana son ganin ka!” Kamar zai fashe da kuka yace ‘’baby ni d’in ne bakya son gani? Ki yi hak’uri komai zai yi daidai, yanzu sai kin d’anyi hak’uri da su am…” Cikin katseshi sannan da k’arfi tace “Ka fita nace!!” Da k’arfi kamar ba mijinta take yi wa magana ba. Ahankali ya lumshe idanuwansa ya bud’e kafin yace “to mu je d’akina sai mu yi magana ko??.. Idan bakya son zama da ita a kusa ne, mu je sama d’akina, ki kwashi kayanki ma gabad’aya daga nan sai ki koma chan da zama ko?” Wani kuka ta sake rushewa da shi ta durk’ushe a wajen tace “Dan Allah ka fita, bana son ganin ka!” Wani irin bugawa zuciyar Yashjub ta yi, dan kalamanta sun dake sa sosai…shiruu ya yi, kafin kawai ya juya kamar mara lakka a jiki haka nan ya fice ya rufo mata k’ofar. d’akin Yadira yace mata”Ko da wasa kar ta kuskura ta je inda Manubiya take, ko sun had’u daga nan har gobe bai yadda ta yi mata ko da kallon banza ba, Infact ta zauna a d’akinta ma kar ta kuskura ta fita koina sai gobe, ai taci abinci..” Da “to” kawai ta amsa shi daga haka ya juya ya fita. Yana fita Yadira ta yi wani murmushi dan da da farko ta d’an ji tausayinsa ta ji babu dad’i, amman da ta tuno hud’ubar su Mommy da Yasira sai ta ware…. A take ta d’auki hoton fuskarta Inda shatin Hannun Manubiya ya fito, tun daga kan Daddy har zuwa kan Yusra babu wanda bata turawa ba tace “Manubiya ta mare ta daga zuwan ta yau!” Daga nan kuma ta kira su Baba larai tace “ta zuba abunda aka bata successfullly.” Yashjub yana fita Mannubiya ta sake sakin wani irin kuka kamar ranta zai fita…. Ta jima tana kuka kafin ta mik’e da kyar ta fad’a toilet, sai a lokacin ta lura da gari gari a zuzzube a cikin bathtub d’in ta da kuma k’asan tiles d’in.. Tashi d’aya ta fahimci mai ya faru a wajen ta kuma fara tunanin ko dai shiyasa ta ji ta tsani Yash lokaci guda!… kawar da tunanin ta yi da sauri ta yi ta’auzi da isthigfari a ranta tace “Mutum bai Isa ya yi wa bawa komai ba sai abunda Ubangiji ya riga ya tsara” Sai da ta fara yin fitsari ta zuzzuba a duk wajajen da ta ga garin daganan ta wanke band’akin ta yi wanka ta d’auro alwallah ta fito still tana jin b’acin rai da takaicin da kuma tsanar Yash amma ba kamar d’azu ba…. D’aukar wayarta ta yi da niyyar kiran Jidda, amma sai ta ci karo da text na rashin mutunci daga Ya’isha!!… ita Manubiya bata ma san wa ya bawa Ya’ishar numberta ba, dan itama ba ta da tata number, sai da taga ta rubuta sunanta a farko kafin ta d’aura da zage zage tukunna ra fahimci ita ce… Hatta kakanninta saida Ya’isha ta zage su tass!!! Gori kala-kala babu kalar wanda ba ta yi mata ba! zage-zage kuwa har da ashar, haka nan ta dinga rubuto sunan musa tana danna masa zagi…kuma ta tabbatar mata cewar ‘wallahi ko budad’e ko bujuma sai ta ramawa Yadira marin da ta yi mata… A zuciye Manubiya ta fara typing d’in reply… kamar kuma wadda ta tuna wani abun sai ta ta tsaya ta danne yatsar ta akan delete ta goge tass!. Hawaye ne suka fara sintiri akan kyakkyawar fuskarta, kafin ta yi jifa da wayar a kan gadon ta zube a wajen ta fashe da wani irin kuka wanda ta dad’e rabon ta da tayi irinsa… Ta jima tana kuka kamar ranta zai fita kafin ta d’auki waya ta kira Jidda… Jidda, tana zaune kiran Manubiya ya shigo wayarta, dama ita take jira dan d’azu bata kaiga tambayar ta daliin kukan da suka sameta tana yi ba Manubiyan tace mata tana zuwa za ta kirata… Tana d’auka ta kara a kunneta tace”assalam alaikom” Muryar jidda da Manubiya ta ji ne ya sa ta sake fashewa da wani sabon kukan. A rikice Jidda ta mik’e tsaye sai kuma ta d’an kalli Inna ganin tana baccinta ya sa ta fita da sauri. Tana fita tace “subahannallah, Adda Manu mai ya faru???..dan Allah ki yi shiru.”Ta fad’i hakan wasu hawaye suna zubo mata itama…… Da kyar Jidda ta samu Manubiya ta yi shiru, ta shiga gaya mata abunda su Yasira su ka yi mata tun safiya har izuwa yanzu. Sai da Jidda ta yi da gaske tukunna ta iya hana kanta kuka, dan ta san tana fara kuka za ta karyawa Manubiya kwarin guiwa ne. Ahankali cikin rarrashi tace “Adda Manu sai da su Innaa suka gaya miki zaman aure dama duk hak’uri ne…ki yi hak’uri, kar ki d’aga hankalinki, ki yi k’ok’ari ki cinye jarabawarki…kuma ni har ga Allah na d’an ji sanyi a raina tunda matsalar ba daga Ya Yash take ba. Su waennan sisters d’in nasa na san dolen ki ne su ɗin amman tunda basuda kirki sai ki ja jikinki ki rabu dasu gaba d’aya, ita kuma Yadira idan nice ke Allah sai na ga dama zan had’u da ita…. Karki d’aga hankalinki ki lalata rayuwar aurenki tun kafin ki somata saboda su. Idan suka zo inda kike ki yi musu iyaka mutuncin da ya kamata, da zarar sun fara miki rashin mutunci ki tartara su ki watsar ki shige d’aki na san Ya Yash zai fahimta. Sannan kamar yadda kika fara yau to ki ci gaba da hakan, ko da wasa karki basu fuskar shige miki d’aki, dan nan ne turakarki, nan ne kaff gidan zaki shige ki zauna idan sun fara haukar su ba tare da sun biyo ki ba, wannan ni kaina na baki goyon baya, ki tsaya ki sanarwa Ya Yash kar su dinga shigar miki anyhow. Sannan maganar fad’uwar gaba da garin da kike tunanin ta zuba miki kar ma ki saka hakan a ranki balle ya yi tasiri..babu bawan da ya isa ya yi wa mutum abunda Ubangiji bai k’addara ba. Ke dai kawai ki yi ta addua ki dage da Azkar kuma zan turo miki da wasu addu’o’i ma dana gani an turo a group na y’an class d’inmu sannan zan san yadda zan yi in sanarwa Inna ba tare da ta fahimci komai ba itama ta dinga yi miki addua. Sannan dan Allah Adda Manu, abunda kika ce kin yi masa muna gama wayar nan ki tashi ki je ki basa hak’uri, tunda ma ya nuna cewa ki tafi d’akin nasa ni a gani na kawai ki kwashe kayanki ki koma chan saman sannan ki ce masa ba kyaso kowa ya dinga shigar muku, idan ya yarda hakan ya fi tunda dama ai turakarku ba kowa ne ya dace ya dinga shiga ba, kuma d’akin yana da girma zai isheku. Dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki cire komai a ranki sanann batun Kausar d’innan itama kar ki ma bari ta d’aga miki hankali, ke dai ki dage da addua a ko da yaushe da sallar dare, InshaaAllah ba su Isa su yi miki komai ba Wallahi….” Ahankali Manubiya ta share hawayenta tana jin sanyi da nutsuwa suna ratsata sakamakon shawarwari da kwarin guiwar da ta samu daga wajen Jidda. Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace “na gode jidda” kamar itace k’aramar. Ko da ta yiwa Jidda zancen makaranta tace”ta ga kamar yanaso ya hanata ci gaba da karatu” Tashi d’aya cike da bata kwarin guiwa Jidda tace “Yashjub ba zai tab’a hanata ta k’arasa karatunta ba. Kawai yanzu tunda tafiya za su yi ta hak’ura ta bi sa ɗin, su je su dawo, ta san daganan zai san abun yi kamar yadda ya fad’a, maybe yace ta k’arasa Online tunda ya fad’a mata baya son cud’anyar ta da maza ne. Amman ita kam tana ba ta tabbacin ‘Yashjub ba zai hanata makarantaba’ tunda shima ya fad’a da kansa yace yanaso ta yi karatun, kuma ai gidan su y’an boko ne so karma ta saka hakan a ranta…..” Sai da Jidda ta kuma jaddada mata ta dage da addua tukunna suka yi sallama da juna suka katse kiran. A hankali ta kife kanta akan gadon ta saki wani siririn kuka… Sam ita ba ma ta san lokacin da Yashjub ya shigo ba sai da ta ji ya zauna nan bakin gadon kusa da ita. A hankali ta d’ago da fuskarta…gaba d’aya sai hankalinsa ya kuma tashi sakamokon yadda ya ga fuskartata ta yi har ta kumbura idanuwanta sun yi luhu-luhu. Kamar zai fashe da kuka sannan kamar mai tsoron tab’ata haka ya matso ya ruk’o hannuwanta ahankali yace”I’m not supposed to make u cry (bai kamata in saka ki kuka ba) dan Allah ki daina” Ya fad’i hakan hawaye suna masu ciccikowa a idanuwansa. A hankali ta share hawayen nata, ta matsa jikinsa..aikuwa bai yi wata-wata ba ya rungumeta yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya. Haka kur’um sai ta tsinci kanta da jin tausayinsa, da kuma jin kunyar sa da ta tuna yadda ta dinga turesa d’azu tana korar sa amma kalli sai da ya dawo…ahankali cikin sanyin murya tace ‘’ka yi hak’uri’’ Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e mai tafe da murmushi yana mai jin nishad’i da tsantsar k’aunarta suna ratsashi, d’ago ta ya yi ya yi cupping face nata a cikin hannunsa kafin yace ‘’Manubiya ba ta laifi a wajen Yashjub! ko ta manta ne?’’ Wani irin kuka ta saka ta sake cusa fuskarta a k’irjinsa.. rungumeta kawai ya yi shima yana mai sauk’e ajiyar zuciya a jejjere, yana bubbuga bayanta a hankali alamun rarrashi. Sun jima a haka dan har ta yi shiru bata d’ago ba, ta yi lamo kawai tana sauraron bugun zuciyarsa. Tukunna a hankali tace”Ina so zan koma d’akin naka, mu biyu kawai” Murmushi ya yi kafin yace “Whatever u say (duk yadda ki ka ce) love….hakan za a yi” Daganan ya gyara musu position suka kwanta a kan gadon ya shiga rarrashinta kamar zai yi mata kuka…… Daman ba ta fara girki ba..kamar yadda Jidda ta gaya mata washegari da safe ta had’a kayanta har waenda ta rufe a jaka kaff ta kwashe, Yash ya tayata kaiwa d’akinsa, dan ta gama tsarawa akan ko sun dawo to ta bar d’akinta kenan muddin Yadira ta na gidan. Tunda kuwa ta haye sama ba ta sauk’o ba dan hatta abinci delivery man yana kawowa idan ya bawa Yadira nata zai wuce da nasu sama…ba ta tashi sauk’owa ba sai bayan azahar lokacin da suka zo fita. Ita a tunaninta ma tare za su fita da Yadirar amman sai ta ga sun tafi iyaka su biyu kawai. Haka suka je suka kammala komai na shirye shiryen tafiyar su. Sai dare wajajen k’arfe takwas tukunna suka dawo. Suna shigowa suka tarar da Yadira da Yassir a zaune a parlourn shi yana waya ita kuma tana kallo …..tabbas idan Yassir bai daina yi wa matarsa wannan d’an iskan kallon ba wallahi zai yi abun ban mamaki!! sai dai duk abunda zai faru ya faru! tsabar Iskanci har wani lashe Baki yakeyi ƙasa ƙasa gashi ya k’ank’ance idanu yana kallonta tun daga sama har k’asa… Tsabar takaici Yashjub ɗin bai san lokacin da yace mata “ta wuce ta tafi d’aki”ba Sai a sannan Yassir ya yi murmushi ya mik’e tsaye ya k’arasa inda suke, Manubiya tana shirin wucewa ya sa hannu ya karb’i ledar hannunta wanda sai da ya had’a da hannnunta da ledar ya runtse ya murza tukunna ya k’arba ledar yana wani kalar murmushi sannan yace “barka da dare antynmu” Da kyar tace “lafiya” Har ga Allah ta tsani Yassir musamman ma yanzu da ta gama tabbatarwa d’an iska ne!! saboda kalar yadda ya runtse mata hannu ko ita Yarinya ce ta san kalar na y’an duniya ne, har wani murzawa fa ya yi.. Shi kam Yassir laushi da taushin hannun nata ne ma ya fi komai d’aga masa hankali, dakyar ya juya ga Yashjub wanda ya kafe sa da idanu yace “Ina wuni” Yana wani killer smile. Dakyar Yashjub ya iya danne fushin sa, dan ya kul’e sosai ba kad’an ba!! ya san case d’in Yadira ya Isa wajen Mommy da Daddy bashi da tantama dan Yahansu tace “tanada magana da shi idan ya zama free ya kira ta” Shiyasa kawai ya danne kansa saboda gudun kar a kuma yin wani case d’in. Cikin kawar da kai yace “lafiya” Kafin ya d’an kalli Yadira itama yace mata “lafiya”wadda sai da ta bari Manubiya ta wuce tukunna ta gaida shi, daga haka ya juya yana mai bin bayan Manubiya wadda ta wuce sama da sauri da kallo, kafin ya maida dubansa ga Yassir.. da mamaki ya k’ura masa ido ya shiga k’are masa kallo dan idan idanuwansa ba k’arya suka yi masa ba tou kamar kayan bacci yake gani a jikinsa, shi sai yanzu ne ma ya lura sannan ya tuno bai ga motarsa a waje ba.. Cikin son fahimtar sa yace “Banga motarka a waje ba, ko dawowa za a yi a d’auke ka?” Murmushi ya yi kafin yace “Bello ne ya kawo ni ya koma, wai zan kai ku airport ne da safe gobe, daganan sai mu wuce gida ni da Yadira” Shiruu Yashjub ya yi a ransa yace ‘’a tak’aice dai kaima a nan ɗin za ka kwana!” A fili kuma kawai sai ya jinjina kai ya sa Hannu yace “bani ledar” Da sauri Yassir yace “No,ga guda biyu masu nauyi a hannunka,bari kawai in kai muku d‘aki Cikin d’an tsare gida Yashjub yace ‘’bani nan, sai da safe’’ Ya fad’i hakan yana sa hannu ya k’arba ledar… Ba dan Yassir ya so ba ya basa, daganan ya zura wayarsa a aljihu ya wuce d’akin bak’i na nan k’asan zuciyarsa tana turiri…so ya yi ya d’an fara k’addamar da shirin sa akan Manubiya tun yau! Ya so ace ya bata ajiyar sak’o mai nauyi mai tsayawa a rai wanda har ta je honeymoon d’in ta dawo yana mata yawo a rai. Ya san rik’e mata hannun da ya yi ma wani abu ne amman ya so ace ya yi wanda ya d’an fi haka… Bai kamata ya dinga jin kishi ba tunda ba Kausar baceba amman har ga Allah haushi yakeji idan ya tuna Yashjub zai tafi honeymoon da ita wata uwa duniya! Anya kuwa ba k’aunar Manubiya yakeyi ba kuwa! dan yanzu haka ma da ya tuna da cewa tare za su kwana ita da Yash wani irin tafarfasa zuciyarsa takeyi…. Ya na shigewa Yadira ta girgiza kai a ranta tace ‘’Ya Yassir kenan!” Shiyasa fa ta k’i yarda da Junior saboda duk kusan halinsu d’aya da shi da Ya Yassir, sai dai Ya Yassir ya fisa sosai dan nasa kam ya fara zama disorder….babban dalilin da ya sa bataji haushin Kausar a lokacin da ta yi futun futun tace ba ta son Yassir ba shine ta san shima ba ita kad’ai yake kulawa ba kuma duk macen da take son zaman lafiya da kwanciyar hankali da ruhi to ba za ta tab’a zab’ar Yassir a matsayin Mijin aure ba… Saboda idan aka bincika Ya Yassir tou tabbas za a tarar yanada matsala ko dai psychological ko kuma asiri aka yi masa da Mata! Dan ita dai tunda take bata tab’a ganin confused d’an iska kamar Ya Yassir ba….za ta iya cewa indai Mace sunan ta Mace tou Ya Yassir yanaso.. Ta san Kausar yakeso da aure amman fa y’an matan da yake so da lalata sam ba za su k’irgu ba! kuma shi sam babu ruwan sa da class ko wani abu makamancin hakan… Yanzu haka a iyaka cikin gidan su kawai ta lura akwai abu a tsakanin sa da Munirat ga Kausar yanzu kuma yadda ta ga tun d’azu da ya zo yana ta faman tambayar ta Manubiya ta fahimci akwai matsala ta nan ɗin ma, dama tun jiya yadda ta ga yana ta shishshige mata ta san da walakin. Bata san mai yake damun sa ba, bata tab’a ganin Namijin da bashi da tsayayyen zaɓi da ra’ayi irin Yassir ba, wani zubin tana lura da shi idan ya ga Mata jikinsa har karkarwa yakeyi, gashi yanzu tsabar idanunsa sun rufe Matar yayansa yake shirin farmawa!”ashe kuwa za’ayi kisan kai! Indai ya Yash ne” ta fad’i hakan a chan k’asan ranta kafin kuma ta tab’e Baki ta mik’e, tanajin haushin Manubiya yana ratsata… a hankali a fili tace ‘’su suka sani’’ daganan ta nufi sama d’akinta……. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 26* Dukda Manubiya a k’ule take da Yassir, amman sam sai ta k’i yi wa Yashjub maganar sa, dan kamar yadda Jidda ta gaya mata inshaaAllah ba za ta sake basu k’ofa su zamo silar b’acin ranta ko na mijinta a rayuwar aurensu ba, sannan ba za ta sake da su ba….addu’a kuwa tun a jiya ta duk’ufa da yi dan ko shiru ta yi to a zuciyarta addu’a takeyi…. Shima Yash d’in bai yi mata maganar Yassir ba, shiyasa ita bama ta san a gidan zai kwana ba. Hira kad’an suka tab’a daganan sukayi nafila suka tofa addu’o’i ko wanne ya bi gado. Tun k’arfe uku ta tashi ta yi wanka ta fara shiri, har breakfast yau ta d’an had’a musu ta ajjiye wa Yadira nata a k’asa, nata ita da Yash kuma ta hau sama da shi ta ajjiye a d’akin… Yassir kuwa wanda yake ik’irarin ya zo kai su airport ne, sai da Yashjub ya zo tafiya sallah tukunna ya tashe sa da kyar… Doguwar rigar abaya ta saka bak’a ta yafa mayafin..babu kwalliya ko k’adan a fuskarta amma ba k’aramin kyau ta yi ba. Ahankali Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya k’araso ya tsaya a gabanta cikin kasala ya amsa gaisuwar ta, kafin ya yi shiruu kawai ya shiga kallonta, sai da ya gama k’are mata kallo tukunna yayi cupping face d’inta a cikin tafukan hannunsa yace‘’I’ll forever love you!a ko da yaushe inaso ki yi ruk’o da wannan kalmar dan daga zuciyata da ruhina ta taho babu hijabi’’ ya karashe maganar tasa yana mai sakar mata light kiss a saman lab’b’anta. A hankali Manubiya ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya, dan kamar yadda yace mata maganar ta taho daga zuci da ruhinsa to itama haka maganar ta shiga cikin zuciyarta ta samu mazauni dan har kwalla sai da suka d’an taru a idanunta. Cikin nutsuwa ya d’auke lips d’insa ya mannna mata wani light peck a kumatunta da forehead kafin yayi hugging nata yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, sun d’an jima a haka tukunna ya cikata dakyar ya d’an gyara tsayuwar tasu ya koma gefenta ya sak’ale hannunsa na dama a cikin na hagun ta yace “shall we?’’ Yayi mata tambayar yana mai d’aga mata gira sama. Murmushi ta yi tana jin tsananin son mijin nata da k’aunarsa suna ratsata dan har wani irin kallo Yash ya ga tana yi masa mai tafiya da imani da zuciyar wanda akeyi ma wa.Ahankali ya ce ‘’Baby wannan kallon fa?so kike ki sumar da ni?’’ Ahankali itama yadda yayi mata maganar kamar mai rad’a tace “Ka yi kyau yau sosai, sosai!!’’ Ta fad’i maganar cik’e da shauk’i. Wani irin blushing Yashjub ya shiga yi mai had’e da dariya yana jin sa a sama…… “Mu wuce ko’’? Muryar Yassir ta katse musu dogon kallon kallon da suke yi wa juna suna masu murmushi,mai cike da shauk’i da sak’onni. Runtse ido Yashjub ya yi, yayinda Manubiya ta yi saurin zare hannunta a cikin na Yashjub ta d’an matsar gefe kad’an. “Babu alamar hankali ko sanin ya kamata a tsarin Yassir kwata kwata” Ta fad’i hakan a k’asan ranta tana mai sake had’e rai sannan ta d’an chuno baki Hakan da ta yi kuwa ba ta sani ba ba k’aramin burge Yassir ɗin ta yi ba…k’arasa shigowa cikin d’akin ya yi sarai ya lura da kallon mamakin da Yashjub yakeyi masa amman ya watsar da shi ya k’araso gaban su ya tsaya yana mai cewa “Waenchan ne luggage d’in ko?bara in fara ragewa. Antynmu Ina kwana” Dakyar tace”lafiya” daga nan ta ja k’aramin trolley d’in da yake a gefenta ta fice daga d’akin. A parlourn chan k’asa ta had’u da Yadira, bata ko sake kallon inda take ba, itama Yadirar haka bata kalleta ba bata kuma kulata ba. Haka Manubiya ta fice ta Isa parking lot d’in gidan ta tsaya dan ba ta san a cikin motoci ukun a wacce za su fita ba. Ta yi mamakin ganin har da Yadira a y’an kwaso kaya dan tana tsaye taga sun sauk’o gaba d’ayansu. Ba ta yi mamakin ganin Yadira ta fito da iyaka akwati d’ayan da ta zo da shi ba maimakon duka biyun, saboda dama ita ta san ba tafiya zatayi ba gaba d’aya, kuma dama bata d’auka a ka ba, k’ark’ari dai abunda ta sani shine bazata d’auki raini ba kowa ya tsaya a iya matsayinsa idan kuma ta ga rawar kan mutun ya yi yawa tou zata dawo da shi saiti, ta yi musu na bak’unta kafin ta gama sanin alk’iblar su yanzu kuwa tunda ta riga ta fahimta shikenan… Bazata wulak’anta su ba ba za ta k’i su ba tunda dangin mijin ta ne su ɗin amman fa bazata tsaya a taka ta ba. Dole sai dai a yi mota biyu dan haka Yashjub ya bawa drivern d’ayar motar aka saka akwatin Yadira a ciki,su kuma akwatunan su a boot d’in motar da za su shiga..har zai hana Yassir ya tuk’asu zuwa airport d’in yace kawai ya zauna shima a motar driver tare da Yadira sai kuma ya kyalesa suka zauna a gaba su biyu Manubiya tana a baya… Hakanan suka musu rakiya zuwa mallan Aminu Kano international airport,sai da sukaga jirgin su yana shirin boardin tukunna Yadira da Yassir suka nufi gidan Daddy shi kuma drivern ya maidawa Yashjub motarsa guda d’aya ya fakata ya rufe harabar gidan da aka bar masa makullin ya kama gaban sa dan Yassir yace masa”kar ya damu zai ajjiye d’aya motar Yashjub d’in a gidan Daddy kawai.” Yashjub so yake yi su dad’e sosai a tafiyar nan su fahimci juna da shi da matarsa, dan ya san su Yasira har ma da Mommy ba za su ba su wannan chance d’in ba…Shiyasa ya riga ya gama tsarawa akan ba za su dawo kwana kusa ba sai sun huta sun sha soyayyarsu kafin nan kuma ya san inshaaAllah Daddy ya huce dan ya san yanzu haka ya sake hawa game da case d’in Yadira dan haka ba fahimtarsa zai yi a kan komai ba,shiyasa zai bar shi ya huce ya d’an yi nesa da su kafin su dawo ya samu ya takawa y’an gidansu burki ba tare da Daddy ya ja masa layi ba, dan ba zai iya rayuwar da suke so ya yi ba, ba zai zuba ido yana kallon hawayen matarsa a kullum saboda su ba, dole a chanza tsari… Kasancewar Airline na Cyprus ba ya zuwa Nigeria a ya sanya tafiyar ta su ta kasance da transit a Egypt dan egypt air d’in suka bi.. A babban hotel na Egypt suka sauk’a dama Yashjub ya san sai sun d’au lokaci ai kuwa ilai sai da sukayi awanni dan sai cikin dare wajajen 2 tukunna komai ya yi settling suka d’auki hanyar Cyprus. Flight d’in su yana landing suna fitowa suka samu mota… Tare suka saka kayayyakin a boot da shi da drivern daga nan suka d’au hanya bayan Yashjub ya basa adress d’in inda zai kai su. Ita kam Manubiya ta yi laushi shiyasa suna shiga motar da ya janyota ta gishingid’a a jikinsa sai bacci. Sai da suka k’arasa tukunna ta ji ana tashin ta a hankali…cikin kulawa kamar ya samu kwai haka yake lallab’ata yana tashin ta kamar baya so dan ba dan drivern na jiran su zai koma ba to da ba dalilin da zai sanya ya tashe ta, yadda yaga tana baccin ta peacefully ya san ba k’aramin dad’i baccin ya yi mata ba. Tana bud’e ido suka yi ido biyu dan haka ta sakar masa wani lallausan murmushi kafin ta d’an gyara ta mik’e ta zauna. Cikin kulawa yace mata “mun iso, bara in bud’e, a rufe ne gate d’in. “Tou” kawai ta ce. Ta na jinsa da shi da drivern suka fita suna ta faman zuge gate, sai da aka gama parking motar tukunna ya lek’o ya mik’o mata hannu yace “muje ko” Jinjina kai ta yi a hankali, kafin ta miƙa masa nata hannun ta ya riƙe sannan ta fito daga bayan motar. dama tunda yace mata zai bud’e gate ta yi mamaki dan ita a tunanin ta za ta ga hotel ne amman sai ta ga gida flat mai d’ankaren kyau mai d’auke da d’an madaidaicin compound.. Murmushi ta yi suna fitowa dan gidan ba kad’an ba ya d’auki hankalin ta ya burgeta gashi dai d’an mitsitsi amman ya k’ayatu iya k’ayatuwa. Sai da driver d’in ya taya Yash suka gama kai kayan bakin k’ofar shiga, drivern ya tafi ya rufe gate d’in tukunna ya dawo. Yana zuwa ya sunkuya ya d’auke ta in a bridal style.. Murmushin ta yi ta zagaye hannunta a wuyansa,a haka suka k’arasa bakin k’ofar.. Tumb d’insa ya saka wata murya ta yi welcomin d’in shi had’e da fad’ar sunansa daga nan ya tura suka shige cikin k’ayataccen parlourn… Saida ya kai ta kan one seater tukunna ya zaunar da ita ya zauna a gefen ta kafin yace “Do u like it ? Gidan! Ya yi miki kyau?” Sai da ta kuma k’arewa parlourn kallo tukunna tace “Sosai ma kuwa, ya yi kyau, over” Ta fad’i hakan tana kallon parlourn.. murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “MashaaAllah, na ji matuk’ar dad’i da kikace ya yi miki saboda dama Inata adduar Allah yasa yayi miki kyau…wannan shine Gida na farko da na fara siya a rayuwata,yana da matuƙar mahimmanci a gareni, its soo dear to me shiyasa na mallakawa wadda ta fi kusanci da ni zuciyata da kuma ruhina… Gidanki ne…da na baki, as a gift, halak malak” Da sauri ta juyo ta kalle shi, sai kuma ta kalli parlourn kafin ta sake juyowa tace “Bai yi yawa ba kuwa?…ba ma a Nigeria ba fa..” Cikin janyota jikinsa yace ‘’gifts ɗin da kika bani Baby sun fi k’arfin wannan, idan na ce zan biya ko zan kamanta to fa sai na baki komai nawa tass ba tare da na kamo k’afar biyan ki ba ma..to amma kinsan an ce yaba kyauta tukuici, shiyasa na baki nawa tukuicin, ki karb’a kawai ke dai ki yi mini alk’awarin kasancewa a tare da ni a ko da yaushe..idan ki ka yi mini haka kin gama min komai Baby…” “Already, takardun a ƙarƙashin sunanki su ke, tomb print d’in kawai za mu mayar ya koma naki shima.” Ahankali tana kallonsa tace”da ni da kai ɗaya ne we are one, remember? Dan haka ba sai an chanja tombprint d’inba..a ko da yaushe za mu kasance tare har abada inshaaAllah” Sai kuma ta sunkuyar da kanta kafin ta d’ago ta kallesa kawai ta kasa magana, dan Wallahi ita ba ma ta san ta Ina za ta fara yi masa godiya ba, gaba d’aya ya saka ta a shock! Da kyar ta bud’e Bakinta tace “Nagode Sosai, Allah ya saka da allhairi na s……” Da sauri ya rufe mata baki yace “ni ne da godiya” Bai sake ba ta damar yin magana ba sakamokon kissing dinta da ya fara yi da sauri da sauri… yadda ta ji jikinsa har karkawa yake yi ne ya sanya ta hak’ura kawai dan ta san ba sarara mata zai yi ba…… Sai da gari ya fara haske tukunna ya samu kanshi.. bayan kamar mintuna biyu haka, ya d’ago yana kallonta yana mayar da numfashi still, yace”mu je mu yi sallah, sai in nuna miki gidan naki, ke kika tsayar da mu ba mu yi tour ba” ya fad’i hakan yana murmushi. Turo baki ta yi ta d’an kauda kai dan haka ya yi dariya ya fara yi mata cakulkuli…. duk yadda ta so dakewa sai ta gagara ta fara dariya itama, a haka ya d’auke ta suka nufi d’aki tana cewa”dole ma ta yi kib’a ko dan yadda yake d’aukarta anyhow ɗinnan in ya so daganan sai ta ga yadda zai yi…..” Wanka suka fara yi suka yi sallar Asubah suka ci abincin da ya yo musu order, tukunna ya ce su je ya nuna mata gidan… D’akuna uku ne sai kitchen da store da tafkeken parlour. Ta baya kuma pool ne da pool house sai garden ata gaban gidan mai d’ankaren kyau…. Suna gama zagayen ya kira masu gyaran gida aka zo aka gyara aka share aka goge koina tass tass. Sun ci sa’a kusa da restaurant suke shiyasa order d’insu ba ya d’aukar lokaci…..sai la’asar tukunna komai ya kammala suka yi wanka sukai sallah. Kwata kwata hutun awa uku ya bari suka yi daganan ya d’aura daga inda ya tsaya…ita kamar wanda ake yiwa ruwan energy ma haka take ganinsa dan sam ba ya gajiya….. To dai kamar yadda Yashjub ya fad’a mata ashe da gaske shi bai ma fara cin amarcinnasa ba sai yanzu dan ita kanta ta tabbatar a Nigeria appetizer ya yi (ɗanɗano ya yi)….Sai da suka shafe sati d’aya da kwana uku ba ta lek’a waje ba, shima haka dan da kyar ma aka samu ya d’an fita ya je ya sissiyo musu abubuwan da za su buk’ata daga nan sai da suka yi sati d’aya da kwana uku tukunna suka d’an fara fita suka fara zageye island d’in… Ita Manubiya har ga Allah so take yi ta zauna a gidan ta yi barci sosai ta huta, amman kuma ta san idan suka zauna a gidan ba barinta ta huta d’in zai yi ba, shiyasa kawai take yarda tana biyosa suna fita yawon ba dan tana jin dad’in yawon ba, gashi dai the view da duk wani abu game da Cyprus ɗin aljannar duniya ne amma ita sam ba ta enjoying tsabar gajiya… A haka dai kafin su yi wata biyu ta samu ta d’an saba kuma ta karɓi mijinta a yadda yake, dan ta fahimci ba wai don ya takuramata bane hakanan halittarsa ta ke, ga kuma gudummawar da soyayyarta da k’aunarta suke badawa.. Shi kansa Yashjub ya na mamakin yadda Manubiya ta taso masa da wani tsumin dake a jikinsa wanda a da sam bai san da shi…dan a da kwata kwata ko kallon mata ba ya son yi ballantana su basa sha’awa..yana jin sha’awa ba wai kwata kwata ba ya jinta ba amman ko ta d’an taso masa to ba zai yi 10 minutes yana jin wannan feeling d’in ba dan tashi d’aya zai ji ya nemi feeling d’in ya rasa, shiyasa a wannan lokacin wani zubin har tunani yake yi akan’Anya kuwa lafiyar sa k’alau!?’. Kafin 2 months itama ta ware ta zama y’ar gari ta shiga farantawa Mijinta rai yadda ya kamata, Wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yi wa Yashjub ba, dan shi sai a wannan lokacin ne ma tukunna ya ke sake experiencing (yake sake jin) wasu ni’imomin da aure ya k’unsa… Zaman lafiya kwanciyar hankali da asalin tattalin so da k’aunar juna shine ma’anar zaman Manubiya da Yashjub a Cyprus..wani zubin idan ya yi mata wani abun har kukan farin ciki takeyi ta yi sujjada ta yi ta godiya ga Allah S W A dan itakam in dai a fannin so da k’auna na tsakani da Allah ne to ba shakka za ta fito ta bugi k’irji tace “ta fi ko wacce mace sa’ar mijin aure…” Hutun su kawai sukeyi gaba d’aya sun manta da matsalolin su, sun yi fari sun yi k’iba abunsu….suna waya da video call da su Jidda haka shima Yashjub ya na waya da Mommy kuma ba yabo ba fallasa suke gaisawa ita da Manubiya, itama Manubiyan da kanta takan kirata ta gaida ita ba yabo babu fallasa take amsawa. Haka suna waya da chattin da su Ummi Yahanasu da Munirat sosai, su Yasira kuwa ko ‘hi’ babu a tsakanin su da Manubiya amma suna kula d’an uwansu. Yashjub ɗin ya lura kuma ya sani, amma bai yi magana ba, itama Manu bata ce komai ba dan ko kiran sa sukayi basa cewa ya bata shima kuma baya bayarwa..Manubiya ba ta nuna masa text d’in da Ya’isha ta yi mata ba 2 month ago kafin su taho amma shi ya gani..so yake kawai ya ga iyaka gudun ruwansu, Daddy kuma ya huce, daganan zai san abunyi. Watansu biyu da sati biyu Daddy ya kira Manubiya..ta yi mamakin ganin kiran amma sai ta d’auka da mutuntawa ta gaidashi.. Da kulawa ya amsa ya tambaye ta ya Cyprus tace alhamdulilah daga haka yace”yaushe za su dawo?” Diriricewa ta yi, ta rasa bakin magana da kyar dai tace” Ya Yash d’in bai gaya mata ba” Jinjina Kai Daddy ya yi kafin yace”ok shikenan” daga haka ya kashe wayar. Sarai Yashjub ya ji komai, kuma ya fahimci me Daddyn yake nufi da yin haka dan haka ya d’au waya ya fita ya kira sa… Bayan sun gama gaisawa Daddy yace “A lokacin da Manubiya ta mari Yadira na ji haushi sosai, kuma kamar yadda ka yi zato tabbas jiranku kawai nake yi ku dawo in had’a ka kai da ita Manubiyan in yi muku warning, kuma in yi riga kafi saboda gaba, amman tunda har za ka iya yi mana k’aura saboda hakan InshaaAllah maganar ta wuce, kuma komai ya wuce, amman a kiyaye gaba…come home..da ni da y’an uwanka da Mommynka muna buk’atarka a kusa da mu, ba ka tashi tare da mu ba, bai kamata yanzu ma ka sake barinmu ba” Shiruu Yashjub ya yi kamar zai faiyyacewa Daddy halin su Yasira ya kare Manubiyan amman kuma kawai sai ya bar maganar yace”ka yi hak’uri Daddy, dama nan da 4 days ma za mu wuce Uk mu yi musu sati biyu, daganan sai mu dawo inshaaAllah”. Ahankali Daddy ya ce “Allah ya kaimu” daga haka ya kashe wayar ya dafe kansa…’he really can’t believe (ya kasa yarda da cewa wai ) Yashjub ya d’auke matarsa, sun yi nesa da su saboda ba ya so a nuna mata ta yi laifi!! kuma bayaso ma a ga laifin nata a kan komai…. tabbas da alama Yarinyar nan ta juya kwakwalwar Yash, kuma son da yake yi mata ba na wasa bane, tabbas zai iya rabuwa da kowa akanta dan gashi ya ga alama nan…. Dan haka zai yi iyaka bakin k’ok’arinsa wajen ganin ba ta raba sa da d’ansa ba, inshaaAllah daga yau ba zai sake ba shi dalilin da zai yi tunanin barinsu saboda ita ba… Shikenan fa yanzu da bai ankare da wuri ba da sai dai Yash ya zo yi musu sallama, dan tsaf zai yi transferring komai nasa garin da yake so ya je ya ci gaba da business d’insa da rayuwarsa a chan su ya barsu a nan. Tabbas ya yi da na sanin aurawa Yash Manubiya dan gashi tun ba a je koina ba tana janye Yash ɗin daga garesu! amma tunda aikin gama ya riga ya gama ba komai, inshaaAllah ba zai sake bawa Yash dalilin da zai guje su saboda ita ba. •••• Tsaraba sosai suka shiga jida a Cyprus dan sun kusa wucewa Uk inshaaAllah. Sarai Manubiya ta fahimci dalilin Yash na tambayar ta akan batun period d’inta kusan kullum… Ko last week har asibiti suka je yace a yi musu checkup d’in su malaria da komai amman ita sai da aka had’a mata har da scanning…. Da farko abun dariya yake bata, dan ita a ganinta ko wata uku basu cika ba amman ace har ya fara k’ulafucin ciki, sai dai kuma yadda ta ga yanayin sa tun jiya da ya ga ta fara period d’inta abun ya bata mamaki matuk’a ita har ya ɗan taɓata, dan tun jiya taga ya zama so silent, da kyar ma yake iya dariya sannan ko bacci bai yi ba a jiyan dan ko da ya tashi ya yi sallar dare ya ida kasa komawa ya yi har asuba… Yanzu kuma da safe tana kitchen ya shigo ya ce mata “ya tafi jugging” bayan da tare da ita suke fita kullum..kafin ma ta gama yi masa a dawo lafiya har ya sa kai ya fice daga kitchen d’in. Ajiyar zuciya ta sauk’e ta juya ta ci gaba da aikin ta jiki duk ba kwari tana ta tunani…a haka ta kammala ta jere abincin a kan dining daga haka ta juya ta nufi d’akin su domin yin wanka. Ta ji matuk’ar tsoron ganin sa da ta yi a d’akin zaune a kan gadon, dan batayi tunanin har ya dawo ba, ba ta ji shigowar sa ba sannan bai ce mata ya dawo ba, kuma idan sun fita jugging d’in sukan d’an jima kafin su dawo… Ta na wannan tunanin ta ga ya sakar mata murmushi kafin ya mik’a mata hannu alamun ta zo garesa. Ahankali ta d’an matsa kamar mai jin tsoro, ta zauna a kan cinyarsa…cikin cusa fuskarsa cikin wuyanta yace “Morning wife!” Ba ta amsashi ba sai da ta mik’a masa tata gaisuwar tukunna . Sannan ta d’an kalle sa ta ce “Kanada damuwa! mun ce ba za mu dinga b’oyewa juna komai ba. Talk to me Dan Allah”. Saida ya d’an shafa cikinta ya kalli cikin tukunna ya d’ago ya kalleta yace”Na ji har yanzu shiru ne!. Baki tab’a shan wani magani mai k’arfi ba ko da na malaria ne? Ko mu je a duba ki sosai sosai..kin san yawanci y’an mata fa kunada matsalar da ku kanku baku sani ba. sai likita ya duba da ikon Allah sai kiga an dace…” Shiruu ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa alamun ta shiga damuwa, shiyasa tashi d’aya kamar zai yi kuka yace “Shiyasa fa kika ga na kasa yi miki maganar tun tuni… Banason b’acin ranki, ni kuma har ga Allah a matse nake inji good news…” Murmushi ta yi tace “ba b’acin rai bane, kawai dai nima kasa na fara tunani ne..” Sai kuma ta d’an yi shiruu kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna tace”Mu yi addu’a !mu yi ta addu’a!” Daga haka ta yi shiruu ta fa’da duniyar tunani….itanma babban burinta a yanzu shine ta ga babyn ta ita da Yash, amma gashi shiru har yanzu, da farko tana gani kamar ya yi wuri amman itanma yanzu ya jefata a damuwa…mai zai faru idan ta kasance a cikin matan da basa haihuwa, ya kenan? Ta ma san shikenan ta rasa soyayyar Yashjub ne! Dan a yadda ta ga k’ulafucin son haihuwa a kwayar idanunsa to ba lalle ya iya zama da ita kad’ai ba tare da ƴaƴa ba sannan ba lalle ya ci gaba da sonta kamar yadda ya ke yi ba. Yashjub ya riga ya saba mata da zazzafar soyayyar sa Idan ya juya mata baya ba ta san ya zata yi ba. Da sauri a cikin ranta tace “Ya Allah ka sa zan haihu nima, Ya Allah ka bamu y’a y’a masu albarka.” Ahankali yace”kar fa ki saka damuwa a ranki.. Ki yi hak’uri idan na d’aga miki hankali” Girgiza kai kawai ta yi tace “ba komai”ta d’an yi murmushi daganan ta mik’e, shi kuma ya fad’a toilet domin yin wanka. Har ya fito a yadda ya shiga ya barta hakan ya dawo ya tarar da mood d’in ta, shiyasa ya yi ta janta da wasa yana k’arfin halin ganin ta sake dan shima a damuwar yake, Ya san it’s too soon amman yawanci ana samu da wuri ai. A haka suka yi breakfast d’in kowa da abunda yake tunani kafin yace “ta zo su je su d’an kammala shirin tafiyar tasu, dan jibi suke so su wuce uk su duba jikin Na’ima su yi musu two weeks inshaaAllah daga nan sai su wuce Nigeria. Ko da suka fita gajiya ga ciwon marar period d’in da take yi ne ya sa Yash ya dawo da ita, bayan ta gama duk abunda ya kamata, shi kuma ya koma. Sai dare ya samu ya dawo Washegari komai nasu ya kammala ta inda zasu bar Cyprus nan da kwana biyu. A cikin kwana biyun nan saida Yashjub ya san yadda ya yi ya cire mata damuwa dan ya lura tunda ya yi maganar ciki hankalinta a tashe yake. Ba wai dan hankalin nata ya kwanta ba ta sake ta ke walwala dan ta lura ba zai barta ba idan har ba ta sake d’in ba Amman a chan k’asan zuciyarta tana da damuwa da ta duk’ufa gayawa Allah. Tun daga nan zaman su ya dawo kamar farko suka koma wasai abunsu dan shima Yash d’in daurewa yayi sosai ya ke k’ok’ari wajen b’oye tasa damuwar. A ranar tafiyarsu Manubiya ji ta yi kamar kar su tafi.Ta ji dad’in Cyprus kwarai ta ji dad’in gidan ta ji dad’in rayuwar da sukayi fiye da komai a rayuwarta, rayuwar da ta tabbata ko wacce mace idan ta samu za ta ji dad’i za ta yi alfahari da sannan zata ajjiye a kwakwalawarta har k’arshen rayuwarta. dan tabbas rayuwa ce mai tsada mai dad’i da mutun bai Isa ya mance ba… Da rana wajajen 2:34 british airways ya sauk’e su a Heathrow Airport London. Suna fitowa Yashjub ya hango Junior ya nufosu yana murmushi, dan haka shima ya sake rik’e hannun Manubiya suka nufe sa. Yana zuwa ya yi hugging Yashjub kafin ya juya ga Manubiya suka gaisa cikin girmama juna, daga nan suka nufi inda ya yi parking motarsa da su da waenda suka d’aukar musu luggage d’insu. “Ga inda ake k’anin miji mai hankali” Manubiya ta fad’i hakan a k’asan ranta. A bakin wani babban gida mai d’ankaren kyau Junior ya tsayar da motar, ya danna horn kafin mai gadi ya ja musu suka nufi ciki. A bakin entrance na shiga babban parlourn gidan suka tarar da Hajiya mama tana jiran su….tunda Manubiya ta fito ta kafeta da ido ta shiga yaba Yarinyar a ranta, gata da nutsuwa dan tunda ta tunkaro ta kanta yake a k’asa kuma tana lure da yadda ta zame hannunta a cikin na Yashjub a hankali a time d’in da ta lura da ita. Murmushi ta yi lokacin da suka k’araso, Manubiya tana shirin durk’usawa Hajiya mama ta yi sauri ta tarota ta sakata a jikinta ta rungume.. dai dai nan mom ma ta fito…haka itama ta yi hugging Manubiya cike da so sunata murna kamar za su maida ita ciki kafin su nufi cikin parlourn da ita! Saida suka zazzauna tukunna Manubiya ta samu ta zamo daga kan kujerar ta gaida su da girmamawa murmushi kawai sukayi suka amsa kafin Hajiya mama ta d’aga Kai ta kalli Yashjub tace “To fad’o mini a ka…yau kenan miskilancin ta kaina ya biyo”. Da sauri Junior yace “Inaaaaa!Hajiya mama ai this is a new B Yashjub fa”ya fad‘i hakan yana mai nuna Yash kafin ya d’aura da cewa”ai ya daina miskilanci yanzu,tunda fa muka taho yake zubawa sweetheart d’insa surutu, yana nuna mata wajaje da favorite places d’insa. Love ya chanja shi ya koma mai surutu” Dariya duk sukayi yayinda Yashjub ya d’an yi murmushi ya na mai sunkuyar da kai a ranshi kuwa shi kansa yana mamakin yadda soyayya ta chanja shi…. Sai da ya kuma yin wani murmushin mai cike da ma’anoni tukunna ya kalli Hajiya mama yace”Ba fa ki kulani ba. A bakin k’ofa kika barni, kika ja hannun kishiyar ki ko ‘hi’ baku ce min ba daga ke har mom..” Murmushi mom ta yi ta mik’e ta k’arasa ta je ta yi huggin nashi tace”welcome welcome” Daga nan ya yarda ya bita ta zaunar da shi kusa da ita. Lek’awa Hajiya mama ta yi ta rankwashe sa tace “Da wani katoton kansa!wa za ka yi wa shagwab’a??” Kwashewa da dariya Junior ya yi, dan haka Yashjub ya d’ago yana masa irin kallon ‘ka fa fita a idona’d’innan! wanda ya sa Junior d’in saurin gimtse dariyar tasa ya shiga yin ta k’asa k’asa sai kuma duk aka sa dariya banda Yashjub wanda ya ke kallon Manubiya da kalar tausayin irin ‘har da ke ake mini dariya’ ɗinnan. Masu abinci ne suka fara gabatar musu da kalolin dishes… saida aka kaisu d’aki suka yi wanka suka yi sallah tukunna aka kaisu wajen Na’ima,jikin nata da sauk’i dan k’afar tata ta d’auko warkewa ma Ba yabo ba fallasa ta amshi Manubiya har da y’ar tsokana, daga nan aka fita parlourn har ita. Suna zama Abhi ya shigo dan haka suka shiga gaida shi, ya ji dad’in ganin su kuwa dan haka aka zauna har da shi aka shiga hira… Dakyar kuwa Manubiya ta samu ta iya cin abinci a cikinsu dan da har Yashjub ya d’auka zai kai mata d’aki da ya lura ba za ta iya ci a tsakiyar su ba amman sai Hajiya mama tace ya barri a bar ta ta saba ta sake da su ita batason wannan takurawa da ake kira da kunyar surukai…ta d’auketa kamar best friend d’inta. Da wasa da dariya da raha haka suka dinga janta har ta samu ta d’an sake ta d’an ci abincin tana ta yaba kara da kirkin su A ranta tace”inama ace sune family d’in Yashjub na Nigeria, da ta more…” Gashi dai sunada komai amma da ta basu tsarabar Cyprus ba kad’an ba ta ga murna a fuskokinsu, nan ta sake tabbatarwa tabbas waennan sun san darajar d’an Adam. Sosai take jin dad’in yadda Junior yake respecting ɗinta! ba wai respect in the form of seniority ba no, respect ta yadda ko a kusa da ita baya zama kamar yadda Yassir yake yi, tsakanin ta da shi mutunta juna. Hajiya mama kuwa da gaske take da tacewa Manubiya ta d’auke ta kamar babbar k’awarta dan janta ta ke yi a jiki suna hira sosai tun Manubiya tana nok’ewa har ta d’an sake dan Hajiya mama har labarin shagalin bikin ta ta bata tace “lokacin maman Mommy itace babbar k’awarta……..” Kamar yau sukazo Uk sai gashi har sun yi two weeks gobe za su tafi tare da tarin alkhairin su Mom.. Tabbas Manubiya ta ji dad’in zama da su, ta ji d’adin yadda suka jata a jiki basu nuna kyama ko wani abu makamancin hakan ba Dan har gaisawa da Inna da Baba sukayi a waya kuma yanzu haka ma sunada number Innar.. A bangaren mutumin nata kuwa, abun ba a cewa komai, tana yin wanka ya ci gaba da honeymoon d’in sa babu kama Hannun Yaro dan shi ba ruwan sa da a inda suke sam bai damu da su Hajiya mama ba… Haka nan ranar da za su tafi Hajiya mama da Mom suka had’awa Manubiyan goma ta arzik’i kayan alkhairi kala kala suna ji kamar kar su rabu da Yarinyar….Sai da Hajiya mama ta yi musu addu’o’i sosai tukunna suka yi musu rakiya compound d’in gidan Junior ya ja su ya kai su airport kamar yadda ya d’ukosu, suka tafi da kewar su da kuma tsammanin su dan Hajiya mama wadda tace “nan da sati biyu zatazo inshaaAllah” saboda akwai aikin da Junior zai yi anan kano ɗin har na tsawon shekara d’aya, so za su taho tare da shi….” K’arfe 2:00pm daidai jirginsu ya yi landing a Aminu kano international airport, Nigeria…. 3 months ago…(watanni uku baya) Da farko su Mommy b’oyewa Kausar batun tafiyar su Yashjub sukayi, dan sun san zata d’aga hankalinta… Ko da labarin ya je mata ba ta yi komai ba, dan zuwa yanzu tama kasa kuka, amma fa sai da ta yi kwana uku bata runtsa ba..sai da Yasmeen ta yi mata prescribing magani tukunna aka samu ta yi bacci..gabad’ayan su tausayi Kausar d’in ta ke basu dan ta zama wata shiru shiru kamar ba Kausar ba, wani zubin har sai ka zo ka na yi mata magana amma ba ma ta sani ba, ko kuma kawai ta zuba maka ido ta yi ta kallon ka har ka gama baza ta iya cewa komai ba. Lamarin ta ba k’aramin sake d’agawa Mommy hankali yayi ba, gashi ita ta ma kasa rarraashin ta dan batasan mai za ta ce mata wannan karon ba! Ita tace ta yi hak’uri kar ta yi komai zata nema musu mafita, amman sai da Manubiya ta basu mamaki saida ta shigo gidan yashjub..amma ba komai!dan wallahi ko da ace za ta bada ranta ne fansa to wallahi gara ta bayar ɗin akan dai ta bari kud’iranta ya tafi a banza,tura ta kai bango! Dan haka komenene zai faru a hanyar cimma manufarta sai dai ya faru bata damu ba! dan sai ta cimma manufarta. Hankalinsu bai sake tashi ba sai da suka ga su Manubiya sun yi fiye da sati biyu amma shiru ba su ma da niyyar dawowa…dukda Mommy ba ta kasance mai yawan laulayi ba amma sai ga ta a asibiti wannan karon jininta ya hau matuk’a, matar da ko a ciki ba ta laulayi iyaka ciwon nak’uda kawai ta sani.Sai da suka shafe sati d’aya cur ba su zauna ba sunata jerawa Yash da Manubiya kiranye amma ko kyallin dawowarsu ba su hango ba,ganin Mommy tana shirin susucewa ne ya sa Baba larai nemo musu sabon solution ta inda ta kawo shawarar kawai su yi wa Manubiya ajiya a ciki sannan su cire mata Yash d’in a rai kwata kwata ta yadda duk nacin sa ba za ta tab’a bashi kanta ba. A ganinta wannan kad’ai ce mafita dan ta san maganar kunce jini da tayi zuwa yanzu har sati uku ba lalle ya yi musu yadda suke so ba… Dan tsabar bala’i a jeji Mommy da Baba Larai suka je suka binne abunda suka yi,a ranar suka yi wa Daddy k’arya suka ce masa an yi musu rasuwa a k’auye suka je suka kwana washegari da yamma suka dawo sunata murna su ala dole sun yiwa Manubiya ajiya a ciki sannan sun saka mata tsanar Yash a rai. A tunanin su, tunda sun yi hakan to su Manubiyan bai fi su k’ara sati d’aya ba daga haka su dawo, amman sai suka ji shiru har fiye da wata biyu, hakan ya sa Mommy ta sake d’aga hankalinta dan a ganinta indai har abubuwan da suka yi suna aiki ai Yash da Manubiya bai kamata ace sun yi zaman su a chan shiruu kamar haka ba, cike da bata tabbaci Baba larai tace”ta kwantar da hankalinta, watak’il har yanzu jinin da aka kunce mata tun farko bai daidaita ba, wataƙil yana on and off ne saboda ita dai bata karya abun da ta yi ba dan haka watak’il sunachan sunata yawon neman magani ne amman ba dai honeymoon ba.” A b’angaren Yassir kuwa yana nan zargin Kausar ya dasu a ransa fiye da ko yaushe, dan ya lura Yashjub yana tafiya ta fara rashin lafiya….sai dai kuma Maganin da take sha na saka bacci ba kad’an ba ya ke taimaka masa, dan in ta sha ta kwanta haka zai shige d’akin nata ya yi ta bidirin sa wani lokacin ta nuna masa bata so amma sai ya yi ta ƙarfi wani lokacin kuma kawai ta rabu da shi dan ta san ba hak’ura zai yin ba ita kuwa bata da k’arfin hana sa ko yin fad’a da shi a wannan lokacin tunda ko ta gwada ɗin ma ba riba…rannan kad’an ya rage Yasmeen ba ta kama sa ba tsabar yadda yake zirya ba d’aga k’afa sam, amma ko a jikinsa bai damu ba..yana sonta kuma hakan yana taimakawa wajen kawar masa da damuwar da yake a ciki saboda kamar yadda damuwa ta yi wa Kausar d’in yawa hakanan shima damuwa ta yi masa k’ad’abaibai!! Shi babban tashin hankalinsa a wannan lokacin shine ‘Yashjub yana chan yana hutawa tare da kyakykyawar matarsa, shi kuma yanannan duk wani plan d’in da ya had’a sai ya tarwatse’ dan hatta a tafiyar nan da Yashjub d’in ya yi sau uku yana k’ok’arin yashe sa amman ya kasa! Har company d’in sa ya je amman komai thumbprint ne bayan thumbprint d’in kuma hadda password Sannan ga zargin sa a kan Kausar ga Munirat da ta fara k’ular da shi da nacin ta…. Ba zai yiu Yashjub ya fi sa komai ba sannan ya fi sa kwanciyar hankali ba…shiyasa kawai ya gama deciding rufe chapter Yashjub da wurwuri dan ya gaji da nad’ar takaici…tunda yayi yayi ya kasa to zai b’arar kawai kowa ma ya rasa… Wallahi ko sunansa ba ya so ya ji an ambata, Allah Allah ya ke ya ga babu shi a doron k’asa, ba don ya san ba zai taɓa iya sake jurar ganinsa a doron ƙasa na tsahon ɗan lokaci ba to da zai so ace ya fara tura masa bak’in cikin da watak’il ma shi ne zai zamo ajalin sa dan tabbas idan akace Yashjub ya mutu da takaici bak’in ciki da kuma tashin hankali abun zai fi yi masa dad’i fiye da komai.…tsabar yadda Yassir ya kwallafa rai da son ganin bayan Yashjub har wata y’ar rama ya yi….. Today.(yau) Daddy, Yash ɗin ya gayawa time na landing d’insu, Ya so ace driver d’insa aka turo masa amma suna fitowa sukayi ido biyu da Yassir. Sai da Yassir ya ji numfashin sa ya d’auke na y’an dak’ik’u tukunna ya dawo da kyar, sakamokon hango Manu da yayi..ta yi wani irin fari ta yi fresh ta k’ara kyau Har kamar ba ita ba!. Da kyar ya d’auke idanuwansa daga kanta ya maida akan Yash yace ‘’Wlcm” Sai kuma ya yi musu jam’i yace “Ya hanya?” “Alhamdulillah” suka ce, daganan suka nufi motar da ya faka, Yashjub yana mamakin yadda ya ga jikin Yassir d’in yayi wani irin sanyi kamar mara lafiya.. Sosai Jeep d’in ta cika taff da kaya dan sun yo tsaraba ga kuma kayyakin su da suka tafi da su sannan ga kayan wajen su hajiya mama….Ana gama lode kayayyakin a cikin motar suka shiga, ya ja motar suka yi gaba. Har suka d’au hanyar gidan Daddy Yassir ya kasa magana, wani irin kishi da zafi da takaicin Yashjub yake ji ta koina, ji yakeyi kamar ya juya ya shak’e sa, kokuma ya cika sitiyarin kowa ma ya mutu! Amma da ya tuna ya kusan kawo k’arshen Yash d’in sai ya yayyafawa zuciyarsa ruwan sanyi dan ya riga ya gama had’a plan d’insa Allah Allah kawai yake ayi ayi lokaci ya cika, bayason ganin sa baya son jin ko da muryarsa ce! Ya kag’u ya rufe babin Yashjub ya fad’a wata sabuwa, dan a yadda Manubiya take yi masa d’innan ya san zai d’an sha fama da ita kafin ta yarda ta auresa bayan mutuwar Yashjub….. “Ya na ga ka d’au hanyar gida?” Muryar Yashjub ta katse masa lissafin sa Sai da ya d’an d’au lokaci tukunna ya juya ya kalle sa ya ce ‘’Mommy ce tace in kai ku chan, ku huta. Zuwa gobe sai su Yasira su je gaba d’aya a tayata gyaran gida, dan ta san ba za ta iya ita kad’ai ba’’ Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya ji gaban sa ya yanke ya fad’i..shiruu kawai ya yi a ransa yace “Allah ya rufa asiri” Daga nan motar ta d’au shiru tsit kawai akeji ta koina har suka k’arasa bakin mansion d’in aka bud’e musu suka shiga, ba wanda ya sake cewa komai. Tun kafin motar ta tsaya ya ga sun fito gaba d’ayansu Har Kausar Ummi da Munirat..shine ya fara fitowa tukunna ya bud’ewa Manubiya gidan baya itama ta fito..kallon Kausar take yi tana mamakin kwalliyarta ta cikin glass d’in shiyasa ma ta kasa fitowa har sai da ya buɗe ɗin… Gashi kayan jikinta k’anana, ga hula ta d’aura a kanta amma ba ta cusa gashinta a ciki ba instead ta fito da shi duka yana reto gefe da gefe da baya ko k’aramin ribbom ba ta mak’ala ba, ga wani irin high makeup da ta yi kamar wadda za ta je gasar saurauniyar kyau! Ko ba a fad’a mata ba ta san saboda Mijinta ne ta yi wannan kwalliyar da shigar shiyasa ta kasa hana kanta jin kishi, dama tun d’azu a jirgi take jin amai da ciwon Kai ga kuma zazzab’i, yanzun kuma ganin Kausar ya sake b’ata mata rai shiyasa gaba d’aya ta shiga jinta wani iri sosai sosai. Ahankali yake nazartar ta kafin yace”muje mana” Ya fad’i hakan yana k’ok’arin ruk’o hannunta, gudun magana yasa ta d’an janye da style ta d’aga masa Kai alamun ‘to’ daga nan suka nufi inda dandazon su Mommy suke a tsatstsaye. Ba abunda ya fi d’agawa Mommy hankali irin farin da ta ga Manubiya ta yi, dan har wani d’aukar ido ta ga tanayi! Ta san sun yi mata ajiya a ciki amma sai ta kasa hana kanta zargin ‘ko dai cikine da ita’!! Har Manubiyan ta k’arasa inda take tsaye, ta d’urkusa a gabanta ta na gaida ita ba ma ta sani ba saida Baba larai ta d’an zungureta tukunna ta dawo cikin haiyyacinta, Ahankali ta dafa kan Manubiya ta ce “lafiya y’ar albarka ya hanya?” “Alhamdulillah”kawai Manubiya tace, daga nan ta gaida Baba larai itama ta amsa mata da kulawa kafin ta mik’e ta nufi Ummi tana shirin durk’usawa Ummin ta rik’eta tace “Sannu ya hanya” cikin tsananin ganin girman matar Manubiya tace “Alhamdulillah” daga nan ta gaida ita sai kuma suka hau murna da hugging juna ita da su Yahanasu yayinda Yashjub yake chan suna gaisawa da su Mommy, Baba larai tana tsokanarshi wai ‘ya yi k’iba.’ Ko kallon Kausar bai yi ba, ko da ta matso ma tana kwarkwasa ta gaida shi bai amsa ba sai da Mommy tace’’Kausar fa tana gaida kai,”tukunna yace ‘’Alhamdulillah’’ ba tare da ya kalle ta ba, dukda haka bata damu ba haka ta matsa kusa da shi sosai ta tsaya ana magana wanda hakan ba kad’an ba ya sake tunzura lissafin Yassir. Sosai ran Ummi itama ya b’aci duba da yadda Kausar d’in ta matso kusa da Yashjub sosai kuma Mommy ta rik’e masa hannu ta hanasa matsawa ana hira ana dariya kamar irin so take ma Manubiya ta gani. Shiyasa tun kafin Manubiyan ta juya ita kuma ta kamo Hannunta suka yi ciki su da Munirat da Yahanasu…. Bata barta ma ta zauna a parlourn ba chan sama side d’inta ta kaita har bedroom d’inta tace “ta huta”daga nan ta cewa Munirat ta kawo mata abincin da suka yi.. Sai dai a ga shishshiginta amman ba za a yi wannan cin kashin a gaban idanunta ta kyale ba, Dama tunda ta ji su Mommy sun dage a kan Yassir ya kawo su nan ta fahimci akwai abunda suke son yi….kuma ita har ga Allah girkin da Mommyn ta yi musu ba ta yarda da shi ba, dan haka ba za ta bari ta ci ba, shiyasa ta cewa Munirat ta kawo wa Manubiyan wanda su suka dafa. Yashjub ya so su zauna a side d’insa amman sai Mommy tace”tunda na kwana d’aya ne, kawai su zauna a guest room inyaso gobe sai su wuce” “To”kawai yace ba dan ya so ba dan 3 months ago Yahanasu ce masa ta yi ‘ya zauna da matarsa kawai a uk har abada In kuma hakan bai yiu ba to kar ya kuskura ya dinga favoring d’inta sannan ya d’an rage nuna mata soyayya a gaban su Mommy’…..shima kuma ya fahimci hakan sannan dama ya sa a ransa ba kwana kusa za su dawo d’in ba amma duk yadda yaso ya dad’e ya yi kamar 2 years haka sai ya ji ya kasa, kuma bazai ma yiu ba saboda aiyyukansa duk suna nan, shiysa ya fara shirin dawowa to a wannan time d’in ne ma Daddy ya kira sa wanda kiran da ya yi masa da yanayin yadda ya yi masa magana da sanyin murya gaba d’aya ya kashe masa jiki, duk abunda ya shirya ma zai fahimtar masa kuma zai yi a kan su Yassira gaba d’aya sai ya ji ba zai iya ba dan Daddy d’in sounds so disturbed (ya ji Daddy ɗin a dame sosai) kamar irin ya gaji da damuwa da cases d’innan, tunda har ya sauk’o da kansa… kuma kamar akwai abunda ya taso masa yake damunsa wataƙilan case d’in marigayiya…shine babba a ganinsa bai kamata ace shine zai saka Daddy a damuwa ko ya k’ara masa damuwa ba..kwanaki ya yi masa wuta wuta yanzu kuma tunda ya sauk’o to Alhamdulillah shi kuma inshaaAllah ba zai taimaka wajen sake d’aga masa hankali ba,shiyasa ya yanke a kan zai yi ta addu’a kawai komai ya daidaita kuma inshaaAllah ba zai yi abunda Manu za ta kwana a ciki ba… Baba larai ce tace “mu shiga ciki mana, ku gaisa da Daddy, a ci abinci ko? Naga su Manubiyan ma har sun wuce. Tun safe Mommyn naka take yi muku girki..babu wanda ya ci abinci ku ake ta jira”. Murmushi ya yi ya kalli Mommy yace ‘’Thankyou Mommy’’ Daganan duk suka shige cikin parlourn, Yashjub ya nufi chan sama wajen Daddy, yayinda su Mommy suka fara rarraba idon neman su Manubiya… Da sauri Baba larai ta matsa kusa da ita k’asa k’asa tace “To!Ummi ta yi sama da ita, kuma in ba da kyar ba ta cika mata ciki da nata abincin, kinga shikenan mun yi shiri da wahalar banza kenan….” A zabure Mommy ta nufi sama d’akin Ummi. Tun d’azu dama Ummi ta lura kamar Manubiyan bata jin dad’i, dan haka suna zama, da Munirat ta fita d’ebo abinci Ummin ta kalli Manu tace “Baki da lafiya ne?” Sai da ta d’an sunkuyar da kanta k’asa dan gaba d’aya kunyar Ummin take ji, gashi ta hanata zama a k’asa kan kafet ta d’aura ta akan gadonta d’are-d’are, tukunna tace “Zazzab’i nake ji da amai” Wani kalar murmushi Ummi ta yi kafin tace “Sannu.. Inaga flight d’in ne ya ja miki hakan, akwai pottage na san za ki ji dad’in sa sosai, yanzu Munirat za ta kawo, sannu ko” Ahankali ta jinjina Kai tace “Nagode Ummi” Daganan ta d’auko wayarta ta shiga kiran su Innaa, tun a mota Jidda ta kirata ita kuma tace mata sun iso, amma ita Jidda tana skul, ta kira Innar kuma bata d’auka ba shine yanzu take sake gwadawa…. Ummi na cikin gaisawa da inna Mommy ta shigo…sai da ta basu mamaki sakamokon ganin ta a hargitse da suka yi, dan haka sukayi sallama da Inna tukunna Ummi ta bata dukkannin attention d’inta tace “ya na ganki a gigice, ince dai lafiya ko?” Tabbas zuwa yanzu Ummi ta fara kai Mommy bango da yanayin maganganunta masu harshen damo marasa respect!!!. Ba ta ita take ba yanzun amman tabbas za ta samu lokacin ta soon, Shiyasa kawai ta k’ak’alo murmushi da kyar tukunna tace “lafiya k’alau Ummi, naga ban ganku a k’asa bane, shine na biyo d’aukar y’ar tawa”. Ita kanta Manubiya sai da ta ji wani bambarakwai, dan yanayin kulawar da su Mommyn suke ba ta yau ɗin ta musamman ce, saboda ko a waya idan za su gaisa da ita ba ta cika yi mata irin hakan ba. Murmushi Ummi ta yi, tana shirin yin magana Munirat ta shigo d’auke da tray..cikin tattausan lafazi tace “Ai ni kam wai da har na yi shishshigi, na sa Munirat ta d’ebo mata abinci, ki bari kawai ta ci anan ɗin dan naga duk kunya take ji, ga kuma gajiya”. Jinjina Kai kawai Mommy ta yi daganan ta juya ta fita..tana fita ta hango Yashjub yana sauk’owa tare da Daddy. Cikin sanyin jiki ta k’arasa, suka gaisa da Daddy, dama Yashjub d’in take nema ga kuma har da Daddy a kusa da shi dan haka a ranta tace “perfect’’. Cikin sanyin murya tace ‘’Am ko za ka yi wa Manubiya magana ta fito mu je ku ci abinci, na gama had’a dining a k’asa Inata jiranku tun dazu’’ Murmushi ya yi yace ‘’ok Mommy. Bara in kira ta, tana d’akin Ummi ko?” Jinjina kai ta yi kawai. Daga haka ya wuce itama ta nufi k’asa Daddy ma ya wuce k’asan. Yashjub yana shiga ya tarar da su Yahanasu suna ta faman k’ok’arin zuba mata abinci… Sai da suka gaisa da Ummi dan d’azu su Mommy ba su bashi dama ba tukunna ya kalli Yahanasu wadda ta gama zubawa Manu abinci ta mik’a mata ta fara k’ok’arin bud’e d’aya kular. Bai so zai ce wani abun ba dan ya san Ummi zata ji babu dad’i amman kuma Mommy ta yi masa magana kuma a gaban Daddy sannan ita da kanta aka ce ta yi girkin shiyasa kawai ya dake ya ce “Am Yaha!ko za ku sauk’o da ita da abincin k’asa ko?,basu gaisa ma da Daddy ba” “Ok”kawai Yahanasun tace, Daga nan shi kuma ya juya ya fita dan baiji dad’i ba! Ummi zata ga kamar ya gwale ta ne. Yana fita Ummi ta girgiza Kai kawai, ta riga ta san ba yin kansa bane ba. Daga haka tace musu su sauk’a da abincin. Ba a dad’e da zama ba, su Manubiya ma suka sauk’o wadda zuwa yanzu zazzab’i ya yi mata ruff! daurewa kawai take yi, ga wani Irin amai da ya taso mata tun d’azu da su Yahanasu suka fara bud’e kuloli har yanzu bai kwanta ba. Suna k’arasawa ta sunkuya har k’asa ta gaida Daddy, da kulawa ya amsa yana tambayar ta ya Cyprus sannan ya suka baro su Hajiya mama, ta amsa masa da “Alhamdulillah,suna lafiya Alhamdulillah.” Da kyar saboda wani jirijiri da ta ji yana d’ibar ta ga amai da ta ji yana shirin taho mata gadan-gadan. Cikin murmushi Daddy yace “MashaaAllah. Bismillah, have lunch with us’’ Ya fad’i hakan yana mai nuni da table d’in dake nan a cike a gaban sa mak’il da abinci. ‘’tam,na gode Daddy” tace, daganan ta mik’e tsaye aikuwa tashi d’aya wani irin gigitaccen jiri ya kwasheta, ta tafi luuu za ta zube, da sauri Yassir wanda shigowar sa kenan ya sa hannu ya tareta had’i da rungumeta tsamtsan a jikinsa!! Tashi d’aya wani yanayi na gigita da fitinar da bai tab’a ji ba ya sauk’ar masa sakamokon tsananin laushi da d’umin jikinta da ya ji… Duk mik’ewa suka yi. A mugun rikice Mommy ta shiga cewa “Subahanallah Manubiya lafiyarki? sannu kin ji, Yashjub dama bata da lafiya?” Cikin tsananin b’acin rai Yash ya ƙarasa ya finciko ta daga jikin Yassir ɗin, tsabar tsananin kishi bai san lokacin da ya rufeta da wani irin fad’a ba ‘’Baki da hankali? Ba za ki iya rik’e kanki ba? Za ki kama ki tafi ki fad’a masa a jiki?yanzu……” Cikin tarar numfashinsa Ummi wadda ta lura da yadda Manubiyan take jin jiki ta k’arasa, ta ce ” yi hak’uri Yash gajiya ce da kuma jiri, a yi mata uzuri ko? duba ka ga halin da take ciki mana.” Sai a lokacin ya fahimci yadda ta fara hawaye ta ido d’aya, gashi ta dafe kanta ta runtse idanuwanta da k’arfi. A hankali ya cika mata hannu kawai ya juya ya nufi cikin parlourn…. Wani kalar farin ciki ne ya lullub’e su Yassira ganin yadda Yash d’in ya yi mata, yayinda Mommy ta fara shiga masifaffan tashin hankali dan yanayin manubiya ya bata tsoro. Ummi ce ta d’an ruk’ota ta share mata hawayen tace “Kar ki yi kuka a gaban mutane mana” Ba tare da kowa ya gani ba ta d’an sake share mata fuska tace”Mu je ki ci abinci sai mu je sama ki sha magani, in ma asibiti za mu je sai aje ko? ki yi hak’uri” A hankali Manubiya ta d’aga mata Kai alamun to dan ita mamaki ma ya hanata jin haushin Yash..anya kuwa shine ya yi mata wannan tujarar a gaban jama a har da wani cewa ‘bata da hankali!’… Da kyar dai ta kawar da tunanin, suka k’arasa Ummi ta ja mata kujera ta zauna itama ta zauna. Sai a lokacin tukunna Mommy ma ta zauna, tana mai jan numfashi da kyar, dan ji takeyi gaba d’aya iskar parlourn ta yi mata k’adan! Yanayin Manubiya da kalar cika da fresh d’in da ta ga ta yi dama a gaskiya indai idanuwanta ba gizo sukayi mata ba tou kuwa ciki ta hango d’anye ma kuwa, yanzu kuwa jirin da ya kwasheta ya sake tabbatar mata…amma taya? Ta san dama shi Yashjub ba kasafai abu yake kama sa ba ko ya kama sa ma to ba ya dad’ewa a jikinsa wannan gado ya yi a jininsa yake, sannan bata tab’a iya juya masa lissafi…to amman ita Manubiya fa?? taya akayi har ta bari wani abun ya shiga tsakanin ta da shi da har ta kai ga samun ciki! Idan ma ta bari d’in to taya ciki zai iya zama a jikinta bayan ajiyar da akayi… Anya ba gaskiya Yasira ta fad’a ba kuwa da tace ‘aikin Baba larai ya daina ci yanzu!’ Tunda gashi dai tun farkon had’uwarsa da Yarinyar nan aka gagara rabasu, aka gagara lalata maganar auren, suka gagara su hana d’aurin auren, suka gagara cireta a ransa da rayuwarsa, yanzu gashi ciki yana neman b’ullowa kuma sun gagara cusa Kausar cikin gidan Yashjub. Dan haka Indai har Yarinyar nan ba waliyyiya baceba tou tabbas da gaske aiyyukan Baba larai sun daina ci.” Mommy ta aiyyana hakan a cikin ranta. Yasira ce ta zuzzuba mata duk abubuwan da suka dafa a plates ta tura mata gabanta tana mata wani kalar murmushi kafin tace “bismillah” Ahankali Manubiya tace “thankyou”sannan ta sa Hannu ta d’an sake jan abincin gabanta. Da kulawa Daddy yace “In duk abincin ba su yi miki ba, akwai cooks ki fad’i abunda kike ra’ayi sai a dafa miki. Ahankali Yassira tace “Idan ma na waje kike so sai a siyo miki” Dakyar Manubiya tace ‘’A’a zan ci wannan d’in ,nagode sosai ‘’ Tana mai jin dad’in yadda Daddy yake yi mata had’e da mamakin Yassira. Sai da ta juya ta kalli Inda Yashjub yake zaune a chan cikin parlour ya yi kicin-kicin da rai, tukunna ta juyo ahankali ta d’auki lomar abincin da Yahansu ta zuba mata ta kai Baki…..ba don kar ta fito da shi waje su ji ba dad’i ba tou da tuni ta fiddo sa dan tashi d’aya ta ji wani irin amai ya yunk’uro mata dan haka ta yi sauri ta had’iye ta d’auka ruwa ta kora ta shiga k’ok’arin danne aman da yake ta so ya fito, a ranta kuma tana mamakin ‘wacce irin fever ce haka wadda bata tab’a yin irin ta ba mai amai’ dan har ga Allah kwata kwata lissafin ta bai kawo mata ciki ba. Cike da k’arfin hali ta d’aura spoon d’in ta a plate d’in da Yassira ta turo mata gabanta gudun kar Mommy ta ji ba dad’i idan ba ta ci nasu ba…a hankali ta deb’o ta yi bismillah a cikin ranta ta nufi bakinta da shi wanda hakan ya sa tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira gaba d’ayansu suka tsaya da cin nasu abincin sukayi mata ‘k’uuurrr!’ da ido suna jira kawai su ga ta kai cikin bakinta. Da mamaki Daddy ya saki Baki kawai yana kallon su…lura da hakan da Baaba larai ta yi ne yasa ta yi sauri ta zunguri Mommy cike da takaici, da sauri Mommy ta juya ta kalle ta, Baba laran tana shirin nuna mata yadda Daddy yake kallonsu suka ji Manubiya ta tura kujerar ta baya da sauri ta mik’e… Ko gama juyawa ba ta yi ba amai ya kece shaaa…….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 27* Da wani irin sauri Yashjub ya taso ya k’araso inda suke, yana zuwa ya rik’eta da niyyar shigar da ita ko da d’akin Yahanasu ne amman hakan bai yiu ba! Dan tashi d’aya ta shiga kwarara masa aman da ta ke yi ɗin a jikinsa ba ji ba gani…ganin yadda jikinta yake karkarwa ne ya sanya ya riketa sosai had’eda d’an tallafota,ahankali ahankali yana d’an bubbuga mata baya. … Sai da ta amayar da gaba d’aya abun da ke a cikinta tukunna ta d’an fara dawowa cikin haiyyacin ta…dukda yadda take cikin jin zafin abunda ya gama yi mata d’azu, sai ta tsinci kanta da jin tausayin sa da kuma rashin jin dad’i ganin yadda gaba d’aya ta b’ata masa jiki. Still layi ya ga tana yi Bayaga hakan wannan uban aman da ta shek’a dama dole ta zama bata da k’arfi a Jikinta, dan haka ya durk’usa bai damu da wai a gaban su Daddy yake ba kawai ya kinkimeta ya nufi d’akin Yahansu da ita. Da sauri Kausar ta goge hawayen da suka silalo mata, sai kuma ta juya ta nufi sama da gudu. Kallon ta kawai Yassir ya yi, saida ta b’acewa ganin sa tukunna ya juya ya kalli su Yashjub da suke shiga d’akin Yahanasu kusan a tare da shi da su Ummi da Munirat da Yahanasun. Sai da ya kaita cikin shower glass tukunna ya dire ta. Sai a sannan itama ta bud’e idanunta. Gaba d’aya fanfunan dake a jikin shower d’in ya ware musu wanda hakan yasa ta sauk’e wata k’ak’k’arfar ajiyar zuciya. Ganin yana shirin fara zuge mata zip d’in rigar tata ne ya sa da sauri ta ce”Dan Allah A’a, su Yahanasu fa suna waje! Idan muka gama wankan ta ya za mu fita??” Murmushi kawai ya yi yana kallon ta yace”Kar ki damu, kafin mu gama mu fita na san za su fita su, ba za su zauna a d’akin ba.” Ya fad’i hakan yana sake k’ok’arin ruk’ota yana mai jin wani so da k’auna da kuma tausayin ta suna ratsashi Add’ua kawai yake yi Allah Ubangiji ya sa tunaninsa ya zamo gaskiya. Turo Baki ta yi ta d’an ja baya da dukkan ragowar k’arfin da take ji kafin tace ‘’A’a ni dai,kuma Allah ka daina d’aukata a gaban su Daddy dan ni yanzu ban san ma ta Ina zan fara kallon su ba” Shiruu kawai ya yi yana kallon ta yana wani irin murmushi kafin a hanakali ya matsa yace “Sorry!ki yi hak’uri akan abunda ya faru ɗazu, amma dan Allah kar ki sake, Har yanzu zuciyata zafi take yi.” Ta fahimci mai yake nufi dan haka ta had’e rai tace ‘’A tunanin ka na fad’a jikinsa da gangan ne?‘’ Shiruu yai yana kallon ta, dan shi sai yanzu ma ya yi wannan lissafin…a hankali ya fesar da iska ya matso ya yi cupping face nata a cikin tafukan hannunsa sannan yace ‘’Mu bar maganar pls, na ji na yi laifi, rashin fahimta ne aka samu, kuma bai kamata in yi miki hakan sannan a gaban Mutane ba, ki yi hak’uri ki yafewa Babyn ki, um…..” Ya yi maganar yana mai lankwasar da Kai. Cikin d’aura hannayenta a kan nasa tana k’ok’arin kwatar fuskarta tace ‘’Kai d’in Babba da kai ai ba Baby bane, sai dai in kwace mini suna kake son yi… Kalli fa yadda ka fini tsayi” Murmushi ya yi yana mai farin cikin yadda ta huce nan da nan, a hankali yana kallon kyakkyawar fuskarta ta cikin ruwan da yake rushing a ta koina na jikin su yace ‘’Ok, bari mu tantance waye ne Babyn……’’ … Kamar yadda ya fad’a, ko da suka fito daga wankan ba kowa a d’akin sai akwatunan su. Murmushi kawai ya yi, ya bud’e ya d’auki towel ya cire vail dinta da ya rufa ya d’aura kafin Ita ma ya d’aukar mata towel ya nufi toilet d’in. Kamar za ta fashe da kuka haka ta fito, ita kam bata san da wanne ido za ta ke kallon y’an gidan ba…d’azu ya d’auke ta yanzu kuma ya sa su Yahansu sun fita sun bar musu d’akin…. Jiri take ji sosai shiyasa ta nemi waje ta zauna a kan gado tana ganin uku-uku. Da kyar da taimakon sa ta shirya cikin wata English dress har k’asa mai dogon hannu,sama sama ya yi mata drying gashinta ya saka mata hula daga nan ya durk’usa a gaban ta yace ‘’za mu je asibiti ne, ko a kira doctor gida?’’ A hankali tace ‘’Ba na jin dad’i, jiri nake yi, kuma inaso in kwanta” “Ok” kawai yace Daga nan ya mik’e ya k’arasa ya d’auko wayarsa ya danna kiran family doctor d’insu… Suna gama wayar ya koma inda take ya saka ta a jikinsa kafin yace ‘’Me kike so? Me kike sha’awar ci in je in nemo miki??” Girgiza kai kawai ta yi tana jin zuciyarta tana tashi dan sunan abinci kawai da ya ambato gaba d’aya sai ta ji kamar za ta yi amai. Sake rungumota ya yi tsan tsan kafin yace ‘’Ki fad’i ko menene zan nemo, ba zai yiu ki zauna a haka ba.” Ahankali tace ‘’Allah ba na son cin komai ni dai’’ Yana shirin yin magana wayarsa ta d’auki k’ara..ganin sunan Yahanasu ne yasa ya d’auka ya kara a kunnensa…. Earlier Su Yashjub suna wucewa su Mommy ma suka nufi sama ba tare da b’ata lokaci ba, parlourn ya rage saura Daddy da Yassir wanda ya ke jin zuciyarsa tana wani irin tafarfasa…. Tabbas zargin sa a kan Kausar ya tabbata kenan son Yashjub take yi!! Dan idan ba haka ba meye na kuka? sannan ta wani wuce sama da gudu! Shi kuma Yashjub wai shin shi ya fi kowa sa’a a duniya ne ga mata nan kyakykyawa Allah ya basa ga d’aukaka da success ga farin ciki sannan yanzu kuma har zai haihu dan in ba da kyar ba ya san Manubiya ciki gareta…yanzu idan ta yi ciki yana ji yana gani haka za ta haihu ba tare da ya same ta ba??! Sai dai ya sameta as maamaa kenan fa..inaa ba zai yiu ba! bayaga haka ba zai tab’a yarda Yashjub ya sake samun wani farin cikin bayaga wanda ya ke a ciki kafin ya mutu ba…. Runtse idanunsa ya yi da k’arfi sakamokon sarawar da kansa ya shiga yi. Mik’ewar da Daddy ya yi ne ya dawo da tunaninsa cikin parlourn, a hankali ya bud’e idanunsa waenda suka rine sukai jazur! Bai gama dawowa daidai ba Daddyn ya wuce sama ranshi fes!! yana murna da adduar Allah ya kawo masa first jika d’insa d’an gidan Yashjub lafiya, tabbas za‘a ga gata!. Daddy yana wucewa su Ummi ma suka fito Direct sama suka nufa yayinda Munirat ta d’an tsaya dube dube tana ganin wucewar su ta zauna kusa da Yassir. Da sauri ya mik’e ya kalleta, da kyar ya yi mata murmushi yace ‘’Daddy cewa yai in bisa sama, we will talk later.” Daga haka ya wuce ya barta zaune a wajen ita kad’ai. Tsabar tsananin tashin hankali mai tafe da dana sani Munirat ba ta san lokacin da ta fashe da wani Irin kuka ba…. Direct sama side d’in Kausar su Mommy suka nufa…Yasira da Ya’isha ne suka shige cikin d’akin wajen Kausar d’in suka shiga bata Baki…dukda zuwa yanzun ba kuka take yi ba amman ajiyar zuciyar da take sauk’ewa ya ishi ya fahimtar da kai tsananin tashin hankalin da take a ciki. A parlourn Mommy Baba larai Yadira Yusra da Yasmeen suka tsaya, dan har ga Allah su Yasmeen bama sa so su had’u da Kausar tsabar tsananin tausayinta da suke ji. Mommy kam tashin hankali ne ma ya hanata k'arasawa ciki…itama ta kanta take yi. Cikin rashin jin dad’i Baba larai ta ja Mommy gefe tace ‘’Khadija sam kin chanja gaba d’aya, bari ki ji wallahi ke kike dawo da aiki baya! Ban san mai ya faru mai ya sa yanzu kike kasa danne kanki ba. Tunda suka tafi na ce miki ki dinga jan Yarinyar nan a jiki a san halin da take ciki a chan ɗin amma kin kasa,kamata ya yi ki dinga kiranta akai akai amma na sha ganin misscalls d’inta ma a wayarki ba ki d’auka ba. Idan fa an yi abu ba wai zuba ido za ‘a yi a nad’e hannu a jira aiki ya ci ba, kai ma sai ka bada gudummawar wayo da kissa tukunna, sannan kuma ka shiga jikin mutun, ta yadda za ka fahimci abun ya yi ko akasin haka, amma sam kin kasa! Gaba d’aya Ummi da Manubiya sun chanja ki..yanzu ko d’azu da Ummi ta hana Manubiya cin girkin ki ta kwaso ta sama na san kin fahimci zarginki take yi ko? Sannan itama Manubiyan kalar kallon da take yi muku da taga kuna nan nan da ita a iyaka yau kawai ai kinsan na mamaki ne ko?. Ko da ace su Yadira sun yi fushi da su ko fad’a ko wani abun makamancin haka it’s okay amman ke kina yi tashi d’aya komai zai tab’arb’are!!! na gaya miki na gaya miki amma kun kasa ganewa, gaba d’aya kun bari zuciyarku tana juya ku sannan tana mulkar ku… Gashi yanzu in ba da kyar ba Wallahi ciki gareta, kuma ban san tayaya akayi hakan ta faru ba. Kun k’i yarda ku shiga jikinta balle ku san kalar tsari da addu’o’in da take yi har a samu a san abunyi.Yanzu na tabbatar inda ace kina waya da ita akai akai kuna video call kuna hira da ita sosai da tuni a cikin watanni ukun nan za mu fahimci abunda mukayi bai yi ba kinga da sai a sake sabon shiri da wuri, amma sam kun k’i ku bani had’in kai, kinga kuwa ai dole a yi ta ganin ba daidai ba…” Da kyar Mommy ta shak’i iska ta fesar kafin ta sa Hannu ta yafito Yasmeen. Yasmeen tana k’arasowa ba tare da shakku! Tantama ko tunanin wani abu makamancin hakan ba Mommy ta ce ”Ki rubutawa Ya’isha allura yanzu kafin mu sauk’a k’asa..muna sauk’a, za mu je ki gwada Manubiya, idan kika gwada ta, kika ga alamun ciki gareta to kar ki bari a yi test kowa ya gani a tabbatar, kawai ki ce musu ba ta da ciki!.. na san ai ba za su fahimta ba, sai ki yi mata allurar da Ya’isha za ta siyo miki ba tare da kowa ya gane ba! A had’o allurar da ta ciwon jiki da ta hana amai. Kin fahimci allurar da nake nufi???” Ahankali cikin tsananin mutuwar jiki da rashin jin dad’in abunda Mommyn take shirin saka ta ta aikata Yasmeen d’in tace ‘’eh,Mommy” sai kuma ta yi shiru kafin ta sake cewa “amma Mommy kina ganin Ya Yash ba zai fahimta ba? Bayaga hakan ma kuma idan aka yi allurar ai za ta yi miscarriage, kuma za‘a gani, sannan za ‘a fahimci ciki gareta amma na yi k’arya nace babu.’’ Cikin fushi Mommy tace ‘’kin fi ni sanin abunda nake yi ne? tunda nace miki haka ayi kawai! Mu samu mu fara yin maganin matsalar da ke a gabanmu yanzu gadan-gadan, next..za mu san abun yi shima’’ Shirun da ta ga Yasmeen d’in ta yi ne yasa cikin tsananin fushi ta sake cewa’’za ki iya ko ba za ki iya ba!?” A hankali Yasmeen ta had’iye wani abuda take jin yana taso mata sannan tace ‘’Mommy! i took an oath to help people! Ba wai in kashe rai ba!..bayaga haka kuma dukda ban so cikin nan ya kasance a jikin Manubiya ba! Na so ace a jikin Kausar yake amma duk yadda na kai ga tsanar Manubiya Mommyn babyn jikinta na Ya Yash ne.. Maganar gaskiya Mommy ba zan iya kashe Babyn nan tashi d’aya ba.Inaga in dai abunda kuke so kenan gara kawai a nemo doctor mu biya sa ya yi mata allurar, dan ni dai a gaskiya Mommy ba zan iya kashewa Ya Yash baby tun kafin ya zo duniy…..” Mahaukacin Marin da Mommy ta d’auke ta da shi ne ya hanata ci gaba da magana…. Cikin tsananin fushi da tashin hankali Mommy tace ‘’dan ubanki ni za ki nunawa jini! kin bi kin wani hak’ik’ance Ya Yash!Ya Yash!Ya Yash d’in da bai damu dake ba tun farko sannan ana so a gyara Abu a had’a kanku kafin wata ta tarwatsa shine za ki yi mini wa’azi? Ni za ki kunyata Yasmeen!! ni za ki yi wa taurin Kai???.” Cikin huci ta fara ja da baya tana cewa “Shikenan! na tsame hannuna daga yau kowa ya yi ta kansa, tunda kallon muguwa kika fara yi min’’ Da sauri Yasmeen tace ‘’A’a Mommy ba haka bane dan Allah…’’ Tun kafin ma ta gama magana Mommy ta fice daga d’akin ta banko k’ofa. Ko gani sosai ba ta yi tsabar tashin hankali…tunda take bata tab’a Jin tsana irin ta yau ba. Da kyar ta samu ta k’arasa d’akinta tana shiga ta fashe da wani irin kuka tana hango faɗuwarta gadan-gadan.. Tabbas Baba Larai ta yi gaskiya dan gashi tunda Manubiya ta shigo a hankali abubuwa suke ta saɓa mata, komai ya ke bijire mata yana going against her, abubuwan da a da suke y’an k’anana a wajenta yanzu gashi suna shirin fin k’arfinta..duk yadda ta yi da Ummi sai ta botsare, sam ta kasa ta shiga tsakaninta da Daddy, Daddyn kansa da farko kamar sun samu kansa amma yanzu ya burkice ko su Yasira ba kasafai yake hira da su da Dariya kamar da ba, yanzu kuma gashi y’ar cikinta ta botsare mata!me ya fi wannan bak’in ciki?kuma ta san in ba da kyar ba sai su Yasmeen d’in sun dasa ayar tambaya a kanta duk a ta dalilin mak’urar da Manubiya ta kai ta. Tabbas sai yanzu ta sake fahimtar Baba larai dan gashi tunda Manubiya ta shigo rayuwar Yash duk abunda ta tsara baya tafiya mata yadda take so, in banda fitina da b’acin rai da k’alubale babu abunda take fuskanta, a tak’aice dai a hankali a hankali kenan Manubiya sai ta yi mata tumb’ir!!inaaa aikuwa ba zai yiu ba!!! she won’t allow it (ba za ta bari hakan ta faru ba) wallahi sai dai a mutu!. Mommy tana fita Yasmeen ta kalli Baba larai tace ‘’ Baaba ki yi mata bayani dan Allah” Da sauri Yasira wadda k’arasowar su yanzu gurin tace “Mai ya faru? Kallon ta ta yi ta kalli Ya’isha kafin ta shiga zaiyyane musu abunda ya faru…. Kamar Ya’isha za ta rufe Yasmeen da duka haka ta shiga surfa ruwan bala’i tana cewa”Ashe baki da lisssafi ban sani ba? Har yaushe kika santa da har za ki tausaya mata dan wannan ba wai Yashjub kike tausayawa ba ita kike tausayi. To bari ki ji in gaya miki idan har wanann Yaron ya zo duniya wallahi ko k’ofar gidan wata rana baki isa ki taka ba!,kinga daganan sai in ga ta k’arshen zumunci da tausayin d’an d’an uwa! Ki na gani dai kwanan ta uku tal a cikin gidan amma da muka je korar mu ya yi! Ki bar ganin wai Daddy ya tsawatar masa yanzu ance mu je anytime wallahi a kwana a tashi watarana Daddyn ma bai isa ya ce komai ba, indai Yarinyar nan ba ta yi waje ba to ba mu da kwanciyar hankali a cikin gidan nan!! Ke kin san su waye talakawa idan suka samu guri kuwa??? sai ta raba sa da kowa ta handame komai daga ita sai y’ay’anta gashi uban dukiyar family karankatakaff duk tana hannunsa’’ Cikin son fahimtar da ita Yusra ma tace ‘’Yasmeen tunda har ga abunda Mommy tace miki ki yi kawai mana, kin fi ta sanin daidai ne?’’ Ahankali Yassira wadda tun d’azu ba ta yi magana ba, ta fesar da iska kafin ta kalli Yasmeen ta ce ‘’ki rubuta, za mu je mu siyo yanzu ni da Ya’isha…abun da Babba ya hango k’arami bai Isa ya hanga ba’’ Cikin rashin jin dad’i Yasmeen d’in tace ‘’Wai me yasa baza ‘a samu mutum d’aya a cikin ku wadda za ta kalli issue d’innan daga point of direction d’ina ba! A samu wata ta kalli al’amarin nan ta fuskar yadda na ke kalla, pls??” Wani wawan tsaki Ya’isha ta ja kafin tace “Ai dama na riga na sani, na san sai kin yi taurin kan naki da kika saba! Yasira kawai ki zo mu je zan yi browsing mu siyo kuma wallahi idan muka kawo dole sai kin yi dan babu wanda kika Isa ki gwadawa taurin kai anan!.’’ Tana gama fad’in haka ta juya ta fice fuuuu zuciyarta kamar ta b’ullo waje. Still cikin son fahimtar da su Yasmeen tace ‘’in da ace mun san zamu aikata haka to da bamu barta har ta rayu dashi a wata k’asa daban ba, Infact da bamu barta ma ta shigo gidan ba.” Cikin tarar numfashinta Baba larai tace “Yasmeen ke shaida ce wanne irin abu ne ba a yi ba amman sai da ta shigo ɗin! Y’an uwanki da mahaifiyarku sun fi ki gaskiya fa….” Cikin katseta Yasmeen d’in tace”to Baaba sai ku duba ku ga yadda akayi ta fama d’in amma sai da auren nan ya d’auru, shin ba za ku yi lissafin watak’il wannan cikin shine rabon da ke a tsakanin su wanda Ubangiji ya k’addara sai sun yi auren kuma sai ya zo duniya ba??ba za ku yi tunanin mai za ta kasance da mu idan muka dage muka ce sai cikin ya fita ba??” Shiruu kawai Baba Larai ta yi tana kallon ta. Ahankali Yasira wadda itama tun farko tsarin bai yi mata ba tace ‘’Yasmeen ki yi abunda ake so, ki yi kawai!! A iyaka sanina Mommy ta fi ki sanin duk waennan abubuwan dan haka dole akwai abunda ta hango. sannan kuma inaso ki sani duk yadda za ki so Yashjub bai kai ga yadda ita za ta so shi da shi da abunda zai Haifa ba, dan haka tunda har kika ji tace haka akwai dalili Babba! We re supposed to stick together (Kamata ya yi ace mun kasance tsintsiya maɗaurinmu ɗaya) Yasmeen, kar kanmu ya fara rabuwa tun a nan! mun fi ki yawa dan haka Ina shawartarki da ki yi hak’uri ki yi abunda kowa anan yake so ayi.’’ Shiruu d’akin ya d’auka kafin chan Yasmeen ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ahankali tace”okay!bara in rubbuto” daga haka ta juya ta fita. Ahankali Yasira ta fesar da iska…ta rasa ganin ta inda abunda suke shirin aikatawa ya kasance daidai ya kuma dace ace sun yi! Tabbas itama a cikin zuciyarta a bayan Yasmeen take d’ari-bisa-d’ari Amman kuma akwai abunda Mommy ta hango tabbas! wannan shine dalilinta na bin bayan Mommyn dan ta san in dai Mommy za ta iya cewa a kashe d’an d’an cikinta to tabbas lamarin Yashjub da Manubiya ya wuce tunanin su,ya fi k’arfin iyakar abunda ta gaya musu suka sani. ……….. Bayan kamar 40 minutes, Su Yashjub suna zaune har da Yahanasu wadda ta kawowa Mannubiya tea take sha, suka ji ana knocking. Sai da Yashjub ya kalli wayarsa ya ga likitan bai kira sa ba, tukunna ya kalli Yahanasu yace “ta bud’e, maybe su Mommy ne” Ai kuwa tana bud’ewa suka yi Ido biyu da Yasira Yasmeen da Ya’isha. Ba musu ta matsa musu suka shigo..sai da suka fara yi wa Manubiya ya jiki tukunna Yasmeen tace “Mommy ce tace in zo in duba ta” Cikin tarar numfashinta Yahanasu tace “Ai Likita yana hanya” Murmushi Yasira ta yi, ta matsa kusa da Yashjub da Mannubiya waenda suke zaune a bakin gadon tace’’Manu, ya akayi kika bari ya kira Dr bayan gamu da soon to be consultant a gida?. Yasmeen matso ki duba ta, Mommy tana jira, ta ce in ta kama sai a wuce asibiti. Gaba d’aya hankalinta har mu duk a tashe yake…aman da ta yi ai dole a dubata da wurwuri ta yadda in ma k’arin ruwa ne ya kamata sai a yi mata, dan na san she’s weak(ba ƙarfi a jikinta)” Shiruu Yashjub ya yi, kafin chan ya d’ago ya cewa Yasmeen d’in “matso mana, mai kike jira?” Sai kuma ya kalli Ya’isha yace ‘’ki je ki cewa Mommy jikin nata fa da sauk’i, ta kwantar da hankalinta”. Murmushi duk suka yi banda Yahanasu wadda gaba d’aya hankalinta yake a tashe! Har ga Allah ta gama shiryawa akan ko da ace cikin ne to za ta san yadda za ta yi ta lallab’a Yashjub su b’oye har sai ya d’an yi kwari tukunna a fad’a, amma gashi yanzu su ne ma za su fara sani! Sannan yadda suka dad’e a saman nan ba su sauk’k’o ba bata da tantama plan suka gama had’awa…. Tana wannan tunanin ta ga Yasmeen ta matsa kusa da su ta shiga duba Mannubiya…dama har da abun auna hawan jinin ta ta taho da ragowar abubuwanta… Duk wani gwajin da ya kamata sai da Yasmeen ta yi mata. ….Tun a kan pulse d’in Mannubiya Yasmeen ta jiyo alamun ciki ga kuma ragowar gwaje-gwajen da ta yi mata waenda suma suke nuni da hakan, shiyasa tashi d’aya gabanta ya yanke ya shiga fad’uwa dan ba ta san ya za ta yi ba, sannan ba ta san ma ta Ina za ta fara ba… Cike da murmushi da tsantsar farin cikin da ya baiyyana a iyaka kan fuskarta Yasira ta matso ta ce ‘’good news ko? pls tell me I’m about to become an aunt(dan Allah yi maza ki sanar mini cewa na kusan zama anty).’’ Ta k’arashe maganar tata da y’ar guntuwar dariya kwance a kan fuskarta. Murmushi Yashjub ma ya yi, yana jira kawai ya ji ance masa Mannubiya na d’auke da ciki ne, amma maimakon hakan sai kunnuwansa suka jiyo masa muryar Yasmeen d’in tana cewa “A’a gaskiya, ba ciki bane ba, dan in da ace shine to da zan ji yanayin pulse d’inta ma ya d’an chanja, sannan ragowar gwaje-gwajen da na yi mata suma duk ba su yi detecting pregnancy ba, inaga gajiya ne da fever… Amma yanzu abu na farko da ya kamata.. bari in fara yi mata allurar tsaida aman nan, saboda da na duba idonta gaskiya she’s very weak sannan bp da ruwan jikinta ma duk suna nuna za ta iya faɗuwa daga yanzu zuwa ko wanne lokaci….!” Gaba d’ayansu jikinsu sanyi ya yi musamman ma Yashjub wanda ya gama kwallafa rai ya gama yarda akan kawai cikin ne, ganin yadda Mannubiyan ta yi ne ya sa cikin son bata kwarin guiwa ya samu dakyar ya aro jarumta yace “ok, dama nima na yi tunanin gajiyar ce, a ina za’a siyo allurar? A samu a yi mata da wuri, a samu ta d’an ci wani abun ta kwanta ko?” Cikin tarar numfashinsa Yahanasu tace‘’Ina ga gara dai a jira Doctor d’in ya zo shima ya dubata tunda kaga shi Babba ne! sai a san da me da me ya kamata a bata.” Da sauri Yasira tace ‘’ba ki ji abunda itama Yasmeen d’in tace ba? Iyaka allurar tsaida amai za ta yi mata saboda itace emergency ana buk’atar a tsayar da gaggawa.’’ Cikin katseta Yahanasu tace’’Yasira allurar tsaida amai fa tanada k’arfi sosai! ki bari a yi kwak’kwaran bincike kafin a fara d’irka mata abubuwa’’ Murmushi Yasmeen ta yi sannan tace “Na yi duk gwaje-gwaje fa! In da ace akwai ciki ko na sati d’aya ne to da zan gani zan kuma fahimta, kar ki manta Gynea na yi specializing a. Also allurar da zan yi mata yanzu ba ta da wani k’arfi iyaka tsayar da aman za ta yi.’’ Zuwa yanzu ran Yahanasu ya b’aci, kuma ta sake tabbatarwa akwai abunda suka shirya dan haka tace ‘’Ai nima ba cewa na yi ciki ba, cewa na yi ki tsaya dai a yi kwakkwaran bincike, dan wannan gwajin da kika yi bai kai ace ya yi detecting komai b..’’ A hankali cikin katseta Yashjub yace ‘’Yaha Mommy ce ta aiko su kar k….’’ Juyawa kawai ya ga Yahanasun ta yi ta fice daga d’akin da alamun ranta ya b’aci. Shiruu kawai Yashjub ya yi, sam bai ji dad’in abunda ya yi mata ba, amma kuma ba ya so Mommy ta yi fushi.. Shiyasa ya bari akan idan su Yasmeen d’in sun gama zai je ya bata hak’uri, gara ace ita ta yi fushi ta bar case d’in akan su Yasmeen su je su gayawa Mommy ta ga kamar ya sace mata guiwa ne daganan ta yi fushi. Tunda sun ce ita ta turo su, kuma ta na chan hankalinta a tashe, to ya san idan ya hana su bazata ji dad’i ba… Gara Yahanasu ya san ita za ta fahimcesa idan ya je ya bata hak’uri zuwa anjima… Iyakar abunda ya sani ya ke kuma da yaƙini akai shine ‘su Yasmeen ba za su tab’a yi masa k’arya ba, kuma ba za su cutar da shi ko Mannubiya ba…’ dan ko kwanaki da aka yi ta case yanzu ya fahimci saboda Kausar suka yi ta abubuwa amma yanzu gashi da ya dage da addu’a ai sun shiryu sun dawo saiti dan yadda suke yiwa Manubiya tun zuwansu ɗinnan har kawo yanzu ya ji dad’i kwarai ya fahimci suna sonta yanzu….shiyasa har ga Allah tunda suka ce ‘babu ciki’ shi kuma ya yarda, kuma ba ya so ma wani likitan ya zo ya kuma duba ta ya ce ‘babu cikin’ saboda shi kad’ai ya san kalar disappointment d’in da ya ji a lokacin da Yasmeen tace ‘babu cikin’…. ya san kuma a b’angaren Manubiya itama hakan ne….. Da waya Yasmeen ta kira Yusra tace ‘’dan Allah ta duba cikin bed side d’inta na left, akwai wata green Leda ta d’auko ta kawo mata… Allurar tsayar da amai ne a ciki da su paracetamol”. …Already dama sun riga sun gama had’a plan d’insu, shiyasa suna gama wayar su Baba Larai suka yi sauri suka bawa Yusran ledar allurorin da su Yasira suka je suka siyo, ta karb’a ta sauk’o ta nufi d’akin Yahanasu da shi…. Ita dai Mannubiya ta yi shiruuu tana ta istighfari a cikin ranta dan lokacin da Yasmeen tace ‘bata da ciki!’ kad’an ya rage ba ta yi sab’o ba….haka shima Yashjub ya yi shiruuu ransa a mugun dagule….yayinda Yasmeen take jin inama akwai wani waje da za ta gudu ta b’uya dan wallahi har ga Allah ba ta son yin allurar! Ba ta son ta kashewa Yashjub Baby!.. Ta kasa yarda da cewa ‘wai yau itace take shirin yin kisan kai, kisan kan ma kuma Babyn yayanta.!’. Suna a haka Yusra ta yi sallama ta shigo, ta mik’awa Yasmeen laidar allurorin. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 28* Yahanasu tana fita, ta nufi sama side d’in Daddy…dan wallahi sai dai fa a yi ta! A cikin gidan nan, amma ba za ta bari Yasmeen ta d’irkawa Mannubiya allura ba tare da an tsaya Likitan kwarai ya zo ya dubata ba!… Ya za’ayi mace tana irin wannan aman ga jiri ga fever sannan kuma Amarya amma tace wani ‘ba ta da ciki!’ Ta san ba ta yi aure ba, kuma bata da sani akan wannan fannin amma tanada shekaru da hankalin da zata iya banbance Mace mai ciki da mara ciki. In banda tsabar rainin wayo a ta ina aka tab’a tabbatar da ciki da rashin sa ba tare da an yi test na jini ko na fitsari ba!… Babu b’oye-b’oye tana zuwa ta cewa Daddy “ga Yasmeen chan za ta yi wa Mannubiya allurar tsaida amai ba tare da ta duba ta ko ta bari Likitan da aka kira ya zo ya dubata ba.!! Kuma allurar tana da k’arfi sosai!ba a cika son yin ta kai tsaye ba”. Shiruu Daddy ya yi, kafin ya mik’e ya ce “mu je wajen nasu.” Kusan a tare Daddy suka k’arasa bakin k’ofar shi da Mommy wadda duk yadda ta so yin fushi ta bar Yasira ta yi dealing da Yasmeen sam ta kasa hak’ura sai da ta sak’k’o a yi komai a gaban idanunta. Tun ba ma da Yasmeen d’in ta kira Yusra tana cewa ta kawo mata ledar ba dan a lokacin sai da Mommyn tasa Yusra ta tambayeta tace “akwai?” Ita kuma tace mata ‘yeah’kawai ba tare da ta bari su Yashjub d’in sun gane ba. Shiyasa sam ta gagara sukuni ta sake burkicewa ta sauk’o ta nufi d’akin Yahansun a gigice, a hakan ma wai Baaba Larai ta ce mata ta nutsu ta ɗan saisaita kanta… Su Daddy suna shiga itama ta shige dai-dai Yasmeen tana shirin zurmuk’awa Manubiya allura a cinyar Hannu. D’an dakatawa ta yi, ta tsaya kawai tana kallon su Suna had’a ido da Daddy yace ‘’Yasmeen an yi duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata ne??? Ku je asibiti a yi test har na jini mana’’ Wani kalar kallo Yassira ta shiga jifan Yahanasu da shi dan ta san ita ta je ta kirawo Daddy. Mommy kuwa ta fi jin haushin Yasmeen! Ji takeyi kamar ta je ta rufe ta da mahaukacin duka! dan in da ba ta tsaya delay ba da tuni tun ɗazu komai ya kammala. Sannan yanzun da ta ga sun shigo tunda har ta riga ta kai allurar kan cinyar Hannun Manubiyan meye nata na wani tsayawa ta d’ago maimakon kawai ta soka ta juye mata ruwan allurar..dama chan ba ta son yi ai shiyasa ta lalata musu komai!… Har wani duhu-duhu take gani tsabar tashin hankali, ganin bakin Yasira take yi yana motsi alamar tana yi wa Daddy magana amman ba ta san ma mai take fad’a ba dan ba ta jin komai tsabar masifar da ta shiga. Tana k’ok’arin ta bud’e Baki ta san dabarar da za ta yi su samu Daddy ya bari su yi allurar cikin sauk’i ta ji muryar Yash yana cewa ‘’Ok,d’an bani 2 minutes,’’ sai da ta kalle sa tukunna ta fahimci waya yake yi…. sai da ya ajjiye wayar tukunna ya kalli Daddy yace‘’Am Daddy family Dr ya zo, Ince ya bari shikenan tunda kace asibiti za’aje ko?’’ ‘’No, bar shi ya shigo d’in kawai, tunda ya riga ya zo. Ya’isha je ki shigo da shi. Idan ya tafi sai a wuce asibitin, ba dad’i ka kirawo babban mutum ya baro aiki ya zo kuma a ce ya koma.’’ Wata kalar zufar da ta ketowa Mommy sai da Yahanasu ta ganta b’aro-b’aro a kan goshinta tsabar yawan ta. Cikin in ina da rashin sanin tudun dafawa Mommyn tace ‘’Daddy nake ganin gara a ce ya tafi, Namiji ne, bai kamata ya tab’a Matar aureba….” “Ya’isha je ki shigo da shi mana!’’ Daddy ya fad’a da d’an k’arfi kamar ma bai san Mommyn tana magana ba, dan ya fara k’ulewa da ita! Ya ga alama tana neman zarce gona da iri tun lokacin da ya goya mata baya a kan case d’in Yashjub da su Yasira ya bata goyon baya ita da su Yasira, ya ga alamar kamar so take ta dinga juyashi ya dinga biyeta akan komai….bayan shi ba wai bayanta ya bi ba ko a wanchan lokacin ma, kawai yana da nasa dalilin shiyasa…. Ganin har ya na shirin fita amma su basu da niyyar fita ne ya sa cikin kakkausar murya ya kalle su yace “A bar Yahanasu, Manubiya, Yashjub da Yasmeen a d’akin kowa ya fito….jikin Mommy har karkarwa yake yi zuwa yanzu.. Ta riga ta san one more move daga gare ta to tsaf Daddy zai b’aro jirginta shiyasa kawai ta hak’ura ta yi kalmar shahada ta fice ta wuce sama d’akinta direct. Ita dai Mannubiya ba da ban Daddy ne da kansa yace ‘a duba ta’ ba, to da babu abunda zai sa ta kuma tsayawa a duba ta, dan ba ta son ta sake ganin wani disappointment d’in a idananun Yashjub… Su Daddy suna tsaye a parlourn Ya’isha ta shigo da Doctor, suna gama gaisawa da Daddy ta wuce da Doctor d’in ta kai sa har d’akin ta fito, itama ta nemi guri ta zauna hankalinta chaaa a tashe. A Chan d’akin kuwa Dr yana shiga suka hau gaisawa da Yashjub, sai da ya kuma yi masa Allah ya sanya alkhairi tukunna cikin zolaya yace ‘’Ai ba wani abun tada hankali bane, amai is a normal thing a pregnancy, but bara dai in duba .” Shiruu duk suka yi kafin ya fara shirin dubata…sai da ya kuma tambayar abubuwan da suke damunta da date na last period d’inta ya ji tukunna ya matsa kusa da ita ya hau aikinsa… Kamar yadda Yasmeen ta ga alamun cikin a tattare da ita hakanan shima amma bai fad’a musu ba Instead sai ya zaro pts a cikin box d’insa ya basu yace “gashi ta je ta gwada” Cikin son fahimtar da shi Yashjub yace “Yasmeen fa ta duba ta yanzu, ba ciki ba ne” Da d’an mamaki Dr d’in ya juya ya kalli Yasmeen kafin yace “da me kika duba ta??” Dibi-dibi ta hau yi kafin tace ‘’ban ji a pulse d’inta ba, sannan na ga bp d’inta bai yi kamar na masu ciki ba” Ta fad’i hakan tana addu’ar Allah ya sa kar ya haddasa mata case. Sai da ya k’ura mata ido sosai kafin cikin d’an b’acin rai yace ‘’Doctor Yasmeen kin san abunda kike yi kuwa?? A bp da pulse dama ake ganin ciki??? What else ki ka yi bayan BP d’in da kika gwada??”. Cikin nemawa kanta mafita tace ‘’Duk na gigice ne saboda na ga tanata amai, I wasn’t myself shiyasa..gaba d’aya duk ta bani tausayi…” Cikin fushi yace ‘’Really??! Yanzu idan aka kawo miki family member d’inki in a critical condition (mummunan hali) Ashe ba za ki iya yin abunda ya kamata ba? Are u really this weak(har haka ki ke da rauni?)!!!” Ahankali Manubiya ta d’an dafe kanta sakamokon sarawar da yake yi mata tace “wash!!!” Sai da ya gama watsawa Yasmeen kallo tukunna ya juya ga su Yashjub ya shiga yi musu bayanin yadda za su yi amfani da pts d’in…. Suna wucewa cikin toilet d’in ya juya ga Yasmeen ya shiga yi mata fad’a had’e da yi mata nuni da abubuwan da ya kamata ta fara yi nan gaba idan an kawo mata patient a irin wannan halin.. Sannan yace “ta cire fargaba ta daina saurin giigicewe dan za ta jawa kanta problem ne kawai, saboda a gaskiya ko shi yau kam ta bashi kunya da mamaki maƙura!!!!” Su Yashjub suna shiga toilet d’in Manubiya ta kalle sa tace ‘’Ko dai za mu ce masa mun yi kawai? Ba na son gwadawa ni kam har ga Allah.’’ Ta fad’i hakan tana hard’e hannuwanta a k’irji. A hankali Yashjub wanda ya samu hope da kwarin guiwa daga jin yadda Doctor d’in yace “Yasmeen ba ta gwada yadda ya kamata ba”ya matso kusa da ita yace “Ki taimaka ki gwada! pls…for me?’’ Shiruu ta yi ta d’an sunkuyar da kanta k’asa tace “to ka fita” Wata dariya yayi yace “Yarinya ba ki da wayo ashe….” …Daki daki yadda aka nuna musu haka suka yi. Dayake doctor d’in ya ce “idan sun gwada su ajjiye for five minutes saboda result d’in ya fito sosai” Ya sa Yashjub ya karb’a ya ce bari ya kai kan window su jira time….. Daga ita har shi gabansu fad’uwa kawai yake yi.. Haka nan ya nufi window da tsinken da niyyar ajjiyewa idanunsa a kai! Kawai ya ga layi na biyu ya fara kamawa Wani irin mahaukacin bugawa k’irjinsa yayi!!! Da wani irin sauri ya juyo ya koma gareta ya tsaya a gabanta ya ma kasa magana kawai ya kafe abun da idanu yana ganin yadda layi na biyun yake kuma fitowa yana turuwa yana dad’a baiyyana. Ganin yadda ya kad’u sannan ya mayar da ilahirin hankalinsa ga tsinken ne ya sa Manubiya matsowa tace ‘’mai kake kallo?’’k’irjinta yana d’an bugawa. Ahankali ya d’ago lumsassun idanuwansa waenda suka cika taf da kwallah ya kafe ta da su kafin ya juyar da fuskar tsinken gareta wanda a yanzu jajayen layuka biyu suka fito rad’au! Hannun ya na rawa ya saita mata shi a dai dai saitin fuskarta a lokaci guda kuma hawayen da suka tarar masa a idanu suka samu damar b’alle masa,a take yayi mata wata mahaukaciyar runguma ya fashe da wani irin kuka….. Ita kanta Manubiya hawaye ne suka b’alle mata. A take wani sanyin farin ciki da annashuwa mara misaltuwa ya mamaye masoyan…lamoo ta yi a jikinsa tana hawaye tana jin yadda yake kuka bilhakki da gaskiya jikinsa har karkarwa yake yi sannan zuciyarsa tana wani irin bugu.. Sun jima a haka kafin Manubiya ta d’an fara k’ok’arin zamewa a hankali tace ‘’Godiya za mu yi wa Ubangiji….’’ Ahankali ya sake matseta a jikinsa yace “Tun d’azu nake godiya,Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah ya rabbi…bayan fatar baki da zuciya ina so in yi godiya ga Ubangijina…..’’ Murmushi ta yi a hankali tace ‘ka yi ta sadaka’’ Sai da ya sauk’e wata k’ak’k’arfar ajiyar zuciya ya tsaida kuka da hawayen nasa da kyar tukunna ya cika ta ya d’ago fuskarta ya yi cupping a cikin tafukan hannuwansa sannan yace ‘’Thankyou Manu, na samu farin ciki sannan na zama cikakken Mutum domin ke, sannan gashi yanzu za ki bani kyautar da na dad’e Ina kwad’ayi, na gode Baby, I love you more than life itself(ina sonki fiye da rayuwa)….” Ahankali ya sake sakata a jikinsa ya rungume. Sun jima a haka yana ji kamar kar ya cikata su tsaya a haka har abada, kafin da kyar suka cika juna ya wanke fuskarsa suka fita. Fuskar Yash kawai Yahanasu ta kalla ta fahimci kuka ya yi kuma tana da tabbacin kukan farin ciki ne, dan haka ta k’arasa garesu da sauri ta had’asu ta rungume cikin tsananin murna tace ‘’congratulations’’ A hankali yayi murmushi ya ce ‘’Thankyou Yaha,‘’ wanda hakan ya sake tabbatar mata ai kuwa Baki har kunne haka ta hau murmushi mai had’e da dariya tana jin tsananin farin ciki. Ita ta k’arba abun gwajin ta kaiwa Dr. Cike da murna ya matsa kusa da su ya yi congratulating d’insu sannan ya d’aura da cewa “a halin yanzu ba zai ce ga exact satuka na cikin ba amma daga yanzu zuwa ko wanne lokaci suna iya zuwa clinic d’insa a yi gwaje gwaje a tabbatar da lafiyar Baby.” A take Yashjub ya ce “su tafi yanzu tare da shi kawai” Murmushi Dr d’in ya yi yana yaba tsananin kulawar Yashjub ga Babyn da matarsa..sai a lokacin tukunna Yasmeen ta matso tana murmushi ta yi congratulating d’insu Dariya Yashjub ya yi yace “young Dr! sai na bawa Baby labarin yadda kika kusa d’ura masa allura ai, saboda rashin kwarewa…” Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa tana murmushi a ranta tana jin kamar ta fashe da kuka tsabar da na sani da kunya da takaicin Mommy…a d’ayan b’angare na zuciyarta kuma tana jin wata nutsuwa dan tabbas ta ji dad’in zuwan Doctor wanda ba dan shi ɗin ba to da tuni ta aikata abunda ita kanta ba za ta tab’a yafewa kanta ba…. Waje suka nufa gaba d’ayansu banda Mannubiya… Ba iyaka Manubiya wadda ke daga d’aki tana jiyo su ba hatta Yahanasu wadda dama ba ta so ma maganar ta fito ba, sai da ta ji kunyar yadda Yashjub ya zage yana mai sanarwa y’an parlourn ai Manubiya ciki gareta!. Har gaban Daddy ya je ya tsaya ya gaya masa cike da tsananin murna da farin ciki.. Sai da ya gama fad’a ya ga kowa ya yi shiruu yana kallonsa a take kuma sai wata kalar kunya ta lullub’esa. Murmushi Daddy ya yi yana jin wani farin cikin da ya dad’e bai ji ba kafin ya dafa kafad’ar Yashjub d’in yace ‘’Allah ya inganta Allah ya raya ya kawo mana sanyin idaniyar mu duniya lafiya. Tun da nake da kai zan iya cewa ban tab’a ganin farin ciki irin wannan akan fuskarka ba.” Sai da ya d’an k’uraa masa ido kafin yace “har kukan murna ka yi ne??” Ya yi masa tambayar da alamun sigar zolaya wanda hakan ya sa Yash d’in sake sunkuyar da kansa k’asa sai kuma ya juya da sauri yace ‘’Bari mu je asibiti’’ Ya fad’i hakan yana mai ficewa waje. Sai da Yahanasu ta koma d’aki tukunna suka kimtsa suka fito. Manubiya ta ji dad’in rashin ganin kowa a parlourn dan dama ba ta san ta Ina za ta fara had’a ido da su ba….. Had’ad’d’en checkup ya sa aka yi mata. Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya sa akayi masa scanning da taimakon bayanin likitan ya ga location d’in jininsa d’an sati biyu tukunna.. Dr kansa ya sha kyauta…sai bayan sallar magrib bayan an gama yi mata allurai da k’arin ruwa leda d’aya suka karb’i magunguna tukunna suka nufi gida cike da murna da farin ciki… Shi yake driving sai Manubiya a gefensa da Yahanasu a baya. Sun zage da shi da Yahanasu suna ta lissafin kayayyakin Baby da abubuwan da ya kamata a fara siya… Murmushi kawai Manubiya ta yi tana sauraron su tana jin wani sanyi a ranta tana kuma sake godewa Allah wanda ya bata Yashjub a matsayin Miji. Sam murna da zumud’in da ya ke yi a kan cikin ya gagara b’oyuwa, dan ko baka tab’a ganin sa ba tashi d’aya za ka fahimci yana cikin tsananin farin ciki a yau. Wayarta ce ta d’auki k’ara, wanda hakan ne ya katse musu hirar tasu shi da Yahanasu. Kamar ba za ta d’auka ba sai kuma ta sa hannu ta d’auka. Tana nan kishingid’e a yadda take haka ta saka wayar a kunnenta ba tare da ta bud’e idanunta ba tace ‘’Assalam alaikom’’ Ahankali Abbakar ya lumshe ido daga d’ayan b’angaren yace ‘’Wslm Manu,ykk kwana dayawa’’ Shiruuu ta yi ta k’i yin magana ta k’i cewa komai Cikin yanayin sanyin muryarsa yace ‘’Abbakar ne’’ Yanzun ma shiruu ta yi dan dama tun farko ita ta fahimci shi d’in ne.. Wato sai yanzu zai waiwayeta sai yanzu zai nemeta bayan haka kurum ya d’auke kafa ya kulle duk wata ƙofa da za ta haɗa su, sai yanzu zai wani kira ta!. Muryarsa take ji yana magana amma ba ta fahimtar sa sakamokon aman da ya taho mata tashi d’aya…dan haka kawai ta kashe wayar ta ajjiye a gefe ta d’ago ta kalli Yashjub. Wanda yake mamakin waye ne ya kira ta haka ta gagara cewa komai Kuma kamar muryar Namiji ya ji yana magana. Da sauri ta toshe Bakinta ta na yi masa nuni da ‘za ta yi amai’ dan haka ya ja ya faka a gefen titin da sauri ya bud’e motar ai kuwa ta shiga shek’awa… Aman da ta yi sai da ya ba su tsoro tsabar yawan sa. Ba yadda ba ta yi da shi kar ya koma ba amma haka ya juya akalar motar aka maida ita asibitin. Suna zuwa kuwa Doctor ya yi admitting d’inta,sai a sannan Yahanasu ta kira su inna ta sanar da su haka ta kira Ummi itama dan ta ji ta shiru bata neme su ko ta ce za ta zo ba kuma d’azu bata ganta a k’asa a parlourn ba dama. Ba ta yi mamakin jin Ummin bama ta san ciki ne da Manubiyan ba Tace mata “d’azu ta je side d’in Daddy ta tarar ya fita da ta sauk’o ta tambayi Yadira kuma tace mata wai sun je gidan su Manubiya ne za ta gaida iyayenta” “Hmm”kawai Yahanasu tace Daganan ta mik’awa Manubiya wayar suka gaisa da Ummi har ma da Yashjub ta yi musu murna daga nan tace musu gata nan zuwa inshaaAllah.A daren kuwa ta zo. Su inna ne dai Yashjub ya kira ya lallab’a su yace “jikin nata da sauki su bari gobe su zo yanzu dare ya yi”. Aikuwa washegari da sassafe d’akin ya cika taff su Inna da Ummi duk suka baiyyana, Manubiya har da kukan shagwab’a da ta ga su Innaa. Gata kam ranar ta ganshi har da d’an hawayen farin cikin ta. Abinci kala kala daga wajen Ummi Inna har da Mama wadda shigar ta gidan kenan ta tarar ana shiri dan haka ta ce “su jira” Haka taje ta had’o mata d’an Malale mai d’an karen dad’i tace a kawo mata bayan ta kira ta ji ya jikin nata…. Yassir gaba d’aya ya fice daga haiyyacinsa!! A tsarin sa sai bayan kamar kwana d’aya zai aiwatar da shirin sa amma kuma farin cikin da ya ga Daddy yanata yi ne ya sake hassala shi dan d’azu ma da Daddyn zai fita ji yayi yana waya a kan Yashjub d’in, wanda ya san kuma gift ko wani abun zai k’ara masa in ba da kyar ba. Ga Kausar kuma da ya lura da yadda ta burkice itama tashi d’aya…abun ba k’aramin sake hassala shi ya yi ba. Shiyasa kawai ya shiga d’aki ya rufe ya shiga aiwatar da shirin nasa. Suna zaune ana ta hira da Ummi da Innaa kawai sukaga an turo k’ofa an shigo. Ita kanta Manubiya ba ta yi tsammanin ganin Mommy ba duba da yadda kaff cikin su babu wanda ya d’au waya ya kirata har ta kwana ta ke shirin wuni…. Cike da sallama faram faram Mommy ta shigo suka hau gaisawa Yasira da Ya’isha suna a bayanta. Yahanasu ce ta bawa Mommy kujera ta zauna bayan sun gaisa. Cike da girmamawa su Jidda da Muhsin ma suka gaida ita sab’anin su Ya’isha da suka koma gefe suka k’ame kamar ba su ga su Innaa ba. Suna zaune d’akin ya yi jugum tun shigowar su Mommy Yashjub suka shigo shi da Najeeb wanda ya d’an rame kana ganin sa ka san yana cikin damuwa… Karairaiyar da Ya’isha ta dinga yi da shishshige masa har zuwa lokacin da ya fita saida ya bawa Jidda kunya,shi kuma yanata basar da ita kamar bai ma san ta na yi ba. Hakanan ya yi wa Manubiya ya jiki bayan ya ajjiye uban tulin laidojin hannusa ya juya ya yiwa su Innaa da Mommy Allah ya k’ara sauk’i ya fita. Murmushi kawai Jidda ta yi a ranta tace”kina nan kina iyayi” “Yana chan yana ziryar zuwa gadon k’aya ba a kula sa.” A d’akin su Inna suka zo suka tarar da Ummi shiyasa Ummin ta mik’e ta fara haramar tafiya dan ta na so ta d’an basu guri kuma ta lura kamar akwai maganar da Innar ta ke so su yi saboda taga matar sai yawan yin shiru ta ke yi kamar tana ta tunani. Ummi tana mik’ewa Yahanasu ma ta mik’e tace “Bara itama ta je ta d’an shirya tanada client da za su had’u in the next 2 hours” Ta riga ta san Yashjub yananan ba inda zai je 24/7 shiyasa hankalinta kwance sukayi musu sallama ta bar su Mommy a d’akin suka tafi tare da Ummi wadda take ta addu’ar Allah ya sa su Mommy ma su yi kan gado su bar Manubiya da y’an uwanta su d’an keb’e, dan ta san rabon da su yi eyes to eyes tun kafin ta tafi honeymoon.. Ita kanta Manubiya so take ta keb’e da ahalin nata, dan ta lura ba iyaka Inna ba hatta Jidda kamar tanada damuwa bayan ta Al’ameen wadda ta riga ta san ta da ita.. Sannan kwana biyu ba ta ji Ya Musbah ba, kuma ta kirasa a waya ko jiya ma bai d’auka ba! “anya kuwa lafiya??” Ta yi wa kanta tambayar a cikin ranta. Illai kuwa! wannan itace damuwar su Innar, saboda tun bayan sati 6 da suka wuce da Baraka ta tare Abu bai yi dad’i ba…zuwa yanzu Inna ta fahimci ashe ladabin kura Baraka ta yi musu, tunda gashi yanzu ta rabasu da Ya Musbah… Tana tarewa ko sati ba ta yi ba tace “ita ta tsani unguwar” Haka nan jikinsa yana rawa ya d’auki d’an kud’in da ya tara zai biya kud’in registration d’insa dan lokaci ya kusa cika Suka tashi a unguwar suka kama wani gidan a Na’ibawa chan nesa da su Inna tsabar rashin adalci irin na Baraka. Kuma ta hanasa fad’a musu sai a ranar da za a tashi d’in. Da dafarko da suka tashi yana zuwa duk bayan kwana biyu a d’an mashin d’insa,sai ya dawo zuwa bayan sati d’aya tou tun daga nan basu sake saka shi a idanunsu ba, gashi kayan abincin su ya k’are. Jiya babu kalar kiran da Jidda ba ta yi masa a waya ba amma ya k’i d’auka…. Tabbas sai yanzu Innaa ta yi da na sanin barin shi ya dawo da Baraka Dama baba yace mata “Indai Baraka ce tou kuwa za ta sha mamaki…” Gashi kuwa k’iri k’iri ta rabata da d’anta kuma tunda ta dawo abu guda da inna ta fara fahimta shine Yaa Musbah mugun mugun tsoron ta yakeji. Gashi ba a Isa a ce abunda ta yi bai kamata ba tashi d’aya zai hau kumbure kumbure… Tun a kan issue na tashin su da Innaa ta so ta hana tashi d’aya ya nuna hakan fa ba zai yiu ba!. Muhsin kuwa da ya yi alk’awarin d’auka ko kalar k’ofar gidansa na Na’ibawa har yau bai sani ba. Ya Nafi’u kuwa ko waya basa yi,tun lokacin da ya dawo da Baraka dama ya fice a harkar sa, ko da ya zo tashin ma bai gaya masa ba dan ya san zai hana shi shima kuma ya Nafi’un har yau bai ce masa ‘Musbahu Ashe ka tashi ba,’ K’ark’ari ya kan je ya duba su Inna shi da Aisha da Khairat duk bayan kwana biyu, amma shi da Ya Musbah kam ko a waya sun daina gaisawa. Baba ne dama ya kamata ya tsawatar ya dawo da Abotar tasu to shi kuma Baba tun lokacin da Inna ta amince a dawo da Baraka tashi d’aya ba tare da ta shawarci kowa ba Ya ce “case in dai na Musbahu da Baraka ne to ba zai bada shawarar komai ko ya ce zai saka Baki a kai ba…” Gashi issue na Baba da su Baba Habu abun ba dad’i nan ma…Kaka mallan ma ya fara gulmace gulmace wai “Baba ya bi kud’i ya aurawa mai kud’i y’arsa amma gashi ya barsu a talauci har yau bai tab’a ganin an kawo ko kwayar shinkafa k’ofar gidan ba.!” Inna tana wannan tunanin Yashjub ya dawo d’akin yanata faman sussunkuyar da kai, so yake ya tambayi Manubiya mai take so ta ci dan tun yoghurt d’in safe sai d’an malelen Mama da ta ci daga su bata sake cin komai ba gashi Doctor yace “ana so ta dinga cin abinci sosai saboda lafiyarta da lafiyar Babyn”…to kuma shi har ga Allah kunyar Inna yakeji dan d’azu ma sai da Ummi ta sa ya ji kunya Haka nan ta tisa shi a gaba tana tsokanar kalar zumud’in da yake ta yi a gaban su Innar… Yana wannan tunanin ya ji wayarsa ta d’au k’ara, kamar ba zai d’auka ba dan da ya zaro bak’uwar number ya gani, sai kuma ya d’auka ya kara a kunnensa kafin yace ‘’Assalam alaikom,’’ A gigice ya ji wata murya kamar ta security d’insa yana cewa”Sir wuta!wuta!! ya kama a estate na kano ka zo da wuri…….’’ Mutumin yana gama fad’in haka ya kashe wayar…. in banda hayaniya da k’arar y’an kwana kwana ba abunda Yash ya ji yana tashi daga background d’in. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ya shiga ambata a fili. Da sauri Yasira ta matsa tace ‘’mai ya faru?’’ Cikin karkarwar murya da kyar ya kalleta yace “Estate d’ina ne, ya kama da wuta’’ Salati gaba d’ayan su suka saka suka mik’e tsaye. Cikin tsananin gigita Yasira tace “subahanallah!! mu je mu je da sauri…” Ta fad’i haka tana yin gaba. Da sauri ya ruk’o Hannunta ya ce ‘’a’a, it’s not safe, kar ki damu zan je ni d’aya, zan kira Yassir a hanya sai mu had’u a chan. “ A hankali ta d’an dawo ta tsaya kafin tace “Allah zai mayar da alkhairi, inshaaAllah’’ Jinjina kai yayi yace”inshaaAllah”sannan yace”ku yi addu’a Allah ya sa Mutane ba su mutu ba!” Jinjina kai ta yi itama, daga haka ya zare hannunsa a nata ya k’arasa inda Manubiya take zaune a kan gadon ya ce “bara in je ko?” sai kuma ya d’an sunkuya yace “Dan Allah kar ki d’aga hankalinki, ba zan jima ba zan dawo, okay?” Ba ta san lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba, ita ya kamata ta rarrashe sa amman kalli shi yake rarrashin ta. Da sauri ta sunkuyar da kanta tana jinjina kai… Murmushi ya yi, daga haka ya yi sallama da su Innaa tukunna ya juya ya fita gaba d’aya suna jajanta masa tare da adduar alkhairi. Yana fita ta sake sakin kukanta tana jin wani iri a cikin ranta A hankali Innaa ta koma kusa da ita ta zauna ta shiga rarrashin ta tana bata baki,Mommy kuma ta shiga kiran Daddy domin ta sanar da shi halin da ake ciki. Cikin rashin jin dad’i Ya’isha tace “Ai dama matsalar had’a jini da mai farar k’afa kenan! Dama ace a iyaka aure aka tsaya to da na san abun zai zo da sauk’i”. Shiruu duk suka yi d’akin ya d’auki shiruu Kafin Ya’isha ta sake cewa “Allah dai ya rufa asiri ya kuma tsayar a iya nan’’ Zuwa yanzu Manubiya ta ji ba za ta iya jurar cin fuska a gaban ahalin ta ba! Ashe dama jiya da suka dawo saboda a gaban Yashjub ne shiysa suka yi mata kissa kenan suke wani nan nan da ita… Shiyasa kawai cikin wani irin fushin da ba ta san tana da shi ba ta mik’e ta cewa Inna “ta zo su tafi” Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Kamar ya ku tafi? Me kike nufi? Idan tafiya kike son yi ai mu za mu tafi da ke ba Innaa kad’ai ba ko?” “A’a inaga tana nufin za ta koma gidan ubanta ne! Ai ta shafa farar k’afar tata yadda ya kamata shiyasa ta ga ya ci ace ta tafi…” Cewar Ya’isha. Ba k’aramin mamaki Innaa ta yi ba, ganin yadda ko gezau Mommy bata yi ba balle asa ran za ta cewa Ya’isha ta yi shiru wadda ta cigaba da fad’o zafafan maganganun kamar wata tab’ab’b’iya. Cikin nutsuwa Innaa ta mayarda Manubiya ta zaunar da ita tace”kar in ji zance mara dad’i, ki zauna ki yi wa mijinki addu’a, ki jira dawowarsa” tukunna ta kalli su Jidda wadda har ta fara kwallah tace mata ‘’ku tashi mu tafi’’ Sai da suka mik’e tukunna Innaa ta juya ta k’arasa inda Mommy take tace mata ‘’Hajiya mun tafi, Allah ya k’ara sauk’i’’ Daga haka ta fice ta na jin yadda kukan Manubiya yake dira a cikin zuciyarta kamar dalma….. Sam ba haka Mommy ta so ba, so ta yi ace Manubiya ko k’anwarta ko Innar tasu wani ya biyewa Ya’isha, daga nan ayi kacha-kacha su yi zuciya su tafi da y’arsu ta yadda za ta raba auren ta kuma ga bayan cikin ta kowacce hanya hankali kwance….. Yanzu haka ji take yi kamar zuciyarta za ta kama da wuta, ita kad’ai ta san halin da take a ciki tsakanin jiya da yau..shiyasa ko Baba larai ba ta gayawa ba ta taho asibitin dama opportunity irin wannan kawai take nema ta samu a yi ta ta k’are dan ta riga ta kai peak.Sai dai Kash!Inna, ta lalata mata komai… Su Inna suna fita, Yasira ta yi tsaki ta juya itama ta fita…. Daddy da Yassir ta fara kira suka yi magana tukunna ta kira wata k’awarta wadda bata dad’e da yin aureba a nan estate d’in Yashjub d’in suke haya, dan haka ta kirata domin ta ji ya abun yake, shin sun samu sun fita lafiya ko?. Ta ji matuk’ar mamakin yadda k’awar tata ta amsa wayar hankali kwance har da y’ar tsokana a ranta tace”to ko dai ta fita ba ta gidan ne” dan haka a hankali a fili tace mata “kina ina?” Sai da gaban Yasira ya yanke ya fad’i da ta ji k’awartata ta ce mata”Ina gida mana, za ki zo ne?” Zaro wayar ta yi ta kalla ta tabbatar da k’awar tata ta kira tukunna ta mayar kunnenta kanta tsaye tace’’ji na yi ance gobara fa ya tashi a estate d’innaku!yanzunnan aka kira Yash aka ce masa ga wuta yanata ci an gagara kashewa” A rikice matar ta rafka salati kafin tace “to inaga gaskiya mak’iya ne, wani ne yake so ya jaa shi ya fito da shi domin a samu ya fita a kama shi!! ko dai wani Abu makamancin haka, dan mu kam nan ko k’aurin wuta babu a nan gaskiya, ki yi maza ki kirasa kice ya juya…..” ai tun kafin ta rufe bakinta Yasira ta yi maza ta kashe wayar a gigice ta shiga kiran Yashjub…ta jera masa miss calls sun fi takwas amma bai d’auka ba, shiyasa hankalinta ya sake tashi dan zuwa yanzu tabbas ta gama gasgata maganar wannan k’awa tata!! tashi d’aya ta fashe da wani Irin kuka a ranta ta gama sakawa ‘shikenan an kashe Yashjub’…….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 29* ..Ko kuma an yi kidnapping d’in sa!. A rikice ta afka d’akin, suna nan a yadda ta bar su, su uku, Manubiya a gefe tana ta faman hawaye. Cikin rikici Yasira ta k’arasa gaban Mommy tukunna tace ‘’Mommy Ina ga magauta ne suka kira Ya Yash! Dan yanzunnan na kira frnd d’ita ta estate d’innasa, tace ‘babu wani gobara,’ shi kuma yanzu haka inata kiran sa a waya ba ya d’auka! Inaga sun sace shi ko sun yi masa wani abun….’’ Ta k’arashe maganar tana mai sake fashewa da wani irin kuka. Manubiya kawai tsintar kanta ta yi a gaban Yasira a rikice tace ‘’Ki sake gwada kira, InshaaAllah babu abunda ya same sa, bara nima in kirasa, idan bai d’auka ba mu yi message, na san in ya gani zai ki kiramu” ta fad’i hakan tana mai juyawa ta nufi wayarta. Sai a sannan tukunna Mommy ta tashi ta tsaya a d’an rikice tace ‘’ikon Allah, to Allah dai ya sa lafiya…babu komai ma ki kautata zato….” Kafin minti sha biyar gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi, dan babu kalar kira da sak’onnin da ba’a yi an tura masa ba amman sam ba ya d’aukar waya kuma bai yi responding messages d’in ba. Banda kuka babu abunda Manubiya take yi, tana kuka tana aikin kiran waya ba’a amsawa abun tausayi… Suna a haka Daddy ma ya kira wayar Yasira yace “da shi da Yassir sunata kiran sa suma amma baya d’agawa but ga su yanzu suke barin gida za su je su duba estate d’in na sa..” Yassira ce ta yanke shawarar ta sake kiran friend d’in tata inyaso ko mai gadin su ne ta sanya ya tayasu ya bincika ko Yashjub d’in ya k’arasa chan…gaba d’aya ta gigice haka ta shiga kiran k’awar tata. Matar tana d’auka tace ‘’ya ake ciki Yasira? kun yi magana da shi?” A tare da matar da Yasira suka fara jiyo hayaniya da ife-ife…ta cikin background d’in Yasira take jiyo k’ara ta ban mamaki kamar ana fasa abubuwa da kuma na bindigu da ihun bayin Allah suna neman ceto…. A hankali jikinta yana wani irin karkarwa ta ji matar tace”Innalillahiwa innalaihirrajiun,Yasira kina jin abunda nake ji?bara in duba…” Sai kuma a rikice taji tace”y’an bindiga ne suka shigo mana sun fi mutum d’ari…..” K’arar harbin da Yasira ta ji ne ya tabbatar mata da k’awartata aka kashe dan a tare ta ji k’arar wani abu ya fashe kamar k’ofar aka fasa da kuma harbin…. K’amewa ta yi ta kasa cewa komai,tana sauraron yadda mutanen suke magana wani a cikinsu yana cewa”a sake duba gidan sosai, idan babu kowa mu yi sauri mu kunnawa wannan ma wuta mu tafi next house bamu da isashshen lokaci…mu yi mu yi mu tafi,yanzu Grenade ya yi min waya yace mu yi retrieving dan sun riga sun kashe gayen, sun k’ona motarsa ma tun a bakin gate….“ K’afafuwan Yasira ne suka shiga kakarwa tashi d’aya ta gagara ci gaba da tsayuwa dan haka ta durk’ushe a wajen ta fashe da wani irin kuka. Daidai nan Manubiya ta matsa kusa da ita kusan a tare ita da Ya’isha suka ce mata “m-m mai ya f fa rru!??’’ Suka yi mata tambayar a tsorace dan yanayin ta ya yi matuk’ar sake firgita su. Da kyar ta iya d’agowa ta kalli Ya’isha ta yi mata bayanin abunda ta ji ya faru sannan ta d’aura da cewa”na ji yana cewa Grenade ya ce sun kashe sa sun k’ona motarsa tun a gate,Ya’isha Ya Yash suke nufi, shi ake so a kashe dama shiyasa aka yi k’arya da gobara aka ja sa wajen saboda su b’adda track d’insu kar a gane manufarsu. Ba y’an fashin gaske bane Ya Yash d’inmu aka shirya kashewa dama Wallahi…” ‘Sululululu’ haka Manubiya ta tafi ta fad’i a wajen sumammiya… Mommy ce ta kira Daddy, wanda ta ji muryarsa a rikice shima, cikin tashin hankali ya ke ce mata“gasu nan sun zo shiga layin motocin sojoji sun taresu, wai y’an fashi sun kaiwa estate d’in hari, an hana su shiga sun ma rufe gate d’in layin gaba d’aya. amma ga su nan dai ana ta k’ok’arin shiga ciki, motocin sojoji biyu sun kutsa kai yanzunnan…” Yadda su Yasira suka ji muryar Daddy yana yi wa Mommy bayani ta wayar yana kuka ne ya sanya suma suka fashe da wani irin kuka. Sun san Daddy ba lalle ya so su je wajen ba shiyasa ba su ce masa za su je d’in ba, maimakon hakan kawai suna gama wayar da shi suma suka fice dan hankalinsu gaba d’aya ya yi wajen….a nan suka fice suka bar Manubiya a yashe a k’asa suka nufi estate d’in suna kuka gaba d’aya su ukun.. ….. A Chan suka tarar da Daddy da Yassir, suma duk hankali a tashe. lokacin har an bud’e gate d’in layin, wajen taff cike da sojoji da y’an kwana kwana dan kusan kaff gidajen sai da suka cinna musu wuta tukunna suka gudu ba a kama ko d’aya ba.! Yadda estate d’in ya k’one ya koma wani abu daban dole ya bawa Mutum al’ajabi, sannan ya sanya ɗan Adam ya sake ka’daita Allah ya kuma tabbatar da cewa abun duniya da duniyar kanta gabaɗaya ba a bakin komai suke ba. Su Yasira suna hango su Daddy suka k’arasa wajen su, suna kuka. shima Daddyn hawaye yake yi, cikin sharar hawayen yace “akwai hope! ga dai motarsa chan a k’one da mutum a ciki, amma gaskiya ba shi bane ba inaga kamar driver d’insa ne, kuma shi har yanzu wayarsa tana shiga, amma wayar mutumin ciki ta k’one da na duba ba ta aiki. Sannan munata dubawa har ciki amma kamar ma shi d’in bai zo nan ba kwata-kwata. Cikin jinjina kai Yasira ma tace “Nima Inada hope Daddy, dan yanzu ma na kirasa wayar tasa tana shiga, Allah dai ya sa ba wani abun ne ya same shi ba. dan gaskiya bai zo nan ba.” Daddy ne ya kira asibiti, dama ga polisawa da sojoji a wajen, dan haka ambulance suna zuwa aka fara fitar da deceased da injured…abun ba dad’in gani, dan mutane sunfi talatin waenda suka rasu injured kuma wajen mutum goma…… Bayan kamar awa d’aya wajen ya cika taff da jama’a, dan har su Baba larai duk sun k’araso suma kowa in ka kalla hankalinsa a tashe. Dukda cewa zuwa wannan lokacin sun tabbatr da cewa Yashjub ba ya wajen, dan kaff jama’ar da ke yashe a harabar wajen da gefe gefen titin a lokacin da abun ya faru an shaida identity d’insu, amman kuma rashin amsa wayar tasa ne ya fi komai d’aga musu hankali a halin da ake ciki. Dan haka Daddy ya kalli Yassir wanda duk hankalinsa ya gama tashi da rashin ganin gawar Yashjub…cikin dafa kafad’arsa yace ‘’ka kwantar da hankalinka Yassir, inshaaAllah babu abunda ya samu d’an uwanka, ka nutsu ka yi addu’a ka ji ko? dan ni kam zuwa yanzu inda hope ‘’ Ahankali Yassir ya had’iye wani k’ululun tashin hankalin da ya toshe masa mak’ogwaro kafin yace ‘’To Daddy’’. Cikin fesar da huci Daddy yace ‘’d’an sake gwada kiran sa mu gani” Still yanzu ma a hankali ya sake cewa “to Daddy” Daganan ya matsa gefe k’irjinsa yana dukan uku-uku dan baya k’aunar ya kira a yi rashin sa’a ya ji muryar Yashjub safe and sound!..Hatta seconds da komai sai da aka k’irga daga inda yake zuwa estate ɗin, sannan ya bada numbobin motocinsa duka incase ma Idan ya chanja mota, kuma sai da suka yi waya da mutanen suka ce masa gashinan ya shiga estate d’in yanzu tukunna suka fara aikin amma bai ga alamun sa a wajen ba!sai driver d’insa wanda yanada tabbacin bai cika yawo da shi ba,mai ya faru???yana ina???? Ya yi wa kansatambayar ba tare da ya san wa zai basa amsar ba… adduarsa d’aya Allah ya sa a wani wajen suka danna gawarsa shiyasa ba a gani da wuri ba!…Allah ya sa a nemota yanzunnan a duk inda take a cikin estate d’in a fito da ita, dan tabbas zuciyarsa za ta iya tarwatsewa idan akace Yashjub ya fita daga cikin wannan abun da ya haɗa masa lafiya ƙalau babu abunda ya same sa…. Da kyar ya samu ya d’an nutsu tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu, hannunsa har karkarwa yake yi haka ya danna kiran Yashjub..bugu biyu a na uku ya d’auka yace ‘’Yassir! kuna Ina??’’ A hankali Yasir ya lumshe idanuwansa wasu zafafan hawayen bak’in ciki da na tashin hankali suka shiga silalo masa… Sai da Yashjub ya sake cewa ‘’Yassir ba ka jina ne?kuna Ina??” tukunna da kyar da mugun kyar ya samu ya iya had’a kalmar ‘’ga mu nan duk, a estate d’inka’’ ‘’Okay gani nan zuwa amma fara bawa Manubiya wayar yanzu, Inata kiran ta ba ta d’auka! Lafiya dai take ko??” Shiruu ya yi ya d’an kalli Daddy wanda ganin kamar waya yake yi ya sa ya tunkaro sa da wani irin sauri, Cikin tsananin rikici Daddyn ya ce “shine??ya amsa?”Sai kuma ya sa hannu ya karb’i wayar. A take ya lumshe idanuwa wasu hawayen farin ciki suka zubo masa sakamakon jin muryar Yashjub lafiya ƙalau yana cewa ‘’Yassir,ka yi magana mana!Ina Manubiya take?ka bata wayar” Dai-dai nan su Mommy ma suka k’araso wajen, suna masu tambayar su “shi ne?ya d’auka?”. Sai da Daddy ya jinjina musu kai yace ‘’eh’’ tukunna ya maida hankalinsa ga Yashjub wanda ya rikice ta waya yana tambayar ‘Ina Manubiya?’ya ce ‘’Yash Manubiya ba tana asibiti ba? ka nutsu mana she’s fine ai ko?….” ‘’Daddy tare na barsu ita da su Mommy na fita, and she was very worried a time d’in, sannan yanzu na ji Yassir yace duk kuna estate meaning har da su Mommy kenan kuma ita ban ji ta ba, sannan Ina ta kiran wayarta bata d’agawa..” Yashjub ya zaiyyane masa hakan a rikice. ‘’Slow down Yashjub” Daddy ya ce kafin ya d’aura da cewa ‘’relax!!ok..”tukunna ya juya ga Mommy yace ‘’Ina Manubiya??” ‘’Tana asibiti” kawai tace da alama ranta a b’ace yake kafin ta d’aura da cewa “Duk ya bi ya d’agawa mutane hankali, kalle mu gabad’ayanmu a rikice, amma shine tsabar rashin sanin ciwon Kai zai ishemu da Manubiya!Manubiya!!, Mannubiyan baby ce?goyota yake so mu yi mu taho da ita crime scene irin haka salon shima idan mun yi hakan yace za ‘a cutar masa da ita??” Numfashi Daddy ya fesar kafin yace”yanzu fa lokacin murna da farin cikin kasancewarsa safe and unharmed ne, godiya ya kamata mu yi wa Allah,ba wai haushi ya kamata ki ji ba‘’sai kuma ya maida hankalinsa ga wayar da yake yi yace ‘’Yashjub Manubiya tana asibiti mu kuma muna estate d’in ka”. Without thinking twice yace ‘’okay bara in je asibitin’’ daga haka ya kashe wayar kitt!!!. Shiruuu Daddy ya yi, ya kusa minti d’aya da wayar a kunnensa…kafin da kyar ya zaro ta ya mik’awa Yassir jikinsa a matuk’ar sanyaye….ya rasa dalilin da ya sanya duk yadda ya so ya kauce ya goce duk dan a zauna lafiya dole shi kuma Yashjub sai ya fito fili ya nuna masa Manubiya ta fi su matsayi a wajensa, itace za ta zo first a sama da kowa da komai na rayuwarsa..he can’t help but to think ‘anya idan ya yi sake ganin Yashjub d’in ma ba zai gagaresa ba kuwa wata rana?!….’ Yahanasu ce ta ce “Daddy mu je asibitin, chan ya nufa ko?” Saida ya juyo ya kalle ta tukunna ya d’aga mata Kai alamar ‘eh’ da ‘to’ daga haka ya wuce cikin tsananin mutuwar jiki. Yana wucewa Ummi ta bi bayansa bayan ta bawa Munirat makullin motarta ta ce ta taho a ciki, dan tanaso ta d’an fahimtar da shi dalilin da ya sa Yashjub d’in ya yi hakan saboda ta fahimci ya ji haushi. Tana wucewa suma suka fara shigewa motocinsu suna bin bayansu…. Wajen ya rage daga Yasira sai Yassir da Mommy da Baba larai, Mommy tsananin mamakin yanayin Yassir da kuma b’acin ran Yashjub ne suka hanata motsi har sai da Baba larai ta tab’o ta tace “mu je ko?” tukunna ta samu ta d’auke kanta daga kan Yassir da kyar, suka nufi motar Yasira. Suna zuwa ta bawa Yassir key amman sai ya zauna a wajen mai zaman banza yace “ta ja su kawai” dan shi kam ba ya jin hannunsa zai iya d’aukar makullin ma ballantaana aje ga jan motar. A rikice Yashjub ya k’arasa cikin asibitin, ko parkin mai kyau da ma’ana bai yi ba hakanan ya fito ya rufe motar ya afka ciki dan tun d’azu dama ya tsinci kanshi da fara jin tsananin fad’uwar gaba, yanzu kuwa da yake ta kiranta bata d’auka kuma ya ji bata tare da su Mommy sai ya kasa hana kansa zarginda tunanin ‘ko wani abun ne ya sameta’ Yana dialing number yana wani irin gudu gudu sauri sauri haka ya afka cikin d’akin. Sai da numfashinsa ya kusan d’aukewa da ya shiga ya ganta yashe a k’asa wanwar kamar matacciya, k’amewa kawai ya yi ya tsaya ya kasa gaba ya kasa baya. Kafin da kyar da taimakon addu’o’in da yake ta jerowa ya samu k’afafuwansa suka basa had’in kai wajen k’arasawa inda take, sai kuma ya durƙusa a rikice…. hannunsa yana wani irin karkarwa haka ya kamo hannunta ya d’aura yatsa a ta wajen pulse d’inta… A take ya saki wata k’akk’arfar ajiyar zuciya, sai kuma ya rarumo gorar ruwa ya b’intike kan ya shiga shafa mata yana d’an tapping fuskarta still hankalinsa a mugun tashe. Wani nannauyan numfashi ta ja ta fesar idanunta a rufe ta shiga magana a rikice a tsorace ‘’Mijina!dan Allah Mommy ku ce ya dawo,mu je mu nemosa,babu abunda zai same shi, Ya Yash d’ina, idan ya bar ni wallahi mutuwa zan yi” Kallon fuskarta kawai yake yi yana jin wani kalar tausayi da tsantsar k’aunarta suna ɗawainiya da shi, a hankali wata kwalla ta ziraro ta biyo ta sauka a kan fuskarsa..cike da taka tsantsan ya d’agota ya saka ta a jikinsa wanda jin k’amshin turarensa da kuma jinta a jikin Mijin nata ya sanya ta dawo haiyyacinta, ta yi sauri ta bud’e idanuwanta domin ta tabbatarwa kanta da shi d’in ne?… A hanakali ya d’ago fuskarta yana kallon cikin idanunta yace ‘’babu inda zan tafi in barki, inshaaAllah muna tare har gaban abada.” A hankali ta lumshe idanunta tana hawaye tana jin wani sanyi yana ratsa ta.. …Da farko gefen kumatunta ya fara murzawa kafin daga baya ya matso da fuskarta sosai garesa cikin shauk’i k’auna da bege ya had’e bakin su waje d’aya….. Kamar ance ‘action’ haka su Kausar suka antayo cikin d’akin gaba d’ayan su. Da wani irin sauri Daddy ya juya, ya fita, har yana d’an tuntub’e. Ya riga ya gan shi kuma ya ga he’s fine, very fine ma kuwa! Dan haka direct kawai sai ya nufi mota ya wuce gida, ya bari kawai akan idan Yash d’in ya koma gida sai ya ji komai daga Bakinsa….meanwhile shi kuma bara ya ji da abunda ya baro ya tafi crime scene ɗin. Daddy yana wucewa Yashjub ya ɗan saki Manubiya ta hanyar yin k’asa da ita ya saka ta a cikin k’irjinsa yana maida numfashi a hankali, ba tare da ya juya ba, yayinda ita kuma kunya ta sanya ta sake ruk’unk’ume sa ta cusa kanta sosai a cikin k’irjinsa. Da sauri Kausar ta juya za ta bar wajen, tashi d’aya suka yi karo da Yassir…cikin son ganin yanayin ta da idanunta ya tare hanyar yace’’Ina za ki je ?’’ Ya yi mata tambayar Fuskarsa babu alamun wasa, dan ransa a mugun mugun b’ace ya ke dama. Ganin ta ƙi magana ya sa ya sake ce mata “look at me” Ba tare da ta kalle san ba tace ‘’matsamin hanya in wuce Yasir, ba ni da lafiya‘’ Ta fad’i hakan tana k’ok’arin zagayesa dan ya tare k’ofar. Wata mahaukaciyar damk’a ya yi wa hannunta wanda har sai da tace”Wayyo!”a hankali, tsabar azaba! Bai damu ba! Hakanan ya dawo da ita gabansa ya tsayar da kyar tukunna yace ‘’I’m not done with you yet,look at me na ce (ban gama da ke ba tukunna!! Ki kalle ni na ce) ko!!?”ya fad’i hakan cikin karsashi kamar wani ubanta, a lokaci guda yana mai sake damk’e hannun nata da take ta k’ok’arin kwacewa. Ganin yana shirin karya mata Hannu ne yasa ta d’ago idanuwanta waenda suka yi jazir suka cika taff da kwallah ta ce ’’Yassir za ka karya mini hannuna fa’’ sai kuma hawaye suka b’alle mata shaar. Da sauri Baba larai wadda ta lura da su ta matso tace’’ikon Allah,Yassir meye hakan kake yi kamar ka samu Hannun k’ato? cika ta mana!”. Ko gezau bai yi ba, ballantana Baba larai ta sa ran zai kula ta ko ya amsa, ya kafe Kausar da manyan idanuwanshi waenda suka yi jazir yana hango tsantsar kishi da k’aunar waninsa a cikin idanunta… Kukan da Kausar take yi ne ya Isarwa su Mommy dan haka duk suka juyo… Da sauri Mommy ta matso ta ce ‘’me ya faru?Yassir cika ta mana” Haka ma Yasira ta matso ta fara k’ok’arin kwatar Hannun Kausar d’in amman bai kula kowa ba… Sai da Mommy ta daka masa tsawa cikin b’acin rai tace’’ka cika ta mana!” Tukunna ya juyo ya zubawa Mommyn ido, sai kuma kawai ya cika Kausar d’in, ya juya ya fita…. Yana fita Kausar itama ta fita, duk da tana tsoron su sake had’uwa da shi, amma ta gwammaci ya daketa ma idan sun had’un akan dai ace ta ci gaba da zama a cikin d’akin nan!. Da ikon Allah kuwa da ta fita babu Yassir babu alamar sa, dan kamar walkiya haka ta neme sa ta rasa, har ta kunna motarta ta fice daga asibitin babu shi babu kyallin sa. Kausar tana fita Yashjub ya mik’e bayan ya gama sauk’e Manubiya daga jikinsa, ya kalli Yassira yace “Yasira ya za a yi ku fice ku bar patient haka? sannan da kuka zo fitar ba ku kira nurse ko wani ba kawai kuka fice ku ka bar ta ita kad’ai, ga shi har ta suma babu wanda ya sani ma, bayan kin san ba ita kad’ai bace ba!”. Sai da Mommy ta yi da gaske tukunna ta danni zuciyarta tace “Am,Yashjub ba ta wannan ake ba! yanzu ka fara fad’a mana Ina ka je ka k’i amsa waya tukunna”. Cikin d’an b’acin rai yace ‘’Mommy a sume fa na shigo na tarar da matata, sannan ku ce ba ta wannan ake ba??” Ai kuwa cikin fushi kamar jira takeyi dama, tace ‘’wai wanne kalar Iskanci da rashin sanin ya kamata ne yake d’awainiya da Kai ne Yashjub??! Ashe baka da hankali kaima ban sani ba? fad’a za ka yi mini yanzun a gaban Yara ko yaya? Tsabar iskanci ina tambayar ka abu kaima kana ce mini wani ‘ya na yi abunda bai kamata ba?’.” Ahankali Manubiya ta mik’e da kyar tace ‘’Mommy ki yi hak’uri nice ban yi masa bayani ba” Sai kuma ta kalli Yashjub tace’’Ya Yash nice na ce su je zan iya…..” Cikin katseta Mommy ta daka mata wata uwar tsawa, ta hanyar cewa “Ke dallah malama rufewa mutane Baki!” Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya d’an firgita, ya d’aga kai yana kallon Mommy cike da mamaki al’ajabi da rashin jin dad’i. Cikin b’acin rai da takaici Mommy ta d’aura da cewa “bana son munafurci da iyayi da kankamba!, A tunaninki idan kika ce masa ke ce kika ce mu tafi mu barki zai fasa dukan mu ne? Ko kina tunanin ke ce za ki gyara tsakaninmu ko kuma ki sanya ya k’i jin haushin mu?. Har yaushe kika zo balle ki yi tunanin yin wannan shishshigin???” Cikin rashin jin dad’i Ummi ta matso tace ‘’haba Mommy, ki yi tunani mai kyau mana, Manubiya fa surukarki ce kuma matar d’anki na farko, a ganinki hakan da kike yi ya dace? Ai ba wai tana tunanin ita zata saka Yashjub ya yi muku wani abun bane, kawai ta so ta rufe maganar ne ta hanyar cewa ita ta ce ku tafi ku barta.’’ Cikin fushi Mommy ta juya ga Ummi sannan tace ’’Tabbas Ummi kwakwalwarki ba ta da rik’e abu! Yara sun gaya miki nima na gaya miki amma har kin manta ko? To bari in sake tuna miki yanzu! Daga yau har abada banaso ki sake yi mini shishshigi… kamar yadda na cewa Manubiya bana son ta yi mini shishshigi to kazalika kema dan baku da bambanci da ke da ita.’’ Shiruu Ummi ta yi kamar ba za ta ce wani abun ba sai kuma kawai ta juya ta kalli Manubiya tace ‘’ki yi hak’uri, kiyi ta hak’uri, haka rayuwar auren yake duk hak’uri ne a ciki, Allah ya baki lafiya’’ daganan ta juya ta kalli Munirat tace ‘’wuce mu tafi.” Suna zuwa daff da k’ofa za su fita, ƙasa-ƙasa Ya’isha tace “gara dai duk wanda ya san shi bare ne ya fita, dama hakan ne ya dace a yi tun farko ai.” Ko kallon ta ba su yi ba haka suka saka kai suka fita. Suna fita Mommy ta d’aura daga inda ta tsaya ta balbale Manubiya kamar ba surukar ta ba, wanda hakan ya sa hatta su Yasira sai da suka yi mamakin ta, sun san cewa Mommy ba ta son Manubiya, amma ba su yi tunanin za ta iya balbale ta a gaban Yashjub ta ci mata kamar haka ba, dama tun d’azu kafin su baro estate d’in Yashjub suka fahimci kamar akwai abunda ya fusatata sosai a tashi d’aya!! yanzu kuwa sun tabbatar, dan in da ace ranta ba a b’ace yake over ba to da bazata yi wannan b’aranb’atamar haka ba. Zuwa yanzu Yashjub ya gama fahimtar tabbas Mommy fa ba ta son Manubiya, kawai dama pretending take yi tun farko, dan ko shi Yaro ne abubuwan da suke gudana a gaban idanunsa sun Isa su fahimtar da shi hakan… Amma meyasa zata dinga pretending a gabansa, sannan me ya fusatata haka? Dan tabbas ba iyaka maganar Manubiya bace ta harzuk’ata ta har ta kaita ga rufe ta da fad’a haka babu ji babu gani. Gabansa ne ya yanke ya fad’i da ya tuna incidence d’in (abunda ya faru) jiya yadda Yasmeen ta ce Mommy ce ta turo ta, da kuma yadda tace Manubiya ba ta da ciki, gashi ta dage sai ta yi mata allura!… Dan tashi d’aya kwakwalwarsa ta bashi anya ba Mommy ce ta turo ta ta zo ta yi wa Manubiya allurar da za ta zubar da cikin ba kuwa?..Dan shi kansa da farko ya yi tunanin rashin kwarewa ne ya sa Yasmeen d’in ta ce Manubiya ba ta da ciki amma da ya zauna ya yi tunani tun a jiyan sai ya fara wani tunanin na daban! But a bayanin Doctor ya fahimci ita kanta Yasmeen d’in ba lalle ace ta fahimci akwai cikin ba ballanta har su yi yunk’urin zubarwa! Sannan tayaya?how? Mommy za ta bayar da goyon baya a kashe masa d’a?noo! Ba hakan bane ba gaskiya!! Dan babu mahaifiyar da za ta aikata haka ga d’anta, babu ita a duniya!…… Yqsh ya aiyyana hakan a ransa. A b’angaren Manubiya kuwa, shiruu kawai ta yi ta k’i cewa komai ta sunkuyar da kanta…da farko hawaye take yi kafin daga baya ta daina, tabbas ta gama tabbatar da Mommy ma a bayan y’ay’anta take! duk ba sonta suke yi ba.. dama sai da ta yi tunanin’ta ya Mommy za ta so ta bayan Kausar niece d’inta ce, amman kuma yadda ta nuna sai kawai ta kawar da tunanin, but yanzu kam ta fahimci ashe shigo shigo ba zurfi ta yi mata…dan gashi yanzu idan banda tsantsar k’iyayyarta babu abunda take hangowa k’arara a tattare da Mommyn. A ko da yaushe k’ok’ari take yi ta ga ta gyara tsakanin su amman ta lura sam waennan sun yi nisa ba sa jin kira… tunda har da mahaifiyarsu a gang d’in tabbas abun ba k’arami bane, sai dai ta d’ukufa gayawa Ubangiji. Ba za ta tab’a yi wa Mommy rashin kunya ba, kuma bazata k’i ta ba tunda uwar mijinta ce amman fa amma fa idan akwai abunda ta san shi tabbatacce to shine ‘ba za ta yarda da cin fuska ba’ shiyasa yanzun ma sai kawai ta yi shiru, ta k’i ba ta hak’urin da ta yi niyya, kawai ta sunkuyar da kanta k’asa…... Sai da Mommy ta yi mai Isar ta tukunna ta kalli Yashjub tace ‘’d’azun Ina ka je da ake ta kiran ka ba ka d’auka???” Kamar ba zai ce komai ba, sai kuma kawai ya lumshe idanuwa ya bud’e yace‘’d’azun Ina fita sai na tsaya waya, saboda a gani na gwara in tafi da ambulance da sojoji da k’arin y’an kwana-kwana…Ina tsaye Ina wayar na ga driver d’ina ya zo ya yi parking dama na aike sa ne akwai takardun da zai karb’o mini. yana zuwa ya yi mini knocking glass, ni kuma na bud’e masa d’ayan k’ofan nace ya ajjiye takardun a wajen….a nan ne ya ji wayar da nake yi ya fahimci abunda ya ke faruwa dan haka ya tsayar na gama wayar ya jajantamin yace mu je tare…motar da ya zo da ita ta fi gudu kuma duk na b’ata lokaci wajen yin waya shiyasa na karb’i makullin nace masa ya maida wannan cikin asibiti ya yi parking, sai ya zo mu tafi… Ina gama magana sai na ga su Innaa sun fito, gashi arean nan ba a samun abun hawa, shiysa na cewa drivern nawa ya fara yin gaba ni kuma na tafi kaisu gida.” Sai da ya d’an yi shiruu ya d’an kalli Manubiya kafin ya d’aura da cewa “muna zuwa muka tarar Baba ba shi da lafiya shine na mik’a su asibiti…” Cikin tarar numfashinsa Mommy tace ‘’saboda ubanta bashi da lafiya shine ka gagara d’aukar wayar uwarka da ubanka??” Da sauri yace “a’a Mommy, ba haka bane, garin kiraye kirayen wayar da na dinga yi ne saboda yadda na rikice inaga na saka wayar tawa a silent sam ban ji kiran ku ko d’aya ba wallahi.” Wani irin kallo Mommy take yi masa kafin chan kawai ta juya ta fice kamar wadda za ta tashi sama ba tare da ta sake cewa komai ba. Hakama Yassira ta matso da ɗan guntun hawayen ta wai “ta kusan mutuwa saboda tsananin tashin hankali a ɗazu da ta yi tunanin wani abun ne ya same sa ne, ashe shi yana chan yana hidimar gabansa, ya barsu hankalinsu duk a tashe, kuma ya zo amman ko ya nuna damuwar sa akan d’aya daga cikin su. gaskiya abunda yake yi bai kamata ba sam! Kuma a gaskiya ko dai ya gyara ko kuma su d’au mataki, dan wallahi tsaf sai su fice a harkarsa shima, saboda gaskiya abun nasa ya yi yawa. ta san shine babba akanta amma dole ta gaya masa ‘he is wrong!’(bai yi dai-dai ba).” Tana gama fad’in haka ta juya itama a fusace ta fice .. haka suka juya one by one suka fita zuciya a kumbure. Su ne suka yi rashin mutunci amma tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wadda ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi, ji suke yi kamar su mutu dan tsabar bak’in ciki!! Takaici!! da tsanar Manubiya wadda ta rufe musu ido ta hanasu walwala, Mommy da Ya’isha har ma da Yasira ji suka yi inama ace bata farfad’o daga sumar da ta yi d’azu ba, kawai da ta wuce lahira….. …Yarinya sai ka ce y’ar gwal?ace estate d’inka ya kama da wuta amma ka tura ɗan aike kai ka tafi hidimar iyayenta ba ka je ba, ina ma laifin ka saka drivern ya kaisu, sannan da ka gama still ba ka je estate din naka ba ka dawo wajenta saboda ka ji bata d’aukar waya!tabbas ba lalle ma ya san da mutuwar driver d’insa da batun y’an fashin ba, tunda har yanzu bai tsaya ya nutsu ya saurari kowa ba ballantana ya ji bayani…… Su Ya’isha suna fita, Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya ta juyo ta kamo hannunsa. Tun kafin tace wani abun yace ‘’Ki yi hak’uri, dan Allah Baby ki yi hak’uri, komai zai yi daidai, inshaaAllah, kar ki sa damuwa a ranki” Ahankali ta d’an yi k’asa da kanta, kafin tace’’ kar ka sa komai a ranka dan Allah, k’addara dama tana zuwarma bawa ta ko wacce irin siga.. InshaaAllah Ubangiji zai mayar maka da abunda ya fi estate d’inka.” Sai kuma ta kallesa tace”InshaaAllah ma ba duka ne ya k’one ba, sannan Allah ya sa ba a rasa rai ba,ni na warke yanzu…ka je ka ga halin da bayin Allah suke ciki….” Jinjina kai yayi, ya jata suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace “ba gobara bane, Najeeb ya ce mini y’an fashi ne, su suka kunna wutar, amma yanzun zan je inshaaAllah, sai in ji komai…” A hankali tace”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun…” Shiruu ya yi ya d’an k’ura mata ido……ya san idan ya zurfafa zancen itama za ta fara zargin abunda yake zargi, sannan hankalinta zai tashi kamar yadda nasa ma yake a tashe wataƙilan ma fiye da nasa d’in, shiyasa ya sauk’e ajiyar zuciya yace”Allah ya tsayar a iya ka hakan…” Ahankali tace “ameen” hankalinta duk a tashe. Cikin ruk’ota izuwa jikinsa yace”sannan kar ki damu saboda businesses d’ina have been successful, kuma tun farkon shekarar nan har kawo yanzu inaga na samu abunda zan iya gina estate d’in ma biyar!! a iyaka ribar shekarar nan kawai. ban saka komai a raina ba na karb’i k’addara. Kuma ko da ace ban samu income da ci gaba a business d’ina ba to banga dalilin da zai sanya in ji takaici ko in shiga damuwa saboda na rasa estate ba. Ubangiji na ya yi mini ni’imomi masu tarin yawa a wannan shekarar…kinga na farko ya bani ke, har da k’aruwa gashi mun samu,sannan abubuwa na da businessess d’ina sai bunk’asa su ke daɗa yi!.. kina ganin dan estate guda d’aya ya k’one zan ji haushi? Ai ya bani abunda ya fi estates dubu ma Baby tunda ya bani ke”. A hankali Manubiya ta sake shigewa Jikinsa ta kwantar da kanta a kan k’irjinsa, ta yi shiruuuu. A karo na biyu, ta ji ya sake cewa “ki yi hak’uri a kan abunda Mommy ta yi miki, dan Allah’’ Ahankali tace ‘’ba komai fa, iyaye basa laifi, sannan kai a matsayin ka na Mijina ka daina bani hak’uri, ka fi k’arfin haka a waje na.” Shiruu duk su biyun sukayi kowa da abunda yake tunani.. “Dan Allah ka kaini in ga Baba’’ Muryar Manubiya ta katse masa rikitaccen tunanin da yake yi. Shiru ya yi kawai bai ce komai ba, dama wallahi ba dan Mommy ta tambaya ba to da ba zai fad’a mata ba! Dan Su kansu su Innaa cewa suka yi kar ya gaya mata saboda kar ta d’aga hankalinta. Muryar ta ce ta sake katse masa tunani jin tana cewa ‘’Dan Allah” a hankali kamar za ta fashe da kuka. Numfashi ya fesar kafin ya sake rungumeta da kyau yace’’ok zan kai ki amma wataƙila sai zuwa gobe, saboda kinga kema baki da lafiya…yanzu bara in kira Doctor ya fara duba mini ku tukunna kin ji ko, ki kira su a waya kar ki sa damuwa zai samu sauk’i inshaaAllah….’’. Sai da ya lallab’a ta sosai tukunna da kyar ta hak’ura a kan goben za ta je, dan haka ta d’au waya ta shiga kiran su, ya ji sun yi magana da Jidda da Inna har ma da Siyama amma bai ji sun yi magana da Ya Musbah wanda tunda ya je gidan kafin su tafi kai Baba asibiti ake ta kiran sa yana cewa”gashinan zuwa”. Ba. shiruu ya yi sai da ya gama had’a one plus one tukunna ya kalli Manu yace mata “Musbah bai je bane??har yanzu?”. Diriricewa ya ga ta d’an yi dan ita kanta lamarin na Ya Musbahu ya fara d’aure mata Kai, dan a bayanin Jidda ta fahimci su hud’u ne kawai a wajen Baban yanzu haka gashi idan ta kira sa a waya ba ya d’auka. Dukda shima yana fama da tasa damuwar amma haka ya daure ya danne tasa cikin nutsuwarsa ya sake ce mata “akwai wani abun ne?is there anything I can do to help (Akwai wani abun da zan iya taimakawa da shi?) saboda jinin Baba fa ya hau ne sosai”. Tashi d’aya tun kafin ya gama rufe bakinsa ta fashe da kuka, cikin kukan tace “dan Allah ka kai ni in gansa” Numfashi ya fesar yace”to bari in kira Doctor ya zo ya duba min ku,tukunna sai in ga ko zai iya barin ki ki fita yanzun” Daga haka ya mik’e ya fice yana ganin dishi-dishi tsabar tension… Yana fita ta kira Jidda shi kuma ya na fita Ya Nafi’u ya kira dan tabbas ya lura family d’in Manu suna cikin damuwa… Da farko Ya Nafi’un b’oye masa yayi, sai da Yashjub d’in ya nace tukunna ya zaiyyane masa komai halin da ake ciki, halin Baraka da yadda ta janye Ya musbah da kuma yadda y’an uwan Baba suka sako shi a gaba..ba su ajjiye wayar ba sai da suka yi wa tufkar hanci daganan suka yiwa juna sallama bayan Ya Nafi’u ya yi wa Yashjub alk’awarin zai sanya Baki ya lallab’a su Baba su yarda su k’arbi gidan da Yashjub d’in ya basu su koma.. Ba k’aramin rarrashi likitan ya yi wa Yashjub ba da ya ji batun Manu har ta suma amma ba su sani ba, ya san ba laifin sa bane ko na nurses tunda sun gama yi mata allurai kuma ita da Mijinta suka barsu a d’akin sannan da aka zo fita ba a kira kowa ba amma hakanan ya yi ta bawa Yash d’in hak’uri dan ya lura ransa a b’ace yake. Dama ba so yake yi ta fita d’in ba, aikuwa likitan yana zuwa da ya duba ta yace”ba zai yiu ta fita yau ba gaskiya jikinta ba kwari”… Hakanan da kyar ya samu ya sake lallab’ata ta hak’ura dan jikinta duk ya yi sanyi daga wayar data gama yi da Jidda yanzu Saboda Jiddan ta gaya mata komai itama……. Yahanasu Yash ya kira ta zo ta zauna da Manubiya yayinda shi kuma ya nufi estate d’innasa…. Sai da ya je Estate d’in nasa tukunna ya ga abunda ya faru da b’arnar da aka yi, tashi d’aya zuciyarsa ta aminta da zargin da yake ta yi tun d’azu ‘tabbas kashesa ake so a yi’ shi aka so a akashe da basaja sai Ubangiji ya kub’utar da shi kuma wannan aikin na jikinsa ne yake yi, da kunce masa tayar mota da aka yi da incidence d’in dole sai na jikinsa wanda kuma ya san shige da ficen sa ne zai iya yi, to amma wanene mai wannan aika aikar??? Dan zuwa yanzu ya fahimci ba Kausar bace ba, wannan aikin sai dai aikin gayya ko kuma kwararren tantiri tunda har da y’an fashi a lamarin…gabansa ne ya yanke ya fad’i a tashi d’aya ya yi istighfari da ta’auzi dan kamar yadda d’azu kwakwalwarsa ta basa ‘Mommy ce ta turo Yasmeen ta yi wa Manubiya allura,’ hakanan yanzu ma lissafinsa ya basa’ita da Kausar maybe da ko Yasira ne suka yi wannan aika aikar, dan aikin ya wuce b’arnar mace d’aya’ Cikin runtse idanunsa ya shiga kokawa da zuciya da kwakwalwarsa dan sam bai ga ta inda mutuwarsa za ta zamo riba wa Mommy ba….ta ya ma zai yi tunanin hakan ita fa ta haifesa. Still shi da kansa a cikin zuciyarsa yace”amma fa some facts cannot be denied(ammafa wasu abubuwan a baiyyane su ke kuma ba zaa iya chanja su ba),… a iyaka d’azu kad’ai ya fahimci kamar ba ta tab’a shiga fushi irin na yau ba, ta ya za ace d’anki ya kusan mutuwa amma da kika gansa ya dawo lafiya lau bai ji kwarzane kwata kwata, ace ba ki yi farinciki ba maimakon farin cikin ma sai fushi da bak’in ciki…kamar irin tana fushin ganin plan d’insu bai ci bane shiysa ta fusata ta kasa controlling kanta…..amma mai yasa? Mai yasa suke son kashe sa, me za su cimma ta hanyar hakan? A take zuciyarsa ta shiga aiyyana masa tana yi masa flashing yadda ‘ba sa son Manubiya!’ To kenan za su kashe sa saboda sun kasa raba sa da Manubiya kenan? Da sauri ya bawa kansa amsa ta hanyar cewa”noo, hakan sam bai bada maana ba!.” Bai san lokacin da hawaye suka shiga ziraro masa ba, yana mai jin wani irin yanayi na tashin hankali da bak’in ciki da rud’ani, a ransa ya ce”Mommy ba za ta iya kashe ni ba amma duk wata alama tana mini nuni ne da tsaf za ta iya aikata hakan….tun ba yau ba na san ba ta sona, sannan tunda na d’auko maganar aure abubuwa suke ta sake tab’arb’arewa, ga kuma abunda ta yi yau.” Rud’ani rikici da kuma rashin sanin gaskiyar lamari ne suka sanya ya runtse idanuwansa da mugun k’arfi, still a cikin ransa yace “akwai wani abun da ya kamata ace na sani…akwai abunda ban gani ba kuma ban sani ba!to amma what is it(menene shi ɗin)????”. Ya yi wa kansa tambayar ba tare da ya san mai basa amsar ba!. dan tabbas a yanayin yadda ya ke ganin abubuwa to dole dole tsakaninsa da mommy ba complete bane ba, akwai wani abun da bai sani ba, wanda sai ya samu ya sani ɗin ne tukunna in ya haɗa komai da ke faruwa a tsakanin shi da ita zai yi makin sense, ya san a take zai bada cikakkiyar ma’ana…. Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e ya dafa shi ganin yana hawaye sannan ya runtse idanuwa yace”Yash sai hak’uri fa!na san me kake tunani, amma ka kwantar da hankalinka ka ci gaba da addu’a, bawa bai Isa ya yi wa bawa abunda Ubangijinsa bai yi ba” A hankali ya bud’e idanunsa da suka koma kamar garwashin wuta, ya zuba su a kan Najeeb. Jinjina kai Najeeb ya yi ya ce ”yeah, tun akan incident na hatsarin motar da ku ka yi kwanaki na fahimci akwai wanda yake harin rayuwarka, kawai na yi shiru ne saboda na ga kaima ka sani amma ba ka son tada maganar, yanzu kuma duba da yadda motarka tana shigowa suma suka baiyyana suka rufe gate suka fara kashe mutumin suka kunna wuta, ya sanya na sake tabbatarwa…amma kar ka damu, a hankali zan taimaka maka za mu yi bincike ko dan rayukan mutane kusan d’ari da aka b’atar inshaaAllah za a kama ko ma waye me aikata wannan mummunan aikin…” A hankali jikin Yashjub ya fara karkarwa, duk yadda ya so hana kansa yin kuka sai da hawaye suka balle masa sosai..yanzu a ta dalilin sa aka kashe duk waennan Mutanen….ta ya zai taɓa iya yafewa kansa?? Ga kuma zargin Mommy da yake yi wanda ya sake hautsina sa… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 30* Duk yadda Yassir ya so ya jira ya d’an saisaita kansa kafin ya fuskanci Kausar kasawa ya yi…ba ya so ya tunkare ta yanzu dan tabbas zai iya illatata amma kuma zuciya da bak’in cikin rashin samun nasarar kashe Yashjub da kuma kishi ne suka k’i su barshi ya iya jira d’in, dan haka kawai ya nufi gida gadan-gadan. A b’angaren Kausar kuwa!! A mugun rikice ta shiga gidan itama sakamokon wani amai mai k’arfi da ya hanata sukuni yake ta faman yunk’uro mata…ta na shiga d’akinta kuwa ya taho da mugun k’arfi.. Da gudu ta nufi toilet amman tun kafin ta k’arasa ta fara sakinshi. Ta jima tana yi kafin ta samu ya d’an sarara mata, ta shiga mayarda numfashi… Yanayin k’arnin aman ne ya firgitata ya tsoratata..dan haka ta na haki ta shiga hargitsa toilet ɗin a gigice tana neman pts, a lokaci guda kuma tana tana addu’a. Da ikon Allah kuwa ta samu, dan haka ba ta yi wata wata ba ta auna kanta. Bata iya ajjiyewa lokaci ya cika ba, hakanan ta shiga safa da marwa a cikin band’akin da abun riƙe a Hannunta idanunta kyam a kai, gaba d’aya ta hargitse ta ma rasa tunanin me za ta yi…tunda take ba ta tab’a jin tsoron shigar ciki da fargaba da tashin hankali kamar na yau ba!. Aikuwa tashi d’aya ta fara ganin alamun positive…kafin ma ya gama tabbatar mata da hakan ta fashe da wani irin kuka ta durk’ushe a wajen, tana kallon yadda abun yake yi mata nuni da tana d’auke da ciki ne. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ta shiga maimaitawa a cikin zuciyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita….. Ganin kuka ba zai fishsheta ba ne ya sanya ta share hawayenta ta mik’e jikinta yana wani irin karkarwa ta ajjiye abun ta shiga lissafin neman mafita…… Tashi d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji, dan haka ta fito ta nufi side d’in Mommy jikinta har yana wani Irin karkarwa. Su Mommy suna isa gida ta wuce sama d’akinta, Baba larai tana ganin haka ta bita da sauri… Sai da ta kai k’ofar d’akinta tukunna ta lura da Baba larai dan haka tace “larai ki je kawai ina buk’atar sarari..” Daga haka ta bud’e ta shiga tana k’ok’arin rufowa Baba larai ta sa hannu ta tare k’ofar ta shiga ta rufo, Mommyn tana shirin yin magana ta ji Baba larai tana cewa”Khadija zama na a cikin gidan na ya k’are, dan haka na zo ne in yi miki sallama, sannan in gaya miki abunda ya faru da kuma taimakon da na yi miki d’azu wanda ya taso na gaggawa. Daga nan ni kam yanzu ba sai anjima ba zan tafi!”. Runtse idanuwa Mommy ta yi, kafin ta bud’e tace”dan Allah Larai ki barni in huta tukunna, za mu yi magana anjima..” Cikin tarar numfashinta Baaba Larai tace “Au wai a tunaninki barazana ce nake yi?…wallahi wallahi na gama sakawa a raina Khadija barin gidan nan zan yi!.. Dan ba zan zauna rashin hak’uri da rashin lissafinki ya kaini prison ba!. Bari ki ji abunda ba ki sani ba d’azu kuna fita na ji Daddy yana waya, ko kin san wanene ya kirasa?” Kallonta Mommy ta yi tukunna tace”A’a” Sai da Baba larai ta sake ce mata “kin san wa ya kirasa?”Mommyn tace “a’a” suka yi haka har sau uku tukunna Baba larai tace”Mallan lawal!” Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Mommy ya yi, kafin cikin in Ina ta ce ”mme yya ce mmasaa??”. “Cewa ya yi yana son magana da shi inaga, dan ji na yi Daddyn yana cewa ‘mallan lawal dama kana raye Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’ sai kuma ya fara basa hak’uri kafin na ji ya yi shiruuu yana sauraronsa sai kuma yace ‘na godewa Allah, nauyi d’aya ya sauk’a a kaina, mallan lawal amma ba za ka iya gaya mini ta waya ba dole sai na zo??’ Daganan na ga ya fice compound ya nufi parking lot, to inaga case d’in Yashjub ne ya tsayar da shi wanda ba dan haka ba da tuni yanzu haka ma yana garin Garin Mallan……” Cikin takaici Baba larai ta d’aura da cewa“wallahi Khadija in da ace ba ki tsaya dawo mana da aiki baya ba da tuni ba mu zo nan ba! Na gaya miki Yarinyar nan barinta tare da Yashjub masifa ne a gareki amma kin k’i ki bada goyon baya a samu a fitar da ita daga rayuwar tasa cikin sauk’i, yanzu ai ga irinta nan! Idan kika ga yadda hankalin Daddy ya tashi gaba ɗayansa ya rud’e lokacin da ya ji mallan lawal yana a raye, za ki yi mamaki…kin san yanzu zai fara wasu wasin mutuwar Khadijah itama ai ko?” A mugun rikice Mommy tace”larai shiyasa tun a lokacin na ce a kashe su, kika ce A’a za ki san yadda za ki yi dasu, yanzu ga irinta nan ai” sai kuma ta fashe da kuka cikin gunjin kuka tace”wannan duk ba laifin kowa bane laifin Manubiya ne, ita ce wallahi, tunda ta zo shikenan ta lalatamin komai, larai na gaji kashe Yarinyar nan zan yi wallahi kuma ba ki isa ki hanani ba…” Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”ba za a yi haka da ni ba, in da ace zan barki ki kashe rai da tuni mun yi tun a kan Khadija..hak’uri za ki yi ki kwantar da hankalinki ki danne zuciyarki tukunna ki ci riba, dan ni dai ba zan tab’a gajiya da gaya muku da ke da su Yassira ba saboda haƙurin ne kad’ai mafita”. Cikin wani irin kuka Mommy tace “Larai yanzu to ba Manubiyan ba, shi mallan lawal d’in larai mun bashi dama ta biyu amma kinga yanaso ya tona mana asiri, na rok’e ki da girman Allah ki taimaka mini ki rufa mana asiri a kawo k’arshen sa, dan wallahi na san gaskiyar lamari zai fad’awa Daddy idan har suka had’u dan in ba hakan ba menene zai sa yace yana son ganinsa?…” Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace”kar ki damu.. Daddy yana fita na kira mutumin da muka ce ya saka mana ido a kansa, ashe ciwon hanta ne ya ke damunsa likita yace masa ba shi da sauran lokaci shiyasa yake neman Daddyn, saboda ya samu ya gaya masa gaskiya.” Numfashi ta fesar kafin ta ci gaba da cewa”tunda dama mutuwa zai yi shiyasa kawai na cewa mutumin ya k’ara masa gudu, mu kuma za mu bashi naira miliyan d’aya…..to dai a halin yanzu Ina tabbatar miki mallan lawal ya tafi kai balance, dan mutumin a lokacin ce mini ya yi a take zai aiwatar da aikin saboda gidan dama ba kowa, shi mallan lawal d’in ne kawai a zaune a gidan da shi da jikarsa wadda take jinyar sa to alokacin ya ga itama ta fita ta nufi kasuwa…… yanzu miliyan d’ayan za a tura masa, dan naga ya kirani d’azu Ina asibiti shiyasa ban d’auka ba.! Muna tura masa ni kuma zan kama gabana dan ba zan zauna ki ci gaba da lalata m….” Cikin Jin dad’in maganganunta Mommy ta rungume Baba larai, wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa abunda take cewa, wani kuka Mommy ta fashe dashi tana cewa”na gode Larai na gode sosai, ki bani accnt number miliyan biyu ma zan bashi wallahi….sannan zan gyara wallahi zan yi yadda kike so, dan Allah kar ki sake cewa za ki tafi.” Da kyar Mommy ta lallab’a Baba larai ta hak’ura da tafiya, daganan suka kira mutumin ya shaida musu cewa”Mallan lawal yana ma shirin shiga k’asa a halin yanzu dan wanka ma ake yi masa.” Naira miliyan biyu Mommy ta tura masa a take, daga nan ta nutsu tana sauraron hud’ubar Baba larai. Da sallama Yasira ta turo k’ofar d’akin ta shigo, kafin ta k’araso ta zo ta tsaya a gabansu. Kallonta kawai Baba larai ta yi ta maida hankalinta ga Mommy kafin tace”a baya da kika iya kwantar da Kai wacce kalar riba ce ba ki ci ba?yanzu kuwa kinga ai komai lalace miki yake yi saboda rashin tunani da lissafin da kika bawa ragamar rayuwarki,kuma bari ki ji ba ni da tantama a yau Yash ya dasa ayar tambaya a kanki wallahi, saboda abunda kika yiwa Manubiya a gaban kowa ya na nuni ne da kin tsaneta dama tun asalin farko, wanda hakan zai sanya ya fahimci dama chan pretending kike yi kuma bakin ku d’aya ke da su Yasira duk ba son matarsa kuke yi ba! Dan haka yanzu ko ciwon yatsa Manubiya ta yi Ina mai baki tabbacin Yashjub ke zai zarga, tunda dama ba wata shak’uwa ce a tsakaninku ba balle ya ki zarginku, kuma ko su Yasira sun je gidan ido zai sanya musu ya dinga d’arr d’arr da su ta yadda ba su isa yin komai ba, shikenan kina ji kina gani Manubiya zama daram! Hakanan abubuwa za su yi ta faruwa da mu, tunda kink’i ki bada goyon baya mu samu a yi abunda za ta tafi. Shiysa na yanke shawarar in tartara ya nawa ya nawa in kama gabana tun kafin bomaboman da za su iya hallaka ni su fara fashewa.” Ajiyar zuciya Yasira ta sauk’e kafin tace”Mommy nima gaskiya abunda kika yi yau ban ji dad’in sa ba….” Cikin tarar numfashinta Baba larai tace”Yasira yo ai har da ku!” Jinjina kai Yasira ta yi kafin tace”ni kam zuwa yanzu Baba larai duk yadda kika ce inshaaAllah hakan za ‘a yi,saboda hakan ne kawai mafita,gara in jure ta, in nuna ina sonta in ja ta a jiki na wata d’aya ko biyu, akan mu rayu da ita har abada, muna fama da ita tana janyo mana masifu kala kala, na tabbatar kashe Ya Yash da aka so yi a yau shima duk a cikin masifun da take tafe da su ne!.” Cikin sauk’e ajiyar zuciya ta kamo hannun Baba larai ta ci gaba da cewa”dama ai ya san za mu je mu tayata gyaran gidan ko?” ba ta jira jin mai Baba laran za ta ce ba ta d’aura da cewa”zan yi wa Yasmeen magana ita da su Yusra. na yi miki alk’awarin inshaaAllah daga yau mun chanza zani, amma Ya’isha ba za ta bimu ba dan na san za ta iya b’ata mana komai…ki had’a duk wasu abubuwan da ya kamata inshaaAllah wannan karon ba za mu baki kunya ba, za ki sha mamaki…” “Allah ya yi miki albarka Yasira, zuwa dare zan ganku ke da su Yasmeen d’in kafin ku tafi” Jinjina kai Yasira ta yi kafin ta kalli Mommy tace mata”Daddy yana son ganinki…” Daga haka ta juya ta fita ta rufo musu k’ofar…. Tana fita Baba larai ta saki murmushi dan tabbas ta hango jajircewa a idanun Yasira, ta san kuma su Yasmeen ma za su yi mata biyayya inshaaAllah wannan karon akwai nasara….cikin jikin Manubiya za su fara farma, a yadda Yash yake ji da cikin nan ta san cikin sauƙi za su samu matsala da shi da ita idan har suka nuna masa kamar Manubiyan ce ta zubar, amma tayaya za su nuna masa hakan??dole su nemo dalilin da zai yarda da shi…… Tana wannan tunanin ta ji Mommy tace”bari in je…” Kallonta Baba larai ta yi kafin tace”Juyin duniya!Khadija, kar ki kuskura ki bari ya fahimci kin san wani abun” Jinjina kai Mommy ta yi gabanta yana dukan uku-uku, ta juya za ta fita…cikin son kwantar mata da hankali Baba larai ta ruk’o hannunta tace”ki kwantar da hankalinki…” Hawayen da suka b’allewa Mommy ne suka sanya ta kasa ci gaba da magana,a hankali ta isa gareta ta rungumota ta shiga rarrashinta..fashewa Mommy ta yi da kuka cikin kukan tace “dan Allah dan annabi larai kar ki sake cewa za ki tafi,a wannan worst situation d’in larai idan kika tafi kika barni Ina makomata??…” Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e ta cikata tace”babu inda zan je amma Khadija kema sai kin chanja zani!kamar yadda su ka yi alk’awari dan Allah kema ki gyara…mu samu Yarinyar nan ta tafi daganan mu aura masa Kausar bayan shekara d’aya ko biyu idan ta haihu muka samu abunda muka so sai mu k’arasa shirin mu a samu a rufe chapter nan, wallahi na gaji, sai abu d’aya ake yi yau kusan shekara nawa amma ba riba!” Ajiyar zuciya Mommy ta fesar kafin tace”Larai, ba zan iya yarda da Kausar akan lamarin Yashjub ba yanzu kam…saboda a da na d’auka soyayyar da take yi masa mai sauk’i ce ko kuma lust(sha’awa) ko wani abu makamancin hakan, shiyasa har na yi tunanin ‘idan ta auresa suka yi shekara d’aya ko biyu, ta samu abunda takeso, ta haihu ta d’an zauna da shi, ya fara fita a ranta to za ta iya yi mana abunda mukeso, dan na san tunda ba ya sonta to musguna mata zai ta yi…’ amma yanzu kam na fahimci masifaffiyar soyayya take yi masa, kuma duk runtsi za ta tsaya masa za ta tsaya a tare da shi ta so shi so ba na wasa ba ma kuma a ko wanne irin yanayi!!! Abunda Yasmeen ta yi mini akan batun zubar da cikinnan ya sanya na fahimci ‘Yaran nan fa ba za a dad’e ba kowacce za ta fara fito da nata ra’ayin da abunda ta ke so itama tana jayayya da ni’ kuma indai har Yasmeen ‘y’ar cikina’ za ta iya yi mini hakan, to abu mai sauk’i ne ga Kausar dan ta bijere mini, shiyasa na gama yankewa akan ‘babu maganar Kausar da Yashjub’! Ba zan bari ta auresa ba!. Za mu san yadda za mu yi dai, dan gaskiya ba zan taɓa yarda in iya trusting Kausar akan wannan Lamarin ba…..” Shiruu Baba larai ta yi kafin tace”to amma kuma ta ya za mu samu wanchan abun kenan? Ko mun b’ata shekaru a banza kenan? Ki duba future d’in Yassir, ki sake tunani….” Sai kuma ta yi shiruu da maganar ta d’an yi tunani kafin tace”to ko Manubiya za mu jira ta haihu, inyaso idan ta haifa sai mu rik’e…….” Cikin katseta da d’an b’acin rai Mommy tace”haba larai!ke fa da kanki ki ka sanar da ni illar kasancewar Manubiya a tare da Yashjub, kuma gashi muna gani muraran!…bayaga haka ma ko dan masifar da wannan cikin da Uwarsa da Ubansa suka sakani a ciki wallahi dole sai ya fita! Ko ana ha maza ha mata……” K’ausar tana hawaye, a haka ta k’arasa side d’in Mommy, ta shiga ta wuce parlourn ta nufi bedroom, har za ta tura k’ofar d’akin ta shige kawai sai ta ji Mommy tana cewa”babu maganar Kausar da Yashjub’!Ba zan bari ta auresa ba!. Za mu san yadda za mu yi dai…..” Wani irin duhu-duhu dishi-dishi Kausar ta fara gani da ji, ko ƙarshen maganar mommyn ma ba ta iya ta ji ba tsabar bala’i …ita da ta zo a kan ta cewa Mommyn ‘mai zai hana a yi tricking Yash (a shirya masa tarko), ta samu ciki, ta yadda dole sai ya aureta…’ amma shine take jin wannan batun daga bakin Mommy?? Dama ita ba ta yi shirin gaya mata tana da ciki ba, dan ta san ba za ta yarda a aurawa Yash ita da cikin Yassir a jikinta ba, shiyasa take so ta bata wannan idear ta yadda ko shi Yassir d’in bai Isa ya san cikin nasa bane kawai kowa a tafi a kan cikin Yash d’in ne,ta samu ta rufawa kanta asiri burinta ya cika.Sam ba ta yi tsammanin haka daga Bakin Mommy ba, wato ta barta ta gama lalacewa shine yanzu take kyamar ta had’a d’anta da ita kenan ko yaya? tabbas blood is thick(jini ya fi ruwa)! Ita kuma ta tabbata ba ta da kowa kenan!!…. Wani Irin kuka ne ya taho mata, dan haka ta yi sauri ta juya gudun ma kar su jiyo ta, ta nufi k’ofar parlourn hannunta a kan bakinta tana mai k’okarin hana sautin kukan nata fitowa. Kusan karo suka yi ita da Daddy wanda ya turo k’ofar parlourn ya shigo. Shi ya wuce ya nufi d’akin ita kuma ta fice ta nufi d’akinta tana kuka kamar ranta zai fita. A tsaye ya same su ita da Baba larai….sum sum haka Baba larai ta sa kai ta fice bayan ta yiwa Mommy wani kalar kallon da su kad’ai su ka san me take nufi. Tana fita ya lumshe idanuwansa ya d’an bud’e kafin ya k’arasa kusa da ita yana mai kallon cikin idanuwanta yace”mallan lawal ya rasu” Gefe da gefe ta kalla kamar irin tana tunani d’innan kafin tace”Daddy mai ya faru??? Kai fa ka ce a daina maganar nan kuma yau kai da bakinka ga shi ka kawo ta?” K’ura mata ido ya yi, dama yana so ne ya ga reaction d’inta (yadda za ta yi), wai ko zai iya kamata da laifi amma sai ya ga babu alamun hakan a tartare da ita! Ya san yadda Mommy ta kula da mahaifiyar Yahanasu, suka zauna lafiya!!! Shiyasa yake ganin kamar idan ya zargeta a kan al’amarin da ya faru a baya to bai yi mata adalci ba, wanda dalilin zargin ya samo asali tunda mallan lawal ya kirasa d’azu ya fara basa hak’uri yana cewa ‘yana son magana da shi’ to tun daga nan ya fahimci anya ba sharri aka k’ullawa Khadijansa a wanchan lokacin ba kuwa! Dan kansa ya d’aure matuk’a ta inda a baya yake da tabbacin mallan lawal d’in ya rasu tun shekaru wajen ashirin da bakwai baya amma yanzu gashi ya ji sa a raye ɗazu, dan ko a mafarki idan ya ji muryar mallan lawal sai ya gane, shiyasa tashi d’aya ya tabbatar akwai k’umbiya-k’umbiya a cikin al’amarin.. Khadija ba ta shiga ko mak’ofta sai tare da Mommy, kuma ko hayaniya ba ta tab’a yi da kowa ba, ita ba ma ta iya fad’an ba….. duba da haukar da Mommy ta yi a lokacin da yace zai k’ara aure da kuma yadda ta shiryu lokaci guda ta rungumi amaryar(khadija) tashi d’aya dama tun a wanchan lokacin ya ke zarginta, kuma ya ke ganin kamar akwai abunda ta ke shiryawa, amma bai yi tunanin za ta iya yi mata wanchan sharrin ba! Sai dai kuma in dai har sharrin ne aka yi mata da gaske to mommyn ce saboda Khadija ko y’an uwa ba ta da shi balle ace wani ne ya yi mata sharri sannan bata da Abokin faɗa!! Dan haka tabbas wannan aikin Mommy ne… Sannan a cikin gidan ya yi waya da Mallan lawal, dan haka ya san wataƙila Baba larai ce za ta gaya mata, shine ta kashe sa kenan??gudun kar asirin ta ya tonu?Tabbas kuwa indai hakan ya tabbata to bai ma san wanne kalar hukunci zai yanke mata ba! Matsalar guda d’aya shine yadda ta yi d’innan wanda ba dan shi da kansa gaba d’aya alamomi suna masa nunin kamar ita ce master mind a al’amarin ba, to ba dalilin da zai sanya ya zargeta. A b’angaren Mommy kuwa in banda lugude babu abunda zuciyarta take yi!k’arfin hali ne kawai take, amma a mugun mugun hargitse take tun lokacin da ya shigo ta firgice… “Daddy ka yi shiru” D’in da tace ne ya katse masa tunani… A hankali yace”yanzunnan ya rasu” Wata zabura ta yi tace”innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Daddy dama chan bai rasu ba??me ya faru?kiranka ya yi?”. Ta fad’i hakan ita kanta ba ma ta san ta fad’a ɗin ba tsabar rashin sanin tudun dafawa, tsoro take yi kar ta yi shiru ya zargeta shiyasa ta zab’i ta yi duk maganar da ta zo mata. Wani kalar mahaukacin bugawa zuciyar Daddy ta yi, dan tabbas Mommy ta k’ulle kanta da kanta..ta ya aka yi ta san kiransa ya yi? Jinjina mata Kai ya yi kawai, yana mai jin kamar ya shak’e ta ya kashe ta a take a wajen, da kyar ya iya cewa”kira na ya yi, ya ce in yafe masa, yana buk’atar gani na da gaggawa.” Zuwa yanzu yadda Mommy ta fara gumi ya gama tabbatar masa da komai, dama abunda ya zo tabbatarwa d’in kenan shiyasa ya zo mata a haka, cikin son sake ganin reaction d’inta (yadda za ta yi) yace”tun lokacin da ya kira ni ya fara magana gaba d’aya hankalina ya karkarta ne a kan watak’ilan Khadija (Amarya) itama tana raye.” A take ya ga idanuwanta sun fara ciccikowa da hawaye kamar za ta yi kuka…da kyar Bakinta yana wani irin karkarwa ta samu tace”Noo Daddy, it can’t be(hakan ba zai yiu ba ai), idan shi ya rayu ita ba zai yiu ta yi rai ba, ko ka manta yadda ita d’in da hannunka fa ka c….” Yadda taga idanuwansa sun yi jaaa a take ne ya sa ta had’iye maganarta ta sunkuyar da kanta,kafin da kyar ta sake d’agowa tace”amma ban sani ba, sai dai mu fara bincikenta,watak’il itanma she made it out alive(ta samu ta fita da ranta)..saboda ka san dama na gaya maka wajen yadda ya koma ba mu iya detecting(gane) ko da biro ba ballantana gawa, dan komai ya kone k’urmus, ruwa kawai muka yayyafa aka yi musu salla a haka…..” Wuff kawai ta ga ya juya ya fita, zuciyarsa ta na wani irin tafarfasa dan ya san tabbas idan ya ci gaba da zama to zai iya aikata abun ban mamaki ga Mommy…Mommy ta yi masa abubuwa daban-daban tun daga kan yadda ta tilasta masa aurenta har kawo yanzu, kullum a cikin b’acin ranta ya ke, amma bai tab’a tunanin za ta iya aikata hakan ba, sannan gashi still k’ok’arin b’oyewa take yi ya san ba zata taɓafaɗin gaskiya ba!!! amma shi ya san ta yadda zai kamata dumu-dumu! Ta yadda zai k’ulleta da jijiyoyin jikinta, ya tona mata aisiri kowa ya ganta…hacking wayarta kawai zai yi ta yadda ko typing take yi sai ya gani. A nan ne kawai zai ji komai da take yi, ya kuma ga komai sannan ya kamata dumu-dumu…ya tabbatar da zarginsa a kanta. He really can’t believe this!he can’t believe (kansa ya kasa ɗauka! Sam ya kasa yarda da cewa) ‘Mommy ta saka shi ya kashe Khadijah da hannunsa, ba tare da laifin ta ba’ dan kamar yadda ita ma Mommyn ta ce yanzun ‘idan mallan lawal ya samu ya fita da ransa to ita Khadijah ba ta Isa ta fita da rai ba, ba za ta iya ba.’ Tabbas hukuncin kisan kai ya yi wa Mommyn sauƙi…shi kansa yana jin tsoron abunda zai yi mata, Wallahi. ……. Kasancewar Yassir a napep ya taho ya sanya sai yanzu ya samu ya shigo cikin gidan….. Yana zuwa a fusace ya haye sama ya nufi d’akin Kausar,zuciyarsa tana wani irin tafarfasa. Kausar ta na wani kalar kuka haka nan ta shiga d’akinta ta fad’a kan gado…..ta yi kuka a wannan rana kamar ranta zai fita kafin ta mik’e ta fad’a toilet ta shiga wanke fuskarta a ranta kuwa ta gama aiyyanawa “wallahi, daga yau!! itama ta kanta za ta yi, farin cikinta kawai za ta duba! Kowa ya yi ta kansa….inshaaAllah sai ta mallaki Yashjub ko ta halin yaya ne, daga nan za ta nunawa Mommy wacece Kausar, sai ta san ta yi betraying d’inta, wallahi daga kanta ko d’an aiki ba za ta sake cin amanarsa ba.” Tana wannan lissafin ta fito daga toilet d’in…a d’akin ta tarar da Yasira, cikin rashin kwarin jiki Yassirar ta mik’e ta k’arasa ta ruko hannunta kafin tace “Kausar na zo ne akan in yi miki gargad’in ki bi Yassir a hankali, kar ki bari ya fahimci wani abun, saboda gudun kar yaje ya yi miki kwab’a. Dan yadda ya yi miki d’azu a asibiti ni kaina na d’an tsorata gaskiya” da “to” kawai Kausar ɗin ta bi ta, daganan Yasirar ta juya ta fita dan ta fahimci kamar Kausar d’in ta na buk’atar sarari. Tana fita Kausar ta girgiza kai a ranta tace’’kwab’a kuma ta nawa?bayan abunda ya aikata,’’ wannan shine karo na biyu da ya so ya kashe Yashjub kuma ta lura Mommy ma ta fahimci wani abun amma ta ga kamar k’ok’ari ma take yi ta b’oye… A hankali tana jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa ta nemi guri ta kwanta. Lumshe idanuwanta ta yi atake hawaye suka shiga sintiri a kan farar fuskarta!!! Wannan wacce irin rana ce ta risketa?…ga ciki tana d’auke da shi, ga Mommy wadda ta juya mata baya ga kuma Yassir wanda take zargi da wannan shirmen a karo na biyu, sannan bata Isa ta tunkare sa da maganar ba, dan ba ta so ya fahimci wani abun… Sannan ga rayuwar Yashjub dake a cikin hatsari, ga Manubiya, ga shi Yashjub d’in ma kansa har yanzu ta kasa samun sa! ta Ina za ta fara ne? dan abubuwan sun yi mata yawa….. K’arar bud’e k’ofar d’akin nata ta ji da mugun k’arfi, dan haka ta tashi a d’an rikice duk da kuwa da ma ta riga ta san waye ne. A tsaye a bakin k’ofar ta gansa yana huci, kafin ya juya ya rufe k’ofar ya murza key tukunna ya nufota gadan-gadan… Duk tsaurin idon Kausar sai da ta tsorata, dan haka tun kafin ya k’araso ta mik’e tsaye tana mai gyara doguwar rigar jikinta ta hau inda inda cikin in’ina tace’’Yassir I’m sick dan Allah ka bar….’’ Mahaukacin marin da ya d’auke ta da shi ne ya sanya ta gagara k’arasa maganar tata, sai da numfashinta ya d’auke na y’an seconds tsabar tsananin shock d’in da ta shiga, a rikice ta d’ago fuskarta wadda ta yi jajir sannan ga shatin y’an yatsunsa sun fito rad’o rad’o a fuskar tata tace ‘’Yassir ni ka mara??’’ Cikin karsashi yace‘’somin taɓi ne ma wannan ɗin, kar ki damu, in kinga dama ki bari in yi miki tambaya ki yi mini k’arya…’’ Ya fad’i hakan yana mai kunce belt d’in wandonsa. Cikin fushi tace “dukana za ka yi?baka da hankali ne? Duk abubuwan da ka yi basu ishe ka ba???’’ Dakatawa ya yi daga nad’e k’asan belt d’in da ya ke yi around his fingers, kafin ya d’ago jajayen idanuwansa ya zuba su akanta tukunna yace ‘’abubuwan da na yi?me da me na yi kenan?’’ Ya fad’i hakan cikin matsowa daff da ita yana mai tsare ta da dara daran idanuwansa waenda suka yi jaaa!!! hatta fuskarsa ta yi jaa tsabar bala’i. Ahankali ta d’an ja da baya dan a mugun tsorace take dashi! Sai da ta d’an kauda kanta gefe tukunna ta yi k’asa da murya tace’’ Wallahi zan tona maka asiri,in har ka tab’a lafiyata sai kowa ya san kai ne ka tura y’an fashi estate d’in Yashjub yau’’ Cak!haka ya k’ame, kafin ya sa Hannu ya juyo da fuskarta cikin karsashi yace ‘’Kausar ni za ki yi wa sharri da borin kunya saboda kinga na kama ki dumu-dumu?’’ Ganin yadda jikinsa ya yi sanyi kuma ta ga ta d’an samu galaba a kansa ne yasanya ta fincike fuskarta tace’’ba iya wannan ba ma, Wallahi har tayar motarsa da ka cire kwanakin baya sai na fad’a kowa ya ji, tunda dama son da nake yi maka ne yasanya nake rufa maka asiri amma in har zaka iya d’aga Hannu ka mareni to na san ka daina sona dan haka nima ban ga amfanin ci gaba da son ka Ina bin bayanka ba,’’ Ta fad’i hakan tana mai rushewa da wani uban kuka wanda yayi tsananin tasiri akan Yassir. Ganin kamar so take ta bugi cikinsa sannan kamar wayo take so ta yi masa ne yasanya ya dake yace’’ke!Kausar bana son hauka da shirme da sharri…idan ba so kike in yi miki fiye da abunda na yi niyyar yi ba to kawai ki bani amsoshina da na zo k’arba, mu yi ta ta k’are. ‘’How dare you! Ta ya ma za ki k’ala mini sharri wani wai ni Ina so in kashe Yashjub! baki da hankali ne?kuma wa kike tunanin za ki gayawa wannan maganar ya yarda?. bari ki ji ko Mommy idan kika gayawa wallahi ba za ta tab’a yarda da ke ba, za ki sha mamaki idan ta juya miki baya har abada, dan babu uwar da za ta yarda wata tazo ta ce mata d’anta yanaso ya kashe d’anta!’’. Goge hawaye Kausar ta yi ta d’ago ta fuskance sa tukunna tace’’Yassir cewa na yi ‘zan fad’awa kowa kaine ka cire tayar mota sannan zan fad’awa kowa kaine ka tura ƴan fashi estate d’in Yashjub’. A kaff cikin maganata ka ji ta inda nace ‘kana so ka kashe Yashjub’?’’. Cikin fushi hargagi da hargowa yace’’Kausar zan illataki fa! ni za ki yi wa wasa da tunani? ai indai aka ji kince na cire taya to an san kashe sa nake son yi kenan!’’ Tsit!haka muryarsa ta tsaya chak!yana mai recalculating (son fahimtar) abunda ya gama faɗa yanzun a cikin kwakwalwarsa’’ Kafin ya yi cilli da belt d’in hannunsa tukunna ya d’aga hannu kamar zai damk’i wuyanta, kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya tsaya chak!! kafin ya juya mata baya yana wani irin huci kamar mayuncin zaki…. Wata bahaguwar ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e kafin ta d’an matsa garesa tace’’ Bari kaji abunda baka sani ba! Ko da ace Mommy bata tab’a shiga aji ba,wallahi ba zan yi kaffara ba itama ta d’an fahimci wani abun,sakamokon yadda ka dinga k’ok’arin tonawa kanka asiri tun a crime scene d’in,har sign na dinga yi maka da ido amma sam ka kasa fahimta….. Shiyasa ka ga hankalina ya tashi raina ya b’aci, ga kuma rashin lafiyar da take damuna,’’ Ahankali ta sake taku d’aya ta kamo hannunsa ba tare da ta zagaya gabansa ba ta ci gaba da cewa’’ranar a d’akinka na gaya maka ina tare da kai a ko yaushe, Yassir tunda har na iya danne zuciyata na had’a ka da Munirat inaso ka san na d’auki mission d’innan (aikin nan) da mahimmanci, duk da na san cewa kashe Yashjub ba ya cikin tsarinmu amma idan har ka gaya mini dalilinka zan goya maka baya, kai ko da ace ba za ma ka gaya mini dalilin naka ba Yassir zan goya maka bayasaboda ina sonka kuma ina so in ga ka yi nasara akan komai, kai kuma a ko da yaushe kamar baka yarda da ni ba shiyasa ban san ta ya zan nuna maka ina son naka ka yarda da ni da gaske ba, da ace na san taimakon ka da muka yi da ni da Mommy zai janyo mini haka daga gareka da ban yi ba tunda na lura tun lokacin da na d’an ja baya da kai saboda mu samu a fasa aurenmu a k’ara maka share har gobe baka yarda da ni ba Yassir’’ Ta k’arashe maganar tana mai durk’ushewa a wajen ta fashe da kuka. Ahankali Yassir ya sauk’e ajiyar zuciya, tashi d’aya ya fara ganin rashin kyautarwar sa,ta ya ma zai kasa yarda da Kausar bayaga dukkan abubuwan data gayamasa da irin gogayyar da take yi wajen ganin ta taimaka masa,shi sai yanzu ma kwakwalwarsa ta d’au charji amma kwanaki da d’azu gaba d’aya duk kishi ya rufe masa ido, tabbas everything is fair in love and war!’they are at war’ dan haka komai is fair kamar yadda ta fad’a dan ta had’asa da Munirat saboda su samu su cimma abunda suke so bai kamata ya dasa ayar tambaya a kanta ba wanda hakan ne farkon zargin nata da ya fara,tunda in komai ya yi daidai ya tafi yadda suke so ai sune da nasara. Ahankali ya juyo yana jin tsananin tausayi da k’aunarta suna ratsa sa ya ce ‘’stand up’’ A ranshi yana mai cewa “inshaaAllah zai yi k’ok’ari ya goge tunanin’watak’il Kausar tana son Yashjub’ daga cikin zuciyarsa. Amma a karo na ƙarshe akwai abunda yake son ya tabbatar ta yadda zai yarda da ita d’ari bisa d’ari. Ganin ta k’i tashi ne ya sanya shi ya durk’usa ya kamota ya d’ago da ita tashi d’aya ya sakata a jikinsa yana mai bubbuga bayanta alamun rarrashi,sun jima a haka sai da ya ji ta yi shiru tukunna yace “Kausar tambayar da zan miki na ƙarshe….na ga kina kuka sannan na ga hankalinki ya tashi kuma muna shiga da kika ga Yashjub da Manubiya kika juya za ki fita wanda hakan yana nuni ne da ba za ki iya jura ba ba zaki iya ganin su a haka ba kenan!,inaso ki faiyyace mini dalilin reaction d’inki ta yadda komai zai tafi daidai a tsakani na da ke.” Da d’an fushi sakamokon tuno mata da abunda ya fi komai d’aga mata hankali da yayi tace “Yassir bani da lafiya, amai nake ji shiyasa na yanke shawarar in tafi” Kallon ta ya yi kafin yace’’amai kuma?….wanne irin rashin lafiya kike yi da zai baiyyana kishi da b’acin rai a kan fuskarki?ko dai ba zaki iya jurar ganinsu…’’ Turesa ta yi da dukkannin ragowar k’arfin da take ji tukunna ta juya a fusace ta nufi toilet…bin ta shima ya yi dan bai gama da ita ba tukunna. Tana d’auko pts d’in ta juya za ta fita suka yi kicib’is da shi, kallon sa ta yi ta kamo hannunsa ta damk’a masa still tana kallon cikin idanunsa tace “Bani da lafiya!” Had’e girar sama da k’asa ya yi kafin ya d’ago abunda ya ji ta saka masa a cikin hannunsa,sai da ya kai hannun nasa saitin fuskarsa kafin ya janye idanunsa a cikin nata ya mayar kan tsinken. Da mamaki k’arara kwance a kan fuskarsa yace “What!!” Sai kuma ya kalleta yace “Tayaya?” Cikin fushi tace “Kut!!!tambaya ta ma kakeyi ‘Tayaya??’.“ Tsabar takaici kasa ma cigaba da tsayuwa tayi dan haka ta bangaje sa ta wuce. Lumshe idanunsa yayi ya furzar da iska, kafin ya bud’e ya juya da sauri ya bi bayanta. Har ta kusan kaiwa bakin k’ofar d’akin nata, dan haka ya bi bayanta da d’an gudu ya cafkota ya juyo da ita. Takaicine ya sanya ta fashewa da wani sabon kuka gwanin ban tausayi. Tashi d’aya jikin Yassir ya sake yin sanyi,bai ma san lokacin da ya janyota ya sake rungume ta ba,yana mai jin tausayi da k’aunarta. Cikin muryar rarrashi yace “Haba Kausar,sai kace wata k’aramar Yarinya? kar ki damu kanki mana, kawai kamar na wanchan karon wannan d’in ma za mu san yadda za mu yi da shi,plss ki daina kukan nan.” Cikin kuka tace”Yassir ka cuceni! Shikenan ni na zama sarauniyar zubar da ciki kenan??? kaf gidan nan a kaff cikin y’an uwanka mata ko ɓatan wata babu wadda ta tab’a yi amman ni k’iri k’iri ka maidani karuwar k’arfi da yaji!! saboda ni ba y’ar uwarka baceba ko? Idan nace ‘A’a’ kuma ka dasa ayar tambaya a kaina.” Kamar zai yi kuka yace “Not at all Kausar,kawai dama ina tunani ne….” shiruu ya yi sai kuma yace “Shikenan Na yarda dake yanzu na fahimci komai komai kuma ya wuce,na yarda da ke daga yau inshaaAllah” Turesa ta sake yi tana kuka kamar ranta zai fita da kyar ta iya cewa “Yassir Me kake zargina da shi a da ɗin?” Sake ruk’ota yayi cikin sigar lallashi yace “Na fad’a miki ki manta kawai” A karo na uku ta sake turesa itama tukunna tace “Dole fa sai ka gaya min, me kake tunani a kaina da! Bayaga tunaninka na bana sonka ba na kishin ka?akwai wani abun, menene shi?” Runtse idanunsa yayi ya d’an sunkuyar da kansa tukunna ya d’ago ya furzar da iska ya bud’e idanuwan nasa sannan yace “Okay fine! Da Ina tunanin kamar kina son Yashjub ne.” Da k’arfi tace “What(me)?” sai kuma ta sake fashewa da kuka kafin ta sa hannu ta kamo sa sai da suka isa k’ofar d’akin ta murza key ta bud’e tukunna tace “Get out Yassir! (Fice min a ɗaki Yassir) Tunda dak’ik’in tunaninka da kishi sun rufe maka ido, ba na jin akwai abunda zan gaya maka kuma ka yarda da ni.ka je ka yi tunanin duk ma abunda ka ke so, ban damu ba, tunda duk bayanin da na yi maka ranar a d’akinka ba ka yarda ba!!. Hatta sirrin da Mommy ta gaya mana wanda ba kowa ake so ya ji ba duk sai da na gaya maka..amma shine still ba ma ka yarda da ni ba?? shikenan!! Ba komai.” Ahankali yace “Kausar” Cikin fushi tace “trust yana da matuƙar mahimmanci Yassir…. taya ma za ka yi wannan tunanin a kaina?. Baka san yadda ka ɓata mini rai yau ɗinnan ba!. Ka fice mini daga ɗaki kawai” Matsowa ya yi da sauri yai hugging d’inta yasa k’afa ya tura k’ofar ya rufe. Ba yadda ba ta yi da shi ba amman sam ta kasa kwatar kanta,dan haka ta sake sakin wani kukan kawai… Lallashinta ya shiga yi a chan k’asan zuciyarsa kuma yana daya sanin zarginta da yayi… Sai da ya ji ta d’an yi shiru tukunna ya cikata ya ce”na yi laifi, a karo na farko gashi na yi yarda na karɓi laifina kuma na yarda na yi miki laifi, ki yi hak’uri. InshaaAllah ba zan sake ba, sannan daga yau ba zan sake dasa ayar tambaya a kanki game da komai ba I promise!. Duk abunda kika yi kawai zan yarda dake ne, ko ma menene. Pls Kausar ki yafe min” Ya fad’i hakan ya na k’ok’arin durk’usawa. Da sauri ta rikesa ta d’an girgiza masa kai…sake yunk’urawa yayi zai durk’usa dan haka tace “Ya wuce, ba komai” Ahankali yace “thanks love..sosai sosai” Sai kuma ya d’an kalli shafaffen cikinta yace”mu zauna sai mu yi magana ko?” Jinjina kai kawai ta yi daga haka ta wucesa ta isa bakin gadonta ta zauna Tana zama shima ya zauna Ba tare da b’ata lokaci ba yace “Yaushe kike so mu je asibitin??” Sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna tace”ba zan je asibiti ba,idan cikin ya kai wata biyar sai in fara zuwa awo InshaaAllah” Da sauri yace “Kausar pls kar mu yi haka da ke mana! Wacce irin magana ce wannan??” Girgiza kai ta yi kafin tace “Yassir ba zan iya yin wani abortion d’in ba fa,ai ka ji dai da kunnenka abunda Doctor yace mana the last time ko?…ko kana so mahaifata ta lalace tun kafin na fara tara iyali?? Bayaga haka ma ai ni na sha gaya maka dama a ko da yaushe ba son rabuwa da babyna nake yi ba, hak’uri kawai nakeyi ina biyeka.” A hankali ta kamo hannunsa ta d’aura a kan cikinta tace “wannan babynmu ne, kasancewarsa jininka ya sa na ji Ina matuk’ar k’aunarsa , saboda tsananin son da nake yi maka, ba zan iya rabuwa da shi ba,wallahi ban tab’a jin so da k’auna bayan wanda nake yi maka ba sai a kan cikin nan!” Damk’e hannunta ya yi da k’arfi dan ba kad’an ba maganganunta sun shige sa sun yi tsananin tasiri sun kuma ci galaba a kansa. Ya jima maganganunta suna ratsa sa kafin a hankali cikin kwantar da murya yace “Kausar!! Daddy will kill me Mommy ma Allah kad’ai ya san mai za ta ce…me” Cikin katseshi tace “Kanka kawai ka ke dubawa??” Da sauri yace “Haba dai,a’a mana.. Baby kema ina duba ki mana, ban san wanne kallo duniya za ta yi miki ba!sannan kema ba wai sauk’i za ki samu daga wajen su Daddy ba. Kinga dama da ni da ke muna da bak’in jini a wajen Daddy, idan ya ji wannan batun ban san mai zai yi mana ba. Ke da kanki kince 1% kawai gareni,na tabbatar idan Daddy ya ji wannan batu tou kashina ya bushe Ni da shi babu taimako babu zaman lafiya daganan har abada Wanda idan hakan ta faru Yash ne zai ci gaba da zama a sama… Tayaya kike tunanin zan kula da ke da Baby idan hakan ya faru? Kausar companies na wannan ɗinma sai a hankali, sannan a wajen Daddy ma 1% gare ni,idan muka haihu Ba tare da mun tsaye da ƙafafunmu ba ya kike so Babyn namu ya rayu?? Ina sonki sannan nima inason cikin nan amman Yakamata mu fara tabbatar da muna da shiri sannan mun tanadi kyaakkyawar rayuwar da za mu bashi kafin mu yanke shawarar kawosa duniya”. Shiruu duk sukayi, kafin chan Kausar tace”Yassir na san abunda zan yi amma har yanzu bani da tabbacin ko ka yarda dani d’ari bisa d’ari…” Ahankali yace”Kausar mun rufe maganar nan fa!na yarda da ke mana” “Ka tabbatar?” “Na tabbatar“ Ya bata amsar yana kallonta sannan ya d’aura da cewa “Na fad’a miki na riga na yarda da ke Kausar,kawai dama inaso in tabbatar ne shiyasa na sake yi miki wachchar tambayr amman tun shigowata cikin d’akin nan da kika fara yi mini maganar farko tashi d’aya na yarda dake.Baki ga ban yi miki denying batun estate da cire taya ba?ko so kike in fito miki ƙiri ƙiri in miki confessing..in ce miki ni ɗinne??” Ba tare da ya jira jin mai zata ce ba yace ‘’ok fine, i did it… ni ne na yi duk biyun”’ “Shin in da ace ban yarda da ke ba kina tunanin zan fad’a miki haka ne?” Ahankali ta sauke ajiyar zuciya tana ji inama ta saita record a lokacin da yake confession d’innan, da ta ajjiye a matsayin shaidar da za ta nuna ta tura shi prison bayan ya gama taimaka mata ta auri Yash…but with time inshaaAllah kafin ya gama taimaka mata amfaninsa ya k’are a wajenta za ta san yadda za ta yi ta sanya shi ya k’ara confessing!” Ahankali ta gyara zamanta ta fuskancesa sosai tukunna ta fara magana “Yassir Inaso ka cire kishi da duk wani tunani marar kyau a kanka, ka duba future d’inka, sannan Ina so ka san cewa ko ka yarda da wannan shawarar tawa da zan fad’i maka yanzu ko baka yarda ba ni dai ba zan tab’a zubar da cikin nan ba. Akwai hanyar da za mu bi mu haifi cikinnan ya rayu cikin farin ciki…kuma inaso ka san cewa hanyar itace silar warwarewar duk wani k’uncinka, amma dole mu tsaya akan raayi ɗaya sannan mu yarda da juna, kafin komai”. Jinjina kai yayi alamun yana jinta kuma yana fahimta. Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya tace”ka ce Daddy zai ji haushinka zai yi fushi da kai watak’il harabada idan har ya ji maganar cikin nan ko??” Jin jina kai kawai yayi “Good! Me kake tunanin zai faru idan Yashjub ne a matsayinka??” Da k’arfi yace “What!!tayaya??” “Kwantar da hankalinka!!! Abunda na ke nufi shine ‘me zai hana mu yi framing ɗinsa… mu yi masa sharri?’!. Ka ga na farko Ni kaina Daddy zai ji tausayi na, sannan zai yi fushi da Yashjub, Kuma mafi mahimmanci zai shirya da kai ya janyoka a jikinsa sannan idan Yashjub yana tunanin wannan cikin nasa ne to tsaf za mu yi amfani da hakan mu samu abunda mukeso” Shiruuu kawai Yassir ya yi ya dafe kansa kafin chan ya d’ago ya kalleta tukunna yace “Taya za ki yi hakan?? Taya hakan zai faru ??” “Good Bari kaji matakin farko” Ahankali ta matso ta zaiyyane masa komai… Da farkon murmushi ya fara yi sai kuma ya mik’e tsaye yace “Inaa! Kai!!! no ba zai yiu ba.” Mik’ewa ta yi itama ta rik’e hannunsa cikin son fahimtar da shi tace “Babu abunda zai faru a tsakaninmu” “Eh na sani mana, kawai dai the fact that za ki kwanta waje d’aya da shi kuma a yanayin da ki ka faɗa ɗinne gaskiya, inaa Kausar ki kawo wata basirar gaskiya banda wannan.” Murmushi ta yi tace “Yasir a lokacin da abun zai faru fa ba ma ya cikin haiyyacinsa ballanta ma ya gane komai. Kuma hakan ita kaɗai ce hanyar da za a iya kamashi dumu dumu… Kar ka bari kishi ya rufe maka ido mu kasa cimma burin mu mana.” Shiruu ya yi kafin yace “Kausar,ta ya zan bayar da d’a na a wani? Tunda idan fa kika haihu kowa Yashjub zai ce shine uban Yaron..ta yaya zan karɓa haƙƙina a matsayin uba?” “Yassir ko wanne family suna da nasu sirrin, dan haka ka bari wnanan ya zama namu (da ni da kai).. Ka duba ka ga fa sau biyu kana ƙoƙarin kashe Yashjub amma hakan bai yiu ba, kuma dukiya har yanzu tana hannunsa, a gani na don ka hak’ura wannan Yaron ya zama nasa na shekara d’aya ko months mun samu da dabara da sharri da abubuwa komai ya dawo hannunka, hakan ya yi dai dai kenan ai… A da kai kad’ai ne ka ke ta had’a shirinka kana faɗuwa yanzu kuwa zan taimaka maka, dan haka na san za mu yi nasara. Idan Daddy ya ga Yash ya mutu ga kuma jaririn Yaro mara gado bani da tantamar tashi d’aya Daddy zai tartara komai ya saka a sunan Yaron kar ka manta yadda Daddy ya ke ji da Yashjub!!! A ganina dan wani abu ya shiga tsakaninsu sun yi fad’a ya daina kulasa ba shi zai sanya ya k’i son d’ansa bayan mutuwar sa ba. Ka fahimce ni Yassir nasara ce atare da mu ta ko wacce kusurwar shirin nan namu fa…kaga Yaro dai yana hannuna kuma kai zan aura a ƙarshe komai zai zama naka, Yashjub ya tafi sannan Yaro kuma ya taso a hannnun iyayensa, mu kula da shi mu haifi k’annensa ya taso cikin ahalinsa,mai ya fi wannan riba??” Shiruu Yassir ya yi kafin yace “Amma idan kuma ita wachchar matar tasa ta haihu kinga mun yi 2 zero ko?dan kowa d’anta zai kwallafawa rai na san. Tunda zuwa yanzu kamata ya yi ace ya mutu! ta yadda zan ga bayan cikin amma ya k’i mutuwa, kuma a yadda yake gadinta d’innan ni ko ke bamu isa zuwa ko da kusa da ita ba ballantana mu yi wani abun…. Murmushi Kausar ta yi kafin tace”kar ka tambayeni dalili sannan kar ka tambayeni tayaya,kawai inaso ka cire batun cikin Manubiya a lissafi, dan wallahi ba ta isa ta haihu ba…kawai ka yarda da ni idan na ce maka cikin nan ko wata ɗaya bai isa ya k’ara a jikinta ba….” Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace”na yarda da ke Kausar.” Murmushi ta sake yi tukunna tace”na gode..na san maganin da za mu yi wa Yash amfani da shi, zan rubuta sunan sai mu je tare da ni da Yasmeen mu siya, amman ita kanta ba zan bari ta gane menene ba kawai zan ce mata wanda ya ke sakani bacci ne akai mini recommending (aka chanja min) sabo. Za ta nuna id card d’inta mu siyo maganin saboda ba za su tab’a bani ba ni, dan yana da masifar ƙarfi.” Kallonta yayi sai kuma yace “Da wuri haka?” D’an zaro ido ta yi kafin tace “Yassir tou sai yaushe? Ai ba wai yanzu yanzu ba amma inaso komai ya zama a tanaɗe ta yadda Ina ganin dama ta samu komai zai kammala. Manya manyan jajayen layukan da suka fito B’aro B’aro a kan tsinken nan ya na nuni da cewa cikin nan ya kwana biyu a jikina, Idan ba da kyar ba ya fi wata ɗaya. Kuma kaga idan ma zan ce inada ciki sai fa kamar irin nan da 2 weeks haka, bayan mun samu abun ya faru.… Shiruu yayi kafin chan yace “Okay kausar. duk yadda kika ce, hakan za a yi”. Murmushi ta yi kafin ta rungumesa tace “na gode Yassir. Na gode sosai da ka yarda da ni kuma ka fahimceni, na ji daɗi” A ranta kuma tace”Ashe ba ka da wayo…wannan shiri na farko kenan wanda dole da kai za’ayi, shirina na biyu kuwa ni kad’ai zan yi abuna, dan ana tabbatar da cikin nan to auren Yash ba zai zama abu mai wahala a gareni ba, sai dai kawai ka ji a salansa… Ya zama dole nima in nemi farin cikina in tsayawa kaina kuma in bawa Yash kariya daga sharrinka…….” ‘Tabbas ya fahimci Kausar kuma ya yarda da plan d’in dan akwai nasarori a tattare da plan d’in…..sannan zaifi jin dad’i idan Yash ya mutu da tabo da mugun suna.” Yassir ya aiyyana hakan a cikin ransa yana mai sake saka ta a cikin jikinsa ••• Yashjub yana fita,d’akin ya rage daga Manubiya sai Yahanasu….a hankali Yahanasu ta mik’e ta k’araso inda take ta zauna a gefen gadon tukunna tace”me zan zuba miki??” Zama Manu ta gyara ta ruk’o hannun Yahanasu kafin tace”Adda Yaha Ina buk’atar taimakonki” Shiruu Yahanasu ta yi ta d’an k’ura mata ido dan kamar ta fahimci mai za ta ce,kafin da kyar tace “anything! Manu..” Ahankali Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace”lokacin da aka kwancewa Ya Yash tayar mota kin san shi da kansa ya san kashesa ake so a yi ko?” Ba ta jira jin me za ta ce ba ta d’aura da cewa”wannan karon ma kinga abunda ya faru ko? amma na ga kamar ba ya so na sani shiyasa nima ban nuna masa na sani d’in ba saboda inaso in taimaka nima kuma na san ba zai barni ba…. Adda Yaha ba zan zauna in zuba ido in nad’e hannu ana wasa da rayuwar Mijina ba….” Hawayen da suka zobo mata ne ya sa Yahanasun ta matso ta shiga goge mata fuska kafin da kyar ta samu ta iya cewa”yanzun ma haka kike zargi ko!nima yanayin yadda na ga abun gaskiya dama na san hakan ne…” Cikin jan hanci Manubiya ta zaiyyane mata abunda Yasira ta ji mutanen suna fad’a da suka shiga gidan k’awarta. “Innalilla wa inna ilaihirrajiun” Yahanasu take ta maimaitawa,tana jin gabanta yana wani irin bugawa.. Addu’arta d’aya Allah ya sa babu hannun Mommy a lamarin nan, dan tabbas itakam za ta taimakawa Manubiya, za su tsaya tsayin daka har sai sun gano gaskiyar lamari an kuma hukunta mai laifin kashe mutanen nan, Dole a tabbatar da adalci. A nan a take suka fara shirye shirye, kuma suka yi alk’awarin ba za su bari Yash ya sani ba, dan sun san zai yi yunk’urin ya hana su musamman ma ita Manu da a yanzu ba shi da wani burin da ya wuce ta yi ta hutawa kawai…. Dama Yahanasu tana da connections ɗinta kasancewarta lawyer, dan haka tun a lokacin ta shiga yin waya da mutane daban daban aka fara shirye shiryen matakin farko…… Yashjub ma sai chan dare ya samu ya dawo….Yahanasu ta wuce gida shi kuma ya nema waje ya zauna ya ruk’o hannun Manubiya….bai so Manubiya ta sani ba gudun kar ya d’aga mata hankali amma kuma ya yiwa kansa alk’awarin ba zai sake b’oye mata komai ba tun lokacin da su Yasira suka kusan had’a masa bomb da zancen Kausar,dan haka ya shiga zayyane mata yadda duk abunda ya faru da binciken da suka fara tun a yau…da ikon Allah cikin nasara cctv ta ɗauki abunda ya faru yau ɗin tun shigowar y’an ta’addan har fitarsu, kuma mutane biyu ogannnin cikinsu babu mask a fuskokinsu, sannan an shaida guda d’aya dama ana neman sa dead or alive…dan haka yanzu mataki na gaba da suka d’auka shine na kama wannan mutumin, dan ta wajensa ne kawai za a gane waye ya turosu, a ji komai dan muddin suka kamasa to kalar interrogation d’in (binciken) da za su yi masa dole ma ya fad’i gaskiya……. Shiruuu Manubiya ta yi, jikinta duk babu dad’i….kusan matakin da ita da Yahanasu suka d’auka shi su Yash d’in suma suka d’auka amma su sun yi nisa dan ita da Yahanasu ko binciken cctv d’in ma ba su kai ga yi ba…. yadda ta ji ya ce ‘ba ya so ya b’oye mata komai’ Ya sanya itama ta fara k’ok’arin gaya masa shirinsu ita da Yahanasu amma sai ta ji yana cewa”dan Allah dan annabi ki kwantar da hankalinki,ba na son ki yi komai..ba dan bana son b’oye b’oye a tsakanin mu ba to da ba zan gaya miki ba, dan haka dan Allah ki kwantar da hankalinki ki kular mun da ku..inshaaAllah komai zai yi dai dai,ok?” Ajiyar zuciya ta sauk’e,a take ta fasa gaya masa saboda har ga Allah tana son ta taimaka dan haka kawai sai ta jinijina kai a hankali ta rungumesa… Ba dan Yash ne da kansa ba to da babu abunda zai sa Doctor ya bar Manubiya ta fita ba tare da ya sallameta ba…sai da ya sake dubata tukunna suka tafi dubo Baba ita da Yashjub… Had’add’en private hospital mai kyau da tsada Yash ya kai sa, dan har ya ma fi na family Doctor d’insu, inda Manubiyan take kwance. A harabar asibitin suka tarar da Jidda a tsaye ta kauda kai gefe da wani, sai da suka k’arasa tukunna suka fahimci ashe Ya Yusuf ne… Da mutuntawa suka gaisa shi da Yash kafin ya kalli Manu itama ya gaida ita daga haka ya yi musu sallama ya tafi… Yashjub ne ya iya amsashi dan daga Manubiya har Jiddan babu wanda ya tanka masa, ita Jidda haushi da tsanar sa ne yasa tunda suka fito ba ta ce komai ba, Manubiya kuwa tsantsar mamaki ne ya hanata yin magana dan ba ta yi tsammanin ganin Yusuf da Jidda a tare ba. Sai da Yashjub ya rakasu bakin k’ofar d’akin tukunna ya juya bayan yace “su shiga zai je ya d’an siyo abu, idan ya dawo sai ya ga jikin Baban su wuce..” Da “to”suka amsa shi, daga haka ya wuce…ko gama fita daga corridor d’in bai yi ba Manubiya tace”Jidda me kike yi da Yusuf a waje???” Numfashi Jidda ta fesar kafin tace”Baba ne ya ce in rako sa…” Kukan da ya taho mata ne ya sa ta yi shiru ta fara kokawar dannewa..cikin rashin jin dad’i da rashin fahimta Manubiya tace “Jidda ai da sai ku tsaya a nan da kika fito ya wuce ke kuna ki juya, meye naki na yi masa rakiya har chan waje?? Jidda Yusuf ne fa!!!” Cikin sauk’e ajiyar zuciya tace”da ya zo ya gama dubiyar ya tashi tafiya shine ya kalle ni yace wai ‘ba rakiya? ‘In zo in rakasa’! a gaban Baba da Inna tsabar ba shi da tarbiyya.Sai da ya fad’a sau uku tukunna Baba ya kalle ni yace”mu raka sa da ni da Muhsin, amma muna fitowa ya cewa Muhsin d’in ya koma ni kuma ya kamo hannuna ya jani kamar wata kayan wanki saboda ya ga Ina shirin komawar, ko da muka fita da na fara k’ok’arin juyawa gani na yi yana shirin runguma ta shiyasa na tsaya kawai. Tsabar rashin sanin darajar manya saboda Allah adda Manu ta ya Baba zai ce mu rakosa amma ya kora Muhsin.” Cikin rashin Jin dad’i Manubiya tace”kuma wai a haka ace Baba ba ya ganin laifin Yusuf??” Ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin cikim share fuskarta tace”yana gani fa! kawai kawar da kai yake yi wasu lokutan saboda gudun magana, amma ni na san yana gani…ba ki da lafiya ne shiysa ban gaya miki abunda ya faru ba….kin san tunda ya yi kud’i ba shi da Aboki sama da Kaka mallan, to shekaran jiya Kaka mallan d’in ya nemi ganin ya Nafi’u da ya musbah, Ya musbah bai je ba sai ya Nafi’u,shine fa tsabar rainin wayo kaka mallan d’in yake ce masa wai ya fad’i ko nawa yake so su basa ya saka baki a yi aurena da Ya Yusuf, wai duba da abunda yake ta faruwa a tsakanin Baba da su Baba habu ya san Baba wataƙila ya chanza ra’ayi dan haka Ya Nafi’u ya yi faɗi ko nawa su bashi ya shawo kan Baba. Shi kuma kaka mallan zai tsayawa Ya Yusuf ko su Uncle ba su yarda ba a d’aura.” Cikin takaici Manubiya tace”kutt me ya ce masa shi kuma?” “Kema kin san ai ya Nafi’u ba zai yarda ba…wane tudu wane gangare suka bi daga haka dai hayaniya ta fara tashi, shine fa akayi fad’a da ya Nafi’u da kaka mallan har da Uncle a case d’in wanda daga jin hayaniya ya afka parlourn ya yi ruwa ya yi tsaki.To dai daga k’arshe Baba ne ya je ya raba da kyar ta hanyar janye ya Nafi’un …shine fa cikin dare wajajen k’arfe d’aya kamar waenda aljanunsu suka tashi haka kurum Uncle ya zo ya shigo har cikin d’aki wai Baba ya zab’a ko su ko ya Nafi’u,saboda ba zai you Yaro ya yi musu rashin mutunci ba kuma ya ci gaba da huld’a da shi yana shigo musu cikin gidan ba. Haka nan dai suka yi ta hayaniya wallahi kamar mata daga k’arshe Baba ya ja bargo ya kwanta kawai ya rabu da su,shine suka yanke mana wutar d’akin da na d’akin Muhsin kuma suka d’auko wasu takardu wai d’akin Muhsin d’in ma rushesa za su yi filin rabi ne na Baba rabi kuma nasu…a ranar babu wanda ya runtsa.Ya Yusuf dai shi yake ta k’ok’arin hanasu Anty Umma ma har kuka ta yi tana lallab’asu tana so ta ga an rufe case d’in amma sai tujara suke yi kaka mallan yana gefe yana mana gori kala kala..har da cewa ya Musbah ya gudu ya barmu,kema wai an bi kwad’ayi an aura miki mai kud’i gashi ba ya tsinana mana uwar komai ko kwayar shinkafa bamu da ita rabon da ya ga mun yi girki har ya manta,wai dama shiyasa ya ke so a aurar da ni a Ya Yusuf, a samu ya rufa mana asiri, ya dinga ciyar da mu amma mu kuma mun k’i yarda.” Mun d’auka maganar d’akin Muhsin fad’i kawai suke yi ashe su sun d’auki abun serious dan da muka zo duba ki bricklayers suka nemo wajen mutun shidda suka nuna musu d’akin aka fara rushewa…Baba yana d’aki sai jin rushe rushe ya yi da hayaniya…..baya so ya kula su, dan yace tun sati biyu baya da suka shige ya lura kawai neman masifa suke yi da shi, shiyasa ya k’i fitowa, ya tsaya a d’aki, ya yi ta kiran Ya Musbah, shi kuma ya k’i d’auka to inaga bak’in cikin hakan ne ya sa muka shigo muka tarar da shi a sume…… “Innalillahi wa Ina ilaihirrajiun” Manu ta ke ta maimaitawa, kafin ta share hawayenta, ita ta ma rasa bakin magana, chan tace”kuma har yau bai zo ba?” Jinjina kai Jidda ta yi alamun “eh”kafin tace “inna tace mini d’azu da na fita siyo mana abinci ya kira Baba ya yi masa ya jiki, inaga message d’in da na yi masa ya gani sannnan ya ce gobe zai zo….” A hankali Manu tace”da ke da Muhsin mu je gidana mana kafin mu ga yadda hali zai yi su Inna kuma tunda suna nan to basa cikin haɗari dan gaskiya Jidda ba za ku koma gidan nan ba, abun ya yi yawa an kai ƙololuwa!” Murmushi Jidda ta yi cikin jin tsananin tausayin kansu tace”Adda Manu kin manta su waye dangin mijin naki ne?ai kema kin san zaman mu a cikin gidanki ba abu mai yiwuwa bane ba….” Shiruu duk suka yi kafin Jidda ta sake cewa”Ya Yusuf dai tunda ya zo ya ke ta bada hak’uri, kuma ya kawo takardu wai ya siye mana gaba d’aya filin daga wajensu har ya kira an fara gyarawa….. To dai wannan karon gaskiya Baba ya zuciya dan tunda Ya Yusuf ya zo bai sake da shi ba, daga amsa gaisuwa ya ja bakinsa ya yi gum!Inna ce ma ta d’an saurare sa kad’an,har da cewa wai ya sayi sabon fili zai yi maaana gini waye waye Baba ya yi hak’uri kar ya damu dan ya Musbah ya daina kula mu, inshaaAllah indai yana raye da shi da Inna ba za su yi kukan rashin d’a ba.” “Wai shi Yusuf yana nufin aikin bankin ne duk ya azurtashi haka??” Cewar Manubiya.. “Hmm”Jidda tace kafin ta d’aura da cewa”Siyama ta ce mini idan fa kika shiga side d’in Baba Habu za ki d’auka a hotel kike tsabar yadda ya gyara sa,ya yi interlock a gaba d’aya compound d’in gidan ya sakawa iyayensa solar shi kuwa gidan da ya gama ya koma akace har abun tsoro hawa biyu fa,motocin sa fa uku,wayarsa wadda ta fito last month ita yake rik’ewa…y’an unguwa sai magana ake yi amma iyayensa da kaka mallan sunce hassada ce! ya ci gaba da business d’insa kawai ya dage da addu’a! ya yi harkar gabansa, kar ya kula kowa….” “Ha’a Manu yaushe kika zo??” cewar Inna wadda ta fito da niyyar bin bayan Jidda, dan ta ji shirun ya yi yawa…a hankali Manu ta tafi jikinta ta rungumeta…cikin rashin jin dad’i inna tace “yanzu Yarinyar nan sai da kika fito?duba fa hannunki har da cannula!to Allah ya kyauta..””Bismillah”daga haka ta juya ta nufi ciki suka mara mata baya. A zaune suka tadda Muhsin yana assignment, Baba kuma yana zaune a kan gadon jinyarsa yana kallon k’ofar da alamun shigowar tasu yake jira dan ya ji Inna ta ambaci sunan ‘Manu!’. A hankali ta k’arasa ta d’an durk’usa ta gaida shi tukunna ta zauna a kujerar mai jinya, ta shiga tambayarsa ya jikinsa.. Murmushi ya yi duk da bai so ta fito ba duba da yanayin jikinta amma kuma ya yi matuk’ar jin dad’in yadda ta damu ta taho dukda itanma a kwance take… Cikin fesar da numfashi ya yi ta’auzi ya kawar da shed’an d’in da ya fara comparing masa himmar Manubiya da Ya musbah a kansa,tukunna yace”ya jiikin naki?” A hankali tace”Alhamdulillah” “MashaaAllah Allah ya inganta”ya ce, kafin ya d’aura da cewa”ki kira mijinki ku koma Manu, dare fa ya yi,ai na warke ma Alhamdulillah” Murmushi ta yi tace”ya tafi siyo abu, sai ya dawo za mu tafi..” Jinjina kai kawai Baba ya yi, daga haka suka d’an tattauna Akan batun su Uncle,Manubiya ba ta so ace Yashjub ne ya bawa iyayenta gidan da za su zauna a ciki ba,amma ba ta da wani zaɓi, tashinsu a kusa da su Uncle shine mafita dan abun nasu ya yi yawa..shiyasa har wani sanyi ta ji da ta ji Baba yana gaya mata “ai Ya Nafi’u ya yi masa batun maganar da suka yi shi da Yashjub shi kuma ya amince,inshaaAllah yana fita daga asibiti za su tare,dan d’azu ma Yash d’in ya zo ya d’auki ya Nafi’u suka je ya basa gidan tare da makullai da takardun.Da Nafi’un ma har yana cewa zai zo ya kawo yanzu to sai yace ya barshi kawai dare ya yi..sa had’u gobe.A gidan ma har da b’angaren Musbahu Allah ya sa dai Baraka ta yarda ya dawo gidan su zauna….” Ahankali Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “zai dawo inshaaAllah Baba, ku dinga yi masa addu’a, kar ku bar b’acin ransa a cikin zuciyoyinku, fushinku a garesa masifa ne.” Jinjina kai Baba ya yi kafin yace”ki na da gaskiya kam,Allah ya sa mu dace.” Knocking suka ji dan haka Muhsin ya mik’e ya je ya bud’e k’ofar….cikin girmamawa ya gaida Yash shi Kuma ya amsa masa da kulawa, tukunna suka k’araso cikin d’akin a tare bayan Muhsin ya maida k’ofar ya rufe. Sai da Yashjub ya d’an russuna tukunna ya gaida Inna da Baba suka amsa ya tambaya ya k’arfin jikin yace”Alhamdulillah” Wallahi dama shiyasa d’azu bai shigo ba yanzu ma kawai ya ga dare sosai ne shiyasa ya shigo tafiya da Manubiya kar ya barta tana yawo ita d’aya da dare…Sam ba ya so su Baba su yi masa godiya amma suna gama gaisawa suka hau yi masa godiya har da su Jidda wadda itama sai yanzun ne ta ji batun daga bakin Baba. Kamar zai nutse k’asa haka ya ji,hakanan ya sunnar da kai yana ta faman cewa”Ameen Ameen.” Ba su wane dad’e ba,suka yi azamar tafiya,Saida duk ta yi musu sallama tukunna ta yi hugging Jidda ta ba ta atm card d’inta da ta d’auko daga jaka tace “gashi” karb’a Jidda ta yi tukunna ta fara shirin rakasu,murmushi Yashjub ya yi ya ce “ta barshi ai su biyu ne.” Daga haka suka tafi Yashjub yana tunanin “Ba dan suma a asibiti suke ba da sun tafi da su Jidda”. A mota Manubiya ma ta so yi masa tata godiyar amma ya yi kicin kicin”wai idan ta yi sai sun yi fad’a” Har da wani turo baki wanda hakan ya sa ta fara dariya…. “Shine amma baka gaya mini ba?” “Na san zugawa za ki yi ai ki hana,shiyasa na zagaye ki!” Ya bata amsar yana mai d’an juyowa ya kalleta. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace”da Ya Nafi’u kuka yi magana kenan?” Sai da ya d’an yi shiru tukunna yace”ni ne na tambayesa na nace shi ne ya gaya mini komai” Cikin mutuwar jiki tace”ba lalle ai ya Musbahn ya yarda ya tashi daga gidan da yake d’in ba.” Kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace”na sa a nemo mini number landlord d’in nasu,kar ki damu zai tashi.” Shiruuu ta yi haka shima Yash d’in daga nan har suka k’arasa asibiti.Kowa da tunanin da ya ke yi,Yashjub gaba d’aya hankalinsa yana a kan wayar Manubiya ne! ya lura wayar a silent take kuma sai faman kiranta ake yi tana rejecting shiyasa ya tafi tunanin ko dai wannan wanda ya kira ta ta k’i cewa komai jiya ne? To kenan ta san waye tunda har take k’in d’auka…bai yi tsammanin za ta b’oye masa wani abun ba shiyasa shima ya yanke a kan ba zai tambayeta ba,zai danne kansa ya ga iyakar gudun ruwanta.Amma fa yadda zuciyarsa take yi sakamokon kishin da ya ke tunzurosa hatta jijiyoyin gaban goshinsa sai da suka fito rad’au!. A b’angaren Manubiya kuwa Abbakar ne yake ta nacin kiranta da messages na ban hak’uri wai yana son magana da ita, yana neman taimakon ta,ta ji zafin yadda ya banzatar da ita amma kuma babban dalilin ta na ƙin kulasa Yashjub ne! Ba ta so su samu matsala ita da shi saboda wani Abbakar kuma Yash ɗin ya fito mata a mutum ya tabbatar mata cewa ba ya son alaƙarta da Abbakar d’in kwata kwata ko gaisawa ba ya so su yi!…ta san ba ya son shi saboda yana tunanin kamar son ta yake yi kuma ta tuna b’acin ran da ta ji a muryarsa ta kuma gani a fuskarsa duk a ta dalilin Abbakar d’in,shiyasa yanzun ta ke jin tsoron gaya masa ‘Abbakar d’in ya na ta kiranta, ya turo mata message yana buk’atar taimakonta.’ Ta zab’i kawai ta rabu da shi, da zarar ta nutsu za ta nemo yadda ake block ta yi blocking d’insa gaba d’aya, ta san Abbakar ya taimaka mata, in ta yi masa hakan ba adadi dan ya kamata ace ta taimakesa yanzun itama, amma Yashjub comes first(Yashjub ne farko) a komai na rayuwarta, kuma tunda ya nuna ba ya son ko gaisawa ne su yi da shi inashaAllah za ta yi masa biyayya….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 31* Sai dare tukunna Baba larai ta tambayi Mommy ‘ya suka yi da Daddy?’… Duk yadda suka yi ta zaiyyane mata,tashi d’aya Baba larai tace mata ‘bugar cikinta ya yi, amma tunda ta ga bai yi mata komai ba to yana so ya tabbatar ne, dan haka ta nutsu!! ta sa ido sosai sannan ta yi taka tsantsan.’ Tashin hankalin da Mommy ta shiga ba zai misaltu ba, dan sai da Baba larai ta yi mata bayani dalla dalla tukunna itama ta fahimci tabbas bugar cikin nata yayi..yo Ina zata fahimta? gaba d’aya d’azun duk a rud’e take hankalinta a tashe. Sai wajajen k’arfe sha biyu na dare tukunna Yassir ya yi sneaking daga d’akin Kausar ya tafi ɓangarensa, a lokacin ya san kowa ya yi bacci babu mai ganinsa…. Ba k’aramin mamakin ganin Munirat a zaune a cikin d’akinsa ya yi ba…shaf ya manta da lokacin da ya bata makullan ɓangaren nasa shiyasa kai tsaye ya ce mata ”ta ya kika shigo?” Murmushi ta yi ta mik’e tace”har ka manta lokacin da ka mallakamin makullan d’akinka har ma da na zuciyarka kenan??” Sai kuma ta girgiza kai tace “hmm..of course you do, (Tabbas ka manta)” Numfashi ya fesar a ransa ya aiyyana”lokaci ya yi da zan daina hulɗa da Yarinyar nan fa” Tunda ya riga ya samu abunda yake so, kuma Ummin bata tafi ba dan munirat ɗin bata bada ƙofar da aka gane suna tare ba, amma dukda hakan dai ya yi nasara dan ko a haka ya barta ya cuceta kuma ya cuci Ummin sannann in wani case ɗin ya taso wanda ya dangancesu ya san Ummin za ta iya tafiya. bayaga haka ma, a sabon plan ɗinsa na shi da Kaudar wanda su ka gama haɗawa yau, shi dai bai ga wani amfanin da Munirat za ta yi musu ba! Dan haka ya kalleta yace”ki je ki yi bacci please, kaina ciwo yake yi..kar ki sa raina ya b’aci” Wani irin kuka ta fashe da shi tace “you snake!!(mayaudari!!!). Ashe dama duk yaudara ce Yassir?? Yau ni ce zan b’ata maka rai? Ka manta yadda kake cewa ba ka iya bacci idan ba na kusa da kai, ka manta duk kalolin k’aryayyakin da ka dinga zuba mini Yassir yau ni kake wulak’antawa kake pushing away…. Ina kiranka ba ka d’auka, ba ka replying messages d’ina, saboda ka riga ka samu abunda kake so, ko???” Runtse idanuwa ya yi da k’arfi, kafin ya bud’e ya matso daff da ita, tukunna ya ce”ki fad’a ko nawa kike da buk’ata zan biyaki fansar budurcinki” Wani mahaukacin mari ta zabga masa wanda sai da jinsa ya d’an d’auke na y’an sakanni!!!. Cikin tsananin b’acin rai ya d’ago ya zuba mata manyan idanuwansa waenda suka yi jazir ya ce ”zan baki mintuna biyu kacal Munirat! ki fice ki bar mini side d’ina, idan kuma baki fita ba to wallahi zan baki mamaki….aikin banza!!!… Ba ma fa ki kai yadda na yi zaton zan same ki ba amma kin bi kin wani d’aga mini hankali sai kace wadda kika ba ni ranki!” Kallonsa kawai take yi jikinta yana wani Irin karkarwa kamar mazari, idanuwanta kuma suna zubda ruwa tamkar fanfo….maganganun cin mutunci da cin zarafi ya ci gaba da fad’o mata, dan haka kawai ta wuce shi ta nufi k’ofa tun kafin ya sa zuciyarta ta buga!!! Har ta fice bai daina magana ba, sai da ya tabbatar da ta yi nisa tukunna ya yi tsaki ya fad’a bathroom…… .. Washegari da sassafe ta rubuto masa doguwar wasik’a mai ƙunshe da tsinuwa da Allah ya Isa kalakala, sannan ta had’o masa da makullayensa da duk wasu gifts da ya tab’a bata, ta kai side d’insa ta ajjiye…. Tabbas Yassir ya koya mata darasi a rayuwa, kuma ya cuceta har gaban abada, amma ba komai ya je zai gani…… Da safe Dr ya sallami Manubiya, dan jikin nata Alhamdulillah, sai d’an abunda ba a rasa ba. Direct gida Yash ya kaita bayan ya tsaya ya siya musu abinci a hanya…sai da suka yi wanka suka ci abinci suka huta tukunna ya ce “bara ya je ya d’auko mata Jidda da Muhsin su taya ta zama, kafin ya je ya d’auko mata gwaggwo mai aiki.” A take kuwa farin ciki ya wanzu a fuskarta, murmushi kawai ya yi yai kissing forehead d’inta ya fice bayan ya tabbatar ba ta buk’atar komai. Ko da ya je Inna ta so ta hana su Jiddan zuwa dan ta san halin k’annensa da mahaifiyarsa, kar zuwan nasu ya zamo case amma sai Baba ya ce”ba komai, su je kawai” Dan a duniyar nan Baba bai ga alfarmar da Yashjub zai nema a wajensa ya k’i yi masa ba muddin bai fi k’arfin sa ba. Hadda Siyama aka taho, dan a lokacin ita da anty Umma sun je duba Baba Yash d’in ya je, hakanan ita da su Ya Nafi’u waenda suka zo da makullan gida suka ta yi masa godiya suma..Anty umma ta na saka masa albarka….. Sai da ya kai su gida yace”su d’ebi kaya”dan a cewarsa “kwana za su yi”tukunna suka kama hanyar nndc quaters. Ba sa so su yi jayayya da shi,shiyasa kawai suka ce masa to suka d’ebo kayan amma sun san ko da ace suna son kwanan ma su Inna ba za su bari ba…. Yana hanya Najeeb ya kirasa ya ce masa yana k’ofar gidansa, dan haka ya ce”ya basa 5 minutes yanzu zai k’araso shima inshaaAllah”. Suna isa tsabar saurin da Siyama take yi ko gama parking Yash bai yi da kyau ba ta fito da saurinta ta nufi entrance..ta ci sa’a kuwa dan Manubiya tana k’asa dama tana jiransu…murnar ganinsu da oyoyo d’in da Manubiyan ta tsaya yi ne ya sa ba ta samu ta shige d’aki ba har Najeeb d’in ya shigo shi da Yashjub.Allah ya so da ma Manubiya da hijab d’inta dan ba ta dad’e da idar da sallar azahar ba. Sama suka nufa Yayinda shi da Najeeb suka zauna a nan k’asan….ba k’aramin tausayi Najeeb ya bawa Yashjub ba dan ya fahimci komai kuma ya lura ko kallonsa Siyama ba ta son yi, dan haka ya gama shirya yadda zai yi ya samu ya ceto rayuwar Abokinsa saboda in banda tsantsar so da k’aunar Siyama babu abunda yake hangowa a tartare da shi…. Siyama da Jidda har ma da Manubiyan ne suka sauk’o suka yi musu fried rice da coslo mai d’an karen dad’i, itakam Manubiya kafin a gama ta jigata dan wani irin amai da zazzab’i take ji gashi aman ya k’i fitowa…… Ana gama cin abinci Yashjub ya kira Manubiya yace “ta turo masa Siyama” Da d’an mamaki Najeeb ya kallesa, sai kuma ya yi shiru kawai ya ci gaba da tunanin da tun d’azu yake ta yi dan ko da suka zauna ma Yash d’in ne yake ta magana. Cikin nutsuwarta ta k’arasa cikin parlourn inda suke ta sake gaida Yash tukunna ta zauna a kan one seater da ya yi mata nuni yace “ta zauna” Kamar ba za ta kula Najeeb ba, sai kuma kawai tace”Ina wuni” Saida ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace”Alhamdulillah,kwana biyu…” Ta san jan magana yake so ,shiyasa kawai ta sharesa. Shiru parlourn ya d’auka kafin ta ji muryar Yash ta d’ira a dodon kunnuwanta, ta inda kansa tsaye yana shiga cewa ”Siyama mai yasa ba kya kula Abokina? Ki ke ta bashi wahala..ko kwata-kwata ba kya son shi ne?” Nauyi tambayar ta yi mata gashi ba ta yi tsammaninta hakan ba..shiyasa ta sunkuyar da kanta ta yi shiruu ta gagara cewa komai. Jan numfashi Yashjub ya yi, kafin yace “A da ban yi niyyar saka muku Baki ba, amma naga abu har wajen 4 months ya k’i gyaruwa sai gara mini Aboki kike yi, shi kuma na san ba hak’ura zai yi ba!” “Na san watak’il a kan Ya’isha ne kuka samu sab’ani da shi…wanda ko baki auri Najeeb ba na san ba zai auri Ya’isha ba, tunda ba sonta yake yi yanzu ba, kinga an yi biyu babu kenan. Kasancewar ni ɗanuwa ne ga Ya’isha ba shi zai sa in k’i bin bayan gaskiya ba,Maganar gaskiya Ya’isha ita ta yi neglecting Najeeb ta yi sakaci da alaƙarsu har ya zo ya had’u dake kuma na san kin san negligence (sakaci) ya kan kashe har aure ma ba wai iyaka soyayya ba….” “Wannan itace gaskiyar maganar Ya’isha da Najeeb, dan haka zaɓi ya rage gareki, amma ni dai ina baki shawarar ki saurari Najeeb ki auresa, saboda na san yana son ki tsakani da Allah, kuma Najeeb yana da kirki, hankali sannan shi ɗin mutumin kirki ne.” Shiruu parlourn ya d’auka kafin Yash ya mik’e ya ce “Bari na baku guri…”daga haka ya wuce chan sama d’akinsa. A hankali Najeeb ya mik’e ya k’arasa ya zauna a gefenta kan three seater da ta ke a zaune yace “Wanne dalili kuma yanzu kike buƙata Siyama da zan ci gaba da azabtar da zuciyata? Na garu haka, dan Allah ki ji k’aina….” Shiruu ta yi ta kasa cewa komai kafin tace”zan yi tunani akai” Wani sanyin farin ciki ne ya lullub’e Najeeb a hankali yace”sai an ja mini rai kenan yanzun ma..” Murmushin da yaga ta d’an yi ne ya sa ya ji kamar an tsunduma sa a aljannah dan haka a fili ya ce”Alhamdulillah” “Yanzu ko zuwa anjima idan na zo za ki fito kuma za ki kulani ko???” Dariya ta yi wannan karon ta d’aga masa kai alamun”eh”sai kuma ta mik’e da sauri ta haye sama….dama chan tana son Najeeb kawai tana jiran wanda zai ba ta kwakkwaran dalilin da zai sanya ta auresa dan ba shi kad’ai ba ita kanta ta garu..yanzu kuwa da ta ji komai ta fahimci komai InshaaAllah za ta rufe ido ta goge babin Ya’isha daga rayuwarsu… Ko da su Manubiya suka ji labarin a take suka goya mata baya d’ari bisa d’ari, suna ta murna suka kira Aisha aka sanar mata, itama kuwa ta ji dad’in batun matuk’a…. Najeeb kam farin cikin da yake a ciki ya k’i b’oyuwa…Tana wucewa ya kira Yash yace masa “zai tafi” Yana sauk’owa ya kallesa yace”har kun gama?” Jinjina kai ya yi kafin ya mik’e yace”Yash Ya’isha kar ta zamo silar…” Dariya ya ga Yash d’in ya fara kafin yace”Najeeb if I were in your shoes (inda ace nine a matsayinka) to da da gudu zan bar sisternka fa in zab’i Manubiya, na san menene so!” Sai kuma ya yi tapping shoulder d’insa ya ce”laifin Ya’isha ne,na dad’e da fahimtar hakan,kar ka damu!” Ganin still Najeeb d’in bai sake ba yasa cikin zolaya yace”Allah ya sa nan da next week mu je mu yi gaisuwar iyaye” Da sauri Najeeb ya ce”Ameen” Dariya Yash ya yi yace”an zo wajen da za ka yi magana kenan…..” “You are welcome” Daga haka suka fad’a zancen case d’in estate d’insa…wanda akwai haske sosai dan ana ta samun ci gaba,soon inshaaAllah suna ganin za a kamo culprit d’in(mai laifin)….. Ba su san waye ya gayawa su Yasira sun koma gidan ba, sai kawai ganinsu suka yi har da babbar jaka…Yasira da Yusra da Yadira, dan Yasmeen ma cewa ta yi ba za ta bi su ba wannan karon, tace ‘ita babu ruwanta, saboda zuwa yanzu da ta zauna ta yi lissafi ta fahimci tabbas idan ba su daina biyewa Baba larai ba to sai ta goge musu duk wani ilimin addini da suke da shi.’ Sosai kanta ya kasa ɗaukar yadda Yasira ta haƙiƙance tana gaya mata ‘wai ai da ma Baba larai ta duba ta gani Manubiya za ta taho da masifu a bayanta..ita za ta ga bayan Mommy, tou kuwa gashi alama sun fara nunawa, dan haka dole su tashi su tsaya…dama ai duk abunda Baba larai ta fad’a sai ya zama gaskiya.’ Bayan ba su san sakawa da suka yi a ransu ne ya sanya Allah ya barsu da halin su ba, shiyasa suke ta ganin masifun suna zuwar musu kamar yadda sukai zato! Dan idan ba hakan ba wacece Baba larai da har za a ce ‘duk abunda ta fad’a sai ya tabbata???…’. Shiyasa Yasira tana gama zaiyyane mata itakuma tace ‘ita dai babu ruwanta,ba za ta hanasu ba, dan ta san ba za su hanu ba, idan kuma ta fad’a to ta san za ta samu matsala da Mommy, dan haka ba zata faɗa ba, amma kar su sake sakota a cikin zancensu….’ Shiyasa Yasirar ta kad’o kan Yadira da Yusra suka taho bayan Baba larai ta cika musu jakankuna da kayan barbad’e-barbad’e, dan tunda suka je asibiti aka ce an sallamesu ta fara harhad’awa. Ba iyaka su Manubiya ba, hatta Yash ya fahimci kissa ce da k’arya su Yasira suka zo da ita wannan karon…dan yadda suka yi musu..suka wani chanja gaba d’aya tashi d’aya abun dole ya bawa duk wani mai hankali mamaki…hatta Yasira da murmushi ta gaida Manubiya sannan ta shiga tambayarta ya jiki, kamar za ta goyata har da zama a kusa da ita, tukunna tace”Mommy ce ta ce su zo su tayata gyare-gyare.” Shi dai Yash ba don kar ya ce su tafi abun ya zama case ba, da tuni ya sallame su! Dan gaba d’aya haka kurum hankalinsa bai kwanta da su ba. Ya san watak’il idan Gwaggo ta zo za su tafi shiyasa yace bara ya je ya d’aukota, amma sai ya ga ko alamun gezau ba su yi ba ballantana a saka ran tafiya, shiyasa kawai ya fita yana jimami. Bayan fitarsa sai wajen ya zama shiru, dan suma su Yasirar tun suna magana da suka ga su Siyama da Manubiyan sun k’i sakewa sai kawai suka d’aga k’afa suma suka yi shiru. Suna a haka suna jimami Ya Nafi’u ya kira su Jidda yace”mutum biyu su fito a bar mutum d’aya a gidan, za su wuce gida su fara tartara kaya an sallami Baba..” Siyama aka bar mata, Jidda da Muhsin kuma suka tafi, dan idan zai yiu a yau suke so su tashi daga gadon k’aya su koma sabon gidansu dake a gandun albasa wanda Yashjub ya basu. Ba su yi ma tunanin za a sallami Baban yau ba, da tuni sun yi parking d’in. Ita Aisha Mama Anty Umma da Inna ne suka tartare komai kafin dare sun kammala komai ya Nafi’u da Muhsin kuma su sakayi ta zirga zirgar kai kaya a motarsa da motar kai kaya. Sai da suka gama kammala kai komai gidan tukunna suka d’auko Baba daga asibiti suka nufi tsohon gidan nasu dashi domin su je su yi wa su Uncle sallama saboda Baba dagewa ya yi yace”shi fa sai ya yi musu sallama.” Suna zuwa Baba da Ya Nafi’u suka nufi wajen su Uncle d’in, Inna da su Mama kuma suka nufi wajen matayensu.…yunwa Jidda ta ke ji dan ba ta tsaya ta ci abinci sosai ba, shiyasa ta je kitchen ta d’aura ruwan zafi da niyyar ta je ta siyo milo da madara ta sha tea… Sai da gabanta ya yanke ya fad’i sakamokon k’amshin turaren da hancinta ya fara jiyo mata,a take a ranta tace “nooo..it can’t be,ta ya ma zai shigo nan.” daga haka ta mik’e bayan ta gama saita murhun ta juya za ta fita kawai ta ga mutum a tsaye kyam!….. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”tace a fili, kafin ta d’an d’ago wayarta ta d’an haska dan ta samu ta tabbatarwa kanta da shi d’in ne… Suna had’a ido ta fashe da kuka ta yi ƙasa da wayar sannan tace”dan girman Allah ka fita Ya Al’ameen kar ka janyo mana masifa” Ahankali ya yi taku d’aya ya matso gareta muryarsa har tana d’an karkarwa yace”D’azu na ji Mama tana gayawa Ammi cewa za ku tashi…” Cikin sharar hawaye tace”eh,mun ma tashi..dan Allah ka fita…” A hankali yace”Jidda ni da ke fa?ba za ma ki tsaya ki ji uzuri na ba?tun safe nake ta faman zirya Ina lek’en gidan nan Jidda duk dan saboda ke amma kora ta ma kike yi?” Bai jira jin amsarta ba yace”a lokacin da na tafi,wallahi wallahi tun a kwana biyu da na kirawo wayarki na ji ba kya amsawa na had’o kayana na biyo jirgi na sauk’a a garin Abuja, inaga cousin d’ina da muka tafi tare da shi ne ya kirawo su Ammi yace musu na taho dan flight d’ina yana shirin boardn zuwa Kano Mahaifina ya kira ni yace idan na zo sai ya tsine mini tunda bani da hankali. Kalar fad’an da ya shiga yi min a wanchan lokacin ni kaina na san akwai abunda Ammi ta gaya masa mai muni shiyasa ya yi fushi sosai ya ji haushi dan ko fad’a bai cika yi mini ba.A wanchan lokacin babu yadda ban yi da shi ba amma ya k’i saurarona, yace in juya in koma. Tun daga ranar ya daina kulani, ya yi fushi da ni, yace kuma wallahi idan ya ji labarin na zo Nigeria ba tare da na gama abunda ya tura ni in yi ba sai ya bani mamaki, yace kuma ko waya na yi miki bai yafe ba. Sai da na dawo tukunna a cikin maganarsa na fahimci ashe Ammi ce ta ce masa saboda ke na rubuta letter na bar course d’in da ya tura ni in yi saboda kince ‘Baba zai aurar da ke a Yusuf idan ban dawo an yi auren da ni ba’. Jidda Course d’in duk yawansa na san ba zai kai wata hud’u ba wanda da ni kwata kwata ban ma san zai kai yawan hakan ba dan na yi tunanin 4 weeks ne sai da na je tukunna na gani, amma da naduba sai naga ai wata huɗun shima ba wani lokaci mai tsayi bane shiyasa na hak’ura na yi masa biyayya na bari akan idan na dawo sai a yi komai, amma ko a wanchan lokacin ɗin ma sai da na saka mai gadin mu ya sa mini ido gudun kar Ina chan Ina shirya ta yadda zan shayo kan iyayena ke kuma a aura miki Yusuf.” Shiruu ya yi kafin ya d’aura da cewa”wannan shine abunda ya faru Jidda shiysa kika ji ni shiru, na san waye mahaifina yana son duk abunda nake so kuma zai tsaya mini a kai, amma muddin na yi masa taurin kai to na san tsaf za a samu matsala, kuma na san halinsa da bin diddigi yadda yace ‘kar in kiraki’ wallahi da ace na kiraki to sai ya sani, ni na san waye shi. na san kuma ya yi hakan ne saboda ya ga shin zan yi masa biyayya ko akasin hakan.” Cikin sake yin taku d’aya zuwa gareta yace”I love you!always and forever, ba zan iya hak’ura dake ba Jidda, gara ma tun wuri ki yi saurin karb’ar uzuri na ki yafe mini mu fara nemawa kan mu mafita!” Shiruu ta yi a ranta ta ji matuk’ar sanyi da dad’i da ta ji ba banzatar da ita ya yi ba, a fili kuma sai tace”Ya Al’ameen ni kam na dad’e da hak’ura da kai,ka duba fa ka ga Mahaifinka ma ba so yake yi ba tunda shi ne yace kar ka ki…” Cikin tarar nufashinta yace”noo Jidda wallahi ba da ke ya ke fushin ba da ni yake yi, kuma na san da ace ya ji batun aurenku da Yusuf ya taso to da zai yi wani abun … A ranar da zan tafi, a airport na yi masa bayanin komai na ce masa Ammi ba ta so, shi da kansa a wanchan lokacin ya tabbatar mini da cewa ‘inshaaAllah ina dawowa za a yi auren mu, kuma kafin ma in dawo za a yi tambaya, batun Ammi kuma kar in damu ya san yadda zai yi da ita, ba matsala inshaaAllah. Amma shi abunda ya ke so dani a lokacin shine in yi k’ok’ari in maida hankali a kan abunda na je yi saboda saboda course ɗin yanada matuƙar mahimmanci wa business ɗinmu!’ Shiyasa da ya ji na shallake sa, na bar ma makarantar shi kuma ya ji haushi ya yi mini haka, amma wallahi ko yanzu Mahaifina a shirye yake ya d’aura mana aure ko a yau!ita ma Ammi ta amince kuma wannan karon da gaske, saboda halin da na shiga ta tsorata ta yi nadama ta gaskiya ba kamar wanchan lokacin ba da ni kaina ban san linke ni ta yi a baibai ba”. Babu wani ragowar dalilin da ya rage wanda zai sanya Jidda ta d’aura laifi a kan Al’ameen, saidai ta san su Baba ba za su tab’a fahimtarsa kamar yadda ita ta fahimce sa ba, shiyasa kawai ta d’an ja da baya cikin sharar kwallah tace”ka yi hak’uri Ya Al’ameen, mu yi hak’uri kawai” Ta fad’i hakan tana mai fashewa da kuka. Da sauri ya sake matsowa yana mai cewa “noo Jidda kar ma ki fara cewa mu yi hak’uri, wallahi ba zan iya ba” Ganin sa daff da ita ya sa ta yi sauri ta sake ja baya ita shaf ta ma manta da murhu da ruwan zafin da ta d’aura,shi kuma abunda ya hango kenan dan haka ya yi saurin ruk’ota zuwa jikinsa ganin za ta afka kan murhun yace”careful!wuta a bayanki” Salatin Ya Yusuf wanda ya haske su tarr da fitilar wayarsa mai masifar haskd da kuma”Jidda”d’in da Baba yace ne ya fargar da su. Da wani irin sauri ta ture Al’ameen shima da mugun sauri ya cikata ya matsa ya shiga ambaton”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” a cikin zuciyarsa. Juyawa kawai Baba ya yi, ransa a mugun b’ace ya fice daga gidan, yayinda Yusuf ya yi kansu zuciyarsa tana wani kalar mahaukacin tafasa..kamar wani mahaukaci sabon kamu haka ya koma, yana zuwa ya rarumi wani k’atoton icce ya makawa Al’ameen a kai da mugun sauri wanda hakan ya yi sanadiyyar fad’uwarsa a wajen, gefen kansa ya shiga zub da jini. Wata razananniyar k’ara Jidda ta saki, ta yunk’ura da niyyar yin kan Al’ameen d’in wandake nan kwance kamar gawa amma tashi d’aya itama Yusuf ya d’auketa da wani gigitaccen mari kafin ya shak’o ta da dukkannin k’arfinsa ya buga ta da jikin bango..dai dai nan su Anty Umma waenda k’arar Jidda ta Isar musu suka afko cikin kitchen d’in,da gudu anty Umma ta k’arasa ta shiga k’ok’arin kwatar Jidda wadda zuwa yanzu idanuwanta suka fara lullumshewa kafin duhu ya maye gurbin ganinta jikinta ya saki a take ta sume a wajen…… A hankali take bud’e idanunta da suka yi mata rauni..dishi-dishi ta ke gani kafin ta fara gani da kyau kad’an-kad’an..ba ta gama tantance a inda take ba…cikin fushi ta ji Baba wanda ta ga ya juya mata baya suna magana shi da Inna yana cewa”saboda su Uncle sun yi mini abu sai in d’aura karan tsana a kan Yusuf, in rufe idanunwana in k’i in bi bayan gaskiya?. Fad’a ni da su Uncle muka yi ba da Yusuf ba! kuma suma su uncle d’in inshaaAllah wata rana za mu shirya, amma ki daina saka Yusuf a cikin fad’anmu, ke ko irin karar da ya yi mana ma ba kya gani? wanne d’a ne kika tab’a gani ana fad’a da mahaifinsa amma ya rufe idanuwansa ya bi bayan k’anin mahaifinnasa da ake fad’an da shi? Kuma fa saboda bugun da su musbah suka yi masa ne ma fa abun ya soma amma yaron nan ya rufe ido yana mutuntani da goyon bayana, ki duba ki ga yadda ya dinga bin bayan mu a gaban Baba Habu har kusan marin sa fa ya yi, suka samu sab’ani, duk a ta dalilin mu, amma duk da haka ke Yusuf bai kwanta miki ba?…….a da gaskiya na sa a raina ba za ta auri Yusuf ba, amma kuma abunda idanuwana suka gane mini yau ya sanya na ga dacewar dole fa in yi abunda na ga ya kamata a matsayina na ubanta!! ko so kike mu zuba mata ido Al’ameen d’in ya gama lalatata? Bari ki ji abunda ba ki sani ba hatta makaranta wasu lokutan shi yake kai ta ya d’auko ta Yusuf ya dad’e da gaya mini hakan dama, ido kawai na zuba mata ina jiran ranar da zan kamata tana kulashi ashe abun nasu ma ya zarce misali!…” Cikin kuka inna tace”yanzu zargin Jidda kake yi ba tare da ka tsaya ka ji bayanin ta ba??” Cikin tarar numfashinta yace”tabbas!tabbas zargin ta nake yi..idan kuma za ki iya gaya mini uban me ta ke yi a ruk’umk’ume a jikinsa a kitchen da duhu cikin dare inda ba a tab’a tunanin ganin Al’ameen d’in ba to Ina sauraronki…” Cikin d’an b’acin rai Inna tace”wallahi zan iya dafa Al’k’urani akan akasi aka samu,Haba Baba Jidda fa? Ashe dama ba ka yi mata sanin da za ka iya shaidarta idan irin haka ta taso ba? sannan kalli fa abunda Yusuf d’in ya yi wa Yarinyarnan har ta kaisa ga sumar da ita amma shine za ka d’auke ta ka aura masa ita? A ganinka hakan dai-dai ne? Sannan idan kace Yusuf a bayan mu yake ka ji ka gani ya zama mijinta me za ka ce a kan baba habu surikinta, wanda hatta yau da ya san tashi za ka yi a kusa da su kuma saboda su bai tsaya kun yi rabuwar arzik’i ba?” Cikin tsananin fushi Baba yace”na riga fa na gama magana! babu wani abunda ya Isa ya sakani in chanja ra’ayina, na tabbata inda ace Musbahu ne ya ganta a yadda Yusuf ya gansu ita da Al’ameen da shima abunda zai aikata a gareta kenan tunda hakan ne dai dai…to shi Musbahu ya gudu ya yaye kansa da kansa dan hakan idan Yusuf ya hukunta Jidda a matsayinsa na yayanta hakan bai zama laifi ba….” Cikin kuka inna tace”ta ya sumar da Jidda ya zama ba laifi ba?” Da mugun k’arfi Baba yace”Aminatu!!!!!” Cikin fushi ya d’aura da cewa”ba na son jayayya, ki barni in ji da abubuwan da suke damuna…ba na so in sake fuskantar tirjiya daga gareki,ina umartar ki da ki yi mini biyayya a yi auren nan a gobe a kaita d’akinta idan ba haka ba wallahi wallahi wallahi za mu samu gagarumin sab’ani da ni da ke!” Yana gama fad’in haka ya juya ya fice… A hankali Jidda ta mayar da idanunta ta rufe…tana jinta kamar ba a duniyar ba…tunda take ba ta tab’a jin Baba ya d’agawa Inna murya ba sai yau duk a ta dalilin ta…ta na son Ya Al’ameen sannan ta san idan ta auri Ya Yusuf tabbas bak’in ciki ne ajalinta, amma kuma inshaaAllah ko alamun tashin hankali ko kuma yunk’urin kare kanta ba za ta yi ba…ta fahimci inna ta yarda da ita ta yi trusting d’inta Manu ma ta san za ta yarda da ita Baba kuma za ta barsa ya aurar ta a Ya Yusuf d’in indai hakan zai sa ya huce,inda rabon wanke kanta wata rana shima zai fahimci ba wani abun suke yi da Ya Al’ameen ba….za ta yi masa biyayya inshaaAllah, dan tunda ta fara tirjiya a Ya Yusuf ta nuna Ya Al’Ameen take so babu abunda alaƙarta da Ya Al’Ameen d’in take ta haifarwa Ahalinta sai masifa……….. Siyama ba ta so kwana a gidan Manu ba, amma haka suka tursasa mata akan sai ta kwana abun mamaki har su Yasira waenda suka yi musu k’abe k’abe ko motsi in suka yi idanunsu a kansu yake ….su dai su Manubiya kawai sun zuba musu ido ne suna kallon ikon Allah da kuma rashin wayonsu, dan wannan rashin wayo ne, saboda yadda suke yi kowa ya riga ya san akwai wani abunda suke son cimmawa, shiysa daga Manubiya har Siyama suke ta addu’o’i da neman tsari daga sharrin su…dukda kuwa d’azu Yasira ta bawa Manubiya hak’uri ta ce “ta yi hak’uri akan abubuwan da suka yi mata, duk sharrin shaidan ne, kuma sun fahimci itace zab’in yayansu, ta yi hak’uri inshaaAllah hakan ba za ta sake faruwa ba, su na so su faro komai saboda da ita, daga fako.”amma hakan bai sa Manubiya ta yarda da su ba…kawai dai ta bita da murmushi tace mata “komai ya wuce” Dukda gwaggwo ta zo, hakan bai sa sun yi shirin tafiya ba..shima kuma Yashjub bai ce musu komai ba ya rabu da su amma dukda haka idanunsa a kansu yake. Ko da dare ya yi su da kansu suka tsara cewa’Siyama ta kwana a d’akin Manubiya na da,su kuma za su zauna a d’akin da Yadira ta zauna’.Gwaggo kuma dama tana k’asa d’akin bak’i. Murmushin yak’e Siyama ta yi dan ta yi tunanin a wajen kwanan ma za su nanik’e musu ne…Yasirar ma gudun kar su ga suna ta manne musu ne ya sanya wannan karon tace a yi hakan. Sun mik’e kenan kowa za ta tafi ta kwanta wayar Manu ta fara haske a karo na biyar daga zaman su zuwa yanzu,duk tsura mata idanu suka yi, a hankali ta yi musu murmushi tace”sai da safe”daga haka ta juya ta nufi sama, tukunna suma suka wuce d’aki. Suna shigewa Manubiya ta dawo da sauri ta Isa gaban Siyama wadda ke k’ok’arin shiga d’aki itama tace”Siyama dan Allah ya ake yin blocking mutum,na kasa” Kallonta ta yi kafin tace”ki duba goggle”kamar ba za ta tambaya ba sai kuma tace”wa za ki yi blocking haka jikinki har yana rawa” “Abbakar”Manubiya ta bata amsa a tak’aice tana mai daddana wayar hannunta kafin ta d’aura da cewa “ya ishe ni da kira,wai dan Allah yana buk’atar taimakona. Kin san shi kuma Ya Yash ya ce ba ya so ko gaisawa ne in yi da shi” Ta faiyyace mata hakan a lokaci guda tana k’ok’arin blocking Abbakar dan har ta gano yadda za ta yin. Shiruu Siyama ta yi tana tunanin”ko dai ta gaya mata Mahaifiyarsa ce a kwance a gadon asibiti rai a hannun Allah, ta san shi yasa yake ta kiranta. Ko kuma kawai ta rabu da ita inyaso ita da Jidda sai su san yadda za su yi su karb’i kud’in a hannunta su basa dan ta san kud’i yake so.” “Done!” D’in da Manubiya tace ne tana haki kamar wadda ta yi y’ar tsere ya katsewa Siyama tunani.Daga haka Manubiyan tace mata sai da safe ta juya ta haye chan sama. Sai da Yusra ta ji Siyama ta shige ciki ta rufo k’ofa tukunna ta juya ta nufi su Yasira waenda suka tsura mata ido tana wani irin murmushi….tana zuwa ta zaiyyane musu abunda kunnuwanta suka jiye mata Manubiya da Siyama suna cewa…ji suka yi kamar an yi musu bishara da gidan aljannah!Tabbas Allah ya na son su,saboda dama neman hanyar da za su bi su nunawa Yash kamar Manu ce ta zubar da cikin da kanta suke yi, yanzu kuwa Yasira tana jin wannan batun tashi d’aya ta san abunda ya kamata ta yi, dan haka ta cewa su Yusran gobe duk runtsi su yi ta kwak’umarta har sai sun ga password d’in wayarta, daga nan kuma sai su nemi number a wayar tata,saboda ita gobe za ta fita office…Yadira tana da kwakwalwa shiyasa tashi d’aya tace mata d’azu dai da yake ta kira ta ga number 090443 ne farkon number k’arshen kuma ba ta gani sosai ba ”Ba damuwa,Allah ya sa ba ta yi deleting history d’in ba idan muka d’au wayar time d’in kawai za mu duba na san lokutan da ya kikkirata ai” Cewar Yasira. Cikin tarar numfashinta Yusra tace”ko ta goge ma ni na san inda zan shiga in dubo,Allah ya kaimu goben da rai da lafiya.” Baba larai suka kira suka sanar mata sannan suka d’aura da cewa”Sun fara zuba abubuwan da ta basu a duk abincin gidan,sannan ba za su samu matsala wajen jefa mata tablet d’in a ruwa ta sha ba saboda lucky for them ba ta shan bottle water ko na dispencer iyaka ruwan borehole kawai take iya tara a cup ta sha sakamokon laulayin ciki shiysa cikin sauƙi d’azu tana ajjiye cup d’in kafin ta je ta dawo suka jefe mata kwayar ba tare da su manubiyan sun farga ba daga ita har Siyama,to dai da ta dawo ta d’an yi sip biyu daga nan ta ajjiye maybe taste d’in ne ta ji ya chanja mata, shiysa suka yanke shawarar su dinga raba kwayar gida uku saboda kar ta gane…. to dai a halin yanzu sun zuba mata a gorar ruwanta na borehole uku da ta tara ta saka a fridge akan za ta dinga sha…” Murna a wajen Baba larai abun ba a cewa komai..ji take kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha…sai da ta gama shi musu albarka kafin tace”amma Yasira cctv fa?” Dariya ta yi tace kar ki damu Baaba, ba zai tab’a ganewa ba, saboda sai da muka shige jikin fridge d’in sosai tukunna muka saka kuma ƙofar fridge ɗin ta karemu sannan ba direction d’in wajen ma cctvn take kallo ba…sannan na cup ɗin shima ɗazu da za mu jefa ba mu yi a yadda cctvn za ta ganmu ba” murmushi baba larai ta yi tace”MashaaAllah, Alhamdulillah,Allah ya ci gaba da taimakon mu” daga haka ta mik’awa Mommy,itama duk da tashin hankali da fargabar Daddy da take ciki, sai da ta yi farin ciki matu’uka, ta yi ta sanya musu albarka, daga k’arshe suka yi sallama suna masu hango silver lining(alamun nasara)… A b’angaren Najeeb da Siyama kam a ranar kusan kwana suka yi suna waya…da kyar ta samu ya yi mata sallama suka katse kiran, nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita ,yayinda shi kuma ya duk’ufa Nafila…Tabbas ya manta rabon da ya shiga farin ciki kwatankwacin wannan..shiysa ya kwana sallah yana godewa Ubangiji, sannan yana rok’onsa ya tabbatar da aurensa da Siyama!… Ya Musbah kuwa da ya yi alk’awarin zuwa, ko alamar sa babu, kuma bai yi waya ba,har cikin dare sai da Ya Nafi’u ya gawada kiransa amma bai d’auka ba, saboda Ya Nafi’un ya lura har da takaicinsa ne suka tarar wa Baba ya birkice musu lokaci guda haka…shi kam zuwa yanzu ya daina jin haushin Ya Musbah dan maimakon yaji haushin nasa ma shi kam tausayinsa yake ji, kuma inshaaAllah zai taimakesa ya fitar da shi daga kaidin Baraka..shiysa ya shirya zuwa gidan nasa gobe da sassafe dan shi da Yashjub dama sun riga sun san gidan…zai je ya samesa su fara ceto rayuwar Jidda wadda take shirin fad’awa halaka a gobe, daganan zai san abunda zai yi dan abun na Baraka ya zama abun tsoro. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 32* A zaune ta same shi yana aiki a computer…zafi sosai take ji sakamokon zazzab’in da ya fara sauka daga jikinta, dan haka ta nufi bathroom domin ta samu ta sake yin wanka bayan wanda ta yi ba da jimawa ba. Sai da ta sauya kaya tukunna ta fito, lokacin shi kuma ya gama aikin yana zaune ya miƙe ƙafafunsa akan gado…kallon ta yake yi yana mamakin yadda ta shiga ta yi wankan ta fito da wayarta rik’e kyam! A hannunta…da sauri ya kawar da zargi a cikin ransa ya mik’a mata Hannu alamun ta zo garesa.. Sai da gabanta ya yanke ya fad’i!…Ta san Yashjub ya yi k’ok’ari, sai dai ita kuma laulayin ciki ya zo mata har da k’in son kasancewa da shi, dan babu abunda ta ji ta tsana kamar yace zai nemi wani abun daga gareta. Murmushin yak’e ta yi ta nufesa, tana zuwa ya gyara zama ya d’aura ta a kan cinyarsa, cikin muryar bege yace”yanzu dai ai jikin da sauk’i ko?” Sunkuyar da kanta ta d’an yi k’asa, kafin ta girgiza kai alamun”a’a”. Ya ji babu dad’i tabbas, dan yana lura da yadda ko Hannunta ba ta so ya rik’e a cikin kwana biyun nan..amma sai ya dake still,yace”haba mana!a ji da ni gaskiya ko in yi miki kuka..” Daga haka bai bata ikon yin magana ba ma ya fara kissing d’inta cike da shauk’i…. Wani irin kuka ya ji ta fashe masa da shi, cikin kukan ta shiga k’ok’arin kwatar kanta. Dakatawa ya yi, ya d’an cikata, sannan ya zuba mata rinannun idanunsa yana kallonta kafin da mamaki yace”Abunda na yi yanzun ne ya sanya ki yin kuka har haka?”. Kasa magana ta yi dan ba ma ta san me za ta ce ba, kafin ta mik’e da sauri ta zagaya d’aya b’angaren gadon ta kwanta, ta juya masa baya, still tana sheshshek’ar kuka.. Ya fi mintuna ashirin a haka, ya k’ame kawai a yadda ta barsa, dan ya ma kasa motsi. kafin da kyar ya samu ya kwanta rigingine yana kalllon sama zuciyarsa tana wani irin tafarfasa ga wani irin ciwon ciki da ya turnik’e shi tashi d’aya. Tashin hankalin zarginta da yake shirin dasuwa a cikin zuciyarsa sam bai sa ya yi tunanin ‘watak’il cikin jikinta ne ya zo da laulayin hakan’ ba, bayaaga haka shi bai ma tab’a sanin masu ciki suna gudun mazajensu ba sai ma son kasancewa a tare da su da ya san anayi….shiyasa gaba d’aya zuciyarsa ta jagule, ransa ya b’aci matuk’a, hankalinsa kuma ya tashi!! dan ya lura ba ta fara basa wannan attitude d’in ba sai da aka fara kiranta a waya…. Gaba d’aya kwakwalwarsa ta yi zafi, haka ma zuciyarsa tunani kala kala ya shiga yi…. ganin zuciyarsa ta na shirin tarwatsewa ne ya sa kawai ya mik’e ya fad’a bathroom ya kama ruwa ya yo alwallah ya zo ya ɗau niyyar nafila….. Sai da ta ji shigewarsa bathroom tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya ta yi addu’o’i ta shiga karatun Al’Qurani a cikin ranta, da haka wani bacci mai d’an karen dad’i ya yi awon gaba da ita….. Sai da ya tashe ta sallar Asubah, tukunna ya juya ya fice ya nufi masallaci…ta lura da yadda ransa yake a d’an b’ace, dan haka ta shirya idan ya dawo za ta yi masa bayani ta basa hak’uri, ta san zai fahimceta. Tana idar da azkar Yahanasu ta kira ta tace”tun jiya cikin dare ta so ta kirata,da kyar ta iya bari asubah ta yi…kamar yadda su Yash suka samu identity d’in mutum biyu su kuma sun samu na mutum biyar har an fara nemansu wataƙila Allah bai yi su Yash d’in za su ga wannan footage d’in ba. yanzu tana ganin su gayawa Yash d’in ne, su k’ara musu haske su had’a k’arfi da k’arfe? ko kuma su yi nasu a daban?” Ajiyar zuciyaManubiya ta sauk’e, ta yi hamdala a fili tana mai jin dad’in good news d’in tukunna tace” Adda Yaha mu yi namu a daban kawai, inaso in taimaka nima, Ina kwad’ayin ganin farin cikin da zai wanzu a fuskar Ya Yash a ranar da muka kama mai laifi sannan idan ya ga muma mun bada tamu gudummawar, mun taimaka. Na ji suma suna maganar da shi da sir Najeeb, and a ta b’angaren nasu suma akwai haske,wanda inda ace sun maƙale sun kasa yin gaba ne to da sai mu k’ara musu haske da namu bayanan, amma tunda suna tafiya suma kawai muma mu yi namun, idan mun riga su yin nasara Alhamdulillah idan sun rugamu hakan ma Alhamdulillah kawai ni dai inaso in taimaka in bada gudummawa ne.” Murmushi Yahansu ta yi kafin tace”shikenan Manu,duk yadda kika ce”. “Yauwa. akwai kud’in da na ajjiye zan baki na case d’in, yaushe za ki karb’a? cash ne” Murmushi Yaha ta yi tace”ai kawai ki barshi…” Da sauri Manu tace”Ina so in yi taimaka ta ko ina ne fa Adda Yaha,pls kar ki ce A’a” “Tam shikenan”Yahansu tace kafin tace”yana Ina?”. Dai dai nan Yash ya k’araso bakin k’ofar d’akin. Tarr ya ji muryar Manubiya tana cewa”ya fita sallah, ai shiyasa ma na samu damar yin wayar, jiya ma na ga misscall, na san watak’il a kan maganar ne shiyasa ban d’auka ba saboda muna tare da shi…” Da sauri ya juya ya bar wajen dan ba ma ya so kunnuwansa su sake jiyo masa wani bala’i da tashin hankalin..har dishi-dishi yake gani, da kyar ya k’arasa kan sofa na corridor ya zauna, yana wani irin haki kamar wanda ya yi y’ar tsere… Manubiya ta san akwai Gwaggwo mai aiki, kuma har ta fara jiyo k’amshin girki, amma hakan bai hanata mik’ewa ta d’an kimtsa domin ta je ta had’awa Mijinta breakfast ba, dukda kuwa morning sickness d’in da ya fara rufar mata mai zafiii. Tana fitowa ta hangesa zaune a corridor kan sofa ya dafe kai da hannu bibbiyu.K’arasawa ta yi da hanzari da d’an mamaki, ta zauna a kusa da shi kafin tace”Ina kwana”sai kuma ta d’aura hannunta a kan nasa tace”Ya Yash”. Cikin kasala ya bata iko ta zame hannuwan nasa da take k’ok’arin yi, daga kansa, kafin ya juyo ya zuba mata ido kawai ba tare da ya ce komai ba. Sai da gabanta ya fad’i sakamokon yadda ta ga idanuwan nasa sun yi jazir…tashi d’aya tausayinsa ya rufe ta sannan gaba d’aya ta shiga jin babu dad’i dan ta san itace silar wannan yanayin da yake a ciki…ta san ba ya iya d’aukar kwanaki masu tsawo ba tare da ya rab’e ta ba. Haushin kanta ma ta soma ji dan haka cikin inda inda tace”Ya Yash dan Allah ka yi hak’uri,ka san ba ni da lafiya shiyasa…” “It’s fine”d’in da ya ce mata cikin katseta ne ya sa ta yi shiru. Tashi d’aya ta ga ya mik’e,yace “idan breakfast ya kammalu ki kawo mini,bari in d’an kwanta, kaina yana mini ciwo,idan na tashi zan ci” Daga haka ya wuce ya shige cikin d’akin. Sukuku! haka ta had’a masa abincin, jikinta da ranta duk babu dad’i, ga kuma zazzab’i. babu yadda Yasira da gwaggwo ba su yi da ita a kan ta kawo su taya ta ba amma tace musu”ba komai,za ta iya”dan haka Yasira ta yi mata sai anjima ta wuce office, Gwaggo kuma ta ci gaba da had’a nasu. Abinci kala uku ta yi masa da coffee, ta d’auka ta nufi saman, ta je ta ajjiye a cikin d’akin,ta so ta zauna a tare da shi amma tana zuwa sai ta ga yana bacci gashi d’azu ta ji yace mata kansa na ciwo, shiyasa ba ta tashe sa ba ta ajjiye a dining table d’in d’akin, ta yi wanka a hankali yadda ba zai ji ba ta fito ta rufo masa k’ofar d’akin. Tana fita ya bud’e ido ya bi k’ofar da kallo… ‘a yadda ta ga yanayinsa in da ace ta damu da shi ai da ta tsaya a tare da shi’ Ya aiyyana hakan a cikin ransa. A d’akin da Siyama take ta tarar da su Yusra suna hira itama Siyaman ta na d’an biyesu ba laifi… Sai da Manu ta zauna tukunna suka gaida ita kafin Yadira ta mik’e tace”bari ta je ta d’ebo mata abinci” Ba yadda ba ta yi da ita akan ta barshi ba amma ta k’i ta fice ta tafi deb’owa. Tana fita Yusra tace”jiya ma kuwa muna rabuwa Mommy ta kira tana so ta ji ya jikinki, ba ta so ta kiraki direct kuma gudun kar ta tasheki dan ba ta sani ba watak’il ko har kun yi bacci,bari in kirata yanzu sai ku yi magana”. Murmushi Manubiya ta yi kafin tace”barshi ni in kirata da layi na” Murmushi Yusra itama ta yi tace”anya kuwa kina da sabon layinta?barshi dai in kira” Daga haka ta kara wayar a kunnenta bayan ta yi dialing… Bugu biyu a na uku Mommy ta amsa, sai da suka gama gaisawa tukunna tace”ga Adda Manu d’in ta sauk’o, jikin nata Alhamdulillah, amma ga ta dai ki ji muryarta.” Tashi d’aya Mommy ta fahimci they are up to something, dan haka ta ce “ok ba ta wayar” Kawai. Yusra tana mik’awa Manubiya wayar ta tsink’e. “Ki yi magana mana kin yi shiru”Yusran tace. “Ai naga kamar ya tsink’e ne” Cewar Manubiya. “Oh God!I forgot fa!wayar tawa ban yi recharging ba!akwai kud’i a wayarki?Yadira ta fita kuma ban san password d’inta ba….” Yusra ta fad’i hakan ta na mai mik’ewa ta k’arasa kan Manubiya ta tsaya tana jira ta bata wayar. Siyama har za ta ce ga tata nan a kira dan kamar ta fahimci akwai wani abun, sai kuma ta tuna babu kud’i a wayarta dan haka ta fara k’ok’arin cin bashi da sauri dan a samu a kira Mommyn da wayartata amma sai ta ji Manu tana cewa”Eh akwai gashi”kafin Siyama tace wani abun har ta danna password d’inta ta bud’e ta mik’awa Yusran wayartata, ita kuma ta sa hannu ta karb’a tana cewa”Bara in saka miki sabuwar number tata in yi saving,ai ta dad’e da daina amfani da wachchar…. Zuciyar Manubiya d’aya, dan ba ta yi tunanin akwai abunda Yusran za ta iya yi daga karb’ar wayarta da making call ba..cikin jinjina kai tace”tabbas kam dan ko na kirata wani zubin ta shiga ba ta d’auka ba, wani zubin kuma ba ta shiga.” “Yeah a saloon aka sace, ita kuma ba ta samu ta yi welcome back ba har yanzu” Ta fad’i hakan tana kwafe number da ta ga anyi ta kiran Manubiyan da ita a jiya ba ta d’auka ba dan gashi ta ga time ɗin da adadin calls ɗin sannan ta ga 090 kamar yadda Yadira ta fad’a, dan haka ba ta da tantama itace ta gayen. Sai da ta gama kwafewa ta adana a wayarta tukunna ta yi copying sabuwar number Mommyn daga wayartata ta loda a wayar Manubiya ta danna call ta mik’a mata tana murmushi. “Lucky morning!na ga password na kwafe number.” Yusra ta fad’i hakan a cikin ranta.Kafin ta juya ta wuce ta koma wajen zamanta ta zauna. Da kulawa suka gaisa da Mommy har da Baba larai,suka tambayeta ya jikinta tace “Alhamdulillah”daga haka suka yi sallama dai-dai nan Yadira ta shigo mata da abinci.Babu yadda ba su yi da ita ba amma ta k’i ci, Siyama ma ta ji dad’in k’in cin da ta yi dan itace ma ta fara yi mata signal da ido saboda yadda suka dage ya sa suka fahimci in ba da kyar ba sun mata abu a cikin abincin ne…shiyasa ta k’i yarda ta ci iyakaci ta d’auki ruwanta na bohole da ta d’ura a gora jiya wanda taga har ya yi k’ank’ara k’ank’ara ta bud’e ta yi bismillah ta kai baki..kalar ruwan bai chanja mata ba hakama taste d’in shiyasa hankali kwance ta sha sosai ta ajjiye tana sauk’e ajiyar zuciya… Murmushi Yusra ta yi a ranta tace”in kin san wata ai ba ki san wata ba!”. Ba su fi minti ashirin da zama ba, Inna ta kira Manubiya ta sanar mata halin da ake ciki tace”nan da 11 za a d’aura aure” Daga Manubiya har Siyama duk kuka suka saka…gashi sunata kiran Jidda ta ma k’i d’agawa. Sama Manubiya ta je ta sanar da Yash halin da ake ciki dan haka ya mik’e yace “bara ya shirya sai su tafi” shima duk hankalinsa a tashe.Ba yadda ba ta yi da shi ya tsaya ya karya ba amma ya k’i yarda yace”su je da wuri kawai ba su da ishashshen lokaci, ya san idan ya yi wa Baba magana inshaaAllah zai d’aga k’afa” A gaggauce ya yi wanka ya shirya cikin wata had’add’iyar b’akar jallabiya daga nan suka d’auki hanyar gandun albasa gaba d’ayansu har Yusra da Yadira. A mota Yusra ta yi chatting Yassira ta tura mata har da number Abbakar…Ya’isha Yasirar ta kira ta tsara mata komai yadda za ta yi kafin tace”idan ya k’i yarda ta kira ta za ta san abun yi”. A b’akin gate d’in gidan suka tarar da Baba Ya Nafi’u da kaka mallan da wasu mutane su uku.Da mamaki su Ya’isha suka shiga kallon juna ita da Yusra dan basu san sun chanja gida ba kuma za su iya dafa Al’Qurani akan cewa Yashjub ne ya basu gidan!tabb!aikuwa yanzu ba sai anjima ba za su gayawa su Mommy, dama sun san irin haka ce za ta yi ta faruwa,gashi kuwa har an fara…. Suna wannan tunanin suka k’arasa suka gaida su Baba, daga haka ya Nafi’u ya ce bari ya bud’e musu gate su shiga da motar amma sai Yash yace ya barshi bari ya bar motar tasa a waje kawai. Shi ya bud’ewa su Manu k’aramar k’ofa suka shige ciki daganan suka juya wajen su Baba da shi da Yash. Manya manyan flat house ne guda biyu iri d’aya gate d’insu da compound d’aya, ko wanne yana d’auke da 4 bedroom da 2 parlours da kitchen da dining area,ga babban tsakar gidan da ya ji interlock wanda atleast sai a gina irin gidajen uku a cikinsa.Har da d’akin mai gadi a kusa da gate d’in. Ba kad’an ba gidan ya burge su Manubiya tashin hankalin da suke a ciki ne ya sa ba su tsaya santin gidan ba suka afka b’angaren da suka ga k’ofarsa a bud’e. A chan waje kuwa sai da Yash ya tsaya tukunna ya fahimci limaman masallacin area d’in ne Baba yake tare da su… Sai da suka gama suka yi sallama suka wuce tukunna Yash ya yunk’ura da kwarin guiwa zai lallab’a Baba amma instead sai Baban ya rigasa ya shiga had’a sa da Allah yana neman alfarmar indai ya d’aukesa a matsayin uba kuma yana ganin girmansa to kawai ya bar maganar ya yi wa su Jidda addu’ar samun zaman lafiya. Sai da Baba ya tabbata ya d’aure Yash da jijiyoyin jikinsa tukunna ya barshi jiki a sanyaye….. Tun daga nesa da ya taho! Ya Nafi’u ya fara murmushi, dan ba kad’an ba ya ji dad’i a cikin ransa matuk’a! Dama d’azu da sassafe da ya je ya yi masa magana a take ya yi masa alk’awarin ‘inshaaAllah zai zo,’ kuma dama tun a d’azun ya lura wannan karon ya Musbah ya ji fad’an da ya yi masa sosai, shiyasa tun a lokacin ya ji sanyi da dad’i a ransa dukda kuwa uwar ramar da ya ga Abokin nasa ya yi. Sai da ya gama parking mashin d’insa tukunna Baba ya lura da shi ya gane sa…..k’uraaa masa ido ya yi gaba d’aya tashi d’aya sai tausayinsa ya lullub’esa, dan ana ganinsa an san yana cikin matsananciyar damuwa. A hankali Baba yake jin duk wani takaicin Ya Musbah da ya k’unsa yana warwarewa sakamokon fahimtar da ya yi tabbas ba yin kansa bane kuma shi kansa ba ya jin dad’in abunda yake yi d’in, dan gashi gaishe da shi yake yi amma sam ya kasa kallon cikin idanunsa kamar ma kuka yake son yi. Ahankali ya had’iye wani k’ululun abu da ya tokare masa mak’oshi yace”Alhamdulillah Musbahu”still yana kallonsa yana karantarsa. Sai da ya sake yin k’asa da kansa kafin yace”ya k’arfin jiki?” ya fad’i hakan a hankali. “Alhamdulillah”Baba yace daga haka ya maida dubansa ga Ya Nafi’u yace”Nafi’u na tura maka kud’in,ka je ka siyo gadon,kaka mallan kai yake jira tun d’azu ku kai gidan.” A hankali Ya Musbah yace”Baba ba za a hak’ura da maganar nan ba,ka yi hak’uri dan Allah ka….” Cikin fushi Baba yace”kai har yaushe ka zo ka ji halin da ake ciki da har za ka tsomo mini baki a cikin al’amurana?Kar fa ka kaini bango Musbahu, kulaka da ka ga na yi ba shi yake nufin na manta abubuwan da ka tafka ba!” Da sauri kaka mallan ma ya tsomo baki,dama d’azu ma saboda Yash ne ya yi magana shiyasa bai tanka ba, dan haka yanzu ya samu bakin magana harda cewa “a cikin duhu aka kama Jidda da Al’ameen, amma shine saboda rashin sanin ciwon kai still suke da bakin k’orafi ga Yusuf wanda ya ji ya gani ya rufe ido zai aureta a hakan.” “Yashjub mu je ciki” Baba ya ce, daga haka ya juya, har Yash zai bisa sai wayarsa ta d’au k’ara, ganin sunan Daddy yasa yace”Daddy yana kirana bari in je in dawo kafin d’aurin auren.” “To”kawai Baba yace, daga haka ya shige cikin gidan dan yana so ya yi wanka ya shirya da wuri gashi har 9:00 ta yi. Su Ya Musbah sun san shawo kan Baba ba abu mai sauk’i bane, dan ransa ba a b’ace ba ma idan ya turje babu mai sa shi ya bari, ballantana yanzu da yake a fusace, shiyasa gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi suka cigaba da addu’a kawai..dan tunda har Yashjub ya sa Baki ya k’i yarda to addu’a kawai za suyi ta yi su jira Ubangiji ya yi ikonsa ya ceto rayuwar Jidda. 28 September 1994 ….zaune take a tafkeken parlourn gidan, wanda ya ji kayan alatu mabambantq…a cikin shekarun da ba su fi hud’u ba Mijin nasu bud’i yake samu ta ko ina Alhamdulillah..sun chanja gida, ya gina musu bungalow guda biyu tafkatafka iri d’aya a cikin gate da compound d’aya, ko wacce da b’angarenta, sai kuma boysquaters babba shima a ta gefe…ya siya musu gwala gwalai har motoci ya siya musu guda biyu iri d’aya, zani kuwa mafi tsada na wannan zamanin shi suke d’aurawa ita da Abokiyar zamanta! Sai dai fa ita duk wannan daula da ake ciki sam hankalinta ba a kwance yake ba, zuciyarta babu dad’i, nutsuwarta ba ta tare da ita!! sakamokon juya mata baya da Mijinta masoyinta abun k’aunarta ya yi tun lokacin da ta haihu shekaru hud’u kenan. Tashi d’aya ya chanja mata ba tare da ta san laifin ta garesa ba. A yadda yake nunawa kamar har yanzu yana k’aunarta tunda yana masifar kishinta har yanzu kishi mai tsanani ma kuwa, amma kuma ko kusa da shi baya so ta je..hantara kyara da tsangwama ne kawai yake shiga tsakaninta da shi, gashi tsabar kishi ya maida ita kamar prisoner ko baranda ta fita indai mai gadi ko mai wanki wani ya ganta to fa ta shiga ukunta a ranar, hakanan tana ji tana gani Abokiyar zamanta za ta tambayi fita a barta amma ita ba ta Isa ba! kitso kawai ta san tana zuwa bayan layi shima tare ita da Abokiyar zaman nata su ke zuwa. Ita sam ta kasa gane kan Imam kwata-kwata, dan kamar ma zarginta yake yi haka take gani, watak’il saboda ya san ba ya sauk’e hakkin ta da ya rataya a wuyansa ne shiysa yake zargin za ta je ta nema a waje… A take hawaye suka shiga sintiri a kan kyakkyawar fuskarta, ‘shin wannan wacce iriyar rayuwa ce??’ Ta aiyyyana tambayar a cikin ranta!! gashi ba ta da gurin zuwa, bata da kowa!! dama Imam d’in shine Uwa shine Uba kuma Masoyi a gareta, yanzu kuwa abubuwan da yake nuna mata ita kanta ta san kora da Hali ne k’arara yake yi mata, ya gaji ita ne..!!! A da tana tunanin ta yi sa’ar Miji yanzu kam tabbas ta san ba ta yi ba, maimakon sa’a Ubangiji ya had’ata ne da mugun Miji Mugu ajin farko! “Khadija wai har yanzu ba za ki bar kukan nan ba?na gaya miki addu’a itace mafita…wallahi Imam har yanzu bai yi miki rabin abunda ya yi mini ba,haka yake, zai daina wata rana, dan Allah ki yi k’ok’ari ki cire damuwa a ranki mana.” Muryar Abokiyar zamanta wadda shigowarta cikin b’angaren nata kenan, ta katse mata tunani. A hankali ta d’ago ta kalleta daidai tana zama da Yaronta a hannunta. Cikin sharar hawaye tace”ba komai Mommy,kar ki damu, nima na san wata rana sai labari.” Cikin son kawar da maganar dan zuwa yanzu ko rarrashi ba ta so a cika yi mata gaba d’aya sai ta sake zama emotional, dan haka ta d’an k’ak’alo murmushi ta ce ”Yassir! Ina ka baro Yasira? ko tana chan tana sana’ar?”. Ta fad’i hakan tana mai mik’awa Yaron Hannu alamun ya zo gareta. “Kamar kuwa kin sani..tun da Baba larai ta yi musu wanka ita da Yahanasu suka koma bacci har yanzu ba su tashi ba..” Murmushi ta yi tace”Allah ya yi albarka, ya had’a kawunansu” “Am khadija ko za ki yi wa Hajiya Mama magana, a samu Yashjub ya dawo..ya yi k’ank’anta a zuwa Hutu ya dad’e haka a wata k’asar, gashi an koma makaranta.” Dariya ta yi kafin tace”yanzu Mommy sai in kira Hajiya Mama in ce mata Yashjub ya dawo ya yi k’ank’anta? ai sai a ga rashin karar mu..ki yi hak’uri, ita kanta na san nan ba da jimawa ba za ta dawo da shi..ke da ya kamata ace yanzu fafutukar ta yadda za ku shirya ma kike yi!? idan ta ji mun ce Yash ya dawo ai bak’in jini za ki sake gogawa kanki har ni sai ta shafa….” Shiruu Mommy ta yi kafin ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya tace”Allah ya sa mu dace” “Ameen”Khadija ce, sannan ta fara yiwa Yassir wanda ta karb’a wasa shi kuma yana dariya. “D’azu dai Daddy ya kori mallan lawal,ai dama na gaya miki yadda ya sakawa Yaron nan k’ahon zuk’a ba zai barshi ba.” Shiruu Khadija ta yi kafin tace”yanzu kenan ta tabbata Daddy zargin na yake yi?” “Ba zarginki yake yi ba Khadija masifar kishi ne kawai, ke dai ki yi ta addu’a, sannan kamar yadda kika fad’a wata rana sai labari.. Ki yi ta sallar dare kina gayawa Ubangiji, na san kina yi amma ki k’ara,jikina yana bani inshaaAllah yana dawowa daga Abuja za ku shirya komai ya zama labari…” A hankali Khadija tace”Au ya tafi?”. Jinjina kai Mommy ta yi kafin tace”bai yi miki sallama ba?” Sai kuma ta kawar da zancen tace”bari in je in had’o y’an kud’ad’e in bawa mallan lawal, Yaron yana bani tausayi wallahi, bashi da kowa fa maraya ne gaba da baya.” Tana gama fad’in haka ta mik’e ta bar mata Yassir ta nufi k’ofa tana cewa “bari na je na d’auko.” Daga haka ta fice…. Tana fita itama ta mik’e ta nufi bedroom d’inta da Yassir a hannunta…wajen ajjiye kud’ad’e ta d’aga ta zaro masu nauyi da niyyar idan Mommy ta dawo ta bata tace ta bawa mallan lawal d’in, dan ko ba komai shima maraya ne kamarta kuma saboda ita a ka koresa….tana d’aukowa ta jiyo kenan suka yi ido biyu da shi, da farko tsoro ya bata saboda ta san mallan lawal d’in da ta sani ko giyar wake ya sha bai Isa shigo mata har cikin bedroom ba, ganin yana magana yana matsota ne ya sa ta fahimci tabbas fa shi d’in ne dan haka cikin tsoron gudun a gansu fushi da hargowa ta fara ce masa”ya fice mata daga d’aki” Ba tare da b’ata lokaci ba. Gadan-gadan ta ga ya nufo ta daga haka bata sake tuna komai ba…sai farkawar da ta yi wadda ta ji inama da ba ta farka ɗin ba inama wucewa lahira kawai ta yi da ya fiye mata kwanciyar hankali. Daga ita sai under skirta kwance a gado d’aya lullub’e cikin bargo d’aya da mallan lawal wanda shima wando ne kawai a jikinsa yana kwance yana sharar baccinsa peacefully. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ta shiga ambato ba k’ak’k’autawa, tana jin wani irin bak’in ciki da tashin hankalin da bata tab’a jin kwatankwacin irin sa ba. Tashi d’aya ta fashe da kuka, ta fara k’ok’arin tashi amma sai ta kasa motsi kwata kwata saboda wani masifaffen tashin hankalin da ya sake mamaye ta sakamokon muryar Daddy da ta ji a parlournta yana cewa”har fa na kama hanya kuka saka ni na dawo saboda takardun! ke da kika gansu a hannun Yarinya ai kamata ya yi ki amshe ki kawo mini.” Cikin kwantar da murya ta ji muryar Mommy tana cewa”to ai Daddy ban yi tunanin naka bane, ni na d’auka na Maman nata ne da na ga ta yo nan d’in da su,ba dan yanzun ka gaya mini kalar envelope d’in ba ma da yanayinta da ba ganewa zan yi ba….” A hankali Khadija ta koma ta kwanta ta ja bargon ta lumshe idanuwanta kawai, saboda ta san no way out, dan a halin da ake ciki ma key ta ji Daddy yana murzawa ta waje zai bud’e k’ofar ya shigo yana cewa”yau kuma Khadija rufe kanta ta yi ta ciki kenan!Allah ya kyauta!”.Gashi ba ta ga makulli a jikin k’ofartata ta ciki ba. Tsabar tashin hankali sumewa ta yi,ruwan da Mommy ta shek’a mata ne ya sa ta farka a gigice!!! chan ta hango Daddy ya nufo ta gadan gadan da wuk’a a hannunsa kafin ta yi wata wata har ya Burma mata a ciki……… Sama sama ta ke jin Mommy tana kuka tana rok’on Daddy tana cewa”kar ka yi haka Daddy,Ubangiji kad’ai ne ya Isa ya yanke hukunci, kar ka yi abunda zaka kai kanka prison, ka bud’e musu su fito dan girman Allah…..” K’aurin wuta ta fara ji kafin hayak’i dga haka ta ga wuta tana ci wanda hakan ya tabbatar mata tabbas Daddy wuta ya cinna musu. Kamar d’azu yanzun ma ba ta yi yunk’urin yin komai ba dan ba za ta iyaba gashi jikinta ba kwari,ba ma ta gani sosai ga tashin hankali..ko yatsarta ba ta iya d’agawa. …..Ba ta san Ina Mallan lawal ya yi ba ita dai ta ji an d’auke ta sannan muryar wani yana cewa”ta nan za ku bi” Wanda har gobe ta kasa tantance muryar mutumin ballantana ta yanke hukunci. A cikin wani d’an madaidaicin gida ta farka ta ganta, ana yi mata k’arin ruwa, ga likita a gefenta da mallan lawal. Rufar mata suka yi suna tambayar ta ya jikinta, itakam bak’in ciki da tsananin tashin hankalin da take a ciki ma bai barta ta ko kallesu ba…duddubata likitan ya yi ya cewa mallan lawal “idan wani abun ya tashi ya nemesa” daga haka ya yi musu sallama da Allah ya k’ara sauk’i ya fice. Yana fita mallan lawal ya gyara zama ya fara magana”Khadija ki yi hak’uri dan girman Allah..wallahi sharrin shaid’an ne, amma inaso ki san cewa babu abunda ya shiga tsakaninmu dan ko da na yunk’ura kasa aikata komai na yi a gareki….na san kin tsaneni ba kya son jin ko murya ta ma shiyasa na zab’i in yi nesa da ke daga yau har abada. Ga gida nan ki zauna a ciki kar ki tambayeni a ina na samu kud’in kawai inaso ki san wannan gidan naki ne, ga takardun nan a cikin wachchar drawer!ki yi hak’uri ki yi hak’uri ki yafe mini dan girman Allah”. Yana gama fad’in haka ya mik’e yace mata”a cikin garin Abuja muke ba a kano ba.” Daga haka ya sa kai ya fita. Sai da ta tabbatar da ya yi nisa tukunna ta mik’e tsaye..d’inki ne a cikinta amma kawai tsintar kanta ta yi da fara takawa a hankali a hankali a haka har ta fice daga d’akin ta fice daga cikin gidan gaba d’aya,ta ya ma za ta fara zama a gidan da lawal ya ajjiyeta?! ba zai yiu ba!. Dare ya yi a lokacin gashi unguwar shiruu babu ma mutane sosai….. Tafiya kawai take yi ba ta san ina za ta je ba, ba kuma ta san abunda ya kamata ta yi ba…wani ikon Allah zuwa yanzu ta nemi zafin da cikin nata yake yi ta rasa, amma kuma ko ba ta kalla ba ta san d’inkin ya warware dan tana jin yadda jini yake bin jikinta…ta lura da yadda wata mota take ta binta a hankali, sai da aka yi kusan tafiyar minti ashirin da mutumin ya ga ba ta da niyyar tsayawa gashi sai faman zubda jini take yi tukunna yayi parking motar a daidai gabanta ya fito yana k’are mata kallo. Sai a lokacin wata juwwa ta kwasheta ta tafi ta zube a wajen. Sai da ta yi kwana huɗu tukunna aka samu ta farfad’o da mugun kyar. A asibiti ta bud’e ido ta ganta,wannan mutumin da ya tsinceta ne yake sanar da ita cewar”kwananta hud’u da kyar aka samu ta farfad’o a ranar.” Babu yadda bai yi da ita akan ta gaya masa inda family d’inta suke ba amma ta k’i magana..ganin kamar ba ta ji kuma ba ta magana ne ya sanya ya hak’ura ya rabu da ita ya had’a ta da nurses ya biya kud’in komai yace “idan akwai emergency a kirasa”daga haka ya tafi. Duk yadda ya so ya manta da al’amuranta sam sai ya gagara,gaba d’aya tausayinta ya hana sa sukuni lamarinta ya tsaya masa a rai..ya san tabbas tanada buk’atar taimako. Ba a yi sati uku da rasuwar k’anwar sa ba, wadda su ka yi wa aure suka kai garin jos!! ashe mijin ba zaman adalci yake yi da ita ba, k’arshe sai ciwon zuciya ne ya kasheta….. Mahaifiyarsu ta rasu kuma su biyu ne kad’ai shiyasa har gobe yake blaming kansa dan in da ace yana yawan zuwa dubo ta kuma ya saka idanu a kanta to da hakan ba ta faru ba. Sai da ya tabbatar ta warware ta fita a shock,na kusan wata ɗaya tukunna ya koma,a lokacin ta warke amma wani ikon Allah damuwa ko kad’an ba ta barta ba asalima kuka ya je shi ya tarda ita ta na yi. Ya kad’u sosai da lamarinta dan haka bayan sun gaisa ya amsa godiyar da ta yi masa da kulawa ya zauna ya shiga tambayarta “menene matsalarta har haka?,kar ta damu ta d’aukesa a matsayin yayanta ta fad’a masa komai.” Sau uku tana bud’e baki da niyyar bashi tarihinta amma tana fara cewa”Mijina ne…” Sai kuka ya ci k’arfinta…… Zuwa yanzu ya fahinci inda gundarin matsalar take shiyasa kawai ya ce “ta yi shiru…..ta yi hak’uri, ko ma me ya yi mata ta yi hak’uri Allah zai saka mata.” Sai da ya tabbata ta d’an nutsu tukunna yace”akwai wanda take so ta kira a cikin y’an uwanta?” Ba b’oye b’oye tace masa ”ba ta da kowa” Jinjina kai ya yi yana mai jin tsananin tausayinta,haka kurum take tuno masa da marigayiya k’anwarsa tun ba ma da ya ji itama sunanta Khadijah kamar k’anwar tasa ba.Ya jima yana nazari kafin yace”kina buk’atar ganin shi Mijin naki ne?a nem…” Tun kafin ya rufe bakinsa tace”A’a” Dan ba wai iyaka Lawal da ya k’ulla mata sharri take jin haushi ba har da Imam wanda ya yarda ya aminta ta aikata abunda aka nunawa idanunsa bayaga haka kuma ya hari rayuwarta. “In kai ki Gidana za ki taya matata zama?,Dr ya ce mini a yau zai sallameki inshaaAllah” Muryarsa ta katse mata tunani. ….Da farko k’in amincewa ta yi tace”ya barta a asibitin ko kuma ya barta ta tafi kawai za ta san abunyi.”Shi kuma ya k’i, dan a yadda take da damuwar nan idan ba ta samu wani da zai yi mata gata ya tsaya a kanta ba tabbas akwai matsala, shi kuma haka kurum ya ji yana so ya taimake ta, kuma yana so ya yi making up to negligence d’in da ya yi (biya bashin sakacin da ya yi) wa sister d’insa, shiysa ya nace ya k’i barinta har sai da ta amince ta bisa suka tafi gidan nasa. D’ansa d’aya mai suna Al’ameen da matarsa suna ce mata Ammi, dan shima mai gidan sunan mahaifiyar sa ne da matar tasa. Dama tun farko Ammi ta fara nuna kishi da Khadija dan ce mata ya yi y’ar uwarsa ce cousin za ta zauna da su. Daga baya kuwa da ya fad’a mata gaskiya dan shi bayason b’oye b’oye,da kuma itama y’an uwanta suka zugata shikenan ta fara hauka!……har ta yi haukar ta kuwa ta saduda babu wanda ya biyeta,ita da kanta ta zauna ta yi lissafi mai kyau ta nemi gafarar mijinta da khadija aka zauna lafiya, dan a lokacin sun kusan shekaru shidda tare shiyasa lissafinta ya bata inda ace fa aurenta zai yi tou da tuni ya aura.Kuma yadda Khadija take kula mata da Al’ameen ko ita ba ta kula da shi..mai d’a wawa!ta haka Khadija ta siye zuciyar Ammi gaba d’aya. A kwana a tashi zama ya dawo da su Kano.Sai a lokacin Khadija ta gaya musu tana da y’a Yahanasu. Addu’ar ta d’aya Allah ya sa ba a chanja musu makarantar da ta san an fara saka su ita da Yashjub tun farko ba,dan haka suka tambayi baban Al’ameen suka tafi ita da Ammi. Ba su sha wahala ba dan tashi d’aya matar ta shaida ta ta amsheta hannu bibbiyu har da hawayenta tana cewa”ai ce musu aka yi ta rasu,amma ta je gida an ganta?ko dai nan wajen Yahanasu ta taho direct??ta je su ganta suma hankalinsu ya kwanta waye waye…” Ita dai Khadija ce mata ta yi tou kafin tace”a kawo mata Yahanasu da Yashjub.” ‘Yashjub ai ya dad’e da komawa Uk,amma Yahanasu dai tana nan,da tare take ma da siblings d’inta, to yanzu bamu da nursery section sakamokon gobarar da muka yi shine aka chanja musu school.” Matar ta faiyyace mata hakan tana mai fita domin ta je ta taho mata da Yaha. Sai da Khadija ta yi kuka,saboda da kyar Yahanasu ta shaida ta. Tana murna tana kuka kamar ranta zai fita haka ta mak’alk’ale y’ar tata. Hatta Ammi da mai makarantar sai da suka yi kuka.. Tun daga ranar duk ran Jumaah kafin su d’auki Al’ameen a school sai sun biya sun ga Yahanasu,Yarinyar ta shak’u da mahaifiyarta sosai zuwa yanzu….Khadija Ammi da Baban Al’ameen suna shiryen shiryen zuwa su je a yi magana ta fahimtar juna a samu Imam ya bawa Khadija Yahansu kwasam rannan sun je mai makarantar tace “Mahaifin Yahanasu yace idan ta sake barinta ta shiga makarantar sai ya k’ulle ta!. Dan Allah dan Annabi ta yi hak’uri ta tafi kuma yace idan har ta sake zuwa kusa da y’ar sa wallahi kowa sai ya ji kansu kuma kowa sai ya ji abunda ta aikata har ita y’ar tata”… ….Babu kalar tambayar da su Ammi ba su yi mata ba a kan ta yi musu k’arin bayani amma ta k’i cewa komai,Baban Al’ameen da har yana shirin shiga kotu a samu a kwato mata y’arta amma ta hana ta kuma rok’esu akan kar su sake yin maganar a bari ya wuce kawai…Zuwa wannan lokacin sun riga sun san Khadija sun san ba muguwa bace ba kuma ba ta da wani mummunan hali,shiyasa ba su dasa ayar tambaya a kanta game da hakan ba kuma suka bar maganar ya wuce kamar yadda ta rok’a ta buk’ata. A b’angaren Khadija kuwa,abubuwa da dama ne suka had’e mata! Kenan har yanzu Imam bai yi bincike ya goge zarginta ba!bai yi nadamar abunda ya aikata mata ba? Sannan ko kewarta ma bai yi ba duk tsawon waennan shekarun bai nemeta ba, bai nemi ta dawo garesa ba maimakon hakan ma yana so ne ya ƙarasa yanke duk wata alaƙar da suke da ita da shi,y’ar cikinta ma ya raba ta da ita kenan yanzu.! Abu na uku kuma ta san tana da gaskiya akan sharrin da Lawal ya yi mata, amma kuma har ga Allah idan akwai Al’amari mafi k’ololuwar tozarci da Muni da masifar tashin hankalin da ba ta son tunawa a rayuwar shine wannan al’aamarin,ita kanta ita kad’ai idan ta tuno ji takeyi kamar ta binne kanta tsabar tashin hankali, ba don k’arfin addu’a ba da tuni ta zauce tsabar yadda abun yake addabar ta a ko da yaushe idan ta tuna, A yadda Imam ya zama wani irin mugun mutum ta san zai yi mata terere ne kamar yadda mai makarantar su Yahansun ta ce yace “kowa sai ya ji kansu shi da ita,har Yahanasu”.A ganinta idan ba ta samu damar shak’uwa da Yahanasu ta bata tarbiyya da kulawar da ta kamata ba to bai kamata ta bada gudunmawa wajen goga mata bak’in fenti ba!Yahanasu mace ce, aure za ta yi, ta san muddin ta bawa Imam k’ofa ya tozartata tabbas abun sai ya shafi rayuwar y’arta. Mommy Uwa ce ta gari kuma za ta iya rantsuwa a kan soyayyarta ta gaskiya ga Yahanasu shiysa ta zab’i ta bisu ta addu’a, dama rayuwa ba a yi ta dan ka samu komai yadda ka ke so ba!…tsakaninta da lawal Allah ne kad’ai zai Isar mata dan ya cuceta ta koina,Imam kuma ya tarwatsa ta gaba d’ayanta!…. kaico!da rashin sa’ar Miji na gari wanda zai tsaya mata ya bugi k’irji ya yi shaidar ta ya kareta a gaban kowa,asalima shi harin rayuwarta da duk wani sauran farin ciki da darajarta yake yi… ko maganar tozarcin da wannan rana ta k’unsa ba ta so ta tuna ballanta a yi mata terere a bainar jama a a gaban y’arta. Dan haka ta zab’i ta bi y’arta da fatan alkhairi kawai tare da addu’ar samun Miji na gari dan tabbas duk macen da ta yi rashin sa’ar Mijin kwarai a rayuwa to ta yi babban rashi….. ………shiyasa tun jiya Hankalinta yake a tashe, take addu’ar Allah ya kawo abunda zai tarwatsa maganar auren Jidda da Yusuf dan tabbas Yusuf bai dace da Jidda ba, mutumin da ba a san silar arzik’in sa ba ta ya za a d’auki y’a a basa saboda Allah………….. Sallamar su Manubiya ce ta katsewa Mama dogon tunanin da ta lula! A hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta shiga goge hawayen da ita kanta sai yanzu ta san suna zubo mata.Sai da ta gama goge fuskarta tukunna ta d’ago ta kallesu tana mai amsa sallamar tasu. Cikin tsananin mutuwar jiki Manu ta k’arasa inda take suka gaisa da Mama da Aisha da Anty Umma,ta gaida Ammi wadda daga ita har Siyama suka yi mamakin ganinta a parlourn nasu tukunna tace musu “Ina su Inna” Aisha ce ta mik’e tace”mu je wajen nasu” Daga haka ta yi gaba suka bi bayanta. Su biyu kawai suka tarar a cikin d’akin,Jidda ta rame a cikin kwana d’aya tak! ta fita a haiyyacinta.. Suna zaune Inna ta na yi mata nasiha a haka su Manu suka shigo suka tarar da su. A gefen gadon suka zazzauna suka sakata a tsakiya kowa idanunta ya cicciko. Bayan gaishe gaishe Inna ta yi sauri ta mik’e ta ce”ga ta, Manu, Aisha ku yi mata fad’a kuma. Baba yace ana d’aurawa za a wuce a kaita gidanta.” Siyama ce ta iya cewa”Inna kuma babu abunda za a yi?” Murmushin da ya ki fi kuka ciwo Jidda ta yi ta rik’o hannunta tace”ba komai Siyama,Allah ya sa hakan ne ya fi alkhairi” Siyama na shirin yin magana suka had’a ido da anty Umma wadda shigowarta kenan dan haka ta yi saurin d’aura yatsanta a kan labb’anta alamun ta yi shiru kafin ta kalli Manubiya tace”Manu d’an zo” Suna fita ita da Inna suka ce mata “tunda har Jiddan ta yi shiru, ta hak’ura itama, to kawai a ci gaba da kwantar mata da hankalli,kar wadda tace wani abun da zai d’aga mata hankali a cikinku. Baba ya riga ya yi nisa ba zai ji kiran kowa ba, ga Ammi Chan a parlour har ita aka had’u aka dinga bashi hak’uri d’azu amma ya k’i hak’ura!! dan haka kawai mu zuba mishi ido.Zab’in Allah muke nema a ko da yaushe..dan haka ba a san meye a k’asa ba, a dai ci gaba da addu’a kawai…” Da “to” kawai Manubiya ta amsa su, daga haka ta nufi d’akin da ke opposite na Jiddahn dan ta san watak’il shine na Inna, tana shiga ta mayar da k’ofar da rufe dan har ga Allah ba ta son had’a idanu da Jidda ba za ta iyaba, gaba ɗaya ta kasa yarda da ‘wai Jidda za ta auri Yusuf amma ba abunda za ta iya yi a kai.’ Waya ta d’auko ta kira Yashjub….a tunaninta har yanzu za ta ji fushi a muryarsa amma sai ta ji sa wasai kamar ba ta yi masa laifi jiya ba har yana tambayarta akwai abunda take so ya siyo ya taho mata da shi?yana hanya Daddy ya d’an kirasa zai je ya dawo.” “A’a”kawai tace. Daganan ta tambayesa ya suka yi da Baba,komai ya gaya mata daga haka shima yace “su yi ta addu’a, zai kirata anjima, yana shiga office d’in Daddy yanzun” Sallama suka yi ta ajjiye wayar tana tunani barkatai a cikin ranta. K’arfe 10:30am guri ya cika taff da jama’a dan Yusuf da kaka mallan sun yi gayya ba laifi,cikin gida kuwa kowa hankalinsa a tashe yake, suma su Ya Nafi’u hankali a tashe dan yanzu suka dawo daga kai gado, shiyasa suka kuma tabbatarwa eh fa Jidda Yusuf za ta aura…kaff wajen daga y’an gaiyyar sod’i da suka ga anata sauk’e kulolin abinci da lemuka da snacks da kajii sai Yusuf da kaka mallan ne kawai suke farin ciki dan hatta Baba hankalinsa ba a kwance yake ba, ba a son ranshi zai aurawa Jidda wanda ranta ba ya so ba musamman ma yanzu da Baban Al’Ameen ya zo ya ja sa gefe ya basa hak’uri, sannan ya ce masa ”a shirye yake su ɗaura auren Al’Ameen da Jidda a yanzu.Ya yarda da Al’ameen har ma da ita kanta Jiddan, amman indai har zargin su yake yi kamar yadda labari ya iske masa to tabbas babu wanda ya fi chanchanta Jiddan ta aura idan ba Al’ameen d’in ba.” “Ya je ya sake tunani,da shi da wakilin Al’ameen suna nan babu inda za su je,fatan Allah ya sa su ji alkhairi.” Tun daga nan jikin Baba ya yi sanyi, tun ba ma da Baban Al’ameen yace”ya yarda da har ita kanta Jiddan” ba! A take a lokacin ya ga rashin adalcinsa ga Jidda…..tabbas ya biyewa dokin zuciya ya yanke d’anyen hukuncin da har abada zai dinga damunsa dan ya san zuwa yanzu kam ba zai yiu ya chanja d’aurin auren nan daga kan Yusuf ya koma kan Al’ameen ba…. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 33* “Na gaya miki dama,ni ne Mijinki…in da ace ba ki tsaya b’ata mana lokaci ba da tuni abubuwa da dama basu faru ba!. Allah ya bamu zaman lafiya Jidderty” Yusuf yana gama turawa Jidda message kamar haka, ya juya ya nufi cikin masallacin, yana zuba wani faffad’an murmushi..yana ji kamar an yi masa bushara ne da Gidan Aljannah. A gefen Baba ya nemi guri ya zauna, idaunsa a kan Baban Al’ameen wanda tun d’azu ya ke ankare da shi!! yana sane da shi ya san so yake a fasa auren a bawa d’ansa. har ga Allah bai yi niyyar yi wa Baban Al’ameen ko Al’ameen d’in wani abun ba amma abunda mutumin yake ta yi tun d’azu ya sa ya k’ullacesu, kuma sai ya nuna musu waye Yusuf! Bari a gama d’aura masa aure da Jidda a kaita gidansa lafiya, Wallahi sai ya b’atar da su. Ana shirin fara d’aurin auren. Sojoji da y’an sanda masu fararen kaya sun fi mota ashirin, suka danno kai cikin layin…a dai-dai wannan lokacin. Sojoji uku da ss guda d’aya ne suka shigo cikin masallacin suka ce “kowa ya fito!”cikin dakakkiyar murya,aikuwa tashi d’aya waje ya hautsine…. cike da fargaba jama’ar suka fara kiciniyar fita ana hayaniya da tambayar “mai ya faru” Baba ne ya juya da niyyar cewa Yusuf “mu je, mu ji mai ya faru, a samu abun ya lafa sai a dawo a d’aura”..amma kamar walk’iya da ikon Allah sai ya ga babu Yusuf babu mai kama da shi, bayan yanzunnan suka gama magana da shi. A b’angaren Yusuf kuwa, tunda ya ga Sojoji hankalinsa ya yi masifar tashi! tsoro ya rufesa, in banda dukan uku uku babu abunda k’irjinsa yakeyi. dukda kuwa ya san cewa fuskarsa ba sananniya bace ba a cikin yaran black snake kuma shi bai yi abun da har ya zamto wanted ak nemansa ba amma hakan bai hanasa tunanin watak’il shi aka zo nemeba, dan yanzunnan ya ga message d’in Abokinsa ta inda yake sanar masa ”an zo kama Black snake a airport, ya yi yunk’urin guduwa an harbesa ya mutu, sannan an bud’e wayarsa an fara binciken neman Yaransa!! dan haka a duk inda yake kawai ya gudu!! kafin a samu komai ya lafa.” Yana gama karanta message d’in ko numfashi bai ja ba ya ga Sojoji sun shigo, shiyasa ana fara hayaniya ya sulale ya bi ta k’ofar liman da sauri ya fice, amma yana fita ya ci karo da wasu a ta gaban k’ofar saboda dama zobe su ka yiwa masallacin….tashi d’aya suka damk’esa dan an raba musu hotonsa shiysa suka yi saurin shaidasa. Baba, Yashjub wanda k’arasowar sa kenan sai su Ya Musbah sojojin suka yi wa bayanin arresting Yusuf ɗin da aka yi…… …..”A cikin wayar black snake suka hararo Yusuf ta hanyar bibiyar chat d’insu da suka yi, an gano yana d’aya daga cikin manya manyan yaransa masu tayashi safarar kwayoyi da y’an mata, dan yanzu haka ma a halinda ake ciki a wannan ranar ba dan an kamasa ba to suna shirye shirye ne a kan shi Yusuf d’in zai taimaka a sacewa Black Snack wata Yarinya ‘Mannubiya’…..” Dan haka za su tafi da shi, kuma babu bailing, har sai sun gama interrogating d’insa, daganan idan suna so za su iya d’aukaka k’ara zuwa kotu kafin a yanke masa hukunci…. Suna ji suna gani aka datsawa Yusuf ankwa wanda yake ta turje turje aka wuce da shi, shi dai Baba bai gama gasgatawa ba amma su Ya Musbah da Yashjub wanda yake ji kamar ya bisa ya fara nad’a masa shegen duka tun a nan saboda tunanin sace masa mata ma da ya yi,duk sun yarda. Kaka mallan kam har da kukan sa a take ya nemi adaidaita sahu ya nufi gida yana tafe yana kiransu Baba Habu a waya….. Limamin ne ya matso ya yiwa Baba jaje kafin yace “yanzu a yi sanarwa Akan an fasa d’aurin auren kowa ya watse kenan? ko za a d’aura ko babu shi?” Murmushi ya Nafi’u ya yi ya kalli Baban Al’ameen wanda ya k’araso yanzun yace”za a yi d’aurin aure yanzu amma ba da wanchan Angon ba,an chanja sabon Ango.” Jinjina kai Baba ya yi yana jin wani nauyi yana sauk’a daga kan k’irjinsa , dan har ga Allah da ya d’aura auren nan yau da bai san ta ya zai kalli Jidda ba,cike da kwarin guiwa ya kalli Limamin yace”sunan sabon Angon Muhammad Al’ameen Muhammad.” Murmushi mahaifin Al’Ameen ya yi a fili yace “Alhamdulillah” Daga haka suka d’unguma izuwa cikin masallacin. Jidda ne kawai da Siyama sai Muhsin wanda shima ya yi jigumm a cikin d’akin…. Kamar a mafarki ta ji ana sanarwa a loudspeaker”An d’aura auren Muhammad Al’ameen Muhammad da Maijidda Musa akan sadaki naira dubu d’ari biyu lakadan ba ajalan ba…. Wani irin bahagon numfashi ta fesar ta sake kwantar da kanta a kan cinyar Siyama wasu zafafan hawaye suka shiga gangaro mata a ranta tace”shikenan na zauce!!gashi dai k’iri k’iri da Yusuf aka d’aura auren nan na riga na sani amma sunan Ya Al’Ameen nake ji…..” “Jidda kin ji abunda kunnuwana suka ji kuwa???” Shiruu ta yi kafin ta tashi a mugun zabure ta mik’e ta zauna sakamokon abunda ita da Siyama da Muhsin suka ji an sake fad’a ana kuma maimaitawa a loudspeaker, dai-dai nan su Anty Umma suka shigo, Anty Umma tana shigowa ta rungume ta haka ma Aisha wadda take waya da Nafi’u domin ta tabbatar…. Sai da ta yanke wayar tukunna ta sanar da su komai abunda ya faru… Nan waje ya kaure da murna Jidda kuma ta fashe da kukan da kowa ya san na farin ciki ne… Har cikin d’akin Ammi ta shigo ta rumgume Jidda ta sake neman yafiyarta tukunna tace”Bari ta tafi ta fara shirye shiryen tarbar amarya…” Tare suka tafi ita da Mama domin su je su d’anyi shirye shirye….Zuwa yanzu Mama ta tabbatar Yashjub dai d’an gidan Imam Manubiya ta aura, dan tana ganin su Yusra ta ga kamanni, ta dad’e da yi wa kanta alk’awarin fita daga harkar Imam da zuri’arsa amma kuma tana so ta ji ya Yahanasunta take,dan haka ta tsara a kan za ta ke tambayar Manubiya halin da y’ar tata take ciki ba tare da ta bari ita kanta Manubiyan ta fahimci wani abun ba…. Akwai tafiyar da Al’ameen zaiyi zuwa Dubai nan da sati d’aya, shiyasa ana gama d’aurin auren Mahaifinsa ya cewa Baba”sai nan da sati d’aya tukunna za su d’au amarya inshaaAllah daganan direct sai a wuce da ita airport” kamar ya sani sai ya d’aura da cewa”amma dai za su fara magana da Angon yanzun duk yadda suka tsayar zai kira sa.” Aikuwa albishir yana zuwar ma Al’ameen bayan ya gama kukan farin ciki ba kunya ba tsoron Allah ya ce shifa kawai a kawo masa matarsa yau su zauna a nan kafin su wuce” Dariya su Ammi suka yi suka kira su Inna suka sanar musu….k’arfe takwas dai dai aka kawo amarya Jidda side d’in Al’ameen da ke cikin gidan. Sai da kowa ya watse tukunna ya shigo…farin ciki da tsantsar nishad’i masoyan suka tsinci kansu a ciki mara musaltuwa….tunda ya shigo ya yi hugging d’inta suka yi shiruu da kyar ya cikata suka yi nafila suka d’anci abinci daga haka ya ja ta ya sakata a jikinsa yana sauk’e ajiyar zuciya yana hamdala suka kwanta…..Jidda har ta fara fargaba..ganin awa d’aya awa biyu bai yi yunk’urin yi mata komai ba ya sa ta kwantar da hankalinta tana mai sauraron yadda k’irjinsa yake bugawa da k’arfi har zuwa wannan lokacin,a haka suka kwana ranar kamar wanda aka cewa wani zai zo kwace masa ita ne,ita kam Jidda jikinta har ya fara tsami tsabar yadda ya ruk’umk’umeta….. Tun a wajen kai amarya Yusra ta kira Ya’isha tace”to fa babu abunda aikin Baba larai ya yi, dan ga Najeeb da Siyama nan kamar za su cinye juna!” Dabass!!!haka Ya’isha ta zauna a kan kujerar parlourn Mommy sai kuma hawaye suka fara bin fuskarta… Da mamaki Mommy da Baba larai waenda suke cikin tsananin farin ciki suka shiga kallonta don yanzunna ta dawo daga ganin Abbakar take ce musu”Da farko ya d’an so ya yi zurfin ciki, amma daga baya ya amince d’ari bisa d’ari it’s like ya ma fi su son mutuwar auren Manu da Yash d’in,kuma yace’ba ya buk’atar sisin kobo kawai su kular masa da mahaifiyarsa su biya duk wasu kud’ad’en asibin ta’.” Hakanan suna ta murna ita da su to kuma me ya saka ta kuka tashi d’aya haka… Mik’ewa Mommy ta yi ta k’arasa inda take ta shiga tambayarta,da kyar ta iya ce mata”ai Najeeb da Siyama aka gani tare har yanzu suna tare ba su rabu ba….” Sai kuma ta mik’e ta fice da sauri tana kuka. Shiruu Mommy ta yi ta fad’a duniyar tunani,har ga Allah tana mutuwar son Najeeb ya auri Ya’isha gashi abun na Y’an matan nata zuwa yanzu shima ya fara damunta..Jiya ta ga d’aurin auren d’an k’awarta wanda suka shirya ita da k’awar tata a kan za a had’asa shi da Yasira,tsabar abun da munafurci ko gaiyyatar ta bikin ma ba a yi ba sai kawai d’aurin aure ta gani…. “Ki kwantar da hankalinki,inshaaAllah duk za su yi aure,Najeeb kuma shima ki barni da shi, bari mu fara gamawa da Manubiya tukunna” Muryar Baba ta katse mata tunaninta. A hankali tace”Baba larai idan kuma ya kai kud’i kafin a gama da Manubiyan fa?” “Kar ki damu ba zai kai ba,ai ita Manubiya inaga ba lalle ta k’ara sati biyu a cikin gidan nan ba fa! Komai a shirye yake, kuma yana tafiya a kan tsari ga kuma wanchan Yaro d’an albaraka Abbakar shima yana side d’in mu, dan haka kawai ki kwantar da hankalinki a kan komai…kar ki damu Najeeb zai dawo sannan shima wanchan na Yasirar ko a ta biyu ne za ta shiga inshaaAllah……” “Allah yasa” Kawai Mommy tace, daga haka ta yi shiruu haka itama Baba larai. Bayan sati biyu!. Satin su Jidda d’aya a Nigeria suka wuce Dubai ita da Al’Ameen, dan cikin sauk’i ta samu visiting visa. Najeeb da Siyama abu ya yi k’arfi, da shi da Yashjub har sun je sun nemi izinin zuwa zance a wajen su Baba Habu wanda hakan idear Baba ce,yanzu haka kuma maganar kawo Kud’i da saka rana ake yi….. Yusuf kuwa babu shi babu labarinsa an hana ma ganinsa,sai dai hakan kamar ya sake ruru wutar bala’i tsakanin Baba da y’an Uwansa ne, a cewarsu”tsabar mugunta a gabansa shi da Yashjub aka tafi da Yusuf amma ba su yi komai ba maimakon bin bayansa kuma su d’aurin aure ma suka ci gaba da yi.” Ya’isha Yassira da Yusra kuma suna gidan Manu har yanzu, sun kafa sun tsare! da farko ba sa samun damar yin chatting da Abbakar ta wayar Manu kamar yadda suka tsara, sai da aka yi sati d’aya suka samu Siyama ta tafi tukunna….sai sun daidaici ta tada sallah za su d’auki wayartata su yi abunda suka ga dama su goge su ajjiye mata wayar kafin ta idar, dama shima Abbakar ya san time d’in da suke samun chance shiyasa a ko da yaushe ya ke available……Ana gamawa za su goge gudun kar ta gani shi kuma Abbakar yana chan yana tarawa a tasa wayar. A b’angaren Baraka da Ya Musbah kuwa, tunda ta ji labarin tashi tashin ma zama gida d’aya da su Inna tace ‘ba ta san zance ba!’ gashi kuma tun a ranar aka basu notice akace ‘su tashi daga wannan gidan da suke a ciki, a cikin sati ɗaya, mai gidan ya siyarwa wani…’ Sai da aka yi fad’a da ita a k’ofar gida ta inda ta haƙiƙance akan ”ai ba a tab’a bada notice d’in da ba na shekara d’aya ba! dan haka ko ubanwa ya siyarwa gidan wannan tsakaninsu shi da sabon mai Gida ne! ita kam ba za ta tashi ba har sai ta cinye shekara d’ayar ta! sannan ba za ta karb’i refund ba.’ Da kyar aka rabata da mutumin, dan shima d’an a yi ne, shiyasa ya biye ta suka dinga hayya-hayya, sai da ta koma ciki tukunna mutumin ya bawa Ya Musbah kud’in hayarsa wanda ya biya, ya sake bashi hak’uri, ya ce ”ya taimaka su nemi gida su tashi, ga kud’insa nan complete ma ya bayar”. Ya Musbah dama yana so ya ci gaba da makarantar da ya soma, kuma har ga Allah zuwa yanzu yana son zama a kusa da su Baba sosai sosai, shiyasa shi abun ma dad’i ya yi masa dan haka ya karb’a yace”ba komai za su tashi a cikin sati ɗayan kamar yadda ya buƙata” Yana shiga gidan da ya so ya yi mata bayani sai abu ya rinchaɓe a tsakaninsu! Dan sam ta k’i fahimtarsa ƙarshe ma ta rufesa da fad’a, a ranar dai ba su yi bacci ba, dan kwana ta yi tana bala’i kuma ta tabbbatar masa da ‘babu inda za ta je…..’ Shi dai ya Musbah a hankali a hankali ya dinga kwasar kayansa, da nashi da na mai sunan Baba suna kaiwa sabon Gida, sannan ya je ya biya kud’in registration d’insa ya ci gaba da zuwa makarantarsa…ranar da sati d’aya ya cika ya zo ya yi mata sallama yace”za su tafi shi da mai sunan Baba”. Da kyar Baraka ta fita daga shock d’in Musbahu wanda tana tunanin ta riga ta saka a kwalba bai Isa ya yi mata hakan ba…a take ta fahimci akwai matsala, shiysa ta danne zuciyarta kawai dan ta san dole sai ta sake sabon shiri kenan kuma a yadda ya botsare mata ɗinnan idan ta ce za ta yi turjiya to kanta za ta jawa shiyasa kawai ta ce “ba komai, ya jira ta itama za ta bishi…..” Sai washegari aka gama kwashe kaya….a plan d’in Baraka idan ta je sai ta yi abunda shi da kansa zai ce su bar gidan kuma sai ta had’a sa da su Inna wannan karon ta kissa asiri da komai za ta had’a…sai dai kuma tunda ta je ta ga danƙareran gida a take a ranta ta ce ‘ba ta ga ta tashi ba!!’ ta san kuma fitar da su Inna a gidan aiki ne ko da zai yiu to ba yanzu ba….gashi ya Musbah gaba d’aya ya juya mata baya, aikin ma ya daina tasiri a kansa Kwata Kwata ba ya sauraronta ba ya jin maganarta, dan yanzu ma k’iri k’iri so take ya d’aga katanga a tsakaninsu da su Innar ya fitar musu da gate d’insu a daban, tama ce ita da kanta za ta bayarda kud’in amma yace”ba ta Isa ba! “Idan kuma ta sake yi mishi wannan maganar shirmen wallahi sai ranta ya yi masifar b’aci” Shiyasa gaba d’aya hankalinta yake a masifar tashe, ta sake dagewa!! gidan kullum idan aka shiga in banda k’aurin hayaki mara dad’i babu abunda yake tashi, dan haka suma su Inna suka sake dagewa da rok’on Allah. Jiya da daddare Hajiya Mama da Junior suka zo….Shiyasa yau da safe su Manu suke ta shiri akan za su je. Ana ganinta an san ta ci kuka, dan fuskarta duk ta kumbura, shiysa tunda su Yusra suka ganta a haka farin cikin su ya nunku ya gagara b’oyuwa har sai da ta d’an lura..a b’angarenta kuwa fad’a suka yi ita da Yash jiya abunda bai tab’a shiga tsakaninsu ba kenan! Tun bayan sati biyu da ya nemeta ta k’i bashi had’in kai ta fara kuka shikenan bai sake neman wani abu a wajen ta ba,abun ya yi mata matuk’ar ciwo dan a tunaninta sun wuce haka ita da shi, ba ta tab’a zaton zai yi irin wannan fushin da ita har haka ba! mutumin da a ko da yaushe ya ke cewa”Manubiya ba ta laifi a wajen Yash,he loves her morethan life itself, ba zai sakata a damuwa ba”amma shine wai zai yi irin wannan fushin da ita! Ba wai fushi na k’in magana ba dan suna wasa suna dariya yana kula da ita yadda ya kamata, kawai dai ko hannunta ya daina rik’ewa….. Dama da haushin hakan a ranta yau kuma k’iri k’iri da ta yi masa maganar makaranta ba kunya ba tsoron Allah yace”ba za ta ci gaba ba!” Daga haka ya shige toilet ya barta a tsaye kuma ko da ya fito ya ga tana kuka bai tsaya ya rarrasheta ba a maimakon rarrashin shima sai ya had’e fuska tamau! ya ci gaba da shirinsa ko a jikinsa…hakanan yana ganinta har ta gama kukan ta ta sauk’a k’asa had’a breakfast bai ce mata komai ba. A b’angaren Yash kuwa..dalilin da ya sa ya d’aga mata k’afa kwana biyu ba ya so ya cika naci ne ya je garin hakan ya fara fita a ranta, shiysa ya hak’ura akan har sai yaga ta shirya masa tukunna…..sannan yana so ya yi k’ok’ari ya ga ya kawar da duk wani abunda zai sa ya yi zarginta ko ya ji haushinta. A yadda ya ji tana waya dole ko ma waye ya dasa mata ayar tambaya amma shi kuma k’ok’ari yake yi ya goge zargi ya bawa hakan kyakkyawar manufa… Ya san dole idan ta koma makaranta ya san hankalinsa ba zai taɓa kwanciya ba tunda ga issue a tsakaninsu dama basu gama sorting out ba!(basu gama sasantawa ba!).shi kuma ba ya son irin hakan a tsakanin shi da ita. sannan ga ciki a jikinta da ake buk’atar ace ta huta,shiysa yanzu da ta yi masa maganar yace mata”A’a”kuma ya had’e rai. Sannan har ga Allah ya na kishi shiyasa ya ga dacewar gara kawai ta yi online… Kukan ta ya tab’a shi sosai amma ya san idan ba hakan ya yi mata ba, to ba za ta hak’ura ba!. Har ta kai masa breakfast ya ci ya fita,sam fuskarsa babu walwala. Sai wajajen 11 bayan sun gama girki Yasira ta ja su ta kai su gidan ita kuma ta wuce office wanda da so ta yi yau ta zauna a gidan itama amma sai Daddy ya kirata. Shiruuu gidan ba kowa suka tarar, dan haka su Manubiya suka ajjiye flask d’in girkin da suka yo, suka nufi sama side d’in Mommy. kamar ko da yaushe, ita da Baba larai sai Ya’isha suka tadda a parlourn nata..zuwan Hajiya Mama babu notice ya d’aga musu hankali matuk’a, ga kuma Daddy wanda yake bin diddigin Mommy kamar ba gobe… Ba yabo ba fallasa suka gaisa, kafin Mommy ta kalli Yadira tace”ta raka Manubiya wajen Hajiya Mama su gaisa.” Suna fita ko tambayar ta su Mommyn ba su yi ba, Yusra tace”yanzu haka ma cikinta ciwo yake yi,ba ta dai fad’a ba amma tun safe take rik’e ciki idan ya murd’a har sai ta durk’usa” “MashaaAllah,Alhamdulillah!!” Baba larai tace cike da farin ciki,kafin ta d’aura da cewa”tunda na ga matar nan da safe hankalina ya tashi, dan na san tsaf za ta iya cewa ku dawo gida..” With full confidence Yusra tace”ai aikin gama ya riga ya gama yanzu kam..dan duk wani ruwa nata muna sakawa a ciki ita kuma tass take shanyewa.. yau sati biyu ta shanye sachet biyu fa!. Ragowar abubuwan ne dai da na toilet da na d’aki duk ba mu samu damar yi ba ai dama na gaya miki..saboda ya Yash ko k’afar benen sa bai bamu fuskar mu tab’a ba, k’iri k’iri ma yace mana ‘ko ba ya nan kar mu shigar musu d’aki.’ Na abinci ita kuma ba ta yarda da mu ba! dan ko girkin mu ba ta ci, kuma tana yawan addu’o’i dan haka na san turaren shima ko ta shak’a ba lalle ace ya yi wani tasiri ba, dukda dai na lura kwana biyu rikici suke yi amma gaskiya ba lalle abubuwan namu bane, dan ba ta cin duk wani abu da muka bata…wataƙilan wata rigimar tasu ce daban.” Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace”Allah ya shige mana gaba,tunda har suka fara rikici su kad’ai ai sun sauk’ak’a mana kinga….sannan ba komai dan ba ku samu kun yi waenchan d’in ba indai komai ya tafi yadda muke so, to maganin da kuka saka da chatting d’in ma kaɗai sun ishi komai. Yanzu Ya’isha ki kirawo Abbakar kice masa zai iya tunkarar Yashjub a yau!” Shiruu Ya’isha ta yi kafin tace”amma bai yi wuri ba?” Murmushi Baba larai ta yi tukunna tace”kina ji fa Yusra tace ta fara ciwon ciki!ai yanzu shine lokacin da ya fi dacewa, dan tunda ta fara ciwon cikin nan ba za ta kai jibi da shi a jikinta ba.” “Tam shikenan,bari in kirasa…” Daga haka ta d’au waya ta kirasa….a gaban su suka tattauna kafin daga baya suka yi sallama,zuciyar kowa fesss!!!. Sosai Manubiya ta ji dad’in ganin Hajiya Mama, haka itama Hajiya Maman…bayan gaishe gaishe Hajiya Mama ta bata tsarabar da ta yo musu ita da Yash, ita kuma ta karb’a tana ta murna da godiya. Dai dai nan Ummi ta shigo dan haka suka zauna su uku gwanjn ban sha’awa suka hau hira bayan Ummi da Manubiya sun gaisa. Hirarsu suke sosai,dukda Manu murmushi da eh ko a’a take ta cewa amma hirar tana yi mata dad’i. A bakin Hajiya Maman take jin maganar Yadira da Junior ta inda take cewa”ta cewa Daddy kawai ya tsayar da date dan al’amarin Yaran gidan ya fara bata tsoro, dan haka tunda har Junior ya nuna Yadira yake so gara kawai a saka rana a yi aure, ragowar suma za ta bincika musu Miji a cikin jikokin k’awayenta na nan Nigeria da suke in contact with! ya zama dole a tashi a tsaya a kansu, dan sun rik’a dayawa.” Ita dai Manubiya murmushi ta yi tace”Allah ya tabbatar da alkhairi” Dan zuwa yanzu ciwon cikin da ya addabeta sama sama tun d’azu ya k’ara k’arfi! Tana ji Ummi tana cewa”ta ji suna cewa Yadiran fa ba ta son Junior d’in…!” Ita kuma Hajiya Maman tace”Wallahi ko za ta mutu sai ta auresa!,Junior ba shi da wani mugun Hali, dan haka dole ta aure sa.” “Washh!” Manu tace sakamokon wani mahaukacin murd’awa da cikinta ya yi. Da sauri duk suka kalleta, sai kuma suka rufar mata sakamokon yadda suka ga ta rik’e ciki ta runtse idanuwa da mugun k’arfi. ‘Sannu’, suka shiga jera mata, bayan Ummi ta rik’eta, Hajiya Mama kuma ta fara k’ok’arin kiran Yashjub. Yadda Manubiya ta fashe da wani irin kuka ta shiga kiran sunayen Allah ne ya sa Hajiya Mama ta ajjiye wayar, ita da Ummi suka fara k’ok’arin kinkimarta dai dai nan Junior ya shigo. Da sauri Hajiya Mama tace”ya fito da mota ga su nan sauk’owa zai kaisu asibiti. Munirat da Ummi ne suka sauk’ar da ita, suka sakata a mota, suna ta faman jera mata sannu!! Junior da Hajiya Mama da Manubiya sai Munirat wadda ta d’aura kan Manu akan cinyarta ne suka fara yin gaba suka nufi asibitin, Ummi kuma sai da ta koma ta sanarwa su Mommy tukunna ta bi bayansu a motarta, da taimakon kwatancen Munirat da suke waya ta Isa asibitin…… Yashjub yana zaune a office, gaba d’aya tunani ya yi masa yawa, dan sai yanzu ya ke ganin rashin kyautawar sa ga Manu…waya ya d’auko da niyyar kiranta amma sai shigowar Racheal ya katse masa hanzari….. Cikin takunta ta k’araso tace”Sir,a guy named Abbakar is here to see you!he said he’s a friend of your wife. (Wani mai suna Abbakar ya na son ganinka, ya ce shi ɗin Abokin Matarka ne Manu).” A take k’irjin Yashjub ya buga, sai da ya d’an d’au lokaci kafin ya samu ya d’ago a hankali ya kalleta yace”send him away(ki sa shi ya tafi kawai)” Duk wani Abu da zai kawo matsala tsakaninsa da Manu ba ya so,gudan sa yake yi. Ya san ya tsani Abbakar,yana kishinsa saboda Manubiya shiyasa ya zab’i k’in ganinsa. Har ta juya za ta fita sai kuma ta juya tace”Sir he said it’s very important and urgent,he need to see you!..(ya ce abun yana da mahimmanci kuma na gaggawa ne, yanada buƙatar ganinka.)” Wannan karon cikin d’an fushi yace”Racheal!send him awayyy!!!(racheal! Ki sallameshi ya tafi kawai!)” “Ok sir” Ta ce,daga haka ta juya ta fita. Dafe kansa wanda zuwa yanzu ya fara sara masa ya yi…ya d’an jima a zaune kafin ya gama yanke shawarar miƙewa da niyyar zuwa gidan nasu ya samu Manubiya, shiruu da kyaliya bai kamata ace ya fara shiga tsakaninsu tun yanzu ba…abunda ya yi kwata-kwata bai kyauta ba…. Yana wannan tunanin ya sauk’a ya shiga motarsa yana shirin kunnawa Abbakar ya k’araso wajen…tunda ya fito ya gansa dama, dan haka ya sake tamke fuska tamau. Cike da kwarin guiwa Abbakar ya k’araso, ya na zuwa ya d’an yi knocking glass d’in motar wajen mai zaman banza kafin ya bud’e ya shiga ya zauna. Shiruu Yashjub ya yi, sai kuma kawai ya kunna motar ya ja ya fice. Sai da suka d’an yi nisa tukunna ya faka ya juya ya kallesa yace”I made myself pretty clear, kuma na san Racheal ta gaya maka..” Cikin tarar numfashinsa Abbakar yace”inada buƙatar ganinka ne dole,shiysa ka ga na yi hakan..” Yashjub ji yake kamar ya bud’e motar ya hanakad’a Yaron waje, dan ya yi tunanin idan ya yi masa hakan zai fita amma sam baiga alamun shakka ko shirin fita daga garesa ba ,shi kuma har ga Allah ba zai iya jurarsa ba…. ko sunan shi ba ya so ya ji an kira wallahi…ga kuma gudun zuciya.. “Am…Yashjub ban yi Mamakin yadda kake yi min ɗinnan ba, dan na san haushina kake ji kamar yadda nima nake jin haushinka!” Muryar Abbakar ta katse masa tunani.. Juyawa kawai ya yi ya zuba masa jajayen idanunsa..wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yi wa Abbakar ba dan ya hango trigger… Cikin sauk’e numfashi ya ci gaba da cewa”A da na so in b’oye maka kamar yadda Manu ta buk’ata, amma kuma sai na ga rashin dacewar hakan, dan bai kamata mu yi ta b’atawa kanmu lokaci ba, shiysa na zab’i in tunkare ka…” Cikin katsesa da tsananin fushi Yashjub yace”Kaii!dan ubanka na yi maka kama da Yaro???ni za ka zowa da wannan shirmen?fice mini a mota kafin na illataka!!!” Murmushi ya ga Abbakar d’in ya yi kafin yace”idan ni ban maida kai Yaro ba ai Manubiya ta maida kai Yaro, jariri ma kuwa..gashi kuma ina k’ok’arin wayar maka da kai amma kak’i ka saurare ni!.” Kama sitiyarin motar Yash ya yi da mahaukacin k’arfi ya d’aura kansa a kai ya shiga karanto addu’o’i dan ya san tabbas tsaf zai iya kai Abbakar lahira muddin ya ce zai biye sa… Tsabar b’acin rai zuwa yanzu sama sama yake iya jin Abbakar d’in yana cewa”Tun Yarinta muka taso ni da Manubiya..ba ta yi tunanin Ina sonta ba shiyasa ta karb’i soyayyarka…yanzu kuma ta fahimci Ina k’aunarta dan haka a shirye take ta barka domin ni Yash! saboda tace ko dan family d’inka ma ba za ta iya rayuwa da kai ba, gashi ba ta son ka…kawai matsalar itace tace mini ba ta san ta yaya za ta gaya maka ba! tana jin kunyarka, har gida ka siyawa iyayenta…ganin duk mu uku muna ta b’atawa kanmu lokacine ya sa na yanke shawarar tunkarar ka a yi ta ta k’are.” A hankali Yashjub ya zare makullin motar ya d’ago kansa ko kallon Abbakar bai yi ba, haka ya bud’e ya sa kai ya fita, dan tabbas shaid’an ya fara kad’a masa ganga maganganun Abbakar sun fara tasiri a kansa gashi zuciya In banda tunzuroshi ya rufarwa Abbakar ɗin babu abunda take yi! shi kuma ya san muddin ya biye Yaron a halin nan da yake ciki to sai dai wani ba shi ba. Bai san shima Abbakar d’in ya fito ba sai hannunsa da ya ji ya kamo ya saka masa wayarsa yace”idan baka yarda da ni ba ka duba wannan.” Duk yadda Yashjub ya so ya yi k’ok’ari kar ya kalli wayar sai da ya kalla…chat d’inta ne da Abbakar har yana ce mata shifa yana kishi gaskiya ta daina yarda da yash, ita kuma ta yi masa alk’awarin ta daina sannan tace”ba za ta iya haihuwa da shi ba, ba za ta iya haifar niece ko nephew d’in su Yasira ba, shi kuma ya yi mata recommending magani ya ce ta dinga sha kullum guda d’aya a hankali cikin zai zube……… Kafin yashjub ya gama karantawa ya had’a wata uwar zufa fuskarsa ta yi jaa…how dare he! ta yaya ma zai fara mishi wannan shegen zancen sannan daɗin daɗawa har yana da ƙarfin halin nuna mishi kamar Irin shi ne ya saka Matarsa ta ke k’aurace masa ɗinnan, sannan har yana da bakin yin magana akan cikin jikinta HOW DARE He!!!….. Cikin son k’aryata zancensa kafin ya ci ubansa ya shiga bincikawa yana dubawa da kyau, sai dai kuma duk ta inda ya so ya k’aryata d’in abun ya gagara…..ya duba number ya fi sau a k’irga amma number Manubiya ne da komai nata… Gashi kuma tabbas wannan itace number da take ta kiran Manubiya amma ba ta tab’a d’auka a gaban sa ba!dan ya ga number ya haddace tsananta bincike ne ba ya so shiyasa bai tab’a kira ba. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Yashjub ya shiga maimaitawa a cikin zuciyarsa, yana jin wani kalar gagarumin tashin hankalin yana yi masa k’awanya. “Actually wannan sirrin mu ne bai kamata in gaya maka ba amma kuma bani da wani zaɓin da ya wuce in gaya maka ɗin..…dalilin da ya sa na nuna maka na san idan ba gani ka yi ba to ba za ka tab’a yarda ba,ni kuma har ga Allah na gaji dan tun kuna Cyprus ake Abu d’aya, shiyasa ita kanta Manu d’in ma na shalllake ta na yi gaban kaina, gara ka san gaskiya mu daina b’atawa kanmu lokaci.… Mahaukacin Marin da Yash ya d’aukesa da shi ne ya saka shi a silent…ba ji ba gani ya rufe sa da duka sai da ya ga ya daina motsi tukunna ya tsallakesa ya shige cikin motarsa yana jin abunda bai ma san me ya ke ji ba!!….. Tafiyar mintuna uku ya yi, ya ja ya faka dan wani irin duhu duhu yake gani…ji yake kamar ya koma ya cinnawa abbakar wuta ko ya samu ya ji sauk’in abunda yake ji a cikin zuciyarsa…kansa har yanzu ya kasa yarda da ɗaukar kalar ƙarfin hali da tsaurin idon Yaron! Ɗayar zuciyarsa kuma tana ta faman tunzurashi da son tabbatar masa da maganganun Abbakar d’in , saboda gashi har gudunsa da take yi Abbakar d’in ne kenan ya hanata ashe, adduarsa d’aya kar maganar zubar da ciki ya zamo gaskiya infact Allah ya sa ma mafarki ne yake yi, ya samu ya farka ! a yanzu, ko kuma ya ga wani abunda zai nuna masa wannan al’amarin k’arya ne….. Wayarsa ce ta d’auki k’ara a karo na bakwai…. da mugun kyar ya zaro wayar daga aljihu da niyyar kasheta gaba d’aya amma sai ya ga sunan Hajiya Mama yana yawo a kan screen d’in, dan haka ya d’auka ya kara a kunnensa ba tare da ya ce komai ba. “Ka zo! Yanzunnan..muna asibiti, Manu ba ta da lafiya….” Daga haka ta gaya masa sunan asibitin da kwatance, ta kashe, dan suma hankalinsu gaba d’aya a tashe yake ganin yadda jini ya kuncewa Manubiya…. Ikon Allah ne kawai ya kai Yashjub asibitin, dan shi kansa gani kawai ya yi har ya iso, amma ya ma manta ta Ina da Ina ya bi. Yana shiga ya tarar da su carko carko a reception, da sauri Hajiya Mama ta k’araso tana zuwa yace”menene yake damunta??” Ya yi mata tambayar yana addu’ar ya ji tace zazzab’i ko wani abun amma sai kunnuwansa suka jiyo masa sautin muryar ta taana cewa”ciwon ciki ne yake damunta…” A hankali ta sake cewa”yanzu kuma ta fara bleeding!.” Wani kalar mahaukacin bugawa k’irjin Yash ya shiga yi, bai san lokacin da ya durk’ushe a wajen ba kamar wani zararre….babban abunda zai tarwatsa shi a halin yanzu ya burkitashi shine idan aka ce cikin nan ya zube! Allah kad’ai ne ya san kalar tsantsar so da k’auna da kuma yadda ya kwallafa rai a cikin nan….. Dai dai nan Dr ya fito ya kalli Hajiya Mama yace”pls follow me!” Daga haka ya wuce ya nufi office d’insa. Da kyar Hajiya Mama ta iya kamo hannun Yash ta rik’e sa ta mik’ar, suka nufi office d’in har da Ummi, aka bar Munirat ta shige wajen Manu. Suna shiga likitan ya kallesu one by one kamar ya ce Yash ya fita dan ya san maybe shine Mijin, sai kuma kawai ya zab’i ya yi maganar a gabansa dan haka ya kalle su yace”have a seat” Saida duk suka zazzauna tukunna ya ajjiye takardar da yake rubutu a kai a gefe, ya cire glasses d’in idanunsa ya kalli Hajiya Mama yace”ke grandma d’inta ce?” A hankali Hajiya mama ta jinjina masa kai alamun”eh”. tsura mata ido ya yi, kafin chan ya sauk’e ajiyar zuciya ya fara magana”ya kamata ku da kuke manya, ku dinga saka idanu a kan y’ay’ayenku da jikokinku..ku dinga gaya musu abunda ya dace da wanda bai dace ba..yanzu gashi saboda kyaliyarku da rashin kula Yarinyar nan ta je ta yi ta shan maganin zubar da ciki kuma mai k’arfi,we lost the Baby!!(cikin ya zube!!), but ni babban tashin hankalina anan ma shine ba lallai ta k’ara haihuwa ba! saboda maganin da ta dinga sha yana da k’arfi kuma ta sha sa over ne…. A hankali Yash ya tura kujerarsa baya, ya mik’e, ya juya ya fice….kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka ya fita daga asibitin ya hau titi ya kama tafiya ba tare da ya ma san inda zai je ba…………. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 34*     Ya yi tafiya mai nisa sosai, dan sai da ya kusan k’arasawa gida ma tukunna ya tari Napep ya shiga ganin jiri yana shirin zubar da shi. Yana shiga gidan dai-dai su kuma su Mommy suna fitowa, har da Yassir domin zuwa asibitin. Ba su kula shi ba shima bai kulasu ba, dan sun riga sun fito shi kuma napep Tana ajjiyesa ya afka cikin gidan. yanayin sa ba k’aramin dad’i ya yi musu ba, dan ko ba’a fad’a ba sun san cikin ya zube ne shiyasa ya zama haka.   Direct side d’insa ya nufa, yana zuwa ya rufe ko’ina ya turawa Siyama message ya ce ‘Manubiya ba lafiya’ Daga haka ya kashe wayoyinsa ya rufe ko’ina ya kwanta ya yi shiruu….   Su Yassir suna ɗaukar hanya, ya turawa Kausar message kamar haka”Yashjub yana gidan Daddy yanzu haka, alamun rauni, rashin kuzari da tashin hankali duk sun baiyyana a tare da shi, dan haka wannan shine lokacin da ya fi dacewa ki tunkaresa…get ready.”       Hajiya Mama da Ummi suka tarar a d’akin, Manubiya tana kwance tana barci dan tunda aka fito da ita ba ta bud’e ido ba.   Hajiya Mama ba ma ta san sun shigo ba, dan ta yi zurfi a tunani matuk’a… idan akwai abu guda da za ta iya rantsuwa a kai shine ‘Manubiya ba za ta tab’a shan kwaya domin ta zubar da cikin jikinta ba’ sannan tunda har Doctor ya ce magani ta sha cikin ya zube tou kuwa maganin ta sha ba tare da ita kanta ta san tana sha d’in ba, bi ma’ana drugging d’inta aka dinga yi har cikin ya zube!… Daga ita sai Yasira, Yusra da Yadira a cikin gidan sai gwaggwo sai Yashjub… “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun rajiun” ta shiga maimaitawa a cikin ranta dan waenda ta zarga su Yasira ne! Tabbas Mommy ta cucesu ta cuci jikokinta muddin hakan ta tqbbata, dan ta san ita ce ta koya musu wannan muguwar dab’iar. “Maama Ina wuni,ya mai jikin?” Muryar Mommy ta katse mata sak’e-sak’enta. D’agowa ta yi kawai ta zuba mata idanu, wanda hakan ya sanya ta sha jinin jikinta ta hau dibi dibi…kallonta kawai Hajiya Mama ta ke yi tana sakewa… a ranta tana mamakin ‘tayaya Mutum ɗan Adam zai iya zama wannan mugun mugun Azzalumi har haka!?’ Tun tana Uk take mugayen mafarkai akan su Yasira da Manubiya, shiyasa tunda ta zo aka ce mata suna gidan sam hankalinta bai kwanta ba, amma kuma dukda haka bata tab’a kawowa za su iya aikaata wannan mugun abu da take zarginsu da shi ba!.   Da kyar ta iya cewa”lafiya Alhamdulillah.Jiki da sauk’i.”   Shiruu duk suka yi, suna so su tambaya su tabbatar da cikin ya zube ne, amma kuma suna shakkar kar Hajiya Mama ta gano wani abun, dan iyaka kallon da take yi musu kad’ai ya sa sun sha jinin jikinsu,shiyasa suka ja bakunan su, suka yi shiru.   Baba Larai ce tace”itakam wannan cikin nata mai laulayi ne, Allah dai ya raba su lafiya!”.   Sai da Hajiya Mama ta d’an k’ura mata ido kafin tace”Ciki kam wanda ya bayar ya karb’a, sai dai mu yi addu’ar Allah ya kawo masu albarkaa, Allah ya sa wannan d’in mai ceto ne.”   Guntun murmushin da Ya’isha ta yi da kuma ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Hajiya Mama ta gani ta kuma ji!! dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa kawai ta hau salati a cikin ranta kanta yana wani irin juyawa..Tabbas an zo gab’ar da ya zamo mata dole ta shigo rayuwar cikin gidan Daddy ta san abun yi, Mommy rub’abb’en seed ce da ya zamo mata dole ta b’intike ta tun kafin ta fara kisan gilla!…ta riga ta cucesu tunda gashi ta yi poisoning (ta gurɓata) tunanin su Yasira, ta kafa musu muguwar d’abia a cikin kansu!! Dan haka ta yi yaɗo kenan a cikin gidan ɗanta da ita da muguwar ɗabi’arta! Amma bata makaro ba! Tana da yak’inin in sha Allahu za ta iya gyara jikokinta muddin ta samu ta ɓintiƙe Mommy aka samu ta yi nesa da su.   A hankali ta d’ago kanta ta kalli Mommy wadda sai a lokacin tace”To Allah ya kawo masu albarka” Ita da su Yasira. Cikin rashin son ganinta tace”ki tafi ki je wajen Yashjub! yana da buk’atar ki, za mu kula da Manubiya.” Babu musu tace”to shikenan Hajiya Mama”dan itama so take ta gudu, saboda ta san tshoho duk inda yake ya fika wayo shiyasa take so ta yi nesa da ita gudun kar ta gano wani abun game da su..dan wannan kallon da taga tana yi mata ta san ba na lafiya bane ba. “Allah ya k’ara sauk’i.” Tace, daga haka tayi musu sallama, suma su Baba larai suka yi wa su Hajiya Mama sallama, daga nan duk suka fice zuciyoyinsu fess! kamar an yi musu bushara da gidan Aljannah.   Hatta Ummi sai da ta dasa ayar tambaya a kansu, itama ta fara zarginsu, dan yadda suka yi da yadda suka nuna halin ko in kula gameda batun zubewar cikin, dole abun ya saka duk wani mai hankali a shakku.   Shiruu d’akin ya d’auka bayan fitarsu,kafin daga baya Ummi ta ce”Bari in je in yi girki kafin ta farka.” “Sannu Ummi, Allah ya yi miki albarka” Hajiya mama tace dan gaba d’aya jikinta ya yi sanyi, ta kad’u kwarai.   Jaka Ummi ta d’auka, daga haka ta fita itama jiki babu kwari. Baya ta fara dubawa dan ya ci ace Munirat ta kammala shanyar kayan Manu da suka  tafi yi, ga mamakinta sai ta ganta ta fito daga lab tana tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, sai da ta zo daff da ita tukunna ma ta lura da ita. Da mamaki ta tsaya take kallon idanunta waenda suka kumbura kamar wadda ta sha kuka..”Ummi za mu wuce ne?” Ta yi mata tambayar ba tare da ta had’a idanu da ita ba. “Kuka ki ka yi?” Itama ta jeho mata da tata tambayr. “Cleaner d’ince ta d’an watsa mini hypo a ido garin wanke zanin Manu shine na je lab d’in suka duba mini, sun ce ba komai, bai ma shiga idon ba.”   Wata bahaguwar ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e saboda da har ta fara tunanin wani abu na daban…..   Sai da itama ta sake duba mata idon tukunna suka nufi gida.   Ummi tana fita, Hajiya Mama ta kira Daddy a waya tace”ya zo yanzunnan tana da buk’atar ganinsa.”   Suna gama magana Inna Siyama da Muhsin suka shigo,har da Sir Najeeb wanda ya je zance ne ya ji zancen, dan haka aka taho har shi, shine ɗin ne ma ya kawosu.   Cike da girmamawa suka gaida Hajiya Mama, ta amsa da kulawa, kafin suka shiga jaje da tambayar jikin nata. Cike da alhini Hajiya Mama take sanar dasu ‘ai cikin ma ya zube har sun yi mata wankin ciki…’ gab’a d’aya shiruu aka yi jiki da zuciya duk ba dad’i. Hawaye kawai suka ga yana bi ta k’uncin Manu wadda shigowar su Inna ne ya farkar da ita, su ba ma su sani ba. Numfashi Hajiya Mama ta fesar kafin ta  tura kujerar ta dai-dai saitin kan Manubiya, a hankali ta shiga rarrashinta tare da yi mata nuni da ta karb’i k’addararta Hannu bibbiyu, Allah ya na sane da ita shi zai sake bata wani.   Da kyar ta samu ta iya bud’e idanuwanta waenda suka yi mata nauyi, tukunna da taimakon Siyama da na Hajiya Mama aka samu ta tashi ta zauna, still hawaye sun k’i su daina sintiri a kan fuskarta. ‘Ya jiki?’suka yi mata, ita kuma ta gaida Inna daga haka ta shiga kallonsu ɗaya bayan ɗaya idanuwanta suna masu begen son ganin fuskar Yashjub..ta samu ta ga halin da yake ciki, su koka tare, su rarrashi juna tare, amma sai ta ga babu shi babu mai kama da shi… Siyama ta tambaya, Siyaman tace mata”ita ma yanzu suka shigo,ba ta gansa ba” Dan haka ta juya ta fara laluben wayarta still hawaye suna sintiri a kan fuskarta sun k’i tsayawa ko na second d’aya. Kallonsu Hajiya Mama wadda ta gama cewa Najeeb ‘ya je ya Kira Doctor ta yi,sannan tace”me kike so Manu?” Ta yi mata tambayar cike da tausayawa don yadda take hawaye jikinta har yana karkarwa dole ta bawa kowa tausayi!   A hankali Inna ta matso ta ruk’o hannunta da niyyar yin rarrashinta aikuwa kamar jira take yi tashi d’aya ta fashe da wani irin kuka ta fad’a jikin Inna ta k’ank’ameta.   Duk dauriyar Hajiya Mama sai da ta yi hawaye….duk kalar kunya da kawaici irin na Manubiya kalli yadda take kuka a gabansu ita da Inna akan cikin jikinta ya zube ai kuwa tab’uwa ta kai tab’uwa, kuma ta sake tabbatarwa ba ita ta zubar da cikin da kanta ba, zubar mata da shi aka yi, tabbas Mommy ta zalinci baiwar Allah nan amma ba ta Isa ta ci bulus ba wallahi……wani irin tausayin manubiyan ne ya lullub’eta, a ranta ta aiyyana ‘a hakan ma Manubiyan ba ta ji abunda Likita ya ce ba,’ tashi d’aya ta shiga addu’a ‘Allah ya sa kar maganarsa ta tabbata, Allah ya sa Manubiya za ta haihu’ shiyasa ma ba ta gayawa ko su Inna ba, kuma za ta cewa su Ummi suma su b’oye gudun ma kar baki ya yi yawa a zancen aje ya tabbata, inshaaAllah Manubiya sai ta haihu, babu abunda ya samu mahaifarta.!!!   Kuka sosai Manubiya take yi kamar ranta zai fita, dan zuwa yanzu ta kasa b’oye kawaicin ta… shigowar Najeeb da Likita ne ya tsagaita hak’urin da su Hajiya Mama suke ta bata, suka d’an matsa gefe domin ya yi aikinsa. A karon farko ya tabbatar musu jininta yayi mugun hawa, sannan tana buƙatar hutu sosai sosai, dan haka ya ce ‘bari ya yi mata allurar bacci.’   Cikin kuka ta shiga cewa “A’a ka fara jira Ya Yash ya zo tukunna sai ka yi min,ina son ganinsa.” Kallonsu Likitan ya yi, zai yi magana Najeeb yace”ka barta tukunna, bari in kira sa.” Cike da kwarin guiwa kanshi tsaye ya shiga gwada numbobin Yashjub, amma duka hud’un da ya ke amfani da su a kashe! Gashi kowa ya tsura masa ido yana jira…shi abun ma mamaki ya basa ‘Anya kuwa Yashjub ne ya aikata haka?’ Manubiya ba lafiya tana asibiti, ba ya wajen, sannan ya kashe gaba d’aya wayoyinsa!gaskiya to akwai matsala kenan..definately.. A hankali ya d’ago ya kallesu cikin in ina yace”wayoyinsa ba sa tafiya, bari in je gidansa in duba”   Shiruuu Manubiya ta yi, hawayen idanunta suka k’afe, ta shiga wani irin rikitaccen yanayi…dama ta san Ya Yash sai ya shiga tashin hankali, amma ba ta yi tunanin zai yi watsi da ita ba! ko a wanne Hali yake a ciki ta yi tunanin zai taushi zuciyarsa ya zo gareta! to ko dai bai san ta yi b’ari ba? Inaa ya sani ta san shine mutum na farko da su Hajiya Mama za su fara kira.   Tana wannan tunanin Likita ya kamo hannunta, ta cikin cannula ya juye mata ruwan allurar bacci, wanda tun kafin ya gama zarewa bacci ya yi awon gaba da ita.     Ba ta dad’e da yin baccin ba Daddy ya zo, dan haka bayan sun gaisa da su Inna suka fita shi da Hajiya Mama. A garden d’in da ke cikin asibitin suka nemi guri suka zauna. Cikin fahimtarwa ba tare da b’oye b’oye ba Hajiya Mama tace “Manubiya ta yi b’ari, kuma Likita ya tabbatar mana magani ta yi ta sha akai akai shiyasa ta yi ɓari wanda ƙarfin maganin ya janyo watak’ila ma ba lallai ta haihu a gaba ba. Na san ka shiga ka ga halin da Yarinyar nan take ciki, kuma ka san ko da wasa ba ita ta yi yunk’urin zubar da cikin nan ba, dan haka inaso ka gaya mini me lissafinka ya baka a halin da ake ciki yanzu?.”     Shiruu ya yi, ya fi minti ashirin…duk su biyun sun yi shiru babu mai cewa komai, kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace”ina riba ga su Yasira idan sun zubar mata da ciki?”   Lumshe idanuwanta ta yi ta bud’e tace”mashaaAllah Imam, na gode Allah da soyayyar ƴaƴanka ta daina rufe maka idanu daga ganin gaskiya. Ina so ka san cewa su Yasira ba su da riba dan sun zubar da cikin Manu, amma Khadijah fa?” A mugun zuciye ya mik’e yana wani irin huci, tashi d’aya idanuwansa suka kad’a suka yi jazir, cikin fushi yace”yanzu ne komai ya baiyyana, ya bada ma’ana” Ya fad’i hakan yana mai juyawa had’i da shirin barin wajen….da sauri Hajiya Mama ta mik’e itama ta ruk’o sa, cikin hikima tace”Imam idan ba ka iya kama b’arawo ba fa shi sai ya kama ka. Yanzu ka gaya mini hujja d’aya da zaka nuna ka kamasu da laifi?” Bata jira ya bata amsa ba ita ta ce “Babu!. Kuma idan ka yi haka to kamar ka sake dulmiyar da y’ay’anka mata ka  saka su a halaka ne, mazan kuma har abada ba za su tab’a yafe maka ba, ka ga ta raba ka da su kenan har abada.” Cikin rashin fahimta yace”Hajiya Mama ni ne Uba, ni zan fad’a a ji, da ni da ke duk mun san ita ce do we really need to prove anything to them? (Ta ina kasa musu gaskiya a faifai su ganta muraran ya zama dolenmu?)”   Girgiza kai ta yi kafin tace”dad’ina da kai kenan, idan zuciyarka ta motsa Imam ba ka ji ba ka gani! Wallahi d’azu da na fahimci abunda Khadija ta saka yaran nan suka yi sai da na yi hawaye, Imam su Yasira y’ay’anka ne jininka ne kai ya kamata ka tashi ka tsaya ka gyara tarbiyyar su da lissafinsu da aka lalata,yanzu idan ka kori uwarsu kana tunanin za su rabu da ita ne? Za ka sha mamaki idan suka kwashe kayansu suka yi maka yaji suka koma gabanta gaba d’aya, tunda bakinsu d’aya, kalli fa abunda ta tura su suka aikata, meye kake tunanin ba za su iya yi mata ko su aikata dominta ba?..kaga daga nan kuma sai abunda Hali ya yi, hakanan za ta lalata maka zuri’a! Allah kad’ai ya san abunda Hali zai yi. Su kuma mazan ba za su tab’a yafe maka ba, cewa za su yi ka kori uwarsu saboda kawai ba ka sonta. Abunda ya kamata mu yi yanzu shine mu nutsu mu karance su, sai mu san abun yi, saboda wallahi Imam akwai abubuwa da dama da bamu sani a kan Khadijah ba, kuma idan muka ce za mu yanke hukunci cikin fushi tou kuwa za mu kwafsa, dan indai har Khadija za ta iya kashe d’an cikin Yash to akwai wasu abubuwa da yawa game da ita wanda mu ba mu sani ba. Sannan yanzu  idan aka yi hayaniya, ta tafi, to fa ba za mu tab’a sani ba, sannan a fannin ƴaƴanka nan ma zai zamana bamu bamu samu mun gyara abunda ta b’ata ba wanda na tabbata Wallahi ko gidan miji ba su Isa su iya zama da wannan mugun halin ba…daga karshe su yi muguwar rayuwa!Imam yaran nan amana ne Ubangiji ya baka, kuma zai tambayeka ranar gobe k’iyama fa!…ka nutsu ka yi abunda nace sai ka ga an dace”   A hankali ya koma ya zauna ya dafe kansa da Hannu bibbiyu, kafin ya d’ago ya kalli Hajiya Mama yace “Mamaa ba zan iya ci gaba da zama a inuwa d’aya da matar nan ba, ta yi mini abubuwa da dama ta cuce ni da yawa,Hatta  lamarin Khadija ba ni da tantama itace wallahi….” Tiryan tiryan ya zaiyyano mata yadda mallan lawal ya kirasa, da kuma yadda ya mutu kafin ya samu ganinsa, sannan ya ɗaura da cewa ”ya yi hacking wayarta amma yana ga kamar ta gane, dan ta ma chanja wayar da layi, ta kashe wanchan,wanda haka ya ke sake nuni da tabbas ba ta da gaskiya.”   Waje Hajiya Mama ta nema itama ta zauna, ta kamo hannun Imam wanda zuwa yanzu yake kuka kamar k’aramin Yaro, cikin tsananin rashin jin dad’i tace”ka yi hak’uri Imam,da ni da mahaifinka mu muka tilasta maka aurenta,ka yi hak’uri ka yafe mana, mun had’aka da…..”   Da sauri yace”ba laifinku bane Mama,na san ba ku yi tunanin za ta zama haka ba ai,saboda da ba hakan take ba,na san tana da masifar kishi amma sam ban yi tunanin zata zamo haka ba.”   Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauk’e kafin tace”kaga ire iren abunda na ke gaya maka ko?kaga lamarin Khadija ma har da sa hannunta sannan recent mutuwar lawal ma muna zargin itace..Ni tunda na ga abunda ta aikata a Yash na san ta yi abubuwa da dama waenda bamu sani ba, shiysa ka ji na ce maka mu bi komai a sannu, mu bincike ta kafin mu san abunyi idan ba haka ba ba za mu ci ribar al’amarin ba…..”   Sun jima sosai a wajen, da kyar Hajiya Mama ta sa Daddy ya hak’ura da korar mommy, suka tsayar akan za su saka ido a kan Mommyn kuma su san yadda suka yi suka nunawa su Yasira abunda suke yi ba dai dai ne ba, a samu su dawo da su hanya…. Ba dan Hajiya Mama ce ta rok’esa ba wallahi da ba zai k’ara kwana d’aya da Mommy a cikin gidansa ba ! kuma sai ya wulak’antata ya k’ask’antar da ita, dukda ya san ba shi da tsayayyiyar hujja da zai nuna ya ce ita ta yiwa Khadija sharri sannan ita ta yi sanadiyyar zubewar cikin Manu, amma ya san itace, kuma shi kawai ba zai iya sake ci gaba da jurarta a cikin gidansa ba ya tsaneta!…. sai dai kuma abunda Hajiya Mama ta fad’a gaskiya ne, shiyasa da kyar ya aminta ya kuma zab’i su biyo mata ta yadda ta bi da su, dan ta hakan ne za su yi nasara a kanta…idan ya koreta yanzu bai rabata da su Yasira ba ai aikin banza kenan, kuma ya barta da gatan ta. Shi kuma so yake yi ta wulak’anta ta shiga masifar da sai ta zab’i mutuwa akan rayuwa, sai ya rabata da duk wani kwanciyar hankali da jin dad’i kamar yadda ta yi masa.   A take a lokacin ya warware ragowar igiyar aurensa d’aya da ta yi saura a kanta, dama kwanaki tun farko da ta hana auren Yassir da Kausar ta taso masa da maganar Khadija ya sake ta ba tare da ya fad’a mata ba gudun ma kar ta tada masa hankali, ya bari a kan sai ta  fita daga idda tukunna zai sallameta,tausayinta ya ji ta kuma ci darajar y’ay’anta shiyasa kawai ya mayar da ita a wannan lokacin yanzu kuwa ya riga ya rufe ya gama babu sauran aure a tsakanin su shi da ita kuma sai ya zo korarta tukunna zai sanar mata ya dad’e ma da sakin nata.!…     Awa biyu su Inna suka yi, daga nan suka tafi ita da Muhsin suka bar Siyama, suna tafiya Yahanasu ta zo,itama tsoro da tsananin tashin hankali sun rufar mata, dan ita kam tana tsaka mai wuya ne a wannan al’amarin saboda itama Ummi tana gama gaya mata lissafinta da zarginta akan Mommy ya dira.   Ita ta zauna a wajen Manu ita da Hajiya Mama da Siyama,dan ita Hajiya Mama ma tace”a asibitin ma za ta kwana da Manubiya”       A chan gida kuwa, zuwan Kausar biyu side d’in Yash amma a rufe, gashi duk wayoyinsa a kashe, dan haka ta gayawa Yassir shi kuma yace”kar ta damu…gasunan zuwa idan suka zo dole zai bud’e, daga nan sai su san abun yi.       Bayan awanni uku!!… Su Mommy ne suka fara dawowa sai Ummi daga baya Daddy…babu kalar bugun da ba a yi wa Yashjub ba amma ya k’i bud’ewa.Najeeb ma ya zo shi da Yahanasu dan zuwa yanzu Manubiya ta farka kamar kuma kamar yadda ta yi bacci da sunansa a bakinta tana farkawa ma da sunansa ta fara. Daddy ne ya je ya nemo spare key da kyar, ya samo ya zo ya bud’e k’ofar suka shiga, amma wani abun takaicin iyaka waiting parlour da corridor kawai suka tarar dan ya rufe k’ofar shiga da ma duk wasu k’ofofi.   Zuwa  yanzu sun fara tsorata, shiyasa Daddy ya ware murya ya shiga kwala masa kira…. Tun a bugun farko Yash ya ji su, duk kuma abunda suke yi yana jinsu, kuma ya saka a ransa ba zai kula kowa ba dan yana matuƙar buƙatar sarari…. Sun fi minti ashirin a wajen Daddy da Najeeb har ma da Yassir da Junior waenda suka zagaya ta baya saitin d’akinsa suna ta faman kwala masa kira! Jin muryar Daddy har ta dashe yana kiransa yana haki da nishi su Najeeb kuma suna cewa bari kawai a nemo masu b’alle k’ofa ne ya sa kawai ya mik’e ba don ya so ba ya nufi k’asan.   Ta cikin glass door d’in suka hangosa ya taho, dan haka hankalinsu ya d’an kwanta, yana zuwa ya d’auki key d’in a jikin k’atoton frame d’in da ya mak’ala ya saka ya murza ya bud’e musu, daga haka ya koma cikin parlourn ya nemi guri ya zauna, dan bibbiyu yake gani..wani Irin mahaukacin jiri yake yi.   Jiki a salub’e hakanan suka shigo suka nemi guri suka zazzauna. Kasa magana duk suka yi, kowa ya yi shiru suna mamakin yadda ya rame tashi d’aya fuskarsa ta yi jazir ya yi wujuga-wujuga. Yahanasu ce tace”Yash bawa fa baya wuce k’addararsa,duk abunda kaga bai zama naka ba it wasn’t yours to begin with! (Dama chan ba nakan bane ba). Allahn da ya baka ya karba, shi zai mayar maka da mafi alkhairi, kar ka azabtar da kanka, ka rungumi k’addara mana! Ka daure kar ka karaya, ita ma Manubiya tana da buk’atarka, a gareka ne za ta samu support da kwarin guiwa….idan har kai ɗin ka karaya haka shin ta ina zaka fara bata support ka kwantar mata da nata hankalin??”   Ga mamakinsu kawai sai suka ga hawaye sun shiga sintiri a kan fuskarsa babu k’akk’autawa, abunda dayawansu ba su tab’a gani ba, dan haka suka shiga al’ajabi!! Mommy kuwa kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha ita da Baba larai, cikin jan hanci da share fuskarsa da tafin hannunsa ya juya ya kalli Daddy yace”Daddy Ina buƙatar sarari…i want to be alone!dan Allah.” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, shi kad’ai ya san me yake ji, ji yake yi kamar ya yi super ya damk’i wuyan Mommy har sai ya ga ta daina numfashi. Cikin jinjina kai yace”okay Yash,amma kar ka sake kulle k’ofofin ka.” Daga haka ya d’an yi tapping kafad’arsa tukunna ya mik’e yace”kowa ya fito” ba tare da ya yarda ya kalli saitin inda Mommy take ba, daga haka ya sa kai ya fice.     Haka nan duk suka fita ɗaya bayan ɗaya, aka bar Yashjub Najeeb sai Yahanasu, Yusra da Yadira tun kafin a je koina har sun fara dana sanin abunda suka aikata, dan basu yi tunannin d’an uwan nasu zai shiga wannan halin ba,a tunaninsu kawai zai sake ta ne ta tafi shikenan a wuce gurin! Sam ba su yi tunanin zai tsaya yana azabtar da kansa har haka ba, su sai yanzun ne ma kwakwalwarsu ta yi lissafin tabbas fa zai shiga damuwa da tashin hankali, dan a yadda yake son Manubiya dole ya shiga masifa idan aka ce ta ci amanarsa…..sannan! Bai kamata ace su ji suna jin tausayinta ba amma yadda suka ganta a asibitin a kwance rai a hannun Allah ga ciki ya zube haka nan sai ta basu tausayi, shiyasa gaba d’aya suka shiga wani yanayi har sai da su Mommy suka lura. Ya’isha kam ko a jikinta, daddana wayarta ma take yi tana bawa Yassira wadda take office update dan ita da Yasmeen ne kawai babu a wajen, sun tafi aiki. Tana gama tura mata ta ja ta tsaya, jiran fitowar Najeeb, su kuma suka wuce.   Suna gama fita Najeeb ya k’arasa ya murza key ya dawo ya zauna a kusa da shi, cikin tattausan lafazi yace”Yash akwai wata matsalar ta daban ne?” Ya yi masa tambayar, yana mai kafe sa da ido. d’agowa shima Yashjub d’in ya yi, ya zuba masa shanyayyun kuma rinannun idanunsa kafin yace”Najeeb tunda nake a rayuwata ban tab’a kwallafa rai akan abu, kamar yadda na kwallafa akan Manubiya da Babyn da na rasa a yau ba,a ganinka hakan bai Isa ya jefa ni a damuwa ba?”   Numfashi Najeeb ya sauk’e kafin yace”sorry for your lost Yash, Allah ya sa mai ceto ne, ya baka masu albarka.” Sai kuma ya sake fesar da numfashi kafin yace “Yashjub baka tab’a b’oye mini komai ba sai yau, dan tabbas na san bayaga b’arin da Manu ta yi akwai wani abun da yake damunka, saboda Yashjub d’in da na sani ba zai bar Manubiya a asibiti ita kad’ai a wannan lokaci da tafi buk’atar sa ba.”   Runtse idanuwa Yashjub ya yi, ba tare da ya bud’e ba yace”Najeeb ka je kawai,kaina ya na ciwo, ina da buk’atar kasancewa ni d’aya!”   Cikin d’an b’acin rai Yahansu tace”Yash amma ka bani mamaki matuk’a!dan inda ace wani ne ya gaya mini cewa ka hau ka zauna akan abunda Doctor ya gaya maka wallahi ba zan yarda ba.” Da sauri ya mik’e tsaye yace”Yaha plssss.Not now!” Ya fad’i hakan cikin d’an b’acin rai. Itama cikin b’acin rai tace”yanzu zamu yi Yash!yanzu za mu yi saboda yanzu nake so in tabbatar kaine kuwa ko ko dai wani ne mai kama da kai ya zo mana, dan Yash d’in da na sani ba zai yarda da k’azafin da Likita ya yi ba.”   Cikin rashin fahimta Najeeb yace”Yahanasu me kike cewa?me kike nufi?, kun bar ni a duhu.” Sai da ta gama zabgawa Yash harara, dan ji take yi kamar ta rufesa da duka,tukunna ta juya ga Najeeb tace”Nima d’azu Ummi take gaya mini,Doctor d’in cewa ya yi maganin zubar da ciki ta yi ta sha har cikin ya zube.”   Da sauri Yash ya lumshe idanuwansa, ya koma ya zauna dab’asss! a kan kujerar, yana jin kansa yana wani irin juyawa, dan Yahansu tana fara maganar ya ji komai ya dawo masa sabo, ciwon da zafin da zuciya da kwakwalwarsa sukeyi sun sake hauhawa.   Cikin rashin jin dad’i sannan a hankali Najeeb yace”kai kuma sai ka yarda da shi?” Ya yi maganar yana kallon Yashjub.   Cikin tarar numfashinsa Yash ya kallesa yace”Nima ban sani ba!iyaka abunda zan iya fad’a kenan ‘nima ban sani ba’!”   “Ka yarda kenan!ka yarda mana, dan idan ba haka ba da baza ka shiga wannan halin ba! Da ba za ka k’i zuwa inda take ba, Yash wallahi ka bani mamaki.” Cewar Yaha.   Kallonta ya yi zuciyarsa tana wani Irin tafarfasa yace”kin san me na gani?kin san me na ji?” “Sai ka fad’a!” Ta bashi amsa cikin takaici…   Tiryan tiryan ya shiga zaiyyano musu yadda suka yi da Abbakar a yau kafin ya je asibiti…..   Cizan labb’a Najeeb ya yi, bai jira ya kai aya ba ya katsesa ta hanyar cewa”Tabbas Yash ba don na san gigin giyar kishi ce take d’awainiya da kai ba wallahi da sai na rufe ka da duka! Bari ka ji abunda ba ka sani a kan Abbakar ba…za ka iya tuna ranar da ka zo ka same ni akan mu je gidan su Manu kanason magana da ita urgent muka kira Abbakar ya yi mana kwatance,bayan y’an mintuna ya sake kira yace mana sun tafi k’auye?” Bai jira jin me zai ce ba yace”to k’arya yake yi, dan a ranar ma sai da Manubiya ta yi exams, kuma ai kaga abunda ya faru next na case d’in black snake wanda hakan yake sake nuni da babu inda ta je tana cikin garin amma ya yi mana k’arya, saboda son da yake yi mata sam ba ya so ka rab’eta!. A ranar da na bashi katin ka, na yi masa bayani nace ya bata tun daga ranar na fahimci son ta yake yi, ban gaya maka ba saboda gudun irin wannan abun da ka aikata da kuma gudun dasa zargin ma shi kansa a tsakaninku, Ashe na yi ta banza tunda gashi Yaro k’arami ya juya maka lissafi!… Saboda ita fa ya nemi transfer, dan tunda aka fara maganar aurenku ya gudu, aashe kwanciyar kura yayi, ya je ya yi sabon shiri! ya dawo da niyyar tarwatsa ku!. A gaskiya Yash ka bani kunya, dan ban yi tunanin za ka yarda da …..”   Cikin tarar numfashinsa Yashjub yace”Najeeb I saw there chat! (na fa ga chat ɗinsu)” Kamar Yahanasu za ta rufe sa da duka tace”kuma sai ka yarda ita ta yi?”   “To wa ya yi? Wayarta ce, kuma numberta, na gani..da dp da komai duk nata ne sannan ga chats nan na gani, waye ya yi idan ba ita ba?bayaga haka ba wai iyaka chats ba na ji da kunnena tana waya da shi tana cewa,sai da na fita tukunna ta samu damar yin wayar….da asubah! Sannan kusan kullum yana kiranta ina gani ba ta d’auka a gabana…”   A hankali Najeeb yace”me ka gani a chats d’in?”   Sai da ya share hawaye tukunna yace”Najeeb shiyasa tun farko da ka tambayeni na ce muku ban yarda ba!saboda i can’t believe wai Manubiya zata yarda ta yi maganata da shi, sannan har ya yi mata prescribing maganin da za ta sha ya zubar mata da ciki na da ke a jikinta.”   “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Najeeb da Yahansu suka ce a tare, kafin Yahanasu ta matso ta zauna a gefen sa ta kamo hannayensa tace “Yash kalleni nan!” Sai da ya juyo ya kalleta, tukunna ta ce ”da ka ji Manu tana waya da asubah, ba da kowa take waya ba da ni ne!” Da mamaki ya kalleta wanda hakan ya sa ta jinjina masa kai tace “tabbas…na yi wa Manubiya alk’awarin ba zan fad’a maka ba, amma yanzu kam ya zama dole in fad’a maka….” Tiryan tiryan ta zaiyyano musu komai game da yadda Manu tace mata ‘…ta taimaka mata suma su yi bada gudummawa a case d’in estate d’insa, ba za ta nad’e hannu ta zuba ido ana wasa da rayuwar mijinta ba!..’ Da binciken da suke yi akan case d’in, da kud’ad’en da Manu ta bayar, duk dan a yi bincike duk sai da ta gaya musu komai ba ta b’oye ba tukunna ta d’aura da cewa”wallahi ka godewa Allah Yash, dan samun mata irin Manu ba kowa ba, Manu mace ɗaya ce tamkar dubu! Allah ya zab’e ka, kar ka yi masa butulci. Maganar chats da shan magani kuma, ni na san aikin su waye!!Amma ba zan fad’a maka ba saboda wani dalilinawa. kawai Ina so ka tsananta bincike a kai, ka duba cctv ai akwai a gidanka, ka yi bincike sosai, ta nan ne za ka gano waye ya d’auki wayarta, waye yake saka magani a abunshanta ko cin ta duk za ka gani.”   Ahankali Najeeb ma ya zauna a gefe, suka saka shi a tsakiya yace”Yash shaid’an ya tsani ya ga ana zaman lafiya, ya tsani ya ga an yi aure ana soyayya tsakani da Allah ,nan za ka ga ya fara saka zargi da abubuwa a zuk’atan maaurata, bayan Abbakar da sharrin zubar da ciki da chats Yash akwai shed’an, dan Allah ka daure ka yi trusting matarka duk rintsi! Ba fa a aure da zargi, babu kyau! ka daina dan Allah kar ka sake wannan tab’argazar, shi kuma Abbakar ka bar ni da shi sai na ci uwarsa, wallahi zai san Ina ya zo”. “Ba na jin har yanzu yana da rai, dan dukan da ni yi masa ba lalle ya rayu ba” Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin yace”mu yi addu’ar ya rayun dai” “InshaaAllah ya mutu” Yash ya fad’a cikin d’aci yana jin wata tsanar Abbakar tana sake taso masa.   A hankali Yahanasu tace”ai yanada magoya baya, dan shi kad’ai ba zai iya aikata wannan b’arnar ba…..”   Shiruu duk suka yi, Hatta Najeeb shima zuciyarsa sisters d’in Yash d’in ta zarga, tunda a baiyyane ba sa sonta, amma kuwa da sun cika dabbobi, dan in har za su iya kashe d’an wansu to kuwa abun nasu Azimun ne! ya godewa Allah da ya rabu da Ya’isha bai aureta ba…….   A ɓangaren Yash ma, yadda Yahanasu ta yi masa bayani da komai da kuma ya tuna yadda Yasmeen tun farko ta ce Manu bata da ciki..babu wasu waenda suka zo kansa sai su Yasira, tunda tare suke da su a cikin gidan. Sai dai kuma duk da yadda komai ya ke masa nuni da su ɗin ne, so yake kawai ya maida zarginsa akan gwaggwo! saboda yanzu haka a cikin tashin hankalin binciken estate d’insa yake, yana jin tsoron sakamokon…shiyasa yake addu’a Allah yasa idan ya yi binciken ya gano gwaggwo ce kawai, ba y’an uwansa uwa d’aya uba d’aya ba.!…   Yahansu ce ta ce”Manu da sunanka ta yi barci a bakinta…ka tashi ka j….” Tun kafin ta rufe bakinta yace”Bara in je in ganta…..” Murmushi duk suka yi, cikin tsananin jin dad’i suka mik’e, Najeeb yace”na san ba zaka fad’awa kowa ba amma pls Yash rashin fahimtar nan  da kuka samu da abunda Doctor yace inaso ya tsaya a iyaka mu uku kawqi! Sannan kamar yadda yaha tace ‘ka yi bincike,’ Allah ya sa mu dace.” Jinjina kai Yashjub ya yi yana jin wani sanyi yana shigarsa kafin yace musu”na gode,sosai”a hankali. Murmushi duk sukayi suka ce ‘ya dage da addu’a, ya cire komai a ransa’ daga haka suka wuce, shi kuma ya hau sama domin ya d’auko makullin motarsa…… Har wannan lokacin Ya’isha tana tsaye tana jiran Najeeb.   Sallama ya yi da Yahanasu, ta wuce, shi kuma ya d’auke kai ya yi kamar bai ganta ba ya had’e rai sannan ya nufi motarsa da sauri, wanda hakan ya sanya itama ta nufosa da sauri, amma kafin ta k’arasa tuni ya shige ya bata wuta ya yi reverse an wangale masa gate ya fice da mugun gudu.   K’amewa kawai ta yi a wajen, ta kasa motsi, kafin da kyar ta ja k’afafuwanta ta wuce garden, tun kafin ta gama shiga ta fashe da wani irin kuka.   Junior kam yau ya samu fuska a wajen Yadira ba laifi, dan suna shiga Yusra ta wuce sama su kuma suka zauna a main parlourn…gaba d’aya jikinta ya yi sanyi shiysa ya sameta yau ɗin, ta d’an sake da shi. wanda murna da farin cikinsa sam suka gagara b’oyuwa.A rayuwarsa yana mutuwar son Yadira, so ba na wasa ba,Allah ya jarabcesa da masifaffiyar k’aunarta.   Ummi tana zuwa za ta d’aura girki, ta tarar gwaggwo har ta kusan kammalawa… dan haka ta sa hannu har da Munirat itama suka taru suka yi na duka gidan, nan da nan kuwa suka gama. daga haka suka wuce asibiti kai abinci, bayan ta had’a na Yash  a daban daban ta ajjiye. Babu yadda ba ta yi da Hajiya Mama akan ta hak’ura ta koma gida ba tunda ga Siyama amma Hajiya maman tace”ba komai za ta kwana da Manubiya, da safe sa chanjeta.”     Yashjub yana hawa sama aka fara kiran sallar Magrib, dan haka ya ga ‘bari ya kama ruwa, ya yi alwallah kafin ya wuce.’ Zuciyarsa ta yi sanyi zuwa wannan lokacin, amma ciwon da kansa yake yi ba kad’an bane ba, yana buk’atar ya sha magaani.. Amma a yadda yake jiri a yanzun ya san idan ya sha babu komai a cikinsa wahala zai sha, gashi a side d’in babu cima, tunda ba zama ake yi a ciki ba, kuma ba zai iya tsayawa cin abinci ba dan ya san yin hakan zai d’auki lokaci… dan haka ya kira gwaggwo a waya yace”ta had’o masa coffe dan Allah yanzu da sauri, zai sha, yanaso ya sha da magani, kafin ya wuce sallah.” Lokacin da ya kira ta tana shirin kawo masa abunci ne dama, dan haka ta ce “to shikenan”. Daga haka ta katse ta ajjiye basket d’in ta shiga had’a masa coffee d’in. Kausar tana cikin kitchen d’in a wannan lokacin, dama tana ta tunanin ta yadda za ta aiki gwaggon a samu ta ajjiye basket d’in Yash ita kuma ta samu hanyar juye abinda ta k’unso a cikin abuncin nasa, a kai..kawai ta ji ya kira gwaggwon. Ba k’aramin dad’i ta ji ba da ta ga gwaggo ta fara had’a coffe saboda dama ta riga ta yi diluting abun kuma ta san idan ta zuba akan farar shinkafa ko miyar agusin da suka yi zai gane, coffee zai fi haɗiye abun lumi ba tare da an gane an zuba komai ba.……         Yana fitowa daga band’akin ya chanza kaya zuwa jallabiya, ya d’auki wayoyinsa ya kukkuna, sai da ya gwada layin Manu akace masa tana barci, tukunna ya zuba a aljihu ya d’au makullin mota ya nufi k’asa dai dai gwaggo tana shigowa da basket. “Yauwa sannu gwaggo iyaka coffee d’in kawai za ki zuba mini” ya fad’i hakan yana mai sauk’owa daga stairs d’in a gurguje.” Itama da hanzari ta shiga zuba masa, kafin ya k’araso cikin parlourn har ta gama zubawa.   Sai da ya nemi guri ya zauna tukunna ya karb’a yace “sannu gwaggo” Daganan ya fara k’ok’arin kaiwa Baki.   Gani yayi ta tsaya tana kallonsa, dan haka ya ajjiye cup d’in ya zuba mata dogayen idanuwansa kafin yace “Lafiya dai ko gwaggwo? Akwai matsala ne!?”   Da sauri ta yi firgigit kafin tace”laa a’a ba komai”sai kuma ta juya ta fice ranta duk ba dad’i…ba ta so ta taso da case kuma a zo a yi bincike aga ba komai ta je ta shiga masifa, amman haka kawai ta ji ba ta yadda da Kausar ba! Ta gama had’a coffee d’in kenan Kausar d’in ta ce mata”ta je sama ta d’auko mata wayarta a sama a parlournta”   Ta so ta lab’e amma sai ta yi gaba kawai amma da ta dawo tabbas taga kamar an tab’a flas d’in coffee ɗin, dukda ba ta ga Kausar ta zuba wani abun ba, cake ma ta tarar da ita tana ci dan lokacin da ta dawo sai da ta d’an lab’e,amma kwata kwata ita dai bata yarda da coffee d’inba, kuma abunda ya sake saka mata zargin Kausar d’in yadda ta dinga cewa “ta d’auka ta kai masa” “ta d’auka ta kai masa”bayan ta dawo d’in. Gashi ta ga ta ci uban kwalliya, dukda doguwar rigar abaya mai bottons ce a jikinta amma ta fahimci kamar k’ananan kaya ne ata ciki  saboda har cinyarta sai da ta hango a waje d’azun da ta zauna tana cin cake, sannan ta gyara gashinta, ta sha jambaki ga uban k’amshi tanayi… Kuma har waje ta biyota, sai da ta ga ta shigo nan ɗin tukunna ta tsaya a wajen ta fara wasa da flowers, tana sinsinawa kamar irin dama abunda ta fito yi kenan……..       Yadda Yashjub ya ga gwaggon ta yi ne yasa ya ɗanji a jikinshi watak’il akwai  abunda take so ta gaya masa amma tana jin tsoro…tashi d’aya lissafinsa ya basa ko dai akan case d’in Manu ne, tunda ai tare suke a gidan har da ita, shi fita yake yi dan haka dole ita ta ga wani abun…..ko kuma maybe taana so ta yi masa basaja ta kare kanta ne.! Yana wannan tunanin yana sipping coffee d’in ahankali ahankali, kafin ya d’auko maganin ciwon kai daga aljihunsa ya b’alle ya sha, ya d’an had’a da cake kad’an daga haka yayi gyatsa yai hamdala ya fara k’ok’arin mik’ewa dan ya ji har an shiga sallah.   Yana mikewa ya ji kansa ya wani irin sarawa, wanda har sai da hakan ya kaishi ga kaiwa k’asa ya durk’usa a nan bakin kujerar. Jiri ya fara yi, mai had’e da wani yanayi na daban da ya shiga tashi d’aya, abun har abun tsoro! “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”ya shiga maimaitawa, dan tashi d’aya gabansa ya fara fad’uwa saboda zai iya cewa bai tab’a tsintar kansa a irin haka tashi d’aya ba!   “Ya subahanaAllah” Ya furta a fili… ga Manu a asibiti, yanzu ya zai yi kenan, a ransa yace “da na sani ban sha ruwan zafin nan ba, na san duk shine sila, amman kuma tou jirin na menene??” Ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya san me bashi amsa ba.   Ganin abun fa gaba yakeyi, yasanya yayi sauri ya lalubo makullin motarsa….ya san Manubiya ba ta da lafiya amma yana buk’atar kasancewa tare da ita, ta hakan ne kad’ai zai iya tseratar da kansa daga fad’awa halaka….saboda wannan abunda ya ke ji ɗinnan mai matuƙar haɗari ne babba.   Dukda baya jin zai iya yin tuk’i a halin da yake ciki, ga kuma jiri, amma gara ya gwada…kar ya je ya yi abunda zai binne kan shi da ransa.   Da k’arfi ya mik’e tsaye…dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi-dishi.   Yana mik’ewa ya ji an fara knocking…Addua ya fara yi akan Allah ya sa ba gwaggwo bace ta dawo, dan ba gwaggwo ba ko Iya ce Indai mace ce to fa akwai matsala muddin suka kasance waje d’aya a tashin hankalin nan da bala’in nan da yake a ciki.   Jin bai yi magana ba, ya sa Kausar ta shigo a hankali ta mayar da k’ofar ta d’an tura ta barta a bude ba tare da ta saka key ba.     Da farko dishi-dishi ya fara ganinta, sai da ta matso daff da shi tukunna ya fahimci ashe Kausar ce….tunda yake a rayuwarsa Kausar bata tab’a burgesa irin na yau ba…sanye take da wata arniyar gown ta roba iya guiwa Fitted Red ga stones a jiki sai walwali sukeyi,ta rambad’a jan jambaki, tasha kwalli!gashi ta gyara gashinta ta yi parking ta yi styling gaban da jel jelar kuma tana reto a tsakiyar bayanta, sannan ga wani uban k’amshi da take zubawa.   Dakyar ya iya cewa”Kausar.” Lumsassun idanunsa suna sake lumshewa. Wata sabuwar k’aunarsa ce ta lullub’e Kausar a take, a hankali ta matso ta sa hannunta a daidai saitin zuciyarsa tana shafawa kafin tace”Dukda kai da Daddy kunce a baka space amma na kasa yin hakan Ya Yash, zuwa na yi in ganka, in ga halinda kake ciki, dan halin da na ganka ɗazu a ciki ya kasa fita daga kaina.” Ta k’arashe maganar cikin wata shuumar murya, sannan cikin shagwab’a da turo Baki, kafin a hankali ta d’an matso jikinsa.   Karkarwa jikinsa ya fara yi, dan haka ya tureta da dukkannin ragowar k’arfin da yake a jikin sa,cikin fushi yace mata “Stay away!!!” Ya daka mata tsawa.   Daga nan ya fara takawa da niyyar fita amma sai ƙofofin suka juye masa, parlourn ma gaba d’aya ya fara juyawa a kwakwalwarsa…ya ma kasa gane wacce ce k’ofar fita!.   Dasauri ta sake zagayowa ta tsaya a gabansa tace”me ya sameka?In kira doctor ne?”   Tunani yayi tabbas idan doctor ya zo to maybe ya bashi magani, dan zuwa yanzu ya san ba zai iya driving zuwa inda Manubiya take ba , dan haka da sauri yace “Yes pls ki kira harda Yasmeen”.ya fad’i hakan a hankali.   Dan sake matsowa jikinsa ta yi tace”Okay mu je in kaika Bedroom sai in kirasa” Daga haka ta matso sosai batayi wata wata ba ta yi hugging d’insa.   Wasu tagwayen ajiyar zuciya ta ji yana sauk’ewa a jere jere, kafin ya d’ago hannuwansa gaba d’aya biyun ya rungume ta da dukkannin ragowar k’arfin sa. Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Kausar, tashi d’aya hawaye suka fara ambaliya a fuskarta tsabar farin ciki…a hankali ba don ta na so ba tace”Let me go, In kira doctor pls Ya Yashhh” Ta fad’i maganar cikin sigar da ta sanya Yash ya sake rungumeta tsam a jikinsa….. Shi dai daganan jin sa ganinsa da komai nasa suka d’auke D’iff!!! Ba shi ya farkaba sai……       Daddy ya yi tunanin zai ga Yashjub a masallaci amman shiru.. Dukdda ya san yana cikin damuwa amma ya kamata ace ya je Masjid ai….   Akwai maganganun da yake so su yi, yana so ya samu ya d’an kwantar masa da hankali tun d’azun, amma sai ya hak’ura ya bari akan idan sun had’u a dinner sai su yi, dan ya san maybe sai ya huta ya yi dinner tukunna zai wuce asibitin.   Shiruuu nan ma har aka fara dinner babu Yash babu alamun shi, kuma wani abun mamakin babu Kausar. Tunani ya yi akan ‘ko dai ya wuce gidansa ne, sai kuma ya tuna ai yanzunma kafin ya shigo Sai da ya ga motarsa.   Yassir kasa zama dinner d’in ma yayi saboda tashin hankali da kishi….ya yarda da Kausar amman idan ya tuna za ta kwanta da waninsa a gado ɗaya ba komai jikinta a ƙarƙashin bargo ɗaya gaba d’aya sai ya ji hankalinsa ya tashi ya gaza sukuni..babu damar ya yi magana yanzu sai tace bai yarda da ita ba!sannan hakan shine kad’ai mafitarsu dan basu da mafita sama da wannan ɗin…shiyasa kawai ya ke ta ƙoƙarin daurewa Kai kawo ya dinga yi, har sai da 40 minutes d’in da suka riga suka tsara ya cika, tukunna ya sauk’o k’asan lokacin ana tsakiyar cin abinci, shi a tunaninsa ma an gama…   Tunda aka zauna dinner Mommy da Baba larai suka sha jinin jikinsu, dan kallar kallon tsanar da Daddy yake jifan mommy da shi sai da ya saka su a al’ajabi.     Da kyar Yassir ya dake ya gaida Daddy, daga haka ya juya ya ja kujera ya zauna ya fara zuba abinci a ransa yana adduar Allah yasa wani ya yi masa maganarta, dan idan ya yi da kansa to ya b’ata komai.   Yassira ce tace “Am Yassir Kausar tana sama ne?”   Kallon ta yayi yana jin wani sanyi a ransa, a zahiri kuma sai ya sake tamke fuska kawai ya d’auke kai.   Mommy ce tace mishi “ba tambayar ka takeyi ba?” Dan itama shirun na Kausar d’in ya d’an dameta, saboda missing dinner ba aladar Kausar baceba, babu abunda ta tsana irin ta kwanta bacci da empty stomach.   Ajiyar zuciya ya sauk’e ya ajjiye spoon d’in tukunna yace “Mommy pls..kar ki yi mini maganarta, ku rabu da ni kawai. Ni da na san ma kuna nan da ba zan sak’k’o ba…” Daga haka ya ci gaba da chin abincin sa.   “Hmm”kawai junior yace, daga haka ya d’auke kai bai ce komai ba.   Ajjiye spoon d’in sa Daddy ya yi, daga nan ya gyara zama ya yi gyaran murya ya kalli Yassir yace “Kai! Ina Yashjub?”     Ahankali ya d’ago ya kalli Daddy yace “Yana side d’insa”   “Okay ni kuma ka raina ni ko?” Mommy ta fad’a.   Kamar irin an dameshin nan ya ajjiye cokalin gaba d’aya, ya ture abincin sannan yace”Mommy Kausar ta tafi side d’in Yashjub dubo sa tun d’azu kafin magrib!” Sai kuma ya yi shiruuu kamar mai tunanin wani abun kafin ya kalli Daddy yace “Wanda ya ci ace ta dawo zuwa yanzu…. Allah dai ya sa lafiya” Sai kuma ya mik’e da sauri ya fita, ya nufi side d’in Yashjub. Gaba d’ayansu mik’ewa suka yi suma, suka bi bayanshi har Yahanasu.   …….. Tun a bakin corridor din da zai sadaka da babban parlourn gidan suka tsinci doguwar rigar abayar Kausar… Da k’arfi k’irjin Daddy ya buga! dan haka suka tura k’ofar suka shige. A tsaye suka tarar da Yassir a parlour ya k’urawa rigar Kausar ido wadda ke nan a yashe a tsakar parlourn. Daddy yana gani tun kafin ragowar mutanen wajen su gani ya juya ya kalli Yadira da su Yusra yace musu “Ku fita!”   K’urawa Yassir ido kawai Junior ya yi…a rayuwarsa wallahi ko tari idan Yassir ya yi ya san me yake nufi, shiyasa tun d’azu da ya sauk’o ya fahimci akwai abunda ya ke shiryawa yanzu kuwa da ya ga sun fara tsintar kayayyakin kausar kai tsaye tun kafin a tafi ga conclusion(ƙarshen al’lamarin) ya fahimci komai, ya gane ina suka dosa…Tabbas Yassir ya tabbata d’an iska…amma bari komai ya lafa zai titsiyeshi ya gaya masa dalilinsu shi da Kausar na aikata hakan kuma wallahi muddin ya ji dalilin bai gamsardashi ba to sai ya tona musu asiri,kasancewarsa best friend d’insa ba shi zai sa ya tsaya yana ji yana gani a k’ullawa Yashjub sharrin da bai ji ba bai gani ba.   Yusra za ta yi magana Daddy yace”Fita nace!” Da k’arfi… Ficewa suka yi ita da Yadira da Junior, tun kafin ace wani abun Munirat ma ta bi bayan su Yusra hakama Yasmeen.   Da sauri Yasira da Ya’isha dan karma a koresu suma suka shiga suka wuce suka nufi d’akin da ya ke a nan k’asan, wanda suka ga k’ofar a d’an bud’e….       Kausar tana jin Yassir ya turo k’ofa ya shigo ta yi tsaki.. tabbas  ta san Yassir da gangan ya bata k’ank’anin lokaci, wato ta samu ta shirya komai iyakar wanda suka tsara..gashi yanzu ko gama hakin jan Yashjub ba ta yi ba har ya zo wanda ba dan hakan ba wallahi ba ta ga dalilin da zai hanata cin moriyar wannan tsadadden lokacin mai muhimmanci ba. Ahankali ta yi kissing Yashjub na kusan sakan biyar kafin ta lalubo sachet water d’in da yake ajjiye a gefenta ta kawo dede setin fuskar su ta matsa da k’arfin gaske ya fashe da k’arfi toss!! A kan fuskarsa.     …..wata bagwariyar nannnauyar ajiyar zuciya Yashjub ya sauk’e, tun lokacin da ya rungume Kausar ya fara ganin dishi dishi tace “Zata kaisa d’aki ta kira Doctor” tun daga wannan lokacin jin sa da ganinsa suka d’auke sai yanzu tukunna suka dawo   Abu d’aya ne ya basa tsananin mamaki, d’ayan kuma ya firgita sa ya saka shi a tashin hankali….na farko yadda gaba d’aya wannan mahaukaciyar desire d’in (sha’awar) da tsananin ciwon kai da jiri suka d’auke masa d’iff ya daina jinsu lokaci guda Komai ya dauke, dan Garau yake jinshi… Sai kuma abu na biyu wanda ya firgita sa dan indai ba mafarki yakeyi ba tou tabbas yau mummunar bak’ar rana ce a garesa saboda kamar naked(tsirara) ya ke jinsa daga shi har Kausar d’in wadda tashi d’aya ya fahimci da ita yake tare, tunda itan ce d’azu a tare dashi daga shi sai ita, kuma har yanzu ga k’amshin turarenta nan yana ji…   A hankali ya d’an fara k’ok’arin bud’e idanunsa domin  ya tabbatar, ya ji Yasira tace “Subahanallah!!” Sai kuma yaji Mutane sun taho rututu!! gaba d’aya sun antayo cikin d’akin…     Runtse idanun naasa kawai yayi, ya koma ya kwanta a kan Kausar d’in, dan bai ma san me zai yi ba! In Banda sunayen Allah babu abunda yake karantowa, yana ji kamar ya shak’e kansa!     Juyawa Ummi ta yi ta fita hankalinta a tsananin tashe ranta a masifar b’ace. Tana fita Baba Larai ma ta fita… Yahanasu kuwa kuka ta fashe da shi…..a ranta tace “wannan wacce iriyar k’addara ce Yash da Manu suke ciki daga an toshe wannan sai wannan!waenna irin mugayen mutane ne haka Ubangiji ya taundumosu a tsakiyar su?!” Ba za ta iya ci gaba da ganin wannan abun bak’in ciki, takaici da tashin hankalin ba, shiyasa kawai ta juya ta fita, dan tabbas idan ta ci gaba da zama to za ta iya kashe Kausar a take.   Kallonsu Yassira Daddy yayi kafin yace”kuma sai na ce muku ku fita!!!. Ba na kori kowa ba tun d’azu???” Ya daka musu tsawa   Dasauri duk suka fice, d’akin ya rage daga Mommy, Daddy Kausar, Yash sai Yassir wanda idanunshi suka kad’a sukayi jazir. Suna had’a ido da Kausar ɗin ta fashe da wani irin kuka, sannan ta fara k’ok’arin tashi Cikin kukan tace “Yassir pls…. Wallahi dole ya yi min..forcing ɗina ya yi.”   D’aga mata hannu kawai yayi,hawaye suna zirara daga idanunsa, sai ya bud’e Baki zai yi magana sai ya kasa.. Yayi hakan ya fi sau uku, kafin kawai ya juya ya fita.   Tausayin shi ne ya lullub’e Daddy…ya fara ji kamar ya rufe su da duka…cikin tsananin b’acin rai yace”Ki tattara kayanki ki bar gidan nan! kafin nan da awa d’aya tak!”. Daga haka ya juya ya fice     Dasauri Mommy ta bisa, har ya kai tsakaiyar parlour, ta rik’o hannunsa tace “Wallahi babu inda za ta je! Wai mai yake damunka ne? Mai ya sa a ko da yaushe idan Abu ya faru sai ka huce a kan Kausar ne? Laifin ta ne? Idan ma tanada laifi shi kuma Yashjub ɗin fa? Kuma fa kana ji tace dole yayi mata a gabansa amman bai musa ba!”   Da mamaki Daddy yake kallonta kafin yace”Khadija ke wacce iriyar dabbar uwa ce??? Baki ganin abunda Yarinyar nan take mayar da ya’yanki ne? Ta lalata Yassir yanzu ta koma kan Yashjub, mutum da aurensa! Brothers fa kuma Ya’yanki Khadijah amman bakya gani???” Ya yi mata tambayar kamar zai rufeta da duka tsabar takaici da tsana! Bai jira Jin amsartaba yace “My decision is final! Kausar za ta bar mini gida kafin nan da awa d’aya!, tun kafin ta fara bin y’ay’ana mata tana lalata musu tarbiyyar da na sha wahala wajen yi,tunda ta riga ta gama lalata mazan…ba ku Isa ba wallahi,da ke da Kausar ba ku Isa ku tarwatsa mini zuri’ata ba.” Daga haka ya  juya zai fita ta sake ruk’o hannunsa, Ido cikin ido tace “Nima bari ka ji nawa decision ɗin! ‘babu inda Kausar za ta je!idan kuma ka nace akan hakan Tou Tabbas nima zan bita.”   Dasauri yace”Alhamdulillah!!! abunda na dad’e Ina son gani kenan! Bari kiji in gaya miki Khadija ranar da za ki bar gidan nan ki bar cikin rayuwata Itace Ranar da nake kwad’ayin gani all my life!!”   Duk yadda Mommy ta so daurewa sai da hawaye suka zubo mata, cikin d’aci da barazana tace”shikenan zan tafi!da Yassira Yasmeen Ya’isha Yusra da Yadira sannan zan had’a har da Yahanasu tunda ni ce na zame mata uwa! Yashjub da Yassir ma na san shekaruna suna yin gaba tare za mu zauna da su da matayensu,kaga wa gari ya waya?kai ne zaka k’are Kai d’aya kwal, daga kai sai Ummi da agolar y’ar ta wadda ba zata ji tausayinka ba idan ka tsufa!” Cikin son fahimtar wani abu tace”kuma wallahi sai na ganka a prison tukunna hankalina zai kwanta, dan sai duniya ta ji abunda ka aikata ga amaryar ka Khadija,ka ce Mallan Lawal yana raye bai dad’e da rasuwa ba na ji shi babu hakkinsa a kanka amma Khadijah kam wallahi sai ka biya sakamokon abunda ka aikata wala da ranka ko kuma da lafiyarka!…. Babu abunda zan b’oyewa duniya , ko Yahanasu, kowa sai ya san abunda ka yi.Tunda ka nuna saboda hakan ne kawai kake jurar ganina a gidan nan ko? To yau nima gashi na fito maka a mutum! Idan ka ga dama ka cigaba da yi mini barazana ni ko Kausar akan barin gidan nan ka ga ikon Allah.Ka riga ka nuna mini babu so ko k’auna a tsakanina da kai, dan haka nima ba zan ji tausayinka kamar shekarun baya ba,fito na fito za mu yi da kai a cikin gidan nan daga yau! Ko dai ka hak’ura ka zauna da ni da Kausar ko kuma ka sha mamaki!.”   Kallonta kawai Daddy yake yi, zuciyarsa ta na tunzura shi da ya shak’e ta ta mutu kowa ma ya huta. Tabbas duk abunda Babba ya hango Yaro bai Isa ya gani ba, Hajiya mama ta yi gaskiya dan gashi tun yanzu ya fahimci tsaff Mommy zata rabashi da ya’yanshi, kuma kamar yadda ta fad’a tsaff za ta kaishi prison wanda shima abunda yake so d’in kenan amman ba zai tafi prison ya bar y’ay’ansa a hannunta babu wanda yayi aure ba, iyaka muguwar illa da gurɓata masa tunanin yaƴa ma da ta yi kad’ai ya isa, kuma dole shi ya kamata ya dage ya gyara ba wai ya bada goyon baya wajen bata k’ofa ta ci gaba da aikata b’arna ga ahalinsa ba….   Ajiyar zuciya Mommy ta shiga sauk’ewa a b’oye dan a yadda Daddy ya yi shiru bai tanka mata game da lamarin Khadija ba ta fahimci abunda take tunani  ba haka bane, dan yadda ransa yake a b’acen nan kuma ta sako maganar, to fa inda ace yana zargintane da tsaf zai yi mata zazzagar kwanyo…to amma me yasa ya yi hacking wayarta, sannan me yasa yake yi mata kallon da kowa ya gani ya san kallon tsana ne tsagwaronsa!!.     Daddy kuwa ya riga ya tsara ne akam zai yi yadda Hajiya Mama tace, shiyasa har zuciya ta ciyo shi zai yi ta ta k’are a take, sai kuma kawai ya yi shiru ya danne zuciyar tasa da kyar, ya zuba mata ido kawai tsanarta tana sake shigarsa. Suna tsaye a haka…suka fara jiyo ihun Kausar.   a minute before now.  (Minti ɗaya kafin yanzu). Su Daddy suna fita Yashjub ya mik’e ya zauna, Jallabiyarsa da ya gani a yashe a k’asa ya d’auka ya saka tukunna ya janye bargon daga jikinsa.   Ya daina jin jiri, ya kuma daina ciwon kai sannan desire d’in ma ta tafi, amman fa dishi dishi yake gani tsabar tashin hankali.   Yana juyowa ya yi sauri ya d’auke kansa,saboda a yadda ya yaye bargon ya barta! a hakanta take still tana nan a kwance ko kyalle bata ja ta rufa ba. Wata kalar arniyar tsanar ta ce ta lullub’esa tashi d’aya!bai san lokacin da ya yi kanta ba! ya hau kifa mata mari ba ji ba gani!. Bayason dukan mata sam, sannan shi kanshi ya san marin da yake kifawa Kausar a halin da ake ciki tsaff zai iya kashe ta! Yasan idan ya  kasheta ya yi babban laifi amma gara ya kasheta ya tafi jail a kan dai ya zauna bai yi mata komai ba ya barta tana rayuwa a doron k’asa bayan shi ta tarwatsa shi ta tarwatsa rayuwarsa……   Ganin ta fara ihu kuma ta k’i mutuwa ne yasanya kawai ya rarumo pillow ya danna mata..Ba dan su Daddy sun shigo da wuri ba da tuni Kausar ta bak’onci lahira.   Da farko duk yadda Daddy ya so ya janyesa su samu su ture pillow d’in kasawa sukayi daga shi har Mommy, saboda Yash gaba d’aya k’arfinsa ya saka ya danne pillow d’in, bashi da wani burin da ya wuce ya ga ta daina motsi! Dan haka Daddy ya daddage ya kifa masa wani rikitaccen mari wanda ya taimaka aka samu Yash ya d’an dawo cikin haiyyacinsa, tukunna da sauri Daddy ya turesa Mommy ta d’auke pillow d’in ta yi sauri ta rufawa Kausar blanket   Ganin Yash d’in yana k’ok’arin sake yin kan Kausar d’in ne yasa Daddy ya rik’esa ya tsayar da shi ya daka masa tsawa yace”one more hit! Yash, ko sau ɗaya tak ne idan ka ƙara bugunta to za ta mutu ne, kuma ka yarda da ni idan nace maka ‘mutuwartata za ta addabeka ne daga nan har ƙarshen rayuwarka!’… muddin ka kasheta Its going to hunt you for the rest of your life. Dan haka ka nutsu!!!!” Ya fad’i hakan cikin tsawa sannan ya girgiza sa.”   Sai a sannan Yash ya d’an kalli Daddy, jikinsa yana wani irin karkarwa fuskarsa da idanunsa sun yi jaaa…. Kawai kuma tashi d’aya sai ya fashe da kuka ya rungume Daddy….   Babu abunda ya fi d’agawa Mommy hankali kamar yadda gaba d’aya pillown ya b’aci da jini kacha kacha! Ga kausar d’in ta ma k’i motsi fuskarta kacha-kacha! Koina jini. Dan haka a gigice ta juyo kan Yash za ta kai masa duka, Daddy ya yi saurin juyawa ya rik’eta.   Tsakiyarsu Yash ya shiga! ransa a mugun b’ace idanunsa suna zubar da hawaye ya fara magana cikin b’acin rai”Ka barta ta dake ni Daddy!ai ba yau ta fara taking sides ba. Ki kasheni kawai idan ma za ki iya, tunda abunda ya rage kenan! Kinsan me ta yi?”bai jira jin amsarta ba yace”Tricking d’ina ta yi na aikata Zina! da aurena! Amman na san dukda haka still bayanta za ki bi…. Dan haka ki dakeni! Ki kasheni!.. Gara ma ki kashenin Dan muddin ba ta riga ta mutu yanzun ba Tou idona idonta kasheta zan yi sai dai duk abunda zai faru ya faru! So inma kasheni za ki yi gara ki kasheni  tun kafin in kashe y’ar da kike fifitawa sama da mu ƴqƴan da kika Haifa a cikin cikinki Musamman ma ‘Ni’.…”   Dakyar Mommy ta samu ta yi lissafi mai kyau ta danne zuciyarta…a gigice ta juya ta fita kiran Yasmeen… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 35* Kallonsa kawai Daddy yake yi, yana nazartarsa. Tashi d’aya ya fahimci tabbas dagaske gadar zare Kausar ta haɗa masa…shakka babu tricking ɗin nasa ta yi. tunda ya haifi Yashjub bai tab’a ganin tsoro firgici da tsananin tashin hankali k’arara a tare dashi kamar na yau ba. Ahankali ya rik’e sa yace”Mu je sama ka huta,ka kwantar da hankalinka ka ji ko?ka sasssauta zuciyarka, ka bi komai a sannu” .. Shiruu ya yi yak’i motsi, dan baima san me Daddyn yake cewa ba, sam ba ya fahimtarsa tsabar tashin hankali… “Mu je Yash” Daddy ya sake cewa. Sai a lokacin tukunna ya bar kallon k’ofar da Mommy ta bi ta fita ta fice daga d’akin…runtse idanunsa ya yi..ya d’an jima a hakan, kafin ya bud’e, bai yarda ya kalli Daddy ba ya fice da sauri…. Yana fita ya ga makullin motarsa a inda ya yar d’azun, tashi d’aya ya sa hannu ya d’auka tare da wayarsa kawai ya fice gaba d’aya, ko bi ta kan Daddy bai sake yi ba. Yana fita ya shige motarsa, alokaci guda ya kunna ya fice daga gidan….. … Test din HIV ya fara zuwa akayi masa, dukda ya san dole ya sake komawa a yi wani nan sati shidda amma dole ya haɗa aka yi masa har da shi a cikin jerin tesatesan da ya lissafa yace duk a yi masa su bayan nahiv ɗin. cikon ikon Allah komai ya fito negative, still sai da aka yi masa allurai ya sha magunguna tukunna ya bar asibitin. Direct Bristol ya wuce, yana zuwa ya kama d’aki, dan ba ma ya so ya je inda wani zai nemo shi…….Idan ya rufe idanunsa fuskar Manubiya kawai yake gani…”innalilla wa inna ilaihirrajiun” yake ta ambata a cikin ransa…idan ya b’oye mata ya ha’inceta, amma kuma bai san ta Ina zai iya kallonta ya gaya mata wannan mummunan al’amari ba, ya san tabbas wannan shine al’amari mafi ƙololuwar tashin hankali da zuciya da kanta za su iya ɗauka kuma su jura… Kaɗan ya rage bai mutu ba! A lokacin da Abbakar ya shirga masa zantukan nan, ba dan su Najeeb sun wayar masa da kai ba ya san tsaf ciwon zuciya zai iya yin ajalinsa shiyasa ya ma kasa iya hasaso halin da Manubiya za ta shiga idan ya gaya mata abunda ya faru tsakaninsa da Kausar, bayaga hakan ma bai ma san ta Ina zai fara had’a ido da ita ba, balle ya yi mata bayani, wani irin tsananin tausayinta da kunyarta kawai yake ji…. Wayarsa ce ta d’auki k’ara, a karo na hud’u. dan haka ya d’ago da niyyar kashe wayar gaba d’aya amma sai yaga ‘Honey’ a kan screen d’in yana yawo…. Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin fuskarsa, hannunsa ya fara karkarwa, k’irjinsa ya shiga dukan uku uku…. Har ta katse bai d’auka ba, haka ta sake kira ta katse bai ɗauka ɗin ba, daga k’arshe ta turo masa message”Baby Ina wuni, hope you are fine..d’azu ka kira Ina barci, yanzu na farka..ba ka d’aukan wayar!ina fatan kana lafiya, i need you, i want to see you (ina buƙatarka, ina so in ganka) plss.” Yana gama karantawa ya yi jifa da wayar ya mik’e ya fad’a toilet, ya sakarwa kansa ruwan sanyi yana wani Irin huci, kansa yana juyawa fiye da misali… Ya fi awa d’aya a cikin band’akin, da kyar ya yi wanka ya yi alwallah ya fito yana istighfari….jallabiyarsa ta riga ta jike tana band’akin shiyasa sai da ya jira ya yi order aka kawo masa, tukunna ya mik’e ya tada ik’ama bayan ya shirya…yana ta istighfari dan bai tashi tuna bai yi sallar Magrib da isha ba sai da ya gama wanka ya fara alwallah, saboda bai tab’a kaiwa war haka bai yi ba, shiyasa ya manta….. Yana idar da sallar ya tashi ya fara jero nafilfili,ko da ya gama ma karatun Al’kur’ani ya zauna yayi, sai wajajen 1 na dare tukunna ya d’an samu zuciyarsa ta fara yin sanyi… Wayarsa ya d’auka… Ya danna dial a number Manu ya kashe, ya fi sau shidda!! kafin daga baya kawai ya rufe ido ya danna, ya runtse idanuwansa, zuciyarsa tana wani kalar mahaukacin bugawa. “Assalam alaikom” Ya jiyo muryarta mai dad’in sauraro da kwantar da hankali. A hankali ya lumshe idanunsa, hawaye suka shiga zirara, kafin ya ce”ameen wa alaiki assalam,ba ki yi barci ba har yanzu?” A hankali Cikin firgice tace”Ya Yash kaima kuka kake yi? har yanzu?.” Bata jira ya bata amsa ba ta ɗaura da cewa “killace kanka da k’aurace mini ba shine zai yi mana maganin damuwar mu ba. Na kasa nutsuwa, hankalina a tashe! ban yi tunanin za ka gujemini a irin wannan lokacin da nake matuk’ar buk’atarka ba Ya Yash.” Kuka sosai ta ji ya saka, kafin ya kashe wayar,yana kashewa ya yi switch off d’inta gaba d’aya. Ta kira sa ya fi sau ashirin amma switch off, dan haka hankalita ya sake tashi!ta fara wasu Irin hawaye masu zafi… Ta shiga tashin hankali da firgici matuk’a a lokacin da aka ce cikin jikinta ya fita, amma dama ita 50%na damuwarta Yashjub ne…da farko ta d’auka fushi ya yi da ita bayan damuwar da yake a ciki, shiyasa ya k’i zuwa gareta, amma yanzu da suka yi waya tashi d’aya ta fahimci tsananin damuwa da tashin hankali ne suka sanya shi ya killace kansa ya k’i zuwa wajenta…ta san Yashjub yana sonta, yana son cikin jikinta amma ba ta yi tunanin abun zai kai ga haka don wanda ya basu ya amsa ba….. Bayan ya gama waya da Manubiya da kamar awa d’aya da rabi lokacin ya san ta hak’ura ta daina gwada layukansa ya kunna d’ayar wayarsa ya kira Yahanasu, bai damu da dare ko kuma kar ya tasheta a barci ba haka nan ya yi ta kira yana sake kira har sai da ta d’auka cikin magagin bacci a d’an rikice tace”Assalam alaikom” “Yash Ina ka tafi ne an je har gidanka ba ka nan, kuma ba ka d’aukar waya?” “Yaha ki taimakeni ki yiwa Manubiya bayanin abunda ya faru, ba zan iya ba, ba kuma zan iya b’oye mata ba..sannan mun riga mun yiwa juna alk’awarin babu b’oye b’oye a tsakaninmu…kuma na san ko yaya mutum ya kai ga iya b’oye sirri dole sai an samu ta inda zai ɗan fita, idan ta ji a wani wajen za ta karaya sannan ba za ta sake yarda da ni ba…ki yi mata bayani ki Ba ta hak’uri, ki fahimtar da ita a madadina, Ina son ganinta amma ba zan iya fuskantar ta ba kunya nake ji sanan a dame nake, kuma tsoro nake ji………” A hankali Yaha ta share hawayenta tace”slow down Yash….!” Kafin ta mik’e ta zauna tana mai kunna bedside lamp tace”maganar b’oye mata kam dama bai taso ba, dan na san ko da gangan sai an samu masu gaya mata!Tunda abu ne wanda kowa ya sani… Ka kwantar da hankalinka, InshaaAllah Manubiya za ta fahimceka. na ji dad’i matuk’a da ka ce ba za ka b’oye mata ba, saboda b’oye b’oye babu abunda yake janyowa sai b’arna, sannan mai gaskiya yana tare da Allah ba zai tab’a tab’ewa ba.! InshaaAllah gobe da safen zan shirye in je in sameta,ka kwantar da hankalinka, Kausar za ta girbi abunda ta shuka Allah yana tare da kai…” A hankali yace”inshaaAllah” yana jin zuciyarsa tana wani irin tafarfasa… Sai da ta sake kwantar masa da hankali tace”ya yi ta sallah da nafilfili, idan ya kasa bacci.. komai zai yi daidai inshaaAllah sannan idan ya samu hali gobe da safe ya kira Daddy saboda hankalinsa a mugun tashe yake…….” Tukunna Daga haka suka yi sallama, yana mai jin sassaucin abunda yake ji kafin su yi magana…. Tabbas Yahanasu tana daga cikin manya manyana kyautar da Ubangiji ya sako cikin rayuwarsa, tana tsaya masa akan komai, tana son farincikin sa sannan ta yarda da shi d’ari bisa d’ari!kalli yanzu ita bata ma da buƙatar ya yi mata bayanin kansa tashi d’aya ta san sharrin Kausar ne….Addu’a ya fara yi a cikin ransa Allah Ubangiji ya sa Manubiya ma ta kawar da kishi, a samu Yahansu tana yi mata bayani itama ta aminta da shi ta yafe komai…….. A b’angaren Kausar kuwa har chan cikin dare ba ta farfad’o ba. Yasmeen ta yi mata duk abunda ya kamata, ta yi dressing mata ciwukan fuskarta amma duk wanda ya ganta a wannan lokacin in ba cikakken sani ya yi mata ba tou ba lalle ya shaidata ba, dan fuskarta ta kumbura ta yi sutu-sutu ga ciwuka ta koina kamar ba ita ba. In banda zubar hawaye babu abunda Mommy take yi…da kyar su Yasira suka lallab’ata aka bar Kausar a gida dan Yasmeen tace musu”she’s fine, kuma idan aka kaita asibiti a haka case ne sannan in akayi bincike aka gano to Yashjub zai iya shiga matsala.” Dakyar Mommy ta yadda amma da cewa ta yi “a kaita asibitin a haka! Inyaso ya shiga matsalar shi ya sani, ita ba damuwar ta bace ba.” Dan ba kad’an ba ta ji mugun mugun zafin halin da Kausar d’in ta ke ciki, ba kad’an ba dukda ta san wataƙil dagaske Yash d’in yake gadar zare Kausar ta haɗa masa har ya kai ga kwanciya da ita amma sam ita ba wannan ne a gabanta ba! Bata ga dalilin da zai sanya ya illata mata Yarinya haka nan ba, wannan ai rashin imani ne!Yarinya y’ar amana!yanzu inda za a tashi uwarta a nuna mata Kausar a sume hakanan da fuskarta a haka ai batasan da wanne ido zata kalletaba ranar gobe k’iyama. Da Mommy da Yassir sun fi kowa tashin hankali a cikin d’akin, sai Yadira wadda yanayin Kausar d’in ya fara bata tsoro itama ta fashe da kuka junior yake ta faman rarrashinta. Yassir har ya fara shirye-shiryen appointment dan yace “tana bud’e ido za su bar k’asar!” Saboda tabbas yadda kumatunta da gefen idanunta suka fashe ya san sai an yi wani abun a wajen…dukda ba shi da enough kud’i amma zai ranta a wajen Abokansa, domin a samu a je a yi mata aiki kafin ya samu ta warke tukunna ya dawo ta kan Yash dan bai ma san ta Ina zai fara ba! Tabbas ya bashi mamaki dan sam bai yi tunanin zai Illata masa Kausar har haka ba…dukda ya san ƙarshen yash ɗin ya zo kenan! dan yanzu Manubiya da Daddy za su juya masa baya saboda ya gama shiryawa da kansa zai tura mata message ya gaya mata komai!amma dole Yashjub ya fuskanci hukuncin abunda ya yi wa Kausar wallahi,dole!… Ummi ce kawai babu a d’akin sai Daddy amma kaff gaba d’ayansu suna d’akin. Junior kawai kallon Yassir yake yi…a yadda ya d’aga hankalinsa tabbas ya tonawa kansa asiri ne a idanun Junior, saboda bai kamata ace ba ya fushi da Kausar a yanzu ba, bayan abunda idanunsa suka gane masa awannin da suka shuɗe. Suna tsattsaye wasun su a zazzaune a kanta, ta d’an fara motsi ,kafin a hankali ta dawo cikin haiyyacin ta! Sai dai ba ta bud’e ido ba… Ta san ta daku dan fuskarta in ba da kyar ba sai ta had’a da plastic surgery amman kuma ba ta jin akwai ranar da ta tab’a tsintar kanta cikin tsananin farin ciki Irin wagga rana!…dan ta riga ta san nan da 10 days inshaaAllah burin ta zai cika ko da balai ko ta wanne Hali! Batajin alamun ciwo ko wani abun a mararta kuma dama ta san Yashjub bai sameta a wajen ba dan haka tana da yak’inin cikin ta yana nan daram!. Yo ai ko ya fita sai ta sake yin wani ta lik’awa Yash!yadda aka kamasu d’innan shine mafi girman abunda za ta riƙa ta yi amfani da shi a matsayin makaminta… Ta ji dad’i matuk’a gameda yadda plan d’insu ya tafi daidai babu targard’a. Sannan bata wani damu da Manubiya ba, dan ba Manubiya ba ko auren irinta uku ne da Yash wuyarta ta auresa Wallahi sai ta yi waje da ita!. Mommy dake daff da kanta ce ta d’an matso tace “Kausar”. Ahankali ta d’an fara k’ok’arin bud’e idanunta… Duk matsowa sukayi sai da ta d’an bud’e idon guda d’aya saboda d’ayan ba zai bud’u ba! Tukunna gaba d’ayansu suka ce “Alhamdulillah”. Da sauri Yassir ya je ta wajen kanta ya d’ago kanta ya d’aura a kan cinyarsa Yace “Yasmeen d’an sake duba ta!idan babu emergency Inaga yanzu za mu fara shirin wucewa kawai!na san dole flight d’inmu ta Abuja zai tashi” sam bai damu da yadda fuskarta ta kumbura kamannin ta suka sauya ba, shi dai kawai ya san Kausar d’insa ce, dan haka yanason ta a ko wanne irin yanayi. Ajiyar zuciya Munirat ta sauk’e tanajin yadda zuciyarta take tafarfasa..a hankali tace “Allah ya k’ara sauk’i” Daga haka ta juya ta fita da sauri. Ba wanda ma ya san ta fita ko ya jita dan tun d’azun ma ba wanda ya kula ta babu wanda ya damu da existence d’inta a cikin d’akin. A b’angaren Munirat d’in itama ba wajen su ta zo ba, dan in banda gaba harara da bak’ak’en maganganu babu abunda yake shiga tsakaninta da su Kausar d’in…Yassir ta biyo lokacin da taga sun kinkimo Kausar an kaita d’akinta ya fito ya fad’a d’akinsa shine ta tsaya akan idan ya fito su yi magana, amma ko da ya fito sai ya d’auke kai kawai ya afka side d’in Kausar ya wani tamke fuska dan karma ta kula sa..itan ma ta yi alk’awarin fita daga harkarsa kwanakin baya amma babu yadda ta iya ne saboda yanzu haka maganar da take so su yi d’in tanada matuƙar mahimmanci shiysa ta tsaya ta yi ta jiran fitowarsa, jin shiru shine itama ta shiga side d’in Kausar d’in…. A yadda taga yake d’innan ta san ba zai saurareta ba shine ta hak’ura ta tsara akan zata nemo numbersa kawai ta tura masa message tunda ta san zai gani…. Sarai ya lura da ita!tana fita ya yi tsaki ya ci gaba da dudduba Kausar yana tambayarta Ina ne yake yi mata ciwo… Ba abunda ya fi d’aurewa su Mommy Kai kamar yadda sam Yassir bai wani damu ko ya nuna jin haushi a kan abunda ya faru tsakanin Kausar da Yash ba, shi ta lafiyar ta ma yake yi.. Ko da ya yi fushi ya fita d’azun suna zuwa suka tarar da shi a d’akin Kausar d’in yana safa da marwa…sun san dole zai tausaya mata amma kuma sam babu alamun kishi ko wani jin haushi a tare da shi, ko irin kishin da ya nuna a d’akin Yashjub sam ba su ga alamarshi a tare da shi yanzun ba…dukda tace masa dole Yashjub ya yi mata amma ya kamata ya ci gaba da jin haushi ko da d’an k’ank’ani ne, kamar yadda ya nuna a wajen dinner ɗazu da ta tafi side d’in Yash d’in da k’afarta. Gyaran murya Mommy ta yi kafin tace”Yassir ka bar batun tafiya tukunna, yanzu a ji da abunda ya faru..indai ba so kake Daddynku ya fusata da kai ba, to ka ja bakinka ka yi shiru ka koma gefe tun kafin a huce a kanka.” Zai yi magana Junior yace”kana fara batun fita da ita waje ma na san tsaf zai saka question mark akan yadda sam ba ka yi kishin komai ba!” Ya fad’i hakan idanunwansa cikin na Yassir wanda ya juyo ya zuba masa nashi shima….lumshe idonta guda d’aya Kausar ta yi dama so take ta yiwa Yassir sign ya gane ya dena abubuwan da yake yi ɗin tun kafin ya tona musu asiri…Aikuwa gashi har an fara magana… Shima Yassir d’in sai yanzu ya d’au haske dan haka ya ce “okay Mommy”kawai..daga haka ya mik’e, sai da ya yiwa junior wani kallo tukunna ya sa kai ya fice saboda ya ji haushi da mamakin yadda d’an uwa kuma Abokin nasa ya so kunce masa zani a kasuwa! Ya san Junior ya sanshi ciki da waje, duk abunda ya yi yana ganewa, ya san wannan d’inma ya gano sa tunda gashi har yana shirin yi masa b’aramb’atama a bainar Nasi, amma ba komai za su had’u ne, zai yi maganin sa dan ya lura Junior ɗin ya fahimci komai kuma ya san yadda yake ji da yashjub, dan haka dole ya rufe masa baki da wurwuri tun kafin ya janyo musu ruwa. Washegari da sassafe Yahanasu ta tashi ta shirya, tana shirin tana fargaba…ba dan Yash ya zab’eta ne kuma ta ji tausayinsa jiya ba wallahi da ba ta ga dalilin da zai sanya ta zamo itace wadda za ta gayawa Manubiya wanna mummunan al’amari ba. Ummi ce ta yi breakfast, suka shirya ita da Yahanasu suka nufi asibitin , akan ‘za su chanji Hajiya Mama da Siyama…’ A d’akin suka tarar da Yashjub ga mamakinsu…lokacin Najeeb har ya je ya d’auki Siyama da Hajiya Mama ya tafi zai maida su gida. ba k’aramin dad’i Hajiya Mama ta ji ba da ta ga Yashjub ɗin ya zo, haka itama Siyama…saboda dama tana ta addu’a Akan Allah ya sa ba fushi ya yi ko ya k’ullaci Manu ba.Ta san dole da zafi shiyasa ta d’aga masa k’afa ya d’an huce gudun kar ta yi magana ta jagula abun, hakanan ta yi ta addu’a sai gashi kuwa yanzu ya zo….. Shi ya tarar da su Hajiya Maman, su Ummi kuwa ba su same su ba iyaka Yashjub d’in suka tarar. Suna zaune, Manubiya a kan gado shi kuma a gefenta ya rik’e hannunta ya sunkuyar da kansa k’asa, ita kuma tana video call da Jiddah wadda Manubiyan ta ji matuk’ar dad’in ganin yadda k’anwar tata ta yi k’iba ta yi fresh a cikin kwanaki k’alilan, alamun Hankalinta a kwance yake. Yadda su Ummi suka ga walwala da murmushi a kan fuskarta ya sa suka fahimci ba ta ji komai ba, tukunna. Gaisawa suka yi da Yash, daga haka ya mik’e ya k’arasa ya shiga had’a mata Breakfast, Yayinda ita kuma suka yi sallama daJidda bayan Jiddan sun gaisa da su Yaha, Manu ta ajjiye wayar suka shiga gaisawa da su Ummi. Yana gamawa ya k’arasa ya ajjiye mata abincin, sannan ya fara k’ok’arin bata… Cikin nutsuwarta tace masa”ai Likita yace akwai allurar da zai yi mata kafin ta ci abinci” “Okay”kawai Yash yace, ya d’an yi mata murmushi, kafin ya mik’e ya fita domin kiran Doctor d’in. Yana fita Yaha ta zauna a wajen da ya tashi tace”MashaaAllah, Jidda ta yi fresh abunta,Al’ameen ya iya kiwo” Dariya duk suka yi har Ummi, kafin Manubiya ta kalli Yahanasu tace”Adda Yaha akwai abunda yake damunsa ne bayaga al’amarin da ya faru da ni? Na ga yanayinsa gaba d’aya ya sauya.” Shiruu Yahanasun ta yi ta d’an k’ura mata ido kafin tace”za mu yi magana anjima,ki kwantar da hankalinki” Daga haka ta yi sauri ta mik’e ta fice, ba itace Yashjub ba amma yunk’urin sanar da Manu da ta yi kad’ai a yanzu tashi d’aya k’irjinta ya fara dukan uku-uku. Kusan karo suka yi da shi, dan tana fita shi kuma yana shirin yin knocking. “Ina Doctor?” Ta tambayesa. “Yace yana zuwa” Ya bata amsa yana kallonta. Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin tace”Yash Inaga gara mu bari ta warke garau, tukunna mu sanar da ita, sannan har ga Allah bana so in yi lalata walwalar da na gani a kan fuskarta.” Jinjina kai ya yi kafin yace”abunda nima nake tunani kenan, da na shigo d’azu ta yi matuƙar farin cikin ganina, dan har kasa ɓoye murnarta ma ta yi a gaban kowa… Ba na jin nima ɗin zan iya lalata farin cikin da nake gani a kan fuskarta, ba zan iya fad’a mata ba Wallahi, shiyasa dama kema tun ɗazun na shirya akan zan ce miki ki yi shiru, to Alhamdulillah tunda tunanin mu ya zo d’aya. Dan haka Mu bari mu koma gida inyaso sai a san abunyi, dan tabbas kam ba zan b’oye mata har abada ba.” Yahanasu ta bud’e baki za ta yi magana kenan suka jiyo k’arar fad’uwa sai kuma salatin Ummi…kafin ta fara cewa”Yashjub Yahanasu kuna Ina Ina likitan?!” dai dai ta bud’e k’ofa za ta fito a gigice suka yi kicib’is da su, dan haka ta juya ta koma ita a tunaninta ma tare suke da likitan… A rikice suma duk suka yi kan Manubiya wadda ke zube a k’asa yashe a tsakar d’akin… Kasa tab’ata Yashjub ya yi, tsabar tashin hankali da tsoro!!! a mugun rikice ya rarumo gorar ruwa ya shiga shafa mata a hankali da hannunsa wanda ya ke wani irin karkarwa…ganin ta k’i motsi ne ya sa ya mik’e a gigice ya nufi k’ofar da niyyar sake kiran Likitan amma sai suka yi karo da shi….ba ma ya iya cewa komai dan ya kasa, kawai Manubiyan yake nunawa Doctor d’in hankali a mugun tashe…da hanzari shima Doctor d’in ya k’arasa gareta… da taimakon Yahanasu suka kinkimeta suka d’aurata a kan gadon ya shiga bata taimakon gaggawa…Yashjub kam ya ma kasa motsi ko magana, hawayen ma sun k’afe, in banda karkarwa babu abunda ilahirin jikinsa yake yi musamman ma k’afafuwansa, dan har zuwa wannan lokacin ba ta farfad’oba! Luu haka ya tafi zai fad’i a wajen, da kyar ya rik’e kansa, ya samu ya zauna a kan kujerar bayansa yana ganin bibbiyu. An kai ruwa rana kafin da kyar aka samu ta farfad’o….ruwa Dr ya sake jona mata ya fita ya je ya kwaso wasu allurai ya yi mata har da ta barci…Sai da bacci ya yi awon gaba da ita tukunna ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya juyo ya kallesu yace da Ummi”jiya jiya na gama ja muku kunne akan d’aga mata hankali ko?za fa ku ja wa yarinyar nan stroke da k’arancin shekarunta idan ba ku yi wasa ba!,jininta maimaikon ya sauk’a hawa yake kuma yi, ku kiyaye fa!.” Cikin d’aurewar kai Ummi tace”lafiya fa muke zaune da ita muna magana,na ga ta fara duba wayarta , sai kuma na ga ta mik’e to daga haka ne ta tafi ta fad’i a k’asa.” Numfashi ya fesar kafin yace “idan ta farka ku kira ni, Allah ya rufa asiri”kawai, Daga haka ya sa kai ya fice. Shiruu duk suka yi suka zubawa Manubiya ido, kafin Yash ya mik’e da kyar ya k’arasa ya d’auki wayar tata wadda har zuwa wannan lokacin take a k’asan gado inda ya ga ta fad’a ,matsawa Yahanasu ta yi saboda itaama wayar tata take shirin dubawa…. Yana bud’ewa ya ci karo da sms daga bak’uwar number ta inda aka sanarwa Manubiya abunda ya faru jiya tsakaninsa da Kausar tiryan tiryan tun daga farko har k’arshe…. Jifa ya yi da wayar cikin fushi yace”enough is enough!!!” Sannan ya fara k’ok’arin fita. Da sauri Ummi da Yahansu suka tare sa, dukda Ummi ba ta ga message d’inba amma itama zuwa yanzu kwakwalwarta ta bata me ya gani. Sai da suka yi da gaske tukunna suka iya tsayar da shi, dan ya zuciya matuk’a, ransa ya b’aci…. Cikin muryar fushi yace”Ummi ki barni in je in same su komai ma ya ishe ni,Wallahi sai na sauya musu kamanni tunda basu san dai dai ba!” Cikin rarrashi tace”Yash wa za ka tunkara? Me za ka yi musu?” Ba tare da sanin inda ya dosa ba ma yace”na san a tsakanin su Yadira so just let me…..” Hawayen da suka shiga zubo masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana, sai kuma ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa A ransa ya shiga aiyyana “me na yi musu da zafi har haka?me yasa y’an uwana suka tsaneni suka tsani farin ciki na?” Sai da Ummi ta share hawayen da suka zubo mata itama, tukunna ta k’arasa gefensa kan sofar ta zauna, cikin sanyin murya tace”kar ka ce haka Yashjub,ba ka ta tabbaci…” Cikin katseta yace”Ummi su ne!idan ba su ba wa ya san maganar in ba y’an gidanmu ba?yaushe aka haifi Yaran nan da za su zama mugaye makirai kamar haka?me na tab’a yi musu da za su yi mini haka?” Shiruu Ummi ta yi dan ta ma rasa bakin magana.Ahankali Yahanasu ta matso tace”Kamar yadda Ummi ta fad’a Yash ba lallai su ɗin bane ba,ka bi komai a hankali kamar yadda na gaya maka jiya…” Dan ta san ko da ace su d’in ne to Mommy ce ta zuga su suka aikata kamar kullum, amma kuma still ba ta jin a tsakaninsun ne, ita ta fi tunanin Mommyn ce da kanta ta aikata wannan d’anyen aikin. Itama cikin katseta ya mik’e yace”Yaha to waye idan ba su ba?Daddy wanda ya haifeni?ko kece?ko Ummi?ko kuma Mommy?….” Shiruuu ya yi, kafin a hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”damn it!!” Sai kuma ya koma ya zauna ya yi shiruuu kawai. Kasa ci gaba da zama a d’akin Ummi ta yi, dan ba ta san ta Ina za ta fara ba..ba ta so tana shigar musu Irin wannan case d’in. Shiyasa ta kalli Yahanasu ta ce”bari in je, Allah ya rufa asiri,Yash k’addara kowa da kalar tasa, ka yi k’ok’ari ka cinye jarabawarka.” Daga haka ta d’au Jakarta ta fice…ba ta da tantama wannan aikin Mommy ne. Tana fita yace”ki je kema,idan ta tashi zan ji da ita,I can face her(zan iya fuskantarta)…” Cikin tausayawa tace”Yash ka yi hak’uri” Wani kalar murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi kafin yace”Yaha hak’urin nake yi a ko da yaushe, amma wani abun dole aga rauni na!…tunda nake a rayuwata ban tab’a jin labarin uwa irin Mommy ba,bani da tabbaci tukunna Akan abubuwan da ta yi mini, sannan ta saka su Yasira suka yi mini amma Yahansu tashin hankalin da nake a ciki ba kad’an bane ba, saboda Ina jin tsoron ranar da zargina zai tabbata Yaha ban san ya zan yi ba. Ina jin tsoro in ji sunada hannu a case d’in estate d’ina! Ina jin tsoro in ji sune suka yi chatting da Abbakar suka bawa Manubiya magani….shiysa nake ta k’ok’arin gocewa amma message d’in nan da aka turo tabbas na san su ne wannan kam ba ni da tantama, kuma hakan ya sanya na sake yarda sune suke yi mini abubuwan da na kasa fahimtar ribar su idan sun tarwatsa ni!” Ya fad’i hakan yana mai sakin hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa, rungumesa Yahanasu ta yi, itama a take wani irin kuka ya kufce mata…Tabbas ta san zafin da Yashjub ya ke ji a yanzu da ya fahimci Mahaifiyarsa ba ta son sa, sannan ba ta damu da shi ba, kuma ba ta damu da farin cikinsa ba! saboda itama ta fuskanci wannan kalubalen kuma har gobe tana rayuwa ne a cikin azabar raɗaɗinsa…. Sun jima suna kuka, babu mai rarrashin wani, kafin da kyar Yaha tashiga rarrashinsa tana basa baki…cikin sheshek’ar kuka tace”Yash har gara kai! InshaaAllah na san akwai ranar da za ta zo maka wadda za ka fahimci Mahaifiyarka ta na son ka ba son kashe ka take yi ba sannan tana son dukkanin abunda kake so infact tana son ka fiye da komai ma da kowa a duniyar nan! Saɓanin ni! da zan rayu da sannan in rungumi gaskiyar cewa ‘mahaifiyata ba ta sona, ba ta k’aunata, ba ta damu da ni ba, iyakar amfanin da take ganin inada shi a wajenta shine ‘ta dinga amfani da ni wajen ganin ta cimma wata manufa tata’…” Cikin katseta Yashjub yace”Yahanasu ki daina cewa haka!babu kyau, kin san fa ta rasu. kar ki k’ara mata nauyi…kwakwalwata ba za ta iya tuno mini ita ba amma a ko da yaushe hajiya mama tana sanar da ni ‘ita d’in mutumiyar kirki ce,’ kar ki ce za ki shiga abunda ya faru tsakaninta da Daddy har ta kaisa ga cewa ‘kar mu sake ko da ambatar sunanta ne!’ wannan tsakaninsu ne, kuma kinga har yau ba mu san menene ba balle mu shiga! kawai ke dai har ma da ni kamata ya yi mu bi ta da addu’a da fatan samun aljannah…dan Allah Yaha kar in sake ji kin yi wannan furucin game da mahaifiyarki!.Mommy kuma tunda Allah ki ka ce to na san gagara misali ne….dan haka nima zan yi addu’ar abunda kika fad’a d’in ya tabbata, zan yi addu’ar ‘Allah ya sa duk zargi ne kawai muke yi ba gaskiya ba.” Kallonsa take yi tashi d’aya wani Irin yanayi na tausayi k’unci da rashin jin dad’i suka lullub’eta.Ba ta san lokacin da ta kuma tafiya jikinsa ta sake fashewa da wani sabon kukan ba.! Sun jima a haka kafin da kyar suka samu suka rarraashi junansu ta sake jaddada masa”ya bi komai a hankali, kamar yadda suka gaya masa, kar ya d’au mataki a kan kowa ba tare da kwakkwaran shaida ba.” Awannnin Manubiya biyu tana barci kafin suka ga ta fara motsi…duk su biyun tashi d’aya k’irjinsu ya buga, kafin Yash ya dake ya mik’e ya k’arasa ya zauna a setin kanta bakin gadon, yacewa Yahansu ta je ta kira Likitan. Tana gama bud’e idanunta Doctor ya shigo…yana nan inda yake aka gama dubata Dr d’in ya fita. Yana fita tun kafin su yi magana ta kalli Yahanasu tace”d’azu kin ce za mu yi magana.Dan Allah kar ki ce mini akan maganar message d’in da aka turo mini ne, dan Allah Adda Yaha ku ce abunda aka rubuta a jiki k’arya ne.” Yahanasu tana shirin yin magana Yash ya ce “gaskiya ne.” A hankali ta saki wani irin kuka mai cin rai….mik’ewa Yahanasu ta yi ta fice zuciyarta sam babu dad’i. Sai da Yash ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya had’iye wani abu mai d’aci da ya mak’ale masa a mak’oshi, tukunna tiryan tiryan ya fara zaiyyano mata duk wani abu da zai iya tunawa wanda ya faru a jiyan, bai b’oye mata komai ba… D’ari bisa d’ari ta yarda da shi, sai dai kishi takaici da bak’in cikin da suka tarar mata ne suka sanya take jin zuciyarta kamar za ta hantsilo ta fito waje, har wani Jan numfashi take yi yana kufce mata. Dai dai nan Mommy ta ja ta tsaya a bakin k’ofar ita da Ya’isha waenda zuwansu kenan. Kamar zai fashe da kuka yace”mun so mu d’an jinkirta, saboda yanayin jikinki daga baya sai mu gaya miki amma kuma sai aka turo miki message…… Ga gaskiya nan na faiyyace miki ita Baby, ga kuma message d’in nan da aka turo miki da kuma abunda ya faru da ni dan haka ya kamata ace in kin haɗa su waje ɗaya su sanya ki fahimci so ake yi a raba mu, dan Allah dan Allah dan Annabi kar ki bada k’ofa, ki yarda da ni plss, dan Allah….” Ya faɗi hakan cikin rungumeta. Tabbas wannan abu ne mai nauyi na tashin hankali da ya sameta, dan za ta iya cewa bata tab’a shiga rikici da k’unci kamar na yau ba amma kuma ya zama dole ta bawa mijinta support sannan kamar yadda ya fad’a tabbas so ake yi a raba su,dan haka ita kuma duk rintsi duk wuya ba za ta bud’e k’ofa a shiga a raba su ɗin ba…..da izinin Allah. Wani irin zafi da rikitaccen tashin hankali ta ke jinta a ciki amma ya zame mata dole ta danne kanta ta taushi zuciyarta ta tsaya musu…dan haka cikin sharar hawaye ta sa hannu ta rungumo sa itama kamar yadda ya yi mata tace”I trust you! (Na yarda dakai) kuma babu wanda ya Isa ya rabamu, ba zan bada k’ofa ba…duk runsti duk wuya ba za mu karaya ba.Abunda ya faru jiya babban al’amari ne , amma na dad’e Ina neman tukuicin da zan k’ara maka na k’aunar da kake yi mini tsakaninka da Allah ban samu ba.. Ya Yash a matsayina na matarka Ina so ka saka a ranka kamar babu abunda ya faru tsakaninka da Kausar, ka goge hakan a kwakwalwarka nima na goge!ina so mu manta da duk wani takaici da bak’in ciki na daren jiya….indai saboda ni ne kake damuwa da fargabar mai zan yi tunani ko mai zan ce a kan case d’in, to inaso ka san cewa Manubiya ta goge komai ba ta rik’e a rai ba, bata saka a gaba ba dan babu komai a gabanta sai burin farantawa mijinta, dan haka ka cire damuwa, ka cire bak’in ciki mu ci gaba da rayuwar mu cikin farin ciki…inshaaAllah da ni da kai har abada ba za a ji kanmu ba.” Kuka sosai Yash ya ke yi ya k’ank’ameta a jikinsa yana godewa Ubangiji da ya basa mar’atussaliha….ya ma rasa bakin magana, in banda sake ruk’umk’umeta babu abunda ya ke yi yana ji kamar ya maida ita cikin cikinsa. Shiruu Mommy ta yi, har sai da Ya’isha tace”hmmm..mu shiga Mommy, za ta ci ubanta ne!.” Tukunna suka d’an gyara daga tsayuwar lab’en da suka yi suka fara knocking. Gaba d’aya Mommy kanta ya d’au zafi, tabbas Manubiya fa sai sun sake tsayuwa a kanta sun k’ara k’arfi fiye da tunani, dan shakka babu Yarinyar nan ta wuce tunanin su gashi shegen naci gareta…ita da ta zo ta d’anyi b’arin zance akan case d’in a samu ta ji ta yadda za ta d’aga hankali har sai ta ji komai daga nan su yi baram baram da Yashjub ɗin ta tafi, sai gashi an samu wani d’an albarka ya tura mata message ma gaba d’aya, amma dukda hakan ji abunda take cewa!..tana da tabbacin Kausar ce ta turo message d’in! tabbas dama tundaga jiya ta fahimci akwai abunda Kausar take shiryawa….ta d’an ji zafin yadda ta tsame su daga duk wani shirinta! ta fara yin gaban kanta ita kad’ai, amma kuma da wata wainar gara wata!da Manubiya gara ta bi bayan Kausar sau million ma, dan haka a nan (bayan kausar) za ta tsaya!….. A yadda ta ji furucin Manu na yanzu ta riga ta gama yanke shawarar abunda za ta yi….ba dare ba rana ita da Baba larai za su duk’ufa daga yau! Wallahi indai ta haifu cikin uwarta da ubanta sai ta juyawa Daddy lissafi ya aurawa Kausar Yashjub, daga nan sai ta ga k’arshen soyayya!!! sai ta ga k’arshen naci!!! za ta ga yadda Manu za ta yi idan Yash ya k’ara aure, za ta ga k’arshen maratussalaha da Manubiya ta ke playing…. Yadda yashjub ya karb’esu ita da Ya’isha sai da suka sha jinin jikinsu…ga Daddy ya juya musu baya yanzu kuma Yashjub! tabbas Manubiya ta tabbata mugun tsuro a cikin family d’insu, amma ba komai inshaaAllah komai ya kusan zuwa k’arshe. An riga an yi abunda suka zo yi, shiyasa kawai suka yi musu sallama suka fito jiki duk ba kwari…..ba kad’an ba yadda Yash ya yi musu abun ya tab’asu, Mommy ta d’an tsorata akan kar fa kwab’arta ta yi ruwa, dan muddin Yash da Daddy suka zargesu suka juya musu baya suka fara gano su to fa akwai Babbar matsala, dan haka dole ta tashi ta tsaya tun wuri ta gyara abunda ya fara lalacewa a tsakaninta da su Yashjub….. A samu Yashjub ya auri Kausar Manubiya kuma ta kama gabanta….. Gashi ta nemi fad’a kacha kacha da Daddy amma ba komai za ta gyara inshaaAllah…. Bayan sati biyu…. Babban abunda ya fi d’agawa Ummi har ma da su Yahanasu hankali shine ‘guduwar da Munirat ta yyi’…haka kurum kwanaki tara da suka wuce ta rubuta wasik’a akan ‘kar a nemeta ta tafi ba za ta dawo ba’ har yau babu inda ba a duba ba babu Munirat babu mai kama da ita,Ummi sai da ta yi sati d’aya a asibiti tukunna aka sallamota tsabar masifa…su Yasira kuwa an samu abunda ake so k’iri k’iri a gabanta suke yi mata dariyar mugunta suke cewa karuwanci Munirat ɗin ta tafi… Mommy ta so su shirya da Daddy, amma abunda ya yi mata sai da ya sakata a al’ajabi! Dan korar kare ya yi mata a lokacin da ta je d’akinsa neman shirin, kuma har yau ko kallo ba ya shiga tsakaninsu, in kuwa ya kalleta to harara ce! Ko abinci ya daina ci a dining d’in k’asa duk dan saboda ita. Wannan al’amari ba k’aramin d’aga mata hankali ya yi ba, har y’ar rama sai da ta yi. Gashi Yash da Manu suma shiruu ba a jin kansu, su da suka zubar da cikin suka k’ulla sharri saboda ya koreta amma sai take gani kamar hakan ma sake had’a kansu waje guda ya yi!..su Yasira kuwa ana sallamar ta a asibiti Hajiya Mama ta ce su dawo gidan Ubansu, shiyasa gaba d’aya mommy ta sake burkicewa, gashi ta ga hajiya mama ba ta da ranar tafiya, dan da farko sunyi tunanin rako Junior ta yi za ta d’anyi sati d’aya daga nan ta koma… Kwanciyar Hankalinta d’aya zuwa biyu a yanzu, na farko ta riga ta san Manu babu ita babu haihuwa, sannan al’amarin Kausar da Yashjub akwai haske dan aiki tuk’uru suke yi babu dare babu rana, dukda kuwa ita da Kausar d’in ba su fahimci juna ba har yanzu..saboda Mommyn ta yi tambayar duniya amma kullum amsa d’aya Kausar d’in take Bata itace”Yashjub raping ɗinta ya yi(fyaɗe ya yi mata)”tsabar ta rainawa Mommyn hankali, shiyasa ita kuma mommyn ta rabu da ita ta d’au fushi da ita, ko taimakon ma da suke yi mata har gobe ba ta sani ba. Su Yasira ma sun d’an ji haushin abunda Kausar ta yiwa Yashjub, gashi suma da suka tambayeta amsa d’aya ta basu irin wadda ta bawa Mommy shiyasa suka daina kulata suka yi fushi da ita…ita kam ko a jikinta, dan idanunta sun rufe, ba ta damu da kowa da komai ba! babban burin ta a halin da ake ciki shine ta ga ta auri Yash, daganan kowa ya yi ta kansa. Abhi ma ya zo, dan Daddy da kansa ya kirasa da ya ji labarin yana Niger sun je wani aiki, shine ya kirasa yace ‘dan Allah idan sun gama ya biyo Nigeria’ saboda kwana biyu gaba d’aya Daddyn a hargitse yake, ya rasa me yake yi masa dad’i, kansa ya d’au zafi..shiyasa ya hana Hajiya Mama ma tafiya, yake kuma buk’atar Abhi d’in shima a kusa da shi. Junior da Yadira ma an saka musu rana, nan da wata uku. su Siyama ma jiya aka je aka yi tambaya aka bayar, kuma an saka har ranar auren wata uku suma…… Ko da Junior ya tunkari Yassir game da zancen Yash…tashi d’aya Yassir ya faiyyace masa komai, bai b’oye ba! saboda ya san ya riga ya fahimta. Cikin tsananin b’acin rai Junior ya hau zaginsa, sannan yace ‘bai taɓa zaton zai iya yiwa Yashjub haka ba, kuma yana gargaɗinsa da ya yi sauri ya gyara kuskurensa ko kuma ya tona masa asiri wallahi.! …..A lokacin da suke makaranta akwai wani video da Yassir d’in ya tab’a yiwa Junior shi da wata Yarinyar da yake ta so itakuma Yarinyar ta k’i sauraronsa…sai da suka bata abu ta sha ta bugu tukunna aka yi video d’in na rashin ɗa’a! abun ba mutunci dai babu kyan gani…..y’ar Nigeria ce, y’ar manyan mutane, gidansu babban gida shiyasa a wannan lokacin suka dinga amfani da video ɗin suna tsoratata da tirsasa mata wajen yin duk abunda suka buƙata daga gareta..ko me suka ce suna so ta yi musu sai ta yi, idan suka kirata dole ta je..ba kalar tujarar da Yarinyar nan ba ta gani daga garesu ba har aka samu ta gama makarantar ta kama gabanta ba tare da sun saki video d’inba..a wannan lokacin an yi ne akan za a yanke fuskar junior da jikinsa a saki video d’in ita kad’ai.To yanzu kuma Yassir ya tabbatarwa Junior muddin ya faɗawa Yash ko wani a gidan abunda ya ke iƙirarin zai faɗa ɗin to wallahi fuska da jikin duka su biyun zai bari ya saki video d’in, kuma ya nunawa kowa har su Daddy da Yadira, daganan sai ya ga ta yadda zai auri Yadira.. Junior Bai ga alamun wasa a fuskar Yassir ba, kuma ya san tsaf zai Iya tunda har ya iya yin dakon video d’in har kawo yanxu saboda shi Junior ɗin ya san sun goge videon sam bai yi tunanin Yassir yana da shi har yanzu ba…. Sai da suka yi kacha -kacha a ranar, tukunna suka rabu baram baram. ba ma a b’angare d’aya suka kwana ba, dan Junior k’aura ya yi ya koma side d’in Yashjub inda Abhi yake. Tambayar duniya ya cewa Abhi ɗin ‘ba komai, yana son zama kusa da shi ne kawai’ dan haka ya rabu da shi ba dan ya yarda ba. .. Yassir ya fi kowa tashin hankali a cikin sati biyun da suka gabata, daɗin daɗawar da ya sa shi zage dantse ya yi wa junior wuta wuta ma kenan dan ya lura in ya barshi ya ƙara masa nashi shirmen akan abubuwan da su ke damunsa to tsaf zai iya yin hauka!! abubuwa sun taru ta ko’ina sun yi nasa yawa! ….Sam bai ga alamun fushi ko jin haushin Yashjub daga Daddy ba kamar yadda suka yi zato shi da Kausar, Sannan Yashjub da Manubiya shiru, kuma ya san ta ga message d’in da ya tura mata, amma ko jiya da ya tambayi spy d’insa na gidan ce masa ya yi ‘tana nan, Yash d’in ma ya daina fita aiki….’ wani irin kishinta yake yi idan ya tuno tana tare da shi gashi shi fa har ga Allah hak’urinsa ya k’are a kanta… ita kuma Hajiya mama da Daddy sun ce daga kansa har zuwa kan Yadira kowa ya zauna a gida, kar wanda ya je musu for now a barsu su huta. Gashi waenda aka kama akan batun lamarin case d’in estate, ya yi musu alk’awarin zai saka a sake su su gudu amma har yau abun ya gagara, dan waenda yake tunanin zai bada cin hanci su taimaka mutanen su gudu sun ce babu ruwansu case d’in a hannu manya yake… Su kuma Yaran waenda aka kama d’in sun ce “hak’urinsu ya k’are, dan haka sun bashi kwana d’aya tak! Ko ya yi wani Abun ko kuma wallahi za su kai sunansa da recording d’in wayoyin da aka dinga yi da shi har ma da wasu videos da bai tab’a sanin akwai su ba.. su tona masa asiri” saboda horo mai tsanani ake yiwa oganin nasu gashi an hana a gansu, yanzu haka ma suna tunanin an kashe d’aya ne…….. Kausar ma jikinta da sauk’i, ko da suka je asibiti cewa aka yi ba sai anyi wani plastic surgery ba, kawai magani aka dinga shafa mata, a jiya kuma da ciwon ya warke har ta fara shafa maganin scar saboda kar ta yi tabo a fuska. Yashjub ma ya tara gaba d’aya footage na cctv camera amma tsoro da fargabar cikar zarginsa sun hana shi dubawa.. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 36* Yau dai ya shirya akan zai daure ya duba.. Sannan zai daure ya je gida ya gaida su Daddy, yana kiransu kullum suna gaisawa, amma ba ya zuwa yau sati biyu kenan, dan tsantsar kunyarsu yake ji! A duk lokacin da ya tuna yadda suka gansa shi da Kausar sai ya ji kamar ya binne kansa,shiyasa sam ya gagara sake fuskantar su. Daɗin daɗawa ya na son ganin Kausar, ya fahimci ba ta mutu ba, dan bai ji ana zaman makoki ba dan haka yanada tambayoyin da yake buk’atar ta amsa masa…kafin ya san abunda zai yi mata na gaba,dan wallahi sai ta zab’i mutuwa a kan rayuwa… Tun bayan kwana biyu da faruwar al’amarin ya fahimci wani Abu da yake adduar Allah ya sa hakan ne ‘in banda coconut oil d’in da ya ji a jikinsa ya kuma gani a ranar da tace wani Abu ya shiga tsakaninsu bai ga komai a tare da shi ba, sannan da ya zauna ya yi lissafi time duration d’in ya yi ƙaranci, shiyasa kwakwalwarsa ta basa babu abunda ya shiga tsakaninsu! To amma a yadda take son shi me ya sa hakan ta kasance? me ye ribar ta idan ta bari aka kamasu kawai ba tare da wani abun ya shiga tsakaninsu ba??’ Ita kad’ai ce za ta iya amsa masa wannan tambayoyin nasa, kuma a yadda ta daku a hannunsa ya san ta d’an shiga saiti ta tsorata, shiyasa ya yanke shawarar ya tunkare ta akan batun.Idan ma wani abun take shiryawa tun wuri ya datse !,shi ya san yadda zai bi da ita ta fad’i masa komai cikin sauk’i. Hajiya Mama kuwa babu tambayar da ba ta yi ba amma aka k’i gaya mata asalin menene ya sami Kausar…Daddy ya lallab’a Ummi ta yi mata k’arya ba don ta so ba tace”daga bene ta fad’o” Abhi kawai Daddy ya gayawa wanda shima sai da Daddyn ya yi da na sanin gaya masa, dan cewa ya yi wallahi sai ta bar gidan a ranar, da kyar Daddy ya rik’esa ya gaya masa komai yadda suka yi da Hajiya Mama da kuma abunda itama Mommyn tace masa a ranar da case d’in ya faru.Ya san idan suka kori Kausar kamar yadda ta fad’a zata tona masa asiri, kuma ta kwashe gaba d’aya y’ay’an sai dai a yi gida biyu…sam abun ba zai yi kyau ba. Tunda Abhi ya ke bai tab’a jin tsanar Mommy da Kausar irin na ranar ba, don sai da ya yi kwana biyu tukunna ya d’an sauk’o…Shiyasa shima ya bayar da goyon baya aka b’oyewa Hajiya Mama saboda sun san idan ta sani babban tashin hankali zata kunnowa kowa! Ta d’agawa kowa hankali har ita kanta ba tare da anbi komai a hankali ba an gano Mommy an tona mata asiri ba. …. Sai da Yashjub ya tabbatar Manubiya ba ta buk’atar komai, ya kira mata Siyama ta zo tukunna ya ce bari ya je ya gaida su Daddy ta basa awa ɗaya yanzun zai dawo, inshaaAllah….. Dama tun a waya ya lura da yanayin Mommy kamar tana fushi ne da shi, Aikuwa yana zuwa ya tabbatar dan ganin sa a zahiri da tayi ya sanya ta kasa b’oye takaicin da haushinsan da take iya dannewa ta waya…da kyar suka gaisa daga haka ta mik’e ta fad’a d’akinta ta barsa shi da Baba larai. Shima d’in a wuya yake da ita, dan Wallahi da kyar ya danne zuciyarsa ma ya shigo side d’innata, ko ganinta ba ya son yi daga ita har Baba larai d’in tata, dama a gis gis suka gaisa tana shigewa shima ya mik’e ya fita ko sallama bai yiwa Baba larai d’in ba. Side d’in Daddy ya je, ya tarar dasu su biyar shi Yahansu, Ummi, Hajiya Mama da Abhi sunata hira ana raha gwanin ban shaawa. yana shiga shima suka ja sa da hira duk yadda yake jin kunya da nauyin Daddy Yahanasu da Ummi sai da ya d’an ware aka yi hirar da shi..kafin a shiga bawa Ummi kwarin guiwa aka d’an kwantar mata da hankali tare da jaddada mata suna nan suna bincike za a nemo Munirat inshaaAllah….. Ya jima sosai kafin ya mik’e yayi musu sallama ya tafi. Yana sauk’owa daga stairs d’in Daddy ya hango Kausar da Yassir suna hawowa saman (tsakiya) daga chan k’asa. Gefen fuskarta ta wajen idonta na dama har yanzu da y’ar guntuwar plasta ragowar ciwukan kuma sun fito rad’au!kasancewarta fara ya sa suka yi tambari ana hangota ake hangosu. Bai tab’a ganinta da Hijab ba sai yau! A take ya ji gaba d’aya ransa ya yi wani irin mugun b’aci, hankalansa ya tashi, Duniyarsa ta tsaya chak! Wani irin kallon tsana ya shiga binta da shi…magana take yiwa Yassir amma sai maganar tata ta tsaya sakamokon jikinta da ya bata kamar yana wajen ne….. Da sauri ta d’ago ta kalli direction d’in da ta ga kamar inuwar mutum. Sanye yake da kaftan Nude colour, da baƙar hula, d’inkin ya yi masifar yi masa kyau…ya d’an rame amman ya k’ara haske, hancinsa ya k’ara tsayi sannan sumar sa ta d’an k’aru both fuskarsa da kansa wanda hakan ya sake fito da ainihin kyawunsa da kuma ramar da yayi..so da k’aunar Yasjub a jininta da ruhinta yake! ba ta ji akwai wata y’a mace da take yiwa wani namiji kwatankwacin k’aunar da take yi wa Yashjub,babu ita a kaff fad’in duniyar nan!. kallonsa kawai take yi kamar wadda za ta had’iye shi ne, Yayinda shima yake jifanta da nasa kallon na tsantsar tsana da kyama..idanunta har ciccikowa suka yi tsabar tsantsar k’auna, a take ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere… Sai a sannan ne Yassir ya gansa tsaye. D’auke kai kawai yayi ya wuce gaba kafin yace mata “Muje” Ya fad’i hakan yana mai nufar side d’inta. Har ta d’an d’aga k’afa zatayi gaba ta ji Yashjub yace “Kausar!”. Gaban tane ya bada wani dumm!!da mugun k’arfi,shauk’i da tsoro suka yi mata k’awanya kafin jikinta ya d’auki karkarwa a take.! Kad’an ta d’an juya ta kalli saitin inda yake kawai ta ga ya nufota gadan-gadan!. Tabbas sun shirya komai itada Yassir kuma ya tafi yadda suka tsara..yadda ya kamata, amma sai yanzu ta san ta yi kuskure da ba su tanadi abunda za ta fad’awa Yash a irin wannan lokacin ba. Sannan ta san Yashjub yanada kwakwalwa, kuma ta san duk yadda ta yi k’ok’ari ta kawar da duk wani shakku dole akwai wani abu da zai d’an fahimta.Sam ba ta shiryawa wannan lokacin ba kawai ita idonta ya rufe, hankalinta ya fi karkata a kan ranar da abun ya faru..kawai ita kowa ya yarda akwai abunda ya faru tsankaninsu… Tana wannan tunanin ya k’araso daff da ita ya tsaya. Yassir ma ya d’an tsorata, dan ya lura da yanayin Yashjub d’in, da kuma kallon rashin yardar da ya ga yana yi wa Kausar tun d’azun…a hankali ya matso yace masa “Yash batada lafiya!daga asibiti muke, Doctor ya bata pain reliever, yace kuma ta huta sosai.” “Wuce ka tafi side d’inka!” Kawai ya ce, ba tare da ya kallesa ba. Cije labb’ansa na k’asa ya yi, yana jin wani tsananin takaici da tsanar Yash d’in tana ratsashi….Cikin d’aci yace”Doctor yace ta huta saboda dukan da ka yi mata ba na wasa bane, har yau bata gama warkewa ba….” Ya fad’i hakan yana ji kamar ya rufesa da duka, a duk lokacin da ya tuna dukan da Yash ya yi mata kuma daɗin daɗawa a lokacin da aka yi dukan har dacikinsa a jikin Kausar ɗin, sai ya ji kamar ya yi hauka!. D’agowa kawai Yash ya yi, ya zuba masa lumsasssun idanunsa waenda suka fara kad’awa sukayi ja kad’an. Yanayin kallon da ya ga yana yi masa ne yasa ya fahimci akwai matsala idan ya biye sa, saboda shima a zuciye yake kamar yadda shima yake a zuciye, dan haka ya san idan ya ci gaba da tsayuwa za a yi b’arna, dan haka kawai ya juya fuuu ya nufi k’asa yana ji kamar zuciyarsa za ta tarwatse. Kasa d’agowa tayi ta kalli Yash bayan wucewar Yassir…duk wani ƙarfin hali da tsaurin idonta yau sai ta nema ta rasa.Gaba d’aya ta rud’e ta rikice, har yanzu jikinta karkarwa yakeyi kad’an-kad’an. Ji yake kamar ya rufeta da wani sabon dukan, amman sai ya danne zuciyarsa..babu alamun wasa ko tantama, a hankali yace”Inaso inji gaskiyar komai daga Bakinki. Na farko ki gaya mini me kika bani na sha,na biyu inaso da Bakinki ki gaya mini cewar babu abunda ya faru tsakaninmu…Kausar kin san ni ba Yaro bane kuma da aurena dan haka na riga na fahimci komai… Amma ina so in ji daga gareki, Ina so da bakinki ki fad’a mini komai! kuma ki sani hakan shine zaman lafiyarki.” A kaff cikin maganganunsa, inda yake cewa”kuma inada aure”ya fi komai d’aga mata hankali da b’ata mata rai dan tashi ɗaya wani sabon kishinsa ya dirar mata. Wasu hawaye ya ga sun hau sintiri a kan farar fuskarta…. Ranta ya riga ya b’aci kishinsa ya fusatata shiyasa ta kai iya wuya ta k’ulu ta k’ule kuma ta riga ta fahimci tabbas fa idan ta bari ta yi laushi to kwab’arta za ta yi ruwa! Dan haka ta dake ta murzawa idanunta toka ta sake matsowa daff da shi tukunna ta fara magana”Yash!!Ina sonka! Ni kaina bansan yawa da adadin son da nake yi maka ba, amman ko da ace sonka zai kashe ni ba zan tab’a aikata abunda kake tunanin na aikata ba! Saboda na san ranka ba zai so ba, kuma ni a ko da yaushe farin cikin ka shine a saman komai na rayuwata. Tayaya kake tunanin zan so ka ji kunya?Tayaya kake tunanin zan so Mommy ta ganmu bayan na san idan hakan ta faru zan rasa yardarta ne… Tayaya kake tunanin zan fito a matsayin karuwa a idanunka bayan ni a ko da yaushe burina shine ‘in gyarru in shiryu’ ko Allah zai sa ka yarda da ni ka amince ka bani matsayin matarka! I’m honored and happy for that night, amman wallahi Yash ka yarda da ni ba haka na so ba! Babu yadda zan yi ne a wannan daren na yi ta ce maka a’a a’a! amma ba ka saurara mini ba, ni kaina na yi mamakin ka shiyasa nake tunanin watak’ilan a office asibiti ko wani gurin ne aka yi mixing drink d’inka ko aka shaka maka wani abun baka sani ba…. Dan wallahi tallahi nikam ban san komai ba, kuma ban yi maka komai ba.” Cikin katseta yace “Ni duk ba wannan na tambayeki ba! Akwai abunda ya faru tsakanin mu ko babu?? Iyakar abunda na ke so in sani kenan ko kuma ince in tabbatar daga bakin ki saboda tuni na riga na san komai.” Ya k’arashe maganar tashi cikin tsananin b’acin rai. Tabbas zuwa yanzu Kausar ta fahimci ta d’an fara yin galaba a kansa, kuma ta lura kamar bai fahimci komai ba kamar yadda yake ta ik’irari dan a maganganun da ya yi yanzu ya riga ya kwafsa, sannan kuma ta fahimci da ta yi maganar wannan rana ne ya fara burkicewa! dan haka tashi d’aya ta san abunyi.A hankali ta matso kamar za ta shige jikinsa wanda hakan ya sa ya d’an ja baya yana watsa mata wani irin kallo.. Itanma shi take kallo ido cikin ido tace”Yash you really don’t remember anything??…da gaske baka iya tuna komai??” Ba ta jira jin amsar shi ba tace”bari in tuna maka!” Wasu maganganu da bayanai ta fara yi masa na rashin d’a’a da tarbiyya!…a cewarta wai duk shi ne ya aikata hakan a gareta a wannan ranar… cikin tsananin tashin hankali ya sa Hannu da mugun sauri ya toshe mata Baki yana kallon cikin idanunta yace”ba ki da hankali,ba ki san nan hanyar wucewar Daddy ba ne??” Sai kuma ya cikata da sauri, ya ture ta, tashi d’aya ya nufi hanyar stairs d’in da zai sada shi da k’asa…har ya juyo zai sake yi mata magana sai kuma kawai ya sauk’a jikinsa yana wani irin karkarwa kansa yana mugun sarawa…”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ya shiga ambata…da ya sani da bai tunkari Kausar da wannan maganar ba, yana so ya sake sakawa zuciyarsa salama ta hanyar tabbatarwa kansa ba abunda ya faru tsakaninshi da ita amma maimakon hakan gashi ya tasowa kansa da tashin hankali..dan a kaff cikin maganganu da yanayin ta sam bai ga alamun rashin gaskiya ba. Gaba d’aya hankalinsa ya tashi, ya sake duburcewa dan d’an guntun hope d’in dayake dashi yanzu kam ya rasa shi, saboda ya gama tabbatarwa gaskiya Kausar take fad’i…shiysa ya zab’i zai rungumi wannan mummunar k’addarar ya yi k’ok’ari ya cinye jarabawarsa kawai, ba zai sake saka hope ko bincike ba…… Yana sauk’a da niyyar tafiya gida aka fara kiran sallah, dan haka ya nufi masallaci…tare suka yi sallar da su Daddy waenda ana idarwa suka tilasta masa ya bisu domin su yi lunch tare. Daddy ya daina cin abinci a k’asa saboda Mommy, dan haka suna shiga suka wuce sama su uku, yayinda dinning area na k’asan ya cika da kowa da kowa saboda Ummi ma zuwa yanzu ta d’an ware da taimakon hope da kwantar da hankalin da Hajiya mama suke ta bata, shiyasa take d’an shiga mutane har da ita ake cin abinci. … Ko da Yashjub ya wuce ya bar Kausar, ciki ta shiga ta wuce bedroom ta fad’a bathroom domin ta watsa ruwa, tana mai jin wani sanyi da farin ciki kamar an yi mata bushara da gidan aljannah…plan A ya kammalu ba tare da wata matsala ba, yanzu saura plan B!tunda an yi sati biyu to ciki zai iya baiyyana kenan, gashi shima Yash d’in ya fara zuwa gida dama tanaso ayi komai a gaban sa ne, dan haka ta shirya akan gobe inshaaAllah dai dai lokacin da ta san yana zuwa za ta yi abunda ta shirya… Tana wannan tunanin tana jin wani tsantsar farinciki hakanan ta kammala wankan ta ta fito d’aure da towel… Sai da gabanta ya yanke ya fad’i da ta ga Yassir zaune a kan gado, idanunsa da fuskarsa sun yi jazur!!! Ya tsoratata sannan yanayin sa ma ya tsoratata matuk’a..kamar mai jin tsoro haka nan ta k’arasa a hankali ta nemi guri ta zauna a gefensa tace”me ya faru?” Ta yi masa tambayar a d’arare… Sai da ya d’auki sama da minti d’aya tukunna ya juya ya zuba mata manyan idanunsa waenda suka yi jaaa yace”Kausar change of plans(shiri ya sauya)..ba za mu tsaya har ki haihu kafin Yashjub ya mutu ba, ya zamo dole ya mutu a yau!yanzu.” Gabanta ne ya yanke ya fad’i, hankalinta ya yi masifar tashi, tashi d’aya yawun bakinta ya k’afe…da mugun kyar ta samu ta ce”me ya faru?” Cikin tashin hankali shima yace”kawai a matsayinki na partner ɗita a komai da komai ne ya sa na ga ya kamata in gaya miki ki sani! Ki bari zan yi miki bayani, amma ba yanzu ba, sai in komai ya kammalu. dan a yanzu ba zan iya ba Kausar, Ina cikin masifa, ba zan iya dogon bayani ba.” Ya fad’i hakan yana mai mik’ewa da shirin fita,da sauri itama ta mik’e ta sha gabansa ta tsaya cikin nemo kalamai da mugun kyar..ta samu ta haɗa tace”Yassir, kar ka yi abunda za ka tona mana asiri ka lalata komai, ka tsaya ka nutsu ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi, ka fad’a mini me ya faru, mu samu mu san abunyi….dan Allah dan annabi.” Ta k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka. Saida ya runtse fuskarsa cikin tafukan Hannayensa, ya murtsuka ya fesar da wani zazzafan huci!!! Tukunna yace”Yaran Grenade sun turawa Yashjub message… yanzunnan nima suka turo mini shaidar sun tura masa ɗin.. Na gani kuma na tabbatar da sun tura masa videos kala kala har da wanda nake kulla yarjejeniya da su, da wanda nake basu kud’i!! Da ragowar maganganu na da su! da muryata da komai ma duk sun tura masa ta watsapp Kausar! komai da kika sani duk wata shaida da za ta nuna nine duk sun tura. A yanzu dai na san bai riga ya gani ba, dan na duba na ga baya online….. Kausar kar ki ce mini a’a, ko kuma ki ce za ki kawo wata mafita ko shawarar, dan ya zama dole Yashjub ya mutu kafin ya ga sak’onnin nan ya bankad’a komai ya saka a kashe ni! Kisan wulak’anci, cikin rashin gata.” Karkarwa jikin Kausar ya d’auka…..ganin yana shirin fita yasa ta sake tare hanya tace”Yassir kar ka je garin kashe sa a kamaka!” Wannan karon cikin tsananin b’acin rai yace”wai ba kya fahimtata ne???duk bayanin da na yi miki ba kya ji na ne?? An riga an tura masa ko na yi yunk’urin kashe sa ko ban yi yunk’urin kashe sa ba zai ga komai kuma idan ya gani aka kamani to kashe ni za a yi! Dan haka gara in yi yunk’urin da fatan samun nasara a samu ya mutu, akan in zauna ban yi komai ba ni in mutu!” Jikinta yana wani irin karkarwa tace”Yassir idan kuma suka turawa Daddy fa?shima binsa za ka yi ka kashe sa?ina ji maka tsoro kar ka je garin hanzari tsoro da fargaba kwab’armu ta yi ruwa! Ka duba fa ka ga yadda kwata kwata plan d’inmu bai yi aiki a kan Daddy ba, dan sam bai ji haushin Yashjub ba, sannan ba mu riga mun ce cikin nan nasa bane ba ya ji ya sani! Akwai abubuwa da yawa a gabanmu da ya kamata mu yi, kar ka lalata komai ka saka mana fullstop, dan idan aka kamaka komai ya zo k’arshe…misali yanzu ka je garin sauri a kamaka me kake tunani?,komai fa ya lalace mana kenan! amma idan muka nustu muka yi tunani za mu samu maf…” Cikin tarar numfashinta yace”idan na tunkaresa ba a kama ni ba kuma fa?sannan idan muka yi slow aka kama ni?” “Yassir a irin wannan situation d’in mutum have to assume the worst!!! saboda Ana so ka shirya kare kanka ka shirya mafita ka san abun yi idan komai ya rincab’e,ba fa a abu sama ta ka!”. Abun nan da ya faru ni a wajena da tunanina gyarasa abune mai sauƙi!! kar ka rikita kanka ta kwab’a komai ka lalata komai..a ganina dan sun tura masa tsaff za su iya gogewa tunda watsapp ne..Yassir kud’i fa aka basu suka karb’a suka yi maka aiki tun a karon farko! Iyakar abunda za ka yi yanzu shine ka k’ara musu kud’i, wallahi in ka ƙara musu ɗin ni na san tashi d’aya za su manta da wani Grenade su bi ta watsapp d’in su goge, tunda kace ba ya online, ni kuma daga nan har zuwa dare ba zan bashi kwanciyar hankalin da zai hau watsapp d’in ba ma!. Ai yana cikin gidan nan har yanzu, dan yanzu ma ta window Ina wanka sai da na hango motarsa a fake dam haka bai tafi ba har yanzu..so kawai ka jira ka zuba mini ido ka ga yadda zan yi da shi.. Sannan ka nutsu dan Allah!!kashe mutum yana da buk’atar plan da shiri,ko kaza za a yanka sai an wasa wuk’a an tanadi ruwa ballantana mutum d’an adam! Ba ka da plan, ba ka da komai, tashi d’aya kace za ka kashesa a rana d’aya!! wallahi ba ni da tantama hakan ba mai yiwuwa ba ne ba, kuma sai an kamaka!kwanakin baya da ka yi yunk’urin hakan da tsararren plans har biyu ya mutu???sai yanzu a cikin rana d’aya ne kake son miracle ya (mu’ujiza ta) faru?”. Shiruu Yassir yayi, yana mai fitar da huci kafin chan ya rungumeta cikin huci yace”I love you Kausar, na gode da kika wayar mini da kai,tabbas maganar ki gaskiyace…amma duk abunda kike shiryawa ki yi da wurwuri, saboda inaga masallaci kawai ya tafi daga nan zai wuce…” “Okay bari in saka kayana” Kawai tace, daga haka ta nufi closet d’inta ta zaro doguwar riga ta saka ta zare towel d’in ko undies da mai bata buk’ata ba haka nan ta wuce drawer ta d’auko turaren da tunda cikin ya shigeta ta tsani warinsa ta fesa a tafin Hannunta ta runtse da sauri dan tashi d’aya ta ji amai ya taho mata…Tana fara shiri Yassir ma ya fara waya da mutanen, ta san ba shi da enough kud’i yanzu shiyasa k’asa k’asa tace masa”ko nawa suka ce ya yarda za ta cika masa” Daga haka ta saka Kai ta fice daga d’akin, tana jin mugun mugun haushinsa,a ko da yaushe idan ya yi yunk’urin kashe Yashjub ji take kamar ta kashe sa!. Addu’ar ta d’aya Allah ya sa mutanen su yarda kar su basu matsala! ita kuma ko nawa suka ce za ta bayar, ba ta so wani matsala ya taso ta koina kafin a yi aurenta da Yash. Tana sauk’a ta tarar da su gaba d’aya suna cin abinci, har da junior Wanda ya zamewa Yadira cingum, itanma kuma ba laifi ya siye zuciyarta zuwa yanzu, musamman ma da ta fahimci yanzu ya shiryu ba kamar da ba, gashi shi aka zab’a mata dan haka aka bata shawara kuma itama ta yarda ta amshe sa hannu bibbiyu. Sosai Kausar ta ji dad’in ganin kowa a ranta tace”perfect!”. Ba ta ko kalli kowa ba, hakanan ta wuce ta nufi kitchen babu wanda ta gaisar har Hajiya Mama, shiyasa ita kuma Hajiya maman cikin fushi tace “tunda kitchen d’in ba na Ubanki bane ba, ki dawo ki zo ki gaida mutane, kafin ki shige”. Wani sassanyan murmushi Kausar ta yi, dama hakan ta ke so ta faru, dan haka kawai ta shige cikin kitchen d’in ba tare da ta ko juyo ba!..kuma kowa ya san sarai ta ji! dan lokacin da Hajiya Maman ma ta fara magana sai da Kausar ɗin ta ja ta tsaya, tana dasa aya kuma Kausar ta ci gaba da tafiya ta shige cikin kitchen d’in. Hatta su Mommy sai da suka sha tsananin mamaki, Hajiya Mama kuwa dire cokalinta ta yi da k’arfi ta mik’e tsaye ta kalli Junior tace”finciko mini Yarinyar chan, ka kawo ta nan, right away!!.” Mik’ewa ya yi ya nufi kitchen d’in ransa shima a b’ace saboda da ma a wuya yake da su ita da Yassir, ga kuma rashin kunyar da ta yi wa Hajiya mama shiyasa yana shiga ya fincikota kamar yadda Hajiya Maman ta buk’ata, da ita da plate d’in hannunta ya fito da ita, sai da ya kawota gaban Hajiya Mama tukunna ya cika mata hannu ta hanyar yin cilli da shi….juyawa ta yi ta shiga zabga masa wata uwar harara yayinda shima yake jifanta da wani irin kallo. Cikin b’acin rai Hajiya Mama tace”ai ni za ki harara ba shi ba..jinin marasa kunya da tarbiyya kawai!! Idan ana gaya muku gaskiya ana cewa ku yi abunda k’uda zai bi ku ƙi yi, yanzu ai ga irinta nan kin fara gani tun a duniya! yaadda fuskarki ta koma izina ce a gare ki, kamata ya yi ace kin fara gyara Hali da ke da iyayen naki.” Shiruu duk aka yi itama Kausar d’in ba ta ce komai ba, kuma ba ta bar kallon Junior wanda shima itan yake kallo ba! Da kyar Mommy ta rarrashi kanta ta danne zuciyarta tace”Hajiya mama ki yi h…” Cikin tsananin b’acin rai da takaici tace “kin san Allah Khadija zan baki kyakkyawan mari wallahi tallahi!!wannan kissar taki ba ta samu guri a cikin kaina ba tun wuri ki daina, idan za ki fito mini a Khadijar ki to ki fito, idan kuma ba za ki fito ba wallahi kin ji na rantse kika sake tsomo mini Baki a cikin issues d’ina sai na make ki!,bak’ar ashana kawai.” Mik’ewa Ya’isha ta yi kamar za ta tashi sama ta wuce sama ranta a mugun b’ace…cikin takaici Hajiya mama tace”an ce da Uwarta bak’ar ashana ta ji haushi bayan gaskiya aka fad’a tunda kalli attitude d’in da bak’ar ashanar ta koyar da ita,nni fa uwar ubanta ce amma kalli abunda ta yi mini…..” Shiruu duk akayi kowa ya yi tsit dan haka Hajiya Mama ta juya ga Kausar tace”zaki gaida mutane ko na saka Junior ya koya miki ladabi yanzunnan?? Ke har kin isa ki bawa mutane wannan attitude d’in? kin hana jamaa sukuni kin yi kane kane a gidan mutum amma dukda haka saboda ke d’in ba y’ar halak bace ba shine za ki fara wannan sabon halin? A baki ci a baki sha Allah na tuba in ba dan mu d’in ba ai da sai dai ki shiga duniya inda kika fito…” Cikin katseta sannan kamar irin kin isheni d’in nan ta juyo ta kalleta ido cikin ido tace”Hajiya Mama Ina wuni” Da k’arfi….. Mik’ewa tsaye Ummi ta yi Hajiya mama ma ta yunk’ura amma kafin su yi wani abun tuni Junior ya d’auke ta da mari!” “Allah ya yi maka albarka imam!” Hajiya mama ta fad’a kafin ta sake kallon Kausar tace”Shegiyar Yarinyar da ba ta san wa yayi mata gata ba!”. Difff!!! Haka kowa yayi tsit. Ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e kafin ta ce”Hajiya Mama ki yi hak’uri, ki bar ta da halinta, ba ta chanchanci lokacinki ba” Wani kallo Kausar ta watsawa Ummi wanda hakan yasa Ummin itama ta kafeta da ido kafin tace” Ko za ki dakeni ne Kausar?? Shin kin chanchanci lokacin nata ne?” Yassira ce ta matso tace”dakata Ummi ba ma son shishshigi,Allah mun gode maka kaff cikin mu babu wadda ta tab’a guduwa yawon karuwanci…wannan al’amarin famiy kaɗai ya shafa, dan haka ki ja bakinkki ki yi shiru ki bar Hajiya mama ita za mu iya d’aga mata k’afa…. Kausar is our sister, ba za mu zuba miki ido ki taka ta haka ba.” Yasira ta kora mata warning ta na huci,kasancewar sun d’an samu saɓani da Kausar ba shi zai sa ta tsaya ta zuba ido a wulak’antata ba. Wani wawan Mari Hajiya mama ta yarfawa Yassira cikin fushi tace”na san uwarki bata baki tarbiyya ba amma ban yi tunanin kin zubar da wadda imam ya baki ba…” Sai kuma ta juya ta kalli Ummi tace “Ai dama na sani wallahi muddin shegiyar y’ar nan tana cikin gidan nan tou babu batun tarbiyya….” A hankali a hankali Kausar take shak’ar turaren hannunta ba tare da kowa ya lura ba amma kuma amai ya k’i zuwa..gashi tana gani kamar har taron ya kusan watsewa. Dai dai nan Yassir wanda sauk’owarsa kenan ya k’araso wajen da hanzari ganinsu carko carko, ya kalli Yassira wadda har yanzu take dafe da k’unci tana kallon Hajiya mama yace “Me ya faru?” Cikin fushi tace”ka tambayeta! Na tabbata ko mai zan ce maka cewa za ta yi ba dai dai bane ba,ka san a ko da yaushe itace mai gaskiya.” Tana gama fad’in haka ta juya fuuu ta haye sama. Kasa ma magana Hajiya mama ta yi tsabar mamaki da al’ajabi kawai ta tsaya sake da Baki. Sai kuma ta juya kan Kausar a fusace tace”Wallahi b’oyayyen Ubanki ma bai Isa shiga tsakani na nida jikokina ba! Imam ja mini ita ka fitar a cikin gidan nan It’s an order…” Dasauri Yassir ya shiga tsakanin Imam da Kausar yace”Hold on!” Cikin fushi, kafin ya kalli Hajiya mama yace”Nobody is throwing nobody out! (Babu wanda zai kori wani a cikin gidan nan). Hajiya mama abunda kike yi fa ya yi yawa…tare kika ga mun taso da Kausar tun Yarinta har kawo yanzu, dan haka zai fiye miki idan ki ka bar ik’irarin korar ta a cikin gidan nan, dan za ki janyowa kanki matsala ne!” Ya fad’i hakan yana me kafeta da manyan idanuwansa da suke nuna tabbacin gaskiyar maganar da ya gama fad’a. Cikin tsananin fushi Hajiya mama tace “Ok!!!..bari in kira ubanka! wanda na Haifa shi kuma ya haifeka, daga nan sai inga shi wa zai zab’a Ni ko Kausar. Dan yau ko ni ko ita a cikin gidan nan.” Tana gama fad’in haka ta Cewa Yahansu ‘ta bata wayarta.’ Cikin nustuwa Yahanasu ta d’auki wayar ta mik’a mata, a ranta tana adduar ‘Allah Ubangiji ya sa a kori Kausar yau!’ Tun ranar da ta shiryawa Yash wannan tarkon ta gama cire duk wani hope na shiryuwa a kan Kausar. Da wannan tunanin ta mik’awa Hajiya mana wayar tata, ita kuma ta karb’a ta gyara zaman gilashin idanunta ta lalumo number Daddy ta danna call, sannan ta d’ago ta kallesu tace”Yassir da Yassira sun janyo mata yau, sai ta tafi.” Dai dai nan Daddy ya amsa kiran cikin bada order tace”ka zo kai da d’an uwanka har da Yashjub duk Ina buk’atar ganinku a k’asa yanzu.” Daga haka ta kashe wayar. Tana kashewa su Yasmeen Yadira da Yusra suka matso suka yanyameta suna rarrashinta amman fur ta k’i sauraron kowa ta nace ta kafe Itafa Kausar yau sai ta bar gidan d’anta. Gashi sai tujara take zubawa Kausar d’in harma da Mommy da Baba larai, shiyasa cikin fushi Kausar ta matso tace”na ji ya Isa haka zan fita zan tafi,tujarar ta Isa haka.” Ta k’arashe maganar cikin tsawa! Zaro ido Hajiya mama ta yi batasan lokacin da ta yi kan Kausar ta kifa mata marin da ya sa ta tafi za ta fad’i ba Da sauri cikin fushi Yassir ya yi kanta amma bai yi nasarar rik’eta ba dan sai da ta fad’i kuma fad’uwar ma ruf da ciki shiyasa tsabar takaici b’acin rai da firgicin ganin yadda Kausar d’in ta fad’i a kan cikinta bai san lokacin da ya d’aga hannu zai kifawa Hajiya mama mari ba!. Da mugun sauri Junior ya rik’e sa cikin tsananin b’acin rai yace”baka da hankali!!! Seriously? Marinta za ka yi?” Dunk’ule hannu Yassir ya yi jajayen idanunsa cikin na Hajiya mama wadda ta shiga tsananin tashin hankali ba na wasa ba. Da style Kausar ta sake saka hannunta a karo na biyar a kan Hancinta, ta shak’i turaren da tun d’azu yake ta taso mata da amai yak’i fitowa, aikuwa tashi d’aya wannan karon ya taho gadan gadan ta shiga shek’awa ba na wasa ba, dan sai da ta zauna a wajen tsabar yadda ya taho da k’arfi. Gaba d’ayan su kanta suka yi kowa hankali a tashe! Har ta gama babu wanda ya iya cewa uffan! A hankali Yassir ya durk’usa ya ce”taso mu je sama sannu” K’asa k’asa yadda babu wanda ya Isa ya ji tace”Yassir ka daina haka mana,kar ka lalata komai.” Shiruuu yayi,ya d’anyi nazari, kafin ya mik’e tsaye ya kalleta ya kalli aman ya yi shiruuu kawai. Ahankali Yassira ta matso tace “Dama ba ki da lafiya??” Ta yi mata tambayar tana yi mata wani irin kallon k’urilla wanda duk sai yanzu suka lura da yadda Kausar d’in ta sake kod’ewa ta yi ɗauuuu!!. Da kyar ta iya cewa”lafiya ta k’alau..haka kurum nima na ji aman ya taho mini!” Wataƙila na ci wani abun ne mara dad’i, shine ya b’ata mini ciki.” “Eh kam tabbas…ya b’ata miki ciki indeed!” Hajiya mama tace, kafin ta kalli Junior tace “Hurry!maza d’auko kit d’inka ka zo yanzunnan.” Sai kuma ta kalli Kausar tace”wallahi ba ki isa kwashe albarkar gidan d’ana a karo na biyu ba!” Da hanzari Mommy ta matso a d’an rikice tace”Hajiya mama kar ki damu! Kince ta fita shikenan za ta fita ba sai su Daddy sun shiga an yi ta case ba. InshaaAllah zan siya mata gida, zan san yadda zan yi da yardar Allah. Muje Kausar.” Ta fad’i hakan tana mai kama hannun Kausar. “Ka ji makira ko!!! Wato kin riga kin san da batun cikin shiyasa za ki janyeta ku tafi ko? Tou na chanja shawara! Za ta tafi amma sai an aunata an tabbatar yadda zan fi samun hujja akanta… na tabbatar shi kansa wannan Yaron bai san da cikin da dalilinshiba duba da yanayin yadda ya shiga shock tashi d’aya.” Yasmeen ce ta matso tace “Bara muje in aunata sai a kawo miki result d’in.” Cikin fushi Hajiya mama tace “Daga kan Khadijah zuwa kan ya’yan da ta Haifa da Larai duk wanda ya sake mini magana kafin Junior ya d’auko Abu ya gwada Kausar sai ranshi ya yi mugun mugun b’aci wallahi! Kun d’auke ni wawiya ko? A tunanin ku zan yarda da ku ne a kan batun wannan ƴar?. Yau sai asirinta ya sake tonuwa, kowa sai ya fahimta kuma ya gasgata shegen cikin da ta sake kwasowa a karo na ba adadi!! Karya kawai!!! kuma kar inga kowa ya bar nan har sai an gama komai Junior wuce nace ka je ka d’auko kit ka dawo yanzun nan!!.” Ta fadi hakan cikin dakawa Junior tsawa. Juyawa ya yi ya fice a take. Junior bai dawo ba, suna tsaye su duka su Daddy suka sauk’o, dan sai da suka tsaya suka d’an yi magana game da kiran da Hajiya Mama ta yi tukunna suka sauk’o. Basuyi mamakin ganin gaba daya y’an gidan a k’asan a tsaye cirko cirko ba!saboda dama tunda Hajiya mama ta kirasu sunsan case ne. K’arni da wari ne ya daki hancinansu wanda hakan ya sa suka fara waiwaye..ba abunda Yashjub ya tsana irin amai shiyasa idanunsa suna kaiwa kan aman ya fara kwala kiran mai aikinsu..Tana chan ciki shiyasa sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna suka fito tare itada gwaggwo. Aman ya nuna musu sai a sannan tukunna hankalinsa ya kai kan Kausar wadda ke tsugunne a wajajen ita da Yassira tana hawaye. Gabansa ne ya ji yayi wani irin mahaukacin bugawa..Adduarsa d’aya Allah ya sa ba Kausar bace ta yi wannan aman! Ba ya buk’atar Kausar ta yi koda ciwon Kai ne bayan abunda ya faru tsakanin su!.. Dama yayi tunanin hakan tun a ranar amma gudun janyowa Kai tashin hankali da masifa ne yasa kawai ya banzatar da tunanin ya kawar da shi ta k’arfi da yaji. Yana wannan tunanin k’irjinsa yana wani irin bugawa Junior ya shigo rik’e da first aid box. Ahankali Daddy da Abhi suka k’arasa inda suke,suna shirin yiwa Hajiya mama magana tace”Na kiraku saboda wani case daban, amma yanzu bari mu fara yin wanda yake a gabanmu emergency!!!……Y’ar ruk’on gidanka! Ciki ne da ita a karo na na tabbatar ita kanta ba ta san adadin ba. Su Khadijah na san watak’il duk sun san da zaman cikin dan ana cewa a yi mata test suka gigice. Wai har ni suka fara k’ok’arin yi wa wayo tsabar raini. Anyways Junior!!” Ta fad’i hakan tana kallonsa kafin ta d’aura da cewa” Ga first aid box! Ga kausar!! Ga ciki!!! Ga jini a jikinta da za a d’auka a gwada. Banaso inji kowa yace Uffan!! har sai an gama test d’innan. Tunda Yashjub yake a rayuwarsa bai tab’a jin mutum yana tsaye kyam amma ji da ganinsa sun d’auke ba lokacin guda tsabar fargaba sai yau!…da kyar ya samu ya fara gani amman fa dukda haka dishi dishi ya ke ganin.! Shi da kansa ya yiwa Kausar iyakar fita k’asar waje anyhow lokacin da ya dawo! har passport d’inta ya kwace, da kyar aka samu ya bata.. Gashi ta nuna kuma tace bata son Yassir, dukda ya fahimci kamar ba su rabu duka ba amma ya san ba za ta kula shi ba, bayaga haka ma in ba ma ta dalilin ciwon nan ba ya san ba sa fita tare, shi da kansa ya tabbatar da hakan kuma ba ta zuwa side d’insa…. sannan ko su suka kawo Iskanci duniya ya san ba za su yadda su yi wani abun anan sama inda d’akinta yake daff da na su Mommy sannan a tsakiyar su Yadira ba….. Durk’usawa Junior ya yi! Abunka da consultant.. Idanuwanta, tafin hannnunta da bayan kunnenta sai k’eyarta kawai ya duba ya tabbatar da tana d’auke da ciki. Sai yanzu ya fahimci komai tun daga kan abunda ya faru 2 weeks ago zuwa message d’in da Yassir ya yi masa yanzun daga fitarsa kafin ya shigo.. a tak’aice dai Yassir ya dirk’a mata ciki kuma suna so su ce na Yashjub ne tunda A message d’in Yassir cewa ya yi ya ce cikin 2 weeks ne exact!. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Junior ya shiga ambata a cikin ransa, saboda ya san tsaf Yassir zai yi abunda yace masa zai yi a cikin message d’in muddin ya k’i bin umarnin sa, shi kuma ba ya so a had’a Kai da shi a cuci Yashjub. D’agowa ya yi a hankali ya kalli Yassir d’in wanda shima shi d’in yake kallo,bai gama nazartar sign d’in da Yassir d’in yake yi masa ta ido ba ya ji Hajiya Mama tace”ya dai???” Tabbas Yassir ya ji masifar dad’i da farko da ya ji ance Junior ne zai yi test d’in amma kuma yanayin sa yanzu sai ya fara bashi tsoro ya shiga tantama a kan ‘anya kuwa zai yi yadda yace masa ya yi???’ Numfashi Junior ya fesar kafin ya kalli Hajiya mama Yace “Bara inyi confirming..” “Ciki ne ko?” Tayi mishi tambayar tana matsowa kusa da su kafin ta kalli Kausar wadda itan ma Junior take kallo tana yi masa sign ta ce”Wallahi yau sai..” Cikin katseta Junior yace “Ban tabbatar ba tukunna, bara mu yi test dai.” Flat Junior ya ce Kausar ta kwanta ya d’auki wani abu ya d’aura mata a kan mararta sannan ya ɗauko y’ar k’aramar allura ya huda tomb d’inta ya d’auki drop d’in jininta a kan PT. Sunayen Allah kawai Yashjub yake karantowa dukda sanyin standin Ac guda hud’u da suke kewaye da makeken parlourn hakan bai hanasa jik’ewa da gumi ba. Ahankali Daddy wanda shi kansa ya sha jinin jikinsa ya juya ya kalli Yashjub..Hatta Abhi sai da ya ji tausayin Yash wanda unlike (saɓanin) Hajiya Mama shi Daddy ya riga ya gaya masa komai, sun san ba da sanin shi hakan ta faru ba, kuma sun san tsanar da yake yiwa Kausar shiyasa gaba d’aya tausayin sa ya lullub’esu. So suke yi su ce wani abu a samu a fasa wannan gwajin Amman suna tsoron Hajiya mama kuma ko da ace sun hana d’in in dai akwai ciki kuma na Yashjub ne tou fa dole za a gani kuma za a fahimta sooner or later. Wayar Junior ce tayi k’ara, bai kula ba saboda ya riga ya san Yassir ne… Tashi d’aya pT d’in ya nuna Kausar tanada ciki kuma yadda result d’in ya fito da wuri hakan ya sa ya fahimci cikin ya dad’e a jikinta. Abunda ya ke gwadawa a cikin nata yakeso ya samu ya k’arasa, dan yana so ya tabbatar sannan ya ga ko zai iya kintata adadin kwanakin cikin…. Kamar ance ya d’ago hakanan ya sake d’agowa, suna had’a ido da Yassir ya kallesa ya nuna masa aljihunsa inda wayarsa take da sauri. Sunkuyar da kai Junior yayi yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa, ba ya so ya d’aurawa Yashjub laifin da ba nasa ba sannan ba ya so asirinsa ya tuno dan ya san muddin Yassir ya nunawa Daddy da Yadira da su Hajiya Mama video d’in nan to Yadira ba za ta tab’a yarda ta auresa ba, su Abhi kuma bayanta za su bi ga kuma kunyar da zai kwasa……sannan idan aka yi rashin sa’a videon ya zaga duniya to fa da shi da Yarinyar sunansu ya ɓaci kenan har gaban abada…. Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya zaro wayarsa a aljihu..tashi d’aya gabansa ya yanke ya yi wani irin mahaukacin fad’uwa sakamokon video d’in da ya ga Yassir ya turo masa, a ƙasan videon ya rubata ”incase idan kana tantama, kamar yadda na turo maka ɗinnan to hakanan zan turawa duk wani wanda yake a family ɗinmu..” Ko bud’ewa bai yi ba dan ya riga ya gani kuma ya san shine…ya san videon farin sani tun a school yanzu ma da ya zo nigeria Yassir ɗin ya sake nuna masa lokacin da suka yi faɗa… da sauri ya kashe wayar yana wani irin haki ya mayar cikin aljihu. “Me kake yi da waya ne haka junior?abun bai yi ba?” Muryar Hajiya Mama ta katse sa. Cikin d’an diriricewa ya d’ago ya kalleta yace “time nake dubawa” Daga haka ya mayar da kallonsa ga abunda ya d’aura a kan cikin nata ya d’an yi shiruu kafin ya sa hannu ya d’auke dan ya kammalu, daga haka ya mik’e tsaye… …… Tsayawa ya yi ya k’urawa abun ido kamar mai son fahimtar wani abu nan kuwa ba su san tunani yake yi ba.Ya riga ya fahimci abun ta inda yake nuni da cikin jikin Kausar zai iya wuce watanni biyu a jikinta… Gashi shi kuma ance yace cikin satinsa biyu idan kuma ba haka ba to ya san me zai biyo baya! Zuwa yanzu tabbas bai san abun yi ba. “Junior ka yi shiru ka k’ank’ame abubuwa ba ka fad’i sakamako ba.” Muryar Hajiya mama ta katse masa lissafi. Ahankali ya d’ago ya kalli kowa kafin yace “She’s pregnant!(ciki ne da ita)”. “Yauwwwa!!ai dama na sani” Hajiya mama ta fad’i hakan cikin tsananin b’acin rai yayinda gaba d’aya parlourn akace”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” kamar an yi rasuwa, Har su gwaggwo waenda suka lab’e a bakin corridor d’insu chan gefe. Wani irin karkarwa jikin Yashjub ya fara yi.. Tunda ya shigo ya ma kasa k’arasawa cikin parlourn, ganin yana shirin zubewa ya sa ya ja kujerar dining ya zauna ya dafe kansa. Yana sake karanto sunayen Ubangiji. A ranshi yana “Ya Allah ka san yadda na ke k’in Yarinyar nan, ka san yadda na tsani zina, Ya Allah ka sa ba zan haifi shege ba Ya Allah ka kawo mini sauk’i da mafita. Ya Allah Ina son Manubiya ban san ta ina zan fara yi mata bayani in fara bata hak’uri wannan karon ba..Ya Allah ka sa wannan cikin ba nawa bane ba.” Dan har yanzu bai cire hope ba! Tunda ta tabbata ciki ne da kausar to yanzu yake son sanin sanin adadin kwanakin cikin… Kamar Daddy ya san meye a ransa hakanan shi da Abhi suka matso kusa da Junior, Abhi ya d’an juyo da shi a hankali, gaban Daddy yana fad’uwa dan bai san ta ina zai fara had’a jini da Kausar ba..yana murna Yassir ya tsallake rijiya da baya yanzu kuma ace innocent Yashjub d’insa ne a ruwa…tausayinsa ya ke ji matuk’a dan tun d’azu ya lura da halin da ya shiga… Ahankali ya kalli Junior yace “Zaka iya aunawa?,kwanakin?” Dan a yanzu bashi da wani burin da ya wuce ya ji ance cikin nan ya fi sati biyu… Sai da Junior ya juya ya kalli Yassir wanda ya ke yi masa wani kalar ɓoyayyen murmushi, Dan tunda ya tura masa last message da video ya lura tarkonsa ya kama kurciya.. Had’e fuska Junior ya yi ransa a b’ace hankalinsa a tashe ya kalli su Daddy yace”Eh amfanin abun nan da na d’aura mata ma a cikin nata kenan,new invention ne(kwanan nan aka ƙirƙirosa)….” BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 37* Gyaran muryar da Yassir ya yi ne ya sanya Junior ya yi shiru ya juya ya kallesa….signal ya yi masa kawai ya nuna masa Yadira da ido, daga haka ya sunkuyar da kansa bai sake yin komai ba. Wani irin kallon fusata da takaici Junior yake jifansa da shi, ya had’e rai da fuska tamau, kafin da kyar ya janye idanunsa daga kan Yassir d’in ya juyo ya kalli su Daddy yace”bai bayarda exact weeks ba amman a yadda na fahimta da k’irgen da na yi banajin ya fi 12 days gaskiya…” Ajiyar zuciya Kausar da Yassir suka sauk’e a b’oye, yayinda Daddy ya d’an tafi Luu zai fad’i Abhi yayi saurin ruk’o sa. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ummi tace, sai kuma hawaye, domin itama tun d’azu da ta lura da yanayin Yashjub wani mugun mugun tausayinsa ya lullub’eta, yanzu kuwa ana fad’a yadda ya mik’e ya nufosu yana tangad’i dole ko waye ya ji tausayinsa….ta san ciwon ɗaukar alhakin abunda baka da masaniya a kai, baka kuma da ikon chanjawa… Yana zuwa a hankali ya shiga tsakanin Daddy da Junior ya rik’e kafad’un junior yace “Junior tsakanin ka da Allah, cikin nan 2 weeks ne??” Shiruu Junior yayi, yana ji kamar ya kurma uban ihu…..wani irin tausayin Yashjub da tsanar su Kausar had’i da bak’in ciki mai tafe da tashin hankali ne suka rufar masa a lokaci guda…. Tabbas Yashjub bai chanchanci haka daga garesa ba, amma kuma ya zame masa dole shima ya tsayawa kansa sannan ya kare kansa…… Ahankali ya ji Yashjub d’in yace “Ba haka bane ba ko? Cikin ya fi 1 month ma, I’m sure of it.” Da kyar Junior ya bud’e bakinsa yace “Am Yashjub…cikin nan bai wuce 12 weeks ba I’m sure of it, dan na gwada yadda ya kamata kuma wannan abun ba ya k’arya sabon shig….” Wata wawuyar shak’a Yashjub ya kaiwa Junior cikin tsananin b’acin rai yace “Ya za ka ce abun nan baya k’arya?k’arfen nasara ne fa!! k’arya yake yi bashi da tabbas,ba gaskiya ya fad’a ba!!”. Sai kuma ya juya ya kalli Daddy yace “Daddy,I’m not responsible i….” Shiruuu ya yi ganin yadda gaba d’aya mutanen parlourn suka tsura masa ido…a hankali ya lumshe idanunsa yana jin duniyar tana juya masa kafin da kyar ya d’aga k’afarsa kawai ya juya ya fice da mugun sauri…bai tsaya a koina ba sai side d’insa na da dan bai shirya fuskantar Manubiya a haka ba.Yana shiga ya zube a kan kujerar parlourn ya fashe da wani irin kuka kamar k’aramin Yaro. Yashjub yana fita, Hajiya Mama wadda tunda aka fara maganar kwanakin cikin da taga yadda Yashjub ya yi ta shiga tsananin tashin hankali! tace “kun dai san Ina da buk’atar a yi mini bayanin komai ko??? Dan kaina ya d’aure tamau tun d’azu, kuma zuciyata ta k’i yarda da lissafin da kwakwalwata ta yi Gameda yadda Yashjub ya yi yanzunnan.” Ta yi maganar tana kallon su Daddy. Ahankali Mommy wadda ta fara kukan munafurci ta matso kusa da ita tace”kar ki ga laifin Kausar, kuma kar ki ga laifin Yashju….” Cikin katseta da tsawa Hajiya mama tace”A’a!!!! A’a sam ba na son jin wannnan maganar! Bana son jin maganar k’azamiya Kausar da kamulalle Yashjub a waje d’aya,ba na so! Tun wuri ma ku nemo wani sharrin ba wannan ba! Ku fad’a mini gaskiya, in je in samesa in yi masa bayani, dan na san yadda ya yi d’innan da kuma abunda kike shirin fad’a mini dole akwai abuunda kukayi wanda ya sa yake zargin wannan shegen cikin nasa ne!” Ahankali Daddy wanda yake ji kamar ya fashe da kuka yace “Hajiya mama mu je sama in yi miki bayani” Wannan karon zabura Hajiya mama ta yi kafin tace”Au kaima??sharrine fa!kar ka yarda da makirci, sharri da asiri…ba batun wata Kausar da Yashjub ba ma naso in ji wannan batun, kawai ku gaya mini gaskiya Inje in fad’a masa a samu ya bar d’aga hankalinsa a aikin banza..” Ahankali Abhi ma ya matso yace “Hajiya Mama mu je mu yi miki bayani, wannan duk b’ata lokaci ne! Ki tsaya ki ji komai dan Allah….” Shiruuu ta yi kafin ta juya ta shiga watsawa Kausar wani kallon tsana!…..Hajiya mama ji take inama ace babu zunubi wallahi yau da sai ta kashe Kausar A nutse za ta shiga kitchen ta d’auko wuk’a ta b’oye a cikin rigarta ba za ta bari kowa ya gani ba, sai ta zo daff da ita tukunna za ta zaro ta lulluma mata…. “Mu je Mama” Muryar Daddy ta katse mata tunanin da take yi. Juyawa kawai ta yi ta nufi sama Sai a sannan su Mommy suka d’aga Kausar suka nufi saman da ita. Yahanasu da Ummi kuma suka bi bayan Yashjub…sun jima suna knocking kafin ya bud’e yace musu”ba komai kar su damu yana buk’atar hutu!” Yahanasu za ta sake yin magana yace”plss”kawai. Dan haka Ummi tace mata “su je, su barshi ya huta d’in.” Daga haka ta ja Hannunta suka wuce suna masu jin tsananin tausayin Yashjub d’in. Suna kai ta d’aki Mommy tace “Kowa ya fita!ta na son za ta yi magana da Kausar.” Suna fita Kausar d’in ta mik’e tace”Ina buk’atar zan watsa ruwa,jikina ya b’aci da amai.” Cikin fushi Mommy ta ruk’o ta tace”ba fa ki isa ba Kausar!!! Wallahi sai kin gaya mini gaskiyar lamari..dukda kuwa na riga na sani amma inaso in ji daga bakinki”. Kallonta Kausar d’in ta yi na y’an dakik’u kafin ta fesar da numfashi tace”A cikin ƴan kwanakin da su ka shuɗe bakya ko kulani, fushi kike yi da ni! Dan haka banga dalilinki na titsiyeni akan sai kin ji ta bakina ba!. Ai Ina ce haushina kike ji? Kin gama rayawa kanki abunda zuciyarki ta aiyyana miki a kaina,ko ba haka ba? To me kuma ya faru yanzu da kike son jin ta bakina? kawai inaga gara ki ci gaba da yarda da duk abunda zuciyarki ta baki.” Kausar ta dire aya cikin tsare ta da idanuwa kafin ta ci gaba da cewa”Besides ai gashi kin ma ce kin riga kin sani, so meyasa kike so ki ji a bakina?ko dai Baki sanin ba?” Cikin fushi Mommy tace “Kausar na san ki ciki da waje na san komai! bari ki ji in gaya miki abunda ya faru abunda kuma kika shirya kike so ya tabbata! …Na san Magani ko kuma wani abun kika shakawa Yashjub a ranar da aka ganku tare ke da shi.A wannan ranar abunda ban fahimta ba shine dalilinki na yin hakan gashi na san mun riga mun gama magana a kan zamu san yadda za a yi ki aureshi. Yanzu kuwa na fahimta Dama burinki ki samu ciiki saboda ki aureshi kenan ko? Bima’ana dai idan na fahimceki da kyau baki gama yarda da ni da Baba larai ba!shiysa kikaje kikayi gaban kanki!! Shiyasa kike ta faman b’oye mini ki ka k’i gaya min komai…. Hakane ko ba haka ba??”. Ajiyar zuciya Kausar ta sauk’e kafin ta matso kusa da Mommy sosai tace”Mommy Taabbas na san Yashjub a buge yake a wannan ranar, Wataƙila daga office ko wani wajen ko asibiti ne aka samu wata ta so cin galaba a kanshi Allah bai yi ba ya dawo gida da wuri abun ya fad’a kaina…dan ni dai da hannuna ban shak’awa ko na sakawa Yashjub komai ba.! Na san kin daina yarda da ni kuma kin daina aminta dani amman tabbas idan kika yarda da abunda nake fad’a miki yanzu to za ki ji dad’i za kuma ki samu salama saboda hakan ne gaskiya… ‘Ban bawa Yashjub komai ba, ban zuba masa komai ba, sannan ba shirina bane in samu ciki da shi wannan tsarin Ubangiji ne.’. Ko a gaban waye hakan zan fad’a tunda hakan ne gaskiya Ruwan ki ki yarda Ruwanki karki yarda..ba damuwa ta baceba!! kawai dai Ina takaicin cewa kin daina yarda da ni sannan kin daina so na.” Tana gama fad’in haka ta juya ta shige toilet da sauri a ranta tace “komin lalacewa na san Yashjub d’anki ne…ba zan bayarda k’ofa a kowa ba banda Yassir, har sai na ganni a d’akin Yashjub zaune a matsayin Amaryarsa. Yadda Yashjub ya gigice d’innan tsaf za ki tausaya masa, shi kuma na san in dai ya ji wani abun to ba zai ɗauki matakin da nake shirin d’auka a gaba! Da mahimmanci ba… Mommy ta dad’e tsaye a dakin tana tunani, amma kwakwalwarta ta kasa yin lissafin abu mai kyau…da kyar dai ta ja k’afafuwanta ta fita bayan ta yanke shawarar yarda da abunda Kausar d’in ta fad’a mata. Shiruuu!!!haka gidan ya koma kamar na zaman makoki…daga jigum sai tagumi….sai da Daddy da Abhi suka gama ji da Hajiya mama tukunna Daddy ya kira Junior yace a kuma yin wani test d’in. Yana fitowa daga wajen Daddy ya nufi d’akin Kausar domin ya d’auki jininta ya wuce office d’insu… Knocking ya yi bai jira an basa izini ba ya tura k’ofar d’akin nata ya shige…a nan ya tarar da Yasssir. Yana shiga Yassir d’in ya fara murmushi ya taso ya nufi bakin k’ofar inda Junior ya ja ya tsaya,kamar zai yi hugging d’inshi haka Yassir d’in ya matso shi yana cewa”Amintaccena! Gwarzonmu..Our savior…” Daddagewa Junior ya yi ya zuba masa naushi yana huci. D’agowa Yassir ya yi yana dariya ga jini yana zuba daga hancinsa dan ya fasa mishi hanci,yana murmushin yace”My pleasure!” Tsaki Junior yayi, bai damu da ya sake bi ta kan Yassir ba ya k’arasa ya kamo hannun Kausar ya d’auko sirinji Cikin rashin fahimta tace “me kuma za ka yi??” “Test zan kuma yi” Kawai yace mata dan ya tsaneta. Matsowa Yassir ya yi yace “Ki barshi ya d’auka,ba komai ai.Kawai dai ka tabbatar ka sake kawo result d’in 12 days! Besides me yasa ma kake buƙatar jinin natat?Tunda dai ka riga ka san k’arya za ka sake rubutowa, ka kawo??” Ya fad’i hakan yana mai dafa kafad’arshi. Juyowa Junior yayi ya zuba mishi ido fuskar nan tamau!! kafin ya tunkud’e hannun Yassir d’in. Ya riga ya gama d’aukar jinin, dan haka ya tartara komai ya fara k’ok’arin juyawa. “Oh no! Haba Junior Da ni da kai amintattun juna ne fa! Ba zan iya jurar wannan attitude ɗin(kyaliyar) daga bestiena ba. Haba mana! A iya sanin da ka yi min ya kamata ace ka san ba zan tab’a fallasa tsaraicinka ba, kawai dai na san za ka yi mini abunda nakeso idan ka ji na fad’i hakan shiyasa..kuma na san hakan shine kad’ai abunda zan yi in iya controlling d’inka wanda controlling ɗin naka danayi a yau ɗin ne ma kaɗai dalilin da ya sanya na ajjiye video d’in dama tun farko, saboda ban san me gobe ta k’unsa ba. amma daga yau ba zan k’ara ba, tunda na ga ranka ya b’aci sosai!!na ma goge video d’in!!ka yafe mini. Pretty please!!” Ya fad’i hakan cikin had’e hannuwansa biyu waje d’aya sannan ya yi kalar tausayi da fuskarsa. K’ura masa ido Junior yayi shima Yassir d’in shi yake kallo da serious face kafin dariyar da ta taso masa ta samu nasarar kufcewa bayan ya fara fesar da ita a hankali a hankali da farko. Kauda kai kawai Junior ya yi cikin fushi ya juya ya nufi k’ofa zai fita.Da sauri Yassir ya bisa ya rik’o hannunsa yace”Pls mana!! Da gaske nake, na ji ba daɗi nima ka yi haƙuri..so sorry Mun shirya??? Ya fad’i hakan yana mik’o masa hannunsa alamun su yi musabaha. Juyowa Junior ya yi kafin ya kalleshi yace “Na san ba ka goge ba!. Kana son mu shirya?” Ya yi mishi tambayar yana kallonshi. Da sauri Yassir yace “Yes,Wallahi.” “Inaso ka goge. ba ma na buk’atar dole sai na ganka ka goge ɗin dan na san za ka iya sake yin kamar ka goge bayan baka goge d’in ba,kawai inaso ka goge tsakanin ka da Allah da kuma darajar friendship d’in da yake a tsakani na da kai! Iyakar abunda nake so daga wajenka kenan Yassir… A wajenka hakan abun tsokana da wasa ne, Amma ni a wajena! Wannan ba abun wasa bane ba.” Numfashi Yassir ya fesar, ya zura hannuwanshi duka biyu a cikin aljihu, cikin yin serious sosai da fuska shima yace “Maganar gaskiya junior, nima ɗin wannan ba abun wasa bane ba a wajena!!! I’m morethan serious, da gasken gaske na ke. Sannan video d’inka is safe Junior, babu mai ganinsa dan na killacesa a wajena Ni kaɗai! Har zuwa lokacin da za ka yi gangancin faɗawa Mutane gaskiya.…..” Yadda Junior yake ji kamar ya rufe Yassir da duka ya b’ata komai ne ya sanya shi juyawa kawai da sauri ya fice daga d’akin ya banko musu k’ofar ransa a mugun b’ace. Yana fita Kausar tace”ka san dai Abotar ku ta lalace harabada ko?” Sai a lokacin Yassir ya juyo,inda take ya nufa ya zauna a gefenta ya ruk’o hannunta a hankali yace”I don’t give a f**k(ban damu ba)!. Ki manta da shi kawai, mu duba kanmu sannan mu saka kanmu a farkon komai! a ko da yaushe, In ba haka ba akwai matsala.” Numfashi ta fesar tace”yeah nima ba wai damuwa na yi da shi ba, kawai dai gaya maka na yi, sannan ko komai ya yi settling ya wuce to kar ka taɓa sake yarda da shi har abada, saboda zai iya cewa shima zai rama.” Cikin kawar a zancen Junior d’in ta d’aura d’ayan hannunta a kan nasu ta damk’e da kyau tace “Thankyou Yassir” Murmushi ya yi kafin yace U re welcome Sweetheart…ai saboda mu nake yi, ba ke kaɗai ba…” Ajiyar zuciya ta sauk’e, ganin ta kusa kwafsawa ya sa ta d’an yi murmushi ta kawar da zancen tace “ya akayi da Yaran grenade?” Sai da ya fesar da iska tukunna yace “da farko 5m suka buk’ata, da kyar muka tsaya a three, na tura musu 2 gaba d’aya kud’in accnt d’ina kenan, yanzu saura 1. Sun ce dai sun ma riga sun goge amma kin san halin Irinsu. 2 hours suka bani akan in tura musu cikon ko kuma su sake yi mini b’arna. Gyara zama ta yi tace “a drawer chan akwai sark’ata, ka d’auka ka saida sai ka cika musu, a samu a wuce wajen.….” Jinjina kai ya yi, yana jin babu dad’i kafin ya ce”inshaaAllah zan siya miki dozen d’in ta.” A hankali ta yi wani d’an guntun murmushi ta zuba mishi ido ba tare da ta ce komai ba. Shima itan yake kallo kafin ya fesar da numfashi yace”bara in tafi… kafin ma wani ya shigo d’akin nan a ganmu tare a san ba haushin ki nake ji ba!” Murmushi duk sukayi, shi yana jin tsananin k’aunarta tana ratsashi ita kuma tana jin tausayinshi kad’an dan ba ta san ya zai ji ba idan ta auri Yashjub….. Sark’ar ya d’auka har da receipt ɗin duk ta haɗa ta bashi, suka rabu bayan yace mata duk abunda take buk’ata ta kira shi ….. Yassir yana fita Yadira ta kira Kausar ɗin ta ce ”Junior yana jiranta a k’asa, Daddy yace scanning mai kyau yake so a yi, dan haka ta fito su tafi…” Hakanan ta shirya ta fito, bayan sun yi waya da Yassir ya ce”ta je,ba komai..shi har ya kama hanya yana so ya gama da Yaran grenade ɗin da wuri.” Har suka k’arasa office d’insa babu wanda ya cewa wani uffan…Yassir kam ya tura masa messages sun fi biyar kuma duk barazana… sun ci sa’a, dan colleague d’insa ba ya nan, dama office d’in nasa na cikin asibitin su biyu ne kawai shi da wani d’an India. Rai a b’ace haka ya yi scanning d’in…dan yana fara scanning ya ga cikin ya fi 2 months kamar yadda ya yi lissafin d’azu a gida. Gashi dai ciki k’ato amma ya na ji yana gani ya dank’ara 2 weeks a jikin report da conclusion amma ya san tabbas ko Yasmeen in ta gani wata rana sai ta gane…shi kuma da gangan ya bar shi a hakan bai ɓoye scanning ɗin ba ya bar komai b’aro b’aro! Ya san ko ba komai ya bar hint kuma ko ta kwab’e zuwa wannan lokacin ya san ba shi da case da Yassir, in sha Allah. Suna gama scanning d’in ya mayar da ita gida, shi kuma ya komo domin ya kammala had’a result d’in jinin da ko tab’a jinin bai yi ba saboda kamar yadda Yassir ya fad’a babu buƙatar jinin tunda k’arya zai rubuta. Har dare gidan shiruu, kowa ya tsit, ko dinner yau kam babu wanda ya tab’a dan kowa da abunda ya damesa… su Mommy kuwa kamar an yi musu bushara da gidan aljannah, dan haka suka sake k’aimi wajen aikin da suka saka a gaba kwana biyu, inshaaAllah yau za ta tunkari su Daddy da maganar auren Yash da Kausar tunda gashi komai ya zo musu da sauk’i sun samu hujja….a da tace ba za ta bari Kausar ta auri Yashjub ba amma Manubiya ce ta farkon da ta fara fusatata dole ta yi using Kausar ta taimaka musu su kawo k’arshen Manubiya inyaso sai ta san yadda za ta yi da Kausar daga baya, dan ba kaɗan ba kalaman Manu na aaibiti da ta ji tana gayawa Yash suka bada gudummawa wajen kammala hautsinata…dalilinta na bari Kausar ta auri Yash na biyu kum shine da ta zauna ta yi tunani duba da yadda Daddy ya chanza mata, abubuwa suka fara rinchab’ewa ya sa ta ga dole fa ta tsaya a kan Kausar d’in ta auri Yashjub, ko ba komai su samu su samu abunda suke so in yaso daganan ba sai Kausar d’in ta san me suka shirya ba cikin sauk’i za su zagayeta su yi abunda ya dace ga Yash ɗin ba tare da ta san su d’in ne suka aikata ba, kuma ta san a yanzu idan ta taimaki Kausar to za su shirya komai zai gyaru tsakaninsu za ta daina ganin kamar ba ta so ta taimake ta ne. Daganan sai ta taimaka mata itama dan akwai aikin da take so Kausar d’in ta yi mata bayan ta auri Yashjub a kan Daddy, ta hakan ne kawai take ganin abubuwa za su gyaru a yadda ya birkice kwana biyun nan………… Yashjub kuwa waya ya yiwa Manubiya yace mata”wani abu ya rik’esa…ta yi hak’uri idan ya dawo zai yi mata bayanin komai.” Sam bai ji alamun ta ji haushi ba, instead ma addu’ar fatan alkhairi da samun nasara ta yi ta jera masa, daga haka suka yi sallama dan ta ji yanayin sa kamar yana gaban su Daddy…shi kuwa tunda ya shiga side d’in nasa wani Irin zazzab’i ne ya lullub’esa. Suna gama wayar ya lumshe idanunsa daganan wani Abu kamar bacci kamar suma ya dannesa ba shi ya samu kanshi ba sai da gari ya yi duhu sosai….yana duba time ya ga har an idar da sallar isha…dan haka ya mik’e da sauri ya nufi bathroom yana istighfari…zazzab’in da ciwon kan sun sauk’a dan gashi har yana iya tafiya saɓanin d’azu da ya kasa tashi ma, amma fa sharkaff yake jinsa cikin gumi shiyasa yana shiga bathroom d’in ya sakarwa kansa shower yana jin yadda zuciyarsa ta shiga dagulewa dan tashi d’aya komai ya dawo masa sabo……. Sai da ya idar da sallolin yana cikin karatun Al’Qurani,kiran Daddy ya shigo wayarsa, yqna ɗauka ya ce “ya zo yana son ganinsa kafin ya wuce gida.” Sama sama hayaniya ta fara tashi a cikin gidan kafin ta karad’e ko’ina. Ko ba a fad’a ba ansan Kausar ce dan ga muryarta ana ji dan haka duk suka firfito parlourn saman…. Akwatuna wajen ashirin suka gani a jejjere… Dafe Kai Hajiya mama ta yi, kafin ta k’arasa inda suke tsaye Yassira rik’e da jakar hannun Kausar ɗin dan ta hanata tafiya ne, ita kuma Kausar tana k’ok’arin kwacewa tana kuka tana cewa”ki bar ni in tafi, kowa ya samu salama.” Hajiya Mama tana zuwa ta fincike jakar daga hannun duk su biyun ta yar kafin tace “Yanzu ke ashe rashin tsoron Allah n naki har ya kai haka? Bayaga tashin tashin hankalin da kika saka mu a ciki throughout shine kika sake cin wani burin hana kowa bacci??. Ki wuce ki shige ciki kafin gobe da safe a san yadda za a yi da ke!”. Ta fad’i hakan tana mai juyawa za ta koma inda ta fito. Cikin kuka Kausar tace “Eh ai dole ku ce in zauna…in zauna a ci gaba da aibanta ni sannan kowa yana jin haushina ana bi na da mugayen tunani da sharri!. Haba Hajiya mama, Ni ce ma na saka ku a cikin tashin hankali Ba ku ba?? Ni na yi wa kaina cikin??”. Cikin tsananin fushi Hajiya mama ta juyo tace”idan ba ki rufe Baki kin daina zancen ciki da ni ba sai na fasa miki Bakin wallahi! Shegiyar Yarinya mara kunya kawai!.” Fashewa Kausar ta kuma yi da wani sabon kuka kafin tace”Eh tabbas kam!!na ji na kuma yarda ni shegiya ce amman kuma yanzu ai ga shege zan haifa muku!jikanki!.” Duk yadda Hajiya mama ta so daurewa kasawa ta yi sai da ta juyo a fusace ta kifawa Kausar mari! Da kyar Yassir wanda suka yi da ita akan za su yi pretending kmr yana fushi da ita na y’an kwanaki,ya iya danne kansa. Cikin fushi Hajiya mama tace “Like I said, ki koma ciki kafin zuwa gobe in gama tunani”. Cikin kuka Kausar tace “Ni kuma na k’i yarda in k’ara kwana d’aya a cikin gidan nan!. Haba mana! wai shin maraici da rashin uba hauka ne?? shikenan sai a dakeni a hanani kuka? ce muku akayi Inada burin in haifi shege??. Bari ki ji in gaya muku last miscarriage d’ina Likita ya tabbatar mini in har na sake samun wani fitar cikin to mahaifata ba za ta sake rik’e ciki na tsawon wata hud’u ba! meaning ba zan sake haihuwa ba!. Tun daga ranar na riga na yanke na kuma gama tsara rayuwata da yadda zan kula da kaina da yadda zan yi aurena in haihu sai dai kash!!!tashi d’aya bagatatan Yashjub ya tarwatsa mini tsari da duk wani abun da na shirya. Amma dukda haka kaff cikinku babu wanda ya duba yadda akayi raping d’ina (aka yi mini fyaɗe) haushina ma ake ji da hantarata da kyarata saboda bani da kowa ba ni da gata ko??. Kowa in banda cin fuska ba abunda yake mini a cikin gidan nan!! safe da dare, dan haka na gama tsarawa zan tafi kuma rest assure idan na fita kowa sai ya san abunda ya faru dan babu wanda zan b’oyewa, wallahi kowa sai ya san wannan d’an na Yash ne! Daganan kuma ba za ku sake ganina ba Ni ko d’ana. Tunda dama abunda kikeso kenan, na yarda zanyi rayuwata ni kad’ai tunda dama bani da kowa”. Da sauri Mommy ta matsa inda take ta rungumeta cikin kuka tace “Kausar kina da ni mana. Kinada ni ga kuma y’an uwanki, Kinada gata mana Kausar.” “Kar ki yi mini haka Mommy, kar ki kashe mini guiwa! Ki ci gaba da fushi da ni kawai kamar yadda kika d’auka da farko, hakan zai fiye miki.” Zuwa yanzu kowa ya hallara har Yashjub wanda Daddy ya kira yace ya zo yana son ganin sa kafin Kausar ta fara dramar tata. Tabbas Mommy tana son Kausar da gaske shiyasa ta sake fashewa da kuka cikin kukan tace “Ke nake gani na ke jin sauk’in rashin y’ar uwata Kausar, idan kika tafi kika barmu ni da Larai kin san ba ki yi mana adalci ba. Haba Kausar, ya za ki yiwa uwar da ba ta san komai ba sai k’aunarki haka??” Hawaye ita ma Kausar d’in ta share tace “Mommy na san kina sona, amman anzo gab’ar da a cikin gidan nan nan da y’an kwanaki dole ki zab’a Ni ko d’aya a cikin y’ay’anki kuma na san dole Yashjub da farin cikin sa da rufin asirinsa za ki zab’a tunda ba zai tab’a yarda a haifi cikin nan ba saboda abubuwa dayawa ni kuma saboda mahaifata da aka ce za ta lalace in na kuma zubar da ciki Wallahi ko sama da k’asa za ta had’e ba zan zubar ba!. Besides in banda gori da masifa da bak’ak’en maganganu babu abunda nake janyo miki a cikin gidan nan fa! Na gode da yadda kika tsaya tsayin daka akaina, kika bani gata amma lokaci yayi da ya kamata nima in tsayawa kaina, shekaru na sun ja Uwa ce ni dan haka zan iya kulawa da kaina and move on…..” Gaba d’aya har Yadira kan Kausar suka rufa suka shiga lallab’ata amma ta birkice furr ta dage akan “itafa sai ta bar gidan” su kansu sun tsorata da Lamarin nata ballantana su Daddy. Ba abunda yafi daga musu hankali Irin yadda ta rantse ta sake rantsewa akan idan ta sa k’afa ta fice ba wanda zai sake ganinta ko ita ko d’an da za ta haifa tunda babu wanda yake buk’atar su. Tsaki Hajiya mama ta yi tace”ai sai ku yi” Daganan ta juya ta wuce ta nufi d’akinta ta shige ta banko k’ofar da k’arfi. Sai a lokacin Abhi ya matsa kusa da ita yace”Kausar ki je d’akinki ki zauna..zuwa nan da 2 hours zan neme ki. Daganan in kin ji hukuncin da na yanke still bai yi miki ba, sai ki tafi babu wanda zai tsayar da ke.” “Kausar plss..ki sauraremu mana, b’acin rai da zuciya ba abunda yake janyowa sai da na sani!.” Cewar Ya’isha. “Fushi ne mukayi dake na y’an lokuta, amma yanzu komai ya wuce..kar ki yi punishing d’inmu ta hanyar rabuwa da mu na har abada. Muna k’aunarki, ke d’in y’ar uwarmu ce, jininmu ce!.” Cewar Yasira Shiruuu kowa ya yi, kafin Kausar ta juya kawai ta wuce ta koma ciki ba tare da ta kalli kowa ba, ranta fess!!… Ba abunda ya fi yi mata dad’i irin zuwan Yashjub, kuma ta tabbata maganganunta sun yi tasiri a kansa duba da yadda ta ga ya tsaya yayi shiruuu a stairs d’in ya ma kasa k’arasowa saman. Tana shiga ta rufo k’ofarta da sauri ganin su Yasira sun biyota suna shirin shigowa suma. Dama Mommy bataso ayi abunda ta shirya ta kuma gama tsarawa a gaban Hjiya mama dan ta san idan sama da k’asa za su had’e ba za ta tab’a yarda ba Shiysa ta yi godiya ga Allah da ta ga tunda ta shiga ciki bata sake ko lek’owa ba. Daddy Abhi sai Yashjub wanda Abhi ya k’arasa ya ja hannnunsa ne suka nufi saman,dan haka da sauri jikinta har yana rawa ta bi bayansu. Suna shiga parlourn Daddy itama ta kutso Kai bakinta d’auke da sallama. A fusace Daddy ya juyo yace”the last time da kika hawo mini side d’ina me na ce miki???” Cikin in Ina tace”Haba Daddy, meeting fa za a yi wanda ya shafi rayuwar d’aana, dole za ka ganni a nan mana sabo…” Cikin katseta da b’acin rai sosai yace”za ki b’ace mini daga gani ko sai na yi ball da ke??” Hawaye ne suka b’alle mata kamar an kunna famfo.. Cikin son tura mata wani bak’in cikin ya matso kusa da ita yace”da ke da frame ba ku da maraba a cikin gidan nan, bi ma’ana sai dai a kalle ki ki kalli mutum shi kenan amfanin ki!. Daga yau! ko da wasa na ganki a wajen da ake magana mai amfani da mahimmanci wadda ta shafi ni ko y’ay’ana Wallahi ranki sai ya yi masifar b’aci, bana buk’atar ki a cikin komai nawa! ko yunk’uri kika yi na son shiga cikin maganata ko ta yarana wallahi bak’anta mini rai kike yi.! Tsabar tsaurin ido ko Ummi wadda na damu da ita ba ki ganta a nan ba amma ke k’ok’ari kike yi ki shigo!….” Da mugun sauri Mommy ta juya tana hawaye kamar ruwan fanfo, bibbiyu haka ta sauk’a daga stairs d’in ta nufi side d’inta inda ta bar Baba Larai tana mai had’a hanya…. Tana shiga ta tarar da su ita da su Yasira… Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali, dan haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”. *MANNUBIYA* *Book 2* *page 38* Tana shiga ta tarar da ita da su Yasira… Ganin yanayinta ne ya sake d’aga musu hankali, dan haka suka rufar mata da tambayar “mai ya faru?”. Ba ta b’oye musu ba, dan zuwa yanzu tana so ta gogawa Daddyn bak’in jini a idanun ƴaƴan nasa ta yadda za su tsaya mata su bi bayanta a kan komai. Dan haka ta zage ta kwashe Komi ta sanar da su, tana kuka abun tausayi..wanda hakan ya sa Yadira da Yusra fashewa da kuka suma… Yasmeen kam ta d’an ji babu dad’i tunda uwa uwace, sai dai kuma har ga Allah ita ba ta ji haushin Daddy ba,Yasira da Ya’isha ne suka fi kowa fusata, Ya’isha har da cewa “ai da ba ta fito ba!” Lokacin da ya ce ta fito d’in. Sosai suka rarrashi mahaifiyar tasu, wadda hakan da suka yi ya sa ta d’an ji sanyi, daga nan ta kalli Baba larai tace mata “suna sama suna meeting Larai, kin san me ya kamata ki yi a halin yanzu ko?” “Dalla dalla ma kuwa!” Baba Larai tace,daga haka ta mik’e ta fice, Ya’isha da Yasira suka bi ta, Yusra da Yadira kuma suka zauna suka ci gaba da rarrashin Mommy yayinda Yasmeen ta fice ta basu guri,dan tunda Mommy ta fara magana da Baba Larai ta fahimci me su ke shirin yi…ba ta againsting wai Kausar ta auri Yash, kawai ita Asiri ta tsafin nan nasu ne ba ta so, sannan makircin su har ga Allah ya yi yawa, gashi ba ta Isa ta ce komai ba. Mommy tana fita Yassir ya shigo…kwata-kwata ya kasa gane kan dalilin wannan dramar da Kausar ta gabatar, zai je ya sameta su keb’e su yi magana ya tambayeta dalili amma for now tun kafin iyayensa su yanke wata muguwar shawarar da zata tarwatsa shi gara ya zo ya fito kawai ya gaya musu shi zai aureta…a yanzu babu lokacin pretending ko acting domin a yadda abubuwa suka gudana da abunda tayi ya san tsaf su Daddy za su ce Yashjub ya d’auki responsibility d’in cikin da ya yi wa Kausar ko dan kar sunan family ya lalace. Ba su kai ga fara magana ba shima Junior wanda sai yanzu ya dawo daga had’o results ya hawo saman ya shigo cikin parlourn. Ganin kowa jigum ya sa shima ya nemi waje ya zauna ya yi shiru….sam ya k’i yarda ya kalli inda Yassir yake ma sakamokon wani haushi da takaicinsa da yake ji. Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Junior yace”ya bayanin result d’in???” Mik’ewa Junior ya yi , kai masa takardun da ya shigo da su na results d’in a envelope tukunna ya koma ya je ya zauna sannan yace” irin na d’azu ne, cikin kwanansa 12 dai dai..na yi kwakwaran bincike yadda ya kamata,sai da na je ma na sake d’aukar jinin nata na yi binciken komai kamar yadda ka ce, ga kuma scanning d’in shima.” Dubawa Daddy ya yi, ya bawa Abhi shima ya duba. Shiruuu parlourn ya kasance daga nan kafin Yassir yayi gyaran murya yace”Daddy idan ba damuwa ni na yarda zan auri Kausar!!! Akan dai ta fita ta tonawa family d’innan asiri sannan kuma ta d’auki d’an d’anuwana ta tafi dashi tayi masa raino da tarbiyyar single parent(Mace).. Ni Na ji na gani zan aureta, tunda dama ina sonta.” Cikin katseshi Daddy yace “Yassir I’m sorry, kawai ka bar maganar nan,ka san cewa Kausar ba za ta yarda ta aureka ba,tunda har mahaifiyarka ta fad’amawa watak’il ba ka sani ba ne amma ta nuna ta kuma ce ba za ta tab’a aurenka ba don ba ta sonka…k’iri k’iri ta bijirewa aurenku kwanakin baya dan haka inaga yanzu ba lokacin fa ya dace ace za ayiwa Kausar dole ba, ta burkice, ba ta ji bata gani dan ina ganin babu abunda ba za ta iya aikatawa a halin yanzu ba….kuma tsaf za ta iya tafiya d’in kamar yadda ta fad’a sannan na tabbatar sai ta yi amfani da wannan Yaron against Yashjub, bayaga haka bai kamata mu bari ta tafi da Yaro ya rayu a hannunta ita kaɗai kamar yadda ka fad’a ba. Sannan akwai abunda ta shirya, tunda har ta fara maganar tafiya dan Kausar d’in da na sani ba za ta yi abunda ta yi yau ba tare da ta tanadi kwakkwaran plan ba….ai ta ga ta samu ciki dan haka tana ganin tanada makami, shiyasa ya zama dole mu kuma mu yi mata shigar sauri kafin ta yi b’arna. Sannan Yassir ko an yi aurenka da Kausar ba za ku zauna lafiya ba, ta dinga taso da fitintunu dan zatace an yi mata dole ne,again kamar yadda ka fad’a kana sonta so za ta ke juyaka ne kawai! In zan baka shawara ka d’auka dan Allah ka hak’ura da Yarinyar nan har abada. Cikin d’an uwanka ke a jikinta, haba mana kwab’ar kar ta yi yawa. Sannan ba zan ji dad’i ba Ni kaina idan aka ce ka d’auki nauyin abunda ba laifin ka bane ba.” Da k’arfi gaban Yashjub ya yanke ya fad’i dan a kaff cikin maganganun Daddy tun kafin ya fito ya fad’i abunda yake ransa ainun ya fahimci inda zancen zai dira, dan haka ya runtse idaunsa da mugun k’arfi yana sauraron Daddy da ya ci gaba da cewa”some facts cannot be denied!!(akwai abubuwan da ba zai yiu a iya chanjawa)… kasancewar ba na son Kausar ba shi zai sa in rufe ido in k’i gaskiya ba!sannan ko babu komai nima y’ay’a mata ne guda shidda a gabana,idan wani ya yi musu haka ba zan ji dad’i ba! A al’amarin nan Abu na farko da zan so ka saka a kanka Yashjub shine ba zan bada goyon baya a zubar da ciki ba, saboda haramun ne. Sannan ka yi hak’uri Yashjub, kaima na san ba laifin ka bane ba amma itama ba laifinta bane ba, saboda kamar yadda ta fad’a da gaske ne maganar da Likita ya yi akan mahaifarta lokacin na ji zancen dan haka ka ga ba za ta so ciki da gangan ba tunda ba zata yarda ta zubarba, kuma ba za ta so ta haihu babu Miji ba. Ta yiu tricking d’in naka ta yi da gaske, amma tabbas na san ba ta yi tunanin za ta samu ciki ba. Abunda nake so ku fahimta a nan shine k’addara ce ta fad’o mana…. idan muka ce Kausar ta zubar da cikin nan bayan kuma mun san yanayi na lafiyarta da halinda take ciki to mun zalunceta, kuma ba zan ma bari a zubar da cikin ba. idan kuma aka ce ta haihu babu Miji shima mun zalinceta kuma na san ma ba za ta yarda ta zauna da mu ba….kuma duk daren dad’ewa kowa ya san Yaro na Yashjub ne dan gaskiya ba ta b’uya.” Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya kallesu ɗaya bayan ɗaya tukunna yace”hakan ya sanya na yanke shawarar abunda ya kamata a yi a rufawa kowa asiri. Yashjub k’addara ta riga fata, kuma an zo wajen da dole sai ka yi hak’uri ka danne zuciyarka an rufawa juna asiri..ni Mahifinka ne, har abada ba zan yi abunda zai cutar da kai ba sai dai in yi wanda ba zai cutar da kai ba, wanda zai rufa maka asiri. Ka dai ji dalilan da na bayar kuma na san ka fahimta…dan haka ka auri Kausar! A samu ta haihu lafiya daganan duk decision d’in da ka yanke ba zan ce komai ba! Ko wanne family suna da nasu secret d’in, cikin jikinta dududu satinsa biyu dan haka idan aka yi aure za ta haihu ne akan lokaci asirin kowa a rufe, duniya ba ta sani ba.Yaro kuma kai ka san yadda zaka yi a gaba ka fitar masa da hakkinsa ba tare da an kwaresa ba. Ka yi hak’uri ka d’auki nauyin da yake naka ne,na san ba laifinka bane ba amma duba da yadda Yaron nan zai zo duniya a ganina idan aka barsa da ga shi sai Kausar a inda ba mu sani ba to gaskiya ba mu yi masa adalciba, kuma kai ka san wacece Kausar! ba ta nutsu ba ma ballantana ta yiwa wani tarbiyyar da ta kamata.” Ajiyar zuciya Abhi ya sauk’e kafin yace”Daddy abunda ka fad’a gaskiya ne! sannan hakan shine kaɗai zaɓinmu mafi sauƙi dan duk wani zaɓin da ba wannan ɗin ba to yana tafe da ƙalubale a bayansa” Mik’ewa tsaye kawai suka ga Yashjub ya yi….yana jin kanshi yana wani irin juyawa yace”Daddy idan na auri Kausar zan iya mutuwa, amma kamar yadda ka fad’a k’addara kowa da kalar tasa…zan je in samu Manubiya in gaya mata komai, duk abunda tace a yi to shi za a yi… Wannan rayuwar mu ce, na ci amanar ta! A ganina ita ya kamata a barwa wannan hukuncin ta yanke…this should be her decision to make. Dukda cewa idan na auri Kausar zan iya mutuwa, amma idan har ta bi bayan abunda kuka hango kuka fad’a to shikenan na yarda zan aureta d’in har zuwa lokacin da za ta haihu!. Idan kuma ba ta yarda ba to ku yi haƙuri dan ba zan aureta ba. Daga nan Kausar is free to do whatever the hell she’s planning on doing(in Kausar ɗin ta ga dama za ta iya zuwa ta yi duk abunda ta shiryama ɗin, ban damu ba”.) Yana gama fad’in haka ya juya ya fita ko bi ta kan Daddy wanda yake cewa “yanzu zama za mu yi mu jiraku kenan kake nufi?”bai yi ba. Sai a lokacin Yassir ya d’an samu nutsuwa… Sosai Daddy ya ji haushi ya fusata…tayaya Yash zai ce sai abunda Manubiya ta yanke tukunna shi za su yi?? A tak’aice dai Yashjub ba shi da zaɓi sai na Manu, su kuma suna zaune suna jira har sai ya je ya tambayota ta fad’i yadda za a yin tukunna ya zo ya gaya musu su Kuma su yi.! Ya san dole abun zai tab’ata tunda abune wanda ya shafi Mijinta da wata Macen amma kuma power d’in da Yashjub ya bawa Manubiya a wannan al’amarin ya yi yawa sosai!!…ya san wannan ba shine lokacin da ya kamata ace ya ji haushin Manubiya a kan wannan maganar ba dan tunda cikin jikinta ya zube shi tausayinta ma yake ji sosai, amma tashi d’aya a take a lokacin sai ya ji takaicinta ya rufe sa….ba zai tsaya a mayar masa da d’a boyi boyi ba fa!. Wato ko abu zai kashe shi kamar yadda ya fad’a indai ta na so to zai yi kenan! matar da ya kamata ace she’s even greatful da Yash ya aureta aka kawota cikin family d’insu shine amma ta kafa ta tsare ta ke juya musu d’a suma take so ta juya su. Lissafin da Daddy yakeyi haka nan shima Abhi yake irinshi Exactly. Dama shi Abhi tun farko da su ka je kai kud’i sai da ya saka hakan a ranshi, amma daga baya sai ya janye, yanzu kuwa power d’in Manu ya yi yawa gaskiya dole a ja mata layi. Dan wannan Yarinyar idan ba su yi da gaske ba har Hajiya mama sai ta juya. Numfashi Daddy ya fesar kafin ya kalli Abhi yace”yanzu me ye abunyi?ni dai ba zan jira sai Yarinya ta yanke hukunci tukunna mu maza mu zartar ba.” Jinjina kai Abhi ya yi yana d’an lissafi kafin yace”Daddy a yiwa kowa adalci sannan a duba Yaron da bai ma riga ya zo duniya ba…kamar yadda ka fad’a duba da yanayin hanyar da akabi aka sameshi ya kamata ace mun tsaya tsayin daka mun sadaukar da abubuwa da yawa wajen ganin mun inganta rayuwa da tarbiyyar sa…” Da sauri Yassir yace”Abhi ni k’anin Yashjub ne, inason Kausar, me yasa ba za ku aura mini ita ba ni??? Wallahi idan kuka had’a Kausar da Yashjub to kun had’a fitina ne saboda ba sa shiri ba sa so…..” Cikin fushi Daddy ya katse sa yace”idan ka ƙara magana Yassir Allah sai ka fita a parlourn nan!!! Mahaukacin banza kawai mara zuciya… Anya Yassir ka san ciwon kanka kuwa??” “Hmmm”kawai Junior yace Wanda hakan ya sa duk sai da suka d’an kalleshi. Atake jikin Yasssir ya d’anyi sanyi dan sai a yanzu ya fara tunanin kar fa ya kwafsa..to amma shi yanzu ya zaiyi???….ga duka ga hana kuka!inaa!!!ba zai bari auren nan ya d’auru ba fa… Sai da su Abhi suka sake yin d’an k’us k’us d’insu tukunna Daddyn ya d’auki waya ya kira Ummi daganan ya kira manyan drivers d’in gidan da aka dad’e da su, yace “su zo!” …Manubiya abar tausayice, duba da zargin zubar mata da ciki da suke yi, sannan Yarinyar ba ta da matsala ga kuma tarbiyya da hankali uwauba d’ansu yana sonta..he’s happy with her!. Amma kuma Tabbas ya kamata a ja mata layi kar ta haura iyaka kar ta haura matsayinta, dan ba zai you su je garin tausayi su kunnawa wani haske su kuma su k’ona kansu ba…soyayyar Yashjub a gareta ta yi yawa!! Amma dukda hakan ba su damu idan ya so ta da yawan ba! kawai su mtsalarsu mahimmanci da kuma power da ya bata waenda su ke k’ok’arin danne su da k’imar su a idanun Yashjub ɗin. Sannan ba a yiwa mace haka! Dan idan su ka zuba ido to a gaba za su samu babbar matsala. Tunda akayi auren yake haka wanda inda ace gigin amarci ne to da tuni ya daina amma abun nasa k’ara gaba ma yake yi. son da Yashjub ya ke yi mata ya yi yawa…ba sa jin haushinta saboda hakan hasalima su tausayi take basu na halinda take ciki ammafa fa hakan ba shi zai sanya su zuba ido Yashjub ya zama boyi boyi ba. Sun san idan ya riga ya auri Kausar, ya saba zama da mata biyu to ko ya rabu da Kausar ɗin bayan ta haihu kamar yadda aka shirya ba lalle ya iya zama da mace d’aya ba… Idan aka barwa Manubiya Yash ita kad’ai akwai gagarumar matsala…. Dan haka suka ga dacewar su jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya…… Yana gama waya da su Ummi ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi shiruuu, yana mai jin kamar ya d’aura Hannu a ka! ya kurma uban ihu…wai yau shine da kansa zai aurawa Kausar Yashjub! Tabbas shiyasa ba a son mutum ya tsananta tsana!saboda ba ka san inda rana za ta fad’i ba. …. Sai da aka kusan yin fad’a da Daddy da Ummi da ta ji wai aure za a d’aurawa Kausar da Yashjub…so ta yi ta fita ta kira shi ta sanar da shi, amma Daddyn ya ce ta zauna Abhi kuma ya shiga bata Baki….ga drivers d’in gidan a zaune sun yi jigum suma kawunansu a k’asa,shiyasa Abhi ya dage ya lallab’ata ba dan ta so ba ita kuma ta hak’ura ta zaune ta na mai jin kamar zuciyarta za ta fito!! babu yadda ta iya haka nan tana ji tana gani aka d’aura auren Kausar da Yashjub akan sadaki naira dubu d’ari, tq inda Abhi ya yiwa Yashjub wakili Daddy kuma ya yiwa Kausar. Ba abunda ya fi d’aurewa Junior Kai kamar rikicewar da Yassir ya yi, Dan ba da shi ma aka yi d’aura auren ba korarsa su Abhi suka yi ganin yana shirin yi musu hauka, da kyar kuwa ya fita yana huci ya nufi side d’in Kausar, amma sama ko k’asa ba ta nan, kuma wayoyinta duk gasunan a zube a kan gado. Ita kuwa Kausar b’uya ta yi a box room na floor ɗin, saboda shi… tana kallonshi ya sauk’o a rikice ya nufi side d’in nata, sai da ya fito ya sauk’a chaan k’asa tukunna ta fito ta shige dan ba ta shirya fuskantar shi ba saboda Bata gama had’a wayon da za ta yi masa wannan karon ba. Dukda tana zullumin son jin dalilin yanayin da ta gansa a ciki amma za ta bari ta ji zuwa gobe. A b’angaren Mommy kuwa, ta fito kenan za ta tafi wajen Baba larai ta ji ya ake ciki ta ga Yassir ya sauk’o kamar ma yana kuka, shiyasa ta kasa hak’ura ta haye saman..ai kuwa tun kafin ta k’arasa jikin k’ofar sosai ta fahimci d’aurin aurene ake yi…. Hamdala da sujjada ta yi, sai da ta ji an ida d’aurin auren tukunna ta juya ta nufi side d’in Kausar har tana tuntub’e. A b’angaren su Daddy kuwa ba a tab’a d’aurin auren da babu wanda yake farinciki ba sai a yau! Kaff wajen babu wanda yake farin ciki da d’aurin auren hatta drivers d’in da aka kira su ka yi shaida ba su yi murna da wannan al’amarin ba, dan su kansu sun san Kausar ba ta dace da Yashjub ba, gashi bai dad’e da yin aure ba. Junior ji yake kamar yayi kuka dan takaici, saboda gani yakeyi kamar hakan duk laifin sa ne amman kuma shima bashida yadda zai yi ne, dan ba zai je garin taimakon Yashjub shi kuma ya lalata nashi relationship d’in da bai ma samu ya fara ba, tare da mutunci, martaba da kuma sunansa gaba ɗaya.. Su Daddy suna gama d’aurawa kuma sai suka fara da na sani..kamar irin ba a cikin haiyyacinsu suka d’aura d’innan ba. Babu tsoron wadda ya fi rufe su a take a lokacin kamar na Hajiya mama!! dan haka suka d’aura alhakin gaya mata a kan Ummi…a ganinsu tunda tana ji da ita tabbas za ta san yadda za ta yi mata bayani ta fahimta ta kuma taushe ta ta hak’ura. Ummi Tana gama jin bayanin su tace”to”kawai, daga haka ta juya ta fice ranta a mugun b’ace. A b’angaren Yassir ma zuwa yanzu ya gama rikicewa, dan yana k’asa drivers d’in suka sauk’o ya tambayesu suka ce “eh an d’aura” bai ma san mataki na gaba da ya kamata ace ya d’auka ba, shiyasa kawai ya zauna yayi shiruuuu dan kwakwalwarshi ta d’auke ta tsaya daga aiki. Mommy tana shiga d’akin Kausar ta sameta a tsaye dan itama shigowar tata kenan. Murmushi Mommyn ta yi, kafin ta k’arasa inda Kausar d’in take ba ta damu da yadda ta turo Baki ba dan ta san yanzunnan za su shirya… Cikin tsananin farin ciki tace “Ki yi mini alk’awari goron albishir d’innan da zan baki yanzu shine za ki daina fushi da mu!!” Gabanta ne ya yanke ya fad’i, a ranta ta shiga adduar “Allah ya sa hasashenta dai dai ne, Allah ya sa tarkonta ya kama kurciya” A fili kuma sai ta kalli Mommyn tace”Inajinki” Cupping fuskarta Mommy tayi kafin tace “Ki yi mini alk’awari tukunna!”. Juya ido Kausar ta yi kafin tace “okay fine!yawan farin cikina yawan daina fushi da ku” Dariya Mommy ta yi sannan tace mata”Y’ata ta girma, ta zama matar aure Matar Yashjub imam kura yanzunnan Ubangiji ya yi ikonsa.” Tun Mommy tana murmushi mai had’e da dariya har ta zo ta daina dan Kausar ta k’ame k’am!!! Ta ma kasa yin ko motsi. Sai da Mommyn ta d’an jijjigata tukunna hawayen farin ciki suka zubo mata,a hankali ta kama Hannunuwan Mommy biyu da suke rik’e da kumatunta, idanunta na zubar da hawaye tace “Mommy da gaske kike, Dan Allah ki yi mini wasa da komai banda wannan”. “Wallahi da gaske nake” Mommy ta fada mata tana murmushi tana goge mata hawayen nata. Fad’awa ta yi jikin Mommy kawai ta fashe da kuka…dai dai nan su Yassira suka shigo ita da su Yusra cikin farin ciki sukace “Mommy da gaske ne abunda muka ji Ummi tana waya yanzu tana fad’a???” Jinnjina musu Kai ta yi still tana rik’e da Kausar dan ta k’i ta cika ta har yanzu… Aikuwa a take gaba d’ayansu suka taho suka had’asu suka rungume… Farin ciki a ranar dai ba mahaluk’in da ya kai su Mommy. Kausar bata ɗauki lokaci ba ta nemi yafiyar dukkansu, na ganin kamar sun daina sonta da ta yi, dan yau kam ta tabbatar da suna k’aunarta duba da yadda suke taya ta murna. Cikin farin ciki suka wanzu a ɗakin kowaccensu Baki a washe Yasmeen ce kawai babu a wajen. A ranar suka yi alk’awarin had’e kansu guri d’aya har Baaba Larai! Sannan A samu su taimaki Kausar su tsaya mata ta yak’i Yashjub su ga bayan Manubiya. Cike da farin ciki Mommy take kallon y’an matan nata, batasan lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba…. Ahankali Baba larai ta kamo hannun Mommy tace “Kar ki damu, na san hawayen me kikeyi inshaaAllah family d’inki ya kusan zaman complete.“ ….. Yassir so yake ya je wajen Kausar, amma ya san tana tare da su Mommy, dan tun d’azu da ya hawo da niyyar sake dubata ya ga su Yasira sun shiga bai ga sun fito ba. shiysa ya hak’ura ya d’aga musu k’afa dan ya san yana shiga a haka akwai matsala, kuma ya riga ya gama yi mata alk’awarin ba zai fallasa plan d’insu a kowa ba, za su yi komai cikin sirrine. Kishi da tashin hankali haɗe da bak’in ciki duk sun taru sun rufesa, ya san Kausar ba ta haramta a garesa ba, kuma ya san a yau idan ya ce a warware auren ba shi da matsala da ita sai dai Mommy, dan haka ya tsara akan za su zauna shi da Kausar da Yashjub gobe inshaaAllah, a warware ba tare da su Momy sun ji ba ,tunda duk su ukun ba so suke yi ba. Sai da ya kai ga wannan matsayar tukunna ya d’an ji sanyi a ransa..amma fa dukda haka kishi sai da ya sauk’ar masa da wani zazzafan zazzab’i..dan idan ya tuna cewa yau fa Kausar matar wani ce sai ya ji kamar ya cinnawa gidan wuta. Shiyasa kawai ya wuce side d’insa bayan ya tura mata message yace”ta kirasa idan ta zama free.” Yana shiga d’akinsa ya ware ac ya rage kayan jikinsa ya kwanta akan tiles flat daga shi sai boxer yanajin yadda kansa yake wani irin sarawa. Assurance yake bawa kansa yana sakewa cewa”Yashjub ma ba zai yarda da wannan had’in ba! dan haka ba shi da matsala ta koina, InshaaAllah a gobe za a ware auren daganan duk abunda su Daddy za su yi wannan daga baya kenan! kuma ko sun yi fushi ya san za su huce.” Yana waennan tunane tunanen zazzab’in jikinsa ya nunku!….ya dad’e yana fama kafin ya samu ya d’an ragu, daga haka wani bacci mai nauyi ya yi gaba da shi……….. Yashjub Yana fita gida ya nufa…har yanzu kwakwalwarshi ta k’i ta bashi kwakkwaran dalili kwaya d’aya wanda ya sanya su Daddy suke tunanin ya kamata ya auri Kausar saboda shi duk wannan bayanin da Daddy ya yi sam baiga ta inda hakan ya zamo hujja akan ya auri Kausar ba. Zai iya kula da ita da ‘danta ba tare da ya kalli inda take bama, Idan kuma tafiya takeso ta yi to ta na iya wucewa, ta tafi duk inda takeso ita ta sani!Abu d’aya da ya ke da tabbacinsa shine idan ta riga ta haihu duk inda take indai a cikin duniyar nan ne to zai nemo ta kuma ya karb’o d’ansa, daganan kuma ita da shi har abada wallahi. Maganar b’ata suna kuma ta je ta yayata ɗin, dan shikam tunda har ya sab’awa Ubangiji sannan Iyayenshi y’an uwanshi da Manubiya kowa ya san abunda ya aikata to tsoro ko kunyar ubanwa kuma zai ji?? Wallahi ba ya shakkar ta d’auki loudspeaker ta hau helicopter ta yi Yekuwaaa! sam hakan ba zai damesa ba,bai damu da mutane da abunda za su ce ba…kawai dai ya san duk shekarunsa da k’arfin tunaninsa bai Isa ya hango abunda su Ddaddy suka hango ba, shiysa ya yi putting maganar tasu into consideration. Tunda ya taho yake addu’a Allah Ubangiji ya sa kar Manubiya ta amince, dan wallahi ba ya jin zai iya shak’ar numfashi muddin akace Kausar ta zama matarsa…ya ma san manu ba za ta yarda a yi mata kishiya ba, ta na son shi ba zata amince ya auri wata ba duk runtsi ,kuma zai yi ta nuna mata hujjoji har ya yi convincing d’inta. Tunda ya taho, ya ke jin yadda wayarsa wadda ke a aljihu take ta faman vibrating… Ganin an jera masa misscalls sama da ashirin ne yasa ya hak’ura ya zaro wayar zai amsa shi a tunaninsa ma daga gida ne amma sai ya ga bak’uwar number…tana katsewa ya fara shirin mayar da wayar aljihu saboda driving yake yi bayaso ya rik’e wayar a Hannu gudun samun distraction, kamar gizo haka yaga message ta notification bar an rubuta”ka duba watsapp, an turo maka shaidu akan wanda ya saka aka kaiwa Estate d’inka hari duk dan a kashe ka.” Sai da sitiyarin motar ya kufcewa Yashjub, da mugun sauri ya rik’e! Allah ya rufa asiri bai bugu ba bai bige kowa ba, dan haka ya yi sauri ya yi parking a gefen kwalta yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa zuciyarsa tana tsinkewa kansa kuma yana juyawa. Wata zuciyar tana hanasa bud’ewa dan bai san mai zai gani ba sannan wa zai gani ba! Yayinda wata zuciyar take azalzalarsa akan ya hau ya gani. Sai da ya yi addu’o’i ya ce ‘Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi’ tukunna ya danne zuciyar da ta ke hanasa bud’ewa..tashi d’aya ya kunna data ya hau Online k’irjinsa yana wani tafarfasa a lokaci guda kuma yana tunanin to waye wannan mai turo evidence haka ko dai tsokanarsa ake yi ana so a raina masa wayo…. to amma ai ba kowa bane ma ya san a na binciken. Sai da messages suka gama shigowa tukunna ya hango number da ta kirasa d’in a ta chan k’asa ga kuma video nan alamun an turo tun d’azu, da messages wajen ashirin a cikin chat d’in. Yanzun ma sai da ya yi da gaske tukunna ya shiga chat d’in ya yi scrolling chan sama ya fara daga farko inda aka turo abubuwa har wajen guda biyar aka goge,kafin a sake turo bayanai da pictures da videos. Maganar farko da idanunsa suka fara yin tozali da ita itace”K’aninka jininka Yassir Imam kura shine ya haye mu ya bamu hotonka ya bada bayanan ka ya tsara mana yadda komai zai tafi a tsari domin mu samu mu kasheka. A k’asa idan ka yi downloading za ka ga komai za ka ga yadda ya bamu kud’i da duk wani shiri da muka yi tare da shi.” Wani irin jifa Yashjub ya yi da wayar jikinsa yana wani irin karkarwa!!ba dan kan kujerar mai zaman banza wayar ta fad’a ba da tuni ta tarwatse!!!! Wani irin karkarwa da huci ya shiga yi yana jin yadda numfashinsa yake shirin d’aukewa! Da kyar a hankali a fili ya shiga cewa”innalillah wa inna ilaihirrajiun, ya Allah kasa hakan ba gaskiya bane ba!”. Ba shi da wani zaɓin da ya wuce ya sake lalumo wayar ya yi downloading ya bud’e ya kalla videos ɗin saboda yadda aka taso masa da tashin hankalin nan idan ba ganin ya yi ba ya tabbatar ko kuma akasin hakan tou ya san tsaf nan da y’an mintuna zai iya samun heart attack…….. Hakanan ya lalumo wayar ya bud’e ya shiga downloading hannayensa suna wani irin mugun karkarwa… da kyar ya danna play, yana addu’ar Ubangiji ya sa kar ya ga Yassir amma sai dai kash!videon yana fara tafiya fuskar Yassir ce farkon abunda ya fara gani ya kuma fahimta,tare da mutumin da yake custody d’insu da wasu guda biyar!! Yassir d’in ya na yi musu bayani dalla dalla yana jaddada musu kar fa a samu matsala su tabbata ya mutu. D’ayan videon kuma inda yake basu mak’udan kud’ad’e ne sai ragowar kuma call recoding ne wanda ya k’unshi yadda suka dinga communicating, har wayar da suka yi d’azu yace su goge suka yi negotiating akan zai basu 3m duk sai da suka tura da receipt d’in 2 da 1m d’in da ya turo daga baya…….. So yake yi ya yi kuka, hawaye su zubo daga cikin idanunsa amma k’aff!!yau kam babu hawayen sun k’afe sun k’are… Wani Irin jaa!idanunsa suka yi, jijiyoyin kansa duk suka baiyyana…so yake ya k’aryata amma babu hanya dan idan ya ce fuskar Yassir aka saka bai Isa ya ce muryar ma sakawa aka yi da yanayin maganarsa ba….. Ya fi awa biyu a cikin motar, dan har sai da Manubiya ta fara waya sakamokon daren da ta ga yayi,tukunna ya kira driver d’insa ya kwatanta masa inda yake. ya zo ya d’auke sa suka nufi gida dan kwata kwata ba zai iya yin driver d’in ba. Shi kansa driver d’in sai da yanayin Yash ya bashi tsoro!Kamar wani zombie d’in robot haka ya zama, da kyar ma ya chanja waje ya koma mazaunin mai zaman banza. Ko da suka isa gida ma bai sani ba har driver d’in ya zagayo ya bud’e masa ya ce masa”mun iso” har sau hud’u tukunna ya yi firgigit ya d’an kallesa kafin kusan bayan mintunan uku ya samu da mugun kyar ya motsa ya fito ya nufi k’ofar entrance. Ba zai iya komawa ya d’auko key a cikin mota ba dan haka ya tsaya yana danna doorbell.. Lokacin da ya dawo Manubiya tana kitchen tana k’arasa soya wainar fulawar da suke yi ita da Siyama kafin su Ya Nafi’u su zo su d’auketa ta tafi.….jin door bell ya sa ta yi tunanin ko dai su Siyaman ne suka dawo maybe sun yi mantuwa dan basu dad’e da tafiya ba. Da wannan tunanin ta fita dan sam ba ta kawo Yash bane da kansa ya tsaya yana danna bell maimakon ya bud’e kawai ya shigo. Manubiya tana bud’e k’ofar suka yi ido biyu da shi a hargitse..dan fuskarsa ta yi jaaa idanunsa ma haka, jijiyoyin kansa sun fito sannan gaba d’aya babu nutsuwa a tattare da shi. Yana ganinta sai ya sake karaya tashi d’aya ya zama emotional cikin tsananin damuwa da neman agaji ya fad’a mata a jikinta ya fashe da kukan da ya nema ya rasa d’azu!jikinsa yana wani irin karkarwa har abun tsoro. Duk k’ok’arinta kasa rik’esa ta yi dan ya yi mata nauyi…a wajen suka zube nan bakin k’ofar ko rufewa ba su yi ba….tsoro da al’ajabi ne suka sanyata fashewa da kukan itama tana yi tana tambayarsa “me ya faru??” Shiruuu, bai ce komai ba, dan ya kasa magana, ya kasa cewa komai kawai ya k’ank’ameta yana kuka bilhakk’i da gaskiya. Sun jima a wajen sosai, kafin ta ji ya shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere yana wani irin numfashi…. Cikin sake fashewa da kuka tace”Ya Yash dan Allah ka fad’a mini koma menene, kana dad’a tsoratani fa!” Ahanakali ya d’an cikata har yanzu jikinsa bai daina karkarwa ba…da kyar suka mik’e da taimakon juna,ya tura k’ofar ta rufu tukunna suka k’arasa cikin parlourn suka zauna ya ruk’o hannuwanta duka biyu ya runtse su a cikin nasa….. Sau biyar yana bud’e Baki da niyyar yin magana amma sam sai ya kasa. Ajiyar zuciya ta sauk’e k’irjinta yana dukan uku uku tace “duk runtsi, sannan a ko da yaushe zan tsaya maka kuma zan goyi bayanka akan dukkan komai! Da ni da kai ba za a ji kanmu ba! Dan haka Ka yi mini magana Mijina, dan Allah ka fad’a min ko ma menene.Mu nemo mafita mu magance matsalar tare.” Da kyar ya samu ya iya bud’e Baki ya shiga yi mata bayani daki daki a kan case d’in Kausar, komi abunda ya faru yau sai da ya zaiyyane mata. Kafin yace”duk abunda kika ce hakan za a yi, amma dan Allah dan Annabi kar ki ce in aureta,wallahi ba zan iya rayuwar aure da ita ba!” Manubiya ba ta iya cewa uffan ba tsabar matsanancin tashin hankalin da ta shiga…shin wannan ɗin mafarkine take yi?? Da gaske wata ce take d’auke da cikin Mijinta a jikinta!kuma ake shirin aura masa ita?!! Yashjub d’inta fa!inaa!!!duk kawaicin ta ba zata iya ba wallahi ba za ta iya ba!!!! Ashe dama haka mata suke ji idan za a yi musu kishiya?ashe kwanakin baya da ta ji kishi da haushin Kausar duk wasa ne!! Dan sai yanzu ne ta san menene kishi! ta kuma san zafin sa ta san yadda ake ji…wani irin feeling take ji feeling d’in da ko mak’iyin ta ba za ta so ace ya ji ba! Ji take yi kamar ta yi hauka!!! ji take kamar za ta mutu!! Hatta b’argo da tsokar dake a jikinta yau kam tabbas sun san tana cikin masifa…. Yanayin da ta shiga ya isa ya sanya Yashjub ya fahimci amsar ta ‘a’a’ ce, dan haka cikin tsananin farin ciki ya rungumota yace”na ji dad’in wannan decision d’in naki,na ji dad’i….” A hankali jikinta da kwakwalwa da zuciyarta har yanzu suna kan karb’ar azaba tace”a yi mata adalci,na yarda ta zo nan ta zauna da mu har zuwa lokacin da za ta haihu…daga nan idan Babynta ya yi wayo zan rik’esa kamar ni na Haifa da zuciya d’aya, ba na son Kausar amma na yarda ta zo ta zauna da mu zan jure! zan jure komai banda kasancewar wata mace matarka Ya Yash!!!” Ta k’arashe maganar cikin fashewa da kuka… Wani irin sauk’i Yash ya ji, dan ya san su Daddy idan suka ji wannan shawarar da Manubiya ta bayar Hatta Mommy duk za su ji sauk’i suma kuma an yiwa Kausar ɗin adalci tunda har za ta zauna a gidansa ya d’auki d’awainiyar ta har ta haihu ai kuwa an yi adalci, kuma itama Kausar d’in ya san tunda ba ta riga ta san su Daddy suna shirin had’asu aure ba tsaff za ta yarda da shawarar Manubiya….ko dan ta zo ta zauna gida d’aya da shi. ya san za ta so ta yi abubuwa da dama idan ta zo d’in amma InshaaAllah shi kuma ba zai bata fuska ba, kuma zai taka mata burki, ba zai bata dama ba. Cikin samun sauk’I ta b’angaren case d’in Kausar ya sake rungumo Manu ya sumbaci goshinta sannan ya share hawayenta tukunna yace”inshaaAllah ke kad’ai ce mace d’aya tak Matar Yashjub,inshaaAllah.” Ajiyar zuciya ta shiga sauk’ewa kafin ta d’aura kanta a k’irjnsa ta yi shiruuu. Dukda tana jin tsananin tashin hankali idan ta tuna Kausar tana d’auke da ciki amma ba ta kishi da Yaro ko Yarinyar da za ta haifa tunda ba laifin sa/ta bane ba,InshaaAllah zata rik’e da zuciya d’aya dan ba ta Isa ta tsani d’an Yash ba, ta san ba ma za ta iya ba….amma Kausar kam!wani kalar zafin kishinta ne yake azalzalar zuciyarta ji take yi kamar ta je ta sameta ta shak’eta!. Sun jima a haka kafin ta ji yace”na san da maganar binciken da kuke yi ke da Yaha a kan case d’in estate d’ina…na gode sosai Allah ya saka muku da alkhairi, na ji dad’i matuk’a da na ji batun kuma na yi farin ciki amma daga yau ku dakatar da komai ku daina.” Ya k’arashe maganar muryarsa tana kakkatsewa kamar zai fashe da wani kukan. A hankali ta d’ago ta kallesa tace”meyasa?” “Saboda na riga na san waye” Ya bata amsar hawaye suna masu saukk’o masa kafin ya zaro wayarsa ya shiga chat d’in ya kunna mata ya mik’a mata, ita kuma ta karb’a… A hankali ya sa hannu biyu ya dafe kansa yana mai zubar da hawaye….da d’an sauk’i da ya kasance ba Mahifiyarsa Mommy bace ba,amma fa dukda haka masifa da tashin hankalin da ya shiga da ya fahimci Yassir ne babu sauk’i. Tabbas dama Manubiya tunda akace insider ne (na jikinsa ne) Yassir ta zarga a karon farko, amma dukda haka itama sai da ta shiga shock ba na wasa ba. Kasa ma magana Mannubiya ta yi, gaba d’aya tausayin Yashjub ya rufe ta tun bama da ya fara magana cikin d’acin zuciya abun tausayi ba!”amma ni kad’ai ne mai irin d’an uwan nan ko?babu wani d’an uwa da na tab’a jin labarin ya aikata hakan ga d’an uwansa uwa d’aya uba d’aya!!babu shi. Ji nake kamar zuciyata za ta fashe!!shiyasa fa case d’in farko na k’i yin bincike saboda in gujewa wannan tashin hankali da azabar da binciken nawa ka iya haifarwa…!!! Abun da matuƙar azabar ciwo sannan bashi da daɗi kwata kwata, ace wai naka ne yake son ganin bayanka! me na yi wa Yassir haka! Ya za a yi ya tsaneni to this extent??? me ya yi zafi har haka?.” A hankali Manu ta rungumesa itama tana hawaye ta shiga shafa bayansa alamun rarrashi. Suna zaune a haka wayarsa ta d’au k’ara!! Sai da aka kira sau uku tukunna ya zaro wayar Da kyar! Da kyar ɗin ya iya karanta sunan Ummi tsabar masifar da yake ciki, a hankali ya amsa ya kara a kunnensa yace”Hello Ummi” Cikin hargitsi da b’acin rai ya ji Ummin tana cewa “Yashjub kana Ina?ka zo yanzunnan,Daddynku yanzu suka gama d’aura maka aure da Kausar.” Kashe wayar kawai ya yi ya ajjiye a gefe ya runtse idanunsa da mugun k’arfi yana jin kansa kamar ba a jikinsa ba! Yana cikin wannan yanayin ya ji k’arar fad’uwa… A mugun rikice ya bud’e ido yana kallon Manubiya da ke yashe a k’asa kan kafet. Sai da numfashinsa ya d’auke, da kyar ya dawo, a take jikinsa ya d’au wani mahaukacin karkarwa. Tabbas ya san abunda aka fad’a ta ji dan wayar tasa tana da murya sosai!!shiyasa tashi d’aya wani sabon tsanar Kausar ya lullub’esa…haka kurum Yarinya ta bi ta d’aga musu hankali babu gaira babu dalili!!!! bai san lokacin da ya shiga tsinewa Kausar albarka ba!. Da hanzari ya rufarwa Manubiya…wadda sai da ya k’ura mata ido sosai tukunna ya lura Ashe ba suma ta yi ba tsabar tashin hankali ne ya sanya ta yanke jiki ta fad’i. Shafa fuskarta ya yi a hankali ya mik’ar da ita ya rungume, ya ce”kar ki bari hakan ya d’aga miki hankali dan Allah saboda Abu ne wanda ba zan tab’a aminta da shi ba” Daga haka ya sa hannu ya d’auki wayarsa…da kyar ya nemo number Kausar a wani group na y’an gidan nasu… A take kuwa dan bai ɓata lokaci ba ya tura mata message daga garesa mai d’auke da saki guda biyu kwarara! Ta watsapp da ta sms duk ya haɗa ya tura mata, da niyyar gobe da safe zai ce ya mayar da ita sannan atake ya sake sakinta, shikenan!!! Ya san idan ya yi uku lokaci guda tsaff za a mayar masa da shi d’aya. Lokacin da Yashjub ya yi sakin, su Kausar suna zaune ita da su Yasira suna zab’ar gado a wayartata messge d’in ya shigo, ta sama duk suka gani amma ba sosai ba dan kad’an suka gani…cikin tsananin tashin hankali Yasira ta amshe wayar ta bud’e gaba d’aya saƙon dan Kausar ta kasa bud’ewa…da kyar ta lek’a suka karanta a tare su duka….. tashi d’aya ta zube a kan gadon ta fashe da wani irin kuka. Salati duk sukayi, Yasira ta mik’e ta k’arasa ta nunawa su Mommy waenda suka mik’e tsaye a tare suma sakamokon salatin da suka ga suna yi da kuma kukan Kausar da rikicewar da suka ga duk sun yi. Suna gama karantawa Mommy ta kalli Ya’isha da Yasira tace “su biyo ta” kafin ta kalli Baba larai tace”bari mu je mu dawo,incase idan Daddy ya tambayi ina ina kice na sha magani na kwanta, Idan kuma sun ji an fita sun tambaya ku ce su Yasira ne suka tafi siyowa Kausar magani…” Tana gama fad’in haka suka saka kai suka fice su uku, ragowar kuma suka ci gaba da rarrashin Kausar. Ya’isha ce ta biya side d’inta ta d’auko musu hijabai, dan Mommy ba ta da kuzarin wannan,daganan ta taho da makullin motarta ta mik’awa Yasira…daga haka suka sauk’a k’asan. Dama Yasira ta san gidan Yashjub suka nufa aikuwa tana kunna motar Mommy tace mata”gidan Yashjub za mu je.” BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 39* Lokacin da su Mommy suka isa gidan, su Yashjub suna chan sama d’akinsa, shi yana wanka Manubiya kuma tana zaune a kan sofa ta fara jiyo k’arar door bell!. Kusan minti biyu suna a tsaye ba’a zo an bud’e ba, dan haka suka fara danna masa call ta wayar Mommy… Wanka yake yi alokacin shiyasa Manu ta d’auko Hijab d’inta ta sauk’o. Sai da ta lek’a ta y’ar b’ular jikin k’ofar, tukunna ta sa Hannu ta bud’e k’irjinta yana wani irin bugu dan tana ganinsu Hankalinta ya tashi zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa. Har k’asa ta durk’usa tace”Mommy Ina wuni” Ba tare da ta kalleta ba ta wuce kawai ta nufi sama tana mai cewa”Ya’isha duba mini k’asan ko yana nan, in baya nan ki hawo mu duba sama”. Tana gani Ya’isha ta k’araci dube dubenta ta zo ta haye saman suka barta nan bak’in k’ofar a durk’ushe dan tun d’azu ta kasa tashi. Da kyar ta samu ta mik’e, ta tura k’ofar ta mayar ta rufe, daga haka ta shige d’akin bak’i na nan k’asan, tana shiga ta fashe da wani irin kuka….A yadda ta ga Mommy ta zo a zuciyen nan ta san ko dai ta saka Yashjub ya mayar da Kausar, ko kuma ta sa itama a sake ta.! Ya fito kenan d’aure da towel kawai ya ga sun shigo su duka ukun. “Subahanallah” ya ambata, daga haka ya juya ya koma cikin closet d’in da sauri hankalinsa a tashe ransa a mugun b’ace….ita kanta Mommy yana da tabbacin ba ta tab’a ganinsa a haka ba da girmansa ballantana su Yasira, sannan yadda ya ganta a gidansa a cikin bedroom d’insa haka ya san ba alkhairi ne ya kawo ta ba, amma fa yau sai dai duk abunda zai faru ya faru dan shima a high yake…. Yana wannan tunanin ya zura jallabiya bai zare towel d’in ba ya fito fuskarsa a mugun murtuke kamar bai tab’a dariya ba. Idanuwansa waenda har yanzu kalarsu bai daidaita ba ya zubawa su Yasira kafin yace”ku fita ku bani guri!!!” “Ba inda za su fita su je!! Ai idan za a yi tsinuwa ana buk’atar wasu a wajen, saboda su bayar da sheda!!!” Zuwa yanzu jikin Yashjub ya fara karkarwa…ya zubawa Mommy idanu kawai ya gagara cewa komai, kafin ya yi taku biyar zuwa shidda ya k’arasa ya tsaya a daff da ita har tana jin hucin numfashinsa yace”Mommy saboda na saki Kausar shine za ki tsine mini????” Ta d’an tsorata, dan yanayinsa na yanzun yanayine na wanda yake cikin tsananin b’acin rai, capable of anything(a shirye wajen iya aikata komai ma). sannan taga kamar furucin nata bai yi wani tasiri a kansa ba, amma sai ta dake!! cikin sake son cin nasara a kansa tace”kwarai ma kuwa Yashjub! Na rantse da girman Allah, Wallahi, Tallah, billahilazim..idan har baka mayar da Kausar ba a yanzu a take to sai na tsine maka, ka bi duniya!!!. Tun muna daga mu sai kai, tun kafin duniya ta ji!su Daddy su ji! ina so ka mayar da Kausar matsayinta na matarka. idan kuma ba haka ba to sai na yi maka Allah ya Isa nonona da ka sha!”. A hankali Yasira wadda jikinta ya yi sanyi ta fara tsorata dan sam ba ta kawo abunda suka zo yi ba kenan,ta matso jiki ba kwari tace”Mommy kar ki yi haka, a nemo wata mafita amma banda wannan.” Wani irin kallo Yashjub ya yi mata kamar zai yi magana, sai kuma ya kauda kai yace “Mommy ni da kaina na tab’a kama Kausar da Yassir a side d’inmu, shiru kawai na yi muku ban fad’a ba!, shin ta ya kike so In yi zaman aure da dadiron k’anina?… A ganina Kausar ta haramta a gareni, dan Allah ki ma janye wannan maganar saboda anzo in da ba zan tab’a yin abunda kike so ba.” Jinjina kai ta yi kafin tace “ko da ace zan tsine maka ko?” Cikin d’an d’aga murya yace “Mommy are you not listening to me?…shin ba kya jinnabunda nake faɗa ne?… Kama ta fa na yi on bed! red handed!! turmi da taɓarya ita da Yassir, ta ya zan rayu da ita a matsayin matata??” “Allah na tuba kana Ina Wa(Yaya) yake sakin Mace k’ani ya aura?!ai ba wai ance haramun bane kawai Halak ake bari dan kunya. Saboda haka dan ka ga Kausar da Yassir wannan tsakanin su ne su da Ubangijin su,kai kuma kai ne wanda duniya ta sani a matsayin Mijinta! Dan haka wannan duk bai shafeka ba!!!!” Mommy ta fad’i hakan tana huci. Cikin d’aurewar Kai haushi, bak’in ciki da tsananin mamaki yace “bai shafe ni ba idan Kausar ta kwanta da ƙanina??? bai shafeniba dan ta kasance karuwa?? Mommy wacce irin uwa ce ke!? Da har kike k’ok’arin ignoring (kike ƙoƙarin share) duk waennan facts d’in (haƙiƙoƙin) saboda kawai ki farantawa Kausar.” A hankali yana kallonta yace “anya Mommy kin san ciwo na kuwa?? kin san zafi na kuwa? wannan rashin adalci haka har ina?ko dai inada wata uwar daban ba ke ba??!!!” A rikice ta d’ago tashi d’aya ta d’aukesa da wani gigitaccen Mari! Sai kuma ta fashe da kuka… Cikin kukan tace”Wata tara ciff ka d’auka a cikin cikina, bayan nauyinka na wata tara haka na kawo ka duniya bayan na sha tsananin wahalar nak’uda! Na shayar da kai na tsawon shekaru biyu.. kashinka, fitsari, tumbid’i duk ni ce mai wankewa mai gyarawa. Sai da ka yi watanni shidda a duniya tukunna ka fara baccin dare, wanda a ta dalilin hakan ne ya janyomini na kamu da ciwon hawan jini, tsabar rashin samun ishashshen bacci. Idan baka da lafiya in kwana a zaune, in wuni a zaune cikin damuwa har sai naga ka warke!ƙiriniyar k’uruciyarka babu kalar wadda ban gani ba, babu wadda ban sha ba amma yau ni ce nake gaya maka abu kana yi mini musu! Ina fad’a kana fad’a Yashjub har ta kaimu ga kana iya kallon cikin tsabar idanuna kana cewa ‘ba ni na haifeka ba!!’ Ka san yadda maganar nan ta sanya ni na ji kuwa? Auren Kausar fa a k’arshe duk kai na ke k’ok’arin yi wa gata amma ka kasa fahimtata!” Ta k’arashe maganar tata cikin fashewa da wani Irin kuka.” Duk shiruu suka yi kafin su Yasira su fara rarrashinta..ganin yadda shima ya yi shiru kamar maganganunta sun yi tasiri akansa ne ya sanya ta goge hawayenta tace”tunda ka ce ban yi maka adalci ba, to ka saurara ka kasa kunne ka ji ga adalci nan zan yi maka… ko dai ka saki Manubiya itama, ko kuma ka dawo da Kausar! A cikin biyun nan ka zab’i d’aya ka aiwatar, na baka mintuna biyu kawai kacal idan kuma ba ka yi ko d’aya ba mintuna biyun nan suka cika Yashjub Allah ya Isa ban yafe maka ba!” Runtse idanuwa Yashjub ya yi da mugun k’arfi, a take wasu hawaye suka zubo masa. Ba tare da ya bud’e idanun nasa ba ya ce mata”ki yi hak’uri!!na dawo da Kausar.” Cikin tarar numfashinsa tace”na gode! Kuma inaso ka sani Muddin ka sake sakinta b’acin ran da za ka fuskanta sai ya fi na yau wallahi!!!” Sannan gobe inshaaAllah za ta tare, ba ma buk’atar ka yi sabon gida ballanta ka tafka rashin adalci! a nan za ta zauna d’akinta kusa da na Manubiya, idan na ga kamun ludayinka daga nan zan yi deciding idan ware gida za a yi,ko kuma Babba za ku chanja wanda ya fi wannan….” Tana gama fad’in haka ta juya ta fice su Yasira suka mara mata baya..Yasira jiki ba lakka Ya’isha kam abun ba k’aramin dad’i ya yi mata ba. Har suka fita bai bud’e idanunsa ba, yana nan a yadda yake…..har Manu ta hawo saman bayan ta ga fitar su ta ta rufe k’ofa, yana nan bai motsa ba. Yanayin yadda ta gansa kad’ai ta san ba lafiya ba. Ta dai san ba sakinta ya yi ba, dan inda ace sakinta ya yi to da tuni su Ya’isha sun nemota a gidan sun yi mata tujara..amma in ba da kyar ba tanada tabbacin Mommy ta saka shi ya maido da Kausar ne. A hankali cikin tsananin k’arfin hali ta k’arasa garesa, tana zuwa ta kamo hannayensa duka biyu ta ja shi… Bai yi mata musu ba ya bita suka zauna a kan sofa, a hankali ta mtsa jikinsa ta rungumesa tukunna cikin son kwantar masa da hankali tace”all will be fine..(komai zai daidaita)wata rana sai dai labari..ka kwantar da hankalinka…” Cikin tarar numfashinta yace”Mommy ta saka na mayar da Kausar,cewa tayi idan ban mayar da ita ba za ta tsine min.” Tunda ya fara magana Manubiya ta fara hawaye..yana iya jin yadda jikinta yake vibrating, k’irjinta kuma yake bugawa sosai shiyasa tashi d’aya wani matsanancin tausayinsu ya lullub’esa. Manubiya ji take yi kamar za ta mutu..kishi, tashin hankali da komai ma duk sun lullub’eta, amma kuma ba za ta biyewa son kanta ta je ta kai Mijin da take masifar kishin da so wuta ba! Indai har tana son Yashjub da gaske to za ta so su rayu har a Aljannah a tare ba wai ta bashi kwarin guiwar da zai tafi wuta ba,dan haka ta tattaro duk wata jarumta da k’ok’arinta da juriya ta fara magana”Ya Yash na gaya maka duk abunda ka ga Allah ya tsara hakan shine mafi alkhairi, ni kam na hak’ura babu komai zan zauna da kishiyar.. Na gaya maka ai, koma menene indai a kanka ne to duk zan jure..ni da kai ba za a ji kanmu ba, dan haka ka kwantar da hankalinka kar ka damu ina tare da kai duk rintsi, we will survive this, together!. dan Allah kar ka sake yin jayayyya da su Mommy, ba zan so ka tafi wuta ba….” Wani irin kuka ne ya taho mata wanda ya katse mata maganar tata…dama tunda ta fara maganar muryarta ta shiga rawa tana kakkatsewa. K’ank’ameta Yashjub ya yi, k’irjinsa yana wani irin mahaukacin gudu. Sun jima a haka kafin yace”ki fara had’a kayanki” Da farko ba ta fahimci inda zancen nasa ya dosa ba sai daga baya,dan haka tace”Ya Yash we can’t just pack up and leave..ko ba komai Kausar matarka ce akwai hakki…” Cikin tsananin b’acin rai ya zuba mata jajayen idanunsa yace”idan kika sake cewa Kausar matata ce za ki ga b’acin raina”. Shiru ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa wanda hakan ya sanya ya ruk’o hannunta duka biyu yace”Mannubiya muma fa mun chanchanci mu yi farin ciki… Annabi Muhammad sallahu alaihiwasallam da kansa a lokacin da aka nuna ba a sonshi Hijara ya yi daga Mecca ya koma Madina!. Ki duba fa kiga, Yassir raina ya ke nema! Mommy tana so ta had’a ni dole in yi zaman aure da dadiron ƙanina! sannan sisters d’ina suma bangama yarda masoya na bane ba! Tsoro nake ji ma in duba abunda na ke son dubawa a kansu saboda na san kamasu zan yi da laifin. Ki gaya mini abu guda d’aya! Dalili kwaya d’aya tak da zai sanya in ci gaba da zama a cikin Mutanen nan? sun nuna ba sa so na ba sa sonki, so kike yi mu ci gaba da zama a haka har sai bak’in ciki ya kashe mu???” Bai jira ta bashi amsa ba ya ce “we deserve to be happy..sannan I’m not suppose to make you cry baby, idan ban cika alƙawarin da na ɗaukarwa kaina na sakaki a ƙololuwar farin ciki ba to bai kamata in sakaki a cikin matsanancin tashin hankali ba.” “Cikin kuka sosai kamar ranta zai fita tace”Rayuwarmu a nan take, bani da mafarki da burin zuwa k’asar wasu in yi rayuwa.. A nan muka had’u da kai Ya Yash ba ni da burin da ya wuce in rayu a nan in tsufa a nan…...” A hankali ya yi cupping fuskarta a cikin tafukan Hannayensa sannan yace”Mannubiya idan akwai lokacin da nake buk’atar asalin zallar goyon bayanki to yau ne! dan Allah dan Annabi kar ki yi mini turjiya. Ba na buk’atar musu ko wani sabon Abu negative(korau), na riga na cika dayawa! Matakin ƙarfin juriyana ya kai k’arshe….ba zan iya sake jurar wata matsalar ba…dan Allah please ko me nace miki kawai ki ce mini ‘to’dan Allah” Ya fad’i hakan hawaye suna masu zubo masa. Wani irin kuka ta sake rushewa da shi, ta rungumesa ta na mai jinjina kanta alamun ‘to’. …….. Najeeb Yashjub ya kira, ya ce masa “dan Allah ya zo yana da buk’atar ganinsa”. Daga nan ya fara nema musu flight d’in Abuja kafin ya yi musu arranging barin k’asar gaba d’aya. … Komai na companies d’insa da ke a nan Nigeria Najeeb ɗin ya d’aura a kai, tukunna yace masa ”ya riƙe masa dan Allah, zai yi tafiya na tsawon wani lokacin, ya rik’e masa amana.” Najeeb bai yi niyyar yi masa maganar ba, dan shi kansa kunyar abun da kuma tausayin Yash ɗin yake ji, amma kuma sai ya ga bai kamata ya b’oye masa cewar ya sani ba, dan haka cikin tsananin jin tausayin Abokin nasa ya dafa kafad’arsa tukunna yace “ba a kanka aka fara ba! Komai ya yi zafi maganin sa Allah.” D’an k’ura masa Ido Yash ya yi kafin ya d’auke kai ya fesar da iska yace”kai ma sun tura maka kenan!” Jinjina Kai Najeeb ya yi ya ce ”a tare suka tura mana! Na san ba za ka so ka zamo wanda zai fallasa abun har a kai ga kashe Yassir ba shiyasa na yi shiru ban yi maka maganar ba kawai!.. Haka suma masu bincike ban ce musu mun gano komai ba amma dai na ari Bakinka na ce musu mun zare hannunmu a binciken, sai dai kuma iyalan waenda aka karkashe a Estate d’in naka gaskiya sun kunno wuta sosai, dan bincike sosai suke yi! cewa ma ya yi ‘ko mu mun janye, yanzu haka sama da mutane ashirin ne tsaye tsayin daka a kan case d’in.’.” A hankali Yashjub ya sunkuyar da kansa k’asa, ya yi shiruu kafin ya d’ago ya ja hanci yace “kar ka gayawa kowa inda nake dan Allah…ba wai iyaka Yassir ne dalilin da ya sanya zan tafi ba” Sai da ya yi shiru ya sake jan hanci tukunna yace”Yau su Daddy suka aura min Kausar….” Dalla Dalla ya gayawa Najeeb bayanin komai da dalilinsa na k’in zama da Kausar…tashi d’aya Najeeb d’in ya goyi bayasa d’ari bisa d’ari. Sai asubah tukunna suka gama shiryawa da had’a kan komai.. Kamar kar su rabu haka Yash da Najeeb su ke ji, Najeeb har da hawayensa dan mugun mugun tausayin Yash ɗin yakeji… hakanan suka yi sallama daga haka driver ya d’auke su zuwa hotel bayan Yash ya damk’awa Najeeb makullan gidan ya ce masa ‘da safe ya kaiwa su Mommy’ dan ta ce za su kawo Kausar. Dalilin ma da ya sanya ya k’i amincewa su zauna a cikin gidan kenan, gudun kar su ce za su kawo masa ita da safe. Sai washegari da safe tukunna Ummi ta samu ƙarfin halin iya tunkarar Hajiya Mama…har ga Allah Hajiya Mama ta yi tunanin Ummi wasa take yi mata da farko, dan kwata-kwata ba ta tab’a tunanin su Daddy za su tafka wannan kwab’etar ba! daɗin daɗawa ba tare da sun shawarceta ba. Sai da ta saka Ummi ta rantse mata tukunna ta yarda, Hankalinta a mugun tashe ranta a masifar b’ace ta kalli Ummi wadda ta fara dibi-dibin bata Baki tace”ke kanki kinsan babu ta inda za ki ce mini hakan ya dace ko?” Shiruu Ummi ta yi, ta sunkuyar da kanta k’asa. Ajiyar zuciya Hajiya Mama ta sauk’e kafin tace”to dan haka ki yi shiruu kawai, kar ma ki bawa kanki wahala.” “Ina shi Yashjub d’in yake, ya sani??a gaban sa shima aka d’aura??” A hankali Ummi tace”a’a..na dai kira na gaya masa nace ya zo a san abunyi, to dai tun jiyan bai zo ba yau kuma inata kiran wayarsa amma daga tashi har ta Manubiyan duk ba ya tafiya.” Jinjina kai Hajiya Mama ta yi,fuskarta har ta yi jaaa! Ta kalli Ummi tace”ki kirawomin su Imam d’in, ki ce na ce su zo yanzunnan!” “Tam”Ummi tace, daga haka ta mik’e ta sa kai ta fice. Ba’a yi mintuna goma ba, Daddy ya shigo da shirin tafiya office, Abhi wanda ke biye a bayansa kuma da jallabiya. Ko gaisuwar su ba ta amsa ba, ta kalli Daddy ta ce ”ashe har kana iya tafiya office bayan masifar da ka k’ulla a gidanka jiya??” A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”ki yi hkr Hajiya Mama, dama yanzu nake shirin shigowa mu tattauna kafin in wuce!” Cikin fushi tace”Imam tattaunawa kuma ta nawa? Sai da ka gama yanke decision da kai da munafuka!muguwa!!makirar matarka!!!!tukunna za ka zo ka ce mini za mu tattauna saboda ka raina ni?? Me za mu tattauna???. Ina sauraronka gaya mini menene ya rage wanda ba ka riga ka yanke hukuncinsa ba da ya kamata ace mun tattauna?” Shiruu ya yi, ya gagara cewa komai. Cikin tsananin b’acin rai ta kallesu su duka biyun tace “da ni da ku, duk mun shirya a kan za a sakawa Khadija ido, a bincike ta, a gano ta, sannan a nunawa Yaranta illarta da illar d’abiar da ta d’aurasu a kai tukunna a sallameta a cikin gidan nan!! Amma saboda tsabar ku d’in ba jajurtattun maza bane ba, shine kuka bari a cikin awannin da basu wuce biyu ba Yarinya y’ar k’arama ‘Kausar’ da kuma Khadija suka juya muku tunani har kuka aurawa Yashjub Kausar!!!.. Daga ta yi y’ar drama da shirmenta shikenan har kun kamu??” Da kyar Abhi ya iya cewa “Hajiya mama cewa ta yi za ta tafi da Yaron. shi kuma Yashjub ko Maganarmu ba ya ji, iyaka maganar Manubiya ya ke bi da farincikinta..a jiyan fa cewa ya yi wai sai abunda ta yanke tukunna shi za a yi” Sakar Baki kawai Hajiya mama ta yi ta na kallonsa har ya dasa aya, tama kasa cewa komai. Da kyar ta iya cewa”idan na fahimce ka, kishi kenan kuke yi da Manubiya kamar wasu mataa!!!shiyasa kuka aura masa Kausar saboda kar Manubiya ta yi dominating d’insa (ta mallakesa) ita kad’ai ko?” “This is the dumbest thing da na tab’a ji tunda uwata ta kawo ni duniya wallahi tallahi! Ina tunaninku ya tafi ina hankalinku ya tafi?? Kausar faaa!!” Cikin son yi mata bayani Daddy yace”ai Kausar d’in ba fa wai mun aura masa ita forever bane, mun aura masa ita ne akan idan ta haihu sai su rabu”. Mik’ewa kawai Hajiya mama ta yi, ta nufi wajen kayanta, ta fara fito dasu tana cewa”Bari Ka ji in gaya maka,Indai Kausar ce to ba za ta tab’a rabuwa da Yashjub ba, ba za ta yarda ba!. Barr ganin wai da Yassir kuka santa,a yadda Khadija ta tsani Manubiya ba za ta bari Kausar ta bar Yashjub ba… A tunanina auren ka da Khadija ya isheka ishara! ya Isa ka gane idan aka auresu ba sa fita, tunda tun yaushe kake so ka saki Khadija ta saku???” Ta yiwa Daddy wanda ya ƙaraso ya rik’e trollyn hannunta tambayar. Ba ta jira jin amsar shi ba tace “kuma saboda ku wawaye ne shine kuke tunanin Kausar za ta yarda a saketa? Wai ma shin ina lissafinku ya tafi da Kausar d’in tace za ta tafi kuka biye mata har kuka yarda?? Khadija fa kad’ai sai Larai gareta a kaff fad’in duniyar nan, Wallahi ko ta tafi ƙarƙari ta yi wata biyu zuwa uku nasan ita da kanta za ta dawo, ko su su Larai d’in su nemota. Kuma indai Khadija ita ta haifi Yashjub to ba zata bari Kausar ta b’ata masa suna ba, dan na san duk bakin su d’aya. Abu simple!! very simple amma kuka gagara tsayawa ku yi lisssafi mai kyau sam, saboda an had’a da asiri da wayo!!!.. Saboda Allah kalli abunda kuka tafka!! Ko Shawara da ni bakuyi ba, kai da ake so a gyara gidanka a kub’utar da kai amma kalli yadda ka sake damalmala komai!!! dan ba ka isa ka ce ka rabu da Khadija ba muddin Kausar ce matar Yash…saboda ko ka kori Khadija a gidan nan indai Kausar tana a matsayin Matar Yash wallahi ka yi ta banza ne…” A hankali Abhi shima ya k’araso dan Daddy yana rik’e trollyn ta sakar masa ta cigaba da zaro kayayyakinta rai a tsananin b’aci tana magana tana had’a kaya…cikin lallami yace”Hajiya mama ki yi hak’uri dan Allah, mun yi laifi. wallahi ni kaina sai yanzu na ke ganin rashin dacewar hakan.” Juyawa ta yi ta kallesa tace”kad’an daga aikin Khadija! Ai ba za ku san lokacin da kuka d’aura ba dama…” Cikin chanja topic d’in tace”ka fara yi mini shirye-shiryen tafiya, meanwhile ka kama mini d’aki a hotel kafin komai ya kammala dan wallahi na gama zaman cikin gidan nan!” “Innalilla wa Ina ilaihirrajiun” Daddy yace, kafin ya d’aura da cewa”Hajiya mama dan girman Allah ki yi hak’uri!! ina cikin garin nan da gidana amma ace kina hotel! dan Allah ki rufa mini asiri. in dai har saboda Khadija ne to a yau za ta fita wallahi.” Ya fad’i hakan kamar zai yi kuka Cikin b’acin rai tace”kar ka soma!!!ba zai you ka koreta saboda ni ba noMatter what! sai dan halinta wanda na so in nuna maka ka runtse Ido. Ku zauna abunku kai da ita da surukarka, Allah ya kareka daga sharrinsu, zan dinga yi maka addu’a Ina daga chan…amma ba zan iya ci gaba da zaman a gidan nan ina tufka Khadija tana warware mini ba, kai kuma kana biye mata!! Ba zai yiu ba ba ni da wannan lokacin considering my age(duba da shekaruna) yanzu lokacine da ya kamata ace na duk’ufa ibada da neman gafarar Ubangijina.” “Hajiya mama a yau Khadija za ta bar gid…” Cikin fushi tace”wai Ya ina magana ba ka ji nane?? Na ce maka ban yarda ba ko? Ko shima taurin kai za ka yi mini ka nuna min iyaka ta? A gaban Yaranta za ka koreta saboda ni ko me?? Ka manta yadda muka yi ni da kai a asibiti, ka manta abunda nace maka?? B’ata mini ran da ka yi ka k’i jin maganata shiyasa zan tafi in bari ka yi komai da kanka dan ni kam na tsame hannuna!. Ka bincika komai da kanka, ka nutsu ka gyara gidanka ta hanyar da ta dace ba wai ka koreta haka kurum a gaban ƴaƴanta saboda ni ba.” Ya Bud’e baki zai yi magana tace”Wallahi zan baka mamaki fa?da musu da kai kakeso In ji ko da b’acin ran da kuka d’ura mini?” A hankali Abhi ya d’an ruk’o hannusa, alamun ya yi shiru, dan ya san Hajiya mama yau kam ta riga ta gama kaiwa high!!!! Daddy yana ji yana gani haka Hajiya Mama ta had’a kayanta tsaf tsaff, ita da Junior suka tafi tsohon gidansa dan tace ‘ko Abhi d’in ma kar ya biyo ta, shima takaicinsa take ji! idan kuma taga d’aya a cikinsu a inda take kafin ta wuce uk to sai dai ta k’arashe kwanakinta a hotel har zuwa lokacin da za ta wuce uk ɗin’ Da Yamma Yashjub ya turo mata da message ta inda yake cewa”Jiya an d’aura masa aure da Kausar ba tare da yardarsaba.! A jiyan ya saki Kausar, to kuma a jiyan Mommy ta zo ta sanyashi ya mayar da ita… Yana da babban dalilin da ya sanya ba zai Iya zama da Kausar ba, sannan akwai abubuwa da dama a halin yanzu da suke damunsa waenda suka sanya ba zai iya ci gaba da zama a gari d’aya da su Mommy ba….dan haka yana da buk’atar sarari da lokaci, dan Allah kar su nemeshi…yanada buk’atar break daga fitinar family d’insa.” Sai da Hajiya mama ta yi kuka a lokacin da ta karanta message d’in Yashjub, dan sosai ya tab’a mata zuciya!!! Ace mutum shi da k’asarsa! shi da gidan Ubansa! amma fargaba da fitintinu sun hanasa ya sake ya rayu a wajen!! wannan wanne irin abu ne haka!! Allah ya Isa tsakaninta da Mommy wallahi!… Junior ta kira tace “ya je gidan ya duba mata..idan sun riga sun tafi to ko driver ne ya tambaya watak’il su gano inda suka nufa” ba wai binsa ko fad’an inda yake za ta yi ba, kawai dai taana so ta san inda yake for her peace of mind (saboda hankalinta ya ɗan kwanta)..saboda itama ta goyi bayan tafiyar da zaiyi d’in d’ari bisa d’ari. Har daren ranar Hajiya Mama a fusace take, ta k’i ta kula kowa ta k’i ta saurari kowa, kuma tace in banda Junior ba ta so ta ga kowa a inda take!! hatta Yahanasu da ta je ba ta samu ganinta ba, dan ta rufe d’akin ma da take ciki abubuwa da tunani sun yi mata yawa. …….Tun ranar da su Mommy suka haifi Yashjub da Yahanasu ta kasa gane abu guda d’aya game da Mommy;kwata-kwata ba ta d’aukarsa ya dad’e a hannunta, kullum tana mak’ale da Yahanasu. A tunaninta (Hajiya Mama) kunyar Haihuwar fari ce ta sanya takeyi masa hakan amma sai ta lura kamar ma haushin Yaron Mommy take ji, tun ba ma da Hajiya Mama ta ga Mommyn ta ce a bashi madara ba, wai ‘ruwan nononta bai zo ba’ amma Likita yana zuwa da aka tilastata aka matso sai ga ruwan Nono fall yana zubowa… Tun daga wannan lokacin ta saka mata ido dan tashi d’aya kwakwalwarta ta bata ‘ko dai saboda maganar dukiya da Imam ya yi ne ya sanya Khadija ta musanya y’arta da d’an kishiyarta!!’ Saboda a lokacin Yahanasu da take jaririya kamanninta sun yi shige da na Baba Larai, da ta fara girma ne dai ta koma kamannin Daddy. Shi kuma Yashjub da Daddy yake kama da yana jariri amma yana fara yin wayo har kawo yanzu da Khadija amaryar Daddy yake kama, sam ba ya kama da Mommy. Har kusan shekara d’aya zuwa biyu Hajiya mama ba ta gano wata hujja da zata sanya ta ce Yashjub ba d’an Mommy bane ba saboda yadda Mommyn take yi masa babu wanda ya Isa yace ba ita ta haife sa ba,kuma a wanchan lokacin ba ta san Mommy da mugayen halaye ba,shiyasa kawai ta kawar da komai ta cire shakku ta cigaba da addu’a, sannan ta mik’awa Ubangiji lamuranta ta barshi ya yi ikonsa, dan zuciyarta ta ƙi ta daina yi mata wasi wasin ‘anya Yashjub dan Mommy ne kuwa!!?’ Gashi ita Babba ce, ba zai yiu ta tada husuma akan wannan gagarumin al’amari haka ba, azo a yi bincike aga ba haka bane gashi Ubangiji da kansa yace “kar ka tsananta bincike” Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru ta ci gaba da addu’a… A lokacin ne kuma Mai gidanta ya rasu mahaifin su Daddy, dan haka zaman ta sai ya dawo Gidan Daddy tunda shine Babba. Sai dai ko sati ba ta iya yi a gidan ba haka kurum ta ji komai ya fita a kanta, ta tsani gidan, ta tsani jama’ar gidan!! Wanda hakan ya sanya ta koma Uk da zama. Dukda tana so ta d’an saka ido akan zaman Daddy da amaryarsa saboda a lokacin dukda Daddyn ba ya yiwa Amaryar tasa abubuwa a gaban Hajiya maman amma ta fahimci akwai matsala, sai dai kuma ba zata iya zama a gidan ba dan haka ta hak’ura ta tafi bayan ta had’a su su biyu Daddyn da Amaryartasa ta tambayesu Daddy yace mata babu komai ba fad’a suke yi ba, Itama amaryar haka. Bayan shekara biyu ta zo hutu,a wannan lokacin ne ta ci karo da layu da abubuwan ban mamaki a d’akin Mommy, k’asan gadonta. lokacin Yashjub yana wasa ya tura Abun wasan nasa a k’asan gadon, ya isheta sai da ta zo ta duba ta d’auko masa dan su Khadijan duk basa nan sun fita kitso… Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba, saboda har da tsaka mai rai a cikin kwalba da abubuwa na tsafi kala kala ta gani a k’asan gadon Yarinyar da kusan rainon ta ma ita ta yi. A lokacin Mahaifiyar Mommy itama ta rasu, kasancewar Hajiya Mama babbar k’awa ga mahaifiyar Mommy kafin rasuwar ta ya sanya ta ga ba laifi bane ba idan ta kirata ta zaunar ta yi mata magana ta kub’utar da ita daga kan Hanyar b’ata da halakar da ta d’auka wanda ba ya b’ullewa. Dan haka suna dawowa ta nemi ganinta, sai da suka keb’e iyaka su biyu kawai tukunna tace mata“ta ga abubuwan da ta ajjiye a d’akinta a k’asan gado”….nasiha sosai Hajiya mama ta yi mata sannan ta jaddada mata “ ta rik’e Allah da addu’a, shi zai sa Imam ya so ta ba wai tsafi ba..a duk lokacin da ka yiwa mutum tsafi ya so ka to fa idan abun ya karye tsanar da zai yi maka sai ta fi ta farko….” Kan Mommy a k’asa lokaci da Hajiya mama take yi mata nasihar kuma daga ‘to’ sai ‘inshaaAllah’ kawai take ta cewa amma tana ji Daddy ya shigo tashi d’aya kawai sai ta fashe da kuka! kuma ya yi tambayr duniyar nan ta k’i magana, ita kanta Hajiya mama kasa magana ta yi tsabar mamaki da al’ajabi. Sai daga baya tukunna da kyar ta bud’e baki ta gayawa Imam d’in cewa “nasiha take yi mata akan biye biyen malamai”ita ba ma tace masa ta ga abu a k’asan gadon Mommyn ba!, Ita Mommyn ce da kanta tace”ai Hajiya maman tace ta ga kaza ta ga kaza a k’asan gadonta waye waye…” Har da abunda Hajiya Mama bata ce mata ta gani ba duk sai da ta lissafo kaff abubuwan da suke a k’asan gadon nata da kanta… Tana magana tana kuka! kukan da duk wanda ya gani sai ya tausaya mata. A take Hajiya mama ta ga alamun b’acin rai a fuskar Imam amma dai bai ce komai ba ya yi shiru,ganin Yarinya tana shirin shiga tsakaninta da d’anta ne yasa tace “to a je a duba” A take cike da kwarin guiwa Mommy ma tace “ta yarda a je a duba” Tun daga nan jikin Hajiya mama ya yi sanyi dan sai a lokacin ta tuna ‘ba ta gyara katifar sosai ba’ dan ba zata iya ba ta yi nauyi, dan haka wataƙil Mommy ta gani sun gane an duba wajen dan haka sun kwashe….ai kuwa hakan ne dan ana zuwa in banda k’ura da akwatuna babu abunda aka gani a k’asan gadon Mommy. Daddy bai ce mata komai ba,sai bayan kwana hud’u Allah kad’ai ya san mai da mai Mommy ta yi masa ta kuma fad’a masa tsabar an shanyesa hakanan ya zo yana ce mata wai”akwai wani Likita da za su je ta gani, idan mutum yana hallucination (yana gane gane) shi ake gani, a kaff garin Kano he’s the best” a lokacin kacha kacha ta yi masa ta koresa, amma tundaga ranar daga ta ga k’adangare a d’akinta, sai ta ga maciji!! kuma idan ta je ta tattaro mutane aka zo aka duba ba’a ganin komai! Hakanan za ayi ta kallonta ana mata kallon tab’abb’iya. Ganin Mommy tana shirin haukatata ne ya sanya ta tattara kayanta ta d’auki Yashjub tace zai je ya yi musu hutu ta tafi da shi,dan abunda Mommy ta yi mata ya sanya ta fahimci tabbas za ta iya aikata fiye da chanjin Yaro ma.Tun daga lokacin ta san yadda ta yi ta d’auke Yashjub gaba d’aya daga gabanta, dan indai harshashenta daidai ne to kuwa ta san tsaff Mommy zata iya cutar da shi ko ma ta kashe sa,tunda indai saboda dukiya ne ta musanya Yaran to kuwa bata ga dalilin da zai sanya mommyn ta barshi a raye ba! Tunda yanzu kam dukiya ta dawo hannunta, ita da su Yassir……… Yanzu kuma da Mommy ta tura su Yasira suka zubarwa da Manubiya ciki hakan ya sake assasa zarginta ta fahimci komai,shiysa ta cewa Daddy ya barta a gidan su yi bincike a kanta sosai saboda tana so ta gano gaskiyar lamari da kuma duk wasu abubuwan da ta aikata a b’oye, su samu su tara shaida a kanta ta yadda za su fi hukuntata da hujja, dan tabbas ta san Mommy ta dad’e tana cutarsu ba tare da sun sani ba..to shi kuma Daddy gashi yanzu ya sake k’ak’abawa Yashjub Kausar. Ta san ba laifin su bane ba, amma kuma ta kasa hana kanta fusata!! dole ta fusata saboda abun ya tab’ata sosai.Dan Auren Kausar da Yashjub kamar an sake kafe Mommy a cikin zuriarta ne…. Sallamar Junior ce ta katsewa Hajiya Mama tunanin da take yi, A hankali ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ta kallesa tace”ba sa gidan ko?” Jinjina kai ya yi ya zauna a gabanta tukunna yace”driver d’insa na samu yana tartare kayansa, shine ya ke ce min wai an sallameshi ne saboda Yash d’in yace masa ‘sun tashi daga gida’ Yau da asubah wai ya kaisu hotel, d’azu kuma ya je ya d’aukesu ya kaisu airport,yace bai san jirgin Ina suka bi ba.” Ajiyar zuciya hajiya mama ta sauk’e bayan ya dire aya, tace masa”ba ni wayata”kawai. Yana mik’a mata ta nemo number Daddy ta danna call ta kara a kunnenta. Ko gaisuwarsa yanzun ma ba ta amsa ba tace “Yashjub ya tafi ba ya nan,ya turo mini message ya gaya mini abunda Khadija ta je gidansa ta yi Jiya,yace min dan Allah kar a nemesa. Dan haka Ina mai baku umarnin kar wanda ya bibiyesa kamar yadda ya buk’ata, ku bar shi ya huta da bala’in Khadija da y’ay’anta. Ka ja mata kunne ka jawa su Yasira kunne sannan ka gayawa d’an uwanka shima ya sani.” Tana gama fad’in haka ta kashe wayar ta ajjiye a gefe zuciyarta tana wani irin tafarfasa. Daga wajen Hajiya mama direct gida Yahanasu ta nufa, dan tana son magana da Mommy, yau kam! ba za ta yi shiru ba!abun ya yi yawa. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 40* A d’aki, side ɗin su Yadira ta same ta ita da su suna hira… Tana shigowa duk suka d’ago suka kalleta, sai kuma suka d’auke Kai babu wanda yace mata ci kanki, hakanan suka ci gaba da hirar su. Mommy tana shirin yi mata magana ita Yahanasun ta riga ta ta hanyar cewa”Ina so za mu yi magana!” Sai da gaban Baba larai ya yanke ya fad’i, dan in ba da kyar ba a yadda ta ga Yahanasu yau kam tabbas za ta iya fasa mata kwai a wajen Mommy, kuma ta san Mommyn za ta ji haushinta. Kallon Yahanasu Mommy ta yi kafin ta d’an kalli Baba larai sai kuma ta mik’e ta nufi Yahanasun ba tare da ta saurari Yusra wadda take cewa”eh lallai rainin hankali ma kenan.”ba. Duk idanu suka zuba musu Baki sake har suka fice daga d’akin. Side d’in Mommy suka nufa, suna shiga Mommyn ta kalleta tace”ya aka yi ??Yahanasu”. Har ga Allah ta san bai kamata ta dinga jin haka game da uwar da ta kawota duniya ba amma she can’t help it! Wani Irin haushi da takaicin Mommy take ji, ba ma ta jin za ta iya tsayuwa su yi wata doguwar magana, dan haka cikin k’aguwa da son barin inda take ta d’an matso kusa da ita tana kallon cikin idanunta tace”ki cewa Yashjub kin janye maganar tsinuwa, sannan ki daina yi masa barazana da tsinuwa idan ba haka ba wallahi tallahi sai na gaya masa cewa ‘ba ke ce kika haife sa ba’!”. Wani irin zabura Mommy ta yi, jikinta ya d’au karkarwa, gaba d’aya ta fice a haiyyacinta, tashi d’aya fuskarta ta yi jazur!!.. D’an k’ura mata ido Yahanasu ta yi kafin tace”kamar yadda na tsammata..ba ki san na sani ba ko?to kuwa wannan karon Baba larai ta munafurce ki.” Hawayen da suka zubo mata ne suka sanya ta yin shiru, itama Mommyn hawaye ta ke yi sosai zuwa yanzu. Da kyar Yahanasu ta tsayar da hawayenta ta goge fuskarta tukunna ta ce “A ranar da kuka dawo daga makarantarmu! A ranar da kuka je kuka had’a guiwa da principal d’inmu kuka saka ta shirgawa Mama k’arya kuka ce Daddy ne ya fad’a! To a wannan ranar ne na ji komai. ….Tun lokacin da Mama ta fara zuwa wajena a makaranta, na so in fad’a muku ke da Daddy, amma sai ta ce mini ba ta so ku sani, wanda a lokacin laifinta na gani da ta nemi in b’oye muku amma da na ji abunda kuka yi kuka saka aka ce mata Daddyn yace! ne ya sanya na fahimci dalilinta na cewa in b’oye muku. Tana zuwa wajena a kai a kai, har ta fara yi mini maganar ‘tana so za ta d’auke ni in zauna a wajenta, shin zan bita?!’ ni kuma na ce mata ‘eh’. A wanchan lokacin shekaruna ba su haura takwas a duniya ba, amma sai na yi lissafin cewa ‘idan na b’oye muku wannan al’amari to kamar na munafurceku ne’ dan haka na yanke shawarar gaya muku ke da Daddy saboda daga ke har shi kuna nuna min tsananin soyayya shiysa na ga rashin dacewar b’oye muku zancen. Ina zuwa dai-dai k’ofar d’akinki na ji muyarki cikin fushi kina cewa “Larai!!wannan yana d’aya daga cikin dalilan da suka sanya na ce miki kar mu fitar da Khadijah har ma da mallan lawal d’in, amma kika k’i yarda kika ce ba za ki iya bari su mutu ba! Yanzu ai ga irinta nan, inda ace Daddy ne ya fara jin labarin zuwan da Khadija take yi wajen Yahanasu! Ya fahimci ta na raye har yanzu ai da mun shiga uku!!!. Kuma yanzun dan mun cewa principal tace mata ga abunda Daddyn yace ke kina tunanin za ta hak’ura ta daina bibiyar y’arta ne?dan kawai ance za a tona mata asiri? ina ce farrak’u kika ce kin yi mata da duk ahalin gidan nan sannan kin kafeta a duk inda take? To ya akayi ta fito?” Sai da Yahanasu ta share hawayenta, tukunna ta kalli Mommyn ta ce “Kai na ne ya d’aure a take a lokacin bayan na gama jin hakan, dan ban gama fahimtar me kike nufi ba, har sai da na ji batun Baba larai tukunna na fahimta,ta inda na je tana cewa”Kar ki damu akasi aka samu, amma zan gyara, sannan saboda Allah Mommy yanzu ace duk Irin taimakon da lawal ya yi mana sai mu barshi ya mutu?? ba dan shi ba ai da tuni Khadija har yanzu tana tare da Imam…” A lokacin shekaruna takwas amma tashi d’aya na fahimci abunda kuka yi, na fahimci komai, saboda a ko da yaushe cewa ake yi gobara ne ya kashe mahaifiyata kuma na tuna yadda ko shekara ba a yi ba Daddy yace mana kar wanda ya sake kiran ko da sunanta, sannan akwai ranar da na ji yana kuka yana cewa Hajiya mama ‘da ya sani ya tsananta bincike, da ya sani bai kunna musu wuta ba.’ Shiyasa na fahimci komai, kuma na fahimci tabbas duk shirin ku ne ke da Baba larai. So na yi in tona muku asiri amma sai na ji kina cewa”shikenan na yarda da ke, amma gaskiya ya kamata ki yi Abu mai k’arfi wannan karon a kansu, ki sake kafe ta a duk inda take, inda Hali ko makwabta kar ta dinga samun jin dad’in shiga! saboda wallahi na tsorata matuk’a sannan inaga Larai gara kawai in fito in gayawa Yahanasu gaskiya, ina so ta san cewa ni ce na haifeta! na san za ta fahimceni!… kalli fa yadda Khadija take zuwa wajenta a b’oye a matsayin Mahaifiyarta itama kuma ta b’oye mana! A gaskiya abun ya fara damuna, kuma Ina tsoron kar ta girma abun nan da na yi kuma na yi shiru ya ya lalata alaƙa ta da ita” Shiruu Yahanasu ta yi tana kaiwa nan, sai da ta jima tana ƙoƙari tukunna da kyar ta iya tsayar da hawayenta ta samu ta ci gaba da cewa “Ban yarda da abunda kunnuwana suka jiye mini ba, sai da na ji Baba Larai ta katse ki itama tana cewa “Khadija ki rufa mana asiri, kar ki ja mana,kar ki je garin soyayya da k’ulaficin y’arki ki je ki tarwatsamu!!Wallahi ko da wasa idan aka san Yahanasu ce y’arki ba Yashjub ba to komai ya lalace mana kenan..kar ki yi tunanin idan kika gaya mata maganar za ta b’uya, ni na san dole za ta fito, dan haka ki ja bakinki ki yi shiru, har mu samu mu cimma burinmu tukunna sai mu san abunyi! As far as I know Yahanasu tana gabanki, za ki kula da abarki, sannan babu wanda zai cutar miki da ita, dan haka idan har zan baki shawara ki d’auka to ki ja bakinki ki yi shiru. Sannan kuma! yadda kike yi a gaban Daddy ki d’an rage, har ma a gaban su Yasirar suma duk ki rage..jiya bakiga al’ajabi da mamakin da Daddy ya shiga ba da akace masa kin daki Yasira saboda Yahanasu, kuma itama Yasira suna cin abinci ina jinta tana cewa ‘Mommy ta fi son Yaha a kansu!!’ dan haka ki ja bakinki ki yi shiru sannan ki Iya takunki tun kafin ki tonawa kanki asiri.” .. Zuwa wannan lokacin har sheshsheƙa Yahanasu ta ke yi, a hankali ta sa Hannu ta goge hawayen da su ka ƙi tsaya mata, kafin ta ci gaba da cewa”Ina jinta tana ce miki kar ki damu ko nan da shekara nawa ne indai kika gaya mini ke ce mahaifiyata ta asali to ba zan guje ki ba, kuma ba zan ji haushin ki ba dan za ta yi mini katanga da Mutane saboda gudun kar in yi k’awaye a gaba in fahimci duniya su zuga ni idanuna su waye in fahimci kin zalinci ni! Sannan za ta rufe mini Baki saboda kar in gayawa kowa na ga Mama, sannan za ta rabani da Mama, ba zan nemeta ba ta inda za ta yi mini abunda ba iyaka Maman kad’ai ba ban Isa in sake shiga jikin wani har mu yi sirri da su in kasa fad’a miki ba! Na k’arshen kuma tace Za ta yi abunda ke kad’ai za ta bari a jikina, bayan ke babu wanda ya Isa ya shiga jikina har ya san cikina, komai kawai kika ce zan bi ki in karb’a hannu bibbiyu ba zan yi jayayya ba.!…. Saboda har abada ba za ki gayawa Daddy gaskiyar tsakanina da ke ba dan gudun matsala, dan haka idan kuka yi mini hakan to za ki gaya min ke mahaifiyata ce ni kuma zan amince in karb’eki Hannu biyu, kuma ba zan gayawa kowa ba sannan ba zan kuma ji haushi ba!. Da farko ce mata kika yi ‘a’a’ amma da ta ci gaba da tsara ki Mommy saboda tsabar son kai da son zuciya tashi d’aya kika amince a yi mini duk wa’ennan abubuwan! Duk dan kar in tona miki asiri, kuma kar in k’i amincewa da ke a matsayin mahaifiyata a lokacin da kika gama tsara plans d’inki kika gama duk abubuwan da kika shiryama yi, kika shirya karb’ata kika shirya gaya mini ni y’arki ce.” Cikin kukan Yahansu ta ci gaba da cewa “sam ba ki yi tunanin hakan da kika yi mini zai iya shiga tsakani na da aure ba!.” ta k’arashe maganar tata cikin fashewa da kuka…..kafin ta ci gaba da cewa “Ina tsaye a wajen Ina kuka har Baba larai ta fito daga d’akin naki ta ganni. na san ta san idan kika ganni a haka kika fahimci na ji komai to za ki karaya ne, kuma ta san akwai matsala, shiyasa a wannan lokacin ta toshe mini Baki ta ja ni d’akinta ta zaunar da ni…. Ita kanta na san a wanchan lokacin ta sha mamaki na, dan bata yi tunanin na yi wayo har haka ba saboda duk yadda ta so yi mini wayo ni kuma na k’i bata k’ofa, kuma ta fahimci na san komai na kuma gane komai, inaga shiyasa ta je ta yi tsafe tsafenta ba tare da ta sanar da ke cewa na ji komai ba. Na san da ke da ita duk kun d’auka asirinku ne ya yi tasiri a kaina na daina shiga jama’a kamar yadda kuka tsara amma a asalin gaskiya Mommy tsanar ki! bak’in cikinki! da haushinki ne suka maidani na zama abunda na zama har kawo yanzu.” .. Sai a wannan gaɓar tukunna Mommy ta iya tsayar da kukanta da kyar tace”Yahanasu dan Allah kar ki ce kin tsane ni! Komai da kika ga na yi wallahi duk na yi ne saboda ku!” Cikin d’an d’aga murya Yahanasu tace”saboda ke dai Mommy! duk abunda kika yi saboda kanki kika yi!!!. Mommy kina kallo fa tun Ina y’ar k’arama ko jama’a idan na gani kuka nake yi, hakanan na tsani komai na tsani kowa nima kuma Mutane suka tsane ni.. Kina ganin yadda aka dinga yawo da ni k’asashen waje domin a gano matsalata, na dinga shan wahala! daga k’arshe aka ce depression gareni lokacin ko shekaru sha biyu ban kai ba amma mommy ba ki yi motsin komai ba. Sau nawa ana fasa d’aurin aurena!!kin san bani da kowa ba ni da komai amma Mommy haka kike murzawa idanunki toka ba kya zuwa ki dad’e da ni ki ji ainihin matsalata saboda kar a zargeki kar asirinki ya tonu. A gaban idanunki su Yasira suke yi mini duk wani kalar cin kashi, amma sai dai ki zuba ido kawai idan anyi sa’a shine za ki ce musu su daina amma ba ki tab’a tsawatar musu ko kuma ki tsayamini ba.! Ta ina hakan ya zama ba son kai ba ba?? ta ina hakan ya zamo duk a ta dalilin neman farin cikina ne????” Yahanasu ta yi mata tambayar cikin d’aga murya.” Cikin share hawaye ta sake cewa”kuma ko tsafin ma da kuke tunanin shine ya yi tasiri a kaina ba ki fa tab’a yunk’urin gyarawa ba dukda kuwa tarin duk waennan wahalwahalun da na sha a rayuwa, amma a haka kike tunanin idan kika ce mini ke mahaifiyata ce a gaba zan karb’eki in yafe miki saboda kina tunk’aho da kin yi mini asiri ko?”. Ba ta jira Mommyn ta bata amsa ba tace”Never!!!” Sannan ta d’aura da cewa”Mama Khadija itace mahaifiyata har gaban abada, shiyasa ma kika ga kawai na zuba miki idanu ban tab’a tunkarar ki da komai ba saboda ban d’auke ki uwa ba!. kamar yadda kema ba ki damu da ni ba nima haka ban damu da ke ba… na san a baya a lokacin da na ji maganganunku na shiga tashin hankali ga k’arancin shekaru ga kuma rashin wanda zan tattauna maganar da, to amma believe u me wallahi wallahi Mommy yanzu abun ba ya gabana. Alhamdulillah na daina damuwa da abun, Ubangijina ya yaye mini damuwar i’ve move on..” Cikin sake matsowa daff da ita tana kallon yadda take kuka billhakki da gaskiya tace”Dan haka Ina mai sake gaya miki ‘ki janye maganar tsinuwa sannan ki kirawo Yashjub ya dawo gida cikin family d’insa, idan kuma ba haka ba, to tabbas Mommy za ki yi mamaki na saboda a yadda na ke jin haushi da takaicinki tona miki asiri shine mafi ƙarancin abunda zan iya yi a halin yanzu.” Dai dai nan Baba Larai ta turo k’ofar ta shigo, a d’an hargitse! Kallonsu ta yi kamar yadda suma suke kallonta, ta riga ta san Yahanasu ta gama fasa kwai! duba da yadda Mommy take kuka kamar ranta zai fita, amma ba ta wannan ta ke ba tukunna dan haka ta kalli Yahanasun tace”D’an bamu guri!” Daga haka ta ja Hannun Mommy suka nufi bedroom d’inta. Had’e rai Mommy ta yi, kamar ta turje ta k’i binta sai kuma kawai ta rabu da ita ta yi mata shiru, dan tsabar mugun mugun takaici da haushin Baba larai d’in ma ya sanyata ta kasa cewa komai. Suna shiga Baba larai ta tura k’ofar, ba tare da ta damu da yanayin Mommyn ba tace”an yanka ta tashi fa! babu aure tsakanin Kausar da Yashjub!..” Ba ta jira Mommyn ta tambayeta k’arin bayani ba, ta d’aura da cewa”kin san ai kawar musu da lissafin duk wani abunda zai sanya a fasa auren nan muka yi dama, shiyasa kwata-kwata ba su yi tunanin ‘ba fa a d’aura aure da ciki‘ ba. Na tabbata Kausar ma da kanta bata sani ba, dan ni ba, sai yanzu ne da na fito zan zo nan na ji suna maganar, Abhi da Daddy..wai har wani babban malami suka sake tambaya ya tabbatar musu da cewa ‘ba a aure da ciki!’ Ban ji bayanin nasu sosai ba, dan k’us-k’us suke yi a chan corridor na babban balcony kamar harda Hajiya Maama suke maganar ta waya,shiyas….” Cikin katseta Mommy tace”Larai me yasa kika b’oye mini batun Yahanasu???” Cikin rashin jin dad’i Baba Larai tace”kash!!! Ki bar wannan maganar za mu yi ta amma ba yanzu ba, yanzu mu ji da wannan, ba mu san wanne mataki su Daddy za su d’auka a gaba ba, dan haka ya kamata mu yi musu shigar sauri!”. Cikin daka mata tsawa Mommy tace “ni kuma wannan maganar nake so mu yi, dan haka ki amsa ni idan na ce miki me yasa kika b’oye min batun Yahanasu sannan me da me kika yi mata?. Har ma da ni ɗin kaina tabbas kin yi mini abu, dan haka ina son jin komai a yau a yanzu ba sai anjima ba, idan ba haka ba kuma wallahi za ki sha mamaki na!!” Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace “shikenan, tunda kin dage sai kin ji!.. Duk abunda na lissafa miki nace shi za mu yi mata shi na yi…” Cikin tarar numfashinta Mommy tace “Sannan nima kika d’auke hankalina daga kanta ko? saboda akwai abubuwan da kika saka ni na yi kika kuma bani na ci waenda duk sai yanzu kwakwalwata take fassaramin ma’anar su, sannnan tunda na yi har yau ban k’ara tunanin fad’awa Yahanasu gaskiya ba! Dan haka ba na son k’arya da b’oye b’oye larai!! Inaso ki gaya mini gaskiya tun rai na bai gama b’aci da ke ba!!!”. Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace “Mommy gani na yi kina shirin tona mana asiri ni da ke, kina shirin kaimu prison… saboda na san muddin Daddy ya san mun musanya Yara to duk wani Abu da muka yi sai ya bnciko ya fito kowa ya gani a hankali a hankali k…” Marin da Mommy ta d’auke ta da shi ne ya sanya ta yin shiru, ta zuba mata jajayen idanuwanta cike da asalin mamaki da al’ajabi. Cikin fushi bak’in ciki da b’acin rai Mommy ta fara magana “a duk tsawon tarayyata da ke ban tab’a ce miki ki je ki yi gaban kanki ki yi kutse cikin rayuwata ki yanke hukuncin da kika ga ya dace miki ba! A tunani na shelter (wajen zama), abinci da gatan da na yi miki ya ishi ace kin yi hankalin yi mini biyayya sannan ki bi umarnina kuma ki girmama duk wani hukuncin da na yanke ba tare da kin yi mini shishshigi ba.!” Cikin fushi sosai itama Baba larai d’in tace”Khadija ni kuma a tunanina na wuce wacce za ki ajjiye hakanan a cikin gidanki tana yi miki duk abunda kike so kawai kamar wata y’ar aikinki!! A tunanina ni yayarki ce shiysa har na yi miki shishshigin da kike magana a kai na yanke hukuncin da na tabbatar it’s for your own best!(domin anfaninki ne)… Amma tunda duk irin rufin asiri da abubuwan da na yi miki tsawon shekaru sama da talatin duk ba ki gani ba, yau ta kai har kin d’aga hannu kin Mareni shikenan!!!. Ba komai, Allah ya had’a fuskokinmu da alkhairi..” Daga haka ta juya ta nufi k’ofa taana tsammanin Mommy za ta tsaida ita, amma har ta fice daga d’akin Mommy ko tari ba ta yi ba. Za ta nemo ta su daidaita su shirya amma sai bayan ta tafi yau ɗin, dan tabbas Yau kam ba za ta tsayar da Larai ba wallahi, sai ta nuna mata abunda ta yi ba ta kyauta mata ba ta yadda gobe ba za ta k’ara ba… Saboda Allah kalli yadda ta saka k’iyayyarta a cikin zuciyar Yahanasu! Duk ata dalilin makircinta, sannan gashi kwata kwata Yahanasun ma ba ta k’aunarta sab’anin yadda Baba larai d’in tace ‘Yahanasu ba za ta iya ko jayayya da ita ba!’ A tunaninta aikinsu ne yake ci shiyasa da ta ga Yahanasun shiru shiru ashe tsana da haushinta ne ya cika mata zuciya shiyasa ta ke yawan yin shiru ba ta kulasu…. Sai da ta tabbata Baba larai ta fice daga side d’inta gaba d’aya, tukunna ta fito daga cikin bedroom d’in nata! kamar yadda ta yi zato ba ta tarar da Yahanasu ba, dan haka ta zauna ta yi shiruu ta shiga lissafin ta hanyar da za ta bi ta daidaita tsakaninta da Yahanasu…. Ta fi minti ashirin a zaune kafin su Yasira suka shigo a mugun hargitse, suna hangota suka kanta suna cewa “ta zo ta hana Baba Larai tafiya, ga ta chan ta had’a kayayyakin ta tsaff!tun d’azu suke rarrashinta amma ta kafe Akan Itafa sai ta tafi, kuma sai kuka take yi, dan Allah Mommyn ta zo su je ta tsayar da ita ta rarrasheta wataƙilan Daddy ko Hajiya mama ne suka yi mata wani abun…..” Mik’ewa kawai Mommy ta yi, ta fad’a cikin bedroom d’inta ta kullo k’ofar! wanda hakan ya sanya suka fahimci matsalar daga wajenta ta taso kenan, dan haka kawai suka sauk’a da niyyar su je su ji da Baba larai first tukunna su dawo wajen Mommy su ji dalilin fad’an nasu…. sai dai suna sauk’a suka tarar da su Yasmeen suna shigowa cikin parlourn, a bakinsu suka ji ‘ai har ta riga ta tafi’ Cikin mayarda numfashi Yasmeen ta ɗaura da cewa “da Jaka ɗaya ma ta samu ta tafi, dan mun rik’e ragowar jakankunan nata mun hanata ita kuma ta tafi kawai ta bar mana su. Mun so mu bita amma ba wani Napep d’in, dan itama sa’a kawai ta ci shiyasa ta samu sannan natan wanda ta ke cikin a baki baki ta zauna ta k’i bamu access bare mu shiga har aka ja aka yi gaba, kuma na san kafin mu shigo mu d’au mota sun riga sun b’acewa ganinmu……” Duk wannan dramar da ake yi su Daddy suna jin su suka manna musu hauka, daga k’arshema garden suka fice suka ci gaba da tattaunawarsu….Daddy ji yake kamar ya fi kowa farin ciki, a ransa kuwa addu’a yake yi ‘in shaa Allahu Baba larai ta tafi ta bar gidansa kenan har abada! next kuma Mommy ce!….’ Hajiya Mama ma ta ji dad’i da suka kirata suka sanar mata, tana fushi da su shiyasa yanzun ma kamar d’azu da suka kirata suka gaya mata zancen aure ba ta biye musu ba, kawai dai tace”a ci gaba da addu’a” daga haka ta kashe wayar tana jin sanyi a ranta, in shaa Allah k’arshen Mommy ya zo kenan, sannu a hankali za ta gani ne….. Har yanzu mamakinsu take yi tana mamakin yadda ita kanta su Mommy suka goge mata hadda!!Amma ba komai, ai gashi nan sun fara gani tun yanzu, kad’an ma suka gani in shaa Allah. A daren ranar Hajiya Mama ta bi jirgin k’arfe hud’u ta nufi Uk, duk da yadda abubuwan da suka wakana suka yi mata dad’i amma tana so ta tafi…fushin da ta yi ɗin ta ga positive effects d’insa sosai a kan Daddy, dan haka ta yanke a kan gara ta tafin..za ta tafi ta je tai ta yi musu addu’a ‘Allah ya sa a dace, in shaa Allah Mommy ta kusa ganin k’arshen ta, kuma duk wasu abubuwa da ta rufe sai sun bankad’a a idanun kowa ya gani.’ Ya’isha ta fi kowa gigita da lamarin tafiyar Baba larai dan ta san Baba larai itace gatan su saboda yanzu haka ma aiki take yi mata a kan Siyama da Najeeb!! Shikenan ta san ta shiga ukunta itakam yanzu..Yasira ma ta gigita sosai dan itama ta san Baba larai d’in dai itace gatan nasu, dan haka da daddare bayan ta bari Mommy ta d’an huce ta je ta sameta.. cikin son fahimtar da ita ta fara yi mata bayanin “illar tafiyar Baba larai a garesu, kuma ko ba komai bai kamata ace sun yi wa Baba larai haka ba! Ko me kuwa ta yi musu, ɓ ba ta chanchanci hakan daga garesu ba.” Kamar Mommy ba za ta kulata ba, sai kuma Cikin nuna halin ko in kula ta ɗan nisa tukunna tace “Yasira ba fa ni na cewa Larai ta tafi ba, ita da kanta ta yi zuciya ta ce za ta tafi, shiyasa ni kuma ban hana ta ba. bayaga hakan abunda ta yi mini ma ya sanya dole in hukuntata in nuna mata iyakar ta, dan haka indai na Isa in fad’a miki ki ji to ki tsame hannunki sannan ki gayawa su Yusra suma duk su tsame hannayensu a lamuranta, ko waya bana so ku yi mata… Allah na tuba idan banda failure (rashin nasara) ma me muke ta fuskanta! aikin nata yanzu duk ya daina ci!” Cikin mamaki da tsanannin rashin jin dad’in abunda Momyn ta yi ta kuma fad’a yanzu Yasirar tace”idan na fahimceki Mommy ‘a yanzu dai Baba larai ba ta da wani amfani a gareki shiyasa kika b’ige da cewa kinaso ki hukuntata ne’, saboda na san inda ace a lokacin da Baba larai take ganiyar taimaka miki komai yake tafiya daidai ne to da ko me ta aikata a gareki ba za ki tab’a barinta ta tafi ba, me ye ne ma ta aikata miki yanzun da ya yi zafi har haka???” Yasira ta yi mata tambayar cikin b’acin rai. Mik’ewa tsaye Mommy ta yi, ta nuna mata k’ofa tukunna tace”get out Yasira, tun kafin ranki ya b’aci!!!” Za ta yi magana ta kuma daka mata tsawa tace “get out nace!!!” Juyawa kawai Yasira ta yi ta fita ranta a b’ace da takaicin Mommy! dan ita a rayuwarta ba ta son mutum mai use and dump!! kawai idan ana tare to duk daɗi duk wuya duk tsanani kawai a kasance a taren har abada! kuma a taimaki juna. amma ita Mommy bayaga use and dump d’inma da ta yi wa Baba Larai, tun ba yau ba ta lura da Mommy kanta kawai ta sani, using d’insu take yi…..gaba ɗayansu amfani da su kawai ta ke yi. … Sai da aka yi kwana biyu tukunna Mommy ta je d’akin Yahanasu, dan ta san zuwa lokacin ta d’an huce. A zaune ta sameta suna waya da Yashjub, tana ganin ta shigo ta yi sauri ta kashe ta ajjiye wayar, ba tare da ta kalletaba ta ce”bacci zan yi” A hankali Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya, ta nemi guri ta zauna a kusa da ita ta kamo hannuwanta. Kawar da kai Yahanasu ta yi,tsabar takaici da bak’in ciki ba ta san lokacin da hawaye suka shiga sintiri a kan fuskarta ba. A hankali tace”na san na yi miki laifi Yaha amma ba laifi na bane ba completely. Na shirya gaya miki komai in gyara tsakanina da ke amma da Larai ta fahimci hakan gudun kar asirinmu ya tonu sai ta je ta yi abunda ta yi ta kawar da tunanin ki daga gabana wanda ba dan hakan ba Yaha da ba zan tab’a bari mu kawo war haka a hakan ba! Amma yanzu komai zai gyaru Yaha, saboda ke da kuma na fahimci Larai ta saka na cuce ki yanzu haka ba ta cikin gidan nan tun jiya saboda ke y’ata. Na san abunda na ke roƙo a wajenki mai nauyi ne sannan za ki ga ya yi yawa dan ni kaina na san its alot to ask for amma dan Allah ki dubi uwar da aka shiga tsakaninki da ita ba tare da saninta ba, ki yi mini adalci ki bani chance ki bani dama Yahanasu….” Mik’ewa da sauri Yahanasu ta yi, tace”dan girman Allah ki fita!ba na buk’atar gyaruwar komai a tsakanina da ke Mommy, kawai ki bari mu k’arashe rayuwarmu a haka! Me ye ne ma ya rage?? You’ve missed out all the important stages na rayuwata(kin riga kin yi watsi da duk wasu matakai masu matuƙar mahimmanci na rayuwartawa)..da na fi buk’atar ki, dan haka yanzu ban ga amfanin ki gyara komai ba wallahi. ba na buƙatarki a rayuwata, na riga na san ba kya so na ba kya k’aunata kin yi amfani da ni saboda ki samu abunda kikeso which u do, dan haka na rok’eki da girman Allah kar ki nemi ki ja ni a jiki saboda ba zan janyu zuwa jikinki ba. Dan haka kawai ki yi harkar ki nima in yi tawa harkar, ba zan tona miki asiriba saboda saɓanin ke ni idan na yi Abu yana damuna kuma na san duk lalacewa ke ɗin mahaifiyata ce dan haka muddin na bada gudummawa ko na zamo silar tafiyar ki prison to na san abun sai ya dameni har k’arshen rayuwata, shiyasa kawai na zuba miki ido na ke jira Ubangiji ya yi ikonsa a kanki. amma fa muddin ba ki daina yi wa Yash barazana kina threatening ɗinsa da tsinuwa ba! Wallahi kamar yadda na gaya miki shekaran jiya tabbas zan fad’a masa ba ke ce kika haifesa ba! Saboda kamar yadda na san guilty conscious zai addabeni idan na fad’i abubuwan da kika yi aka hukuntaki haka zalika guilty conscious zai addabeni idan na bari bak’in cikin ki ya kashe Yashjub, dan haka ki daina threatening d’insa!!! daga nan ni da ke mu ci gaba da mu’amala da juna kamar yadda muke yi kafin ki san na san ni ƴarki ce, iyakacin abunda nake buk’ata kenan daga gareki ba wai sulhu da fahimtar juna ba! Kin riga kin cuceni wata shari’ar sai a lahira,Mommy ba wai iyaka hakki na ba wallahi ko da Hakkin Mama khadija kad’ai aka barki ke da Mallan lawal da Baba larai ya isheku…..” Shiruuu Mommy ta yi haka itama Yahanasu…tun shekaran jiya da Yahanasun ta je d’akinta ta yiyyi threatening d’inta, a take ta san tsaff za ta iya yin abunda ta fad’a ɗin, shiyasa ta ke so ta lallab’ata..tana son y’arta kuma ta na so su fahimci juna Sannan da gaske ne Baba larai asiri ta yi mata ta kawar da Yahanasun daga ranta gaba d’aya, amma ita Mommy a halin yanzu Babban tashin hankalinta shine kar Yahanasu ta tona mata asiri! Ta ji haushin Baba Larai kuma ta na so ta san ta yi mata laifi ta yadda ba za ta sake yunk’urin yin wani ba shiysa ta barta ta tafi kuma ta hana a nemota amma fa Yahanasu tana daga cikin dalilin da ya sanya ta yiwa Baba larai abunda ta yi saboda tana so Yahanasu ta gani sannan ta san ta yi abu Babba haka duk dan ita, sai dai kuma ta lura hakan ko a kwalar rigar Yahanasun, gashi a iyaka maganganunta na yanzu ma ta lura Yahanasu fa ta san har case d’in abunda ta aikatawa Khadija(amaryq)….dan haka dole ta d’auki risk ta aikata dukkan abunda za ta iya domin ta samu ta yi manipulating Yahanasu, ta shawo kanta su fahimci juna tun kafin ta b’allo mata ruwa. Dan haka A hankali ta ce mata “ki zauna mu yi magana Yaha, zan fad’a miki duk abunda na yi tare da alk’awarin ba zan sake ba..kuma na san idan kika ji bayani na za ki yi mini adalci idan kika fahimci dukkannin abubuwan da na yi na aikata su ne saboda ku y’ay’ana.” Yahanasu ba ta zauna ba ganin ba ta da niyyar zaman ne ya sanya Mommy ta fara magana. “Kamar yadda na fad’a, ba zan b’oye miki komai ba, saboda Ina so ki yarda da ni, mu fahimci juna. ……….Idan ana maganar rashin jituwa da rashin zaman lafiya da rashin so da k’auna to shine asalin ma’anar zamana da mahaifinku tun lokacin da muka yi aure…ko Irin soyayyar nan ta amarci bai nuna mini ba, iyaka k’arshen rashin mutunci da kyara shi Imam ya dinga nuna mini. Tunda muka yi aure sam ba ya ja na a jikinsa, ba ya nuna mini kulawa. Ban rufe watanni biyu a gidan Imam ba ya tubure ya dage ya d’agawa kowa hankali akan shi fa sai ya k’ara aure…sai ya auri budurwarsa wadda na san yana masifar so kamar ransa, dan k’iri k’iri ya kan ce mini saboda sunana ya zo d’aya da ita ne dalilin da ya sanya yake d’an kulani. Babu kalar masifar da ban yi ba, amma sai da aka d’aura auren nan, lokacin ma da aka d’aura ba na nan ya kaini gidanmu yace a yi mini fad’a, Abban mu kuma ya goyi bayansa aka mini horo mai tsanani ta inda aka ce ba zan koma gidan ba, Ina ji Ina gani aka yi auren Khadija ta tare suka gwangwaje amarcinsu ni kuma Ina gidanmu hankalina a tashe. Yadda na fita daga haiyyacina sai da ya bawa mahaifiyata da Hajiya Mama tsoro dan haka suka fara ƙoƙarin yin wani abun, amma sai mazajensu suka tsawatar musu, aka ce a rabu da ni hakanan. sai da na gama shan wahala, imam ya gama cin amarcinsa tukunna Abbanmu ya ce in koma! tare da zazzafan warning d’in ‘idan har ya ji case ya taso daga waje na to na bar Imam kenan har abada! ba zai bari in koma gidansa ba.’ Ina mutuwar son Mijina, ba zan tab’a iya rayuwa babu shi ba. gashi ba zan iya zama da kishiya ba, shiyasa na shiga tsaka mai wuya! na rasa abunyi! na rasa tudun dafawa… A dai-dai wanchan lokacin ne kuma dama larai ta dawo hannun Mahaifiyata da zama (matsayinta na y’ar uwar mahaifiyarta), saboda an samu matsala da ita a k’auyensu an d’aura mata sharrin maita. Itama tana da damuwa nima Inada damuwa shiyasa muke zama muke tattaunawa…Larai ta tausaya mini sosai haka kurum da na zo komawa tace ‘Tana so za ta biyo ni.’ A wanchan lokacin da kyar su Abba suka amince saboda Larai a k’alla ta bani shekaru sha biyar, kuma suna so in je in zauna lafiya ni kad’ai in yi hankali shiyasa suka ji tsorom kar mu je da larai in ga mu biyu ne in yi ta rashin mutunci..amma sai mahaifiyata tace ‘ba komai, mu je kawai’ saboda ta ga mun shak’u muna d’ebewa juna kewa, sannan tunda Larai ta zo ba mu sameta da wata muguwar d’abi’a ba in banda addini da sanin ya kamata da muka santa da shi. Haka nan aka tambayi Imam ya amince shima dan haka muka tafi gidana tare da Baba larai. A ranar da na koma ma Imam ba a d’akina ya kwana ba, ko kallona ba ya son yi. sai bayan kwana hud’u ya kiramu ya raba mana kwana Akan za mu dinga yin kwana uku uku ni da Abokiyar zama na. Sai da girki na ya zagayo sau hud’u tukunna ya fara kwana a cikin d’akina saboda da a parlour yake kwana, ko da ya fara kwana a d’akin nawa shima kuma babu abunda yake shiga tsakanina da shi! Dan sai dare wajajen 12 ma tukunna zai shigo, Idan aka kira assalatu kuma ya fita, daga nan ba zan sake saka shi a idanuna ba sai wani daren, a cewarsa ‘aiki ya yi masa yawa!’. Da gaske na san ba ya gidan tun safe har dare, amma kuma sai ranar girkina ne ya ke yin scarce (ƙaranci da wuyar gani) dan duk ranar da aka ce miki yau girkin Khadija ne to tun kafin Magrib yake shigewa d’akinta ba abunda yake fito da su sai sallah da cin abincin dare da ake yi tare, daga sun yi isha kuma ya ke kiranta daga nan ba za mu kuma sake ganinsu ba sai washegari, haka nan wasu lokutan zan yi ta jin hirarsu yana dariya yana raha. Abun ya ishe ni, gashi ban Isa yin rigima ba dqn na san in na yi tsaf su Abba za su raba auren! ni kuma ba zan iya rayuwa babu shi ba, shiyasa na yanke shawarar kashe kaina kawai!!!!… ranar da zan yi abun Allah ya taimakeni na d’aga kwalbar fiya fiyan kenan zan sha Larai ta shigo, ganin yadda na firgita ta fahimci ba ni da gaskiya aikuwa tun kafin ta gama dubawa ta gane menene a ciki. Hankalinta ba k’aramin tashi ya yi ba, dan haka ta fito min a Mutum k’iri k’iri tace min ‘Itafa dama ta biyo ni ne saboda tana so za ya taimaka mini..’ Ba ta b’oye mini komai ba tace ‘akwai wani boka a k’auyensu, mutumin tun yana zuwa mata a mafarki sama sama, har ta gano location d’insa (inda ya ke) a cikin mafarkin, a wata bukka chan a cikin daji, ta je..nan yake sanar mata tun ranar da aka haifeta ya san dama itace za ta gaje sa… Tun bata d’auki abun da gaske sannan da mahimmanci ba har ta d’auka!!! bata da uwa sai Matar uba, dan haka bata yi shawara da kowa ba ta biye masa! Ba a yi wata d’aya ba ta koyi kusan komai, ta inda ya zage ya kokkoya mata abubuwa, yace ‘ta rik’e da kyau, hannunta yana da zafi fiye da zaton mai zato’. Akan wata k’awarsu da suka yi fad’a ta fara gwadawa, ta inda matar har yau tana nan a k’auyen namu ba ta gani, daga nan sai ta gayawa babbar k’awarta…tun daga ranar duk wani abu da k’awar take so ko ta kwallafa rai akai to sai Larai ta yi mata aiki a Kai, ta samu!! Itqma kuma da kanta ta kan yi wa kanta abubuwa.. A b’oye suke yin abun nasu kuma daga ita sai waenda ta yarda da su shiyasa abun bai baza gari ba. Amma ta ce mini abu d’aya ne har yau ta kasa yi wa kanta aiki a kai shi ne ‘mijin aure,’ dan har wajen bokan da ya koya mata duba da abubuwa ta je suka taru suka duba ranar aurenta amma sai su ka ga ‘babu!’.. Dukda hakan bai sa ta fidda rai ba, hakanan har gobe Larai take neman mijin aure ido a rufe amma babu shi babu alamarsa. Ragowar k’awayenta da k’annen k’annen k’awayenta duk sun yi aure, kuma ba laifi sun rik’e mata sirrinta ba su fad’awa kowa ba… Mutuwar wannan boka itace ta tona mata asiri, dan da ya kusa mutuwa sai ya raba sunanta ma clients ɗinsa (kwastomominsa), to ta hakane da wata mata ta zo wajenta ta sanya Laran ta yi wa d’an kishiyarta asiri ya yi ta rashin lafiya d’aga k’arshe Yaron har ya zo ya rasu..shine fa da bincike ya yi bincike aka ganota aka ce za a k’onata a k’auyen! ai mayya ce! tunda gashi dama ta rasa miji kuma zan iya ce miki kaff k’auyen mu har yau ba ayi mai kyan larai ba, shiysa su kuwa suka ce ai mayya ce. Ina gama jin labarinta ko wasu-wasi ban tsaya yi ba na amince da tayinta, muka fara aiki babu dare ba rana a kan Khadija(amarya) da Imam. Ba a yi sati d’aya ba kusan gaba d’aya hankalin Imam ya dawo kaina, dan kusan yaddda yake mu’amala da Khadija amaryarsa nima haka yake mu’amala da ni, sai dai kuma ni kaina na san soyayyar Amaryarsa ta daban ce kuma ta gaskiya ce duba da yadda ba ya kishi na kamar yadda yake kishinta, dan haka muka sake zage damtse, aiki ba dare ba rana, ga kuma kissa da muka bawa mahimmanci, dan ko wani abun aka yi sai dai in shige d’aki in yi kuka in goge daga ni sai larai ba ma tab’a bari wani ya ji ko ya gani… Haka kurum kwata-kwata sai na kasa d’aukar ciki. Hankalina bai gama tashi ba sai da Imam ya kwashe dukiyarsa gaba d’aya ya damk’awa d’an cikin amaryarsa !!! dama chan ba so nake yi Yaron ya zo duniya ba saboda Larai ta ce mini tabbas Namiji Amarya za ta haifa…dan haka Ina jin wannan batun na jajirce kuma na dinga yi wa Larai kuka har sai da ta tsaya tsayin daka ta taya ni muka kashe Yaron tun yana ciki! saboda ita Larai ta ce za ta yi komai amman banda kisan Kai, dan shi ya rabota daga garinsu ya kusan tona mata asiri, bayaga haka ita har ga Allah ba ta son yin kisa..to kukan da na dinga yi mata da kuma zancen raba dukiya da ta ji ne ya sanya ta biye mini a wanchan lokacin. Tun daga nan muka k’ara k’aimi akan asirin da muke yi wa Khadija (amarya) akan ta bar gidan Imam, mu bata ta ci! mu ba ta sha! mu zuba mata a ruwan wanka amma sam abu ya k’i yin tasiri a kanta! kwata kwata ba ta ma da shirin tafiya, abun yana kama ta ba wai ba ya kama ta kwata-kwata ba kawai dai ba ya yin tasiri ne a kanta. A kwana a tashi a haka har muka samu ciki a tare ni da ita… Tunda muka samu ciikin Larai take aiki Akan ni in haifi Namiji ita kuma ta haihu babu rai, kamar yadda ta yi na farko… cikin yana yin watanni biyar Larai ta fahimci Tabbas fa Khadija (amarya) sai ta haihu kuma Namiji za ta haifa, sannan Yaron mai tsananin albarka ne! Da sa’a! Dan dukkannin abunda ya saka a gaba sai ya cimm masa kuma attajiri ne mai masifar kud’i, sa’a da nasara ta ko wacce kusurwa ta rayuwarsa!. Sai da na suma a tsaye!! Bayan na gama jin wannan mummunan batu daga Larai, dan hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba, saboda a ranar ne na lab’e musu na ji Imam d’in yana sake damk’awa cikin jikin Khadija dukiyar sa kamar yadda ya yi a na farko, ita kuma tace ba zai you ba shine yace mata to a cikin mu ni da ita duk wadda ta haifi Namiji ita za a bawa… shiyasa na nufi wajenta a hargitse dan na san idan muka yi kunnen doki to tsaff Imam zai yi son kai! Dan haka na nufi wajen larai direct domin mu samu mu tattauna a nemo mafita to shine ita kuma ina shiga ta tare ni da mugun zancen…. Da kyar! Dan sai da Larai ta yayyafa mini ruwa tukunna na dawo haiyyacina da mugun kyar. Ganin Ina shirin had’iyar zuciya in mutu ne ya sanya tace mini ‘’me zai hana mu musanya Yaran, ni in karb’i mai albarkar..’ tashi d’aya tun kafin ta k’arasa na k’i amincewa, na ce kawai a cigaba da aiki a kansa ta yadda ba zai yi albarka ba kuma ya yi rayuwa mara dad’i mara nasara ya mutu wulak’antacciyar mutuwa, tunda mun riga mun san sai fa ya zo duniya. Wani babban tashin hankalin saida na yi scanning na tabbatar ni mace zan haifa! saboda ban tab’a kawowa zan haifi mace ba duba da yadda muka dinga aiki akan in haifi Namiji. A wannan lokacin ma Baba larai ce ta sake bani shawara kamar farko a kan mu musanya Yaran, inyaso bayan mun haihu an bayar da dukiyar idan ma kashe Yaron za mu yi sai mu yi tunda dai Yaro yana a hannunmu ai tsaf za mu iya yin kome muka ga dama sab’anin yanzu da yake a ciki. Kuma kar in damu zata toshe duk wata hanya da za a zargemu ko da kuwa Yaron ya yo zubin uwarsa ne. Tashi d’aya na amince dan a wannan karon kam na gamsu kuma na fahimta…tun a lokacin muka san yadda muka yi muka siye likitan da muke zuwa asibitin wajensa…ta hanyar yarda da shi da Baba Larai ta yi bayan ya fad’i mana shi hakan kawai yake da buk’ata daga garemu. A ranar da na fara labour muka bata magani itama muka tayar mata da nata labour ɗin ta hanyar ba ta kwayar da ya bamu a ruwa ta sha ba tare da ta sani ba. Tana shiga d’akin haihuwa gudun kar ta fahimci wani abun aka shak’a mata anesthesia aka yi mata cs!! Kusan a tare muka haihu Ita aka fito mata da Yashjub ni kuma na haifoki, Likitan da nurse d’in da Baba larai suka yi sauri suka sauya, aka fitar da ke a matsayin Y’ar da ta haifa, ni kuma bayan y’an mintuna aka fitar da Yashjub aka ce na haihu. Daddy ya bada rabin dukiya kamar yadda ya yi alk’awari, amma fa ba ni da burin mallakar wannan dukiya kamar yadda nake da burin kashe Yashjub saboda kwata kwata ko fuskarsa ba na son kalla, gashi aka tilasta mini hakanan Ina ji Ina gani na dinga shayar da shi. Kwatsam!!ina ta shirye shiryen yadda za a yi in raba shi da duniya ba tare da kowa ya zargemu ba sai ga ciki a jikina, cikin y’an biyu.. Tun cikin yana da watanni hud’u Baba Larai ta fara mafarkai marasa dad’i game da Yaron da zan haifa..Tabbas mun fahimci Namiji ne kam wannan karon ammafa Yaron kwata-kwata bashi da albarka, ga kuma mutuwa da zai yi wulak’antacciya idan har bai yi arzik’i ba!!! sannan duk abunda ya soma to ba zai yi albarka ba… Hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba, dan sai da jini na ya hau na kwanta a asibiti sau bakwai saboda wannan duba da Baba larai ta yi ta gano mini bala’i..sai da muka nutsu muka yi lissafi Sosai muka bincika tukunna muka gano Ashe ‘asirin da muka yi wa Yashjub tun kafin ya zo duniya ne ya fad’a a kan Yassir!’ tunda asirin an yi sa ne a d’an Khadija matar Imam kuma kinga nima sunana Khadija, sannan nan gidan imam aka jefa shi shiyasa duk daɗewar abun sai ya dawo ya faɗo nan ɗin. Sannan ko bayan da muka fahimci abun bai kama Yashjub ba bamu damu mu yi wani abun a kai ba dan kwata kwata ba mu kawo cewa zai fad’a kan Yassir ba bayaga haka babu ma ta yadda za a yi mu karya abun saboda ba zamu iya nemosaba, dan a babban ruwa mai tafiya muka jefa dan haka kinga la shakkah ba ma ya cikin Nigeria, ya bi ruwa. Babu abunda ba mu yi ba, babu kuma abunda bamu gwada ba amma idan muka yi aikin muka gwada in banda wasu sabbin masifu a kan na da babu abunda muke gani a tauraron Yassir, amma ita d’ayar Yarinyar lafiya lau dan zuwa wannan lokacin mun fahimci twins ne. Kamar kullum a wanchan lokacin ma Baba larai ce ta sake kawo shawarar’mai zai hana mu yi hak’uri mu taushi zuciyoyinmu mu raini Yashjub! tunda shi zai yi albarka, in ya so idan ya girma ya gama tara abunda ya tara sai mu san yadda muka yi muka d’aura Yassir a kan dukiyarsa, shi kuma Yashjub mu kashesa! Daga nan komai ya dawo hannunmu, in ya so sai Yassir ya kula da komai tunda ba Yassir d’in ne ya fara tarawa ba..dukiyar ba tasa bace ba dan haka in sha Allahu ta san komai zai tafi cikin sauk’i, abun zai yi albarka! dan shi Yassir d’in abunda ya fara ne dakansa ba zai yi albarka ba. So inshaaAllah komai zai yi kyau. Sannan idan hakan ta faru babu batun wulak’antacciyar mutuwa a Yassir tunda a yadda ta gani sai idan ya rasa komai ya rasa kowa ne tukunna wannan al’amarin zai faru da shi.’ Ko kad’an ban yi mata jayayya ba, dan nima plan d’in ya yi mini d’ari bisa d’ari. Dan haka muka tashi muka tsaya tsayin daka na danne zuciyata, na ja Yashjub a jikina, na kula da shi duk dan saboda y’ay’ana, sai dai kuma tun lokacin da Yashjub ya kai shekaru 4 a duniya na fahimci kamar ma ya tsane ni! Sam ba ya son magana ma da ni, ba ya son shiga jikina, baya jan y’an uwansa a jiki… Gashi duk cikinku mahaifinku ya fi son shi… Daga k’arshe ma Hajiya mama ta d’aukesa gaba d’aya ya koma wajenta…na so ya dawo a wanchan lokacin amman a banza, dan yadda Hajiya mama ta ga na d’aga hankalina na san shiyasa ita kuma ta ce ba zai dawo ɗin ba. Yashjub tun yana zuwa mana hutu sau 2 a shekara, daga baya ya koma sau d’aya ko bayan shekaru biyu, daga k’arshe ma ya daina..sai dai Daddy da su Yassir su je, ni kuma a lokacin mun yi kacha kacha da su Hajiya mama tace idan ta ganni a inda take sai ta yi mini abunda ban tab’a tsammani ba. Tun Yashjub yana shekaru 17 na so ya fara saka su Yassir d’in a jikinsa, da suka girma suka yi wayo sosai nan ma na yi masa maganar ya fara saka shi a business d’insa amma ya k’i, na zo nace to ya bashi jari nan ma ya k’i, gashi a lokacin na fahimci son kan da Daddy ya kuma yi a lamarin yadda ya kasafta share na company d’insa. shima gashi (shi Yashjub d’in) ba ma ya nan ballantana in san yadda zan yi in yaudare sa ya ja d’an uwansa, gashi kuma asiri bai cika tasiri a kansa ba kamar Khadija(uwarsa). Hankalina ba k’aramin tashi ya yi ba da na ji ƙishin ƙishin d’in Na’ima ta cewa Yassir Yashjub take so, dan dukda cewa na san mun cire masa son mata da sha’awar su a rai! amman kuma na san in dai har Na’ima ta gayawa su Daddy tana son shi tofa dole ya aureta, kuma yau da gobe sai Allah, na san duk girman abunda muka yi dole wata rana Na’ima ta iya samun ciki…Shiyasa muka k’arawa abun namu k’aimi, gaba d’aya ya kuma tsanar mata sannan muka fara aiki a kan ya dawo a yi ayi ko shi ya ɗaura ko kuma mu san dabarar da muka yi aka d’aura Yassir da Yassira a kan komai na dukiyarsa before or after (kafin ko kuma bayan) mun kashe sa! Dan na daɗe da yiwa kaina alk’awarin ‘jinin Khadija (amarya) bai Isa ya rayu ya ji dad’i har ya yi aure ba, saboda yadda Yashjub da mahaifiyarsa suka d’aga mini hankali ba su chanchanci rayuwa ba!’ That is my revenge…. (Hakan itace sakayya ta a garesu). Kwatsam!! Sai kuma tauraron Mace ta fara b’ullowa wadda Baba larai tace ita za ta kawo k’arshena muddin muka bari aka yi auren…. Yo dama ai ko ina hauka Yash bai Isa ya yi aure ya haihu ya ji dadi sannan Yaro ya shigo cikin gadon sa ba….ga kuma maganar Matar ma ta zo har da su batun kawo k’arshena! shiyasa na tsani kuma bana son Manubiya kamar mutuwa ta!”. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e, kafin ta kalli Yahanasu tace “yanzu na san kin fahimci dalilina na aikata duk wani abunda na aikata, kuma inda ace ba na sonki ko ban d’auke ki a matsayin jinina ba Yahanasu da ba zan tab’a zama in faiyyace miki komai in bud’e miki cikina kamar haka ba!!. Na san na yi laifi, na san na yi kuskure amma Yahanasu Daddynku shine ummulaba’isin komai da na fara aikatawa, sannan da tafiya ta yi tafiya na san kema kin fahimci saboda Yassir da kuma ku na aikata ragowar abubuwan da na aikata…. Sannan Manubiya had’ari ce ga rayuwata, shiyasa ya zame mini dole in….” Cikin tarar numfashinta Yahansun tana wani irin kuka kamar ranta zai fita tace “Mommy babu ruwan Mannubiya da duk wani abu da ya sameki da kuma yake shirin samunki! Ubangiji ne ya fara nuna miki k’arshenki!!…” Wani irin abu ne ya rik’e mata zuciya da mak’ogaro dan haka ta yi shiru dan numfashinta ya tsaya…da kyar ta samu ya dawo, ai kuwa tashi d’aya ta matsa ta kamo hannun Mommy ta fara janta, sai da suka isa bak’in k’ofa tukunna ta bud’e tukunna ta had’e hannuwanta waje guda tace”dan girman Allah ki fita, ki fita kafin ki sa zuciyata ta buga!!!!” Tabbas Mommy ta fahimci tarkon ta ya kama kurciya, dan yadda tayi ɗinnan ya sanya ta fahimci ba za ta iya yin komai ba kamar yadda take ik’irari…kuma yadda ta bud’e mata cikinta ta fad’a mata sirrinta ta san hakan ma sake k’ulle Yahansun ta yi da jijiyoyin jikinta, dan haka ba za ta iya yin komai ba. Shiyasa kawai ta shafa fuskarta a hankali ta d’an goge mata hawayenta, daga haka ta sa Kai ta fice hankalinta a d’an kwance dan tun d’azu da Yahansu tace ‘guilty conscious zai addabeta idan ta fad’i abubuwan da ta aikata aka hukuntata’ Ya sanya ta fahimci iyakar abunda ya kamata ta ƙara yi shine ‘ta sake nunawa Yahanasun itan fa itace mahaifiyarta, kuma tana sonta’ daga nan ta san za ta ƙarasa rufe mata baki ta sanyata ta yi shiru cikin hikimarta, shiyasa ta bud’e mata cikinta saboda tana so Yahanasun ta ga ita mommyn ta yarda da ita, kuma ta d’auke ta y’a. Kafin Yahanasun ta gama fita daga al’ajabi da mamaki ta dawo dai dai, ita kuma InshaaAllah kafin nan za ta san yadda zata yi da su Daddy, za ta san yadda za yi destroying ɗinsu, kar ma su sake bata ciwon kai Mommy tana fita da sauri Yahanasu ta mayar da k’ofar ta rufe, k’irjinta yana dukan tara tara, dan bayaga haushi da takaici har ga Allah zuwa yanzu kam tsoron Mommy take ji!! Anya kuwa Mommy tana da zuciya a cikin k’irjinta?? ita da Baba Larai anya kuwa za su ga Annabi? ashe dama akwai mutane irinsu har yanzu a duniya?…. A da ita tana jin haushin Mommy saboda abubuwan da ta yiyyi ashe ba ta ji duka ba, ba ta san duka ba!!!! “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ta shiga ambato a cikin zuciyarta kanta yana wani irin sarawa… tabbas kamar yadda Mommy ta yi zato a yadda ta zauna ta bud’ewa Yahansu cikinta hakan ya sanya Yahanasun ta d’an ji d’arr sannan kuma ta yarda Mommy ta d’auke ta a matsayin y’a!! Ba wai ta yafe mata abubuwan da ta yiyyi ba kawai dai hakan ya sanya ta sake fad’awa cikin duniyar tsoron tona mata asiri saboda ta san idan ta tona mata asirin to fa azabar lamarin ba zai bartaba ya dinga addabarta kenan yana bibiyarta yana damunta har ƙarshen rayuwata, tunda duk dai lalacewa uwa uwace, ta san dole za ta ji guilt, dan haka gara kawai ta barta Ubangiji ya nuna mata iyakarta… Ba za ta sake da ita ba ba kuma za ta kula ta ba, babu ruwan kowa da kowa kamar dai da, dan tabbas Mommy ba uwar da zaka sake ka yi mu’amala da ita baceba,she is everything Bad!….. Sai da Baba larai ta yi sati d’aya tukunna Mommy ta basu izini suka fara nemanta, sai dai kuma babu kalar kiran da ba su yi mata ba amma wayarta ba ta shiga kuma sun kira k’auyensu ance bata je ba, dan haka hankalinsu ya tashi matuk’a. A b’angaren Kausar da Yassir kuwa ko da yayi mata maganar aurenta da Yashjub nuna masa ta yi itama ba ta so, kuma wai abunda ta yi a ranar da aka ɗaura musu auren ta yi ne saboda ta yi tunanin Yash d’in zai fara bata wani abun daga cikin dukiyar sa, ko ya ba ta gida ya ce ta zauna a inda za ta je d’in…amma ita sam ba ta yi tunanin su Daddy za su yi musu aure ba. Dan haka ya taimaka ya taya ta nemo Yash ta samu ya sauwwak’e mata, ita kam aurensa ba ya cikin plan d’insu.’ Dukda wannan bayanin nata still Sai da Yassir ya nuna mata b’acin ransa na k’in tuntunb’arsa da ta yi kafin ta yi abun, ita kuma ta basa hak’uri sosai tare da alk’awarin ba za ta k’ara ba, tukunna ya yi mata alk’awarin nemo Yash a duk inda yake ko ta message ne a samu ya sake ta…Hakanan suka rabu daga shi har ita babu wanda ya san ba aure ma tsakanin Kausar da Yashjub d’in. Bayan kwana biyu Kausar ta san yadda ta yi ta bincika wayarsa ta d’auki number mutanen nan masu evidence (Yaran grenade) Sai da ta b’oye numberta, tukunna ta tura musu message ta inda take cewa ”su turawa Yashjub da duk wasu mutanen da suke neman wanda ya yi aika aika a Estate d’in Yashjub ɗin shaidun da suka turawa Yash Yassir ya saka suka goge, ita kuma za ta basu ko nawa ne su ke so.” Saboda ita har ga Allah Yassir ya ishe ta kuma ta san idan ba kama shi aka yi aka kashesa ba to tabbas ba zai barta ta sakata ta wala ba. Abuja su Manubiya suka fara zuwa, kafin su gama shirye shiryen tafiya….sai bayan sati biyu tukunna suka isa Copenhagen Denmark suka yi settling! Cikin rarrashin da tsoron shiga Hakki ta shiga k’ok’arin fahimtar da shi cewa “ko ba komai fa Kausar matarsace!!” Har ga Allah sai da ya yi mata bayanin da shi kansa sai a cikin jirgi da kwakwalwarsa ta d’an huta tukunna ya tuna sannan itama ta tuna tabbas fa da gaske babu aure tsakanin Kausar da Yashjub saboda ba a d’aura aure da ciki! A ranar tsakanin Manubiya da Yashjub ba za a ce ga wanda ya fi wani murna ba……daga nan suka kawar da duk wani b’acin rai suka shiga shimfid’a rayuwarsu mai dad’i a Copenhagen dan basu ga ranar dawowaba…. Mommy kuwa zuwa yanzu ta riga ta gama sanin me za ta yi game da auren Kausar da Yashjub………… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 41* A b’angaren Mommy kuwa zuwa yanzu ta riga ta gama sanin me za ta yi game da auren Kausar da Yashjub. Ta riga ta san zuwa yanzu Yashjub ya san babu aure a tsakaninsa da Kausar..kuma ita kanta zuwa yanzu ta san ba ta da lokacin da zata ce sai sun cire Manubiya tukunna za su kashe Yashjub! Shiyasa kawai ta ma hak’ura da sake k’ulla auren Yash da Kausar d’in a karo na biyu. Ta dai ji Daddy yana cewa Ummi”Kausar d’in tana a matsayin matar Yash a idanun duniya har zuwa lokacin da za ta haihu. Gudun b’acin suna.” So ita kuma kafin nan da zuwa lokacin da Kausar d’in zata haihu inshaaAllah burinta zai cika! kud’irinta zai cika! Kuma ta san barin Kausar d’in ma da aka yi a mazaunin matar Yash d’in Allah zai nuna hanyar da za su ci moriyar hakan inshaaAllah.. Kawai ita yanzu wuyarta ta san inda Baba Larai take, dan tana buƙatarta matuƙa yanzu kam, saboda ta riga ta gama tsarawa akan duk bala’i wuyarta Yashjub da Manubiya su sako k’afa a cikin k’asar Nigeria wallahi sai ta ga bayan su!… Dole a yita ta k’are abun ya yi yawa, kuma anzo gab’ar da dole ta yi musu hakan cikin gaggawa idan ba haka ba kuwa to tana cikin masifa!!!!… Zuwa wannan lokacin idanunta sun rufe..a iyaka saninta Ita da Yassir suna cikin gadon Yashjub dan haka ba sai ta wani jira sun yi abunda suka yi an mallaka masa dukiya gaba ɗayanta ba, iyaka kason da za su samu ma idan an raba gado ya isa! Daganan su kuma su Daddy da Ummi da su Hajiya Mama duk za ta saka su a saiti InshaaAllah ta san me za ta yi musu, gara kawai a yita ta k’are…… rashin sanin inda Baba larai take shine kawai yake kawo mata babban fullstop a mission d’in nata saboda Baba larai d’in ce za ta yi komai tun daga kan dawowar da take so suyi cikin gaggawa har zuwa kan mutuwarsu. Tsakanin Mommy da Yahanasu sam babu jituwa kwata-kwata! Yahanasun ta k’i yarda ta ba ta chance har y’an gidan sun fara lura da yadda Mommyn take binta ita kuma tana kaucewa… Mommyn har da ce mata “InshaaAllah za a karya abunda aka yi mata a samu ta yi aure!” Ita kuwa Yahanasu tace”dan girman Allah kar su karya komai! su barta a yadda ta ke ta yi Imanin Ubangiji ne kad’ai zai iya yin ikonsa a kanta.” Kamar yadda Mommy ta yi zato, Yahansun ba ta tona mata asiri ba, ammafa tun daga wnanan ranar ko had’a hanya Yahanasu ta daina yarda ta yi da Mommy, k’ofar d’akinta kuwa kullum a rufe. ….. ……Wata d’aya wata biyu tun su Mommy suna d’aukar b’atan Baba Larai abun kamar wasa har suka zo suka fara tsorata, dan yau kwana sittin kenan babu ita babu alamarta, wayarta ba ta shiga, gashi suna tsananin buk’atarta dan Ya’isha ta d’aga musu hankali akan auren Najeeb da Siyama gashi Yash da Manubiya babu su babu dalilinsu! ba ma ta jin za su dawo bikin, Yassir kam ya sake tab’arb’arewa company d’in da Yash ya bud’e masa ma ya tashi a aiki!! Hatta building d’in nasa ya sayar, motocinsa masu tsada ma ya siyar, kuma har yau ba a san Ina yake kai kuɗaɗen ba.. Kausar kam ba k’aramin Namijin k’okari take yi wajen danne zuciyar ta game da shi ba, gashi mutanen da ta addaba da kira a kan su tona masa asiri a samu a kashe sa ta hutu! sun daina ma sauraronta kamar waenda ya yi musu tsafi! A fannin lamarin Yash kuwa ita kad’ai ta san me take ji ita kaɗai kuma ta san halinda take ciki!! Ta kira sa! ta yi message!! amma duk baya shiga, ba ya tafiya! tsabar bala’i har depression ta kamu da! Da kyar ta samu ta nutsar da kanta ta ke shan magani ganin tana shirin haukacewa!! Inda ace babu aurenta a kan Yash ya yi wannan dogon zangon da baza ta tab’u sosai ba amma wannan zumar da aka lasa mata a baki aka janye shi yafi komai haukatata!! ……saboda Allah ace ranar da ake shirye shiryen kai ka gidan Miji mijin ya gudu!! kuma har yau bai dawo ba!(dan ita har yau ba ta san ba matar Yashjub bace ba ita.) Dukda wannan bala’in da take ciki amma tana namijin k’ok’ari wajen rik’e kanta da saisaita kanta, zuwa yanzu ba ta da komai against su Mommy amma haka kurum take jin ba za ta iya tattauna matsalarta da su ba! Ba za ta iya sake yarda da su ba….. abunda Mommy ta yi wa Baba larai ma ya sanya Kausar d’in ta d’an tsorata da Mommyn, ta ja jikinta sosai… Doctor d’inta dai yace mata hakan alamace ta ciwon damuwan da ta kamu da shi saboda ta yi going through a lot a rayuwarta da yawa shiyasa ba za ta iya sake yarda da kowa ba(ta zama komai nata a sirrance), sai dai sam ita ba ta wani yarda ba,ta fi raja’a akan kawai dai shekarunta da suka ja ne suka sanya ta yi wayo ta zamo shiru shiru ta kuma koyi rik’e sirrinta. A kaff y’an matan gidan har ma da Mommyn babu wanda ya lura da cewa ba ta ma da lafiya saboda kamar yadda take cikin masifa hakanan suma kowa a cikin masifar take! Su Yasira zuwa yanzu rashin aure ne matsalarsu, dan auren Yadira da suka ga ya taho gadan gadan ya sake uzzura musu son aure a cikin zuk’atan su musamman ma Yasira wadda ta fissu shekaru, sai dai kuma ko talakan saurayi babu mai shi a kaff cikinsu, Ya’isha kuwa tata damuwar daban ce dan ji take muddin Najeeb ya auri Siyama a gaban idanunta to kuwa sai ta mutu!!! Mommy kuwa nata tashin hankalin ya fi na kowa dan itama rashin auren nasu yana damunta amma ba kamar yadda komai ya rinchab’e mata ba!! Ta ko’ina babu haske babu sauk’i babu nasara……Kausar d’in ma da ta shirya akan za ta yi mata Abu da Yashjub a kan Daddy gashi yanzu babu auren, kuma a yadda take ganin Daddy kwana biyun nan in dai ba irin wannan aikin aka yi ba tabbas akwai gagarumar matsala. Da kyar ta samu ta dake ta sanarwa Kausar d’in da su Yasira ‘babu fa maganar aure’ dan tausayinta take ji gara kawai ta sani ta cire hope, aikuwa ranar duk dauriyar Kausar kasawa ta yi,sai da suka yi sati d’aya a asibiti tukunna ta dawo dai-dai da kyar ta fara gane waye ma a kanta. Dole ta sanya Mommy ta fito mata a mutum ta ce mata ‘kawai ta hak’ura da Yashjub!!! Ta yarda ta aminta da ita kawai idan ta ce mata ta taimaki kanta ta cire Yash a ranta, dan zuwa yanzu ya kamata ace ta fahimci zuciyar Yash ta Manu ce,dan haka dan Allah ta hak’ura kawai!… Tana cikin masifa, gashi babu Baba Larai dan haka dan Allah ta ajjiye komai a gefe ta tashi ta tsaya mata dan tana buƙatar ta tsaya mata ɗin a matsayinta na ƴaruwata kwara ɗaya wadda ta yi mata saura. Dan haka ta taimaka mata, akwai labarin da zata bata amma ba yanzu ba sai nan gaba. Ta ajjiye batun soyayya haka nan ta taimaka mata ta rai da tsira ake yanzu dan duk abunda ya sameta to itama ya shafeta farinciki da nasara ko kuma akasin hakan… sannan su Daddy sun ce har ta haihu a idanun duniya tana a matsayin matar Yashjub ne…InshaaAllah a tsakankanin nan Ubangiji ta san zai nuna musu hanyar da za su bi komai ya tafi musu dai dai.” Ita dai Kausar tace mata “to” ne kawai, amma bata gama fahimtar inda zancen nata ya nufa ba sakamokon bala’in da take a ciki, ita kanta yanzu kam ba ta san ta Ina za ta b’ullo ta sake zama mata ga Yashjub ba!! Ta kasa yarda kanta da zuciyarta sun aminta da cewa ‘gaba d’aya hard work d’inta da baƙar wahalar da ta sha duk dan ta mallaki Yash sun tafi a banza lokaci guda kenan???inaa da sake!. Ba zai yiu ba gaskiyq! Har yanzu babu Munirat babu labarinta, Ummi ta kuma zama abun tausayin Hankalinta gaba d’aya a tashe! Daddy ne yake dan tausar ta shi da su Hajiya mama wanda shima Hajiya Maman ce take tausar sa take tsayar da shi ba dan itan ba da tuni ya san na yi da Mommy…dukda ya san ba shi da wata hujja a kanta amma kawai shi jurarta ne a cikin gidan ya ke masa azabar wahala! Ba zai iya ci gaba da jurarta ba,ya tsaneta. A bangaren Mama itama zuwa yanzu ba ta da wani burin da ya wuce ta saka Yahanasu da Yashjub a idanunta dukda tana tambayar Manubiya ya suke tana jin komai dan har gaisawa sukeyi ma da Yashjub amma tana buk’atar ta saka su a idanunta musamman ma da ta ji har yanzu Yahanasu ba ta yi aure ba! Tashi ɗaya duk ta damu hankalinta ya kasa kwanciya dan ta san dole tana da buk’atar ta….. Bayan watanni uku!!! An yi auren Siyama da Najeeb gidansu yaana unguwar Badawa,haka shima Junior ya auri Yadira suna zaune a d’aya daga cikin gidajen Daddy dake a Unguwar Darmawa kafin ya kammala abunda ya zo yi ta karb’i transcript d’inta su wuce Uk. Duk cikin aure biyun nan da aka yi, su Manubiya ba su zo ko d’aya ba, sun dai turo gudunmawa sun kuma yi addu’a. Su Hajiya Mama ma da suka zo na su Junior ba su wani dad’e ba suka juya, dan ita dama da kyar ma ta yarda ta zo. Ya’isha tana nan yau lafiya gobe ba lafiya, dan yadda ta kad’u ta damu da al’amarin sai da ya girgiza su Mommy, gashi har yanzu batama da shirin hak’ura da Najeeb ɗin. Kausar ma tana nan tana fama, kullum ba lafiya ga ciki ya tsufa..jira kawai take yi su Yashjub su dawo wllahi duk bala’i sai ta san yadda ta yi ta koma masa sai dai ta rasa ranta a hanyar raba sa da Manubiya da kasancewa tare da shi. Ya Musbah ma ya kammala karatun da ya yi, takardar tana fitowa ya fara shirye shirye cikin nasara kuwa ya zana waec ya yi jamb, yanzu haka neco ya ke yi, kuma ya ci jamb d’in, dan haka Najeeb ya sake zage damtse wajen nema masa gurbin karatu a fannin Business Administration a jami’ar Bayero uni,Kano. Gwaggo Suwaiba ma ta zo,yanzu Mijinta shima Allah ya fara nuna masa k’arshensa kuma Itanma ta dage da addu’a sosai, dan cikin ikon Allah tana cikin wnnan hali na ha’ula’i Allah ya kawo mata wasu makwabta jajirtattu wajen fannin addu’a har Al’k’urani suke rubuwata da littafai… sama-sama suka fara gaisawa, su kad’ai suke iya shiga gidan, sai da zama ya yi dad’i labari ya yi labari tukunna suka fahimci ashe ma Matar (maƙwabciyar tasu) tana da dangantaka da Mahaifiyarsu Inna da Gwaggwo suwaiban, amma irin dangantaka ta nesa ɗinnan. Matar ce ta bawa Gwaggo Suwaiban addu’o’i, kuma ta ce ta dage da Azkar da sallolin dare..Aikuwa da taimakon Ubangiji cikin ikonsa yanzu Mijinnata har islamiyya ya barta ta shiga, sannan yanzu kam ana iya zuwa wajenta kuma wannan tsangwama ta kyarar duk babu, ba shi ma da lafiya ya kwanta jinya…. Ko da ta tambayesa zata zo ta ga Inna an yi auren su Jidda duk ba ta zo ba! Nan ma sam bai yi yunk’urin hanaawa ba, dukda ba ya so amma shi kansa ya san yanzu kam surk’ullensa sun daina tasiri a kanta…hakanan ta taho kano ita da d’aya daga cikin y’ar mak’oftan nasu mai suna Hadiza bafulatanar Yarinya mai shekaru 17 kyakkyawar gaske siririya doguwa fara sol gashi har gadon baya. Tunda suka zo da Ya Musbah ya kyalla ido ya ga Hadiza itama ta gansa suka kamu da k’aunar juna, abun kamar had’in baki. Satinsu biyu ya ga dai ba zai iya daurewa ba ya amayar da abunda ke zuciyarsa itama kuwa Hadiza ko irin d’an jan ajin nan na mata da kunyar fulani gagara kwatantawa ta yi tashi d’aya tace masa ‘Yes!!’ Dama su Inna sun fahimci take takensu, ai kuwa Yarinyar tana gayawa Gwaggo Suwaiba suka hau murna, itama kuma Inna Ya Musbah ya gaya mata, ba kad’an ba Inna ta ji dad’in had’in shiyasa Murna ta zame mata biyu, ga farin cikin ganin y’ar uwarta ga kuma farin cikin had’in Hadiza da Ya Musbah da Ubangiji ya had’a! Hausawa sun ce ba ‘a yabon d’an kuturu sai ya shekara da yatsu amma tabbas ita kam za ta yabi Hadiza saboda Yarinyar tana da hankali, ga ilimin addini, ga son mutane da girmama na gaba da ita,sannan gwaggwo Suwaiba ma da suka yi watanni goma sha uku tare da su ta bada kyakkyawar shaida a kanta, kuma itama ta ji dad’in had’in matuk’a. Dama su Inna so suka yi a b’oye abun sai an saka rana komai ya kankama tukunna a fito da maganar, ba dan komai ba sai dan saboda Baraka… amma Allah da ikonsa tun kafin kowa ya ji ma ita Barakar ce ta fara ji kamar wata mai duba…aikuwa nan da nan ta kunno masa wutar bala’i ta koina, ba ta tashi masifar ta sai dare ya yi idan ya zo bacci, nan za ta hanasa bacci sai dai su kwana idanunsu biyu..amma har gobe shi nuna mata ma yake yi bai san a kan me take bala’in nata ba!!!shi inama ya ga lokacin yin wata budurwa???… Dukda hakan bai sa Baraka ta hak’ura ba, kuma bai sa ta bar Hadizar ta zauna sakayau ba, dan yanzu tun safe har dare a wajen su Inna take wuni! dukda idan ta shiga wajen nasun fuskarta kullum kamar ta shanu sannan hakanan za ta yi tai musu kallon hadarin kaji, amma kuma hakanan za ta zauna a tsakiyar su ta na ta yada maganganu a Hadizan har ma da su Inna! ko a jikinta. kuma zuwa yanzu hakanan ta hana Ya Musbahn keb’ewa da ko Innar ne, wai duk dan gudun kar ya samu lokaci da momment da Hadiza. Kamar mai gadin sa haka ta koma, ta kafa ta tsare, haka nan za ta yi ta zaman jiransa a side ɗin su Innar…yana dawowa daga aiki kuwa zata fara hamma har sai sun tafi. ko wajen Baba ya je haka za ta yi ta safa da marwa a bakin k’ofar parlourn nasa ta baya har da lab’e, har sai ya fito sun wuce tukunna hankalinta zai kwanta. Tsabar bala’in da ta sakawa kanta ko girki ba ta iya zama ta yi, ballantana gyaran gida! koina ya yi datti…gashi ba girki, gida duk tsami kuma a da Baraka kam tanata tsafta gwanin ban sha’awa. Sai dai kullum idan ta gama gadin nasa suka koma b’angaren su yace mata’ta d’an saka turaren wuta ta kimtsa gidan yana kyankyami’ shi kuma ya fita ya je ya siyo musu gurasa da nama…abunda Baraka ba ta sani ba shine idan ya yi fita siyan gurasa da naman ne yake samun ganin Hadiza, dan sam ba shi ne yake zuwa siyowa ba, almajirin su mai wanki da sharar gidan yake bawa shi kuwa ya dawo ciki ya wuce wajen Hadiza inda suke had’uwa kullum wajen wanke wanke ta baya. Yana lura da sa idon da Baraka take yi masa, dan ko fitar zai yi sai ta lek’o ta tabbatar ya fita d’in tukunna take komawa ba ta san yana kallonta ba. A yadda yake son Hadiza ba ya so a samu matsala a aurensu, kuma zuwa yanzu ya fahimci Baraka ta hau Buzu, shiyasa ko su Inna da suke ta cewa ya fad’a mata idan auren ya rage saura sati biyu jin su kawai yake yi, dan sai ya samu kansu tukunna zai nutsu ya zauna ya yi musu bayani sosai..domin shi kam inshaaAllah sai dai kawai Baraka ta ga Hadiza a d’akinsa matsayin matarsa ko kuma ta ji ana d’aura aure. A b’angaren Baraka kuwa har yau ba ta kama Hadiza da Mijinta ba, amma dai ta san akwai abunda ya ke wakana a tsakaninsu, gashi wayarsa koina password ballantana ta yi masa bincike…Bokan ta ne ya fara sanar mata, yanzu kuma ya sake d’aga mata hankali ta inda yake ce mata ai maganar aure ma ake yi… dama chan Baraka a cikin masifa take sakamokon yadda komai ya k’i tafiya yadda take so, Ya Musbah ya k’i ya dawo mata kamar da! Sam ta gagara mallakesa kwata-kwata, sannan so take a raba gidan biyu ko a sayar da gidan a sayi wani su rabu da su Inna amma abu ya ci tura!!! Gashi gaba d’aya ta rasa soyayyarsa kuma ta gagara dawo da hankalinsa gareta, kuma sai yanzu ita kanta ta fahimci masifaffiyar k’aunar da take yiwa mijin nata musamman ma da ta ji zancen maganarsa da wata….shiyasa ta tashi ta tsaya tsayin daka! Ta ƙudiri aniyar ‘wallahi indai ta haifu, to Ba’a isa a yi mata kishiya ba, kuma Inna da take zugasa ta hana ruwa gudu ta toshe mata duk wata hanya wallahi sai ta haukatar da ita, ko kuma ta maida ita kamar yadda take farko ta hanyar kwantar da ita, ta yadda za ta zama da ita da gawa babu maraba!’ saboda Bokan ta yace mata”Inna ce take yin addu’o’i ba dare ba rana, babu ji babu gani, shiyasa komai nata ba ya ci, komai nata yake tab’arb’arewa.” Yahanasu ma ta yi sabon saurayi mai suna Egnr Doc Kamal sumaila vice governor d’in Kano state…sun had’u da shi ne ta sanadiyyar tsaya musu da ta yi a matsayin mataimakiyar lawyer su na shar’iar da suka yi ta fafatawa yau kusan shekara d’aya kenan akan mulkinsu da aka yi musu almundahna, to yanzu dai Alhamdulillah komai ya daidaita sun hau kan mulki wanda sai a lokacin ne ya fito mata da k’udirinsa! Ya fi wata d’aya yana binta tana cewa a’a, shi ya d’auka ma ko saboda kasancewarsa babban mutum amma bai tab’a aure bane ya sanya tace masa a’an, sai da ta fito masa ta basa labarinta tukunna ya fahinceta…cikin ikon Allah shima d’in hakan ce ta yi ta faruwa da shi, dan sau hud’u ana samun matsala a batun aurensa (ana fasawa) dan haka yace mata ta yi hak’uri ta daure su bawa alaƙartasu chance inshaaAllah wannan karon daga shi har ita za su dace… Da kyar da taimakon su Manubiya da ta gayawa suka dinga bata shawarwari aka samu ta amincewa Alhaji kamal, yanzu dai ya zo sau biyu jiya kuma sunzo shi da Abokinsa sun gaida Daddy. Hatred, tsagwaron tsana da tsantsar takaicin Mommy ne ummul’aba’isin kwanciyar Daddy rashin lafiya, ga kuma damuwa daban-daban, gashi Yashjub ba ya kusa. Last week Abhi ya zo ya dubasa, sam bai ji dad’in yadda ya ga jikin nasa ba, dan ba don yana da aiki ba ma to da ba zai koma gida ba…. Hankalinsa duk ba a kwance ba, Hakanan ba dan ya so ba ya wuce Uk…tun a jirgi ya kira Yashjub yace”yana son ganinsa a Uk idan ba damuwa.” Ya san suna waya da video call da Daddyn, amma ya kamata ya je ya gansa gaskiya. Bayan kwana uku da dawowar Abhi su Manubiya suka zo ita da Yashjub d’in…ta yi fari k’all, ta yi k’iba ta yi fresh ta k’ara kyau abunta amma babu ciki babu alamun sa a tare da ita, wanda hatta su Hajiya mama sai da suka d’an ji d’arr!! Amma kawai sai suka basar, suka ci gaba da murnar ganin juna. Abhi kam ya ma fi su Hajiya mama damuwa, har ga Allah fa wannan yana daga cikin confidential reasons d’insa(ɓoyayyen dalilinsa) da ya sa ya so ace Yashjub yanada mata biyu ne, ba wai Kausar ba! A’a, bayan ya sake ta(kausar ɗin), ya so ace Yash ɗin ya auri wata saboda ba zai yiu ace Yash ya k’are rayuwarsa a haka ba, duk wannan uban dukiyar ace shege ne kad’ai zai juyata……… “Abhi Ina wuni!” D’in da Yash ya ce masa ne ya katse masa tunani… Ahankali ya ke kallonsu shi da Manubiyan, kafin ya d’an yi murmushi ya amsa gaisuwar tasu tukunna ya d’aura da cewa “duk kun yi k’iba kun yi kyau abunku tubarkallah!” Sunkuyar da Kai Manu ta yi cikin tsananin jin kunya, yayinda Yashjub ya d’an sosa k’eyarsa yana murmushi…. Ciki su Hajiya Mama suka wuce da Manubiya bayan an gama gaishe gaishe..suna wucewa Abhi ya gyara zama ya kalli Yash yace masa “yaushe za ka je ka dubo mahaifinka??” Tashi d’aya yanayin fuskar Yash d’in ta chanja, idanunsa suka d’an fara kad’awa. Sai da Abhi ya sake jeho masa tambayar a karo na biyu, tukunna da kyar ya samu yace”ba rana!” “Saboda me??” Abhi ya tambayesa cikin tarar numfashinsa. Wata nannauyar ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace”Abhi pls, dan girman Allah ka bar maganar kawai.” Jinjina Kai kawai Abhi ya yi, daga haka ya d’auki waya ya danna kiran Hajiya mama tana d’auka yace “Mama sai fa kinzo saboda ya k’i gaya mini.” Runtse idanu Yash ya yi da tafukan hannunsa, kafin ya cika ya d’ago ya kallesa yace”Abhi saboda Kausar ne fa, dan Allah kawai ka bar…” “Kausar dai is one of the reasons Yash! ko har ka manta message d’in da ka turo mini da Hannunka??” Muryar Hajiya mama ta katse sa tana mai k’arasowa inda suke, kafin ta zo ta nemi guri ta zauna, tana mai fuskantar sa tace”Yash an baka sarari kamar yadda ka buk’ata, Kausar is no longer your wife! Dan haka menene dalilinka na k’in komawa Nigeria, ko kanada waenda suka fi mu ne da ba za ka gaya mana matsalarka ba sai su?” Hawayen da ya zubo masa ya sa Hannu ya goge kafin ya ce ”barin maganar nan shine mafi alkhairi ga kowa Hajiya mama, bana son yinta…” Sake gyara zama ta yi da zaman gilashin idanunta, ta fuskancesa sosai tace”ni kuma yau na nace sai na ji komai, dan haka the sooner you talk the better,,dan ka san ba zan tab’a hak’ura ba ko?.!” Jinjina mata Kai ya yi, dan haka tace”perfect..muna sauraronka!” Sai da Yashjub ya d’auki sama da mintuna goma, ya yi shiruu kawai… kafin chan ya zaro wayarsa ya kai musu inda videos d’in Yassir suke, ya mik’awa Hajiya mama, ya yi sauri ya mik’e ya fita…… …. Sai da hawan jinin Hajiya Mama ya tashi! Abhi kansa sai da ya yi Hawaye ba sau d’aya ba….ba su iya b’oyewa Daddy komai ba hakanan suka sanar da shi komai, wanda shima ɗin sai da suka yi da na sanin fad’a masa ɗin da suka yi ta waya! dan sosai ya gigita ya kad’u matuka da al’amarin, da kyar Ummi ta taushe sa aka samu ya sha magani ya yi bacci bayan sallar asubah dan throughout ranar ba su runtsa ba. Da kyar da mugun kyar suka lallab’a Yashjub, aka samu ya yarda zai zo Nigeria! dan ba k’aramin Takaici ya ji ba da ya ji sunce har sun turawa Daddy, saboda shi har ga Allah ba hakan ya so ba… sai da Hajiya mama ta zaunar da shi ta yi masa fad’a ta nuna masa illar yin shiru da kuma guduwar da ya yi, tukunna ya yarda da kyar ya amince ba dan ya gamsu ɗari-bisa-ɗari ba. Sai da suka yi sati d’aya, tukunna suka samu zuwa… Yashjub Manubiya Abhi da Hajiya mama… Manubiya kanta Hankalinta a masifar tashe yake, dan tunda Yash ya sanar da ita komai ta fahimci yau case ne a gidan, shiyasa ta nemi alfarmar ‘ya bari su Ya Musbah su zo su d’auketa a airport, ta yi missing su Inna dayawa, bata samu ta yi musu sallama ba, gashi har gwaggo Suwaiba itama ta zo.’ Ya fahimci zillewa take son yi, kuma shima baya son a yi a gabanta, shiyasa ya amince….tun kafin su yi boardn ta sanar da su Ya Musbahn, ai kuwa a airport d’in su suka fara gani shi da Ya Nafi’u kafin su Junior suma su ka k’araso. ……Ba daban Yassir ba ya cikin gidan ba to da tuni Daddy ya dad’e da d’aukar mataki a kan sa, dan ya tafi Abuja tun last week bayan ya cewa kowa ya je yin business ne… Da farko da Daddy ya ji zancen masifa ya shiga, da tashin hankali mai tafe da tausayin Yassir d’in..yanzu kuwa haushi da tsanar Yaron yake ji maƙura!! Baya jin ma zai iya kallon fuskarsa. Ba ya son jin ko da sunansa ne…. Kaff gidan zuwa yanzu kowa ya san Daddy yana cikin b’acin rai! On top of na farkon da yake a ciki da kuma rashin lafiyarsa, shiyasa kowa ya sha jinin jikinsa harda Mommy wadda ta fara shirye-shiryen yi masa bori ata dalilin kwata-kwata ya daina raba musu kwana ita da Ummi, dukda ko da chan d’in ma tana zuwa dama yake korarta, amma dai ai ya fi mutunci da daraja akan yanzu da ya had’ewa Ummi kwanakin gaba d’aya kaff. Jirginsu Yashjub ya sauk’a da safe around 6:00am na su Yassir kuma ya sauk’a around 6:40am, Shiyasa ya zamana sun shigo cikin gidan kusan a tare dan su Yashjub suna gama shiga shima ya shigo. Side d’insa ya fara nufa ya je ya yi freshening up! Daga haka ya fito a gurguje dan ya yi misssing Kausar over!! Dukda wajen sabuwar budurwarsa da suka had’u a instagram ya je ya gwangwaje abunsa, amma da kewar Kausar yake kwana yake tashi, har ga Allah shi kansa bai san wanne kalar so yake yi wa Kausar ba. Ita kuwa Kausar tana chan, ta shiga damuwa..dan mutanen sun ce mata ‘ba za su tona Yassir ba, dan ya cika alƙawarin da ya yi musu ta inda ya dad’e da taimakawa oganninsu suka gudu.’ Ba k’aramin tashin hankali Yassir ya shiga ba da ya fara jiyo kamar muryar Yash suna magana shi da Ummi a baki bakin k’ofar. Aikuwa yana shigowa da shi ya fara cin karo! ya juya baya yana magana shi da Ummi…. Tashi d’aya hankalinsa ya tashi, ransa ya yi masifar b’aci, zuciyarsa ta fara tafarfasa….wani irin sabon haushi tsana da k’iyyayyar Yash d’in suka yi masa k’awanya.. “K’araso ciki Yassir!!” Muryar Abhi ta katse masa tunani, a dake!. Kasa juyawa Yashjub yayi, sakamokon wani irin yanayin da ya tsinci kansa a ciki. Yassir d’in kamar ba zai kula sa ba, sai kuma ya d’an matsoshi yace”sauk’ar yaushe?” Bai jira jin amsar sa ba yace”welcome” Daga haka ya wuce ciki dan he can’t stand him. Parlourn taff cike yake, daga Mommy sai Kausar wadda take ta uban bacci ba ma ta san sun dawo bane kawai babu. Shiruu kowa ya yi, har su Yadira da basu san me ke faruwa ba! Yayinda su Daddy suka tsura masa idanu kawai. Cikin nutsuwa Yassir d’in ya k’araso, ya nemi guri ya zauna ya fara kallonsu one by one dan zuwa yanzu kam ya san tabbas akwai matsala. Gyaran murya Abhi ya yi kafin ya kalli su Yasmeen yace “ku d’an bamu guri” Girgiza kai Daddy yayi cikin tarar numfashinsa ya ce ”ka barsu Abhi,Ina buk’atar shaidu.” Bai jira d’aukar lokaci ba ya kallesu ɗaya bayan ɗaya yace “ina so duk ku zama shaidata! Daga yau har gaban abada babu ni babu Yassir!!!” Sai kuma ya kalli Yassir d’in yace “mintuna arb’ain kawai na baka! Ka tartara ya naka ya naka ka bar mini cikin gidana!!!!”. Da mugun sauri Yashjub ya juya ya fita, Yayinda su Yusra suka kaure da kuka suka shiga rok’ar Daddy suna basa hak’urin ya taimaka ya bar Yassir, ko me ya yi bai chanchanci hakan ba!….dan Allah ya janye maganarsa. Daina ji Yassir ya yi na y’an sakanni… Ya riga ya san duk inda aka je aka dawo su grenade ne Ummul’abaisin wannan mummunan al’amari da ya faru da shi a yanzu, dama ya san ɓata lokacin da ya yi wajen kuɓutar da su dole ya fuskanci hukunci daga garesu, amma kuma a tunaninsa 3 million d’in da ya bayar ta isa ta rufe musu Baki ai. “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ya shiga ambato a cikin ransa, dan bai ma san mai zai yi ba, ko ya zai yi ba, ko kuma mai zai ce ba!!!!. Shin da gasken gaske ne wannan al’amarin ya ke faruwa da shi, kokwadai mafarki ne yake yi….zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai tab’a zama helpless cikin matsanancin tashin hankali ba irin wannan!! Na farko ya san tabbas an san me ya yi , na biyu kuma yanzu shi idan ya fita ta ina zai fara? Ba shi da halin da zai iya ciyar da rai biyu, besides da ma ya gama tsarawa ita kanta yanzu kam sai dai ta ci gaba da ciyar da kanta dan last kud’in hannunsa ne ya yi amfani da su ya je Abuja ya dawo…… Da farko zuciyarsa tunzurasa ta fara yi akan ya yiwa Daddyn bori yace”babu inda zai je, sannan yace sharri aka yi masa” amma kuma indai videos da voice d’in da mutanen suka turo masa shi suka turawa su Daddy tou tabbas bai Isa ya fara cewa sharri baneba..Idan ya yi hakan kamar ya sake tsunduma kansa a wani sabon bala’in ne…dan haka zai fiye masa idan ya kwantar da kai a halin yanzu da halin da yake a ciki. Cikin fushi ya ji Abhi yace “we are morethan disappointed in you Yassir, ka bamu kunya! ban tab’a tunanin za a samu b’ata gari a cikin zuri’armu ba! dan haka tun kafin mu fara yi maka Baki ka b’ace mana daga gani a yanzu-yanzu ba sai anjima ba!.” Dai-dai nan Mommy ta sauk’o k’asan. Wani Irin rikicewa parlourn ya yi da koke-koke, hatta Yahanasu sai da ta yi hawaye kafin daga bisani ta mik’e ta shige d’akinta. Dai-dai nan Mommy kuma tana k’arasowa cikin parlourn, ta tsaya a tsakiyarsu, ranta a mugun b’ace, hankalinta a masifar tashe, jikinta yana wani irin karkarwa, tace “Ashe dama gulma da munafuci aka shirya, shiyasa na ganku gaba d’aya kun yo family kun zo????” Bata ga mik’ewar Daddy ba sai k’arasowar da yayi ya d’auketa da wani mahaukacin mari!! Cikin tsananin fushi hargagi da hargowa yace “dabbancin naki yau har ta kan Mahaifiyata ya biyo Khadija!!!Saboda ke mahaukaciya ce wadda ba ta san wa ya yi mata gata ba shine a gaban idanunmu za ki furta wannan kalmar?? Waye ya ke yi miki munafurcin??” Ya yi mata tambayar kamar yana shirin rufeta da duka! Tashi d’aya Mommy ta sha jinin jikinta, tashin hankalin da take a ciki ya sake hauhawa…Tabbas a yadda ta ga Daddy ya fusata d’innan ta san muddin ta biye masa to fa za ta janyowa kanta matsala…. Shiyasa tashi d’aya ita ta sauk’o, a take ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen cikin kuka tace “ka yi hak’uri Daddy dan Allah, ka yi hak’uri b’acin rai da tashin hankalin jin abunda kuke ik’irari ga Yassir ne ya janyo hakan, amma ka yi hak’uri da abubuwan da na fad’a ba zan sake ba, sannan dan Allah ka yiwa Yassir adalci, ka yi hak’uri, ko me ya aikata a ganina bai chanchanci hakan daga gareka ba!” Da mugun sauri Yassir ya mik’e ya fice..inshaaAllah tunda har Mommy ta sauk’o ya san za ta san abun yi. Cikin kuka Ya’isha ta tari numfashin Mommyn itama tace “Daddy ka yi hak’uri akan komai, dan Allah. Sannan ka duba yadda fa ka ke yiwa Mommy!!! Ka sanyata ta durk’usa haka a gaban kowa!! A gani na kamar yadda ranka ya b’aci muma namu fa zai b’aci idan ka tab’a mana mahaifiya!” Cikin tsawa junior yace mata”bar nan kafin na yi ball da ke!! Manya suna magana kina saka musu baki daɗin daɗawa kuma ‘rude tone’!!” Harara ta zabga masa wanda hakan ya sanya ya mik’e ya nufota gadan-gadan, cikin bashi kwarin guiwa Hajiya mama tace”kana zuwa ka rufeta da duka kar ka raga mata!!” Ganin yadda ya taho kuma ta san tsaf zai aikata ne ya sanya ta mik’e ta bar wajen da gudu ta haye sama tana sharar hawaye.” Tsaki Hajiya Mama ta yi tace”marar kunyar banza” Sai kuma ta kalli ragowar tace”duk wadda na sake jin muryarta a cikin ku za ta sha mamaki.” Yayinda Daddy ya had’iye wani abu mai d’aci a mak’oshinsa, da kyar ya juya kawai ya k’arasa ya d’auki wayarsa ya fara k’ok’arin playing video d’in, da sauri Abhi yace”ka yi hak’uri ba sai kowa ya ji ya gani ba” Cikin fushi Daddy yace”tabbas Abhi ya kamata kowa ya ji ya gani sabida idan ba haka ba wannan makirar matar sai ta k’unsa k’iyayyata a zuk’atan dukkannin jama’ar gidan nan,,dan cewa za ta yi Yassir bai yi mini komai ba hakanan na koresa, kalli fa kukan kissa da kisisinar da take yi bayan itace silar komai! Muguwar zuciyarta da gurb’atacciyar tarbiyyar ta su suka janyo komai dan haka kawai ka bari kowa ya ji ya gani.” Daga haka ya wuce ya k’arasa inda take ya cilla mata wayar yace”bud’e ki kalla ,kalla ki ga abunda rashin tarbiyyar da kika yiwa y’ay’ana ya janyo mana!! Ki duba kiga abunda Yassir ya aikata a d’an uwansa…..” Tarin da ya sark’afe sa ne ya sanya ya gagara ci gaba da magana… Da sauri Abhi da Hajiya Mama suka k’arasa inda yake suka ruk’osa suka kaisa kan kujera suka zaunar, Junior ya yi saurin matso masa ruwa daga dispenser ya kawo…. Shiruu parlourn ya d’auka in banda sheshshek’ar kukan Mommy da na su Yassira ba ka jin komai!!. Mommy ce take kallon video d’in amma iyaka voice d’in Yassir da bayanansa sun fahimtar da kowa na wajen abunda ke faruwa!!! A tare Yasmeen da Yadira suka mik’e suka bar wajen suna wani irin kuka kamar ransu zai fita, dan ba ma su san abun cewa ba. Da kyar aka samu Daddy ya dawo dai dai, tarin ya d’an lafa…cikin gajiya da komai ya d’ago ya kalli Hajiya mama yace “ki gafarceni Hajiya mama, ba zan iya ci gaba da zama da matar nan k’ark’ashin inuwa d’aya ba!” Gaba d’aya a tare Yasira Yusra da Mommy k’irjinsu ya yi wani irin mahaukacin bugawa..Ummi kuwa ta san me Daddy zai yi dan ya dad’e da gaya mata matsayin Mommy a cikin gidan, dan haka ta mik’e da sauri ta wuce sama….. Har ga Allah Junior ya ji dad’in abunda ya faru da Yassir, amma kuma sam bai ji dad’in abunda yake da shirin faruwa da Mommy ba shiyasa ya ce”Daddy koma me Mommy ta yi ka yi hak’uri…” Cikin tarar numfashinsa yace”Junior ba ka san me ta yi ba!!!” A hankali yace”Daddy ta ci albarkacin y’ay’anta!!!” Girgiza Kai kawai Daddy ya yi yace”not anymore!!!” Daga haka ya kalli Mommy yace”shekaru 32 kina zaluntata Khadija..na san nima wasu lokutan na kan sab’a miki ta hanyar nuna soyayyar wata fiye da taki, ko kuma nuna halin ko in kula da nake yi a kanki, amma Khadija wannan ma duk laifin ki ne! Saboda kin san ba na sonki ba na k’aunarki amma haka kika tilasta mini zama da ke…tsakanina da ke wata shari’ar sai a lahira, dan wallahi ko da zunubin tarbiyyar Yarana da kika lalata aka barki ya isheki!! Duk wata cutarwa da kika yi mini da su Ubangiji zai saka mana!!. A alamarin Khadija Sam ban kama ki da komai ba! Tabbas kin yi k’ok’ari wajen kare kanki, amma na san komai laifinki ne, kuma shima zaki had’u da Ubangiji zai yi mana hisabi mu uku ya bi mata hakkinta wanda a ko da yaushe idan na tuna hankalina tashi yake yi matuk’a, amma dole na san sai na fuskanci Ubagiji da wannan tarin zunubin da kika yaudareni kika sanya na aikata …..” Kukan da ya kufce masa ne ya sanya ya gagara cewa komai kafin da kyar ya samu ya ci gaba da cewa”zamu had’u da ke a lahira!!! Amma for now Khadija a halin yanzu bana k’aunar in sake jin ko da labarinki ne dan haka ki bi Yassir ku b’ace mini daga gani, har gaban abada ba na so in sake jin ko da muryoyinku ne!!!!!” Tabbas wannan itace rana mafi muni a rayuwar Mommy…wani irin kuka take yi tana janyo numfashinta da mugun kyar….duhu-duhu kawai take gani!! tabbas ta san Idan ta biyewa Daddy tsaff zai sake ta a take a yanzu shiyasa ta yanke shawarar tafiya kamar yadda ya buk’ata tun kafin ta b’intike igiyoyin aurenta ta je ta tonawa kanta asiri ta tarwatsa kanta….gara ta samu ta je ta yi sabon shiri a samu ya biyota ya rarrasheta ya d’aukota da kansa ya dawo da ita gidan, daga nan kuma sai ta san abunyi saboda ta riga ta san ba kowa bace silar wannan bala’in da take a ciki face Manubiya, dan haka dama ta gama tsarawa tunda ta k’i fita daga rayuwar Yashjub gara kawai su mutu tare cikin gaggawa……tun kafin su zamo ajalinta….. Tana cikin wannan tunanin kamar a mafarki ta ji muryar Daddy yana cewa”kwanaki da kika tarwatsa auren Yassir da Kausar na sake ki!! Da na fahimci abunda kika koyawa y’ay’ana kika turasu suka je suka aikata a gidan Yashjub shima a take a wannan lokacin na sake sakinki!!! Kuma na san baki manta da sakin farko ba.. dan haka yanzu ni da ke babu maganar aure har abada!.” …..Da farko duhu Mommy ta gani ya mamaye ganinta, sai kuma ta daina ji gaba d’aya kafin ta ji k’afafunta da hannunwanta da duk wani sassa na jikinta kamar ma babushi!! Daga ƙarshe kuma ta tafi luuuuu ta zube a wajen sumammiya. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 42* Gaba d’aya Yaran kanta suka nufa har Junior, babu kalar ruwan da ba su yayyafa mata sun shafa mata ba amma ko gezau! Dan haka Yasira ta kalli Junior hankali a masifar tashe tace”Junior taya ni mu d’auketa mu kai ta sama, sai in kira Dr…” Ko gama rufe bakinta ba ta yi ba Daddy yace”amma ba ku ji abunda na fad’a ba ne?!! Wanne saman za a kai ta?” Cikin tsananin mamaki Yasira ta d’an cika Mommyn ta d’ago tana kallonsa idanunta jazir tace”Daddy suma fa ta yi?a hakan still baka hak’ura ba, so kake ta fitar maka daga gida? Atleast ka tsaya a samu ta dawo cikin haiyyacinta mana, inyaso sai a yi komai, dan girman Allah.” Hajiya Mama ta so ta saka musu baki tun d’azu, amma kuma sai ta ga wannan hukuncin Daddy ya kamata a barwa ya yanke, ita dai ta basa shawara ne, dan haka kawai sai ta ja bakinta ta yi shiru. Cikin d’aci Daddy yace”Yasira ban bawa kowa ikon ya hau mini da ita sama ba, sannan iyaka mintuna biyar na bayar a fitar mini da ita daga cikin gidana!”. Sosai zuciyar Yasira ta hau tafarfasa ta fusata sosai, dan a ganinta duk lalacewa dai ai ko dan darajarsu bai kamata ace ya kori Mommy ba daɗin daɗawa kalli fa halin da take a ciki amma dukda hakan ya dage kawai shi a fitar masa da ita daga cikin gida kamar wata annoba!! Idan ta gaskiya za a bi ai ba ita ta sanya Yassir ya yiwa Yashjub abunda ya yi ba!….. Cikin sharar hawaye ta mik’e zuciyarta a iyaka wuya tace”Daddy muddin fa Mommy ta fita to muma binta za mu yi tabbas!!!” Cikin matsowa kusa da shi ta ci gaba da cewa ”shin ka shiryama rasa mu muma akan dai ka tsaya a yi magana a yi sulhu??” Shiruu ya yi kamar ba zai ce komai ba (dama wannan shine abunda shi da Hajiya mama suke gudu!!!) kafin chan ya d’ago ya kalleta, yace mata”time d’in da na baku ku fitar da ita ya kusan cika…Yasira nan gidan ku ne dan haka feel free ki zab’i wajen Mahaifiyarki sannan ki dawo nan a duk lokacin da kika ga dama, babu wanda zai dakatar da ke. Iyaka abunda na sani, na kuma tsaya akai shine a yau a yanzu sai Khadija ta bar cikin gidana! ta bar rayuwata, bari na har abada!!!!.” Wani irin kuka Yasira ta fashe da shi, ta juya ta fita daga parlourn gaba d’aya rai a b’ace sannan hankali a masifar tashe……. Tana fita Daddy ma ya sa Hannu ya share hawayen da ya zubo masa, tukunna ya wuce sama da sauri….. Ba tare da ɓata lokaci ba Hajiya mama ta bisa….. A tsaye ta same shi yanata faman safa da marwa, yana ganinta ta shigo ya k’arasa gareta ya rungumeta ya fashe da wani irin kuka, cikin kukan ya shiga cewa ”ki yi hak’uri, na gagara ci gaba da jurar ganin Khadija a cikin gidana da kuma rayuwata gashi kuwa abunda kike gudu ɗin shi zai faru da ni ‘za ta rabani da y’ay’ana Maamaa’!”. Cikin tsananin jin tausayinsa Hajiya mama ta shiga Bashi baki tana cewa”kar ka damu ba komai…dukda ba haka na so ace ka yanke hukuncin da wuri cikin fushi ba, amma ba komai, inshaaAllah komai zai yi dai-dai,mai gaskiya shi ke da riba a ko da yaushe, inshaaAllah za su dawo gareka, za su gane gaskiya . mu dai namu addu’a!!”. ….. Har sama su Yadira suka bisa, suka d’urkusa suka rik’e k’afafuwansa! suna kuka akan ‘ya yi hak’uri, ko babu aure a tsakanin shi da Mommy ya barta ta ci gaba da zama a gidan, ko a k’asa ne ya bata d’aki’ amma furr!! Daddy ya k’i yarda ya k’i amincewa, k’arshema a gaban su ya kira y’an sanda ya cewa ƴan sandan “su zo gidansa!” Yana gaama wayar ya kallesu yace”Wallahi idan Mommy da Yassir ba su fice masa daga gida ba, har suka bari y’an sandan nan suka zo, to sai ya sa an tafi da su cell!”. Kuka sosai Yaran suke yi suna magiya, amma Daddy sam ya k’i sauraronsu. Hatta Ummi wadda suka zo suka tarar da ita tare da shi a d’akin sai da Yadira ta rik’e Hannunta tana kuka tana cewa “dan Allah ta saka baki, ta tayasu bashi hak’uri.” Hakanan Ummin ta fara bawa Daddyn hak’uri itama dan sosai zuciyarta ta tab’u da al’amarin gwanin ban tausayi, ta san Mommy ba ta kirki amma ko dan Yasmeen da Yadira da ta tabbatar sun shiryu sosai tun kwanakin baya yanzu kuma suke irin wannan kukan ya kamata a ce an tausaya musu…… Sai dai fa duk wannan abun da suke yi ko a kwalar rigar Daddy, fad’a musu kawai yake yi yana sake maimaitawa “wallahi idan har suka bari y’an sanda suka zo to sai sun tafi da su Mommy.!” Suna cikin wannan halin Ya’isha ta kira su tace “idan har za su bisu to su sauk’o, ita da Yasira suna k’asa suna jiransu!” Dan ita dama tun lokacin da Yasira ta kira ta ta sanar mata ko yunk’urin lallab’a Daddyn ma ba ta yi ba, kuma wallahi ta gama sakawa a ranta sai ya nemesu ruwa a jallo!!!. A b’angaren Yassir kuwa, yana chan side d’insa yana jiran azo a ce masa ai Mommy ta wankesa komai ya wuce, amma kawai sai ganin Yasira ya yi a hargitse, da kyar ta ɗan nutsu ta samu ta ita ce masa”Mommy ta suma, Ashe Daddy yanata sakinta ita ba ma ta sani ba, yanzu babu aure a tsakaninsu, sannan su Yasmeen suna chan suna ta lallab’ata Daddy amma ya k’i yarda su ci gaba da zama a gidan, ya ma kira y’an sanda ya ce ‘a zo a tafi da su(shi da Mommy)’. Dan haka kawai ya taho su tafi gidan Mommy wanda ke a tudun Yola, Ya’isha ta kwaso keys, a samu a kira Likita Mommy ta farfad’o dan Yasmeen ta kasa yin komai kuka kawai take yi, idan ta farfad’o suka nutsu sai su san abun yi!.” Da farko dafe kai Yassir ya yi da mugun k’arfi da hannuwansa duka biyun, kafin ya cika ya fara fatali yana fashe fashen da hattaHannuwan nasa duk sai da suka tsatstsage suna fidda jini! Haushinsa Yasira take ji d’azu, amma har ga Allah zuwa yanzu duk sai ya bata tausayi, dan haka ta matsa ta rungume sa, wanda hakan ya sa ya fashe da wani Irin kuka ya sakar mata dukkannin nauyinsa suka zube suka durk’ushe a wajen duk su biyun suna kuka!! Cikin wani irin kuka yace”Yasira ba laifina bane ba, Daddy ya fi fifita Yashjub ya bashi duk dukiyar family d’innan bayan kamata ya yi ace ni da shi munada equal right….” Muryarsa ce ta sark’afe sakamokon kukan da ya ci k’arfinsa, dan haka ya sake sakinsa da mugun k’arfi… Tabbas zuwa yanzu kam Yasira itama ta yarda ‘idan Yassir yanada mugun mugun laifi tou Daddy ne silar komai tun asalin farko! wallahi duk Daddy ne ya damalmala komai ya hargitsa komai! Saboda tsantsar kafiya da son kansa, sannan yanzu ma gashi yana shirin sake maimaita kuskuren da ya yi a farko a karo na biyu, tunda gashi saboda ba ya son mommyn ayanzu baya buƙatar zama da ita shiyasa ya zaɓi shi ya samawa zuciyarsa salama ta hanyar daina ganinta kwata kwata su kuma ya baƙanta musu rai..’ shiyasa tausayinsu ita da y’an uwan nata da Mommynsu ya sake lullub’eta, kawai sai ta kuma rushewa da wani kukan…. Sun jima a haka suna kuka kafin dakyar Yasira ta d’ago fuskarta tace”Yassir a situation d’innan da kake a ciki, kar ka bari ka shiga case da hukuma, kamar yadda ya fad’a gara ka tashi mu bar masa gida! Tabbas abunda ka yi ba ka kyauta ba Yassir amma kar ka damu kana da mu! Kana da y’an uwa tunda na fahimci pushing d’inka aka yi…ka taso mu tafi mu je mu fara ji da Mommy, a samu ta farfad’o sai a san abunyi…..” Kamar wani k’armin Yaro hakanan ya shiga d’aga mata kai, dan a mugun tsorace yake bai saba shiga masifa da tashin hankali irin wannan ba… abubuwansa masu mahimmanci kawai ya kwasa, daga nan ya rufo side d’in nasa suka nufi motocinsu. Dai-dai nan Yusra ta sauk’o itama da akwatinta dan Yasmeen tace a nan ita za ta zauna. tuni, Ya’isha da Junior sun saka Mommy a motar Ya’ishan, shiyasa tana ganin su ta kunna motar tata amma sai fitowar Kausar wadda ta hango a gigice ya sanya ta kashe motar ta fito. ….. Da kyar suka sanya Kausar ta hak’ura da binsu, a cewarsu ‘ta zauna a nan ta zame musu ido a nan d’in kafin su dawo, sannan ta samu ta haihu a nan dan sai ya fiye mata tunda ga Yash ɗin ma nan ya dawo’. inshaaAllah za su san abun yi! Akan duk wata matsala tasu, ta kwantar da hankalinta komai zai gyaru! za su dinga waya suna communicating, kar ma ta soma binsu yanzu gudun kar Daddy ya samu damar korarta itama….. Sun ci kuka sosai Yassir ma ce mata ya yi kawai za su yi waya, daga haka suka shige motocinsu suka fice daga gidan Yasmeen kuma wadda ba ta bisu ba ta kamo hannun Kausar d’in suka koma ciki dan ta yi nauyi sosai…duk su biyun suna kuka wiwi haka nan suka nufi cikin gidan… Su Yadira kuma direct gidansu suka wuce dan kukan da take ta yi sosai ya d’agawa Junior hankali, Shiyasa ya hanata binsu ma saboda condition d’inta. A tunanin Kausar Daddy zai koreta itama, amma sai ta ga ko kallonta bai yi ba.. hakanan ya wuce ta ya fita wajen y’an sandan da suka k’araso yanzun domin ya sallamesu, a ransa ya gama tsara’itama zai koreta ne amma sai ta haihu tukunna bayan sun karb’i d’an sun bawa Manubiya….’ Yashjub tun d’azu yake ta jin k’arar bud’e gate ana rufewa shiyasa hankalinsa ya sake tashi dan tashi d’aya kwakwalwarsa ta bashi Allah dai ya sa ba harda Mommy aka bar gidan ba. …… Duk yadda suka yi tunanin abun zai yiu a gida gagara ya yi, dan bayan sun kai kayyakinsu, abun na mommy sai ya ci tura, har sai da suka danganata da asibiti tukunna ta farfad’o da kyar.! Ai kuwa tana tari tana hawaye hankali a tashe kamar tab’abb’iya ta shiga tambayarsu “ya ake ciki? A ina take?” Ya’isha ce ta iya yi mata bayani… Aikuwa cikin masifa da tashin hankali ta rufe su ta fad’a tace “dan meyaasa suka yarda suka fitar da ita daga cikin gidan??..” Sai kuma ta fashe da kuka ta fara jero Allah ya isa a Hajiya Mama da Manubiya dan sam batajin haushin Daddy kamar yadda takejin masifaffiyar tsanarsu a cikin ranta ba! Hatta su Yasira ma sai da ta dasa musu matsananciyar tsanar su Abhi da Hajiya mama a cikin ransu bayan ta Manubiya da take zaune daram a ransu dama. Duk yadda suka so su rarrashi mommy su bata baki sam abun ya gagara, gashi dama suma a wuya suke, shiyasa kawai suka fashe mata da kuka…ba ta damu da kukansu ba ballanta ta sarara musu, magana kawai take yi kamar tab’abb’iya kuma ta nace akan Itafa sai sun d’auketa sun mayar gidan Daddy dan Kwata Kwata jikinta babu kwari itan dan haka tama kasa tashi da kanta, shiyasa kawai Yassir ya juya ya fita ya je ya kira likita, yana zuwa ya yi mata allurar bacci da kyar dan sai da su Yassir suka danneta tukunna aka samu aka yi amma da sam ta k’i tsayawa. Sosai Yassir yake jin tsanar Yashjub tana dad’a shigarsa, ga tsoro ga tashin hankali… Suma su Yasira sun ji haushin rashin zuwan Yashjub d’in asibiti domin ya ga Mommy, matuk’a. Sai chan dare tukunna Mommy ta farka…tashi d’aya komai ya dawo mata sabo wanda hakan ya sanya ta ji inama ba ta farka ba. Ɗaya bayan ɗaya ta fara kallonsu tashin hankalin ta yana sake hauhawa sakamokon yadda ta ga fuskokinsu sharkaff da hawaye dagaje dagaje, kowa ta yi tagumi.. Yassir da Yassira kuma basa nan. A d’an rikice ta tashi ta zauna ta kallesu tace “Ya’isha mai kuma ya faru??” Sai a lokacin ma suka lura ashe ta farka, dan haka daga Ya’ishan har Yusra haka nan suka nufeta da sauri suka fad’a jikinta suka fashe da wani irin kuka. Zuwa yanzu jikin Mommy har wani irin karkarwa yake yi! A hankali ta zaro su daga jikinta k’irjinta yana dukan tara tara tace”ku fad’a mini menene kafin zuciyata ta buga” Sai da ta sake tambayar su!ta maimaita!!ta daka musu tsawa a karo na uku! tukunna da kyar Yusra ta bud’e wayarta ta kai mata wajen hoton sannan ta mik’a mata tana wani irin kuka. A hankali jiki na karkarwa Mommy ta saka hannu ta karb’a hoton…………..Babu idanuwa sannan an yanke nonuwa da private part da y’an yatsun k’afa da hannu amma hakan bai hanata gane Larai tashi d’aya ba. Jifa ta yi da wayar a mugun tsorace sai kuma ta turesu ta mik’e ta d’aura Hannu a ka ta fasa wata razananniyar k’ara. Dai-dai nan Yassir da Yasira suka shigo, da sauri suka k’araso suka rik’eta, Yasira itama cikin kuka tace “addu’a za ki yi mata Mommy, dan Allah ki yi salati ki daina ihu…” Sai a lokacin Mommy ta shiga ambaton ‘innalillahi wa inna ilaihirrajiun’ ba k’akk’autawa a gigice tana wani irin kuka jikinta yana karkarwa. Shiruu duk suka yi, suna kuka kafin Ya’isha tace”an baku ita?” Jinjina kai Yassir ya yi yace”Tana mortuary, sun yi saurin saka ta a k’ank’arar saboda ta kumbura gawar ta fara wari! zuwa gobe da safe inshaaAllah sai a yi mata wanka a binne ta!” Wani irin kuka mai k’arfin gaske Mommy ta fashe da shi.. Haka suma su Ya’isha, babu mai rararahin wani, kowa kawai kuka yake yi gaba d’aya d’akin ya birkice, dan ko kusa da d’akin aka zo a wannan dare to sai an fahimci an yi musu rasuwa. A tsaye ranar suka kwana babu wanda ya runtsa. Washegari da sassafe suka nemi sallama aka sallami Mommyn daga nan suka d’auki Larai suka wuce da ita gida domin su yi mata wanka a mik’ata gidanta na gaskiya!!!. Kamar yadda su Yasira suka ci karo da labarin gidan tsafin da jami’an tsaro suka binciko a garin kano tare da hotunan victims d’in ta watsapp hakanan yau suma su Daddy suka gani har da Kausar…Hankalinsu ba k’aramin tashi ya yi ba..Yashjub ma yana idar da sallar asubah ya gani.. Daddy ya so ya hanashi zuwa inda suke, amma kawai sai ya rabu da shi ya tafi, Hajiya Mama kuma ta kira Yusra da Yasira ta yi musu gaisuwa tace su mik’a gaisuwarta zuwa ga su Ya’isha. Motocin su Yasira suna gama yinparking a k’ofar gidan Momy wanda ke a tudun yola dai-dai nan Yash ma yana k’arasowa kamar had’in baki, da ma ya san nan d’in suka nufa. Mommy tana hangosa ta fito a fusace, ko ta kan su Yasira da suke ce mata “ta tsaya su shiga ciki tukunna sai a yi” ba ta bi ba, hakanan ta nufi Yashjub tana zuwa ba ta yi wata wata ba ta zabga masa wani Irin rikitaccen mari………. Da mamaki ya dafe wajen yana kallonta kawai, ya ma kasa magana. Ita kanta sai da ta mareshin ta d’an ji sanyi a cikin ranta tukunna ta yi tunanin duba da yadda Yassir fa da kashe sa ya so yi bai kamata ace ta maresa ba, dan haka tace”tsabar kai dak’ik’i ne Yashjub! ace a had’a video da voice d’in d’an uwanka amma ka gagara gane k’arya ne aka shirga? ina karatunkka da ilimin ka suke? sannan ka je ka wani tartaro mini su Hajiya mama ka sako su cikin case d’in nan saboda baka san ciwon kanka ba?” Ba ta jira jin ta bakinsa ba ta d’aura da cewa “To bari ka ji, ba ni ka wulak’antaba wallahi kanka ka wulak’anta, kuma inaso ka sani wallahi tallahi muddin baka je ka wanke d’an uwanka ka shiryasa da mahaifinka ka gyara abunda ka lalata ba to ni da kai har abada!! Ka b’ace mini daga gani duk ranar da ka gyara b’arnar da ka yi sai ka zo gareni!” Tana gama fad’in haka ta juya fuuu ta wuce ciki ta shiga ta gate d’in da su Yasira suka bud’e suke ta k’ok’arin shiga da motocin. Har suka gama shigewa Yash yana nan yadda yake ya ma kasa motsi.. ‘shin da gaske Mommy ta yarda da cewar sharri aka yi wa Yassir, kokodai son Yassir ne ya sanya ta yi masa wannan borin??’ Ya yi wa kansa tambayar a cikin ransa..Saboda ya tabbatar ko k’aramin Yaro idan ya ga video d’innan da voice da shaidu ya san ba had’awa aka yi ba. Juyawa kawai ya yi, ya shige cikin motarsa ya kunna ya wuce, yana tafiya ya turawa Yasira mesaage ya yi mata gaisuwar rashin da suka yi, dan Mommy tana shiga ya ga ta fito za ta zo wajensa shi kuma ba zai iya sake ci gaba da tsayuwa a k’ofar gidan ba zuciyarsa za ta iya tarwatsewa ..Tabbas Mommy ta tsaneshi!!! Sai da Yasira ta bari Yassir da su Yusra sun shige ciki tukunna ta yi saurin ruk’o hannun Mommy k’asa k’asa tace”Mommy videos d’innan da gaske ne fa!! Yassir da kansa jiya ya yi mini confessing, ya tabbatar min bai ƙaryata ba…….da kin sani ba ki yi wa Ya Yash haka ba gaskiya, jiya dai na ji haushinsa da bai zo ya ganki ba amma yau ai da mun tsaya mun sauraresa tunda ya zo ɗin.” Shiruuuu ta ga Mommyn ta yi..ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta tubure kawai tace sharri aka yiwa Yassir dan haka ta cewa Yasirar “rikicewa Yassir ya yi jiya, shiyasa yace miki shine, amma tabbas ni na san sharri ne aka yi masa……’ Rabuwa da ita kawai Yasira ta yi, ta bari akan sai an kai Baba Larai, zafin mutuwar da komai ma ya fara raguwar mata tukunna sai su yi magana da ita ta fahimtar juna. …. Gaba d’ayansu kashe wayoyinsu suka yi, saboda Mommy tace ba ta son y’an gaisuwa su san tana nan, bama ta buk’atar ganin kowa a halin yanzu…da kyar da mugun kyar suka samo matan da suka yarda suka yiwa Baba larai wanka dan a k’ank’arar da aka sakata jiya ya sanya yanzu kuma duk sai ta lagwab’e da k’ank’arar ta narke, dan ko jikin nata kana tab’awa sai ka ji kamar zai biyoka ga uban wari! Suma Matan dai daga k’arshen wankan kawai ruwa suka yayyafa mata aka yi mata sutura….. Sai la’asar tukunna suka samu aka sallaci Baba Larai aka kaita makwancinta… Ana dawowa daga kaita Mommy ta cewa Kausar ta tafi, ita tsoranta d’aya kar itama Kausar d’in Daddy ya koreta dan tabbas suna da buk’atar ta a cikin gidan…tare suka tafi ita da Junior Yasmeen da Yadira….. Suna tafiya Yassir shima yace musu”zai wuce za su ci gaba da zama da wani Abokinsa kafin komai ya yi settling” Mommy ta so ta tsayar da shi gudun kar wani abun ya same sa, amma da ta fahimci video d’in a iyaka family ne ya zagaya aka gaggani hukuma ba su riga sun gani ba sai kawai ta rabu da shi ya tafi….ba ta kuma yi masa maganar ba saboda ta lura kamar ba ya son zancen! Har ga Allah ita she’s proud of Yassir saboda ya yi yunk’urin kawar mata da matsalar ta (Dama ita tun a wajen da abun ya faru ta so ta fahimci shine, ta kuma fusata da Yash d’in bai mutu da gaske ba) dan haka ta bisa da kyawawan addu’o’i da fatan alkhairi, su Yasira kuma ta ci gaba da yi musu borin ai sharrin aka yi wa Yassir d’in. Sai da Yash ya je ya ga Manu, tukunna ya fara haramar wucewa gida shi kaɗai, saboda dama tun jiya take rok’ansa akan ‘ya barta ta yi kwana uku’ tunda gida ma za su chanja, ai kuwa da ya barta ɗin ta ji dad’i kwarai, amma kuma yanayinsa da ta gani wanda ya sanya ta fahimci akwai matsala ne ya ɗan ɓata mood ɗin nata, dannhaka ta hau tambayarsa….. bai b’oye mata ba, ya gaya mata cewa”Daddy ya kori Yassir, kuma k’arshen abun bai yi dad’i ba, dan har da Mommy itama sai da ta bar gidan” ,sosai Manu ta tab’u daga jin zancen, da kyar ta taushi kanta sannan ta yi namijin k’ok’ari wajen kwantarwa da Mijin nata hankali, tukunna suka rabu shi ya wuce gidan Daddy shi da Najeeb wanda ya zo bada jimawa ba, har da Siyama. Ita Manubiya ba ma ta yi tunanin da Siyaman aka zo ba, dan basu dad’e da yin waya da ita ba, kuma bata gaya mata ba.. sai da su Yash d’in suka wuce tana shiga parlourn nasu daga parlourn Baba kawai ta ganta a zaune, ai kuwa nan suka hau murna har da hawayen farin ciki. Sai da su Yash suka kama hanya tukunna ya tuna bai sanarwa su Manubiya rasuwar Baba Larai ba,dan haka ya bari a kan sai zuwa anjima sai ya gayamata, ya san dole za ta kirasu ko ma ta je har gidan ta yi musu gaisuwa…addu’arsa d’aya ‘Allah ya sa kar Mommy ta yi mata abunda ta yi masa itama’ Tunda da ma gashi ba ta sonta. A b’angaren Kausar kuwa, zuwa yanzu ta gama tsarawa da sanin abunyi, dan haka jimamin Baba Larai yana d’an sakinta ta kira Ya’isha tace”tana so ta had’ata da Abbakar, akwai abunda zai yi mata” Da kyar Ya’ishan ta had’ata da shi kuwa! Saboda last time Abbakar d’in ce mata ya yi “kowa kawai ya yi ta kansa daga yanzu! dan plan d’in da suka had’a last time ɗin bai yi masa ba, gashi ba su yi nasara ba sannan kuma sai da yayi watanni uku a asibiti…” Hakanan dai ita Kausar ta nace sai da aka had’ata da shi tukunna hankalinta ya kwanta, saboda shi ne kawai ta ga niyyar su ta zo d’aya tunda yana son Manu itakuma tana son Yash dan haka za su taimaki juna bilhaƙƙi da gaskiya, dan ta zauna ta yi tunani sam ba za ta wani biyewa Mommy ba wallahi! Ba za ta iya hak’ura da Yashjub ba…kowa kawai ya yi ta kansa………. Ita dai Yasira tana jinsu suna wayar da Ya’isha..har aka tura number tana mamakinsu a ranta tace”wato dai wanda ya mutu ya riga ya tafi!duniya kuma kowa sai ya ci gaba da abunda ya saka a gaba. Kalli yadda suka ci gaba da k’ulle k’ullensu kamar ba yanzunnan aka dawo daga kai Baba Larai kabari ba.” Ita ma Yusra lissafin da take yi kenan. Ita sam ba ta yi tunanin Kausar d’in ta san da issue d’in Abbakar d’in ba ma, wataƙila sai dai in ko Ya’ishan ce ta fad’a mata. Su Yassir suna gama tafiya, Mommy ta cewa su Yasira su zo su raka ta…su sun yi tunanin ma kayan abinci da abubuwan buk’ata za su sissiyo, sai da suka ga ta d’auki hanyar inda za su je tukunna suka fahimci inda suka nufa… Aikuwa suna isa suka shaida wajen… Mutumin tsoho tukuff dashi, duk wanda ya gansa ba zai yi tunanin ko gani yanayi ba ma tsabar tsufa..hakanan ya k’araso inda suke dan suna yin parking suka ga ya fito dama…. yana zuwa yace”lale marhaba Khadija, yau kuma ina Larai??” Sunkuyar da kai Mommy ta yi ta girgiza kanta a hankali wasu siraran hawaye suka zubo mata…. Shiruu ya yi, ya d’an k’ura mata idanu, kafin yace”Allahu Akbar! amma an yi babban rashi..Allah ya ji k’anta!mu je daga ciki” Daga haka suka nufi cikin. Shi wannan tsohon! wanchan bokan na k’auyen su Baba larai shi ne ya had’ashi da ita tun asalin farko kafin ya rasu kafin ta baro ma k’auyensu ta dawo nan Kano inda yake…..idan abubuwa suka shige masa duhu ya kan tambayeta, itama haka,har nan suna zuwa ita da Mommy idan aikin da suke son yi ya had’a da wanda mace ba zata iya yi ba sai su kawo shi ya yi musu. …. Sai da ya sake yi mata gaisuwa ta amsa, tukunna ba tare da b’ata lokaci ba tace masa ”Yashjub ya yi aure ba ta samu abunda take so ba har yau, kuma Yarinyar ta zo da farar k’afa! mutuwar Baba larai na daga cikin masifun da Manubiya ta zo mata da shi! saboda dama Baba larai tace muddin aka aurota to fa an yi ta ganin bala’i kala kala. Yanzu haka ma ba ta gidan Daddy jiya ya yi musu korar kare ita da Yassir….” Salati tsohon ya yi, kafin ya janyo wata tukunya mai ɗauke da ruwa fall a cikinta, ya hau duba cikin nata yana jimami…. Sun fi mintuna ashirin a haka, kafin chan ya d’ago ya kalleta ya ce ”ai kin yi kuskure! irinsu waennan ba a barinsu a doran k’asa! ai idan aka yi aiki akaga ya k’i ci ya k’i cinyewa to rabasu da duniyar gaba ɗaya ake yi, tunda sun fi k’arfinka dan haka ta ya zaka tsaya fafatawa da su? ai ba zai you ba! Dan fafatawa da irinsu babu riba!.” Ajiyar zuciya Mommy ta sau’ke, dan ba k’aramin dad’i ta ji da jin wannan batun ba, saboda dama itanma takanas abunda ya kawota kenan!!a yi ta ta k’are kawai. Cikin k’aguwa tace”aikin gaggawa nakeso ka yi mana, ba na so Larai ta kwana uku a kabari ba tare da Yarinyar nan ta bi ta ba!” Cikin tarar numfashinta Yasira tace “Mommy wai kisan Kai kike nufi??” Murmushi tsohon ya yi, kafin yace”to ai hakan kawai ce mafita! saboda Wallahi Allah muddin Yarinyar nan tana raye tou fa bala’i da masifu yanzu kuka fara gani!!!”. K’ura masa ido Yasira ta yi, kafin chan ta d’auke kanta ta mayar ga Mommy tace”Mommy mu je gida ma yi magana, Plss, dan Allah ki bar maganar nan!”. Girgiza Kai kawai Mommy ta yi kafin ta ce”Yasira har yanzu ke Yarinyace..dan gashi duk abubuwan da suke faruwa a gaban idanunki ba kya gani! inaga sai na mutu kin binne ni tukunna za ki fahimci abunda muke nufi!!!” Da d’an zafi Yasira tace”Mommy Manubiya b….” Cikin katseta da tsawa sosai Mommyn tace”za ki yi mini shiru ko kuma in kora ki waje????” alamun ta yi shiru su Ya’isha suka yi mata, dan haka kawai ta yi shiru ba dan ta so ba, kuma wallahi wannan tab’argazar ba da ita ba, ba za ma ta bari a yi ba… Sai da Mommy ta yi kusan minti d’aya tana hararar Yasirar, tukunna ta mayar da kanta ga tsohon wanda shima yake cewa Yasirar “ki tsaya ayi abu a nema muku mafita, hatta rashin aurenku duk itace dan gashi nan na gani a nan! ko ba kwanan nan wanda za ki aura ya yi aure ba???” Ita dai Yasira banza ta yi da shi, Yayinda Mommy da Ya’isha suka aminta da maganar ta shi d’ari bisa d’ari… Murmushi kawai ya yi, ya mayar da dubansa ga Mommy yace”kar ki damu, komai ya zo k’arshe inshaaAllah!” Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace”yanzu nake so a yi aikin..saboda na gaji na tsani…” Cikin tarar nunfashinta yace”sai dai a yi aikin a yau da daddare gobe a tashi babu ita!!” Jinjina kai ta yi tace”hakan ma ya yi” “To Alhamdulillah” yace, kafin ya d’aura da cewa”yanzu akwai yadda za a yi in samu hularta???” Kallon juna suka yi ita da Ya’isha suka yi shiruu, kafin chan Ya’ishan tace”eh!! Da me kuma??” “Iyaka hula, kawai!. Ki tabbatar tana cirewa daga kanta kin kawo mini kai tsaye ba tare da kowa ya saka ba! Shikenan abunda na ke da buk’ata.” Sai kuma Cikin yin serious da fuska sosai, ya ture tukunyar gabansa ya mayar gefe ya kallesu da kyau tukunna ya ce ”da farko dai inaso ku fahimci cewa shi RAI!! Bayar da shi da karb’arsa wannan Ubangiji ne kad’ai ya isa! bi’ma’ana Ubangiji ne kad’ai yake bayar da Haihuwa yake kuma kashewa, bayan shi babu wanda ya isa ya yi hakan, duk bala’in mutum bai Isa ya kashe ko ya raya ba…” Jimm Mommy ta yi, tana jin wani sabon tashin hankali yana rifeta, kar dai mutumin nan yace ba zai iya yi mata komai ba kuma!!! Tana wannan tunanin ta ji ya ci gaba da cewa”Abunda mukeyi idan matsala irin taki ta taso shine wannan aikin da zan yi muku a yanzu, ammafa yanada matuk’ar haɗari kuma yana buk’atar taka tsantsan!” Sai da ya sauk’e numfashi tukunna ya d’aura da cewa”ita wannan hula da za’a kawo! itace nake so a kiyaye kar a samu matsala wani ya saka bayan ita Yarinyar kafin a kawo min, ko kuma a samu matsala ta hanyar kawo min wadda ba tata ba, ko kuma dai wani abu makamancin hakan… saboda idan aka samu matsala, to fa shi wanda ya saka bayan itan, ko kuma shi wanda aka kawo tasa a maimakon ta Yarinyar, ko kuma dai duk wani wanda ya gilma a tsakani har ya ja matsalar ta samu, uwa uba wanda ya ɗauko hular ya kawo! Duk ɗinsu aikin zai haɗa ya faɗawa. Bima’ana dai duk wanda ya ja aka samu matsala a aikin ko wacce iri ce to maimakon aiki ya faɗa akan Yarinyar (Manubiya) aiki zai faɗa ne a kansa ko a kansu!… saɓanin idan ba a samu matsala ba, aikin zai faɗa ne akan ita Yarinyar (Manubiya) ita ɗaya kawai… kuma idan aka yi aikin aka kammala komai ya kankama to ba’a janyewa, bima’ana idan aka yi ya kammalu komai ya hau saiti to an riga an yi kenan ba a taɓa iya karyawa.” Jinjina kai Mommy ta yi tace “na ji na fahimta, inshaaAllah za a ayi taka tsantsan..ya aikin yake?” Ta yi masa tambayar tana kallonsa. Murmushi ya yi kafin kanshi tsaye yace”rik’e mata numfashi zan yi!…idan kaff likitocin duniya ne za ace su zo su taru a kanta to fa babu wanda ya isa yace tana da rai! saboda komai tsayawa zai yi. Daganan Idan aka yi mata wanka, akai mata sutura aka kai ta kabari aka binneta! muka tabbatar an kai ta ɗin, ni kuma sai in saki numfashin nata ya dawo..kinga dai ai bata isa ta fito ba ko? sai dai ta k’arasa a chan!!” Ya k’arashe maganar tasa yana sakin dariya… Da sauri Yasira ta mik’e ta fita, hankali a tashe ranta a masifar b’ace..Tabbas bayin Allah marasa Imani suna da yawa a duniya..ta ya mutum zai iya aikata haka a d’an Adam musulmi d’an uwansa?. Wani sanyi da nutsuwa Mommy ta ji daga jin bayaninsa, dan bata tab’a jin hukunci mafi dacewa da ya dace ace ta yankewa su Manubiya ba kamar wannan!!! Har za ta yi magana, sai kuma ta tuna da su Yusra a wajen, dan haka ta kallesu tace”ku d’an bamu guri!” Sai da ta tabbatar sun fice daga cikin gidan gaba d’aya, tukunna ta kallesa tace”Ana iya yiwa Namiji ma ko?” Dariya sosai ya yi kafin yace”Yashjub ko? Tsaff za ki yi masa shima, amma shi gashin kansa za ki kawo.” “……….Samun gashin kan Yashjub zai d’an yi wuya, amma hular Manubiya yanzunnan ka jira a daren nan za ka samu, za ‘a iya kawo ribbom ma?” Cewar mommy.. Jinjina kai yayi yace”indai ya tab’a kuma ya yi muamala da gashin kanta to ku kawo!!” Wani irin farin ciki ne ya lullub’e Mommy, gudun ma kar su ci gaba da b’ata lokaci ya sanya ta mik’e da sauri tace masa ‘ya bata awa d’aya da rabi’ daga haka sukayi sallama ta fita jikinta har yana b’ari, ranta fess. A mota duk ta samesu a zaune, Yasira ta had’e rai kamar ba ta tab’a dariya ba!! Mommy Ta san idan ta biyewa Yasira b’ata mata lokaci kawai za ta yi, dan haka ta sa Hannu ta d’auki Jakarta ta kalli Ya’isha tace mata “zo” Su kuma su Yasira tace”ku wuce gida.” Yasira za ta yi magana tace”na rantse da girman Allah Yasira zan yi miki Baki!! idan kuma kema Yasmeen da Yadira za ki zama to bismillah, ki tattara ki koma gidan ubanki kar ki damu da damuwata! Allah zai yi mini gata!” Sai kuma tafashe da kuka tace”Larai ce fa ta rasu, amma kalli Yadira da Yasmeen ko yunk’urin zama inda nake basuyi ba ballanata su taushe ni, tunda Manubiya ta zo cikin rayuwarmu komai ya hargitse, ku kanku ƴaƴana an juya muku lissafi kalli fa abunda kuke yi mini sannan a haka ki ce wani in hak’ura?” Cikin zubar hawaye Yasira tace”gaskiya fa nake gaya miki Mommy, kuma son da nake yi miki ne ya sanya nake k’ok’arin kub’utar da ke daga hanyar halaka in saita ki a hanyar tsira! Saboda Allah ta Ina kashe Manubiya ya zamto hanyar warwarewar waennan abubuwan da kika lissafa, Ina riba a kashe rai??….kece fa baki tsaya kin nutsu kin fuskancemu ba shiyasa kike ganin kamar mun juya miki baya, Yadira fa ciki ne da ita amma baki ma lura ba kina ta abubuwan gabanki! tunda ta yi aure ba ki damu ki duba ya take ba! ko d’azun ma amai ta yi shiyasa junior d’in yace su wuce asibiti, kuma na san za ta dawo ba wai k’in zama ta yi a wajenki ba. kawai bamuga kin nustu bane balle har ki bamu listening ear shiyasa kika ga bama…” Cikin katseta tace”to duk ba uban ku bane ya rikitani kwana biyun nan!wai Yasira “ Itama cikin katseta tace”Mommy babu laifin kowa ba….” Marin da ta d’auke ta da shi ne ya sanya ta yin shiru…cikin fushi tace”ku wuce gida!!!” daga haka ta ja hannun Ya’isha suka wuce suka tari napep…. Sun dai san gandu ne Gidan, amma sai da Ya’isha ta kira Yadira ta yi mata kwatance tukunna suka d’au hanya….k’asa k’asa gudun kar mai napep d’in ya ji Mommy tace”kina da idear yadda za a yi a samo??” Jinjina kai Ya’isha ta yi itama k’asa k’asa tace”zuwa zan yi kawai in gaya mata abunda ya faru da Yassir da ke, in ce mata na zo ne akan in rok’eta ta yi wa Yash da Hajiya mama magana a samu ku dawo!… Durk’usawa wada ba gajiyawa bane ba, mu dai kawai mu samu abunda muke so… A ganina hakan shine kad’ai option d’inmu, dan idan ba hakan ba kin san halinsu da rashin yarda na san ba lalle ta sake da ni mu keb’ance in samu in d’auki abunda nake so d’inba.” Jinjina kai Mommy ta yi tace “to. ni kenan ba sai na je ba ko? tunda ban jiyo ni a cikin plan d’in naki ba!” “Eh. kawai ku juya idan na gama zan same ku a gidan mutumin ai na gane ba wani nisa ma.” “To shikenan” Mommy tace daga haka ba ta sake cewa komai ba, har suka kaita ta shige ita kuma ta juya…….. A gate ta same su ita da Siyama, ta rakosu har da Najeeb, suna ta hira suna dariya….da kyar da mugun kyar Ya’isha ta hana kanta kuka saboda ko waye ya kalli Najeeb da Siyama ya san hankalinsu a kwance yake, kuma suna matuk’ar k’aunar juna!… Sunyi wani irin kyau sun yi k’iba sun yi fresh har wani glowing suke yi musamman ma Siyaman dan in ba kwakkwaran sani ka yi mata ba to ba lalle ka iya gane ta ba, sannan idan baka santa ba in har ba bakinta ta bud’e ta yi maka Hausa ba to ba za ka tab’a cewa y’ar Nigeria bace ba….. Wani k’ululun bak’in ciki tashin hankali da kishi ne ya tokare mata mak’oshi! dama tun d’azu da aka fara maganar tsayar da numfashi Siyaman kawai ta hararo…inshaaAllah ana gama na Manubiya itama za ta san yadda ta yi ta nemo nata yanzu haka ma dan ta lura tafiya za su yi Wallahi da a yau zata had’a har da nata….. “Ya’isha sannu da zuwa!” Muryar Manubiya ta katsewa duk su ukun tunani…ko juyawa Najeeb bai yi ba, Siyama kuma haka kurum gabanta ya yanke ya d’an fad’i yayinda Ya’ishan ta d’an yi murmushi tace”yauwwa”kawai,daga haka ta yi gaba ba tare da ta san wanne a cikin flat biyun za ta shiga ba,dan ba za ta iya jurar ganin Siyama tsaye jikin Najeeb ba suna wannan rahar ta san tsaf zata iya mutuwa..shi kuma ta lura har wani sake ruk’o hannun Siyaman ya yi…… Tana wucewa Najeeb ma yace”bari su tafi” Hakanan suka rabu Manubiya tana masa tsiya akan ‘gaskiya itadai bata gama ganin k’anwarta ba, haka kurum ya zo da wuri!’ shi kuma yanata dariya. A tsaye ta sameta gaban flats d’in, dan haka suka sake gaisawa tukunna suka nufi ciki. Ba yabo ba fallasa Ya’isha ta gaisa da kowa har Hadiza da Baraka, kafin ta nemi ganin Manu in private…a ranta tana addu’ar Allah ya sa komai ya zo mata da sauk’i. Suna shiga d’akin, Manubiya ta cire hijab d’in jikinta ta linke ta ajjiye… sanye take ta wata riga y’ar kanti mai k’aramin hannu pink da hula pink mai d’an karen kyau. Sosai Ya’isha ta ji dad’in ganin hular, dan haka ta shiga tunanin ta Ina za ta fara!ya za ayi ta samu!… Da kyar ta iya yiwa Manubiya bayanin yadda suka shirya ita da Mommy d’azu a Napep, tana yi tana hawaye, itama Manubiyan sai da ta yi hawayen tukunna tace mata ‘ta kwantar da hankalinta, inshaaAllah zata saka Baki a al’amarin Mommy, kar ta damu itama Mommy ai uwa ce a gareta…’ sam bata ce zata yi komai a case d’in Yassir ba, dan babu ruwanta a case d’in Yassir. Sosai ta girgiza da ta ji ance Baba Larai ta rasu! A take ta gayawa su Inna aka kira su Mommy itama Ya’ishan aka yi mata gaisuwa sannan suka fara shirye-shiryen zuwa amma sai Ya’ishan tace”ba komai su bari sai gobe”dan ta san Mommy ba ta gidan yanzu. Hakanan shima Yash da Manu ta kirasa ta tanbayesa akan zuwan sai yace “ta bari sai gobe” a ransa yana mamakin mai ya kai Ya’isha gidansu Manu!!. Kiraye-kirayen sallar Magrib aka soma, dan haka duk aka tashi aka shiga alwallah ana gabatar da salla….a d’aki Ya’isha ta yi alwallah ta fito waje domin yin sallah, jikinta duk a sanyaye dan zuwa yanzu hanakalinta ya fara tashi saboda tun d’azu Manubiya ba ta cire hula ba bare ribbom.. Sai da ta ji kamar ta doka tsalle sakamokon pink d’in hular Manu da ta hango a kan Hannun kujera a ajjiye, itakuma Manu ɗin ta d’aura k’aton jilbab d’inta na d’azu a kanta da jikinta ya rufe ko’ina, tana sallah ita da Inna wadda ke a gefenta. Ya’isha bata ta yi wata-wata ba, ta k’arasa, dan parlourn babu kowa, tana zuwa ta zauna a kan kujerar ta d’au hular ta danna a jaka jikinta har yana karkarwa. Ko sallar ba ta yi ba, su Innar suna idarwa Ya’ishan ta cewa Manubiya ‘za ta tafi’ da aka tambayeta ‘ta yi sallah?’ tace musu “eh” Ba yadda basu yi da ita akan ta tsaya ta ci abinci ba, nan ma ta ce “ba komai, ta ƙoshi” Hakanan Manubiya ta yi mata rakiya, suna fita ta samu Napep. har ga Allah sosai tausayinsu ya lullub’e manu! wai yau Ya’isha ce ta zo neman alfarma a wajenta! tabbas daman idan mutum ya yi hak’uri komai ya yi farko zai yi k’arshe…. Fad’an kalar murnar da Mommy ta yi da Ya’isha ta kai hular b’ata baki ne..hakanan ta yi ta sanya mata albarka… A gabansu tsohon ya d’auko wata k’atuwar babyn roba! Ya sanya mata hular Manubiya a kanta bayan ya yanka kaza a kan hular jinin ya gama zuba a kai! daganan ya nemo allurori ya caccake wajen zuciya da kuma kan y’ar tsanar da guda shidda ko Ina uku uku, guda d’aya kuma ya chaka a mak’ogwaronta….…haka nan dai ya yi ta abubuwansa har abun tsoro akan y’ar tsanar…ya fi mintuna talatin yana aiki a kan y’ar tsanar nan kafin ya nad’e ta yadda ake yi wa gawa aka bar iyakar fuskarta a buɗe tukunna ya tambayesu cikakkun sunayen Manubiya su kuma suka sanar maasa, ya ambata sau uku tuukunna ya mik’e ya ce musu “mu je”…. Hakanan suka zagaya bayan gidansa inda yake kiwon kayan daji kala kala har da macizai. suna shiga wajen ya nufi wani k’aton biri kamar gunki, ƙarasawarsu wajen birin ke da wuya, birin ya tashi daga kan dutsen da yake zaune akai, shi kuma tsohon ya ɗan ɗaga dutsen dukda flat ne amma da mugun kyar! Sannan ya saka Babyn robar a k’asan dutsen ya mayar ya ajjiye, birin ya koma kai ya zauna.. With full confidence ya ce musu “an gama!!..” Sannan ya ƙara da “kar ma ku biya ni, har sai kun tabbatar an kai Manubiya kabarinta…….” Hakanan suka nufi gida ransu fess…ko da suka je su Yasira suka nemi d’aga musu hankali ce musu suka yi ‘ba su yi abun ba!’ Ya’isha har da rantsuwa, dan haka suka yarda da su. A b’angaren Kausar ma tana chan tana ta shirinta…akwai wata k’awarta y’ar babban jami’in tsaro mai fad’a a ji a Nigeria da kewaye, da ta ga hoton baba larai itama takanas tazo yi wa Kausar ɗin gaisuwa… Ta yi mamakin ganin ta da ciki tsoho, dan haka ta tambayeta ba’asi itakuma Kausar d’in tace”Yashjub ta aura, amma har yau kishiya ta hanata tarewa” Dan haka k’awar tata tace “‘ta kwantar da hankalinta za ta taimaketa.. yanzu haka Ita kanta tanada sojojin da idan ta saka suka k’ulle mutum Wallahi ba Yashjub ba ko waye bai Isa ya fito da shi ba’ Dan haka yanzu abunda za a yi, ta bari idan ta haihu ranar suna za su k’ullawa Manubiya sharrin sata, inshaaAllah indai sojojinta suka tafi da ita ba a Isa a karb’ota ba sai ta dad’e sosai in lokacin sakinta ya yi suka ga dama sai su sakota kafin nan ita kuma Kausar d’in inshaaAllah ta gama samun Yashjub ta saka shi a corner har abada…”. Sosai Kausar ta ji dad’in plan d’in, dan haka ta bari akan sai ta haihu d’in sai ta had’a har da abunda suka shirya ita da Abbakar za su yi d’azu! a yita duk a lokaci d’aya ta yadda ko bibiyarta ma Yash d’in ba zai yi ba, kuma dama still akwai abunda ta shirya zata yi wa Manubiya a kan Yaron da za ta haifa ɗin wanda nan ma ta san dole abun ya sake zama super effective… InshaaAllah kafin ta fito ita kuma ta san yadda ta yi ta ko wacce hanya ta kanainaye Yashjub ta auresa sannan suka zama cikakkun ma’aurata, tunda har ga d’a a tsakani kuma babu Manubiya to ta san samunsa ba zai yi mata wahala ba inshaaAllah. Sosai Kausar ta ji dad’I, hakanan suka rabu ita da k’awar tata tana ta murna ranta fess kamar an yi mata bushara da gidan Aljannah. A b’angaren Yassir shima yanzu ya sake hawa ya koma gidan jiya..saboda da farko ya ji tsoro matuk’a, amma yanzu da ya d’inke da Abokinsa ya gaya masa komai ya samu goyon baya d’ari bisa d’ari daga wajen Abokin nasa sai zuciyarsa ta sake bushewa musamman ma da ya tabbatr video d’in a iyaka family yake yawo bai je ga hukuma ba! tashi d’aya tsoronsa ya kau! Kuma ya ji Mommy tana cewa sharri aka yi masa, dan haka zai fake da sharrin aka yi masa ya dage har sai su Daddy sun yarda ya samu sun shirya.. daga nan zai yi mai kankat dan Abokin nasa yace”InshaaAllah zai tsaya masa zai taimaka masa su ga bayan Yashjub, kuma ba za su sake tura wani ya kashesa ba! saboda kar a sake samun matsalankamar lokutan farko! Next time kawai sakawa za su yi a d’auko musu shi su kashe sa da Hannunsu. But first, ya samu ya fara wanke kansa ya shirya da su Daddy, inyaso daga nan sai su k’addamar da shirinsu saboda yanzu wani abun yana samun Yash shi za a zarga.” A ranar da daddare Ya’isha tana tafiya daga gidan su Manu, itama Baraka ta je ta karb’o garin maganinta wanda za ta barbard’a ta haukatar da Inna, dan zuwa yanzu tace ‘ba za ma ta sakata jinya ba, haukatata za ta yi dan sai ta fi wulak’anta idan ta haukace akan jinya.’ Sam ba ta da mu da sharad’in bokan ba da yace mata”idan ta b’arbad’a abun Inna ba ta bi ta kai ba to itace za ta haukace” Tashi d’aya tace masa “ta amince!” Hakanan ta zube masa mak’udan kud’ad’e ta amso ta taho saboda ta san a inda za ta zuba ta yadda dole innar sai ta bi ta kai, ai abun ma ya zo mata da sauk’i tunda yace”kowa zai iya bi kawai dai ta tabbata itama Innar ta bi ta kai.Kuma awa ashirin da hud’u abun zai yi bai lalace ba saboda yana da k’arfi.” Dan haka ta san babu ta inda za a samu matsala, kuma ta gama tsarawa ne akan a bakin k’ofar ban d’akinta za ta zuba, inda ta san ko cikin dare ko da safe ko da rana dole ta shiga ta yi uzuri ta yi alwallah! ai Inna ta tafka babban kuskure tunda har ta bata damar shigar mata ɗaki anyhow sannan a duk lokacin da ta ga dama! Dan haka tunda har tana da access da bedroom ɗin innar to komai ta san zai zo mata da sauƙi….… Hakanan, Baraka tana ta sak’e sak’e a ranta ta iso gida, jakarta kawai ta ajjiye, ta nufi cikin gidan…a nan ta samesu duk d’insu gaba d’aya har Baba ana hira, inna kuma tana zaune a kan darduma tana lazimi dan har ta yi shirin barci. Tana shiga suka fara tambayarta “ya jikin maman Abbakar d’in” Itq kuma tace musu “da sauk’i,” daga nan ta fara rarraba ido…lucky for her ta ji Manubiya tace mata”ya yi barci, yana d’akin Inna, in kun zo tafiya sai in d’auko miki shi.” Ita ba ma shi ɗin take nema ba, amma daga jin hakan ko gama rufe Baki ba ta bari Manubiya ta yi ba ta yi wuff ta mik’e ta afka d’akin tana mai cewa”ai yanzu za mu tafi ma, bari in d’auko shi!” Tana shiga ta tura k’ofar ta mayar ta rufe,sai da ta zuzzuba tukunna ta mayar cikin bra d’inta ta d’auki mai sunan Baban ta fito ta yi musu sallama ta tafi, yau ko jiran ya Musbah ma Bata tsaya ta yi ba…shima kuwa ya yi zamansa, har sai da ya gama zancensa da Hadiza tukunna ya koma kuma da ya je ya balbaleta da masifa dan bai san da zancen zuwanta dubo maman Abbakar da daddare ba sam ba ta tambayesa ba, sannan yace”idan Inna tana cikin d’akinta to za ta iya shiga amma in har Inna ba ta ciki kuma babu kowa a cikin d’akin to kar ta sake afka mata d’aki kamar yadda ta yi d’azu, tunda d’akin ba na sa’arta bane ba!” Saboda shi har ga Allah haka kurum bai yarda da shigar tata da ta yi ba da yanayinta na yau ɗin gaba d’aya duk bai yarda da ita ba. Ga mamakinsa har k’asa Baraka ta durk’usa tace”ya yi hak’uri ba zata k’ara ba!” Ita kuwa a ranta cewa tayi “kar ka damu,zuwa gobe mai karekan ba za ta sake samun dama ba!daganan wallahi ko kara idan na ajjiye baka isa ka shallaketa ba.!!”. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *page 43* Ya Musbah yana tafiya su Inna ma suka fara k’ok’arin shiga domin suma su samu su kwanta barci, dan Baba shi kam ya jima da wucewa d’akinsa tun lokacin da suka gama yiwa Yash da Daddy gaisuwa, ya wuce ciki abunsa… Hijab d’inta ta cire ta linke ta ajjiye a kan dardumar, tukunna ta d’auka bayan ta had’e su waje ɗaya ta yi folding d’insu, sannan ta tsaya kawai tana kallon Hannun kujera inda ta ajjiye hularta tun d’azu da Magrib lokacin da zata yi sallah amma da ikon Allah yanzu ba ta ganta a wajen ba. Manubiya ta kalla ta kalli hular kanta wadda gwaggwo Suwaiba ta basu tsarabarta su biyu iri d’aya tace”Manu hularki ce a kanki ko? Ni Ina tawa??” Murmushi Manubiya ta yi tace” Dama na sani!” sai kuma ta d’aura da cewa”ai dama kinsan Siyama tace itama kalar take so..ba ta son kalar tata ita da Jidda! bani da tantama itace ta d’auke takin a tunaninta tawa ce na ajjiye shine ta d’auke ta tafi da ita!”. Shiru Inna ta yi kafin tace”Anya kuwa? Kuma inda ace ita ta d’auka ai da na san za ta ajjiye tatan.. kuma ai kafin Magrib Siyama ta tafi,ni kuma sai da na zo yin sallar Magrib d’infa tukunna na cire!.” Cikin tarar numfashinta gwaggo Suwaiba tace”To,watak’ilan mai sunan Baba ne ya d’auka ya saka a wani wajen. yanzu dai mu je mu yi barci, idan Allah ya kaimu gobe da safe sai a duba!. Idan ma ba a samu ba, sai in je kasuwa in siyo yadi kalarsa ai ba za a rasa ba, duk ku hud’un sai in had’a Hadiza ta kai tela ya d’inke a yi muku iri d’aya, kinga an huta ai ko?” Dariya Manubiya ta yi kafin tace “Allah ni fa Ina tunanin Siyama ce ta d’auke! Ta yi tunanin tawa ce, saboda fa tunda ta ga tamu(ni da Inna) tace ita za ta yi anko da Inna, kuma kalar ta fi so dan shine favorite colour d’inta, shiyasa ni kuma tun d’azun har ta tafi har bayan ma ta tafin ban yarda na cire ba! Tsabar yadda na saba da hular a kaina” tana dariya ta ci gaba da cewa “wuyan Hijab d’ina ma fa ya yi mini kad’an amma haka nake d’aurawa a kan hular ina yin sallah tun d’azu”. Ta fad’i hakan tana dariya….. daga haka suka nufi d’aki gaba d’ayansu…ita dai Inna abun ya d’aure mata kai, saboda har bayan tafiyar Siyama fa hularta tana kanta…amma kawai sai ta tsaya akan watak’il mai sunan Baban ne ya d’auka ya jefa a wani wajen, dan haka ta bari akan gobe da safe idan Allah ya tashemu lafiya sai ta duba!!!!. Manubiya da gwaggo Suwaiba ne kawai suka shiga suka kama ruwa suka yi alwallah, dan ita Inna da alwalarta, dardumarta da Hijab d’in kawai ta ajjiye ta kwanta saboda haka kurum ta ji ta wani iri ga kuma kasala!!! da mugun kyar ma ta iya kaiwa kan gadon, tana kwanciya kuwa wani wahalallen barci marar dad’i ga takura ya yi awon gaba da ita…. Su kansu su Manu sun yi mamakin baccin da Inna ta yi nan da nan gashi a karkace ma ta kwanta amma sai sukayi tunanin wataƙila ko gajiya ce, Manu ce ta d’aura mata Kai a kan pillow tana mamakin yadda take fitar da numfashi da kyar, daga haka ta rufa mata abun rufa ta d’an rage k’arfin ac dan a tunanin ta sanyin ne ba ta so…daga nan suka d’an tab’a hira ita da gwaggo Suwaiba suka yi addu’o’i suka bi gado suma. Da asuba!!…kiran sallar farko ne ya farkar da Manubiya da Gwaggo Suwaiba. Band’aki gwaggwo Suwaiba ta wuce, yayinda Manubiya ta d’an zauna a kan gadon ta yi shiruu har sai da ta wartsake sosai tukunna ta juya cike da mamakin Inna ta shiga tashinta, dan kullum idan suka farka a zaune a kan darduma suke tadda ita. Sau uku ta kira sunanta tana mai d’an tab’a mata Hannu amma shiruu…cikin tashin hankali ta mik’e ta k’arasa ta kunna wutar d’akin ta koma gareta da sauri ta shiga k’are mata kallo tana kiran sunanta kafin ta zauna a daidai kanta a firgice ta d’an shafa fuskarta ta ajjiye Hannunta daidai saitin hancinta. A firgice cikin tsananin masifaffen tashin hankali! firgice da tsoro ta tashi daga kusa da ita da mugun sauri ta d’an ja baya ta tsaya a kanta tana ci gaba da kallonta jikinta yana wani irin karkarwa! Daidai nan gwaggwo Suwaiba ta fito daga band’akin…yanayin Manubiyan ne ya sanya ta yi saurin k’arasawa inda take ta ruk’o hannunta itama idanunta suna a kan Inna tace”me ya faru?” Ta yi mata tambayar jikinta itanma yana karkarwa dan yanyin yadda Innar take a yashe da kuma yanayin Manubiya sun mugun firgigita. Juyowa Manubiya ta yi ta kalleta dai dai nan hawaye suka samu damar b’alle mata cikin tashin hankali tana magana da kyar tace”ba ta numfashi, kuma jikinta ya yi sanyi” Ta yi mata maganar tana mai nuna mata Innar da yatsa… Da kyar Gwaggo Suwaiba ta samu ta yi namijin k’ok’ari wajen k’arasawa inda Innar take ta zaune a gefenta ta shiga dubata…..tashi d’aya ta fashe da wani irin rikitaccen kuka ta shiga ambaton “innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!!”. Luuu!!! haka Manubiya ta tafi ta zube a wajen sumammiya……. Sama-sama take jin muryar Ya Musbah shima yana kuka yana yayyafa mata ruwa yana kiran sunanta! A hankali ta shiga k’ok’arin bud’e idanunta kanta yana wani irin mahaukacin sarawa…dishi-dishi ta fara gani kafin ta samu idanunta suka ware tarr,,tana iya kallon fuskar ya Musbah shab’e-shab’e da hawaye wanda hakan ya sake tabbatar mata tabbas Inna ta rasu!!! Mik’ewa ta yi ta zauna ta shiga k’are musu kallo, kowa ya hallara har da mai sunan Baba ya Nafi’u da Aisha da Likita yana duba Inna. Fashewa ta yi da wani irin kuka kanta yana wani kalar mahaukacin sarawa ta samu ta mik’e daga kan sofar dake a d’akin(inda suka d’aurata) da mugun kyar ta wuce Ya Musbah ta k’arasa inda Likitan yake duba Inna tana shirin yin magana dai dai shi kuma ya d’ago ya kalleta tukunna ya kalli su Baba cikin karyewar zuciya yace”rai ya yi halinsa!sai dai mu yi mata addua!!..i’m so sorry…..” Gaba d’ayansu har mai sunan Baba da Khairat fashewa suka yi da kuka! Yayinda ita kuma Manubiya ta nemi nata kukan ta rasa hawayen idanunta suka k’afe k’aff saboda tsabar masifa da tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki wanda ba ta tab’a jin kwatankwacinsa ba tunda Inna ta kawo ta duniya!! Tabbas zafi rad’ad’i zugi da d’acin rashin Mahaifiya daban yake! Ta yi going through hell a rayuwarta dan masifa kusan kaɗan ne za ta ce bata ɗanɗana azabarsu ba amma ba ta tab’a jin kalar bala’in da ta ke jinta a ciki a halin yanzu ba.! Ita ba ta fad’i ba ita ba ta zauna ba hakanan ta tsaya musu k’ememe ta k’ame kamar gunki dan haka gwaggo Suwaiba ta ja ta ta kaita kan kujerar da ta taso ta zaunar da ita ta rungumeta tana wani irin kuka kira take”Mannubiya ki yi kuka,dan Allah ki yi kukan nan ko kya rage zugi da zafin zuciya……..” Dai dai nan Baraka ta shigo d’akin d’ankwalinta rik’e a Hannu….haka kurum d’azu suka ga ta fita a rikice yanzu kuma gata ta dawo a hargitse!!!!… Ba ta ita suke ba, shiyasa babu wanda ya ko sake kallonta ma har ta Isa ta je ta bintik’e Manubiya daga jikin Gwaggo Suwaiba ta mik’ar da ita cikin tsananin tashin hankali tace”Manu ya ake ciki?” Girgiza kai Manubiya ta yi cikin rauni ta durk’ushe a wajen tana k’ok’arin janyo kuka amma sam ya k’i zuwa! Sake mik’ar da ita Baraka ta yi tace”ta mutu kenan yanzu shikenan??” Cikin fara jin haushinta gwaggo Suwaiba tace”ta rasu zaki ce Baraka ba wai ta mutu ba, kuma addu’a za ki yi mata ba hauka ba!” D’amara Baraka ta yi da d’ankwalin Hannunta tace”ki gaya mini tsakaninki da Allah..shin A tsakankanin jiya da muka rabu da ku zuwa yau shin ta bi ta kan k’ofar band’akinta ta wuce? bi ma’ana ta shiga b’andakin ta kafin ta mutu!???” Cikin k’unci Ya Musbah yace”Baraka bar nan!!” Kansa ta nufa tana zuwa ta tsaya a gabansa tace”Amsa d’aya za ku bani sai in tafi!! Shin kafin Inna ta mutu ta bi ta kan k’ofar band’akinta? ‘eh’ ko ‘A’a’? Dan Allah ku bani amsa in san makomata saboda idan ba ta wuce ta shiga band’akinta ba to akwai matsala fa!! wallahi akwai matsala!!!!”. Sai kuma ta nufi Inna tana zuwa ta fara k’ok’arin ruk’ota tana cewa “Allah yau sai kin tashi kin fad’a mini shin kin bi ta kai ko baki bi ba, ki tashi idan ba ki bi ba to ki bi yanzu a gabn idanuna in gani…..” Dai dai na Ya Musbah ya k’araso ya juyo da ita ya d’auketa da wani kalar rikitaccen mari. Kuka ta fashe da shi tace”ba ta haukace ba ta mutu ni kuma na haukace!!!saboda Allah in banda mugunta irin tata ta ya zata kwanta ta mutu ba tare da ta bi ta kan abunda na zuba mata ba? salon ta jaza mini bala’i!!!!” sai kuma ta fincike ribbom d’in kanta ta hau barbaza gashin kanta ta fara tsalle tana dira tana cewa “ai ku barshi ba sai kun fad’a mini komai ba ma, yadda na fara ji a jikin nan nawa na san ba ta bi ba ni kuma asirina ya dawo kaina, Innalillahi wa inna ilaihirrajiun mun tafi ba zamu dawo ba, da ni da Inna mun tafi inda ba a dawo wa!! ita ta tafi garin matattu ni kuma na tafi garin mahaukata daga ni har ita ba zamu tab’a dawowa ba!!… Bokan yace mini asirin baya karyewa ba a tab’a iya k’aryawa…” Daga haka ta juya ta kinkimi takalmin da ta gani a k’ofar band’akin ta rungume ta fice da wani irin mahaukacin gudu tana kurma uban ihu!!!… … Iyaka maganganun Baraka sun isa su faiyyace musu komai!!! shiyasa kawai duk suka bita da ido kowa yana Allah wadai!!!. Halin da suke a ciki bai sanya kowa ya sake bi ta kan Baraka ba..tana wucewa suka ci gaba da koke kokensu. Kafin awa d’aya gidan ya cika taff da jama’a, har da matan su Uncle da Mama kowa ya hallara, har Najeeb da Siyama su Jidda suma sun ce suna airport. A nan parlourn Baba mai k’ofa ta baya, Gwaggo Suwaiba da Mama suka yi wa Inna wanka amma da ikon Allah ana gama yi mata wankan Gwaggo Suwaiba ta hana a yi mata sutura, har kawo yanzu, kawai dai sun rufa mata zani sunata yi mata addu’a, ita kuma Gwaggo suwaiba ta k’ura mata idanu tana ta kallonta. ……. Najeeb da Manubiya sun kira Yash amma bai d’aga ba, kuma bai biyo kiran ba shiyasa Najeeb yace bari ya je gidan ya dubosa. Tun cikin dare Yash ya kasa barci sakamokon mummunan mawuyacin halin da ya dinga ganin Mommy da Ya’isha a ciki a mafarki…shiyasa ya kasa hak’ura duk da yadda Mommy ta ja masa kunne kar ya je inda suke! k’arfe bakwai ta na yi ya fita ya nufi gidan saboda zuwa wannan lokacin ko rufe idanunsa ne in ya yi to kamar Irin a cikin gobara haka yake ganinsu, shiysa ma ya yi tunanin ko gobara ce ta kama a gidan gashi duk d’insu babu mai d’aukar wayarsa. Yasira,da! ta yi fushi, tace Wallahi Hatta office d’in ma ta daina zuwa, amma sai Mommy da Y’aisha suka yi mata magana jiya da daddare suka ce “ta je, ai bazasu zuba masa ido su kyalesa hakanan ba, kuma idan ba ta je ɗin ba to tsaf zai iya d’aura Ummi a kan komai tunda Yash bai gama resumin aiki ba”…dan haka ta shirya saboda dama yau ta san da zuwan manya manyan bak’i. Tare suka fita ita da Yusra, wadda zata ga invigilator d’inta a yau,ta sauk’e Yusran ita kuma ta wuce office…… Sosai yau Mommy take jinta a sama, ta dad’e bata samu soundsleep (bacci mai daɗi) kamar na jiya ba, saboda ta riga ta san yau zata ji labarin mutuwar Manubiya….: Tun a jiyan da suka gama magana da Ya’isha ta yi musu sai da safe ta shige d’aki, har suka gama breakfast su Yasira suka fice sam Mommy ba ta ji motsinta ba, dan haka ta lek’a d’akin da yake mallakinta.. Da wani irin mahaukacin gudu ta k’arasa cikin d’akin sakamokon hango Ya’isha da ta yi wanwarr a k’asa a yashe….. Tana zuwa ta d’agota ta d’aurata a kan cinyarta ta shiga kiran sunanta amma ko gezau!! Duddubata ta hau yi amma sam ba ta ga alamun rai a tartare da Ya’ishan ba, ga idanunta sun k’afe suna kallon sama wanda hakan ya sanya tashi d’aya Mommyn ta fashe da wani irin kuka ta rungumeta da k’arfi a jikinta cikin kuka ta shiga cewa “I’m so sorry Ya’isha, Innalillahi wa Innailaihirrajiun….” Sai kuma ta mik’e zumbur ta fita waje…. Sai da Mommy tabbatar ta kulle ko’ina, sannan babu kowa a gidan tukunna ta koma ta d’auko makullin mota da Hijabi ta zo ta bud’e boot d’in motar gudun kar a kamata dan motarta babu tint. Tana wani irin kuka ta je ta kinkimo Ya’isha da kyar ta sakata a booth, hakanan tana ji tana gani ta rufe y’ar tata a booth a ranta tana k’iyasta yadda zata yi da su Yashjub muddin ta samu Ya’isha ta farfad’o dan wannan duk laifinsu ne!!! tunda uwarsa ta shigo rayuwar Daddy har yau ba ta samu kwanciyar hankali ba, gashi yanzu saboda shi da Manubiya ta zo wannan flat house d’in d’an mitsitsi ta zauna sannan kalli a booth ta saka y’arta yo Idan bata ga bayan su Manu ba ma ai ba ta cika sunanta Khadija ba wallahi….. Sannan ad’uarta d’aya ‘Allah dai ya sa ba aikin bane ya lalace, Allah ya sa dai abun ya kama Manu’ dan tabbas jiya Ya’isha tace mata bata yi mistake ba, to amma kuma mai ya faru!!!? Me yasa abun ya tab’a mata y’a!!!!? Hakanan tana ta sak’e sak’e hankalinta a masifar tashe ta je ta zuge gate d’in tana wani irin kuka…tana gama zugewa ta koma ta fitar da motar ta fito ta mayar da gate d’in ta rufe, sannan ta koma ta ja motar ta nufi gidan tsohon jiya dan ta san shi kad’ai ne zai iya farfad’o mata da Ya’isha……… Sosai tun d’azu Yashjub wanda sam ba ta lura da shi ba ya ke tsaye yana kallonta yana mamakin yadda take kuka…….sannan yadda ta zuge gate da kanta ta fita da asussubah, tabbas hakan abun mamaki ne. Sai da ta Isa k’ofar gidan tsohon, tukunna ta tuna ba ma ta d’auko wayarta ba, ballantana ta kirasa ya bud’e mata, dan haka kawai ta fito ta Isa bakin k’ofar gidan nasa ta hau bugu. Ba ta wani dad’e tana bugawa ba tsohon ya zo ya bud’e mata k’ofar, dan dama daga shi sai dabbobi ne a gidan. A rikice ta afka ta tura k’ofar ta mayar ta rufe, cikin tsananin tashin hankali tana ganin dishi-dishi tace masa “Mun wayi gari babu Ya’isha, ka taimaka mini ka san yadda ka yi y’ata ta dawo!!. Ina son y’ata, ita kad’ai ce ba ta tab’a yi mini jayayya ba wallahi!. sannan in har su Yasira suka ganta haka to sun san ni ce!! sun san me ya faru! tunda a gabnsu aka fara maganar jiya, dan haka na san wallahi ba za su tab’a yafe mini ba!!! dan girman Allah ka yi wani abun….” “Biyo ni” Kawai yace, daga haka ya nufi cikin gidan…. Wajen Birin jiya suka je, kamar jiyan suna zuwa birin ya matsa musu shi kuma tsohon ya saka hannu ya d’aga dutsen ya turasa gefe! tun kafin ya d’auko babyn robar ya kwab’e fuska ya ce “too ikon Allah, mai ya faru kenan?” Da sauri Mommy ta matso tace”ya akayi? mai ya faru? Ba dai aikin ne ya lalace gaba d’aya ba dai ko??” Ta yi masa tambayar a gigice Girgiza kai yayi, ya sa Hannu ya d’auko Babyn robar yana kallo tukunna yace “gaskiya kun yi kuskure, amma bansan ta Ina ba! Saboda yadda y’ar tsanar nan ta yi bak’i, kalli kinga fuskarta, “ Ya yi magaar yana nuna mata ƴar tsanar ta hanyar kai Mata ita saitin fuskarta tukunna ya ɗaura da cewa “to hakan yana nuni ne da aiki ya ci kuma ya kama sannan yana kan yi, kuskuren ne ban fahimci ta ina kuka yi ba! Saboda tunda har abun ya shafi Ya’isha tou tabbas akwai wani abu da kuka yi ba daidai ba.” Sai kuma ya kalleta yace”ke fa??lafiya kike jin ki dai ko??” Jinjina masa Kai ta yi da farko sai kuma tace”idanuwana dai suna ta yi mini dishi-dishi tun d’azu!!!!” Jinjina kai ya yi, ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace “dama na yi zaton hakan a kema ɗin, idanunki ne kenan za su tab’u” sai kuma ya mayar da gabaki d’aya hankalinsa gareta yace”idan kinaso za a iya karyawa, tunda kinga aiki dai gashi ya ci ya kama amma bai kammalu ba, dan inda ace ya kammalu to da ƴar tsanar za ta ƙone ne daga nan to shine ba za a taɓa iya karyawa ba. Dan haka yanzu muna da damar karyawa amma fa idan aka karya ɗin Na farko ba za a sake iya yiwa ita Manubiya irinshi ya kamata ba, sannan abu na biyu babu tabbacin Ya’isha za ta tashi!”. Kuka ta fashe dashi sannan tace”kamar ya zaka ce mini Ya’isha ba za ta tashi ba!! idan fa Yarinyar nan ba ta tashi ba wallahi na san duk su Yasira sai sun fahimci komai, kuma ba za su tab’a yafe mini ba, k’arshentama su tona mini asiri…” Cikin tarar numfashinta ya ce ”ai dama sai da na gaya miki aikin yana buk’atar taka tsantsan, kuma yanada haɗari….” Cikin yi mata nuni da babyn robar a karo na biyu, yace”dan ci kam aiki ya ci kuma kun ce hularta ce sannan ba a samu matsala ta ko ina ba dan haka tabbas ya ci kuma ya kama Manubiyan dan ga zahiri nan nima na gani….amma kuma halin da Ya’isha ta shiga yana nuni ne da aiki ya riga ya fara tab’arb’arewa kenan…..kuma a yanzu tunda har bai kammalu ba to zan san yadda zan yi, zan gwada in sha Allahu zamu iya warwaresa….wanda idan an warware ɗin ta you Ya’isha ta tashi ta you kuma ta tafi kenan har abada, amma tabbas Manubiya kam za ta tashi ita wannan a rubuce yake tunda ga ƴar tsanar nan har yanzu bata ƙone ba…..” Cikin tarar numfashinsa tace”to mu bari mana sai an kaita (manubiya) inyaso sai mu warware a tare!” Girgiza Kai yayi yace”sam ba haka abun yake ba..kuma ni yanzu mintuna uku ne ma suka ragemini, suna cika za ki ga y’ar tsanar nan ta kama da wuta! (idan har ta kama da wuta ba a fara kwanceta ba to aiki ya riga ya ci kuma ya kammalu kenan..an gama komai baza a taɓa iya warwarewa ba)saboda daga nan abun ya fita daga hannuna kenan!!.. dan haka ki yanke hukunci da wurwuri, kin riga kin lalata komai da ke da y’arki, dan haka iyaka bayanin nan da na gama yi miki shine kawai taimakon da zan iya yi miki a halin yanzu….” Shiruu ta yi kafin tace”idanuwan nawa da na fara ganin dishi dishi dasu a haka za su dauwwama?” Shiruu ya d’anyi kafin yace”akwai taimakon da zan baki, tunda ke kinga abun da alamun shafarki ya yi kawai ba wai ya rikito gaba ɗaya a kanki kamar Ya’ishan ba ne, dan haka inshaaAllah in na yi miki maganin za a dace” Cikin sake jeho masa wata tambayar tace”tashin Ya’isha k’ila wak’ala ne ko?” Jinjina kai ya yi yace”Bari ki ji ba zan b’oye miki ba Ya’isha ba ma na jin tanada rai a halin yanzu, dan haka ba zan iya yin komai a kai ba, saboda kun damalmala komai ne, gashi kuma bamusan ma ta ina matsalar take ba taƙameme…ga dai aiki ya yi kuma yana ci wanda hakan yake nuni da ya kama har Manubiyan da aka yi wa tabbas…to shafar Ya’isha da aikin ya yi ne matsalar, shiyasa abun zai fi k’arfina!” A hankali Mommy ta lumshe idanuwanta hawaye suka zubo cikin d’acin zuciya tace”ka bar shi kar ka karya!!!” Ta ji tsananin zafin mutuwar Ya’isha tabbas, amma da ta tuna abunda ya ke faruwa da Manubiya a halin yanzu sai ta d’an ji sanyi, ko banza ta san kwalliya ta biya kud’in sabulu!!!!…. Ba ta dad’e da gama rufe bakinta ba Babyn robar ta kama da wuta, tana jin tsohon yana cewa “Aiki ya kammalu kenan, yanzu kam ba zai yiu a taɓa iya warwarewa ba, sannan a halinda ake ciki shi kansa bai san ranar da numfashin Manubiya zai komo mata ba, aiki ba a hannunsa yake ba ba zai iya yin komai ba tunda sun riga sun damalmala masa komai!!” Itadai Mommy ta ji sanyi a ranta, tunda ba a warware ba to ta san duk bala’i ko nan da shekara nawa ne Manubiya ba ta Isa ta fito ba!. Da shi da ita suka yanke shawarar ‘gara su binne Ya’isha, maganar ta tsaya a iyaka su biyu kawai. dan idan wani ya sani tofa akwai matsala…. Inyaso Mommyn sai ta cewa ƴan uwan Ƴa’ishan ta aike ta k’auye ne, kafin su kuma (ita da tsohon) su san abun yi. Sannan shi kuma ya yi mata alƙawarin inshaaAllah kafin a nemo abunda za a ce ya samu Ya’ishan har a samu zancenta ya gushe, zai rufewa duk wani wanda zai d’aga mata hankali wajen bin diddigi da tambayar ‘Ina Ya’isha’ Baki. Hakanan suka je wani k’ungurmi daji, ya hak’a rami! yana shirin d’auko Ya’isha ya sakata a ramin aka kirasa….. Kiran mai matuk’ar mahimmanci ne, dan haka ya cewa mommy ‘ta yi masa hak’uri, dole zai tafi, ita ta k’arasa sakata ta rufe ramin ta koma gida’. hakanan ya wuce ya barta a wajen, jikinsa yana karkarwa dan babban mutum ne ya kirasa wanda ya san a k’allan a lalace yau sai ya samu sama da miliyan biyu….. Tsoro da fargabar dajin gata tare da gawa ne suka sanya Mommy saka Ya’isha cikin ramin anyhow! ba tare da nutsuwa, tsari ko hankali ba…dan ta Ka ma ta fara zurata kuma ta tura gangar jikin akan kan nata wanda har sai da wuyan Ya’ishan ya yi ƙara, sannan ko gama rufewa ma ba ta yi ba, hakanan ta yi sauri ta bar wajen jikinta ya na karkarwa, tana kuka. Bata wani jima da komawa gidan ba, su Yasira suka dawo… Jikinsu daga ita har Yusra duk a sanyaye, haka dai suka gaisa Yasira tana mai bin Mommyn da wani irin kallo itama Yusran haka… kafin chan Yasira ta d’an yi waige waige tace mata “Ina Ya’isha?” hakanan Mommy ta had’e fuska, tace musu”ta turata k’auye! tunda sun hana a tsayar da numfashi, to ta turata k’auye zata yo musu mai sauk’i…” Shiruu Yasira ta yi kawai Tana kallonta…sam ba ta son ta zargi Mommy amma kuma duba da inda suka je sannan da abunda ta ji ta gani a jiya, ya sanya hankalinta ya kasa kwanciya ɗari bisa ɗari da Momyn tun lokacin da ta ji labarin rasuwar Inna… Ta jima tana tunani kafin tace mata “Ina fatan bakiyi komai ba Mommy” cikin alhini ta d’aura da cewa”Mahaifiyar Manubiya ta rasu yau! ki shirye mu je, mu yi musu gaisuwa.” Daga haka ta mik’e da niyyar kimtsawa ta fito inyaso sai su tafi. Shiruu ta ga Mommyn ta yi, ta shiga mugun shock! kafin kawai ta ga ta mik’e tsaye….. K’iri k’iri tashi ɗaya ta hau bori!! Ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba! Ta nace akan “ba zata je ba, sannan suma kuma ta hanasu zuwa ba za su je ba!! Wai ai suma su Manubiyan jiya ba su zo mata gaisuwar Larai ba!” Da mugun mamaki Yasirar ta bi ta da kallo har ta shige cikin bedroom d’inta ta banko k’ofar… Tana shiga ta sak’ala key k’irjinta yana dukan uku uku, ta durk’ushe a nan bakin k’ofar… kar dai maman manubiya ce ta rasu ba manubiya ba…Gidan babu wuta bata jona wayarta ba babu charji shiyasa dama bata samu ta yi waya ta ji batun wanne hali Manubiya ke ciki ba tun d’azu…inna lillahi wa inna ilaihirrajiun, kenan yanzu duk wani effort jajircewa da sacrifices d’inta sun tafi a banza kenan? Kaii inaa ba zai yiu ba, inshaaAllah ma ba haka bane ba, inshaaAllah Manubiya da mahaifiyarta tata ne suka mutu tare…amma kuma inda Manubiya ta rasu ai da Yasira zata gaya mata….. Wani Irin bugawa k’irjinta ya shiga yi, gashi zuwa yanzu dishi dishi take gani sosai sosai, ga wani irin juyawa da kanta yakeyi, dan haka ta mik’e da kyar ta k’arasa kan gadonta ta kwanta ta lumshe Idanuwanta tana jin kamar ta saka Hannu a cikin k’irjinta ta kwak’ulo zuciyarta ta jefar, tsabar azabar da ta ke yi mata……… Bata da wani zaɓin da ya wuce ta tirsasawa zuciyarta akan ‘Ta tsaya ta d’an jira zuwa anjima, in sha Allah zata ji labarin mutuwar Manubiyan itama’. Saboda ko da wasa bazata taɓa iya Hasaso ko ta yi tunanin cewa ‘wai Manubiya ba zata mutu ba! Kenan Duk waniaiki da sadaukarwarta sun tafi a banza fa kenan, inaa.’ Tabbas Yasira ta tsorata, kuma ta shiga al’ajabi da lamarin Mommy, ko bayan shigar Mommyn d’aki har Yusra ta wuce d’aki ita Yasirar tana nan a yadda take ta ma kasa motsi, kafin da kyar ta nemi waje ta zauna tukunna ta zaro waya ta Kira Manu ta yi mata gaisuwa sannan ta ce mata “zasu zo inshaaAllah” Daganan ta kashe wayar ta yi shiruuu…chan ta ɗago wayar tata ta danna kiran Ya’isha!…. Ta san Ya’isha tanada taurin kai amma zata gwada lallab’ata a samu ta hak’ura da aikin da Mommy ta turata yi kawai ta dawo, ba wai son Manubiya take yi ba, kawai ta ga Mommy ta wuce gona da iri ne, dan haka tun kafin ta kai kanta ga halaka ya kamata a dawo da ita saiti! Wanne Irin bala’i ne har ka tashi mutum gari ya gari dan kawai ya je ya yo maka asiri ya dawo! Har mai ya yi zafi haka……. Layin Ya’isha yana shiga ga mamakinta kawai sai ta jiyo k’arar wayartata a d’akin da Ya’ishan ta kwana, dan haka ta mik’e ta shige…. … Tana shiga ta ga wayar Ya’ishan a ciki, har da charger da su AirPod d’inta da watch duk ba ta d’auki ko d’aya, ba sannan kayanta suma gasu nan ciff suke! Alamun ta d’iba ba, daga gani tun jiya ba ma ta tab’a ba…dan haka kawai ta juya ta fita ta je ta shiga buga d’akin Mommy… Ta fi mintuna ashirin a wajen a tsaye! Har Yusra itama ta fito ta jona ta suka dinga buga ɗakin, tukunna aka samu Mommy ta bud’e… yadda suka ganta dagaje-dagaje sannan idanunta duk kwantsa sai da abun ya basu tsoro, ya kuma basu mamaki, dan haka Yasira ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi (ta sauƙa daga fushin da ta hau) amma dukda haka sai cewa ta yi”Mommy ki gaya mini tsakaninki da Allah, Ina Ya’isha? saboda na duba d’akinta Hatta wayarta ba ta d’auka ba!!” Shiruu mommy ta yi, dan ita sai yanzun ne ma kwakwalwarta ta bata duk waennnan abubuwan…..da kyar ta nemo mafita, dan haka a hankali ta buɗe Bakinta tace musu “da k’aramar wayata ta tafi, saboda hanya, kaya kuma ta d’auki dogayen rigguna biyu. Dan Allah Yasira ki bar ni in huta mana bakiga situation d’ina ba ne??? Ki huta kema ki zo ki je mini pharmacy ki siyo min maganin ciwon Ido, saboda wannan d’ayan har na daina gani da shi, sannan ki fita ki nemo min chargi ina buk’atar in yi waya da gaggawa….Yusra ke kuma ki d’aura girki…” Tana gama fad’in haka ta juya ta rufo k’ofarta hankali a masifar tashe……… ••• Sai azahar tukunna Yash ya zo…zuwa wannan lokacin kowa ya fara jin tausayin gwaggo Suwaiba saboda sun fahimci zafin abun ne ya sanyata yin hakan! Ta inda kwata kwata ta k’i bari a nad’e inna a yi mata sutura…..ta zama kamar wata tab’abb’iya. Manu tana zaune a parlourn ita da su Siyama da su anty Umma suna kuka su mama kuma sunata lallab’a gwaggo Suwaiba, Baba shima yana gefe shi da Ya Musbah in banda hawaye babu abunda suke yi, sun ma kasa tsawatar mata! Suna a haka Muhsin ya shigo yacewa Manubiya “ga Ya Yash a waje yace ta je…” Manu tana mik’ewa Gwaggo Suwaiba tace mata “tace masa tana son ganinsa ya shigo” Sannan ta kalli su Baba tace “dan Allah tana buk’atar magana da Yash shi kad’ai…….” Sai da suka gama kukan su shi da Manu ya lallab’a ta da kyar tukunna ta iya gaya masa sak’on gwaggo Suwaiba, ya d’an yi mamaki amma kawai sai ya bi bayan Manu, ta yi masa rakiya zuwa cikin parlourn. Manubiya ta so zama amma itama Gwaggo Suwaiba ta sallameta, parlourn ya rage daga ita sai Yash sai Inna…. Sun jima sosai sun fi 1 hour dan har mota Yash d’in ya fita ya shigo da ita kafin ya tafi ko sallama bai yi wa Manubiya ba! Ta ji mamaki matuk’a, dan tun d’azu dama da ya zo ta Lura da yanayin da yake a ciki na tashin hankali firgici tsoro da kuma rud’ani!…tunda ya zo ɗin tana kallon idanunsa ta fahimci ya ci kuka ba na wasa ba, da farko ta yi tunanin rasuwar inna ce ta tab’asa haka amma yanzu yadda ya tafi kuma ya k’i d’aukar wayarta ya sanya ta fahimci tabbas wata matsalarce ta sake tasowa bayan waenda suke a ciki. Bayan tafiyar Yashjub suna shiga suka tarar Gwaggo Suwaiba har ta shirya Inna an sakata a makara ma wanda hakan ya sanyasu sake rushewa da kuka, ko zama ba su yi ba Ya Musbah ya shigo yace “Baba yace ku ake jira.” Da kyar aka b’amb’are Muhsin da Manubiya daga jikin gawar! Hakanan Ya Musbah shi da Ya Nafi’u suka d’auketa a cikin makarar aka je a ka yi mata sallah suka mik’ata gidanta na gaskiya….. Ana tafiya kaita su Yahanasu sukazo dukkansu har Yasmeen Yadira da Hajiya Mama da su Daddy…. Hajiya mama ba su had’u da Mama ba, saboda da wuri suka tafi tare da su Daddy ita da su Yasmeen, Yahanasu ce ta zauna. Ita kuma Mama a lokacin ta koma gida, sun d’an kimtsa tukunna suka taho ita da Ammi. Yahanasu tana zaune a d’akin da Manubiya ta ajjiyeta kawai ta ga Mama ta shigo, wadda dama ita maman ta san tabbas yau kam za ta had’u dasu, amma fa dukda haka sai da ta kusan fad’uwa a lokacin da sukayi ido biyu ita da Yahanasun, Yahanasun kanta ta kusan suma, gashi lokacin babu kowa a d’akin sai ita kaɗai… … A hankali jiki ba lakka ta mik’e tsaye, bakinta yana wani irin karkarwa ta ce ”maa maa!”sai kuma ta tafi da gudu ta fad’a jikinta ta fashe da wani irin kuka… Itama Maman kuka ta saka a nan wajen ta yarda tray d’in hannun nata ta rungumeta a cikin jikinta! Ba abunda ya fi yiwa Yahanasu dad’i kamar yanzu da ta san ta san inda mama take! Dan A take a ranta ta aiyyana ‘shikenan za ta had’a Yash da mahaifiyarsa cikin sauk’i!’ nauyin da ya ke a kanta shekara da shekaru yanzu zai sauk’a. Cikin sharar hawaye ta d’ago ta kalleta tace”Mama dama kin san su Manubiya? Ya aka yi kuka had’u?” Ta yi mata tambayar waensu hawayen suna sake zubowa….. Hannu ta saka ta share mata hawayen nata, kafin ta ja hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna…nan ta faiyyace mata duk wata alak’a da take tsakaninta da su Manubiya… Tana kuka tana hawaye sannan tana dariya at the same time tace” da ma kece mama da nake yawan jin sunanki a bakin Manu? Alhamdulillah!! Mama na ji matuk’ar dad’in ganinki, bari Manu itama ta zo, na san zata ji dad’in jin wannan labari kwarai!” Ta fad’i hakan cikin sake rungumeta. Da sauri Mama tace mata “A’a Yaha, kar ki gaya mata komai!” Cikin rashin fahimta Yahanasu tace”ko me yasa Mama?” A take wasu hawaye suka zubo mata cikin ruk’o hannun ta tace”Yahanasu a halin yanzu ba zan iya fuskantar Hajiya mama da sharrin tarin abun kunya da aka yi mini ba, sannan mahaifinku ya sanar mini muddin ya ganni ko da a kusa da ke ne to fa abunda zai aikata a gareni mummuna ne!!” Cikin tarar numfashinta Yahanasu ta d’ago tace”Mama duk sharri ne ba shi ne ya fad’i waennan maganganunba! duk makircin su Momny ne!” Da mamaki ya kalleta tace”su Mommy kuma?” “Tabbas ita ta had’a Baki da mai makarantarmu a wanchan lokacin, sannan asalin abunda ya faru shima duk laifinta ne! Kar ki hukunta Daddy ta hanyar cewa kar a gaya masa an ganki, dam na tabbatar shima neman naki yake yi yanzu haka.” Cikin gyara zama da sake ruk’o hannunta ta d’aura da cewa” Akwai abubuwa da yawa da nakeso in faiyyace miki, but first yanzu bari in kirawo su Daddy su zo Allah kad’ai ya san kalar murnar da za su yi idan suka ganki!” Shiruu Mama ta yi, dan ba kad’an ba ta shiga shock da jin sunan Mommy a cikin lamarinta!!! Mommy Mommy dai??anya kuwa? Sai kuma ta kalli Yaha kamar mai nazari kafin cikin hanzari ta sa hannu ta karb’e wayar hannun Yahanasun ta kashe kiran…. Da mamaki Yahanasu ta kalleta kafin tace”Mama pls mana, dan Allah ki bari in…..” Cikin tarar numfashinta tace”Yahanasu ki yi mini alfarma guda d’aya a matsayina na mahaifiyarki kar ki gayawa kowa kin ganni, inaso ace Daddy ya nemo ni ya maidani cikin zuri’arsa da kansa kamar yadda ya yi mini yankan k’auna da kansa…shekaru kusan talatin Yahanasu amma ace har ke da kanki kin fahimci sharri aka yi mini ta ya zan yarda Daddy da kansa bai fahimci hakan ba, sannan meyasa bai neme ni ba???. Ni dai kawai inaso ya kasance ya nemo ni ya mayar da ni da kansa da hannunsa Akan ace kece kika mayarda ni ba tare da yarda da amincewarsaba, kuma inajin tsoron had’uwa ta da shi, ban san ya zata kasance ba, kince abunda mai makarantaar ku ta fad’a sharrin su Mommy ne ko? To na ji na yarda amma kuma wat if ya yi mini kamar yadda suka ce zai yi d’in? dan na san zai iya aikata hakan Yahansu mutumin da ya kashe ni zai iya aikata fiye da abunda suka k’aga suka fad’a suka ce ya ce zai yi.” Ciki girgiza kai Yaha tace “Na tabbata idan na yi masa bayani zai fahimta zai yarda. Kumafa Mama shi a tunaninsa kin rasu ne, muma a da duk hakan muka d’auka, ki bari a yi masa bayani” “Yahanasu inda ace ya damu, to ya kamata ace zuwa yanzu ya fahimci gaskiya kamar yadda kema kika fahimta” Yahansu zata yi magana Mama ta katseta ta hanyar cewa”dan Allah kar ki yi min jayayya, bana son musu daga gareki, ki yi yadda nace hakan shine farin cikina. Na fi so ya fahimta da kansa ya nemoni da kansa, hakan shine kad’ai zai goge mini abunda ya faru. Sannan bamuda tabbacin zai karb’eni Yahansu idan aka yi rashin sa’a ya tozartani Ina riba? Ba zan so a ci mini mutunci a b’atamin suna ba, dan haka na rok’ek’i da girman Allah kar kiyi komai kar kice komai, alfarmar mutunci da darajata a idanunki ki bari mu yi addu’a ya yi yadda nakeso d’in ko na samu peace of mind da sauk’in radadin da nakeji a cikin zuciyata!”. Da kyar Mama ta samu ta sanya Yahanasu ta yarda kuma ta hak’ura akan ‘ba zata gayawa kowa ba, har sai Daddy ya huce ya nemo maman da kansa ya fahimci komai…’ ba dan Yahansu ta so ba ta yarda da hakan, amma InshaaAllah ba za ta yi k’asa a guiwa ba har sai ta nuna masa hanya, shi kuma ya gane gaskiya ya nemi sanin inda take da kannasa kamar yadda Maman takeso. Washegari Jidda suka zo ita da Al’ameen, nan kuwa komai ya dawowa su Manubiya sabo fil…..sun ci kuka kamar ransu zai fita, Jidda da Siyama masu d’auke da juna biyu wata uku uku kam sai da aka dangana da kwantar da su a asibiti tsabar kuka da damuwa…. A ranar ne kuma Gwaggo Suwaiba ta tashi tafiya, babu yadda basuyi da ita ba amma furr tace musu “ita tafiya zata yi..” Wanda hakan sam bai yiwa kowa dad’i ba, dan kai tsaye hakan rashin kyautawa ne…hakanan su Ya Nafi’u suka kaisu tasha ita da Hadiza suka kama hanya, gidan ya rage daga Manubiya sai su Jidda abun tausayi , dan ma Anty Umma tana tare da su saboda Siyama ba ta wani dad’e ba aka sallamota daga asibitin ta dawo gidansu manu ɗin, Mama kuma ita take tare da Jidda a asibiti itakam sai da ta yi sati biyu a kwance, dama cikin nata ya zo da laulayi sosai tun usulinsa. Yahansu har asibitin take zuwa ta duba Jidda su tattauna da Mama, amma har yau bata samu ta yi convincing maman ba, ganin fa bazata tab’a yarda ba ne ya sanya ta mayar da hankalinta ga tunanin ta yadda za ta bawa Daddy ko da clue ne a samu ya fara binciken nata, dan maman ta sanyata ta yi mata alk’awarin ba zata tab’a cewa kowa komai ba. Sosai mama ta ji dad’in ganin kamal a matsayin wanda Yahanasun zata aura, dan shima ya je ya duba Jidda kuma ya je ya yi gaisuwa. Sai da aka yi kwana ashirin da rasuwar Inna tukunna su Manubiya suka koma gidajensu, anty Umma ma ta koma gida, gidan ya rage daga mai sunan Baba sai Baba Muhsin da Ya Musbah dan Bararka tunda ta fita da gudu har yau ba’a ganta ba, cigiya har a gidan radio mahaifiyarta ta bayar amma shiru…shi ya Nafi’u ma ya d’auka da mahaifiyartata ta ji labarin zata yiwa mutane hauka, amma sai suka ga ta big’e da bada hak’urin abunda Barakar ta yi, sannan ta roƙi ‘dan Allah a yafe mata, a tayata addu’ar nasarar samun ganin ta……..’ …. Bayan kwanaki goma.. Yau kwanakin Inna talatin da rasuwa, su Manubiya kuma goma da komawar su gidajen mazajensu…Jidda ma a nan Nigeria Al’Ameen ya barta ya tafi dan saura kwana sittin ya kammala abunda ya je yi ɗin, kuma exams ne da shi Masu zafi a gabansa, shiyasa tace masa ‘tana son zama a nan’ su Ammi ma suka ce ‘ya barta a nan ɗin’ saboda jikin nata ya yi tsanani sosai…. Ya siya mata gida mai kyau a Na’ibawa, ya zuba kaya ya yi komai, amma dai a Hannun Ammi ya barta for now, saboda kusan kullum sai an k’ara mata ruwa..sosai kuwa Ammi da Mama suke kula da ita dan abunda suke yi mata ko Inna iyakacin abunda zata yi mata kenan. Siyama ma ta koma gidanta, lafiya k’alau itakam bata wannan fitinannen Laulayi kamar na Jiddah. A b’angaren Manubiya kuwa gaba d’aya ta gagara gane kan Yash!! Tun ranar da Inna ta rasu shikenan ya chanja gaba d’aya. kuma ba wai ita kad’ai ba kowa yake yiwa hakan….haka kurum sai dai ya yi shiruu ya zauna ya tusa Mutane a gaba babu um babu um’um ya yi ta kallon kowa..amma iyaka idanuwansa kad’ai idan aka kalla tashi d’aya za’a fahimci yana cikin masifa da tashin hankali… Hatta office ma da Najeeb ya zo zai yi masa handing over cewa Najeeb ɗin ya yi ‘ya cigaba kawai ba zai iyaba……..’. Shima da so ya yi ya chanjawa Manubiya gida, amma sai Hajiya mama ta ce ”kawai ya zo Mansion d’in Daddy su zauna a side d’insa na da, dan tabbas yanayinsa yana mugun bawa har su su Hajiya maman tsoro, gashi an yi tambayar duniya yace mus ”he’s fine!! Babu abunda ya ke damunsa!” Mommy kuwa har yau bata cire rai ba……Ya’isha dai ta tafi dahirr! ta ma cire rai….….amma tsohon yace mata “ta kwantar da hankalinta, indai hular Manu aka d’auko akayi aikin da ita to fa ta zuba ido zuwa ko wanne lokaci labarin rasuwar Manu zai iya riskarta!! watak’il inna itama ta saka hular ne shiyasa abun ya shafeta kuma shiyasa aka samu jinkirin mutuwar Manubiyan amma tabbas tana hanya itama….Su Yasira kuwa zuwa yanzu sun dawo daga rakiyar Mommy…babu Ya’isha babu labarinta zuwa yanzu kuma idan suka yi mata maganar Ya’ishan ma fad’a take rufe su dashi…dukda sun san itama tana cikin masifa amma sam wannan ba abunda za su yi shiru bane ba dan haka Yasira ta shirya akan zata je ta samu Daddy tace masa ‘ba fa su ga Ya’isha ba, kuma Mommy ko maganar ba ta so ayi!!!’ Ta san ko da matsalar ganin da take fama da shi aka barta ya isheta(dan zuwa yanzu kwata kwata idonta na dama ba ya aiki na hagun shima ya tab’u sosai)amma fa ba zata iya cigaba da yin shiru ba wallahi, dan wannan al’amarin serious case ne. A lokacin da Yasira suke maganar za su je su samu Daddy ita da Yusra Mommyn tana jinsu… Shiyasa hankalinta ya sake tashi matuk’a, dama masifar rashin gani da tsohon ya ke ta amshe kuɗaɗenta ana ta yin magani amma a banza ta isheta, ga Manubiya da ranta har yanzu Yash ma haka…a halin da take ciki dai yanzu ta ajjiye komai a gefe, dan ita babbar damuwarta itace a samu ta fara gani tarr tukunna sai a yi komai, su Yasiran kuma ta san ta rufe musu Baki a kan case d’in Ya’isha to amma kuma gashi yanzu kwatsam! Suna shirin jik’a mata aiki,… Har fa su Yasmeen ta hana zuwa gidan, duk dan kar a tambayi Ya’isha, a lamarin waya kuwa da suka ji ta shiru tace musu ‘bata da lafiya ne’… ita kanta sai yanzu ta san tanada matsala fa! dan Bata san me zata ce game da Ya’isha ba a gaba, sabida ba zai yiu ta yita b’oye b’oye har abada ba. A b’angaren Abbakar shima tunda aka yi rasuwar kusan kullum sai ya je musu gaisuwa da daddare lokacin da ya tabbatar ba zai had’u da Yash ba!. Ita dai Manu gaisawa kawai suke yi, daga haka ta wuce d’aki, dan abu da Abbakar sam ba ta so…to yanzu kuma ya isheta a waya yanason taimakon ta, ta yi blocking d’insa amma a banza a rana sai ya kirata sau bakwai da different layuka ga uban messages, dan ma Allah ya taimaketa Yash bai tab’a gani ba saboda shima he’s not himself (baya cikin haiyyacinsa) kwana biyun nan duk sai a hankali kawai. … Ta san watak’il akan rashin lafiyar mahaifiyarsa ne wanda ya k’i ci ya k’i cinyewa (saboda ta ji anata maganar ciwon nata) Abbakar ɗin yake ta nemanta, amma ita har ga Allah tsoron d’aukar wayarsa ma take yi, Shiyasa jiya da ta je gida ta tura Muhsin gidansu ya karb’o mata accnt numbersa ta tura masa dubu d’ari amma kuma dukda haka Abbakar bai bar kiranta da tura mata sak’onni ba. A b’angaren Kausar kuwa, tana nan cikin tashin hankali dan ga Yash da Manu a cikin gidan kusa da ita amma kamar basa nan…..ba ta Isa ta je inda suke ba kuma tunda suka zo ko ganinsu bata yi ba, Yasmeen dai tana zuwa wajensu har Yadira idan sunzo, amma shi kam saboda ita ko lek’owa bayayi itama Manu ya hanata shiga main cikin gidan kuma su Hajiya mama sun yarda da hakan, Daddy dai da asubah suke gaisawa Hajya mama kuma ta kan je musu da kanta……. .. Tun daga kan Hajiya Mama har zuwa kan Yadira wadda suke yawan zuwa gidan….duk y’an gidan mamakin Kausar suke yi dan ta ma fi su energy. Kwata Kwata ba ta jin nauyin cikin jikinta, sannan babu alamun ciki ya d’auko tsufa a tartare da ita……. Kwatsam!! yau suna zaune aka yi musu waya daga asibiti wai ‘Kausar ta haihu, ta haifi baby boy!’ Matarda Ba ma su san lokacin da ta fita dafa cikin gidan har ta tafi asibitin ba. Ummi da Yasmeen ne kawai suka je asibitin…sai da Ummi ta firgita a lokacin da ta d’auki Yaron! sakamokon tsananin kamannin da suke yi ita da Yaron, hatta Yasmeen sai da ta lura da hakan, dan haka kanta ya sake d’aurewa tamau game da al’amarin Kausar da haihuwarta… Basu dad’e da zuwa ba su Mommy suka k’araso, dan haka Su ummin suka yi mata sallama suka wuce gida kawai, hatta Yasmeen ma wadda Ummi ta yi tunanin zata d’an zauna da su mommuyn bata zauna ɗin ba, biyota kawai taga ta yi. Su kansu su Mommy sun yi mamakin tsananin kamannin Yaron da Ummi, amma kawai sai suka bari akan watak’il saboda tana yawan kallon ummin kullum ne, shiyasa. Mommy har da cewa”akwai wani d’an makwaftan su itama da ya tab’a yin kamanninta lokacin suna yawan shiga gidan!!”. Daganan kuma suka hau murna, sannan aka fara zab’e zab’en suna aka zab’i ‘Alan’, ba kad’an ba sun ji matuk’ar dad’i da Yaron ya kasance Namiji dama tuntuni mommy take cewa ta yi scanning ita kuma tace bazata yi ba, gara kawai ta Haifa a gani. Kausar ba ta b’oye musu abunda ta k’ullawa Manubiya ranar suna ba! Su dai su Yasira basu ce komai ba, dan zuwa yanzu komai ya fita a kansu! Mommy ce ta bada goyon baya, dama tana neman ta inda zata rage bak’in cikin Manubiya kafin a samu asirin ya kamata ta tafi forever… Idan kuma ma ta mutu kafin ranar sunan to falillahilHamdu!!! Daganan kuma suka shiga tattauna akan kud’in da zasu had’a bayan suna a samu Mommy ta ga likitan ido,dan suma zuwa yanzu al’amarin idon nata ya na tsorata su. … Bayan kwana d’aya aka kaiwa su Hajiya mama Yaron har gida ,Yash kuwa Ana ce masa za a kawo Yaron ya gani ya fita ya bar musu gidan sai dare tukunna ya dawo. Wanda hakan ya kusa haukata Kausar a lokacin da mai aikin nata ta dawo mata da Yaron take bata labari, dan ita a tunaninta Yaron ne zai sanya ta samu kusanci da Yashjub daganan kuma ta sameshi yadda take so………. Itadai Yasmeen har gobe gaba d’aya mamakin lamarin haihuwar Kausar take yi, ta lura kowa ma hakan take a wajenaa, amma kawai ba a son yin maganar ne…kwata kwata jikin Kausar bai nuna alamun jego ba, kuma duk girman Yaron ance bata samu tear ba, sannan har zuwa ranar suna ruwan nono bai zowa Kausar ba hakanan ake ta d’urawa Yaron madara. Gagarumin suna aka had’a na gani na fad’a suka gaiyyaci Mannubiya…ita Manubiya da farko cewa ma ta yi bazata je ba, shima Yashjub yace “ta huta kawai” Saboda yau ɗin za su je gida, jibi arba’in d’in inna, amma sai su Anty Umma sukace “ta je kawai tunda sunan da yamma ne kuma ma har sun gama shirye shiryen sadakar da za a yi jibi… saboda idan bata je ba kowa mummunar fassaara zai yi mata, tunda har sun gaiyyace ta to ta je kawai.” Dan haka ta tashi ta fara shiri…. Bata jima da fara shirin ba Yash ya yi mata waya ya ce ya taho dan haka ta ƙara sauri…. tana cikin shiri kiran Abbakar ya shigo wayarta a karo na ba adadi…..tun d’azu basu zauna ba, shiyasa bata samu ta saka wayar tata a charji ba, dan haka yana kira wayar ta katse ta mutu gaba d’aya! Tabbas ta san zai ga kamar kashewa ta yi, kuma Abbakar bai chanchanci wulak’anci daga gareta ba, ko ba komai yadda ya dinga d’awainiya da Inna da Baba bai kamata ace ita ta banzatar da al’amarin tasa mahaifiyar ba..har harbinsa aka yi a ranar da akayi case d’in black snake duk saboda ita da ahalinta…..tana cikin wannan tunanin Muhsin ya shigo cikin d’akin kamar ba zata yi komai ba sai kuma kawai ta karb’a wayar hannunsa mai tochila ta saka sim d’inta a ciki ta kira asalin layin Abbakar…. ga mamakinta bayan ya amsa sai ji ta yi ya ce mata “dan Allah ta fito, dama ya zo ganinta ne, yana neman alfarma a wajenta.” So ta yi tace ya shigo, amma ta san su Aisha ma sai sun yi mata magana muddin suka gansu tare shiyasa kawai ta fita tanata jero istighfari….A nan wajen ta samesa zaune a kan machine d’insa, yana hangota ya mik’e ya nufota wanda hakan ya sanya jikinta sake d’aukar karkarwa…. Gaisawa kawai suka yi daga haka ta fito masa k’iri k’iri tace “dan Allah ya daina yawan kiranta, Mijinta baya son mu’amalarsu, ya yi hak’uri kar ya janyo mata matsala….” Sosai ya nuna mata ya fahimta yace “ta yi hak’uri dama godiyar kud’in da ta tura masa ya zo yi mata, sannan ta k’ara hak’uri da shi amma kud’in basu kai ba..aiki za a yi wa Mahaifiyar tasa a zuciya, yanzu haka dai cikin kud’ad’en da yake ta tarawa saura dubu d’ari biyu…..” A take ta sake tura masa kud’in ya cika, tace “ya yi hak’uri ta san yayi mata halaccin da bazata iya k’irgawa ba, amma dole ta yanke alak’arsu har abada, ta yi saving aurenta, idan yana buk’atar wani abun ya gayawa Muhsin shi kuma zai gaya mata” Hakanan suka rabu yanata jera mata godiya, zuciyarsa k’all dan chan ya hango Yashjub ya danno kan motarsa tun d’azu amma da ya gansu sai ya tsaya ya ja ya yi parking, ita kuma Manu sam ba ta lura da shi ba. Tunda ta fito yake ta addu’a Yashjub ya zo dan Kausar tace masa mai gadin yace “tun d’azu ya fito……” Tun a jiya ya tura masa mesaage ta inda yake cewa “a tunaninka sharri na yiwa matarka ko?to yanzu haka halinda ake ciki kud’i take bani nake tarawa zan siya mana gida,mu ja jari kafin ta rabu da kai. Manubiya ni take so ba Kai ba za ta iya yin komai saboda ni….idan Baka yarda da maganata ba ka duba alert a wayarta.” Shiyasa tunda Manu ta fito yake ta addu’ar Yash d’in ya zo saboda ya samu ya sake k’ulleta idan Yash d’in ya gansu tare. A b’angaren Yash kuwa kwata kwata bai yarda da maganar Abbakar ba! Haba mana!! Abu kamar na wasan Yara, amma fa da ya gansu tare ya kusan suma a cikin motar dan ko last week sai da yace mata ba dai ta kula Abbakar ba ya fakewa da zuwa musu gaisuwa ko? ita kuma tace masa “eh” Sai gashi yau ya gansu tare a tsaye a waje ba ma a cikin gida ba, kamar wasu masu zance!!! Su Siyama sun tafi Umrah, Jidda kuma bata da lafiya, shi kuma Muhsin da shi ake aikin kimtsa gida ga aike, shiyasa ba ta samu me rakata ba…Bata dad’e da komawa cikin gidan ba Yash ya kirata yace”ta fito ya zo!” Peach colour lace ne a jikinta da white vail takalmi da y’an kunne da agogo…Bata yi kwalliyar komai ba, amma sosai ta yi kyau, shiyasa da ta fito ya tuna a haka fa ta ga Abbakar ya ji zuciyarsa kamar zata fashe…. Tana fitowa ta bud’e motar ta shiga suka gaisa sama-sama ya kunna motar ya ja suka yi gaba fuskar nan a tamke kamar bai tab’a yin dariya ba, wanda hakan ya d’aure mata kai matuk’a! Dan ya kan yi shiru ya yi ta tunani amma bai cika had’e rai kamar hakan ba.. Duk da alhinin rasuwa da take a ciki haka nan ta daure ta dinga yi masa magana..wanda daga um sai um um kawai ya dinga binta da shi….. A haka har suka k’arasa wajen.. iPhone d’inta ta zaro ta jona a jikin motar tasa dan ta ga bashi da niyyar shiga, ita kuma ta d’auki purse d’inta ta fara k’ok’arin fita bayan tace masa ta gode, Kamar daga sama ta ji yace “muga wayarki!” A hankali tace “gata nan tana charji, wanna kuma ta Muhsin ce na saka layina a ciki” Ta yi maganar tana mik’a masa wayar” Karb’a ya yi kanshi tsaye ya shiga message ya duba. Yadda ya mik’o Mata wayar sai da ta tsorata tana karb’a yace mata”jeki!!” da d’an k’arfi! A ransa yana ji inama bai duba ba…shiyasa fa tun d’azu yake ta tausar kansa amma zuciya ta tunzurashi sai da ya duba!!! Ya san maganar Abbakar k’arya ne da ya ce tana basa zai siya musu gida, to amma kuma meyasa ta tura masa kud’i ba tare da ta tambayesa ba, sannan meyasa ta fita waje wajensa…… iPhone d’inta da ta kawo haske ya shiga ya duba nan ma yaga ta tura masa.. ‘Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! me yasa manubiya zata yi masa haka??” Ba shi da mai basa amsa, a take kawai ya ji hawaye sun b’alle masa, dama ga masifar dayake a ciki tun kwanaki talatin da bakwai baya yanzu kuma ga kishin da yake shirin tarwatsa masa zuciya da kwakwalwa. shiyasa kawai ya kafa kansa a kan sitiyarin motar ya fashe da wani irin kuka. Ya jima yana kuka kafin ya shiga jero istighfari, yq ɗago ya goge fuskarsa yana maida numfashi, dai-dai nan ya ji ana knocking masa gilashin motar tasa…. Ba k’aramin mamakin ganin Aslam M T ya yi ba (Abokinsa da suka yi karatu tare a Uk) Abunda bai sani ba kuwa wajen taff!! cike yake da Abokansa dan Kausar diary d’insa ta tsinta a d’akin Mommy dan haka ta turawa kusan kaff friends d’insa da invitation na ranar sunan!!! Yana fitowa Aslam ya yi murmushi yana kallonsa ya ce ”Yash, ya akayi ka yi aure?” D’an guntun murmushin da ya fi kuka ciwo Yashjub ya yi, kafin ya d’aura kwayar idanunsa a kan matar da ke gefen Aslam d’in yana rik’e da hannunta yace”kai ya akayi ka yi auren?!” Duk dariya suka yi har ita Hudan..dai-dai nan wasu friends d’insu su biyu suma suka k’araso wajen, d’ayan yana cewa “da ikon Allah Yash da Aslam sun rigani yin aure gaskiya ku nema mini mata” Dariya d’ayan ya yi kafin yace”ai Yash matansa har biyu amaryar ce ma ta haihu!!” Ai kuwa nan suka tusa shi a gaba da shaƙiyanci har Aslam wanda duk suka yi mamakin magana da walwalar sa dan hakan sam ba d’abiarsa bace ba kowa ya shaida…sun d’an jima a wajen suna ta tsokanar Yash, kafin suka yi masa murna suka nufi cikin hall d’in gaba d’ayansu.. Shi dai Yash bai so shiga ba sam, amma haka nan suka tilasta masa, gashi ba zai yiu ya yi musu bayani ba, ga tashin hankalin da yake a ciki ! shiyasa ya ji kamar ya d’aga Hannu ya d’aura a ka ya yi ta kurma uban ihu…. Sai da ya shiga cikin ma tukunna ya had’u da ragowar friends d’insa, hakanan aka had’u aka yi ta murna kowa yana cewa Yash ya kyauta da ya had’a musu wannan reunion d’in dan sun dad’e basu had’u ba. … Hannu bibbiyu su Mommy suka amshi Manubiya kamar za su goyata, daga su har Kausar d’in…ita dai Yassira binsu take yi da ido amma wallahi tsaf sai ta tona musu asiri saboda ta gaji gashi zargin Mommyn ma ita takeyi da rufe musu Baki dan kwata kwata ta gagara yin maganar Ya’isha a kowa. Bayan sun shiga ne Yash ya nuna musu Manu, wadda ke zaune a chan gefe yace musu “ga wife d’insa chan!” Huda dama she’s uncomfortable a tsakaninsu shiyasa ta cewa Aslam ‘bari ta je wajenta….’ Mommy d’ayan Abokin nasa ya hango, dan haka suka je suka gaida ita suka dawo suka ci gaba da tsokanar Yash wanda shi ya k’i yarda ko kallonta ma ya yi….hakanan itama Kausar ya k’i amincewa su je wajenta ko jaririn ma ya k’i basu fuskar su d’auka saboda shi har yau bai ko kalli fuskar Yaron ba, hud’uba ma Junior ne ya yi masa…su Daddy kuma basuce komai ba, har yanzu! wanda hakan ya sake fusata Kausar, ta san duk dan Manubiya ne hakan take faruwa da ita, shiyasa da ta tuna a yau zata kawo k’arshenta sai kawai ta basar ta d’an ji sanyi a cikin ranta. Manubiya tana zaune Huda ta zo ta zaune a kusa da ita, suka gaisa tace mata”sunanta Huda Matar Abokin Mijinta Aslam” Itama Manu ta ce mata sunanta Manubiya, daga nan suka sake gaisawa suka zauna tare suna kallon masu rawar k’oroson da aka d’auko suke ta chasewa… Ita dai Huda har ga Allah kwata kwata Kausar ba ta yi mata ba..ta wani zauna a kan kujerar alfarmar ta had’e rai kana ganinta ka san bata da mutunci, gashi ita da Manubiyan sam babu had’i! shiyasa take ta tunanin dalilin da yasanya Yash ya auri Kausar bayan Allah ya basa Manu a matsayin mata…… Suna zaune aka kira Hudan a waya, akwai kid’a sosai ta san ba za ta ji ba, shiyasa ta mik’e ta cewa Manubiya ‘bari ta amsa call ta dawo’ daga haka ta fita……ba ta yi mintuna uku da fitan ba ta dawo, ta inda suka shigo kusan a tare ita da Kausar wadda ta shigo ita kuma ta k’ofar kusa da wajen zamanta…tun kafin Hudan ta fita ta ga Kausar d’in ta mik’e ta fita, kuma bata ga lokacin da ta fita da jaririn a Hannunta ba amma tabbas da ta ganta a waje tare da Yaron ta ganta! ita da wata maid a wani dogon lungu! inda ita kuma Hudan ta je ne domin ta amsa waya a lungun…bata ma iya yin wayar a wajen ba ta chanja guri, saboda duk wanda ya gansu tashi ɗaya zai fahimci basu da gaskiya! kuma ba sa so a gansu a wajen ba sa so a ga abunda su ke yi, sannan tabbas indai har ba gizo idanunta suka yi mata ba sannan abunda ta gani dai dai ne to kamar a buhu fa ta ga suna shirin saka Yaron! Noo it can’t be! Ba zai you ba! Dan babu uwar da zata saka jaririn d’anta a cikin buhu! Gaskiya babu ita! Amma kuma what are they up to?me su ke ƙullawa??” Hudan ta ƙarashe saƙe saƙen nata cikin yiwa kanta tambayar, kanta yana sake d’aurewa….. Ita kam Manu al’amarin Yash, damuwa, alhini da kuma halin da take a ciki ne suka sanyata a gaba! Ta ma kasa magana, ga kuma ciwon cikin period d’in da take yi, sannan gashi ta ji kamar har ta fara b’ata jikinta tsabar yadda pad d’in jikinta ya jik’e! Ba ta k’aunar chanjin pad a unguwa Idan ta fita, amma ya zame mata dole! Allah ya so ta dama ta taho da pad d’inta, dan haka a gaban idanun Huda ta bud’e jakarta ta d’auka bak’ar ledar mai zip da ta sako pad d’in a ciki, ta ɗauka ta mayar ta rufe tukunna ta bata tace “ta rik’e mata jakar dan Allah, bari ta je yanzu za ta dawo….” Ba ta dad’e da fita ba itama ta dawo…tana zama baba ya kirata suka yi magana, sai da ta kashe tukunna ta cewa Huda “jibi sadakar arba’in d’in Mahaifiyarta” Sosai Huda ta tausaya mata, nan ta yi mata gaisuwa tanata bata Baki… Kwatsam y’an sanda da sojoji tare da masu gadin event centre d’in suka danno kai cikin hall d’in gadan-gadan wanda hakan ya tada hankalin kowa matuk’a…gasu kuma rik’e da jaririn da ake sunansa wanda jama’ar wajen kaff basu ga lokacin da aka fita da shi ba a tunannin kowa Yaron yana chan a cikin gadonsa ne. Mik’ewa tsaye suma su Manu suka yi, ita da Huda, dan mutane sun fara hayaniya da guje-guje kowa ya nufi k’ofa… Da gudu Kausar ta je ta karb’e Jaririn daga Hannunsu ta fashe da wani irin kuka… babban sojan da aka zo da shi ne ya d’auki mike ya yi harbi sama yace kowa ya zauna, wanda hakan ne ya nutsar da mutanen wajen…maid d’in da suka kama da Yaron ya saka aka kawo masa gaban hall d’in itama..dalla dalla yayi musu bayani akan cewa”satar sark’a aka yi wa hajiyarsu (matar da suke gadin ta), to kuma suna shirin shigowa ne suka kama wannan maid d’in da jaririn zata fita da shi a buhu…tace musu sakata aka yi aka bata mak’udan kud’ade, dan haka kowa ya zauna za ta nuna wadda ta turota!!” Ko da wasa sam Manubiya ba ta yi tunanin ita maid ɗin zata nuna ba…a cikin zuciyarta tanata alhinin rashin imani irin na masu satar Yara…. Kawai tana k’ok’arin zama kwatsam tana d’agowa taga maid d’in ta yi pointing saitin ta!! A rikice ta juya ta kalli gefe da gefenta amma babu kowa ita d’ince dai….Bata Ida fita daga shock ba mutumin ya nufota gadan-gadan har da ankwarsa…… Aslam ne kad’ai ya rage zuwa wannan lokacin a cikin Abokan Yash bai tafi ba, dan ragowar k’uluwa suka yi da attitude d’in Yash d’in kawai suka yi masa sallama da barka suka wuce abunsu, saboda ya k’i dariya ya k’i basu baby su gani kuma ya k’i tsayawa a yi hoto, sannan gaba d’ayansa a rikice yake kana ganinsa…shiyasa kawai suka basa sarari ta hanyar tafiya…….. Da sauri Aslam ya nufi sojojin da Manu, dan ya lura Yash bashi da niyyar yin komai!!! Kawai ya tsaya ne ya k’ame…. Yana zuwa ya warce ankwar ya yar yacewa sojan ”Atleast ka yi bincike sosai mana, dan kawai ta fad’i abu shikenan sai mu hau kai mu yarda?ka san wacece wannan d’in da kake shirin arresting?” Da gudu Kausar ta yo kan Manubiya tana kuka wai zata daketa, da kyar aka rik’eta aka hanata tab’ata, su Mommy suka janyeta aka fita da ita tana cewa”Allah ya isan Yaronta da ta saka mata a cikin buhu, wallahi Allah sai ya yi musu hisabi, muguwa!! azzaluma, saboda ita bata haihu ba shine zata kashe mata nata!!!” Ita dai Manu uffan ba ta ce da su ba , dan tunda sojan nan ya nufota da ankwa har kawo yanzu kawai ta k’ame a wajen ta kasa motsi ta kasa cewa komai!! babu wanda ya fi bata mamaki kamar Yashjub wanda kawai ya tsaya ya kafe su da idanuwa ya gagara cewa komai!!! Shi kuwa Yash bak’in cikin Kausar ne ya ke jin kamar zai kashesa, bayan jama’ar da ta tattaro ta nunawa duniya d’an nasa ne shine hakan bai yi mata ba sai da ta had’a da wannan makircin!? Ga kuma Mommy wadda wata zuciyar take ingizasa da kawai ya had’ata da sojoji tunda gasu gatanan, watak’il ya san idan ya yi hakan zai ji sauk’in azabtuwar da zuciyarsa takeyi!!… Gashi shaid’an sai sake hasko masa moment d’in Manu da Abbakar na d’azu yake yi a kwakwalwa da Idanunsa. Tsabar bala’in da yake a ciki kasa ma motsi ya yi…ga dai Manu da Aslam yana kallo amma kwata kwata ya gaza tab’uka komai, ya kasa Isa garesu ko yatsarsa kasa d’agawa ya yi.. Sai da Aslam ya yi da mugun gaske, shima ya nuna musu k’arfin iko suka fahimci wayene shi ɗin! Tukunna suka hak’ura bazasu tafi da Manu ba! Dai-dai nan Hajuyar tasu (k’awar Kausar) tace”to a yi binciken sark’arta tunda an gama case d’in jariri….. Haka kurum da Manubiya ta juya ta hangi Jakarta chan a yashe wadda bata san ya aka yi ta fad’i ba, tashi d’aya sai ta ji jikinta ya bata nan ma an gama k’ulleta ne, aikuwa ana fara bincike na jakankuna da akazo kan tata aka duba tashi d’aya akaga dankwaleliyar sarkar k’awar Kausar a ciki ta asalin ɗanyen gold… Suna tamabaya batayi musu ba tace musu “jakarta ce” Aslam ya san sharri aka yiwa Yarinyar, amma kuma duba da yadda mai sark’ar take influencial ya sashi kawai yin shiru, dan ya san bata da mafita, amma inshaaAllah zai san abunyi….. Huda tana kuka kamar ranta zai fita itama Manu haka, hakanan suka kaita har office d’insu a motarsu, dan Aslam ya nemi alfarmar su bari su kaita da kansu su kuma sun yarda! Ba wai kukan sharri ko arresting d’inta da akayi manu take yi ba…tana kukan yadda aka wuce da ita ta gaban Yash amma bai ce komai ba, bai tab’uka komai ba…. … Babu yadda Aslam bai yi ba, amma duk inda ya zaga ya zagayo sai ya ga ba fa zai iya fitar da Manu ba, ga Hudan ta d’aga masa hankali sai kuka take yi, ko magana ma ta kasa yi duk ta gigice…… Shi kansa tausayin Manu d’in ya addabesa kunyar kallon ta ma yakeyi, shiyasa kawai yace mata “bari ya mayar da Hudan gida(dan zuwa lokacin dare ya yi sosai), kar ta d’aga hankalinta zai san abunyi….” Huda ta so ya barta tare da Manubiya har a san abunyi amma yace mata “A’a su tafi gidan” Hakanan ta bata kwarin guiwa, daga haka suka fita suka tafi suka barta ita kad’ai a wajen cikin masifa tsoro da tashin hankali, dan ma a office aka ajjiye ta ba a cell ba. Ana tafiya da Manu k’awar Kausar ta yi mata waya ta sanar da ita. A gate su Mommy suka ajjiye Kausar suka wuce…su kansu Mommy da Kausar d’in sun sha jinin jikinsu dan yadda su Yasira suka had’e rai suka k’i kulasu ya ishi ya sanya su fahimci ba su ji dad’in abun ba…. Tana shirin shiga ita da mai aikin ta da jaririnta kawai ta ji an fincikota ta yi baya kamar zata fad’i! sai kuma ya mayar da ita ya buga mata kanta da jikin gate d’in yana huci….suna had’a ido da shi ta kalli mai aikin nata tace”wuce mini ciki da Yaro” Sai da Yarinyar tagama shiga tukunna ta kallesa tace”Yassir!ban yi tsammanin ganinka a nan ba” Sake matsowa daff da ita ya yi tukunna yace”na ji labarin abunda kika aikata a Yarona saboda baki san ciwon sa ba ko? Wallahi wallahi Kausar ko da wasa kika sake yunk’urin cutar mini da ɗa ba zaki sake ganinsa ba! Mahaukaciya kawai!” Daga haka ya sake bugata da jikin gate d’in har sai da ta yi k’ara tukunna ya juya ya wuce, dan a mugun zuciye yake dama…har yau Daddy ya ma k’i ya sauraresa, duk ya bi Abokan Daddyn ya roƙesu akan “su yi masa magana, ya yi laifi ne, a shirya su dan Allah” amma dukda haka ko saurarensa Daddyn bai yi ba, gashi he’s broke!!! Gaba ɗayansa Bashi da kuɗi! Infact bashi da ko sisi!. Motarsa tana barin wajen Kausar ta yi tsaki,a ranta tace”na dai kusan ya da kwallan mangoro in huta da k’uda!” Saboda ta gama shawo kan su grenade ta basu miliyan huɗu cif cif! gobe inshaaAllah za su saki videos d’in Yassir a polisawa, sojoji, dss duk sai sun turawa kowa!!…. Yassira ce ta sanar da Yahanasu halin da ake ciki! Ita kuma Yaha ta sanarwa su Daddy, Ummi da su Ya Musbah… Abbakar da Ya Musbah ne suka fara zuwa dan a lokacin suna tare aka kira Ya Musbahn. Suna shiga suka ganta a zaune ita kad’ai ta yi shiruu ta zabga uban tagumi, waani irin tausayinta ne ya lullub’e Abbakar bai san lokacin da Hawaye ya zubo masa ba!! Tana d’agowa da ta gansu kawai sai ta fashe da wani irin kuka, ta tashi ta k’arasa ta fad’a jikin ya musbah tana kuka abun tausayi fad’i takeyi “na hak’ura da Ya Yash, na hak’ura da shi har abada… A gabansa aka tafi da ni, amma bai ce komai ba! Ina sonshi kamar Raina amma wallahi na hak’ura da shi, mak’iya ba za su tab’a barinmu tare ba!” Sosai Abbakar ya ji guilty conscious ya lullub’esa, dama shi tunda aka ce masa an kama Manubiya hankalinsa ya tashi dan hakan baya cikin tsarinsu…kwata kwata bai yi tunanin abun zai iya cutarda ita ba, amma kuma ta ya yi tunani mai zurfi a ransa, a take sai ya fahimci to ai duk abubuwan da ya ke ta yi ɗin cutar da itan ya ke yi a baɗini kawai dai wannan a zahirance ne an ga an yi arresting ɗina amma ragowar abubuwan da ya yiyyi mata tabbas nauyin cutarwarsu idan aka auna ya ma fi na kamata ɗin da aka yi a yau….. A ransa ya shiga cewa”Tabbas na biyewa sharrin zuciya, na cutarda wadda nakeso da sunan so… Tabbas Manu bata chanchanci hakan daga gareni ba, dan idan na ajjiye soyayya a gefe ko dan friendship d’inmu sam bai kamata in yi mata haka ba…. What was i even thinking? ta ya akayi na bari shaid’an ya rinjayi zuciya da kwakwalwata har haka??? Ta ya na kasa gane Manubiya ta Yash ce, ta ya na kasa gane ko da na aureta to fa zuciyarta ba tawa baceba! Ba zan tab’a samunta yadda nake so ba, sai dai na wahalar da kaina da ita na lalata mana rayuwa da farincikinmu gabad’aya…kallifa yanzu a halin da take a ciki amma cewa takeyi ‘tana son Yash kamar ranta!!!’ How can i be this selfish to the person who stood by me through thick and thin(ta yaya zan zamo mai son kai haka ga Matar da ta tsaya min a lokutan wahala da lokutan sauƙi na rayuwata..) my first sannan kuma last love?!” Bai yi auni ba kawai ya ji hawaye sun wanke masa fuska, da sauri ya juya ya fita zuciya fall danasani!……. …. Kusan duk a tare su Anty Umma, Baba, Daddy, Yaahanasu suka isa wajen har da Duputy Governor saurayin Yahanasu wanda tana gaya masa ya taho…ai kuwa yana saka Baki a al’amarin aka saki Manu tare da bata hak’uri….. Sai a lokacin ne kuma Yash suka ƙaraso suma, shi da Aslam wanda ya je ya ɗadd’akosa a event centre d’in bayan ya ajjiye Hudan a gida. (dan kowa ya watse amma shi ya kasa tafiya,yana inda suka barshi) A hanya Aslam ya gaggaya maasa abunda Hudan tace…ta inda ya sanar masa ‘duk sharri ne, gashi-gashi, Hudan duk ta gaya masa komai, ta tabbatar masa ‘ita Kausar ɗin ce ta saka d’an nata a buhu, ita maid d’in bakinsu d’aya da Kausar, sannan jakar Manu babu komai a cikinta da farko! Huda ta gani. saka mata sarkar aka yi daga baya lokacin da wajen ya hargitse….” Sannan ya ɗaura da cewa “Amma yanzu su fara zuwa wajen nata dai, idan abu yak’i ci yak’i cinyewa sai su je su d’auko Huda ta bada shedar sarƙar….” Suna zuwa suka tarar an sake ta, har suna ma shirin tafiya! Sai a lokacin Yashjub ya ji kamar ya rufe kansa da kansa da duka!!!. Da mugun kyar ya samu ya d’aga k’afafuwansa ya nufe ta, yana zuwa dai dai inda take ta juya ta kamo hannun Ya Musbah tace masa”take me home, dan Allah, pls…” Zai yi magana tace masa”plsss”hawaye suna masu bin k’uncinta Su Ya Musban za su yi mata musu, Daddy yacewa Ya Musbah ya tafi da ita…..dan shi kansa ya ji mugun mugun haushin abunda ya ji Manu tana gayawa Yahanasu Yash d’in ya yi mata…ko a wanne irin Hali kake a ciki ai bai kamata ka bari a tafi da matarka a gaban idanunka ba!. Duk watsewa suka yi, aka bar shi da Aslam a wajen…sai a lokacin Aslam ya dafa kafad’arsa yace”Allah ya kare gaba” daga haka shima ya juya ya wuce ya tafi, dan tabbas Yashjub yana buk’atar space!…ya san menene damuwa da k’unci, shiyasa tun ɗazu suna yin ido biyu da Yash ɗin kai tsaye ya fahimci ‘Yasjub yana cikin masifa..’ dan haka ya tafi yana mai yi masa addu’ar ‘Ubangiji ya yi masa maganin damuwarsa……’ Shi Yash bai ma lura da Abbakar ba, sai da aka gama watsewa tukunna ya hangesa a chan nesa zaune shi kaɗai ya yi shiruu ya yi tagumi..kafesa kawai Yashjub ya yi da idanuwa, kamar an ce ya ɗago shima Abbakar ɗin ya ɗago dan hakansuka yi ido biyu…suna had’a idanu Abbakar ya mik’e ya nufosa,a zuciye Yashjub shima ya nufi Abbakar d’in yana jin ‘tabbas yau kam ko shi ko Abbakar…..’ …..suna zuwa kusa da juna Abbakar ya yi sauri ya durk’usa a gaban Yash ya rik’e k’afafuwansa da hannu bibbiyu, kawai ya fashe da kuka… Da farko Yashjub ya d’auka wani sabon plan d’in Abbakar d’in ne yin hakan, shiyasa a zuciye ya fara k’ok’arin wafce k’afarsa amma sai ya ji Abbakar d’in yana kuka yana neman yafiyarsa sannan ya shiga zaiyyano masa dukkannin abunda suka yi shi da su Yasira da Kausar!.. Dan haka Yash ya fahimci nadama ce ta zowa Abbakar,wanda hakan ya sanya zuciyarsa ta d’anyi sanyi jikinsa ma haka….. Babu abunda Abbakar ya b’oye bai gayawa Yashjub ba, ya kuma nuna masa proof a wayarsa, sannan ya gayamsa yadda suka yi da Manu d’azu.. komai dai duk sai da ya fad’a masa, tun daga farko har zuwa k’arshe… Dare ya yi sosai amma hakanan Yash ya tisa k’eyar Abbakar suka nufi gidansu Manu……. Da farko cewa ta yi bazata saurari Yash ɗin ba, Allah ya so Baba ya ji lokacin dan haka ya fatattake ta zuwa parlourn Bak’i wajensu… Ta yi mamakin ganinsa tare da Abbakar, amma sai kawai ta zauna ta juya kai ba tare da ta kula ko wannen su ba…. Kamar yadda Abbakar ya yi masa bayani, hakanan ya maimaita sak a gabanta, sannan ya tashi ya kaimata proof ɗin itama ya nuna mata a wayrsa. Abbakar yana kuka ya durk’usa a gaban Manubiya yace”dan Allah dan Annabi ta yafe masa!!!…….” Manubiya ba ta iya ko kallonsa ba, da kyar itama tana kuka sosai ta mik’a masa wayarsa tace”ya tashi ya fita , ba ta son ganinsa!” Dama ya yi tsammanin hakan daga gareta, amma ya ji dad’in nauyin da ya sauk’e a kansa, dan haka ya mik’e ya yi musu addu’ar ‘Allah ya barsu tare, ya kawar da idanun mak’iya daga kansu’ daga haka ya sa kai ya fice…. …..wasu lokutan a rayuwa dole mu aminta sannan mu rungumi cewa ‘ba fa komai ne abunda muke so zai zamo mallakinmu ba!….asalima wasu lokutan abun kwata-kwata ba alkhairi bane a rayuwarmu! Sannan idan muka tilasta muka nace akan sai mun samu abunnan to fa in banda koma baya da dak’ile kai babu abunda muke yi wa rayuwartamu!!!… Tabbas inda ace ya raba Manu da Yash to da ya tarwatsa rayuwar mutane uku! da shi! da ita! da Yash! Tarwatsawa ta har gaban abada, kuma ba zai tab’a samun farin cikin da yake nema ba. Dan haka Ya godewa Ubangiji da ya wayar masa da Kai ya nuna masa gaskiya..ya san yana son Manubiya fiye da tsammani, amma zai yi k’ok’ari ya manta da ita ya yi moving on a rayuwarsa, ya nemi farin ciki ya daina mayar da kansa baya yana b’atawa kansa lokaci…. Da wannan lissafin ya fice daga cikin gidan yana sharar kwallah, zuciyarsa fal da na sani. Abbakar yana fita Yash ya mik’e ya k’arasa inda Manubiya take nan a zaune tana kuka….a hankali ya sa hannu ya dafa ta wanda hakan ya sanya ta juyo da sauri ta fad’a jikinsa ta fashe da wani sabon kukan da ya fi nafarko...cikin kukan tace”yanzu ta tabbata ba zan haihu ba kenan??” Da sauri ya sa *MANNUBIYA* *Book 2* *page 44* Abbakar yana fita Yash ya mik’e ya k’arasa inda Manubiya take nan a zaune tana kuka….a hankali ya sa hannu ya dafa ta wanda hakan ya sanya ta juyo da sauri ta fad’a jikinsa ta fashe da wani sabon kukan da ya fi nafarko...cikin kukan tace”yanzu ta tabbata ba zan haihu ba kenan??” Da sauri ya sa Hannu ya toshe mata Baki tukunna ya ce ”fad’arsu ba fad’ar Allah baceba! Sannan abunda suka yi miki bai isa ya hanaki haihuwa ba sai dai izinin Ubangiji..ki kwantar da hankalinki Baby ki tuna na sha gaya miki ba zan taɓa bari ki yi kuka ba dan sam bai kamata in bari ki yi kuka ba Munnubiya, sannan na daɗe da yi wa kaina alƙawarin in dai har kinada ni to zan gwada ƙarshen abunda zan iya yi in share miki dukkan hawayenki sannan in baki dukkan farin ciki….shiyasa tun a wanchan lokacin na fara shirye-shirye… Akwai Doctor d’in da za ki gani a Berlin daga yanzu zuwa ko wanne lokaci, dan zai bamu Appointment very soon, na sani…ki daina kuka Manu na san Ubangiji zai bamu haihuwa InshaaAllah Allah ba zai barmu haka ba..na dad’e da yin believing akan zaki haifa mini Yara inshaaAllah zamu zama parents muma...” Ya ƙarashe maganar a hankali cikin sake janyota Jikinsa ya rungume tukunna ya ci gaba da kwantar mata da hankali, sosai. Har sai da ya ga ta daina kuka hankalinta ya d’an kwanta tukunna ya kyaleta. Cikin sharar hawaye ta d’ago ta kallesa tace”inaso insan abunda yake damunka tun kwanakin baya..kar ka b’oye mini dan na san kana da damuwa bayan wannan!!” Shiruu ya yi, ya d’an k’ura mata ido kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yace”Ya’isha ta rasu! Rana d’aya suka rasu ita da Inna..ban san wanne tudu wanne gangare ba amma Mommy ce sila. A jeji ma ta je zata binne ta ko sutura ba ta yi mata ba…. kuma har yau bata gayawa kowa ba… Tun a ranar nake k’ok’ari nake so in d’auko y’an sanda a tafi da Mommy amma na gagara kulle mahaifiyata da Hannuna..kuma shirun nan da na yi ni kaina na san ban kyautawa Ya’isha da kaina da kowa ba ma!!!….” Kukan da ya ci k’arfinsa ne yasanya shi yin shiruuu…kafin chan yace”Mannubiya na tsorata da lamarin Mommy, na firgita sosai, Mommy ta firgita ni, al’amarin ya gigitani da yawa….” Yadda yake kuka yana magana ne ya sanya ta rungumesa da sauri, wanda hakan ya sa ya yi shiru da maganakawai ya ci gaba da kuka, kamar yadda itama take kuka kamar ranta zai fita….. Sun fi awa d’aya a parlourn, kafin ta je ta samu Baba, Allah ya so ta bai yi bacci ba, nan tace masa”za su tafi!” Dare ya yi sosai sosai, amma bai Hana ba dan ya ji dad’in shiryawar da suka yi, dan tunda har tazo ta ce zata tafi to ya san komai normal kenan, dama shi bayaso ta yi yaji ta zo ta kwana masa a gida….hakanan ya je suka yi sallama da Yash ya sanya musu albarka..suka wuce gida tare…..: Washegari da sassafe su Manu suka hau shiri, dan za su fita su fara shirye-shiryen tafiyar da ta taso musu bagatatan saboda jiya cikin dare suka yi receiving letter daga babban likitan da zata gani a Berlin..zai gansu in the next ten days. Tun a masallaci Yash ya sanar da Daddy cewa ”Ya dawo da Manu tun jiya, yau kuma suna so za fita da sassafe dan za su fara shirye shiryen tafiya, Manu zataje ta ga Doctor”… suna gama shiri, sun fito kenan, Yashjub yana reverse kawai suka ga Munirat ta kutso kai cikin gidan, sanye da baban Hijabi! Ta yi k’iba sosai, fuskarta ta kukkumbura dan da kyar ma Yash ya iya ganeta Manu ce dai tana ganinta ta ganeta. Fita duk su biyun suka yi daga cikin motar, suka tsaya suna kallonta har ta k’araso garesu……. Jiya su Junior basu koma gidansu ba, direct daga wajen Manu gidan Daddy suka wuto kawai suka kwana a nan!. Suna zaune da shi da Daddy, Yasmeen, Yahanasu da Ummi suna breakfast Yash da Manu suka shigo…. Murmushi Daddy ya yi, haka itama Ummi da suka gansu… Suna shirin yin magana Yash ya k’araso cikin parlourn ya ware murya ya shiga kwala kiran “Kausar!!!” Da mugun k’arfi. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *Book 2* *final episode* Idanunta biyu a lokacin, Yaron ya dameta da kukan yunwa! Dan rabonsa da abinci tun jiya kafin ta tafi wajen makeup. Kamar ba zata je ba, sai kuma ta mik’e ta nufi k’asan.. Duk mik’ewa su Ummi suka yi, suna masu buk’atar k’arin bayani…tashi d’aya Ummi ta tafi Luu zata fad’i sakamokon ganin Munirat da ta yi ta shigo tana hawaye, da sauri Daddy ya yi saurin rik’eta shima ya mayar da hankalinsa ga Munirat ɗin cikin kid’ima ya ce ”Munirat!!” Duk sai a lokacin su Yasmeen suka lura da ita, Kausar kuma ta yi turuss ta ja ta tsaya ta gagara k’arasowa nan k’asan, idanunta kyam!! a kan Munirat…. A zuciye Yash ya k’arasa ya fincikota ya wurgota tsakiyar parlourn, wanda sai da ta kai k’asa ta zube tsabar yadda ya yi cilli da ita….cikin tsana da kyama ya k’arasa ya tsaya a gabanta ya ce mata “ina d’anta????” Gaba d’aya kowa kansu ya yi, dan babu wanda ya fahimci inda Yash d’in ya dosa…. Ganin an zagaye su asirinta yana shirin tonuwa ne ya sanyata ta mik’e cikin in ina tace”Ya Yash, D’an wa kuma??? ban gane ba..” Mahaukacin Marin da ya zuba mata sai da ya yi sanadiyyar fashewar hancinta da bakinta! cikin tsawa ya ce ”Kausar ina d’anta!????” Dafashi Daddy ya yi, jikinsa yana karkarwa ya ce ”Yash, me kake magana akai haka ne, mai ya faru??” Dai-dai nan Hajiya mama da Yadira waenda suka ji ife ifensa suma suka sauk’o k’asan…… Jikinsa yana wani irin karkarawa yace”Daddy ka barta ta bani amsa, sannan ta yi bayani da Bakinta!!” Sai kuma ya kalli Kausar a karo na uku ya daka mata tsawa yace “Kausar ina d’an Munirat???” Luuu haka Ummi ta tafi ta zube a wajen!!! Saboda dama ita tunda Munirat d’in ta shigo da ta kalleta ta fahimci kamar haihuwa ta yi, kuma sai da Yash d’in ya fara waennan maganganun tukunna kwakwalwarta ta shiga tariyo mata alamomi da dama data gani a tartare da Munirat d’in kafin ta gudu…… Salati duk y’an parlourn suka d’auka dan suma sun fara d’aukar haske, yayinda Kausar ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen tace “wallahi ni bansan mai kake magana a kai ba…..” Zuwa yanzu Yahanasu da Manu da Munirat sun samu Ummi ta farfad’o, dan haka Munirat ta mik’e ta k’arasa inda take ta tsaya tace “Kausar baki fahimci abunda yake nufi ba? har kin manta yadda kikayi ta kuka kina rok’ata in rufa miki asiri kenan???” Kallon kallon aka fara yi kafin Daddy ya shiga gaban kausar ya tsaya a gaban Munirat yace”ki yi mana bayani dalla dalla!” …. Hawayenta ta share kafin ta fara magana “Daddy ku yafe mini, na biyewa sharrin zuciya da son da nake yi wa Yassir na jefe kaina halakar da nakasa fuskantarku da tabon, wanda hakan ya sanya sai da na gudu na bar gidan nan dan ba zan iya facing kowa ba!! Yassir ya yaudareni da kalmar so, ni kuma na biye masa saboda rashim wayo da biyewa son zuciya…haka muka taru da ni da shi muka dinga tafka b’arna har ta kaini ga samun ciki, kuma Likita ya tabbatar mini muddin na yi yink’urin zubarwa to kodai in mutu ko kuma in rasa mahaifata…shiyasa na dawo na samu Yassir dan a lokacin ma har mun rabu…sai da na dinga kuka a gabansa Ina magiya jinina ya hau na shiga masifa mai tayin yawa tukunna ya yarda zai taimakeni, hakanan ya kaini wani gida flat mai two bedroom ya zuba mini kayan abinci ya yi gaba, bayan yace ‘idan na haihu in kirasa sai mu kai Yaron gidan marayu…….’. Ban sake ganin Yassir ba, sai da cikina ya cika wata na biyar kwatsam suka zo mini da shi da Kausar, suka ce min ‘Kausar ta yi b’ari, suna buk’atar idan na haihu in bata Yaron a samu a rufawa juna asiri…’ Da farko ban yarda ba, dan ko da Yassir yace za a kai Yaron gidan marayu jinsa kawai nake yi amma na gama tsarawa Ina haihuwa zan bar garin da d’a na mace ko namiji, saboda Ina matuk’ar son abuna. Magiya kuka da kuma nuna mini alfanun yin hakan da yadda za mu taimaki juna da Kausar da Yassir suka yi ne ya sanya na chanja ra’ayina na amince akan ‘idan na haihu Kausar sai ta karb’a, ni kuma sai in dawo gida gareku ba tare da kowa ya san abunda ya faru da ni ba, in yi rayuwa ta kamar farko.’ Tunda na haihu na ji ba zan iya bata d’ana ba….da mugun kyar na amince bayan Yassir ya lallab’ani, amma a jiya da na ji yana waya ana sanar masa abunda Kausar d’in ta yi wa Yarona ya sanya na fahimci bayarda shi a Kausar is the worst thing (shine abu mafi muni) da zan taɓa yi a rayuwana… Shiyasa yanzu na dawo, kawai ku karb’i ɗana daga Hannunta ku bani abuna, inason ɗana wallahi, ba zan iya rabuwa da shi ba, ba zan iya bar mata shi ba. daganan ku yafe ni, ku yafe min, na san na yi muku laifin da ni kaina ba zan iya yafewa kaina ba.” Cikin kuka Kausar tace”Wallahi k’arya take yi” itama Munirat cikin kuka tace” Wallahi gaskiya nake fad’a….” sai kuma ta kalli Yash tace “and again…cikinta ba 12 days bane ba tun asalin farko k’arya ta yi muku suka had’a Baki da Junior akace naka ne, amma a lokacin da tace tanada ciki, cikin jikinta watanninsa biyu na ji komai kuma na ga komai a wayar Yassir!!!”. Damk’ar wuyanta Kausar ta yi, cikin ihu da kururuwa ta hau cewa “wallahi k’arya take yi mini, sharri ne, Munirat waye ya turo ki??” K’arasowa Junior ya yi da kyar ya kwace wuyan Munirat daga Hannun Kausar, kowa su yake kallo…kunya kamar k’asa ta tsage ya shiga hakanan ya kallesu ya ce ”da gaske Munirat take! cikin Kausar da na duba a wanchan lokacin ya ma haura 2 months, amma na ce muku bai wuce 12 days ba saboda……………” Tiryan tiryan ya zaiyyano musu komai da yadda Yassir ya yi tricking d’insa komai bai b’oyeba, kafin ya juya ga Yash ya Had’e hannuwansa biyu yana kuka Yash d’in ma yana hawaye yace”ka yafe mini dan Allah, kar ka rik’eni a rai, ka taimaka ka yafe mini…..” …… Tuburan!! Haka Kausar ta kafe ta dinga rantse rantse akan ‘k’arya Munirat da Junior suke yi…’ …. Scannning d’in da yayi aka nemo, Yasmeen ta duba, ta tabbatar sannan ya nuna musu messages d’in da Yassir ya dinga yi masa a wannan rana amma dukda hakan Kausar tana tsaye tana kuka tanata faman rantse rantse akann ‘Itafa k’arya aka yi mata…’ Yashjub bai san lokacin da ya k’arasa ya damk’i wuyanta ba! Kamar ya samu k’ato haka ya kaita bango ya dinga gwara kanta wanda hakan ya yi sanadiyyar da har jini ya fara fitowa ta kunnenta… Da mugun kyar su Daddy suka kwaceta daga Hannunsa, tana ganin haka ta fita da gudu….ta riga ta san asirinta ya tonu, kuma a halinda Yash yake tsaff zai iya kasheta, shiyasa kawai ta nufi gidan Mommy a hargitse, ta san idan ta je chan ɗin za su nemi mafita!!! Dan she ain’t giving up wallahi, bata shiryama haƙura ko saduda ba!. Hakanan ta nufi titi, kowa yana kallonta, dan daga ita sai riga da wando manya na barci, da hula. Ita kam sam bata damu ba..da kyar ta samu napep ta hau, ta yi masa kwatancen gidan Mommy suka wuce a haka, sanyi yana kad’ata kamar zai d’auke ranta. Tana fita Yash ya rushe da wani irin kuka ya juya ya rungume Daddy faɗi yake “AlhamdulillahC Alhamdulillah Alhamdulillah” babu k’ak’k’autawa….Allah kad’ai ya san adadi da kalar dad’i da farincikin da ya tsinci kansa da nutsuwar da ya samu a lokacin da akace d’an Kausar ba nasa bane ba, kuma yanzu ya sake tabbatarwa babu abunda ya shiga tsakaninsa da ita. Shima Daddy hawaye yake yi, a ransa cewa yake”Astaghfirullah Astaghfirullah how did I end up With a son like Yassir!!!…total shame….” Daddy da Hajiya Mama where very disappointed in Junior, amma kuma yanada nashi dalilin na yin hakan, kuma yanzu ya fito ya fad’i gaskiya shiyasa suka yi masa fad’a, sannan suka nuna masa illar k’arya a ko wanne hali!!! Yadira ma da yake tunanin zata yi wani abun, bata yi komai ba, ta dai ji zafin al’amarin kasancewarsa da wata sosai, dukda kuwa abun ba yanzu baneba amma ba komai..inshaaAllah,zata rungumi mijinta su zauna lafiya ta kula da shi yadda ya kamata. Sosai Junior ya sake luntsumawa kogin dana sani, dan da ace ya san haka zasu karb’i al’amarin to da bai zalinci Yashjub har hakan ba. Hakanan aka d’auko Yaro a sama yanata tsala Ihu aka bawa Munirat ɗin shi, sai a sannan Yash ya yarda ya kalli fuskarsa…. Har ta juya zata tafi, Ummi ta ruk’o ta, ta rungumeta, cikin kuka ta shigacewa “Munirat kar ki sake tafiya ki barni..kin yi laifi, amma nima inada nawa laifin…Dan kwata-kwata bai kamata ni da Ƴaruwarki mu yi dogon fushi da ke ba, wanda har ta kaiki ga rasa abokin shawara. sannan ni kaina munirat na san bana paying attention a kanki sosai yadda ya kamata, dan inda wata uwarce to da ya ci ace ta gane y’arta tana d’auke da ciki ne tun a karon farko!…Saɓanin ni, da na fi maida hankali akan al’amuran rayuwata sama da ke ƴata wadda kika kasance Mace! Kuma budurwa! Da kowa ya san tana buƙatar Mahaifiyarta a ko da yaushe, domin kuwa duk wata uwa kamata ya yi ace ta shiga jikin ƴaarta sun saba sosai ta hanyar zamtowa Ƴarttata a ƙawa! Abokiyar shawara! Malama! ƴaruwa! Sannan abokiyar sirri… amma ni kalli saboda tsabar sakacina ya ja mini har kika iya yarda da Yassir a kaina, dan inda ace na baki dama mun saba to da na san tabbas za ki nemi shawarata kuma idan na gaya miki to za ki ɗauki maganata sama da huɗubarsa… Ki yi hak’uri ki yafe mini Munirat, mu yafewa juna, mu taru mu gyara kuskurenmu…” Ummi ta ƙarashe faɗin hakan cikin sake fahshewa da kuka. Sai da su Daddy suka saka Baki, tukunna Munirat ta yarda akan ‘zata zauna ɗin’ sannan ta sake neman yafiyarsu… A nan parlourn gefe kad’an Ummi ta zaunar da ita ta ce ”ta bawa Yaron nono, dan ba a tab’a basa ba” Ai kuwa tana saka masa a Baki ya kama yana sha a haukace yana sauƙe ajiyar zuciya, duk sai da ya basu tausayi. Ummi da Daddy basu so samun shege a cikin zuriarsu ba, amma za su rungumi k’addara su karb’i Yaron hannu bibbiyu, inshaaAllah za su cinye wannan jarabawar…. … Suna nan tsattsaye ana koke-koke da neman yafiya, su Yasira suka shigo ita da Yusra. Da gudu Yusra ta tafi jikin Daddy ta fad’a, sannan ta fashe da kuka, hakama Yasira ta je ta rungumesa…. cikin kuka Yusra ta fara neman Yafiyarsa ta hanyar cewa ”ya yafe musu, sun yi kuskure amma yanzu sun gane gaskiya…basu san inda Ya’isha take ba…Mommy tace ta aiketa k’auye, saidai har yau ba ta dawo ba…ya taimakesu a nemota, tabbas sun san akwai abunda Mommy take b’oyewa…..” Sosai kan Yashjub ya fara juyawa…Da kyar ya yi gyaran murya, dan haka duk suka kallesa, tukunna tiryan tiryan ya shiga zaiyyano musu yadda ya ga Mommy ta fito daga gidanta, da yadda ya bi bayanta har zuwa inda ya ganta a gaban rami ta saka Ya’ishan…. Sannan ya d’aura da cewa “A gani na bai kamata a binneta a haka babu sutura ba, shiyasa bayan mommy ta tafi na ɗaukota, to kuma ina gama sakata a mota sai na ji labarin rasuwar Inna….” Manubiya ya kalla wadda take kuka kamar ranta zai fita yace “Ina zuwa gwaggo Suwaiba ta nemi ganina….tashi d’aya Ina shiga ta sanar da ni Inna fa ba mutuwa ta yi ba, amma ita kanta bata gama sanin mai ya faru da ita ba..saboda lokacin da suna yi mata wanka ta ga babbar yatsarta ta Hannun dama ta yi motai alamun akwai rai a tare da ita amma kuma ba ta numfashi, kuma Likita ma ya tabbatar da ta mutu…a wannan lokacin ta ce mini bata so ta ce bata rasu ba ta sakawa su Manubiya rai, kuma a zo daga baya aga ta rasu d’in, saboda ta tabbatar mini aikin asiri ne ba na asibiti ba, to komai zai iya faruwa a gaba ta yiu ta tashi ta you kuma ta wuce…shiyasa tace mini za ta wuce da Inna k’auyensu, a taru a yi mata addu’a dan suna da manya manyan hafizai a k’auyen masu tsoron Ubangiji da sani, daga nan sai a ga abunda Ubangiji zai yi, Idan bata tashi ba to za su binne ta a chan, idan kuma ta tashi za su dawo da ita da izinin Allah…. Zannuwa da cottons kawai da kara muka had’a aka saka a makara aka je aka binne dan bama so kowa ya san maganar……inajin batun Gwaggwo Suwaiba tashi d’aya na fahimci komai sharrin Mommy ne, wani abun suka yi shiyasa take ta nuk’u nuk’u da rasuwar Ya’isha musamman ma da na tuna yadda na ji Ya’isha ta je gidansu Manu a day before, shiyasa na had’a har da Ya’isha aka kaisu k’auyen su Inna a tare da zummar ayi musu addu’ar tare dan itama na yi tunanin watak’il asirin ne ya shafeta, sai dai kuma ita Ya’isha suna zuwa aka tabbatar ta rasu dan har ta fara kumbura ma shiysa na je aka yi mata sutura aka binneta a chan ɗin……..” Gaba d’aya parlourn kaurewa ya sake yi da koke koke…da kyar Manu ta k’araso gabansa ta tsaya jikinta yana karkarwa tace”inna fa?” Murmushi ya yi yace,kwana talatin ta yi ta warke, yanzu haka ma suna hanyar dawowa, tun jiya gwaggo Suwaiba tace mini sammako zasu yi yau inshaaAllah, yanzu haka da ma da shirin muna gama abunda muka fita yi sai mu wuce……” K’amewa Manubiya ta yi, ta kasa motsi, sai da su Yasira suka zo suna kuka suka rungumeta tukunna ta dawo cikin haiyyacinta… Share mata hawaye Yasira ta yi ta fara k’ok’arin durk’usawa a gabanta…da sauri Manu ta tarota ta shiga girgiza mata kai tace”na ji na san me kuka yi… Yasira tun Ina cikin mahaifiyata Allah ya k’addara hakan zata faru da ni ,idan na haihu Alhamdulillah idan ban haihu ba haka Allah ya tsara, kawai inaso ki san cewa kome kuka yi na yafe muku na rungumi k’addarata….let’s just start a fresh…..” Rungumeta suka yi gaba d’ayansu har Yasmeen da Yahanasu suna wani Irin kuka…. Dai dai nan Gwaggo da wata mai aikinsu suka fito, cikin sunkuyar da kai ta ƙaraso wajen tukunna tace”itama tanada magana!” Ashe ranar da Mommy ta yi magana ita da Yahansu a ɗakin Yahanasun, Gwaggo ta ji komai, har ta yi recording ma, dan haka tana ɗan ɗari-ɗari tace “tanata so ta kunnawa Daddy amma bata san ta Ina zata fara ba….” nan kuwa ta kunna musu, kowa ya ji muryar Mommy tarr tana bayani dalla dalla, kamar yadda ta yiwa Yahanasu a wachchar rana…… Hajiya Mama ita dai k’arshe k’afafuwanta kasa d’aukarta suka yi, dan haka ta nemi guri ta zauna a naan kan kujerar. Kowa kuka yake yi a parlour..suna gama jin recording d’in Gwaggo ta cewa Yashjub “a wachchar ranar ma tana gani kamar Kausar Abu ta zuba masa, dukda dai bata tabbatar ba amma ta lura da ita da yanayinta..” nan ta zaiyyane masa yadda suka yi da kausar ɗin a ranar….. Numfashi Yashjub ya fesar, ya share hawayensa, ya nemi guri ya zauna yana mai jinsa kamar wani sabuwar halitta….kasancewar sa ba d’an Mommy ba yana daga cikin abubuwa mafi dad’i da ya tab’a faruwa da shi a tarihin rayuwarsa, shiyasa wani sanyi nutsuwa annashuwa suka mamaye sa…… Da kyar ya iya bud’e Bakinsa ya cewa gwaggwo “yanzu kam babu batun Kausar, ta bar cikin rayuwarmu har abada….halinta ya bita.” Duk parlourn “Ameen” suka ce, kafin Daddy ya kalli Yaha yace mata “Maiyasa kika yi shiru, wannan gagarumin al’amari haka Yaha???” Sabon kuka ta fashe da shi, tana kukan ta k’arasa ta ruk’o Hannun Yashjub tace”I’m so sorry….” Dan ta fi jinsa ta san ta fi yi masa laifi akan Daddy tabbas!… Rinannun idanunsa ya d’ago, ya zuba mata,,kafin yace “Yaha ba zan b’oye miki ba! Sam ban ji dad’in yadda kika yi shiru game da wannan al’amarin mai matuk’ar mahimmanci a rayuwata da ke ba, har iyau kuma na fahimceki kuma na fahimci uzurinki, dan haka karki damu, komai ya wuce..” Su Yasira ya kalla waenda suka matso garesa suma, ya ce ”kuma abunda kuka yi mini ba komai, ba zan ce na manta da shi kamar bai faru ba, amma kar ku d’au hakan ku saka a ranku dan inshaaAllah ba zai zamo silar shiga tsakani na da ku ba..rashin walwala da shak’uwata da ku ya sanya Mommy ta samu damar shiga tsakanina daku, ta yi poisoning mind d’inku against me, har ta kai kuka yarda cewa bana sonku, wanda ni hakan nature d’ina ne kuma kasancewarku mata da kuma yanayin rawar kan Yassir ya sanya na ga dacewar in sake zama mai tsauri a kanku saboda kyautuwar tarbiyyarku, amma inshaaAllah daga yau zan gyara! na gane kuskurena..in sha Allahu zan jaku a jikina mu zamto abu d’aya! Abokan juna, ta yadda babu wanda zai sake iya shiga tsakaninmu…kasancewata step brother a gareku ba wai yana nufin zumuncinmu zai samu rauni ba sai dai ma ya k’ara k’arfi InshaaAllah…” Rungumesa gaba d’ayansu suka yi a lokaci guda har ba a iya hangoshi ma, cikin kuka suka shiga ce masa “kar ma ya sake cewa shi step brother d’insu ne, har abada za su zama d’aya, babu y’an ubanci a tsakaninsu inshaaAllah…..” Da kyar suka iya had’a ido da Yahanasu, suka nemi gafarar ta, they really can’t believe wai ‘Yaha cikinsu d’aya!’ kuma suka dinga yi mata wulak’anci, ta yi shiru, sannan itama Mommy ta sani amma ta yi shiru! duk dan cikar burinta, tabbas Allah ne kad’ai zai yiwa Mommy hisabin da ya fi dacewa da ita…. Hajiya Mama ma tun d’azu ta fara hawaye, fad’i take”Alhamdulillah Alhamdulillah” Ta godewa Ubangiji da ya bata Aron rai ta ga wannan rana…Alhamdulillah da ya fallasa rub’abb’en irin gidan Imam a gabn idanun kowa, matsalar gidansa ta zo k’arshe. Cikin sharar hawaye Yash yace”hak’ik’a yau tana daga cikin ranakun da suka kai k’ololuwar dad’i da farin ciki a cikin ranakun rayuwata…Hak’ik’a Ubangiji mai kun faya kun ne! Ya kan yaye damuwa ya chanja al’amari ya kawar da matsala mai girman gaske a cikin k’ank’ani lokaci… Mu dai kawai abunda ya kamata mu yi a ko da yaushe shine mu yi trusting d’insa mu saka gaba d’aya fate d’inmu akansa sannan mu mik’a dukkannin al’amuranmu garesa, daga nan komai zai yi falling into place cikin sauk’i…..in da Rabbana ba wahala…. Alhinina d’aya a halin yanzu ‘rasuwar Ya’isha, da mahifiyata wadda bama ta san tanada ni ba…..” Ya fad’i haka cikin zubar hawaye.. Cikin sharar hawaye shima Daddy yace”Tabbas Khadija ta dad’e tana zaluntata tun asalin farko…da ace Ubangiji zai bani dama to da na koma baya na janye abunda na yiwa Mahaifiyarka Yash…da na gaya mata cewa ‘na yarda da ita d’ari bisa d’ari kuma na san sharri ne akayi mata…dan ko ba a gaya min ba na yarda na san sharrin ne.” Inama ace Khadija (mahaifiyarka) bata rasu da bak’in cikina da takaicin na ƙi yarda da ita ba…inama ace tana raye da na sauk’e wannan nauyin, na nemi gafararta…..” Yahanasu ta san ta yiwa Mama alk’awari, amma kuma an riga an linke Daddy ta baibai! Ta yadda ba zai tab’a fahimtar Mama tanada rai ba muddin ba nuna masa ita akayi ba….dan haka ta goge hawayenta tace “tanaso kowa ya biyota, tanada surprise d’in da takeso zata nuna musu, kar wanda ya tambayeta menene, kawai kowa ya biyota…” Daga haka ta shiga d’aki ta kwaso key sannan ta Kira Mama tace mata”tana Ina?” Maman tace”Tana gidansu Manu, tun jiya Gwaggo Suwaiba ta kirata tace su had’u a gidan da sassafe gasunan yanzu haka ita da su Ammi suna shiga gidan….” Yahanasu tana fitowa suka taru suka tsara akan ‘za a d’auko y’an sanda, su tafi da Mommy, su mik’ata kotu a yanke mata hukunci…’ Daga nan suka nufi gidansu Manubiya akan sai sun gama da nan d’in, tukunna za su je a tafi da Mommy, dan bayan Inna dake hanya Yaha tace musu nata surprise d’inma yana gidansu Manu. ••• Kausar bata tarar da su Yasira a gidan Mommy ba, dan ko da ta yi knocking ma Mommyn ce ta zo ta bud’e mata da kanta, wanda ganin Kausar ɗin a yadda ta je mata ya yi matuk’ar d’aga mata hankali dan haka ko shiga bata bari sun yi ba tana gama rufe gate ta shiga tambayar ta “mai ya faru?!.” Sosai Kausar ta zama emotional, dan haka ta fashe da kuka cikin kukan ta shiga zaiyyane mata abunda ya faru… Har wani irin huci kuwa Mommy take yi tsabar b’acin rai!!! Enough is enough fa!! wallahi zata yi fito na fito da mutanen nan inyaso komai ta fanjama fanjam!!! Ba ta kai ga bud’e bakinta ta yi magana ba suka ji knocking… Ko da Mommy ta lek’a da kyar ta iya gane Yassir!! dan sanye yake da kayan sanyi ga hula ta rufe masa kai, goshi da kunnuwa sannan ya sanya bak’in gilas… da sauri ta sa Hannu ta bud’e masa ya shigo…. Wani Irin sanyi Yassir ya ji a ransa sakamokon idanu biyu da ya yi da Kausar…saboda dama zuwa ya yi akan ya d’auki Yusra su je ta je ta fito masa da Kausar ɗin saboda shi an hana masu gadi barinsa ya shiga gidan sannan yana ta kiran wayarta ba ta d’auka. Mommy tana shirin yin magana ya sa Hannu ya rik’o hannun Kausar yace mata “Mommy d’an bamu mintina goma za mu je mu dawo” “To” kawai ta ce masa, ta bisa da kallo tana jin wani irin yanayi…. Har ya juya zai fita, sai kuma kawai ya dawo ya sa Hannu ya rungume Mommyn sosai a jikinsa tukunna ya cikata, ya ja Kausar suka fice suka bar Mommy a nan tsaye kamar gunki. Sosai k’irjin Kausar yake dukan uku uku, dan a yadda ta shirya komai ta tsara komai bai kamata ace ta ga Yassir free har yanzu ba!!! A ranta tace “Ko dai ya fahimci abunda na yi ne?” dan kayan sanyi ne a jikinsa ga bak’in glass amma she can tell’ransa a masifar b’ace yake’!. Sai da ya zaunar da ita a seat ɗin gaba na motar, tukunna ya zagaya ya shiga ya zauna ya kunna motar ya saka lock ya bata wuta!!!! .. Wani irin uban gudu yake tsulawa, wanda tun daga nan Kausar ta fara dana sanin biyosan da ta yi….gashi tace masa”Yassir” Daga fitowarsu zuwa yanzu ya fi sau talatin amma ko kallonta bai yi ba! Sai da ta ga sun d’auki hanyar barin Kano tukunna ta fashe da kuka, cikin kukan tace”Yassir baka da hankali ne?ina zaka kaini??” Ba tare da ya kalleta yace “Zuwa ga mutuwarki!!” Sosai ta firgita, gashi ta fara hango wani mahaukacin k’aton rami kuma shi ta ga Yassir ɗin ya durfafa, dan haka jikinta yana wani irin karkarwa ta sa Hannu ta zare key d’in, da sauri shi kuma ya taka burki kafin ta Ida cirewa…. Cikin kuka sosai tace”Baka da hankali ne?” Sai kuma ta juya ta fara k’ok’arin bud’e k’ofa domin ta samu ta fita amma inna sam sai ta gagara…. Komawa ya yi kawai ya kwanta a jikin seat d’in da yake a kai, har ta k’araci bige bigen ta…ganin bafa za ta iya escaping bane ya sanya ta juyo garesa ta fara yi masa magiya… Ahankali ya juya ya fuskanceta sannan ya Zuba mata ido ta cikin glass d’in, ya ɗan jima a hakan kafin ya furzar da huci yace “Kausar, su grenade sun tura mini duk wasu chat d’inki da su, saboda suna so in san who is behind it all….. kamar yadda kika so, an saki videos d’ina a wajen hukuma, yanzu haka nemana ake yi dead or alive(a mace ko a raye)… sannan satin nan da ya shige! A gidan Abokina, muka yi raping wata y’ar minista to death! wanda mu kanmu bamuyi tunanin fyaɗen zai kaita har ga mutuwa ba! Shiyasa da muka ga ta mutu sai muka b’oye gawar, muka saka ta a fridge… kwatsam! kuma yau da aka zo arresting d’ina sai aka ga gawar!!. Ba su samu sun kama ni ba! shi kuma Abokin nawa ba ya nan… Da kyar da mugun kyar na samu na iya guduwa, amma kuma sai da na gudu d’in tukunna na ga guduwar tawa ma ai ba ta da wani amfani tunda na san dole sai an nemo ni, kuma hukuncina kisa ne!!! Bani da mai bani shelter yanzu kam..saboda Abokina da yake bani hatta abinci da kayan sakawa da motar hawa shima ta kansa yake yi kuma laifukana sun fi k’arfinsa! bani da gatan da wani zai tsaya mini ko ya kare ni, ko kuma ya taimaka mini in gudu….” Kin yi betrayin d’ina Kausar kin ci amanata, kin tarwatsa mini trust, sannan kin tarwatsa duk wani hope ɗin da ya taallaƙa sannan ya ƙunshi burukana!!… Idan wani yace mini zaki bada kud’i sabida a kamani a kashe ni Wallahi Kausar tsaf zan kashe mutumin saboda abune wanda na yarda sannan na tabbatr ba za ki yi ba! amma kwararan shaidun da na gani su suka tabbatar mini da tabbas kin ci amanartawa kin yi betraying d’ina sannan a lokaci guda na fahimci kuma na gane cewa ‘ashe yaudarata kike yi kina using d’ina tun usuli, kuma ba nine zab’in ranki ba…..’ Amma dukda haka inaso ki san cewa da sanki na rayu kuma da son ki zan mutu kuma wallahi babu wanda zan barwa ke a doron k’asa…ni yanzu tawa ta riga ta k’are! da a kan a kamani a yi hanging d’ina ko a fille mini kai gara ni in kashe kaina da kaina!! amma Kausar kamar yadda na fad’a miki ‘ba zan barwa kowa ke ba! ke d’in tawa ce ni kad’ai! dan haka you are coming along with me, tare za mu mutu!!” Wani irin zabura Kausar ta yi, ta sake fashewa da kuka, sannan ta manne a jikin marfin motar ta shiga magiya da basa hak’uri bil hakk’i da gaskiya…… Fincikota kawai ya yi, ya fara k’ok’arin k’arb’ar key d’in daga Hannunta, amma sai ta hana, dan haka ya sa k’arfi ya lankwasa hannun nata wanda hakan da ya yi ya janyo Hannun ya k’arya ya bada k’arar k’asss!!! Alokaci guda itama ta saki wata razananniyar k’ara!!!! Key d’in kawai ya d’auka, a fili yace mata”ke da zaki mutu ma Kausar menene na ihu dan hannunki ya karye???” Daga haka ya zura ya kunna ya bawa motar wuta ya nufi d’urmemen ramin da ke a gabansu da wani kalar mahaukacin gudu…. … Kausar kira take”Yassir!! Yassir!!!Yasssir!!!!!” Da masifar ƙarfi! Amma inaaa! sam bai saurareta ba, sai da suka kusan fad’awa cikin ramin tukunna ya juyo ya kalleta yace mata “I love you!” Daga haka ya take gudu da k’afarsa sosai! ya saki sitiyarin ya d’aga hannuwansu duka biyu sama yana kallonta yana murmushi ita kuma tana ihu tana kuka tun k’arfinta..a haka suka fad’a cikin ramin…. Sai da motar tasu ta yi galantoyi ta bubbugu sau wajen biyar tukunna ta Isa k’asa, tana fad’awa kuwa ta kama da wuta…….. ••••• in banda dukan uku uku babu abunda k’irjin kowannensu yake yi tsabar zullumi….da Ya Musbah suka fara had’uwa a bakin gate shi da Ya Nafi’u da Aisha waenda suma duk Gwaggo Suwaiba ce ta kirasu…Manubiya cikin zumud’i ta fara kokarin fita domin ta je ta sanar da su amma sai Yash yace mata ta tsaya tukunna surprises ne kar ta gayawa kowa…hakanan ta ja bakinta ya yi shiru tana jin farinciki kamar zai fasata…haka Suka nufi ciki gaba d’ayansu. Daddy a waje ya tsaya shi da Yashjub sai da Baba ya zo tukunna ya shigar da su parlourn bak’i, Yayinda su Ummi suka nufi ciki gaba d’ayansu….Hajiya mama ta na shiga sukayi ido biyu da Mama wanda hakan ya sanya duk su biyu suka k’ame a yadda suke kowacce ta kasa motsi. Kuka Mama ta saka a take ta durkushe a wajen tana jin wani kalar nauyin Hajiya Mama yana lullub’eta…k’arasawa inda take Yahanasu ta yi tana zuwa ta durk’usa itama, cikin kuka Mama tace”sai da kika yi abunda na hanaki ko?” Dai dai nan Daddy Yashjub da Baba suka shigo dan suna ce masa Yahanasu ce ta kawosu gashi gashi yace to su shiga cikin suga menene surprise d’in……. A hankali Yahanasu ta girgiza kai tace”kamar yadda na gaya miki basuyi tunanin kinada rai ba, kuma Daddy bashi da wani burin da ya wuce ya had’u dake a halin yanzu..d’azun nan ya gama fad’in haka a gabana a gaban kowa shiyasa na kawo su…..” Shi dai Daddy zuwa yanzu hatta tsokar datake a jikinsa karkarwa take yi…bai riga ya ga wadda Yahansu take magana da ita ba amma dukkan bayananta suna nuni ne da Khadijarsa ce…… Tashi d’aya numfashinsa ya d’auke jinsa ya d’auke a daidai lokacin da Hajiya Mama ta k’arasa ta mik’ar da ita tsaye tace”Khadija!!!” Sai kuma ta rungumeta ta sa kuka… Kallonsu Yashjub ya ke yi saboda saɓanin Yahansu shi tun yana Yaro da aka ce ta rasu bai sake sakata a idanunsa ba, shiyasa bai ganeta ba.. ammafa tashi ɗaya tunda ya ganta ya ji wata kalar k’auna da son matar suna shigar sa bana wasa ba…. Yana jin Hajiya Mama kuma tace”Khadija”, sai ya tabbatar tabbas ita d’ince, dan haka ya taka izuwa gareta idanunsa suna zubda hawaye! Yana zuwa wajen, Hajiya mama ta matsa, shi kuma ya tsaya a gaban Mama idanunsa suna fidda ruwan hawaye…duk yadda ya so ya yi magana sai ya ji ya kasa, dan haka kawai sai ya rungumeta ya fashe da wani irin kuka wanda hakan ya sanya gaba d’aya suma su Manubiya suka saka kuka….. cikin k’ok’arin zaro shi daga jikinta take ɗan tapping bayansa alamun rarrashi tana mamakin kalar so da tausayinsa da take ji suna shigarta a take a lokacin sannan kuma da suka yi ido biyu ita da shi sai taga Yash d’in kamanninsa d’aya da ita… Hajiya Mama ce ta share hawayenta tukunna ta ce ”ki rungumi d’anki Khadija! d’an da makircin Mace ya sanya ba ki san ke ce mahaifiyarsa ba” A rikice ta juya tana kallon Hajiya Mama! Wadda hakan ya sanya Hajiya maman Jinjina mata kai sannan tace”tabbas! kece mahaifiyar Yashjub ta asali… makirci! rashin tsoron Allah! da son zuciya ne suka sanya Larai da Khadija suka musanya miki shi da Yahanasu..amma yanzu komai ya zo k’arshe. ranakun kuka, bak’in ciki, k’umbiya-k’umbiya da munafurci duk sun k’are a zuri’ar Imam kura….” gaba d’aya parlourn a tare sukace “inshaaAllah” kowa yana sheshek’ar kuka banda Mama da Daddy waenda suka yi mutuwar tsaye tun d’azu… Ba kad’an ba Ammi ta shiga shock! Ba na wasa ba…. A kanta ta ke ta juya maganar tana mamaki, a ranta ta ce ‘yanzu Yash d’in Manu shine asalin d’an Mama?!Tabbas a duk yadda ka ga mutum kar ka taɓa rainasa…Bata ci zarafin mama ba sannan bata wulak’antata ba tun bayan da ta fahimci Maman ba ta da interest a kan Mijinta amma dukda haka a take sai ta ji wata kalar kunya da nauyinta sun yi mata k’awanya. Da kyar Hajiya Mama ta b’anb’are Yash daga jikin Mama, ta kamo hannunta, ta ja ta ta kaita gaban Daddy wanda ya yi mutuwar tsaye, sannan ta kamo hannunsa ta saka hannun Mama a ciki tukunna ta juya ta shige cikin parlourn da su Daddyn suka fito a ciki yanzun…Yashjub ne kawai ya tsaya tare da Mama da Daddy yayinda kowa ya bi bayan Hajiya Mama suka shige parlourn Baba Tabbas inda ace Mama tana gidan Daddy tuntuni to su kansu su Yasira sun san da tuni sun daɗe da fahimtar ita ce Mahaifiyar Yash, dan tabbas suna kama.. Daddy kuwa la shakka ya ga kamannin tun ba yau ba, amma kuma cikin hukuncin Ubangiji sai bai bawa hakan mahimmanci ba ballantana har ta kaisa ga yin magana ko ya zargi wani abun, daɗin daɗawa kuma shi har ga Allah bai taɓa tunanin cewa mommy zata iya musanya Ƴaƴan ba, ko da wasa da ikon Allah sam hakan bai taɓa zuwa kansa ba.. Shiyasa ko da ya ga kamannin sai ya bari akan wataƙila zaman da suka yi tare ta yawaita kallonta ne ya janyo hakan ko kuma dai wata mu’ujizar ta ubangiji ce ta sanya Yash ɗin yake kama da Khadija ko kuma ma idanunsa ne su ke nuna masa hakan, tunda ya ga Hajiya mama da Abhi sam basu taɓa yin maganar ba suma, dan haka sai ya yi zato ko shi kaɗai ya ke ganin fisgen kamannin Yash ɗin Da Khadijahnsa… … Su Hajiya Mama suna shiga cikin parlourn Baki’in dai dai nan kamar gwaggwo Suwaiba ta san suna nan itama ta shigo, Inna na biye a bayanta. Suna shigewa Daddy ya fashe da wani irin kuka, sai kuma ya durk’usa a gaban Mamaa yana kuka yama kasa yin magana… A hankali ta durk’usa itama, tana hawaye da kyar ta iya cewa”sharri aka yi mi….” Cikin tarar numfashi yace Baki da buƙatar ki yi mini bayanin komai saboda Wallahi na dad’e da gane gaskiya, na dad’e da fahimtar cewa sharri ne aka yi miki…ki yi hak’uri ki yafemini abunda na yi miki, wallahi kunyar kallon kwayar idanunki nake yi, ban kyauta miki ba, bai kamata ace na yarda da sharrin da aka k’ulla miki ba, ki yi hak’uri, ki yafe mini, ki manta da komai, ki yarda da ni a karo na biyu, inshaaAllah ba zakiyi dana sani ba….” Kuka duk su biyun sukeyi, Mama tana mamaki da al’ajabin Mommy, dan tunda Yahanasu ta ce mata itace silar komai shikenan gaba ɗaya ta tsorata da lamarin d’an Adam! matar da a ko da yaushe take yi mata kamar zata goyata ashe ba sonta take yi ba…… A hankali Yashjub ya k’arasa, ya had’e iyayen nasa su biyu waje guda ya rungumesu…tabbas inda ace a gida d’aya ya rayu da Mama to da ba za a ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin ya fahimci itace asalin mahaifiyarsa ta gaskiya! saboda iyaka so da k’aunar matar da yake ji suna ratsashi a halinda ake ciki da kuma yadda yake jinta a cikin jinin jikinsa kad’ai ma ya san sun isa su fahimtar da shi itace Mahaifiyarsa. Sun jima a haka kafin Yash ya cikasu ya kalli Daddy yace”mun yafe maka Daddy, zamu baka second chance…” Duk murmushi suka yi, daga nan suka shiga tambayarta Ina ta shige, ita kuma ta gaya musu komai tun barinta gidan Daddy har kawo yanzu…. Sosai suka sake girmama da Al’amarin Ubangiji Ga ta dai tare da Manu, amma kalli sai da Ubangiji ya k’addara saduwarsu a yau tukunna suka had’u..dama shi Yash a ko da yaushe idan za su gaisa da ita ta waya ya kanji yanayinsa ya chanja, itama kuma Maman haka Ashe duk jini da asalin soyayyar tsakanin uwa da d’a ne dalilin abunda sukeji. Sun jima kafin su shiga parlourn da suke ta jiyo koke-koke da murna yana fitowa daga cikinsa, dama shi Yash da Daddy duk sun san menene, Mama kuwa sai da ta kusan suma da suka yi idanu biyu ita da Inna dan haka ta tafi taje suka rungume juna cikin tsananin farin ciki. nan kuwa murna ta zame musu biyu , farinciki shima ba a magana, musamman ma Yash wanda yake ta mak’ale da Mama duk inda ta zauna a nan shima zai zauna kamar wani d’an yaye…… Kabarin Ya’isha suka nufa daga nan wanda ke anan k’auyen su Inna, suka yi mata addu’a, kowa yana kuka cike da alhini. sai dare tukunna suka dawo dama already Yash ya yi magana da y’an sanda, dan haka suna zuwa suka tarar da su a k’ofar gidan Mommy suna jiransu….Mama Manubiya Yahanasu da su Yadira k’in shiga suka yi, Daddy Hajiya Mama da Yash ne suka shiga har cikin gidan. sai da suka damk’a Mommy a hannun y’an sanda suka tabbata an tafi da ita tukunna suka wuce gida rayukansu fess!. Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ya fahimci ba ta gani…ya san lokaci yayi da zata fara ganin masifu da bala’i reflection d’in abubuwan da ta shuka…. A Daren ranar aka sake d’aurawa Daddy da Mama aure…Daddy ya lura da yadda jikin Ummi duk ya yi sanyi matuk’a dan shi kansa ya san zumud’i da rawar kan da yake yi ba kad’an baneba. Shiyasa ya sameta ya taushe ta sosai, kuma yace mata ta kwantar da Hankalinta itama yana sonta kuma ta kasance tare da shi a worst times na rayuwarsu dan haka iinshaaAllah ba zai tab’a juya mata baya ba…”. Ya san ba zai tab’a had’a son Ummi da Khadija ba amma in sha Allah zai kamanta adalci wannan karon. Sai a lokacin itama Ummi ta samu kwarin guiwa ta d’an sake, Mama kuwa dama tunda ta ga Ummi ta san matsayinta kuma sam bata ji haushi ko kishinta ba tunda dama ita hakan ba d’abiarta baceba.. nan ta rungumi Ummi itama Ummin haka suka rungumi juna zaman lafiya abun sai wanda ya gani!…… Sai bayan kwanaki uku tukunna y’an sanda suka tsinci gawar Kausar da Yassir! da taimakon wallet d’insa suka gano identity d’insa da gidansu… Dama a lokacin da basu ga Kausar tare da Mommy ba tunaninsu basu ya yi tana tare da Yassir ai kuwa ilai… Hannu bibbiyu su Daddy suka karb’i gawarwakin suka yi musu wanka aka yi musu sutura aka sallace aka mik’asu gidanjensu na gaskiya. Yasira ce taje ta sanar da Mommy rasuwar tasu…aikuwa nan ta haukace jininta ya hau..gashi ta so ta d’an karkato hankalin Yasirar wai ko ta samu wani by her side amma tun daga ranar ko mai irin muryaar Yasira ba ta sake gani ba…ga ba ido ga rashin lafiya gashi ba ta da kowa shiyasa ta sake shiga cikin masifa. Ana i saura kwanaki huɗu appointment d’in Manu wanda Dr ya basu su cika, suka wuce Berlin Lokaci yana ciki suka wuce asibitin, nan kuwa aka fara bincikata ciki da waje. ‘….da gaske mahaifarta ta tab’u kamar yadda Dr ya fad’a musu a Nigeria! due to maganin da ta sha, amma kuma za a iya treating d’inta ta samu ta haihu, sai dai ba lalle ta iya haihuwar sama da Yara biyar ba….’ Manu ta ji dad’in good news d’in Alhamdulillah, amma dukda haka sai da ta koka!… …Astaghfirullah, amma a k’aiyyadewa Mutum haihuwa a ganinta hakan ma damuwa ce….. Yash kuwa kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha, haka ya ji!! hakanan ya yi ta jero hamdala ga Ubangiji subahanahu wata ala.. …Manu d’insa zata haihu, kuma har morethan 4 kids ma ai kuwa shi kam Alhamdulillah… Ya san dai babu dad’i ace mutum yanada matsala kuma ga iya Ƴaƴan da zai iya Haifa, amma shi kam Alhamdulillah!!!Alhamdulillah!!! …. Sosai ta samu cikakkiyar kulawa, sannan aka d’aurata a kan magani… Watannnin uku suka yi a Berlin suka juyo da d’an cikinta, cikin da su kansu basu san da shi ba sai da suka dawo Nigeria da sati d’aya tukunna ta fara ganin alamu, aikuwa tana gwadawa ta ga positive. Sai da ta yi kuka ta godewa Allah ta yi sujjada, hankalinta ya ɗan dawo jikinta..tukunna ta fad’a wanka ta yi ta fito, ta chab’a kwalliya dan Yash ya kusan dawowa. Dama ta gama girki dan haka ta jere girke girken da ta yi akan dining…..Gwaggo tana tafiya ta d’auko disposable plate mai murfi ta saka masa pt d’in a ciki akan tissue ta rufe ta ajjiye, kamar had’in baki dai dai nan ya turo k’ofa ya shigo… Murmushi suka sakarwa juna, kafin ya ware Hannuwansa alamun ta zo garesa, kamar jira take yi kuwa ta tafi ta fad’a jikinsa ya mayarda hannuwan nasa ya k’ank’ameta yana mai sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya a baiyyane, a dai-dai saitin kunnenta yace”I love you!irin sosai d’inna!!!” Dariya duk suka yi, sun jima a hakan kafin ta jasa zuwa dining d’in ta zaunar da shi.. Sai da ya sakar mata murmushi tukunna yace”yau kenan tun kafin in yi wanka za a bani abinci?” Itama murmushin ta yi kafin tace”Inada surprise ne” Wani irin kallo ya shiga yi mata yana murmushi kamar zai cinye ta, kafin yace”to bismillah,zuba mini.” Waje ta nema ta zauna a kan cinyarsa ta zagaye wuyansa da hannayenta tukunna tace”special na girka maka…shi yana ciki, sannan ga kuma waenanna a kan dining… A cikin kalmomi biyun da zan fad’a yanzu ka d’auki guda d’aya ‘Ni’ ko ‘Kai’” Dariya ya yi sosai, har sai da kyawawan hak’oransa suka baiyyana kafin yace”abun game ne kenan? yau babyna tab’ara take ji naga alama. Shikenan ki gama taki nima zan yi tawa!” Ya fad’i hakan yana mai kashe mata ido d’aya kafin ya sakata a jikinsa sosai tukunnan yace “na zab’e ki!” Dariya ta yi sosai tace”ka yi winning! Ka zab’i in kawo maka special ɗin yanzun kenan! Inda ace ‘kai’ ka d’auka to da sai nan da dare tukunna zaka samu special d’in.” Daga haka ta Mik’e, ta je ta d’auko disposable plate d’in ta dawo ta koma Inda take zaune nan kan cinyarsa ta zaune rik’e da plate ɗin, sannan tace masa “gashi” Murmushi ya yi yana kallonta, tashi d’aya ya sa hannu ya bud’e ya kai idanunsa wajen. …. Shiruuu ya yi yana kallon pt d’in dake nan ajjiye a kan tissue wanda yake nuna masa positive…. Yadda ya yi shiruun sannan ya k’ame ya sanya ta d’an d’ago ta kalli fuskarsa shima a dai dai nan ya kalleta da Idanunsa da suka yi jazir hawaye ya fara zirara bakinsa yana karkarwa yace”d-daaa g-ask-e??” Jinjina masa kai ta yi ta kamo free hand d’insa ta d’aura a kan cikinta tukunna tace”Eh!!” Bata Ida rufe bakinta ba a zafafe ya had’e bakinsu waje guda ya shiga kissing d’inta yana mai sake sakata a jikinsa kamar wanda zai mayar da ita cikin jikin nasa ne….. ……….. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, cike da zallar farinciki…. An saka ranar Yahanasu da Dr Engr Kamal haka Hadiza itama an bayar da ita a Ya Musbah har an saka rana suma. Najeeb ya sauk’a, ya mayarwa da Yash gaba d’aya companies d’insa da businesses d’insa dan shima aiyyukansa sun yi masa yawa zuwa wannan lokacin dama kawai maneji yake yi… Ummi da Mama kuwa shi kansa Daddy ya fad’a ya sake maimaitawa ‘ko a labari ko a film bai tab’a ganin kishiyoyin da suka had’e Kai suke shimfid’a rayuwar asalin zaman lafiya na tsakani da Allah da kwanciyar hankali ba! Kamarsu.’ Gashi sun rungumi su Yasira, ta ko wanne b’angare sun zame musu Uwar da sukayi rashin sa’arta, idan aka shigo cikin gidan in ba wai Mutum ya riga ya sani ba dama chan ko kuma an fad’a masa to ba wanda zai tab’a sanin mahaifiyarsu bata cikin gidan, dan su Ummi basu rage su da komai ba. Hakanan suma su Yasirar suke girmama Ummin da Mama, sun d’aukesu iyaye, suna zaune da kowa tsakani da Allah. Tsakanin su Yasira da Manubiya kuwa abun sai dai ace ‘Alhamdulillah!’, dan sosai suke nuna mata da gaske fa sun shiryu..sosai kuma suke kyautata mata suke mutuntata da nuna mata asalin k’auna da tsantsar tattali kuma har cikinn zuciyoyinsu babu mix a dukkan abubuwan da su ke yi mata ɗin… A fannin Manubiya itama ta tashi sosai ta tsaya wajen jaansu ajikinta kamar ƴan uwanta! Kwata kwata babu jirwaye ko mix itama a cikin ƙauna da kulawar da ta ke musu, dan tsakaninta da Allah sannan da zuciya ɗaya ta ke yi musu komai. A fannin kuɗi dai Yash yana da shi dan haka komai in ya tashi ta kafa ta tsare tare take cewa a yi musu ita da kowa, amma opportunity kam idan ya zo ya zamana ba zai yiu a yi musu su duka ba to Manubiya ta kan hakura ta barwa su Yasira…Shiyasa a ko da yaushe suke sake jin regtret!…suna sake jin Zallar dana sani yana daɗa shigarsu saboda gashi Manubiyan da suke tunanin zata yi musu mugunta ko kuma za ta raba su da ɗan uwansu ita ce tsaye tsayiin daka wajen ganin sun haɗu kuma sun shaƙu da ɗan uwan nasu dukda shima Yash ɗin dama ya ɗau alƙawari kuma hakan ne burinsa amma da ace Manubiya bata so ba to da sun san abubuwa da yawa ba su kankama a tsakaninsu da Yash ɗin ba. A gaban kowa sannan a ko da yaushe za su iya tsayawa su bugi ƙirji su ce sister in law ɗinsu is the best! Dan abunda ta ke yi musu kamar itama ɗin tasu ce ba wai Yash ɗin shi kaɗai ne nasu ba. Yadda take yi musu addu’a akan aure tsakaninta da Ubangiji kuwa, ko a kanta ne inda ace ba ta yi auren ba to iyakar addu’ar da za ta yi kenan, dan ta san abun yana damunsu kwarai da gaske. Rayuwar gidan dai asalin jin dadi da farin ciki zallah, gashi arzik’in Daddy da Yash sai sake bunk’asa yake yi. Manu kam wani zubin har kuka take yi…saboda indai farin ciki ne da tsantsar soyayya ta miji da dangin sa to itakam ta samu….tabbas Ubangiji ba yadda ba ya iyawa; ya kan chanja situation daga bak’ik’irin ya koma fari k’alll!!. Bayan dangin miji da Miji ita kanta rayuwarta da rayuwar gidansu aya ce, dan zuwa yanzu cikin hukuncin Ubangiji rayuwarsu ta zam abar sha’awa ga kowa tabbas!! Kusan za a ce sun samu komai su kam, Alhamdulillah. Har islamiyya su Yasira suka koma saboda su samu su yi repenting da kyau sannan su koma ga Allah yadda ya kamata, dan da gaske sun shiryu shiryuwa ta tsakani da Allah, sun yi danasanin abubuwan da suka dinga yi a baya….Miji ne dai ko saurayi har yau shiru, dan bayaga Yaha wadda ta auri Kamal har zuwa wanan lokacin babu wadda take da mashinshini a kaff cikinsu. Daddy ya so su Manu su tashi su yi gidansu a daban, dan shi gani yake yi kamar an takura musu, amma ita da su Yasira suka ce sun fi jin dad’in zaman taren, dan haka aka sake gyara mata side d’in Yash suka ci gaba da zama a nan. ………… Bayan shekara bakwai. Babu zancen Yusuf babu labarinsa har gobe, an gagara amsoshi. Company da Businesses d’in da Yashjub ya so ya d’aura Yassir akai shi ya bawa Ya Musbah, kuma abun ya bunk’asa ya yi albarka fiye da tunanin mai tunani…. Ya Musbahn ya kammala degree d’insa a buk, yayi masters d’insa a cairo duk a fannin business admin, gashi Allah ya dafa masa kasuwancinsa dan duk wanda ya tab’a to sai ya yi albarka, yanzu haka a kaff layin nasu babu wanda ya kaisa bud’i da arzik’i jama’a har maula suke zuwa wajen Ya Musbah, haka masu buk’atar taimako suma…Daga ya dawo daga tafiya za a fara layi a kofar gidan, kowa yana son ganinsa…. Ya sake gyara musu gidan gaba ɗayansa, ta inda ya mayar musu da gidajen duk biyun masu bene, ya kyalkyalce su ta koina, dan ana shigowa cikin layin katangar da gate na gidan da kuma gidanjen guda biyu ne suke fara ɗaukar idanun mutane. Shekaru uku baya da suka wuce su Baba Habu suka yi wata mummunar gobara! babu dai wanda aka rasa duk an fitar dasu akan lokaci ammafa ko cokali basu samu sun d’auka ba, komai sai da ya k’one….a lokacin ya Musbah ya fara tashen arzik’insa shi ya kwashessu ya kama musu haya na shekara d’aya…a cikin watanni tara aka gina musu gidaje a cikin filin nasu masu bene hawa d’add’aya part uku Uncle Baba Habu har da anty umma, da babban parlourn kaka mallan…. Sai da su Baba Habu suka yi da gaske tukunna kunya danasani da nauyin Baba suka barsu suka zo gidan suka yi godiya!. suna kuka sosai suka nemi yafiyar Baba bisa ga abunda suka dinga yi masa!!….murmushi kawai Baba ya yi ya ce musu “‘komai ya wuce, burinsa kawai shi a yanzu a yi zumunci, bai rik’e kowa a cikinsu a rai ba!’ A rayuwa kowa ya kan yi kuskure, amma abunda ake so shine mutum ya gane kuskurensa kuma ya gyara, shi kuma wanda aka yi wa laifin ya yi k’ok’ari ya yi hak’uri kar ya ce zai rama, ta hakan ne za a ga dai dai sannan komai ya tafi bisa tsari.” Ai kuwa Baba ya ga zumunci ganin idanunsa, kuma yana kan ganin zumunci saboda a halin da ake ciki Hatta d’inki tare Baba Habu da Uncle suke yi da shi! komai iri d’aya, wani zubin har agogo iri d’aya suke sakawa, gidansa kuwa suna yawan zuwa, wanda kasancewarsa k’aramin cikinsu ya sanya shima yake zuwa nasu gidajen sosai domin ya hutashshesu. Anty Umma kuwa tunda akayi gobarar da ta dawo gidan Baba har yau su Inna sun ce kawai ta zauna tare da su…Gwaggo Suwaiba itama tana yawan zuwa, Mijinta har yau yana nan amma fa ciwo ya ci ya cinyesa ko tafiya ma ba ya iya yi, haka nan take fama da jinya. Kaka mallan shima tun shekaru shidda baya ko bakin maganar ma babu, yanzu kuwa ba ma ya sanin waye a kansa.ciwo ya ci ya cinyesa sosai. ……. Hannun Ya Musbah a bud’e yake sosai, shiyasa yake dad’a samun bud’i, kwata kwata bashi da rowa bashi da kyashi…Ya Nafi’u shima ya samu chanjin aiki, yanzu yana da rufin asirinsa amma duk da haka Ya Musbah sai da ya siya masa gida ya chanja masa mota tukunna hankalinsa ya kwanta, sannan har gobe kayan abinci! kayan sakawa nasa da na Yaransa biyu mace da Namiji da na matarsa kullum ya Musbahn ne yake siya! k’iri-k’iri ya hana Ya Nafiu yin duk wata hidima, ya d’auke masa komai, dan idan duniya da alk’awari ba zai tab’a mantawa da Nafi’u ba.! Duk wani business da yake yi sai ya san yadda ya yi ya sako Nafi’u a ciki shima ya samu abunda ya samu. Sosai rayuwa ta chanja tables suka juya! Yaransa uku a halin yanzu duk maza dan Hadiza ta Haifa masa Yashjub da Naf’iu. A ko da yaushe Ya Musbah idan ya samu hali da dama ya kan yi ƙoƙarin wajen ganin ya sanar sannan ya fahimtar da Mutane cewa ‘duk yadda tsanani ya kai tsanani duk yadda hanyar ta kai ga ƙullewa toshewa sannan duk yadda komai ya rufe koina ya yi duhu, har ta kaiga Bawa yake ganin no way out! Babu mafita kwata-kwata! To bawan Allah kar ya taɓa fidda rai daga rahamar Ubangiji! Sannan wayo dabara ko kwarewar Mutum ba ita ta kaisa zuwa ga nasara ba rahamar Ubangijice. Kuma a duk yadda ka ga Mutum a yau kar ka taɓa rainasa saboda baka san wayene shi ɗin ba a gobe. Jidda itama suna zaune cikin Jin dad’i dukiya da daula da tsananin k’aunar juna, suna son juna ita da Ammi ma Sosai suke zamansu lafiya….Yaranta uku, biyu mata d’aya Namiji, ta kammala karatunta a northwest, yanzu haka tana businesss. Siyama ce mai Yaro d’aya, saboda sai da ta haihu tukunna ta durfafi karatu, shiyasa suka tsayar akan ‘sai ta gama karatun tukunna sai ta d’aura haihuwar daga inda ta tsaya’. Sosai suma suke zaune lafiya, dan shima Najeeb mijin marainiya ne, ma sha Allah. Mijin Yahansu Kamal yanzu shine governor na Jahar Kano state, dan shekara d’aya asalin governor d’in ya yi ya yi ya rasu, shi ya maye gurbinsa aka basa ruk’on kwarya da aka zo zab’e kuma jama a suka sake zabaar sa. Yasmeen ta yi aure. Munirat ma ta auri Alhaji bashir (asalin saurayinta)matarsa ta rasu ata sanadiyyyar ciwonta da ya motsa mata haka kurum..ta yi jinyar sati biyu Allah ya karb’i ranta. Ko da ya dawo yace zai auri Munirat su Ummi basu b’oye masa komai ba, amma sai ya ce ‘ya ji ya gani, ai k’addara tana kan kowa kuma har Yaron ma zai rik’e..’ Aikuwa ya rik’e amana, dan shekara ta hud’u kenan suke a ciki amma bai tab’a nuna mata rashin mutunci ko gori ko banbanci a kan d’anta ba. sosai ya had’a da Yaron nata (ɗan gidan Yassir), da wanda ta Haifa masa, da y’ay’ansa na wajen uwargidansa marigayiya yake kula da su tsakani da Allah, itama kuma Munirat ta rik’e masa Ƴaƴa bilhakk’i da gaskiya…. Yadira da Junior sun koma Uk da zama, d’ansu d’aya yanzu take da cikin na biyu, suma zamansu Alhamdulillah. Hajiya Mama kam k’iri k’iri Ummi da Mama sun yi wa Mom wayo dan sunce suma ta bari su samu nasu ladan. Za ku sha mamaki idan na ce muku Abbakar Yusra ya aura! Wanda itance ta ce ta ji ta gani duk duniya ita shi take so…da farko farko ma b’oyewa ta yi, sai da ta ga k’aunarsa ta na shirin yi mata illah tukunna ta fito ta fad’a…da farko su Manu k’in yarda suka yi, amma da suka ga k’anwar tasu ta mato da yawa kuma Abbakar ya yi nadama sai kawai suka nemi zab’in Allah, ai kuwa tunda aka fara maganar har aka d’aura aure komai sumul…yanzu haka Shekarar su biyu da aure suna zaune a garin Abuja inda yake aiki d’ansu d’aya mai sunan Daddy. Muhsin ma yana Abuja yana karantar English a nile university, level 1. Yasira ce dai Allah ya d’aura mata jinkirin aure dan sai yanzu ne tukunna Allah ya fito mata da miji alhaji isma’il matansa biyu itace ta uku…yanzu haka an saka rana wata uku…. An yankewa Mommy hukuncin d’aurin rai da rai…. Na kisan da suka saka aka yiwa mallan lawal.. mutuwar Ya’isha, da kuma d’an Khadija (Amarya) na farko wanda ita da Baba Larai suka dinga d’ura mata magani har sai da suka kashe tun a ciki. Dama tun kafin y’an sanda su tafi da ita ta daina gani…Shekarar ta d’aya a prison kuma mugayen prisoners suka jefa mata bonk gado na k’arfe a k’afafuwanta, ba a bata kulawa da wuri ba har sai da k’afafun suka rub’e!! hakanan tana ji tana gani daga ƙarshe sai yankewa aka yi..kuma har yau an gagara a samu yadda aka yi akai mata transfer zuwa gidan gajiyayyun, hakanan take fama a prison ba ido ba k’afa. Ƴaƴan Manubiya da Yashjub uku..ta farkon mace takwarar Hajiya Mama ‘Yahanasu’ suna ce mata Noor, sai maza guda biyu masu sunan Baba da Najeeb, Yaran Masu tsananin shiga rai, kamannin Manu duk suke d’aukowa gasu da k’ok’ari da wayo tubarkallah. Itama ta kammala karatunta ta yi masters yanzu haka PhD takeyi kuma tana lecturing a buk….. A ko da yaushe idan Manubiya ta zauna ta kalli rayuwarta sai ta yi kwallah….Duniya rawar y’an mata… Kasancewarta y’ar talaka, talakan ma maskini hakan bai hana Ubangiji yin ikon sa a kanta ba, dan gashi abunda mutane wasu suke gani impossible(kamar ba zai yiu ba) ita ya faru a kanta, kuma tana rayuwa a cikinsa…ta samu miji mai masifar sonta wanda sam ba class d’insu d’aya ita da shi ba! Ta aura, kuma ya sota yana kan sonta tsakaninsa da Allah Tabbas komai yayi farko zai yi k’arshe, farkon rayuwarta da kuma kusa da tsakiyar rayuwarta (lokacin da su mommy suka sakota a gaba kowacce hanya ta kulle) inda ace wani zai ce mata za ta ji wannan dad’in da take ciki sannan za ta samu wannan kwanciyar hankalin, a gaba, to da ba zata tab’a yarda ba..amma with faith haƙuri da kuma addu’a everything find its place perfectly… addu’a ita ce makamin mumini dan tabbas in da Rabbana komai ma ba wahala. Mugu ba shi da riba, musamman ma mugun da yake zalinci yake cin riba baya tuba kullum ribar kawai yake gani! Tabbas irin su waennan sun fi kowa wulak’anta daga k’arshe, sannan kuma azabar su ta fi tsanani ranar gobe k’iyama. A ko da yaushe idan mutum ya yi hak’uri ya dogara da Allah Tabbas komai mai wucewa ne kuma komai akwai lokacin sa. A bangaren Yashjub shima babu abunda zai ce sai Alhamdulillah!! Ga matarso Allah ya basa, ga Ƴaƴa Alhamdulillah, ga Mahaifiya ta gari, ga mahaifi mai k’aunarsa, ga y’an uwa masu sonsa, sannan ga arzik’i dukiya farin ciki da jin dad’i da tsantsar kwanciyar hankali duk ya samu yana kuma kan samu ta koina!! Tabbas a ko da yaushe bashi da kalmar da ta fi dacewa yacewa Ubangiji sai ‘ALHAMDULILLAH!!!!!.’ Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Na godewa Allah da ya bani ikon kammala littafina mai taken suna’MANNUBIYA’. Kuskuren da na yi a ciki Allah Ubangiji ka yafe mini, darussan da suke a ciki Ubangiji ka sa mu amfana. GODIYA TA MUSAMMAN GA Nazeefa Sabo Nashe. Da Maryam Bulama. Ba zan tab’a mantawa da ku ba,alkhairin Ubangiji ya isar muku a duk inda kuke. JINJINA da GODIYA mai tarin yawa zuwa ga mutanena Oum Zahra Maman Aliyu Fauziyya Gwandu Hannah OC Binta Muhammad Yumin Aliyu Shamsiyya wada Sadiya Ka’oje Ummi Muhammad Indo Aysha Fati Abbas Kudra Maman Hafeez Zahra Auwal Iymert Habiba Idris Salmerh Maryam Mustapha Hannah collection Mrs MB Sadiya Oumhanan Da duk wani member na group d’in MANNUBIYA group one and two..ba zan tab’a mantawa da ku ba,ba ni da bakin gode muku sai addu’a wallahi!na gode na gode sosai Allah ya bar zumunci ya kuma kare mini ku kullum da ko da yaushe!na gode kwarai!! Ina muku fatan alkhairi. FATAN ALKHAIRI ga duk wani fans ɗina a duk inda suke, Alkahirin Allah ya isar muku, ina godiya kwarai da addu’o’inku da kulawa… Taku har kullum Humayrah Bulama.