*MANNUBIYA* *01* BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM. Kano, Shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa’in….(1990) A gefen titi sannan a hankali ya ke tuƙin motar tasa k’irar ‘Daewo Nubira’ tamkar ba ya son ƙarasawa inda ya tasarma zuwa ne. ‘Sannu-sannu bata hana zuwa’ In ji Mallan Bahaushe dan a hakan ya samu ya ƙarasa gidansa wanda ya ke a Unguwar sharaɗa. Ko da ya ƙarasa bakin gate na gidan bai yi horn ba. Alamun tsayuwar Mota da mai gadin gidan ya ji a ƙofar gidan ne ya sanya ya leƙo wanda ganin Mai gidan nashi ya na jira ya sanya ya koma da sauri ya wangale gate na Madaidaicin flat house ɗin. Ko da ya shiga ya ƙarasa ya yi parking, kashe Motar kawai ya yi ya ɗaura kanshi a jikin sitiyarin Motar ba tare da ya fito daga cikinta ba. Ya fi mintuna talatin a haka ya na tunani shi kaɗai kafin tashi ɗaya gabanshi ya yanke ya faɗi! Ranshi ya sake ɓaci! Sakamokon jin fitowar ta da ya yi dan ko ba’a gaya masa ba ya riga da ya san ‘Khadijah’ ce, kasancewar ba su da mai aiki, a gidan daga shi sai ita sai mai gadi wanda shi ke yi musu har wankin kayansu da guga. Shiruu, kawai ya yi ya na jin ta ta rufo ƙofar parlourn tukunna ta tunkaro Motar da ya ke ciki a zaune. Kamar yadda ya zata, ta na zuwa da rashin mutunci ta soma ta inda ta buɗe ƙofar Motar da ƙarfi kamar ta iso filin daga, sannan ko sannu da zuwa ba ta yi masa ba, cikin fushi ta soma da cewa “shine sai da ka kira Abba ko?” Ba ta jira ya bata amsa ba ta ɗaura da “ashe cin fuska da rashin adalcin da ka kusan aikatawa bai isheka ba kenan? tunda gashi har an kashe magana an gyara komai amma ka ɗauki waya ka kira Abba, me kenan kake so yanzu? So ka ke ya goya maka baya ko me?” Bata jira jan numfashi ba a hassale ta ɗaura da cewa “Tou bari ka ji, ko da ace Abba ya goya maka baya akan abinda kake so ni ba zan bari hakan ta taɓa faruwa ba wallahi… Zan baka mamaki dan in ka na tutiyar ka na da Abba (zai tsaya maka) to nima ina Daddy (yana bayana)” Ta ƙarashe maganar tata cikin tsananin bacin rai da takaici. Tun lokacin da ta iso ta fara magana shima ya haɗe rai, Fuskar nan tamau kamar bai taɓa dariya ba. Ba tare da ya kalle ta ba ya zare key ɗin Motar ya ɗauki abubuwan buƙatar shi tukunna ya fito daga cikin Motar. Ko kallon inda ta ke bai yi ba ya fara ƙoƙarin wuceta. Da ɗan ƙarfi sannan da sauri ta riƙo Hannunsa! Cikin tsananin bacin rai ta ce “IMAM ,Wallahi na fi ƙarfin ka wulaƙanta ni, ai so ba hauka bane ba, bar ganin wai Ina sonka wallahi idan har ba ka janye maganar nan ba to zan yi maka abinda sai ka yi da ka sanin haɗuwa ma da ita kanta ‘Khadijar’, zan baka mamaki, zan sanyaka ……..” “Sannu Uwarsa” Su ka ji Muryar Abba daga sama dan sam ba su san lokacin da ya shigo ba ma. Tabbas, ta sha jinin Jikinta amman dukda hakan kishi da baƙin cikin da ya ke kwance a kan kyakkyawar farar Fuskarta bai kau ba sannan Zuciyarta in banda turniƙi da tafarfasa ba abunda ta ke yi. Ganin yadda har zuwa wannan lokacin Abban ya kafeta da Idanuwa yana mai ƙarasawa zuwa inda suke ne ya sanya ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa da sauri, kafin kuma ta cikawa Imam ɗin Hannu. Abban yana ƙarasawa Imam ya durƙusa har ƙasa ya gaida shi, bayan sun gaisa ya ɗaura da cewa “Abba ai da ka bari mun ƙaraso, dan yanzu dama na ke shirin in yi wanka mu karaso wajen naka.” “kada ka damu, ai babu nisa, kuma Ina buƙatar yin tattakin nima” Haka kawai Abban ya ce ya na kallon Khadijah wadda ta ke gaishe shi da “ina wuni” Cikin ɗan russunawa. Bai amsata ba, ya juya ya bi bayan Imam wanda ya juya ya nufi ƙofar parlourn nasu da ɗan sauri yana ce wa “Bismillah Abba.” Bayan sun shiga ciki, Abban ya zauna, Imam ɗin ne da kansa ya shiga kitchen ya kawo masa lemo mai sanyi da ruwa sai snacks a gefe, dan Khadija ba ta riga ta shiga parlourn ba ta na waje ta na ta faman lissafe-lissafe, hankalinta chaa ya tashi dan tabbas a yadda ta ga Abba a wannan lokacin ta san ba zai bi bayan ta ba! Sannan ba ɗaga mata ƙafa zai yi ba, gashi ta san Abban nasu in ya ƙule sam ba ya tolerating nonsense da tirjiya… ‘Za ta iya cewa ba ta taɓa ganin soyayyar ƴa da uba mai zafi kala ta Abban da sister ɗinta ba amman tunda sistern nata ta yi masa laifi ya fita harkarta shikenan ya yafe ta har gobe ita kanta ba ma ta san inda ƴaruwar tata take ba.’ Shiyasa hankalinta ya ke a tashi maƙura, har ba ta san lokacin da ta soma kuka ba. Tsoronta ɗaya kar ya goyawa Imam baya kuma ya kafe akan itama sai ta bi ta yarda da abunda Imam ɗin ya ke so dan in dai hakan ta faru tou wallahi ta shiga ukun ta. Ita kanta ta san ta na da tsananin kishin da ko da ace ba Imam ta aura ba to fa ba ta jin za ta iya zama da kishiya, ballantana kuma Imam ɗin ne, Mutumin da ta ke da tabbacin a yadda ta ke masifar sonshi tabbas ba za ta taɓa iya jurar ganin wata ƴa Mace a matsayin Matarsa ba, bayan ita babu kowa kawai, sannan daɗin ɗaɗawa kishiyar ma ace wai ‘Khadija’ Yarinyar da ta san ya ba tsananin so da ƙauna! Ko satin da ya wuce haka nan ya fito ƙiri-ƙiri ya ce mata ‘albarkacin sunan su ya zo ɗaya ita da Khadijarsa ne ya sanya ya ke yi mata raha sannan ya ke ɗan kulata.’ ……. Ta san rashin shigarta a kan lokaci zai iya sake hasssala Abba, dan haka ta yi ƙoƙari da kyar ta iya tsayar da kukan nata, ta goge hawayenta, tukunnan ta nufi parlour itama. Abba ya na zaune a kan kujera Imam a gefen shi, zaune a ƙasa A haka ta shiga ta samesu, dan haka itama ta ƙarasa ta zauna a ƙasa ta ɗayan gefen ƙafar Abban. Ba tare da ya kalleta ba, Abban ya ce ‘’Sai yanzu ki ka ga daman shigowa kenan “ Bai bata damar cewa komai ba ya ɗaura da cewa ‘’Inaso ki nutsu ki ji abunda zan fada miki yanzu…. Na farko shawarace! Na biyu ma kamar shawarar ta ke! Sai na uku kuma umarnine daga gareni wanda ya zame miki dole ki ji, sannan ki yi.” Still bai ɗau lokaci ba ya ɗaura da cewa ‘’Idan Mata uku Imam ya ce zai ƙaro to baki da hurumin shiga cikin lamarin da zummar hanawa” ‘’Ki zauna a matsayin ki sannan ki yi wa Mijinki biyayya, ki kuma bashi goyon baya. Ni ma a matsayina na Mahaifinki ki yi mini biyyayya ki yi abunda na ce. Sai da ya jaa numfashi ya sauƙe tukunna ya ce ‘’Khadijah” Wanda hakan ya sanya ta ji gabanta ya yanke ya sake faɗuwa, ba ta kai ga dawowa dai-dai ba Abban ya ɗaura da cewa “Imam zai ƙara aure! Ba na son in ji wata matsala ta kuma kunno kai daga gareki daga yau har a yi auren nan a gama Idan ba haka ba kuma wallahi …..’’ Kukan da ta rushe musu da shi tamkar ana yankata ne ya sanya duk su ka zuba mata ido kawai, su na kallon ikon Allah. Cikin kukan ta ce “Haba Abba, ko fa wata na biyu ban gama rufawa a cikin gidan nan ba amma ace za a yi mini kishiya! Kuma ku ce in yi haƙuri in yi shiru?. Shi mai ya sa ba zai yi haƙurin ba, mai ya sa ba zai haƙura ba?. Daddy fa ya ce bai yarda ba, ya ce ba ya ma son ya sake jin maganar. “ Cikin katse ta Abban ya ce ‘’A lokacin da Daddyn bai san cewa ita wachchar Khadijar Imam ya fara so ba kenan…a lokacin da bai san itace budurwarsa tun asalin farko ba… Bari ki ji abunda ba ki sani ba, tun kafin shi Daddyn ya fara maganarku Ke da Imam, tun a lokacin shi Imam ya yi mini maganar Khadija!. Maganar aurenku ke da shi ce ta sanya ya ɗaga ƙafa dan haka yanzu banga dalilin da zai sanya ya fasa aurenta saboda ke a karo na biyu ba wallahi” Cikin kuka ta ce ‘’Abba har fa ciki ta zubar, kuma tsabar cin fuska har gidan nan ya kawo mini ita, lokacin ko sati biyu ban yi ba, a chan boys quarters ɗin aka yi jinyar ta! Saboda bata da kowa. Fisabilillahi ta ya za a haɗa ni kishi da wadda ta gama shigo mini gida ta san sirrina, wadda batta da iyaye, mai yawo a titi suna tallan Nono …..’’ ‘’Ya Isa haka, Khadijah”!. Abban ya daka mata tsawa cikin tarar numfashinta. Kafin ya ce ‘’Tashi ki tafi ki bani guri‘’ Za ta yi magana ya kuma daka mata wata uwar tsawar dan haka ta miƙe ta wuce zuwa ɗaki tana wani irin kuka. Ko da ta shiga ɗakin ma ta jima ta na kukan, kafin daga karshe ta yanke shawarar neman ‘Larai’. Saboda ta lura hatta Mahaifiyarta ita ma bayan Abban ta ke bi…. Iyayenta su na da matukar kawaici da kara, duk an san Imam ba ya son ta! Biyayya ce ta sanya ya aureta, shiyasa su kuma iyayen nata ba za su taɓa goyon bayan ta ba saboda gudun kar su shiga hakƙinsa..kuma sosai su ke gudun dasa matsala tsakaninsu da ‘Family friends’ ɗin nasu, shiyasa duk wani abun da zai buɗe wannan ƙofar ba sa ƙaunarsa sam. Dan haka ta ga gwara ta nemawa kanta mafita! Tun kafin kawaicin Fulanin Iyayenta ya cutar da ita. A nata lissafin…. kamata ya yi a ce an barta da Imam ta juyo da hankalinshi zuwa gareta, tunda an san bai son ta, ba wai a haɗata kishi da wata chan daban wadda za ta zo ta lalata komai ta kuma janye mata hankalin masoyi ba…. A chan parlour kuwa, Khadijah ta na shigewa ciki, Abba ya ɗan gyara zama ya kalli Imam kafin ya ce ‘’Na ji Khadijah ta faɗi wani abu akan Khadijar da kake son ka auro wanda ni ban san da shi ba! Ina fatan za ka ce mini ba dai-dai bane ba.” Lumshe idanu Imam ya yi, kafin ya yi amfani da tafin Hannunsa wajen shafa farar Fuskarshi wadda ta yi jaa zuwa wannan lokacin tsabar tashin hankali…. Abba ne kaɗai hope ɗinsa..ya san kuma shi kaɗai zai iya juyo da hankalin su Daddy a samu su barshi ya auri Khadija. Abunda ya ke ta tsoro dama shine kar su san ƙaddarar da ta afka wa Khadijan dan ya san muddin su ka sani to da wuya Abban shima ya yarda…. ‘’Imam, ka yi shiru” Muryar Abba ta katse masa lissafi. A hankali ya sauƙe numfashi tukunna cikin sanyin jiki ya soma magana ‘’am Abba… Kamar yadda na gaya maka Khadija ba ta da kowa, ita da ƴar uwarta marayu za a ce musu kai tsaye, na santa ne a silar kawo mana Nono office da su ke yi talla daga ita sai ƴar uwarta na sani danginta sai kuma wani Kawunta da ta taɓa haɗani da shi, wabda su ke zaune a gidansa. A halin yanzu shima ya rasu kuma dama Matar tashi azabtar da su ta ke yi, tun a lokacin da ya ke a raye ma. Shiyasa ya na rasuwa ta tattara ta barsu ta yi gaba, su sun ce mini Uncle ɗin nasu da Mahaifinsu kawai su ka sani… Ba su taɓa zuwa garinsu ba, bama su san garin ba har Mahaifin nasu ya rasu. To kuma su na saka ran zuwa da shi kawun nashi shima sai Allah ya yi masa rasuwa. Shiyasa tun a lokacin na so in auri Khadijar saboda itama ƴaruwarta Miji ya fito mata ta auri wani mai mata uku da ƴaƴa ashirin a layin nasu amman ya ce ba zai riƙe Khadijah ba. Na san zaman ta ita kaɗai akwai haɗari! Shi kuma Daddy ya dage akan duk uzuri na ya jira, ko ma menene ya jira har a yi auren mu da Khadija tunda an riga an gama magana. Ko uzurin nawa bai tsaya ya ji ba, gani kawai ya ke kamar turjiya na ke shirin yi masa, shiyasa na haƙura a wannan lokacin kamar yadda ka buƙaci in yi haƙurin. Itama ba yadda ban yi da ita akan ta biyo ni ba amman ta ce za ta iya zama ita kaɗai! Ni kuma abubuwa sun sha mini Kai a wannan lokacin ga hidimar biki! Ga aiki! To a wannan tsa-kan-ka-nin ne aka samu wani Marar Imani ya je ya yi mata fyaɗe!” Sai da ya ɗan yi shiruu, zafin abun ya na ratsashi tukunna ya ɗaura da cewa “Sam ba laifinta bane ba Abba. Dan sai da ma ta yi kwanaki biyu a asibiti ba tare da ta san inda kanta yake ba ma. Tun daga lokacin ni kuma sai na ƙi amincewa ta ci gaba da zama a gidan ita kaɗai…. Laifina ɗaya shine da na kawota nan ɗin! Na san bai kamata in kawota nan ba tunda gidan aure na ne! Amman kuma banida wata mafitar, tunda su Daddy ba za su bari in kai musu ita chan ba tare da sun san wacece ita ba! Gashi cikin da ta samu ata dalilin ƙaddarar da ta afka mata ya zo da matsala! Ana yin sati biyu ta fara bleeding muna zuwa asibiti kuma ya zube. Ga rashin lafiya ga rashin tsaro da wajen zama mai kyau shiyasa na kawota nan ita da nurse, sai dai kuma tunda Khadija ta yi bincike ta gano asalin gaskiya shikenan ta fatattakesu… Sai da na yi kwana uku tukunna na nemota da kyar.” Shiruu ya ɗan yi kafin ya ɗaura da cewa ‘’Dan Allah Abba ka duba lamarin nan.. Mu taru ni da Kai mu ceto rayuwar baiwar Allah.” Ya ƙarashe maganar cikin haɗe Hannuwanshi biyu waje guda kamar zai fashe da kuka. Numfashi Abban ya fesar bayan dogon nazari….. Kafin ya kalli Imam ɗin ya ce ‘’Zan haɗa ka da driver gobe ku je a yi duk wasu gwaje-gwaje da suka kamata! Allah ya sanya alkhairi Allah ya yi maka albarka. Zan yi wa Daddyn naku magana! Kar ka damu zai fahimta shima, in sha Allahu.’’ Wani tsananin sanyi ne ya lulluɓe Imam ,har sai da wasu hawayen farin ciki suka wanke mishi fuska. Murmushi kawai Abban ya yi, daga haka ya miƙe da shirin tafiya…. Tsakanin uba da ƴa sai Allah! Ya san abunda ya yi, ya ke kuma shirin yi tabbas shine dai-dai amma kuma a take tausayin ƴar tashi sai ya lulluɓeshi ya hanashi jin walwala… Saboda ya fahimci tunda har Imam ya rufe ido ya sake yi mishi zancen wata bayan ya aura masa ƴarshi ko watanni biyu ba a rufa da yin aurensu ba, to fa hakan ya na nufin ba ƙaramin so ya ke yi wa ita wachchar bafulatana mai tallan Nono ba. Har ga Allah, da ya ji maganar ta yi shiru bayan wata ɗaya da yin auren nasa ya ɗauka Imam ɗin ya haƙura ne, ashe abun ya na nan! Tabbas rayuwar ƴarsa Khadijah ta na cikin garari…saboda tun shekara ɗaya da ta gabata (a lokacinda aka fara maganar aurensu) har kawo yanzu, bai taɓa ganin ɗigon son ƴar tashi a cikin idanun Imam ba. Daddy, babban Abokinsa ne tun yarinta, wanda ba dan albarkacin hakan ba da kuma yadda ya ga Daddyn ya nace da son ya ga ya ƙulla auratayya a tsakanin su tabbas da babu dalilin da zai sanya ya yarda da auren Khadjansa da Imam tun farko, tunda ya san ba sonta ya ke yi ba. Yana ta fatan su samu su ɗan sasanta, ya so ta wata rana to kuma yanzu gashi zai auri wadda ya ke so! Fatanshi ɗaya ‘Allah ya sa Khadijan ta yi hankali ta kwantar da hankalinta ta yi biyayya ta zauna lafiya… Wataƙila ta samu matsugunni a zuciyar Mijinta… In ba haka ba kuwa Ba ya jin tana da rabo a Zuciyar Imam …… An ɗan kai ruwa rana kafin Daddy ya yarda aka ɗaura auren Khadija(Mai tallar nono) da Imam a cikin sati ɗaya. Wanda a tsakankanin kwanaki bakwai ɗinna babu kalar haukar da Khadija (uwar gida) ba ta yi ba! Har kalanzir ta zuzzuba a gidan koina lokacin yana bacci ana i gobe ɗaurin auren! Allah ya taimaka, ya ji warin kalanzir ɗin cikin barci dan haka ya farka da wuri…. Yana zuwa ya tarar da ita ta na ta ƙoƙarin kyasta ashana…. Da kyar ya samu ya karɓe ashanar ya jefar, ai kuwa ya na jefarwa ita kuma ta rarumo wuƙa. Fahimtar da ya yi da gaske kishi ya haukatata kuma idan ya barta kashe shi za ta yi, hakan ya sanya ya fincikota zuwa parlour sannan da kyar ya fitar da ita tsakar gidan ya saka ta a mota….. Iyayenta tamkar iyayenshi su ke, dan zai iya cewa shi da ɗan uwansa especially ma shi ɗin kusan a hannun Mahaifiyarta ma ya girma! To amma kuma ya kamata a takawa haukar tata burki! Tun kafin ta yi ɓarna, shiyasa ba dan ya so ba ya kaita gidansu ya faɗawa su Abba duk abubuwan da ta ke yi masa har ƙoƙarin kashe shi ɗin da ta soma yi. .. Sallamar Imam kawai Abba ya yi bayan ya bashi haƙuri.. ya ce a barta a nan kar ya koma da ita. A tunanin ta faɗa kawai za a yi mata, daga nan a maida ita a ranar amma sai ta ji Abba ya hana! Sannan ya hana a barta ta fita ko da ƙofar gida ne… Tana ji ta na gani haka nan aka ɗaura auren Imam da Amarya Khadijah… Ba abunda ya fi ɗaga mata hankali kamar yadda ta ji Abba yace ‘’ba za ta koma gidan Imam ba kwata-kwata‘’ Gashi auren da ta yi haukar a kai an riga an ɗaura dan haka a take ta fara da ta sani.. Hankalinta ya sake tashi sosai dan sai ta ga kamar ma ta bawa Imam damar cin amarcin shi hankali kwance kenan!. Ko sati ɗaya ba a yi ba ta ƙara gigicewa ta fita a haiyyacinta, kamar mahaukaciya haka ta koma. Ba dan Baabaa Larai wadda ta zo musu ta ke bata Baki da kuma Mahaifiyarta wadda itama ta ke tausar ta tabbas da ba tuni ta zauce!! …. Sai da ta sha wahala ta ƙara fita a haiyyacinta tukunna da kyar su Maama Mommy da Daddy su ka takurawa Abba ya kira Imam ya ce masa “ya zo ya ɗauki Matarsa” A Lokacin Amaryarsa watan ta ɗaya a gidan har da ɗan cikinta. ….. Tare da Larai suka koma gidan nata saboda itama Laran a lokacin an ɗan samu matsala da ita a ƙauyensu, ta ƙi komawa. Sosai Imam ya yi mamakin yadda Uwargidan tasa ta chanza lokaci guda…. Ba kishi ba hauka sannan ta ja Abokiyar zaman ta a jiki kamar za ta cinye ta domin so… Cikin jikinta kuwa ko ita uwar iyaka yadda za ta kula da shi kenan. Sai wani nan-nan ta ke da ita ko abu mai nauyi bata taɓa bari ta ɗauka…gashi sun hanata girki shima sun ce ta huta kawai ita Uwargidan da Larai ne su ke yin komai! Ko ruwa in ta je tafasawa haka Uwargidan za ta amshe Ita ko Larai a samu wani ya tafasa mata a kai mata har ɗaki. Wani Abu da Imam ya yi noticing shine kullum fuskar Uwar gidansa da idanunta a kumbure su ke, ya yi tambayar duniya ta ce mishi kawai ciwon ido ne ya ke damunta…. A yadda su ka haɗe kansu gidanshi kullum cikin zaman lafiya da lumana ya sanya kawai ya kauda duk wasu shakku ya kwantar da hankalinsa ya guji tsawwala bincike sannan ya rungumi matanshi Hannu bibbiyu. Dan sosai a ta ɓangarensa ya ke iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen kwatanta adalci, shi kan sa ya san yana Namijin ƙoƙari tabbas wajen ganin ya yi adalci a tsakanin Matan nasa duba da yadda ya ke ji game da ko wacce a cikin zuciyarsa…… A yadda uwar gidan tasa ta ke kula masa da Amaryar ya kamata ko Albarkacin haka ne a ce ta ci itama ta samu guri a zuciyarsa Amman har gobe ya kasa bata ko da kaso ɗaya ne a cikin ɗari na zuciyar sa saboda Amaryar ta riga ta haɗe ta mamaye gaba ɗaya kaso ɗari ɗin Itace zuciyar tashi ma gabaɗayanta. Amman kuma dukda haka Yana iyakar bakin ƙoƙarinsa sosai wajen boye hakan. Abu ɗaya ya ke yi wasu lokutan ya ke tonawa kan sa asiri…. Kasancewar sa mutum mai masifaffen kishi ya sanya kishinsa ba ya ɓoyuwa akan Amaryarsa amma Uwargidan sam ba ya nunawa sosai. Tsananin kishin sa a Amaryar ya janyo ko Abokan shi ba ya bari su gaisa da ita. Idan za a fita ya dinga gyara mata zaman hijabinta ya na rufe koina, ko gaisuwar mai gadi in ta amsa su ka ɗan gaisa sai ta haɗu da mita na ƴan kwanaki Saɓanin yadda ya ke nunawa uwar gidan sa halin ko in kula. Shiyasa ko ba a faɗa ba ko ya ɓoye su sun riga sun sani. Ba tare da shi kanshi ya san sun gama ganewa ɗin ba. Cikin Amaryar ya na watansa na biyar Imam ya tattara gaba ɗaya dukiyarshi ya damƙawa babyn da za ta haifa! Mace ko Namiji ya ce shi bai damu ba, kawai dai shi ya san ya daɗe da gama yanke shawarar idan aka Haifa mishi baby na farko a rayuwarshi to ya bada komai nashi a babyn kenan… Amaryar har kuka ta dinga yi akan ya janye wannan ƙudiri nashi dan a ganinta zai janyo mata baƙin jini ne amma furr ya ƙi ji ya ƙi gani. Daga ƙarshe dai ya tilasta ta ba yadda ta iya ta haƙura ta bi tsarin nasa sannan su ka tsayar akan ‘Maganar za ta tsaya iyaka su biyu’ Idan Allah ya sa ta haihu shi zai ci gaba da kula da dukiyar har sai Yaron ko Yarinyar ta/ya kai munzalin aure tukunna za a damƙa mishi komai… A cewarshi sannan a yadda ya faiyyace mata wai kyauta ce kawai ya ga damar bayarwa sabooda farin cikin samun haihuwa ne shiyasa ya shirya hakan a ɗan da zai haifa na farko kuma ko da ace uwar gidansa ce ta haifa tou hakan zai yi… Amman a chan cikin zuciyarshi har ga Allah ya yi hakan ne saboda tsananin so da ƙaunar da ya ke yi wa Amaryar tashi! Dan yadda ya ke sonta ya kuma kwallafa rai a kanta haka ya ke ji da cikin jikinta shima, kamar ranshi. Ba ya fatan wani abun ya sameshi ta wulaƙanta. Ya san su Abba ba za su bar Yaron ya wulaƙanta ba amma ita fa! Dan ta Uwargidansa ta na da nata gatan Amaryar ce abun ji… Wani sabon abu da ya fara lokacin da cikin ya kai wata bakwai shine rashin godewa abunda su Larai su ke yi! Duk kalar ƙoƙarin da su ke yi waAmaryar sai ya daina gani.. Ko maganinta ne idan ba ta sha a kan lokaciba to ranar sai an ga abun mamaki! Dan rashin kara ya dinga masifa kenan har washegari. Kuma in dai Amaryar ta yi missing magani tou ko dai ita Uwargidan su na girka mata abinci ne sun sha’afa ko kuma wani abu makamancin haka…amma sam Imam ba ya fahimta. Ganin rigima ta na shirin fara kunno kai hakan ya sanya ita da kanta Amaryar ta karɓi magungunan nata daga Hannun Abokiyar zaman tata ta ce za ta dinga sha da kanta. Dan ita kanta abubuwan da Imam ɗin ya ke yi sam ba ta jin daɗinsu… Ko dan yadda su Laran su ke sonta da gwada Namijin ƙoƙari wajen bata kulawa ita da abunda ya ke cikinta ya kamata ace ya yaba amma kamar ma ba ya gani. Shi komai kawai ita da cikin Jikinta. Abunda Imam ya ke yi a kan cikin nan za ka ɗauka a kan shi aka fara haihuwa a duniya! Abu ɗaya da uwar gidanshi ta yi shine kau da Kai! Sosai ta yi ƙoƙari wajen ɗauke kanta ta rufe Idanunta, sam ta ƙi yarda ta biye mishi, kuma sarai ta san da maganar ‘bawa ɗan da Amaryar za ta haifa kakaf dukiyarshi da ya yi amman shima ba ta ce masa ƙala ba! Dan ita a wannan lokacin babbar damuwarta Ita ce yadda ta gagara ɗaukar ciki! Dan haka ta duƙufa addu’a sannan ta bar Imam ya na ta kinibibin shi shi ɗaya. Ƙarƙari idan ya ce ba ta yi wa Amaryarsa abu ba ta bashi haƙuri kawai a wuce wajen, ko yana mita bata biyeshi. A kwana a tashi…. edd ɗin Amarya ya cika har ya wuce amman sam ba ta ji motsi ko alamun labour ba, dan haka su ka nufi asibiti. Su na zuwa tun a gwajin farko aka fahimci Babyn babu rai ya ma daɗe da mutuwa dan har kamar ya fara dagargajewa ma. Sumewa Imam ya yi a wajen da jin wannan mummunan batu! Dan tabbas bai taɓa shiga tashin hankali kwatankwacin na wannan lokacin ba. Har aka yi aikin aka gama aka cire babyn aka mata wankin ciki bai farfaɗo ba. A tare su ka yi jinya a asibiti ita da shi dan ba kaɗan ba jinin shi ya hau ! A bangaren Amaryar itama abun babu sauƙi sam! Dan bayan kwana biyu da yi mata wankin ciki Yayarta itama ta rasu! Ta sanadiyyar haihuwa da ta zo yi duk su biyun ita da Yaron ba wanda ya rayu. Shiyasa abun sai ya haɗe mata biyu, gaba ɗaya ta burkice… Ba dan ƙarfin Imani ba da tuni ta zauce tsabar yadda abubuwan su ka daketa. Imam ma sosai ya yi fama dan kamar wani ƙaramin Yaro haka ya ke kwana ya na wuni kuka, ga rashin lafiya, sai da Mahaifiyarsa(Yahanasu) ta tsawatar masa ta yi masa nuni da muhimmancin karɓa da yarda da ƙaddara tukunna da kyar da taimakon Allah da addu’o’i ya ɗan dawo dai-dai. Ko a gidan nashi ma sai da aka kwashe duk wasu kayayyaki na babyn da ya kashe uban kuɗaɗe ya yi ta siya ya na jibgewa a ɗakin da aka ware guda domin babyn tukunna aka samu sa’ida! Dan kafin a kwashe ɗin haka nan zai shiga ɗakin ya rungume kayan Yaron ya yi ta uban kuka kamar wani ƙaramin Yaro abun tausayi! Dama shi tun ya na Yaro yana da masifar son ƴaƴa Shiyasa ya kwallafa rai akan cikin jikin Amaryar tashi masoyiyar shi, sai dai kuma Ƙaddara ta riga fata……….. *Bayan Watanni Uku* Kamar haɗin Baki, a lokaci guda duk su biyun su ka samu ciki. Sai dai edd na uwar gidan ya fi na amaryar A yadda ya nuna Ita uwargidan ce za ta fara haihuwa da sati biyu daga nan amaryar itama ta haihu … Murna wajen Imam ba a magana amman a wannan lokacin ma duk yadda ya so ya ɓoye kowa sai da ya fahimci ya fi farin ciki da cikin jikin Amarya. Kasancewar Uwar gidan itama ciki gareta wannan karon shiyasa aka ƙaro mai aiki, wadda ta ke zuwa da tafiya su ka haɗu ita da Larai su ka yi ta kula da su. Kamar yadda Imam ya yi wanchan karon haka ya yi wannan ma Ya kwashe komai ya damƙawa ɗan cikin Amarya. A nan ne kuwa ya ga ɓacin ranta kalar wanda bai taɓa gani ba dan burkice masa ta yi, ta ce ba zai yiu ba, in har gaskiya za a bi ai itama yayar tata ciki gareta…. Har kuka ta dinga yi masa sannan ta haɗa da nasihar kar ya yarda ya zamto cikin Maza masu zalinci babu kyau sam. Ita Amaryar babban abunda ya sake ɗaga mata hankali ma shine tunda ta ke da Uwargidan ba ta taɓa cutar da ita ba! Abunda ta ke yi mata ko Ƴar uwarta wadda ta rasu ba ta yi mata shi ba…dan haka ta yaya zai dinga yi mata haka saboda Allah ita kuma ta naɗe Hannu ta zauna ai ba zai ma yiu ba. Ita kam babu ruwanta kuma idan ya matsa sai ta je ta samu su Daddy ta faɗa musu dan ba da ita za a yi wannan zalincin ba …… Yanayin yadda cikin Amaryar ya yi tsini kamar wanchan karon na farko hakan ya saka masa yaƙinin Namiji za ta haifa in sha Allahu saɓanin na uwar gidan wanda ya bi jikinta sosai yasanyata ta yi ƙiba. Shiyasa ya zauna ya yi ƴan lissafe lissafensa tukunna ya yanke shawara, ya zo ya sanarwa Amaryar cewa tunda ta ɗaga hankalinta kuma ta ce ya yi adalci shikenan zai yi… Na farko ya fasa bada duka dukiyar maimakon hakan zai rabata gida biyu ne ya bayar da rabi ya riƙe rabi Sannan zai bayar a duk wadda ta haifa masa ɗa Namiji Idan kuma duk su ka haifi maza tou sai a rabata gida biyu a bawa kowa kashi ɗaya, kuma kamar tsarin farko shi zai ci gaba da kula da ita har sai Yaron ya kai munzalin aure ko shekaru goma sha takwas tukunna zai damƙa masa abunshi. A wannan karon ma ya kawo mata wani dalilinsa na yin hakan, inda ya ce Yaro Namiji na farko ya kamata a bashi support tunda duk ƙannensa a ƙarƙashinsa su ke sannan kuma dama ya na so ya bada kyautar saboda farin ciki dan haka gara kawai a barshi ya yi… Sai dai ita Amaryar sam ba ta fahimci fa’idar yin hakan ba. Tun ba ma yadda ya ware ta ita kaɗai ya gayawa ba bayan itace ma ƙarama…. A ganinta kamata ya yi ya haɗe su duk su biyun ya yi shawara da su, Idan ma hakan ne decision ɗinsa tou ya gaya musu a tare. Ganin da ta yi ranshi ya na sake ɓaci game da tirjiyar da ta ke ta yi ne ya sanya kawai ta haƙura ta rabu da shi… Amman har ga Allah a chan ƙasan ranta addua ta ke yi Allah Ubangiji ya sa Uwargidan ta haifi ɗa Namijin. Sarai ta san Matar tana fahimtar wasu abubuwa na bambanci da Imam ɗin ya ke nunawa a tsakanin su amman dukda haka ta ke kauda Kai kamar ba ta san me ke faruwa ba, but fa ta san ko zuciyar gwal gareta muddin akace yau sun haihu tare ita ta haifi ɗa Namiji an ɗauki rabin dukiya an bata tou fa ta san zaman lafiyar ta da Abokiyar zaman na ta tsaf sai ya taɓu! Ita kuma bata son abunda zai haɗata da Abokiyar zaman nata dan ta yi mata abunda ba za ta taɓa mantawa da ita ba..yadda ta kula da ita da ɗan cikin ta na fari ba ko wacce kishiya ce za ta iya ba, ko ɗanuwa na jini iyakar abunda zai yi maka kenan. ………… A kwana a tashi….. Watan haihuwa ya kama, cikin hukuncin Ubangiji ko wacce ta sauƙa lafiya, sai dai fa abubuwa ba su tafi yadda Imam ya tsara ya kuma yi zato ba domin Amarya Mace ta Haifa! Uwar gidan shi kuma ta haifi ɗa Namiji… Sam-sam Imam bai yi zaton hakan ba. A ranar da suka haihun ma ba ya nan…. Ya yi tafiya zuwa Abuja, A ranar da zai tafi ɗin Uwargida ta fara labour da sassafe dan haka ya bar musu duk abunda ya san za su buƙata sannan ya ce shi da Amarya za su je su ƙaro wasu kayan, basu dawo ba sai da ya biya da ita asibiti aka tabbatar masa sai nan da two weeks tukunna edd ɗinta zai cika! Inda ya ji daɗin hakan sosai saboda dama ya fi so ta haihu yana a tare da ita kuma shi sati ɗaya kawai zai yi a Abujan ya dawo… Dan haka ya maida ita gida cike da farin ciki, yayinda ita kuma ta ke ta faman kumbure-kumbure ta na ta yi masa wa’azin ya dai dinga adalci. Cike da fatan alkhairi da kuma tsananin kewar Amaryarsa ya tafi, tare da fatan yana dawowa ita ma in sha Allahu ta haifa masa sanyin idaniyar shi. Sai dai kuma yana tafiya itama Amaryar ta fara samun contractions, dan haka akayi asibiti da su duk su biyun. Suna zuwa akace sai dai a yi wa Amarya cs dan ba za ta iya haihuwa da kanta ba. Ba tare da ɓata lokaci ba Daddy da Mama su ka cike takardun amincewa aka shige ɗakin tiyata da ita. Itace kuwa ta fara haihuwa aka ciro mata babynta Mace ƙatuwa tubarkallah, Larai ita ta miƙawa su Mommy waenda su ke a wajen labour ɗin kowa yana ta farin ciki, fuskokinsu tamkar gonar auduga…. Basu gama murna ba! Likitan ya fito musu da kyakkyawan Yaro mai tsananin kama da Ubansa ɗan wajen Khadijah (uwar gida.) Kowa idan ya kalleshi sai ya ce MashaaAllah, dan tun ya na jariri kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci kyakkyawa ne. …… A ranar Imam ya biyo flight ya dawo a hargitse dan ɗoki ….. Tun a chan ya gama yanke shawarar fasa bawa ɗan gidan uwar gidan ta sa rabin dukiyar sa da tunanin neman wata mafitar tunda ba kowa ya san da zancen ba dama…..saboda shi babban dalilinsa da ya ɓoye ya ƙi gayawa kowa shine ba ya so ya riga Amaryarsa gidan gaskiya ta wulaƙanta ba ya so wani abun ya sameshi ba tare da ya kafata ta tsaya da ƙafafunta ba. …. Imam ya na zuwa da ya ɗauki Yaron a take ya ji duk duniya ba abunda ya ke so sama da shi. Dan har kuka ya yi tsabar asalin farin ciki. Wata irin soyayya Allah ya dasa masa ta Yaron, mai tsayawa a rai. Ya na son itama ɗayar Yarinyar da aka haifa masa amman ba kamar yadda ya ke son Yaron ba, wani irin kalar so ƙauna da tausayi na Yaron ya ke ji suna ratsa dukkan ɓargo jini da tsokar da ke jikin shi. ….. Bai yi tunanin su Maama sunsan maganar alƙawarin da ya ɗauka na raba dukiyar shi biyu ba, sai da ta yi masa maganar. Ashe wannan karon ma uwar gidan ta sani kuma ta gaya mata tun farkon sanin zancen da ta yi. Wanda kai tsaye Maama ta fahimci son kai ne ya ke shirin yi ta kuma ji haushi duba da yadda ya yanke shawarar a cikin Amaryar na farko ma ba tare da ya tuntuɓi kowa ba, shiyasa ita kuma ta cewa Uwargidan ta yi shiru ta barta da shi, za ta yi maganin shi. Ya so ya ziille!. Tabbas ya na son ɗanshi fiye da komai, amma kuma yana duba rayuwar Amaryarsa. Ya so ace ita ta Haifa masa wannan Yaron da tuni ya bayar ba tare da shayi ko kokwanto ba. Fahimtar da ya yi Uwargidan har ma da Mahaifiyarsa sun fara fahimtar dama chan ba adalci ya so yi ba, hakan ya sanya kawai ya haƙura ya bayar da rabin dukiyar tasa a ɗan nashi ba dan ya so. ………… Wani ikon Allah.. Tun daga wannan lokacin abubuwa sai su ka sauya! Gaba ɗaya soyayyar Imam ga Amaryarsa sai ta yi rauni. Ita sai ta ke ganin kamar ma haushinta ya ke ji! Dan ko kusa da shi ta fahimci ba ya so ta je. Itama uwar gidan tashi ba wani sake mata ya ke yi ba, amma dai ya fi tsanar amaryar akanta. Indai ka ga yana dariya tou ya ɗauki ƴaƴansa ne! Amman baya ga haka ba shi da wata walwala kuma. Tashi ɗaya ya koma wani irin murɗaɗɗen Mutum mai wuyar sha’ani, lamarin nasa har abun tsoro ma. Dan har ga Allah ita kam Amaryar zuwa wannan lokacin ya fara bata tsoro. Ga ga hantara, kyara da tsangwama wadda ya ke gwada mata ƙiri-ƙiri. Ga wani irin masifaffen kishinta da ya ke yi marar misali, har ya janyo zargi, wanda hakan ya sanya ta ke tunanin ko dan ya san ya daina bata kulawa da bata dukkan hakƙinta ne shiyasa ya ke tunanin za ta je ta kula wani a waje. Gaba ɗaya tashi ɗaya sai duniya ta yi mata zafi!. Da ga Uwargidan sai Larai ne kawai ta ke da su, ta ke ɗan hira da su ta ji sauƙi. Sai ko ƴar jinjirar Yarinyar ta wadda da aka ƙara ƴan kwanaki itanma sai ta lura kamar ƙiyayyar da Imam ɗin ya ke yi mata ta shafi hatta jinjirar Yarinyar wadda ba ta ji ba bata gani ba. Dan kafin ya ɗauki Yarinyar sau ɗaya to ya ɗauki ɗanuwanta sau ashirin….. Ba ta da yadda za ta yi, tunda bama ta san laifinta a gareshi ba ballanta ta gyara…. Shiyasa ta duƙufa addu’a kawai ta ke kuma ƙoƙarin wajen riƙe kanta kar ta gigice dan yadda ya ke sonta a baya itama haka ta ke son shi har gobd wanda hakan ya sanya daya juya mata baya komai nata sai ya tsaya mata chak!. Shiyasa ko Mutum bai santa ba tun farko to da zarar ya ganta a wannan lokacin kallo ɗaya tak za a yi mata a fahimci ta na cikin tsananin tashin hankali. …… *Bayan Shekaru Talatin* BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *02* *Bayan shekaru talatin* *AUCKLAND(okland)* ….. Babban jirgin ruwa ne, na alfarma(superyatch) mai kyawun gaske, tsaye a chan tsakiyar ruwa, keɓance daga dukkannin gidaje da al’ummar garin. Kwata-kwata jirgin ruwan ba zai ɗauki sama da mutane 70 ba kasancewar ba wani girma gareshi ba…. Walwali na kalolin fitilu mabanbanta, da haskensu ke ratsowa ta cikin jirgin ke bada tabbacin party ake yi a ciki. Tun daga nesa da su kaɗan sautin ƙiɗa ke tashi alamun an ƙure speakun sun kai ƙarshe kenan, cikin jirgin kuwa muddin Mutum ya kasance ba ma’abocin son kiɗe-kiɗe bane to ko sakanni ba zai iya ɗauka a ciki ba. Sama da ƙasa ne da jirgin kamar girman madaidaicin gida mai bene (duplex). A ƙasan ake gudanar da event ɗin, wanda yanayin decoration da cakes ɗin wajen zai sanya a kira hidimar da ta ‘birthday party’…. …… Ƴan Mata ne guda biyu tare da wata farar budurwa wadda ba za ta haura shekaru ashirin da bakwai a duniya, keɓance a ɗakin da ke sama su uku kawai yayinda dukkannin al’ummar cikin jirgin ƴan Mata da Samari su ke a babban parlourn da ke a ƙasan sun cika shi taf har ma da ƴar varander da ta fita waje itama ta cika da Mutane in banda kiɗa da rawa ba abunda ake gudanarwa a wajen. Wine rack na nan cike da kwalabe, duk kalar abunda su ke buƙata zuwa kawai su ke yi bar tender ya tsiyaya musu su kora ta maƙoshinsu. Ta na kwance akan makeken gadon da ke a cikin ɗakin sanye cikin wasu matsatstsun riga da wando, Rigar ko cibiyar ta bata gama rufewa ba… Fara ce ita ɗin tass dan hasken fatarta kalar na turawa ne ma!! Ba za a kirata da kyakkyawa ba ba kuma mummuna bace ba, tana da doguwar fuska, madaidaitan Idanuwa dogon hanci da matsakaicin Baki! Gashin kanta shima a cike ya ke taf ga kuma tsayi dan har ya kusan kaiwa tsakiyar gadon bayanta. Doguwa ce sosai sannan siririya ce ta gaske. ‘’KAUSAR!!!!’’ Ɗaya daga cikin ƴan Matan ta kira sunanta…. A hankali ta lumshe idanuwanta ta buɗe su kafin cikin asalin jan aji da yauƙi ta miƙe ta zauna a kan gadon. Sun san halinta da yauƙi dama ga kuma rashin son takura, dan haka kowacce sai ta ja Bakinta ta yi shiru, ba su sake tanka ta ba. Ta fi mintuna biyar ta na ta yamutse fuska kafin ta miƙe kawai ta faɗa toilet….. Ta jima sosai a cikin banɗakin tukunna ta fito. Kallon gadon ta yi sakamokon ƙarar da ta ji wayoyinta waenda ta bari a kan gadon, su na yi . Ko kallon wayoyin bata sake yi ba, ta nufi ledar da ta hanga wadda ke a nan gaban dressing mirrow tun ɗazu, tana zuwa ta zaro wata 3 quarter gown black! Ta jefar da ledar a ƙasa tare da ragowar abubuwan ciki. Ba abinda ta shafawa fuskarta sai jan jambaki daga nan ta zura gown ɗin ta feshe turarurruka, ta saki gashin ta wanda ta ɗaure gudun kar ruwa ya jiƙa mata shi garin yin wanka. Bata kalli kowa a cikin ƴan Matan da suke nan a shirye tun ɗazu suna ta jiran ta ba… Wayarta guda ɗaya kawai ɗauka daga haka ta kama hanyar fita… Suna ganin hakan su ka mara mata baya duk su ka fice kusan a tare…. …. Suna sauƙa ƙasan wajen ya karaɗe da ihu, masu cewa “happy birthday Kausar” ma, su na yi. Murmushi kawai ta yi ta shiga hugging friends ɗin nasu waenda suka taru ana gaisuwar yaushe gamo… Anayi su na bata gifts ita kuma tana miƙawa friends ɗinta da suka sakƙo tare. … Tunda ta saƙƙo su ka haɗa ido da shi amman sai ta ɗauke kai ta yi kamar ma bata ganshi ba, bata ma yarda ta sake kallon inda ya ke zaune shi da Abokanayen sa su biyu, ba. Direct inda babban cake ɗinta ya ke nan ta nufa ta je ta yi cutting daganan ta yi wa kowa godiya tare da basu uzurin ‘ta na da important interview’ Daga haka ta yi excusing kanta ta juya ta nufi sama inda ta fito…. Party kuma ya ci gaba da gudana. Wata mahaukaciyar Dariya ɗaya daga cikin Abokansa ya kece da ita kafin ya ce ‘’Tunda nake a rayuwata ba a taɓa yin disgin da ya bani tausayi da dariya at the same time kalar wannan ba.” Kallon shi ɗayan Abokin nasu ya yi kafin ya ce “Dude!”. Yana ɗan yi masa alamun ya yi shiru mana sannan ya nuna masa YASSIR ɗin da ido wanda ke nan zaune a tsakiyansu su biyu…. Tun lokacin da Ƙausar ta sauƙƙo ya ɗauke wuta, ta saba wulaƙanta shi dama kwana biyun nan amman tunda su ke bata taɓa yi mishi abun da ya ji haushinsa kalar wannan ba… Dukkan Mutanen da su ke a wajen shi ya kwaso su wasu daga Nigeria wasu daga ƙasar da su ke duk shi ya yi musu kuɗin jirgi saboda yana so ta ga friends ɗinsu na school tare a waje ɗaya ranar birthday ɗinta, a wajen da soyayyarsu shi da ita ta soma wajenda ta soma yarda dashi wato ‘Aucland’ wajen da ya san nan ne favorite wajen da ta fi so… Amma its like ba ta yi farin ciki da surprise ɗin nasa ko kaɗan ba. “Wats wrong with Ƙausar ne wai kwana biyu?” Ya yi wa kanshi tambayar a cikin Zuciyarsa, ranshi yana ƙarasa dagulewa. A hankali ɗayan Abokin nasu ya ce “Yassir, Magana ta gaskiya… Yarinyar nan abun nata ya fara yin yawa..You are better than this, haba mana! Pls move on, ga girls nan kala-kala amma ka nace kai sai wadda….” Kallon da ya ga Yassir ɗin ya ɗago ya na yi masa ne ya sanya shi kasa cigaba da maganar tashi..kafin a hankali ya ɗan sunkuyar da kanshi sai kuma ya juya ya bar wajen ma gaba ɗaya, dan tabbbas yadda ya ga Idanuwan Yassir ɗin sun kaɗa sun yi jaaaa! To fa tsaf zai iya juye haushin sa a kan shi. Shi kanshi ɗayan Abokin nasu da ya ke ta yi mishi dariyar shaƙiyanci shiru ya yi ya kauda kai bai sake yunƙurin cewa komai ba….. Ya jima a wajen kafin ya miƙe ya nufi sama inda Kausar ɗin take. Yana ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin da ta ke ciki ya hango ta zaune gaban madubi ta sunkuyar da kanta sosai, kamar ma kuka ne ta ke yi… A hankali ya ja ya tsaya a bakin ƙofar ya shiga ƙoƙarin fahimtar yanayin ta daga nan inda yake tsaye “leƙe, ba halin kwarai bane, musamman a Macen da ta keɓance kanta ta ke buƙatar space ɗinta ita kaɗai!!’’. Ya ji muryarta cikin yanayin kuka. Numfashi ya fesar kafin ya kutsa Kai ya ƙarasa cikin ɗakin! Idanuwanshi a kanta, duk tsananin ɓacin ran da ya ke ciki sai ya ji yana ta raguwa a hankali a hankali….. A gefenta ya je ya tsugunna kafin ya miƙa Hannu ya kamo nata… Bata kula shi ba sannan bata hana shi ba, tana jin shi ya shiga murza tafin Hannun nata, a hankali cikin kwantar da murya ya ce ‘’Kausar abinda ki ka yi mini yau banji daɗinsa ba! Na haɗa wannan abun ne fa domin ke kawai, ga friends ɗinmu wasu na tabbatar rabon ki da su tun a Makaranta, na kawoki inda na san ki na so na haɗa miki duk abubuwan dana san ki na so amman yadda ki ka nuna kamar irin ba ki gode ɗinnan ba, kamar ma na kwaso kashi ne na zo na yaɓa miki a Jikinki! Ko arziƙin kallo fa ban samu daga gare ki ba, ballantana in ji yadda ki ka ji daɗin surprise ɗin. Sannan na sanar miki tare za mu yanka cake amma ba ma ki tsaya kin jira ni ba, kawai ki ka je ki ka yanka ke kaɗai. Idan wani abun na yi miki dan Allah mu yi maganar in baki haƙuri a wuce wajen dan wannan abubuwan da ki ke min barazana ne ga relationship ɗinmu, ba kya helping kwata-kwata sai ma ƙoƙarin lalatawa da ki ke yi. Ni kaɗai na ke ta faɗi tashin ganin mun gina alaƙar nan tama, Ƙausar ina ƙoƙari fa duk domin ki…. Ko iyaka wannan birthday ɗin da na haɗa miki kawai don in ga farin cikin ki shin kin san nawa na kashe kuwa?” Duk maganganun da ya ke ta yi sai da ya kai nan tukunna ta fesar da Numfashi sannan ba tare da ta kalle shi ba ta miƙe ta ɗan ja hannuta wanda ke a cikin na shi da ɗan ƙarfi, ta bar wajen cikin takun ta mai jan hankali ta nufi bed. Jakarta kawai ta ɗauko ta zaro check ta fara neman biro. Tunda ta fara rubutun ya fahimci me ta ke shirin yi dan haka ya miƙe shima ya ƙarasa da hanzari ya wafce takardar dai-dai nan ita kuma ta gama rubuta mishi kuɗin. Cikin ɓacin rai ya kalli takardar sannan ya maida dubanshi gareta ya ce ‘’Cewa na yi ki biyani???’’ A hankali ba tare da ta kalleshi ba ta ce “Nop! Amma Ina buƙatar space dan haka zan yi ko ma menen domin in ga na samu, dan haka ko biyanka ɗinne ma sai in yi in dai zan samu ka daina yi mini wannan jarababban nacin naka”. Cikin takaici ta ɗaura da cewa ‘’Kuka fa ka shigo ka ga Ina yi Yassir, amman kawai kai ta matsalar ka ke yi, kanka kawai ka sani, har ga Allah ka takura ni dayawa, ina jin matsi sosai a duk lokacin da na ke tare da kai.’’ Ɗan zaro idanu ya yi, har zai yi mata magana da ƙarfi! Sai kuma ya runtse Idanun nasa da tafin hannunshi da ƙarfi!!!… Ya ɗan jima a haka kafin ya buɗe Idanun ya ɗan sake matsawa inda ta ke tukunna a hankali cikin tsananin mutuwar jiki ya ce “Kausar, ni ne na ke nacin, ni na takuraki kuma yau??” Shirun da ya ga ta yi ta kauda Kai ne ya sanya shi sake matsawa sosai gareta a hankali ya ce ‘’har yanzu, akan abunda ya farun nan ne ki ke jin haushi na, ko?” Sai a sannan ta ɗaago Idanuwanta ta kalleshi, a hankali itama ta ce ‘’Yassir bana son yawan magana ayanzu amman sai surutu ka ke ta sakawa Ina yi.. Bari ka ji, idan ka ga dama ka je ka nemi duk ƴan matan duniyar nan, na faɗa maka ba damuwa ta bane ba! Sannan in dai cikinka zai iya ɗauka to dan Allah ka je ka juye masa dukkan nin giyar da ke a cikin duniyar nan shima duk ba matsalata bace ba, iyaka abunda na ke so daga gareka shi ne “space!!” Don Allah Yassir ka ɗan ƙyaleni na wani ɗan lokaci, ba na son takura”. Ta na gama faɗin haka ta juya ta shige toilet da sauri ganin ya na shirin ruƙota. Aikuwa har bakin ƙofar toilet ɗin ya je ya yi ta faman knocking Ya na rarrashinta ta amman sam ta ƙi ta tanka shi. Ya jima a wajen kafin da kyar ya jaa ƙafafuwansa ya bar ɗakin yana mamakin abun da ya ke damun Ƙausar…. Tun suna da shekaru 14 a duniya su ke soyayya ya kuma san ta na tsananin ƙaunarsa, kawai dai bai san mai ya faru kwana biyun nan ba, gaba ɗaya ta hargitse, kamar ma ko kallon sa ba ta son yi….. …. Sai da ta ji fitar sa, tukunna ta sauƙe wata nannauyar ajiyar Zuciya ta buɗe ƙofar ta fito… Ba wai ba ta son Yassir kwata-kwata bane a yanzu. Tabbas akwai ragowar burbuɗin soyayyar sa a cikin Zuciyar ta har kawo wannan lokacin. Tun suna Yara ta san YASHJUB ya na burgeta amma ba ta taɓa sanin soyayyarshi za ta iya yi wa zuciyarta mahaukacin kamu ba sai da ta ganshi after 10 years!!. Sannan bayan soyayyar ta gare shi, babu ta inda za a haɗa Yashjub da Yassir… Kyau, Ilimi, class, haɗuwa! Uwa uba kuɗi duj Yashjub ya fi Yassir komai, ta koina. Tabbas ta san za ta sha fama. Ta san dq wuya Yassir ya haƙura cikin sauƙi sannan da wuya shima Yashjub ya yarda cikin sauƙi, ga kuma Iyayensu waenda ta san ba ƙaramin rikici za fa kunno a tsakaninsu ta hanyar yin hakan ba! To amma ya ta iya?! Dan har ga Allah ba ta jin ta na da sauran numfashi a gaba muddin rayuwarta babu Yashjub a ciki…. Duk yadda Yassir ya so daurewa kasawa ya yi! A yadda ya ke jinshi tsaf zai fashe da kuka, shiyasa bai kula kowa ba haka nan ya zo ya wuce taron jama’ar wajen ya shige cikin wani ɗan ƙaramin ɗaki a nan jikin parlourn…. Yana shiga ko ida rufe ƙofar bai yi ba! Hawaye su ka wanke mishi fuska!. Duk wani abu wanda ya ke za a iya fasawa a cikin ɗakin sai da ya fasa shi! Wanda hakan ne ya janyo hankalin jama’ar da ya bari a waje! bari Har ta kai ga Abokanan shi guda biyu shigowa…. Dama a yadda su ka ga ya sauƙƙo ɗin sun san ba lafiya ba. Da kyar ɗayan ya iya kwace kwalbar Hannu shi wadda ta yi masa jina-jina… Ya yar da ita Cikin ɓacin rai ya ce ‘’Haba Yassir!! Kana hauka ne? Wai duk akan Mace ne ka ke wannan jahilcin? A haka kana mata naci zata soka ne an gaya maka?. In bata sonka ka haƙura mana A Ina aka taɓa yin so dole.” Cikin tsananin fushi Yassir ɗin ya shaƙo wuyan shi Wanda hakan ya sanya ɗayan Abokin nasu ya matso ya fara lallaɓa shi da bashi haƙuri, dan ya lura ba ya tare da hankalinsa… Da kyar kuwa ya samu ya cika shi, Abokin nasu ya juya yana wani irin huci da sauƙe ajiyar zuciya a jejjere… Cikin tsananin ɗacin zuciya Yassir ya cewa ɗayan “Ka shirya komai. Kowa ya watse.” ••••••• B U K Kano Bayani tuƙuru lecturen ya ke yi, wanda ya yi tsaye a gaban whiteboard na lecture hall ɗin. Gaba ɗaya hankulan ɗaliban ya na a kan shi ne, ajin ya yi tsit kowa ya nutsu wanda hakan ke tabbatar da Ana jin tsoron lecturer din… Kowa ya nutsu kalli ɗaya za a yi musu a fahimci babu mai buƙatar yin laifi. Tunda ya shigo ajin ya lura da ita da kuma yanayinta….. Farar budurwa ce, sai dai ba ƙal ba amman yanayin farin na ta mai tsananin kyau da ɗaukar hankali ne.. Zaune ta ke a cikin ajin sai dai zaman nata bai ɓoye yanayin halittarta ba…ta na da tsayi sannan ba ta da jiki amman ba za a kirata da ƴar siririya ba sakamokon yanayin ƙirar da Allah ya yi mata… Sannan kyakkyawa ce ajin farko, Yauma kamar kullum tun shigowar ta ajin nasu lecturern ya fahimci hankali da tunanin ta ba sa ajin, dan tun farko fara ɗecturen ya ga ta zabga Uban tagumi da Hannu ɗaya. Yana shirin ɗauke Idanunsa daga kanta kawai ya ga hawaye sun fara zubowa daga cikin idanunta! Wanda ya fahimci ita kanta ba ta san hawayen sun taho ba har sai da su ka samu nasarar sauƙa akan kumatunta tukunna ta ji ta fahimta, dan haka da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, kawai kuma sai ta fashe da kuka marar sauti. Har aka yi lecture ɗim aka gama aka ɗauki attendance bama ta san an yi ba Saboda yau ɗin zagewa ta yi sosai ta zubar da hawayen da suka tarar mata a ƙirji su ke bada gudunmmawa a ƙaruwar ƙuncin ta. Ta kuwa dan ji sanyi ba kaɗan ba ….. ‘’MANU!! Za mu wuce‘’ Muryar budurwar da ta ke zaune a gefen ta ta katse mata hawaye da ajiyar zuciyar da take ta faman sauƙewa a jejjere. Da sauri ta sa Hannu ta goge fuskarta, kafin ta ɗago. Ko kallon su ba ta yi ba, kawai ta ɗan matsar da ƙafar ta gefe domin su samu damar wucewan… Tana jin ɗayar ta ce ‘’Allah ya kyauta!! Kowa dai yana da damuwar nan daurewa kawai akeyi.” Bata da lokacin su, dan zuwa wannan lokacin abunda ya ke kanta ma ita kam ya ishe ta ya yi mata yawa ma, tunda gashi yau har da kuka tuƙuru ta yi a aji, dan haka ko shirin biyesu ma ba ta yi ba, ta barsu su ka wuce. Kafin itama ta ɗan sunkuya ta ɗauki koɗaɗɗiyar Jakarta tukunna ta miƙe, ba ta yarda ta kalli kowa ba, kawai ta nufi ƙofa. Ai kuwa kamar wata tv haka ragowar students ɗin suka bita da kallo, wasu ta basu tausayi wasu kuma ta basu mamaki! Dan tashi ɗaya duk wanda ya kalli fuskarta to ya san kuka ne ta yi. Gaba ɗaya duk sai ta ji ta muzanta ganin kalar yadda ake ta kallon ta.. Ta ji sauƙin raɗaɗin zuciyar ta tabbas amman kuma duk sai ta ji takaicin kanta na kukan da ta zage ta rasga a aji, dan haka tana fita ta wuce Ko ABBAKAR yau ba ta tsaya jira ba. Tana fara tafiya ta jiyo shi ya biyo ta a baya yana kiran ta “Manu ! Manu !! Manu!!!.” Sai da ta ɗan gyara fuskarta wai ita ala dole kar shima ya gane kuka ne ta yi! Tukunna ta ɗan tsaya ba tare da ta juya ba… a haka ya ƙaraso ya sameta a wajen ya na ɗan haki wanda ya ke nuni da sai da ya haɗa da gudu tukunna iske ta, ya na hakin ya ce ‘’Hope dai ba ki yi attendance ba. Kar Sir Najeeb ya ga sunanki biyu ya fito, ɗazu na ga kin sunkuyar da kanki s kuma na gefen ki da su ka gama basu tashe ki ba shine na rubuta miki.” Jinjina kanta ta yi kawai alamun ‘Eh’ Sannan ta sa Hannu ta ɗan goge fuskarta sam ta ƙi yarda ta kalleshi ita ala dole kar ya fahimci kuka ta yi. A hankali ta ce ‘’na gode abbakar ‘’ Murmushi ya yi kafin ya ce ‘’oh com on Manu! Na san fa kuka kika yi ’’ Girgiza kai ta yi, kafin ta ce ‘’Ban yi komai ba ‘’ Murmushi yayi mai ɗan haɗe da dariya kafin ya ce ‘’kalle ni ‘’ Bata ɗago ɗinba dan haka ya zagayo ya tsaya a gaban ta sosai ya tsare ta da Idanu ya na kallonta kawai kafin a hankali ya samu Bakinshi ya sake furta kalmar ‘Kalle ni ‘ Yanzun ma ba ta ɗago ba, suna a haka wani ɗan ajin su ya zo ya cw ‘’Yauwa ku nake nema… Sir Najeeb ya na kiran ku” Har ya yi gaba sai kuma ya dawo ya ce ‘’ I mean, yana kiran ta dan ita yace in kira but na san tare za ku je shiyasa na ce muku yana kiran ku ‘’ Ya fadi hakan yana dariya ƙasa-ƙasa sannan ya ɗaura da cewa ‘’Ku yi sauri yana ajin har yanzu’’ Kafin yace musu ‘’sai anjima‘’ Daga haka ya juya ya wuce.. Addua MANNUBIYA ta shiga yi…. Ta na roƙon Allah yasa ba wani abu serious bane ba, dan in dai ka ji kiran sir Najeeb tou ba alkhairi bane ba… Dan haka tashi ɗaya sai ta ɗan tsure! Wanda hakan ya sanya har ba ta ma jin Abbakar wanda ya ke ta yi mata magana har sai da ya sake cewa ‘’Manu. Kar fa ya haushi ‘’ Tukunna suka jera su biyun suka nufi ajin da suka gama lectures ɗin a cikinsa yanzunnan… Waya suka sameshi yana yi dan haka suka tsaya jira… Ya fi minti huɗu kafin ya yi sallama da wanda ya ke wayar da shi tukunna ya miƙe ya fara harhaɗa takardun shi… Yana haɗa takardun ba tare da ya kallesu ba ya cw ‘’Next time, idan kin san kuka da rashin maida hankali za ki yi mini a aji to kar ki sake shigowa‘’ Daga haka ya sa kai ya fice , ko haƙurin da suka fara bashi bai tsaya ya saurara ba…. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *03* Ya na fita Abbakar ya fesar da iska kafin ya ce ‘’Allah ya taimake mu…mun ci sa’a.” Dan tabbas shi kan shi ya ɗan tsorata kuma ya san ba ƙaramar sa’a su ka ci da sir najeeb ɗin ya bar Manubiya a iyaka warning bai ce kar ta sake shigar masa aji ba.” A hankali itama Manubiyan ta sauƙe numfashi, bata gama tunani ba ta ji ya ce ‘’Nima ina son ganinki. Bismillah, zauna.” Ya faɗi hakan yana nuna mata wajen zama, sannan shima ya nemi seat ya zauna dan zuwa wannan lokacin babu kowa a ajin. Shiruu ta yi kamar ba za ta zauna ɗin ba, sai kuma ta nema seat na kusa da ita row ɗin farko ta ja ta zauna tukunna ta ce ‘’Ina jinka.” Cikin rashin jin daɗi ya ce ‘’Manu, bana jin daɗin ɓoye-ɓoyen nan da kike yi mini kwana biyun nan, idan akwai wata matsalar da ban san da ita ba Talk to me…ki gaya mini, mu samu mu nemo mafita tare, ko kin daina trusting ɗina ne?” ya ƙarashe tambayar tashi a hankali yana mai kallon ta. Sai da ta sauƙe ajiyar zuciya tukunna ta ce ‘’Ba haka bane ba.’’ Cikin tarar numfashinta ya ce ‘’To yaya ne?’’ Girgiza kai kawai ta yi tana jin wani takaici ya na sake lulluɓeta, kafin ta ce “Kaka Mallan ne, ya ke so ya ɓullo da wani sabon issue.” A hankali ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya kafin ta ci gaba da cewa ‘’sai kuma Baraka itama…” Sai kuma ta ɗan yi shiru, chan kuma kawai sai ta ce ‘’Kaka Mallam ne ya ce wai in bar makarantar in yi aure.” Da sauri Abbakar ya ce ‘’what? Saboda me wai?” A hankali ta ce ‘’Nima ban san dalilin sa ba, kawai ya ga kwana biyu ciwon Inna ya motsa shine ya ke son sake ɗaga mata hankali ita da Baba…” Saboda In ba hakan ba meye zai sa ya ɓullo da wani case ɗin? Ai ya san Baba ba ya so ace ba za mu yi karatu ba,kuma ya san baya son yawan yin jayayya da su.” ‘’Ya kamata a yi wani abun akan wannan tsohon fa‘’. Abbakar ɗin ya ce cikin rashin jin daɗi. Sai kuma ya ɗaura da cewa ‘’me Baba ya ce?” Cike da damuwa ta ce ‘’Shiru ya yi, kuma ni har ga Allah ina jin tsoron shirun nan da ya yi… Ina Jin tsoro kar ya amince saboda ka san san shi baya son yin hayaniya da su.” Da sauri Abbakar ya ce ‘’Ba na jin Baba zai yarda su hana ki karatu fa, No matter what‘’ Cikin gyara zaman sa da bata dukkannin attention ɗin sa ya ce ‘’Ki nutsu ki daina ɗaga hankalinki dan Allah, ki kwantar da hankalinki kar ki damu inshaaAllah sai kin yi har PhD, kar ki taɓa bari tsohon nan ya hanaki walwala ya saka ki a damuwa, kalli yadda kike kuka a aji fa.” Ya ƙarashe maganar cikin rashin jin daɗi. Jin jina kai kawai ta yi, daga haka ta fara ƙoƙarin miƙewa. A hankali ya na kallonta ya ce ‘’Ita kuma Barakan mai ta yi?” Sai da ta ɗan kalle shi da kyawawan rinannun idanuwanta tukunna ta kauda kai gefe ta ce ‘’Ba komai ‘’ Daga haka ta miƙe tsaye. Da sauri shima ya miƙe ya ƙarasa gareta sannan ya ce ‘’Ya jikin Inna? An haɗa kuɗin kai ta asibitin?’’ Da sauri ta ce ‘’An haɗa” daga haka ta juya ta nufi ƙofar fita. Tun ɗazu dama ya so ya gano a inda main problem ɗin da ya sanyata kukan ya ke! Yanzu kuma yadda ta yi ya tabbatar masa da hakan…. Ya riga ya san ko me zai yi ba zata yarda ta karɓi sisi a wajen sa ba sannan ya fahimci Baraka ta kuma yin abunda ta fi komai ƙwarewa akai wannan karon ma! Inda ya ke da tabbacin ta ɓullo da wani abun ne ta amshe gaba ɗaya kuɗaɗen Haannun Ya Musbah… Ya rasa gane dalilin da ya sanya Baraka ta ke wannan rashin imanin, bai san menene a kanta ba! Bai kuma san dalilin da ya sanya Baba da Ya Musbah su ke biye mata suke ɗaga mata ƙafa ta ke tsula duk tsiyar da ta ga dama ba! Ganin da Abbakar ya yi Mannubiya har ta fice hakan ya sanya shima ya bi bayan ta da ɗan saurinsa, a ranshi kuwa ya riga ya gama yanke shawarar abunda ya kamata ya yi wajen taimaka mata domin a samu a kai Innar Asibiti.. Matar satin ta kusan ɗaya ta na fama da ciwonta wanda ya motsa mata, tabbas ya kamata ace ta je ta ga Likita. Yana fita ya hango ta har ta ɗau hanyar da zai sada ta da gate… Dan haka ya ƙarasa su ka nufi gate ɗin tare shi da ita. Ba gida zai yi ba shiyasa basu tafi gidan tare ba, amman sai da ya sanya ta a adaidaita sahu ya biya kuɗin kamar kullum tukunna ya juya shima ya tari tashi adaidaita sahun ya shige ya yi gaba…… Anguwar su ɗaya da Abbakar shine best frnd ɗinta…tun daga sakandire Abotar tasu ta yi ƙarfi, amma tun su na Yara su ke shiri dama. Abokanayen sa Maza har dariya su ke yi masa, dan tun yana ɗan mitsitsi ya ke wanke ƙafa ya tafi gidan su Manubiya wasa, tun Inna ta na hanawa har ta zo ta daina. Har kawo yanzu kuwa shi kaɗai ne Abokin ta tun da ita ɗin Ba kula ƴan unguwar su ta ke yi sosai ba saboda munafurce munafurcen su….. a makarantar ma ta ƙi yarda ta yi ƙawaye, dukda yadda ake son yin ƙawance da ita amma ita ta ƙi yarda, duba da yadda yaran su ke ƴan gayu a ganin ta idan ta biye su za a iya zuwa gaɓar da za ta kasa godewa Ubangiji na na’imomin da ya yi mata. gashi kullum idan aka je wajen cin abinci sai dai su yi ta biya mata kuɗin Ba wai suna complain bane kawai dai itace ba ta feeling comfortable (ta kasa sakewa da hakan) kuma ta san yau da gobe sai Allah shiyasa ta ke ta zizzillewa. Tun suna yi mata naci tana zillewa har suka haƙura suka rabu da ita. Su suna ganin girman kai gare ta, yayinda Ita kuma a nata ganin bai kamata ta ɗaurawa kanta abunda ya fi ƙarfin ta ba, Matsalar ta ma ita kam ta isheta. Tana wannan tunanin mai Adaidaita sahun ya ƙaraso cikin layin nasu wanda ke a Anguwar ‘Gadon ƙaya’,. Ita ta nuna masa ƙofar gidan ya yi parking daga haka ta fito ta nufi gidan bayan ta ce masa ta gode . Tun a kallo ɗaya, in aka yi wa gidan ya ke faiyyace daɗewarsa a doron ƙasa, sannan bai ma san me ake nufi da renovation (sabunta gini) ba. Katangar gidan both side sun tsatstsage, yayin da fentin ya goge gaba ɗayan shi! Ba’a ganin komai sai jar ƙasar ginin gidan wanda ya baiyyana daga tsakiya zuwa ƙasa, ta saman katangar kuma ragowar farar ƙasar fentin da bata gama gogewa ba ce itama duk ta yi dishi-dishi, sai zanen Yara na shirme wanda akayi da baƙin gawayi, duk a jikin katangar. Normal ƙaure ne a gidan sai dai shima ya ji jiki matuƙa…… Tana ƙarasawa jikin kyauren ta kama ta tura ƙofar ta kutsa kanta cikin gidan… Dama tun daga waje yanayin gidan ya ke nuna Babban gida ne, saboda yanayin faɗin tsayin katangar… Ta wani dogon soro ta bi kafin ta ƙarasa ainihin cikin farfajiyar gidan! A ta farko-farko gefen dama babban kitchen ɗin gidan ya ke wanda murhu da kurfeti suka cika shi taf ta inda hakan ya ke nuni da kowa girkin shi ya ke yi a daban. Farfajiyar asalin cikin gidan kuwa ɗauke ta ke da fanni-fanni wajen guda takwas! Wasu sabbi ƙal ginin zamani wasu tsofaffi tukuf ginin ƙasa Wasu manya ne domin tun daga kallo ɗaya in an musu an san za su ƙunshi wajen ɗakuna uku sannan a ciki har a samu parlour ma sai kuma masu ciki da parlour, yayinda wasu kuma ɗaki ɗaya ne kawai sai banɗaki….. Ginin daya fi ko wanne tsufa kuma ɗaya daga cikin jerin ƙananun buildings ɗin Manubiya ta nufa, tana zuwa dai-dai bakin ƙofar ɗakin ta sa Hannu ta ɗaga labulen ta shiga ciki da sallama. Babban ɗaki ne sosai da manya manyan taga guda biyu suna kallon juna sai ƙofar banɗakin da ta ke a chan kusurwar ɗakin. Ƙatuwar katifa ce kawai a yashe a gefe cikin ɗakin. Sai babban wardrobe na katako.. Laidar ɗakin bata wani yayyage ba ammanfa ta ji jiki dan ta yi laushi matuƙa…kallo ɗaya za a yi mata a fahimci takatsantsan da kula ne kawai su ka kawota war haka ba ta fatattake ba. Wata farar budurwa, fara ƙal, ce, zaune a kan katifar ƙafafunta su na ƙasa. dududu budurwar ba za ta wuce shekaru sha bakwai a duniya ba, sai gefen ta kuma wata dattijuwar mata ce kwance a kan katifar, budurwar na yi mata fifita. Tun a kallo ɗaya yanayin Matar ya ke nuni da abun tausayi dan sosai ta ke jin jiki, a zahirance da baɗini. Saitin su kuma wani dattijon tsoho ne zaune da wani Yaro a gefen shi, Yaron ba zai wuce shekaru sha ɗaya a duniya ba, dattijon kuma ba wani mai shekaru bane a baɗini a zahirance ne kawai tsufanshi ya fito ya baiyyana muraran saboda yanayin rayuwa. Fuskokin su gaba ɗayasu, babu walwala! Kowa ya yi jigum, ana ta tunani, Ba ma su san Manubiyan ta ɗaga labulen ba har sai da su ka ji sautin muryarta, sanda ta shigo da sallama. Jidda, wadda ke zaune a kusa da Inna ce ta ɗago ta kalle ta a hankali ta ce ‘’har kin dawo? Sannu da zuwa.’’ Jinjina kai kawai Manu ta iya yi kafin ta juya ta kalli Muhsin wanda ya ke yi mata sannu da zuwa shima, ta yi masa wani guntun murmushi tukunna cikin nutsuwa ta ƙarasa ta durƙusa a gaban Baba ta ce ‘’Baba Ina wuni.’’ Kamar ba zai yi mata magana ba sai kuma ya ce ‘’Mai yasa baki ɗauki kuɗin motar da na ajjiye miki ba? Bana ce miki munada kuɗin abun karyawa ba?. Mai yasa kike da taurin kai ne?’’ ya jero mata tambayoyin a jere kafin ya ɗaura da cewa ‘’Ce miki akayi nan da b.u.k ɗin tafiyar wasa ce?” Ya ƙarashe tambayar ta sa ta ƙarshe cike da rashin jin daɗi da takaici. A hankali ta sunkuyar da kanta ƙasa tukunna ta ce ‘’ka yi haƙuri Baba ba zan ƙara ba.’’ Sai da ya ɗan fesar da iska tukunna ya kauda kai gefe ya ci gaba da tunanin da ya ke yi kafin ta shigo. Su Jidda ta juya ta kalla kafin ta ce ‘’Ya jikin nata?” Da kyar dan sai da ta haɗiye wani abu wanda ya tokare mata maƙoshi tukunna Jidda ta ce ‘’Da sauƙi. Alhamdulillah .’’ A hankali Manu ta ce ‘’Allah ya ƙara sauƙi.’’ Kamar Muhsin zai fashe da kuka haka nan ya ɗago ya kalli Manubiyan kafin ya ce ‘’Adda Manu, sai da fa ta kuma suma da ki ka tafi makaranta ɗazu’’. Shiruu ta yi chan kuma sai ta sunkuyar da kanta ƙasa, wanda hakan ya bawa hawaye damar fara gangaro mata… Haka ita ma Jidda ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fara nata kukan… Ganin hakan ne ya sanya shima Muhsin ya fara nashi kukan…. Haka nan suka tusa Baba a gaba kowa ya na hawaye. A hankali Baba ya zaro wayarsa daga aljihu ya danna kiran Ya Musbah… Kamar ɗazu yanzun ma wayar a kashe! dan haka ya ɗago ya kalla Jidda bayan ya maida wayar cikin aljihun malun malun ɗin da ke a Jikinsa ya ce ‘’Maijidda kikace ɗazu ya ce miki Mu jira shi zai zo ko?’’ Sai da ta ɗan yi shiru tukunna a hankali ta gyada masa kai sannan ta ce ‘’Eh, Baba.’’ Tsaki ya yi daga haka ya miƙe tsaye ya ce ‘’Muhsin taso mu je .’’ Da sauri Jiddan ta ce ‘’Baba ka bari ni in sake komawa, in dubo shi, ba sai ka je ba.’’ Kallon ta ya yi kamar ba zai ce wani abun ba Sai kuma ya ce ‘’kar ki damu! yanzu za mu je mu dawo InshaaAllah… Ina son ganawa da shi.’’ Daga haka ya kalli Manubiya ya nuna mata gurasarta wadda suka ajjiye mata a cikin kwano ya ce “ki tabbatar kin ɗauka kin ci.” Sannan ya sa kai ya fice cikin tafiyarsa da ke baiyyana nakasar da ke tare da shi, dan ƙafa ɗaya gareshi yayinda ɗayar ta kasance ta roba. Ya na fita Muhsin ya mara masa baya da hanzari, dan shi ma Yaron hankalinsa a mugun tashe yake, Allah Allah kawai yake a san yadda za a yi a kai innar tasu asibiti, dan jikin nata ya tsorata kowa! Babba da Yaro. Suna fita Manubiya ta miƙe ta cire hijabin Jikinta. Daga haka ta ƙarasa inda su Innar su ke, (ita da jidda). Sai da ta tabbatar innar bacci ta ke yi tukunna ta kalli Jiddan ta ce ‘’Mai ya faru ɗazu da kika je gidan? kin gan shi?’’. A hankali Jidda ta share hawayen da su ka zubo mata. Kafin ta shiga koro mata bayanin yadda su ka yi…. Da yadda Ya Musbah ya ce kawai ta zo gida, su jira shi. Gashi kuma har yanzun bai zo ba. Shiruuuuu, duk su biyun su ka yi! Ko wacce zuciyarta babu daɗi. Suna kuma tunanin a ina za su je su samo kuɗi! Dan sun san tunda Ya Musbah ya fara wasar ƴar ɓuya da su tou shima bashi da yadda zai yi ne. A take zuciyar Manubiya ta fara bata shawarar ta cire kunya kawai ta gayawa Abbakar gaskiya, ta san zai taimake su. ……… A ƙofar gidansa su Baba su ka hango shi. Kamar wani saurayi haka yanayi da jikinsa ya ke, sam bai yi kama da magidanci ba. Fari ne sol kyakkyawan gaske, bai cika tsayi ba amman yana da faɗin ƙashi. Cikin sanyin jiki Baba da Muhsin su ka ƙarasa inda Ya Musbahn ya ke alwallar sallar Maghrib ɗin da ta gabato, shi da wani maƙwafci kuma Abokinsa mai suna ‘Nafi’u’. Cike da girmamawa shi da Abokin nasa su ka gaida Baba. Kafin Abokin ya cewa Ya Musbah ‘’Bara in wuce. In fara karatu kafin ku kammala.’’ Jinjina kai kawai Ya Musbah ya yi, dan gaba ɗaya hankalinsa a mugun tashe ya ke, ga shi ya ga Baban sai wani irin kallo ya ke ta yi ma sa wanda ya kasa gane ma’anarsa. Rashin sanin abun yi da kame-kame ne su ka sanya shi cewa ‘’Bismillah Baba Mu shiga daga ciki ko?’’ Sai da Baban ya sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya ce ‘’Naa shiga kuwa?’” A hankali Ya Musbah ya ce ‘’to ko soro ne ka shiga dan Allah. Akwai bayanin da na ke so in yi maka ne.” Ba dan Baba ya so ba! Ya Kama Hannun Muhsin su ka bi bayan Ya Musbah. Anan soron kuwa ya shimfiɗe musu tabarma….. Dan a wannan lokacin bai isa shigar da su cikin gidan ba! Daff da zuwan su Baban Nafi’u ya gama yi musu shari’ah shi da Baraka! Saboda kawai Jidda ta zo ɗazu, shikenan tunda Yarinyar ta zo ta tafi Baraka ta ke ta bambami ‘Wai ta zo har gida ta yi mata rashin kunya!!!!’ Kuma sarai ya san ƙarya ta ke yi! Kawai ta na neman hanyar da za ta bi ta datse zuwan ƴan uwan nasa gidansa ne! Gaba ɗaya. Bayan a yanzu kamata ya yi ma ace shi ya ke riƙe da Jidda ko Manubiya….. ‘’Tunanin mai ka ke yi???’’ Muryar Baba ta Katse ma sa tunani. A hankali ya sauƙe ajiyar zuciya! Ya na shirin yin magana Baban ya sake katseshi ta hanyar cewa ‘’Innar ku har yanzu ta na kwance, babu kuɗin magani, babu na zuwa asibiti. Musbahu! Kai ne ka hanani aikin ƙarfi, Sannan kai ne ka ce ƙannen ka Mata ba za su yi Aikatau ba wanda ba daban hakan ba na san da yanzu mun san yadda mu ka yi aka kai ta asibiti. Tun shekaran jiya mu ke ta tsammanin ka! Ka kashe wayarka kuma ka ƙi ka yarda ka zo inda muke. Wanda in m kuɗaɗen ne ba su samu ba a gani na dai a ya kamata ace ka zo ka duba Mahaifiyar ka dai ko?’’ Cikin yin ƙasa da murya sannan a hankali Ya Musbah ya ce ‘’Baba, kalli fa ƙafar ka. Ba za ka iya aikin ƙarfi da ita ba! Ina tsoron ka saka mata nauyi da yawa haka nan mu je Itama ƙwaya ɗayar wadda ta rage maka ya zamana itama ta samu matsala. Su Manubiya kuma ba wai girman kai bane ya sanya na ce ba za su yi aikatau ba! Kawai a ganina bai kamata ace ina raye muna zaune a unguwa ɗaya amman ace ƙanne na Mata su ne za su na kula da iyayena, ba. Dan Allah Baba ka yi haƙuri, ka bar maganar dakon da ka ke so ka yi, da duk ma wani aikin ƙarfi. In sha Allahu zan yi ƙoƙari in san yadda za a yi. InshaaAllah zan iya kula da kowa. Kuɗin asibitin ma na nemo, ba wai ban nemo ba! Amman sai jikin Baba ƙarami ya ɗan mot……’’ Shiru ya yi kafin ya ci gaba da cewa ‘’Amman karka damu Nafi’u ya yi wa ɗan uwansa magana kuma ɗan uwan ya ce za’a san yadda za ayi… Mu jira shi zai kawo kuɗin. Shiyasa ma ka ga ban zo ba saboda bana so in zo muku ba tare da kuɗin ba. Shi nake ta jira na fi so in ya zo ya bani ni kuma sai in zo a kaita asibitin‘’. Sai a sannan Baraka wadda ta laɓe musu tun ɗazu ta shigo cikin soron. A hankali ta ƙarasa inda su ke ta zauna! Cikin ladabi ta gaida Baba. Inda ya amsa mata da Kulawa ya na mai tambayarta “Ina takwaran sa” ta ce masa “yana ciki yana barci.” Da ladabi Muhsin ya gaida ita ta amsa daga nan soron ya ɗauki shiruuuuu, kafin a hankali sautin kukan Baraka ya soma tashi. Da sauri Baba ya ce ‘’Subahanallah, Baraka lafiya? Mai ya faru?”. Cikin kukan da kyar ta ɗan tsagaita sannan ta ce ‘’Ba komai Baba, ba komai. Ku yi haƙuri, suɓuce mini ya yi.’’ Tana gama faɗin haka ta fara ƙoƙarin miƙewa. Cikin ɗan tsare gida Baba ya ce ‘’Koma, koma Baraka. Koma ki zauna’’. Ya bata umarni ransa duk babu daɗi. A hankali ta koma ta zauna ta na ɗan satar kallon Ya Musbah wanda ya haɗe rai! Yana ji kamar ya rufe ta da shegen duka. Cikin kulawa Baba ya shiga rarrashin ta…. Har sai da ta yi shiru tukunna ya nemi ta faɗa masa me ke faruwa. Cikin yin ƙasa da murya ta fara zaiyyane masa cewa “dama kwanakin baya ne Ya Musbah ya karɓi kuɗinta, kuma itama kuɗin ba nata bane ba na wata ƙawar Mamanta ne To a halin da ake ci Maman tata ta biya rabi, amma ta kasa biyan rabi shine ƙawar ita Mahaifiyar tata ta ce ‘za ta je da ƴan sanda ta tafi da Mahaifiyar tata’. Tun jiya ta ke bin Ya Musbah akan ya bata kuɗin shi kuma ya ƙi ya bata, yanzu gashi ƴan sandan sun je za’a tafi da Mahaifiyarta.….” Shiruuu Baba ya yi, da jin batun Baraka. Kafin ya miƙe tsaye ya kama Hannun Muhsin. A hankali ya kalli Ya Musbah ya ce ‘’Musbahu, idan an kawo kuɗin da akayi maka alƙawari ka bata.’’ Da sauri Ya Musbah ya ce ‘’Amman fa Baba..’’ Cikin katse sa ya ce ‘’Bana son musu! Sannan bana son ja-in-ja! Ka bata kawai. Kar ka damu, zan san abun yi ‘’. Tukunna ya kalli Baraka wadda ta yi kalar tausayi ya ce ‘’Kar ki damu, ba za a tafi da Mahaifiyarki ki ba. Inada mara lafiya a gida, shiyasa ba zan iya bin ki mu je in ga komai ya lafa ba. Yanzu ki yi sauri ki je wajen ta, Musbahu zai biyo ki da kuɗin InshaaAllah. In basu cika ba ma In na san yadda nayi na haɗa kan ƴan kuɗaɗe na kashe wutar gaba na… Ki yi mini magana sai in cika miki ‘’. Yana gama faɗin haka ya jaa Hannun muhsin su ka fice daga soron. Cikin ɓacin rai Ya Musbah ya kalle ta kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya miƙe shima ya fice! Ya bi bayan Baba ranshi a mugun ɓace!. Yaso ya fahimtar da Baba a samu ya yi haƙuri ya karɓa kuɗin ya bar batun Baraka! Amman furr Baba ya ƙi sauraron sa, karshe ma faɗa ya rufe sa da shi! Sannan ya ce “ya koma kar wanda zai kawo masa kuɗin ya zo bai same shi ba, kuma Wallahi idan ya sake karɓarwa Baraka kuɗinta sanna ya hana ta tabbas ransa sai ya yi mugun ɓaci.” Ganin yadda ran Baba ya ɓaci sosai ne ya sanya kawai Ya Musbah ya haƙura…. Sannan ya ba shi haƙuri, daga nan ya juya ya nufi hanyar gidansa. Bai shiga ba! direct masallaci ya wuce, ana idar da sallar ɗan uwan Nafi’u ya kawo kuɗin kamar yadda ya alƙawaranta. Ya Musbah, ji ya yi kamar ya cewa ɗan uwan Nafi’un kawai ya bar kuɗin ya fasa ranta…. Dan ya san idan ya sa Hannu ya karɓa kuɗin ya baiwa Baraka To fa bai san ranar biya ba, gashi yana tsananin jin kunyar Nafi’u wanda ya ke bin sa bashin kusan dubu ɗari kuma bai san ranar biya ba….. Gashi yanzu na ɗan uwansa shima ya fara hawa kan shi. Dama saboda ya ga na asibitin Mahaifiyar sa ne Shiyasa kawai ya rufe ido zai karɓa…… Kamar Nafi’un ya san me Ya Musbah ya ke tunani. A hankali ya dafa Abokin nasa wanda suka taso tare tun ƙuruciya ya ce ‘’Ka kwantar da hankalinka. Kar ka damu! Ko yaushe ne in ka samu kana iya biya.” Sai da ya ɗan sauƙe ajiyar zuciya tukunna a hankali ya sa Hannu ya karɓi kuɗaɗen, waenda ko bai ƙirga su ba ya san ba su fi naira dubu goma ba! Ya so ace sun ɗan fi haka da sai ya bawa Baraka dubunta goma ragowar kuma a yi hidimar asibiti da shi… Godiya Sosai ya yi har sai da ya bawa ɗan uwan Nafi’un kunya ma. Daganan Mutumin ya yi musu sallama ya burga mashin ɗin sa ya wuce, ya barsu anan tsaye. Kafin suma su ka juya a tare su ka nufi ƙofofin gidajen su…. Har su ka ƙarasa ƙofar Gidanjen nasu guda biyu.. Ya Musbah tunani kawai ya ke ta yi… Tausayin sa Nafi’u ya ke ji sosai dan ya san in ba matsalar Baraka ba tou matsalar rashin lafiyar Mahaifiyar su ce ta sanya shi a damuwa haka. Yana shirin yi masa magana ya ji Ya Musbah ya ce “Nafi’u kuɗin nan fa Baraka zan bawa‘’. A ɗan fusace Nafi’un ya ce ‘’Saboda ka zama Mijin ta ce?’’ Ya Musbah, bai ɓoyewa Abokin nasa komai ba haka ya zaiyyane masa abunda ya faru… Sannan ya ƙara da cewa ‘’Ba wata maganar ƴan sanda, Biki ne take da shi! tsabar bala’i wai ankon super za su yi! Me sunan Baba kan sa ta yi masa kaya masu kyau da tsada sama da kala uku! Amman saboda Allah ace wai Mahaifiyata bata da lafiya amma sam Baraka ta kasa mini kara, kwata-kwata ba ta damu ba….’’ Ya ƙarashe maganar hawaye su na silalo masa. Da kyar Nafi’u ya iya danne fushin sa, gudun kar ya sake tunzura Abokin nasa. Sai da ya ɗan daidaita kan sa daga takaicin Baraka, tukunna a hankali ya dafa shi sannan ya ce Ka yi haƙuri Musbah! Komai in ya yi zafi to maganin sa Allah. Tunda ta yi maka haka kuma Baba ya ce a bata to kawai a bata ɗin. Ita ta sani, in dai duniya ce, dai dai ta ke da ita. Kawai yanzu matsalar ita ce inda za mu nemo wasu kuɗin. Saboda nima Wallahi babu a waje na, da ace ina da shi da na baka. Ka san lokacin biyan kuɗin gida ya yi, Mutumin nan sam ni baya taɓa ɗaga min ƙafa, har gara kai ma ya ce ai ya san baka aiki…. Gashi wannan term ɗin Khairat ta shiga makaranta shiyasa nima duk na zama a matse, ba ni da shi.” Shiru ya ɗan yi kamar me tunani kafin ya ci gaba da cewa ‘’kuma kaga yaya na guda ɗaya tak a duniya na tambaya maka shi shima amma bara muga ko akwai….’’ Da sauri Ya Musbah ya katse shi ta hanyar cewa “Nafi’u kar ka damu. Na gode wallahi ban san da wanne Baki zan yi maka godiya ba. Ba na jin akwai Aboki irinka har yanzu a duniyar nan in har kuma akwai tou tabbas ba ku da yawa. Nagode nagode. ka kwantar da hankalinka, bara inje in bata kuɗin. dole haka zan haƙura in leƙa Innar babu ko sisi! Idam na je ɗin sai a san yadda za a yi’’. ‘’Ok’’ Nafi’un ya ce, cikin rashin Jin daɗi. Kafin ya sake cewa ‘’Nima bara in duba gida, Idan komai normal sai mu tafi wajen Innar tare….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *04* Ba kunya ba tsoron Allah haka Baraka ta sanya Hannu ta amshe kuɗaɗen nan, duk da kuwa ragowar kwallar da ta gani a Idanun Mai Gidan nata wanda hakan ya tabbbatar mata da kuka ya yi! Dan hatta ga jijiyoyin gaban Kansa sun fito raɗau! Ga kuma farar Fuskarsa itama ta yi jajawur gaba ɗayanta. Ka na ganinsa ka san yana cikin tsananin tashin hankali. …… Tana amshe kuɗaɗen ta shige cikin parlournsu mai ɗauke da ɗakuna biyu, dama fitowarta daga banɗaki kenan ta ganshi tsaye da kuɗaɗen yana jiran ta. Ya daɗe tsaye a wajen, kafin ya samu ya iya jan Ƙafafuwansa ya juya ya fice daga cikin gidan, gabaɗaya. Sai a sannan ta bar bakin windown inda ta laɓe tana kallon sa tana mai taɓe Baki! A fili ta ce ‘’Haka kurum in bada kuɗaɗena a kai uwar wani ba tawa ba asibiti, bayan ga biki a gabana…. Idan na biye maka Musbahu naga alamun sai na gagara shiga cikin ƙawayena watarana wallahi. Da mutunci na da kyalli na ka auro ni amma iyakar inda ka ajjiye ni da suturun da ka jere mini a lefe ya sanya yanzu ko hamshaƙiin taro idan za a yi ƙawayena basa gaiyyata ta! Yo ina dalili fisabilillahu.’’ Hakanan tayi ta mita ita kaɗai daga ƙarshe ta shiga kasafta mai da me zata siya da kuɗaɗen…… Tun lokacin da suka rabu da Ya Musbah, ‘Baba’ ya ke tunanin ta Ina zai samo kuɗi , duk inda ya duba ya zaga ya zagayo babu hanya! Hakan ya sanya gaba ɗaya hankalinsa ya sake tashi!!! A haka suka yi alwallah su ka yi salla shi da Muhsin daganan suka fito daga masallacin suka zauna akan ɗan dakalin ƙofar gidan. Yana cikin tunani ya ji wasu zafafan hawaye suna zuba akan kyakkyawar tsohuwar Fuskarsa… Sai da ya faki idon Muhsin wanda ya yi shiruu shima ya sunkuyar da Kansa ƙasa tun ɗazun da su ka zauna tukunna ya sanya Hannu ya share Hawayen nasa kafin a hankali ya faɗa duniyar wani tunanin na daban .. <<<< Yanzu haka, a tsakiyar ƴan uwansa yake! Babban yayansu BABA HABU da Matansa guda biyu Umma DIJE da Umma KULUWA Umma dije Ƴaƴanta mata uku Zainab, Hauwa sai Maryam, gaba d’ayan su sun yi aure. Sai Umma Kuluwa tana da Yaro ɗaya Namiji ‘Ya Yusuf’ wanda ya girmi Ya Musbah da shekara ɗaya amma shi bai yi aureba. Sai ɗayan Yayan nasa UTHMAN Wanda kowa yake kiran sa da UNCLE Uncle yanada mata uku Kasancewar yana aiki a banki ya sanya duk ya ɗan fi su rufin asiri Matarshi ta farko FATIMA Umma Fati Yaro ɗaya tak ta Haifa Ya iliya (yayi aure)daganan ta samu matsala bata sake haihuwa ba ta biyun sunanta Khadija Ita kam ko ɓatan wata ma bata taɓa yi ba. Sai ta ukun Anty RUMASATU (Anty amarya) tanada Ƴaƴa biyu mata twins Shamsiyya da Salaha masu shekaru goma a duniya. Sai Yayarsa Anty Umma (Binta), wadda Mijinta ya rasu ta komo gidan da zama Ƴaƴanta biyu Mata ta farkon sunan ta Fiddausi tana aure a illorin sai autar ta wadda ta ke tare da ita ‘Siyama’ Siyama ta girmi Jidda Manubiya kuma ta bata shekara ɗaya. Sai shi Baba (MUSA) Matarshi ɗaya Aminatu (Inna) Da Ƴaƴansa huɗu! Na farko Musbahu mai shekaru 27 Sai Manubiya mai shekaru 22 Sai Maijiddah mai shekaru sha bakwai Da auta Muhsin wanda bai ƙarasa rufe shekaru sha ɗaya ba. Duk a cikin ƴan uwan nan nasa(Baban) da suke zaune tare a gida ɗaya babu wanda zai tambaya kwandala a cikinsu yau ace ya ɗauuka ya basa! Idan ana maganar asalin rashin haɗin kai Tou shine definition(ma’anar) rayuwar Baba da ƴan uwansa!. Babu hassada babu faɗa babu hayaniya a tsakaninsu amma fa kowa na sa kawai ya sani, hatta Anty Umma, kaff cikin yayun nasu Maza babu mai ciyar da ita kuma sunada rufin asiri ba wai babu ba amma sai dai ta ci da kanta ta ci da ƴarta (Siyama) Da taimakon ƴar sana’ar siye da siyarwar da take yi, sai kuma Yayar Siyaman itama tana taimakawa ba laifi. A taƙaice dai kowa ta kansa yake yi a gidan…kowa nasa kawai ya sani, sannan babu ruwan kowa da kowa. Yanayin zaman sam babu daɗi. Ga baki ga hanci..compound ɗaya amma idan ba su Manubiyan ba babu me leƙawa ya ga ɗan uwansa idan wani abun ya faru domin a ji ko a ga halin da yake ciki. Mai ƙananun maganganu, rigima da son haɗa faɗa a gidan Mutum ɗaya ne ‘Kaka Malan’ Wani ɗan uwan Mahaifinsu da Allah bai ba shi haihuwa ba suka ɗauko suka bashi ɗaki mai banɗaki a cikin compound ɗin nasu. Wanda shima sai ya yi da gaske tukunna ake kula shi ake zuba masa abinci, dan Kaka Mallan irin tsoffin nanne masu tijara, gulmace-gulmace, shishshigi da zalama. Su kam ragowar Mutum gidan a tsakanin su babu jita-jita! Sai dai sam basa tausayin juna, basa kuma taimakawa juna… A yanayi da tsarin gidan ‘Idan ɗan uwanka zai kwana bai ci ba! Babu ruwanka, ba abunda ya shafeka bane ba.’. Tun suna Yara, su uku. Mahaifinsu ya zaunar da su ya tambaye su ‘abun da kowa ya ke son yi a rayuwa….’ Ƴan uwan Baba (Yayyunsa Maza su biyu) Uncle da Baba Habu suka zaɓi karatu Shi kuma Baba ya zaɓi Sana’a. Kamar yadda Mahaifin nasu yayi alkawari kuwa Karatu har sai da Uncle da Baba Habu su ka ce “sun gaji!” Shi kuma Baba aka damƙa masa maƙudan kuɗaɗe aka ce ya je ya yi Sana’a. Sai dai kuma abun nashi kamar sa Hannu!! Dan duk sana ‘ar da ya soma bata albarka! A haka har jarin na sa ya ƙare tass!!. Uncle, Baba Habu da Anty Umma Mahaifiyar su ɗaya Yayinda shi kuma Baba ya kasance ɗan gidan Amarya. Mahaifiyarsu Uncle ce ta fara rasuwa kafin tashi Mahaifiyar wadda ta rasu wajen haihuwarsa. Tun suna Yara sun taso basu da wani haɗin kai. Tun lokacin da Iyayen nasu Mata suka rasu Mahaifinsu bai ƙara aure ba shima har ya bar duniya. Hakanan suka tashi a wannan gida wanda suka gada kowa yayi aurenshi yake yin rayuwarshi daga shi sai iyalinsa. Duk cikinsu shine (Baba) mai ɗan ƙaramin waje sakamokon siyar musu nashi portion ɗin da ya dinga yi saboda ya samu ya sake jan wani jarin sannan kuma aci abinci a gidansa. Ko da ya haifi Musbahu, Yaron ya kai minzalin hankali Baba ya so ya ɗaura shi akan layin sana’a shima, har rantar kuɗi ya dunga yi yana bashi jari amma shima sam sanar tashi bata yi Albarka ba! Ganin sana’ar ba zata yiu ba ya sanya suka haƙura!. Da ragowar ƴan kuɗaɗen Hannunsu waenda basu wani kai sun kawo ba Baba suka haɗa suka fara makanikanci dan a lokacin shekarun Musbahu sun kai sha bakwai babu damar komawa makaranta. A wannan lokacin ne kuma Allah ya ɗaurawa Baba Musa tsananin son yaga Ƴaƴansa sun yi karatun… Haka ya sanya ya tsaya tsayin daka akan karatun nasu, dan bai yi ƙasa a guiwa ba wajen sanya su a makaranta. A lokacin Manubiya har dariya ake yi mata dan ta yi girma a ajin Yara! Saboda tare ya haɗa ya sanyasu su uku aji ɗaya Manubiya Muhsin da Jidda Duk a aji ɗaya. Hatta jidda a lokacin ta yi girma a ajin, amma sam Yaran(su Manubiyan) basu wani damu ba Saboda suma suna tsananin son karatun! Sannan suna da tsananin ƙoƙari da naci akan karatun, hakan ya sanya cikin ikon Allah hazaƙar su ta sanya aka dinga yi musu double promotion wanda har ta kaisu ga taddo sa’o’insu. Da farko private suka fara amman yanayin rayuwa ya sanya dole Baba ya maida su ta gwamnati wanda duk gidan su kaɗai ne su ke yin karatu a makarantar gwamnati. Jamb ne ya so bawa Manubiya matsala amman waec ɗinta da neco har mamaki ya dunga bawa mutane saboda yanda ta fito da flying colours. Rashin cin jamb ɗin da bata yi bane ya sanya ta shiga poly ta yi diploma tukunna ta wuce BUK da D E , yanzu haka tana level 3 suna karantar English ita da Abbakar wanda suke karatun tare da shi tun a poly shine kaɗai Abokinta har gobe kuma shi ɗin ne, bata da ƙawa mace…. Saboda yanayin rayuwarta da ta zauna ta duba sai ta ke ganin kamar ƙawance ba nata bane ba kullum Kayanta a koɗe! Gashi ko kuɗin handout wani lokacin sai dai ta ara ta yi karatun a iya makarantar Sannan idan an zo tafiya cafeteria (wajen cin abinci) sai dai ta gudu Dan indai an je sai dai a siya mata ba dai ita ta siya da kanta ba! Shiyasa da ta fahimci rayuwa ba zata yiwu a haka ba sai ta shafawa kanta lafiya. Abubakar ne kawai Abokinta, anan unguwar tasu yake bayan layin su… Mahaifiyarshi ƙawar Maman Baraka ce! Tare suka buɗe gidan abincinsu tun shekarun baya da daɗewa… Jidda kuma wannan shekarar ta zana waec, ta ci itama kuma cikin Ikon Allah ita taci har jamb, yanzu saura mata post utme. Muhsin kuma yana js2 tun last year, yanayin rayuwa yasa ya kasa ci gaba da karatun. >>>> ‘’Baba Ina wuni” Muryar Abbakar ta katsewa Baba tunanin da yake yi. A hankali sannan a ɗan ɓoye ya sake goge Idanuwansa tukunna ya juya yana kallonsu shi da Muhsin. Da kulawa ya amsa shi yana tambayar sa ya Mamansa shi kuma Abbakar ɗin yace masa ‘’tana lafiya’’ kafin cikin yin ƙasa da Kai ya ce ‘’Baba ɗazu a aji ana ta bayani amma sai na lura sam hankalin Manubiya baya a ajin…. daga baya ma sai na fahimci ashe kuka take yi. Na so in taimake ta dan na san akan rashin lafiyar Inna ne amma sam sai ta ƙi yarda. Dan Allah Baba ga kuɗi nan na bawa Muhsin a kai Innar asibiti dasu.. Kar kace a’a, nima kamar uwa Inna take a waje na” Sai da ya ɗan yi shiru tukunna a hankali ya ɗaura da cewa “Allah ya bata lafiya, ya kawo mata sauƙi’’ Yana gama faɗin haka ya musu sallama ya juya ya wuce… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *05* Sai da Muhsin ya ɗan taɓa Baba tukunna ya yi fir-gi-git ya ce ‘’Na’am.’’ Sai kuma ya fara neman Abbakar ɗin amma sai yaga babu shi babu alamun sa… A hankali ya cewa Muhsin ‘’ka je gidansu, ka ce masa na gode! Sam banga wucewar sa ba.” ‘’To’’ Muhsin ya ce, kafin ya miƙa masa kuɗin ya na mai cewa ‘’gashi.’’ Sai da kwallah ta zubowa Baba kafin ya sanya Hannu ya karɓa tukunna ya miƙe ya wuce cikin gidan da sauri…. Muhsin kuma ya wuce gidan su Abbakar. Kusan karo suka yi shi da Manubiya wadda ta fito da gudu! Suna haɗa idanu da Baban nata sai ta fashe da kuka ta fara waiwaye, tana nuna masa ɗakin tana juyowa tana kuka wiwi, tama kasa yin magana. Da sauri ya wuceta ta bisbi a baya, suka ɗunguma zuwa ɗakin. Abunda yayi tunani ɗin ne kuwa!! Dan haka ya durkusa ya fara ƙoƙarin kinkimar Inna wadda ta sanƙame Idanuwanta suka ƙaƙ-ƙafe… dai-dai nan Ya Musbah ya shigo ….. .. Allah ya taimake su Nafi’u ya taho da Motarsa 206, dan haka aka saka Innar a ciki, suka wuce zuwa asibitin su huɗu: Baba, Ya musbah, Nafi’u wanda ke driving da Innar. Rashin gurin zama da kuma jiran Muhsin ne ya sanya su Manubiya suka haƙura ba don sun so ba, amman har waje bakin ƙofa suka biyo su kowacce tana kuka, sai da suka ga wucewar su tukunna suka fara ƙoƙarin komawa ciki da kyar…. Ba su kai ga komawar ba..a nan bakin ƙofar gidan su Baba Habu shi da Uncle wanda dawowar sa kenan daga parking motarsa a gidan makwafcin su, inda yake ajjiyewa kullum, su ka iskesu. Gaisuwarsu kawai Uncle ya iya amsawa daga nan ya shige ciki ya barsu tsaye su da Baba Habu, wanda shima ɗin ya fara ƙoƙarin shigewa ciki kamar ba zai tambaye su ba, sai kuma ya ce musu ‘’lafiya kuwa?’’ Jidda ce ta iya bashi amsa dan ita Manubiya haushin sa take ji saboda son zuciyar da ya ɓullo da shi kwana biyun nan…ba sa shiga harkarsu sannan ba sa taimaka musu amman ya tashi ya tsaya yana ƙoƙarin ƙulla aure tsakanin Jidda da Ya Yusuf, bai damu da yadda Jiddan bata son Ya yusuf ɗin ba kawai shi dai farin cikin ɗansa yake dubawa…. A tunanin Jidda zai bi bayan su Baba tunda ta lura tunda aka fara maganarta da Ya Yusuf ya na ɗan kula su amma sai ta ji ya ce ‘’Allah ya bata lafiya’’ Daga haka shima ya ja ƙafafunsa ya shige ciki. Yana wucewa dai-dai nan Muhsin yana ƙarasowa wajen dan haka suka wuce ciki duk su ukun. Sai chan dare tukunna Ya Nafi’u ya dawo, ya zo ya ce musu “su kwantar da hankalinsuc jikin Innar da dauƙi.” Wanda a take yanayinsa ya sanya tashi ɗaya suka fahimci ya faɗa musu hakan ne kawai dan su ɗan kwantar da hankalunsu. Daman ba su yi girki ba! Tashin hankali kuma ya sanya suka kasa ma jin yunwar. jugum!! Haka suka kwana ita da Jidda sam basu runtsa ba! Muhsin shima barcin ɗan kaɗan ya yi. safiya tana yi zazzaɓi mai zafi ya rufe Manubiya dan har da yau ɗin kwanan ta na uku kenan batayi bacci ba …… ••••••••• Tun lokacin da Yassir ya fita daga ɗakin da Ƙausar take ciki bata sake ganin sa ba. Hada-hadar komawa ma Abokinsa ya ɗaurama wa komai, shi kuma ya yi wucewar sa. In banda addua babu abunda Ƙausar ta ke ta yi a ranta akan ‘Allah Ubangiji ya sa Yassir Zuciya yayi. Sannan ya haƙura da ita kenan har abada’ Haka nan ta kwana tana wannan adduar tare da tunani barkatai a ranta! washegari itama suka haɗa komai nasu itada ƙawayenta suka nufi airport…… … Da safe around 8, flight ɗinsu ya yi landing a gida, Nigeria. Suna fitowa suka tarar da Sister ɗinta ’Yasira’ ta na jiransu …. … Sai da suka fara ajjiye ƙawayen nata waenda suka dawo tare tukunna suka ɗauki hanyar gidansu wanda ke a sultan road, Kano state. shiruuuu! Haka motar ta ɗauka babu mai cewa komai kafin chan Yasira ta yi murmushi ta ce ‘’tun jiya da ya dawo dama na fahimci faɗa kukayi, yanzu kuma mood ɗinki kaɗai ya tabbbatar min da hakan. Kin gaya masa ne?’’ Ta ƙarashe maganar tata da tambaya tana me ɗan waiwayawa ta kalle ta kafin ta maida hankalinta akan tuƙin da take yi. Kamar Ƙausar ba zata amsa mata ta ba, sai kuma ta ce ‘’kina nufin na sanar masa ‘bana son shi, yayan sa nake so???’.” Wata ƴar siririyar dariya Yasirar ta yi, kafin ta ce ‘’Noo! Ki dai san ta yadda za ku yi breaking up tun wuri kawai kuma cikin sauƙi, saboda in har kika bari kuka yi baram-baram da shi, to fa ki tabbata auren ki da Ya Yashjub ba mai yiuwa bane ba!. So, find an easy way out (Ki nemo mafita mai ɓullewa, mafi sauƙi) soon. Rikitacciyar zuciyarki data ɗauko mana aiki mai zafi, ta nemo mana mafita, a samu a rabu cikin sauki.’’ Wata nannauyar ajiyar zuciya Kausar ta sauƙe kafin ta ce ‘’Abun da nake ta so in yi kenan, amma shi kuma Yasir nacin bala’i ne da shi, kamar maye haka yake, ya ƙi ya bani haɗin Kai, ban….’’ Ganin yadda Yasirar ta yi shiruuu ta ɗan ɓata fuska ne ya sanya Kausar ɗin yin shiru kafin ta ɗan yi gyaran murya, tukunna a ankali tace ‘’Sorry.’’ Murmushi kawai Yasira ta yi sannan ta ce ‘’Kausar, inda ace zan ji haushin ki akan issue ɗin Yasir, tou da tuni tun farko da kika gaya mini yadda feelings ɗinki sukayi bouncing (tsuntsuwa) daga kan Yasir zuwa kan Ya Yashjub, da tun anan zan ji haushinki! Amma banji ba, saboda You are my best friend (ke babbar ƙawata ce) hakan ne ya sanya na goyi bayanki dan kasancewar Yasir twin brother ɗina ba shi zai sanya in zuba ido Inaji Ina gani ki cuce sa sannan ki cuci kanki ba, domin kuwa na san tunda har kika iya kallon Idanuna kika ce mini ba kya son Yasir tou tabbas bakya son nasa kenan, dan haka idan na bari kuka yi auren a haka akwai babbar matsala. wannan dalili ya sanya ko da ace baki samu Ya yashjub ba, ba zan so ki auri Yasir ba ….’’ A hankali Kausar ɗin tace ‘’InshaaAllah ma zan samu Ya Yash, da izinin Allah. I just need your support (goyon bayanki kawai nake buƙata) Yasira.’’ Ta ƙarashe maganar a hankali tana kallon Yasirar abun tausayi. Murmushi Yasira ta yi kafin ta sanya Hannu ta kamo na Kausar ɗin tana Murmushin ta ce ‘’Zan taimake ki har sai inda ƙarfi na ya ƙare InshaaAllah, tun muna Yara kin kasance ƙawata kuma ƴar uwata wadda take tsaya mini tsayin daka akan komai!. Idan na ƙi yi miki wannan taimakon kwaya ɗaya wanda na san shine farin cikin ki Ƙausar ai na zama butulu.’’ Cike da jin daɗi Kausar ta ce ‘’Thankyou’’ tana Murmushi. Daganan suka shiga tattaunawa akan yadda za su yi da Yasir, saboda sun fahimci sai sun yi da wayo, dabara sannan da gaske tukunna za su ci nasara! Dan sai yanzun ne suka fahimci ashe su sun raina adadin yawan ƙaunar da yake yi wa Ƙausar ɗin, basu yi Tunanin ya yi zurfi a sonta har hakan ba…. …. Kamar yadda suka yi zato.. A compound na dank’areren mansion ɗin suka tarar da Mommy tana jiran su, murmushi Yasira ta yi kafin ta juya ta kalli Ƙausar wadda ta haɗe rai tamau, ta ce mata ‘’Your guarding angel, ai na san ta daina fushin dake dama, gashi har ta zo tarbarki. Jiya da Daddy ya ce mata zai dawo yau, bakiga yadda hankalinta yayi bala’in tashi ba, saboda gudun kar ya dawo bai tadda ki ba. Tun jiyan take tambaya ta ‘Flight ɗin naku dai 8:00am ne ko? In tabbatar na je na dauƙo ki da wuri…. Kar Ya Yash ma ya fahimci bakya ƙasar kuma kar Daddy ya zo ya ga bakya nan’.” Duk da yadda Ƙausar ta shirya ƙin yin murmushi sai da wata ƴar siririyar dariya ta suɓuce mata! A chan ƙasan ranta tana mamaki da yaba tsantsar ƙaunar da Mommyn nata takeyi mata! Amma dukda haka ba zata bari Mommyn ta ga lagonta ba dan in ta bari ta ga sauƙinta to ta san yau sai ta sha faɗa!. Dan haka ta sake haɗe rai sannan ta turɓune fuska kamar bata taɓa dariya ba, tukunna ta murza handle ɗin marfin motar ta fito. Duk yadda mommy ta so sauƙewa Ƙausar ruwan bala’i, suna haɗa ido sai ta ji fushin nata yana ɗan sauƙa!! Tabbas ita kanta ba zata iya auna adadin ƙaunar da take yi wa Kausar ba. Ganin yanayin fuskar Kausar ɗin kuma sai ya sanya ta ta ɗan fara d’ar-d’ar, amman dukda haka yau kam ba zata bari Kausar ta ga lagonta ba, Ita ce uwa! Ita ya kamata su bi, ba wai ita ta dunga binsu ba. Tana cikin wannan tunanin kawai ta ga Kausar ta zo ta wuce ta ba tare da ta ko gaida ita ba. A fusace Mommyn ta juya ta bita sannan ta shiga kwala mata kira…. Ɗaga mata Hannu kawai Kausar ɗin ta yi tana wani yatsine fuska kamar irin kin isheni ɗinnan, daganan ta wuce ta bi ta kan haɗaɗɗiyar Barandar da ke kewaye da main door ɗin gidan, ta murza handle na ƙofar ta tura ta shige ciki abunta. Ba mommy ba hatta Yasira sai da ranta ya ɗan ɓaci! kamar zata bi Kausar ɗin ta yi mata magana sai kuma ta tuna yadda su ke ita da mommy ‘ba’a shiga faɗan su, yanzun sai su shirya su barta tana fushinta ita kaɗqi’ Dqn haka sai ta zaɓi ta zuba musu ido kawai. A mugun fusace, gudu-gudu, sauri-sauri mommy ta bi bayan Kausar. A bakin stairs ta hange ta tana shirin fara hawa, dan haka ta tafi da gudu ta finciko ta ta dawo da ita gaban stairs ɗin, tukunna ta soma faɗa! Baki da kumfa!! ‘’Ki yi laifi , kuma ki dawo mini da wannan attitude d’in? Me kike nufi kenan ? Tou bari ki ji, wallahi zan barki da Daddyn naku wannan karan, dan naga abun naku daga ke har Yasir ɗin fitina yake k’ok’arin zamewa mutane!! Idan auren kuke so ku faɗa a yi muku mana kowa ma ya huta!. Dan Wallahi na gama rufa muku asiri. Bazai yiu ace kina bin sa kuna yawo k’asa-k’asa mu kuma muna gida a shantake ba! In Banda iskanci wanne irin birthday celebration ne wanda ba za a iya yi miki a Nigeria ba? Har Sai ya d’auke ki kun tafi wata uwa duniya?”. A hankali Yasira ta ɗan matso ta taɓo ta kafin ta ce ‘’Mommy.’’ Cikin fada mommyn ta ture Hannun Yasirar kafin ta ci gaba da cewa ‘’Rabu da ni Yasira! Kausar ta kaini bango Wallahi. A gaban ki ai na ce mata ban amince su tafi ko Ina ba! Amma da yake ta raina ni shine ta wanke ƙafa ta bi shi….. To kuwa kamar yadda ta wanke kafa haka nima zan wanke hannayena daga rufa musu asiri da nake yi tund…’’ A karo na biyu Yasira ta sake katseta ta hanyar cewa ‘’Mommy!!!’’ Da d’an k’arfi. Juyawa Mommyn ta yi a fusace zata rufe Yasirar da fad’a amma sai ta ganta duk a ɗimauce tana kallon ta tana waiwayawa tana kallon ƙofar shigowa…. ….Giant ne sosai mai faɗin ƙashi, sanye cikin riga da wando (pyjamas) farare tass masu ratsin silver. Yanayin kalar fatar jikinsa (light brown ne)…..ruwan tarwaɗa mai haske. (Kamar na half cast) mai tsananin kyau, sheƙi da ɗaukar idanu. Normal lowcut da tsadadden gyaran fuska ya yi waenda suka taimakawa baƙa ƙirin ɗin sumar kai da fuskarsa damar sake haskaka kyakkyawar fuskar tasa….. Babu alamun sanƙo ko kaɗan a tare da shi hakan ya taimaka wajen sake fitowa da kuma ƙawata matured handsome face ɗinsa wadda ƙawataccen saje da ɗan siririn gashin Baki haɗe da ɗan guntun gemunsa da ko Hannun Yara ba zai iya kamawa ba suka taru suka yiwa fuskar tasa k’awanya. Yanayin yadda sumar tashi ta ɗanyi coiling dukda kankantar ta a ka da fuskarsa ke nuni da lallausar suma gare sa. Dogayen Idanuwa gareshi, manya kamar na mai jin bacci waenda suka yi dai-dai da tsararriyar girarsa. Hancinsa dogo ne sosai, har baka! Mai v shape ta chan ƙasa Sai d’an mitstsin light nude lips ɗinsa mai asalin kyawu da ɗaukar hankali… .. Ita kanta Kausar sai yanzu ta lura da YASHJUB, tsaye a bakin k’ofar. Wani irin sanyi take ji yana ratsa ta tun daga tsakiyar kanta har izuwa babban ɗan yatsar kafarta. Duk da yadda taga ya sake tamke fuska fiye da yadda take a kullum amma sai shauƙin da ta shiga na ganin sa ya lulluɓe fargabar tata. A hankali ya lumshe dogayen Idanuwansa kafin ya buɗesu ya zuba akan Kausar! Wanda hakan da ya yi ya bawa Yasira damar silalewa ta gudu zuwa kitchen, dan ta lura zuwa wannan lokacin hankalinsa ya koma kan Kausar. Wani ɗan mitsitsin tsaki ya jaa! Ganin yadda take kallon sa tana wani lumlumshe idanu. Sai da ya sake haɗe rai tukunna ya tunkaro ta cikin takun sa mai cike da ƙasaita da kamala. Har ya k’arasa gareta Ƙausar bata cire Idanunta a cikin nasa ba,shima kuma haka, dan yana so ya ga k’arshen tsaurin idon nata. Sai da ya matso daff da ita tukunna da kyar ta cire kwayar Idanunta a nashi ta hanyar lumshe idanuwan nata wanda hakan ya bawa wata ƴar siririyar kwalla damar zubo mata daga ido ɗaya…. Idan akwai abunda ya ke yi masa wahalar yi tou shine ‘magana’ Shiyasa kawai ya tsaya ya yi shiru Har ta gama sauk’e ajiyoyin zuciyar da take (a jejjere) sannan ta sake buɗe Idanuwanta tana kallon sa. He can’t stand her (ba ya iya jurar ta!) ko kallon ta baya son yi. Wallahi inda ace yarinyar ba Marainiya bace ba to da sai ta koma gidan su dan shi da kansa zai maida ita. Babu abunda ya tsana a rayuwar sa kamar ‘ƴa mace marar kamun kai.’ Bai yi cikakken 3 months da dawowa gidan ba amma ya fahimci sam yarinyar bata da hankali, dama tun suna Yara ( kafin ya koma Uk da zama) ya fahimci hakan dabi’ar ta ce amma sam bai yi tunanin har yanzu bata nutsu ta shiryu ba . Cikin kakkausa kuma dakakkiyar murya ya ce ‘’ATM’s , phones ,car keys &passport.’’ A rikice ta buɗe Idanunta a kansa tace ‘’Ya Yash pls I ….’’ Wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata da har sai da ta kai ta ga tsugunnawa a ƙasa! ‘’Bani nan!!!’’ Sannan ya d’aura da cewa ‘’Kar ki bari raina ya k’arasa b’aci’’ Taso ta ɗan ɓoye waya ko atm amma tana ɗago handbag d’inta ya wafce. Ba tare da ya sake kallon ta ba ya juya tukunna ya ce ‘’Mommy ki turo min Yasir.’’ Yana gama faɗin haka ya juya kamar walkiya, fitt! Haka ya fice daga parlourn, ya bar musu mayataccen kamshin turarensa. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *06* Har ya fice Idanuwanta basu daina kallon inda ya bi ya fitan ba. Cikin fushi Mommy ta kamo Hannunta ta ta juyo da ita saitinta sannan ta ce ‘’Ai ga irinta nan, yanzu kinga magana kam ta riga ta je kunnen Daddyn ku ta gama!!! Kin janyowa kanki da kanki.’’ A hankali Kausar ta matso kusa da ita, daf! Sannan ta ce ‘’Ko kuma dai kin janyo mini ba, dan inda ace ba ki zo kina hargagi da shouting(ihu) ba ai da bai ji ba, na san dama ai abun da kike so kenan…so kike yi ya ji ɗin kuma gashi ya jiii!!! Sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha, tunda burin ki ya cika!!!’’. Tana gama faɗin haka ta wuce sama da gudu tana kuka…. Ko akwatinta bata jira ɗauka ba. Mommy ta daɗe tsaye a wajen kafin da kyar ta jaa k’afafuwanta, ta wuce… Hawayen Kausar suna ɗaya daga cikin abubuwan da bata ƙaunar gani a duniyar nan… ••••••• Tunda garin Allah ya waye su Manubiya su ke zuba idon ganin su Baba, amma shiru. Ganin har k’arfe 10 ta yi, ga jikin Manubiya itama sai ƙara tsanani yakeyi, hakan ya sanya suka yanke shawarar Jidda ta je ta dubo su Baba tun da sun san asibitin da aka kai Innar. Da kyar suka haɗa naira hamsin kuɗin mota, ta bata tace ta hau bus, idan ba ta gaban asibitin murtalan za su bi ba sai su ajjiye ta a hanya ta ƙarasa. A hankali ba don tana so ba ta miƙe ta shiga toilet ta yi brush ta wanke fuskarta, ta ɗan kimtsa tukunna ta fito ta yi musu sallama ta fita. Unguwar shiru ba kowa, ƴan kasuwa sun tafi harkokin gaban su masu zuwa aiki sun wuce haka ma ƴan makaranta… A takaice dai kowa ya tafi neman abunda zai fishshe sa. …..Tun lokacin da ta fito shi ya hango ta, amma yadda ta taho ya sanya ya fahimci ita bata lura da shi ba. Ƙare mata kallo kawai yake yi yana maimaitawa, yana mai sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya… Shi fa tunda yake bai taɓa ganin farar mace tass!!! Kuma farin mai asalin kyau kamar na Jidda ba! Dan duk wanda ya ganta ba zai taɓa tunanin Mahaifinta talaka ne ba. Fatarta har wani shek’i take yi! Ga idanuwa dara-dara manya sosai, oval shape, tubarkallah. hancinta pointed nose ne, ba dogo chan bane kalar wanda za a ce masa ‘har baka’, pointed ne mai asalin kyau da ɗaukar hankali. Bakinta shima mai kyau, laɓɓan masu ɗan cika! ba chan ba, sannan na ƙasan tsakiyar sa a ɗan rabe kamar an tsaga. Sai dimples ɗinta a wajen hab’arta (k’asan lips d’inta gefe guda). Ga shape da Allah ya yi mata, dan Jidda asalin figure 8 ce. Yadda Jidda take, haka sak Manubiya take. Suna tsananin kama da juna, Sai dai Jidda ta fi Manubiya hasken fata Manubiya kuma ta ɗan fi Jidda tsayi da jiki, kuma Idanuwan ta basu kai na Jidda girma ba, amman sun fi na Jidda kyau da kyalli da d’aukar hankali. Sannan ta fi Jidda tsayin gashi, dan nata har gadon baya yake , sab’anin na Jidda wanda bai ida kaiwa har gadon bayanta ba. Yanayin dimples ɗinsu shima ya banbanta jidda guda ɗaya ne a k’asan hab’arta na Manubiya kuma a kumatunta suke (both side) Masu kyau da ɗaukar hankali. A halayya ma sun bambanta dan Manubiya tanada ɗan faɗa, Jidda kuwa in za’a saka mata hannu a baki, ba lalle ta ciza ba …… .. Jikinta ne ya bata kamar ana kallon ta, dan haka ta ɗan ɗago da kanta, ai kuwa da shi ta fara tozali. Suna haɗa idanu ta yi saurin mayar da kanta k’asa, ta k’ara sauri domin ta samu ta wuce sa… amma sai ya yi saurin ƙarasawa inda take yana wani kalar murmushin da yake sanyawa take k’ara tsanar sa. … ‘’Ina wuni’’ tace da shi. Daga nan ta fara ƙoƙarin zagaye shi zata wuce. Hannu kawai ta ga ya saka zai kamo ta, dan haka ta yi saurin kaucewa. Da kyar ya iya ruƙo bakin hijabinta fuskarsa har zuwa wannan lokacin d’auke da murmushi… Sai da ya dawo da ita gabansa ta hanyar janyo ta tukunna yace ‘’Matas, wai har yanzu ba za ki sakawa zuciyarki da rayuwarki salama ba ko? Kin fa riga kin san ni ne mijinki har gaban abada! To kuma mai ya sa ba za ki tursasawa zuciyarki ƙauna ta ba?’’ Yayi mata tambayar yana mai matsowa kusa da ita. Da sauri ta ja baya, Idanuwanta har sun kawo ruwa. Muryarta na rawa tace “Ya Yusuf ka sakar mini hijabina, Ina sauri ne’’. Kwaikwayar ƴar siririyar muryar tata mai cike da rauni yayi ta hanyar cewa ‘’A’a, ni ba zan saki hijabin matata ba’’. Duk yadda ta so hana kanta kuka kasawa ta yi, dan haka kawai ta saki kukan da take ta k’ok’arin riƙewa…. da sauri ya cika mata hijabin kafin ya ce ‘’to to sorry!!!… Wasa fa nake yi miki, mai ya faru har haka? Are u okay?’’.” bata san lokacin da tq ce ‘’Inna ce fa bata da lafiya, tun jiya su Baba suka tafi kaita asibiti har yanzu basu dawo ba. Shine zan je wajensu, kai kuma ka tare mini hanya.’’ Cikin rashin jin daɗi ya ce ‘’yi hak’uri ai ban sani ba ne shiyasa. Jira ni anan, bara in je in d’auko mashin ɗina sai mu je, ko?’’. Kafin ma ta basa amsa har ya wuce da ɗan sauri, da alama yanayi nata da maganar rashin lafiyar Innar ya kid’ima sa. Kamar wata Yarinya! Tana ganin shigewarsa gida ta ɗiba a guje, ta shige wani lunga ta ɓuya!. Ta san babu kyau ka ce ka tsani Mutum amma wallahi ta tsani Ya Yusuf!!. Tabbas! dama sai da ya shiga cikin gida tukunna yayi wannan tunanin, aikuwa ilai sai gashi ya fita da gudu. Sai dai kuma gudun nashi bai amfaneshi da komsi ba dan babu inda bai duba ba amma ya rasata….. Saboda da Jiddan taga ya fara neman ta, sai ta yi wuff ta shige gidan da yake a cikin lungun! Allah yaso sun tab’a yin Islamiyya ɗayq da ƴar gidan dan haka ta gaida Maman Yarinyar (Matargidan) tace “dan Allah za ta yi fitsari” matar ta ce mata “tou” daga nan ta afka toilet. Ta jima tukunna ta fito tayiwa matar sallama da godiya, dan ita kaɗai ce a gidan Yaran duk sun tafi makaranta. Tana fitowa ta ɗan tsaya opposite gidan jikin katangar wani dank’areran gida wanda katangar ta shanye gaba ɗaya lungun, ta ɓangaren dama… A tsorace shiga kalle-kalle kamar marar gaskiya, sai da ta tabbatar bata ga Ya Yusuf ba tukunna ta fara shirin nufar titi…. Ko taku biyu bata yi ba suka yi ido biyu da Ya Musbah. Dan haka bata samu ta je asibitin ba sakamokom ce mata da ya yi “ ta taho su koma gida a je a yi wa Innar girki. an kwantar da ita, wai aiki za ayi mata, kuma daga yau ba za su sake bari ta ci komai ba har sai bayan an yi aikin da kwana uku.” … Sai da suka shiga gidan tukunna Ya Musbah ya san ashe Manubiya itama bata da lafiya dan Jidda bata samu damar gaya masa ba, tunda ta ji wai ‘aiki za’a yi wa Innar’ gaba d’aya sai ta d’imauce ta rikice. Ba ƙaramin tashi hankalin Ya musbah ya kuma yi ba, sai da ya ga Manubiyan ta tashi ta zauna tanata maimaita masa cewa ‘jikin nata fa da sauki‘ tukunna ya ɗan ji relief(sauƙi). Daganan ya shiga sanar musu “Kidney ɗin Innar guda ɗaya ya samu matsala! sannan ciwon zuciyarta shima ya motsa! Ga hawan jini!. Kuma basu san garin yaya ba amma jiya cikin dare ta samu stroke! Maybe ko mak’udan kud’ad’en da ta ji Likita ya lisaafo ne suka d’aga mata hankali, Allah kad’ai ya sani. But yanzu dai an ce ana buƙatar a cire kidney ɗin da ya samu matsalar da wuri gudun kar mai kyaun itama ta kamu.” Kuka suka saka gaba ɗaya su ukun, tun kafin ma ya dasa aya, ya so ya daure ya rarrashe su amma sai ya gagara! shima kawai ya b’ige da hawaye. Da kyar Manubiya ta tsaida kukan nata ita ta shiga rarrashinsu, tukunna sukayi shiru. Sun ɗan jima a ɗakin shiruuu kafin Manubiya ta ce ‘’Ya Musbah, yanzu ya za’ayi mu haɗa kan uban kuɗaɗen nan na aikin, da na gado da na magani? Sannan za su kai kimanin naira nawa??” A hankali ya ce ‘’Baba ya saida filinsa dama tun a jiya, da namu. Sannan Al’ameen ya cika mana wasu kud’ad’en,’’. Shiru ya yi kamar mai tunani kafin ya kalli Muhsin ya ce ‘’Zo, mu je mu siyo abun kari mu yo cefane’’. Suna fita Manubiya ta juya ta zubawa Jidda kyawawan idanuwanta ba tare da ta ce ko ta yi niyyar cewa komai ba. Sarai Jidda ta gane tuhumar ta Manubiyan take yi Don haka ta ce ‘’Ban san maganar ba, bama mu had’u da shi ba, rabo na da shi tun wanchan satin.’’ Ajiyar zuciya kawai Manubiya ta sauƙe kafin ta ce ‘’Jidda kina fita ɗazu ba ki daɗe ba na tsinci naira hamsin a cikin littafina na makaranta dan haka na aika Muhsin na ce yayi gudu ya je titi ya ƙara miki kud’in mota tunda na san ba lalle kin kai ga zuwa titin ba ma. Amma sai ya dawo ya ce mini bai ganki ba!. Kuma Ya Musbah yanzu cewa ya yi a jikin gidan su ya ganki, wanda shi kan sa na san kawai maganar ce baya so shiyasa yayi miki shiru.’’ A hankali Jidda ta ce ‘’Wallahi rabo na da Ya Al’ameen tun wanchan satin, ki yarda dani, dan Allah.’’ Ta ƙarashe maganar kamar zata fashe da kuka. A take kuma sai tsananin tausayin ta ya rufe Manubiya, ko babu komai ta san ba ƙaramin Namijin ƙoƙari Jidda take yi wajen ganin ta rabu da Al’ameen ɗin ba. ……. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *07* Sai bayan sallar isha tukunna, Mommy ta tattara gaba d’aya ragowar kwarin guiwarta, ta nufi side ɗin Kausar. A parlournta ta same ta, kwance cikin luntsumemiyar resting chair ɗin dake yashe a balcony na parlourn wanda glass ne kawai ya raba balcony ɗin da parlourn. A hankali Mommy ta ƙarasa kusa da ita, ta zauna a dai-dai wajen k’afafunta, tana tunanin ta ina zata fara rarrashin nata. Tun lokacin da Mommy ta turo k’ofar ta shigo Kausar ta lura da ita amma sai ta yi kamar ma ba ta san mutum ya shigo ba, tana kwance Idanunta suna kallon sama har zuwa lokacin da Mommyn ta zauna a kusa da k’afafunta Idanunta ba su motsa ba, ta na nan a ƙame kamar farko alamun ta yi zurfi a tunani kenan, ta ke so ta ce. A hankali Mommy ta ce ‘’Kausar’’ Jin shiru ya sanya ta d’an sake k’ura mata ido kafin ta sake cewa ‘’Kausar’’ Nan ma shiru taga Kausar d’in ta yi, babu ko gezau! Dan haka ta kama k’afafunta ta d’an jijjiga kafin da d’an k’arfi ta sake cewa ‘’Kausar!!’’ tana me kallon fuskarta. A firgice Kausar ta ɗan kalli Mommy, sai kuma wasu hawaye suka tsinke mata, a lokaci guda. Aikuwa nan take Mommyn ta rikice! Ta shiga tambayar ta “menene?” a lokaci guda ta na mai k’ok’arin zaunar da ita. Sun jima kafin dakyar ta samu Kausar d’in ta d’an yi shiru, tukunna a hankali Mommyn ta kamo Hannayenta tace ‘’In dai akan fad’an da na yi miki ne ɗazu, ki yi hak’uri, ba zan sake ba inshaaAllah, ki daina kuka komai ya wuce.’’ Wani kalar murmushi Kausar ta yi wanda ake cewa yafi kuka ciwo, kafin ta shiga girgiza kanta sannan a hankali ta ce ‘’Ba shine ya saka ni kuka ba, kawai dai ina tunanin ‘ina ma ace Ammina tana da rai’, ne’’. Cika Hannuwan nata Mommy ta yi a take kafin ta ce ‘’Kar ki yi min haka Kausar’’. Da sauri Kausar ta ruk’o Hannayen Mommy kafin ta ce ‘’Kar ki yi misunderstanding ɗina. Mommy ko da ace Ammi tana nan na san iyakar soyayyar da kike yi mini ita ma zata min! Maybe ma ba lalle ya kai naki ba. Kawai ina tunain ‘ina ma ace tana raye’ saboda na san inda ace tana nan to ba lalle in zauna a gidan nan ba, babu ruwana da takurar Yasir da kuma tsangwamar Yashjub. Har ga Allah Mommy bani da matsala dake ko su Yasira, amman Yassir!! Shine matsalar da ya fi damuna sannan saboda Yash ne naji inason barin gidan nan gaba ɗaya, dan akwai wani abun da yake damu na wanda in dai ba Ammi na ba to wallahi ko ke kanki ba za ki taɓa iya fahimta ta ba.’’ Ta ƙarashe maganar tata tana mai fashewa da kuka. A hankali Mommy ta share hawayenta kafin ta ce ‘’Na fahimce ki, na fahimci dalilin furucin ki na ɗazu. Abunda nakeso dake yanzu shine Ki faɗa mini abu uku… Na farko mecece matsalar ki da Yasir Na biyu Meye damuwarki da Yash, Na uku kuma wanne irin abu ne yake damun ki wanda har kike tunanin Ammin ki ce kad’ai zata iya fahimta?’’ Ba tare da tantama ba Kausar ta ce ‘’Mommy bana son Yasir, shi kuma naga alamun kwana biyun nan kamar wanda aka yi wa wahayi aka ce dole sai ya aure ni.’’ Duk da Mommyn ta ji ba dad’i yadda Ƙausar ɗin ta gaya mata direct bata son Yasir, amma sai ta yi k’ok’ari ta danne ta sake riƙe hannun Kausar d’in duka biyu kafin ta ce ‘’Faɗa kukayi? wani abun ne ya faru ?’’ Ganin kausar ta ƙi ta bata amsa ne ya sanya tace ‘’To, koma dai menene ya faru ina mai baki shawarar ki yi hak’uri ki auri Yasir domin shine rufin asirin ki, ko kina tunanin akwai namijin da zai aure ki ba tare da ya san wacece ke ba?’’ Sai da Mommy ta runtse idanuwanta ta bud’e tukunna ta kalli Kausar d’in ta ɗaura da cewa ‘’Kausar ki yi hak’uri ki rufa mana asiri, kar ki ɓata mana sunan family’’. Da sauri ƙausar ta ce ‘’Mommy ni fa ba wani wajen na ce miki zan je in yi aure ba! A cikin gidan nan zan yi, dan haka kinga wanda zan aura ɗin already shima ya riga da ya san maganar haihuwar da na taɓa yi da kuma maganar Mahaifi da komai nawa.’’ Cikin tsananin ɓacin rai Mommy ta yi wurgi da Hannun Kausar da ke a cikin nata kafin ta mik’e tsaye ta ce ‘’Kar ki kuskura!!!! Wallahi kar ki soma Kausar. Ba na son iskanci da yayen sabon rikici a cikin gidan nan!!! Ba zai yiu ba. Dan haka tun wuri ma ki farka, dama naga take-taken ki tun wanchan watan da ya shige ashe kuwa hassashen da nake yi gaskiya ne. To bari ki ji, ki bud’e kunnuwanki da kyau!!! Wallahi ba zan yarda ki raba mini kan ƴaƴana ba, Ina raye.’’ A hankali hawaye yana zubo mata Kausar ɗin tace ‘’Saboda ni ɗin ba ƴar ki bace ba?’’ Rikici da ɗimaucewa ne suka sanya Mommy ta ɗauke ta da wani gigitaccen mari!!! Cikin fushi ta fara magana ‘’Kar ki kuskura ki murƙushe tunanina da dabararki saboda son ranki wawuyar Yarinya kawai, doluwa. In banda rashin tunani ma irin naki tayaya ma za ki bar Yasir wanda ya ke tsananin ƙaunar ki da tausayin ki saboda Gawurtaccen miskilin Mutum irin Yashjub??? Mutumin da na san ba zai taɓa ƙaunar ki ba ko da ace baki kasance budurwar ƙaninsa tun asalin farko ba’’. Wannan karon mikewa tsaye Kausar ta yi! Cikin faɗa-faɗa itama ta ce ‘’Mommy kinga ta inda ake cuta ta ko? Ko kuma ince ta inda ni da kaina na lalata komai sannan na ɗaure kaina da jijiyoyin jikina..ta hanyar kasa cewa kowa ‘ba son Yasir nake yi ba’. Kuma kina so ki san dalilin da ya hanani yin magana?’’ Bata jira jin amsar Mommy wadda ta kafe ta da idanuwa ba ta ɗaura da cewa ‘’Saboda kawaici da kunyar in kalli idanun ƴan gidan nan in ce musu bana son Yassir. In banda hakan Wallahi tallahi kin ji dai na rantse miki ni ban taɓa son Yasir ba tunda na yi wayo na san kaina…. friendship dai tun Yarinta na san akwai shi, Ina son sa a matsayin ɗan uwa kuma Aboki amma bayaga hakan babu komai kuma tsakaninshi da zuciyata. Yashjub shine wanda na san inaso tun tasowata har kawo yanzu da soyayyarsa take neman kashe ni Mommy, wallahi inda ace ba Yash nake so ba tou da zan iya haƙura in auri Yasir amman matsalar shine ba zan iya auran ƙanin wanda zuciyata take ƙauna ba.” Ta ƙarashe maganar tana mai durƙusawa ta kamo ƙafafuwan Mommy cikin kuka ta ce ‘’Mommy dan Allah ki fahimce ni na yi kara na yi kawaici amma zuwa yanzu idan na ce zan ci gaba da yin kawaicin tabbas cutuwar zata yi mini yawa, wallahi mutuwa zanyi!!! Ki fahimce ni Mommy dan Allah.’’ Suna a hakan, Yasira ta shigo ta same su. Da sauri ta ƙarasa ta ɗago Kausar ɗin sannan ta shiga rarrashin ta kafin ta kalli Mommy ta ce ‘’Daddy ya dawo, yana ta neman ki’’. Da kyar Mommy ta iya jan ƙafafuwanta, ta fice daga balcony ɗin tukunna ta bar parlourn ba tare da ta kalle su ko ta sake ce musu uffan ba. Tana fita Yasira ta kalli Kausar wadda har yanzu take ta faman gunjin kuka ta ce ‘’Sannu, dan naga k’ok’arin ki, amma kuma mood ɗin Mommy kaɗai ya sanya jikina yayi sanyii…. Ina matuƙar son in ga na taimaka miki game da lamarin nan Kausar (really wanted to help u) amman inaga gara kawai ki haƙura haka nan, dan gashi Mommy kanta bata baki goyon baya ba, dama na san tunda case ɗin ya shafi favorites ɗin ta to ba lalle ki yi nasara ba! no matter yadda kuke ke da ita’’. Shiru Yasirar ta yi kafin ta ci gaba da cewa ‘’ki yi hak’uri sis, ki hak’ura kawai.’’ A hankali cikin goge hawaye Kausar ta ce ‘’Yasira!! Yasir da Yash and me ne favorites ɗin Mommy ko kin manta? Za ki ce na gaya miki Mommy tana side ɗina.’’ Da mammaki Yasira ta ke kallon ta. With full confidence Kausar ɗin ta sake cewa ‘’yeah, za kuma ki ce na faɗa miki.’’ Ta na gama faɗin haka ta juya ta bar wajen, ta shige toilet domin ta wanko fuskarta….. Duk da tana fargabar yadda zata kaya tsakanin ta da Daddy, Yash da kuma Yassir amma ta san tunda yanzu Mommy ma tana bayan ta to komai zaizo mata da sauk’i. Although Mommyn bata riga ta faɗa mata cewar tana bayan nata ba amma ta gani a yanayin ta da kuma idanunta dan haka ta san definitely tana bayan ta. Tun kafin Yashjub ya dawo Nigeria ta lura da yadda Mommy ta ɗaga hankalinta akan tarin dukiyarsa, tabbas Yash bai saba da Mommy sosai ba kuma bama a gabanta ya taso ya girma ba hakan ya sanya Mommyn duk ta bi ta ɗaga hankalin ta. Babu abunda ta lura Mommyn bata so kamar Daddy yq yi maganar auren Yash da wata! kuma ta san ba dan komai yasanya Mommy bataso Yash ya yi auren ba sai dan saboda kar wata ta zo ta ƙarasa janye mata Yash ɗin da shi da dukiyarsa gaba ɗaya ba tare da ita Mommyn ta samu sun shaƙu da Yash ɗin ba. Ta san Mommy kamar yunwar cikin ta! Duk yadda ta kai ga ji da Yassir ba zata taɓa bari ga Kausar wadda ta nuna tanaso ace wai Kuma Yash ɗin ya je ya auri wata daban ba.! Dan ta san in dai Yash ya auri Kausar tou da shi da dukiyar sa kamar sun dawo Hannunta ne sun gama……… ••••••• Shinkafa mai kyau da kayan miya harda nama Ya Musbah ya kawo. Babu yadda Jidda bata yi da Mannubiya ba akan ta barta za ta yi amma sai da ta saka mata Hannu a aikin. Dama tun suna girkin suka dunga shiga one by one suna yin wanka dan haka Girki yana kammaluwa dai-dai nan suma sun shirya abunsu tsaf. Babu fannin da basu shiga a gidan sun sanar musu da rashin lafiyar Inna ba, amman Baba Habu ne kawai ya bada kuɗin lemo ragowar kuwa ba wanda ya basu ko sisi Anty Umma ce ma ta ce “inshaaAllah zuwa anjima za ta je ta asibitin ta duba ta in Siyama ta dawo.” Baba Habun shima naira ɗari biyu ya basu ya ce “su siya mata lemon zak’ii su gaishe ta su ce yana mata ya jiki, Allah ya bata lafiya.” Muhsin ne ya karba sukayi godiya shi da Jidda daganan suka fito suka kama hanyar asibitin…. A ward Ya Musbah ya san ya bar su amma suna zuwa Nurse ɗin ta ce masa ai an maida ita aminity 2. Yana mamaki yana tunani haka nan ya wuce shi da su Manubiya suka nufi aminity inda aka nuna musu. suna shiga suka tarar da Al’ameen a zaune, In banda ƙamshin Kaji da youghurt ba abunda ɗakin yake yi, hatta ruwan sha ya siyo wajen katan goma da lemuka suna kusan goman duk an jibge sai kace waenda za su buɗe shago ne. Tunda suka fara shigowa ya kafesu da ido. kasancewar Jiddan ce a ƙarshe ya sanya bai ganta da wuri ba har sai da dukkan su suka ida shigowa tukunna…. A hankali ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya a ɓoye kafin ya sunkuyar da kansa k’asa ya lumshe idanunsa. Itama Jiddan tunda ta shigo suka haɗa ido gaba daya duk sai ta diririce. Cike da damuwa da rashin jin daɗi suka matsa kusa dasu Baba, da kulawa suka gaida Mahaifin nasu su duka huɗun, tare da tambayar sa ya “jikin Inna”wadda suka tarar tana bacci. A hankali shi da Al’ameen suka ce ‘’Alhamdulillah’’. daga nan Al’ameen da Ya Musbah suka yi musabaha cikin mutanta juna da girmamawa, Muhsin kuma ya gaida shi, haka itama Jiddan ta shiga gaida shi dakyar ba tare da ta yarda ta kalle sa ba. Sai da ya kalle ta ya ɗan yi murmushi tukunna ya amsa da kulawa. Cikin rashin kuzari Ya Musbah wanda ya gama ƙarewa ɗakin kallo ya kalli Al’ameen ɗin yace ‘’Al’ameen, wannan duk aikin ka ne ko? wahalar bata yi yawa ba kuwa?’’ Sai da yayi murmushi tukunna ya miƙe tsaye ya ce ‘’ko d’aya Ya musbah, ka mai daina kiran hakan da wahala dan Allah, fatan mu Allah ya bawa Innarmu lafiya. ni bari in wuce, zuwa anjima inshaaAllah zan dawo.” Har Manubiya za ta yi magana sai kuma suka haɗa ido da Baba wanda tun ɗazu ta ga ya kafeta da ido. Cikin ɗan sigar zolaya Al’ameen ɗin ya k’arasa kusa da ita ya ce ‘’Adda Manubiya ina wuni’’ yana ɗan murmushi. Ta so ta amsa sai dai kuma takaicin da ya taso mata ya turnuƙe ta lokaci guda ya sanya bata ma san lokacin da ta wuce shi ta isa kan kujerar da ya tashi akai ta zauna ba. A hankali ya kalli Jidda wadda take kallon su tun ɗazu Ya ce ‘’Sai anjima,Allah ya ƙara sauk’i’’. Sai da ta sunkuyar da kanta ƙasa tukunna tace ‘’Ameen, mun gode’’. Murmushi kawai ya yi, daganan yayi musu sai anjima, yasa kai ya fita. Yana fita Manubiya ta ce ‘’Haba Baba, ya zaka yarda Al’ameen yayi mana wannan hidimar haka?! salon mahaifiyarsa ta zo ta d’agawa kowa hankali??’’ Da sauri ya ɗaga mata Hannu Kafin ya xɓce ‘’Fad’a kike yi min?’’ Cikin yin ƙasa da kai ta ce ‘’ka yi hak’uri’’ A hankali. Sai da ya duba Inna ya tabbatar da baccin nata yayi nisa tukunna ya kalli Ƴaƴan nashi gaba d’ayan su… Kafin a hankali ya fara magana ‘’Ku yi hak’uri, na san na gaza muku a matsayi na na Mahaifinku. A ko da yaushe ina jin takaicin halin da muka tsinci kanmu a cikin sa duk a ta dalilin taurin kaina, dan na san inda ace tun farko da sana’a ta ƙi karbata na haƙura na koma karatu da wuri to da yanzu ina da aiki na. Ina jin tausayin ku a ko da yaushe sai dai yanzu ban san da wanne ido zan iya ci gaba da kallon ku ba. Tun wanchan watan da ya wuce Mutumin da ya ara mini kud’i lokacin da za a yi mini aikin ƙafa a yanke ya zo da takardar sammaci, bana so ya d’aga maganar kowa ya ji, domin a lokacin ma Innar ku tana asibiti, shiyasa da ya buk’aci zai fanshi kud’in sa da garejina na yarda na amince akayi komai cikin lumana.’’ Sai da Baba ya runtse idanunsa ya bud’e su tukunna ya d’aura da cewa ‘’Jiya kuma na siyar da fili na wanda ake rini a ciki ake biyana duk shekara, da naku na ƙauye sannan a halin da ake ciki yanzu, mai gareji ya ce yana buk’atar kangon zai fara gini a ciki wai d’ansa zai yi aure. Dama ba wani abun kirki ne a ciki ba sai ƴan kayan gyaran mota da benchi. Ba komai yasa nake fad’a muku a yanzu ba sai dan ku san a yanzu bani da komai! Dama filayen nake shirin siyarwa in fanshi gareji na na san koda rabin kud’in ne in na ba sa zai iya jira daga baya in cika ma sa ragowar, to kuma sai maganar aikin Innar kun da ya taso jiya gadan gadan ya sanya dole in siyar da filin a fara shirye-shirye tunda lafiya itace a kan gaba. Ku yi hak’uri ku yafewa mahaifinku na gaza maku, tun farko ban baku kyakkyawar rayuwa ba yanzu kuma ban san wacce irin rayuwa za mu yi a gaba ba, babu fili babu gareji’’. Ya ƙarashe maganar tashi yana me fashewa da kuka. Da sauri Ya musbah ya matsa kusa da shi ya durk’usa a gaban sa ya kamo Hannayensa, cikin karyewar zuciya ya fara magana ‘’Baba kar ka ce haka dan Allah, ai ba dole bane sai ka bamu rayuwar daula, abun da yake akan ka shine ka bamu tarbiyya sannan ka yi iyakar k’ok’arin ka wajen tufatar da mu da kuma ciyar damu sai kuma muhalli, wanda baka tab’a gazawa ba. Bamu da abun da za mu ce maka sai godiya, fatan alkhairi da kuma adduar Allah ya saka muku da gidan aljannah kai da Inna, Allah kuma yasa ku gama da duniya lafiya. Baba kana cikin iyayen da ko wanne ɗa zai yi alfahari da. kuma dama yanzu ai lokacin hutun ka ne, nema yana a kaina yanzu! Dan haka ka daina ɗaga hankalinka dan Allah’’ A hankali itama Manubiya ta matso ta ce ‘’Baba gaskiya Ya Musbah ya fad’a, na san bamu tashi a had’ad’d’en gida cikin daula ba Amman Allah ya azurta mu da mahaifi mai tsananin son mu da k’aunar mu, dan Allah ka kwantar da hankalin ka, dan ni kam ko da ace za a dawo da duniya farko a bani damar in zab’i Mahaifina wallahi Baba kai zan zab’a.’’ Cikin sharar kwallah Jidda tace ‘’Iyaka soyayyar ka da kulawar ka a garemu ta wadatar Baba. InshaaAllahu za mu taimaki juna daga yanzu, kar ka damu da salwantar da garejinka ya yi na san Ubangijin da ya halicce mu ba zai hanamu abin da za mu ci ba, Kuma inshaaAllah ubangiji zai kawo mana mafita cikin sauƙi’’. .. Garejin na sa ba wani kud’i yake kawo masa ba tunda babu ciniki sakamokon kayan aiki da suka yi musu k’aranci kuma babu kud’in saye, sai filinshi wanda masu rini suke biyan sa dubu talatin duk shekara, Da su ya dogara da su yake ciyar da iyalin nasa to gashi yanzu ya rasa su a lokaci guda!!! Bai san ya zai yi ba bai san ya za su ci abinci ba amma kamar yadda yaran suka faɗa yanzu, Allah zai san yadda zai yi da su…. Yarda da k’addara da kuma kalaman su masu dad’i da kwantar da hankali ne suka ɗan kwantarwa da mahaifin nasu hankali. … ….. Jidda ce ta zuba masa abinci suka tilasta masa har sai da suka ga ya d’an ci da dama tukunna suka kyale shi. … Hamdala da tasbihi Baba Musa ya ke ta jerowa a chan ƙasan zuciyarsa, dan shi kam Ubangiji ya gama azurta shi da Ƴaƴan da ko wanne uba zai yi alfahari da, hankali, nutsuwa da tsantsar sanin abun da ya dace duk sun had’a. Gashi dai ko yanzu k’iri-k’iri sun dage su na ta k’ok’arin ganin sun kwantar masa da hankali sun kuma nuna masa ba komai amma ƙarara yake iya hango tsantsar tashin hankalin da suke ta ƙoƙarin ganin sun danne a idanun gaba d’ayan su, har Muhsin. …………… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *08* Kausar tana fitowa daga banɗakin, suka sauƙa k’asa tare, ita da Yasira. A dining table suka hango gaba d’aya ahalin gidan a zaune. Inda Daddy ya ke suka nufa domin su gaida shi sannan su yi masa sannu da zuwa. Suna isa suka durkusa cikin girmamawa suka gaida shi a tare, tare da yi masa sannu da zuwa. Da kulawa ya kalli Yasira ya dafa kanta ya amsa kafin ya kalli Kausar kamar zai amsa sai kuma ya dauk’e kai ya dauk’i ruwa yana shirin sha ya ji ta sake cewa ‘’barka da dawowa Daddy’’ Ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘’Yauwa’’ daga nan ya fara shan ruwan da ya kai Bakinsa. Ba iya Kausar ɗin ba hatta Yasira da kyar ta iya mik’ewa daga wajen, suka wuce suka nema waje suma suka zauna. Babban dining table ne sosai mai ɗauke da kujeru wajen goma sha biyar! Daddy ne zaune a seat ɗin tsakiya ata farko wanda yake facing na ƙarshe inda Mommy ta ke zaune. Yashjub da Yasir sun saka Daddy a tsakiya a ta gefe da gefen sa(kujerunsu suna kallon juna) a kusa da Mommy kuma Yasmin da Ya’isha ne. Yasmin ita ke bin Yasir da Yasira Shekarunta 25 a duniya,likita ce. Sai Ya’isha mai shekaru 24 a duniya wadda ta fara masters kwanan nan a Dangote Business School. A kusa da su kuma Yusra da Yadira ne, Yusra shekarunta ashirin a duniya ita take bin Ya’isha tana karatu a B u k tana level 3 Sai auta Yadira wadda take itama a buk level one shekarunta sha bakwai a duniya. Cikin nutsuwa Daddy ya yi serving kan shi, daganan kowa ya shiga zuba abunda ransa yake so. Ganin har tsawon wani ɗan lokaci Daddy bai kai ko loma d’aya Bakinsa ba ya sanya suma duk suka tsaya!. Shiru dining d’in ya d’auka gaba d’aya…. Kafin chan Mommy ta ce ‘’Na lek’a ta ɗazu, tun kafin ka sak’k’o, amma sai ta ce mini a k’oshe take.’’ Shiru ya yi bai tanka mata ba, ganin hakan ya sanya ta mik’e ta nufi k’ofar wani d’aki wanda ke a nan cikin main parlourn, tana ta faman guna-guni. Bata yi mintina hud’u da shiga ba suka fito tare ita da wata farar budurwa wadda ak’alla zata kai kimanin shekaru 29 a duniya, bata da jiki sai dai doguwa ce sosai, kallo d’aya tak za a yi mata a gano tsantsar kamanninta da Daddy wanda tun fitowar su ya kafe ƴar tashi da idanuwa yana mamakin tsantsar ramar da yaga ta sake yi. A kusa da Yashjub Mommy ta zaunar da ita. Daga nan ta koma mazaunin ta itama ta zauna. A hankali suka shiga passing mata kulolin abincin zuwa gabanta.. Bata zuba ba sai da ta fara sunkuyar da kanta ta gaida Daddy cikin girmamawa tare da yi masa sannu da zuwa dan itama ba ta san ya dawo ba… da kulawa ya amsa ta tukunna ta shiga zuba abunda ranta yake so. Tana gamawa Daddy ya yi bismillah ya fara…. Bismillah suma duk sukayi daga nan aka gabatar da dinner d’in cikin nutsuwa. Sai da kowa ya kammala, tukunna Daddy ya juya ya kalli Yahanasu ya ce ‘’Lafiyar ki kuwa ? duk naga kin sake ramewa’’. Murmushi ta yi ahankali kafin ta ce ‘’Lafiya ta k’alau Daddy, Alhamdulillah’’. Ya jima yana nazartar ta kafin daga baya ya d’auke kai ya maida hankalinsa kan Mommy ya fara magana ‘’Akwai Aboki na ‘senator Bashir’! Ba wai ya kaini shekaru bane ba, kawai dai tamu ta zo d’aya da shi ne shiyasa muka zama Abokanai. Matar sa d’aya, ya yi min maganar yana son ya k’ara aure ne Shine na ba sa izinin ya zo yaga Yahanasu! Is an sun daidaita Alhamdulillah. Na san shi tun ba yau ba, shima haka ya sanni so banajin za’a samu matsala wannan karon, InshaaAllah. Na bar komai a Hannunki, ku shirya tarbar sa da kyau ranar juma’ar nan zai zo.’’ A hankali mommy ta ce ‘’InshaaAllah Daddy. sannan da yardar Allah ba za a samu matsala ba.’’ Ta yi maganar tana mai yi wa Yahanasu addu’ar dacewa a wannan karon, ko ba komai hankalin kowa zai kwanta. A hankali yahanasu wadda gaba d’aya hankalinta ya tashi lokaci guda ta ce ‘’Daddy, Dan Allah…’’ Cikin rashin son ya saurare ta ya ce ‘’Sai magana ta ta biyu.’’ A take duk suka tattara hankulan su suka maida akan sa! Ganin yadda lokaci guda ya sake tamke fuskar sa ne yasanya duk suka sha jinin jikinsu. ‘’Yashjub ya sanar da ni Irin taɓargazar da Yaran nan su ke shukawa’’ Daddy yayi maganar yana nuna Yasir da Kausar. Kafin cikin b’acin rai ya kalli Mommy ya ce ‘’I’m really disappointed in you, da ke da su bansan wa ya fi wani ba. Anyways, na riga na gama yanke shawarar d’aura musu Aure gobe da safe in sha Allahu!!! dan ban shirya d’aukar shege a karo na biyu a cikin gidana ba’’… Tun kafin ya kai k’arshen aya Kausar ta fashe da wani irin kuka, cikin sheshshek’ar kuka ta ce ‘’Allah ba zan aur……’’ Ai kuwa a take Daddy ya mik’e da shirin isa inda take, ganin haka ya sanya ta kwasa a guje ta yi sama. Ya so ya bita, ya ci k’aniyar ta dan dama a mugun k’ule yake da ita, bayajin haushin Yasir kamar yadda yake jin haushin ta, sannan a ganin sa ita ta b’ata Yasir tun asalin farko shi kuma bai farga da wuri ba, shikenan garin tausayi gashi Yarinya tana neman tarwatsa masa tarbiyyar Yaro ko ma ace ta riga ta tarwatsa d’in… Muryar Mommy ce ta katse shi jin tana cewa ‘’Daddy u need to reconsider(ka sake tunani), wannan abun da kake shirin yi ba dai-dai bane ba! kuma lokacin da ka d’auka a gaskiya ya yi kad’an, dan Allah ka sake tunani.’’ Cikin tsananin ɓacin rai ya ce ‘’Bar ganin a gaban ƴaƴanki kike, wallahi yanzun nan zan kifar da ke. kin bar Yara suna shashanci sannan yanzu ana k’ok’arin gyara abu amma kina k’ok’arin kawo tangard’a akai ?? karfa ki bari rai na ya k’arasa b’aci da ke! wallahi ba za ki ji dad’i na ba’’. Yana gama fad’in haka ya juya fuuu ya wuce saman shima ya nufi side d’insa. A zuciye Mommy itama ta mik’e ta k’arasa inda Yashjub ya ke tsabar fushi bata san lokacin da ta rufe sa da fad’a ba! Baki da kumfa ta shiga cewa ‘’Mai yasa kake da muguwar zuciya ne? Yanzu kukan da take yi dad’i yayi maka ko mai? ka fini sanin ciwon kaina ne? ko kuwa ka fini sanin abun da ya fi dacewa a yi? Tunda har ka ga na yi shiru ai ka san akwai dalili dai ko?’’ A hankali ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zuba mata ba tare da yace uffan ba….. Ganin yanayin kallon da ya ke yi mata ne ya sanya ta yin shiru a take ta kauda kanta daga gareshi ta had’iye ragowar maganganun nata. Ya jima yana kallonta kafin ya d’auke idanuwansa daga gareta ya fesar da iska ya mik’e tsaye! daganan ya fara k’ok’arin barin wajen. Cikin tsananin sanyin jiki ta ce ‘’Yash’’ Juyowa kawai ya yi ya tsaya yana kallon ta. Gaba d’aya kuma sai ta diririce ta gagara cewa komai Ta hau kame-kame ‘’am dama a ganina bai kamata ka gayawa Daddy…..” A hankali ya ce ‘’Mommy ..’’sannan ya ɗan girgiza mata kai yana mai lumshe idanunsa ya bud’e daga haka ya juya ga Yahanasu ya ce ‘’Allah ya tabbatar da alkhairi.’’ Yana gama faɗin haka ya sa Kai ya fice daga parlourn ko sai da safen su Yadira bai tsaya amsawa ba. Mommy ji ta yi kamar ta d’aura Hannu a ka! Ta yi ta kurma ihu!!! Tabbas idan akwai Yaron da bai San darajar mahaifiyarsa ba tou Yashjub ne….kalli fa bashi ma da lokacin yi mata magana ballantana a je ga sauraronta ko bata haƙuru. Tana tsananin k’aunar Yasir amman ya zama dole ya hak’ura da Kausar Yashjub ya aura dan bata hango shak’uwar da take kwad’ayin samu daga gare sa ba muddin ya yi aure ya tare chan da wata ba Kausar ɗin ta ba! Musamman ma idan ya samo wadda yake so! Shikenan ta zama ƴar kallo a gefe.. Tana wannan tunanin ta dake ta cire tsoro ta nufi sashen Daddy da niyyar tana gamawa da shi kuma zata lek’a d’akin Baba Larai saboda tabbas a yau take so a yi ta, ta k’are!!. Ɗaya bayan ɗaya aka dinga watsewa daga dining table ɗin, ya rage saura Yasir shi kaɗai. Ya yi mamaki haɗe da jin zafin yadda k’iri-k’iri ya hango rashin amincewar auren nasu a kwayar idanun Mommy! shiyasa tun lokacin ya fad’a duniyar tunani ya gagara cewa komai har izuwa yanzu da kowa ya watse ya bar sa a wajen. A hankali ya mik’e ya nufi sama sashen Kausar amman ko da ya je ɗin sai ya tarar da k’ofarta a rufe ruff!! Babu kalar bugu da kiran wayar da bai yi mata ba amma sam ta ƙi yarda ta bud’e, ta ma ƙi kula shi. Haka nan ya gaji ya kama hanya ya sauk’a ya fita daga sashen gaba d’aya ya nufi nasu, wanda yake a jikin mansion d’in amma k’ofar su ta baya take da wani makeken compound a wajen wanda ya ma fi na gaban gidan dan tsaf za a iya gina irin mansion d’in guda a wajen! Da har da gate d’insu daban a wajen amma saboda yawan yawon dare da Yasir ya tsira yakeyi ne ya sanya aka rufe gate d’in Daddy ya hana fita ta nan gabad’aya. …. Parlour ne babba sosai sai kitchen, dining area da 2 bedrooms a k’asan sama kuma 2 bedrooms ne ko wanne da parlourn sa sai saperate d’aki guda d’aya, Side d’in nasu ta b’angaren mansion d’in mai hawa ɗaya ne sab’anin na su Daddy wanda ya had’a hawa biyu…. A nan main parlourn ya tarar da Yash yana zaune yana sipping tea yana waya a hankali. Mommy ta gaya masa yana nemansa! Sannan So yake ya tambaye sa abu dan haka ya nema waje ya zauna shima akan d’aya daga cikin kujerun parlourn. sai da ya zauna tukunna ya fahimci ashe da Abokinsa ‘Najeeb’ yake wayar Wani dan guntun Murmushi Yasir ya yi a ransa ya ce ‘’Haba, dama ni dai na san ba da Mace yake wayar nan ba Mutum sai kace waliyyi …..’’ Ya fi 1 hour yana waya kafin finally ya ajjiye wayar ya d’ago ya na kallon Yasir ya ce “Ka je kawai, maganan da za mu yi an gama ta tun ɗazu a wajen dinner, an rufe komai ai” Murmushi Yassir ya yi ya ɗan sunkuyar da kanshi ƙasa ya ce “eh”sai kuma ya ƙi tafiya, dan haka Yashjub ɗin ya ce masa ‘’Lafiya?’’ Sai da Yassir ya ɗ’an sosa kansa tukunna ya ce ‘’Um, dama ina d’an son…’’ Tun kafin ya k’arasa Yash ya ce ‘’Kud’i,ko?’’ Murmushi ya yi kafin yace ‘’yess,a lot (masu yawa)” A hankali Yash ya mik’e tsaye sannan ya ce ‘’Yadda Daddy ya Zuciya da ku ɗinnan Yassir idan ka yi dinner ko wani shirme a auren nan ka san ranka ne zai yi mummunan b’aci,therefore ba za ka samu kud’i daga gareni ba, gaskiya’’. Yana gama fad’in haka ya wuce sama. Yasir ji yayi kamar ya bi shi a baya ya make shi! a ransa ya ce ‘’Munafuki!!! Ai kaine ka janyo Daddyn ya ke fushin da mu, duk da dai munafurcin naka yau ya yi mini rana tunda gashi gobe za a aura min farin ciki na .’’ Mutsutstsuka idanunsa ya yi, ya fesar da iska kafin ya mik’e shima ya wuce saman yana tunanin ta yadda zai yi raising kud’i!! dan ba zai yiu ace bikin su shi da Kausar amma wai babu dinner ba wani shagali ba…… ……. A bakin gado Mommy ta samu Daddy, a tsaye yana shirin shiga wanka. Ya ji shigowar ta, dan haka ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘’Don’t try anything stupid (kar ki gwada yin shirme a lamarinnan) Khadijah daga nan har gobe. Ban san wasan da kike son bugawa wannan karon ba amma ina shawartar ki da kar ma ki fara shirin yin komai, idan kuma ba haka ba to zan baki mamaki.’’ Ba tare da fargaba ko tantama ba ta ce ‘’Ba wai shirin wani abu sabo zan yi ba, dan na riga na gama shiri na, kawai dama naga kamatar in sanar maka abunda ya kamata ka yi ne domin ya tafi dai-dai da shirin nawa! Dan haka ka saurara ka ji ‘Inaso ka janye maganar auren Yasir da Kausar, dan ba mai yiuwa bane ba’.’’ Sai yanzu Daddy wanda ya gama d’aura igiyar bathrub ɗin da ke Jikinsa ya juyo gareta, ya d’an taka inda take ya tsaya tukunna ya ce ‘’Dole, a gobe Kausar za ta fitar mini daga gida Khadijah, It’s either ta wuce gidan Yasir ko kuma ta san inda zata je, na yi iya yina!!.’’ Wani kalar murmushin takaici Mommy ta yi kafin tace ‘’Ai dama na sani, na san ka gaji da rik’e ta ne shiyasa za ka yi mata auren dole.’’ Cikin fushi Daddy yace ‘’A kul d’inki Khadijah!. Idan ke dak’ik’iya ce baki san ciwon kanki ba baki san kishin d’an da kika haifa a cikinki ba tou ni na sani. Ki godewa Allah ma da har na yarda Yasir zai auri Kausar d’in… Allah na tuba Maraici ai ba hauka bane ba! Yarinyar nan fa har haihuwa ta yi sannan bata da uba! Amma duk da haka na amince na yarda zan aurawa Yasir ita.. Shine amma har kike da bakin cewa za a yi mata auren dole?’’ Daddy bai tsaya jin amsarta ba ya d’aura da cewa ‘’Bari kiji, ba don na san Yasir yana da ikon k’ara aure ba to da ba zan bar shi ya auri shegiya ya rayu da ita ba wallahi.’’ Kamar an kunna fanfo haka fuskar Mommy ta jik’e sharkaf da hawaye, Cikin kuka ta ce ‘’Na gode ‘Imam’ na gode sosai. Alk’awarin kenan ko? Allah ya ji ƙan Abba da Daddy… A gaban su ka amince za ka rik’e Kausar, ruk’o na amana amma yau da kanka da Bakinka kake cewa ta fitar maka daga gida da kanka kake kiran ta da sunan ‘shegiya’ D’an Adam butulu, walllahi Allah sai ya yi mana hisabi.’’ Cikin tsananin b’acin rai ya ce ‘’Dole in ce Kausar ta fitar mini daga gida, Khadija ‘Ƴaƴana takwas a duniya amma babu wadda a kullum take d’aga mini hankali take janyo min abun kunya da magana sai y’ar ruk’o, ko su Mazan ba sa yin fitinar da Kausar take yi!!!. Kalli yanzu yadda ta lalata Yassir, shikenan ni kullum gidana cikin case saboda ita?. Ki duba fa ki ga yau tafiya na yi na dawo amma ko isashshen sannu da zuwa da hutawawa ban samu ba ban yi ba na fara da case din y’ar ruk’o.’’ Cikin d’aga Hannu (alamun stop ) Mommy ta ce ‘’Dakata daganan Daddy. Maganganun ka ga Kausar sun ishe ni, sannan idan ba zaka kirata da Kausar ba to ka yi shiru! dan shegiya ko y’ar ruk’o ba sunanta bane ba, gorin ka da cin fuskar yayi yawa haka ya isa!!!. kuma ta Ina kausar ta lalata Yasir?fyad’e ta yi masa? da aka ce maka sun tafi Auckland d’in tare shi munafukin naka camera ya mak’ala musu ya ga sun yi wani abun? Baya ga haka ba fa su kaɗai suka yi tafiyar ba?? har da Abokansu suka tafi. Kawai kai dai ka tsani Kausar! Na riga na sani tun ba yauba ka tsane ta shiyasa kullum burin ka ka ga ka k’untata mata. Tayaya ma za ka ce wai Kausar ta lalata maka ɗa! haba Daddy, ka dinga adalci mana, ko kara babu?’’ Cikin takaici Daddy ya ce “karar da na yi tun farko ita ta cutar da ni, gashi inaji Ina gani Yasir zai auri Matar da sai addua kawai, kuma a matsayin uwar gida, Idan jikokina suka tashi a gagara nuna musu dangin uban Mahaifiyar su’’. Cikin jin-jina kai Mommy ta ce ‘’shikenan tunda kai ba Mahaifinta bane ba! ka faɗa ka nuna kuma ka furta. Tou nima daga yau Inaso ka tsame Hannunka a duk lamari da rayuwar Yarinyata. Aure kuma da Yasir tunda har kana ganin kamar za a cuce shi ne to wallahi ba za a d’aura ba! Idan kuma ka d’aura to za a sha mamaki na. Tunda baka son had’in ta fi nono fari muma bama so. Kuma inshaaAllah daga yau Ni zan dinga kula da ƴata, babu ruwan ka da duk wani abun da ya shafe ta! Zan nemo cook inn siyo kayan abinci a dinga yi mata girkinta a daban… k’arshen wata kuma zamu dinga biyan ka kud’in haya, ruwa da na wuta!!! Iyakar abunda nake nema daga gareka shine ka daina takura mata, kuma ka daina yunk’urin yi mata dole. Iyakar tsakaninka kai da ita gaisuwa. Tunda a iya sani na babu inda Kausar za ta je muddin Ina cikin gidan nan, dan haka sai ka jira har sai ranar da Allah ya kawo mata wanda take so ta aura tukunna.’’ Tana gama fad’in haka ta juya zata fita sai kuma ta juyo ta dawo inda yake nan tsaye ranshi a mugun b’ace ta ce ‘’Allah dai ya so ba y’ar uwata kad’ai bace ta fara haifar shege! kafin ta yi kafin Kausar ta yi sai da aka yi!!! Ko in je in kawo maka Yahanasu? Na san wataƙila idan ka kalli fuskarta zaka iya tuno da wadda nake nufi da kuma abubuwa da dama, saboda kalamanka da k’iyayyar ka ga shege sun sanya na fara tunanin maybe ko dai ka yi loosing memory ne. A yadda ka tsani Kausar kake kyamar ta inada tabbacin ta fi dubu! saboda na tabbata in dai Kausar ta auri wanda take so kuma yake son ta to ba za ta tab’a cutar sa ba baza kuma a kamata da waninsa ba! saboda ƴata tanada ruƙon amana kuma na san ta san darajar soyayya……….. Cikin tsananin fushi Daddy ya yunƙura da dukkannin ƙarfinsa ya ɗauke ta da wani gigitaccen mari. Dagowa ta yi da niyyar ci gaba da tsiwa amma sai yanayinsa da idanuwansa suka sanya ta had’iye maganganunta da tsiwar tata domin a yadda ta ga yana kallon ta da jajayen idanuwansa tsaf zai iya illatata. Da kyar ya iya cewa ‘’Fita kar in sake ganin fuskarki idan ba ni na neme ki ba.’’ Babu musu, haka nan ta juya ta fice daga d’akin dan ta tsorata da yanayinsa. Tana fita kuma sai ta ji wani sanyi ya lulluɓe ta, a haka ta fita daga side ɗin nasa gaba ɗaya ta sauƙo tana mai jin zuciyar ta fess!!! Tabbas ta san dama idan ba da gaske ta yi ba to ba lalle ta iya hana auren nan ba! Amman a yadda ta tsokalo Daddy ta tuna masa da baya to fa ba lalle ya iya shan ruwa ba ma daga nan har Jibi, ballanta har a zo ga maganar ɗaurin aure!! Yayinda a chan k’asan zuciyarta kuma sai ta ji kishi yana taso mata! Sakamokon k’unci, damuwa da tsananin kishin data gani a Idanuwan Daddy kamar jiya jiya abun ya faru………… •••••• Kamar yadda Al’ameen ya ce, Da yamma kusan magrib sai ga shi ya dawo da laidoji nik’i-nik’i. Ya kuwa ci sa‘a dan Jiddah ce a wajen, Manubiya an tafi yi mata test saboda tunda Baba ya lura ba ta da lafiya duk sai ya damu da kyar ma ya wuce gida shi da Muhsin ya barsu tare da Ya Musbah akan idan komai yayi settling shi sai ya dawo ya bar Jidda da Manu su kwana washegari kuma ya koma su dawo su yi girki, idan Allah ya kaimu. Tunda ya shigo ta diririce gashi Inna ma bata jima da komawa bacci ba. Dariya ta so ta ba shi dan kamar irin zai sace ta d’in nan haka yaga tana yi…. Cikin sanyin murya da sanyin jiki ta gaida shi, shi kuma ya amsa mata da kulawa yana mai tambayar ta “ya jikin Inna?” A hankali ta ce ‘’da sauk’i’’ Har zai zauna sai kuma ya ƙarasa gaban gadon ya ajjiye ledojin ya ce mata ‘’gashi’’ tukunna ya dawo ya zauna. Da kyar ta ce ‘’mun gode’’ Sai kuma ta ɗan yi shiru kafin ta ce ‘’Ya Al’ameen ka daina, dan Allah’’ Wani d’an guntun Murmushi ya yi kafin ya ce ‘’in daina me?’’ Ya faɗi hakan yana mai kafeta da idanuwa. Sai da ta ɗan ɗauki lokaci tukunna da kyar ta ce ‘’ka daina kallo na sannan dan Allah ka daina zuwa, mun gode sosai, amman Ina tsoron Ammi. kar a zo ta gane kana zuwa nan, kaga Inna bata da lafiya dan haka idan aka fara wani case na daban kuma abun ba zai yi dad’i ba’’. A hankali ya sauk’e ajiyar Zuciya kafin ya ce ‘’Ko yanzu kafin in taho saida na gayawa Ammin inda zan je’’ Da sauri Jidda ta ɗago manyan Idanuwanta tana kallon sa! Shima itan ya ke kallo dan haka ta yi saurin yin ƙasa da kanta. Murmushi kawai ya yi kafin ya ce ‘’Jidda I love you. Na san Ammina tana son duk abun da nake so, wanchan karon ma mishkila aka samu kuma bana nan amma yanzu komai ya daidaita. Ki kwantar da hankalinki dan Allah, ta ce ma zata zo har nan ta duba Inna, sannan ta ce in cewa su Baba su yi hak’uri komai ya wuce. Kuma ko yau kafin in fito ma sai da muka yi magana da ita akan ‘Ina dawowa daga tafiyar nan da zan yi im sha Allah za a fara maganar auren mu kuma ta amince d’ari-bisa-d’ari, ta ce ba za ma a d’auki lokaci mai tsayi ba, Abba kam dama shi ba shi da problem da auren tun farko. So please had’in kanki kawai nake nema a yanzu. Na san kwanakin baya dole kun ji babu dad’i kuma kun ji haushi amma pls darling ki yi hak’uri ki yafewa Al’ameen d’inki ki yafewa Ammi itama kin ji…”. Ya ƙarashe maganar kamar zai fashe mata da kuka. Shiruuu Jidda ta yi ta fad’a duniyar tunani… Ita kanta ta san k’arya takeyi idan ta ce bata son Ya Al’ameen wanda tun tana ss1 su ke soyayyar su a b’oye a layin, saboda a lokacin ta san Baba ba zai tab’a barinta kula samari ba. Haka Al’ameen ɗin ya yi hak’uri yayi ta jiran ta har ta kammala tukunna ya baiyyanawa Baba da Ya Musbah manufar sa… Sun kuwa yi farin ciki ba wai dan saboda tsananin arziƙin Mahaifin shi ba wanda kaff Unguwar ba za’a nuna wanda ya kamo k’afarsa a kud’i ba! Sai dan hankali da sanin ya kamatan Al’ameen d’in. Duk arzik’in Mahaifinsa shima bai nuna k’in amincewa ko kyama ba, farin ciki ma ya yi da ɗansa ya samu wadda ya ke tsananin so har haka… Amminsa ce a lokacin ta kafa ta tsare ta zuba musu tujara sosai Sannan ta ce ‘sam bata yarda d’anta ya auri y’ar talakan miskini ba’. To yanzu kam in dai Ammin tasa ta amince kamar yadda ya fad’a shikenan ai bata da wani issue sam, Ammi kamar uwa take a wajen ta kamar yadda Al’ameen ya nemi ta yafe mata tsaf zata yafe mata dukkannin abunda ta yi mata ita da ahalinta wannan ba matsala bace ba.. ‘’Jidderty’’ Ta ji ya kira sunan ta. A hankali ta ɗan kalle sa sai kuma ta sunkuyar da kanta. Zai yi magana kenan Manubiya ta turo k’ofa ta shigo… Suna had’a Ido da ita ya fara murmushi kafin ya ya ce ‘’Yayata wadda bata k’aunar gani na’’. Cikin tarar numfashinsa ta ce ‘’Ka fad’a da k’arfi ka buga a jaridar da zata fita gobe, dan maganarka hakan take’’’ Da sauri Jidda ta ce ‘’Adda ‘’ Wani kallo Manubiya ta yi mata dan haka ta ja Bakinta ta yi tsit! Sannan ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba. Kusa da Inna kawai ta k’arasa ta nemi waje ta zauna ta had’e rai, taso ta wanke Al’ameen amma sai takaicinsa da na jidda suka hanata iya cewa komai. Sun fi mintuna talatin a haka kafin daga baya Al’ameen ɗin ya mik’e ya ce ‘’ni zan wuce’’ ‘’Mun gode’’ kawai Jidda ta xe Manubiya kuma ta mike ta ce ‘’Mu je, ina son ganin ka’’ Ko da suka fita nicely Manubiya ta rok’e sa akan ya daina bibiyar su… Amman sai ya tabbatar mata da cewa ‘’Ai Ammi ta sauk’o, ta ce a basu ma hak’uri kuma zata zo da kanta ta duba Inna’’ Ita dai Manubiya still cewa tayi ‘’Ya d’an jira sannan ya daina yawan zuwan har sai an tabbatar da amincewar Ammin, domin su a yanzu rikici da tashin hankali is the last thing da za su yi involving kansu a ciki ‘’ Ba dan ya so ba sai dan yadda Manubiyan ta dage, haka nan ya ce mata’’ tou ‘’ kawai ya wuce. Ko da ta koma ciki ma sai da ta zubawa Jidda serious warning kuma ta ga jiddan ta yarda tukunna ta kyale ta. Tana kokwanton maganar Al’ameen ‘Wai Ammi ta yarda ya auri Jidda ‘ *Bayan Sati Biyu* Successfully aka yi aikin Inna, Manubiya da Jidda ne suke yi mata wanka da komai dan har yanzu b’arin Jikinta sam baya aiki, ko magana ba iyawa take yi ba. Sun so su koma ward amma sai aka ce musu ai Al’ameen kud’in wata d’aya ya bayar so koda ace ba a kai one month d’inba ya ce su za a bawa chanjin. Tunda Jidda take a rayuwar ta bata tab’a b’oyewa Manubiya wani abu ba sai wannan karon.. Dan a washegarin ranar da Manubiyan ta ce kar ta sake kula Al’ameen sannan shima kar ya sake zuwa ma sai da ya dawo kuma ya sake cin sa’ar samun Jiddah ita kad’ai lokacin Manubiya ta tafi allura. Ganin tsoro k’arara a Idanun Jiddahn ne ya sanya ya ce mata “gobe zai dawo Karfe 4 na yamma”yayi mata kwatancen in da za su had’u. Haka nan su ka dinga yi Idan lokacin zuwan sa ya yi sai ta kwashi wanke-wanke ko ta karb’a sak’o In ta je bata dawowa sai sun sake had’a Appointment na inda za su had’u washegari. Shi Al’ameen baya son causing mata problem da su Manubiya kuma Ammin nasa bata samu daman zuwa ba ta tafi ummara Shi kuma yana ganin tunda har mahaifiyarsa da mahaifinsa sun amince a gaskiya ba zai iya yin nesa da Jiddah ba, dan yana mutuwar k’aunar ta. Ita ma jiddan tana son abunta Kuma saura masa sati uku a lokacin yanzu kuma saura sati d’aya ya tafi wani course da zai yi na 4weeks Shiyasa kawai ta amince kuma ta b’oyewa Manubiya dan kar ta hanata…. A cikin sati biyun nan kuwa soyayya da shaƙuwa ta sake ƙulluwa tsakanin su bata wasa ba. ••••• BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *09* *2 weeks ago* *(sati biyu baya)* Kamar yadda Mommy ta yi tsammani… Washegari da safe ba zancen auren Yassir da Kausar! Sannan babu Daddy babu alamun sa. Ita a tunanin ta fushi yayi ya zauna a ɗaki, sai da dare yayi ta je domin ta kai masa dinner tukunna ta fahimci ashe bama ya gidan gaba d’aya! Dan a nan inda ta ajjiye masa breakfast da lunch a kan dining table ɗin parlourn nasa anan ta dawo ta same su yadda ta ajjiye babu ko alamar an tab’a ma. Tabbas ta d’an firgita musamman ma da ta shiga d’akinsa ta tarar ya kwashe kusan kaff kayansa,tun anan ta sha jinin jikinta sannan ta fara da na sanin ambato masa ‘Khadijah’ da ta yi a jiyan bayan k’wak’kwaran warning ɗin da ya zabga mata ita da su Yahanasu akan kar wanda ya kuskura ya yi zancen ko ya ambato ko da sunan Khadijahn ne a cikin gidan.. Tana tsaye tana tunanin ta hanyar da zata bi ta shawo kan Daddy domin ta san ba k’aramin yaji yayi mata ba, Yassir ya shigo. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya domin tun safe yake tambayar ta ‘ina Daddy’ ita kuma ta zabga masa k’aryar ‘Daddyn ya ce sai gobe za a d’aura musu auren sannan ya tafi shirye shiryen gidan da za su zauna ne, shiyasa bai gansa ba.’ A b’angaren Yasir kuwa dama tun d’azu da safen da ta fad’a masa maganar bai wani gasgatata ba shiyasa gaba d’aya tun safe hankalinsa a tashe yake! Kausar itama ta k’i ta bari ya ganta, ta kashe wayoyinta! Daddy baya amsa calls d’insa, Mommy kuma ya lura kamar avoiding d’insa ma takeyi(wasar ƴan ɓuya take yi da shi). Jiya bai yi barci ba sai da ya had’a Dinner ta gani ta fad’a wadda za a gudanar a yau da daddare bayan an kai masa Kausar gidansa,kusan kaff Abokanayen su babu wanda bai fad’ama yau auren shi da Kausar ba, a dai dai wannan lokacin side d’in su shi da Yashjub a cike yake taff da abokanayen su waenda suke gari maza,matan kuma ya kaisu side d’in Yasira dan kausar ta yi wuyar gani. Abhankali ya taka ya isa gaban Mommy ya tsaya, farar Fuskarsa har ta yi jajawur dan tashi d’aya ya hango rashin gaskiya a tare da Mommyn… Manyan Idanuwansa da suka yi jazir ya zuba mata kafin ya ce ‘’Mommy stop toying with me(Mommy ki daina yi mini wasa da hankali) na rok’e ki da girman Allah ki fad’a mini me ke faruwa’’ Sam, Mommy bata yi tsammanin wannan ɓacin ran daga Yasir lokaci d’aya ba! Dan hatta jijiyoyiin kansa sun fito sun yi rud’u-rud’u, kan dogon hancinsa ma yayi jaa sosai. A hankali cikin in ina ta ce ‘’Son,mun d’an samu matsala ne da Daddyn naku jiya,so ya yi fushi ya tafi.’’ Ba tare da ya daina kallon ta ba Cikin tarar numfashinta ya ce ‘’Ina yaje???’’ A d’an rikice ta ce ‘’In da ace na sani da zan fad’a maka,’’ Da d’an k’arfi ya ce ‘’Dole kin sani, ai na san da gangan kika janyo fad’an saboda ba kya son auren ba kya son farin cikina, dan haka dole ki sani kuma dole ki nemo sa,haba Mommy how could u???? kin fi son farin cikin Kausar akan nawa ne??? kamar ba ni ne d’anki ba.’’ Da sauri ta matso ta kamo Hannusa kafin ta ce ‘’Ba haka bane ba Yassir, wallahi duk abun da ka ga nayi Gaba nake hango maka, farin cikinka da dauwwamar cikar burin ka shi nake tayaka nema… Kai farin cikin yanzu kake so ka samu Ni kuma hangen nesa nakeyi maka. Yassir ka fahimce ni ka yarda dani duk abun da na yi wallahi nayi ne saboda kai kad’ai, Trust me.’’ Cikin fushi ya fincike Hannunsa a nata kafin ya ce ‘’I’m not interested in anything u have to say Mommy(ba na son jin komai daga gareki Mommy), na baki 3 hours ki nemo shi Idan kuma ba haka ba to nima zan bar gidan nan kamar yadda Daddy ya bari har sai kin gyara abun da kika b’ata an d’aura mana aure da Kausar tukunna za ki ganni.’’ Yana gama fad’in haka ya juya zai fita, da sauri ta sha gaban sa da niyyar rarrashi. Amma tun kafin ta yi magana ma ya d’aga mata yatsunsa guda uku! Cikin tsananin ɓacin rai wanda ya had’e masa da tashin hankali ya ce ‘’3 hours Mommy,awanni uku kacal.’’ Bai iya jira awanni ukun sun cika ba ma tsabar maɗaukakin ɓacin rai, yana fita ko bi ta kan frnds d’in nasu bai yi ba, dan bai san ta yaya zai yi facing d’in su ba. Hatta ɗayar wayarsa bai biya ya d’auka ba! Allah ya so shi akwai car key a jikin sa dama dan haka ya nufi mota ya shiga ya kunna ya ja ya fice daga cikin mansion d’in. .. Tun daga nan babu Daddy babu labarin sa Ba kuma Yassir shima. Ko da Abokin Daddyn ya zo ganin Yahanasu, Yashjub ne ya tsaya ya tarbi bak’on, haka ita kuma Yasira da Mommyn suka san dabarar da suka yi suka sallami frnds d’insu ƴan biki waenda Yassir ya tara…….. ••••••• Yau satin Inna biyu a asibiti, tunda ta kwanta a asibitin sau biyu kawai Mannubiya ta samu ta je makaranta. Ita kanta ba wai lafiyar gareta ba dan zazzab’i da ciwon kai sun sakota a gaba. Yau suna zaune da rana gaba d’ayansu sai ga Baraka! Ita da Mamanta da Abbakar da Mamansa shima. Tun lokacin da Innar ta kwanta jinya yau ne zuwan Baraka na farko kuma shima haka nan ta taho ko ruwa bata ruk’o ba ballantana azo kan maganar yi wa marar lafiya girki… Ƴan gidansu Manubiyan suma Siyama ce kawai Anty Umma ta turo, bayan ita babu wanda ya zo. Abbakar, Ya Nafi’u da Al’ameen wanda yake zuwa a b’oye ne kullum sai sun zo, Matar Ya Nafi’u itama zuwanta har hud’u….. A nan kan k’atuwar taburmar da suka shimfid’e a tsakiyar d’akin suma ƴan dubiyar duk suka nemi waje suka zazzauna. Cikin mutunta juna suka gaisa da Baba tare da tambayar sa “ya mai jiki” ya amsa musu da ‘’da sauk’i’’daga nan ya mik’e ya fita ya bar musu d’akin… Haka shima Ya Musbah ya mik’e ya fita bayan sun gama gaisawa da surukan nasa. Ɗakin ya rage saura Matan kawai da Innar sai Abbakar dan Muhsin ma Hannun Baba k’arami ya kama suka fita tare da Ya Musbah. Gaisawa suka sake yi daga nan suka shiga tambayar su ya mai jiki da yanayin jikin nata. Baraka bata wani dad’e a zaune ba ta mik’e ta bi bayan Ya Musbah, bayan ta gama ƙarewa ɗakin kallo. Tana fita Abbakar ya kalli Manubiya ya ce ‘’Jiya fa sir Najeeb ya yi test’’ A firgice ta ce ‘’Wasa kake yi,Amma ko?’’ Cikin dariya ya ce ‘’A’a wallahi, da gaske nake,ya yi test jiya’’ Kamar za ta fashe da kuka ta ce ‘’Haba Abbakar, shine kuma baka gaya mini ba, na zo tun a lokacin na yi’’ Da sauri cikin katse ta ya ce ‘’in da ace kin je ɗin mai za ki iya rubutawa? Ai na san sai dai ki yi ta kukan da baya so, a ajin’’ Still yanzun ma kamar mai shirin yin kuka ta ce ‘’Still dai, ai da ko attendance ne na yi. Yanzu shikenan bani da test d’in?’’ Cikin son sake firgitata Abbakar ya ce ‘’Kuma ya ce shine na continuous assessment’’ ‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’ Manubiya ta ce duk ta rikice. Ganin yadda duk ta gigice ne ya sanya ya yi dariya sannan ya ce ‘’Matsoraciya kawai, na yi miki tou’ Da sauri tana mai sauk’e ajiyar Zuciya ta ce ‘’Da gaske ? Test din ?’’ ‘’Eh mana’’ ya bata amsa yana murmushi. A hankali ta ce ‘’Allah sarki, Abbakar Na gode sosai’’ A tare duk su ka yi dariya har Jiddah. Mik’ewa ya yi, ya ce ‘’bara in wuce kasuwa, Allah ya k’ara sauk’i. Mu je in baki handouts d’in da ya fitar a jiya, ya ce gobe zai kuma yin open test shima part of CA ɗinmu ne’’. ‘’Okay’’ ta ce, tana mai mik’ewa sannan ta k’ara da cewa ‘’Mutumin nan d’an wahala ne Wallahi Da shi da test 5&6’’. Dariya ya yi daga nan suka saka kai suka fita a tare. A bakin ward d’in ta hango Ya Musbah shi da Baraka a tsaye! Kallo ɗaya za a yi wa Fuskokinsu kai tsaye a fahimci fad’a su ke yi. Baraka ce take facing d’in ta dan haka tana ganin tahowar ta ta yi shiru, har suka zo suka wuce. A cikin garden ta chan gefe ta hango su Muhsin da Baba a zaune…… Allah sarki Abbakar… Duk wasu handouts d’in da aka fitar na course d’in da suke yi sai da ya siya mata, daman exams ta taho! Duk haka ya had’a ya bata sannan ya sake tabbatar mata Da ‘ta zo gobe.’ Ta san saboda mamansa ne ya sanya ya ce ‘iya na sir Najeeb ya siyo mata’ dan ta lura da yadda suka yi a lokacin da ya ce ‘yayi mata test d’in’ ma. Shiyasa itama da ta karb’i jakar ta yi godiya ta goya a bayanta, ta ci alwashin b’oyewa…… Har ta karya kwana ta nufi inda su Ya Musbah suke sam ba su lura da ita ba! Ranshi a tsananin b’ace yake ita kuma Baraka ta bata baya shiiyasa duk basu lura da ita ba. Tun kafin ta k’arasa kusa da su ta ji Ya Musbah yana cewa ‘’Yanzu Baraka ya kike so in yi? Ko sata kike so in je in yo? Na fad’a miki wallahi babu kud’i a Hannuna’’ Cikin tsiwa ta ce “Eh kam babu kud’i a Hannunka ga alama nan ai na gani! Rashin kud’in naka ne ya sanya Innar ka take kwance a aminity d’aki cike da kaji da lemuka!! Ko y’an uwanku ne suka kawo? ‘’. A zuciye ya ce ‘’Ba na son cin fuska kuma.! Na ce miki ba ni da kud’i hidima kuma da kika gani ba ni nake yi ba! Ki yarda ko kar ki yarda wannan ba matsala ta bace ba. Akwai kud’i a hannun ki na sani ba wai babu ba dan haka idan za ki yi hidimar gida dasu Bismillah… Duk ranar da na samu zan maida miki, Idan kuma za ki iya barin ɗan da kika haifa a cikin ki da yunwa saboda rashin sanin ciwon kai to shima Bismillah… Sannan idan kinga ba zaki iya ci gaba da zaman ba nan ma kin san mai za ki ce min inyi ni kuma in sha Allahu zan yi miki yadda kike so’’ Cikin tsananin b’acin rai ta ce ‘’Eh lalle Musbahu ka yi arziƙi, ga alama nan na gani…ai dama ku Maza haka kuke, wato kud’i sun fara zama maka shine ni Baraka yau nice abar wulakantawa ko? Ka barmu da yunwa ni da d’anka ka dauko Babarka ka kawo aminity kuma na yi magana ka ce za ka sakeni Saboda yanzu ka san kana da kud’in da za ka yi wani auren idan na tafi ko …’’ Cikin katse ta ya ce ‘’Ba wai cewa na yi zan sake ki ba, cewa na yi idan kinga ba zaki iya zama ba to ki fad’i abun da yake ranki ni kuma in aiwatar. Magana ta ta ƙarshe anan ‘ki yarda ko kar ki yarda Ba nine nake hidimar asibitin nan ba, saboda bani da shi. Dan haka idan zan baki shawara ki d’auka to, ki je ki siyo kayan abinci ku ci da ke da mai sunan Baba kar ki damu da cikina In sha Allah zan samu abun da zan ci, kuma duk lokacin da Allah ya bani kud’i zan mayar miki’…’’ Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce ciki! Yana adduar Allah yasa Manubiya ba ta ji conversation d’in nasu ba dan shi sai yanzun ne ya lura da ita. Takaici kamar ya kar Manubiya, sam bata yi niyyar kula Baraka ba, dan haka ta zo za ta wuceta da sauri ta na jin wani takaicin ta na musamman yana rufe ta!. Ita kuma Baraka dai-dai ta juya dan haka suka yi kiciɓus!!!… Wani tsaki Baraka ta jaaa! Kafin ta ce ‘’Ni kam wannan aure, a cuce ka kuma ka yi magana aji haushi! Sannan ga ido ta ko ina…’’ Har Manubiya ta ɗan yi gaba sai kuma ta juyo ta dawo ta sha gaban Baraka, ta tsaya. Gyara tsayuwa kawai Baraka ta yi itama ta shiga watsa mata kallon wulaƙanci. Cikin takaici Manubiya ta ce ‘’Wallahi kin bada Mata, ai ko kishi da rashin hankalin ma yanzu an daina yayin irin wannan. Duk abubuwan da kike yi zuba miki ido kawai muka yi ba wai dan bamu san me kike yi ba ne sai dan a kullum adduar mu itace ki shiryu. Haba Baraka Mahaifiya fa? Itace abar kishi? Inda ace ma lafiyar ta ƙalau tou da da sauk’i amman bata fa da lafiya, a kwance take, a gani na idan baki taimako ba to bai kamata ki d’agawa kowa hankali ba. Kaico!!Wallahi Ya Musbah bai yi sa’ar Mace ba.’’ Yadda Baraka ta zazzaro Idanuwa waje duk wanda yagansu a wajen zai yi zaton daddanawa Iyayenta zagi Manubiya ta yi… Ta san dama Manubiya bata da hak’uri amman bata tab’a tunanin zata iya gaggaya mata magana har haka ba. Tijara da Zuciya da suka ciyota ne suka sanyata ta figo Hannun Manubiya da dukkannin k’arfin da Allah ya bata suka yi ciki tare. Tun daga bakin k’ofa ake kallon su, ga security ya biyo su yanata faman yi wa Baraka magana Yana cewa “ta sakar mata Hannu” amman sam Baraka bata da niyyar sauraren sa, ita kuma Manubiya taso yin tirjiya ko kuma ta fisge Hannun nata amman kuma a ranta sai ta ce ‘bara kawai ta barta’ gudun kar su yi kokawa ta sake tada wani case d’in a tsakiyar asibitin.. Ta fahimci d’akin da Inna take take shirin kaita shiyasa ta gama rayawa a ranta ‘suna shiga d’akin in ta cika ta ita kuma zata fice ta barta’ dan ta lura burin Baraka tabbas bai wuce ta ga gawar Inna ba… Da k’arfi ta tura k’ofar suka shiga tare ita da Manubiyan. Da sauri su Jidda su ka mik’e tsaye saboda a yadda Baraka ta shigo kamar wata mahaukaciya sun yi zaton wani gagarumin abu ne ya faru. Duk yadda Manubiya ta so ta cika mata Hannun sai ta kiya, ta rik’eta gam! Sai a sannan Manubiya ta yi dana sanin k’in kwace Hannunta tun a waje su yi ta ta k’are dan tana shigowa d’akin da Inna ta fara tozali ta bud’e idanuwanta sab’anin ɗazu da ta barta tana bacci. Da kyar Ya Musbah ya samu ya had’iye wani k’ululun takaici wanda ya tokare masa maƙoshi tukunna ya k’arasa wajen su. Ba tare da ya kalli Baraka ba ya cewa Manubiya ‘’D’auki jakarki ki wuce gida’’ Dan ya fahimci akan maganar da Manubiyan ta ji suna yi ne shi da Baraka, ta yi wa Barakan magana shine ita kuma ta janyo ta nan domin ta d’agawa Inna hankali. Cikin d’aga murya, hargowa da hayagaga Baraka ta ce ‘‘Ka san me ta yi mini ne da za ka ce ta tafi haka kawai, wato ta zagi banza ma kenan ko?. Allah na tuba in banda k’addarar aure da ta kanainaye ni a gidanka Manubiya ta isa ta taka inda na taka? Ballantana har ta kalle ni ta fad’a min maganar banza? A hankali Ya Musbah ya lumshe Idanuwansa waenda su ka yi jazirrr!! Kafin ya bud’e su ya zubawa Baraka ya ce ‘’Baraka saki Hannun Manubiya ta wuce gida. Zan yi mata magana.’’ Cikin gurb’atacciyar Hausa security d’in da ya biyosu shima ya matso ya ce ‘’Madam, cika mishi Hannu, ki bar fad’a, ba’a hayaniya, kalle patient fa” Ya yi maganar yana nuna Inna wadda ta kafesu da Idanuwa. A hankali Ya Musbah wanda ya ke ji kamar ya nutse a cikin ƙasa ya ɗan waiga ya kalli Innar kafin ya juya da ɗan zafi ya ce ‘’Baraka ki sake ta, ta wuce nace, ko?’’ Cikin tsananin tsiwa rashin kunya sannan da ƙarfi ta ce ‘’Kaga rufe Bakinka, tunda ba za ka yi adalci ba! Ƙanwarka ta zage ta zuba mini rashin kunya sannan ko bin ba’asi ma baka yi ba kace kawai in cika ta ta tafi? wato ban isa bama kenan ko? To Bari ka ji bayan cin kashin da kake yi mini da azabtar dani ɗin da kake yi wallahi ban shirya sake d’aukar rashin kunyar k’annenka ba, dan haka ba zan cika ta ba kuma sai ta bani hak’uri yanzu ba sai anjima ba sannan ka kora mata zazzafan warning idan kuma ba haka ba to wallahi sai mun kwashi y’an kallo ni da ita’’ Da mamaki Manubiya ta ke kallon Baraka… ba abunda ya fi bata mamaki irin yadda Barakar ta ke ihu bayan ga Inna a kwance sannan ta bi ta wani dage akan wai an yi mata rashin kunya bayan ita Manubiyan ta bata wata biyu a duniya! Yanzu haka ita ta cika shekaru ashirin da biyu ita kuma Barakar sai watan gobe…. Security ya yunk’uro kenan zai yi magana Maman Abbakar ta mik’e ta ce masa ‘’Yi hak’uri, je ka. Za su yi shiru, bara in yi musu magana’’ Ba dan ya so ba ya juya ya fita dan ya k’ule sosai da Baraka. Yana fita Baba yana shigowa rik’e da Hannun takwaransa, Muhsin na biye a bayan su. Dama tun kafin ya k’arasa ya ke jiyo hayaniya gashi kuma ya tadda su cirko-cirko dan haka ya hau tambayar su ko lafiya…. Maman Abbakar ce ta ce ‘’Tou Baba Musa, ka san dai Manu da Baki da kuma rashin kunya! To inaga yau abun nata ya biyo ta kan yayar tata ne, dan gashi har janyo ta ta yi ta kawo k’ara shi kuma Musbahu ya ma k’i ya bari a yi maganar, sai cewa yake ta yi Manubiya ta wuce ta tafi kawai zai yi mata magana’’. A cikin ransa Baba ya shiga karanto sunayen Allah. Tsit haka d’akin ya d’auka. Sai da Baba ya ji ya d’an dedeta tukunna Ya ce ‘’Musbahu ya ce Manubiya ta tafi za su yi magana saboda nan d’in d’akin mai jinya ne wadda take fama da kumburin zuciya, hawan jin, k’oda da kuma mutuwar b’arin jiki. Ina fatan kun fahimci dalilin da ya sanya ba ya so a yi wata rigimar a gaban Idanunta kar ku yi masa mummunar fahimta, ba wai son kai yake shirin gwadawa ba ….’’ A hankali ya juya ya kalli Baraka tukunna ya ce ‘’Me kike so Manubiya ta yi miki yanzu?’’ A hankali ta sunkuyar da kanta ta cika Hannun Manubiya tukunna ta ce ‘’Baba ta bani hak’uri, karta sake kuma’’ ‘’InshaaAllah” Baban ya ce Sannan ya juya ga Manubiya har Idanuwansa sun yi jajir suna kyalli tsabar ɓacin rai, zai yi magana da sauri Manubiyan ta ce ‘’Ki yi hak’uri, sharrin Zuciya ne, ba zan sake ba, inshaaAllah’’ Ajiyar zuciya Maman Baraka ta sauk’e sannan ta mik’e, Baba kawai ta cewa ‘’Allah ya k’ara sauk’i’’ daganan ta taho kamar zata bangaje Manubiya ganin haka yasa tayi sauri ta matsa Itakuma ta bud’e k’ofar ta fice. Baraka ma Hannun Baba k’arami kawai ta kama suka fita bata cewa kowa uffan ba. Maman Abbakar ce ta d’an tsaya ta yi musu sallama daga nan ta saka kai ta fice Jidda da Baba suna masu ce mata sun gode. A hankali Baba ya ga wasu hawaye suna tsilalalowa Inna ta ido d’aya da sauri ya k’arasa ya sunkuya dai dai fuskarta ya shiga share mata hawayen nata yana girgiza mata kai alamun ta yi shiru…. Sun jima a haka kafin ba tare da ya juyo ba ya ce ‘’Manubiya ki kwashi duk Kayanki da suke anan, Ki wuce gida.’’ Fashewa ta yi da kuka Cikin kukan ta ce ‘’Baba dan Allah ka yi hak’uri, wallahi ban yi tunanin Baraka za ta yi haka ba’’ Still bai d’ago ya kalle ta ba ya ce ‘’Ni kuma ban yi tunanin har yanzu ba ki yi hankali ba, ban yi tunanin har yanzu ba za ki iya barin abu d’an k’ank’ani ya wuce ba tare da kin yi magana ba’’ Cikin fushi Ya Musbah ya ce ‘’Ko ma menene ki ka ji tsakanina ne ni da ita! Dan mai yasa za ki shiga ciki har ki yi mata magana?” A hankali tana kuka ta ce ‘’ku yi hak’uri’’ Ya d’an jima yana kallon ta kafin ya ce ‘’Ki kwashe Kayanki ki wuce gida, ki je ki fara karatu Jidda za ta ci gaba da zama anan, Ke kuma kya dinga yin girki daga gida.’’ Za ta yi magana ya ce ‘’Manubiya ki je a ka ce ko?’’ A hankali ta d’aga kanta alamun ‘to’ tukunna ta k’arasa ta je ta shiga had’a kayanta, har ta gama bata yarda ta d’ago sun had’a ido da Inna ba dan ta san ita take kallo, sai da ta zo tafiya tukunna ta je ta rungumeta ta ce’’Inna Allah ya baki lafiya’’ Still bata yarda ta kalle ta ba. Daganan ta yi wa su Jidda sallama, Baba ya bata kudi’n mota ta sa kai ta fita. Ya Musbah ji yake kamar ya fashe da kuka, tabbas Baraka ta kai shi bango!!! k’iri-k’iri duba fa yadda ta disga shi ta wulak’anta shi a gaban jama’a harda wani cewa ‘k’addarar aure’!! babban takaicin sa shine idan ya d’au mataki a wannan gaɓar ya san sai ya had’u da fushin Baba saboda cewa zai yi dan mai yasa zai biye mata a case d’in da ya had’a da su Manubiya, tunda wani abun yana faruwa kowa cewa zai yi ya bi bayan k’anwarsa sam baza’a duba rashin d’a ‘a da furucin da ta yi a gaban iyayensa ba………. … Chaaan yamma. Jidda na zaune ita kad’ai gashi lokacin zuwan Al’ameen ya yi ta rasa yadda za ta yi ta fita. Sai da Innar ta yi bacci tukunna ta samu ta fita, tana ta sauri. A cikin mota ta same shi yana ta jiran ta Ba tare da b’ata lokaci ba ta ce ‘’ya zo su je d’akin, Adda Manu bata nan yau, ta bar Inna ita kad’ai’’ Murmushi yayi Daganan ya fito suka jera suka nufi d’akin gwanin ban sha’awa. Sun jima kuwa suna hira, tukunna ya yi mata sallama ya wuce. Allah da ya taimaki Jidda sam Ya Yusuf bai had’u da Al’ameen ba dan tana dawowa daga raka Al’ameen d’in ta tarar da shi a d’akin, ko waye ma yayi masa kwatance, sai Allah . Tunda ta shigo ta gan sa sai ta tamke fuska, daga gaisuwa bata yarda sun yi wata hirar kirki ba. Ita sai da ya fad’a mata ma tukunna ta gane wai ashe fushi ya yi tun ranar da ta gudu shiyasa shi kuma ya ƙi zuwa ya duba Innar sai yanzu…. Ganin dai duk yadda ya yi fad’a, fushi da rarrashi sam ya gagara samun fuska a wajen Jiddan ne ya sanya kawai ya tashi ya tafi dan ya riga ya gama tsara yadda zai yi da ita next tunda ya lura bata san a bita ta sauk’i ba. Katamau!! Haka shima ya wani tamke fuskar nan tukunna ya fice bayan ya ajjiye musu dubu d’aya akan gadon, wai su sayi abun da basu da shi….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *10* Ko da Baba ya koma gida da daddare sai da Manubiya ta sake roƙon sa akan ‘ya barta ta je asibitin washegari’ amman furr ya ƙi amincewa illa ya ce mata’’ta yi karatu ta dinga zuwa makaranta akai-akai” kawai. Da asubah ta tashi ta shirya musu breakfast, har lunch, ta cewa Muhsin “ya d’umama miyar idan an zo kaiwa” daganan ta wuce makaranta saboda tana so su yi karatu da Abbakar yau sosai, gashi lecture ɗin Sir Najeeb gare su da sassafe shiyasa take ta sauri saboda ta san baya bari a shiga muddin ya riga ya shiga. Duk saurinta kuwa sai da ta yi rashin sa’a, dan ta na karya kwanar inda k’ofar tafkeken hall d’in ya ke ta hangoshi yana shiga dan haka ta k’ara sauri amma dukda hakan kafin ma ta k’arasa bakin k’ofar har ya rufe. Haka nan ita da ragowar d’aliban da suka yi letti suka ja suka tsaya a bakin k’ofar hall d’in dan waatak’ila idan sun ci sa’ar shi In ya fito ya karb’a sunayen su da Matrc number ɗinsu ya raba musu ko da half half maki ne. 3 hours ne lecture d’in kuma Sir Najeeb d’an ƙa’ida ne shiyasa sai da ya cike 3 hours d’in sa tsaf tukunna ya fito. Bai yi musu kamar yadda suka yi zato ba dan kamar ma ransa a b’ace yake lokacin da ya fito d’in dan ya had’e girar sama da ta k’asa fuskar nan tamau!!! Kamar bai tab’a dariya ba, shiyasa kowa a wajen ya sha jinin Jikinsa. Ko da wani a cikin su ya je yana k’ok’arin gaya masa uzurin sa ma, a take ya daka masa tsawar da ta ƙarasa ruɗa su! Dan haka duk sai suka ƙarasa rikicewa, kowa kuma ya jaa ya yi tsit suna ganin sa ya wuce ya tunkari parking lot. Har ya nufi inda ya yi parking motarsa, sai kuma ya juyo, dan in dai ba gizo ta yi masa ba tou Yarinyar da yake nema ya hango a cikin dandazon ƴan letti. Ya na juyawa kuwa su ka yi ido biyu shi da ita dan itanma bayansa ta raka da harara saboda ba kad’an ba ta ji haushin tsawar da ya dakawa wannan wanda ya zo zai ba sa uzuri, sosai. Da sauri Manubiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tana adduar Allah ya sa bai fahimci hararar sa take yi ba. ‘’Manubiya Musa, follow me’’ Ya faɗa ba tare da ya damu ta ji ko bata ji ba, haka kawai ya sa Kai ya wuce ya shiga motarsa ya jaa ya nufi building d’in da office d’insa yake, a nan cikin BUK ɗin. Bata ji d’in ba kuwa, ragowar Mutanen da suke wajen ne suka ce mata ‘’ya ce ta bi sa’’. Dan haka hankalinta ya gama tashi a take saboda laifi a makaranta wanda zai janyo su Baba su sake yin fushi da ita is the last thing da take tunanin za ta yi involving kanta a ciki.’’ A take ta gama yanke shawarar tana zuwa zata durk’usa ta basa hak’uri sannan ta ce masa Itafa haka Idanuwanta suke, ya yi hak’uri ba hararar sa take yi ba. Tana shirin barin wajen Abbakar na fitowa daga cikin hall ɗin, kana ganinta ka san a rikice take, a haka ta k’arasa kusa da Abbakar ta ce ‘’Yauwa Abbakar, dan Allah zo mu je ka yi min shaida, ka cewa Sir Najeeb tun muna Yara haka Idanuna suke, ba harara ce na yi masa ba’’. Kallon ta sosai Abbakar ya yi kafin ya ce ‘’Cewa ya yi ki bi shi?’’ Da sauri ta ce ‘’Eh, saboda ya kama ni Ina hararar sa’’. Wata nannauyar ajiyar zuciya Abbakar ya sauk’e kafin ya ce ‘’Inaa! Ba saboda harara ya ce ki je ba, Manu! yau ni da ke kashin mu ya bushe, ni ma ya ce min in biyo sa’’. Za ta yi magana ya ce ‘’Mu je, mu je da sauri ke dai ki yi ta addu’a kawai’’. ..Da hanzari suka ƙarasa block ɗin da office ɗin Sir Najeeb yake, ba tare da b’ata lokaci ba suka kutsa kai cikin building d’in… Manubiya ba ta san hanyar office d’in ba Abbakar ne ya yi musu jagora. A corridorn office d’insa ne na farko-farko dan haka suka k’arasa da hanzari, duk saurin da su ke yi sai da suka tsaya suka yi addu’a tukunna Abbakar ya d’aga Hannu da kyar ya fara knocking a hankali kamar wanda baya son yi… Sun fi 5 minutes a bakin k’ofar office d’in idan Abbakar ya d’an buga sai ya tsaya ya ji ko za’a basu izinin shiga, amma shiru. Badaban sun ga motarsa ba Kuma yanzu haka ma da su ke knocking ɗin kamar suna d’an jin murya k’asa-k’asa, to da sai su ce ba ya nan. Sai da suka cire rai knuckles ɗin Abbakar har sun fara ciwo, Tukunna suka ji ya ce ‘’Come in’’. Abbakar ne ya ɗan murza handle d’in ya fara shiga da sallama, dan Manubiya sai da ta tsaya ta karanto addu’o’in da za su saka Zuciyarta ta yi sanyi tukunna ta bi bayansa ta shiga da sallama itama, kanta a k’asa. A hankali ta lumshe kyawawan Idanuwanta tana me shak’ar kamshin AC, room freshner da na zafafan designer turarurrukan su waenda su ka had’e waje guda suka bada wani zazzafan ƙamshi mai tsayawa a rai!. Dama tunda suka shigo ta fahimci kamar ba shi kad’ai bane ba, yanzun kuwa da suka sake bawa iska ajiyar su suka ci gaba da hirar su ya sanya ta tabbatar da ba shi kad’ai d’in baneba duk da kuwa har yanzu bata yarda ta kalli direction ɗin da table da kujerun da su ke zaune a kai yake ba… sam ta rasa dalilin da ya sanya ta tsinci kanta da samun faɗuwar gaba tun farkon shigowar ta cikin office ɗin. Abbakar kuwa ganin computer har uku a kan table ɗin nasu gashi daga gani da shi da Abokin nasa abu mai mahimmanci su ke tattaunawa, hakan ne ya sanya ya ja Bakinsa ya yi shiru gudun kar ya katse su ya je ya yi laifi Dan tun ɗazu a rikice ya ke!!! Jiya dama tunda Mamansa ta ji ‘ya yi wa Manubiya test’ shikenan take ta faman surutai kuma ta tabbatar masa “muddin ya janyowa kansa kora daga makaranta to wallahi sai dai ya koma ƙauye ya yi noma ko kuma ya yi aure!! Dan ba zai yiu ace ta yi ta kashe kud’i akan karatunsa tun yana k’ank’ani amma yanzu ya b’arar a banza ba, saboda wata Manubiya. Sannan a yanzun da ya kamata ace ta ji dad’in karatun nasa shine yake so ya sake zame mata liability duk saboda wata Manubiya. To ba zai yiu ba.” Gaba d’aya ta d’aga masa hankali ta dagawa kanta, dan tun jiya take fad’a masa tana sake nanatawa akan muddin aka gano su tou kamar ya gama shiga masifa ne a cikin makarantar…… Abbakar yana tsananin son karatu gashi ba k’aramar wahala ya sha ba kafin finally ya samu gurbi ya ci gaba da karatun nasa, shiyasa ta yi nasara wajen rikita sa da kalaman ta.. A hanakali Manubiya ta shiga bin office ɗin da kallo a ranta ta ce ‘’Aljannar duniya, ina ma za a bani aron nan in kawo Inna ko shekara d’aya ne ta yi ta huta sosai, a haɗa mata tare da abinci mai kyau sannan ba hayaniya, Na san tabbas za ta rage wata damuwar.” Ba abunda ya fi burge ta da office d’in irin yadda aka ware wajen Hutu daban wajen aiki daban… Inda su ke zaune shi da Abokinsa ya yi kamar office, sai kuma chan gefe wasu lumtsuma-lumtsuman sofa ga fridge, dispenser, tv da center table, kamar dai wani parlourn amarya…. ‘’You Guys Are Very Stupid, GET OUT !!!!!’’ Suka ji muryar Sir Najeeb ya daka musu tsawa.. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *11* Tsananin rikici da tsoro ne suka sanya Abbakar durƙushewa a wajen, ya shiga ba shi haƙuri. Manubiya kuwa takaici da baƙin ciki ne suka sanyata fashewa da kuka…. Tun farkon zuwan su dama da ya shanyasu a waje takaici ya isheta, daurewa kawai take yi! Yanzu kuwa abun na shi ya kaita bango gaskiya. ….Haƙuri sosai Abbakar yake badawa amma sam ya ƙi ma ya tsaya ya saurare shi, tijara kawai ya ke zuba masa da ihu kamar wani ubansa, ba abun da ya fi sake ɓatawa Manubiya rai irin yadda ya sako iyayensu a lamarin Ta inda ya ke cewa ‘’..in da mom d’insu ko Dad d’insu suka zo suka gani a wajen ai da za su gaishe su! amma da yake shi sun raina shi shine suka zo suka tsaya musu kyam!! A Ka, ko shirin gaida su ma basu da shi, da yake ga sa’annin su sun tarar, ko ?. To idan basu sani ba yau su sani Malamanka suma kamar parents su ke a wajenka, in kuma suna da ja akan maganar tashi to su kama hanya su fita, shi kuma ya basu c.o in fact har spill ma sai sun yi wallahi!!!! Idan sun isa su je Iyayen su uwa ko uba wani a cikin su ya basu A a course d’in sa……..’’ Kukan da Manubiya ta sake fashewa da shi sai da ya sanya Hatta Sir Najeeb d’in yin shiru. Idan wani ya zo wucewa ta bakin office ɗin ba abun da zai hana yayi tunanin dukan ta ake yi a cikin office d’in… Duk tsura mata idanu suka yi suna kallon ta! Banda Yashjub wanda tun lokacin da ta fara kukan in fact tun farkon shigowar su ma haka nan ya daina fahimtar Najeeb, yanzun kuwa kukan nata gaba d’aya ya sake dagula masa lissafi, bai ganta ba dan bai juya ba sai dai kuma wani abun mamaki Iya muryarta kad’ai da ya ji lokacin da ta yi sallama da kuma sautin kukan ta wanda a wannan lokacin yake ji har cikin ransa ne ya sanya shi jin kamr ya tashi ya je kawai ya rarrashe ta. Tun a lokacin da ta fara kukan Abbakar ya fahimci takaici da kuma tuno Inna ne suka saka ta kuka. Sir Najeeb kuwa takaicin ta ne ya sake lullub’e sa, ya lura da yadda bata ma yi attempting ta ba shi hak’uri ba tun farko, yanzu kuma ta cika masa office da koke-koke, abun da yace ta daina yi masa a aji shine yau ta kwaso ta kawo masa har office, dan haka a fusace ya zagaye tebur d’in da ke a gaban sa ya wuce Yashjub da niyyar nufar inda take kamar wanda zai dake ta. Cikin hanzari Yashjub ya tashi tsaye, ba tare da ya juyo ba ya ruk’o Hannun Najeeb da sauri dan already har ya gota sa ‘’Wait pls!’’ Kawai ya iya cewa. Daga haka ya cika masa Hannu tukunna ya juyo ya nufi inda Abbakar ya ke a durk’ushe ya ce masa ‘’Stand up!.’’ Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna ya ce ‘’ki yi shiru ko ki fita’’ yayi mata maganar ba tare da ya kalle ta ba. Da kyar Manubiya ta samu ta haɗiye sannan ta share hawayenta ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere itama har yanzu bata bari sun yi ido biyu ba. Da sauri Abbakar ya mik’e ya na cewa ‘’Wallahi , I don’t want to interrupt you ne, thats y (wallahi bana so in katse ku ne, shiyasa) muka yi shiru, dan Allah ku yi hak’uri’’. Kamar ba zai ce komai ba sai kuma kawai ya juya ya ce ‘’Sir Najeeb a yi musu afuwa mana’’ Shiruu kawai Najeeb ya yi ya ƙurawa Yashjub ido yana mamakin shi, tun da ya san shi bai tab’a gani yayi irin hakan ba… lamari wanda ya shafe sa ma barin wajen yake yi ballantana wannan da bai shafe sa ba. Shi har gq Allah da ya ji ya ce masa ‘wait pls’ yayi tunanin so yake ya mik’e ya fita inyaso daga nan sa cigaba da hayaniyar tasu ….. Sai da Najeeb d’in yaga Yashjub ya d’an yi masa murmushi tukunna ya kawar da nazarin da ya soma ya d’aga masa kai kawai ya juya ya koma wajen zaman sa ya zauna, Ya zubawa Abbakar Idanu. Chan kan sofa Yashjub ya koma ya zauna ya tsurawa tV ɗin da ba a jone take ba ido. Da sauri Abbakar gudun kar su sake yin wani laifin ya ce ‘’Morning ! Sir,ka ce mu biyo ka shine..’’ Cikin katse shi Najeeb ya kalli Manubiya ya ce ‘’Discuss on Email and Linguistics’’ Dibi-dibi ta hau yi kafin kawai ta yi bismillah ta rufe idanunta tukunna a hankali ta ce ‘’Ban iya ba’’. Cikin fushi ya ce ‘’Ko kuma dai kin manta,ko? Saboda a takardarki in da ace ban gano yi miki akayi ba! Da tsaf zan baki A.’’ A hankali gaban ta yana fad’uwa ga b’acin rai ta ce ‘’Ka yi hak’uri Sir, Mahaifiyata ce bata da lafiya, tana kwance a asibiti ma yanzu haka! Shiyasa ya yi mini, ka yi punishing d’ina amman dan Allah ka kyale Abbakar, tausaya min yayi, bashi da laifi. dan Allah.’’ Tabbas ya tausaya mata, dan ko ba a bashi tabbaci ba ya yarda da gaske take duba da yadda yanayin kalar idanunta suka chanza da kuma zafafan hawayen da ya ga sun zubo mata, kaɗai, sun isa tabbatar masa gaskiya take fad’a. Tun yana k’ank’ani mahaifiyarsa ta rasu bayan doguwar jinya amma sam bai manta zafi da raɗaɗin rashin lafiyar mahifiya da kuma rasuwar ta ba! Hakan ya sanya ya d’an sauk’o, zuciyarsa ta d’an yi sanyi. Tsit office d’in ya yi, baka a jin k’arar komai sai na Ac yayin da Manubiya take ta faman sauk’e ajiyar Zuciya a jejjere, ahankali. Yashjub yana nan a yadda ya ke tun ɗazu ya k’urawa waje d’aya ido, k’arar wayarsa ce ta katsewa kowa tunani…. A hankali ya zaro wayar daga cikin aljihu ganin sunan Daddy ne ya sanya shi mik’ewa ya amsa wayar ya kara a kunnensa kafin ya nufi k’ofa da ɗan hanzari cike da k’asaita. Tun lokacin da Manubiya ta shigo dama take tsaye a bakin k’ofar har kawo wannan lokacin, ganin da tayi ya mik’e kuma ya nufo ta ne ya sanya gaba d’aya ta diririce…. d’azu ta ji k’arar waya amma a zaton ta bai amsa ba ko kuma ma maybe ta Sir Najeeb ce ya bari akan in sun fita ya amsa, sam Bata lura da wayar da ke kare a kunnensa ba dan ba shi take kallo ba directly kawai dai tana iya ganin Motsin sa ne. Ganin da ta yi dai da gaske itan ya nufo hakan ya sanya ta yi sauri a k’ok’arin kaucewa dai-dai shima ya kauce da niyyar zagaye ta ya bi ta bayanta ya fice! A tare suka sauk’e ajiyar zuciya sakamakon d’an kusancin da suka sake samu wanda ya sake dilmiya su a wani yanayi na daban. Sai da Yashjub ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna ya sake k’ok’arin kaucewa domin ya samu ya wuce ta inda take da farko, ba tare da ya kalle ta ba yanzun ma, amman sai akai rashin sa a dan a dai-dai wannan lokacin ne itama ta kauce da niyyar ta bashi hanya a karo na biyu!. Ɗan taku ɗayan da ya yi da niyyar kaucewa kuma sai ya sanya suka matso daff da juna kamar za su yi gware. Zuwa wannan lokacin Manubiya ta tabbatar fad’uwar gaban da take samu da yadda bugun zuciyarta ya sauya tun farkon shigowar ta office d’in a ta dalilin wannan bawan Allahn ne Saboda The more yana kusanto ta The more bugun zuciyarta yake k’aruwa….. Haka kurum sai ta tsinci kanta da son kallon fuskarsa dan haka ta d’ago kyawawan idanuwanta waenda ruwan hawaye,takaici, bak’in ciki, damuwa da k’unci Suka cikasu taff.. Ganin sun kusan yin gware a karo na biyu ne ya sanya Yashjub saita kwayar idanunsa a fuskarta da niyyar ce mata ‘Ta tsaya shi zai matsa, ya wuce,ya fita’… Karaff!idanuwansu suka sark’e a cikin na juna. Sai da numfashin Manubiya ya d’auke na y’an sakannni tukunna da kyar ta samu ta nemo shi ta daidaita shi ya dawo mata dai-dai, A Chan ƙasan zuciyarta ta ce ‘’Ma shaa Allah!!!!’’ Duk yadda Yashjub ya so ya d’auke idanuwansa daga kanta kasawa yayi, a lokacin in da za a tambaye shi yanayin Bakinta ko hanci hatta ma da kalar fatar ta to ba lalle ya iya fad’a ba! Saboda tsabar yadda zuciyarsa da ruhinsa suka karkata sannan suka dulmiya a cikin kwayar idanunta…… ……. Kamar irin idan Mutum yana bacci ɗinnan ya dinga jiyo muryar Mutum daga chan nesa ana tashin sa, haka Yashjub ya fara jiyo muryar Daddy a chan nesa yana cewa ‘’Hello,Yash!Yash!!Yashh!!!!are u with me, kana jina kuwa?’’ Wani bagwaren numfashi ya fesar sannan ya yi saurin lumshe idanunsa, a hankali ya sake runtse idanuwan nasa waenda bai riga da ya bud’e su ba har kawo wannan lokacin… da kyar ya had’iye wani abu wanda ya tokare masa mak’oshi!!! Kafin ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ‘’Yes!,Daddy’’ Daga nan ya zagaye ta tukunna ya bud’e idanunsa ya kama handle d’in ƙofar da sauri ya murza ya fita.. Sai da Abbakar ya ce ’’Manu!’’ tukunna Manubiya ta dawo office d’in, a take kunya da takaici suka lullub’e ta dan ta san tabbas sun lura da irin kallon da ta yiwa wannan bawan Allah da kuma yanda ta k’ame k’am! Ko bayan fitar sa. ‘’Hmm’’ Kawai Sir Najeeb ya ce, kafin ya fara magana ‘’Dole zan yi cancelling test d’in ku both of you, sai ku dage a exams. Bai kamata a ce na d’aga muku k’afa har haka ba bayan gashi na kama ku dumu-dumu!!! Amman uzurin ki shi ya taimake ku, ku dage a exams sannan ko da wasa karku k’ara yi mini wannan shirmen a test ko assignment, idan mom d’inki bata da lafiya ki zo ki yi reporting’’. Da sauri suka had’a Baki suka ce ‘‘In sha Allah, mun gode Sir, Sosai.’’ A hankali ya jawo computersa ya fara latsawa kafin ya ce ‘’U can leave’’ Ba tare da ya kalle su ba. ……………………… BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *12* Tun lokacin da Yashjub ya baro office d’in Najeeb, gaba ɗaya ya rasa nutsuwar sa. Har ya k’arasa gida ya yi wanka ya yi sallah ya nufi side d’in Mommy domin ya Isar mata da sak’on Daddy gaba d’aya hankalinsa yana kan Yarinyar da ya gani ɗazu a office d’in Najeeb. Sai da ya yi addu’a sosai tukunna ya samu tunanin ta ya bar shi ya yi sallah a nutse. Bai samu Mommy a parlour ɗinta ba dan haka ya wuce d’aki sai dai nan ɗin ma bata nan…. Har ga Allah Kansa har ya fara ciwo shiyasa ya bi gadonta ya kwanta shi kad’ai ya yi shiruu. So yake ya lumshe idanuwansa ya d’an huta amma ba ya son yin hakan saboda ya san yana lumshe su idanuwan wannan Yarinyar zai ke gani. Abun takaicin shine ko sunanta bai sani ba sannan ya san idan za’a jere masa mata blindfolded(a rufe musu Idanuwa da kyalle) ace masa ya nuna ta a cikin su sam ba zai iya gano ta ba. Ya san bashi da wata alak’a da ita amman kuma sam muryarta da idanuwanta sun addabi zaman lafiyar sa ya rasa nutsuwa ya kasa yakiceta sam ya rasa sukuni, tun ɗazu da ya ganta har kawo yanzu babu daƙiƙar da ta wuce wadda bai yi tunaninta ba. Sai da ya yi da gaske ya had’a da addu’o’i tukunna ɗazu ta ɗan lafa a ransa ya samu ya yi sallah cikin nutsuwa….. Wani bahagon tsaki ya jaa ya miƙe ya zauna a kan gadon, kafin ya zaro waya ya danna kiran Najeeb…. Sai da ta katse ya sake kira nan ma ta kusan katsewa tukunna ya d’auka da sallama… A hankali Yashjub ya amsa, tun kafin ya yi k’orafi Najeeb ya ce ‘’Sorry, ina wanka ne, yanzun nan fitowa ta na ga wayar tana haske’’ Ya k’arashe maganar yana mai shirin ajjiye wayar dan ya san tunda Yashjub d’in ya ji haka zai ce ‘ok, Idan ya shirya ya kira sa kawai.’ Har ya maida wayar kan side drawer sai kuma ya ga still ba’a kashe ba, shiruuu ya d’an yi kafin ya sunkuya ya d’auki wayar ya mayar ya kara a kunnensa, a ransa yana tunanin ‘shin me yake damun Yashjub haka, ko dai family matter ne? tunda dama ya ga Daddy ya kira shi d’azun, kuma tunda ya fita ko sallama bai dawo yayi masa ba kiran sa kawai yayi ya ce masa ya wuce!. It’s very unlike him….’. Yana cikin wannan lissafin a hankali ya ji Yashjub d’in ya ce ‘’Am..Najeeb, Yaran d’azu ya sunansu? I mean, ya sunanta?’’ Shiruuuu Najeeb d’in ya yi ya zaro wayar daga kunnensa ya kalli sunan da kyau ya tabbatar Yashjub d’in ne tukunna ya mayar ya d’an tab’e Baki ya d’aga gira yana murmushi kad’an -kad’an yana jinjina Kai alamun ‘yes’ tukunna ya ce ‘’Okay!!…’’ sai kuma ya kwashe da dariya. Da sauri Yashjub wanda dama tunda ya yi masa tambayar a take ya fara jin inama he can take it back(inama bai yi ba), ya ce ‘’ka ji matsalar ka, ko? Ba abun da kake tunani bane ba tou, she just looks like someone (ta yi min kama da wata) shiyasa nake so in yi confirming (in tabbatar) Ita d’in ce ko ba ita bace ba, that’s all.” Cikin son k’ok’arin danne dariyar tasa dan ya lura mutumin nasa har ya dan k’ule, Sir Najeeb ɗin ya ce ‘’Maybe ita ce, a ina ka san wacchar d’in?’’ Cikin rashin gaskiya Yash ya ce ‘’A uk, neighbor d’in mu ce, amma gidan nasu gaba d’aya sun dawo Nigeria, har ita. Last year’’ ‘’Girlfriend??’’ Najeeb ya sake jeho masa tambayar yana mamakin yadda Yash d’in ya k’irk’iro k’arya haka tashi guda ya zabga masa. Cikin d’an d’aga murya Yashjub ya ce “I said neighbor!!(maƙociya fa na ce maka) Ko ife-ifen d’alibai ya kurmantar da kai ne ban sani ba?. Maƙociya ce kawai. ka fad’a min sunan ta kawai mu wuce gurin’’ Ya k’arashe maganar tasa a k’age, dan ji yake yi kamar ya shiga ta waya ya zak’ulo sunan nata daga cikin bakin Najeeb d’in. A hankali Najeeb ya ce ‘’Gaskiya ba ita bace ba!.. Yarinyar da ka gani ɗazu I don’t think ta san ko hanyar airport ma. ko last time da kyar ta yi registration fa, har aka fara exams tana cike crf, da farko ma k’in yi mata signing mukayi sai da hod ya ce ‘mu yi mata tana da d’an issue’ tukunna’’ Zuwa wannan lokacin Yashjub ya fara ji kamar ya shiga ta waya ya shak’o Najeeb! Dukda tashi d’aya ya ji damuwa daga jin labarin nata amman kuma jan ran da Najeeb yake ta yi masa ya gama k’ular da shi dan haka ya kira sunansa da dakakkiyar murya, ya ce ‘’Najeeb!’’ ‘’Na’am,Yash.’’ Najeeb d’in ya amsa Ya sunan Yarinyar da na gani ɗazu a office d’inka?’’ Sarai dama Najeeb ya gano shi, ya fahimci inda ya nufa.. Kwana-kwanar da ya tsaya yi masa ce ta sanya shima ya so ya ja masa rai amma jin yanayisa ya sanya kawai ya hak’ura! Ya san zai dawo gareshi, soon. Dan haka kawai sai ya ce masa ‘’Manubiya Musa’’ Ajiyar zuciyar da Yash ya sauk’e saida Najeeb d’in ya ji, dan haka kawai ya yi murmushi a ransa Ya na adduar ‘Allah ya sa su daidaita’ dan ya san idan Yashjub ya samu ya auri wadda yake so to zai fita daga wannan k’uncin da ya d’aurawa kansa k’arfi da yaji ta dalilin miskilanci… Yo miskilanci mana, saboda in ba hakan ba Mutum successful kamar Yashjub ace wai ba shi da aiki sai yamutse fuska da fushi da rashin hira da dariya da walwala, kullum………… Yashjub yana gama jin sunan Manubiya ya yi sallama da Najeeb. ko komawa bai yi ya kwanta ba Ya hau instagram ya shiga searching ‘Manubiya Musa’ dan ya san idan ya samu ya ga pictures ɗinta complete maybe zai samu ya ɗ’an rage damuwa ya samu ta daina yi masa yawo a ido da kunne…. Sai dai kuma sam bai samu ba! Shine twitter!! Shine Facebook!!! Ko ina sai da ya duba amman sam bai samu ba Dan ko da ace bai santa ba idanuwan waenda ya ke gani masu irin sunan ta sam ba irin nata bane ba… Dan haka tashi d’aya yake fahimtar ba ita d’in bace ba. Tunani yayi ‘ko dai ya sake kiran Najeeb ya tambaye sa ko tana da wani nick name’ sai kuma ya ga in ya yi hakan Najeeb ɗin zai ga zak’ewar sa, kuma ya san yana tambayar sa ma shikenan zai fara judging d’in sa, dan haka sai kawai ya hak’ura ya koma ya shiga searching ‘Manubiya eyes’ A tunaninsa maybe friends d’inta da hakan suke kiran ta! Tunda shakka babu Idanuwanta are one in a million. Ya jima yana Abu d’aya kafin chaaan kuma ya yi shiruuuuu! Ya fara tunani da auna wawtar sa. Shiruu yayi shi kaɗai! Yana mamakin yadda ya haukace tashi d’aya, dan shakka babu wannan d’an k’aramin haukane yake yi… A hankali ya ajjiye wayar ya dafe goshin sa, sai da ya d’an nutsu tukunna ya ja ya kwanta ya shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere. Yana kwanciya tashi d’aya tunaninta ya dawo masa… Me yake damun ta?! Me ya ke saka ta saurin kuka?! Me yake saurin breaking d’inta!!! Ya akayi bata samun kud’in registration da wuri??!…. Runtse idanunsa ya yi da k’arfi cikin b’acin rai ya yi tsaki!!! kafin a fili ya ce ‘’Yau ni kam na had’u da aljana’’. ‘’Wacece aljanar??’’ Muryar Mommy wadda ta shigo yanzu ta daki dodon kunnuwansa. Sarai, ya ji ta. Sai dai bai bud’e idanunsa ba ma ballantana ta yi tunanin samun amsa daga gare shi. Wani maɗaukakin tashin hankali ta danne da kyar, kafin ta k’araso ta tsaya a kansa tukunna ta sake cewa ‘‘Wacece aljanah??’’ Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya bud’e Idanuwansa ya kalle ta sannan ya ce ‘’Daddy ya ce gobe zai zo, da daddare. Yana buk’atar ganin kowa. Sannan kin gayawa Yasir da Bakinki yadda kukayi da shi?”. Cikin inda inda ta ce ‘’Shi Daddyn me ya ce maka mun yi da shi?? Me yace maka na ce?’’. Ta yi maganar ta na mai zama a Bakin gadon wajen ƙafafunsa. Sai da ya d’an yi murmushi kafin ya ce ‘’Nothing. Ya ce dai kawai ki san yadda za ki yi da Yasir kafin ya zo, dan idan ya zo a goben baya son jin wata magana game da komai kuma, akwai important abun da zai kawo shi! So kar a zo ku bashi kunya’’. Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ce ‘’sai anjima’’ daga haka ya nufi k’ofa. Da sauri ta mik’e ta ce ‘’Yash. Wacece aljanah?’’ Juyowa kawai ya yi ya kalleta, kamar zai ce wani abun! Sai kuma kawai ya sauk’e wata nannuyar ajiyar Zuciya daga nan ya sa Kai ya fice ya barta nan a tsaye…… Gaba d’aya Kan Mommy d’aurewa ya yi, ta rasa mafita game da lamarin Daddy da kuma Yashjub, da su da maganganun su duk sun taru sun d’aure mata Kai kwarai. ……. Kamar yanda Daddy ya fad’a, washegari da daddare bayan sallar isha’a,ya zo. Tare suka shigo da Yashjub wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya had’u da su suna parking dan haka ya jira suka shigo tare. Suma gama zama ya haura sama domin yana son magana da Mommy kafin ta sauk’o saboda kar ta ga bambarakwai. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *13* Waya ya same ta tana yi, da alama da Uncle d’intane (yayan Abban ta….) Yanayin maganan nata ya sa ya yi tunanin maybe ko k’ara ta kai. A hankali ya nemi guri ya zauna yana mai lumshe idanuwansa a ransa ya ce ‘’In ban da abun Mommy, ta bar Abb’oi ya huta mana, Mutum ko gani bayayi sosai shekaru sun ja amman tana d’aga masa hankali, tabbas shiyasa bata shiri da ya’yan da jikokinsa dan sun lura kashe musu shi take k’ok’arin yi da tension d’in matsalolin ta……” ‘’Yash!’’ Muryarta ta katse masa tunani. A hankali ya bud’e idanuwansa kafin ya mik’e ya k’arasa bakin gadon ya zauna ya ruk’o Hannayenta. Tunda ta ga yayi mata haka ta fahimci abu mai matuk’ar mahimmanci zai fad’a mata, dan haka ta tarkata ilahirin hankalinta zuwa gare sa, kirjinta yana mai dukan uku-uku. Gaba d’aya tashi d’aya sai tausayin ta ya lullub’e sa, dan haka ya sake runtse Hannuwanta a nasa tukunna ya fara magana ‘’Mommy dan Allah ki yi hak’uri, duk abun da zan fad’a miki yanzu inaso ki danne Zuciyarki, ki yi hak’uri, ki fahimce ni’’. Zuwa wannan lokacin gaba ɗaya hankalin Mommy ya gama tashi, da kyar ta samu ta iya ce masa ‘’in shaa Allah, Yash’’. A hankali ya ce ‘’Su Daddy sun zo, suna k’asa shi da bak’uwa, mun samu k’arin member a family d’in nan, jiya……. Inaso ki fahimci ba wai saboda kun samu matsala ne shiyasa ya yi miki kishiya ba, dama chan akwai plan d’in b’oyewa yayi. Nima ban sani ba sai last week But I think an d’an matso da d’aurin auren kusa saboda a yadda na sani kamata yayi ace yanzu saura two weeks. Mommy dan Allah ki yi hak’uri na san dole za ki ji babu dad’i, ni kaina ina jiye miki, kinga dai bani da ko budurwa amman ko tunani na yi ‘For instance (misali)ace Inada budurwa, ta je tana kula wani’ to bansan ya zanyi ba!!! Ballantana kuma ku da ku ke ma’aurata. Ki yi hak’uri, na san babu dad’i amman a yadda Daddy yake a yanzu Idan kika b’ata masa rai tabbas ban san kuma mai zai yi ba!. Ki yi hak’uri Mommy na san kina hak’uri da Daddy amma dan Allah ki ƙara ki sake hak’uri!!! For us ….’’ Tunda ya fara magana ta kafe shi da idanuwa ta kasa motsi, sai da ya sake runtse Hannunta dake cikin nasa tukunna ta yi fir-gi-git!!! Tabbas they saw it coming(dama sun gani), amman ba su yi tunanin kwana kusa ba! “Innalillahiwainnailaihirrajiun” Ta shiga ambatowa a k’asan ranta.. Ta manta rabon da ta shiga tashin hankali Irin wannan a rayuwarta, sam ta manta!! Ta ma kasa kuka…..ji take yi kamar an tsunduma Zuciyarta a cikin talge! Saboda tsabar azabar da tsananin tashin hanakalin ya tsunduma Zuciyar tata a ciki. ‘’Mommy!’’ Yashjub ya sake kiran sunanta. A hankali sannan da kyar ta k’ak’alo wani murmushi wanda ya fi kuka da ife-ife ciwo! Tabbas wannan babban tashin hankali ne da aiki ya same ta, amma ta wata fuskar kuma dama ce ta samu na gyara tsakaninta da Yash, dan yadda ta hango tsantsar tausayinta da kulawa a gareta A idanuwan Yashjub yau wataki’ila wannan auren da Daddy yayi ya janyo mata kulawa da shaƙuwa a wajen d’annata. Ta lura kamar yadda kishi yake weakness d’in Daddy haka Yashjub shima… A hankali ta ce ‘’Zan sak’k’o Yashjub, ka je k’asa kawai, zan taho. I need some time alone(ina buƙatar kasancewa ni kaɗai, yanzun.” Har zai mik’e sai kuma ya janyota zuwa jikinsa ya yi hugging nata ya shiga bubbuga mata baya alamun rarrashi… kafin ahankali ya ce ‘’Ki yi hak’uri Mommy, Allah zai baki lada’’ Daganan ya cikata ya mik’e ya fita. A bakin k’ofar d’akin suka yi kiciɓis shi da Baaba Larai alamun shiga take shirin yi shi kuma ya fito. Murmushi kawai ta yi masa daga nan ya nufi k’asa inda su Daddy suka jiran su, ita kuma ta shige. *Baaba Larai* cousin d’in Mommy ce, kamar yadda Mahaifiyar Mommy ta haifesu su biyu kawai (ita da Ammin kausar) Haka itama kakarta ta haifi maman ta da maman Baaba Larai kawai, sai dai ita Baaba Larai ita kad’ai aka haifa sannan har gobe Allah bai bata Mijin aure ba!! Tun tana budurwa dama bata da samari…. Idan k’awayenta suka yi aure sai ta koma wajen k’annen su da k’awance!! Hatta da niece d’in k’awarta Baaba Larai ta tab’a yin k’awance. A lokacin da ta kai shekaru talatin a duniya sai y’an k’auyansu suka fara d’aura mata sharrin *Maita!* wataƙila ko dan sun ganta fara sol ga gashi sannan kyakkyawa amman babu Miji ne, oho. A lokacin Mahaifiyarta ta jima da rasuwa, shiyasa Mahaifiyar Mommy ta d’aukota daga gaban Mahaifinta da Matarsa ta ce za ta ci gaba da rik’eta, dan sharrin dama ya samo asali ne daga bakin Matar uban. A yanzu kuwa iyayennasu duk sun rasu shiyasa suka rungumi juna su uku Ita(Mommy), Baaba Larai da kuma y’arsu Kausar. Badaban shi Kansa Yashjub ya san Yahanasu y’ar kishiyar Mommy ce ba to da sai ya ce ‘Maybe a wajen Baaba Larai ta gado rashin auren’ amma dukda haka a kullum adduarsa itace “Allah ya sa kar y’ar uwar tasa ta k’are kamar Baaba Larai’’ Dukda kuwa cewa ‘ita Yahanasu tanada samarin kawai idan an zo maganar aure ne ganga-ganga da ikon Allah sai wani abun ya zo ya tarwatsa…….’ Amma still yana yi mata adduar kar ta ƙare kamar Baaba Larai, a kullum da ko da yaushe…. ‘’Tana Ina?’’ Muryar Daddy ta katsewa Yashjub tunani. ‘’Tana sauk’owa’’ ya basa amsa yana me k’arasawa cikin parlourn sannan ya nemi waje ya zauna suka sake gaisawa da Anty Amarya. Dama shi ya riga ya santa dan employee d’insu ce, kawai dai bai san akwai abu tsakaninta da Mahaifin nasa ba sai yau da ya ganta a matsayin Matar ubansa. Kafin su Mommy su sauk’o, Daddy ya kira Yadira ya ce mata ta kirawo mada kowa hatta drivers da masu gadi da Kausar…. Yassir ne kawai bai hallara a wajen ba saboda har zuwa wannan lokacin bayan sati biyun da ya shafe baya gidan bai kai ga kenan dawowa ba, ya ma kashe wayar da ya tafi da ita gaba d’aya. Mommy bata wani b’ata lokaci ba suka sauk’o itama tare da Baaba Larai! She looks calm amman fa ana ganin fuskarta za a fahimci ta yi kuka. Tana zama Daddy ya umarci Yashjub da ‘ya bud’e musu taron da addua’ Ana shafawa ba tare da b’ata lokaci ba Ya gabatar musu da Hajiya Saddik’a a matsayin Amaryarsa, kafin ya d’aura da cewa ‘’Na san ta, wajen aikinmu ɗaya! Shekaru sha biyar kenan muna tare da ita… Mijinta ya rasu, shekaru ashirin da suka wuce. Tanada Ƴaƴa Mata, guda biyu.’’ Daga haka ya ce ‘Ya na so tun daga kan Yahanasu har izuwa kan Yadira kowa ya bata girma da respect, har masu aiki yana so duk kalar respect d’in da za su bashi to itama su bata, baya so ya ji wani case ko ya ga ana gwada mata rashin d’a’a , in kuwa hakan ta faru to zai sab’awa ko ma waye’. Masu aiki, Yahanasu sai Yashjub ne kawai suka ce ‘’InshaaAllah Daddy’’. Daganan masu aikin suka yi introducing kansu sannan suka sake gaisheta. Sab’anin su Yasmeen waenda suka d’auke Kai ba tare da sun ce mishi uffan ba. Baya son creating scene shiyasa kawai ya rabu da su! Da niyyar cin k’aniyar su idan ya samu lokacin su. Cikin kulawa ya juya ga Hajiya Saddiqa Itama ya ce ‘’ta d’auki Ƴaƴan nashi kamar nata, In sha Allah ba zata samu matsala da su ba ‘’. A hankali ta na murmushi ta ce. ‘’InshaaAllah’’. Sai a sannan Yasira ta daure, da mugun kyar ta ce ‘’Daddy tou me zamu dinga ce mata’’ Cikin jin dadi da sauri ya ce ‘‘Ummi. Ƴaƴanta da Ummi suke kiranta’’ Murmushi Yasmeen ta yi, ta ce ‘’sannu da zuwa Ummi, We are glad to have u (Mun ji daɗin zuwanki cikinmu)‘’. Cikin tsananin jin dad’i Hajiya Saddik’a ta ce ‘’Nagode y’ar albarka’’. Saboda da farko gabanta har ya d’an fara fad’uwa, dan ta yi tunanin Yasira za ta amsheta fiye da yadda ta ga ta yi mata duba da yadda suka riga suka san juna tun a office, shiyasa ta yi mamakin yadda suka yi mata ita da y’an uwanta! Gasu duk mata. Bayan an sallami masu aikin, hira ce sosai ta biyo baya tsakanin Yasira,Yasmeen da Ummi! Mommy ma tana d’an sako musu Baki sama-sama… Kafin daga bisani Daddy ya ce “za su wuce.” Sun yi mamaki sosai da sukaji Daddy ya ce “ba a nan za ta zauna ba! Already an kaita ma sabon gidanshi wanda ya ke a nndc quarters.” Tsit!! Haka parlourn yayi daga jin hakan, dan hatta Yashjub sai da ya ji ba dad’i… Har d’aurin auren sai da ya je, jiya. Amman Daddy bai ce masa ba tare da su zata zauna ba! Kuma shi ya ce masa kar ya gayawa kowa ya yi shiru amman gashi shi ya b’oye masa abu, bayan haka sabon gidan ai Mommy ya kamata ya kai tun da shima mansion ne kamar girman nan ‘’Okay ba damuwa,zamu zo inshaaAllah,’’ Muryar Mommy ta dawo da gaba d’ayan su daga duniyar tunanin da suka dulmiya. Ba yadda Ummi bata yi da Ya’isha akan ta biyota su tafi tare ba Saboda y’arta Munira age mate d’in Ya’ishan ce kuma jibi zata baro gidan Yayarta ta komo wajenta da zama a chan nndc d’in! Amman Ya’ishan tak’i yarda… Ta bata excuse ɗin ‘tanada shirye-shirye na masters d’in da ta fara recently, so tana buk’atar time domin ta nutsu ita kad’ai ta shirya abubuwa.’ Ba dan Ummi ta so ba ta tafi bayan sun yi mata alk’awarin za su je, inshaaAllah. Har mota suka rakasu saida suka ga fitar su, tukunna suka koma ciki. Yadira ce ta ce ‘’Yanzu dan Allah Daddy ya ..’’ Da sauri Mommy ta kalle ta, dan haka ta ja Bakinta ta yi tsit. Har suka yi dinner aka tashi babu wanda ya yi zancen Ummi ko Daddy! Yashjub ya yi musu sai da safe ya wuce, Kowa ta nufi side d’inta. Ba abunda ya fi yiwa Kausar dad’i irin yadda ta ga babu Yassir babu dalilin sa. Dan ita sam case d’in sabuwar kishiyar Mommy bai wani d’aga mata hankali ba! saboda ta riga ta san k’aramar alhaki ce……. Tunda Yashjub ya koma Ɗaki, sam sai ya kasa tab’uka komai! zuwa wannan lokacin tabbas ya fahimci yana buk’atar sanin more about Manubiya. Ya riga ya tsaya akan cewa ba son ta yake yi ba saboda to tayaya ma za ayi ya so ta!? in fact idanuwanta kawai ya gani dan haka if there is anything ma (idan akwai ma abun) da yake drawing nasa towards her maybe it’s the eyes, dan ya tabbatar bai tab’a ganin kwatankwacin masu kyawun su ba, ko kuma maybe akwai wata k’addarar da take jan sa zuwa gare ta wataƙila shi ya taimake ta a wani abun ko kuma ita ta taimaka masa…… A mazaunin haka ya bar lamarin, daga nan ya d’auki wayarsa ya kira Najeeb… Ya san zai sha tsokana amman gwara tsokanar Najeeb akan wannan rashin kwanciyar hankalin da yake fuskanta daga zuciyarsa dan in banda azalzalar sa ba abun da takeyi…. ‘’Kawai ina buƙatar sanin fiye da sunanta ne, daganan na san shikenan! Ba wani abun da zai sake biyo baya kuma’’ Ya fad’a hakan a fili cike da son gasgatawa kansa iyakar abunda yake buk’ata kenan. Sai da Najeeb ya yi murmushi yana mamakin taurin kai irin na Yash, dan ya san yau ɗin ma in ba da kyar ba akan Manubiya ne ya sake kiran sa…. Sai da ya girgiza kai, ya ce ‘’hmm’’ tukunna ya d’au wayar ya kara a kunnensa ya ce ’’Hello Yash,how far’’ ‘’Kar ka ce komai kuma kar ka tambaye ni meyasa, kawai Ina da buk’atar sanin ƙarin bayanai akan wannan Yarinyar’’ Yashjub d’in ya fad’a yana mai runtse idanu, sannan ya yamutse fuskarsa kamar irin ‘Meyasa ma na tambaye sa’ d’innan. Tabbas sai da Najeeb ya yi da gaske tukunna ya samu ya danne dariyarsa sannan ya ce ‘’To a gaskiya Yash ni dai bana tara bayanai akan ɗalibaina.. Iyakar abunda na gaya maka jiya shi kad’ai na sani a game da ita. Amma y not (mai zai hana) in karb’a maka numberta in yaso kaga sai ka binciketa ka ji komai da daga Bakinta?” Tun kafin ya rufe Bakinsa Yashjub ya ce ‘’Kana hauka ne? Ka ga bafa wani abun bane ba, i just saw her jiya jiya(jiya jiya na ganta) so kar ka yi mini tunanin wani shirme’’. Yana gama fad’in haka ya yi sauri ya kashe wayar, dan tabbas idan ya ci gaba da magana ba iyakar Najeeb ba shi kansa zai iya gano abun da yake ta k’ok’arin k’aryatawa tun a jiya. “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Ya shiga maimaitawa a ransa dan yana ajjiye wayar sai kuma ya fara jin haushin kansa na Kashe wayar da ya yi ba tare da ya nacewa Najeeb d’in ya nemo masa information (bayanai) game da iya ba. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *14* •••••• Lokacin tafiyar da Al’ameen ya ce zai yi,ya cika! Dan haka ya je ya samu Dr da nurses d’in, duk wasu abun buk’ata sai da ya biya kuma ya bada numbersa ta k’asar da zai je ya ce a kira sa in wani abun ya taso. Da kyar ya samu Jidda ta yarda ta k’arba waya daga Hannunsa. A ranar da zai tafi kuwa kamar kar su rabu, haka nan suka dunga yi wa juna rakiyar kura kafin ya samu ya rakata bakin k’ofar d’akin da Inna take jinyar ya bud’e mata ya ce “ta shiga” tana shiga ya jaa ya rufe ya juya ya wuce da sauri yana murmushi…. Sai da Innah ta k’ara sati biyu a asibitin tukunna aka sallamo ta. Ba laifi jikin nata da d’an sauk’i. A cikin sati biyun nan kuwa Manubiya bata je ba dan k’iri-k’iri Baba ya hana ta zuwa, dole haka nan ta hak’ura ta ci gaba da karatunta dan exams za su fara yau saura kwana d’aya. Y’an gidansu ma tun zuwan da Siyama ta yi har yau ba wanda ya koma sai Ya Yusuf da ya je sau uku. Baraka itama bata sake komawa ba dan cewa ta yi ‘’Ba zata je inda za a dinga wulak’antata ba, zata dinga yi wa Innar fatan samun sauk’i tana daga Gida.” Matar Nafi’u kuwa kusan kullum sai ta je, dama ita tun fil’azal basa shiri da Baraka! Amma dukda haka da ta lura bata zuwa sai da ta je har gida ta bata shawara, ai kuwa basu k’ark’are k’alau ba dan k’arshe ma Baraka k’ofar fita ta nuna mata ta ce ‘’Ta fice mata a gida’’ Rufe-rufen files ne da wasu ƴan gwaje-gwaje suka d’an tsaida su Baba daga dawowa da wuri. Tun safe da Jidda tacewa Manubiya an sallame su, Manubiyan ta gyara d’akin tass ta share ta yi girki ta kunna turaren wuta ta wanke band’aki! Sai zumud’i suke yi itada Muhsin dan shima ba kasafai aka cika zuwa da shi ba, basu samu sun k’araso ba kuwa sai wajajen k’arfe uku. Suna zaune a d’aki lokacin, kaar daga sama suka ji Baba yana gaisawa da Anty Umma. Da zumud’i suka mik’e sukayi waje, anan tsakar gidan suka tadda rabin y’an gidan kowa ya fito yana duba jikin Innar. Taɓe Baki Manubiya ta yi a ranta ta ce ‘’daga baya kenan’’ daganan suka nufe su ita da Muhsin, a tare suka rungume Innar wadda take zaune akan wheelchair, Manubiya har da hawayenta kafin daga bisani suka wuce ciki y’an gidan suma kowa ya wuce Fanninsa. Suna shiga Manubiya ta shiga gabatar musu da abinci. ita da Jidda ne suka bawa Inna, ta ci kuwa ba laifi duk da rabi duk ya zube saboda har yanzu gefen Bakin nata ba aiki yake yi sosai ba. Haka suka zauna suna y’ar hira ana cin abinci gwanin ban sha’awa ba wanda zai kalle su ya ce sunada wata matsalar, dan hankalin Baba a mugun tashe yake saboda bai san yadda zaiyi ya biya ƴan basusssukan da ya ci waenda suka zama dole ba, sannan bai san yadda zai yi ya ci gaba da kula da iyalin nasa ba, amma sam bai bari sun gano halin da yake ciki ba haka nan ya biye su akayi ta raha. To haka a b’angaren Ya Musbah shima yayi k’ok’ari ya danne tashi matsalar aka ci gaba da hirar suna ta yak’e daga shi har Baba. Kiran sallar la’asar ne ya tashi zaman nasu, Maza suka tafi masallaci Matan kuma suka yi a gida. Sai a lokacin Jidda ta samu damar zama da Manubiya dan Inna har ta samu bacci. .. A hankali suna ida addu’a Jidda ta kamo Hannuta ta ce ‘’Adda Manu ina ta so mu yi magana amma ban samu right time ba sai yanzu’’. Da kulawa Manubiya ta juyo tana kallonta tare da bata dukkannin attention d’in ta. Tun daga ranar da ta hana Al’ameen zuwa ta kuma hanata kula shi ita kuma ta cigaba Ba abunda Jidda ta b’oyewa Manubiya sannan ta mik’e ta je jakarta ta kawo wayar da ya bata ta nuna mata. Cikin son fahimtar da ita Manubiya ta ce ‘’Jidda ban hanaki kula Al’ameen ba, saida na duba na ga abun da hakan kan iya janyowa. Jidda Mahaifiyarsa bata k’aunarki…ki duba ki ga halin da muke ciki, kar ki je ki sake janyo mana wata matsalar. Tunda ya ce miki Ammin nasa zata zo kin ji ko waya ne ta yi??’’ A hankali Jidda ta ce ‘’Ya ce min ta yi tafiya ne, Adda Manu ki fahimce ni dan Allah, Ina son Ya Al’ameen nima, kawai ki tayani da addu’a dan shine farin cikina. banajin zan iya rabuwa da shi, a matsayin ki na y’ar uwata ina tunanin ke zaki fara fahimtata..” Cikin katse ta Manubiya ta ce ‘‘Jidda,ba wai inaso inyi going against farin cikinki na yanzu bane ba, Inaso ki samu dauwamammen farin ciki na har abada ne shiyasa kika ga Ina haka. Idan ya ce Mahaifiyarsa ta yi tafiya ai ya kamata ace ko waya ne kun yi ke da ita considering (idan aka yi la’akari da) abunda ya faru a baya, saboda a samu a tabbatar da yess tana son ki yanzun..” Sallamar Siyama ce ta katse su dan haka duk suka d’ago a tare suna kallonta da murmushi. Itama murmushin ta mayar musu kafin ta ce ‘’Tare nake da bak’uwa, ta shigo?’’ Ba tare da sun san wacece ba suka ce mata ‘’eh.’’ Tana shigowa gaban Manubiya ya yanke ya fad’i amma sai ta dake tace mata ‘’Ina wuni’’ daganan ta miƙe ta je ta d’auko darduma ta shimfid’a mata. Cikin sunkuyar da kai Jidda ma ta gaida Mahaifiyar Al’ameen (Ammi). Duk jimla Ammin ta yi musu ta amsa gaisuwar tasu, kafin ta juya ga Siyama ta ce ‘’ta je ta kira mata Uncle, dan ta ga shigowar sa yanzun’’. Kana ganin yanayin fuskarta ka san ba dubiya ta zo yi ba. Dan haka duk suka zauna shiruu kowa da abun da yake tunani. A tare Uncle,Ya Musbah,Baba da Muhsin suka shigo d’akin. da sallama. Tunda Baba ya ganta a gidan dama ya san ba lafiya ba! amman sanin da ya yi ya riga ya raba y’arsa da d’anta hakan ya sanya ya d’an ji sauƙi… Duk da ya san ba lalle Al’ameen d’in ya gaya mata ya basu kud’i ba amma dama a shirye yake yana ta k’ok’arin neman bashi ya samu ya had’a kan kud’ad’en da Al’ameen d’in ya basu ya biya saboda ya san fitinar Mahaifiyar tasa, kuma a lokacin da Al’ameen d’in yace zai taimake su Inda ya k’i amincewa ya san Yaron ba zai ji dad’i ba, bayaga haka ma basu da yadda za su yi a wannan lokacin. Da Uncle suka fara gaisawa sai Ya Musbah da Muhsin kafin Baba Musa ya kalle ta ya ce “Barka da yamma,Ammi.” ‘’Barka dai,Musa’’ Kawai Ammin ta ce ba tare da ta kalli inda yake ba. Daganan kowa yayi shiru a d’akin kafin Uncle ya kalli Manubiya ya ce ‘’Manu ke da su Muhsin ku d’an bamu guri ko?’’ Da sauri Ammi ta ce ‘’A’a,ai zuwan nasu ne,ma’’. Bata jira jin mai za’a ce ba ta juya ta kalli Baba ta fara magana ‘’Kwanakin baya, mun samu matsala da ku akan wannan Yarinyar Maijidda da take mak’alewa Yarona, ta shiga tsakanina da shi har sai da ta kai ta kawo ya dena yi mini biyayya. To an samu an gyara matsalar kwanaki da kyar!! Yanzu kuma an koma ruwa… Da sauri Uncle ya ce ‘’A’a fa Misunderstanding (rashin fahimta) dai aka samu Ammi, dan rabon Jidda da Al’ameen ai tun kwanaki da muka yi musu tsakani ko ba haka ba? Maijidda’’ Yayi maganar yana mai kallon side d’in da Jiddah take nan Kai a durk’ushe. Kafin ya juyo ya kalli Ammi ya ce ‘’Kuma ina Al’ameen d’in baya nan ma? jiya na ji Yaran nan Maza suna cewa ya tafi England ko’’ ‘’Eh ya tafi akwai course d’in da zai yi a chan shiyasa ma na samu na zo nan ɗin, dan cewa ya yi muddin na yi wani yunk’urin sake raba shi da Jidda to babu ni babu shi’’ Cewar Ammi Sannan ta d’aura da cewa ‘’Already Al’ameen yana da Matar da zai aura, an riga an gama magana. Shi kad’ai Allah ya bamu da ni da Mahaifinsa!! Muna da burin mu ga ya samu rayuwa da Abokiyar rayuwa wadda ta dace da shi!!. Ba zan b’oye muku ba Jidda is the last person (ita ce Mace ta ƙarshe)a duniyar nan da zan so Yarona ya aura!! A kwanakin baya ban fuskanci Jidda da lamarin nan ba na fuskance ku ‘Mahaifanta’ saboda na ga kune magabatanta kuma a tunani na Ita ɗin Yarinya ce amma yanzu ta nuna mini cewa ta girma kuma ta fi k’arfin ku dan haka Ki saurara ki ji!!’’ Ta yi maganar referring to Jidda wadda ta fara kuka k’asa-k’asa. ‘’Duk zuwan da yake yi da irin kud’ad’en da ya ke kashewa na san komai Dan haka …..’’ Da sauri Manubiya ta ce “Ammi Mahaifiyarmu bata da lafiya, at least idan baki yi considering d’in ta(la’akari da ita) ba..’’ Cikin d’aga murya Ammin ta ce ‘’Na tabbatar idan na bar Al’ameen tare da Jidda to nima condition d’ina sai ya dawo irin na Mahaifiyar taku saboda tsabar baƙin cikin da za ta dinga d’ura mini.’’ Ciki d’acin Zuciya ta juya ta kalli Uncle ta ce ‘’tunda na haifi Al’ameen bai tab’a yi mini musu ba sai da ya had’u da Yarinyar nan, Wallahi’’. Cikin katse ta Manubiya ta ce ‘’Kar ki d’aura alhakin taurin kan d’anki akan mu, tunda ba ke kad’ai yake yi wa ba…ki tambaye shi ki ji yadda muka dinga cewa kar ya zo inda muke amma sai da ya je!!! bayaga haka a gani na ai ke kika haifi Al’ameen dan haka idan yayi taurin kai ko ya ƙi yi miki biyayya hakan yana nufin ke ce kika kasa sannan ke ce kika sangarta abunki …..’’ ‘’Manu!!’’ Ya Musbah ya kira sunanta da kakkaurar murya yana kallonta da idanuwansa waenda suka kad’a suka yi jaa. Sai a sannan Ammi ta d’auke idanuwanta daga kan Manubiya ba tare da ta ce komai ba ta mik’e ta kalli Uncle ta ce ‘’Shigowar da na yi cikin d’akin nan ya ishi k’ask’anci ba sai na tsaya wannan y’ar ta gaya mini maganganu ba! Idan ka lura ko uban su bai isheni kallo ba shiyasa na kira ka akan ka yi mana alk’alanci ni da Jidda, amma tunda basu san sulhu ba sannan basu san banbancin da yake tsakani na da su ba, inaso ka gaya musu nace ‘duk abunda Al’ameen ya kashe musu su dawo mini da shi!! kafin nan da awanni ashirin da hud’u, idan kuma ba haka ba to wallahi kotu ce za ta raba ni dasu’.’’ Tana gama fad’in haka ta juya ta fita fuuuuu. Cikin rashin jin dad’i Uncle ya kalli Baba ya ce ‘’Haba Musa, yanzu ina amfanin haka? wutsiyar rak’umi fa ta riga ta yi nesa da k’asa, bayan haka ma Ina ce ita Jiddan Yusuf za ta aura, mai ya sake had’ota kuma da Al’ameen ɗin da aka raba ku da wannan Matar kwanakin baya da kyar????’’ Cikin tsananin ɓacin rai Ya Musbah ya ce ‘’Ta je ta tafi kotun, idan bata da hankali, waye take tunanin zai kalle ta? kud’i ai Al’ameen ne ya bayar ba ita ba’’. Cikin katse shi Uncle ya ce ‘’Kai Yaro ne har yanzu Musbahu, kamar yadda ta ce akwai fa bambanci mai k’arfi a tsakanin ta da ku, Allah na tuba ko police station ta kai ku ta kulle wallahi sai kun ji a jikinku!! dan babu d’an sandan da zata zubewa kud’i ya ƙi sakawa a narkeku, barin ma idan ta ce kud’i take binku tsaf za a yi ta jibgarku, tunda an san baku da shi har sai kun biya, idan ma za a tsaya muku to fa kafin a yi wani abun kun ji jiki…. gashi yanzu kowa ta kansa yake yi ban san taya ma za a fara biyanta kud’in ba, thats in ba a yi rashin saar kullenkun ba… Kai yanzu instead of ka ji da rashin lafiyar Matarka mai yasa ka je kana amshe kud’in Yaro?.’’ Uncle ya Ƙarashe maganar tasa cikin b’acin rai. A hankali Baba ya d’ago gajiyayyun idanuwansa yana kallon Yayan nasa, bai bashi amsar tambayoyin sa ba maimakon hakan sai shima ya jefa masa tashi tambayar ta hanyar cewa ‘’Menene yake damun Matar tawa?’’ Cikin rashin fahimta Uncle ya ce ‘’Ban gane ba’’ Cikin son fahimtar da shi Baba ya ce ‘’Wanne kalar ciwo ne yake damun matata wanda har ta shafe sama da wata d’aya a kwance a gadon asibiti?. Kai d’an uwana ne dan haka na san ka je ka duba ta kuma ya kamata ace ka san abubuwan da suke damun ta’’. Cikin kame-kame Uncle ya ce ‘’Magana za ka gaya min? baka san yanayin tsarin aikin banki ba ko? to bari ka ji Matana ma hak’uri suke yi da ni! Ni kaine bani da lokacin kaine balle kuma..’’ ‘’Balle kuma wani ni,ko?’’ Baba ya k’arashe masa maganar tasa cikin sanyin murya. Cikin d’an fad’a-fad’a Uncle ya ce ‘’Kaga Musa, ba ta wannan muke ba yanzu, kar ka zille ta wannan hanyar, ka fito ka fad’i ta yadda akayi ka karb’i kud’in yaro da kuma dalili, ni kuma in gayawa su Baba Habu daga nan mu ga abun da za mu iya’’. Kamar Baba ba zai yi magana ba sai kuma ya yi murmushi tukunna yace ‘’Ba zillewa zan yi ba, amsar da zaka bani ita zata sa ka fahimci yadda akayi na karɓi kud’in. Ciwon k’oda ne ya ke damun Amina wanda saida ta kai ga an cire (guda ɗaya). sannan ta samu stroke!! hawan jini, ga kumburin zuciya.. Iyakar allurai da magungunanta kad’ai aiki ne. Ba daban Al’ameen ɗin ba to da ban san ya zan yi ba’’ Ya k’arashe maganar wasu zafafan hawaye suna zubo masa…. A hankali ya share hawayen kafin ya kalli Uncle ya ci gaba da cewa ‘’Waennan sune abubuwan da suke damun Matata suka sanya har na karb’i kud’in Al’ameen Saboda ya nuna kwad’ayin yanaso ya taimakeni sannan shi kad’ai ne ya zo mini ya kuma taimakeni. Inaso ka gayamin In da ace kaine a matsayina shin, ‘Ba za ka amshi kud’in ba’?”. Uncle ya dad’e yana kallon Baba kafin ya ce ‘’Anjima za mu had’u a parlourn Kaka Mallan, a nemo mafita tsakanin kai da Ammi!. Sannan a tabbatar da maganar Jiddah da Yusuf dan ta hakanne kawai ja’irar Yarinyar nan ba zata sake nemo mana magana ba’’ Ya fad’i hakan yana mai kallon direction d’in da Jiddan take, kafin ya juyo ya kalli Ya Musbah ya ce ‘’Har ga Allah ina jin tsoron Matarnan(Ammi), fad’a da mahaukaci sai sarki, ka fahimtar da su dan Allah.’’ Ya na gama fad’in haka ya kama hanya ya fice . Sai a lokacin Manubiya ta samu ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa. A hankali Jidda ma ta ci gaba da nata kukan. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *15* Cikin rashin jin dad’i Baba ya ce ‘’Ban yi tunanin zan kafa miki doka ki shallaketa ba Jidda, yaushe har kika yi wayo da girman da za’a raba ki da shi ki kasa hak’ura? Ashe dama ziryar da yake ta yi wajen ki ya ke zuwa a b’oye? Kenan har yanzu kuna tare? Amman shine da ke da shi kuka ce mini babu komai tsakanin ku, kun rabu ko?. Ni kika yi wa k’arya Jiddah?’’. Cikin fashewa da wani irin kuka ta ce ‘’Baba dan Allah ka yi hak’uri… Cewa yayi zai samu right time ya yi maka bayani ta yadda zaka fahimce mu’’. Cikin fad’a sosai Baba ya ce “Bayanin me? Ni za ku yaudara?. yanzu shi Al’ameen ashe ba zai iya taimako na saboda Allah ba sai in da wani dalilin kenan, yaushe aka haifeku daga ke har shi da zaku raina min wayo?’’ Ya k’arashe maganar cikin fushi. A hankali Ya Musbah ya ce ‘’Baba ka yi hak’uri dan Allah, bara in fita in ga yadda za’ayi da kud’in Matar nan, gara kawai a rabu lafiya.’’ A hankali Manubiya ta share hawayenta ta ce “Zan je mu yi lissafi da ita, ta lissafa kud’in ta zan biyata ta hanyar yi mata aiki! A gidan ta.” Da sauri Ya Musbah ya ce ‘’za mu san yadda za mu yi ni da Baba ki maida hankali akan karatunki ki yi shiru,kawai.’’ Murmushi ta yi kafin ta ce ‘’Ka bari nima in taimaka dan Allah, in kuka kawo naku sai a had’a ragowar da bai cika ba In yi mata aiki na Iyaka kwanakin, kud’in suna da yawa fa ka barni inaso in taimaka nima. Makaranta kuma ba matsala zan iya had’a aikin da makarantar karka damu.’’ A hankali Muhsin ya ce ‘’Za mu dinga zuwa tare, sai in dinga tayaki da wani abun’’. Jinjina Kai ta yi alamun ‘to’ Tana kallon sa tana murmushin da ya fi kuka ciwo. Kafin ta kalli Ya Musbah Ta ce ‘’Bara in je tun da wuri mu ji ko zata amince’’ Sai a sannan Jidda tace ‘’Adda da kin bari na….’’ Cikin katse ta ta ce ‘’Ba komai Jidda, kar ki damu, zamu gyara komai, inshaaAllah’’. A hankali Jidda ta matsa ta rungumeta ta na kuka sosai kanta fal da na sani, ba tare da Baba ya gani ba ta saka mata wayar da Al’ameen d’in ya siya mata Kafin ya tafi a Hannu, ita kuma karb’a kawai ta ɗan jinjina Kai, daganan ta d’auki hijab d’inta ta sake sakaya wayar sannan ta cewa Muhsin ya taho. … A gaban Baba ta je ta durk’usa tana addu’ar Allah Ubangiji yasa kar yace a’a… cikin kwantar da murya tace’’Baba,dan Allah ka bar ni inje, kar ta zo ta tozarta Mutane ka ga inna bata da lafiya, kar a kuma d’aga mata hankali, gara mu bi ta a sannu a rabu lafiy….’’ Yafi mintuna biyu bai yi magana ba kafin chan ya had’iye wani k’ululun bak’in bak’in ciki da tashin hankali tukunna ya jinjina mata kai alamun amincewa. Chan k’asan ranta ta ce ‘’Alhamdulillah’’.Sannan suka mik’e da niyyar fita, har sun d’an gota ta ji yace ‘’Manu’’. Sai da ta lumshe idanunta tukunna a hankali ta ce ‘‘Na’am Baba’’ Ahankali yace ‘’Kar ki yi ja’inja da ita sannan ki yi mata magana da tattausan lafuzza’’. ‘’InshaaAllah Baba’’ tace Daganan ta jaa Hannun Muhsin suka wuce. Suna fita Baba ma ya juya ya fita. Chan bayan gidan inda ba kowa yaje, yana zuwa ya fashe da wani irin kuka, ya manta rabon da yayi feeling helpless irin yau, ba irin wannan rayuwar ya so ƴaƴansa su yi ba,ba irin wannan uban yaso ya zamto ba amman ba yadda zai yi ba shi da yadda zai yi,ko wacce hanya ko ina ya juya a toshe yake gani.. Ya jima ya na kuka kamar wani k’aramin yaro kafin daga bisani ya share hawayen nasa yayi istighfari sannan ahankali ya ce ‘’Alhamdulillah’’ tukunna ya mik’e ya koma d’akin. A nan ya tarar da Ya Musbah shi da Jidda suna ta lallab’a Inna wadda take ta faman hawaye. Dan Baban yana fita sukayi la’akari da ita ashe ta farka tun tuni basu sani ba, saida Baba ya fara umartar Ya Musbah akan ya je gida ya duba Baraka da mai sunan shi yaga komai kalau tunda tun safe yake asibiti kuma da suka dawo bai je ya lek’a gidan nasa ba. Ba dan yaso ba ya tafi, tukunna shi da Jidda suka ci gaba da lallab’a Inna……… Sai da su Manubiya suka kusa awa biyu tukunna suka dawo daga gidan Ammi duk su biyun jikinsu a sanyaye. Jidda kawai suka samu a d’akin ita da Inna wadda suka lallab’a dakyar daga nan ta sha maganinta bacci ya d’auke ta,Jiddan ce ta ce musu ’’Baba ya fita yanzu bai dad’e ba’’. A hankali Muhsin ya ce’’Bara in je wajen shi, na san yana masallaci’’ daga haka ya fice ya bar musu d’akin. Yanayin yadda Jiddan ta ganta ne ya sanya itama cikin mutuwar jiki tace ‘’lafiya dai ko? na gan ki wani iri’’. A hankali Manubiya ta ce “Wai har mun fara yau fa, shiyasa ma kika ga mun dad’e. Aikin ba sauk’i gaskiya kuma a haka kinga yanzu dare ne so na san na safe zai fi wahala… wanke-wanke da shara mukayi yau, tace kuma gobe har da girki. Muhsin kuma da muka je da niyyar ya dinga tayani ta ce shi zai dinga sharar wannan makeken tsakar gidan mai uban girma, albashin mu dubu goma goma, a wata dubu ashirin mu biyu. In Allah yasa su Baba sun samu kud’i masu nauyi watak’ila wata d’aya ko biyu kawai za mu yi muna aikin, na bata har wayar da ya baki ma’’. Manubiya ta k’arashe maganar tana mai cire hijabin jikinta. Ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e kafin tace ‘’Adda Manu ko ni in karb’a ke ki huta ki yi karatun ki cikin kwanciyar hankali’’. A hankali Manubiya ta koma kusa da ita ta zauna kafin ta ce ‘’Jiddah,a yadda matarnan take jin zafin ki idan kikaje mata gidan da sunan aikatau tsaf za ta iya cutar da ke, kuma bayaga haka ma bai kamata ke d’in ki je ba so ki bari karki damu ni da Muhsin d’in za mu yi, za mu iya’’. Cikin zubar hawaye Jidda ta ce ‘’Adda Manu,ta yaya za ayi ni na yi laifi amma ace kune zaku biya price d’in A Ina aka tab’a yin haka?’’. Cikin d’an jan kumatunta Manubiya tace ‘’A gidan Baba, gidan da y’an uwa suke matukar k’aunar junan su, gidan da kai yake a had’e! Har ta kai Idan abu ya shafi d’aya tou ya shafi dukkan mu, gidan da mu ke so mu nunawa Jiddan mu tana da gata’’. This time around fashewa da kuka Jidda tayi ta fada jikinta ta rungumeta a hankali ta ce ‘’Nikam kar ku yi ku barshi zan yi in kuka yi bazan tab’a yafewa kaina ba.. Kullum zan dinga gani kamar na shiga hakkin kune’’ A hankali Manubiya ta ce ‘Jidda ki kwantar da hankalinki, bau komai kinji ko? Kuma inaso ki saka a ranki muddin za ki ci gaba da kula Al’ameen tou abunda zai faru damu kenan. dan Allah Jidda For the last time ki fita harkar Al’ameen har abada’’. Ahankali Jiddan ta cika ta ta d’ago tana kallon ta kafin ta ce ‘’na riga na gama yi wa kaina wannan alk’awarin! InshaaAllah babu ni ba Yw Al’ameen, kawai dai dan Allah kar ku bari a aura min Ya Yusuf, Wallahi bana son shi’’. Cike da bata assurance had’e da kwarin guiwa Manubiya ta ce “Su su uncle d’in wacce rawa suka taka tun daga haihuwarki har kawo yanzu da kike tunanin zamu bar su su yi miki auren dole? ki kwantar da hankalinki kin ji ko! InshaaAllah Yusuf sai dai ya ganki ya bari.’’ Ahankali Jidda ta sake hugging d’in Manubiya tanajin wani kwanciyar hankali a cikin ranta, harga Allah bata son Ya Yusuf! bata san ya za ta yi ba Idan k’addarar Ubangiji ta sanya ya zamto mijin ta ba, da sauri a ranta tace ‘’ya Allah kar ka sa in auri ya Yusuf,alfarmar annabi s.a.w’’. Shiruu ta yi tana tunani kafin ta d’ago ta gyara zamanta tukunna ta ce ‘’duk naga kin yi kalar gajiya kin gaji sosai ko? bari in je in d’eba miki ruwan wanka, in d’aura na fanfon ya d’auke’’. Murmushin yak’e Manubiya ta yi kafin ta ce ‘’Mun riga mun tara ni da Muhsin kafin mu shigo,sai da ma muka d’aura a kitchen tukunna muka shigo nan, na san zuwa yanzu dai bai yi ba’’… …Tun ranar da ta gan shi notunan kanta suka kwance, sanin da ta yi cewa sam shi d’in ba sa’an ta bane ba ta ko Ina, hakan ya sanya ta yi wa kanta fad’a! sannan ta dage da addu’a da sallar dare da nafilfili…. Ta samu sauk’i kuwa! sai dai kuma bata san k’addarar da ta kai ta gidan Ammi ba yau ɗin gidan da tun da take a rayuwarta bata tab’a shiga ba! Shin wacce irin kama ce tsakanin Matar da ta tarar tana yi wa Ammi kitso da wannan bawan Allahn da ta gani a office d’in Sir Najeeb sati biyu baya da suka wuce?… Tunda ta ga Matar kuma tashi d’aya sai tunanin Mutumin ya dawo mata sabo fil. “Innalillahi wainna ilaihirrajiun!! Ya Allah kar ka d’aura mini abun da zai zama ajalina, ya Hayyu ya Qayyom kar ka ɗaura mini abunda ba zan iya ba’’. Ta fad’a a chan k’asan ranta….. Anya kuwa zata iya ci gaba da aikin gidan Ammi tana karo da wannan Fuskar kullum,dan ta lura matar kamar a gidan take saboda inda ace zuwa ta yi tou da da ta gama yi wa Ammin kitso da zata tafi amma sai ta ga ta kama wani aikin kuma na daban, babban tashin hankalita shine kar ta je shima Mutumin a gidan ya ke!!! Dan tabbas maybe in dai ba tsananin kamanni ba to matar nan yayar sa ce. Ta san cewa Ammi d’a d’aya gare su ‘Al’ameen’ to kenan wannan mutumin y’an uwansu ne? da shi da yayar tasa a gidan suke kenan? Inaa ba zata iya ba, saboda gani d’aya ta yi masa lissafinta ya kwance shin ina kuma ga idan ta ci gaba da ganin shi kulliyaumin?…… ‘’Adda Manu, ya kawo ruwan fa’’ Jidda wadda take ta faman yi mata magana bata kula ta ba tun dazu, ta fad’i hakan da d’an k’arfi. A d’an firgice Manubiya ta yi firgigit ta d’ago tana kallon ta kafin ta samu da kyar ta had’iye wani abu wanda ya tokare mata mak’oshi tukunna a hankali tace’’Ok‘’. kafin ta kalli Muhsin wanda ya dawo daga mik’a ruwan band’akin ta ce ‘’Na gode auta,bari in yi in rage maka’’. Tana gama fad’in haka ta mik’e ta d’auki abubuwan da zata buk’ata ta fad’a band’akin. … BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *16* Tana fitowa daga wanka, aka aiko kiran su daga wajen Kaka Mallan. Muhsin kawai suka bari a wajen Inna su duka suka d’unguma. Uncle,Ya Yusuf,Baba Habu Anty Umma sai Kaka Mallan suka tarar. Ko gaisawa Uncle bai bari an yi ba dan yana lura babu Ya Musbah ya d’au waya ya hau kiransa yana mitar ‘ya an ce za’ayi meeting, amma an bar shi ya tafi,bai zo ba’. Sai da aka jira ya zo ya fara bud’e taron da addu’a tukunna Uncle ya bari ma aka gaggaisa. Ba tare da b’ata lokaci ba Kaka Mallan wanda ya amsa gaisuwar su Baba da kyar ya kalli Baba ya ce ‘’Musa’’! Sai da Baba ya lumshe Idanunsa ya bud’e tukunna ya ce ’’Na’am,Kaka.’’ Sai ya d’an nisa tukunna ya ce ‘’Dazu d’an uwanka ya zo ya same ni akan batun Matar senator da y’ar wajen ka, an yi part 2 kenan?’’ Shiruu Baba ya yo kafin chan ya ce ‘’InshaaAllah hakan ba zata sake faruwa ba, na tsawatar mata’’. Cikin d’an daka tsawa Kaka Mallan ɗin ya ce ‘’Kai dallachan gafara, ka tsawatar kuma na yaushe, kwanakin baya ba an tsawatar matan ba amman ka ga alamun ta yi amfani da tsawatarwar?. kuma tsabar cin fuska da rashin sanin ya kamata MUSA, Yusuf fa da Mahaifinsa suna cikin gidan nan amman kuka barta take kula wani ‘Al’ameen’. Dama na fahimce ka tun ba yau ba,komai naka daban yake….. Duk wata hanyar da zaka bi ka salwantar da had’in kan zuri’ar nan tou ka sani, kai kenan ace komai naka a botsare? kuma duk in ka je ka dawo baka ganin dai-dai sam amma taurin kai ya ƙi bari ka saduda? Ka duba kaga yadda ka kafe akan kasuwanci kana ganin babu riba amma dukda haka sai da ka d’aura Musbahu akan kasuwancin shima, kana gani y’an uwanka suna karatu amma kai ka nacewa abu d’aya gashi yanzu a ta dalilin botsarancin ka kai da iyalin naka gaba d’aya kun zama abun tausayi.” Da sauri Manubiya ta mik’e ta juya za ta fita. Cikin karsashi Kaka Mallan ya ce’’Wallahi zan ci ubanki, ni zaki mik’e ki fitarwa ina tsaka da magana, saboda na fad’i gaskiya?dawo ki zauna tun kafin in saka Yusuf ya ladaftarmin da ke’’. Ko gezau Manubiya bata yi ba, bata fitan ba kuma bata koma ta zauna d’in ba, har sai da Ya Musbah ya daka mata tsawa ya ce ’’Wai ba da ke ake magana ba?’’Tukunna ta koma ta zauna tana ji kamar ta fashe tsabar takaici. Baba, Kaka Mallan ya kalla kafin ya ce ‘’Ka gani ko? kalli ka ga!! Wannan ƴar sai ta gagare ka wallahi’’ ya fad’i hakan yana nuna Manubiyan kafin ya d’aura da cewa ‘’Babu yadda ba a yi da kai akan ka aurar da ita ba amma ka nace akan karatun da aka kwad’aita maka tun farko ka k’i yi,shi za tayi. Ita da take y’a mace wadda ya ci ace yanzu ta yi Yara biyu ko uku ma, amma ka ja mata har ta yi kwantai… tunda ni dai rabon da in ji sallamar zance da sunan ta har na manta, ta d’auki shegen girman kai ta azawa kanta bata kula waenda suke zuwa mata ai gashi duk sun gudu, ba fata nake miki ba Amman da wuya ki auru sai ki je ki rungumi littafi.’’ Shiruu kowa ya yi baka jin maganar kowa sai ta Kaka Mallan ta inda ya d’aura da cewa ‘’Duk da ka nuna ban Isa da kai ba dole zan saka baki a maganar Jidda wanda dalilina na biyu kuma shine ba zai yiu ka tara Yara da kai kanka ku na ta kurmutsa a d’aki a takure kuma kak’i d’aukar shawara sannan ka yi tunanin za mu yi shiru ba. Ba zan zuba ido Yaranka mata har biyu su tagaiyyara ba.! Ita Manu yanzu ta riga ta zama sai an had’a da addu’a, shiyasa tun kafin Jidda itama ta yi kwantai na riga na gama yanke shawara kowa ya saurara ya ji.. Nan da sati biyu dama za’a kawo kayan sa ranar Siyama dan haka a tare a kuma rana d’aya Yusuf shima zai bada na Jidda, in Allah ya kaimu nan da wata uku za ‘a had’a a d’aura auren tare da nasu Siyama a mik’a ta d’akinta, in kuma anan cikin gidan ma zai zauna shima sai a ware ma sa nashi fannin. Sai maganar kud’in Matar senator, Ummaa da Uncle sun bada dubu bibbiyu Habu ya bada uku nima zan bada uku a had’a a bata kai kuma sai ka nemi cikon ka cikata mata, Allah ya rufa asiri. Akwai mai magana?’’. Ahankali Anty Umma ta ce ‘’A’a Kaka’’. Tana mai jin takaici a ranta, ita da take Mace kuma za’ayi auren y’arta, babu wanda a cikin su ya bata ko sisin kwabo, Yayar Siyaman sai ita ne kawai suketa fafutukar komai, hatta lemukan da za’a tarbi bak’i ita ce zata siya, an sakar mata komai an zuba mata ido kuma ta sab ba bayarwar za su yi ba daga nan har akai siyama d’akinta,amma yanzu ita an hura mata wuta sai da ta bada dubu biyu… A hankali Baba ya ce ‘’Kaka Mallan,Ina da magana’’ Sai da Kaka Mallan ya d’an k’ura masa ido tukunna ya ce ‘’Muna jin ka’’. Sai da ya fara yin godiyar karo karon kud’ad’en da suka yi masa tukunnna. Cikin rashin jin dad’in maganar da zai fad’a ya ce ‘’Ka yi hak’uri Kaka, ba wai jayayya zan yi da kai ba amma Ina ganin maganar auren Jidda da Yusuf gara kawai a barta’’ Ba tare da Baba Habu ya ce komai ba kawai ya mik’e ya fice daga parlourn gaba d’aya. Cikin fushi Uncle ya kalli Baba ya ce ‘’To ai shikenan, gata nan sai ka kwad’ata ka cinye, amma wallahi idan ta sake janyo magana kar a kuskura a sake involving d’ina a ciki’’. Daga haka ya juya ga Ya Yusuf wanda ya sunkuyar da kansa yayi shiruuu ya ce ‘Yusuf dan Allah dan Annabi ka hak’ura da Yarinyar nan, kana da degree d’inka da sana’arka babu gurin Yarinyar da zaka je ta k’i ka’’. Anty Umma dai bata tanka musu ba hakanan ta jaa Bakinta kawai ta yi gum, tana kallon kowa. Da dakakkiyar murya Kaka Mallan ya ce ‘’Musa, inaso ka gaya min laifin Yusuf kwara d’aya tak’’. Ba tare da shakkah ba Baba ya ce ‘’Yusuf bashi da laifi Kaka kawai dai na ga a halin da Jidda take ciki na damuwa da rashin lafiyar Mahaifiyarta bai kamata a yi mata auren dole ba, kuma ni ban shirya aurar da Jidda ba har sai mahaifiyar su ta samu lafiya, InshaaAllah.’’ Sai yanzu Anty Umma ta ce ‘’Ita Jiddan ta ce maka bata son Yusuf d’in?’’ Tun kafin Baba yayi magana Jidda ta yi k’arfin hali da sauri ta ce ’’Eh,Umma’’ a hankali. ‘’Uhm, to ai shikenan’’ Anty Umma ta ce, daganan ta ja bakinta ta sake yin shiru. Tabbas ran Kaka Mallan ya b’aci dan haka kawai ya ce “kowa ya tashi ya tafi’’ Yanayinsa kad’ai ya sanya kowa ya fahimci tabbas in ba da kyar ba to kuwa sun d’aura gaba kenan da shi da Baba har abada.. Hakanan taro ya watse zuciyar kowa da k’unci, dan shi kansa Baba saboda yaga ba yadda zai yi ne shiyasa yayi magana bayaso ya sako karatu su yi masa chaa amma yanaso Jidda ta fara ko da level one ne ta d’an saka k’afarta a jami’ar tukunna a yi auren, ga kuma damuwar da suke ciki ga rashin lafiyar Inna, abubuwan da yawa!! Ya san dama ba lalle su fahimce sa ba. Shiyasa washegari ya bi Kaka Mallan anty Umma Baba Habu da Uncle, dan yana so su sasanta a tsakaninsu su manyan sannan ya fahimtar da su. Amman sai abun bai yi masa dad’i ba sam dan Anty Umma ce kawai ya samu ta d’an saurare sa ya gama bayanin sa, ta ce ‘Ba komai’ kawai. Dama ita ƴar i don’t care ce. Uncle kuwa tun a masallaci ya ce masa yana son ganin su shi da Baba Habu in an fito amma suna fitowa ya shiga gidan da yake parking motarsa ya zari mota yayi gaba gashi ranar lahadi ne bare ace aiki ya je. Baba Habu kuma ya ce masa bacci zai yi, lokacin siesta d’insa yayi. Kaka kuwa tun kafin ya k’arasa shiga wajen nashi ma ya kore sa. Tun daga ranar kuwa kan y’an gidan ya sake tarwatsewa, da farko lamarin nasu rashin had’in kai ne kawai yanzun kuwa abun ya had’a har da jin haushin juna da fushi. …. Satin Manubiya d’aya da fara zuwa aiki gidan Ammi. most atimes (mafi yawanci) exams ɗin nata da safe suke yi shiyasa take zuwa gidan tun kafin gari ya fara haske saboda ta samu ta yi ta gama ta tafi on time,ranar na Sir Najeeb ne kawai ta rok’i Ammi, tun ana i washegari exams ɗin ta ce mata ’Dan Allah ta yi mata hak’uri 10 za ta taso InshaaAllah zuwa 11 za ta iso gidan ta yi aikin nata.’ Allah ya taimake ta a lokacin da ta je ta na neman alfarmar Mama tana d’akin Ammin tana shirya mata wardrobe d’inta,ai kuwa tashi d’aya Maman ta saka Baki… Dan haka ba dan Ammin ta so ba sai dan girman Maman a idanunta ya sanya ta hak’ura ta yardar ta amince….. Itafa so take ta maidawa su Manubiya rayuwar su living hell (mafi ƙololuwar azaba) amma ta lura Yarinyar ita da k’aninta (Muhsin) kamar waenda ake jona musu charji, duk kalar uban aikin da ta tula musu kafin ace kwabo sun kammala shi tsaf. A b’angaren Manubiya kuwa sam aiyyukan da Ammi take tula mata basa damun ta, ita babban tashin hankalin ta a gidan ita ce’Mama’, kamanninta da wannan Mutumin sun yi yawa sannan in dai ta kalli fuskar Mama tou sai ta tuno shi kuma indai ta koma gida ta kwanta barci tabbas sai ta yi mafarkin shi maimakon ta yi mafarkin Mama tunda ita ta ke gani, A’a Mafarkin Mutumin take yi kuma kullum kamar sake ingiza mata tunanin sa ake yi. Hakan ya sanya a ko da yaushe take k’ok’arin ganin ta yi nesa da Mama. Wanda zuwa wannan lokacin Hatta ita kanta Maman ta fahimci Manubiya wasan y’ar b’uya take yi da ita, bata san dalilin Yarinyar na guje mata ba gashi ita kuma har ga Allah Yarinyar ta shiga ranta, sosai……… ••••• Amaryar Daddy tana cika sati biyu da tarewa rana tsaka ya ce ’ta had’a kayanta za su koma main house d’insa,’. *Ummi* Mace ce mai sauk’in Kai da fahimta ga hak’uri, shiyasa tun kafin auren ma da ya ce mata ta ajjiye aikinta tashi d’aya ta ajjiye, sam bata yarda ta yi jayayya da shi ba shiyasa yanzun ma da ya ce su koma main house ɗin nasa tashi d’aya ta ce ’’to’’, Kuma ita har ga Allah bata ji komai ba dan by then (zuwa wannan lokacin) sun saba da Mommy da Ƴaƴanta saboda bata yi k’asa a guiwa ba sai da ta amshi numbers d’in su kaf su ke gaisawa, sam bata damu da yadda a ko da yaushe ita take kiran su ba. Basu samu dawowa ba sai washegari, dama gado da set d’in kujeru kawai ta yi amma hatta kayan kitchen a gidan ta je ta tarar dan haka aka kunto mata iya gadonta da kujerun aka zo nan mansion d’in aka kafa mata a side d’in da Daddy ya nuna mai d’auke da parlour mini kitchen dining area da two bedrooms, k’ofar side d’in nata yana kusa da na Kausar na Yasira kuma kusa da na Mommy. Tare ta zo da Ƴarta Munirat, mai kirki sosai da hankali ga nutsuwa Ga ta kyakkyawa sosai doguwa dirarriya black beauty, ga gashi tubarkallah. Ummi ta so Munirat ta zauna a d’ayan d’akin gefenta(na cikin fanninta) amma sai Mommy ta yi insisting akan itama a ware mata nata d’akin a gefen na su Yasmeen, hakan kuwa aka yi, aka ware mata d’aki anan side d’in nasu su uku Ita, Yasmeen sai Yadira kowa da d’akinta amman suna sharing parlour…. Lamarin Yasir ya ishi Mommy gashi gidan an dawo kamar komai bai faru ba dan hatta Kausar ta ware sosai ta ci gaba da shiga mutane… Daddy shima ya d’an sak’k’o yana d’an wasa da yaran Shi da Mommyn ne dai har yanzu daga gaisuwa shikenan shima sai in a gaban yaran ne ya ke amsawa amma Idan iyaka su biyu ne ko kallonta baya yi. Amman shi Yasir har yanzu shiru Allah kad’ai ya san inda ya je ya zauna. Dan haka ta yanke shawarar tunkarar Daddy da maganar yau duk da bata san ya za su kaya ba amma ta saka a ranta zata yi koma menene muddin za a nemo mata Yasir d’inta. Dama yau ɗin ita ce da girki dan haka ana gama dinner bayan an d’an tab’a hira kowa ya watse itama ta je ta d’an kimtsa ta nufi chan sama hawa na biyu inda side d’in shi yake. A parlournsa ta same shi yana waya dan haka ta koma gefe ta samu guri ta zauna. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *17* Ya fi 1 hour yana wayar kafin finally ya katse kiran ya ci gaba da danna computer dake a gaban sa. Ta ji zafin yadda ya yi mata, dama a wuya take dashi yau ko kunya babu haka ya dinga zolayar Ummi ɗazu a wajen dinner a gaban kowa ita kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba. Da kyar ta samu ta danne abunda takeji yana taso mata, ahankali ta ce’’barka da dare,Daddy’’. Ba tare da ya kalle ta ba Ya ce ‘’za ki iya tafiya, na gode.’’ Yana gama fad’in haka ya mik’e ya tartare kayayyakinsa waenda ke zube a gabansa kan centre table ɗin, daga nan ya nufi hanyar d’akinsa. Da sauri itama ta mik’e ta ce ’’a kan Yasir na zo mu yi magana’’. Kamar ba zai kula ta ba sai kuma ya ce ’’what about him?( me ya faru akanshi?). Ba tare da ya kalle ta ba. Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce ‘’Ba ka lura baya gidan nan ba? Ya fi 4 weeks fa ba ya nan’’. Sun fi 2 minutes a tsaye dan sam Daddy bai so ya kula ta. Ya so ya danne fushin sa ya manna mata kawai ya yi wucewar sa amma sai hakan ya gagara.. A hankali ya juyo ya ajjiye computersa da wayoyin a kan kujerar dake kusa da shi sannan ya taka ya k’arasa inda take ya ce ‘’Khadijah, kar ki yarda ki kai ni bango a cikin gidan nan, ba ki san ya nake ji ba idan na kalli fuskarki, ina zaune da ke ne kawai saboda Ƴaƴan da ke a tsakaninmu da kuma alk’awarin da na yiwa su Abba kafin su rasu sannan na dawo gidan nan ne domin na lura in dai na zauna a daban daban ni da Ƴaƴana tou tabbas za ki iya raba ni da su. Banason yawan magana ta da ke! saboda na lura baƙin ciki, da tashin hankalina kike son gani, a ko da yaushe kin fi so ki ganni cikin tashin hankali…. Dan haka na zab’a yin nesa da ke!. Ina samu lumana da kwanciyar hankali daga wajen Saddik’a, abun da kika gagara ki bani.’’ Bakin Mommy har rawa ya ke yi, ganin tana shirin fara magana ya sanya yayi saurin d’aga mata Hannu alamun ‘wait(jira)’ ya ce ‘’Ba na buk’atar komai daga gareki, kin yi kuma kin ce me isarki….. Kin san bani da lafiya amma a wannan shekarun ki ka zab’i ki tuna mini da case d’in ‘Khadijah’. Ban san mai zan ce miki ba. Amma kamar yadda na yi miki sutura na bar ki a cikin Ƴaƴanki sannan bayan na zab’i raba gida da ke na hak’ura na dawo na ci gaba da zama da ke a k’ark’ashin inuwa d’aya tou nima inaso ki yi mini alfarma d’aya tak,ina so ‘ki fita a harka ta’!!!! Iyaka wannan kawai nake da buk’ata daga gare ki. Case d’in Yasir na ce a gaya miki ki yi solving tun kafin mu zo ni da Saddiƙa, yanzu kuma da ya ƙi dawowa wannan ma matsalarki ce, ke kika san yadda za ki yi ki je ki nemo sa, amma Yasir ba jariri bane ba da zaki fake da case d’in sa ki k’ulla wata alak’a a tsakanin mu, duk inda ya je idan ya gaji zai dawo in bai gaji ba kuma Ubangiji ya sada fuskokinmu A aljannah…. abu na k’arshe da zan ce da ke shine ki tabbata wannan ita ce maganata mai tsayi ta k’arshe da ke, in ba haka ba wallahi zan baki mamaki.’’ Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Mommy, a hankali yana shirin wucewa ta ce ‘‘Ubangiji ma muna yi masa laifi mu rok’i gafara kuma ya yafe mana, na ce ka yi hak’uri Daddy! Ka bani last chance! I love u, kar ka yi mini haka…..’’ Cikin fushi ya ce ‘’Ba kya so na ba kya k’aunata sam, shiyasa kike turturing d’ina(azabtar da ni). ko kin san cewa akan maganar da kika yi mini kad’an ya rage in mik’a kaina ga hukuma?kuma na san kin san menene hukunci na ko?’’ Cikin zubar hawaye Mommy ta ce ‘’Ka yi hak’uri mu bar wannan maganar ta wuce…..’’ ‘’Get out!’’ Daddy ya fad’a cikin katse ta. Za ta yi magana ya sake cewa ‘’ki fita ,na ce.’’ Da d’an k’arfi. A hankali ta sa Hannu ta share hawayenta ta toshe Bakinta saboda kar sautin kuka ya sake fitowa, sai da ya ɗan lafa tukunna cikin tsananin mutuwar jiki ta ce’’ka yi hak’uri’’ daga nan ta juya ta fita tana mai sake toshe Bakinta. Ya dad’e a wajen kafiin da k’yar ya samu ya juya ya wuce d’akinsa. …. A d’akinta ta tarar da Kausar da Yasira… Ta so ta b’oye musu damuwar ta amma suna had’a idanu da su sai ta karaya bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba. Sai da suka yi da gaske tukunna suka samu suka rarrashe ta, ta yi shiru, Yasira ta d’au waya ta kira Baaba Larai, tana zuwa suka shiga tattaunawa. Ba su suka bar d’akin nata ba sai wajajen k’arfe d’ayan dare bayan sun saka Kausar ta yi musu alk’awarin kiran Yasir washegari, Idan Allah ya kaimu….. … Washegari da sassafe Kausar ta tashi ta shirya cikin wata dress mai kyau wadda bata k’arasa rufe mata k’afafunta ba. Jan jambaki da kwalliya ta rambad’a sosai wanda hakan ya sake fito da ainihin kalar farar fatarta… Hula kawai ta saka a kanta daga nan ta kama hanya ta fice ta nufi side d’in su Yashjub tana adduar Allah yasa bai fita ba, dan dukda yau ba aiki ta ji Yasira tana cewa sunada important meeting. A parlourn ta same shi shirye tsaf cikin suite ga briefcase d’insa a gefe yana zaune yana sipping tea. A hankali ta saki wani lallausan murmushi kafin ta k’arasa ciki, cikin takun ta mai tsananin d’aukar hankali. sai da ta je kusa da shi tukunna ta ce ‘’Salam alaika’’. Tun lokacin da ta turo k’ofar ta shigo ya lura da ita dan haka ya sake tamke fuska tamau kamar bai tab’a murmushi ba. A hankali ta nema waje ta zauna a gefen sa, sannan ta ce ‘’Ya Yash, Ina kwana’’. Ci gaba kawai yayi da sipping tea d’in sa yana kallon tv still bai ce mata uffan ba. Badaban Kausar A ce a fagen tsaurin ido ba to da a yadda ya tamke fuska kaɗai ya Isa yasanya ta tsorata, ta fita. Duk da tana d’an fargaba haka ta daure a karo na uku ta ce ’’Ya Yash’’. Lumshe kyawawan idanuwansa yayi a hankali ya juyo gare ta sannan ya bud’e yana mai kallon ta ido cikin ido tukunna ya ce ‘’Duk abun da kike buk’ata ki turomin Yadira anjima, tashi ki fita.’’ Ganin yadda ta kafe sa da idanuwa ne ya sanya kawai ya mik’e ya d’au briefcase d’insa ba tare da ya sake bi takanta ba ya nufi hanyar fita. Da sauri ta sha gabansa cikin d’an gudu ta ce ‘’Ya Yash Mommy ce fa ta aiko ni wajen ka’’ Ta fad’i haka tana k’ok’arin matsawa jikinsa sosai sannan ta saka Hannu zata kamo briefcase ɗinsa. Duk kalar tsaurin idonta sai da ta ji tsoron kalar kallon da yayi mata dan haka ta d’an ja baya kad’an ta sunkuyar da kanta k’asa. Da kyar Yashjub ya samu ya d’an rarrashi kansa, kawai ya wuce ba tare da ya yi mata komai ba ya fice ya barta anan wajen amma da farko yadda zuciya ta taso masa so yayi ya d’an wanke ta da mari watakila zata dawo saiti!!! Idan akwai abunda ya fi tsana a rayuwar sa bayan cin amana to shine Mace marar kamun kai! tabbas Kausar y’ar uwarsa ce amman kwata-kwata jininsa bai d’auke ta ba tun filazal, gashi yanzun kuma rashin kamun kanta ya sanya ta kuma fita a kansa ko ganin Yarinyar baya son yi,wallahi. Da wannan tunanin ya k’arasa motarsa ya shiga ya zauna ya lumshe idanuwansa…. A take idanunta waenda izuwa yanzu abun ya zame masa jiki suka hau yi masa gizo. A ransa ya ce ‘’Ga inda ake Mace nan, gaisuwar ta ma tsada ne da ita, sannan ta yi laifi amman tsabar sanin darajar Kai bata yi gigitar da d’ayan Namijin ya yi yana bada hak’uri ba…. Ana ganinta kuma za a fahimci yadda itama take a ruɗe amma ta dake sam bata yarda ta zubar da class d’inta ba….” A hankali wani lallausan murmushi ya sub’uce masa A fili ya ce ‘’Sai shegen kukan shagwab’a kamar wata y’ar baby’’… Yana nan zaune yanata tunani kira ya shigo wayarsa… Ba k’aramin fad’uwa gabansa yayi ba a lokacin da ya d’auko wayar zai amsa idanuwansa suka sauk’a akan time, ‘Wato zaman sa anan har ya yi 30 minutes kenan??’ ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya samu mai basa amsa ba. Ganin kiran yana shirin tsinkewa ne yasa yayi sauri ya d’auka ya kara a kunnensa ahankali ya ce ‘’Daddy Ina kwana,sorry wani abu ya ɗan tsaida ni,gani nan zuwa’’ . Yana gama fad’in haka ya kashe wayar ya kunna motar ya bata wuta ya wuce…. A ransa yace ‘’I really need to see Najeeb.(tabbas dole zan ga Najeeb) Zuwa yanzu ya fahimci in dai ba son Yarinyar nan yake yi ba to tabbas akwai dalilin da ya sanya Ubangiji ya turo ta cikin rayuwar sa, ya san ma ba zai you ace yana son ta ba tun da bai san ta ba… ya kuma yi addu’o’i dan haka definitely ba aljana ko mayya bace ba tunda gashi har yanzu bai bar tunanin ta ba! Tun yana k’ok’arin yakice tunanin nata ma har ta kai ta kawo zuwa yanzu ya daina saboda in yana tunanin nata wani nutsuwa, annashuwa da farin ciki na musamman ne suke dirar masa wanda har ya kan ji baya k’aunar abun da zai gilma ko ya gifta a tsakanin sa da tunanin nata…. Dan haka kawai ya gama yankewa akan zai ajjiye b’oye-b’oye a gefe ya fuskanci Najeeb akan maganarta yau yau d’innan inshaaAllah, tun kafin a samu matsala, yana da buƙatar ya santa. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *18* Da wannan tunannin Ya ƙarasa makeken company d’in Daddyn nasu. Sanin da yayi suna da bak’i ne yasanya bai wani tsaya ko ya biya ta office d’insa ba, kai tsaye kawai ya wuce in da ake meeting d’in… Bai samu sun kammala komai ba kuwa sai wajajen k’arfe biyu, duk saurin sa bai samu damar k’arasawa office d’in Najeeb ba sai pass 3. A parking lot suka had’u da Najeeb d’in yana shirin fita shi kuma ya shigo. Tunda ya hango Yashjub d’in ya taho ya tsaya daga k’okarin bud’e k’ofar motar tasa da yake yi ya zuba masa ido yana murmushi yana girgiza kai a ransa ya ce ’’Allah mai halittar kowa da yanayin nasa halin, ya san zai zo kuma ya san ba lallai ya same shi ba amma ya d’auki waya ya ce masa ‘ya jira sa’ kawai, shine yake ganin aiki, ya gwammaci ya zo ɗin in bai same shi ba ya juya’’. ‘’Kai lafiyar ka kuwa!’’ Yashjub wanda ya k’araso kusa da shi yayi masa tambayar cikin tsare gida. Y’ar guntuwar dariya Najeeb ya saki kafin ya ce ‘’Mamakin ka nake yi, ka san wani abu ne ya d’an rike ni, ba dan haka ba da na dad’e da fita daga nan’’ ‘’Hmmm’’ Yash ya ce kafin ya d’aura da cewa ‘’Ka kyauta kuwa, bani key d’in in shiga idan ka gaji da tsayuwa ka same ni a office d’in.’’ Murmushi Kawai Najeeb yayi daganan ya mik’a masa key d’in ya wuce shi kuma ya bud’e motarsa ya zuba kayayyakinsa a ciki ya rufe tukunna ya bi bayan Yashjub d’in. Kusan a tare suka shiga Office ɗin wanda ya ke nan k’all gwanin ban sha’awa sai faman tashin ƙamshi yake yi. Fridge Yashjub ya nufa ya d’auki ruwa da cup tukunna ya nemi guri ya zauna akan sofa kusa da Najeeb d’in, yana zama ya b’alle marfin ruwan ya zuba a cup ya kafa a Baki yayi bismillah ya shiga sha….. Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin ya ce ‘’Uncle ya ce in baka hak’uri, In sha Allah nan da sati biyu za’a gama ginin estate ɗin.. k’ofofin ne suka d’an yi wahala gashi ka ce dole sai irin na estate d’in Abuja da Kano za a saka shiyasa abun ya d’an yi musu tsauri amma yanzu haka an samu an yo order, ya ce kawai za’a fara fenti da fixing electronics in ya so idan an kawo ƙofofin sai ya zamana shine last aikin da za a yi kawai.’’ Kallon da ya ga Yashjub d’in yana yi masa ne ya sanya ya ce ‘’Menene kuma? Yash!..Uncle d’ina ne dai, ido ya san na gida.’’ Murmushi Yashjub yayi kafin ya ce ‘’Kallon da kaga Ina yi maka na mamakin yadda ka hau zuba ba tare da ka ji dalilin zuwana ne,ba. Ko ce maka aka yi akan maganar estate na zo nan?’’ Yayi masa tambayar yana me kafesa da ido. Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin ya ce ‘’To naga ai shine priority d’inka a yanzu mu kuma muna ta yi maka delay’’. ‘’Yeah, days ago shine priority d’ina amma yanzu kam ba shi bane ba, kawai dai tunda ka taso da maganar tou ka gayawa waenda ka ce sun ce suna son guda d’aya rent su jira sai nan da one month idan za su iya.’’ Yash ya fad’a hakan yana sake zuba ruwan a cup sannan ya kai Baki. ‘’Ok’’ Kawai Najeeb ya iya cewa yana mai k’ok’arin fahimtar mood na Yashjub d’in. Wani d’an guntun murmushi yaga Yash yayi, ba tare da ya kalle sa ba Ya ce ‘’Ina Manubiya?’’ Da d’an k’arfi Najeeb ya ce ’’what!’’ Kafin ya d’aura da cewa “wai dama da gaske kake kenan, kuma amma ka tsaya ka na ta yi mini kwana-kwana da fulatanci? Ba fa a zurfin ciki a harkar nan dan in ka tsaya wasa tsaff sai dai ka ji sold out!wallahi. Kaii amma na ji dad’i, ni zan fara kaiwa Mommy good news ɗinnan. Alhamdulillah ‘dutse’ is in love finally’’. Najeeb ya k’arashe maganar yana mai fashewa da dariya. Tsayawa kawai Yashjub ya yi yana Kallon sa bai ce masa uffan ba. Haka nan Najeeb ya tisa shi a gaba yayi ta zolayar sa, sai da ya gaji dan kan sa yayi shiru tukunna Yashjub ya ce masa ‘’Ka gama? Za ka iya saurarata yanzu mu yi abun da ya kawo ni, ko in tafi kawai?’’ Cikin dariya k’asa-k’asa Najeeb ya ce ‘’Sorry, Ina jin ka Angon Manubiya’’. A hankali ya lumshe lumsassun dogayen idanuwansa ya bud’e tukunna ya ce ‘’Najeeb ba wai son Yarinyar nake yi ba…..’’ Cikin tarar numfashinsa Najeeb ya ce ‘’Yet(tukunna..) Amma ta burgeka ai ko?. ai dama abunda za ka ji kenan yanzu tunda kwata-kwata sau d’aya ka tab’a ganin ta,haka abun yake ai. Ka yi ƙoƙari ka santa ku shaƙu! InshaaAllah nan da ƴan watanni za mu sha biki…’’ ‘’Ya Allah, duk wani iri abun nan ya ke sa ni ina ji’. Yash ya fad’a yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya. Dariya Najeeb ya saka kafin ya ce “Ai yanzu zan baza ka a groups, kaff friends d’inmu sai sun san aljannar da ta aureka ta rabu da kai finally ko kuma ta mutu, wannan abun farin cikin har walima zamu had’a.’’ ‘’Pls don’t (dan Allah kar kayi hakan), haba Najeeb ya kake yi min haka? Na zo maka da matsalata a matsayin ka na Abokina kai da ya kamata ace ka tsaya ka saurare ni amma sai faman shirme kake yi min,shikenan kawai bara in tafi…’’ Yashjub ya fad’a yana k’ok’arin mik’ewa da alama ransa ya d’an sosu. Da sauri Najeeb Ya ce ‘’Yi haku’uri’’ yana mai rik’o hannunsa sannan ya yi serious face ya ce ‘’na daina, Talk to me friend(mu yi magana Abokina).” Sai da Yashjub ya d’an k’ura masa ido tukunna ya koma ya zauna. Ya dafe kansa da Hannu d’aya ya d’an sunkuyar da kan nasa ya lumshe ido a hankali ya ce ‘’Ba wai son Yarinyar nan nake yi ba Najeeb, saboda wallahi yanzu inda ace za a kawo mata guda goma a kulle musu Iyaka Idanunsu a bar ragowar fuskar a bud’e to ba lalle in iya nuna ta a cikin su ba. iyakar idanunta kawai na gani that very day(a wachchar ranar) amman tun daga lokacin na gaza sukuni… Idan fa na lumshe idona har ganin idanunta nake yi, sannan haka kurum sai in dinga ji kamar muryarta tana yi mini gizo a kunnuwana.. sannan in ba tunaninta nake yi ba ko maganarta as in(misali) idan na yi forcing kaina in cireta a raina to gaba d’aya sai in ji Ina neman susucewa kaga alal misali yanzu haka maganar ta muke yi da kai ko?To ni kad’ai na san irin peace of mind d’in (kwanciyar hankalin) da nake samu, wani sanyi nake ji har k’asan zuciyata da annashuwa sannan with each passing second na rayuwata all i want to do (sannan duk wata daƙiƙar da za ta zo ta shige a rayuwata iyakar abunda na ke ganin ya kamata in yi) shine In san ta!!!. Its like (ji nake) kamar akwai abun da yake pushing d’ina (tura ni) akan in je in santa in yi bincike akan ta, in zama very close to her, like sooooo close..may be a friend (In samu mu shaƙu da ita, shaƙuwa sosai, wataƙila kamar ko mu ƙulla Abota haka)” Ya k’arashe maganar tasa a hankali yana mai d’agowa ya kalli Najeeb wanda ya ga ya yi shiruu ya k’ura masa ido kawai, sai da ya fesar da iska tukunna ya ci gaba da cewa ‘’Na san me kake tunani amma dan Allah karka fad’a, I can’t love her (ba zan iya in so ta ba) tunda ban riga na san ta kuma na ganta ganta sosai ba, shiyasa ma na riga na yi concluding abun as (na bar abunda na ke ji a kanta a matsayin) ba so bane ba!!!!. it’s definitely something else (dole wani abu ne chan na daban, amma ba so ba). Dan haka Ka bani shawara, mu tattauna a nemo mafita amma kar ka ce min son Yarinyar nan nake yi dan na san ba son ta nake yi ba.’’ Da kyar Najeeb ya samu ya iya danne dariyar da take ta faman taso masa, duk da tausayin da Abokin nasa ya bashi amman kuma ya ba shi dariya duk a lokaci guda. Gashi dai Yashjub is in love da ikon Allah saboda gaba d’aya bayanan shi akan Manubiya amsar d’aya ce tak ‘KAUNA’ although (dukda)bai ganta sosai ba amma idanuwanta da muryarta da ruhinta sun riga sun hana shi sukuni tun yanzu Ina kuma ga in sun kasance frnds d’in (abokan)kamar yadda ya ke da buk’ata a yanzun, Lokacin da zai amayar da abun da yake ransa ma ba zai saniba!…. Tabbas kuwa za a yi soyayyar da ba lalle an taɓa yin kwatankwacin irin ta a tarihi ba dan ya lura da Manubiyan itama a ranar da suka fara had’uwa da Yash d’in. ‘’Najeeb’’ Yashjub ya kira sunansa. Kame-kame Najeeb ya fara yana tunanin mai zai ce masa, saboda shi dai ya riga ya gama fahimtar Yashjub d’in tsaff to amma shi kuma gashi yace kar a ce masa yana son Yarinyar ne Which is the absolute truth(wanda hakan ne haƙiƙanin gaskiyar)… Dan haka a hankali cikin son fahimtar da shi ta ruwan sanyi Najeeb yace ‘’Mai yasa kake tunanin ba son ta kake yi ba? soboda kai ba Mutum bane?’’ Ganin ya ƙi ma ya kula shi ne yasanya Najeeb cewa ‘’Shikenan bara zan san abun yi amma gaskiya ni a yanzu ba zan iya nema maka mafita ba. Frnds d’in dai da ka ambata inshaaAllah zan had’aku friendship (Abota) dukda ni ban ma san ta Ina zan fara ba tunda kaga ni Malaminta ne amma in sha Allah zuwa gobe za ka ji ni, zan nemo idea soon, bari zan jira dan kamar suna da exams d’in Dr Auwal” Shiruu Najeeb d’in yayi daga magana kafin ya sake cewa “bari zan san yadda zan yi kar ka damu, na ma nemo idea’’. ‘’Ok’’ Kawai Yashjub ya ce Kafin ya sake cewa ‘’Kuma wannan wanda na gan su tare kana tunanin akwai wani abun a tsakanin su’’? Dariya najeeb yayi a ransa yace ‘’Ga wani sign din ‘kishi ‘ A fili kuma sai ya ce ‘’I don’t think so, amma dai zan yi finding out’’ Shiruu Yashjub yayi dan sai kuma ya d’an fara jin haushin kansa na tambayar da ya yi wa Najeeb d’in ta yanzu. Ganin yayi shiru ne Yasanya Najeeb kawo wata hirar daganan suka hau tattaunawa… .. Kiran sallar laasar ne ya tashi zaman nasu Yashjub ya wuce Najeeb kuma ya nema wani ya aika shi inda su Manubiya suke exams yau yace masa ya kira mishi Abbbakar. Daganan ya wuce masjid….. •••• Tun rabuwar Kausar da Yashjub da ta shige d’akinta ta rufe bata bud’e ba! Mommy ta je har sau biyu… Jin ta yi knocking ba a bud’e ba yasa ta yi tunanin ko ta fita ne maybe dan haka ta hak’ura ta hau zaman jiran ta. Ganin har yamma ta yi bata ganta ba yasa ta sake komawa domin ta sake dubawa dai-dai nan ita kuma Kausar d’in tana shirin fitowa daga side d’in nata. Kana ganin fuskarta ka san ta ci kuka ba kad’an ba. A hankali cikin rashin jin dad’i Mommy ta ce ‘’Haba Kausar, yanzu ashe tun ɗazu kike ta faman kuka, mai ya faru haka, mai ya sameki?’’ Ta yi mata tambayar tana mai tsare ta da idanuwa. Fad’awa ta yi jikin Mommy ta sake fashewa da wani irin kuka cikin kukan ta ce ‘’Mommy ko kallo ban ishi Ya Yash ba, ni gani nake ma kamar yq tsane ni, tayaya kike tunanin zai kalle ni ma Talkless of ya bani time da chance d’in da zan kafa kaina a cikin Zuciyarsa?. Ke da Baaba Larai kullum sai cewa kuke yi in jira in jira yau an fi wata d’aya kuna cewa in jira, so kuke yi in yi ta jira har sai lokacin da ya had’u da wata ya fara son ta tukunnna ni kuma in nuna mishi ra’ayina?. nikam a gaskiya Wallahi ba zan sake bin ta maganar ku ba ko zai ko zai kasheni da duka zan gaya masa in yaso ke da Baaaba Larai ku san abun yi daganan.’’ Da kyar Mommy ta samu ta zaro ta daga jikinta cikin son fahimtar da ita ta ce ‘’Kausar gaggawa aikin shed’an ne, ki tsaya ki nutsu!!! Na gaya miki na san abun yi kin ji ko? saurin me kike yi ? Yash naki….’’ Cikin ture Hannun Mommyn daga jikinta tana kuka sosai ta ce ‘’Mommy dole in yi sauri, baki san ya nake ji game da shi a cikin zuciyata ba, ina tsoron kar ya sub’uce min sannan ga fargabar kar Yasir ya sanya Daddy yayi min dole… Ko da yaushe fa a cikin fargaba nake. Kar in rasa Ya Yash In ya sub’uce min mutuwa zan yi, wallahi mommy inban aure sa ba”……… Tsit maganarta ta katse ganin Yash d’in yana hawowa sama cikin main parlour d’in saman Cikin zuciyarta kuma sai ta ce ‘’Ai da ban yi shiru ba gara kawai in fad’a ya ji ko zan huta,’’ dan haka ta yi saurin kau da kai kamar ba ta gan shi ba, ta bud’e baki za ta yi magana kenan shi kuma ya ce ’’Mommy’’ da d’an k’arfi. Da sauri Mommy ta saka Hannu ta toshewa Kausar Baki dan har ta cigaba da cewa’’wallahi…’’. Ba tare da ya kalli Kausar d’in ba ya k’araso wajen ya na kallon Mommy Fuskarshi a murtuke kamar bai tab’a dariya ba ya ce ‘’Barka da gida Mommy’’ bai jira jin me zata ce ba ya d’aura da cewa ‘’Mommy dan girman Allah kar ki sake aiko min Yarinyar nan side d’inmu, tun da kin san bata da hankali kuma bata san ciwon kanta ba to da baki turomin ita ba…. ko mayafi fa babu a jikinta ɗazun, a haka ta je min.’’ Cikin rarrashi Mommy ta ce ‘’Yash wayoyinta fa da atms har ma da passport duk ka had’a ka kwace yau kusan wata ko in ce fiye da wata d’aya ma, kaga kuwa ai kai ka kira ta side d’inka ba niba’’. Cikin fushi yace ‘’Au dama ba ke kika turo ta ba zuwan kanta ta yi?’’ Ya fad’i hakan yana nufar Kausar d’in a zuciye kamar zai make ta. Da sauri Mommy ta sake shiga tsakanin su cikin rarrashi tace ‘’A’a ni na turota mana Hausa ce nayi maka.. Anyways tunda baka gane ba shikenan yanzu ka yi hak’uri ka bata wayarta muna son ta kira Yasir dan ya kamata ace yayi hak’uri haka ya dawo gida, naga alama Daddyn ku yana k’ok’arin mantawa dashi a cikin ya’yan sa’’. Tunda Mommy ta fara magana idon Yashjub yana kan Kausar wadda ta sunkuyar da kanta k’asa,wata kalar hararar tsana yake jifan ta da shi. Ahankali Mommy ta d’an kamo hannunshi ta ce ‘’Ka ji Yash, d’an uwanka ne kar mahaifinku ya yi zuciya ta har abada da shi ata dalilin shirmen nan nasa, ka bata wayoyinta ita za ta san yadda za ta yi ta yi contacting ɗinsa,in ta yi masa magaa zai dawo.’’ Sai yanzu ya d’auke idonshi daga kan Kausar ya maida kan Mommy tukunna yace ‘’Na san inda yake,anjima zan je in taho dashi Dan naga alama absence d’insa yana k’ok’arin janyo min bala’i’’. Shiruu duk su biyun sukayi Mommy tana adduar Allah yasa ba maganar su ta yanzu itada Kausar ya ji ba, Kausar kuma tana adduar Allah yasa ya ji d’in. Muryarshi ce ta katsewa duk su biyun tunani Jin yana cewa ‘’Mommy dan Allah dan annabi kar ki sake turomin Yarinyar nan, zan kawo miki phones d’in nata da komai anjima, Ina shikenan?’’ Yayi maganar yana mai d’aga hannunshi duka biyu da gira d’aya. Murmushi Mommy ta yi sannan ta sa hannu ta shafa kumatun shi a hankali tana murmushin ta ce ‘’Shikenan son,shikenan na gode’’. Kama Hannun Mommy wanda yake a fuskar tasa yayi kawai yana kallon ta, Itanma shi take kallo tana nazartar shi So take ta gano ‘ya ji zancen nasu ko a ‘a.’ Bai bata dama ba kuwa dan k’asa yayi da kansa ya furzar da iska ba tare da ya ce uffan ba ya cika Hannun nata ya juya ya fita ya nufi side d’insu bayan ya tsaya ya d’auki belongings d’insa daga motarsa… Ko shiga side d’in nasu dama bai yi ba ya nufi wajen Mommyn dan ba kad’an ba ya ji haushin zuwan da Kausar ta yi masa ɗazu da safe bagatatan….. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *19* Kamar kullum yau ma tare Abbakar da Manubiya su ka fito daga ɗakin jarabawa. Suna tafe yana bata labarin Baraka a jiya da ta je gidan su…. Adashe ta ke yi ashe, ta kwashi nata har naira dubu d’ari uku a jiyan! Yana d’akinsa na soro ya ji ita da maman shi da mamanta suna hirar ‘wai fili zata cika ta siya ta yi gini’. A hankali Manubiya ta sauk’e wata nannauyar ajiyar Zuciya a fili ta ce ’’Allah ya sa ta fi haka! Allah ya bata ikon siyan wasu filayen dayawa nan gaba..’’ ‘’Abbakar!’’ Suka ji an kira sunan shi. Cikin yanayin maganarsa ta masu sanyin jiki ya juya ya kalli mai kiran nasa ya ce ‘’Na’am’’. Dariya saurayin ya yi kafin ya ce ‘’ka bi ka dagewa k’awance da Mace dama kai ga ka ga yanayin ka yanzu kam ba marabar muryarka da ta Macen…. ka je Sir Najeeb yana neman ka’’ Ya k’arashe maganar tasa yana me tapping shoulder d’in Abbakar d’in daga nan ya yi gaba ya wuce ya bar su nan tsaye. Yana wucewa Manubiya ta ce ‘’Allah yasa lafiya’’ Murmushi ya yi ya ce ‘’InshaaAllah ma lafiya, mu je sai mu ji menene’’ Dasauri ta ce ‘’Wa?Ni?tab!inaaaa..’’. wata kalar harara ya yi mata kafin ya ce ‘’Ban gane ba, ba za ki raka ni ba?’’. Cikin nemo mafita da sauri ta ce “Abbakar na fa gaya maka na bar aiki burjik a gidan Ammi, gashi yanzu 4har ya wuce, dan Allah ka yi hak’uri kar mu je yau ma mu tarar yana da bak’o mu yi ta zaman jiran sa in yi letti wajen Ammi, sannan kaga ga karatun exams d’in jibi, ta yau ma ta bani wahala wallahi.’’ Cikin sigar tsokana ya ce ‘’Ko dai ba kya so yau ma ki sake yin gamo da crush d’in ki ba.’’ Da sauri ta zaro ido sai kuma ta buga masa littafin Hannunta tana mai cewa ‘’To k’arya dak’ik’in tunaninka ya baka, wallahi ba wani crush’’. Dariya ya yi yace ‘’Auch’’.yana sosa inda ta buga masa littafin sannan still yana dariyar ya ce ‘’Shikenan, ki je sai mun had’u gobe inshaaAllah.’’ Hararar sa ta yi daga nan ta juya ta wuce. A hankali ya sunkuyar da kansa yana murmushi kafin ya d’aga kai ya bi bayanta da kallo….. sai da ta b’acewa ganin sa tukunna ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya juya ya nufi office d’in Sir Najeeb… Yana zuwa wajen ana shiga sallah, sanin halin Sir Najeeb d’in ne ya sanya sai da ya je office d’in nasa ya tabbatar da baya nan tukunna ya nufi masallacin shima. Yana shiga ya tarar da shi a sahun gaban sa. Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar la’asar ana idarwa shi da wasu a cikin masallacin da suka rasa raka’a suka tashi domin ramawa masu addu’a kuma suna yi. Yana idarwa shima yayi addu’a ya shafa daganan ya zauna zaman jiran Sir Najeeb yana mai ha’dawa da adduar ‘Allah dai yasa ba wani laifi ya kuma yi ba’ dan bayan class rep in dai ka ganka a office d’in Sir Najeeb to ba k’aramin abu bane ba. Ko wani abun ne ma kake da buk’atar yi ko gaya masa to daman an san ka’idarshi’ka gayawa class rep shi kuma ya fad’a masa’…. Ganin fitar sa ne ya sanya Abbakar d’in mi’kewa da sauri ya bi bayan sa. A bakin office d’in nasa suka had’u yana k’ok’arin bud’ewa dan haka yana bud’ewa suka shiga tare Abbakar ya shiga da sallama sannan ya shiga gaida shi da ladabi. Cikin nutsuwa ya amsa masa yana mai neman guri ya zauna akan d’aya daga cikin sofa d’in dake a office d’in kafin ya d’ago ya kalle sa ya ce ‘’d’an zauna.’’ Cikin d’an d’ari-d’ari Abbakar ya nemi waje ya d’an d’osana mazaunansa ya yi shiruu, zuciyarsa tana masa sak’e-sak’e kala-kala. Shiruu shima Najeeb ya yi yana tunanin ta ina ma zai fara ne, Wallahi ba dan Yashjub bane Allah da babu abunda zai sa ya yi wannan abun haba!student d’insa fa abun ya yi wani iri da yawa, amma ya ya iya dole ya daure ko ba komai shima yana so ya ga Yashjub ya yi aure, kuma tunda har ya ga Yashjub ya zo ya same sa a kan maganarta tou kuwa ya san abun na gaske ne, wanda hakanne ya sa shima ba zai yarda ya ɗauki batun da wasa ba. Ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an yi gyaran murya wanda hakan ya sanya Abbakar ya mik’a masa dukkannin hankalinsa. Cikin nutsuwa Najeeb ya ce ‘‘Akan wannan ƙawar taka na kira ka, Manubiya” Shiruuu Abbakar d’in ya yi da farko kafin a hankali ya ce ’’Ok,Sir.’’ Dan zuwa wannan lokacin Kwakwalwarsa ta gama bashi amsar dalilin kiran da aka yi masa. ‘’Tana da wata matsala ne?,as in family issue besides rashin lafiyar Mahaifiyarta?’’ .. Manubiya ƙawarsa ce da yake yi mata kallon kamar ma ta zama ƴar uwa, a ganin sa bai kamata ya kunce mata zani a kasuwa ba. Dan haka ya ce ‘’A’a rashin lafiyar Maman nata ne kawai issue d’in ta’’. ‘’Shiyasa take kuka kusan kullum a class?’’ Sir Najeeb ya sake jeho masa wata tambayar cikin katse sa. Shiruu ne ya d’an biyo baya kafin Sir Najeeb d’in ya ce ‘’Kamar yadda na fad’a muku the other day Malamai kamar iyaye su ke, a yadda na ke ganin ta so disturbed (a dame) kullum na yi tunanin tana da financial issue ne. Am na san ba hurumin mu bane but Aboki na wanda ka ganmu tare ne yake da offer na aiki very simple wanda Mace ko tsoho za su iya yi…” A Ta’kaice Sir Najeeb ya yi wa Abbakar bayanin aikin da ya ga damar had’awa a kansa a take a wannan lokacin kafin ya d’aura da cewa ‘’Na yi tunanin tana da financial problem shiyasa na ce mishi akwai wadda zan nemo ta yi mishi aikin but tunda ka ce ba haka bane ba shikenan zan ce mishi ya nemi wata kawai’’. Shiruuu Abbakar ya yi, ya hau tunani…... ‘Tabbas ya san Manubiya za ta yi farin ciki da offer d’in nan, to amma kuma….’ Cikin katse masa tunanin Sir Najeeb ya ce ’’Shikenan, u can leave, dama reason d’in kiran naka kenan’’. Duk da b’oye-b’oye da kwana-kwanar da Sir Najeeb yayi tashi d’aya Abbakar ya fahimci inda suka dosa daga shi har Abokin nasa, hakan ya sanya ya shiga tsaka mai wuya dan on the other hand, no matter how (a ta wani fannin, duk rintsi)…ko ma menene yake ji yake kuma tunani to fa bai kamata ya yi wa Manubiya bak’in ciki ba! Besides (baya ga haka ma) shi a rayuwa da ko da yaushe yana saka farin cikin ta ne a saman nashi.. Dan haka ya ɗan gyara zama! Da kyar ya iya danne zuciyarsa ya d’ago manyan fararen idanuwansa waenda suka d’an fara surkuwa da kalar ja ya ce ’’za ta yi, baku da matsala za ta yi cikin farin ciki ma, in sha Allah.’’ Yana gama fad’in haka ya maida kansa k’asa. Har cikin zuciyarsa ya yi wa Manubiya farin ciki da samun wannan aiki dan daga gani mai tsoka ne, ya san zata rage damuwa kwarai sannan za ta yi maganin matsalolinta, duk da kuwa ya riga ya san akwai wata ɓoyayyiyar manufa a bayan aikin da aka bata, amma dama tun ba yau ba ya dad’e da yankewa ‘indai rana mai kama da ta yau ta zo, to ba zai bari zuciyarsa ta rinjayi tunanin sa ba’. Ya san ba wai Sir Najeeb d’in ne yake son ta ba amma shakka babu kamar yadda ya lura da itama ta tab’u da ganin wannan Abokin nasa haka zalika shima Abokin, tunda gashi ya fara fakewa da bata aiki….. A hankali ya fesar da iska a ransa yana sake jaddadawa kansa cewa ‘’inshaaAllah, ba zai tab’a bari shirme da mafarkinsa su shiga tsakanin Manubiya da auren wannan Mutumin ko aikin da ta samu ba..’’ A b’angaren Najeeb shima shiruu kawai ya yi yana nazartar Abbakar d’in kafin daga baya ya ce ’’ok,ga katin friend d’in nawa, idan ta shirya sai ta kira shi ta ce masa itace Manubiya Musa wadda za ta yi masa aikin da Najeeb ya ce zai had’asa da wadda za ta yi’’. Ya fad’i hakan yana mik’awa Abbakar katin. A hankali kamar marar lakka a jiki Abbakar ya mik’e ya k’arasa ya je ya amsa, sannan ya ce ‘’Mun gode kwarai Sir,Allah ya k’ara d’aukaka da arzik’i, Allah ya ji k’an magabata’’. A hankali Najeeb yayi murmushi ya ce ‘‘Ameen Abbakar, ta kira soon’’ ‘‘In sha Allah’’ Abbakar d’in ya ce da murmushi kwance akan fuskarsa. Daga nan Sir Najeeb ya sallame sa suka yi sallama ya tafi… Tashi ɗaya!! Najeeb ya gama fahimtar komai game da Abbakar amma ko hauka ya ke yi ko da wasa bai isa ya gayawa Yash ba! dan ya san zai kunno fad’an da ba lalle ya iya kawo k’arshen sa ba ne, saboda a yadda ya ga kishi k’arara a Idanun Yashjub ɗazu ya san tabbas in ya bari ya ji wannan batu to fa sai ya raba su ko da bala’i ne. Shiyasa ya bari akan ba zai fad’a mishi ba, shi ya san ta yadda zai bi ya taya Abokin nasa akan Abbakar da komai ma In sha Allah komai zai tafi normal.. Abbakar kuwa abubuwa biyu ne suka had’e masa na farko damuwar sa wadda yake ta k’ok’arin b’intikewa wadda ya ji mamakin yadda ta ke shirin cin galaba akansa na biyu kuma farin cikin ta ya Manubiya murnar samun riba biyu da ta yi na aiki da masoyi in sha Allah. A hankali yayi murmushin da ya fi kuka ciwo a chan k’asan zuciyarsa yana adduar ‘Allah yasa yadda ya tsara yake kuma tunani ya tafi yadda ya ke zato, Allah yasa yadda yake tunanin zuciyarsa zata huta zata samu nutsuwa idan Mannubiya ta yi auren ta, hakan ya kasance. sannan Allah kar yasa yayi da na sanin wannan ƙudirin nasa da ya yanke .’. Hakanan ya na tafe yana tunani ya nufi gate dan ya san dama ta riga ta tafi gida tun ɗazu, ya san zai ga farin ciki a kan fuskarta in ta ji labarin aikin dan haka yake ta sauri domin ya je ya sanar mata saboda ba kad’an ba yake kwad’ayin ganin wannan farin cikin nata. Duk da yadda yake fargaba amma hakan bai sanya ya ji zai fasa ba dan ya fi bid’ar ganin farin cikin ta da walwalar ta sama da komai….. Adaidaita ya samu ta kai shi har k’ofar gidan su Manu amma sai Jidda ta ce masa ‘’Da ta dawo jakarta kawai ta ajjiye ta yi alwallah ta nufi gidan Ammi.’’ A k’ofar makeken gate d’in ya tsaya ya d’an buga kad’an.. Dakyar, bayan mai gadin ya ji buk’atar shi ya yadda zai je ya kira masa ita dan a cewar sa k’a’ida ne sai an fad’a a day before (ana i gobe) tukunna visitors suke zuwarma masu aikin gidan. Ba a yi 5minutes ba Manubiya ta d’an lek’o da fuskarta ta k’aramar k’ofar gate d’in, suna had’a ido ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ‘’Ashe da gaske kai d’in ne’’. Ta fad’i hakan tana mai fitowa daga gidan gaba d’aya.. ….. Ahankali cikin tsananin sanyin jiki ta fito ta tsaya tukunna tace “Na yi mantuwa ne? ko handout aka bada?’’ Sai da Abbakar ya fesar da iska tukunna ya ce “yau dai na tabbatar da duk abun da yake sanya ki tunani kike ta faman b’oyemin for the past few weeks (kwanakin da su ka shuɗe) a gidan Ammi ya ke, meye ne Manu? Akwai abun da take yi miki na cutarwa ne?’’ Murmushin yak’e Manubiya ta yi kafin ta ce ‘’Kawai na gaji ne, shiyasa ka ga haka. meyafaru ance kana nema na wai ka ce it’s important,ko?’’ Ta yi mishi tambayar cike da son kaucewa tambayar ta shi dan bata san amsar da zata bashi ba. ‘’Manu yau fa ba zaki kaucemin ba wallahi sai kin fad’amin damuwar ki.’ Ya fad’i hakan yana mai zama akan tebur d’in dake anan ta gefen gate d’in Kad’an Kafin ya sake cewa ‘’Sam ba haka mood d’in ki (yanayinki) yake ba lokacin da muka rabu da ke d’azu-ɗazun nan a school,so definitely (dole) anan gidan ne kike da damuwa. Talk Ki gaya min mu nemo mafita kafin ya zamana lokaci ya ƙure. Kinga ba inda ma fa zan je har sai kin fad’a min, kin dai sanni da naci ko?’’ A hankali Manubiya ta lumshe idanuwanta ta bud’e, ta san halin Abbakar da shegen naci, a yadda ya kafe d’innan in bata gaya masa ba to ko ruwa ba zai barta ta sha ba, bayaga haka ma in ba shi ko Jiddah ba bata san wa zata gayawa ta samu sauk’i ba, dukda bama ta san inda damuwar tata ta dosa ba bata san ta yaya za ta fassara ko ta fasalta damuwar tata ba saboda ba lalle ta yi making sense to anyone ba(bada ma’ana a kwakwalwar kowa ba) dan ita kad’ai ta fahimci sannan ta san me take ji take kuma fuskanta dan haka ba lalle a fahimce ta ba.. ‘’Manu ke nake saurare’’ Abbakar ya fad’a yana sake gyara zaman shi. Cikin tsare gida Manubiya ta ce ‘’Ok. zan fad’a maka amma sai ka yi min alk’awarin ba za ka yi min mummunar fahimta ba’’. Murmushi ya yi kafin ya ce ’’inshaaAllah,ina jinki’’. Sai da ta had’iye wani abu da kyar wanda ya tokare mak’oshinta tukunna ta ce ‘’Wannan Mutumin na office d’in Sir Najeeb na ranar nan, to shine nake ganin wata Mata mai kama da shi anan gidan kuma in dai na ganta to sai in yi ta tunanin sa har mafarki fa… Ni kuma bana so ina yawan tunanin sa, bana buk’atar abun da zai had’ani da shi sam, shi yasa nake tunanin barin aikin nan..’’ Ta k’arashe maganar cikin tsananin sanyin murya da rashin jin dad’i. Shiruu Abbakar ya yi yana tunani, har sai da ta sake cewa ‘’Ka fahimce ni?’’ Tukunnan ya d’an yi firgigit Ya ce ‘’Yeah, yeah na fahimceki’’. Daganan ya yi shiruuu ya sake dulmiyawa duniyar tunani. ‘‘Shikenan tou tunda ba ka ma da abun da zaka ce, yanzu gaya min abun da yake tafe da kai’’ Ta fad’i hakan cikin d’an had’e gira alamun ta ji haushin kanta na fad’a masa ta kuma ji haushin shirun da ya yi dan in ba dakyar ba to tasan tunanin abun da bata so ɗin shi kwakwalwarsa ta bashi yake yi. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *20* Murmushi Abbakar ya yi kafin ya ce ‘’Yi hak’uri, ban san me zan ce ba ne shiyasa kika ga na yi shiru…. abun ne ni kaina ya sakani a tunani da damuwa ballantana kuma ke, shawara d’aya itace ‘kawai kiyi ta addu’a..Allah ya sa mu dace.’.” A hankali ta ce ’’Ameen’’ Sai da Abbakar ya d’an sake yin nazari tukunna ya ce ‘’Am..kiran da Sir Najeeb ya yi mini ɗazu akan ki ne fa.’’ Da sauri ta zaro idanu waje, sai kuma ta ce ‘’A kan me wai???’’ Ta yi masa tambayar a d’an tsorace. Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘’kwantar da hankalinki, abun alkhairi ne. Aiki kika samu, a wata a yadda ya ce min 30k, kuma sau d’aya kawai za ki dinga zuwa a sati ragowar kwanakin duk ta waya za ki dinga bada rahoto.’’ Da sauri ta ce ‘’Da gaske? Tayaya? a ina kuma?’’ Ta yi masa tambayar cikin zumud’i da d’aurewar Kai. Yana murmushi ya ce ‘’Kina cewa sir Najeeb bashi da kirki ko? To ba haka abun yake ba, sannan kuma wataƙila ina tunanin yana da wani rauni a duk lamarin da ya shafi mahaifiya… Dan Ce mini ya yi yana yawan ganin ki a damuwa ‘dayake kin san ranar ai kin ce masa Inna bata da lafiya to inaga yana tunanin ko akwai wani problem d’in da ba za ki iya fad’awa kowa ba, shiyasa ya ga ya dace ya taimaka miki ke kuma ki taimaki Inna’.’’ Abbakar ya zaiyyane mata hakan cikin son rufe duk wata k’ofar da zata sa ta fahimci wani abun. A hankali ta ce ‘’Allah sarki Sir Najeeb, Allah ya saka masa da gidan Aljannah. Amma aikin nasa ne? I mean (ina nufin) a Ina ne?company ne?’’. ‘’Eh to nima ban sani ba gaskiya amma inaga kamar na Uncle d’insa ne or something like that(ko kuma wani makamancin hakan), ga dai katin wanda aka ce ki kira nan, shi zai yi miki bayanin komai’’. Abbakar d’in ya bata amsa, yana mai mik’o mata card d’in Yashjub wanda Najeeb ya ba sa. A hankali ta sa Hannu ta karb’i katin tana mai jin yanayinta yana chanjawa, haka kurum…. Cikin nutsuwa take kallon had’ad’d’en business card d’in mai d’auke da sunan ‘Yashjub Imam Kura’. Shiruu ta yi tana sake kallon sunan tana sake maimaitawa… kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta d’ago da sauri ta kalli Abbakar sannan ta ce ‘’Abbakar ko dai wannan Mutumin ne wanda muka had’u da shi a office d’in Sir Najeeb ɗin wanda na gama maka maganar shi yanzu?’’ Cikin katseta ya ce ‘’A’a ba shi bane ba, in da ace shine da zai gaya mini… wannan d’in Sir Najeeb ce min ya yi kamar Uncle d’insa ne fa, Kinga wanchan kuma ai bashi da shekarun da za’a ce masa Uncle ko?’. sannan duba katin da kyau wannan fa landlord ne Estates gareshi har a su Abuja da nan garin, yaushe aka haifi wanchan Mutumin wanda bana jin ya kai 30yrs da har zai gina estates haka??’’. ‘’Eh kam.’’ Manubiya ta ce. Tana mai k’ok’arin son yarda da maganar Abbakar d’in, daga nan ta saka a ranta maybe kawai ta ji fad’uwar gaban da ta saba ji in ta yi tunanin shi ko ta had’u da Mama By mistake ne, Amman wannan ba wanchan Mutumin bane ba. A hankali ta ci gaba da karanta sunan tana sake maimaitawa dan ya yi mata dad’i sosai A fili ta ce ‘’Yashjub’’ A hankali,sai kuma ta d’an yi murmushi. Ba tare da ta kalli Abbakar ba Still idanunta na akan katin ta ce ‘’Nagode kwarai Abbakar, Allah ya sa mu dace’’. Sai kuma ta d’ago kyawawan idanuwanta tana kallon sa tukunna ta ce ‘’Amman ka san sai na yi shawara da su Ya Musbah da Baba, mu yi adduar Allah ya sa su yarda dan ka san halin su ba sa so su ga ni ko Jidda wani a cikin mu yana contributing (kawo gudummawa) wajen ciyar da gidan. Ya Musbah ya dage yana k’ok’arin d’aurawa kan sa abun da ba zai iya ba, wuni yake yi yana guga da wanki A shagon Mati kullum in ka gan shi a gajiye ya ke abun tausayi.’’ Ta k’arashe maganar tata idanuwanta suna ciccikowa da kwallah. Murmushi Abbakar ya yi kafin ya ce ‘’Ai har aiki yake yi a wajen masu ginin chan na bayan layi ya tura suminti ya tura bulo duk dai wani aikin k’arfi yi yake, ni fa yana burgeni Manu, Namiji da neman na kanshi aka san shi.’’ Cikin karyewar zuciya ta ce ‘’eh, hakane Abbakar, amma shi abun nasa ya yi yawa kuma kar aje ayi biyu babu, ka duba fa ka gani saboda d’aurawa kai aikin wahala Baba ya rasa k’afarsa guda d’ayar kuma ta ji rauni, Inna ma saboda yawan tunani kalli halin da take ciki! Kar mu je shima Ya Musbah abu ya yi mishi yawa shima ɗin aje ya samu wata matsalar, in hakan ta faru( Allah ya rufa asiri ) da ni da Jiddan da basa so mu wahala mu zamu zama a wahale ai ga Muhsin shima. A rayuwa in dai ana so a ga abu ya yi perfect (dai-dai) to fa sai an had’a Hannu da Hannu k’arfi da ƙarfe tukunna.’’ Ta k’arashe maganar tata wasu siraran hawaye suna zubo mata, da sauri ta yi ƙasa da kanta. A hankali Abbakar ya sauk’e ajiyar Zuciya kafin ya ce ‘’Manubiya k’addara kowa da irin tasa, ki daina kuka dan Allah, ki yi addu’a, ki kwantar da hankalinki. wata rana sai labari.’’ A hankali kanta a ƙasa har yanzun ta ce ‘’Astaghfirullah! amman Abbakar k’addara ta mai zafi c…’’ Cikin katse ta ya ce ‘’shiii‘’ Sai kuma ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ya ce ’’Taki kawai kika sani.’’ Kamar zai ce wani abun sai kuma ya mik’e ya ce ‘’Bara in wuce,duk yadda kukayi kya gaya min gobe’’. A hankali ta ce ‘’To’’. Daganan suka yi sallama ta sake masa godiya sannan ta koma gidan Ammi shi kuma ya wuce yana tunanin Allah yasa Manubiya kar ta ji haushin sa sosai idan ta fahimci ya san Yashjub za ta yi wa aiki amma ya b’oye mata..dama bai yi niyyar gaya mata ba, ya fi so ta je ta fara aikin tukunna ta fahimci Yashjub d’in ne, ya san kafin nan ba lalle ta iya bari ba. To kuma yanzu a yadda ya ji tana ik’irarin zata bar gidan Ammi saboda mai kama dashi ya san babu dalilin da zai sanya ta aminta da aikin in ta san shi d’in ne… wannan dalilin ya sanya shi ninke ta ta bai-bai.. Sai dare tukunna ta samu gayawa family d’inta har Inna, duk da sun san ba iya magana zata yi ba amma za ta ji su kuma ance in ta amince ta lumshe idanuwanta za su fahimta. Kamar yadda suka yi zato tashi d’aya Baba da Ya Musbah suka ce “A’a”, shi Ya Musbah ma cewa yayi ‘’mutumin d’an kidnapping ne ko kuma dai yanada wani mummunan nufi akanta, dan in ba hakan ba tayaya za a yi Mutumin da kullum shine yake bata tsoro a cikin Malamanta ace tashi d’aya ya bata aiki kuma aikin ma ba zuwa zata dinga yi kullum ba iyaka sau d’aya a sati kawai, sannan a wata ya d’auki dubu talatin zuwait!! Ya bata.” cike da bin bayan ya Musbah Baba yace ‘’Tabbas maganar ka haƙƙun Musbahu, ke Manubiya ina so ki..’’ Cikin katse su su ka ji Jiddah ta ce ‘’Inna ta amince’’. Da mamaki duk suka maida duban su gare ta, ai kuwa ta sake lumshe idanuwanta kamar yadda ta yi da farko. Cikin rashin jin dadi Ya Musbah ya ce ‘’Inna,Manu Mace ce, nauyin family d’in nan akaina ya ke Pls karki…’’ Ahankali ya ji Baba ya dafa kafad’arsa,Kafin da sanyin murya ya ji ya ce ‘Shikenan’’ Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya ya ce ‘’Ki kira Mutumin. Duk Ranar da ya baki ya ce ki je sai ku tafi tare Ke da Musbahu’’. Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice daga d’akin. Ko bayan fitar Baba sai da Ya Musbah ya kuma yi wa Inna bud’ad’d’an bayani akan illolin da shi yake hangowa game da aikin Manu da kuma yadda ya kamata ace shi ne ya ke d’awainiya da family d’in ba wai ita Mace ba. Amman yana gamawa da ya sake ce mata ‘’Kin yarda Manubiya ta je ta yi aikin da aka nemeta ta yi?’’ Sai ya ga ta lumshe masa idanuwanta ta bud’e. Cikin rashin jin dad’i ya kalli Manu, shima ya ce ‘’Ki kira sa, duk yadda kukayi kya gaya min gobe, sai da safen ku.’’ Ya fad’i haka yana mai mik’ewa ya fita. Haka kurum kuma itama Manu d’in sai ta ji duk bata son kira, sai da Jidda da Muhsin waenda suke ta murna da zumud’i suka tisa ta a gaba tukunna ta fita ta je ta aro wayar Siyama ta dawo d’akin. … Gani suka yi kawai Manubiyan tana ta kallon wayar da katin tana juyawa dan haka Jidda ta sa Hannu ta karb’i wayar da katin ta kwafe nambobin farko a cikin jerin nambobin waya guda ukun da ta gani ata chan k’asan katin,ta dannna call ta saka a speaker.. Yadda wayar take ringing tana d’uu-d’uu haka zuciyar Manubiya take bugawa kamar zata faso k’irjinta ta fito. Jin har ta tsinke ba a d’aga ba ya sanya ta sauk’e wani bahagon numfashi, dan haka kurum ta ji tana fargabar jin muryar wanda zai amsa kiran. A hankali ta lumshe kyawawan idanuwanta tana mayar da numfashi a hankal a hankali… Tana shirin bud’e idanunta ta yi magana ta ji Jidda ta sake danna kiran a karo na biyu ta shiga ringing.. Da sauri ta bud’e idanuwanta ta wafce wayar ta ce ‘’Ke ya isa haka, ba ki ga dare ya yi ba, Mutum Babba da matarsa kin dame sa da kira haka ki bari gobe ma sake gwadaw……’’ ta fad’i haka tana duban wayar dan ta ga ko ta kashe ne saboda ta ji ta daina ringin d’in… Tsit!haka muryarta ta katse sakamokon ganin timer da ta yi tana tafiya akan fuskar wayar alamun wanda aka kira ya riga da ya d’auka. Ganin yadda Manubiyn ta yi tsit ta zubawa fuskar wayar ido ne ya sanya Jidda da Muhsin su ka lek’a fuskar wayar suma, cikin zumud’i k’asa-k’asa Muhsin ya ce ‘’Adda Manubiya an d’auka fa, ki yi magana mana.’’….. A hankali Yashjub ya lumshe idanuwansa ya rintse pillow d’in da ya d’aura akan k’irjinsa yana mai sake tabbatarwa da kanshi Tabbas ita d’in ce……. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *21* Earlier.. Zuwan Abokin Daddy, senator Bashir biyu wajen Yahanasu, yau zai yi na uku. Suna waya sosai da Yahansun sannan suna chatting, ta fahimci yana k’aunarta sosai dan yana nuna mata kuma yana yawan gaya mata. Itama kuwa ta kamu ba kad’an ba dan hatta Daddy da Mommy da su Yashjub duk sun fahimci hakan dan har walwala yanzu suka ga tana yi shiyasa Daddy Mommy da Yash suka duk’ufa da addu’ar ‘Allah ubangiji ya tabbatar da auren ta, yasa kar a samu matsala a wannan karon’. Yau tun safe take shirye-shirye, k’arfe biyu tana yi ta shiga kitchen ta fara girke-girke dan ya ce mata yau yana son cin girkin matarsa, saboda already a jiya suka tsayar ita da shi a kan Next week zai turo a saka rana kamar wata uku haka a yi aure, so yau suka tsayar za su sanar da Daddy. Tana cikin aikin Munira ta shigo, tana son Yahanasu dan haka ta dage akan sai ta taya ta. Duk y’an gidan they are nice to her(ba sa yi mata rashin kirki) duk da basa zama su yi hira especially da Ya’isha wadda take ganin itace sa’ar ta amma kuma babu kyara ba kallon banza tsakanin su iya gaisuwa ne da murmushi daganan kowa ta shige d’akinta, duk ranar da bata da makaranta ta kan je d’akin su Yasmeen domin su yi hira amma tana zuwa daga gaisuwa suke shareta ko kuma su fara waya tunda ta ga haka itama sai ta ke zama kawai a d’akinta wani lokacin kuma ta tafi wajen Mamanta ko Yahanasu su yi hira. Ba laifi suna shiri da Baaba Larai itama da kuma Mommy ma, ba wai za’a zauna a yi hira ayi wasa da dariya ba amman dai ana gaisawa cikin mutunta juna da kulawa. Mutum d’aya ce ta fahimci ta tsane ta a gidan ‘Kausar’ sai ko ‘Yashjub’ wanda shima in ta gaida shi da kyar yake amsawa ciki-ciki! Kausar d’in kuwa ko ta gaishe ta bata amsawa, bata san mai ta yi mata ba amman tabbas ta fahimci ta tsane ta gashi kuma ta lura kamar kaff gidan su Yasira da su Mommy sun fi son ta da k’aunarta. … Ba yadda Yahanasu bata yi da Munira ba amma ta dage akan sai ta tayata, a cewar ta dama zaman shiru ya isheta kuma ta riga ta gama exams(finals d’in ta)tun last week so bata da abun yi… 4 tana yi ta je ta yi Sallah ta dawo daga nan itama Yahanasu ta tafi domin ta yi Sallah sannan ta shirya bayan ta cewa Munirat d’in idan yayi kafin ta dawo ta juye a cooler dan already komai ya kusan kammaluwa. Sai da Munira ta had’a komai tukunna ta saka masu aikin suka tayata ta kai parlourn bak’i! Ta kunna burner ta saka turare ta gyaggyara komai sannan ta wuce d’akin Yahanasu. A gaban madubi ta sameta sanye cikin wata Turkish gown mai tsananin kyau da tsada, kwalli kawai ta sanya wa idanuwanta sai powder da lipgloss amma ta yi tsananin kyau!! asalin kyawun siririya kuma kyakkyawar fuskarta ya fito sosai. Murmushi Munira ta yi kafin tace ‘’Adda Yaha, yau in senator ya ganki sai ya hantsila’’ ta fad’i hakan ta na mai k’arasawa cikin d’akin. Dariya duk sukayi kafin Yahanasu tana dariya ta ce ‘’Ba ki da dama wallahi’’. Suna tsaye Munira tana taya ta rolling wayar Yahanasu ta fara k’ara. Tun kafin ta d’auki wayar dama ta fahimci shine dan ringing tone d’in da ta saka masa daban ne. Tana d’auka kuwa ya ce mata “ya k’araso, yana ma parlourn bak’i, Kausar ta shigo da shi.” Da sauri suka kammala, Yahanasu ta nufi parlourn bak’i, Munira kuma ta yi sama dan itama zafi take ji tana buk’atar ta d’an watsa ruwa.. Ya yaba kwalliyarta da girkin kuwa, sosai haka ya yi ta zuba santi. Sai da ya kammala tukunna ya zaro kud’i ya bata ya ce ga tukuicin girkin ta sannan ya sake zaro wani ya ce wannan kuma na masu aikin da suka d’an taya ta da y’an yanke-yanke ne . Tashi d’aya ta ce masa “Masu aiki wanke-wanke kawai suka yi, girkin kuma tare suka yi da sister d’inta Munira y’ar amaryar Daddy.’’ Ya san lokacin da Daddy ya k’ara aure amman basu tab’a had’uwa da Amaryar ba, balle y’arta sannan haka kurum tun da ta ce Munirat yanayinsa sai ya chanja. Haka de suka d’an tab’a hira, Sai da ta zo fita domin ta je ta kira masa Daddy dan yana so su yi maganar akan zai turo tukunna ya ce “ta turo mishi Munirat d’in, ya bata tukuicin ta sannan su gaisa’’ Da ‘’to’’ ta amsa tukunna ta sa kai ta fice. Har Yahanasu ta k’arasa d’akin Munira d’in tana d’an jin ba dad’i musamman da ta tarar da Munirat d’in ta yi wanka ta shirya… fuskarta babu kwalliya amma yarintarta da kyawunta sun fito matuk’a, dan haka atake sai ta ji d’an guntun kishi yana taso mata, amma kawai sai ta saka kyakkyawan zato a kyakkyawar zuciyarta ta tura masa Munirat d’in ita kuma ta wuce wajen Daddy domin ta sanar masa da sak’on Senator Bashir d’in. Tana fita itama Munira ta d’auki hijabinta ta zura ta nufi k’asa d’akin bak’in, ba dan ranta yana so ba. A hankali ta k’arasa bakin glass door d’in ta yi knocking tukunna ta shiga kanta a k’asa da sallama ‘’Ashe rai kanga rai’’ Muryarsa ta daki dodon kunnuwanta. Da sauri ta d’ago, ai kuwa suna yin ido biyu ta juya da sauri zata fita. Amman sai aka yi rashin sa’a ya riga ta zagayawa ya tare hanyar, dama tun da ya ga ta shigo ya mik’e daga wajen zaman shi ya Isa kusa da ita. Da sauri ya ce ‘’Haba Munira, after long time no see (bayan lokaci mai tsayi ba a haɗu ba) shine kuma za ki yi min haka kamar kin ga wani Aljani? Kin sa yadda na dinga neman ki kuwa?‘’ Already Munira har ta fara kuka, dan haka ta d’ago a gigice ta ce ’’Dan girman Allah ka rufa mun asiri, mamana zata iya ganin ka, a gidan nan take aure mijinta kuma shine Mahaifin Adda Yahanasu wadda za ka aure’’ Cikin katseta ya ce ‘’Munirat ai yanzu maganar aure kuma ta tashi tsakanina da Yahanasu sai dai a yi maganar auren mu ni da ke,dan ni ke zan aura yanzu kam.’’ ‘’Cin fuskar da zaka yi min kenan ??’’ su ka ji muryar Daddy a kansu. Wani irin kuka Munirat ta fashe da shi, daman abunda take jin tsoro kenan.. Yahanasu ta riga Daddy k’arasawa bakin parlourn, yadda ya ga tana hawaye ya san ba k’aramin abu ta ji ba tunda gashi shima iyakar maganganun senator na karshe ya ji amma gaba d’aya hankalinsa har ya tashi. Idonshi a kan senator ya k’arasa cikin parlourn, ba tare da ya kalli Munirat ba cikin fushi ya ce ‘’bamu guri’’ Da sauri ta juya ta fita har da tuntub’e. A bakin k’ofar suka yi karo da Yahansu tana hawaye, tana ganin ta ta juya da sauri ta nufi main parlour yayinda Munirat d’in ta bi ta da gudu, sai da suka kusa shiga parlourn tukunna ta samu nasarar cafko Hannun Yahanasun tana kuka ta shiga bata hak’uri sannan ta shiga ƙoƙarin fahimtar da ita ‘wallahi bata da niyyar cin amanarta, kuma ko Maza sun k’are bata ga dalilin da zai sanya ta saurari senator Bashir ba ma ballantana a zo ga batun aure’’ Wani kalar murmushin takaici Yahanasu ta yi kafin ta ce ’’kar ki damu, sam ba laifin ki bane ba Munirat, Idan ba ki sani ba yau ina so ki sani ‘wannan shine aure na 8 da aka so a kulla min yana warwarewa’! sam ban ji haushin ki dan ya ce ke yake so ba, kawai dai ina kuka ne sabo da…..” Salatin da Kausar ta rafka ne ya katse su, tashi d’aya ta figo Hannun Munirat sai da ta kai ta tsakiyar parlourn tukunna ta ce ‘’oya oya! 20 minutes kawai zan iya baki! Ki tartare garbage d’in (sharar) tsummokaranki ki bar gidan nan tun kafin in yi miki abun da za ki yi regretting (da na sanin) haihuwar ki da aka yi a duniya’’ Cikin tsananin b’acin rai takaici da kuma tausayin Yahanasu waenda suka had’e waje d’aya suka tunzura Munirat ta kalli Kausar da idanuwanta da suka jik’e da hawaye ta ce ‘’Ai ba ke kika kawo ni gidan ba, ballantana ki ce za ki koreni’’ Kamar jira Kausar d’in take yi tashi d’aya ta d’aga Hannu ta d’auke Munirat da mari!!! dai-dai nan Mommy Ummi da su Yasira suka faara firfitowa sakamokon hayaniyar da su ke ji sama-sama tana d’an k’ara yawa. Kallon ƙasƙanci da tsana Kausar ta yi mata kafin ta matso daff da ita ta ce ‘’Ko Yasira kin tab’a jin ta gaya mini magana anyhow a cikin gidan nan?’’ Da sauri Ummi ta k’araso ta ce ‘’Kausar, mai ya had’aki da k’anwar taki haka?’’ Cikin rashin kunya da tantiranci ta kalli Ummi sama da k’asa ta watsar sannan ta juya ga Mommy wadda ta k’araso garesu yanzun ta ce ‘’Mommy, senator ya ce ya fasa auren Yahanasu, Munirat zai aura!!! All thanks to abun da ta zuba masa a cikin abinci ya ci yau’’ Kusan duk a tare Ya‘isha, Yasira, Yusra da Yasmeen su ka ce ‘’watt!’’ Suna zaro ido ‘’Dama tun da na ga tanata faman kai kawo a kitchen da sunan tayata girki wallahi na san za a rina!!! Idan ba haka ba tayaya tashi d’aya zai ce wani ita yake so? Kaff y’an Matan gidan nan bai ce yana son kowa ba, sai ita’’ Cewar Kausar. ‘’Ya Isa haka Kausar’’ Ummi ta fad’a cikin d’an tsare gida ‘’Ke Saddik’a bai Isa ba!!! ko kowa ba zai yi magana ba ni zan yi magana kuma sai in da k’arfina ya k’are wallahi, sai kun warware abun da kuka yi kafin ta bar gidan nan, dan ba za mu iya ci gaba da ganin Yahanasu a wannan situation d’in ba’’. Kausar ta ce tana kallon cikin Idanun Ummi… Da sauri Yasira ta matso ta ce ‘’Tabbas nima zan yi magana, kuma bayaga haka ma yau in ta yi mata aka yi shiru gobe d’aya a cikin mu zata sake yi wa dan haka dole a d’auki mataki’’ Kamar yadda Kausar da Yasira suka ce ‘sai Munira ta bar gidan After ta warware asirin da ta yi wa senator yau ba sai gobe ba’ haka ma su Ya’isha da Yasmeen da su Yusra suka yi wa Ummi da Munirat chaa!! A ka! chin kashi Kala-kala babu kalar wanda ba su yi musu ba a wannan ranar… Ganin rashin kunyar tasu ta yi yawa ne yasanya Ummi ta kalli Mommy da Baabaa Larai ta ce ‘’Yanzu sai na ce ku hana su tukunna za ku yi magana??’’ Dai-dai nan Daddy ya shigo cikin parlourn ransa a b’ace da alamun ya sallami Senator ya fita ta k’ofar baya sannan daga gani basu k’ark’are k’alau ba.. A hankali Mommy ta ce ‘’Saddik’a, situation d’in nan is out of my hand(al’amarin ne ya fi ƙarfina), Yaran nan sun fi ku gaskiya… Yahanasu has sufferd a lot (Yahanasu ta sha wahala sosai) a kan irin wannan issue d’in. a ko da yaushe idan irin hakan ta faru mu kan ji inama ace munada ikon gyarawa, yanzu kuwa muna da iko kinga kuwa ai bamu da abun yi wanda ya wuce mu gyara d’in ko?. Idan ba ki duba komai ba to ina so ki duba maraicin Yahanasu dan Allah ki yi wa Munirat magana, a samu a daidaita komai, wallahi Yarinyar nan tausayi ta ke bani, ba zan iya ci gana da ganinta cikin wannan pain ɗin ba.” Wani sanyi Daddy ya ji a zuciyarsa, in akwai abunda zai iya rantsuwa akai to shine ‘tsaftatacciyar zallar ƙaunar da Mommy take yi wa Yahanasu!..’ dukda ta kasance y’ar kishiyarta kishiyar da ya fifita nesa ba kusa ba a sama da ita amma sam Mommy bata kishi ko jin takaicin Yahanasu. Cikin kaiwa iya wuya Ummi ta ce ‘’Haba Mommy.. Ita kuma Munirat d’in ba marainiyar bace?. kamar yadda Yahanasu ta ke marainiya haka Munirat itama, Hasali ma maraicin Munirat ya ma fi na Yahanasu tunda ita uba ta rasa’’. Cikin tsananin fushi Daddy ya ce Saddik’a………. …….. Sai da Yashjub ya yi sallah, ya yi wanka ya d’an huta tukunna ya d’au makulli ya nufi gidan da Yasir yake. Shi Yasir a tunaninsa ya b’oyewa kowa ne bai san tun lokacin da ya saka Ƙafa ya bar gidan idanun Yashjub yake a kansa ba.. da farko Abuja ya wuce sai last week tukunna ya dawo shi da tawagar y’an Mata da Abokansa suka tare a guest house d’insu d’aya daga cikin Abokanayen nasa su ke cin karen su babu babbaka. Wallahi,ba daban yana jin tausayin Mommy da halin da take ciki kwana biyu ba sannan shi kan shi yana jin Yasir d’in a ransa tunda duk lalacewa dai d’an uwansa ne shi ɗin ciki d’aya suka fito, to da tuni ya turawa su Yasir y’an Hisbah!!! Kuma ya cikawa y’an Hisbahn aljihu ya had’asu da manyan sojoji sun nad’e kaff d’in su ta yadda ba uban wanda ya Isa ya amsosu…. .. Yana zuwa bakin gate d’in tun kafin ya gama mik’a hancin motarsa ga gate d’in wani mutum k’ak’k’arfa sanye da gajeran wando da vest ya taho daga majalisar chan gefe da gudu yana cewa ‘’kai! Kaii!! Kaii!!’’ Sai da ya zo Jikin glass d’in motar ta dai-dai inda yake ya d’an buga tukunna Yashjub d’in ya ma lura da shi. Glass d’in motar tasa bullet proof ne sannan hankalinsa ya tafi ga lissafin ta yadda zai shiga gidan saboda ya san Yasir da shegen wayo da taka tsantsan ba zai tab’a zama babu security ba.. Sai da ya gama k’arewa mutumin kallo tukunna ya zuge glass d’in motar tasa,ya zuba masa dogayen idanuwansa kawai ba tare da ya ce komai ba. Cikin girmamawa mutumin ya ce ‘’Oga ai masu gidan basa nan, sun yi tafiya,sannan ni ban ma sheda ka ba …’’ Dai-dai nan wasu samari guda biyu suka k’araso suka saka mutumin a tsakiya fuskarsu babu alamar wasa. Sai da Yashjub ya d’an lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna ya d’an matso mutumin yana kallon cikin idonsa ya ce ‘’Ni yayan Yassir ne, na san ka san shi.. Yasir wanda ke a cikin wannan gidan yanzu haka’’ ya yi maganar yana nuni da gidan kafin ya d’aura da cewa ‘’Ban zo ba sai da aka tabbatar min da yana nan yanzu haka. Ka bud’e min ko in kira maka sojoji da y’an Hisbah, dan in baka barni na shiga ba hankalina ba zai kwanta ba sai na tabbatar na yi maka d’aurin goro. Amman in ka barni na shiga zan baka kud’i yanzu ka kama gaban ka dan kar ma su hukuntaka kuma zan hana Yasir nemo ka ya hukuntaka shi kuma Yasir na san zai yi maka tsakani da Abokansa. Shiruu Mutumin ya yi yana kallon Yashjub…. Suturar jikinsa, motarsa da kuma yanayinsa kad’ai sun isa su sanya a fahimci tabbas kud’i sun zauna sannan ya jik’u a naira, yana lura da yadda Abokan Yasir d’in suke yi masa fadanci saboda duk ya fi su kud’i to Ina kuma ga yayansa,kar ya je garin gadin y’an tsaki ya janyowa kan sa fad’a da giwa.. ‘’Ina da abun yi ka tsaida ni’’. Yashjub ya fad’a yana d’an kallon tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar Hannunsa. Sai da mutumin ya kalli Mazan dake a gefe da gefen sa su ka yi masa sign da ido tukunna ya kalli Yashjub ya d’an jinjina kansa alamun amincewa. ‘’Hmmm’’kawai Yashjub ya ce yana mai d’an girgiza kansa daga nan ya d’auko bandir biyu na kud’i ya mik’a masa. Wani kalar murmushi Mutumin ya yi shi da samarin biyu daga nan ya sa Hannu ya amshe ya yi godiya.. A tare su duka ukun suka shiga gidan ta k’aramar k’ofa suka wangale masa gate ya shige su kuma suka d’auki ghana most go d’insu dake a d’akin mai gadi suka yi gaba abun su.. Gida ne mai kyau flat babba sosai dan compound d’in zai d’auki motoci kamar 15 haka,sai pool da pool house d’in shi a ta baya. Flat din kuma daga gani d’akunan ba zasu wuce 5 ba da maybe 2 two parlours da kitchen haka. Yana yin parking ba tare da b’ata lokaci ba ya bud’e motar ya d’au wayarsa ya fito ya nufi main door d’in gidan. Tsaki yayi ganin ta a rufe dan haka ya d’an danna bell ya koma gefe ya tsaya. Budurwar da take parlourn zaune tana kallo ce ta mik’e a ranta tana cewa’’i wonder who that could be (Waye kuma ya zo mana?’’. Tana zuwa bakin k’ofar ta d’an tsaya ta lek’a… duk da ta y’ar b’ular k’ofar ta gan shi hakan bai hanata ganin tsananin kyawaun sa ba, jikinta da hannunta har rawa suke yi haka ta sa Hannu ta bud’e k’ofar cike da zumud’i. Tana bud’ewa ta d’an saita kanta kana ta d’an karkace tana wani irin shu’umin murmushi. “Innnalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ya ambata a ransa a zahiri kuma ya sake tamke fuska yana mai jin kansa yana tsananin sarawa, sanann yana da ya sanin zuwa gidan. Da kyar ya samu ya iya bangaje ta ya wuce ciki dan har ta nufo shi tana shirin yin magana. .. Ransa a mugun b’ace haka ya nufi cikin parlourn, ya nemi guri ya zauna yana mamakin yadda take yawo a cikin gidan daga ita sai wannan guntuwa sannan shara sharar bathrobe d’in wadda ko pant d’inta bata gama rufewa ba sannan in dai idanuwansa ba gizo suka yi masa ba to tabbas ko bra babu a jikinta. Sam ba ta damu da yadda ya yi mata da farko ba dan ta riga ta gama rikicewa da ganin sa. Haka nan ta wuce kitchen ta had’o masa juice da cake. ta fito tana rangwad’a ta zo gaban sa ta ajjiye sanann ta koma gefen sa ta zauna daff da shi. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘’Ina Yasir??’’ Cikin sake matsowa kusa da shi ta ce ‘’Ooh,he’s a little busy at the moment (akwai aikin da ya ke yi yanzu) sai dai ka d’an jira shi kad’an, but don’t worry I’ll keep you company(amma kar ka damu zan tayaka cinye lokacin)’’. Ta fad’i haka tana mai d’aura hannunta akan cinyarsa ta fara shafawa tana masa tafiyar tsutsa tana yin sama da kad’an da kad’an. Tsabar yadda ransa ya b’aci bai ma san ta ya aka yi ya mik’e tsaye ya zare belt d’in jikinsa ba dan tsintar kan sa kawai yayi yana kimarta da belt tana ihun ceton rai… Kafin su Yasir su fito har ya farfasa mata jiki, sai da suka yi da gaske tukunna Yasir Abokinsa da d’ayar Yarinyar da suka fito tare daga ɗaki ɗaya su uku! suka iya kwatar budurwar nan a hannun Yashjub wadda zuwa lokacin har ta suma. Cikin tsananin tashin hankali Yashjub ya ke yi wa Yassir wani irin kallo….daga shi sai boxers haka shima Abokin nasa sai d’ayar Yarinyar ita kuma da towel. Wata mahaukaciyar shak’a ya kaiwa wuyan Yassir cikin hargagi da hargowa ya ce ‘’Dan ubanka gay ka zama?’’ Su kam wannan budurwa da saurayi sun ga tashin hankali, dan a still sai da suka kuma yin da gaske tukunna suka iya kwatar wuyan Yassir daga hannun Yashjub. Dakyar Yasir ya iya cewa ‘’A’a, Wallahi ba abunda kake tunani bane ba, ka tsaya zan yi maka bayani.’’ Da kyar Yashjub ya iya danne zuciyar da take tunzura sa… da yatsarsa manuniya ya nunawa Yasir k’ofa, kawai…… Duk hauka,iskanci da rashin kunyar Yassir yana tsananin jin tsoron Yashjub a irin wannan yanayin dan yadda ya tunzura d’in nan abun ba sauk’i ko last month da yayi irin haka a gida hatta Daddy sai da yayi shakkar sa da kyar da mugun kyar aka ci sa a Yahanasu ta samu ta iya lallab’a sa, amma duk da haka ya fi wata d’aya a kumbure. Da kyar yana jin maganar tana harhad’e masa yana ganin dishi-dishi ya sake cewa Yasir ɗin ‘’Za ka wuce ko sai na baka mamaki?’’ A hankali Yassir yana d’an d’ari-d’ari ya ce ‘’Na san motarka babu tint, ka yi hak’uri in shiga in d’auki kayana, dan Allah’’ ‘’In tsaya in jira ka kenan??’’ Yayi masa tanbayar yana sake tunkaro shi da idanuwansa waenda suka yi jajawur abun tsoro. Da gudu wannan budurwar wadda gaba d’aya ta gama tsorata ta wuce d’akin ta janyo akwatin Yasir ta fito da shi. Tana fitowa Yashjub kuma ya juya ya fita dan ya fahimci in dai ya sake damƙar Yassir tou tabbas zai iya kai shi lahira, cikin fushi ya nufi gate d’in gidan ya na jin kamar ya fincike zuciyarsa ya jefar tsabar tafarfasa da azabar da take yi.. Da Sauri Yassir ya bud’e akwatin nasa ya zaro jallabiya ya bi bayan Yashjub da mugun gudu yana zuwa ya bud’e motar dan Yashjub har ya kunna yana shirin bata wuta, dan ma ya tsaya wangale gate ne shiyasa yaci sa’ar samun shi amma da tuni ya tafi. Ko rufe motar Yassir bai yi ba Yashjub ya figee ta suka fice da guduu da kyar ya iya rufe motar ya zura jallabiyar shi dan mutane har sun d’an fara kallon su duk inda suka bi……… Hakanan suka k’arasa gidan da ikon Allah saboda tsananin gudun da Yashjub ya tsula Allah ne kawai ya kaisu gidan lafiya. Tun kafin su k’arasa main door su ke jiyo hayaniya, dai-dai suna shiga suka ga Daddy ya dakawa Ummi wata mahaukaciyar tsawa sannan ya nufe ta gadon gadan kamar zai rufeta da duka…… .. Cikin fushi bayan ya isa gareta ya ce ‘’Wacce irin Mace ce ke? Eh? Ashe son kan naki har ya kai haka?’’ ‘’Yarinya ta yi laifi k’iri-k’iri amma kina k’ok’arin b’oyewa?’’ Sai da ya kalle su tukunna ya juya ga Ummi ya ce ‘’To laifi mana, in ba haka ba lokacin da ta je ta ji ya fara yi mata maganar banza ai kamata yayi ta bar gurin ko? A matsayin shi na wanda yayarta za ta aura’’ Yadda yake mata ihu da hargagi da kuma tuhumar Munirat akan abunda bata tab’a tunanin zai yadda ta aikata bane ya sanya wasu zafafan hawaye zubo mata cikin d’acin zuciya ta ce ’’Daddy tuhumar ta kai ma kakeyi? wanne kalar asiri ne zai juyar da lissafin Mutum mai kimanin shekarunka a cikin lokaci k’ank’ani haka?’’ Cikin b’acin rai da d’acin zuciya ta share hawayenta kafin ta d’aura da cewa ‘’Maybe sai dai ko irin wanda akayi maka aka juyar da kanka daga gare ni ne kwana biyu’’. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *22* ‘’Babu irin wannan a tsarin mu, ke kan ki kin san inda ace muna irin haka Wallahi da baki Isa shigowa ki taho har da agola cikin gidan nan ba. Sannan duk abun da za ki yi, ya tsaya a iyaka kanmu amma kar ki kuskura ki sako Mommy’’ Cewar Ya’isha. Cikin jaddada mata Kausar ta ce ‘’Tabbas, dan in dai kika tab’o Mommy to kuwa muma ba za mu ji shakkar rama mata ta ko wacce hanya ba… yanzu dai a komawa maganar da ake yi tun farko dan naga alamar so kike yi a rufe lamarin Munira.” Da mamaki Ummi take kallon Daddy wanda sam ya kasa tsawatarwa ya’yan nasa. Su kansu su Yashjub sun d’an ji mamakin sa. Yusra ce ta k’arasa ta juyo da Munirat wadda take ta faman kuka ta ce ‘’Munirat tun muna shaidar juna mu da ke….’’ Cikin fushi Munirat d’in ta fincike hannunta sanann ta katse ta ta hanyar cewa ‘’Kar mu shedi juna daga yau dan Allah ki yi duk abunda kika ga dama, ki illatani ta yadda ba ke kad’ai ba kowa ma ba zai iya sheda ni ba’’ “Munirat wai ya ana k’ok’arin gyara abu kina turjewa ne? kin fi kowa Baki da Zuciya ne? we are all the same (duk ɗinmu ɗaya ne) anan, so kar ki yi tunanin wai ko ana k’ok’arin nuna miki bambanci ne, ko waye a cikin sisters d’ina yayi irin abun da kikayi dole irin haka za a yi mata!!!! We all love Yahanasu (duk ɗinmu muna son Yahanasu) dan haka ya kamata mu tsaya mu fahimci juna a samu a gyara abun da kike son ki b’ata’’ Yasira ta ce tana mai k’arasowa inda Munirat d’in su ke tsaye ita da Yusra. Ta bud’e Baki za ta yi magana kenan cikin d’an d’aga murya suka ji Yahanasu tace’’Ya isa haka’’ sanann ta k’arasa inda Yasirar ta ke ta saka Hannu ta juyo da ita tukunna ta fara magana “Da ni da ke da kowa duk an san daga ke har Kausar d’in ba ku wani damu da ni ba! Infact har su Ya’ishan suma duk ba damuwa suka yi da ni ba! Dan haka na rok’e ku da girman Allah kar ku yi amfani da ni wajen baiyyana abun da yake a ranku game da su Ummi… Alh Bashir da farko ya ce yana so na yanzu kuma ya ce ya fasa Munirat yake so!!! Ni har ga Allah ban ga wani abun tashin hankali anan ba… iyaka kawai mu yi musu addu’ar Allah ya basu zaman lafiya shikenan magana ta k’are!!! Dan Allah kar wanda na sake ji yayi amfani da bak’in jini na da bad luck d’ina wajen nuna real face d’in shi!!… ku bar ni in ji da abun da yake damu na’’ Ta fad’i hakan wani irin kuka yana sub’uce mata da mugun k’arfi. A hankali Yashjub wanda ya k’araso yanzun ya sa Hannu ya juyar da ita ya rungume ta yana jin wani tsananin b’acin rai da takaicin senator Bashir suna taso masa. Cikin kuka ta ce ‘’Yash dan Allah ka ce su daina maganar nan, su bar shi ya auri Munirat d’in su dena maganar bana so, suna rubbing salt a wounds d’ina (suna fama min gyambon da ke a zuciyata) ne, sanann dan Allah kar wanda ya sake ce min in yi aure, dan Allah dan Annabi’’ Wani kalar kuka abun tausayi take yi wanda yasa gaba d’aya jikin Daddy wanda ya harzuk’a ya fusata ya yi sanyi haka ma Mommy da Ummi duk sai jikin su ya yi sanyi. Munirat kuwa ji take kamar ta je ta chakawa senator wuk’a! Yahanasu is the most nice calm and friendly person da zata ce ta tab’a had’uwa da a rayuwarta, gashi jinin su ya had’u matuka ….. A hankali Yashjub ya ja ta tana a rungume a jikinsa suka wuce d’akinta. Suna wucewa Ummi ta ja hannun Munirat suka wuce sama suma. Gaba d’aya kuma kallo sai ya koma kan Yassir wanda tun ɗazu da suka shigo ya gagara janye manyan idanuwansa daga kan Munirat. Ganin duk sun tsura mishi ido ne ya sanya ya d’an sunkuyar da Kai ya fara sosa k’eya kafin da kyar yace’’Daddy I’m sorry for..” Kafin ma ya rufe Bakinsa tuni Daddy ya zo ya wuce shi ya fice daga gidan gaba d’aya dan a wuya yake dama Ummi, bata san a cike yake da itaba kwana biyun nan dama, haka kurum yake jin takaicin ta! yanzu kuma ji abun da ta yi, ta wani bud’e Baki tana cewa ai itama Munirat marainiya ce sannan har tana da Bakin cewa wani an juya mishi tunani akanta,duk irin yadda yake k’ok’arin bata kulawa amma sam ita bata gani how dare she!!!! tunda yake da Mommy bata tab’a yi masa irin haka a gaban Yara ba amma ita ta iya bud’e Baki yana fad’a tana fad’a…. y’ar shi tana cikin wannan halin kalli yadda Mommy take tausaya mata amma ita tata y’ar kawai ta sani. Yahanasu batayi deserving haka ba y’arshi mai hankali nutsuwa da sanin ya kamata, cikin fushi a fili ya ce ‘’Allah ya tsinewa Alhaji Bashir’’ …… Daddy yana fita Mommy ta k’arasa inda Yassir yake tsaye ta hau duddubashi kamar wani k’aramin Yaro, idanuwanta suna kaiwa kan wuyansa wanda har zuwa wannan lokacin yake nan jajir ta rikice ta hau tambayar sa abun da ya same shi. ‘’A hankali ya ce ‘’Mommy I’m fine, favorite son d’inki da kika tura ne ya je ya jiwa Abokai na ciwo ya sumar da d’aya sannan nima ya shak’eni da kyar aka kwace ni daga hannunsa, da tuni yau sai dai ki ga gawa ta.” Kamar zai kurma ihu ya d’aura da cewa “da kika san yana da anger issue da sai ku taho tare ke da shi ta yadda ko haukar tasa ta motsa za ki iya shiga tsakanin mu, na san in kina nan maybe ya d’an nutsu’’. Cikin rashin jin dad’i Mommy ta ce “Subahanallah, wallahi Yassir ban san zai yi haka ba… I was so worried ne (na damu ne sosai) shiyasa na barshi ya je. ga shi naga Daddynku yana neman mantawa da kai ma gaba d’aya tun da yayi aure komai ya lalace bai damu da ni ba ma kai kam ko zancen ka baya yi,wannan Matar da ka gani auntyn ku ce ….’’ Cikin katse ta ya ce ‘’Yeah na fahimta daga shigowata da kuma scene d’in da na yi witnessing (abunda na gani)” A hankali ya kama lips d’inshi na k’asa ya d’an ciza kafin ya d’ago idanuwansa ya sauk’e a kan k’annen nasa waenda sukayi cirko-cirko. A hankali Baabaa Larai ta k’araso ta ce ‘’Ka ji maganar mahaifiyarka ka ji d’an albarka, duk abun da Babba ya hango Yaro ko ya hau kan dala ba zai gani ba! kar ka sake yunk’urin barin gidan nan. Yanzu lokaci ne da ya kamata ace kun had’a kai da mahaifinku kun shiga jikin shi sosai, dan duk wanda ya yi gangancin yin nesa da shi to kuwa kanshi yayiwa.’’ Tana gama fad’in haka ta kama hanya ta wuce d’akin Yahanasu. A hankali su Yadira Yusra da Yasmeen suka matso kusa da su suka ce ‘’Welcome home Ya Yassir(Sannu da zuwa Ya Yassir)’’ Sannan Yasmeen ta ce ‘’we missed u(mun yi kewarka)’’ tana d’an murmushi. Kallon su kawai ya yi, daga nan ya maida duban sa ga Kausar wadda ta d’an tsura masa ido tana mamakin ramar da ta ga yayi. Yana kallo ta ya ce ‘’Mommy bara in je in watsa ruwa as usual nobody cares about me (kamar ko yaushe babu wanda ya damu da ni) na tafi kuma na dawo da kaina ba tare da an yi min abunda na buk’ata ba,a tunani na Inada loved one’s waenda za su damu da damuwata… I guess i was wrong(inaga tunanin nawa ya bani ba dai-dai ba kenan).’’ A hankali ya d’auke dubansa daga gareta ya maida kansa k’asa ya fesar da wani numfashi Sannan ya ce ‘’Bara in je in d’an watsa ruwa.’’ Tun kafin ya juya Yashjub wanda ya fito yanzu daga d’akin Yahanasu ya ce ‘’Yasir, wait!.’’ Lumshe idanuwansa ya yi ya d’an bud’e tukunna ya ce ‘’Wanka zan je in yi” ya fad’i hakan yana mai kallon cikin idanunsa. Ba tare da Yashjub d’in ya sake kallon sa ba ya juya ga Mommy ya ce ‘’A gyara masa d’aki a sama kusa da side d’inki.’’ Gaba d’ayan su a tare suka ce ‘’Whattt!!!!’’ Cikin b’acin rai Yassir ya ce ‘’Look here,Man!( ka ga Mallan kalli nan) tura ta kai bango fa, haba mana wanne cin fuskar ya rage ba ka yi min ba??? Ka je ka ce in biyo ka na biyo ka bayan b’arnar da ka yi min sannan yanzu kuma za ka saka ni a tsakiyar Mata? To gaskiya baka isa b…..’’ Kallon da Yashjub yake yi masa ne ya sanya ya d’auke Kai ya kalli mommy Ya ce ‘‘Mommy, ki yi min tsakani da shi fa, idan kuma ba hakaba to wallahi za mu kwashi y’an kallo.’’ A hankali Yashjub ya matsa daff da shi ya kamo kafad’unsa ya juyo da shi sannan ya ce ‘’Yassir, kar ka ga wai muna a gida kuma a gaban su Mommy ka ce za ka yi min shirme… Raina already a b’ace yake kar ka sake provoking d’ina(fusata ni). Ka wuce masu aiki za su gyara maka d’aki a chan sama kusa da side d’in Mommy ta yanda za ta fi saka maka ido saboda ni fita nake yi kuma yanzu zan dinga kai dare sosai, sannan ina so in yi tafiya dan haka ba zan iya kula da kai ba! Tunda ka nuna har yanzu ba ka yi hankali ba, dan haka dole za ka zauna a inda za’a saka maka ido a kuma kula da kai. Anjima kuma za mu zauna da ni da kai da Mommy da Daddy a yi magana akan abun da na gani a gidan da kake cewa na yi maka b’arna. for the last time Yassir, ka wuce sama’’. Iya k’uluwa Yassir ya k’ule, ya san tsaf Yashjub zai iya sake fad’in wata maganar da zata sanya Kausar ta d’an fahimci wani abun tunda gashi har ya fara dan haka kawai ya yanke shawarar wucewa sama amma tabbas zuwa wannan lokacin yayi girman da zai gyarawa Yashjub zama, da sake!!! Dan gaskiya ba zai yiu a dinga juyashi da girman sa ba. A hankali Mommy wadda ta fara firgita da yanayin Yashjub ta kamo Hannun Yassir ta ce ‘’Son!mu je,mu je saman. anjima ba ya ce za mu zauna ba! sai mu zauna d’in, amma for now mu je ka ji ko’’. Ta fad’i haka tana k’ok’arin janye Yassir d’in daga ruk’on da Yashjub ya yi wa kafad’unsa.. Ai kuwa da kyar sai da ta d’an tab’a Yashjub d’in ta ce mishi ‘’Cika shi za mu wuce’’ Tukunna Yashjub ya samu ya janye idanuwansa waenda su ka yi jazir daga kan Yassir ya cika sa da kyar, daga haka kuma ya juya ya fice kamar zai tashi sama. A hankali Kausar ta ja numfashi ta bi bayansa da kallo har ya wuce tukunna ta lumshe idanuwanta tana ji a ranta’tabbas bata da hutu bata da sukuni bata da nutsuwa muddin bata samu Yashjub ba!!! yanzu ne wasan zai fara dan ko ta halin k’ak’a ne wallahi sai ta mallake shi, bata ga dalilin da zai sanya ta rasa shi ba.’. Su Mommy suna wucewa sama ita ma ta bi bayan su haka ma su Yadira. Yasira kuma ta wuce d’akin Yahanasu… bata damu da cewar ‘shirin aurenta ya tarwatse a karo na takwas ba’ dole ta kora mata warning, Wallahi. .. Wani irin karkarwa jikin Yashjub ya ke yi tsabar takaici! Abun zai yi wani irin banbarakwai idan ya je ya samu senator Bashir da fad’a ko da rarrashi dan zai ga kamar yana neman kai da y’ar uwarsa ne….. Ya jima rabon da ya shiga b’acin rai irin wannan a rayuwarsa, baya so ya dinga jin maɗaukakin ɓacin rai irin haka amma yau senator Bashir da Yassir sun kai sa bango!! Da wannan tunanin ya k’arasa part d’in nasa yana zuwa ya fad’a bathroom ya sakarwa kan shi ruwa mai sanyi… Sai da ya ji ya fara atishawa tukunna ya d’auro alwalla ya fito ya chanja kaya zuwa jallabiya… ya na shiriin yanata faman tsaki dan yana fitowa ya ji ana idar da sallah a masallaci. A nan d’akin nasa ya yi sallarsa ya idar ya zauna zaman addu’a. Yana zaune sai ga Kausar ta yi knocking, ta shigo da zumbulelen hijabinta. ta zo ta zauna kusa da shi wai Mommy ta ce tunda course d’aya suka karanta ta zo ya k’ara duba mata project d’in ta gobe time zai cika kar a sake dawo da ita wannan shekarar ma,sannan ya manta bai bata wayoyin nata ba. A yadda ya ke jin kansa tabbas inya ce zai kula Kausar tou zai iya ji mata rauni, wacce irin mahaukaciyar Yarinya ce wannan mai shegen tsaurin ido haka. Mik’ewa kawai yayi ba tare da ya ko kalle ta ba ya koma kan sofa ya nemi guri ya zauna. Duk da tsoron da take ji hakan bai hana ta matsawa dai-dai wajen k’afafunsa ta zauna ba, sannan cikin wata kalar murya mai tsananin had’ari ta ce ‘’Ya Yash dan Allah’’ Gaba d’aya tashi d’aya sai ya ji tsigar jikinsa yayi wani iri… Kallon ta ya yi da rinannaun idanunsa cikin b’acin rai ya ce ’’Tashi ki fita, in kuma tsaurin ido zaki gwada Bismillah ki k’ara second goma a nan za ki ga ikon Allah’’ ya riga ya san k’arya take yi ba Mommy ce ta turo ta ba. A hankali ta ce ’’ka yi hak’uri’’ daga haka ta mik’e ta fita tana jin zuciyarta k’all dan ta san ko dai hijabin ko kuma muryar ta da salon ta tabbas akwai abun da ya ba ta ko da k’ank’anuwar nasara ne akan shi yau!!. ‘’Slowly but surely (Sannu sannu bata hana zuwa)’’ Ta furta hakan tana murmushi a lokacin da ta fito daga b’angaren nasu. A ranta tace ‘’kwalliya ta biya kud’in sabulu, next level kam zan girgizaka!! ai da na d’auka kai d’in dutse ne.’’ .. Shakka babu idan kausar bata fita a hanyar shi ba tou zai bar gidan nan, baya son tab’a lafiyarta kwata kwata amma kullum sake pushing nashi (tunzurashi zuwa) bango take yi.. Yarinya ba jan aji ba nutsuwa ba sanin darajar kai kamar ba tarbiyyar Hausawa ba!!!. Kalli yadda ya ke korarta kullum amma sam ba ta damu ba!! shak’iyyiyar Yarinya ji irin muryar da ta yi amfani da ita… Yash ke aiyyana hakan a ranshi.. A fili kuma sai ya yi tsaki ya ce ‘’Allah wadaran naka ya lalace’’.. A hankali a hankali tunanin Manubiya ya fad’o mishi…. jingina ya yi da jikin gadon ya lumshe idanuwansa, nan muryarta da idanunta suka fara yi masa gizo, da kad’an da kad’an ya ke jin b’acin ran nasa yana sauk’a har ya samu ya d’an ji dama dama tukunna ya mik’e ya koma kan gadon ya kwanta ringigine yana mai kallon sama yana mamakin ta yadda tunanin ta yayi maganin anger d’insa a cikin lokaci k’ank’ani haka.. Kad’an-kad’an ya fara jin bacci dan haka ya jawo pillow ya d’aura a kan k’irjinsa ya d’an rungume a fili ya furta ‘’Alhamdulillah’’ saboda ya san in yayi baccin ya farka b’acin ran nasa zai ragu sosai da yardar Allah. Bai dad’e da lumshe idanuwan nasa ba kuwa bacci yayi awon gaba da shi…. Mafarki ya fara mai masifar dad’i da annashuwa…. ‘Ga shi ga Manubiya a zaune a cikin wani lambu mai cike tabb da korayen ciyawa, yana sanye da farar jallabiya yayin da ita kuma ke sanye cikin baƙar Abaya da niƙabi, iyaka idanuwanta kawai yake iya gani. Suna zaune suna fuskantar juna suna hira amma sam ba ya iya jin me suke cewa, sai da ya d’an nutsu tukunna ya ji yana cewa ‘’I just want to see your face get to know u(fuskanki kawai na ke ao in kalla sannan in san wacece ke) shikenan na san inshaaAllah zan samu nutsuwa, pls ki fad’a min komai game da ke da rayuwar ki sannan ki nuna mini fuskarki, ina so in san ki’’. Sai da ya sake nutsuwa tukunna ya ji ta ce “Ka kwantar da hankalin ka jibi inshaaAllah za ka ganni’’ Cikin katse ta ya ce ‘’Manubiya ba ki san ya nakeji a raina game da ke ba, ki nuna min fuskarki yanzu dan Allah. ɗazu raina a b’ace yake amma da na fara tunanin ki a take na ji fushin ya fara raguwa…. na san ina ganin fuskarki b’acin ran zai b’ace gaba d’aya’’. Ya k’arashe maganar tasa yana k’ok’arin sanya hannu da niyyar janye nik’abin nata. A hankali ta ce ‘’Na ce maka fa jibi za ka ganni..‘’ sai kuma ya ga ta d’an yi shiruuu kamar mai tunani ko sauraron wani abun kafin ta d’ago ta tsare shi da kyawawan idanuwanta tukunna ta ce ‘’Answer your phone (Ka amsa wayarka)’’. Da d’an mamaki ya ke kallon ta sai kuma ya yi murmushi yana shirin yi mata magana, ya farka daga baccin. Wani wawan tsaki ya ja dan ya manta rabon sa da yayi bacci da mafarki mai d’an karan dad’i irin wannan, da sauri ya lumshe idanuwan sa ya shiga addu’ar Allah yasa ya samu ya koma baccin ya cigaba da mafarkin kawai ya ji wayarsa ta fara k’ara… Shiruu kawai ya yi yana sauraron ringin tone d’in har ta katse. He just wish Ina ma ace itan ce, although mafarkin da yadda ta ce ya amsa wayar shi kuma ya farka a ka fara kiran sa is a little bit wired (ya ɗan yi abun al’ajabi) Amma Shi fa a halin yanzu a yadda yake ji ko da ace aljana ce to zai iya zama friend d’inta muddin za ta dinga ba sa wannan nutsuwa da kwanciyar hankalin da yake ji a ko da da yaushe in yana tunanin ta. Yana wannan lissafin Ya ji wani kiran ya sake shigowa Gudun kar ta sake tsinkewa ne yasanya shi ya d’an juya ya d’auki wayar da ta ke k’ara a cikin wayoyin da ya zube a gefen gadon tun farkon shigowar sa d’akin… business phone d’insa ne shiyasa bai yi mamakin ganin bak’uwar lamba ba. Ahankali ya ɗaga ya kara a kunnensa ya koma ya gyara kwanciyarsa ba tare da ya ce komai ba. Tashi d’aya ya ji gabansa yayi wani irin mahaukacin faɗuwa sakamokon jin muryarta da ya yi tana cewa ‘’Ke ya isa haka, ba ki ga dare yayi ba, mutum Babba da matarsa kin dame sa da kira haka ki bari gobe ma sake gwadaw……’’ Tsit kuma sai ya ji ta yi shiruu.. A hankali ya d’an runtse idanunsa yana jin k’irjinsa yana bugawa a ransa ya ce ’’is she really the one?(da gaske ita ɗin ce?) ta ya aka yi ta samu number na?,noo it can’t be (ba zai yiu ba)” tabbas yanzu ma gizo take yi masa har a waya ga kuma mafarkin da yayi Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Ya Allah na yi gamo da aljana amma wallahi bana son rabuwa da ita,Ya Allah ka sa ba muguwa wadda zata cutar da ni bace ba.’’.. Ya aiyyana hakan a ransa. Yana wannan addu’ar ya ji an ce ‘’Adda Manubiya an d’auka fa, ki yi magana mana.’’… A hankali ya lumshe idanuwansa ya rintse pillow d’in da ya d’aura akan k’irjinsa yana mai sake tabbatarwa da kanshi tabbas ita d’in ce……. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *23* Da kyar Manubiya ta samu ta tattaro gaba d’aya courage d’in ta (kwarin guiwarta) ta ce ‘’Assalama alaikom sir Good evening. Sir Najeeb ya ce zaka bani aikin da zan dinga reporting maka duk sati, he gave me your card and ask me to call you for more information(ya bani card ɗinka ya ce in kira ka za ka yi min cikakken bayani)…’’ Kitt!! Haka suka ji an katse kiran. Da sauri ta d’ago tana kallon su Jidda waenda suka zuba mata ido su ka yi mata k’urr, A hankali Muhsin ya sauk’e ajiyar zuciya ya koma ya zauna daga tsugunnon da ya yi domin lek’a wayar tukunna ya ce ‘’Adda kema kin kwafsa, ya za ki yi masa mix d’in Hausa da turanci..’’ Da sauri Jidda ta ce ‘’Eh! Nima ina tunanin Hausar da kika yi ce ta b’ata masa rai.’’ A hankali Manubiya ta ce ‘’Allah yasa ba Matar shi ce ta d’auka ba’’ Daga haka ta koma ta jingina da jikin bango.. A b’angaren Yashjub kuwa tunda Manubiya ta fara magana ya ji numfashinsa yana shirin d’aukewa, the fact that ‘tana yi masa magana referring to shi kaɗai’ ne ya sanya nishad’i da annashuwa suka mamayesa sannan ga zuciyarsa wadda ya ji tana shirin tarwatsewa, tsabar uban gudun da take yi. Ganin Yarinya k’arama tana shirin sumar da shi ta waya ne yasanya shi yanke shawarar ya kashe wayar idan ya nutsu ya yi calming down tukunna sai ya fahimci wanne irin aiki take magana akai dan kwata kwata kwakwalwarsa ta ƙi ta d’auki charji, kuma ya san in ya ce zai yi mata magana a haka to tabbas za’a samu matsala. A hankali ya runtse idanuwansa ya na maida numfashi kamar wani wanda ya yi y’ar tsere……. Ya fi mintina goma a haka sam ya kasa tab’uka komai…. yana nan kwance a hakan ya ji ana knocking k’ofar d’akin nasa….. Sai da aka yi sau wajen uku tukunna ya ce ’’come in’’. Ya riga ya san wacece shiyasa tana shigowa ya ce ’’Mommy kar ki damu fa, i’m fine’’. Murmushi ta yi kafin ta k’arasa bakin gadon ta nemi waje ta zauna sannan ta ce ’’in kai kana ganin ka yi girman da za ka b’oye min damuwar ka to ni har gobe ganin ka nake yi kamar yau na haifeka. yanzu tashi in zauna sai ka kwanta in yi maka massage a goshinka na san ciwon kan zai ragu ko?’’ Bud’e idanunsa yayi ya kalle ta na y’an sakanni kafin ya mik’e ya zauna a kan gadon sanann ya sake kallonta yace ‘’Mommy da gaske nake miki fa I’m okay now.’’ Sai da ta d’an k’ura masa idanu na y’an sakanni kafin ta ce ‘’How? ko aljannar da na ji kana maganarta kwanaki a d’akina ce ta kwantar maka da hankali?’’ Wani sassanyan murmushin da Yashjub ya saki a take sai da ya sanya Mommy a al’ajabi. Ba ta san lokacin da ta ce ‘’Akwai ta kenan da gaske, a ina take? talk to me(yi min maganar), ka fad’amin, kar ka b’oye mini komai’’ This time around (wannan karon) dariya Yashjub ya yi kafin ya juyo ya kalle ta sosai sannan ya ce ‘’Relax! Mommy… Idan lokacin sanin nata ya yi za ki santa amma ba yanzu ba, kuma na san tunani kike yi akan wai ko budurwata ce ko kuma ina son ta wanda sam abun ba haka yake ba, she’s just my friend (ƙawata ce kawai) ko kuma ince za ta zamto ƙawar tawa, soon(nan ba da jimawa ba)” Ya fad’i hakan yana komawa ya kwanta kamar yadda ta shigo ta same sa. Ganin da yayi kawai ta yi shiruu ta fad’a duniyar tunani ne ya sanya shi cewa “okay!bye. bara in d’an huta kafin in shigo anjima’’. A hankali ta ce ’’Byee’’ ba tare da ta motsa ba. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace ‘’Your mood?(na ga yanayinki ya sauya?)mai ya faru?’’ Ya yi mata tambayar yana kallon ta sannan ya sake mik’ewa ya zauna. D’an murmushi ta yi a hankali daganan ta ce ‘’Bye, sai mun had’u anjiman’’ Tana gama fad’in haka ta mik’e za ta fita, da sauri ya ce ‘’Yauwa’’ sai kuma ya mik’e ya k’arasa drawer da ya ajjiye wayoyi da atms d’in Kausar ya d’auko envelope d’in da ya saka komai nata a ciki ya kaiwa Mommyn ya ce ‘’ga shi”. Dukda hakan bai ga chanji a mood d’in nata ba(yanayin nata ba), dan kawai karb’a ta yi ba tare da ta kalle sa ba ta juya ta fita. Ya dad’e yana nazarin Mommy daga k’arshe ya yanke wa mood d’in nata (yanayin nata) hukuncin ‘wataƙila ta d’an ji zafin yadda ya ƙi tsayawa ta yi masa massage saboda wata friend wadda ya sani jiya-jiya already ta riga da ta kwantar masa da hankali.’ Daga haka ya janyo wayarsa ya turawa Manubiya message kafin ya danna kiran Najeeb… Yana d’auka kuwa ya kwashe da dariya. Shiruuuuu Yashjub ya yi yana sauraron shi sai da ya yi mai isar sa tukunna ya ce “ya aka yi ne?’’ ya yi masa tambayar still yana dariya k’asa-k’asa. ‘’Iyakar plan d’in naka da idear taka kenan? wanne aiki to zan bata?’’ Yashjub yayi masa tambayar kai a d’aure. Cikin dariya Najeeb ya ce ‘’Iyaka taimakon da zan iya yi maka kenan wallahi, tunda kaga ka zo mini da sharud’a, my hands are tied ta ko ina (ka ɗaure ni ta koina) shiyasa na barka ka yi figuring out komai da kanka, cikin sauk’i.’’ Ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin ya ce ‘’To ai ni aikin da zan bayar a dinga zuwa duk sati sau d’aya ne ban san shi ba’’ Yadda Najeeb ya yi wa Abbakar tak’aitaccen bayani akan aikin haka ya yi wa Yashjub, daganan ya d’aura da cewa “chatting nake yi da k’anwarka ka kira ni, kar ka ja min in je garin gyara maka ni kuma madam ta yi fushi, sai anjima.” Yashjub yana shirin yin magana ya ji Najeeb ya katse kiran… shiruu ya yi yana tunani kafin kuma ya fara wani kalar murmushin da ya dad’e bai yi ba…. …. Su Manubiya har sun cire rai suna shirin maidawa Siyama wayarta kawai suka ji message ya shigo.. Da farko kamar ba za su duba ba dan basu sani ba ko na siyaman ne sai kuma suka ga kamar number da suka kira ce dan haka suka duba. Suna bud’ewa suka ga an turo Time da Adress d’in inda zata same shi, jibi Monday da safe inshaaAllah… A take suka turawa Ya Musbah message d’in ta wayar Siyaman, duk da sun san gobe za su had’u, amma duk cikin su Baba ne kawai mai waya dan haka gara su ajjiye message d’in a wayarsa, in ya so goben sai su shirya komai, jibi su tafi tun da ya ce 8 na safe za ta je. Suna gama tura masa Jidda ta maidawa Siyama wayarta ta dawo ta zauna ita da Muhsin suka shiga surutu da murnar aikin da Manubiya ta samu, tun Manubiyan bata kula su har ta d’an fara saka musu Baki a hirar tasu wadda duk suna yi ne a kan albashin Manubiyan: za su siya kayan abinci da na farko, idan an sake biyan ta kuma sai su siyawa inna da Baba kayan sakawa, sannan suka ce za su biyawa Muhsin ya yi jarabawa ya wuce ss1 ya ci gaba da karatunsa shima…. Kusan duk a lissafin nasu ba su sako kan su ba kawai komai su iyayen su sai Muhsin wanda yake ta murnar ya ji an ce zai ci gaba da karatu.. wannan dalilin ne ya sanya hawaye suka b’allewa inna wadda ta farka daga bacci ba da dad’ewa ba.. da kyar ta samu ta rarrashi kanta ta yi shiru. A haka Baba ya shigo ya same su hannunsa rik’e da bak’ar leda. sai da suka yi masa sannu da zuwa tukunna Manubiya ta mik’e ta d’auko faranti ta na zuwa ya mik’a mata ledar ta karb’a ta yi godiya tukunna ta bud’e…. Kunun tsamiya ne a ciki d’an sachet guda d’aya sai gurasa guda hud’u mai gishira an d’an yayyafa mata mai. Jidda ce ta karb’a kunun tsamiyar ta je ta ta damo wa inna ta dawo Manubiya da Muhsin kuma suka d’auki gurasar d’aya d’aya su ka ci bayan sun yi sun yi da Baba akan shima ya ci amma ya ƙi, ya ce musu “ya ci tasa a waje kafin ya shigo” ba dan sun yarda ba sai dan basu son yin ja in ja da shi ne yasanya suka hak’ura suka d’auki tashi guda d’ayar suka sake raba ta gida uku suka barwa Jidda wadda take bawa inna kunu nata su kuma suka ci nasu suka sha ruwa, daganan Manubiya ta d’auki bargon Baba da Muhsin ta yi musu shimfid’a ta ajjiye musu abun rufuwa… dai dai nan ita kuma Jidda ta gama bawa Inna kunu, dan haka ta zauna zaman cin tata gurasar Manubiya kuma ta je ta d’an d’umamo ruwa ta dawo ta kaiwa Baba rabi toilet rabin kuma ta zo ta shiga gogewa Inna jiki. Cikin sanyin jiki Baba ya mik’e ya je ya gasa k’afar sa wadda ta addabe sa kwana biyun nan, daganan ya yi uzuri, brush da alwalla ya fito ya zo ya yi addua ya kwanta yana tunanin mai gobe kuma zata k’unsa…. babbar damuwar sa itace ‘abinci’ dan wannan ma a bashi aka basa da kyar, dan haka ya san ba lalle wanda ya basa bashin ya kuma basa gobe ba….. Yana jin su (Yaran) suka shiga one by one kowa ya yi brush ya yi alwallah ya fito daga nan Manubiya ta kunna musu mosquito coils Jidda ta yi musu shimfida suka nema waje suka kwanta.. Har bacci ya kwashe su gaba d’aya amma shi ya gagara kawai dai ya lumshe idanuwansa ne kamar mai bacci …. ••••••• Ummi bata cewa Munirat komai ba har suka k’arasa d’akin Ummin. Sai da suka shiga ta rufe k’ofar d’akin nata tukunna ta juyo Munirat tana shirin yin magana Ummin ta kwashe ta da wani kalar gigitaccen mari, cikin fushi ta ce ’’na baki minti biyar ki yi mini cikekken bayani. Munirat kina haukane? Yahansu fa? Ba wai ina zargin ki da yi mata snatching (kwace) ba amman kamar yadda Daddy ya fad’a da Mutumin ya fara yi miki zancen banza da sai ki yi fitar ki ki bar shi, a iya d’azun yana ganin ki kawai ya ce miki zai aureki ko kuwa ya abun ya ke?’’ Cikin kuka Munirat ta ce ‘’Ummi alhaji Bashir ne fa kuma tare mun hanya yayi, amma wallahi Ina ganin sa na so in juya amma sai ya tare min hanya…’’ Shiruuu Ummin ta yi ta kasa cewa komai kafin chan ta cewa Munirat d’in ‘’je ki yi alwallah ki yi sallah ki kwanta,’’ Daga haka ta juya ta fice daga d’akin. Ko da Ummin ta fita a parlournta ta zauna ta yi tagumi, ta jima sosai a haka kafin daga baya ta mik’e ta nufi side d’in Daddy.. A d’akin Munirat ta ci y’an biscuits da apple ɗin da ta tarar a fridge ta sha ruwa bayan ta yi sallah ta kwanta tun tana tsammanin ganin Ummi har bacci ya kwashe ta tana sheshek’a tana ajiyar zuciya. … Kamar yadda Yashjub ya fad’a,sai da ya huta ya tabbatar Daddy ma ya gama duk wasu aiyyuka da uzururrukan sa tukunna ya nufi cikin gidan, bai tarar da kowa ba dan gidan yayi shiruu, dare yayi kowa yana d’akin sa. yana tafe ya turawa Mommy massage daganan ya nufi sama side d’in Daddy yana k’arasawa k’ofar parlourn ya d’an yi knocking tukunna ya shiga da sallama. Yana shiga ya hango sa ya rafka tagumi ya zurfafa a tunani, sai da ya je kusa da shi sosai ya zauna a kan 1 seater d’in da take facing 3 seater da yake zaune akai ya ce ‘’Daddy’’ Tukunna ya yi firgigit ya d’ago yana kallon sa BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *24* Numfashi Daddy ya fesar kafin ya gyara zama ya bawa Yashjub dukkannin attention d’insa tukunna ya ce’’kana da buk’atar wani abu ne?’’ Ganin Yashjub d’in ya yi shiru ya gagara cewa komai ne ya sanya Daddy d’in sake cewa’’ina jin ka, akwai matsala ne?’’ A hankali Yashjub ya sunkuyar da kanshi yana tunani, sai da Daddyn ya sake basa dukkannin hankalinsa ya ce’’Talk,mana.’’ tukunna Yash d’in ya sauk’e ajiyar zuciya cikin nutsuwa da sanin kan zance ya fara magana ‘’Daddy.. Allah ya huci zuciyarka akan abun da zan fad’a maka yanzu, Idan ya yi maka zafi ka yafe min” sai da ya d’an yi shiru tukunna ya ce ‘’Daddy abun da aka yi wa Ummi a gidan nan yau bai kamata ba, sannan su Yasira a gaban ka suka dinga yi mata rashin kunya amma aka kasa tsawatar musu, bayan ba ma laifin Yarinyar nata bane ba, tunda ba ita ta ce tana son Mutumin ba… kar so da tausayin Yahanasu ya rufe mana ido mu d’auki alhakin Ummi da y’arta bayan kai ne ka yi alk’awarin za ka zame mata uba. Sannan magana ta biyu su Ya’isha ya kamata a taka musu burki tun yanzu, kar su saka Yarinyar nan a gaba, and also tun daga kan Yasir har izuwa kan Yadira gaskiya Daddy ya kamata a yi wani abun saboda kwata-kwata basu san ya kamata ba, ko ni da na tashi a Uk ba zan yi abubuwan da suke yi ba, na san muna iyakar k’ok’arin mu wajen basu tarbiyya amma abun nasu kullum k’ara gaba yake yi!.. Kalli abun da suka yi wa Munirat da Ummi yau sannan Yassir yau da na je gidan da ya ke abunda na gani ba zan ma iya sake maimaitawa ba saboda k’azantar ta yi yawa…. da shi da Abokansa guest house guda suka ware suke zaune da y’an Mata abun babu kyan gani, ya kamata a tsawatar musu tun wuri Daddy, B4 it’s too late (Kafin lokaci ya ƙure).” Shiruu Daddy ya yi yana nazari ‘Tabbas shima sai da ya shigo ya nutsu yanzun tukunna ya fara ganin rashin kyautarwar sa, kawai dai itama Ummin bai kamata k’iri-k’iri ta bi bayan y’arta ba, ya san wannan dalilin ne ya sake fusata shi. Sannan bai san daliliba amma tana yawan bashi haushi, haka kurum wani lokacin ko magana in ta yi sai ya fusata!!! Saddik’a ba ta da laifi tana da biyayya ga tsafta shiyasa ya ke ta k’ok’arin danne zuciyarsa a samu su zauna lafiya sannan ya ke danne duk wani takaicin ta da yake ji, ya ke kuma kyautata mata amma duk da haka bata appreciating sam kalli yadda yau ta bad’a masa k’asa a ido a gaban jama’a, yana fad’a tana fad’a’.” ‘’Assalama alaikom’’ Sallamar Mommy ta katsewa Daddy tunani. Cikin nutsuwa ta k’araso, Yassir yana biye mata a baya… A kan one seater Yassir ya nemi guri ya zauna Mommy kuma ta zauna akan 2 seater, daganan parlourn ya yi shiru. Da kyar sannan ciki-ciki Yassir ya ce ‘’Daddy ina wuni’’. Ko kallon shi Daddy bai yi ba instead sai ya juya ya kalli Mommy sannan ya ce ’’Kin san d’anki a guest house ya je ya zauna yana shed’ana? Ya ce ki yi masa aure kin k’i bada had’in kai kin tarwatsa abun, to gashi yanzu ya nuna miki kalar b’arnar da zai yi idan aka k’i a yi masa auren. Mai yasa ba kya so ya auri Kausar?’’ Daddy ya k’arashe maganar tasa da tambaya, kansa tsaye yana mai sake fuskantar ta. Gaba d’aya diriricewa Mommy ta yi, tana mai jin takaicin yadda Daddy ya ke k’ok’arin had’a mata bomb tsakanin ta da Yassir, har ma da Yashjub. Cikin katse mata tunani Daddy ya ce ‘’Anyways shikenan, ku kuka sani! na riga na cire Hannuna a lamarin kuma wallahi I’m very glad about the fact that (na yi farin ciki sosai da) Yassir bai auri Kausar ba!! Dukda cewa shima naga alamun ya zama d’an duniya amma duk lalacewar giwa ta fi kare….. yanzu dai abu biyu zuwa uku nake so in yi miki magana kuma in ja miki kunne akai, ki saurara ki jini da kyau… Ki san yadda za ki yi ki gyara d’anki ‘Yassir’ idan kuma ba haka ba to zan kwace company d’in da na bud’e masa, saboda na ga sai ya shafe morethan one month ma bai je ba dan haka a gani na babu amfanin a bar masa… akwai Yaran Abokaina architecture’s da yawa, zan iya bawa d’aya daga cikin su!! C’e’o kawai zan chanja cikin k’ank’anin lokaci za a chanja suna da komai. Sannan idan bai shiryu ba to ba k’aramin aiki bane in kore sa a cikin gidana gaba d’aya!! Saboda ba zai yiu ya dinga yin yadda ya ga dama anyhow ba!!! Ban ga dalilin da zai sa ya je yayi iskancinsa kuma ya dawo min nan ni kuma in bashi shelter ba!!!! Ya nuna zai iya rayuwa shi kad’ai, tunda gashi ya fi 1 month (wata ɗaya) ba ya tare da mu, dan haka idan na sake jin wani shirme daga garesa wallahi sai na baku mamaki….. Amma for now a matsayina na ubansa zan saka a yi masa sauk’a, a raba sadak’a, a saka shi a addu’a ‘Allah ya shirye shi..’ daganan kuma idan bai shiryu ba ya nuna min ya fi k’arfina to sai dai mu raba gari ni da shi..” Daddy ya k’arashe maganar cikin tsananin fad’a da takaici. Yassir ji yake kamar ya tashi ya rufe Yashjub da duka, tabbas ya san shi ne ya zo ya had’a masa munafurci a wajen Daddy. Saboda Allah d’an k’aramin company d’in nasa da aka bud’e masa shine yake so a kwace ko yaya? it’s obvious shi ne (a baiyyane ya ke Yashjub ɗin ne) favorite d’in Daddy ya san Daddy ya fi son shi, shi kuma ya san Daddy ya tsane sa. Already Yashjub ya fi shi a fannin kud’i da ɗaukaka da komai ma tou amma dan me yasa zai saka masa ido ya sakawa d’an business d’insa ido sannan ya sake hura wutar k’iyayyar sa a zuciyar Daddy!!! “Anya kuwa jininsu d’aya da Yashjub?” Yassir ya yiwa kansa tambayar yana jin yadda zuciyarsa take sake tafarfasa. A hankali Mommy ta ce ‘’InshaaaAllah Daddy za a gyara, kuma za mu kiyaye, ba za mu baka kunya ba.’’ Dai-dai nan Ummi ta shigo, har za ta koma dan tana ganinsu ta fahimci meeting suke yi amma sai Daddy ya ce mata “ta zo ta zauna ba komai..” Cikin nutsuwa ta gaida Daddy daganan ta juya ta gaida Mommy suka amsa ba yabo ba fallasa Yashjub kuma ya gaida ita… sai da Daddy ya zabgawa Yassir harara tukunna ya ce ‘’Ina wuni’’ Ba tare da ya kalle ta ba… da kulawa ta amsa kafin ta kalli Daddy cikin sunkuyar da kai ta ce’’ Ka yi hak’uri Daddy akan abunda ya faru ɗazu, In shaaAllah hakan ba zai sake faruwa ba’’ A hankali Daddy wanda duk ya ji jikinshi ya yi sanyi ya ce ‘’ba komai’’. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta fara magana ‘’Alhaji Bashir, ya san Munirat 3 years back, sun had’u a instagram ne, tun kafin ya ganta in person (ido da ido) suke tare. tunda ya zo suka had’u kuwa sai ya fara maganar aure. Cikin watanni biyu, komai ya k’ullu, aka saka ranar auren su wata uku. A ranar hennah party d’inta ne muka ji labarin ashe matarsa psyco ce (tana da taɓin hankali), ita ta kashe y’arsu ta farko ma amma da yake mahaifinta influential person (babban mutum) ne, sai aka rufe abun aka ce depression ne yake damun ta shi yasa take hauka… daga baya ma aka ce ba ita ta kashe yarinyar ba. A ranar d’aurin auren Munirat da Bashir ne matar tasa ta d’auki karamar y’ar tasu wadda ta rage ta tafi da ita Cairo, ta turo masa video tana treatning d’insa (yi masa barazana) akan ‘ko dai ya fasa auren Munirat, ko kuma ta kashe wannan yarinya wadda ta gudu da ita sanann itama ta kashe kanta’. Sai a lokacin ne muka ji labarin ashe haukar tata tana tashi ne idan Bashir d’in ya kula wata ko kuma yayi yunk’urin k’ara aure, shiyasa shi kuma yake b’oye mata. Ko ba komai a wannan lokacin mun fahimci yadda Bashir yake k’aunar matarsa duk da a lokacin ya ce saboda y’arsa yayi abun da yayi amman yadda matar ta hanasa dawowa bayan tafiyar sa despite (dukda kuwa) yadda ya bar Munirat ya ci ace an fahimci yadda yake gudun b’acin ranta. Bai tashi fad’ama wakilinsa ma ya fasa auren ba sai da ya isa airport ya tabbatar ya samu jirgi tukunna ya iya nutsuwa ya turawa wakilin sa da na Munirat message…. Watan Munira d’aya tana rashin lafiya saboda yadda k’awayenta makwafta da kuma y’an uwa suka dinga gulmace-gulmace, gashi ko ba komai itama na san tana son Bashir a wannan lokacin. Tun wannan lokacin bai tashi dawowa ba sai after five months (bayan watanni biyar) bayan ya gama theraphy d’in matarsa ya gama lallab’ata ta zauna achan Cairo d’in, sai gashi ya dawo da niyyar auren Munirat ba tare da sanin matar tasa ba ni kuma nace a’a Munirat ma tace a’a ta hak’ura. Da farko lallab’a mu ya fara yi da yaga dai mun dage, sai ya fito mana da asalin fuskarsa….. Duk da mun maidawa gidan su duk wasu kayan lefe da na Al’ada sannan an janye batun bashi itan da akayi amma sai ya dage akan cewa ‘shi fa an riga an bashi danhaka a duk lokacin da ya ga dama ko muna so ko bama so zai je a d’aura musu aure.!!’ A lokacin Munirat har ta yi wani saurayin ana shirin saka rana amma sai da Bashir ya shiga ya fita ya raba ta da wannan Yaron. Ganin yana neman takurawa rayuwar mu kuma dama na gama sabon gini na ne Ya sanya na d’auke Munirat muka tafi chan garin mu, muka yi wattanni bakwai kuma da muka tashi dawowa bamu tare a gidan da ya sanmu ba. Yayarta itama cewa ta yi sai da mijinta yayi da gaske tukunna Alhaji Bashir ya d’aga musu k’afa dan da ya neme mu ya rasa kanta ya koma wai sai ta fito masa da fiancé(matar da zai aura)…….’’ Sai da Ummi ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace ‘’ Munirat bata da niyyar cutar da Yahanasu, kuma daga ita har ni kwata kwata ba mu taɓa kawowa a kanmu shine wanda Yahanasu za ta aura ba, dan Allah kar abun da aka d’an samu misunderstanding sannan ya riga ya wuce ya zama silar samun matsalar mu’’. Ahankali Daddy yace ‘‘InshaaAllah Ummi, kema kuma ki yi hak’uri ke da Munirat d’in bamu san da haka ba kuma shima Bashir ko da na yi masa magana ɗazun bai yi min wannan bayanin ba, zan samu samu lokaci in saka su Yasmeen d’in su baku hak’uri a fahimci juna komai ya wuce inshaaAllah’’. A hankali Mommy ma ta ce ‘’Allah yasa mu dace’’. A tare Daddy da Yashjub da Ummi suka ce’’Ameen’’ Daganan Ummi ta mik’e ta ce musu ‘’sai da safen su’’. Tana fita,Daddy shima ya mik’e ya ce’’we are done here,Allah ya bamu alheri.’’ Sai da safe su Yashjub suka yi musu suka fice, yayinda Mommy ta mik’e ta bi bayan Daddy amma tana shiga yauma kamar kullum ya sallame ta, haka nan ta fito hankalinta a tashe!!…… Tabbas ita kanta ta san tana da kissa amma bata jin wannan karan she can keep on hiding her pain,(za ta iya ci gaba da ɓoye damuwarta,), abubuwan sun yi mata yawa, abunda ta raina yana k’ok’arin fin k’arfin ta. Ga shi yanzu zargin su a kan Yashjub ya tabbata, dukda ya ce mata friend d’in shi ce amma ita bata wani yarda ba bayaga hakan ma shin a ina ake wani k’awance tsakanin mace da namiji, tunda ya gaya mata d’azu har yanzu hankalinta bai kwanta na second d’aya ba…. ‘kar dai fa ace wannan ita ce Yarinyar da zata zamto obstacle d’in (shamakin) nasu…….’ Mommy ta aiyyana hakan a ranta. Bayan kwana d’aya,(Monday!.) Da asubah Manubiya ta tashi, tana idar da sallah ta yi karatun Qur’ani ta idar, daga nan ta d’auki handout d’inta ta hau karatu bayan ta je ta d’aura ruwa. Sai da garin ya d’an yi haske tukunna ta mik’e ta je ta d’an d’ebi ruwan ta watsa ta barwa su Jidda nasu. Tunda Baba ya fita sallah bai dawo ba har ta gama shirin ta, ta san kuma dalilin da ya hana shi dawowar! Dan haka ta hau tunani tana lissafin ‘ko dai su hak’ura da zuwa office d’in mutumin nan ko kuma su je a k’afa idan za su iya in yaso d’an kud’in motar da suka tanada sai a siyawa inna kununta su Muhsin suma su ci abinci’ dan ta san shima Ya Musbah ba lallai a samu wani abun daga wajen sa ba. K’arfe 7 dai-dai ta fita zuwa gidan Ammi tana addu’ar Allah yasa yau d’aya dai ta samu ko da left over d’in jiya ne. Kamar yadda ta yi expecting (zato) kuwa sai da suka fafata ita da Ammi…dan jiya basu had’u ba wai ta tafi sunan k’anwarta tun sassafe so manubiyan bata samu ta tambaye ta akan fitar da za ta yi yau ba!! Sai da Mama ta saka Baki yau ma tukunna Ammin ta barta akan nan da k’arfe goma za ta zo. Abincin da ta yi tunanin samu kuwa san bata samo ba, haka nan ta dawo hankalinta a mugun tashe dan bata san mai za su ci ba. Da ikon Allah tana shigowa ta tarar Ya Musbah ya zo musu da koko Jidda har tana bawa inna nata.. ba k’aramin dad’i ta ji ba kuwa dan haka ta yi wa Allah godiya, itama ta karb’a ta sha nata daga nan Baba ya yi musu addu’a su Jidda suka yi musu a dawo lafiya, su kuma suka fito ita da Ya Musbah kowa a d’akin yana musu fatan alkhairi. Lokacin karfe 7:36. A hanyar bakin k’ofa suka tarar da ya Yusuf yana tsaye yana daddana waya sanye cikin suite. da murmushi Ya Musbah ya k’arasa ya mik’a masa Hannu yana mai cewa ‘’Yusuf ina ta so in lek’a in yi maka murna… Na ji Baba yana cewa ya ji Kaka mallan a masallaci yana gayawa Abokinsa ka samu aiki a banki ko? Allah ya sanya alkhairi’’ Ya k’arashe maganar tasa da tsananin murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarsa. Ko kallon sa Ya Yusuf bai yi ba ballantana ya yi tunanin zai bashi Hannu su gaisa! A hankali Ya Musbah ya janye hannunsa kafin cikin rashin kuzari ya sake cewa “Allah ya sanya alkhairi.’’ Yanzun ma bai ko kalle sa ba sai wayarsaa da ya ci gaba da dannawa. Juyawa Ya Musbah ya yi, ya kalli Manubiya wadda ta k’ule ta zo iya wuya, ya ce mata ‘’Manu,mu je’’daga nan ya sa kai ya fice daga gidan jikinsa a mugun sanyaye. Manubiya har zata fita itama sai kuma ta juya ta kalli Yusuf d’in dai dai shima ya d’ago yana kallon ta, a hankali k’asa-k’asa ta ce’’Jidda ce dai,ba za mu bayar ba! dan Allah in kaga dama ka zama sarkin gaba.’’ Tana gama fad’in haka ta fice da sauri tana mai jin takaicin yana d’an raguwa. ….. Ƙarfe 7:56am Adaidaita sahun su ta yi parking a bakin ‘Yashjub Limited’. Sunayen su kawai masu gadin suka tambaya, Manubiya tana fad’ar sunanta suka shiga yi musu sannu da zuwa, suka bud’e musu k’aramar k’ofa su kuma suka shiga. A reception suka zauna bayan sun je sun fad’i sunayen su an ce ‘su d’an jira.’ Cikin nutsuwa Ya Musbah yake kallon gurin yana adduar ‘Ina ma ace ya samu aiki a gurin, ko da masinja ne, in dai zai samu abun da zai ciyar da Inna da Baba da y’an uwansa da kuma Baraka da d’ansa to Alhamdulilla…’ aikin gini da wanki da gugan nan da ya ke yi ba k’aramin wahala yake sha ba sannan ogannin nasa basa biyan sa sosai, ga shi kullum a gajiye ya ke!!!, Baraka har ta fara yi masa mitar baya sauk’e mata hakkinta na aure wanda yake a kansa saboda kullum yana zuwa gida ya ke bajewa sai barci, tsabar gajiya. A nan kam ya san ba zai dinga yin gajiyar da yake yi a wankau ba, ga gurin ko Ina AC…. ‘’Ya Musbah dan Allah ka daina kula Ya Yusuf, tunda bashi da mutunci.’’ Muryar Manubiya ta katse masa tunani, murmushi kawai ya yi kafin ya kalle ta tukunna yace’’Manu,idan na biye masa ai sai zumuncin namu ya fi yanzu lalacewa…’’ ‘’Miss Manubiya, pls follow me(taso mu je).’’ Wata baturiya cikin suite da skirt ta ce da su kafin ta juya ta nufi hanyar sama. A tare suka mik’e ita da Ya Musbah suka bi bayan matar…. a bakin lift matar ta tsaya, sai da ta juya ta tabbatar suna bayan ta tukunna ta danna lifter ya bud’u sannan ta shige ta kallesu ta ce ’’come in,pls(ku shigo)’’ A hankali suka shiga k’irjin Manubiya yana dukan uku-uku,dan bata tab’a shiga ba, ta dai san menene amma bata tab’a shiga ba. 4th floor dama Matar ta danna wanda shine last floor dan haka suna isa lift d’in ya tsaya k’ofar ta bud’u matar ta fice suma suka bi ta a baya. Sai da numfashi su ya kusan d’aukewa saboda tsananin had’uwa da kyawun wajen, ko ina glass! dan kana iya hango har chan waje har titi, ga wasu fitilu da suka haska wajen suka sanya yayi wani irin haske tarr…. Hijabin idi ɗinta na last year ne a jikinta brown colour, a wanke tass a goge har k’asa, sai shek’i yake yi, dan tun sallar da ta saka bata sake sakawa ba! Ya Musbah shi kuma yana sanye da jallabiya bak’a da hula fara (tashi ka fiye naci)…. kayan Jikin duk su biyun a goge suna shek’i amma duk da haka sai suka raina kansu saboda had’uwar wajen da kyawun shi sai ya fito da rashin kyau da tsadar kayan nasu. Apart from wannan baturiyar da take yi musu jagora basu ga kowa a wajen ba, a k’asa ma kwata-kwata mutum shida suka gani daga receptionists sai wani a cikin suite sai masu gadi da cleaner, da alama dai company d’in bayan kasancewar sa private to mai company d’in ma baya buk’atar mutane da hayaniya tunda gashi itama ce mata aka yi dama ’sau d’aya za ta dinga zuwa a sati’. Suna tafe ita da Ya Musbah suna bin bayan wannan baturiyar kowa da abunda yake aiyyanawa a ransa… wani dogon corridor suka bi kafin su k’arasa wani babban guri tsakiyarsa na ɗauke da wani abu kamar round about cikinsa duk flowers masu asalin kyau da ƙamshi.. A ta chan gefen hagu suka hango wani waje kamar d’an k’aramin parlour mai d’auke da wasu d’urma d’urman sofa, 3seaters guda uku, masu tsananin kyau da d’aukar hankali sai center table a tsakiyar su da fridge da dispenser a gefe da gefen su. Yayin da tsakiyar wajen ke d’auke da wani makeken roundabout wanda aka cika sa da shuke shuken flowers masu tsananin kyau da kamshi, sai kuma wuta kamar na pop yana ratsowa ta k’asan flowers d’in yana k’arawa shuke-shuken asalin kyau da d’aukar hankali… Manubiya bata gama tunanin ta ya ake bawa flowers d’in ruwa ba ta ji baturiyar ta ce mata “this way miss(nan za mu yi’’ Kafin ta kalli Ya Musbah ta ce masa ‘’U can wait,right there(ka ɗan jira ta, a chan).’’ Ta fad’i hakan tana mai nuna masa wannan d’an mini parlour d’in da yake ata chan gefen hagu. Kwata-Kwata k’ofofi uku ne a wajen na glass,biyu suna kallon juna d’aya kuma yana opposite wannan mini parlourn da aka ce ya Musbah ya zauna duk da roundabout d’in flowers d’in da yake a tsakiyar su tsaf kake iya hango komai da ya ke a ciikin dukkan wajajen. Biyun da suke facing juna, a d’ayan kana iya hango tebura da chairs d’insu da computer a kan ko wanne tebur, yayinda wanda yake kallon sa kuma yake d’auke da k’atoton tebur (dogo) da kujeru wajen sama da arba’in zagaye da shi, sai doguwar micro a gaban ko wacce kujera a ajjiye kan tebur d’in sai projector d’insu da suka bari a kunne. Sai last one d’in wanda yake kallon mini parlourn, a saman shi an rubuta C.E.O, kana iya hango normal tebur sai kujeru biyu a gaban tebur d’in da kuma d’aya tana kallon biyun sai parlour mai kyau a gefe da kuma wani mutum sanye cikin white suite dogo k’ak’k’arfa giant ya juya baya yana kallon waje da waya a kare a kunnensa…. … Da farko Ya Musbah ya so ya yi musu da aka ce kar ya shiga, sai kuma yaga ai yana iya hango komai na cikin inda aka ce Manubiyan ta shiga dan haka ya je ya nemi waje ya zauna, yana kallon su har wannan baturiyar ta shiga Manubiya ta bi bayanta suka mayar da k’ofar suka rufe …. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *25* Tun lokacin da suka shigo cikin company d’in ya gan su ta cctv, kuma ya fahimci ita ce dan ba shi da appointment da kowa yau sai ita… Babban abunda ya d’aga masa hankali shine Ya Musbah, ba ya ganin fuskokin su sosai shiyasa bai fahimci fusgen kamannin da suke yi ba dan shi a tunanin sa ma Abbakar ne tunda tare ya gansu the other day(a wachchar ranar). a ran sa ya ce ‘’to ko dai saurayin ta ne da gaske’’ A take wata zuciyar tace masa’’to idan ma saurayin nata ne ina ruwan ka, kai naka ba kawai ka san more about her ba(santa bane ba)..’’ Yadda yake jin zuciyarsa tana tafarfasa ne ya sanya ya kasa jurewa, ya rufe computer, ya mik’e ya bar gaban tebur d’in nasa ya isa jikin glass ya juya baya yana mai kallon waje. A haka secretary d’in tasa ta shigo ta same shi ta ce masa ‘Ga Manubiya ta zo’. Yana bata izinin ta je ta shigo da ita ya zaro waya ya hau kiran Najeeb dan ji yake yi kamar ya sanya security su fitar da wanda yake tunanin Abbakar ne…. yana so ya san alak’ar ta da shi kafin ma su shigo masa office.. ‘’You are suppose to be busy by this time(kamata ya yi a ce kana busy a dai dai wannan lokacin), ko ba da safe ka ce mata ta zo ba?’’ muryar Najeeb ta katse masa tunanin da yake yi. ‘’Yeah, gata nan ta zo amma basu shigo ba. amm..Najeeb, wanann yaron da na gansu tare ranar a office d’inka waye ne shi d’in saboda yau ma gasu nan ta taho min da shi.’’ D’an guntun murmushi Najeeb ya yi yana mai jiyo kishi k’arara a muryar Yashjub d’in,kafin ya ce ’’inaga kamar d’an uwanta ne.. Maybe ko cousin dan surname d’in su ba d’aya bane, amma wani lokacin ma tare suke shigowa aji, so ina ga kamar a gida d’aya suke zaune. are u jealous?’’ Najeeb ya k’arashe bayanin nasa da tambaya, yana mai dariya k’asa-k’asa. Tsaki Yashjub d’in ya yi, dai dai nan Racheal ta d’an yi knocking tukunna ta yi sliding k’ofar ta shigo Manubiya na biye da ita a baya. Sama-sama ya fara jin Najeeb saboda lokaci d’aya jikinsa ya yi sanyi sannan yanayin bugun zuciyarsa ya k’aru. A hankali ya cewa Najeeb “I’ll call you back’’ bai jira jin mai Najeeb d’in zai ce ba ya katse kiran, yana jin yadda yanayinsa ya sauya tashi d’aya. Cikin nutsuwa Racheal ta ce ’’Sir she’s here(ga ta nan)” A hankali ba tare da ya juyo ba ya ce ’’Thankyou,you can leave(za ki iya tafiya, na gode)” Racheal d’in ce ta nunawa Manubiya inda zata zauna kafin ta juya ta fita bayan Manubiyan ta zauna da kyar, tunda suka shigo company d’in jikinta yayi sanyi..tunda ta hango shi a tsaye ya juya baya ta nemi kuzarinta ta rasa!!! gashi yanzu kuma tunda ta shigo office d’in k’irjinta ya hanata sukuni… Gashi ƙamshin turarensa wanda ya karad’e ilahirin office d’in ya yi mata kamar na mutumin da ta had’u da shi a office d’in Sir Najeeb, dan tabbas hancinta ya shak’i ƙamshin sosai a wachchar ranar a lokacin da ya matso kusa da ita zai fita… sannan babu abunda ya fi d’aga mata hankali irin muryar da ta ji a yanzu a lokacin da ya yi wa wadda ta rakota( Racheal) magana, kar dai fa ace wannan mutumin ne, dan in dai ba gizo muryarsa ta yi mata ba to kuwa tabbas wannan Mutumin shine wanda suka had’u da shi a office d’in Sir Najeeb kwanakin baya. Da kyar Yashjub ya d’an nemo nutsuwa ya sakawa gangar jikinsa tukunna ya juyo, cikin takun shi na k’asaita ya nufo tebur d’in, ba tare da ya kalle ta ba. Wani irin bugawa zuciyar Manubiya ta shiga yi dan yana juyowa ta shaida shi ‘’amma Abbakar bai kyauta min ba’’ ta fad’i hakan a chan k’asan zuciyarta, kafin a hankali ta sunkuyar da kanta k’asa tana jin kamar ta tashi ta fita da mugun gudu. Idanuwanta da zuciyarta sam sun gagara daina zuzuta mata tsananin kyawun da yayi ga wani haiba da kwarjinin da yayi mata wanda suka taimaka wajen sake hautsina mata lissafi… A ranta ta shiga aiyyana cewa “ashe wanchan karon ban gansa sosai ba.’’ Tana wannan tunanin Yashjub ya nemi waje ya zauna a kujerar da take facing d’in ta, yana mai jin k’irjinsa yana bugawa, kafin a hankali ya d’ago lumsassun idanuwansa ya zuba su a kanta….. Wani irin sanyi ya ke ji yana ratsa shi tun daga saman kansa har izuwa kan babban d’an yatsan k’afarsa….a take wata nutsuwa da kasala suka sak’e rufar masa yana mai jin wani irin nishad’in da bai tab’a jin kwatankwacin irin shi ba. Duk da yadda ta sunkuyar da kanta hakan bai hana shi k’arewa kyakkyawar fuskarta wadda ke zagaye a cikin hijabi kallo ba, a hankali a chan k’asan zuciyarsa ya ce ‘’Subahanallah, MashaaAllah, Allahu akbar!..’’ Tun lokacin da ya zauna ya fara kallon ta ta diririce… da kyar da mugun kyar ta samu ta iya d’ago fuskarta da niyyar gaida shi amma sai ta ga ya kafeta da kyawawan idanuwansa, cikin sauri ta kauda kanta gefe saboda girma da nauyin da ta ga kwayar idanun nasa sun yi mata…a hankali ta ce ‘’Good morning,Sir,’’ da kyar. Lumshe idanunsa yayi ya bud’e yana kallon yadda take kallon gefe kad’an ita ala dole ba za ta had’a ido da shi ba bayan kwanakin baya da kyar ta iya zare idanunta a nashi..bai san lokacin da wani murmushi ya kufce masa ba wanda har sai da ta d’an jiyo sautin kad’an, kafin cikin kamala da dad’in sauraro ta ji ya ce ’’’Morning, you called me day before yesterday(kin kira ni shekaran jiya)’’ ya fad’i hakan har zuwa wannan lokacin idanuwansa na a kanta yana yi mata wani irin kallo kamar wanda yake so ya k’irga duk wata b’ular gashin da ke a fuskarta ne. Shi kan sa yana so ya d’an d’auke idanun nasa daga kanta amma sam ya gagara, babu abun da ya fi d’aure masa kai kamar yadda tashi d’aya ya shiga nutsuwa walwala da farin ciki da annashuwar da bai tab’a shiga ba. A hankali ya ji ta ce “Sir Najeeb said you have a job for me, that’s why I called.(sir Najeeb ne ya ce kana da aikin da za ka bani, shiyasa na kira).” Ta k’arashe maganar a hankali kamar tana jin tsoro. Shiruu ya yi, yana kallon ta kafin chan yace’’Yeah,i do,can i see your credentials.(eh, ina da aikin da zan baki, zan iya ganin takardunki?.)” A hankali ta lumshe idanuwanta dan sai a wannan lokacin ne ta tuna bata d’auko na secondary school ba wanda ya ke shi a chan sama yake a cikin akwati, dama tana ta zuci zucin za ta d’auko ta had’a da ragowar sai dai kuma har ta fito Allah bai bata iko ba, haka nan ta mik’a masa na primary da diplomar ta tukunna ta ce masa’’ ta manta na secondary school d’in’’ dan haka ya ce ‘’ba damuwa, next zuwan da za ta yi, ta zo da shi’’. Ya d’an jima yana nazari kafin ya fara yi mata bayanin aikin nata yadda zata fahimta……. ‘’Akwai estate a Kano, Lagos da Abuja. Bana so idan abu ya b’aci a dinga kira na direct almost everyday (kusan kullum) sannan secretary d’ina is very busy (aiyyuka sun yi mata yawa) itama, dan haka zan tura musu number d’inki ta yadda duk wani complain idan za su yi kawai za su gaya miki ki tara ki ajjiye, sai ki dinga reporting to me ranar Friday, duk Friday… Kinga yau Monday to in four days time(to nan da kwanaki huɗu) za ki zo nan kenan, Amman idan akwai abu urgent(abunda ya ke buƙatar a duba cikin gaggawa), za ki iya kirana ko kuma ki gaya min ta online, ba sai kin jira friday ba… k’arshen wata zan dinga baki 30k. Mun fahimci juna?’’. A hankali ta jinjina kai kafin ta ce ‘’Yes,Sir Thankyou so much.’’ Jinjina kai kawai yayi yana mai sauk’e wata b’oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya mik’a mata wata takarda mai d’auke da wajen saka; Full name Address Personal sickness Email Phone number,da sauran su…… ya ce’’ki yi filling wannan.(ki cike wannan).” Cikin nutsuwa ta zaro biro a jakarta, ta hau cikewa… wajen phone number ne ta bari blank dan bata san ya za ta yi ba, da farko ta yi tunanin ta saka number Siyama tunda ita bata da waya sai kuma taga ai aiki ne bai kamata ta d’aura mata komai a wayarta ta takura mata ba sannan anytime za ‘a iya kiran ta kar aji wata ta d’auka ya zamana kamar bata d’auki aikin ma da mahimman ci ba, shiyasa ta ga gara a yi k’ok’ari a san yadda za ayi inshaaAllah ko mai torchlight ce su nemo sai ta taho da number tare da certificate d’in nata, dan haka ta bar wajen blank ta cike ragowar. tana gamawa ta mik’a masa, tana addu’ar Allah ya sa daga wannan ya sallame ta. D’auka ya yi, ya kalla yaga ta bar wajen phone number blank dan haka ya ce ta k’arba ta k’arasa cikewa. Sai da ta d’an yi shiruu tukunna tace masa ‘’a yanzun ba ta da waya,amma inshaaAllah zata taho da phone number d’in a next zuwanta tare da secondary school certificate d’in nata.’’ Shiruu yayi kawai ya zuba mata ido yana mamakin ‘ta ya kamar ta ace bata da waya’ Wanda hakan ya sanya Manubiya ta ji kamar ta kurma ihu!..dan gaba d’aya ya d’aure ta da idanuwansa, ta koina jin kwayar idanunsa take yi suna yi mata yawo a jiki. Ya jima yana k’are mata kallo kafin ya d’an sunkuya ya janyo d’aya a cikin drawer da ke jikin tebur d’in ya zaro wata farar leda, jiya ya sayi A1 d’in zai bawa mai wankin su da ya ce masa wayarsa ta fad’a a ruwa… A hankali ya mik’a mata ya ce ‘’ga shi,idan kin yi charji sai ki turomin messge da number ki meanwhile zan basu email d’in ki idan number ya zama ready sai ki turomin in tura musu ta yadda za ki fara aikin asap.’’ ya fad’i hakan yana mai mik’a mata wayar. sai da ya sake cewa ‘’ki karb’a mana,consider it as an allowance’’ tukunna a hankali kamar mara lakka a jiki ta sa hannu ta karb’a ta ce ’’Nagode,sosai,’’ dan dama har ga Allah bata san ta ina zata fara neman waya ba su da suke fama da abinci. Ganin ya yi shiruu ya koma ya jingina kawai yana k’are mata kallo ne ya sa ahankali ta sake cewa’’na gode’’ daga nan ta yi masa sallama ta mik’e ta nufi k’ofa tana adduar Allah ya sa kar ya sake tsayar da ita, a haka har ta fice daga office d’in. .. Tana fita ya lumshe kyawawan idanuwansa, ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake kai a zaune, a hankali a fili ya ce ‘’It’s official,I’m in love (Ta tabbata son Yarinyar nan na ke yi.)” Sai da ta fita daga office d’in, ta tabbatar ta zugo k’ofar tukunna ta bud’e hancita ta shaƙi iska sosai sannan ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya…. Da kyar ta samu ta ja k’afafuwanta ta nufi inda Ya Musbah ya ke wanda ya riga ya mik’e tsaye tun lokacin da ya hango fitowar ta. Kallon sa take yi tana jin k’auna da tausayin d’an uwan nata suna ratsa ta.. ‘dole haka nan za ta hak’ura ta yi aiki da Yashjub ko dan y’an uwanta….domin ta samu ta bawa Ya Musbah jari sannan ta kula da ahalinta. dukda kuwa bata san ta yaya zata iya rayuwa da wannan mutumin wanda yake k’ok’arin tarwatsa mata zuciya ba amma dole ta dage ta taimaki ahalinta under any circumstances(duk rintsi), zata tsaya tsayin daka InshaaAllah ta yaƙi tunaninta sannan ta taimaki kanta ta hanyar tirsasawa zuciyarta da tunaninta akan su daina yaba mata kyau,kwarjini,jarumta da nutsuwar Yashjub…. inshaaAllah daga yau duk wani abu mai kyau nasa ita kuma zata yi k’ok’ari wajen ganin ta maidashi mara kyau a idanu da tunanin ta… Opportunity comes at ones (Dama ta kan zuwarma wani lokaci ɗaya kawai) hakan ya sanya ba za ta zubar da wannan damar ba, inshaaAllah za ta yi k’ok’ari ta daure ta dage ta yak’i zuciyarta,ta samu ta taimaki ahalinta..’ Da wannan tunanin ta k’arasa inda ya Musbah yake tsaye. Jarumta ta aro ta yafawa gangar jikinta ta k’ak’alo murmushi sannan tace “Na samu aikin, ya bani har da allowance na waya ma.. Aikin dole yawanci ta waya ne..” nan ta d’an yi briefing masa (masa taƙaitaccen bayani) akan yadda suka yi da Yashjub.’’ Cikin tsananin murna ya Musbah yace mata ‘’congratulations Manu. kin ga rabo ko? lecturer d’in da kika tsana ga shi yau yayi miki gata. na miki murna gaskiya… gashi aikin ba wahala kwata-kwata, kuma na yarda da company d’in a yadda yake d’innan nasan an sanshi kuma ya na bin k’a’idoji, kinga kuwa ba za’a cutar da ke anan ba..mu je’’ Ya fad’i hakan yana wucewa gaba, a hankali Manubiya tace ‘’Tam’’ daga haka ta bi sa suka kama hanya suka fita…… ‘Tana jin tsoron kasancewar ta tare da Yashjub amma ya zame mata dole ta taimaki ahalinta’ Ta sake aiyyana hakan a ranta, ahankali ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya.. ‘tabbas gaskiya Abbakar ya fad’a ranar chan da ya ce mata Yashjub ne ‘crush d’in ta,’ Ta aiyyana hakan a ranta, da sauri kuma sai ta kawar da tunanin, a ranta ta ce ‘’Manubiya wake up(farka!!)… mutumin nan ba sa’an ki bane ba, ki duba ki ga ko shekaru talatin ba lalle ya rufa ba amma ya mallaki estates nashi na kan sa… matsalolin rayuwarki ma kad’ai sun ishe ki, kar ki je ki jefa kanki ga halaka…” BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *26* Tun Shekaran jiya Munirat ba ta fito ba, kasancewar ta gama exams ɗinta bata da abun yi da gurin zuwa ne ya sanya ko lek’owa bata yi.. abinci ma bata sauk’a ta ci kuma ko Ummi ta kai mata ba iya cin mai nauyin take yi ba, sai dai ta yi y’ar kwalamar ta a fridge d’in Ummi ko kuma idan dare yayi sosai ta sakk’o ta dafa indomie ta ci ta koma. Tun sassafe Yahanasu ta fita dan tana da client kasancewar ta independent lawyer, ko da ta gama abun da zata yi bata komo gida ba direct sai ta wuce gidan k’awarta. Ya’isha itama tana so ta d’an yi wasu aiyyuka dan haka ta fita tare da Kausar domin ta rakata ta yi depending project d’inta daga nan, yayinda Yasmin take da surgery itakam tun 6 ma ta fita. Yusra da Yadira suma duk suna da exams d’in sassafe Yadira ƴar level 1 ita kam biyu ne ma da ita safe da yamma…. Yassira itama tun sassafe ta fita aiki ! Dan haka gidan ya rage daga Mommy sai Ummi Baaba Larai Yassir da Munirat. Sai wajajen 2 tukunna da kyar Munirat ta fito ta shiga taya Ummi aiki saboda yau Ummin za ta karb’a girki kuma ta na so ta burge Daddy domin ta samu su sake shiryawa da shi sosai. Sai kusa da k’arfe 4 tukunna suka samu suka kammala, kasancewar Munirat tana fashin Sallah ne ya sanya Ummi ta barta a kan ta jujjuye a flask ta kai side d’in Daddy ita kuma Ummin ta tafi yin sallah da wanka. Cikin nutsuwa take juye abincin a cooler suna hira da gwaggo mai aiki dan su Husaina da Asabe y’an Matan (masu aikin) sun tafi shirin islamiyya…. ji tayi kamar ana kallon ta dan haka ta d’an juya a hankali.. da sauri ta d’auke kanta ta juya ranta a d’an ɓace sai kuma ta ja kujera ta zauna saboda riga da wando sai ƴar k’aramar hula ne a jikinta, wandon pencil kuma ya kama ta sosai, sam bata yi tunanin anan yake ba ta d’auka a side d’in Yashjub yake, ta san kuma Ummi ma ta manta ne da bazata bar ta ta zauna a hakan ba… babu abunda ya fi bata haushi irin yadda ya kafe ta da dara-daran idanuwansa yana k’are mata kallo.. ‘’Ina wuni, d’an albarka’’ Muryar Gwaggo ta katsewa Yassir da Munirat tunani… a hankali ya k’araso cikin kitchen d’in yana mai cewa ‘’lafiya’’ yayinda idanunsa su ke yawo a jikin Munirat wadda ko kallon inda yake bata yi ba.. ganin da yayi bata da niyyar gaida shi ne ya sanya shi ya gaida ita ta hanyar cewa’’Anty Munirat,Ina wuni.’’ Da mamaki ta d’ago manyan idanuwanta ta d’an kalle shi dan bata yi tunanin ya san sunanta ba, sai kuma ta sunkuyar da kanta tace’’ina wuni’’a hankali. Murmushi kawai yayi daga haka ya juya ya kalli gwaggwo ya ce ’’gyaran jiya bai fita ba fa, sannan kinsanni bana son white bedsheets, a cire a saka wani sannan a sake gyara d’akin.’’ Yana dire aya, da sauri gwaggo ta ce ‘’Yanzu kuwa d’an albarka.’’ Ta fad’i hakan tana mai ficewa daga kitchen d’in, daga nan ta nufi sama d’akin nashi kusa da na Mommy, amma fa a ranta ta gama aiyyana yadda zata zaiyyanewa Munirat halayen Yasir, dan ba zata bari Yassir ya cuci y’ar marainiyar Alllah ba, sarai ta lura da yanayin kallon da yake yi mata!! bayaga tijarar da y’an uwanshi suka yi mata shekaran jiya shine shima yake so zai d’aura mata da nashi kalar cin zalin. Gwaggo tana fita Munirat ma ta mik’e zata fita, da sauri Yassir ya ce’’We haven’t met(ba mu samu mun haɗu sosai ba sai yanzu) sunana Yassir,3rd born (ɗa na uku) na wannan family d’in, I’m an architect C.E.O Yassir Limited’’ Ya fad’i hakan yana mik’o mata Hannunshi alamun su gaisa yana d’an murmushi. Ba tare da ta kalle sa ba ta ce ’’nice to meet you(madalla da haɗuwarmu)” ta fad’i hakan tana k’ok’arin wucewa Da sauri ya sha gabanta yace ‘’Am..dama Ina so in baki hak’uri a kan abunda su Ya’isha suka yi miki the other day…’’ Cikin katse sa tace ‘’Dan Allah ya Yassir ka bar maganar, za mu yi resolving (sasanta) a tsakanin mu, girls(Mata).’’ Murmushi yayi yana yi mata wani irin kallo kafin kansa tsaye yace “you don’t like me,Y? (Kamar kin tsaneni! Amma Maiyasa? kar ki damu ki fad’a min ba zan ji haushi ba’’ Cikin k’aguwa tace “a gajiye nake, sannan Ina da damuwa, kai kuma ka zo kana ta magana, bana son yawan magana.’’ A hankali yace “Sorry dear! Na fahimta, kuma ban ji haushi ba.’’ ya fad’a hakan yana mai matsawa sannan ya nuna mata hanya da hannunsa ya d’an rissinar da kai yana wani kalar murmushi. Da sauri ta wuce ta fita tana waiwayen sa kamar wanda akace zai biyo ta ya kama ta ne. A Chan corridor ta lab’e sai da taga hawan shi sama da juice da cake da alamun su ya zo d’auka, tukunna ta fito ta koma kitchen d’in ta k’arasa zuba abincin ta kai d’akin Daddy,bragowar kuma ta jere musu a kan babban dining table d’in tukunna ta zuba nata ta ci a kitchen d’in dan sai yanzun ne yunwa ta fara kwak’ular ta saboda rabon ta da abinci mai nauyi tun shekaran jiya…. Gwaggo ta riga ta gama wanke wanke shiyasa itama tana gama ci ta shiga d’auraye plate d’in da ta b’ata. Tana cikin wankewa Ya’isha da Kausar suka shigo suna hira… ko kallon ta ba su yi ba haka suka ci gaba da hirar su kamar ba su ga mutum a kitchen d’in ba, suna hira suna shewa Kausar ta d’auko pizza a fridge ta sa a microwave ta d’auko cake da drinks suka nufi d’an mini dining d’in da ke a cikin kitchen d’in suka zauna. Su ne ya kamata su kula Munirat duba da abunda ya faru a tsakanin su tunda itace bak’uwa, sannan yanzu ma ita suka tarar a cikin kitchen d’in….Amma basu ko kalle ta ba..gudun magana ne ya sa har Munirat ta juya za ta fita sai kuma ta koma inda su ke ta tsaya tace “Am..Ya’isha sannun ku da zuwa, dama tun jiya ina so mu yi magana, amma sai ban samu ganin ku ba sai yanzu… dama a kan abunda ya faru ne, ku yi hak’uri mu fahimci juna, a samu komai ya wuce.” Dai-dai nan Kausar ta mik’e ta nufi microwave d’in da ta fara k’ara Ya’isha kuma ta d’auko wayarta ta hau daddannawa. ‘’Ya’isha’’ Munirat ta sake kiran sunanta tana mai k’ok’arin danne zuciyarta. Ba tare da Ya’ishan ta d’ago ta kalle ta ba ta ce “Ni fa, waya zan yi da boyfriend d’ina, so pls leave..dan na tabbata turare ko wankan da kika yi shekaran jiya bai gama barin jikinki ba!! Najeeb is a very handsome and nice guy (Najeeb kyakkyawa ne kuma ya na da kirki) sannan ina son shi, dan haka ban shirya bar miki shi ba…’’ Ya’isha ta fad’a mata hakan tana mai daddana wayarta ba tare da ta kalli Munirat d’in ba, kamar ma ba da ita take maganar ba. Dai-dai nan Kausar ta dawo da pizza ta ajjiye musu suka shiga ci. Har Munirat za ta ce wani abun sai kuma ta juya kawai ta fita zuciyarta tana wani irin tafarfasa. Tana fita Kausar ta kalli Ya’isha ta ce “na san ni cousin d’inku ce amman a yadda muka taso Ni kamar sister nake a wajen su Yash da Yassir, sab’anin Munirat dan haka ya kamata mu yi wa Ummi magana ta daina barin katuwar y’arta tana yi mana yawo tib’ir-tib’ir a gida, dan naga kamar ma tallar y’ar tata take yi.’’ Kausar ta k’arashe maganar cikin tsananin takaici tana addu’ar Allah yasa ba a yi rashin sa’a Yashjub d’inta ya shigo by mistake ya ga Munirat a haka ba. Murmushi Ya’isha ta yi cikin kamo hannun Kausar d’in tace’’ Kausar ki dena cewa ke cousin d’inmu ce saboda you are more than a sister ma to all of us, muna son ki muna k’aunar ki fiye da zaton ki,’’ cikin sake ruk’o hannunta ta ce ‘’bara in baki misali,‘’ sannan ta d’aura da cewa “in da ace wata ce ta yi breaking heart d’in Yassir a tunanin ki ya za mu yi mata? k’iri-k’iri kika ce bakya son Yassir on top of that kika ce Yashjub kike so amma mu ka goya miki baya ɗari bisa ɗari ba tare da mun ji haushin ki ko mun tuhume ki ba dan haka dan Allah ki daina cewa ke cousin d’in mu ce, ki yarda ki saka a ranki You are part of this family and we love you,always &forever(kema ƴa ce kamar mu a cikin wannan Ahali n kuma har abada muna sonki). ita kuma wachchar ki bar ni da ita, zan san maganin ta soon, in dai ina numfashi sai ta bar gidan nan da k’afarta walllahi..d’azu ai Yasira ta turo message a group akan labarin da uwar tata ta bayar, kin gani?’’ Tab’e Baki kausar ta yi sannan ta ce ’’eh!na gani,amman hakan ba zai chanja komai ba, dole sai ta bar gidan nan tunda babu gadon ubanta a ciki.’’ ‘’Ita da uwarta’’ Ya’isha ta k’arashe mata maganar tata tana dariya. Dariya duk suka yi kafin su ci gaba da cin abincinsu suna yi suna tattaunawa. Duk yadda Munirat ta so ta hana kanta kuka sam sai ta kasa, tana fita hawaye suka fara tsiyaya daga idanuwanta. Abun yayi mata ciwo sosai… gashi Ummi tace kar ta sake mayar musu da magana, maimakon rikice tana so a ko da yaushe ta nemi zaman lafiya da su..tana tafe tana hawaye a haka har ta k’arasa d’akin Ummi… bata tarar da ita a d’akin ba dama abunda take so kenan dan haka ta zaro akwati ta je d’akinta na b’angaren su ta jido kayanta ta had’a komai tana gama had’awa ta kira sister d’inta ta ce mata “za ta zo ta yi mata kwana biyu…” yayar tata tanata murna a haka suka yi sallama ta zauna zaman jiran Ummi ta samu ta yi mata sallama daga nan ta kama gaban ta..sai dai kuma Ummin tana zuwa tace bata san zance ba!!! Ba yadda Munirat bata yi da ita ba amma Ummin ta hana ta tafiya, k’arshema sai ta rufe ta da fad’a, tana ji tana gani haka ta hak’ura ba dan ranta ya so ba… …. Kamar kullum bayan sallar isha, sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta yarda ta bita suka sauk’a domin yin dinner. Dama sun san yau su Daddy suna da meeting, dan haka shi da Yassira da Yashjub basu zauna dinner ba. A dining d’in suka tarar da kowa har Yahanasu… a kusa da Mommy Ummi ta ja kujera ta zauna da murmushi a fuskarta tace ‘’Barka da dare Mommy’’ ba yabo ba fallasa da d’an murmushi a kan fuskar Mommyn ta ce’’Lafiya Ummi ya gida ?’’ ‘’Alhamdulillah’’ta bata amsa daga nan Munirat ma ta gaida Mommy da Baaba Larai da Yahanasu kafin ta ja kujera ta zauna… sai da ta zauna tukunna ta lura ashe opposite d’in Yassir ta zauna, ta so ta tashi amma kuma in ta tashi duk inda za ta koma to dole sai dai ta shiga tsakiyar su Kausar ne dan a rarrabe suka zazzauna, dan haka kawai sai ta hak’ura ta zauna. Cikin girmamawa Yahanasu ta gaida Ummi ita kuma ta amsa mata da kulawa. Tana shirin zuba abinci suka had’a ido da Yassir, a hankali ya d’an motsa bakinsa alamun ‘Hi’ D’auke kanta kawai ta yi ta ci gaba da zuba musu abinci itada Ummi. Murmushi yayi kafin ya juya ya kalli Ummi ya ce “Ummi ina wuni’’ Da sauri Ya’isha da Baaba Larai suka kalle sa, sai kuma suka d’auke Kai suna mamaki. Cikin jin dad’i da murmushi Ummin ta ce ‘’Lafiya Alhamdulillah,Yassir.” Wata kalar dariya Yasmeen ta yi ciki-ciki kamar irin Mutum yana k’ok’arin gimtse dariyarsa d’innan amma kuma ta yadda ta tabbatar da Ummin za ta ji. Ta kuwa ji! amma sai bata kulata ba, daga haka kowa ya shiga cin abincinsa. Yassir ne ya fara mik’ewa yayi musu sai da safe yana ta satar kallon Munirat, ita bata ma lura da shi ba amma Ya’isha da Yadira sun lura. Yadira tana shirin mik’ewa Ummi ta ce ‘’Yadira d’an zauna ina son magana da ku’’. Kamar ba za ta zauna ba, sai kuma ta koma ta zauna ba tare da ta kalle ta ba, ta wani had’e rai ta d’auke Kai. Kausar ko rabin abincinta bata ci ba bata da niyyar tashi da farko amma tana jin Ummi ta ce ‘tana son magana da su’ Kawai sai ta mik’e ta wuce sama. Shiruu Ummin ta yi, kamar ta ce kowa ya tafi kawai sai kuma ta fesar da numfashi kafin ta ce ‘’Ya’isha in kun hau sama sai ku gayawa Kausar da Yassira abunda na ce…’’ Daga nan tiryan-tiryan haka nan Ummi ta zaiyyano musu labarin senator da Munirat kamar yadda ta gayawa su Daddy kafin ta d’aura da cewa ‘’Munirat ba za ta tab’a auren shi ba, dan in da ace zan bari ta aure shi to da tun lokacin da ya dawo an d’aura musu aure, ballantana kuma yanzu da yake a matsayin saurayin Yahanasu.’’ cikin lallami Ummi ta ce “Dan Allah komai ya wuce, let bygones be bygones(a bar baya ya zamto baya).” ‘’Ummi komai ya riga ya wuce, what more do you need from us(me kuma ki Ke sake buƙata daga garemu?)’’. Yusra ta yi mata tambayar cikin tsare ta da Idanuwa. Cikin rashin jin dad’i Ummi ta ce ’’Yusra zumunci da zaman lafiya nake so a tsakanina da ku, sannan a lokacin da Daddyn ku ya aure ni ya yi alk’awarin zai rik’e Munirat kamar y’ar cikinsa, ya ce za ta ji dad’i a tsakanin ku… zaman gidan nan ba zai tab’a yi mata dad’i ba indai kuna yi mata irin haka… Ɗazu fa tarar da ita na yi ta had’a kayanta zata bar gidan nan, kinga ai hakan bai yi dai-dai ba, pls ku zauna lafiya, dukkanmu a k’ark’ashin mutum d’aya muke… duniyar ma duka duka nawa take?d’an zama ne fa na k’anƙanin lokaci bayaga haka ma na tabbata nan da five years ba lalle a tarar da hatta Yadira a cikin gidan nan ba.. Ya’isha ki gayawa Kausar in kin hau sama ki yi mata bayanin da na yi muku ita da Yasira tunda su ne ba….’’ Da k’arfi Ya’isha ta dire kofin juice d’in da ke Hannunta wanda hakan ya katsewa Ummi maganarta! Allah ya so cup d’in unbreakable ne da tuni ya fashe saboda yadda ta wani buga shi. Cikin tsananin b’acin rai ta mik’e ta kalli Munirat wadda ta d’ago itama tana kallon ta, zuciya a wuya ta ce ‘’Dan girman Allah yadda kika had’a kayanki kar ki kwance ki kwashe su ki yi gaba yau! kar in sake ganin k’afarki anan.’’ Sannan ta juya ta kalli Ummi tace’’Ummi do you know wat your problem is? (Ummi kin san menene matsalarki?)” bata tsaya jin mai Ummin zata ce mata ba ta ce’’Son kai!. son kai shine matsalar ki… kalli yadda kika tisa mu a gaba kina mana maganar dole sai mun so y’arki!! dole sai mun yi zaman lafiya da ita, shin wai ana dolene!??. kuma na ga ita ta janyo komai tun asalin farko tunda tun da ta zo gidan nan babu wanda ya Kyamaceta Despite the fact that She’s not even our class but (dukda kuwa cewar ita ɗin ba ajinmu bace ba amma) a hakan muka ja ta a jiki duk dan a zauna lafiya amma duk bataga wannan ba haka nan ta zo ta tafkawa Mutane shirme… Kasancewar wani wai saurayintane tun farko ko ma mijinta ne tun farko hakan ba zai goge laifinta ba tunda ai dai yanzu Yahanasu ya zo zai aura amma bataga wannan ba tsabar cin fuska haka ta biye masa.. Although (dukda)Yahanasun ta ce babu ruwanmu da case d’inta amma yadda ki ke supporting y’arki kike k’ok’arin goge laifinta k’arfi da yaji ni shine matsalata da ke!!!!! sannan bari ki ji in gaya miki ni kam har abada i’ll never be friends with her (babu zaman lafiya tsakanina da ita) tunda na lura ba ki san mutunci,kawaici da arzik’i ba ke kawai naki kika sani, you are morethan selfish (kin fi son kai son kai) dan haka babu zaman lafiya a tsakani na da ke da y’arki har abada wallahi… ba da irinku ake zaman lafiya ba dan naga idan aka baku fuska next time sai kun yi abunda ya fi wannan, dan haka dole mu taka miki burki mu nuna miki matsayinki a cikin gidan nan tun yanzu, ke ba kowa bace ba, you are just holding a place here(cike waje kawai kike yi a cikin gidan n…..)’’ Cikin tsawa Ummi ta mik’e tsaye ta ce ‘’Ya’isha!!’’ Itama Ya’ishan cikin tsawar da ta fi ta Ummi ta ce ‘’Kar ki sake d’aga mini murya!!! gaskiya ce dole in fad’eta. kuma naga da farko ba ku san mu ba muma bamu san ku ba amman ai mun rayu kuma kun rayu, to a kan wanne dalili ne za ki tilastamana yanzu akan dole sai mun kula y’arki?. Sannan last warning gareki ‘kar ki sake cewa za ki tara mu da ni da siters ɗina ki yi mana fad’a ko kuma ki bamu wani useless labarinki wanda mun riga mun san shi dan an fad’a mana tun d’azu da safe… and one more thing(sannan abu ɗaya da nake so in sake jaddada miki)…. Idan kina son magana da Yasira ko Kausar to kin san hanyar inda d’akunan su yake, kar ki sake cewa za ki aikeni tunda ni ba y’ar aiken ki bace ba…” Tana gama fad’in haka ta wuce ta bar wajen fuuu kamar za ta tashi sama…. Tana wucewa Yusra itama ta mik’e ta bi bayanta haka ma Yadira. A hankali Yasmeen ta mik’e ta ce ’’Mommy good night, muna da wani surgery d’in gobe da sassafe… Baabaa Larai a yi min faten doya irin na jiya pls’’ Ta fad’a hakan tana langab’ar da Kai. Murmushi Baaba Larai ta yi, daga nan ta ce ‘’inshaaAllah y’ar albarka, Allah ya taimaka. sai da safe.’’ ‘’Na gode Baaba Larai d’inmu’’ Yasmeen ta fad’i hakan da murmushi akan fuskarta kafin itama ta wuce abunta ba tare da ta kalli inda Ummi take nan a daskare ba. A hankali Yahanasu ta lumshe idanuwanta a ranta ta ce’’inama Bashir bai shigo cikin rayuwarta ba,” Tunda gashi dai yanzu ba auren ta zai yi ba amman kuma ya zamto silar da zai tarwatsa auren Daddy da Ummi wanda take addu’ar a samu ya d’auree har abada. Da gudu Munirat ta mik’e ta bar wajen ta na hawaye…. wannan shine duka biyu!!! ga cin mutunci gashi kuma Ummi ta hanata yin magana. A hankali Mommy tace ‘’Sai da safen ku’’ Daga nan ta mik’e ta bar wajen. Ummi za ta bar wajen kenan Yahanasu ta mik’e ta matso ta kamo Hannunta tace “Ummi dan Allah ki yi hak’uri, ko da ace kowa bai fahimce ki ba to ni na fahimce ki, tun a jiya Yash yayi min bayanin komai ta waya, nima kuma a jiyan duk na yi wa Yasira bayani kuma na ji suna maganar Yassira ta tura a group d’in su dan haka kinga sun san labarin kenan kawai dai gaskiyar ce ba sa so kuma suke k’ok’arin dannewa tunda dama abunda ya farun ba shine asalin dalilin su na kyarar ku ba. kawai ki yi hak’uri Ummi, ki daina k’ok’arin had’a kansu da Munirat dan ba zai tab’a had’uwa ba… ki zuba musu ido kawai. ki kwantar da hankalinki Munirat is not alone (ba za ta ji kaɗaici) a cikin gidan nan ba, tunda ina nan, ba za ta yi zaman kad’aici ba, inshaaAllah…’’ Cikin takaici Ummi ta ce ‘’Na gode Yahanasu, amma ko ba komai ya zama dole in ji takaicin yadda Mommy ta ke yin burus akan lamarin nan… ki duba ki ga yadda nake bata girmanta amma ita in Yaran nan za su wanka min mari ba za ta tab’a hanawa ba.’’ Cikin katseta Baaba Larai ta ce ‘’Ummi, sai dai fa ki yi hak’uri, duk cikin Yaran nan ki gaya min waye kika ga yana jin maganar Mommy a cikin su? Tun daga kan Yassira har izuwa kan Yadira Yahanasu kada’i ke yi mata biyayya amman ragowar duk binsu kawai take yi. Dalilin da kika ga yasanya bata saka muku Baki Shine Bata so ta shiga fad’an kuma su disgata a gaban ki, dan itama ba jin maganarta akeyi a cikin gidan nan ba!! hatta shi kanshi Daddy d’in ba bi ta kanta yake yi ba kuma na san kin san me ke faruwa a tsakaninsu shi da ita tunda ta ce min rannan a gabanki ya koreta……. Ba wai Ina gaya miki hakan dan ki raina ta ba, A’a ina gaya miki ne dan ki daina jin haushin ta, ki yi mata uzuri ki barta da abunda ya ke damunta…. Dan haka idan zan baki shawara ki d’auka to ki daina k’ok’arin tilastawa Yaran nan akan dole sai sun bi ki dan hakan da kike yi kamar kina sake rura wutar rikici a tsakaninki da su ne. Sannan wani abunda na lura kamar baki sani ba shine ko dambatuwa kuka yi da ke da Yaran nan to fa idan ubansu ya zo bayansu zai bi, dan babu abunda ya tsana a duniyar nan kamar ka tab’a masa ƴaƴa… Dan haka tunda har kika ga uwarsu ma ba ta tilasta musu to kema ki koma gefe ki zubawa kowa ido.’’ Tana gama fad’ar haka ta wuce, ta nufi sama wajen Mommy.. .. A d’akinta ta sameta tanata faman safa da marwa… tana ganin shigowarta ta yi maza ta k’arasa wajen ta, a d’an rikice ta ce “yauwa Larai, ke nake ta jira, ya ake ciki? Ajiyar zuciya Baaba Larai ta sauk’e kafin ta ce ‘’Na barta a k’asa, ita da Yahanasu’’ Cikin katseta Mommy ta ce ‘’Ba maganarta nake yi miki ba, maganar Yashjub nake yi..na gaya miki tun jiya ai..maganar ki gaskiya ce, da Bakinsa ya tabbatar min amman har yanzu ban ji kin ce komai ba.’’ Murmushi Baaba Larai ta yi kafin ta nemi waje ta zauna sannan ta ce ‘’Tunda kika ji na yid shiru akwai dalili…. yanzu Yahanasu ce naga Bakinta ya fara bud’uwa, kina ganin ba matsala kuwa?. Na lura da ita, bata shakkar kowa kwana biyun nan, yanzu haka a gabana ta gama aibanta su Kausar sannan k’iri-k’iri Ina kallon idanunta tana kallon nawa amma ta bi bayan Ummi ta bata gaskiya… shiyasa na ke ganin gara a yi wani abun tun kafin ta je ta b’allo ruwa.” Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin ta ce ‘’Larai bar batun Yahanasu tukunna, Ina tunanin shurun nata da rashin fitar da take yi ne ya shafe ta har a ta b’angaren aure fa, ko ke ba ki yi wannan lissafin ba? Ba ki fahimci komai ba?. Saboda har ga Allah na fara jin tsoron zalintar Yahanasu da nake yi dayawa har haka saboda nawa gain d’in(ribar)’’ Shiruu Baaba Larai ta yi kafin ta ce ’’gaskiya ni kam ba zan bi ta taki ba Khadija, saboda idan Bakin Yahanasu ya bud’u ba ke kadaice a wahala ba, bari ki ji in gaya miki yau tun safe da ta bar gidan nan bata dawo ba sai magrib.’’ Cikin rashin jinn dad’i Mommy ta nemi guri ta zauna itama a kusa da ita kafin a hankali ta ce ‘’shikenan Larai, ki yi abunda kike ganin ya dace.’’ Murmushi Baaba Larai ta yi kafin ta gyara zama ta ce ‘’Ita kuma Ummi………..’’ BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *27* Sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta fasa zuwa gidan yayarta…da fad’a da rarrashi duk ta haɗa tukunna ta samu ta d’an kwantar mata da hankali, dukda kuwa ita ma hankalin nata ba a kwance ya ke ba… abun tausayi haka itama Munirat d’in ta shiga kwantarwa da mahaifiyar tata hankali. sun jima suna magana kafin Ummi ta mik’e ta nufi wajen Daddy jiki ba kwari. A bakin k’ofar shiga parlourn suka had’u da Yasmin, tana shiga Yasmeen d’in kuma tana fitowa..ko kallon ta bata yi ba Itama Ummin bata kulata ba. Da sallama ta shiga, ba ta same shi a parlournsa ba sai a chan cikin d’akinsa a zaune a kan gado, Ya yi shiruu alamun tunani yake yi. A kusa da shi ta je ta nemi guri ta zauna kafin a hankali ta ce ‘’Barka da dawowa Daddy, ya meeting d’in?’’. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘’Alhamdulillah’’ Daga nan ya mik’e ya fad’a toilet. Har ya fito tana nan a zaune, ta yi zurfi a tunani.. Sai da ya gama shirin bacci tukunna ta ce ‘’Bara in kawo maka abinci’’ Ta fad’i hakan tana shirin mik’ewa. Cikin dakatar da ita yace ‘’don’t bother, a k’oshe na ke.’’ Cikin kwantar da murya tace ‘’Daddy, ka d’an ci ko kad’an ne m….’’ ‘’Wai Saddik’a ni k’aramin Yaro ne?d’ura zaki yi min ko me? Na ce miki a k’oshe nake amma kin bi kin ishe ni… daga meeting na dawo Ina buk’atar hutu shin baki da fahimta ne????” A hankali ta ce ‘’ka yi hak’uri, Allah ya huci zuciyarka’’… Har zai kwanta sai kuma ya ce ‘’Ki koma parlour ko kuma ki zab’i wani bedroom d’in ki kwana, ban ce ki fita a side d’ina ba…kawai ki nemi wani bedroom d’in a parlourn..’’ Sai da ya sake cewa’’bakya ji na ne?’’ Tukunna da kyar Ummi ta ce ‘’to Daddy, sai da safe.’’ Washegari da sassafe ta tashi, tunda ta yi sallar asuba ba ta koma ba, dama tun a daren jiyan ta fitar da abincin da ya ce ba zai ci ba ta saka a fridge dan a lokacin hatta gwaggo ta riga ta tafi side d’insu na masu aiki. Had’add’en breakfast mai rai da lafiya yau ma Ummi ta shiga had’awa Daddy… tana cikin yi su gwaggo suka shigo dan haka ta shiga akayi har na gaba d’aya gidan tare da ita. K’arfe bakwai da kwata suka kammala, dan haka ta d’auki na Daddy ta nufi sama da shi cike da sassarfa. A bakin k’ofar d’akinshi ta same sa yana gyara zaman necktie d’insa, tun kafin ta gaida shi ya ce ’’koma da abincinki yanzu ma, na k’oshi’’ A hankali ta nufe sa da tray d’in a hannunta da niyyar idan ta je ta durk’usa ta bashi hak’uri, amma tana zuwa kusa da shi tun kafin ta durk’usa ya yi wani irin fatali da abincin wanda ta sanadiyyar hakan gaba d’aya parlourn, kayan jikinsa da kayan jikinta suka b’aci…. Cikin fushi ya juya ya koma d’aki ya bar ta nan a tsaye cikin tsananin tashin hankali da mamaki, bata san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka shiga tsilalo mata ba. Da kyar ta samu ta goge wajen tana yi tana kuka haka nan ta je ta chanja kayan jikinta tukunna ta dawo ta tattare kwanukan ta nufi k’asa. A hanyar stairs ta tsaya ta goge hawayenta tukunna ta k’arasa sauk’a ta nufi kitchen. A kitchen d’in ta tarar da Yasira Kausar Yasmeen da Ya’isha, da alamun kowa fita zata yi kuma masu aikin ba su gama jerawa a kan dining d’in ba shine suka zo suke d’iba anan d’in… a cikin su ba wanda ya ce mata ci kan ki haka ta wuce ta ajjiye kwanukan ta shiga wanke Hannunta… Cikin rashin mutunci ta ji Ya’isha na cewa ‘’Dad’ina da talaka bai iya samun guri ba, a yi employing d’inka amma ka nemi zak’ewa, na rantse da Allah Asabe duk ranar da kuka sake yin letti ba ku jera mana abinci har kuka ja muka makara ba to ko wacce shegiya sai ta koma inda ta fito, sai ku dinga yin abu kamar ku kuka haifi Mutum….. Mtswwwww’’ Ta k’arashe maganar tata tana mai jan wani uban tsaki, daganan ta sa Kai ta fice. Wata dariya Yasmeen ta yi, Irin wadda ta yi wa Ummi jiya ciki-ciki. Dariya sosai Kausar ita kuma ta yi kafin tace ‘’Kin ga Malama, ki saki Baki ki yi dariyarki dan babu uban wanda ya Isa ya hanaki.’’ Ahankali amma yadda ta tabbatar Ummin za ta ji Yasira ta ce ‘’Tana jin tsoron a shiga tsakanin ta da Daddy ne’’ Cikin dariya k’asa-k’asa ta rainin hankali Kausar tace ‘’au,haka ne fa’’ Daganan duk suka d’auka abincin da suka zuzzuba suka fita suka nufi dining table banda Yasmeen wadda ta tsaya haɗa tea a cikin kitchen d’in. Har Ummi ta fita sai kuma ta tuna akwai flask d’in da ferfesun ciki bai gama zubewa ba dan haka ta juya da niyyar komawa ta cewa gwaggwo su juye mai kyau ne… a k’ofar kitchen d’in suka yi kiciɓus da Yasmeen wadda ta yi kamar irin ta tare k’ofar nan ne..ita ba ta matsawa Ummin ta wuce ba sannan ita bata fito ba.. da mamaki Ummi take kallon yarinyar tana so ta ga iya gudun ruwanta. A hankali Yasmeen wadda ta hango Daddy yana sauk’owa daga bene tace “na ga kin shigo da kwanuka a hargitse kuma idonki kamar kin yi kuka, gaya min gaskiya dukan ki Daddy ya yi?’’.. Dama tun ɗazu da kyar Ummi take danne kanta dan bata so ta kula Yaran amman duk maganganun da suka yi a kitchen d’in ta san da ita suke ga kuma takaici da tashin hankalin da Daddy ya tsoma ta a ciki tun jiya shiyasa duk yadda ta so hana kanta ta kasa dan haka ta d’aga Hannu ta zabgawa Yasmeen wani irin gigitaccen mari, dai-dai nan kuma Daddy ya k’arasa saukk’owa cikin parlourn. Wani irin kuka Yasmeen ta saka ta durk’ushe a wajen ta dafe kunnnenta tana ihun ‘’Wayyo Allah kunnena’’ Dai-dai nan Daddy ya k’araso wajen a gigice, da k’arfi ya ce ‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’ sakamokon ganin jini yana zubowa ta kunnen Yasmeen. Sai a lokacin Ummi ta ji ashe wai ‘Yasmeen tana da abu a cikin kunnenta wanda ya ke zuk’o mata magana sakamokon rashin aiki da kunnuwan nata basa yi sosai.’ kuma ba kunya ba tsoron Allah a take Kausar har da rantsuwa ta yi tsalle ta dire wai “ai sun gayawa Ummin jiya da ta yi yunƙurin marin Yasmeen d’in amma shine yau sai da ta mare ta, shikenan yanzu in ba da kyar ba ta danna mata abun chan ciki ta lalata mata kunne gaba d’aya.” Cikin tsananin gigita Ummi ta ce ‘’Kausar ki ji tsoron Allah, yaushe…. Wata rikitacciyar tsawa da Daddy ya buga mata ce ta sanya ta kasa ci gaba da magana…cikin tsananin fushi ya ce ’’ki b’ace min a wajen nan tun kafin na illataki .’’ A hankali sannan k’afafuwanta suna wani irin karkarwa ta samu da kyar ta juya ta kama hanyar sama zuciyarta tana wani irin tafarfasa. Yayinda su kuma suka d’unguma kai Yasmeen asibiti, gaba d’ayan su. •••••• Sai yau Manubiya ta d’auki wayarta a jikin charji daga gidan Ammi, dan sai da ta bar wayar ta yi awannin da aka rubuta ana buk’atar ta yi a jikin charjin. Layinta na jiya da suka yi wa register ta saka, bayan kamar 30 minutes ta d’auki wayar ta dudduba daganan ta d’auko katin Yashjub cikin nutsuwa ta juye numbersa tukunna ta tura masa sak’o kamar haka ’’Good morning Sir(ina kwana sir), yau na kunna wayar tawa daga charji, my mail is empty as for today(yau, mail ɗin nawa ba komai a ciki)..idan sun turo I’ll report everything to you on Friday (zan haɗa in sanar maka komai ranar juma’a).. InshaaAllah Thankyou(na gode)... Manubiya Musa..’’ Fitowar Yashjub daga wanka kenan dan lokacin 7 dai-dai,itama Ammi ce ta ce mata ta tabbata ta je da wuri fiye da yadda take zuwa kullum, wai tana da bak’in da za su zo daga Abuja so akwai aiki sosai.. Yana fitowa ya ga wayarsa ta yi k’ara dan haka ya k’arasa ya d’auka ya shiga duba message d’in, dama ya saka a ransa maybe ita d’in ce dan tun jiya yake ta jiran ya ga kira ko messge d’inta. Murmushi kawai ya yi, ya sake karanta sak’on ya kuma maimaitawa ya sake maimaitawa kafin ya ajjiye wayar da kyar yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya… yanzu mene ne abun yi, saboda duk taurin kansa da kauce-kaucen sa ya riga ya sak’k’o, ya fahimci yana mahaukacin son Manubiya..duk yadda ya yi ta denying yana kaucewa, a iya jiya kad’ai ya tabbatar k’aunarta yake yi, k’auna ba ta wasa ba, amma kuma ta ya zai fad’a mata abunda ko Najeeb yana tunanin anya zai iya fad’awa kuwa…. numfashi ya fesar ya nemi guri ya zauna a ransa yace ‘’Yashjub a yadda kake son Manubiya, b’oye b’oye ba naka bane ba,’’ domin shi kansa ya san yana da buk’atar wani abun ya faru soon…a fahimci juna a yi aure tun kafin sonta ya zautar da shi sannan ga wannan cousin d’in nata da ya ga take-taken kamar shima sonta yake yi, kasancewar sa na gida ne ya sanya Yashjub yake ganin gara ya d’auke Manubiya tun wuri tun kafin iyayenta su yi abunda zai kai sa lahira ta hanyar aura mata Abbakar. A part from all these (bayaga duk waennan abubuwan ma) a yanda yake jin Manubiya a zuciyarsa da ransa to tabbas ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa daga nan zuwa watanni hud’u ko uku gaba ba tare da ya mallake ta a matsayin matarsa ba….. Da wannan tunanin ya shirya ya fice office, ko Daddy bai tsaya jira ba dan yana buk’atar ya yi tunani sosai sannan ya san ta inda zai fara Kafin Daddyn ya zo su fara aiki,kuma yana da buk’atar lek’awa d’ayan company d’in nasa duk a yau. …… Manubiya tana ajjiye wayar ta juya kenan su ka yi ido biyu da Maamaa, da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace’’Maamaa Ina kwana.’’ sai kuma ta fara k’ok’arin fita daga kitchen d’in. Murmushi Mama ta yi sannan ta ce’’ni kam Manubiya tsoro na kikeyi ne? naga kwata kwata kin k’i ki yarda ki saki jiki da ni ga shi kuma k’addara ta had’a mu zama guri d’aya,ya kenan?’’ Ta k’arashe maganar tata da tambaya tana murmushi. Murmushi Manubiya ta yi kafin a ranta ta ce ‘’Tabbas k’addara ta had’a ni zama guri d’aya bama da ke kad’ai ba har da wanda nake gudun ki domin shi.’’ A fili kuma sai tace ‘’Ba komai Maama ba gudun ki nake yi ba kawai dai abubuwan ne suka d’an yi min yawa,shiyasa.’’ Cikin rashin jin dad’i Maama tace’’Ayya!na ji Ammi tana cewa mamanki ma ba lafiya ko?’’ Ahankali Manubiya ta d’aga kanta alamun’’eh’’ Cikin tsananin jin tausayin ta maama ta ce ‘’Allah ya bata lafiya Allah ya sauwwak’e, ku yi ta addu’a za ta warke inshaaAllah, kin ji ko?’’ Ahankali ta jinjina mata kai tukunna tace ‘’nagode Maama’’ ta fad’a hakan tana mai Jin tsananin k’aunar matar na shiga ranta. Murmushi Mama ta yi, ta matso ta d’an shafa fuskar Manubiya tukunna ta ce ‘’Allah ya yi miki albarka” daga nan ta wuce ta fita daga kitchen d’in.. so gamon jini!! ita dai haka kurum Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar, tana jinta ne har cikin ranta……. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *28* Har wajajen 11 shiru babu Daddy ba Yasira a company. Baƙin da suka yi ma Yashjub ne ya yi handling d’insu shi kad’ai, gashi yana ta kiran number Daddy amma baya d’auka ita kuma Yasira nambobinta duk ba sa shiga. Dan haka Baƙin suna tafiya shima ya kamo hanyar gida. Sai k’arfe 10 tukunna likitocin da su ka karb’i Yasmeen suka fito, cikin son fahimtar dasu Babban Likitan ya kalle su ya ce “It’s nothing serious(ba wani babban abu bane ba), dan bai tab’a komai ba kawai dai d’an kurjewa ta yi shiyasa kuka ga jini. abun nata dama ina so in bata sabo shine kawai muka tsaya aka d’an yi dressing wajen na bata sabo na bata drugs da 1 week off ta huta a gida, Allah ya kare gaba.’’ Cikin samun relief dukkan su suka ce ‘’Ameen’’ sai a lokacin tukunna Yasira ta d’au waya ta kira Mommy take gaya mata komai. Office Yasira ta wuce Yusra da Ya’isha da Yadira kuma school, yayinda Daddy da Kausar suka kama hanya domin maida Yasmeen gida. Suna shiga Daddy ya cewa Kausar ta kai Yasmeen d’akinta shi kuma ya nufi b’angaren Ummi….. Bai same ta a d’akin nata ba ashe ya baro ta a k’asa a d’akin Yahanasu wadda zazzab’i ya rufe tun jiya da daddare ba wanda ya sani. Munirat ya tarar tana share d’akin, cike da girmamawa ta durk’usa har k’asa ta gaida shi, ba yabo ba fallasa ya amsa kafin ya ce mata “Ina saddik’a?’’ A hanakali tace masa ‘’Tana d’akin Adda Yahanasu wadda batada lafiya’’ A ranta tana mamakin Allah dai yasa lafiya dan bata tab’a ganin shi a dai dai wannan lokacin a gida ba, kuma a side d’in Ummi. Cikin fushi ya juya da niyyar fita, a bakin k’ofa suka yi kicibis da Ummi wadda ta ji shigowar su ta biyo domin ta ji ya jikin Yasmeen d’in…. tunda suka fita ta ke trying numbers d’insa, saboda ita shi kuma ya saka wayoyinshi gaba d’aya a silent.. Da kyar Daddy ya iya cewa ‘’Munirat give us a moment (Munirat bamu waje)” ya fad’i hakan idanuwansa a kan Ummi, ba tare da ya kalli Munirat d’in ba. Da sauri ta ajjiye parker da abun sharar ta fice daga d’akin, tana tafe tana waiwaye gaba d’aya hankalinta a tashe tana mamakin me ya had’a su haka dan ita Ummi bata ce mata komai ba tun ɗazu, gashi ta ga ran Daddy a mugun b’ace!!! ba abunda ya fi d’aga mata hankali irin yadda ta ga mood d’in nasa, tsoronta kar ta je ya bugi Umminta… tana tafe tana lissafi tana waiwaye haka ta fice a parlourn, bata yi auni ba kawai ta ji ta afka kan Mutum, da sauri ta ce ‘‘Innalillahi’’ sai kuma ta fara k’ok’arin kwace kanta daga rikon da Yassir ya yi mata. Tunda ta taho tana kallon baya ya ganta dan lokacin dai-dai shi kuma ya fito daga corridor na side d’in Mommy , ahankali ya wani lumshe ido ya bud’e saboda yauma riga da wando ke jikinta na bacci irin me bin jikin nan, rigar iya cinya wandon kuma har k’asa,dan haka a ransa ya ce ‘’lucky me’’ Ganin bata gansa ba ne ya sanya shi sake nutsuwa ya ƙi motsi gudun kar ya ankarar da ita,ai kuwa da ikon Allah ta afka jikinsa!!! Without thinking twice shi kuwa ya rungume ta gamgam…. tana d’agowa su ka yi ido biyu da shi, cikin tsananin firgici ta ce ’’get off me, (ka cika ni) baka da hankali ne’’ Ta k’arashe maganar cikin tsawa. Wani irin murmushi ya yi kafin ya ce ‘’Munirat yo ai ko malaikan mutuwa ne ya zo d’aukar raina to Sai ya d’aga min k’afa na gama appreciating moment d’innan (godewa lokacin nan) tukunna ..’’ Wani irin kuka ta saka kafin ta fara k’ok’arin kwace kanta tana magiya tana kai masa duka, ganin tana neman cika masa kunne ne ya sanya ya fara k’ok’arin kissing d’inta….. A gigice ta kwala wata mahaukaciyar k’ara dai-dai shima Yashjub ya ce ‘’Yassir’’ Cikin tsawa …………. Achan d’aki kuwa, Munirat tana fita Daddy ya cewa Ummi ‘’Ki had’a kayanki, duk wani abunda kika san naki ne, ki tartare, ki bar min gidana’’ A hankali Ummi ta ce ‘‘Daddy har me ya yi zafi haka? Wallahi Kausar k’arya take yi, ban san Yasmeen tana da matsala a Kunne ba! Sannan ya kamata ka tsaya ka ji abunda Yaran nan su ka yi min kafin ka yanke wannan d’anyen hukunci hak….’’ Cikin katseta Daddy ya ce ‘’Na san k’arya Kausar ta yi miki, na san basu gaya miki Yasmeen tana da matsala a kunne ba. Kinsan abu na farko da ya fara had’ani da ke?’’. Cikin zubar kwallah Ummi ta girgiza kanta alamun’’a’a’’ Cikin fushi Daddy ya ce ‘’Ranar da kika zo d’akina kika bamu asalin labarin Munirat da Bashir, me na ce miki ??’’ Cikin inda inda saboda duk ta rikice ta ce ‘’Cewa ka yi komai ya wuce, amman Daddy su Kausar basu..’’ Cikin tsawa ya ce ‘’ba wannan ba!d’ayar maganar tawa ta k’arshe, me na ce miki Saddik’a?’’ A gigice ta ce ‘’Cewa ka yi zaka saka su su bani hak’uri’’ ‘’Good’’ Daddy ya furta yana mai sake matsowa kusa da ita wanda hakan ya sanya Ummi ta d’an ja baya dan ba kad’an ba ta tsorata da Daddyn, bata tab’a ganin shi a haka ba tunda su ke. Cikin zafin zuciyar da ya ke ji tana taso masa ya ce ‘’na fad’a miki bara in sake maimita miki! dan naga kamar kin manta, Abu uku na fi tsana a yi min waenda su ne suke janyowa Mutum ya ga other side d’ina; A yi crossing d’ina A ci Amata na uku, a nuna min ban Isa ba!! Duk yadda na kai ga son Mutum da ganin girman sa muddin ya yi min haka to babu dalilin da zai hana ni yin kacha-kacha da shi…... da nace miki ki jira zan sanya su su baki hak’uri dan me yasa kika yi gaban kanki? saboda kin raina ni? saboda ban isa ba?..na ji sarai na kuma san me kika yi Yasmeen ta gaya min yadda kika tara su a dining table kina cewa su zauna lafiya da Munirat, kina gindaya musu sharud’a kina jera musu warning alhalin su already komai ya riga ya wuce a wajen su….. Me kike so ki yi proving by doing that??(ki nuna ta hanyar yin hakan??) bari kiji nan gidan ubansu Yasmeen ne, Munirat kara kawai na yi mata nake bata shelter saboda ke, and if za ki nemi ki takurawa ƴaƴana saboda ita har ta kai ga kina k’in jin maganata kina k’etare umarni na to kuwa ban ga dalilin da zai sanya in ci gaba da zama da ita a gida d’aya da ke kan ki ba!!! Sannan yau har kina da guts d’in da za ki d’aga Hannu ki mari Yasmeen?kin tab’a gani na yi wa Munirat kallon banza??? Ko ma me Yasmeen ta yi miki ko ma menene Saddiƙa ban ga dalilin da zai sanya ki mare ta ba’’ Cikin share hawaye Ummi ta ce ‘’ko menene?’’ Ciikin fushi Daddy ya ce ‘’Ko uwar ki ta zaga ban baki ikon ki tab’a d’aya daga cikin Ƴaƴana ba!!! Kin tab’a ganin uwar da ta haife su ta d’ora Hannu akan su??’’. Wani Irin kuka Ummi ta fashe da shi ta durk’ushe a wajen, dan ba wanda ya fad’o mata a rai a dai dai wannan lokacin sai Marigayin Mijinta.. Sam bata bawa Daddy tausayi ba, dan shi wani irin haushi ma ta ci gaba da bashi, ji yake yi kamar ya yi ball da ita. Kwanakin baya Mommy ta tuno masa da Khadija yanzu kuwa Saddik’a ce ta tuno mishi da ita..ta yadda ta nuna masa bai Isa ba, bashi da girma da daraja!!! ta yadda ta nuna son kanta ta fifita y’arta k’iri k’iri sama da shi. Cikin fushi ya sake cewa “ki tashi ki had’a kayan ku…” Maganarsa ce ta mak’ale sakamokon ihun Munirat da suka jiyo..da gudu Ummi ta nufi waje..kafin ta k’arasa ta fara jiyo na Yassir shima….. Ummi na fita Daddy ya bi bayanta da kallo cikin takaici…. kafin kuma ya nufi wardrobe d’inta da kansa ya fara firfito mata da kayanta yana sauk’e akwatunanta sannan ya ja akwatunan ya fitar parlournta daga nan ya wuce ya fitar dasu daga side d’inta gaba d’aya!! ya nufi chan babban parlourn da ke a saman… ko damuwa da ife-ifen Yassir bai yi ba kawai shi a halinda ake ciki babban burinshi shine Ummi ta fitar masa daga gida, kawai shi dai ta fita, ya san in ta fita shine zai samu nutsuwa….. … A chan parlourn kuwa… Yashjub yana hango su bayan ya daka masa tsawa, sai kuma ya nufe su cikin tsananin tashin hankali. yana zuwa bai yi wata wata ba ya janyo Yassir ya kifa masa wani gigitaccen marinda har sai da ya sanya Yassir d’in ya kai k’asa yana shirin tashi ya zaro belt d’in jikin wandon shi ya rufe shi da duka yana ball da shi. Yanayin dukan da Yashjub ya ke yi masa ba irin dukan da normal Mutum zai yi bane ba saboda k’arfin Yashjub d’in na daban ne shiyasa duk yadda Yassir ya so daurewa sai ya kasa ga shi ya kasa tashi dan yana yunk’urawa zai tashi Yash d’in yake kuma kai masa duka da k’afa ya kwantar da shi. Kusan a tare Mommy Kausar da Ummi suka k’araso wajen…. Kausar ce ta fara k’arasawa kusa dasu da niyyar rabawa ai kuwa itama ya zula mata belt dan dama haushin ta yake ji. Da sauri Mommy ta matsa ta janyo Hannunta ta mayar da ita gefe, tukunna ta yi kan Yashjub d’in… Da kyar ita da Ummi suka samu suka rik’e Hannun Yashjub wanda idanuwansa suka yi jaa sosai. Cikin tsananin b’acin rai Mommy ta fashe da kuka ta ce ‘’haba Yash, wanne irin abu ne wannan? Ko Yaro d’an shekaru sha takwas ai ba ka saka a gaba da duka irin wannan ba’’. Cikin rashin jin dad’i da dauriya Ummi ma ta ce ’’Yash baka kyauta ba, ko ma me ya yi maka bai kamata ka dake shi haka ba.’’ Sai kuma suka juya ga Munirat wadda ke durk’ushe a wajen Mommy ta ce ‘’me ya faru’’ Gaba d’aya ta tsorata ta gigita daga abun da Yassir ya yi mata ga kuma dukan da taga Yash yayi masa shiyasa da gudu ta tafi jikin Ummi ta fad’a ta fashe da kuka tukunna ta ce ’’Ummi dan Allah dan Annabi ki zo mu bar gidan nan, idan kuma ke ba za ki tafi ba ni gaskiya zan tafi’’. Dai-dai nan Daddy wanda ya gama janyo akwati ya cillo waje ya ce ‘’Kar ki damu, yanzun nan za ku tafi’’. Da sauri Yashjub wanda tun ɗazu yake ta karanto sunayen Allah yana k’ok’arin daidaita kan shi, ya runtse idanuwansa da k’arfi. Dai dai nan su Yahanasu da Baba larai suka hawo saman sakamokon hayaniyar da suka ji. Yahanasu ce ma ta lura da yadda gefen kan Yassir ya ke zubar da jini sai kuma taga kamar ma baya motsi da sauri ta k’arasa kansa ta shiga tattab’asa tana kiran sunan shi’’yasssir! yassir!!’’sai kuma ta juya ta kalli Baaba Larai a rikice ta ce ’’baya motsi fa’’. Cikin tsananin tashin hankali Mommy ta kalli Yassir itama ta tabbatar ba ya motsin, bata san lokacin da ta juyo ta kifawa Yash wani irin gigitaccen mari ba sai kuma ta sake fashewa da kuka ta durk’ushe a kan Yassir, cikin tashin hankali ta ce ‘’Shikenan ya kashe min Yarana, ya kashe min d’ana mafi soyuwa a gare ni, shikenan ya kashe min gudan jinina….’’ Da sauri Baba Larai ta ce ‘’Haba Khadijah, ki yi shiru mana, bai mutu ba inshaaAllah’’ Sai kuma ta durk’usa ta mikar da ita, tana tittirjewa tana kuka haka suka jata ita da Kausar suka nufi b’angarenta da ita, tana kuka kamar ranta zai fita. A hankali Daddy ya k’arasa ya dudduba sa, ba tare da ya kalli Yash ba ya ce ’’kama min shi mu kai sa d’akinsa.’’ Yana gama fad’in haka ya d’auko waya ya kira family Dr.d’insu, daga nan suka fara k’ok’arin kinkimar Yassir. Har sun kama hanyar k’ofar d’akin Yassir d’in Daddy ya d’an tsaya ya juyo ya kalli Ummi ya ce ‘’kar ki k’ara minti biyar a cikin gidan nan’’. Daga haka suka yi gaba suka wuce shi da Yashjub. A hankali Munirat ta k’arasa kusa da ita ta rungume ta cikin zubar hawaye ta ce ’’ sorry Ummi, it’s for the best InshaaAllah( ki yi haƙuri Ummi, hakan shine mafi alkhairi, in sha Allah)” Munirat ta fad’a hakan dan ita duk a tunaninta ita ta sake tunzura Daddy dan taga Daddy ya ji lokacin da ta ce su bar gidan…… A kan gado suka kwantar da Yassir, Daddy ya sake zaro waya ya shiga kiran Dr domin ya ce masa ya zo da sauri, yayinda Yashjub ya faki idon shi ya juya ya fice, ya nufi wajen su Ummi. Bai same su a main parlourn saman ba dan haka kanshi tsaye ya wuce side d’in Ummin. A bakin k’ofar d’akinta ya tsaya yana knocking, lokacin suna tsaye suna mamakin yadda Daddy ya watsar da gaba d’aya kayan wardrobe d’in Ummin, ahankali Ummi ta faki idon Munirat ta goge hawayenta ta nufi k’ofar da ta ji ana bugawa tana addu’ar Allah yasa kar Daddy ya sake creating wani scene d’in a gaban Munirat dan ita a tunanin ta shine ya sake dawowa, amma tana fita sai ta ga ashe Yashjub ne. Dukda halin da take ciki haka ta daure ta b’oye tata damuwar ta ce ‘’Yash, dan Allah dan Annabi kar ka sake yi wa d’an uwanka irin wannan dukan, Dan Allah’’ A hankali Yash ya had’iye wani k’ululun da ya mak’ale masa a mak’oshi yana mai mamakin kyakkyawar zuciya irin tata tukunna ya ce ‘’Na ji Ummi, ba zan k’ara ba amma kema kar ki je koina, I’ll speak with daddy (zan yi magana da Daddy), In ya huce’’. Murmushi ta yi kafin ta ce masa ‘’shigo’’ Ta fad’i hakan tana matsawa ta bashi hanya ya shigo cikin d’akin nata da sallama a bakinsa… da mamaki shima ya ke kallon d’akin sai kuma ya kalle ta. Cikin karyewar zuciya ta ce ‘’Ni kaina Yash bana son barin gidan nan, banaso aurena ya mutu, amma kuma kalli abun da Daddy yayi, shiyasa na ga tunda har abun ya kai ga haka gara in fita tunda lafiyata da mutuncina..tun kafin ya zo yayi fata fata da ni kamar yadda yayi da kayana, amma Ina so ka fad’a masa ko bayan na bar gidan nan cewa ina son Y’ay’ansa kuma ba zan tab’a cutar da d’aya daga cikin ku ba.’’ Yadda Ummi take hawaye da kuma abunda Daddy ya aikata tabbas ya san Ummi ba za ta yarda ta k’ara minti uku ba ma a cikin gidan, shiyasa a hankali ya jinjina mata kai kawai alamun fahimta, yayi hakan yana mai kallon windunan d’akin da kuma hanyar closet d’inta har zuwa toilet ya tabbatar babu ta inda za su fita, ya ji dad’i da balcony d’inta ya kasance a parlour ne dan wallahi ko shi ne Daddy ya yi mishi wannan tijarar sannan ya ce ya fice mishi a gida to sai ya fita ko ta window ne, daga baya ya dawo a sasanta….. A hankali ya ce ‘’Na fahimci ki, Ummi.’’ Murmushin da ya fi kuka ciwo ta yi ta ce “ka kula da y’an uwanka, Allah yayi maka albarka’’ ‘’Ameen’’ ya ce, daga nan ya juya yana zuwa k’ofar yayi sauri ya sa Hannu ya zare makullin kafin ta k’araso ta ce wani abun har ya fice ya sak’ala key d’in ta waje tana k’arasowa jikin k’ofar ta ji ya rufe su ya zare makullin…. …. Ko da Dr ya zo, ce musu yayi “ba wani abun tashin hankali bane ya samu Yassir d’in, kawai azaba ce ta saka shi ya suma sannan kurjewa ne kawai kan nasa ya yi ba wai dukan ne ya fasa masa kai har yasa yayi jini ba… Dan haka su kwantar da hankalin su” Daga nan, ya basa allurai da duk abunda ya kamata, ya tabbatar musu da “inshaaAllah he’ll be fine..” Yashjub ne ya raka shi har mota yana dawowa ya tarar da Daddy har yanzu a tsaye a kan Yassir wanda ɗazu ya farka Dr ya yi masa allurar bacci kafin ya tafi. K'arasawa ya yi ya tsaya shima yana kallon Yassir d'in…. tabbas yana son d'an uwansa amma kuma halayen Yassir kullum sake tab'arb'arewa suke yi sannan shi kuma ga yanayin zuciyarsa wadda yake sake tunzura sa ga aikata wasu abubuwan….saboda Allah bayaga girman shirmen da Yassir ɗin ya yi wa Munira ai ko ba komai bai kamata ya yi mata hakan iyayensu suna cikin gidan ba!!! Da sauri ya dakatar da tunanin gudun kar ransa ya sake ɓaci, a hankali ya sunkuyar da kansa a ransa ya ce ''bai kamata ace na dake sa ba, inda ace Yassir ya yi aure da wuri to da yanzu maybe yana da ƴaƴa biyu ma..'' Cikin dakakkiyar murya ya ji Daddy ya ce “abun da ka yi yau was incredibly stupid(gagarumin shashanci ne), ko da wasa kar ka sake yin wannan shirmen, Ranar da case d'in Yahanasu da Munirat ya faru cewa ka yi saboda ka ga muna wajen ne shiyasa baka hukunta su Yassira ba! It would be nice of u(za ka fi burgeni) idan ka ci gaba da bar mini komai a Hannuna… ban haifi ya’yana dan wani ya ci kashi a kanku ba kuma na san ka fi kowa sanin wannan.” Sai da ya juyo ya kalleshi ido da ido tukunna ya ce “Next time idan Yassir yayi laifi U report To me! (Nan gaba idan Yassir ya yi laifi, ka kawo min ƙararsa kawai)” Yana gama fad'in haka ya juya ya fita…. Daddy yana fita daga wajen Yassir fannin Ummi ya biya…..ya je ya murza ya ji a rufe kuma bai tarar da akwatunanta ba, dan haka ya yi tunanin ta tafi ne… a take ya ji wani irin sanyi yana ratsa shi, yayinda a chan wani b'angare na zuciyarsa kuma yana takaici da jin haushin tafiyar tata da kuma abunda ya yi mata…. Gaba d’aya Yashjub a hargitse yake, mari da maganganun Mommy sun yi mugun b’ata mishi rai!! Ga kuma abunda Daddy ya yi masa, sannan ga yadda ya ga Yassir and yana kyautata zaton su Yasmeen ne suka shiga tsakanin Daddy da Ummi…. Ba zai yiu fa ya zuba ido ya tsaya tarbiyyan k’annensa ya zama haka ba!!! amma matsalar shine ta Ina zai fara tunda gashi k’iri-k’iri Daddy ya ja masa barrier(ya shata masa layi)…. ganin da yayi gaba d’aya yana neman sake b’atawa kansa rai ne yasanya kawai ya fice ya nufi side d’insa ransa a mugun b’ace. Yana shiga parlourn shi ya tarar da Najeeb a zaune…. ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce ‘’zuwa babu sanarwa?’’ Murmushi Najeeb ya yi sanann ya ce ’’inata kiran wayarka baka d’auka, driver d’inka na kira ya ce min kana nan, shine na zo,’’ ‘’anything important? (Akwai wani abu mai mahimmanci ne)’’ Kawai Yashjub ya iya cewa. Murmushi Najeeb ya yi kafin ya ce “ko in tafi ne ?’’ Dai-dai nan Yashjub ya k’araso ya zauna kusa da shi, sai a lokacin Najeeb ya lura da yadda idanuwansa suke wanda hakan ya basa tabbbacin ransa ne a b’ace. ‘’Me kuma ya faru ??’’ Najeeb ya yi masa tambayar. Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya ce ‘’ba komai’’. Tunda ya ce hakan Najeeb ya fahimci maybe family issue ne ko kuma ba shi da niyyar gaya masa ne, dan haka ya kawar da zancen ta hanyar cewa “tun jiya Ya’isha ta k’i d’aukar wayata, ban san me ya faru ba. Yash sai ka saka baki a lamarin nan fa dan Yarinyar nan tana wahalar da ni da yawa.’’ Tsaki Yashjub ya yi tukunna ya ce ’’k’aton banza kawai.’’ Dariya Najeeb ya yo kafin ya ce “ai gara ni, I’m not living in denial sannan bana fakewa da employing mutum..k’arara nake fitowa, speaking of which..how is she. (Ai gara ni kai tsaye ƙarara nake fitowa in yi abuna, kuma bana fakewa da ɗaukar Mutum aiki.. Ni ka ma tuna min, Ya take.??)” Kamar Yashjub ba zai yi magana ba sai kuma ya ce ’’she’s ok(tana dai dai)’’ Ya yi maganar yana mai jin wani sanyi yana maye gurbin b’acin ransa. ‘’Gaya min yadda kuka yi da ita, lokacin da ta je.’’ Najeeb ya fad’i hakan ya na mai gyara zamansa ya fuskanci Yash d’in sosai . Tiryan-tiryan haka Yashjub ya bashi labarin komai, wanda kafin ya gama gaba d’aya b’acin ran da yake a ciki ya b’ace b’at!. Shi kansa Najeeb sai da yayi mamakin yadda Yashjub ya zage ya yi doguwar magana haka. Dan haka yana dasa aya Najeeb ya ce ‘’Yashjub Yarinyar nan ba na jin iyayenta za su barta ta k’ara shekara d’aya ma ba tare sun yi mata aure ba, kar ka tsaya b’atawa kanka lokaci ka je garin hakan miskilanci ya cuce ka, ka san dai kana son ta ko?’’ Shiruu Yashjub ya yi a ranshi yana lissafin ‘ko dai ya cire kunya da taurin Kai ya gayawa Najeeb ne, dan yana buk’atar shawara! Saboda har ga Allah bai san ta Ina zai fara ba, kuma kamar yadda Najeeb ya fad’a tabbas tsaf iyayenta za su iya aurar da ita anytime..ya zama dole ya ajjiye komai a gefe dan Manubiya ce peace of mind d’insa(kwanciyar hankalinsa) Strength (kuzarinsa) Happiness (farin cikinsa) da komai na shi’’ ‘’Yash….’’ Muryar Najeeb ta katse masa tunani ta hanyar kiran sunansa da ya yi cikin k’ura masa idanu. A hankali Yash ya gyara zama yana kallon Najeeb d’in tukunna ya ce ‘’menene abun yi yanzu?’’ D’an fiki-fiki Najeeb ya yi da idanuwanshi tukunna ya ce ‘’kana son nata kenan?’’ Murmushi Yashjub ya yi tukunna ya d’an d’aga masa Kai alamun “yes” kafin a hankali ya ce “a lot(irin sosai ɗinnan)” sai kuma da sauri ya nuna Najeeb d’in da yatsa alamun warning sannan ya ce ‘’don’t laugh, kuma wallahi kar in ji maganar nan a Bakin kowa.’’ Duk yadda Najeeb ya so hana kan sa yin dariya sai da ya yi, kafin daga baya ya yi shiru sannan ya ce ’’sorry Man, na ji dad’in abun ne sosai shiyasa… congratulations Allah ya baka Manubiya.’’ A hankali Yash ya ce ‘’Ameen’’ yana wani irin blushing. Kafin Najeeb d’in ya yi serious face sannan ya maida gaba d’aya hankalinsa a kan Yashjub tukunna ya ce ’’yanzu abunda ya kamata ka yi shine……’’ BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *29* A hankali Yash ya ce ‘’Ameen’’ yana wani irin blushing. Kafin Najeeb d’in ya yi serious da fuska, sannan ya maida gaba d’aya hankalinsa a kan Yashjub tukunna ya ce ’’yanzu abunda ya kamata ka yi shine, ka yi k’ok’ari shaƙuwa ta shiga tsakaninku ta hanyar friendship… In ya so idan Allah ya kaimu kamar nan da one week (sati ɗaya) to kana iya tunkarar ta da maganar, in ya so mu kuma sai mu je mu samu uncle, brother ko Mahaifinta a san da zaman ka’’ Wani irin kallo Yash ya yi masa wanda ya sa Najeeb ɗin yin wata y’ar siririyar dariya kafin ya ce ’’a tunanin ka yanzu idan ka ce mata kana son ta direct za ta amince ne?ai ya yi wuri sosai Yash.. Gara ka fara neman friendship d’inta first. kuma ba fa nan da wata d’aya ko biyu na ce ba, iyaka sati d’aya na ce maka, sarkin zalama.” Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya ce ’’Najeeb, Manubiya fa ba zata saki jiki da ni har ta yarda mu zama friends ba, that too in one week time that’s impossible(daɗin daɗawa a cikin iyaka sati ɗaya, gaskiya abu ne wanda ba zai yiu ba) Saboda tanada kamun kai da nutsuwa sosai..she is not the type (ba irin ƴan Matan nan bace) da zata zama friends da duk wani baƙon da ya shigo cikin rayuwarta bane tunda a yanzu dai hakan nake a wajenta(baƙo/stranger). Amma tabbas maganarka ma gaskiya ce tunda ko da ace ban tab’a soyayya ba na san kafin mutum ya samu guri a cikin zuciyar Mace ana buk’atar shak’uwa da kuma yarda da sauran su amma ni yanzu a hanlinda nake ciki yanzu haka Najeeb Ina so ka fahimceni ka fahimci yadda nake jin ta a cikin zuciyata..dan haka Ina ganin gara kawai in nemi su yardar tata daga baya amma for now abu na farko shine ta san Ina son ta… kar fa ka manta bayan na gaya mata ta amince da ni akwai fa su tambaya saka rana da buki a gaba kafin ɗaurin aure wnda na san Daddy da Mommy sai sun d’an d’auki lokaci dole su na shirye shirye kafin ayi auren, Ni kuma gaskiya a matse nake ta zamto matata, ba wai lust(sha’awa) ko wani abun ba a’a abunda kawai na fi buk’ata a yanzu shine ta yarda da ni ta aminta da ni in mallake ta ta zama tawa ni kad’ai, ka fahimceni??’’. Numfashi Najeeb ya fesar kafin ya ce ’’Yash na fahimce ka amman kuma kaima ka fahimce ni, gaggawa fa aikin shed’an ne.. Gara mu bi komai a hankali.’’ Najeeb d’in ya fad’i hakan saboda shi yana so su d’an fara shaƙuwa kafin komai dan ba zai yiu ace ya bata aiki Monday kuma Friday tashi d’aya ya ce mata yana son ta ba, ba lalle ta fahimce sa ba zata ga kamar yaudarar ta ya zo yi… … A hankali, bayan zurfin tunani shima Yash d’in sai ya ce ‘’ok, bara in jira one week d’in.” …….. Tunda Daddy ya koma d’akinshi yake ta faman kai kawo, gaba d’aya ranshi a dagule ya ke hankalinsa a tashe yake, sam ya rasa gane me yake damun sa ma! dan shi kansa zuwa wannan lokacin ya fahimci a mugun birkice ya ke. Tun kafin aje ko’ina har ya fara tunanin bai kamata ya kori Ummi ba! ta chanchanci hukunci tabbas dan bai kamata ta tab’a masa y’a ba amma kuma shima bai kamata ya ce ta bar gidan ba, ko ba komai ya san tana son shi tun ba yau ba so na tsakani da Allah dan itama ba matsiyaciya bace balle ya ce kud’i ta bi, tana business tana aiki kuma ya san mijinta ya bar musu mak’udan kud’ad’e.. saboda shi (Daddyn) ta yi resigning aiki sam bata damu ba ta ce itama tafi so dama ta kula da shi da y’ay’an su… A hankali ya dafe kansa yana jin yana wani irin sarawa …. Da sallama Mommy ta turo k’ofar d’akin ta shigo a hankali ta k’arasa kusa da shi tana d’ar-d’ar tace ‘’Daddy Yassir fa har yanzu bai farka ba, lafiya kuwa?’’ Ba tare da ya cika kan nasa ko ya d’ago ya kalle ta ba ya ce ’’lafiya,allurar tana da nauyi ne.’’ Ahankali ta matso ta d’an riƙe Hannun shi ta ce ’’am..i’m sorry about umm..’’ Hannunsa rik’e da Kai har yanzu ya d’ago ya kalle ta tukunna ya ce ’’Get,out!’’ Ta bud’e Baki za ta yi magana ya yunƙura ya kamo kafad’unta da Hannu biyu ya ce ’’in kin san kina da Hannu a koma meye ne to tun wuri tun kafin mu dena sheda juna ki janye ki fita a idanuwana Khadijah!’’ Wasu hawaye ne suka zuba mata wanda hakan ya sa Daddy ya ji ina ma bai yi maganar ba. A hankali ta ce ‘’daddy i…’’ Wuce ta kawai shi yayi ya fita da sauri yana da na sanin yi mata hakan dan bai kamata ya d’aurawa kowa laifin abunda ya aikata ba. Yana fita aka fara kirana sallar azahar dan haka ya wuce zuwa masallaci. A masallacin suka had’u da su Yashjub, bayan an fito… cikin girmamawa Najeeb ya gaida shi Daddyn kuma ya amsa da kulawa daganan Najeeb ya wuce side d’in Yash ya barsu a wajen dan ya ga kamar suna buk’atar space. Najeeb na wucewa Yashjub ya bawa Daddy hak’uri kafin ya fad’a masa abunda ya yi wa su Ummi. Bai yi murna ba kuma bai yi bak’in ciki ba, makullin kawai ya karb’a a hannun Yash ya wuce sama. A zaune ya same su, su biyu, a kan gado. Kowacce ta yi tagumi amma fa sun had’a kayayyakinsu tsaf gaba d’aya sun juye a cikin akwatunan da jakankuna sun jere su a gaban su. Tun kafin ya ce wani abu suka mik’e, ba tare da ta kalle sa ba ta ce ‘’Yashjub ne ya kulle mu, ka yi hak’uri, yanzu za mu tafi’’ Ta fad’i hakan tana k’ok’arin jan akwatuna biyu waenda suke cikin jerin akwatunan gaban su. A hankali Munirat itama ta mik’e ta fara k’ok’arin jan wasu akwatunan… cikin sanyin jiki Daddy ya matso kusa da ita(ummi) ya ce ‘’Ki tsaya mu fahimci juna …..’m” Munirat ji ta yi kamar ta kwala k’ara dan takaici, ya gama ci musu mutunci sannan yanzu ta ga da alama so yake ya hana su tafiya… har ta bud’e Baki za ta yi magana sai kuma ta ajjiye akwatin Hannunta ta fita dan already Daddy har ya kamo hannun Ummi ya hanata fara jan akwatin. A parlourn ta nemi waje ta zauna tana addu’ar ‘Allah kar ya sa Ummi ta yarda su ci gaba da zama a cikin gidan nan. Shigowar Mommy ce ta katse mata tunani.. Ahankali Mommy ta sauk’e nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce ’’Munirat na godewa Allah da baku tafi ba. na kira wayar mamanki bai shiga ba. kar ku d’au zafi kamar yadda shima ya d’auka kin ji ko? bara in shiga In yi mata magana itama’’. Ahankali Munirat tace ‘’ita da Daddy ne.’’ Da sauri Mommy ta ce ‘’Yauwa perfect, bari in same su duk su biyun.’’ Har ta nufi k’ofar sai kuma tace ‘’Am..Munirat dan Allah, d’an je ki kitchen akwai soup d’in da na d’aurawa Yassir, kar ya k’one kafin mu gama. ki juye a bowl ki kai masa d’akinsa’’. Kamar Munirat za ta yi mata musu, sai kuma kawai ta mik’e ta wuce. ‘…..Tun ranar da ta fara ganin Yassir ya d’an burge ta! Kyakkyawa ne ajin farko, halayyarsa ce da ta fahimci ba ta da kyau da kuma yadda gwaggwo ta ja mata kunne kawai ya sanya ta cire rai da shi, dan a tashi d’aya ma tun daga ranar ta ji ta tsane shi…. amma duk kalar tsanar da ta yi masa ta kasa jin tausayinsa a yau ɗin, dan ta tabbatar inda ita aka yi wa wannan mahaukacin dukan to da tuni ta mutu…..’ Tana wannan tunanin ta ƙarasa kitchen d’in, ta juyo soup d’in a bowl… Ɗakin da ta ga su Daddy sun shiga da shi ɗazu ta nufa, tana zuwa ta d’an yi knocking…. jin shiru ya sanya ta tura k’ofar ta shiga bakinta d’auke da sallama. Tana shiga ta ganshi a kwance a kan makeken gadon shi… A hankali ta k’arasa ta d’an tsaya akan sa tana kallon yadda fuskarsa ta kumbura… A take kuma sai ta fara da na sanin zuwa dan sai da ta ganshi ta ga yanayin jikin nasa tukunna ta fara jin haushin kanta na kasa hak’ura da ta yi har sai da ta zo, dan haka ta ajjiye bowl d’in da niyyar juyawa ta ji ya kira sunanta!. Da sauri ta juya da niyyar fita amma sai ta kasa sakomakon magiya da hak’urin da ya shiga bata yana cewa ‘sharrin shaid’an ne! ta yi hak’uri ba zai sake ba, kawai he got carried away by her beauty ne (tsananin kyawunta ne ya ruɗe sa) ya biyewa feelings d’insa towards her(shi kuma ya bari feelings ɗinsa gareta su ka yi galaba a kansa).. Wallahi bai san me ya shiga kansa ya aikata mata hakan ba! amma inshaaAllah ba zai sake ba.’’ Yadda jikinta yayi sanyi shi kanshi Yassir d’in ya lura da hakan, yana shirin ci gana da magana ta juya da sauri ta fita, dan tabbas in ta ci gaba da zama a d’akin tou za’a samu matsala…… Munirat tana fita Yassir ya yi wani killer smile(shu’umin murmushi)…. ‘…..Tun ranar farko da ya fara ganinta, dama ya fahimci Yarinyar za ta yi saurin shiga Hannu!!!! Kum ya lura kamar tana d’an son shi. Dole ya san yadda zai yi ya samu abunda ya ke so daga gareta, ta ko wacce hanya!!!! Sannan ya yi amfani da ita wajen hukunta Ummi! Dan ya lura lamarin Mommy da Daddy ya sake tab’arb’arewa kuma yana da tabbacin Ummi ce sila. Sannan Yarinyar ta tafi da imaninsa, ya san baya sonta, amma fa tabbas a cikin Mata idan za a tara a raba su kashi d’ari tou kashi 1 zuwa biyu ne za a same su da irin zubin Jikin Munirat….’ Yana wannan lissafin yana murmushi, ya juya da niyyar d’aukar bowl d’in dan yunwa ya ke ji amma sai ya gagara sakamokon tsamin da Hannun sa yayi, dole haka nan ya hak’ura..a hankali ya koma ya sake langab’ewa saboda ko’ina na jikinsa ciwo yake masa ‘…….ya kasa yarda! Har yanzu ya kasa yarda da cewar wai Yashjub ne ya yi masa haka da girman sa da kud’in shi da class d’in sa!!!! Abun kamar a mafarki. Tabbas abunda Abokansa suke gaya masa na cewar ‘’In yayi wasa sai ya zama d’an kallo a gidan’’. Ya tabbata, kenan. Shi fa daman tun farko kokawa kawai yake yi da zuciyarsa saboda ya san Yashjub d’an uwansa ne kuma Mommy ba za ta so taga basa shiri ba amma wallahi tun yarinta shi kam ya tsani Yashjub! Duk wani abu da ya ke so ko yake son yi to sai abun yayi ta zuwar ma Yashjub d’in cikin sauk’i. Tun yana Yaro yake da burin zama business man babba sosai kamar Daddy… Daddy ya ce sai sun yi phd tukunna zai basu jari amma Yashjub ko da ya gama phd d’inma already yanada estate all thanks to son kan da Daddy ya yi tun ranar da aka haifi Yashjub d’in wanda hakan ya sanya da Daddy ya basa nasa jarin sai arzik’insa ya sake nunkuwa, shi kuwa da aka bashi nasa aka bud’e masa company compared to na Yashjub(da na auna nashi da na Yashjub ɗin) duk sai ya rena nashin, dan a lokacin har ma a yanzu bai Isa ya tsaya ya ce zai goga da Yashjub a harkar business da kud’i ba saboda ya fi shi ya tsere masa ta koina.. kuma har gobe Yashjub d’in kamar wani aljani duk abunda ya saka a gaba tou sai ya cin masa kuma sai ya yi albarka, baya jin tun tasowar su ya tab’a ganin abunda Yashjub ya nema bai samu ba.! Shi yasa tun kafin a zo nan Abokanayensa suke ba sa shawarar ya tashi ya tsaya, dan it’s clear (dan a baiyyane ne ga kowa) Daddy ya fi son Yashjub, ga shi ya fi shi kud’i da fame, kuma shakka babu shekarun Mommy itama suna sake yin sama wanda ya fi arzik’i a tsakanin su shi zata fi so… Yana k’ok’ari, yana danne zuciyarsa ne dan baya so ya cutar da Yash amman gaskiya he can’t take it anymore(ba zai iya ci gaba da dannewa ba!!) ya tsane shi tsana ba ta wasa ba! dariya kawai yake yi masa kasancewar shi d’an uwanshi dolen shi sannan ya san ba shi da yadda zai yi da shi amma yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata ya tashi tsaye ya nemawa kanshi mafita kuma ya ga bayan Yash…… ta hakan ne kawai k’ima da martabar sa za su dauwwama a idanun y’an gidan da ma duniya gaba d’aya…. ……… Munirat tana fita Ummi ta ce ‘‘Daddy kar ka ja in yi maka musu, ka yi hak’uri komai ya wuce, amma dole in tafi. Yaran ma ba sa k’aunata, ba za mu zauna k’ark’ashin inuwa d’aya da su lafiya ba’’ Cikin katse ta ya ce ‘’Ummi I’m not going to apologize (ba zan baki haƙuri ba) ke kin sani. Kawai na ce ki zauna! kuma i‘m expecting u to obey me As my wife (kuma a matsayinki na Matata ina tsammanin ganin kin yi min biyayya, kin zauna ɗin.). sannan su Yasmeen dolen ki ne A cikin gidan nan, dan haka zai fiye miki idan kika nemawa kan ki mafita game da yadda za ki zauna ƙalau da su…’’ Ummi za ta yi magana kenan Daddy ya toshe mata Baki da Hannunsa, yana kallon k’ofa… ba tare da b’ata lokaci ba ya yi sauri ya yi wuff ya fice. Da sauri Mommy ta shiga gyara d’aurin zaninta wanda ta kamo bakin za ta kunto. a d’an rikice ta ce ‘’wajen ka na zo’’ bata jira jin mai zai ce ba! sannan bata damu da kallon tuhumar da ya ke yi mata ba ta d’aura da cewa “am..an bugi Yassir akan Munirat, but itama ya kamata a ja mata barrier (layi) akan zuwa d’akin shi. ita yarinya ce kar mu je Yashjub ya ce zai yi mata shegen dukan da ya yi wa Yassir dan kaga in hakan ta faru mamanta na san ba za ta daliliba ga kuma halin da ake ciki Daddy dan Allah ka d’aga musu k’afa mana….” Cikin rashin fahimta Daddy ya ce’’ban gane ba’’ dan gaba d’aya zancen nata a hargitse ya ke kamar yadda ita ma ta hargitse ganin an kusan kamata. Dai-dai nan Ummi ta fito, da sauri Mommy ta matsa kusa da ita ta rungume ta ta ce ‘’Dan Allah ki yi hak’uri akan abunda ya faru d’azu, na yi masa magana hakan ba za ta sake faruwa ba, ki zo mu je kuma ina son ganin ki, akwai maganar da za mu yi ni da ke in babu damuwa’’ kafin ta kalli Daddy ta ce ‘’za mu iya tafiya, dan Allah ?’’. A hankali ya d’aga mata kai, yana tunanin… ‘tou lab’e take yi musu, ko kuma dai da gaske zuwan ta yi akan su yi magana? dan har ga Allah bai ganta lokacin da ya fara magana ba, yana ganin inuwar ta kuma ya yi sauri ya fito which means (wanda hakan ya ke nufin) bata dad’e a wajen ba kenan. ‘ Mu je, muje dan Allah?’’ ya ji muryar ta cikin sanyi a hankali. D’aga mata kai kawai ya sake yi a karo na biyu, ya bari akan in sun had’u su biyu ya tambayeta… ya san ba lalle ta fad’a mishi gaskiya ba amma zai tsoratata dan ba zai iya sake ɗaukar wata sabuwar gurɓatacciyar halaiyya daga Mommy ba Bayaga waenda take da su. Suna fita shima kawai ya wuce ya bi bayan su… suna fitowa daidai itama Munirat ta fito daga d’akin Yassir, haka kurum duk sai ta diririce!! Kamar mommy bata ganta ba hakanan ta yi, kawai ta ja hannun Ummi suka nufi fanninta. Daddy ma bai ce mata uffan ba, Ummi kuma jira ta yi akan in sun koma d’aki Munirat d’in ta yi mata bayani dan bata fahimci hak’urin da Mommy ta bata ba sannan ko tana hauka ai d’akin Yassir ba wajen zuwan ta bane ba. .. Ko da suka je d’akin Mommyn hak’uri Mommy ta bawa Ummi sannan ta ɗan gaya mata halayen Daddy ta ce kuma “in dai ya nuna baya son abu to kar ta yi sannan itama musabbabin farkon fad’an ta da shi akan ta daki Yadira ne. Kuma da sam ba haka yake ba. ta yi hak’uri kawai ta yi tolerating din su Yasmeen mata ne kamar yadda ta fad’a nan da 5 years (shekaru biyar ma) ba za ta tarar da kowa a gidan ba, duk aure za su yi inshhaaAllah… dan haka kar ta bari a ta sanadiyyyar su ta tafi ta bar gidan auren ta.” Sun d’an tab’a hira,har Ummi tana mamakin sakewar da Mommy ta yi da ita tanata janta a jiki. Ummi ta na da asthma shiyasa taketa so ta bar d’akin dan suna shiga Mommy ta kunna musu turare wai tun safe da ta gyara d’akin yau ba ta saka ba, shiyasa har wani d’ad’d’aukewa Ummi ta ji numfashinta ya soma ga shi kuma Mommy ta k’i barin ta ta tafi sai sake rik’eta ta ke yi da hira,ita kuma kawaici yasanya ta kasa ce mata bata son hayak’in. Sai da Yadira ta shigo ta ce musu ‘’Ya Najeeb ya zo, yana k’asa yanason gaisawa da su’’ Tukunna ta samu suka fita a d’akin suka sauk’a k’asa. Ummi, Ta gama rayawa a ranta zata zauna ba za ta tafi ba amma wallahi sai Daddy ya san ya tab’o ta, da farko ta yafe mishi! amman yanzu kuwa komai ya chanza besides tunda ya yi mata wannan wulak’ancin kuma ya fifita ‘ya ‘yan shi akan kowa to tabbas ita ma ba zata sake saka shi a priority ba!!!! ita bama ta san ya aka yi ba amma wallahi fit ya fice a ranta a cikin mintinan da ba su fi talatin ba, gaba d’aya ta tsaneshi…… Cikin mutunta juna da kulawa suka gaisa da Najeeb Mommy ta gabatar mata da shi a matsayin wnda yake neman Ya’isha da aure kuma Abokin Yash sannan family friend d’in su. A nan parlourn Mommy ta barsu ita kuma ta mik’e ta je kitchen dan ta nunawa masu aikin abunda za a d’aura, dan haka Ummi ma ta mik’e ta bi bayanta suka bar Yash da Najeeb a zaune wanda yake ta zaman jiran dawowar Ya’isha. Ummi tana zuwa za ta hau dining ta nufi kitchen Ya’isha ta shigo, ba tare da ta kalle ta ba ta ce ’’Ban yi tsammanin ganin ki ba ai, ko da yake na manta ashe zuciyar kare ya cinye.’’ Ta yi maganar kamar ba da ita take ba dan ko kallon Ummin ba ta yi ba kuma bata daina tafiya ba..daga haka ta wuce cikin parlourn. Suna gaisawa da Yash ya mik’e ya fice daga parlourn ya bar ta ita da Najeeb. Zama ta yi a kujerar da take facing d’insa kafin ta ce ‘’Sorry Ya Najeeb, Ina y’an wasu abubuwa ne’’. Cikin nutsuwa ya d’an k’ura mata idanu kafin ya ce ‘’shine kika kasa yi mini ko da message ne?’’ D’an turo Baki ta yi tukunna ta ce ’’Ya Najeeb daga shigowata sai fad’a? To raina ne a b’ace tun safe, da kyar na yi abunda na fita yi d’in ma’’ …Ya’isha tana yi masa abubuwa da yawa masu zafi yana kau da Kai amma na yau ya yi mishi ciwo sosai!! Wato ranta ne a b’ace kuma ba ma shine ya yi mata laifin ba laifin wani ne ya shafe sa shiyasa ta gagara d’aukar wayarsa! shi yana chan yana ta tunanin ko maybe fushin da ta Saba yi da shi ta yi ashe abun ba haka bane ba wani sabon iya shege ne ta fito da shi… Bai sake cewa komai ba haka kawai ya mik’e ya ce mata ‘’Allah bamu alkhairi’’ daga nan ya sa Kai ya fice. Bata damu ba, kanta tsaye ko alamar nadama ko tunanin ta bashi hak’uri babu, haka nan ta ce ‘’sai anjima’’kawai, saboda ta riga ta san ba zai ma iya kwana biyu bai neme ta ba. Yana ficewa ta nufi sama a gigice…. direct d’akin Kausar ta nufa, tana shiga ta tarar da ita tana waya da Yasira, cikin tsananin tashin hankali ta ce ‘’she’s still here(har yanzu tana nan), bata tafi ba har yanzu, how?(ta ya hakan ta faru?)”. Numfashi Kausar ta fesar kafin ta ce “ba ki fi Mu tashin hankali ba, ki nutsu ki zo ki zauna ki ji”. Da kyar ta nemi waje ta zauna Jikinta har ɗan karkarwa yake yi, daganan Kausar ta saka wayar a hands free suka shiga magana da Yasirar har ita…. ……..Thursday…….. Cikin ikon Allah jikin Inna da sauk’i sosai, dan har zama tana iya yi idan an zaunar da ita, kuma tana iya cewa “eh” da ‘a’a’, wanka ne dai da ragowar abubuwa har yanzu sai an yi mata. A b’angaren Baba shima ya siyo musu buhun shinkafa, katan d’in taliya da macaroni, mai da maggi da tomato paste katon biyu. Rabon da su Manubiya su shiga farin ciki irin haka har sun manta, sai dai kuma suna d’an fargaba dan basu san a inda Baba ya samu kud’in ba, ba kuma yadda ba su yi da shi ba amma ya ƙi gaya musu kawai dai ya ce musu “ba bashi ya ci ba!” k’arshema da suka dame sa da tambayoyi sai ya rufe su da fad’a.. dan haka suka hak’ura suka ja bakinsu suka yi shiruu. Ba yadda ba su yi da Ya Musbah ba akan ya d’an d’iba kayan abincin ya kai gidansa shima amman sam ya k’i yarda yak’i d’iba! A cewar sa ‘idan bai kawo ba to bai kamata ya d’auka ba kuma ai yanada aikin yi Alhamdulillah suna samu su ci su sha suma, yanzu kam ba laifi.’ Ba dan sun so ba haka suka hak’ura suka barshi dan ya dage akan ba zai d’iba d’in ba… gaba d’aya tausayin d’an uwan nasu sukeji especially yanzu da matsalar kud’in haya ta sako sa a gaba, k’iri-k’iri ya hana su gayawa Baba da Inna, dan su ce musu ya yi ya biya saboda gudun kar ya d’aga musu hankali, su Jidda ne kawai suka san bai biya d’in ba, mai gidan ya d’aga mishi hankali a haka ma Ya Nafi’u ya bashi dubu hamsin ya bayar yanzu sauran sabain, shiyasa su Manubiya suka gama deciding ita da su jidda akan tana d’aukar albashinta za ta ba sa ya bayar, ta san dole yanzu haka yanata fafutuka dan haka wataƙila ya samu ya had’a kan 40 d’in saboda tun wachcharr shekarar da ya biya dama ya fara shirye-shiryen biyan na wannan shekarar.. Allah sarki, bawan Allah duk ya rame, farar fatarsa mai shek’i da kyan gani ta d’an yi duhu fuskar nan hanci ya k’ara tsayi! idanuwan sun sake fitowa zurr! Hakan ya sanya gaba d’aya suke tsananin jin tausayin shi, dauriya kawai suke yi dan ba sa so su karaya su nuna mishi ne su je su kashe mishi kwarin guiwar…. A b’angaren Ya Musbah kuwa, kud’in haya bai d’aga masa hankali ba kamar yadda Baraka ta d’aga masa hankali! gaba d’aya ta birkice mishi musamman ma kwana biyun nan, rigimar yau daban ta gobe daban! yanzu haka ta d’aga masa hankali akan wai k’awayenta y’an unguwar su na yi mata gani-gani, a ganin ta bai kamata ya ci gaba da wanki da guga ba saboda za ‘a raina ta, wai an yi bikin k’anwar wata k’awarsu ba a gaiyyace ta ba saboda tana a matsayin matar mai wanki da guga, Dan haka ya nemi wata sana’ar amma gaskiya ba wannan ba!!! ya yi low class da yawa. Shi kuma Ya Musbah da wanki da gugan ya ke samu ya ke ciyar da iyalin nasa yake rufawa kan shi asiri, shiyasa ya k’i hak’ura, ita kuma ta dage…. hakan ya sanya kullum cikin fad’a suke ita da shi, bai san ya zai yi da ita ba dan in ya bar wanki da gugan ita ce ta farkon fara d’aga masa hankali. Gashi yanzu ta tsiri wani salo wai tana da low bp dan haka miyar ta kullum dole sai an saka mata nama a ciki sannan sai ya siyo mata maltina, yanzu haka ta koyawa me sunan Baba shima Idan babu nama a abinci to ba zai ci ba sannan shima in be sha maltina ba to fa ya dinga zunduma musu ihu kenan duk makwafta sai an jiyo su. Ya Musbah yanada guilty conscious (. )hakan ya janyo masa muddin ya siyawa Baraka nama da maltina to hankalinsa baya tab’a kwanciya har sai ya siya ya kaiwa Inna da Baba suma ko kuma ya bawa Baba kud’i ko ya siya wani abun ya kaiwa su Manu…. Shiyasa gaba d’aya ya sake zugewa wani lokacin ko abinci baya samu ya ci dan babu enough.. Kuma kullum idan ya fita aiki tun safe sai dare yake samu ya zauna ya d’an huta. Tun suna Yara yake son Baraka, ba dan ragowar birbid’in son da yake yi mata ba da kuma darajar me sunan Baba wallahi da tuni ya sallame ta, ya gaji! har ga Allah Baraka ta kai shi bango a kwanakin nan,wayar hannunta kad’ai abar kallo ce amman ta siya maggi guda d’aya a gidan aiki ne babba a gareta, ta gwammaci ta dame sa a waya idan me sunan Baba ya fara kukan yunwa. Ba abunda ya fi sake bak’anta masa rai irin yadda ta raina iyayensa, Kwanaki baya Yayan Nafi’u ne ya yi hatsari dama ba shi da Mata (gauro ne) Dan haka yana gida a kwance ba lafiya… irin girkin da Matar Nafi’un Aisha ta yi ta tafi dubiya sai da ya bashi mamaki dan ranar shima har zubo masa aka yi, tun daga nan kuma bata yin sati ba ta je ta dubo sa ba, hatta Inna..Aisha bata yin sati bata je ta duba ta ba.. amma ita Baraka ta ce su Manubiya sun raina ta kuma ba a ganin girmanta a gidan, tunda Inna ta fara rashin lafiya sau d’aya ta je ta dubata lokacin tana asibiti kuma shima sai da yayi da na sanin zuwan nata, k’iri k’iri ta hana k’annensa zuwa gidan kuma itama bata zuwa inda suke…… A b’angaren Jidda itama abun ba sauk’i dan hankalinta a tashe yake kwana biyun nan… Ko waje da kyar take iya fita dan sai ta tabbatar kuma ta lura Ya Yusuf baya gidan ko kuma in in yana wajen aiki, saboda ta tsorata da shi sosai tun ranar da suka had’u ya yi treatning dinta (ya yi mata barazana), ta inda ya sanar mata ‘…….Abunda suka yi masa ita da su Baba...disga shin da suka yi a gaban kowa, k’iri-k’iri suka ce basa so ta aure shi! To ta sani ya ji zafin hakan sosai. Kuma yana so ta yarda ta tabbatar sannan ta saka a ranta har abada yana sonta sannan bata da wani mijin bayan shi! Dan haka ko dai ta haƙura ta aure shi watak’il ya manta da rashin mutuncin da sukayi mishi a gaban su kaka mallan ya fasa d’aukar revenge d’in da ya yi niyya ko kuma ya kunnowa ahalinta bala’in da ba za su tab’a iya kashewa ba, wallahi. Ta je ta yi tunani, yana jiran amsarta, ya bata kwana biyu, kacal!…….’ Shiyasa tun lokacin da kwana biyun ya cika take wasan y’ar b’uya da shi dan bata san me zata ce masa ba. Duk da wata zuciyar tana bata shawarar ta hak’ura ta aure shi akan dai ta bari ya tab’a mata ahalinta amma kuma ba wai iya bata son Ya Yusuf baneba har ga Allah ko kallon shi wani lokacin bata son yi, sannan Barazanar da ya yi mata ɗinnan ya sanya ta sake tabbatarwa ba mutumin kirki bane ba… A ganinta rashin mutuncin Baraka ma ita kaɗai ya ishesu!! Sam bai kamata ace ta k’arawa su Baba da wani mugun surukin ba kuma du….. matsalar su ma ta ishe su. Gashi ya ce kar ta fad’awa kowa, ta san kuma idan ta fad’a d’in zai sani dan ta san su Manubiya ba za su yi masa da sauk’i ba, ita kuma har ga Allah tsoro takeji dan a yadda ta ga idanunsa a ranar sam bata ga alamun wasa a cikinsu ba. BULAMA ✍️ 0903 441 3252 *MANNUBIYA* *30* Duk da wata zuciyar tana bata shawarar ta hak’ura ta aure shi akan dai ta bari ya tab’a mata ahalinta amma kuma ba wai iya bata son Ya Yusuf baneba har ga Allah ko kallon shi wani lokacin bata son yi, sannan Barazanar da ya yi mata ɗinnan ya sanya ta sake tabbatarwa ba mutumin kirki bane ba… A ganinta rashin mutuncin Baraka ma Ita kaɗai ya ishesu!! Sam bai kamata ace ta k’arawa su Baba da wani mugun surukin ba kuma du….. matsalar su ma ta ishe su. Gashi ya ce kar ta fad’awa kowa, ta san kuma idan ta fad’a d’in zai sani dan ta san su Manubiya ba za su yi masa da sauk’i ba, ita kuma har ga Allah tsoro takeji dan a yadda ta ga idanunsa a ranar sam bata ga alamun wasa a cikinsu ba. ‘’Tunanin me kike yi?’’ Muryar Manubiya wadda ta shigo yanzun ta katsewa Jidda tunani. Da sauri ta d’an matse kwallar da ta tarar mata tana shirin zubowa sannan ta ce ‘’Ba komai, ya aikin?’’ Ajiyar zuciya Manubiya ta sauk’e kafin ta ce ‘’Huh!Alhamdulillah… Ammi fa ta tafi next level, dan ma Allah ya taimake ni gobe zan gama exams d’ina..wallahi abubuwa duk sun yi min yawa especially a gidan Ammi, dan ma akwai Maama.. Mace mai kirki wani lokacin fa ita take taya ni wasu abubuwan, ta ma ce za ta shigo ta duba Inna.’’ Manubiya ta k’arashe maganar tana mai neman waje ta zauna a kusa da Jidda. ‘’Allah sarki,sannu!ki yi hak’uri duk ni na janyo muku’’ Jidda ta fad’i hakan cikin rashin jin dad’i. Murmushi Manubiya ta yi tana kallon ta kafin ta ce ‘’Ba komai kar ki damu, Allah yasa mu dace’’ Ahankali Jidda tace’’Ameen’’dai dai nan Baba ya shigo bakinsa d’auke da sallama. ahankali ya nemi guri ya zauna..cikin girmamawa suka gaida shi ya amsa kafin Jidda ta mik’e ta fita domin ta je ta kawo masa abinci, daga haka d’akin ya yi shiru kowa da tunanin da yake yi a ransa. Manubiya Yashjub ne ya b’ata mata rai, jiya aka yi mata ƙorafin abu dan haka ta ce masa “akwai report via watsapp.. (Akwai ƙorafi ta watsapp)” Kanshi tsaye ya amsa mata da reply ɗin da ya dame ta ya hanata sukuni ’’Okay dear, you can report to me tomorrow as planned, take care. (Tam dear, za ki iya sanar min da ƙorafin nasu gobe kamar yadda muka tsara, ki kula da kanki)”. Tabbas ya kusa tarwatsa mata zuciya da ta gani, dan me yasa zai ce mata wani ‘dear’, bai san yadda zuciyarta ta buga ba da taga reply d’in har yanzu bata gama dawowa daidai ba. Gaba d’aya ya sakar mata da kasala daga reply d’in, anya kuwa ba za ta tura masa bayanan ta watsapp ba goben ta ƙi zuwa ta yi k’aryar bata da lafiya… dan tun jiya ta fara fargabar had’uwar su ta gobe, bata so ta fara feeling wani (jin wani) abu na daban game da bawan Allahn nan dan bata shirya shan wahala akan soyayya ba..iyakar ganin sa da muryarsa ma kad’ai kid’ima ta su ke yi dama yanzu kuma ya kama ya wani ce mata ‘dear’ Tun safe ya rikitata…… Shigowar Jidda ne ya katse musu tunani gaba d’aya su biyun, da ladabi ta k’arasa ta ajjiye abincin a gaban Baba sannan ta koma gefe ta zauna. A hankali Baba ya d’ago ya kalli Manubiya kafin ya zaro bandir na kud’i daga aljihunsa ya mik’a mata…. cikin nutsuwa ta matsa ta sanya Hannu ta karb’a, tana shirin yin magana ya ce “gashi gobe idan kin je ki bawa Ammi, na ke da Muhsin, kun bar aiki kenan inshaaAllah. ku samu ku huta Allah ya yi muku albarka. InshaaAllah wani satin idan aka koma makaranta da shi(Muhsin ɗin) za a shiga…. Idan kin huta zuwa ko anjima ne sai ki je ki tambayi kud’in uniform da shiga da duk abubuwan da ya kamata a makarantar Mazan chan, zuwa dare inshaaAllah zan bawa Musbahu kud’in ya je ya biya masa in Allah ya kaimu aka koma sai a fara tare da shi.” A hankali Manubiya ta ce ‘’An gode Baba Allah ya saka da alkhairi, ya k’ara bud’i, ya bawa Inna lafiya’’ Cikin tsananin sanyin jiki Jiddah ma ta ce ‘’an gode Baba’’ A hankali Baba ya ce ’’Ameen’’. Daga nan duk su biyun suka yi shiru…. …A Ina ya ke samun kud’i? Gashi tun last time ya kora musu warning d’in ‘kar wadda ta sake tambayar sa a inda ya ke samun kud’i, idan ba haka ba kuma ransu zai yi mummunar b’aci, Wallahi….’ Har ya gama cin abincin ba wadda ta iya sake cewa komai, ya na gamawa ya mik’e da shirin sake fita…cikin girmamawa su ka yi masa a dawo lafiya, sai da ya je ya shafa fuskar Inna wadda take baccin ta cikin kwanciyar hankali tukunna ya sa Kai ya fice daga d’akin… Yana fita Jidda ta ce ‘’Adda Manu inajin tsoro fa, ta Ina Baba yake samun kud’i haka lokaci guda??’’ Ajiyar zuciya Manubiya ta sauk’e kafin tace ‘’Jiddah ni kam ta ya za a yi in sani? let’s just hope for the best(kawai mu yi fatan hakan alkairi ne), dan nima gaskiya kaina a d’aure yake. kina karatu kuwa sosai? post utme d’in ku fa ta matso. ‘’ Ahankali jiddda tace ‘’eh,Ina yi, ku taya ni da addu’a’’ ‘‘InshaaAllah’’ Manubiya ta ce,kafin ta mik’e ta koma gefe ta d’auki takarda ta shiga karatu…dan gobe mai tashin kafin asuba ce saboda exams d’in 9 gare ta, ga shi a goben ne za ta had’u da Yash, Allah ya taimake ta ita da gidan Ammi sun yi bye bye, ba dan haka ba da bata san yaya zata yi goben ba. …. Kalar tsalle da murnar da Muhsin yayi lokacin da ya ji labarin tafiyar sa makaranta sai da ya bawa su Manubiya mamaki, amma da suka tuna yadda Yaron yake da k’ulafucin makaranta sai suka yi masa uzuri, dan bai yi murnar barin su aiki a gidan Ammi ba kamar yadda ya yi murnar saka shi a makaranta da za ‘ayi.. Tun daga lokacin da ya ji zancen kuwa..in dai ya san sunan abu da turanci to fa ba zai fad’a da Hausa ba, murna da shak’iyanci kala-kala haka ya dinga yi ya yi ta saka su dariya da walwala kuwa dan wunin ranar haka suka kasance cikin farin ciki wanda hakan ne ya taimakawa Manubiya ta samu fargaba da tunanin had’uwarta da Yash ta gobe ya d’an yi skipping mind d’in ta(ya ɗan bar kanta). •••••••• Da ikon Allah yau har aka fara gabatar da dinner su Yasira ba su yi wa Ummi rashin ɗa’a ko kallon banza ba, wanda hakan ya riga ya Zamto d’abiar su..dan in dai suka had’u to wajibi ne ta fuskanci rashin mutunci daga gare su. Ba su gaishe ta ba dai kuma Daddy bai ce su gaishe tan ba kamar kullum, haka ake kan gabatar da dinner d’in.. ta kuwa ji zafi amma yadda ta yi alk’awarin fita harkar Daddy da ya’yansa ne ya sanya ta tartarasu ta zuba a kwandon shara. Sai da aka kusa kammalawa tukunna Yassir ya sak’k’o k’asan. Daddy kawai ya gaisar daga nan ya cewa Yusra ta yi serving d’in sa… A hankali Munirat ta d’an d’ago ta kalle sa ai kuwa suka had’a ido, murmushi yayi mata daga nan ya d’auke Kai da sauri gudun kar Kausar ta kama sa.. Ɗaya bayan ɗaya duk suka shiga watsewa har dining d’in ya rage daga Yassir sai Daddy, Ya’isha da Yash. Yassir yana shirin tashi Yash yace ‘’Days ago (kwanan baya) na je d’akinka kana bacci’’ ‘’Yeah’’ kawai Yassir d’in ya ce ba tare da ya kalli inda Yash yake ba ma, daga haka ya mik’e da niyyar barin wajen gaba d’aya. Har ga Allah Yash ya d’an so su fahimci juna a kan abunda ya faru amma attitude d’in da Yassir( yadda Yassir ɗin) yayi masa ne yasanya ya fasa, dan haka cikin b’acin rai ya ce ’’ban gama da kai ba’’ Still ba tare da Yassir ya kalli Yash ba ya ce ’’good 9te,Daddy(Daddy sai da safe)” A zuciye Yash ya mik’e amma kafin ya yi wani abun tuni Daddy ya tsaida shi ta hanyar ruk’o hannunsa, da sauri ya maida shi ya zaunar da shi. Hakanan Yassir ya sa Kai ya wuce, yana wucewa Ya’isha ma ta yi musu sai da safe ta wuce.. Da kyar Yashjub ya d’an yi controlling kansa tukunna ya bawa Daddy labarin abunda ya faru wanda har ta kai sa ga dukan Yassir d’in. Sannan ya d’aura da cewa “ya kamata Yassir ya bar cikin gida haka tun kafin a samu matsala’’. Cikin son fahimtar da shi Daddy ya ce ’’Yashjub, kai ne ka ce Yassir ya dawo cikin gida, bai yi ja-in-ja da kai ba haka Yaron nan ya yi maka biyayya duk da baya so amma a hakan ya hak’ura ya dawo ya zauna, duk dan a zauna lafiya..kaga kuwa idan ka ce sai ya sake komawa wajen ka yanzu a gaskiya ba ka yi adalci ba Yash, besides i don’t think (Bayaga haka ma bana jin ) bayan abunda ya faru a tsakanin ku zai yarda ya dawo ku zauna tare. Ya yi min maganar kafin kai ka yi. Ka kwantar da hankalinka zai bar cikin gida amman sai nan da three months idan an gama masa nashi ginin wanda za a fara a wanchan filin da yake jikin gidan nan in yaso in an gama sai a fasa a had’e da nan… Yassir is not a kid (Yassir ba Yaro bane ba) dan haka bai kamata mu ce za mu dinga juya shi muna controlling d’insa haka ba, he deserves to make his own decisions(ya kamata a barshi ya yi yadda ya ga daman tsara rayuwarsa). Maganar Yarinyar nan kuma, na fahimci komai da kaina, tun kafin ma in ji wannan bayanin naka tsaf na fahimci ‘ita take kai kanta gare shi’ so na same shi na ja masa kunne kuma ya yi min alk’awarin zai fita a harkarta har abada.. therefore Yassir is good to live here (Dan haka babu aibu da damuwa a cikin zaman Yassir a nan), har zuwa lokacin da za a gama masa ginin sa shima, ya koma. Kar ma ka ce ya koma side d’inka a gaban shi ya yi maka musu daganan raini ya shiga tsakanin ku, dan nima ban goyi bayan ya koma d’in ba bayan abunda ya faru a tsakanin ku, na fi ganin dacewar ku zauna a saperate wajen zama(wajen zama daban daban), dan na san ba zaku zauna lafiya ba, na san ka da zuciya..za ka ce ya yi abu which na san definitely ba zai yi ba (wanda inada tabbacin shi kuma ba zai yi ba)..zai yi maka rashin kunya kai Kuma zaka ce zaka dake shi shi kuma zai ce zai rama daganan kuma abun ba zai yi dad’i ba…! so tun kafin abun ya kai ga haka..maganin bari kar a soma.Ina yi masa addu’a kai ma ka taya ni..Allah ya shirya sa, bana so in sake jin wata maganar.’’ Da kyar bayan kamar mintuna biyu Yash ya samu ya iya cew Daddy “to “ dan sai da yayi da gaske tukunna ya iya danne fushin sa. Daga nan ya yi masa sai da safe ya mik’e ya fice, ya bar sa yana tunanin Ummi, Matar da da har farce take yanke masa! biyayya kala-kala amman wai ita ce yanzu banda gaisuwa ba abunda yake shiga tsakanin su, yadda take yi wa kowa a gidan haka take yi masa shima babu wannan kulawar ta musamman da take bashi, abincinsa d’azu da ta kai masa (breakfast) kawai direwa ta yi ta juya sannan ba ta je ta wanke masa toilet da gyaran d’aki ba kuma yau ta karb’i girki, yana da tabbacin ba lalle ma yau ta kwana d’akinsa ba dan ko kallon sa bata yi.. Wallahi! ba dan shekaran jiya jiya ya gama yi wa Hajiya Mama alk’awarin zai zauna da Ummi ba da tuni ya salleme ta…. He apologized(ya bada haƙuri), tunda har ya ce mata ta zauna a gidanshi ai kuwa kamar he apologized ɗinne (ya bada haƙurin ne) amma duk da haka kalli attitude d’in da take bashi…. Ya jima a wajen kafin da kyar ya samu ya mik’e ya nufi sama ranshi a mugun b’ace, kamar yadda ya yi zato kuwa har asubah ba Ummi babu alamarta, dan haka ya kuma kumbura ya nad’i takaicin ta shima ya ci alwashin zuba mata ido kuma wallahi mistake d’aya idan ta yi sai ya koya mata hankali a cikin gidan duk kuwa da shekarunta ai itama bata san darajar shekaru ba tunda gashi ta raina shi. Takaici da mamakin Daddy ne suka hana Yash bacci, babu yadda bai yi ba amma sam ya gagara yin bacci. He really can’t believe(Ya kasa yarda da) wai Daddy ne ya ja masa layi a kan Yassir, kenan dai yanzu abunda yake nufi ‘a zubawa Yassir ido yayi duk abun da yaga dama…’ ta ya ma zai ce laifin Munirat ne bayan ranar dakyar ya kwaceta daga Hannun Yassir d’in, he hates to think about it amma maganar gaskiya Daddy is very selfish when it comes to his children (Baya so ya dinga irin tunanin nan amma Daddy yanada son kai sosai a duk harkar da ta shafi ƴaƴansa). Ganin takaici yana shirin saka shi d’an k’aramin hauka ne ya sanya kawai ya d’auki waya ya shiga kiran Manubiya lokacin 10 har da rabi. Sai da wayar ta fara ringin tukunna ya fara tunanin anya kuwa ya dace ya kira ta kar ya je ko ta yi bacci, bayaga haka ma me zai ce mata idan ta d’auka. Amma kuma he needs her (Amma kuma yanada buƙatarta), yanada bukatar ya ji ko da muryarta ne, ba shi da wani zaɓin…. Yana cikin wannan tunanin ya ji sautin muryarta a hankali ta ce ‘’Assalama alaikom’’ A hankali ya lumshe idanuwansa yana sauraron ta tana ta hello!hello!!’’ Sai da ta jera wajen hud’u tukunna da kyar ya ce ‘’Ki zo da wuri gobe, sannan ki zo da SScertificate ɗin naki’’. ‘’Ok,inshaaAllah’’ Ta ce, daga nan ta yi shiru.. Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya samu ya iya kashe wayar dakyar yana jin yadda k’irjinsa yake bugawa…. Washegari.. Ya Musbah ya so ya raka ta sai aka yi rashin sa’a me sunan Baba ba shi da lafiya, dan haka ya barta ta tafi ita kad’ai su kuma shi da Baraka da Muhsin suka tafi kai Yaron asibiti. 7:3O ta Isa bakin company d’in na shi, k’irjinta yana abunda ya saba a duk lokacin da ta san ta kusanto shi. haka nan ta nufi gate d’in, sauri take so ta yi ta gama dan tana da exams kuma bata samu ta lek’a gidan Ammi ba dan sai da suka ɗan yi meeting ita da Ya Musbah akan ‘ya karb’i kud’in da Baba ya bata ya biya kud’in hayan su sa ci gaba da aikin ba komai’ dama ta san ba zai yarda ba ai kuwa ilai yak’i amincewa, , shiyasa bata samu ta je gidan ba saboda bata gama yanke shawara da farko ba da kuma ta gama yanke shawarar lokaci ya riga ya shige mata, dan haka in dai ta gama da nan da wuri tana so ta biya gidan Ammi su gama da ita tukunna ta wuce exams saboda kar matar ta ga ko dan ta bar aiki shine yau zata yi mata wulak’anci ta bar ta da aiki ya kai rana…… .. Tana zuwa bakin gate security ya gaisheta ya bud’e mata k’aramar k’ofa ta wuce ciki. Yau ma Racheal ce ta yi mata rakiya har chan sama office d’in nasa amma yau ba ta shiga ba suna zuwa ta ce mata ta shiga ita kuma ta juya ta koma. Tana hango shi fad’uwar da gaban ta yake yi ya tsananta… yau black suite yake sanye da amman ya cire babban suite d’in ya sak’ale ya bar k’aramar ta ciki armless (marar Hannu) da white long sleeve (farar riga ta ciki mai dogon Hannu) din da suka yi masa asalin kyau, ba ta san ya aka yi ba kawai sai ta shagala da kallon sa tana mamakin tsananin kyawu da kwarjinin da Allah ya ba shi. Tana tsayawa a wajen jikinsa ya ba shi da Mutum a gurin dan haka ya d’ago da niyyar tabbatarwa yana d’agowa kuwa suka had’a ido da ita. Da sauri ta sunkuyar da kanta dan tashi d’aya duk sai ta diririce…..kafin da kyar ta samu ta d’an d’aga hannunta ta yi knocking a hankali tukunna ta tura k’ofar ta shiga a hankali bakinta d’auke da sallama……. *MANNUBIYA* *31* A hankali ya amsa..yau ma kamar ranar farko haka ya kafe ta da idanu tun lokacin da ta shigo har ta k’araso ta zo ta zauna a hankali ta ce ‘’Good morning Sir. (Ina kwana, sir).” A hankali ya samu ya ɗan motsa ɗan mitsitsin bakinsa ya ce ‘’Morning’’ ya fad’i hakan still idanunsa na a kanta…. yana son blue a rayuwar sa gashi yau Manubiya ta sako royal blue d’in hijab wanda colour d’in ya fito sosai, har da kwalli da man leb’e yau ta saka wanda hakan ya sake rikita Yashjub dan lokaci d’aya ya ji komai ya tsaya masa chak!..tashi d’aya ta tafi da imanin sa. Ganin da Manubiya ta yi Yashjub ba shi da niyyar daina kallon ta ne ya sanya ta d’auko wayarta ta shiga yi masa bayanin k’orafin da aka bata… baiwar Allah har printing ta yi ta taho da shi dan ita har gobe ganin sauk’in aikin ta ke yi sosai! duba da yadda za’a dinga biyan ta har 3Ok a wata… sai da ta karanta masa ta d’ora da bayani tukunna ta hada da certificate d’in nata da takardar ta tura masa gaban shi. Shi dai Yash ya ga ta ajjiye takardu kuma ya san tanata magana tun d’azu amma wallahi shi bai fahimci komai ba..duk bayanin da ta yi sam bai fahimci ‘Alif’ daga ciki ba. kallon ta kawai ya ke yi yana jin wani sanyi da nutsuwa sannan yana lissafin mallakar ta a matsayin Mata…....yana mai addu’ar Allah yasa idan an fara maganar auren su kar a d’auki lokaci mai tsayi...shi kad’ai ya san me yake ji game da baiwar Allah n nan,a hankali ya fesar da numfashi ya lumshe idanunsa… lokacin da yake ganin Abokansa a makaranta suna hauka a kan y’an matan su haushi suke ba sa,yanzu kuwa ya daina ganin laifin su dan a halin da yake ciki baya jin akwai abunda ba zai iya aikatawa akan baiwar Allah n nan ba muddin bai sab’ama addinin musulunci ba, ko ihu ne idan Manubiya tace tana so ya yi ta kurmawa tou tabbas a shirye ya ke, zai kurma!!!! Ashe haka so yake?…. Yahanasu ta yi gaskiya,dan yana bata labarin Manubiya ta ce masa “in bai yi sauri ya gaya mata yana son ta ba to nan da y’an kwanaki kad’an sai ya ji kamar ya yi hauka.” “Sir I’m done(sir, na kammala bayanin)” Muryar Manubiya ta katsewa Yashjub tunani wadda ta fad’i hakan ba tare da ta kalle sa ba. ‘’You look cute today! (Kin yi kyau yau!)’’ Muryar Yashjub ta dira a cikin dodon kunnuwan Manubiya. Wani irin fad’uwa gabanta ya yi wanda har sai da ya sanya ta d’an sake sunkuyar da kanta k’asa. Kamar ta fashe da kuka haka ta ji… Tabbas Yashjub so yake ya karya juriyarta dan in aka ci gaba a haka ba zata iya ci gaba da tsayawa kai da fata a kan abunda ta yi wa kanta alƙawari dan ta ga alamar ya dage sai ya ga bayan d’an guntun kwarin guiwar tata, bai san a ta ya take iya yin aikin nan da shi ba! bai san me take ji ba! bai san yadda take kokawa da zuciyarta bane ba….. Tana buk’atar aikin nan saboda ta samu ta kula da ahalinta amma muddin zai dinga torturing d’inta(wahalar da ita) irin haka gaskiya ba zata iya jura ba gara ta nemi wani hanyar taimakawa ahalin nata, dan ba za ta yadda ya juyar mata da tunani ba. Tana sane da shi akan kiran da ya yi mata jiya akan maganar certificate….bayan tuni a zuwanta na farko ya riga ya ce mata ta taho da certificate d’in nata photocopy, amma shine ya kama ya wani kira ta jiya cikin dare. Ba ta san takun da yake haɗawa akanta ba amma tabbas ba za ta ba shi k’ofa ba, tunda ta san ba auren ta zai yi ba dan wannan ba sa’an auren ta bane ba, dan ko da ace ya yi niyya ma ta san yana zuwa idan ya ga yanayin gidan su zai fasa, bayaga haka ma ta ma san yana da matar shi tuni dan wannan a shekarunsa ga kud’i ga kyau ya ci a ce yana da mata da Yaro ko Yara…. Sosai Yashjub ya yi mamakin yadda Manubiya ta had’e rai ta tamke fuskarta tamau!!! Ta k’i cewa komai. Yadda ta chuno d’an mitsitsin bakinta ne ya bashi dariya kuma ya burge sa. A hankali ya d’an yi murmushi mai sauti wanda har sai da ta ji sa, ba tare da shakku ba ya sake cewa” You look cute today! breathtaking,to be precise ( kin yi kyau yau, a taƙaice irin mai tafiya da numfashin nan)” Saboda yana so ya tabbatar da ‘shin maganar tasa ce ta ɓata mata rai har haka kuma yana so ta sake cuno bakin dan ba kad’an ba kara mata kyau yake yi sannan har ga Allah daga cikin zuciyarsa direct maganar take fitowa.’ Shiyasa tashi d’aya Manubiya ta rikice dan har cikin gangar jiki da tsoka maganganunsa suke shigar ta..jin tana shirin bada Kai ne ya sanya ta ta mike tsaye da sauri… ba ta yarda ta kalle sa ba kawai ta fara magana “Sir! with all due respect, our relationship is strictly professional (Sir! Cikin girmamawa, dangantakarmu ni da kai ta aiki ce kawai!) ka ba ni aiki saboda Sir Najeeb yana jin tausayi na amma hakan ba wai yana nufin zan barka ka ci min fuska ta ko wacce siga ba! Yes, I know I’m poor (eh, na san ba ni da shi) amma hakan ba shi zai sanya in barku ku ci zarafin talaucina ba, dan haka ko ma wanne irin tunani ne a ranka game da ni ka daina, Banaso!.. Sau biyu kawai ka ganni ta ya har ka samu ƙarfin halin iya gaya mini kalar kyawun da na yi?. Mu ba komai ba ne face baƙi ga juna. A gaskiya, kirana da ka ke yi cikin dare da kuma yadda kake mu’amala da ni suna sa ni jin rashin kwanciyar hankali. Aiki ne kawai ya had’a ni da kai, babu wata alaƙa ta ƙashin Kai da ke a tsakaninmu… Ka je gida ga Matarka! Na tabbatar tana chan ta yi maka kwalliya..ita ya kamata ka cewa she looks cute (ta yi kyau) ba wai ni ba.’’ Tana gama fad’in haka ta juya da sauri ta nufi k’ofa, ji take yi kamar ta kurma ihu a ranta ta ce ‘’ku yi hak’uri Inna, na san na yi muku bak’in cikin albashi na duk wata amman ba zan yarda yayi wasa da tunani ba’’…. Dama tun farko yanayin yadda aka bata aikin ya ɗan so ya d’aure mata kai amma kamar yadda Abbakar ya ce ‘tausayin ta Sir Najeeb ya ke ji’ ne ya sanya kawai ta kawar da duk wani tunani na rashin kyakkyawan fata, In ba haka ba a ganin ta tsaf secretary d’insa za ta iya dan aikin sam ita ba ta ga wani dalilin hiring d’in ta (ɗaukarta) da aka yi ba. Tun lokacin da ta mik’e ta fara zazzaga masa bala’i ya kasa cewa komai, kuma ya kasa d’auke idanunsa a kanta..dama tun ranar farko da ya fara ganinta a office d’in Najeeb! Yadda ta ƙi yin magana da kuma yadda ta saka kuka ya sanya ya fahimci tana da temper but she’s also very weak (tana da zafin rai amma kuma tanada raunin Zuciya) tunda ga shi yanzu ma sam ta gagara jure tasirin da kallon sa gareta da maganarsa ta yau suka yi mata!!! Sai da ya fesar da numfashi tukunna ya aiyyana a ransa ‘Kawai ni fatana, Allah ya sa ta ɗan ji wani abun da ya shafi so da ƙauna a kaina, ko da ɗan kaɗan ne! Ba wai iya ɓacin rai maganganu da kallona suka janyo mata ba’…….. Ba abunda ya fi ba sa mamaki irin yadda sam ko sau d’aya bai ji zafin maganganunta ba! In banda burge sa ma shi kam ba abunda ta yi kuma ta sake samun mazauni ta zauna daram a cikin zuciyarsa, tabbas Manubiya ta san darajar kanta. Babu kuma abunda ya fi bashi dariya irin yadda ta balbale shi da masifa kamar ta samu d’an cikinta amman kuma sam ta gagara kallon idanunsa ko da sau d’aya ne. Tana kama hanyar k’ofar, Yashjub ya danna wani abu a kan tebur d’in nashi, ya koma ya jingina da jikin kujerar yana kallon yadda take tafe tana sassarfa kamar wadda aka ce mata zai biyo ta ya kama ta ne. Tana zuwa jikin k’ofar ta fara k’ok’arin jan glass d’in amman sai ta rasa ta ya ma za ta ja! Saboda ɗazu k’ofar a d’an bud’e take kad’an amma yanzu kuma kamar an yi sealing (haɗe) glass d’in an manne su duka a waje d’aya dan sam babu alamar ta inda zaka ce zaka zuge ko kuma ka tura ka bud’e… “innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Manubiya ta furta hakan a fili sai kuma wani irin tsoro ya lullub’e ta! Tabbas Yashjub ne ya rufe k’ofar nan, ko shakka babu. A yadda ta zuba masa rashin kunya sannan ta wuce za ta barshi a nan wurin.. to fa in dai babu mummunar nufi a cikin zuciyarsa game da ita kai tsaye yana zuwa ta san zai koreta ne bayan ya dake ta ko kuma shima ya rama bak’aken maganganun da ta zuzzuba masa!! Waenda ita kanta sai yanzun ne take tariyo wasu maganganun da ta faffad’a masa masu zafi waenda bai kamata ace ta gayawa Babban Mutum kamar shi ba, a ranta ta ce ‘’shikenan yanzu na tonawa kaina da kaina asiri, dan shi dai ba cewa yayi yana sona ba amman na bi na tak’arkare ina ta faman cewa ‘dangantakarmu ta aiki ce kawai’.” In dai kuma mummunan nufi ne a zuciyarsa game da ita to kuwa yadda ya rufe k’ofar nan Yana zuwa raping d’inta zai yi shikenan tata ta k’are yau. Ta aiyyana hakan a ranta Jikinta yana soma karkarwa. Juyawa ta yi da niyyar ganin me ya ke yi.. ta ganshi zaune ya hard’e hannuwansa biyu a k’asan k’irjinsa ya jingina da jikin kujera ya zuba mata ido sai kuma ta ga ya taso ya nufo inda take… Ai kuwa da sauri sannan a rikice ta juya ta fara kiciniya tana shashshafa k’ofar tana addu’ar Allah ya sauk’o da mu’ujizar da idanuwanta za su nuna mata wata tsaga ko alama a jikin glass d’in domin ta samu ta bud’e ta fice. .. A rikice take dudduba glass d’in tana yi tana waigen sa a gigice. ganin dai da gaske itan ya nufo ya sanya ta fara dukan glass d’in tana kwala k’arar ‘‘Help’’ Murmushi kawai Yashjub yayi, dai-dai nan ya k’arasa inda take. Tsoro da rikici ne suka sanya Manubiya ta juyo ta runtse idanunta ta d’aga hannuwanta sama kamar irin mutun yayi laifi ƴan sanda sun zo za su kama sa d’in nan, kafin a rikice ta ce’’Dan Allah ka yi hak’uri’’... *MANNUBIYA* *32* Murmushi kawai Yashjub yayi, dai-dai nan ya k’arasa inda take. Tsoro da rikici ne suka sanya Manubiya ta juyo ta runtse idanunta ta d’aga hannuwanta sama kamar irin mutun yayi laifi ƴan sanda sun zo za su kama sa d’in nan, kafin a rikice ta ce’’Dan Allah ka yi hak’uri’’ Yashjub bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba, aikuwa ya shiga yi kalar wadda ya dad’e bai yi ba. Ba k’aramin k’ulewa Manubiya ta yi ba kuwa, sannan ga tsoron da ya bi ya dabaibaye ta dan haka ta yi k’asa da kanta a take hawaye suka shiga wanke mata fuska. A rikice ya ce ‘’Ooo’O!sorry,i’m so sorry’’ dan tashi d’aya sai hawayen nata suka d’aga masa hankali. Bata kalle sa ba kuma bata daina kukan ba sai ma yawa da yaga hawayen nata sun k’ara, sannan ya lura da yadda hatta jikinta ya ke karkarwa…… A hankali ta d’aga hannunta, ta juya ta shiga k’ok’arin bud’e k’ofar a karo na biyu, wanda hakan ya ke nuni da alamar so take kawai ya bud’e mata ta samu ta fice. Ba zai tab’a iya jurar ganin ta a hakan ba, dan yadda hawayen nata yake zuba akan kumatunta haka yake ji kamar ruwan zafi ne ake kora masa a cikin k’irjinsa.. So yake ya bud’e mata k’ofar, amma kuma ya san muddin ya bud’e ficewa za ta yi , ba tare da sun fahimci juna ba. Jin kukan nata ya fara fita da sauti had’i da jan hanci ne ya sanya kawai ya d’aga hannunsa, a nan jikin glass d’in ya danna abunda ya bawa k’ofar damar bud’uwa wanda ba kowa ne ma zai fahimci za a iya bud’e k’ofar da shi ba. Tana ganin glass d’in ya ɗan motsa ta saka hannu ta jaa ta bud’e ta yi waje da wani irin sauri… Zai zama wani iri idan ya bita, kuma ya san ba za ma ta so hakan ba dan haka kawai sai ya juya a hankali ya koma ya zauna akan kujerarsa! ya dafe kansa wanda har ya fara sara masa. Sai yanzun ya fara jin haushin kansa da ya kasa fahimtar ya kamu da kaunarta ne tun a ranar farko..tun asalin farko soyayyarta ta yi wa zuciyarsa sahihin kamu, amma ya gagara fahimta bayan ga gaskiya nan k’iri-k’iri amma bai iya ya fahimta ba ya dinga wahalar da kansa da kuma ita kanta Manubiyan har da su bata aiki gashi ynzu ta tashi ta dank’ara masa matsayin boss d’inta a kwakwalwa da tunaninta… baya jin za ta yarda da shi cikin sauk’i..a yadda yaga ta rikice ta kid’ima sannan ranta ya b’aci daga ya ce mata ta yi kyau ɗinnan, ya san idan ba yayi da gaske ba to ba k’aramar wahala zai sha ba kuma sai ta d’auki lokacin da baya so a ɗauka a lamarin nasu kafin ma ya samu matsayinsa na ‘sir’ya goge a idanunta na ‘masoyi’ ya shiga. A hankali ya sake fesar da iska, kafin tashi d’aya ya yanke shawarar zuwa gidansu!… Ba zai sake d’aukar lokaci ko jira ba tunda ga abunda kwana kwana da jiran ya haifar. Sai da ya jera mata misscalls sama da biyar amma bata d’auki ko d’aya ba. A take gaba d’aya hankalinsa ya sake tashi ya yi dan haka ya ga gara ya kira Najeeb.. ko gaisawar kirki bai bari sun yi da Najeeb d’in ba ya ce ‘’ya nema masa adress d’in Manubiya yanzu, gashin nan zuwa wajen sa, idan ya zo zai ji komai’’. Yana gama fad’in haka ya katse kiran ya bar Najeeb kare da waya a kunne.. Wanda ya shiga lissafin …ya kamata ace a dai-dai wannan lokacin ya fara yi wa Yash dariyar mugunta, duba da yadda a baya yake zaginsu idan yaga suna abu a kan soyayya dan gashi alhakin su ya kama shi, tunda gashi yana nema ya susuce tun kafin a je ko’ina ma…..da kuma alhakin y’an matan da suka sha yin kuka a gaban sa saboda matsananciyar buƙatar samun kulawar Yash ɗin, amman kuma gaba d’aya tausayin Abokin nasa sai ya hana shi, sakamokon rikici, fargaba hatta da tsoron da ya jiyo k’arara a cikin muryar Yashjub d’in yanzunnan… A hankali ya fesar da iska kafin ya furta kalmar ‘’so gamon jini’’ a fili. daga haka ya datse ya kira class rep ya ce “ya tura mass number Abbakar yanzunnan” A ransa yana mai cewa “k’iri k’iri dai Yash sai ya janyo min raini a wajen Yaran nan, dan yanzu kam babu batun kwana kwana saboda ana ji na tambayi kwatancen gida za a fahimci inda muka dosa…” Gaba d’aya hankalin Abbakar tashi ya yi, tunda Sir Najeeb ya kira sa ya tambayesa kwatancen gidan su Manu. ji yake inama bai yi wa sir Najeeb ɗin kwatancen ba…tsabar halinda yake a ciki tashi d’aya idanuwansa suka ka’da su ka yi jajawur. Ya tsani abunda zuciyarshi ta gama aiyyana masa akan ya yi, amman kuma bashi da yadda zai yi.. ya san abunda yake shirin aikatawa bai kamata ba amman fa zuwa yanzu ya fahimci hukuncin da ya yanke kwanakin baya ba shi ne mafita ba! don tun kafin a je koina ya fahimci idan bai d’au mataki ba tou tabbas hakan na iya zamtowa ajalin sa. Ba ya so! sam baya k’aunar abunda zuciyarsa take gaya masa take saka tunzura sa akan ya aikata dan ya san hakan bai dace ba amma kuma babu yadda ya iya, dan haka ya d’ago wayar tasa ya bi number sir Najeeb wadda ya kira sa da ita yanzun ya danna call…. Najeeb yana zaune a office d’inshi yana duba wasu takardu Yashjub ya shigo tare da sallamar sa… Murmushi kawai Najeeb ɗin ya yi ya mik’e yana kallon sa kafin ya ce ’’na Manubiya bada kanka a sare’’. Kallon sa kawai Yashjub ya tsaya yana yi, dukda ya ji dad’in furucin nasa amman kuma yadda ya gansa ba a shirye chap ba ne ya b’ata masa rai! Dan haka cikin rashin jin dad’i ya ce ‘’Najeeb, ni da nake tunanin zan same ka a parking lot amma shine kalla ko socks babu a k’afarka ballantana takalmi sannan duba suits d’inka a gefe! Ina wayarka? Itama na san sai ka nemo ta ko??’’. Dariya Najeeb ya yi, sannan ya yi sauri ya saka socks d’in ya d’auka suit d’in da takalminsa ya rik’e a Hannu tukunna ya d’au wayarsa da makullin office d’in ya na me kashe computer ya ce ‘’muje Oga’’ ya fad’i hakan yana dariya. Suna fita a office d’in ya samu ya saka takalminsa sannan ya rufe office d’in ya bi bayan Yashjub wanda ya riga ya yi gaba da d’an sauri, yana tafe yana saka suit d’in tasa. Suna shiga motar, Yashjub yana shirin yi wa motar key kira ya shigo wayar Najeeb…. bai d’auka ba dan baya buk’atar takura a yanzu saboda yana so Yashjub ya bashi labarin mai ya faru tsakanin sa shi da Manubiya da ya rikice ya gigice har yake buk’atar zuwa gidansu da gaggawa haka!… Ganin an kira har sau biyu bai d’auka ba sannan ga na uku ya shigo ya sanya ya zaro wayar yana mamakin waye ne haka.. ya d’an yi mamakin ganin sunan Abbakar da yayi saving d’azun, dan haka ya d’auka ya kara a kunnensa ba tare da ya ce komai ba. Daga d’ayan b’angaren Abbakar ya ce “Assalam alaikom, Sir! Ɗazu na ji ka tambayeni gidan su Manu, shine ban sani ba ko zuwa za ka yi?’’ Sai da Najeeb ya ɗan juya ya kalli Yashjub wanda ya cilla kan motar ga titi tukunna ya d’an jinjina kai kafin ya ce ’’Eh,muna hanya ma’’ Dum!! Haka k’irjin Abbakar ya buga, ya ma kasa magana, ya kasa cewa komai..kafin da kyar ya samu ya ce ‘’yanzunnan su ka tafi k’auye, gaba d’aya y’an gidansu, sai jibi Za su dawo’’. Shiruu Sir Najeeb ya yi, yana d’an nazari kafin ya ce ‘’okay shikenan, ma zo jibin idan sun dawo’’ Daga haka ya kashe kiran ya juya ga Yashjub wanda yake tambayar sa “kai da waye ne?”. Shiruu Najeeb ya ɗan yi, yana so ya fahimci wani abun game da Abbakar…kafin kawai ya kalli Yashjub sosai, sannan ya ce’’ba fa sa nan, yanzunnan suka tafi k’auye’’ K’iiiiii!!!! haka Yashjub ya ja burki, tukunna ya juyo a d’an fusace ya cewa Najeeb d’in ‘’kuma shine ban ji ka tambayi wanne k’auye ne ba?ko ka san k’auyen?’’ Ɗan ƙuraa masa idanu Najeeb ya yi yana kallon shi kafin chan ya ce ‘’idan na tambaya zuwa za mu yi?’’ ‘’Ba tare da b’ata lokaci ba ma kuwa’’ Yash d’in ya ba sa amsa ya na me matsar da motar tasa gefen titi dan ya tare hanya har ya fara tara goslow. Sannan ya sake cewa Najeeb ‘’Wai tunanin mai kake yi ne?, ka kira da wuri mana mu samu mu kama hanya time is against us(bamu da isashshen lokaci)’’ ya fad’i haka yana kammala parking d’in sannan ya juyo ya zubawa Najeeb lumsassun idanuwansa!. Sai kuma cikin fushi sosai ganin Najeeb d’in still shi yake kallo sannan yak’i ya sake kiran wayar ya ce ‘’Bani number in kira su, bani mana da wuri ‘’ ya fad’i haka yana mik’awa Najeeb hannunsa. A hankali cikin kwantar da murya Najeeb ya ce ‘’dan Allah, ka d’an nutsu ka sarrafa komai ko da ace na mintuna biyar ne a cikin kwakwalwarka, saboda ita kanta idan ka wanke k’afa ka bita har k’auyen su a haka tou akwai matsala, ka tsaya ka fad’a min abunda ya faru sai a san abun yi, dan Allah.’’. Shiruu Yashjub yayi, kafin kawai ya d’auke kai! dan in ya biyewa jayayya da Najeeb yaga alamar ransa ne zai sake b’aci… A hankali ya kwantar da kansa a jikin seat d’in da yake zaune a kai… sun kusa mintuna talatin a haka kafin Yashjub ya gyara zamansa ya kunna motar ya ja suka koma inda suka fito. Har ya sauk’e Najeeb bai sake kallon inda yake ba haka nan ya juya ya wuce ko sallamar Najeeb d’in bai tsaya ya amsa ba, girgiza kai kawai Najeeb yayi daga haka ya nufi tasa motar ya shiga yayi mata key shima yayi gaba yana mamakin Yashjub da zazzafar soyyayar Manubiya wadda ya lura ta d’an fara tab’a masa Aboki… Zuwa wannan lokacin Najeeb ya fahimci k’arya Abbakar ya yi masa dan sai yanzu ya tuna suna da exams ma yau da safe around 9 yanzu haka ma maybe sun shiga, but baya so Yashjub ya je wa manubiya a haka dukda bai san me ya had’a su ba, zai bari in Allah ya kaimu gobe sai ya je ya lallab’a Abokin nasa ya fad’a masa me ya faru daganan su san abun yi dan a yadda suka rabu da Yashjub ya san ba zai tab’a sauraron sa yau ba. Lamarin Abbakar kuma akwai sark’ak’iya.. ya lura Manubiyan kanta tana ji da shi, shiyasa yake so ya nemi bakin zaren ya san abunyi dan ya san idan Yashjub ya san wani abun tou abun ba zai yi dad’i ba shi kuma bayaso Yash ya samu matsala da Manubiya saboda wani Abbakar….. In banda ciwo ba abunda kan Yashjub yake yi, tashi d’aya idanuwansa suka kad’a suka yi ja, in da ace zai san inda Manubiyan take to da sai yaje…. Kawai dai ya tabbatar tunda Najeeb ya masa haka to fa ba zai tab’a fad’a masa ba shiyasa kawai ya hak’ura ya yanke shawarar ya tafi gida yayi sabon shiri…… Yau ma kamar kullum haka Manubiya ta tartara Abbakar ta zuba a kwandon shara, tak’i kula shi. Ya riga ta kammalawa dan haka yana gama submitting ya yi sauri ya d’auke jakarta daga inda ake tara jakankuna ya fice ya tsaya jiran fitowar ta. A wajen ta same shi yana tsaye yana jiran fitowar tata. ‘’Ba ni jakata’’ shine kawai abunda ta ce da shi cikin tsare gida. Murmushi ya yi ya k’arasa inda take tsaye kafin ya ce ‘‘Ki yi hkr tou, dan Allah’’ ‘’Ba komai ya wuce Abbakar, kawai dai na ji haushi ne..bai kamata kai, musamman kai ba wai ace ka b’oye min abu irin wannan ba .shiyasa na ji zafin abun, yanzu kuma na huce so ba komai ya wuce.’’ A hankali cikin sanyin murya da mutuwar jiki sannan idanunsa a kanta kyam ya ce ‘’Sure? ba za ki tambaye ni dalilinna na yin hakan ba??’’ Da sauri ta ce ’’komai ya riga ya wuce, in da ace bai wuce ba da ko kallon ka ba zan yi ba kai ka san halina, tunda har ka ga na kula ka tou ya wuce kenan, kuma bana so ka sake yin maganar’’ Ajiyar zuciya ya sauk’e, ahankali yace ‘’Thankyou’’ ‘’Um’’ kawai ta ce, daganan ta yi gaba shi kuma ya bita rike da jakartata a hannunsa, suna tafe suna d’an tab’a hira. Gaba d’aya Abbakar haushin kansa yake ji na k’aryar da ya yi wa sir Najeeb sannan bayaga hakan ga ta nan a gaban sa amman ya kasa fad’a mata abunda yayi, shi sai yanzu ma ya yi tunanin watak’ila fa sir Najeeb d’in zai iya ganin su a cikin makarantar kuma tare dan haka yayita addua Allah yasa har su fita kar su had’u da shi. Kafin su k’arasa gida har sun shirya kamar basu tab’a yin fad’a ba. Manubiya ta lura da waensu ƴan change-change daga Abbakar tun ba ma da ta ba sa labarinta da Yashjub na yau ba! dan tashi d’aya ta ga gaba d’aya hankalinshi ya tashi kuma ransa ya b’aci, saboda sam ya kasa danne kansa wannan karon… ta so ta tambaye shi sai kuma kawai ta kawar ta basar da zancen ta sako wata hirar.. Da kyar Abbakar ya dinga yak’e har suka isa gida, ya yi mata sallama tare da fatan hutu mai albarka daga nan ya wuce gida shima. Dakyar ya iya k’arasawa ya tsaya ya gaisa da mamansa wadda take zaune a tsakar gida daganan ya koma d’akinshi da ke a soro, yana shiga ya tura k’ofa ya sak’ala sakata tukunna ya saki zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa tun a makaranta… bai yi tunanin ba zai iya hak’ura da Manubiya ba sai yanzu, tsananin k’aunar da yakeyi mata ne yasanya ya hak’ura yayi saurin had’a ta da Yash. A ganin sa da lissafin sa… na farko Manubiya ta fi k’arfin sa! sannan kusan age mates suke (shekarunsu ɗaya) shi da ita dan ko kwak’kwaran watanni biyu bai bata ba, sannan a kalar matsin rayuwa da wahalar da Manubiya ta sha ya kamata ace ta auri mai arzik’i ta yadda zata kula da kanta da ahalinta itama ta samu ta huta ta ji dad’in rayuwa, Waennan dalilai su suka sanya ya hak’ura da ita domin ta samu ta ji daɗin rayuwa kuma ya yi saurin had’ata da Yash dan a tunaninsa zai iya saka farin cikinta a saman nashi kuma ya zauna ƙalau sannan yana zaton idan ya had’a ta da wani ya ga tana farin ciki tou zai hak’ura ya samu zuciyarsa ta samu salama sai dai kuma a tashi d’aya a iya yau kad’ai ya fahimci abun ba haka yake ba!! kuma ya fahimci ya tafka babban kuskuren da in dai bai gyara ba to shine ajalin sa…. Tunda gashi tun yanzu ya fara shiga tashin hankali Ina kuma ga in soyayya ta yi nisa tsakanin ta da Yash….?.. … Ya yi kuka ranar kamar ransa zai fita, kafin daga baya ya yi shiru ya shiga duniyar tunanin nemawa kansa mafita dan tabbas da sake….. *MANNUBIYA* *33* Manubiya Tana shiga gida ta d’auki kud’in da Baba ya bata na Ammi ta nufi gidan, dan bata samu ta tsaya sun yi magana ba d’azun. Tana shiga ta tarar da aiki birjik!! Ammi ta hana d’ayar mai aikin nata tab’awa, dan hadda natan ma tace duk ta haɗa ta barwa Manubiya yau duk ita za ta yi .. Wai punishment d’in lettin da ta yi kenan.. haka nan suka zauna babu wanda ya had’a tsinke da tsinke a cikinsu, ana jiran Manubiya ta zo ta yi, dan Ammi ta fusata yau da lettin da Manubiyan ta yi ba da wasa ba, hakan ha sanya ko da Maama ma ta saka Baki wannan karon Ammi ba ta saurare ta ba dan haka itama maman sai ta kyaleta dan ta lura yau matar tijara take ji. Ba k’aramin tashi hankalin Ammi ya yi ba, da ta ji wai su Manubiya za su bar aiki….. babu damar ta ce bata yarda ba tunda dai ga kud’in ta an riga an bata.. dan haka ta shiga gaggaya mata maganganu, ta hakan ne ta samu ta d’an rage takaici kuma tace sai ta yi aikin yau!! Manubiya so take su rabu lafiya dan haka ta yi aikin ta gama tsaf ta je ta yi mata sallama… Bak’in ciki a gun Ammi kamar ta d’aura Hannu aka ta yi ta kurma uban ihu. Har k’ofa maama ta rakota, matar ta ji dad’in aikin da Manubiyan ta bari saboda ta lura Ammi so take ta wahalar da yarinyar dan ko Muhsin k’iri k’iri ta hana sa shigar mata cikin gida idan ya zo ko Manubiya baya samu ya gani dan iyakar sa tsakar gidan, yayi shara ya tafi,a cewarta ba ta so namiji ya shigar mata cikin parlour da kitchen ba……. ••••• Zuwa yanzu Yassir ya warke garau, dan har ya koma office ma. Ba k’aramin tashi hankalin Mommy ya yi ba ganin yadda Yassir ya k’ulla gaba da Yashjub! gashi Daddy ya ƙi ya sa Baki…. Ita ta rasa wanne irin dak’ik’in Yaro ne Yassir wanda ba a isa a gaya masa ya ji ba, sam ya k’i yarda da ita akan ‘ya hak’ura ya kula d’an uwansa..’ ta san muddin Yashjub ya tsame Yassir a lamarin shi Wallahi in ba da kyar ba sun rabu kenan har abada. Gashi yanzu ita kanta Yashjub d’in fushi ya d’auki yi da ita gadan-gadan tunda ta mare sa sannan ta yi waennan furucin garesa duk akan Yassir, shikenan ko sunanta baya kira! Iyakaci ya ce mata Ina kwana ko Ina wuni ruwanta ne ta amsa ruwanta karta amsa. Ita kanta ta fara da na sanin marin da ta yi masa da furucin da ta yi, dan gashi sun janyo mata ya k’ullace ta! ita gani take yi ma kamar gaba d’aya ya tsaneta…. kamar ba uwar da ta tsugunna ta haife shi ba! Shiyasa gaba ɗaya duniyar ta yi mata zafi. … Tsakanin Ummi da yaran gidan ma abun ba dad’i sam, d’azu da safe har bangajeta Kausar ta yi .. Yassir ma ya samu gindin zama a wajen Munirat, tun bata kula shi har ta zo ta fara kula shi sakamokon nacin da yake yi mata, sannan duk wani abunda ya san zai janyo ta so shi to shi ya ke yi tun ba ma da ya lura tanaso ta ga yayi repenting akan abunda yayi ba dan haka ya maida bata hak’uri d’abi’ar sa ba dare ba rana… kullum sai sun had’u a wajen dining kitchen har back yard binta ya ke yi in ta fita shan iska. ta sake da shi kuwa, dan Munirat irin matan nan ne masu raunin zuciya ga tausayi, kuma Yassir ya ci sa’a dan tun a ranar farko kyawunshi ya tafi da hankalinta, yanzu kuma kulawar sa da tausayin sa sun k’ara ingiza ta zuwa gareshi. A ranar da Ummi ta ganta ta fito daga d’akinshi, ta ja mata kunne sosai, ta kuma hanata shiga d’akin shi! Gaisuwa ta mutunci dai tunda ya nuna yanaso a yi su yi, amma ta tabbatar mata da ‘kar ta sake shigar mishi d’aki dan yin hakan ba dabi’a mai kyau bace ba…’ Ita kanta Munirat ta yi mamakin yadda ta kasa gayawa Ummi dalilin da ya sanya Yashjub ya daki Yassir a wannan ranar…. Wataƙila ko dan bata so Ummin ta tsani Yassir d’in ne, ko kuma ta ce za ta raba su har abada… Ita kuma Ummi bata tambaya ba, kawai a tunanin ta fad’an su ne ya had’o su shi da Yashjub d’in. …. Da Allah ya tashi kama Munirat kuwa, ranar Yassir ya biyo ta har d’akinta akan ta zo su je d’akinsa yanada surprise d’in da zai nuna mata..kawai sai ga Ummi ta shigo d’akin a daidai lokacin da Yassir ya janyo hannun Munirat ɗin ita kuma mistakenly ta fad’a jikinsa. Da kyar Ummi ta ɗan danni kanta ta cewa Yassir ya basu waje, ya na fita kuwa Munirat tana shirin yin magana Ummi ta wanka mata mari sannan ta rufeta da fad’a, kuma ta ce “ta bata sati biyu, ta fito da miji a yi mata aure..” Ba abunda ya fi b’atawa Munirat rai irin yadda Ummi ta k’i tsayawa ma ta saurareta, da kuma yadda ta yi zargin wani abun su ke yi ita da Yassir d’in….. .. Munirat ta ci kuka kamar ranta zai fita, dan bayan Ummi ta tafi da kamar awa d’aya ta kira yayarta za ta labarta mata amman sai ta ji itama yayar tata ta rufe ta da fad’a ashe har Ummin ta kirata ta kora mata jawabi…. sai da ta yi mata fad’a sosai, tukunna ta kashe wayar ko sallama ba ta tsaya sun yi ba.. Ranar haka y’an gidan suka gabatar da dinner d’insu babu Ummi babu munirat… Kausar kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha. Tabbas ta fara hango silver lining(alamun nasara) ba kamar da da komai yayi musu duɗum!!!. Sai k’arfe sha biyu na dare tukunna Munirat ta sauk’o k’asa ta d’ebi abinci ta nufi sama, wasu ma har an saka su a fridge haka ta d’auka ta yi warming a micro wave.. tana hawa saman ta nufi hanyar side d’in su kenan ta ji Yassir ya ce ’’Munirat’’ A zuciye ta juyo amma sai ya yi sauri ya rufe mata Baki da tafin hannunsa, ya karb’e plate d’in nata ya ajjiye akan centre table na parlourn saman kafin ya ja ta zuwa d’akinsa…. ko da suka shiga sai da ya sa ta yi masa alk’awarin ba za ta yi ihu ba tukunna ya cikata, ya cika mata Baki ya matsa gefe. Duk masifar da Munirat take ji, tashi d’aya ta b’ace ɓat!! Sakamakon abunda ta gani a gabanta…… Sosai ya yi decorating d’akin da candles, gashi an rubuta “I love you Munirat” da ballon’s, gwanin ban sha’awa… cikin sanyin jiki ya ce mata ‘’dama surprise d’in da na ke so na nuna miki kenan… Ina so in gabatar miki da kaina a matsayin masoyi kuma me neman aurenki, amma kuma na rasa a ina zan yi dan na san ba za ki yarda ki bi ni mu je wani wajen ba, kuma ba zai yiu na yi miki a cikin gidan ba…” Daga nan ya durƙusa a gabanta a hankali, sannan ya yi mata sahihin proposal. Duk yadda Munirat ta so ta d’an ja aji kasawa ta yi dan tashi d’aya ta ce masa ‘yes’ sai kuma ta juya da sauri ta fita, dan duk sai ta ji wata kunyar shi ta lullub’eta. Ko abinci nata bata tsaya ta d’auka ta ci ba dan tashi d’aya ta ji ta a ƙoshe… Tana fita Yassir ya saki wani kalar murmushi a ransa ya ce ‘’Allah sarki! zuciyar Mace bata da wuyar samu. very innocent soul(mai tsarkakakkiyar Zuciya)’’. ‘’Na san kin san ta fita ko? so za ki iya fitowa, Sannan nan gaba dan Allah ki daina motsi da k’ofa wajen yin lek’en, dan kad’an ya rage ba ki yi drawing attention d’in ta towards inda kike ɓoye ba (ba ki ja hankalinta zuwaga inda ki ke ɓoye ba).’’ Yassir ya fad’i hakan ba tare da ya juya ya kalli k’ofar bathroom d’in ba, kafin a hankali ya durk’usa ya fara d’auke candles d’in yana kashewa. Dai-dai nan Kausar wadda ta fito daga toilet d’in ta k’araso kusa da shi itama ta sunkuya ta fara tayashi, suna kwashewa suna kashewa a tare. …. Ganin ya ƙi kulata ne ya sanya ta ce ‘‘Haba dear! wai har yanzu fushin ne?’’ Mik’ewa ya yi fuskarsa babu alamun wasa ya ce ‘’Kausar!it’s either you talk (ko dai ki faiyyace min komai) ko kuma in yi fatali da wannan plan ɗin naki gaba ɗaya wallahi!. kin san dai yin hakan ba k’aramin aiki na bane ba ko?’’ Murmushi ta yi kafin ta ce ‘’ka tabbata? Na fa san halinka, Kuma take-taken ka ma akan Yarinyar na gani shiyasa na zo maka da wannan tayin, domin mu samu mu jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya. Are you sure(ka tabbata) za ka iya yin fatali da mission d’in nan (manufar nan tamu) ba tare da ka samu abunda kake so ba?’’. Cikin fushi ya mik’ar da ita tukunna ya ce ’’and you are not even jealous!(Kuma ba ma kya kishi!!)… tabbas yanzu na sake tabbatarwa raina min hankali kike son ki yi..kin ga Kausar i’m not your pet (ni ba abun wasanki bane ba) sannan ni ba k’aramin Yaro baneba….. Kwanakin baya da suka shuɗe kin nuna kin tsaneni, yanzu kuma a cikin kwana biyu kawai kin dawomin!. Idan kin san wasa za ki yi min da hankali saboda ki samu ki cimma wata manufa taki to wallahi tun wuri ki janye!! Idan kuma ba ki janye ba to this time around (wannan karon) zan ba ki mamaki!! bar ganin wai Ina son ki wallahi I can be your worst nightmare(wallahi zan iya zame miki babban masifarki)… Ba wanchan Yassir d’in da kika sani baneba har yanzu, Yanzu na chanja. Sannan kin ce akwai reason d’in (dalilin) da ya sa kukayi calling off auren mu ke da Mommy(da ya sa kuka janyo aka fasa aurenmu, ke da Mommy)….. Inaaso in ji dalilin da komai, inaso ki fad’amin komai, inaso in san menene shirinku dan ba zan yi participating a game d’in (ba zan bada gudummawa a wasan) da ban san inda aka dosa ba… Ba zai yiu ki dinga yi min abu ta bai bai ba, akwai abubuwa da dama da na ke so ki fahimtar dani If not (idan kuma ba haka ba to) kawai inaga gara abar……’’ Rungumeshi tayi wanda hakan ya sanya ya kasa ci gaba da magana.. sun d’an jima a haka tukunna ta d’ago ta na kallonsa ta ce ‘’Yassir ba zan iya gaya maka dalilin mu ni da Mommy ba, ka yi haƙuri. Na fad’a maka mun fasa ne saboda Kai da kuma farincikinka duk abunda mukayi mun yi shi ne saboda Kai! Idan ni ba ka yarda da ni ba! na san ka san dai Mommy ba za ta tab’a nemo bak’in cikinka da hannnunta ba dai ko? You just need to trust us on this one (Naka shine kawai ka yarda da mu a wannan lamarin) Saboda ba zan iya fad’a maka ba. Abu na biyu kuma kai nake so Yassir, Ina sonka tun farko.. fushin da ka ga Ina yi da Kai kwanakin baya kawai Ina yi ne saboda ina so ka bani space (iska) a samu a fasa auren mu da gaske. Ba za ka tab’a samun abunda kake so ba tare da ni ba! Dan haka ka taimakemu, ko kuma in ce ka taimakeni in samu in fitar da Ummi daga cikin gidan nan! In gyara tsakanin Daddy da Mommy! ta yadda za mu samu mu yi maka gatan da muke son yi maka, daga nan in ya so sai a yi maganar aurenmu. ka fahimceni?’’. Kanshi tsaye ya girgiza mata Kai kafin ya matsa daga Jikinta da inda take sannan ya juya mata baya tukunna ya ce ’’ban fahimceki ba Kausar! not untill you tell me (har sai kin gaya mini) ko da ace d’an single hint(ƙaramar alama) ne. Ba zan tab’a fahimtarki ba idan ba gaya min kika yi ba kuma in ban fahimceki ba ba zan taimake ki ba.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce “shikenan Yassir, amma kar ka bari Mommy ta san ka sani dan Allah’’ ‘’I promise (Na yi alƙawari) kawai yace, yana mai juyowa ya kafeta da idanuwa. Sai da ta sauk’e numfashi tukunna ta fara magana ‘’Ka san tun lokacin da aka haifi su Yahanasu, Daddy ya bawa Yashjub rabin dukiyar shi ko?’’. ‘’Continue (Ki ci gaba)” Yassir yace yana mai gyara tsayuwarshi A hankali Kausar ta ci gaba da cewa “Da wannan rabin dukiyar da kuma taimakon ƙwazo da aiki tuƙurun da Yashjub ya ke da su ne suka zamto silar da a yanzu haka hatta Daddy bai isa ya kamo k’afarsa a kud’i ba!. Bayan estates d’in da muka sani, Yashjub yanada hannun jari a companies daban-daban da kuma gidanjen man fetur!… Ita kanta Mommy bata san da hakan ba sai last two years ago (shekaru biyu baya da suka wuce) ne ta fahimci d’umbin arzik’in Yashjub. Daddy ne kawai ya san komai nasa amma abunda zai baka mamaki shekarar nan da ta wuce da ya tashi raba wasiyyar masu Hannun jari a companynsa(shi Daddyn)… Kamar haka ya raba; share d’in Yashjub (kason yashjub)a company d’in Daddy 50%ne (Kaso hamsin a cikin ɗari) Na Daddyn 18% (Sha takwas a cikin ɗari) Su Yasira su 6 kowacce tanada 1% masu hannun jari dama nasu already (tuntuni) 5% ne Mommy bata da komai ita dama Mama 20% naka kai kuma 1%.” Da k’arfi Yassir ya ce ‘’watt??’’ ‘’Kwarai da gaske’’ Kausar ta ce kafin ta d’aura da cewa ‘‘Mommy ta b’oye maka ne saboda ta san idan ka sani ba za ka ji dad’i ba. Yassir Idan ta ji na fad’a maka ba za ta min da sauk’i ba, ko su Yasmeen basu san da maganar nan ba! Yasira ce kawai ta sani Dan haka kar ka fad’awa kowa dan Allah sannan ina so ka yi min alƙawarin ba zaka yi komai ba. A hankali ya ce’’I promise (na yi alƙawari) Cigaba Ina jin ki .’’ Cikin son fahimtar da shi Kausar ta ɗaura da cewa ‘’Ka san a yanayin tsarin Daddy Idam Mutum ya yi graduating (kammala karatu) ya fara aiki ma to tsame hannunsa ya ke yi a kansa kuma tun ba yau ba ya riga ya ce ‘a cikin ku idan kuka riga kuka yi aure to tsakanin sa da ku sai dai ku dinga kawowa gida, dan ya gama baku kwandalarsa,’…… Tuni, ya riga ya gama gina Yashjub ya kafa shi! Wat about you(kai Kuma fa)?. Yassir idan ka kuskura ka yi aure a yanzu shikenan ka tashi da 1 percent da kuma company d’inka wanda bana jin a shekara ma yana kawo maka sama da million biyu, Shin ta yaya za ka iya ciyar da iyalinka? kuma na san idan baka kawowa gida kamar yadda Daddy ya tsara ba to kuwa ka had’u da tijarar sa kenan. Ita Mommy abunda take so shine ‘ta samu ta san yadda zata yi ta janyo hankalin Daddy a samu ya k’ara maka wani abun, ko da a cikin share d’in Mama da nasa dana Yashjub ne! A samu ayi maka karo karo kaima ka yi sama..’ To kuma an d’an fara samun nasara sai Hannun agogon gaba ɗaya ya koma baya tun lokacin da wannan matar Saddik’a ta shigo rayuwar Daddy, shikenan komai ya tab’arb’are! We need to get her out (Dole mu fitar da ita)! mu gyara tsakanin Mommy da Daddy, a k’ara mata share ka tsaya da k’afafunka kaima tukunna ayi maganar aure Yassir. A yanzu balance d’inka na duk shekara wanda Daddy yace yana tarawa kowa nasa Idan aka tashi baka na shekara ukun da suka wuce ba a baku ba dai dai fa kake kai da su Yasira! A matsayinka na ɗa Namiji!…. Daddy ya tartara komai ya damk’awa Yashjub wanda ba shi da wata kyakkyawar alaƙa da ɗaya daga cikin mu hatta Mommy… Iyaka Daddyn ne kawai ya san cikinsa kuma ya ke ɗan shiri da shi… Ka ga kuwa duk ranar da aka ce ya yi aure to komai hannun matarsa zai koma! Mu sai dai mu zama y’an kallo a gefe.. Daddy can take care of himself (Daddy zai iya kula da kanshi) daga nan har tsufan sa yanada kud’in da zai temaki kansa da shi da Mommy! Kai fa? kai da su Yasira…. Allah ya rufa asiri Idan ba ayi wani abun ba sai dai mu zama a gefe y’an kallo, abun tausayi! Gaba d’aya arzik’in gidan nan ya koma hannun shi shi kad’ai daga shi sai matarsa tunda tun yanzu dama ba kulamu yake yi ba…… Amman idan kuka zamto equal (ɗaya) da kai da shi, ko ma ace ka fi shi samu to tanan ne kad’ai komai zai tafi normal! tunda munsan kuma muna da tabbacin kai za ka kula da su Yasira da ita kanta Mommyn sannan ni za ka aura ba wata stranger (bare) ba dan haka arzik’inmu yana nan a wajen mu. Ba abunda ya fi d’agawa Mommy hankali irin yadda ya yi maka duka ranar nan! Kuma ka kasa ramawa saboda baka da power, shiyasa take so ku zama ɗaya a fannin arziƙi da samu, bata so wani ya taka wani…. kuma tana jin tsoron kar a yi ta zalintar ka ka zo ka ce zaka rama ta hanyar da bata kamata ba… Wannan itace gaskiyar magana Yassir, so muke yi mu taimake ka amma sai ka bamu hadi’in kai tukunna za mu iya. sannan dan Allah kar ka bari Mommy ta san ka sani dan bata so kowa ya ji! Saboda ta san ba lalle a fahimceta ba, dan za’a ga kamar ta fi sonka ne akan Yashjub’’.” Rungumeta Yassir ya yi, kafin a hankali ya ce ‘’Sorry Kausar, na d’auki alhakinki kwanaki, na yi tunanin gudu na kike yi, ki yi hak’uri, na fahimci komai yanzu.’’ Shiruu ya d’an yi kafin ya ce ‘’Amma ta ya Munirat za ta taimaka wajen case d’in (lamarin)Ummi? da har kike ta k’ok’arin haɗa ni da ita, sannan shin ba kya kishina??’’. Murmushi ta yi sannan ta ce “Yassir Ina kishin ka, amma bana so in zama kamar Ina controlling d’in ka(juya ka), sannan na san duk rintsi ni d’in dai ni ce a cikin zuciyarka. na riga na san halinka ba wai ban saniba.. na san ko na yi haukar rabaka da ita a yanzu ba zan yi nasara ba! Inaso mu zama d’aya ni da kai.. Shiyasa akan ka je ka yi abu a bayan idona gara ka yi a gaban idona, daga haka ni kuma in ci moriyar halinda ake cikin….dan Wannan yarinyar itace lagon Uwarta! Muddin ka kafa mata k’ahon zuk’a lokacin da uwartata zata hak’ura ta bar gidan nan tare da ita ma ba za a sani ba… Ba ka ji a labarin Yahanasu ba? saboda senator ta bar garin nan ita da y’ar sai bayan watanni tukunna suka dawo…. Tuni yanzu ita da Daddy sai dai kallo We make sure of that (Mun tabbatar da hakan) fitar ta a gidan ne kawai matsala, Wanda godiyar hakan ta tabbata ga Hajiya wadda ta hana Daddy sakin ta in dai har ba ita ta tafi da kanta ba. Ita ma kuma na lura idan ba sakin nata aka yi ba to ba zata tafi cikin sauƙi ba! Shiyasa Muke so mu sakata ta bar gidan da k’afarta daga nan Daddy ya rakata da takardarta.’’ Wani zazzafan numfashi Yassir ya fesar kafin a hankali ya ce ’’Na fahimci komai yanzu” daganan ya sake k’ank’ame ta A ranshi yace “Na gode Kausar.. ke da Mommy ku saka Daddy ya k’ara min share(kasona) Ni kuma zan shiga cikin dukiyar Yashjub.. In kwashi rabi In tarwatsa rabi Idan kuma abun ya zo da tangard’a in dagargaza komai, kowa ma ya rasa!. Bayan na gama da shi kuma zan dawo gareki, sai dai kawai ki ji ana d’aura mana aure! Saboda duk da bayanin nan da ki ka yi min I still don’t trust you (ban gama yarda da ke ba) Dan Inda ace da gaske kina sona to da zan ga ko da d’an guntun kishina ne a cikin idanunki da aiyyukanki,. Allah dai kawai yasa ba yaudarata kike yi ba! sannan ba ki da shirin shiga hanyata ki taremin abunda nake son cimmawa…dan cikin duk Mutane ke kad’ai ce banaso ki shiga hanyata saboda a shirye nake in bi ta kan duk wanda ya yi k’ok’arin tare min hanyar cimma abunda nake so in cimma….’’ Tunda Kausar take a rayuwarta bata tab’a jin shakkar Yassir irin na yau ba, dan kamar yadda ya fad’a mata tabbas ‘wannan ba shi ne Yassir d’in da ta sani a baya ba’! Idanuwanshi sun tabbatar mata da hakan, Hakan ya sanya ta d’an tsorata da shi dan ta san idan ya fahimci gaskiyar lamari to akwai matsala, dan ita har ga Allah baya gabanta! asalin gaskiya ma ita so take ta yi getting rid of him (ta kawar da shi a hanyarta) cikin sauk’i, shiyasa ta zo suka shirya…. Da gaske, akwai shiri maganganun da ta gaya masa ba wai babu ba! kuma duk gaskiya ne, da batun arziƙin yash da batun yadda Daddy ya kasafta kason company ɗinsa duk gaskiya ne, amma ko su Mommyn kawai biye su take yi saboda ita a cikin zuciyarta bata da mu Yassir ya ji dad’i ko kar ya ji ba dan ba shine a gabanta ba… ita kwata kwata babu shi a cikin tsarin ta na asalin gaskiya ma… …shirinsu ita da su Yassira shine su fitar da Ummi. …shirinsu ita da Mommy da baba larai kuma Shine su saka a bawa Yassir kaso mai tsoka sannan hatta Yash suna so ya janyo shi ya saka shi a cikin company d’in shi. …Ita kuma shirinta shine ta yi wa Yassir wayo, gudun kar ya je ya yi mata wani shirmen… ta samu ya bata lokaci da iska ta samu ta shiga jikin Yash shi kuma ta kwak’uma masa Munirat daganan sai dai kawai ya ga ana d’aura mata aure da Yash. Amma yanzu kam dole ta chanja taku! Saboda Ta san Yassir tun suna Yara idan zuciyarsa ta motsa babu abunda ba zai iya aikatawa ba! Dan haka ya zame mata dole ta yi betraying (ci amanar) Baba larai da Mommy dan ba za ta tab’a bari Yash ya ja Yassir a jikinsa saboda a yadda Yassir yake a zuciyen nan tsaf zai iya cutar da Yash ko dukiyarsa. Kuma dole ta yi sauri ta ko wachche hanya ta auri Yash daga nan ta san yadda za ta yi ta kare kanta ita da Yash daga sharrin Yassir. Zuwa yanzu Ummi ba matsalarta baceba dama so take yi ta bak’antawa Daddy rai sannan ta hana sa jin dad’i sakamokon abubuwan da yake yi mata a cikin gidan,! Shiyasa ta had’a guiwa da su Yassira.. Ai kuwa gashi ta ci riba! tunda gashi baya samun farin ciki da soyayyar Ummin, kuma ba ya jin daɗi! Dan haka ta tsame hannunta daga yanzu su ɗin su je su yi ta fama dan tana da abubuwan da sukafi lamarin Ummi barkatai a gabanta… Ita kad’ai ce a kan wannan nata shirin dan haka dole ta so kanta fiye da komai da kowa. A hankali ta ji yanayin ruk’on da Yassir yayi mata yana sauyawa.. wani k’ululun bak’in ciki ne ya tokare ta, da kyar ta iya danne zuciyarta ta ɓoye takaicinta tukunna ta d’ago ta kalleshi tana murmushi ta ce ‘’ba zan kwanta tare da Kai Da sunan wata a sak’ale a saman mu ba‘’ Murmushi ya yi kafin ya ce ’’sorry’’ daga haka ya cika ta ya je ya cire ballon d’in da suka had’a sunan Munirat ya jefar a k’asa ya dawo….. Yana shirin rik’e ta ta ce ‘’Yassir a ganina bai kamata mu….” ‘’Shii’’ ya ce a hankali cikin katsera kafin ya d’aura da cewa ‘’Come on! dont be a grandma mana, you know i miss u, ryt?… (Wayyo! ya kamar ba wayayyiya ba, kin san dai na yi kewarki, ko?) Daga nan ya janyo fuskanta da Hannuwansa duk biyu ya haɗe Bakinsu waje guda… Ba yadda ta iya dan bata so ya gano ta ko ya dasa ayar tambaya a kanta, hakanan tana ji tana gani ta hak’ura ta zuba masa idanu.. …….. A b’angaren Yash kuwa yana chan bai ma san suna yi ba..damuwa da tunani sun saka shi a gaba dan za’a iya cewa yadda ya ga rana haka ya ga dare, saboda k’iri-k’iri ya gagara yin bacci… ganin hakan ya sanya ya tashi ya dinga jero nafila, tukunna ya d’an ji sanyi a ranshi…. zuwa yanzu ya huce daga fushi da Najeeb dan haka ya sa a ransa inshaaAllah gobe suna fitowa daga meeting d’insu na sassafe da suke dashi, da shi da su Daddy, zai kira Najeeb, ya san yadda zai yi da shi ya tambaya masa kwatancen k’auyen su Manubiya.. yana wannan lissafin ya sake zaro waya bai damu da cikin dare bane haka ya yanke shawarar gwada sa’ar sa sai dai tun kafin ya kai ga kara wayar a kunnensa yanzun ma ya ji an ce masa a kashe kamar yadda tun d’azu da safe yake jin layin nata’a kashe.’ •••washegari da safe••• A rikice Baba ya shigo cikin d’akin su, bai tadda kowa ba sai Inna dan Manubiya ta fita siyo sugar Muhsin ya je gidan Ya Musbah Jidda kuma tana wanka Yana shiga ya nufi wajen kayansa ya hau duddubawa…. duk wasu ragowar kud’ad’en da yake da su haka nan ya kwaso ya tara su a gabansa ya hau lissafi, dai dai nan Jidda ta fito daga wanka tana mai gyara zaman hijabin a fuskarta. Ganin bai ma lura da ita bane yasa ta k’arasa kusa da shi a hankali ta ce ’’Baba’’ Sai a sannan ya yi fir-gi-git ya mik’e sai kuma ya fara kalle kalle da dube dube kamar yana neman wani abun… Sai da ya tabbatar babu kowa tukunna yace ‘’Yauwa Jidda ki kira Manu, zan fita yanzu idan kuka ga na kai awa uku ban dawo ba to ku d’auki innarku ku je wani gidan ku b’uya. Idan na samu na dawo zan yi muku bayanin komai. ku kira Musbahu ki ce masa shima su b’uya shi da Baraka….” *MANNUBIYA* *34* Yana shiga ya nufi wajen kayansa ya hau duddubawa…. duk wasu ragowar kud’ad’en da yake da su haka nan ya kwaso ya tara su a gabansa ya hau lissafi, dai dai nan Jidda ta fito daga wanka tana mai gyara zaman hijabin a fuskarta. Ganin bai ma lura da ita bane yasa ta k’arasa kusa da shi a hankali ta ce ’’Baba’’ Sai a sannan ya yi fir-gi-git ya mik’e sai kuma ya fara kalle kalle da dube dube kamar yana neman wani abun… Sai da ya tabbatar babu kowa tukunna yace ‘’Yauwa Jidda ki kira Manu, zan fita yanzu idan kuka ga na kai awa uku ban dawo ba to ku d’auki innarku ku je wani gidan ku b’uya. Idan na samu na dawo zan yi muku bayanin komai. ku kira Musbahu ki ce masa shima su b’uya shi da Baraka….” “Ba ni da ishashshen lokaci, inshaaAllah idan na samu na dawo zan yi muku bayani, ba wani abun cutarwa ko zalinci na aikata ba..kuskure ne na yi amma da yarda Allah komai zai gyaru.” Yana gama fad’in haka, ya juya ya nufi k’ofa yana zuwa ya d’aga labulen d’akin ya fice, fitt!. Da kyar Jiddah ta samu ta d’an dawo dai-dai tukunna ta juya ta bi bayan Baba da sassarfa tana mai cewa “Baba,Baba,Babaa!’’ A mugun firgice, gaba d’aya ilahirin jikinta yana karkarwa. Tana bud’e labulen su ka yi karo da Ya Yusuf, Murmushi ya yi mata kafin ya ce ‘’Sai mun dawo’’ daga haka ya juya ya bi bayan Baba wanda already ya riga ya yi gaba shi. A gigice ta fito ta bi bayan su, kafin ta kai soron ta fara hangensu a ta chan waje su biyu akan mashin d’in Ya Yusuf d’in amman kafin ta kai ga fita tuni Ya Yusuf ya burga mashin d’in nasa sun wuce. Kasa tab’uka komai ta yi tsabar rikici, kafin kawai ta fashe da kuka, ta durk’ushe a wajen abun tausayi… Ta dad’e a haka tukunna da kyar ta samu ta tsayar da kukan nata, ta na shirin mik’ewa Manubiya ta shigo… A rikice ta k’arasa inda take ta shiga tambayar ta “mai ya faru?” Da kyar Jidda ta iya yi wa Manubiya bayani, aikuwa a take ita ma ta gigice ta fita a hankalinta duk yadda ta so k’in yin kuka kasawa ta yi dan haka ta bar hawayen suka shiga sintiri akan kyakkyawar fuskarta… da kyar suka rarrashi junan bayan wasu lokuta tukunna suka share hawayen su, gudun kar su shiga su je maybe ko Inna ta farka ta gane sun yi kuka. suna shiga kuwa suka tarar da ita ta farka, dan haka suka danni kansu suka Bata abinci da maganinta da kyar, duk da sun lura da yadda take ta kallon su ma’snar ta gane suna cikin matsala kuma tana buk’atar k’arin bayani amma cikinsu ba wadda ta ce mata komai, suka nuna kamar basu fahimci me take nufi ba….. haka nan ta hak’ura ta kyale su. Har sama da mintuna talatin, amman sun gagara tab’uka komai, dan gaba d’aya a gigice suke ga kuma k’ok’arin b’oyewa Inna damuwar su da suke ta faman yi… da kyar suka d’an fara sauk’k’o da jakankunan, suna tunanin inda za su ganshi ko su san abunda ya faru, daganan sai a san abun yi. Ganin bazama su iya had’a kayan bane gashi sun ma kasa yin lissafi mai kyau tsabar rikicewa ya sanya kawai suka yi alwallah suka shiga jero nafilfili suna masu kaiwa ubangiji kukan su… ahaka har aka shafe kusan awa biyu da rabi! sai da suka ji sun d’an dawo dai-dai tukunna k’asa-k’asa Manubiya ta ce mata ‘su had’a kayayyakin nasu kamar yadda yace, in ya so sai su san inda za su kai inna daga nan su shiga neman Baba da neman mafita..’ sai da suka gyarawa Inna kwanciya…ta hanyar juyar da ita ta yadda ba za ta ga mai su ke yi ba tukunna suka shiga had’a kayan a hankali gudun kar ta fahimci mai suke yi.. tsaff!! suka had’a komai, suka zauna suka yi jugum! A haka har aka shafe wata awa biyun babu Baba babu labarin shi, sai a lokacin sukayi lissafin su nemi Ya Musbah dan tsabar yadda suka gigice sam ba su yi wannan tunanin da farko ba! Manubiya ce ta ce bari ta je ta dubo shi dan wayarta ba kud’i kuma ta ma kashe, Jiddah kuma ta zauna da inna wadda ta fara bacci yanzunnan…. Ganin har kusan mintuna ashirin ba Manubiya ba alamarta ne ya sanya Jidda ta mik’e ta nufi k’ofa da niyyar zuwa kiran Manubiya. Tana d’aga labulen ɗakin suka yi ido biyu da Ya Yusuf… bayansa ta kalla sannan ta d’an lek’a wai ko za ta ga Baba amman sai ta ga wayam!!! ba tare da ta sake kallon sa ba ta dake sannan ta danne tsoron sa, ta fito ta zo za ta wuceshi. Hijab d’inta ya janyo ya fisgo ta ya dawo da ita gabansa ya tsayar! Da sauri Jiddah ta sunkuyar da kanta, dan tashi d’aya hawaye suka shiga silalo mata….. hab’arta ya kama ya d’ago da fuskar tata da k’arfi wanda hakan ya sanya ta yi saurin runtse idanuwanta hawayen suka shiga sintiri da sauri da sauri akan kyakkyawar fuskarta. Ya jima yana kallonta tana kukan kafin ya ce ‘’Ok,sorry!(ok, yi haƙuri)” Ya fad’i hakan yana cika hab’ar tata kafin ya d’aura da cewa ‘’Gani na yi kina neman ki nunamin taurin kai, shiyasa ni kuma na dawo da ke seti..wannan kukan da kika yi ya nuna min ke d’in ce dai Jiddahta’’, sai da ya fesar da iska tukunna ya ce ’’za mu iya yin magana yanzu’’ ba tare da ya jira jin mai zata ce ba ya fara da cewa ‘’Baba bai dawo ba har yanzu, na ji d’azu yace ku gudu ko?? So a gani na a yanzu gaskiya gudawar itace kad’ai zaɓinku, amman kuma tsaf za ki iya gyara komai dan komai a hannunki yake. Ga Baba mallan chan a d’akinshi, Babana shima yana nan, Ki zo mu je kawai a d’aura mana aure, daganan ni kuma na yi alk’awarin zan saki Baba.’’ A rikice ta d’ago ta ce ‘’Ya Yusuf kai ne ka kama sa? mai ka yi wa Babana? ta ya akayi ya yarda ya bika?’’. Ta k’arashe tambayar tata cikin tsananin rud’ani da tashin hankali. Murmushi ya yi kafin ya ce ‘’Ba ni na kama sa ba, amma ni na yi silar da aka kama sa….. Jidda abun takaicin shine akan naira miliyan d’aya tak za’a kulle Babanki kina ji kina gani!!saboda tsabar taurin kanki, haka nan zai yi ta shan wahala, bayan kina da ikon da za ku taimake sa… bari in faiyyace miki abunda ya faru…. Ranar chan a masallaci na gan sa yana kuka, sai na nuna masa na ji tausayin sa ne, na ce masa ‘ana bada loan a bankin da nake aiki, idan yana so zai iya k’arba ya yi business da shi, bayan shekara uku ya biya’ na yi masa alk’awarin a k’asan suna na ma zan saka shi! ta yadda ko da ace ta kwab’e ya kasa biya ba za’a kama sa ba tunda sunana ne a wajen, kuma ma inshaaAllah kafin nan za mu biya kud’in…’ A take ya ce min ‘akwai business d’in dama da yake da shi a rai, ya ke son yi! InshaaAllah a cikin shekara biyu ma zai had’a kan kud’in ya cire ribar sa.’ A lokacin alhaji Baba har rungume ni ya yi, Allah sarki na ji tausayin shi kuwa na so in janye k’udirina da na k’ulla akansa amma kuma da na tuno da kalar cin fuskar da kukayi min Sannan na riga na fahimci indai ba ta haka na biyo ba to ba zan tab’a samun ki ba… Sai na kauda tausayin shi a raina, na d’auke shi muka je ya cike form kala-kala ba tare da ya san mai yake cikewa ba…..wanda a ranar tabbas rashin zuwa makarantar Baba ya taimaka min ya kuma yi min amfani matuk’a!! saboda dama Inata adduar Allah ya sa kar ya fahimci wani abun amman sai naga ashe…’’ sai da ya d’an guntse dariyarsa yayi k’asa da murya sosai tukunna ya ce ’’ashe Baba ko cikakken sunansa ma bai iya rubutawa ba’’ Ya fad’i hakan yana mai kwashewa da dariya… Sannan ya ci gaba da cewa “Ni na dinga yi masa spelling, na nuna masa inda zai yi tumbprint, shi kuma ya yi ya mik’a. Bawan Allah har muka dawo gida yana ta yi mini godiya, Ina ga Ya san in ya gaya muku za ku tuhume shi shiyasa ya yi shiru dan har d’azu ma sai da na tambaye shi, shi kuma ya ce min ba ku sani ba, ni kuma na ce to zan zo in yi muku bayani ta yadda za ki fahimceni dalla-dalla, dan har ga Allah dama na ji dad’in shirun da yayi saboda dama banaso kowa ya sani sai a yau d’in. Na san za ki ce min mai naci ko kuma mara zuciya Jidda amma inaso ki san cewa duk abunda na yi na yi sa ne saboda farin cikinki! sai kin aure ni tukunna za ki fahimci gatan da nake ta k’ok’arin ganin na tsunduma ki a ciki. Ki taimake mu ki yi abunda nake so, daganan sai mu je mu ceto Baba, dan muddin suka riga suka tafi da shi to ko an biya kud’in tabbas fito dashi ma aiki ne!!! inada dubu d’ari tara zan bada cash na san ba za’a rasa cikon da zai had’a kan kud’in ba har intrest d’in ma. Iyakar abunda za ki yi hargitsin nan ya mutu shine ‘kawai ki aminta da ni!’ Daga nan komai zai tafi cikin tsari. Ya yarda da ni sosai, yanzu haka yana chan yana jirana in je in fitar da shi, dan ce masa na yi zan zo in yi muku bayani in kwantar maku da hankali daganan in tafi neman kud’in da za’a harhad’a a fito da shi. To ni kuma kinga sai kin yi min abunda nakeso tukunna zan fitar da shi Dan haka kinga ƴancin Babanku a hannun ku ya ke. Sannan bayan an tafi da shi, za’a zo a kama ku dukkanku har sai kun fito da kud’in nan!! daga nan kuma a fara kiciniyar fito dashi..’’ Wani irin kuka Jidda take yi abun tausayi, da kyar ta samu ta d’ago kenan za ta yi magana idanuwanta suka sauka akan Manubiya wadda ta gama yawon neman Ya Musbah a wajen wankin su da Gidansa amman bata same shi ba. Da gudu Jidda ta tafi ta fad’a jikinta ta sake fashewa da wani Irin kuka…. Tsabar tsananin mamakin Ya Yusuf da takaicin sa da kuma tsananin tashin hankali sam Manubiya ta ma kasa kuka ta kasa magana… haka kawai ta kafe Ya Yusuf da idanu kafin ta samu ta janye Jidda daga jikinta a hankali idanunta har zuwa wannan lokacin suna akan Yusuf d’in tukunna ta nufesa… yadda Yusuf ya ga ta nufosa sai da ta yi masa kwarjini, aikuwa tana k’arasawa inda ya ke bata yi wata wata ba ta d’aga Hannu ta zabga masa wani irin gigiceccen marin da ita kanta bata san tana da k’arfin yin irinshi ba….. A rikice Ya Musbah wanda suka dinga tafka sab’ani da shi da Manubiya ya iso hanyar d’akin nasu..tun d’azu Baba ya bada numbersa aka kira sa har ma sun yi magana da Baban. Bai ga marin da Manubiya ta yi wa Ya Yusuf d’in ba sakamokon k’ofar d’akin nasu da take a ta d’an lungu amman fa yana karya kwana ya hango Ya Yusuf ya shak’e Manubiya da dukkanin k’arfin da Allah ya yi masa, ga Jidda a gefe tanata k’ok’arin kwatar Manubiya amma ta kasa. Dama Ya Musbah neman Ya Yusuf d’in yake yi, dan a iya bayanin da Baba ya yi masa d’azun ya fahimci Baban bai lura tarko ne Yusuf ya d’ana masa ba, amman shi yana fara yi masa bayani ya fahimci hakan…a ganin Ya Musbah duk hauka da iskancin Ya Yusuf bai kamata ya sako Baba a cikin rashin mutuncinsa ba. Da gudu ya nufesu ya je ya fara k’ok’arin kwatar Manubiya daga Hannun Ya Yusuf, ganin ya ƙi cikata ne yasanya Ya Musbah ya fara kai masa duka, kamar jira Jidda take yi haka itama ta saka dukkannin k’arfinta ta dinga zuba masa duka a baya… Cikin ƙanƙanin lokaci abun sai ya yiwa Ya Yusuf yawa, shiyasa bai san lokacin da ya cika wuyan Manubiya ba, yana cikata kuwa itama ta sa hannu suka had’u har ita suka rufe Ya Yusuf da duka… duka bana wasa ba dan dukkan su su ukun a zuciye suke da shi, sai da suka kaisa har k’asa… Duk da haushin sa da Ya Musbah yake ji, sai kuma ya ga rashin dacewar hakan, ga kuma halin y’an gidan dama! kar Babansa ko wani nashi ya gansu ya ce sun yi masa taron dangi, haka nan su je su b’ullo da wani sabon hargitsin na daban kuma….. Dan haka ya tsayar da dukan da ya ke yi masa sannan ya fara k’ok’arin janye su Manubiya. Amman sai akayi rashin sa’a Baba Habu ya k’araso wajen sakamokon hayaniyar su da ta fara fita harabar gidan kuma ya ji kamar muryar Yusuf d’in. Da kyar Ya Musbah da Baba Habu suka samu suka janye su Manubiya dan rufarwa Ya Yusuf sukayi, suka yi masa dukan mata ta koina kamar sun kama b’arawo. Haushi da takaici ne suka sanya Baba Habu yarfawa Ya Yusuf mari bayan ya d’ago sa, A cewarsa ta ya zai tsaya su Manubiya su dake sa. Da kyar! dan ya jigata ko gani bayayi sosai saboda Ya Musbah ya fasa masa gefen ido..ya samu ya iya cewa Baban nasa “ai har da Musbahu.. shine ma ya fara kai masa dukan da ya kai sa k’asa.” Cikin fushi Baba Habu ya juya ya kalli Ya Musbah, kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya ja hannun Ya Yusuf suka wuce wanda gaba d’aya jikinsa! baki! hanci da gefen ido suke fitar da jini, gashi ya kasa mik’ewa ya tsaya sosai yanata faman rik’e ciki alamun sun dake sa a wajen…. *MANNUBIYA* *35* *BARKAN MU DA BABBAR SALLAH,UBANGIJI ALLAH YA KARB’I IBDUNMU YA MAIMAITA MANA.* Suna wucewa Ya Musbah ya dafe kansa.. ya fi second ashirin a haka tukunna ya d’ago ya ce ‘’bari in kai Inna gidana, sai in zo mu tafi wajen Baba. Muhsin dama tun d’azu na mik’a sa gidan Nafi’u.’’ Da sauri Jidda ta ce ‘’Ya Musbah kar ka je su ganka kai ma namiji su kamaka. A ganina gara ka bari mu Mata mu je…dan kai ba lallai su d’aga maka k’afa ba, inaga shiyasa Baba bai nemi ka je d’in ba ya ce ‘mu gudu’!. Ka bari za mu je na san idan suka ganmu Mata za su tausaya mana su d’aga mishi k’afa.’’ Ajiyar zuciya Ya Musbah ya sauk’e yana mai kallon ta ya ce ‘’D’azu Baban ne suka sanya ya kira ni da kanshi. Na ji tsoro tare da firgici mai tsananin a cikinnmuryarsa. Shin wanne irin d’a zan kasance idan na gudu na barshi a wannan halin saboda ni in ceci kaina? Jidda babu inda d’aya a cikinmu zai gudu ya je, ko da kuwa za su d’auke ni a matsayin fansar kud’in da Baba ya ci ne. Inna ma zan kaita gidana ne saboda kar a barta ita kad’ai anan, Dan gaba d’aya mu ukun nake so mu tafi tare.” Cikin katseshi Manubiya ta ce ‘’Ya Musbah ka san dai Baraka ba za ta kula da ita ba ko’’. A hankali ya ce ‘’Manu na sani. Yanzu haka Muhsin yana wajen Matar Nafi’u, so idan na kai Inna zan tura mata shi kuma zan ce masa in Inna tana buk’atar wani abun da ya san ba zai iya ba ya je ya kira matar Nafi’u. Ina so mu tafi mu dukan mu mu uku saboda Baba yana buk’atar mu dukkan mu, sannan kinga ni ban iya karatu ba dan haka ba zai yiu in je ni kad’ai ba… Jidda ba zai yiu mu je da ita kad’ai ba, kema kuma ba zai yiu in je dake ke kad’ai mu bar Jidda anan ba hankalinta ba zai kwanta ba, Ni kuma ba zan barka ku tafi iya ku biyu ba. Ba za mu bar Inna anan ba, kar mu tafi Yusuf ya shiga ya yi mata wani abun dan izuwa yanzu na gama tabbatarwa Yusuf babu abunda ba zai iya aikatawa ba….na Kira Nafi’u ya ce yana hanya, ku zo mu je mu had’a k’arfi da k’arfe mu hud’un tunda ba mu da wanda zai tsaya mana, na san Allah zai taimakemu, shi zai tsaya mana InshaaAllah… In ma sunk’i yarda su hak’ura ni zan bada kaina a matsayin fansar kud’in ba komai, a samu Baba ya dawo gida”. Shiruu duk sukayi kafin Manubiya ta yi sauri ta wuce tana share hawayenta tana mai cewa “zan jira ku a titi’’. Ya Nafi’u yana zuwa suka saka inna a motarshi suka kaita gidan Ya Musbah, kana ganinsu ka san suna cikin tsananin tashin hankali Jidda kam in banda hawaye ba abunda takeyi, ya Musbah ma da kyar ya ke iya rik’e kwallarsa, dan basu da tabbacin dawowar tasu… Baraka tana kitchen ya lek’a ya ce mata ‘’za su je wani waje, ga inna nan a d’akin bak’i.’’ Bata ko kalle sa ba ballantana yayi tunanin zata amsa shi. Hakanan ya juya ya bar mata kitchen d’in, ya samu Muhsin yace masa “in yana buk’atar wani abu ya je ya kira anty Aisha” daga haka ya kama hanya ya fito ransa duk ba dad’i. Yana zama a cikin motar, Nafi’u ya lura da yanayin shi dan haka ya ce ’’in ba zata yarda ba Musbahu kawai mu kai Inna wajen Aisha, tun d’azu da ka kirani dama na kira ta na gaya mata, dan da ni da ita duk mun d’auka a gidana ma za a ajjiye innar a wajenta…shiyasa ma har ta gyara mata d’ayan d’akin bak’in dake a tsakar gida.’’ Girgiza kai kawai ya Musbah ya yi kafin yace’’karka damu Nafi’u. ba zai yiu ace ni da gidana amma mahaifiyata ba zata shiga ba! ba zai yiu ba!. Ka bar batun Baraka kawai, dan bata da lissafi da ishashshen hankali, mu yi sauri mu yi abunda yake a gaban mu kar mutanen nan su fara shirme.’’ A bakin titi suka tsaya suka d’auki Manubiya tukunna suka kama hanyar Bankin… cikin d’aurewar Kai Ya Nafi’u Ya ce ‘’Ni fa duk ban gane komai ba, wanne irin banki ne za su ranta kud’i iya na kwana uku kuma su ce za su kama Mutum tashi d’aya? Sannan na ji kace Baban ya ce maka da kansa ya je bankin to ya akayi kuma suka kamashi????’’ Ajiyar zuciya Ya Musbah ya sauk’e kafin ya ce ’’wallahi nima kaina a d’aure yake da lamarin nan, na dai san sharrin Yusuf ne bani da tantama shi ne ya had’a komai. Shi kuma Baba ya yarda da shi, kuma ka san shi da b’oye b’oye, sannan ya ƙi yin shawara da kowa har ta chab’e. Bara dai mu je d’in, sai mu ji komai, Allah ya shige mana gaba.’’ ‘’Ameeen’’ gaba d’ayansu suka ce, daga haka motar ta d’au shiruuu kowa yana tunani da fargaba, dan haka suka shiga jero addu’o’i a cikin ransu. Aikuwa da suka je abun da suka yi zato d’in ne, dan ko cikin bankin ma ba su shiga ba a waje ake case d’in, saboda babu bashin banki tsakanin Baba da banki. Bashi! a tsakanin Baba da wani mai kud’i ne wai shi ‘Black Snake’ wanda k’asa take zarginsa dan a file d’in nashi ma har da case da efcc suna kan yi…. A jikin takardar ….Baba ya tambayi Mutumin aron miliyan d’aya, akan yana buk’ata urgent kud’insa sun d’an mak’ale amma suna fitowa nan da 2 days zai maida masa har da interest!. Idan bai maida ba kuma to ya yarda Mutumin ya yi masa duk abunda ya ga dama… Su ya Yusuf su suka yi shaida suka tsaya a tsakani da shi da wasu Abokan shi guda biyu. Babban abun takaicin shine yadda Mutumin ya ƙi baiyyana su gansa balle su samu su yi mishi magana!!! an ma ce musu baya ma k’asar gaba d’aya… Wasu mutane ya aiko su biyu bak’ak’e murd’ad’d’u, waenda ana ganinsu kallo ɗaya an san babu d’igon Imani a tare da su. Ana cikin haka aka ce ‘’ai case ya tashi anan, awa uku da aka bada ta cika dan haka yanzu sai dai a tafi da shi Police station. Kamar wani shahararren b’arawo haka aka datsa masa ankwa, aka saka shi a mota. Gaba ɗayansu Yaran suna kuka haka aka tafi da shi. Ba tare da b’aata lokaci ba suka bishi a motar ya Nafi’u. Suna zuwa suka tarar da wani sabon tashin hankali ‘Wai an bada order, a yi masa horo mai tsanani,’ Gashi an k’i a basu bail d’in shi. D’ayan police d’in ma ce musu yayi “su gudu.” Saboda wai black snake d’in tun d’azu ya bada order a kama har family d’in Baban a had’asu waje d’aya.. Suna tsaye a reception suka fara jiyo ihu, babu yadda ba su yi ba amma aka hana su shiga…. d’ayan police d’in ne ya d’an kwantar musu da hankali ta hanyar ce musu “ai ba ihun Baba baneba” sannan ya basu shawarar ‘su je su nemo kud’in, tun kafin abun ya fi haka lalacewa’ Da kyar dai aka samu suka hak’ura suka yi waje a gigice masu hawaye suna yi masu kuka sunayi. suna fita Ya musbah da ya Nafi’u kowannensu ya d’au waya suka shiga neman mafita a rikice. Sun shafe sama da awa d’aya suna tambayar jam’ar da suka sani bashi amma daga Ya Musbah har Ya Nafi’un kwata-kwata dubu ashirin suka had’a…. Uncle kanshi dubu uku ya turo ta acc d’in ya Nafi’u ya ce “su jira sa, in ya tashi a aiki zai zo ya duba Baban.” Gefe Jidda ta koma ta fashe da wani sabon kuka, ji take kamar ta gudu….. Saboda ita Manubiya ta yi aikatau a gidan Ammi! sannan yanzu ma gashi saboda ita aka kama Baba! in ba dakyar ba kuma ta san Ya Yusuf ne ya ce ayi masa horo mai tsanani, so yake ya rama dukan da suka yi mishi. Kuka gaba d’ayansu suke yi daga ita har Manubiya… Su ya Musbah kuma in banda waya ba abunda suke yi dan kaff d’an kud’in hannunsu ma duk ya k’are a siyen kati. Suna tsaye a harabar police station d’in sukaga wasu polisawa sun fito da tray da almakashi da wasu k’arafuna akai duk jini, sun nufi fanfo suna ƙarasawa su ka hau wankewa…. Tun kafin kwakwalwar Manubiya ta gama d’aukar charjin ‘watakil jinin Baba ne wannan…’ ta kwasa a guje ta yi cikin police station d’in, da kyar ta iya tsayawa ta shiga tambayar police d’in da ya biyota da niyyar taro ta. Tana kuka ta ce “ka bar ni in ga Baba, saboda Allah da Annabi.” Tausayi ta bashi dan haka ya nuna mata k’ofar inda Baban yake, ya juya kawai, a ransa yana mamakin ‘mai ya had’a waennan kamilallun mutanen da Black snake.’ Juyawa ta yi zata koma dan ta baro d’akin a baya, suka yi ido huɗu da su Ya Musbah, ashe sun biyota a baya suma, duk a gigice. sai da suka je bakin k’ofar d’akin kuma duk sai suka kasa shiga,kowa yana jin tsoron abunda zai shiga ya tarar. Da kyar Ya Musbah ya yi ta maza ya tura k’ofar ya shige! daga haka suma suka samu kwarin guiwar mara masa baya. Turuss! ya Musbah da ya Nafi’u suka ja suka tsaya…. Su manubiya kuma suka saki wani irin kuka. A kwance suka sameshi daga shi sai vest da dogon wando… In banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, da alamun bai ma san waye a kansa ba, ga jini a zuzzube a k’asa! Sai da suka matsa kusa dashi sosai, dakyar, tukunna suka lura ashe har da faratunsa na k’afa d’aya guda d’aya da na Hannu yatsu biyu suka fara zarewa. Da sauri suka zauna a gabanshi Jidda ta d’aura k’afafun shi akan cinyar ta Manubiya ta shiga goge masa gumi tana yi masa fifita, suna yi suna kuka a rikice. A zuciye ya Nafi’u ya mik’e cikin fushi ya ce ‘’Wanne irin rashin imanine da dak’ik’anci wannan? A haka zai fito musu da kud’in nasu?’’ Sai kuma ya nufi hanyar waje. Da sauri Ya Musbah ya sha gabansa ya tare sa. Cikin fushi ya Nafi’u yace ‘’matsa,matsamin in je in samesu” Cikin son fahimtar da shi ya Musbah ya ce ’’Nafi’u idan rai ya b’aci hankali ba ya gushewa… ka je ka samesu ka ce musu me? kud’i fa aka basu aka basu order kaga kuwa dole su yi abunda aka ce, kuma baka karanta takardar bane? mutum bai saka hannu bama ya aka k’are ballantana an saka hannu? Dole su yi abunda aka ce! Kuma ko Ina za mu je babu wanda zai tsaya mana, idan ka yi fad’a ko kuma ka ce zaka tada rikici yanzu sai a had’a da kai saboda baka da kud’i nima bani da kud’i shima Baba bashi da kud’i. Ka tsaya yanzu mu nutsu mu San abunyi mu ceto Baba, dan hayaniya da rikici ba namu bane ba.’’ Da kyar dai ya Musbah ya samu ya d’an kwantarwa da ya Nafi’u hankali aka samu ya nutsu kaɗan. Yana huci ya ce ’’na ji, ka fi ni gaskiya, ba zan je in same su ba amma wallahi tallahi duk wanda ya shigo da niyyar sake yin wani hauka anan wajen sai na illatashi. Ina nan ba inda zan je’’. Lumshe ido kawai ya Musbah ya yi ya bud’e ya ce ’’ba za su sake ba, in ma bamu samu mun had’a kan kud’ad’en ba, ba komai ni sai in fanshe sa’’. daidai nan Abbakar ya shigo wajen shima a rikice. Yana ganin Manubiya da yanayin kukan da take yi hankalinshi ya sake tashi..hankalin nashi bai gama tashi ba sai da idanuwansa suka kai ga Baba. Da sauri ya k’arasa ya na salati sai kuma ya kalli Manubiya, kamar jira take yi kuwa a take ta sake fashewa da wani sabon kukan.Ji yayi kamar shima ya sa kuka, da kyar ya samu ya tsugunna inda take a ahankali ya d’aga hannu kamar zai shafa fuskarta sai kuma ya sauk’e hannun jiki a sanyaye kafin ya runtse idonshi da k’arfi ya bud’e tukunna a hankali ya ce ‘’Ki yi hak’uri Manu, za mu san yadda za a yi inshaaAllah.. d’azu ya Musbah ya kirani yake gaya min, 3k ne kawai a acc d’ina na tura mishi yanzu kuma ga 20 na sake nemowa…ki kwantar da hankalinki za’a samo, kin ji, dan Allah ki daina kuka’’ Da kyar ta samu ta ce ‘‘Abbakar kafin nan mukasan mai za su sake yi masa? kall …..” K’arar bundugun da suka ji ba k’ak’k’autawa tare da hayaniya da k’arar motoci ne ya sanya duk suka yi tsit. Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k’ofar da mahaukacin k’arfi an shigo da gudu… *MANNUBIYA* *36* K’arar bundugun da suka ji ba k’ak’k’autawa tare da hayaniya da k’arar motoci ne ya sanya duk suka yi tsit. Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k’ofar da mahaukacin k’arfi an shigo da gudu… Body guards ne bak’ak’e k’irin da su sanye da bak’ak’en kaya da bak’in glass… biyu na farkon suna rik’e da manya manyan bindigu, ragowar na bayansu kuma k’anana ne a sak’ale a gefen k’ugun ko wannensu. Yanayin wajen suka kalla dan haka d’aya a cikin su ya juya ya fita da gudu, ya je ya kawo kujera ya ajjiye, kafin ya koma ya shiga cikin layi biyun da suka yi a jere tundaga bakin k’ofar har izuwa inda suka ajjiye kujerar a gaban Baba. Tsayawa kawai su Manubiya suka yi gaba d’ayansu suna kallonsu.. Basu kai ga gama tunani da lissafin abun ba, tashi ɗaya suka fara jiyo wata iriyar dariya ana yinta cikin wani kalar sauti da kuma murya marar dad’in sauraro…. Yadda ake dariyar ne zai sanya tashi d’aya a fahimci rashin kamala da rashin sanin ciwon kan mamallakin muryar…Yana magana da turanci yana dariya sosai kamar wani tab’abb’e!. Yadda su ke jiyo muryar tana matsosu ne ya sanya suka fahimci Mutumin nan cikin d’akin zai shigo.. Ta tsakiyar body guards d’in nashi waenda suka hau layi ya bi ya shigo… Ƙato ne sosai, dogo, lukuti, fari sosai..farin nasa irin jaaa!! Ɗinnan. Babu gashi ko guda d’aya tun daga scarf d’insa (fatar kansa) har gemun sa da gashin baki duk babu gashi! Iya kar girar sa da gashin idanunsa ne kawai masu gashi a kaf ilahirin kansa zuwa fuskarshi wanda hakan ne ya basu damar ganin asalin yanayin fuskartashi wadda take d’auke da k’ananan Idanu jajaye, da ɗan guntun Hanci, yayinda Bakinsa ya kasance madaidaici. Yadda dpo yake binsa yana russuna masa yana yi masa magana kamar zai kwanta abun dole ya k’ular da jama’a… dariyarsa kawai yake ta yi shi kam at the same time yana bawa dpo amsa, har ya iso inda Baba ya ke!. Shiruu ya yi ya tsayar da dariyar tasa kafin ya kalli dpo tukunna ya ce ’’ku ka ce yana kan karb’an punishment (hukunci) But (amma nagani he’s still conscious,Y(har yanzu yana cikin haiyyacinsa, mai yasa?)?’’. Yayi tambayar yana mai zubawa dpo jajaye idanuwansa. A take dpo d’in ya rikice ya fara kame-kame ya shiga karanto addu’o’i daban-daban a k’asan ransa yana mai neman tsari daga sharrin ‘Black Snake’! Dan kasancewar yanzunnan ya gama raha da dariya da shi ba shi zai hana shi sauya masa kamanni a take a wurin ba!.. kamar kuwa ya sani dan tashi d’aya black snake ya gama rayawa a ransa ‘zai sanya body guards d’in shi su yi wa dpo asalin horo, a yanzu a gaban kowa, ta yadda next time zai fahimci mai ake nufi da horo!!’ dan haka ya d’an d’ago kansa da niyyar juyawa ya kira biyu a cikin body guards d’in shi amma sai Idanuwanshi suka sauk’a akan Manubiya wadda gaba d’aya tashi d’aya ta rikice sannan tsoro ya lullube ta daga ganinsa! Ba abunda ya fi d’aga mata hankali irin zanen bak’in macijin da ya fito tarr!! wanda yake nan a kwance a hannunsa na dama…tun daga kwanjinshi har kan bayan tafin hannunshi kamar na gaske ga wasu uban sark’ok’i a jikinsa wuya da hannu da wani burgujejen wando shima mai sark’ok’i a jiki amma kuma rigar jikinsa armless(marar Hannu). Wata mahaukaciyar dariya ta ga ya kwashe da, ga mamakinta kawai sai ta ga ya nufota aikuwa kafin ya k’araso tuni ta shige bayan Ya Musbah ta b’uya. Da mamaki ya kalleta ya juya ya kalli Jidda sai kuma ya juya ya kalli d’aya daga cikin bodyguards d’in nasa ya ce ‘’John!dama ita biyu ce?’’ ‘’A’a ai dama Kabir d’in ya ce tanada sister, remember(ka tuna)?’’ Dariya ya yi kafin ya juya ya shiga yi wa Manubiya wadda ta b’uya a bayan ya Musbah wani irin kallo har da lek’awa yake yi yana sakewa saboda a yadda Abokin Ya Yusuf ya yi masa bayani tabbas Yarinyar ta fi haka kyau a fili.. Ya Musbah ya kalla ya kalleta kafin ya yi wani kalar murmushi.. Ba su gama fahimtar ma’anar murmushin nashi ba suka ga ya yi fito!. Da sauri ɗaya a cikin body guards d’inshi ya zo ya hankad’e Ya Musbah ya fisgo Hannun Manubiya ya dawo da ita gaban black snake ya tsayar, tukunna ya juya ya koma ya je ya tsaya a wajen tsayuwarshi. Cikin d’an d’aga murya ya Nafi’u ya ce ‘’Me ye haka wai?’’ Ba wanda ya ko kalle sa balle su bashi amsa, a hankali black snake d’in ya sa Hannu ya d’an kamo hab’ar Manubiya ya d’ago yana mai k’are mata kallo. Da sauri ta kawar da kanta gefe, tana wani irin kuka…dan gaba d’aya a tsorace take ga tashin hankalin da take a ciki tun farko dama ga kuma zuwan wannan abun tsoron shiyasa duk ta bi ta sake duburcewa, in banda karkarwa babu abunda jikinta yake yi. ‘’Mallan kana haukane!’’ Ya Musbah wanda ya taso yanzu ya fad’a a Zuciye yana shirin yin kan black snake d’in… A take wani a cikin bodyguards d’in nashi ya saita masa bindiga.. Da sauri Baba ya ce ’’dan Allah kar ku yi musu komai, dan Allah” sai kuma ya fashe da Kuka. Shi kam black snake gaba d’aya hankalinshi ya tashi da ganin Manubiya!.. Babu k’asar da bai je ba a rayuwarshi sai dai in da ba’a rasaba, amman ba zai yi k’arya ba duk yawonsa da gane ganensa bai tab’a ganin Mace mai kyawu sannan Macen da ta d’auke hankalinshi lokaci guda kamar Manu ba. Kallonta kawai yake yana sakewa kamar ya samu television…. Sai da ya lashe Bakinshi tukunna ya kamo hijabinta ta k’asa bata yi auni ba kawai ta ji ya d’ago shi ya zare ya yar a gefe… Tabbas ba k’aramin zafin tozarcin da ya aikata mata ta ji ba, dukda kuwa doguwar riga ta Abaya ce a jikinta amma ji ta yi kamar ta kurma ihu. Tashi d’aya ta ji wani irin bak’in ciki ya lullub’eta, bata san lokacin da ta d’aga Hannu za ta kifa mishi mari ba. Ya Musbah da Ya Nafi’u ma duk nufar sa suka yi dukda bindigar da ke saite a kan Ya Musbah bai ma san lokacin da ya motsa ba. Abbakar shima yana ganin haka ya yi kansu cikin fushi. A lokaci guda black snake ya zaro pistol daga cikin aljihun wandonshi ya saita k’afar Abbakar ya sakar mishi bullet sannan ya rik’e tattausan Hannun Manubiya da d’ayan Hannun nashi. ‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’ gaba d’ayansu suka ce, sai kuma suka yi kan Abbakar wanda ya fad’i a wajen, ya yi suman wucen gadi, tsabar azaba ya ma kasa kuka ya kasa magana Yanajin azabar da tunda uwarshi ta kawoshi duniya bai tab’a ji ba tana ratsashi. Black snake bai huce ba sai da ya kuma harbin d’aya a cikin bodyguards d’insa a kafad’a wanda d’azu ya saitawa Ya Musbah bindiga Cikin dakakkiyar murya ya ce ’’da ka saita masa bindiga ka ga ya motsa harbesa ya kamata ka yi, next time you should take note (Ka ɗauki darashi saboda gaba)!’’. Ba tare daya cika Hannun Manu wadda taketa k’ok’arin kwacewa tana kuka tana kallon Abbakar ba Ya kalli kowa a wajen tukunna Ya ce ‘’yanzu na samu attention d’in kowa ko? Perfect(dai-dai kenan) bari ayi magana’’ ‘’My name is black snake (suna na Black snake) wanda ya kamata ace kuna jin tsoro amma na ga ku da Babanku kun raina ni, wanda hakan ne ya nuna min cewa ba ku san wayene ni ba ba kuma kusan what i’m capable of ba(abunda na kan aikatawa ba).” “Baba na nan kwance’’ Ya yi maganar yana nuna Baba, Kafin ya d’aura da cewa “ya ci kud’ina!. Ban san ta ya aka yi this old man (wannan tsohon) ya samu guts da audacity d’in (ƙarfin guiwar) cin kud’ina ba but duk nan mun san ya ci min kud’ina, sannan a statement d’inshi ya rubuta in yi mishi duk abunda na ga dama idan har bai biyani ba.’’ Dariya ya yi kafin ya d’aura da cewa ‘’sai da na saka aka dubamin aka tabbatar min da mutumin nan ba mahaukaci baneba Tukunna Saboda na yi mamakin mutum mai hankalin da zai yi wannan rubutun a statement na tsakanina da shi I’m the black snake (Ni ne fa black snake)” Ya fad’i hakan yana d’aga hannuwanshi biyun sama still yana rik’e da hannun Manubiya, kafin ya ci gaba da cewa “ni mutum bai ce in azabtar da shi ba ma na azabtar ballantana kuma ya fad’a?!. Anyways I was overseas (Ko dai yaya ma, ina ƙasar waje) ba na k’asar aka fara case ɗinnan. Ni da Kabir a friend of your nephew Yusuf (Abokin ɗan wanka Yusuf) muka tafi and ya ji ni a waya ina magana akan hargitsin shine ya bani labarin da na ji dad’i kuma da idanuwana suka gani na sake jin dad’i…. Da farko ya ce min ‘wannan Baban ko kashe shi zan yi ba zai biya ni kud’ina ba saboda bashi da kud’i! Amma akwai wata hanyar da zan iya fanshewa…. Baba yanada kyakkyawar yarinya fara k’al! akwai wata rana da ya je a gidan su Yusuf d’in ya ganta ya cewa Yusuf yana sonta to ashe wai budurwar Yusuf d’in ce’.” Cikin yin k’asa da murya ya ce “ban gayawa Yusuf komai ba, bai ma san na dawo Nigeria ba as we speak(yanzu haka), dan Kawai Ina jin maganar budurwa na hayo private jet na na taho Na zo in yi betraying d’in shi (in ci amanar shi)’’ Ya k’arashe maganar yana mai kwashewa da dariya haka suma guards d’in shi duk suka kwashe da dariya. … ‘Da kyar Abbakar ya iya zaro wayarshi ya fara k’okarin kiran sir Najeeb. … Sai da suka gama dariyar su tukunna Black snake ya ci gaba da cewa “da farko ina ɗan tantama but yadda na ga Kabir ya rikice yana zuzutamin kyawun Yarinyar ne ya sa na amince na bi shawarar da ya bani na zo Akan ‘Baba ya auramin ita ni kuma in bar mishi 1 million, na yafe har intrest d’in’!‘’. Manubiya bata san tanada k’arfi ba sai da ta samu damar fincike hannunta daga cikin na black snake dan ba k’aramin girgiza ta maganar sa ta k’arshe ta yi ba. Dariya ya kwashe da ita kafin ya ce ‘’Ai ba ki ji best part d’in ba ma (Ai ba ki ji mafi ƙayatarwar shirin nawa ba ma),’’ Bai jira jn magana ba ya d’aura da cewa ‘’na yi zaton ke d’aya ne, to kuma da na zo sai na tarar ku biyu ne kyawawan matan, shiyasa na zo da better plan(shirin mafi dacewa) ‘Zan auri ɗaya in ajjiye d’aya mistress(ƙwara)’. What a smart boy am i, ko?? (Ni ɗin mai wayo ne, ko???’’)”. Ya k’arashe maganar tasa da tambaya yana d’an rawa kad’an-kad’an sai kuma gaba d’ayansu suka sake kwashewa da dariya. Kasa ma motsi Manubiya ta yi dan gaba d’aya kanta ya d’au zafi, In banda ambaliyar hawaye ba abunda take yi kamar an kunna famfo. Su Blake snake sun jima suna dariyar da su Manubiya suka kasa fahimtar abunda yake sakasu yin dariyar kafin black snake ya d’aga bindigar sa ya harbi window dan haka duk suka yi shiru suka nutsu.. su Manubiya kuwa in banda karkarwa ba abunda jikinsu yake yi, Addu’o’i kawai su ke karantowa dan tabbas black snake masifa ne. A kan Baba ya k’arasa ya tsaya tukunna ya ce ‘’Okay Baba, komai yana Hannunka yanzu, kaga dai na harbi mutane har biyu… But bafa wai na yi releasing gaba d’aya temper d’ina bane ba(ammafa a hakan ba wai na saki gaba ɗaya fushina bane), dan na yi iyakar k’ok’arina wajen danne Zuciyana shiyasa ka ga na harbesu a wajen da na tabbatar ba za su mutu ba! saboda bana so in yi mugun abu a gabanka a matsayinka na father inlaw d’ina(surukina) Amma, na yi maka alƙawarin muddin ka yi mini gardama! musu! ko taurin kai! to zan kashe maza guda ukun nan Sannan in tafi da matana! Ruwanka ne ka yarda ko kar ka yarda, kuma ba za ka sake ganinsu ba sai wataƙila bayan shekaru sha biyar in sun tsufa sai su dawo maka. Dan haka idan ni ne kai Baba to zan yi wa black snake biyayya in aura masa mata d’aya in bar masa d’aya kamar yadda ya ke so kowa ya tafi safe…. A rabu ba tare da wani fad’a ko grudges (riƙon haushi) ba, kaga ta hakan sai mun fi kare dangantakar da ke a tsakaninmu a samu ta zamto lafiyayyiya kuma dauwwamammiya. Sannan wani hanzari ba gudu ba, Inaso ku san cewa ba za ku iya sharia da black snake ba! Dan haka idan ma kuna tunanin court ne na wuce nan tun tun tun tuni…. I have my ways! (Inada hanyoyi da dabaru na).’’ .. Da kyar Abbakar ya iya d’ago wayarshi ya kira sir Najeeb, bai d’auka ba dan haka ya samu ya tura mishi message da taimakon Ya Nafi’u wanda ya tambayeshi ‘’mai zai yi?’’ shi kuma ya ce masa ’’wanda zai taimakesu ya ke so ya kira’’ Daga nan ya gaya mishi shi kuma ya rubuta; ‘Manubiya tana buk’atar taimakon Yash da gaggawa’ Da Address d’in police station d’in da suke a k’asa.’ Daga haka suka tura ba tare da an gansu ba. Kishi haushi da kuma takaicin abunda ya sake aikatawa wanda ya yi wa kansa alk’awarin ba zai kuma ba ne…suka taru suka sake zuzutamasa azabar da ya ke a ciki…dishi-dishi ya fara gani, daga haka idanuwansa suka rufe, ya sume a wajen yana mai addu’ar Allah ya sa Yash d’in ya zo, dukda kuwa kishi da takaicin sake had’ashi da Manu da yayi a karo na biyu yana ta addabar zuciya da ruhinsa amman kuma ba zai iya barin Manubiya a cikin wannan bala’in ba, bayan ya san akwai hanyar da zai bi ya cece ta. A chan gefe kuwa, wani a cikin guards d’in black snake ne ya tak’ark’are yana yi masa bayanin yadda ake auren Musulmai dalla-dalla, dan bai gama sani ba kasancewar sa Christian. A take suka yanke shawarar za a yi na musulmai kuma za a yi na Christian’s duk a wajen a yau! Dan haka ya cewa d’aya a cikin guards d’in nasa ya tafi ya d’auko pastor ɗinsu na church ya zo da shi kafin a gama d’aura na musulman. ……… Kuka gaba d’ayansu suke yi, ga Abbakar a yashe an ce za a kaishi asibiti Amma Black snake ya ce ’babu uban wanda zai yi motsi a wajen har sai an gama aura masa Manubiya.’ Zuwa wannan lokacin su kam sun d’auka ma Abbakar d’in ya rasu ne saboda dogon suma ya yi mai nauyi, duk wanda ya ganshi ba zai yi tunanin akwai rai a jikinsa ba. Sai da aka sake saitawa Ya Musbah da ya Nafi’u bindigu tukunna suka nutsu! Baba kuma ya ce “shikenan ya yarda zai d’aura auren” ya fad’a musu hakan, a ransa kuma yana tunanin ta yadda zai nemi mafita su samu su zille. Wani kalar murmushi black snake yake ta zubawa wanda ya ke nuna tsantsar farin cikin da ya ke a ciki… bai tab’a had’uwa da Macen da ta sace zuciyarsa tashi d’aya kamar Manubiya ba, shiyasa har Allah Allah yake ayi ayi a d’aura musu aure, ya samu cikakken iko a kanta, za ta ga soyayya, ya san za ta yarda da shi, duk da kuwa taurin kanta da yadda ya fahimci tana jin tsoronshi amma ya san idan ta ga ya riga ya zama Mijinta to dole ta yarda da shi sannan zai sameta yadda yake so dan ya san za ta yi mishi biyayya…. Ga Manubiya matarsa wadda zata haifa mishi y’a y’a ga kuma jidda a gefensa mistress.. wannan wacce iriyar rana ce haka mai sa’a ta riskeshi! Tabbas ya zama dole ya yi wa Kabir babban kyauta idan komai ya tabbata. •••• Around 2:OO pm, yana tsakiyar meeting kira ya shigo wayarshi, kamar ba zai kalla ba sai kuma ya d’an zaro wayar, ganin sunan Najeeb ya sanya shi saka wayar a silent ya ajjiye ta a gefensa, dukda kuwa ya san koma menene tou it’s very important tunda har Najeeb ya yi kiran shi a dai dai wannan lokacin…dan ba su dad’e da gama waya da shi ba ya ce masa ‘zai sake shiga wani important meeting d’in da su Daddy, bak’in nasu har yanzu basu tafi ba, but in ya fito zai kira shi.’ Ba zai yiu ya amsa wayar ba, dan meeting d’in da su ke yi mai matuƙar mahimmanci ne, shiyasa ya bari akan idan sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb ya ji dalilin kiran.. Kawai dai yana fatan Allah ya sa dalilin kiran ba abune mai mahimmanci sosai sannan wanda ake buƙatarsa da gaggawa ba, sannan yana fatan Allah ya sa har zuwa lokacin da za su gama meeting ɗin nasu lokaci bai riga da ya ƙure game da kiran da Najeeb ɗin ya yi masa ba…. *MANNUBIYA* *37* Ba zai yiu ya amsa wayar ba, dan meeting d’in da su ke yi mai matuƙar mahimmanci ne, shiyasa ya bari akan idan sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb ya ji dalilin kiran.. Kawai dai yana fatan Allah ya sa dalilin kiran ba abune mai mahimmanci sosai sannan wanda ake buƙatarsa da gaggawa ba, sannan yana fatan Allah ya sa har zuwa lokacin da za su gama meeting ɗin nasu lokaci bai riga da ya ƙure game da kiran da Najeeb ɗin ya yi masa ba….. ….. Kiran Yashjub Najeeb yake yi yana sake maimaitawa..ganin ya jera masa kira sun fi sha biyar amman bai d’aga ba ne ya sanya Najeeb d’in yanke shawarar ya tura masa message kawai, dan haka ya rubuta:’Yash, Manubiya tana da buƙatarka, ban san menene ya faru ba amma her friend(Abbakar)ya ce min It’s very urgent!.’ Daga haka ya tura masa tare da address d’in police station d’in da su Abbakar suka turo, yana adduar Allah yasa ya gani ya kira. A bangaren Yashjub kuwa dama tun d’azu ya nemi nutsuwarsa ya rasa, haka kurum ya ke ta jin wani iri.. so yake ya amsa kiran ko ya yi excusing kan sa ya fita amma kuma ya san idan yayi hakan zai gamu da b’acin ran Daddy ba na wasa ba!… Yana cikin wannan tunanin ya ji k’arar shigowar message dan haka ya juya ya kalli wayar tasa. Wani Irin bugawa k’irjinsa ya yi! Bai san lokacin da ya mik’e tsaye ba sakamokon message d’in sir Najeeb daya samu damar karantawa ta saman notification bar. Da sauri Daddy ya ce ‘’Yash.’’ A d’an rikice ya kalli Daddy sai kuma ya kalli Yasira da ragowar turawan da ke a wajen kafin ya ce “sorry,i have to go, it’s very important (Ku yi haƙuri, zan je ga wannan kiran, yanada matuƙar mahimmanci)” Ya fad’i hakan yana mai kallon wayar tasa sannan yana kallonsu, kafin ya tura kujerar tasa baya riƙe da wayar ya fita daga hall d’in gaba d’aya kamarwalkiya yana mai cewa “pls excuse me(dan Allah a yi min afuwa)”. Yana fita ya shiga kiran number Najeeb…in banda bugawa ba abunda k’irjinsa ya ke yi..Manubiya a police station kuma!ta ya?garin yaya!….. shi da yake ta fafutukar zuwa k’auye wajen ta, mai ya dawo da ita har ya kaita ga zuwa police station. Yana wannan tunanin ya ji Najeeb ya d’auka, a d’an rikice ya ji muryar Najeeb d’in sannan kamar ma driving yake yi, dan yana amsa kiran ya ji Najeeb ya fara magana “kaga message d’ina ko? Abbakar ne ya kirani yanzun, ban samu na d’auka ba shine ya turomin message, inaga shima yana wajen. Ina ganin message d’in na kira shi, an d’auka amma ba a magana.. Babban abun tashin hankalin kamar muryar black snake na ji a wajen, kuma Yash kamar maganar aure su ke yi da shi da Manubiya! Amma ka kwantar da hankalinka ganinan na ma kusan ƙarasawa police station ɗin.’’ Kashe wayar kawai ya ji Yashjub yayi….. A yadda ya nufi k’asa sai da ya bawa wasu tsoro da mamaki, dai-dai nan Daddy yana fitowa dan akwai speech wanda Yashjub zai bada kuma lokaci ya yi. Cikin fushi Daddy ya bi shi a baya amman kafin ma ya gama sauk’a k’asan ya hango tashin motar Yashjub ta glass ɗin dake ajikin gefen stairs d’in… ‘Tabbas zai ci uwar Yashjub kam yau!’ Daddy ya raya hakan a cikin ransa, amma yanzu bari ya koma ya gama da waennan mutanen,first. Kafin ya koma cikin hall d’in ya turawa Yasira message ya ce ta shirya ita za ta bada speech d’in a madadin Yash… hakan kuwa aka yi Allah ya taimaka Yasirar ta san kan abun, dan haka ta d’an had’a abubuwan da za ta iya ta bayar taron ya watse. Daddy kamar ya fashe saboda tsananin takaici, dan ko da ya koma kiran Yashjub ya ci gaba da yi amman sam bai d’auka ko d’aya ba, k’arshe ma message ya yo masa wai ‘’wani abu mai mahimmanci ya taso masa, su k’arashe meeting d’in babu shi kawai!’’. Me zai fiye mishi wannan meeting ɗin da su ke yi mahimmanci? Menene har ya fi mahimmanci a wajensa sama da kare mutuncin company da kuma mutuncin shi kansa Daddyn. Har wanne irin abu ne zai sanya ya tafi ya bar shi stranded (babu madafa) cikin bak’in mutane haka ya kunyatashi….. …. Tun kafin ya k’arasa police station d’in ya kira babban office na dss yace ‘yana buk’atar su, Black snake yana Nigeria, kano.’ Sannan ya fad’a musu sunan police station d’in.’ Ashe dama neman sa ake yi, ruwa a jallo. Sun tab’a yin case da Yashjub ta inda ‘black snake ɗin ya so ya cinye masa filinsa, da kyar ya kwato filin nashi’ a ta dalilin hakan ne Yashjub ya san wayene black snake da kuma record d’insa dan ko satin da ya shige ma sai da suka yi maganar sa da Najeeb akan ‘ya je ya gina hotel a filin wani yace filin nasa ne, ana tsakiyar yin case d’in da ya ga za a damk’e sa shine ya gudu’. Kuma still an banka’do ‘yayi sanadiyyar sace y’an mata, y’an secondary school guda ashirin’. Shiyasa da yaga za a yi masa tunb’ir a tona masa asiri sannan a kamasa shine ya gudu zaman Nigeria ya gagare sa, ya bari akan in komai ya lafa sai ya dawo. .. Yash yana gama waya da DSS ya kira AIG yace ‘’a dakatar da duk wani abu da ake gudanarwa a police station d’in da Najeeb ya gaya masa su Manubiyan su ke” sannan yace’’ kar a bar kowa ya fita,dss suna hanya za su kama black snake’’. Tafiyar mintuna goma ce ta kai shi police station d’in dan bashi da nisa da su, sannan bai bi k’a’idodin hanya da titi ko guda d’aya ba sakamokon uban gudun da ya tsula kamar ba gobe. Motarsa tana yin parking ta wani dss shi d’aya ko uniform babu a jikinsa ta yi parking, da sauri ya k’araso ya nunawa Yashjub id card d’in sa kafin yace ‘’kai ne ka yi waya ko? ina kusa sosai na ga assignment d’in shine na k’araso da wuri but mota biyar tana hanya, yanzunnan zaka gansu inshaaAllah. “ Sam Yashjub bai ji dad’i ba, dan so yayi ace tawagar su ce tazo da wuri haka saboda ya san black snake baya yawo shi kad’ai, dan ga police station d’in ma yanzu haka ya cika tapp da motocin da ya tabbatar nasa ne da shi da Jama’ar sa. Kamar yadda jami’in dss d’in ya nunawa Yashjub Id card haka ya k’arasa ya nunawa ragowar y’an sandan dake harabar wajen id card d’insa dan haka a take suka sara masa suka bi bayan sa su ka yi ciki gaba d’ayan su…… …..4 minutes before now. (Mintuna huɗu da suka shuɗe)… Ana shirin fara d’aura aure Dpo ya fita domin amsa waya, kafin minti d’aya sai gashi ya dawo…jikinsa har yana d’an karkarwa. Da mamaki black snake ya ke kallon sa yana shirin yin magana Dpo d’in ya k’arasa inda yake ya ce ‘’Muna da problem fa! an san kana nan’’ Dariya black snake yayi kafin yace ‘’Relax(kwantar da hankalinka), babu wanda ya Isa ya yi arresting ko ya iya dakatar da ni’’ Cikin yin k’asa da murya dpo ya ce ‘’Ban san ya akayi ba, amman Dss ne a hanyar zuwa nan fa black snake, sun san kana nan gurin Sun kusan ƙarasowa ma yanzu haka, sannan oga kwata kwata ya kirani ya ce In tsayar da koma me ake yi anan ɗin sannan in kama ka!! da farko ma da suspending d’ina ya yi, sai da na rantse masa akan ban san da case d’in ‘ana neman ka’ ba tukunna ya bar ni yace in tabbata na kama ka!’’ Take a alokaci d’aya fuskar black snake ta chanza daga jin batun dpo, cikin fushi ya d’ago yana kallon kowa….sai kuma yayi lissafin ai mutanen nan basu da ƙarfi da hanyar da za su kira someone influential (babban mutum) haka. Wataƙilan dai wani Abokin hamaiyyarshi ne ya ji labarin zuwan sa shine akayi masa chune!. Bayaga hakan ma ai tun d’azu yana tare dasu Manubiyan kuma babu wanda ya ga yayi waya a cikin su. Yana wannan tunanin ya ji dpo yace ‘’Sir,wannan ba lokacin tunani baneba,u need to leave, now!(ya kamata ka tafi, yanzu yanzu). ka san su kamar aljanu, yanzun nan za ka ga sun k’araso.’’ Cikin fushi black snake d’in ya juya buguzun-buguzun Ya je shi ya damk’i hannun Manu ya fara janta sannan ya cewa yaran nasa su kamo Jidda duk wanda kuma yayi yunk’urin hanasu to su kaishi lahira. Ya Nafi’u ne ya danne zuciyarsa da kyar ya iya rik’e Ya Musbah dan ya san muddin suka shiga to kashe su mutanen nan za su yi kuma in sun mutu ba za su samu su kwato su Jiddan daga hannunsu ba. Da kyar Baba ya iya had’a gaba d’aya k’arfinsa da ragowar kuzarin da ya rage masa ya samu ya mik’e tsaye,jikinsa yana karkarwa ya tsaya a inda black snake yake k’ok’arin bi ya wuce,yace’’ka kashe ni kawai! A kan dai in bari ka tafi da y’ay’ana har biyu a gaban idona, gara kawai ka kashe ni!’’. Wani wurgi black snake ya yi dashi wanda ya sanya shi ya tafi ya je ya daki gini…. Cikin fushi black snake ya cd ‘’Ban tab’a had’uwa da tsoho mai audacity (tsaurin ido) irin ka ba! kar ka damu ba zan kashe ka ba amma tunda na lura kamar ka fi son wanchan Yaron naka mai kama da kai a cikin y’ayan naka maza to shi zan kashe’’. Ya yi maganar yana nufin Ya Musbah. …Now(yanzu)… ‘’Ba za ka kashe kowa ba black snake’’ Muryar jami’in dss d’in da suka shigo taree shi da Yash ta katsesu, sannan ta maida hankalin kowa gare su. A take Yashjub ya ji ransa yayi wani irin b’aci na ban mamaki, zuciyarsa ta cunkushe tana tafarfasa sakamokon yadda ya ga black snake ya k’ank’ame Hannun Manu, gashi sai k’ok’arin kwacewa takeyi tana wani irin kuka, kuma ko damuwa ma bai yi ba. Sannan daga ita sai doguwar riga da hula, wuyanta duk a waje!. Bai san lokacin da ya k’arasa ya fincike hannunta daga cikin na black snake d’in ba sannan ya hankad’asa gefe. Wani irin murmushin takaici black snake yayi kafin ya ce ‘’Yashjub!the hero..we meet again! (Jarumi Yashjub, mun ƙara haɗuwa kenan…)” Banza Yashjub ya yi dashi, kawai ya juya inda ya hango hijabin da ya gani a yashe wanda yake da tabbacin na Manu ne, ya k’arasa ya je ya d’auko ya mik’a mata yana mai k’ok’arin danne fushin sa. Dai dai nan jami’in dss tare da dandazon y’an sandan da suka biyo bayan su da shi da Yashjub suka yi kan black snake Ba tare da tantama ba Black snake ya harbi ss d’in a ciki wanda hakan ya sanya gaba d’aya y’an sandan suka rufar masa, dama rabi a cikinsu duk bakinsu d’aya da dpo ba wai son kama black snake d’in sukeyi da gasken gaske ba. Ai kuwa hakan ya bashi dama da shi da tawagar sa suka fice da gudu Bayan ya kalli Baba ya ce masa “zan dawo d’aukar matata, nan ba da jimawa ba’’ Da sauri Yashjub yayi kan jami’in da aka harba, ganin yana motsi yasa yace gara a yi sauri danne gurin su kai sa mota a wuce dashi asibiti. Shi kuma ya bi bayan su black snake da gudu amman ya na zuwa sai k’urar motocin su kawai ya tarar. ‘’Damn it!!’’ Ya furta da k’arfi, yana jin takaici kamar ya kurma uban ihu. Dai-dai nan motar Najeeb ta k’araso cikin harabar gurin tare da dandazon motocin jami’an dss. Najeeb yana k’arasowa yace ‘’Kar ka damu,rabin motocin sun bi su,za’a kama shi in sha Allah,bai dai tab’a kowa ba ko?’’ Cikin b’acin rai Yashjub ya ce ‘’Ya harbi mutane uku’’ A rikice Najeeb yace’’subahanaallah,da wa da wa?? ina Manubiyan take?’’ ‘’Tana ciki!’’ kawai Yash ya iya cewa, daga haka ya juya ya nufi ciki bayan ya kira ambulance, dan wani irin takaici yake ji,ya riga ya san dole ba za a iya kama black snake ba. Suna shiga polisawan da wasu a cikin ss d’in suna fitowa d’auke da jami’in da aka harba. Statement ya tarar ragowar ss d’in suna karb’a a wajen ya Musbah da ya Nafi’u yayin da Jidda da Manubiya suke kuka suna dudduba Baba. Dukda abunda black snake ya aikata sai da Yashjub ya karb’i acc number d’insa a wajen dpo ya tura masa 1 million d’insa da yake bin Baba, bayan ya ji bayanin komai da ga Bakin dpo. Zuwa wannan lokacin gaba d’aya ran Yashjub ya kammala b’aci daga jin bayanin, tabbas in da ace zai ga black snake yanzu to kuwa in bai kashe sa ba sai ya sumar da shi, musamman ma da ya ji cikakken labarin maganar auren da ya so a d’aura masa shi da Manubiya!… ‘wato da niyyar auren Manubiya ma yake yi!’ Idan ya yi tunani akan ‘Black snake d’in fa yayi tunanin auren Manubiya, kenan ta kwanta masa shima son ta yake yi’, sai ya ji kamar ya bazama ya nemo shi ya chaka masa wuk’a. Dan mai yasa zai yi wannan tunanin a kanta!. how dare he!. *MANNUBIYA* *38* Shiyasa har aka gama case ɗin….aka gama karb’ar statements d’in su, suka nufi asibiti sam fuskarsa babu walwala! Ya had’e girar sama da ta k’asa, ko magana ma ya daina yi. Private hospital aka nufa da Baba da Abbakar, suna zuwa aka karb’esu emergency. …… Wayar da Yashjub ya yi aka tabbatar masa da ‘black snake ya gudu, ba a samu damar kamasa ba’ ne ya sake harzuk’a shi. Dukda halin da take a ciki sai da ta lura da shi dama tun ɗazu.. yanzun kuma ta tabbatar wayar da aka yi masa ce ta sake b’ata masa rai… So take yi atleast (ko ma ƙa-ƙa dai) ta je ta ce musu sun gode, dukda ta ga su Ya Musbah sun yi musu godiya sosai har karɓar nambobin juna ma taga sun yiyyi, amma dai dukda haka ya kamata su je su yi musu godiya suma ita da Jidda, sai dai kuma tana shakkar kar ta je ya maketa! Dan in ba lokacin da su ke exchanging numbers shi da su Ya Musbah ba to bataga ya saki fuska dede da na second d’aya ba!…Sannan kuma tana jin kunyar sa dan in ta tuna abunda ta yi masa jiya da safe gaba d’aya sai ta ji wani iri babu dad’i! duba da yadda yanzu yake tsaye tsayin daka akan al’amarin da ya kusan tarwatsa rayuwarta da ahalinta. Gashi yanzun kwata-kwata bata hango walwala a tare da shi ba, masifa ya ke yi wa kowa hatta sir Najeeb yanayin yadda ta ga yana masa magana kamar zai rufe sa da duka take gani…. waennan dalilan ya sanya ta d’an dakata tana mai tunanin ta yadda za ta yi masa godiyar. Sallar la’asar aka kira, dan haka gaba d’aya Mazan suka fita masallaci, su kuma suka nufi band’akin da suka tambaya aka nuna musu… Sallah kuma suka nemi waje inda babu mutane sosai, suka gabatar da ita cikin nutsuwa. Bayan sun idar sukayi addu’oin samun lafiya wa Baba da Abbakar, har ma da Inna. Basu dad’e da dawowa wajen ba su Yashjub ma suka shigo, shi da sir Najeeb su Ya musbah a bayansu. Ba k’aramin dad’i Manubiya ta ji ba, dan bata yi tunanin za su dawo su jira har sai an gama treatment d’in su Baban ba, hakan ya sanya har bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba, tana murmushin tana kallon Yash d’in…. dai-dai shi kuma ya d’ago kansa shima da niyyar ya d’an saci kallon ta ai kuwa karaff suka had’a ido da ita tana kallon sa tana murmushi. Da mugun sauri ta sunkuyar da kanta k’asa, ta fara wasa da y’an yatsun hannun ta… murmushi sosai ne ya kufcewa Yash wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili! Dasauri sir Najeeb ya d’ago yana kallon sa… ganin inda yake kalla yana murmushin ne yasanya Najeeb d’in yin wata y’ar guntuwar dariya kafin ya ce ’’Romeo, a asibitin ma ba za’a d’aga k’afa ba?’’ ‘’Hmm’’ Kawai Yashjub ya iya ce wa Najeeb, dan gaba d’aya Manubiya ta sanya shi a wani yanayi, shiyasa ko iya juyawa ya kalli Najeeb d’in ma bai yi ba, saboda gaba d’aya idanuwansa da hankalinsa kacokam suna akan ta ne! So yake ta sake d’agowa ya kalleta amman sam tak’i, ta ma yi k’asa da kanta sosai. Ganin ta ƙi d’agowa shi kuma zullumi yana shirin susuta shi ne ya sanya kawai ya nufi inda take. Dama kuma yanata so ya d’an yi mata maganar ‘ko akwai wani abun bayan wanda dpo ya gaya mishi’ amma ya lura tanata kuka, shiyasa ya d’aga mata k’afa saboda jin kukan nata yake yi har cikin ransa a lokacin da take yi….dan har ga Allah ya san in ya je kusa da ita tana wannan kukan to tsaf za’a iya samun matsala, kukanta yana cikin abubuwa mafi munin da baya buk’atar gani a duniyar nan……. A take Manubiya ta fahimci inda take yake nufowa, dan haka tashi d’aya fargabarta ta k’aru, dama ga fargabar jikinsu Baba dan ma an tabbatar musu da jikin na Baba Ba wani abu me muni bane Abbakar kuma yanada rai. Tana wannan tunanin ta ji shi a tsaye a kanta, ji ta yi kamar ta mik’e tsaye ta ruga a guje. Ba ta ida jan numfashin da ya mak’ale take kokawar janyoshi da kyar ba ta ji yace’’in zauna??’’ Dakyar da mugun kyar dan sai da ya sake maimaitawa tukunna ya ga tad’an matsa kusa da Jidda sosai sannan ta ce masa’’eh’’ a hankali. Murmushi yayi kafin a hankali ya nemi gefenta da d’an tazara kad’an ya zauna cikin nutsuwar sa bayan yayi bismillah. Yanayin zaman da ta yi sai da ta bashi dariya, ya lura da yadda ta wani zabura lokacin da ya zauna d’in ma sannan ta kuma matsawa jikin Jidda sosai. Murmushi kawai yayi, ya amsa gaisuwar Jidda yana mai kallon ta a hankali ya ji tace’’Mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi’’ Murmushi ya yi kafin ya ce ’’ba komai, Allah ya kare gaba ya ba su lafiya’’ ‘’Ameen’’ ta ce,daganan ta yunk’ura zata tashi dan ta lura kamar yana d’an bukatar space da Manubiyan amma sai ta ji Manubiyan ta yi saurin damk’ar Hannunta ta rik’eta gam. A hankali Jiddan ta gyara ta zauna a wajen ba dan ta so ba, itama ta sunkuyar da kanta ta shiga wasa da bakin hijab d’in jikinta… Har ga Allah ta jinjinawa Yashjub da abunda ya yi musu, dan tun d’azu da Manubiya ta ce mata ‘ai shine wanda take yi wa aiki’ Jiddan take ta mamaki, dan a ganinta a zamanin nan na yanzu wanne employer (Oga) ne yake damuwa da matsalar employee d’insa (ma’aikatansa) har haka, a take wata zuciyar kuma sai ta ce mata ‘’kodai!kodai!!’’ dan haka ta d’an yi murmushi ita kad’ai, ta ci gaba da lissafe lissafen ta. Ba k’aramin burge Yash su Manubiya sukayi ba…yadda suke da kunya da kamun kai tabbas ya san iyayen su sun yi k’ok’ari wajen tarbiyyar su, dan ko ba a fad’a mishi ba ya fahimci jiddda k’anwar Manubiya ce sakamokon tsananin kamanni da ya ga suna yi.. Banbancin Jidda da Manubiya yanayin girman jiki, kalar fata da ido ne kawai..Manubiya ta fi Jidda tsayi da jiki kad’an, kalar fatar Jidda fara ce ita tass sosai Manubiya kuma ba b’aka bace ba kuma ba fara bace sosai, Idanuwan Jidda sun fi na Manubiya girma sosai amma na Manu sun fi na Jidda kyau da d’aukar hankali..a ransa ya ce ’’ idanuwan da suka kusan haukatani” sai kuma ya d’an yi murmushi kad’an. Shiruu duk suka yi kafin Yash ya katse shirun ta hanyar cewa Manubiya ‘’Sister d’inki ce ko?’’ A hankali ta d’an jinjina kanta sai kuma tace ‘’eh’’daganan shiru ya sake biyo baya. Still shi ne ya sake kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa ‘’Baba zai samu sauk’i, inshaaAllah. kar ki damu komai zai daidaita. inshaaAllah’’ A hankali ta ce ‘’InshaaAllah,’’itama Jidda tace’’inshaaAllah’’a cikin ranta. A hankali Manubiya ta lumshe idanuwanta, tana mamakin yadda k’iri-k’iri ta gagara yi masa godiyar da take ta zumud’in son yi… gaba d’aya duk sai ta ji ba dad’i ta inda ko ishashshiyar gaisuwa ta gagagara shiga tsakanin su.. Yo ta inama zata iya? itafa tunda ya zo ya zauna a kusa da ita shikenan ya sakawa tunani, kuzari da duk wasu lissafe-lissafenta full stop. Ganin rashin kyautuwar abunda ta yi ne yasanya ta yi da gaske da kyar ta samu ta d’an d’ago kanta da niyyar ta kalle shi ta yi mishi godiya, suna had’a ido ta yi sauri ta fara kallon gefen kunnensa sakamokon wani irin kallo da ta ga yana yi mata gashi sai wani tsadadden murmushi yake zuba mata. Babu yadda ba ta yi ba amma da ikon Allah sai ta gagara cewa komai, ga wani mahaukacin bugu da zuciyarta ta shiga yi… ganin da ta yi ba zata iya bane ya sanya ta yi sauri ta sunkuyar da kanta tana tunanin ta yadda zata aro jarumta ta yi masa magana ko da ace bata kalleshin ba dan zuwa yanzu ta fahimci abun kamar da wuya,a ranta ta ce ’’wannan wanne irin abu ne haka, wanne irin feelings ne wannan?’’ ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsar ba. A b’angaren Yashjub kuwa kad’an ne ya rage bai fashe da dariya ba a ransa ya ce ’’.to wai menene nata na k’in kallon cikin idonshi ne?’’ yadda take yi tana kallon gefen fuskarshi abun ba k’aramin burge shi da bashi dariya ya ke yi ba.’’ Murmushi kawai yayi yana kallon yadda ta sunkuyar da kanta yana jin wani sanyi yana ratsatsi… baisan wanne Hali zai shiga ba in da an yi rashin sa’a black snake ya tafi da ita ko yayi mata wani abun, ganin ransa yana shirin b’aci ne ya sanya ya yi saurin kawar da tunannin cikin taushin murya ta ji yace “Allah ya ci gaba da karemin ke, tare da family d’inki a duk inda kike’’. Dumm!! Haka ƙirjinta ya buga,a take ta runtse idanunta tana jin yadda kalaman nasa na yanzun suke ratsa zuciya da dukkkannin sassan dake a jikinta tare da sauk’ar mata da wata sabuwar kasala mai tafe da fad’uwar gaba… cikin mutuwar jiki a chan k’asan ranta ta ce ’’Not again Yashjub,plsss (Kar ka kuma, Yashjub, dan Allah!)”. Tunani Yashjub ya fara yi akan ko dai ya sako maganar incidence d’in jiya da safe, dan haka ya bud’e Baki zai yi magana kenan aka bud’e k’ofar d’akin da aka shigar da Baba da Abbakar aka fito, da sauri su Manu da Ya Musbah da sir Najeeb suka rufarwa Doctor d’in da ya fito. Yayinda Yashjub yake nan a inda yake ko motsi ya gagara yi, bayan Manubiya wadda ta mik’e da sauri ta nufi doctor kawai ya bi da kallo yana murmushi yana jin wani nishad’i yana ratsashi…ashe haka so yake? shi fa ko wanne irin takaici yake ciki to wuyarta ya yi magana da ita ko ya ganta kai ko tunanin ta ne ya samu ya yi to fa da yardar Allah tashi d’aya sai ya ji b’acin ran nasa ya kau. Cikin nustuwa sir Najeeb wanda ya gama jin bayanin Likitan ya juya ya nufi inda Yash d’in yake a zaune, har ya k’arasa ya tsaya a kansa sam Yashjub bai lura ba sai da Najeeb d’in ya kyasta ƴan yatsunshi a setin fuskar Yashjub tukunna ya d’an d’ago yana kallon sa. Murmushi Najeeb yayi ya zauna a gefen sa tukunna ya ce “ya dai?’’ Bai da niyyar b’oyewawa dan haka tashi d’aya ya ce ‘’Najeeb! Manubiya ce rayuwata, adadin yadda nake numfashi kullum haka k’aunarta take k’aruwa a cikin zuciyata, ku yi sauri ku nema min aurenta tun kafin in haukace muku.’’ K’amewa Najeeb ya yi kawai yana kallonshi yana mamaki, a ransa yace “Ubangiji mai’kun fa ya kun’!’’ Kafin ya yi murmushi ya ɗan bubbugan kafaɗan Yash d’in cikin sigar zolaya yace “Mutumina! Ai ka riga ka fara hauka, kalli yadda ni kaina ka maidani bawan students d’ina.. mun gama duk wasu abunda suka kamata amma ka hanamu tafiya, sannan ka ji yadda kake magana kuwa?.. Gaskiya kam ya kamata mu yi wani abun da sauri’’ ya k’arashe maganar yana dariya k’asa-k’asa. Kafin ya sake cewa “yanzu dai zo mu je ka ga sirikin naka,,mu samu mu wuce, Inada aiyyuka da yawa wallahi. Doctor yace Abbakar d’in an cire bullet an yi komai amma bai farfad’o ba tukunna, Sirikin ka kuma he’s well and conscious so let’s go say hi (Ya farfaɗo yaana lafiya, dan haka mu je a gaisa), daganan mu wuce ko?’’ Ya k’arashe maganartashi da tambaya yana mai mik’ewa tsaye. Har ya d’an yi gaba sai kuma yaga Yashjub bai ma taso ba, dan haka ya koma ya ce “ya akayi kuma?’’ Tunda yake bai tab’a ganin Yashjub yayi kalar tausayi ba sai yau, har da wani karkata wuya… Dan haka kawai sai Najeeb d’in ya saki baki yana kallon ikon Allah.. Muryar Yashjub d’in ce ta katse masa tunani jin yana cewa “I’m serious (da gaske fa nake) Najeeb, ka fara yi wa Hajiya Mama magana ita kuma ta yiwa Daddy, ka san halinta yanzun sai ta birkice a kasa gane kanta, shiyasa bana so ni in yi mata magana da kaina dan na san idan ta ga na damu kuma na rikice akan maganar to ba za ta taimakamin ba, cewa za ta yi tun yanzu Ina haka ina kuma ga idan anyi auren, ni kuma na san a yadda nake ji d’innan ba zan iya yin komai a nutse ba. Ka yi mata magana, a samu a fara maganata da Yarinyar nan Najeeb tun kafin a samu matsala.” Shiruu Najeeb ya yi kafin ya bud’e Baki yana shirin yin magana k’arar wayarsa ta katse shi, dan haka ya cewa Yash d’in “a minute pls (Ina zuwa dan Allah)’’ kafin ya sanya Hannu a aljihunsa ya zaro wayar. Yashjub ya kalla kafin ya sake maida hankalinsa ga wayar sakamokon ganin sunan Daddy da ya yi a matsayin wanda yake kiran nasa, sai kuma ya sake kallon Yash d’in tukunna ya ce ‘’Ina wayarka??’’ ‘’Tana mota’’ Yash ya bashi amsa a tak’aice, yana mai ci gaba da tunane-tunanen sa…’ya riga ya k’arbi har number Baba, zai jira ya d’an warke daganan sai ya bawa Daddy number d’in tasa su yi magana a tsakanin su ya san inshaaAllah kafin nan Najeeb kuma ya tsara masa hajiya Mama ita kuma ta yi wa Daddyn magana, daga nan ya san inshaaAllah komai zai zo masa da sauk’i, ta b’angaren Manubiya kuwa yana addu’a tare da yak’inin inshaaAllah za ta aminta da shi da yardar Allah ba zai sha wahalar samun soyayyarta ba, shiyasa ma yake so ya je mata ta koina har ta sama ta yadda zata fi d’aukar sa serious.’…. Cikin nutsuwa da girmama Najeeb ya gaida Daddy shi kuma ya amsa masa kafin cikin fushi ya ji Daddyn ya ce ‘’kana tare da Yashjub ne??’’ Sai da Najeeb ya kalli Yash yaga sam hankalinsa bama ya gurin ya tafi ga tunanin da yake ta yi tukunna ya ce ’’eh Daddy,‘’ kafin ya d’aura da cewa’’gashinan, bara in basa’’ Da sauri cikin katseshi Daddy yace “A’a barshi. Ka ce masa na ce dan ubansa ko me yake yi ya bari ya zo yanzunnan’’ Daga haka ya kashe wayar kit. A d’an duburce Najeeb ya kalli Yash dan bai tab’a jin Daddy da irin wannan fushi haka ba, kafin yace’’Yash!Daddy fa a zuciye yake, mai ka aikata?’’ A hankali Yashjub ya maida kallonsa da tunaninsa ga Najeeb kafin ya yi shiruu kamar mai tunani sai kuma chan ya ce ’’kash!wallahi mantawa na yi’’ Cikin tarar numfashinsa Najeeb d’in ya ce ’’me ka manta? yace ka je right away fa(yanzu yanzunnan) tashi mu wuce, na ji b’acin rai sosai a muryarsa’’ Najeeb d’in ya fad’i hakan yana mai juyawa. Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya kalli inda Manubiya ta bi ta shige… wallahi ba daban Daddy ne ya kirasa ba to da bai ga dalilin da zai sanya ya fita a asibitin nan ba tare da sun yi sallama da Manu ba, bayaga hakan shi fa bai ma gaji da ganin ta ba. A gaggauce suka tsaya suka biya duk wasu bills daga nan suka fice suka nufi motocin su Najeeb yanata sauri yana cewa ‘’ka yi sauri fa Yashjub,kar ka dad’e ransa ya sake b’aci..’’ *MANNUBIYA* *39* A zaune su Manu suka tarar da Baba, ana gwada masa sugar dan complete checkup Yash ya biya ya ce a yi musu. suna had’a ido da shi gaba d’ayansu sai suka sake zama emotional(sai raunin zuciyoyinsu ya tsananta) Tashi d’aya Jidda da manubiya suka fara hawaye, ya Musbah shima sai da ya yi da gaske tukunna ya iya hana kansa kuka…ji yake kamar ya d’aura hannu aka ya yi ta kurma uban ihu!… Wai akan naira miliyan d’aya tak!kalli abunda aka yi wa mahaifinsa sannan aka yi shirin tafiya da k’annensa Mata har biyu amma babu abunda ya iya tab’ukawa. Nurse d’in tana fita suka rufarwa Baba, har suna y’ar rige-rige wajen k’arasawa tare da tambayar sa “ya jikinsa?” murmushi ya yi dan dukda hali na tashin hankalin da yake a ciki sai da ya ji wani sanyi da fariin ciki suna ratsashi na ganin yanda y’ay’an nasa suka damu sannan su ke ta d’awainiya da shi, dan haka ya shiga kwantar musu da hankali kafin ya kalli ya Musbah ya ce ‘’Ina Yaran su ke? Ai bai kamata ku barsu a waje ba ko? ku je ku shigo da su da wuri, kar su tafi ban yi musu godiya ba.’’ Jinjina kai ya Nafi’u ya yi suka fita da shi da ya Musbah amma ko da suka fita basu tarar da kowa ba wnda hakan yake nuni da cewar su Yash d’in sun tafi kenan, dan haka suka koma ciki! Suka sanarwa baba…sai da suka ce masa ai suna da nambobin wayarsu, tukunna ya d’an ji sanyi, sannan ya ce ‘ko da sun Kira su a waya ya zama dole su je har office d’insa ko gidansa ayi masa godiya, dan duk Mutumin dayayi musu alkhairi irin wanda Yashjub yayi musu to tabbas ya chanchanci kulawa ta musamman daga garesu suma. Ta wayar ya Nafi’u aka kira Yash ɗin wanda gaba d’aya kunya ta lullub’esa sannan duk sai ya ji wani iri na daga godiyar da baban yake ta yi masa… Hakanan dai a kunyance suka yi wayar daganan Yash ya yi masa sallama tare da fatan ‘Allah ya basa lafiya, ya kuma kare gaba’. Har Najeeb sai da Baba yasa aka kira masa shi shima yayi masa godiya tukunna hankalinsa ya kwanta…dukda kuwa Baba k’arfin hali ne kawai yake yi amman gaba d’aya abun wani iri yake jin sa ace wai ‘ka ci kud’i har za a tafi da y’ay’anka Mata, amma ka gagara tab’uka komai….’ A hankali ya lumshe idanunsa a ransa ya ce ‘’Innalillahi a inna ilaihirrajiun,’’ Daidai nan kiran wayar Aisha ya shigo wayar Manubiya, dan haka ta d’an fita waje domin ta amsa…bataso ta yi wayar a gaban Baba dan bata sani ba ko wani abun ne ya taso daga b’angaren Inna, dan ta san yana ji zai ce zai tafi gida, to kuma shima ga yanayin jikin nasa sai a hankali…. dan haka ta fita tana mai addu’ar Allah yasa lafiya…. Jidda ma tana ganin fitar Manubiyan itama ta mik’e ta mara mata baya. Baba yana jin fitar su ya bud’e idanunsa ya zubawa inda su ka bi suka fita idanu yana jin tsananin tausayin su yana ratsashi dan tabbas shi kansa ya san ba za su ji dad’in hukuncin da ya gama yankewa a kansu ba. Ya ji dad’in fitar da suka yi dan haka ya gyara zama ya kalli ya Nafi’u da ya Musbah ya ce’’ inshaaAllahu nan da sati biyu nake so in aurar da Jidda da Manubiya…’’ Kwarewar da Ya Musbah ya yi ya fari tari a wahale ne ya katse Baba…Da kyar!! Dan sai da ya sha ruwa sosai ya d’an zauna tukunna ya d’an ji dama-dama still yana tarin kad’an-kad’an… Bai iya jira tarin ya tsaya gaba d’aya ba ya ce ‘’Baba aure a cikin sati biyu kuma sab….’’ Cikin tarar numfashinsa Baba ya ce ‘inshaaAllahu Rabbi… Yanzu Manubiya nake so ku nemawa tsayayye wanda yake a shirye tsaf, nan da sati biyu sai a had’a a yi… Jidda ita dama Yusuf a shirye ya ke, inshaaAllah Ina fita daga nan zan samu Baba Habu mu…’’ Duk yadda Ya Musbah ya so ya danne fushin sa kasawa ya yi, Dan bai ma san lokacin da ya katse Baban ba.. cikin tarar numfashinsa a hassale ya ce ’’Baba amma dai ba Yusuf d’an gidan Baba Habu na gidanmu kake maganar za ka aurawa Jidda ba dai ko?! Ba dai Yusuf d’an iska wanda ya jefa mu a cikin wannan bala’in za ka d’auki Jidda ka aurawa ba ko?! Dan in dai shi kake nufi to a gaskiya Baba ba zan tab’a barin Jidda ta aure sa ba…’’ Cikin fushi da fad’a Baba ya ce ‘’a kul ɗin ka Musbahu!!! Wannan iftila’in da ya fad’o min babu ruwan Yusuf a cikinsa! Dan haka kar ka d’aura masa laifin da ba nasa ba. eh! Na san muna yawon samun sab’ani da su amma na san ko Hauka Yusuf ya ke yi ba zai tab’a yi mini abunda zai jefani cikin wannan halin ba,’’ Cikin fushi Ya Musbah ya ce ’’baba habu fa shi y…’’ Cikin tarar numfashinsa a hasale Baba ya ce “Musbahu bana son rashin kan gado fa? So nawa nake ce maka ko da wasa kar ka yarda ka k’ullaci ƴan uwana da y’ay’ansu akan abubuwan da suke yi? Idan ka k’ullace su kaima ai ka zama su kenan!! Ka ga sai ka bada gudummawar tarwatsewar zumuncin namu cikin sauk’i. In ba rashin kirki ba Musbahu har kai ne wai za ka kalleni kana cewa wani bazaka bari Jidda ta auri Yusuf ba Kaine ka haifa min ita???” Sai yanzu Ya Nafi’u ya fesar da iska ya k’arasa gaban Baba ya zauna akan kujerar da ke a bakin gadon tukunna ya ce ’’Baba ka yi hak’uri, kar ka yi (wa furucin Musbahu fahimta ata bai bai) misunderstanding d’in sa, maganar gaskiya Baba Yusuf bai cancanci a bashi Jidda ba duba da yadda….” Cikin katseshi Baba ya ce ‘’Bari ka ji Nafi’u! Dama na san za ku yi Tunanin wai ko ata sanadiyyar Yusuf ne na fad’a wannan halin, wanda sam abun ba haka yake ba! Yusuf taimakona ya yi amma sai abun (taimakon) ya zo da tangard’a! Ya yi mini bayani kuma na fahimci komai dan haka bana son jin komai daga Bakin kowa illah ku ce mini ‘to’ kawai. Yusuf zai auri Jidda nan da sati biyu, Manubiya kuma ku nema mata Miji, wannan shine kawai abunda nake so ku fahimta sannan ku yi mini biyayya a kai.’’ Shiruu Ya Nafi’u ya yi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce ‘’amma Baba auren gaggawa da….” Cikin katse shi Baban ya ce ‘’Nafi’u baka ji abunda Mutumin chan black snake ya fad’i mun kafin ya tafi ba? Idan ba ka ji ba bari in maimaita maka. Ce min yayi ‘sai ya dawo d’aukar Matansa’!’’. Shiruu Baba ya yi kafin zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin rik’ewa suka samu nasarar zubo masa, cike da rauni ya ce ‘’Nafi’u tunda na haifi Yaran nan ban jiyar da su dad’i, farin ciki da walwala ba!! Allah ya rufa asiri amma idan aka ce yau ga black snake ya dawo kamar yadda ya fad’a ɗin ya d’auki Yaran nan ban san ta ya zan fuskanci ni karan kaina ba ballantan asu kansu yaran, Mahaifiyarsu, uwa uba ubangijina, Nafi’u ban san da wannne Bakin zan yi masa bayanin yadda na kula da amanar da ya bani ba’’ Baba ya k’arashe maganar tasa yana mai fashewa da wani irin kuka. Jiki a sanyaya Ya Nafiu ya shiga ƙoƙarin ganin ya lallaɓa Baba dan a samu ya yi shiru… shi kansa ya Musbah ya ji ba dad’in kukan da mahaifin nasa yake yi shiyasa gaba d’aya jikinsa yayi sanyi, yayinda zuciyarsa take wani irin tafarfasa!!! tabbas Hausawa sun yi gaskiya da sukace’’munafuki in ya rigaka shiga d’akin uwarka, to ko ruwa baka isa ka sha ba.’’ Allah kad’ai ya san me da me Yusuf ya gayawa Baba shi kuma ya hau kai d’aram ya zauna. Gashi ya san halin Baba da wata iriyar rikitattiyar kafiya, dan haka ya riga ya san ko ta ya zai yi masa bayani ba zai tab’a yarda ba. Gashi yanzu ya saka shi a gaba yana kuka, shiyasa tashi d’aya gaba d’aya jikin Ya Musbah ya yi sanyi, dan jin kukan Baba yake yi har cikin ransa, ji yake yi kamar ya je ya samu Yusuf ya d’aga shi sama kawai ya goce… zai bar maganar yanzu, ya samu ya lallab’a Baba amma inshaaAllah ba zai taɓa bari Jidda ta auri Yusuf ba’’. A hankali ya matsa ya shiga rarrashin sa shima yana mai bashi hak’urin abunda ya yi masa yanzun… Cikin sanyin jiki Baba ya ce’’mutumin nan ya gudu, basu kama shi ba. ku bar ni in aurar da su Jidda tun kafin wani abun ya sake faruwa, na san inshaaAllah idan sunada aurensu darajar aure da kariyar ub…..” Shiruu ya yi sakamokon shigowar da su Manu sukayi. cikin nutsuwar su, suka k’arasa suna zuwa wajen ya Musbah ya juya da sauri yace ‘’bara in duba jikin Abbakar!” Ya fad’i hakan yana nufar labulen da aka saka a tsakanin baba da abbakar d’in. Doga jin haka ya Nafi’u ma ya biye masa baya. Ya Musbah na gaba ya Nafi’u na biye da shi a baya yana tafe yana dialing number Aisha dan sai yanzu yaga misscalls dinta birjik, haka suka shiga inda Abbakar d’in yake a kwance. Suna shiga ya Musbah ya naushi iska da k’arfi, jikinsa har wani irin karkarwa yake yi tsabar takaici. Dasauri ya Nafi’u ya rik’e shi yace’’haba Musbahu! kayi hak’uri a bi komai a hankali, lokaci zai sa komai ya yi daidai inshaaAllah.’’ Kamar zai fashe da kuka ya ce ‘’Astaghfirullah, Nafi’u wacce iriyar rayuwa ce wannan? kalli family d’ina! kalli halin da suke a ciki! amma wai ace banida yadda zan yi in taimakesu? ka duba kaga yadda ake shirin aurar da su Manubiya kamar wasu Kaji? kuma a yadda Baba yayi bayanin nan tabbas yana da gaskiya ta wani fannin tunda daga ni har shi ɗin ba za mu iya karesu ba.. amma dukda haka bai kamata Jidda ta auri Yusuf ba, kuma ya kamata ace na yi wani abun amma banida……’’ Kukan da ya kufce masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana. Ya Nafi’u ji yayi kamar shima ya fashe da kuka, dan haka cikin sanyin jiki ya matsa kusa da ya Musbahn ya rungumesa, sannan cikin sigar rarrashi ya ce ’’kuka da k’unci ba shine mafita ba Musbahu, kar ka dasa ayar tambaya a kan k’addararka ka je garin hakan ka kauce hanya, sannan kar ka karaya ka ce wai dan baka da k’arfi ba za ka Iya yin komai ba. inshaaAllah za mu fahimtar da Baba kuma zai fahimcemu, dan ko da ace za’a aurar da su Jiddan to ni kaina ba zan goyi bayan a aurar da su da wuri haka ba kuma ba zan bari Jidda ta auri Yusuf ba inshaaAllah. kawai dai yanzu abunda nake so ka fahimta shine ‘Baba ya d’au zafi!. Sannan hankalinsa a tashe yake!’ Dan haka ka bari nan da kwana biyu inshaaAllah idan ya d’an sak’k’o mu ka lallab’a shi na san zai fahimce mu. Ubangiji yana tare da mu, komai zai yi dai-dai inshaaAllah’’. Cika shi Ya Musbah ya yi, ya je jikin window ya dawo ya sake komawa…yana yi yana share hawayensa, kafin da kyar ya samu ya tsayar da kukan nasa tukunna ya ce ‘’Allah ya dafa mana. Allah ya tsaya mana. Nafi’u na san zafin rashin dace da Abokin rayuwa, idan akayi rashin sa’a Baba ya k’i amincewa da mu ya je garin neman mafita ya ɓurma su Jidda a Hannun mugaye shin ya kake tunani kenan? Kar mu je duk mu ukun mu k’are da…..’’ Da sauri ya Nafi’u ya ce ‘‘Musbahu, ka kyautata zato dan Allah…think positive!. inshaaAllah hakan ba za ta faru ba’’. Shiruuu, ya Musbah ya d’anyi da farko! yana me sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere, kafin ya jinjina kai kawai, daga haka ya k’arasa bakin gadon da Abbakar ya ke nan a kwance ya zubawa guri d’aya ido ya yi shiruuu. Numfashi Ya Nafi’u ya fesar, kafin ya d’ago wayarsa da sauri dan shi sai yanzun ne ma ya tuna ya yi dialing number Aisha tun d’azu, yana d’ago wayar kuwa ya ga timer tanata tafiya alamun ta d’auka kenan tun d’azun. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya kara wayar a kunnensa ya ce ’’lab’e kika fara kenan!’’ Murmushi ta yi, sannan ta ce ’’na d’auka sai su khairat suka fara fad’a ita da mai sunan Baba, shine na ajjiye wayar na je raba su da ke hankalina ya yi gaba a tunanina na kashe. amma kuma dukda haka da na d’auka d’in da farko kafin in ajjiye na ji maganar da ta d’an kid’ima ni shiyasa ma na manta ban kashe d’in ba tsabar kid’imar da na yi’’….shiruu ta d’an yi kafin ta ce ’’da gaske Manubiya aure ta yi???” Dafe Kai ya Nafi’u ya yi kafin yace’’kinga irin ta ko, baki tsaya kin ji kan zance da k’arshen sa ba kawai daga kin ji ance aure shikenan ke har kin je ga ƙarshen zancen.’’ Fahimtar da Aisha ta yi kamar ran maigidan nata a d’an b’ace yake ne yasanya cikin kwantar da murya tace ‘’Allah ya huci zuciyarka, ba zan k’ara ba. Dama na ga kamar Inna tana jin yunwa ne shine na kira inaso in tambaya a bata madara ne ko abinci, to kuma sai baka d’auka ba, a lokacin kuma wayar Manu bata shiga amma na same ta ma har ta yi min bayani tun d’azu mun gama magaana.” ‘’Okay, sannu Aisha, Allah yayi albarka’’ ya Nafi’u ya fad’i hakan cikin sanyin jiki. Ahankali tace ‘’ameen’’ daganan suka yi sallama bayan yace mata ‘ai sun ma kusan dawowa’ Dan haka ta bari akan idan sun dawo sai ta ji koma mene ya kaisu suka dad’e har haka. …………. Tun lokacin da Ya Musbah ya kai Inna gidansa ya fita! Baraka ta kumbura, ta rasa Ina za ta saka ranta. Tashi d’aya ta ji gaba d’aya duniyar ta yi mata zafi…ita fa dama tun farko abunda take ta tsoro kenan, dan ita babban tashin hankalinta kar rikon Inna ya dawo hannun Ya Musbah! Dan wallahi ita bazata tab’a iya jurar ganinta a cikin gidan ba!….dad’in dad’awa kuma gata liability, saboda Allah in banda rashin adalci ta yaya ma za’a had’ata da jinya, ai ba dan haka aka aurota ba!. Takaici da bak’in ciki ne ma suka saka ta kasa tab’uka komai a cikin gidan, dan haka ta fito tsakar gidan ta zauna akan y’ar kujerar tsugunno tanata faman cika tana batsewa, ko d’akin da aka ajjiye Innar bata lek’a ba tunda su ya Musbah suka kawo ta suka fita… Muhsin ne da me sunan Baba wanda tunda ya gansu yaketa murna ya shige d’akin shima suke ta yiwa innar hira. Baraka kuwa tana tsakar gida ta d’aurawa kanta bala’i in banda tafarfasa babu abunda zuciyarta takeyi…a haka Aisha ta shigo ta same ta. Sama-sama suka gaisa da Aishar daga haka ta tambayeta d’akin da innar take, ta nuna mata, Aishar ta shige. Tana shigewa Baraka ta mik’e tsaye dan zuwa wannan lokacin ta ma kasa zama kwata-kwata, kamar wata wadda aka aikowa da rikitaccen sak’o haka ta shiga safa da marwa a tsakar gidan ta kasa tsaye ta kasa zaune….itafa ba zai yiu a maida mata gida asibiti ba wallahi! Tunda gashi y’an dubiya har sun fara zuwa, wannan ya shigo wanchan ya fita shikenan ita ba ta da sirri a cikin gidanta kenan? Gashi har yanzu su Ya Musbah shiru, ta kirasa kuma ya k’i d’agawa, Itafa wallahi Inna ba za ta kwanar mata a cikin gidanta ba yau.!. Sama-sama ta fara jiyo muryar Aisha kamar tana waya da ya Nafi’u dan haka ta je ta lab’e….. wani irin gumi ne ya shiga keto mata sakamokon kunnuwanta da suka jiyo mata lokacin da Aisha take cewa “da gaske Manubiya aure ta yi???’’. Tashi d’aya Baraka ta shiga cikin maɗaukakin tashin hankali, a ranta ta ce “Manubiya ta yi aure! Abunda suka je yi kenan? To ina batun Baba kuma dan d’azu maman Abbakar ta kira ta take gaya mata cewar “kamasa akayi! Shiyasa suka kawo innar suka tafi gaba d’ayansu, itama ta so ta tsaida Abbakar amma yana gaya mata an kama Baban ya fice a gigice har yanzu shiru babu shi babu labarin shi tanata kiran wayar sa kuma baya d’auka’’ … “Wato Shiyasa aka kawo mata inna da Muhsin tun yanzu kenan… Manubiya tana tarewa a gidanta ta san jidda ma nan za ta dawo! Kut!ai wallahi bazaiyiu ba, wannan abu ba zai tab’a sab’uwa ba, ba za ta zauna a gida d’aya da su ba wallahi! Sannan yanzu haka ma ya aka k’are, tayaya ya Musbah yake iya ciyar da su biyu kawai Ina kuma ga in nauyi ya sake yi masa yawa.’ Waennan sak’e-sak’en da Baraka take ta yi ne ya sanya ta fara jin jiri, dan bala’i har wani dishi-dishi ta fara gani! dan haka ta koma ta zauna a kan y’ar kujerar ta tana ji kamar zuciyarta zata kama da wuta. Bata dad’e da zama ba, Aisha ta fito ita da khairat ta ce mata ‘’ta d’aura girk, bara ta je ta duba’’ ‘’To’’ Kawai Baraka ta iya ce mata shima kuma da kyar, dan wani irin tafarfasa zuciyarta takeyi. Aisha tana fita Baraka ta mik’e. Ta ma rasa me yakeyi mata dad’i! ta rasa Ina zata saka ranta ta ji sanyi… Tabbas idan fa ta yi sake tou wallahi ruk’on inna ya dawo hannunta kenan har abada tunda ko da ace daakwai Jiddah ai Jiddan in dai ta ci post utme d’inta to makaranta za ta fara zuwa!!! Muhsin yarone ya Musbah kuma aiki zai ce ze dinga fita, shikenan ita a barta da inna kenan…. Ita kam a barta da talaucin da ya Musbah ya tsundumata a ciki ma mana ba sai an k’ara mata da zama gida ɗaya da dangin miji ba!. Tsulum! Haka Muhsin ya ga Baraka ta afko cikin d’akin da suke a ciki shi da inna… Da sauri ya mik’e yana cewa “anty, kin ji yanzunnan Na ji inna ta ce ‘Manu’ wallahi! Ki matso ki tambayeta ki ji’’ Ya fad’i hakan cikin tsananin farin cik, yana Jan hannun Baraka yana dariya… Wafce hannunta ta yi da k’arfi ta... *MANNUBIYA* *40* Wafce Hannunta ta yi ta k’arfi ta ce ’’dalla ni cikani” A hankali Muhsin wanda duk jikinshi ya yi sanyi ya ce ‘’Da gaske nake fa’’ Da kyar Baraka ta d’an k’ak’alo murmushi sannan ta ce ‘’Na yarda mana, nima ai tun daga waje na ji lokacin da ta fad’a’’ Da sauri ya ce ‘’au haba! bara mu kira su……” Cikin katseshi ta ce ’’yi maza ka je shagon Audi ka karb’o mata madara, Idan ta ce ’Manu’ to madara take buk’ata. Bari in je in kawo maka kud’in” Baraka ta fad’i hakan tana mai juyawa da niyyar fita. Shiruu Muhsin ya yi, tana shirin fita ya ce mata ’’A’a fa,bata ma tab’a cewa Manu ba sai yau! Adda Manubiya take nufi, kuma ai yanzun nan muka bata madara ni da anty Aisha.” Cikin d’an fushi ta ce ‘’Muhsin za ka yi abunda nace ko kuwa??’’ ‘’Tam’’ Ya ce mata, sai kuma ya sake cewa ‘’Akwai madarar da Ya Musbah ya siya mata me yawa a gida, bara in je in d’auko’’. Shiruu ta yi, kafin ta nufo sa, tana zuwa ta kama kafad’unsa ta ce ‘’Muhsin su ya Musbah sun rufe d’akin naku kafin su tafi, ka wuce ka je ka siyo mata a shagon Audi yanzu-yanzun nan, bara in kawo maka kud’in. Kana sakani yawan magana, kai na ciwo ya ke yi.” Ahankali ya ce ‘’tou Anty’’ a ransa yana tunanin nisa da tafiyar shagon audin. Kamar ya ce mata ‘ba zai iya siyowa a shagon kusa ba?’ sai kuma kawai yayi shiru dan ya san halinta yanzun in ya cika ja-in-ja da ita tsaf sai ta makesa! Dan haka ya ja Bakinsa yayi shiru, ya tsaya ya jirata har ta je ta kawo masa naira d’ari ta ce ’’gashi, ka yi sauri’’. Da ‘’to’’ya amsata, tukunna ya sa hannu ya karb’i kud’in ya fita…har ya kusan kai k’ofa kamar wanda ya tuna wani abun sai kuma ya koma d’akin ya ce ’’Anty in je in kira Anty Aisha? Ta ce idan zan fita in je in kirata, saboda kar a bar inna ita kad’ai.” Wannan karon cikin fushi sosai Baraka ta yi masa dak’uwa tukunna ta ce’’ ungo naka Muhsin! Innar ita kad’ai ka gani anan? ni ba mutum baceba?. Za ka wuce ka je min aike ko sai jikinka ya gaya maka?” A hankali ya kamo hannun me sunan Baba ya ce ‘’zo ka rakani’’ Daganan ya juya kawai ya fita ba tare da ya sake cewa komai ba. Yana fita ta kalli Inna tana raya abunda za ta yi, kafin ta kalli k’ofar da Muhsin d’in ya bi ya fita a ranta tace “sai dai kawai ka dawo ka gani, na san in kana nan tsaf za ka kawo min cikas! Ba k’aramin aikinka bane ba ma ka tara min jama’a shegen Yaro mai shegen surutu…” Tana gama fad’in haka ta nufi inda innar take. … Tana zuwa ba tare da shayi ko tantama ba ta yaye zanin da aka lullub’ewa innar k’afafu da shi, ta d’auki pillown da ke ajjiye a gefenta ta fita waje… A nan tsakar gidan da sumintin duk ya farfashe ta yi shimfid’a ta zanin da pillown tukunna ta koma d’akin. Da kyar, da mugun kyar ta samu ta kinkimi Inna, k’arshema da ta ga baza ta iya ba janta ta yi ta fitar ta shimfid’eta anan tsakar gidan Inda ta shimfid’a zani ta saka pillow. Tana ganin lokacin da hawaye suka shiga sintiri a kan kumatun Inna amman ko d’ar Baraka ba ta ji ba!idanunta sun riga sun rufe.. Ita babban tashin hankalinta shine ‘Manubiya ta yi aure kuma da alamun wani wajen za’a tafi da Baba tunda an riga an kama shi wataƙila shikenan ya tafi har abada, ko me ma yayi oho musu! Dan haka dole dole ta san gidanta Muhsin Jidda da Inna za su dawo kenan da zama’… Dan haka Wallahi ita kuma ba za ta yi k’asa a guiwa ba wajen nuna musu ba su Isa ba…tun wuri ma su nemi gurin zama! yau za su yi ta ta k’are!garama idan suka dawo su gani sannan su tabbatar da cewa uwar tasa ma bata da wajen zama a cikin gidan ballantana kuma k’annensa. Dama tun d’azu a k’ule take….saboda da ya tashi kawo Innar ma ko shawartarta bai yi ba haka nan kawai sai ganin su ta yi. Ai kuwa yanzu zai gani kuma zai san itama ta Isa wallahi!! taga alama idan ba nuna masa ta yi ba tou ba lalle ya tuno ‘waccece Baraka ba’. Hakanan ta yi ta zancen zuci tana huci ita kad’ai!!!. Ko bi ta kan inna bata sake yi ba, ta fad’a band’akin da ke nan a tsakar gidan tana jin nauyi da zafin da zuciyarta ta yi yana raguwa kad’an-kad’an….. A ganinta rainin wayon su ya ma yi yawa! A barta taji da hak’urin zaman auren ma da takeyi da shi ba sai an k’ara mata da wani takaicin ba, yau za’a yi ta ta k’are Wallahi dan bata tsoron uban kowa a cikin su. ……. Su Ya Musbah suna tsaye a d’akin da Abbakar ya ke, su Jidda suka shigo. a take wani irin tausayin su ya lullub’e ya Musbah, dan haka ya kalli ya Nafi’u ya ce ’’bara in duba Reception, in ji ragowar bill d’inmu dan a samu a biya…” Daga haka ya sa kai ya fice… Sun san su Yash sun biya d’azu amma basu san duka suka biya har da na Abbakar ba. Yana fita ya Nafi’u ya d’auki wayar Abbakar, Manubiya ta bud’e musu password d’in shi kuma ya kira maman Abbakar. Ko mintuna ashirin ba ayi ba kuwa suka k’araso cikin asibitin a hargitse ita da maman Baraka. A reception suka had’u da ya Musbah wanda yake ta faman sak’a da warwara, sam ya kasa komawa cikin d’akin bayan ya je an ce masa “ai su Yash sun riga sun gama biyan komai’’. Hangosu ya yi a hargitse suna tambayar wani cleaner, dan haka ya k’arasa ya yi musu iso har cikin d’akin. Dama shima d’in da kyar suka amsa gaisuwar shi yanzu kuma ko kallon baba da yake kwance ba su yi ba haka suka wuce shi suka d’aga labulen da ya ke tsakaninsu da Abbakar Inda ya Musbah ya nuna ya ce musu yana ciki… kawai suka afka ciki. Shi kuma Ya Musbahn ya tsaya a wajen Baba da ya Nafi’u wanda bai dad’e da fitowa daga wajen Abbakar ɗin ba, yake sanar musu ‘’ su Yashjub sun riga sun biya komai’’ Baba yana shirin yin magana suka jiyo maman Abbakar ta kurma wani irin ihu…. Da sauri su Ya Musbah suka nufi inda suke suna addu’ar Allah dai yasa ba wani abun ne ya samu Abbakar d’in bayan fitowar su ba. A durk’ushe a bakin gadon suka hangeta tana wani irin masifaffen kuka. Kafin daga baya ta (maman Abbakar) mik’e ta nufi Manubiya gadan-gadan, tana zuwa ta shak’o ta ta mik’ar da ita tsaye tukunna ta cikata, cikin fushi da kuka ta ce ‘’ai duk ke ce kika janyo komai! munafuka! muguwa! kawai, haka kurum kin maidamin Yaro kamar wani boyi-boyin ki…’’ ‘’Haba mama, baki yarda da k’addara bane?’’ Ya Nafi’u yayi mata tambayar cikin rashin jin dad’i. Cikin fushi ta ce ’’ai dama na san ba za ku ga laifinta ba, to wallahi ku jirani a kotu dan ba zan yarda ba sai mun yi shari’a da ku. Amman kafin nan inaso in ja miki kunne!…. Manubiya in dai har kin haifu cikin Musa da Amina tou kar in sake ganin ki a kusa da d’a na. Kalli cikin azabar da kika jefa sa da ke da y’an uwanki da iyayenki…masifa ce ku wallahi!!! shiyasa duk wanda ya rab’e ku sai ya shafa, na yi k’ok’arin nunawa Abbakar ba so d’aya ba ba sau biyu ba amman dayake kin riga kin shanyemin Yaro kalli sai da kika kusan kai shi lahira…’’ Kukan da ya kufce mata ne ya sanya ta d’an dakata, kafin ta sake d’agowa a zuciye ta ce ’’na gaya miki yanzu zan sake maimaitawa ‘in dai kin haifu cikin tsinannun iyayen k…’’ Nufar matar Ya Musbah yayi da niyyar kai mata duka amman sai maman Baraka ta shiga tsakiya ta rik’e sa, zafin zuciyar da ta ciwo sa ne ya sanya cikin rashin sani ya yi cilli da ita, ya sake yin kan maman Abbakar ɗin… Ganin yana shirin yin b’arna ne yasa ya Nafi’u ya taresa ya ce ‘’Musbahu ka yi haƙuri ka kyaleta ba dan itaba, ka duba fa Abbakar shi ne ya kira su Yashjub, ka rabu da ita, ta ci albarcin d’anta.’’ Daga haka ya juya ya ce mata ‘’mu za mu wuce yanzu. Ga Abbakar nan, zan dawo in duba shi inshaaAllah zuwa anjima…muna buk’atar mu yi mishi godiya. An biya duk wasu charges, abinci kawai zaki dinga basa, Allah ya basa lafiya.’’ Daga haka ya cewa su Manubiya “su wuce su tafi’’. Sai da kuwa yayi da gske tukunna shi da Jidda suka samu suka janye Manu dan ta tsaya kawai tana kallon maman Abbakar ne, so take yi ta maida mata da martani amman kuma darajar d’anta ya sanya ta kasa yin magana. Aikuwa har suka fice maman Abbakar ba ta yi shiru ba…babu kalar zagin da batayi musu ba… Maman Baraka itama tana tsomo Baki A cewarta ‘’sirikinta ya hankad’eta, ta fad’i kuma ko kallon inda take bai yi ba kamar ba y’a ta d’auka ta basa ba!!!! ‘Saboda shi ɗin d’an marasa tarbiyya ne…shiyasa bai san darajar ta ba’.” Hakanan Baba ya tsawatar musu yace ‘’kar wanda yace uffan, su rabu dasu’’ dan haka suka tartara yanasu yanasu suka fice bayan ya Musbah ya je ya karb’i magungunan Baba. K’arfe shida dai-dai suka bar harabar asibitin suka nufi gida. A gida suka fara tsayawa suka ajjiye Baba, tukunna Baban ya ce musu “su duka su je su d’auko inna, kar su damu ba komai zai iya zama shi kad’ai’’. Da ‘’to’’ suka amsa shi, daga haka suka nufi gidan Ya Musbah gaba d’ayansu domin su je su d’auko Innar. ce ’’dalla ni cikan….’’ *MANNUBIYA* *41* Suna fita Baba ya saki hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa… Dama baya so ya yi kuka a gaban su gudun kar ya karya musu guiwa ya d’aga musu hankali..shiyasa yace su tafi gaba d’ayansu. Da ace yana da yadda zai yi to da ba zai tab’a aurar da su Jidda yanzu ba, ya so ƴaƴansa su yi karatu, yaso ace Jidda ta gama ko da level one ne tukunna, amma yanzu kam sai dai ya bita da addu’a da fatan alkhairi tare da rok’on Allah ubangiji ‘ya had’a Manubiya har ma da Jiddan da surukai na gari, ya sa su so su’ Dan kasancewar ya san mahaifin Yusuf ba shi zai sa ya k’i yiwa y’ar sa wannan addu’ar ba! yana rok’on Allah ya sa su jata a jiki bayan auren, Manubiya kuma Allah ya bata na gari, a samu kowacce ta zauna lafiya a gidan ta, dan tabbas abunda su maman Baraka sukayi musu yau a asibiti ya tab’a shi sosai, ya ji zafin abun. A k’ofar gidajen nasu biyu motar Ya Nafi’u ta yi parking, dan haka suka fara firfitowa….. Ya Musbah ne ya fara shiga cikin gidan nasa, su kuma suna biye da shi a baya. A k’arshen soro kafin ya k’arasa shigewa cikin gidan sukaga ya ja ya tsaya chak! Ya ƙi yayi gaba sannan yak’i yayi baya. K’arasawa kusa da shi ya Nafi’u yayi yana mai cewa ‘’Ya dai? kar ka…’’ A take maganarsa ta tsaya chak sakamakon hango Inna da shima yayi a yashe a tsakar gidan. Da farko tunanin su basu ya yi ’watak’ila ko ta yi k’ok’arin tashi ne sai Allah ya bata iko, shine da ta fito kuma sai ta fad’i a wajen’… amman kuma yadda suka ga an shimfid’a mata zani sannan aka d’aura kanta akan pillow ne ya basu tabbacin wannan aikin Baraka ne. Cikin d’aga muryar Ya Nafi’u ya hau kwala kiran ‘’Aisha! Aisha!!’’ Sai kuma ya juya zai fita dai-dai suka yi kicib’is da Aishar dan tana jin tsayuwar motar tasa a k’ofar gidan ta d’auko kular da ta gama juye abinci a ciki ta janyo hannun y’arta suka yo gidan. Cikin fushi ya ce ’’ya akayi kika barta kika fita? ina Muhsin??’’ Inda-inda ta fara yi, tana shirin yin magana ta ga su Manubiya sun yi cikin gidan da gudu, wanda yadda ya Nafi’u ya d’an gota suka wuce ne ya bata damar hango Innar itama dan haka ta yi ciki da sauri tana salati. A take Jidda da Manubiya suka fashe da kuka saboda yadda suka ji jikin Innar ya d’au zafi sosai! hatta kayan jikinta ya d’au zafi! ga ranar la’asar da ta kusan fad’uwa ta haske mata fuska sosai gashi babu damar motsawa……. Dishi-dishi ya Musbah ya fara gani tsabar tsananin b’acin rai da tashin hankali…da kyar ya samu ya iya cewa ‘’Baraka!!’’ Da d’an k’arfi, dan jikinsa wani irin karkarwa yake yi, hatta muryar tasa rawa takeyi. Tun lokacin da suka shigo ta jiyo su…..dan ta gama watsa ruwa a jikinta kenan sakamokon zafin da akeyi ta ji tsayuwar motar ya Nafi’u. Dan haka ta d’auro zaninta, ta yafo mayafinta ta rik’o kayanta a Hannu ta fito fuskarta a had’e tamau!. … Tana fitowa Ya Musbah ya k’arasa inda take ya tsaya..so ya ke yayi magana amman sam sai ya gagara, in banda karkarwa babu abunda jikinsa yake yi, dan haka kawai sai ya kafeta da idanu, ya shiga karanto addu’o’i a chan k’asan ransa yana mai neman tsari daga shaid’an saboda a yadda yake jin zuciyarsa a halin da ake ciki ya san muddin ya ce zai ɗauki mataki ko ya yi wani abun to ya san wallahi kashe Baraka zai yi! sai ya kaita har lahira. Tunda Baraka take a rayuwarta bata tab’a ganin Ya Musbah a irin wannan yanayin ba, babu abunda ya fi tsoratata irin yadda taga idanuwansa sun yi jajawur hatta farar fuskarsa ta yi jaa! gashi jikinsa sai wani irin karkarwa yake yi… Shiyasa gaba d’aya duk sai ta ji tsoro ya lullub’eta, abunda bata tab’a tunanin za ta ji ba kenan dan ko a mafarki bata tab’a kawowa akwai ranar da zata zo ace wai’ta ji tsoro ko shakkar Ya Musbah a rayuwar ta ba’. A lokacin da suke soyayya soyayyarshi kawai ta sani, da suka yi aure kuma..hak’uri juriya da lallashin sa kawai ta sani. Shiyasa a yanzu da ta ga asalin fushinsa abun sai ya bata tsoro matuk’a. Sai da ta d’an yi k’asa da kanta tukunna ta ce ‘’feshi na yi a d’akin, shine na fito da ita waje…..’’ Basu ga k’arasowar Ya Nafi’u ba, sai sauk’ar gigitaccen marin da ya d’auke Baraka da shi kawai suga gani. Da sauri ta d’ago ta kallesa sai kuma ta kasa cewa komai kafin hawaye sharr ya wanke mata fuska, tama kasa maganar. Dakyar da mugun kyar Ya Nafi’u ya yi k’ok’ari ya danne zuciyar da take tunzura sa akan ya rufe Baraka da duka, yana wani irin huci ya juya ya kalli Ya Musbah Ya ce ‘’Yi hak’uri Musbahu’’ Daga haka ya wuce ya fice daga cikin gidan da sauri, dan ya san in ya cigaba da tsayuwa to tabbas sai an samu matsala. Yana fita Baraka ta juya tana kallon Ya Musbah wanda yake nan tsaye ya kafeta da idanuwa… A ranta tana mamakin yadda yana gani Nafi’u ya d’aga hannu ya zabga mata mari amman bai tab’uka uwar komai ba, sannan ba shi da alamar yin komai a kan hakan har yanzun, dan haka ta bud’e Baki zatayi magana kenan shi kuma ya riga ta ta hanyar cewa “ki tafi na sake ki! saki biyu’’ Dede nan Manubiya wadda suka gama kai inna cikin d’aki ta fito ta yo kan Barakar da niyyar ko dai ta illatata ko kuma su illata juna. Da sauri Aisha wadda dama ta lura da abunda Manubiyan take shirin yi ta taho da gudu ta rik’e ta. Sai yanzu Baraka ta samu ta goge hawayen da suke zubo mata babu k’ak’k’autawa tukunna da kyar ta ce ‘’Cika ta, cikata ta dakeni tunda ita mahaukaciya ce, nace muku Feshi na yi amman hakan bai ishe ku ba, uwar taku gwal ce?’’ Cikin fushi Aisha ta ce ‘’Mahaukaciya! Jahila! Dak’ik’iya! Idan baki saniba to yau ki sani Baraka ‘uwa ta fi gwal’. Da bata haife shi ba to da baki same shi ba, dak’ik’iya kawai. Ya Musbah ya ce ya sakeki, dan haka za ki iya tafiya. ki tartara kayanki ki koma gida a sake yi miki tarbiyya wataƙil in kin gyaru ya dawo dake, dan tabbas ko ni ba zan bada goyon bayan aci gaba da zama da ke da wannan halin da wannan zuciyar taki ba.’’ Tana gama fad’in haka ta juya ita da Jidda suka ja Manubiya da kyar suka shige d’aki dukkan su Manubiya tana kuka sosai kamar ranta zai fita! dan ji takeyi idan bata daki Baraka ba yau tou sai ta mutu!. Ita kanta Aisha ta san tabbas in ta tsaya tsaf za su kwashi y’an kallo ita da Baraka kuma a ganinta in bata kwantar da husuma ba to bai kamata ta iza wutar ba, dan haka ta zaɓi su zauna a ɗaki sannan ta duk’ufa tausar Manubiya. Duk bakin Baraka yau kasa cewa ko yin komai ta yi daga k’arshe kawai sai ta juya Fuuuuuu ta wuce d’akinta…. Ya Musbah ma bai ci gaba da zama a gidan ba! Baraka tana wucewa d’aki ya lek’a ya cewa su Manu “kar wanda ya kulata a cikin su,su barta da duniya’’ daga haka ya juya ya fita. Baraka tana shiga d’aki ta fashe da kuka marar sauti mai tsananin cin rai! Bata tab’a tunani ba bata tab’a kawowa a ranta Ya Musbah zai iya sakinta ba!! “to me ya faru, ya akayi har ya iya sakinta! Yanzu ya za ta yi kenan???” Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsar ba. Ta jima tana kuka tana tunani kafin ta share hawayenta a ranta ta shiga aiyyana “Tabbas sai ta nunawa Musbahu kuskurensa wallahi! sai ta jaa shi a k’asa.Kallifa kalar cin mutuncin da suka taru sukayi mata,inaa!bazaiyiu ba wallahi da sake dole ta sake shiri zai ga ikon Allah, bama shi kaɗai ba gaba d’ayan su sai ta nuna musu wacece Baraka’’. Da farko da ta yanke ne akan babu inda zataje, sai kuma ta bawa kanta shawarar ta je ta samu su mamanta itama, a yadda su Ya Musbah suka hayayyak’o sukayi mata wannan aika aikar tabbas bai kamata ta yanke shawara ita kad’ai ba…. Tana wannan tunanin ta had’a kayanta kaf, ko d’an kunne bata bari ba a ganinta in tayi haka Ya Musbah zai ji tsoro ya zo biko da wuri. Su Manubiya suna d’aki sun zagaye inna suna yi mata fiffita sukaji fitowarta tana ta jidar kaya. Babu wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu,haka suna jinta ta dinga kwasar kayanta tana fitarwa one by one har ta gama…… Ya Musbah yana fita direct wajen Baba ya nufa, dan ya gama rayawa a ransa ‘Idan ma za su maida Inna gida tou sai dare, dan so yake yi ya nunawa Baraka iyakar ta! Ta yadda tana ji tana gani sai dai ita ta fita ta barwa Inna gidan Wallahi’. A hanya ya had’u da Muhsin da mai sunan baba sun dawo daga siyo madara, dan haka suka wuce wajen Baban da su… Dama bayaso Baraka ta tafi akan idon me sunan Baba gudun kar yayi ta kuka ya ce sai ya bita. Sun d’an jima a wajen Baba bayan ya ce mishi ‘’Sunje sun tarar Aisha tana bawa innar abinci ne shine aka tsaya ta gama tukunna a kawo ta’’ Sai da suka kuma d’aukar lokaci tukunna ya bar Muhsin anan, shi kuma ya kama Hannun me sunan Baba suka nufi gidan nasa… bai yi tunanin tarar da Baraka har zuwa wannan lokacin a gidan ba amma yana karya kwana ya tarar da ita da adaidaita sahun ta har uku tanata loda kayayyakinta ita da masu napep d’in a ciki. Ko iskar da ta d’ebo ta bai yarda ya kalla ba, ya sake rik’e hannun Yaron ya zo zai shige cikin gidan…suna zuwa da Yaron ya gane ashe uwarsa ce tare da masu adaidaita sahun ai kuwa nan ya hau ihun sai ya bi ta. Tana gani ya fara tsalle ana jan shi yana tirjewa ta dawo ta kama kunnesa ta ja tukunna tace “in na sake jin sunana a bakinka sai na ci uban ubanka! shegen Yaro kawai sai kace dashi na zo’’ daga haka ta juya zata wuce ta ji Ya Musbah ya ce ’’Babana yi hak’uri, mu wuce mu shiga gida, yawo a titi bai kamace ka ba’’ Ai kuwa cikin fushi Baraka ta juyo ‘’Ai sai ka bari in gidan naka ne sai ka yi tink’aho da shi, talaka mara matsugunni kawai, gara ni idan na tafi yawo a titin ba’a gidan haya zan k’are ba! kai kuwa nan da y’an kwanaki za a zo ayi waje da kai dama darajata yasa mai gidan yake d’aga maka k’afa yanzu kuwa na san ba zai barka ka cigaba da zama daga kai sai uwarka b……” Da sauri ya d’auke me sunan baba, ya wuce ciki ya banko k’ofar dan bai shirya biyewa Baraka a k’ofar gida ba… Ta jima kuwa tana ta tijara ita kad’ai sai da masu mashin d’in suka ce mata “in bata shirya tafiya ba, zasu sauk’e mata kayanta su yi gaba’’ tukunna ta shiga ta zauna a take kuma sai ta fashe da kuka. To dai Baraka tun kan aje koina sai da ta ji dama bata fito daga gidan mijin nata ba saboda d’ayan mai mashin d’in bai rik’e mata amana ba…dukda kuwa tafiyar da sukayi bata wuce ta mintuna biyar a tsakani ba amma da yayi wura wura ya ga babu ido a kansa chan ya chanza hanya. Sai da ta Isa k’ofar gidansu tukunna ta lura babu napep d’aya. •••••••• Tun lokacin da Yashjub ya bar office Daddy ya k’ule, ganin la’asar har ta gota bai kira kuma bai zo ba ne ya sanya shi ya kira Najeeb a fusace ya bashi sa’ko amman gashi har bayan Magrib Yashjub d’in bai iso ba. Yassira ce ta guntsawa su Mommy abunda Yashjub d’in yayi yau a office, gashi kuma har yanzu bai dawo ba..hakan kuwa ba k’aramin sake d’aga musu hankali yayi ba dan tashi d’aya suka yanke cewa ‘’wannan yarinyar da suke zargi ce ta kirasa’’ Saboda Yasirar ta ce musu ko bayan da aka tashi daga office sai da suka biya d’ayan company d’in Yash d’in ita da Daddy amma akace musu yau throughout bai je chan ba. Ta tambayi Racheal kuma, ta ce mata ‘’batun estates d’insa komai stable(dai-dai)’’ dan haka matslar ba anan take ba kenan. Shiyasa suke da tabbacin wannan yarinyar ce kenan…tabbas kuwa zama bai kamasuba dan Indai har matsalarta zata sanya ya mik’e tsulum ya fice ana tsakiyar meeting sannan ya ƙi d’aga wayar kowa har yanzu saboda tsabar yadda ya bata mahimmanci, to hakan ya nuna da akwai babban bound (abu) a tsakanin sa da ita wanda ya zame musu dole su tarwatsa shi tun wuri su yakiceta daga cikin rayuwarsa, tun kafin ya k’ak’abo musu k’adangaren bakin tulu!. Hakanan gidan ya kasance shiruu kowa da abunda yake tunani har aka yi dinner aka watse babu Yashjub babu alamar sa. Zuwa wannan lokacin Daddy ya sauk’o daga duk wani fushin da yayi da Yashjub! dan duk hankalinsa ya tashi, shiyasa ya yanke shawarar idan k’arfe goma ta yi Yash bai dawoba tou zai kira y’an sanda da sojoji su saka Hannu a nemo masa d’anshi. Tunda sukayi dinner kowa ya bar dining ya koma cikin parlourn ya zauna…. In banda safa da marwa ba abunda Ddaddy ya ke yi, a kallo d’aya ake iya hango tsantsar damuwa da tashin hankali kwance akan fuskarsa, ya kasa tsaye ya kasa zaune…tabbas yau ya sake tabbatarwa Yashjub shine rayuwarsa. *MANNUBIYA* *42* Tun asalin farko baya k’aunar ganin fushi ko b’acin ransa wannan dalili ya sanya hajiya Mama ta d’auke shi ta maida shi gabanta dan ta ce ‘muddin ta bar masa shi a yadda yake tsananin son nan nashi to ba zai iya yi masa tarbiyya mai kyau ba.’ Daddy ya kasance Mutum mai tsananin k’aunar ya’yanshi amma son da yake yi wa Yashjub wani irin so ne na daban wanda bai tab’a jin kwatankwacin kalar son akan kowa ba bayan uwar da ta haifesa sai ga Khadijah mahaifiyar Yahanasu. Bayaso ya yarda da cewa ya fi son Yash dan baya son ya samu banbanci a tsakanin Ƴaƴan nasa amma yau kam ya yarda ya tabbatar, dan gashi kwata-kwata ko awanni 12 ba ayi ba amma rashin sanin inda Yash ɗin ya ke yana neman haukatasa, ji yake yi kamar ya d’aga Hannu ya zunduma ihu. Gashi dai laifi ya yi masa amma zuwa wannan lokacin har laifin ya gogu a idanun Daddy…..kawai shi matsalar da ke a gabansa a halinda ake ciki itace ya san inda Yashjub d’in yake da lafiyar sa. Gashi ya kira gidan su Najeeb shima ance bai Isa gida ba kuma duk wayoyinsu a kashe, hakan ya sanya tashin hankalin nasa ya sake hauhawa. Mommy kuwa za’a iya cewa tashin hankalin nata ya kusan k’etare na Daddy dan dai kawai ita ɗin tana iya danne nata ne. Babban tashin hankalinta shine ‘wannan Yarinyar da ko sunanta basu saniba ballantana su samu su fara bi takanta, dan indai har ita ce ta kira Yash ta sanya shi ya yi wannnan dogon zango haka to kuwa sunada babbar matsala, dan haka abar a fara bi takanta tun da wuri. Kausar itama daurewa kawai ta ke yi amma had’iyar zuciya ne kawai ya rage batayi ba…. basu riga sun gama tabbatarwa ba amma tabbas in dai maganar Baba Larai ta zamto gaskiya ce! To wallahi sai ta nemo yarinyar nan a duk inda ta ke ta halaka ta! Bata da wani zaɓin da ya wuce ta kaita lahira dan ba a halicci Macen da ta Isa ta shiga zuciyar Yashjub ba wallahi! Ko ta shiga sai ta fito….. A b’angaren Yassir kuwa, ba k’aramin sake hawa ya yi ba, yadda hankalin Daddy ya tashi ne ya fi komai d’aga masa nashi hankalin….duba da yadda laifi fa Yashjub d’in yayi fushi ya kamata ace Daddyn yayi da shi amman ya b’ige da damuwa akan rashin sanin inda yake sai kace wani jinjiri. Zuwa wannan lokacin shi kam ba ya buk’atar wasu shaidun da za su sake tabbatar masa da ‘Yashjub na musamman ne a cikin gidan nan’ dan ya riga ya yarda sannan ya aminta da hakan…. Ya tabbatar inda ace shine ya b’ace haka to da babu wanda zai damu..kwanakin da suka shuɗe lokacin da ya yi fushi ya tafi, Daddy bai san inda yake ba amma bai damu ba! haka aka share kwanaki ko neman sa bai yi ba, kuma bashi da niyyar neman nasa…. Inaa, gaskiya da sake! dan ba zai yiu a dake shi sannan a hana shi kuka ba..ba zai kuma yiu ace uwa d’aya uba d’aya su haifesu ba amma ace ya fi shi fada !kud’i!farin jini!jama’a!ilimi sannan ya d’auke soyayyar iyayen su…ya zama dole ya gyara hakan, in kuma ba zai gyaru ba to dole ya bi ta ko wacce hanya ce yayi maganin wannan matsalar tun kafin bak’in ciki ya kashe sa!! Dan shi kad’ai ya san me yake ji a cikin zuciyarsa…a halinda ake ciki k’ok’ari kawai yake yi yana danne kansa amma ji yake yi kamar ya had’a Daddy da Yashjub d’in ya saka musu bomb!! Musamman ma da ya tuno da abunda Kausar ta gaya masa ‘’ace wai Yashjub yanada 50% (kaso hamsin) shi kuma wai 1 %’’ wannan rashin adalcin har Ina haka!?. •••••• A chan b’angaren su Manubiya kuwa, tun tafiyar Baraka… tsabar b’acin rai tsakanin Aisha Jidda da Manubiya babu wadda ta iya cewa komai, ko abincin da Aishar ma ta kawo duk kasa ci suka yi. Inna kuwa ta lumshe idanuwanta kawai dan bata so ta bud’e hawaye su fito ta sake d’aga musu hankali, shiyasa kawai ta lumshe idanun nata ta yi shiruu iskar fiffitar da suke yi mata su duka ukun tana ratsata. Suna a zaune Ya Musbah ya shigo, shi da mai sunan baba wanda yaketa faman zabga ihu da shure-shuren shi sai ya bi mamansa…. Ganin khairat abokiyar wasan shi ne ya d’an rage zafin abun, kafin dare sharr Yaron ya sake ya shiga mutane yanata wasa. Ba su dad’e sosai ba, ya Nafi’u ya zo, dan haka gaba d’ayansu suka nufi gida bayan ya Nafi’u ya sanya su Manubiya sun yi mishi alk’awarin ba za su gayawa Baba komai game da zancen Baraka ba tukunna. A ranar Baba ya ga gata, har da kwallar farinciki sai da yayi. Kamar komai bai faru ba haka suka zauna har Ya Nafi’u da Aisha aka sha hira, aka ɗan kwantarwa da juna hankali. Sun jima tukunna Ya Nafi’u da Aisha tare da khairat suka yi shirin tafiya, dan haka Baba ya cewa Ya Musbah shima ya tashi ya bisu kar a bar Baraka ita kad’ai. Da “to” ya amsa shi, daganan ya yi musu sallama suma suka fice shi da mai sunan baba. Su Ya Musbah suna fita su Jidda suka sanarwa Baba ‘ai d’azu ma Siyama ta kira, lokacin suna asibiti, wai mamanta ba lafiya, shiyasa ma bata je ba.’’ Ba tare da b’ata lokaci ba ya ce musu “su mik’e su je su dubota, ai da sun fad’a tun d’azu, Allah yasa su Siyaman ba su riga sun yi bacci ba.’’ Da “to” suka amsa, daga haka suka fita….bayan fitar tasu ne Baba ya matsa kusa da Inna… duk abinda ya faru yau ba abunda ya b’oye mata, saboda yanaso ta sani domin ta fahimce sa kuma ta goya masa baya akan aurar da su Jidda da yake shirin yi cikin gaggawa. Yaga alamar amincewa kuwa a fuskarta dan har lumshe masa idanuwa ta yi ta bud’e, dan haka ya sake jin dad’i ya kuma samu kwarin guiwa….hakanan yayi ta mata magana dukda ya san ba za ta mayar masa ba amma ya san tana sauraronshi, kuma ta fahimcesa. Jikin anty Umma kam ba sauk’i sam, sannan har gara Baba ma shi an samu an kaishi asibiti Ita kuwa ko asibitin ma ba a samu me kaita ba. Siyaman ce take gayawa su Jidda cewa “babu wanda ban kira a cikin manyan gidan nan ba, amman kowa sai dai yace min ba shi da ko sisi. Uncle shi kam ma rufe ni yayi da fad’a! wai yanzu Ya Musbah ya kira shi, ya tura masa kud’i shine nima zan kuma kira… gaskiya shi fa an saka mishi ido!Ɗan shige da ficen da aka ga yanayi shine ake ganin kamr wani k’arfi ne da shi. Daga yau in dai na san maganar kud’i ne tou kar ma in sake kiranshi yana wajen aiki, shima bashida shi…’’ Muryarta ce ta katse ta dalilin kukan da ya taho mata. Cikin kulawa Manubiya ta shiga rarrashinta tana bata Baki….. duk da damuwar da su Manubiya suke a ciki basu yarda sun bar parlourn ba sai da suka d’an kwantarwa da y’ar uwar tasu hankali, suka ga ta d’an ware, tukunna suka yi wa anty umma ‘Allah ya k’ara sauk’i’ suka mik’e za su tafi. Mik’ewa itama Siyaman ta yi ta cewa Umman nata “bari in d’an raka su’’ ‘’To’’ kawai anty Umman tace daga haka ta yi musu sai da safe tace su gaida Baba. Suna fita Siyaman ta ce “Manu, akwai abunda nake so in gaya muku, kar ku ji a Bakin wani gara ku ji a Bakina’’. Tsayawa su ka yi duk suna kallonta, dama sun lura kamar akwai abunda take son fad’a! Anty Umma kuma sai gargad’i take ta yi mata da ido. Cikin sanyin jiki Siyaman ta sanar musu ’ashe Suraj..wanda zai aureta ne ya fasa. wai akan an zab’a masa y’ar uwarsa… shine ma dalilin da ya sanya Anty Umma ta d’aga hankalinta har ta kwanta rashin lafiya.’ Tausayin ta ne ya lullub’e Manu dan haka sai tama kasa cewa komai. Jidda ce ta iya cewa ‘’Siyama dan Allah ki kwantar da hankalinki kema karki wani d’aga hankalinki. InshaaAllah hakan shine mafi alkhairi, Allah ya riga ya rubuta dama ba mijinki baneba, inshaaAllah shi zai baki wanda ya fi shi.” Ajiyar zuciya Siyama ta sauk’e kafin ta ce ‘’Jidda sam ban d’aga hankalina ba wallahi ni kaina ina mamakin yadda abun bai wani dameni sosai ba, amma yadda Umma take yi ne bana so, sannan Itafa har yanzu ta ƙi ta hak’ura, shiyasa ma kika ji bata gayawa kowa ba, ni kuma na riga na san tunda har suka ce sun fasa to sun fasa d’in kenan saboda matsalar daga b’angaren mahaifinsa ne fa tun da y’ar k’anwar mahaifin nasa aka basa ashe shiyasa suke ta ja mana rai wajen kawo kaya su ce yau su ce gobe. Amman wai duk da wannan abunda suka yi wa mutane in kika ga yadda Umma take waya da mahaifiyarsa tana wani lallab’a ta abun sai ya b’ata miki rai, sai kace irin ana neman kai da ni ɗinnan…. Da ya ke itama mahaifiyar tasa ba so take ya auri ita wachchar Yarinyar ba.’’ ‘’Haka iyaye mata suke Siyama, gani takeyi kamar za ki shiga damuwa… Duk abunda za ki ga ta yi domin ke ne take yinsa” cewar Manubiya wadda gaba d’aya jikinta yayi sanyi. Cikin sanyin murya Siyama ta ce “da wannan kam gaskiya, sannan kuma na lura kamar tana so ma ta nunawa kaka mallan iyakar sa, a nawa tunanin kenan. saboda kin san ai ya yi wa makwaftanmu magana akan karb’ar kaya, tou yanzu duk ya je yanata yayatawa wai an fasa auren nawa… A bakin yayata fa da take aure a illorin mukaji, wai wata makwafciyar mu anan ta kirata takanas dan ta tabbatar, kinga kuwa ai ya gama yayatawa kenan. Amma dukda haka ni ban san me yasa Umma ta ji haushi ba, dukda a yanayin da yaketa sanarwar bai dace ba amman kuma ni a ganina gara ma a sani tun wuri, tunda dole dai za’a fasa d’in, kuma kowa zai ji.’’ Ajiyar zuciya ta sauk’e cikin son kawo k’arshen zancen ta ce ‘’ko ma dai menene… mai faruwa ta riga ta faru. Ni kuma Ko ba komai yanzu da na yi muku maganar na d’an samu sauƙin abun wallahi’’. Murmushi Manu ta yi kafin ta ce ‘’Siyama ai iyayenmu ne basu gane hakan ba tun wuri, zaman tare dole akwai sab’ani wasu lokutan ma har da rashin fahimtar juna amma muddin aka ce akwai had’in kai a tsakani to sai ki ga an dace’’ Da sauri Siyama ta ce ‘’Wallahi Manu rashin had’in kan y’an gidan nan namu nima yana damuna, har gwara ma ku ku biyu ne Ni fa? Wani zubin fa idan aka k’unsa mana sai dai mu zauna Umma tana kuka nima ina taya ta, babu mai rarrashinmu’’. Murmushi Jidda ta yi daga haka ta kamo Hannun Siyama tukunna ta ce ’’rashin had’in Kai wannan zab’in iyaye da yayyen mu ne. amman mu za mu iya gyarawa, ko da a tsakanin mu ne, wanchan tsarin su ne dan haka inaga muma za mu iya shimfid’a namu tsarin! watak’il idan suka ga ribar had’in kan a tsakanin mu suma su gyara…. kasancewarsu manya ba shine zai sanya ace duk abunda suka yi shine daidai kuma muma sai mun bi ba’’ Murmushi Siyama ta yi kafin ta ce “tabbas Jidda maganarki hakan take. Tun tasowata bani da burin da ya wuce inga mun had’a kai ni da y’an uwana, amma kash! Ɓangaren Mahaifina sun fi nan gwanancewa a fannin rashin haɗin dan su kam zan iya cewa da su gara babu ma, tou nan d’in ma dande kawai muna zaune a waje d’aya ne Ina ganin ku Ina jin sauk’i amma ta fannnin had’in kai kam duk sammakal…. Na cire rai da gyaruwar al’amura a tsakanina da ɓangaren Babana amman nan kam dama Ina saka ran dacewa. Na ji dad’in wannan goyon bayan dana samu daga gareku y’an uwana, Ina rokon Allah Ubangiji ya dafa mana ya bamu ikon gyara zumuncin mu.’’ Ta k’arashe maganar tata tana mai rungumo su gaba d’aya….. … Siyama ta yi waec, takardarta ce dai batayi wani kyau ba, ta ji kwad’ayin inama ace itama itace zata zana post utme jibi kamar Jidda, dan haka suka k’ara k’arfafa mata guiwa akan ‘ta sake yin waec, ta yi jamb ta koma makaranta…’ Idan Allah ya kawo aure ta yi in kuma bai zo ba ta maida hankali akan karatu da gina rayuwarta, kar ta bari wani chan Suraj dashi ya saka mata damuwa.’ Sun tab’a hira, tare da shawarwari a tsakanin su sosai. kafin suka yi mata sallama suka wuce d’akinsu itama ta koma fanninsu. ••• K’arar zuge gate tare da parking d’in motar Yashjub ne ya katsewa kowa tunani. A kurkusa ya yi parking d’in shiyasa har ya samu damar shigowa kafin Daddy wanda ya nufi k’ofa kamar wani zararre ya Ida fita. A bakin k’ofar suka yi karo da shi da Daddyn wanda ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya sakamokon ganin Yashjub d’in da yayi a kan ƙafafunsa lafiya lau. Cikin kwantar da murya Yashjub ya d’an yi kalar tausayi ya ce ‘’Daddy I’m so sorry, dan Allah ka yi hak’uri… Tun 5 lokacin da ka kira Najeeb muka fito, to muna fitowan ne sai motar Najeeb ta lalace, shine na tsaya na ara masa battery ɗina wai dan a samu a tashi nasa ashe wata waya ce ta lalace dan haka nima sai nawa battery d’in ya samu matsala…. Da waya d’aya na fita, to da yake tun rana muke yawo ni da shi munata waya kuma akayi rashin sa’a duk ba wasu isashshen charge ne a wayoyin namu ba shiyasa duk sai suka d’auke, bamu samu mun kira kowa ba. D’azun kuma da na fita daga meeting wani abune mai matuƙar muhimmanci ya taso, zan yi maka bayani akai anjima amma yanzun dai ka yi hak’uri akan fitar da na yi da komai ma, ka yi hak’uri pls Daddy.’’ Ya k’arashe mganar tasa yana me had’e hannuwansa guri guda alamun roƙo. Juyawa Daddy yayi, ya kalli yadda gaba d’ayansu har Ummi da Munirat suka zuba musu idanu sannan suka yi musu cirko cirko. A hankali ya juyo ya kalli Yashjub d’in ya ce ‘’ka je ka ɗan huta, ka ci abinci, sai ka same ni a sama.’’ Daga haka ya juya ya wuce. Yana wucewa Yahanasu da Mommy suka taho a tare. Fuskar Mommy kamar wadda za ta fashe da kuka har da hawaye yaga ya taru a idanunta. Dasauri ta ɗan ture Yahanasu ita ta k’arasa, ta na zuwa ta rungume Yashjub d’in kafin ta cikashi ta shiga tattab’a fuskarshi tana dudduba jikinshi, sai da ta tabbatarwa idanunta da lafiyarsa k’alau tukunna ta ce ’’Gaba d’aya hankalin mu a tashe yake Son…’’ Wani guntun murmushi Yashjub ya yi wa Mommy, da kyar, kamar irin an saka shi dole d’innan. tukunna ya kamo hannunta wanda yake rik’e da kumatunsa a hankali ya sauk’ar mata da hannun nata daga haka ya matsa kusa da Yahanasu wadda ta ja ta tsaya tun lokacin da aka ture ta gefe. Murmushi yayi mata kafin ya ce ’’sorry, na d’aga muku hankali…. Am anjima inaso za mu yi magana dake,kar ki yi bacci da wuri pls’’ Murmushi ta yi ta d’an shafa fuskarsa da alamun kulawa tukunna ta ce ‘’tam, I’m just glad you are okay (Na ji daɗin da ya kasance ba abunda ya same ka).” Ahankali ya ce ’’na gode’’ kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta turo baki ta ce ’’you owe me an apology…(gaskiya ina binka bashin ban haƙuri)….. Ka saka na bada speech d’in da ban shirya ma ba.’’ Murmushi ya yi kafin ya ce ’’Ina buƙatar hutu yanzu, sai da safenku.’’ Har ya juya zai fita sai kuma ya sake juyowa ya kalli Yahanasu ya ce ’’kar fa ki yi bacci!’’ daga haka ya sa kai ya fice. Tun lokacin da Yash ya ture hannun Mommy, ta k’ame a wajen, ta gagara motsi. Gaba d’aya kanta ya d’aure ya d’au zafi dan kwata-kwata ta ma kasa fahimtar yanayin Yash d’in. Chaan kuma sai tashi d’aya kwakwalwarta ta d’au chargi gumi ya shiga keto mata dan in dai abubuwan da ta ji daga bakin Yasira da wanda ta fahimta yanzu a take gaskiya ne to kuwa tanada babbar matsala a gabanta! A take k’irjinta ya shiga dukan uku uku, ta shiga add’ua a ranta akan ‘’Allah dai ya sa bata riga ta makara ba’’ A take kwakwalwarta ta fara lissafawa tana haska mata yadda abubuwanta da shirye-shiryenta na sama da shekaru za su zagwanye a gaban idanunta, muddin bata tashi ta tsaya ta yi da gaske ba!. A chan k’asan ranta ta ce ‘’Wacce irin shuumar Yarinyace wannan? Da zata shigo mana bagatatan haka ta tarwatsa min duk wasu taka tsantsan d’ina’’. Tsabar rud’ani da rikici Mommy bata san lokacin da a fili a hankali kamar me mumbling ta fara cewa “ba zai yiu ba, ba zai yiu duk wasu sadaukarwar da na yi su tafi a banza ba….’’ Da sauri Baaba Larai ta matso ta rungume ta, a cikin kunnenta ta ce mata ’’ana dai kallon ki, ki zo mu je sama tukunna, sai mu yi magana’’ Jinjina Kai Mommy ta yi kamar ta fahimta sai kuma ta d’ago ta kalli Baba Larai ta ce ’’kikace Mace ce a rayuwarsa ko? kin tabbatar d….’’ ‘’Innalillahi!!! Na ce ki zo mu je sama ko?!!’’ Baaba Larai d’in ta fad’a mata hakan da d’an zafi. Sai a sannan tukunna Mommy ta samu ta ɗan dawo cikin haiyyacinta. Ba tare da ta kalli kowa ba, ta juya ta wuce sama jiki ba lakka.. Baaba Larai na bin ta a baya. Anan suka bar Yahanasu wadda ta bisu da ido kawai a tsaye. “hmmm’’ kawai ta ce, kafin ta juya ta nufi d’akinta, ba tare da ta kalli su Yassira ba. Ummi ma bayan Mommy ta bi dan gaba d’aya duk sai ta ji tausayinta ya lullub’e ta.. A gaskiya Yashjub bai kyauta ba, taya za ka dinga yi wa uwar da ta haifeka irin hakan?….. Da wannan tunanin ta haye sama ta bi bayan Mommy da Baaba Larai dan tana so ta d’an taya Baaba Laran tausar Mommyn. Achan parlour k’asa kuwa, wata hirar su Yassira suka shiga yi gaba d’ayansu suna raha suna dariya….Yayinda Munirat ke tsaye a gefe tana mamakin yadda basu damu da damuwar mahaifiyar tasu ba, suka hau hira haka. sai da tafiya tayi tafiya tukunna ta fahimci ashe don ita da ummi suka kafa hirar dan babu komai a cikinta sai habaice habaice, tun suna habaici har suka fara sako sunayen su suna zagi suna dariyar rashin mutunci dukkansu banda Kausar wadda tun d’’azu ta yi shiruu. Nazartar ta (kausar ɗin) kawai shi kuma Yassir yakeyi shiyasa ya ƙi tashi a wajen. Munirat ce ta katse masa tunani ta hanyar nufar sama da wani irin sauri dan ita sai yanzun ne ma ta yi tunanin ‘to me ma ya tsayar da ita a wajen ne tun fako?’ Wani irin wawan tsaki Yassir ya jaa, dan bai riga ya gama fahimtar Kausar ba amma kuma dole ya tashi ya bi bayan Munirat. Cikin had’e fuska ya mik’e ya bi bayanta a ransa yana aiyyana ‘’gaskiya shi fa yana gama samun abunda yake nema a wajen ta to zai yi fatali da plan d’in Kausar… baya son damuwa, bayajin zai iya ci gaba da jurar yarinyar nan muddin ya samu buk’atarsa ta biya.’’ yana tafe yana mita a cikin ransa fuskar nan tamau haka ya haye saman…. A hankali Kausar itama ta mik’e ta nufi sama jiki ba lakka. *MANNUBIYA* *43* Sai da su Mommy suka kusan shiga d’akinta tukunna suka lura da Ummi a bayansu… Mommy ji ta yi kamar ta zurma uban ihu, dan a halinda take ciki bata buk’atar ganin kowa da yin magana da kowa in ba Baaba Larai ba….ayanzu da ya kamata ace sun keb’ance daga ita sai Baaba Larai shine wannan matar zata kama ta wani biyo su. Da kyar kuwa ta d’an sake ta bata fuska suka shige d’akin nata gaba d’ayansu. ….. ‘’Babe!Babe!!’’ Muryar Yassir ta katsewa Munirat tunani. Da kyar ya samu ya d’an daidata fuskarshi, dai dai nan ita kuma ta juyo… dama ta san sai ya biyota dan haka tana juyawar ta ce ’’i’m okay,sai da safe.’’ Ruk’o hannunta ya yi, dan haka ta juyo ranta a b’ace ta ce ‘’Yassir na ce ka daina tab’ani ko??’’ Cikata yayi yana mai d’aga hannuwansa sama kafin ya maidasu k’asa ya zura su duk biyun a cikin aljihu tukunna ya ce ’’kin tabbatar?’’ Murmushi ta yi tukunna ta ce ’’eh, i’m okay! Ina buk’atar hutu, sai da safe’’ Bata jira jin me zai ce ba ta shige ciki ta banko k’ofar!. Runtse idanunshi ya yi da k’arfi sosai, ya dunk’ule hannunsa, a ransa ya raya ’’ Tabbas idan burinsa ya cika akan yarinyar nan sai ya ci uban ta Wallahi’’. Gyaran muryar da Kausar ta yi ne ya sanya shi bud’e idanuwan nasa, kafin ya juya ya zuba mata idanu yana kallon ta har ta k’araso inda yake, sai da ta kalli k’ofar da Munirat d’in ta banko tukunna ta kallesa tace “Rashin kunya fa kenan” Sai da ya furzar da iska tukunna ya matsa kusa da ita sosai ya ce “kuma dole in jure duk wannan abun nata ba, tunda kin had’ani yin soyayyar dole da ita’’ Murmushi ta yi kafin ta ce ‘’Shiyasa k’aunarka take sake nunkuwa a cikin zuciyata… Ammafa dukda haka Yassir ba fa ka yin yadda ya kamata da kyau, dan ni dai bana ganin wani shak’uwa a tsakaninku’’ Motse Bakinsa yayi ya d’an chuno lips d’inshi, still idonshi yana akan Kausar d’in ya ce ’’ko d’azu ma kamar za mu cinye juna a waya, kawai dai tanada attitude ne sannan bata iya danne ɓacin ranta ba ..na lura idan ranta ya b’aci a kaina take hucewa’’ Cikin katseshi ta ce ‘’Ko kuma haushi ta ji akan baka tsaya mata agaban su Yasira ba’’ Murmushi ya yi ya d’an sunkuyar da kansa tukunna ya d’ago ya ce ‘’Tabbas hakan ne ma. Kinga, ni yanzu mu bar maganarta haka, ke mene ya ke damu ki?’’ Yayi mata tambayar yana me tsare ta da idanuwa. Itama idon ta zuba masa na y’an dak’ik’u..tashi d’aya ta fahimcesa tsaff dan haka ta ce ‘’Mommy ce take bani tausayi, ko kai baka lura da ita tun d’azu ba? In nufin lokacin da taji labarin Yashjub ya bar office.’’ Sai da ta d’an sunkuyar da kanta ta fesar da iska tukunna ta d’ago ta ce ’’muna tunanin yana tare da wata ne, kuma ka san dama na gaya maka yadda take ji game da batun aure a lamarin Yashjub batare da mun samu mun karb’o dukiyar gidannan daga hannunshi ba……d’azun baka lura da yadda ta yi kuka ba kafin su hawo?’’ Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya ce ’’yeah na lura’’ A ranshi kuma yana jin wani sauƙi yana zuwar masa dan shi kansa baya so zargin da yake yi akan Kausar ya tabbata, saboda bai san me zai zama ba kuma. ‘’Ya akayi?’’ Muryarta ta katse masa tunani Murmushi ya yi tukunna ya ce ‘’ba komai’’ Ya fad’i hakan yana d’an ruk’ota. Dariya ta yi kafin a hankali da style da wayo ta samu ta zille tana mai cewa “ka je ka kira budurwarka ku shirya, bari in je na ji da Mommy’’ daga haka ta wuce ta barshi a nan tsaye. Yashjub yana fitowa a wanka ko abinci bai ci ba saboda dare ya riga ya yi…. Ya d’auki waya ya kira Manubiya…dan zuwa wannan lokacin kam ya san ta kunna tunda ya ganta da ita a asibiti. Lokacin basu wani jima da dawowa daga wajen Siyama ba, suna zaune ita da Jiddah suna shawara… Ta inda Jiddan ta ke cewa Manubiyan ‘ta siya masa jallabiya da Alkur'ani, ta kai masa a matsayin gift na godiyar abunda ya yi musu….’ Suna cikin lissafin ta Ina kud’in za su fito ne wayar Manubiya ta fara k’ara, dan haka ta yi sauri ta mik’a Hannu ta d’auka daga inda take, ta yi saurin saka ta a silent, gudun kar ta tashi su Inna…. Dukda ta goge numbersa tun lokacin da ta yi fushi ta bar masa office ɗinsa amma tana ganin number kallo d’aya ta gane shi ne! dan haka ta zubawa screen d’in idanu tana kallo kawai, yayinda k’irjinta yake bugawa a hankali a hankali. Lek’awa Jidda ta yi, kafin ta d’an d’ago ta kalleta tana murmushi ta ce ’’shine ko?’’ sai kuma ta kalle ta ta ce ’’Adda Manu, anya kuwa mutuminnan…ko dai ko dai, d’azu fa naga irin kallon da yake ta miki’’ Da sauri Manubiya ta d’ago ta kalleta, sai kuma ta shiga girgiza mata kai alamun ‘A’a’ kamar za ta yi kuka. Dariya Jidda ta yi ta ce ’’to ki d’auka da wuri kar ta tsinke, in yaso sai ki je ko bakin dakalin gefen k’ofa ne, kar ki tashi su Baba. Kamar wata Yarinya haka Manu ta d’an jinjina Kai alamun tou, sai kuma ta mik’e ta fice da sauri dan itanma tanaso ta d’auka d’in…tun d’azu take ta tunanin sa, sam bataji dad’in yadda har ya tafi bata samu ta yi masa cikakkiyar godiya ba, kar yaga rashin kyautawarta.. Tun kafin ta Ida fita ta d’auka ɗin tukunna a hankali ta maida k’ofar ta rufe, ta nemi waje gefen dakalin ta zauna kafin ta ce ‘’Assalama alaikom’’ A hankali. Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e, yana jin wani sanyi yana ratsa shi tukunna ya nemi waje ya zauna a bakin gadon shima. A hankali ya fesar da iska sannan ya ce ‘‘Ameen. Wa alaiki Assalam’’ Daganan shiru ya d’an biyo baya kafin ta ce ‘’Ina wuni.’’ ‘’Alhamdulillah’’ ya ce tukunna ya sake cewa ’’ya jikin Baba?” Itama ‘’Alhamdulillah’’ ɗin tace, daga nan suka sake yin shiruu. A b’angaren Yashjub tunanin kawai yakeyi yana fatan Inama ace tana gefen shi a yanzu haka. Manu kuwa ta lumshe idanunta ne kawai, ta jingina da jikin bango dan zuwa wannan lokacin tabbas zuciyarta ta yi galaba akanta… wani farinciki da nutsuwa kawai ta tsinci kanta a ciki. Bata san meyesa yake son kiran ta ba amma kuma kiran nata da yakeyi ɗin da kulawar sa gareta da kuma taimakon su dayayi ayau tabbas sun k’ara bada gudunmawa wajen tsundumata cikin tafkin k’aunarsa. Ta san ba lalle ta sameshi ba, ta san za ta sha wahala, ta san ya kamata ta yaƙi zuciyarta amman kuma ta san ta makaroo dan ta san ko ta yi yunk’urin hana kanta ba za ta hanuba! she can’t help it… saboda ta riga ta kamu. sannan abunda take ji a duk lokacin da ta yi tunanin shi ko kuma take tare da shi ‘aljannar duniya ne’ haka za ta fasalta abun, dan ya ƙunshi duk wani nishaɗi, farin ciki, annashuwa d.d.s….. Dan haka bata son ta rasa wannan abun da ta ke jin ko da na second d’aya! Ita kaɗai ta san me take ji….shiyasa a take tausayin kanta sai ya lullubeta. ‘’Na yi tunanin za ki kirani’’ Muryarsa ta katse mata tunani. A hankali ta ce ‘’tun d’azu ban zauna ba, sai yanzu’’ ‘’Yeah, nima haka… Na san ai ko da ace kin zauna d’in ma, ba kiran nawa za ki yi ba.’’ ‘’Saboda me’’ Ta yi saurin tambayar sa. ‘’Saboda na lura kamar tsoron kulani kike yi, bakya so mu fahimci juna alaƙarmu kuma ta bunƙasa. idan kuma na yi making move (wani yunƙurin da zai bunƙasa alaƙar tamu) sai a balbaleni da fad’a, a yi fushi a bar min office d’ina” Wata iriyar kunya ce ta lullub’eta, kamar tana gabansa haka ta rufe fuskarta da tafin Hannunta d’ayan, saboda gaba d’aya kunyarsa da kunyar abunda ta yi masa jiya da safen take ji… Sai kuma ta yi saurin dafe k’irjinta, dan sai yanzu ne kwakwalwarta ta gama mata lissafin abunda ya ke nufi ‘Making move (Bunƙasa alaƙa) kamar yaya? Ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba. Shiruu ne ya biyo baya kafin da mugun k’arfi kirjinta ya buga jin a hankali cikin wata kalar murya ya ce ‘’Mannubiya’’ Bata san lokacin da ta kashe wayar da wani irin sauri ba, tana hak’i kamar wadda ta yi y’ar tsere! Sai kuma ta lumshe idanuwanta, ta sake kishingiɗewa a jikin bangon kamar mai shirin shigewa cikinsa, a lokaci guda kuma ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere a jere. Ta d’an d’auki lokaci a hakan, kafin ta ji kira ya sake shigowa wayar. ta riga ta san shi ne shiyasa ta yanke shawarar k’in d’auka, amman kuma sai zuciyarta ta ƙi bata goyon bayan yin hakan, dan haka ta amsa kiran… Tana d’auka ta ce masa “zan duba inna yanzu, sannan za mu zo da ni da su Ya Musbah mu yi maka godiya, a office. ban sani ba ko kana nan gobe sunday’’ ta so daga haka kawai ta kashe amma kuma sam sai ta gagara. Shiruu ya d’an yi kafin ya ce ‘’Ba za a abar godiyar nan ba kuwa? zaku sa in yi ta jin kunya fa’’ A hankali ta ce ‘’ba komai ai, da har da Baba ma zamuzo’’ Da sauri yace ‘’Innalillahi. dan Allah ku rufa min asiri…. In Baba ya zo yi min godiya da kanshi ai sai in b’ace. d’azu ma duk sai da na ji wani iri da ya min a waya Wallahi.’’ Murmushi ta yi kafin ta ce ‘’Eh muma mun lallab’a shi ya hak’ura, amma dai ka bari mu d’in mu zo saboda ba zai yarda ba, ko na ce masa ka ce ba sai mun zo ba! bazai bari ba. kuma nima ina son in yi maka godiyar, dan ban samu na yi maka a asibiti ba’’ Shiruuu ya d’an yi, har sai da ta zare wayar daga kunnenta ta kalla taga still yana kan layin kafin ta ji ya ce ’’Ni kam ba godiya na ke buk’ata daga wajen ki ba.. Akwai abunda nake da buk’ata amman sai ido da ido tukunna zan gaya miki. Allah ya kaimu goben. inanan. Akwai aiki dama, kinga goben sai ki nuna min, daganan idan mun kammala ni kuma sai in gaya miki tukuicin da nake so a bani,’’ Shiruu ta yi har sai da yace ‘’Mannubiya’’ Tukunna ta ce ‘’to. amma fa babu aiki mutum d’aya ne kawai, sannan ya akayi ka sani?’’. Murmushi yayi yace ‘’aikin nasa yana da matuƙar muhimmanci.” Shiruu ta kuma yi kafin ta ce ‘’Ai be kamata ka tambayi tukuici da kanka ba, ni ce zan ga dama in bayar kuma bai ma gama zama ready ba (bai ma gama kammaluwa ba).” Dariya ya yi, yana jiyo wauta a cikin maganar tata kafin ya ce ’’banaso ki siyamin komai… In ma wani abun kike shirin siya, dukda kuwa na ji daɗi kuma na gode amman da gaske ba na son ki siya min komai. Ni a ɗaɓi’ata idan na yi abu aka yaba to ni zan fad’i tukuicin da nake so a bani.” Sai da ta ɗan juya maganar a Bakinta tukunna ta ce masa “Iyakar maidamin zuwan nawa sau biyu da ka yi a wannan satin, a ganina ai ya ishi tukuici to” ‘’Um um bai Isa ba, sannan ai ba iya wannan satin nace ba, zuwan ki gaba ɗaya ya dawo sau biyu kenan Friday and Sunday’’ yace hakan yana murmushi. Turo Baki ta yi gaba kamar tana gaban sa, sai kuma ta yi shiruu tana tunani kafin ta samu tayi kokawa da zuciyarta wadda take ta faman d’aurata akan tunanin abunda zai fad’a mata goben….. ahankali tace ‘’bara in duba Inna, sai da safe’’ Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya ce “dare bai yi sosai ba ko? in ba damuwa inaso za mu gaisa’’ A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce ’’ai bata da lafiya’’. ‘’Eh, Najeeb ya fad’a min kuwa…Allah ya bata lafiya. ki kai mata wayar in yi mata ya jiki’’ Ya sake nanata mata batun gaisawar, a karo na biyu. Sai da Manubiya ta d’an lumshe idanuwanta ta bud’e tukunna ta ce ‘’ai bata magana, bata iya yin komai’’ Da sauri ya ce ‘’subahanallah, Stroke?’’ Ya yi mata tambayar a d’an rikice. A hankali ta ce masa “eh’’ Shiruu ya yi yana nazari kafin ya ce ‘’wanne physiotherapist d’in take gani?’’ A hankali ba dan ta so ba tace mishi ‘’in mun kaita tana ganin normal Dr’’ Zuwa wannan lokacin ya fara fahimtar wani abun dan haka a hankali ya ce ‘’wanne asibiti take zuwa, da magungunan da take sha?’’ Sai da ta sauk’e y’ar siririyar ajiyar zuciya tukunna ta ce ‘’asibitin murtala’’. Ahankali ya lumshe idanuwan shi, yana mai jin tsananin tausayin ta yana ratsa shi….ji yake yi kamar yayi mata kuka. Sai da ta ce bara in je, sai da safe. tukunna dakyar ya ce ‘’Ok’’ sai kuma ya sake cewa ‘’zan iya kiran ki nan da 3O minutes haka, dare bai yi ba?’’ A hankali ta ce ‘’tam, ba damuwa’’ daganan suka yi sallama.. A ranta tana mamakin tsantsar tausayin ta itada ahalinta tare da kulawa da ta jiyo ƙarara a cikin muryarsa. Ba a cikata mintuna ashirin ba ya kirata, ya sanar mata ‘’gobe su shirya around 8, akwai babbar likitar da ya yi booking, za ta zo ta duba Innar. Idan ta zo ɗin za ta tafi da ita asibitinta a goben, in suka gama aka maido Innar gida kuma Matar za ta dinga zuwa gida kullum (ko ita ko wakilliyarta) ana duba Innar ‘’ Daganan ya ce ‘’ta tura masa adress d’in gidan nasu zai turawa Likitar’’ Shiruu Manu ta yi, dan ita har ga Allah batayi tunanin Likita zai kira a daren nan ba, bayaga hakan ba ma ta yi tunanin abun zai damesa har haka ba… ta ji dad’i matuk’a da ya damu da damuwarta, kuma ta ji dad’i da innar tasu za ta samu kulawar lafiya ta musamman dan ta san InshaaAllah da taimakon ubangiji za ta warke in ta samu kulawa ta musamman, wanda hakan shine babban burinta ita da y’an uwanta a halin yanzu(inna ta warke) To amma kuma sai take gani kamar ɗawainiyar da Yashjub ɗin yake yi da su ta yi yawa, ba wai ko dan tana tunanin za ta d’aura masa nauyi ko kuma aljihunsa zai yi k’asa ba dan ta san hakan ba zai tab’a aljihunsa ta koina ba tunda ya riga ya tara, kawai dai tana ganin kamar in hakan ta faru su d’in za’a ga kamar sun zira jiki sun sakankance da shi dayawa, kar kuma aga kamar ko kwaɗa’…..’’ Muryarsa ce ta katse ta jin yana cewa “Likitan Babba ce ta kware sosai a aikinta. kar ki damu inshaaAllah innarmu ta kusan warkewa’’ Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin a hankali ta ce ‘’bansan ta Ina zan fara yi maka godiya ba’’ Cikin katseta ya ce ’’Mannubiya, tsakani na da ke babu godiya’’ Sai kuma ya d’an yi murmushi tukunna ya ce ’’kawai dai tukuicin da na ke da shirin tambayar ki gobe ne nake addu’ar Allah yasa kar ki ce A’a’’ Ahankali ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce ‘’good 9te, sweet dreams’’ A hankali kamar itama bataso ya ji tace masa “good nyt’’… Murmushi kawai ta ji yayi daganan suka yanke kiran a tare kowannen su yana yi kamar bayaso. Yana katse wayar ya koma ya kwanta rigingine akan gadon yana wani kalar murmushi…. Ƙarar wayarsa ce ta katse shi… yana d’auka da ya kalla kawai sai ya maida kanshi ya kwanta ba tare da ya amsa ba! Yana mai jin yanayin rai da zuciyarsa suna chanjawa….tun d’azu Mommy take kiran sa, tun yana wayar da Manubiya har yayi da Doctor ya koma ya sake yi da Manubiya…. Shi da farko ma bai san ita bace ba dan bai duba mai kiran nashi ba, sai da ya gama shirya appointment da Doctor tukunna ya ga ashe ita ce. Ya riga ya san ba wani abun bane kawai wayar da ta ji yana yi ne ya kuma d’aga mata hankali tunda tun daga d’azun har izuwa yanzu bata d’aga k’afa na minti uku ba! kiran sa kawai take ta yi akai akai…ba ƙaƙƙautawa Ya san yana d’auka za ta fara tambayar sa da wa yake waya kamar wani k’aramin Yaro, ba zai iya yi mata dogon bayani ba gaskiya, gashi kuma dama a fusace yake da ita. Zai san abunda zai fad’a mata dan har ga Allah sai komai ya kammala tukunna za ta ji, saboda bai yarda da Mommy ba akan duk wani abunda ya shafi Kausar!!! Sarai ya ji abunda Kausar d’in take fad’a mata a ranar da ya je sama wajen Mommyn zai yi mata magana akan ‘ta daina turo masa Kausar side d’in sa’, Shiyasa ya yanke akan ba za su ji yanzu ba sai Daddy ya amince sannan komai ya shiryu ya zama ready tukunna, sannan bayaga wannan dalilin ma yanada dalilai dayawa…. Kiran wayar ne ya sake shigowa dan haka ya kalla, kafin ya sake d’auke kai…har ga Allah bai san me zai ce mata ba idan ya d’auka, shiyasa ya bari akan in ya gama shawarar me zai ce mata ɗin da zuciyarsa sai ya saurareta amma ba yanzu ba, dan baya so ta chanja mishi yanayi na nishaɗin da yake a ciki yanzu.. Ya san abunda ya ke yi baya kyautawa amman itama Mommy bata kyauta mishi ba! Ba zai iya yi mata dariya ko ya sake mata ba, yana jin zafin ta har yanzu.….na marin da ta yi masa a gaban k’annensa sannan ta fifita Yassir sama da shi, har gobe idan ya tuno maganganunta ji yake kamar ya yi kuka, abun yayi masa ciwo sosai, ya tsaya a ransa, ya kasa mantawa….. Cikin son kawar da tunanin ya maida hankalin shi ga Manubiya, wadda tausayinta gaba d’aya ya mamayesa tun ɗazu, a hankali ya ce ’’Allah ya sa a dace da magani da pt ɗin doctor sofia, a samu mshaifiyarta ta warke ta fara magana’’ yana wannan tunanin text na adress d’inta ya shigo wayarsa dan haka ya turawa Dr sofia d’aga haka ya mik’e ya fice. Wajen Daddy ya fara biyawa ya bashi hak’uri sosai tukunna yayi masa sai da safe ya wuce. Ya san cewa uwa daban take kuma tanada daraja, shiyasa duk yadda ya so sai ya gagara wuce side d’inta ba tare da ya shiga ba dan ya san hakan bai kamata ba duba da yadda tayi ta kiranshi ma ya ƙi d’auka. Ba dan ransa yana so ba, haka nan ya k’arasa bak’in k’ofar side d’in nata ya shige cikin parlourn ya wuce zuwa bedroom d’inta. murd’a k’ofar yayi amman ga mamakinsa sai ya ji ta a rufe. Yana shirin fara knocking ya ji magana k’asa-k’asa….kamar zai tsaya kuma sai ya juya kawai ya fita dan ya san ita da Baaba Larai ne kuma magana mai mahimmanci ce sukeyi tunda har ya mud’a handle amman suka gagara lura sannan ko yaro ne shi ɗin, ya san bai kamata ya yi musu laɓe ba. Da wannan tunanin ya fice ya nufi d’akin Yahanasu yana mamakin yadda sam baya jin Mommy a jikinshi, dan har ga Allah shi kansa abun yana damun sa…. kwata-kwata baya jin ta kamar yadda yake jin Daddy da su Yasira wanda kamata yayi ma ace ya fi jinta a zuciyarsa fiye da kowa tunda ita soyayyar uwa daban take… Har a bakin ka’aba ya yi adduar ‘Allah ya saka masa soyayyar mahaifiyarsa a cikin zuciyar sa’ saboda wani zubin har tsoro ya ke kar ya je shi bai sani ba rashin shak’uwar su ta ja yayi wani abun da za ta ji haushi, ta ga kamar ba ya kula da ita yadda ya kamata, ya je garin hakan ya fad’a halaka. Shiyasa ko da yaushe ya ke iyakar bakin k’ok’arin sa wajen ganin ya samu ya jata a jiki to ita kuma gashi yanzu ta zo ta kuma bak’anta masa rai akan Yasir!!! da sauri ya kawar da tunanin saboda in ya tuna ma ransa sake dagulewa yake yi dan maganganun da ta farfad’a a ranar sun tsaya masa a rai matuk’a….. Cikin takunsa ya k’arasa dak’in Yahansu, bayan ya gama yankewa akan ‘sai Daddy ya gama hucewa tukunna maybe ko zuwa gobe ya same shi da maganar Manubiya.’ Ya san bashi da matsala tunda Daddy da bakinsa ya sha gaya musu cewa “ko wanene ko wacece in suka kawo zai aura musu a duk lokacin da suke so in dai tarbiyyan su yayi masa’’ Amma dukda hakan yana adduar Allah yasa ya dace, kar Daddy ya baɗa masa ƙasa a ido. Sai da ya shiga da sallama tukunna ya ɗan sake yi mata knocking dan ya fahimci kamar ma bata san ya shigo ɗin ba…saboda a chan kan tebur ya hangeta ta barbaza takardu da alamun aiki takeyi. Glasses d’in idonta ta zare ta mik’e ta nufesa tana murmushi. .. A gefen gado ta zauna tukunna tace masa’’Bismillah’’ta yi maganar tana nuna masa gefenta, ganin yadda ya tsura mata idanu. Sai a sannan ya d’an sauk’e ajiyar zuciya yana me zama a gefen nata ya ce ’’baki gama warkewa ba amma kika zauna aiki har twelve? ya jikin naki?’’ Yayi mata tambayar yana kallon ta. Murmushi kawai ta yi kafin ta ce ‘’Alhamdulillah’’ Zata yi magana ya katseta ta hanyar cewa ‘’Tunani kike yi ko? shiyasa ki ke ta tulawa kan ki aiki.. har yanzu kin k’i ki kwantar da hankalinki’’ Murmushin ta sake yi sannan tace ‘’Bafa na tunanin komai Yash, mu bar maganar nan, yanzu fad’a min meye kake so ka gaya min?” Ta fad’i hakan da murmushi kwance akan fuskarta. D’an k’ura mata ido yayi kafin ya ce ’’Mun fara b’oye-b’oye a tsakanin mu kenan! Kin san dai za ki iya tattauna koma mene dani dai ko?. ki kwantar da hankalinki dan Allah Yahanasu, ni wallahi har ga Allah ban ga wani tsufan da kikayi ba, meyemarabar ki ke da su Kausar d’in?? Kausar ta kusa 28 fa haka itama Yassira, ita kam tama rufe 28 d’in… meye marabar ku da za ki bi ki d’aga hankalinki??’’. A hankali ta ce ‘’Yash, ba zaka gane ba, na tare musu hanya. in ban wuce ba taya za su saki jiki su ga dacewar suma ya kamata su wuce???’’ K’ura mata idanu ya yi, wanda har sai da ya sanyata d’an sunkuyar da kanta tukunna ya ce ‘’Mommy ko Baaba Larai wani a cikinsu ne ya gaya miki haka ko? ko kuma su Kaisar d’in?’’ ‘’Yash dan Allah mu bar maganar nan, ka san dai yadda nakeji idan ana irin wannan maganar ko? ka bar maganar kawai’’ Ajiyar zuciya ya sauk’e tukunna ya ce ’’tam, na ji, zan bar maganar amman sai kin yi min alk’awarin kin daina tunani kuma kin daina ɓoye min abubuwa, idan kinada damuwa ki dinga tattaunawa da ni pls za ki ji sanyi a ranki! zama a d’aki ke kad’ai daga ke sai matsalolinki ba abunda zai ja miki sai depression! Ki kwantar da hankalinki, Aure nufi ne na Ubangiji… yanzu ne fa za ma ki fara 30s d’in ki Yahanasu sai yanzun ne ma fa kika zama lady, kar ki biyewa al’adar Bahaushe ki kashe kanki, kalli yadda kika rame fa.’’ Hawayen da ya zubo mata ta ido d’aya ta sa Hannu ta share kafin ta ce ’’Yash,dole abun ya dameni….tun Inada shekaru 15 nake so inga na yi aure. so nayi Ina gama secondary school ace na yi aurena, ba wai dan komai ba sai dan kawai ni inaso in ga na yi aure na haihu na kula da family d’ina, amma kalle ni har yanzu”. Ajiyar zuciya ya sauk’e, ya matsa kusa da ita ya kama kafad’unta tukunna yace’’kalle ni nan Yaha’’ Sai da ta d’ago ta kalleshin tukunna ya ce ‘’Bawa, kowanne da akwai tashi kalar k’addarar, ki d’auka ke wannan ce taki… Ubangiji dama ya kan jarabcemu da abunda muke matukar so, za mu samu delay amma da ikon shi in mukayi hak’uri sai ki ga mun samu har ma da k’ari. Ki godewa Allah ma ke da ya jarabceki a yanzu, ba sai kin tsufa ba, saboda a kullum Ina yi miki addua ‘InshaaAllah wannan ita kad’ai ce mummunar k’addarar ki! kuma itama ɗin inshaaAllah kwanan nan za ki yi auren ki, komai ya daidaita. InshaaAllah za ki samu mutum mai hankali mai tsananin k’aunar ki, ki yi aure, ki hayayyafa, hankalinki ya kwanta, ki samu kwanciyar hankalin da in kika tuna kin tab’a shiga wannan damuwar ma sai ki nemi b’acin ran da kika shiga a yanzu ki rasa, ki ji kamar bai tab’a faruwa ba. InshaaAllah za ki samu yalwataccen farin ciki a gaba wanda zai goge duk wannan bak’in cikin da kike a ciki.’ Amma yanzun ina so ki rungumi k’addararki ki cinye jarabawarki sannan ki kwantar da hankalinki, kin ji ko?’’ A hankali ta jinjina Kai ta goge hawayenta ta ce ’’na gode Yash, Thankyou so much(na gode sosai)”. ‘’You are welcome (Babu komai ai)” Ya ce, yana murmushi kafin ya cikata sannan ya ce ’’akwai Labari mai daɗi, amma ki fara yi min alƙawarin ba za ki fad’awa kowa ba a yanzu sai in gaya miki… saboda inaso sai komai ya kankama tukunna kafin kowa ya ji’’ Tana wani faffaɗan murmushi ta d’aga mishi kai ta ce ‘’na yi alƙawari’’ Wani kalar murmushi irin kamar ya na ɗan jin kunyarta ɗinnan ta ga yana yi kafin ya ce ’’kin kusa ki yi k’anwa… InshaaAllah inaga wani watan ko wataƙila kafin ma nan da wata ɗaya Zan yi aure, in har Daddy ya bani haɗin kai ita kuma Yarinyar ta bani dama da”. Yahanasu ba ta san lokacin da ta ce ‘’what!? (Da gaske!?)’’ cikin farin ciki ba. Tana mai zaro idanunta Kafin ta d’aura da cewa “eh lalle Manubiya ta ciri tuta,’’ A hankali ya yi murmushi ya ce ’’eh, da gaske, ki tayani da addu’a da k’ok’ari a yi auren nan kamar yadda na tsara da sauri, saboda Manubiya ta riga ta sace zuciyata’’. Dariya sosai Yahanasu ta yi kafin ta mik’e ta ce “ina zuwa” tukunna ta Isa jikin k’ofa ta bud’e, ta d’an duba tare da sak’ala key.. saboda yadda ta ji jikinta ya bata akwai Mutum a wajen. Tana dawowa ta zauna sannan ta ce ‘’Yanzu tou ya ake ciki? Itama ta amince ne? sannan Yash kana ganin ƙin gayawa su Mommy ba zai janyo wata matsalar ba kuwa? Kar su ga ka b’oye musu sannan ka gaya musu a k’urarren lokaci, Ka san ba za su ji dad’i ba, za su ce bama su san kana da budurwar ba. Dole na san in suka ji aure kwatsam zasuga kamar ka b’oye musu ne ko wani abu makamancin haka’’ Iska ya fesar kafin ya ce ‘’Yaha, kin san abunda na gaya miki kwanaki akan Kausar.. In ta ji labarin Inada budurwa aiki ne, kuma kin san Mommy bayanta za ta bi! Dan haka Pls, ki bar maganar nan, bana so in gaya musu saboda Kausar wadda banaso ma Ina tuna abunda na ji ranar ta fad’a a kaina, wallahi raina b’aci yake yi!!!. Maganar Manubiya kuma gobe zan gaya mata dai.. inshaaAllah Ina fatan Allah yasa ta amince da ni, dan ba zan ma iya tunanin wai bata amince d’in ba. Ina adduar Allah yasa zargina ya zamo gaskiya dan na ga kamar itama tana so na. In komai ya kammala za ai auren ciki gaggawa dan ba zan tsaya ɓata lokacin da zai bawa Mommy ko Kausar damar kawo min cikas ba.” Murmushi yahanasu ta yi, kafin ta ce ’’na fahimceka, kuma inshaaAllah ba za ma a samu matsalar komai ba. sannan na san dole ma Manubiya ta ce maka yes! goben nan, dan bana jin a kaf fad’in duniyar nan akwai Macen da za ta ƙi amincewa da lil bro ɗina(ƙanina)’’. Dariya ya yi kafin ya d’an harare ta cikin sigar wasa, sannan ya ce ’’lil bro kuma? ko cikakkiyar awa d’aya fa ba ki bani ba’’ ‘’Amma dai na girme ka! ko da da second d’aya ne, na dai girme ka’’ Dariya duk sukayi kafin Yahanasu ta ce ‘’amma ta ya kake tunanin iyayen ita Manubiyan za su amince su aura maka y’ar su a cikin wata d’aya kamar yadda ka fad’a? Ko zaka d’an d’aga k’afa ko wata uku hak….’’ Girgiza Kai kawai ya yi kafin ya ce ‘’gaskiya ba zan iya ba, dukda ban san ta ya za’ayi su yarda da auren a haka ba amma zan yi ta addu’a, kema ki tayani,’’ Yayi mata maganar cikin yin kalar tausayi, har da wani karyar da wuya . Tausayi da dariya ya bata dan haka ta ce ‘’inshaaAllah, komai zai tafi yadda kake so’’. A hankali ya ce ‘‘Allah yasa” daga nan suka shiga tattaunawa game da lamarin….’’ Yahansu ta san menene so duba da yadda itama ta so first love ɗinta(saurayinta na farko a duniya) kamar ranta,,saurayin da ya fara yin watsi da ita… Shiyasa yanzu sam bata ganin laifin Yashjub da ya gigice akan Manubiya…. Adduarta d’aya ita ce ‘Allah yasa a bashi ita a yi auren kamar yadda suketa tsarawa yanzun, Allah yasa kar su Mommy su kawo cikas d’in komai.’ Yash yana k’aunar y’ar uwar tasa sosai..ya lura da yadda su Yasira basa janta a jiki..dukda bai ma san wasu daga ciki hantarar da suke yi mata ba amman yana yawan tsawatar musu da nuna musu gaskiya, kawai dai ya san tunda suka riga suka nuna basa sonta to ba lalle ya iya gyara tsakaninsu su dawo su k’aunace yadda ya kamata ba. Yanaso ta ji itama ta musamman ce…itama ta ji tanada ɗan uwa me kaunarta a ko da yaushe, shiyasa ya ke bata kulawa ta musamman, kuma har ga Allah yana ji da itan da gasken gaske kuma ita kad’aice zai yi shawara da ita ya ji dad’i dan sun saba sosai, shiyasa yanzun ma yake ta neman shawarwarin ta… Ta kuwa ji dad’i tun ba ma da ya ce ‘itace za ta had’a masa lefe ba!’ bata san lokacin da ta fashe da kuka ba…. Yahanasu…. Ta kan yi kukan rashin jituwa tsakaninta da y’an uwanta mata, amma a duk lokacin da ta tuna tana da Yash sai ta ji duk damuwarta ta Kau. Bata jin a duniya akwai d’an uwan da ya ke tsananin k’aunar ƴar uwarshi kamar yadda Yash ya ke ƙaunarta ya ke ji da ita, ko shawara ce da ita ya ke yi, ko menene sai ya gaya mata…. shiyasa har yau har gobe ta kasa yafewa kanta duba da yadda ita ta kasa gaya masa abu mafi mahimmanci na rayuwarsa bayan ta sani, kuma tana da ikon da za ta taimaka mishi wajen samun abunda ta san zai sanya shi farinciki fiye da komai….. Ta jima tana kuka har sai da ta d’an fara bawa Yash ɗin tsoro. Tukunna ya samu ya rarrasheta da kyar, ya d’an jata da wasa da hira daga nan suka shiga wata maganar…. Kafin daga baya ya yi mata sallama, ya tafi bayan ya samu ta hak’ura ta karb’i number Manubiya kawai dan da farko cewa ta yi sai ya kira mata ita sun yi video call,, da kyar ya lallab’ata ta hanyar ce mata “Manubiyan ta yi bacci by now.’’ daga haka suka yi sallama, ya tafi. ……..2 hours before now……… …….awanni biyun da suka shuɗe(kafin yanzu).. Ummi bata wani dad’e a wajen su Mommy ba, ta fita ta wuce d’akinta. Bata dad’e da fita ba, su Yassira suka shigo, suka taru a d’akin har Yasmeen kamar wasu masu meeting. Mommy ce ta cewa Yasira ‘ita da Kausar, su je su saka mata ido a k’ofar Yahanasu’ dan ta san tunda ya ce yana so yayi magana da Yahanasun yau to komin dare sai ya je sun yi, su kuma ta maganar da za su yin ne kawai za su samu haske akan zargin nasu…. Ba k’aramin tashin hankali ta sake shiga ba lokacin da ta kira shi ta ji yana waya, kawai ita ta yadda ta gama amincewa ta bada amanna akan maganar Baaba Larai!! Shiyasa kwata-kwata kwakwalwarta bata bata cewa ‘ai waya yake akan business ko wani abun ba! tashi d’aya ta amince kawai da wannan Yarinyar yake ta waya.’. Yassira ce ta samu ta ga Yash d’in, dan Kausar ta saman balcony ta tsaya tana jiranshi, ta yadda yana fitowa daga side d’inshi ita kuma zata gani daga nan sai ta jira in ya shige d’akin Yahanasu ta je ta lab’e!! saboda ta fi kowa k’aguwa da son jin menene asalin gaskiyar maganar amma sai Allah bai bata ikon ganin nashi ba dan lokacin dai-dai ya zo zai wuce sai aka yi mata text dan haka bata ga shigar tasa ba. … A kitchen Yasira ta jira har ya gama da wajen Daddy ya sauk’o ya shiga d’akin Yahanasu, tana ganin ya shige ya turo k’ofar ita kuma ta fito ta Isa bakin k’ofar da sauri ta lab’e. Shiruu Yassirar ta yi tana sauraron su… Wato dai zargin su ya tabbata kenan, sannan bayaga hakan kuma aure cikin wata d’aya ma yake son yi!!! “Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” Ta aiyyana hakan a cikin ranta hankalinta a masifar tashe, ta shiga lissafin…. ‘Shin ta ya za su iya cin nasara akan wannan abunda ya taho musu gadan-gadan haka?. Babu tausayin wadda ya lullub’eta sai Kausar! Saboda zuwa wannan lokacin idan Kausar ɗin ta yi wani abun har mamaki take bata, kamar wata wadda ta fara samun taɓin hankali haka so da k’aunar Yash suka maida ita, sam bata ji bata gani aduk abunda ya shafeshi …’ Yasira tana cikin wannan tunanin ta ji Yahanasu za ta bud’e k’ofar dan haka ta yi sauri ta wuce ta fad’a kitchen. …Now… …yanzu.. Sai da Yassira ta ji fitar Yash, tukunna ta fito, tana ji kamar zuciyarta za ta tarwatse, ta nufi sama. *MANNUBIYA* *44* Kausar na tsaye, ta saman balcony ta hango fitar Yash.. ta yi mamakin rashin ganin shigar shi ɗin da bata yi ba dan haka ta fito da sauri tana adduar ‘Allah ya sa Yassira ta samu ikon saurarar su.’ Dai dai tana fitowa ta hangi Yassirar ta nufi side d’in Mommy a rikice, dan ko lura da fitowar Kausar d’in ma bata yi ba. Da k’arfi k’irjin Kausar ya buga! yayinda k’afafuwanta su ka fara karkarwa… Da kyar ta samu ta tattaro gaba d’aya kuzarinta ta bi bayan Yassira tana jin kamar zata fad’i a k’asa dan tabbas wannan rikicewar da ta ga Yassira ta yi tou akwai matsala kenan. Yassira tana shiga d’akin Mommy, duk suka mik’e tsaye!. Dama gaba d’ayansu sun taru Yusra da Yadira ne kawai babu. Yasmeen ce ta matso kusa da ita ta ce ‘’Lafiyan ki kuwa? Me ya faru?’’ Wani k’ululu da ya tokare mata mak’oshi Yasira ta hadiye tukunna da kyar ta ce ’’Ya‘isha, ku d’an fita, Ina son yin magana da Mommy ita kad’ai’’ Cikin d’an b’acin rai Baaba Larai ta ce ’’zancen banza kenan, waye kika gani Bare a cikinmu?’’ A hankali Yasira ta lumshe idanunta ta bud’e ta na jin tsananin tausayin Kausar har ma da Mommy yana sake lullub’eta, kafin ta ce ’’Ba haka bane Baaba, bana son maganar ta yayatu da yawa ne gudun kar wata a cikin ku ta manta ta yi suɓutar Baki a gaban Kausar.’’ Dai-dai nan Kausar wadda ta k’araso bakin k’ofar d’akin Mommy ta jaa ta tsaya… Tabbas a yadda ta ga Yasira d’azu da kuma yanda ta ji muryarta a yanzu da abunda ta ji ta fad’a, ta san idan ta ganta ba za ta fad’a mata komai ba duk runtsi!. Dan haka kawai sai ta yanke shawarar lab’ewa a wajen. A hanakali Mommy wadda gabanta ya fara fad’uwa sosai, ta k’arasa inda Yassira take ta ce ‘’Yi magana Yassira, ko menene ma fad’i, za mu iya fuskanta in sha Allah!. Me ya faru? Wacce maganar ki ka ji Yash suna yi da Yahanasu?’’. Dafe Kai Yassira ta yi, ta matsa gefe ta juya sannan ta d’an runtse idanunta ta yi shiru kafin ta bud’e ta ce ‘’Abin baƙin ciki ne sosai!! Ace lokaci guda gaba d’aya aikin da ku ka yi tuƙuru na shekara da shekaru ya tarwatse, ba tare da mun ci riba ko guda d’aya ba’’. Da sauri Mommy ta ruk’o ta, ta juyo da ita sannan ta ce ‘’Yassira, ina son abu na gaba da zai fito daga Bakinki ya tafi kai tsaye zuwa ga ainihin maganar da duk mu ke son ji! Ki fad’a min abunda ya faru tun wuri saboda raina ya fara b’aci.’’ Kallon ta Yasirar ta yi kafin ta ce ’’ai ba ki ji b’acin rai ba Mommy sai na ce miki Yash zai yi aure! Kuma nan da wata ɗaya na ji ya ce dan haka kinga kuwa an riga an gama komai ma kenan…ba maganar budurwa ake yi ba yanzu, maganar aure ake yi’’ Cikata Mommy ta yi da sauri, sai kuma ta k’ame, sam ta kasa sake yin motsi. Cikin takaici Yassira ta ce ‘’Yes Mommy, Yash zai yi aure ba tare da kun fahimci juna ke da shi ba, ba tare da mun samu damar amso uban dukiyar da Daddy ya mallaka masa ba, ba tare da ya damu ko ya had’a Kai da d’aya daga cikinmu ba Sannan mafi muni Yash zai auri wadda bamu sani ba kuma ga dukkan alamu yana matuk’ar sonta da k’aunarta, kinga kuwa zuwa nan da y’an shekaru kaɗan komai ya zama nata, daga ita sai ya’yan su! mu kuma sai dai kallo!’’ Cikin fushi Mommy ta ce ‘’Yi shiru Yassira, ya Isa haka!’’ ‘’Mai yasa? Saboda me zan yi shiru? Ba kya son ji ne? Ai gaskiya na fad’a, in ba haka ba Mommy ki duba fa ki gani aure ne Yash zai yi ko kuma in ce yake shirin yi nan da wata ɗaya fa!!! Amman kaff d’inmu nan babu wadda ya gayawa, ko kyallin zancen ma babu wadda ta taɓa ji saboda tsabar yadda kanmu da nashi yake ba’a had’e ba!…. Wannan shegiyar Yahanasun ita kad’ai ce ta sani, ita kad’ai ya gayamawa, ashe tun farko dama ta san da Yarinyar amman ta yi mana shiru..’’ Cikin fushi Yasmeen ta ce ‘’Ai ita take cin dunduniyar mu dama, ku gaya min dalilin da zai hanani cin uwar Matar nan yau a cikin gidan nan!’’ Ta fad’i haka tana shirin fita da niyyar zuwa ta sami Yahanasun. Da sauri Baba Larai ta sha gabanta, ta rik’eta kafin ta ce ‘’Ba za ki tab’a Yahanasu ba Yasmeen, ba za ki ce mata komai ba’’ A harzuƙe Ya’isha ta ce ‘’Haba Baaaba! Ya za ki ce haka???yanzu inda ace ta gaya mana tun farko ai da mun san abun yi, da tuni ba’a kawo ga haka ba, amma yanzu kalli abunda b’oyewar da ta yi ya janyo. saboda Allah idan mu tana ganin bata shiri da mu ai ko ke ko Mommy ya kamata ace ta gayamawa, tunda na san ta san dole ba’a san da zancen ba. Har ga Allah Yahanasu ta fara wuce iyakarta kwana biyun nan, Ranar chan fa da ta gaggaya mana magana a parlour ranar da akayi case d’in senator da Yassira ta je d’akinta idan kika ga yadda ta yi wallahi za ki sha mamaki, Yasira tana fad’a atake itama take mayar mata k’arshema toilet ta shige ta banko mana k’ofa. Kwata-Kwata bata shakkar uban kowa a cikin mu amma dukda haka kuna gani kun yi shiru sannan da ance za a gyara mata zama sai ku hana….yanzu kalli abunda saken da kukayi ya janyo’’. A hankali Mommy wadda zuwa yanzu tama daina gani sosai tsabar b’acin rai ta ce ’’Ya’isha so kuke ku kasheni? Aka ce ku bari tukunna yanzu a fara sanin abun yi in ba hakaba wallahi zan tura ku d’akinku kamar Yusra da Yadira tunda kuma Yaran ne… Ku tsaye ga matsalar da ya kamata ayi magana akai nan amman kun tsaya kuna shirme?’’ Mommy ta k’arashe maganar tata cikin d’an d’aga murya da tsananin b’acin rai. Komawa Yasmeen ta yi ta zauna, haka itama Ya’isha, ammafa dukda haka a kumbure suke kamar za su fashe.. Shiruu d’akin ya d’auka kowa ya shiga tunani…. ‘To kenan Daddy shima ya sani amma ya b’oye mata ko dai ya abun yake ne???’ Mommy ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba, a take wata zuciyar ta ce mata “da wuya idan ya sani, kuma ko da ace bai sani d’in ba ma ta san wuyarta Yashjub ya ce masa yana son aure! Ko a cikin sati d’aya ne ba abunda ya shafesa tsaf zai d’aurawa Yash aure, in dai har Hajiya Maama ta amince kuma an yi bincike’’… Sabodahaka ta san yanzu Baaba Larai ce kad’ai za ta iya taimakon su, dan haka ta d’ago da niyyar yi mata magana kenan Idanuwanta suka sauk’a a kan Kausar wadda ta turo k’ofar d’akin a dai dai lokacin ta shigo. Lumshe idanu Mommy ta yi ta bud’e saboda yadda ta ga hawaye shab’e-shab’e a fuskar kausar d’in ta san ta riga ta gama jin komai. A hankali ta d’an matsa kusa da ita da niyyar yi mata magana amma sai Kausar d’in ta yi saurin d’aga mata Hannu alamun ‘stop!’ Kafin kuma ta juya da sauri ta bar wajen…… Da sauri su Ya’isha su ka bita da hanzari, su Mommy suma suka rufa musu baya..duk suka d’unguma side d’in Kausar inda suka ga ta shige. Suna zuwa suka tarar har ta shige ta turo k’ofar bedroom d’inta dan haka suka tura suma, cikin ikon Allah bata rufe ba. Suna shiga suka tarar da ita ta fasa kwalba tana k’ok’arin yanka jijiyan wrist d’in ta(wuyan Hannunta). Da sauri sannan a tsorace suka je suka rirrik’eta Mommy tana cewa ‘’Haba Kausar, ba fa auren aka ce miki an riga an d’aura ba’’ Inaa! ko jin ta Kausar bata yi ba, in banda kuka da hauka ba abunda take musu.. Dan haka Mommy ta juyo da ita ta wanka mata wani kalar gigitaccen mari. Wani sabon kukan Kausar ta sake fashewa da shi kafin ta fad’a jikin Mommy ta rungume ta tana kuka sosai kamar za ta shid’e ta shiga cewa ‘’Mommy kawai ki barni in mutu, all my life I’ve been unlucky (ni duk tsawon rayuwar da na yi ba ni da sa’a) Ammina ta rasu! Mahaifina bana jin ma ya san da ni!Daddy shima ya tsaneni! Sannan tare muka fara karatu da su Yassira su duk har sun gama sun kama aiki amman ni har yanzu Ina project!… Dan Allah ku bar ni in mutu, Idan na zauna Yash ya rayu da wata a matsayin Mata mutuwa zan yi Mommy, gara kawai in mutu….” A hankali Mommy ta rungumota itama zuwa jikinta sannan ta ce’’Na yi miki alk’awari, Yashjub ba zai auri kowa ba sai ke.” Cikin katseta ta ce ‘’Mommy haka kike cewa kullum, gashi yanzu har yayi budurwa yana shirin aurenta bama mu sani ba’’ A hankali Mommy ta saka Hannuwanta ta d’ago da fuskarKausar ta yi cupping a cikin tafin hannuwan nata kafin ta ce mata ‘’kin yarda da ni???’’ tayi mata tambayar tana kallonta A hankali kausar wadda duk ta miƙa wuya ta jin jina mata kai alamun’yes’ Idanuwanta shab’e-shab’e da hawaye, har ga Allah ta karaya da yadda ta ji maganar ta taho gadan gadan dan ta san tunda akace nan da wata ɗaya to hatta su Hajiya mama sun sani kuma sun amince, ta riga ta san duk bala’i ba’a isa a chanjawa hajiya mama ra’ayi ba, shiyasa kawai ta zab’i ta mutu amma wannan alƙawarin da mommy ta yi mata ya sanya ta ɗan ga alamun haske dan haka ta zaɓi saka rai da dacewa sannan ta zaɓi ta yarda da mommyn ɗari bisa ɗari ko bayaga hakan ma yarda da mommyn dama shine zaɓinta mafi sauƙi wanda ta ke so ɗin, dan akan ta mutu ta barwa wata yash ɗinta gara a fafata su yi nasara ta hanyar raba shi da Yaroinyar, in sha Allah. Dan haka ta sake cin ɗamara, bayan ta ɗaura gaba ɗaya yardarta akan abinda mommy ta faɗa mata ɗari bisa ɗari ta kuma aminta da momnyn za ta cika mata burinta. Sai da Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ci gaba da cewa “ki kwantar da hankalinki, babu wadda ta Isa ta shigo cikin gidan nan a matsayin matarsa, ki zuba ido ki ga ikon Allah’’ Ya’isha ce ta ce ‘’Mommy me za a iya yi a cikin sati uku zuwa wata d’aya? Wataƙila ma fa an riga an kai komai.” “Ba dai ni nace muku ku zubamin ido ba?….dan haka bana so in sake jin wata magana game da batun auren Yash a cikin gidan nan’’ Sai da ta sake sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce ’’zan ga ta yadda zai yi auren, zanga ta yadda zai aureta.’’ A hankali ta kamo fuskar Kausar ta ce ’’alfarma d’aya nake so daga gareki…’ki kwantar da hankalinki!’. Ki cire komai aranki, kar ki damu in dai kinada ‘Ni’ na dad’e da yi miki alk’awarin ba za ki yi kuka ba………..” •••••• Washegari da sassafe Manubiya ta tashi, ta shirya tsaf, dan tun a jiyan Ya Musbah yace mata “ta shirya da wuri, za su je su dawo saboda Ya Nafi’u yana da interview by ten‘’ shiyasa take ta sauri ta shirya ɗin, sai dai bata ko fara karyawa ba sai gashi sun shigo shi da mai sunan Baba. Bayan an gama gaggaisawa ne Manubiya ta sanar dasu yadda sukayi da Yash d’in jiya da kuma yadda ya ce yau Likutar za ta zo ta duba Inna. Shiruu Baba ya yi da jin bayanin nata kafin chan ya nisa ya ce ’’Manubiya daga wannan, kar ki sake gaya masa wata damuwar ki. Ɗawainiyar tayi yawa haka’’ A hankali ta sunkuyar da kanta tace ‘’to Baba,’’ saboda dama ta san za’a rina, har ga Allah ita ta ma yi tunanin zai yi mata fad’a idan ya ji. Shiruu kawai Baba ya yi, yana wani lissafin na daban. Kafin ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, tukunna ya mik’e da kyar dan ciwo Ƙafar takeyi masa..inda aka ciccire masa faratun duk sun kumbura sun sake taso masa sannan sun assasa ciwon k’afar nasa wanda dama yake ta fama da shi, dauriya ce kawai yakeyi tun kwanakin baya amma yanzu abun yana cin ƙarfinsa dan azaba yake sha sosai!! Hatta faratun hannunsa waenda aka cire suma duk ciwo su ke yi masa. Ahankali ya d’ingisa ya nufi toilet domin ya watsa ruwa, dan tun d’azu Manubiya ta kai masa ruwan wanka. Yana shiga Jidda ta shigo musu da breakfast, dan haka suka zauna su uku suna ci har da mai sunan Baba wanda Ya Musbah yaketa tsokanar sa yana ce masa acici dan sai da suka ci wainar gero tukunna suka fito. Inna ma tun ɗazu an bata nata abun karin, an shirya ta. Ganin sun kusan kammalawa ne ya sanya Ya Musbah mik’ewa ya fita domin ya dubo ko Nafi’u ya zo, in kuma bai ƙaraso ba sai ya kira sa. Sai da Muhsin ya mik’e ya fita tukunna Jidda ta kalli Manu ta ce “na d’auka Muhsin zai yi fushi ko kuka da aka ce an fasa kaishi makaranta, ashe ya girma yayi hankali yanzu’’ Murmushi Manu ta yi kafin ta ce ‘’Ya ban tausayi, Allah ubangiji ya bamu ikon sanya shi a makarantar’’ ‘’Ameen’’ jidda ta ce, daganan ta zare hannunta a abincin ta d’an matsa kusa da Manubiya sosai sannan ta ce ’’yanzu ya za’ayi? Za ki siya masa ne a hanya tukunna ku wuce office d’in nasa? Dan gaskiya bai kamata ku had’u ba tare da kin bashi ɗan gift ba’’ ‘’Babu gift d’in da zan bashi’’ Manu ta fad’a hakan ba tare da ta kalleta ba. Da sauri Jiddah ta d’an zabura sai kuma ta ce ’’amma wasa kikeyi ko?’’ Sai a sannan Manu ta d’ago kyawawan idanuwanta ta kalleta tukunna ta ce ‘’Da gaske nakeyi, ya riga ya fara rok’on tukuici da kanshi, kinga kuwa ai ya yi wa kansa’’ Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ‘’kamar yaya?’’ ……yadda su ka yi da shi jiya akan batun tukuici Manu ta kwashe tsaf ta gayawa jidda… Kafin ta d’aura da cewa ’’tun d’azu nake ta faman fargaba, ban san me zai ce yana so ba, na riga na yarda da shi akan ba zai cutar da ni ba, amma dukda kawai ni I’m so nervous( ina cike da fargaba)” Ta k’arashe maganar tata tana mai mayar da idanunta kan jellof d’in taliyar da ke a gaban su. Shiruuu Jidda ta yi, ta zuba mata idanu, har sai da Manubiyan ta gaji dan kanta ta d’ago ta kalleta Tukunna Jidda ta yi murmushi kanta tsaye ta ce ’’kema kina son shi ko??’’ Wata mahaukaciyar zabura Manu ta yi a lokaci guda ta yi amfani da d’ayan Hannunta na hagu ta toshema Jidda Baki, ta fara rarraba ido a cikin d’akin. Dai-dai nan Baba ya fito daga toilet d’in sanye da kayan da ya chanja a ciki wanda ya cire kuma riƙe a hannunshi tare da brush da vaseline d’in shi. Kallonsu ya yi kafin ya ce ’’d’azu Kaka Mallan ya kira akan yana buk’atar ganin mu ni da su Uncle da gaggawa. idan Likitar ta zo ku yi komai in kunga ban dawo ba sai ku wuce kawai ba sai kun jira ni ba’’ Daga haka ya ajjiye kayan wankin a wajen da suke tarawa ya ajjiye brush da Vaseline d’in suma a wajensu sannan ya wuce yana mai cewa “idan na dawo na ci nawa abincin’’.. Yana fita Jidda ta ce ’’Adda Manu yanzu y….’’ Cikin katseta Manubiya ta ce ’’Jidda dan Allah kar ki yi min haka, kar ki ƙarasa rikitani’’ Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ‘’ki tsaya tou mana ki ji abunda zan fad’a ma’’ Kamar Manubiya za ta fashe da kuka ta ce ’’Plss Jidda….’’ Daganan ta mik’e ta fad’a toilet ta wanke Hannu tare da kuskure Bakinta sannan ta d’auro alwallah ta fito. Fitowarta ke da wuya, wayarta ta d’auki k’ara… Tana dubawa ta ga Yash ne me kiran. Batayi mamaki ba, dan itama tunanin sa take yi dan haka ta d’auka a hankali ta kara a kunnenta…. …bayan kashe mata jiki da doguwar gaisuwa, ya ce mata ’’Dr Sofia fa tana waje, ta zo tun ɗazu’’ Da “to” ta amsa masa, tukunna suka yi sllama daga haka ta nufi k’ofa da niyyar fita ta je ta shigo da ita amman sai suka yi karo da ya Musbah da ya Nafi’u dan haka ta gaya musu ita kuma ta koma ciki. Su ne suka je suka shigo da baturiyar likitar mai suna Sofia matar mai kirki sosai da bagwariyar Hausar ta… Sama da awa d’aya ta d’auka tana examining (gwadawa da bincika ) innar kafin ta ce ’’su wuce asibitin ta’’ A inda ta gaya musu asibitin nata yake ya baud’e sosai da office d’in Yashjub! Gashi sun riga sun ce masa za su zo, kuma shi kansa Ya Nafi’u ya kamata ace yana wajen interview ɗinsa ma yanzu haka…shiyasa suka yanke akan ‘Ya Nafi’u ya tafi interview d’inshi, Manubiya ta je ta yi wa Yashjub godiya a madadin dukkansu sannan ta gaya masa dalilin da ya sanya ba su zo su duka ba. Ya Musbah shi kuma ya tafi asibiti tare da Inna. *MANNUBIYA* *45* A inda ta gaya musu asibitin nata yake ya baud’e sosai da office d’in Yashjub! Gashi sun riga sun ce masa za su zo, kuma shi kansa Ya Nafi’u ya kamata ace yana wajen interview ɗinsa ma yanzu haka…shiyasa suka yanke akan ‘Ya Nafi’u ya tafi interview d’inshi, Manubiya ta je ta yi wa Yashjub godiya a madadin dukkansu sannan ta gaya masa dalilin da ya sanya ba su zo su duka ba. Ya Musbah shi kuma ya tafi asibiti tare da Inna. Babu kalar lallamin da Manubiya ba ta yi wa Jidda akan ‘ta zo su je tare’ ba, amma k’iri-k’iri Jidda ta ce mata ‘’A’a!, idan na bi ki wa zai kula da su mai sunan baba da Muhsin?’’ Da sauri Manubiya ta ce ‘’To duk ku zo mu tafi tare’’ Cikin tarar numfashinta Jidda ta ce ‘’kuma in Baba ya dawo sai ya ga ba kowa?’’ Haka suka yi ta fama, dan duk ta inda ta b’ullo sai Jidda ta toshe. Ya Musbah ma bayan Jidda ya bi ya ce ’’ko baya ga hakama ta ya an cewa Yashjub d’in za su zo su uku yanzu kuma kawai yaga Yara. Kawai ta je d’in in yaso ta ce masa inshaaAllah shima shi da Ya Nafi’u suna nan zuwa’’. Hakanan Manubiya ta fita ko sallama bata yi wa Jidda ba, Jiddan tanata tsokanarta k’asa-k’asa da ‘‘Oga wife’’ Ita dai Manubiya bata kulata ba, ta barta kawai akan sai ta dawo sai su yi ta. Har ta Isa company d’in kuwa tana fargaba! bata san tukuicin da zai ce yana so ba sannan ga matsayar da Jidda ta riga ta gama cimmawa, da kuma abunda ita kanta zuciyarta take raya mata shiyasa gaba d’ayanta ta bi ta sake diriricewa. Yau tana zuwa receptionist d’in ya ce mata ‘’an ce in ta zo kawai ta wuce office d’in ceo, ba sai an rakata ba’’ ‘’Okay’’ kawai ta ce, daga nan ta nufi office d’in nashi dake a chan sama kai tsaye. A bakin glass door d’in ta tsaya ta d’an yi knocking glass d’inc tukunna ta tura ta shiga da sallama. A zaune ta sameshi ya k’urawa k’ofar ido…fuskarsa tamau kamar bai tab’a dariya ba, dan har sai da ya d’an bata tsoro amman kawai sai ta dake ta k’arasa ta nemi waje ta zauna, a hankali ta ce ’’ina kwana’’. Tunda yake a rayuwar sa bai tab’a ganinta da mayafi ba sai yau, mayafin ma kuma mai shara shara….sanye take da doguwar riga d’inkin Ashape, atamfar army green da d’an kwalliyar milk da black, rigar bata wani kamata ba amma yanayin jikinta da kuma mayafin da ta rufa (black clour)wanda bata saba sakawa ba ne ya taimaka wajen fito da surar Jikin nata, mayafin nata babba ne sai dai ya d’an yi shara-shara.Ta yi normal d’aurin d’ankwalinta ta gaba ta baya kuma ta nannad’e sa akan ribbon d’inta wanda ta tufke uban tulin gashinta da shi, sannan ta d’aura mayafin nata akai. Kwalli, powder sai man leb’e ne kawai a fuskarta amman ba k’aramin kyau ta yi ba, dan har wani fisfisga Yash ya ji numfashinsa yanayi…. ‘‘Yanzu duk inda ta bi ta wuce tun daga gidansu har nan haka Maza suka ganta kuma suma haka suka dinga ji kenan? bata tab’a saka mayafi ba sai yanzu da ya ke jin masifaffen kishin ta’’ Yashjub ya aiyyana hakan a cikin ransa. A b’angaren Manubiya kuwa ita kanta tun d’azu a takure take dan ba wani sabawa ta yi da mayafin ba, ta yi kuskure ta bar hijabanta duk sun yi datti, kuma bata samu sun yi wanki da wuri wannan satin ita da Jidda ba, sannan ga abunda ya zo ya faru gaba d’aya ya d’auke musu hankali shiyasa basu nutsu ba ma ballantana ayi maganar yin wanki. A hankali ta d’an kalleshi ta ga still ita yake kallo, dan haka ta sake yin k’asa da kanta ta ce ’’ina kwana’’ Kamar wani mai jin bacci haka ya lumshe lumsassun idanuwansa ya had’iye wani k’ululun abunda ya tokare masa mak’oshinsa yake shirin hanasa numfashi tukunna ya ce ‘’Me ya faru da hijaban ki yau?’’ Yayi mata tambayar yana mai matsar da computer dake a gabanshi gefe wanda hakan ya bashi damar sakata a gaba ya tsura mata ido sosai. Gaba d’aya diriricewa Manubiya ta yi, sam ta kasa magana dan haka kawai sai ta sake yin k’asa da kanta… Zuwa yanzu ta fahimci wataƙila mayafin da ta rufo ne ya b’ata masa rai shiyasa duk sai ta ji ba dad’i, dan sam bataso ta zamto silar b’acin ransa ta ko wacce siga. Ga kuma tunanin ta na ‘maybe kishina yakeyi’ gaba d’aya sai ya sake kashe mata jiki. Yanayin yadda ta yi ‘k’asa da kai ta yi shiru’ ne ya sanya yayi tunanin ‘maybe ranta ya d’an b’aci’ne, ga kuma yadda ya tamke fuska ko maraba bai yi mata ba wanda shi kanshi sai yanzun ya lura da hakan, shiyasa tashi d’aya shima duk sai ya ji ba dad’i dan haka ya sauk’e wata y’ar siririyar ajiyar zuciya kafin ahankali ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna yace’’Sorry!(yi haƙuri)” kawai. Duk shiruu sukayi kafin ya sake cewa ‘’Ya jikin Baba??’’ Ba tare da ta d’ago fuskarta ba sannan a hankali ta ce “Alhamdulillah’’ Murmushi ya yi kafin ya ce ‘’Fushi kikayi?’’ Girgiza kai ta yi da farko sai kuma bata san ya akayi ba amman kawai sai ta tsinci kanta da ce masa ‘’’(yi haƙuri)!’’ itama. Murmushi mai sauti ya yi kafin yad’an had’e rai tukunna ya ce ‘’Kar ki damu next time idan kika sake saka wannan abun, ni kad’ai na san me zan yi miki’’ Ya k’arashe maganar yana dariya ahankali ahankali. Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba itama kafin a hankali ta fara magana “Sofia ta zo, tun a yau kawai har ta k’ara mana haske akan yadda za mu dinga yi wa Inna, na ji tace kullum itama za ta dinga zuwa ko?’’ ‘’Um’’ kawai yace Idanunsa akanta. A hankali ta ci gaba da cewa “ban samu na yi maka godiya yadda ya kamata ba, da tare za mu taho da su Ya Musbah tou kuma dole sai da shi tukunna za’a kai Inna asibiti, shiyasa ya ce in baka hak’uri in ce suma suna nan zuwa kuma mun gode sosai Baba!Jidda!da Muhsin suma duk sun ce ayi maka godiya… Allah ya saka maka da alkhairi’’. Murmushi ya yi kafin ya ce ’’Allah ya k’arawa su Inna lafiya, bana buk’atar godiya daga gareki ko Ahalinki.. Dan Allah ki cewa su Musbah suma ba sai sun zo ba…’’ A hankali ta ce ’’a ganina ya zama dole mu yi maka godiya’’ Jin ya yi shiru yanata kallonta ne kawai ya sanya ta ce ’’once again mun gode, Allah ya biyaka.” Kamar wadda ba zata yi magana ba sai kuma ta ce ’’zan tafi’’ ta fad’i hakan tana mai sunkuyar da kanta k’asa sosai. So takeyi kawai ta tafi tunda ta gama abunda ya kawota, maganar aikin da ya ce akwai yau dama ta san kawai jan magana ne. A hankali ya sauk’e nannauyar ajiyar zuciya sai kuma ya sunkuyar da kanshi yana murmushi kafin ya d’ago ya ce ’’nima, a ganina ya zame min dole in bawa abunda nake tsananin k’auna kariya.’’ ‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’ Haka Manubiya wadda ta runtse idanuwanta tashi d’aya ta shiga nanatawa a cikin zuciyarta, tana mai jin wani kalar fad’uwar gaban da bata tab’a ji ba tunda take a rayuwarta. A take gaba d’aya ilahirin Jikinta yayi wani irin sanyi, kamar babu jini ko rai a k’afafuwanta haka ta ji.. dan tabbas inda ace za a tsikara mata allura a wajen tou da ba lalle ta ji ba!… A haƙiƙanin gaskiya ba ma ta jin dukkannin ilahirin Jikinta saboda tsabar yadda ta ɗauke lokaci guda koina ya yi mata sanyi. Dakyar ta samu ta fara dawowa dai-dai ta d’an fara jin jinin jikinta yana kai mata a jikin nata, sai kuma ta d’an fara kyarma ahankali ahankali. Ganin yadda ta runtse idanunta ta k’ame a waje d’aya ne ya sanya Yashjub ya furzar da wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya tashi ya koma inda take ya zauna a kujerar da ke a gefenta. Kamar jiya yau ma yadda ya ga ta zabura sai da ta kusan bashi dariya…Kamar zata fashe da kuka haka ta juyo ba tare da ta yarda sun had’a ido ba ta ce ’’Dan Allah ka daina, banaso.’’ ‘’Bakya so in ce miki Ina sonki? K’arya kike so in yi miki? Ko so kikeyi in ci gaba da azabtar da zuciyata ta hanyar hanata muradin ta??’’ Ya ce da ita yana kallonta. Mik’ewa Manubiya ta yi da wani kalar sauri, ta juya za ta fita amma kafin ma ta yi taku d’aya kawai sai ta ji ya damk’o Hannunta!. Da sauri ta juyo sai dai kafin ma ta ce wani abun tuni ta ji hawaye sun b’alle mata. A hankali Yashjub ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna a hankali ya mik’e tsayen shima still yana rik’e da Hannun nata wanda ya ke jinsa kamar kar ya cika kamar ya rik’e har abada kar ya barta ta je ko ina, ga wani musulmin taushi da d’umi da Hannun nata ya ke ƙunshe da! Wanda atake suka taru suka d’imauta sa. Da kyar ya iya cewa “ki yi hak’uri Mannubiya in abunda na gaya miki ya b’ata miki rai ne ki yi hak’uri, Dan Allah. Ba na son ganin hawayenki, ba ki san yadda nake ji a cikin raina ba, pls ki daina kukan nan….burina in sanya ki farin ciki in kula dake a ko da yaushe, ba zan so in zamto silar zubar hawayenki ba, kar ki sa in kasa yafewa kaina pls. A ganina ba laifi bane idan na gaya miki sirrin zuciyata shiyasa tun jiya nace miki alfarma da kuma tukuici, saboda na san dama ba lalle kema kina jin abunda nake ji ba, amma in har kikayi min wannan alfarmar kika bani wannan damar kika amince da ni kika bani damar kasancewa tare da ke har abada Mannubiya kin gama min komai. Tun ba yau ba a matse nake, inaso in faiyyace miki sirrin raina, inaso kuma in ji naki, Inaso in ji abunda yake cikin zuciyarki kema gameda ni, amman tabbas a yanzu ina jin tsoro sani saboda hawayen nan naki da na gani ba alama ne mai kyau ba!.. Dan haka in har kin san amsar da za ki bani ‘No’ zata kasance, to na rok’e ki da girman Allah kar ma ki ce min komai, ki je ki sake tunani kawai dan tabbas na san zan iya rasa raina idan kika ce mini A’A …..’’. Bata ce dashi komai ba, bata ma da niyyar cewa komai, kukanta kawai take yi tana d’an k’ok’arin kwace Hannunta daga cikin nasa. A hankali ya lumshe idanunsa yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya bud’e ya d’an sunkuyar da kanshi k’asa..ba abunda ya tsana a ynzu irin kukan nan da takeyi, sam ko da wasa baya son ganin hawayenta…Shiyasa ya bud’e idanunsa ya d’an runtse hannunta da ke a cikin nashi sannan a hankali ya sake matsowa kusa da ita, ya d’aga d’ayan Hannunsa wanda ba ya riƙe da komai, ya kai dai-dai setin fuskarta. Tabbas ta fahimci so yake ya goge mata hawaye, dan haka cikin kuka wanda yake d’auke da b’acin rai ta ce “iyakar Hannuna da ka rik’e bai ishe ka ba??’’ ‘’Oh no (Wayyo)” Yashjub ya fad’i hakan a fili, dan shi wallahi sai yanzu ya fahimta ya kuma fara ganewa… Shi fa Indai yana gabanta to mantawa yake yi da kowa da kuma komai. Har ga Allah bai san lokacin da ya damk’i Hannun nata ba da farkon da kuma ya rik’e d’in sam sai ya gagara saki. “Damn it!” Ya fad’a a chan kasan ranshi yana jin takaicin kanshi, dan tabbas ya san ya kwasa. Da ikon Allah kuma gashi har zuwa wannan lokacin ya gagara sakar mata Hannun nata yana nan riƙe da shi gam. Da k’arfi Yassira ta daki glass d’in k’ofar wanda hakan yake nuni da alamun knocking… A tare gaba d’ayan su suka d’aga Kai suna kallon k’ofar shigowar. Sun yi mamakin ganin Kausar da Yassira a tsaye a cikin office d’in, dan basu san lokacin da suka k’araso ba ballantana su san lokacin da har suka shigo. Da sauri Manubiya ta juya, ta goge hawayenta, daganana bata sake yarda ta juyo ba. Cika mata Hannu Yashjub ya yi, sannan ya janye d’ayan Hannunshi wanda ya d’aga da niyyar goge mata hawaye, tukunna ya d’an matsa kusa da su ya kalli Yassira, fuskarshi ba yabo ba fallasa Yace ‘‘Lafiya dai ko?’’ Da kyar Yassira ta samu ta iya cewa ‘’eh!lafiya, mun zo wajenka ne, sai dai na ga kamar kana busy….” ‘’Eh kam, very busy” Ya bata amsar kanshi tsaye, kafin ya ce ‘’Ki jira in mun had’u a gida sai mu yi’’ Ya k’arashe maganar tasa cikin takaici, dan sam bai so su ka ga Manubiya yanzu ba. Daga haka ya fara k’ok’arin juyawa ya ji ta ce ‘’Akan Mommy ne fa. Ba zai yiu mu yi a cikin gidan ba dama shiyasa muka biyo ka nan’’ Wannan karon had’e fuska Yashjub yayi tamau kafin yace “Yassira, i’m busy, ki jrani ko ma menene, idan na dawo gida sai in ji ko?!.Thankyou’’ Shiruu Yasirar ta yi kafin daga baya ta d’an k’ak’alo murmushi, a hankali ta ce ‘‘Okay Yash’’ Jinjina Kai yayi, still fuskarshi a had’e ya ce ‘’sai anjima’’ har ga Allah Allah Allah kawai yakeyi su yi su fita, saboda gaba d’ayanta Kausar! Da ita da shigarta! Da kwalliyarta! Duk juya mishi kai kawai takeyi. Sai da Yassira ta sake kallon Manubiya wadda ta juya baya tun shigowarsu tukunna ta kamo Hannun Kausar wadda itama tunda suka shigo ta yi ido biyu da Manubiya ta sunkuyar da kanta k’asa ta k’i cewa komai. Ahankali Yasira ta ce mata ‘’mu je!’’ Ganin da ta yi kamar ma Kausar d’in bata jin abunda take ce mata ne ya sanya kawai ta ja Hannunta suka fice daga office d’in . Suna fita Yash ya zagaya ya d’auki wayarshi ya turawa Yassira massage …’idan kika sake zuwarmin da ita office ɗina, I’m going to humiliate the two of you like hell…. (Sai na haɗa da ke da itan na yi muku wulaƙancin da ba za ku taɓa mantawa ba)…..’ *MANNUBIYA* *46* Yana gama turawa Yassira message ya ga Manubiya ta sak’ala jakarta, tana shirin juyawa ta tafi. Dan haka ya k’arasa da sauri ya tare gabanta. Kasa magana ta yi shiyasa kawai sai ta kawar da kanta gefe. Cikin sanyin murya ya ce ‘’nima ban shiryama hakan ba…ki yi hak’uri, ba zan sake rik’e miki Hannu ba, yanzun ma mistake ne..let’s start a fresh (yanzu, mu sake farowa daga farko) InshaaAllah ba zan sake ba.’’ Ya fad’i hakan yana kallonta, shi a karon kanshi yana mamakin yanda ya koma, dan sam bayar da hak’uri baya daga cikin tsarinshi, bai ma iya ba! Amma a iya yau a iya shigowarta cikin office d’insa kawo yanzu ya bata hak’uri ya fi a k’irga. …….’’sam ba su yi kama da d’ayar ba dan tama fi kama da y’an china. Har gara ma d’ayar ita sun d’an yi kama wataƙila ko cousin d’inshi ce, to ita kuma d’ayar fa wacece? Dan sarai ta lura da yadda idanuwanta suka cicciko lokacin da suka had’a ido, wacece ita? Su waye su? Sannan wacece Mommy!? Dan ta tabbatar inda ace wadda aka ambata da Mommy Mahaifiyar sa ce to da ba zai k’i tsayawa ya saurari abunda suka zo takanas fad’a masa akanta ba”…. Manubiya ta aiyyana hakan a cikin ranta. Tunanin ta ne ya katse jin ya ce ‘’Mannubiya’’ A hankali Ajiyar zuciya ta sauk’e tukunna ta d’ago ta d’an kalleshi. Kalar tausayi ya yi mata kafin ya ce ‘‘Plsss’’ Ya fad’i hakan yana k’ok’arin durk’usawa a wajen Ita kanta ba ta san lokacin da ta ce “a’a dan Allah kar ka sunkuya’’ Ba tare da ya damu ba ya ce ’’ai ba ki ce ya wuce ba’’ Ya fad’i hakan yana me durk’usawa a gabanta. Gaba d’aya kunya da takaicin kanta ne suka lullub’e ta, bata san lokacin da ta ce ’’ya wuce! nima sai yanzu na lura baka ma sani ba, dan Allah ka tashi’’ Murmushi ya yi kafin ya mik’e a hankali yana kallonta sannan ya ce ’’ashe dai ana so na!’’ Da sauri ta runtse idanunta a ranta ta ce ‘’Tabbas Ina sonka Yashjub!’’ Dariya ya yi kafin ya ce ’’dole ki runtse ido mana’’ A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa ta yi shiruuu, kafin chan ta ce ’’wacece Mommy?’’ Murmushi ya yi kawai… a hankali yake kallon fuskarta yana karantarta, yana jin wani sanyi yana ratsashi…. Sai da ta sake cewa ‘’um?’’ Tukunna ya ce ‘’Sisters d’ina ne dukkan su, Mommy kuma is my mom(mamana ce).” Bai bata damar cewa komai ba Ya ce “mu bar wannan maganar, yanzu mu yi maganar da ta shafe mu’’ Ahankali ya ji ta ce ‘’Kuma ita ta haife ka?’’ Lumshe idanunsa ya yi ya bud’e tukunna ya ce ’’ki bar maganar mana, um??’’ Girgiza kanta kawai ta yi kafin ta ce ’’kawai na ga yadda ka yi ne kamar baka wani damu ba Wanda hakan sam bai dace ba!. Na san bai kamata in shiga cikin abubuwanka na kashin kai ba amman uwa ta fi k’arfin wasa.. Indai har wadda suka kira da Mommy Mahaifiyarka ce to a gaskiya abunda ka yi bai kamata ba. Ni yanzu haka so nake ace Innata ta turo wani ya bani sak’o ko mu yi magana Baki da Baki ma ni da ita amman ba ni da damar yin hakan. Shawara ce nake baka dukda na san na yi maka shishshigi amman na kasa haƙuri ne tunda naga abun ya shafi Uwa! dan babu abunda yake ɓata mini rai kamar inga ana d’aukar Mahaifiya ba da muhimmanci ba Dan haka dan Allah idan zai yiu ka yi k’ok’ari ka gyara hakan, Once again ka yi hak’uri idan na zarce iyakata.’’ Shiruuu kawai ya yi yana sauraron ta, tunda ta fara har ta dasa aya. Jin ya yi shiru yasa ta d’an d’ago ta kalleshi…ganin kawai ita ya ke kallo ne yasa ta d’an kauda idanunta daga garesa a hankali. A lokaci d’aya ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce ‘’Thankyou! inshaaAllah na yi miki alk’awarin zan gyara. Kawai dama mun d’an samu rashin fahimta ne amman inshaaAllah komai ya wuce daga yau! Na yi miki alƙawari. Sannan Kar ki sake cewa kin zarce iyakar ki a cikin rayuwata ko hurumi na kashin kai na saboda Mannubiya kece rayuwar tawa ba ki da iyaka a komai nawa duk abunda ya shafe ni to ya shafe ki…. Inaso ki yi kutse, ki shiga, ki yi duk yadda kika ga dama, dan tabbas in kikayi hakan zai sanyani farin ciki. A yanzu amincewarki gare ni kawai nake jira, daganan idan mun zama d’aya komai nawa ya zama naki. Na dad’e da gama tsarawa ‘matata ita ce ni nine ita.’ Kawai ina fatan za ki bani damar da zan nuna miki how much I love you (yadda na ke son ki)…….’’ Manubiya ji take yi kamar ta ce mishi “eh, itama tana son shi. amman kuma tana buk’atar shawara da su Jidda kafin ta ce komai, dan ita kanta ta san kuma tana gani kamar Yash ya fi k’arfinta amma dukda hakan tana buk’atar shawara da wani nata wanda zai bata izinin ta kulashin saboda itama a karon kanta abunda take so d’in kenan. Abu na biyu kuma ko da ace zata ce masa tana son shi har ga Allah ba za ta iya kallon cikin idanunshi ayanzu dai ta fad’a mishi ba, dan wata tsananin kunya kwarjini da girmansa take ji take kuma gani. Abu na uku kuma abunda yayi mata yanzu ta ji zafi dukda kuwa ya bata hak’uri kuma ita kanta ta lura dagaske bai sani d’in ba amman tanaso ta sake jaddada mishi sannan su fahimci juna sosai akan ‘Ko bakin hijabinta bata yarda ya sake tab’awa ba’….’’ Dan haka kawai sai tace masa ‘’once again (Har ila yau), mun gode kwarai. bari in wuce gida’’ Murmushi kawai ya yi kafin ya ce ‘‘Okay ranki ya daɗe! duk yadda kika ce hakan za a yi. In kai ki? Ko in saka a maidake?’’ Yayi mata tambayar yana mai tsare ta da idanuwa. A hankali ta girgiza Kai kafin ta ce ’’na gode’’ daga haka ta juya ta wuce Numfashi ya fesar sannan yace ‘’Ina jiran amsata’’ Tsayawa ta yi i ta kasa gaba ta kuma kasa juyowa Bata san lokacin da ya matso kusa da ita ba sai da ta ji maganarsa a setin kunnenta A hankali yana cewa ‘’pls dear, don’t keep me waiting‘’ Da sauri ta yi gaba ta fice daga office d’in tana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya…… Shima ajiyar zuciyar ya sauk’e sannan ya fesar da iska yana wani sihirtaccen murmushi kafin ya koma ya zauna a fili ya ce ‘’Alhamdulillah’’ Kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya mik’e, ya bi bayanta da sauri….. Sai da ya nemi adaidata sahun da ta kwanta masa ya sakata tukunna hankalinsa ya kwanta…haka nan suka rabu kamar basa so bayan ya ce mata ‘akwai ƴar uwarsa ta musamman da zata kirata, mai suna Yahanasu.’ Sai da suka k’ule ya daina ganinsu tukunna ya juya ya koma builɗing d’in, har ya isa shi kad’ai sai faman murmushi yake ta yi.. Ba drivers ba hatta securities na company d’in nashi sun sha mamaki yau, dan haka sukayi ta y’an ƙus-ƙus d’in su a tsakani shi kam Yashjub bai ma san sunayi ba. Sai da suka yi nisa da company d’in tukunna Manubiya ta samu ta shak’a sanann ta fesar da wani bahagon numfashi, dan tun d’azu ji takeyi kamar an shak’e ta, gaba d’aya kunya!k’auna!shauk’i!da asalin mamakin Yash sun hanata sukuni… Yashjub yana zama a office, aikin Yassir wanda ya saka a gaba ya d’an tab’a, kafin daga baya ya fad’a duniyar tunani…. Ya kuwa dad’e yana lissafe-lissafenshi kafin ya mik’e ya fice daga company d’in gaba d’aya dan dama saboda Mannubiya ne ya zo yau….. A b’angaren su Kausar kuwa, suna fita ta samu gaban company d’in chan da d’an nisa ta yi parking. Kallonta kawai Yassira ta ke yi tana mai jin wani tsananin tausayinta ya na sake lullubeta a lokaci guda kuma tana da na sanin gaiyyatar ta ɗin da ta yi akan su zo nan ɗin, dan inda ace ta san za su yi wannan mugun ganin to da ita kaɗai za ta zo abinta, su tattauna ita da Yash d’in akan Mommy su magance matsalar iyaka su biyu’ kawai! Dan ba zai yiu ace ta zuba ido tana gani yana gaba da uwar su ba’. Ta lura da yadda Kausar d’in ta ci uban kwalliyar da ita kanta ta ma manta rabon da ta ga ta yi kwatan kwacin irinta, gashi ta zo amma ko kallonta Yash d’in ma bai yi ba, gashi kuma sun yi mugun gani….. Yassira tana cikin wannan tunanin ta ga Kausar d’in ta zaro wayarta. Wani cleaner wanda su ke shiri kuma suka shirya akan zai ke fad’a mata shige da ficen Yash ɗin! Ta kira. Yana zuwa ya fara sosa k’eya, bayan sun gaisa kuma yayi shiru, ya sunkuyar da kanshi k’asa dan tun a ranar da yaga Manubiya ta zo an kaita har office d’in Yash ya kamata ace ya kira Kausar ya sanar da ita a yadda suka tsara amman kawai shi baya son wannan harkar ne dan ya zama kamar munafurci da cin dunduniyar Yash kenan Mutumin da wani lokacin in wata ya k’are har k’ari yake yi musu akan salary d’in su….. ‘’Ka san laifin ka kenan’’ Muryar Kausar ta katsewa cleaner d’in tunani Murmushi yayi ya d’an sosa k’eya, ahankali ya ce ‘’Afuwan hajiya! na d’an yi tafiya ne, nima yau na fara ganinta da na tambaya shine aka ce min ai ta d’an kwan biyu’’ Sarai Kausar ta fahimci k’arya ya shirga mata, shiyasa ta ce ‘’Ina da recording d’in wayoyin da muka yi ni da kai, ba zan damu ba dan Yash ya san me nakeyi dan haka idan baka bi min Yarinyar chan ka gano min gidansu ba tou zan kwashe komai in tura masa.’’ Da sauri yace ‘’ki yi hak’uri dan Allah, inshaaAllah zan bi ta, yanzu ma kuwa. Tana fitowa zan bi ta.” ‘’Ka d’auko min number gidan adress d’in ta da sunanta da komai’’ Dasauri yace ‘’To to,angama…’’ Kafin ma ya gama amsawa har ta kunna motar, bata sake bi ta kansa ba ta figi motar suka wuce. Sai a lokacin Yassira wadda tun d’azu ta kumbura sannan al’ajabi ya rufeta ga kuma tausayin Kausar ɗin ta ce ‘’Kausar! me za mu yi da adress d’in ta? Kin dai san duk abunda kika je kikayi mata zata gaya masa ko?? Baya ga haka ma ba ajin mu bace, sannan bai kamata ace mun tsaya muna chachar Baki da wannan Yarinyar wadda bana jin ta kai sa’ar Yusra ma. Kuma idan ya sani ko ya ji labari ina fatan kin san kashinki ya bushe ko? Ki duba ki gani dai yadda duk ya burkice ya rikice yake ta faman rarrashinta saboda kawai ya ga tana hawaye….’’ Mahaukacin burkin da Kausar ta ja wanda sai da Yassirar ta buga kanta kad’an ne ya sanya ta yi shiru, dama Yasira a zuciye take kuma ranta a mugun b’ace yake ‘na ganin Manubiya da ta yi’ dan haka rai a ɓace ta d’ago ta ce ’’Girl! Are you crazy? (Ke! Kin haukace ne?) kallifa ya…’’ Maganar tata ce ta mak’ale sakamokon hawayen da ta gani ya fara zubowa ta cikin Idanun Kausar d’in.. Shiyasa gaba day’a sai tausayinta kuma ya lullub’e Yasirar….tabbas ko da ace itace take da saurayi ya yi budurwa kamar wachchar Yarinyar da suka tarar a office d’in Yashjub to fa ko dai ta hak’ura da shi ko kuma ta bi ta ko wacce hanya ta rabasu, dan ita kanta tunda ta ganta tashi d’aya sai da ta raina kanta ga wani irin kishi da ta ji ya taso mata a take duk ya bi ya lulluɓeta lokaci guda!! To Ina kuma ga Kausar ɗin?! Allah kad’ai ya san me take ji! Bata riga ta samu hankalin Yashjub d’in bama, gashi har wata ta yi wuff da shi, dan a iyakar abunda ta gani a yau kawai tabbas ta san sunada aiki jaaa! A gaban su. ‘’Yassira har mu je gida kar ki sake cewa komai Dan Allah’’ Muryar Kausar ta katsewa Yasirar tunanin. Tana gama fad’in hakan ta ja motar da gudu suka wuce. Suna zuwa gida ba ta ko kalli Yasira ba, ta bud’e motar ta fice ta wuce sama. Kai tsaye fanninta ta nufa, tana tafe Zuciyarta tana wani irin tafarfasa. Tana shiga parlournta ta yi cilli da wayarta da d’an ficicin mayafinta sai kuma ta fara kai kawo….tana safa da marwa a cikin ɗakin, kafin kuma ta fara d’aukar abubuwa tana farfasawa!!! Wanda hakan ya janyo hankalin Mommy, dan haka ta nufo side d’in nata. Tana shiga ta zaro idanu waje, sai kuma ta k’arasa inda Kausar d’in take ta rik’eta cikin tashin hankali ta ce ‘’Lafiyar ki kuwa?’’ ta yi mata tambayar tana mai shafa fuskarta wadda ta yi jajawur idanunta suka sake k’ank’ancewa. Tsabar tashin hankali kasa ma magana ta yi, kuma so take ta yi kuka sosai amma ta kasa dan shima hawayen ya k’afe… Suna tsaye a haka Yasira ta iso, tun daga bakin k’ofar ta fara cewa “Kausar bani takardun nan akwai wanda ya ke jirana a office kins…’’ Maganartace ta mak’ale sakamokon kutso kai da ta yi cikin parlourn. Da sauri ta ce’’Ya subahanallah!’’ sai kuma ta k’arasa inda suke tsaye su duka biyun. Tana zuwa ta rungume Kausar d’in, sannan a hankali cikin son kwantar mata da hankali ta ce ‘’kar ki damu, za mu nemo mafita’’ Da sauri Mommy ma ta shiga rarrashin Kausar d’in dukda kuwa bata san dalilin fashe fashen da ta tarar ta na yi ba da ɓacin ran nata amma dama tunda Yassira ɗazu ta ce mata ‘’za su je office d’in Yash itada Kausar” ta san za a rina…. Suna nan tsaye wayar Kausar ta d’au k’ara…. Dan haka ta janye Jikinta daga na Yassira a hankalia ta koma gefe ta durk’usa ta d’auki wayar tata wadda ta duk farfashe dan tana shigowa dama da ita ta fara yin cilli. Ganin mai kiran nata ne yasa ta d’auka a take, sannan a hankali ta ce ‘’ina jin ka’’ Daga chan d’ayan b’angaren ya ce mata “gani nan yanzunnan aka ajjiyeta a k’ofar gidan nasu ta shiga’’ daganan ya fad’i mata adress da number gidan tukunna ya ce ‘’ban samu sunan yarinyar ba dai amman Ina kan bincike.’’ ‘’Tam’’ kawai Kausar ta iya cewa daga haka ta zare wayar daga kunnenta ta kashe sannan ta shiga cikin contact d’inta…. Zuwa wannan lokacin Yassira ta fahimci da wa ta gama yin waya dan haka ta matsa kusa da ita ta ce mata’’Kausar me za ki yi ne??’’ Dai-dai nan ta kara wayarta a kunne ta ce ’’Hello!na’am…zan turo maka adress d’in wani gida yanzu!Inaso ku je duk wata budurwar da bata kai 25 ba a gidan ku yi resetting d’inta….’’ A zabure Yassira ta wafce wayar ta yi jifa da ita cikin fushi ta ce ’’Eh!lalle kam zuciyarki ta kama da wuta!! kuma ba ki da hankali!” Cikin rashin fahimta sannan a d’an tsorace Mommy ma ta matso ta d’an rik’e Hannun Kausar d’in sannan ta ce ‘’Kausar! Su wa kika bada order a kashe?? Yaushe kika fara harka da y’an daba ba mu sani ba????’’ Ba tare da Yassira ta kalli Mommy ba ta ce ’’Matar da Yash yake so zai aura take so a kashe saboda mahaukaciya ce ita’’ ta fad’i hakan still idanunta na akan Kausar d’in. Sai a sannan Kausar ta d’ago ta kalleta itama tukunna ta ce ’’kina da wata idear(shawarar) ne bayaga ‘ku bani hak’uri ku ce za a san abun yi’ Bayan wannan ɗin?? Ki fad’a min idam akwai wata mafitar da ta fi wannan yanzu, ina so in ji’’. Cikin takaici da tsananin b’acin rai Yassira ta ce ’’ban tab’a tunanin abun naki ya kai har haka ba! Ban tab’a tunanin za ki iya kai har izuwa wannan hatsabibin matakin ba! Kausar kin san menene rai kuwa??.. A kan Yashjub wanda idan Ubangiji bai rubuta Mijinki bane shi ɗin ko sama da k’asa za ta had’e baki Isa ki auresa ba shine za ki d’auki jinin bama mutum d’aya ba?” A ɗan tsorace sannan a rikice ta kalli Mommy ta ce “Tunda bamu san y’an mata nawa ne a cikin gidan ba.’’ Sai kuma ta yi shiruuu kawaui ta runtse Idanunta ta tsaya da magana saboda tsabar yadda al’amarin Kausar ya k’ulle mata kai ya bata tsoro gaba d’aya yasa kanta har wani jujjuyawa yakeyi. Sai da ta d’an dawo dai-dai tukunna ta bud’e Idanunta ta kalli Kausar ido cikin ido ta ce ’’ki saurara ki kasa kunne ki jini da kyau! Ina mai shawartar ki! had’e da gargadi! mai tafe da zazzafan warning(jan kunne)! Da kuma threat(barazana!)… Na rantse da Allah idan wani abun ya sami Yarinyar nan to da Bakina zan fad’awa Yash komai sannan babu ni babu ke har abada!Dan ban shirya zama a k’ark’ashin inuwa d’aya da murderer (masheƙiya) ba. Idan ba ki nutsu kin dawo cikin hankalinki ba to za ki rasa komai kuma za ki rasa kowa…duk tak’amar ki da kuma isar ki baki kai Yash ba dan haka inaso ki saka a ranki cewa ‘idan kika kashe ta da shi za ki yi shari’ah!’. Kar ki lalata rayuwarki da Hannunki! wannan zafin da kika d’auka babu inda zai kai ki sai garin da na sani, mu d’in da muke ce miki ‘ki yi haƙuri, ki bi komai a hankali za a nemo mafita’ mu ne masoyanki, kuma mun fi ki gaskiya. Ki nutsu ki yi lissafi ki ga yadda duk iyakar k’ok’ari muna yi amma sai da yayi budurwa, gashi yanzu har ana maganar aure! Ba ki san menene a k’asa ba ba ki san me Ubangiji ya binne ba dan haka mu bi komai a hankali, a samu a nemo mafita amman kashe ran d’an Adam sam ba namu baneba Kausar!. Tun Yarinta ina tsaya miki tsayin daka akan dukkan al’amura amma wallahi Kausar idan kika zarce iyaka na fad’a miki na sake maimaitawa Ni da ke pam!pam!!pam!!!.” Ta fad’i hakan tana mai karkad’e tafukan hannayenta duk biyun. Jinjina kai Kausar ta yi cikin b’acin rai ta ce ‘’Tabbas a yau Yassira na san cewa blood is thick(Jini ba ya ruwa)” Cikin tarar numfashinta Yasira tace‘’this isn’t about blood Kausar (Wannan ba akan batun ƴan uwantaka bane ba Kausar)’’ Cikin fushi Kausar ta ce ‘’To dan mai yasa kike komawa ɓangarensa? Ba ma fa ki san wannan Yarinyar ba amman a yadda ki ke yi ɗinnan ya sa na ji kamar har kin so ta, kuma na tabbatar farin cikin da kika gani a fuskar d’an uwanki ne ya sanya kika fara sonta da har kike tunanin kareta. Na san banida kowa Yassira amman ban yi tunanin kaɗaicin nawa ya kai har haka ba sai yau’’ Matsowa Yassira ta yi ta kama kafad’unta tukunna ta ce ‘’Kausar, wallahi yadda kika tsani Yarinyar nan nima haka na tsaneta, abu d’aya da nake so ki gane shine Duk rintsi ba zan tab’a goya miki baya ki yi abunda kike shirin yi ba, kuma idan har ma kika aikata hakan ke a karan kanki kin san me hakan ya ke nufi???’’ Bata jira jin amsar Kausar d’in ba ta ce ‘’yana nufin kin tsorata, kin ji tsoronta! Kin bada Kai kin san ta fi ki da komai, kin yarda babu ta yadda za a yi ki iya kwace shi daga hannunta Shiyasa har ki ka yi mata mai kan-kat!’’ A hankali Mommy wadda tun d’azu ta yi shiruuu kawai tana kallonsu ta ce ’’bari in je kiran Daddyn ku, shi ne ya kira ni na na fito. Ina zuwa yanzu zan dawo’’ ‘’Tam’’ kawai Yasira ta ce mata daganan ta ci gaba da cewa Kausar “ita Mace ce! Kema Mace ce dan haka ki yaƙe ta! A yi duk kalar yaƙi da kissa da faɗan da za a yi har mu samu mu yi galaba a kanta.. Wannan na yi miki alƙawarin zan tsaya miki akai duk rintsi Kausar amman batun kisan kai kam ya fita daga tsari da lissafi dan haka a barshi, dan gaba ɗaya tunanin naki Kausar ya fita a kan hanya” Ta k’arashe maganar tata a hankali. ‘’Wanne tunanin nata ne ya fita akan hanya? And what exactly happen in here(sannan me ya faru a nan haka?)” Yassir wanda shigowar sa kenan ya fad’i hakan yana bin parlourn da kallo. A hankali Kausar ta ce ‘’ba komai’’ Sai kuma ta juya da sauri ta wuce d’akinta ta rufe k’ofar. Ya jima yana kallon k’ofar d’akin nata kafin ya furzar da iska ya k’araso ciki inda Yassira take ya tsaya yana kallon ta. Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce ’’na yi tunanin ka na office, na ji Daddy ya ce ka samu contract, me ka ke yi a gida??’’ ‘’Yasira yau fa Sunday, tun jiya ma kuma na gama abubuwan da na san su ne masu mahimmancin, yau kuma P.A d’ina yana chan. Inada buƙatar hutu kuma na san zai yi handling (yin ) komai’’ Yassir ya faiyyace mata hakan kansa tsaye. Cikin rashin jin dad’i Yasira ta ce ’’Yassir wannan dalilin fa ya sanya Daddy ya fi bawa Yashjub jari, saboda ya san ko an baka asara ne. Saboda Allah kalli yadda ka tarwatsa company d’inka in banda ci baya ba abunda yake yi kullum!!! Sannan ka d’an samu contract da kyar amma dubi yadda kake wasa da damarka?… Ka yi haƙuri da abunda zan gaya maka kai tsaye kuma a gaban idonka Amma Yassir kana da matuƙar son jiki da kasala…’’ ‘’Am, Yassira! Me ya faru da Kausar?? Me kuke tattaunawa kafin na shigo?’’ Yayi mata tambayar yana mai gyara tsayuwar shi. Fusata Yassira ta yi, ganin yadda k’iri-k’iri ya gwale ta, ya ma k’i sauraron ta… dama ga takaicin Manubiya da Kausar shiyasa cikin fushi ta ce ’’in ka matsu ka shiga ciki ka je ka tambayeta da kanka.” Daga haka ta bangaje shi ta fice. Ta nufi d’akin Mommy da niyyar jiranta ta dawo daga d’akin Daddy su yi magana amman sai ta ganta a d’akin nata a zaune ta zabga uban tagumi. Ta d’an yi mamaki amma sai ta kawar kawai ta ce ‘’Mommy, sai kin bud’ewa Kausar ido fa! Ina tsoron kar ta je ta yi wani shirmen, ganin wannan Yarinyar nan da ta yi ya haukatata!!… Ni kaina na tsorata Mommy dan in dai wannan ce Yarinyar da ya ke so zai aura to gaskiya ba na jin za mu iya kai labari….. Sannan ga dukkan alamu yana tsananin santa! Dan na manta rabon da in ji Yash yana bada hak’uri amma ita in kinga yadda yake rarrashinta wallahi sai kin yi mamaki… Dan haka in dai har muka bari ta shigo gidan nan To a idanunsa da mu da kashi duk d’aya! Dan na san ita kawai zai dinga gani…. Shiyasa ya zame mana dole mu yi wani abun amma kafin nan ya kamata ki tsawatarwa Kausar, kwata kwata wannan shirmen nata ba shine mafi dacewar mafita ba…’’ *MANNUBIYA* *47* A hankali Mommy ta ce ‘’InshaaAllah zan yi mata magana, amman Yassira ban ji dad’in yadda kika yi mata magana ba yau sam, kalaman da ki ka yi mata amfani da su sun yi tsauri da yawa’’. Ajiyar zuciya Yassira ta sauk’e kafin ta nemi guri ta zauna a gefen Mommyn, ta ce ‘’zan bata hak’uri Mommy, amma ya kamata mu fara nuna mata kuskurenta tukunna. I love her ne shiyasa kika ga na yi mata hakan. Kinga na farko abunda take shirin yi bai kamata ba Abu na biyu kuma Mommy ni kad’ai na san abunda na gani a kwayar Idanun Yash game da Yarinyar nan, idan Kausar ta yi gigin raba ta da duniya wallahi ba ita ba bincike in ya biyo har ta kanmu sai mun ga tashin hankali dan kashinmu ya bushe har ke kanki kuma mu da shi har abada. A ganina gwara ya tsaneta da kansa cikin sauk’i, tsana ta har abada. Akan ya tsanemu tsana ta har abada saboda ita.’’ Dafe Kai Mommy ta yi tukunna ta ce ’’Kausar ba za ta yi komai ba inshaaAllah, Yash kuma na ce muku ku barni da shi, da shi da yarinyar duk ku bar ni da su. Yanzu ki je abunki, ina buk’atar hutu sosai, ki koma office kin ce ana jiranki.” Shiruu Yasira ta yi tana jin wani kalar tausayin mahaifiyar tasu yana mamayeta! Saboda Allah ace wai d’anka ba ya kulaka, zai yi aure bama ka saniba sai y’ar kishiyarka ya gayamawa. Sannan yanzu ga Kausar ta sake d’aga mata hankali….shiyasa dole ta shiga damuwa…. Har Yasirar ta mik’e za ta fita sai kuma ta koma ta rungume Mommyn, sun jima a haka tukunna ta cika ta ahankali ta ce ‘’komai zai gyaru Mommy, inshaaAllah’’ A hankali Mommyn ta ce ‘’Na gode Yassira, Allah ya miki albarka’’ Murmushi Yassirar ta yi tukunna ta cikata ta ce ’’ameen,sai na dawo’’ daga haka ta fita A ranta tana adduar ‘Allah ya kawo ranar da Mommy Yash Daddy za su had’a Kai su so juna su k’aunaci juna komai ya dawo dai-dai Family ya gyaru ya yi dad’i……’ A b’angaren Yassir kuwa, Yassira tana fita ya k’arasa k’ofar d’akin Kausar da niyyar shiga amman sai ya ji ta a rufe, dan haka ya sake tabbatarwa kansa ‘Tabbas akwai abunda Kausar take b’oyewa’ Amma kuwa in ta yi masa haka to ta yi mugun janyowa kanta bala’i da masifa…. Bai bar bakin k’ofar ba sai da ya gama tsara abunda zai yi ‘Zai jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya’ Tsuntsun farko…zai kawo k’arshen matsalarsa. Tsuntsu na biyu kuma…zai fallasa masa Kausar…zai gano abunda take b’oyewa, dan ya san in dai har da gaske Kausar son Yashjub take yi kamar yadda ya ke zargi to Idan ta ji labarin mutuwar Yashjub ɗin sai ta yi haukan da zai fallasa ta b’aro-b’aro. Ta hakan ne zai gane gaskiya, a daina wasa da hankalinsa kamar wani wawa! Daga nan kuma ya ci ubanta na wasa da hankalinsa ɗin da ta yi sannan ya aureta ba yadda ta iya…… Ko gida Manubiya ba ta kai ga k’arasawa ba Yahanasu ta kira ta…Tashi d’aya kuwa ta ji Yahanasun ta kwanta mata a rai, itama Yahanasu nutsuwa da hankalin Manubiya yasa ta ji ta k’ara sonta… sun d’an tab’a hira daganan ta taya d’an uwanta campaign kafin suka yi wa juna sallama. A k’ofar gidan nasu aka ajjiye ta, kamar had’in Baki! Mai adaidaita sahun yana wucewa tana shirin shiga gida ta ji an kira sunanta dan haka ta juya. Murmushi ne ya wanzu akan kyakkyawar fuskarta sakamokon had’a idanu da suka yi da Mama. Sai da ta gaida ita ta amsa tukunna Maman ta ce ’’ki yi hak’uri nima kwana biyun nan ban ji dad’i ba shiyasa ban samu na shigo na duba innar taku ba.” Murmushi Manubiya ta yi, tana mai jin k’aunar Matar tana ratsata a lokaci guda kuma tana mamakin tsananin kamanninta da Yashjub kafin cikin kwantar da murya ta ce ‘’Allah sarki! Allah ya baku lafiya gaba d’aya… Innar ma na san bata nan, dan ba lalle sun dawo ba amman mu shiga dai mu duba’’ Daga haka suka wuce tare bayan Mama ta ce ‘’ameen’’ Sai da ta yi sallama ta shiga tukunna Maama ta bi bayanta itama ta shiga Bakinta d’auke da sallama. Da ikon Allah kuwa har sun dawo dan ‘a cikin wata na’ura kawai aka saka Innar aka fitar’ amman Dr Sofia ta ce ‘’ta mayar da pt d’in sau biyu a rana sannan su kwantar da hankalinsu dan babu wata matsala saboda abun nata ma ashe minor ne dan haka su tsammaci warkewarta a ko wanne lokaci muddin aka bata kulawar da ta kamata.’’ Manubiya ta yi mamakin yadda ta gansu a zaune gaba d’ayan su sun yi jugum har Ya Nafi’u, bata gama nazartar su ba aka fara gaisawa da Mama wadda hankalinta ya tashi matuk’a daga ganin jikin Inna dan sam ba ta yi tunanin jikin nata ya yi tsanani har haka ba. Itama ba wani k’arfi ne da ita ba balle ta taimaka musu, dan ta lura lamarin na Inna har da d’an rashi da babu. Cikin rashin jin dad’in ganin Innar a haka ta ce ’’akwai baba mai gadi na gidan ammi, malamin tsangaya ne kafin ya dawo gadin ya barwa ya’yansa, zan ce masa ya dinga yi wa inna rubutu duk jumaah sai Musbah ya dinga karb’a mata tana anfani da shi, sadak’a saboda Allah’’ Sun ji dad’i kuwa sosai haka nan suka yi mata godiya tanata cewa ‘kar su damu ai ba komai’ daga nan suka d’an tab’a maganganu kafin daga bisani ta yi musu sallama ta tafi. Manu ce ta rakata har k’ofar gate na gidan Ammi, daganan ta juyo ta komo. Tana shiga d’akin ta gansu sun koma jigum d’insu kowa kana ganinsa ka san yana cikin damuwa. Dan haka ta shiga tambayar su ‘’me ya faru?”. Ya Nafi’u ne ya iya bata amsa ta inda yake cewa ‘kiran da Kaka Mallan ya yiwa Baba d’azu, akan wai su Baba Habu sun kai k’arar ku ne game da dukan da kuka yi wa Yusuf…wanda duba da hakan yanzu sun yanke shawarar Uncle zai siye nan d’akin da band’akin da d’an filin baya wanda yake mallakin ku, sai ku tashi a gidan’’ Cikin fushi Manubiya ta ce ’’ashe kuwa da sun tabbata mahaukata, mu bamu yi magana akan abunda shi Yusuf d’in ya yi ba sai shi me uba ??’’ Ciki fushi Baba ya ce ‘’Manubiya bana son shirme fa… Tun farko ai kamata ya yi ace da kuka zargi ya yi wani abun ku tuntub’eni ku ji asalin bayani ba wai ku rufe shi da duka sai ka ce wasu taɓaɓɓu ba! Yusuf d’in d’anku ne da za ku d’aga Hannu ku dakeshi?? Baya ga haka ma ai sai da na gayawa Musbahu k……’’ Cikin fad’a fad’a ya juya ya kalli Ya Musbah ya ce ‘’Lokacin da ka zo ka same su ba ka gaya musu taimakon da Yusuf d’in ya yi min ba?? shine ka biye musu kuka dake shi??. Har yau yana asibiti kuma Baba Habu ya ce duk mu za mu biya kud’in jinyar sa.’’ Tsabar takaici Manubiya bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, cikin kukan ta ce ‘’Baba yaudarar ka ma fa yayi! cutar ka yayi! Takardun da ya baka ka saka Hannu ba abunda ya fad’a maka ne rubuce a jiki ba!. Baka ga black snake ya zo ba? Me ya had’o ka da shi tou tunda shi Yusuf d’in cewa ya yi banki ne’’ Rai a ɓace Baba ya ce ‘’Ko da ace ban yi karatu ba na san abunda yake a rubuce a jikin takardar nan tunda na san kuma na yarda Yusuf ba zai cutar da ni ya had’ani da wannan mugun Mutumin ba. Shi kansa Yusuf d’in yanzu haka a cikin danger yake….. Shi wannan black snake d’in shi ne ya had’a da ni da shi gaba d’ayanmu ya biyo mana ta k’ark’ashin k’asa’’ ‘’To tayaya akayi shi Yusuf d’in ya san Mutum irin….’’. Maficin da Baba ya jefa mata ne yasanya ta yin shiru….cikin fad’a sosai ya ce ‘’Ungo naki’’ ya fad’i hakan yana yi mata dak’uwa kafin ya d’aura da cewa “ina fad’a kina faɗa! Ce miki akayi ban san me nakeyi ba??’’ Ya Musbah ta kalla wanda ta ga yana yi mata alamun ta yi shiru kawai ta hanyar d’aura yatsunsa a kan Bakinsa. Kuka kawai ta sake fashewa da shi tsabar takaici da bak’in ciki, hakanan ta yi shiru Baba ya balbaleta ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kafin daga k’arshe ya tashi ya fita. Bai ma san ta ina zai fara ba gashi Uncle ya ce ‘’Idan ya k’i yarda ya siyar da d’akin nashi da filin cikin sauk’i to zai sako hukuma ya fad’i abunda y’ay’ansa sukayi’’. Saboda Allah ta ya za su yi masa haka? taya za su tsame sa a cikin gidan! Bayaga haka ma ta Ina zai fara neman wani d’akin a wannan d’an kud’in da suka ambata za su siye d’akin. Yana fita direct masallaci ya nufa ya ci sa’a kuwa babu kowa a ciki….tun tasowar su su Uncle ba su tab’a yi masa abunda ya ji zafinsa kamar na yau ba, wato sun nuna cewa su uwarsu d’aya kenan shine bare a cikin su abunda ba su tab’a yi ba kenan…. Fisabilillahi in ba haka suke son nunawa ba ta ya za a yi case da Yusuf d’an gidan Baba Habu wanda yake kamar d’a a tsakanin su su duka ukun abunda ya kamata ace su yi sulhu a tsakaninsu su gyara amman ace wai Uncle ya shigarwa Baba Habu! Wannan wanne irin nuna banbanci!wulak’anci! da cin fuska ne……!. Duk yadda Baba ya so daurewa kasawa yayi bai san lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba…… Baba yana fita su Ya Nafi’u suma suka mik’e suka fita aka bar Manubiya Inna Jidda da Muhsin… Jidda gaba d’aya ta yi laushi dan gani take yi kamar komai duk laifinta ne shiyasa ta ma kasa rarrashin Manubiyan dan ita ba ma ta san me zata yi ba tsakanin kuka ko ihu! Da kyar ta lallab’a ta iya mik’ewa ta je ta kwanta a gefen Inna ta yi shiruuu. Sun jima a haka kafin Manu ta tashi ta fita dan azahar har ta yi. A kithchen d’in ta zauna tunda ta fara girkin har ta gama sam ba ta damu da hayak’in ba sai da ta gama tukunna ta juye a kula ta koma d’akin. Hakanan gidan ya kasance jigum mai sunan baba ne kawai yaketa faman tsalle-tallen sa. Ya Nafi’u da Ya Musbah kuwa ba su zauna ba har dare, duk inda suka je ko dai a lissafo musu uban kuɗaɗe ace su nemi lawyer ko kuma tashi d’aya ana ganinsu ma ace su yi haƙuri kawai dan ansan ba iyawa za su yi ba. Manubiya ma sai dare tukunna ta d’auki wayarta, ba ta yi mamakin ganin misscalls kusan takwas duk na Yashjub ba dan tunda ta dawo bata bi ta kan wayar ba kuma tun jiya lokacin da ya ce zai kira ta after thirty minutes ta saka wayar a silent gudun kar ta tashi su Baba. Bataso ta kira shi dan kunya takeji amman haka nan ta daure ta danna call tana sauk’e numfashi a hankali a hankali. Har ta katse bai d’auka ba dama addua takeyi kar ya dauka d’in saboda na flashing ne kawai da ita ta san kuma yana d’auka mtn za su katse. Tana tsinkewa kuwa a take ya biyo kiran. Cikin nutsuwarta ta d’auka ta kara a kunnenta bakinta d’auke da sallama …….……..bayan kamar awa biyu Jidda ta fito ta zauna a gefenta ta na yi mata nuni da alamun lokaci. Jinjina Kai Manu ta yi kafin ta zaro wayar ta d’an kalli screen d’in, ba k’aramin mamaki ta yi ba kuwa da ta ga har sun wuce awa biyu suna wayar dan haka ta fara yi masa sallama…. Da kyar ya hak’ura ya kashe bayan ta ce masa bacci take ji sosai…… Murmushi Jidda ta yi bayan Manubiya ta kashe wayar cikin d’an sigar tsokana ta kalle ta ta ce ’’yau ansha till down. Dama gani na yi tun d’azu Baba yana zaune kar ya fara tambayar ki shiyasa. Dan naga kamar kun manta da kowa a duniyar sai faman I love u ilove you ake…’’ Toshe mata Baki Manubiya ta yi tana d’an hararar ta kafin ta ce “ba wani I love you kusan ma duk labarin ku ke da Muhsin nake ta bashi’’ A hankali Jidda ta ce ‘’amman dai zuwa yanzu ke kan ki na san kin yarda son ki yake yi ko?’’ A hankali Manubiya ta d’an gyara zama ta kalli Jiddan, tun d’azu basu samu hankalinsu ya dawo Jikinsu ba bare su zauna Shiyasa bata gaya mata komai ba, sai yanzu ne da ta d’an ga walwala a fuskar Jiddan yasanya itama ta samu kwarin guiwar zaiyyane mata yadda sukayi ita da Yashjub d’azu da safe…..tiryan tiryan haka ta bata labarin kafin ta d’aura da cewa “yanzu ma muna fara waya ya ce wai yanaso zai kira Ya Musbah a fara magana, ba yadda ban yi da shi ba amman ya dage wai gobe da safe inshaaAllah zai kira shi’’ Dariya Jidda ta yi kafin ta ce ’’to da farko dai ‘Alhamdulillah’wallahi na ji dad’i sosai saboda kun dace, abu na biyu kuma shi wannan bawan Allah haka ake yi? Irin wannan zumud’i haka? Ke da baki riga kin ce masa ‘eh’ ba ma, saurin me yake yi?’’ D’an turo Baki Manu ta yi kafin tace “Nima dai abunda na gani kenan’’ Dariya ce take ciyo Jidda ganin yadda Manubiyan take so ta yi mata basaja k’iri-k’iri Dan haka ta ce ’’to kawai ki fito ki gaya masa gaskiya mana, ki ce masa kawai bakya son shi’’ Da sauri Manu ta d’ago ta kalle ta ganin yadda Jiddan take guntse Baki tana dariya k’asa-k’asa ne ya sanya ta fahimci jan magana Jiddan take yi dan haka ta kai mata dukan wasa ta ce ’’ja’ira’’ Ahankali Jiddan ta matso ta rungume Manubiya tukunna tace “Ba sai kin fad’a min ba Adda Manu kema na san kina son shi tun ba yau ba, Ina miki addu’ar Allah Ubangiji ya tabbatar da alkhairi sannan ya dauwwamar da farin ciki a rayuwar ku, ya tabbatar da aurenku ya sa kar a samu matsalar komai.’’ A hankali Manubiya itama ta sa hannu ta rungumo k’anwar tata tana mai jin tsananin tausayin ta yana ratsata…..ba dan Ammi ce mahaifiyar Al’ameen ba da ba abunda zai hanata tsayawa tsayin daka har sai ta ga Jidda ta auri Al’ameen, dan ta san yadda Jidda take son Al’ameen tun kafin ta yi wayo shiyasa take tsananin jin tausayin ta dan soyayyar da ta ke yi wa Yashjub ta sanyata ta sake fahimtar yadda Jidda ta ji a lokacin da aka rabata da Al’ameen, dan tabbas in da ace itace wani ya yi gigin rabata da Yashjub to da batasan ya zata yi ba, da wuya idan bata rasa ranta ba. A hankali ta zaro Jidda daga jikinta cikin rarrashi da bada Baki ta shiga kwantar mata da hankali tare da yi mata addu’ar Allah ya bata wanda zata so sama da Al’ameen wanda zai so ta shima tsakani da Allah. Sun jima Sosai a wajen suna kwantarwa da juna hankali tare da bada shawarwari kafin su mik’e suka shiga d’aki. Sai da kowa yayi bacci tukunna Manubiya ta yi. Tunanin ta ya karkata ga Abbakar wanda tun ranar da suka bar asibiti ya daina d’aukar wayarta baya kiranta gashi su Baba sun hanata zuwa ta dubosa, su ya Nafi’u dai sun koma duba shi dukda kuwa abunda mahaifiyarsa ta yi hakan bai hanasu zuwa ba amma ita sun ce ba zata je ba. Ta d’an ji haushin abunda yayi mata dan bata yi tunanin zai d’auke mata wuta lokaci d’aya haka ba, duk da ta san dama dole mahaifiyarsa za ta kora masa warning a kanta amman bata yi zaton wannan d’aukewar d’iff d’in daga garesa ba amma kuma da ta tuna daraja irinta uwa sai ta goge duk wani takaicinshi a ranta. Tabbas ta san za ta yi misssing Abbakar saboda shi ɗaya take da shi a matsayin Aboki, amman tunda haka shi da mahaifiyarshi suka tsara ba komai za ta jure Allah yasa hakan ne mafi alkhairi…. tana wannan tunanin itama ta ja abin rufa ta yi luff sai kuma ta fara tunanin Yash kafin ta fara karatun Al’kurani ahankali ahankali a cikin ranta daganan bacci yayi awon gaba da ita…. A b’angaren Abbakar kuwa dama tun kafin ya farka mahaifiyarsa da maman Baraka suka gama had’a plan d’in su…….yana farkawa kuwa ko likita ba su kira ya duba shi ba suka shirga masa k’aryar “ai Manubiya ta yi aure Babanta ya aurar da ita a wani mutum yanzunnan aka gama d’aura auren a cikin asibitin.’’ Tashi d’aya Abbakar ya amince kuma tunanin sa ya bashi ai Yashjub aka aurawa Manubiya watak’il ya zo ya taimakesu Baba kuma ya ji dad’in taimakon da ya zo yayi musu shi ne ya ba sa Manubiya. Shiyasa gaba d’aya hankalinsa ya tashi, tashi d’aya ya birkice musu ita kanta mahaifiyar tasa sai da ta tsorata……abu d’aya da yayi dana saninsa shine farkawar da yayi! Dan sai da ya yi fatan inama ace black snake a k’irji ko ciki ko kai ya harbesa!! ya san babu kyau amma a ranar ji yayi ina ma ya wuce lahira kawai Ina ma bai tashi ba. Tun daga ranar kuwa ya daina magana sam, maman nashi ta kasa gane kanshi… Iyakar shi ya bud’e ido ya ci abinci, tayi mishi alwala yayi sallah ba um ba um um Kuma Doctor ya tabbatar mata komai nasa lafiya lau. So yake kawai a sallameshi ya je ya nemi transfer ya yi nesa da garin Kano first, daganan sai ya san abun yi dan a yanzu kam ya san Manubiya ta yi masa nisa shi kuma ba zai iya jurar ganinta da kowa ba. Amman fa in akwai abu d’aya da ya sani shine ‘zai yi duk yadda zai yi ya san yadda zai mallaketa, bai damu ba ko ya’ya goma ta haifa yana nan dawowa dan ba’a haifi mutumin da zai barwa Manubiya ba……..’ *MANNUBIYA* *48* Kamar kullum, yau ma tunda Yashjub yayi sallar asubah bai koma bacci ba, yana gama azkar da karatun Alk’urani ya hau aikin Yassir wanda yake so ya kammala a yau in sha Allah… Yana cikin aikin Najeeb ya kira sa, dama yanata tsammanin sa tun jiya da ya ce masa za su yi waya da hajiya mama in sun gama zai kira sa amman ya ji shiruu……. Ba k’aramin dad’i Yashjub ya ji ba da Najeeb d’in ya ce masa ‘’ai hajiya mama ta amince ɗari-bisa-ɗari, tana ta murna ma kuma ta ce ‘za ta yi magana da Daddy, shima Yash d’in ya je ya same shi su yi magana, ana gama bincike sai maganar aure in sha Allah.’ Sannan itama da kanta ta nuna bata so ma a d’au lokaci me tsayi’’. Tashi d’aya wani kalar farin ciki ya lullub’e Yash, ya ma kasa b’oye murnar sa har sai da Najeeb d’in ya tisa shi a gaba da tsokana tukunna ya d’an sassauta yayi masa godiya suka yi sallama. Sai da ya shirya shirin office tsaf, tukunna ya d’au waya ya kira Ya Musbah dan baya so yayi masa kiran asubah gudun kar ya saka shi a al’ajabi, amma dukda hakan sai da Ya Musbah yayi mamakin ganin kiran Yash d’in k’arfe 7:48 na safe. Ba maganar b’oye-b’oye dan bayan sun gaisa kanshi tsaye ya sanar da shi fa Manubiya yake so, yana so ya samu Baba yayi mishi maganar zai turo magabatansa. Ba k’aramin shock Ya Musbah ya shiga ba, amman kawai sai ya bar Yashjub d’in akan ‘in sun tattauna da Baban, duk yadda suka yi zai sanar masa….’ Yashjub ya ji dad’in yadda Ya Musbah yayi masa, dan tun daga hakan ya silver lining (hasken a al’amarin) dan haka ya fara shirya samun Daddy kawai ta yadda in sun ce ya turo ba sai ya tsaya k’umbiya-k’umbiya ba, dukda ya san a tsakankanin jiya ko yau dole Daddy zai ji maganar daga wajen hajiya mama amma dukda hakan shima ya kamata ya d’an cire kunya ya same shi. A b’angaren Ya Musbah kuwa, ya saka a ranshi kuma ya san Yashjub zai yi magana da Baba amman fa a asalin gaskiya shi ba zai yi magana da Baba ba har sai ya ji ta bakin Manubiya, sannan ya gama bincike tare da tsaida matsayar abunda ya kamata ayi tukunna. Dan a yadda Baba yake kwana biyun nan tsaf zai iya cewa Yashjub ya zo a d’aura masa auren da Manubiya ba tare da an yi wani ƙwaƙƙwaran bincike ba. Sai da ya yi wa me sunan Baba wanka ya shirya shi shima ya yi wanka ya shirya suka karya tukunna suka fita suka nufi gida da niyyar in sun gama tattaunawa da Manubiya zai d’auki Jidda ta zo ta gyara masa gidan, dan yayi datti a cikin kwana biyu kacal kyankyamin koina yake yi. Inna da Jidda ya samu kawai a dak’in Jidda tana ganinsa, sai da ta fara gaida shi ya amsa tukunna tace’’dan Allah ga inna nan, bari in je nan baya in aro wani littafi da na tab’a gani a wajen su mami kwanaki gobe post utme, inaso in duba sosai.’’ ‘’To’’ kawai yace da ita, daganan suka zauna shi da me sunan baba a gefen innar suka shiga gaida ita. Ba su yi mintuna biyu da zama ba Manubiya ta shigo cikin d’akin da laida a Hannunta ta siyo omo da maggi Kallonta ya yi ya kalli laidar kafin yace ‘’meyasa ba ki aiki Muhsin ba??’’ Sai da ta zauna ta gaida shi ya amsa tukunna ta ce ’’ai ya tafi islamiyyar safe’’ ‘’oh haka fa, na manta’’ Ya Musbah ya fad’i hakan kafin ya d’aura da cewa “ke kika bawa Yashjub damar ya kirani?’’ Diriricewa ta yi, ga wata kunya da ta lullub’e ta tashi d’aya, a ranta ta ce “wato har ya kira shi?, wai zumuɗin me Yashjub yake yi ne har haka?’’ Ta yi wa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba. ‘’Kin yi shiru!!’’ d’in da ya Musbah ya ce mata ne, ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, ahankali ta jinjina masa Kai alamun’’Eh!’’. ‘’Kin san akan maganar me ya kira ni?’’ Ya sake jeho mata tambayar. Sunkuyar da kanta ta kuma yi kamar wuyanta zai karye kafin ta ce ’’Eh!!’’ a hankali. Shiruu Ya Musbah ya yi kawai yana kallon ta kafin cikin fad’a sosai ya fara cewa ’’kuma amma shine kika bashi damar kiran nawa? Kin shirya kenan kema ko? So kike a aurar da ke da wuri? Ba ki san Mutum ba, ba ki san daga ina ya fito ba, ba ayi bincike ba shine har za ki ce ya kira ni ayi maganar aure? Yaushe har kika san shi yaushe ma kuka fara soyayyar da har kuka fahimci juna wanda yasa kika samu kwarin guiwar ce masa ya kira ni akan maganar aure??? Daga ya ce miki ilove you sau d’aya zuwa biyu shikenan har kin aminta da shi?? Tou bari ki ji abunda baki sani ba!dama Baba so yake ya aurar da ku da wurwuri, tun a asibiti ya riga ya gama yankewa kuma ya fad’a mana, kinga idan kika yi wa kanki kika bari Baba ya ji wannan zancen ba tare da an yi wani cikakken bincike akan Yashjub ba tou ina tabbatar miki ko sati biyu ba za’a rufa ba za ki ganki a cikin gidan Yashjub a matsayin matarsa, Wallahi! Dan haka Baba ya tsara ya ke kuma fata.’’ Motsin da ya ji ne ya sanya shi d’aga Kai ya kalli bak’in k’ofar toilet ɗin. Ba k’aramin bugawa k’irjinshi yayi ba sakamakon had’a idanu da suka yi shi da Baba wanda ya fito a wanka. In-i-na Ya Musbah ya fara, yana shirin yin magana Baba ya kalli Manubiya ya ce ‘’ki ba sa number ta, ki ce na ce ya kirani’’. Yana gama fad’in haka ya wuce yana d’ingishi yana tafiya da kyar, ya fice… dan kamar gyambo haka yake jin y’an yatsunsa, ba k’aramin zugi suke yi masa ba. Yana fita Ya Musbah ya ce ‘’innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’ ‘Ya san halin Baba, ya san waye Baba, ya san in ya saka kanshi abu babu wanda ya Isa ya hana shi. Babban tashin hankalinsa shine kar aje Yashjub yana da wani mugun hali wanda ba a san da shi ba, su je su aura masa Manubiya… Har gara Baraka da Ya Yusuf Allah ya rufa asiri in sukayi abu za a iya hukuntasu aci ubansu, wannan Yashjub d’in yanda yake da arzik’i Ina su Ina yin rigima da shi?….’ Ahankali Manubiya ta ce ‘’Ya Musbah cewa fa yayi kawai….’’ Wani uban tsaki ya ja, ba tare da ya kalli inda take ba ya mik’e ya fice ranshi a mugun b’ace. Sai da Jidda ta yi da gaske bayan dawowar ta, tukunna Manubiya ta yarda ta turawa Yashjub number Baba ta ce ‘’ya kirashi, number Baba ne,’’ Already dama yanada number dan haka yace mata “ai yanada ita, dama izini kawai yake jira, dan haka ya gode’’ Haka nan ya yi ta murna kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljannah, kafin daga baya suka yi sallama gaba d’aya jikinta babu kuzari. Saboda itama sai yanzu ta fara da na sanin basa damar ya kira ya musbahn tun farko da ta yi da wuri haka..shikenan zai raina ta tun yanzu, dan zai ga kamar tana neman Kai ne da kanta, ga kuma abunda Ya Musbah ya gaya mata wanda gaba d’aya ya d’aga mata hankali….. A take a lokacin…ba b’ata lokaci, ya kira Baba. Sai da Baba ya sake yi masa godiya tukunna suka fara tattaunawa… Baba da so yayi su yi magana a waya kawai amman sai Yashjub d’in ya ƙi amincewa..a ranar suka zo da shi da Najeeb suka had’u a masallaci ya amsa tambayoyin Baban. Daganan Baba ya nemi da ya tura masa da adress d’in sa, ya ce masa “inshaaAllah bayan kwana biyu, za su neme sa.” Ba abunda ya fi b’atawa ya Musbah rai irin yadda Baba ya sake d’aura masa alhakin yin bincike akan Yash, kuma ya hura masa wuta ko d’aga Ƙafa babu ko duba halin da suke a ciki ma bai yi ba. A b’angren Baba kuwa babu abunda zai iya shiga tsakanin sa da maganar Yashjub da Manubiya dan har ga Allah ya yi farin ciki matuƙa da ya ji Yash d’in yana son Manu ba wai kwad’ayi ko wani abun ba kawai dai ya san idan Manubiya ta auri Yashjub to hatta Jidda za ta samu kariya daga sharrin black snake…. Tun jiya da suka samu matsala da su Baba Habu hankalinsa yake a tashe dan ya san auren Jiddan da yake gani tana da Miji a Hannu ba mai yiwuwa baneba… Shiyasa gaba d’aya hankalinsa ya sake tashi, sai gashi da ikon Allah Allah ya kawo Yashjub…..in dai aka yi bincike ya ji komai daidai akansa to inshaaAllah a cikin sati biyu kamar yadda ya fad’a zai aura masa ita. ….. A cikin kwana biyu Ya Musbah ya yi bincike ya gama, ya so ya ƙi gayawa Baba amman sai Ya Nafi’u ya soma da yi mishi nasiha, ta inda ya ke cewa ’’ka kalli komai da kyakykyawar fuska, kar ka yi mummunar zato. Mu bi komai da addua tunda bamu Isa mu hana Baba yin abunda yayi niyya ba, uwa uba idan Ubangiji ya riga ya rubuta matarsa ce to fa ba mu Isa mu hana ba’’ Kamar ya Musbah zai fashe da kuka ya ce ’’Nafi’u ba fa anan ya girma ba, taya za ayi amfani da shaidar da aka bayar akansa anan Nigeria??’’ Nasiha da fahimtarwa sosai ya Nafi’u yayi masa, sannan ya masa nuni da rashin son tsananta bincike kafin ya k’are da cewa “mu bi komai da addua, za a ga alkhairi inshaaAllah’’. Ya Musbah bai iya gayawa Baba komai ba Ya Nafi’u ne ya same shi yayi mishi bayani. Sai washegari tukunna Baba yana shirin kiran Yashjub d’in shi ya kira sa. Dan shi Yashjub har ga Allah ya k’agu, abu har kwana uku sun ce za su neme sa amma har yanzu shiru…Ya san ba shi da wani mummunan hali amman ya kasa hana kansa jin fargaba da tsoro. Dukda ya san za a ga zumud’in sa amman shi fa akan Manubiya aga komai ma bai damu ba. ………Bayan doguwar gaisuwa da tambayar Baba ya jiki da jikin inna kuma sai kuma ya hau kame-kame. Murmushi Baba yayi yana yaba yanda Yashjub d’in ya ke son Manubiya, shifa tun lokacin da aka bata aiki dama ya fara tunanin wani abun Shi a zaton sa ma sir Najeeb d’in ne sai da yaga Yashjub da yanda yayi lokacin da ya ga black snake rik’e da hannunta tukunna ya tabbatar Yashjub d’in ne. Cike da kamala Baba ya ce ’’yanzu nake shirin kiranka’’ Sai da Yashjub ya d’an sosa k’eya tukunna ya ce ’’to Bara inzo yanzun Baba’’…kamar wachchar ranar Baba so yayi kawai su gama a waya tunda ba wata magana mai tsaho bace ba amman sai Yash d’in ya dage akan yana so ya zo d’in….bayan kamar mintina ashirin sai ga shi…. A masallaci yau ma suka sauk’e shi, Baba ya so ace su Uncle sun d’an shiga maganar amman ko da ya je musu ma ko kallo bai ishe su ba dan gaba suke yi da shi k’iri-k’iri, dan haka suka tari Yashjub iya su uku, Baba Ya Nafi’u da Ya Musbah. Cike da fahimtar juna Baban yace ‘’zuwa ko yaushe ya turo! In ta shi ne yanaso ayi a cikin sati biyu ma amman ko yaushe suka shirya sai su fad’i lokacin da suka ga ya fi musu’’ Godiya da murnar Yashjub saida ta bawa Baba dariya dan kasa b’oyuwa ta yi, musamman ma da ya ji Baba ya ce a cikin sati biyu! Abun yayi masa dad’i matuk’a, shiyasa farin cikin sa ya kasa b’oyewa haka yai ta murmushi bayan yayi godiya kafin daga baya suka yi wa juna sallama tare da fatan alkhairi,ya wuce. Washe gari ….. Yau ya shirya samun Daddy, jiya kwana ya yi yana sallah, yau ɗin ma sai addu’o’i yake ta yi tare da fatan ‘Allah kar ya sa a samu matsala ta ko Ina’ Dukda ya san tunda har hajiya mama ta amince to a rubuce yake Daddy shima ya amince, dan ko jiya sai da ta kira shi suka yi maganar amma dama shi addu’ar sa ‘Allah yasa su yarda ayi a cikin 2 weeks d’in, sannan Allah ya toshe duk wata matsala da take shirin tasowa.’ Suna gama waya da Manubiya wadda rikicin ta na kwana biyun nan yake basa dariya sosai, ya mik’e ya nufi parlourn Daddy, dan ya san zuwa wannan lokacin Daddyn ya gama duk wasu aikace aikacensa…… A zaune ya same su shi da Ummi kamar wasu mak’iyan juna! Ita ta juya fuska tana kallon makeken aquarium d’in da yake a parlour ta had’e rai, shima Daddyn ya kauda Kai yana daddanna wayarsa fuskar nan tamau!. Ko isashshiyar gaisuwa Ummi bata tsaya sun yi da Yashjub ba, ta mik’e ta ce ‘’sai da safen ku’’ daga haka ta yi wuff ta nufi ƙofa kamar wadda take zaune akan k’aya. Bin ta kawai Daddy yayi da kallo har ta fice ta rufo musu k’ofar….sam ya kasa gane kanta gaba d’ayanta, abun nata kamar wata mai aljanu, tun abun bai dame shi ba har ya zo ya fara damunshi…yanzu haka shi ne ya kirata akan su samu su d’an yi magana su d’an dedeta amma tana shigowa daga gaisuwa ta d’auke Kai ta had’e rai! Shi kuwa wallahi ta yi kad’an ya bita ya rarrasheta! Idan ma abunda take jira kenan…… Ahankali cikin kwantar da murya Yashjub yace mishi ‘’Daddy, wani lokacin fa muma sai mun d’an sak’k’o tukunna zaman yake yin dad’i, kuma na tabbatar inda ace rikicin na iyakar kai da ita ne to da tuni komai ya wuce na san da bazata d’auka da zafi har haka ba, amman abun ya had’a da Yara shiyasa ta ji ciwo sosai.’’ K’ura masa idanu Daddyn yayi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce ’’Yash!! Ko a gidan giya akwai babba. Ban auri Matar da zan dinga bin ta tana raina ni tana raina min wayo ba, yi haƙuri da abunda zan faɗa a gaban idonka..ba wai cin fuska ba amma Yash ko Macen da na so fiye da kowa batayi min wannan abun ba. Sannan nan gidansu Yasmeen ne, abu d’aya wanda na sani kuma ba zan tab’a komawa baya akan maganar tawa ba shine ‘Dole a lallab’amin Ƴaƴana a gidan ubansu, kuma babu wanda ya Isa ya zo nan ya ce zai juya min su!’ Idan ta yarda da hakan a zauna lafiya, in kuma ba ta yarda ba ta je ta yi ta fushi Itace ita kaɗai……’’. Ahankali Yashjub ya ce ‘’Amman Daddy…’’ Cikin d’an fushi Daddyn ya katseshi ta hanyar cewa ‘’Yashjub bar maganar Matar nan, banaso!’’ Shiruu Yashjub d’in yayi, kafin ya sauk’e ajiyar zuciya, sai kuma ya mik’e daga inda yake ya koma 3seater da Daddyn yake zaune akai shimanya zauna,a hankali ya ce ’’am Daddy’’ Murmushi Daddyn ya yi tukunna yace “za a yi min wayo kenan’’ Dariya duk sukayi sannan Yashjub ya fara magana ahankali “am..Daddy, dama alfarmar ka da rufin asirin ka nake nema.’’ Bai jira komai ba ya ci gaba da cewa “na san hakan yana iya zama kamar abu mai wuya amman idan ka yi min wannan gatan to ban san wanne irin farin ciki ni kaina zan shiga ba. A baya ka sha gaya mana cewa ‘ wacece/wanene muke so a matsayin abokiyar/abokin zama, in dai tarbiyyar su ya kwanta maka to ba za ka yi k’asa a guiwa ba wajen ganin mun mallaki juna. To Daddy ni a yanzu mahaifin Yarinyar da nake so yana buk’atar d’aurin auren nan da sati biyu ne, shiyasa nake neman alfarmar ka In ba damuwa a d’aura a cikin sati biyun masu zuwan kamar yadda ya buk’ata.’’ Shiruu Daddy ya yi, har sai da Yashjub ya d’ago dan kalar shirun da Daddyn ya yi ya yi yawa, had’a ido suka yi kamar an fisgi maganar daga bakin Daddy ya ce ’’yaushe ka yi budurwa ??’’ fuskarsa tana baiyyana mamaki Sunkuyar da Kai Yashjub ya yi da sauri dan tashi d’aya ya ji wata kunya ta lullub’esa. Lokaci guda ya ji Daddy ya fara dariya, cikin dariyar ya sake cewa “Dan Allah dagaske Yashjub ya akayi ka yi budurwa, abun ya bani mamaki ne, Hajiya Mama ta yi min magana tun lokacin dama nake so ka yi min maganr saboda a tunanin na ita ta had’a ka da Yarinyar ashe da gaske kai ka kyallo abarka.’’ Ya fad’i hakan yana dariya…. Kamar Yashjub zai fashe da kuka cikin yin kalar tausayi ya ce ‘’Daddy dan Allah ka daina’’ Ai kuwa ya sha tsokana a wajen Daddy, dan har ga Allah Daddyn ya ji tsananin mamaki, kafin daga bisani kuma ya yi gyaran murya ya gyara zama tukunna ya ce ’’Yash ka tabbatar kana sonta, itace zabin ka?’’ Ahankali yace ‘’Eh Daddy, da dukkan Zuciyata.” ‘’Alhamdulillah’’ Daddyn ya ce kafin ya ci gaba da cewa ‘’Yash, tabbas alk’awarin da na yi muku yana nan, babu abunda ya chanza amma ka san ba zan bari ka cutu ta ko wacce irin hanya ba. Abu d’aya da na yi mamaki shine ta inda Mahaifinta ya dage akan a yi a cikin sati biyu wannan shine abunda zan fi sakawa na’urar bincikena akai wanda ina fatan ya kasance ba wata matsala baceba dan nima farin cikin naka nake son gani. Idan an duba an ga ba matsala sannan aka yi bincike shima akaga ba wata matsala to da yardar Allah sai a d’aura auren a cikin sati biyun kamar yadda suka buk’ata. Allah ya yi maka albarka.” Ahankali Yashjub ya sauk’e ajiyar zuciya yana mai jin wani farin ciki mara misaltuwa kafin a hankali a fili ya ce ’’Alhamdulillah’’ Muryar Daddy ce ta katse shi jin yana cewa “Ka bani adress d’in da wuri, saboda ina gama binciken nake so zan aikawa su Hajiya mama, dan a samu su taho da wuri suma.’’ D’an b’ata fuska Yash yayi ya d’ago ya ce ’’Daddy yanzu wannan tsohuwar itama sai ta zo?’’ Dak’uwa Daddyn ya yi masa kafin ya ce ’’Dole ta zo, kuma in ka yi mata abunda bata ji dad’i ba tsaf sai ta ce a fasa, kasan kuma daga ni har uncle d’in naka dole abunda tace shi za mu yi, daganan sai in ga k’arshen soyayya’’ Da sauri Yashjub ya ce ‘’Na gode sosai Daddy, zan turo maka adress d’in yanzu inshaaAllah’’ daga haka ya mik’e da sauri yace’’sai da safe’’ tukunna ya fice tun kafin Daddy ya sa shi ya nutse cikin k’asa a take a wajen dan ya lura sarai yau Daddy tsokana yakeji shikuwa ba zai iya ba. Hakanan ya wuce zuciyarsa cike taff da farin cikin da bai tab’a tsintar kanshi a cikin kwatan kwacin sa ba…. Bayan fitar Yashjub, A hankali Daddy ya lumshe idanuwanshi… Tabbas ya yi matuƙar farin ciki da Yashjub ya samu wadda yakeso, kuma gashi da izinin Allah zai aureta. Yana tuna lokacin da ya auri Mommy……shiyasa a ko da yaushe yake addu’ar Allah kar ya sa d’aya a cikin ya’yan shi ya ɗanɗana kwatankwacin wannan feeling ɗin (yanayin), dan shi kad’ai ya san mai ya ji, shi kad’ai ya san zafin aurar wanda ba ka so!. Har i yau kuma yana tuna lokacin da ya auri amaryarsa Khadijah…farin cikin da ya rayu a ciki shi yake yi wa gaba d’aya ya’yansa kwad’ayin su samu, shiyasa ya dad’e da yi musu alk’awarin ko waye sukeso A ko wanne irin yanayi InshaaAllah zai shige musu gaba ba zai yi k’asa a guiwa ba wajen ganin sun mallaki juna!!! Wannan dalilin ne yasa bai takurawa kowa a cikinsu akan yayi aure ba, saboda yana so su nutsu kowa ya nemi wanda yake k’auna cikin nutsuwa… Yahanasu itama gani yayi kamar tana cutuwa ne shiyasa yake saka baki a cikin lamuranta ba dan haka ba to da ba zai tab’a cewa komai ba, dan bashida wani burin da ya wuce yaga gaba d’aya y’ay’ansa sun samu asalin ƙauna da sahihin farin ciki na gaskiya kamar yadda shima ya samu A lokacin da Khadijansa take da rai!! A hankali wasu zafafan hawaye suka shiga bin k’uncinsa… wannan wanne irin feeling (yanayi) ne? Ya tsaneta! Sannan kuma har yanzu yana mahaukacin sonta da k’aunarta Kuma Ji ya ke kamar ya kashe kansa saboda abunda ya yi mata… Wanda Zuwa wannan lokacin ya gama yanke shawarar Idan Allah ya ba shi ikon ganin auren hatta Yadira, ya kuma tabbatar da Ƴaƴansa duk sun girma sun kama ƙasa za su iya kulawa da kansu to inshaaAllah zai mik’a kanshi ga hukuma!! Ba zai iya ci gaba da jure wannan radaɗin ba ,shi kad’ai ya san me yake fuskanta me ya ke ji a cikin zuciya da ranshi! Babu wanda ya lura ba kuma wanda ya sani amman a ko wacce rana ta duniyar nan yana fuskantar azaba mai tsanani ne. …….. Tun ranar da Yassir ya je d’akin Kausar ya tarar da ita suna magana da Yassira…..tun daga wannan ranar bai sake saka ta a Idanunsa ba dan wasan y’ar b’uya ta hau yi da shi gadan-gadan. Sai yau ne tukunna ta daure da kyar ta ce ‘bari dai ta lek’a sa’. Sai chan dare wajajen sha biyu, tukunna ta samu ta lek’a d’akin nasa, ita ala dole za ta yi mai basaja gudun kar ya fahimci komai… Ba yabo ba fallasa ya karb’eta, dan haka ta samu kwarin guiwar zama a kusa da shi suka gaisa tukunna ta ce “kwana biyu ka ji ni shiru, sorry mun d’an sake samun matsala ne ni da Daddy shiyasa ka ga Ina kuka ranar da ka zo, to kuma tun daga ranar bani da lafiya sai yau ne na d’an ji dama-dama,’’ Ta fad’i hakan tana mamakin yadda tun ranar da ya zo ta rufe k’ofa bai nemeta ba, sannan bai sake lek’a d’akin ta ba, ko a waya bai ce mata hi ba, yau kwanaki hud’u kenan. Murmushi kawai ya yi mata ya ce ‘kar ta damu ba komai’ daganan ya d’an ja ta da hira… faram-faram dai haka ya yi mata kamar ba komai. Abu d’aya ne ya bata mamaki ta inda ‘ta nuna za ta kwana a d’akin nasa’ amman sai ya ce mata ‘’its fine(ba komai), ta tashi ta tafi kawai, ita da bata da lafiya ma’’ Itanma daman hakan take so, dan haka ta yi masa sallama daganan ta fice, tanata mamakin sa. Sai kamar bayan mintuna goma da fitar tata tukunna ya d’auki wayarsa ya shiga ya kira wata number, tana fara ringin ya mik’e ya fice ya tsaya a balcony d’insa wanda yake opposite inda ake parking motocin gidan…. Har ga Allah bai shirya yin haka tun yanzu ba! Ya so ace ya bashi wahala ya kassara shi tukunna sai yayi shawara abunda zai yi masa a gaba amma Kausar ta janyo komai, ya lura barin shi a doran k’asa yana numfashi had’ari ne a garesa ta ko wanne fanni!!..dan haka dole a yi gama kawai. Dakyar yana jin yanda tunanin ya sake tunzura zuciyarsa ta fara tafarfasa ya ce ’’ba kowa ta nan, cameras d’in ma na tsaida su Ka yi sauri kafin su yi zagaye.’’ Yana nan tsaye a wajen a yadda ya ke d’aya daga cikin masu yi wa gidan hidima wanda suka gama wayar dashi kenan Ya lallab’o ya je shi jikin motar da Yashjub yake fita aiki da ita kullum ya kunce tayoyi biyu ba duka ba…ya kunce su ta yadda ba za ayi tafiyar mintuna biyu da motar ba tayar gaba da ta baya waenda ya kunce d’in za su fita . Sai da Yassir ya ga Mutumin ya kammala komai ya koma inda ya fito tukunna shima ya koma d’akinshi ya rufe k’ofar balcony d’in, yana jin wani nauyi yana sauk’a daga kan k’irjinsa. Addu’arsa d’aya ‘Allah yasa kar Yashjub ya bashi mamaki gobe ta hanyar chanza motar hawa’ Yayinda a d’ayan b’angaren zuciyarsa yake mamakin Kausar da kuma tunani da lissafin abunda zai yi mata idan zarginsa a kanta ya tabbata, hatta Yassira itama sai ta karb’i rabon ta wallahi, dan ya lura tabbas itama ta san wani abun daman tun ba yau ba! Za su san sun yi wasa da hankalin shi kuwa. ……. A gidan dai ranar Yashjub ne kawai yayi baccin kirki.. Mommy da Baba Larai, za a iya cewa sun fi kowa tashin hankali!Saboda zuwa wannan lokacin su kansu sun san da tahowar auren gadan gadan! Gashi sun nemi ko wacce kalar mafita sun rasa…dan aiki akeyi tuk’ura amma kamar ma rura wutar abun ake yi wanda hakan ne ya sake hautsina su saboda ba su tab’a zaton abun zai gagare su har haka ba. Yahanasu kuwa tana chan shoppping online, dan Yashjub ya sanar mata yadda suka yi da Daddy shiyasa ta fara dudduba kayayyaki tun ayau saboda ta ga babu lokaci. Daddy kuma takaicin abunda Ummi take yi masa ne ya hanasa bacci. Kausar da Yassira ma kowacce a rikice. Ummi takaici da tsanar Daddy ne ya hanata bacci. Munirat kuma d’abiun Yassir ne suka taru suka d’aure mata Kai! Shiyasa ta b’ata lokaci tana Shawara akan ‘ta ci gaba da kula shi ko ta rabu da shi kawai’ ita dama bata da wani abokin shawara dan bata iya hulɗar ƙawance ba ƴar uwarta kuma da Ummi duk fushi sukeyi da ita har yau, sun k’i su sake mata bayaga hakan ma ko da ace sun sake mata d’in ita kanta ta san bata isa ta tunkare su da maganar soyayyar ta da Yassir ba wanda ta san hakan ne ummulaba’isin fushin na su da ita. Yasmeen da Ya’isha suma duk hankalin su a tashe yake,,ga kuma k’unci da tashin hankalin da suka gani tartare a fuskar Mommy da kuma abunda Yashjub da Yahanasu sukayi duk sai hakan ya taru ya b’ata musu rai, shiyasa suma suka gagara runtsawa. Yassir kuwa abubuwa biyu ne suka had’ar masa Na farko yanaso ya kawar da Yashjub saboda komai ya dawo Hannunshi kuma ya na so ya yi hakan da wuri ko dan ya samu ya gano gabas d’in Kausar Amma fa duk da taurin Zuciya irin tashi tun d’azu yake fargaba…ba wai fargabar kashe d’an uwanshi da ya shirya yi ba, Yana fargaba ne akan kar zarginsa akan Kausar ya tabbata dan idan ya tabbata ɗin to bai san me zai ji ba! bai kuma san mai zai zama ba muddin ya tabbatar da cewa ‘Kausar tana son wanin shi, wanin ma yayan shi, sannan har su Yassira sun sani amman suke yi masa rufa-rufa suka munafurcesa’ tabbas ya san in zarginsa ya tabbata hakan ne to ya zama ba shi da kowa a tare da shi kenan dan haka kansa kawai zai ke dubawa ko Yassira da yake ji da ita a matsayinta na tagwayensa ba zai sake bi takanta ba tunda suma basu damu da damuwar sa ba.! Waennan tunane-tunanen da kuma zullumin son ganin gobe ne suka hana shi bacci. Sai da aka fara kiraye-kirayen assalatu tukunna da taimakon shed’an ya samu wani bacci mai d’an karen dad’i ya kwashesa……..