[6/25, 4:05 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/CoSIFObGSJeG4TLAuJwo3J 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 1 Mashin ne yake tafiya a hankali, mutane biyu ne a kan mashin ɗin, mai tuƙawa sai kuma wani farin mutumi wanda yake sanye da jallabiyar fara tas da hular larabawa sai hirami rataye a wuyansa. Tun da suka shigo cikin ƙauyen Ƙundu, mutane suka zubawa mashin ɗin ido ba komai suke kallo ba sai wanda yake goye a bayan mashin ɗin. A tsakiyar garin mashin ɗin ya tsaya kusa da wata majalisa da mutane suke zazzaune. Sakkowa mutumin ya yi yana rataye da wata jaka a kafaɗarsa inda mai mashin ɗin yake miƙo masa jakar da ya ɗora masa a gaban mashin wacce da alama kayansa ne a ciki. Cikin wata murya mai taushi da yake furta hausa kamar ɗan koyo amma cikin furucin akwai ƙalƙala na larabci ya ce "Nawa ne kuɗin" Mai mashin ɗin ya faɗa masa, amma maimakon ya bashi abin da ya faɗa sai ya fito da kuɗi mai yawa daga aljihun ya miƙa masa ya ce ya ɗauki kuɗinsa, yana mai cewa "Wannan kuɗin ma sai da na iso nigeri'a na yi canji, ban san ya lissafin kuɗin yake ba" Ya faɗa yana ɗan shafa lallausan gashin kansa wanda yake haɗe da saje suna sheƙi kana gani ka ga balarabe usul. Bayan mai mashin ya ɗauki kuɗinsa ya miƙa masa sauran, ɗauke da jakarsa ya nufi wajen majalissar nan cikin hausar mai kamar larabci ya ce "Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh ya ahlu hazihil ƙarya" Ya faɗa yana ɗaga musu hannunsa da yake saƙale da carbi yana ja. Duk suka mayar da hankali kansa, suna amsa masa a tare, hannu ya shiga miƙa musu suna musabiha kowa yana jin daɗin gaisawa da balarabe farar fata. Cike da ɗan girmamawa ya ce yana son a kai shi gidan shugaban garin, nan wani ya masa jagora yana cewa gidan mai gari. Balaraben nan yana faɗin "Ayyuwa, mafi mushkila" Da haka suka kama hanyar gidan mai gari, kasancewar yammaci ne, sai suka samu majalisar mai gari a cike da jama,a ana fadanci, mai gari yana zaune ya ƙwame a kan kujera. Ganin farin mutumin nan yana biye da ɗaya daga cikin mutanen ƙauyen sai kowa ya zubo masa idanu, amma bai karaya da kallon ba, ya maje yana ɗan murmushi mai bayyana haƙoransa wanda suke ɗauke da haƙorin makka guda biyu. Mai gari kuwa ya saki baki da idanu yana bin mutumin da kallo, shi in ba a waya ba idan ana nuna hoton ka'aba da yake ganin fararen fata, sai ya ce bai taɓa ganin farin mutum kamar wannan ba. Tun kan su yi magana, mai gari ya yi ƙarfin halin faɗin "Audu daga una ka samo balaraben mutum?" Ya faɗa yana kallon wanda ya rako baƙon. Audu ya hau masa bayanin cewa yanzu aka sauke shi a mashin, kuma wajen mai garin ya buƙaci a kawo shi. Mai gari ya hau faɗin cewa jama'a su matsa su ba mutumin waje, haka Audu ya ajiye jakar a gefe ya koma gefe ya tsaya, suka zubawa baƙo na mujiya. Mai gari ya kalli baƙo ya ce "Barka da zuwa Malam, daga ina kuma wajen wa ka zo" Ya faɗa yana kallonsa, har mai gari ya fara tunanin ya fara yi wa baƙon maganar bebaye, don sai ya yi tunanin ko ba ya jin hausa, amma dai ya san tun da har Audu ya ce ya faɗa musu wajen mai garin zai zo to tabbas yana jin hausa. Har ya ɗauke tsammani sai ya ji baƙo ya yi gyaran murya, ya ciro jakarsa ya ta rataye, Shek ya ɗan sunkuya kaɗan, yana murmushi da kamun kai ya ce “Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu “Ni sunana Sheikh Abu Abdurrahman Al-Yamanini ɗan Yemen ne daga Al-Mukalla. An turo ni nan Najeriya domin taimakawa al’umma wajen magance matsalolin da suka shafi ruƙiyya ta shaiɗanun aljannu, da cututtuka na zuciya da jiki.” “Na karanci ilimin hadisi da ruƙiyya tun ina ɗan shekara 9, kuma Alhamdulillah, na yi aiki a masallacin Umar bin Khattab a can ƙasarmu.” “Ban zo nan domin neman duniya ba, sai dai in taimaka da abin da Allah ya bani. Na riga na shirya tsari na musamman da za a gudanar da ruƙiyya ta jama’a kowace da kuma maganin mantuwa, ruɗu da zalunci" Ya faɗa yana ɗorawa da faɗin “Na riga na fara shirya ruwan da aka karanta masa ayatul kursiyyu da suratul jinn sau 70. Da yardar Allah, wannan ƙauye zai zama mai kwanciyar hankali, dama na samu labarin matsalolin garin nan ne a wajen wani bawan Allah, a inda ya mini kwatance aka sako ni a hanya don na zo na taimaka" “Wannan hidima kyauta ce, sai dai idan wanda aka warkar ya ga dama ya kawo sadaka... kamar yadda ake yi a Yemen!” Yana sunkuyar da kai, jama’ar wurin suna cewa "Allahu Akbar!" Mai Gari yana gyara rawani da kallon mutanensa ya ce “Wallahi wannan ba ƙaramin bako bane, jama'a ku kalli yanda yake fari kamar an wanke shi da ruwan zamzam!” Ya cigaba da faɗin “Ka ce Yemen? To wannan kauyen namu na Ƙundu bai taɓa samun baƙo daga ƙasar larabawa ba. Kai ne farko, to tabbas alheri ya shigo ƙauyen Ƙundu da yammacun nan!” Ya ce ba tare da ya jira cewar kowa ba ya ɗora da faɗin “Mun dade muna fama da matsaloli, mazajen da suka daina kataɓus a wajen matansu, matan da suke magana da kansu, kawai ka ga zabgegiyar mace ta dage tana zance ita kaɗai, yaran da suke kuka ba dalili ba dare ba rana sy damu jama'a muna ta zargin shaiɗanun aljannun nan ne suke buɗe musu maganai(Idanu) Amma yanzu Allah ya kawo mana ƙare kukan ka muna yi wa Allah godiya" Ya kai ƙarshen jawabin yana juyawa ga mutanen da suke kewaye da shi, wanda dama asali a wajen suke zaune da wanda suka zo daga baya. Ya ce daga yau, Sheikh Al-Yamani zai zauna da mu, za a bashi ɗakin baƙi na gidan baƙina da sannan za a riƙa kai masa tuwo da dare da ɗumamen safe, da rana za a kai masa dambu ko fura ni a matsayina na Mai Gari na ɗauki wannan nauyin” Ya ce yana gyaran zaman rawaninsa, don a nasa ganin ya ƙure iya ƙurewa. A ɓangaren mutanen wajen suna jinjinawa Mai Gari bisa namijin ƙoƙarin da ya yi, amma a zucuyar Sheik ba haka bane, ransa ne ya ɓaci jin an ambaci tuwo da dambu, saboda ba zai lamunta ba, ya baro tuwo a ƙauyensu sannan yanzu ma yake fama da tuwo da dambu. Kai ya ɗago yana faɗin "Ma sha Allah, Alhamdulillahi hamdan-hamdan, sakallahu bil kairi" Mai Gari ya washe baki don furucin balaraben kaɗai ya masa nuna da cewa baƙon ya jinjina masa. Don haka cike da ƙarfin gwiwa ya dubi jama'a ya ce kun ji sai larabceni yake yana mini addu'a wataƙila har da addu'ar zuwa makkah ya mini" Jama'ar garin kasancewar jahilci ya musu katutu suka hau gyaɗa kai, balarabe kuwa a ransa ya ce 'Tashin hankali gobarar gemu, wallahi in na yarda da wannan wawancin in nutse a wajen nan, dole in nemawa kaina mafitar cin daɗi ko na murmure, a kan me zan zo in ke ruƙiyya da ƙarfin tuwo da dambu, wallahi dole na samarwa kaina ƴanci daga cin tuwo da dambu' A fili kuma ya ce "Liy su'alun(Ina da tambaya) Ya faɗa yana ɗaga yatsa, duk da basu san mai ya ce ba, don shi ma kansa ba wai ya ƙware bane a larabcin, larabci ne na ƙarfin hali da ya zauna yake koya a wajen wani saurayi, sannan a ƙamus na larabci mai fassarar hausa yake ƙara samun ƙwarewa. Mai Gari cike da ɗan razana yake kallon baƙon balaraben nasu, don bai san wannan larabcin da ya yi ba cike da ƙarfin hali ya yi namijin ƙoƙarin faɗin "Ya Sheik, mene ne sussu,aliy(Liy su'alun yake nufi). Balarabe ya ce "Ina nufin ina da tambaya" Murmushi ya yi ya ce a zuciyarsa 'Allah sa dai ba wata tambayar ƴar ƙure zai mini ba, ni da ko bihim ban sani ba a yaren larabci, kai ko cewa aka yi zo in kashe ka Mai Gari ba sani na yi ba' A fili kuma sai ya ce "Allah sarki mene ne tambayar?" Baƙo ya ce "Na ji ka ce za a ke bani tiwi da dimbo(Tuwo da dambu yake nufi, amma cikin ƙalƙalar larabcin rainin hankalinsa ya ce tiwi da dimbo shi a dole bai san tuwo ba. Shiru Mai Gari ya yi don bai fahimci komai ba, sai da Audu wanda ya rako baƙon da yake ya fahimci manufar Sheik sai ya ce "Yana tambayar tuwo da dambu" Mamaki ya so kama Mai Gari amma kuma da ya yi tunanin baƙon daga ƙasar waje yake ta larabawa sai ya ce "Ikon Allah na kwance ya faɗi, wallahi an samu akasin lissafi Malam abincinmu ne na hausawa, mu nan duk wanda bai san tuwo ba sai muke ganin kamar saɓo ma ya yi, don shi muka ci muka girma kuma shi muke ci har yanzu" Ya Sheik ya ɗan yatsina fuska ya ce " La a'alamu hazihil ism(Ban san wannan sunan ba) Shiru Mai Gari ya yi yana tunanin kar baƙon ya ɓaro masa wani gagarumin abu tun da shi ya ce zai ke ciyar da shi saboda bajinta. Sheik ya ce "Mu a namu ƙasa dajaja wato kaza safe da rana dare sai mutum ya ci, kuma muna shan shayi mai kauri wanda madara ta isa sosai, bama cin komai bayan wannan sai shimkafa ƴar gwamnati ta buhu" Ya faɗa yana ɗago carbi ya shiga ja. Mai Gari gumi ya shiga haɗawa, kasancewar duk kiwon da ake a gidansa ba a ci ko tattabara ba a ci bare kaza, idan har an yi yanja a shekara ne ake layya da sallah, shi ma gudun jama'ar gari su yi da shi, suke ganin yana shugaba bai yanka ba. Kamar ya yi kuka haka ya amsa da ceww za a yi bakin ƙoƙari don ganin an ciyar da Sheik ɗin da abincin da ya saba ci, duk da yanzu ya musu bayanin cewa ya yi wata guda a wani gari yana koyan harshen hausa dakyar ya samu ya ɗan iya, a can garin ne ma ya ji labarin halin da garin Ƙundun yake ciki shi ne ya zo. Sheik ya ga ikon Allah, Mai Gari duk ya rikice saboda tunanin ciyar da wannan baƙo, dan dai babu yadda zai yi tun da yanzu yana yin wani furuci mutanen gari za su ji babu daɗi tun da suna ganin waraka ta zo. Haka mutane suka yi ta tittiɗowa daga gidajensu suna fitowa tamkar wanda ake rabon buhhunan shinkafa, aka kewaye fadar Mai Gari maza da mata da yara, ana ta kallon baƙon balarabe. Sai daf da magriba, Mai Gari ya umarci jama'a da su tafi, haka suka tafi shi kuma ya sa aka ɗauki jakunkunan Malam, Mai Gari da kansa ya taso ya kama hannun Malam domin bai taɓa riƙe ko da rigar balarabe ba, bare kuma hannunsa. Wani irin laushi ya ji hannun Sheik, tunaninsa tsabar zaman ƙasar larabawa ne da rashin aikin wahala, bai san cewa tsabagen shafa mayukan bilicin ne da Sheik ya yi ba da mayuka masu sanya laushin fata duk don cim ma manufarsa ta zama MALAMIN BOGI. Suna tafiya wasu ƙamshin turaruka suna tashi daga jikin Sheik, wanda wannan ƙamshi shi ne yake ƙara tabbatarwa da Mai Gari cewa yana tare da balarabe ɗan larabawa. Suna gaba masu ɗauke da jaka suna biye da su, gidan saukar baƙin Mai Gari suka nufa, gida ne na jar ƙasa aka shafe da siminti, ɗakuna uku ne gidan a share ƙal, kasancewar ba a daɗe da wasu baƙi suka zauna a gidan ba. Ledar tsakar ɗaki ce shimfiɗe a ɗakon, sai katifa mai tudu, nan ne ɗakin da Sheik zai sauka. Mai Gari ya kalli Sheik ya ce "Ya Sheik wannan ɗakin ne za ka sauka a ciki" Sheik da ya ga ɗakin a ransa ya ji daɗi, amma a fili sai ya ce "Wannan ɗakin babu shara!" Haka Mai Gari ya sa samarin da suka ruƙo jakunkunan Sheik suka share tas aka goge, sannan Sheik ya shiga yana faɗin "Alhamdulillah, ma sha Allah" Yake faɗa cikin muryar lanƙwasar harshen larabci. Bayan su Mai Gari sun tafi don Mai Gari ya ce zai kawo mutane biyu da za su zauna a sauran ɗakunan biyu suke taya Sheik zama, amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama ya ce kar a kawo komai ya riƙe ayar Allah ba ya jin tsoron komai. Ɗakin ya rufe ya garƙama mukulli tamkar dai marar gaskiya duk da dama marar gaskiyar ne wanda ko a ruwa sai ya yi gumi. Hular gashin nan nan ya cire kasancewar zafi yake ji, kansa da babu ɗigon ko gashi ya bayyana wanda yake ƙwalƙwal, hatta fuskar babu wani gashin saje da gemu duk ya ɗaye. Jakar kayansa ya buɗe gabaɗaya kayan jallabiyoyi da turaruka masu ƙamshi ne da hulana carbuna, da sauran su, wani zip ya buɗe a cikin jakar kuɗi ya fito da shi ƴan dubu dubu rafa uku, wani murmushi ya saki a fili cikin yin ƙasa da murya da hausa raɗau ya shiga faɗin "Allah sarki Lami uwar ƴan jaraba ana can ana baloƙoƙo ko ya suka ƙare da mai zubin adashe" Ya faɗa yana tuno cewa matarsa uwar gidan ita ce ta shiga adashe ɗauka dubu ɗari biyu sai da ɗaukanta ya zo mai adashe take mata hanya-hanya Lami da ta gaji ta je gidan mai adashe ranar bata nan ta tafi wani ƙauye sai kishiyarta a gidan, tana ganin Lami ta since saniyar mai zubin adashe, tana fitowa riƙe da igiya bata zame ko ina ba sai wajen mijinta Ibra dama cin kasuwa zai tafi haka ta damƙa masa saniyar ta ce ya kai kasuwa ya karɓo kuɗin ta ɗauki dubu ɗari biyun ta, ta ba mai zubin adashe sauran kuɗin ko mai za a yi sai dai a yi ko ta mutu ko ta yi rai bata tsoro. Ibra ya karɓi saniya bayan ya je ya siyar daga kasuwar ma bai hau motar garin Mai mangoro ba, wato can garinsu, sai ya hau wata motar da bai san garin da ,a ta je ba, wannan ne silar barowarsa gida, da kuɗin ya sayi komai da komai na kayan larabawan da kayan magungunan ƙaryar da ya zo da su. Kuɗin ya mayar yana ƴar dariya, yana cewa sai ya zama maloniya a harkar maluntar bogin nan, yadda zai wuce raini idan ya koma ya biya kuɗin saniyar don yana ganin lokacin ko jirgin sama zai iya saya a yadda ya tsara in komai ya tafi daidai kenan, in ba a samu mushkila ba. Mayukan bilicin ɗinsa wanda su ne taimakon farar fatarsa, da ƙwayoyi da yake saya na bilicin har allura ake masa ta sanya fari, duk don ya yi ɓadda kama a cikin fatarsa ta asali. Yanan nan zaune har aka kira sallar magriba, bai ankara ba sai ya ji ana ƙoƙarin turo ƙofa, a kiɗime ya lanƙwasa muryarsa zuwa maganarsa da hausa bata gama kama bakinsa ba ya ce "Waye?" Mai Gari da suke tare da limamin garin ya ce "Ya Sheik buɗe mana mun zo mu tafi da kai, za a yi jam'in sallar magriba" Hannu Sheik ya kai ya taɓo tsakiyae kansa da yake salle babu gashi, ya mayar da kallonsa kan hular gashinsa mai haɗe da gemo da saje tana yashe a ƙasa, ba na wannan ba, magungunan bilicin ɗinsa da ya fito da su ya yi ɗai-ɗai da su. Jin suna ƙara turo ƙofar da ƙoƙarin buɗewa ya mie tsaye babu shiri yana muzurai, a zuciyarsa yana faɗin 'Allah kar ka bari asirina ya tonu ban cika burina ba, wayyo Allah, yau na san matsawar suka gane waye ni ba lallai in fita daga garin nan da ƙafafu ba' Ya faɗa jikinsa yana karkarwa duk ya ruɗe... Yanzu za a fara don ba zan ce an fara ba, yanzu ne za mu fara ƙoƙarin buɗe labarin ma don ko wuri bamu ɗauka ba, kar ku shagala kuna tare da MAMAN AFRAH wacce alƙalaminta ba ya rubuta shirme na san za ku so labarin nan🥰 *MAMAN AFRAH* *09025576222* [6/26, 5:17 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 2 Cikin muryarsa tabakin balarabe da husa bata gama zama a ciki ba ya fara cewa "Afwan, afwan, afwan ya Mai Gari a bani minti biyu ina cikin yin wani aiki ne kuka iso" Ya faɗa yana ambatar hailala da ɗan ɗaga murya yadda za su ji sauti. Mai Gari da liman juna suka kalla, suna jin daɗin furucinsa don sautin hailalar sa yake ya musu nuni da cewa wataƙila yana cikin yin wani aiki ne ko addu,a irin tasu ta manyan malaman larabawa. Malamin bogi kuwa bai yi ƙasa gwiwa ba ya shiga saurin saita kansa, ta hanyar ɗaukan dukan kayan da ya cire a fuskarsa ya mayar, sai da ya saisaita nutsuwarsa sannan ya ɗakko dogon carbinsa hularsa riƙe a hanunsa ɗayan. Har da gyarawa jakankunansa wuri don in ba don an ce sallah za a je ba, to babu mai raba shi da jakar kuɗin nan saboda jin kuɗin yake kamar ransa. Yana buɗe ƙofar ya fito ƙamshin turarensa yana yi wa su Mai Gari sallama, ganinsu ya yi tsaye a gefe suna ta kallonsa kamar sun ga sabon halitta, shi Liman kawai kanannaɗaɗɗan gashin Sheik yake kallo, ji yake ina ma gashin nan lallausa ya dawo kansa, da ya ji daɗi. Ƙofar ya jawo ya kulle ya cire mukullin ya saka a aljihu yana mai cewa "Assalamu alaikum, marhababikum" Ya faɗa yana ɗaga hularsa mai rubutun larabci daga gaban da aka yi da wani golding, shi kansa da za a daɓa masa wuƙa bai san mai aka rubuta a jikin hular ba. Yana ɗora ta a kan hular gashinsa da yake basaja a matsayin gashin sa, sai ya shiga mismis da baki alamar azkar yake. Su kuma amsa masa sallamar suka yi suna washe baki, sun san dai ya musu sallama marhababikum ɗin kuma basu san ma'anarta ba, sai dai sun san ko a hausa ana cewa mutum marhabin, wato dai sai suka saka hakan a matsayin duk barka da zuwa yake musu. Mai Gari ne ya ce "Dama sallah za a gabatar muka zo takanas mu tafi da kai" Sheik ya ce "Laisal mushkila" Kallon kallo aka shiga yi da Mai Gari da Liman, duk da basu san mai ya ce ba sai suka washe haƙora suna haɗa baki wajen cewa "Ai dama shi ya sa ba a gabatar da sallar ba sai an kirawo ka" Murmushin jin daɗi Sheik ya yi don ya fahimci ba ƙaramin ƙasurgumin garin jahilai bane ya dira, kuma ya ji daɗin hakan, domin hakan yana masa nuni da cewa zai ke cin karensa babu babbaka, saboda dole tun da basu san komai a larabci ba wataran kwaɓawa ma kawai zai ke yi, saboda ya samawa kansa kima a wajensu. A fili kuma sai ya ce "Za mu iya tafiya" Turus suka yi don sai suka ji ba za su iya shiga gabansa ba sai dai yake tafiya suna take masa baya, saboda su ba ƙaramin daɗin bayyanarsa a garin nan nasu suke ji ba domin garin Ƙundu yana buƙatar hawa jirgin annabi Nuhu ma'ana suna buƙatar ceto da taimako. Sheik ya ce "Dama ina ɗaki bayan fitarku na yi alwala shi ne nake, gabatar da addu'a domin kawo muku kwanciya lafiya a wannan rana, kowa ya yi baccinsa kun san mu a ƙasar larabawa akwai addu'o'i da ake gabatarwa kullum da dare don samun bacci mai daɗi ga kowa na gari kai har garuruwan da suke kewaye ma, don samun kariya" Mai Gari ji ya yi ransa fari ƙal da wannan batu, ya san addu'a da sadakar ƙuli-ƙulin da ake yi ne a garin ya sa Allah ya kawo musu wannan babban malamin kuma balarabe. Har za su tafi ya tuna bashi da alwala, tun da wacce ya ce musu ya yi faɗa ya yi don ya faranta musu don ya san hakan zai kankaro masa mutunci. Amma saboda gogewa a tsara zance sai ya ce yana son sake alwala, saboda su larabawa suna da yawan sake alwala domin tana kankare zunubi. Haka suka jira shi ya shige bayin a ciki ya yi alwalar ma, saboda gudun cire hularsa wajen yin shafar kai. Yana gaba suna bin sa a baya sai jan carbi yake bakinsa yana kai wa da kawowa alamar ba ya sake da hailala da salatin annabi S.A.W. Tun da suka taho mutane suke ta gaishe da shi cikin girmamawa wannan abin ya ƙara ƙayatar da shi, kuma ya sa kansa ya amsa wani gingirigim don jinsa yake tamkar wani basarake ko mai mulki tabbas zai ja zugar mutane yadda zai samu kuɗi. Sun ƙaraso masallacin inda mutane suna tsaye carko-carko, suna zuwa kowa ya fara darewa ana ba balarabe waje don ya samu sahu kowa yana son tsayuwa kusa da shi. Mai Gari ne a kusa da shi liman sai wani baza babbar riga yake shi ala dole zai jagoranci limanci har da balarabe. An yi sallah an idar, sai da aka yi isha'i sannan kowa ya watse bayan Mai Gari da jama'ar gari sun yanke shawarar naɗa Sheik a matsayin limamin garin, abin ya yi wa liman ciwo amma ya danne tun da ya san babu yadda za a yi a saurare shi tun da yanzu kowa yana ganin Sheik ya zo zai kawo musu waraka daga cutukan da ake fama da su a garin. Bayan Mai Gari da liman sun raka Sheik gida masaukinsa, Mai Gari ya ce za a kawo masa abinci yanzu nan suka masa sallama suka tafi, liman yana ta muzurai za a ƙwace masa matsayinsa na liman yana ganin hakan zai rage masa kima a idanun mutanen gari. Mai Gari yana komawa gida ya je wajen matarsa da take dafa kazar da aka kama cikin kajinsa aka yanka, yana hango tukunya a kan wuta ransa ya ƙara ɓaci don ya tabbatar kafin Sheik ya bar garin nan sai ya nakasta masa dukiya sai dai ya ci alwashin sai ya yi ramako don kadararsa da kuɗinsa ba za su tafi a banza ba. Bayan an gama aka juye a ƙatuwar samira, sai tururi yake, ƙamshi yana tashi Mai Gari sai haɗiyar yawu yake saboda rabon ya ci wani abu mai suna nama har ya manta. Ɗaki ya shiga da kwanon da kuma jug ɗin da aka sayo shayi a wajen mau siyar da shayi, aka zuba madara haɗin kauri, buɗewa ya yi ya saka a gaba yana kallo, a haka matar tasa ta shigo, ganin haka ta ce "Mai Gari ya haka, kai da za a kai wa baƙo abu ka zauna ka saka a gaba, kana kallo kamar ka samu wata sabon kamawa?" Yawun da ya taru a bakinsa ya haɗiye, kamar zai yi kuka ya ce "Dama ina kallo ne saboda in kore kwaɗayin da nake ji" Ta ce "Haba dai dama kallon abu yana kore kwaɗayi?" Ya amsa mata da cewa haka ne. Tana fita ya kasa jurewa, cinyar kaza ya ɗauka guda ɗaya, zafi ne da ita dakyar ya ɗauka, ya kai baki ya ciri tsokar ya cika baki da ita kamar daga sama sai jin takun matarsa ya yi da sauri ya rasa inda zai saka cinyar kazar kuma ba ya so ya mayar cikin kwanon a kai balarabe ya gani an ci ko ma dai ya ce ba zai ci guntun baƙar fata ba, ya san kuwa shi ne a ciki tun da dole a kama wata kazar a yanka a dafa, in ba haka ba jama'ar gari su yi da shi a ace abu ya gagare shi. Da sauri ya kai hamatarsa da yake ƴar shara ce a jikinsa sai ya zamana hamatar a buɗe ai kuwa yana saka naman nan mai zafi ya danne hamatar ya matse ta, ya yi saurin goge hannun a jikin rigarsa. Bidik Asabe matar Mai Gari ta shigo ɗakin ko sallama babu, muduk Mai Gari ya haɗiye naman bakinsa da sauri ba tare da ko taunawa ya yi ba, gashi da zafi duk ya ɗane harshe. Tana shigowa ta ce "Mai Gari ga Audun ya zo" Idanu ya ɗan runtse jin zafin naman da yake ratsa hamatarsa ya buɗe idanun cikin ɗan gigicewa ya ce "Gonar za su tafi yin shuka?" Galala ta saki baki tana kallonsa ta ce "Haba Mai Gari lafiyarka kuwa? Mu da ba a damuwan muke ba wane irin tafiya gona, kai fa ka ce a kirawo shi zai kaiwa baƙo abincin" Wata ƴar dariya ya saki yana sosa ƙeya da ɗaya hannun nasa ya ce "Allahu akbar ashe fa haka aka yi ina jin mafarki na yi" Ya faɗa yana tura mata kwanon da jug ɗin gabanta, saboda ya matsu ta fita ya cire naman hamatarsa ko ya samu sauƙin raɗaɗin zafin yaji da na wutar da suka haɗe masa. Kallonsa take da mamakin jin furucinsa da sauti ta suri kwanukan ta fito daga turakar tasa, tana tunanin ko dai aljannun garin Ƙundu sun fara taɓa Mai Gari. Audu ta ba kwanukan ta juya ta shige ɗakinta gudun tsautsayi ko ɗakin Mai Gari bata koma ba, a yadda ta ga yanayinsa ta fara tsoron ya mata wani abu. Mai Gari tana fita fa sauri ya ɗaga hamatarsa, naman faɗowa ya yi, amma tsabar raɗaɗin zafin barkono da na wutar bai bi ta kan naman ba, illa barin hamatar da ya yi a ɗage ya karkata bakinsa ya shiga hura iska a hamatar ko ya samu salama. Haka ya dinga yi sai da ya ji sawaba, sannan ya ɗauke naman ya cinye ya taune ƙashin ya haɗiye, fitowa waje ya yi yana ƙwalawa matarsa kira, bakam ta fito daga ɗaki tana ɗan ɗari-ɗari da shi, sai cewa ya yi "Asabe anya baki cika yaji a wanann dahuwar naman ba?" Shiru ta yi tana kallonsa da mamaki ta ce "Yaji kuma Mai Gari? Kai da baka ci ba ya aka yi ka sani ko dai baƙon ne ya faɗa ya ce an cika yajin?" Sai sannan ya fahimci ya yi ɓaran-ɓarama cikin wayincewa ya ce "A'a fa, kawai dai tun ɗazu nake atishawar yajin da na shaƙa garin jin ƙamshin naman" Baki ta taɓe ba tare da ta ce masa komai ba, ƙuri ta yi wa ƴar sharar jikinsa ganin wani abu kamar man miya, fuska ya ɗaurr ganin tana kallonsa gudun kar ta harbo jirginsa, don haushinta ma yake ji da ta zo ɗakin bai kurɓi shayin nan mai madara ba. Ruwa ya cika a buta ya wanke hamatarsa da klin, don ita matarsa ɗakinta ta koma. A ɓangaren Audu tun da ya je gidan da aka sauki Sheik, ya shiga rafka sallama ganin Sheik ya rufe ɗaki, Sheik kuwa tun daga sallamar ya ji yawunsa ya tsinke don ya gane saƙon abincinsa ne ya zo. Sai da ya ɗan yi jim sakamakon mayar da mayukan bilicin ɗinsa da yake shafawa, don dama yana shafawa da dare sai ya kwana da su, saboda an ce masa man ya fi bin jikin fata in ana kwana da shi. Ƙofar ya buɗe ya fito yana cewa. " Man yatahaddas(Waye yake magana?) Ya ce yana ɗan ƙara fitowa . Audu da bai san mai aka ce ba ya juya da gayya zai koma, tun da ya ga ba hausa zai masa ba shi kuma babu abin da ya sani na larabci. Cikin sauri Sheik ya fito ko takalmi babu yana faɗin "Ya za ka koma gani fa ko ba wajena ka zo ba" Audu juyowa ya yi yana mamakin ɗan rikicewar da malamin ya yi ya ce "Dama abinci ne Mai Gari ya ce a kawo maka" Karɓa ya yi yana ta wasu zantukan larabci da shi kansa Sheik ɗin bai san mai yake faɗa ba, Audu kuma sai ya ji abin ya birge shi, saboda a rayuwa yana spn ya ji yana wani yare da ba hausa ba sai dai bayan hausa bai iya komai ba. Sai da ya juya zai tafi, malam ya ajiye kwanukan ya bi bayan Audun wannan karon fa hausa yake zabga godiya, saboda tsabagen rowa so yake Audun yana fita ya rufe ƙofar gida, don kar wani ma ya zo yana cikin cin naman shi kuwa ba zai bayar ba. Audu sallama ya masa zai tafi ganin ya kama ƙofa zai rufe Audu ya yi gyaran murya cikin yin ƙasa da murya ya ce "Malam da kake barin ƙofar gidan nan a buɗe, in son samu ne ma har ƙofar ɗakin da kake ciki, idan ma ba damuwa da sai ka ce a baka masu tayin kwana..." Tun kan ya kai ƙarshen maganar Sheik ya katse shi da faɗin "Ni bana buƙatar kowa ya zo ni kaɗai ma zan zauna" Ya faɗa a fili a zuciyarsa kuma ya ce 'Aikin banza mutane da shegen kwaɗayi da son samu kuke, wato ka ga an haɗo kayan daɗi an aiko mini shi ne za ka yi dibara don in ce ka zo ka kwana wato duk wani abin daɗi in ke kasawa ina baka, to alharam giya a gidan liman' Audu ya ce "Malam wannan gidan da kake gani gidan kakan Mai Gari ne, mutumin nan ya kashe shekaru masu yawa a duniya kafin ya mutu, tsabar tsufa da kuma malamin tsubbu ne mai aiki da aljannu sai da gabaɗaya jikinsa ya yi fari gashi..." Sheik ya kalle shi ya ce "Audu ni fa ban tambaye ka tarihin Kakan Mai Gari ba" Ya katse masa hanzari. Audu ya ce "Ba tarihi nake baka ba, abin da nake faɗa maka ya danganci zaman ka a gidan, wato duk jikinsa sai da ya yi gashi farin gashi, ko da ya mutu aka binne shi kullum sai raminsa kabarinsa ya buɗe wataran a gan shi a wajen kabarin, to a ƙarshe dai sai rami aka masa a cikin gidan nan aka binne shi, ka ga wancan zagayen da aka saka langa-langa to kabarinsa ne a ciki, kuma gidan nan matattarar aljannu ne, tun daga ranar da ya mutu cutuka suka baibaye garin Ƙundu, aljannu suka addabi jama'a mutane ɗai-ɗai ne basu da aljann... Gaba ɗaya Sheik ya jiƙe sharkaf da gumi, tsabar ruɗun da ya saukar masa a zuciyarsa, hatta jikinsa ya ɗan fara karkarwa amma bai bari Audu ya fahimci hakan ba, idanunsa duk sun faɗa tamkar wanda ya yi sati bai ci abinci ba, bakinsa ya haɗa kalmomi yana shirin faɗin wani abu sai ya tsinkayi maganar Audu yana faɗin "Ni zan koma sai da safe" Tsabar rowa da Sheik yake da ita sai dai ya ji duk da haka ba zai gayyaci kowa a taya shi kwana ba, musamman ma da ya san ya riga ya cewa Mai Gari shi kaɗai zai kwana ya riƙe ayoyin qur'ani. Har Audu ya juya cikin haɗo jarumta ya ce "Kuma baƙin da ake saukar da su a gidan fa?" Audu ya ce "Basa yarda su kwana su kaɗai, sannan duk da haka suna faɗawa ƴan garinsu kaima ina ga abin da ya sa Mai Gari bai maka bayani ba saboda ya ga kai babban malami ne" Kai ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, a haka Audu ya tafi ya bar Sheik, dakyar ya iya kara ƙofar kamar dai ya jinginata amma bai rufe ta da ƙarfi ta rufu ba, bare a yi maganar saka sakata. Yana juyowa daga zauren idanunsa suka sauka a kan kewayen langa-langar da aka ce kabarin tsohon nan ne, ƙwiiiiwitttt wata tusa da bai shirya fitowarta ba ta ƙwace masa, tsabar tsoratar da ya yi amma dai zai yi iya yinsa ya ga bai kunyata kansa ba, wajen cikar burinsa na zama Malami a garin, tun da neman kuɗi ya fito dole ya jure. Kwanukan ya ɗauka ya shige ɗaki ya rufo ƙofa, amma bai kulle ba, domin ya tsorata da furucin Audu na cewa akwai kabari a gidan, sannan akwai aljannu. Duk halin da yake ciki yana buɗe kwanon kaza sai ya manta komai, romo ya dangwala ya ɗanɗana wani ɗanɗanon farin maggi da na daddawa ya ziyarci harshensa, tuni ya tashi yana wata rawar larabawa yana juyi a tsakiyar ɗakin, gijif ya faɗa kan katifa a reran tsabar murna, ya tashi ya dawo gaban kwanon, ƙuri ya yi wa kazar yana ɗakkowa yana ɗorawa a kan marfin, tsaf ya irga sai ya ga babu cinyar kaza guda ɗaya, tsaki ya ja a ransa yana ayyana don maita sai da suka taɓa masa, amma dai zai sanar da su cewa su a ƙasar larabawa idan za a ba malami kaza kai da ƙafa kawai ake fitarwa amma ba a cire wani sassa ya faɗa saboda ƙarfin hali. Tas ya cinye ya shanye wannan ruwan shayin mai uban yawa, dam ya ji cikinsa yana sakin gyatsa, ta window ya miƙo hannunsa ya wanke, da yake akwai ruwa a ɗakin. Sai da ya gama danne-dannensa a waya, sannan ya cire hularsa da saje haɗe da gemu ya ajiye, rigarsa ya cire daga shi sai gajeran wando, kan nan sai sheƙi yake, magungun ƙwaya na bilicin ɗinsa ya sha, ya kwanta, ya yi ɗai-ɗai a kan katifa, a take ƙoshin da ya yi da kuma samun ɗaki mai iska ya sanya bacci ya yi awon gaba da shi, ko addu'a bai yi ba, shi ya sha'afa ma da maganar da Audu ya faɗa masa. Yana cikin bacci ya fara mafarki da ƴan garin a mafarkin suna cewa "Sheik, wannan gidan... uhm... ka dai dinga karanta ayatul kursiyyu da suratul Jinn a kai -a kai. Saboda kowa ya san gidan…” Duk a mafarki ne amma sai da gabansa ya faɗi Cike da ruɗewa ya ce " Mai gidan yake? Sheik ya tambaya yana jan carbi da azama. "Dama... Uhmm... Komai lafiya ne. kawai gidan yana da...” Ba a faɗa masa mene ne a gidan ba ya farka daga nannauyan mafarkin, gabaɗaya ya haɗa gumi gabansa sai faɗuwa yake. Lalume ya hau yi a jakar kayansa, ya ɗakko wata rigarsa wacce ta fi jallabiyar da ya cire tsawo, zai saka amma sai ya kasa saawa kasancewar ta wuyan rigar yake ƙoƙarin sakawa, ganin bashi da nutsuwar sakawa sai ya rataya ta a kafaɗa, ko sallaya bai shimfiɗa ba ya zauna a ƙasa ya kalli gabas yana karanta “A'uzubillahi”Har sai da numfashinsa ya fara daidaita. Yana cikin wannan halin sai ya ji ƙara daga ƙofar ɗaki "Gum, gum, gum!" Sheik ya yi firgigit! Ya miƙe yana ƙoƙarin lalumo wayarsa sai kawai ya kara ta a kunne yana faɗin "Wayyo Mai Gari a kawowa Sheik ɗin yemen ɗauki" Ya faɗa cikin raɗa, sai lokacin ma ya tuna bashi da number Mai Garin ashe. Wata iska mai sanyi ta fara ɗaga labulan windown, sai ya hangi wani haske kamar walƙiya ya wulga, sai ya ji ana buga katako. Sheik ya miƙa hannu ya ɗakko wani littafi da yake yashe a tsakiyar ɗakin, duk tunaninsa ba qur'ani ne saboda tsabar ruɗun da yake ciki, buɗewa ya yi yana karantawa, kawai yana girgiza kai yana cewa “Wallahi ni dai ban taɓa ganin irin wannan ba a ce ba damina ba ana walƙiya Allah mun tuba" Ya faɗa yana ɓarkewa da kuka marar sauti, sai dai har yanzu bai ji yana da na sani a kan fitowa harkar maluntar bogi ta cutar mutane ba. Yana a haka sai ya ji kamar ana tafiya, ma'ana ya fara jin taku a tsakar gidan, bai san lokacin da ya yi cilli da littafin hannunsa ba, shi da yake kallon gabas sai gashi ya juya zuwa yamma, bakinsa yana kaiwa da komowa, wannan karon, babu ƙalƙalar larabcin bogin nasa hausa ce sak yake yi babu lanƙasa, shi kansa bai san mai yake faɗa ba. Yana cikin wannan hali ya ji wani sauti ana cewa "Sheeiiiik Ibra mun san kai ba malamin gaske bane na bogi ne, to ka sani muna sane da zuwanka wannan ƙauye" Shi da yake zaune ya kalli yamma, bai san ya tashi ba sai ganinsa ya yi a tsaye ya kalli kudu ƙafafunsa, suna barazanar kasa ɗaukansa, saboda karkarwar da suke, tunaninsa ɗaya wai aljannun ne suka san da haka ko kuma shi tsohon da aka binne ne ya yi fatalwa? Tun da gashi har sunansa na asali an kira shi da shi wato Ibra. Wannan yasa Sheik ya buɗe ƙofar ɗaki da sassarfa, ya fito yana kwalalo ido kamar wanda ya yi fashi aka kama shi. Ya yi gigin barin gidan da sassarfa. Cikin sanɗa ya fito daga ɗakin daga shi sai gajeran wando, da rigarsa rataye a kafaɗa, Yana fitowa ya ji gidan ya ruɗe da surutai kamar ana wani gagarumin taro, bai tsaya wata-wata ba ya durfafi hanyar ƙofar gida, sai lokacin ya tuna lokacin da ya ɗauki wayarsa ta kawo haske ya ga ƙarfe biyu da rabi na dare, amma da bala'in da ya fara fuskanta a gidan gwara ya fita. Cike da tsoro ya buɗe ƙofar gidan, shiruuu garin tamkar babu kowa sai carar zakaru da yake tashi da kukan dabobi lokaci zuwa lokaci. Yana fitowa ya kalli, gabas da arewa ya ɗaga ƙafa zai fara sheƙa gudu ya tuna kansa babu hularsa ta gashin larabawa mai haɗe da saje da gemu, sannan ƙafarsa babu takalmi, uwa uba a tuɓe yake bashi da riga don bashi ma da nutsuwar saka rigar da take rataye a wuyan, amma dai ya san ba ƙaramin abin kunya bane ya tafi cikin gari a haka a zo a ganshi da kai a ƙwalƙwale, kai sunan zuwansa a haka mutuwa kusa don batu ne wannan na tonuwar asirinsa, yana a wannan halin na cewa ko ya koma ya yi shigarsa ta balarabe, in ya so ko gidan ne sai ya ce a sauya masa, duk da bashi da hujjar da zai faɗa a sauya masa tun da shi dai ba zai ce yana tsoron aljannu ba, a wannan yanayin ne ya ji an ce "Sheik, baby nah ina jiranka mu je mu kwanta" Idanu ya zaro yana mai juyawa inda ya ji sautin wato ƙofar gidan da ya fito, wata budurwa ce tsaleliya riƙe da fitila mai haske, tana sanye da sari na indiyawa" Ga birni ga ƙauye, shi dai ba zai koma gida ba tun da ya san dai budurwar nan aljana ce, sannan ba zai je cikin gari a haka ya bugawa mutane gida ba, tun da gidan kusan shi ne na ƙarshe a inda yake, ganin ta doso inda yake sai fitsari ya suɓuce masa, ya fara sakin wata tusa mai ƙara a kai- a kai... MAMAN AFRAH 09025576222 [6/28, 6:21 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 3 *ƘAUYEN MAI MANGWARO* Lami matar Sheik tun daga lokacin da ya tafi take cike da tsammanin jiran dawowarsa, tana son idan ya kawo kuɗin nan ta ɗauki nata ta mayarwa mai saniya nata, shi ma Ibran ta sammasa wani abu daga ciki saboda ta san shi da idon son naira. Tun bayan sallar la'asar motocin kasuwa suka fara dawowa, tun daga lokacin take ta sintiri wajen da motocin suke sauka amma duk motar da ta kawo mutane bata samub mijinta a ciki,duk sai ta shiga damuwa tana fatan dai ba saniyar ce bata siyu ba, ko kuma ta ƙi yin daraja shi ya sa bai dawo da wuri ba, duk da ta san ta faɗa masa ya siyar ko ma nawa ne ita ba asarar ta bane indai ta ɗauki kuɗinta. Dab da magriba tana tsaye riƙe da tsantsa ta rasa mai yake mata daɗi, don zuwa lokacin hankalinta ya fara tashi, tana tsaye kamar daga sama sai ta ji an fisgi kafaɗarta, juyowarta ke da wuya idanunta ya sauka a kan Jummai tudun adashe, tana wani muzurai sai huci take kamar kububuwa. Rai Lami ta haɗe itama tana aika mata harara, cike da masifa Jummai ta ce "Lami ashe baki da hankali ashe tunanin yara ne da ke, saniyar marayun kike je kika kunce? Ina kika kaita, kin san dai tsohon mijina da ya mutu gadon ƴaƴana da aka bani na saya saniyar nan tun tana ƙanƙanuwa na kiwata musu ita, a kan wani kuɗin adashe ki je ki since mini ita?" Ta faɗa tana dawowa gaban Lami har zanin Jummai yana neman kuncewa ta gyara. Kallon ko in kula Lami ta jefe ta da shi ta ce "Wato kuɗin adashe ba kuɗi bane ko? Saniyar marayu ita ce abun kirki da tattalawa... Katse ta Jummai ta yi da cewa "Ni ba wannan ba mu je ki bani saniyar nan tun muna mu biyu kin dan dai ta marayu ce na faɗa miki" Wata dariyar rainin wayo Lami ta yi ta ce "To sai su ɗauki na annabawa, ki jira dawowar Ibra mijina daga kasuwa in ya kawo kuɗin saniyar sai in ɗauki kuɗin adashena in baki ragowar in ya so sai ki sayi wata ƙaramar ki kiw... Tun kafin Lami ta ƙarasa Jummai ta wani zaro idanu tana dafe ƙirji ta ce. "Kanki ɗaya kuwa Lami?Saniyar kika bada aka kai kasuwa?" Ta faɗa cike da takaici dama dawowar ta kenan, aka faɗa mata ko gida bata je ba ta kama hanyar gidan Lamin shi ne ta hange ta tsaye. "Ras kuwa, ai da nake kai miki kuɗin zubin adashen kike karɓewa baki taɓa sanin kaina ɗaya ne ko ba ɗaya ba sai yanzu da na ɗauki saniya" Masifa Jummai ta shiga yi tamkar za ta hau Lami fa duka, ita ma da ba kanwar lasa ba suka haɗu suna yi har mutane suka fara taruwa ana basu haƙuri, Jummai tana cewa ko Ibran ya dawo da kuɗin daga kasuwa sai ya koma ita saniyar ta kawai ta sani. Wani dattijo yaa basu haƙuri a kan a jira Ibra ya dawo amma har motar ƙarshe ta kasuwa ta dawo amma babu Ibra a ciki, nan hankalin Lami ya tashi don ta fara wani tunani da ban, sai da ta samu wani direban motar shanayen da Ibra ya shiga ta tambaye shi, nan yake ce mata suna sauka a kasuwa ko cikin kasuwa Ibra bai shiga da saniya ba, aka fara tayawa, nan ya samu wani ya saya ya bashi kuɗin don har la'ada ya bayar.Ya ce wata mota ma Ibra ya shiga, don a yanayinsa ma bashi da niyyar komawa Mai Mangwaro. Jummai kamar ta yi hauka sai zage-zafe da tsinuwa take, amma kuma tana riƙe da mayafin Lami a kan cewa ƙafar Lami ƙafarta sai ta nemo Saniya, magana ya girmama har gaban mai gari. Bayan an faɗawa mai gari komai, sai ya rasa ma yadda za a yi da Ibra tun da komai dai na maganar yana hannunsa, don haka sai mai gari ya aika wani yaro ya zo da Tasallah kakar Ibra, yaron da zuwansa ya samu Inna Tasallah tana kwance a kan tabarma daga yin sallar isha'i ta ɓingire a kan sallayar. Sallamar da saurayin yake rafkawa ita ta falkar da ita daga ɗan baccin da ya ɗauke ta. Bayan ya gaishe ta ya ce "Inna saƙon kira ne daga fadar mai gari" Inna warai ta ware daga ɗan baccin, tana zaro ido da mamaki ta ce "Idirisu Allah sa dai lafiya, ya za a yi a ce mau gari yana kirana da wannan daren?" Idrisu ya ce "Inna Ibra ne dai yake son tada miki zaune tsaye, ya karɓi saniya a wajen Lami, kuma saniyar ta Jummai ce, kasuwa Lami ta ce ya kai ya siyar amma har kowa na kasuwa ya dawo amma babu Ibra, yanzu dai suna can gufane a gaban mai gari Jummau ta ce sai an biyata" Salati Inna Tasallah ta shiga zabgawa tana tafa hannuwa ta ce "Wannan yaro an yi taƙadari, yanzu Ibra ina zai je da saniyar mutane, a ce mutum ya girma bai san ya girma ba, yanzu a ce mutum da iyalinsa shi ba wani yaro ba amma sai jan rigima, ni yanzu ai ni ya tsunduma a masifa, ni da ko kaza bani da ita, wallahi Ibra albasa bata yi halin ruwa ba, iyayensa mutanen kirki ne amma tun da suka mutu nake jigila da shi, tun yana yaro bai barni na huta ba" Ta faɗa tana fashewa da kuka irin na tsofaffi. Haƙuri Idrisu ya shiga bata, taba goge idanu tana face hanci ta shiga ɗaki jim kaɗan ta fito da wata roba mai ɗan girma tana riƙe da ita, waje suka fito ta saka mukulli ta kulli gidan, suka farw tafiya ta shiga faɗin "Wannan kalwa da barkonon da kuka da suke cikin robar wannan su kaɗai ne mallakina a duniyar nan, su nake kira suke amsawa, yau ban da cinikin naira ɗari ban yi ciniki ba, ita ma ɗarin gata nan a cikin robar, idan mun je ko da an buƙaci wani abu daga gareni in biya kuɗin saniyar sai in juyewa mai gari wanann kayan don su kaɗai ne da ni. *GIDAN ALHAJI ADNAN JIBO* Hajiya Nuritya ce zaune a tangameman falon ta da ya gaji da kayan alatu, tana zaune ta harɗe ƙafafunta hannunta riƙe da waya ƙirar iphone 16 pro mx sai wani ɗan yatsina fuska take lokaci zuwa lokaci. Shigowar mai aiki falon ɗauke da tire wanda aka ɗora plate da ta yanka kayan marmari, ko sallamar da ta yi bata amsa ba, haka ta ƙarasa gaban Hajiya Nuriyya ta durƙusa ta ajiye tiren tana mai cewa "Barka da hutawa Hajiya, na kammala yankawa" Shiru Hajiya ta yi bata amsa ba, kamar ba za ta yi magana ba zuwa can ba tare da ta kalli mai aikin ba ta ce "Ki je ɗakin Rahma ki sanar da ita kin gama yanka mata" Da to ta amsa cike da girmamawa, sama ta haura ta je ƙofar ɗakin ta tsaya, tana tsoron ta ƙwanƙwasa ta yi laifi, amma haka ta daure son babu yadda za ta iya tun da in bata sanar da ita ba ɗin ma, laifin ne gwara dai ta sanar ɗin. Kamar tana jin tsoro haka ta shiga ƙwanƙwasawa a hankali, duk don gudun laifi" Sau biyu kawai ta buga sai ta dakata tana jiran jin amsa, tun da ta san dai in har idanun Rahma biyu to tabbas za ta ji bugun sai dai amsar ce sai an kai ruwa rana. Sai da ta ɗauki kimanin minti biyu zuwa uku tana jira sannan ne cikin muryar Rahma mai sanyi ta ce "Waye?" Cike da girmamawa ta ce "Ni ce Hajiya ta ce an gama yanka kayan marmarin" Cike da izza Rahma ta ce "Na ji" Baki mai aiki ta taɓe tamkar Rahma tana ganinta, juyowa ta yi ta bar ƙofar ɗakin, tana zuwa ta sanar da Hajia ta fita don zuwa ta cigaba da aikinta. Sai bayan kamar minti goma sha biyar, sai ga wata kyakkyawar budurwa wacce ba za ta fi shekaru ashirin ba kuma ba za ta gaza shekara sha tara ba, tana tafiya kamar bata so, sanye take da fararen kaya tas riga da wando a jikin gaban rigar an yi zanen heart da pink colour, sai aka rubuta BEAUTY. Kyakkawa ce ajin farko, sai dai bata da ƙiba, ƙarasowa ta yi ta zauna a kusa da Hajiya Nuriyya, Hajiya cike da soyayya da son nuna kulawa ga tilon ƴar tata, ta ajiye wayar hannun, ta mayar da hankalin ta kanta ta ce "Mai kike so ne eh baby nah?" Ta tamabaya tana kallonta cike da soyayya. Ɗan yatsina fuska ta yi tana ɗan tura baki ta ce "Fruit ɗin ne ba zan iya ci ba" Ta faɗa cikin muryar sangartattun yara. Murmushi Hajia ta yj ta ɗakko ta shiga bata, suna cikin haka sai Alhaji da Yaya Ma'aruf suka yi sallama suka shigo, Yaya Ma'aruf ɗan gidan yayan Alhajin ne a ƙauye yake shi ne ya zo karatu birni ya sauka a gida ƙanin mahaifin nasa. Yaya Ma'aruf mutum mai ibada da kula da addini, yana son ganin mutum yana riƙo da sallah, sai dai kuma ya sauka a gidan kawunsa inda yake ganin ana wata rayuwa ta da ban. Da gudu Rahma ta tashi ta je ta rungune mahaifinta tana cewa "Oyoyo Daddy nah" Yana nuna farin cikinsa ya raba ta da jikinsa yana riƙe da hannunta yake cewa "Oyoyo baby fatan kin ci abinci" Ɗan tura baki ta yi ta ce "Ban son cin abinci yau Daddy fruit nake ci" Murmushi ya yi yana riƙe da ita suka ƙarasa tsakiyar falon. Yaya Ma'aruf cike da girmamawa ya shiga gaishe da Hajiya, amma ta amsa kamar bata so, don ita har yanzu kallon wanda bai waye ba take masa, kallon baƙauye, ita dama ba don dai ɗan gidan ƙanin mijinta bane kuma mijinta yana jin maganar Yayansa da tuni ta kore shi daga gidan. Ganin Rahma ta tashi tsaye tana wani buga ƙafa alamar ɓaci, wai Daddy ne zai cigaba da bata fruit, da sauri Yaya Ma'aruf ya ɗauke kai, ganin kayan sun kama mata jiki, kuma ya san shi ba muharraminta bane. Sallama ya musu yana shirin juyawa ya ji Rahma tana cewa "Daddy ka ce Yaya Ma'aruf ya miƙo fruit ɗin ka cigaba da bani" Ta faɗa lokacin da Daddy ya zaunar da ita kusa da shi yana lallashin ta yana faɗin zai bata har sai ta ƙoshi. Idanu Yaya Ma'aruf ya runtse jin rainin wayon wannan, ba don yana son ilimi ba, kuma yana da burin ya je garinsu ya kawo musu cigaba daga jahilcin da suke ciki da tuni ya bar gidan nan ya koma ƙauye. Maganar Daddy ce ta katse mata tunani. "Ma'aruf miƙo fruit ɗin can na ƙanwarka" Daddy ya faɗa hankalinsa yana kan Rahma da take ta zuba masa shagwaɓa, yana mugun son ƴar tasa. Haƙori Yaya Ma'aruf ya sanya ya danne leɓensa na ƙasa yana jin takaicin wanann aiken, amma babu yadda zai yi, kasancewarsa mai biyayya, cike da ladabi ya je gaban Hajiya ya ɗauki tiren, Hajiya tana aika masa wani kallo saboda ita kawai bata ƙaunarsa. Sai da ya je zai ajiye amma Rahma ta miƙo hannu ta ce ya bata plate ɗin, ya mayar da tiren kicin. Daddy bai ji daɗin abin da ta yj ba amma babu yadda zai yi don ba ya son abinda zai mata ran Rahma. Haka Yaya Ma'aruf ya danne zuciyarsa ya ɗauki plate ɗin fruit ya miƙa mata ashe dai bata riƙe ba, ai kuwa plate ɗin ya kuɓuce gabaɗaya kayan marmari suka yi masauki a jikin fararen kayan Rahma, duk ruwan kankana ya fito jawur a jiki, tana kallon jikinta ta fashe da wani kukan ɓaci, da sauri Hajiya ta tashi har tana neman yin tuntuɓe, tana zuwa vata yi wata-wata ba ta ɗaga hannu ta saukewa Yaya Ma'aruf yatsunta biyar a kumatunsa, kuncin ya safe cike da mamaki ya ɗago idanu yana kallonta Daddy kuma ya miƙe tsaye, duk da ya ji zafin abin da Ma'aruf ya yi na zubaw Rahma kayan marmarin a jiki amma kuma ya ji haushin marin da Hajiyar ta wanke Yaya Ma'aruf da shi a ganinsa abin da ya yi bai kai a mare shi ba, hakan ya sa Daddy ya ce "Hajiya... *SHEIK* Yana cikin wannan halin wandonsa jargaf da fitsari, ya fara ganin wasu ƙananan yara kamar jarirai amma tsaye suke a kan ƙafafunsu suna doso shi, kusan su goma, da alama daga cikin garin suke, abin da ya tsorashi ma babu wani mai sutura a jikinsa su duka tsirara, bai gama tunanin jinsin mutane ne ko na aljannu ba sai ya ji budurwar nan ta ƙofar gidan da take kiranshi ta ce " Sheik waɗannan ƴaƴanmu ne ni da kai, wanda na haifa maka su daren yau, gasu nan zuwa kowanne ka masa kuɗuba ka raɗa masa suna" Galala yake kallonta, ganin jariran suna dab da zuwa suna faɗin "Baba Sheik" Kawai Sheik ya yanke shawarar ya tsira da rai da lafiyarsa, don da alama wanann yaran suka rafke shi wato suka ɗane jikinsa kowa fisgar inda ya samu zai yi ba lallai su bar shi da fatar jikinsa bama, fakar idanun budurwar yayi kawai sai ya zura da uban gudu, ganin wata kwana sai kawai ya sha kwanar, amma kamar almara sai ya ji ƙarab takun gudu a bayansa, haka ya tabbatar masa da biyo bayansa ake yi, ganin wata bishiya ya yanke shawarar hawa kanta, a nashi tunanin idan ya hau bishiyar in wanda suka biyo shi sun zo sun wuce sai ya sakko in ya so ya gwammace ko gadin gidan wasu ya je ya yi da ya zauna a wannan bala'i da tashin hankali, da shegen kaɗayi da son abin duniyarsa ya kawo shi ciki. Yana hawa bishiyar yana jin wani santsi dakyar ya samu ya haye sai da ya hau can sama, ya samu waje ya zauna, sai ganin jariran nan ya yj sun tasho suna gudu suna kiransa, haɗe da wanann budurwar mai fitila, suka zo suka wuce bishiyar, wata dariya Sheik ya fashe da ita marar sauti a zuciyarsa ya ce. 'Ashe aljannu ma ana iya guje musu, ka ga sakarkaru wato ni ina saman bishiya ku kun wuce kuna kirana, wannan shi ake kira hotiho!' Yana kallonsu har suka yi nisa kifta idanun da zai yi sai ya neme su ya rasa a fili ya ce "Ai indau zan samu cikar burina to da in fallasa kaina a gane MALAMIN BOGI ne gwara kullum in ke kwana a saman bishiya, a to don na ga wajen zama ni sai in ke kwantawa ma a kan bishiyar in kr baro musu gi... Jin an zungure shi daga bayansa shi ne abin da ya dakatar da shi daga maganar da yake, cike da faɗuwar gaba ya ɗan waiwaya, jariran nan ya gani su duka suna kan bishiyar da yake muryar ɗaya mai amo a cikin su ita ta katse shi da faɗin "Baba Sheik muna ta nemanka ashe dai ka zo gidanmu" Jin an ambaci gidansu sai lokacin hankalinsa ya kai ga kallon bishiyar da yake kai a nan ya ga bishiyar kuka ce wato matattarar aljannu" Hawaye ne suka taru a idanunsa, ya tashi dakyar jikinsa yana karkarwa, rigar wuyansa ya ɗakko ya ɗaure tsantsa, bai jira komai ba a fili ya ce "Innal hamda, wal ni'imata laka wal mulk, la sharikala, Allahu akbar! " Yana gama faɗar haka ya yi tsalle ya diro daga saman bishiyar nufinsa sai dai su tsera, da aljannun yaran, amma abin mamaki maimakon ya ji shi a ƙasa sai ya ji shi ya dira a kan hannaye, yana dubawa ya ga wannan jariran ne su duka suka masa ɗaukan makarar mamaci. Babu damar guduwa ya zubawa sarautar Allah ido, don shi kansa ya san riƙon ma ba na jarirai bae, tamkar wanda aka tara ƙattan maza. Suna tafiya suna faɗin "Mama mun ɗakko miki Babanmu" Sheik kuwa sai ruwan ido yake tamkar an buɗe famfo. Suna zuwa ƙofar gidan suka samu wannan dai budurwar, shi bai san wane irin tunani zai yi ba ma. Tana ta musu sannu da kawo Babansu ta matsa gefe suka shige da Sheik yana ji yana gani, suna gama shiga, ta rufe ƙofar gidan ta saka sakata. Ɗakin da Sheik ba a can ya sauka ba can aka nufa da shi, suna shiga suka zaune da shi yana ta kallon ikon Allah, da suka ajiye shi suka fara kama jikinsa kowa yana mamula, guda biyu sun kama breast ɗinsa suna sha wasu kuma jikin fatarsa da babu riga, a zuciyarsa ya ce 'Wai ni Ibra yau ni ɗiyan aljannu suke mamular fatar jikina da bakinsu marar haƙori, har da masu sha mini mama, na ga ta kaina duk tsorona amma yau an ƙure mini gudu' Ya faɗa a zuciyarsa hawaye suna zuba shaaaaa. Yana nan zaune suna ta faman tsotsarsa, idanunsa a rufe don ya lura duk idanunsu babu ƙwayar ido a ciki. Idanun a rufe ya ji kamar daga saman matar nan ta ce "Ka raɗa musu suna ka zo mu kwanta dare ya yi" Cike da faɗuwar gaba ya buɗe, ya ganta zaune a bakin wani gado mai kyau. Haka ya ringa kai bakinsa wajen kunne jariran yana musu gwalan gwalantun larabcin da bai san mai yake faɗa ba bare ya san addu'a ce ko mene ne. Abu ɗaya ya sani duk wanda ya gamawa gwalan gwalantun sai dai ka ji daga ƙarshe ya ce, Mamuda, Lawwali, Amiru a haka ya gama raɗawa kowa suna. Yana gamawa suka tashi suna masa bye-bye suna cewa sai sun dawo, haka budurwar nan ta miƙo masa hannu, wannan karon a zuciyarsa ya ce zai gwada sa'arsa don yadda ya ga za su kaɗaice a gado da aljanna yana tsoron wani abu ya wakana a tsakaninsu ma'ana ta je ta masa cikin gaske, tun da yanzu ma gashi tana cewa ƴaƴan can nasa ne. Ganin ta fara wani abu kamar mai shirin yin dambe sbai san lokacin da zuruf ya tashi tsaye ba, sai kawai ya ga ta fara sawaya ta koma tsohuwa tukuf, a guje ya fito daga ɗakin, ɗakinsa ya shige, yana haki yana shiga ya banke ƙofa ya saka sakata, kan katifa ya faɗa ya ja wani tsohon bargo da ya gani a kan katifar, da gari lafiya ƙalau ne ya san, sai dai ya cewa ƴan garin larabawa basa shiga tsohon bargo, amma yanzu da yake neman mafaka yake gani yake ko cikin kashi aka ce ya shiga babu musu zai shiga kashin in da hali har wanka sai ya yi da kashin.. Tun da ya rufa da bargon nan yake ta faman gumi amma bakinsa sai warto addu'a yake wacce bai san wace iri ba ce shi dai fatansa ya tsira dafa halin wannan, sai ya ji a ransa zai bar garin Ƙundu a gobe amma in ya tuna irin kaji da shayi mai kauri da zai je sha to tabbas sai ya ji zai jure komai. Tun da ya rufa shi ba a kwance ba, shi ba a durƙushe ba kawai dai ya yi goho ya nutsa kansa a katifa, a haka yake ta jin ife-ife da guje-guje wani lokacin ya ji an buga ganga wani lokacin a ƙwala masa kira, fitsari ya yi wajen kala biyar, har sai da aka fara kiran sallar asuba, sannan ya ji komai ya lafa, can kafin shigar masallaci ya fara jin tashin muryoyi a ƙofar gidan, yana ji ana ta bugawa, amma ya ƙi fitowa ma don shi yanzu babu wanda zai kira shi ya je, gani yake aljannu ne, duk da yana ganin rashin fitarsa masallacin asuba barazana ne ga maluntarsa, amma dai a halin da yake duk ya yi wurjanjan, da kuma jiki da fitsari jargaf in ya fita ya buɗe ƙofar abun kunyar sai ya fi na ƙin zuwa masallaci. Sai da ya ga rana ta fito tangararau ya tashi ya fito har lokacin rigarsa tana ƙugunsa a ɗaure, ya since a zuciyarsa yana faɗin 'Wuya in ji tsula, yau malamin balarabe na ƙasar Yemen ya ga ta kansa cikin dare' Ya faɗa yana shafo breast ɗinsa da suka sha damƙa a bakin aljannu. Dakyar yake tafiya haka ya je ya buɗe ƙofar gidan sannan ya shiga ɗaki ya saka hularsa ta gashi da gemunda sajensa, yana gamawa ya shiga bayi ɗaure da towel bayan ya kai ruwa, jikinsa ya shiga sallewa da daddaɗan sabulun bulicin mai ƙamshi, ya gama saɓa jikin bai ɗaureye ba, dib ya ji wani abu ya faɗo daga sama, yana dubawa ya ga kunnen jariri ne. A can ƙofar gida kuwa Liman ne da Mai Gari suka zo da manyan ƙartai za a ɓalle ƙifar gidan a shiga a ga ko lafiya sabon malamin balarabe bai fito sallar asuba ba, kuma an zo an buga masa shiru, sun san dai malamai kamar Sheik ba ya ƙi yin sallar jam'i da gangan ba su da suke ganin an kawowa ƙauyensu waraka daga jahilci, amma har rana ta yi ba a ganshi ba. Ganin kunnen da Sheik ya yi, hakan ya yi daidai da saƙa ƙafa da wani ƙaƙƙarfan saurayi ya yi ya hankaɗa ƙofar gidan, kasancewar Sheik sakatar ya cire bai buɗe ƙofar ba. Buga ƙofar da ta daki bangon bayin shi ya ƙasa assasa tsoro da ruɗanin da Sheik yake ciki, tunaninsa ya bashi aljannun ne suka kawo masa ziyara, don ya san yadda mutanen garin suke girmama shi, babu yadda za a yi su banko masa ƙofa haka har ta gwaru da bango, towel ɗinsa ya fisgo a inda ya rataye ya naɗa a ƙugunsa ko ɗaurewa bai yi ba, ya bazamo da gudu daga banɗakin takalminsa ma ɗaya can ya barshi a bayin, sannan ga jikinsa kumfar da bai wanke ba, fitowarsa a rikice ya nufi ɗaki ko kallon hanyar ƙofar gidan bai yi ba burinsa kawai ya shiga ɗaki ya kulle, Mai Gari da tawagasarsa su Malam Liman ganin abin da yake faruwa sai suka tsorata, sun san duk abin da zai sanya Ya Sheik babban malami balarabe gudu to ba ƙaramin abu bane, ganin shi da ya san qur'ani da ayoyin Allah, da addu'o'i yana gudun ceton rai ina ga su ƙasurguman jahilai. A take aka shiga ƴar tsere zuwa ɗakin Malam inda ya nufa, sai suke ganin nan ne wajen tsira, samari guda biyu sai Malam Liman da kuma Mai Gari aka fara rige-rigen zuwa ɗakin Malam Sheik, shi kuma Sheik sai da yana dab da shiga ɗaki ya lura da tawagar Mai Gari, ganinsu da gudu a kiɗime sun nufo hanyar ɗakinsa alamar kamar an biyo su, sai ya yi tunanin gari ma babu lafiya, tunaninsa su ɗin ma daga waje aka biyo su suka taho wajensa kasacewarsa malami basu san a halin da ya kwana ba, basu san shi bacci ma tun na farkon dare bai runtsa ba haka ya kwana tsakanin waje da cikin gida, yanzu ma yana wanka yana son bayan ya yi wanka ya yi alwala ya yi sallah don yadda jikinsa yake sharkaf da fitsari sai ya yi wanka. To sai kuma aka samu an jefo masa kunnen jariri a banɗakin, bayan ya fito hallaw gashi ya ci karo da su manyan garin su ma sun zo. Da Sheik da Mai Gari aka yi karo wajen shiga ɗaki, shi Mai Gari yana fatan kar Malam ya ƙulla musu salalan tsiya wato ya shige ya banke ƙofar ɗakin, don su tunanin komawa baya ma su fita daga gidan hakan bai zo musu a ƙwaƙwalwar su ba, bare ma sun san tun da aka samu matsala a masaukin malam to garjn ma yana dab da rikicewa, don wani sa'in gabaɗaya aljannu garin suke rikitawa. Karon da suka yi babu wanda ya lura, kowa ta kansa yake, a haka Malam Liman ma ya totsu suka zama su uku a bakin ƙofar suna ƙoƙarin shiga, ƙofar ta musu kaɗan kuma kowanne ya kasa dakatawa wani ya fara shiga. Samarin nan ma suna jira su ma su shige. Malam Liman yana kai kansa suka yi gware da goshin Mai Gari, Sheik ne ya fara nasarar shigewa ɗakin, sai dai da takalmin nan ƙafa ɗaya ya shige santsin ledar tsakar ɗaki ya kwashi Sheik, sai gashi wancakal a gefe, yana ta yaƙi da towel ganin bai masa tsirara ba. Su kuea su Mai Gari basu lura da wani towel ɗinsa ba bare su kawo zai yi wani tsirara, don gani suke tamkar a filin ƙiyama inda ake cewa kows ta kai - ta kai yake. Sheik da rarrafe ya ƙarasa saman katifa, sai Mai Gari da Malam Liman suka mara masa baya, samarin nan ma suna shiga ɗayan ya banka ƙofar, su duka cakuɗe a kan katifar, Sheik ya warto tsohon bargon nan, zai rufa ai kuwa Mai Gari ya ce da wa Allah ya haɗa shi in ba da bargon hannun Sheik ba, nan ya shiga yaƙin warta don ya rufa shi ma, haka Malam Liman ma, ya shiga jan bargon da ya gama shan duniyarsa, kasancewar bashi da ƙwari sai ya yage a biyu, Malam Liman ya ɗauki ɓangare ɗaya, Mai Gari da Sheik suka shiga ɗayan, samarin nan suka totsa kawunansu a babbar rigar Liman... 😂😂😂😂😂 Na ba kaina daria yau Allah sa ju dara amma akwai cakwakiya. Mu haɗu next page akwai gwarama, za ku ji yadda Sheik zai kare kansa saboda rainin wayo, su kuma sai su bada kai bori ya hau. MAMAN AFRAH 09025576222 [7/2, 4:03 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 4 *SHEIK* Suna tunanin samun nutsuwa amma abin ya ci tura!. Abin da yake faruwa shi Sheik ga tsoron kunnen da ya gani a banɗaki ga kuma tunanin yadda ya hango su Mai Gari a sukwane, shi bashi da nutsuwar da za tambaye su ba'asin gudunsu tun da har ya ga suna tseren shiga ɗaki da masu garin to tabbas ya san wataƙila cikin garin yana can a rikice kamar filin yaƙi, kuma ya san kowa shi zai jira, shi ma kuma ga a halin da ya kwana ga kuma a halin da ya falka ko sallah bai yi ba, kenan lamarin garin Ƙundu ba ƙaramin lamari bane in dai a ce aljannu da ranar gari ma sai sun addabi jama'a to lallai akwai sake. Kowa gabansa faɗuwa yake, shi Malam Liman sai yanzu yake jin da na sani da sun juya baya sun koma cikin gari, amma gashi sun shigo wannan gida mai ruɗani bayan sun san cewa wannan gidan shi ne kan gaba wajen matattarar aljannu amma kuma ƙarfin gwiwar tasu shi ne Sheik to shi ma babu yadda yake, sun lura a ruɗe yake ruɗun ma iya ruɗewa, bayan shi suke ganin zai kawo musu ɗauki amma sho ma kamar dai yana neman ɗaukin ne. Mai Gari kasancewar shi kaɗai ne a cikin yankin bargon da ya shiga, duk da a katifa ɗaya suke amma sai yake jin tsoro yana ƙara baibaye shi, ya so a ce bargo ɗaya suke da malam balarabe mai jar fata kuma babban malami wataƙila aljannun sa yi sassauci a lamarin. Samarin nan guda biyu sai numfashi suke ƙasa-ƙasa kwata- kwata a ruɗe suke. Ya Sheik shi idan ya tuna da kunnen da aka jefo masa a banɗaki sai ya ji cikinsa ya murɗa alamar gudawa, yanzu haka yana ta fafutuka wajen danne wata guntuwar tusa da take son ta fito masa wacce yake da tabbacin matsawar ta fito kashi zai iya kuɓuce masa. Wannan dalilin ne ya sa yake ta mutsu-mutsun dannewa, don ya san matsawar ya saki tusar to su Mai Gari za su ji wari kuma hakan kamar zubar da kimarsa ne a matsayinsa na bababan malami, shi ba ma wannn ne matsalar ba yadda suka biyo shi suka cika masa ɗaki, ya san cewa yanzu kowa shi yake son ya kawowa ɗauki bayan shi kansa ta kansa yake. A daidai wannan lokacin kuma ɗaya daga cikin samarin nan ne ya ji ɗayan ya janye masa inda ya rufu don haka ɗan jijjiɓin yaƙi ya kaure a tsakanin su biyun, shi ɗayan so yake ya rufe har ƙafafunsa, shi kuma ɗayan an janye masa don kansa ma yanzu a tantagayyar waje yake, wannan ya sa yake ganin va zai yarda ya ɗauki dala ba gammo ba. Hakan ya sanya suke ta jaye-jaye da rigar Malam Liman wamda fitsari ya cika masa mara, duk fusgar rigarsa ɗaya da suke barazana ne ga mararsa da take cike da fitsari, hakan ya sa ya damƙe baki, a zuciyarsa yana faɗin 'Lahaula wala ƙuwwata, kar ku mini haka ƴan samari, ina zan kai wanann abin kunyar a ce limamin gari guda amma ya yi fitsari a wando, ku taimake ni kar ku kunyata ni' Ya faɗa a zuciyarsa yana wani damƙe idanu tare da haɗe ƙafafunsa waje guda yake fafutukar matse su. Ɗayan ne ya fisge rigar da ƙarfi ya zungura kansa wanda kan nasa yake a saitin mazaunan Malam Liman, Malam liman ana zungurar mazaunansa ya ji guntun fitsari kaɗan ya kufce masa da sauri ya sake haɗe ƙafafun don ya lura in bai yi da gaske ba sai an saka shi ya saki fitsarin nan duka. Hannu ya miƙa ya sakarwar kan wannan saurayin wanda yake kusa da mazaunansa, ya sakar masa ranƙwashi a zuciyarsa yana faɗin 'Shegun yara, kamar da ubanku muka haɗa kuɗi muka sayi rigar, sai ja kuke kamar kun samu guga a rijiya' Ya faɗa a zuciyarsa yana jin da a lafiya ƙalaw ake ko iyayensu ba za su yarda su shiga rigarsa ba saboda yadda yake da kima ana girmama shi, a matsayinsa na Limamin garin. Saurayin nan da Liman ya kaiwa ranƙwashi, zafin ranƙwashin ya saka shi ƙara cukuikuye rigar Liman da gangan, dama shi ne wannan me ƙarfin da aka taho da shi zai buɗe ƙofar gidan, wato ƙaƙƙarfan. Jan rigar da ya yi shi ma ɗaya saurayin yana ta ƙoƙarin ja ya rufe kansa, sai ya zamana gabaɗaya an shaƙewa Liman wuyansa, jin shaƙe wuyan yana barazana ga maƙogwaronsa sai ya lanƙwasa kansa da sauri ya zame kansa daga cikin babbar rigar, hakan ya sa garin ya zame rigar sai kansa ya fita daga cikin bargon da suke tare da Sheik, shi kuma Sheik sai ya ja bargon ya ƙara duƙunƙune kansa, don yana a goho ne duk da yana jin kashin. Samarin nan jin Liman ya sakat musu rigar sai suka cure waje guda suka rufa, tun da yanzu ta ishe su sun rufa tare dama saboda tana jikin Liman ta musu kaɗan. Malam Liman kasancewar a firgice yake kuma a tsorace kansa yana fitowa daga rufar da yake sai idanunsa suka masa gizo da ganin Kakan Mai Gari wanann marigayin da aka binne a gidan, ya tsago jikin ƙofa yana tahowa sanye da likkafaninsa, ya ɗan duƙa kasancewar yana da ƙusumbi. A kiɗime Liman ya nayar sa kansa ya cusa a katifa haɗe da cewa "Wallahi marigayi kakan Mai Gari wato mai ƙusunbi ya tatso ta jikin ƙofa ya shigo ɗakin nan" Ya faɗa yana miƙa hannu a niyyarsa ya samo bargon da ya fito ya shiga, sai ya cafko towel ɗin jikin Sheik, Sheik kuwa jin furucin Liman na cewa Kakan Mai Gari ya shigo ɗaki, hakan ya tuna masa da jawabin da Audu ya masa a daren jiya na cewa Kakan Mai Gari ƙasa ta ƙi karɓarsa da ya mutu, saboda saɓon da yake yi, sai gida aka dawo aka masa kabari aka binne. Kenan wanda ake zuwa maƙabarta ana samun sa yana gefe kabarin da aka saka shi ma a gefe, to ba abin mamaki bane in aja ce yanzu ya taso da ƙafafunsa, wataƙila fatalwa ya yi. Tsabar ruɗanin da Sheik ya shiga yana jin an iska ta fara shiga jikin mazaunansa alamar mazaunan nasa a buɗe suke tantagarya, amma tsoro ba zai bari ya suturta su ba, don shi tunaninsa towel ɗin zamewa ya yi. Samarin nan jin furucin Liman sai suka rungume juna kamar sa zama mutum ɗaya, haka kowanne yake jin bugun zuciyar ɗan uwansa alamar dai ana cikin fargaba da tashin hankali, Malam Liman da ya samu towel ɗin Sheik ya rufe yana ta ƙoƙarin son ya ga ya samu ko da addu'a ɗaya ce cikin wanda ya iya don yake karantawa ko a zuciyarsa ce amma ji ya yi gabaɗaya ya manta komai a halin da yake ciki yanzu gani yake sunansa ne kaɗai zai iya tunawa. Yana wannnn halin ne ya ji saukar hannun Mai Gari a bayansa, wanda hakan ya sa ya ɗauka hannun marigayi mai ƙusumbi ne wanda ya masa gizo, duk tunaninsa a zahiri ya gan shi, hakan ya sa gumi ya shiga zarya a gabaɗaya ilahirin jikinsa tare da kufcewar wannan fitsari da yake ta dannewa, saboda yanzu an zo wajen da ba ta girma da martabarsa ta Liman ake yi ba, ana magana ne ta ceton rai tun da har yana ganin gawa ta taɓa shi, gawar ma ta marigayi mai ƙusumbi. Liman a zuciyarsa yake faɗin 'Allahu akbar! Tamu ta zo (Yana nufin mutuwa) Allah ka bamu ikon amsa tambayar kabari, Allah ni nake jan sallah a garin ƙundu ka bani cikawa da imani' Wannan yake ta maimaitawa a zuciyarsa. Mai Gari kuwa hannun da ya miƙa shi lalumen bargon Sheik yake yi, so yake ya koma cikin bargon Sheik ko ya samu salama a ransa, tun da yana ganin bargon Sheik za a samu tsari kasancewar malamin balarabe ba za a ce ruɗani ya hana shi addu'a ba. Jin ya sauke hannun nasa a jikin riga, kuma ya san dai Sheik bashi da riga suka shigo ɗakin, tun da idanun Mai Garin a rufe suke ba ya so ya buɗe bare ya ga fatalwar kakansa mai ƙusumbi, son ya fara tunanin ma kar dai mai ƙusumbin ya ce ya zo ya tafi da shi ne. Hannun da ya fara matsarwa a jikin Liman kasancewar rigar Liman ta shadda ce ta ci uban duniyar ta da tsinke, domin daga baya a yage take kasancewar ya ɗora babbar riga shi ya sa ba a ganin yagar, yanzu kuma da samarin nan suka sa ya cire babar rigar sai yagar ta bayyana a bayansa. Hannun Mai Gari ne ya shige cikin bayan Liman ta wanann yagar, hakan ya sa ya shafo bayan fatar jikin Liman. Liman mutuwar kwance ya yi don zuwa yanzu ma kawai bakinsa ne yake karkarwa kamar wanda zazzaɓi ya yi wa mugun kamu, haƙoransa suna haɗuwa da juna, saboda ya gama saddaƙarwa cewa fatalwar mai ƙusunbi ce ta dama masa baya take shafa fatarsa, ya san yau babu makawa da shi za ta koma lahira Mai Gari da sauri ya ɗauke hannunsa, saboda fatar da ya taɓa ya ji wani karsansan, alamar fatarsu ce irin ta baƙaƙen fata, ya san ta Sheik tana da laushi da santsi irin na larabawa, shi zai tabbatar da haka tun da jiya ya kama hannun Sheik mai laushi kamar na jarirai, bai san cewa tsabar amfani da allurai da magunguna da kuma sabulai na garan fata ne ya sa take duk a yanayin da ya ji fatar. Yana ɗauke hannun ya miƙa wani wajen tun da gabaɗayan su a kan katifar suke, duk sun cushe, tun da su biyar a kan katifa ɗaya, yana ƙara miƙa hannun ya sauke a kan ƙafafun samarin nan shafawa ya yi sai ya ji wani gautsin fata, don har ya shafo kaushi da faso a ransa ya ce 'Kai jama'a har yanzu dai ina ta dawurwuri a jikin ƴan ƙasar nigeri'a Allah ka kaini a kan daidai wato in taɓo fatar balarabe' Ya faɗa yana jin tausayin kansa. Samarin nan kuwa jin an taɓo musu ƙafafu, kowanne sai numfashinsa ya tsaya cak! Tunanin su fatalwar da Liman ya gani ce za ta yi awon gaba da su. Juna suka ƙara ƙanƙamewa kowanne yana ta ƙoƙarin warto addu'a a zuciyarsa domin ya kuɓuta, sai dai a cikinsu babu wanda ya yi nasarar ambatar kowacce addu'a don ruɗanin ya kai ruɗu. Gwiwarsa ya ja bargonsa yana ƙamale a kafaɗarsa idanunsa a rufe, ya miƙa hannunsa bai masa masauki a ko ina ba sai a kan mazaunan Ya Sheik, laushi luɓus ya ji, hakan ya sa ya miƙa ɗaya hannun ma ya zamana hannayensa biyu a kan mazaunan don yana son tabbatar da cewa tabbas a kan fatar Ya Sheik ya sauke hannunsa, amma fa duk abin nan da yake bai san cewa a kan mazaunan Sheik ya sauke hannu ba. Sheik kuwa jin an taɓa masa mazaunai a lokacin ya ƙara gane mazaunansa a tantagarya yake babu rufi ba ma wannan ba lalumen da Mai Gari yake yi nema yake ya wuce gona da iri a wajen Sheik domin kuwa hannunsa yana neman taɓo mafitsarar Sheik, Sheik wanda tunaninsa ya fara bashi cewa fatalwa ce take lalumen jikinsa sai ya ƙara tsorata ya shiga ruɗu, da tunanin kar dai fatalwar mai ƙusunbin tana so ta tsinke masa mafitsarar ne gabaɗaya ma, wani sashen na zuciyarsa yana bashi cewa ko dai shayi ake son a masa(Kaciya,sallatu) Idanu ya zaro bai san lokacin da ya buɗe baki ba gabaɗaya ya manta sa ƙalƙalar sa yake yi ta larabci wajen yin magana, wato yadda ko hausa yake sai ka ɗauka ɗan koyo ne. Wanann karo da hausa sak irin yadda bahaushe yake magana babu gargada ya ce "Wallahi na rantse da Allah an mini kaciya, don Allah kar a cire mini mafitsara" Ya faɗa a fili ɗakin har yana ɗaukan amsa kuwwa. Don ya fara tunanin kar a je ko dai a tsinke masa mafitsarar ko dai a je garin masa kaciyar a yanke fiye da rabin mafitsarar a bar masa ƴar guntuwa. Yana faɗa wani hawayen tausayin kansa ya cigaba da zubo masa domin ya fara tuno matansa su Lami da ya baro a ƙauyansu ya san duk inda fatalwar kakan Mai Gari ya gabce masa rabin mafitsara, ko ta cire masa gabaɗaya to in har ma bai mutu ba kenan, ya san shikenan sai dai kowacce ta ce ya bata takardar saki, tuno da wannan kuma ya san yana son matansa sai ya ƙara ware murya duk da yana cike da tsoro ya ce "Wallahi ina son matana, ba zan sake su ba wani ya aura" Mai Gari tun maganar da Sheik ya yi ta farko wato inda ya ji Sheik yana batun kaciya da cire mafitsara, bai san lokacin da ya ɗauke hannuwansa salin alin da sauri ya koma wajensa da ya taso ya kifa kansa yana ambaton 'Lahaula wala ƙuwwata ' A zuciyarsa, don shi ya san dai ya ji an yi magana amma ko za a saka masa wuƙa a maƙoshi ba zai gane ga wanda ya yi maganar ba, sannan ruɗanin da yake ciki bai bari ya gane cewa Sheik ne ya yi maganar hausa sak ba, babu ƴar ƙalƙalar larabcin. Malam Liman jin ana ambaton kaciya sai ya fara tunanin ko dai fatalwar ta yanke shawarar yayyanke musu mafitsara ne hakan ya sa ya saki towel ɗin da ya rufe kansa da shi, ya mayar wajan matse matsin ƙafafunsa a nufinsa ya yi shirin ko ta kwana, saboda kar a masa sakiyar da ba ruwa. Gabaɗaya kowa da zaman jiran tsammanin da yake, Sheik ya yi ƙarfin halin jan bargon ya rufe mazaunansa, yana jin da na sanin zuwa garin ma baki ɗaya, sai dai shegen kwaɗayi da son abin duniya ba za su bari ya bar garin ba, ya yi wa kansa alƙawarin zama daram sai ya ga abin da ya turewa buzu naɗi. Mai Gari ya jiƙe da gudmi sharkaf ga gwiwarsa ta ƙafa da ya tsunduma a fitsarin Liman, amma dai yanzu a matsayinsa na Mai Gari gashi kuma yana tsoron mutuwa dole zai yi ƙoƙarin yin magana don a samu mafita, tun da tana ganin duka manyan garin ne a ɗakin, idan kuwa fatalwar mai ƙusumbi ta musu fata-fata to gari yana cikin garari. Su kaɗai suka san gari lafiya lau yake, amma shi Sheik har yanzu tunaninsa wani gudun famfalaƙin tsoron ne ya sa suka yi hijira daga cikin gari zuwa gidansa. Da muryar kuka kuma muryar a shaƙe kai daga ka ji maganar ka san mai yinta ƙarfin hali yake Mai Gari ya ce "Ya Sheik, muna buƙatar taimako, muna buƙatar addu'a kar fa a mana ɗauki ɗai-ɗai, ka yi addu',a mana, mu baƙaƙen fata muna cikin wani hali kaima babban malami kana... Tun Mai Gari bai kai aya ba Sheik ya daure ya yi ƙarfin halin saita ƙalƙalar hausar larabcinsa ya fara cewa "A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Tun da ya sanu nasarar yin a'uziyyar nan shikenan yake maimaitawa don shi ita kaɗai ya iya kamowa, don haka bai damu da cewa yana ta maimaitawa za su ce wani abu ba. Mai Gari da yake jiran ya fara jin ana zayyano addu'o'in larabci masu yawa bayan gama a,uziyya da bismillah sai ya ji ba a fara ba ana ta maimaita abu ɗaya. Can ya ce "Haba Ya Sheik ka fara addu'ar da muke ji ana karantowa a ƙasar makka mana" Ya faɗa yaba ɗan ɗaga muryarsa da take ta zillo tana rawa, tare da saurin gyara fuskarsa daga inda ya nutsa ta a jikin katifa jin ya danne hancinsa numfashi yana neman gagararsa shaƙa, amma fa duk maganar nan da ya yi Sheik bai ce uffan ba kuma bai fasa faɗar abin da yake faɗa ba, saboda shi a ganinsa ya samu makamar ceton kansa. Liman da samarin nan jin muryar Sheik ta karaɗe ɗakin yana faɗin "A'uzubillahi minash shaiɗanir rajim, Bismillahir rahmanir rahim" Cikin muryar larabawa tamkar wanda wani balaraben gaske yake yi, basu san cewa Sheik sai da ya daɗe yana yi wa muryarsa training a kan ƙalƙalar kafin ya zo garin nasu ba. Liman da samari basa bambance abin da yake faɗa, don yadda yake maganar tamkar wata doguwar sura ce yake karantawa sai suka shiga mishi amshi da faɗin "Allahu akbar!" Idan ya faɗa sai Liman ya ce "Attakabir" Sai samari su ce "Allahu akbar!" Mai Gari ma tuni ya bi yarima yake shan kiɗa, don ya lura shi kaɗai ne muryarsa bata fitowa a cikin ɗakin, yana tsoron abin ya zama shi kaɗai zai samu. Sun kwashe sama da awa suna a haka, sannan ne Sheik ya ji ƴar nutsuwa, ya buɗe ido ɗaya ya ƙyallara ya ga dai ɗakin babu kowa, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tunanin abin da ya faɗa ne ya sanya fatalwar ta fita daga ɗakin. Daƙyar ya ɗago daga gohon ya zauna, ganinsa babu towel ɗin nasa, sai ya ƙura ido a mafitsararsa yana son ganin ko an masa shayin, amma sai ya ga yadda take haka take, sai dai ta yamushe a waje guda ta tattare saboda wahala. Har lokacin bakinsa bai yi shiru da abin da yake faɗa ba, hannu ya kai ya fisge towel ɗinsa na wajen Liman, Liman da dama bai riƙe towel ba kasancewae hannuwansa suna matse a matse matsinsa, sai ji ya yi an buɗe masa kansa, hakan ya sa ya ƙara runtse ido haɗe da bada ƙaimi wajen ƙara danna hannuwansa don ganin ba a yi kaciyar nan da shi ba, har lokacin yana faɗin "Attakabir" Da sauri Sheik ya ɗaura towel ɗin ya ɗan muskuta ya koma kan sallayar da take shimfiɗe, tare da miƙa hannu ya ɗakko hirami a jakarsa yana gyra zaman hularsa da gemunsa, sai da ya zauna yana kallon gabas , ya rufa hiramin yana ta cigaba da a'uxiyya. Dakyar ya samu nasarar warto suratul fatiha a bakinsa, ya shiga karantowa, sai da ya yi sau uku, sannan yana zaunen ba tare da ya juyo ba ya ce "Alhamdulillahi, na samu nasarar korar fatalwa, komai ya dawo daidai" Ya faɗa cikin muryarsa ta balarabe. A hankali suka fara tashi zaune kowa yana ɗan ƙyallara ido, ganin babu fatalwa a ɗaki, sannan Sheik yana kan sallaya ya rufa hirami sai suka fara hamdala Mai Gari faɗi yake "Allah mun gode maka da ka kawo mana babban malamin larabawa da yau ya za mu yi?" Ya faɗa yana kallon gwiwar ƙafarsa, da ta jiƙe, shi kuma Sheik bai ma san inda gudawarsa ta yi ba domin yanzu ba ya ma ji. Malam Lima cewa yake "Ai ba ƙaramar sa'a muka yi ba" Ya faɗa yana ɗan satar kallon wandonsa da ya jiƙe ya ce "Wannan yara an yi yaran banza, yanzu a cikin ku aka samu wani marar imanin ya zage wando ya mini fitsari a jikina?" Ya faɗa yana kallon samarin nan da suke sharkaf da gumi. Ɗaya ya buɗe baki zai yi magana Mai Gari ya yi saurin cewa "Kai ba a son wani tone-tone ku bashi haƙuri" Haka suka bashi haƙuri ba don son so ba, sai don ba yadda za su yi kuma dai ga wandonsa ya fi nasu jiƙewa tun da shi ya yi fitsarin su dai kawai sun shiga lemar ne. Liman daɗi ya ji a ransa ganin girmansa bai zube ba. Nan suka kalli Sheik da ya juyo daga kallon gabas yana gyara zaman towel ɗin da hiraminsa, gumin da yake yi tamkar ya dawo daga filin tsere. Mai Gari yana kallonsa ya ce "Sannu Ya Sheik lallai ka yi artabu" Sheik a zuciyarsa ya ce 'Artabun yau ka gani, da ka ga na jiya da na sha da ina ga wano zancen ake ba wannan ba' Amma a fili sai ya ce "Kai wannan ai ƙaramin abu ne, ai ina tabbatar muku kuna zuwa cikin gari za ku ga aljannu sun lafa komai ya daidaita" Da mamaki suke kallonsa jin yana batun cikin gari, Malam Liman ne ya ce "Cikin gari babu lafiya ne dama?" Shiru Sheik ya yi yana tambayar kansa a zuciyarsa cewa 'To da uban me ya taho da ku da gudu idan ba tashin hankali kuka baro a cikin garin ba?' A fili ya ce "Dama cikin garin lafiya, na ɗauka ai babu lafiya da na ga kun shigo gidan nan a kuɗime" Mai Gari ya ce "A'a gari lafiya ƙalaw dama zuwa muka yi, mu ga ko lafiya mun zo da asuba kiranka a yi sallah amma aka gaji da bugawa shiru, to shi ne muka samo samarin nan muka ce su ɓalle ƙofar a duba lafiyarka, da aka tura ƙofa kuma sai muka hango ka taho a guje da takalmi ɗaya a ƙafa jiki duk kumfa, wannan dalilin ne ya sa mu ma muka ga tun da har kana gudu to akwai gagarumar matsala gwara mu bika mu tsira ka ji dalili amma gari kowa yama sabgar gabansa lafiya" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana jin wani mugun haushin su, da suka firgita shi, shi a nashi tunanin garin ne a ruɗe suka taho ashe dai shi ya ruɗa su. Cike da ƙarfin gwiwa ya sheƙo wata sheƙeƙiyar ƙarya don kar a ga gazawarsa ya ce "Ai nake faɗa musu ina cikin banɗaki ina wanka, nan na ga wani aljani mai ƙaho bakwai ya tsaga bango ya fito, yana fitowa ta sheƙe da dariya yana cewa, wai yanzun nan za su saki manyan aljannun da za su rikita gari, kai har cewa ya yi mai gari ma ɗauke shi, za su yi, wannan dalilin ne ya sa ina nuna shi da yatsa wani hayaƙi ya tashi da shi sama, ya bi iska ya ɓace, to ni kuma tuno halin da garin zai kasance shi ne na fito hankali a tashe domin na kai muku ɗauki cikin gari, ganinku a guje kun shigo ya ƙara sanya hankalina ya tashi, saboda bana son jama'a su shiga damuwa, sai yanzu bayan na gama addu'ar nan na gano ashe dai aljanin nan ne ya shiga jikina ya haifar da tsuma da ruɗu da tsoro, don kar in taimaka muku, shi ne fa muke rige-rige tsakanin ni da ku wajen samun maɓoya" Ya faɗa yana dafe goshi alamar damuwa. Mai Gari har da ƙwallar farin ciki ganin ba ƙaramar ƙauna Sheik yake yi wa garin nasu na Ƙundu ba, sannan ba ƙaramin taimakon su yake yi ba, bai san cewa Sheik kasuwanci ya zo yi a garin nasu ba, don ba a aikin banza a ko ina. Cike da girmamawa ya ce "Allah saka da alkairi Malam ashe kana ta fafutuka ne a kan garinmu, silar haka har aljani ya shiga jikinka ya saka muke tsere, bawan Allah dama na yi mamakin ganin muna ta neman mafaka tare da kai ashe dai ba da kai muke nema ba, da aljani ne" Ya faɗa yana kallon Sheik. Liman ya ce "Ai ni na yi mamaki dama, malamai ai magada annabawa ne" Sheik ya ce "Ina ai ƙaryar aljani in ji tsoronsa, su kansu sun sanni" Ya faɗa amma yana ɗan rage murya saboda tuno kunnen jaririn da aka jefo a banɗaki. Liman ya ce "Allah mai baiwa, ku dai Allah ya baku" Sheik aka wani gyara zama gudun kar towel ya kunce ya ce "Ai aljanin ya yi niyyar hanani yin addu'a ma lokacin da fatalwa ma ta shigo hatta bakina sai da suka so riƙe mini, yanzu ma sai da na sha fama na hau sallayar nan, so suka yi kar in yi addu'a" Gabaɗaya suka ce "Allah ya fi su" Nan dai aka sa samarin nan su fita da katifa su gyara ɗakin, a nan ne ma Mai Gari ya ƙarewa Sheik kallo ganin idanunsa luhu-luhu alamar ko dai kuka ko rashin bacci ya ce "Ya Sheik ka ga idanunka kuwa, hatta fuskarka a kumbure take" Sheik tuno artabun da suka sha jiya da jarirai da aljannu har ya hau bishiyar kuka, sai ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Haba Mai Gari wanann tambayar ma ai ɓata baki ake yi, ni da na zo taimako ina ni ina bacci, ai ni nan da na gama cin abinci kawai alwala na yi na hau sallaya, nake salloli ina addu'a ban tashi ba sai da aka fara kiran assalatu, shi ne na sake alwala na yi shirin fita masallaci, sai kuma na tuna ku ne za ku zo mu tafi tare, to dai ni ban ji zuwanku da asubar bama don ni nan na yi sallah da nafiloli, wataƙila aljannu sun saka mini auduga ne a kunne shi ya sa ban ji bugun naku ba" Ya faɗa yana kai hannu ya share zufa a goshin sa. Sosai suka jinjina masa, daga nan suka ce za su je a kawo masa abin kari, nan ya ce wainar ƙwai da dafaffan ƙwai sai a biredi da shayi me kauri. Mai Gari sai da gabansa ya faɗi, jin abubuwan da ya zana, sai dai har da wasu sunayen abubuwan larabci da shi kansa Sheik bai san mene ne ba, ya zayyana sai da Mai Garin ya ce vasu san abubuwan ba sannan Sheik ya ce a barsu dama abincin su ne na ƙasar larabawa. Bayan samarin sun gama gyaran suka tafi da su Mai Gari. Lokacin ya saka jallabiya, ya ce zai yi wanka, suna tafiya ya gabansa yana faɗuwa, amma haka ya je ya garƙama sakata ya ɗauki ruwa ya tuɓi ya yi wanka a tsakar gidan, don ba zai iya komawa banɗakin a lokacin ba. Yana gamawa ya buɗe ƙofar gidan saboda masu kawo abincin don an ce masa mutane za su fara zuwa neman magani yanzu gidan zai cika maƙil in ya gama cin abinci. Juyowar da zai yi ya yi arangama da wani ƙaton hanci yashe a tsakar gidan, amma girman hancin ya yi kan mutum da gudu Sheik ya doshi ɗaki towel a hannu don da ya kunce gani ya yi bashi ma da nutsuwar tsayawa ya ɗaura. Yana shiga ɗakin ya banke ya jingina da jikin ƙofar yana mayar da numfashi, a fili ya ce "Ko a ni ko a ku aljannun garin nan, wato kun ga ana girmamani hassada da tsana suke damunku, yadda zan ke shan ganimar girki, da kuɗaɗen magani ana biyana yasin babu inda zan gudu, ba hanci da kunne ba kai ko karo zan ke ci da mafitsara kuna jefowa aradu sai dai na gudu ɗaki amma dai arziƙi sai na dagwala a garin Ƙundu" Ya faɗa yana ƙarasawa ya zauna, ya shiga shafa mayukansa, sai da ya gama tsaf a saka kayansa ya samu turarukansa masu ƙamshi ya shafa saboda su kashe warin mayukan bilicin yake yawan amfani da turaruka. Yana gamawa ya kabbara sallah, sai lokacin ne ya yi sallar asuba, a lokacin kuma Audu yake rafka sallama, gyaran murya ya yi, sai da ya sallame sanann ya amsa, amma da ya leƙo bai ga hancin nan ba, haka ya buɗewa Audu ɗakin ya ajiye masa kayan abincin bayan ya gaishe da shi, ya nuna masa kwanukan jiya ya ɗauka, har ya jiya zai tafi Sheik ya ce "Mu manyan malamai ba a gutsure mana cinyar kaza ko wani sashe na jikinta, yadda aka ba mutum saƙo ya ji tsoron Allah ya kawo daidai" Da rashin fahimta Audu ya kalle shi amma sai ya ce "Malam ban gane ba" Sheik ya ce "Jiya kazar nan da ka kawo bata da cinya ɗaya" Mamaki ne ya kashe Audu jin wai shi da aka bashi abu har lissafawa ya yi, hakan ya sa ya ce "Wallahi ni ban ɗauka ba, sai dai ko a gidan Mai Garin ne da aka dafa suka ɗauka suka rabawa yara" Maganar Audu ta nunawa Sheik asalin gaskiya ya faɗa masa, don haka sai yayarda ya ce ya tafi. Tun da ya buɗe kwanukan ƙamshin wainar ƙwai ya cika ɗaki, ya cinye tass ya sha shayin bayan ya saki gatsa ya ce "Bari in yi shiri na san yanzun nan masu buƙatar magani za su fara zuwa, ni ko buhun hatsi ma zan ce Mai Gari ya bayar a kawo min? Saboda in ke zuba kuɗin sadakar magungunan da zan ke bayarwa" Ya faɗa a fili yana ciro hular kansa ya shiga taje ta da brush kumb ta kwanta sosai ya ɗauko wani mai me sheƙi ya shafa a take ta shiga walwali. Ajiyewa ya yi a gefe ya buɗe inda kuɗinsa yake ragowar kuɗin saniya, ya shiga ƙirgawa, yana cikin hakan sai ya ji tashi hayaniya an shigo gidan, sai ya ji ana masa wani kira kamar na ƴan farauta ana cewa "Sheik ka fito gari babu lafiya, aljannun mai farfaɗiya sun tashi, ƙartai goma aka tara suka riƙe ta amma ta watsar da su" Gaban Sheik ne ya harba da ƙarfi wai me farfaɗiya, kuma ƙartai goma ta watsar kenan yanzu shi kuma in zai mata maganin ya zai yi?. Bai yi magana ba kuma dama ɗakin nasa a rufe, sai ya ji wani ya shigo yana cewa "Innalillahi wallahi matar nan mai farfaɗiya ta ɗaga Mai Gari da hannu ɗaya hannunta na dama, hannun hagun ɗin ta ɗaga Malam Liman, Sheik ka fito da gaggawa ,a ta hau saman kukar bulukiya da su" Gabaɗaya idanun Sheik sun ciko da ƙwalla, hankalinsa ya tashi gabansa ya hau dukan uku-uku. Dakyar ya yi ƙarfin halin faɗin "Ya subhanallahi, mai farfaɗiya a yi haka kuma, ki ɗaga Mai Gari da Malam Liman, jama'a gani nan zuwa" Ya faɗa yana zufa, sai dai abin da ya bashi mamaki wanann hular tasa wacce ita ce rufin asirinsa, wacce ya cire ya taje gashin ya ajiye a gefe yana lissafin kuɗi, babu ita babu dalilinta, wato hula dai mai gashi da gemo da saje ta yi ƙafa don bai ganta ba. Hankali a tashe ya kai hannunsa biyu saman kansa yana shafo tsakiyar kansa zuwa fuskarsa, hankali tashe, jin ya shafo ƙwal kwabon kansa da kuma fuskarsa da babu saje babu gemu lallai yau akwai cakwakiya, ya ake so ya yi wajen fita zuwa ruƙiyyar. Wani ƙaramin mudubi ya ɗakko a jakarsa ya duba fuskarsa yana ganin tabbas idan ya kuskura aka ganshi a haka ya kaɗe har ganyensa, don za a gano ba balarabe ba ne. Wani mai ƙarfin hali ne ya takarkare ya ce "Sheik ka fito su Liman rai a hannun Allah, tana hawa kukar nan ɓacewa za ta yi, don idan aljannu suka ɗauke ta sai ta yi wata biyu ma ba a ganta ba" Ya faɗa a ruɗe ganin Sheik bai fito ba. Wannan furucin ya sake sanya shi diriricewa yana ƙara shafa sallallan kansa ya ce "Gani nan zuwa ai ƙaryarta ta sha ƙarya" *Mu haɗu a gaba don jin ya SHEIK zai yi wajen fitowa babu hula, shin ina hular tashi? Ko dai aljannun ne suka saci don su ga ƙarshen ƙarya?* Yanzu muka fara ku dai ku biyo ni don jin ya za ta kaya✍️ MAMAN AFRAH 09025576222 *Dan Allah masoya ina neman alfarmar addu,arku gareni da bakunanku masu albarka, Allah kaɗai ya san bakin wani, ina nema domin Allah🤲 ko a zuciya ne ki mini addu'a NGD sosai ana tare😍* 🤝 [7/4, 4:00 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/EBurrU2vz6OFGbE37xLhPS 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 5 *ƘAUYEN MAI MANGWARO* A fadar Mai Gari dakyar aka dakatar da Jummau daga kukan da take tana ta faɗar cewa yau sai an biya ta saniyar marayu. Ita ma Lami tana faɗin sai Jummai ta biya ta kuɗin adashen ta, tun da ita ma saniyar ba ita ta siyar ba don haka sai dai ta biya ta kuɗinta in ya so idan Ibra ya kawo kuɗin sai ya bata, sai dai Mai Gari ya tsawar musu sannan suka yi shiru. Isowar Kakar Ibra Inna Tasallah fadar Mai Garin na Mai Mangwaro tana sakin ɗan kuka tana face hanci shi ya dakatar da kowa aka ɗago ana zuba mata na mujiya, wuri ta samu ta zauna har lokacin tana ɗan matse hawaye ita takaicin ta ɗaya jarin kayan miyar nan idan ta bayar ina za ta samu? Mai Gari ne ya yi gyaran murya ya fara magana kamar haka yana mai cewa "Tasallah shin kin san kiran da na aika aka miki?" A maimakon ta bashi amsa sai ta ƙara gudub kukan nata, kasaƙe ya yi yana kallon ta, sai da ta ɗan tsagaita kukan ta ce "Yo na sani mana Mai Gari, ai Idrisu da ya je ya kwashe komai ya faɗa mini, to zuwa wajenka kuwa ai ya zame mini farillah tusa a masallaci, in da sabo na saba a kawo ni ƙara wajenka, yau a ce Ibra ya cinyewa yarinya me tallah ƙosai, gobe a ce ya warci sandar rake a dandali, har ta kai ya fara kame kajin mutane yana yankewa ya cinye, yau kuma saniya sukutum ya gudu da ita wallahi albasa bata yi halin ruwa ba"Ta faɗa tana rungume robar kayab miyar ta tamkar wani ya ce zai ƙwace. Jummai ce ta yi tsoma baki ta ce "Wallahi in har ya saba cin ƙasa ya kiyayi ta shuri, in har tun yana ƙarami yana wartar kayan jama,a ana ƙyalewa kawo samartakarsa, to yau ya taɓo gidan rina don ko sama da ƙasa za su haɗe sai kin biyani saniyata" Haɓa Inna ta dafe ta ce "Haba Jummai kema kin san alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba, in ba tada zaune tsaye ba, ni yanzu a kan kuɗin ƙafar kaza ma sai a harbe ni, bare wata saniya, ni ban ci nanin ai nanin bata ci ni ba ko?" Ƙirji Jummai ta buga tana hayayyaƙowa Inna kamar ta kai mata duka ta ce "Ai dama ɗan kuka shi yake jawa uwarsa jifa, nima dai kayan marayu ne, don Inna ko kan ki za ki kai kasuwa a yi cinikin ki masu yankan kai su saye ki yasin sai kin siyar kin biyani kuɗin saniya" Da wani kuka mai jiniya Inna ta fashe jin ana batun ta sayarwa ƴan yankan kai kanta ta biya kuɗin saniya, Mai Gari ne a fusace ya ce "Wai shin ni zan yi hukunci ko kuwa ku za ku yi, idan har ku za ku yi babu amfanin zuwanku, kuma nima babu amfanin zumana a wajen nan" Mutanen fadar Mai Gari suka haɗa baki wajen faɗin "Wannan gaskiya ne ranka ya daɗe, Allah ja zamaninka mai gudumar dukan talauci" Wani zama ya gyara yana gyara babbar rigarsa, don maganar da ya yi ba iya su Inna ya katsewa hanzari be har da Lami da ta ƙunso nata maganganun amma sai ta ja bakinta ta ƙunshe. Mai Gari ne ya shiga faɗin "Tasallah yanzu magana tana hannunki amma dai kafin nan sai na fara da Jummai, ke Jummai me ya sa kika cinyewa Lami kuɗi har dubu ɗari biyu?" Ƙeya Jummai ta sosa irin ta mararsa gaskiya sai ta ce "Tsautsayi zagin mahaifi" Wani kallo ya mata ya ce "To in har cinye kuɗinta tsautsayu ne to ke ɗin ma ɗaukan saniyarki tsautsayi ne" Ɗagowa ta yi tana kallonsa da sakakken baki, sai kuma ta kalli Lami da take aika mata harara kamar idanunta za su faɗo. Bai jira cewarta ba ya ce "Kowa a cikin ku yana da laifi, ke Lami bai kamata ki taka har gidan Jummai ki since saniya a turke, ki ba mijinki ya kai kasuwa ba, mene ne amfanina a wannan garin, da kin kawo ƙaranta ai da na san abin yi" Kai Lami ta sunkuyar tana jin haushin Mai Gari ganin zai ɗora mata jakar tsaba kaji su bita. Bai ba kowa damar magana ba ya ce "Yanzu Tasallah kina da kuɗin da za ki biya wanann cakwakiya?" Inna kamar jira take ta sakin wani kuka mai ɗan sauti tana jin ciwo kayan miyarta da za ta bayar ta ce "Ya na iya da abin da ya fi ƙarfina, ai dama faɗan da ya fi ƙarfinka wasa kake mayar da shi, ni nan bani da komai amma ga kayan miyar nan da wannan naira ɗarin da na yi ciniki, su kaɗai ne na mallaka, ta karɓi jingina har zuwa ranar da Ibra zai bayyana, idan ya bata kuɗin saniyarta sai ta bani kayan miyata, amma da sharaɗi ko kalwata ko kuka suka yi ciwon kai ba zan yarda ba yadda zan bata kayan miyar nan salin alin ta ajiye kar ta sake ta taɓa" Ta faɗa tana ɗaga robar ta juye kayan miyar a kan tabarma a gaban Mai Gari. Tsabar takaici Jummai bata yi magana ba, ƴan fadar ne suka shiga danne dariyarsu, Mai Gari cike da takaici ya ce "Haba Tasallah a gabana kike mayar da babbar magana ƙarama, ana batun saniya kina batun kalwa da kuka da barkono?" Ɗan karkata kai Inna ta yi ta ce "To ai kowa da abin hannunsa yake ado, guntun gatarinka ya fi sari ka bani, ita saniya gare ta ni kuma kayan miya ne Allah ya bani" Mai Gari bai sake bi ta kan Inna ba, ya shimfiɗa sharaɗin za a jira daga nan zuwa kwana uku, a ga ta inda Ibra zai dawo, in ya so sai a san abin yi. Haka ya kashe rigimar ba don ta mutu ba, ya ce idan Ibra ya dawo da saniya ko kuɗin saniya sai Jummai ta karɓi kayanta, sannan ta biya Lami kuɗinta. Inna wani irin washe baki ta yi, tamkar ba ita ce wacce take wannan kukan ba, dama kukan takaicin za a raba ta da kayan miyarta ne. Haka ta kwashe ta saka a robar tana jerawa Mia Gari godiya, ta tafi gida a ranta tana Allah wadai da halin Ibra mutum kusan shekara arba'in amma bai san abin da ya kamata ba sai tunani irin na yara. Lami da Jummau kowa a ƙufule da ɗan uwansa ya bar fadar Mai Gari. Lami tana komawa gida ta samu kishiyarta Sa'a a tsakar gida tana riƙe da ƙugu, shigowar Lami ko zaunawa bata yi ba Sa'a ta ce "Sannu Lami wato ke kin iya ɗauki ɗam baki ajoye ba ko? A kan me za ki ɗaukar mini gayan tuwo?" Lami wacce take cike da ɓacin ran rashin dubu ɗari biyun ta, da kuma yaudarar da Ibra ya mata a tsawa ce ta ce "Sa'a hawainiyarki ta kiyayi rama ta, saboda rainin wayo ni da nake da dubu ɗari biyu kuɗin adashe uban me zan yi da gayan tuwo, to Allah tsari gatari da saran shuka" Sa'a hannuwa ta tafa ta ce "Da ba a san asalin barbela ba sai ta ce daga madina take, kuɗin adashen da ko naira biyar bata zo hannunki ba, kika ɗauki saniyar mutane kika ba wanann marar imanin ya tafi to ai kin yi saki na dafe. Sa'a ta ci gaba da cewa "Shi ne za ki ɗauke mini gayan tuwona ki fice da shi, na san a gyalenki kika duƙunƙu ne tuwon kika je maƙota kika yi kwaɗo da mai da yaji kika cinye" Galala Lami take kallonta sai dai takaicin da yake cikin ranta ya fi wannan wanda Sa'a take takalarta faɗa da shi don ta san ita da Sa'a basa jituwo ko kaɗan, haka ta tashi ta shige ɗakinta tana jinta tana jera mata Allah ya isa amma bata ji za ta iya biya ta su yi ba, don ita a halin da take ciki ko yunwa bata ji bare har ta saci gayan tuwo ta san kawai neman masifa ne irin na Sa'a. *WASHE GARI* Sa'a ce a tsakar gida tana shanya kayan wanki, Lami tana bakin ƙofar ɗakinta tana zaune ta kifa uban tagumi, bata da buri illa ta ga Ibra ya dawo da kuɗin wannan ko saniya amma shiru malam ya ci shirwa. Wata uwar sallama ake rafkawa a zauren gidan, da murya wacce hausa bata gama ratsa ta ba, alamar yare ne yake maganar. Wani takaici ne ya turnuƙe Lami ta taso rai a ɓace ta zo bakin zauren ta tsaya ta ce "Tunde sai aka yi yaya kuma? Ya za ka zo da safen nan ka ishi mutane da rafka sallama" (Tunde inyamuri ne da ya zo daga Lagos yana zaune a garin Mai Mangwaro yana da gidansa da matarsa ɗaya da ɗansa, sai kuma shagonsa da yake a ƙofar gidansa nasa). Kallon Lami ya yi ya ce "Ba wajenki na zo ba wajen mijinki na zo" Ya faɗa cikin hausar sa da bata gama kama bakinsa ba. Ambaton mijinta da ya yi ya ƙara sosa mata mikin takaicin Ibra da ta kwana da shi, cikin takaici ta ce "Baya nan ya ɓata, hijira ya yi da saniyar mutane ba a san duniyar da yake ba" Idanu ya zaro ya saka hannu a lajihu ya fito da takarda wacce rubutu ne rututu a jiki ya ce "In na yarda shegiya nake, kalli basukan da mijinki ya ci" Ya faɗa yana nuna mata takardar. Kallon sheƙeƙe ta wa takardar ta ce "To ai ka yi ta banzar ni da ba boko na yi ba ina zan san me aka rubuta" Yana zaro idanu ya ce "Idan ma ɓoye mijinki kika yi ki fito da shi, don yau ba zan bar nan ba sai da kuɗina, shinkafa kwano uku wake rabin kwano, sabulun bilicin da ya sha karɓa, da mayukan bilin har allurai da nake masa na sanya fari bai biya ni ba wallahi ko a ni ko a shi jiya ya ce zai dawo daga kasuwa ya biyani yanzu ki ce wai ya yi hijira" *SHEIK* Kukan zuci ya shiga yi wanda ya fi na fili ciwo, ya san tabbas yau watan tonuwar asirinsa ne ya kama in ba haka ba hular da ita ce kaɗai rufin asirinsa kuma ita ce take fito da asalin kamarsa da larabawa a ce babu ita. Shiru ya yi yana nazarin yadda zai kuɓuta amma iya tunaninsa bai tuno komai ba, don babu mafita, kansa gabaɗaya ya kulle. Ga abin da ya fi ɗaga masa hankali ma shi ne yadda samarin sukemta azalzalarsa a kan ya fito ana jiransa. Cikin ɗaga murya ya ce "Afwan ya shabbab, gani nan ina zuwa, ina yin shirin ko ta kwana ne, saboda aljannu dubu saba'in ne a kan matar nan mai farfaɗiya" Ya faɗa yana ta safa da marwa a ɗakin ya haɗa uban gumi yana ganin yau dai ƙarya nema take ta ƙarewa ɗan kada, saboda ya lura yana cikin tsaka mai wuya. Kamar zai yi kuka a hankali ya ce "Allah ka taimake ni, Allah kar ka bari in kunyata" Ya faɗa yana ciccira ido a ɗakin, fani yake kamar zai ga hular amma babu niyya wai ango ya kwana da wando. Wata dabara ce ta faɗo masa ya buɗe baki ya ce "Gabaɗaya ku fita daga gidan nan, gani nan fitowa saboda maganin aljannun da zan fito da shi yana da ƙarfi, wataƙika idan na fito guguwa ta taso ta haɗe gidan da ƙura... Tun bai kai ƙarshen maganar ba, samarin nan kowa ya yj ta kansa, sai lokacin ya ɗan ji sawaba, kamar ƙiftawar ido da fitar su Sheik ya fara ganin labulen windown ya fara kaɗawa da ƙarfi kamar dai ana iska mai ƙarfi ne, Idanu ya zaro cikin taku biyu ya koma jikin bango ta raɓe, bakinsa yana karkarwa ya fara addu'a, kawai sai ganin hular gashin nasa ya yi tana reto a saman ɗakin, kai ya ɗaga yana ta kallonta, a ransa yana jin daɗi da ya ganta sai dai ba a nan gizo yake saƙar ba yanzu tunaninsa ɗaya ya za a yi ta zo hannunsa. Bai ankara ba ya ga an wurgo dogom gemun jikin fuskarsa sai kuma sauran sajen da hular gashin suka ɓace, kamar zai yi kuka ya hau faɗin "Ku taimaka mini, ya zan yi da gemu shi kaɗai, damuwata gashin kan nan nawa da babu yadda yake salsal su kuwa sun san Sheik da gashi laɓaɓa na larabawa." Yana rufe bakinsa sai ga sauran ma sun fito sai kuma suka faɗo, duk da yana tsoro haka ya lallaɓa ya je ya ɗauka yana godewa Allah a ransa yana jin daɗin cewa ashe dai da sauran shan ruwansa a garin Ƙundu tun da gashi dai asirinsa bai tonu ba lallai akwai damfara. Shirinsa ya yi tsaf ya ɗauko wani baƙin takalmi sabo a jakarsa ya saka, ya ɗakko turaruka ya shafa ya saka hular gashin ya manna gemun ya saita sajen da yake wani abu ne a jiki da ake ɗayewa mai danƙo daga ya ɗaga wajen sai ya manne kamar a fuskarsa a ka halicce su. Ɗakinsa ya kulle ya fito yana riƙe da wata roba mai ɗauke da ruwa da wani garin magani da aka jiƙa a ciki ya fito daga gidan gabansa yana faɗuwa, yana tunanin yadda za a ƙare da wannan lamari, shi ya sa ko wayarsa bai ɗauko ba gudun masu aljannu su warce ko ma a fasa masa ita. Tun da ya fito yake hangar mutane jefi -jefi suna yin wata hanya sannan kuma sai wani girmama shi ake ana bashi hanya, wanann ya ƙara masa jin kansa ya ƙara girma, duk da yana cikin yanayin tsoro haɗe da fargaba. Sheik haka ya doshi cikin garin ya yi inda mutane suke yi da alama nan ne wajen da su Liman ɗin suke.Duk da idanunsa sun kumbura saboda fargaba da rashin baccin da bai samu jiya ba, kai har da kukan da ya yi ma. Tun kan ya ƙaraso yake jin ana ta yin salati, yana kusa ƙarasowa ya ji ana faɗin "Shikenan ma ga Sheik nan, ga ƙare kukan ka nan, balaraben malami yanzu komai zai zo ƙarshe. Mutanen gari sun taru suna jiran ya fitar da maganin da zai kori aljannu kuma ya kuɓutar da su Liman. Amma Sheik yana cikin firgici har yanzu saboda abin da ya faru da dare. Yana ganin taron mutane sai ya fara rawar baki da hannun yana murza carbi, yana faɗar kalmomin larabci marasa ma'ana, don shi kansa bai san abin da yake faɗa ba yayin da yake karanta addu'a sai wani ƙaramin yaro ya faɗi a gabansa ya fara rawa ɗari tamkar yana shi ma mai farfaɗiyar ne, mutane suka shiga faɗin suna cewa "Aljannu yanzu za ku gane shayi ruwa ne" Shi kuwa Sheik ganin yaro ya zube a ƙasa idanunsa sun kakkafe sai ya sha jinin jikinsa gabansa yana tsanata faɗuwa, ya yi shiru don bai san me ya faru ba, amma ya ci gaba da murza carbi yana ambaton maganganu. Jama'a suka fara mamaki da tsoron Sheik suna ganin tsabar maluntarsa ce ta sa yaron ya zube a ƙasa. Bai bi ta kan yaron ba ya ɗaga kansa sama, mutane uku ne a kan bishiyar kukar da mutane gari suke kira da kukar bulukiya saboda tarin aljannun da suke kanta Hannu ya saka ya kama yaron nan da ya faɗi ya ɗaga shi, ƙirjinsa ya dukan uku-uku ya shiga karanta fatiha da ƙarfin halinsa yana tofawa yaron a fuska, wani gurnani yaron yake, Sheik kuwa ji yake kamar ya sheƙa da gudu amma babu hali. Ɗan ranƙwafowa ya yi yana cigaba da tofa masa karatun idanun yaron a kakkafe ya miƙa hannu bai masa masauki a ko ina ba sai a gemun Sheik. Sheik a zuciyarsa ya ce 'Shikenan asirina ya tono zai fisge min gemun a bainan nasi, kowa ya gane bogi ne' A fili kuma sai ya fara faɗin "Subhanallahi, ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba, hasbunallahu wa ni'imal wakil" Duk abin nan da ake yaron ya ƙi sakawa, shi kuma Sheik hannunsa ɗaya yana riƙe da carbin da robar maganin nan ɗayan yana riƙe da yaron, ji yake kamar ya yi kuka, bai yi wani yunƙuri ba kawai sai yaron ya naɗe jikin malam yana cewa "Ka kaini saudiyya" Sheik a zuciya ya ce "Ni kaina ko filin jirgi ban taɓa zuwa ba' A zahiri ya ce "Kai mutum huɗu su zo nan" Ya faɗa yana ƙara miƙa haɓarsa jikin yaron don ba ya so ya ja yaron ya ciro gashin gemun. Samari da mata da magidanta da suke wajen sai aka fara darewa jin malam yana kiran mutum huɗu Malam ganin yaron yana miƙa hannu wajen wuyansa gudun kar ya shaƙe shi ya kashe shi a banza, inda Sheik yake riƙe da hannunsa ya nutsawa yaron farce ya shiga tsunkonsa da ƙarfu ba tare da kowa ya lura ba, mutane duk sun koma gefe. Sai aka ji yaro ya fashe sa wani kuka, lokacin ne mahaifiyarsa da ta uso wajen tana kuka ta ƙaraso, kukan da yaron ya fashe da shi sai Sheik ya shiga faɗin "Allahu akbar! Ya dawo hayyacinsa sun fita" Ya faɗa lokacin har jikin yaron ya saki kamar mai jin bacci yana lunshe idanu, babar yaron ce ta karɓe shi da hannu biyu, tana miƙawa Sheik 3k ƴan dubu-dubu tana cewa "Allah saka da alkairi, Malam ga abin sadaka" Ko fulaki bai yi ba ya karɓa yana cewa. "Babu komai ai yi wa kai ne don ma an ce babu kyau mayar da hannun kyauta baya" Mutane ganin Sheik ya warkar da yaro aljannu sun fita daga jikinsa sai girman Sheik ya ƙaru a idanun su, suka shiga yin kabbara. Kuɗin nan ya saka a aljihu yana faɗi a zuciyarsa cewa. 'Allah kawo dubbanku, da a ce za a ke samun abin sadaka mai yawa haka ai da wuri zan cika buhu da kuɗi' Gabansa yana faɗuwa ya matso daga gaban kukar da su Liman suke ka,reshen kukar ne manya guda biyu a can saman amma ba tsililiko ba, ɗaga reshen Liman ne a maƙale kamar ɓeran da aka tsamo daga ruwa, ɗayan kuma Mai Gari, sai wani lanƙwashashshen reshe wannan matar mai farfaɗiya tana zaune a kan, su kuma suna maƙale da hannuwan su a kan reshen. Sheik ya yi shiru jin wajen babu abin da yake tashi sai kabbara, matan gari an taru wasu ma sai yanzu suke ƙarasowa wajen, a baya idan haka ta faru sai dai kowa ya yi ta kansa, a ringa shiga gida ana kullewa, amma yau ganin balaraben malami kowa sai tsoro ya ragu daga zuciyarsa. Sheik ya fara tunanin Malam Manniru, wanda yake zaune a wani ƙauye a daji a can wajensa yake bashi magungunan da ya zo don yon bogin da su, har ruƙiyar ma ya koya masa, sai dai ya san yin magani dace ne ga shi maƙudan kuɗi malamim yake karɓa. Baki ya buɗe ya shiga jan fatila, nasi, falaƙi, yana ta maimaitawa, ya buɗe wannan ruwan ya tsiyaya a marfin ya watsa wajen bishiyar kukar, wata irin kururuwa da su Liman suka ɗauka sai da Sheik ya ja baya kamar zai fita da gudu, sai kuma ya tuna ashe shi ne jagaba a garin. Ya daɗe yana ta karatun nan sai uban gumi yake sharɓawa, ruwan maganin na kuwa sau uku ya watsa, cikin taimakon Allah sai Liman da Mai Gari suka fara atishawa, kawai sai ga su an sakko da su ƙasa, mai fardaɗiyar ce aka sakko ta kamar wanda aka jefo ta, ta zo da rubda ciki, gabaɗaya wajen ya kaure da faɗin "Allahu akbar! Allahu akbar".Wani daɗi ya rufe Sheik yana jin kawai ya warke, shi dai da talauci sai ko ya ga ana yi amma kam sun yi hannun riga da shi da talauci, tun da ga shi har ta ci nasarar warkar da yaro da kuma su Mai Gari, duk da ya san cewa da alama aljanin jikin yaron nan wahala ce ta tsinkon da ya masa ta sanya ya fita. Mai Gari da Malam Liman sai washe baki suke, su kuma jama'a maza da mata sun dunƙule hannu suna jinjinawa Sheik suna faɗin Allahu akbar!. Sun san ba ƙaramin aiki ne a sakko da mutane daga saman kukar bulukiya ba, matar nan wasu mata biyu aka sa suka kinkime ta aka ce a kaita gidan ta. Mai Gari da Liman faɗi suke "Jajirtaccen balaraben malami, garin Ƙundu ya yi babban kamu, sai inda ƙarfinmu ya ƙare dole gari ya kyautatawa Malam kai jama'a ku ce Allahu akbar!" Gabaɗaya wuri ya kaure da kabbara a tare. Sheik bakinsa ya ƙi rufuwa, sai jin kansa yake yana ƙara girma, har ya fara hango yadda zai yi kuɗi a saya kadarori. Yana shafo gemunsa ya ce "Kar ku damu, mu dama taimako ne muke yi, indai aljannu ne ko ido biyu za mu fafata da su bare kuma a jikin ɗan adam, ai na gani duk aljannu ne suka baibaye kukar amma yanzu sun tarwatse" Ya faɗa yana ɗan murmushi, a take mutanen gari suka fara kawo kuɗi suna ba Sheik tun yana zubawa a aljihu har dai aka ara masa fanteka yake sakawa, mutane suna murnar ceton su Liman da ya yi da kuma murnar garin su zai yi lafiya za su rayu babu tsoro. A cikin kunnesa iska take kawo masa maganganun matan sa suke wajen wata tana cewa "Ai mun samu wajen zuwa, mun huta kaiwa malamai da bokaye kuɗaɗenmu suna bamu maganin mallakar miji, da wanda ake yi wa kishiya, shikenan yanzu a wajen balaraben malami za muke baje haja" Wata ta ce "Ai na faɗa miki yanzu malamin nan sai ya rasa lokacin kansa in aka ringa tururuwa" Duk abin da suke faɗa Sheik yana ji har ya fara hango yadda zai ke tsula musu kuɗin aiki. Ana cikin haka kamar an ce Sheik ya ɗaga kai, sai kuwa ya sauke idanunsa a kan kukar bulukiya. Wani kan ƙwarangwal ya hango ajiye a saman kukar, sai ƙaho a jiki, da sauri ya sunkuyar da kansa, yana haɗiye wani yawu muduk. Carbinsa ya shiga ja da sauri-sauri dama robar ruwan maganin tana cikin fantekar kuɗin, gabansa ne ya shiga faɗuwa ya tuno furucinsa da yake cewa ko ido da ido za su fafata. Liman ne ya ce "Ya Sheik ya dai?" Ya faɗa ganin duk ya diririce yana ta faman haɗa gumi" Ya san babu wanda ya lura da abin da ya gani, bai sani ba dai ma ko shi kaɗai aljannun suka buɗewa ido yake ganin kan ƙwarangwal ɗin. Yaƙe ya yi ya ce "Ah babu komai fa dama"Ya faɗa yana ɗan ɗaga kai kaɗan ya hangi saman kukar, dariya ya ga kan yana masa, kafin ka ce kwabo sai aka ga an fara sama da Sheik alamar ƙafafunsa sun fara barin kan ƙasa, idanu ya zare don kafin ƙiftawar ido har ya wuce saman kan mutane shi kaɗai yana shawagi a saman ba tare da ya riƙe ko ina ba, yana riƙe da fantekar kuɗi. Jama'aka shiga faɗin "Subhanallahi!" Ana ta maimaitawa kowa yana ganin ikon Allah, Sheik gabaɗaya ya tsure sai hannu yake miƙawa alamar a kawo masa ɗauki, tun da aka fara sama da shi yake faɗin "Yauma tublar sara'ir, jama'a taimako" Kowa jin Sheik da kansa yana ambatar taimako sai suka fara ja baya, jar su Mai Gari kowa ya koma can nesa, sai da aka kai Sheik saman kuka, wuyan jallabiyarsa da shi aka rataye shi a jikin kuka, yana ji yana gani kan wanann ya ciro hirami daga wuyan Sheik ya masa ɗaurin ɗankwali gwaggwaro a kansa, babu wanda yake ganin kan sai Sheik... MAMAN AFRAH 09025576222 *TALLAH TALLAH TALLAH* 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 ???????????? *KIN KARANTA* ?????????????? *Shin kin karanta littafin nan? Kin ji cakwakiyar da ake yi a ciki? Ta kamu da mugun son sa wanda da shi ta raini zuciyarta tun tana ƙarama, tun bata san mene ne so ba, sai dai tana daf da sanar da shi aka saka aurensa da yayarta da yake ƴan uwa ne, ta ji takaici a hakan take fafutukar jan hankalinsa duk da yana mijin yayarta, mutuwar yayarta shi ya bata damar cin karenta babu babbaka, ta shiga ta fita ta aure shi tun dafin mutuwar matarsa bai barshi ba, sai dai shegen kishin ta, ya sa ta raba mijinta da kowa ciki kwa har da uwar da ta kawo shi duniya, hatta ƙawayenta mararsa aure sai da ta daina hulɗa da su dk don kar a aure mata miji, mai zai faru? Aminiyarta da ta yarda da ita take faɗa mata sirrinta ita ce mafarin komai, kwatsam mijin ya tashi ƙara aure, da aminiyarta suke fafutuka wajen toshe ɓarakar auren da mijin ya ɗakko, ashe dai ita ce ta yi wufff da mijin nata sai a washe garin ranar da ta tare suka yi ido huɗu, shin ya zaman zai kasance? Kin taɓa jin inda kishiya take yin asiri ta rufewa kishiyarta HQ a toshe wurin gabaɗaya a gefe guda a fito mata da mazantakar namiji? To a buk ɗin nan an yi wannan badaƙalar, da 500 kawai zan baki book ɗin har ƙarshe* . 09025576222 [7/5, 6:08 PM] Mom mashkr & Afrah: https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 Mums & mums-to-be! 👶🧺 Adashen washing machine🥳🥳🥳🥳bby & kids’ clothes + accessories ya dawo!🔥 Easy payment, zero stress! Ki shiga kafin a gama! 📥💃 +234 707 753 2253 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 6 *MA'ARUF* Yana dafe da kuncin yana jin zafi da kuma haushin abin da Hajiya ta masa. Daddy ya ce "Haba Hajiya yanzu abin da ya yi har ya ci hukuncin mari haka?" Ya tambaya yana kallon ta Rahma ce ta taɓe baki ta ce "Haba Daddy ko duka aka masa ai hukuncin ya yi kalli fa yadda ya ɓata mini kaya" Shiru Daddy ya yi duk da bai ji daɗin abin da aka yi wa Ma'aruf ɗin ba, amma sai dai son ƴarsa ya rufe maaa ido. Hajiya ce ta ce "Alhaji kai kake sangarta wannan yaron, in ba haka ba har ya ɓatawa tilon ƴar tamu jikinta kake tambayar dalilin dukan da aka masa, kuma har kana ganin hukuncin da aka masa ya yi tsauri" Daddy iska ya furzar mai zafi ya ce "Bai kyauta ba kam amma dai da baki mare shi ba" Ma 'aruf ya danne takaicin da ya ji yana mai sauke hannunsa daga fuskarsa ya ce "Ba komai Daddy ai ita ma mahaifiya ce a gareni, duk abin da ta yi daidai ne... Kafin ya ƙarasa maganar Hajiya ta katse shi da faɗin "Ai indai tsara magana ne kai dai sai ko a samu na biyunka amma babu na ɗayanka, ka iya kalallame mutane wannan da mace ne kai kishiyarka ta shiga uku saboda kissa" Bai ce komai ba ya juya jiki a sanyaye zai fita, Daddy ne ya ce "Ina kuma za ka je" Ya ce "Zan je in ɗan watsa ruwa ne" Amsa masa Daddy ya yi shi kuma ya fita. Hajiya ta taɓe baki tana cewa "Wannan uztazun yaron miskilin gaske yana abu kamar dai bai san me duniya take ciki ba" Ta faɗa tana kama hannun Rahma. Daddy bai ce komai ba ya mayar da hankalinsa ga danna waya. Sai shagwaɓa take zubawa a haka suka haura sama wai za ta yi wanka ta sauya kayan wanann na jikinta. Ma'aruf yana zuwa ɗakinsa ya mayar da ƙofa ya rufe tare da jinginuwa a jikin ƙofar, ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya yana tuna irin yadda Hajiya da Rahma suka ɗora masa karan tsana, ya san kuma ba komai ba ne dalili illa kasancewarsa ɗan ƙauye kai ba ma ƙauyancin kaɗai ba babban abun shi ne bashi da masu gidan rana, ya san da a ce yana da kuɗi ko da kasancewarsa ɗan ƙauyen ne to zai samu sassauci da salama, sai dai ba sa ganin ilimin da yake da shi na addini a nasa ganin da tunanin ilimin addini kamar shi ne zai zama ginshiƙin da za a ƙauna ce ka, ko yaya dai ka fi ƙarfin jahili, amma a hakan suke masa kallon bagidaje saboda addininsa. Goshi ya dafe jin yanayin da ya fara ziyartarsa a ƴan kwanakin nan, wato wasu sababbin abubuwa da suke son ɓullowa daga zuciyarsa, wanda a halin yanzu shi kansa yake yaƙi da xuciyarsa, saboda ya san tabbas tana son ta kai shi ta baro ne, to in ba tsautsayin takaba auren shiɗaɗɗe ba, mene ne yake jin zuciyarsa tana son ta kai shi ta baro shi?. Ya san tabbas ba ya son halayyar Rahma, ko kaɗan baya damu da sallah ba, ga raini da ɓaci a gaban iyaye saboda an sangarta ta, sai dai yanzu yana jin wasu ƴan canje-canje a game da ita, wanda ba ya raba ɗayan biyu wannan kalmar ce da ake kira SO, wannan kalmar dai da bata duba cancanta ko matsayi, tun da ya san so babu ruwansa da ɗaukaka, matsayi, ƙanƙanci, talauci mulki kyau ko muni, idan ba zuciyarsa tana son yaudararsa ba mai ya kaita take son faɗawa tarkon son Rahma. A fili ya furta "Zuciyata karki mini haka, kar ki yaudare ni, kar ki ja mini abin da zai zama da na sani, kar ki saba da abin da ba za ki taɓa samu ba, idan mafarki kike yi ki falka, Rahma ta masu kuɗi da ƴaƴan masu faɗa a ji ne"Ya ƙarasa faɗa yana faɗawa kan katifarsa ya yi rubda ciki. Ya ci gaba da faɗa a zuciyarsa cewa 'Ta yaya ina baƙauye, sannan ni da albarkacin zumunci na zo gidan nan cin arziƙi amma kike ɗakko mini dala ba gammo haba zuciyata ki mini lamuni, ki rufa ni ki saya, ki rufa mini asiri kar ki ja mini tozarci, don abin da kike so ba za ki samu ba ni na sani' Ya ƙarasa faɗa a zuciyarsa yana fito da wayarsa, number mahaifinsa Mai Garin Ƙundu wanda yake ɗan uwa ne na jini ga Daddy, ya shiga kiransa, amma bai ɗauka ba, sai da ya kira sau uku ba a ɗauka ba sannan ya mayar da wayar ya akiye a kan katifar yana mai kifa kansa a jikin katifar yana jin yadda son Rahma yake fara huda zuciyarsa a hankali. *LAMI* Kallon Sheƙeƙe ta yi wa Tunde tana riƙe da ƙugu ta ce "Tunde na faɗa maka ba ya nan, ni nan da ka ganni da haushin kuɗin da ya guje mini na kwana, amma in kana ganin kamar yana nan na hana shi fitows ga ƙofa ka zo ka shiga ku fafata, ka ga sai a yi ko a kai ko a shi" Idanu yake zarowa jin furucinta shi dama ya tsani bayar da bashi saboda ba yadda zai yi ne ya ba Ibra amma gashi cibi yana neman zama ƙari. Kamar zai yi kuka ya ce "Ba zan yarda ba sai kin biya ni kuɗin da nake bin mijinki" Wani uban tsaki ta yi ta ce "Da na san lokacin da kuka yi, to ko biyar ba zan bayar ba idan rigima kake ji na dame ka na shanye, ni na fi inyamuri iskanci dan ka ji in faɗa maka" Ta faɗa tana wani zazzare ido. Haushi da takaici ya cika shi ya ce "Ko za ka daure ki ranta masa" Hanci ta yatsina ta ce "Ko naira biyar ɗita ba za ta yi ciwon kai ba, ka kama hanya ka je gidan kakarsa wataƙila tana da abin biyanka" Tana gama faɗar haka ta juya ta bar shi a tsaye yana riƙe da takarda yana sababi cikin gurɓatacciyar Hausar sa . Yana fita bai zame ko ina ba sai gidan Inna Tasallah kafin ya ƙarasa can ya haɗu da wani wanda jiya yana zaune a fadar Mai Gari aka yi wa su Lamu shari'a. Ganin Tunde yana tafiya yana ɗaga takarda yana masifa ya masa magana, bayan sun gaisa da shegen tsegumi sai cewa ya yi "Ah, ah Oga Tunde sai ina kake sauri" ,Kamar jira yake ya ce "Tsausayi mana ya sa na ba wannan Ibra bashi, ya ce zai dawo daga kasuwa jiya ya mini blance amma yanzu na je gidanaa wai ba ya gari yanzu sai cewa ta yi matarsa wai sai dai in je gidan Kakarsa ta biya ni" Buɗar bakin mutumin sai cewa ya yi "To ai kai faɗuwa ta zo daidai da zama" Tunde ya saki baki cike da jin haushin wancan ɗin yace "Wannan wulaƙanci ne, ashe kana mini baƙincikin kasuwancina in ba haka ba ni kake wa fatan faɗuwa?" Ya faɗa yana nuna kansa. Da sauri wancan ɗin ya ce "Haba Oga Tunda ya za a yi in maka fatan faɗuwa a sana'a Hausa ce fa na maka wato karin magana, abin da ya sa ma na faɗa saboda ina sp in jaddada maka cewa wannan Kakar tasa kuɗi gare ta jiyan nan a fadar Mai Gari muna zaune sai da ta biya kuɗin saniyar Jummai... Tun bai gama bashi labarin ba Oga Tunda ya yi gaba yana sauri yana zabga masa godiya, saboda so yake ya je kar kuɗin ya ƙare. Inna Tasallah ce zaune a bakin gadonta ta sha ɗaurin ɗankwali gwaggwaro, tana zaune robar kayan miyarta a ƙasa a gabanta, hannunta kuɗi ne naira ɗari da saba'in dama da safe ta yi cinikin naira ɗari ya zamana tana da 200 shi ne ta saya koko na talatin ta sha a haka ko suga bata saka ba, duk don kar ta saya sugan tun da ita bata ƙaunar abin da zai taɓa mata kuɗi sai dole. Sai maimaita irgen kuɗin take tana ta washe baki a fili ta ce "Kai jama'a wato a jikin kuɗi akwai wani maganaɗisu wanda idan kana irgawa duk ɓacin ran da kake ciki sai ka ji ya washe, Allah ka ƙarawa kuɗi daraja" Ta faɗa yana gyara naira ashirin ɗin, da yake ɗari ce guda, sai hamsin sai ashirin ɗin. Tana cikin wannan yanayi na nishaɗi kamar daga sama ta fara jin ana rafka mata sallama, abin mamakin ma yadda ta ji muryar ba ta bahaushe ba ce, da sauri ta ɗaga filo ta cusa kuɗin a cikin rigar filon ta gyarawa rigar filon wajen ta gyara ta ja robar kayan miyarta ta tura ƙasan gado a zuciyata tana faɗin "Yanzu na shirya ko tashin bob(Bomb) Za a yi na ɓoye kayan sana'a ta kadarata, haka kawai ka ji inyamuri yana rafka sallama, har ta buɗe baki za ta amsa sai ta fasa, fitowa ta yi daga ɗakin, wani tsohon gatari ta ɗauka ta nufi ƙofae gidan a ganinta koyaushe gwara ka zauna cikin shirin kar kana zaune a zo a cika da yaƙi" Ta faɗa tana dosar zauren tana ɗan ɗar-ɗar. . Tunde yana tsaye ya ga Inna ta fito riƙe da gatari, a tsorace ya fara ja da baya yana faɗin "Ba tashin hankali bane ya kawo ni" Ganinsa sai Inna ta sauke gatarin da ta ɗaga saman, ta shiga kallonsa da mamaki ta ce "Bayerabe mai kuma ya kawo ka gidan nan?" Kallonta ya yi ya ce "Dama Ibra ne ya ci bashi a wajena... Tun bai ƙarasa ba Inna ta fara sababi tana faɗin "Allah sa uban bashi ya ci ba bashi ba, ni ina ruwana ko na san lokacin da kuka yi, ko ka taɓa gani ko siyen ashena na je shagonka, saboda ba na son arne ya ƙaru da ni, in sha fafutukar neman halal ɗina ta hanyar siyar da kayan miya amma in je in yi wa arne ciniki, on bar musulmi to na san ciwon kaina ehe" Ta faɗa tana muzurai Cike da jin haushin ta cw za ta yi wa musulmi ciniki ya ce "To in ma liman za ki yi wa ciniki ni babu ruwana, yanzu ki shiga ki fita ki biyani kuɗin da nake bin jikan ki tun da lika biya kuɗin saniya ma... Tana masifa ta ce "Wato ga Tasallar mahaukata, sai aka ce ni gabaɗaya rayuwata a biyan bashi za ta ƙare, ni ba zan yi abin kaina ba sai dai in yi ta biyawa Ibra rigimar da ya ɗakko, tun yana ƙarami nake faman asarar kuɗi a kansa, kuma wanda ya ce na biya kuɗin saniya ƙarya ya shirga maka, don ni wallahi Jummai ko kuɗin igiyar ɗaurin saniya ban bata ba bare kuma kuɗin wata saniya" Ransa a ɓace ya ce "Ko baki biyata ba ni dai dole ki bani, mayukan bilicin ɗin da ya karɓa kaɗai ma ba na ƙananan kuɗi ya karɓa ba idan baki bani ba sai na je birni na ɗakko ɗan sanda... Kamar za ta kai masa duka ta ce "Gwafar uban ɗan sandan, idan ka yi asarar kuɗin motar zuwa birnin ka ce ɗan sandan na ce ba sanda ba ko ƙota ce na bi ta kanta da gudu aikin banza da wofi, wani shegen ya ce ka bashi bashin man bilitin(Bilicin) Gabaɗaya ka sauyawa yaro kamanni da man turawa ka mayar da shi fata kamar ƙullin ƙosan da ya sha jan tattasai, fuska tana masa tabbare-tabbare, ni ba don na yi wa Ibra farin sani ba wallahi tsabar wannan shafe -shafen da yake ba zan gane shi ba, duk ya sauya halitta da jikinsa da baƙin bayan tukunya bambancin kaɗan ne wajen baƙi, amma yanzu gabaɗaya jikinsa babu baƙi, ban da ma Ibra ya girma yanzu na tabbata ko mazaunansa aka kwataye aka buɗe sai an samu sun yi fari ina dalili" Ta faɗa tana hararar Tunde da yake jin ba don kar a kore shi daga garin ba, ko kuma a yi shari'a da shi da tuni ya make Inna ta faɗi sumammiya saboda takaici. Ganin bashi da niyyar tafiya ta yi wurgi da gatarin tana faɗin "Yanzu zan yi maganin ka, ka bari in shiga in fito, kai ba kai kaɗai ba duk wanda ya ƙara zuwa neman bashi wajena, bayan ba ni na ci ba aradu sai ya gwammace kiɗa da karatu" Ta faɗa a fili a zuciyarta kuma ta shiga cikin gidan tana faɗin 'Anya Ibra zai ga annabi kuwa, a ce ka gudu da saniyar mutane, jiya ma da tsakar rana sai da me wainar rogo ta zo karɓar jaka biyu da rabi (500) Yo in ba fashi da makami nake yi ba ina zan samu wannan maƙudan kuɗi in biya ta in na biya kuɗin bashin Ibra sai na daina siyar da kalwa da kuka wallahi' Murfin wata ƙatuwar tukunya irin ta girkin gidan biki ta ɗakko, tana ɗauka ya fara rinjayarta kasancewar yana da nauyi, amma a haka ta nufi zauren da ɗan saurin ta, Tunde yana ganin Inna ya fita a guje don takardar ma a zauren ya barta, yana gudu yana masifa cikin yarbanci. Inna har ƙofar gida ta fito riƙe da murfin tana huci saboda nauyin da ya mata.... *A yi haƙuri da wannan yau ko malam bamu leƙo ba, in sha Allah sai a next page* MAMAN AFRAH 09025576222 [7/7, 7:36 PM] Mom mashkr & Afrah: 👳🏻‍ *MALAMIN BOGI*👳 NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 7 IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha. Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE 👉join Here. Za ki sha mamaki!🤩 Muna da ✅Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅Kayan gyaran gida masu kyau 📞Tuntubi mu:+2347077532253 📩DM ;Whatsapp 📸IG/Tiktoc:@imzeed-venture *SHEIK* Gabaɗaya sai hankalinsa ya tashi ganin mutane da ya zo wajen don ya taimaka musu suna gudunsa, wato wasa tare amma ci bamban. Duk mutane an koma can nesa da kukar ana kalllon ikon Allah, Sheik kuwa gabaɗaya ya yi saranda ya san tabbas abin kunya yana dab da bayyanuwa, don bai san yadda zai kuɓuta daga wannan tarkon ba. Kan ƙwarangwal ɗin nan ya fara yawo a saman kukar da yake mutane babu wanda yake ganin kan sai Sheik abu ɗaya dai suka sani shi ne in ba aljannu ba babu wanda zai ɗaga Sheik ya kai shi saman kuka. Kan ne ya nufo kusa da fuskar Sheij, yana ji yana gani kan yake nema kaiwa bsminsa sumbata, Sheik ya shiga kawar da kai gefe, don ya san tabbas akwai gagarumar matsala a ce , amma kan kamar an ce dole ne ya sumbaci Sheik, duk ya ruɗe amma har lokacin saboda ƙarfin hali fantekar kuɗinsa tana ƙanƙame a hannunsa. Gashi yana son ya ɗakko robar ruwan maganin nan ta cikin fantekar ya watsawa kan amma kuma tsoro da fargaba ba zai bari ya yi hakan ba, ba ma a nan gizo yake saƙar ba so yake ya maje, ya jajirce kar ya bari rauninsa ya bayyana ga ƴan gari don idan ya bari suka gane yana tsoro to kuwa akwai babbar matsala, kuɗin da yake saka ran ci daga gare su ma zai zama ya masa wahala saboda za suke masa kallon kamar dai ba malamin bane. Lura da ya yi basa ganin kan wannan ya san hakan ba ƙaramar matsala ba ce amma da hakan yake ƙoƙarin saita kansa. Baki ya buɗe zai yi magana kan ya karkata ya saka masa kunne a baki, ma'ana ƙwarangwal ɗin ya saka kunnesa a bakin Sheik. Sheik a zuciyarsa ya ce 'Mai Gari a kawo taimako saboda aljannu sun fara mini ɗaurin goro' A fili kuma ya shiga ciccira idanu, amma saboda ƙarfin hali yana so ya ɓoye halin da yake ciki, duk da abin yana neman cin tura. Mai Gari a zuciyarsa ya ce 'Shikenan ma in suka ɗauke ka, uban kuɗin nan da ka tara ai sai na maye gurbinsa, kafin Allah ya sa ka kuɓuto' Ya faɗa idanunsa a kan fantekar kuɗin saboda gani yale matsayinsa na Mai Gari da a ce mutanen gari haka suk tara masa kuɗaɗe da yanzu ya yi ban kwana da talauci. Sheik da wani irin sauti ya ji wannn kan yana masa magana yana cewa "Ibra, ka baro garinku ka zo wannan gari baka san matsalolin da suke ciki ba, to ka kawo kanka cilin gagarumar matsala, ko dai ka haɗa kayanka ka koma inda ka fito ko kuma mu shiga fafatawa da kai" Tsuru Sheik ya yi yana jin maganar kamar tana amsa kuwwa amma ya lura shi kaɗai yake ji, idanu ya sauke a kan uban kuɗin da aka saka a cikin fantekar nan masu uban yawa, duk da yawanci ƙananun kuɗi ne amma ya lura akwai ƴan dubu-dubu. Ganin kuɗin nan sai ya ji babu gudu babu ja da baya tun da gani yake babu mai ja da cikar burinsa, wani yawu ya haɗiye yana muzurai, kai ya ƙara cewa "Ka amince za ka bar garin Ƙundu a yau?" Wannan tambaya ta sanya ya ji wani takaici saboda ga shi dai a kwana ɗaya ya haɗa wannan uban kuɗi babu aikin fari bare na baƙi, to ina ga ya yi watanni, duk da shi a ransa yana ganin in har ya samu dama a shekara goma ma ba zai bar garin Ƙundu ba, tun da ya ga wannan hanyar arziƙinsa. Shiru da ya yi sai kan ya ce "Shirunka ya nuna ba za ka tafi ba to mu zuba mu da kai" Ana gama faɗa masa haka sai ya ga kuɗaɗen cikin fantekar sun fara ɓacewa, idanu ya shiga zarewa yana son yin ihun kuka amma babu dama, ba ya so ya bayar da kansa a wajen Mai Gari da mutanen gari. Gabaɗaya cikin fantekar sai robar maganin kaɗai ta rage sai wata tsohuwar naira biyar. Takaici ne ya kama shi yana ji a ransa da a ce shi malamin gaske ne ba MALAMIN BOGI ba da sai ya yi addu'ar da zai ƙona aljannun garin gabaɗaya, tun da gashi yanzu ya ga samu ya ga rashi. Kafin ya gama wannan mamakin sai ya ji an fara tura shi daga baya kamar dai idan mutum ya hau lilo ake tura shi yana yin gaba yana dawowa baya, to haka ya ji, idanu ya runtse tun da shi banda fantekar wannan da ya riƙe babu wani reshe da ya riƙe, illa wuyan rigarsa ne kawai yanzu a maƙale da bishiyar kukar. Turashin da aka fara sai ya fara ganin kamar zai hantsila ƙasa, suratul nasi ce kaɗai ya samu nasarar wartowa a bakinsa ya shiga karantowa babu sautin yana fita a hankali sai shi kaɗai yake ji, su Malam Liman da suke ƙasa da mutanen gari suna kallon yadda ake shilla Sheik bakinsa kuma sai kaiwa da komowa yake alamar yana magana sai dai kasancewar a can sama yake basa iya jin furucin nasa. Ya daɗe a haka har ya fara fidda rai da rayuwa, hawaye suna safa da marwa a saman fuskarsa. Dakyar ya samu ya daina hangen ƙwarangwal ɗin kan wannan don ya ɓace ɓat, sannan an daina cilla shi yana lilo. Ganin haka sai ya fara tunanin mafitar da zai wanke kansa ba tare da mutanen gari sun gano ainihin abin da yake faruwa ba. Hannusa ɗaya ya cire daga jikin fantekar ya kaiwa jikin reshen kukar wani uban naushi, har sai da bayan hannun ya fashe alamar ƙumewar da ya yi, ya buɗe murya yana faɗin "Allahu akbar!" Sai da ya kaiwa reshen nan naushi sau biyar yana ambaton kabbara, duk da azabar da take ziyartar hannun nasa. Ji ya yi an finciko rigar tashi daga inda take a maƙale, idanu ya waro ganin ya nufi ƙasa gabaɗaya mutane aka dare daga wajen, Sheik fatansa da addu'arsa Allah ya sa ya faɗa a kan Liman ko Mai Gari, sai dai saboda ƙarfin hali yana dab da faɗowa ya buɗe murya yana faɗin "In sha Allahu balaraben malami ne da nasara a kan ku, garin Ƙundu ya fi ƙarfin ku aljannu" Da wanann kalaman ya faɗo sai gashi wancakar a tsakiyar wajen, ƙatuwar fantekar wannan ta kife kansa, gabaɗaya jama'a aka yi kansa, faɗuwar da ya yi ya ji hular gashin sa tana neman cirewa. Ga faɗowar da ya yi ƙugunsa kamar zai cire amma dai saboda wannan ce hanyar cutar jama'a da zai yi wajen samun kuɗinsa dole ya daure. Mai Gari ne ya miƙa hannu saman kan Sheik ya cire fantekar yana ta faman jera masa sannu. Duk da ya jigata kuma idanunsa a rufe amma a haka yake jero kabbara. Jin hular gashin kansa tana nema zamewa ya yi azama ya dafe kansa da hannu, mutane duk an kewaye shi ga hawayen nan da ya yi ga bayan hannunsa ɗaya a dauje, da kaɗan-kaɗan ya shiga buɗe idanun kowa ya zuba masa na mujiya ana jiran a ji ta bakinsa. Hannu biyu Mai Gari da Liman suka saka suna ƙoƙarin tada shi zaune, duk fa haka bai yi wasa dafewar da ya yi wa hular gashon kansa. Mai Gari ne ya buɗe baki ya ce "Sannu Ya Sheik, Allah ya maka alam nashra" Ya faɗa cike da tausayawa. Cike da ƙarfin hali Sheik ya ce "A haba kar ka damu Mai Gari ai mu Allah ya riga ya bamu, duk runtsi ba zan bari a cutar da garin nan ba sai inda ƙarfina ya ƙare" Liman ne ya ce "Kamar ya Sheik kai da ka sha wahala amma kake kiran sai ƙarfinka ya ƙare?" Sheik a zuciyarsa ya ce 'Ka ji masu hana ruwa gudu, waɗannan basa mutuwar tsakar ɗakinsu, wato zani zai kuncr mini a kasuwa' A fili kuma ya ce "Ai ni nan na hangi wani bala'in tashin hankali, gingimeman yaƙin duniya na uku ne aljannu suka shirya tsakanin su da mutanen garin Ƙundu, gabaɗaya so suka yi su tarwatsa ku, su yi muki bazata, cikin ƙoƙari don ba na so ku firgita hankalinku ya tashi, shi ya sa a zuciyata na ringa addu'a a kan iska ta kai ni saman kukar, domin daga can ne aka shiryo dakarun yaƙin, shi ne ma kuka ga na tashi a saman iska, to a can ma ku abin da idanunku yake gani da ban abin da yake faruwa da ban, kuna ganina a rataye amma bakwa ganin gwagwarmayar da take faruwa, yaƙi ne ake tafkawa suna kawo sara fa suka da wuƙaƙe da adda ta aljannu a ƙarshe duk na ƙwace makaman na ci su da yaƙi hatta wanann hannun nawa haɓar wani aljani na yi ta naushi da shi kun ga yadda na ji ciwo, ku za kuke gani ina naushin kuka amma ni ina ganin aljani ne mai ka bakwai, ganin dai zan musu lahani duk suka watse don duk na jinyata su, saboda baƙin talaucin da suke ciki ma, na raba musu kuɗin da kuka tara mini, domin na ji suna cewa za su bazo garin duk wasu kuɗaɗe su kwashe" Gabaɗaya maza da matan wajen suka yi wata kabbara tamkar a filin sallar idi. Suka ce "Allahu akbar" Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin ƙaryar da ya zabga ta kuɓutar da shi, a take Mai Gari ya saka ƙasan babbar rigarsa yana sharewa Sheik ƙasa a bayan rigarsa ganin faɗuwar da ya yi duk ya kwashi ƙasa. Cike da tausayawa yana miƙa hannunsa kan hular Sheik daga ƙeya yana karkaɗe masa ƙasa, Sheik kuwa sai ƙara danne hular yake gudun afkuwar matsala, Mai Gari ya ce "Lallai garin Ƙundu ya yi dace mai shahada da sadaukar da kai ga mutanen garo domon ceton rayuka, in ba haka na ta yaya za ka amince da garin nan har haka?, Ni da ya kamata a ce ni zan yi wannan sadaukarwa" Sheik cike da lanƙwasa kuryarsa ya ce "Ina ai in har ina garin nan babu wata matsala da za ta tunkaro ku in ƙyale ta, saboda mu can a ƙasashen larabawa haka muke yi bare ni da na baro ƙasata don in zo in taimaka muku" Gabaɗaya sai aka shiga jinjinawa Sheik bisa namijin ƙoƙarin da ya yi, haka ya ƙara girma a idanun jama'a kowa yana yaba masa. Haka aka yi yuya guda don raka Sheik gida ya huta saboda faɗa da aljannu. Amma a ransa baƙinciki ne fal na yadda aljannun suka ɗauke masa kuɗin da ya tara, yana murna ya samu kuɗi ashe dai da sauran rina a kaba. Har cikin gida aka rako shi ana girmama shi, da zai shiga ɗaki Liman ya ce "Sheik Allah gafarta malam ga robar ruwan maganinka, da naira biyar ɗin nan, ita da ka rage ta a cikin fantekar ko maganin aljannun za a yo da ita" Ya faɗa cike da girmamawa yana miƙa masa don an ba mai fantekar fantekar ta. Sheik kamar ya yi kuka ya ce "Eh ai ina sane na rage ta, ka san har hawayen tausayin garin nan na yi a saman kuka na ji tausayinku sosai" Ya faɗa yana danne takaicin da yake ji a ransa ga zafin da hannunsa yake yi. *DA YAMMA* Ƙofar gidan Sheik ya cika da jama'a maza da mata, masu karɓar magani, saboda ya ce ba za a ke bada magani a titi ba saboda kowa abin da zai nemi magani sirri ne a wajensa bai kamata ake faɗa ba, hakan ya sa aka yi dogayen layi biyu na maza da ban na mata da ban, aka ce idan mace ɗaya ta shiga sai namiji ɗaya ya shiga. Wata mata ce ta fara shiga gidan da sallama, Sheik ya amsa, yana mai mata umarnin ta shiga, shiga ta yi ta samu waje daga can nesa wajen ƙofar ɗaki ta zauna, shi kuma yana daga kan sallay ya lanƙwashe ƙafa sai wani ƙaton baho a ajiye daga can bayansa. Gyaran murya ya yi ya ce "Mai yake tafe da ke?" Matar wani daɗi ne ya cika mata rai jin muryarsa, sai yanzu take tabbatar da maganar mutanen gari da ake cewa maganarsa hausar ma bata fita, ba ma wannan ba farar fatarsa kaɗai ji take kamar wanda ta je garin makka. Cike da ɗan diriricewa irin tana magana da balarabe ta ce "Malam dama mijina ne ko kaɗan ba ya kiran sunana, sai ya kira kishiyata sa sunanta amma ni sai yake kirana madam, kamar wata inyamura mai bashi hayar gida" Ta faɗa cike da takaici don dama ta daɗe tana son ta magance wannan matsalar amma du wajen malaman da ta je sai a ce mata wai soyayya ce da girmamawa, waɗanda kuma take ganin sun cinye mata kuɗi ko an bata maganin ma ba ya yi, amma dai yanzu tun da ta samu balaraben nan wanda aka ce aljannu ma yana maganinsu, to tabbas ta san ta zo ƙare kukan ka. Sheik a zuciyarsa ya ce 'Mata masu duniya, mata iyayen kishi wato ita ba wata babbar matsala ba ce da ita ma"' Amma a fili sai ya ce "Allah sarki haƙiƙa na jimanta miki, wannan ba ƙaramin abu bane a ce mijinki yana kiranki da suna madam, kamar dai wata tunkiya, ko kuma bayerabiya mai gasa masara a bakin titi" Ya faɗa yana ɗan mayar da fuskarsa abin tausayi. Kai ta kaɗa irin ka ji dai ji, a zuciyarta tana jin daɗi don ta tabbatar da cewa wannan ba sunan soyayya bane ko na girmamawa. Yana ɗakko wani ƙullin magani ya dube ta da kyau ya ce "Wannan maganin ki samu ƙatuwar zabuwa ko kaza ki dafa da wannan maganin, ki juye masa ita duka amma sai ranar bakin girkin ki, kar ki ci ko ƙafar kazar, ki ce masa takanas kika dafa saboda kina son sa don ki faranta masa, sai ya kusa cinyewa ki ce masa kina da wata buƙata in ya tambaya sai ki ce daga yau ya daina ce miki madam, zai buƙaci sunan da zai kira ki da shi sai ki zaɓa ki faɗa masa, daga ranar zai daina kiran ki Madam!" Wani daɗi ne ya baibaye ta, ashe ma aikin ƙarami ne take ta ƙunsar baƙin ciki, kullum in ta ji ya kira kishiyarta da sunanta ita ranta ɓaci yake, ta lura idan ya ce mata madam kishiyarta har wata ɓoyayyar dariya ta cusa haunshi take mata. Maganin ta karɓa ta ce "Malam nawa ne abin sadaka" Sai da ya ƙare mata kallo yana son gane tana da halin kuɗaɗe masu yawa ko kuma kuɗi kaɗan take da shi, sai ya daure ya ce "Ai abin sadaka ba ya kaɗan ba ya yawa" Ita kuma jin haka sai ta buɗe jakarta ƙarama, ta fito da wasu uban kuɗi ƴan ɗari biyar-biyar da ƴan dubu-dubu kuɗin gyaɗar yin ƙuli-ƙulinta ne wanda za a sayo mata buhu guda, mai da ƙarago take na siyarwa, malam sai washe baki yake a ɓoye yana ganin yana zaune a ɗaki zai ci bati. Amma sai ya ga ta ajiye kuɗin a gefenta tana ta duba cikin jakar, a tunaninsa wani za ta ƙaro sai ya ga ta fito da naira hamsin, sai kuma ta ɗauke kuɗin mai yawan da ta ajiye a gefe ta mayar cikin jakar ta zige zip ɗin, ta ɗakko hansin ɗin da hannu biyu ta zo gabansa tana cewa "Gashi Malam, Allah ya biya buƙatu, muna godiya babban balarabe na ƙasar larabawa" Tamkar Sheik ya saki ihu haka ya ji, kamar shi Sheik amma ta bashi hamsin. Tsaye ta miƙe bayan ta ajiye tana gyara mayafinta, ta juya tana masa sallama, ko amsawa bai yi ba, duk takaici ya ishe shi, yana jin da na sani dama bai ce mata abin sadaka ba ya yawa ba ya kaɗan ba. A fili ya ce "Haka kawai shi fa za a dafawa zabuwa ma ai ya fini morewa, ni da na masa silar cin zabuwar haka kawai na ƙare a kuɗin siyan goro, yo siyan goro mana hamsin in ba goro ba mai za a saya da ita" Duk maganar nan da yake cikin hausa sak yake yinta, jin tahowar mutum ya ja bakinsa ya yi shiru, yana mai yin sauri ya jefa hamsin ɗin cikin bahon gudun ma kar a ganta a gabansa a zaci kuɗi kaɗan yake karɓa. Wani saurayi ne gajere baƙi ya shigo da sallama, malam ya amsa saurayin bayan ya zauna ya ce "Malam ina da buƙata mai girma" Sheik ya ce "Ina jinka" Suarayi ya ce "Matsalata guda ɗaya duk wajen budurwar da na je bata so na, sai ake cewa ba a son gajarta ta, kuma wai na yi baƙi da yawa shi ne na ce ko za a bani maganin da zan kore baƙin jinin nan daga jikina wato a bani maganin farin jini?" Shiru Sheik ya yi yana nazarin maganar, ya ƙara kallonsa sai ya ga har wani sheƙi baƙin nasa yake, ga wani muni kamar me, hakan ya sa a ransa ya ce 'Ni ɗin ma da kake gani duk bula ce, a toh ni ma ba farin bane mai ne ba don kar a yi saurin gano ni ba da man bilicin ɗina zan ke tsiyayewa ina ɗaurawa a leda ina ba masu buƙata irin taka, to kar a ce ni ɗin ma hakan take gwara in tsaya matsayina' A fili kuma ya ce "Subhanalla, lahaula wala ƙuwwata illa billa, hasbunallahu wa ni,imal wakil, iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in" Saurayin gabaɗaya sai gabansa ya shiga faɗuwa jin abin da Sheik yake faɗa, don har ya fara tunanin kar a ce aljana ce ta aure shi, ko kuma a ce ba zai taɓa auruwa ba a haka zai rayu, gashi yana buƙatar aure. Tun kafin Sheik ya ƙara magana ya ce "Malam ba dai babu maganin jinyata ba?" Ya ƙarasa kamar zai yi kuka. Sheik ya ce ",A haba ɗan saurayi ai kowace jinya Allah ya saukar da maganinta, mutuwa ce kawai bata da magani" Wani gauron numfashi ya sauke ya ce "Alhamdulillah" Sheik ya ce "Matsalarka tana da magani amma da sharaɗi" Ya ce "Zan bi kowane sharaɗi ne in dai mace za ta amince in na ce ina sonta har ta yarda ta aureni" Sheik ya ce "Zan baka wani ruwa da za kake shafawa a fuskarka tsawon kwana bakwai, amma fa ka tabbatar a kwanaki bakwai ɗin nan ka samu wata ƙwaƙƙwarar sana'a da za take kawo maka kuɗi, sannan a ranar da ka cika kwana bakwai, ka nufi wajen budurwa da kake so kana zuwa kafin ka gabatar da kanka ka bata dubu goma" Idanu saurayin ya zaro saboda shi ko kyautar naira ɗari bai taɓa ba wata mace ba. Yana kallon Sheik ya ce "Malam dubu goma? Ni ai bana ba mace kuɗi" Sheik a zuciyarsa ya ce 'Ashe shi ya sa ake gudunka, yo ga muni ga cin zanzana, ma'ana ga talauci ka muni wace mace ce za ta yarda, da aka bayar da kuɗi ai babu wanda zai ga muninka" A fili kuma sai ya ce "Wannan shi ne sharaɗin maganinmu" Shiru ya yi sai kuma ya ce in dai da biyan buƙata to zai yi. Sheik ya san muddin saurayin nan yake bada kuɗi budurwa ba za ta ƙi son sa ba duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba wasu ƴan matan basu da son kuɗi. Ruwan da Sheik ya tsiyaya masa a ƴar kwalba ya karɓa, ya ce masa na farin jinin ne da kuma wanke shi da munin mata su daina ganin muninsa, godiya yake kamar zai ari baki, bai san cewa ruwan ma a randa Sheik ya ɗuro shi ya ajiye, don ya lura in ya ce maganin da ya saya wajen malam zai ke bayarwa ba lallai ya haɗa kuɗin ya ƙara komawa ya karɓo wasu ba, wanda ya san zai iya warware matsalarsu ba tare sa magani ba sai ya basu maganin BOGI. Yana karɓa ya tashi zai fita ba tare da ya bada kuɗin sadaka ba, ran Sheik ne ya ɓaci ganin zai fita ya ce "Ɗan samari babu abin sadaka ne ?" Juyowa ya yi cike da girmamawa ya ce "Ai a gari aka yi sanarwa cewa a zo nan a karɓi magani an samu baƙo daga ƙasar larabawa na ɗauka ba a biyan abin sadaka" Cike da jin haushi Sheik ya ce "Hankali za ka taka aljani burubutu a gabanka dama su ne masu karɓar kuɗin sadakar" Da sauri sairayin ya ja baya yana mai ɗakko dubu biyu hannunsa yana karkarwa ya ajiye a gaban Malam ya juya cike da tsoro ya buɗe ƙofar ya fita. Yana fita Sheik ya ɗauke dubu biyu. Wani tsoho ne ya shigo yana dogara sanda, saboda tsufa har ya ranƙwafa, dakyar ya zauna, yana sauke numfashin gajiya hannunsa yana karkarwar tsufa jikinsa duk ya yi yaba sannan kansa da gemunsa duk furfura. Sheik kawai kallonsa yake ya rasa ma mai zai kawo tsohon nan shi da ya dace ya zauna a gida yakenta sallah yana neman gafara ya jira zuwan mutuwarsa. "Bakinsa yana karkarwa ya ce "Ɗana balarabe, na sha wahala a waje wajen bin layin shigowa, yanzu ma ganin an bige ni a turarreniya shi ne wata mata ta bar min layinta na shigo, ka san ai namiji ɗaya sai a mace ɗaya aka ake shigowa, shi ya sa ka ga na shigo" Har lokacin Sheik yana mamakin abin da zai kawo tsohon. Daurewa ya yi ya ce "Baba maganin basir kake so ko maganin ciwon baya?" Tsohon ya ce "Haba ɗan nan balarabe, ni nan maganin maida tsoho yaro za ka bani, wato maganin ƙarfi ka gane?Ƴan mata ne guda biyu zan ɗauka a rana ɗaya dukansu kowacce budurwa" Mamaki ne ya mamaye Sheik dakyar ya danne harshen sa ganin bai yi magana da yaren hausa sak ba ya ce "Budurwa fa Baba?" Tsoho ya ce "Rass kuwa ba ma budurwa ɗaya ba ƴan mata biyu ake saka mini su a lalle gobe za su tare ka ga kuwa aiki ya ganni dole in nuna musu basu auri tsoho ba" Shiru Sheik ya yi ya rasa ma abin da zai faɗa masa, kawai ya ɗakko wani garin magani ya ce ya saka a ruwan wanka ranar da amaren za su tare. Godiya kamar wanda aka bashi maganin da tsofa zai barshi. Dubu goma ya ba Sheik amma sai da Sheik ya kama shi ya iya dogara sandar ya tafi. Wata mace ce mai ƙiba ta shigo, tana wani wurwurga idanu, ganin yadda take zazzare ido tana wani soshe-soshen jiki sai Sheik ya ji duk ya tsargu, juyawa ta yi ta rufe ƙofar bai lura ta saka mukulli ba, kuma sai ta cire mukullin, cike da ƙaguwa ya ce "Mai yake tafe da ke?" Ta ce "Ina so ka bani maganin da kullum mijina sai ni, sannan ka bani maganin da zan zubawa kishiyata ta mutu, da wanda idan na shafa a hannuna duk inda kuɗi yake zai zo wajena" Ganin kamar yadda take magana yanayin ya nuna kamar umarni take bashi ya ce "Ayya ai ba a kisan kai a wajen nan, kuma kuɗin mutane ai kamar sata ce, zan baki dai wanda mijink... Bai ƙarasa ba kawai sai ya ga ta tashi tsaye idanunta sun juye ta fara dalalar da yawu, gabansa ne ya bada rasss ya shiga faɗuwa tamkar zuciyarsa za ta huda ƙirjin ta fito, gadan-gadan ya ga ta biyo shi, ya ja baya ta matso ya yi wani tsalle sai ya ji ta riƙe masa hiramin da yake rataye a wuyansa, jin za ta sheƙe masa wuya suka shiga kunce. Idanunsa cikin nata ya gane aljannunta ne suka tashi ba ita ba ce, salati ya hau janyowa yana ji a ransa anya ba zai haƙura da maluntar nan ta BOGI kuwa ba? Da gudu suka yi wajen ƙofa sai lokacin ya lura ƙofar a kulle, idanu ya zaro gabansa yana faɗuwa ganin daga shi sai ita kuma bashi da nutsuwar mata ruƙiyya, kafin ya yi wani yunƙuri sai ji ya yi ta fisge hular gashin kansa, salati ya ɗauka a zuciyarsa kafin ya ƙarasa wani ya kamo wani , yana juyowa ya ga ta tuƙunƙuna hular ta ɗaga rigarta ta totsa hular da gemo da sajen boginsa a bireziya. Kafin ya gama tunanin asirinsa zai tono ta yi wani kukan kura ta shaƙo shi, rasa abin yi ya yi ya buɗe baki ya ce "Gabaɗaya na ƙofar gida ku shigo a guje ana ruwan kuɗi a ɗakin malam" Ya faɗi hakan ne don a yi saurin kawo masa ɗauki, ya manta da cewa kansa babu hula, haɓarsa babu gemo, gefen fuskarsa babu sajen larabawa... MAMAN AFRAH 09025576222 💃💃TALLAH TALLAH💃💃 *INA MANYAN MATAN SUKE?* *Masoyana ina ƙara talalta muku kayan sana,ata kamr su* *Less, atamfa, laffaya, kamfala, mayafai zannuwan gado, kayan yara, takalma na yara da manya, abayas, huluna na maza, mata, yara frames, sarƙa ɗan kunne zubuna banguls.* *Akwai kayan maganin mu na kamfanin meera b herbs, maganin sanyi, maganin ƙiba, maganin rage ƙiba maganin rage tumbi, maganin cire tabo ga wanda suk shafa mai ya ɓata musu jiki ko fuska, sannan uwa uba maganin mata.* *A ƙarshe ina tallata muku FURA dakan mai, wacce muke yi mai garɗi da ƙamshin man shanu, muna yi don biki, ko suna, ko taron naɗin sarauta da dai sauransu muna aikawa ko ina, akwai nono galan galan da bokitai ga masu buƙata, ku nuna min ƙauna ta hanyar siyar abin da nake siyarwa* . *Mai so ya min magana a number ta 09025576222 idan ba saya za ki yi ba kar ki min mgn.* https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Da sauransu Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 8 Sanye take da doguwar rigar less wacce ta kama jikinta, ta yi ɗaurin ɗankwali wanda ya zauna daram a kanta sai mayafinta wanda yake kala ɗaya da leshin da ta saka, ƙarami ne mayafin yana rataye a gefen kafaɗarta ɗaya. Ƙaran takalmin ta mai tsine wanda take sakkowa da saman benen shi ne ya janyo hankalin Hajiya da take zaune a kan kujera tana waya. Tana riƙe da wayarta ta ƙaraso tsakiyar rangameman falon, lokacin ya yi daidai da gama wayar Hajiya. Ɗagowa ta yi ta kalle ta, ta ce "Inyeee ka ga ƴan matan Daddyn ta, kyakkyawar mace kuma matar manya ƴan boko masu faɗa ji, sanann matar masu kumbar susa" Wani daɗi ne ya mamaye zuciyar Rahma tana jin daɗi jin furucin da Hajiya ta mata, tabbas a duniya ta tsani talaka, ta tsani talauci kuma, tana son saurayi ɗan manya wato ɗan gidan masu kuɗi sannan ɗan gayu ko ma dai yaya yake in har za a iya nunawa sa,a shi to tana son shi sosai. Kai ta langaɓae gefe cikin shagwaɓaɓɓiyar fuskarta ta ce "Ai ni sai na zaɓa sai wanda ya isa ne zai aure ni Mummy bana son duk wani namiji in har bashi da masu gidan rana" Murmushi Hajiya ta yi ta ce "Da gaskiyar ki ko ni talauci ya yi gabas na yi yamma, kuma ke da kika tashi a gidan naira ai dole sai ɗan naira" Murmushi ta yi ta ce "Bari na je baby nah yana jirana" Hajiya ta ce "Ya zo kenan" Rahma ta ce "Eh ya zo" Tana faɗa ta kiya cikin takunta na maau aji irin na mata masu ji da kansu. Yana zaune a wajen da aka tanada don zama a sha iska zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun wajen, hango ta ya yi ta taho tana tafiya tamkar tarwaɗa, tana tafiya tana yanga da wani jan a ji da mata masu aji ne kawai suke yin irin taku. Sulaiman tun da ya hango ta kwacakwam ya mayar da hankalinsa a kanta, dama yana chartin ne da wata budurwarsa, amma ganin Rahma ta taho sai ya yi saurin kashe data ya sauka ma daga kan whatspp ɗin gabaɗaya. Ma'aruf yana daga can ɗaki ya zo buɗe labulen window saboda ya ji ɗakin ya ɗauki zafi, dama dawowarsa daga makaranta kenan, ya shiga ya yi wanka shi ne zai shirya. Ganin Rahma sai ya ji gabans ya faɗi, musamman da ya hango irin kallon da Sulaiman yake mata mai cike da soyayya. Kishi ne ya tsaya masa a rai. Idanu ya runtse yana jin irin yadda zuciyarsa take bugawa. Da son samu ne yana so ya samu ko da kwatar matsayin da Sulaiman ne ya samu a wajen Rahma, shi in ba ma jarabawa ba da kuma zuciya da baka tursasa ta, ina shi ina kamauwa da son Rahma bayan ya san ko suma yake yana falkowa ba zai same ta ba. Cike da jin haushi ya rufe labulen dan sai ya ji gwara ya dawwama a cikin zafin ɗakin, a kan ya bar windown a buɗe yake kallon takaici. Rahma kuwa ƙarasawa ta yi tana ɗan murmusawa, ta samu kujerar da take kallon ta Sulaiman ta zauna, idanun da ya kafe ta da su, hakan ya sanya ta sakar masa da wani shu'umin murmushi mai bayyana haƙora, yadda hakoranta suke a jere reras kamar masara sai ya ji ya ƙara mutuwa a kanta, ya san za a saka Rahama a sahun farko na kyawawa. Cike da murya irin ta mayaudarin namiji, irin muryar da dama ta saba da yi digiri a yaudara ya ce "Sannu da zuwa sarauniyar matan duniya, alkairin Allah yana lulluɓe da ke, ina so ki sani mutuwa ce kawai za ta raba mu, don na san na gama dacen mace ta kece raini ta nunawa sa'" Ya faɗa yana kafe ta da idanunsa wanda har aai da ya sa ta ɗan sunkuyar da kai tanaƴar dariya kaɗan. Hannunsa ya miƙaya ajiye wayarsa a kan teburin da yake a tsakiyarsu ya ce "Da a ce zan mallake ki da kuwa na gama dace a duniya, ke ni bana jin zan sake bacci a duniya, don an sallame ni, a baya in jin tamkar wanda na rako maza duniya, in na ga suna da budurwa mai aji kuma ana nuna musu kulawa da soyayya ashe dai ni ɗin ma zan samu rabona" Sai da ta ɗago fuskarta ta sauke idanunta a cikin nasa sannan ta ce "Ba kai kaɗai ne ka yi sa'a ba ni ɗin ma har kullum ina alfahri da kai, yanzu daga zuwana ko gaishe da kai ban yi ba amma kana ta zuba mini yabo" Ta faɗa don kaf ta rasa inda za ta saka ranta, tana son ta ji ana yabonta ko ana koɗa kyawunta sai take ji kamar duk duniya babu kyakkyawa kamar ta. Idanu ya lumshe ya buɗe su tarrr a kan nata idanun yana jifanta da wani kallo na mayaudara wanda duk macen da akw mata sai an sace zuciyarta ya ce "Ke ɗin ce kin cancanci haka, ke ɗin ce duk kin rikita mini lissafi, bana iya kallon kowace mace sai ke, bana son kowacce mace sai ke, har abada na gama zamar mace sauran duk kallon maza nake musu" Wani mugun daɗi take ji Tana kallonsa yana kallonta, hannunta da ta ɗora a kan teburin ya miƙa hannunsa ya ɗora a kan hannunta, Ma'aruf da fitowarsa daga ɓangarensa kenan sanye yake da farin yadi ɗinki tazarce yadin marar nauyi, ya yi matukar karɓar jikinsa, Sulaiman ganin Ma'aruf ya fito ya yi saurin janye hannunsa, ita kuma da yake ta ba Ma'aruf baya bata san ya fito ba, kuma ita bata ma ɗauki cewa taɓa hannun nata wani laifi ne da har za ta janye hannunta, tun da tana ganin yanzu dan ma saurayi ya taɓa hannun mace ma wani abun ƙarama bane, tun da yanzu har wajen hoto saurayi da budurwa suke zuwa, kuma a kama hannun juna, har ma da abin da ya fi hakan, kuma a ɗora a status mutane su gani babu mai cewa an aikata haramun sai dai ake cewa sun yi kyau, idan aka samu wanda ya ce hakan bai dace ba, sai a ce ai saurayin da za ta aura ne, ko a wane hadisi ko ayar aka bayyana haka? Kawai dai ƙarshen duniya ne duk da ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Ma'aruf zuciyarsa ce ta fara tafasa shi fa dama ya lura cewa duk mazan nan da suke son Rahma ba wai son aure suke mata ba duk mayaudara ne. Wani mugun kallo yale jefaw Sulaiman daga nesa, Rahma ce ta lura da Sulaiman hankalinsa ba ya kanta baya ta waiwaya ta ga Ma'aruf ta yatsina fuska ta ce "Baby mene ne" Ta faɗa lokacin da ta mayar da kallonta kan Sulaiman ɗin. Haushi ne ya kama zuciyar Ma'aruf jin Rahma ta kira Sulaiman da wanann sunan, sunan da ko a mafarki zai ji daɗi ta kira shi da shi, shi ya rasa ma yaushe ya kamu da son Rahma abin nan yana ci masa tuwo a ƙwarya ya san dai ko a tsarinsa babu mace irin Rahma, wacce bata san darajar ɗan adam ba amma gashi so yana neman ya kai shi ya baro. Idanu Sulaiman ya ɗauke jin Ma'aruf yana masa kwarjini, shi dama ya tsani ya zo gidan su Rahma ya ga wannan baƙauyen da bashi da komai sai gidadanci da rashinw wuyewa. Ma'aruf kuwa ji ya yi da a ce yana da dama da ya je ya kora Rahma cikin gida, sai dai bashi da iko da wannan damar. Sulaiman ne ya yi ƙasa da murya ya ce "Baby ki sa wannan baƙauyen yayan naki ya kawo min ruwa" Ta kalli Sulaiman cike da jimanta abin da ya ce ta ce "Ruwa kake so sha bari na kira Mummy ta sanya ƴar aiki ta kawo" Yana ɗan haɗe rai ya ce "Ni ba na son wata ƴar aiki wannan nake son ya kawo mini" Murmushi ta saki cike da kulawa ta ce "Kar ka damu ai yanzu kuwa" Ma'aruf da ya nufi get zai fita so yake ya je masallaci ya karanta qur'ani ko ya samu sauƙi da salama a zuciyarsa, jin ƙaran wayarsa da take aljihu ya fito da ita, ganin sunan Rahma abin ya bashi mamaki har sai da ya tsaya ya juyo don ya tabbatar da cewa ita ɗin ce take kiransa, don ya san saboda wulakanci irin nata kwanaki cewa ta yi ta goge numbersa saboda bata son take jin maganar baƙauye a kunnenta. Juyawar da ya yi sai ya ga ita ɗin na wajen take kallo, kamar wasa sai ya ga tana ɗaga masa hannu alamar ya zo, bao je ɗin ba kuma bai cigaba da tafiya ba don ya san wannan kiran akwai wani abu a ƙasa kuma shi bashi da wata daraja da zai rama ko ma mai suka masa, saboda tana faɗawa Daddy shikenan ko kuma Mummy wacce a dole son babu yadda za ta yi ne yake zaune a gidan. Yana mayar da idanunsa kan wayar hakan ya yi daidai da tsinkewar kiran, yana katsewa ya ga wani kira ya shigo, juyawa ya yi yana tafiya ya ɗaga wayar ya kara a kunne yana lumshe ido, a hakan yake tafiya kasancewar gidan babban gida ne, akwai tazara daga harabar gidan zuwa get ɗin. Yana karawa a kunne sai ji ya yi ta ce "Na ce ba" Ta daɗa cike da iko da raini. Cikin nutsuwa ya ce "Ina jinki" Ta ce "Ka dawo ka ɗakkowa Sulaiman ruwa zai sha" Ransa ne kawai ya yi mugun ɓaci kasanceqar ya san al'adar Rahma ce ta tsani a kashe mata waya sai kawai ya kashe domin ita ma ya ƙunsa mata ɓacin ran da ta sa ya shaƙa. Yana kashewa ya cigaba da tafiya har ya buɗe get ɗin ya fita waje. Rahma ranta ne ya ɓaci kamar yadda ya yi zato, cike da jin kunya ta ce "Ya ce sauri yake zai je wajen suturar abokinsa da ya mutu" Ta tsinci kanta da sheƙa ƙarya. Sulaiman banza ta mata ko da ta ce za ta ɗakko masa da kanta sai ya ce ta bari ma ya daina jin ƙishin. Haka dai ranar hirar tasu ta wakana babu wani armashi. Da zai tafi ya shiga mota ya ɗakko rafar ƴan ɗari biyar guda biyu ya bata wai ta sha ice cream. Motar ya shiga direbansa da yake ciki zaune yana jiransa ya tada motar, tana tsaye tana ɗaga masa hannu, har mai gadi ya wangale musu get suka fita tare da haurawa titi. Tana komawa ciki ta kwashe abin da Ma'aruf ya mata ta faɗawz Mummy inda ta ringa faɗa ta inda take ahiga ba ta nan take fita ba, tana faɗin zai dawo ya same ta, tun da ba ubansa Mai Gari bane ya gina gidan, da har yana zaune ba za a amfane shi ba. Daddy sai bayan magriba ya dawo gidan, ko da aka zo cin abinci Mummy ta kwashe komai ta faɗa masa na tsinka Rahma da Ma'aruf ɗin ya yi a gaban saurayinta, duk da Daddy ya san abin da Rahmar ta yi bata kyauta ba sai dai ba zai iya tsawatar mata ba saboda soyayya da kuma Hajiya ya san ba za ta bari a ga laifin ƴarta ba kasancewar ƴar tata ƴar ido ce. Ma'aruf dama sai dai ya ci abincinsa da ban saboda Hajiya da Rahma wai basa iya cin abincin idan yana waje zuciyarsu tana tashi, wai suna jin yana warin ƙauye, kuma kawai tsabar rainin wayo ne. Sai da aka yi ishasha'i ya dawo don karatu suke tsakanin magriba da isha'i a masallaci, Daddy ne ya kira shi yana masa faɗan rashin gaskiya, Ma'aruf ya ce "Haba Daddy ni ne fa gaba da Rahma amma sai ta aike ni kuma a gaban saurayinta, kuma ma saurayin fa zan ɗakkowa ruwa, duk ƴan aikin gidan nan, yanzu fa ko Yayan da ka ce take faɗa min ta daina Ma'aruf take kir... Daddy ne ya katse shi da cewa "Haba kai kuwa ana ga yaƙi kana ga ƙura, ana maganar baka je aike ba kai kana maganar bata ce maka Yaya. Hajiya ce ta katse da cewa "An ƙi a ce maka Yayan ubanta ne kai da sai ta girmamaka" Kai ya sunkuyar don ya san Daddy kawai yana tsoron Hajiya ne amma ai ya san shi ne da gaskia, haka ya masa faɗan ya tashi ya fita ya koma ɓangarensa. *BAYAN SATI UKU* Zaune take a lambu ta ɗora ƙafa ɗaya a kan ɗaya tana zaune ne bisa kujerar roba sai ta ɗora ƙafafunta a kan wata kujerar, jarida take dubawa sai kayan maƙulashe a kan plate a gabanta tana ci. Tun da fa shigo lambun yake kallonta da yake idanunta a kan jaridar bata san da tahowarsa ba ma, sanye yake da riga blue mai ƙaramin hannu sai jeans baƙi sai ƙamshin turare yake mai daɗi. Rahma da ta jiyo ƙamshin iska ta kawo mata ta lumshe idanu, don ƙamshin turaren ya mata, kasancewae sabo ne ya saya ƙamshinsa ya sha bamban da wanda yake shafawa. Sai da ya zo dab da ita ta ji ƙamshin ya ƙaru alamar ma ƙamshin ba iska ce take kawowa ba mai ƙamshin yana dab da ita. Murmushi ta saki, saboda ta san sun yj waya da Sulaiman ya ce zai zo su fita su shaƙata kuma ta faɗa masa tana zaune a lambu, a tunaninta shi ne ya zo zai tsokane ta take son ya rufe mata ido ko dai wani abu makamanci haka. Cike da shauƙi ta ce "Barka da zuwa Babynah" Gaban Ma'aruf ne ya faɗi yana tunanin ko dai addu'ar da ya kwana yana yi a kan Allah ɗora shi a kanta ta amince da shi, ita ce ta karɓu. Ta cigaba da cewa "Ƙamshin turarenka ne ya sanar da ni ƙarasowarka, zuciyata tana maka marhabin, tana maka tuni cewa da kai kaɗai za ta rayu!" Kaɗan ne numfashin sa bai bar gangar jikinsa ba, tsabar irin yadda maganar ta dake shi, a hankali ya fara taku a dawo gabanta, sai lokacin ta ɗago fuskarta daga kallon jaridar tana murmushi mai ƙara mata kyau da kwarjini. A kan kyakkyawar ƙafarsa da take cikin baƙin takalmu ta fara yi wa idanunta masauki, ko a mafarki bata taɓa zaton Ma'aruf bane, cikin murya mai taushi, wacce take damfare da nutsuwa ya hau faɗin "A nawa ɓangaren ma haka ne, da ke kaɗai za ta rayu, kuma zuciyarta ta janyo linzamina ne zuwa wannan wajen, don ta bayyana miki asirin da yake cikinta, tana fata da addu'ar mu rayu a tare har mutuwa... Waɗannan kalaman sun sauka a kan dodon kunnen Sulaiman da ya nufo wajen, wanda kuma ya ƙara shiga kunnuwan Mummy da ta zo za ta sanar da Rahma cewa za ta fita, saboda ta kira wayar ta ta ji bata shiga ba, shi ne ta tasho don ta faɗa mata sai kuma kunnuwanta suka yi arba da wannan babbar maganar... *INNA TASALLAH* Zaune take a tsakar gida da yammacin ranar asabar, tana zaune hannunta riƙe da mangwaro irin mai ƙamshin gawasa, nunanne ne jawur da shi, tana sha tana lunshe ido har wani karkaɗa kai take saboda zaƙin da take ji har tsakar kanta. Tana a wannan halin Lami ta shigo da sallama, idanu Inna ta buɗe ganin Lami afujajan ta dakata da shan mangwaron ta ce "Lami lafiya kamar an hakaɗo ki?" Lami cike da jin haushin Inna tana wani ɓata rai ta ce "Wato ke Inna har kin samu damar sha mangwaro har kina lumshe ido" Galala Inna take kallonta cike da takaici ta ce "Haba Lami wai ni ku mutane mai ya sa bakwa son ku ga wasu sun ci gaba? Da raina da lafiyata ma ba zan sakata in wala na sai ana sanya min ido, yanzu kayan miyana sun ƙare duka don cikin ribar na ɗauki naira talatin na saya mangwaro in sha a ruwan raina shi ma sai ya zama ana mini baƙinciki, mutane bakwa so ku ga mutum duniya tana gara masa, wato kun fi so ake zaman kashe wando... Wata harara Lami ta aikawa Inna ta ce "Inna tsakani da Allah ko ana yi wa wani baƙinciki wa zai miki, ni wallahi a sana'ar kalwa da barkono da kuka ban ga abin baƙinciki ba" Kamar Lami ta yi saɓo haka Inna ta zaro ido ta ce "Kina wasa da maƙiyi, maƙiyi ai shi ko alawa kake siyarwa sai ya maka baƙinciki, yanzu ni a wajena ai cigaba na samu tun da gashi a cikin ribar har ina shan mangwaro" Ta faɗa tana gutsuro fatar mangwaro, Lami a zuciyarta ta ce 'Yanzu zan rikita miki lissafi, yanzu za ki kiɗime don na tabbatar baki san da abin da nake tafe' A fili kuma sai ta ce "Inna saƙon kira ne aka bani wajenki" Sai da ta suɗi mangwaron ta ce "Kai zaƙu har cikib kaina wallahi, wannan mangwaro da zan samu iri ai da na shuka, to ke waye yake kirana in ka ji kira ai samu ne" Baki Lami ta damƙe cikin dakewar murya ta ce ",Inna, ina ce dai kina sane yau kwana ukun da Mai Gari ya ɗauka a kan maganar saniyar da Ibra ya tafi da ita" Tari ne ya sarƙe Inna jin wata gagarumar matsala sabod ita kwata-kwatanta manta don maganar ta kwanta mata , sanadin tarin da ta yi mangwaron hannunta ya suɓuce ya faɗi a ƙasa amma ko ta kansa bata bi ba ta ce "Lami waye ya faɗa miki wannan magana, yanzu haka ma Mai Gari ya manta da zancen nan amma saboda ke ce mai tada zaune tsaye kika je kika tado da maganar ko?" Lami ta ce ",To ba ni ɗin ba ce, Jummai ce tun da sanyjn safiya ta je faɗawa Mai Gari cewa kwana uku sun cika amma Ibra bai dawo gari ba, to da ta je da safen Mai Gari ba ya nan sun yi asubanci sun je wani ƙauye gaisuwa, shi ne yanzu ta koma da yamma, tana can ma fadar Mai Gari cike maƙil da mutane, yanzu ma daga can aka aiko ni kiranki, saboda kowa ya hallara amma ban da ke" Idanun Inna suka yi rau-rau tana tunanin abin yi sai ta ji hankalin ta ya tashi domin ita ta manta da wannan maganar kwata-kwata ashe dai yau wa'adin kwanakin zai cika. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ce "Kai jama'a ba dan na shiga ban ɗauka ba bata fitar da ɓarawo wallahi da babu abin da zai kai ni fadar Mai Gari, saboda bani da kuɗin saniya, ban ajiye ba " Lami ta ce "To Inna ni ina zan gane wannan yaren naki, Mai Gari za ki yi wa bayani" Banza ta yi da Lami ta wanke hannunta, ɗaki ta shiga ta haɗo kan kuɗin kayan miyan da ta sayar, akwatin ƙarfen ta ta buɗe tana zaune a gaban akwatin ta fito da atamfofi guda uku ɗinkakku, wanda a wanke suke tas sun sha linki takaicin ɗakko atamfofin take ji a ranta amma haka ta zuba a ledar Viva ta fito ta ɗakko wata samira irin ta ƴan da mai hawa huɗu duk sun yi lamba a jiki, ta ce Lami ta riƙe mata, ita kuma ta yafa gyalenta ta ɗauki ledar atamfofin ta rufe gidan suka kama hanya a ranta tana cewa 'Ba saniya ba ko giwa ce Ibra ya gudu da ita in na bada kayan nan ba zan ƙara komai ba' Ta faɗa tana kallon setin samirarta da yake kan Lami... MAMAN AFRAH 09025576222 [7/9, 3:38 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 9 *SHEIK* Jin kamar dai babu alamun wani da zai taho daga ƙofar gidan ya kawo masa ɗauki, wato ya tabbatar muryarsa bata isa waje ba, don haka yanzu kam matar ta cim masa ba zai iya ma bari ta cigaba da azabtar da shi ba, dakyar ya ƙwace kansa ta shiga binsa da gudu suna tsere a ɗakin bai ankara ba sai ya ji ya kama rigarsa daga baya a haka yake gudun tana jansa tana rinjayarsa kasancewarta ƙatuwa ta fishi ƙiba, sai ya zamana dakyar yake iya gudun kasancewar rigarsa jallabiya ce a zuciyarsa ya ce 'Ina ganin ikon Allah, in ban da maluntar nan da na ɗakko ta larabawa ina dalili mutum zai kafa fama kullum da doguwar jallabiya kana tafiya tana taɗe ka' Ya faɗa a daidai lokacin sun zo saitin ruwan da ya ajiye, wanda yake kwalfa yana ba mutane, ruwan ne suka ture ya zube, tsautsayi ya sa suka shiga ciki gabaɗaya Sheik ya yi gaba ya yi baya ji kake tim santsi ya kwashe shi ya faɗi, ya yi zaman ƴan bori a cikin ruwan ita ma tana ɗora ƙafarta sai ta zame ta tiƙu da ƙasa. A reran ta je ƙasa, ganin haka Sheik ya yi ta maza ya daure ya matso don ba ƙaramin buguwa mazaunansa suka yi da ledar ba, qulhuwallahu ahad ya shiga karanta mata yana tofa mata sai dai wannan karon ba tofi ƙarami yake yi ba tsabar bala'in da yake ganinsa a ciki, yawu kawai yake tofa mata ba kaɗan ba. Karkarwa ya ga jikinta yana yi kuma ya fahimci kamar jikinta ya yi sanyi alamar aljannun za su sake ta, da hanzari ya janyo hularsa ganin ta ɗan leƙo daga bireziyar da ta saka ta a ciki, bai sake bi ta kanta ba sai ya shiga suturta kansa wato ya saka hularsa da gemun, mukullin ya gani a inda ya faɗi daga hannunta ya ɗauka ya buɗe ƙofar yana mayar da numfashin wuya, jin maganar wani mutum yana rafka sallama sai Sheik ya ɗauki wata ƙatuwar bulala da take ajiye ya ɗaga ya tsulawa matar nan da ƙarfi ta ce "Zan fita" Gabansa ne ya faɗi sai yanzu ya fahimci ashe aljannun basu saka ta ba, sai ya ji mutumin nan na waje yana cewa "Ah ashe dai ruƙiyya ake yi wa matar nan, shi ya sa ta daɗe ta bar mutane a layi ana jiran fitowarta, bari in fita in faɗawa jama'a halin da ake ciki" Ta haka Sheik ya fahimci cewa mutumin da ya shigo ya zo ne ya ga dalilin daɗewar matar. Can kusa da katifar ya koma yana raɓe, har sai da ya ga matar rana sakin atishawa wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin yana sha n wahala a maluntar nan ta BOGI amma ƙarfin hali da sa kai wanda ya fi wauta ciwo ya hana shi barin maluntar bogin. Duk da ya san yana amfani da maluntar yana damfarar jama'a bayan ya san shi jahili ne babu abin da ya sani, ko surorin qur'ani da yake karantawa izun ƙasa ne, tun lokacin yana zuwa makaranta kafin ya kangare da ya kangare kuwa ai makarantar ma ba ya zuwa. Ko karatun bokon ma ko secondary bai gama ba. Zaune ta tashi tana kalle -kalle ta ce "Waye ya kawo ni nan" Sheik ya ce "Magani aka miki maza tashi ki je gida, kike shan sauran ruwan alwalar la'asar da magriba, sauran aljannun kan naki za su kama gabansu" Shiru ta yi ba don ta gama fahimta ba, ta muskuta ta tashi tana ganin yadda duk ta jiƙe, fita ta yi Sheik a fili ya ce "Gwara in faɗa miki bogi ki tafi yo ina na ga nutsuwar baki magani ma ki je ki ƙara shaƙo ni, ni na rasa mai hular gashin nan nawa ta yi wa aljannu da mutane, duk abin jikina ba a kaiwa komai farmaki sai hula ta" Ya faɗa yana gyara zaman hular, yana tuno artabun da ya sha da aljannu suka ɗauke masa ranar nan. Dakatar sa masu shigowa ya yi, ya sauya jiƙaƙƙiyar rigarsa ya goge ruwan, a haka ya cigaba da karɓar mutane suna bashi kuɗin yana tarawa ransa fari ƙal yake ji idan ya kalli kuɗin nan yana zaune yake samu. Sai da ya gama da jama'a ya ce sai kuma gobe za a cigaba da karɓar mutane. Tun daga wannan rana Sheik ya zama limamin garin Ƙundu, shi yake jan sallah, sai dai waɗannan ƙananun surori na ƙasa su ne kullum yake jan sallar da su, idan yana jan sallah ya ƙara maƙe murya ya lanƙwasa sai ka ɗauka cewa a masallacin makka ne ake jan sallar amma dai a wajen mutanen Ƙundu, saboda su ne basu gama tantance asalin karatun balaraben mutum da kuma Sheik baƙar fata wanda mayuka da sabulai suka wanke masa fata. Idan za a yi sallah mutanen ƙauyen kafin Sheik ya zo masallaci sai masu manyan wayoyi adroid su zo su kunna recording su ajiye wayoyin, daga an yi sallah an idar, sai ka ga idan sun fita daga masallacin suna samun wuri su kunna, suke ji sai ka zo wucewa ka ga mutum ya duƙufa da earpiece a kunna sai dai ka ji yana faɗin "Allahu akbar, uhmmm, ma sha Allahi, Allah ƙara lafiya babban malamin ƙasar larabawa" Sai ya zamana hatta mata masu waya sai su ba mazajen su, wayar in za su je masallaci su ɗakko musu sallar Sheik. Wanann dalilin ne ya sa Mai Gari ya ce Sheik ya musu karatun qur'ani wanda za suke saurara a waya, na izu sittin irin wanda ake turawa na su Ahmad Sulaiman da yake Mai Gari yana da irin su a waya. A nan ne fa gizo yake saƙa, don Sheik ya san dai bai sauke qur'ani ba hakan ya sa ya ƙaƙalo ƙarya kamar yadda ya saba ya ce "Ai an fi so mutum yake sauraren abin da ya iya, wato tun da basu sauke qur'ani ba ba za suke saurara, na fi so kuke sauraren izufin ƙasa saboda kuke biyawa yadda za ku ƙara ƙwarewa a hadda" Ya faɗi haka don ganin ya tsira daga tarkon wannan, hakan sai ya sa Mai Gari ya gamsu Sheik ya musu rukodin ɗin iya surorin ƙasa da ya iya, suke saurare. Batun magani kuwa duk waɗan da Sheik ya ba magani sai suka zo suke godiya da saka albarka a cewarsu magani ya musu amfani, saboda Sheik yana zama ya yi wa'azi a kan cewa ba a ƙaryata malami ko a tuhume sa, hakan ya sa ko da mutum bai ga amfanin magani ba sai yaja bakinsa ya yi shiru, sannan ma dama duk abin da aka baka a matsayin magani in dai ka yarda cewa zai yi to ko ba maganin bane yana maka magani. Bare kuma Sheik da yawanci matan dama kissa ce yake faɗa musu, da kyautatawa mijin kuma ko wanda ya ce mata suna gudunsa saboda muninsa da ya je ya yi abin da Malam ya ce na bayar da kuɗi ga budurwa sai gashi ya samu mai son sa har an ɗaura aure, hakan ya sa kowa ya ƙara yarda da maganin Malam. Sanann masu aljannu yana cewa suke karanta nas da falaƙi kullum wanann ya sa suke samun kariya tun da sun yi amfani da ayar qur'ani, idan kuma aljannun wanda ya fitarwa suka aara tashi, sai ya ce dama ciwo na ɗaya rana ne sauƙi sai a hankali. Duniya ta yi wa Sheik daɗi yana cin karensa babu babbaka, gabaɗaya ya ƙara ƙiba saboda cin kayan daɗin da yake, duk da cewa yanzu Mai Gari yana sanyawa a masallaci ana haɗa sadaka to da su yake amfani wani lokacin ana ciyar da Sheik, sannan wasu ma suna kawo gudunmuwar kaji, wasu zabbi wasu ma dama idan daga rugar da suke maƙotaka da Ƙundun za su zo magani da kaji da nono suke zuwa a matsayin abin sadaka. Wata rana ana zaune Sheik yana faɗakarwa, Liman sai muzurai yake don shi yanzu bashi da maƙiyi sama da Sheik, tun da an ƙwace masa Limancinsa wanda tun yana saurayi yake yi. Duk da a ganin Liman ɗin Sheik ya fishi ilimi kuma yana karatu irin nasu na larabawa amma dai duk da haka yana jin haushi. Wani ne ya ɗaya hannu ya ce "Ya Sheik ni ina so a fassara min Assalamu alaikum, kuma a fassara mini karatun cikin suratul fatiha wacce ake karantawa a kowacce sallah, ina so in san me yasa a kowace sallah sai an karanta ta?" Ƙululuuuu cikin Sheik ya bada wani sauti a hankali ba tare da kowa ya ji ba. A zuciyarsa ya ce 'Na shiga uku yau an ƙure ni?' A fili kuma sai ya ce "Ma sha Allah, su'alun mai kyau" Ya faɗa yana ɗan lashe baki. Gabaɗaya waje ya kaure da cewa "Yawwa ni ma ina so in sani" Kowa sai ya ce yana son ya sani har Mai Gari. Da gangan Shei ya tsiri wani tari yake yi ba ƙaƙƙautawa daga tarin ya lafa sai ya ce "Ma sha Allah ya ikwan... Sai kuma ya sake fara tarin alamar tarin ba zai bar shi ya yi magana ba, nan aka shiga masa sannu aka kawo masa ruwa amma ya ƙi dainawa saboda dama da gangan yake tarin saboda bai san amsar da zai bayar ba. Ganin haka sai Mai Gari ya ce Sheik ya je gida ya huta, daga haka maganar fassarar ta sha ruwa. Wata rana da daddare Sheik ya fita daga gida ya saci hanya, gidan wani matashi da yake babu nisa da inda aka sauke shi ya je, ƙogar gidan ko kara ta ba a yi ba kasancewar sairayin yana shaye-shaye idan ya dawo daga yawonsa a buge sai ya shiga ya kwanta. Can Sheik ya shiga ya ga sausayin kwance a tsakar gida a ƙasa yana bacci. Machine ɗin saurayin ya ɗauka ya fito daga gidan, sai da ya ɗan tura machine ɗin ya wuce gidan saurayin, ya tada mashin ɗin dama ko mukulli ba a sakawa mashin ɗin a hakanake tashin sa. Hawa ya yi ya tafi ƙauyen da malamin wanda Sheik yake karɓar maganin da yake ba mutane, ya same shi ya bashi kuɗi mai yawa daga kuɗin da yake samu, nan malamin ya bashi magungunan amma Sheik ya ce maganin matsalolin mata ya fi yawa saboda sun fi zuwa da matsaloli. Ya bashi kuɗin mayukansa da sabulai da turaren oud da sunayen su a rubuce ya ce zai dawo ya karɓa, dama malamin yana zuwa birmi. Bayan ya karɓo ya dawo gidan saurayin ya akiye mashin, ya tafi gidansa. Yau ta kama laraba misalin ƙarfe goma Sheik yana zaune a ɗakinsa yana karantar ƙamus mai larabci da hausa, yana ta haddar kalmomin larabci don ya haddace saboda sakowa a magana, duk da cewa ya san ko kwaɓa larabcin ma ya yi ba ganewa suke yi ba, Allah ma da ya taimake shi rubutun larabcin akwai inda aka yi fassarar hausar larabci. Shigowar mutane ya ji zaure gidan suna rafka sallama kamar dai ma a kiɗime suke, da sauri ya mayar da littafin ya tashi ya hau sallaya, jin suna ta cigaba da sallamar sai ya shiga jan gyaran murya alamar baya rabuwa da bauta da ibadad kowane lokaci. Jin suna ɗan surutai sai ya saurara ya ji suna cewa "Ai shikenan kuma matsalolin Ƙundu sun fara dawowa, har muna murya an maganace ashe dai da sauran rina a kaba" Didimmm ƙirjinsa ya buga, kafin wani yinƙuri sai ya ji muryar Mai Gari alamar shi ma ya shigo yanzu, ya ji Mai Gari cikin karkarwar murya yana cewa "Kabarin Hashimu da na wa hallaw?" Sheik ya ji wani ya ce "Da kabarin Fatsime" Gabaɗaya Mai Gari ya kwashi salati. Zufa ce ta fara ketowa Sheik jin ana maganar kabari shi dai duk da bai fahimci kurman baƙin ba amma dai ya san shi ne a cikin matsala tabbas. Haka ya koma ya zauna daɓas sai da ya ji ya ɗan samu ƴar nutsuwa sannan ya buɗe baki ya ce "Bismillah a shigo" Ya faɗa yana janyo dogon carbinsa mai dubu ya fara ja yana mismis da baki tsabar rikicewar da ya yi shi kansa bai san abin da yake faɗa ba. Su duka suka ɗoro ɗakin Mai Gari ne a kan gaba sai wasu mutum huɗu a bayansa. Mai Gari yana baza malun-malun ya zauna amma kana ganinsa ka san babu lafiya, yana zama ya ce "Barka dai Ya Sheik" Sheik sai da ya yi yaƙi da idanunsa wajen ganin basu bayyana taoron da yake ciki ba tsumu-tsumu don shi a duniya in dai maganar aljannu ne da maganar mutuwa to ya ƙi jinin maganar nan, ko kabarin mai Ƙusumbi da yake zaune a gidan da shi saboda, kar ya bayar da kansa a ga gazawarsa, don dai ba yadda zai iya kuma yana son samun kuɗi ba ya so ya bar garin wato ya bar cima mai daɗi da kuma samun kuɗi, shi ya sa yake wanann siyar da rai, to in ba siyar da rai yake yi ba kake tunkarar aljannu kai tsaye, bayan shi ƙasurgumin jahili ne ya shiga MALUNTAR BOGI. Amsawa Sheik ya yi yana ɗan washe bakin dole, duk gumi ya wanke masa goshi, saboda lura da ya yi da sauran mutanen nan su a tsugunne suke basu zauna ba, hakan duk yana nuni da ana cikin ruɗu da masifa. Mai Gari ya ce "Ya Sheik abu ne na gaggawa, garin Ƙundu babu lafiya, wannan ƙaiyen da muke maƙotaka da su ne maƙabartar su ta cika, to shi ne idan aka yi rasuwa sai su kawo maƙabartar garin nan su binne, yanzu wani yaro ne ya mutu a garin sun zo ya za su binne shi aka samu gawa biyu an tono su daga kabari, kuma an ce masu haƙar kabari da suka zo suka tona kabarin da za a binne yaron lokacin da suka gama kabarurrukan da aka tone lafiya lau ba a tone suke ba, sai yanzu da suka zo suka tarar da hakan, kuma sun ce ɗaya gawar da aka tone ta yi motsi bayan ta shekara nawa a binne, yanzu dai sun bar gawar yaron a maƙabartar kowa ya gudu" Mai Gari ya faɗa yana ɗago kai ya kalli Sheik. Tun da Mai Gari yake bayani ƙirjin Sheik yake fat-fat-fat, ya yi wani tsumu-tsumu tamkar an tsamo ɓera daga ruwa, dama sunkuyar da kansa ya yi idanunsa suna kallon ƙasa don kar su fallasa asirin zuciyarsa na tsoron da ya ji ya kunyata. Sheik ya ɗago da kansa idanunsa tamkar wanda aka tada daga baccin sa yake mafarkin tsoro, ya yi wujiga-wujiga, ruwan da yake gefensa a kwano ya ɗauka ya kurɓa, bayan ya ce musu da sai ruwan roba da na leda yake sha, ajiye kwanon ya yi ya ɗago carbinsa yana ja tsabar ya ruɗe ma ba ɗaɗɗaya yake jan carbin ba, wani lokacin ƴaƴa goma wani lokacin biyar kawai ja yake babu ƙaƙƙautawa, sai da ya ji zuciyarsa ta daina bugun da in ya yi magana za a harbo jirginsa na tsoro ya yi ta maza ya ce "Subhanallahi, subhanallahi, subhanallahi, wannan aikin aljannun garin ne yanzu abin har ya kai a tono gawa a kabari kai abin ya girmama, yanzu ya za a yi?" Ya tambaya har lokacin tamker ana fisgo maganganun daga bakinsa. Ɗaya daga cikin mutanen ne ya ce "Ya Sheik yanzu dai ka yi gaggawar zuwa maƙabartar nan ka rufe kaburburan da aka tone, gudun kar a yi bori da sanyin jiki su cigaba da tone sauran kaburburan maƙabar nan, tun da hatta yaron nan da ya mutu yana nan ajiye a makara ba a binne shi ba, an bar sabuwar gawa ajiye a maƙabarta" Nannnauyar ajiyar zuciya ya sauke wacce ta kasa ɓoyuwa a ɗakin ya ce "Tabbas wannan iblisan aljannu ne, da ifiritai" Mai Gari ne ya zaro ido duk da yana ganin za a magance matsalar garin amma jin wannan sunaye na aljannu ya ƙara rikita shi ya ce "Yanzu waɗanann aljannu ya za ka yi ka fitar da su daga garin nan, bayan ƙauyen ya yi lafiya amma kuma yanzu za su dawo mana da hannun agogo baya" Sheik ya ce "Kar ku damu, na taho daga ƙasarmu ne don in kawo ɗauki ga mutane masu neman taimako babu gudu babu ja da baya" Ya faɗa yana miƙewa tsaye, ganin haka sai suka fita suka bar shi, gabaɗaya ji yake kamar ya rufe ido ya gan shi a garinsu MAI MANGWARO ji yake kamar dai ya bi wata hanyar ya bar garin ba tare da sanin kowa ba, sai dai wata zuciyar tana tuna masa irin badaƙalar da ya baro a garinsu, da basussukan da ake binsa kuma dai bai akiye ba bai bayar ba ajiya, ya san tabbas in ya koma zaman banza ne zai cigaba da yi, amma tun da ya samu sana'a a nan dole ya jajirce. Ruɗin da yake ciki ya sa bai rataya hiramin a wuyansa ba kamar yadda yake saƙalawa, yau sai ya masa naɗin gwaggwaro, daga gaban goshin ma naɗin ya ɗan zamo ya karkace sai ya yi tamkar tsohuwa, ya ya ɗauki zumuƙeƙen carbinsa, ya ɗauki littafinsa na ƙamus, sai wani ruwan magani da ya karɓo cikin magungunan da ya siyoa wajen malaminsa, shi tsabar ruɗani ma ya manta ko ruwan maganin mene ne. Yana fitowa ƙofar ɗaki ya ga saka takalminsa ya ga su Mai Gari tsaye suna jiransa, fitowarsa ke da wuya duk da ruɗun da suke ciki sai suka fara magana cikin girmamawa. "Allah ya taimaki balaraben Malamin, Allah ƙara ilimi, haƙiƙa mun samu jajirracce da yau sai dai kowa ya yi hijira daga garin nan don ba za mu iya da wanann aljannun ba" Sheik a zuciyarsa ya ce 'Kwa mini kirari mana tun da kun haɗani da aikin tsohuwar gawa da sabuwa, yau ai sai ta Allah' Ya faɗa yana yin yaƙe tare da ƙara ƙanƙame littafinsa a ƙirjinsa yana jan carbin haka suka fito daga gidan bayan ya kulle ƙofar. Abin da basu sani ba shi ne, Sheik ya fi su shiga ruɗani da tashin hankali. Tun da suka fito tsakiyar garin maza suka fara tururuwa don sai lokacin, suka ji ƙarfin gwiwar fitowa tun da Sheik ya fito gani suke aljannu ba za su fafata da Sheik ba ko su ja da shi. Sheik ne a gaba mutane gari suna take masa baya, sai wani bada faɗi yake shi ala dole masanin qur'ani da addu'o'i, ana cikin tafiya, sai lokacin ya kalli ƙafarsa, idanu ya zaro ganin takalman ƙafarsa gamin bauta ne, wato takalmin ƙafar dama takalminsa ne sandal amma kuma na ƙafar hagun ne ba wai na ƙafar dama bane, don haka a juye yake, shi kuma takalmin ƙafar hagun ɗin silifas ne na wankansa, amma kuma ƙafar dama ne a hagun ɗin wato dai shi ma a juye yake a zuciyarsa ya ce 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, mutanen garin nan kun saka ni a masifa, da tashin hankali tun da uwata ta haife ni ban taɓa wannan gamin bautar takalmin ba, amma yau saboda kun jefani a ruɗani gashi nan, takalmin kwalliya da na wanka na saka, su ɗin ma kowanne ba ƙafar ba ce' MAMAN AFRAH 09025576222 [7/10, 4:03 PM] Mom mashkr & Afrah: https://chat.whatsapp.com/BcJ4LIJJQlfHRgfiJUnBJo?mode=r_c 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 10 *MAƘABARTA* Tun da Sheik ya lura da takalminsa sai ya wayince ya je kusa da Mai Gari ya masa raɗa cewar garin saurin ya zo ya ceci gari ya sako takalmi ba iri ɗaya ba, Mai Gari ya ce "Allahu akbar! Tabbas Sheik kana ƙaunar garin nan" Nan ya nuna masa babu komai ruɗun da jama'a suke ciki ma ba zai bari su lura da takalmin ba, kuma ko sun lura ma sai a musu bayani. Wannan bayanin ne ya sa Sheik ya ji daɗi tun da ya lura yanzu dai ba za a zargi cewa tsabar ruɗani ne ya sa ya sako takalmi gamin bauta ba daidai ba. Tun da suka zo dab da maƙabarta Sheik gabansa ya fi na kowa faɗuwa, amma a haka ya daure yake jan carbi, da yake maƙabartar ƙauyen ba a kewaye take ba, sai dai akwai bishiyoyi da suka mata ƙawanya, sannan akwai hanyar da aka ware don ake shiga ta wajen. Gabaɗaya jama'ar sai suka yi turus kowanne yana tsoron shiga, Sheik ne a kan gaba sannan suka mara masa baya. Suna shiga jikinsa yana karkarwa amma sai ya maje ya nuna ba karkarwa jikin nasa yake ba, mutane gabaɗaya suka tsaya suna jiran su ba abin da zai faruwa, kowa yana gefe. Ƙarasawa ya yi gaban kabarin guda biyu gabansa yana faɗuwa, kallon ɗaya da aka tono ya yi, wani yawu ya haɗiye muƙut ya juya ya kalli Mai Gari ya duk kamar a ce asss su zura da gudu, ɗan wayincewa ya yi ya ce "Babu tsoron Allah a wannan lamari, a ce a tone gawa tsohuwa da sabuwa, kai Allahumma ajirni min wannan mummunan aiki, ya subhanallah," Ya faɗa yana girgiza kai irin na malamin da ya ga an yi wani aiki marar kyau. Wani ne daga cikin tawagar mutanen ya ce "Ni fa a hanya na haɗu da masu binne yaron can, na ji suna cewa wai ji suka yi yaron ya saki kuka shi ne aka rasa mai tsayawa a cikin su... Kafin saurayin ya gama magana Sheik ya kai hannunsa mai carbi ya sharce gumi, ya ce "Alkazibu, ƙarya haramun, babu gawar da za ta yi kuka" Duka wurin babu wanda ya tona don shi Sheik sani ne bai yi ba kafin ya zo garin wataran tsakiyar dare ake jin ƙaran turmi ana daka a cikin maƙabartar ko dai a ji ƙaran injin markaɗe, abubuwa dai barkatai. Mai Gari ya kalli Sheik ya ce "Ya Sheik ko da matsala ne?" Sheik ya ce "Ah haba matsala da kanta ƙarya take ta doshi balaraben Malami daga Yemen" Wani sanyi ne ya ratsa zukatan mutanen wajen. Sheik ya matsa gaban gawar guda ɗaya, ya buɗe littafin hannunsa, ya shiga dubawa kamar mai duba qur'ani ki littafin addu',oi ya ji ya kasa komai so yake ya karanta wata addu'a ko sura amma bakinsa ya ƙi basa haɗin kai, ganin haka ya juya ya kalli jama'a ya ce "A karanto" Suka kalle shi da rashin fahimta. "Mai za a karanto?" Mai Gari ya tambaye shi Sheik ya ce "Kowa ya karanta karatun da ya iya" Ya faɗa don shi ya kasa saamun kowacce sura ma bare ya karanta, haka kowa ya buɗe baki yana karatu a nan Sheik ya fisge wata surar ya fara, kowa yana kaiwa ƙarshe sai aka yi ɗif, matsawa ya yi ya ɗauki shebir ya fara kwashe ƙasar kabarin, saboda gabaɗaya ƙasar ta koma ta rufe inda za a mayar da mutumin yana cikin kwasowa ya ga cinyar mutum a ciki, gabansa yana faɗuwa ya juyo zai sanar da mutane tun da su suna can baya sun bashi wuƙa da nama. Kafin ya furta komai sai ji ya yi gawar wajen ta saka ƙafa ta tura shi sai ga Sheik ya kusa ya faɗa ciki, dakyar ya yi nasarar komawa gefe yana haki lokacin mutane duk sun ƙara ja baya, littafinsa da ya ajiye ya ɗauka tare da maganin nan da ya ɗakko na wajen Malam yana nufo mutane gabansa yana faɗuwa don ya tabbatar gawar nan ta tura shi gashi tsohuwar gawa. Yana zuwa ya ce "Kar ku damu wannan ba wani abu bane, akwai siddabarun aljannu a lamarin, kuma wannan mayar da gawar kabari ba na mutum ɗaya bane ku matso mu taru mu yi aiki tare" Kowa ya fara zare ido Sheik ya ga suna masa kallon tuhuma. Da sauri ya nuna musu robar maganin hannunsa ya ce "Wannan magani ne daga ƙasar Yemen na taho da shi idan aka yayyafa a bakin kabari aljannu suna guduwa cikin daƙiƙu" Si ya ga kowa ya ɗan saki jiki. Bai nuna musu ya ga cinya a cikin ɗaya kabarin ba haka suka mayar da gawarwarkin don sun yarda da maganin da Sheik ya barbaɗa basu san cewa shi kansa Sheik ɗin bai san maganin mene ne ba wataƙila ma yana cikin magungunan mallakar da za a ba mata. Kabarin yaro nan ne kawai ya rage, Sheik ya ce tun da ba gawar garin ba ce a nemo ƴan garin su zo su binne, don tun da ya ji saurayin nan ya ce an ce gawar ta yi kuka sai ya tsorata dama gabaɗaya ma ƙarfin hali yake yi. Mai Gari ya ce ai kawai su binne tun da yana cikin tawagar mutane ai su ma garin namu ƙarƙashin mulkinsa yake. Kai Sheik ya gyaɗa tana wayincewa, sun kewaye kabarin mutane damƙam, Sheik tun da shi ne balarabe shi ne yake jagorantar komai. Hannu ya miƙa zai ɗauki yaron , da ya miƙa hannu ta wajen kan yaron sai ya ga kamar ba shi ya ɗago kan yaron ba, kamar dai gawar ce ta ɗago da kanta, da sauri ya janye hannayensa ya ɗago sai ya ga ba a lura da abin da ya gani ba, kamar gawar ta san mai yake tunani kawai sai ya ga ta fara ɗagowa sai ga yaro a zaune dakaka duk da yana sanye da likkafani, Sheik da ya tashi a firgice ya tsallake yaron sai ƙafarsa ta maƙale da likkafanin da aka ƙulle ƙafar yaron yana fisga ya yi tsalle da yake yana ɗaya gefen ne Mai Gari kuma suna ɗaya gefen, sai lokacin kowa ya lura da abin da yake faruwa, tun da dama gawar yaron daga can gefen kabarin take ba a dab da kabarin ba, tsalle ɗaya Sheik ya yi ya tsallake ramin kabarin sai gashi a gaban Mai Gari ya kama rigar Mai Gari, jama'a kowa ya fara kama gabansa da yake dama maƙabarta ba wani a kewaye take ba sai kowa ya fara kama gabansa wasu gabas waau yamma wasu arewa, Mai Gari da Sheik suna cikin mutanen da suka fita ta yamma. Don Mai Gari ya warce riƙon da Sheik ya masa haka suke falla gudu kowa yana ta kai- ta kai. Babbar rigar Mai Gari sai tashi sama take, rawanin ya kunce yana binsa yaraf, ko takalmi babu a ƙafarsa ya sille, Sheik ƙafarsa maƙale da dogon tsumman likkafanin da aka ɗaurewa yaron ƙafa, haka suka ratsa ta cikin gonaki suna sheƙa gudu, Sheik ya tattare jallabiyarsa saboda gudun samun akasin faɗuwa, suna cikin gudu da yake Mai Gari ne a gaba Sheik yana take masa baya, jama'a kuwa kowa ya yi tashi hanyar, kamar daga sama sai ganin wannan yaron da suka baro a maƙabarta zaune a kan makara ya diro a gabansu, Sheik ya taka wani uban birki shi ma Mai Gari haka, sai Sheik ya juya a guje ya bi wata hanyar sai tafiyar ta kasance Sheik ne a gaba Mai Gari a baya gawar yaro tana take musu baya. Da yake Sheik a wuyansa ya rataya carbinsa, littafinsa yana aljihunsa, Mai Gari ganin gawa tana son cim masa sai ya miƙa hannu ya kamo carbin wuyan Sheik a haka suke gudu, sai da suka zo dab da shiga gari Sheik ya ja wuyansa sai carbin ya tsinke, a nan Mai Gari ya saki carbin, kamar an ce su waiwaya bayansu a tare suka hango gawar bagatatan tana binsu, wanann karon yaron tsirara ya riƙe likkafaninsa a hannu hancinsa toshe da auduga, yana cewa "Sheik, Mai Gari ku zo ku mayar da ni kabarina ku binne ni" ,Amma bahu wanda ya tsaya bare ya saurare shi. Tun daga gidajen farko -farko suke cin karo da gidaje a rurrufe, alama ce ta gabaɗaya magana ta ratsa gari tun da dama a tsorace ake da maganar tone kabari bare kuma yanzu aka ce gawar ta tashi zaune, tabbas sai inda mai ya ƙare shiga motar mahaukaci!. Sun zo tsakiyar gari suke ganin mutane suna ɓullowa ko ta ina, wani babu takalmi wani hula a maƙale a hamata wano ya tuɓe rigar ma yana zangaya gudunsa a haka. Mai Gari maimakon ya yi hanyar gidansa sai kawai ya bi bayan Sheik, Sheik kuwa ganin gawar yaron tana son cin musu sai ya tura wata ƙofar gida haka Mai Gari ya mara masa baya suka shige, gidan wata tsohuwa ne wacce kp fita bata iya yi, ɗaki suka bankamu suka rufe suna mayar da numfashi. Sheik ya fito da robar magani daga aljihunsa ya buɗe yake tuttulewa a fuskarsa, Mai Gari ma ya karɓa ya watsa a tashi fuskar sai suka ji da wata muryar yaro an ce "Ku zo ga likkafaninku, raminku yana can na haƙa muku kabarin" Suna juyawa suka ga yaron ya ratso ta bango, da rarrafe suka fito Mai Gari yana miƙewa sai gida ya yi, Sheik ma ya yi nasa gidan yana shiga ya banke ya zauna ya kifa tagumi, carbinsa ɗaya ya ɗauka ya fara ja yana jin tsoro sosai idan ya tuno wai gawa ce ta tashi da ƙafarta take bin su riƙe da likkafani. Yana cikin wannan halin ta tuno yadda ya ji wani a maƙabarta ya ce, ya ga wani kabarin yana motsi tunanin da ya fara kar sai gabaɗaya gawarwakin su fito su bazo gari shi bai san ma abin da zai ce ba. Tun da ya shige ɗaki bai fito ba, ranar haka garin ya tsaya cak baka jin motsin kowa hatta masallaci ma ladan bai kira sallah ba, bare kuma mai gayya mai aiki wato Sheik ya fito ya ja sallah, to shin wa zai ja sallar ma? Bayan mutanen gari kowa yana gida a ɓame ana tsoron fitowa a yi arba da gawa. Salloli dai Mai Gari sai a ɗaki ya samu ya yi alwala a wani kwano ya gabatar sa sallolinsa cikin tsoro. Ranar dai babu watandar kayan daɗi yo waye zai dafa kayan daɗin. Ɓangaren Mai Gari ma tun da ya kwasa da gudu ya yi gida, lokacin matarsa ta ji ana cewa gawa ta bazo gari hakan ya sa ta taho za ta kulle gida, ta tura ƙofar kenan hakan ya yi daidai da zuwan Mai Gari ya kai kansa ta banko masa ƙofar a goshi, haka suka shiga turarreniyar ƙofar shi yana turawa yana so ta buɗe masa ya shiga, ita kuma tunaninta gawar da aka ce ta bazamo gari ce, shi kuma tsoro ma ya hana shi furta komai, saboda ko da ya taho ma ya sha haɗuwa da mutane kowa yana ta kansa, babu ma wanda ya lura da shi bare a girmama shi, yo shi ina zai tsaya karɓar girman ma. Jin yana neman ya ci ƙarfinta sai ta ƙara dagewa ta tura ƙofar, Mai Gari sai cewa ya yi "Ke buɗe Mai Garin Ƙundu ne" Jin muryar mijinta a rikice sai ta matsa daga ƙofar ko kallonta bai yi ba ya wuce ta ya shige cikin gida a guje, ganin haka bata tsaya rufe gida ba don abin ya girmi tunaninta yadda ta ga Mai Gari yana zabgar gudu ta san tabbas akwai lauje cikin naɗi. Baya ta take masa sai dai kafin ta je ya shige ɗakinsa ya banki sai ƙaran saka sakata ta ji, nata ɗakin ta nufa, wanda tana shiga ta rufe ƙofar runawa da ta yi sakatar ta cire, sai kujerar zaman tsakar gida ta mata ta saka a bayan ƙofar ta zauna tana haki tana tunanin to ina Balaraben Malamin garin nasu da yake yaƙar aljannu. Washe gari sai da gari ya waye tangararai aka fito sallah, saboda ƙarfin hali irin na Sheik ya baro wata baƙar rigar jallabiya tana ta sheƙi ta ƙara haska shi, ya sheƙa uban turaren oud, ya fito yana jan carbi, yana muzurai don kar a kawo masa raini, a haka ya ja sallar, bayan an idar ya zauna a mazauninsa bayan ya juyo ya fuskanci mutanen masallacin ya ce " Alal haƙiƙa jiya mun haɗu da wani ibtila'i, wanda aka samu wani aljani marar imani ya shiga jikina don kawai yana son ya rikita wanann gari ku shiga halin ha,u'la'i, saboda sun san ni kaɗai ne zan kawo mafita a wanann gari, sun san ni zan magance duk wata matsala da za ta tunkaro gari, shi ya sa suka tura mini wani ƙasurgumin aljani ya shiga jikina, sai da daddare na ƙure karatun qur'ani a wayata sanann na hau yi wa kaina da kaina ruƙiyya, a nan ne da ya buɗe baki ya yi magana na gane ashe ba ni bane aljani ne" Kowa ya yarda da maganar Sheik sai suka ji dk ya fara basu tausayi don sun yarda da abin da ya faɗa. Mai Gari da yake da shi suka yi gudun famfalaƙin da Sheik sai ya kalle shi da mamaki ya ce "Yanzu dama Sheik duk wannan abin da muka yi na gudun ceton rai ba kai bane?" Wani yawu Sheik ya haɗiye jin kamar dai tambayar ta yi kama da tambayar tuhuma ko rashin yarda. Cikin son ya kankarowa kansa mutunci ya ce "Ashsha Mai Gari, haba kai kuwa ni ne zan yi gudu saboda gawa? Ko ana ha maza ha mata ai ba zan yi gudu ba, sannan kuma ina horar mutane a kan rashin dacewar tuhumar malaman su musamman malaman larabawa ko abu suka yi ba daidai ba, ba a tambayar mai ya sa" Shiru Mai Gari ya yi sai ya ce "Ni ma duk mamaki ne ya cika ni, ni ina ta gudun gawar yaro ashe ina tafe da aljani" Ya faɗa yana ji babu daɗi. Haka dai Sheik ya yi ta kawo maganganun da zai kama zuciyarsu, ya ringa faɗar maganganu masu shiga rai, saboda cewa ya yi ma ko joya da suka ji shiru bai fito ba aljanin ne da bai sake shi ba shi ya sa bai fito jan sallah ba, basu san abin da ya hana su fitowa ba shi ɗin ma shi ne ya hana shi fitowa wato tsoro. A ƙarshe dai ya ce musu wannan yaron ba mutum ba ne, aljannu ne suka ɗauke gawarsa wanda ya taso ya shigo gari aljani ne ya yi shigar yaron, sai washe bari aka ga gawar yaron a ƙofar maƙabarta, haka dai Sheik ya ari jarumta aka binne yaron. Bayan sati uku, komai ya kankama, a inda mata suke tururuwar zuwa wajen Sheik karɓar magani, gabaɗaya a sati rana biyu ce ta maza amma kwanaki biyar duka mata ne aka warewa suke ziyartar Sheik ɗin. Hatta ƴan mata suna layi a wajensa, maganin farin jini, maganin karɓar kuɗi a hannun saurayi, maganin samun bazawari marar mata, haka suka yi ta zuwa suna karɓar magani, Sheik kuma kasuwa ta kankama yana ta damƙar kuɗaɗe. A wata ranar laraba ne Sheik ya yi arba da wata budurwa da iyayenta suka kai masa ita ya mata ruƙiyya tun da ya ɗora kansa a kan yarinyar nan ya ji ya kamu da son ta, yana so ya aure ta amma kuma yana tsoron su mutanen gari su zargi wani abu ko ma wani ya harbo jirginsa, a ga shi yana balarabe ya ce yana son baƙar fata, amma dai ya fara ƙagauta da zama babu mace ya baro matansa biyu. Shiru ya yi a fili ya furta "Ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, in baro mace tana gugar mace har mata biyu amma in zo ina zaman gwauranci, shi ma Mai Garin ban da sakarai ne ka bar baƙo babu mace haba ko da na ce ni malami ne ina kwaana sallah da salatin annabi S.A.W ai ni ma ba dutse bane kuma ba katako bane da zan ƙare kullum a cire aljannu da bayar da magani, ina nan ina zaune da abu sanƙamƙam a jallabiya" Ya faɗa yana jan wani dogon tsaki. Bayan kwana biyu da yamma ya ce zai yi lazimi ya dakatar da ba maza magani dama ranar maza ce, shi kuma ya fi son ranar mata saboda wuni yake yana wadaƙarsa yana kallon su shegen son mata. Kuma maza basa bada kuɗin sadaka da yawa, amma ya fi morar kuɗin mata. Yana kishingiɗe bayan ya gama kallon film a wayarsa, wanda ya sauke a youtube, wayar da ya cewa su Mai Gari wayar babu komai sai karatun qur'ani. Ɗan baccin da ya ɗauke shi ne yake mafarkin ya auri budurwar nan da ya ɗora rai. Bugun ƙofar gidan ne ya falkar da shi, ji yayi ana ta rafka sallama, ya taso ya leƙo, jin ana hayya- hayya, wata matashiyar mace ce aka shigo da ita maza ne ƙattai uku sun riƙo ta tana togewa, dakyar ake janyota sai kamce saniya, da wata mata tana share hawaye da alama mahaifiyarta ce, sai da Sheik ya kalle ta ya gane ido ɗaya ne da ita. Aljannunta ne suka tashi, ɗaki aka sakawa Sheik ita duk da yana jin ɗarɗar haka ya shiga mata ruƙiyya kafin a gama ruƙiyyar ta haɗa shi da ƙasa sau uku, yana cikin bayan ya fitar mata da aljannun sai ta miƙe ƙafa ta ƙura masa idonta guda ɗaya har sai da ya tsargu, ko kuɗin sadaka bai karɓa ga burinsa kawai su fitar masa ita. Da daddare yana zaune ya gama cin abinci sai ga Mai Gari, Liman, da wasu dattijai guda uku, suka zauna aka sake gaisawa, Mai Gari ya yi gyaran murya ya ce "Ya Sheik a matsayina na Mai Gari na zo da wata buƙata" Buɗar bakin Sheik sai cewa ya yi "Haba Mai Gari ai babu abin da za a nema a rasa a wajensa, har da cewa ya yi alƙawari tun bai ji abin da ake buƙata ba. Mai Gari ya ce "Wannan yarinyar da ka yi wa ruƙiyya da yamma mai ido ɗaya... Gaban Sheik ne ya faɗi tunaninsa ko za a ce aljannun ne suka sake tashi, saboda dama dai ya san lafawa suka yi ba wai sun bar jikinta bane. Mai Gari ya cigaba da cewa "Aljannu sun karɓi ƙarfin jikinta, sun hana ta sakat sun ce sai an ɗaura mata aure da kai, in ba haka ba wani gagarumin bala,i zai sauka a garin nan sai sun kashe rabi da kwatar jama,ar gari... MAMAN AFRAH 09025576222 [7/11, 4:08 PM] Mom mashkur & Afrah: IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 11 *RAHMA* Tsabar firgici da mamakin furucin Ma'aruf tsaye ta miƙe, shi kuma Ma'aruf ganin Sulaiman sai hakan ya sanya ya shafawa idanunsa toka, don a yau ya ci alwashin babu gudu babu ja da baya, dole ya bayyana sirrin zuciyarsa ko ta halin ƙaƙa ko da kuwa hakan zai zama sanadiyyar afkuwar gagarumar matsala. Hannu biyu ya saka a aljuhunsa ya yi wata irin tsayuwa ta yaran zamani, in ban da su da suka san shi kuma suka raina masa hankalin cewa shi baƙauye ne babu wanda zai ce ya taɓa zama a wani ƙauye, cike yake yau da kwarjini haɗe da haiba kyawunsa ya ƙara bayyana, yana sakin wani shu'umin murmushi, yana mai kafe masoyiyar tasa Rahma da idanunsa da ta ji sun zame mata tamkar miki, don yau sai ta ji ya mata wani kwarjini sai dai ba za ta bar kwarjininsa ya rinjayi zuciyarta ba, dole za ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, saboda ma kar ya yi gigin furta wata kalma a gare ta. Mummy kuwa kallon ƙasƙanci da raini ta shiga jifan Ma'aruf da shi, ganin yana tsaye a inda tilon ƴarta take sannan ga ɗan minista da take fatan ya zama sirikinta wato Sulaiman. Sulaiman kuwa tun lokacin da ya ji furucin Ma'aruf sai zuciyarsa ta buga, tsanar da ya yi wa Ma'aruf ɗin ta ƙara linkuwa a zuciyarsa, a gefe ɗaya su duka yana jifansu da kallon tuhuma, musamman tauraruwar tasa wato Rahma. Rahma ita ta rasa ma abin cewa don furucin Ma'aruf ya bata ɗimbin mamakin da ta kaaa furta uffan duk da a ƙoƙarinta na ganin ta masa tatas. Mummy ce ta katse shirun da ya ratsa wajen, da kuma kallon tuhumar da wasu suke jifan wasu, sannan da zulumi da taraddadin da zukatan wajen suke ciki ta ce "Ma'aruf lafiyarka kuwa, wanann wane irin daƙiƙanci ne? Ko an faɗa maka bakin rijiya wajen wasan makaho ne" Ta faɗa tana masa alama da hannu na tambaya. Amma abin mamaki maimakon ya girmama ta kamar yadda yake yi a kullum sai ta ga ya ɗan murmusa ya ce "Mummy ina baki haƙurin furucina sai dai, furucin da zan yi yanzu zai sha gaban wanda kika saurara, amma sai dai ina so matsayinki na Mummynah ki tayani neman karagar mulki a zuciyar Rahm... A ƙufule Mummy ta ɗaga masa hannu alamar dakatarwa tana huci kamar kumurcin zaki ta ce "Allah wadaran naka ya lalace wai jakin dawa ya ga na gida, an faɗa maka ni ina da wani ɗa a duniya da ya wuce Rahma? Idan mafarki kake ka falka daga mummunan mafarkin da kake yi, ka wartsake idanunka ka san da wa kake magana, Rahma ta fi ƙarfin talaka baƙauye irinka ka taka a sannu in ba haka ba za ka ɗakko ruwan dafa kanka" Rahma ce da ƙwallar takaicin furucin Ma'aruf ya cika mata ido saboda takaicin cewa yana neman karagar mulkin zuciyarta ta shiga nuna shi da yatsa ta ce "Wallahi ahir ɗinka, ko giwa ta faɗi ka sani ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, wallahi, wallahi, wallahi, idan har baka taka a sannu ba za ka yi da na sani na har abada, rainin ma ya yi yawa, ni Rahma kake wa wannan furucin? Ina so ka sani matsawar baka dawo cikin hankalinka ba to za ka taka dakalin da yake ɗauke da ruwan ɗanyar kuɓewa, a ƙarshe ka zame ka karkarye a banza a wofi" Ta faɗa tana hayayyaƙo masa. Sulaiman fara takawa ya yi a sannu sai da ya zo har gaban Ma'aruf ya tsaya, kallon kallo aka shiga yi, tsakanin Ma'aruf da Sulaiman, shi Sulaiman ransa a mugun ɓace shi kuma Ma'aruf yana sakin wani shu'umin murmushi. Hannu Sulaiman ya sanya a cire glases ɗin fuskarsa, ya kafe Ma'aruf da idanunsa da takaici ya sa suka yi jawur, yana masa wani kallo irin na raini, ba komai yake baƙanta masa zuciya ba sai yadda Ma'aruf ya fi shi kyau da cikar haiba, kai zai iya cewa Ma'aruf ya fi shi komai kuɗi ne kawai zai Sulaiman zai faɗa masa. Sai dai inda gizo yake saƙar shi ne, Sulaiman babu ɗigon ko da son Rahma a zuciyarsa, ba komai bane a zuciyarsa sai yaudara yana so ne kawai ya raba ta da mutuncin ta, shi ya sa ya yi amfani da zaƙin baki da nuna soyayya da kulawa na ƙarya har ta amince da shi, a halin yanzu duk ta rabu da samarinta duk da dama su ɗin ma za ni ce ta tarar da muje mu, ma'ana babu wani na kirki duk ƴan ƙarya ne ƴaƴan manya masu kuɗi. Baƙincikinsa ɗaya shi ne ya fahimci matsawar Ma'aruf ya furta so ga Rahma to ko da a ce bata son sa to zai yi iya yinsa ya ga ya hana shi cim ma burinsa, haka ya fahimta saboda ya lura ko a cikin gidan za su hira, sai yake neman zame musu ƙadangaren bakin tulu, yana hana su rawar gaban hantsi. Ba ma wannan ba kawai zuciyarsa ta bashi raina masa hankali suka yi, ma'ana ya fara zargin Rahma tana son Ma'aruf ne in ba haka ba ya zai zo ya tarar da su a lambu tare ya yi shiga mai kyau, sannan shi da kansa ya ji Rahmar tana faɗin wasu kalmomi na soyayya ga Ma'aruf shi ma kuma Ma'aruf ɗin ya mayar da martani, zuciyarsa ma ta bashi cewa zuwan Mummy wajen ne ta musu alama da cewa ya iso wajen shi yasa suke masa wasa da hankali suke raina masa wayo. Ya dara tunanin kawai ma amfani ake yi da shi ana cin kuɗinsa. Hannu Sulaiman ya kai ya dafa gefen kafaɗar Ma'aruf amma sai Ma'aruf ya saka hannu ya ɗauke hannun Sulaiman daga kafaɗarsa ya warɓar da shi, daga Rahma har Mummy baki suka saki saboda yau ɗaya Ma'aruf ya sauya musu, ran Sulaiman ne ya ƙara ɓaci a ganinsa wannan baƙauyen har ya kai ya masa haka? A ƙufule ya nuna shi da yatsa ya ce "Kai ƙaramin ƙwaro, ƙaramin ɗan iska, ina so ka sani ko da mai ka zo an fika, ruwa ba sa'an kwando bane kuma ni na fi ƙarfin in yi tarayya da kai a wajen mace ɗaya... Rahma jin wannan furucin sai ta lumshe idanu, tare da sakin wani murmushi saboda ta lura Sulaiman zai ladabtar sa Ma'aruf ko da kuwa da kalamai ne, Mummy kuwa jinjina ta hau yi wa Sulaiman a zuciyarta, tana jin gwara ma a bar shi da Sulaiman ɗin ya nuna masa kudu ba arewa ba ce. Sai dai me? Sai suka ji saɓanin abin da suke tunanin ji wato Sulaiman ya cigaba da cewa "Don haka in dai Rahma ce ka je na bar maka" Daga Mummy har Rahma sai da gabansu ya yi mummunar faɗuwa, suka shiga zare ido jin za su yi babbar asarar ɗan masu kuɗi, duk da suna da kuɗi amma sun san Sulaima tsani ne a wajensu na cim ma wasu burika a rayuwarsu. Da sauri Rahma ta matso tana kafe Sulaima da idanu ta ce "Ka san mai kake faɗa kuwa Baby? Yanzu my love wannan ƙazamin kake yi wa furucin ka bar masa ni, in ce dai wasa kake ko?" Ta faɗa tana kallonsa don so take ta ga ya wawwanke fuskar Ma'aruf da kyawawan maruka, don ya zame masa izna kuma darasi a nan gaba, don su basa so su masa wani abu cibi ya zama ƙari idan Daddy ya dawo. A zuciye Sulaiman da yake jifan Rahma da kallon tsana ya ce "Ke dalla malama dakata! An ce miki kowa sakarai ne, ko kin ɗauka ni ɗin ma sakarai ne irin samarin da kika yaudara saboda kin same ni kika sallame su? To ni da hankalina, na san abin da nake, ni za ki rainawa hankali, in zo in same ki kuna soyayya amma ki nuna mini bariki, to ni nan na fiki sanin bariki idanuna a buɗe suke yadda bakya zato" Ya faɗa yana hayayyaƙo mata tamkar zai kai mata duka. Ma'aruf ya ji daɗin hakan ya san kuma ko da bai auri Rahma ba to tabbas ya cire mata mugun iri a rayuwarta, saboda ya san Sulaiman mayaudari ne ba don Allah yake sonta ba, yana amfani da ita ne saboda cim ma wata dama tashi daga ya samu biyan buƙata ya tabbatar zai cikawa rigarsa iska, in ma bai barta da guzurin ciki ba. Mummy ce ta dafe ƙirji ta ce "Haba Sulaiman ya za ka yanke wannan ɗanyen hukunci marar ma'ana da madafa? Kai kanka ka san Rahma ta fi ƙarfin wannan bagidajen, kai take so kuma kai za ta aura" Juyowa ya yi yana yi wa Mummy kallon baki fahimci rayuwa ba. Ma'aruf ya ce "Mummy dama fa ba son ta... Kafin ya kai aya Mummy ta ɗaga hannu ta kai masa wani mummunan marin da ya sa ya ga giftawar taurari. Sulaiman ne ya fashe da wata dariya da sai da ya komawa kowa madubi abin kallo wato kowa ya tsaya yana kallonsa da mamaki, sai dai yana cikin dariyar sai ya haɗe fuska, ya ɗaga kai yana kallon Ma'aruf da yake dafe da kunci, ya juya ya kalli Mummy sannan ya sauke idanunsa a kan Rahma cike da izza da taƙama irin ta ɗan gidan masu faɗa a ji ya ce "Rahma ki sani daidai da second ɗaya ban taɓa sonki ba" Idanu ta zaro cike da fargaba zuciyarta ta bugu da ƙarfi, Mummy kuma baki ta saki tana kallonsa da tsantsar mamaki, Ma'aruf kuwa da dama ya san kwanan zancen sai hakan bai ɗaɗarashi da ƙasa ba, bai ba kowa damar magana ba ya cigaba da faɗin "Na san saboda ina da kuɗi kike sona, da bani da kuɗi na tabbata ba za ki ƙaunace ni ba, tun da dai kika guji ɗan uwanki saboda bashi da kuɗi, bayan ya fini komai na ɗa namiji nagarta kyau da komai, to kin ga saboda na guje ki kar hakan ya dameki, ni dama don kawai a yi soyayar sharholiya don ki sani ma akwai wacce nake so, dama da a ce soyayyarmu ma ta ɗore sai dai ki ji an ɗaura mini aure, ina miki tuni da waɗanda kika yaudara a baya, kika fasa son su saboda kin sameni kika guje su, to ke ɗin ma yau gashi zan nisance ki, dama an ce duk abin da ka shuka shi kake girba, sannan duk abin da ka yi shi za a yi maka" Yana kaiwa nan ya mayar da kallonsa ga Ma'aruf wanda ba ya mamaku furucin Sulaiman ɗin don shi abu ne da ya gama fahimta tun ba yau ba. Yana kallonsa ya ce "Ɗan jagaliya ga ƙanawarka nan na bar ta zan je na tafi" Rahma ita mutuwar tsaye ta yi don kuwa maganganun Sulaiman sun ɗaure mata kai, ta kasa furta komai tana a hakan ya nuna mata fuskar wayarsa ya ce "Kin ganta wacce nake da burin na aure ƙiris ya rage" Ya ce yana nuna mata hoton wata a wayae, sai ya juya ya nuna wa Mummy kawai sai ya fara taku ya fara tafiya. Ma'aruf ya ce "Ka je da mugun nufinka, Allah raka taki gona" ,Mummy ta ɗaga murya ta ce "Shege mai baƙin hali, mummunan halinka ya bika Allah ya isa, sai ka samu wanda zai maka abin da ka yi" Juyowa ya yi ya ce "Kamar yadda kuka sameni na muku abin da kuka yi wa wasu ba" Rahma juyawa ta yi da gudu ta yi hanyar da za ta sada ta da cikin gida. Mummy ta ɗaga kai ta kalli Ma'aruf tana surfa masa zagi kamar ta ari baki, tana jaddada masa cewar ya ɗauko ruwan dafa kansa, don ta ɗauki aniyar saita gintse masa ɗan karatun bokon da yake taƙamar yana yi don dole sai ungulu ta koma gidanta na tsamiyata. Ko fitar da za ta yi fasawa ta yi, ta koma ta hau lallashin Rahma da take ta kukan maganganun Sulaiman duk da abin da ya furta amma sai da ta koma tana faman kiransa a waya amma yake katsewa daga ƙarshe ma sai wayar ta ji a kashe. Ma'aruf kuwa godiya ya yi wa Allah da ya sa halin Sulaiman ya bayyana ko ba komai ya ceci ƴar uwarsa daga mummunan nufin da Sulaiman ɗin yake yi a kanta, ko bai auri Rahma ba duk da cewa dama ya san abu ne mawuyaci ya aure ta duba da yadda ita da mahaifiyarta suka tsane shi amma dai zai so ta samu namiji mai sonta da aure ba wai ɗan a hole ba. Tun kafin Daddy ya dawo gidan Mummy take doka masa kira a waya, yadda ya tsinci muryarta ne ma ya sa gabansa faɗuwa, saboda a nasa tunanin ko ɓoyayyan sirrin da yake ɓoye mata ne ta sani. Amma bayan ta shiga faɗa masa akwai matsala a gida sai ya ji ya ɗan samu sassauci don shi ba ya fatan Hajiyar ta ji ƙudurin sirrinsa a yanzu, ya san dai za ta sani amma akwai lokaci!. Da dare yana dawowa ko ruwa bai watsa ba bare a yi batun cin abinci, Hajiya da Rahma suka saka shi a gaba da batun abin da ya faru, Rahma sai kuka take abin da ya sa hankalinsa ya tashi saboda ba ya haɗa damuwar Rahma da komai. Ransa ya ɓaci duk da Mummy ta cewa Rahma kar su bayyanawa Daddy furucin Sulaiman na cewa dama ba son ta yake ba da gaskiya kawai soyayyar shan minti yake son su yi, kuma sun ɓoyewa Daddy hakan nr don ya ɗauki maganar da muhimmanci ta yadda zai yanke tsatstsauran ra'ayi a kan Ma'aruf. Ran Daddy ne ya ɓaci ya ɗaga waya ya kira Ma'aruf, sai gashi ya shigo da sallama, Hajiya sai aika masa harara take tamkar idanunta za su faɗo. A ƙasan kafet ya zauna yana ɗan sunkuyar da kai ya shiga gaishe da Daddy. Rahma sautin kukanta ta ƙara saboda Daddy ya yi hukuncin da ba zai yi wa Ma'aruf daɗi ba. Daddy ko amsa gaisuwar bai yi ba ya ce "Ma'aruf mai ya kai ka shiga sabgar da ba ruwanka? Mai ya sa ka bari haka ta faru a kan mai za ka yi yadda ka yi ka raba Rahma da mijin da za ta aura?" Baki ya buɗe zai masa bayani cikin nutsuwa amma sai Mummy ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu ta ce "A cikinmu babu mai maka ƙarya don haka ba bayaninka ake nema, ko kuma kare kanka, hujja kawai ,a ka bayar" Shiru ya ratsa falon saboda ya rasa ma mai zai ce. Daga haka Mummy ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, har Daddy yana ce mata wataƙila shi Sulaiman ɗin ya dawo su shirya amma Mummy ta ce ai ba zai taɓa dawowa ba. Tashi ta yi ta fita, jim kaɗan sai gata da akwati niƙi-niƙi tana zuwa ta dangwarar da akwatin a gaban Ma'aruf ta ce. "Alhaji ni dai daga yau na bar zama da wanann mai nufin mutane da sharrin a gidan nan, dole ya koma ƙauye don ba zai zauna yake korewa ƴata samari ba, idan su basu yaudare ta ba shi ai ya yaudare ta da kalamai ya ya gusar mata da abin da kowace ƴa mace take taƙama da shi.... *INNA TA SALLAH* Tun kafin su ƙaraso fadar Mai Gari take hango rawanin Mai Gari take aikawa rawanin harara, ji take gabaɗaya har Mai Garin ma haushinsa take ji, a nata ganin ai shi ma ba zai ce kwana uku ba, tun da ya san a magana ta gaskiya ba lallai Ibra ya dawo ba a kwana kusa ma bare kwana uku ai dama sai ya ce daga wata uku zuwa shekara uku, wannan shi ne magana ta adalci. Zaunawa ta yi ta ce "Lami miƙo min saitin samirar wanann" Lami tana muzurai ta miƙa mata samira. A gabanata ta ajiye tana jiran abin da uban gayya wato Mai Gari zai ce domin ita ko arziƙin gaisuwa bai samu daga gare ta ba saboda tana ganin ai bai kamata tun da ya san ba ita ta ɗauki saniya ba yake mata aike kamar ta ci bashi. Gyaran murya ya yi ya ce "Tasallah ya za ki zo ki mana gurum da tsoffin kwanuka a gabanmu? Duk tunanina ma ko kaji ne kika soyawa fada kika taho da shi don in ke ci ina gabatar da shari'a cikin adalci, amma sai na ga an miƙo miki shafal da su samirun babu wani nauyi sai wata uwar lamba duk sun kwankwatse" Wani kallo ta masa ta ce ",Ai da kana son cin kaji sai ka aika mini zakara da kaza tun jiya da yamma, ka ga zuwa yanzu da na gama soyawa sai in taho maka da su" Ta faɗa tana kawar da kai gefe. Ƙwafa ya yi bai ƙara maganar naman ba don ya gane magana Innar ta faɗa masa. Ya cigaba da cewa "Ko gabatar da kanki baki yi ba kika yi gurum da ke" Idanu ta ɗago ta ce "Wai Mai Gari shari'a za ka yi a kan saniya ko kuma dai cin fuska za ka mini a gaban jama'a sanin kanka ne babu wanda bai san sunana ba Tasallah nake matar Malam kaka a wajen Ibra, mai ake neman sani kuma?" Ta tambaya tana kafe Mai Gari da ido. Taɓe baki ya yi don ya ji hashin yadda ta bashi amsar ya ce "To ina maganar mu ta kwana?" Shiru ta yi sai kuma ta ce "Yo tana inda ta kwana mana, a inda ka tsayar da ita ranar nan ina ganin ai bata motsa ba" Cike da jin haushi ya ce "Tasallah kar fa abin naki ya fara wuce gona da iri, ana batun saniya amma kina mayar da abin wasa kamar ana maganar tsuntsuwa" Ta ce "To mai kake so in ce in ban faɗi haka ba fisabilillahi, yaron nan an bashi saniya ya tafi bai shawarce ni ba ban san ma ua bar garin ba, amma sai tuhuma ta ake kamar tsohuwar ɓarauniya ina dalili" Mai Gari ya ce "Abu ne da ya zama dole, in ba a faɗa miki ba wa za a faɗawa yanzun nan kika gama gabatar da kanki har da inkiyar kakar Ibra, kin ga kenan ba laifi ba ne don mun nemi ki a cikin laifinsa" Kallon Jummai da take muzurai ta yi ta ce "To fa! Allah ya dawo da mu ke dai wannan mata baki da haƙuri a ce a kan saniya ɗaya kina azalzalar mutane" Jummai kamar jira take dama ta ce "Guntun gatarinka ya fi sari ka bani" Ta ce tana mata kallon up and down. Mai Gari ya ce "Ya isa haka Tasallah ku dakata yanzu dai duk magana tana wajen ki Tasallah" Cike da takaici Inna ta ɗauko ledar nan ta fara fito da atamfofin nan ranta yana ƙuna, sai da ta fito da su gabaɗaya tana duddubawa ta ce "Tsakani da Allah na kai zuciyata nesa, kafin in ɗakko wannan atamfofin ka gansu dai a wanke suke karrr, sun sha linki " Mai Gari ne ya ce "In za ka yi alheri ai ba sai a idanun mutane ba, sai ki bari sai kin je wurin wanda za ki ba jacen kayan sai ki fito da su yanzu dai batun saniya ake" ,Galala ta saki bari tana kallonsa hannunta riƙe da rigar atamfar ta mai dogon hannu, Lami ta shiga danne dariyarta don ta ga kamar dai Inna tana son bada kayan ne a maimakon kuɗi. Cike da masifa ta ce "Wane jace wai? Ni ina na ga arziƙin bayar da jacen atamfa sabbil dal ya wannan basu sha jiki ba, ai ni in ka ga na bayar da zani to na ga yana darewa ne ta wajen mazaunai, sai in ba mai so ya ƙarasa, amma waɗannan basu ji jiki ba daga wacce na saka sau goma sai wacce na saka sau sha biyar dama dama ɗayar ce ma na saka sau bakwai ita ce ta ganin aarki" Jummau ta ce "Mu duk wanann bai shafe mu ba... Inna ta katse Jummai da faɗin "To Almunafunfun masu zuwa lahira da ƙoƙon bara" Ta faɗa tana ɗaukan cinikin kayan miya ta miƙawa Mai Gari ta ce "Irga min nan" Da kamar ba zai karɓa ba sai kuma ya karɓa ganin dubu biyu da ɗari takwas da hamsin sai ya washe baki don ya ɗauka ko ladan rufe baki ne ta bashi saboda ya sassauta mata a wajen shari'a. Yana gama doɓara yawu ya yatsansa ya irga ya faɗa mata yawansu, tana jin babu daɗi a ranta ta tura masa setin kwankwatsatstsun samirun nata kamar za ta yi kuka ta ce "Abu uku dai dole ya famshi abu ɗaya, ga atamfofi, ga samiru, ga kuɗi" Ya ce "Ban gane ba" Ta ce "Duka fa na bayar Jummai ta zauna a matsayin saniyarta" Tsaye Jummai ta tashi tana baloƙoƙo ta ce "In na yarda da wannan tatsuniyar in daskare a wajen nan, duk inda saniya take sai an nemo min" Inna tana kama haɓa ta ce "To tun da haka ne sai ki jira dawowar Ibra ya biya amma ni dai iya arziƙina kenan" Mai Gari ya ce "Tasallah baki da gaskiya, yanzu fa a wajen nan kowa ke yake jira ki ba Jummai kuɗinta don ta warawa Lami haƙƙinta" Inna ta ce "To sai dai a kaini mahauta wajen mahauta masu yankan nama, a yi cinikina su saya su yi tsirena su sayar in Allah ya sa na yi kasuwa shikenan sai a biya su amma dai ni bani da wani kuɗi wannan ma ƙundubala ce na yi zan koma in zauna in rungumi ƙaddara don jarin kayan miyar ne karkaf na kawo" Jummai masifa kawai take surfawa Mai Gari yana taka mata birki amma ta ƙi yin shiru hakan ya sa Inn tashi tana goge ƙwalla ta ce "Ni dai wannan abu bai mini rana ba, a ce baka ji ba baka gani ba ana maka titsiye a kan abin sa baka da laifi a ciki, Mai Gari bani wannan kuɗin" Mai Gari ganin Inna ta fitittike sai ya miƙa mata, ƙullewa ta yi a hannun zaninta, ta kwashe atamfofin ra mayar cikin leda ta ajiye a gefe ta janyo setin samirun ta daga gaban Mai Gari ta ajiye kusa da ledae atamfofin. Komawa ta yi ta zauna ta ce "Haƙiƙa tashin hankali ba a saka masa rana, sannan shi ya sa ba a son yin alƙawari saboda wata rana, da na ɗauki alƙawarin tun da Malam mijina ya bar duniya ba zan sake yin aure ba, amma yanzu ƙaddara ta gifta dole in yi aure, Mai Gari ina so tun da ga mijin Jummai a zaune, kaima gaka kuma ga mutane nan matsayin shedu" Dakatawa ta yi da bayanin tana share hawaye tsakaninta da Allah kuka take kowa ita yake kallo duk da basu gane inda maganar tata ta dosa ba ta ce "Na yarda na amince a ɗaura min aure da mijin Jummai, na yafe masa sadaki aurena da zai yi shi ne biyan bashin saniyar Jummai wallahi na amince zan aure shi" Jummai wacce ta koma ɗazu ta zauna yanzu sai gata a tsaye ba shiri... MAMAN AFRAH 09025576222 [7/13, 7:00 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 12 IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture *INNA TASALLAH* Kamar Jummai za ta kai mata duka haka ta hayayyaƙo mata tana kumfar baki, Lami kuwa tsabar mamaki ta rasa bakin magana baki sake take kallon Inna ganin jiki duk yaba amma tana ambaton a aure ta kuma ma wai a fansar saniya, bayan kowacce mace ta tsani kishiya bare ma wai da bashin ta. Cike da masifa ta ce "Tasallah cin fuskar taki har ya kai haka a ce wai ni da kuɗina zan wa kaina da kaina kishiya, wato ga Jumman mahaukata ke ko kunya ma bakya ji" Inna haɓa ta kama ta ce "Mene ne abin kunyar a aure sunnar ma'aiki? Kuma ni a ganina da a zauna ana ɗauki ba daɗi ai gwara na aure shi shiknn" Jummai ta ce "Tsofai tsofai da ke sai ki auri jikan cikin ki?" Inna ta ce "Yo haramun ne kuma da kike wannan maganar sai ki ga ni tsohuwar na fiki kataɓus a gidan auren... Cike da haushi ta katse Inna da cewa "Yo Sale mai zai yi da ke" Inna ta ce "A'a Jummai tsakani da Allah kar ki ari bakinsa ki ci masa albasa ai sai ki bari ya bada amsa da kansa" Jummai tana nuna Inna da yatsa kamar za ta tsone mata ido ta ce "Yo wannan abu ai a bayyyane yake gwara tun muna shaida juna ki biya bashi in ba haka ba birni zan je in ɗakko miki ɗan sanda" Inna ta ce "Kulki za ki ɗakko mini, ke ko ƙarewa ki ɗakko soja" Sale ya ce "Haba Jummai ya ana neman masahala kina ƙin karɓa ko kin gwammace ake abu ɗaya wato faɗa" Juyaw Jummai ta yi bakinta sake tana son tabbatar da manufar mijin nata, saboda a yanayin maganarsa sai ta ji kamar dai yana goyon bayan Innar ne. Ya cigaba da faɗin "Tun da har ta amince ai babu komai in har hakan zai zama masalaha" Inna wani murmushi ta yi saboda ita dai ta san wannan ce mafita babu inda za ta samo kuɗin saniya. Jummai ta ce "Babu wani masalaha munfurci dai irin naka in ba haka ba, ta yaya za ka amince da auren tsohuwa" ,Mai Gari ya dakatar da su ya ce "Haba Jummai wai ni ku mata wani lokacin me ya sa bakwa son gaskiya, duk wani abu in dai aka ce warwarar matsala ne shikenan kuma mutum ba ya fita a wajenku" Zuwa wannan lokacin Jummai ta kai linta a ɓacin rai, ji take tamkar ta yi da dukan Sule, Inna da kuma Mai Gari, tsabar haushi. Lami ta ce "Inna wai da kike maganar aure da mijin Jummai da wasa kike? Idan ba da wasa kike ba ni kuma ya za a yi da nawa kuɗin" Inna ta ce Lami kin san dai ni guda ɗaya ce ba biyu ba, kuma dai jikana kike aure bare ke ɗin ma in ce zan aure mijinki a fanshe kuɗin, sannan tun da ba wani shegen ya aike ki basho sanoysr ba sai ki jira ya dawo ya biya ki" Mai Gari ne ya katse da cewa "Ni kaina na gaji da shari'ar nan kuma shi wanda ya cinye saniya ba a san inda yake ba ma, yanzu tun da Tasallah ta amince da auren Sale za a ɗaura auren... Jummai ce ta koma ta yi zaman ƴan bori ta ce "Yanzu Mai Gari wanann ne adalci? Ya za a yi a dakeni a hanani kuka, a cinye min saniya kuma a aure mini miji" Mai Gari ya ce "Idan har kin amince kin haƙura har ranar da Ibra zai dawo to, amma da sharaɗin kar in ƙara ganin ƙafarki a fadar nan" Jummai ta fitittike ta ce bata yarda da jiran Ibra ba kuma ba za a auri Inna ba. Sale ya ce ai ko an fasa shari'ar nan to fa shi dai aure da Inna babu fashi, a cewarsa ma zai biya Jummai kuɗin saniyar idan ya yi noma da damina" Kafin ya gama rufe baki Jumma ta je tsakiyarsa inda yake zaune tana ruwan bala'i, a ƙarshe dai Inna ta ce "Jummai ki kwantar da hankalinki auren nn na wuce gadi ne, idan na aure shi duk inda Ibra ya dawo to takardar sakina za a bani in bar muku gida, in ba larura ba ma ina ni ina aure a wannan shekarun nawa" Mai Gari bai jira komai ba ya fara gabatar da shawara a wajen jama'ar fada kowa ya ce wannan ce mafita, Sule ya kyallara idanu yana kallon Inna da wani murmushi Inna ta rufe fuska irin na jin kunyar nan. Har za a fara gabatar da ɗaurin auren Inna ta ce ",Mai Gari a ja kunnen Jummai fa kar a zo bayan aure take ce mini ƴar sadaka, ko take kiran aurena da auren biyan bashin saniya" Mai Gari ya ce "Ai sai dai in bana garin nan na Mai Mangwaro" Sule ya ce "Daga na bata kuɗin ta in na yi noma ai kin zama mallakina ma" Wani farrrr da idanu Inna ta yi. Mai Gari ya ce " A yi wa annabi salati" Jama'a suka ce S.A.W" Yaraf Jummai ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. *MA'ARUF* Da sauri Ma'aruf ya ɗago kansa yana kallonta, Rahma kuwa sai ƙwafa take a ranta tana cewa Allah ya ƙara maganin mai shishshigi da shiga abin da babu ruwansa. Daddy jikinsa ne ya yi sanyi jin furucin Hajiya tabbas yana son Rahma amma ba zai kori Ma'aruf daga gidansa ba saboda ya san Mai Gari yayansa shi ne sanadiyyar dawowarsa garin abuja da zama sannan a taƙaice ma shi ne silar arziƙinsa, yanzu yana jin nauyinsa ya kora masa ɗa gida saboda wanann maganar sannan ba zai iya yi wa su Hajiya musu ba hakan ya sa ya ce "To shikenan Ma'aruf ke ɗauki kayanka mu je in sauke ka a tasha sai ka je gida, idan ka je ka haɗani da Mai Gari in masa bayani" Cike da takaici da kuma da na sani Ma'aruf ya ɗago kai ya sauke a kan ɗan uwan mahaifin nasa, amma abin mamaki sai ya ga Daddy ya faki idanun su Hajiya ya ƙifta masa idanu, duk dabya kasa ganewa cewa gizo idanunsa suke masa ko kuwa dai ya ga Daddyn ya masa wata alama. Daddy ya ce "Amma yanzu tun da dare ya yi da safe sai ka tafi" Haka ya buɗe baki zai yi magana Daddy ya dakatar da shi, akwatin ya kinkima Hajiya tana murmushin nasara, na ganin sun jefar da ƙwallon mangwaro sun huta da ƙuda, Rahma har da cewa Allah raka taki gona. Da daddare bayan kowa na gidan ya yi bacci, Hajiya da ta gama ƙwawar Alhaji ya kwana a ɗakinta ya ce shi ba ya jin daɗin katifar ɗakinta saboda bata da laushi ya fi so ya kwana a ɗakinsa, ta rasa mai ya sa yanzu ya fi son kwana a ɗakinsa, ita kuma kawai bata son gadon ɗakinsa saboda irin ƙaramin nan ne bashi da wasaci sosai, wannan dalilin ya sa sai ta yi kwanciyarta. Yau ma kamar kullum hakan ce ta faru, Alhaji da tun da ya shiga ɗakinsa ya rufe ƙofa ya hangi wayarsa da take kan bed side drower tana kawo haske wani murmushin gefen baki ya saki yana shafa haɓarsa, wajen wayar ya nufa kamar yadda ya yi zato kuwa hakan ce ta kasance sunata ya gani kamar yadda ya yi saving my zee bakin gadon ya koma ya zauna ya ɗaga wayar cikin muryarta mai ɗauki da sinadarin shagwaɓa ta ce "Haba baby ka barni sai tsoron nake ji ina dakon jiran dawowarka" Ta faɗa tana sakin kukan kissa. Wata ajiyar zuciya ya sauke tana jin ta har cikin kunnenta cikin ƙasa da murya ya ce "Haba amarya ke kin san sai dai in wani abu ne zai riƙe ni amma ina nan zuwa gare ki, kin san dai daga kasuwa ma a nan na yada zango, to yanzu ma ina so ta yi nisan zango a bacci in lallaɓo in taho" Daɗi ne ya rufe Zee ta ce "Sai ka ƙaraso" Amsa mata ya yi yana lunshe ido tonowa da ya yi da cewa yanzu idan ya je tana nan sanye da kayan baccin nan nata masu taushi da kama jiki. Sai da ya ɗauki kamar minti talatin ya fito ya nufi ɗakin Mummy yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin, tun kafin ya shiga ɗakin kunnuwansa suka yi arba da munsharin da take sakin tamkar an shaƙewa raƙumi wuya, kasancewar tana da nauyin bacci har ya ɗan tsaya amma ko motsi bata yi ba ta yi shame -shame. Ƙofar ya jawo mata a hankali, ya rufo, ɗakinsa ya koma ransa fari ƙal, yana zuwa ya ɗauki wayarsa da kuma mukullin ƙofar baya wacce yake bi ya yi ɓadda kama ya tafi gidan Zee. Zee ƙawar Rahma ce amma ba ƙawa ta jiki sosai ba, sun yi aure da Daddy ba tare da sanin Hajiya ba kasancewar tsananin kishin Hajiya ya saka ta sanya shi ya mata alƙawarin ba zai mata kishiya ba, yanzu kuma da tafiya ta yi tafiya yana son ya yi auren amma babu hali. Don ba za ta bari ba, sun haɗu da Zee ne watarana ta zo wajen Rahma, bayan ta fita shi kuma yana ƙoƙarin shiga get ɗin gidan, hakan ya sa ya ɗauke ta a motarsa ya kaita har gida, daga nan ya karɓi lambar wayarta. Komai a ɓoye ya yi hatta bikin Zee Rahma bata san an yi ba, saboda lokacin ta je hoto Kaduna gidan wata ƙawar Mummy. Ya fito cikin dunu da yake gabaɗaya ƙwayayan gidan an kashe su, sannan shi ma ya kashe na ɗakinsa, yana lallaɓawa zai sauka daga matakalae kasancewar a sama suke, kamar daga sama ya ji an buɗe ƙofar ɗaki, da sauri ya ɗauke sawub takalminsa yana saurin ƙarasa sauka daga matakalar. haske ya hango an kunna fitilar harabar wajen, jin ƙaran tafiya ya yi saurin laɓewa, yana nan a laɓe sai ya ga Rahma ta sakko tana sanye sa doguwar rigar bacci hannunta riƙe da waya ta kunna fitilar. Gabansa ne ya faɗi saboda ya san matsawar ta ganshi sai ta gane shirin fita ne a jikinsa, don bai yi kama da mai bacci ba, kuma ya san idan ta ganshi tamkar a kunnen Hajiya sai ta faɗa mata. Fitilar falon ta kunna ta nufi frige ta buɗe ta ɗakko ruwan roba ta rufe, fitilar ta kashe ta haura sama, sai da ya ga duhu ya rasa saman alamar ta kashe fitilar kuma ya ji ƙaran buɗe ƙofa da rufewa, alamun ta koma ɗakin ta. Ƙofar falon ya buɗe ya fita ta ƙofar bayan gidan ya kulle ta, machine ya samu ya tsare ya hau ya nufi gidan amaryarsa. Yana zuwa ya ƙwanƙwasa mai gadi ya buɗe masa ya shiga, yana zuwa part ɗinta ya ta buɗe ƙofar ya shiga ta rufe, yana kafe ta da idanunsa sai wani bubbuga ƙafa take wai ya ƙi zuwa tana ta jiransa, a rayuwarsa shagwaɓa da ɓacin da take masa shi yake rikita masa lissafi. Kimanin wata biyu da yin aure suna cin amarcin su suna cin karensu babu babbaka, yana fitowa daga gidan Hajiya in ya ce zai tafi kasuwa gidan amarya yake zuwa, sai a shelaƙe zai je kasuwar, sai dai yaransa ne a kasuwar, sannan da wuri yake tashi ya koma gidan amarya, a can sai dare zai dawo gida kullum da uzurin da yake ba Hajiya, ko Ma'aruf bai sani ba, abu ɗaya ya sani shi ne Daddyn yana sanya shi ya ajiye shi a gidan amma bai san mai Daddy yake a gidan ba. Sannan da dare ma sai ya lallaɓa ya je su kwashi soyayya ita Hajoya tana can kwance basho bata san wainar da ake toyawa ba.. Don haka amarya bata san bakin uwar gida ba saboda kullum ita ce take da miji safe rana da dare ma su kwana, sai ya yi asubanci ya koma, don a mota mai gadi yake mayar dashi da yake a gidan akwai motar Zee ɗin. Ido biyu suka kwana suna bankar amarci tamkar ba za su rabu ba, Daddy ji yake yanzu kaf duniya babu abin da Zee za ta buƙata ya ƙi yi mata saboda yana samun yadda yake so daga wajenta. Tare suka shiga suka yi wankan su, ganin ƙarfe huɗu da wani abu ya ce zai tafi gudun samun matsala, dakyar ya samu Zee ta bar shi ya fito, mai gadi ya ɗauke shi kamar kullum a motar ya nufi gidan da shi a ƙofar bayan ya ajiye shi, ya buɗe ya fita ya buɗe ƙofar gidan ya shiga ua mayar ya kulle. A can cikin gidan Daddy kuwa Mummy ce ta tashi zaune, tana murtsuka idanu, tare da sakin doguwar hamma ta rufe bakinta, ta sakko daga gadon ta nufi bayin cikin ɗakin nata domin yin fitsarin da ya tashe ta, da ta fito har za ta koma kan gadon sai kawai ta fasa, ji ta yi kawai tana son jin ɗumin mai gidan nata, ita da ta ma manta rabonta da shi saboda ita a nata hankalin yanzu sai ta shafe tsawon lokaci basu kasance tare ba, tana ganin ai sun girma, bata san cewa shi namiji ba ya girma da buƙatar sunnar aure, haka nan namiji ba ya tsufa da haihuwa. Wayarta ta ɗauka ta kunna fitilar bayan ta kashe fotilar ɗakin nata da ta kunna, duk da ta san ana kiran sallag zai ce masallaci zai tafi amma dai ta san kafin lokacin sun kashe arnan soyayya ya haɗa alwala da wanka, tun da ta ga ƙarfe huɗu ta wuce. Ɗakin nasa ta dufafa gadan-gadan ta kama hannun ƙofar ta murɗa tare da tura ƙofar ta buɗe... *SHEIK* A kiɗime ya ɗago yana kallon Mai Gari ya ce "Aure kuma Mai Gari ni Sheikul Yemen, balaraben malami daga ƙasar larabawa?" Ya tambaya lokacin yana nuna kansa da yatsa. Mai Gari ya ce "Haba Ya Sheik kar ka manta ka sauka a garin nan don ka ceto garinmu daga halakar da shi da aljannu suke yi kuma yanzu wata gagarumar matsala ta taso a ce kana tambaya mai kamar tuhuma?" Wani yawu Sheik ya haɗiye yana son nuna musu ba haka bane, cike da wayincewa ya ce "Haba kai kuwa ina ni ina wannan babban al'amari ina so ne in san shin wa kuka samu ya mata ruƙiyya har ya gano wanann baban al'amari na aurena a tare da ita?" Mai Gari da bai zaci waɗannn tambayoyin ba ya ce "Sai an mata ruƙiyya za a gane haka, ita da kullum bata cikin hayyacinta ita fa koyaushe aljannunata suna tare da ita, ga shegen leƙen asiri da tone-tone, ai gwara ma da ta zaɓe ka to ai kai ne maganin iskancin nasu idan suka je maka leƙen asiri su ganowa kansu maganin su" A zuciya Sheik ya ce "Kun kashe ni, leƙen asiri kuma? Ni da ba gaskiya gareni ba ina ɗan rurrumawa amma yanzu a ce wai za a mini aure, auren ma da mai aljannu, in ƙi auren ku gano lagona' A fili kuma sai ya ce "Kash aljannun nan basa kyautawa wataran" Ya faɗi hakan a ransa yana cewa sai ya , yanzu ni ai ba zan ke garajen faɗar laifukansu ba kar in je a yi ta kife da shi. Ɗaya daga cikin dattijan sa suka zo ya ce "Amma Allah gafarta malam, me ya sa ka ce basa kyautawa wataran ni a nawa tunanin aljannu ai kullum ma basa kyautawa, ka ga fa yadda yanzu suka ce idan baka auri amaryarka ba za a tashi yaƙi a garin nan a kashe rayukan garin rabi da kwata, kenan akwai wani abu ko dai kan tsoron su ne?" Sheik jin za a harbo jirginsa ya ce "Ashsha Malam Wada ai ni nan aljannu ko wucewa na zo yi suna waje sai sun sara mini, ni ai ba zan ƙi aurenta ba bare ma kun ce ido ɗaya gareta ai mu a ƙasashen larabawa jihadi ne ka auri mace mai nakasa, kamar mai ido ɗaya ma muna kiranta mar'atul mubaraka, wato mace mai albarka" Gabaɗaya suka ɗauki kabbara " Allahu akbar!" Don sun jinjina masa, shi kuma a zuci kuka yake yana jin wannan auren kamar dai wata ƙulalliya ce aka shirya masa, tun da in akamce matarka ai dole za a ce za ta san sirrinka, shi kuma da yake da manya sirrika, ya zai yi rayuwar aure da mai ido ɗaya kamar ɓera ya leƙa buta, bayan nasa matan ma masu lafiyar ido ma ya bar su a can. Haka ya ringa janyo kalmomin larabci wanda bai san ma'anarsu ba yana ta faɗa musu tare da kwaɗaita musu cewa duk wannan larabcin ayoyi ne yake janyowa a kan falalar auren mace mai ido ɗaya, yana yin hakan ne ko Allah zai sa ɗaya daga cikin su ya ce zai auri mai ido ɗaya amma sai ya ga babu niyya ango ya kwana da wando. Ya amince da buƙarar auren saboda ba ya so ya ƙi su ga gazawarsa, ba ma komai ne ya ɗaga masa hankali ba sai da ya ji Mai Gari yana bayanin cewa asali da idanunta biyu aka haife ta amma daga baya kuma aljannu ne suka cire mata idon guda ɗaya, buɗar bakin Sheik sai ya ce "Garin yaya?" Ya faɗa gabansa yana tsananta bugu. Mai Gari ya ce "Ai wataran aljannunta sun tashi sai aka ɗauke ta zuwa wajen mai magani, to mai maganin ne ya shiga dukanta da dorina, ashe dai aljannun sun ji haushi shi ne suka cirewa mai maganin mafitsara ita kuma suka cire mata ido ɗaya. Dadammm gabansa ya yi wani irin bugu musamman da ya ji an yi batun mafitsara, tun da ya san dole in ya aure ta a yi sunna to kuwa ina zai yarda ya tuɓe a gabanta ya je a masa mai kankat wato a guntule shi kamar yadda aka bashi labarin an guntule wani malamin mai magani, lallai yana cikin jalala amma dai hakan ba zai sa ya nuna karayarsa ba, a matsayinsa na wanda ake girmamawa. Haka suka yi ta saka masa albarka a ƙarshe suka ce gobe za a ɗaura auren tun da gudun kar aljannun su fara aika-aika a garin. Duk da Sheik yana da son mata amma yana ji yana gani, wannan macen ba ya ɗokinta. Bayan tafiyarsu haka Sheik ya kwana da zulumi bai runtsa ba, saboda ga damuwar aurensa da mai ido ɗaya, ga kuma yadda aka kwana ana taɓa jikin langa-langan da aka binne mai ƙusumbi a gidan. Washe gari aka ɗaura auren Sheik da mai ido ɗaya, kowa sai kiransa ango yake, amma Sheik ransa ƙuna ma yake da aka ce an ɗaura auren. A ranar ne aka ce za ta tare gudun shaiɗacin aljannun kar su yi abin da suka ce za su yi a garin. Ranar kaji biyu aka dafawa Sheik saboda sun zama su biyu, kuma dai a gidan da yake za su zauna shi tunaninsa ma buhun kuɗinsa da yake taro, da kuma ya zai yi in zai je wajen Malam karɓar magani, shi dai kawai gani yake wata maƙarƙashiya aka shirya masa don a tona masa asiri. Bayan magriba yana zaune a ɗaki yana tunanin yadda zai ke yi da hular gashin kansa kar amarya ta harbo jirginsa. Turowar ƙofar gidan da kuma shigowar Mai Gari da mahaifiyar amaryar ta Sheik dukansu a kiɗime suna rafka sallama, shi ya sanya hantar cikin Sheik ɗin kaɗawa ya fito daga ɗakin a ransa yana ambaton Allah sa ma aljannun ne suka ɗauke ta da ya huta. Mai Gari a rikice ya ce "Sheik akwai matsala fa, aljannun nan dai sai ka tashi tsaye a kansu, suna son yin fito na fito da kai a gurin amaryarka, yanzun nan muna jiran fitowarka mu yi sallar isha'i sai ga sirikarka a kiɗime wai amarya tana shirin da za a kawo ta gidan miji, tun da ka ce ba sai an kawo ta da komai ba katifar ɗakin ma ta isa, abinku ku malamai mai sauƙi ne kar a yi wahala, to shi ne fa amarya ta kurma ihu mahaifiyar tana zuwa ɗakin ta ga amarya kwance amma abin mamaki abubuwan nan guda biyu sun ɓace ɓat babu su" Gabansa faɗuwa yake duk sun ruɗa shi, ya kasa ma gane inda maganar ta dosa, uwar amaryar ce ta karɓi maganar da faɗin "Wallahi sun ɗauke mata mashayar shayar da yara duka biyun(Breast) Babu ko ɗaya wajen ya shafe shafal kamar ƙirjin babe, ko in ce kamar bayan silba" *MUNA DAB DA GAMA BOOK 1 WANDA PAGES KAƊAN SUKA RAGE MANA, KAMAR KULLUM KUN SANI INA BAKU BOOK 1 FREE BOOK 2 PAID, WANNAN KARON MA ZA A BIYA 500 KACAL DON KARANTA LABARIN HAR ƘARSHE, AKWAI CAKWAKIYA KUN SAN DAI YADDA AKE CAKWAKIYA TO NAN MA BA ZA A BAYAR DA KUNYA BA IN SHA ALLAH.* *MAI BUƘATA ZAI IYA TURA KUƊIN KARATUNSA TUN YANZU DON WASU TUNI MA SUKA BIYA, ZA A TURA ZUWA FAIZA ABAUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222 IDAN AKA KAMMALA CMPLT DOCMENT 800.* MAMAN AFRAH 09025576222 [7/15, 8:21 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 13 IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture *INNA TASALLAH* Har aka ɗaura auren Jummai tana sume bata falka ba, Lami tana gefe mamaki ya kashe mata jiki, ta rasa ma ina za ta sanya wannan lamari shin waye mai laifi Jummai da ta kawo a karɓa mata haƙƙinta ko kuwa ita ma da aka cinye mata kuɗin adashe, ko dai Mai Gari ne mai laifi wajen rashin aiwatar da komai bisa adalci. Inna ta sanya mayafinta ta kare fuskarta sai wani murmushi take dokawa, bayan an shafa fatiha sai Mai Gari ya yi gyaran murya ya ce "Sule ga amaryarka nan aure dai sunan ce ta ma'aikin Allah S.A.W ka riƙe ta da amana kar ka ga ta fika shekaru ka ce za ka mata abu na rashin kyautawa ko dai ka bari matanka su mata, ba zan lamunta ba, tun da dai ka ga ta yi hakan ne saboda ta sadaukar da kanta a matsayin kawo masalaha ga wannan tashin tashina da ake yi, ta yi biyan bashi da kanta ka ga hatta ni ta sama mini lafiya a kan wannan shari'a da ban san ranar ƙarewarta ba" Sulen yana wani murmushi sai washe haƙora yake ya ce "Ai kar ka damu Mai Gari babu abin da zai faru kuma ai amarya ko ta buzuzu ce dole za a so ta a yi ɗokinta" Inna jin wanann lafazin sai ta ƙara jin wani daɗi a ranta. Abin da basu fahimta ba shi ne Inna ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse ɗaya, ma'ana ta auri mijin Jummai saboda kawo maslaha sannan kuma saboda take samun abinci tun da yanzu ta ga dai idan aka kafa mata ƙahon zuƙa a kan biyan bashin nan hatta abinci ma sai ya gagare ta amma yanzu in ta yi auren dole dai a ciyar da ita, tun da ta lura abincin ta yana dab da ƙarewa kuma yanzu tun da da biyan bashi ba za ta samu sararin siyan abubuwa ba. Cikin jin kunya ta ce "Mai Gari a samo ruwa a yayyfawa ƴar uwata ta tashi mana" Kowa sai da ya jinjina lamarin wani ne daga cikin mutane wajen ya ce "Kai Inna amma dai bakya ma kishi da Jummai" Inna ta ce "Haba ina ni ina kishi da ita" A daidai nan aka miƙo ruwa Lami da take cike da al'jabi da jin kunya ganin an ɗaurawa kakar mijinta aure a wajen ta karɓi ruwan ta yayyfawa Jummai, sai ga Jummai wuruf ta tashi tana waiwaye ganin jama'ar wajen da kuma Inna da take kakkare fuska da mayafi hakan ya tabbatar mata da cewa ba mafarki take ba a zahiri ne. Tana tashi tsaye ta kalli Mai Gari ta ce "Ni ba ni aka yi wa amarya ba tun da ni ce mai bin bashi ni za a biya kuɗina tun da Sule ne ya auri mace" Mai Gari ya ce "Jummai Tasallah fa ta ce bata kishi da ke, kin fa zaman nan da za ta yi na ɗan lokaci ne, daga Ibra ya dawo za a bata takardar saki ta bar muku gida... Sule ne ya ce "Aure ai ba abin wasa ba ne tun da har aka ɗauka babu batun saki, a bar Tasleey ta ƙarasa rayuwarta a gidana" Sunan Tasleey da Sule ya kira a maimakon Tasallah shi ne abin da ya ƙara fusata Jummai, sannan shi ne abin da ya faranta ran Inna ta ji ta dawo tamkar ƙaramar yarinya. Cikin harzuƙa Jummai ta ce "Mu zuba mu gani sai na zame muku ciwon ido a gidan nan" Tana faɗar hakan ta juya fuuuu ta bar fadar kamar za ta hantsila. Mai Gari ya ce ya sallami kowa, ya kalli Inn yana dariyar wasa ya ce. "Ka ga amarya ran gida, amarya bakya laifi Tasallah amaryar Sule" Wani daɗi Inna ta ji, ta kunce ƙullin hannun zaninta da ta yi ta ɗauko kuɗin kayan miyarta haka ta zaro ɗari biyar ta ce "Mai Gari ga jaka biyu da rabi (500) Ka ci goro" Sosai ya ji daɗi yana washe baki ya ce "Yaushe za ki tare?" Ta ce "Yo tun da aure ya ɗauru ni kuwa tariyar mai zan jira ai a yau ba sai gobe ba" Sule ya ce "Dama akwai ɗakina kawai sai ta zauna a ciki". Lami tsaye ta miƙe ta ce "Mai Gari ni ina nawa zancen ya kwana tun da ita Jummai an samu mafita?" Kallon sheƙeƙe ya mata ya ce "Ana batun giwa wa yake maganar ɗan tsako, amma dai ai kin san wanda ya zai je sama ya taka leda ya ci ƙarfin tafiya ko?" ,Takaici ya sa bata sake cewa komai ba, juyawa ta yi sai Inna ta ce "Yanzu Lami maimakon ki tsaya ki ɗauka mini samirar nan da ledar kayana, ki raka ni gidan in kintsa, amma kya tafi ki barni ai an yi ba a yi ba rufin ƙofa da ɓarawo" Cike da jin haushi Lami ta ce "Haba Inna tun yanzu ai a tunanina duk gaggawar asara ta jirayi samu" A faɗa ce Inna ta ce "Ke kika sani ƴar baƙinciki wato kina jin babu daɗi na samu jirgina ya ɗaga na yi aure bayan a gari ga yan mata nan galla-galla da zawarawa masu jini a jika amma ni na tashi na barsu, to ai dama abin rabo ne auren mace da ciki" Takaicin ta ta danne ta ce "Haba Inna ai ba batun baƙin ciki ba ne, ai ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ni ma ba zan so ki ƙarasa rayuwarki babu aure ba, gwara ki yi ko a sama mana ƴan ƙanne" Kallon kallo aka shiga yi a fadar Lami ta sunkuya ba don ta so ba ta ɗauki samira da ledar Inna ta yi gaba, ita kuma Inna ta tashi tana ta jin kunyar jama'ar wajen Mai Gari ya ce "Tasallah babu batun kunya ba a aure kuma ai jahadi kika yi" Ya faɗa yana saka ɗari biyar ɗin da ta bashi a aljihu. Inna ta ce "Haka ne ai da rashin tayi ake barin araha, kuma da rashin kira karen bebe ya ɓata" Gabaɗaya ƴan fadar aka amsa mata ana mata jinjina, har ta yi gaba Sule ya tashi yana washe baki ya ɗan bi ta suka keɓe ya ce "Amarya bakya laifi, yaushe za ki zo" "Ta ce ahaf dag an yi sallar isha'i mana za a rako ni, kar in je in zauna Jummai ta zo ta min tijara a kan kuɗin saniyar da na fansa da aurenka" Haka ya tafi yana wani waiwayen Inna, wasu daga fadar suna masa kallon sha-sha-sha. Tafe suke a hanya Lami tana barin Inna a baya har Inna ta gaji ta ce "Lami sai wani cin magani kike, wai ke baki san mata tsoffi ƴan da basa tsufa ba, mu fa nan mu ake yi wa laƙabi da mace daki bari" Cike ta haushi Lami ta ce "Daki bari kamar wata atamfa?" Inn ta ce "Yo ai atamfa wataran tana yagewa ko ta mutu a jefar da ita, amma mutane da ƙarko garemu kuma shi namiji ba ya ganin tsufan mace waɗannan matan nasa sai ki ga na je na fiye masa su sau miliyan, duk wannan hayagagar da Jummai take wiyarta in tare ai duk wanda ya daka rawar wani zai rasa turmin daka tasa rawar, dama alƙawarin Malam na ɗauka na ce ba zan yi aure ba amma yanzu na fasa aurena zan zauna yo malam ɗin ma da shi ne ba lallai ya bari a mini arba'in ɗin mutuwa ba zai gallo wani auren, ita ma Jumman kallon raini take min bata san cewa idan makaho ya ce a yi wasan jifa to tabbas ya take dutse ne, amma dai zan nuna mata gani ya kori ji" Banza Lami ta mata, har ta fara tunanin ma dama duk rawar kan Ibra da rashin jin nasa wajen Inna ya yi gado. Suna dab da ƙofar gidan Inna Lami ta ce "To Inna ga kayan ni zan wuce gida, Inna amarya ta ango" Ta faɗa cike da gatse. Inna ta kalle ta ta ce "Kin ga Lami kar ki mini fallasa auren bashi, idan ba za ki kai mini gida ba, ba sai kina mini terere a titi ba, amma dai ki sani duk wanda ya ƙona rumbunsa ya san inda toka take tsada" Tana karɓar kayanta ta shige gida, Lami kuwa baki ta taɓe ta yi tafiyarta. Inna gidan ta buɗe ta shiga, tana murna ta shiga haɗa ƴan komatsanta da ta san za ta buƙata . Kawayenta guda huɗu ta je ta gayyato suna ta mata barka sa fatan alhari don babu wacce ta ce bata kyauta ba. Haka mata biyu suka yi gaba da yara aka je da kayan Inna ƴan samiru da kayan sawa, sai randunanta da aka ɗauka a baro da sauran kaya, aka je dakyar aka shiga da kayan kasancewar Jummai tana tijara, sai da Sule ya tada jijiyoyin wuya. Bayan an kintsa ɗaki da gadon Inna na ƙarfe, sannan aka rako Inna a ƙafa ana ta rangaɗa guɗa, haka aka shigo da ita aka zaunar da ita a bakin gado.Bayan kowa ya watse , Inna ana zaune ana ta murmusawa ango ya shigo da ledar tsire da pure water, Jummai tana zaune a ɗaki ta kasa ta tsare tana jiran zuwan ango, ita kishiyar tata ma cewa ta yi babu ruwanta ita ma Jummai abin da ya sa ta damu saboda ga babu kuɗin saniya ga kishiya. Bayan Sule ya shige ɗakin amarya dama ko ta kan su Jummai bai bi ba, ya rufe ƙofa yana washe baki tare da mata kirarin amarya mai daɗin tuwo. Ƙasa ta sakko suna zaune a tsakiyar ɗakin, ya saka hannu ya buɗe fuskar da ta rufe da mayafi, Inna tana ta kare fuska tana zabga murmushi, Sule saboda ƙarfin hali har da shan magani don abokansa sin zuga shi a kan cewa tsohuwa ma ai mace ce, kuma ita ma tana da tata ni'imar hakan ya sa ya shawo ya yi tatul, don gabaɗaya mararsa hargitsa masa take Inna kuwa babu abin da ta sha sai maganin zafi wato maganin rana, sai wani abu da wata matashiyar mace maƙociyarta ta bata mai suna ƙwaƙwalwar raƙumi ta ce ta saka a gabanta, gabaɗaya sai ta fi sauran matan ɗanɗano. Ya fito da pure watern da takardar tsiren ƙamshin ya cika musu hanci Inna tana ganin ita gaba ta kai ta gobarar titi don sai ta ji gwara ma da Ibra ya gudu da saniya tun da gashi ta tsinci dami a kale, ga abinci za take samu ga kuma kayan daɗin amarci, tun da ta ga har da ruwan leda(Pure water) Da har tana jin haushin an katse mata shan mangwaro ashe dai rabo ne yake kiranta. Sule ne ya ɗakko tsoka ɗaya ya nufi bakin Inna, tana ɗan kauda kai ta karɓa tana jin kunya sai ƙarfin gwiwa yake bata a kan cewa babu kunya tsakanin miji da mata. Tana taunawa ya tulla ruwan guda ɗaya, ya miƙa mata ta kurɓa bayan ta cinye naman, ita ma hannu ta kai ta ɗauki ɗaya tana kare fuska ta miƙa masa, Sule kansa ya ji ya wani ƙara girma don shi har ya manta da a bashi abinci a baki ko dai ya ci ko ya zauna da yunwa duk ɗaya a wajen matan nasa. Baki ya wangale sai dai kash, naman bai kai ga sauka a kan harshen sa ba sai aka banko ƙofar ɗakin, a tare suka ɗago suna kallon wanda ya banko ƙofar a tare suka zaro ido ganin Jummai sanye da wani tafkeken gajeran wando da wata riga mai ƙaramin hannu, sai wata adda sabuwa dal a hannunta, ƙofar ta mayar ta rufe har da saka sakata, su duka sun tsorata sun fara tunanin ko dai kashe su za ta yi. Inna bata san lokacin da ta saki naman hannun ta ba, shi kuma ango ya ajiye ruwan hannunsa a take ruwan ya fara malala a tsakar ɗakin. Jummai tana zare ido ta kalli Sule cike da kakkausar murya ta ce "Sule saniyar da ake shari'a taka ce?" Cike da tsoro yana kallon yadda sabuwar addar take ƙyalli ya shiga girgiza kai alamar a'a Ta ce "To wannan ba amaryarka ba ce tawa ce, don haka dole ta bini ɗakina muke kwana, in ha haka ba sai dare ya tsala kun sakankanci da cin amarci, zan shigo in datse maka mafitsara" Idanu ya zaro yana saka hannu biyu ya dafe mararsa, don ya san kaɗan daga aikin Jummai. Ta ɗora da faɗin "Ita kuma na sare mata mazaunai" Inna da sauri ta kai hannu biyu ta dafe mazaunan ta tana zare ido gabanta yana faɗuwa domin kuwa ta ga samu ta ga rashi. Tana nuna su da yatsa ta ce "Shawara ta ragewa mai shiga rijiya" *SHEIK* Yana zaro idanu amma bakinsa ya kasa furta ko uffan sakamakon yadda zuciyarsa take zilli tamkar za ta huda ƙirjinsa ta fito. Tunani yake wace irin baƙar ƙaddara ce a shegen neman kuɗinsa a ce za a ɗaura masa aure da mace mai aljannu, mai aljannun ma wacce aljannu suka raba ta da ido ɗaya, sannan yana ji aka ce an cirewa mai maganin mafitsara amma kuma sai a ɗora masa jakar tsaba gashi nan yanzu kaji suna bin sa. Managar Mai Gari ta katse masa tunani da faɗin ",Ai yarinyar nan Allah ya taimake ta ba ƙaramin sa'a ta yi ba da ta auri Sheik amma in ba Sheik ba wa zai iya auren ta?" Sirikar Sheik ta karɓe da faɗin "Yo ai dama riƙon mahaukaci sai sarki" Numfashin sa ya samu daidaitawa ya ɗan saka harshen sa ya laso bushashshen leɓansa da ya bushe ya ce "Kai amma wannan dai sun takurawa rayuwarta, dama ana yi a ce an ɓatar da mashayar jikin mace?" Ya tambaya cike da tsoro don shi yanzu ya kasa bambance komai ma, duk tsoro ya hana shi sakat musamman idan ya tuna cewa yau da ita za su kwana a gida ɗaya kuma a ɗaki ɗaya. Cike da alhini mahaifiyarta ta ce "Kayya malam yo aljannu mene ne basa yi, yarinyar nan wataran fa ko rashi ta yi za ta yi fitsari sai ka ji ta ce babu wajen sun toshe mata, sai ranar da suka bushi iska suke buɗewa ai tana wata rayuwa, yanzu dai Allah ya kawo mata ƙarshen wahala, in ma ba malamai irin ku magada annabawa ba waye zai yarda a ce mace an cire mata mashayar ɗa(Breast) Kuma ya yarda bai sake ta ba, kai wani mai aljanun ma ba zai yarda ya aura ba, kai ɗin ma jahadi ne ka yi" A fili Sheik ya ce "Yo ai dama kura ma ta san gidan mai babbar sanda, amma su sani rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya" A zuciyarsa kuma ya ce "Za ku yi sake reshe kama ganye, wannan dai wayon a ci ne an kori kare daga bakin ɗinya, in ba haka ba kawai kuje fakewa da malami kuna turo mini mutuwa yo mutuwa mana wannan da aljannu suka zama danginta jinin jikinta za a kawo min ita, baku san ni ɗin ma ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama ba, babu wani malam kawai MALAMIN BOGI ne' Cike da murnar kalamansa Mai Gari ya ce "Ai sai mu je ko? Dama mutane sun kewaye ta in ji mahaifiyar amma kowa cewa yake ai matar babban malamin larabawa ce daga ya zo komai ya ƙare" Baki Mai Gari ya washe ya ce "Shi ya sa nake alfahri da shi a garin nan Allah ya tarfawa garinmu nono" Sheik a ransa ya ce Ai dama ba wahalalle sai kwaɗayayye, haka kawai garin neman gira in je in rasa ido, ni ban amfani kuɗin da na tara ba in rasa abin da kuɗi ba zai saya ba, amma ya na iya haka zan ringa tarar aradu da ka, in ta yi ruwa rijiya in bata yi ba masai' A fili ya ce "Ai kar ka damu mai gari, mu ko a ƙasashen larabawa bamu san tsoro ba, zan yi ta ba mutanen garin nan magani mata na basu na gyaran aure kai kowa sai ya samu abin da yake nema" Sirikar da Mai Gari suka yi kabbarar jin furucin ta, tana murna ƴarta ta samu mijin nunawa sa'a. Ɗaki ya shiga ya ɗauko magani ya ɗakko dogon carbinsa ya fito, Sirikar Sheik ta ce "Ai Allah ya kawo mana ƙarshe wahala, yo wahala mana da asubar fari idan aljannunta suka tashi kowa na gidan nan sai jikinsa ya faɗa masa, haka za ka ji saukar doka da dorina" Gabaɗaya sai ya ƙara kiɗimewa zuwa yanzu ya gama tabbatarwa cewa matsala ya aura wato har tana duka. Tsabar ba ya hayyacin sa sai ya bi bayan su a haka. Mai Gari da ya waiwayo ya ce "Subhanallahi Ya Sheik kana lafiya kuwa, baka saka takalmi ba" Cike da wayincewa ya ce "Ashsha duk saurin zuwa nemowa amarya lafiya ne" A ransa ya ce 'Lallai akwai lauje cikin naɗi, yau dai na yarda cewa dalili ne kaɗai yake sa a leƙa gaban sirika' Takalmin ya ɗakko, lokacin da suka doshi gidan, sai haɗuwa da jama'a suke a hanya ana girmama Sheik basu san cewa ba ya gane abin da suke faɗa ma, shi hankalinsa ba ya jikin sa musamman da suka kusa shiga gidan suka ringa jin wani kururuwa da iface-iface. A zaure suka tsaya, Sheik zuwa yanzu ko magana ba ya iya yi ta fito sosai sai jan carbi da yake ta faman yi yana addu'a a ransa cewa, Allah ya ɗora shi a kan aljannun nan, shi yanzu so yake ya cigaba da bayar da magunguna amma batun aljannun nan ba so yake yi ba. Sai tashin hanyaniya da suke ji ta mata a cikin gidan, jim kaɗan sai ga sirikar Sheik ɗin ta dawo tana cewa "Bismillanku ai gata can ma jikin ya matsa, amma abin mamaki sunan Sheik take ta faman faɗa" Sheik da ya ji faɗuwar gaba an ce ana kiran sunansa sai ya yi zaton ko dai sunan sa na asali ta faɗa wato Ibra tun da ya san su aljannu babu abin da basu sani ba. Da ɗan diriricewa ya ce "Ya subhanallahi wane sunan daga ciki?" Ta ce "Sheik kawai take cewa, amma idanunta a rufe" Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ta shiga gaba suna biye da ita, duk mata ne da alama ƴan taron bikin ne da kuma kai amarya. Ɗakin da take karaɗin ihun ne wanda sai da aka rufe daga window ake leƙen ta. Mai Gari ne ya ja ya tsaya yana mai cewa "To Ya Sheik a fito lafiya" Ɗiff Sheik ya yi yana jin faɗuwar gaba tana ratsa dukkanin gaɓoɓin jikinsa da zuciyarsa, amma haja ya daure ya gyaɗa masa kai yana mai faɗin "In sha Allah" Haka sirikar tasa ta buɗe masa ƙofa ya shige, har da rufo ƙofar. Tana kwance reran sai wani gurnani take tana surutai da ihu. Gabansa yana tsananta bugu ya haɗiye wani yawu ya ce "A'uzubillahi minsh shaiɗanir rajim" Ya faɗa da ƙarfi saurin yana karaɗe ɗakin, kamar aljannu jira suke ya yi magana sai ta ɗifff kamar an ɗauke wuta, murmushi ya yi a ransa yana faɗin 'Ashe dai ku ɗin ma matsorata ne kamar ni, yanzu kuwa za ku faɗawa ƴan garinku don wallahi sai na mori faɗuwar gaban da kuka sakani sai na baku wuju-wuju, mu zuba mu gani' Ya faɗa a zuciyarsa yana ajiye maganin da ya taho da shi, carbinsa, da kuma hiraminsa ya naɗe hannun jallabiyarsa. A can tsakar gida kuwa jin ta yi shiru sai aka shiga ƙusƙus kowa yana murna, ana yabawa lamami daga ƙasar larabawa. Mahaifiyar ta ta ce "Kai jama'a aiki ga mai ƙare ka, ashe dai duk ihu suke bayan hari ka ji dai ya fara maganin su" . Mai Gari ya ce "Yo dama mai zai gagara ai da kike ji da gani ƴarki ta yi babar sa,a saboda yanzun nan za ki ji ya fitar da su, ke hatta nonuwanta dole su dawo mata da su" Wannan maganar da suka yi a kunnen Sheik da yake suna a ƙofar ɗakin ne. Sheik jin haka sai ya ƙara ƙaimi, ya leƙi da window yana cewa "A samu murɗuga-murɗugan bulali, guda biyar wannan dole sai sun ci ubansu" Ya faɗa da muryar hausar larabcin sa. Da sauri Mai Gari ya saka samari suka ciro a dalbejiyar ƙofar gidan, aka miƙawa Sheik, nan da nan sai ya hau karatun suratul fatiha ita kaɗai ya karanta har lokacin dai bata ƙara ko motsi ba ta yi ɗif kowa bata cewa komai sai dai yanzu ta buɗe idanunta sun yi faral kamar na gawa. Ganin hakan ya hau zagarta da bulala, yana faɗin "Za ku fita ko sai na koya muku hankali, sai na nuna muku kudu ba arewa ba ce matar malamin ƙasar yemen za ku ɗaukewa mashaya, baƙin ciki kuke min, kar in angwance" Ya faɗa yana tafka mata bulala. Sai da bulala uku ta karye duk ya burɗa mata jiki. Ya ɗaga ta uku zai zabga mata sai gani ya yi ta miƙe a fusace, yanayin yadda ta iyo kansa sai da hanjin ciknsa sa ya kaɗa, bulalar ta riƙe bai ankara ba ya ji ta warce, ja ɗaya ta yi wa bulala sai ga Sheik ya saka yana zare ido cike da tsoro, gabansa yana bugawa, ɗagawa ta yi ta tsula masa, tsabar yadda zafin ya shige tsalle ɗaya ya yi sai gashi a gefen gado, taku ɗaya ta yi sai gata a tsakiyar gadon, ta ɗaga bulalar tana rama dukan da ya mata, amma saboda gudun kar a gano lagwansa bai yi ihu ba, ko wani furuci da zai sa a gane halin sa yake ciki. Mai Gari ne cikin laga murya ya ce. "Aikin ka yana kyau Sheik kar ka bar su sai sun dawo mata da abubuwan nan masu muhimmanci a jikin mace(Breast)" Sheik dakyar ya mayar da kukan da yake ƙoƙarin ƙwace masa ya ce "Ai sai sun maido... Bai ƙarasa faɗa ba ta buge masa baki tana zare ido yana kallon ta ya san ba a hayyacin ta take ba. Shammatar ta ya yi ta ya fito daga lungun gadon sai ga shi a tsakiyar ɗakin, farɗo ta ya yi yana ɗaukan ɗaya bulalar ya zabga mata sai ta zube a kan gadon idanunsa ƙurrr a ƙirjin ta ya ga wayam babu breast kamar ƙirjin yara. Baki ya buɗe yana karanta qulhuwallahu ahad, yana zabga mata bulalar yana cewa "Ku maido da nonon da kuka ɗauke, ku maido da shi aka ce... Bai rufe bakinsa ba mai zai ji? Wani abu ya ji kamar an hura masa iska a ƙirjinsa, kafin ka ce kwabo sai ya ga tudu nan da nan sai ga breast ɗin duka biyu a ƙirjin Shaikul yemen. Idanu ya zaro cike da fargaba a zuciyarsa ya hau cewa 'Ƙirjin ta nake nufi fa aljannu, ƙirjinta nake nufi ku mayar ba ƙirjina ba na shiga uku ni Ibra jikan Inna' Ya faɗa yana kai hannu cike da tashin hankali ya shafo ƙirjin, breast ne ya ji tamkar ƙirjin mace.... *BOOK 1 free BOOK 2 500 shiga grp cmplt docment 800 za a biya ta asusun faiza abubakar 9030283375 opay. Saura page 2 a gama book 1* *MAMAN AFRAH* 09025576222 💃 TALLAH TALLAH💃 *Kamfanimu na MEERAH B HERBS muna da kayan mata masu kyau da inganci, akwai maganin sanyi maganin gyaran breast, maganin hips, na rage ƙiba, na ƙara ƙiba, maganin rage tunbi, da kuma maganun MAN POWER ga matan da mazajen su ba sa uin kataɓus a wajen aikata sunna da sauransu.* *Mai so ya tuntuɓeni a layina 09025576222* [7/16, 6:52 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 14 IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_venture *MUMMY* Shigewa ɗakin Daddy ta yi, kasancewar fitilar a kashe sai kawai ta durfafi kan gadon, cike da shauƙin soyayya ta ɗare gadon, sai dai wani abu da ya ratsa ƙwaƙwalwar ta shi ne, jin gadon kamar ma wayam yake babu kowa a ka, ma'ana kamar dai ita kaɗai ce da ta hau gadon yanzu a ka, mamaki da al'ajabi suka haɗe lokaci guda a kwanyarta tambayoyi da tunani barkatai suna safa da marwa a ƙwaƙwakwar tata. Da yake tun tana dab da zuwa ƙofar ɗakin ta kashe fitilar wayarta, saboda ta fi so sai ta hau gadon zai san da zuwanta, hannu ta kai ta gama zagaye kan gadon amma babu alamar mutum, fitilar wayar ta kunna sai yanzu idanunta suka ƙara tabbatar mata cewa ba ya kan gadon a zuciyarta ta ce 'To ko dai yana banɗaki?' Wata zuciyar ta ce 'Kuma banɗakin ne ba zai kunna fitilar ɗakin ba, sannan kuma ita ma ta banɗaki ba zai kunna ta ba?' Ƙafafunta ta zaro daga kan gadon, banɗakin ta nufa, bata kunna fitilar banɗakin ba sai ta yi amfani da fitilar wayar, amma sai ta ga babu shi babu alamar sa. Haka ta rufo ƙofar banɗakin ta dawo ta zauna, nazari take amma kwanyarta ta ƙi bata haɗin kan gano inda mai gidan nata yake, fitilar wayar ta kashe, tana jira ta ga ta inda zai fito. Daddy kuwa ransa fari tas ya fara haurowa sama, fitilar wayarsa a kashe saboda kar a samu akasin lissafi, saɗaf-saɗaf ya zo ya wuce ƙofar ɗakin Hajiya, ganin fitilar a kashe a zuciyarsa ya ce 'Ka ga sarakan bacci ana can ana fama, ni ai da kike da nauyin baccin nan gaba ta kai ni gobarar titi' Ya faɗa a zuciyarsa yana kama hannun ƙofar ɗakin nasa ya buɗe ƙofar, Mummy da take zaune har sai da ta ji gabanta ya daɗi saboda bata tsammace shi ba, sannan bata kawo cewa zai shigo a duhu bai kunna fitila ko da ta wayarsa ba ce. Ɗif ta yi tamkar bata cikin ɗakin, Daddy kuwa yana shigowa ya yi wata miƙa yana salati, tare da sakin doguwar hammar biyan bashin baccin da bai yi ba a daren na jiya. Kan gadon ya nufa kasancewar ba ta wajen da Mummy take zaune ba ne, har ya hau gadon bai san tana zaune ba, sai da ya ja filo ya tada kansa yana sakin wata hammar a karo na biyu, hannu ta ɗan miƙa ta sauke a jikinsa, gabansa ne ya buga da mugun ƙarfi kasancewar bai ma taɓa kawo cewar Mummy ba ce, gabaɗaya sai ya razana, fitilar wayarta ta kunna a takw haske ya gauraye ɗakin, sai a lokacin idanunsa suka yi tozali da ita, duk da ya tsorata da kama shi ɗin da ta yi, kuma ya ga fuskarta ma babu yabo babu fallasa amma kuma sai ya maje ya ɗan saita kansa. Mummy ita dai haushin inda ya fita da tunanin amsar da zai bata take, amma kuma bata taɓa kawo cewar wai aure ya yi kai bata ma yi tunanin har zai iya fita daga gidan ba. Cike da tuhuma ta ce "Alhaji daga ina haka?" Ta tambaya tana kafe shi da idanu don gani ta harbo jirginsa musamman da ta ji wani ƙamshin turare da ba nashi ba, yanayin ƙamshin mai sanyin ya sa ta ji tamkar ma turaren na mata ne, sai dai ba za ta yanke hukunci ba, kai zuciyarta ma ba za ta bari ta zargi Alhajin ta ba, saboda ta bashi yarda, ba ma wannan ne abin yin ba, sai alƙawarin da ta sanya ya ɗauka na dole, a kan cewa ba zai mata kishiya ba. Cike da iya sarrafa harshe ya ce "Ni ke ce ma kika bani tsoro kawai sai ki zo cikin duhu ki zauna? " Sai ta ji gabaɗaya ma ranta ya ɓaci kasancewar tana tambayarsa yana tambayar ta. Rai ta haɗe ta ce "Kai ɗin ma ai a cikin duhun ka fita, da ka dawo ma a duhun ka dawo" Gabansa ne ya bada rass jin furucin ta, tunaninsa ko dai shuka ya yi a idon makwarwa wato Mummyn ya ga tafiyarsa ko kuma dai Rahma dama ta gan shi ƙyale shi ta yi ita ce ta faɗa mata, wani gumi ne ya karyo masa, ya san in her Rahma ta ganshi amma ta nuna bata ganshi ba sai da ya fita ta bi sawunsa to tabbas babu abin da za ta ɓoye wa Hajiya. Jarumta ya ara ya ce "Haba Hajiyata ai ni na fita a duhu ne saboda kar in kunna haske ki hango daga ɗakin ki, ki ce na bar miki idanuna basu runtsa ba wato ban yi bacci ba, kuma da na dawo ma wannan dalikin ne ya sa ban kunna hasken ba" Ya faɗa zuciyarsa cike da zulumin Allah tarkonsa ya kama tsuntsu. Wani daɗi ne ya baibaye Hajiya don yanzu kam na gane komai ma saboda soyayyarta ya yi, wani farrrr ta yi da idanunta ta ce "To yanzu dai ina ka je?" Hannu ya kai ya shafo gashin kanta da babu hula ya ce "Kawai fa ina kwance na falka nake jin motsi a ƙasa shi ne na sauka na duba, ashe ma dai kunena ne don ban ga komai ba" Murmushi ta yi tana cewa "Kai kam baka son abin da zai taɓa iyalinka" Murmushin jin daɗin samun nasara a kanta ya yi, don ya san tabbas matuƙar ta gano shi to akwai gagarumar matsala ko da kuwa ganin budurwarsa ne bare kuma a ce matar aure, auren ma kuma a ɓoye ba tare da sanin ta ba duk da cewa ya san ita ce ta ja koma mene ne, a ce mace ta ce ita ba za a mata kishiya ba, wannan son zuciya ne da dannewa namijin haƙƙinsa tun da Allah ya halatta masa. Washe gari tun da sanyin safiya Hajiya take famar a je a sallami Ma'aruf da kuɗin kota ya kama hanyar ƙauye, Daddy kuwa da ya gama shirin fita ya ɗauki Ma'aruf ɗin suka fita tare, bai zame da shi ko ina ba sai gidan Zee a nan ne yake gabatar da Zee a wajen Ma'aruf tun da ita dama ta san shi a bakin Daddy. Daddy ya ce ya zauna a ɗakin baƙi kafin ya gama sama masa admission a wata ƙasar inda yake ganin zai dace da cigaba da karatun sa. Ma'aruf ya yi mamakin jin cewa Daddy yana da wata matar bayan ya san babu wanda ya sani kuma ya san akwai matsala ko dai ya ce tashin hankali duk ranar da ƙwan ya fashe za a yi ɗan jijjiɓin yaƙi. Ya ji daɗin cewa Daddy za fitar da shi ƙasar waje karatu, wannan ya nuna cewa Daddy har yanzu yana riƙe da zumunci kuma, zugar Hajiya da Rahma bata yi tasiri ba kuma dama bashushe ya ce hassada ga mai rabo taki ce. Zee ta karɓe shi hannu biyu shi kuma yana girmama ta duk da cewa ya girme ta amma kuma, tun da dai matar Daddy ce babu wani batun girmansa tun da idan ana dara fitar da uwa ake. Daddy ya kammala masa komai na tafiya, inda zai tafi China nan da kwana uku, murna kamar zai yi mai, ashe da rabon ya shiga jirgi. Ana jibi zai tafi ya je Ƙundu ya musu sallama, duk da a tsaitsaye ya yi saboda bai gama shiri ba, har ya je ya dawo basu haɗu da Sheik ba. Ranar laraba misalin ƙarfe biyu jirgin su ya tashi, Zee da Daddy ne suka raka shi airport yana ta farinciki saboda shi yana son karatu. *(A page 15 buk 1 zai ƙare mai buƙatar book 2 zai biya ɗari biyar* Haka rayuwa ta cigana da tafiya, Rahma tana fantamawar ta, sai samari take yi kala-kala ƴaƴan masu faɗa a ji, don ita ta ƙi jinin masu ƙaramin ƙarfi ƴaƴan malam shehu. A ɓangaren Daddy kuwa har yanzu yana ta cin karensa babu babbakaa, domin babu ranar da za ta zo ta faɗa bai kwana a gidan amarya ba, ita kuma Mummy da yake hotiho ce bata taɓa lura ba, saboda idan ta je ta hangame baki sai bacci bata taɓa sanin abin yake wakana ba. Sannan basu da masaniya a kan tafiyar Ma'aruf karatu su duk tunanin su yana can ƙauye, don Mummy takan ce Ma'aruf ana can ƙauye an kama sana'ar sayar da rake. Ranar wata juma'a ne Mummy tana kwance bayan ta dawo daga fitsari, bacci bai ɗauke ta ba, sai ta ji kamar alamar hayowa saman benen, shiru ta yi tana son gano cewa ko dai kunnen ta ne amma sai sai bata kawo komai ba tana dai kasa kunne tana jiran ta bambance, kamar daga sama haka ta ji, ƙaran buɗewar ƙofar ɗakin Daddy mamaki ne ya yi masauki a kwanyarta, zaune ta tashi, amma yau kawai sai ta ji tana son sanin mai ya saukar da shi ƙasa, don zuciyarta ma ta fara wasi-wasi wato shaiɗan ya fara mata biyar ko dai ɓangaren masu aiki yake zuwa, ba komai ya sa wanann zargin ya ɗarsu a zuciyarta ba sai furucin wata ƙawarta da ta ce mata ba a gane gaban namiji bare bayansa, haka ta faɗa mata bayan ta bata labarin cewa ba zai msta kishiya ba kuma shi mata ma basu ishe sa kallo ba. Da sanɗa ta sakko duk da tana masa zato mai kyau amma kuma dai tana son idan ta yi abin da za ta yi ɗin ta tarar da shi a kan gaskiya. Abin da ma ya sa ta fara wannan tunanin sai tunawa da ta yi da wannan ranar ma da kamar wannan lokacin ne ya dawo inda ya ce mata ƙasa ya sauka ya ji motsi, a nata ganin ai ba kunnen maciji ne da shi ba da za a ce wani ƙaramin motsi ya je kunnensa. Jinginuwa ta yi a window tana ɗan ɗaga labule a zuciyarta tana cewa. 'Idan ka ji ana cewa raka no in yi kashi to tabbas kashin ba gudawa ba ne' A daidai lokacin da ta ɗaga labule Daddy yana dab da shiga ɗakinsa, abin da ya ɗaure mata kai kuma shi ne yadda yake wani sanɗa yana waige-waige, alamomin rashin gaskiya dai sun bayyana ƙarara a yanayinsa. Gabanta ne yake faɗuwa, amma haka ta daure tana kallonsa har ya shige ɗakin, kuma a duhu bai kunna fitilar waya ba ko kuma fitilar ɗakin. To in har ba babu gaskiya a tare da shi ba mai ya sa zai yi hakan. Sai da ta bari ya ɗan jima da shiga sai ta buɗe tata ƙofar ta fito, Daddy da ya shagala da yin waya da Zee bai ma san Hajiya ta buɗe ƙofa ba don ba ya cikin nutsuwar da zai ji ƙaran ƙofar. Sai da ta zo za ta buɗe ƙofar ta ji dirin maganarsa sai dai bata ji mai yake cewa ba, mamaki take da wa za su yi waya a doshin asubar nan. Ƙofar ta murɗa, Daddy da yake waya ya danne wayar da sauri ta ɗauke, idanu ya rufe kamar mai baccin ƙarya. Fitilar ta kunna abin mamaki har da munshari yake saki, wanann ne dalilin da ya sa ya fara jefa masa ayar tambaya a ranta, tana tunanin wane irin sake ne wannan ta yi a cikin gidanta, sai yanzu ne ma take mamakin yadda Alhajin ba ya ƙulafucin ta zo ɗakin nasa wanda a da can baya ba sa ɗaukan wannan tsawon lokacin ba tare da sun kusanci juna ba, amma sai yanzu ta lura da ita da babu ma duk ɗaya, bata san cewa sabuwar fulawa ya samu yake ban ruwa ba. Yadda ya mata bariki ita ma barikin ta masa, gaban gadon ta ƙarasa ta ɗan buga ƙafarsa tana kiran sunansa, idanu ya buɗe dakyar yana wani ƙanƙance su irin na mai bacci, sai ta ji wani haushin sa ma tun da ta ga zai munafurce ta. Ɗan washe fuska ta yi tana masa murmushi take cewa ya tashi lokacin sallah ya yi, ko kunya haka ya tashi yana wani murtsuka idanu, duk da ta san ba a ma fara kiran sallar ba, amma dai dama ta zo ne don ta tababtar da baccin makaho, da a ce yana da gaskiya Daddy da ba zai yi baccin ƙarya ba, sai dai ta ci alwashin sai ta gano abin da yake sauka yi a ƙasa. Ɗakin ta ta juya ta koma shi kuma ya shiga banɗaki, yana suuke ajiyar zuciyar kuɓuta don shi a nashi tunanin ko ta ji yana waya ne, don bai taɓa kawo cewa ta ga shigowarsa ba, bare har ya yi tunanin ta ji yana waya ya san ma ba zai yiwu ta yi shiru ba. Bata sauya masa ba ko a fuska bata nuna masa ba, sai dai a ɗauki alƙawarin sai ta ƙurewa motarsa gudu. Sai da dare ya yi ta hau ƙawar ya kwana a ɗakinta amma firrr ya ƙi yana cewa shi katifar ɗakin ce ba ya so, da ta nuna cewa ko ɗakinsa za su je, sai ta ga ya ɗan basa da zancen, ita kuwa bata wani nuna masa ta damu ba ko kuma ta damu, sai kawai ta kwanta a nata ɗakin ya mata sallama ya fita ya rufo ƙofar. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, tana jiran ta ga abin da zai faru. Har ta fara ganin lafin kanta da kanta cewa ta zargi mijinta kamar daga sama ta ji an buɗe ƙofar ɗakinsa, bizigir ta miƙw zaune daga kwanciyar da take ba tare da ta shiryawa hakan ba. A hankali ta lallaɓo ta zo window sai gashi ya fita, tana nan tsaye ta ji ya buɗe ƙofar falon ƙasa, shi ma don idanun ta biyu shi ya sa ta ji kuma saboda ta kasa kunne. Gabanta ne ya tsananta bugu tana jin faɗuwar gaba don zuwa yanzu ta tabbatar da cewa wajen ƴan aiki yake zuwa, tun da dai babu abin da zai fitar da shi da dare, windown da ake hango harabar gidan ta zo ta leƙo sai kawai ta hangi Daddy ta cikin hasken farin wata yana ta sauri, kallonsa take hawaye cike a fuskarta don a halin da take yanzu gani take ko rantsuwa za ta yi cewa biyan buƙatarsa ce ta wajen ƴan aiki ta fita da shi. Sai dai akalar tunaninta ya sauya ne a lokacin da ta ga ya nufi ƙofar fita daga gidan ta baya, a sannan ne ƙirjint a ya shiga bugu da mugun ƙarfi,, ji ta yi hankalinta ya tashi, da sauri ta bar jikin labulen bayan ta ga fitarsa, a kiɗime ta juyo ta kunna fitilar ɗakin, haske ya gauraye ko ina, ƙaramar lokar jikin madubi ta janyo inda take ajiye mukullai, dakyar ta samu mukullin ƙofar fita daga bayan gidan, jikinta yana ta ƙyarma, saboda jikinta ya bata akwai wani gagarumin abin da yake faruwa. Ko ƙofar ɗakin bata rufe ba, haka ta fito fitilar wayarta a kunne, da matakala bibiyu take sauka daga saman benen, ƙofar falon ma a buɗe ta bari ko takalmi babu a ƙafarta, ita fatan ta ɗaya shi ne Allah sa dai ba wai fira yake da wata macen ba, shi ne ba ya zuwa sai dare ya tsala saboda gudun ɓacin ranta, amma wace mace ce za a ce tana fitowa daga gidansu a wannan daren, sai dai in mutuniyar banza ce, haka take ta saƙawa har ta zo wajen ƙofar, ganin ƙofar a kulle , zargin ta ya zama gaskiya, mukullin ta saka ta buɗe ƙofar sai dai bata da nutsuwar rufe ƙofar, amma sai ta laɓe ta leƙo, daga can ta hange shi tsaye da alama wani yake jira, tana hango shi tana jin tsanarsa a ranta, wato su iyalansa suna nan suna bacci shi kuma lokacin ne safiyarsa ta waye. Wani machine ne ya tsayar ya hau, suna fara tafiya sai ga wata mata a mota, nan Hajiya ta tsayar da ita ko tsoro ma bata ji, matar kasancewar ta likita kuma sama da gidan su Mummy take, ta fito ne za ta je karɓar haihuwar wata mata, haka ta ɗauki Mummy ganin kamar ba a hayyacinta take ba machine ɗin ta nuna mata a kan cewa ta bi bayansu, ganin sai kuka take tana mata bayanin abin da ya sa ta biyo bayan mijin nata. Ta tausayawa Mummyn, sun ɗan tsaya daga ɗan nesa ganin machine ɗin ya tsaya a ƙofar wani gida, Mummy ta mata godiya bayan an buɗewa Daddy ya shige ta fita daga motar ta ƙarasa a ƙafa. Ganin katangar bata da wani tsayi a ranta ta ce 'In ka ji kana ba za ka iya ba to bai same ka ba ne, ai ni yau sai na ga ƙwal uwar daka' Ta faɗa a zuciyarta tana komawa daga can bayan gidan ta kama katanga ta ɗare, haka ta ti dabara ta dira amma fargabar abin da za da tarar sai ya sanya bata ji buguwar da mazaunanta suka yi ba. Tashi ta yi ta yi saurin laɓewa ganin ana hasko fitila, sai da ta dakata mai gadin ne ya zo ya yi ɗan haske haske ya juya bai ganta ba, da alama bai fuskanci cewa gidan aka diro ba. Ƙofar falon ta lallaɓa ta tura a hankali jin ba a saka mukulli ba zuciyarta tana ta ayyana mata cewa "Namiji ba ɗan goyo ba ne, tun da ta yarda da mijinta ashe dai saka reshe kama ganye ta yi, sai dai ta ɗaukarwa kanta alƙawarin za a yi kan mai uwa da wabi, domin ta lura tsugunne bata ƙare ba amma sai ta nuna musu tun kafin a haifi uwar mai sabulu barbela take da farinta, tun shi Alhaji ganin hadarin nesa zai sa shi yin wanka da kashi, don ta lura wadatar biki ne tsarki da romo, tun da har ya iya zuwa wajen wata mace za ta nunawa matar cewa abincin wani gubar wani ne, don abin nasu aikin banza ne shafa lalle a ɗuwawu' Ɗan hasken da ka bari a falon wanda yake kawowa yana ɗaukewa hasken mai kalar blue, ganin falon shiru hakan ya bata tabbacin suna sama, saman ta hau tana jin cewa yau duk sai sun baƙunci lahira, a ɗaki na farko ta fara jin magana ƙasa -ƙasa muryar Zee ta ji tana cewa "Haba kai kuwa gaskiya yau ka makara baka fito da wuri ba, ka san dai ai bana iya bacci sai da kai, sai ka je ka tare a gidanka ni ka barni da kewa" Mummy ji ta yi kamar ta fasa ihu, Daddy ta ji ya ce "Haba ƴar lele ai komai nake hankalina yana kanki, kin sha gaban duk matan duniya ke kaɗai idanuna yake iya gani da kuma hange, haba amarya mai capacity, amarya kin fi quality, mu kwanta... Banko ƙofar da Mummy ta yi shi ya ankarar da su juyo, zumɓur Zee ta miƙe daga cinyar Daddy, a take idanun Mummy suka sauka a kan cikin wata huɗu na Zee wanda ya yi kufkuf a jikinta kamar ƙaramar ƙwarya... *BOOK 1 free shiga grp na BOOK 2 500, cmplt doc 800* *Acc no faiza abubakar 9030283375 opya shaidar biya 09025576222 gobe za mu gama book 1* *Yau ba samu leƙo inna amarya ba da kuma ango Sheik mai breast* 😂😂😂😂😂😂 *Sai gobe in muna raye* MAMAN AFRAH 09025576222 [7/17, 7:31 PM] Mom mashkur & Afrah: 👳🏻‍♂️ *MALAMIN BOGI*👳🏻‍♂️ NA MAMAN AFRAH First Class Writer's Asso.📝 Daga marubuciyar: Ƙazamin miji Bonono Rufin ƙofa... Ruɓaɓɓiyar igiya Ƴar zaman wanka Ƙara'in inna delu Beelal Ƴan adaidaita sahu Ungozoma Jalli joga Da sauran su. *09025576222* BOOK1️⃣ PAGE 15 *END OF BOOK 1 LAST FREE PAGE* *BOOK 2 500 naira pay in to faiza abubakar 9030283375 opay* IMZEEDVENTURE https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Duniyar kayan kitchen da na yara masu kyau da araha! Kina neman kayan kitchen masu kyau, luxury da adashe, ko kayan yara masu kyau da tsada ko gonjo mai kama da sabo? To shiga group ɗin IMZEEDVENTURE! Za ki sha mamaki! 🤩Muna da: ✅ Adashe na kayan kitchen ✅ Kayan yara sabbi da gonjo ✅ Kayan gyaran gida da na mata masu kyau 📞 Tuntuɓi mu: +234 707 753 2253 📩 DM: WhatsApp 📸 IG/Tiktok: @imzeed_ventureƊ *INNA TASALLAH* Cike da tsoro take kallon sabuwar addar hannun Jummai gabanta yana faɗuwa, ta ɗauka Sule jarumin maza ne zai yi iya yainsa don ganin ya dakatar da Jummai daga wannan barazana ta mummunan aikin da take so ta yi amma sai ta ga har lokacin yana dafe da mararsa yana ciccira idanu tamkar kwarton da aka kama a ɗakin amarya. Jummai kuwa babu alamar wasa ko kuma yin barazana a kalamanta ko yanayinta kana ganinta ka san iya gaskiyarta take faɗa iya abin da yake cikin ranta ne kuwa alwashin da take ci babu gudu babu ja da baya. Inna a zuciyarta ta ce 'Tabbas ƴan magana sun ce kifin fadama ba ya gasa da kifin kogi, amma wannan mata tana son kawo min cikas a ɗan amarcin da na ɗora rai zan dangwala, tana son shuka min salalan tsiya' ,A fili kuma sai ta ce "Haba Sule ka yi wani abu mana, kana dai jin abin da take faɗa tana neman kawo tsaiko a lamarin kasancewarmu tare, kuma sanin kanka ne Mai Gari ya kashe wannan maganar, kuma maganar ta mutu murus" ,Wani yawu Sule ya haɗiye ya lura Inna bata san abubuwan da sukw faruwa a duniya ba, shi da yake ma'abocin sauraren rediyo ne babu abin da bai sani ba saboda yana jin labaran yadda wasu matan suke yankewa maza mafitsara musamman a kan lamarin kishi, bare Jummai da haka nan ma tarar aradu da ka ne da ita bata barin ta kwana. Yana ɗan sakin murmushin yaƙe ya ce "Haba Tasleey ai kin san Jummai a kan gaskiyarta take, haƙiƙa saniya ba tawa ba ce ke ma kuma kin sani" Wani takaici ne ya rufe Jummai jin wai Sule yana kiran Inna da Tasleey wato ta lura maza basu da gaba basu da baya wato sawun keke ne su, amma in ba haka ba ita yake kiranta Jummai amma Inna daga tarewa har ya sauya mata Tasallah zuwa Tasleey. Inna kuma wani haushin Sule ne ya kamata tana ji kamar ta hau shi da duka, yana ji za a mata sagegeduwar amarcin amma babu wani kataɓus da ya yi, ita ba ma wannan ne tunanin ta ba yadda maƙociyar yarinyar nan ta bata ƙwaƙwalwar raƙumi ta yi amfani da shi gashi yanzu ana neman sakawa ta shiga uku. Inna ta ce "Ban gane a kan gaskiyarta ba?" Ido ya shiga ƙiftawa Inna yana mata alama da addar hannun Jummai, ita ma Inna hannunta riƙe da mazaunai ta ce "To shikenan saboda ta ɗauki adda sai a ƙi faɗar gaskiya, kana ji fa ta ce wai ni za ka bata in koma ɗakinta, ka taɓa jin wannan ɗanyen aiki ni fa tun da an ɗaura mana aure ni ɗin fa na zama mallakinka ita kuma tana a matsayin kishiyata ne, yanzu kawai sai in koma ɗakin kishiya?" Jummai ce jin har suna shawara, kenan suna ja da maganarta hakan ya sanya ta fara taku ta zo gaban gadon ta zauna ta miƙe ƙafa ranta a ɓace ita kuma adda sai walwali take, wannan ƙallin da addar take shi yake ruɗawa Sule ciki. Sule ganin haka ya ce "Tasleey maganin kar a yi kar a soma... A hargitse Jummai ta katse shi da faɗin "Wane suna ne wannan ɗin?" Da sauri ya gyara da faɗin "Tasallah a bar maganar nan Jummai iya gaskiyarta take faɗi" Inna saroro ta yi tana kallonsa ganin da gaske dai Jummai yake tsoro, duk da ita ma tana tsoron amma tana so ne ta yi yaƙi ta karɓi ƴancin ta. Inna ta ce "Jummai kin san dai na yi jika da ke, ni ba na son tashin tashina, tun da Allah ya yi na auri mijinki ki ɗau dangana, duk ranar da Ibra ya dawo da kuɗinki zan sa Sule ya warware igiyar" Kai Jummai ya ɗaga tana wani yatsina ta ce "Sule ya muke ciki ne? Ka ga yadda na kulle ɗaki daga ni sai ku, sannan ga sabuwar adda" Sule cike da zuga da kambamawa ya ce "Jummai ikon Allah, Jummai masallacin kura kike ba a ba kare limanci, ƙarfe duka ƙarfe ne amma a cikin ƙarfe akwai zinare da azurfa" Ya faɗa cike da kirari don ganin ya faranta mata ta janye batun ta, don shi yana tsoron mutuwa saboda bai shirya tafiya ba, kar a je ta guntule shi tsakiyar dare ya shiga uku. Inna jin ta yi sake reshe kama ganye, wato dai amarcin nan ba ciyuwa zai yi ba, sai kawai ta fashe da kukan takaici" Sule bai lallashe ta ba ko bata baki gudun kar ya yi laifi. Jummai ta sheƙe da dariya ta ce "Wato an ga samu an ga rashi, to ai sai ki tashi ki koma ɗakin mijinki, wato ni kenan ɗakin mijin ki Jummai" Cewar Jummai tana ƙara bushewa da dariya Kai Sule ya shiga gyaɗawa kamar ƙadangare, alamar eh, Inna ta kalli Jummai ta kalli sule wanda zuwa yanzu ya fara motsu-motsu da harhaɗa ƙafafu wanda ba komai ba ne ya haifar da hakan sai maganin da ya sha ne yake tambayarsa. Cike da sanyin murya ya ce "Tasleey au... Ya dakatar da maganar tunowa da ya yi Jummai ta yi magana ɗazu. Yana sauya akalar maganar ya ce "Tasallah ki tashi ku je ku kwanta" Wani haushinsa ne ya kama Inna tana ganin saboda tsabar shi saunan namiji ne kana da amarya amma ka ba mace saboda namijin hotiho ne shi. Jummai ta miƙe tsaye tana wata hamma, ta je saitin ƙofar ɗakin ta tsaya, ganin Inna bata taso ba, sai ta saka addae a jikin bango ta karta alamar wasawa ta yi, tsabar ruɗewa a kuɗime Sule ya miƙe bai san ya aka yi ba sai ganinsa ya yi a gaban Jummai, sai da ya ganshi a gabanta ya tuna cewa ashe ba shi ne za a tafi da shi ba. Inna kuma karta addar a bango sai ya sa ta miƙe tsaye har zani yana neman kwancewa ta gyara, Jummai ce ta ce "Sule ko har kai za a tafi ne?" Yana wayincewa ya ce "A haba da girman kujerarki ai da Tasallah ne za ku tafi" Ya faɗa ransa yana ƙuna gabansa kuma yana faɗuwa a lokaci guda, don shi duk abin da za a ce an haɗa da rai to tabbas ba ya son maganar mutuwa. Inna tana yin yaƙe ta ce "Eh da ni ce" Dariyar cin nasara Jummai ta saki a ranta tana saka hannu ta buɗe sakatar ta saka Inna a gaba suka nufi ɗakinta suna fita Sule ya yi zaman ƴan bori yana ambatob Lahaula wala quwwata. Kai ya dafe da hannu biyu a fili yana faɗin "Kin cuce ni Jummai, sai da na gama ɗora rai zan kwashi garaɓasa kika mini shigar sauri, yanzu a ce sai da na gama bankar magani abokaina suka gama zuzuta maini amarcin zan kwashi ganima amma ki zo ki min haka" Ya faɗa idanunsa suna masa jawur. Inna kuwa ɗakin Jumman suka shiga, warin fitsarin yaran ne ya ankarar da Inna cewa an shigo ɗakin ƙazama Jummai, don yaran sun isa su daina fitsarin kwance ma. Cike da umarni ta nunawa Inna gado, haka Inna ta hau gadon tana jin tsinkon da marar ta take mata. Amma babu yadda ta iya haka ta hau ta kwanta, tana tuno tsiren amarcin ta da kuma ruwan ledar da aka kawo mata na amarci. Jummai wuri ta samu ta ajiye addar ta hau gefen Inna ta kwanta, sai yanzu Jummai ta ji sauƙin zafin ranta da yake mata raɗaɗi tun lokacin da aka ɗaurawa Inna auren, ga kishi ga rashin saniya, yanzu kuma tun da Inna ta dawo ƙarƙashin ta sai take ji daidai yake da saniyarta ce a kusa. Sule a nan tsakar ɗakin ya yada zango, don ko gadon ƙarfen Inna bai samu hawa ba, haka nan tsire ma bai samu shiga ba saboda yanzu amaryarsa kawai yake buƙata amma babu hali, don da alama Jummai da gaske take ba za ta bar Inna a ɗakinsa ta kwana ba, tun daɗewa yake jiran dawowar Inna ya ɗauka Jumman za ta barta ta zo amma dai har har yanzu shiru, kamar maye ya ci shirwa ba amo ba labari, tun da dai babu niyya ango ya kwana da wando. Har dare ya tsala yana nan tsakar ɗakin yana murƙususu, ganin dai abin ba zai masa ba, tashi ya yi ya lalaɓo ya fito yana sanɗa ya nufi ɗakin Jummai, tun kafin ya ƙaraso yake jin tashin munsharin Jummai, da na yaran da suke kwance a tsakar ɗakin. Da yake akwai fitilar ƙwai irin ta mutanen da, an barta a kunne amma kuma an rage hasken. Inna wacce ita ma baccin ta kasa tana ta juye-juye, a kan idanunta Sule ya shigo ɗakin, ai kuwa ta ɗan ɗago kai yake mata zancen kurma da hannu yana tambayarta ina adda, da hannu ta nuna masa inda ta ga Jummai ta ajiye, lallaɓawa ya yi ya ɗakko ya tura ƙasan gadon, gaban gadon ya ƙarasa ya juya bayansa Inna da sauri ta tashi ta ɗare bayan Sule ya goya ta, cike da zumuɗi suka baro ɗakin Jummai ransu fari ƙal. Ashe tun shigowar Sule Jummai ta falka tana kallonsa munsharin ƙarya take, kawai ta bari ta ga gudun ruwansa, suna fita ta sakko daga gadon ta ɗauki addarta, ta fito ta bi bayansu Sule yana shiga ɗakin ya garƙama sakata, sai kuwa ga Jummai ta sake dawowa, amma kasancewar a rufe sai ta kasa shiga, ta window take musu magana tare da cin alwashin muddin Sule ya kusanci Inna sai ta ɓalla ƙofar ta zo ta musu aika -aika. Tsabar tsoro sai Sule ya kasa komai, tun da tana tsaye ma Jumman tana kallon su, haka ya zauna a ƙasa yana kifa wani uban tagumi, don shi ya ga mace a ɓagas yana ganin ya tsinci dami a kale, babu sadaki babu kuɗin aure ko biyar bai kashe ba. Inna tana zaune ta miƙe ƙafa tana jin kamar ta shaƙe jummai, a haka suka kwana babu wanda ya runtsa a cikin su. Da asuba haka Inna ta yi alwala sai da ta ɓata buta guda a wajen tsarki saboda ni'imar da ƙwaƙwalwar raƙumin nan ta sanya mata a zuciyarta ta ce 'Wannan yarinya Jummai an yi ƴar kan uwa, da bata kasa ta tsare ba jiya Allah kaɗai ya san ganimar da za mu kwasa, amma don asara kalli yadda nake wanke ni'imar a banza tana bin makwararar banɗaki' Haka ta yi sallah ranta duk ba daɗi shi dama tun da ya tafi masallacin ma bata ganshi ba, ita kuma Jummai sai da ya fita sannan ta bar ƙofar ɗakin, amma Inna a ranta ta ci alwashin yau sai ta kai ƙara wajen alwalin ta wato Mai Gari. Haka kowa ya kama sabgar gabansa, Duduwa kishiyar Jummai ce ta yi ɗumame ta kaiwa Inna,, haka yaran Jummai suka tare a ɗakin Inna suna ta murna Inna mai kayan miya ta zama amaryar babansu, haka ta ɗauki tsiran nan ta raba musu. Jummai kuwa wata kaza ta kama aka yanka ta gyara ta dafa, ta juye a kwano ta bayar aka kaiwa Mai Gari ba tare sa kowa ya san wanda aka kaiwa ba. Dama ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya ta san dole ta amsa kiran Mai Gari yau, shi ya sa ta yi riga malam masallaci, ta dafa kaza ta aika masa saboda toshiyar baki da kuma cikar burinta. Wajen ƙarfe goma aka aiko kiran Jummai daga fadar Mai Gari, haka ta tarar da Inna da Sule a can, bayan ta zauna Mai Gari ya kalli Inna ya ce "Tasallah wai lafiya kike ta tagumi kina cika kina batsewa?" A ƙufule ta ce "Haba Mai Gari ya kake so in yi to? Ko baka ji a akan abin da muke ƙaran Jummai ba" Mai Gari ya ce "Na sani mana" Inna ta ɗora da faɗin "To wannan ne dai ai ka ji kan maganar, amarcu dai daren jiya bai ciyu ba" Ta faɗa tana gallawa Jummai harara. Amma buɗar bakin Mai Gari sai ya ce "To ai Jummai ta fiku gaskiya" Sule da Inna suka kalli juna suka kalli Mai Gari, Jummai ta saki wani murmushi, don ta san tabbas Mai Gari ya ji daɗin dahuwar kalwar da ta yi masa wacce ta sha farin maggi. Nan ya shiga faɗin dole a bi abin da Jummai ta ce har zuwa dawowar Ibra wannan shi ne adalci. Kowa ya ji ba a kyauta amma amma mai gari in ya tuna dabgen kazar da ya ci da sanyin safiyar nan sai ya ji ba zai iya musawa Jummai ba An yanke hukunci a kan Inna ta zauna a ɗakin Jummai takaici kamar ya kashe Sule, Inna kuwa ba a magana, haka aka tashi daga fada kowa yana jimami ban da Jummai da ta san amasar tambayar. Tsawon kwana biyar Inna tana kwana a ɗakin Jummai, saboda yanzu an kasa kwana ma tsakanin Duduwa da Jummai amma ban da Inna Tasallah. Yau da ya kama alhamis tun da yamma Jummai take gyare gyare sannan kuma Inna tana lura da magungunan mata da take sha, sai dai kuma ta san yau bakin Duduwa ne ba na Jummai ba. Abin da ya ba Inna mamaki yau yaran ba a ɗakin za su kwana ba, tun da wurin ta musu shimfiɗa a wani ɗaki da ake ajiye tarkace ta gyara musu tas. Tsakanin Inna da Sule sai gani daga nesa Jummai ta kasa ta tsare duk da Inna ta ci wani alwashi da zai rusa duk wani shirin Jummai, saboda tana ta ayyana yadda za ta zamewa Jummai ƙadangaren bakin tulu. Haka ta ga an gyara ɗakin, gadon ta hau ta kwanta, ita ma Jummai ta hau. Tsakiyar dare Inna tana bacci sai ta ji an dafa mata kafaɗa ranta fari ƙal ta buɗe idanu tunanin ta ko Sule ne, amma abin mamaki sai ta ji Jummai ce, Jummai ta ce "Inna tashi matata" Idanu Inna ta zaro tana tunanin ko ta yi makuwa ne amma saj ta ji da gaske take, cike da mamaki ta ce "Mai kike cewa Jummai?" Jummai ta ce "Tashi za ki yi ki biya ni sadakina" Inna ta ce "Na ce miki sai Ibra ya za a biya ki" " Jummai ta ce "Ai kin san a birni an ce akwai abin da ake yi mace tana auran mace to nima yanzu kin zama matata, don haka dole ki bani haƙƙina" Ta faɗa tana farwar zanin Inna, sai ga zanin Inna an warɓar gefe sai ɗan tofin ta(Skirt ɗin ciki) A take Inna ta tuna da ana cewa ana lalata mace da mace in bata manta ba an ce hakan yana faruwa a gaske to yaushe Jummai ta zama a haka ba a sami ba, a take Inna ta hau ihu tana cewa ",Ihu kwartuwa, Sule taho ka ga marar imanin nan za ta mini fyaɗe... *MUMMY* Babu wanda zai gane ko ya iya fasalta yadda tanji wani abu ya caki ƙahon zuciyarta, jikinta ne ya hau karkarwa a lokacin da ta yi wa idanunta masauki a kan fuskar yarinya, ko daga bacci ta tashi tabbas ba za ta kasa shaida Zainab Zee ba ƙawar ƴarta. Hannu ta saka ta dafe bango ɗaya hannun tana nuna su da yatsa. Duk rikicewar Hajiya Daddy ya fi ta rikicewa saboda shi ji ya yi wani irin tsoro da fargaba a masa dirar mikiya, bai taɓa zato ko mafarkin wannan rana ba, kenan duk wannan sirrin da yake binnewa ya aka yi Hajiya ta sani. Mummy kanta ne ya shiga juyawa, a take ta yanke jiki yaraf ta zube a ƙasa, Alhaji ne ya yi kanta yana kiran sunanta, ita kuma Zee ganin yadda duk ya birkice sai take ganin kamar ya fi son matarsa a kanta ita a nata ganin tun da ba zaman dadiro ne suke yi ba, ai ba komai ba ne don Mummyn ta sani, ita a ranta ma daɗi ta ji doin za ta saki jiki ta yi rayuwarta son ranta, duk da ta san dai yanzu tun da Hajiya ta sani da wuya ta ci gaba da samun Daddy a ɓagas kamar a baya da kullum ma yake mallakin ta, babu ranar bakin ta babu na Hajiya. Haka ya kira mai gadi ya fito da mota shi kuma ya kinkimo Hajiya ya saka a motar Zee kuma ganin yana rawar ƙafa kawai sai ta ce ita banu inda za ta je. Asibiti ya kai Hajiyar inda aka shiga bata taimakon gaggawa. Bata farfaɗo ba sai wajen asuba, ta falko da kiran sunan Rahma, Daddy yana riƙe da hannun ta ko da ta kalle shi sai abin da ya wakana jiya ya dawo mata a take ta warce hannunta tana fashewa da kuka. Misalin ƙarfe bakwai aka sallame su, amma Hajiya ta ƙi shiga motar ta hau napep duk da cewa Daddyn yana tabbayar mata cewa ba fasiƙanci yake yi ba matarsa ce ta sunna. A ganinta ya ci amanar ta tun da ya yi aure matar har da ciki. Daddy yana bin bayan napep ɗin da take ciki har suka je gida, ko parking bai gama ba ya kashe motar ya fito shi ya sallami mai napep ɗin ma ta hanyar masa transper tun da bai fita da kuɗi ba. Yana shiga falon ya haura sama kasancewar bai ganta a ƙasa ba, zaune ya tarar da ita a ɗakinta a bakin gado tana ta faman rasgar kuka Rahma tana bata haƙuri, duk da Mummy ta mata bayani amma ta ji haushin Daddy da kuma Zee da ta auri ubanta. Daddy yana shigowa Rahma wani takaici ya cika mata zuciyarta, a take ta yi ƙunci, fita ta yi daga ɗakin ta shiga ɗakinta ta kwanta a kan gado ta fashe da kuka, tunanin ta ɗaya yadda mahaifinta ya auri ƙawarta yanzu abin da ya tsaye mata a rai wai har Zee tana ɗauke da cikin mahaifin nata kenan Zee ta ga Daddyn ta babu kaya a jikin sa har wani abu yana shiga tsakani. Mummy kuwa ko sauraren sa bata yi ba ta ce ya fita mata a ɗaki, haka ya fita yana tunanin gwara ya bari idan ta huce ya yi aikin lallashin. Rahma ta kasa jurewa, wajen sha biyun rana da ya fita ta je ta cewa Mummy za ta tafi Ƙundu ta je ta faɗawa Mai Gari halin da ake ciki, don ita abin ya mata ciwo tamkar dai wanda aka ce Daddy babu aure ya yi wa Zee ɗin cikin. Tana fita Mummy ma ta rufe ƙofar ta kwanta ranta yana ƙuna tana tunanin mafita da kuma yanda za ta yanke shawara. Rahma mota ta ɗauka ta saka jakarta a ciki, direba ta sa ya tuƙa ta suka doshi garin na Ƙundi wanda rabon ta da ƙauyen har ta manta kuma ta san dai Mai Gari yayan Daddy ne kaɗai yake iya sanya Daddy ya yi ko ya hana shi. *SHEIK* Cike da tashin hankali Sheik ya yi cilli da bulalar hannun sa, yana kai hannu biyu ya taɓa ƙirjin yana faɗin "Innalillahi, na shiga uku ya zan yi?" Ya faɗa a hankali yana kallon amaryar tasa da ta zube a ƙasa kamar wacce ta suma. Mai Gari da ya ji Sheik yana cewa su maido da nonon da suka ɗauka, kuma dai sai ya ji Sheik ɗin ya yi shiru wannan dalilin ne ya sa murna ta cika Mai Gari don a tunaninsa Sheik ya sa aljannu sun maido da nonon amaryar, baki ya buɗe yana cewa mahaifiyar yarinyar "Kin ga abin da nake faɗa miki ko? Ai balaraben malami mashayar ɗa ba ko mutum sukutum aka ɗauka sai Sheik ya dawo da shi bare wani nono ai abu mai sauƙi ne fitar da wando ta ka" Ya faɗa yana dariya mai sauti, duk matan tsakar gidan a kunnen su aka yi wannan magana, a take aka fara ƙusƙus kowacce tana cin alwashin ta samu wajen zuwa neman maganin damuwarta. Mahaifiyar amarya ta washe baki tana jin daɗin sa'ar sirikin da zai zama silar warakar ƴar tata. Duk maganar nan da ake a kunnen Sheik da ya jiƙe jagaf sa gumi ƙirji da tudun breast. Maganar Mai Gari ce ta katse shi da faɗin "Ya Sheik sun maido ko?" Sheik yana kallon ƙirjin sa ya buɗe baki dakyar ya ce "Ina ta fafatawa dai da su suna gab da maidowa" Ya faɗa yana hawaye da jin da na sanin wannan maluntar BOGIN Ya cigaba da karanta qulhuwallahu wacce ita kaɗai yake iya tunawa zuwa yanzu, yana tofawa amaryar don yanzu bashi da ƙarfin dukanta ma. Yana yi sai ya ga ƙirinta ya fara tasowa kamar almara sai ga tudun ƙirjinta ya dawo, a rikice ya kalli nasa ƙirjin ganin bai ɓace ba kuma dai natan ya dawo das dashi. Da sauri ya tsugunna yana yin ƙasa da murya ya ce "Haba aljannu kar mu yi haka da ku, ni na yafe nonuwan nan domin Allah ku raba ni da shi" Amma atishawar amaryar tasa ce ta tabbatar masa da cewa aljannun sun sake ta. Ƙuri ta masa da idon ta ɗaya tana washe baki, fuska ya tamke yana ganin duk ita ce silar shigarsa matsalar da yake ciki. A wayince ya shiga kare ƙirjinsa gudun kar ta gani, ya janyo hiraminsa ya yafa a kafaɗa yana dibara wajen kare ƙirjinsa. Magana take masa yana amsawa a daƙile, ya buɗe ƙofar ya fito ta biyu bayansa tana tafiya dakyar alamar ƙarfin jikinta bai dawo ba, mahaifiyarta ta rungume ta cike da murna, kowa na wajen ya zo ana kallon yadda Sheik ya sa aljannun suma maido mata da nonon ta, sai dai babu wanda ya lura da ƙirjin Sheik bare a ha ajiyar da aljannun suka masa. Mahaifiyarta tana ta masa godiya, tana cewa yanzu ai za a kawo masa ita gidan, amma buɗar bakinsa sai ya ce aljannun sun ce ba yau za ta tare ba idan ta tare yau za su haifar da gagarumar matsala a garin. Jin haka sai Mai Gari ya ce a dakata da tarewar yau, shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda rufuwar asirin sa, don ya san matsawar aka kai amarya to tabbas ita ce za ta fara tona masa asirin ajiyar da aljannu suka masa a ƙirji, bare kuma shi da rayuwarsa gabaɗaya sirri ce yana sana'arsa ta MALAMIN BOGI. Daga nan masallaci suka wuce ya ja su sallar isha'i basu lura da yadda yake ta kare-karen ƙirji ba. Ana gama sallah ya ce zuwa zai yi ya kwana yana lazumi saboda matsalar garin, amma ya faɗa ne kawai don yanzu tashin hankalinsa bai wuce ƙirjinsa ba, so yake ya ce ya ga ta yadda zai yi da breast ɗin ƙirjinsa. Bayan ya je gidan ko ta kan abincin da aka kawo bai yi ba, ɗakin ya bankawa sakata, ya yi saurin cire hirami ya jefar ya kama riga ya cire. A razane yake kallon ƙirjin nasa ganin wani baƙiƙƙirin ɗin breast ne, musamman da suka haɗu da farar fatarsa da ta sha bilicin, sai baƙin su suka ƙaru, kamar a jikinsa suke tun asali haka suka yi, ya rasa ma ya zai yi da su. Ya fara tunanin mafita cewar yake yafa hiraminsa a wuya yana dabara yadda zai ke ɓoyewa ba tare da kowa ya gani ba, har zuwa lokacin da Allah zai yanke masa wahala, don shi bai taɓa jin an ce namiji yana da breast ba in har ba mata maza ba. Ya san mata maza ne suke da breast sannan suna da HQ da kuma mazantakar namiji a jikin su, amma dai bai taɓa jinw wanda shi ba mata maza ba kuma aljannu su fito masa da breast rana tsaka tashin hankalin ya yi yawa. Haka ya kwana ranar da zulumi sai bacci ɓarawo ne yake ɗauke shi. Washe gari aka kawo masa wata mata ƴarnuwar Mai Gari an ce masa bazawara ce sakin wawa, an kawo ta ne a mata magani saboda tun da suka rabu da mijin har yau ta rasa mashinshi ni, shi ne ake tunanin ko mijinta na farko ne ya mata asiri. Sheik tun da ya ƙyalla idanu a kanta ya ji yawunsa ya tsinke, sannan a ransa yana tunanin ina ma a ce wannan ce aka ɗaura masa aure da ita ba waccan mai ido ɗayan ba, yanzu kuma da kunya matsayinsa na balarabe ya ce ya ga baƙar fata yana so, domin ita ma farar bafulatana ce gashi har kafaɗa ga shi tana da cikar halitta wacce ita ce ta sanya Sheik ya rasa nutsuwarsa don sai ya ji ko fatar jikinta ne yana so ya taɓa. Saboda wannan dalilin na ba ya son ya daina kallon ta ya ce maganin na kaana uku za a yi, sai wanda suka kawo ta suka koma garinsu ita aka barta a gidan Mai Gari a kan cewa idan an gama maganin ta koma. Da yamma motar su Rahma ta yi wa garin Ƙundu dirar mikiya, a ƙofar gidan Mai Gari motar ta tsaya, tun kafin ta fito ta hangi Sheik yana tsaye da wasu mutane, gabanta ne ya yanke ya faɗi ganin wani balarabe fari tasss da shi yana sanye da baƙar jallabiya ga gashin kansa kwance lufff kamar na jarirai. Sajensa da ya ƙara ƙawata fuskarsa shi ne abin da ya ja hankalin ta cikin sauƙi, gemunsa da ya tashi ziyat a habar shi kaɗai ma abin kallo ne. Ta shagala da kallon Sheik bata san lokacin da ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ba. Sheik bai ganta ba saboda hankalinsa ba a wajen motar ma yake ba, dakyar ta samu ƙwarin gwiwar fitowa daga motar. Abin yana bata mamaki ya aka yi aka samu balarabe a wannan kwaraɓaɓɓan ƙauyen, ko ita da take bahaushiya ba don wannan damuwar da suke ciki ita da Mummyn ta ba, babu abin da za ta shigo ƙauyen nan ta yi. Direban ne ya bita da akwatin kayanta wanda ta ɗakko kala uku da kuma su madara kwanfiles da sauran abubuwan buƙata saboda ba za ta iya cin cimar garin ba, kuma dai a yadda ta yi fushi da Daddy tana so ta ɗan nesanta kanta da shi, sannan sai ya zo har garin an magance matsalar wannan dalilin ne ya sa ta taho da kaya. Mai Gari ganin Rahma ya cika da murna, har ya kasa zaune da tsaye ganin ƴar ɗan uwansa da ya fi ƙauna. Mutane suna ta mata sannu amma ko kallo basu ishe ta ba, tana ta waiwayen inda za ta ƙara ganin balaraben nan amma bata ga inda ya yi ba. Direban komawa ya yi a cewarta za ta masa waya ya zo ya ɗauke ta, in buƙatar hakan ta taso. Da suka yi sallar isha'i Sheik yake cewa Mai Gari ya fara sha'awar saka kayan hausawa babbar riga da ƴar ciki, Mai Gari ya yi mamaki ganin dai Sheik bai saba da saka kaya in ba na larabawa ba, amma ganin ya ce tana so sai ya ce za a siyo shaddodi da yadika masu tsada a ɗinka masa. Shi kuma Sheik ya yi hakan ne saboda ya fara ɓoye breast ɗin ƙirjinsa, sannan yana so idan ya je wajen malamin da yake karɓo magunguna ya bashi kuɗi a siyo masa bireziya saboda ya fara suturta ƙirjinsa tun da yana ganin bra ɗin za ta sanya ba za a lura da tudun ba kuma musamman idan ya saka kayan hausawa da babbar riga. Rahma ta faɗawa Mai Gari gabaɗaya damuwar da ta kawo ta, Mai Gari dama ya san cewa ɗan uwan nasa ya yi aure amma kuma bai san cewa bai sanar da iyalinsa ba, don haka sai ya nunawa Rahma zai kira shi ya masa magana za a san abin yi a hukunta Daddy, ta ji daɗin furucin shi ma kuma ya mata hakan ne don ta fita daga damuwa. A nan take tambayarsa labarin wani balarabe da ta hanga lokacin da ta iso, Mai Gari ya kwashe komai ya faɗa mata, dangane da Sheik a take ta ji ta kamu da muguwar ƙaunarsa, kuma in dai shi ne ta amince ko a cikin kara ne tw zauna ba wai a ƙauye ba. Ta sa a ranta idan Daddy ya zo garin nan ba za su tafi ba sai ta mallaki Sheik a matsayin miji, dole Daddy ya gina musu gida mai kyau inda za su rayu, ta haifi ƴaƴan larabawa, idan kuma Sheik ɗin yana so sai su tafi Abuja su rayu a can amma dai bata da mijin sai balarabe daga ƙasar Yemen. Bata faɗawa Mai Gari ba ta dai bar maganar a zuciyarta zuwa safiya. Haka ta kwanta cike da shauƙi da ƙaunar Sheik tana fatan ya zo mata a mafarki. *DARE* Darebya tsala, kowa yana bacci sai dai Sheik sa tun da ya ga baƙuwar nan ya kasa sukuni, idanunsa yanzu ma sun hana shi ya runtsa saboda ya sanya tunanin ta a ransa kawai burinsa ya ji matar nan a kusa da shi. Juyi ya yi yana jon tunanin da ya saka a ransa ya hana shi sukuni. A take ya yanke shawara, tsaye ya tashi ya ɗako wani zani da hijabi cikin kayan da yake tsinta idan aka zo aka taru ana karɓar magani, sai a ga hijabi wani lokacin a rasa mai shi ko ɗankwali ko hula ta mata ko zani. Zanin ya ɗaura ya saka hijabin, yana jin cewa yau ko ta halin ƙaƙa sai ya je ya ji ɗumin jikin baƙuwar nan, shaiɗan yana ta zuga shi yana masa linzami. A zuciyarsa ya ce "Ai na lura tana cikin buƙatar kulawa da soyayya, kuma ai ba za ta gane waye ba, buƙatar maje hajji sallah" Ya faɗa yana fitowa waje, yana duba gabas da yamma arewa da kudu ya ga babu kowa sai kukan karnuka kawai. Katangar Mai Gari ya kama ya ɗare, da yake bata da tsawo ya sauka a hankali, yana lashe baki ya shiga ƙarewa ɗakunan gidan kallo yana so ya gano inda zai samu baƙuwar, ko dogon tunani ba ya yi ya fi so kawai ya ganshi a ɗakin. Ɗakin matar Mai Gari ya fara leƙawa amma jin ana sakin munshari kamar an shaƙe raƙumi sai ya zaci ɗakin Mai Gari ne a tunaninsa Mai Garin ne yake munsharin. Wani ɗaki ya shiga yana ji a jikinsa tabbas a nan masoyiyar tasa take, da sanɗa ya ƙarasa ya haye katifar ganin ta lulluɓe ruf da bargo shi na ya bankaɗa ya yi wa kansa masauki a ciki. A hankali ya lallaɓa ya rungumo na bargon, a zuciyarsa yana cewa 'Alhamdulillahi, ƴar fara zo ki ji lallausar fatar balarabe' Bai tsaya a nan ba ya kai baki zai kamo bakin, amma cikin rashin sa'a sai ya cafko hancin, ya manta ma da ƙirjinsa da aljannu suka masa ajiya, jin an cafki hancinsa sai hakan ya hana na cikin bargon shaƙar numfashi da kyau, yana riƙe da hancin a bakinsa yana sauke numfashin cin nasara da cikar burin sa. Fisge-fisge na cikin bargon ya fara, yana son ƙwacewa amma Sheik ya ƙara zage ƙarfinsa ya maƙalƙale. Cikin hargitsi aka ce "Kai wai waye a nan ne, wane shegen ne ya shigo mini bargon yana lasar mini hanci kamar tsohon maye?" Sheik a zuciyarsa ya ce 'La'ilaha ilallahu ba baƙuwa ba ce Mai Gari ne ai!" Gaban Sheik ne ya doka da ƙarfi ya fara janyo salati a zuciyarsa da fatan Allah kuɓutar da shi, a take ya fara ƙoƙarin ficewa daga cikin bargon, Mai Gari jin haka sai ya kai hannu ya riƙo shi, tunanin Mai Gari rigar mutumin ce ya riƙo ashe hijbin ne ya riƙe saitin fuskar, Sheik ya rasa ta ina zai fito da kan nasa ma domin Mai Gari ya cukwikuye, yana faɗin "Wane kwarton ne wai, wato an ga na yi baƙuwa daga birni" *A NAN NA KAWO ƘARSHEN BOOK 1 MAI SON SHIGA GROUP YA ƘARANTA ZAO BIYA 500, MAI SON CMPLT DOCMENT 800* IDAN KINA SON JIN YA ZA TA KAYA KI BIYA KI KARANTA A NUTSE *MAMAN AFRAH 09025576222* *ZA A BIYA TA FAIZA ABUBAKAR 9030283375 OPAY SHAIDAR BIYA TA 09025576222*