61&62 Wani irin kallo take masa. bakinta na rawa magana ta take so tayi amma tsabar tashin hankali! da mamakin al'amarin ya sa bakinta yin nauyi, ta gagara furta komai sai kallonshi take tana ayyana abubuwa da yawa a kansa, gaskiyar magana yau ne ta tabbatar da cewa yana da matsalar kwakwalwa, kamar yanda jama'a suke zarginsa, idan ba mara hankali da tunani ba waye zai d'auki matar auransa ta sunnah ya mi'ka ga wani 'kato, tabbas basu da hankali! gabadaya har maigidan nasa dukkaninsu suna bukatar ganin likitan k'wak'walwa! ita kam ba zata yarda da wannan yahudancin ba, tana ganin duk abinda zai faru sai da ya faru, ba zata amince da wannan manufar ba. To bayan tafiyarsa sai ta kasance cikin damuwa da tunanin hanyar da zata bi gurin ganin ta warware matsalarta, gaskiyar lamari barin gidan shine samun nutsuwarta, ashe dama wannan matsalar Baba Asabe ke hango mata, gashi kuwa tun ba a je ko'ina ba al'amura sun jagwalgwale. Ita kanta Hajiya Saude kwana biyu ta kasa gane me yake damunta, domin ko ta je gurinta ba ta iya sakin jikinta, suna gaisawa take tafiya domin ba ta yarda ta zauna maigidan ya same ta, gabad'aya ta sanja taku a gidan, da wurwuri take kukkule ko'ina na sashenta, sai ta shige can uwar daki ta kulle kanta, duk a kokarinta na tsaretar da rayuwarta. Sai dai duk yunkurin da za tayi masu tsaron gidan idonsu a kanta, domin zuwa yanzu sun santa a gidan, amma ba su san matsayinta ba. Sai ta sanja shawara da kuma shirya yanda za tayi ta gudu daga gidan. Ranar Juma'a ita ce ranar da gidan ke cika da jama'a maza da mata domin a ranar ne maigidan ke raba kud'i ga mabukata. To tana ganin za tayi basaja ne kawai ta shiga cikin jama'ar a matsayin mai neman taimako. Gidan ya cika sosai da jama'a gabad'aya masu tsaron gidan suna can suna shirya mutane domin su daidaita layi kafin ya fito, wannan ya bata damar shiga jerin matan da suke ja dogon layin da ba zai 'kirgu ba. Sule ya fito ya sanar musu da cewa; saboda yamma tayi kuma dab ake da a kira sallar magariba su yi hakuri sai anyi sallah tukkuna maigidan zai fito. Babu wanda ya nuna damuwarsa da hakan, kowa dai burinsa ya samu abinda zai sa a aljihunsa. Fitowarsa ta hango sai tayi saurin sunkuyar da kanta. tana addua Allah yasa kada ya gane ta. Jama'a su ka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa, ya amsa daidai gwargwado kafin ya wuce zuwa massalacinsa dake jikin gidan, wasu suka bi bayansa wasu kuma suka gabatar da sallarsu a cikin gidan mussaman mata tunda akwai manya manyan rumfuna dake shimfide da kafet da tabarmi. Kan wata kujera ya zaune a nutse ya fara gudanar da abinda ya tarasu a gurin. Duk wanda aka bawa zai yi godiya ya kama hanya ya fita cikin farin ciki da annashuwa. Layi yana ta tafiya har aka zo kanta, kallo daya yayi mata ya gane ko wacece a gabansa, mamaki sosai ya kamashi, sai ya tsira mata idonsa kamar koda yaushe, ita kuma sai jikinta ta daburce! da sauri ta dauke kanta tana sake gyara zaman hijab din da ya rufe mata fuska sai 'kwayar idonta kawai ake gani. Sannu take mik'a masa tana risinawa wai ya bata kudin. bai yi 'kasa a gwiwa ba ya bata domin ganin abinda take shirin aikatawa domin ya tabbatar da zarginsa. aikuwa tana kar'ba hanyar fita ta nufa da saurin gaske. Da azama ya juya in da escort d'inshi biyu ke tsaye a kansa. Duka suka sunkuyo domin jin umarninsa. Da sauri wanda yake hannun damarsa ya nufi bakin gate wanda a lokacin har tasa kafarta a waje za ta fita, aka dakatar da ita. Gabanta ya buga da karfin gaske! shikkenan ta faru ta kare. Jami'in tsaron ya nuna mata bindiga kafin ya bata umarnin komawa ciki da hannunsa. Da sauri ta bi umarninsa ta koma ciki domin ba ta so hankalin jama'a ya dawo kansu, dama yanayin kallon yayi mata tasha jinin jikinta cewa ya sheda ta. Ganin masu tsaro gidan da masu gadin hankalin su ya karkata wani guri da sauri ta kama hanyar sashenta tana ta addua a cikinta. Rurrufe ko'ina tayi ta zube kan kujera! sai kawai kuka ya 'kwace mata, wannan masifa dame ta yi kama? shikkenan haka za tayi ta zama cikin fargaba da damuwa, wai shin ya za tayi ne da rayuwarta. Abokiyar shawararta wato zuciyarta ita ce ta tunasar da ita cewa dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma Allah yana nan saboda haka ta nemi sauki a gurinsa. Don haka sai ta ji k'warin gwiwa! lallai wannan shawarar ita ce abin yi. Alwala tayi ta gabatar da nafila raka'a biyu sannan ta daga hannunta tana zubar da hawaye take rokon Allah ya kawo mata sassauci a rayuwarta, Allah ya zaba mata abinda ya fi alheri. Da safe ta tashi sakayau! lallai ta yarda al'kur'ani yana maganin kowace irin masifa, kuma dukkan wanda ya shiga damuwa ya mika lamuransa ga Allah zai isar masa. Kwana d'aya biyu babu wani lamari na tashin hankali da ya biyo baya duk da cewa sun had'u amma bai yi mata komai ba ballantana ya tuhume ta akan matakin guduwa da ta d'auka! Ranar litinin da sassafe Hajiya ta je asibiti domin a duba lafiyarta, tare da Shukura su ka tafi domin daga Asibitin za su wuce wata unguwa. Da k'warin gwiwarta ta shiga da sallama a bakinta. Sai dai ganinsa a hakimce! a kan kujera ya tsoratar da ita, da sauri ta juya da nufin fita. Ya dakatar da ita babu yabo babu fallasa ya ce." Ya zaki juya kuma ko ba gaida Hajiya ki ka zo ba?" Kanta kawai ta iya daga masa alamun "Eh hakane" Ya bata umarnin zama da fadin." Zo ki zauna yanzu za ta fito.'' kallonsa tayi amma bata yarda da maganarsa ba domin a irin wannan lokacin take samun hajiyan a zaune a falo a duk sanda ta zo gaishe ta. Ya ce." Matsalata dake gardama zo ki zauna na ce." Yafada yana nuna mata saman kujera. A jiyar zuciya ta sauke a tsarge ta je ta zauna kasan k'afafunsa domin babu yanda za a yi ta zauna kan kujera bayan yana kai. K'amshinsa ne duk ya cika mata hanci! jikinta yayi la'asar, a duk sanda za ta ji 'kamshin jikinsa sai ta rasa gane abinda yake damunta, ita dai 'kamshin yana mata dad'i Tsaye ya mi'ke tayi saurin kallonsa sai ta ga ya nufi hanyar fita, ta sauke sanyayyar azuciyar zuciya domin duk a zaton ta fita zai yi ga mamakinta kawai sai ta ga yana kulle kofar da key (mukulli) "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! wannan kalmar ta kira kafin ta tashi tsaye suka hada ido a lokacin da ya juyo. ta tsorata da ganin yanayin fuskarsa don babu fara'a ko kad'an. Daf da ita ya tsaya saura kadan jikinsu ya had'u. Ta ja da baya, ya sake matsowa ta sake ja da baya! Still ya sake kusantarta! sai ta daga hannu da niyyar tayi masa gargad'i! ya bar abinda yake, ya r'ike hannun ya had'a da nasa yatsun suka had'u guri d'aya! wani irin taushi tafin hannunsa. Jin saukar hannunsa kan mazaunata yana kokarin rungumeta, ta fizge jikinta ta matse gefe kwalla duk ta cika kwarmin idonta. Wannan mutumin shu'umi ne! Gabad'aya ta sanya hannu ta 'kan'kame kirjinta. domin ganin yanda ya tsira musu ido. Murmushi yayi gabad'aya kwayar idonsa ta sauya. Bud'e muryarsa yayi sosai kafin ya ce." Kwanaki ina ki ka shirya zuwa ne? ki ka yi basaja cikin mutane, ko kin dauka ba zan gane ki ba. Kai tsaye ta ce." Zan gujewa sharrin ka ne." "Da gaske?" yafad'a yana lumshe mata tsummamun idanuwansa da suka 'kankace! Kai ta daga da fadin." Kwarai kuwa domin zama a wannan gidan had'ari ne ga rayuwata. Le'bansa ya d'an lasa kafin yayi wani munafikin murmushi ya ce." Ai kin shigo gidan nan kenan har abadah." Wani kallo tayi masa mai kama da harara! sosai kallon ya tafi dashi, jikinsa ya 'kara rikicewa. Ya nemi kujera ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. "Sonki nake yi." ta ji sautin maganarsa yana fad'in wannan kalma. Ta dinga kallonsa a lokacin da yake ta nanata maganar...."Sonki ne keyi ina sha'awar ki mallaka min kanki" Wani tashin hankali ta shiga a lokacin ta kalle shi wanda har yanzu ita yake kallo irin kallon da ta tsana! ta ce." Har abada na haramta a gare ka domin komai kulafucin ka na fi karfinka." Murmushi yayi ya d'an sake lasar le'bansa a karo na biyu! gabad'aya sha'awa ta gama kashe masa, Ya ce" Ki daina cika min baki domin idan kin shiga hannuna ba zan sassauta miki kawai ina so mu yi komai cikin nutsuwa da walwala shiyasa nake rarrashinki." Ta ce" Ba zaka ta'ba samun biyan bukatarka." Sai ya tashi ya nufi gurin da take. tayi sakare domin ta d'auka wani abin zai mata. kawai sai ta ga ya zube a gabanta gwiwarsa a 'kasa ya 'kask'antar da kansa tare da rauntar da murya cikin sigar lallashi da yaudara ya ce.... [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 63&64 "So nake ki amince da b'ukata ta, ina nufin ki mallaka min kan ki koda na rana d'aya ne, wallahi ni kuma nayi miki alkawarin faranta miki rai, tun daga kan miliyan d'aya zuwa miliyan d'ari zan mallaka miki mutukar zaki bani kanki, sannan zan saya miki mota mai tsada, na kuma gidanawa mahaifinki gida, ke nayi miki alk'awarin duk danganinki za su fita daga cikin kangi na talauci muddun kin amince min na dand'ana zumar ki, wallahi zan iya sadaukar miki da duk abinda na mallaka." Yana maganar ne a lokacin da yake ka'sk'antar da kansa amma ya bud'e muryarsa sosai yanda za ta ji sa'kon nasa! Ta dinga girgiza kanta tana auziyya a cikin ranta, wasu hawaye masu d'umi! ne suka shiga sauka a kumatunta, dama duk wani kwane-kwane da yake ta riga ta fahimci abinda yake bukata kenan da ita, ko ga yanayin kallon da yake mata a duk lokacin da suka had'u! ai talauci ba hauka bane, tana ganin ko me zai mallaka mata ba zata amince da bukatarsa ba. Ganin tayi shuru kawai tana kallonsa da hawaye a fuskarta, sai ya tashi jikinsa na rawa! ya 'kan'kameta yana shashshafa bayanta sai kisses yake mata har ya samu nasarar cire mata dankwalin kanta yana hargitsa mata gashi wanda ta wanke ta d'aure shi da ribbon. Wani 'karfi ne ya zo mata a lokacin, ta ture shi tare da kurma uban ihu! ta sa hannuwanta duk biyun aka tana kiran sunan Allah! kuka take tukuru! dan ganin yanda yanayin sa ya sauya gabad'aya! ya rikirkice! yana nema ya kwantar da ita a saman kujera tana duddukansa ta ko'ina! kuma ba ta fasa kurma ihu ba tana kiran Allah ya kawo mata dauki. K'arfi ya sa mata sosai ya ri'ke ta da kyau! don ganin ihun da take yana nema ya tarwatsa 'kwanyarsa! ya matse ta a jikin bango! sannan ya had'e bakinsa da nata! gam! ya ri'ke ya hana ta ihu! a lokacin da bakinsu ya had'u ji tayi kamar an bubbuga mata 'tabarya a k'afafunta sai kyarma take tana ta so ta k'wace bakinta abin ya fassakara, ya ri'ke harshenta da kyau! so yake kawai ta samu nutsuwa! Sanyi jikinta yayi sai uban hawayen da yake gararanba a saman fuskarta, wanda shima tasa fuskar duk ta ji'ke da ruwan hawaye, ba kuka yake ba amma tsabar tashin hankalin da ya ke ciki a lokacin ya sanya kwayoyin idanuwansa mugun ja! ita da shi suka dinga rawar jiki ita dai na tsananin tashin hankali da fargaba ne, shi kuwa na tsantsar sha'awa ne da bukatuwa zuwa wani abu da yayi shekara da shekaru bai samu ba. Sai da ya tabbatar ta nutsu jikinta ya mutu sannan ya cire bakinsa daga nata, ya dan ja baya tare da zuba hannuwansa cikin aljihu yana yi mata wani irin kallo na tausayi da mugun so! Ta zube 'kasan 'kafafunsa tare da ri'ke daya ta ce" Don darajar Allah da Annabi ka da ka aikata fasadi dani, kada ka janyo mana fushin ubangiji! zina babu kyau! mussaman ga masu aure hukunci mai tsanani Ubangiji ya tanadar ga masu aikata wannan lamari, wallahi tunda nake ban ta'ba zina ba, kuma bana fata na fara da kai, bana bukatar komai daga gare ka, ni na yarda na cigaba da zama matalauciya mai rangwamin gata, shin wai ma me za kayi da ni? duk ga mata nan a gari kyawawa masu aji da kyawun jiki, mai za kayi da iri na nakassashiya mara gata, kana da kudi ka je ka nemi irinka amma ni don girman Allah ka fita daga cikin rayuwata. Cikin tsantsar tashin hankali da kuka matsananci take wannan maganganu. Amma ko a fuska bai nuna sadudarsa ba ya cire k'afarsa tare da komawa kan kujera ya zauna yana kallonta babu alamun sassauci a tare da shi ya ce.'' Wannan shine karo na farko dana bukaci wani abu a gurin wata 'ya mace ta yi min gardama! kamar ni, na nemi da ki bani kan ki, amma ki cika min kunne da ihu! har kina kai min duka da cizo da yakushi! wai shin meye a ciki ne? na farko dai wannan lamari idan ya faru tsakanina dake ne, babu wanda ya ji ko ya gani, amma duk kin tashi hankalinki a banza a wofi wanda ni kuma duk abinda za kiyi ba zan janye kudiri na ba, dole sai na kwanta dake domin zuciya da gangar jikina suna bukatar hakan, saboda haka zan baki kwana uku ki je kiyi tunani, amma ki zo min da abinda zan gamsu, tunda na fada miki ni dai ba zan iya hakuri dake ba. cikin jaddada aniyarsa ya kai karshen maganar. Hannu tasa ta goge ruwan hawayen da yake zuba ta ce." Wai kai baka tsoron Allah? ba ka tsoron ranar da zaka tsaya a gabansa, ranar tonan asiri, ranar da kudi da mulki ba za suyi tasiri ba, a ranar ne Allah zai nuna wa jama'a waye kai cikinsu kuwa harda mutanan da suke ganin girma da mutuncinka, a gidan duniya, kowa yana ganin girmanka, dalilin taimako da sadaukarwar da kake da dukiyarka, a zahiri kai mutumin kirki ne, amma kuma wani 'bangaran ka samu nakasu! saboda miyagun halayen da kake aikatawa irin wanda Allah ya haramta. A cikin al'kur'ani mai girma Ubangiji subahanahu-wata'ala ya umarce ku da ku aura daga d'aya zuwa biyu da abinda yayi sama, mutukar kuna da iko kuma za kuyi adalci." Ta d'an sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da cewa; Allah yayi maka komai na daga jin dadin duniya ya wadataka da arziki da rai da lafiya da ji da gani bai tauye ka ba, to mai zai sanya ka butulce masa? kana da dukiyar da zaka auri mata hud'u ka ajiye a gidanka domin raya sunnar ma'aiki salallahu alaiyi wassalam, amma kana zubar da 'kima da mutuncinka, ka sani cewa duk abinda ka yi a kan dan wani sai anyi da naka, saboda haka ka ji tsoron Allah ka daina bibiyar rayuwata." A maimakon jikinsa ya mutu da nasihar ta, sai kawai ta ga yana murmushi tare da wasa da gemunsa kamar wacce tayi abin dariya sai kallonta yake yana murmushi, tsayin mintina uku kafin ya ce" Na gode da nasiha malama, amma ina sheda miki cewe; ina nan akan bakana, ba zan janye kudiri na ba, dole zaki bani kanki ko kina so ko ba kya so, ki je kiyi shawara na baki kwana uku kamar yanda na fad'a miki da farko." Ya na gama maganarsa ya tashi ya haye sama ya bar ta zaune a gurin cikin tsantsar damuwa da tashin hankali. A tsakanin kwanakin sosai ta mayar da hankalinta gurin karatun al'kurani mai girma tare da shedawa Allah damuwarta, a yanzu dai ba ta ga tsuntsu ba ta ga tarko, dalili babu wanda za ta je ta fada masa damuwarta saboda wayar da take hannunta ma tun ranar da su kayi magana da Saliha ya 'kwace! har ya tafi bai bata ba. Tana dai zaune a gidan tare da mi'ka lamuranta ga Allah. Yau ne cikar kwanakin da ya gindaya mata. Tayi ta k'o'karin danne damuwarta amma hakan bai samu ba, sai da Hajiya Saude ta fahimci damuwa a tattare da ita a lokacin da ta shiga domin gaishe ta. Ta kalle ta, kafin ta ce." Shahida cikin kwana biyun nan ina ganin damuwa a tare dake ko da akwai wani abu da mu ke miki?" Ta ji kamar ta fad'a mata abubuwan da suke faruwa, sai kuma wata zuciyar ta tsawatar mata saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo, watakila idan ta tona maganar ita ce zata kwana a ciki, domin babu wanda zai yarda da ita. Ta girgiza kai da fadin." Hajiya babu komai kawai dai bana jin dadin jiki na ne." Tayi murmurshi kafin ta ce" Wai cikin naki wata nawa ne?" Da sauri ta ce." Hajiya bani da ciki fa." "Ke haba dai 'yar nan, to wannan laulaye-laulayen da ki ke na menene?" Shuru tayi ba tace komai ba. Shukura ta fito daga d'akinta ta shirya tsaf sai kamshin turare take, ta nemi kujera ta zauna hankalinta a kan wayarta ciki bada Umarni ta ce." Ke Shahida ki shiga dakina ki gyara min sannan kuma ki wanke toilet." Hajiya Ta ce." Ai yau sai dai kiyi da kan ki ba ta da lafiya" Wani irin kallo tayi wa Shahidan tana ta'be baki da fad'in." Hajiya gaskiya ba zan iya wani abu ba yanzu na riga nayi wanka ai d'akin nawa babu wani datti sosai! kawai ta tashi ta je tayi dama aikin ta ne" Ta ce." A'a ki sa Marka mai aiki tayi miki mana ita wannan d'in ki kyale ta rana daya dai da huta." Tana k'okarin magana ya k'araso gurin, duk sai su kayi shuru, suna kallonsa amma banda Shahida kanta yana 'kasa domin tunda taji 'kamshin turaransa ya cika gurin, hankalinta ya tashi, gabanta in banda fad'uwa babu abinda yake. Ya ce." Hajiya maganar me ku ke ne? zuwa na gurin kun yi shuru sai kace wani mala'ika" Murmushi ta yi kafin ta sheda masa maganar da suke. Ya harari Shukuran kafin ya ce." Ke aikin me ki ke da ba zaki gyara abinda ki ka 'bata ba." Tayi shuru ba tace komai ba. Ya ce." Kada ki kuskura ki sake sanya ta aiki, ke kika 'bata kuma ke zaki gyara abinki." A sanyaye ta ce."To Daddy." Jin haka yasa ta tashi da niyyar tafiya gurinta ta d'an risina da fadin." Hajiya a tashi lafiya zan ni koma guri na." Ta ce." To sannu, ubangiji Allah ya baki lafiya amma yana da kyau! kuje asibiti likita ya dubaki sosai laulayin yayi yawa gashi kin ce baki da ciki.'' Murmushi kawai tayi ta juya tare da kallon gefen da yake zaune, bata yarda ta kalle shi ba ta ce."Alhaji a tashi lafiya." Shima ba tare da ya kalle ta ba ya amsa hankalinshi a kan wayarsa. A gaggauce ta fita tana cigaba da neman tsarin Ubangiji akan mummunan al'amarin da yake bibiyar rayuwarta. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 65&66 Lamarin dai babu dad'i domin wani lokacin idan tsanani yayi yawa sai mutum ya gwammace mutuwarsa akan rayuwar da yake, sai dai kuma hausawa suka ce idan aski yazo gaban goshi to ya fi zafi! hakane kowane bawa akwai irin tasa kaddarar wanda babu wanda ya isa ya goge ta, to ita kam tana tunanin wannan ce kaddararta wanda ta tazo da kafafunta ta sameta har inda take, babu shakka wannan mutumin ya zame mata jaraba da kuma kaddara, ba kowa ne sila ba sai Mijinta wato wanda ta kwallafa rai a kansa take ganin shi din mai kaunarta ne, ashe kallon kitse takewa rogo, mutum ne shi azzalimi mayaudari, ta amince masa ya cutar da ita. Har ta gaji da zubar da hawaye, watakila rashin kukan ne ya janyo mata toshewar mak'ogwaro domin wani k'atoton abu ne ya zo ya tsaya mata a wuya! sai kuma damuwa da fargabar da tayi mata katutu! Da 'kyar ta iya tsakurar abinci cokali biyar kacal ta ci gabad'aya cikinta ya cushe! tasha ruwa ta kwanta lamo a tsakanin kujeru! wannan duhun ma babbar masifa ce, domin tuntuni batiran fitilar suka mutu! sunyi ruwa basa bada haske, gashi kwana biyu bata ga Sule ba ballantana ta fad'a masa. Sosai kanta yake mata ciwo domin ba wani cikakken bacci take samu ba saboda tunani yayi mata yawa shiyasa bacci ya kauracewa idonta sai dai ta yi shi a tsin-tsinke. Lumshe idonta tayi tare da kiran sunan Allah da ya kawo mata d'auki! a rayuwarta. Motsi ta ji a kanta bayan masifaffen kamshin turaransa da ya bakunci hancinta, sai tayi gaggwar bud'e ido ta tashi a razane! shine ya shigo, to ta wace hanya? bayan duk ta rurrufe k'ofofi! Innalillahi-wa'ina ilahi raji'un! abinda ta fada kenan kafin ta ja jikinta ta matsa can gefe tare da takurewa a jikin kujera. Gurin yayi shuru bayan zamansa da minti biyar ya bud'e muryarsa sosai kafin ya ce." A ina maganarmu ta kwana ina fata baki mance cewa yau ne cikar kwanakin dana baki ba. Shuru tayi tana kallonsa amma ba sosai ba, saboda babu hasken a dakin sai na wayarsa da ya kunna. Ya ce"Shurun da ki kayi ya tabbatar min da cewa kin amince kenan?" Uffan ba tace masa ba, wata mummunar shawara ta yanke a zuciyarta. kawai sai ta tashi ta nufi kicin cikin zafin nama! Ya bi ta da kallo tare da tunane-tunane a ransa. Hannu bibbiyu ta ri'ko zabgegiyar wuka gayawa jini na wuce, irin ta cikin set ta zo ta tsaya a kansa tana wani irin huci! kamar kububuwa! Gabansa ya fad'i! amma bai nuna a zahiri ba sai ma gyara zamansa da yayi ya kalle ta a lokacin da jikinta ke wani irin rawa ga wu'kar a rik'e a hannunta sai kyalli take! Ya ce."Me ki ke shirin aikatawa?" Kai tsaye ta ce." Kashe ka zanyi, na kashe mugun iri." sai maganar ta bashi dariya, da murmushi a tare dashi ya nuna kirjinsa da fadin." Ni zaki kashe?" Ta ce." K'warai kuwa, meye amfaninka a wannan duniyar ai baka da amfani wallahi" Yayi dariya tare da cewa" To na ji yanzu ya ki ke so ayi?" ''Ka fice daga rayuwata mutukar kana so ka cigaba da numfashi a doran duniya. Tafada tana gyara ri'kon wukar da hannunta "Ba zan iya ba domin na fada miki cewa zuciyata da gangar jikina ne suke bukatarki" "Ashe kuwa za kayi asarar rayuwarka" Ta fad'a tana wani irin nishi! ba kuma tare da yayi tsammani ba ta kai masa wani irin sara! yayi saurin kaucewa wuk'ar ta sauka a hannun kujera tsabar yanda wukar ta huda kujerar sai da soson ta fito! Jikinta na rawa! ta ce"Sai dai a kashe ni amma nayi alkawarin raba ka da rayuwarka mutukar ka keta min alfarma. Ya shiga rud'ani sosai! yarinyar da gaske take, kuma ya yaba da k'okarinta kwarai da gaske, sai dai makamin dake hannunta yana nufin abubuwa da yawa, wani tunani yayi kafin ya ce." Ajiye wannan makamin na hannunki mu yi magana." 'Kin ajiyewa tayi ta kalle shi sosai da fad'in." Ashe kana tsoron mutuwa" "Bana tsoron mutuwa sai dai ina fargabar a ce kece sanadiya domin zaki kare rayuwarki a wahalace! Ta ce" Bana nadamar hakan, ni dai burina rage mugun iri, irinka wanda baya tsoron Allah." Kansa ya girgiza tare da auna maganganunta. ''To yanzu idan nace na janye aniyata a kan ki zaki yarda?" "Wallahi ba zan yarda ba domin ban ga alama ba" Yayi yun'kurin tashi! ta sake kai masa wani saran a karo na biyu nan ma Allah ya kiyaye bata same shi ba. Wannan karon ya tsorata sosai! ya kuma fahimci da gaske take tana iya kashe shi, domin tseratar da rayuwarta. A halin yanzu ta sa shi a tsaka mai wuya domin daga yayi motsi zata zabura! ta nemi illata shi da wukar hannunta. "Na janye kud'iri na a kanki idan na rantse da Allah zaki yarda?" Yafada da alamar roko da tsoro a tare dashi. Ganin haka yasa ta ce." Ka rantse da zatin Allah da buwayarsa" Ya ce."Ni Alhaji Saddiku na rantse da girman Allah ba zan aikata abinda nayi niyya ba, na tuba ga Allah na tuba gare ki" Ta matsa gefe tana numfarfashi tare da sauke wu'kar 'kasa. Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi tsaye tare da zuba hannunwansa a cikin aljihu! Cikin nutsuwa ya nufi gurin da take tsaye! gabanta ya fad'i! ganin ya nufo ta sai tayi yun'kurin sake d'aukar wukar yayi sauri ya riga ta har sai da ta yanke musu hannu ita dashi, amma ba sosai ba, saboda halin da suke ciki yasa babu wanda ya damu. Fuskarta yake kallo jikinta na ta wani irin rawa! ya kama hannunta suka zauna a kujera! matsawa tayi can gefe tare da nuna masa hanyar fita da hannunta, Ya gane abinda take nufi sai ya girgiza kansa alamar "A'a" Da muryar Baban-baba ya ce"Ba zan fita anan ba domin ke mallakina ce kuma matar rufin asiri uwar 'ya'ya na anan gaba. Da mummunan tashin hankali take kallonsa a lokacin da yake maganar gabad'aya rasa miyau tayi a bakinta. "Baban baba kuma? shine kuwa domin muryarsa ce ke mata amsa kuwwa a kunne! "Ni ne Alhaji Saddiku Dan gaske, kuma ni ne Baban-baba mahaukacin nan na bakin kasuwa mai kwanciya a k'ar'kashin mota." Shikkenan ta faru ta 'kare! innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wai shin me yake shirin faruwa ne da rayuwarta! Hannayenta ya ri'ke tsabar tashin hankali ta kasa k'wacewa sai wasu irin tunane-tunane take wanda suke nema su haukatar da ita. Ya ce."Na san dole kiyi mamakin haka amma ina neman afuwa a gare ki matata! duk wannan abubuwan da suka faru tsakanina dake ina da manufa kuma ina so ki bani hankali da nutsuwarki" Hannu ta d'aga masa tana so tayi magana amma ta kasa! sai kawai ta fashe da wani irin kuka! jikinta in banda rawa babu abinda yake. Rungumeta yayi a jikinsa yana rarrashinta tare da shafa bayanta, bata hana shi ba, domin a wannan lokacin rarrashin take bukuta, tayi lamo a jikinta shi kuma yana ta aikin jijjigata kamar wata jaririya! A hankali ta cire jikinta tana kallonsa shima din ita yake kallo tausayinta duk ya cika masa zuciya ya rasa wane kalar rarrashi zai mata, domin ya san dole hakan zata faru idan ya fito mata da gaskiyar lamari. Kokarin tashi ta fara sai yayi gaggawar ri'ke mata hannu da fadin" Ina zaki je?" Shuru tayi masa tana dauke kanta. Ya janyota ta zauna a cinyarsa! ya ri'ke ta sosai suna kallon juna! ya ce." Ki kwantar da hankalinki fa wannan duk ba abin damuwa bane! wallahi nayi hakan ne domin wata manufa tawa, za kuma ki fahimce ni idan na baki labarin abinda ya faru da rayuwata a shekarun baya, saboda haka ki cire shakku ko mamaki a ranki, Ni ne Alhaji Saddiku d'an gaske! kuma ni ne Baban-baba." "Me yasa kayi min haka?" tayi magana a karo na farko da faruwar al'amarin. Ya ce." Ina da hujjoji da yawa, amma ina so ki bani aron hankali da nutsuwarki domin na sheda miki abubuwan da suka faru a shekarun da suka wuce. Ido kawai ta zuba masa tana kallonsa, shi kuma sai ya sake matseta jikinsa, ta kwantar da kanta a kafad'arsa tayi sanyi sosai domin al'amarin ya tsorata! Muryarsa ya bud'e sosai yanda za ta ji ya ce." [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 69&70 Jin saukar ajiyar zuciyarta, yasa ya d'an shafa gashinta, a hankali yasa bakinsa daidai kunnanta ya hura iska kad'an, kafin ya ce." Kinyi shuru, na cigaba da baki labarin ko?" kanta ta d'aga tare da sake gyara kwanciya a kirjinsa, gabad'aya jikinta ya mutu sakamakon labarin rayuwarsa da yake bata ashe da sauran rina a kaba, domin kukan da take shafar mai ne akan wanda za tayi anan gaba. "Mahaifina ya samu jama'a sosai wad'anda suka sallaci gawarsa da wad'anda suka bada sheda arziki a kansa! sai dai kuma tun bayan da aka kai shi gidansa na gaskiya kowa ya watse babu wanda ya zauna, suma 'yan uwanshi zaman da su kayi na 'yan mintina ne, suka kama gabansu, al'amarin ya bani mamaki sosai, a nan na gane cewa babu wanda yake saurin kaskanta a duniya sai talaka, wato mutane sun san ko da sun zauna zaman makoki babu abinda za a fito musu dashi daga gidan mamacin, shiyasa suka watse! sai nake tunanin yanda jama'a ke tururrubi gurin zaman makokin wanda yake da farcen susa, wani ma don ya ci abinci ya ke zuwa ya zauna, ko da bashi da alaka da mai mutuwar, wannan kuwa talaka ne wanda bai ajiye ba, kuma bai bawa kowa ajiya ba, amma dai ko da kowa bai zauna ba, 'yan uwansa sa zauna domin kar'bar gaisuwa, duk da cewa zaman ba dole bane a shari'ar musulunci, amma ai an mayar dashi al'ada, a lokacin zan ji dad'i mutukar da wani a kusa dani, sai ya kasance ni kad'ai nake kar'bar gaisuwa domin babu wanda yake zaune gefe da gefe na, sai dai ina farin ciki sosai idan na tuna cewa mahaifina yayi mutuwar shahada, ya kuma shiga ranar juma'a, bayan kyakykyawar sheda ta mutane. Ranar sadakar uku ni da k'anwata Sadiya muka yi masa saukar al'kurani maigirma, bayan haka kuwa babu wani abu da 'yan uwasa suka yi masa na sadaka, a tsaitsaye suka tafi mussaman Baba Auta don shi ko zama beyi ba yace yana da uzuri, gwara Baba Audu ya d'an zauna na 'yan mintina kafin ya tashi ya tafi. Hakan bai dameni ba, domin ni babban buri na da fata na, ace mahaifina ya dace da rahamar ubangiji. Sosai na tashi hai'kan! da neman kud'i, duk abinda za'ayi da jiki k'arfi ina zuwa na yi mutukar zan samu abinda asiri na zai rufu, ni ne wanki da guga! gyaran takalma, aikin gini, dako cikin kasuwanni, gefe guda kuma ina yin gyaran babura da siyar da fetur a bakin titi, asiri na kuwa ya rufu, domin na d'aukewa mahaifiyata da k'anwata nauyin komai, don ba naso suyi kukan maraici! shiyasa nake fita nema ba dare ba rana. Ganin haka yasa Hajiya dawowa gidan, a cewarta ai suma suna da hakki a kaina, duk neman da nake uwata nake wahaltawa, sai ta dawo gidan ta share d'aki ta zauna, tsirfar yau daban ta gobe daban, gashi ita kuma mamana bata da hayaniya! kuma bata son tashin hankali, shiyasa duk abinda Hajiyan tayi mata sai ta kawar da kanta, amma abin yana damunta mutu'ka, ni ma abin yana yi min ciwo, ranar da na samu zama a gidan, zan shiga har dakinta na zauna domin na nusar da ita cewa abinda take ba daidai bane, sai kawai ta fashe min da kuka ta lauya zancen da cewa; don naga 'kasa ta rufe idon mahaifina shiyasa nake nuna mata cewa mamana tafi ta girma a guri na, ganin haka yasa kawai na rabu da ita sai dai na daina sakar mata fuska, ko wasa take min bana saurararta nake shigewa na tafi harkokina, sai ta rarrafo ta fito tsakar gida ta zauna ta dinga habaici! wanda yake damun zuciyar mamana! bata kaunar tashin hankali da damuwa, haka za suyi ta kuka ita da Sadiya a daki abin na damun ransu. Cikin ikon Allah da wannan buge-buge da nake na samu na sayi fili, sai dai tunda Hajiya ta ji labari, ta dame ni kan lallai sai na fito da matar aure tunda ina samun kudi, nayi kokarin nusar da ita cewa; kudin da nake samu na rufin asiri ne, zanyi aure amma ba yanzu ba. Ta 'ki yarda da maganata, kawai ta kira Baba Auta ta fara sheda masa halin da ake ciki, 'kiri-'kiri na ga hassada a cikin idonsa, jin cewa na sayi fili har na soma gini, ya dinga fad'a mara dalili wai akan me duk abunda zanyi ba zan nemi shawararsa ba, ni dai shuru kawai nayi ina kallonsa. Ya ce." Shikkenan Allah ya sanya alheri, maganar aure kuwa dole mu yi maka ka fito da mata, idan kuma baka da ita to na baka Fatima." Gabana ya fadi! na kalle shi da mamaki a tare da ni na ce." Wace Fatima?" Ya ce"Ta waje na mana ko kana ganin kafi karfin ka aureta ne?" Na ce." Gaskiya bana ra'ayinta Baba auta babu maganar rufa-rufa a tsakaninmu, Fatima 'yarka ce amma kasan bata da kamun kai ko?" Ya ce." Magana zaka fada min a gaban ido na?" Na ce" Ba haka bane na jaddada maka abinda ka sani ne, ni d'in ba mace bane, ballanatana ayi min irin auran da bana ra'ayi, a kyale ni da kaina zan duba matar da ta cancata. Sai kawai ta fashe! da kuka da fadin" Saddiku wannan sharrin na mahaifiyarka ne, domin ita take zama ta kitsa maka komai, amma ina laifin wanda yayi maka kyauta, Fatima dai 'yar uwarka ce duk lalacewarta ba zaka sanja ta ba. Ya ce." Ki rabu dashi Hajiya tunda shi bashi da mutunci, a gaban idona yake cin fuskata, to shikkenan tunda kace baka sonta sai ka fito da wacce ka keso." yana gama maganarsa ya tashi fuuuu! ya fita. Nima tashi nayi na bar gurin raina a 'bace! gaskiya ba zan lamunci wannan kama karyan ba. domin dai yarinyar kowa ya san halinta, sam bata da nutsuwa da tarbiya ga shegen kula maza da sauraran abubuwan da basu dace ba, a wannan zamanin kowane uba yana so ya za'bawa 'ya'yansa uwa ta gari, to akan me yana ganin kashi da rana ya taka, ba zai yuwu ba. Ko da na shedawa mamana halin da ake ciki, sai ta ce tunda abun ya riga ya zama haka to nayi gaggawar fito da matar da nake so na aura, domin a ganinta hakan zai sanya su janye maganar Fatima. Na shiga tsaka mai wuya a lokacin, domin kuwa tunda na girma na kai munzali na samartaka ban ta'ba kula wata budurwa ba, ba don bani da bukata ba, a'a asali ma ni mutum ne mai yawan sha'awa, shiyasa sa'i da lokaci nake azimi domin tseratar da kaina. Ina son aure sosai, to amma ina cizawa! domin na riga na san aura a yanzu dole sai ka shirya, nauyi biyu ne zai hau kaina dana iyalina da na mahaifiyata da 'yar uwata. Amma tilas tasa na yankewa kaina shawara domin gujewa auran Fatima wacce babu ita a cikin tsarin rayuwata Na je na samu mahaifiyata da maganar Na'ima 'yar 'kaninta ce Baba Salihu, yarinyar tana da tarbiya sosai da kunya, wannan shine abinda ya ja ra'ayi na akanta har na ji ina sha'awar auranta. Tayi shuru tana nazarin al'amarin kafin ta ce." *D'an gaske* da yake sunan da take kira na dashi kenan, sakamakon sunan mahaifinta ne, ta cigaba da cewa" ina gudun abinda zai biyo bayan al'amarin, domin bana son tashin hankali, kuma ban mance da wasiyyar mahaifinka ba, kan cewa lallai na kula da mahaifiyarsa ka da tayi kuka damu, muyi kokarin ganin mun rabu da ita lafiya, wannan dalilin yasa duk abinda Hajiya take min a gidan nan, bana d'aga kai na kalleta, domin zama na amana da mutunta juna nayi da mijina, duk da mahaifiyata bata yare, ya zama dole na girmama tasa, saboda haka ban hana ka nemi auran Na'ima ba, amma ka je ka shedawa 'yan uwan mahaifinka domin mu ji hukuncin da za su yanke. Hajiya tayi tsalle ta dire tace bata amince ba, wato naje na had'a baki da uwata ta dauki 'yar kaninta ta bani, na guji 'yar uwata Fatima, to bada yawunsu ba, muddun nace dole sai na auri Na'ima sai dai na sanja iyaye, gabad'aya suka had'e bakinsu, Kawu Audu dashi Baba Auta din, babu wanda ya fahimce ni. Mamana ta umarce ni cewa na janye maganar auran Na'ima na amince da auran Fatima domin samun kwanciyar hankali, amma zata tsananta da yi min addua insha Allahu ba zan lalace ba. Jin haka yasa na amince ba don raina yaso ba, sai don samun zaman lafiyarmu bakid'aya. amma sam Fatima bata daga cikin tsarin matan da nake so na aura. 'Bangaran wacce ake dambawar don ita, ko da ta samu labarin abinda yake faruwa, sam bata nuna damuwa ba, domin ta jima da sona a cikin zuciyarta, duk da bata furta min ba, amma duk alamomi sun bayyana, idan zamu had'u a ko'ina ne sai tayi min magana irin ta rashin kamun kai, "Wallahi kana burgeni, ina son namiji dogo giant (ingarma) wanda na san ya cika cif, zai gamsar da ni a shimfida, ire-iren wannan maganganun banzan take min a duk sanda za mu had'u, sai nayi mata jan ido sannan! na nuna mata cewa; ni nafi k'arfinta, amma hakan baya hana ta sake zuwar min da maganganun banza makamanta wannan. a duk sanda zamu had'u a wani guri Tunda ake maganar auran ban taka k'afa na je gurin yarinyar ba, komai suke ina kallonsu ne kawai, nayi iyakar abunda zan iya na lefe da sauran abubuwan bukata na aure. Sai ga ta tazo ta same ni a gurin aiki na tare da 'kawarta, kallo daya nayi musu na kawar da kaina domin raina ya 'baci da ganin sutturar dake jikinsu, komai a bayyane. ''Magana na zo nayi da kai" tafada a lokacin da take tsaye a kaina. Na kalleta tare da fadin."Me yake tafe dake?" kai tsaye ta ce."Kudin 'kunshi da kitso nake bukata. Dubu uku na bata amma na gargade ta kan cewa; kada ta kuskura ta zo min gida da gashin doki, domin gwanar 'karin gashi ce da tara farce, ga uban bilicin da take, duk ta lalata fatarta! Ta'be bakinta tayi ta ja hannun 'kawarta suka tafi, tana maganganu kasa-kasa wanda na san dani take. 'Daki da rumfa kawai na samu na kammala, na dan kwaskware! dai-dai gwargwado. amma kicin da band'aki da sauran aiki, dan babu fulasta ballanatana rufi, haka nan na hakura, saboda yanda wahala tayi yawa, ga bikin ya matso komai ya kacame! babu mataimaki sai Allah. To tunda aka d'aura auran, ban wani saki jikina da ita ba, na dai sanya mata ido ne kawai ina nazari a kanta. Duk wani hakkinta da ya rataya a wuya na, ina kokarin ganin na sauke shi, amma kuma ban ta'ba had'a shimfida da ita ba, a falo nake kwanciyata ita kuma a cikin uwar daki, haka nan, za tayi shigar fitar da tsaraici a gabana tayi ta juyawa, amma cikin ikon Allah ba ta iya jan ra'ayi na zuwa gare ta. Sai kawai ta je ta fad'awa Hajiya cewa; bani da lafiya domin tunda akayi auranmu wata hud'u ban ta'ba kwanciya da ita ba. Hajiya ta samu abin yi ta je har d'akin mamana ta rufe ta da fad'a, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, cin mutumci iri-iri abin mamaki! Fatima har tana sanya baki, anan ne Sadiya ta gaza hakuri ta fara mayar da martani, Hajiya ta gaura mata mari tana fadin" Wato za ta goyi da bayan uwarta kenan! to shikkenan zata sanya kafar wando daya dasu gabad'aya! Sai da nazo gidan Sadiya ke sheda min abinda ya faru, sosai raina ya 'baci! idan Hajiya ta ci zarafin mamana na rabu da ita to babu shakka Fatima ba zata wanye lafiya ba, domin bani da hakuri a kan mahaifiyata da nake jinta a cikin ko'kon raina! Sosai ta ga 'bacin raina akan abinda tayi, na ce kuma lallai in tana bukatar zama dani to ta je ta bata hakuri, idan ta'ki wallahi sai na sake ta. wannan shine hukuncin dana yanke mata. 'Kwana d'aya biyu shuru ba tabi umarnina ba, a cikin kwana na ukun, na rubuta mata saki daya a takarda na ce lallai kafin na dawo ta fice min daga gida. Yanda na fahimta al'amarin ya bata tsoro sosai, domin ba tayi tunanin zan iya sakinta ba, haka na fita na barta cikin damuwa mai tsanani, wanda ni hakan bai dameni ba, mutukar zata ta'ba martabar mahaifiyata to wallahi na gama zama da ita. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 67&68 ASALIN LABARI. "Ni mutumin jahar katsina ne, a cikin karamar hukumar jibia a ka haife ni, tare da 'yan uwa na biyu wanda suka kasance mata, sai dai Allah yayi wa babbar cikinmu rasuwa a lokacin da ta zo haihuwar fari, tayi mutuwar shahada, ina rokon Allah ya jikan Amina yasa aljanna makomarta, mahaifinmu Malam Sani kafinta ne ma'ana mai sarrafawa katako ta kowace siga, daidai gwargwado yana samun rufin asiri da wannan sana'ar duk ya d'auki d'awainiyarmu, ci da sha suttura da harkokin karatunmu. Ya kasance mutum mai sha'awar karatun boko tun yana yaro, amma Allah bai sa yayi ba, dalili mahaifinsa bashi da wannan ra'ayi a cewarsa duk wani karatu ya bi bayan na addinin musulunci, wannan dalili yasa ya daukeshi ya kai shi can jamhuriyar nijar karatun allo, anan ya sauke al'kur'ani mai girma ya kuma haddace shi, sannan ya dawo gida domin taimakawa mahaifinsa akan sana'arsa ta gado, wacce shima ya gada a gurinsa, yake kuma cin abincinta da ita tare da biyan buk'atar yau da gobe. Sosai ya tsaya min da 'karfinsa dana aljihunsa har sai da ya ga na samu gurbin karatu, a jami'ar bayaro university dake jahar kano, hankalinsa ya kwanta, burinsa kawai nayi karatu sosai wanda zan samu aiki na d'auki nauyin kaina, na kuma yi aure domin rike iyali. A lokacin mahaifiyarsa tayi ta k'orafi da k'ananun maganganu, kan cewa; da Mahaifinsa yana raye wannan d'anyan aikin ba za'ayi ba, domin itama akwai 'karancin rashin fahimta a tare da ita, a ganinta duk wani karatu da za ayi a yanzu mutukar bana al'kurani bane to bashi da amfani, kuma a lokaci fa nayi saukar al'kur'ani, nasan hadisai da sauran littaffan addinin musulunci, kawai dai ita bata son karatun bokon ne, ganin haka yasa mahaifiyata yin shuru da bakinta, domin tana iya magana laifin ya dawo da kanta, sai tayi shuru kawai, amma cikin zuciyarta addua. take min. Tun ina yaro 'karami nake jangwale-jangwale, duk lalacewar abu idan nasa masa hannu sai ya tashi, musamman irinsu tv keken d'inki babur, mota da sauransu, wannan dalilin yasa mahaifina ya bani shawarar karantar Engineering, cikin ikon Allah kuwa cos din beyi min wahala ba, ni nake zuwa na d'aya duk jarrabawar da za muyi bana fad'uwa, sosai nake taimakawa wasu daga cikin abokan karatuna. Na kammala karatuna cikin narasa takarduna sun yi kyau sosai! irin yanda ake bukata, sai dai fafur! aiki ya'ki samuwa, tunda na dawo gida nake yawon neman aikin abin ya fassakara a cikin jahata babu local goment din da ban je neman aiki ba, amma Allah bai sa na samu ba, A lokacin Hajiya ta samu bakin magana, fad'i take dama ai na fad'a! wannan karatun bashi da wani amfani, gashin tsayin shekara hud'u kana fagauniya duk ka lalace! ka yi rama, shi kuma da yake daure maka gindi yayi asarar kudinsa a banza, sai a zo a rungumi sana'ar gado tunda abinda ake nema bai samu ba. Mahaifina dai shuru kawai yayi mata ba wai don bashi da abin fada ba, amma ya fi kowa jin ciwon abin a cikin ransa. Haka na ajiye takarduna, na sanya hannu domin tamaikawa mahaifina alokacin dama k'arfinsa yayi rauni. Rayuwa tayi mana tsanani domin mahaifina bashi da wani cikakken jarin da zamu juya mu kasa mu sayar, sai dai kullum idan mun fita shago mu zauna jiran masu kawo kwaskwarima, idan hakan ta samu kenan, domin watarana yanda muka fita haka zamu dawo babu ko kwabo cikin aljihunmu, gashi rayuwa tayi tsada kullum 'kara tsanani take. Ganin abinda zamu ci yana nema ya fi k'arfin bakinmu, yasa na fara shiga cikin kasuwani domin daukar dako, to anan ne na samu na tara kud'in da na sayi kayan gyaran babur da faci, sannan na nemi albarkar iyaye na, na fita bakin titi, domin gwada sa'a ta akan sana'ar ko Allah zai sa a dace. Cikin ikon Allah kuwa sai Ubangiji ya bani sa'a, kullum idan nayi sana'oi na, na kan tashi da kud'i masu kauri wanda zanyi awo da cefene a gidanmu sannan da safe na basu kudin karin kummalo. Iyaye na sunyi farin ciki sosai da wannan sana'a da nake, kullum cikin yi min fatan alheri suke, ita kuma Hajiya lokacin ta matsanta min lallai sai na fito da matar aure, duk yanda naso na fahimtar da ita abinda ke da akwai amma fafur! taki saurarata, ita dai tunda na samu sana'a to nayi aure. Ni kuma tunani a yanzu shine, shi aure sai mutum yana da kwakwarar sana'a! saboda yau da gobe gashi bani da muhalli uwa uba nauyin iyayena da 'kawanta Sadiya dake kaina Haka dai rayuwa ta cigaba da gurgurawa, yau da dadi gobe babu, cikin wannan yanayi ciwon ajali ya kwantar da mahaifinta! gabadaya ya daina fita yana gida a kwance sakamakon wani irin tari da ha-ki! da ya ci k'arfinsa, na d'auk'e shi na kai shi asibiti, a lokacin akayi masa gwaje-gwaje! amma cikin ikon Allah ba'a gane abinda ke damunsa ba, sai dai likita ya rubuta masa maganin da yake ganin zai taimaka masa. To koda naje gurin siyan maganin hankalina ya tashi sosai sakamakon yanda mai siyar da maganin ya fada min adadin kudin da zan biya domin a bani magungunan da likita ya rubuta a katin. Kudin dake aljihuna duka-duka dubu biyu ne, wanda ko guda daya ba zai siya ba, gashi likitan yace lallai a sayi magungunan duka domin suna da mutukar amfani. Jiki a sanyaye na koma gida da tunanin hanyar da zan bi gurin samun dubu ashirin da hudu wanda zan sayawa mahaifina magani, 'Yan uwansa ba su dashi, amma ya zama dole na je gurinsu, domin na sheda musu halin da ake ciki, saboda haka kai tsaye gurin sana'ar Malam Audu na nufa inda yake sana'ar faskare na icce. duk na sheda masa halin da ake ciki, na kuma nuna masa katin asibitin domin ya tabbatar. Sosai ya jajanta al'amarin, ya kuma tausayawa d'an uwansa halin da yake ciki, da karshe ya dauko dari uku ya bani tare da bani hakuri kan cewa shima bashi da kudi ga wahalhalu na iyali sunyi masa yawa. Kwata-kwata ban ji haushinsa ba, domin na san da gaske bashi dashi, d'an abinda ya ke samu bai taka kara ya karya ba, kuma dashi yake daukar nauyin iyalinsa. Gurin d'an autansu na nufa wanda muke kiransa da Baba Auta babu laifi shi yana d'an samu a kasuwa tunda harkar hatsi yake gidansa babu yunwa kuma sannan a cikinsu duk yafi su rufin asiri. Kallona yayi a lokacin dana gama yi masa bayani, ya girgiza kansa da fadin." Lallai Sani yana cikin jarrabawa, Allah ya ba shi lafiya" na amsa da "ameen" ina jin sanyi a zuciyata, domin duk a zato na zai taimaka mana, kawai sai ji nayi ya ce." To Saddiku kasan dai yanda rayuwa take, duk wanda ka ga yana nema to saboda iyalinsa yake, saboda haka zan taimaka daga abinda naga zan iya domin kuwa ba zan takurawa kaina ba." Yasa hannu cikik aljihu ya dauko kudi d'aure da kyaure ya zaro dubu daya ya miko min da fadin." Ga wannan a hada a saya masa maganin, Allah ya ba shi lafiya." Jikina a sanyaye na kar'ba da fadin." Allah yasa ka alheri ." Ya amsa da ''ameen" tare da shigewa cikin gidansa ya bar ni tsugune a gurin. To koda na shedawa Hajiya abinda ya faru, sai cewa tayi ai sunyi 'kokari ma a hakan, abinda yanzu wahala tayi wa kowa yawa, wa zaka je ka daura nauyinka" Sai na kasa fahimtar inda maganarta ta dosa, wato tana nufin ta goyi da bayan abinda sukayi kenan daidai ne a gurinta. girgiza kaina kawai nayi na tashi na bar gurin, zuciyata cike da jin ciwon rashin kulawar da take akan mahaifina kamar ba ita ce ta haife su duka ba. Wani abokina ne ya bani shawarar zuwa gidan redio domin na kai kuka na, cikin ikon Allah kuwa kwana biyu da zuwa na wani bawan Allah ya biya kudin maganin, sosai nayi farin ciki, addu'a kuwa munyi masa sosai dani da mahaifiyata da k'anwata Sadiya. Cikin ikon Allah yana fara shan maganin sai sauki ya fara samuwa, muna ta murna da godewa Ubangiji, sai dai kuma mune muke haukanmu ashe saukin na tafiya, daran alhamis ya rasu! da kalmar shahada a bakinsa. Mutuwar mahaifina ba zan ta'ba mancewa da ita a tarihin rayuwata ba." Shuru yayi, ya kasa cigaba da bata labarin. saboda yanda mutuwar ta dawo sabuwa, kukan zucci kawai yake, Lokacin ita kuma tausayinsa duk ya gama mamaye zuciyarta, sai ajiyar zuciya take saukewa tana sake shigewa jikinsa kukan da take dannewa ne ya su'bce! sai sautinsa ya ji a kunnensa! sosai take zubar da hawayen tausayinsa. Hankalinsa ne ya tashi ya dinga rarrashinta cewa tayi shuru saboda dare yayi sosai! sautin kukan zai iya fita, duk da cewa gurin da suke da tazara mai tsayi da cikin gidan. Ganin ta'ki ta daina kukan ne yasa ya d'auke ta kai tsaye d'aki ya nufa da ita a rungume a jikinsa yana cigaba da lallabata, kan kirjinsa ya kwantar da ita ya matseta tsam! da zai samu shima kukan zai yi domin komai ya dawo masa sabo. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 71&72 "Ina gurin aiki sai ganin Sadiya nayi a kaina. Na san dama hakan zata faru, ko ga yanayin da naga yarinyar, idanuwanta sunyi jawur! da alama ta ci kuka ta 'koshi. na ce" Menene? nan take sheda min cewa gida babu lafiya na je ana nema na." hankalina na kan babur din da nake gyarawa, na ce "taje kawai gani nan zuwa." Koda na shiga gidan hayaniya hayaniya ce kawai take tashi. muryar Hajiya tafi ta kowa sai sababi take, ta inda take shiga ba tanan take fita ba. shigowata yasa suka saurara, Inna Samira ce 'kanwar mamana, suke musayar yawu da Hajiyan, yayin da mahaifiyartawa ke cikin d'aki tana zubar da hawaye, wannan shine abinda ya d'aga min hankali, kuma nayi nadamar abinda na aikata, wanda na san shine musabbabin tashin hankalin da yake afkuwa a gidan. " Ka shige ciki zanyi magana da kai." Hajiya ce ta bani wannan umarnin, ban yi mata jayayya ba, na bi bayanta. nan na gan su a zaune ita da mahaifinta wato Baba Auta fuskarsa a murtuke! ina mika masa hannu domin mu gaisa amma bai ko kalle ni ba. Na samu gefe na tsuguna ina sauraran abinda zai biyo baya. Ta fashe! da kuka! fuskarta kaca-kaca da hawaye! take fadin" Saddiku cin mutuncin da za kayi mana kenan? saboda 'kasa ta rufe idon ubanka, shiyasa kake nuna min iyakata, babu damar na yanke hukunci a gidan nan, sai kasa kafa ka tsallake, amma kara wannan, idan mahaifiyarka ta ajiye baka iya tsallakewa saboda kana gudin 'bacin ranta, amma ni dana haifi ubanka ka raina ni, Sadiya ta shirya maka karya da gaskiya ka hau kai ka zauna, shin yaushe Fatima ta zagi uwarka da har zaka sake ta, akan wannan dalilin da bashi da tushe ballanatana maka ma." Zanyi magana ya daga min hannu da fad'in" Dakata" sai nayi shuru ina kallonsa. yayi 'kwafa! yana girgiza kansa da fadin" Aure duka wata hud'u da 'yan kwanaki har ka soma wulakanta min yarinyata! menene abin jin haushi anan, saboda kawai ta nemi hakkinta na aure shine zaka sake ta, idan baka da lafiya ba sai ka fada mana ba, a nema maka magani." Murmushin takaici nayi na ce" Lafiyata lau, kawai ban yarda da nayi kwanan aure da ita kai tsaye ba, sai mun je asibiti likita ya aunta, domin gabad'ayanku kun san abinda yake faruwa. Sai ya fusata! ya rufe ni da fad'a zagi ta uwa ta uba! duk ina kallonsa ina kuma 'kara jin haushin 'yarsa a cikin zuciyata, an aura min ita ba don ina sonta ba, amma ana bina da cin mutunci. Ta sassauta murya da fad'in" Saddiku kada ka bani kunya mana kayi wa Allah da annabi ka dau aniya a zuciyarka ka mayar da matarka dakinta, kada ka manta fa 'yar uwarka ce, duk abubuwan da suka faru a baya ka daina tunawa, ka fuskanci abinda abinda yake gabanka. Ganin ta sassauta yasa na ce"To shikkenan zanyi shawara akan al'amarin... ya katse ni ta hanyar fadin." Kada ma Allah yasa ka mayar da ita mana, ko ka d'auka kai kad'ai ne namiji a duniya shashasha mara mutunci kawai" Na ce" Baba auta idan an ciza a hura! kai babba ne kuma kanin mahaifina, ka dinga sanin irin maganar da zaka fada a kaina, domin ina tsoron watarana ka fusatani na mayar maka da martani" Da kumfar baki ya ce" Ka mayar mana, ai babu lefi tunda kana ganin ka isa" Ta ce" Ya isa haka Auta abi komai a sannu a hankali, domin shima duk abinda yake yana da hujja akai saboda haka rarrashinsa za ayi" Shuru yayi yana cin magani. ita kuma Fatiman sai ta hau kuka! tana fadin" Sai Allah ya saka mata a kan zargin da ake mata, tunda ita dai bata ta'ba sanin wani d'a namiji ba. Ni dai tashi nayi na bar su a gurin suna mayar da magana, na shiga dakin Mamana na same su a zaune jigum! Inna Samira na kwantar mata da hankali, itama zuwanta gidan kenan, sai ta riski irin cin zarafin da akewa 'yar uwarta, wannan dalilin yasa ta shiga ciki fad'an, domin kare mutuncin yar uwarta. Ta kalle ni kafin ta ce" 'Dan gaske, wannan ya zama na farko kuma ya zama na 'karshe! kada ka kuskura wani sa'bani ya sake had'aka da matarka ka sake ta, ko bayan raina ban amince da hakan ba. Na ce" Umma ba zan iya zama da matar da zata zage ki ba, wallahi duk son da nake mata zan rabu da ita, muddun ba zata martabaki ba, to ballantana wannan da kin san ba sonta nake ba, akan me zata ci mutuncinki ba." Ta ce" Wannan ba hujja bace, ba kuma dalili ne da zai sanya ka saki matarka a kai ba." Na ce" Wallahi Umma kin fi karfin komai a guri na, kamar yanda na fada miki da farko ba zan zauna da matar da zata ci zarafinki ba." Ta ce" A gaban idonka Fatima ta zage ni?" na girgiza kai da fadin" A'a amma Sadiya ta tabbatar min, kuma na san ba za tayi k'arya ba." Ta 'bata rai da fadin" To na gargad'e ka, ka daina yanke hukunci sai ka tabbatar da gaskiyar lamari, domin sakin Fatima na nufin abubuwa da yawa a gidan nan, ciki kuwa har da rashin kwanciyar hankalina, bayan haka kuma ina mai baka umarni yanzu-yanzu ka mayar da matarka, wannan shine farin ciki na" Cikin 'bacin rai ta kai k'arshen maganar . Na ce" Shikkenan Umma na mayar da ita kamar yanda ki ka bukata. Ta ce" Allah yayi maka albarka, ka je ka d'auke ta ku tafi gida, kuma ka tabbatar da cewa ka bata hakkinta na aure, kada ta sake zuwa gidan nan, da wata matsala." Na ce" Insha Allahu komai ya wuce zanyi k'ok'arin bin umarninki. Addua sosai tayi min kafin na tashi daga gurin. To wannan shine abinda ya faru, hakan yasa na kwanta da Fatima kwanciya irin ta sunnah, amma kash! ban same ta cikakkiyar mace ba, wanda dama na san hakan zata iya faruwa. Koda na tsira ta a d'aki domin ta fad'a min iyakacin mazan da take mu'amula dasu, sai ta rushe! da kuka ta dinga ranste-rantse! kan cewa; babu wani namiji da ta kwanta dashi, na ce to ya akayi ban same ta cikakkiya ba, nan ta sheda min abinda suke yi da 'kawayenta (Madigo) hankalina ya tashi sosai! a lokacin, amma ban yi 'kasa a gwiwa ba, nayi mata nasiha mai ratsa jiki, ta ce min insha Allahu ba zata sake ba. Saboda yanayin magungunan matan da take sha yasa kullum sai na neme ta, kuma bana iya ha'kura nayi sau d'aya sai nayi sau biyu zuwa uku sannan nake jin daidai, babu lefi ina jin dadin auratayya da ita sosai, saboda ta gama fahimtar abinda nake so. Rayuwa tana tafiya da dad'i babu, haka muke zaune, amma duk wani hakki nata ina kokarin saukewa, to sai da tabbatar da cewa na saki jikina da ita sannan ta 'bullo da wata manufa, kullum bata yarda da na kwanta da ita sai na bata kud'i! Ni kuma bani da hakuri ko kadan ta wannan 'bangaran, gashi na riga ba saba da ita bana iya kwanciya bacci sai nayi tara da ita, wannan dalilin yasa hankalina yake tashi a duk lokacin da bani da kudin da zan bata, domin sai an kai ruwa rana, take amincewa da b'ukata ta. Cikin wannan halin ta samu ciki, sai ta tsiri nu'kufurci! 'bacin rai iri-iri! idan na tambayeta abinda ke damunta, sai ta ce min babu komai, ashe cikin ne bata so, ni kuma a lokacin farin ciki yasa na kasa hakuri na shedawa Mamana da Hajiyata, sunyi murna sosai! mussaman mahaifiyata da kullum idan naje gidan sai ta bani tsaraba irin ta masu ciki ta ce na kai mata. Yanda na kai mata sak'on haka za ta bari su lalace! suyi funfuna, sai dai a zubar a shara, ga k'azanta domin ta daina komai a gidan, sai dai da safe kafin na fita aiki na gyara. Ranar litinin 'Kawarta Jamila ta zo da sassafe! sam! bana 'kaunar yarinyar, dalili bata da kamun kai ko kad'an, shiyasa bana sakar mata fuska. Ta same ni a d'aki ina shiryawa domin fita aiki, "Asibiti zan je." ta fad'a kamar bata so. na ce" Ai yana da kyau, dama tuntuni nake ce miki kije domin a duba lafiyarki, data baby, yanzu me kike bukata?" "Ku zaka bani." a lokacin na dauki dubu biyu na bata, tayi wa kudin wani irin riko kafin ta ce"Dubu biyu me za tayi min gaskiya sai dai na fasa zuwa" Na ce" Yau ban tashi da kudi ba, kiyi hakuri kiyi maleji mana" "Gaskiya ba zan iya ba" tafad'a tare da ajiye min kud'in tana kokarin fita, sai na ce "Zo ga dubu daya na kara miki." Ta ce" Dubu biyar zaka bani domin har scanning za ayi min." Da yake ina so taje asibiti a lokacin, haka na dauki dubu biyar din na bata, ashe zubar da cikin suka tafi. Ni dai na dawo gidan na ganta a galabaice, na ce" lafiya dai." sai ta ce" Gajiya ce kawa." Na ce" Ba kiyi girgi ba kenan? kai ta daga alamar eh! da kaina na shiga kicin din nayi mana shinkafa da wake. Da daddare kafin mu kwanta nake tambayarta takardar scanning, sai ta ce" ai sakamakon bai fito ba." ban kawo komai a raina ba, na kwanta domin huta gajiya. Sati biyu da faruwar al'amarin, sai naga ta warware! tana ta walwala babu alamun laulayi a tare da ita, al'amarin ya bani mamaki sosai, na ce" Da alama dai magungunan da na siyo miki suna da kyau, naga kwana biyu kin samu lafiya" Ta'be bakinta tayi can kasan ma'koshi ta ce" Na dai rabu da jaraba." Na ce." Me kika ce?" shuru tayi bata tanka ba, sai nasha jinin jikina domin duk da tayi maganar a can k'asan mak'oshi, sai da na fahimta. Na ce" Baki da gaskiya Fatima kin rabu da jaraba ko?" Ta ce" Eh mana ni wallahi ba zan haihu yanzu ba." Gabana na faduwa na ce" Me kike nufi kenan?" "Zubar dashi nayi" ta fada hankalinta kwance! Ban san sanda na kai mata wani mugun mari ba wanda yasa hancinta fitar da jini! Jikina na rawa na ce" Cikin nawa ki ka zubar akan me?" Ta tashi tsaye hannunta dafe da kumatunta ta ce" Saboda yana bani wahala kuma ban shirya haihuwa yanzu ba" A zafafe! na sake zabga mata wani marin! na ce" Me na rage ki dashi a gidan nan? duk neman da nake akanki yake 'karewa, me yasa za kiyi min wannan wulakancin?" Tana kuka take fadin" Kada ka sake mari na" na ce " Duka zanyi miki ma yanzu" da sauri na je na rufe kofar d'akin, na sanya blet na zane ta ciki da waje sai da na huce! fushina! sannan na kyale ta, na ce kuma lallai kada na dawo na sameta a gidana. Tana kuka take fad'in"Ai dama ko baka fad'a ba, mugu azzalimi kawai" fita kawai nayi na k'yaleta domin idan ba hakan nayi ba, to zan iya kashe ta har lahira, saboda takaicin da ta 'kunsa min." [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 73&74 'Bacin rai ne mai tsanani ya biyo bayan al'amarin da ya faru tsakanina da Fatima, domin zuwa tayi ta juya maganar, ta ce na rufe ta a daki nayi mata dukan tsiya! har sai da cikin jikinta ya zube! duk yanda naso da na kare kaina abin ya fassakara domin babu wanda ya tsaya ya saurareni, mussaman mahaifiyata da ta dauki fushi! mai tsanani! wanda ya d'aga min hankali mutu'ka! na dinga bata hakuri, amma fafur! taki saurarata, sai dai 'kyar na samu tayi min magana kan cewa; muddun ina so naga farin cikinta, to naje na bawa matata hakuri akan abinda na aikata, sannan na nemi gafarar Hajiya da shi kansa Baba Auta, to fushin Ummana yana da ala'ka da rashin kwanciyar hankalina, wannan dalilin yasa dole na sauke duk wani 'bacin raina, na je na samu Hajiya na bata hakuri, itama dai magana d'aya ce wato na je na bawa Baba Auta Hakuri da 'yarsa, haka nan, ba don raina yaso ba na nufi gidan, sai dai nasha wulakanci ba k'arami ba a gurin Baba Auta ya dinga nannago ba'kaken maganganu ya narka min, haka dai na daure na dinga bashi hakuri, kafin ya bari Fatima ta dawo gidana sai da ya kafa min sharad'ai! na ce na amince duk don samun zaman lafiya, da gujewa fushin mahaifiyata. To koda ta dawo gidan, sai dana kai zuciyata nesa sannan na fara mu'amula da ita, amma na daina sakar mata fuska, kuma na sanya mata matakan tsaro sosai domin na hana duk wasu 'kawayenta zuwa gidan. Da yake idan na fita tun safe bana dawowa gida sai wajejen sha biyu na dare, domin wani sa'in da daddare kasuwa tafi bud'ewa ga wad'anda basu da bukatar shiga gidan mai, sai su tsaya a gurina su saya, gefe guda kuma idan faci ko gyara ya samu ina yi duk domin asiri na ya rufu. Tun safe na tashi da ciwon kai, na san hakan baya rasa nasaba da rashin samun wadataccen bacci, na daddafa na fita domin nasan ko na zauna a gidan don hutawa, 'bacin rai ne zai biyo baya gwara fitar tawa tafi alfanu. Ina tsammanin ko rabin awa banyi da zama gurin aikin ba, na kasa jurewa domin saboda tsananin ciwon kai har jiri nake, sai na yanke shawarar komawa gida na samu nasha magani na kwanta Sai dai me? tun daga nesa na hango 'katon 'kwado! a jikin kofar gidan, raina ya 'baci ainun! wato a duk sanda na sanya 'kafa na fita daga gidan, itama rufewa take ta tafi nata guri. Allah yasa ina da mukulli a hannuna kawai sai na bude gidan na shiga, yanda na fita na bar shi a hargitse babu gyara haka yake bata gyara ba. Damuwa sosai na shiga da wannan abu da faru, kuma zuciyata ta dinga munanan tunane-tunane a kanta. A takaice! dai Fatima bata dawo gidan ba sai bayan isha'i! tayi sallama ta shigo jikinta duk a sanyaye, lokacin ina kwance kan doguwar kujera na d'an ji dadin jikina, sakamakon magungunan dana sha, amma duk da haka sai da mai chamis din ya bani shawara cewa naje asibiti likita ya duba ni saboda yanda nake kuka da ciwon kai. Ta zo ta tsaya a kaina tana wuri-wuri! tare da shirya karya da gaskiya, wai gidansu taje Mamanta bata da lafiya. Na kalleta kafin na ce"Kin san dai ban yi kama da wanda zai yarda da wannan shirmen ba ko?" "Wallahi tallahi ba 'karya nake yi ba ko za kaje ka tambaya ne" Tafad'a tana kokarin kare kanta Zaune na mi'ke na d'aga mata hannu da fadin " Ki fad'a min gaskiya idan kina so ki tsira da lafiyarki, don wallahi tallahi rufe kofa zanyi naci ubanki sai dai duk abinda zai faru ya faru.'' "Ubana kake zagi?" ta fad'a tana nuna 'kirjinta. Na ce" Ba shine yake daure miki gindi ba?" Shuru tayi tana kallona . Na ce" Na fi ki iya sharri! da mugunta! Fatima, duka zanyi miki na zubar miki da ha'kora! don ba zan yarda da munafurci ba, da aure na ki ke zuwa kina neman maza a waje" Sai ta fashe! da kuka da fadin" Wallahi sai Allah ya saka min sharrin da kake min ni 'ban ta'ba kwanciya da wani namiji ba sai kai, amma kullum cikin zargi na kake. Na ce" 'Karya ki ke yawon ta zubar ki ke zuwa bayan na fita dame na gaza miki? na d'auka ko bana son kwanciya dake sai kinyi min dole kuma haka nake 'kure miki gudu! amma shine zaki je ki kwaso mana cuta" Ta tsuguna 'kasan 'kafafuna tana kuka da fadin "Ni dai don Allah ka daina jifa na da irin wannan munanan kalaman, wallahi bana zina, shima lesbian din tunda nayi aure ban sake yi ba, kuma zan gaya maka gaskiyar gurin da nake zuwa. Na zuba mata ido ina kallonta ta ce" Gidan Jamila nake zuwa muna sana'ar dillanci, shine nake samun 'yan kud'i domin nima ina sha'awar na tsaya da k'afafuna, tunda dai kai baka da wata gwagwgwa'bar sana'a." Raina ya 'baci mutu'ka na ce"Yanzu Fatima da 'kananun shekarunki ki ke wannan sana'ar? masifa kike so ki janyo mana ko me?" girgiza kanta tayi. Na ce" Kin ce bani da gwagwagwa'bar sana'a! shin na ta'ba barin ki, da yunwa?" kai ta girgiza. na cigaba da cewa; na gaza miki ta fannin ci dasha da suttura da lafiya da gurin kwanciya? " Ta ce" A'a." na ce" To mai zai sanya ki zubar min da mutunci?" Hakuri ta dinga bani, Na ce" Wannan ya zama na farko da 'karshe kada ki sake fita bada izini na ba, sannan kuma na rabaki da Jamila har abada babu ke babu ita, zan je har gidanta na sameta da wannan maganar." Kamar gaske ta ce" Shikkenan ba zan sake ba nayi alkawari, kuma na rabu da jamila har abada'' jin haka yasa hankalina ya dan kwanta na sassauta mata. To ashe tsugune! bata 'kare ba, domin dai Fatima ha'inata take ta kowanni, idan na siyo kayan abinci na wata guda sai ta kwashe rabi ta siyar, abin ya dinga bani mamaki! ganin cewa mu biyu ne kacal! amma 'karamin buhun shinkafa baya wata d'aya haka nan kwalin taliya ma, mangyada da manja jarka-jarka nake saya da ledar maggi, amma basa kwana goma zuwa sati biyu sun 'kare, sosai na sanya mata ido, anan na gane cewa kwashewa take ta siyarwa da wani mai kanti, dake bayan layinmu, duk na samu wannan hujjojin ne daga gurin al'majirin da yake mana aike-aike! tunda na gane haka sai na daina siyan komai ina aje wa, sai dai kullum idan zan fita zan bata dubu daya ko dari bakwai, tayi awo da cefane! Sai ta shiga damuwa! kullum cikin 'korafi! cewa; kudin da nake bata basa isa komai yayi tsada! shareta kawai nake na kan ce ta cigaba da yi min addu'a idan na samu kudi zan cigaba da siyo mata komai da yawa. Wata da'bi'a da ta tsira kuma shine, duk sanda na dawo gida na cire rigata na shiga wanka sai tayi min binkice ta dauki dubu daya ko biyu a cikin abinda na samu, da yake bana lissafi a can sai na dawo gida shiyasa ban gane ba, sai watarana dana shiga wanka sai naga babu sabulu, na fito kawai sai naga tana zazzage min kudin cikin aljihu tana lissafawa, nan naga ta dauki dubu uku ta daure a bakin zaninta, tashi tayi da sauri zata mayar da rigar sai kawai muka had'a ido! duk sai ta gigice! ta fara wuri-wuri! na daga mata hannu da fadin" Bani kudi na" babu kunya ba tsoron Allah ta kwanto kudin ta bani. Na ce" Tun yaushe ki ke min sata?" "Wallahi yau ne kawai" Tafada muryarta na rawa" Na juya na rufe dakin da sakata na ce" Zaki fada min gaskiya ko sai naci ubanki" Ganin ina kokarin dukanta yasa ta fara kuka da fadin" Ka tsaya don Allah kada ka doke ni zan fad'a maka wallahi wannan shine karo na bakwai ." "Iya adadin nawa ki ka dauka?" na fad'a zuciyata a 'kuntacce! "Dubu goma sha shida kenan" Tafad'a tana yin nesa dani. Na ce" Me za kiyi da kudin?" "Ankon bikin Abulle zan saya dubu talatin da biyar ne, na san idan na fad'a maka ba iya saya min za kayi ba." Wani kuttun bakin ciki ya tokare min wuya.Na ce" Ya akayi ki ka yanke min hukunci bayan baki fad'a min kin ji ta bakina ba" "Dubu talatin fa duka-duka jarin naka guda nawa yake wallahi ba zaka iya say......." Wani bahagon mari na kwada mata, jikina na rawa na ce" Don ubanki da kudin wa za ki saya yanzu?" tayi shuru tana kallona hannunta dafe a kumatu. Na cigaba da cewa; ina jin yanzu har kin had'a dubu goma sha biyar da kudina wanda duk sanda ki ka tashi magana zaki ce bani da jari, ko kuma gwagwgwabar sana'a wannan din kudin ubanki?" Kuka take sosai! na ce" Fito min da kud'ina ko na lahira ya fi ki jin dadi yanzu. Tana kuka ta ce" Ai na riga na bayar dasu na ce zan ciko sauran, don Allah kayi hakuri ka saya min" Na ce"Ai baki biyo hanya ba, wallahi da kin fad'a min cikin mutunci ni mai iya saya miki ne, amma tunda ta wannan hanyar ki ka biyo shikkenan, gobe da wurwuri ki je ki kar'bo min kud'ina idan ba haka ba, ni dake ke ne" Zubewa tayi a kasan dakin tana kuka, ni kuma nasa rigata na fita domin sayo sabulun wanka. Sai da ta kar'bo min kud'ina sannan na 'kyaleta ta sha'ki iska. Kwana biyar da faruwar al'amarin, na dawo gida naga babu kujeru a falo. na tambayeta suna ina? kai tsaye tace ta sayar dasu, domin ta sharewa kanta hawaye! tunda dai nata ne. na ce to shikkenan, mutukar kuwa ta fita zuwa gurin bikin nan, a bakin auranta. Ko a jikinta, biki na zuwa ta dinga zurga-zurga duk ina kallonta ban ce mata komai ba, sai da suka gama bikin tukkuna, da safe ta kwaso wanki za tayi, da zan fita na bata takarda saki, nace" wannan ita ce shedar sakin da nayi mata idan ta manta to na tuna cewa muddun ta fita da niyyar zuwa gidan biki 'kawarta a bakin auranta. Kuka sosai ta dinga yi tana bani hakuri, ban ko saurareta ba nasa 'kafata na fita daga gidan. Wannan abun dana aikata sai da nayi nadama! domin shine silar kwanciyar mamana 'bacin rai da tashin hankali ya janyo mata mutuwar 'barin jiki! kuka sosai nayi da idanuwana ganin mahaifiyata magashiyan rai a hannun Allah, nayi tur! da auran Fatima da kuma 'bakar zuciyata, duk da nasan duk abinda nake yi akan gaskiyata nake domin na kare darajar aure na. Har Mamana ta gama zama a asibiti babu wanda ya taka kafa ya je domin dubata, gabad'aya 'yan uwan mahaifina da ita kanta Hajiyar sun dauki laifi sun d'ora mata cewa; da umarninta nake aikata komai, saboda haka babu su babu ita. Nayi nadama sosai! kuma na zubar da hawayena ganin yanda 'bacin rai da damuwa suka haifarwa da Ummana matsala, 'bari guda na jikinta ya daina aiki, sai an taimaka mata! haka Sadiya take kula da ita, ni kuma ina yi da jikina da aljihuna, kuma nayi mata alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba, sosai tayi min fad'a ta kuma nuna min kuskuran abinda na aikata, cewa saurin saki ba shi da fa'ida ko don gaba kada na sake, tunda yanzu saura igiya daya to nayi kokarin ri'ke ta da kyau muddun raina! har cikin raina nayi nadama na kuma yi mata al'kawari cewa duk abinda Fatima za ta aikata ba zan 'kara daukar matakin sakinta ba. tana daga kwance ta dinga yi min kyawawan addu'o ina amsawa da "Ameen" **** Bayan wasu 'yan wattani da faruwar al'amarin. zamana da Fatima babu yabo babu fallasa, idan rikicin ya ratso mu nayi sosai! kuma ina ladabtar da ita yanda ya kamata don bana daukar wargi, amma ban sake yun'kurin sakinta ba duk irin 'bacin ran da zata sanya ni a ciki ina hakuri, don ko da naga magungunan planning (tsarin iyali) cikin kayanta, ban yi mamaki ba, saboda na san zata aikata abinda ya fi haka, kawai sai na d'auke! maganin na zuba a cikin masai! (shaddah) da yake bata da gaskiya ba ta tambayeni ba, sai dai kawai naga tana ta dube-dube a dakin. A tsakankanin lokacin nake ta shirye-shiryen aurar da Sadiya domin tuntuni aka sanya ranar auran ana d'agawa, saboda yanayi na rayuwa komai ni nake na hidimar auran, cikin 'yan uwan mahaifina babu wanda ya tambayeni me nake shiryawa. Na samu na had'a kudi dubu dari da saba'in wanda zan sayi kayan aikin da zan had'a mata gado da kujeru, da yake duk na iya komai, tunda sana'ar gidanmu ce, bisa tsautsayi na shiga da kudin gida, ashe Fatima taga lokacin dana d'aga kasan gado na ajiye kud'in! wallahi a daran na shiga wanka ta kwashe kudin, kwabo bata bari ba, tana zaune a falo na fito daga wanka na same ta, na ce" Ke kuma zaman me ki ke baki kwanta ba" A sanyaye ta ce" Yanzu Ummana ta kira ni a waya bata da lafiya sun tafi ma asibiti! kasan tana da ciwon suga to shine ya tashi a daran nan. Cikin alhini na ce" Allah sarki! addua za kiyi mata Allah ya bata lafiya." Ta amsa da ameen kafin ta ce"Don Allah ka bari na je tunda dare beyi ba kaji kuma babu nisa a tsakaninmu" Ganin yanda take had'ani da Allah da annabi yasa jikina ya mutu! na ce ta tashi taje Allah ya sawwak'e! aikuwa da saurin gaske tasa hijabi ta kama hanya fita. Har 'karfe goma sha biyu da rabi bata dawo ba, hakan yasa na rufe gidan, domin zuciyata ta aiyyana min cewa a can zata kwana. Har ga Allah ban kawo komai a raina ba, domin sai sauri nake na shirya na fita don gabatar da uzurirrikan dake gabana, ciki kuwa harda zuwa gidansu Fatima domin duba jikin mahaifiyarta Sai dai me ina d'aga kasan gado da niyyar d'aukar kud'i na ga wayam! hankali ya tashi ainun! na sauke katifar gabad'aya tare da karagar gadon wai ko sun fad'a 'kasa! sai dai duk iyakar dubawar da nayi ban ga komai ba sai tarkace da 'kura! Na zube kasan d'akin kaina na wani irin juyawa! tabbas ba kowane ya d'auki kudin nan ba sai Fatima domin na riga na san halinta ciki da waje, amma ya akayi ta san na ajiye kudi a k'asan gadonta, tunda lokacin tana kicin tana aiki. Da 'kyar na rarrafa na fita zuciyata cike da damuwa da tunanin faruwar al'amarin. Sai da na samu saukin aiki tukkuna na kira wayarta nake tambayarta, duk da ina da tabbacin ita ta dauki kudin, amma sai na tsinci kaina da tambayarya, kawai sai ta fashe da kuka da fad'in" Kullum idan na nemi abu na rasa a gidan sai na dinga zarginta, ina d'ora mata sata, alhalin ita bata kwana a gidan ba, gaskiya ita ta gaji da wannan abu. Kashe wayar kawai nayi na rabu da ita, domin dai gabad'aya kaina ya k'ulle na rasa irin tunanin da zanyi. Ko da na shedawa mahaifiyata halin da ake ciki, ta ce nayi hakuri kada na sake maganar, abunda ya samu ayi haka. Na ce"Mama yanzu haka za a kai yarinyar nan gidanta babu gado? hakan kamar bai da ce ba, kuma kin ga daga b'angaran mu ake samun matsala! a kowane lokaci bai kamata a sake d'aga bikin nan ba" Ta ce" Ba za a d'aga ba insha Allahu. za a yi abinda ya sawwa'ka idan ya so da kud'in sadakinta sai a saya mata katifa, ni kuma da 'yan uwana za mu had'u mu saya mata labulaye da kayan kicin, zanin gado da sauran abubuwan bukata" Na ce" Amma Mama ba haka naso ba wallahi, kuma ina da tabbacin cewa Fatima ce ta d'auki kudin nan. Ta ce" Tunda na ce ka bar maganar to kada ka sake tayar da ita. Ajiyar zuciya na sauke da fad'in" Shikkenan Umma Allah yasa mu dace." Ta amsa da "Ameen ya Allah. To a takaice dai haka aka aurar da Sadiya babu gado ballanatana kujeru, hakan yayi wa zuciyata ciwo sosai da sosai, amma na kudire a raina cewa; duk sanda na samu faraga zan sharewa yarinyar hawaye. Sosai na shiga takatsantsan! da Fatima bana yarda na shigo da kudi gidan, ballanatana ta gani ta d'auka, amma ban d'auki matakin komai a kanta ba, kawai na zuba mata idona, cikin zuciyata nake mata adduar shirya a gurin Allah. Cikin watannin da suka gabata, gabad'aya ta sauya hallita lokaci guda tayi wata irin 'kiba da haske na d'aukar magana, fatar jikinta tayi luwai! bayan manya-manyan sutturun da take sanyawa, haka zan dawo gidan na samu tayi abinci mai rai da lafiya, bayan kayan d'aki da ta sanja sabbi irin na company, abin ya dame ni sosai! na zaunar da ita ina tuhumar ta, ta ce" Business suke da Jamila. Na ce "Wane irin business ne wannan da yake kawo muku wannan mahaukatan kudi haka? kuma bana raba ki da Jamila ba?" Ta ce" Order kayan kicin mu kayi daga india, kuma babu yanda za a yi na rabu da Jamila domin abokiyar rufin asiri na ce." Na ce" To naji a ina ki ka samu kud'i? har ki ka fara kasuwanci?" Shuru tayi. Na ce" Yanzu kin tabbatar da zargin da nake miki ko?" Ta'be baki tayi ta ce" To meye ai gashi nan, ni da kai muna cikin jin dad'i! lokaci guda rayuwarmu ta sauya, amma da ka tattare kud'i zakaje kayi gwaninta" Takaice ya rufe lullubeni, na ce" Saboda na rufawa 'kanwata asiri shine gwaninta, Fatima anya kuwa kina da hankali?" D'auke kanta tayi tana surutai! zuciyata tayi zafi sosai! amma sai na daure ban yi mata komai ba na tashi na bata gurin, zuwa nayi na kwanta domin samun nutsuwa, kwana biyu sam bana jin dadin jikina, ciwon kai mai tsanani da jiri, dole dai ko ina so ko bana so naje asibiti likita ya duba ni. Likita ya tabbatar min da cewa jinina ya hau sosai! dole ne kuma na kiyaye shiga damuwa da gujewa duk abinda zai janyo min 'bacin rai! kuma na dinga samun isashen bacci! Banyi mamaki ba, domin na san halin da nake ciki zan iya kasancewa a jerin masu 'karancin lafiya, na tabbatar da cewa; hakan baya rasa nasaba da tashin hankalin da Fatima take jefe rayuwata a ciki. Akan magani aka d'ora ni, na dawo gida ina bin ka'ida, amma na san hakan bashi ne maslaha ba, samun lafiyata yana da ala'ka da Fatima. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 75&76 To ko da taga ina shan magani, bata tambaye ni dalili ba, sai rama nake a tsaitsaye, babu abinda ya dameta, sai narka 'kiba take tana gogewa tare da tu'ammali da sutturu na alfarma, babu wanda zai ga Fatima a lokacin ya ce ita d'in matata ce domin tafi kama da matan hamshakan masu kudi sosai abin yake damuna tare da cin rai! don haka sai na samu iyayenta da maganar, kan cewa su binkici a ina take samun kud'i, domin abinda take yayi yawa. Bud'ar mahaifita wato Baba Auta sai ya ce" Halak take nema domin shi yana da labarin komai, saboda haka kada na sanya mata ido ko nayi mata ba'kin ciki, tunda dai ni bani 'kwakw'kwarar sana'a to babu lefi don ta nema duk rufin asirinmu ne.'' Wannan shine abinda Hajiya ta maimaita domin itama tayi goyi da bayan Fatiman. Sai kawai na tattara na rabu dasu, amma duk sanda na dawo gida ta kawo min abinci, wanda nasan bani nayi cefenan ba, to bana ci haka zai wayi gari ta d'auka ta bawa almajirai tana surutai irin na rashin kunya. Duk da shan 'kwayar da take hakan bai hana Allah Zartar da ikonsa ba, ciki ta samu, kuma bai tashi bayyana kansa ba sai da yayi wata hud'u a jikinta sannan ta gane cewa tana da ciki lokacin da taje asibiti likita ya tabbatar mata da watanninsa. Halin damuwa ta shiga mai tsanani! ta daina walwala a gidan, kullum idan na dawo daga gurin aiki cikin damuwa nake samunta, har dai na gaji na tambayeta, kawai sai ta fara min rashin kunya tana k'okarin zagi na, wai ba zata sake amincewa da bu'katata ba. Na ce" Duk me ya janyo hakan?" tana kuka ta ce" Ciki ne dani watansa hud'u harda kwanaki." Na ce" Na gode Allah! yanzu kin tabbatar da cewa; ba a yiwa Allah wayo ko?" Tayi shuru tana kallona, na ce" Duk abinda ki ke a gidan nan ina sane, nasan cewa kina amfani da k'wayoyin hana daukar ciki, amma na zuba miki ido kawai, saboda kin fi k'arfina Fatima, amma yanzu Ubangiji ya nuna miki cewa baki da dubara." "Wallahi sai na zubar dashi" tafad'a tana gurshe'ken kuka! na ce" To babu lefi sai ki d'aura d'amara" tashi nayi na bata guri, domin ina kallonta zuciyata zata iya tarwatsewa saboda b'akin ciki! Bayan kwanaki shida da faruwar al'amarin, na fita gurin aiki da kamar minti talatin, sai kawai na gilmawar mota ta wuce ta gabana. babu shakka Fatima ce a ciki domin ita d'in ba sabuwar hallita bace a gurina, sai dai wacce take tuka motar ce ban gane ba. Hankalina ya kasa kwanciya domin ba muyi da ita cewa zata fita ba, aiki nake amma gabad'aya hankalina can wani guri. Daf da mariba na tashi daga aiki na nufi gida domin hankalina ya kasa kwanciya, a bud'e naga gidan, sai naji nutsuwa a raina, domin na tsani yawon dare, amma duk da haka sai na tuhumeta wane guri taje d'azu! Ina sanya 'kafa ta a d'akin na ci karo da wata leda viva! a bakin k'ofa, ban kawo komai a cikin raina ba, na shiga dakin na sameta a kwance duk tayi zuru-zuru! Na ce" Fatima ina ki kaje d'azu?" Shuru tayi min, sai da na sake maimaita tambayata tukkuna ta ce" Wani guri na je" na ce" Kin gaya min zaki fita ne?" Ta girgiza kai. na ce" Ina ne wani guri? ko bashi da suna" Zum'bura baki tayi ta ce" Ni fa bana son damuwa don Allah ka rabu dani na ji da ciwon da yake damuna" Na ce" Billahil-lazi la'ilahaillahuwa sai kin fad'a min gurin da ki kaje, idan ba haka ba sai na ji miki ciwo a gidan nan" Zaune ta tashi tana kallona kafin ta ce" Sai dai kuwa ka kashe ni wallahi domin zuwa nayi na zubar da wannan jarabar daka 'kunsa min, ga d'anka can a leda a bakin k'ofa! Da saurin gaske na juya ina kallon bakin kofar, ashe abinda na ci karo dashi gudan jinina ne, jikina na rawa na kalleta da fadin" Yanzu sai da ki ka zubar da cikin nan Fatima?" "To meye amfaninsa, ni wallahi ba zai katse min hanzari ba, domin saudia za mu tafi tare da Jamila zaman shahada" "Innalillahi-wa'inna-ilahi rajiun! wannan adduar nayi ta nanatawa kafin na samu nutsuwa! Na kalleta tana zaune turmin danya babu abinda ya dameta, na ce" Da izinin wa zaki tafi zaman shahada?" "Kai nifa dama na gaji da zama da kai wallahi! dube ka, kullum jiya i yau, babu wani cigaba a tare da kai, ka dube ni da kyau kai kanka, kasan yanzu nafi 'karfinka don haka wallahi dole ka sake ni na gaji" Na ce"Shine hujjarki na zubar min da ciki?" "Kwarai kuwa domin ba zan tafi da nauyinka a kaina ba" Wallahi a lokacin rasa bakin magana nayi domin duk wasu dabaru na sun 'kare, jiki a mace babu kuzari na shiga daki na dafe kaina, hawaye masu tsananin zafi suka shiga kwaranya a saman fuskata. Koda ta shigo d'akin ta sameni ina zubar da hawaye, ko a jikinta, ina kallonta ta shirya ta kama hanya ta fita tana 'kananun maganganu, cewa ita ta gaji da zama cikin talauci, bayan ban gaza mata da komai ba. Ashe kukan da nake shafar mai ne, domin ledar gudanan jinin da aka fara yiwa hallita ta d'auka ta nufi can gidanmu, har d'aki ta samu Mamana a kwance tana fama da kanta ta ajiye mata ledar, tare da fad'in" Gashinan an fara yi masa hallita saboda haka sai ayi masa suttura a aje a binne, ita bata shiryawa haihuwa yanzu ba, bayan haka kuma ta gaji da zama cikin talauci lallai ita a sawwa'ke mata, domin ta je ta auri daidai da ita" Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! ai tana fita daga dakin da 'yan mintina Mamana ta had'iyi zuciya ta mutu, sai gawa muka tarar! likita kuma ya tabbatar min da cewa zuciyarta ce ta buga sakamakon 'bacin ran da ta jima a ciki. Wallahi na shiga tashin hankali da damuwa a lokacin, domin kamar zautacce haka na dawo, babu ci babu sha! na rasa ina zan tsoma rayuwata na ji sanyi, gashi a lokacin kowa ya san Fatima ce sanadin mutuwar mahaifiyata amma saboda rashin adalci suka ce a lullub'e maganar kada wasu a waje su ji abinda yake faruwa. Amma Hajiya jikinta yayi sanyi sosai! domin kuka sosai ta dinga yi lokacin da aka fito da Mamana za a kai ta, gidanta na gaskiya sai neman afuwarta take. Har aka share makoki Fatima bata tako k'afarta gidan ba, daga karshe ma sai samun labari nayi cewa; sun tafi saudia ita Jamila 'kawarta. A lokacin Hajiya tayi tur! da Allah wadai da halinta, ta kuma kira Baba Auta ta rufe shi da fad'a sosai! da yake 'yar tasa ta toshe masa baki da kud'i ko gezau! bai nuna damuwarsa ba, sai ma ya ce" Shi ya gaji idan auran nan, ba zai yiwu ba to a rabu kawai domin ya gaji da sasanci." Hajiya ranta ya 'baci sosai! a take gurin ta umarce ni dana sake ta, ban jira komai ba na furta cewa na sake ta, na kuma rubuta a rubuce, na bashi sheda! bai damu ba, ya kar'ba tare da buge rigarsa ya ta tashi ya tafi ya bar mu a zaune a gurin cikin tsananin mamaki. A tsakankanin lokacin sai da na kwanta a asibiti domin tsananin ciwon kai da ya addabe ni, jina ne ya hau sosai! sai da likitoci suka rufu a kaina da kuma taimakon Allah na samu lafiya, na dawo gida da tarin magunguna tare da kokarin cire damuwa daga cikin raina, kamar yanda likitana ya bu'kata. Wata uku da rasuwar Mamana wani abokina da mu kayi karatu tare dashi a kano, ya kira ni a waya ce maza na zo ya samar min aiki a wani kamfani, amma nazo da takarduna. Banyi 'kasa a gwiwa ba, na shedawa Hajiya halin da ake ciki, tayi min addu'a sosai kafin na kama hanya na tafi. Faruk ya dafa kafad'a ta da fadin Abokina insha Allah wahalarmu ta 'kare domin "Babban kamfanin sarrafa shinkafa ne dake unguwar harad'a suke neman injiniyoyi irinmu, wannan dalilin yasa na kira ka nace maza kazo ko Allah zai sa a dace, domin ni har na fara zuwa aiki cikin satin da ya gabata" Na ce" Na gode sosai Faruk Allah ya 'kara zumunci" ya ce."Babu komai abokina duk yiwa kai ne. To shi dama lamarin ubangiji ne yana faruwa ne a lokacin da ba kayi tsammani ba, kuma wani lokacin baka samun farin ciki kai tsaye sai an jarabce ka. Kasancewar takarduna sunyi kyau sosai! yasa aka daukeni aiki, akan matsayi mai girma! da albashi mai tsoka, kuma da yake shugaban company yana da tarihin rayuwata, wallahi gida ya dauka ya bani tare da abun hawa mota sabuwa mai kyau da 'kwari! Nayi masa addua sosai da sosai! kuma na d'auki alkawarin yin aiki cikin gaskiya da amana. Wannan shine mafarin dawowata garin Kano da zama, tare da Hajiya na tare a sabon gidana domin tun bayan rasuwar mahaifiyata take tausaya min, wannan dalilin yasa ta ce " Duk inda nake tana gurin" Baba Auta ya dinga kishi! ya kuma kasa 'boye hassadarsa akan abun alherin dana samu. 'Bangaran Baba Audu kuwa addua yayi min sosai, wannan yasa na dauki kudi masu yawa na bashi. Sadiya ma har gidanta na je na kwantar mata da hankali, na ce duk abinda take bukata ta kira ni, a waya insha Allah zan share mata hawaye! cikin damuwa muka rabu da juna. *** Bayan shekara biyu da fara aiki na, rayuwa ta sauya min sosai! hankalina ya kwanta domin bani da wata matsala gagarima, kullum cikin nasara nake fita aiki na kuma dawo cikin fatahi! Rana tsaka Fatima ta kira ni a waya, nayi mamaki sosai! na d'aga wayar muka gaisa, na ce "Ina fatan lafiya? Sai cewa tayi " Kayi hakuri da abinda ya faru" Na ce"Shine dalilin kiran?" Ta ce"A'a" na ce" To ina sauraranki" Ta ce" Na samu labarin abun alherin da ya sameka Allah ya sanya alheri ya kara d'aukaka" Na amsa da "ameen ya Allah" Ta ce"Ka bani address din gidanka zan zo maka da wani albishir wanda zai sanya ka farin ciki." Tsaki na ja da fadin" Baki da hankali har yanzu Fatima" sai kawai na kashe waya ta na rabu da ita, tayi ta kira ban daga ba har ta gaji ta hakura Ina tsammanin number wayata ta bibiya har ta samu gidana.karfe takwas na dare sai ganinta mu kayi tare da wata 'karamar yarinya da bata fi shekara daya da rabi ba. Duka muka zuba mata ido da kallon mamaki a fuskokinmu, kawai sai ta zube kasan kafet tana kuka! tare da rungume yarinyar a jikinta! Hajiya ta je ta kama yarinyar tana duddubata, sai ta kalleni bakinta na rawa, nima yarinyar kawai na zubawa ido ganin fuskarta irin tawa sak! sai dai bata da haske sosai! gabana ya dinga fad'uwa ina kiran sunan Allah a zuciyata cikin raina naji cewa wannan yarinyar 'yata ce domin kama take da Sadiya 'kanwata. Hajiya ta ce"Fatima wannan kukan da ki ke bashi da wani amfani, kiyi mana bayanin matsayin wannan yarinyar." Ta share hawaye murya a dashe ta ce" 'Yarsa ce" gabad'aya muka zuba mata ido. Ta cigaba da cewa" Bayan naje likita yayi min allurar zubar da ciki, ashe tagwaye ne (twins) kuma d'aya ne ya fita. shima likitan be gane ba, saboda Allah ya 'boye al'amarinsa, sai bayan na je saudia domin fara gudanar da harkokina, kawai ciki ya bayyana, koda na je asibiti domin a zubar, likitan ya tabbatar min da cewa ba zai fita ba, domin kuwa ya riga ya girma, idan kuma na tsananta to zan iya rasa rayuwata, wannan dalilin yasa na hak'ura har na haifeta, amma na shiga damuwa sosai, saboda ina fargaba kada na kawo maka yarinyar kace ba kai ne ubanta ba, sai dai nayi farin ciki sosai da Allah yasa yarinyar tayi kama da kai, don Allah Hajiya ku yafe min." Hajiya ta dinga kuka tana fadin" Fatima kinga ikon Allah ko? yanzu kin tabbatar da cewa, ba a yiwa Allah wayo tunda ya saukar da ishara a kanki, ya kamata kiyi hankali kuma" Ta ce"Wallahi Hajiya nayi nadama sosai, na san kuma abinda na aikata ba dai-dai bane don Allah ki bashi hakuri ya mayar dani d'akina" Na kalleta zuciyata cike da b'akin ciki abinda ta aikata Na ce"Har abada aure ya haramta a tsakaninmu, idan kin manta to bari na tuna miki, saki d'aya sau uku nayi miki, ba kuma a lokaci guda ba, ballanatana ki kawo min wani k'auli da ba'adi! saki uku ya halarta a kanki, ni dake har abada mun gama zaman aure, wannan yarinya kuma na 'karba Allah yayi mata albarka" Sosai take kuka tana bani hakuri wai idan aka tambayi malamai za su iya gyara lamarin, kallon mahaukaciya kawai nake mata, ina ji Hajiya na tambayarta sunan yarinyar ta ce" Sunan mahaifiyarsa nasa mata wato Aisha, amma sai nake kiranta da Shukura" Ta ce"Aikuwa kin kyauta da ki ka sanya mata sunan Aisha, Allah yasa ta gaji halinta. Tashi nayi na basu guri domin zamana a gurin ina kallon fuskarta yana tuna min da munanan abubuwan da suka faru a baya. Wannan shine mafarin dawowar Shukura hannuna, domin hana ta tafiya nayi da ita, Hajiya ta cigaba da rainonta, ita kuma tunda ta tabbatar da cewa ba zan mayar da ita ba, sai ta fara biye-biyen malamai, daga 'karshe dai ta je tayi auran kisan wuta wanda ko wata uku ba tayi ba ta fito, ta zo ta matsanta min cewa lallai sai na mayar da ita gidana, sai da nayi mata jan ido sosai! ta saurara min, na nuna mata cewa ko babu mata a duniya sai ita wallahi ba zan 'kara zaman aure da ita ba. "Wannan shine tarihin rayuwata da Fatima matata ta farko, kuma Uwar Shukura, kasancewar asubah ta gabato zan tsaya miki a nan kafin na cigaba da baki labarin abinda ya wuce.. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 78&79 Hannunsa ri'ke da fulas mai d'an girma ya shigo dakin, ido na tsira masa har ya 'karaso gurin da nake zaune, cikin taushin murya ya ce" Tashi ga abincin na samo miki gurin Hajiya." Shuru nayi ban ce komai ba, kuma bani da niyyar tashi. Ya ajiye fulas din kan dirowa, ya hayo gadon yana k'okarin janyo ni, Na cire hannunsa da fad'in" Don Allah ka daina ta'ba ni." A sakarce ya kalle ni, kafin ya girgiza kansa, yanayinsa ya nuna kamar ya fara gajiya da abinda nake masa, ni kuwa duk abinda nake yi, baya damuna, domin har yanzu ban yi na'am dashi a cikin zuciyata ba, amma kuma ina mamakin yanda yake min rawar jiki, kuma ina kallon tsagwaron sona a cikin 'kwayoyin idanuwansa. Kansa ya sunkyar k'asa yayi shuru tare da tsirawa k'asa ido! wannan ya sake tabbatar min da cewa; ransa a 'bace yake da abubuwan da nake masa. Jiki a sanyaye na sauko daga gadon, na shiga band'akin dake cikin dakin, na wanko hannuna na fito, na same shi a yanda yake, kusa da kafafunsa na zauna tare da janyo abincin na bud'e, abinci ne mai rai da lafiya, sai 'kamshi yake, lokaci 'kank'ani yunwar da nake ji ta dawo sabuwa, hannu nasa da bissimillah a bakina na fara cin abincin. Tashi yayi ya fita, minti uku ya shigo da ruwa da lemo ya ajiye a gabana, kunya duk ta rufe ni ganin irin hidimar da yake min, ni kaina na san abinda nake masa bana kyautawa. a hankali na ce" Sannu" bai amsa ba, kawai ya nemi gefen gado ya zauna tare da kunna wayarsa yana dubawa. Har na kammala cin abincin, hankalinsa yana kan wayarsa, na je na wanke hannuna, na zaune can 'karshen gado. A nutse ya kalle ni tare da fad'in" Kin 'koshi?" shuru nayi ina kallonsa don ban ji abinda ya fad'a ba. Murya ya bud'e kafin ya sake maimaita maganarsa. kai na d'aga masa alamar "Eh na ko'shi. Ya ce" Kin shirya saurarata yanzu?" Cikin jin nauyi na ce"Eh" sai ya ajiye wayar hannunsa a kusa dashi, wannan karon beyi yun'kurin rungume ni ba, sai dai ya mayar da hankalinsa kaina sosai kafin ya cigaba da bani labarin rayuwarsa. "Zinaru, 'kanwar maigida na ce, ina nufin mutumin da nake aiki a 'kar'kashinsa, ni dai da bakina da nasa ban ta'ba fad'a masa cewar bani da aure ba, sai kawai ya same ni da wata magana wacce na kasa yin jayyaya dashi. "Saddiku na yaba da hankali da nutsuwarka, wananan dalilin yasa nake neman wata alfarma a gurinka, ina fatan zan samu. Na ce" Alhaji wace irin alfarma ce wannan?" domin ni a gani na mai nake dashi da har zai nemi alfarma a guri na. Ya ce" 'Kanwata nake so ka aura" gabana ne ya fad'i! na kalle shi tare da fad'in" Alhaji ai ina da aure" Murmushi yayi kafin ya ce" Allah ta'alah hud'u ya ce mu aura mutukar muna da iko! to ballanatana kuma na san da cewa; baka da aure, na samu labari a bakin abokinka Faruk, wannan dalilin yasa na nemi wannan alfarmar a gurinka. Wato Faruk ne ya fad'a masa cewa; bani da aure, amma gaskiya ban ji dad'in abinda yayi min ba domin kwata-kwata babu maganar aure a tare dani, amma tunda al'amarin ya kasance haka, dole nayi hakuri, domin ba zan iya jayayya da wanda ya rufa min asiri ba. Na ce" Alhaji Na gode da wannan kyauta da kayi min, tabbas hakane, bani da aure a yanzu, amma shekarun baya na auri 'yar uwata har da rabo a tsakaninmu." Ya ce" Ma sha Allah. ai duk Faruk ya fad'a min komai. amma idan kana ganin da akwai matsala sai na janye. Na ce" Haba Alhaji ai kafi 'karfin komai a guri na wallahi, zan auri 'kanwarka kamar yanda ka bu'kata" Ya ce" Na gode sosai Saddiku da wannan rufin asirin da kayi min, sai dai kuma hanzari ba gudu ba" Shuru yayi fuskarsa da alamun damuwa. Na ce" Alhaji da akwai matsala kenan?" Ya gyad'a kansa da fad'in" 'Kwarai kuwa Saddiku ba zan munafurce ka ba, yarinyar nan ta d'an yi yawo gaskiyar magana kenan, bana tsammanin za a samu budurci a tare da ita, bayan haka kuma tana da aljanu, wanda muke tunanin sune suke sanyata aikata munanan ayyuka" Gabad'aya jikina ya mutu! cikin zuciyata nake tasbihi ga Ubangiji duba da irin kaddarar da take wanzuwa a tattare dani, ba zan ta'ba bijirewa umarnin Alhaji Harazimi ba, domin yayi min abinda ba zan manta ba. Na ce" Alhaji kada ka damu. auran Zinaru a gare ni, kamar jahadi ne, mutukar tayi istibura'i zan aureta na kuma zauna da ita da zuciya d'aya, maganar aljanu kuma, ba su fi k'arfin Allah ba, insha Allahu zanyi iyakar bakin kokarina akan hakan. Nan da nan, ya saki fuskarsa cikin jin dadin lafazi na, ya ce" Na gode sosai Saddiku Allah ya saka maka da alheri, hakika ka rufa min asiri a lokacin da nake bukatar hakan, a duniya bani da matsalar komai, sai ta Zinaru, 'kanwata ce, mu biyu iyayenmu suka haifa, asali mutumin Nijar ne, cikin zinder aka haife ni, neman kudi ya kawo ni Najeria, har nayi aure na tara iyali na, bayan rasuwar iyayenmu, Zinaru ta dawo hannuna, wallahi tunda ta zama cikakkiyar budurwa ta gagare ni, babu irin dukan da ban yi mata ba, amma k'arshe sai ta tattara kayanta ta gudu, sai tayi wata uku hud'u sannan zata dawo gida, wannan dalilin yasa na daina dukanta, sai na tsananta da addu'a tare da sanya matakan tsaro a gidana, amma duk da hakan, sai ta fita yawo, maza na d'aukarta a mota su tafi uwa duniya, wannan shine dalilin da yasa na yanke shawarar yi mata aure, ko Allah zai sanya ta shiryu. Cikin damuwa na ce" Ranka ya dad'e ka kwantar da hankalinka, duk abinda yayi farko, yana da 'karshe! ni nayi maka al'kawarin ri'ke yarinyar nan amana, zanyi iyakar bakin 'kok'ari na insha Allahu. Sosai ya dinga yi min godiya har sai da ya bani tausayi. Wallahi Shahida idan kin ga Zinaru, sai ki dauka ita tayi kanta saboda tsananin kyau! domin ta ko'ina tayi, cikakkiyar mace kyakykyawa, tana da duk abinda namiji yake bukata, dama na fad'a miki asalinsu, 'yan nijar ne, buzaye ne gashinta har baya gata da kyau! sai dai rashin kyawun hali. Amma kin san wani abu, wallahi kwata-kwata ni ba ta kwanta min a raina ba, kawai dai na aureta ne saboda d'an uwanta, dama can a tsari na bana son auran kyakykyawar mace, saboda wasu dalilai nawa. Zuwa na gurinta sau d'aya aka d'aura aure ta tare a gidana, washe garin ranar d'aurin auran Alhaji Harazimi yayi min kyautar d'aya daga cikin kamfaninsa na shinkafa! sosai al'amarin ya bani tsoro mutu'ka! na kalle shi a lokacin da yake bani takardun kamfanin, na ce"Alhaji kada muyi haka da kai, don Allah ka janye wannan kyautar, wallahi ban auri yarinyar nan don abun hannunka ba, na aureta ne tsakani da Allah, da kuma darajarka, amma ban aureta don ka bani wani abu ba. Murmushi yayi tare da cewa" Saddiku ba ka ji bahaushe yana fad'in" Yaba kyauta tukwici ba, wallahi zan iya mallaka maka duk kadarorina, saboda rufamin asiri da kayi, ka auri 'yar uwata ba tare da ka 'kyamace ta ba, a wannan zamanin da kowane uba yake kokarin samawa 'ya'yansa uwa ta gari, sannan ba kowa ne zai yarda ya auri mace irin Zinaru ba, ai ni ka gama yi min komai, saboda haka kyauta nayi maka, kuma babu mai canza ta, ina bukatar ka tsaya da k'afafunka saboda nauyin iyali, tunda akwai yaran da su kayi iya aiki ta dalilinka, to za su cigaba da zama a 'kar'kashina, amma kai na 'yantaka insha Allahu. Gabadaya sai jikina yayi sanyi da kalamansa, hannu biyu nasa na 'karbi takardun ina godiya. Ya ce" Zaka cigaba da gudanar da komai na kamfanin, domin ya riga ya bar hannuna, kuma na tara duk ma'aikatan dake karkashin kamfanin na sheda mu su komai, saboda haka kanka tsaye, zaka cigaba da gabatar da komai." Na ce" Na gode sosai Alhaji Ubangiji Allah ya 'kara suttura duniya da lahira, Allah ya amfani zuria" ya amsa da "amen ya Allah tare da mi'ko min hannu mu kayi sallama. Abota ta da Alhaji Faruk babu ganin 'kyashi, ya taya ni murna sosai, kuma ya taimaka min ta hanyoyi da dama, har kawowa yanzu muna tare muna gudanar da harkokinmu. Hajiya tayi farin cikin alherin da ya same ni tare da duk wani mai k'aunata, amma a zahiri ina ganin masu yi min hassada! sai dai tsakani na dasu addu'a ce. Zama na da Zinaru da farkon fari, yayi dad'i sosai, don har na dinga k'ok'arin sanyata cikin zuciyata domin a lokacin ina ganin kamar tayi hankali ta nutsu ta shiryu kamar yanda muke bu'kata, don tun da na fahimci cewa; tana cikin jerin jarababbun mata nake kokarin ganin na kawar mata da sha'awarta a duk lokacin da ta bukaci hakan daga gare ni, sai dai ashe duka aikin banza nake, domin duk kokarin da nake akanta fita take yi tabi abokan shashancinta da aurena a kanta. Hajiya ce ta tare ni da maganar ranar litinin da sassafe na fito da shirin fita ta ce" Saddiku ina son magana da kai." Yanayin fuskarta kawai na kalla na fahimci cewa maganar da za tayi tana da muhimmanci, duk da sauri nake a lokacin, sai na nemi guri na zauna tare da fadin" To Hajiya ina sauraranki. Ta ce" Duk dai shiga tsakanin ma'aurata babu kyau, amma ni gaskiya abinda ake a gidan nan, ya fara damuna. Na ce" Hajiya wani abu yana faruwa ne?" Shuru tayi tana girgiza kai kafin ta ce" Matarka bata da gaskiya Saddiku, domin tana aikata abubuwa marasa kyau! Gabana ya fadi jin abinda tace, da saurin na ce" Me take aikatawa?" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Kullum bata zama a gida, ka na fita take ficewa, kuma bata dawowa sai dare, sannan duk san da take gida wani mutum kullum sai ya zo gurinta su shiga daki, na ta'ba tambayarta shin wanane shi? sai tace ai d'an uwanta ne, ban yarda ba domin kwata-kwata basa kama da juna, wannan dalilin yasa nake zarginta." [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 77&78 Saukar ajiyar zuciyarta yake ji tare da sheshshekar kukanta, wanda yake masa tsananin zafi a cikin ransa, shima kukan zucci yake, sakamakon tuna abunda ya wuce na daga rayuwarsa, hannu yasa ya dinga goge mata hawaye yana rarrashinta da kalamai masu sanyi, har ya samu tayi shiru ta daina kukan, ya matse ta tsam! a kirjinsa yana jijjigata kamar 'yar goye. Kiran sallar asubahi ne ya raba tsakaninsu, a hankali ya cire ta daga jikinsa ya tashi ya shiga toilet domin d'aura alwala. Sai da yayi wanka tukkuna sannan ya d'aura alwala a gurguje ya fito daga band'akin, nan ya sameta a zaune gefen gado. kallon juna sukayi, yayi mata murmushi na mussaman kafin ya bud'e k'ofa ya fita, sai ta bishi da kallo tana mamakin al'amarin, gabad'aya jikinta ne ya mutu sakamakon jin labarinsa, ta rasa wane tunani za tayi domin gani take kamar ita d'in ba ta dace dashi ba, duba da matsayi da mu'kamin sa, ya kere mata nesa ba kusa ba, ya za'ayi ta saki jiki dashi ta kwantar da hankali har tayi rayuwar aure dashi. *** Tunanin da na jima a cikinsa shine rayuwar aure da talaka dai-dai da ni, don wallahi ban ta'ba sanyawa raina auran mai kudi ba, duba da lalura ta, bayan haka kuma bani da wani kyau na kuzo a gani, sai kuma gani a matsayin matar babban mutum! wanda jama'a suke alfahari dashi, wannan kad'ai ya isa na godewa Allah a bisa ni'imar da yayi min. to amma a raina nake jin kamar auran namu akwai matsala ta kowane 'bangare. Wanka nayi na shirya jikina cikin riga da siket na atamfa, mai kawai na shafa a jikina na gyara gashin kaina, ban d'aura dankwalin ba, sai kawai na yafa a kaina na fito falo na zauna, tunani yayi min katutu! domin kwata-kwata na kasa shiga kicin ballantana nayi tunanin abinda zan ci, da damuwa gami da fargaba sun taru sun cushe min ciki bana sha'awar komai . Haka ya shigo ya same ni cikin wannan halin. kallo d'aya nayi masa nayi saurin kawar da kaina, yayi bala'in kyau cikin 'kananun kayan da yake sanye a jikinsa, mutum ne shi mai wani irin kwarjini da haiba wanda da yawa mutane basa iya had'a ido dashi, sosai k:ananun kayan su kayi masa kyau, ya dawo matashin saurayi, farin gilashin da yake tu'ammali dashi a koda yaushe, yana 'kara masa kyau mutu'ka! Kusa dani ya zauna jikinmu har yana had'uwa 'kamshin turaransa duk ya dabaibaye gurin. Gefe na d'an matsa ina wasa da yatsun hannuna. Ya kama hannun da fad'in." Yaushe za a yi min lalle ('kunshi) irin na amare ina bukata" yana maganar ne lokacin da ya had'a yatsunmu guri daya. Jikina ya d'an mutu sakamakon jinsa a kusa dani, namijin 'kokari nayi gurin gaishe shi. Ya amsa tare da sa bakinsa daidai kunne na ya ce." Ya gajiyar kuka?" Murmushi nayi na ce" Labarinka ya bani tausayi sosai! amma kayi hakuri jarrabawa kowa da irin tashi, sannan ka godewa Allah da ni'imar da yayi maka." Ya ce" Kullum a cikin godiyar Allah nake, gashi yanzu ya amsa min addu'a ta, ya azurtani da mar'atussaliha" "Nayi mamakin sosai da wannan al'amarin, amma ya akai kake sauya hallitarka? don wallahi ban ta'ba tsammanin kaine kake kasancewa mutum biyu. Dariya yayi ya ce" Zan baki labari anan gaba, ni dai burina ki saki jiki da ni, ki ri'ke ni amana, domin nasha wahala a hannunku, shiyasa nake tsoronku, amma dai ina da tabbacin ke ba zaki wahalar dani ba ko?" Yanda ya fad'i maganar ne ya bani dariya da tausayi. Na ce" Auranka nawa?" "Wannan shine na uku kuma ina rokon Allah yasa nayi dace." Ya fada tare da rintse hannuna da nasa. Shuru kawai nayi ban ce komai ba. "Kinyi shuru ko baki amince dani a matsayin miji ba" Na ce" Ni dai gaskiya sai nayi tunani tukkuna, domin naga kamar kana da dabi'ar auri saki, ita mace tana da rauni me yasa ba za kayi hakuri da hallayar mata ba. "Bangane abinda ki ke nufi ba" yafada da alamun rashin dadi a tare dashi. Na ce" Ni ina tunanin wani abu ne" Hannuna ya ri'ke jikinsa na rawa ya ce" Ki daina tunani a kaina matata kuma kada ki dauki abinda nayi miki da wata manufa! nayi hakan ne domin na gwada ki kuma alhamdulillhi, kin yi d'ari bisa d'ari! ni yanzu na ga matar aure." Ido kawai na zuba masa ina auna maganganunsa, yayin da shi kuma ya zage! sai kalaman soyayya yake zuba min tare da rarrashi da daukar alkawari. Na ce" Ni dai gaskiya zan fad'a maka abinda yake zuciyata shine, ba zan iya rayuwar aure da kai ba" Cikin rashin jin dadin furucina ya ce." Saboda me ki ke wannan maganar menene dani da ba zaki amince mu raya sunnar ma'aiki ba" Kasa magana nayi saboda yanda ya bani tausayi, nasan har cikin zuciyata nake tausaya masa, amma kwata-kwata bana jin sonsa a cikin raina. Cikin rashin jin dadi, ya tashi ya fita, sai na bishi da kallo, ina tunanin abubuwa da yawa a cikin raina. Minti ashirin da fitarsa, ya dawo amma tare da Hajiya suke, gabana ya fad'i, dama cikin tunanin yanda zata kar'bi al'amarin nake, duba da cewa; yayi abun a rufe bai bayyana gaskiya ba, fuskarta a sake ta nemi kujera ta zauna tana kallona. Saukowa 'kasa nayi na gaisheta, cikin sakin fuska ta amsa gaisuwata sai kallona take wanda ya sanya na tsargu, na shiga wasa da yatsun hannuna tare da k'ok'arin mayar da hawayen dake kokarin zuba. Sai da ta bud'e muryarta sosai sannan ta ce" To ke Shahida idan ban da abunki menene abin damuwa a cikin wannan al'amarin, ai komai na Allahu ne , ni wallahi nayi murna sosai da jin wannan abu, kuma nayi muku fatan alheri, dama buri na kenan yayi aure, to Alhamdulillhi, bukatata ta biya, saboda haka ki kwantar da hankalinki, duk abinda ya same ki, na alheri to halinki ne ya ja miki, domin mijinki yayi min bayanin dukkanin abinda ya faru, don haka ki saki jikinki damu, sannan kuma kiyi hakuri ki 'karbi wannan aure hannu biyu, domin hakan alheri ne. Ajiyar zuciya na sauke na ce" Hajiya al'amarin ne na rasa ina zan ajiye shi a raina, amma cikin zuciyata sai nake tunanin kamar ni ba tsaran auransa bace, bayan haka kuma ina tunanin wani abu." Shi ya rigata magana da fadin" Wannan ba hujja bace Shahida, na san abinda kike tunani, amma bari kiji wani abu, ko kin fi haka rauni ko nakasu! wallahi zan aureki, domin ni bana bukatar kyau! ko wata d'aukaka! tarbiya nake buk'ata da amana, kuma na samu da yardar Allah, saboda haka kisa a ranki cewa; ni naki ne har abada kuma uban 'ya'yanki." Kallonshi nayi, tare da girgiza kaina, domin ni abinda nake dubawa daban da tunaninsa. Ta ce" Nima hankalina ya kwanta da yarinyar nan Alhaji Habu, saboda haka kayi k'ok'arin rarrashinta domin ta samu nutsuwa." Ya ce." Insha Allahu Hajiya." Ta kalleni tare da cewa" Shahida ni zan tafi amma don Allah kada ki bijirewa auranan, kiyi hakuri ki zauna tare damu kinji ko" Tausayi ta bani sosai! na ce" To shikkenan Hajiya nima na gode sosai" To tunda ya fita bai sake shigowa ba sai bayan isha'i, ya shigo ya same ni kan dadduma na idar da sallah, ina addu'a. Zama yayi kusa dani tare da d'aga hannunsa sama yana fadin" Allah ka mallaka min zuciyar matata ka bamu zuria masu albarka. Ina jinsa yana ta addu'oi, nima ina yin nawa, na shafa a fuskata, shima shima ya shafa, ya kalle ni da murmushi na mussaman a fuskarsa, babu yabo babu fallasa na gaishe shi, ya amsa a lokacin da yake 'kok'arin rike hannuna. da sauri na janye, na tashi na bar shi a gurin. Beyi zuciya ba, ya sake zuwa kusa dani ya zauna tare da rungumo ni jikinsa, kawai sai na fashe da kuka! ina ture shi! " Ka matsa daga kusa dani" Ya ce" Me yasa zan matsa bayan ke din halalina ce'' "Ni ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba, domin baka cikin tsari na" Na fad'a tare da cire hannunsa da d'ora a saman cinyata. Ido ya zuba min da alamun damuwa a tare dashi ya ce" Menene abinda ba kya so a tare dani?" Shuru nayi masa, ya ce" Kada fa ki butulcewa Allah Shahida." Ajiyar zuciya na sauke da fad'in" Nafiso na auri daidai da ni, mai rauni da rangwamin gata. Ya ce"Sai kuma Allah ya baki Saddiku a matsayin miji shin ya za kiyi kenan? da yanayi na 'bacin rai yayi maganar. Tashi nayi na shiga d'aki na kwanta tare da tsirawa rufin d'akin ido! hawaye masu zafi suke zuba, shin ya zanyi ne? na san Ubangiji ya gama yi min komai da ya mallaka min babban mutumin mai daraja irin wannan, amma a jikina nake jin kamar akwai abinda zai faru mara dad'i dangane da auransa. Shigowarsa d'akin yasa nayi saurin goge hawayena, ya ce" Kina yi min asarar hawayenki wanda ya fi gold tsada a gurina, bari kiji wallahi duk abinda za kiyi ba zan rabu dake ba, domin ni naga matar aure. Kallonsa nayi a lokacin da yake maganar, nan naga tsagwaron sona a cikin k'wayoyin idanuwansa. Ya ce" Yini guda duk kin rasa sukuni! kinyi rama ta ba gaira ba dalili, kowane bawa fa, da kaddararsa, ke taki k'addarar auran dattijo wato Saddiku, kuma kin shigo hannunsa kenan, domin ba zan iya rayuwa babu ke ba. Na ce" Aikuwa ba zaka samu nutsuwar da kake bukata ba, tunda dai ni bana 'kaunarka, tausayinka kawai nake ji, kuma ban san ya za'ayi nayi rayuwar aure da kai ba. Murmushi yayi kafin ya ce" To tunda akwai tausayi ni na tabbata da akwai k'auna, amma mu je zuwa dai tunda kin fad'i haka. Juya masa baya nayi tare da rintse idona! sai kawai na jishi a kusa dani, yana k'okarin rungume ni! na ture shi da karfi! na tashi zaune tare da matsawa 'kuryar gado! Kallo na yayi na minti biyu kafin ya ce" Kin san dai hukuncin matar da take 'kauracewa mijinta ko?" Gabana ya fad'i! da jin maganarsa. Cikin rawar murya na ce" To me kake nufi?" Murmushi yayi wanda ya tsaya iya fatar bakinsa ya ce." Bana nufin komai sai alheri, ko zan kar'bi hakkina ba yanzu ba sai zuciyarki ta aminta dani, amma yanzu ina so ki bani hankali domin cigaba da warware miki abinda ya faru da rayuwata wanda baki sani ba, ina so na baki labarin d'aukakata da kuma cigaban labarin zaman aure na da matata ta biyu. Jin haka yasa na kalle shi da fad'in" Ya sunanta?" "Zinaru" yafad'a yana kallon fuskata. baki na ta'be da fad'in" Yunwa nake ji yanzu" sauka yayi daga gadon, ya kama hanyar fita ba tare da yace min komai ba, nima na bishi da kallo tare da nazari da tunanin abubuwa da yawa a tare da ni, da shi. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 80&81 Kafin nayi magana sai ga ta fito, kamar wacce take la'be, ta tsaya 'kerere! a kan mu, ta nuna Hajiya da yatsa tare da fad'in'' To magulmaciya tsohuwa mai zuwa lahira da 'ko'kon dambu, duk na ji abinda ki ke fad'a masa sharri za kiyi min Allah ya isa tsakani na dake." tana wata irin girgiza irin ta rashin mutunci take maganar. Kaina ya d'aure mutu'ka! na kalli Hajiya dake zaune idanuwanta sun ciko da ruwan hawaye sakamakon cin mutuncin da Zinaru ke mata, zuciyata ta cika da tausayinta, na kalle ta har yanzu tana tsaye a kan mu babu alamun risina a tare da ita, raina a 'bace na tashi tare da tsinka mata mari a fuskarta, cikin takaici da bak'in cikin abinda ta aikata na ce" Hajiyar tawa ki ke kira da magulmaciya saboda baki da mutunci." "To idan ba magulmaciya ba mai zai sanya ta zaunar da kai tana shirya maka magana wallahi duk abinda ta fad'a sharri tayi min" Ta karasa maganar cikin k'okarin kare kanta. Na ce" Wallahi ki iya bakin ki, muddun kina bukatar zama da ni to dole ne sai kin daraja Hajiyata mutu'kar kuwa ba haka ba, to zamu sa kafar wando daya dake. "To sai me ? tafad'a tana buga cinya kafin ta cigaba da cewa; kai bari ka ji wallahi ba zan zauna kana taka ni ba, al halin na san da dukiyar d'an uwana kake fankama, akan me? wannan tsohuwar zata sanya min ido a gida har tana fada maka cewa; ina fita yawo to 'karya take munafuka ce" Jikina na tsuma! na sake kai mata wani marin, ta kauce ban same ta ba, Hajiya ta tashi ta rirri'ke ni tana hana ni dukanta, ganin haka yasa tayi mana kallon banza tare da jan dogon tsaki! ta shiga daki ta bugo kofar da karfin gaske! Zubewa nayi kan kujera tare da dafe kaina zuciyata in ban da zafi babu abinda take, Hajiya ita ta dinga tausar zuciyata har na samu sukunin tafiya ofis, amma duk da haka da 'bacin rai na yini, har sai da abokina Alhaji Faruk ya fahimci ina da damuwa. ya matsanta min sai na sanar dashi halin da ake ciki. Ya ce" Ban yi mamakin faruwar wannan abu ba, domin dama can yarinyar bata da mutunci, sai dai shawarar da zan baka shine ka kula sosai, kuma ka sanya matakan tsaro a cikin gidanka, gudun kada ta je ta dauko wani ciwo ta kawo maka gida, ko kuma ta d'auko cikin wani ta kawo maka. Na ce" Aboki na wallahi ni duk a tunanina yarinyar nan, ta shiryu ta daina duk wasu halaye marasa kyau! wannan dalilin ne ma ya sanya na saki jikina da ita har nake mu'amular aure da ita, ashe yaudarata take, tana ha'inta ta. "Kayi hakuri abokina kaddara kowa da irin tasa amma ni kaina ina jajanta maka auran Zinaru, sai dai nayi maka alkawari insha Allahu, zan sanya ka cikin addu'ata, Allah ya kawo maka mafita. Jikina a sanyaye na amsa da "ameen suma ameen abokina. Gabad'aya daina shiga sabgar ta nayi, sannan kuma na saka matakan tsaro sosai a gidan, duk a k'okarin na ganin na kare martabar aurena. Hakan da nayi sai ya sanya ta cikin damuwa mai tsanani, ashe kullum idan na fita zuwa take har d'akin Hajiya ta ci mata mutunci iya son ranta, watarana dai Shukura ta kasa daurewa ta mayar mata da martani, tunda a lokacin yarinyar tana da shekara goma sha biyu, ta fara sanin ciwon kanta. Aikuwa kamar jira take, sai ta zari wayar redio ta kama yarinyar ta dinga dukanta kamar wacce Allah ya aiko, Hajiya tayi-tayi ta 'kwace yarinyar daga hannunta ta kasa, k'arshe ma ta dinga had'awa da ita tana duka. Sosai ta farfasawa yarinyar jiki, da wayar redio, amma abin mamaki! ina dawowa gidan ta same ni tana kuka tare da fadin" Shukura tayi mata rashin kunya har da zagi, na tambayeta dalili sai ta fara kame-kame, ganin haka yasa na ce ta je zan d'auki mataki akan hakan. Lokacin da Hajiya take yi min bayanin abinda ya faru. sai ta fito ta zauna duk abinda Hajiyar ta fad'a sai tace 'karya ne ba haka bane, na kalle ta da tsananin b'acin rai a tare dani na ce" Zinaru idan na sake jin maganarki sai ranki ya 'baci." shuru tayi tana zabgawa Hajiyar Harara. Hajiya ta gama yi min bayanin duk abinda ya faru, raina ya 'baci sosai tunda na fahimci cewa babu laifin tsaye bare na zaune ta kama yarinyar da duka har sai da shatin waya ya fito a jikinta, na ce" Wallahi Zinaru, duk sanda ki ka sake dukan yarinyar nan sai na rama mata, domin ita d'in ba jakarki ba ce, da zaki kama duka sai kace an aiko ki, ina so wannan ya zama na farko ya kuma zama na 'karshe. 'Budar bakinta sai ta ce" A wai! to ai 'yar taka ba cikakkiya bace, domin ita da shegiya ba su da maraba, duk ina da labarin komai, tsohuwar matarka ta je yawo can saudia ta d'auko cikin shege, ta haife ta kawo maka, saboda kai shakatafe ne kazo kana murna, wannan yarinyar duk ina da labarin komai a kanta" Hajiya ta fashe da kuka tana fadin" Ki ji tsoron Allah Zinaru, ki bi duniya a sannu." Tsaki ta ja mana kafin ta tashi ta shige daki ta bar mu cikin damuwa da tashin hankali. Hajiya da Shukura kuka suke, ni kam! gabad'aya ma na rasa tunanin me nake, Shukura na tabbata jinina ce amma a gaban idona ana sheganta min ita, a lokacin idanuwana suka ciko da 'kwallah, babu shakka Fatima tayi mana gi'bi a rayuwarmu. Gabad'aya gidan haka muka kwana da b'acin rai! in ka cire ita wacce ta haddasa mana damuwar kwana tayi tana shaye-shaye! na tabbatar da hakan ne, lokacin dana shiga d'akinta domin na nuna mata kuskuran da ta aikata. Wallahi numfashi kasa sha'ka nayi sakamakon mugun warin da ya cika dakin, kwayoyi ne da kwala'ben kayan maye har da guntayen sigari wanda ta sha, tana kwance a kasan kafet tana ta sharar bacci. Hankali a tashe na je ofis na kasa katabus! tunani da damuwa sunyi min katutu! ashe ba iyakar bin maza Zinaru keyi ba har da shaye-shaye? wannan abu ya tsaya min a rai sosai da sosai. Bala'i ne ya faru bayan fita ta, domin Fatima ce ta je gidan, bayan dawowarta daga dubai! da yake kasuwanci take sosai, to duk sanda ta samu sukuni tana zuwa ta gaishe da Hajiya sannan ta duba Shukura, sai ta same su cikin damuwa! domin ita bata san ma nayi aure ba a lokacin, 'bacin rai da kishi suka rufe mata ido, lokacin da Hajiya take kuka tana fad'a mata abubuwan dake faruwa. Ta duba jikin Shukura ta ga shatin duka a ko'ina, mayafi ta cire kawai ta nufi dakin Zinaru domin d'aukar fansa. Fad'a da zage-zage su kayi sosai a d'akin, kafin su fito falo, nan ma suka cigaba da cin mutuncin junansu, tare da jifan kansu da munanan kalmomi. Zinaru ita ta fara d'auko makami (wu'ka) wai sai ta kashe Fatima sai ta ga wanda ya tsaya mata. Hajiya Hankalinta ya tashi sosai, gudun kada suyi aika-aika, yasa ta umarci Shukura ta kira ni da wayar mamanta, tana kuka take sheda min abinda yake faruwa. Taimakon Allah ne kawai ya kawo ni gidan, lokacin dana shiga na samu Fatima a ruwan cikin Zinaru! sai dukanta take, don Allah ne ya bata sa'a ta 'kwace wukar, ta samu galaba a kanta. Da 'kyar na iya janye Fatima na juya ina yi mata fad'a, kawai sai saukar wu'ka na ji a baya na, Zinaru ta soke ni da ita, lokaci guda jini ya jika riga ta yana d'iga a gurin. da gudu ta shiga dak'i ta kulle 'kofa! Hankali a tashe suka rirrik'e ni suna kuka, ni kam ni kad'ai na san azabar na da nake ji, sosai wu'kar ta hud'a jikina. Asibiti muka nufa. Emagency su ka bani taimakon gaggawa, sai dana na kwana tukkuna na dawo gida da tarin magunguna, bayana nannad'e da bandaji. Ban iya fad'awa Alhaji Harazimi komai ba, kawai dai na ce dashi tsautsayi ne ya ritsa ni wani mai babur ya buge ni lokacin dana fito daga mota ta. Bayan tafiyarsa abokina Alhaji Faruk! Ya ce" Gaskiya ka bani mamaki Alhaji Saddiku mai zai sanya ka rufa mata asiri, wallahi bari na fada maka da yarinyar nan da ta samu nasara a kanka kashe ka za tayi, to mai yasa za ka cigaba da zama da ita, tunda ta zama annoba, kamata yayi ka shedawa d'an uwanta halin da ake ciki, cewa; tunda akayi auran nan baka samu kwanciyar hankali ba. Girgiza kaina nayi na ce" Ba zan iya fad'awa Alhaji Harazimi wannan al'amari ba, domin ni nayi masa al'kawari cewa; zan jure zanyi hakuri da halayen 'yar uwarsa, kuma idan ka duba akwai shekaru a tare dashi, wanda ya kamata a ce yana samun nutsuwa da kwanciyar hankali a irin wannan lokacin, wallahi da bakinsa ya sheda min cewa, a duniya bashi da damuwar kowa sai ta Zinaru, ita kad'ai ce matsalarsa, to mai zai sanya na fad'a masa abinda zai d'aga masa hankali, wallahi ko yarinyar nan, zata kashe ni ba zan fad'a masa abunda zai d'aga masa hankali ba, zan cigaba da bashi amsa d'aya a duk lokacin da ya tambaye ni zan ce masa muna zaune lafiya. Shuru yayi yana jinjina kai! na san yana mamakin karfin hali na, wanda ba kowa ne zai iya jurar wannan al'amari ba. To har na 'karaci jinyyata Zinaru ba ta ce min sannu ba, sai dai duk san da ta ji muryar Fatima a gidan, za ta fito daga d'akinta ta nemi fitina, ni nake tsawatarwa da Fatima, a lokacin zata ci mutuncinta sosai tare da fad'in sai dai gani daga nesa amma Saddiku ya fi 'karfinta, wani lokacin Fatima har kuka take saboda takaici da 'bacin rai! Tsayin sati hud'u bana kula ta, don gabad'aya na ajiye ta a gefe guda, sabgogin gabana kawai nake, sai ta same ni a daki bayan na dawo daga ofis, ta nemi guri ta zauna tana kallona. Na ce" Kina bukatar wani abu ne?" "Eh ina da magana da kai" tafada tare da tsira min ido, lokacin na karanci abinda yake damunta. Babu walwala a tare dani na ce" Ina sauraranki. "Ka san dai ba dutse ka ajiye a gidanka ba ko?" Shuru nayi tare da tsira mata ido! ta cigaba da cewa" Tsayin sati hudu da kwanaki baka kula ni ballantana ka bani hakkina na aure, to gaskiya ni dai wallahi na gaji, idan ba zaka iya ba ka sake ni na fita na samu wanda zai d'ebi min kewa" Zama nayi ina fuskantarta na ce" Zinaru lafiya ta ki ke bu'kata ko?" "Ban gane ba?" tafad'a tana ta'be baki. Na ce" Kwanana nawa a kwance ina jinyya wanda kece sanadi amma baki duba ni ba, ballanatana kiyi min sannu, yanzu Allah ya bani lafiya kin zo kina min wata maganar banza. Shuru tayi tare da sunkuyar da kanta. Na ce" Kin yi min abubuwa masu muni! amma na ajiye su a gefe ba don komai ba, sai don ina duba wani abu, kada ki dauka kin fi k'arfi na, ko kuma tsoro ya hana ni, d'aukar mataki a kanki, ko d'aya, ina da yanda zanyi dake wallahi ina duba wani abu ne amma da ba don haka ba, zaki san asalin waye Saddi'ku" "Ka ga nifa ban nemi wata magana ba, ni fa dole akayi min na aureka amma wallahi na fi jin dad'in zama a haka, idan namiji nake bu'kata akwai su kala-kala sai wanda nayi ra'ayi. Cike da takaici nake kallonta kafin na ce" Ki ji tsoron Allah wallahi, kuma ki bi duniya a sannu idan ba haka ba zaki yi nadama a rayuwarki, menene abin tunk'aho gurin aikata zina? menene abin burgewa? da har ki ke tutiya da aikata alfasha! kina ta 'kama da kyau! da surar jiki ko? to ki sa ni lokaci guda ubangiji na iya juya hallitarki, ki zama abar tsoro abar 'kyama, a gurin mazan dake bibiyarki, su guje ki, babu abun burgewa a gurin aikata abinda Allah ya haramta don haka wallahi kiyi hattara" Lokacin jikinta yayi sanyi, da alama nasiha ta, ta ratsa mata jiki. Na cigaba da cewa" Kada ki sake kiran Shukura da shegiya domin yin hakan, zai sa ni dake mu sa kafar wando d'aya domin ita kad'ai gare ni, kuma ni ne ubanta. Ta ce" To ai nima 'kawata ce ta fad'a min cewa; sun zauna d'aki d'aya da Fatiman a saudia kuma ta tabbatar min da cewa Fatiman 'yar iska ce tana bin maza." Takaici ya cika min zuciyata, na ce" To 'karya take miki, lokacin dana rabu da Fatima tana tare da ciki na, idan kin duba sosai za ki ga kama a tsakanina da Shukura don haka kada na sake jin wannan maganar ta fito daga bakin ki." Ta ce" To na ji ni dai gaskiya idan kana so mu samu zaman lafiya ka cigaba da bani hakkina, domin shine dalilin da yasa zuciyata take zafi wani lokacin. Na ce"Babu damuwa in dai wannan ne, zanyi kokarin sauke hakkinki da yake kaina." lokaci 'kan'kani ta saki fuskarta har tana bani labarai, ni dai jin ta kawai nake cikin zuciyata nake mamakin halayenta, wani sa'in ina gazgata maganar d'an uwanta, lallai tana da matsalar mutanan 'boye! [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 82&83 Haka na cigaba da zama da Zinaru da dad'i ba dad'i nake ha'kuri da halayen ta ina kawar da kaina gudun 'bacin rai da rikice domin duk ranar dana dau'ki mataki akan rashin arzi'kin da take a gidan, iskokai! take tayarwa ta yini ta nayi wani sa'in har kwana take tana buge-buge da birgima! duk abinda ya zo hannunta d'auka take ta kai min duka dashi!Zinaru ta yi min rauni a jikina wanda ba zai lissafu ba, damuwa da fargaba gami da tashin hankali yasa ciwona ya ke tashi akai-aikai, wanda kusan duk sati sai na ga likita ya duba ni tare da bani shawarwari! wasu al'amuran nawa duk sun tsaya sakamakon masifar da nake ciki, gashi a lokacin Allah ya bud'e min 'kofafin samu ta ko'ina, bayan kamfanin shinkafa da Alhaji Harazimi ya bani kyautarsa, cikin hukuncin Allah na bud'e wani kamfanin amma na sumunti, sai gonaki uku da na saya nake noma wake da alkama da kuma gero, harkoki na sun bud'e sosai! kuma ina samun alheri fiye da tunaninki, a lokacin abokina Alhaji Faruk yake tsokana ta da fad'in "Zinaru ita ce matar arziki na taurarinmu sun zo d'aya, wai tunda na aure ta nake samun d'aukaka da cigaba, murmushi kawai nayi a lokacin na tabbatar masa da cewa; ni ban yarda da wannan hasashen ba, na fi yarda da cewa; Ubangiji ne kawai yake saukar da ikonsa akaina, domin shi yake bayar wa, kuma shi yake hana wa, sai kuma tasirin addu'ar iyaye na dake bibiyar rayuwarta. Hajiya na mutu'kar ha'kurin zama da Zinaru domin rashin kunya take mata sosai! bata shakkar zaginta a ko'ina, ga gori kala-kala! duk ranar da Shukura tayi gangancin mayar mata da martani, to babu zaman lafiya a gidan, domin dukan tsiya take mata har sai ta fitar da mata da jini, 'karfi ne da ita sosai! wanda na tabbata da cewa; aljanun da take tare da ita ne suke tunzurata aikata munanan ayyuka! domin wasu lokutan na sha farkawa daga bacci na ganta a tsaye a kaina da wu'ka! sai nayi namijin 'ko'kari! nake fita daga dakin, wannan dalilin ya sa na daina kwana a d'akinta, sai dai duk ranar da take da wata bu'kata sai kawo kanta d'aki na. Ranar Asabar ban fita ba saboda ba na jin dadi, cikin baccin da nake na dinga jin hayaniya! a firgice! na tashi zaune, ina kiran sunan Allah. can na ji muryarta tana d'urawa Hajiya zagi! rai na a 'bace! na tashi na fita sai na same ta tsaye a kan Hajiyan tana nu na ta da yatsa sai rashin mutunci take mata, Hajiyan kanta a sunkuye sai share hawaye take, raina ya 'baci mutuk'a! mari na tsinka mata tare da yin ball da ita gurin! Hajiya ta rirri'ke ni tana bani hak'uri! ina sake kai mata duka da 'kafata! ji nake kamar na fashe da kuka saboda ba'kin ciki, tabbas auran Zinaru bai 'kare ni da komai ba sai tozarci! kai na tayo tana kuka ta ci kwalar riga ta ta dinga zagi na tana kuka wai dole sai na sake ta, ko kuma ta kashe ni. Nayi-nayi na k'wace! daga hannunta na kasa saboda ri'kon kamar ba nata ba, zagi na take ta uwa ta uba, bakinta duk ya tara wata irin kumfa! a lokacin na tsorata! sosai sai kawai na dinga karanta mata ayatul-kursiyu ina tofa mata a fuska! hakan yasa ta sassaura ri'kon da tayi min, na finkice! da sauri na nufi d'aki na. Kafin nayi wani yun'kuri! ta shigo dakin, ta buga 'kofar da k'arfi ta rufe! tayo kaina! da kokawa sosai ta kama ni! mu dinga bi kusurwa-kusurwa da ita, nayi mamakin 'karfinta dan ban samu galaba a kanta ba, da 'kyar! na samu na rarrashe ta na ce ta zauna muyi magana ta fahimta, ta ce itafa ba zata zauna ba sai na rubuta mata takardar saki. na ce ni ba zan sake ta ba har abada domin al'kawari nayi wa d'an uwanta. nan ta tabbatar min da cewa; wallahi sai ta kashe ni mutu'kar ban rabu da ita ba. jin haka sai jikina yayi sanyi na kalle ta tare da fad'in" Zaki iya kashe ni Zinaru? ta ce" 'Kwarai kuwa mutukar baka rubuta min takardar saki ba. na ce to shikkenan kiyi hakuri zanyi shawara ki bani kwana biyu. jin haka yasa ta sakar min wuyan riga ta fita daga d'akin tana numfarfashi! Kwana nayi ina tunanin hanyar da zan bi gurin ganin nayi wa tufkar hanci, tabbas Zinaru tana iya kashe ni tunda ta furta to hakan yake a zuciyarta, maslaha kawai na samu d'an uwanta da maganar domin mu tattauna. Alhaji Harazimi bai yi mamakin jin haka daga gare ni ba, ya ce." Abinda ya fi haka Zinaru za ta aikata, shiyasa na ce maka wasu lokotan ba ita take aikatawa wasu abubuwan ba, mutanan da suke tare da ita ne, amma ina 'kara neman alfarma a gurinka, wannan ita ce ta 'karshe idan abin ya ci tura to na baka wu'ka da nama ka sake ta domin ba zan bari ta cutar da kai ba. Na ce" Alhaji wace alfarma ce wannan?" Ya ce" Za mu d'auko malamai su yi mata ru'kiya idan Allah yasa an dace iskokin sun rabu da ita shikkenan, domin dana ta'ba tuntu'bar wani malami da maganar, nan yake tabbatar min da cewa; iskokin da suke tare da ita da wuya su rabu da ita saboda na gado ne, wallahi tun daga lokacin jikina yayi sanyi, domin ba zan manta ba, Mahaifiyarmu ma haka tayi ta fama dasu a lokotan baya, don dai ita tana da rik'o da addini ne shiyasa basa wahalar da ita sosai. Ajiyar zuciya na sauke na ce"Shikkenan Alhaji yanda ka ce hakan za 'ayi ina rokon Allah yasa ayi asa'a, domin ni kaina ina tausaya mata wallahi, gabad'aya daga ni har ita muna cikin tashin hankali da damuwa." To malamai uku ne suka rufu a kan Zinaru suna ta karatu har sai da suka sauke al'kur'ani mai girma kana suka fara karatun ru'kiya! a lokacin bacci ne ya kwashe ta wanda ta d'auki tsayin kwana uku ta nayi, domin ni har na tsorata da al'amarin, sai da na kira d'aya daga cikin malaman ya kwantar min da hankali, tare da fad'in" Insha Allahu za ta tashi. Washe gari kwana hud'u kenan, ta tashi idonta cike da kwansa! fuskarta duk ta zurma! gabad'aya ta fita daga hayyacinta, sosai ta bani tausayi don da kaina na had'a mata ruwan wanka na ri'ke hannunta muka shiga band'akin tare na taimaka mata tayi wankan. Kwanciya tayi kan gado bayan ta shirya jikinta tayi lamo! tare da tsirawa rufin d'akin ido, na ce" Kina jin yunwa ko?" kai ta d'aga min alamar Eh, na fita da sauri, na umarci Shukura ta shirya abinci ta kai mata, tare suka shiga da Hajiya suka duba jikinta kafin su fito jikinsu duk a sanyaye! domin duk wanda ya ga Zinaru a lokacin sai ya tausaya mata duba da yanda hallitun ta suka sauya. Sati biyu da faruwar al'amarin. ta warware sosai! kuma muna zaman lafiya domin wata hatsaniya bata sake faruwa ba, tsakaninta da Hajiya ma babu wata matsala. hakan ya sa hankali na ya kwanta, sosai na dinga godewa Allah. na cigaba da gudanar da harkokina na yau da gobe. Ranar talata ya kama kwana ashirin da biyar da yi mata Ru'kiyar muka nema ta muka rasa a gidan. hankali na a tashe na kira wayarta ina tambayarta. kai tsaye ta ce min ta na Swaziland ('kasar waje) gabana na fad'uwa na ce" Me ki ka je yi a can?" Ta ce" Aure za tayi tare da tsohon saurayinta wanda yake aiki a can.'' wani kuttun! bakin ciki ya tokare min a wuya, na ce "Zinaru da aure na za ki auri wani?" ta ce" Eh man, yanzu ai ka sake ni don dole! bana k'aunarka munafiki macuci kawai." Kashe wayar nayi sai kwai na zube a gurin tare da dafe kaina. "Innalillahi wa'ina ilahi raji'un! ka kawai na kira, har na samu sassauci! na dauki waya na kira d'an uwanta na sheda masa halin da ake ciki. cikin 'bacin rai ya ce." Saddiku yanzu na tabbatar da cewa; idan da akwai iska a tare da Zinaru, to akwai hali, wallahi nayi iyakar bakin 'ko'kari na don haka na gaji, na gode sosai da alfarmar da kayi min, saboda haka ka rubuta takardar sakin yarinyar nan ka aiko min da ita, dama ni ne na tilas taka auranta duk da na san da cewa; ba ta dace da kamilin mutum irinka ba, wallahi don ka saki Zinaru hakan ba zai yi min ciwo ba." Cike da tausayinsa cikin raina, na ce" Alhaji kayi hakuri don Allah kada kasa damuwa a cikin ranka har wani ciwo ya kama ka, hakika ina tausaya maka wannan jarabawa da Allah ya dora mana, sannan kuma ka daina cewa; ka gaji, ka cigaba da yi mata addu'a babu abinda ya gagari Ubangiji." Fashewa! yayi da kuka a lokacin tsabar bakin ciki ya kasa cewa komai! kawai sai ya kashe wayar ya bar ni cikin tsananin damuwa! Wannan shine abinda ya faru tsakanina da Zinaru, har Alhaji Harazimi ya rasu ban iya furta kalmar saki ga Zinaru ba, har hazar yau, saboda ina ganin idan na aikata hakan, kamar na so kaina kuma nayi rashin adalci, sosai nake k'aunar mutumin, nake kuma tausaya masa da irin jarrabawar da Allah ya d'ora masa, tunda Zinaru ta bar gari, har yau ba ta dawo ba, sai dai ina samun labari a gurin iyalin Alhaji Harazimi cewa; tana can Swaziland din tayi aure akan aure har da 'ya'ya biyu. Bayan rabuwar mu, hankali na ya kwanta na cigaba da bun'kasa harkokin kasuwanci na, cikin ikon Allah nayi suna a 'kasata da duniya, yanzu haka ina da gidajen mai biyar, tare da kamfanoni da dama, sannan ina harkar sufari ina da jirage uku tare da manyan motoci na daukar kaya, alhamdulillhi, Ubangiji ya azurta ni, da dukiyar da ni kaina ban san adadinta ba, kuma daidai gwargwado ina 'kokarin ganin na sauke hakkin Allah dake kaina, domi duk wanda Ubangiji ya bashi dukiya kamar ya d'ora masa babban nauyi ne, wanda dole sai yayi takatsantsan! ina kokarin ganin na taimaki 'yan uwa da abokanan arziki tare da jama'ar gari da duk wani ma'bukaci. Wannan shine abinda ya faru, shine kuma dalilin da yasa na shirya shiga cikin unguwanni domin neman matar aure, na kuma sauya kammani na zuwa mahaukaci, don kin san a wannan zamanin ba kowace mace ce zata yarda ta auri garma-garma! (mai ta'bin hankali) irina ba, tun lokacin da na fara ganinki na ji kin kwanta min a raina, sai a ka ci sa'a kema kina tausaya min, tun daga lokacin na sanya ki, a raina nake addu'a akan Allah ya tabbatar min dake a matsayin matata, domin ni lalurar ki, sam bata dame ni ba, abubuwa da yawa suka ja hankali na a kan ki, saboda haka ki kwantar da hankali, insha Allah zan nuna miki soyayya fiye da wacce ki ke tunanin mahaukacin nan zai yi miki.'' Ya 'kare maganar da lallausan murmushi a kwance a fuskarsa. Kallon sa kawai nake ina mamakin yanda ya sha gwagwarmaya, zahirin gaskiya ba shi da laifi don ya aikata hakan, domin neman matar aure, na farko wata macen za ta aure shi ne saboda dukiyarsa, mafi akasari abinda yake faruwa kenan, auran kud'i! amma yanzu da yayi hakan ya tabbatar da son gaskiya, kuma yayi abinda duk 'kwa'kwar mutum ba zai gane ba. Hannuwa na ya ri'ke tare da sassauta murya ya ce." Kin yi shiru ba ki ce komai ba. Murmushin ya'ke nayi na ce." Ni kam ba ni da abinda cewa domin har yanzu ina kokwanto akan ka." Shiru yayi na minti uku kafin ya kalle ni da fad'in"Ta shi mu je na nuna miki wani abu wanda zai sake tabbatar miki da gaskiya ta." Ban yi jayayya da shi ba, na tashi kamar yanda ya umarce ni, sai ya ri'ke hannuna muka fita harabar gidan... [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 84&85 Ni dai bin sa nake duk in da ya ajiye 'kafarsa nan nake ajiye tawa, har muka isa wata 'kofa dake wani d'an korido, tsoro na ji ganin gurin yayi duhu da yawa! na ja na tsaya ina 'kokarin cire hannuna dake cikin nasa. a nutse ya kalle ni da fad'in" Menene?" na ce" Wannan d'akin fa?" murmushi yayi kafin ya ce." 'Dakina ne, da nake ajiye muhimman abubuwa, kada ki ji komai ba zan cutar dake ba." Nayi shuru ina kallonsa tare da tunanin wani abu a cikin raina. na ji mutane na fad'in yawanci masu kud'in da sukayi shura a duniya suna da wani 'boyayyan sirri wanda suke aikatawa na sa'bon Allah! haka kawai zuciya bata amince da shi ba, duba da yanayin gurin da ya kawo ni, wani irin d'aki a cikin ciyayi! da wata doguwar 'kofa zururu! gabana na fad'uwa! na ce" Ni dai ba zan shiga ba." Kallona yayi da mamaki a tare da shi ya ce." Saboda me? ko har yanzu ba ki amince da ni ba?" Baki na ta'be da fad'in" A'a kawai ina zargin d'akin ne watak'ila ba abin arzi'ki ne a ciki ba" Yanayinsa ne ya sauya don na fad'in wannan maganar, jikinsa duk yayi sanyi kawai sai ya tsira min ido! ya d'an ban tausayi, amma ban nuna a zahiri ba, sai kawai ma na tafi na bar shi a tsaye a gurin. Sosai ransa ya 'baci da abinda yarinyar take masa, gabad'aya ya rasa gane abinda take nufi, yanayin kallon da take masa shi kad'ai ke damunsa, ya riga ya gama sanya ta a cikin ransa, domin wani irin so yake mata wanda ba zai fasaltu ba, amma yana ganin sai ya sha wahala kafin ya samu kanta, don ganin irin kallon da take masa kamar wanda yayi mata gagarimun laifi. Bai sake tunkarar inda take ba sai wajejan goma da rabi na dare ya shiga gurun da take cikin kayan bacci masu taushi, yana 'kamshin azababben turaransa. Salamarsa kawai na amsa na sunkuyar da kaina don ban yi tsammanin zai shigo ba shiyasa na zauna da vest tare da siket wanda ya tsaya iya gwiwa! da sauri na d'auki dankwalina na yafa a jikina na d'an ture plate din da na ci abinci gefe na had'e jikina guri guda. Zama yayi yana fuskanta ta, yayin da 'kamshin turaransa ya addabeni yana neman ya kashe min jiki. ganin yanda ya tsura min ido yasa duk na tsargu! sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce." Haka ki ke zaune a cikin duhu?" shima ya fad'i maganar ne kawai saboda ya ji dad'in bakinsa, waye ya ajiye ta a duhun idan bashi ba. Shuru kawai nayi masa saboda raina ne ma ya 'baci da maganar tasa, wacce tayi kama da ta rainin hankali. Shirun nawa shi ya bashi amsa da kuma yanayin fuskata don 'kiris ya rage na fashe da kuka! "Babu gaisuwa ko?" Ya fad'a yana haske ni da fitilar wayarsa. Hannu nasa na kare fuskata, babu fara'a na ce" Ina wuni?" Ya amsa babu yabo babu fallasa kafin ya d'ora da fad'in." Kin ci abinci?" Kaina na d'aga masa. Falon yayi shuru na 'yan mintina kafin ya sake wata maganar da ta sanya nayi saurin kallonsa. Ya ce." 'Kwarai kuwa ina da bu'katar matata a wannan daran, ai nayi ma 'kokari kusan watanni uku ina kallonki ban yi komai ba, kada ki manta a cikin labarina na sheda miki cewa; ina da yawan bu'kata! saboda haka sai ki shirya domin ina so ki zama jaruma! mai d'aukar d'awainiyata." Kuka ne ya 'kwace! min da sauri na ce" Ni wallahi ban shirya wannan al'amari da kai ba, domin dai ni ba kai nake so ba, saboda haka ka ajiye wannan maganar ni kawai ka dauke ni ka mayar wa da iyayena" Murmushi yayi mai ciwo kafin ya ce." Ai kin shigo hannun Saddiku dattijon nan mai furfura! babu rabuwa a tsakanina dake yarinya sai dai mutuwa." Tashi nayi da gudu na shige d'aki na kwanta a kan gado ina kuka! ni gaskiya ba zan iya bashi kaina ba, sai dai duk abinda zai faru ya faru, amma ban shirya zaman aure dashi ba. Gadon ya hayo ya janyo ni jikinsa yana so ya rungume ni ina turjewa tare da fizge-fizge! sai kawai yasa min 'karfi ya matse ni tsam! a jikinsa yana ta jijjigani tare da shafa gashin kaina! rarrashina yake tamkar 'yar goye yana ta fad'a min kalaman soyayya a cikin kunnena har ya samu nasarar kashe min jiki ta hanyar fad'in" Da wasa yake babu abunda zai yi min. jin haka yasa nayi shuru, tare da gyara kwanciyata a jikinsa. Cikin wata murya na ji maganarsa a kunne na. ya ce. "Me yasa ki ke tunani mara kyau a kaina?" Shiru nayi ban bashi amsa ba. Ya cigaba da cewa; ba zan gaji da fad'a miki cewa ni ba zan cutar dake ba, kuma duk abinda ya faru, akwai dalili wanda na sheda miki, amma ban yi tunanin haka daga gare ki ba don Allah kiyi hakuri mu zauna domin mu raya sunnar ma'aiki tare." Jin yanda yake had'a ni da Allah yasa jikina ya mutu! na ce" Ni fa muddin kana so na zauna da kai domin yin rayuwar aure sai ka kasance yanda na sanka a farko, domin ni fi bukatarka a haka." Ya ce." Hakan ba zai yuwu ba, ki so zahiri na, shine abinda na fi buk'ata, amma wancan da ki ke so duk gaibu ne, shiri ne, nayi domin cimma wata manufa kuma Alhamdulillhi na samu nasara, amma ba zan zauna cikin yagaggun kaya da 'kazanta ba, wannan zai janyo min wani abu daban." Na ce" Ni kam na fi bu'katar ka a haka, tunda kana ganin hakan ba zai yuwu ba shikkenan." Murmushi kawai yayi bai sake magana ba. ganin haka yasa na tashi daga jikinsa na matsa can 'karshen gado! na ja bargo na rufe jikina. Bacci ne mai nauyi ya d'auke ni, ko da na tashi da asubah! baya d'akin, ban damu ba, kawai na tashi na shiga band'aki da tunani mai yawa a cikin raina. Sai da na shirya tsaf sannan na nufi cikin gidan don gaishe da Hajiya. Da sallama a bakina na shiga falon, Hajiya da Shukura suna zaune a gurin cin abinci. na 'karasa a nutse na tsuguna har kasa na gaishe ta, ta amsa da fara'a mai yawa a fuskarta. Cikin wani irin yanayi mara dad'i Shukura ta gaishe ni kamar anyi mata dole. nima na amsa babu yabo babu fallasa. Hajiya ta ce" Ki zauna ki karya kummalo mana. Na ce" Hajiya na ci abinci a guri na kafin na fito. "Allah sarki." Ta fad'a kafin ta d'ora da fad'in." Mijin naki ai tun asubah ya tafi can garin mu jibia da yake duk 'karshen wata yana zuwa, ina fatan kunyi sallama da juna?" Da sauri na ce" Eh Hajiya ya fad'a min, Allah ya dawo dashi lafiya" Ta amsa da "Ameen ya Allah." Tsaye na mi'ke tare da fad'in" Hajiya zan koma guri na sai an jima. Ta ce"To shikkenan mu jima da yawa." Tana fita Shukura ta kalli Hajiya da fad'in "Wai Daddy ya rasa wacce zai aura sai kurma! wallahi Hajiya abin yayi min ciwo sosai! tuntuni Mommyna take so ya dawo da ita ya'ki ya je ya kwaso wannan k'azamar." Hajiya ta ce" Ke dai ki iya bakin ki Shukura bana son tashin hankali don Allah. domin abin farin ciki ne a guri na da Allah yasa yayi auran ina raye, maganar babarki kuma ki ajiye ta, a gefe domin da zai dawo da ita da tuntuni anyi an gama, saboda haka ki d'auki matar babanki a matsayin uwarki, kin fi kowa sanin halin mahaifinki, don haka kada ki ga kuna sa'anni da yarinyar nan, ki raina ta, duk 'kan'kantar ta uwarki ce, tunda tana auran mahaifinki." Kawai sai ta buga tevur d'in cin abinci tare da fad'in" ba zai yuwu ba wallahi." hanyar d'akinta ta shiga tana surutai! Hajiya tabi ta da kallon mamaki! "Mommy kina da labarin Daddyna yayi aure kuwa?" ta fad'a cikin ba'kin ciki da takaici! Daga d'aya 'bangaran Hajiya Fatima ta ce" Aure? yaushe yayi babu labari?" Nan duk ta kwashe komai ta sheda mata. Ta ce" Amma gaskiya 'Dan-gaske ya ba ni kunya, duk diddigin nasa anan ya tsaya? auran kurma wacce take da nakasu, mtsww! kada ki damu idan na dawo zan zo gidan, ai ko yana so ko baya so sai ya mayar dani d'aki na, ko kuma na hana shi kwanciyar hankali da matar tasa. Ta ce."Mommy ni na rasa wace irin zuciya ce da Daddy, ke fa 'yar uwarsa ce, yana kallon yanda ki ke katangala! kiyi nan kiyi can, duk saboda shi amma ya 'ki ya saurareki, gaskiya Momy kiyi wani abu akai, domin ba zan iya bud'e idona na kalli kucakar yarinyar can a matsayin matar mahaifina ba, wai har Hajiya tana fad'in" Dole sai nayi mata biyayya" Hajiya Fatima ta ja tsaki tare da cewa; ki rabu da Hajiya Saude tuntuni na fahimci cewa; ba ta son lefinsa, saboda yana da kud'i! babu yanda ban yi da ita ba, akan tasa baki ya mayar dani, amma ta'ki, saboda haka idan na dawo daga dubai, a gidan zan sauka duk sai na rikirkita musu lissafi tunda abin ya kasance haka." Ta ce." Yawwa Mommy Allah ya dawo dake lafiya." Ta amsa da "Ameen kafin ta kashe wayar zuciyarta a 'kuntacce! [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 86&87 Ranar na yini cikin zullumi da tunanin hanyar da zan bi gurin ganin na yi zaman aure da shi kamar yanda yake bu'kata, gaskiyar magana ba shi da wata makusa ta kowane fanni yana da kyawun hali, uwa uba kyawun zuciya tare da nagartar da ba kowa ne mai arzi'ki ne yake da ita ba, yanda na fahimce shi, bai d'auki kansa wata tsiya ba, irin yanda masu kud'i da mulki sukeyi, ya ajiye kansa dai-dai yake da kowa, kuma arzikinsa bai rufe masa ido ba, yana alheri sosai, tunda ni ganau ce, domin duk sati ranar juma'a kenan, gidan cika yake yi da bil-adam yara da manya dattijai da matasa har da mata masu buk'ata, kuma da kansa yake fitowa ya gaisa da kowane sashi kafin ya zauna ya fara robon kayan abinci da kud'i! shiyasa a kullum bakin gate d'in gidansa baka raba shi da al'majirai kala-kala, daga wata uwa duniya ma zuwa suke kuma duk yawansu sai ya faranta mu su rai, mutuk'ar kaga sawun 'kafa ya d'auke a gidansa, to ka tabbata cewa; baya gari yayi tafiya, amma duk da haka dai ba'a fasa aikin alherin ba, al'majirai irin na tsangayu suna zuwa kar'bar sadakar abinci mai rai da lafiya, wanda ya bada umarin cewa; ko baya gari kada a sauke tukunyar abincin sadaka. Maganar shekaru, gaskiya ya kwana biyu a duniya domin ya wuce shekaru ar'ba'in da biyar don a 'kalla zai yi shakara hamsin, amma saboda yanda yake kula da kansa shekarun basu nuna ba, bayan haka kuma yana da kyawun jiki, dogo ne amma bashi da ki'ba mai muni! sai dai kowace ga'ba a jikinsa a bud'e take, wannan ya samo asali ne, sakamakon atisayen da yake a duk ranakun karshen ma'ko, yana da kyau! daidai gwargwado don bashi da muni! ya fi ni kyau! nesa ba kusa ba, gashi da gayu da tsafta! kowace mace ta same shi a matsayin miji ta more! amma ni har yanzu zuciyata ta kasa aminta da shi, domin na zauna nayi rayuwar aure dashi, kuma na rasa a wane matsayi zan ajiye shi a cikin raina. Da wannan tunanin na yini, don sai bayan magariba ma na shiga kicin na dafa taliya fara tunda na kan yi miya ta kwana biyu zuwa uku, don na kori yunwa na zauna na tuttura abincin ba don baki na yana so ba. Wanka nayi na sanya doguwar rigar bacci ma dan taushi, saboda yanayin garin ana zafi, falo na fito, kafin na zauna sai dana zuge labule domin haske ya shigo, tunda harabar gidan, da fitilu ko ina, gurina ne, kawai babu fitila, to idan na bud'e labule haske yana shigowa, don tun ina jin tsoro har na saba. Zama nayi ina sa'ka wasik'ar jaki, har lokacin da na ji agogo ya buga goma daidai na dare, na sauke zazzafar ajiyar zuciya tare da gyara kwanciyata kan dugowar kujera, ina tunanin Baba Asabe da sauran 'yan uwa da mahaifi na, hawaye ne suka zubo min nasa hannu na goge wasu na na sake zubowa, cikin wannan yanayin ya shigo ya same ni, nayi saurin juya fuskata baya ina rintse idona. Sallama yayi bata amsa ba, kuma ya ga sanda ta juya baya a lokacin da ya shigo. Bai ajiye abin a ransa ba, ballananta ya dame shi, kawai abinda yake nazari shine, yarinyar ta samu dama a kansa ne, tunda ta fahimci irin azababben son da yake mata, dama kuma ta'kidin mata ne hakan, mutu'kar sun fahimci namiji na k'aunarsu shikkenan iskanci iri-iri zai biyo baya. Ya zauna a gefan ta tare da riko hannunta kafin ya 'bud'e muryarsa yanda za ta ji ya ce" Na zama dodo abin gudu ko Shahida?" Shiru ba tayi magana ba, sai ya d'ora da fad'in." Ki tashi mu tafi can cikin gidan, na gaji da zaman ki anan gurin, tunda wasan kwaikwayon ya 'kare." Ta shi nayi ina kallonsa shima ya tsira min nasa idon, wanda nake hango tsantsar gajiya a ciki. Na ce" A'a ka bar ni anan tunda dai kai ka ajiye ni kuma nan d'in kaga ya fi cancanta da ni.'' Ya ce." Ba zai yuwu ba dole zaki koma cikin gidanki da zama kiyi rayuwa mai kyau kamar yanda ko wace mace take a gidan auranta." Cikin rauni! na ce" Ka da ka manta fa, da bakinka ka ke fad'in kud'i ka bayar aka baka ni, to mai zai sanya ka ajiye ni a guri mai kyau?" Shiru yayi yana kallona, na goge hawayen dake zubo min na ce, idan ka manta ni ban manta ba, babu irin cin mutuncin da ba kayi wa mahaifina ba duk da na san halinsa ne ya janyo masa cin zarafi, saboda haka ni me zanyi a cikin gidanka domin ni wannan auran har yanzu wasan kwaikwayo na d'aukashi'' Ransa a 'bace ya ce." Kada ki sake kiran auranmu da wasan kwaikwayo kin ji ko." Kaina na d'auke tare da fad'in" Ai kai ka shirya kuma kai ka bada umarnin sunan shirin film din naka wasan kwaikwayo." Na sake maimaitawa duk da ya nuna baya so ban ji shakka ba. Shiru falon yayi ni da shi kowa da nazarin da yake, ganin kawai ya tisa ni a gaba yana kallo yasa na yun'kura zan tashi, sai ya ri'ke min hannu, still idonsa yana kaina, gabadaya jikina ya mutu! domin bana iya jurar wannan kallon nasa. Ya ce" Na je jibia ban fad'a miki ba, duk suna gaishe ki, za kiyi 'bakuwa cikin satin Sadiya za ta zo ku gaisa." Shiru nayi masa. ya sake rintse hannuna dake cikin nasa, kafin ya ce." Ina ganin dai har yanzu wahalata ba ta 'kare ba, zan cigaba da addu'a tare da fara dubawa daga cikin masu rubibi na." Kallonsa nayi tare da jin fad'uwar gaba, duk da cikin zaurance yayi maganar na fahimci abinda yake nufi, duk sai na ji rashin dadin furucinsa, amma ban nuna a fuskata ba, nayi saurin d'auke kaina. Ya mi'ke tsaye tare da zuba hannuwansa cikin aljihu, ya ce" Na tafi ko na zauna na taya ki kwana?" Da sauri na ce" Ka je kawai." Yayi tsayiwar minti biyu kafin ya kama hanyar fita, na bishi da kallo! zuciyata na wani irin tunani akan kalamansa. Washe gari na tashi sukuku! babu kuzari ko kad'an a jikina, dalilin mafarkin da nayi, haka dai na gudanar da komai cikin rashin nutsuwa! na gama uzurirrika na sannan na zauna karya kummalo kana na sa hijabi a jikina, kamar dai ko da yaushe na nufi cikin gidan. Lokacin dana shiga falon shiru babu kowa, jikina a sanyaye na sake wata sallamar a karo na uku, babu wanda ya amsa, sai jikina ya 'kara mutuwa! cikin zuciyata nake addu'ar cewa; Allah yasa lafiya. Motsi na ji can saman bene in da ya kasance turakar mai-gidan, da sauri na d'aga kaina ina kallon gurin, Hajiya ce take saukowa daga benan idanuwanta jawur! da alama kuka tayi. gabana ya yanke ya fad'i! cikin rawar baki na gaishe ta amsa a sanyaye kafin ta ce" Ki hau sama mai-gidan naki bashi da lafiya jiya da daddare ciwonsa ya tashi ba mu rintsa ba" 'Kafafuna suka shiga rawa! na kasa gaba na kasa baya kawai na zuba mata ido, k'walla duk ta cika kwarmin idona. Ta ce" Kiyi wa Allah da Annabi ki kwantar da hankalinki a gidan nan, ki bawa mijinki kulawa, wallahi ba mu da mummunan nufi! a kanki, bana raba d'aya biyu 'bacin ran ki ne, ya haddasa ciwonsa ya tashi. Da sauri na ce" Wallahi ba haka bane Hajiya, ni kuma me nayi masa da har ciwonsa zai tashi a kaina, kada fa ki manta manya irinsu, dole ba zaki raba su da cututtuka ba, bayan haka kuma abubuwa sunyi masa yawa, na harkokin yau, da gobe, amma kada ki ala'kanta ciwonsa da damuwata." Murmushi takaici tayi kafin ta ce." Duk abubuwan dake faruwa a tsakaninku ina da labari, domin Saddiku baya b'oye min komai, ki sani cewa; a gurinki ne kad'ai muke sanya rai za mu samu nutsuwa, gashi ke kuma kina yi mana wani irin kallo na rashin yarda, wannan ce babbar damuwarsa, gashi ya sanya ki a ransa sosai, ki duba irin 'kaunar da yake miki don Allah ki zauna dashi." Duk yanda na so dana daure abun ya gagara, hawayen da nake 'boyewa suka su'bce! na ce" Hajia wallahi bani da laifi zuciyata ce, amma insha Allahu zanyi 'ko'karin ganin na kawar da komai na zauna tare da ku kamar yanda kuke bu'kata." Ta saki fuskarta tare da fad'in" To shikkenan Allah ya baki iko." na amsa da "ameen" kafin na fara hawa 'kafar benan cikin sassarfa. Zaune a kusa dashi na samu Shukura tana kuka tare da rungume hannunsa a 'kirjinta fuskarta ji'ke da hawaye! sai duk suka bani tausayi ita da shi, mafarkin da nayi yana nema ya tabbata. A sanyaye na 'karasa bakin gadon, wanda tun da na shiga d'akin yake kallona, kuma bai daina ba har na zauna a kusa da shi. Ta kalle ni a banza ce kafin ta ja tsaki! mai tsayi wanda duk rashin ji na, sai da kunnuwa suka amsa sautin tsakin! kaina kawai na sunkuyar, ita kuma ta tashi ta fita daga dakin tare da bugo 'kofar da k'arfin gaske. Tun da na sunkuyar da kaina bai d'ago ba, domin na ji ciwon kallon banzan da tayi min tare da tsakin da ta ja min. Sautin maganarsa na ji, na d'ago kaina ina kallonsa, ya sake maimaita maganarsa wacce yake da tabbacin cewa; ban ji ba, wannan karon da sauti mai 'karfi yayi maganar. "Kiyi hakuri." Ya fad'a tare da kamo hannuna yana 'kokarin tashi zaune. sai kawai na tsinci kaina da taimaka masa ya tashi na jingina masa fillo a bayansa kafin na koma na zauna. A nutse na ce."Ai ku za a bawa hakuri." Ya ce." Saboda me?" murmushin takaici nayi kafin na ce" Na ga gabad'aya kun d'auki lefi kun d'ora min, domin na shigo na ga Hajiya tana kuka tana sheda min cewa; damuwata ce ta haddasa ciwonka ya tashi, bayan haka kuma, a gabanka Shukura ta ja min tsaki tana min kallon banza! idan da matsala kawai ka rabu da ni, domin ni bana so shiga cikin zargi, bayan da bakinka kafad'i ga wacce ta haddasa maka ciwon tun fil-azal, amma ana neman d'ora min jakar tsaba." "Kiyi hakuri." Wannan kalmar ya furta kafin ya rintse idonsa, alamun sun nuna baya bu'katar doguwar magana. Na ce" Ya jikin naka?" da sauk'i ya fad'a ba tare da ya bud'e idonsa ba. Shiru d'akin yayi na 'yan mintina kafin na ce" Yanzu me kake bu'kata?" Bud'e idonsa yayi yana bi na da kallon mamaki! Fuskata na saki amma ban ce komai ba. Ya girgiza kansa tare da fad'in" Ba abinda nake bukata a gare ki, sai alfarmar ki zauna tare da ni, ki kuma cire shakku a kaina, bayan haka kuma ki ri'ke ni amana." Jim nayi na minti biyu kafin na ce" Shikkenan zanyi 'kokarin ganin nayi hakan muddin zan fita daga zargi don bana so wani abu ya same ka mutane su ce ni ce sanadi. Murmushi yayi, yana min wani irin kallo kafin ya ce'' Babu wanda zai zarge ki don kin taka sawun 'barawo, kin 'karasa gawar da ba taki ba, dama can bani da cikakkiyar lafiya, ko da Hajiya tayi wannan maganar, ba da wata manufa ba, tayi ne domin ki gyara kuskuranki, ma'ana ki zama mai kula da mijinki domin ki samu rabauta ranar gobe 'kiyama." Sunkuyar da kaina nayi tare da wasa da yatsun hannuna, ya tashi a hankali ya nufi band'aki cikin 'kwarin jiki, sai kawai na tsinci kaina da bin sa da kallo da tausayinsa 'kadan a cikin raina. [1/12, 11:25 PM] Binta Umar Abbale: 88&89 Gadon na shiga bi da kallo kamar me neman wani abu. wayoyinsa ne akai sai farin gilashinsa da kuma littafin husunul muslim a ajiye a gefe, sai kuma 'kamshin turaransa da ya mamaye d'akin, komai nasa a tsanake babu harigido a ciki, dattijo ne mai kamala da hallin dattako. Ajiyar zuciya na sauke tare da tsirawa k'ofar 'bandakin ido! fitowarsa daga band'akin yasa nayi gaggawar d'auke kaina, kai tsaye 'katuwar wardrobe din da ta cinye bango guda ya nufa yana neman kayan sawa. A nutse na je na tsaya a kusa dashi tare da fad'in" Ka je ka zauna na duba maka kayan. Kallo na yayi da mamakin magana ta. Sai na d'an saki fuskata tare dasa hannuna kan kayan nasa ina dubawa. Ban an kara ba kawai na ji shi a jikina, ya zagaye k'ugu na da hannuwansa tare da d'ora ha'barsa a kafad'ata. Cikin fad'uwar gaba na juyo rigar dake hannuna ta fad'i a gurin. 'Kokarin k'wace jikina nake yana sake matse ni a jikinsa dake wani irin karkarwa! 'Kafafuna suka shiga kyarma! jin yanda yake yawo da hannuwansa a sassan jikina. Kuka nasa tare da ture shi da 'karfi na matsa gefe ina gyara zif d'in rigata da ya zuge min. Da azama! na kama hanyar fita, sai yayi saurin tarar gabana, ya sanya mukulli a jikin 'kofar d'akin, ba tare da ya ce komai ba ya ja jikinsa da babu 'kwari ya hau gado ya kwanta har da jan bargo. A sanyaye na ce" Ka bud'e min 'kofar na fita. Shiru yayi be ce min komai ba. Ganin haka yasa na zauna kan kujera tare da zabga tagumi! abinda yayi min yanzu ya tsorata ni, mutumin da bashi da lafiya. Motsin ta'ba 'kofa na ji sai nayi sauri na kalle shi har yanzu yana cikin bargo a lullu'be. Na ce" Za'a shigo fa." Shiru babu amsa. Gurinsa na nufa domin neman mukkulin, ya bud'e fuskarsa da alamun bacci ya bani mukullin da fad'in."Amma don Allah kada ki ce zaki koma wannan gurin ina bukatar ki zauna tare dani, ina neman wannan alfarmar." Jikina ne yayi sanyi jin yana had'a ni da Allah kamar ya san kud'iri na kenan. Ni kaina ina jin wani iri a duk lokacin da yake 'kas'kantar min da kai. A sanyaye na je na bud'e 'kofar. Shukura ce ta shigo hannunta ri'ke da kwandon abincin. wani irin wula'kantaccan kallo tayi min kafin ta wuce cikin d'akin. Sosai raina ya 'baci da iskancin da yarinyar take min, idan tayi min wulakanci a can baya nayi ha'kuri, to yanzu zahirin gaskiya ba zan iya jura ba, domin kuwa a matsayin uwa nake a gurinta ko tana so ko ba ta so dole ta girmama ni kamar yanda zata girmama mahaifinta. idan ma ba zata gaishe ni ba to ba zan jure kallon banza da zagi ba. K'ofar na rufe na je na zauna ina kallonta tana fad'in" Daddy ka tashi ka ci abinci ka sha magani." Na kalle ta babu walwala a fuskata na ce" Ki rabu da shi mana ko ba kya ganin bacci yake?" Ta juyo a fusace! tare da cewa" Kin ga malama kada kiyi min shishshigi" Kafin nayi magana har ya 'bud'e fuskarsa. rai a 'bace! ya kalle ta da fad'in" Tun da kin kawo min abincin, tashi ki je kawai." A sanyaye ta tashi ta fita kamar ta fashe da kuka. Na kalle shi yana 'ko'karin sake rufe fuskarsa na ce" Yana da kyau! ka tashi ka ci abincin sai ka sha magani ko." Minti biyu da magana ta ya ta shi tare da cire bargon dake jikinsa ya sauko da 'kafafunsa 'kasa! sai kuma na ga ya dafe kansa da duk hannuwansa. Ganin haka sai jikina yayi sanyi na tashi na je kusa dashi na zauna. Cikin zuciyata nake jin d'an tausayinsa, da alama yana jin jiki daurewa kawai yake. kafad'arsa na dafa a hankali na ce"Sannu kan ka ne yake ciwo ne?" Girgiza kansa yayi ba tare da ya kalle ni ba. Na sauke ajiyar zuciya da fad'in" Na ga ka dafa kai ne, shine nake tunanin ko ciwon kai ne ya matsanta maka. Ya cire hannuwan nasa tare da zuba min ido. Kasa kallonsa nayi sakamakon ganin yanda 'kwayoyin idanuwansa suka sauya jajawur! yanayin kallon da yake min ne yasa jikina mutuwa! gabana kuma na cigaba da fad'uwa! Hannu na ya ri'ke tare da fad'in" Ina da damuwa mai tsanani." Nayi shiru ina kallonsa. Ya cigaba da cewa; Kasancewar ki a kusa da ni ya janyo min sha'awa mai tsanani, gashi idan ina cikin wannan halin bana iya sarrafa kaina." Na kalle shi a lokacin da yake bin ilahirin jikina da kallon kurulla, gabad'aya yanayinsa ya sauya yayi sanyi sosai, hannunsa dake ri'ke da nawa sai karkarwa yake. "Yanzu me ka ke bu'kata?" Na tambaye shi duk da na harbo jirgin nasa. "Ki mallaka min kan ki a wannan lokacin." Ya fad'a tare da kusantar jiki na. Kai na girgiza. alamar ba zan iya ba. Ya ce."Saboda me?" Shiru nayi ban bashi amsa ba saboda na san da cewa bani da wata hujja. Rungume ni yayi tsam! a jikinsa! yana makyarkyata! kuka nasa ina ture shi tare da fad'in" Ka rabu da ni don Allah. Cikin kunnuwana na ji yana fad'in" Ki taimaka min na rage damuwa ta shekara da shekaru matata ba zan cutar dake ba." "Ni dai A'a ban shirya faruwar hakan ba.'' Cikin shagwab'a da sangarta nayi maganar ina kokarin raba jikina da na sa. Yanda na fahimta hakan da nake kamar 'kara masa 'karfin gwiwa nayi domin rikicewa yayi yasa 'karfi sosai ya kwantar dani kan gadon yayi min rufa! Sosai nayi mamakin abubuwan da yake min tamkar ba mara lafiya ba, hannayensa sai yawo suke a sassan jikinta. Gabad'aya gwiwa ta tayi sanyi sakamakon abubuwan da yake min, 'kamshin jikinsa ma ya taka muhimiyyar rawa gurin hana ni 'kwatar kaina. Kamar a mafarki mu ka ji an bud'e 'kofar d'akin an shigo da saurin gaske ya sauka daga kaina tare da juyawa domin ganin waye ya shigo. gefen rigarta kawai mu ka yi katarin gani domin da saurin ta bar gurin ba tare da ta rufe 'kofar d'akin ba. Takaice yasa na fashe da kuka da fad'in" Ka gani ko?" Ba tare da ya ce komai ba ya juyo da nufin sake kwantar da ni, sai na matsa gefe da sauri ina gyara wuyan rigata, sauka nayi daga gadon, k'afafuna sai rawa suke, na ce" Yanzu kayi wannan abun ya za a yi su yarda baka da lafiya. Murmushi kawai yayi ya tashi ya shiga band'aki ba tare da ya ce min komai ba. Na zauna kan kujera gabana sai bugawa yake, komai yana bu'katar sirri ya zama dole ya takawa yarinyar nan burki ta daina bankad'o mana d'aki tana shigowa ba tare da neman izini ba. Ko da ya fito daga toilet din ban iya kallonsa ba, saboda tawol ne d'aure a jikinsa, cikin zuciyata na ce" Dole ciwo yayi ta damunsa ko da yaushe cikin watsawa jiki ruwa. Band'akin na shiga na tsafta ce jikina, domin ni kaina ban yarda da kaina ba, abinda ya faru a tsakaninmu yasa wandon dake jikina ya 'baci! wanke wa nayi na shanya a band'akin na fito na same shi a zaune kasan kafet yana duba wayarsa. Har nayi nufin zama kan kujera, na ji maganarsa. "Kada ki zauna zuba min abinci nan." Ya fad'a ba tare da ya kalle ni ba. Na zuba masa daidai gwargwado na ajiye a gabansa, niyyar barin gurin nayi, ya ce" Zauna ina so muyi magana. Zama nayi kaina a 'kasa Ya ajiye wayar hannunsa a gefe, kafin ya kalle ni, ya ce." Za mu ci abincin tare ko?" Girgiza kai nayi. Ya ce." me ki ka ci to?" shiru nayi masa tare da d'auke kaina. Ya ce." Na fara gajiya fa da wannan abubuwan da ki ke min zan kai 'karar ki gurin mahaifinki" Kallonsa nayi da mamakin maganarsa, ya ce." 'Kwarai kuwa! ki kalle ni da kyau! kin san a shekaru na haife ki ko? amma na ajiye girmana ina rarrashinki duk don mu zauna lafiya kina min wasu abubuwa saboda kin fahimci cewa Allah ya jarrabe ni da sonki shin ko ba haka bane?" Ban ce masa komai ba. Ya cigaba da cewa" Ki kula da ni a matsayin mijinki, kiyi kokarin sauke hakkina dake kanki kada ki zalince ni, sannan ina so ki d'auki wannan al'amari a matsayin 'kaddararki, kada ki butulcewa Ubangiji mana, da can kin yi soyayya da mahaukaci mara galihu! sai kuma Allah ya sauya tunaninki ki ka tsinci kanki a matsayin matar babban mutum wanda ya shallake tunaninki, shin me ya kamata ki yi?'' Jin nayi shiru ban ce komai ba ya cigaba da cewa" Allah subahanahu wata'alah za ki godewa a bi sa ni'imar da yayi miki, duk wad'an nan abubuwan da ki ke min kamar 'kara min 'karfin gwiwa ki ke domin ni ba zan iya rabuwa dake ba har abada don kin zama jinin jikina. Ya 'kare maganar tare da tsira min ido. Na ce" Ni yanda zanyi rayuwar aure da kai ne ban sani ba." Sihirtaccen murmushi yayi kafin ya ce." Saboda nayi miki tsufa ko?" Shiru nayi masa. Sai ya cigaba da cewa" Wace rayuwa ki ka shirya yi da masoyinki Baban-baba?" Kallonsa nayi sai na gana yana murmushi wanda ya 'kara masa kyau! Da sauri na ce"Rayuwa mai sau'ki da sau'ka'awa." Dariya yasa sosai yana mamakin yarinyar. 'kuruciya ce kawai take damunta, a ganinsa ai rayuwar da za ta yi dashi a yanzu sai ta fi armashi da wacce za tayi dashi yana fa'kiri (talaka) gabad'aya ya gaza fahimtar inda ta nufa, wata irin bahaguwa ce, ko da yake yana yawan ji daga bakin mutane suna fad'in (Kurame) ba su da saurin yarda domin duk abinka sai sun zarge ka a wasu lukatan( A yi min afuwa masu wannan laluran ban yi dan na ci fuska ba) Ya kalle ta da fad'in "Me yasa lokaci guda ki ka aminta da ni a lokacin da nake mahaukaci na 'kar'kashin mota" "Tausayinka na ke ji har cikin raina ina jin takaicin irin rayuwar da ka ke, kuma ina shiga 'bacin rai a duk lokacin da na ji ana kiran ka da mahaukaci! har kuka nake wani sa'in." Ya sake jin wani irin k'aunarta a cikin ransa. "Ni ma a lokacin ji nake duk duniya bani da mai 'kauna ta kamar ke, domin baki 'kyama ce ni ba, kin bani abinci kin bani ruwa, kin share min makwancina, wannan dalilin yasa na tsaya kai da fata naga na mallake ki domin samun mace irinki a yanzu babban aiki ne." 'Dakin yayi shiru na minti biyu, kafin ya cigaba da cewa; ki sa a ranki cewa abinda mahaukacin nan zai yi miki na kulawa da soyayya, to ni zan yi miki wanda ya fi shi, buri na kawai ki amince da ni cewar ba zan cuce ki ba, kuma nayi miki al'kawarin ba zan gaza miki ta kowane fanni ba. Kalamansa su suka sanyyayar min da jiki cikin zuciyata na ji ina sha'awar zaman aure da shi, sa'banin tunanin da na keyi , ganin kamar ya fi 'karfina, tabbas duk maganganunsa akan hanya suke, yanda yake rantsuwa da Allah a kan 'kaunar da yake min, hakan ya 'kara min 'karfin gwiwa, sai dai kuma tils na cigaba da addu'a akan Allah ya kore mana fitina a cikin al'amarin. Tare muka ci abincin, yana ta jana da hira, ni dai umm kawai nake cewa, sosai ya warware kamar ba mara lafiya ba, ya saki jikinsa yana ta zuba min kalaman soyayya wanda suka ragargaza min ga'bo'bin jikina, domin da abincin ma wai a baki zai ba ni, na no'ke don gabad'aya kunyarsa nake ji ganin kamar yana so ya wuce gona da iri. Har dare ina d'akinsa kunya nake ji na sauka 'kasa, shi kuma tun bayan da ya fita sallar magariba bai dawo ba, duk na takura! a dak'in, gashi ina da bu'katar zuwa tsohon guri na, domin d'auko rigar bacci amma ya hana ni, daga ni sai doguwar rigar atamfar dake jikina sai kuma mayafin dana yafo ina zaune nayi tsuru tare da tunanin abunda zai faru tsakanina dashi a wannan rana. [1/12, 11:28 PM] GARKUWAR MATA: 90&91 Hajiya da kanta ta shigo ta kawo mana abinci. Fuskarta kawai na kalla na fahimci cewa tana cikin farin ciki da abinda nayi, don babban burinta shine na zauna tare da su, ganin haka yasa na k'arawa kaina 'karfin gwiwar ha'kurin zama a d'akin mijina, ko don saboda 'yar tsohuwar ta kasance cikin walwala da farin ciki. A can 'kasa kuwa Hajiya na zama Shukura ta fara 'kananun maganganu na rashin mutunci, domin kishi 'karara take nunawa akan matar mahaifin nata, ita dai bu'katar ta mahaifiyarta ta dawo gidan. Hajiya ta katse ta da fad'in" Idan zaki kwantar da hankalinki akan wannan al'amari to, domin da mahaifinki zai dawo da Fatima gidansa da tuntuni ya dawo da ita, sannan kina fadin na tilasta shi, akan me zanyi masa dole? shine mai auran kuma yace ba zai zauna da ita ba saboda wasu dalilai, to akan me zan matsanta masa, don Allah Shukura ki samu nutsuwa, kada ki tayar mana da hankali a gida da fitina mara dalili. Hawaye ta share ta ce" Hajiya ni kawai yarinyar ce ba tayi min ba, ai ba tsaran auransa ba ce, don wulakanci shine zai auri 'yar 'karamar yarinya bayan duk ga mata nan a gari." Cike da mamaki! ta ce" Mahaifin naki shine wulakantacce?" Hanci ta sha'ka ta zumbura baki ta ce" Ai dama ba kya 'kaunar Mommyna kamar ba ke ki ka haifi Ubanta, 'kiri-'kiri ki ke nuna fifiko saboda kawai Daddyna yana da kud'i." Hajiya ta ri'ke baki da d'umbun mamaki! a tare da ita ta ce" Rashin kunya za kiyi min Shukura yanzu ni ki ke fad'awa wannan magana?" Ta bud'e baki za tayi magana ya shigo falon, duk sai su ka yi shiru, amma fuskokinsu da alamun 'bacin rai! don ita Shukuran ma kuka take. Cike da kulawa ya kalle ta da fad'in."Menene?" yana son yarinyar sosai! saboda ita kad'ai gare shi, halayenta ne baya so shiyasa ba kasafai yake yarda ta je gurin gurin uwarta ba. Sake rurucewa! tayi da kuka tana takure jikinta a cikin kujera! Ya zauna yana kallon Hajiya domin tayi masa 'karin bayani. Tsaki! ta ja ta ce" Wannan yarinyar sam bata da hali wallahi. kuma yanzu na fahimci abinda ka ke gudu tsakaninta da mahaifiyarta, domin dai wasu halaye take masu kama da na uwarta. Ya ce." Menene ya faru?" Nan ta kwashe komai ta fad'a masa. Ya sha kunu sosai! yana kallonta da kakkausar murya ya ce." Wallahi ki kiyaye ni Shukura ki bar ganin ina biye miki ko ina nuna miki 'kauna, akan Shahida za mu 'bata sosai ranki zai 'baci mutuk'ar baki daidaita hankalinki ba, ina ruwanki da ita? muddin kin d'auke ni uba to itama uwarki ce, saboda haka kada na ji ko na gani kinyi mata rashin kunya, duk ranar da hakan ta faru sai na 'bata miki rai." Cikin kuka ta ce" Daddy kayi hakuri don Allah, amma ina neman alfarma a gurinka. Ya kalle ta babu fara'a a fuskarsa, ta ce" Don Allah ka dawo da Momnyna wallahi tayi nadama, kuma 'yar uwarka ce." Shiru na minti biyu kafin ya ce." Zanyi shawara akai." Daga haka bai sake magana ba ya tashi ya hau sama. Itama Hajiya tashi tayi ta shige dakinta cike da takaicin abinda yarinyar tayi mata. Ganin saura ita kadai a falon yasa ta dauki wayarta "Mommy kin san wani abu?" Daga d'aya 'bangaran Hajiya Fatima ta ce" Sai kin fad'a min." "Na roki alfarma a gurin Daddy zai mayar dake d'akin ki." Cike da murna ta fadi maganar. Hajiya Fatima kamar ta zuba ruwa a 'kasa ta sha don farin ciki, ta ce"Shukura da gaske ki ke ?" Tafad'a cike da zumud'i. "Wallahi kuwa Mommy amma ya ce"Zai duba ya ga ni, nan da kwana biyu zan sake yi masa maganar." Ta ce" To shikkenan zan zo a shirye in sha Allahu. amma ki cigaba da matsanta masa akan maganar, kuma kada ki bar matarsa tasha iska a gidan, 'yar iska nakasashshiya." "Mommy cewa yayi fa akanta zai 'bata min rai! wai dole sai na girmama ta! kamar yanda zan girmama shi." Tsaki! ta ja ta ce" A gaban idonsa ki bata girma amma a bayan idonsa ki ci ubanta, idan na shigo gidan, da k'afafunta zata gudu. "To shikkenan Mommy yaushe zaki dawo?" "Cikin satin da za mu shiga in sha Allahu." "Mommy kada ki manta don Allah ina son abaya masu kyau da takalma." Ta ce" Su nayi order baki da matsala daughter sai na dawo in sha Allah." Sallama su kayi da juna, kafin ta shiga d'akinta cikin farin ciki da an Nashua's mamanta zata dawo kusa da ita. Zaune a gefen gado ya same ni ina ta nazari da tunanin abinda zai biyo baya. Koda ya shigo d'akin, can wata kusurawa ya nufa ya cire wani babban zani akwatina ne a jere guda bakwai sababbi kar kuma daka gani masu tsada ne. Ya juyo yana kallo na kafin ya ce." Ga kayan lefanki nan na jima da had'a miki, duk yawanci a dinke suke, akwai komai na bu'kata a ciki kama daga kayan kwaliyya rigar nono kayan bacci wando siket da dai sauran abubuwan b'ukata na mata, daga yau kada ki sake amfani da kayan dake wancan sashen, tunda dai wasan kwaikwayon ya 'kare." Murmushi nayi wanda yayi kama dana dole na kaucewa maganarsa ta hanyar fad'in"Ga abinci Hajiya ta kawo" na nu masa kwadon dake cike da kwanukan abinci. Yana 'ko'karin sauke akwati nan 'kasa ya ce." Ni kam a 'koshe nake kin manta ban jima da jin abinci ba, ko da zan ci wani sai an jima, amma dai ke ina bu'katar ki ci abinci sosai! Yana maganar ne yanda zan ji sosai! don ya riga ya saba da d'aga sauti idan zai min magana. Na ce"Nima na 'koshi." Girgiza kansa yayi a lokacin da yake 'ko'karin zama a kusa da ni hannunsa ri'ke da wata figalalliyar riga, da kuma sababbin pant da brez. A cinya ta ya ajiye min pant da brez din kafin ya fara warware! rigar yana fad'in" Yau wannan rigar za kiyi min ado da ita." Gabana ya yanke ya fad'i! kallonsa nayi naga sai dudduba rigar yake mussaman ma'ajiyar nonon dake jikinta kafin ma nayi magana na ji yana fad'in" Anya kuwa Wannan gurin be miki kad'an ba ?" Ya fad'a yana nuna min gidan nonon rigar. da saurin gaske na kawar da kaina kunya kamar na nutse a gurun. Abubuwan da yake kamar wani matashin saurayi! na lura shima kunya tayi masa 'karanci. Ya sake maimaita maganar. Na ce" Nima ban sani ba. Sai kawai na ji saukar hannunsa a :kirjina yana lalubawa! a gigice! na sauka daga gadon! ina harararsa! dama abinda yake bu'kata kenan! a ganinsa wannan ba harara bace kallon soyayya ne. Ido ya kashe yana bina da wani shu'umin kallo! duk sai na tsorata, kamar na bud'e dakin na fita, amma sai na daure, na zauna kan kujera gabana na cigaba da fad'uwa! babu shakka akwai babban al'amarin da zai faru a tsakaninmu. Kira ne ya shigo wayarsa na ji yana fad'in" Yaushe ka dawo babu labari?" Shiru na 'yan second biyu kafin ya ce." Allah ya kai mu lafiya idan ka shigo sai ku gaisa da amarya ta." Dariya naga yayi kafin ya ce." Ai babu wasa a tsakaninmu, wallahi da gaske nake nayi aure kimanin wata uku da suka wuce." Shiru yayi yana sauraransa kafin ya ce." To Idan ka zo zaka dai tabbatar da magana ta, Allah ya ba mu alheri." Kashe wayoyinsa yayi duka ya ajiye kan dirowa kafin ya kalle ni, babu wasa a fuskarsa ya ambaci sunana da sautin da zan ji maganarsa. Amsawa nayi nima ina kallonsa. Ya ce." Za mu yi sallah ta godiya ga Allah ko?" A sanyaye na d'aga kaina. Sai ya tashi ya nufi band'aki! ya bar ni a zaune ciki tararrabi da fad'uwar gaba! Alwala yayi ya fito nima na shiga nayi alwalar na fito na same shi ya shimfida mana babbar dadduma! Hijabi ya mi'ko min na kar'ba nasa a jikina, na tsaya a bayansa ya tayar da sallar. Raka'a biyu mu kayi, ya daga hannu sama, ya dinga kwararo addu'a har sai da na tausaya masa jin yana rok'on haihuwa da samun wadatacciyar nutsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, da kuma zuria masu albarka, muryarsa sai rawa take kamar zai fashe da kuka yake fad'in "Ubangiji Allah kasa nayi auran nan kenan! mutuwa ce zata raba ni da matata, ya rabbi ka bani zuria da yawa da ita, kasa na samu nutsuwa da ita, Wahidun ahadun! kayi min wannan arzi'kin don alfarmar Annabi Muhammadu S.A.W." Hawaye ne suka fara zuba a saman fuskata, gabad'aya tausayinsa ya gama kashe min jiki, ro'kon Allah yake akan ya samu zuri'a da ni, ya na kuma bukatar ya samu nutsuwa da ni, duk ni kad'ai! tabbas Allah yayi min tagomashi! kuma yayi min kyautar da ba kowace mace ba, domin samun nagartaccen namiji a wannan zamanin sai anyi dace. Bayan ya shafa addu'ar ya juyo yana kallo na, lokacin na kasa tsayar da kukan da na ke yi, hannuna ya ri'ke kafin ya ce." Menene?" zuciyata ta sake karyewa, hawayen suka cigaba da zuba, yasa hannu yana goge min, ya ce"Zubar hawayenki yana min zafi a cikin raina, yau babbar rana ce a gare ni, na had'a ki da girman ALLAH ki daina yi min asarar hawayen nan" Kallonsa nayi, naga yayi wani irin rama a gabana, kamar mai neman gafara sai rarrashina yake da kalamai kyawawa! na ce" In sha Allahu! zan zama farin cikin ka, ai ban za ci 'kaunata ta kai haka a cikin zuciyarka ba. Murmushi yayi wanda yake 'kara masa kyau! ya ce." Kin wuce haka a can cikin zuciyata, domin k'aunar da nake miki tayi nisa ta bi ilahirin jinin jikina gabad'aya idan babu ke rayuwata zata salwance, a kanki na san meye so! duk matan dana aura akwai dalili, amma ke ce ra'ayi na, buri na shine ki bani dukkanin kulawarki, kuma ki zauna lafiya da ni." Hannuna na ri'ke a karo na farko! ban ji nauyin had'a yatsuna da nasa ba, na ce" Zanyi 'kokari in sha Allahu." Murmushi kawai yake yana jifa na da wani irin kallo, wanda yasa nayi saurin sunkuyar da kaina kasa. To duk da ya ce a 'koshe yake sai da ya taya ni cin abincin, nima ba wani da yawa na ci ba saboda fargaba, kad'an na tsakura, na shiga bandaki nayi wanka tare da wanko bakina na fito, duk jikina babu 'kwari, domin ina jin tsoron abinda zai wanzu a tsakaninmu, yanayin kallon 'kurrulan da yake min, shi yake tabbatar min da cewa; da wuya yau wani abu bai faru ba. Rigar ya mi'ko min yana kashe min ido. Kasa 'karba nayi saboda kunya, na sa hijabi a jikina. Ya tashi ya je ya kashe fitilar dakin, da ya dawo ya zauna yana lalube na. Can gefe na matsa tsigar jikina sai tashi take. Sai da ya lalubo ni, ya rike hannuna sosai kafin ya fara kici-kicin cire min hijab, dama kuma daurin kirji ne a jikina. Kuka nasa masa ina ture shi, ni gabad'aya al'amarin banbarakwai nake jin sa. Bai damu da yanda nake kuka turje-turje ba, haka ya cire hijan din jikina ya ajiye ya kwantar da ni saman gado. Ni dai tun daga lokacin na shiga d'imuwa, domin kasa fahimtar kaina nayi, don jikina saki yayi tunda ya d'ora min nauyinsa, ban san ya akayi ba har ya gano abinda na fi muradi, nan naga ya mayar da hankalinsa a gurin, har ya samu kaina na dinga biye masa ina rawar jiki, sai dai kuma lokacin da mai afkuwa ta afku na raina kaina mutuka gaya! domin dai nan na gane cewa maza suna suka tara, dattijon 'karfi! ne dashi sosai! ya k'urewa duk wata fitina ta, kuka na dinga rizga tare da kokarin kwatar kaina daga hannunsa, a lokacin da shi kuma yake kan ganiya, ya hana ni k'atabus! jikina ya laushi sarrafa ni kawai yake ta kowace siga, yana yi tare da numfarfashi! [1/12, 11:30 PM] GARKUWAR MATA: 92&93 Ba zai iya tantance wane irin hali yake ciki ba sakamakon tarayyarsa da yarinyar. ita ce mace ta uku da wata mu'amula ta shiga tsakaninsu. amma ya bata lamba ta d'aya a cikin jerin matan da ya yi mu'amula irinta ta auratayya. babu shakka Ubangiji baya tarawa bawa damuwa! domin ko da ya halliceta cikin jerin masu rangwamin gata sai kuma ya wadata ta da ni'ima tare da sauran abubuwan da ba kowace mace ke da irin shi ba, shi dai ya tabbatar da cewa; yarinyar ta zarce duk matan da yayi tarayya da su don ya samu gamsuwa da ita sosai, babu wani abu da yayi saura a mararsa, sakayau! ya ke jinsa tare da wani irin nishad'i da bai ta'ba shigarsa ba, lallai dole ya godewa Allah bisa ni'imar da yayi masa gurin azurta shi da 'yar baiwa wacce take da tarin nagartattun abubuwa masu alfanu a gare shi. Da wannan tunane-tunanen bacci mai nauyi ya d'auke shi ya matse ta tsam-tsam! a jikinsa. Da gari ya waye kuwa duk hidimar da ya kamata na yi da kaina shi ya yi min, yanda yake nuna kulawarsa a kaina hakan ya faranta min raina mutuka! sosai nayi farin ciki da ya samu budurci na domin kuwa shine abin alfaharin kowace 'ya mace, da kansa ya kai ni band'aki tare da had'a min ruwan wanka yana tattare hannun riga ya ce" Ko nayi miki wankan ne?" Kai na girgiza! alamar A'a na tsuguna sai kace wata sabuwar maijego gabana ciwo kawai yake min, ba tare da na kalle shi ba na ce" Ka d'an had'a min wani ruwan amma kada yayi zafi sosai. Da sauri ya had'a min ya taimaka min na shiga ruwan na zauna, rintse idona nayi sosai lokacin da zafin ruwan ke ratsa jikina, zugi da zafi suka sanya hawaye zubo min. Duk sai ya tashi hankalinsa yana ta bani hakuri, juye-juye kawai naka a ruwan kamar na fito, wata zuciyar ta hana ni, nasan cewa ruwan zafin shine zai dakusar da ciwon dake gurin. Hannunsa ya tsumbula cikin ruwan yana so ya ta'ba gurin "Ko dai na sa likita ta zo ta duba ki?" yana maganar yana so yasa hannanusa a gurin, ina kaucewa, na ce" A'a zai daina ciwon insha Allah. Ya ce." Ina so na gani ne domin hankalina ya kwanta. Kallonsa nayi naga da gaske yake maganarsa, na ce"A'a ba sai ka gani ba. Cikin wata irin murya mai taushi ya ce." Saboda me? bayan na zama wani jigo a rayuwarki, kin zama ni, na zama ke, meye abin jin kunya. Shiru nayi, domin bana tsammanin zan nuna masa. Ya fara 'kokarin tayar dani tsaye wai dole sai ya gani, kuka nasa tare da ri'ke bahon ruwan ina ture hannunsa da fad'in" Ka fita ni dai." Fita yayi ya bar ni a band'akin ba don ransa ya so ba. Na jima cikin ruwan d'umin. sannan nayi wankan tsarki! na fito na d'aure da towel mai girma a jikina. Ko da na fito baya cikin d'akin, amma ga kaya na nan, ya ajiye min a kan gado. Na shirya cikin atamafa java mai ruwan ganye kuma dinki yayi min cif! a jikina, mai kawai na shafa tare da fesa d'aya daga cikin turarunkansa dake jibge a kan madubi, na gabatar da sallar asubah da ta wuce ni, kafin na rarrafa na hau gado na kwanta bacci ne fal a cikin idona, ga wani irin ciwo da jikina keyi min, abu dai goma da ashirin! sun dabaibaye ni, jiya dai na yabawa aya za'kinta, har bana so na tuna gumurzun da mu kayi saboda tsigar jikina ce take tashi, amma na godewa Allah da ni'imar da yayi min, duk isar mace mutuncinta ta kai budurcinta gidan mijinta, na yi farin ciki da ya same ni cikakkiyar mace, kuma yanda na fahimta ya samu gamsuwa da ni ko ga irin addu'ar da yake min tare da d'aukar min al'kawari iri-iri, cikin zuciyata nake adduar Allah yasa hakan yake a zuciyarsa, don gaskiya bana k'aunar kishiya duk da na san umarni ne na Ubangiji amma ni kam na fi buk'atar na zauna ni kad'ai da mijina. Tare suka shigo d'akin da Hajiya, sai nayi saurin rufe idona, kunya nake ji kada ta fahimci wani abu ya faru. ashe zuwa yayi ya fad'a mata abinda ya ke da akwa. shine ta shigo ta duba ni. Kamar na fashe da kuka saboda takaici! ban iya cewa komai saboda nauyi da jin kunya baccin 'karya na tsira, ina jin suna ta maganganu nayi luf! sai da ta fita daga dakin sannan na bud'e idona na kalle shi. yana zaune kusa da k'afafuna yana waya! Cikin dubara na tashi zaune na d'an jingina da fuskar gado! ganin na tashi yasa ya katse wayar da ya kalle ni, cikin kulawa ya ce." Sannu kin ga yanzu Hajiya ta fita ta shigo duba ki." Zum'bara baki nayi tare da fad'in" Me yasa ka fad'a mata wani abu ya faru a tsakaninmu?" "Me yasa ba zan fad'a mata ba? bayan ta damu da nayi aure na haihu, sannan kuma yanda ki ke kuka da gurin shi ya bani tsoro na je na sanar da ita ko da wani taimakon da za tayi mana." Yafad'a idonsa a tsaye a kaina. Na ce" Gurin fa zai dusashe in sha Allahu. To "Allah ya yarda, amma na yi waya da likitana duk nayi masa bayani abinda ke da akwai, ya bani tabbacin cewa; idan ana bu'katar gurin ya zama normal sai an 'kara wani abun, shine na ce ko zaki bari nayi wani yanzu ko da sau d'aya ne. "Bangane ba." Na fad'a gabana na duk uku-uku! don gabad'aya hankalina ya tashi jin abinda ya ke fad'a. Sai ya fashe da dariya yana kallona. Ganin haka yasa na juya masa baya domin na fahimci tsokanata yake. Da sauran dariyar a tare da shi ya ri'ke hannuna da fad'in" Da wasa nake miki my love ba zan miki komai ba sai gurin ya warke in sha Allahu." Ba tare da na juyo ba na ce" Ka tabbata?" Shiru yayi be bani amsa ba. Shukura ta shigo da'kin da sallama a bakinta. shi ne ya amsa, ni kam kunya tasa na rufe idona, ina 'kokarin 'kwace hannuna dake cikin nasa, ya ri'ke da kyau! 'Bangaran Shukura kuwa ganin ta, kwance lakadan a gadon mahaifinta, sai wani bakin ciki ya turnu'ke ta, ga shi kuma a zaune ya kusa da ita hannunsa cikin nata, kamar ta kurma ihu! saboda takaici. A sanyaye ta ajiye kwandon abincin dake hannunta, ta ce"Daddy ina kwana?" Ya amsa cikin kulawa yana nazarin fuskarta domin ya hango damuwa a tare da ita. Sai da ta daure zuciyarta sannan ta ce" Antina ina kwana." Ba tare dana kalle ta ba na amsa da "Lafiya lau." daga haka ban ce komai ba, amma cike nake da mamaki ya akayi yarinyar ta sauko har take gaishe ni. Ta ce"Daddy Hajiya ta ce na kawo muku abin karin kummalo idan anti ba za ta iya saukowa 'kasa ba" Hankalinsa gabad'aya yana kaina ya bata amsa da cewar" To babu laifi hakan." Hanyar fita ta nufa jikinta duk a sanyaye. sai kuma ta kasa daurewa ta tsaya tana kallonsa kafin ta ce"Daddy ya maganar da mu kayi da kai kwana biyu da ya wuce?" Ya ce." Wace magana kuma?" domin shi ya manta ma sunyi wata magana. Ta ce" Akan dawowar Mommyna d'akinta da kuma al'kawarin da kayi min." Tsawa! ya buga mata tare da nuna mata hanyar fita. " Wuce ki bani guri shashashar banza." Da saurin gaske ta bud'e k'ofar ta fita tana sgare hawaye. Na kalleshi sai na ga duk babu walwala a tare dashi. Na ce" Ya za ayi ka kore ta har kana yi mata tsawa! kada fa ka janyo min 'bakin jini, Shukura 'yar ka ce bai kamata kayi haka ba." Babu fara'a a tattare dashi ya ce." Ke a ganinki abinda tayi ya da ce?" Ido na tsira masa da fad'in." Magana kayi da ita har kayi mata al'kawari lefi ne don ta sake tuntu'barka da maganar. Ya ce." A'a ni ban yi mata al'kawarin dawo da mamanta ba, ta dame ni da maganar sai na ce mata zan duba na gani." Dama abinda nake so na ji kenan daga bakinsa. Sai kawai nayi shiru raina gabad'aya ya 'baci! ban san me yasa ba haka kawai nake jin kishin matan da yayi tarayya dasu duk da cewa a yanzu basa tare, amma haushinsu nake ji sosai! Shiru d'akin yayi na 'yan mintina, kafin ya kalle da cewa" Ki tashi ki ci abinci ga farfesu Hajiya tayi miki." Yana 'kokarin bud'e fulas din yake magana. Motsi ban yi ba ballanatana yasa ran zan sauko na ci wani abu. Ya gaji da maganarsa ya had'a shayi da kansa ya karya ya sha, kafin ya zuba farfesun ya dangwala da biredi. Cikin bacci da ya fara fizgata na ji shi yana laluben hannuna dake cikin bargo, ya saka min wasu takardu. "Tashi zaune za muyi magana." Yafad'a babu wasa a muryarsa. Sai da na mula tukkuna na tashi zaune. har yanzu na kasa sakin fuskata, duk na damu jin maganar dawo da uwar gidansa. Cikin nazari ya ce " Duk kin sauya fuska saboda wani dalili mara tushe! kada fa ki damu, na riga na shafe babin Fatima a rayuwata, domin da zan dawo da ita to da tun kafin na aure ki na dawo da ita, don haka ki samu nutsuwa. Daurewa nayi na ce'' Waye ya fad'a maka na damu? kaina ne fa yake min ciwo ba wani abu ba. Murmushi kawai yayi tare da fad'in ''Ai na gane ana 'kaunata yanzu tunda na ga kishi 'karara a cikin idonki." Shashantar da maganar nayi ta hanyar fad'in" Wannan takardun fa?" Ya ce" Naki ne." Na tsira masa ido domin yayi min 'karin bayani. Ya fuskance ni sosai kafin ya ce." Kasancewar na samu abu mai muhimmanci a gurinki yasa nayi miki wannan kyautar. takardu biyu ne a hannunki, akwai na gidan mai da kuma na rumfar kasuwa dake kwari, yanzu haka ana cigaba da hada-hada na kasuwanci a kowane sassa, abinda aka samu duk ya zama mallakinki, ina miki fatan alheri. Na kalle shi da mamaki mai yawa a tare dani, na ce"Saboda kawai ka samu budurci a tare dani zaka bani gidan mai sukutum! nayi me da shi to?" Sai ya 'bata fuska da fad'in" Ba wai ba ne a gurina, kuma budurcinki ya cancanta da komai. domin zan iya tattare duk abinda na mallaka a duniya na baki saboda farin cikin da ki ka sanya ni a ciki, saboda haka ki dauki al'amarin da muhimanci, ki kuma sa a ranki cewa; kin bani abu mai daraja wanda bani da abinda zan biya ki dashi. Gabad'aya jikina yayi sanyi da kalamsa. kawai na ri'ke takardun tare da zuba masa ido, ni dai ban ga abinda zanyi da gidan mai ba, ina lefin rumfar kasuwar. Kira ne ya shigo wayarsa ya d'auka! nan na ji yana fad'in" In sha Allahu gobe zan shigo kano d'in sai a san yanda za a yi. Na ce" Don Allah mu tafi tare." Girgiza kansa yayi da fad'in" Za ki je amma ba yanzu ba sai kinyi nauyi. Sai na rasa inda maganarsa ta nufa, sai nayi nauyi kamar yaya? Ya katse tunani na ta hanyar fad'in." Kina bu'katar zama a wannan sashen ko za ki koma naki domin na riga na gama shirya miki komai." Girgiza kai nayi da cewa" A'a gwara nan d'in." Ajiyar zuciya ya sauke da tare da cewa "Shikkenan abinda ki ka za'ba shine za'bi na."