🥀🌹MAILAAH🌹🥀 Follow the 🌹MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS AND MORE 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 🥀🌹𝑴𝑨𝑰𝑳𝑨𝑨𝑯🌹🥀 𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰 𝑴𝑬 𝑪𝑰𝑲𝑬 𝑫𝑨 𝑭𝑨𝑫𝑨𝑲𝑨𝑹𝑾𝑨 𝒁𝑨𝑳𝑳𝑨𝑹 𝑪𝑨𝑲𝑾𝑨𝑲𝑰𝒀𝑨 𝑫𝑨 𝒁𝑨𝒁𝒁𝑨𝑭𝑨𝑹 𝑺𝑶𝒀𝑨𝒀𝒀𝑨 𝑴𝑬 𝑻𝑺𝑨𝒀𝑨𝑾𝑨 𝑨𝑲𝑶𝑲𝑶𝑵 𝑲𝑨𝑰 𝑾𝑹𝑰𝑻𝑬 𝑩𝒀 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐ 𝒀𝑨𝑹 𝑩𝑨𝑰𝑾𝑨𝑹 𝑱𝑨𝑱𝑰𝑹𝑻𝑨𝑻𝑻𝑼. 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 PAID BOOK FREE PAGES BOOK ONE بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ الْحَمْدُ لِلَّهِ نَحْمَدُهُ وَنَسْتَعِينُهُ وَنَسْتَغْفِرُهُ وَنَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْ شُرُورِ أَنْفُسِنَا وَمِنْ سَيِّئَاتِ أَعْمَالِنَا مَنْ يَهْدِهِ اللَّهُ فَلَا مُضِلَّ لَهُ وَمَنْ يُضْلِلْ فَلَا هَادِيَ لَهُ وَأَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ ---------Chapter 1 & 2 Miƙa na yi tare saka hannuna na rufe bakina da wa ta iriyar waskekiyar hamma ta kwace min ba tare dana shirya ba, ahankali na fara warware ƙafafuwana daga tankwasar da nai musu ta tsawon awanni, sai na ji sunyi min tsami har wa ta ƙara suke saki ƙas-ƙas, amma ahaka na daure na miƙe su a zaune, zura hannuna na yi tare da shafo daga dokin wuyana zuwa wuya, ina jin yanda ƙashin wajen kemin wanu iri saboda tsabar gajiya da duƙiyar da nayi, yawata idanuwa na nike a ko wane saƙo da lungu na ɗakin ina mamakin sanda har duhun dare ya mamaye ko ina ba tare dana ankara ba, sai na koma baya ina tariyo abin da ya faru. Hayaniyar muryoyi mabanbanta ke tashi, kowace murya da abin da take faɗi, sai na girgiza kaina da naji yayimin wani irin nauyi kamar dutse, na tariye wurin hayaniyar da koma daidai inda najiyo muryar wacce nikewa kallon bango abar jinginata ke faɗin. "Yo maraici hauka ne da za'a gallabi rayuwar baiwar Allah wacce bata ji ba bata gani ba, dan anga bata da wani zaɓi sai yanda rayuwa ta juyata shine za'abiyewa son zuciya acutar da ita, dan anga tana nuna kamar batason farin ciki ba shine za'a kashe ma ta rayuwa a tsaye, na rantse da girman Allah babu inda zanje imbar MAILAAH a wannan baƙin gidan me kama da akurkin kaji, dan kawai Allah ya jarabceta da ciwo sai a maidata kamar kamar mujiya a cikin mutane, wallahi ba zata zauna agidannan da sunan aure ba, sai na tafi da ita inda babu me sake jin ɗuriyarta. Kyakkyawar fara tas ɗin matar da hutu da naira suka nuna jikinsu akanta ta faɗi tare da warware mayafinta ta ci ɗamara dashi a ƙugu ta na jijjiga jiki. "Haba Hajiya Munubiya, dan Allah ki kyale musu yarinyarsu suyi yanda suke so da ita, Allah yasan zuciyarki da niyyar taimakonta da kike tun tana ƙanƙanuwa, yanzu ba lokacin tada jijiyoyin wuya ko yin faɗa bane, kawai kibita da fatan alkairi da addu'ai Allah yasa auren ya zama silar canzawar ƙaddararta, dan Allah kiyi haƙuri kowa yasan kina tsananin son MAILAAH kuma kin ɗauketa kamar ƴar cikinki, yanzu kiyi ma ta nasiha da huɗuba akan abin da ya shafi zaman aure." "Hajiya Umma ba za ki gane yanda nike ji ba, ba za ki gane yanda nike tsananin tausayin MAILAAH ba, ina jin rashin dacewa akan banzatar da ita da ake yi dan kawai an ganta a haka, yarinya tun tana ƙarama take shan wahalar rayuwa har girmanta haka, sannan ace abiyewa son zuciya ayi ma ta irin wannan auren, ki kalli gidan da ke amsa sunan gidan mijinta, wallahi ko me gadin gidnsu yafi ƙarfin zama a irin wannan gidan bare ita." tana magana tana kuka, idanuwanta suka kaɗa sukai jawur, cikin hanshaƙan matan da ke tsaitsaye su na yatsine fuska wa ta taja dogon tsaki tare da faɗin. "Mtswwwww aikin banza da wofi, kinsan kina jin tausayinta har haka kika gagara aura ma ta ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴaƴanki, sai yanzu da waɗanɗa keda ita suka aurar za ki zo da guntuwar gulmarki kina kuka munafurci wai ke gamai tausayi." maganar da matar ta yi ta sake tunzura tunzurarra, wato Hajiya Munubiya, nan ta koma kanta ta fara gaggasa ma ta magana, matar itama ba daga baya ba, sai ta zage ta dinga macifa tare da zagin Hajiya Munubiya, nan take ɗan ƙaramin ɗakin amarya ya hauci aka hau faɗa. Ina zaune akan ɗan ƙaramin madaidaicin gadon ɗakin, tun da aka zaunar da ni akai na duƙe ina kallon farin zanin da aka shimfiɗa, jin hayaniyarsu nike tana zaman lafiyar kwanyata, nan take jikina yahau tsuma, hannayena da ƙafafuwa suka hau karkarwa kamar wacce aka jonawa shocking, iya yanda hayaniyarsu ke ƙara yawa iya haka nike sake birkicewa, nan take da kwarara wa ta iriyar ƙara me shiga har tsakiyar kwanyar du wanda yaji ta, lokaci ɗaya na miƙe tsaye tare da soma neman guduwa ina kwarara ihu, kafin kace me, tuni rabi da kwatar mutanen ɗakin sunyi waje a mugun kiɗime, ina shirin fitowa naji anfizgeni baya tare da ɗagani saka sannan aka sake ni ƙasa na faɗi timmm, nan take kaina ya bugu da ƙasa, sai nayi wani shiru ya gifta, hayaniyar da nike ji anamin a cikin kai ta daina, sai duhu daya lulluɓe ganina duniyar tai min tsif kamar babu kowa acikinta. Ban san tsawon wane lokaci na ɗauka bana hayyacina ba, sai farkawa na yi naga wacce muke kira da Anty Ummie riƙe da ƙaramar fanka a saitina tana yimin tofi, kamar kullum bance komi ba sai tashi da nayi na zauna inabin saura da kallo, wasu suce min sannu wasu kuma su kalleni su taɓe baki, sai da marice yayi sannan kowa yayimin sallama suka watse bayan sun lulluɓemin fuskata da farin mayafi, daga inda nike zaune ina iya jin yanda motocinsu ke tafiya ɗaya bayan ɗaya, duƙar da kaina na yi na shiga tunanin iska dan babu abin da nike iya tunawa sai de inyi shiru ko inyi kamar na zurfafa a tunani, haka nike kaina babu komi sai fanko. A hankali na sauke ƙafafuwa zuwa ƙasan gado, sai nayi saurin janyesu jin na taka wani abu me sulɓi, haka nike inada wuyar sabo musamman da sababbin abubuwa, rayuwa tafi yi min sauƙi a ɗakina na gidanmu, du bayan lokaci ana yin aiki da sauye-sauyen abubuwa, amma bani yarda ayi a ɗakina, du randa aka sauyamin wani abu sai na daɗe ban sake a ɗakinba, haka zanta zama a takure kamar raƙumi a keji. Har nakoma na sake jingina sai kuma na sake tashi tunowa da ai Sallah nike so inyi, ahankali na sauko duka ƙafafuwa tare da yunƙura kamar me tsoron taka ƙasa na miƙe tsaye akan ƙafafuwana da nike jinsu kamar ba ajikina suke ba saboda tsami da ciwon da suke yi, ahankali na shiga takasu harna fice daga cikin ɗakin wanda duhu ya mamaye babu haske ko kaɗan, tsayawa nayi ina ƙarewa tsakar gidan kallon badan komi ba sai dan tap da nike nema, wani ɗan ƙaramin tanki na gani a kusa dashi ga famfo shima ƙarami, sai na tsugunna nayi fitsarin da cika min mara, sannan nai tsarki tare da ɗauro alwala, du sai da na jiƙe farar lafayar da ka naɗamin, a haka na koma ɗaki ina jina wani daban, sai tin da Anty Ummie ta nuna inda makunin haske yake kafin tafiyarsu na kalla, sai na miƙa hannuna bayan na rintse idanuwa gam na kunna haske, da sauri nakai zaune ina shesheka lokacin da nike ji a jikina farin hasken ya gauraye ko ina, kuma da alama hasken me ƙarfi ne sosai, nakai kusan mintuna arba'in ahaka ba tare dana tashi kona buɗe idona ba, sai da hasken yabi jikina, du wani gashi daya miƙe sai da ya kwanta sannan na tashi, jakar da nike aje kayan sallahta a ciki na gani agefe tare da wasu sabbin akwatinan, ban tsaya kallon komi dake wajen ba na kwalle kayana na saka rigar sallah da abayata. Zazzaune suke agaban wanda daga gani babbane ko me faɗa aji, nasiha yake musu me ratsa jiki, fuskar kowanensu aɗan maraurace, amma banda shi, zaune yake a tsakiyarsu baice komi ba, kuma ko kaɗa kai alamun amsawa bayayi kamar yanda sauran suke, aduƙe yake ba'a iya ganin ainahin fuskarshi, saboda baƙi wuluk ɗin gashin kanshi daya zubo har gaban fuskarshi, ganin sauran sun miƙe ya saka shima ya miƙe, ba tare daya ko kalli kowa ba ya saka kai gaba ya juya ya kama tafiya, tafiya yake cike da sadaukantaka kuma cikin isa da ƙasaita kamar wani jinin sarauta, matasane biye dashi a baya har suka zo daidai inda ya tsaya a ƙofar wani ɗan ƙaramin gida, gidanda a ido zaka iya hango ƙanƙantar da zaiyi a ciki, tsayawa yai saitin ƙofar daya buɗe, ya juyo da baya yana kallon matasan da birkitattun idanuwansa waɗanda suke sheƙi a cikin hasken farin watan, ganin yanda ya tsaresu da ido yana kallo, sai kawai suka juya suka tafi, sai da sukai mashi nisa a ido sannan ya juya ya shiga gidan ya kulle. Kanshi tsaye ya nufi kwalli ɗayan ɗakin da ke gidan ya shiga, ɗan turus yayi ganin yanda duhu ya mamaye ko ina, ba tare da jinkiri ba yashiga laluben makunin fitilar ɗakin dake jikin bango, bai yi aune ba ya ji ya sauke ƙafarshi akan wani abu lallausa kuma me ɗumi, da hanzari ya ja da baya, sai yai rashin sa'a ƙafarshi ta zame, ki kake timm ya faɗa akan wani abu me laushi kuma tattausa wanda ke fitar da lumfashi da alama hallitace me rai a wajen. Tun shigowarshi ina iya ganinshi, musamman da yake sanye cikin farare tas ɗin tufafi masu haske, naga sanda ya ke ta laluben bango da alama abu yake nema, ban motsa daga inda nike zaune ba, sai de na ɗaga kaina acikin duhun na dubi wajen da swetch ɗin ya ke, ban sa'ilin da ya ƙaraso inda nike ba, daidai saitin ƙafata, juyowar da zanyi dai kawai naji lallausa tafi me tsananin taushi ya taka ƙafata, ba halina bane zabura ko tsorata aduk lokacin da naga wani abu wanda zai cutar da ni, sam ni bana tsorata kamar sauran mutane, sai de in shiga wani yanayi me wuyar fassara, yanayin da ke tsorata du wanda ya raɓe ni. Second ɗaya, biyu, uku, har zuwa sakannin goma banji abin da ya tausheni me taushi da tsananin nauyi ya ɗagani ba, can cikin maƙoshi na furta sauti, "auch" saboda ji danayi zuciyata na zullo har tana ƙoƙari fucewa ta maƙogarona, wani irin luguden duka take min lokcin da naji hannunshi na laluben jikina kamar meson tantance wani abu, saurin tallafe hannunshi na yi ina girgiza kai kamar yana gani na, ina jin yanda ya sauke wa ta ƙaƙƙarfar ajiyar, sai kuma ya janye jikinshi gefe ya kwanta a ƙasa, wani irin shiru marar hayaniya ne ya mamaye ɗakin yayinda sautin komi ya ɗauke saina shaƙa da fesarwar iskar numfarfashinmu, mu kanmu bamusan iya adadin tsawon lokacin da muka kwashe a haka ba.....✍️ SOMIN TAƁI KENAN A CIKIN LABARI ME TAKEN MAILAAH KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZATA ƘARKE Follow the 🌹MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS AND MORE 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133 🥀🌹𝑴𝑨𝑰𝑳𝑨𝑨𝑯🌹🥀 𝑾𝑹𝑰𝑻𝑬 𝑩𝒀 𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐ 𝒀𝑨𝑹 𝑩𝑨𝑰𝑾𝑨𝑹 𝑱𝑨𝑱𝑰𝑹𝑻𝑨𝑻𝑻𝑼. 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* PAID BOOK FREE PAGES BOOK ONE بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ الْحَمْدُ لِلَّهِ نَحْمَدُهُ وَنَسْتَعِينُهُ وَنَسْتَغْفِرُهُ وَنَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْ شُرُورِ أَنْفُسِنَا وَمِنْ سَيِّئَاتِ أَعْمَالِنَا مَنْ يَهْدِهِ اللَّهُ فَلَا مُضِلَّ لَهُ وَمَنْ يُضْلِلْ فَلَا هَادِيَ لَهُ وَأَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ ---------Chapter 3 & 4 Ban saniba ko ƙosawa yai da yanayin sai jin motsinshi nayi ya tashi, fita yayi zuwa waje kafin ya dawo hannunshi riƙe da wani abu me haske, banyi aune ba sai ji nayi anhaske saitin inda nike a zaune, a mugun zabure na miƙe tsaye jikina na karkarwa, cikin ƴan sakanni ƙalila du nabi na ruɗe inata faman kare farar fuskata da hasken ke neman nakasa min ido, ja da baya na yi ganin yanda yake sake tunkaro ni da hasken, yaraf na faɗa akan gado inata faman shesheka, lokaci ɗaya hasken ya fitilar da yasamu damar kunnawa ya bibaye ɗakin, direct ya sauke birkitattun idanuwansa akaina, sai wasu maganganu suka shiga yi mashi amsa kuwa cikin kunne. "Haske!!!, ka kiyaye kunna haske kai tsaye a inda ta ke, bata son haske, yana kassara zaman lafiyarta, kuma yana zautar da ƙaramar ƙwaƙwalwarta, haske ne matakin farko da ke fara rikita tunaninta, takan shiga tsoro da firgici a lokacin da haske ya haskata kai tsaye ba tare da dabara ba." Ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke, kafin a hankali ya shiga taka dogayen ƙafafuwansa har ya ƙaraso inda nike zaune dafe da kaina inata faman shesheka idanuwana a warwaje, wani itin tartsatsin haske ya gilma ta cikin kaina lokacin da na ɗago da fuskata wacce tafara tirewa zuwa kalar jah, saukar idanuwa a cikin nashi birkitattun idanuwa wanda nike hango sheƙi da walwali wani kalar rauni, raunine irina na tsoro da fargabar faruwar wani abu, ban gama tantace inda kaina yake ba kawau naji na tafi luuuu duniyar na juya min, daga nan ban sake sanin komi ba, duhun da yake lulluɓe cikin ƙaddarar rayuwata ya ratsa da masarrafar tunani da ganina, shirun da ke cutar da tuhina ya ziyarceni ba tare dana shiryawa hakanba. Jijiyoyine ruɗu-ruɗu duka firfito a gaban goshi da kanshi, yayinda gumi ke tsatstsafo mashi ta kowace hudar gashi dake jikin fatarshi, da iya ƙarfin da Allah ya azurtashi yake riƙe da kafaɗuna yana jijjigani da tsananin ƙarfi ko zan dawo hayyacina, amma ina, a maimakon ihu da gurnani me ban tsoro da nacika gidan da shi, sai kaina ya shiga lauyewa gefe da gefe, wani irin fari tas ɗin yawu ya dinga gangarowa daga bakina, nan take jikina ya saki sautina ya ɗauke dif jikina yai wani irin sanyi ƙalau, a mugun tsorace ya sake ni nai baya bakinshi a buɗe idanuwan a waje ya dafe kanshi da ƙarfi sannan ya furta. "MAILAAHHHHHHHHHH!!!!!!!." Da wani irin hanzari magidancin da ke zaune akan sallaya yana tasbihi ya miƙe, lokaci ɗaya shaƙuwa ta kama shi, cikin sarkewar murya ya ke faɗi bayan ya dafe saitin zuciyarshi dake barazanr tarwatsewa. "MAILAAH, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, hasbunallahu wani'imal wakil, yah Rahaman." sai kuma ya duƙe a wajen wasu irin zafafan hawaye na ɓalle mashi, ga kuka da zafin zuciya sannan ga shaƙuwar data addabeshi. Wannan shine karo na babu adadi datai juyi kamar me barci, ranta a mugun ɓace bayan ta buɗe ido kaɗan ta ga har lokacin zaune ya ke yana tasbihi, ji take kamar ta tashi ta shaƙoshi ta kwantar a gefenta, sai babu adadi take baƙin ciki da zagayowar ranar a matsayin ranar girkinta, da tasan haka abin zai juye da bata yi wannan tafiyarba, ta na tsaka da tunani mahita sai ta ji sallatinshi, ba tare da ɓata lokaci ba har tana mancewa da ashe barci take ta miƙe zumbur tare da ƙarasawa zuwa inda yake a durƙushe yana saƙuwa, hannunshi a saitin zuciyarshi, idan ta ce batai farin ciki da hakan ba to ta gillara ƙarya, cike da kwarewa da sanin makamar aiki tashiga bashi taimakon gaugawa, bayan ta bashi ruwa me matsakaicin sanyi ta kwantar dashi akan gado da kyar, sannan ta dallara mashi allurar barci me tsananin ƙarfi, bai haura ƴan sakanni ba barci yai awon gaba da shi, cike da murna ta fice ta na jin daɗin yanda ta samu wannan damar, kanta tsaye ta haura samman dogon stirs ɗin dake fitar da dum light a gefen matattakalarshi, bayan ta shiga sai da ta tabbatar da ta rufe ko ina, sannan ta sunkuya a ƙasan gaɗo ta janyo wani ɗan ƙaramin jan akwati, nan take sarka me tsananin tsada ta bayyana, cike da nishaɗi ta shafa bayan sarƙar sai sarƙar ta fara rikiɗewa tana sauyawa yayinda hayaƙi fari fat ya cike ɗakin ta yanda ba'a iya ganin komi, can bayan wasu ƴan mintuna hayaƙin ya soma raguwa ahankali har ya ɓace ɓat, abin mamaki sai wannan matar ta bayyana zaune, farar fuskarta ta ƙara haske, yayinda hancinta ya ƙara tsayi kamar anja shi, laɓanta suka sake rinewa zuwan dark pink, sai ɗaukar ido ta ke, ga wani gwarjini na bala'i dake bayyane akan fuskarta, cikin ƙanƙanin lokaci kyawunta ya linku sosai fiye da yanda ta shigo ɗakin. Barci ya ke amma zuciyarshi naga ƴarshi jininshi, wacce yake zargin kanshi akan wofintar da rayuwarta, da ace ya rungumeta ya karɓeta da lalurarta, da rayuwa ba zatai ma ta ƙunci irin haka ba, da ace ya tsaya tsayin daka wajen kula da lafiyarta tare da juriyar nema ma ta magani, da yanzu wataƙila ta samu lafiya, yana matuƙar son ƴarshi MAILAAH, amma bai san dalilinda yasa ya kasa kulawa da ita ba, wani bin yakan mance da rayuwarta sai idan anyi zancenta ko Allah yasa ta fito waje su haɗu, yakan kalli tsakiyar jemamun idanuwanta waɗanda ruwa ke kwance masu sheƙi kamar hawaye, tsaf ya ke karantar rauni da kuma jarumtarta a cikin idonta, yakanji ya tsani kanshi daya kasa inganta rayuwarta, idan yayi niyar janyota jikinshi don ya kyautata ma ta, kuma ya zama inniwa a gareta, sai wa ta doguwar katanga wacce yayiwa laƙani da katangar ƙaddara ta gifta a tsakaninsu, taƙi ɗaya bazai ƙaraba daga inda yake sai de ya farka yaganshi kwance ana saka ma shi drip, tun abin na damunshi harya rasa sukuni har takai daya sadaƙar, yakuma cire hannunshi gaba ɗaya cikin safgar MAILAAH dan yana so ya tsira da lafiyarshi, badan abin baya nuƙurƙusar zuciyarshi ba, kawai de ya janye jikinsh daga ita ne dan samar musu da nutsuwa daga shi har ita. Bai taɓa zartar da hukuncin da yai danasanin ba irin aurar da MAILAAH, bai samu halartar ɗaurin aurenba, saboda ciwon zuciya daya addabeshi a safiyar ranar, gaba ɗaya guyagunshi sun gama sakewa akan cakuɗaɗɗun al'amurranda ke faruwa da rayuwar ƴarshi, muddin zaiyi hwaɓɓasa akan yi ma ta wani abu babu shakka sai yaji a jikinsa, sau dayawa zuciyarshi kanyi rawa akanta, har yakan ji kamar ya yarda da zancen da ake faɗi akanta na lallai ta haɗa jinsi da Aljannu, amma idan ya tuno yanda yai rayuwa tare da mahaifiyar sai ya tuhumi kanshi, mahaifiyarta itace wadda ta sadaukar da komi nata, ta sallama rayuwarta akanshi, idan zaiyi tunani iri ɗaya da sauran mutane tabbas ya zama butulu, gaba ɗaya kanshi a kulle yake, yanada buƙatar sarari domin ya nutsu yayi tunanin komi tun daga tushe, sai de bai da wannan lokacin, lokaci yayi ƙaranci a gareshi, idan yace zai matsanta kuma, to abubuwane masu tarin yawa zasu ɓullo marasa daɗi. Haka yaita tunane-tunane har lokacinda barci ya sake ɗauke shi. Tunda gari ya waye ta caɓa uban ado, gwala-gwalai ne keta walwali a jikinta, ga wani haske da kyau da tayi kamar wa ta sarauniya, ba tun yau ba, ba jiya ba, ba shekaran jiya ba, tun shekaru masu dama da suka shuɗe zuciyoyin ilahirin mazauna gidan ALHAJI SHA'ABAN ke rawa akan matarshi ta biyu me suna SALIMA, ba kyawunta da kullum yake ƙaruwa ne ke rikita tunaninsu ba, hatta izza da kwarjinin da take da shi abin zargi ne a wajensu, amma kamar an saka kwaɗo an kulle bakunansu, haka suka kasa tattauna zancen koda a tsakaninsu ne. Kamar yanda al'adar gidan ta ke na haɗuwa kowace safiya a ranakun aiki tun ƙarfe bakwai domin karyawa, yauma hakan ce ta faru, rankatakaf iyala Alhaji Sha'aban wanda suke kira da Alhaji ne zazzaune akan dogon dinning table, mecin mutane sama da ashirin, kowa ka gani daga matan har mazan shirye suke a cikin shirin fita aiki, yara kuma kowanne sanye da uniform, sai hayaniya ke tashi kamar gidan biki, da zuwanta wajen kowa yai tsit, hatta yaran du suka kama bakunansu suka nutsu, Hajiya Salima ta saki murmushi cike da ƙasaita sannan cikin izza da taƙama ta zauna akan kujerar da aka ware dan zamanta ita kaɗai, lokaci ɗaya suka haɗe bakunansu wajen gaisar da ita, sai da ta ƙare musu kallo one by one, sannan ta saki murmushin ƙasaita, tai amsawa ɗaya, daga nan kowa ya shiga sarving kanshi, tsit dinning ɗin yayi bakajin komi sai ƙarar cokulla, fuskokin mazauna wajen du sun nuna alamun ƙosawa da takura, muddin Hajiya Salima ta bayyana a waje wannan yanayin ne zai bayyan a fuskokinsu, basa sakew sai ta wuce ta basu waje, wannan ya saka idan ba dole ba babu me zama a kusa da inda ta ke, ita a wajenta tana ganin hakan kamar kwarjini ne, yayinda su kuma suke ɗaukar hakan a matsayin takurawa. ☆☆☆☆☆☆☆☆☆ Dummmm!! haka na ji kaina na sarawa da tsananin ƙarfi, yayinda na saka hannayena na dafe kan ina jujuyashi cike da azaba, idan akwai abin da nikewa zullumi, bai wuce gusowar dare ba, ni kaina bana iya tantance ainahin abin da nike ji, amma dazarar duhun dare ya kusanto, ina shiga matsanancin tashin hankali, zafin abu biyu kacal na sani, daga zafin azababben ciwon da kaina ke yi, sai zafin baƙar azabar da bansan yanda zan kwatanta ko misaltata ba, kwanyata bata aiki sam, hasalima bana iya tantance wacece ni karan kaina, amma nakan tantance nau'o'in azabar da a kullum dare nike kwana a cikinta. Buɗe idanuwa na da suka rine zuwa jajaye na yi, ina jin kamar in ciresu in huta saboda ciwon kan da nike ji har cikinsu, ban sauke su ako ina ba sai a saman farar fuskarshi wacce ke zagaye da lallausan saje, "ɗin,ɗinn,ɗinn". na ji wannan sautin ya doka a ƙoƙon kaina, a daidai lokacin da nayi tozali da ɗigo-ɗigo ɗin jinin da bansan ta inda yake fitaba a jikina, ya ɓata gaban farar rigarshi, ban san mi nike yi ba, amma naga hannuna ya miƙe zuwa kan ƙirjinshi a daidai saitin da jinin ya ɗiga, bazance ga abin da nike yi ba, sai kawai naga hannuna na zagaye inda jinin ya ɓata, caraf ya riƙe hannayena, tare da buɗe idanuwanshi ya watsosu a kaina. Wani tartsatsin haske ne me cike da tarin abubuwa waɗanda ke cakuɗe da hayaniya suka gilma ta cikin idanuwa, acikin abubuwanda suka gilma min nai nasarar cafke wani hoto, a cikin duhu ne a bakin ruwa, ina a tsaye yana a zaune ƙarƙashin bishiya na juya ma shi baya ina jefa ƙananun duwatsu a cikin ruwanda ke gabana, idan ruwan ya yo tsallo yalle sa'ilin da na jefa dutsen yakan fallatsa da ƙarfi har saman fuskata da ke a rufe ruf ba'a iya ganin komi, daga nan hoton ya yanke, sai kawai na damƙi gaban rigarshi da ƙarfi tare da rintse idona, ban san abin da zanyi kuma ban fahimci komi ba amma hakanan naji ina so in idasa ganin wannan hoton daya gilma min. Wa ta iriyar mummunar dokawa ƙirjinsa yayi, babu shiri ya rintse idonshi da ƙarfi, jijiyoyin da suka zagaye saman kanshi na sake fitowa raɗo-raɗo, wa ta iriyar zufa ta shiga karyo ma shi daga saman kai tana bin fatar fuskarshi, lokaci ɗaya jikinshi ya mutu murus, dama gashi ba wani isashen ƙarfi ne da shi ba, ko ina ciwo yake mashi a jikinshi, sake rintse ido yayi yana tunano mawuyacin halin da yaganni a ciki jiya da daddare. A CIKIN DARE Kwance ya ke kamshi na kallon sama, duda baya iya ganin komi saboda duhun da yayiwa ɗakin ƙawanya, tun da yaga yanda na firgita da ganin haske sai kawai ya kashe hasken yana tariyo maganganun kamikin mutumin da tun da yai tozali da shi, ya kasa mancewa da yanayinda yaganshi a ciki, zai iya ganewa idan wani na cikin damuwa koda kuwa yaso ya ɓoye hakan, kallon farko da yaiwa mutumin da aka sheda mashi ya zama suruki a gareshi, ya karanci tarin damuwa me ɗumbin yawa kwance akan fuskarshi, ya kasance cikin mutanen nan waɗanda basu damu da kowa ba, amma bai san yanda akai yaji ya damu da yanayinda yaga mutuminba, kalamanda yai amfani da su wajen yi mashi magana basada tsawo, amma sun samu wawakeken muhalli sun zauna daram a zuciyarshi. "MAILAAH ƴata ce, ka riƙe min ita amana, ka kula da ita, ka zame mata garkuwa kuma kariya ga dukanin wani abu dazai kusancet walau na cutarwa ko akasin haka, suna yi ma ta kallon mahukaci, sai de ba haka bane ƙaddarce ta mayarda rayuwarta haka, idan ka riƙeta amana nan gaba kaɗan zaka yi alfahari da ita, MAILAAH yarinya ce ƴar baiwa, wacce take rayuwa da ikon Allah kaje na miƙ ragamar rayuwarta a hannunka, Allah ya baka ikon kulawa da ita amin." .........✍️MARYAM STAR⭐ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HbYjxC6ucFxK95Gxo1yN9i 🥀🌹MAILAAH🌹🥀 WRITE BY MARYAM STAR ⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* PAID BOOK BOOK ONE FREE PAGE بسم الله الرحمن الرحيم. Chapter----------- 5 & 6 Bai mance yanda yaga Alhaji Sha'aban yakai hannu na ɗauke guntayen hawayen da suka sulalo daga idonshi ba, ya amshi amanarta tun a lokacin, ko da ace Alhaji bai roƙeshi akan ya kula da ita ba, zaiyi hakan, kodan albarkacin sunanda ya zama sillar haɗuwar ƙaddararsu waje ɗaya, daga lokacinda matar da yaji sam bata kwanta mashi arainba ta ambaci sunan MAILAAH ya rasa nutsuwarshi, akan sunan kaɗai ji yake zai iya sadaukar da rayuwarshi gaba ɗaya, MAILAAH sunane me matuƙar muhimmanci a rayuwarshi, zai iya mance da kowa, da komi amma banda sunan da mamallakitar sunan, a du faɗin duniyarnan babu abin da ke saka shi tsananin farin ciki irin tunowa da ƙanƙanin lokacin da ya yaru da ita, ya gama sadaƙarwa akan ya rasa farin ciki tun da ta kubce ma shi, ya tabbatarwa kanshi zai yi rayuwa amma bata farin ciki ba, zai rayune kawai dan karya ɓata gyara da kwaskwarimar data sadaukar da lokacinta wajen yi ma shi, itace wacce ta gyara ma shi rayuwa, a lokacin da ya fita yawon neman mutuwa ido rufe, bayan ya tsallake wahalhalun rayuwa sai kwatsam ta diro cikin rayuwarshi, ta shafe ma shi du wani tabo da dattin wahalar da yake ciki, ayanzun da babu ita sai yake tattalin rayuwarshi kamar yanda a lokacinda take a tare da shi take tattala masa, bai yadda ko ƙuda ya haushi da sunan cizo ba, kiyaye lafiyarshi ya ke sosai da sosai, shiyasa yau daya wayi gari yaji jikinshi na ciwo kamar wanda akaiwa duka, sai yaji ƙunci ya dabaibaye rayuwarshi. Idan bai manta ba yana a kwance ya fara jiyo nishi da gurnani, da farko bai maida kai ba, amma ji da yayi abin na sake yawa ya saka shi tashi zaune ya watsa idanuwanshi a daidai saitin inda take a zaune, da sauri ya tashi zaune zuciyarshi na dokawa, bazaice ga sadda ya miƙe tsaye ba, kawai ya tsinci kanshi ne riƙe da ita. Cikin ficewar hayyaci na shiga fizge-fizge a sa'ilinda ya riƙeni gam a cikin hannayensa, har lokacin ban daina gurnani ba, da nayi nasarar fuzge jikins daga nashi, sai kawai na shiga buga kaina da nike jin wa ta iriyar hayaniya na tashi a ciki a bango, da tsananin ƙarfi nike doka kan nawa cikin fitar hayyaci, sake kamoni yayi ya rungume ni tsam, sai na shiga sauke ma shi duka tako'ina ina ihu, na ɗauki lokaci me tsayi a haka, yayinda shi kuma yake riƙe da ni har lokacin, duda ihuna na tsananin shiga ma shi kai, amma bai sake ni ba haka ya dinga haɗa gumi, a sa'ilinda ya ke gab da fita hayyacinsa gaba ɗaya, ni kuma jikina ya fara saki sannu a hankali, kafin ya ankare har na fara sakin numfashi irinna me barci, lumshe idonsa yayi shima nan take barci me nauyi yayi awon gaba da shi. Damƙar hannuna yayi daga kan ƙirjinsa, a hankali ya zameni daga jikinsa sannan ya miƙe tsaye yana rangaji har ya fice daga ɗakin zuwa ɗan madaidaicin tsakar gidan, ruwa ya tara a tanki ya shiga ɗan mitsilin kewayen da ke tskar gidan dan yayi wanka. Kallon bayanshi na yi har ya fice daga ɗakin, tashi na yi tsaye ina jin yanda ƙafafuwana ke zugin azaba gasu sun kumbura sunyi suntum, ina jin zafi da azabar da suke min amma haka na takasu cikin rashin sanin abin da kemin ciwon, kaina tsaye na nufi hanyar toilet ɗin ko buta ban ɗauka ba na shige kaina tsaye. Wanka ya ke, kuma na ganshi amma ban damu da wanzuwarshi wajen ba na tsugunna gefe na tattare rigata da ruwan fitsari ya fara ɓatawa na tsula fitsarina, tashi na yi bayan na gama babu maganar tsarki na taka ta cikin fitsarin na wuce. "Mutane da yawa suna yi ma ta kallon mahaukaciya, sai de ba haka bane, ƙaddara ce ta zaɓi mayar da rayuwarta haka." Fes kalan Alhaji Sha'aban suka dawo ma shi lokacinda komi nashi ya tsaya da aiki na wucin gadi, rasa abin da zai yi yayi lokacin da na danna kaina cikin kewayen yana tsaka da wanka, hakanan ya ji yana ƙaryata zuciyarshi da take son aminta da cewa niɗin mahaukaciya ce, akwai wani abu wanda bai san minene ba da yagani a tattare da ni, shidai iya ganin mintunan da basu gaza biyu ba da yayi min cikin haske, sai ya yardarwa kanshi ni ba mahaukaciya bace, akwaide wani sarƙaƙen ƙulli dake dabaibaye da ni, wanda idan aka sakashi ya kunce zai sha matuƙar wahala kafin ya gane ainahin bakin zare, hakanan wa ta iriyar fargaba ta dirar ma shi, yayinda tsoro ya lulluɓe shi wanda shi kanshi bai san na minene ba, a gurguje ya idasa watsa ruwan wanda yake jin sanyinsu na ratsa gaɓɓan jikinshi suna sakar mashi kasala. Hannunshi riƙe ta fari ƙal ɗin towel yana goge ruwan jikinshi ya shiga ɗakin, sai yayi turus baki a sake yana kallona. Sallah nike yi hankalina a kwance, kuma anutse du iya kokonton mutum ba zai gane waje ɗaya da nayi kuskure ba, da mamaki ya idasa shiga ɗakin yana kallona, harna sallame, sai yayi kamar zaiyi min magana sai kuma ya fasa, dan shi ba mutum ne meson yawan magana ba, zai iya wuni zungur bai ce kanzil ba, koda yaushe bakinshi a rufe yake ruf Wani abu ɗaya da na yi wanda ya kusa sumar da shi da mamaki shine, ina gama sallar na kalleshi a ɗan fizge sannan nace. "Alhaji barka da kwana ka tashi lafiya." A mugun zabure ya ja da baya, yayinda sautin muryata ya dira a kunnuwansa a bazata, nan take wani abu ne nauyi ya motsa a ƙirjinsa, bai san ya buɗe raunanniyar muryarshi da yake ɓoyoba yace da ƙarfi. "Kkkekeke ke, kece!!! inmalillahi." Sai kuma ya zabura ya miƙe tsaye ya nufo ni kamar mayunwacin zaki, wa ta iriyar damƙa yayimin ya shiga girgizani da tsananin ƙarfi kuma a birkice kamar zautacce yake faɗin. "MAILAAHHHHHHHH! ki amsa min pls ke,,,, keece MAILLAH ɗin Tajjjjj ko?, nasani ai kece, baki gane ni ba, nine Taj ɗinki, wannan wanda kika taimaka kuma kika tafi kika barshi cikin kewa da nemanki, why' why zaki tafi ki barni, zuciyata ba zata iya jurewa ba, mi nayi maki da za ki nisanceni???."......✍️ TOFAH WATA SABUWAR, KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZA'A ƘARKE🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ M STAR⭐..........✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HbYjxC6ucFxK95Gxo1yN9i 🥀🌹MAILAAH🌹🥀 WRITE BY MARYAM STAR ⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* PAID BOOK BOOK ONE FREE PAGE بسم الله الرحمن الرحيم. ------------Chapter 7 & 8 Dummm, haka na ji kaina yayi sa'ilin da yake magana, du da fahimtar shi nike yi ba, amma akwai wani abu a tattare da shi wanda ke gilmawa a ƙwaƙwalwata, ina jin zafin yanda ya ke jijjiga jikina, da kuma yanda hannuwansa suka matse kafaɗuna, amma ban san mi zanyi ba, sai kawai na buɗe ƙaramin bakina ina kallonshi, kamar daga sama na ji ance. "Taj." da wa ta iriyar murya me tsananin rauni, na ji yanda sautin ya doka tare da bugun zuciyata, amma tunanina bai bani damar gane nice nai maganar ba. Da wani irin sauri Taj ya jefani a ƙirjinshi yai min murfi da hannayenshi sannan kuma kanshi daya kwantar akan kaina nawa kan, wasu irin zafafan hawaye na kwaranyowa daga idonshi, da wa ta iriyar murya me tsananin rauni ya ce. "MAILAAH!!!! ke ce ko, kece Mailaar Taj, miya faru da ke haka, Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, na sadaukar da lokacina ina neman ki, miyasa Mailaah, why kika zaɓi ki sabauta zukatanmu da ƙaddara ta haɗesu a waje guda, miyasa kika zaɓi ki tafi ki barni ba tare da sanina ba, kin mance alƙawarin da kika yi min cewa idan za ki tafi atare da ni za ki je, kin mance kince za ki kula da rayuwata ki ingantata, ko kin mance kince min zaki bani gata ki kula da rayuwa ta yanda zan mance rayuwata ta baya, ban taɓa son kowa ba sai ke, ban taɓa yarda da kowa ba sai ke ban taɓa jin zan iya rayuwa kamar yanda sauran mutane ke yin rayuwaba sai da kika shigo rayuwa, na rantse da tsarkin mulkin Allah bazan yi sake wajen kulawa da ke ba, ke ɗin tawa ce ni kaɗaina, bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya cutar da ke." Haka ya dinga sakin sambatu yana kuka kamar ƙaramin yaro, yayinda rayuwar da muka gudanar a baya ke sake haskowa ta cikin idonshi. MIYE ALAƘAR MAILAAH DA TAJ A BAYA???. 2024-1-1 KATSINA MAKURƊA. Sanye yake cikin riga da wando na yadi, dogone sosai kuma yana ƴar ƙiba ba laifi, fari tas, amma yayi duhu da alama dauɗa ce danƙare a jikinshi, kayan jikinshi kansu kamar wanda aka tono daga rami yayi futu-futu, ƙafafuwanshi babu ko takalmi suna sunyi buɗuɗu da ƙura da dauɗa, yayinda ya isa daidai waje wa ta bishiya da ke kusa da ƙodama, zama yayi a wajen yai shiru yana ƙarewa ruwan da sanyinsu ke ratsa shi kallo, kafin ya fara jin ƙarar takun takalmanta, waɗanda a tsawon kwanaki biyu kenan da take zuwa wajen kullum da daddare ya haddace yanayin ƙararsu, du tako ɗaya da zata yi tana tunkaro wajen yana ji kamar tana takowa da nutsuwarshi ne. Kamar kullum fuskata a lulluɓe ta ke ruf cikin niƙabi, wanda bada son raina nike saka shi ba sai dan babu yanda zanyi, da taimakon hasken farin watan daya haske ko'ina nike ganin gabana, ina jin yanda sautin takalmin kwalbar ƙafata ke amsakuwa saboda shirun wajen. A daidai bakin ruwan na tsaya, ina jin nutsuwa na safko min, lumshe idona na yi dake rufe ina shaƙar ƙamshin ƙasar wajen, zan iya rantsuwa cewa tun daga ranar da ƙafata ta dira a garin ban taɓa samun nutsuwaba kwatankwacin wacce nike samu idan ina a bakin ruwa, nayi iya yina wajen ganin na hana kaina juyawa kallon ƙasar bishiyar, amma abu yaci tura, sai da na juya na kalli wajen, kamar kuma ko yaushe idan na kalli wajen gabana kan doka da ƙarfi, yanzuma ina iya jiyo sautin yanda zuciyata ke tsallen bugu kamar zata faso ƙirjina, a hankali na fara takawa zuwa inda yake a zaune yana kallon ƙafafuwana, kamar meson haddace wani abu. Zillo zuciyata ta yi a daidai lokacin da na tsugunna agabanshi ina kallon fuskarshi wacce nagaza gane yanayin da yake ciki, ban damu da yanda zuciyata ke dokawaba na tsinci bakina na faɗin. "Mi kake yi anan, inane gidanku, kaci abinci miyasa bakayi wanka ba, bakada lafiya ne ko wani ya biyoka?." na dinga jera mashi tambayoyi muryata a karye, danakai dubana zuwa ƙafarshi bansan sanda na zauna a ƙasa tare da kama ƙafar tashi wacce nike iya ganin dauɗar da tayi ta cikin hasken farin watan, idona na tsiyayar hawaye ta cikin niƙabina na ce. "Ya Allahu ya Rahama!!! a ina kaji ciwo, akwai zafi ko, sannu, sannu kaji bara inje gida in ɗauko maka magani, jirani mintuna biyu yanzu zan dawo." Na faɗi muryata na sarƙewa saboda kuka, a hankali na aje ƙafar tashi tare da tashi da hanzari na fara tafiya gudu-gudu, har naɗanyi nisa sai kuma na dawo da sauri ina faɗin. "Kaci abinci, ko kanajin yunwa bara in taho maka da tuwo ban saniba ko zaka iya ci tunda bakada lafiya." Sai kuma na sake juyawa na tafi da hanzari.....✍️ KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZAMU WARWARE ZAREN SARƘAƘIYAR LABARIN. KUYI HAƘURI BA YAWA INA BUSY. MARYAM STAR⭐....✍️