Book 3 001           Yaya Adam yana zaune a falo shida matar sa Aisha yana cin abinci tana zaune a gefen sa ya kalle ta yace, "Ameena ta fito yau kuwa?." Aisha ta kalli hanyar d'akin da Ameena take ya kalle shi tace, "bata fito ba, abincin ma aika mata dashi nayi." Ya kalle ta yace, "Meyasa baza kice ta fito ba wai? Baki San Zaman dak'in yana k'ara mata damuwa ba?" Ya fad'a zai mik'e tayi saurin rik'e hannun sa tace, "Dan Allah ka zauna." Ya zauna din kamar yadda tace yana kallon ta yace, "meyasa?." "Tana buk'atar zama ita kad'ai din wani lokacin, kar ka manta ka sanar dani tana son mijin nan nata sosai, watakila bata kawo rabuwa a yanzu tsakanin su ba dole tana buk'atar keb'e kanta ba ko yaushe zata kasance mai son magana ba. Bata iya yi maka musu shiyasa in kace ta fito take fitowa, ka kyale ta dan Allah kar ya zama an shiga hakkin ta kuma." Yace, "baki san zama ita kad'ai zai iya k'ara mata ciwo ba? Hawan jini gare ta fa, likita ta tabbatar min da ana bukatar tadinga kasancewa cikin jama'a ana hira da wasa da dariya da ita akan me zan barta ita kad'ai? Fitowa ta cikin mu shine zai saka ta nishadi ko da batayi magana ba hirar mu zata saka ta cikin farin ciki." "Na sani, amma wani lokacin tana son zama ita kad'ai din ka fahimta, koda ta shigo cikin namu wallahi bata sakewa ka dinga kula da hakan. Kuma Amira na tare da ita suna hira saboda tafi sakawa da Amiran ne ma mahaifiyar ta ta bar mata ita sai ta warware Amiran ta koma, dan Allah ka kyale ta anjima zata fito." Bai sake cewa komai ba ya cigaba da cin abincin sa kafin yace, "mijin nata ma yana neman sake b'ata min rai, hukuncin da na k'iyi masa saboda Iyayen sa shi yake so nayi masa da alama" ya fad'a yana kwafa tare da girgiza kansa. Tayi murmushi tace, "kafa daina zaqewa a lamarin mata da miji, kar kazo kaji kunya nan gaba." D'aure fuska yayi babu alamun wasa ya kalle ta yace, "Kamar ya zanji kunya? Kina nufin zata koma masa ne?, kinga Asiha  bana son b'acin rai kar ki sake fad'amin wannan maganar koda wasa. Wanne irin na daina zaqewa me kike nufi?." Mik'ewa tsaye tayi ganin ransa ya b'aci  tace, "Allah ya Baka hakuri." Zata wuce kenan aka sallama aka shigo falon duk suka kalli masu shigowa tare da amsa sallamar suka k'araso ciki suna tsuguna suka gaishe da Yaya Adam, yayi murmushi yace, "Zakiyya da Rukayya, Barkan ku da zuwa." Murmushi duka sukayi cikin mamaki Zakiyya tace, "Yaya ban d'auka zaka gane mu ba ai wallahi." Shima murmushi yayi yace, "ashe bazan gane Ameena ba kenen." Rukayya tace, "Gaskiya ne." Murmushi kawai baice komai ba suka gaishe da matar da ta amsa fuska sake yace, "Aminai kenan a wajan Ameena, ki nuna musu d'akin da take." "Kaga ai ga masu saka ta nishadi sun zo sai hankalin ka ya kwanta" ta fad'a tana yin gaba tana dariya suka bi bayan ta har inda Ameena take. Ta zaune akan katifa ita kadai ta jingina da bango tana kallon bangon yake gaban ta tayi shiru kamar mai d'aukar darasi. Aisha tace, "Ameena kina aikin tunanin ne? Ina Amira da Zaitun suke?." Sai a sannan ta kalli wajan da taji maganar ganin su Ruky sai tayi murmushi tace, "Aunty sun dame ni da hayaniya ne shine nace su fita, saukar yaushe? Ta fad'a tana kallon su Zakiyya. Aunty Aisha ta kalle su tace, "kuyi mata fad'a dan Allah ku sanar da ita k'addara tana kan kowa, rabuwar aure  kaddara ce tun kafin auren ta Allah ya rubuta haka, ta karb'i kaddarar ta saki jikin ta shi yana can tare da matar sa har yanzu bai zo gidan nan ba koda sunan ganin y'ar sa balle ita, ita kuma tana nan zaune kullum a d'aki tana kuka tana tunani, ku sake nusar da ita ko zata fahimta kune k'awayen ta zata fi amincewa da maganar ku"ta fad'a tana fita ta basu waje. Zakiyya ta zauna a gefen ta na dama Rukayya ta zauna a haggu suka saka ta a tsakiya duk suka dafa ta Zakiyya tace, "Ameena abinda Auntyn ki ta fad'a gaskiya ne, ki duba yadda kika sake komawa fa dan Allah , wallahi Yaya Adam bazai ji dadi ba kina gidan sa ace kina wannan ramar ba." Rukayya tace, "gata yayi miki dan in ba shi ba babu wanda  zai karb'o ki daga wajan Yusuf." Ameena ta sauke numfashi tace, "kawai ina tunani ne daman nima zan kasance a cikin layin mata zawarawa?." Rukayya tace, "kaddarar ki kenan ai kuma dole sai ta same ki, shi kuma tunda ya samu wata ya wulakanta ki." Ameena tayi murmushi tace, "Wai a ina kika samu labarin ina nan? Nidai nasan bamu yi maganar ba." "Daman ai baza ki fad'a mana ba, kiran ki nayi Amira ta d'auka nace mata zan zo gidan sai take fad'a min ai kina nan ga abinda ya faru" Rukayya ta fad'a tana kallon ta. Ameena ta sauke numfashi tace, "Abun kamar a mafarki nake kallon sa". "Ai nan taba ganin namiji kamar Yusuf din ki ba Ameena, Tunda Rukayya fa fad'a min na dawo daga rakiyar maza, Tunda ya iya yi miki kishiya yazo kuma yana wulak'anta ki a akanta har abin ya kai ga kin dawo gida naji duk duniya babu wanda na tsana kamar Yusuf, wallahi sai Allah ya saka miki dan bai miki halacci." Ameena bata ce komai ba Zakiyya ta sake cewa, "ki saki jikin ki Hajiya kina gida ne kema ki kawar da komai a ranki yana can tare d a matar sa ke kina nan da damuwa a zuciyar ku ciwo ya same ki ki shiga uku, dan shi bai san kina yi ba ki mik'awa Allah lamarin ki kawai ki fara sabuwar rayuwa kamar ko wacce mace. Wannan damuwar ba abinda zata k'ara miki sai ciwo da wata damuwar, dan Allah ki cire batun Yusuf a zuciyar ki." Ameena tace, "babu Yusuf a tare dani yanzu Zakiyya, ni burina yanzu ma yazo yace ya sake ni din dan bana mafarkin komawa gidan sa, ni kad'ai nasan me a cikin gidan. Kawai abu kad'an ne yake saka ni damuwa bayan shi babu komai." Rukayya tace, "to shima ya daina saka ki damuwar, damuwa dai ciwo ce a tare dake, yanzu kika samu ciwo kan ki kika cuta ba shi ba." Tayi murmushi tace, "mu bar maganar nan ta wuce in sha Allah na manta da Yusuf kenan, wai ina labarin Fidyn New York?." Zakiyya tayi dariya tace, "Tana can ana chilling ana buga uwar soyayya." Ameena tayi murmushi tace, "Hajiya Fidy buri ya cika, ga mai kud'i gata kuma a America k'asar da tafi so." Rukayya tace, "buri ya gama cika ai a wajan ta." Ameena ta kalli Rukyy tace, "Ya batun Umar din? Komai yayi daidai?." Rukayya ta sauke numfashi tace, "yana nan magana tana neman yin k'arfi ma, zancen aure ya shigo tsakani sosai." Zakiyya tace, "Alhamdulillah, amma ya naga bakya farin ciki? Akwai wani abun ne?." Rukayya ta d'aga kai tace, "Akwai." Ameena ta tashi zaune sosai tace, "meye?." Rukayya ta kalle su tace, "Kun san wanda ya samu Baba da batun aurena kuwa?." Suka kalli juna suka girgiza kai alamun basu sani ba Rukayya tace, "Ibrahim tsohon mijin Fiddausi mahaifin Amir dan ta." A tare suka zaro idanu waje Ameena tace, "Wai tsohon mijin Fiddausi tamu?." Rukayya ta d'aga kai sama tace, "shi fa, yanzu haka maganar da nake muku Baba ya bashi damar yazo mu gaisa. Ban San me zance ba wallahi gabad'aya ji nake kamar na aikata wani kuskure babba. Bana so yazo ma balle ace mun zauna nida shi a matsayin wai wanda yake neman aurena, wani iri nake ji a jikina wallahi sam babu dad'i." Zakiyya ta girgiza kai tace, "ikon Allah! Ibrahim yazo wajan Baba yana neman auren ki? Bayan Fiddausi ta rabu dashi." Rukayya tace, "ni wallahi zancen ma fad'uwar gaba yake saka min." Zakiyya tace, "Kin san wani abu Rukayya?." Rukayya ta girgiza kai alamun A'a tace, "Sai nake ji a jikina kamar fa daman haka Allah ya shirya shiyasa ya jinkirta miki yin auren har sai da Ibrahim ya rabu da Fiddausi." Rukayya tace, "Kina nufin wai shine mijina? Haba Zakiyya tsohon mijin Fidy ne fa, ai ba easy ace na auri tsohon mijin k'awata Fiddausi, wacce nasan sirrin gidan ta kaf, Haba ai babu dadi." Ameena tace, "shi abinda Allah ya tsara babu wanda zai canj shi duk abinda mutane zasu ce kuwa a kai, in haka Allah ya k'addara akwai abinda zakiyi ne?. In daman shi Allah ya rubuta shine mijin ki ya zaki yi?." "Amma dai akwai cin amana a lamarin nan, sai Fidy taga kamar ma tun baya son mijin nata nake yi wallahi. Ni in yazo zan fad'a masa yayi hak'uri kar ya sake zuwa inda nake da sunan yana sona ni bazan aure  shi ba. In na aure shi mutanen unguwa ma ai sai su tsine min, ga Baba yayi na'am dashi sosai, a yadda Umma ta fad'a min sai da yaje gidan su Fiddausi suka gana da Abban su akan batun Ibrahim din tunda  ya dawo yake ce mata shi ya amince da İbrahim. Wallahi gabana fad'uwa yake bana so ace hakan ta kasance." Zakiyya tace, "in hakan ta kasance din ai me Rukayya? In ma lokacin da Fiddausi take auren sane dan ya aure ki wani abun ne balle bata tare dashi tayi masa nisa a yanzu tunda  tana da aure. Saboda talaka ne Fiddausi taga bazata iya zama dashi ba, kin san komai ai akan abinda ya raba su; ke kuma kina ganin zaki iya zama dashi to meye a ciki?. Ita arzuk'in sa bai mata ba ke kuma yayi miki meye to?." Ameena tace, "wai daman saboda haka Fidy ta rabu da Ibrahim?." Rukayya tace, "hmm bakin su d'aya da Zakiyya fa, duk abinda ya faru da saka hannun Zakiyya itace take zuga ta." Zakiyya tace, "k'aramar yarinya ce da zan zuga ta? Babu wata zugata da nayi akwai ni na taya ta cika burin ta ne kawai kuma burin ya cika." Ameena ta kalli Zakiyya tace, "zugar kenan ai." Zakiyya tace, "wannan ya wuce Ameena, muyi magana akan abinda yake gaban mu a yanzu. Bara na kira Fiddausin na tabbata abinda na fad'a shi zata maimaita, duk hankalin Rukayya ya tashi Akan wannan gwara tasan ba wani abun bane ba" ta fad'a tana d'auko waya ta shiga kiran Fiddausi ta katse bata d'auka ba ta sake kira a lokacin ga dauka ta saka a speaker daga can tace, "Kiyya yane? Kin kira ina wanka ina fitowa kiran ki ya sake zuwa." "Amaryar Alhaji Bello, ko ne mana ma bakya yi" Ameena ta fad'a daga gefe." Fiddausi tace, "Muryar wa nake ji kamar ta uwar gidan Yusufa?." "Nice." "Wallahi Ameena baki da kirki, message nawa na yi miki ta WhatsApp bakya bud'ewa?." Ameena tayi murmushi tace, "wallahi ni na manta ma rabon da na shiga WhatsApp,  tuba nake amarya." Fiddausi tayi dariya tace, "wallahi nayi kewar ku sosai, ina amaryar Ibrahim kuma?" Ta fad'a tana dariya sosai. Kallon juna sukayi Zakiyya tace, "daman kin san maganar ne?." Fiddausi tace, "na sani mana, jiya ake bani labari a gidan mu Baba yaje ya samu Abba da maganar shi kuma ya fad'awa Mama, Mama tace sai farin ciki Abba yake yi dan wai Ibrahim yana son Rukayya kamar wani gwamna ne yake sonta. Kar dai su Abba suyi mata dad'in baki ta yarda ta kai kanta gidan talauci wallahi." Zakiyya tace, "Maganar muke yanzu da da Ruky kin ganta a zaune duk tayi tsuru-tsuru wai ita ji take kamar ma zuwa da yayi yace yana sonta kamar taci amanar ki ne." "Amanar wa? Ni Fiddausin Abba?, Rukayya ko lokacin da nake gidan sane yace zai d'auko ki meye zai dame ni balle bana gidan?. Nifa sai yanzu nasan meye aure nasan meye ma kishin miji, wallahi da bana kishin wani Ibrahim balle naji haushi da zaiyi aure, kina ji Ruky in zuciyar ki ta amince da Ibrahim bismillah ki shiga babu abinda zai damu Fiddausi, kuma in na dawo har gidan zan zo wajan ki mu gaisa dashi matsayin mijin ki naci shinkafa da wake in akwai kunu na kora dashi babu abinda ya shafe ni. Ai na rufe chapter wannan talakan a rayuwata wallahi. Kawai dai kema ki yiwa kanki fad'a kowa gidan jin dad'i yake zuwa ke zaki tafi gidan wahala." Zakiyya tace, "Kamar a gaban ki haka nace mata yanzu nan, dan ma fa hankalin ta ya kwanta ne ya saka na kira ki, duk da basu zauna shida ita ba ya samu Baba da maganar ne kawai shine hankalin ta ya tashi haka wai mutanen unguwa sai suce daman tun can baya tana son sa ita ta kashe auren ku dan ta aure shi." Fiddausi tayi dariya son ranta harda su tafa hannu  kafin tace, "to su fad'a mana, in zata biyewa mutane ai baza ta yi komai a rayuwar ta ba. Ni kaina dana biye mata ai da yanzu bana inda nake, ni wallahi in da zata aure shin ma farin ciki zanyi saboda nasan Amir dina ya samu uwar da zata kula dashi fiye dani." Sai a sannan Rukayya tayi magana tace, "balle ma babu abinda zai kai ni Allah ya had'a kowa da rabon sa." Fiddausi tace, "gwara dai ki yiwa kanki fad'a ki samu mai kud'i ba irin su Ibrahim ba. Sai yanzu nasan da zaman cutuwa kawai nayi wallahi." Murmushi kawai Rukayya tayi Zakiyya tace, "Wai yaushe zaki dawo ne?." "Ke nima ban sani ba wallahi, Ina nan ina Shan soyayya me zai dawo dani Nigeria?. Wai kuna gidan Ameena ne na jiku tare?." Zakiyya tace, "eh Muna can, kin San da yake...." Ameena ce ta tab'a ta tare da girgiza mata kai alamun kar ta fad'a mata Zakiyya ta fasa fad'at abinda zata ce tace, "sai dai kin dawo akwai labari, amma ina jin bakya nan za'a yi bikin Ruky." "Maganar tayi karfi kenan?." "Eh akwai wani ai da yake sonta da gaske kuma bana jin auren zai d'auki lokaci." "Mai kud'i ne?." Zakiyya tayi dariya tace, "Mai kudi ne, sai dai yana da mata." Fiddausi tace, "in ma mataye ne dashi ba mata ba kawai ta shiga, Allah ya sanya alkhairi. Kai amma naji dadi wallahi Rukyya zata shiga daga ciki itama." Dariya sukayi dukkan su kafin suyi  Zakiyya tace, "kar ki kwashe min katin ma k'arasa a whatspp" ta fad'a tana kashe wayar ta kalli Ruky tace, "kin ji ahında na fad'a miki ko?. Rukayya kar ki yi gaggawar korar Ibrahim kice masa ke bakya son sa, ki tsaya ki yi addu'a kawai wanda ya kasance alkhairi Allah ya zab'a miki a cikin guda biyun, in dukkan su babu alkhairi Allah ya kawo miki wasu. Ke zuciyar ki ba irin tamu bane ta son mai kud'i ba, dan haka Ibrahim daidai da ke ne." Ameena tace, "shine akwai abin yi." Rukayya ta girgiza kai zuciyar ta na yin sanyi da kalaman Fiddausi da kuma nasu Zakiyya domin sai taje jin tsoron da take ji game da Ibrahim gabad'aya ya kau, zuciyar ta sai take bata k'arfin guiwar zata iya sauraren sa koda bazata aure shi ba. Ameena taji dad'in zaman su sosai sun jima suna hira ta sake ana dariya da ita har bayan la'asar sannan suka tafi.      Rukayya tana komawa gida shigar ta soron gidan su kenan suka had'u da Baba  yana niyar fitowa ya kalle ta yace, "ina kika je ne ina ta neman ki?." Rukayya tace, "munje wajan Ameena ne nida Zakiyya." Baba yace, "maza kije ki shirya kina da bak'o yana jiran ki." Gaban Rukayya ya fad'i  ta d'aga kai Baba ya fita ita kuma  ta shiga wajan Umma. Da Zuhra suka had'u a tsakar gida tayo wajan ta tana fadin, "Aunty kin san waye yazo wajan ki? Ibrahim fa mijin Fiddausin ki." Rukayya tace, "Shine bak'on da Baba yake fad'a?." Ta d'aga kai tace, "Shine, kije kar baba yayi miki fada tun d'azu yake neman ki wayar ki bata shiga."         Falon Umma ta shiga Umma na ganin ta tace, "tun d'azu ake kiran wayar ki bata zuwa, kin shiga wajan bak'on?." Ta girgiza kai alamun A'a tace, "Umma anya hakan ya dace kuwa?, mijin Fiddausi ne mahaifin yaron ta fa." Umma tace, "Jeki dai kiji mai zai ce ki dawo sai muyi maganar daga baya" da to kawai ta amsa ta juya ta fita ba tare da ta canja komai ba ta nufi d'akin da Baba yace mata gaban ta yana mugun fad'uwa bata san dalilin hakan ba a haka ta tunkari d'akin zuciyar ta na bugawa sosai. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid Book3 002 Sai da ta tsaya a bakin k’ofa ta daidaita nutsuwar ta sannan ta shiga da sallama kanta yana k’asa. Daga ciki taji ya amsa ta k’arasa ta zauna a kan carpet ta d’an yi shiru bata ce komai ba kafin ta d’ago ta kalle shi tace, “Barka da yamma.” Kyankyawan murmushi yayi mata wanda ya saka ta saurin mayar da kai ‘kasa yace, “Barka dai Malama Rukayya, ina fatan n same ku lafiya.” Rukayya kanta yana kasa tace, “Lafiya lau, ya su Hajiya?.” “Alhamdulillah, tanas gaishe ki.” Bata iya amsa ba domin zuciyar ta bugawa take yi sosai ya lura da rud’anin da take ciki sai ya tausasa murya yace, “Rukayya nazo wajan mahaifin ki akan ina so na shiga sahun masu neman auren ki, shine ya bani dama yace nazo yau na ganki kuma gashi nazo, sai dai ke naga kamar bakya son ganina ni kuwa ganin naki nake so.” Kai ta girgiza kawai bata ce komai ba ya sake cewa, “ilimin ki, nutsuwar ki da kuma shaidar da kika samu daga bakin mutane itace ta jawo hankalina zuwa ga auren ki. Kamar yadda Baba ya sanar dake sunana Ibrahim na tab’a aure amma bana tare da matar, ina da yaro guda d’aya mai sunan mahaifina wanda nake kira da Amir. Ina aiki a masana’antar sarrafa siminti.” D’ago ido tayi ta kalle shi cike mamakin sa jin yana fad’a mata abinda ta riga ta sani hakan kamar ma ya raina mata hankali ne. Ganin tana kallon sa sai yayi murmushi dan ya fahimci dalilin kallon kafin yayi magana tace, “Duka nasan komai a kanka kamar ka sani a kaina, amma ka manta wacece ni a wajan….” Saurin dakatar da ita yayi yace, “Baki sanni ba ban sanki ba, yau kika fara ganina nima yau na fara magana dake, ban zo nan da a tuna wata magana da ta wuce ba, ban zo nan da a tuna wani ko wata ba, haka ban zo nan dan a bani labarin wata alaqa ba. Shi aure yana faruwa ne in Allah ya qulla babu ruwan Allah da alaqa ko wani ko wata, kuma ita k’addara takan zo a kan abinda baka yi tunanin ba, domin wani lokacin sai wani abun ya faru sannan k’ofar alkhairi zata bud’e maka ba tare da ka fahimci hakan ba, kafin faruwar hakan baza ka kawo ba amma in ya faru in ka zauna zakayi tunani ashe daman saboda kaddarar da Allah ya rubuta min aka yi kaza da kaza.” Shiru tayi tana jin sa kalaman Fidy suna fad’o mata musamman in tana cewa akwai kalamai a bakin Ibrahim ta kuma yadda domin yadda yake magana dole ba su shiga zuciyar ka, yace, “Rukayya ki saka a ranki baki sanni ba, nima zan saka a raina ban sanki ba sai da nazo neman auren ki, in kika ce zaki tuna baya babu abinda zaka ciki cimma a rayuwar ki domin kuwa duk abinda ya wuce ana so ka barshi a ya wuce ka kalli abinda zai zo kuma. Ki d’auke ni matsayin mai sonki har abada baza kiyi dana sani ba, kamar yadda na nake so na d’auke ki mai sona dan nasan bazan yi dana sani ba nima.” Rukayya tayi shiru bata ce komai ba har lokacin ya ake cewa, “Na amince dake dari bisa dari zuciyata ta amince da auren ki, ban san naki b’angaren ba zaki amince ko kuma akasin hakan. Ina rok’on ki dan Allah in zaki amince dani ki amince dani dan Allah, in kika tashi akasin haka ma ki k’i ni saboda zuciyar ki badan wani dalili naki ba.” Rukayya ta d’ago idanu ta kalle shi ta girgiza kai tace, “har yanzu in na kalle ka ina kallon ka matsayin mijin k’awata wacce nasan sirrin gidan ta, bana jin zan iya abinda kake cewa domin ina kallon abun tamkar cin amana.” “Amma ai na rok’e ki nace miki kar ki tuna baya ki d’auka baki san Ibrahim ba yanzu yazo gare ki, wannan ne kawai zai baki damar amfani da zuciyar ki Rukayya. Amma in kika kalle ni ta wannan fuskar da kike fad’a zaki amfani da tunani ne kawai ba tare da zuciya ba.” Ganin tayi shiru bata ce komai ba yayi murmushi yace, “Na gode da damar ganin ki da kika bani, ina fatan sake dawowa a sake maimaita irin wannan zaman, amma ina fatan salon kalaman ki zuwa lokacin sun canja.” Ya mik’e tsaye yana kallon ta daga zaune ko motsi bata yi ba yace, “na barki lafiya Malama Rukayyan Ibrahim, ki gaida mutanen gidan” yana fad’a ya fita ya barta a zaune a wajan zuciyar ta na sake maimaita mata _Malama Rukayyan Ibrahim._ Har Baba ya shigo bata sani ba ya kalle ta yace, “A’a Rukayya baki shiga gidan ba? Lafiya dai ko?.” Ta kalli Baba tare da mik’ewa tace, “Lafiya lau Baba, yanzu zan shiga” ta fad’a tana wuce Baba ta shiga cikin gida ya bita da kallo yace, “Allah yasa lokacin tashin ki yazo Amin.” Rukayya tana shiga falon Umma suka had’a ido da Umma tasan feedback take so ta bata sai ta zauna kusa da ita tace, “Umma Mun gama.” Umma tace, “to kin amince dashi?.” Shiru tayi ta sauke numfashi tace, “wallahi bana ce ba Umma, amma ki taya ni addu’a kawai Wanda ya kasance alkhairi a gare ni Allah ya zab’a min.” “Amin” Umma ta furta a takaice ita kuma ta mik’e ta shiga d’aki. Tana shiga wayar ta nayi k’ara taga sunan Umar ta tsaya tana kallon wayar ba tare da ta d’auka ba, Umar yana sonta sosai yana kuma qaunata ta sani, gashi dan gayu matashi mai kudi mai kyau, in ta aure shi ita kanta tasan ayi dacen wanda yake sonta. Gashi yasan dajarar iyalan sa sau d’aya bai tab’a yi mata maganar matar sa ba balle ya aibata ta akan wani abun. Kulle ido tayi ta bud’e ita bata da zab’i kawai ta barwa Allah zabi wanda ya zab’a mata shi zata karb’a hannu biyu. A can New York bayan sun gama waya dasu Ameena tana zaune a gefen gado Alhaji ya shigo ya kalle ta sai ya d’auke kai ya karasa inda ya ajjiye kayan ya bud’e ya d’auki abinda zai d’auka ya mayar ya rufe har lokacin bai kalle ta ba. Da sauri ta tashi ta tare gaban sa tana kallon sa tace, “Haba Baby wai fushi kake dani haka?.” Bai mata magana ba ya wuce ta ta bishi da kallo har ta daina ganin sa ta zauna tana kallon wani wajan daban zuciyar ta babu dad’i ko kad’an dan tunda taga yayi haka tasan fushi yayi. Kaya ta saka kamar yadda ta saba tsukewa dan wandon da ta saka iya rabin cinyar ta ya rufe, rigar kuwa gabad’aya cikin ta a waje yake haka bayan ta ma an kwashe tsakiya. Tayi kyau sosai ita kanta ta sani domin jikin ta akwai d’aukar kwallaiya ta fito ta zuba tea da yake cikin kettle ta fara sha ta zauna a falon tana zaman jiran dawowar sa. A lokacin su dare yayi dan akwai tazarar awa shida tsakanin su da Nigeria amma baza kace dare bane saboda hasken da yake cikin falon. Tana zaune tana kallon tv tana shan tea ya sake shigowa tana ganin sa sai ta ajjiye tea din ta mik’e tsaye ta k’araso kusa dashi tana kallon sa shima iya yake kallo tace, “Baby wai fushi kake?.” Hannun ta ya rik’e dan bazai iya tsallake tarkon nan nata ba yace, “ba fushi nake ba Baby, kawai ina mamaki daman akwai abinda zan nema na rasa a wajan ki?.” Jan ta yayi zuwa kan kujera ya zauna ya zaunar da ita a jikin sa yana shafa jikin ta tace, “To ai na baka hak’uri kuma na fad’a maka hakan sab’on Allah ne kaima kuma ka san da hakan.” Ya juyo da fuskar ta yana kallon ta yace, “Na fad’- miki ba halina bane kawai ina so na tabbatar da abinda ake fad’a min ne.” “Ai bai kamata ma ka dinga mu’amala da irin wannan abokan ba Baby, duk wanda zai dinga sab’awa Allah har ya dinga baka labarin dadin abun ai ba na gari bane Babyyyy…” ta ja sunan da k’arfi cikin wani salo mai daukar hankali a lokacin da yake tsaka da shafa jikin ta. Bai sake mata magana ba itama bata kuma cewa komai ba domin bata hayyacin ta shima a lokacin haka shafa jikin ta yake yi har ya raba ta da komai na jikin ta cikin soyayya da shauk’in junan su. Sun yi nisa dukkan su babu kamar ita da take kasa yana sama yadda yake sarrafata ya saka idanun ta a kulle yake gabadaya jikin ta ya gama yin sanyi. Jin abinda yake kokarin yi ya saka ta zabura ta ja baya ta fad’o daga kan kujerar tana kallon sa tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu tana kallon sa kamar yadda yake kallon ta, zata yi magana yayi saurin zuwa kusa da ita yace, “Fiddausi dan Allah ki barni iya yanzu kawai daga yanzu bazan sake ba dan Allah ki barni.” Fiddausi tayi d’aki da sauri jikin ta yana rawa sosai ta rarumi towel ta daure jikin ta tana sauke numfashi kamar tayi gudu mai tsahon gaske zuciyar ta sai bugawa take, a lokacin ya shigo yana cewa, “Yanzu Fiddausi daman baza ki iya bani abinda nake so ba?.” “Bazan iya ba wallahi bazan bari kayi luwad’i dani ba, ni musulma ce bazan sab’awa Allah ba akan gwaji kawai, bazan iya ba ka hak’ura da gwajin dan bazan tab’a aikatawa ba.” Ya matso ya rike kafadarta yace, “na fad’a miki ba halina bane, an fad’a min dad’in da abin yake dashi Ina so na gwada kuma ke kadai nake da ita Fiddausi. In ba’a wajan ki baba wajan wa zan samu? Dan Allah ki taimaka min kar kiyi min haka.” Fincike jikin ta tayi tace,” Zan iya yi maka komai amma banda na bari kayi amfani dani ta baya ba, kayi hak’uri bazan iya ba wallahi.” “Na fad’i miki bawai ina son hakan bane zan gwada ne kawai.” “Gwajin ma wani babban zunubi ne tunda kasan sab’on Allah zaka yi, kasan haramcin abinda kake niyar aikatawa dan haka laifi kake kokarin yi? Kasan da cewa al’arshi girgiza yake a duk lokacin da aka aikata abinda kake niyar yi dani da sunan gwaji?. Wallahi bazan ba na fad’a maka.” Da hannu ya tankad’a ta fad’a kan gado ya saka k’afa ya take hannun ya yace, “Ko bakya so sai na gwada a wajan ki kawai zan d’and’ana naji abinda ake ji.” Ganin da gaske yake yi fa ya saka ta dage ta ture shi ta shiga bandaki a guje. K’ofar ya k’arasa yana bubbugawa yana fadin, “Fiddausi! Ki bud’e ko ka b’allakofar, bana son shirme ki bud’e nace Malama.” “Wallahi bazan bud’e ba, bazan bari ka saka na aikata babban laifi daga cikin manyan laifuka ba” ta fad’a muryar ta har rawa take yi kamar zatayi kuka. “Shikenan na fasa amma ki fito.” “Bazan fito ba.” “Shikenan na fita” ya fad’a tana barin wajan da sauri. Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta fito tana sauke numfashi tana lek’owa kamar munafuka ganin baya nan sai tayi sauri k’arasawa ta kulle k’ofar ta jingina da k’ofar tana sauke numfashi. A hankali ta k’arasa ta zauna akan kujera tana kallon d’akin kamar da wani abun a ciki tace, “na shiga uku, me hakan yake nufi wai?.” Gumi ne yake tsatstsafo mata ta saka hannu ta share gumin ta kwanta da baya ta rasa tunanin me zatayi. Hankalin ta ya tashi sosai abinda ko a mafarki bata zata ba sai gashi yana k’ok’arin faruwa da ita. Sau hud’u kenan yana yunkurin yin luwadi da ita shin bai tab’a tsamari kamar yau ba, sai tayi magana sai yace wai labari aka bashi gwaji yake so yayi yaji ya ake ji. Hannu biyu ta saka ta dafe kanta sai kuma ta mik’e jikin ta a sanyaye ya koma band’akin. Ta jima a cikin sannan ta fito ta saka doguwar riga ta fito falon ta kalli kayan ta na d’azu ta tsuguna ta kwashe kayan ta ajjiye akan kujera ta zauna sharaf akan kujerar tana sauke Ajiyar zuciya cikin tunani. Tun tana zaman na dad’in rai har ta gaji babu shi babu alamun sa, a nan bacci ya kwashe ta har alarm d’in wayar ta da yake tashin ta da asuba ne ya buga ta tashi tana kallon falon kafin ta mik’e ta shiga d’aki taga baya nan alamun bai dawo ba. Alwala tayi ta dawo tayi sallah tana zaune akan sallayar sai kuma bacci ya kwashe ta akan sallayar. Bubbuga hannun ta taji ana yi hakan y saka ta bud’e ido ta tashi zaune tana kallon sa shima haka sai yayi murmushi yace, “a nan kika kwana ne?.” Ta girgiza kai alamun A’a kafin tace, “da na idar da sallah ban San bacci ya d’auke ni ba.” “Tashi ki zauna sosai to” ya fad’a yana mik’ar da ita ta zauna akan gadon ya zauna kusa da ita yace, “kiyi hak’uri abinda ya faru jiya bazan sake ba kin ji.” Jin abinda yace sai tayi murmushi cikin jin dad’i tace, “har naji dad’i, da ina ta jin tsoro ko laifi nayi maka shiyasa baka kwana a nan ba. Baby kai kasan haramcin da yake cikin abinda kake son yi Allah ya hana, abinda mutanen annabi lud suke yi kenan a zamanin sa Allah ya hallakar dasu, meye riba ko dadi’i ga abinda Allah baya so?.” Murmushi yayi jin abinda take fad’a wai zata yiwa wa’azi ya shafa kansa yace, “haka ne kam babu riba, yanzu dai ya wuce. Ki shirya kayan ki da misalin karfe biyu jirgin mu zai sauka a Abuja.” Ta kalle shi da mamaki tace, “Amma kace a nan ni zan zauna mai zai kaini Abuja kuma?.” Yayi murmushi yace, “taya zan iya aiki an Abuja babu ke? Aikin gaggawa ne ya taso min Zamu je mu dawo, ina tabbatar miki da zarar mun dawo ma Paris zamu wuce.” Murmushi tayi ta rungume shi shima ya rik’e ta yana girgiza kai yana ayyanawa a ransa lokacin Fiddausi ya k’are sai dai wata ba ita ba kuma. A bangaren Yusuf duk yadda ya kai da son daurewa yaje wajan Yaya Adam abin yaci tura, gabadaya ya rasa abinda zai yi yaji dad’i jin sa yake kamar bashi ba zuciyar da tayi nauyi sosai. Ko ya ya rufe ido Ameena yake gani zuciyar sa na mararin ta sosai amma gangar jikin sa tak’i bashi had’in kai akan hakan. Gabad’aya ya rud’e ya rasa gane inda rayuwar sa ta saka a gaba balle ya San inda ya dosa. Asiya ce ta shigo falon tana bin falon da kallo tare da tab’e bakin ta ta rasa meyasa tunda Ameena ta tafi yafi son zama a b’angaren ta ko me yake ji a ciki oho masa. kallon sa tayi bayan ta zuba masa harara sannan tace, “Wai ni me kake ji a b’angaren nan ne wanda babu shi a nawa?.” Sai a sannan ya d’ago kai ya kalle ta yaga tana bin falon da kallo sai zaga shi take yi. Dawo da kallon ta tayi gare shi tace, “ka tashi mu koma can bana son zaman da kake yi a nan.” Kamar bazai mata magana ba yayi banza wayar sa tayi k’ara yana dubawa yaga sunan Abbah gaban sa ya fad’i har ta tsinke bai d’auka ba aka sake kira dole ya d’auka ya saka a kunne daga can b’angaren Abbah yace, “Yusuf ka kaiwa Adam takardar sakin k’anwar sa kuwa?.” Yusuf yace, “ban kai ba Abbah, amma zan kai.” “Yaushe? Kai bana son iskancin banza da wofi fa, ni zaka mayar karamin mutum ina saka ka abu kana cewa zakayi har yanzu baka yi ba?.” “Kayi hak’uri Abbah zanje yanzu in sha Allah.” “Ka tashi ka tafi yanzun nan in ba haka ba wallahi baka je yanzu ba sai ranka yayi mugun b’aci. Baka son yarinya ka sake ta kai takarda kuma ya gagara? Wanne irin iskanci ne wanann?.” Kafin Yusuf ya sake magana Abbah ya datse kiran. Yusuf ya dafe kansa da hannaye duka biyun gabad’aya ya rasa abinda yake masa dad’i ya furzar da iska daga bakin sa idanun sa a kulle har lokacin ya kasa koda motsi balle yayi magana. A bayyane yace, “ya zanyi ni Yusuf? Komai ya tsaya min cak.” Asiya tace, “lafiya?.” Kallon ta yayi baice komai ba ya d’auke kai. Asiya da take kallon sa take jin abinda yake cewa a waya tace, “ina zaka je yanzu?.” Ya kalle ta bai magana ba sai kawai ya tashi ya hau sama bai jima ba ya sakko ya fita ba tare da yace mata kanzil ba ta bishi da kallo kafin itama ta fito daga b’angaren zuwa nata b’angaren. #Mai daki #Book3 #paid #500 Book3 03              Yaya Adam yana zaune a falo shida matar sa da yaran sa da kuma Ameena suna kallo,  dan Indai yana gıda to Ameena tana kusa dashi baya bari ta ware kanta ko kad'an balle ta zauna tana tunanin da baya so yaga tana yi. Duk motsin da za'a yi sai ya kalli Ameena sai yaga kallon tv take yi wani abun tayi murmushi wani abun kuma tayi akasin sa. Wani abun tayi magana wani abun tayi shiru ko tace Uhum kawai. Aisha sai hira take janta da ita a haka ta dan sake suna hira amma ba sosai ba. Bud'e k'ofar falon akayi aka shigo da sallama duk suka amsa suka kalli wanda ya shigo yana tsaye daga bakin kofa yace, "Ranka ya dad'e kana da bak'o a waje." Yaya Adam yace, "Bako kuma? Daga ina?." "Bai fad'a min daga inda yake ba ya tambaye ni kana nan nace eh yace dan Allah nayi maka magana." "Sai kuma ka baro wajan ka barshi shi kadai?." "A'a ai bai shigo cikin gidan nan ba yana daga waje na kuma kulle gate din." Yaya Adam ya ajjiye Zaytun da take cinyar sa mik'e yace, "Shikenan muje" ya fad'a yana niyar fita Zaytun ta rik'o shi alamun zata bishi ya d'auke ta suka fita tare. Yana fitowa k'ofar gidan yaga Yusuf a tsaye a jikin mota ya hard'e hannayen sa a kirji kansa a sunkuye yana kallon kafar sa kamar wanda bashi da lafiya. "Kaine kake nema na?" Yaya Adam ya fad'a yana kallon sa. Yusuf ya kalle shi sai yayi saurin d'auke ido daga cikin nasa yace, "Barka da dare Yaya." "Daddy!" Zaytun ta fad'a da farin ciki tana mik'a masa hannu, sauke ta Yaya yayi daga jikin sa sai kuwa ta k'arasa inda Yusuf yake ya d'auke ta yana mmurmushi shima da farin cikin ganin ta yace, "Ammata kin manta dani." "Daddy ina ka tafi? Ina chocolate?." Yusuf ya girgiza kai yana kallon ta yace, "na kawo miki." Yaya Adam da yake kallon sa Zaytun ta kalle shi cikin maganar ta da take fita zaka gane mai take cewa tace, "Abba daddy ya zo da chocolate." Yaya Adam yayi murmushi yace, "ai ya kyauta." Yusuf ya kalle shi ya kasa magana balle ya aiwatar da abinda yazo yi zuciyar sa bugawa take sosai ko kallon Yaya Adam yayi sai gaban sa ya fad'i Yaya Adam yace, "Daman ganin y'ar kane ya kawo ka kenan?." Yusuf ya girgiza kai alamun A'a gabad'aya ya rud'e  ya rasa ta yaya zai bashi takardar sakin Ameena Gashi kuma harga Allah yana so ya ganta amma yasan babu damar hakan, zuciyar sa na fad'a masa hakan ba daidai bane akwai  rashin kyautawa a cikin tunda kamar mahaifi yake a wajan ta bashi takardar sakin Ameena tamkar cin fuska ne. Yaya Adam yayi tsaki yace, "in kana so zaka iya d'aukar ta ka tafi da ita daman taka ce ni tawa tana cikin gida." Yusuf yayi shiru ya rasa abinda ma zaice ganin hakan Yaya Adam yace, "ina fatan ka tawo da takardar sakin Ameena ko? Dan na fad'a maka kar na ganka a nan in ba takardar ka kawo min ba." Gaban sa ya fad'i ya kulle ido ya bud'e ya furzar da iska daga bakin sa. "Daddy wani a nan". Zaytun ta fad'a tana saka hannun ta a daidai zuciyar sa dan sosai take jin yadda take bugawa a hannun ta hakan ya bata mamaki shiyasa ta fad'a masa. Yusuf baice komai ba ya motsa daga inda yake ya bud'e gaban motar ya d'auko leds fara babba mai kyau ya dawo kusa da Yaya Adam ya mik'a masa yace, "Wannan na Zaytun ne." Kallon sa yayi ya kalli ledar ya sake kallon fuskar sa kafin yayi magana yace, "Dan Allah ka karb'a Yaya." Bai mu sa ba ya karb'a ya bud'e ledar a nan yayi karo da takarda fara a kai ya saka hannu ya d'auka ya bud'e yana dubawa. Baice komai ba ya saka takardar a aljihun sa yace, "Kar na sake ganin k'afar ka a k'ofar gidan nan daga yanzu, in Kana da ra'ayin ganin y'ar ka zaka iya aikowa a d'auke ta amma bana bukatar sake ganin ka daga nan har karshen duniya. Zaytun tawo" ya fad'a yana mik'a mata hannu sai ta kwanta a jikin Yusuf alamun bazata zo ba tana alamun zatayi kuka. Yaya Adam yace, "Shiekan kaje da ita" ya fad'a yana niyar juyawa ya koma gıda. Yusuf gabad'aya ya rasa abinda yake damun sa gaahi bakin sa yayi masa nauyi in ya tafi da Zaytun wajan wa zai kaita? Bata saba da Asiya ba sannan in ya kai ta wajan Ammah bai  san me zaice ba, shi bazai iya zuwa gidan su da ita ba Allah ya sani dan kowa yana ganin ta yasan abinda ya kawo shi ya karb'a ta kunyar hakan yake ji shiyasa gwara ya barta. Da sauri yace, "A'a Yaya kaje da ita kawai, Zaytun ki shiga gida wajan Mummy." Yaya Adam ya tsaya cak ya juyo yana kallon sa Zaytun ta saka kuka tace, "A'a ni zan bika." Yaya Adam yace, "kaje da ita gobe a dawo da ita kawai tunda tana so" yana fad'a ya juya zai shiga gida Yusuf yace, "Dan Allah ayi hakuri Yaya, nayi kuskure amma" juyowar da Adam yayi ya kalle shi sai ya kasa k'arasawa yayi shiru baice masa komai ba ya shiga gıda ya bar masa Zaytun d'in a hannun sa. Badan yaso ba haka ya saka ta a gaban mota suka bar unguwar yana kukan zuci wanda yafi na zahiri ciwo da tab'a zuciya.            Yaya yana shiga falon ya samu waje ya zauna ya kalli Ameena da take kallon sa k'aramar yarinyar sa mai shekarun Zaytun tace, "Abba ina Zaytun?." Ya kalli Ameena yace, "taga baban ta tak'i zuwa wajena, nace yaje da ita ya dawo da ita gobe tunda ta ganshi a barta a wajan sa kar tazo tana kuka" ya fad'a yana kallon Ameena dan yaga reaction din ta. Sai kuwa yaga ta kalle shi da sauri suna had'a ido sai ta d'auke kanta amma yanayin ta ya canja duka gabad'aya jikin ta ya saki yayi sanyi sosai alamun bata ji dad'in maganar ba, ajjiye filon kujerar da ta rungume tayi ta tashi kawai ta wuce daki da sauri dan bata so ma Yaya yayi mata wata maganar. Tashi yayi yabi bayan ta ya ya same ta sa tsaye a jikin bango tana sauke numfashi ya kalle ya yace, "Ameena me ya faru?." Murmushin yaqe tayi tace, "babu komai Yaya." Ya dafa kafadarta yace, "Kiyi hak'uri na bashi ita ba tare da na nemi izinin ki ba, zai dawo da ita gobe bana so ta dawo tana kuka tunda tana son kasancewa da mahaifin ta a barta tayi hakan." "Babu komai Yaya, duk abinda kayi daidai ne." "Ga chocolate nan da ya kawo mata sai ki ajjiye in ta dawo zata sha" Ajjiye mata ledar yayi a kan katifa kafin yace, "Ameena Yusuf ya sake ki saki d'aya." K'irjin ya buga da sauri ta runtse ido tana sake Jan numfashi tana saukewa a hankali, hawaye yaga sun sakko daga idanun ta sai ta bashi tausayi sosai a shekarun ta in ba kaddara ba me zai kaita ga zaman gida da sunan mutuwar aure, sannan  ya tabbatar tana son Yusuf duk da ya ragu sosai amma shi bazai iya barin ta tare dashi bane dole sai ya raba su. "Kiyi hak'uri Ameena tunda har ya furta baya son ki banga amfanin zama dashi ba, Ameena koda yana sonki abubuwan da suka faru sai na saka ya sawwake miki balle ma baya son ki. Gwara ace baya son ki yana zaune dake Lafiya akan ace yana sonki yana azabtar dake. Ameena matsayin mahaifi nake a wajan ki bazan cutar dake ba, duk Inda nasarar ki take a duniya da cigaban ki shi nake nema miki. Raba ki da Yusuf da nayi ba cutar ki nayi ba ko hanaki abinda kika so face nema miki mafitar damuwar ki dan gudun nan gaba." Sai a sannan ta bud'e ido ta goge idanu tayi murmushi yaqe tace, "Wallahi babu komai Yaya, kar ka manya nima ina goyan bayan raba mu din kuma ina ji a jikina shine alkhair a gare ni, kawai dai naji wani iri ne da naji ka ambaci saki a kaina" ta fad'a tana sauke kanta kasa tana goge idanun ta. Yace, "nasan zaki ji hakan amma ki cire ranki daga gare shi, ki kalli rayuwar ki ta yanzu kar ki  tuna ta baya domin ta riga ta wuce. Ki saki jikin ki duk abinda kike so zan miki, in ma makaranta kike so ki koma Ameena zaki koma kafin ki sake yin wani auren." Kai take d'agawa tace, "To Yaya na amince da duk abinda kace, in sha Allah zan yi." "Yauwa Ameena, wannan d'ar-d'ar din da kike yi ne bana so bana jin dad'i ko kad'an, ki saki jikin ki ba'a kanki aka fara mutuwar aure ba, ki manta da komai dan Allah ki sake kiyi. rayuwar ki ta farin ciki. Ina jin babu dad'i in naga kina zaman d'aki ko kina kuka, bana son hakan Ameena ki daina." "Daga yanzu na daina in sha Allah Yaya." Yayi murmushi yace, "Ko Kefa, Saura na dawo naga kina kuka" ya fad'a yana fita daga d'akin yana fita ta k'arasa kan katifar ta zauna tana kallon ledar. Baya tayi ta kwanta ta lumshe idanun ta tana jin wani iri in ta tuna a yanzu fa bata da aure sai gaba ta ya yanke ya fad'i tunawa Itafa bazawara ce a yanzu, idanun ta ta sake gogewa tace, "in sha Allah zan manta da komai daga yau in sha Allah, kodan saboda Yaya na daina saka damuwar komai a zuciyata." Hawayen take so ta tsayar amma sun k'i tsayawa sai kawai ta tashi ta shiga band'aki.         Yusuf a haka ya koma gida yayi parking mota ya fito ya rik'e hannun Zaytun suna takawa a hankali zuwa cikin gidan, kulle k'ofar yayi ya shiga ciki ya sau saman a nan ya samu Asiya a tsaye daga ita sai d'aurin kirji ta bishi da kallo tana kallon Zaytun zuciyar ta na bugawa. Bata ce masa komai ba shima bai ce ba ya shiga d'aki ya zauna a gefen gado ya zaunar da Zaytun akan gado yana kallon ta tana tacin biskit din da ya bata ta b'ata bakin ta gabad'aya da madarar dake jiki, ya kalle ta yace, "kin b'ata jikin ki." Asiya ce ta shigo tana kallon Zaytun ta kalle shi tace, "A ina ka samo Zaytun kuma" sai ta tsuguna a kusa dashi tace, "zuwa gidan su Ameena din kayi?, me kaje yi to? Sakin ta kayi ko kuma me?." Yadda jikin ta yake bugawa saboda wari shine ya saka shi yin baya ya yamutsa fuska  bai ce komai ba. "Magana nake maka fa, wajan Ameena kaje ne?." Kallon ta yayi kamar zai magana sai akwai ya share ta ta sake cewa, "magana fa nake yi, an ina ka samo Zaytun ka tawo da ita? Kar kace min fa a nan zata zauna." Baice mata komai ba ya tashi ya shiga band'aki ta bishi da kallo kafin ta kalli Zaytun da take cin biskut din ta tace, "Chab, ai wallahi in ma ka dawo da ita ne wallahi bazan rike yarinyar nan ba gwara ma a san nayi" ta fad'a tana kallon ta a lokacin itama ta kalle ta sai kuwa ta zare mata idanu. Zaytun sai ta tsorata ta kama kanta ta nutsu sosai Asiya ta fita ta bar d'akin, bai jima ba ya fito yana yamutsa fuska gabad'aya baya son zama a b'angaren da komai na dakin wari yake har bandaki. Tana ganin sa Zaitun ta sakko daga kan gadon taje ta rike shi tace, "tsoron ta nake ji." Kallon wajan yayi yaga bata nan ya rik'o hannun ya ya zauna da ita shima ya zauna ya saka tissue yana goge mata baki. "Daddy ka kaini wajan Mummy" ta fad'a zata yi masa kuka yace, "kar ki yi kuka zan kai ki, wajan Mummy kike so kije?." Ta daga kai alamun eh yace, "to zaki je." Asiya ce ta sake shigowa sai Zaytun ta rik'e shi tana kallon Asiya ya kalle ta  shima yace, "me kika yi nata daga shiga ya band'aki take tsoron ki?." Asiya tace, "Ka ji min mutum, me zan yiwa wannan yarinyar? Kawai makirci ta gado daga wajan uwarta shiyasa take wannan rarraba Idon kamar munafuka." Kallon ta yayi yana jin zafi a zuciyar sa  musamman uwarta da tace sai bai kula ta ba ya cigaba da rarrashin Zaytun ta kalle shi tace, "yauwa ka saka ta tayi bacci dan ni yau sai an bani hakkina ko me za'ayi. Haba kwana kusan goma sha fa kenan Kullum kace min baka jin dad'i yau dai bazan iya hak'uri ba wallahi. Ai nayi hak'uri na baka dama dan naga kana cikin damuwa na kyale ka amma yanzu ni wallahi bazan iya ba." Bacci Zaitun ta fara a jikin sa ya kwantar da ita yana bubbuga bayan ta har tayi bacci ya kalle ta tana tsaye a gaban sa tace, "kaji ai abinda nace, ni na gaji wallahi kazo muje dakina ko kuma mu kwanta a nan" ta fad'a tana murgud'a baki. "Asiya fita ki bani waje." Da mamaki yake kallon sa ganin kamar ma abinda take yi a kansa baya tasiri wani lokacin taga yana aiki wani lokacin taga akasin haka kamar mai aljanu tace, "kamar ya na fita bayan na fad'a maka abinda ya kawo ni?, babu inda zani sai ka bani hakkina bazan iya jurewa ba n fad'a maka." "Asiya nace ki bani waje." "Wallahi bazan fita ba." Da sauri ya kalle ya yaga idanun ta kyam a kan fuskar sa babu alamun tsoro a tare da ita tace, "har yanzu ace ko ciki na kasa yi saboda rashin kula da nake samu daga wajan ka, wallahi bazata sab'u ba ko ka bani hakkina ko na kai k'arar ka wajan iyayen ka." "Ki kai karata wajan wa?." "Wajan na gaba dakai mana, ai wannan abu ne mai mahimmaci da duk wanda na fad'awa sai ya tsaya ya saurare ni." Mamaki take bashi sosai ya girgiza kai kawai ya kalle ta yace, "to baza ki samu ba, ki fita ki bani waje Malama." "Wallahi in ban samu ba sai na kira Ammah na fad'a mata" ta fad'a tana niyar fita ya dakatar da ita yace, "Baki da hankali? Da gaske kike zaki iya fad'awa Ammah?." Ya matso kusa da ita yana kallon ta yace, "Sai ki fad'awa Ammah haka? Kice mata nak'i baki hakkin ki?." "To ba so nake ba, kuma ai hakkına ne ko gaban alqali naje sai ya Karb'ar min" ta fad'a tana kallon wani wajan daban. Kallon ta akwai yake yi kafin ya koma da baya ya zauna yayi shiru baice komai ba dan ya rasa bakin magana sai kallon ta kawai. Matsowa tayi kusa dashi ta dafa kafadarsa tace, "My love kwana biyu kawai daurewa nake, dan Allah ka saurare ni yau din nan" tav fad'a tausashe tana kallon sa. Wallahi shi warin da take yi yafi komai d'aga masa hankali a wannan lokacin, taya zai iya yin wani abun da ita tana wari haka ai sai yayi amai. Ya cire hannun ta daga jikin sa yace, "kije ki yiwanka dan Allah." Ta Harare shi tace, "ni bazan wanka ba sai bayan an gama, Nidai ka amince kawai bazan iya bacci ba." Kallon ta yayi suka had'a ido ta sake marairaicewa ya d'auke kai daga kallon ta ya kalli Zaytun da take bacci ya sunkuyar da kai baice komai ba. Masifa yake so yayi mata ya kora ta waje  inda hali ma mare ga ma amma sai yaji ya kasa yin hakan sai shiru ma da yayi ya sunkuyar da kai ya rasa ma abinda zai yi yaji dadi. Shafa jikin sa take yi dan towel ne kawai a jikin sa da ya fito daga wanka bai saka kaya ba ya d'auke hannun ta yace, "ki jira ni a dakin ki gani nan." "Ka tabbatar zaka zo?." Ya d'aga kai alamun eh  ta fita ya bita da kallo ya kalli Zaytun sai ya shafa goshin ta ya mik'e ya k'arasa kusa da window yana kallon window din Ameena dakin duhu kamar Kullum. _Shikenan Ameena ta tafi?._ sai yayi saurin barın wajan jin zuciyar sa na kawo masa abinda gangaar jikin sa bata so. Sakin labulen yayi ya rasa abinda yake masa dadi a zuciyar sa ji yake kamar ya zubar da hawaye, bashi da mafita a wannan lokacin tunda tace zata kira Amma yasan zata iya shi kuma bazai zo hakan ba. taya zai iya had'a jiki da Asiya tana wari?, fatar ta na maik'o tana jiki duk Gashi?. Tsigar jiki sa ta tashi dan tunawa da abinda hakan zai haifar masa dan Allah ya sani baya son wari ko kusa. kai ya girgiza kawai yaje ya kulle k'ofar ya karasa wajan kayan sa ya saka ya dawo ya kwanta kusa da Zaytun baya tunanin zai iya aikata wani abun da Asiya a yanayin da take. Kusan mintina talatin yana a haka shiru bai ji tana buga masa k'ofa ba sai ya kwanta da niyar bacci amma sai y kasa sam zuciyar sa a cushe take yana ta hasashe abubuwa kala-kala akan abun  sai akwai ya sakko daga kan gadon ya fita zuwa d'akin ta. Bud'ewa yayi ya shiga yana kallon ta a kan gado gaban sa yana fad'uwa zuciyar sa na yin rawa saboda abinda ya gani wanda bai kawo hakan a zuciyar ba shine ya kwo masa sanyin jiki da tsinkewar zuciya lokaci d'aya. #Mai daki #Book3 #Paid #500 #Nana Haleema Book2 004 Duf duf duf haka gaban sa take bugawa ya had’d’iye abinda yazo masa wuya yana takawa a hankali yana sake wara idanun sa akan Asiya da bata san ma yana shigo ba saboda hankalin ta da tunanin ta basa tare da ita a wannan lokacin balle taji sautin bud’e k’ofa ko sautin takun takalmin sa. Idanun ta a lumshe suke sai sauke numfashi take yi tana k’ananun maganganu hannun ta d'aya yana kirjin d’ayan kuma tana wasa da gaban ta cikin fitar hankali da son cimma abinda zuciya take so. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya maimaita a bayyane ganin har lokacin fa bata san ma yana wajan ba da hanzari ya k’arasa inda take yace, "Asiya!." Yadda yayi maganar da k’arfin gaske a zabure ta mik’e zaune tana kallon sa shima ita yake kallo yana sauke numfashi saboda abinda ya gani ita kuma tana saukewa idanun ta akan fuskar sa. Ba alamun tsoro ko kunya a tare da ita sai ma hararar sa da tayi idanun ta kyam a kan nasa, muryar sa har rawa take yace, "me kike aikatawa haka? Kina da hankali kuwa?, meye hakan?." Bata yi magana ba har lokacin numfashi take saukewa a hankali sai tana so ta tattaro nutsuwar ta gabad’aya ta dawo da ita jikin ta daga baya tace, "Abinda ka gani shi nake aikatawa." "Kina da hankali kuwa?, wai kin San me kika aikata kuwa? Mastrubation fa kike aikatawa?, hauka kike Asiya?.” "Koma me na aikata ai kaine sıla; laifin kane kaine kaso hakan da baka so ba da bazan yi ba" ta fad'a tana kallon sa sai kuma ta fara kuka tana fad’in, "Allah ya isana, ka saka na aikata abinda ban tab'a yi ba saboda rashin samun had’in kanka. Inda ka bani abinda nake so da duk hakan bata kasance ba. Na fad’a maka ai ina buk’atar ka k’arshe sai kace nazo nan ka kulle kofar ka, ya kake so nayi maka?, ne kake so nayi in ba hakan nayi na samarwa kaina mafita ba?. Tunda abin naka haka ne wallahi bazan d’auka ba zan kai k’arar ka zan kai wajan iyayen ka." Yusuf da yake kallon cikin tashin hankali da mamakin abinda ya gani wanda bai tab’a gani a zahiri ba yace, "It's just a few days fa, ba wata ba balle shekara shine har abin ya kai da nazo na same ki a wannan yanayin?, ina hankalin ki da tunanin ki ya tafi? A ganin ki wannan abun wasa ne?” Ya fad’a a fusace cikin fad’a yana kallon ta. "Kar ka soma yi min masifa ko kace zaka d’aga min murya, kai a ganin ka kwanakin ai basu da yawa ni a ganina suna da yawa kuma wallahi bazan d’auka ba dole na sanar da na sama dakai a dauki mataki da gaggawa.” "Amma kin sa aikata hakan haramun ne ko? Sannan lafiyance babbar illa ce a gare ki ko?." Ta kama k’ugu tana kallon sa tace, "Mata kake so na nema ko maza to? Fad’a min sai na canja daga salo daga yau." Sai ta sake fusata shi ya zabura kamar zai dake ta yace, "ina miki magana akan abinda kika aikata kina min maganar wai maza zaki bi ko mata?, meyasa baki da hankali ne kewai?, kin san illar abinda kika yi?.” Ta ja baya tana kallon sa tace, "koda wasa kar hannun ka yazo jikina da sunan duka wallahi daga ranar zaka yi dana sanin fara dukana. Ina ruwan ka da illar da abin yake dashi naga jikina ne ko?.” "İn na dake ki din me zaki yi?." "Ka gwada ka gani mana sai ka gwada zaka tabbatar da abinda zanyi, ni ka fita ka bani waje bazai yu ayi min laifi ba kuma azo an yi min ihu a kaina ba, ga mari ga tsinka jaka kai kasan bazai yu ba.” Sai kuwa yayi kwafa ya fita daga d'akin ta bishi da harara ta tashi ta shiga band’aki. Tana fitowa daga bandakin ya sake shigowa ta kalle shi ta d’auke kanta ya k’araso ya zauna itama ta zauna yace, "kar ki sake aikata abinda kika aikata Asiya, na yarda laifina ne amma hakan bai kai da ki jefa kanki cikin wannan mummunar dabi'ar ba. Yanzu in kika sabarwa kanki shikenan ko me za’a yi miki sai kin yi zaki ji dad’i, hakan ba daidai bane ba abu bane mai kyau na fad’a miki. Daidai yake da aikata zina.” "Kar ma ka yarda laifin naka ne mana, ka zauna kana yi min fad’a ni kuma naje na sanar da na gaba dakai.” "Wai ke baki iya magana bane?, baki San ta yadda zaki magana da mutane ba?. Ina kyale ki amma bakya ganewa kika kai ni bango wallahi zaki mamakin waye ni.” Ta murguda baki bata sake kallon sa ba balle tayi magana. Yace, "Nidai na fad’a miki kar na sake ganin kina wannan abun in ba haka ba zan d’auki mataki a kanki wallahi, bazan zauna da mace mai irin wannan Hali ba, ba dabi'a ta gari bace ba kuma abin burgewa bane, cutar kanki zaki yi domin abinda kika fara zai iya hana ki zaman aure.” Shiru tayi bata amsa ba yace, "Daman kin saba aikata hakan ne?." Ta kalle shi ta girgiza kai tace, "ban tab'a ba sai yanzu, kuma laifin kane ai na fad’a maka amma sai ka k'i ji" ta fad'a kamar zatay kuka. "Shikenan nasan laifina bazan sake ba amma dan Allah kar ki sake abinda kika yi domin zai iya sakawa na yanke wani hukuncin a kanki.” Kai ta d’ag alamun to ya kalle ta yace, "ba gudun ki nake ba Asiya matsalar daga wajan ki ne, bakya gyara jikin ki gabad’aya ko turare bakya amfani dashi taya kike ganin zan iya wani abun dake a wannan yanayin?. Da da nake zuwa gidsn ku ba haka kike ba ko yaushe cikin khamshi kike yanzu kin canja. Zuciyata har tashi take wani lokacin kamar zan yi amai in nazo kusa dake, dan Allah ko gyara in ba haka ba samun kaina zai dinga miki wahala." Lallai ma gayen nan ya raina min hankali, ni zai kalla yana fadawa wannan maganar ba kunya ba tsoron Allah?, lallai ya kamata na sake d’aukar mataki a kansa tunda aka fara zuwa wannan gab'ar, tace, "Me kake nufi?." "Kin San me nake nufi, dan Allah ki dinga gyarawa; gabad’aya gidan nan ya canja saboda rashin kulawar ki, bana son k'azanta wallahi, hankalina tashi yake in naga ina waje kuma ana k'azanta a wajan." Ta zuba masa ido tace, "kenan ni k'azama ce?." Ya kalle ta shima yace, "Nidai ban ce k'azama bace ba amma ya kamata ki gyara." Shiru tayi bata ce komai ba sai ya mik’e zai fita ya rik’o hannun sa tace, "to ina kuma zaka je?." Ya dawo ya zauna yace, "ai naga rashin kunya kike ji da ita ne shiyasa zan baki waje kafin na kasa jurewa.” "To kayi hakuri" ta fad'a tana matsowa jikin sa ta kwanta duk da tayi wanka amma wallahi wari yake ji a jikin ta amma babu yadda zai iya. Shi dai kawai ya daure yayi abinda take so tunda yaga hakan yana neman kawo matsala amma wai dan son ransa ko dan yana so bazai aikata komai ba domin sai da tsafta zai samu nutsuwa.                 Yana komawa d’aki Zaytun ta farka tana cewa, "Mummy ruwa." Ji abinda take cewa sai ya d’auki ruwa ya karasa inda take ya zauna ya bata ta kalle shi cikin karamin hasken d’akin tace, "Daddy wajan Mummy zan je." "Shiii ki yi bacci zan kai ki" ya fad'a yana kwantar da ita a jikin sa a hankali ta fara komawa baccin. Tunani ya tafi yi rabon sa da wani abun ya had’a shi da Ameena kusan watanni zai ce ba kwanaki ba, ya kwantar da Zaytun lokacin bacci ya dauke ya ya sake tashi yaje yana kallon tagar Ameena, _indai Asiya zata aikata abinda ta aikata dan anyi kwanaki goma zuwa sama da haka ban kula ta ba Ameena ya kenan?, wanne irin yanayi ta shiga a wannan watannin dan nasan Ameena bazata aikata abinda Asiya ta aikata ba._ yayi Ajiyar zuciya ya sake labulen ya koma ya zauna ya dafe kansa gabad’aya ya rasa abinda yake yi masa dadi a zuciyar sa. Wayar sa ya d’auka ya shiga WhatsApp ya dubo lambar ta message din ta na karshe shine wanda take fad’a masa zata je asibiti, online ya gani a k’asan My Choice sai ya kifa wayar a kan gado ya saka hannu yana shafa dukkan fuskar sa a bayyane yace, "Meyasa nake jin wani iri in ana yi min maganar Ameena? Meyasa ma...?" Sai kuma yayi shiru ya dafe kansa ya koma ya kwanta da baya yana kallon sama kafin ya kulle idanun sa.           Kukan Zaytun ne ya tashe shi  ya mik’e zaune ya kalle ya ta mik’a mata hannu ta taso wajan sa yace, "ya akayi Ammah." Ta rik’e shi sosai tana kuka alamun akwai abinda ya bata tsoro sai ya mik’e ya d’auke suka fita daga d'akin. Bai ga Asiya ba kai tsaye b’angaren Ameena ya wuce ya hau sama har dakin Ameena Zaytun tana kiran, "Mummy!." Ya kalle ta ya zaunar da ita akan gadon ya bud’e inda kayan Zaytun din suke an kwashe rabin su amma har lokacin akwai Saura sai dai basu da yawa ya d’auko guda d'aya zuciyar sa na bugawa sosai burin sa kawai ya bar d’akin. Zaman d’akin ne yaji ya ishe shi sai yayi k’aramin tsaki ya d’auke ta suke fito da kayan a hannun sa ya koma wajan Asiya suka had’u a falo  ya mik’amata kayan yace, "Karb’i kije kiyi mata wanka taci abinci." Ta kalle shi tace, "ban gane bafa, Wai ta dawo gidan nan ne da zama ko ya ya?." "Kiyi abinda nace kawai" ya fad'a yana kallon ta shima. Zaytun din ta kalla taga ta kwanta a jikin Yusuf ta rufe ido tace, "to gashi nan ai tama k’i kallona balle ta sakko nayi mata wanka." Ya kalli Zaytun d’in yace, "Zaytun jeki Auntyn ki tayi miki wanka." Maqale kafada tayi tace, "A'a tsoro nake ji." "Dodo ce ni da kike jin tsorona dan Uwar ko?" Asiya ta fad'a tana sake zare ido tana kallon ta. Sai kuwa Zaytun ta fashe da kuka tana kiran Mummy, a fusace ya kalle ya yace, “Wai Asiya baki da hankali ne? Wannan yarinyar kike yiwa haka kika zagin ta?.” “Ta koyo halin uwar tane ai shiyasa.” “Kika sake min zagi a nan wallahi na buge bakin ki.” “In nayi sai ya?.” Bai san lokacin da ya buge mata baki ba cikin b’acin rai ta kalle shi tace, “Akan y’ar Ameena?.” bai samu damar magana ba saboda kukan Zaytun ya hau sama ya zaunar da ita a kan gado tana kuka sosai yace, "Daina kuka Zaytun din Daddy me kike so?." "Mummy! Mummy!" Ta fad’a da karfi tana sake fashewa da kuka. "Wajan mummy zaki?." Ta d’aga kai alamun eh yace, "to ina zuwa" ya fad'a yana tashi ya shiga band’aki yayi wanka ya fito ya samu ta kwanta tayi shiru kamar mai bacci amma ba baccin take yi ba. Kai ya girgiza lallai ya kamata ya takawa Asiya burki akan yarinyar nan dan bazai dauki abinda take yi masa ba dole ta karb’i Zaytun domin y’arta ce .” Da sauri ya shirya ya d’auki kayan ta da ya d’auko da key na mota ya sauka ko kallon ta bai yi ba ya fita. Da kallo ta bishi tace, "kan uban nan kayyasa, na rabu da uwa yanzu kuma a kawo min y'a? Wallahi bazata sab'u ba dole na sake shiri daman naga kamar ma bayi nake ba, kamar ina tufka Ana warware min ne dole na d’aura d’ammara domin bazan d’auka ba wallahi” ta fad'a tana d’aukar waya ta hau sama da sauri dan dole Umma taji labarin nan.        Yusuf kuwa yana hawa mota kai tsaye gidan su ya wuce da Zaytun sai da ya faka motar ya kalle ta yace, "Zaki je wajan Ammah?." Ta girgiza kai tace, "nidai Mummy." Ya sauke numfashi yace, "to mu je mu gaisa da Ammah sai mu je wajan Mummyn ko?." Ta d’aga alamun eh ya fito da ita suka shiga cikin gidan. Humaira ya gani a zaune tana karatu a falon ganin Zaytun ya saka ta bud’e mata hannu cikin fara’a tana fadin, "Zaytun d’ina." Sai kuwa ya tafi wajan ta a guje itama ya ajjiye kayan ta a kusa da ita yace, "ki mata wanka ki bata abinci sannan ki mayar da ita." Humaira ta kalle shi tace, "ina zan kai ta?." Ya jiyo ya kalle ta yace, "zata fada’a miki" ya fad'a yana shiga wajan Ammah. Bai jima ba ya fito ya sake fita ita kuma suka shig wajan Ammah da ita.         Fiddausi lokacin da jirgin su ya sauka a Nigeria dare yayi tana zaune a kusa dashi suna jiran driver da zai d’auke su ya kai su gida sai ga mota guda biyu d'aya babba daya k’arama amma dükkan su masu kyau ne bak’akme hatta glass din jikin su bak’i ne baka ganin na ciki sai dai na waje. Ya kalli Fiddausi yace, "Baby ki shiga wannan zai kai ki gıda, zanje office yanzu." "Da daddare nan Baby?" Ta fad'a tana kallon sa da mamaki. Ya mik’e yace, "bazan jima ba" ya fad'a yana shiga bayan Babbar motar ita kuka ta shiga k’aramar suka fita. Tafiya suke tana kallon garin Abuja ko ina da haske kamar ba dare ba amma shiru babu kowa sai jami'an tsaro da mota tsilli-tsilli. Duk inda suka bi Jami’an tsaro zasu tsayar dasu amma da anyi bayani sai a barsu su wuce. Gaban wani babban gate taga sun tsaya kafin a bud’e a shiga ma sai da aka tsaya ana magana kafin su shiga suka yi tafiya suka sake zuwa wani gate din aka sake bud’ewa suka wuce, babban gida ne sosai iya ganin ka wajan ajjiye motocin ma abin kallo ne gashi ko ina da haske sosai kamar ba cikin dare ba. Driver ya kalle ta yace, "ranki ya dad’e mun iso." Fitowa tayi tana kallon gidan shi kuma ya fito da jakar ta yana kallon ta cikin girmamawa yace, "muje." Gaba yayi tana bin sa a baya tana kallon gidan domin kuwa yayi mata daidai da ra’ayin ta sai murmushi take yi suna har zuwa wata k’ofa ya bud’e yaja baya yace, "bismillah." Shiga tayi taga babban falo ne sosai mai d’auke da k’ofofi da yawa amma dukkan suna kulle suke, falon babu kowa sai sanyin a.c yana da girma kuma yana da kyau sosai.  Ya nuna mata k’ofar da take can gefe yace, "Waccen k’ofar itace ta bangaren ki, ga mukullin." Ita mamaki take yi shi da yace an America zata zauna to me ya dawo da ita Nigeria har ana cewa ga b’angaren ta?. Karb’a tayi ya juya ya fita ita kuma tana kallon falon taja jakar zuwa inda ya nuna din, bud’ewa tayi nan ta sake karo da wani falon mai kyau sosai komai sabo kuma komai akwai a cikin sa sai khamshi yake tana bin sa da kallo tare da girgiza kai, jakar taja zuwa inda take tunanin d’aki ne ta sake bud’ewa nan ma taga falo ne wanda sai ka sauka daga steps zaka shiga ta shiga nan ma tana kallon sa. Murmushi tayi tana jin sanyi a ranta nida farin ciki ta wuce zuwa wata k’ofar ta bud’e sai taga kitchen ne ta kulle ta bud’e wata taga waje ne amma ta baya, rufe wa tayi tace, "oh kenan nan ne hanyar shigowa ba tare da ka biyo ta baban falo ba, wow amazing" ta fad'a tana sake bud’e wata a nan taga doguwar hanya da d’akuna guda hud’u manya. Sai da ta duba ta zab’a taga wanda  yafi Kyau da girma sannan ta shiga ta ajjiye jakar ta shiga wanka. Tana fitowa ta nufi wajan wardrobe da niyar zuba kayan ta abin mamaki duk kayan ta na gidan da ta fara sauka an dawo dasu d’akin, ta kama k’ugu tana kallo kafin tace, "kenan wai a nan zan zauna? Ko da yake bara na jira yazo muji ya abin yake" ta fad'a tana d’aukar Riga ta saka ta kwanta a kan gado tana juyo cikin farin ciki sai bacci.      Mata ne guda biyu a tsaye a window suna kallon shigowar Fiddausi har aka raka ta part ta d’aya ta kalli daya tace, "Alhamdulillah lokacin fita na daga gidan nan in sha Allah yayi." D’ayar tace, "Ke kam kin ji dadi ina ma nice ke, na gaji da zama a gidan nan wallahi sam bashi da dad’i. Zaman gidan nan dashi gwara ace a prison kake" ta fad'a tana goge idanun ta da suka ciko da kwallah. D’ayar ta dafa ta tace, "Zaki fita in sha Allah, Tunda wannan ta shigo wata ma zata shigo kinga kenan mune zamu fita nan gaba" ta sauke numfashi tace, "Allah sarki amarya tana murna ta shigo babban gida, tana murna tazo gidan jin dad’i, tana murna tazo gidan hutu bata san da kwanciyar hankali da gidan nan sunyi hannun riga. Hmmmm! Muna taya ta murna da shigowa gidan da zaman prison ya fishi dad’i, ina taya ta bak’in cikin shigowa gidan nan, domin kuwa zaman gidan nan sai ya saka ta kusa fita daga hankalin ta, domin kuwa zaman gidan nan ya kasance tamkar kabarin bature ne, daga waje akwai kyau da k’yalli amma daga ciki Allah kad’ai yasan abinda yake faruwa.” D’ayar tace, "muje mu kwanta dare yayi sosai ma had’u da amarya da safe. Dan na tabbata itama irin mu ce bata amince ba shiyasa ta dawo nan ayi mata ta k’arfi ko tana so ko bata so.” D’ayar tace, “abin tausayi wallahi. Allah yasa mu dace kawai.” Sallama sukayi ko wacce ta wuce b’angaren ta. #mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid #500. Book3 005 Washe gari Fiddausi bata tashi ba sai goma da rabi na safe tana tashi bata fito ba sai da tayi wanka ta shirya cikin kaya masu kyau kana kallon ta Kaga matar Alhaji ta tsaya tana kallon kanta tana murmushi tace, "Gaskiya na dace ni Fiddausi, ba karamar sa'a nayi da na fito daga wancan gidan nazo nan ba wallahi. Kalle ni kai kana kallona kasan babu raini a jikina domin kuwa ko matar gwamna baza ta fad'a min kyau da jin dad'i ba" Tayi dariya tare da yin juyi tace, "kudi duniya ne, wannan b'angaren gabadaya ace shine nawa, ai akwai farin ciki sosai." Cikin taku na isa ta fito zuwa falon nan tayi karo da wata babar mace a tsaye tana ganin ta ta duk'a tace, "Barka da fitowa Hajiya." Fiddausi ta bita da kallo tace, "barka dai." Ladidi tace, "sunana Ladidi nice mai kula da b'angaren ki gabad'aya, nice mai share-share da girki da aike in ya tashi." Fiddausi ta sake jin wani abu na hawa kanta ya zauna aka d'ora k'afa kan d'aya tace, "Allah sarki, ke kika gyara falon?." "Nice ranki ya dad'ega abinci ma na kammala. Akwai shayi, akwai kunu, akwai dankali akwai doya da kwai, akwai kunun gyad'a da farfesun Kaji." Fiddausi ya sake yin murmushi tace, "to na gode." "Aikina ne ranki ya dade, akwai abinda kike so?." Fiddausi tace, "eh, ki shiga ki gyara min daki a wanke bandaki." "To hajiya" ta fad'a tana tashi ta wuce zuwa d'aki da Fiddausin ta fito. Fiddausi tayi dariya ta tafa hannu tace, "Duniya sabuwa" ta d'ora kafa akan center table ta kad'awa tace, "Allah ya ka bamu kud'i." Tashi tayi zuwa inda abincin yake taja kujera ta zauna ta had'a tea shegen kauri tana sha tana danna waya suna gaisawa da mutanen gidan su. Tana cikin karyawa ta fito tace, "Hajiya na gama, akwai abinda za'a yi?." Fiddausi ya kalle ta kalle ta tace, "No kije in akwai zan kira ki."ta amsa da girmamawa zata bar wajan Fiddausi tace, "ina ne wajan ku?." Ladidi tace, "Nan baya ne, ga waya nan a ajjiye in kina nemana zaki danna sifuli zan d'auka." Fiddausi ta d'aga kai Ladidi ta tafi ta cigaba da cin abincin ta . Sai da taci ta koshi sannan ta taso tana sake kallon falon ya fito zuwa babban falon ta. Tana fitowa mata guda biyu suka shigo da sallama ta amsa tana kallon su d'aya daga cikin su tace, "Amarya barka da warhaka, zamu iya zama." Fiddausi tayi murmushi tace, "barka dai, bismillah ku zauna." Dukkan su suka zauna harda ita ta bisu da kallo ganin su kyawawa farare kamar ta dan a shekaru ma baza su wuce sa'anin ta ba. D'aya daga ciki tace, "Amarya ya kwanan bak'unta?." "Alhamdulillah" ta fad'a da murmushi tana kallon su. D'aya tace, "Ni sunana Aliya mata a wajan mijin ki nice ta biyu a yanzu." D'ayar ma tace, "Ni kuma sunana Naja'atu nice mata ta uku a wajan mijin ki, ke kuma kin kasance da hud'u kenan" ta fad'a tana kallon sa tana murmushi. Fiddausi ta bisu da kallo tace, "wai da gaske ko da wasa?." Sukayi dariya Aliya tace, "Wallahi da gaske muke, kinga kamar ba haka ba ko?." Fiddausi tace, "amma ni ai matan sa uku na sani." Naja'atu tayi murmushi tace, "eh ta uku har ke ba, ai ta farko ba'a saka ta a lissafi domin itace uwar gida uwar yaran sa ita daban damu, ko nace itama ba matar sa bace amma akwai ta farko kafin Aliya." Fiddausi tace, "ban gane ba." Aliya yayi murmushi tace, "Zaki gane sai nan gaba. Baki fad'a mana sunan ki ba." Fiddausi tace, "Sunana Fiddausi nazo daga Kano." Aliya tace, "Ma sha Allah, Allah ya bamu zaman Lafiya , daman shigowa mukayi mu gaisa kuma mun gaisa zamu koma b'angaren mu" ta fad'a suna mikewa itama ta mike Fiddausi tace, "muje na raka ku nima sai naga wajan naku." Tare suka fito zuwa babban falon ta bi falon da kallo ganin yara k'anana dukkan su kusan kansu d'aya su biyar suna wasa. Kallon yaran take yi ta kalli Aliya sai tayi murmushi tace, "Duka yaran kine, y'ay'an sane." Fiddausi ta sake kallon yaran tace, "Y'ay'an sa? Ba yaran sa bakwai ba?." Aliya sukayi dariya tace, "Zaki fahimci komai sai a hankali yanzu ko Mun fad'a miki baza ki yarda ba." Girgiza kai take yi tana kallon yaran zuciyar ta cike da wasi-wasi akan abinda suka fad'a mata amma bata nuna ba ta share zancen kawai. Fiddausi ta sake kallon su tace, "Ina mijin namu kuma?." Naja'atu tayi dariya tace, "Ai ked ganin mijin nan naki yanzu kuma ai sai Allah." Fiddausi ta sake kallon su tace, "kuna yi min maganar da bana fahimta wallahi, ban gane ba fa.." Aliya ta dafa ta tace, "Zaki gane nan gaba ke zaki yiwa wata bayani in bama nan" ta fad'a tana shiga b'angaren ta ta bar Fiddausi a tsaye tana kallon su. Mamaki take ganin su ko kishi ma basa yi kamar y'an uwa sannan ga maganar da suke yi abaibai bata ganewa. Juyawa tayi ta koma zuwa mata b'angaren ta d'auki wayar ta ta shiga kiran lambar sa dan sun jefa mata wasi-wasi a zuciyar ta, kusan sau biyar ta kira ba'a d'auka ba sai a na shidan aka d'auka kafin ayi magana tace, "Baby kana ina ne ina ta kiran ka baka d'auka? Na dawo gida kace min kuma jiya meeting zakayi har yanzu ba'a gama ba?." Daga can b'angaren aka ce, "Ohh kece sabuwar amaryar kenan, Allah sarki baki san komai ba ai. Anyway bacci yake ki jira in ya tashi zan fad'a masa kin kira in da lokaci sai ya kira ki." Gaban Fiddausi ya fad'i jin muryar mace tana mata magana hankali kwance kamar wata matar sa ko kuma yar uwar sa kuma tana ce mata wai yana bacci Fiddausi tace, "wacece ke?." Tayi dariya tace, "shiyasa nace miki ke sabuwa ce ai,kar ki damu da sanin wacece ni zan zo na kwanta har a kan gadon ki, sai anjima" ta fad'a tana yanke wayar Fiddausi tabi wayar da kallo zuciyar ta na bugawa. Hannun ta har rawa ta sake kiran sa ba'a d'auka ba ta sake kira aka d'auka kafin ayi magana tace, "Wacece ke kike tare da mijina har kike fad'a min wannan maganar?. Meye had'in ki dashi da zaki cemin yana bacci?." "Ke Fiddausi! Tunda ta riga ta fad'a miki bacci nake ki yarda mana, bana son takura itama bata son takura da. haka kar ki sake kirana sai na neme ki. İn kud'i kike so ki duba account din ki zan saka miki yanzu amma bana son yawan yin waya." Daga cikin wayar taji yarinyar tayi dariya tace, "Wallahi Sugar kana da abin dariya, Wato in kud'i take so..." duf taji an yanke wayar Fiddausi ta zame ta zauna a akan kujera kirjin ta na bugawa a bayyane tace, "Wai me yake faruwa ne haka?." Babu mai bata amsa tayi shiru tana tunani kafin ta tashi zuwa daki zuciyar ta duk ta cika da abubuwa iri-iri. Yana yanke wayar yarinyar Alhaji Bello da yake dariya tace, "Naga alama yarinyar nan tana da rawar kai, in ban da raini da rashin mutunci bata yarda da abinda nace bane sai da ta kuma kiran ka?." Alhaji Bello ya taso daga inda yake daga shi sai karamin wando ko riga babu ta saka kusa da ita tana zaune tana busa sigari ya jawo ta jikin sa ko warin sigarin baya ji yace, "Haba Sugar, kin San sabuwa bata san wacece ke ba shiyasa, amma nan gaba in akace ta sake aikata abinda tayi bazata yi ba." Ta hura masa hayakin a fuska tace, "ohh! Kenan har son da kake mata yayi yawan da zaka kare ta?." Yayi murmushi yace, "Ai kaf duniya in akwai wacce nake so to kece. Ina fad'a miki gaskiya ne da tasan matsayin ki baza tayi ba." "Itama kana son ta tunda ka d'auko ta kawai dan ka kasa samun abinda kake so ne ya saka ka shata mata layi kamar sauran." "Ke kin San ta badan ce a wajena." Ta kashe sigarin ta kalle shi tace, "Ban yarda ba, inda ni daban nake da bazata sake Kiran ka ba kamata yayi taji magana ta kamar yadda zata ki maganar ka, dan taga na bata dama Kun zauna a New York shiyasa take kokarin raina min hankali, Sugar ni yarinyar nan bata yi min ba sam." Alhaji Bello yace, "Me kike so ayi mata? İn so kike a kora ta gıda yanzun nan wannan mai sauki ne." Ta girgiza kai tace, "Zan fad'a maka abinda za'a yi mata ina so ya banbance ta tabbatar ni ba sa'ar ta bace." "An gama Sugar." Tana ji yana yawo da hannun sa jikin ta tace, "Sugar wai meye kake shafa ni?." "Sugar Kari nake so, a taimaka min." Ta kalle shi tace, "kaje wajan amarya mana." "Ai ni kece amaryar ta." Tayi dariya kad'an tace, "dadin baki." Ganin tayi dariya sai ya samu damar abinda yake so a lokacin suka aikata Zina suka aikata luwadi duk a lokaci d'aya. Tare suka fito daga wanka a lokacin wayar Alhaji Bello ta sake yin k'ara yarinyar da take amsa suna Nabila ta k'arasa wajan wayar ganin mai kiran sai tayi dariya tace, "Sugar amarya ce fa, bara naji ne zata ce" ta fad'a tana d'aukar wayar. Daga can bangaren Fiddausi tace, "Baby wai kana ina ne? Ina son ganin ka yanzu dan Allah kazo. Wacece wacce kuke tare har take fad'a min magana?." Dariya Nabila tayi jin abinda take cewa tace, "Ke wai bakya jin magana ne? Sau nawa zan maimaita miki in lokacin neman ki yayi zai neme ki?." A fusace Fiddausi tace, "Wai ke wacece da zaki dinga d'aukar wayar mijina in na kira shi? Wacece ke din sa da zaki cemin bana jin magana? Kin San wacece ni kuwa?." Cire wayar daga kunne Nabila tayi tana kallon sa tana yamutsa fuska alamun maganar tayi mata k'arfi tace, "ni kike d'agawa murya?." "Na d'aga miki, me zaki yi min?. Dallah malama ki bawa mijina waya ba ke nake nema ba." Nabila ya kalle shi tace, "Sugar kana jin abinda amaryar ka take cewa min ko?." Ya matso yace, "Sugar na fad'a miki sabuwa ce bata san wacece ke ba, bata san ma labarin ki ba amma yanzu zata sani kiyi hak'uri." Fiddausi da take jin me yake cewa tace, "Baby wacece ita wai? Meyasa za'a bani labarin ta? Meyasa kake bata hak'uri?." Tayi murmushi tace, "Zaki gane wacece ni, ki shirya amsata a gidan ki ganin nan zuwa" tana fad'a ta yanke wayar ta kama k'ugu tare da daure fuska. Hankalin sa ya tashi sosai ya m rud'e yace, "kinga Sugar nifa zan iya rabuwa da ita akan wannan b'acin ran naki, Kiyi hakuri dan Allah ki saki ranki ganin damuwar ki tana tayar min da hankali sosai." Ta kalle shi tace, "Ina so na nuna mata ni ba sa'ar ta bace da zata fad'a min magana haka har tana yi min tsawa." "To me kike so ayi mata?." "So nake yau mu kwana a gidan ta a kuma kan gadon ta nake so mu kasance da kai." Ya rike fuskar ta tace, "in akayi hakan zaki huce?." Ta girgiza kai ya lumshe ido ya bud'e tace, "zan wuce, sannan ta bani hak'uri ta kuma gyara kan gadon da muka tashi." Yayi murmushi yaja hancin ta yace, "An gama Sugar." Murmushi tayi tana kallon sa tace, "muci abinci zuwa dare sai mu tafi ." Kafad'a ya d'aga alamun to tayi gaba ya bita a baya dan cin abinci. Basu jima ba suka gama cin abincin suka sake komawa ruwa har dare sannan suka shirya ta d'auki jakar ta ya dauki key ma mota itama Haka suka fita tare, ya shiga mota daban itama ta shiga suka d'auki hanyar gidan. Suna shiga gidan ya ajjiye mota itama ta ajjiye ya nufi b'angaren da ya saka a ajjiye Fiddausi itama tana bayan sa tana takun isa da tak'ama da son nunawa Fiddausi iyakar ta. Gidan shiru babu motsin kowa sai kukan tsuntsaye a haka suka k'arasa har k'ofar da zata kai ka falon Fiddausi ya bud'e mata ta shiga ya biyo ta a baya. Bata wannan falon suka shiga d'ayan tana zaune akan kujera tana charting Nabila tace, "Sugar ka ganta ma hankali kwance charting take yi." Jin muryar mutane ya saka Fiddausi tashi zaune tana kallon su shida da ita ba, kamar ita kallon ta take yi domin kamar aljana saboda kyau gata siririya sai kad'a jiki take tana tauna cingom tana yi mata kallon d'ay-d'ay. Fiddausi ta tashi tsaye ta matso kusa dashi tace, "Baby Ina ka shiga ne? Wacece wannan?." Nabila tayi murmushi ta wuce ta zauna a kan kujera ta dauki remote tana canja channel bata ce komai ba. Fiddausi ta kalle ta ta sake kallon sa tace, "Wai Wacece wannan? Da alama da ita muka yi magana d'azu a waya, Wacece ita?." Ya kalle ta yace, "kinga fiddausi tambayar wacece ita ba naki bane zaki gani a zahirance, kar na sake ji kin tambayi Wacece ita indai kina son zaman Lafiya." Nabila ta mik'e tsaye tace, "Baby bacci nake ji fa, muje ciki" ta fad'a tana wucewa sai kuma ta tsaya tace, "Sugar ina ne hanyar ne?." Da Sauri ya k'arasa ya bud'e mata suka shiga suka bar Fiddausi baki sake tana kallon su cikin tashin hankalin da bata tab'a shiga irin sa ba, shin me hakan yake nufi wai...? Matar sacs itama ko kuwa wacece din sa.....?. #Mai daki #book 3 Book2 006 A fusace ta nufi d’akin da suka shiga ta banka k’ofar ba tare da ta kwankwasa ba ta samu Nabila ta cire dankwalin kanta shi kuma yana tsaye a kusa da ita yana yi mata magana, jin k’arar bud’e k’ofar ne ya saka duk suka juya Fiddausi ta shigo a fusace tace, “Wai wacece wannan ne? Wacece ita da zaku shigo d’aki tare da ita? Itama matar kace ko Wacece nan ka fad’a min.” Nabila da take zauna a gefen gadon tace, “ni ba matar sa bace amma nafi matar sa a wajan sa, duk wannan rawar kan da kike yi ke ba komai bace a wajan sa, ko yau nace ki bar gidan nan sai kin bari” ta kalle shi tace, “Ka tabbatar mata da abinda na fad’a yanzun nan dan kasan bana son raini ko kad’an.” Ya kalli Fiddausi da take tsaye ya dawo da kallon ta ga Nabila yace, “kina ji Sugar muje waje muyi magana.” “Babu inda zani sai ka tabbatarwa da yarinyar nan matsayina yafi nata, ni zata zo tana d’agawa murna a gaban ka kuma ka tsaya kana kallon ta? Wacece ita a wajan ka? Wanne matsayi ne da ita da ka kasa nuna mata wacece ni a wajan ka?.” Ya kalli Fiddausi da take kallon sa yace, “Fiddausi jeki waje ki bar dakin nan.” Fiddausi tace, “Wallahi babu inda zanje sai ka fad’a min wacece wannan? Meye tsakanin ku da baza ka fad’a min ba?.” “Nace kije waje ko?!” Ya fad’a da karfi yana kallon ta Fiddausi ma tace, “Wallahi babu inda zanje, sai ka fad’a min wacece ita, in kuwa baka fad’a ba babu inda zanje wallahi.” Nabila ta kalle shi tana tab’e fuska fuska tace, “Kenan ta fini ko? Shikenan na gode” ta fad’a tana niyar barin wajan yayi saurin rik’o hannun ta ya dawo da ita baya ya kalli Fiddausi yace, “Wallahi in baki bar d’akin nan ba zan fasa miki baki.” Fiddausi tace, “Wallahi bazan fita ba sai dai kayi duk….” Kafin ta karasa ya zabura ya tsinke ta da mari yana zade mata idanu yace, “ni zaki yiwa iskanci ina miki magana kina mayar min da amsa? An fad’a miki ni irin lusarin tsohon mijin ki ne?” Ya nuna ta da yatsa yace, “Ki fita nace yanzu nan kafin na yi miki dukan tsiya.” Kallon mamaki da tsoro mai hade’e da tashin hankali idanun ta a waje hannun ta dafe da kuncin ta tace, “ni ka mara saboda na tambaye ka wacece ita?.” “Nan gaba in kika sake abinda yafi mari zanyi miki, babu ruwan ko da ko wacece abinda na sani kawai tana da mahimmaci da ke baki dashi a wajena kin gane? Tana da ikon zama a gidan nan a kuma duk inda taso abinda ke bashi dashi, Dan haka fita ki bani waje yanzun nan ko nayi miki abinda baza ki manta ba” ya fad’a yana nuna mata hanya zata kuma magana yace, “ki fita nace Malama!.” Ta kalli Nabila da take zaune tana kad’a k’afa ta juya jiki a sanyaye ta fita tana fita ya saka lock a k’ofar ya koma kusa da Nabila yana kallon ta yace, “Amma kin san na fad’a miki sabuwa ce ita bata san kan komai na gidan nan abi komai a Sannu a hankali zata gane matsayin da kike dashi, su Aliya ai basu isa suyi miki haka ba saboda sun san wacece ke, ita bata san komai ba shiyasa kika ga bana zak’ewa akan lamarin ta. Dan Allah kiyi mata uzuri na kwana biyu na cimma abinda nake so na rabu da ita.” Nabila tace, “Yanzu ai ya kamata ta sani dan naga alama tafi sauran rawar kai, kai kasan sauran bana yi musu hakan saboda su biyayya suke yi min babu ruwana dasu har kai nake bar musu ka kwana dasu saboda basa gabana, amma ita ka kalla fa ni take d’agawa murya tun ba’a je ko ina ba.” “Na sani Sugar, amma Ina so ki tuna amfanin ta bai kare a wajena ba akwai saura, in kika fusata ta fa?.” “Ta bar gidan.” “Kin san babu inda mata ta take zuwa matuk’ar ba sakin ta nayi ba.” Ta kawar da kai gefe tana kallon wani wajan daban kafin ta fara cire kayan jikin ta ya rage daga ita sai Bra da pant ya zauna kusa da ita yace, “Kiyi hak’uri ki bata lokaci Sugar, akwai abu mai mahimmaci da nake son samu a wajan ta in tayi fushi yanzu a Ina zan samu?.” Ta kalle shi tace, “me kake so ka samu din Wanda ni bani dashi?.” “Kedai ayi shiru kawai” ya fad’a yana tallafo fuskar ta tare da fara kissing din ta. Fiddausi tana zaune a jikin k’ofar d’akin da suke sai raba ido take kallon abun take kamar a mafarki, ta saka hannun ta a kuncin ta ta mara ta tabbatar dai ba mafarki take yi ba ta sauke numfashi kirjin ta yana bugawa a guje tashin hankali ya bayyana a tare da ita kana kallon ta kasan a firgice take. Nishi take jiyowa k’asa-k’asa daga cikin d’akin kafin ta fara jiyowa sosai musamman muryar Alhajin ta da take ji da alama baya cikin hayyacin sa. Da sauri ta tashi ta mik’e tsaye ta kasa kunne sosai a daidai lokacin da Alhaji yayi wani irin ihu ba shiri tayi baya ta zube a wajan idanun ta a waje baza ka tantance suma tayi ko kuma idanun ta biyu ba. A haukace ta mik’e tana dukan k’ofar d’akin da iyakar k’arfin ta amma k’ofar kk motsin kirki bata yi, wani irin abu Fiddausi take ji hankalin ta a tashe ta tashi tana waige-waige nan ta hango wani bottel mai kyau na kwaliyya da yake a ajjiye ta d’auko a fusace ta dinga makawa k’ofar amma kamar ba yi take yi ba. A wajan ta zube tana kuka sosai wanda yake fitowa daga k’asan zuciyar ta cikin rashin sanin abinda zata yi, ji take zata iya yin ko meye ma akan ta bud’e kofar hakan ya saka ta zabura zata tashi aka bud’e k’ofar sai tayi cikin dakin ta fad’i ruf da ciki ta d’ago tana kallon Nabila da take tsaye tana kallon ta daga ita sai k’aramin towel wanda bai wuce cinya ta kalle ta tace, “ki shiga cikin miji ki zaiyi magana dake” ta fad’a tana tsallake ta ta fice tana baza gashin kanta. Cikin d’akin ta kalla tana kuka sosai harda majina taga Alhaji daga shi sai k’aramin wando ya nufo ta a nan ta samu k’arfin guiwar zabura ta fita a guje ya bi bayan ta amma kafin yaje ta kulle k’ofar yana jin kara da alama watsar da kayan dakin take yi dan yaga alamun kamar abun ya d’an tab’a mata kai, Kai ya dafe sam bai so hakan ba shima baya son nuna mata waye shi sai ta gama amfanin da ya d’auko ta dan shi tukunna sai komai ya bayyana, amma baya son b’acin ran Sugar dole yayi abinda tace kodan ya samu farin ciki shima. K’arar wayar sa da ya jiyo ya saka shi komawa d’akin a lokacin Nabila ta dawo tana shan tea tana kad’a k’afa. Wayar ya d’auka ya fita ganin mai kiran ya koma can dakin k’arshe ya shiga bandaki ya saka wayar a kunne yace, “Malam barka da dare.” Daga can b’angaren Malamin yace, “Barka dai Alhaji Bello, na kira ka da daddare fatan babu damuwa.” “Babu damuwa malam ko yaushe kana da ikon kirana, komai Lafiya dai?.” “Ka samu damar kasancewa da matar ka ta baya?.” “Wallahi tak’i bani had’in kai ne, nayi-nayi amma yarinyar nan tak’i na rasa ya zanyi.” Malamin yace, “Ai kuwa haka zaka samu ko ta tsiya ko ta arzuki, kasan dalilin da ya saka aka auro ta kenan in akace ana zaune har zuwa yanzu ba’a yi komai ba akwai yuwar arzukin ka zaiyi kasa da kashi sittin cikin d’ari. Sannan kuma akwai yuwar samun nak’asu a fannin kasuwancin ka abokin adawar ka kuma zaiyi sama. . Cikin tashin hankali Alhaji Bello yace, “Da farko na d’auka zata amince Kasancewar ta mace mai son kudi amma nayi-nayi tak’i yarda sai ma ayoyi da hadisai da take jawo min, gashi kace anfi so ta amince aikin zai fi yin kyau.” “Yadda kayi kokari ka samo ta a matsayin wacce aka lissafa ana so a samo a aura saboda wannan burin dole kasan yadda zaka kasance da itata baya kamar yadda aka tsara, in hakan ta kasance shikenan komai zai cigaba fiye da baya, sannan ka tabbatar bata yi ciki ba dan ba’a so hakan ta kasance in da ciki a jikin ta. Kafin hakan ya faru ka tabbatar babu ciki a jikin ta, inda hali ma anfi son hakan ta kasance tana cikin jini dan tabbatar da rashin ciki, amma saboda d’aukar lokaci in kasan babu ciki zaka iya aiwatarwa.” Alhaji yace, “Zanyi malam zan tabbatar nayi maganin komai, Tunda a yanzu zan iya amfani da ita ta k’arfi hakan yazo da sauki ko maganin bacci zan bata nayi in yaso in ta farka zan iya sakin ta tunda amfanin ta ya riga ya kare.” Malam yace, “kayi komai banda maganin bacci, ka dai saka a d’aure ta kamar yadda kake yiwa masu taurin kai irin ta, amma maganin bacci in aka bata ai bata hayycin ta kenan zai zama a banza aikin tunda ba’a cika sharud’an ba. ka tabbatar dai babu ciki in ba haka ba za’a yi a banza.” Da to ya amsa da girmanawa kafin ya sake cewa, “matuk’ar ta sanar da wani wannan abun komai zai lalace, kar ka bari wani ya sani ka hanata fita in ta kama ta daina amfani da waya har sai tayi wata guda da aikata luwad’i da ita a wannan lokacin zaka iya sakin ta.” Ya amsa cikin gamsuwa kafin ya kashe wayar yana tunanin hanyar da zai bi wajan ganin ya kusanci Fiddausi ba tare da ya sha wahala ba. D’akin Fiddausi yazo zai koma halin da ya hango Nabila a ciki ne ya saka shi kasa wuce ta ya koma ciki da sauri ya kullo k’ofar yayi kanta. Duk wani hankali da ake samu a jikin d’an Adam ya fita daga jikin Fiddausi, numfashi kawai take ja ta zubar da komai na d’akin gabadaya bata cikin hankalin ta tayi wani iri lokaci d’aya.Jikin ta mugun rawa yake yi ko mafarki bata tab’a kawo hakan ba, ko a film bata tab’a ganin irin wanna k’azantar da Alhaji ya aikata ba. Har lokacin gani take mafarki take yi ta kasa tabbatarwaa gaske ne ba mafarki ba sai juya kai take cikin yanayi Mara dad’i. Ta rasa ma abinda zatayi gabadaya ta gigice ta fita daga hankali ta rasa abinda yake mata dadi sai numfashi take yi dakyar kanta ya kulle ta rasa irin tunanin ma da zatayi. _mijin ki fa da wata har cikin dakin ki, mijin ki ne yake kwanciya da wata a daki kuma kike a zaune?._ abinda zuciyar take fad’a mata kenan sai kuwa ta zabura ta fito daga d’akin ta nufi d’akin da suke ta bud’e ta shiga. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ta fad’a tana Jan wani irin numfashi tare da zubewa a wajan a sume ganin abinda bata tab’a gani ba yana wakana a tsakanin mijin ta sa wacce bata san wacece ba. Jiyowa yayi ya kalle ta Nabila taja tsaki muryar ta a shak’e tace, “Cigaba Sugar, ka cigaba ka kyale ta kawai.” Kamar daman jira yake ya cigaba da abinda yake yi tana sake rik’e dan ta rikita shi da kukan da take masa yana sake bada himma wajan aikata abinda yake yi Fiddausi ta kwance a wajan a sume. Sai da suka kammala Nabila ta sakko daga kan gadon ta wuce ta tayi wanka ta fito shima ya shiga ya fito ya saka doguwar riga sannan ya k’arasa inda take ya yafawa fuskar ta ruwa amma bata motsa ba yayi tsaki ya juya ya d’auki waya ya saka a kunne yace, “Kana ina ne?.” Yayi shiru alamun Ana bashi amsa kafin yace, “okay kar ka damu ba wata babbar matsala bace.” Yana fad’a ya yanke wayar ya d’auki ruwa roba guda ya juye a fuskar Fiddausi sai a lokacin taja numfashi amma bata bud’e ido ba. D’aukar ta yayi cak zuwa d’akin ta ya kwantar da ita a kan gadon ya zauna yana kallon ta a lokacin ta bud’e ido, ta bud’e baki zatayi ihu yace, “Shiiii! Kar ki yi min wata magana, tun farko ai na fad’a miki ga abinda nake so kika k’i laifi ne dan na nema a wajan wata? Ki bani ki gani in bai daina kula ta ba mana.” Ita dai Fiddausi kallon da take yi zuciyar ta nayi mata wani irin abu dan ta kasa banbance abinda take ji sai kallo kawai ya rik’e ta ta fincike tace, “Kar ka sake tab’a ni.” Murmushi yayi yace, “ke ki shiga hankalin ki kin gane ko? Bana son shirme da hauka. Kina da ciki?.” Bin sa kawai take da ido ta kasa magana yayi tsaki ya sake d’aukar waya ya saka a kunne kafin yace, “İn ka kammala kazo gida yanzu Ina so za’a gwada min jinin wata ne” yana fad’a yana yanke wayar yana girgiza kansa dan so yake ayi komai a gama kafin Fiddausi ta bashi matsala Shiru babu wanda ya sake magana aka yi masa waya ya fita ta bishi da kallo ta rasa ma wanne irin tunani ya kamata tayi, kanta ya toshe gabadaya bata da nutsuwar da zatayi tunani ta jingina kawai ta lumshe idanun ta zuciyar ta nayi mata zafi sosai. Shida wani dogon mutum suka shigo ya kalli Fiddausi yace, “jinin ta nake so a d’aukar min aga tana da ciki.” Ba musu yayi inda Fiddausi take ya kalle ta ya kalli Alhaji yace, “Ai a yanayin ta ma Alhaji ya nuna tana da ciki k’arami, amma saboda ka tabbatar bara mu duba” ya fad’a yana rik’e hannun Fiddausi ya d’aure ya d’auki jinin ta. Ita dai kallon sa akwai take yi kamar wacce ta samu tab’in hankali dan abinda ta gani ya saka ta zama mahaukaciya ta wucin gadi likitan ya fita shi kuma ya zauna a kusa da ita yana jira ga dawo yaji abinda zai ce. Nabila ce ta shigo ta kalle shi tace, “Sugar” ta fad’a tana k’arasowa inda yake tana kallon sa tana kallon Fiddausi. Murmushi yayi mata yace, “Sugar ina zuwa yanzu zan dawo.” Ta tsaya ta hard’e hannu a kirji tana kallon Fiddausi tace, “Akwai cikin ne?.” “Bamu tabbatar ba har yanzu.” Ta tab’e baki tana kallon Fiddausi kafin tace, “kaima kai ta raba jikin ka a wajan irin wad’anan gidadawan matan wanda basu San mutunci ba, ai wallahi kana bani kunya banga abin nema a wajan wannan yarinyar ba.” Murmushi yayi yace, “banda abin ki sugar ai irin su ake samu a d’auko cikin ruwan sanyi ba tare da ka sha wahala ba, ki duba ki gani kwata-kwata a kwana nawa ya d’auko ta tazo gidan nan?. İrin su Sune daidai ni dan nafi jin dad’in su.” Ta tab’e baki bata ce komai ba. Likitan ne ya dawo da sallama Alhaji Bello ya kalle shi yace, “Ya ake ciki? Akwai cikin kuwa?.” Likita yace, “Eh akwai na sati biyu, ga sakamakon” ya fad’a yana mik’a masa takardar. Alhaji yace, “basai na gani ba ai, ka tawo da allurar?.” “Eh gata” ya fad’a yana d’auko allurar yaja a sirinji ya kalli Alhaji shima shi yake kallo yace, “yi mata allurar.” Abinda yazo kunnen Fiddausi kenan ya ratsa zuciya ya kaiwa kwakwalwar ta ziyara ta zabura ta mike tana cewa, “A’a kar a yi min allura kar a zubar da cikin.” Kamar mahaukaciya haka take magana tana kallon su, Likitan ya dakata da nufar inda take ya kalli Alhaji shima ya kalle shi sai ya mik’e tsaye ya nufi inda take ya rike ta yace, “Zo kayi mata sai an zubar da cikin ko tana so ko bata so, ban kawo ta dan tayi ciki ba.” #Mai daki #Paid #500 #Nana Haleema #Book3 Book3 07 Fiddausi ta fara fizge-fizge amma ya rik’e ta gam yadda ko motsi ta kasa tana ji tana gani aka yi mata allura a bayan ta ya gama ne ya sake ta ya kalli likitan yace, “Zuwa nan da yaushe cikin zai fita?.” Likitan ya kalli agogo yace, “Zuwa nan da minitina goma zai iya fita saboda karami ne sosai bai fara girma ba kuma allurar mai k’arfi ce sosai.” Alhaji Bello ya kalli Fiddausi da idanun ya suke a kulle hawaye na sauka yace, “Da zarar ya fita shikenan ko?.” Likitan yace, “Shikenan Alhaji babu wata matsala sai dai in da matsala yazo.” Alhaji Bello yace, “Shikenan na gode.” Likita yayi godiya ya fita shi kuma ya kalli Nabila yace, “Sugar muje mu barta a nan ta gama jinyar ma dawo.” Nabila ta k’araso kusa da Fiddausi ta shafa fuskar ta tace, “Sorry amarya lokacin haihuwar ki baiyi ba, ki jira lokacin yayi amma yanzu dole wannan cikin ya fita” tana fad’a ta juya ta fita har ya fita sai ya dawo ya k’araso inda take ya d’aga rigar jikin ta ya zare pant din ta yace, “yadda zaki fi samu sauki My Baby” ya fad’a yana shafa fuskar ta ya fita ya barta. Tun Fiddausi tana jin abun ciwo sama- sama har ya zama tana ji sosai cikin ta da marar ta kamar an had’e su waje d’aya saboda azaba, sai wani kuuuuu cikin ta yake mata kamar an saka masa wani abun a ciki yana vibrating a cikin sa. Jikin ta rawa yake tana juyi tana kukan azaba sai juya kai take tana gumi dan sosai take jin ciwo musamman marar ta da take ji kamar zata b’alle. Ta d’auki mitina goma a haka kafin ta fara jin jini na zuba daga jikin ta kukan ta ya k’aru tayi karamar k’ara a lokacin da jini yake zuba. Numfashi take ja a hankali azabar da take ji tana raguwa a lokacin ta kalli jikin ta taga jini ga kuma gudan abu da take ji a jikin ta. Kuka take sosai ta mike tsaye sai tayi saurin komawa ta zauna jin kanta na juyawa kamar zata kofa ga ciwon da take ji har lokacin bata daina ji ba sai dai ya ragu sosai. K’ofar aka bud’e bata kalli wanda ya shigo ba aka k’araso akace, “Hajiya Alhaji ne ya turo ni akan na taimaka miki.” Kallon wacce aka turo tayi ta mayar da ido ta kulle tana ji kamar ba’a duniyar take ba a wata duniyar take daban ba wacce ta saba rayuwa ba. Da taimakon ta Fiddausi ta iya tashi ta kaita bandaki kuma ta fito tana gyara wajan tana girgiza kai cikin tausayin Fiddausi tace, “ban san meyasa kyawawan mata suke kawo kansu wannan gidan ba, ban San me suke gani a jikin Alhaji suna maqale masa ba, basu san azabar da take cikin sa ba amma duk shekara sai wata tazo kamar basu da na gaba dasu da za’a bincika a gano waye ma Alhajin. Mtswww Allah ya kyauta ya kiyaye mu daga kwad’ayin abun duniya.” Wajan ta gyara tsaf ta koma bandakin ta samu Fiddausi tana niyar fitowa bayan tayi wanka ta taimaka mata ta dawo da ita ta zauna tace, “Hajiya kina son jin wani abun ne?.” Fiddausi ta kalle ta tace, “k’arfe nawa?.” Ladidi ta kalli agogo tace, “karfe shida ta safe yanzu, anyi sallar asuba.” Fiddausi ta sauke numfashi tana kanta nayi mata ciwo sosai haka marar ta tace, “bani riga a kayan can.” Ba musu ta tashi ta d’auko mata a cikin kayan da ta nuna mata ta kawo mata, tana daga zaune ta saka Ladidi ta fita ta barta a wajan. Ba jimawa ta dawo da shayi a hannun ta mai kauri da maganin da Alhaji ya bta ta kawo mata amma sai ta tarar Fiddausin tayi bacci sai ta ja mata k’ofar ta koma inda ta fito. Fiddausi ta jima tana bacci har rana tayi sosai bacci take yi shigowar sa ce ta tashe ta ta ganshi a tsaye a kanta yana kallon ta da murmushi akan fuskar sa, kallon sa tayi taga ba fuskar ta yake kallo ba sai ta duba jikin ta taga gabad’aya rigar da ta saka ta tattare daga k’asa haka daga sama ma na ganin komai na jikin ta. Da sauri ta mik’e zaune ya gyara rigar tana dafe kanta dan ciwo yake mata sosai har lokacin ya zauna kusa da ita yace, “Fiddausi my Baby, ya jikin naki?.” Mugun haushin sa take ji a zuciyar ya mai had’e da tsana ta lokaci d’aya hakan ya saka bata ma kalle shi ba yayi murmushi yace, “to meye kuma? Laifi nayi?, to ki yi hak’uri shikenan?.” Bata kula shi ba ya yi dariya ya mike yana kallon ta yace, “Zanje na dawo, ko shirya Karb’ar mijin ki” ya fad’a yana murmushi sosai ya fita yana darıya ya barta zaune kamar gunki. Da kallo ta bishi har lokacin ta kasa gasgata abinda ya faru ba mafarki tayi ba, dan yadda ta farka yanzu taga shigowar hakan ya bata tabbacin mafarki tayi a bayyane tace, “kodai daman mafarki nayi? Tunda gashi yazo yana ce min Baby, mafarki nayi ko ba mafarki bane?.” Kiran sallah taji a wayar ta kalli agogo taga karfe d’aya Saura na safe ta tashi ya shiga bandaki tayi wanka ta fito ta saka kaya tayi sallah tayi shiru tana tunanin abubuwan da suka faru gaske ne ko kuwa ba gaskiya bane ba dan ita ta kasa gasgawata ganin abin take kamar fa mafarki ne. Sallama aka yi aka shigo d’akin jin muryar matan da suka gaisa ya saka ta kallon wajan suka karaso da murmushi Aliya tace, “Amarya ashe baki da lafiya?.” Zama sukayi a kusa da ita suka saka ta a tsakiya Naja’atu tace, “Baba Ladidi itace ta sanar damu kin yi b’ari da safe, Allah ya tsayar miki iya haka ya saka baza ki sake wani cikin ba.” Fiddausi ta shafa cikin ta ta kalle su tace, “kenan abubuwan da suka faru ba mafarki nayi ba da gaske ne?.” Aliya tace, “ai indai a gidan nan ne zaki ta ganin abubuwa tamkar ba’a duniya ma kike ba. Abinda kika gani ba komai bane indai a duniyar gidsn Alhaji Bello ne.” Fiddausi ta dafe kanta zuciyar ta nayi mata bugu tace, “baza ku gane abinda ya faru ba shiyasa, gaskiya ba a gaske hakan ta faru ba mafarki nayi.” Aliya tace, “Yazo da Nabila sun kwana a daki d’aya sannan ya saka an zubar miki da ciki.” Jin hakan Fiddusi ta kalle ta jin tasan abinda ya faru sai Aliya tayi murmushi tace, “Fiddausi wannan ai karamin abu ne a gidan nan, ki gode Allah ma da iya hakan abin ya tsaya bai had’a ki Keda Nabila a lokaci guda yayi amfani daku ba, shi yayi amfani dake itama tace kin burge ta kina ji kina gani zaki aikata lesbian babu abinda kika isa ki yi kuma.” Hankalin Fiddausi ya tashi sosai tace, “kenan kuma kun san da hakan?.” Naja’atu tace, “dukkan mu babu wacce hakan bai faru da ita ba, ke kinji dadi ma da aka zubar da cikin mu da muka Haifa fa? Gasu nan a ajjiye har bana so na tuna ina da d’a tare dashi. Domin ban samarwa d’an nawa uba na gari ba, gwara ace a waje nayi cikin sa na haife shi da ace a gidsn nan na haife shi.” Fiddausi ta rasa ma tunanin da zatayi jijiyoyin kanta suna harbawa ta kalli Naja’atu tace, “Wai dan Allah Kun San daman yana aikata abinda yake yi?.” Aliya tayi murmushi tace, “Ai Tunda muka ga an dawo dake gidan nan daga k’asar waje muka san kema irin mu ce kina bashi matsala ta wajan yin mu’amala dake ta baya, inda kina bashi had’in kai kamar Nabila da yanzu bakya Nigeria kina can duk abinda kike so kuma zaki samu. Dan in jirgin sama kike so yana da kudin da zai iya siya miki, domin manyan mutanen da yake dasu a turai jirgin sama ba komai bane a wajan sa face k’aramin alhaki.” “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Kenan Kun San da cewa Alhaji yana luwadi da matan sa?.” Naja’atu tayi dariya sai ga hawaye ya sakko mata tace, “nida Aliya babu wacce bai kusanta ta baya ba Fiddausi, na tabbata kema hakan zata zo gare ki. Ba wai fata muke miki ba amma da wahala ki tsallake wallahi.” Fiddausi ta fara girgiza kai tana hawaye tace, “A’a wallahi badai ni ba, wallahi bazan amince ba, badai ni ba, bai isa ya saka na aikata sab’on Allah ba.” Suka yi murmushi ko wacce tana kuka Aliya tace, “kar ki cika baki, in ba Allah ne ya taimake ki ba wallahi sai yayi dake. Kinga ni maza ya saka har guda hud’u suka rik’e ni, biyu suka rik’e k’afa biyu suka rik’e hannu a gaban su yayi amfani dani ta baya ina kuka a karshe sai da na suma na kwana ban San lokacin dana farfado ba, Naja’atu maganin ya bata tasha yayi amfani da ita cikin maye, kema kuma ki jira naki lokacin.” Fiddausi jikin ta rawa yake yi sosai tana kuka hankalin ta ya kai k’arshe wajan tashi Naja’atu tana kuka tace, “Baya kishin ko wacce mace indai ba Nabila ba, ita kad’ai ce yake kishin ta kuma ba matar sa bace karuwar sace amma ta fiki a wajan sa. Zai iya amfani dake a gaban maza masu irin halin sa amma bazai iya yi da Nabila a gaban wani ba saboda iya yake kishi ba mu ba. Gwara Aliya Tunda yayi amfani da ita sau d’aya bai sake ba ni kuwa sau uku yana yi dani, babu yadda na gani jaka zai saka a rik’e ni ko a d’aure masa ni ban isa nayi motsi ba daga ranar bazan sake ganin sa ba sai hakan ta sake rayo masa” ta fad’a tana kuka sosai wanda ya bayyana ya cika dakin. Fiddausi tayi suman zaune baza ka banbance a wanne yanayi take ba a lokacin sai zare idanu take yi ta rasa abinda zata ce dan abun fa yafi karfin kanta Aliya tace, “a gaban idanun ki zai kwanta da Nabila baki isa kiyi magana ba, kema yana lallab’a ki ne a yanzu saboda bai samu abinda yake so ba amma da zarar ya samu shikenan kin zama tamkar bolar sa, sai sanda ya ga dama yaji yana ra’ayin ki zai neme ki kuma dole kije babu uzurin kina al’ada indai yaso sai yayi amfani dake ko da tsarki ko babu. Bawai zaki kai kanki bane ta karfi za’a yi amfani dake dan zai shammace ki ne yazo a lokacin da bakiyi tsamani ba kafin Kiyi k’ok’arin guduwa ya kama ki.” Jiri Fiddausi taji yana d’aukar ta kanta ya sara ta dafe kai tana juya kai ta rasa ma abinda zata ce dan bakin ta yayi nauyi sosai harshen ta ya sarqe ta kasa cewa komai Aliya ta dafa ta tace, “kiyi hak’uri kawai addu’a ce zata fitar dake daga gidan nan.” Wani irin abu Fiddausi ta fara kamar mai shaquwa tana kuka da sauri Naja’atu ta d’auko mata ruwa ta sha sai ta bud’e murya sosai tana kuka sosai. Dukkan su kuka suke yi babu mai bawa wani hak’uri kusan mintina biyar a haka kafin Fiddausi tace, “zaman ne kuke a gidan da baku gudu ba?” Ta fad’a muryar ta na rawa sosai. Aliya tayi dariya kad’an mai nuna zallar ciwon da yake zuciyar ta tace, “Ai duk wanda ya shigo gidsn nan bai isa ya fita ba sai in babu igiyar auren sa a kanta.” Fiddausi tace, “kamar ya?.” “Da alama kema irin mu ce duk ba’a yi bincike Akan Alhaji ba aka aura masa mu. To wallahi ko nan da gate din farko baki isa kije a ‘kasa ba, sai dai a kai ki a mota kuma duk motsin ki ana kallo baki isa kije wani wajan ba sai dai in ya sake ki babu auren sa akan ki. Kinga ni daga Katsina ya auro ni amma tun bayan da naje gıda sau d’aya lokacin Muna tsaka da soyayya ban kuma zuwa ba har yanzu, akwai lokacin ma da amfani da waya sai ya hanaki gabad’aya.” Naja’atu tace, “duk Inda kike son zuwa za’a kai ki Fiddausi amma ke dai ki fita ke kad’ai k’arya kike kuma babu inda zaki sake zuwa daga wannan waje da kika je sai gidan nan.” Fiddausi tayi shiru sai hawaye kawai da take yi ta ma rasa ne zata ce Aliya ta sake cewa, “Addu’a ce maganin mu kawai a gidan nan amma duk yadda kike tunanin uqubar gidan na ta wuce haka” ta fad’a tana danna wayar ta ta fito mata da wani hoto tace, “Kalli wannan hoton ki gani.” Fiddausi ta d’aga jajayen idanun ta ta kalli hoton Aliya tace, “nice a jikin hoton kafin nazo cikin gidan nan” ta kashe wayar tace, “a baya ni mai kib’a ce wacce za’a kira da y’ar lukuta, amma yanzu baza ki tab’a cewa Allah yayi kib’a a jikina ba Fiddausi saboda tashin hankalin mijin ki komai zaki dinga ci wallahi bak’in cikin sa bazai barki k’iba ba.” Fiddausi tace, “amma meyasa baku yiwa iyayen ku waya ba?.” Aliya tace, “duk wata hanya da zata Sada ki da wanda kika sani ya toshe ta, in waya ce ya saka anyi masa blocking kaf lambobin wayar ki, amfanin wayar ki kawai ki kalli wani abun ko kiji wak’a amma ko internet baza ki bud’e ba balle ki samu damar turawa bloggers kice hide my id.” Fiddausi ta fesar da iska tana girgiza kai cikin rashin sanin abinda zata ce dan ita jin ta take yi wani iri kamar ba waccan Fiddausin ba Naja’atı tace, “ki daure ki fara addu’a in bakya yi Allah ya raba ki da wannan gidan domin zaman sa yafi zaman gidan prison.” Aliya tace, “Akwai kud’i ko nawa kike so zai baki, akwai mota duk wacce kike so zaki hau, in Nigeria kike so ki bari zai kai ki amma kwanciyar hankali ta minti daya babu ita a wanann gidan. Amma akwai kudi dan tashin farko sai ya saka miki miliyan goma an account amma basu da amfani dan baza ki more su ba.” Fiddausi tayi shiru ita dai ta tallafe hab’a tana zare ido tana jin maganar Aliya ta k’arshe da take cewa, _Akwai kudi, akwai mota akwai kuma zuwa duk ina kake so, to wannan ba shine kwanciyar hankali ba?._ Fiddausi ta d’ago ta kalli Aliya tace, “wannan abubuwan da kika lissafa ba Sune kwanciyar hankali ba?.” A tare Aliya da Naja’atu suka kalli juna sukayi murmushi Aliya tace, “Duk irin tunanin mu daya dake Fiddausi, amma na tabbata daga yanzu zaki fara gane kud’i ba shine kwanciyar hankali ba, kwanciyar hankali daban kudi daban Fiddausi. Domin daga dawowar ki gidan nan zuwa ynzu nasan kin tabbatar da akwai kwanciyar hankali sannan akwai kud’i, akwai kwanciyar hankalin da tafi kudi.” Naja’atu tace, “Inda anyi cikakken bincike baza’a baki auren Alhaji Bello ba, to iyayen mu saboda shuran da yayi a fannin kudi ya aka suka bamu shi ba tare da dogon bincike ba. Wallahi Fiddausi har kud’in aurena an kawo an saka rana amma tunda Alhaji ya bayyana na bijirewa waccan auren sai da aka hak’ura hankalina ya kwanta. A budurwa ya d’auko ni ya kawo ni gidsn nan ko nace ya kaini london dan ni a can muka fara zama, ji nake babu kamata a lokacin duniya tayi min dad’i saboda na samu rayuwar da nake mafarki, daga k’arshe ga Inda na k’are” ta fad’a murya nayi rawa kafin tace, “tun ba’a je ko ina ba na fara yin dana sani wacce bata da amfani a wajena.” Aliya tace, “Dukkan mu k’addara d’aya ce fa had’a mu a wannan gidan, kawai Fiddausi ki yi hak’uri zaki ta ganin bak’in abubuwa a gidan nan wanda ko a film baki tab’a ganin su ba. Ki kuma daure ki yiwa Nabila biyayya in ba haka ba wallahi zata saka yayi miki dukan tsiya wata ran kuma tace sai kin bata hak’uri.” Fiddausi tace, “ina yaran nasa da yace min yana dasu?, ina Uwar gidan sa?.” “Yana da manyan yara sosai wacce uwar gidan sa ta haifa amma yanzu basa tare tunda ya fara harkar nan ta tattara komai mata ta bar shi ita da yaran ta. Bamu sani ba ya sake ta ko bai sake ta ba Allah ne ya sani. Yana da wata matar a can New York wacce ya barwa mai gidan sa bature shugaba su a wannan fanni ita yana abinda yake so da ita bamu sani ba ko ya sake ta ko har yanzu matar sace. Yanzu sai ni sai ke sai kuma Naja’atu sai kuma wacce k’addarar take a kanta zata shigo nan gaba.” Naja’atu tace, “a duk shekara yake yo auren budurwa ko bazawara ya danganta da abinda bokan sa yace ya samo. Dan boka zance ba Malami ba. Ki gode Allah ma da kika je New York kika dawo wannan mai gidan nasa baice yana sonki ba.” Fiddausi ta kalle ta yace, “Bokan sa kuma?.” Naja’atu tayi dariya tace, “Eh bokan sa, kin d’auka wai ya ganki dan yana so ne? Kin d’auka duk abinda ya dinga yi yayi ne dan yana son ki?. Hmmm Ki sani tun daga kan halayyar ki, kammanin ki, komai naki bokan sane yace a nemo mai irin ki ayi amfani da ita saboda samun wani abu nashi. Babu lallai ki yarda yanzu amma nan gaba da bakin sa zai fad’a miki Fiddausi kamar yadda ya fad’a mana. Ni ya auro ni saboda aikin da ake so za’a yi masa dan cin galaba akan mai gidan sa na New York kuma anyi aiki yayi nasara. Babban burin sa a yanzu bai wuce yayi amfani dake ta baya ba dan shine mafarin aikin sa a kanki.” Fiddausi ta girgiza kai jikin ta har rawa yake yi dan abubuwan da taji kamar shocking aka jona mata a jikin ta ta girgiza kai tace, “bazai tab’a samu ba kuwa har abadah!. Indai a wajena ne ni Fiddausi bazai samu abinda yake so ba, nafi karfin sa wallahi.” #Mai daki #Book3 #Nana Haleema Book3 008 Aliya da Naja'atu sukayi murmushi a tare bayan sun kalli juna jin kalaman Fiddausi Wanda a wajan su tamkar busa ce Aliya ta girgiza kai ta mik’e tsaye tace, "Kawai ki cigaba da addu'a Fiddausi, amma wallahi duk yadda kike tunanin mijin ki wallahi ya wuce haka. Allah dai ya kare ki kawai." Naja'atu ma ta mik’e tsaye tace, "Abinda ya kamata kenan ba wai ko cika baki kice ke bazai yu a wajan ki ba, Alalh ya k'ara Lafiya amarya" suka fad’a suna fita suka barta a zaune tana bin su da kallo. "Wai da gaske abinda suka fad’a gaskiya ne kuwa?." Ta fad'a a bayyane tana sake kallon k’aton d’akin da take ciki dan har lokacin zuciyar ta bata wani gamsu sosai ba. Sai ta girgiza kai tace, "Ke Anya ba amfani sukayi da mafarkin da nayi ba suka sake tsorata ni ba? Taya hakan zata kasance wai a zahiri ba a film ba?. Ko a film din America ba’a wannan k’azantar balle a zahiri.” Tayi k’aramin tsaki tace, "Kai wannan ba gaskiya bane taya hakan zata faru kuma suke zaune a gidan nan basu nemi hanyar guduwa ba?. Kawai suna so su tsorata ni ne amma ba gaskiya bane.” Dukan kanta tayi dan ta ma rasa wanne tunani da zatayi ta kwanta a kan gado tana sake tunanin abinda suka fad’a mata wanda take jin sa tamkar almara. Tsaki ta sake yi tace, “wannan karyar banza ce ba gaskiya bane.”             Rukayya tana kwance a kan gado suna waya da Ameena akan abinda yake gaban ta a lokacin tace, "wallahi Ameena ganin abun nake kamar a mafarki wai nice Baba yake jira yau na bashi amsar wa nake so a cikin Umar da Ibrahim. Sai naji kamar ba ni ba dan a baya in akace min wannan lokacin zai zo ko sai naga kamar kawai ana fad’a min ne dan naji dad’i.” Ameena daga b'angaren ta tace, "Shiyasa nake fad’a miki ki yi hak’uri lokaci ne gashi kuma lokacin naki yazo yanzu sai labari. Yanzu wanne kika d'auka a cikin su? Wanne zuciyar ki tafi amin cewa dashi?." Rukayya tace, "wallahi Ameena na rasa abinda zanyi ni akan lamarin nan, dukkan su bazan ce ga wanda nake so a cikin su ba, abinda na sani ko wanne yana k’ok’ari wajan ganin ya nuna kin yana sona ba kamar Ibrahim da ya manta ni k'awar Fiddausi ce. Shi Umar yana da aure ba ko yaushe yake sakewa ayi waya ba saboda matar sa hakan kuma yana burge ni sosai, Ibrahim kuwa kalaman sa suna saka ni a nishadi, Gashi Bawai na soyayya yake amfani dashi ba; magana irin wacce muke yi yanzu haka yake yi amma sai ya bani nishadi a zuciyata. Ni ban sani bama ban san me zan ce ba wallahi Ameena, har bana so anjima tayi Baba ya kira ni dan ban San me zance masa ba.” Ameena tace, Kiyi addu'a ki kuma istikhara duk wanda yake da alkhairi Allah ya zab’a miki. Amma kin San me?." "Sai kin fad’a." "Wallahi nafi son ki auri Ibrahim akan Umar?.” Rukayya tace, "Ibrahim fa tsohon mijin Fidy ne Ameena." Ameena tace, "Tsaya mana, ki tambaye ni meyasa nake so kiji hujjata mana." Rukayya tace, "to meyasa hujjar taki?." "Na farko kinga an san ibrshim an san halin sa da yanayin iya rik’e matar sa da yayi a baya nasan ke kanki kin shaida da hakan, an san bashi da wata halayya mara kyau yana kokari a kan gidan sa duk da bashi da wani k’arfi sosai amma iyalan sa sunfi k’arfin ci da sha. Na biyu kuma bashi da mata a yanzu in ya aure ki ke kad’ai ce matar sa sai Amir wanda nasan zaki masa tarbiyya fiye da yadda Fiddausi zatayi masa. Na uku kuma dangin sa basu da matsala zasu so ki su qaunace ki baki da fargabar dangin miji ko abinda yayi kama da haka ba. Na hud’u yana sonki da gaske ba da wasa ba, soyayyar da yake miki ce ta saka ya furta zai aure ki. Shi kuma Umar an san shi amma ba'a san wacece matar sa ba, watakila bata da ra’ayin zama da kishiya zata iya yin komai da ta fitar dake, sannan dangin sa sun karb’e ki ko A'a, wanne irin rik’o yake yiwa matar sa?, duk ba'a sani ba saboda duk binciken ka akwai abinda sai ka shiga zaka gani. Duk binciken Yaya Adam bai gano wata halayyar Yusuf ba sai da na shiga shiyasa nidai Allah ya sani nafi son ki auri İbrahim." Rukayya da take jin ta tace, "Baba ma yafi son Ibrahim kawai baya so lokaci d’aya yace min na auri Ibrahim ne naga kamar yayi min dole shiyasa ya bani dama na Zab’i wanda nake so amma in a son ransa ne na d’auki Ibrahim. Ni kuma wani iri nake ji wallahi in na tuna mijin Fiddausi ne fa har d'a akwai tsakanin su sai naji yana fice min daga tunani gabad’aya." "Yanzu fa ba mijin Fiddausi bane ki dinga cewa tsohon mijin ta." "Tsohon mijin nata fa, meye bata sani nasa ba? In na aure shi nan gaba nasan tabbas zata zo gidan dan kin San ta ba kunya gare ta ba kuma zasu had’u zata ga kamar ma ragowar tane Ibrahim din ta rage ta yar na d’auka. Kin sanni da kishi in na tuna hakan sai naji ni auren sa baya zuwa kaina." Ameena tayi dariya tace, "to ai a baya take matar sa ba a yanzu ba, dan ya aure ki kece kike a matar da ita kuma tsohuwar matar sa." "Amma meye bata sani ba nasa?." Ameena ta sake yin dariya tace, "ke dallah ki kawar da wannan tunanin daga zuciyar ki shaid’an ne kawai yake kawo miki wannan tunanin, nagartar sa zaki gani da cancantar sa ba wannan k'ananun tunanin da kike yi ba mara amfani." Rukayya tace, "Shikenan dai kawai Allah zab’a mana abinda yafi alkhairi." "Ameen. Ki dai tsaya kiyi tunani kar ki yi abinda zakiyi dana sani. İn zuciyar ki bata İbrahim kar ki d’auka ki zab’i Umar din.” "Ni yanzu har bana so yamma tayi Baba ya kira ni yace na fad’a masa wa na d’auka, gabana har fad’uwa yake." "To ke yanzu wa kika d’auka?." "Ban sani ba wallahi." Ameena tace, "yanzu in Baban ya kira ki zuwa zaki kice masa baki sani ba?." "Ni kawai zan bashi dama Ameena ya zab’a min duk wanda yaga yafi cancanta dani, dukka su biyun zan iya zama dasu kawai ya zab’ar min in Ibrahim ne Allah yasa haka shine alkhairi, in Umar din ne Allah yasa shine mafi alkhairi." "Shikenan kin huta, Allah ya tabbatar da alkhairi." "Ameen ya Allah. Sai na shigo." Daga nan sukayi sallama ta kashe wayar. Jingina tayi da bayan gado tayi shiru tana sauke numfashi idanun ta a kulle kafin ta bud’e ido a lokacin kiran Ibrahim yake shigowa cikin wayar ta, kamar bazata d’auka ba sai kika ta d’auka ta saka a kunne tayi sallama daga can b’angaren ya amsa tare da fad'in, "kin wuni Lafiya?." Rukayya tace, "Lafiya lau, yasu Hajiya?." "Tana gaishe ki." "Ina amsawa." Bata sake cewa komai ba tayi shiru yace, "Rukayyan Ibrahim zance ko?." "Yaushe na zama ta Ibrahim?." Yayi murmushin da sai da taji shi a zuciyar ta yace, "Ni na fad'a kuma hakan ne zai tabbata." "Sanin gaibu ai sai Allah." "Nima bance nasan gaibu ba ai Rakiya, ina fadar abinda nake ganin zai yu ne." Kamar yana gaban ta ta turo baki gaba tace, "nifa ba sunana Rakiya ba." Yayi dariya mai sauti wacce ta saka ta murmushi itama daman da ya tsokana tane ya fad’a yace, "ya sunan ki?." "Rukayya!" Ta fad'a cikin salo wanda ya saka shi sake yin murmushi yace, "ni Rakiya na sani sunan ki." "Allah nima zan ce maka Iro." Yayi dariya kad’an yace, "ni ai ba sunana bane dan Mu'azzam nake ke kuwa sunan ki Rakiya." Itama tayi murmushi tace, "kai kad’ai kake fad’a min sunan nan kaima dan tsoho ne daman tsofaffi ne suke b'atawa mutane suna." Yayi dariya yace, "na yarda da abinda kika ce kema ki amsa sunan ki Rakiya." "Allah bazan amsa ba." "Zaki amsa fa ni na fad'a miki." Murmushi tayi bata ce komai ba jin hakan ya saka yace, "Rukayya!." Lumshe ido tayi ta bud’e a duniya tana jin dad’i in yace Rukayya tun suna tare da Fiddausi ta kan cewa Fiddausi ibrshim da larabci yake cewa Rukayya balle yanzu da in ya fad'a take ji har ranta tace, "Na'am." "Zan kula da rayuwar ki in kika amince kika bani amanar kan ki ina tabbatar miki da babu dana sani a cikin zama dani, zan saka ki farın cikin da baki tab'a hasashen zaki kasance a cikin sa ba Rukayya. Nasan akwai wani tabo da kike kallona dashi amma ajjiye shi nake so ki yi a gefe ki kalle ni matsayin wanda yake neman auren ki baki san shi ba ya kawo kansa wajan ki dan neman alfaramar shiga zuciyar ki. Bana so ki dinga kallon baya ki kalli yanzu ki d’auka baki sanni ba ban sanki ba Rukayya, indai zaki kallo baya baza ki amince dani a zuciyar ki ba, fatana ki amince dani ina tabbatar miki da baza nadama ba sai farin ciki wanda zai mamaye dukkan rayuwar ki.” Shiru tayi tana jin kalaman sa har zuciyar ta domin kuwa a nutse yake yin maganar dole ka saurara koda baka so saboda yadda yake kalaman a nutse zasu shiga jikin ka. Kafin tayi magana ya sake cewa, "Dan Allah Rukayya ki daina kallona a yadda kike kallona, ki kalle ni matsayin wanda zai aure ki kuma masoyin ki. Rukayya da gaske ina sonki son da nake miki shine ya kawo ni wajan ki, in kin tashi yanke hukunci ki tausaya min domin zuciyata tayi rauni sosai in taji akasin abinda take so taji zata iya shiga yanayin da baki yi tunanin zata shiga ba." Kasa magana tayi sai shiru da tayi tana jin sabon yanayi a cikin zuciyar ta amma ta kasa ce masa komai, "Rukayya!." Ya sake fad'a tace, "Uhum!." "Kina jina?." "Eh." "Naji kin yi shiru baki ce komai ba." "Jira nake ka gama" ta fad'a tana wasa da gashin bargon da yake jikin bargon da take kwance a kai. Yayi murmushi yace, "to na gama fad’i abinda zaki ce." Tayi dariya tace, "Baka gama ba ka cigaba da fada kawai." Murmushi ya sake yi yace, "Ina zuwa ana Kira na" ya fad'a yana datse wayar tabi wayar da kallo ganin sunan da tayi masa saving ya d’auke daga kan screen din alamun ya kashe ta kulle ido ta bud’e a bayyane tace, "Ibrahim kar ka manta kai fa tsohon mijin kawata ne Fiddausi, taya zan iya auren ka ina kallon ka matsayin mijina bayan kayi rayuwar aure da kawata?." "Rukayya!." Jin muryar Umma ya saka ta mik’e zaune tace, "Na'am Umma." "Ga bak’i kin yi ki fito ku gaisa" tana fad'a ta fita ita kuma ta tashi ta fito. Cousins dinta ta gani mata suka zauna suna hira sosai har akayi sallar la'asar suna tare. Bayan sallar i'sha Baba ya saka Zuhra ta kira ta tunda taji kiran gaban ta ya fad’i haka ta tashi zuwa  d’akin sa ta same shi a zaune yana cin abinci ta shiga da sallama ya amsa yana kallon ta har ta samu waje ta zauna tace, "Baba gani." Ya ajjiye cin abincin yace, "ya maganar mu dake? Kin San yau nace zaki fad'a abinda kika tsayar ko?." Ta d’aga kai alamun eh yace, "To ina Jinki." Ta da’go ta kalli Umma da take kallon ta ta sake sunkuyar da kai tace, "Baba ni na baka dama a cikin su biyun wanda Kaga ya dace dani ka aura min shi kawai." Baba ya kalle ta sosai a nutse yace, "meyasa kika ce haka? Bakya son su ne dukkan?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "to meyasa kika ce kin bani dama? Ai in kina son  mutum d'aya shi zaki fada, wannan Zab’i da kika bani kamar dukkan su bakya son su ne ai ko?" Ya fad'a tana kallon umma. Umma tace, "Eh to, watakila dukkan su tana jin zata iya zama dasu ne shiyasa ta baka dama ka bata wanda kaga yafi cancanta." Baba ya kalle ta yace, "Haka ne?." Ta d’aga kai tare da fad’in, "eh haka ne Baba." "Kin tabbatar dukkan su zaki iya zama dasu a matsayin mijin ki?, duk wanda na baki kin tabbatar zaki iya zama dashi a matsayin mijin ki?.” "Eh Baba zan iya." "Kar ki cutar da kanki fa ki tilastawa zuciyar ki abinda so. Na fad’a miki in duk su biyun basu yi miki ba Wallahi babu mai miki dole, ki fad’i abinda yake zuciyar ki.” Ta gyara zama tace, "Zan iya Baba." Baba ya girgiza kai yace, "Shikenan to Allah yayi miki albarka yasa zab’in nawa ya kasance alkhairi a gare ki." "Amin Baba" ta amsa a hankali yace, "Tashi kije zuwa gobe zaki gane wanda na zab'a miki a cikin su." Ta tashi ta fita Umma ta kalli Baba tace, "Nasan zab’in ka Ibrahim ne ko?." Yayi dariya yace, "Kamar kin shiga zuciyata, daman bana so naji ta ambaci akasin Ibrahim wallahi, inda tace Umar zan amince mata saboda shine zab’in ta saboda babu yarda zanyi, amma yanzu da ta bani dama Ibrahim shine mijin ta in sha Allah." Umma tayi murmushi tace, "Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Ya amsa da amin yana cin abinci yana ji a zuciyar sa matsayin sa na uba na gari ya zabarwa y'ar sa miji na gari wanda baza tayi kuka ba ko bayan babu ransa zai mata miji kuma uba. #Mai daki #Book3 #Paid #Nana Haleema Book3 009 Rukayya haka ya koma d’aki jiki a sanyaye ta zauna ta dafe kanta cikin rashin sanin abinda zatayi Zuhra da yake gefen ta tace, “Yaya wa kika d’auka a cikin su?.” Rukayya ta kalle ta tace, “Zuhra ban san za d’auka wa zan bari ba.” “Nidai nffi so ki d’auki Umar dan yafi Ibrahim din nan kudi.” “Ba kudi ne a gabana ba Zuhra, kawai ki taya ni da addu’a Allah ya zab’a min wanda yafi alkhairi.” Zuhra tace, “To Amin. Allah yasa a had’a bikina da naki.” Murmushi kawai tayi ta tashi ta shiga band’aki. Haka ta kwana cikin tunani kuma cikin ikon Allah a daren babu da wanda suka yi magana dashi a cikin su babu wanda ya Kira ta sai hankalin ta yafi kwanciya tayi bacci cikin tunanin wa Baba zai bata a cikin su?. Tana zaune akan kujera tana kad’a k’afar ta kamar Kullum jikin ta kaca-kaca riga daban zani daban tana danna waya, Yusuf ne ya shigo kallo daya zaka yi masa ka tabbatar da ramar da yayi a bayyane ya kalle ta yace, “bakya ji ina yi miki magana ne?.” Ta d’ago ya kalle shi tace, “naji kawai babu amfanin na amsa ne, amma yanzu da kazo da kanka ai Gashi kasan ina jin ka.” Mamaki shi hana shi magana yake yi in tana yin wani abun kamar itace mijin shine matar haka take masa gadara Akan komai yace, “Kina ji babu amfanin kiyi magana haka kika ce fa.” Ta sake cewa, “to meye amfanin ka maimaita min nasan abinda kaji shine abinda nace.” “Asiya wannan wanne irin iskanci kika d’auko ne? Ni zaki dinga yiwa rashin kunya an fad’a miki sa’an ki ne ni?.” Kallon sa tayi sai ta juya tayi tsaki ta cigaba da abinda take yi. Kwace wayar yayi daga hannun ta a fusace yana kallon ta yace, “Dan iskanci ni kin yiwa tsaki?.” Ta sake yin wani tsakin bai ssn ya tsinke ta da Mari ba sai ganin ta yayi ta mik’e tsaye a fusace tana kallon sa shima haka tace, “Ni ka Mara Yusuf?.” “Na mare ki ko zaki rama ne?.” “A yanzu bazan rama ba wallahi ka sake dukana sai na rama, ai ba’a kawo ni dan ka dinga dukana ba.” “Allah yasa ki sake yin abin dukan ki gani in ban mare ki ba, ni zaki mayar dan iska ki dinga yi min tsaki kamar kece mai gidan nice matar?. Ya zan dinga ajjiye kud’i a gidsn nan daga ni sai ke na dinga neman su ina rasawa? Ina suke zuwa?.” “K’afa ce dasu fita suke yi. kaga malam ni ba irin uwar gidan ka da ta fita bace bana sata ban iya sata ba. Kaje can ka nemi inda ka ajjiye kud’in ka amma ba a wajena ba.” Yusuf ya bita da kallo ganin sai wani jijjiga jiki take yi cikin rashin kunya yace, “in bake ce kike d’auka ba to waye?.” A fusace tace, “Wannan kuma kai ka sani, ni dai ba barauniya bace ba kaje can ka samu b’arauniyar ka. Haka kawai kaje a b’ata maka rai ka zubar da kudin ka zaka zo ka wuce a kaina? To wallahi nidai ka sake mari na sai na ra….” Kafin ta gama fad’a ya sake tsinke ta da mari dan yaga zata rama din ta tsaya tana kallon sa shima ya kalle ta sai kuma yayi tsaki ya juya ya fita ransa a b’ace sosai. Ransa a b’ace yake sosai ko kallon gaban sa bayayi yadda ya kamata ya fita zai shiga b’angaren Ameena mai aikin Ameena Baba Habi ta tsayar dashi tace, “Alhaji barka da Rana.” Ya tsaya ya kalle ta yace, “Baba Habi an tashi lafiya?.” “Lafiya lau Alhaji. Dama akan maganar zaman gidan nan, Tunda hajiya bata gidan nan gaskiya zamun mu a gida…..” kafin ta k’arasa magana suka ga Asiya ya fito wajan a fusace tana fadin, “wallahi ka sake saka hannu ka dake sai na nuna maka ni ba irin wacce zaka daka ta kyale bace, ni zaka kalla kace nayi maka sata? Kudin me zaka shigo dashi da zan d’auka?. An fad’a maka ni irin banzar Uwar gidsn kace da zaka dinga yiwa abinda Kaga dama tana kyale ka? To wallahi ni baka isa ba domin kuwa daidai nake dakai.” Jikin Yusuf sanyi yayi sosai ya kalli su Baba Habi da suke tsaye suna kallon Asiya ya kalli mai gadin sa yaga duk suna kallon abinda yake faruwa sai ya kulle ido ya bud’e jikin sa gabad’aya ya mutu domin kuwa ba’a tab’a wulak’anta shi a duniya ba kamar yadda Asiya tayi masa yanzu. Ba’a tab’a yi masa tozarcin da tayi masa ba a wannan lokacin, ba’a tab’a yi masa abinda ta aikata masa ba shiyasa ya kasa yin ko motsin kirki ya kulle idanun sa kawai. Bai kula ta ba ganin baiyi magana ba tace, “kayi magana mana ko ka sake dukana kaga in ban rama ba, Aikin banza aikin wofi, na d’auka rashin kunyar taka taje inda taje take, na d’auka zaka kuma dukan nawa dana nuna maka yadda ake zallar hauka wallahi.” Kallon ta yayi yace, “Koma ciki.” “Bazan koma ba ai ba kai ka fito dani ba daman, ka jira duk sanda naso komawa zan koma.” d’auke kai yayi daga kallon ta kawai ya shiga b’angaren Ameena ba tare da ya sake cewa komai ba dan ya Lura in ya cigaba da kula ta zata iya yin kokawa dashi a gaban ma’aikatan gidan sa. Koda ya shiga rasa abinda zaiyi ma yayi gabad’aya komai baya yi masa dad’i ransa a b’ace yake sosai, kamar shi Asiya zata fito gaban masu aiki tana yi masa hauka dan kawai ta wulak’anta shi?, abinda bai tab’a faruwa dashi ba tun da yake zaune a gidan. Falon yake k’arewa kallo kamar mai neman wani abun komai yana nan yadda yake sai k’ura da falon yayi amma babu komai da yake ajjiye komai yana mahallin sa hatta khamshin turaren falon bai fita ba dan ya Riga ya kama d’akin sosai. Hoton sa da ita da Zaytun ya gani dukkan su sunyi dariya yayi saurin d’auke kansa zuciyar sa na mugun harbawa ya bar wajan yana ji kamar ya zubar da hawayen da bai san dalilin su ba. Asiya tana komawa gida waya ta kira Umma na d’auka tace, “Umma na gaji da d’agawa Yusuf wallahi, yau mari na yayi har sau biyu na rantse da Allah ya kuma dukana Umma sai na rama.” Umma daga can b’angaren tace, “Me kika yi masa da ya mare ki?.” “Wai ina kudin sa da ya ajjiye suke zuwa in ya ajjiye baya ganin su, kuma ta kud’in dana turo miki ne aka yi hidimar kawo kudin Fauziyya shine fa yazo yake d’aga min murya harda mari na.” Umma tace, “kuma kina jinina namiji ya d’aga hannu ya mare ki ki zauna kina kallon sa?, ai kafin ya sauke hannu kema yaji naki hannu a fuskar sa. Ke dan fa Muna son zaman ki da Yusuf ba hakan yana nufin ya saka hannu dake ki mu kyale shi bane, ai duka baya cikin zaman aure, in ya dake ki tabbatar kafin ya sauke kema Kinyi abinda zai ji zafi a tasa fatar shine ya jawo. Na Riga nayi masa abinda bazai iya yi miki ko barazanar komai ba bazai tab’a iya sakin ki ba ko yace kije gida, kar ki sake kuskuren Bari ya dake ki koda nan gaba domin zai samu lagon sake dukan naki a nan gaba.” Asiya tace, “Ai na fad’a masa wallahi ya sake dukana sai na rama, nifa Umma so nake na mayar dashi tamkar Keda Baba, sai abinda kike so za’a yi amma ni naga yak’i koma min haka.” “Sai a hankali, shima baban naki ai ba lokaci d’aya ake samu abinda ake so ba, zaki same shi fiye da yadda na samu mahaifin ki kedai kar ki cigaba da yin abinda nace sannan koda wasa banda duka.” Umma ta sake cewa, “shinkafar mu fa ta kare ki san abinda zaki yi.” ASiya tace, “yak’i koya min mota ne wallahi da yanzu na zubo su a baya na kawo babu wanda yasan meye na kawo miki har gida, amma zan aiko da kud’i sai a siya.” Umma tace, “yayi” Daga nan ta kashe wayar Asiya na sake girgiza jiki da tabbatar da ya sake dukan ya wallahi sai ya rama. Bayan kwana biyu. Fiddausi ta rame sosai tun bayan da suka rabu da Alhaji bata sake ganin sa ba har aka kwana biyu kullum sai ta Kira shi amma baya d’auka sai dai taga gajeren text in taci sa’a yace ta duba account ya saka mata kud’i. Tun abun baya damun ta har ta kawo damun ta yake yi ta kasa sukuni har ta kai ga ta fara ramewa. Duk abinda ya faru a baya ta d’auka mafarki ne tak’i gasgawata ko zuciyar ta naso gagagata abun sai ta kawar da tunanin. A daren ranar tana zaune a falon ta tsahon kwana biyun su Aliya basu zo ba itama kuma bata je ba tana zaune ita kad’ai cikin tunanin da ta fara saka kanta a ciki. Motsi taji a kanta hakan ya saka ta d’ago ta kalli wanda yake kanta ta ganshi a tsaye yana kallon ta ta mik’e tsaye tana kallon sa tace, “meyasa baka d’aukar wayata in na kira ka? Meyasa sai dai ka turo min kud’i? Baka San kaii nake son magana dashi mai ba kudi ba?.” Yayi murmushi ya rik’o hannun ta yace, “Haba Baby kema kin san ai nayi kewar ki sosai ai.” Ta bishi da kallo tace, “Meyasa bana samun y’an gidan mu a waya? Duk wanda na kira sai tak’i tafiya.” Ya kawar da kai gefe kafin yace, “Watakila basu da network ne, zo kiji” ya fad’a yana Jan hannun ya zuwa d’aki. Daki’n da suka kwanta da Nabila suka shiga tabi d’akin da kallo gaban ta yana fad’uwa tace, “A dakin nan nayi wani mafarki ya faru, amma sai nake Jin matarkin kamar gaske ne.” Yayi murmushi jin abinda tace ya zauna a gefen gado yace, “Baby ni ba wannan ba, a matuk’ar buk’ace nake dake fa Baby. Ya za’ayi?.” Ta zauna a kusa dashi zuciyar ta na sake tabbatar mata da bafa mafarki tayi ba zahiri ne amma sai ta kawar tana so ta sake tabbatarwa tace, “Nima haka Baby.” Jin abinda tace sai yayi murmushi dan daman bazai tab’a bari abinda ya faru ya hana shi samun ta ba dole yayi abinda zaiyi dan kawar mata da tunani ya kawo ta jikin sa ya fara sarrafata ta fara fita daga hankalin ta shima haka. Sai da ya tabbatar komai yayi nisa sannan ya fara kokarin aiwatar da abinda ya dawo dashi a kanta, kamar an tsire mata allura ta firgita ta mik’e zata sauka daga kan gadon ya rik’o ta yace, “Baby kar ki yi min haka ki tsaya dan Allah.” Kai take girgizawa tace, “ban tabbatar da abinda ya faru ba mafarki bane sai yanzu, ban tabbatar da bani da hankali da na sake sauraren ka ba sai yanzu, ban tabbatar da nayi kuskure ba sai yanzu, wallahi baza ka smau abinda kake so ba a wajena” ta fad’a tana fita da gudu yayi saurin diriwa ya tsaya a gaban ta yace, “Dan Allah Baby ki tsaya kiji, Haba baby ni ne fa dan Allah ko tsaya sau d’aya kawai.” A guje ta fita ya bita amma kafin yaje ta kulle k’ofa ya daki k’ofar yace, “Wallahi in baki bud’e ba sai na b’alla k’ofar nan, Fiddausi kizo ki bud’e saboda abin nan na auro ki, Kizo ki bud’e wallahi na bud’e da kaina sai na yi miki abinda baki tunani ba.” Shiru yaji alamun bazata bud’e ba sai yayi kwafa ya juya ya koma ya shiga d’akin d’azu ya d’auki wayar sa ya kira Malam bugu biyu ya d’auka Alhaji Bello yace, “Malam Yarinyar nan tak’i amincewa fa, kuma kace sai idanun ta biyu shine aikin zaiyi na rasa ya zan mata wallahi. Kai ka ce nazo mata a yau amma gashi nazo ta gudu harda kulle k’ofa.” “Da girman ka da komai mace guda d’aya ta gagare ka? Guda d’aya ce fa ba guda goma ba. Kasan yadda zakayi komai ya faru a yau in ba haka ba sai dai ka jira a samu wata ranar da hakan zai faru, kayi kokarin ganin kayi komai a yanzun nan ai ba k’arfin ka tafi ba kuma saboda haka ka auro ta, ya kamata ka tabbatar da abinda nake fad’a maka kafin kazo kana dana sani.” Alhaji yace, “shikenan Malam nasan abinda zanyi m yanzun nan.” Kashe wayar yayi ya cigaba da danna wayar kafin ya saka a kunne yace, “ku shigo cikin gidana yanzu nan.” Ajjiye wayar yayi ya koma ya fita suka dawo tare da maza manya guda biyu k’arfafa har kofar d’akin Fiddausi ya kalle su yace, “ku cire min k’ofar nan.” Da k’arfi mutum d’aya ya dake ta motsa ya sake dukan ta ta sake motsawa a taree mutum biyun suka dake ta sai ta balle suka shiga suka ganta a zaune a kan gado tana kuka sosai dan duk dukan k’ofar da ake bata ji ba ba’a hayyacin ta take ba. Ganin sun shigo sai ta zabura zatayi bandaki ya kamo hannun ta y kalle su ya ce, “ki d’aure min ita akan gadon nan, Kuyi mata ruf da ciki kamar yadda aka saba .” Kuka take tana son kwacewa tana cewa, “Dan girman Allah ka kyale ni kar kayi luwadi dani, ni musulma ce dan Allah ka kyale ni kar ka saka na sab’awa Allah.” A lokacin ta kwace daga rik’on da yayi mata ya kalle su yace, “ku kamata nace.” Kafin ta kai ga shiga band’akin mutum d’aya y d’auko ta cak kamar yar tsana tana wutsil wutsil da k’afa ya jefa ta kan gadon. A lokacin d’ayan ya shigo da doguwar igiya ya danne Fiddausi suka d’aure ta a kife kamar yadda yace suyi haka sukayi mata. Bayan sun gama ya kalle su yace, “kun tabbatar baza ta kwace ba?.” “Bazata kwance ba Oga, anyi nata d’aurin da sai da a kwance ta.” Ya mats kusa da ita sannan ya kalle su yace, “Kuje.” Ba musu suka fita shi kuma ya k’arasa inda Fiddausi take kwance tana ihu. “Kar kayi min haka dan Allah ka kyale ni, bana son aikata abinda kake so na aikata dan Allah ka kyale ni. Na amince ko mai kake so zanyi amma banda wannan, komai kake so a gangaar jikina ka yanke amma dan girman Allah kar kayi min haka.” Ya fara tartare rigar ta daga baya yace, “da kin amince ta ruwan sanyi da ba’a zo wajan nan ba, amma sai kika k’i ke ga mai taurin kai ko? Baki San saboda abin na auro ki kenan ba?. An fad’a miki duk abinda nayi a kanki saboda na auro ki ne kawai na kwanta dake kiyi ciki ki haihu? Haba Fiddausi zaman wannan ai ya wuce.” Kuka take sosai har muryar ta na dashewa tace, “Na amince ka sake ni ka rabu dani amma kar ka aikata abinda kake niyar yi dani dan Allah, ka taimaka min ka agaji rayuwata bana so. İn kashe ni ne ka kashe ka kai inda zaka kai gangaar jikina amma dan girman Allah ka dakata da abinda kake niyar aika min.” “Keda barin gidan nan kar ki kawo shi kusa a zuciyar ki, zaki bar gidan amma ba yanzu ba sai lokacin da naga damar hakan, kuma wallahi sai nayi dan abinda na kawo ki dan shi Kenan baki isa ki saka ni asara ba.” ya fad’a yana hawa kan gadon a daidai Lokacin Fiddausi tayi k’ara mai k’arfi. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid #500 Book3 010 Idanun ta sun yi mata mugun nauyi da ta fara bud’ewa sai ta mayar ta kulle saboda ji take kamar an saka wani abu an danne mata su a haka ta fara bud’e Idon ta a hankali duk da nauyin da suka yi mata haka ta bud’e su tun tana gani biyu-biyu har ta bud’e idon tass a cikin d’akin tana sake kallon d’akin kamar ya canja mata. Hawaye ne ya sakko daga idanun tana jin zafi a bayan ta ta kalli gefen ta taga ruwa ne aka saka mata yana shiga jikin ta da alama suma tayi a lokacin ta farfad’o. Hannu ta saka tana shafa jikin ta tana hawaye sosai kafin ta kalli gefen ta taga Aliya ce a zaune a kusa da ita tana kallon ta ganin ta bud’e ido tace, “Sannu Fiddausi.” Sai kukan yafi na baya gudu muryar ta na rawa tace, “Daman duk zantukan da muka tattauna ba mafarki nake ba? Kenan har zubar da cikin da ya saka aka yi min ba mafarki nake yi ba?. Zafin da nake ji a jikina hakan yana nufin yayi luwad’i dani ko Aliya?.” Itama hawaye ya sakko mata cikin tsananin tausayin rayuwar su ta rik’e hannun ta tace, “Ba mafarki kike ba Fiddausi, da gaske ne kin auri Alhaji Bello mai amfani da matan sa dan neman duniya, da gaske ne cikin sa da yake jikin ya saka an zubar, da gaske ne yayi amfani dake ta baya Fiddausi.” “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!!. Ina zan saka raina ni Fiddausi? Na sab’awa Allah na aikata luwadi, Hasbunallahu wani’imal wakil, Wayyo Mamana.” Aliya tana kuka sosai itama tana kuka kamar ita aka yiwa abinda aka yiwa Fiddausi dan tasan zafin abun da rad’ad’in da zaka dinga ji a zuciyar ka da ruhin ka tace, “na fad’a miki daman ki yi addu’a kika nuna ke bai isa ba saboda kina ganin kamar kina da k’arfi, wallahi saboda hakan ya auro ki kawai ki yi hak’uri Allah yana gani yasan ba da son ranki hakan ta faru ba, Alalh bazai kama ki da laifin aikatawa ba dan ta k’arfi akayi amfani dake. Kiyi hak’uri kawai kiyi addu’ar Allah yasa wanna shine na farko kuma karshe kawai. Dan in ba addu’a ba anjima zaki sake ganin sa ya maimaita abinda ya saka aka yi miki ya sake cika burin sa akan ki, bai damu da baki da lafiya ba indai zai samu biyan bukatar sa wannan ke kika jiyo.” Fiddausi tace, “bazan sake zama a gidan nan ba balle ya sake lalata dani ba, wallahi bazan zauna ba yau d’in nan zan bar garin nan; a Kano zan kwana yau gidan mu zanje” ta fad’a tana cire allurar hannun ta ta mik’e zaune sai ta kasa zama ta koma ta kwanta tana cewa, “na kasa zama Aliya na kasa, Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, na kasa zama ya zanyi?” Ta fad’a a gigice tana kuka sosai wanda yake nuna tsantsar k’unar da zuciyar ta take ciki. Aliya ta koma kusa da ita sosai ta rik’e ta tace, “sai dai ki yi hak’uri fa dan zaki ji zafi sosai a hankali zaki dawowa daidai, baza ki iya zama a yanzu ba ki daure ki kwanta zaki samu Lafiya zuwa wani lokaci.” Kuka take yi sosai mai tsuma zuciya Aliya ta rungume ta tana kuka itama dan rayuwar da suke ciki sai dai kawai Allah ya fitar dasu. “Aliya bazan zauna ba, bazan zauna ba Aliya gidan mu zan tafi, bazan iya zama a gidan nan ba walalhi gida zanje. Mutuwa zanyi in na zauna a nan zuciyata zata buga, na hak’ura da komai zan tafi gida.” Aliya bata ce komai ba domin taga wanda ya shigo yana kallon su duka biyun ganin suna kuka ya saka shi ya tsaya a gefe yana kallon Aliya yace, “ki fad’a mata ta cire ran komawa gida yanzu” ya fad’a yana k’araso inda suke yana kallon su. Aliya tace, “Ka sani Allah sai ya saka mana sai kayi mutuwar wulakanci, sai Allah ya nuna maka sakamakon ka tun a duniya.” Yayi k’aramar dariya yace, “Dani daku za’a ga wanda yake ganin sakamako ai. Ku tun a yanzu kuke ganin naku sakamakon gashi nan duk Kun firgice Kun kasa tsayar da hankalin ku waje d’aya.” Fiddausi tana kuka ta kalle shi tace, “Allah ya isa ban yafe maka ba wallahi sai ya saka min abinda kayi min. Mugu, azzalumi, d’an neman maza.” “Ohh! Kin farfad’o daga suman kenan, yayi kyau” ya fad’a yana kallon ta yana wani irin murmushin rainin hankali. Aliya ya kalla itama shi take kallo yace, “ki fad’a mata irin wannan addu’ar kun saba yi min ita tun lokacin baya kafin tazo, ke tun kafin ku akwai wanda suka yi min irin ta babu adadi amma babu abinda ya same ni. Itama ki fad’a mata babu abinda fatan ta zaiyi min sai dai ya k’ara min k’arfi da kuzari.” Fiddausi tace, “mugu, kaci amanar yardar da nayi maka, ka cuce ni ka yaudare ni, ka lalata min rayuwa ka saka na sab’awa Allah. Ban tab’a tunanin aikata abinda ka aikata dani ba ko a tunani bai tab’a zuwar min ba, Allah ya isa bazan yafe maka ba.” Yayi dariya mai sauti yace, “ke ai amfanin ki bai k’are a wajena ba, dan kaf matan da nake mu’amala dasu banji wacce naji dadin ta kamar ke ba, dan haka zan iya ce miki yanzu aka fara gwara ma ki kwantar da hankalin ki zaki fi samun duk abinda kike so” ya fad’a yana rik’e fuskar ta. Kwace fuskar tayi fuskar ta duk hawaye taji sosai tace, “kuma wallahi nafi k’arfin ka, baza ka sake sab’on Allah dani ba sai dai kayi duk abinda zaka yi min, in kashe ni ma zaka yi sai ka kashe ni amma wallahi bazan bari ka sake ba. Allah ya isa nan yafe ba kuma sai na bar gidan nan ko baka sake ni ba.” “Hajiya Fiddausi Kenan, ai daga yanzu har lokacin amfanin ki ya k’are a gidan nan baza ki sake koda waya da kowa naki ba har sai lokacin dana ga damar hakan, amma daga yanzu babu ke babu waya, duk kuma wayar wanda zaki karb’a da niyar sanar da wani babu wanda zaki samu” ya fad’a yana nuna mata wayar ta a hannun sa yayi murmushi yace, “nasan kin haddace lambar mutane da yawa zaki iya Karb’ar wayar wani kice zaki kira su, ina tabbatar miki da duk wayar wanda zaki karb’a baza ki tab’a samun wani naki ba, koda wannan k’awar taki ce baza ki same ta ba har sai lokacin da naga dama sannan hakan zata kasance.” “Wallahi sai na gudu na bar gidan nan, bazan zauna dakai ba, na tsane ka, bana sonka, bana son mai sonka” Fiddausi ta fad’a tana kuka sosai tana kallon sa. Yayi dariya yace, “nima ba sonki nake ba sannan ba kaunar ki nake ba, dalilin da ya saka na aure ki shi na aiwatar miki jiya kuma shi zan cigaba da aiwatar miki a duk sanda amfanin hakan ya tashi. A banza na saka kika kashe auren ki an fad’a miki? An fad’a miki soyayyar gaskiya ce zata saka na nace ki kashe auren ki Fiddausi?” Yayi dariya tare da tafa hannu yace, “duk kashe kud’in da kashe na yi shi ne akan abinda nayi miki jiya, ban auro ki dan ina sonki ba sai dan ina da manufa a kanki kuma ita nake cimmawa a yanzu.” “Ke kuma kin aure ni saboda kud’i, mota, babban gida, fita kasar waje. Duk kin samu kuma ko yanzu kika ce min kina son zuwa wata k’asar Fiddausi you’re free to go, zan barki ki je ko ina amma banda Saudia. Duk inda kike so a fad’in Abuja zaki je amma baki isa ki tsallaka titin Abuja ba tare da ikona ba. Duk wani motsin ki ina gani ko ina kika je na sani dan haka taku d’aya baki isa ki yi ba sai ni naso. Abinda kika aure ni dan shi ai kin samu meye kuma kike fatan na sake ki kuma Fiddausi?. Kince kudi shine komai a duniya gashi kina cikin kudi to meye na kuka kuma? . A ganina farin ciki zakiyi domin in kika amince da abinda nake so wallahi ba kud’i ba kud’ad’e zan baki ba.” Kasa magana tayi sai kuka kawai da take yi tunawa da abubuwan da tace a baya sai zuciyar ta ta karye kuka babu full stop. Ganin hakan ya saka shi yin murmushi yace, “In kuna da ra’ayi a yau din nan zan siya muku ticket ku tafi England, kuna so?.” “Bama so, ko bango duniya zaka kaimu so, kaje ka k’arata da k’udin haram mu bama so. Allah ya isa bamu yafe ba” Aliya ta fad’a tana kuka sosai. Yayi dariya ya yace, “Kedai bakya so, amma nasan Fidy tana so ko My Baby?.” Kuka take sosai ta kasa magana balle ta tanka masa yayi dariya kawai ya fita ya barta ba tare da yace komai ba Aliya ta kalle ya tace, “Kinyi kuskuren kashe auren ki kika shigo wannan gidan Fiddausi, Kinyi kuskuren zab’ar kud’i a matsayin farin ciki. Daga shigowa ki wannan gida gashi kin fara tabbatar da kud’i ba shine farin ciki ba, gamu a kud’in a zaune amma ko wanda suke hannun kidnappers baza su sha irin wahalar da muke sha ba” tana fad’a ta tashi ta bar Fiddausi wajan tana kuka kamar ranta zai fita. Dana sani take ji tana mamaye mata zuciyar ta hakan ya saka kukan tak’i tsayawa sai zuba yake kamar an kunna fanfo. Tunda suka samu sab’ani da Asiya ya fita sabgar ta ko wajan ta baya zuwa sai yaje d’aukar wani abun , a b’angaren Ameena yake zaman sa a d’akin sa ko ta kanta baya bi dan gabad’aya ta fita masa daga rai amma kuma ya kasa yin komai a kanta. Hukunci yake so yayi mata ya d’auki mataki a kanta amma da sun had’a ido sai ya kasa yin komai ya rasa a inda Matsalar take. A Daren Umma Sakina tazo gidan Asiya a lokacin tana zaune a falo tana kallo daga ita sai d’aurin kirji kai ko dakwali babu ga kitson ya gama tsofewa ba’a gyara ba. Umma Sakina tana yin sallama ita da Maimuna suka toshe hanci saboda k’arnin falon yake ganin su ya saka ta taso a guje ta rik’e Umma Sakina tana cewa, “Umma Sakina Sannu da zuwa.” Janye ta tayi daga jikin tana k’are mata kallo tace, “Asiya ashe daman duk fad’an da nake miki akan wannan kazantar baki daina ba? Ke kinji yadda kike wari kuwa ga hammatarki kamar kan jariri?.” Asiya ta zauna tace, “Umma Sakina Ina k’ok’ari ai wallahi, kin San ina da ciki ne shiyasa ba komai nake iyawa ba.” Maimuna tace, “ina y’an aikin naki?.” “Suna nan, suna gyara gidan.” “Amma yake wannan k’arnin kamar an zubar da Kwai? K’arnin ma na rasa wanne iri yake yi.” Asiya tace, “kinji Yaya meye yake k’arni a nan dan Allah?” Sai ta tsaya da maganar ta d’aga filon kujera ta tofa yawu ta kalli Umma Sakina tace, “Cikin nan ne baya bari na yin komai wallahi.” Umma Sakina ta yamutsa fuska tace, “Ai gashi nan na gani.” Asiya ta mik’e tace, “bara na kawo muku ruwa da abinci.” Umma tayi saurin cewa, “A’a nidsi bazan ci ba, ki barshi kawai ba sai kin kawo komai ba.” Asiya ta koma ta zauna tace, “Yauwa Umma daman ina so muyi magana dake, tun fad’an nan da nace miki munyi yau kwana biyu kenan ko shigowa nan baya yi yana b’angaren matar sa, ni abun ya dame ni nayi fushin naga bai zo yana rarrashi na ba.” Maimuna tace, “A haka zai rarrashe ki kina fama da wari da d’aurin kirjin?.” “Kinga Yaya babu ruwan ki dani, in ma bana wanka ai jikina ne” ta fad’a ta murgud’a baki. Umma Sakina tace, "Shugabar marasa kunya ta Nigeria, To ya rarrsshe ki yace ya rarrashi wa kenan? matar sa ko kuma k’azama?." zata yi magana ta dakatar da ita tace, "Indai a haka zaki cigaba da zama ba rarrashi ba sake kallon ki ma bazai yi ba. Shiyasa aikin mu baya tafiya mana ashe kece kike daqile komai saboda wannan shegiyar k’azantar taki, ai ko wanne aiki sai da gyara sannan za’a samu abinda ake so.” Asiya tace, “To ni ya zanyi? Ina iya k’ok’arinw ai.” “Sai ki yi ai amma ina so ki sani a haka babu maganin da zaiyi miki aiki, domin kuwa baki da wani abun da zai yi marmarin sa, kin lalata komai kin bar komai ya tsofe kamar ba sabon aure ba. Daman nazo miki da wani wanda in zaku kwanta zaki shafa to naga babu amfani dan ko ni bazan iya zaman minti d’aya a a kusa dake ba balle kuma shi da zai jima jikin ku a had’e.” Asiya tace, “ku bani Umma zan gyara.” “Ai ko kin gyara baza ki daina wannan warin ba, wanna gashin da kika ajjiye a hammatar ki ko shi kad’ai ya isa ya saka ki wari, hammata a cike haka kamar kan taro ina gakuma na k’asa.” Asiya tace, “yanzu zanje nayi wanka sai na cire shi, ni wahala yake min ne shiyasa nake barin kayana ai shima ado ne.” Umma Sakina ta tab’e baki tace, “gashi nan, in kin gyara anyi abinda ake so kanki, in baki gyara bama kanki ke zaki cutu ki dawo gida da zaman zawarci.” Asiya ta karba tace, “Yanzu zanje nasha, Umma Sakina na meye shi?.” “Daman gaddamar da yake miki ne da Babar ki ta fad’a min na nemo naki mafita, amma naga alama babu aikin da zaiyi miki wallahi yanzu da naga yanayin ki. Haba nidai ina mamaki wallahi, in aka ce min wai yana k’aurace miki ko kuma yana miki tsaya, dan ni nasan abubuwan da nake baki ba na wasa bane, a cikin abubuwan da nake baki Wallahi akwai wanda ko kara kika ajjiye bai isa ya tsallake ba, amma sai naga babu wani cigaba ashe Matsalar daga wajan ki take.” Asiya tace, “Zan gyara ai” ta sake tofa yawu a bayan kujera Maimuna tace, “tabdijam, Yusuf yana k’ok’ari wallahi, Umma ni kam zuciya ta tashi take yi nayi waje in kin gama mu had’e na cigaba da zama amai zanyi” ta fad’a tana tashi ta fita Umma tace, “nima bazan iya zama ba ai, Ke sai anjima” ta fad’a tana tashi ta fita ba tare da ta sake kallon Asiya ba. Asiya ko a jikin ta dan ita bata ga k’azantar da ake fad’a tana da ita ba, a ganin ta tana tsafta daidai gwargwado wanka ne daman tasan wannan sai taga damar yi shima ba k’azanta bane ba ai tattalin ruwa ne. Ta tashi ta hau sama ko wankan bata yi ba ta fesa turare ta saka kaya ta sauko k’asa ta sha maganin ta nufi b’angaren Ameena. Tana shiga falon sai da ta lumshe ido taja numfashi tace, “Wai aljanu ne suke yiwa b’angaren nan turare oho.” Saman ta hau nan ma yana nan tas dashi sai dai k’ura kawai amma d’ankwali babu ta wuce falon ta hau saman da zata je d’akin sa. Tana shiga ta hange shi a zaune da kofi a hannun sa yana shan abu a ciki duk a tunanin ta lemo ne tana zuwa taga babar kwalba a kusa dashi ta kalli kwalbar ta kalle shi taga idanun sa sunyi ja sosai sai lumshe su yake yi, d’aukar kwalbar ta duba jiki ta wara ido ta ajjiye tace, “Giya kake sha?.” Sai a nan yaji muryar ta dan bai ma San tazo ba ya bud’e ido yana kallon ta ya mik’e tsaye yace, “ke ni zaki yiwa abinda kika yi ko?” Ya fad’a yana nuna kansa da yatsa. “Yusuf daman kai d’an giya ne ban sani ba?.” Cikin muryar maye yace, “keee ni kike cewa dan giya d’an Uwar ki?” Ya fad’a yana tsinke ta da mari. Tayi baya tana kallon sa da mamaki ya saka hannu a gefen sa ya d’auki belt ya nad’a hannun sa yace, “ba kince in na dake ki sai kin rama ba?, bani kika yiwa rashin kunya ba?, To rama na gani” yana fad’a ya fara dukan ta da belt d’in tana ihu tana yin baya yana saka binta ta rasa abinda zatayi sai ihu da take yi dan dukan na shigar ta sosai, a haka ta k’arasa ga k’ofa ta fita a guje tana kuka dan ta daku. #Mai daki #Book 3 #Paid #500 #Nana Haleema Book3 011 A gidan su Ameena ta ware kamar ba ita ba harkokin ta kawai take yi bata tunawa ma da Yusuf sam rayuwa take cikin farin ciki a a gidan Yayan ta mai son ta. Hakan ya yiwa Yaya Adam dad’i ganin ta saki jikin ta ta manta da rayuwar baya ta karb’i rayuwar da tazo mata ta zaman tunani, ko kad’aice kanta bata yi sai dai ka ganta tana danna waya ko tana wayar tana darıya nishad’i. Tana zaune a dak’i suna waya ita da Humaira sai dariya take yi tace, “Kice bikin naki dai yazo, wata uku ai kamar yau ne.” Daga can b’angaren tace, “Eh wallahi, ni naji dad’i ma da aka kai shi wata uku.” “Meyasa?.” “Lokacin kin fita daga idda kizo a sha shagali, dan wallahi sai kin zo.” Ameena tayi dariya tace, “Lallai ma Humaira, Umarni kike bani?.” Humaira tace, “shi nake baki, ai kema kin san Ammah baza ta yarda kice baza ki ba ko?.” Ameena tace, “nima ai bance miki bazan zo ba, me zai hana ni zuwa? In kinga ban zo ba sai rashin lafiya.” Humaira tace, “Yauwa ni daman nasan ni ta musamman ce.” Tayi dariya Humaira tace, “Zan zo ma na d’auki Zaytun tayi min Hutu.” Ameena tace, “Sai kinzo, kizo kafin ta shiga makaranta dan first term ma nake so mu shiga wallahi na saka ta a makaranta surutun ta yayi yawa gwara ta fara karatu.” Humaira tace, “Kinji wai ki saka ta a makaranta, Yaya Yusuf dai ya saka ta a makaranta ke meye naki?.” Ameena tayi murmushi tace, “nice zan sakata mana, in aka biye tashi ta kai shekara biyar ma bata fara ba.” Humaira tace, “Wai dan Allah bakya jin haushi in aka ambaci Yaya Yusuf a kusa dake?.” Ameena tace, “Haushin me kuma?.” “Akan abubuwan da yayi miki bakya jin haushin da dan Allah?. Abi mamaki yake bani sai naga in ana maganar sa bakya jin haushi sai dariya da nishadi ma da kika k’aro.” “Hmmm! Humaira kenan, ai dashi da babu duk d’aya ne a wajena yanzu, kin San Allah mantawa nake ma ji dashi a duniya, sai Zaytun tana zancen sa nake tunawa dashi.” Humaira tace, “ai gwara hakan, ya cancanci ki manta dashi din, haushi yake bani gabad’aya ko magana bana so yayi min.” Ameena tayi dariya tace, “ke dai kika sani.” “Da wata b’arauniyar matar sa.” Ameena zatayi magana sai ga Shukra y’ar Yaya Adam ta shigo tana cewa, “Munmy Kizo Inji Abba.” Ammeeena tace, “Yaya Adam yana kırana sai anjima” ta fad’a tana kashe wayar ta fita zuwa falon. Su biyu ta tarar a zaune a falo shi da wani a zaune a kusa dashi tana zuwa yace, “To ga Ameena nan.” D’ago ido mutumin yayi ya kalli Ameena suka had’a ido sai tayi murmushi domin ta san shi tun a baya abokin Yaya Adam ne sosai ma kuwa tace, “Ina wuni.” Kallon ta yake yi fuskar sa da murmushi sosai yace, “Ameena kece kika koma haka?.” Tayi dariya kawai Yaya Adam ya kalle ta yace, “Koma ciki.” Ameena ta juya ta Zaytun ta bita tana kiran Mummy. Tana barin wajan ya zare glasses d’in fuskar sa yace, “Wai dan Allah Ameenata ce wannan?.” Yaya Adam ya Harare shi yace, “na hana cewa Ameenan ka tun ba yau, amma ka kasa dainawa indai za’a zancen Ameena sai kace Ameenan ka.” “Astagarifullah ashe tana da aure, nayi mamakin ganin ta ne wallahi rabona da ita fa tun kafin tayi aure, wannan yarinyar mai kyau y’ar tace?.” Yaya Adam yace, “y’ar ta ce mana, baka ji tana cewa Mummy ba?.” Yayi murmushi mai bayyane da tsantsar haibar sa yace, “Gaskiya duniya na gudu sosai, har Ameena ta shekara hud’u da aure ko nace biyar ma. Allah ya cigaba da basu zaman Lafiya ya raya abinda aka Haifa.” Yaya Adam yace, “Amin, amma basa tare da mijin ya sake ta.” A firgice Al’ameen yace, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Yarinya k’arama kamar Ameena ace a sake ta?. Adam yaushe hakan ta faru?.” Yaya Adam yace, “wallahi, kwata-kwata bata fi sati uku a gidan nan zuwa hudu, dan har yanzu bata gama iddah ba.” “Kace kwanan ne ma.” “Eh wallahi.” “to Allah ya daidaita su yasa ta koma d’akin ta shine rufin asiri. Yarinya kamar wannan ace tana zaman gıda abun ai babu dad’i.” “Ta bar wannan mijin nata, in kaga na bari ta koma to bani da rai.” “Amma meyasa? Ka sani ko tana son sa?, ka sani k akwai wani rabon a tsakanin su?. Ka daina fad’ar haka in lokacin mutuwar auren baiyi ba zata koma.” Ya kalle shi yace, “baza ka gane ba ai shiyasa, amma da zan warware maka komai da kace tayi zaman ta ta samu wani mijin tayi auren ta. To bazan fad’a ba.” Jin abinda Adam yace sai yayi dariya kad’an yace, “kar ka fad’a nima bance ka fad’aba ai, Allah yasa hakan ya zaman mata alkhairi. In kuma daman haka Alalh ya shirya mana nida ita to. Kasan babu ruwan Allah shiyasa ya baka damar hana ni ita a waccan lokacin, sai kaga a wannan lokacin ka kasa komai har na same ta.” Yaya Adam yayi tsaki kawai baice komai ba dan yasan daman Al’ameen sai yayi wannan zancen ganin hakan sai Al’ameen yayi dariya suka fara tattaunawa akan abinda ya zaunar dasu a wajan. Tunda yamma tayi akace ga dangin wanda zasu kawo kud’in Rukayya sun zo ta kasa sukuni gabad’aya, ta kasa zaman d’aki sai kai kawo kawai take yi ta kuma kasa gasgata abun ta kasa tantance yanayin ta farin ciki ne ko akasin sa iya kanta bata sani ba. Umma ce ta shigo ganin tana ta zagaye ta kasa zama ya saka tace, “Rukayya!.” Jin kiran ta da Umma tayi ya saka ta jiyo ta kalli Umman tace, “zagayen me kike yi haka kika kasa zama?.” Tayi shiru batayi magana ba Umma tace, “ba ke kika bawa Baban ku zab’i ba?.” Ta d’aga kai alamun eh tace, “Meyasa to kike tantama akan zab’in nasa? Ko kuma akwai Wanda kike so a cikin su?.” Rukayya tace, “A’a Umma ba haka bane, na kasa banbance yanayin da nake ciki ne shiyasa na kasa sukuni.” Umma tayi dariya tace, “ki kwantar da hankalin ki kawai, ki jira su tafi na tabbatar zaki farin ciki sosai da zab’in mahaifin ki.” Umma har ta yi gaba zata fita Rukayya tace, “Umma!.” Umma ta juyo tana kallon ta tace, “Wa Baba ya zab’ar min dan Allah?.” Umma tayi dariya tace, “ki jira bak’i su tafi za’a fad’a miki waye a cikin su.” Zama tayi a gefen gadon bayan Umma ta fita Zuhra ta shigo tana kallon ta tare da fad’in, “Yaya wai ya na ganki ba’a nutse ba?.” “Zuhra wallahi gabana fad’uwa yake ban San meyasa ba.” “To Yaya meye na fad’uwar gaban ke da zaki yi farin ciki?.” “Na kasa tantance yanayi na wallahi.” “Zaki tantance in Baba yace Kizo.” Tana nan zaune har akayi kiran sallar magriba a lokacin Baba ya fito ya raka bak’in waje suka tafi bai dawo gida ba ya wuce masallaci yayi sallah sannan ya dawo gida duk wanda ya ganshi yasan yana cikin farin ciki sosai daga kallon fuskar sa zaka gane hakan. Sai murmushi yake tun a hanya yake ta basa yara sadakar y’an chanjin da suke aljihun sa yara sai murna suke yi. Yana shiga gida ya kira Umma ta jima a wajan sa sannan aka kira Rukayya ta shiga gaban ta yana fad’uwa ko kallon su ta kasa yi, waje ta samu ta zauna Baba ya kalle ta yace, “Rukayya kina ya jiran tsammani ko?.” Ta sunkuyar da kai tana murmushi shima yayi murmushi yace, “kar ki damu alkhairi ne a baibaiye dake Rukayya, alkhairi shine ya kai kinga wannan lokacin.” Bata ce komai ba ya mik’a mata kud’i yace, “Karb’i wannan.” Rukayya ta kalli abinda yake mik’a mata taga kud’i ne zasu yi dubu d’ari ta karb’a Baba yace, “kud’in sadakin kine Rukayya.” Gaban ta ya yanke ya fad’i ta kalli Umma taga sai murmushi yake tana goge hawaye da alama na farin ciki ne ta sauke kai k’asa Baba ya sake yin murmushi yace, “nasan mun saka zuciyar ki a rud’ani ko?.” Bata ce komai ba Baba yace, “farin ciki da nishad’in da ya cika zuciyar mu, kowa farin cikin ganin d’an uwan sa matsayin siriki ya saka aka kasa b’oye wannan farın cikin sai da aka karb’i sadakin ki a matsayin matar aure, shaidu sun shaida d’aurin auren ki a d’azu Rukayya ga goro da alawa. Mahaifin k’awar ki Fiddausi shine ya bada sakadin gabad’aya naira dubu d’ari.” Dam dam dam gaban Rukayya yake bugawa ta d’ago ta kalli Baba suka had’a ido sai yayi murmushi yace, “Kinga lokacin ko Rukayya? Lokacin da kike fad’awa Umman ki kice Umma lokaci ne in lokacin aurena yazo zanyi amma bata ganewa, yau gashi da lokacin yazo basu tafi ba sai da aka d’aura auren ku. Zaman ki a gidan nan ya k’are, zaman ki matsayin wacce babu aure shima ya wuce yanzu matar aure kike Allah ya rubuta baza ki kai gobe babu igiyar aure a kanki na. Kamar mutuwa ce kiji ana cewa haka ta shiga d’aki lafiya lau amma sai gawar ta aka fito da ita saboda lokacin zaman ta a duniya ya k’are lokacin na komawar ta ga Allah yayi, koda ciwo ko babu ciwo sai anje. To haka auren ma; ban tabbatar da hakan ba sai yanzu, da lokacin auren naki yayi gashi bamu shirya ba ba zato babu tsammani anyi auren ba tare da dukkan mu munyi tunanin hakan zai faru ba. Wato in akace ka barwa Allah lamarin ka wallahi baza ka tab’a dana sani ba, in akace kana addu’a Allah ya zama maka na gari kuma mafi alkhairi wallahi baza ka gushe ba sai kaga alkhairin da zai same ka.” Baba ya sake cewa, “Rukayya hak’urin da kika yi, da zab’in da kika barwa Allah, da kame kanki da kika yi a gida kika tsare mutuncin ki gaba da baya Allah bazai bari ki wulak’anta ba duniya da lahira. Kin karb’i k’addara kin jure duk wani abu daga wajan mahaifiyar ki da y’an uwan ki da k’awayen ki dama mutanen Unguwa, kin kawar da kai daga duk wata magana da ake miki, kin jure hanaki aiki da karatu da nayi kin zauna a gida har aka aurar da k’anwar ki aka kawo kudin kanwar ki ta biyu amma a fuska baki nuna bak’in ciki ba sai dai kice Allah ya sanya alkhairi kina farin ciki kina murna. Taya Allah zai bari ki tozarta Rukayya? Addu’ar da kike yi itace ya canja k’addarar ki Allah ya fito miki da miji mai nagarta ya aura miki shi a lokacin kad’an wanda baki yi tunanin hakan ba.” Kuka Rukayya take yi sosai wanda ake jin sautin sa sosai a falon Baba yace, “ba kuka zakiyi ba, ki gode Allah Rukayya yayi miki abinda bai yiwa sauran mata ba yayi miki zab’in da ina tabbatar da baza ki yi dana sani ba. Lokacin yazo ko nace yama wuce daman lokaci baya jira sai dai a jira shi, ke kin jira shi gashi da yazo sai yazo da gaggawa akayi komai aka gama cikin hukuncin Allah.” Kuka take mai sauti Umma kanta kuka take yi domin kuwa taga kalmar LOKACI NE da Rukayya take yawan fad’a mata a yanzu taga lokacin da take cewa zai zo amma bata san ko yaushe ba gashi yazo a lokacin da dukkan basu shirya ba sannan ba suyi tunanin zai zo da sauri haka ba. Baba yace, “A cikin kwanakin nan za’a yi komai na bikin ki ki tare a gidan ki. Da Muna cewa zamu had’a auren ku dana Zuhra ashe ke lokaci tashin naki yazo na Zuhra bai zo ba kuma lokaci baya jira.” Ya kalli Rukayya yace, “ki gode Allah, kije ki yi sujjjadar godiya ki godewa Allah dan ya yi miki ni’imar da bai yiwa sauran mata ba da yawa ba a duniya, yayi miki zab’in da baza Kiyi kuka ba koda nan gaba. Tunda kika ce kin bashi zab’i bazai miki zab’in da zaki yi dana sani ba. Shi ya halicce ki komai na rayuwar ki shine ya tsara, wannan auren naki ba yana daga cikin hukuncin sa, shi zaki godewa ba kuka ba Rukayya.” Idanun ya ta goge tana Jan numfashi Baba yace, “nasan kina ta tunain waye mijin naki ko?.” Yayi murmushi kad’an yace, “kar ki damu, kije ki shirya an jima mijin ki zai zo ku gaisa ku tsayar da lokacin da kuke ganin kun shirya zaku tare. Tashi kije.” Jikin ta a sanyaye ta mik’e zata fita sai ta koma ta zauna tace, “Na gode Baba, Allah ya saka maka da gidan aljanna. Allah ya azurta sauran mata da mahaifi kamar ka Baba, bani da abinda zance sai dai nace Allah yasa zaman kabari yafi maka zaman duniya dad’i, Allah ya da ranka yasa ka cika da imani.” Umma tana amsawa da Amin tana hawaye Rukayya ta tashi ya fita jikin ta a sanyaye sosai. Farin ciki ya hana Rukayya sukuni kuka take yi tana sallar i’sha tana godewa Allah tana murna da ta kasance mai bautawa Allah, tana murna da ta kasance mai mik’a masa lamarin ta, ta gode masa da ya saka mata imanin zai amsa rok’on ta bata tab’a ji a zuciyar ta baya Karb’ar kukan ya ba, gashi ya karb’i kukan ta ya amsa ya kuma biya mata a lokacin da batayi tunanin hakan ba. Ta jima a sujjada tana kuka tana mik’a godiya ga Allah sannan tayi sallama lokacin Zuhra ta shigo ita kuma ta mik’e tsaye Zuhra cikin murna ta rungume ta tana kuka itama tana kuka. Zuhra tace, “ki gode Allah Yaya, Allah ya share miki hawayen ki.” Kuka take yi sosai kafin ta raba jikin ta dana Zuhra ta k’arasa wajan jakar ta ta d’auko kud’i ta bawa Zuhra tace, “dan Allah kiyi sadaka yanzun nan, ki bawa wanda kika san zai y farin ciki a daren nan Zuhra.” Zuhra ta Karb’a ta fita ita kuma ta zauna a gefen gadon tana jin abun kamar a mafarki wai itama a yanzu matar aure ce. Tana zaune so take ya tantance yanayin ta amma ta kasa ita dai tasan tana farin ciki a zuciyar ta amma kuma dai taji kamar ba Rukayya ba Umma ta shigo ta zauna a kusa da ita tace, “Rukayya!.” Ta kalli Umma jin sunan da ta kira ya tabbatar mata itace dai Rukayya tace, “Na’am.” Ta sauke numfashi tace, “Mijin ki yazo yana jiran ki a setrroom din Baban ku.” Gaban ta ya fad’i ta rik’e hannun Umma tace, “Gabana fad’uwa yake Umma.” Umma ta rik’e hannun ta tace, “Nima kaina haka nake ji balle ke Rukayya, fad’uwar gaban ta alkhairi ce a wannan lokacin. Tashi kije kar a barshi yana jiran ki.” “Umma ji nake kamar bazan iya zuwa ba.” “Zaki iya, tashi kije Rukayya lokacin da kika jima kina jira ne yazo yanzu, taya zaki ce baza ki iya ba? Mijin ki ne yanzu ba mai neman auren ki ba, tashi maza kije in kin dawo sai muyi magana.” A sanyaye ta mik’e ta fita daga d’akin cikin hijjabin da ta idar da sallah ta nufi d’akin Baba gaban ta yana cigaba da fad’uwa sosai ba kad’an ba. Kafin ta shiga sai da ta tsaya ta dinga jawo duk addu’ar da tazo bakin ta kamar wacce tayi laifi take tsoron hukunci, “Ki shiga mana Rukayya.” Muryar Baba taji a bayan ta hakan ya saka ta shiga babu yadda zatayi ganin yana tsaye yana kallon ta, kanta yana k’asa k’afar ta kawai take kallo tana shiga ciki. Tsayawa tayi cak ba tare da ta cigaba da tafiyar ba taji anyi murmushi mai sauti ance, “k’araso mana Rukayya, ko nazo nazo na k’araso dake ne?.” #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid #500 Book3 012 Jin muryar wanda bata kawo ba a zuciyar ta ba ya saka gaban ya sake fad’uwa ta d’ago kai ta kalli inda yake yana zaune a cikin manyan kaya shadda fara kal sai kyalli take yi kansa da hula annurin fuskar sa ya bayyana a zahiri kana kallon sa zaka san yana cikin farin ciki sosoi sai murmushi yake yi yana kallon ta tare d’aga mata gira guda d’aya cikin salo na nuna soyayya da shaik’in da yake ciki a wannan lokaci. Cak ta tsaya kamar an tsayar da ita bata yi gaba ba sannan bata yi baya ba kallon sa kawai take zuciyar ta na bugawa sosai, kamar an d’aure mata k’afa haka take ji shiyasa ta kasa motsawa sai kallo kawai, ganin ta tsaya ba gaba babu baya ya saka shi ya taso yazo inda yake tsaye yana kallon ta itama kallon nasa take yi yace, “Ya kika kasa k’arasowa ?.” Yadda yayi maganar a hankali kuma yana kallon idanun ta ya saka ta sauke kai k’asa ya saka hannu ya d’ago da fuskar ta sai ya rufe idanun ta yayi murmushi ya saki fuskar ya koma ya zauna yace, “Ki zauna Rukayya.” A hankali ta zauna ta sunkuyar da kanta k’asa bata ce komai ba tana share hawayen tana mamakin wai ita dashi yanzu mata da miji ne, akwai igiyar auren sa guda uku a kanta sai taji wani abu na yawo a jikin ta shiyasa ta kasa banbance a wanne yanayi take ciki, yace, “Kinga lokaci ko Rukayya? Yazo mana a lokacin da ba mu yi zato ba daga ni har ke.” Shiru tayi ta kasa cewa komai har lokacin ta kasa banbance yanayin ta kamar a mafarki haka take ganin komai da yake faruwa ba gaskiya bane. Ya gyara zaman sa yace, “Na gode da kika amince dani kika bani amanar rayuwar ki, na gode da kika zab’e ni a matsayin mijin da zaki zauna dashi na har abada, na gode da kika zab’e ni a matsayin abokin rayuwar ki. Ni kuma nayi miki alqawarin bazan bari ki yi hawayen bak’in ciki ba sai dai hawayen farin ciki, bazan ce bazan b’ata miki rai ba saboda dan adam ajizi ne yau da gobe sai Allah amma nayi alqawarin farin cikin da zakiyi sai ya ninka akasin sa a zamana dake. Ban San me kike ji a zuciyar ki ba a yanzu amma ko ma meye ki ajjiye shi a gefe, ki manta da batun Ibrahim din baya da kika sani ki canja masa suna ya koma Mu’azzam a yanzu ina tabbatar miki dashi zaki zauna bada Ibrahim din da kike tunani nara tushe a kansa ba. Rukayya!” Ya fad’a Tana kallon ta. D’ago kai tayi ta kalle shi idanun ta sunyi ja haka fuskar ta yace, “Subahanallahi kukan na meye haka?.” Ta mayar da kanta k’asa bata ce komai ba yace, “Rukayya ana kukan farin ciki amma naki bai yi kama dana farin ciki ba, in akwai damuwa ki fad’a min a yanzu babu wanda kike dashi da zaki fad’awa abinda yake zuciyar ki sai ni; saboda ni ne mijin ki a yanzu.” Kalmar mijin ki da ya fad’a ya saka ta lumshe idanu har lokacin ta kasa tabbatarwa da gaske ne ba karya ba. Sai a sananan tace, “Babu komai.” “Ban amince babu ba, nasan kuma meye yake zuciyar ki.” Ta d’ago ta kalle shi yace, “Eh kin san nasan abinda yake ranki a yanzu, na kuma fad’a miki ni kaina bana son tuna abinda ya wuce amma ke ban San meyasa kike son barin sa a zuciyar ki ba. Bana son abinda zai saka ki a damuwa ko kusa, zan iya yin yak’i da ko meye dan nan na Kore shi daga zuciyar ki farin ciki ya maye gurbin sa. Babu Wanda zai canja abinda Allah ya rubuta, Allah ya rubuta zai jinkirta miki aure har sai Ibrahim yayi aure ya haihu yaron ya girma ya rabu da matar sannan zai aure ki, babu wanda ya isa ya canja wannan k’addarar saboda wani baya auran matar wani, ni ne dai mijin ki bayan ni babu wanda zai aure ki tunda ni Allah ya zana a cikin k’addarar ki. To meye kike damun kanki bayan Allah ne ya rubuto miki? Meye na tunanin wani abu da ya riga ya wuce Rukayya?.” Ya taso ya dawo kujerar kusa da ita ya karkace yana kallon ta yace, “babu wanda zai goge abinda Allah ya rubuta koda iska ce ko ruwan sama, ni ne a zanen k’addarar ki nima kece a tawa kaddarar. Rabuwa ta da wacce yake zuciyar ki ba komai bane face daman hakan Allah ya tsara dole sai ta bar gidan sannan zan aure ki, inda an samu jinkirin rabuwar har yanzu da ina tabbatar miki da Alalh zai iya Karb’ar rayuwar ta saboda lokacin ki ya shiga dole sai na aure ki shi kuma lokaci baya jira Rukayya.” Hannun ta ya kalla ta had’e su waje d’aya tana ta juya su sai ya rik’e su duka biyun ta kalle shi shima ya kalle ta yace, “Ki goge komai daga zuciyar ki ki fuskanci sabuwar rayuwar da tazo miki a wannan lokacin, indai ni ne baza ki tab’a samun matsala dani ba in sha Allah.” Hannun ta ta zame daga nasa ta girgiza kai alamun gamsuwa yace, “magana zaki yi min.” Tace, “Haka ne abinda kace, zanyi in sha Allah.” “Yauwa ko Kefa, sai ki yi dariya na gani.” Bata yi dariyar ba ta sunkuya tana kallon fuskar ta yace, “Kiyi dariya na gani.” Murmushin yaqe tayi yace, “wannan murmushin bai kai zuciya ba.” Bata san lokacin da murmushi ya bayyana akan fuskar ta ba sosai jin abinda yace shima yayi ya tashi ya koma wajan sa kafin yace, “naga alama baki da nutsuwa sosai a yanzu” sai ya mik’e yace, “zan tafi ki samu ki yi bacci ki huta sosai, in Allah ya kaimu gobe zamu tattauna.” Tashi itama tayi tace, “To sai da safe, a gaida Hajiya.” Yazo kusa da ita da niyar wucewa yace, “Hajiya zata ji in sha Allah. Shikenan abinda zaki ce?.” Sai ta kalle shi suka had’a ido ta sauke ido k’asa domin kwarjini yake yi mata sosai musamman yanzu da fuskar sa take a sake sosai ya sake cewa, “tambayar ki nake, shikenan abinda zaki ce?.” Ta d’aga kai alamun eh yayi murmushi yace, “kin tabbatar?.” Ta sake d’aga kai alamun eh yayi dariya mai sauti yace, “shikenan ki kwana Lafiya” ya fad’a yana niyar fita tabi bayan sa da kallo sai ya jiyo ya kama ta tana kallon sa tayi saurin kawar da kai yayi dariya yace, “Na kama ki kuma Rakiya, ni nasan akwai abinda yake ranki amma a na bar miki bashi zaki fad’a min nan gaba.” Murmushi ta samu kanta da yi a lokacin ya fita daga d’akin ta sauke numfashi tana kallon sama kamar ne duba wani abun kafin ta fito ta dawo falo ta tarar da Umma a zaune tana ta buga waya tana sanar da y’an uwa an d’aura auren Rukayya, kai da ka kalle ta kasan cikin farin ciki take yin wayar. Zama Rukayya tayi tana kallon Umman da murmushi domin yanzu ta tabbatar da maganar Ameena da take ce mata Umma ta fita damuwa da tayi aure kawai maganar mutane ce ta saka take takura mata amma sai tafi kowa farin ciki in hakan ta kasance, sai gashi ta ga hakan a bayyane akn fuskar Umma. Umma ta kalle ta tace, “Rukayya ya naga kamar bakya farin ciki?, ko Umar kika so Abban ki ya zab’a miki ba Ibrahim ba?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “kawai ina jin abun ne kamar a mafarki yake faruwa Umma, wai nima a yanzu matar aure ce ina da miji ko yanzu ya mutu sai nayi masa takaba. Wallahi Umma sai naji kamar ba a duniyar nake ba, sai naji kamar ba nice Rukayya ba wata ce daban aka canja.” Umma tace, “Lokacin da kike ta fad’a min kenan koda yaushe Rukayya, Gashi yazo da yake lokacin yazo baza ki sake kwana ba tare da igiya uku a kanki ba sai gashi a yau aka d’aura auren ki ba tare an shirya wa hakan.” Rukayya tace, “Umma ashe daman zaman jiran Ibrahim nake yayi aure ya haihu ya saki Fiddausi sannan ya aure ni? Ashe daman shine ya kawo jinkirin? Ashe saboda Allah ya rubuta shine mijina ba wani ba shiyasa qalubale Kala-kala suka dinga faruwa har sai da akazo gab’ar da muke ciki a yanzu. Allah gwanin hikima in ya tsara babu wanda zai canja sai dai in shine yaso Hakan, da gaske ni matar Ibrahim ce tsohon mijin Fiddausi wanda suka rabu, ashe duk zaman jiran da nake yi a gidan nan shi nake jira, Allah kenan” ta fad’a tana girgiza kanta imani da tsoron wanda ya halicce ta suna sake shiga zuciyar ta sosai. Umma tace, “Allah al-Hakeem kenan gwanin hikima da tsara abubuwan da zai faru a rayuwar bayin sa. Wallahi sai yanzu na amince da duk wani abu bai isa ya faru ba tare da lokaci yayi ba, lokacin yayi shiyasa babu jira akayi komai aka gama ba tare da shiri ba, kamar yadda Baban ku yace in mutuwa ce ma haka za’a tafi ba tare da an shirya ba gashi auren ki ma ya nuna min lokaci ne sai kuma yanzu yazo. Dan nice naga ishara dan keda mahaifin ki kun amince da hakan nice na kasa amincewa. Rukayya badan na tsane ki ba, sai dan ina so naga kinyi aure kamar yadda sa’anin ki sukayi, kowa a y’an uwa tambayar sa yaushe Rukayya zatayi aure?, in naga wanda shekarun ku suke d’aya da yara d’aya ko biyu wallahi sai naji babu dad’i a zuciyata. Yanzu da nake waya ina sanar da mutane auren ki kowa mamaki yake harda masu cewa zasu zo gobe gidan nan, wallahi Rukayya in kin fini farin ciki a auren nan naki to da kad’an ne, amma in da ana shiga zuciya zan bada dama ki shiga tawa kiga adadin murnar da nake yi. Addu’a da mik’a lamarin ki ga Allah da kika yi sai yayi miki zab’i mai kyau dan na tabbatar Ibrahim miji na gari ne a wajan ki.” Rukayya ta girgiza kai tana hawaye tace, “Haka ne Umma, nima na amince da hakan wallahi. Tunda nasan ina addu’a ba dare babu rana na kuma bawa Allah dukkan lamarina na kuma bar masa zab’i na tabbata shine ya zab’a min Ibrahim, zab’in Allah shine zab’i dan haka na karb’i abun hannu biyu Umma.” Umma tace, “Haka nake so naji daman daga bakin ki, Nima na tabbatar miki da baza Kiyi kukan bak’in ciki ba Rukayya, in sha Allah farin cikin da zaki yi sai ya ninka wanda kike yi a yanzu, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman Lafiya yasa babu saki ko yaji a zamantakewar auren ku.” A hankali ta amsa da amin ta tashi ta shiga cikin d’aki ta d’auki waya da niyar ta sanawar dasu Ameena abinda yake faruwa. Tunda Yusuf ya shiga wajan Asiya da safe ya same ta a zaune bakin ta a kumbure alamun dukan da yayi mata jiya ne ya jawo hakan ya zauna yana kallon ta jiki a sanyaye kafin yayi magana tace, “Ashe daman kana shan giya ban sani ba?.” Ya runtse ido yana jin zafin kalmar yana shan giya har zuciyar sa, Allah ya sani yana so ya daina amma in ransa ya b’aci in bai sha ba baya jin dad’i. Ya gyara zama yace, “Asiya tsautsayi ne ya kaini ga hakan amma ba halina bane, Kiyi hak’uri da abinda nayi miki a jiya ban san hakan ya faru ba.” “Kenan ka daki banza ko? Ka shayu ka dake ni kana tunanin ka yiwa banza ko me?.” “Shiyasa nazo na baki hakuri nasan ban kyauta ba.” “Wallahi bazan hak’ura ba sai na sanar da iyayen ka, akan ne zaka dinga dukana ai ba dan duka aka kawo maka ni ba. Sannan daman har giya kake sha kuma nake zaune dakai ban sani ba?, ai wallahi bazan iya zama da dan giya ba sai maganar nan taje wajan iyayena, ko ka daina shan giya ko kuma kasan abinda za’a yi.” Yusuf yace, “Haba Asiya hak’uri fa nake baki meyasa baza ki iya b’oye sirrin mijin ki ba?.” Asiya ta kalle shi tace, “na b’oye ka sake sha nan gaba kenan ko? In kaje ka sha tafi k’arfin kanka kazo ka sake dukana ga jaka an kawo maka har gida, wallahi bazan iya ba.” Yusuf yace, “Meyasa kike haka ne? A kaf duniya daga ke sai Ameena ne kuka san da maganar nan, dan Allah ki fad’awa kowa nayi alqawarin zan daina In sha Allah.” “Ita Ameena din sau nawa kace mata zaka daina? Ka daina din?. Kaga Yusuf ni wallahi ba Ameena bace bazan d’auki abinda ta d’auka a kanka ba, in manya suka shiga maganar ko baka so ai ka daina.” Yusuf ya dafe kai babban tashin hankalin sa bai wuce iyayen sa su san da maganar yana shan giya ba yace, “Dan Allah kar ki fad’awa kowa.” Ta kalle shi tace, “Amma ka iya dukana bayan kasan ina da k’aramin ciki.” “Na karb’i laifin nawa, Kiyi hak’uri.” “Zanyi hakuri amma sai ka bani wani abun.” Da sauri yace, “Kamar ne kenan kike so?.” “Zan rike sirrin bazan fad’awa kowa ba tunda kace baza ka sake ba, amma sai ka bani naira miliyan d’aya.” Da mamaki yake kallon ta jin abinda tace yace, “miliyan d’aya? Yanzu dan zaki rufawa mijin ki asiri sai ya biya ki?, baza ki iya b’oye sirrin sa ba sai ya baki wani abun?. Kina da hankali kuwa?.” Ta Harare shi ta ce, “bani da hankali, ka bar kayan ka ni kuma wallahi sai yau Ammah tasan da labarin nan” ta fad’a tana niyar tashi zata bar wajan yayi saurin cewa, “shikenan zan baki, amma miliyan d’aya yayi yawa ai ba hauka ake ba, zan baki dubu d’ari.” Banzan kallo tayi masa tace, “Almajira ce ni da zaka bani dubu d’ari? Ko ni yanzu na kai matakin kyautar ta, in zaka bada dubu d’ari bakwai ka bayar in baza ka bayar ba gidan Ammah kai tsaye.” Yusuf ya lumshe idanun sa ya rasa wacce mata Allah ya had’a shi da ita ace matar sa baza ta iya rufa masa asiri ba sai ya biya ta, ya kalle ta yana jin d’aci a zuciyar sa kafin yayi magana tace, “Wallahi bazan rage ba, in zaka bayar kanka in baza ka bayar ba duk bai shafe ni ba.” Ya zaiyi baya so Ammah tasan labarin dan Allah kad’ai yasan tashin hankalin da zata shiga hakan ya saka yace, “shikenan zan tura miki, amma koda wasa bana so wani ya samu labarin nan.” Tayi murmushi sannan ta jiyo ta kalle shi tace, “hannun kuturu da makaho, tura min sannan nayi nawa alqawarin.” Waya ya d’auka yana dannawa kafin ya hasko mata wayar yace, “Gashi na saka miki.” Ta kalla taga kud’in sun shiga tace, “Nayi alqawarin babu wanda zai sani, amma wallahi ka sake sha ka dake ni sai na fad’a in baka so na fad’a kuma naira miliyan biyu, in kuma ba haka ba wallahi Ammah da Abbah sai sun San kana shan giya.” “Ke baki iya rufin asiri ba a rayuwar ki?.” “Ban iya ba, kud’i kawai na sani.” “Wai ya akayi na d’auko ki ne?.” Da sauri ta kalle shi tace, “me kace?.” Baice komai komai ba ta kalle shi tace, “koma me kace zama da Asiya dole, kuma dole ayi abinda nake so in ba haka ba aga ba daidai ba”tana fad’a ta barin wajan ya bita da kallo ya sauke numfashi mai nauyi yana jin sa kamar ya rasa wani abu mai mahimmaci a tare dashi. #Book3 Book3 013 A zaune suke a babban falo kai da ka kalle su kasan mayan mutane ne wanda suka ajjiye naira suke kan tara ta domin shigar su kawai zata tabbatar maka da ko wannen su ba k’aramin mutum bane ba. Suna zaune da alama tattaunawa ake mai mahimmaci dan kowa ya bada hankalin sa ga abinda ake yi Alhaji Bello yace, "ni ban gane abinda Boss yake nufi bafa, wa yake nufi a cikin mu." D'aya daga  cikin su yace, "kai yake nufi fa, Taya zaka ce baka gane ba bayan kaine zuwan k’arshe New York da matar ka? Mu ai sai dai muyi maka murna harka ta sauka.” Wanda yake zaune kusa da Alhaji Bello yace, "Shine abinda na gani, ita ya gani yace yana so a karo na biyu a bashi ita ta sati d’aya kasan akwai ribar da zaka samu ai, nawa ka samu da wacce take can wajan sa?, kawai ka fara murna mu ma kuma a cire mana namu in an samu kar a manta damu.” Alhaji Bello yace, "ni bawai bana son kaita bane tana da taurin kai bazata amince ba, kasan kuma shi bature ne bazai iya mata dole ba." "Sanin da kayi masa, wallahi yanzu da k’arfi shima sai yayi abinda yake so, kawai ka d’auke ta gobe a kaita shine kawai. Dan wannan ba k’aramin business bane yazo mana.” Alhaji Bello yaja numfashi d’ayan ya kalle shi yace, "Ko kishi kake?." Ya kalle shi yayi dariya yace, "Kai kasan babu macen da zanyi kishi a yanzu, kawai dai ina jin babu dad’i ne in na tuna wacece ita." Mutane biyun suka mik’e d'aya yace, "haka zaka yi hak’uri ka San dabara da zaka yi ka a kaita, kar ka bari lokaci ya wuce in ba haka ba zaka rasa babbar damar da ka samu.” Alhaji Bello ya mik’e yace, "nasan ma abinda zanyi zata je kuma koda bata so." Sukayi dariya suka d’aya yace, “Ai dole ma taje, ta isa tayi mana asarar wannan damar da muka samu.” Tare suka fito ya hau mota ya nufi gida dan dole ma Fiddausi ta amince ya kai ta New York dan ya samu kudi. A gate na biyu na cikin gidan da ya hango Fiddausi da Naja’atu da kuma ma'aikatan wajan ana fad’a akan sai ta fita su kuma sun hana, Naja’atu tana janta baya tana sake kwacewa lallai sai ta fita. Kana ganin ta kasan akwai fitar hankali a tare da ita komai yin sa take ba a daidai ba kamar mahaukaciya. ganin motar sa duk sai suka bar wajan tayi sufa zata fita zuwa gate na gaba mai gadin wannan gate d’in ya d’auke ta cak yayi baya da ita a lokacin Alhajin ya faka mota ya fito yana kallon komai. "Wallahi sai na tafi na bar gidan nan, ku barni na tafi dan Allah" ta zube a wajan tana kuka sosai Alhaji balle ya k'araso yana kallon ta. Naja’atu ta tsuguna kusa da ita tace, “ki tashi mu koma ciki Fiddausi baza su barki kije ko ina ba wallahi.” “Babu inda zanje sai na bar gidan nan yau.” Alhaji ya k’araso inda take yace, "kina so kije gida ko?." Bata amsa ba sannan bata kalle shi ba yace, "in kin shirya anjima kad’an zan saka a kai ki a jirgi, in kina so ki taso ki biyo ni ki shiga gida in bakya so ki ta zama wallahi ko gate na gaba baza su barki kije ba.." Ta d’ago tana kallon shi jikin ta har rawa yake yitace, "da gaske zan tafi?." "Zaki tafi na tabbatar miki." Naja’atu tace, “kar kije Fiddausi kar ki bishi wata yaudarar ya shirya miki wallahi bazai kai ki gıda ba, kar ki shiga motar nan.” Fiddausi ta kalle shi dan a tsorace take dashi kafin tayi magana yace, “wallahi babu abinda zan miki jirgi zamu shiga na kai ki har gida, ban tab’a miki alqawari ba ko? To nayi alqawarin babu abinda zanyi miki.” Kallon Naja’atu tayi ta girgiza mata kai tace, “kar kije bai san mahimmancin alqawari ba, bai San meye rantsuwa ba kika bishi kin yiwa kanki.” Ya kalli Fiddausi yace, “kar ki amince da abinda take fad’a miki, naga ban kyauta miki ba na d’auko ki daga gidan ki ga d’anki bai kamata nayi haka ba shiyasa zan kai ki gida, kar ki amince da abinda take cewa ki shiga mota muje in ba haka ba baki da damar zuwa ko ina.” Kallon Naja’atu tayi tana hawaye itama hawaye take tace, “Zanje Naja’atu gida za’a kai ni.” A guje ta tashi ga shiga cikin gidan tun kafin ya shiga ta riga shi yayi dariya ya kalli Naja’atu yace, “ki koma malama.” “Sai na kashe ka” ta fad’a tana barın wajan da sauri yayi dariya ya d'auki waya ya saka a kunne yace, "A shirya jirgin yanzu gamu nan zamu tawo da ita" fad'a ya yanke wayar yabi bayan ta ya shiga suka shiga cikin gidsn. A falon ta ta tsaya daga nesa dashi kana kallon sa kasan bata da lafiya ta rame a lokaci d'aya kamar zuk’e ta tace, "Da gaske zaka kaini gidan mu?." Ya matso kusa da ita tayi saurin yin baya kamar zata fad’i tace, "Kar ka tab'a ni, bana so ka tab'a ni ka fad’a min gaskiya zaka kaini gidan mu?" Sai ta fara kuka hawaye na sauka daga idanun ta wani yana bin wani tana kallon sa. Yayi murmushi yace, "inda bazan kai ki ba ai bazan miki magana ba, ke kin san ban tab’a yi miki irin haka ba, kije ki shirya kayan ki." Fiddausi jikin ta har rawa yake yi tace, "basai na canja kaya ba zan tafi a haka basai na d’auki komai ba." Yayi dariya ya kalli ta yace, "muje to" ya fad'a yana yin gaba ta biyo bayan sa jikin ta har rawa yake yi sosai zuciyar ta na fad’a mata kar ta bishi amma ta kasa sarrafa kanta domin idanun ta a rufe yake gida kawai take son zuwa. Mota suka shiga gabad'aya a tsorace take dashi shi kuwa farin ciki yake a zuciyar sa sosai  zai samu ninkin kudin da ya samu a lokacin da ya gabata, nan da nan suka isa airport da yake a private jet zasu je babu zancen ticket suna sauka jirgi suka hau ya tashi zuwa k’asar America. Tafiya ake yi sama da awa d'aya a sannan ta kalle shi tace, "wai har yanzu bamu shiga kano ba?.” Kallon ta yayi yana dariya a zuciyar sa yace, "kiyi bacci ki tashi mu kusa zuwa." Bata son yin magana dashi hakan ya saka ta yin shiru amma a zuciyar ta mamaki take har yanzu basu zo kano ba bayan tasan tafiyar Abuja zuwa kano baya wuce mintina arba’in amma ace har yanzu kusan awa biyu basu shiga Kano ba. Bacci take son yi amma tsoron sa take ji sosai baza ta iya ba gani tane in tayi bacci zai sake yi mata wani abun shiyasa ta kasa baccin duk motsin sa tana gani bai kuma yi k’ok’arin koda rik’e hannun ta ba. Idanun ta biyu har jirgi ya fara sauka suka fito daga ciki tana bin airport din da kallo ganin kamar fa ba ta Kano bace amma batayi magana ba dan bata son magana dashi kawai ta biyo shi saboda rashin mafita. babbar mota ce bak’a tazo d'aukar su ya shiga amma Fiddausi tak’i shiga sai kallon sa da take yi. Yace, "ki shigo muje." Kai take girgizawa tana ja baya yace, "in baki shigo ba babu inda zaki iya zuwa, ki shigo babu abinda zan miki." Bata shiga ba sannan bata daina kallon sa ba yace, "Ba'a Nigeria kike ba a k’asar America kike, in baki shigo ba baki da inda zaki je kuma wallahi suka kama ki sai kin je prison." Sai a lokacin ta kalli mutanen da suke yawo a wajan taga duk turawa ne ta kalle shi tace, "Amma ba haka kace min na, meyasa ka kawo ni nan? Me zanyi a nan? Ni gida nake so naje bazan bika ba” ta fad’a tana kuka sosai dana sanin bin sa na mamaye mata zuciyar ta. "Ki shigo kawai Malama koma meye ai zaki ji." “Bazan shigo ba” ta fad’a zata gudu yayi hanzarin kamo hannun ta ya jata da k’arfi ta fad’o motar aka kulle aka tafi. Jikin ta rawa yake tana kuka tace, “Allah ya isa, ban yafe ba Allah ya tsine maka albarka.” Bakin ta ya toshe dan bata son maganar ma da take yi duk da ba ji mai motar yake yi ba, kafin su je zazzab’i ya rufe mata jiki. A harabar gidan suka tsaya ya fito Fiddausi tak’i fitowa ya kalle ta yace, "ki fito mana." Tace, "bazan shiga ba." "İn baki fito da k'afar ki ba wallahi zan saka sa d’auko ki." "Bazan shiga ba wallah, ka mayar dani gidan mu bana son zama a nan." Turawa guda biyu ya kalla cikin harshen turanci yace, “a kawo ta ciki" ya fad'a yana yin gaba abin sa kafin tayi aune an d’auke ta a sama an bi bayan sa da ita. A falon aka ajjiye ta zata fita yayi saurin rik’o hannun ta yaga ba a hankalin ta take ba yace, "ki nutsu Malama bana son hauka da shirme, ba burin ki zuwa kiyi rayuwa a America ba? Yanzu Gashi kin samu meye na wannan rashin hankalin?." Girgiza kai take yi tana cewa, "yanzu bana so, ka mayar da bai Nigeria bazan zauna ba, bazan zauna ba ka mayar dani. Bana son zaman nan gida zanje, ka mayar dani gida na gaji da rayuwa da kai, ka barni na koma kafin na mutu.” Ganin tana yi masa hauka ya saka shi tsinke ta da marin da sai da gefen bakin ta ya tashe cikin fusata yace, "Ko ki yi min shiru ko na saka ayi miki mugun duka, ina yi miki magana kina yi min shashanci sa'an kine ni? Ban haife ki ba?." Sai da ganin ta ya d’auke na wasu lokacin kafin ta dawo daidai jikin ta na rawa sosai tana kuka yaja tsaki ya zauna ya kalle ta yace, "kud’i zaki samu kudi zan samu, ki nutsu ki shiga hankalin ki muyi maganar abinda zai kasance kin k’i.” Kuka take yi sosai ta lafe a jikin bango kamar marainiya yaja k’aramin tsaki ya tashi ya fita daga gidsn ya barta a wajan. Bata san adadin lokacin da ta kwashe a wajan ba a nan baccin wahala ya d’auke ta ta cure waje d'aya kamar almajira, magana ta fara ji a kanta hakan ya saka ta mikewa zaune tana kallon su ta ganshi tsaye shida wani bature sai kallon ta yake yi yana murmushi. Alhaji ya kalli Fiddausi yace, "ke baya jin hausa nasan kin iya turanci, to kiyi duk abinda yake so ki d’auka shima mijin ki ne kamar ni. Ko nawa kike so zai baki, ko me kike so zai miki kar Kiyi masa hauka" ya dawo kusa da iya ya tsuguna yace, "wallahi in kika sake kika aikata akasin abinda nace sai na lahira ya fiki jin dad'i, ki amince masa yayi duk abinda yake so dake ki saka a ranki dani kike tare ba shi ba. Fiddausi in kika yi masa abinda kika yi min wallahi maza zai saka su rik’e ki sai yayi abinda yake so sannan ya kyale ki gwara ma ki hak’ura ayi komai cikin nutsuwa a gama dan nan ba Nigeria bane,” Fiddausi jikin ta dai rawa yake kawai ta rasa ma abinda zatayi dan kamar bata ma fahimtar me yake cewa sai kallon kawai da take bin sa dashi kamar  ta zare. Bata san ya akayi ba taga dai babu mijin ta sai bature da yake kallon ta yana ta murmushi kafin taga ya matso kusa da ita yana shafa fuskar ta. Abinda ya dawo da ita daga da ita hankalin ta kenan ta zabura ta mik’e tayi baya ya sake biyo ta yana murmushi cikin harshen turanci yace, "meye yake faruwa ne Baby? Tunda na ganki naji ina sonki zan baki duk abinda kike so indai zaki amince dani. Ina son dan Nigeria kamar ki ki amince dani zan baki duk abinda kika nema." Jikin ta bai daina rawa ba bata daina ja da baya ba yana biyo ta, ganin yadda jikin ta yake rawa a nan ya tabbatar tsoro take ji ya d'auki waya ya Kira Alhaji Bello yana d’auka yace, "ya naga bata amince ba? Bata so ne?." "Sir kayi amfani da ita koda ta k’arfi ne in akace za'a bita a hankali bazata yarda ba." "A'a bana son tilasta ta gashi kuma ina sonta" ya fad'a yana kallon Fiddausi da bata ma fahimtar abinda yake cewa dan bata nutsuwar ta. Alhaji Bello hankalin sa ya tashi baya son rasa wannan harkar yace, "ta haka kawai zaka same ta in ba haka ba bazata amince ba." Datse kiran yayi ya matsa kusa da Fiddausi yana kallon ta sai yaga tana baya da sauri ta d’auki kwalbar lemo da yake kan table a wajan tana nuna shi da ita shi kuma yana murmushi yana binta. "Kar ka tab'a ni, kar kazo Inda nake, kar ka tab'a ni" daidai lokacin da ya kawo hannun sa gare ta sai kuwa ta buga masa kwalbar gefen kansa nan take ta fashe ya sunkuya dafe da kai ita kuma ta fita a guje. Caraf taji an yi sama da ita a lokacin da ta fito d’in kafin wani lokaci police sun bayana a wajan aka saka mata handcuffs aka saka Fiddusi a mota aka tafi.             A gidan su a Ibrahim gabadaya y'an uwan sa sun zo an saka shi a gaba ana ta tsokanar sa ana cewa angon Rukayya shi dai sai murmushi kawai amma baya cewa komai. Yaya Hadiza tace, "sai murmushin murna kake ka kasa magana." Hajiya tace, "ke kuwa ba dole ba, yarinyar akwai shiga rai wallahi. Fatana da burina Allah yasa ba irin halin k’awar tane da iya ba." Mariya tace, "in sha Allah wanna ta daban ce, addu'ar da akayi ai bazata fad’i k’asa a banza ba." Hajiya tace, "abin mamaki mahaifin ku yace mahaifin Fiddausi ne ya amashi auren Rukayya kuma shine ya bada sadaki. Yace sai murna yake kamar komai bai faru ba." "Ai Hajiya daga jin yadda aka k’are da d'aurin aure daga zuwa kai kudi kema kin san farin ciki ne ya jawo hakan, Alhaji yace ai baki ji yadda ya dinga bashi hak’uri akan abinda Fiddausi tayi ba nace ashe sun sani" Hadiza ta fad'a tana d’aukar lemon da yake Leda tana b’arewa . Hajiya tace, "sun sani mana, ai zancen duniya baya b’uya. Kinga wannan kulle shi din da ta saka akayi? Wallahi kamar yayi kuka haka ya dinga bawa Alhajin ku hak’uri. Shi kansa ya san d’iyar sa tayi rashin miji, Bawai yabon kai ba amma duk inda taje sai dai a fishi da kud’i ba dai kwanciyar hankali ba." Mariya ta kalle shi baice komai ba har lokacin tace, "ikon Allah kenan, kaga sai ku tare a sabon gidan ka. Kai babu Wanda ya kai Allah iya tsara wa mutum lamuran sa, ka rabu da tsohuwar mata, tsohon gıda, tsohuwar damuwa, tsohon aiki. Yanzu kuma sabon gida, sabon abin hawa, sabuwar amarya, sabon aiki. Ka gode Allah Ibrahim Allah yana shiga lamarin ka” ta fad'a tana dan dukan sa a kafad’ar sa a lallai sai yayi magana. Murmushin ya sake yi amma bai yi magana baHajiya tace, "Yanzu sai a fara batun lefe ko? Kud’in da kake tarawa a wajena sai a fito dasu ayi hidima. Yadda suka karrama mu muma mu karrama su." Sai a sannan Ibrahim yace, "Eh  gobe in Allah ya kaimu Yaya da Mariya zasu je su fara siyo abinda ya kamata, Tunda akwai kudi a hannnuna ina ganin zasu isa dan ba karya za'a yi ba." Mariya tayi dariya tace, "Allah ko ango? Wallahi a shirye kake tsaf abin ka.” Yayi dariya ya tashi ya fita yana jin su suna cigaba da tattaunawa akan lamuran auren yana jin dad'i a har zuciyar sa kamar auren fari yayi.           Ameena tana zaune a falo suna charting ita da Rukayya tana bata labarin abinda ya faru sai murmushi take yi na farin ciki in kaga yadda take yi sai ka d'auka kalaman soyayya ake fad’a mata take murmushi. Yaya Adam ne ya shigo ganin tana ta murmushi ita da waya ya zauna yace, "Aminatuwa keda wa kike murmushi haka?." Sai a sannan ta kalle shi tace, "Rukayya ce Yaya, Sannu da zuwa." Bin ta yake da kallo cikin farin ciki ganin ta dawo kamar ba ita ba ta manta da komai yace, "Yauwa. Da Rukayyan kike wannan murmushin?." "Ai abin farin ciki ta fada min ne Yaya." Yayi dariya yace, "ai naga alama." Dariya tayi ta cigaba da danna waya kafin yace, "in kika gama idda ne kike so kiyi Ameena? Aure ko karatu?." Sai da gaba ta ya fad’i ta ajjiye wayar a cinyar ta tace, "Karatun dai Yaya." "Auren fa?." Ta sauke numfashi tace, "nayi daga baya." "Allah ya bada nasara" ta amsa da amin kafin tace, "Yaya gobe zanje gidan su Rukayya." Ya kalle ta yace, "waye yace miki wacce take idda tana fita?." Ta rausayar da kai tace, "ai ba wani wajan zance ba iya gidan su ne kawai." Yayi shiru na wani lokaci kafin yace, "zan gani zuwa goben in akwai damar na bari kije din." Tayi murmushi tace, "to na gode." Zaytun ce ta tawo tayi wajan sa tana kiran Abba ya d’auke ta yana yi mata wasa iya kuma ta cigaba da danna wayar. Bud’e k’ofar akayi aka shigo ya kalli wanda ya shigo ya kalli Ameena ya ganta da riga doguwa kamar yadda ta saba shigar ta ya kalli Al'ameen yace, "muje ko?" Ya fad'a tana tashi tsaye. A sannan Ameena ta kalli wanda ya shigo tayi murmushi tace, "ina wuni Yaya Al'ameen?." Murmushin shima yayi yace, "Lafiya lau Ameena." Daga haka bai sake cewa komai ba itama haka suka fita. Tare suka shiga mota guda d'aya Al'ameen yayi shiru yana tuk’a motar baice komai ba shima Adam din baya magana sai daga baya Al'ameen yace, "Adam dan Allah ka bani Ameena a karo na biyu." Adam ya kalle shi yace, "Wai meye ya shiga kanka ne? Na fad’a maka idda yarinyar nan take yi meyasa kake kawo zancen ta a wannan lokacin?." Al'ameen yace, "na sani, ai ba tunkarar ta nayi ba kai na samu da maganar. Kai kasan tun kafin Ameena ta girma nake sonta Allah baiyi ni zan aure ta ba. A wannan lokacin ka bani dama dan Allah ina sonta har gobe, kafi kowa sanin waye ni." Adam yaja tsaki yace, "ka daina min wannan maganar dan Alalh ka bari ta fita daga idda komai zai biyo baya." Da to ya amsa ya cigaba da tuk’in sa amma zuciyar sa na wajan Ameena. A b’angaren ta ma bayan ya fita Anti Aysha tazo ta zauna tace, "Ameena yayan ki shida waye suka fita?." Ameena tace, "Al'ameen ne, wai Yaya bashi da aure ne?." Tayi dariya tace, "bashi da aure." Ta wara ido tace, "sa'an Yaya ne fa?.." "To shima yaushe yayi auren?." "Amma dai yayi ai." "Ke ya tab'a aure, matar ce ta rasu a wani hatsari da sukayi da ciki a jikin ta." Ameena tace, "Allah sarki, Allah ya jikan ta." Aisha tace, “Ameen. Kowa baki ga murnar da yake yiwa matar sa ba saboda ta same shi, Wato namijin ne tsayayye kan abinda ya shafi iyalan sa wallahi, lokacin da suka yi auren ma baiyi kud’in haka ba ana tunanin in yayi kudi zai canja mata amma ko kusa bai canja mata ba gashi ta jima babu ciki, aka dinga zai k’ara aure bata haihuwa amma bawan Allah nan bai d’aga kai ma ga kalle su ba balle yayi auren.Kai yana da nagarta sosai.” Ameena tace, "Allah ya bashi wata mai alkhairi." Ta amsa da amin suka cigaba da wata hirar. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid #500 Book3 014 Fiddausi tana cikin cell na turawa an kulle ta sai kuka take tana zaune a jikin bango tana kallon kowa sama-sama dan jiri take ji sosai. Ba komai ne yake zuwa kanta ba sai lokacin da ta saka aka kama mata Ibrahim, kallon inda take tayi gashi mai kyau harda gado ta tunda inda Ibrahim yake duk fitsari wajan ga daud’a ta lumshe idanun ta hawaye na cigaba da sakkowa. A bayyane tace, “ka yafe min ibrahim, ka yafe min hakkin kane yake bina, duk abinda nayi maka sai da ya faru dani, ka yafe min” ta fad’a cikin kuka sosai kamar yana gaban ta. D’ago kai tayi tana kallon waje ta hango Alhajin a wajan y’an sandan yana tayi musu magana amma ina sun k’i amincewa su bashi dama yaje inda take, dakyar suka amince ya k’arasa ya tsaya yace, "ke wacce irin mahaukaciya ce iyee? waye ya fad’a miki a wannan danyen aikin a k’asar turawa?, waye ya fad’a miki nan Nigeria ce? Dan baki da hankali sai ki d’auki kwalba ki fasa masa kai da ya mutu fa?.” "Kaina ciwo yake yi, ka bani magani zan mutu, kaina zai rabe gida biyu, ka taimaka min ka bani magani” abinda take cewa kenan tana juya kai cikin mayuwacin hali yaja tsaki ya bar wajan ya koma yana ta zagaye bai san ya zaiyi ba. Zuciyar sa ta fara kitsa masa kawai ya tafi ya barta in sun kaita prison shikenan ita ta jiyo shi bai dame shi ba. Ana haka sai ga Ogan nan ya shigo kansa d’aure da bandage daga gefe ya k’arasa wajan y’an sandan yayi musu bayanin yadda zasu bar Fiddausin yayi singing aka fito da Fiddausi. Ganin yanayin da take ya saka aka wuce da ita asibiti aka kwantar da ita aka saka mata ruwa da allurai. A lokacin Alhaji Bello ya samu damar yi masa magana yace, "Sir kayi hak'uri da abinda ya faru, bata jin magana ne na rasa ta yadda zan nuna mata mahimmaci ka a wajena ta gane, ban san ya zanyi mata ba.” Yayi murmushi cikin yaren sa yace, "ina sonta kar ka damu , zan bi da ita ta ko wacce hanya dan samun cikar burina a kanta. Ka koma Nigeria ka da ita zanje meeting k’asar Germany in na dawo zaka dawo min da ita, kafin lokacin zan saka maka balance na kawo ga da kayi in komai ya faru zan mallaka maka duk abinda kake so domin kuwa ba’a tab’a kawo wacce ta burge ni kamar ta ba.” Alhaji Bello yayi dariya yace, “godiya nake Boss.” “Ka tafi da Zainab ma, amfanin ta ya k’are.” “An gama boss.” Alhaji Bello yaji dad’i sosai dan baya so ya fasa in yace ya fasa ya tafi da ita gida yayi asarar kud’i masu shegen yawa, amma yanzu da yaji wannan bayanin ya gamsu sosai duk da ta b’ata masa rai da ta amince da yanzu an cika masa bankin sa da kud’i. Da wannan b’acin aka d’auke ta aka kaita gıda aka kwantar akan gado aka barta ita kad’ai sai bacci take yi bata an ma an dawo da ita ba. Mafarki tayi wanda ya saka ta zabura ga mik’e sai a sannan ta tuna rabon ta da sallah tun a Nigeria ta sakko dakyar ta shiga band’akin da ta gani a d'akin tayi alwala ta fito tana kallon d’akin nan taga alama ta alqibla ta tayar da sallah ba tare da ta canja kaya ba dan bata dasu. Bayan ta idar ne tana zaune tana tunani mai had’e da dana sani aka kwankwasa k’ofar aka shigo sai ga wata yarinya a gaba bayan ta wata mai aiki ce baturiya ta rik’e da babban tray na abinci ta ajjiye ta juya ta fita ita kuma tabi Fiddausi da kallo da take zaune. "Sannu fa y'ar uwa." Jin tayi hausa ya saka ta juya da sauri ta kalle ta tayi dariya tace, "kinyi mamakin jin ina hausa ko? Nima bahaushiya ce kamar ki matar mijin ki kuma, abinda ya kawo ki ayi dake shi ya kawo ni ayi dani nake zaune har wannan lokacin." Gaban Fiddausi ya fad’i tsoran ta ya ninka na baya dan lamarin Alhaji ya fara b’atar mata da hankali gani take Anya ma mutum ne, ta kasa magana sai kallo kawai waccan ta zauna tace, "inda zan baki shawara da nace ki amince kawai ayi a wuce wajan dan wallahi in baki amince ba kika koma hannun mijin ki wahalar da zaki sha Allah ne kawai ya Santa, kawo ki din nan da akayi ba k’aramin kud’i zai samu ba in kika k’i ki amince har ya saka a mayar dake kin shiga uku." Fiddausi murya na rawa tace, "kema matar sa ce?." Tayi dariya tace, "matar sace ni, da yawa an d’auka ya sake ni basu San nan ya kawo ni yake kasuwanci dani ba." Fiddausi tace, "kuma kika amince ana lalata dake?." "To ya zanyi? Bani da kowa bani da komai, hatta waya baza ki rik’e a gidan nan ba ko wanne motsi kika yi ana kallon ki. Ya zanyi in ban amince ba? Zan haura na gudu ne?.” Fiddausi ta dafe kai tace, "na shiga uku ni Fiddausi na kawo kaina inda za'a hallaka ni, wacce irin masifa na jefa rayuwata a ciki?.” Yarinyar tayi murmushi tace, "kin ganni nan sunana Zainab ya auro ni shekara uku kenan dan a bayana aka auro Aliya da Naja'atu sai ke a yanzu, nida ke a yanzu bai d’auke mu matan sa ba ya barwa ogan su wannan Baturen dan nasan Kun had’u dashi wad’ancan ma sun zama hoto lokaci yake jira ya kore su ya auro wasu." Fiddausi tana Jan numfahsi dakyar tace, "mutumin nan anya mutum ne kuwa?." "Mutum ne, duk wacce kika gani a gidan sa son zuciya ne ya kawo ta kamar ke kamar ni kamar kowa ma, dukkan mu an aura masa mu babu bincike dan da akwai bincike babu wanda zai amince y’arsa ta aure shi. Dukkan mu yawanci son duniya ne ya kai mu ga auren sa, ke kin san y’an matan wannan zamanin mai kud’i kawai ko wanne Hali yake dashi ji muke zamu iya zama dashi indai akwai kud’i, gani muke kudin shine farin ciki shine kuma cinyewa saboda za’a dinga labari a cikin k’awaye ace ai wance matar mai kud’i ce,” Fiddausi hawaye ya sakko mata kanta yana k’asa Zainab tace, "Yanzu kika fara kuka duk da ban San abinda kika aikata kika zo nan ba amma ina tabbatar miki da sai kinyi dana sanin zuwan ki nan. Da yawan mu guduwa mukayi muka aure shi wata kuma iyayen ta bijirewa, ni gani nake Anya baya yi mana asiri kafin yazo gare mu?.” Ganin Fiddausi ta kasa magana sai kuka da take yi tace, "Na tabbata kin tuna abinda ya wuce ne, kin ganni nan iyayena na gudawar aka d'aura mana aure dashi, babana baya so" muryar ta fara rawa kafin tace, "amma saboda kud’i da son kasancewa matar mai kud’i haka na tsallake umarnin sa na bar gıda ban koma ba sai da aka d'aura mana aure dashi, na baro iyayena suna fushi dani akan hakan amma ban damu ba kawai ina hangen zan shiga gidan sa na zama matar mai kud’i da nazo na kai su umrah shikenan zasu yafe min" sai ta tashe da kuka sosai itama ta sake cewa, "Sai gashi ranar da aka kaini wajan sa ya kawo ni k’asar nan mukayi sati biyu a lokacin ya fara bijiro min da son amfani dani ta baya, nak’i yarda yayi min ta k’arfi sai da na kwana biyar a asibiti na dawo daidai ya mayar dani Nigeria ya jibge ya hana ni waya da kowa nawa" ta goge idanun ta tace, "A wannan lokacin ya auro Naja'atu ni kuma ya dawo dani nan ashe yarjejeniya ce a kaina za'a bashi kud’i masu yawa shi kuma zai barni a nan Ana amfani dani kamar karuwa, ko a jikin sa bai damu ba kuma bai sake ni ba. Haka nazo nan garin da farko na fara gaddama aka daina bani abinci aka daina bani abin sha tsahon kwana biyu ban sha ruwa ba" kukan ta yayi k’arfi sosai kafin ta tsagaita tace, "ina ji Ina gani wannan baturen yayi amfani dani ta gaba da ta baya a lokaci d'aya, daga rana aka fara bani abinci. Sai kuma aka bijiro min da saka min maganin bacci duk sanda yaso yin amfani dani za'a bani abinci nayi bacci daga nan ban San me yake faruwa sai dai na ganni a kwance babu kaya ko na ganni asibiti. Har gobe haka ake min na tabbata kema haka za'a yi miki dan indai ina cikin hayyacina bazan amince ba.” Kuka suke sosai su biyun cikin k’unar rai ko wacce tana dana sanin abinda ta aikata sai ga wata baby mai kyau fara ta shigo d'akin ta nunawa Fiddausi ita tace, "yarinyar dana haifa masa ce y’ar uwa, nayi cikin shege da aure a kaina na haifawar baturen da ban San shi ba y’a gata nan ina kalllo." "Na shiga uku ni Fiddausi, ina zan saka kaina naji dadi?, Mama da Abba kuzo ku taimaka min kafin na mutu!. Alhaji zai kashe ni bak’in cikin sa sai saka zuciyata ta buga.” Abinda ta fad'a Kenan tana kuka sosai dan abin yafi k’arfin abinda su Aliya suka fad’a mata. Dukkan su kuka suke yi babu mai rarrashin wani a cikin su dan ko wacce dana sanin abubuwan da ta aikata take yi, ba kamar Fiddausi in ta tuna har ciki ta zubar sai taji kamar ta kurma ihuu ta dinga Marin kanta. yarinyar mai suna smart tana ta kallon su tana tsaye a gefe kamar ta san kukan ne suke yi. Bud’e k’ofar akayi aka shigo ganin wanda ya shigo ya saka Zainab mik’ewa ya bita da kallo yace, "Zuwa kika yi kina fad’a mata zancen kema haka akayi miki?." Zainab tace, "ka kiyayi karshen ka wallahi, sai kayi dana sanin abinda kayi mata." Yayi dariya yace, "kune zakuyi dana sani, ke iyaye kika gudarwa kika aure ni ita kuka mijin ta mai sonta da kula da ita ta gujewa saboda ta auri mai kudi. To Gashi ya aura kasar da take burin zuwa gata a cikin ta sai tayi abinda take so." Magana Fiddausi take so tayi amma babu hali sai hawaye da yake ambaliya fuskar ta kamar tumatur saboda Jan da tayi. “Kaicona, kaicona ni Fiddausi. Allah ka yafe min Ibrahim ka yafe min, iyayena ku yafe min abinda na aikata. Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!.” "Duk a cikin matan dana aura nafi sonku shiyasa na kawo ku nan dan ku samu kud’i kuji dadin rayuwar ku, ke Fiddausi yanzu yace mu koma Nigeria dake tafiyar gaggawa ta kama shi zuwa Germany a k’alla zaiyi sati biyu. Ke kuma zaki bar masa masa y’ar sa a nan daga nan ki tafi gidan ku na sake ki." Wani irin numfashi taja cikin farin ciki sai kuma hawaye ya biyo baya da tunawa da abubuwan da ta aikata kafin a sake ta din ta zube a wajan tana kuka mai matuk’ar yawa. Sai ya kuma ta kalle ta yace, "Zee kafin ki tafi bazan barki haka ba ya kamata" ya fad'a yana jefa ta kan gadon ta tayi baya ta dire sai yayi dariya kawai yace, "bazan sake waiwayon ragowar bature ba, zamu wuce gobe zuwa Nigeria har ke daga nan ki kama gaban ki, baki San wani Alhaji Bello ba ko a mafarki." Jikin ta rawa take yi sosai ya juya ya fita har lokacin jikin ta bai daina rawa ba tana kallon Fiddausi itama ita take kallo ko wacce kuka take yi mai tsuma zuciya sautin sa ya karad’e d’akin gwanin ban tausayi. Babu mai iya yiwa wani magana a cikin su suna nan zaune bacci ko wacce ya kauracewa idanun ta har safiya tayi ko wacce na zaune idanun ta kyam suka fito suka hau jirgi zuwa Nigeria. Zuciyar Zainab na farin ciki wani b’angaren yana bak’in ciki a haka suka tawo Nigeria. Asiya tana tsaye a jikin madubi tana shiryawa shi kuma yana gefe yayi tagumi kamar ko yaushe ya rasa abinda yake masa dad’i ya rasa meye yake addabar zuciyar sa ya rasa sukuni, juyows tayi ta kalle shi tace, "My love dan bani kayana na saka." Bai ce komai ba kamar bazai tashi ba sai ya tashi zuwa inda kayan suke ya bud’e yace, "wanne kike so?." "Duk wanda yayi maka shi nake so.” Ta fad’a tana murmushi tana kallon sa shi kuma gabad’aya ba wannan ne a gaban sa ba. Kayan Gasu nan a hargitse babu gyara ko na sisi baka gane ma wanda zaka d’auko, ya tab’e baki ya jawo wata atamfa da yake gano daga can k'asa sai yaji abu ya biyo atamfar ya fad’o kan k'afar sa. Atamfar ya cilla mata yana kallon abinda ya fad’o yayi ya sunkuya ya d’auka ya kalla ya kalle ta ya sake kalla yace, "Kaii! Wannan ba sark'ar dana nema na rasa bace ba?." Asiya ta diririce tsoro ya bayyana a tare da ita sosai amma sai ta basar ta daure tace, "a nan ka ajjiye kenan? Kaga ban ma San ka ajjiye din ba." Kallon ta yake yi da mamaki gaban sa yana fad’uwa matuk’a yace, "ya akayi tazo hannun ki? Kenan a waccan ranar kece kika dauk'a?." Banzar harara tayi masa tace, "kamar ya ni na d’auka? A ina nasan inda take da zan d’auka? Ka ajjiye abu kuma kace min nice na d’auka?. Inda ni na d’auka zata Kai yanzu ban je na siyar ba?.” "Kar ki raina min hankali mana Asiya, ba ke kika shiga d’akina ranar da muka dawo daga Saudia ba? Kin mata ne?." "Kodai kai ka dainawa rainawa kanka hankalin ba, ta ina nasan inda abu yake da zan d’auka daga dawowar mu ban tab’a shiga d’aki ba ace har nasan inda sark’a take?. Kaga malama bana son sharri." "Ni nake miki sharrin?." Tayi tsaki tace, "kai din mana, ubana ne kai?. Ba sharrin kayi min ba? In ba sharri ba an ina nasan inda sark’a take balle na d’auka?.” Bai san ya tsinke ta da maruka biyu ba sai da yaji saukar nata hannun a fuskar sa tana zare idanu ta nuna shi da yatsa tace, "ai na fad’a maka ake ka sake kuskuren dukana sai na rama ko? Na fad’a maka ranar da ka sake dukana sai na rama kuma gashi na rama din. Ka sake kuskuren sake marina wallahi sai na rama.” Suman tsaye yayi yana kallon ta dan kwakwalwar sa taje hutun rabin lokaci dan ya daina gane komai sai kallon ta akwai da yake yi zuciyar sa na bugawa sosai saboda abinda aka yi wanda bai tab'a zaton za'a yi shi ba. Shi mace ta saka hannu ta mara macen ma matar sa da yake sa iko da ita tace ta mare shi dan raini da kuma iskancin da bai san da me zai Kira shi ba. "Me nayi maka da zaka dake ni? Dan kaje kasha giyar ka tayi maka yawa zaka zo kana yi min hauka? To wallahi nawa yafi k’arfin ka duk abinda kayi min daidai nake dakai wallahi. Uban me zanyi da sark’ar ka da zan d’auka? İn sata nayi ai baza ka ganta a wajan ba tun lokacin har yanzu ai da tuni na siyar, Uwar gidsn kace b’arauniya bani ba.” Har lokacin bai dawo daidai ba maganar da tayi ce ta saka shi dawowa hankalin sa ya tuna marin sa fa tayi ya kalle ta dan ya rasa ma abinda zai mata ma ya wuce ya kalli sark'ar da take hannun sa ya tuna abinda ya faru a lokacin da ya rasa sark’ar bai San lokacin da ya saka k’afa yayi ball da ita a ba a wajan. Ihu tayi ta mik’e tayo kansa ta chakumi rigar sa tana cewa, "wallahi baka isa ba, shege dan giya dan iska, kuma ka sake dukana wallahi sai na nuna maka mahaukaciya ce ni.” Fincike ta yayi daga jikin sa ya sake ba marika guda biyu wanda ya sakata gigicewa tace, "Allah ya isana, banza dan giya, na fad’a dan giya" ta sake fad’a da ihu ya sake tsinke ta da mari. Kuka take sosai tana zagin sa ya fita yana jiyo gudun a bayan sa ta biyo shi har bakin gate daga ita sai d’aurin kirji sai mayafi da ta yafa, "na fad’a sai dai kayi duk abinda aka yi min, wallahi ni bazan d’auki ka dinga dukana a banza a wofi ba. Kuma na fad’a dan giya, karya nayi maka ba Shan giyar kake yi ba?. Sai kayi dana sanin kirana b’arauniya a rayuwar ka, wallahi sai na nuna maka ni ba irin matan da zaka wulak’anta a banza bace” Ta fad’a da k’arfi hakan ya fusata shi ya juyo ya tankad’a ta baya ganin tana k’ok’arin rik’o rigar sa ta fad’a jikin mota da ciki tayi k'ara mai k’arfin gaske shi kuma ko ta kanta bai ba ya hau mota ya fita daga cikin gidan ransa a matuk’ar b’ace. #Mai daki #Paid #Book3 #500 Book3 015 Motar Yusuf tana fita k’anwar ta Momi ta shigo gidan gano a kwance a k'asa ta k’arasa wajan a guje tana kiran sunan ta cikin mamakin abinda ya kawo ta wajan, hankalin ta ya tashi ganin idanun ta biyu amma yadda take cize baki tana yarfe hannu zai nuna maka tana jin ciwo sosai. A guje tayi waje k’arasa inda taga direban Asiya din aka taimaka aka saka Asiya a mota aka tafi asibiti. Da yake private suka je karb’ar gaggawa aka yi mata aka kwantar da ita Momi ta kira Umma ta sanar da ita abinda yake faruwa zuwa wani lokaci kad'an Umma ta hallara a asibitin hankalin ta a tashe sosai. Bayan sun fito daga d'akin da Asiya take dan ba private room bane d’aki ne mai mutane guda biyar dole suka fito waje dan su tattauna ta kalli Momi tace, "Wai Meya faru ne haka? Meya same ta?.” Momi tace, "wallahi ban sani ba, Nidai nasan motar mijin ta tana fita na shiga na ganta a kwance a harabar gidan masu aiki na kawaye da ita." Umma tace, "kenan yasan tana wajan a kwance ya fita ya barta? Karfa shine ya sake dakar min ita wallahi bafa kyale shi zanyi ba." "Wallahi ban sani ba Umma, sai dai in ta farka zamu ji abinda ya faru." Umma tace, "da aka duba ta ne aka ce?." "Nurse din cewa tayi cikin jikin ta bai zube ba amma in aka sake maimaita irin buguwar da tayi zai iya fita dan ta bugu a cikin nata sosai.” Umma ta girgiza kai tace, "nasan sai zuwa gobe zamu bar nan, zanje gida zan dawo zuwa anjima keda Fauziyya ku zauna da ita kafin na dawo. In ta farka goben naji abinda ya faru" daga haka Umma tayi gaba ta koma gida Asiya tun daren ta tashi daga bacci ta tashi zaune Fauziyya ta kalle ta tace, "Sannu, ya ciwon ciki?." Asiya ta shafa cikin tace, "kar kice min cikina ya zube." Fauziyya tace, "bai zube ba yana nan, amma dai yana gab da zubewar dan bugewar da kika yi kiris ya rage mai zubar dashi ba." Bata sake cewa komai ba tayi shiru tana kwafa a zuciyar ta dan wallahi sai Yusuf ya gane kuren sa akan abinda yayi mata. Da safe kafin Umma tazo ma sun baro asitinin kai tsaye gida suka wuce Asiya sai cize baki ake kamar wacce take nak’uda. Bacci tayi sosai koda ta farka abinci taci sai yatsina take abincin ba nama ba haka ta saba ci ba, sai da Umma ta tabbatar ta huta sosai sannan ta kira ta ta zauna duk suka zagaye ta kowa so yake yaji abinda ya faru Umma tace, "ya kike jin jikin naki?." Asiya tace, "da sauki Umma." "Meya faru haka? Fad’uwa kika yi a harabar gidan naku?." Asiya ta had’e rai tace, "Yusuf ne ya dake ni, wai ni zai kalla yace nayi masa sata harda marina shine na rama dana sakko sai ya ture ni na fad’i cikina ya bugi mota. Yanzu da cikin ya zube bashi da asara.” Umma da mamaki tace, "ya kuma dukan ki kuma dai? Wai shi waye ya fad’a masa na kai ki gidan sa dan ya dinga dukan ki? Dan yana da kud’i muna samun abinda muke so ba hakan yana nufin zai mana iskanci mu d’auka bane bafa. Zan bashi mamaki fa bai San wacece ni akan y’ay’ana ba.” Maimuna tace, "Ai wallahi Umma laifin ki ne, ace wai namiji kamar Yusuf ya gagara zama yadda muke so?." Umma tace, "Barni dashi ai ya tab'a abinda yafi karfin sa yanzu kuma ai. Ke Asiya kiyi wanka anjima muje gaban iyayen sa a yiwa tufkar hanci domin bazan lamunci duka ba wallahi. Dan na kai shi kotu a wannan yanayin ba wani abun bane ba a wajena. Gwara na sanar da iyayen sa san abinda za’ayi.” Momi tace, "kuma dan wulakanci ta kwana ta tashi a asibiti amma ace ya gagara zuwa ya ganta yasan wanne hali take ciki, an raba shi da uwar gidan ma amma duk da haka bai zama yadda ake so ba, Kullum lamarin sa sake yin gaba yake yi, in aka taro shi a nan sai ya koma nan.” Umma tace, "ai bazan jira komai ba wallahi daga nan sai gidan su dani da ita zamu je, banga dalilin da zai dinga dukan ta ba ai ba baiwa aka kai masa ba, shi ya gano yace yana so. In ma satar tayi sai me ba kayan mijin ta bane ba?." Baba da ya shigo yake jin mai yake cewa ya kalle ta yayi murmushi tare da girgiza kansa ya rasa wacce irin macece da ba’a tab’a mata yara a zauna lafiya, ko waye kai zaku yi fito na fito dashi bata kunyar hakan ko kad’an yace, "Ai Atika a haka duk yaran ki zasu k’are wallahi, akan turbar da kika d’ora su babu mijin da zai iya zaman aure dasu. Duk inda suka je sai sun dawo gaban ki kamar yadda babbar su take a gaban ki yanzu, Ita kanta Asiya din k’arshen ta irin na Maimuna zai zama indai baki d’ora su akan turbar gaskiya ba. Ko bani da rai ki rubuta ki ajjiye matuk’ar baki canja daga yadda kike ba a haka za’a k’are wallahi.” Umma ta kalli Baba tace, "a kanka, babu abinda zai samu auren ta in sha Allah. Ni ban tab’a ganin uban da yake yiwa yaran sa bak'in ciki ba sai kai, tana zaune a gidan ta muna samun duk abinda muke so kace wai k’arshen ta irin na Maimuna zai zama?, bana son irin haka in baza kace Allah ya gyara ba kayi shiru ba ka kyale mu ai babu lallai sai kayi magana a kai. Wannan ai bak’in Hali ne kamar ba kai ne uban su ba?.” Baba baice komai ba ya wuce su kawai Fauziyya ta kalle shi bayan ya wuce tace, "Baba yana da damuwa wallahi." Umma tace, "kyale shi, ke tashi kije ki canja kaya kizo muje gidan nasu kafin dare yayi."  Asiya ta tashi dakyar ta shiga d'aki tana jiyo Umma na mita ta saka kayan Momi da hijjabi ta fito ta tarar Umma har ta saka hiijjabi suka fita daman driver Asiyan yana waje tunda suka dawo ko ya fita zai dawo dan haka aka ce masa suka shiga mota sai gidan su Yusuf.        A can gidan su Yusuf yana zaune a cikin iyayen nasa yayi shuru kai da ka ganshi kasan yana cikin yanayi na damuwa mai yawan gaske fuskar sa ta nuna hakan sosai a bayyane kana ganin sa abinda zai zo ranka kenan, Abbah yana ta masa fad'a yace, "Dan hauka da rashin sanin ciwon kai da rashin sanin dajarar matar ka ace d’an aikin kane zasu Kira mahaifiyar ka ya fad’a mata kuma fad’a da matar ka a harabar gida? Meye yake damun kane Yusuf?. Me ya shiga kanka kake aikata mugayen abubuwa haka?.” Kansa yana k’asa ya kasa magana saboda ciwon da yake ji a zuciyar da Ammah tace, "Akwai zubar da mutuncin da ya kai wannan? Y'an aiki ace Sune suke raba ka fad’a da matar ka?” Ta kalli Abbah tace, “Wannan ba shine na farko ba anyi wani kuma nan gaba ma za'a sake tunda haka ya zab'arwa kansa." Abbah yace, "wannan ai hauka ne da rashin tunani, matar ka ta aure har k’ofar gida gaban masu aiki kuzo kuna fad’a kamar wasu y’an bariki Yusuf?." Abbah yace, "yanzu tana ina?." Yusuf yace, "Tunda na baro gidan ban koma ba, ban sani ba ko tana nan." Abbah ya sake yin tsaki ciki takaici yace, "ba’a tab'a yin irin wannan tozarcin ba a kaf zur'iar mu, mu ba’a san mu da d’aga hannu mu daki mace ba balle fad’a balle kuma ya kai ga duka a gaban masu aiki. Gabad’aya halayyar ta ta zamantakewar aure ka ta fita daban da ta kowa a gidan nan kamar kai kadai ne mai zuciya a cikin maza. Komai duka? Kai a ganin ka shine hukuncin da za’a yiwa mace? Baka San in ka saba mata ba wallahi kana d’aga hannun ka ka dake ta kafin ka sauke hannun ta rama har abada kuma mutuncin ka ya zube kuma kai ne ka jawo hakan.” Humaira ce ta shigo da sallama Ammah ta amsa tace, "Abbah ga Asiya matar Yaya Yusuf da babar sun zo suna son ganin ka." Gaban Yusuf fad’i sosai ya d’ago ya kalli Humaira Abbah ya kalle shi kafin ya kalli Humaira din yace, "jeki ki shigo dasu." Humaira ta juya Abbah ya kalle shi yace, "Kaji kunya wallahi." Da sallama Umma ta shigo Asiya na bayan ta suka k’araso Asiya ta zauna a k'asa kamar yadda Yusuf yake Umma ta zauna a akan kujera tace, "Barkan ku da dare da fatan na same ku lafiya." Abbah ya amsa da fad'in, "Alhamdulillah, ya masu jikin?." Umma ta kalli Asiya tace, "gata nan, daman abinda ya kawo mu kenan." Umma tace, "Tsakani da Allah bazan d’auki duka a zamantakewar auren Yusuf da Asiya ba, ranar nan ya dake ta tayi hak’uri ta fad’a min nace tayi hak’uri yau an sake har hakan ya kai ga bazarana ga abinda yake cikin ta badan Allah ya kare ba da yanzu babu shi, akan me ai ba dan duka aka kawo masa ita ba." Ammah tace, "Gaskiya ne." "Yauwa shiyasa nazo dan a yiwa tufkar hanci, bazan lamunci duka ba wallahi in wani abun tayi ya kawo k'arar ta ayi mata fad’a amma duka ai ba na ma'aurata bane." Abbah ya girgiza kai yana kallon matar kafin yace, "haka ne, fad’an da muke yi masa Kenan yanzu." Umma tace, "sannan koda wasa kar ka sake kira min ya da b’arauniya, me aka ajjiye ta d’aukar maka da zaka ce mata b’arauniya? Dan ita uwar gidsn ka tana yi maka sata itama sai kace tana yi maka akan me?. A'a Yusuf zamu samu matsala da kai akan abubuwa guda biyu dana fad’a yanzu, na farko sharrin sata da kuma duka. Irin haka ne yake kawowa mace ta fara rama duka a wajan mijin ta dan shine yake saba mata da dukan dole in ta gaji ta d’auki hannu ta rama, daga ranar da ta rama shikenan Kun zama y’an dambe.” Ammah da Abbbah suka kalli juna babu wanda yace komai Umma ta sake cewa, "kai me ka kamata ta satar maka da zaka ce mata b’arauniya?." Yusuf dai ya kasa magana gabad’aya kamar an d’aure shi haka yake ji domin an tozarta shi kam sosai ya muzanta a gaban iyayen sa. Ace babar matar sace take wannan abun a cikin gidan su me ya kai wannan bak’in ciki. Asiya tace, "balle ma Umma babu abinda na d’aukar masa kawai yasha tafi karfin kansa ne shiyasa" ta fad'a tana hararar sa ta k’asan idanu shi kuwa ji yayi ina ma k’asa ta bud’e ya shige ciki ya b’uya kafin a kai ga fad’ar abinda yasan sai ta fad’a. Umma tace, "kar kice min yana shan k’waya?." Asiya tace, "ba k’waya yake sha ba giya yake sha wallahi, ranar nan da ya shiga b'angaren tsohuwar matar sa na same shi yana sha har yayi min duka bakina ya fashe. Ya dinga rok’ona kar na fad’a, daman na fad’a masa indai ya kuma dukana walalhi sai na fad’a kuma gashi na fad’a kowa yaji.” Ta kalli Ammah tace, "Wallahi Ammah yana shan giya, in ana ganin k’arya nake azo aje d'akin sa na b’angaren Ameena a duba za'a ganta, ko kuma a tambayi Ameena ai ita tasan yana shan giyar ai.” Umma tace, "giya! Ahh gwara da akayi maganar nan a gaban iyayen sa. Bazai yu ba wallahi bazata sab'u ba wai bindiga a ruwa. D’an giya da y'ta ta cikina wacce na haifa inaaa!" Ta kalli Abbah da shi ya k’asa magana sai kallon ta da suke yi kamar tv tace, "Alhaji tsakani da Allah abubuwan da yawa, ko ya daina shan giya ko ya sakar min y'ata domin kuwa bazata zauna da dan giya ya dinga dukar min ita a banza ba wallahi bazai yu ba. In ya kashe ta Kun fi mu kud’i ya kashe banza, to bazai yu ba bazan d’auka ba wallahi.” Abbah da Ammah dai sun kasa magana sunyi shiru babu wanda yake magana a cikin su dan basu da ta cewa shiyasa suka tsaya suna jin abinda take cewa Umma ta sake cewa, "ni zancen duka ya kawo ni sai ga maganar da tafi k’arfin dukan ma, dan giya da y'ata ina ai abun bazai yu ba wallahi, ko ka daina ko kuma ka sakar min ita bazan lamunci dukan da zata sha in ka bugu ba salon ka kashe min ka saka ni asara rana tsaka wacce bazan mayar da ita ba.” Ta kalli Agogo tace, "To Alhaji Mun zo kuma gaban ku bani kunce komai ba.” Sai a sannan Yace, “Abinda Kika ce gaskiya ne, za’a san abinda za’ayi.” “mu zamu koma zan tafi da y'ata gıda in ya daina abinda yake yi yazo ya tafi da ita, amma batun shan giyar nan da akayi yanzu a sake dubawa sosai domin kuwa abu ne babba in ya sha zai iya kashe min y’a, in yaga bazai iya ba ya sake ta.”Abbah yace, "in sha Allah za'a san abinda za'a yi, Kiyi hak'uri dukkan ku." Umma ta tashi tace, "Yauwa, na barku Lafiya." Ta rik’e hannun Asiya suka fita daga falon aka barsu  su uku kowa ya kasa motsin kirki a cikin su abinda aka yi a wajan suke juyawa. Yusuf ji yayi kunyar duniya tazo ta lullub'e jikin sa, bai tab'a dana sanin shan giya a rayuwar sa ba sai a wannan lokacin, bai tab'a jin an ci mata musu mutunci ba sai a wannan lokacin, bai tab'a jin komai ya fita daga ransa ba sai a wannan lokacin. Bai tab’a jin rana d’aya an zare masa Shan giya a zuciyar sa ba sai wannan lokacin, bai tab’a gamsuwa da ya daina ba sai a wannan lokacin dan anyi mas abinda yafi tozarci tozartawa. Ammah dai ta kasa magana tayi shiru domin abun babba ne yafi k’arfin tunanin ta tana so ta tabbatar da batun shan giyar nan dan tafi komai tsaya magana zuciya. waya ta d’auka tana dannawa kafin ta tsayar da dannawa ta saka wayar a speaker ana jin alamun tayi kira. "Asslamu alaikum Ammah barka da dare." Maganar Ameena ta bayyana sa cikin wayar Amma ta kalle shi taga ya lumshe idanun sa yana jan numfashi ta d’auke kai tace, "Wa'alaiki Salam, Ameena barka dai, ya gida?." "Lafiya lau Ammah." "Ameena kiran ki nayi na tambaye ki wani abu Allah yasa kar ki yi min k’arya." "In sha Allah Amma bazan miki karya ba." Ammah tace, "kin tabbatar?." "In sha Allah." Ammah tace, "tsakanin ki da Allah a zamantakewar ku da Yusuf yana shan giya ko baya shan giya?." Shiru Ameena tayi kamar bata ji mai Ammah tace ba Amma tace, "kince zaki fad’a min gaskiya tambayar ki akwai nayi eh ko A'a?." Ameena tace, "Ammah." Ta dakatar da ita tace, "baku da wata alaqa a yanzu rufa masa asiri ba naki bane Ameena, a yanzu ba mijin ki bane balle ki kare shi kamar yadda kike yi a baya. Ameena Yusuf yana shan giya eh ko A'a?." Jin yadda Ammah tayi magana a tsawace da alama ranta a b’ace yake sai Ameena tace, "eh." "Yana sha kenan?." "Uhum." Amma bata sake jin wani abun ba ta datse kiran ta juyo a fusace ta tsinke shi da mari mai zafi ta d’auki wayar ta cilla masa tace, "kaji kunya, Allah yayi wadara halin ka, ka cuci kanka ka kuma cuci Ameena hakkin tane ya fara bibiyar ka yanzu, ina so ka saka a sanka ba’a yi komai bama, yanzu ka fara ganin sakamakon abinda kayi Yusuf. Bana fad’a maka ba in kaine kake cutar Ameena zamu gani, in itace take cutar ka zamu gani yanzu waye yake kwashe kashin sa a hannu?. Kayi asarar rayuwar ka wallahi, ka b’ata tarihin ka ka b’ata na gidan nan.” Kuka Ammah take yi sosai shi kansa Abbah ya rasa ma abinda zaice dan Umman Asiya ta shayar dashi mamaki sai yanzu ya fahimci maganar Ammah da take yi kafin auren ta kan ce basu da tarbiyya yau gashi ya ga rashin tarbiyya daga wajan babar su bama ita ba. Yusuf ya kasa koda motsi ya sunkuyar da kai k’asa jikin sa yayi masa sanyi sosai kukan Ammah yake ji a har cikin zuciyar sa sai dai ko kusa ya kasa jin haushin Asiya akan abinda tayi masa, yana jin b’acin rai amma kuma daga wani waje daban ba daga wajan Asiya ba. Abbah yace, "to ai kaji abinda iyayen ta suka ce maka, ko ka daina shan giya ko kuma ka sakar mu ya. Kaga wacce take da gata kenan ba wacce ka dinga wahalarwa dan kaga babu iyaye ba, ban tabbatar da cewa yarinyar da ka bari ka cutar da ita ba sai yanzu, ban tabbatar da cewa ka tafka babbar asara ba sai yanzu Yusuf. Bazan ce ka daina shan giya ba kasa. daidai k'asan ba daidai ba, in ka daina kanka in baka daina bama kanka babu abinda zai dame ni. Abinda na sani ban tab'a zaton a cikin ahlina za'a samu baragurbi kamar ka ba, ban tab'a d’auka za'a samu mai shan tab'a bama sai gashi mai shan giya aka smau gabad’aya. Komai ka aikata rayuwar ka ka cuta Yusuf kaje kayi duk abinda kake ganin daidai ne, matar dai da ka zab’a tana tare d akai ga rayuwar da ka zab’arwa kanka nan kaje Allah ya bada sa'a." Yana gama fad’a ya tashi ya bar masa wajan Ammah kuwa ta kasa tashi kuka tane sosai. Magana yake so yayi mata amma ya kasa cewa komai lokacin Humaira tazo ta zauna a kusa da Ammah duk da bata san meya faru ba amma tasan damuwar Yusuf ce ya kalli Amma zaiyi magana tace, "bana son aji komai daga bakin ka Yusuf, tashi ka baki waje ko kallon fuskar ka bana so." Baice komai din ba kuwa ya mik’e tsaye ya fita zuciyar sa nayi masa mugun d'ci yana kuma sake yin alqawarin ya daina shan giya daga wannan ranar, ya raya a zuciyar ss ya kuma yiwa Allah alqawarin bazai kuma Shan giya ba daga wannan lokacin. Book3 016 Yusuf tuk’i yake yana hawaye yana kuma gogewa da bayan hannun sa gabad’aya duniyar tayi masa zafi sosai ya rasa inda zai nufa yaji dadi a zuciyar sa. Tafiya yake kawai har yaje k’ofar wani gıda ya faka ya kifa kansa a sitiyarin motar ya rasa meye yake damun sa abinda ya sani baya Jin haushin Asiya a gangar jikin sa amma zuciyar mugun tsanar ta yake ji akan abinda tayi sannan kuma yana dana sanin Shan giya a rayuwar sa. D’agowa yayi ya d’auki waya ya saka a kunne kafin yace, “ina kofar gidan ka dan Allah fito.” Abinda yace kenan ya yanke wayar ya mayar da kai ya kwantar kamar wanda aka yiwa mutuwa. Usman ne yazo yaja handle din motar yaki bud’ewa sai ta dan daki glass din ya d’ago ya kalle shi sai ya danna lock ta bud’e ya shiga ya zauna yana kallon sa yace, “Meyasa baza ka shiga ciki ba?.” Shiru bai bashi amsa ba hakan ya saka ya kalle shi sosai yaga gabad’aya ya canja yace,”kai kuma lafiya kake?.” Yusuf ya d’ago ya jingina da kujera yace, “Usman ban san me yake damuna ba.” Usman ya bishi da kallo yace, “Meya faru?.” “Yau Ammah tasan ina shan giya Usman, kuka Ammah take a gabana tana cewa Allah yayi wadarai na. Meyasa nake b’ata mata rai ne?. Meyasa dani kad’ai Amma take kuka?.” Umsan yayi tsaki cike da jin haushi yace, “Au kai tun da baka shirya wa wannan ranar ba ka fara sha giya? Da kai duk baka shirya wa b’acin ran Ammah ba kake kafa kanka a shan giya Yusuf?. Ai na d’auka ka shiryawa ranar ne ta yadda Ammah tana samun labari kasan abinda zaka yi bazata shiga damuwa ba. Ka gode Allah da bata yi maka baki bana dan abinda ka aikata ba abu bane n wasa Yusuf.” Yusuf yace, “nayi dana sani Usman, na tsani kaina, naji abinda ban tab’a ji ba. daga yau in sha Alalh bazan sake ba nayi alqawarin bazan kuma ba.” “Alqawarin na biyar kenan da kayi min akan baza ka sake ba ka daina?.” A raunane yace, “zan daina yanzu, wallahil azim zan daina, ban tab’a jin kunya kamar ta yau ba Usman, nan tab’a jin an muzanta ni kamar yau ba. Na kasa had’a ido da iyayena Usman.” Usman yace, “kunyar duniya ma kenan, ka kasa had’a ido da iyaye saboda abinda kayi sai ka tuna da had’a ido da zakayi da mahaliccin ka in ka mutu a wannan yanayin shi kuma ya abin yake?.” Girgiza kai yake cike da Dana sani da nadama da alqawarin dainawa yace, “na daina, nayi alqawari da wanda ya halicce ni, nayi alqawari da wanda yake bani ikon numfashi daga yau ni Yusuf na daina shan abinda shan. İn kuma na sake Allah kar kasa naji dad’i zaman duniya da lahira.” Usman ya kalle shi da sauri yace, “kana da hankali kuwa? Wannan fatan da kake yiwa kanka fa?.” “Dan ka tabbatar na daina ne Usman, dan ka tabbatar yanzu da gaske nake bazan sake sha ba in sha Allah. daman tsautsayi ne da zaman k’asar turawa, amma na daina kuma in sha Allah.” Usman cikin jin dad’i yace, “in da gaske kake sai nace Allah yasa hakan, zan fi kowa jin dad’i in hakan ta kasance ai.” Ya sauke numfashi sannan ya kulle ido yace, “Amin. Na gode Usman.” Usman yace, “amma waye ya fad’a musu?.” Ya kalli Usman sai Umma ya sake cewa, “to naga kace Ameena ce kawai ta sani naga kuma yanzu bakwa tare, me zai saka ta fad’a yanzu bayan tun a da bata fad’a ba?.” Yusuf ya runtse ido yace, “in kuka ambaci sunan nan ji nake kamar ana tafasa min jinina wallahi, ni kadai nasan abinda nake ji duk sanda aka ambaci sunan ta, dauriya kawai nake. Zuciyata na son sunan ta amma gangar jikina kamar Ana zuba min ruwan zafi.” Usman ya bishi da kallo yace, “tofa, to Allah ya kyauta. Waye ya fad’a mata?.” Yusuf ya sauke numfashi yace, “Asiya ce.” “Sabuwar matar ka kenan, Wato ita baza ta iya rufa maka asiri ba sai ta fad’a, tayi min daidai ai watakila silar shiryuwar taka Kenan.” “Usman ko kusa bana jin haushin ta, soyayyar ta tana nan a jikina bana so na rasa ta Usman.” Usman ya bishi da kallon mamaki yace, “wai ita Asiyan?.” Ya d’aga masa kai alamun eh Usman yace, “to waye yace zaka rabu da ita?.” Shiru yayi bai amsa ba yayi shiru Usman ya dinga binsa da kallo kafin yace, “Yusuf anya kana addu’a kuwa?.” Sai kuma Usman ya sake cewa, “to ina kaga lokacin addu’a ma?, kaje aiki ka gaji ka dawo kasha giya ka kwanta ina lokacin neman tsari da bautawa wanda ya halicce ka?.” Yusuf bai iya bashi amsa ba ya sake cewa, “lamarin ka akwai buk’atar addu’a a ciki ka mayar da hankali akan rok’on Allah komai kake ji zai zama tarihi. Amma sai kana addu’a dan gabad’aya rashin addu’a ya saka kake jin abinda kake ji a yanzu, mai taimaka maka kayi ibadar ka rabu da ita wannan kuma ba abinda tazo yi kenan ba.” Idanun sa ya bud’e ya kalli Usman yace, “zanyi.” “Ya dai kamata.” Yusuf ya kunna motar yace, “zan koma.” “Zaka iya tuk’a motar?.” Ya d’aga masa kai alamun eh Umsan ya bishi da kallo yace, “to Allah ya kiyaye” ya fad’a yana fita shi kuma ya juya motar ya koma ta inda ya biyo. Washe gari da safe Yusuf ya shirya ya hau mota kai tsaye gidan su Asiya ya wuce dan dakyar ya iya yin bacci saboda jikin sa kasa kwanciya yayi saboda babu Asiya. A k’ofar gidan su ya faka zuciyar sa ta hana shi fitowa ya kulle ido ya bud’e ya kira wayar ta a lokacin tana zaune a falo ama shan shayi sai yamutsa fuska take yi ita baza ta sha haka ba sai an soya mata Kwai. Ganin yana waya ya saka ta kalli Umma tace, “Umma shine yake waya fa.” Umma tace, “Dan banza, d’auki muji.” Ta d’auka ta saka a kunne sai kuma ta sauke tace, “Umma wai yana k’ofar gida.” Umma tayi shewa ta tafa hannu tace, “Momi tashi kije ko shigo dashi, ke kuma tashi ki koma ciki, Fauziyya tashi ki gyara falon kafin ya shigo.” Asiya ta tashi tana cewa, “ni gwara ma na koma na jima ban sha shayi babu madara ba sai yau” ta fad’a tana shiga ciki. Kwashe kayan falon akayi da gaggawa aka fesa air freshener kafin suji sallamar Yusuf ya shigo, Umma ta masa tana cewa, “maraba, shigo ka zauna mana kamar bak’o.” K’arasowa yayi jikin sa a sanyaye ya zauna a kan carpert yace, “Umma barka da safiya.” “Barka dai Yusuf, an tashi lafiya.” “Lafiya lau, a same ku lafiya.” “Lafiya lau muke.” Yusuf ya gyara zama yace, “Umma nazo mu koma da Asiya ne, in sha Allah abinda ya faru bazai sake faruwa ba, nayi kuskure wannan shine ma k’arshe.” Umma ta gyara zama tace, “yanzu naji batu ai Yusuf, da ace kana dukan yarinya da cikin ka a jikin ta kamar baka sonta?. Har suka girma ban tab’a dukan su ba sai dukan wasa, akan me ka d’auke ta da haqoranta guda talatin a bakin ta ka ce zaka dake ta?, kaima kasan ai kuskure ne hakan baka yi daidai ba. Kar a sake wannan kuskuren dan anayi na gaba bazan d’auka ba wallahi.” Yusuf yace, “anyi na k’arshe da yardar Allah.” “Sai batu akan giya, Gaskiya baba amince yarinta ta zauna da dan giya ba, haka kawai kaje ka shayu kazo ka cillo ta taga ka balla min ita ka cuce ni ba.” Kamar zai zubar da hawaye haka yake ji, zuciyar sa na bashi umarnin ya tashi ya bar musu gidan amma ya kasa sai yace, “Shima daga wannan baza’a sake ba in sha Allah, ayi hak’uri.” Umma ta bishi da kallo tayi murmushi tace, “to yayi kyau. Sai kuma kudin da aka kashe da aka kaita asibiti, Mun kashe dubu d’ari biyar saboda asibitin kud’i muka je, ka bada kudin yanzu.” Yusuf yace, “sai dai bani account number na saka.” Umma ta kalli Maimuna tace, “bashi ya saka.” Maimuna ta karanto masa yana rubutawa kafin yace, “na saka kudin.” Umma tace, “ina zuwa bara na turo maka ita dan tayi fushi akan lamarin sosai.” Yana zaune Umma ta tashi ta shiga ta samu Asiya har ta saka kaya Umma tace, “au har kin shirya ma kenan?.” Asiya tace, “to ga gidana inda zanje naci abinda nake so nan an bani bak’in shayi babu madara.” Umma tace, “aikin mu ya kama shi sosai, duk aikin da muke ma zan iya cewa sai yanzu ya shiga jikin sa tunda kika ga ya kawo kansa har yana neman a bashi ke ku koma. Lokacin mulkin ki yayi yanzu sannan lokacin da zaki tara mana yayi.” Asiya tace, “Allah yasa dai, wani lokacin kamar aikin ya kama shi sai kiga ya sake komawa daidai.” “Wannan ya kama shi kenan kuma ai. Yanzu ina abinda yace kin d’aukar masa dan nasan kin d’auka wallahi.” Asiya tace, “Kai Umma, sark’a ce fa tana nan kuma.” “Ki turo da ita a siyar a ajjiye kudin.” Asiya ta turo baki tace, “to Umma duk abinda na tara indai zan dinga aiko muku ai bazan tashi da komai ba kenan.” “To dan uban ki kin san kudin dana kashe kafin ma ya aure ki? Bana son shashanci da shirmen banza in badan ni ba kin isa ma ya aure ki kina fama da wannan shegiyar k’azantar?.” Ta saka hijjabin Momi tace, “Nidai a bar min sark’ar zan samo kud’i na turo miki dashi.” Momi da ya shigo tace, “kika saka min hijjabi? Wallahi ki cire min domin sai ya kwana goma yana warin jikin ki.” Umma tace, “meye haka ke kuma?.” Momi ta Harare Asiya tace, “Wallahi Umma in ta saka duk wankin da za’a yi masa kafin ya fita sai an sha wahala.” Asiya suka fito ita da Umma yana ganin Asiya sai yayi murmushi amma zuciyar sa kuka yake yi ya mik’e tsaye Umma tace, “gata nan na sake dawo maka da ita Yusuf kar wani abun ya sske faruwa dan Allah.” Yusuf yace, “in sha Allah babu abinda zai kuma faruwa.” “A’a Yusuf.” Baba ya fad’a yana shigowa. Yusuf ya tsuguna har ‘kasa ya gaishe shi ya amsa yana cewa, “Yusuf ka tsaya tsayin daka akan iyalan gidan ka, kar ka bari wani ki wata ta shiga tsakanin ka da iyalan ka, in namiji bai zama tsayayaye a gidan sa ba zai zama tamkar bola a wajan matar sa komai ta d’auko zata watsa masa ne, koda yaso gyarawa a gaba bazai yu ba domin ya riga yayi sake tun farko ya bar ragamar gidan sa a hannun mace. Ina mai baka shawara da kar ka bar ragamar gidan ka a hannun mace domin nan gaba zaka yi dana sani. Sannan ka tsaya ka nutsu akwai abinda bazai gyaru ba koda kayi k’ok’arin gyarawa domin hakan ya samo asali tun daga tushe, haka zaka gaji da magana ka gaji da yawo k’arshe sai ka bar wannan abun hankalin ka zai dawo jikin ka. Ka kuma dinga addu’a rashin ta yana daga cikin abinda ya kawo ka nan.” Shi dai Yusuf gabad’aya ya rasa gane inda maganar Baba ta nufa amma sai yayi murmushi yace, “In sha Allah.” Baba yace, “Allah ya kiyaye hanya ya bada zaman Lafiya” ya fad’a yana shigewa ciki Yusuf suka fita. Umma tabi bayan Baba zuwa d’aki tace, “malam me kake nufi da bayanin da ka yiwa Yusuf?.” Baba ya kalle ta yace, “in kina tunanin akwai abinda nake nufi to ki d’auka akwai din kawai.” Umma tace, “in ma dai zuga shi kake akan Asiya wallah babu abinda zai faru In sha Allah, Haba ni tab’a ganin uban da yake yiwa yar sa bak’in ciki ba sai kai” ta fad’a tana fita yayi dariya ya girgiza kai domin kuwa yasan za’a gab’ar da Yusuf zai dawo da Asiya gida. Bayan kwana biyu. Bikin Rukayya ya kankama ana ta shirye-shirye ta ko wanne b’angare babu kamar gidan su Rukayya da ake fito da tsofaffin ajiyar kayan kitchen da aka siya mata ana wankewa. Amarya Rukayya ita da Ameena da Zakiyya suke shirin su sun d’auke mata kewa gabad’aya sun cire mata fargabar auren Ibrahim ta sake sosai dashi suna shansoyayya dashi. Ya rage saura sati d’aya ta tare suna zaune ita da Zakiyya suna jiran Ameena tace zata bata zo ba Rukayya tana yi mata waya sai gata ta shigo Rukayya tace, “Na d’auka baza kizo ba ai.” Ameena tace, “Yaya ne baya barina fita wallahi, dakyar ya barni nazo m yanzu ma wallahi.” Zakiyya tace, “eh gashi nan ai sai kyau kike yi wallahi kin mayar da jikin ki kamar ba ke ba.” Tayi murmushi tace, “ke wai har yanzu ba’a samu Fiddausi a waya bane? Rashin samun nan nata yayi yawa sosai.” Zakiyya tace, “Bari kawai, wallahi shiru ba’a samun ta ta ko wanne bangare. Amma yanzu gidan su zan shiga wajan Mama naji ko sun samu labarin ta.” “Ya dai kamata wallahi, ke baki da lambar Alhajin?.” “Wacce nake da ita batayi yanzu wallahi.” “To Allah yasa dai Lafiya” Rukayya ta fad’a tana zama kusa dasu. Suka amsa da amin Ameena tace, “yanzu ya ake ciki?.” “Jiya baki zo ba muje gidan amarya, ke kinga gidan İbrahim Ameena?” Zakiyya ta fad’a tana dariya kafin tace, “hmmm gida mai kyau da falo da dakuna ke baki gani ba, komai ma sha Allah babu inda ba’a sakawa kaya ba nace daman wannan ai shine bikin y’ar gata.” Ameena tace, “Alhamdulillah, haka muke so ai, nima nazo a kaini in Yaya ya barni. Ya batun maganin kin Shan na sanyin?.” Rukayya tace, “eh Zakiyya ta bani na wajan wannan Surayya Halin yau din gaskiya yana da kyau sosai nima na gani.” Ameena tace, “to kar dai kice zaki sha wani kayan matsi ko wani abun, kije masa a natural taste din ko ya kika je Zakiyya?.” Sukayi dariya tare da tafawa Zakiyya tace, “Gaskiya ne wallahi. Abin mamaki wai Rukayya matar Ibrahim ce a yanzu, ikon Allah kenan.” Ameena tace, “babu mamaki an ikon nasa ai daman Kiyya. Yanzu me kike ganin zaki gabatar a bikin?.” Rukayya tace, “ni babu komai wallahi, da zaku zo dai a hadu ayi saukar alkur’ani zai fi min dad’i.” Ameena tace, “me zai hana muzo? Bikin kine fa Ruky.” Zakiyya tace, “zamu zo in sha Allah, Allah dai ya nuna mana wannan lokaci.” Suka amsa da amin suka cigaba da hirar bikin. A gidan su Fiddausi Maman su ce a tsaye tana jiran Abban su ya fito daga d’aki yana fitowa tace, “Alhaji.” Ya tsaya ya kalle ta yace, “Lafiya dai?.” Mama tace, “Fiddausi.” Abba ya gyara ta tsayuwa yace, “me ya same ta?.” “Malam rabon da mu samu Fiddausi a waya har mun manta, mun rasa dalilin da ya saka bama samun ta a waya dan Allah ko zaka taimaka a kira mana mijin nata ko hankalin mu zai kwanta,” Abba ya kalle ta yace, “Ni nake da lambar mijin ta?.” Mama tace, “na d’auka kana da ita ai.” “Auren da kuka d’aura shi bana nan an ina zan samu lambar sa? Kije ki samu Kawun ta ai ta inda aka hau ta nan ake sauka ya samo muku lambar sa sai kuyi magana.” Mama tace, “munyi magana dashi yace baya samun lambar sa, dan Allah Alhaji ka daure ko wani daga gidan dangin mijin nata ne a nema a tambaya. Hankalina ya tashi wallahi ko Lafiya ce ta haifar da shirin ya kamata mu sani.” Alhaji yace, “babu wanda na sani a dangin mijin ta ki koma wajan wanda ya bada auren nata ki tambaya bani ba. Baku sam mutum ba baku yi bincike a kansa ba kuka d’auki yarinya kuka bashi a cikin sati biyu kawai dan kar na dawo na hana auren akayi aka kaita Abuja a jirgi. Watakila dan yankan kaine ya kai an yanke mata kai amfanin ta ya k’are a wajan sa.” Mama tace, “Haba Alhaji, dan Allah ka daina fad’ar wannan maganar mahaifin tane kai fa.” “Kun bani mahimmacina ne a lokacin auren? Ba aurar da ita kuka yi ba kuka kaita ai ta samu gidan mai kudi. Bara na fad’a miki abinda baki sani ba Fiddausi da kanta ta kashe auren ta, wannan wanda ku ka bata auren sa ya jima suna tare dashi shine ya zuga ta ta kashe auren ta da Ibrahim ai talaka ne zata auri mai kudi.” Mama tace, “Haba Alhaji taya zata aikata haka da ilimin ta fa?.” Zaiyi magana Kenan Zakiyya tayi sallama ta shigo ta durk’usa har kasa ta gaishe su bata d’ago ba tace, “Mama dan Allah ana samun Fiddausi a waya kuwa?.” Alhaji ya kalli Mama yace, “ki bata amsa ba’a samun ta a waya baku san ta wacce hanya zaku nema ta ba, ba dai ta d’ora rayuwar ta akan motar kwad’ayi da hange ba? Wallahi a tashar wulakanci zata ajjiye ta” ya fad’a yana saka hular da ya fita Mama ta bishi da kallo kamar zatayi kuka. Mama ta kalli Zakiyya da ta mik’e tsaye tace, “Zakiyya jikina yana bani wani abun ga samu kawar ki.” Ta fashe da kuka Zakiyya tace, “in sha Alalh babu abinda ya faru mama, Kawu bai San dangin sa ba?.” Mama tace, “Zakiyya duk waliyan da ya kawo na karya ne, sunan sa dai shine amma komai da yayi amfani dashi na k’arya ne. Ban san a wanne hali Fiddausi take ciki.” Zakiyya tace, “in sha Allah tana cikin kwanciyar hankali, zan saka a bincika in da hali ma zanje har Abuja gidan da aka kaita na dubo na gani.” Mama tace, “anje har gidan, yayar su taje ita da mijin ta har gidan an tabbatar musu da babu mutane a cikin gidan, hankalina ya tashi sosai ban San abinda yake faruwa da ita.” Zakiyya ta girgiza kai da mamaki lamarin da kuma tsoro tace, “zamu dinga addu’a in sha Allah babu komai, zamu samu wayar ta Mama kar ki damu.” Mama ta girgiza kai ta wuce d’aki ta bar Zakiyya a wajan itama ta juya ta fita jikin ta a sanyaye tunanin ta ya tafi wajan meye ya samu Fiddausi ba’a samun ta a waya…?. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid Book3 017             Yusuf ya canja gabad'aya ya rame sosai ko yaushe yana gıda babu inda yake iya zuwa ko yaushe ka ganshi cikin tunani yake shi kansa bai San abinda yake damun sa ba balle ya nema wa kansa magani. Yana zaune a kan kujera yayi shiru yana tunani cikin kwanakin da ya rufe idanun sa Zaytun yake gani da Ameena amma ya rasa me yake jawo hakan. Ga zuciyar sa ta dinga bugawa a duk sanda ya tuna su sai yaji ruwa yana k'ok'arin taruwa a cikin idanun sa. Asiya ce ta shigo tana kallon sa ta zauna tace, "My love me yake damun ka?." Ya kalle ta ya zauna sosai yace, "babu komai." Ta tab'e baki ya sake kallon ta yace, "har kin dawo daga bikin?." Ta cire mayafi tace, "eh wallahi, gidan zafi shiyasa na dawo." Baice komai ba yayi shiru yana kallon tv badan yana fahimtar abinda ake cewa ba sai dan ya tsani doguwar magana da ita. "My love ina buk'atar a canja min mota gaskiya." Ya d'ago ya kalle ta yace, "har yaushe aka siyi motar da za'a canja miki?." "Ai ko jiya aka siya dan nace a canja min yau ba wani abun bane ba Tunda akwai kud'in, kawai in za'a canja a canja in baza'a canja ba sai a fad'a min." Banza yayi mata bai amsa ba ganin bai amsa ba sai tace,  "Sannan kayan abincin gidan mu ya k'are fa, wai kana sane da wata yayi nisa amma baza a siyi abinci a  aikata su Umma ba, Haba wannan fa ba daidai bane kana gani ga azumi yana gabatowa haka za'a shiga Ramadan din sai na tuna maka zaa kai musu abinci?." Yusuf ya kalle ta yace, "na manta ne amma yanzu zan saka a kai musu." Asiya ta girgiza kai cikin b'acin rai tace, "in su Ammah ne baza ka manta ba." Da sauri ya kalle ta  yace, "ke wai ban miki warning akan sakoAmmah a cikin maganar mu ba? Meyasa baki da mutunci ne wai?. Iyayena daidai suke da iyayen ki ne?." Ta murgud'a baki bata ce komai ba shi kuma yayi tsaki ya mik'e dan da ace ta tanka masa da Allah kadai yasan abinda zai mata ya bar wajan. Sama ya hau ya tsaya a bakin taga yana kallon mai shigowa, ya rasa meyasa ya kasa d'aukar mataki akan Asiya duk abinda yake masa, ya rasa meyasa take masa abinda taga dama yake iya shiru ya kyale ta. Ya sauke numfashi ya kalli wajan tagar sosai ganin mata suna shigowa harabar gidan wajan Ameena, ganin ana ta magana dasu sai ya bud'e window din yace, "Baba Lafiya?." Baba ya d'aga kai ya kalli Yusuf yace, "Alhaji wajan Hajiya suka zo." Yusuf yace, "barsu su shigo" ya fad'a yana kulle window din ya sakko shima dan yaga kamar ba Lafiya ba. Yana sakkowa sun gama shigowa falon d'aya daga cikin su ta nuna Asiya da take zaune tace, "gata nan, wallahi itace ta d'auka na ganta ganin idona, ashe matar gidan nan ce." Asiya ta mik'e tana kallon su duk da taji tsoro sossi amma bata nuna ba tace, "ku kuma lafiya kuka shigo min gida? Su waye ku?." D'aya daga cikin su tace, "ai nasan kin gane ni kuma wallahi ke kika d'auki zoben, ko ki fito dashi ko kuma na had'a ki da y'an sanda yanzu wallahi." Yusuf da ya ke kallon su yace, "Dan Allah ayi abun a nutse, Meya faru?." Wacce take maganar tace, "ai naga tazo da rainin hankali, kuma wallahi in bata fito da zoben nan sai dai hukuma ta raba mu." Asiya tace, "an ina na sanku har muka had'u da zan d'aukar muku zobe? Dan kun raina min hankali kaf gidan bikin a rasa wacce za'a ce tayi sata sai ni? Ku kalle ni ku kalli gidana Kun san nafi k'arfin nayi sata wallahi." "Ke da kika ce baki san inda muka had'u ba taya kika san a gidan biki muka had'u?." Asiya ta dan rud'e amma bata nuna ba ta kalli Yusuf tace, "My love ban san wad'annan mutanen ba akan me zasu zo gida na suna cemin barauniya? Nayi kama da mai sata ne?." Wacce take tsaye bata ce komai ba ta kalli Yusuf tace, "Zoben da ake magana a kai nawa ne, a kalla kudin sa ya kai miliyan biyu da wani abun. Wallahi in bata fito da zoben nan ba hukuma ce zata raba mu." Yusuf yace, "ku ya akayi kuka san itace ga dauka Tsakani da Allah?." "Saboda na kamata tana bincika min a jaka, dana kamata sai tace min tissue take nema ban d'auka barauniya bace na d'auka mace ce mai aji wacce dan ta duba jaka ta ba komai bane ashe mai halin b'era ce. Ina kwatanta ta aka ce min itace kuma halin tane na biyo ta ta bani, wallahi ko ki bani zobe na wallahi ko ki kwana a wajan y'an sanda." Asiya tace, "babu abinda zan bayar saboda babu abinda na d'auka." Wacce take magana da Yusuf tace, "haka kika ce?." Asiya tace, "eh haka nace." Tayi kwafa ta juya ta zata fita Yusuf yace, "dan Allah ki tsaya abun bai kai haka ba" ya kalli Asiya yace, "in kin san kin d'auka ki fito musu da abin su." "Yanzu my love kaima kana tunanin na d'auka din ne? Babu abinda na d'auka balle na bayar barazanar su baza tayi min komai ba." Basu ce komai ba akwai suka juya suka fita Yusuf ma bashi da ta cewa ya kalli Asiya yace, "Asiya" tayi saurin dakatar dashi tace, "ban d'auki komai balle na bayar ka gane ko?" Tana fad'a ta bar wajan ya tsaya ya rasa abinda yake masa dad'i ya zauna a wajan yana tunanin tsautsayin da ya kai shi auren Asiya a cikin rayuwar sa gabad'aya. Kusan mintina ashirin da fitar su sai ga su sun dawo da y'arr sanda mace suna shigowa Asiya na sakkowa da jaka da mayafi zata fita tace, "Yauwa gata nan."  Jin magana ya saka Yusuf tasowa ya fito yana kallon su yace, "Officer Lafiya?." Matar ta kalle shi tace, "ta d'auki abu kuma tayi gardama shiyasa na nuna mata bani da mutunci wallahi sai ta fito dashi." Asiya ta tsorata ta kalli Yusuf tace, "my love babu abinda na d'auka." Yar sandar tace, "Ko ki fito dashi a yanzu ko kizo muje can sai ki fito dashi." Ta rik'e Yusuf tace, "kar ka bari a tafi dani ban d'auki komai ba Kaga kuna ciki ne dani dan Allah kar ka bari a tafi dani." Yusuf ya kalle ta yace, "Dan Allah Kuyi hakuri abin duk bai kai haka ba, matar aure ce kuma juna biyu ne da ita zubar da mutunci ne ace an ganta a police station. Dan Allah ku tsaya muyi magana ta fahimta." "Ai ta nuna taurin kaine shiyasa na nuna mata na fita iya iskanci. Da ta tashi satar ai ta manta ita matar aure ce tayi dan haka nima zan manta da Hakan, officer ki kama ta muje kawai." Yusuf yace, "baza'a yi haka ba, dan Allah ku zauna muyi magana wacce zamu fahimci juna." Officer tace, "Ai matar taka ce take  da taurin kai da basai nazo nan ba, da ta amsa ta bayar duk da ba haka ba amma ta k'i." "Nifa babu abinda na d'auka, duk abinda za'a yi sai dai ayi amma ban d'auki komai ba babu wanda zai kama ni kuma." Yar Sandar ta kalli Yusuf tace, "kayi hak'uri kawai zamu je da ita." Yusuf yace, "baza'a yi haka ba dan Allah kiyi hak'uri" ya kalli Asiya yace, "Asiya ki saita harshen ki." "Bazan saita ba, haka kawai azo har gida ayi min sharrin sata a gaban ka kuma ka yarda?. Babu Wanda ya isa ya kama ni kuma wallahi sai nayi k'arar su suma." Yusuf ya rasa abinda zai ce sai kallo kawai yar sandar tace, "indai kin san kina da gaskiya kizo muje yanzu zaki dawo." Asiya ta kalle shi taga yayi shiru sai tayi tsaki tace, "muje din sai me" ta fad'a tana bin bayan su suka fita shi kuma dai Yusuf yana tsaye yana kallon su domin kuwa gwara ma aje da ita din watakila tayi hankali nan gaba kar ta sake dan ya tabbatar tayi. Sai bayan sun fita ne ya tuna ya kamata ya bisu ya fito amma kafin ya hau motar ya fita ya neme su ya rasa. Waje ya samu kawai ya faka ya tsaya ba tare da yaje ko ina ba zuciyar sa tana fatan Allah yasa suyi mata dukan tsiya kowa ya huta. Yana cikin motar Abbah ya kira shi yana d'auka yace, "kana ina?." Yusuf yace, "ina mota." "Yanzu DPO din police station din nan na cikin gari ya Kira ni wai har gida an kama matar ka tayi sata, kai kana ina?." "Abbah a gabana suka tafi na rasa me zanyi, nace ta fad'a in ta d'auka tak'i sai rashin kunya take musu shiyasa ban hana su tafiya da ita ba gwara taje tayi hankali." Abbah yace, "Baka da hankali ai, malam ka wuce kaje ka fito da ita In ma ta d'auka ka d'auki alhakin biyan kudin zoben ku dawo gida." Da to kawai ya amsa ta kashe wayar yana d'auki hanyar station din. Yana zuwa yaga Asiya a zaune a gaban DOP ana magana tayi shiru ta sunkuyar da kai ga zobe nan kato a kan table din sa. Ganin Yusuf ya shigo ya samu waje ya zauna suka gaisa da shi ya kalli Yusuf yace, "ai ban san matar ka bace sai da tayi min bayani da cikakken sunan ka gashi bani da lambar ka dole na kira Alhajin ka na sanar dashi." Yusuf yace, "yanzu ya ake ciki." "Ga dai zobe ta fito dashi, Gasu a zaune zan basu abin su a kashe case din a nan komai ya wuce. Dana san matar kace ma da baza'a zo nan ba wallahi amma komai ya wuce ai." Ya d'auki zoben ya mik'a musu yace, "ga zoben ku." Ta taso ta karb'a yace, "an rufe wannan case din tunda ga abun ku ya fito, koda nan gaba kar a sake tayar da maganar nan." "Shikenan ranka ya dad'e, ai da ta fito dashi tun farko da ba'a zo nan sai tak'i tana yi mana taurin kai." "Yanzu dai komai ya k'are." "Shikenan ranka ya dad'e." Ya kalli Asiya yace, "ke ki basu hak'uri." Ta kalle su tace, "kiyi hak'uri." Mai zoben ta Harare ta tace, "babu komai ya wuce." Ya kalle su yace, "na sallame ku" sukayi sallama suka fita. Bayan sun fita ya kalli Asiya yace, "koda nan gaba ki daina wannan gangancin, mijin ki babban mutum ne haka mahaifin sa hakan ba k'aramin b'ata masa suna zaiyi a duniya ba." Asiya tace, "baza'a sake ba in sha Allah." "To ma sha Allah. Yusuf zaku iya tafiya babu komai yanzu komai ya wuce." Yusuf ya tashi tsaye suka sake gaisawa dashi sannan ya kalli Asiya ya fita itama ta tashi sum sum tabi bayan ta. Ko a mota baice mata komai ba itama bata ce ba har suka isa gida ya faka a bakin gate yace, "ki shiga gıda." Bata ce komai ba ta bud'e ta fita shi kuma yana motar ya nufi gidan su. Sai da ya tsaya yayi sallar magriba sannan ya shiga gidan ya samu kuwa kaf yayyen sa suna nan mazan da k'anin sa ya shiga da sallama ya zauna baice komai ba. Kallon sa dukkan su suke yi kafin Humaira tace, "Yaya Yusuf lafiya kake kuwa?." Bai ma ji abinda tace ba ganin yayi shiru bai amsa ba ta kalli Abbah sai Abbah yace, "Kai Yusuf lafiya kake kuwa?." A sannan ya kalli Abbah yace, "Abbah mai kace?." "Lafiya lau kake kuwa? Kaga yadda ka koma?." "Babu komai Abbah." Ammah da take gefe face, "to ana samun lafiya a wajan mai sab'awa Allah ne? Mtsww har a tsaya tambayar Yusuf Lafiyar sa Qalau dan b'ata lokaci?." Yusuf yayi shiru tun abinda ya faru a gidan Asiya tace yana shan giya shikenan ko murmushin Ammah ya daina gani yazo ya bata hak'uri yace ya daina amma tak'i yafe masa kuma har zuciyar sa daga wannan lokacin bai sake koda kallon abin ba, tunanin ta ma ya daina balle ya aikata hakan. Abie ya kalle ta yace, "Dan Allah Ammah ki bar batun nan haka, Yusuf ya daina wallahi ni na tabbatar da hakan ba tun yanzu ba. Tun daga wannan ranar bai sake ba." Tayi tsaki kawai bata ce komai ba. Abbah yace, "Yacase din matar taka?." Yusuf ya kalli Abbah yace, "anga zoben an basu sun tafi." Abbah ya jinjina kai yace, "to Allah ya kiyaye gaba, sai kayi mata fad'a tasan inda zata dinga d'aukar abun magana." Ammah tace, "ga b'arauniyar dai ta bayyana, yanzu aka fara ai badai kace marainiyar Allah ba komai bace? Badai ka sab'a alqawarin da ka d'auka ba?. Hmmm ayi dai mu gani" ta fad'a murmushi tana kallon wani wajan daban. Yusuf yayi shiru baice komai ba sai yaji zaman wajan ya ishe shi  sai ya mik'e ya yiwa Abbah sallama ya fita daga gidan. Abbah ya kalli babban yyayan su yace, "Anya lamarin Yusuf babu wani abun kuwa?." Abie yace, "nima na gani Abbah, munyi magana da Umsan yace min gaskiya a dinga amsa addu'a yarinyar da yake tare da ita kamar ba haka ga barshi ba gaskiya." Ammah tace, "Qalau yake fa sakayya ce kawai take bibiyar sa, tun ba'a je ko ina ba ai gashi ya fara ji a jikin sa ina ga nan da kwana biyu?. Ga b'arauniya nan dai ya d'auko ya kawo har gidan sa." Abbah yace, "koma meye Allah ya kawo k'arshen sa, satar da yace Ameeena tayi masa ga b'arauniya nan ta bayyana yanzu, babu abinda kuma zai iya yi mata" ya fad'a yana tashi ya fita saboda sallar I'sha.                   Bayan kwana biyu. Yau ta kama ranar Alhamis ranar ake taron saukar alkur'ani na bikin Rukayya su Ameena ne a gaba ita da Zakiyya ana ta karatu sai da aka sauke alkur'ani a gidan sannan aka ci abinci mai rai da lafiya abin rabon da Ameena tayi mata aka raba a wajan kowa ya tafi da murna a fuskar sa gwanin burgewa. Bayan an watse Ameena ita da Zakiyya da Rukayya suna zaune suna zancen Fiddausi Ameena tace, "rashin jin Fiddausi ya fara damuna wallahi, abin yayi yawa sosai." Zakiyya tace, "bari kawai, ni kaina ya dame ni ga wata damuwar." Rukayya tace, "meye kuma?." "Baban Fahad mana ya tabbatar min da ko na zubar da cikin jikina ko ya sake ni." A tare suka had'a Baki suka ce, "Saki kuma?, akan ciki?." Zakiyya tace, "Saki wallahi, abin ya d'aure min kai sosai cikin halak bana shege ba amma yace zai sake ni a kai." Ameena tace, "Akan me to?." "Wai baya son haihuwa yanzu, baiyi niyar yinta ba ban kuma isa na saka yayi ba." Rukayya tace, "ikon Allah, yanzu ya za Kiyi?." "Ban sani ba wallahi kaina ya kulle gabad'aya nima damuwa tayi min yawa, sabbin halaye ya samo Wanda a baya da ita ko kad'an." Ameena tace, "to Allah ya kawo mafita, amma kar ki zubar da ciki gaskiya ki bari zaku daidaita." Ta amsa da amin  suka cigaba da tattaunawa akan lamarin kafin ko wacce ta tafi. Washe gari juma'a bayan sallar juma'a aka saka Rukayya a gaba ana nasiha wannan yace wannan wannan yace wancan, dangi a taru ana biki kowa yana fad'ar albarkar bakin sa. Gıda ya cika sosai da mutane ana ci ana sha cikin wadata da farin ciki. Rukayy tun tana ganin abun kamar wasa sai da ta tabbatar gaske ne a lokacin aka kai ta gidan su İbrahim wajan iyayen sa kafin a dawo da ita gida da yamma Baba ya saka ta a mota ya tafi kaita gidan ta kansa ba tare da anyi taron kai amarya kowa yaje kafin zuwan ta. #Book3 Book3 018 Amarya a gidan ta tayi sallar magriba tana zaune bayan ta idar tana k’arewa falon kallo madaidaici mara girma sosai kuma ba k’arami ba an saka mata kujera saiti d’aya da table a tsakiya a kan carpert din da yake tsakiya mai kyau mai gashi kamar jikin mage. Tv tana ajjiye Akan tv stand madaidaici itama tv ba babba ba sosai kuma ba k’arama bace ba. Falon sosai ya burge ta duk kyaun da ake ce mata yayi sai taga yama fi haka san kana ganin sa kaga na amarya dole ya burge ka, da yake akwai hasken wuta ko ita yayi tarr gwanin ban sha’awa sai d’aukar ido yake yi kamar ka d’auke shi ka saka a jaka. Hawayen da take rik’ewa ne suka sakko mata ta goge da sauri dan bata son zubar da hawaye akan tunanin da yake ranta, ganin abun take kamar a mafarki wai wannan gidan ta ne komai na cikin sa nata ne, yanzu tayi aure tana zaune a gidan ta zaman gidan su sai dai taje ziyara ta dawo ta bud’e wannan tace gidan tane. A bayyane tace, “Allah mai iko mai kuma yadda yaso.” Bata goge hawayen ba bata kuma daina kallon falon ba ta tabbatar ba mafarki take ba gidan mijin tane da Baba ya kawo ta da kansa tayi zaman aure a cikin sa. “Asslamu alaiki” aka fad’a ana shigowa falon sai ta kalli inda taji sallama suka had’a ido da İbrahim da ya shigo yana sanye cikin shadda blue dinkin babbar Riga yayi kyau sosai fuskar sa d’auke da annuri kamar ko yaushe yana kallon ta. “Fuskar amaryar a bud’e sannan kuma ga hawaye tana yi kuma ta kasa daina kallon angon nata” ya fad’a cikin tsokana yana kallon ta sai tayi saurin d’auke kanta ta kallo kasa amma bata rufe fuska ba sannan kuma goge idanun ta ba. Murmushi yayi mai sauti ya shigo yana kallon ta ya dawo kusa sa ita ya zauna akan carpets kamar yadda take kansa ta yana k’asa hawayen bai kuma daina zuba ba sai ma sake yawa da hawayen yayi ya zuba mata ido kawai yana kallon ta, “Yanzu wannan hawayen da yak’i tsayawa na meye Rakiya? Na farin ciki ne ko kuma na akasin sa?.” Bata ce komai ba ta saka hannu ta goge idanun nata bata d’ago ba har lokacin balle ta sake kallon sa, sautin murmushin sa taji sai ta d’ago ta kalli gefen sa ta gefen ido sai suka had’a ido yayi dariya ganin tayi saurin d’auke fuskar ta yace, “ana kiran sallar Isha zanje nayi sallah na dawo” ya fad’a yana tashi tsaye yace, “amma dan Allah kafin na dawo hawayen nan su tsaya ganin su yana sakawa wani abu ya d’arsu a raina sai naga kamar baki farin ciki da kasancewa a gidan nan” ya koma ya tsuguna a gaban ta ya saka hannu ya d’ago fuskar ta idanun ta suna kallon kasa yace, “ganin hawaye a wannan fuskar yana tab’a zuciyar Ibrahim, dan Allah ki daina zubar da hawaye yana sakawa naji d’aci a zuciyata.” Naga motsa ba balle ta dago kai yace, “ki d’ago idanun ki ki kalle ni.” Bata d’ago ba yayi murmushi yace, “baza ki d’ago ba?.” “Za’a tayar da sallah” ta fad’a a hankali tana motsa bakin ta cikin salo na musamman. Har cikin ransa yaji d’adin yin maganar da tayi yayi murmushi yace, “in na fasa zuwa masallacin fa?.” Ta d’aga ido ta kalli fuskar sa tace, “sallar fa?.” “Sai nayi da matata, ko akwai aibu a hakan?.” Ta sake mayar da idanun ta k’asa bata ce komai ba ya tashi ya fita. Kallo tabi wajan dashi tayi shiru na wani lokaci kafin ta tashi itama ta tayar da sallah. Har ya dawo bata idar da sallah ba sallah take tayi kamar baza ta tsaya ba ya zauna yana kallon gidan sosai ya masa kyau kamar ba mallakin sa ba. Har mamaki yake wai wannan gidan mai kyau da tsari mallakin sane shi Ibrahim, abun yana masa dad’i sosai dan shi kansa yasan abubuwa da yawa sun canja a rayuwar sa. A lokacin ta idar zata tashi daga inda take yace, “kar ki taso, bara nazo muyi wata sallar.” Ta koma ta zauna ya taso sukayi sallar kamar ko wacce amarya da ango. Bayan sun idar ya kalle ta yace, “Kici abincin ko?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “bacci nake ji.” “Zaki iya ci ai sannan ki yi bacci.” Ta sake girgiza kai yace, “meyasa?.” “Dare yayi in naci na kwanta zan ji kamar zanyi amai.” “In kika ci ba sai ki k’i kwanciyar ba.” Ta d’ago ido ta kalle shi tace, “to me zanyi?.” Ya d’an bud’e idanun sa yace, “kina so kusan abinda zakiyi?, kina so kice ma baki sani ba? Lallai ma to na fad’a miki?.” D’auke idanun ta tayi bata bashi amsa ba ya tashi yace, “sai kinci abinci ba’a kwanciya da yunwa a gidana.” Abincin ya bud’e mata a roba irin ta wajan biki fara harda cokalin roba a kai alamun siyowa akayi daga wani wajan abincin yace, “ki d’auka kici ko kuma na zauna na baki da kaina.” _na shiga uku, wai wannan mutumin daman haka yake? Ni duk ya takura ni wallahi._ abinda take fad’a a zuciyar ta kenan sai taga ya zauna kusa da ita ya bud’e robar cikin nutsuwa kamar ko yaushe yace, “rashin cin abinci bazai hana abinda yake zuciyar ki, cin abincin ma bazai hana ba. Tunda kin san da hakan kin san kuma sai ya faru meyasa baza ki ci ba kawai ki huta? Rashin ci ai ba mafita bane ba.” Ya fad’a yana bud’e robar ba tare da ya kalle ta ba. Gaban ta fad’uwa yake sosai ta kalli abincin bata fara ci ba sannan bata motsa ba yace, “kici abinci.” Hannayen ta ta fito dasu daga cikin mayafin ya kalli hannyen ta farare marasa kauri sosai tasha kunshi gaba da baya yayi mata kyau sosai a hannun kamar an d’ora shi a kai. Hannun ta rik’e ya bud’e tafin hannun ta yana sake kallon zanen kunshin yace, “yau na rik’e hannun matata Rakiya.” Yana d’ago ido suka had’a ido da ita sai ya kawar da kai yayi dariya yace, “ko na tab’a rik’ewa ne ake kallona?.”sai yayi murmushi dan yasan baza ta bashi amsa ba tace, “kina son kallon mijin ki amma ban San meyasa da Mun had’a ido sai ki kawar da fuska ba.” Abincin ya d’iba a cokali ya kai bakin ta amma bata karb’a ba yace, “na gane, bakya cin shinkafa kin fi son kazar ki ko?.” Da sauri ta kalle shi sai taga ya d’aga mata gira sai ta saka kawar da kai zuciyar ya bugawa take tana so ya fahimci halin da take ciki amma bazai yu ba ya sake da ita sosai baya jin wani nauyin ta ko kunya kamar sun shekara haka yake mata magana baya jin komai ita kuma ba haka yake ji ba. Sai kuwa ya tashi ya d’auko wata ledar ya ajjiye mata yace, “to gata ai sai ki ci.” Babu abinda take tunawa sai lokacin da aka kai Fiddausi gidan sa itace kan gaba wajan Karb’ar kudi a hannun abokan sa na siyan baki, suna ta yiwa Fiddausi rad’a ana dariya suna ce mata sai sunzo jinya ana tayi mata tsokana irin ta k’awaye balle ita aka fara aurarwa a cikin su. Tunanin ya dabaibaiye zuciyar ta ta kasa kawar dashi. a wannan lokacin shiyasa ta kasa sukuni kwata-kwata. “Rukayya tunanin me kike?.” Ta kalle shi ta girgiza kai alamun babu yayi murmushi yace, “Kici abinci ki bar wannan tunanin babu abinda zai miki.” Haka kuwa akayi ta d’an ci abincin kad’an tace, “ya ishe ni.” Baice komai ba ya rufe baya son takura mata dan bata sake dashi har lokacin, tana so ta tambaye shi bazai ci ba amma kuma ta kasa dole tayi shiru. Ya tashi tsaye ya saka hannu ya d’ago ta gabad’aya ta tashi itama yace, “muje ki kwanta inda gaske kike baccin zaki yi.” Sai a lokacin taje inda dakuna suke taga guda biyu ne d’aya yana kallon d’aya ya bud’e na hannun haggu taga gado ne babba a ciki an gyara shi tsaf yayi kyau sai khamshi yake yi. Gidan amarya daban yake dan kana kallon gidsn Rukayya kasan na amarya ne komai daidai da ita. Ya tsaya daga gefe yace, “ina zuwa.” Ganin ya fita ya saka ta kallon d’an sosai a nan fa fahimci shi Zuhra yake fad’a mata ta ajjiye mata kayan ta a ciki ta tashi ta shiga band’aki ta fito ta canja kaya har lokacin bai dawo ba ta kashe hasken d’akin ta kwanta. Shima yana sane ya kyale ta dan ta sake sosai tayi abinda take so sai bayan ta kwanta taji an bud’e k’ofar an shigo, tayi kamar bacci ya d’auke ta shi kuwa yasan ba bacci take yi ba amma bai nuna mata ba ya fita ya kyale ta dan ta samu tayi baccin sosai in tayi baccin ya shiga ya kwanta. Bayan kwana biyu. Ameena na zaune a gaban Yaya Adam yana kallon ta yace, “Yauwa daman kiran ki nayi akan kar na sake ganin kina tuk’a mota da kanki. Ko makarantar zan samar miki mai kai ki amma ban yarda ki sake fita da kanki ba kin gane?.”Ameena ta girgiza kai yace, “in ba fita ta gaggawa ba ban amince da ki dinga driving ba sai in Kinyi aure. Ba kuma saboda wani abun ba kawai haka tsarina yake.” Ameena tace, “in sha Allah Yaya.” “Ya batun makarantar? Komai yana tafiya daidai ko?.” “Sosai ma Yaya, naji dad’in makarantar duk da daga level two na fara amma bana jin wahalar karatun gaskiya, sai dai math ne bana ganewa.” Yayi dariya yace, “Nima ba iyawa nayi ba balle na dinga koya miki, sai dai ko Al’ameen in wani abun ya shige miki duhu ki tambaye shi ya iya lissafi fiye da tunanin ki.” “Ai kuwa zan tambaya, dakyar nake iyawa in an koya mana.” “To yayi kyau, Allah ya bada nasara.” “Amin Yaya, na gode.” “An kawo min iv na bikin gidan su Yusuf, zaki je amma dai ko?.” Ameena tayi shiru kamar baza tayi magana ba kafin tace, “eh zanje.” Yaya yace, “ya dai kamata kije din, suna sonki sosai gwara kije in baki je ba baza su ji dad’i ba.” Ameena tayi murmushi yace, “tashi kije Allah ya taimaka mana.” Ta tashi ya shiga d’aki a lokacin wayar Humaira ta shigo. Tana d’auka Humaira tace, “Sis ranar alhamis za’a fara fa.” Ameena tayi murmushi tace, “Humaira babu lallai nazo duka gaskiya, nafi daman tunanin zuwa kamu kawai ranar juma’a.” “Ai da Ammah bata ji dadi ba kuwa, iya kamu banda dinner banda yini? Haba Sis yanzu a bikin nawa?.” Ameena tace, “kiyi hak’uri ba da wani abun nace bazan zo ba.” “To dan meye? Dan Alalh kizo kawai ayi shagali dake.” “To naji zan zo.” Humaira tayi dariya tace, “Ko Kefa, har naji dad’i wallahi. Zan shigo gobe ai in sha Allah.” Ameena ta amsa mata kafin sukayi sallama. Ajiyar zuciya tayi bayan ta kashe wayar tana kallon wayar tace, “taya zan iya zuwa gidan ku Humaira?, bazan iya sakewa ba musamman akan…..” Sai kuma tayi murmushi ganin kiran Rukayya yana shigowa ta d’auka ta saka a kunne tace, “Amaryar Ibrahim kin sha khamshi daga waja ma jin khamshi nake.” Rukayya tayi dariya tace, “fadi ki sake fad’a amaryar ce ta gaske ba ta wasa ba.” Ameena tace, “Allah? Lallai Ruky baki ya bud’e.” Tayi dariya tace, “har yanzu baki dawo ba ko?.” “Bari akwai Ruky makaranta ta sako ni gaba, so nake na nutsu nayi karatuna da kyau wallahi.” Rukayya tace, “ya labarin Fiddausi kuwa?.” “Har yanzu babu labari wallahi, ni abun tsoro yake bani fa wallahi.” “Nima haka wallahi, Allah yasa ba wani abun ne ya same ta ba.” “Amin dai. Ya amarci?.” Rukayya tace, “ban sani ba.” Ameena tayi dariya sannan Ruky tace, “kin san da muka je gidan su yadda Hajiyan sa tayi min inda kika san ta goya ni, Gashi daman nayi girki na tafi dash ke baki ji saka albarka ba. Ai naji dadi dana samu iyayen miji masu qaunata kamar ke da Ammah.” Ameena tace, “ke samun dangin miji masu sonka yana da dadi sosai wallahi, yana daga cikin abinda ya saka nake juriya a zamana da Yusuf. Wani abun badan shi nake yi ba dan iyayen sa nake yi.” “Ai yanzu na gane wallahi, inda kika san yadda Ammah take miki haka Hajiya take min. Komai ta samu aiko min dashi su albasa, kuka, daddawa, kub’ewa harda kayan Miya komai a bani.” “Ke ai ta ko ina auren nan alkhairi ne a wajan ki wallahi.” “Na gani Ameena, duk da akan ce amarya bata gane halin mijin ta amma juma’ar da zatayi kyau tun daga laraba ake gane ta. Wallahi Ameena bani da abinda zan cewa Allah sai gode, jinkiri kuwa ya zamar min alkhairi.” Ameena tace, “Ana ta soyayya, Allah yasa baki da ciki soyayyar sai tafi armashi.” Rukayya tayi dariya tace, “ku wallahi baku da kunya, haka Zakiyya ma da tazo ke baki ji magana ba.” Ameena tayi dariya tace, “banza, ke ai itace dake “Ameena kinga yadda Zakiyya ma ta koma kuwa? Tunanin mijin ta bai san da cikin ba ya d’auka ta zubar baban tashin hankalin ta kar ya sani yace ya sake ta ya zatayi.” Ameena tace, “mu dai Mun shiga uku, daga wannan sai wannan?. In wannan ta fita daga matsala sai wannan ta shiga, nida ke mu fita ita da Fiddausi sun shiga. Allah ya kawo mafita kamar yadda ya baki mafita nima ya bani.” Ta amsa da amin kafin tace, “bikin Humairan Ammah za’a yi fa.” “Amma dai zaki je?.” “Tunanin da nake yi kenan Ruky.” “Ki ajjiye ko wanne tunani yana da kyau kije gaskiya.” Ameena tace, “ni wallahi nauyi nake ji.” Rukayya tace, “Akwai nauyi amma haka zaki je saboda Ammah.” Ameena tace, “to zan san abinda zanyi.” suka cigaba da hira kafin su kashe wayar. Rukayya tana yanke wayar aka shigo falon ta kalli wanda ya shigo ganin mijin ta sai tayi dariya tace, “banji motsin ka ba.” Ya k’araso ya zauna yace, “daman ai baza kiji ba kina waya.” “Sannu da zuwa.” Kallon ta yake yi bai amsa ba sai tayi murmushi ta sunkuyar da kai yace, “wannan sunkuyar da kai yaushe za’a daina shi Rakiya?.” Tace, “nifa ka daina cemin Rakiya Allah bana so.” Ya rik’o hannun ta ya dawo kusa dashi sosai yace, “ni kuma ina so saboda yadda kike shagwab’a in fad’a miki yana burge ni.” Tayi dariya ta kwanta a jikin sa yayi murmushi yana jin farin ciki a zuciyar sa tace, “na kawo maka abinci?.” “A’a ruwa kawai zaki bani abinci sai anjima.” Ta tashi ya d’auko ruwa ta kawo masa yace, “babu sanyi ruwan, rashin wutar nan yana damuna ga gidan babu haske in dare yayi, ya kamata ayi wani abun ko k’aramin inji ne a samu.” Rukayya ta zauna tace, “ni banga amfanin siyan wani inji da kake magana ba wallahi, yanzu aka siyi inji kud’in fetur din ma ai zaman kansu suke yi. Gidan nan bashi da zafi ko kad’an in da wutar ma ba’a cika kunna fanka ba saboda babu zafi, haske kuma akwai wanda ake kunna kuma ba’a rasa wuta a unguwar injin me za’a siya?. Da siya ma gwara a biya kud’in school bus din su Amir ka huta da yawon d’auko shi Kullum.” Kallon ta yake yi yana tuna wani abu da ya gabata baice komai ba yana kallon ta itama haka sai yayi murmushi yace, “ni zaman duhun ne bana so.” “Ni kuma bai dame ni ba, indai a Nigeria kake a zaman duhu ka saba dashi.” Yayi murmushi kawai tace, “ka dawo da wuri, Allah yasa lafiya.” Shiru yayi baice komai ba yana jin dad’in yadda take kula da lamarin sa, in bai dawo da wuri ba bazata tambaya ba sai ta jira ya huta sannan zatayi magana haka in ya dawo da wuri ma sai ta jira ya huta zata tambaye shi. Yace, “Waya akayi min ana ne mana a unguwar nan shiyasa na dawo.” “Allah yasa lafiya.” “Lafiya lau sai alkhairi.” Ya kalle ta yace, “dawo kusa dani zanfi jin dad’in baki labari.” Tayi murmushi ta dawo ta zauna tace, “ina Jin ka.” Ya rungumo ta jikin sa yace, “Kamfanin Airtel ne suke so zasu yi service a unguwar nan shine suke ya searching waje suka gano area nan da muke a nan ya kamata ayi.” Rukayya tace, “meye ma service?.” “Wannan dogon karfen.” “Oh na gane.” “To gidan nan yana daga cikin wajan da suka nema zasu rushe su had’e waje d’aya suyi services din, shine aka kira ni ake zancen zasu ninka mana kudin gidajen mu sau uku. Kinga ni wannan gidan nan sunde zasu bada naira miliyan sha biyar amma a cikin sati d’aya zamu tashi mu basu wajan. Yanzu sun bamu daga nan zuwa gobe kayi shawara ni na rasa me zance musu wallahi.” Rukayya tace, “to me ka yanke?.” Ya kalle ta bayan ya had’a fuskar sa da ta ta yace, “shine nazo muyi shawara dake ai, ya kike ganin za’a yi?.” Rukayya ta zame fuskar ta ta kwanta a kafadarsa tace, “ni sai nake ganin da ka karb’a kawai.” Ya katse ta yace, “mu karb’a dai ba na karb’a, ki daina saka ni ni kad’ai har dake.” “To mu karb’a, amma kayi shawara da Alhaji Kaji me zaice.” “Kece a kusa dani a yanzu kafin Alhaji, dake zan fara shawara kafin naje wajan su.” Rukayya dad’i ya mamaye mata zuciya samun mijin da zaiyi shawara da ita hakan yana yi mata dad’i sosai tayi murmushi tace, “to nidai a ganina a shawara ta a karb’a, sai a samu wani gidan a siya sauran kud’in ba sai ayi amfani dasu ba.” Ya girgiza kai yace, “kamar me za’a yi dasu?.” “Kamar a juya su mana daga biyar su koma goma, ko ka siyi adaidaita sahu ka bayar ana aiki dashi ana kawo maka balance. Yana da riba sosai Baba ana yi masa.” “Banji kince a siya mota ko a siya wani abun ba.” Rukayya tace, “eh to, siyan mota yana da amfani amma ta wani b’angaren bashi da amfani a yanzu. A Bari nan gaba a siya a juya kud’in in Allah ya saka albarka sai kaga an samu ninkin su kafin shekara.” Yayi murmushi yace, “haka ne maganar, zanje wajan Alhaji in na d’auki Amir zamu wuce zuwa dare sai mu dawo zanji me zaice.” Tace, “to shikenan Allah ya saka mana albarka.” Ya amsa da amin yana ji a zuciyar sa yanzu yasan yayi aure. Fiddausi ta rame sosai ta fita daga hankalin ta gabad’aya ta koma kamar ba ita ba ko abinci bata iya ci m kullum cikin tunanin gida take ko bacci babu dan da ta kwanta sai taji kamar zai so ya sake amfani da ita ga baya sai ta girgiza ta tashi gabad’aya ta koma kamar mai tab’in hankali. A daren ranar tana zaune a kan tiles a cikin d’akin ta ta gama kukan ta ya shigo yana kallon ta yace, “ke bakya gajiya da kuka ne? Baki ga y’an uwan ki su Aliya sun saki jikin su ke kin kasa hakan?.” D’ago kai tayi tana kallon sa dan rabon ma da ta ganshi ta manta hawaye ya zubo mata ya bita da kallo yace, “haka kika koma? Duk abincin gidan nan bakya ci ne ya saka kika koma kamar mahaukaciya?.” “Ka mayar dani gidan mu dan Allah, iyayena hankalin su ya tashi dan Allah ka barni na tafi.” Alhaji yace , “kinzo rayuwar farin ciki ne fa, na ajjiye ki a babban gida ga mota ga kudi ga komai to meye na damuwa ki koma gıda?.” Ta goge idanun ta tace, “meye amfanin kudi wannan gidan? Meye amfanin kud’in da babu farin ciki?. Ka rik’e kud’in ka mayar dani gida na gaji da zama dakai wallahi.” “Ni ban gaji da zama dake ba Fiddausi, Nidai yanzu nazo ki bani hakkina” ya fad’a yana matsowa kusa da ita tayi baya da sauri tace, “baza ka sake samun jikina ba, ka barni dan Allah ka tafi.” Ya kamo ta da k’arfi yace, “ai baki isa ba wallahi, sadaki na bayar na aure ki dan haka dole ki bani abinda nake so.” “Wallahi bana cikin tsarki dan Allah kayi hak’uri.” “Ina ruwana dan kina cikin jini? Babu abinda zai hana ni.” “Innalillahi, dan girman Allah kayi min haka kar ka saka na sake aikata haramci dan Allah kayi hak’uri.” Tsaki yayi ya cilla ta kan gado yabi bayan ta bata da k’arfin kokawa dashi sai kuka da hawaye amma bai saurara mata ba sai da yayi abinda yake so da ita sannan ya tsallake ta ya fita ya barta a wajan tana kuka sosai. Godiya take a zuciyar ta da Allah ya saka tana da tsarkin babban tashin hankalin ta ace babu da ya gama cutar ta. Ta kasa tashi balle ta gyara kanta ta rasa me zatayi kuka akwai yake zuciyar ta har bugawa take yi sosai kamar zata fito waje. Tafi awa d’aya a wajan bayan fitar sa bata motsa ba sai daha baya sannan ta iya tashi ta yi wanka ta fito tana ji kamar ta kashe kanta akwai ta huta da rayuwar dadbobin da take a gidan nan gwara ace ta mutu ta huta kawai. Bata so ya sake samun jikin ta ba duk da ba abinda bata so yayi da ita ba amma bak’in ciki take ji a zuciyar ta da hakan ta sake faruwa tsakanin su. #Mai Daki #Book3 #Paid #Nana Haleema Book3 019 Nan da nan zazzab’i ya rufe Fiddausi, jikin ta sai rawa yake yi a lokacin Aliya ta shigo ganin hankalin da take ciki hankalin ta ya tashi tace, “Bara na kira a kai ki asibiti.” Ta rik’o hannun tatace, “gida zanje, ki kaina gida, ki fitar dani daga nan dan Allah.” “Ban san yaya zan fitar dake ba Fiddausi dana sani da yanzu na fitar da kaina, Kiyi hakuri kawai ki karb’i kaddara ki da hannun dama.” “Na cuci kaina, na cuci rayuwata, Wayyo Allah ni Fiddausi na shiga uku. Na baro gidan da ake bani farin ciki, ake bani abinda nake so, komai nace shi ake yi, har ba’a so nayi kuka. Na kawo kaina inda kuka ya zama abincina” ta fad’a tana kuka sosai jikin ta ya sake d’aukar zafi sosai. Alhajin ne ya sake shigowa shida wani babban mutum kamar sa suna kallon Fiddausi yace, “ka ganta nan, kuma tana cikin jini lokacin da aikin ka zaiyi kyau kenan.” Mutumin ya kalli Fiddausi yayi murmushi ya shafa gemi yace, “Tayi wallahi, yanzu ka bani kenan?.” “Ahh na baka mana, ai kasan ni dai bani na baka ne” ya kalli Aliya tace, “ke tashi ki basu waje.” Aliya tace, “kaji tsoron Allah, ka tuna zaka mutu wata rana kaima kuma zaka koma ga Allah.” Yayi tsaki yace, “zaki wuce ko sai na buga ki da k’asa? Ina magana kina min maganar banza?.” Aliya tace, “bazan fita ba” ta fad’a tana kuka Fiddausi ta rike ta sosai jikin ta sai rawa yake yi sosai kamar zata shid’e saboda abinda take ji a zuciyar ta da gangaar jikin ta. Ya kalli Alhaji yace, “kayi akwai abinda yake gaban ka kar wannan kar ta dame ka.” Yayi murmushi yana cire hula yace, “daman mu ai mata mutanen mu ne dan mun tub’e a gaban si ai ba wani abun ba” ya fad’a yana yin inda Fiddausi take yana kallon ta. Sake kankame Aliya tayi jikin ta na mugun rawa hankalin ta ya tashi sosai ta masa magana sai rawa da jikin ta yake yi. Hannun sa ya kai jikin Fiddausi sai ya kalli Alhaji Bello yace, “jikin ta akwai zafi sosai kuma a yadda abun yake sai mai Lafiya fa, yanzu ya za’ayi?.” Alhaji Bello ya kalli Aliya tace, “wannan baza tayi ba?.” Ya kalli Aliya yace, “yanayin ta baiyi daidai da wacce akace ba gaskiya, sai dai ayi manage kawai” ya fad’a yana kallon Aliya da take kallon sa itama. Zabura tayi ta k’arasa jikin madubin Fiddausi ta d’auki kwalbar turare tace, “wallahi duk wanda ya matso kusa Dani sai na buga masa, wallahi duk wanda ya tab’a ni sai na fasa masa kai.” Ganin da gaske take sai bata hankalin ta Alhaji Bello yace, “Mutumin zo muje kawai, wannan hauka zatayi maka daman da dai waccan zatayi ne sai a San abinda za’a yi. Amma zan saka likita yazo ya duba ta anjima sai a ka dawo” tare suka fita ta ajjiye kwalbar ta k’arasa da sauri ta kulle k’ofa ta koma wajan Fiddausi nan ta tarar da ita bata numfashi. A guje tayi kan Fiddausi tana girgiza kafad’ar ta tana kuka tana cewa, “Fiddausi! Fiddausi!! Innalillahi wa’inna ilahir raji’un.” Da sauri ta k’arasa cikin band’aki ta d’auki kofin ruwa ta d’ebo ruwan ta dawo da sauri tana shafawa Fiddausi a fuskar a lokacin ake kwankwasa k’ofa ana cewa, “Aliya ku bud’e nice.” Jin muryar wacce take magana ya saka Aliya zuwa ta bud’e a lokacin Naja’atu ta shigo d’akin Aliya ta kalle ta tace, “k’araso dan Allah, bata numfashi wallahi na shafa mata ruwa duk da haka a sume take.” Da sauri ta k’araso tana cewa, “Meya faru haka?.” “Mijin ki ne ya kawo wani har nan wai yayi amfani da ita tana cikin jini, har da cewa yayi amfani dani tunda ita baza’a samu ba.” “Mun shiga uku mu kam, Mun kawo kan mu inda ba’a san darajar aure ba balle darajar mace.” Aliya kuka take a lokacin Fiddausi ta bude’e ido ta dafe kanta da hannun guda d’aya tana kallon su suna ta aikin jera mata Sannu. Kanta take dafewa saboda ciwon da yake mata sosai sai kallon su da take yi amma ta kasa cewa komai saboda yadda jijiyoyin kanta suke harbawa kamar zasu tsinke bata son yin magana gabad’aya. Aliya ta kalli Naja’atu tace, “Ko lokacin mu bamu sha wahalar da yake bawa Fiddausi ba, yafi takura mata sosai ya kamata mu san abinda zamu yi akai kafin ya kashe ta da ranta.” Naja’atu ta koma da baya ta kulle k’ofa ta dawo ta zauna kusa da Fiddausi da take kwance tana hawaye tace, “Na samu waya a hannun masu aikin gidan nan bai sani ba, Akwai lambar wanda kika haddace a gidan? Fad’o na rubuta ko za’a dace ta shiga.” Jin abinda akace sai ta samu k’arfin guiwa ta mik’e zaune dakyar ta jingina da bangon gadon tana fad’ar lambar Abba ana sakawa. Ana kira ya nuna number busy Naja’atu tace, “fad’i ta k’anin ki ko yayar ki amma na tabbatar ta baban ki da babar ki baza tayi ba.” Fiddausi ta rutse ido tana juya kai cikin azaba tace, “su kawai na haddace.” “Ki tuna Fiddausi koda maqocin ku ne ko k’awayen ki, ki tuna bamu sani ba ko za’a dace ta shiga.” Kai take juya suwa domin kuwa daga lambar Abba sai ya Mamata haddace bayan su babu lambar wanda ta rik’e a kanta Aliya tace, “ki tuna ko waye ko wace zamu kira shi yanzu mu sanar dashi halin da muke dukkan mu ko za’a taimaka mana,” “Ban haddace ba!, ban haddace ba!!.” Naja’atu tace, “ko tsohon saurayin ki ne ki tuna wannan ne lokacin da muke dashi. Na gwada na y’an gidan mu kaf bana samu ke mu gwada naki ko za’a dace.” _ibrahim._ zuciyar ta fad’a mata sai ta bud’e ido da sauri ta kalli Naja’atu ta bud’e baki da niyar fara fad’a mata lambar sa sai kuma ta kasa ta lumshe idanu sai kuka ya dawo sabo. “Kin tuna ko? Fad’o a rubuta.” Kai take girgizawa tace, “bazan iya ba, bazan iya kiran sa ba Naja’atu.” Aliya tace, “indai kin haddace zamu iya kiran sa ko waye, a wannan halin da ake ciki neman taimako muke yi babu ruwan mu da waye shi.” Ta sake juya kanta tana kuka tace, “bazan iya ba, ban san da wacce fuska zan masa magana ba, Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un na cuci kaina ni Fiddausi.” Naja’atu tace, “Dan Allah ki fad’a ko za’a dace dan Allah. A yanzu neman d’auki muke ba zancen baza’a iya ba, ki tuna wannan damar kawai muke da ita in baki magana ba zamu rasa ta itama. Ni zan masa magana in ke baza ki yi ba.” Bud’e ido tayi ta fad’i lambar Ibrahim da yake kanta har lokacin aka kira kowa yana jira yaji zata shiga, number busy ta sake sakawa Naja’atu ta sake kira ta sake rubuta haka ya sake kira cikin ikon Allah ta fara ringing. Kallon su tayi cikin farin ciki dukkan su kallon ta suke ko wacce kuka take yi ana jira aji za’a d’auka amma shiru ba’a d’auka ba har ta yanke. Hannu na rawa suka sake kira amma tak’i yi duk yadda suka kai ga naci tak’i shiga. Aliya tace, “ki adana mana lambar na tabbata zata yi mana amfani gaba dan bamu tab’a gwada kira ta shiga ba sai a kanta, waye shi d’in ki?” Ta tambaya tana kallon Fiddausi. Ta lumshe ido tace, “tsohon mijina.” A tare suka kalle ta Aliya tace, “amma dai babu matsala ko? Kina ganin in muka fad’a masa koken mu zai taimaka mana?.” Cikin muryar kuka tace, “ban sani ba wallahi, abinda na sani kawai nayi masa abubuwa marasa kyau a zaman mu dashi, tunda nazo gidan nan na fara ganin sakayya akan abubuwan da nayi masa. Tun daga kan zubar da cikina da akayi, amfani dani ta k’arfi, saka ni a cell da duk abinda yake faruwa” ta nuna kanta tana kuka tace, “nice nayi silar rabuwar mu kawai dan nazo gidan nan.” Hawayen nasu sun tsaya Aliya ta sauke numfashi tace, “babu wanda yake zuwa gidan nan sai ya aikata kuskure makamancin wannan, amma in sha Allah zai taimaka mana in muka same shi a waya.” Ta girgiza kai tace, “duk yadda kuke tunanin abun ya wuce haka, nayi masa abubuwa masu yawa dan ina jin kaf cikin ku na fiku aikata kuskure.” Naja’atu tace, “Gashi kina ganin sakayya ai kina kuma dana sani wacce bata da amfani.” Shiru kawai tayi ta kulle idanun ta bata ce komai ba tana ji kamar ta had’d’iye zuciya ta mutu saboda bak’in ciki. Ibrahim lokacin da akayi masa waya wayar tana chaji a falo Rukayya tana zaune ita da Amir tana koya masa assignment taji kiran wayar amma bata motsa ba suka cigaba da abinda suke yi. A lokacin ya shigo falon ya kalle ta yace, “Amir baiyi bacci ba? Dare yayi akwai makaranta.” Rukayya tace, “na manta ba muyi assignment bane shiyasa muke yi yanzu. Amma mun gama yanzu sai ya kwanta.” Ya zauna Amir ya kalle shi yace, “Abba kasan a makaranta Ya Sayyada tace na iya hadda ta.” Yayi murmushi yace, “dakyau haka ake so, ka cigaba da dagewa indai kayi kokari ka iya zan siya maka keke.” Sai kuwa farin ciki ya bayyana a tare dashi yana ta murmushi Rukayya ma haka. A sannan suka gama ta rufe littafin ta saka masa a jaka tace, “d’auki school bag din kaje ka ajjiye a d’aki.” Ba musu ya d’auka ya shiga d’aki ya ajjiye ya dawo Ibrahim yace, “bani waya ta Amir gata can.” Zuwa yayi ya d’auko ya kawo masa Rukayya ta tashi suka shiga d’aki ita da Amir Jim kad’an ta fito ya kalle ta yace, “har ya kwanta?.” Ta zauna sannan tace, “Uhum ya kwanta.” “Number ce aka yi min waya na kira kuma bata zuwa.” Rukayya tace, “sharrin network ne.” “Meyasa baki d’auka ba da aka kira?.” “Kawai sai na d’aukar maka waya in an kira ka ban san waye ba?.” Ya kalle ta yace, “ai ni na baki damar hakan ko?.” Sai tayi murmushi tace, “kai wai ko irin b’oye waya da mazasuke yi yiwa matan su baka yi?.” Yayi dariya kad’an yace, “to me zan b’oye miki? Y’an mata ne dani da zasu kira ni?. To yau ko y’an matan ne dani ai ke zaki fara sani.” Tayi murmushi tace, “Nidai bazan d’auka ba in kana kusa ka d’auki kayar ka amma bada ni ba d’aukar wayar ka in an kira .” “Tsoro kike ji?.” “Eh hakan ne, gwara naji tsoron na k’i d’auka dana d’auka kuma naji wani abun ba daidai ba.” Ibrahim ya kalle ta yace, “babu abinda zaki ji ba daidai ba a wayata, zan iya bar miki ita na fita na dawo babu abinda zai faru na tabbatar miki. Rukayya nida nake da mace kamar ki me zai had’a ni da wasu matan na waje?.” Murmushi kawai tayi bata ce komai ba sai yaga ta fuskar ta canja daman tun d’azu ya lura da yanayin ta ba daidai ba yace, “Me yake damun ki?.” Ta kalle shi tayi shiru batayi magana ba yace, “tambayar ki nake, me yake damun ki?.” “Mun kasa samun wayar Fiddausi gabad’aya, bata kira ba’a kiran ta hankalin mu dana iyayen ta a tashe yake sosai shirun nan ko na alkhair ne yayi yawa.” Ibrahim ya kalle ta yace, “wace haka kuma?.” Kallon sa tayi taga babu alamun wasa a tare dashi sai tace, “Fiddausi k’awata.” “Allah Sarki! Ban santa bama Ameena nafi rikewa, shine kika koma haka kamar mars Lafiya?.” Rukayya tace, “tamkar y’ar uwa take a wajena kamar Zuhra da Sajida haka nake jin ta a jikina wallahi. Mu saba sosai rashin ta zai saka naji babu dad’i.” Ya tab’e baki yace, “To yayi kyau.” Kallon da tayi taga ba ita yake kallon ba alamun baya son maganar sai ta canja maganar tace, “ya kuka yi da Alhaji akan maganar gidan?.” “Maganar nazo muyi dake sai hankalina ya bar wajan. Alhaji ya bada goyan baya sosai bama shi kadan ba har su Yaya Sulaiman, suma kamar yadda kika ce haka suka ce.” Tayi dariya tace, “kayi magana dasu?.” “Sai zuwa gobe zan musu magana sai mu fara shirya kayan mu neman gida indai da kud’i ba abu bane mai wahala.” Rukayya tace, “to Allah ya saka musu albarka gabadaya.” Ya kalle ta yace, “Amin. Makarantar su Amir da naje d’azu sun sanar dani Amir yana k’ok’ari sosai musamman a b’angaren addini, alkur’ani da an yi musu da ya rik’e hakan ya saka suka kira ni akan a cigaba da k’arfafa masa guiwa ana cigaba da bibiyar karatun nasa dan hakan shine ya saka shi yake iyawa da sauri. Principal din yace min da aka tambaye shi an ina ake koya masa yace Ammin sace.” Rukayya murmushi take bata ce komai ba ya rik’e hannun ta yace, “ni dmaan nasan zaman ki da Amir alkhairi ne a cikin tasa rayuwar, domin baza ki barshi yayi kuka ba sannan baza ki yi masa tarbiyya banza ba. Amir da anyi kira yake tashi yayi sallah alwala in yana yi sai ka tsaya ka kalla saboda yafi wani babban iyawa. Haka akayi a masallacin juma’a da muka je da yana alwala kallon sa mutane suke yi ana dan Allah wannan d’an waye alwala babu kuskure kamar ba yaro ba, farin ciki hana ni magana yayi da alfahari nake sanar da mutane d’ana ne.” Murmushi take yi kawai hannun ta na cikin nasa yace, “mace ta gari itace take samar da y’ay’a na gari, Allah yayi miki albarka Rukayya shigowa ki rayuwar Ibrahim da ta d’ansa tanka haske ne a cikin duhun daji, Allah ya cigaba da baki ikon hak’uri dani.” Tayi dariya ta kalle shi tace, “har wani abu ne dakai da za ayi hak’uri?.” Yayi dariyar shima yace, “ni nasan akwai ai ko ya y baza’a rasa ta inda nake yin wani abu bakya so ba, kinga ni ina hak’uri dake musamman a b’angaren wannan kunyar taki da ta kasa tafiya har yanzu.” Sai kuwa ta sake kulle fuskar ta tana dariya shima haka tace, “kin gani ko? To hak’uri nake dake akan wannan babu yadda zanyi.” Murmushi take yi ta bud’e fuska tace, “dukkan mu alkhairi ne a rayuwar junan mu, kai alkhairi ne a rayuwata samun ka yafi samun diamond.” Ya wara idanu yace, “kin San diamond kuwa?.” Tayi dariya tace, “darajar sa bata kai da mijina ba.” Ya kwanta a jikin ta yana kallon ta yace, “in kika ce mijin nan naki ko sai naji kamar an d’auke ni sama ana zagawa dani.” Tayi dariya tace, “kana bani nishad’i.” “Allah yasa na dinga baki nishadi har abada.” “Allah ya amsa bakin ka.” Yace amin yana murmushi ko wanne su farın cikin kasancewa da dan uwan sa yake yi domin rayuwar su ta canja gabad’aya kamar ba Sune suka sha wahala a baya ba. Yusuf yana zaune yana danna waya Asiya ta shigo ta bayan sa bai san ta shigo ba dan a lokacin transfer yake yi ta tsaya a bayan sa tana kallo har taga pin din da ya danna ya gama tura kud’in sai tayi dariya cikin farin ciki a sannan ta k’araso ta zauna tace, “Yauwa batun kudin siyayyar kayan jaririn cikina.” Kallon ta yake yi jin babu sallama babu sannu balle kuma gaisuwa yace, “ke baki iya sallama bane ba wai?.” “Ban iya ba, abinda na saka a gaba shi kawai nake yi.” Kai ya girgiza yana jin d’acı a zuciyar sa da k’una da kuma tsanar ta mai muni tace, “nayi lissafi miliyan biyu zaka bani dan ko keken da za’a siya masa na kwanciya naira dubu dari biyu ne, akwai gado da sauran kayan sawa.” Ya kalle ta yace, “ke wai baki da magana sai za’a zancen kudi?.” “Su na fito nema, dole ka bani kuma koda baka so.” “Sai ki kwace tunda naki ne.” Tayi dariya kad’an tana kallon sa kafin ta kalli ledar da take gefe ta d’auko tana dubawa ganin atamfa guda biyu da kuma lace kala biyu yace, “kayan bikin humaira ne Ammah tace a kawo miki.” Ta fito da katina daga cikin kayan tana kalla ganin bikin ma cikin satin ne tace, “lallai ma, jibi juma’a za’ayi kamu amma ba’a kawo min ankon ba sai yanzu da yake an daina min hankali, To baza’a saka ba” tayi tsaki tana cillar da kayan gefe. “Kee!.” Ya furta yana kallon ta zuciyar sa na tafasa sosai fushin sa ya bayyana a kan fuskar sa ta kalle shi tace, “na fad’a, sai me?.” Bata yi tsammani ba taji ya mare ta daman kiris yake jira ya mik’e tsaye tana kallon sa itama ta mik’e kawai ta chakumi wuyan rigar sa tace, “na rantse da Allah kar ka kuma dukana ina fad’a maka ka daina wannan kuskuren amma ka k’i ka daina.” Ya cire hannun sa daga jikin sa yace, “ke wacece da kika mayar da Ammah tamkar abokiyar wasan ki? Asiya in baki shiga hankalin ba zaki yi dana sani wallahi.” “Bazan shiga hankalin nawa ba, an fad’a kuma baza’a dinka kayan ba sai kayi abinda zakayi. Naga dama ko bikin ma bazan je ba akwai abinda za’a yi min ne?.” “Gwara ma kar kije ai zuwan ki bashi da amfani, da ki je ki yi sata ai gwara ki zauna a gida ki saci kanki.” “Naji ni sata nake kai kuma giya kake sha, d’an giya kawai mai sab’awa Allah wanda yake aikata abinda ya haramta. Gwara ni wanda ya yiwa abin sa ajiyar banza nake d’auka na gyarawa zama kai kuwa fa? Dan giyan banza da…..” kalmar da ya tsana kenan yaji tana fad’a masa a duk lokacin da hakan ta faru yana saurin harzuk’a zuciyar sa ta tafasa bai san lokacin da ya sake marin ta ba ai kuwa kafin ya d’auke hannu sa ta kai masa mari itama ya rik’e hannun nata ya tsaya yana kallon ta tace, “Baka isa ba wallahi, kai baza ka sake dukana na kyale ka ba dan ba jaka bace ba ni. An fad’a kuma d’an giya kayi abinda zakayi” tana fad’ar hakan ta kwace hannun ta bar masa wajan ya bita da kallo har lokacin mamaki yake da ya bari sake Marin sa zatayi kenan?. Wani irin kuzari ne yazo masa a lokacin wanda ya jima bai ji irin sa ba yabi bayan ta da sauri ya samu tana k’ok’arin shiga d’aki ya zari wayar fanka ya k’arasa inda take ya manta ma ciki ne da ita ya fara dukan ta ta ko ina tana ihuu tana cewa, “Allah ya iss, Shege mugu dan giya. Wallahi sai kayi dana sani abinda kayi min sai na d’auki mataki a kanka.” Hankalin sa ya gushe dukan ta kawai yake yi bai kula da jinin da ya fara zuba daga jikin ta ba burin sa yayi mata dukan da zata kasa tashi ko nan gaba zata daina yi masa abinda take yi. Sai da ya gaji dan kansa ya cillar ya bar wajan ya fita daga gidan gabad’aya yana jin zuciyar sa na tafasa sosai domin fushin zuciyar da tsanar ta da take ciki ne yayi tasiri a gangar jikin sa. Momi ce ta hau saman a lokacin tazo gidan Asiyan ta kira ta akan tazo ta kwana gobe ta karata asibiti ganin halin da yake ciki gata a kwance kamar bata numfashi hankali ya tashi tayi waya gida hankali tashe ta fad’a. Hankalin ta ya tashi gashi bazata iya sauka da Asiya ba ga masu aikin duk sun gudu dole ta jira har su Umma suka zo aka d’auki Asiya aka fita da ita hankalin su ya tashi sosai. Karb’ar gaggawa aka yiwa Asiya a asibiti aka shiga bata taimako gaggawa dan a ceto abinda yake cikin ta. Da yake private ne likitan yana fitowa ya kalli su Umma yace, “dukan ta akayi?.” Umma tace, “bamu sani ba tana gidan ta muka je muka same ta a haka.” “Duka ne dan jikin ta akwai shatin duka sosai, dukan da aka yi mata ya jawo cikin ta da ya kai matakin zama mutum ya mutu, in mijin ta yana kusa ya saka hannu a nan za’a yi mata aikin gaggawa domin cire shi,” Umma ta dafe k’irji tace, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, d’an ya mutu?.” Likita yace, “ya mutu, ayi a saka hannu dan za’a yi mata aiki a cire.” Yaya Maimuna tace, “Babu wani babba a kusa damu yanzu, wannan Maman ta tace ni kuma yayar ta zan iya saka hannun?.” Likita ya yiwa nurse nuni da ta bata takardar ta saka hannu suka koma dan cire yaron cikin Asiya. Momi tace, “lallai Yusuf ya d’auko ruwan dafa kansa, sai yayi dana sanin abinda ya aikata mana.” Umma ta kasa cewa komai sai kallo kawai da take yi tana kwafa dan Allah kad’ai yasan abinda zata yiwa Yusuf a wannan lokacin. Suna nan har washe gari an yiwa Asiya aiki an cire yaron a lokacin Umma bata nan tana barin asibitin gida taje tayi wanka ta shirya ta sake fita kai tsaye wajan ya’n sanda taje ta sanar dasu duk abinda yake faruwa aka had’o ta da y’an sanda guda biyu suka tafi gidan Yusuf kai tsaye. Koda suke je mai gadi yace ya fita bata yi k’asa a guiwa ba tace su wuce store d’in sa ta tabbatar yana can. kai tsaye can suka wuce dan kamo shi dan tayi alqawarin sai yasan y’ar ta ya yiwa duka har d’ancikin ta ya mutu, daga kan Asiya bazai sake dukan wata mace ba koda ance yayi ta tabbatar bazai yi dan zata koya masa hankalin da nan gaba shine zai hana wani aikata irin abinda ya aikata. #Mai daki #Book3 #paid #Nana Haleema #500 Book3 020 Abbah yana zaune a dashi da yaran sa kaf harda jikoki ana ta lissafin wanda ba’a kaiwa katin d’aurin auren Humaira ba, Abbah yace, “ku dai tuna dan Alalh bana son korafin ban bada kati ba. Gwara a tuna Wanda ba’a kaiwa ba a kai dan Allah.” Mubakar yace, “nidai wanda na sani duk na rubuta an kuma kai musu kati, sai dai ka kira Yusuf akwai wanda ya sani wanda ni ban san su ba.” Abbah yace, “Gaskiya ne, ban san ma inda ya tsaya ba mun yi dashi zai zo nan din yace min yaje store shiri bai k’araso ba” ya fad’a yana d’aukar waya da niyar kiran sa.” Wani kiran ne ya shigo wayar Abbah yace, “to DPO kuma?.” D’aukar wayar yayi ya saka a kunne yace, “Dpo barka da rana.” Daga can b’angaren yace, “Barka dai Alhaji, ya shirye-shiryen biki? An kawo iv ai nace ashe abun har yazo.” “Wallahi yazo yanzu haka maganar katinan nake yi.” “Allah ya kaimu ya sanya alkhairi.” “Amin.” Yace, “Alhaji Yusuf aka kai station na bompai babar matar sa tana k’arar sa akan ya daki y’arta har d’an da yake cikin ta ya mutu, yanzu akayi min waya daga can aka fad’a min dan yace ya sanni tunda ba station dina aka aji da case din ba.” Abbah yace, “Subahanallahi, yaushe akayi hakan?.” “Yanzun nan ne, ba shiri muke da DPO din can ba shiyasa ban neme shi bama na Kira ka na sanar dakai nasan baza ka rasa sanin sa ba, aje ayi magana dashi dan babar matar tace ita kotu take so a kai case din tsaf kuma zai aika kotu din.” Abbah yace, “to na gode sosai yanzu zan tura Sulaiman yaje a San abinda za’ayi.” “Yauwa ayi hanzari aje kafin wani abun ya faru.” Sallama sukayi Abbah ya kashe wayar ya kalli kowa da yake kallon da yace, “Wai Yusuf aka kama yana station na bompai.” Yaya Sulaiman yace, “Wanne Yusuf din?.” “Akwai Yusuf din da ya wuce wanda yake gidan nan?.” Ammah tace, “Akan me aka kama shi?.” “Wai Babar matar sace tayi k’arar sa ya daki y’ar ta dukan da yayi silar mutuwar abinda yake cikin ta, ita kotu take so kai maganar kai tsaye.” Ammah tace, “shi kuwa yana da hankali? Dukan mace mai ciki har d’a ya mutu?. Wanne irin duka yayi mata haka?.” Abbah yayi karamin tsaki kawai yace, “Hankali ne dashi? Waye ya fad’a masa Ana dukan mace ma? Matar ka ka dinga dukan ta dan hauka da rashin hankali?. Babana dakai da Mubarak ku tashi kuje can sai ayi abinda za’a yi sai ku had’a ni da shi Dpo din a waya.” Yayan Abuja tayi tsaki tace, “Wai Yusuf aka kama, ji wani abun haushi dan girman Allah. Gabad’aya ya zubar da dajarar sa tunds ya auro yarinyar nan mai halin b’eraye shikenan ya zama gashi nan dai kawai, yau ana nan gobe Ana can.” Babu Wanda yace komai Abie da Muabakar suka tafi dan jin yadda abun zai kasance a can amma kowa zuciyar sa babu dad’i dan wannan ba mutuncin dangin su bane. Lokacin da suka je a cell suka tarar da Yusuf Abie ya kalle shi sai kawai yayi tsaki ya wuce zuwa wajan Dpo din ya jima kafin azo a fitar da Yusuf a shiga dashi office din. A nan ya samu Umman su Asiya a zaune ita da Fauziyya ya zauna Dpo din ya kalli Umma yace, “Hajiya Gashi ya fito, abinda nake so a bar maganar nan akwai duba da shi din sirikin kine tozarta shi tamkar tozarta yar ki ne. Babu riba in kin Kai shi kotu ko babu komai za’a ce sirikin ta ne kuma ta kai shi kotu.” “Saboda su masu kudi ne ko? To bazan iya hak’uri ba kotu nake so aje sai an karbarwa y’ata hakkin ta na abinda yayi mata. Ai ya san tana da ciki yake dukan ta, yanzu abinda yake cikin ta ya mutu watakila shine kawai jinin ta da zata gani a duniya amma yayi silar mutuwar sa. Tana can a a kwance asibiti ba lafiya sboda dukan da yayi mata ace kuma a bar maganar? Bazai yu ba ai ba ni nace yasha giya ba da zai dinga jibgar ta kamar jaka ba.” Ya kalli Umma yace, “Hajiya a gaban hukuma kike ya kamata ki saita harshen ki ki san kalaman da zasu dinga fitowa daga bakin ki.” Ya kalli Yusuf yace, “Yusuf da ilimin ka da hankalin ka me ya kai ka dukan mace mai ciki kuma matar ka?.” Yusuf yayi shiru baice komai ba sai Dpo ya sake cewa, “Yanzu dai sulhu za’ayi wannan hayaniyar bata kamaci dangi kamar ku ba, mata da miji ace kuma babar mata na k’arar mijin y’ar ta abun ai sam baiyi dad’i ba.” Ya kalli Umma yace, “Hajiya ki yi hak’uri an san anyi ba daidai ba amma ki janye batun zuwa kotu akan maganar nan, ayi maganar iya nan wajan a rufe ta kowa ya tashi tunda dai matar sace shima kuma mijin tane, duk yadda akayi wani b’acin ran ne ya jawo yayi mata haka ai a akwai sab’ani tsakanin ma’aurata ko?.” “Ranka ya dade sab’ani ai ba hauka bane da zai mata dukan da sai da abinda yake cikin ta ya mutu, yanzu in da itama ta mutu haka za’a ce nayi hak’uri kenan?.” Dpo yace, “ai bata mutu din ba Allah ya kare, a bar maganar nan tunda dmaan ta gıda ce ba ta hukuma ba.” “Za’a bar maganar nan amma ai ya biya diyar ran dan da ya mutu.” Yayi dariya ya kalle ta dan yaga alama tana da son kud’i ba kuma mutunci ne da ita ba yace, “kin san nawa ne diyar rai da kike cewa a biya?.” Umma tace, “Yana da daraja kenan tunda har ka tabbatar da yana da tsada diyar sa dan haka ko a biya ko naje kotu.” Dpo yace, “Hajiya babu batun zuwa kotu magana za’a gama a rufe ta anan tunda mijin tane in kin kai shi k’ara babu riba.” Umma tayi shiru kafin ta tausasa murya tace, “fisabinillahi ace yarinya mai ciki mijin ta ya dake ta har abinda yake ciki ya mutu wannan darajar miji ce? Ba yau ya saba dukan ta ba amma tunda tana da ciki kamata yayi ya anada dukan nasa ya bari ta haihu sai y d’ora daga inda ya tsaya. Haka kwanaki ma ya dake ta aka tabbatar mana da cikin ya kusa fita nayi hak’uri na bar maganar yanzu kuma ya sake, wannan daidai ne?.” Dpo yace, “Gaskiya bai kyauta ba.” Umma tayi shiru bata ce komai ba ganin hakan ya saka yace, “Yanzu dai ki yi hak’uri tunda mijin tane komai ya wuce Allah da ya basu cikin zai sake basu nan gaba, magani da komai daman a wuyan da yake dan haka kiyi hak’uri a bar maganar nan haka.” Ya kalli Yusuf yace, “ka bata hak’uri dan baka kyauta ba.” Yusuf yayi shiru bai ce komai ba bai ma kalli Umman Umma tace, “ka gani bazai bada hak’uri ba, da nasan haka za’a yi fa bazan kawo case din nan wajan nan ba wallahi. Wani wajan zanje daban inda nasan za’a yi min abinda nake so.” Abie ya kalli Yusuf suka had”a ido sai Yusuf yace, “Kiyi hak’uri.” Ta zabga masa garar tace, “haka kazo har gida kace baza’a sake ba sai gashi a sake abun yayi gaba ma fiye da baya. Ranka ya dad’e ina so ayi rubutu kowa ya saka hannu indai ya sake dukar min yarinya wallahi sai maganar nan taje gaba.” Shi dai mamaki ma yake yi a ina suka samo wannan sirika masifaffiya wacce bata girmama masu matsayin sirikai? Sai a lokaci ya tuna ya Santa a kwanaki yayi case da ita kuma itace tayi nasara shiyasa ta kawo abun gaban sa amma baice komai akayi rubutu kamar yadda tace aka bar copy d’aya a hannun dpo d’aya a hannun ta tace, “Gashi nan ya saka hannu in ya amince.” Dpo yace, “Yusuf ka saka hannu.” Babu yadda ya iya haka ya saka hannu akan rubutun bazai sake dukan Asiya ba sannan aka sallami case din. Umma na fita daga office din Dpo kalli Abie yace, “A ina kika samo wasa nan matsayin sirikai? Na San matar bata da mutunci daga ita har y’ay’an ta bata ganin darajar kowa , Yusuf ne ya kai ka hada zuri’a da wad’annan dan Allah?.” Abie yace, “Sakyya ce da rashin jin magana.” Dpo yace, “yanzu badan kazo ba inda wani wajan takai case din nan sai yayi prison fa dan ba abu bane na wasa, dukan mace mai ciki har d’an ya mutu in badan Nigeria ba Wallahi duk da mijin tane wannan ba abu bane da za’a barshi. kaima bai kamata ka daki mace mai ciki ba wannan ba dabi’a mai kyau bace ba Yusuf. Yanzu gashi da mutuncin ka dana ahlin ku an d’auko ka an kawo ka nan da sunan ana k’arar ka. Ina dad’i a wannan lamarin dan Allah?.” Abie yace, “bari kawai, Allah ya kyauta kawai za’a ce” ya fad’a yana tashi tsaye suka gaisa tare da yin sallama suka fito. A lokacin sallah ake sai da suka yi azahar sannan suka wuce zuwa gida. Suna shiga falon Ammah ce da Yayan Abuja ganin harda Yusuf ya shigo suka kalle shi Yaya tace, “An Sako shi kenan.” Mubarak ya tab’e baki yace, “Allah ya raba mu da sirikan banza wanda zasu tozarta ka a idanun jama’a, wai sirika ce zata kai k’arar sirikin ta saboda lalacewa” yana fad’a ya wuce Yusuf baice komai ba yana tsaye har lokacin sai kuma ya waje ya zauna a kusa da k’afar Ammah kawai ya kwantar da kansa a k’afar ta amma baice komai ba. Kallon sa suke yi babu wanda ya iya magana kafin Abie yace, “Sai ka tashi kaje asibitin inda take ka biya komai kafin ta sake biyo ka nan tayi maka sabon lissafi.” Bai isa motsawa ba yana kan k’afar Ammah baice kanzil ba dan bazai iya magana ba a wannan lokacin ba. Abie yace, “Ammah ni na wuce sai anjima, naga an fara yin decoration, me humaira zatay ne yau?.” Yayan Abuja tace, “Wai henna party zatayi.” “Bidi’a Kala-kala” ya fad’a yana fita har lokacin Ammah bata ce masa komai ba shima bai ce ba bai kuma d’ago kansa daga k’afar ta ba. Humaira ce ta shigo tana waya tana cewa, “Yauwa sis na gode sosai sai na ganki.” Ta fad’a tana kashe wayar tace, “Ammah Ameena ce tace ta saka masu small chops zasu zo yanzu nan daman kuma kamar na sani ban kira ko ba.” Ammah tace, “banda kayan rabon da tayi harda wannan wahalar? Zata zo din ne?.” “Tace min dai wai gata nan dai amma gobe dai zata je.” Ammah tayi murmushi akwai bata cse komai ba Humairs tace, “Wai Yaya Yusuf ne a kwance haka?.” Yayan Abuja ta tab’e baki itama haka bata ce komai ba ta wuce zuwa ciki dan an kusa fara mata make up. Ammah ce ta gaji da shirun da yayi sai ta d’ago kansa daga jikin ta taji jikin sa zafi sosai tace, “Subahanallahi Yusuf baka da lafiya daman?.” Kallon sa tayi taga fuskar sa kamar an zuqe ta tace, “me yake damun ka? Jikin ka yayi zafi sosai.” Baice komai ba sai kallo kawai ya mik’e tsaye ya fita daga falon Ammah ta kalle shi tace, “Yaron nan akwai abinda yake damun da fa. Kalli yadda ya koma kamar ba shi ba.” Yayan Abuja tace, “ba haka suka bar Yusuf ba fa Ammah sun had’a da asiri wallahi, tun farkon neman auren yadda yake rawar kan nan wallahi nasan akwai asiri a ciki, amma sun min daidai ita wacce bata asirce shi ba ai azabtar da ita yake yi.” Amma bata ce komai ba tayi shiru kawai dan duk abinda ya faru shine ya jawowa kansa da kansa. Yusuf baice asibitin ba gida ya wuce kawai ya shiga b’angaren Ameena ya wuce sama har d’akin Ameena ya kwanta a kan gadon ta da har lokacin yana nan kamar tana gidan dan ba komai suka d’auka ba, a wannan lokacin ne zuciyar sa ta kasa rik’e abinda yake zuciyar ya fashe da kukan da bai san dalilin sa ba a wannan lokacin kawai yaji zubar su ne dan bazai iya cigaba da rik’e su ba. Kuka yake sosai kamar d’an yaro gashi bai san dalili ba abinda ya sani in baiyi kukan ba zuciyar sa zata iya bugawa. Ya jima yana kukan sosai kafin ya koma sauke numfashi a hankali bacci ya d’auke shi. Sai la’asar ya tashi ya shiga band’akin ta yana kallo ga shower gel dinta nan da komai a ajjiye kamar tana ciki ya jingina da bango yana kallon komai yana ji a ransa kamar zai ganta. Dakyar ya lallab’a yayi alwala ya fito yayi sallah a d’akin nata ya zauna inda take zama tana jan charbi yayi tagumi ba tare da yasan abinda yake damun sa ba. Abinda ya sani yana tunanin Ameena a wannan lokacin, yana jin kewar ta sosai a zuciyar sa da gangar jikin sa, yana ji kamar a mafarki in ya tuna wai babu Ameena a gidan sa, wai shi da kansa ya sake ta abin yana d’aure masa kai sosai. Abbah ya gani yana yi amsa waya ya d’auka Abbah yace, “malam duk inda kake ka wuce asibitin da matar ka take kaje can ka biya abubuwan d aka kashe, dan rashin hankali ka yiwa yarinya illa kuma kayi zaman ka a wani wajan baka je inda take ba? Ka tashi ko me kaka yi ka tafi kaje can ka biya komai, wallahi na sake kira baka je ba sai ranka ya b’aci.” Datse kiran Abbah yayi Yusuf babu yadda zaiyi dan badan Abbah ba wallah baza shi ba ya tashi ya fita ya hau sama yayi wanka ya canja kaya ya fito kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ya hau mota ya tafi asibitin da Abbah yace masa. Sai baya ya shiga ne ma ya tuna ashe fa bai san a inda suke ba gashi babu wanda zai tambaya balle a raka shi, yana ajjiye motar yaga Momi k’anwar ta tana magana da wani mutum a tsaye sai ya fito lokacin yaga ta shiga ciki yabi bayan ta har d’akin da yaga ta bud’e ta shiga, shima bud’e k’ofar yayi ya shiga da sallama ya same su a zaune gabad’aya su harda Umman da Umma Sakina suka amsa kowa fuska a d’aure ana kawar da kai a lallai anyi musu laifi, “Barkan ku da yamma.” “Sai yanzu kaga damar zuwa kenan?” Umma ta fad’a tana kallon sa. “Yanzu na samu lokaci” ya fad’a Tana kallon Asiyan da take kwance. Umma da mamaki tace, “da Baka da lokacin zuwa ka ganta kenan? Ka yiwa yarinya wannan asarar kace sai yanzu ka samu lokaci?, dan Kaga na bada dama a sake ka shine kake min gadara?.” Banza yayi mata bai amsa ba dan yadda yake ji a zuciyar sa tsaf zai iya fad’a mata magana. “Bashi bill din abubuwan da aka kashe wanda kika biya ya biya ki kudin ki” umma ta fad’a tana kallon Maimuna. Maimuna ta mik’a masa takarda ya karb’a yana kalla ganin kudin kasan k’arya ne sai ya kalle ta yayi murmushi kawai yace, “Zan tura miki.” “Tura yanzu” ta fad’a tana kallon sa yayi dariya kad’an ya d’auko waya yana dannawa tana fad’a masa yana rubutawa har ya tura mata Umma tace, “Wallahi ko nan gaba kar ka sake dukar min yarinya ba jaka bace ba.” Yusuf yace, “a ja mata kunne ko nan gaba kar ta sake saka iyayena a maganar ta, daga yau kuma in ta sake yi min sata ko mai aka kashe a asibiti za’a dauka a kudin satar da take ajjiyewa a biya. İn kuma ta saka duka yanzu ta fara shan sa” ya fad’a ba tare da ya kalle su ba ya juya ya fita Umma Sakina tace, “Lallai akwai sake akan lamarin nan, mu yake kalla ya fad’awa wannan maganar?. sai mun sake mik’ewa akan wannan yaron matuk’ar ba so muke nan gaba yafi karfin mu ba.” Umma mamaki ya cika mata zuciya ganin abinda yayi amma sai tace, “shi d’in banza ai bai isa ba wallahi, amma zamu sake zage dantse dan nuna masa wanda ya tab’9 ba wanda aka ake tab’awa a zauna lafiya bane ba wallahi, Mun fi karfin sa nesa ba kusa ba.” Maimuna tace, “Wai harda a ja mata kunne, Kaji wannan mutumin dan Allah.” Duk sukayi kwafa alamun za’a sake had’uwa dan sai sunyi maganin sa. Washe gari juma’a Ameena ta shirya ta fito tayi kyau sosai dan kayan da ta saka sun amshe sosai ta riga da siket ta saka rigar har guiwa mai fad’i tayi rolling kanta da mayafi ta d’auki jaka yayi matuk’ar kyau sosai kamar wacce bata haihu ba. Aunty Aisha ce take kallon ta tunda ta fito tana cewa, “kai yarinyar nan kinga yadda kika yi kyau kuwa?. Wallahi babu wanda zai ce ke kika haifo Zaitun.” Tayi dariya tace, “Kai Aunty, dan Allah wai yanzu baza ki je ba?.” “Babu Inda zani mijina zai dawo anjima, kije kedai amma banda ni.” “Wallahi bana son zuwa ni kad’ai ga Zaytun tana can.” “Ba Rukayya kika ce zata raka ki ba?.” “Bata da lafiya bazata je ba.” “Sai ki yii hak’uri ki tafi haka, nikam na wuce sai kin dawo” ta fad’a tana wucewa ciki dole Ameena ta fita harabar gidan amma babu wanda Yaya yace ya dinga kaita duk inda zata je. Dawowa ciki tayi ta masa waya bai d’auka ba tana nan zaune har akayi magriba Aisha ta fito tace, “baki tafi ba?.” Tace, “eh Aunty, baya nan wanda zai kai ni din.” “Gashi ya hana ki Jan mota, kuma fita ki gani ko yana nan yanzu, ni ban san dalilin sa na hana ki Jan mota ba wallahi.” Ta amsa da to ta tashi ta fita amma baya nan sai Al’ameen da yake a tsaye a wajan mai gadi sun magana ta nufi wajan da niyar tambayar mai gadin. Kallon Ameena yake da dukka hankalin sa dan tayi masa kyau fiye da tunanin sa a lokacin ta k’araso wajan sa tace, “ina yini.” Yayi murmushi yace, “lafiya lau Ameena, ina zuwa da magriba nan?.” Ameena tace, “biki zanje ga Yaya yace akwai Salisu zai dinga kaini amma ban ganshi ba.” Mai gadin gidan Yaya yace, “Salisu yaje Wudil wallahi, duk yadda akayi bai san da fita yau din ba.” Ameena tace, “shikenan to bara na hak’ura na koma ciki.” Al’ameen yace, “an ina ne wajan bikin?.” “A nan cikin nasarawa wajan yake.” “To bara na d’auko mota sai na kai ki.” Ta amsa da to ta shiga ta fad’awa Aisha ganin ta bada goyan bayan hakan sai hankalin ta ya kwanta dan tsoron fad’an Yaya take yi. Ba jimawa Al’ameen yazo suka tafi wajan bikin shida Ameena tana gaba a zaune, suna tafiya babu mai magana a cikin su yace, “wacce makarantar kike yanzu?.” Ameena tace, “wata private university ce a nan cikin hotoro.” “Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya bada nasara.” Ta amsa da amin tayi shiru bata sake magana ba sai satar kallon ta yake ita kuma kallon ne bata so dan tana Lura dashi kawai tana basarwa ne kamar bata gani ba. Wajan bikin suka zo ya tsaya ya kalle ta yace, “to k’arfe nawa zaki gama bikin?.” Ameena tace, “wallahi ban sani ba dan ban sani bama ko an fara.” “To ki saka min number ki in yaso in kin gama sai ki kira ni nazo na d’auke ki.” “Da ka barshi ma ba sai ka dawo ba bazan rasa wanda zai kawo ni a ciki ba sboda duk na san su.” Fuska taga ya d’aure ya kalle ta yace, “nima kamar Adam yake in baya nan nine madadin sa, ban amince ki shiga motar kowa ba ki bani number ki in kin gama zan zo mu tafi.” Ameena tace, “To.” Waya taga ya mik’a mata ta saka number nan take ya kira ta shigo yace, “Yauwa jeki.” “Na gode.” Ta amsa tana fita ta shiga wajan bikin. Kid’a ne yake tashi tun daga bakin gate daga can gefe kafin ka shiga wajan bikin ta hango Ammah da su Yayan Abuja a tsaye sunyi kyau sosai kowa ya sha kwallaiya ba kamar Ammah kamar ba ita ba. kamar baza ta k’arasa ba dan ji take wani iri a jikin ta sai kuma ta daure kafin su gani ta Zaytun ta ganta tace, “Mummy!” Ta fad’a tana yin gudu zuwa wajan duk sai suka kalli wajan. Nan take farin ciki ya bayyana a fuskar Ammah ganin Ameena ta k’arasa Ammah tace, “ai Humaira tana nan tayi fushi dake.” Tayi dariya suka gaisa Yayan Abuja tace, “ko ni nayi fushi ba Humaira ba, sai yanzu ma zaki zo.” Ameena tayi dariya tace, “na rasa wanda zai kawo ni ne Yaya ya hana ni tukin dare shiyasa na jima ban zo ba.” Ammah tace, “ai kam ya kyauta dan tsaf a tare ki a kwace motar. Ma sha Allah Daughter kinga yadda kika yi kyau kuwa?.” Ameena tayi dariya Yayan Abuja tace, “Wallahi Ammah, kamar ba ita ba dan baza kice tayi aure tana da yarinya kamar wannan ba, lallai Ameena mai Yaya Adam yake baki?.” Dariya tayi kawai bata ce komai ba dan wallahi nauyin su yake ji sosai Ammah tace, “Allah kamar ba ke ba, kodan na jima ban ganki bane?.” Ita dai murmushi take yi kawai Ammah ta kalli Yayan Abuja tace, “wai ina wanda nace ya kawo min jakata ne? Wayata tana cikin jakar nasan ana ta kira na ina ya tsaya bazai kawo min ba.” Mubarak da yake tsaye yace, “Yusuf ne wallahi shi yace gashin an zai kawo miki har yanzu bai zo ba, gashi nan ma.” “Mtsww! Kuma ku rasa waye zai kawo min jakata sai Yusuf? Meyasa kai baka koma ka d’auko min ba?.” Mubakar yace, “zan koma kika ce fa na tsaya a nan akwai bak’in da zasu zo na basu kati” ya fad’a yana kallon bayan su ko zai ga Yusuf din. Mubakar yace, “Yauwa gashi nan ma ai.” Zaytun ce tayi wajan sa suka k’araso tare Ameena tana wajan a tsaye ko gezau batayi ba dan tayi alqawarin baza ta nuna ta ganshi ba in kuma ya zama dole baza ta nuna amsa komai ba, kamar yadda zasu gaisa da Mubakar haka zasu gaisa dashi ta wuce. Yana zuwa Ammah tace, “Kai komai sai ka b’ata lokaci.” Baice komai ba ya bata jakar bai ma kula da wacce a wajan ba Zaytun tace, “Daddy ga Mummy” ta fad’a tana nuna masa ita gaban Yusuf ya fad’i sosai ya d’ago ido ya kalle ta yaga bashi take kallo ba ita da Yayan Abuja suke magana kamar ma bata san yana wajan ba. Juyawa kansa yake yi tun ranar da suka rabu sai ranar ya ganta hankalin sa yaji yana neman barin jikin sa zuciyar sa na bugawa sosai yayi kamar zai fad’i Allah ya taimaka ya tsaya ya dafe kansa baice komai ba. Ammah na kallon sa tana kuma kula da yanayin sa Ameena ta burge ta sosai da bata rud’e ko ta nuna wani abun ba da ta ganshi tayi tsaki tace, “muje ciki.” Tare suka wuce Ameena suna ta hira da dariya kamar bata ganshi ba nan kuwa sarai ta ganshi akwai bata da lokacin masa magana ne. Dakyar ya iya barin wajan ya shiga mota ya tafi zuciyar sa na bugawa sosai ba tare da yasan dalilin faruwar hakan ba. Ameena ta sake a cikin mutane Ana ta hidima da ita da yawa wanda basu san Yusuf ya sake ta ba d’auka suke matar Yusuf ce har lokacin. Sai gab da za’a tashi ta kira Al’ameen yazo ya mata waya yace gashi tazo ta fito kamar su Ammah suce ta tsaya mama baby yadda zasu yi haka ta fito gashi tace baza taje dinner ba. A waje ta ganshi a mota ta shiga da sallama ya amsa yaja motar yace, “Har an gama bikin?.” Tayi murmushi tace, “eh an gama.” “Yayi kyau.” Ya fad’a yana cigaba da tafiya har suka zo k’ofar gidan ya tsaya ta kalle shi tace, “Na gode Yaya Al’ameen.” Yayi murmushi yace, “Nima na gode sosai.” Ta kalle shi ganin irin kallon da yake mata sai ga d’suke kai ya fita daga motar ta shiga cikin gidan, sai da yaga an mayar da k’ofar an rufe sannan ya k’arasa nasa gidan yana ji a ransa ya zama dole ma ya san abinda zaiyi ya mallaki Ameena. Bayan kwana biyu. #Book3 #Mai daki #Nana Haleema Book3 021 Adam da Al’ameen suna tsaye a k’ofar gida suna hira Ameena ta dawo daga makaranta tazo wuce su a k’asa tace, “Ina wuni.” Al’ameen ya amsa yana kallon ta yace, “ya na ganki a k’asa? Ina Salisu din?.” Ameena tace, “Yaya ne ya aike shi ya tsaya a nan farkon layi ni kuma na gaji gida nake so shiyasa nace zan k’araso k’afa shi ya tsaya.” Al’ameen yace, “ai dole, shiga k’i huta.” Ta bud’ egate din gidan ta shiga ya bita da kallo har ta kulle sannan ya kalli Adam yace, “Dan Allah na tambaye ka.” Yaya Adam yace, “ina jinka.” “Ina da wata dabi’a mara kyau da ka hana ni tunkarar Ameena da abinda ya jima a zuciyata?.” Yaya Adam yayi murmushi yace, “ai ina jin ni ne zan zo a mutum na farko da zai fara yabon halayyar ka, in ban zo a na farko ba zan zo a na biyu. Ba hana ka magana da Ameena nayi ba Al’ameen kawai dai….” Ya katse shi ta hanyar cew, “Kawai me? Indai har da gaske bani da wata dabi’a mara kyau ka bani dama nayi magana da ita, kai kace min masu sonta suna ta zuwa kai kake dakatar dasu meyasa ni baza ka bani dama nazo ba?. Adam kafi kowa sanin ina son Ameena so na hakika meyasa kake yin abu kamar zan cutar da ita in ka bani ita?.” Adam ganin Al’ameen ya d’auki zafi sai yace, “Ko kusa Al’ameen, ni kunya nake ji ashe kana abokina babba amini kazo kace kana son kanwata. Abun kamar da raini a ciki.” Al’Ameen yace, “Kai kake ganin haka ni bana gani, kaine sarkin son girma ni babu wannan a gabana wallahi, ka bani dama naje ga Ameena na fad’a mata abinda yake zuciyata watakila ni ne mijin ta na biyu.” “Shikenan to zan sanar da ita zuwan ka sai ku zauna ku tattauna.” “Yau nake so hakan ta kasance ba gobe ba.” Adam ya kalle shi yace, “umarni kake bani kenan?.” Al’ameen yace, “oho maka dai. Kai bafa sai ka bani dama ba, wallahi naga dama zanje na same ta kai tsaye ai Nima Yayan tane ina da ikon bada auren ta sai na bawa kaina.” Yayi dariya ya kalle shi yace, “to a haka zan baka ita baka girmama ni?.” Al’ameen ya harare shi shima yayi dariya baice komai ba ya shiga gida. Aisha matar sa ya samu a d’aki ya shiga yana cewa, “Aisha Al’ameen ya takura akan sai yayi magana da Ameena, ni ban san taya zan fad’a mata Al’ameen yana sonta ba wallahi” ya fad’a yana dariya tare da zama a kan gado. Aisha tayi dariyar itama tace, “Fad’a mata zaka yi ai kawai, Al’ameen irin mijin da zaka aura mata ne.” Ya girgiza kai yace, “dari bisa dari kuwa, Al’ameen mutum ne yasan darajar ilyalan sa sosai. Duk inda kike tunanin Al’ameen ya wuce haka. In ma kud’in ne yana da kud’i fiye da tunanin ki kawai shi ba wani lokacin bai da ya nuna ba ne.” Aisha tace, “to ka gani ai abu ne mai kyau.” “hutun mu ya kusa k’arewa zamu koma Kalaba nan da y’an kwanaki in na zan jima ban dawo ba, ban sani ba da ita zamu tafi ko an ina zamu barta?.” “Tafiya da ita ai bazai yu ba ka manta tana makaranta? Tafiyar da in mukayi bamu San lokacin da zamu dawo ba?. Ai baza mu tafi da ita ba sai dai na zauna a nan mu zauna tare.” Yaya Adam ya jinina kai yace, “bara na same ta naji ya zata karb’i batun Al’ameen” har zai fita sai kuma ya dakata yace, “in anyi sallah naje yanzu tana hutawa naga ta gaji sosai.” Aisha tace,”ni so nake tayi auren ma wallahi a kwanakin nan.” “Meyasa kika ce haka?.” “Saboda a cikin abinda ya raba auren ta harda maganar rashin sauke hakki da bata samu har yake shan magani, duk da yanzu tasan bata da aure baza ta saka abun a ranta da zai dame ta ba amma yau da gobe sai Allah.” Yayi shiru yana jinta yace, “haka ne maganar ki, zan same ta naji ga zamuyi da ita” ya fad’a yana tashi ya fita. Bayan sallar magriba suna tare da ita a falo Yaya Adam ya kalle ta yace, “Ameena ta.” Ta kalle shi tana murmushi yace, “Akwai bak’on da zai zo wajan ki in anyi sallar i’sha.” Ta d’ago da sauri ta kalle shi ya d’aga mata kai yace, “ya takura akan sai kunyi magana Ameena na dakatar dashi ya dage akan na taimaka na bashi dama ku tattauna. Zai zo anjima Kuyi magana.” Ameena tace, “Amma Yaya kace sai na gama makaranta.” Aisha tace, “ko a gidan ki zaki k’arasa karatun ai Ameena.” Yaya yace, “babu wanda zan bari ya aure ki sai anyi yarjejeniya akan zai barki ki cigaba da Karatu. Sannan ai ba auren sa zakiyi ba kawai na bashi dama ne akan yazo ya ganki ba wani abun ba.” Ameena tace, “To Yaya.” “In Anyi sallah sai yazo ku gaisa.” Ta amsa da to tana zaune bata sake cewa komai ba har akayi kira ta tashi ta shiga d’aki tayi sallah. Bayan ta idar da wani lokaci taji yana kiran ta hijjabi kawai ta saka suka fito tare da Zaytun Yaya ya kalle ta yace, “Yanzu zai shigo, ki zauna.” Ba musu ta zauna suna ta hira da Zaitun a zuciyar ya tana mamakin itace ta fara zuwa kafin shi maimakon shi yazo kafin ita, Al’ameen ya shigo da sallama tare da k’arasowa ta amsa tana kallon sa da murmushi tace, “sannu da zuwa Yaya Al’ameen .” “Yauwa Ameena sannu” ya fad’a yana zama Zaytun taje wajan sa ya d’auke ta yana yi mata wasa. Kallon Ameena yayi yaga da alama bata san shine bak’on naya ba sai yayi murmushi yace, “Zaytun jeki wajan Anty zan aiko miki da alawa.” Da sauri ta shiga ciki tana tsalle-tsalle ya kalli Ameena yace, “Nime bak’on da Adam ya fad’a miki zaka yi.” Da sauri ta kalle shi jin abinda yace wai shine bak’on nata da akace zatayi to ta ya ya?. Ganin yana mamaki sai yayi murmushi yace, “kinyi mamaki ko?.” Ameeena ta sunkuyar da kai dan ita abun dariya ma yaso bata tayi sa’a ta rike dariyar yace, “Nasan zaki yi mamaki Ameena amma ba abun mamaki bane dan tun kafin ki yi auren farko naso Yayan ki ya bani ke amma sai yak’i.” Murmushi yayi tare da girgiza kai yace, “A karo na biyun ma yanzu dakyar ya bani wannan damar nan, ban sani ba ko gani yake yi na miki tsufa dai shi ya sani.” Dariyar tace ta fito fili tayi kad’an amma bata ce komai ba yace, “Gani nazo ina so na shiga cikin jerin masu son auren ko a wannan lokacin, bazan bari ki kubce min ba kamar lokacin baya ba zanyi abinda zanyi dan ganin na rik’e ki da kyau kin kasa kwacewa.” Ameena ta d’ago tayi murmushi amma bata ce komai dan ita fa mamakin abun ma take yi wai shine yake sonta, Al’ameen yace, “Na tab’a aure amma matar tawa da abinda yake cikin ta tun kafin yazo duniya sun rasu a hatsarin mota da suka yi, yanzu bani da kowa iyaye sun jima da barin duniya mata ma haka, sai y’an uwa.” Ameena tace, “Allah ya gafarta mata yasa tana aljanna.” “Amin na gode. Ke nake so ki zamar min komai Ameena, ke nake so ki zamar mata ki zaman min iyaye wanda zan dinga kalla ina farin ciki kamar ko wanne yaro. Ameena da gaske ina sonki so na tsakani da Allah wanda tun kina k’arama yake a zuciyata. Tun wannan lokaci har yanzu soyayyar ki tana nan a zuciyata dan ke na fara so bana tunanin soyayyar ki zata gushe koda mutuwa nayi nasan da ita zan bar duniya a zuciyata. indai kika bani dama baza ki yi dana sani ba Ameena zan kasance miki tamkar Yaya Adam wajan kula da tarbiyyar ki, sannan zan zamar miki tamkar dan aikin ko komai kike so shi zan miki Ameena.” Shiru tayi bata ce komai ba ya sake cewa, “Tsakani da Allah kina ji a zuciyar ki zaki iya aurena?.” Ameena bata d’ago ba tayi shiru yace, “amsa zaki bani Ameena zaki iya aurena?.” “Wallahi ban sani ba duk abinda Allah ya tsara min shine daidai a wajena, bani da Zab’i zan iya ko bazan iya ba indai Allah ya iya min Alhamdulillah” ta fad’a a sanyaye bata kalle shi ba. “Hankalin ki da nutsuwa kamar yadda kika nuna yanzu shine ya sake dasa min soyayyar ko a zuciyata, ina ji a jikina kamar silar aurena dake ne Allah ya kaddara mutuwar auren ki. Ko wacce kaddara tana da sila komai na duniya yana da mafari yana kuma da k’arshe.” Ta girgiza kai tace, “haka ne kam.” “Ina fatan mafarin k’addarar mu nida ke ya kasance a wannan lokacin, ina nan ina fad’awa Allah ya sa Ameena ta kasance mallakina a wannan lokacin.” Tayi dariya kawai bata ce komai ba yace, “yadda kike dariyar nan da murmushi Allah yasa har zuciyar ki kike yi ba iya fuska ba.” Ta sake yin murmushi dan ita dariya yake bata ba wani abun ba tace, “Amin.” “Kar na cika ki da magana ya kamata na tafi na barki amma bana son tafiyar ji nake ina ma mu kasance a haka har abada.” Sai kuma ya mik’e yace, “na tafi Ameenatu ina fatan in na sake dawowa zan samu kalamai masu dadi’i daga wajan ki.” Ta mik’e itama tace, “Na gode sosai, Allah ya bamu alkhairi” ya amsa da amin ya fita yana jin zuciyar sa fess ko babu komai ya fad’i abinda yake zuciyar sa wanda ya jima yana damun sa. Yana fita Anty Aisha ta fito falon sai Ameena ta kalle ta ta fashe da darıya tace, “Anty wai Yaya Al’ameen ne yake sona, abin mamakin bai ji kunya ta ba ya zauna dani yana fad’a min yana sona kamar ba shine abokin Yaya ba.” Anty Aisha ganin Ameena ta mayar da abin wasa sai tayi dariya tace, “Bafa abin dariya bane Ameena da gaske sonki yake kuma auren ki zaiyi in kin bashi dama.” “To ni da ba aure zanyi yanzu ba.” “Za dai kiyi ko wanne lokaci ne zaki yi auren, kuma gwara irin su masu hankali wanda aka san halin su akan wanda ba’a san hali ba.” “Tab, ni wallahi dariya abin yake bani sosai fa Anti.” Anti tayi dariya tace, “zai daina baki darıya ranar da akace an d’aura auren ku.” Ameena ta wara idanu tace, “wai!” Sai ta sake yin dariya sosai kafin ta shiga cikin daki tana jin nishadi a zuciyar ta bata san dalilin zuwan sa ba. Yusuf yana zaune a falon Ammah shida Amma yana cin abinci amma babu wanda yake magana a cikin su ita waya ma take dannawa shi kuma ya saka abincin a gaba yana ci kad’an-kad’an ture abincin yayi ya jingina da kujera ya kulle idanun sa kafin yace, “Ammah zuciyata bugawa take yi ban san dalili ba.” Ammah ta kalle shi cikin kwanakin tausayi yake bata sosai ya gama fita daga hayyacin sa kana kallon sa zaka gano hakan a tare dashi tace, “Sannu, kai ta maimaita Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un zaka ji dad’i.” Ya lumshe idanun sa baice komai ba tace, “kaci abincin wannan ramar da kake yi da yunwa Yusuf.” Ya girgiza kai yace, “Babu Yunwa Ammah, ba Yunwa bace damuwa ce tayi min yawa.” “Allah ya yaye maka” ta fad’a tana cigaba da danna wayar ta amma zuciyar ta na tare dashi. Mubakar ne ya shigo ya shigo Tana cewa, “Ammah dan Allah bani lambar Mummyn Zaytun.” Ammah ta kalle shi tace, “lafiya dai?.” “Mtsw! Tun bikin Humaira ranar kamun nan wani abokin ango ya ganta aka had’o dashi ya takura min shi ko lamabar tace na bashi, wallahi a kullum sai yayi min magana yafi sau biyar. Naga alamun serious sonta yake shiyasa zan bashi lambar ta na huta da magana dashi.” Ammah tace, “ai da gidan su ka kwatanta masa yaje yayi magana da Yayan ta kafin ita indai da gaske.” Mubakar yace, “Hakan za’a yi, ai ban san gidan ba” sai yayi gaba yace, “bara na kira Humaira ta bani full address din gidan sai na tura masa na huta Nima” ya fad’a yana ficewa Amma tace, “in ya samu Ameena yayi sa’ar da ba kowa ne yake yin irin ta ba. Wasu ko sunyi irin ta sai suyi wasa da ita ta kubce musu.” Kallon Yusuf tayi taga ya runtse idanun sa sosai yaja numfashi mai tsaho kafin ya cize bakin sa yace, “Ammah zuciyata tana yi min zafi sosai, ki bani magani dan Alalh, Ammah zafi nake ji” ya fad’a a gigice kamar bashi ba, da sauri ya taso tazo inda yake tace, “Yusuf lafiya kake? Me kake ji a zuciyar taka?.” Nuna mata kirjin sa yake yana jan numfashi sosai kamar ciwo yana hakki yana gumi kamar yayi gudu. “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!” Amma ta fad’a hankali a tashe tana buga fuskar sa tace, “Yusuf! Yusuf!! Kana jina?.” Numfashi yake ja a hankali ta d’auki ruwa ta d’aga kansa ta bashi yasha ya kwantar da kansa akan table din da yake zaune yana cigaba da jan numfashi a hankali a wahalce. A hankali numfashin nasa yayi daidai ya bud’e idanun sa da suka yi ja sosai ya kalli Ammah ta rik’o hannun sa tace, “taso ka dawo kan kujera zaka fi sakewa” tashi yayi ya dawo kan kujerar ya zauna ta zauna kusa dashi tace, “Sannu, babu abinda kake ji yanzu?.” Girgiza kai kawai yayi baice komai ba ta zuba masa ido kawai tana kallon sa bata ce komai ba itama. Abbah ne ya shigo falon ya k’araso ya zauna yana kallon su ita da Yusuf din yace, “to Lafiya dai?.” Ammah ta nuna masa Ysusuf da kana kallon sa kasan ba Lafiya yake ba yace, “bashi da lafiya?.” “Babu Lafiya, Kaga yadda numfashi sa ya dinga yin sama d’azu kafin ka shigo ? Bai jima da dawowa daidai ba.” “Yusuf akwai abinda yake damun ka ne?.” Ya kalli Abbah yace, “komai damuna yake Abbah, ina jina kamar ba mutum bane ba ni.” “Allah ya kawo mafita.” Ammah ta amsa a bayyane shi kuma yayi shiru. Abbah ya kalle shi yace, “ka tashi kaje gida ka huta.” Yusuf ya mik’e ya fita baice komai ba yana fita Ammah ta kalli Abbah yace, “lamarin a Yusuf Wallahi akwai saka hannu a ciki.” Ya kalle ta yace, “maganar da muka gama yi da Usman abokin sa Kenan, yace min dan Allah a mayar da hankali aman Yusuf dan yana cikin damuwar da zata iya yi masa illa fiye da tunanin mu.” “Kaji ko, dan Allah mu dage a kansa a fara yi masa addu’a da saukar alkur’ani ko zai dawo daidai.” Abbah ya kalle ta yayi murmushi yace, “Keda kika ce ko mallake ke shi matar zata yi ta mallake babu ruwan ki? Meyasa kike son a samo masa magani yanzu?.” “Yayi kuskure, kuskuren da ya aikata ne suke bbibiyar sa sakayyar Ameena yake gani tun ba’a je ko ina ba. Amma hakan ba yana nufin zamu watsar dashi bane in bamu taimaka masa ba waye zai taimaka masa?.” Abbah yayi murmushi jin yadda take magana a sanyaye yace, “haka ne, na saka ayi saukar alkur’ani akwai kuma wani maganin sirihi da naji wani malami ya bayar na ganyen magarya na saka a had’a masa sai ki dinga bashi yana sha tunda yanzu kusan kullum yana wajan ki. Na jima da sakawa Ana yi masa addu’a sannan kema ki dinga dagewa a kansa wajan sallah, in kuna tare kice masa ya dinga karanta alkur’ani ko yayi lazumi, ki daina barın sa haka yana zaune yana wannan tunanin na banza.” Ammah tace, “to Allah yasa a dace.” “Amin, ki kwantar da hankalin ki haka sakayya take akwai zafi sai ka fita daga hankalin ka wallahi. Yusuf ma ai tayi masa da kyau.” Ammah ya girgiza kai bata ce komai ba Abbah ya shiga ciki ya barta da tunanin mafita, daman yasan dole magantu ita uwa ce bazata so ta cigaba da ganin sa haka ba dole zuciyar ta ta karye. Yusuf yana komawa gida wajan Asiya ya shiga bai same ya a falo ba ya hau sama zai shiga d’akin sa ya jiyo shewar ta tana cewa, “Shiyas nake yin ki uwata gari, yanzu sabon salon da ya dauko kenan zama a gidan su, ni so nake ya daina ya ma daina zuwa gidsn kamar yadda ya fara a baya ya zama daga ni sai ni, Ameena kuma ta barshi har abada dsn yadda muka raba su bazai sake waiwarta ba in sha Allah.” Abinda yaji kenan bai tsaya ya sake jin wani abun ba ya bud’e d’akin ya kalle ta maimakon taji tsoro ta kashe wayar sai tayi dariya tace, “gashi nan ma ya dawo daga wajan Ammah din, Sannu d’an Ammah” ta fad’a tana kallon sa cikin rainin hankali. Kashe wayar tayi ya kalle ta kamar zai magana sai kawai ya fasa ya fita ya zauna a falo. A tsaye ya ganta a kansa tace, “sai ka dinga shigo min gida babu fara’a akwai abinda nayi maka ne?.” Bai magana ba tace, “kana jin ai abinda nace ko?.” Nan ma yayi shiru tace, “kana ji fa.” “Ameena bana son magana.” “Kutmar uban can, Ameena kace fa?.” Kallon ta yayi ya kulle ido sunan ne kawai yazo bakin sa yaji ya furta ya bud’e ido zaiyi magana tace, “sai ka fad’a min wajan ta kaje? Dawo da ita kake so kayi kenan ko?. Dan tsabar wulakanci da iskanci ka kalli idona kace min Ameena dan bura’ubanci?. Tambayar ka nake wajan ta kaje?.” Ihu take masa a kansa shi kuma baya so ko maganar ma baya so amma hakan ya saka ya mata banza kamar ba shi take ba tace, “to wallahi in ma dawo da ita zakayi ya kamata ka San abin yi, dan na rantse da Allah baka isa ka dawo da Ameena gidan nan ba, ta riga ta fita kenan gidan nan nawa ne ni kadai babu shegiyar da ta isa ta sake zama a cikin sa in ba ni ba.” Tashi yayi ya bar mata falon ya sauka ya fita daga b’angaren ta zuwa b’angaren Ameena, dan baya son magana balle tashin hankali shi kad’ai yasan abinda yake ji a zuciyar sa. yana shiga ya zauna akan kujera sai kuma ya zamo kan tiles dan babu carpet a falon ya kwanta a k’asa din yana juyi zuciyar sa kamar zata buga haka yake ji yace, “Allah ka kawo min mafita, Allah ka yafe min” abinda yace kenan yana sake juya kansa ji yake damuwa zata iya saka zuciyar sa ta buga a wannan lokacin. Ya jima a haka kafin ya daina juye juyen da yake yi yayi shiru yana kallon hoton Ameena da yake kafe a falon har lokacin ba’a cire ba kawai yaji hawaye suna sakko masa gudun zuciyar sa na sake yin yawa ya kulle idanu sa sai kuma ya bud’e ya sake kullewa yaga fuskar ta dai yake kallo a lokacin da take kuka ranar da suka rabu yace, “Ameenaaa!” Ya fad’i sunan da k’arfi tare da saukewa a hankali ya sake bud’e idanun sa ya rasa abinda yake ji a wannan lokacin shi kansa bai San wanne irin yanayi yake ciki ba. Shin farin ciki yake ko bak’in ciki? Damuwa ce ko kuma tashin hankali ne?. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid Book3 022 Suna zaune a babban falon sabon gidan Rukayya mai kyau suna cin lafiyayar shinkafa da miyar Kaji ga lemo da had'a musu mai sanyi dan 24 hours solar take da ita shiyasa take lemo na siyarwa mai shegen dad'i ga sanyi. Zakiyya kallon falon take yi tana girgiza kai tana mamaki wai gidan İbrahim ne wannan, ta rame sosai tayi bak’i kamar ba ita Zakiyya ba ya kalli Rukayya tace, "Wato duk Wanda yayi hak’uri a rayuwar sa zai ga alkhairi, mai hak’uri baya tab'a fad'uwa kasa na gani a kanki keda da Ameena. Kalli wannan gidsn yanzu gidan ki ne, da Fiddausi ta zauna da yanzu watakila Keda ita ne a cikin gidan nan.” Rukayya tayi murmushi tace, "nima naga amfanin hak’uri da kuma Karb’ar k’addara Zakiyya, ban tab'a hasashen samun farin ciki kamar wanda nake ciki a yanzu ba, duk inda zai kwatanta kwanciyar hankalin da nake ciki a gidan nan babu wanda zai fahimci hakan." Ameena tace, "ai ko baki fad'a ba mun gani a zahiri, Gashi nan sai kib’a kike abin ki kin sake yin haske duk da kina da ciki baki bak'i ba saboda hutu kawai kike yi." Rukayya tayi dariya tace, "makaranta nake so na koma a wannan lokacin amma yak'i wai sai na haihu." Zakiyya tace, "ku kam kunji dad’i keda Ameena baku da wata damuwa a yanzu kyau kuke yi kuna k’ina, ni gani ban san a wanne mataki aurena yake ba dan nasan yana dawowa yaga cikin nan saki na zaiyi." Rukayya tace, "ki daina yiwa kanki fata bazai sake ki ba in sha Allah." "Hmmm Rukayya ni kad’ai nasan tashin hankalin da nake ciki, gabad’aya bani da kwanciyar hankali a gidan sa kullum cikin fad’uwar gaba nake yi. Yanzu in ya sake ni ina zanje? Ku kun san yadda gidan mu yake karami ne a yanzu bani da wajan zama in akace na koma gida. Nice nake taimaka musu da abinci dana cefane in akace Nima na koma na zauna me gari ya waya kenan?. Tashin hankalin da nake ciki ban san adadin sa ba wallahi.” Ameena tace, "Taimakon iyayen ki da kike yi Allah bazai barki ki wulak’anta ba. Kuma a yanayin da kike ciki bai kamata ki dinga sakawa zuciyar ki damuwar nan zata cutar da lafiyar ki ba, duk kin rame kamar ba ke ba." "Rashin kwanciyar hankali shine ya ramar dani, yanzu na gane maganar da kuke cewa kud’i daban kwanciyar hankali daban, gani dai a yanzu a cikin kud’in amma wallahi bani da kwanciyar hankali, Kullum fargaba kar Abbahn fahad ya dawo ya samu cikin nan har ya girma haka." Rukayya tace, "ki ta addu'a babu abinda zai faru in sha Allah, ki saka Inna ta dinga miki addu’a wallahi in sha Allah babu abinda zai same ki. Har yanzu babu labarin Fidy ko?." Zakiyya tace, "hmmm! Fiddausi ina jin ai d’an yankan kai ta aura ya kai an yanke mata kan, dan indai ba haka ba to watakila ta mutu." Ameena tace, "Haba Zakiyya, meyasa kike cewa haka?." "To shirun yayi yawa ne Ameena, tun Abban su bai damu ba yanzu shima ya damu ya dame shi sosai ana ta saukar alkur'ani akan Allah ya bayyana ta. Ba’a samun wayar ta an kuma rasa tana ina." Rukayya tace, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Allah ka bayyana mana wanna baiwa taka cikin aminci. Wallahi Kullum da itanake kwana nake tashi, Kullum sai nayi mata addu'a tun Amir yana tambayata Mama har ma ya daina.” Ameena tace, "Wallahi nima kullum tana raina, addu'a indai zan yiwa kaina zan muku gabadayan ku amma abin yayi yawa shirun nata yayi yawa sosai." Zakiyya tace, "ba fata nake ba amma wannan shirun na Fiddausi ba alkhairi bane ba, alkhairi bazai b’oye Fiddausi ba sai ma ya sake bayyana ya dan kowa yana tana cikin sa." Ameena ta girgiza kai tace, "wannan haka yake, Allah dai ya bayyana mana ita." Suka amsa da amin suna cigaba da hirar su har suka tafi.        Sai yamma gab da magriba suka tafi bayan tafiyar su Ameena  school bus ta kawo Amir tana jin horn ta saka hijjabi ta fita ta bud’e sai da suka ga ya shiga gida sannan suka ja motar suka tafi, wanka ta yi masa tasan suna sallah a makaranta yaci abinci. Suna nan tare da Amir har suka yi i'sha ta koya masa karatu a wajan yayi bacci Ibrahim bai dawo ba. Waya take masa baya d'auka duk ta damu dan baya kaiwa dare kamar haka, tana tsaye a bakin gate din gidan sai kai kawo take yi hankalin ta ya tashi tana kira baya d’auka gashi kuma bai dawo ba. Horn taji a k'ofar gidan tayi saurin bude k'ofa taga shine tayi Ajiyar zuciya ta zare sakata gate din ta bud'e ya shiga da motar sa mai kyau sabuwa madaidaiciya daidai k’arfin sa ya ajjiye a inda ake ajjiye ta daman parking space din gidan na mota d’aya ne. Fitowa yayi daga motar ta gama kulle gate din ya kalle ta itama shi take kallo yace, "Meyasa kika kulle bayan kin san aikina ne? Na hana ki aikin gate d’in nan amma bakya ji ko?.” Shiru bata amsa masa ba sai kallon sa da take yi ya murmusa yace, “kiyi hakuri." Kallon sa tayi kawai bata ce komai ba yayi murmushi suka shiga ciki ya tarar da Amir a kwance a falon yana ta bacci yace, "lallai nayi dare har Amir yayi bacci?" Ya fad'a yana zama ta wuce shi ta kawo ruwa da lemo da abinci ta zauna bata ce komai ba yayi murmushi yasan tayi fushi shi kuma dad’in hakan yake ji dan ko babu komai yasan kula dashi ne ya jawo haushin. Abincin yaci yasha ruwa sai a sannan ya kalle ya yace, "ayi hak’uri a daina fushi naje wani waje ne shiyasa na jima." "Shi wajen da aka je ba’a d'aukar waya kenan?." Ya dan sosa kai yace, "ai kinga babu dadi ina wajan wata na d’auki wayar ki ko?." Da sauri ta kalle shi sai taga baiyi dariya ba alamun da gaske yake yi ba zolayar da ya saba bace yace, "Shiyasa bana d'auka in na dawo nace zan miki bayani. Kin san dai kece k’awar shawara ta ko? To wata na gani ina sonta shiyasa naje gidan su daga wajan aiki." Kallon sa kawai yaga tana yi amma bata ce komai ba kana ganin kallon kasan bana Lafiya bane yace, "ta karb’e ni hannu biyu sosai amma ta sanar dani iyayen ta basa son bikin ta ya d’auki lokaci, ni gashi ban wani shirya sosai ba ya kike gani za’a yi?.” Shiru nan ma bata ce masa komai ba sai ta tashi daga inda yake ta shiga d'aki yayi dariya mai sauti yana jin dadin tsokanar ta har zuciyar sa. İn yana tsokanar ta nishad’i yake yi sosai shiyasa baya rabo da zolayar ta. Da kansa ya kwashe kayan ya kai kitchen ya kashe hasken falon ya d'auki Amir ya kai shi d’akin ya kwantar dashi  ya shiga wanka sai da ya gama shiryawa sannan ya shiga inda take. A kwance ya ganta a kan gado ta juya baya ya kunna hasken d’akin ya k’arasa Inda take kwancen ya tashe ta zaune yaga tana kuka, yace, "Subahanallahi wai kuka kike? Haba Habibty kin San wasa nake miki fa meye na dawowa d’aki kina kika bayan kin san ba ke kadai bace ba?." Hawayen ya share mata yana murmushi yace, "Kiyi hak’uri na d'auka zaki tunanin wasan nake yi shiyasa na tsokane ki amma wallahi wasa nake yi, ki daina kuka dan Allah. Da nasan zakiyi kuka ai da ban yi ba.” Ta kalle shi yace, "in wasa ne meyasa baka d'aukar wayata? Bayan kasan dare yayi baka tab’a kaiwa haka a waje ba kasan dole na damu, meyasa baka ni ka fad’a min ba? Indai da gaske ba inda kaje din ba kenan meya hana ka sanar dani?." Ya zauna a kusa da ita sosai yace, "Allah wasa nake miki nace a wallahi ya kamata ki yarda." "To ina kaje? Me ya hana ka d'aukar wayata?." Yayi dariya kad'an yace, "Ina Wanda na bawa kudina ana juya mana?.” Ta kalle shi ya d’aga kai yace, "To an siyar da kayan riba ta samu Habibty fiye da tunanin ki. An samu albarka sosai Allah ya sakawa kasuwacin nan albarka. Wajan sa naje akayi lissafi aka bani ribar, kin San abin da yawa shiyasa na jima sosai, kuma muna zaune a wajan shiyasa ban d’auki wayar ki ba." "Amma da ka fito meyasa baka kira ni ba?." "Na karb’i laifin ayi hak’uri bazan sake ba." Ta kalle shi tace, "Meyasa ka tsokane ni?." Yayi dariya yaja hancin ta yace, "ina so naga kina nuna kishin ki a kaina, ina jin dad’in tsokanar ki Allah ya sani.” “Saboda me kake son tsokanata?.” “Sboda yana bani nishad’i.” Rukayya tayi murmushi tace, "wata ran wannan kalaman naka zasu iya zama na gaske." "Kinga mu bar zancen nan, muyi maganar wannan alkhairin da muka samu. Ribar da yawa ya kike ganin zamu yi da ita?. Daman kin san akwai kudina na gidana na farko da aka siyar canjin aka fara juyawa ga wanda nake tarawa na albashi ga kuma na gidan da muka baro kinga shi yafi yawa ma, shiyasa aka samu riba Alhamdulillah." Rukayya ta gyara zama tace, "to yanzu ya akayi kenan?." "Me kike ganin za'a yi da kudin?." "A sake juya su mana, ka k’ara a kan jarin naka a sake juyawa su ninka abinda aka samu." "Uhuummm nayi wannan tunanin amma sai na fasa na dai rage wani abu a ciki a k’ara ragowar suna wajena, ki fad’i abinda za'ayi dasu me kike so?." "Me kake ganin za'a yi dasu?." "Alhaji da Hajiya nake so na yiwa bazata wacve zasu yi farin cikin sosai, dalilin farin cikin nasu ya haifar min da wani cigaban a rayuwa ta, to na rasa me zan musu wallahi.” Rukayya tayi dariya tace, "Shawara." Yace, "ina ji." "Ka kai su umrah indai kud’in zai isa, ina tunanin duk abinda zaka yi musu bazai kai wannan farin ciki ba." Murmushi yayi yana kallon ta cikin jin dadin abinda tace, "Ban mu tafa dan Allah." Dariya tayi ta bashi hannu suka tafa ya rike hannun yace, "Gaskiya shawarar nan taki tayi sosai ba kad’an ba, tabbas zasu yi farin ciki musamman Hajiya ace yau ga a saudia ai sai ta suma saboda murna." Rukayya tace, "ai kowa ma sai yayi murna koda ya tab'a zuwa balle basu tab’a zuwa ba.” Ibrahim yace, "kinga dai ni yanzu ban san nawa ne kud’in zuwa ba bana tunanin kuma kud’in zai iya na kai su su biyun sai dai mutum d'aya." Rukayya tace, "to wa zaka kai?." "Zab'i naji a cikin su wa za'a kai?." "A’a bani da zab’i a cikin su duk wanda ka kai daidai ne." Yayi dariya yace, "to ko a kyale su muje nida ke nan gaba sai su je?." "A'a wallahi, su ya kamata ka fara kaiwa sannan mu biyo baya, zuwan da zasu yi farin ciki da addu'ar da zasu yi maka wallahi sai kafa kafin su dawo Allah ya hore wanda zamu je nida Kai din." Kai ya girgiza cikin gamsuwa yace, "haka ne, Ina ma Allah ya hore muje ni da ke da hajiya da Alhaji duk a rana d’aya." Rukayya tace, "yanzun ma baka san me  Allah zaiyi ba." "Haka ne. Yanzu gobe bazan fita ba tunda Amir babu makaranta zaki raka ni muje mu tambayi kud’in da za'a kashewa mutum d'aya in zai isa suje su biyu in bazai isa ba sai ki zab’i wa za'a kai." Tayi dariya tace, "nifa babu wanda zan zab’a a cikin su kowa a kai daidai ne." Ya dungure mata Kai yace, "Allah ke zaki zab’a bara dai muje mu ji." Ta kwantar da kanta a kafadar sa tace, "ashe baza'a zab'a ba.” Cikin ta ya shafa yace, "baki fad'a min ya akayi a asibitin ba." "Ban je ba wallahi, Ameena da Zakiyya ne suka zo muka zauna Muna ta hira." "Amma ya kamata kije." Tayi shiru kafin tace, " zan je . Su Ameena suna gaishe ka, sun so ka dawo ku gaisa ma baka dawo ba." Yace, "ina amsawa" abinda yace kenan yayi shiru itama haka zuciyar ta ta tafi tunanin Fiddausi shi kuma yayi shirun ne dan kar ta sake cewa wani abun tayi masa zancen Fiddausi. Wayar sa ake kira ya d'auka ganin lambar da bai sani ba ya saka shi saka wayar a speaker yace, "hello." Daga can b'angaren akace, "Hello kana jina? Hello kana jin abinda nake cewa?." Ya kalli Rukayya da take kallon sa yace, "ina ji,wacece?." "Nice Naja'atu daga nan Abuja, Mun tare da tsoh......!" Dufff sai wayar ta d'auke ya kalli Rukayya yace, "Naja'atu, daga ina kuma?." Rukayya tace, "ka kira kaji naji kamar hankali tashe ake maganar." Ya ajjiye wayar yace, "ban Santa ba bazan kira ba watakila ma kuskuren lamba akayi." Rukayya tace, "maybe." Ta fad'a tana kulle idon ta dan bacci take ji sosai. Daga b'angaren su Fiddausi Naja'atu tana fara magana a wayar suka ji motsi sai suka kashe da gaggawa suka zauna amma kana kallon su kasan basu da gaskiya ko kad'an. Alhajin ne ya shigo yana bin su da kallo d’aya bayan d’aya yace, "wannan zaman meeting din da ake yi akai-akai fa ban amince dashi ba, in ma wani shiri kuke shiryawa gwara ma ku daina babu abinda zai fitar daku daga gidan nan sai in ni naso." Ya kalli Fiddausi ya kalli wanda yake kusa dashi yace, "ga amaryar can in tayi maka a akai maka ita d’aki dan tana da gardama sosai." Ya kalli Fiddausi yace, "tayi, ni ai baza tayi min gardama ba saboda ba harkar ku nake ba ni ba irin ku bane ba, kai kasan gaba zan bi ba baya ba." Yayi murmushi yana kallon ta yace, "y’an mata muje ko? In akwai abinda kike so ki fad’a min sai a baki." Alhaji ya kalli Fiddausi yace, "tashi kuje, ba abinda kike tsoro zaiyi dake ba Malama." Girgiza kai take yi alamun bazata ba ya kalli Alhajin yace, "ka gani na fad'a maka daman taurin kai ne da ita, ina zuwa" ya fad'a yana juyawa ya fita shi kuma yazo wajan Fiddausi da niyar tab'a ta sai tayi baya ta tankad'a shi da karfin ta da ya rage mata. Aliya ta d’auki plate din da yake kusa ta buga masa a kansa Naja'atu zaro drawer da take jikin bedside drawer ya maka masa da karfin gaske. Da sauri yayi hanyar waje ko waigen su bayayi Naja'atu ta kalle su tace, "mun daina bari ana mana abinda ake so daga yanzu wallahi, koda Alhajin ne abinda zamu yi masa kenani in ta kama mu kashe shi wallahi kashe shi zamuyi. Mu koma zama waje d’aya hatta kwana mu dawo yi a d’aki d’aya daga lokacin zai fara shakkar mu. An daina cutar wata a cikin mu mu kasa komai sai dai muyi kuka mu share hawaye, wannan lokacin ya wuce wallahi.” Shigowa yayi da maza biyu d’aya ya rik’e Aliya d’aya ya rik’e Naja'atu cikin b’acin rai y rik'e Fiddausi ya fara marin ta ta ko ina yana cewa, "Dan uban ki dan uwar ki bana ce miki duk wanda na sake kawo harkar samuwa kika sake b'arar min da ita ba sai na kashe ki?." Duk da dukan ta yake yi amma cewa tace, "ka kashe ni din, zanfi jin dad'i ace ka kashe din na huta da wannan bala’in da nake ciki." "Zaki ci uban ki kuwa" ya fad'a yana janta ya fita da ita inda security sa suke ya cillar da ita yace, "ku zane min ita sannan ku yi abinda kuke so da ita" yana fad'a ya bar wajan. Ja baya Fiddausi take yi suna kusanto ta d'aya ya fara dukan ta ta ko Ina tana ihuu tana kuka amma bai daina ba duka yake mata da bulala, neman d'auki take amma babu wanda zai kawo mata d'auki sai Allah sai da suka yi mata duka sannan suka ja ta wani d'aki na farkon yace, "waye zai fara?." D’aya yace, "A'a Nidai na yafe." D’ayan ma yace, "nima haka, matar Alhaji Bello ce watakila ma tana da kanjamau bazan gogawa kaina ba haka kawai Ina zaune Lafiya. Wannan mutumin shi kansa bai San adadin halittar da yayi mu’amala dasu ba, har akuya ma ance bi yake yi.” Sukayi dariya a tare baban yace, "mu kyale ta zuwa anjima ma fito da ita mu kaita matsayin mun yi." Ai kuwa haka sukayi sai kusan mintina talatin sannan suka d’auki Fidy kamar jaririya aka mayar da ita b'angaren ta aka ajjiye tana kwance cikin jini dan duk sun fasa mata jikin ta. A lokacin wanda suke tsaron su Aliya suka bar wajan duk aka yi inda Fiddausi take kwance fuskar ya ta kumbura baki ya fashe . Naja'atu tace, "Yanzu haka zamu cigaba da zama a gidan nan baza mu samu hanyar fita ba?." Aliya ta kalli ko Ina ta tabbatar babu camera sannan tace, "gashi mun samu d’azu ya d’auki wayar amma kafin mu kai ga magana suka shigo, kafin mu sake samu wayar ta shiga ma yanzu aiki ne." Naja'atu tace, "ki bar batun waya mafita ya kamata mu samu mu har gidan nan kafin ya kashe mu." "Ta ya ya zamu fita Naja'atu?." "Gwadawa zamu yi, rashin gwadawar shine ya kaimu har yanzu a gidan nan bamu fita ba. mu gwada mu gani in a dace mun dace dukkan mu." "Ni zuciyata zuga ni take yi mu kashe Alhaji kawai." Naja'atu tace, "na jima da wannan tunanin indai zaku iya aiwatarwa nima zan iya mu kashe shi." Aliya tace, "in muka kashe shi baza mu tsira ba za'a kama mu k’arshe mu kare rayuwar mu a prison guduwar mu daga nan itace mafita. "Muna da dama a yanzu na tabbatar baya nan yana wajan Nabila, gashi dare yayi sosai ya ku ke ganin zamuyi?." Aliya tace, "Fiddausi baza ta iya tafiya ba." Fiddausi da jini yake ya bata mata jiki tace, "zan iya." Naja'atu tace, "da rashin lafiyar nan ta ta zamuyi amfani mu shiga mota a kai mu asibitin gabad’aya." Aliya tace, "amma kin san na cikin gidan nan za'a je ko?." Naja'atu tace, "jira ni kawai, kafin na dawo ki tabbatar kema kin zama mara Lafiya wacce za’a had’a a kai. Kuyi addu’a Allah yasa mu dace. Ina zuwa" ta fad’a tana tashi ta fita jim kad’an sai gata da security gidan su biyu tace, "kinga halin da suke ciki itama Aliya yanzu ta gama amai, ku taimaka mu tafi dan Allah kafin su mutu. Tausayi Fiddausi ta basu amma basa su aikata babu umarnin Alhaji ba d'aya yace, "wayar Alhaji a kashe yake baice mu kai ku asibiti ba dan haka babu inda za'a je." "Yanzu in suka mutu bakwa ganin kuma da alhaki? Kuma shima Alhajin in suka mutu a hannun ku bakwa ganin zai yi muku ba daidai ba?." D’ayan yayi shiru sai ya k’arasa inda Fiddausi take ya sab’ata a kafad’a yace, "muje kawai." Naaatu ta rik'e Aliya suka fito aka saka su a mota Naja'atu zata shiga yace, "ke ai lafiyar ki qalau Ina zaki je?." Gaban ta ya fad’i sosai sai tace, " indai a gidan nan ne ba’a zama Lafiya lau, yace naje a zubar min da ciki." Da kai yayi mata alamun ta shiga suka shiga baya su kuma suka shiga gaba suka fita. Asibitin gidan suka je suka dinga kiran wayar likitan amma tak'i shiga driver yana taksi yace, "likitan baya d'auka yanzu ya zamuyi dasu? Kaga numfashi waccan har ya kusa d’aukewa" ya fad’a yana kallon Fiddausi. "Muje cikin gari nasan yana can.” Gaba yayi da motar zuwa asibitin da yake kusa dasu private aka karb’e su aka kwantar dasu duk a d’aki daya suna tsaye a k'ofar d’akin su kuma suna gadi. Ruwa aka sakawa Fiddausi aka gyara mata ciwon fuskar ta da hannun ta  nurse d’in tana fita Aliya ta mik’e zaune ta kalli ko ina na d’akin ga taga nan amma kawai k’arfen da zai hana ka fita ta dafe kai ta sakko daga kan gadon ta shiga band'akin nan taga akwai taga kuma babu k’arfen sai dai k’arama ce. Fitowa tyi a hankali suka taimakawa Fiddausi ta tashi suka shiga ba d’akin aka rufe murfin masai aka taka amma tsahon su yak’i kaiwa, drum din Naja’atu ta gani suka zuba ruwa a ciki ba mai yawa ba suka d’auka aka d’ora a kan masan Naja’atu ta ta cire tagogin ta sakko suka fara d’ora Fiddausi suna tura ta har ta fad'a ta tagar ba tare da sun san ina ne ba, Aliya ce ta fara hawa itama ta dira Naja'atu tana ji ana buga k'ofar hankalin ta ya tashi sosai ta rud’e Allah ya bata sa'a ta dira itama sai gasu a bayan asibitin Aliya ta bugu a k’afa sosai Naja’atu kuma a hannu suka d'aure suka mik’e dakyar suka tashi suna tafiya da sauri har suka je bakin gate mai gadin yana bacci suka fita, suna fita daga gate din sai gudu kamar wanda suka gudu daga hannun masu garkuwa da mutane. #Nana Haleema #Book3 #Mai daki #Paid #500 Book3 23 Gudu suke sosai basu san inda suke jefa k’afar su ba dukkan su babu mayafi balle hijjabi. hanyar asibitin babu komai sai fitilin titi tafiya suke suna fatan Allah ya kai su cikin gari. Fiddausi ce ta gaza gudun ta tsaya tana hakki duk suka tsaya suna jan numfashi mak’ogwaro ya bushe Aliya tace, “ki daure kizo mu tafi.” Kai take girgizawa tace, “bazan iya ba, kuje zan kub’uta nima ku tafi kar a kama ku.” Kuka take yi sosai Naja’atu tace, “baza mu tafi mu barki ke kad’ai a nan ba, ki daure mu cigaba da gudu kar su gane bama cikin asibiti kuzo ku tafi.” Dakyar ta iya tashi suka cigaba da gudu ba suyi nisa ba ta sake zama tace, “Wallahi bazan iya ba, kuje kawai Allah zai kubtar dani ku tafi.” Haske su akayi da fitila dukkan su suka tsorata suna tunanin shikenan a kama su sai suka ga ma’aikatan tsaro ne suka k’araso inda suke d’aya yace, “ku kuma daga ina kuke? Su waye ku?.” Aliya tace, “Kama mu akayi mun gudo ne, ku taimaka ku d’auke mu daga nan kar su biyo mu su sake kama mu.” “Kidnapping din ku akayi?” Naja’atu tace, “Eh, ku taimaka mana dan Allah.” Wanda yake kusa da wanda yake musu tambaya yace, “Sir yanayin su ya tabbatar da abinda suke fad’a, mu taimaka a kai su asibiti a duba su, suna jin jiki musamman waccan” ya fad’a yana nuna Fiddausi da take kwance akan kwalta. Shugaban nasu yace, “ku d’ago ta ku shiga mota muje asibiti.” Dakyar suka iya d’aga Fiddausi aka saka ta a mota suka shiga akayi gaba. Kasancewar da hukuma nan da nan aka karb’e su Fiddausi a asibiti dan dukkan su sai da aka basu gado, Aliya wajan dirowa ma taji ciwo sosai a hannu Naja’atu kuma ta karye a hannu amma da yake ceton rai yafi fitar ran wahala basu ma sani ba burin su kawai su Gansu a cikin gidan su. Washe gari. “Kamar ya sun gudu? Kun San abinda kuke fad’a min kuwa? Kun San me kuke cewa?” Alhaji yake fad’a cikin ihuu yana kallon wanda suka fita dasu Fiddausi jiya. Direban yace, “Alhaji bamu san guduwa zasu yi ba da bamu fita dasu ba, kuma tsakani da Allah mun ga yanayin su suna jin jiki sosai shiyasa…..” kyakykyanwa mari Alhaji ya sauke masa a kuncin sa yace, “da kai da jin jikin kunci uban ku, meyasa baku tambaye ni ba? Meyasa kuka yi komai bisa umarnin kan ku?. Saboda haka na ajjiye ku daman? Badan komai a fad’a min na bada Umarni nake ajjiye daku ba?.” Shiru sukayi basu ce komai ba ya dafe kansa yana zaga falon cikin tashin hankali yace, “na rantse dan Allah matuk’ar suka tsallake Abuja suka shiga wani garin kashin ku ya bushe, wallahi sai nayi maganin ku sai kunyi dana sanin da baki tab’a yi ba.” Kai da Kaga Alhaji Bello kasan yana cikin rud’ani da rashin hankali wanda ya bayyana k’arara akan fuskar sa, ya cire babar rigar ya ajjiye yana girgiza kansa dan abinda ya faru dashi gwara ace duka mutuwa sukayi a dace sun gudu. Bai tab’a hasaso hakan ba da ya d’auki mataki tun kafin abin ya faru. Ya rasa abinda yake masa dad’i domin guduwar su illa ce ga rayuwar sa gabad’aya. Waya aka yi masa kamar bazai duba ba sai kuma ya duba ganin mai kiran sai ya d’auka ya saka a speaker aka ce, “Alhaji bamu gansu ba, mu tabbatar da guduwa sukayi dan cameras da take gate din asibitin ta d’auke su lokacin da suka fita.” Cillar da wayar Alhaji yayi Allah ya saka a akan carpet ne babu abinda tayi ya zauna sai kuma ya mik’e tsaye kamar mahaukaci ya kalle su yace, “dole nayi muku hukuncin abinda kuka aikata min, sai Kun….” K’arar wayar sa ya saka bai gama fad’a ba ganin sunan malamain sa da sauri ya d’auka ya saka a kunne daga can b’angaren yace, “me yake faruwa nake ganin bak’i yana kokarin mamaye lamarin ka?.” Alhaji Bello yace, “Na shiga uku, malam sun gudu matan guda uku duk sun gudu a lokaci d’aya.” Malam yace, “sun gudu? Garin ya ka bari suka gudu a wannan yanayin da ake ciki? Ka manta ba’a so sirrin nan ya fita matuk’ar baka saki matar ba?.” “Nan sani ba, masu kula dasu ne suka ci amana ta suka fita dasu ba tare da na bada izini ba. Malam ya zanyi yanzu?.” “Ayi kokarin nemo su kafin su kai ga fad’awa wani ahinda yake faruwa, in hakan ta faru zan iya cewa shikenan lamarin ka ya lalace, kamar yadda ka sani lokaci d’aya komai yake b’aci haka zai faru a kanka.” Hankalin Alhaji Bello ya kuma tashi rud’ewar sa tafi ta baya ya kalli inda suke a zaune sai yaga basa nan alamun sun gudu hankalin da ya tashi ya cillar da wayar, tv da take kusa dashi ya jawo ya da k’arfi ta fad’i k’asa ya saka k’afa yana taka ta cikin fitar hayyaci saboda rud’anin da yake ciki a wannan lokacin. “Na shiga uku ya zanyi?” Ya fad’a a bayyane cikin rashin sanin abinda zaiyi d’in, da sauri ya d’auki key ya fita dan ya tuna wani abu. Su Fiddausi tunda suka farfad’o suke kukan a kai su gıda hankalina tashe sun kasa ko magana kawai a kai su gıda, ganin hakan ya saka aka had’a su da d’an sanda guda biyu aka shiga dasu mota za’a sauke Naja’atu a kaduna, Fiddausi a kano Aliya Katsina. Hankalin su bai kwanta ba sai suka ga an fita daga garin Abuja a nan ko wacce ta fashe da kukan farin ciki. A safiyar Yusuf yana tsaye a kan titi a cikin mota ya fita yaje ya siyo fura da ya tashi da son sha yana tsaye ana check point. Tsaki yayi yace, “da safiyar nan ace za’a yi wani checking kamar b’arayi” ya fad’a yana kokarin juya motar ya koma. Ganin zai koma sai d’an sanda d’aya ya sha gaban sa suka kalli Yusuf yace, “ina zaka koma?.” “Zan canja hanya zanyi ne ne gaji da tsayawa.” Ya bashi amsa yana kallon sa ba tare da tsoro ba. D’an sandan ya kalli Yusuf sosai yace, “oga ban yadda da wannan ba azo a duba motar.” Yusuf ya tab’e baki suka zo suna duba motar Yusuf ya bud’e musu boot yana jiran su gama abinda suke yi ya kama gaban sa. Wani ihuu yaji sunyi da sauri ya kalle su a lokacin suna duba bayan motar nan da nan aka kewaye shi da bindiga babban cikin su yace, “fito!.” Yusuf yace, “me nayi?.” “Ka fito akace malam.” Yusuf ya fito ya tsaya yana kallon wanda ledar take hannun sa yace, “safarar cocaine da safiyar Allah, ku saka shi a mota a tafi office.” “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Cocaine kuma? Ni din aka ganta a mota ta?.” Tsaki yayi ya daki kewar Yusuf aka saka shi a motar da aka rubuta NDLEA aka tafi dashi. Sai Yamma su Fiddausi suka shiga garin Kano bayan an sauke Naja’atu lokacin da ta ganta a kano farin ciki ya mamaye zuciyar ta sai kuka kawai take yi saboda farin cikin da ya cika mata zuciyar ta. Har k’ofar gidan su aka tsaya Fiddausi ta fito ita da d’an sandan guda d’aya ta shiga cikin gidan shi kuma ya tsaya daga waje ba tare da ya shiga ba. Had’a ido sukayi da Mama tana shiga amma Mama bata gane ta ba sai ta sake kallon ta tace, “Baiwar Allah daga ina haka?.” Sai kawai ta zube a wajan ta a kuka muryar ta ko fita bata yi tace, “Mama Fidd…au…si ce” ta fad’a a rarrabe tare da zubewa a wajan a sume. Mama tayi ihuu tayo kanta tace, “Fiddausi” ta fara girgiza ta amma bata numfashi Mama tace, “Alhaji! Alhaji! Alhaji!! Ga Fiddausi ta dawo kazo a kaita asibiti ta suma.” Abba da yake waje suna magana da d’an sandan jin ihun Mama ya saka ya shigo ciki da gaggawa aka d’auki Fiddausi aka wuce asibiti da ita dan dole taga likita. Emergency na asibitin murtala aka kai ta akayi sa’a akwai gado aka kwantar da Fiddausi aka fara bata taimako da take da buk’ata. Cikin mintina kad’an y’an uwa an cika kowa yazo Mama yake tambaya tace ita bata sani ba a tambayi Abba. Har dare suna wajan Fiddausi bata farfad’o ba har wannan lokacin gashi ba’a barin shiga gwara Mama ta shiga ta gano ta amma bayan ita babu Wanda yake shiga. Sai lokacin da zasu koma Abba ya kalli Mama da y’an uwan Fiddsuin yace, “waye zai zauna a wajan ta? Mai jinya akwai zasu bari ya shiga.” Mama tace, “ni zan zauna, an kawo min abin kwanciya ma.” Abbah yace, “shikenan ko mai ake ciki ki yi min waya komai dare.” Mama ta amsa ya d’auki kud’i ya bata yace, “koda za’a nemi wani abun sai ki yiamfani dasu.” Mama tace, “to sai da safe.” Tafiya sukayi ita kuma Mama ta shiga ciki dan komawa inda Fiddausin take. Har safiya babu wanda yaji labarin ba’a ga Yusuf ba Asiya bata fad’a tace bai kwana a gida ba, waya ake yi tana shiga amma ba’a d’auka. Abbah da yake masa waya yana zaune yace, “Yusuf yana da shiririta wallahi, tun daren jiya mukayi zai kawo min sak’o har yanzu shiru gashi amfani zanyi dashi yanzun nan.” Ammah tace, “ka tura Mubakar gidan ya gano maka in yana nan.” Baice komai ba ya kira Mubakar a waya yace, “jeki gidan Yusuf kace masa ya baka Sak’ın ka kawo min amfani dashi zanyi, yasan jirgi na k’arfe sha biyu zai tashi amma bazai hanzarta ya kawo min ba.” K’aramin tsaki yayi ya kashe wayar ya ajjiye Ammah tace, “Kuma da aka fara yi masa addu’a wallahi na ga canji a tare dashi sosai. Kaga yanzu bashi da wajan zama sai gidan nan bai cika zama a can ba sai dai kwanciyar bacci da take Kai shi.” Abbah ya kalle ta yace, “Nima na gani, Matsalar daga wajan sa take ai shiyasa. Baya ibada yadda ya kamata kuma matar sa itace Matsalar.” “Da wannan, dama ya sake ta su rabu kowa ya huta.” “Ya dawo da Ameena?” Ya tambaya yana kallon ta dan yaga yanayin ta. Ammah ta sauke numfashi ta girgiza kai tace, “Ameena ai tayi masa nisan da bazai same ta ba a yanzu.” Abbah yace, “koma meye dai shi ya kawowa kansa, nan kika nuna bakya son auren sa da yarinyar nan ya dage sai anyi yanzu ga abinda yake faruwa nan. Ya d’auko mana k’ananun mutane marasa tarbiyya ya kawo mana zuri’ar mu, addu’a ta Kullum Allah yasa ma kar ta haihu dashi dan baragurbi zai zamar mana gashi bamu isa muce ba namu bane ba.” Wayar da Mubakar yake yi ya saka Amma batayi magana ba ya d’auka ya saka a speaker Mubakar yace, “Abbah Yusuf baya gidan nan.” “Ka tambayi matar da Ina yaje.” “Baba isihu ya tabbatar min da tunda ya fita jiya da safe bai sake dawowa ba har yanzu.” Abbah ya kalli Ammah ya ce, “to Ina yaje?.” “Baba yace min ce masa yayi zai je ya siyo fura ya dawo har yanzu bai dawo ba.” Abbah yace, “duk da haka ka shiga ciki ka tambayi matar s.” Mubakar ya amsa ya kashe wayar, Ammah tace, “to ina yaje?.” Abbah yace, “watakila ko yayi tafiya ne bamu sani ba.” Waya ce ta sake shigowa Abbah ya d’auka Mubakar ne sai yaga sabuwar number ya d’auka ya saka a speaker daga can b’angaren aka ce, “Muna magana da mahaifin Yusuf?.” Abba yace, “eh shine.” “Muna kiran ka daga nan NDLEA akan d’an ka Yusuf yana hannun mu.” “NDLEA!? Me Yusuf din yayi da yazo hannun ku?” Abbah ya fad’a a gigice yana tambayar sa. Ya cewa Abbah, “National drugs law enforcement agency, kamar yadda Kaji ita nake nufi NDLEA. daga nan muke yi maka waya akan mun kama d’anka yana hannun mu tun jiya.” “Innalillahi wa’inna ilahiri raji’un! Dan Allah yana wanne station din ku?.” “Muna nan club road, kazo kafin mu tura case din zuwa kotu.” Abbah yace, “gani nan zuwa yanzu in sha Allah.” Ammah tace, “Yusuf din aka kuma kamawa?.” Ya kalle ta yace, “wannan yafi wancan illa, an kama shi da miyagun kwayoyi tunda kika ji NDLEA ne a case din.” Bai sake cewa komai ba ya fita Ammah ta mik’e tsaye tace, “Allah ka kawowa Yusuf sauk’i a lamarin sa, nasan sakayya ce take bibiyar sa yake fad’awa wannan iftila’i kala-kala, ya Allah ka yafe masa ka sassauta masa wannan lamarin da yake faruwa dashi.” Kuka Ammah take yi sosai a lokacin Mubakar ya shigo ganin tana kuka hankalin sa ya tashi yace, “Ammah Lafiya? Me ya faru haka kike kuka?.” “Yusuf aka kama Mubarak, wai a NDLEA, me Yusuf yayi suka kama shi?.” Mubarak ya wara idanu yace, “NDLEA Ammah? Yusuf din?.” Ammah tace, “Nan fa Mubarak.” Ya d’aga k’afa zai tafi ta rik’e shi tace, “zo ka fad’a min me mutum yake yi a kai shi can.” Mubakar yace, “Ammah ki bari ina zuwa.” “Sai ka fad’a min zaka bar wajan nan.” “Ammah in aka kama mutum da k’waya ko kayan maye shine ake kai shi can, kuma wallahi basa sakin mutum gashi wahalar da mutane suke yi domin shine hukumar yak’i da kwayoyi” yana fad’a ya fita ta zauna tayi shiru kawai tare da tagumi. Abbah sai da ya kira Abie da Yaya Abubakar da Usman abokin Yusuf suka tafi can, koda suka je a inda suka ga Yusuf sai da zuciyar su tayi rawa ya basu tausayi fiye da tunani, yayi bak’i daga jiya zuwa yau saboda babu ci babu sha babu kwanciya sai dai zama suka kalle shi babu Wanda yayi magana Abie yaje wajan ma’aikacin yace, “Dan Allah da wa zamuyi magana akan Yusuf?.” Wanda yake yiwa magana yace, “oga ne kuma bai zo ba, zaku iya zama.” Zama sukayi suna kallon Yusuf idanun sa na lumshe kamar mara lafiya jiriii yana d’aukar sa daga inda yake, Abbah ya girgiza kai yana kallon sa zuciyar sa ta karyar kamar yayi kuka haka yake ji dan in ka kalle shi ka sake kallon sa dakyar baka ji idanun ka sun taru da hawaye ba. Suna nan a zaune har sha biyu tayi Abbah ya kalli Agogo ya dafe kai yace, “ina da flight yanzu na manta ma.” Abie yace, “Kaje Abba zamuyi komai.” “A’a dai mu zauna kawai na tafi zuwa dare.” Suna wajan har akayi azahar suka tashi sukayi sallah Usman ya sake tambayar su aka ce Oga bai zo ba. Suna wajan akace Oga yazo ya shiga ya baya zaman jiran a basu dama suyi magana da Oga har la’asar ta kusa, Yaya Abubakar ne yayi tashi dan shi baya jurewa ya ya same su yace, “Ya ana yi muku magana kunce yazo tun d’azu shaya mutane? Kun San waye mahaifin mu da zaku wulak’anta mu haka? Ai ko dajarar girman sa kwa duba ayi wani abun ya bar wajan nan Kasancewar ba saba zama akayi a waje irin wannan ba.” Wanda yake yiwa magana yace, “Kaga a man aikin mu muke ka bamu waje.” “Ank’i a baku waje din, wannan wanne irin wulakanci ne tun d’azu ake magana d’aya har yanzu taki k’arewa, in baza mu ganshi ba kuce baza mu ganshi bama sai kin bata mana lokaci.” Abie ya taso ya janye shi ya kalli ma’akkacin yace, “in Zaku bamu dama ku bamu, in baza ku bamu ba mu tafi.” Abbah da yake kallon sai a lokacin ma ya tuna da yayi waya mana ya d’auki waya ya fita waje yana kiran wanda ya sani a sama dan a shiga maganar. Yana shigowa Oga ya fito suna hira shida wani da ya juya baya sannan suka gaisa ya juyo suka had’a ido da Abbah. Yaya Adam yace, “A’a Alhaji.” Ya fad’a yana k’araso wa wajan har k’asa ya gaishe da Abbah yace, “Alhaji me kuke yi a nan haka?.” Abie yace, “a Yusuf aka kama wallahi, har yanzu anki fad’a mana laifin ma me yayi tun kafin azahar muke a nan har Abbah.” Adam yace, “Subahanallahi, Yusuf dai” ya fad’a yana juyawa ya hango Yusuf a kwance kamar ma baya cikin hayyacin sa. Adam yace, “kai a fito dashi kamar ma bashi da lafiya.” Oga ya kalle su yace, “a fito dashi yanzun nan.” Da sauri aka fito da Yusuf dan sai janyo shi akayi dan a sume yake aka kwantar dashi a wajan. Adam ya kalli abokin sa kuma shugaba a wajan yacc “Meyasa yaran nan naku suke ke yin haka ne? Kalli bashi da lafiya amma sun k’i bari ayi magana ma balle a san abinda ya faru. Harda mahaifin a wajan nan ace tun safe har yanzu an kasa magana balle ma san wanne laifi ya aikata?.” Oga ya kalli Abbah yace, “Alhaji kayi hak’uri dan Allah ba san abinda ya faru ba kenan” ya fad’a yana d’aukar wayar sa yayi gefe ganin mai masa waya. Bai jima yana wayar na ya juyo yace, “kayi hak’uri alhaji yanzu ma wayar da akayi min akan maganar ne.” Adam yaja tsaki yace, “wannan ai rashin sanin aiki ne wallahi.” Ya kalli Oga yace, “yanzu ya za’ayi dashi emergency ne kana kallon sa unconsciously.” Ogan yace, “case ne Babab soja, kama cocaine akayi a motar sa.” “K’aryar banz ce wallahi baya shan cocaine kuma baya siyar da ita, ajjiye masa akayi na tabbata bazai aikata ba.” “Ka San shi ne?.” “K’anina ne fa, kai a banza nake wannan tayar da jijiyoyin wuyar.” Ogan ya kalle su yace, “Waye case din yake hannun sa?.” Ya taso da sauri ya kalle shi yace, “Meyasa baka fad’a min tun d’azu ba?.” Adam yace, “ba aikin ka zan ko ya maka ba Mujahid amma wannan ba aiki bane, ya mutum yana kwace a sume kana wani tambayar banza da wofi. Kaga ni ka bani Yusuf din na kai shi asibiti in ya gudu ka kamo ni kawai, snake dashi yanzu su kayi magana dasu.” Ya kalli Adam yace, “bazai yu bane hakan har yanzu ana zargin sa da abin bazai yu ba dole sai munyi magana tukunna.” “A kai shi emergency na k’arkashin ku mana, wannan wanne irin bincike ne?.” Ogan ya kalli Adam yace, “Dan Allah ka nutsu Adam za’a yi komai yadda ya kamata, matsala ta dakai hargagi. Kai ku d’auke shi a kai shi emergency” ya kalli su Abba yace, “Abbah mu je.” Adam yace, “ni zamu je dashi asibitin.” Mubarak da ya yake wajan yace, “A’a Yaya Adam ni zan bisu ka zauna a nan.” Ya kalli Mubakar yace, “Yauwa dan Allah ka bisu.” Aka d’auki Yusuf aka fita dashi su kuma suka shiga office din Muhajid. Cocaine din da aka kama a motar ya ajjiye akan table yace, “Alhaji Kaga abinda aka kama a motar sa a safiyar jiya.” Adam yace, “au tun jiya ma yake a hannun ku amma ba’ayi yi waya ba sai d’azu? Wannan wanne irin abu ne wai haka? Baku da tabbas akan tasa ce ko ba tasa bace a ajjiye mutum ba ci babu sha sama da awa ashirin da hudu? Yanzu in ya mutu a hannun ku fa?.” Ya kalli Adam yace, “da zahiri muke aiki Adam, kasan doka ya take ai ka ajjiye wannan hargagin naki dan Allah.” Alhaji yace, “Abinda na sani Ysusuf baya harkar k’waya gaskiya sai dai in saka masa akayi a motar.” Yace, “to bamu da tabbas tunda dai babu shi a wajan nan yanzu, kaya dai tunda a motar da aka gani nasa ne in kuma ba nasa bane a dokar mu sai ya kawo mana mai kayan sannan zamu sake shi.” Adam zaiyi magana ya katse shi yace, “NDLEA ne nan fa Adam ba police station ba, Muna da ka’ida kan aikin mu, amma saboda wayar da akayi da kai za’a san abinda za’ayi amma dole Yusuf ya kasance a karkashin kulawar mu har sai munji magana daga bakin sa.” Adam yace, “In saka masa akayi a motar fa?.” “Wannan bai dame mu ba, mu dai a motar sa muka ga kaya dan haka na sane” ya kalli Abbah yace, “Alhaji ku kwantar da hankalin ku in sha Allah babu matsala za’a san abinda za’ayi amma dole sai ya farfad’o gaskiya.” Alhaji yace, “Babu damuwa mu gode. Amma zamu iya zuwa mu duba shi?.” “Za’a iya amma dai dole akwai masu kula dashi ma’aikatan mu in ya farfad’o akayi magana za’a iya bada belin sa tunda anyi magana daga sama ga kuma Adam.” Abbah yace, “babu damuwa in gode sosai, bara na kira Mubakar muji abinda suke.” Ogan yace, “ Alhaji in sha Allah a gida Yusuf zai kwana gobe.” “Har sai gobe? Kenan yau ma a wancan wajan zai kwana?.” Ya kalli Adam yace, “yanzu ai yana asibiti ko? A can zai kwana da safe sai ayi magana a wuce wajan.” Adam yayi tsaki ya tashi ya fita yayi murmushi ya kalli Abbah yace, “Adam dan rigima kenan, Alhaji wannan d’an naka kana fama dashi bashi juriya ko kad’an komai ayi a gama kawai. Baya son b’ata lokaci gashi bai iya fushi ba, mantawa yake da waye shi in ran ya b’aci Abbah yayi murmushi yace, “sojojin kenan.” “Tare muka fara aikin dashi na fad’i a wani training sai na dawo nan, abokin a ne sosai yana da kirki akwai zumunci baya yarda ya sani ko waye shi.” Abbah yayi murmushi kafin yayi magana yace, “Kar ka damu Alhaji walalhi ko ba’a yi waya daga sama ba saboda Adam za’a san abinda za’ayi, so nake muji daga bakin sa sannan sai mu yanke hukunci.” Abbah yace, “na fahimce ka, babu damuwa mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi.” Aka amsa da amin suka fito tare sukayi alwala akayi sallah sannan suka wuce inda aka kai Yusuf dan su ganshi. Book3 24 Lokacin da suka je asibitin an kwantar da Yusuf ana k’ara masa ruwa da yake da Mubarak private aka je d’akin shi kad’ai sai mai tsaron sa a k’ofa a tsaye shi kuma yana kwance yana bacci. Kallon sa suke yi dukkan su dan ya rame sosai yayi bak’i kayan jikin sa sunyi daud’a sai ga nurse t shigo Abbah yace, “Dan Allah me yake damun sa?.” Ta kalle shi tace, “muje waje ayi muku bayani.” Tare suke fito ta kalli Abbah tace, “damuwa da yunwa sune suke damun sa, jinin sa ya d’an hau ta dalilin damuwar ko kuma ya jima baiyi bacci mai yawa ba duk shine suka had’u suka saka ya suma lokaci d’aya. amma yanzu Alhamdulillah komai zai dawo daidai da ya tashi.” Abbah yace, “to mun gode sosai.” Bayan ta bar wajan Abbah ya kalli Adam yace, “Soja na gode sosai fa Allah ya bar zumunci.” Adam yayi murmushi yace, “Babu komai Alhaji, zan koma yanzu zan san abinda za’ayi bazai koma wajan nan ba in sha Allah. So nake ya tashi muji ya akayi ta shiga motar sa ya bawa motar kafin ya hau an ina kuma ya ajjiye motar.” Abbah yace, “Gaskiya ne wannan, Allah ya taimaka mana baki d’aya.” Ya amsa da amin yayi musu sallama ya wuce. Mubakar ya kalli Abbah yace, “Hankalin Ammah ya tashi sai waya take yi na rasa me zance mata.” Abbah yace, “kaje ka d’auko ta ka kawo ta nan anjima sai ta tafi kai ka zauna dashi a nan, Nima zan koma yanzu zamu je a san yaddda za’ayi a kashe case din nan.” Mubakar yace, “Tafiyar taka fa Abbah.” “Sai dai wani lokacin kuma.” “to bara naje na d’auko Ammah din”ya fad’a yana barin wajan Abbah ma ya tafi su kuma suka zauna a kujerun da suke kofar d’akin. Fiddausi ta farfad’o ta idanu ta biyu a kwance a kan gadon amma tak’i magana sai kuka kawai da take yi wanda Mama ta rasa kukan na meye. Gaji tayi da ganin ta tana kukan tace, “Fiddausi Ki yimagana naji ki daina wannan kukan dan Allah. Tunda kika tashi baki yi magana ba ko wani abun ya same ki kika daina magana?.” Ta lumshe ido ta bud’e ta kalli Mama kamar zatayi magana sai ta share kawai bata ce komai ba. “İn baza ki magana ba ki daina wannan kukan ance jinin ki ya hau kukan ma zai k’ara miki.” Sai a sannan tace, “Mama dama na mutu.” Jin tayi magana sai hankalin Mama ya kwanta tace, “Alhamdulillah! Da na d’auka kin daina magana ne ai, bara na fad’awa likita” ta fad’a tana fita Jim kad’an suka dawo da likita yazo kan Fiddausi ya tsaya yace, “me kike ji yanzu?.” Fiddausi tace, “babu komai.” “Kanki baya ciwo?.” “Yana yi amma ba sosai ba, sai dai jikina babu dadi.” “Eh naga alamun duka a jikin ki, wannan dukan ne ya saka kike jin haka amma a hankali zaki dawo daidai.” “Likita an yi min test?.” “Anyi miki?.” “Bani da HIV?.” Da sauri ya kalle tajin abinda tace Mama ma kallon ta take yi yace, “Bamu gwada jinin ki a wannan b’angaren ba, amma yanzu a siyo sirinji sai a gwada a gani.” Fiddausi ta kalli Mama kamar zata yi magana Mama tace, “ga wani d’azu da akace a siyo za’a yi mata gwajin malaria kuma ace anyi.” Karb’a yayi yaja jinin ta yayi rubutu a takarda ya bawa Mama yace, “aje lab a gwada.” Mama ta karb’a tana kallon Fiddausi gaban ta yana fad’uwa sosai tace, “gwajin k’angamau Fiddausi? Me ya had’a ki dashi?.” Fiddausi tace, “ayi kawai Mama.” Mama tace, “bara naje.” Jim kad’an sai ga Mama ta dawo ta bawa likitan Sakamakon gwajin ya kalla ya kalli Fiddausi yace, “Baki da cutar hankalin ki kwanta?.” Tayi Ajiyar zuciya bata ce komai ba ya kalli Mama yace, “To ai zaku iya tafiya gida, aje tayi wanka taci abu mai kyau a sake bata dama tayi bacci sosai dana akwai rashin sa sosai a idanun ta.” Mama tace, “to shikenan bara na kira mahaifin ta sai mu tafi.” Waje ta fita ta samu yana wajen ta fad’a masa ta koma ta kwaso kayan su a dawo ta rik’e Fiddausi suka fita daga d’akin suka shiga mota suka tafi. Kamar yadda yace kuwa an saka tayi wanka ta sha shayi tayi sallah ta sha magani sai kuwa baccin ya sake d’auke ta. Sai bayan i’sha ta farka ta fito falo ta tarar da Mama da y’an gidan su gabad’aya harda Abba da Kawu tana fitowa kowa ya kalle ta tace, “Sannun ku.” Yaya tace, “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Fiddausi haka kika koma?.” Bata ce komai ba ta wuce tayi alwala ta dawo tayi sallar i’sha a falon a zaune dan bata iya tsyauwa sosai bayan ta isar ta kwanta akan sallayar bata ce komai ba. Mama tace, “sannu Fiddausi.” Kai kawai ta d’aga bata ce komai ba Abba yace, “sannu Allah ya baki Lafiya.” Lumshe ido tayi ta bud’e sai ta fara kuka Mama ta lura da ita tace, “Wai kukan nan da kike aikin yi na meye?.” Batayi magana ba sai ta share hawayen ta a nan bacci ya sake d’auke ta. Ganin hakan y’an uwa ta duk sai suka tafi aka kashe mata haske aka barta tayi baccin. Washe gari tun kafin ta tashi y’an uwan ta sun zo kowa burin sa yaji me ya same ta ina kuma mijin nata yake ta koma kamar alamajira haka, sai da tayi wanka aka bata abinci taci sannan Abba ya zauna da ita ya fara jera mata tambayoyi daman tasan sai anyi haka yace, “Fiddausi d’an sandan da ya rako ki yace kun gudo ne daga wajan yan garkuwa da mutane haka ne?.” Ta girgiza ki alamun A’a hawaye ya zubo daga idon ta Abba yace, “to me ya faru? Ina kika shiga ko a waya ba’a samun ki? Ina mijin ki yake?. Meya same ki kika koma haka?.” Cikin muryar kuka tace, “Daga gidan sa muka gudo ba wajan garkuwa da mutane ba, mun fad’awa y’an sanda haka ne kawai dan kar su mayar damu gidan.” Abba yace, “to ina kika shiga har gidan da aka kai ki anje amma bakya nan?.” Sai ta fashe da kuka mai sauti tace, “karya yayi min Abba, naga tashin hankali da bala’i a gidan sa, na wahala naga masifa kala-kala wacce ko a mafarki banyi tunanin ganin irin ba.Shi ya hana ni amfani da waya ya kulle ko wacce number ta mutanen gidan nan babu wanda zan samu ko daga wacce waya zan kira. Kullum cikin fargaba nake da tashin hankali, bana bacci, bana iya cin abinci, kuka shine abokina shine abokin shawarata” ta fad’a tana kuka sosai wanda ya hana ta kasa cigaba da maganar. Abba yayi murmushi ya kalli Mama ya sake kallon Fiddausi yace, “ina jin ki.” Ta tsayar da kukan tace, “Abba dan luwad’i ne.” A tare kowa yace, “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!.” Mama tace, “luwadi Fiddausi?.” Ta daga Kai tace, “eh Mama, ba kuma da iya maza ba har matan sa babu wacce take tsallakewa.” Abba ya sauke numfashi ya kalle ta sosai yace , “kema baki tsallake ba kenan?.” Ta runtse ido ta sake fashewa da kuka ganin hakan kowa yasan ne yake nufi jikin kowa yayi sanyi banda Abba. Tace, “Alhaji ba mutum bane dabba ne, rayuwar gidan sa babu wanda zai sani sai ya shiga Abba. Domin kuwa duk wata hanyar da zaki bada labari ya toshe domin baza kije ko Ina ba har sai in shine ya sake ki. Nida Aliya da Naja’atu matan sa muka had’a plan Allah ya bamu sa’a muka fad’a hannun y’an sanda. Baya bari aje ko ina saboda kar ki fad’a wani halin sa, in ma fitar ta zama dole za’a had’a ki da masu kula dake ta yarda waya baza ki yi ba dan hatta bandaki zaki je sai an raka ki. Na sha wahala ko mak’iyi na bana fatan yasha wahalar da na sha a gidan sa.” Abba yace, “wahala ai basai kin fad’a ba Fiddausi gata nan a bayyane a tare dake.” Ta kalli Abba tace, “Abba duk yadda zan kwatanta tashin hankalin da na shiga baza ku fahimta ba ni kawai nice nasan halin dana fad’a.” “Daidai kenan ai Fiddausi, Ba ke kina zab’i kud’i akan kwanciyar hankali ba? Yanzu kin banbance tsakanin guda biyun kenan?.” Ta runtse idanun ta danasani ta gama mamaye zuciyar ta da jikin ta tace, “na banbance Abba, na gane yanzu kwanciyar hankali daban kudi daban. Ko a gidan akwai kudin duk abinda kike so akwai amma babu kwanciyar hankali Abba. Nayi danasanin zab’ar kudi, nayi nadama wallahi.” “Nadamar ta banza ce ai ba tunda ba ta Tsakani da Allah kika yi nadamar ba sai da kika sha wahala sannan kika yi, saboda tsabar son duniya kika kashe auren ki da kanki, kika kashe dan cikin ki da kanki kawai saboda zaki auri mai kud’in da kike ganin shine farin ciki a wajan ki. Kuka had’a baki da Kawun ki akayi aure bana nan balle nace zan hana saboda bincike ko wani abun. Yanzu gashi kin je kin dawo kina kuka kina dana sani bayan kin aikata babban zunubi a wajan Allah. Ke a tunanin ki wannan abubuwan da ya faru a kanki meye?.” Kuka take yi sosai ta kasa magana dan muryar ta ta dashe tana shashsheka a haka ta bude’e baki tace, “Ban aikata ina sane ba Abba, ta k’arfi akayi amfani dani, wallahi nan aikata ina sane ba.” “K’arya kike, akan kud’i babu abinda baza ki yi ba dan an biya ki anyi luwadi dake a wajan ki ba komai bane. Tunda kika iya kashe d’an cikin ki akan kud’i dan ance min an biya ki Kinyi luwad’i ai ba wani abun bane ba.” Kai take girgizawa hawaye wani yana bin wani tace, “A’a Abba, wallahi ban aikata ba, wallahi banyi ina sane ba, wallahi Allah d’aya kenan fin karfina akayi.” Abba yace, “to my yanzu da kika dawo mana me zamu yi miki? A abinda kika fada kaf banji kince ya sake ki ba kinga matar sace sai ki tashi ki koma gidan kud’i da kwanciyar hankali dan a nan bamu dasu.” Tayi hanzarin rik’e kafafun Abba tace, “ka yafe min Abba nayi kuskuren da bazan manta dashi ba, na aikata abinda har abada bazai daina bibiyata ba ka yafe min dan girman Allah. Gwara ka yanka naman jikina da kace na koma wannan gidan, kayi hak’uri Abba ka yafe min.” Abba yace, “ni ance miki kin yi min laifi ne? Zab’ar abinda kika ga shine daidai a rayuwar ki kika yi to meye na laifi a nan?. Kin kashe auren ki, kin kashe d’an ki, kin saka an kama tsohon mijin ki kin wulakanta shi saboda kawai kina ganin ke a lokacin ba d’aya kuke ba. Kin auri mai kud’i daidai ke wanda kika ce shine farin ciki ki je kina farin cikin ki to meye na dawo min gida kina kuka?.” Kowa yayi shiru a falon babu maganar wanda yake magana kowa jikin sa yayi sanyi sosai kikan ta kawai ake ji tace, “duk abinda kace na aikata Abba, amma wallahi nayi badana nayi dana sani domin na banbance tsakanin kud’i da kwanciyar hankali Abba. In na koma kashe ni zaiyi bak’in ciki zai iya silar bari na duniya.” “Ai sai kin koma, baki gama ladaftuwa ba har yanzu Fiddausi dole ki koma kije ki cigaba da rayuwar jin dad’i mu ki bar mu muyi rayuwar wahala da talauci a nan.” Ta rud’e ta gigice tayi wajan Mama tace, “Mama ki bashi hak’uri, Yaya, Kawu ku taya ni bashi hak’uri nayi kuskure amma dan Allah kar yace sai na koma, in na koma da gawata za’a dawo gidan nan.” Abba yace, “sai me in an dawo da gawar taki? Ai bake kad’ai na haifa ba ina dasu da yawa dan na rasa ki bazan ji komai ba. Baki da d’a ko y’ar da zan tausayawa in akace babu ke a duniya. Babban abinda yake bani takaici dake bai wuce karyar da kika shirya kika fad’a mana akan mijin ki ba, ashe plan kika shirya duk akan burin ki kashe auren ki ki tafi gidan masu kud’i. Tashi ki koma baza ki zauna a gidan nan ba, bazan zauna da matar dan luwadi a gidana ba, ko da yake kema kin zama shi ai bazan zauna dake ba ki tashi ki koma can ki yi rayuwar ki mu ma muyi tamu.” Kawu yace, “Haba Yaya, dan Allah ka daina wannan maganar tayi laifi kuma ta tuba in da wanda za’a yiwa hukunci nine ba ita ba. Hannun ka bazai rube’e ka yanke ka yar ba.” Abba yace, “sai dai in bai dame ka da ciwo ba, in ya dame ka lokacin da zaka yanke ka cire ka y’ar ma baka sani ba. Na fad’a mata ta bar gidan nan kafin na dawo kar na same ki a nan” yana fad’a ya fita Mama ta tashi tabi bayan sa ta same shi a d’aki tace, “Alhaji nasan ka tausayawa Fiddausi dan Alalh ka yafe mata. Wannan fad’an da kake mata zai iya jawo mata wani sabon ciwo, kasan ance jinin ta ya hau in aka mata irin haka wallahi sai zuciyar ta ta buga.” Ya juyo ya kalli Mama yace, “in na tuna abinda ta aikata ina bak’in ciki, ina bak’in cikin abubuwan da tayi a baya kawai saboda wani buri nata na banza da wofi. Haushi nake ji in na tuna yanzu tsohon mijin ta yayi mata nisan da baza ta tarar dashi ba, duk uban da ya samu siriki kamar sa farin ciki yake yi baya so yaga yarinyar sa ta fita daga gidan sa amma ita ta k’arfi da yaji ta fita banda rashin kunyar da ta dinga yi har iyayen sa bata kyale ba. To me zata zauna tayi a nan? Ta koma can take ta cigaba da rayuwar jin dadin da ta zaba matsayin farin ciki.” Mama tace, “na sanabinda kake ji Alhaji, amma kayi hak’uri akwai hakan da kake fad’a kuma akwai k’addara dole hakan sai ya faru.” “Wannan ba k’addara bace ganganci ne, yanzu kika sani ko ya saka mata wani ciwon.” “Kayi hak’uri dai ka yafe mata dan Allah.” Yayi shiru baiyi magana ba tace, “ka daina cewa ta koma ka yafe mata dan Allah mu barta a nan.” “Da aure a kanta har yanzu shi muyi ya dashi?.” “Za’a San abinda za’a yi ko zuwa gaba in sha Alalh. Amma dan Allah ka yafe mata.” Yayi ‘karamin tsaki baice komai ba ya fita Mama ta bishi da kallo ita kanta zuciyar ta tayi rawa sosai. Lokacin da ta koma Fiddausi take basu labarin komai da ya faru har kama ta din da akayi a New York sai da ta fad’a, su kansu y’an uwan ta kuka suke dan sun tausayawa mata sosai. bayan ta gama basu labari tace, “nayi dana sani kuma na tuba na gane kwanciyar hankali daban kudi daban, na gwammace gidan da babu ci ko sha nake a zaune indai hankalina zai kwanta. Kwanciyar hankali ke kawo jin dad’i ba kudi ba na yarda.” Mama tace, “daman a gaske akwai masu irin wannan rayuwar?.” Wacce take bin Fiddausi tace, “ko an american film ban tab’a jin wannan kazantar ba, lallai addu’ar da aka saka ana yi miki daga nan Allah ya amsa kika gudo da ba’a San a inda abun zai tsaya ba. Watakila ma ya bada jinin ki ayi tsafi dashi.” Shiru kawai bata ce komai ba amma zuciyar ta zafi take yi. Danasani, nadama, ina ma banyi ba, sun taru sun yi mata yawa a zuciyar ta, ta rasa me zatayi taji daidai a zuciyar ta da jikin ta, ta rasa farin ciki gabad’aya a ko wanne bangare na rayuwar ta. Yusuf yana zaune akan kujera ya dafe kansa an office din su Abbah dasu Abie su Adam duk suna zaune a wajan Oga yace, “Yusuf akayi aka samu cocaine a motar ka?.” Yusuf da yake cikin rashin lafiya yace, “ban sani ba, yadda aka ganta nima haka na ganta amma ban San taya ta shiga ba.” “Wa ka bawa motar taka ya hau kafin kai?.” Yusuf ya dan yi shiru aka sake cewa, “an ina ka ajjiye motar?.” “a gida.” “Baka ajjiye ta a ko ina ba? Ka tuna wa ka bawa motar sannan a ina ka ajjiye?.” Yusuf yace, “direban gidana Sani ya fita da matata a cikin motar, dan ko da naje gida ba a ita nake ba ban hau ba sai da safiyar.” Oga Muhajid ya kira waya ya bada umarnin aje a kawo Sani. Adam yace, “ba iya Sanin ba har matar ai tana cikin motar.” Yayi dariya Abba ma dariya yayi yace, “banda abin Adam ina mace ina wannan harka.” Oga yace, “suna yi alhaji wallahi suna yi, sai kaga mace da ciki ka d’auka d’a ne a ciki ashe cikin kwaya akayi mata ciki dan a b’atar da hankalin mutane daga kanta.” Abbah yace, “kai amma lamari ya b’aci.” Ya kalli Yusuf tace, “wa kake zargin zai ajjiye maka a cikin motar ka?.” Ya girgiza kai yace, “Gaskiya babu.” Ya girgiza kai yace, “za’a san abinda za’a yi in sha Allah.” Sani aka shigo dashi aka zaunar dashi ya kalle shi yace, “Malam Sani kaine direban gidan Yusuf?.” Ya daga Kai yace, “kwarai nine.” “Kwana biyu da suka wuce ka d’auki matar sa Kun fita da ita a motar ina kika je?.” “Wajan biki na kai ta.” “Sai ka bar motar an ina?.” “Ina ciki babu inda naje.” “Babu wanda suka tsaya a motar aka dan yi hatsaniya ko wani abun?.” Sani yace, “eh to, gaskiya anyi.” Yace, “Meya faru?.” Ya kalli Yusuf ya kalli wanda yake masa tambayar yace, “Hajiya ce ta fito da sauri tana cemin na kunna motar ta shiga da gaggawa kafin mu tafi wasu mata da wani namiji sun zo wajan kamar zasu daki motar ana cewa a kamo ta ta had’a harda kayan ta sace ni kuma a lokacin ina motar muka tafi. Muna tafiya ta bud’e abinda ta fito dashi sai naji tayi tsaki ta cillar da jakar ta window tana juya wata Leda a hannun ta sai kuma ta ajjiye tace, aikin banza babu komai sai hoda daga nan tayi shiru muka cigaba da tafiya.” Ya girgiza kai yace, “in na fahimce ka ina its Hajiyan ce ta sato jakar da hodar take ciki, da ta duba taga babu kud’i ko wani abun a ciki sai ta yar a motar.” Yace, “haka aka yi, bayan wannan ba’ayi komai ba gaskiya ban kuma tsaya ko na fita daga motar ba.” Ya kalli Yusuf yace, “matar ka muna son ganin ta a wajan nan.” Baice komai ba Abbah yace, “a tura a d’auko ta.” Nan take aka yi waya aka gida mace da na miji du tawo da Asiya. Suna zaune babu wanda sake magana sai Ogan da ya fita ya dawo ba jima wa sosai sai ga Asiya a shigo da ita. Zama tayi ya kalle ta yace, “Kin San wannan?.” Ya fad’a yana nuna mata Yusuf. Ta daga kai tace, “na San shi.” “Wannan fa?”. Ya nuna mata Sani ta kalle shi tace, “shima na San shi.” “Kwana biyu da suka wuce ya kai ki biki a motar mijin ki hana ne?.” “Eh haka ne.” “Kin d’auki wasu kaya har mutane suka biyo ki da kika duba a motar kika ga ba abinda kike so bane a ciki sai kika cillar anyi haka?.” Asiya tace, “eh, amma ni ba d’aukar kayan nayi ba kuskure ne nayi da jakar na d’auka tawa ce.” “Me kika gani a ciki kika yar?.” “Wata hoda ce fara a cikin Leda sai na yar kawai.” “Kin San meye a ciki?.” “A’a.” “Kin San cocaine?.” Ta zaro waje tace, “na dai ji ana fad’a amma ban sani ba.” Ya girgiza kai yace, “to itace kika yar a cikin motar.” Kafin tayi magana yace, “zaki gane masu jakar da kuka yi canjen?.” “A’a bazan gane ba” ta fad’a tana kawar da kai gefe. Ya girgiza kai yace, “Alhaji zaku iya tafiya gabad’aya ku amma dan Allah a kula in za’a shiga mota a dinga duba ko ina dan kana tare da makiyin ka naka sani ba wani zai iya ajjiye maka dan ya tozarta ka.” Abbah ya girgiza kai yace, “Gaskiya ne.” Ya kalli Asiya yace, “ki san abinda zaki dinga d’auka ko da yake ki san irin jakar da zaki canje da ita, a dinga kula in ba haka ba wata ran zaki kai kanki kurkuku.” Asiya ta d’auke kanta gefe kawai bata ce komai ba ya kalli Adam yace, “To Soja an gama hankali ya kwanta ko?.” Mubakar yace, “Tasan abinda zata dinga satowa zaka ce ba canje ba.” Ta kalli Mubakar da sauri yace, “k’arya aka yi miki? Ba satowar kika yi ba? Yau kika fara?. Garin sace-sacen ki na banza da wofi zaki kai mijin ki gidan yarı ba dan Allah ya kiyaye ba, kina can gıda kina bacci baki damu ba saboda ba ke aka kama ba” ya mik’e tsaye yace, “me ake da mata b’arauniya?.” Abbah ya kalle shi yace, “Mubakar ya isa haka, ku tashi mu tafi bana son wata magana.” Tayi shiru bata tanka ba suka tashi suka yi masa sallama suka tafi aka wuce da Yusuf Asibiti dan sake duba Lafiyar sa. Babu Wanda ya sake magana akan Asiya kowa yayi shiru domin duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa yake duka. #Mai daki #Nana Haleema #Book3 #Paid Book3 025 Ameena na zaune a falo tana karatu Anti Aisha ta fito ta zauna kusa da ita tace, "y'an boko, ana tayi." Ta kalle ta tayi dariya tace, "wallahi Anti, Bauchi nake so naje gidan Yaya amma wannan karatun bazai barni ba."  Asiha tace, "kuma yana da kyau kije ba tunda ga aure ki nan yana tunkaro ki." Ta rufe littafin ta kalli Anti tace, "nifa ba yanzu zanyi aure ba ku barni na sake hutawa sannan batun aure ya shigo." Tayi dariya tace, "sai kiyi hutun a gidan mijin ki." Sai tayi dariya tace, "kin San meye Anti? Yaya Al'ameen dariya yake bani yana saka zuciyata nishadi in naji ya dage shi a lallai soyayya yake yi, sai naji ina nishad'i  wallahi dan darıya abin yake bani. Da girman sa wai yace yana sona, dan Allah meye nawa bai sani ba lokacin ina yarinya? Komai da tare suke yi da Yaya amma yace wai ni yake so" ta sake fad'a tana dariya a bayyyane.  Anti ma dariyar tayi tace, "ita soyayya ina ruwan ta da babba da yaro? Kuma wai kwata-kwata nawa yake da kike zancen wai babba?, sa'an Yayan ki ne da kike gani  ko babar y'ar yayan ki bata yi shekara takwas ba har yanzu." Ameena tayi dariya tace, "to ki duba su Yaya mana duk k'annen sa ne kuma ko wacce ta kusa da aurar da y'a, ga Yaya Sumayya nan har an sa  ranar Ummi, ga Yayan Bauchi ma Amira ta kusa aure, kawai shi dan namiji ne." Anti ta sake yin dariya yace, "naga alama lamarin Al'ameen kin mayar dashi comedy, to shi wanda ya ganki a bikin su Yusuf din fa?." Ameena ta yatsine fuska tace, "shi kuma yayi yaro." Ganin kallon da Yaya take mata sai tayi dariya sosai Anti tace, "kyayi dariya mana kema kin san kin d'auko sabon iskanci ne ai. Wannan yayi girma wannan kuma yayi yaro." "Allah Anti ni maganar auren nan ma dariya take bani, ba yanzu zanyi ba sai na gama Digree in sha Allah." "Ai wallahi baki isa ba, yadda mazan auren suke wahala ke kin samu kice baza kiyi wasa ba." Ameena tayi dariya tace, "za dai mu gani." Sallamar Yaya Adam ya saka suka katse hirar suka kalle shi yace, "Ameena tun daga waje ake jin dariyar ki, me ya baki dariya haka?." Ta sake yin dariyar sai Anti tace, "Wai lamarin Al'ameen ne yake bata dariya wallahi, in yana magana nishadi yake bata, Kaji sabon iskanci dan Allah sai kace tana tare da mai wasan kwaikwayo." Yaya Adam  yayi dariyar shima yace, "Ameena ina ganin ki shiru-shiru ashe kema shak'iya ce." Tayi dariya tace, "babu ruwana Yaya." Yace, "Yanzu aka sake damuna akan Ana son auren ki." Ta kalli Anti itama ta kalle ta tace, "Kya kalle ni ai, wallahi cikin ukun nan da aka samu dole ki d'auki daya sai ki gama karatun a gidan ki."  Yaya Adam yayi dariya yace, "ina wani gida na farkon layin nan wanda yafi ko wanne girma a layin nan?." Anti tace, "na gane shi, gidan Alhaji Mu'az naji Ana cewa ko?." "Yauwa nan kuwa, ni na d'auka mai gidan da babba ne wallahi dan yanayin gidan na d'auka na babban mutum ne haka ya ajjiye mata hudu ashe mai gidan ba babba bane bai fi ni ba." Ameena ta kalli Yaya tace, "au kai yanzu ba babba bane ba Yaya?." Aisha ta dake ta tace, "ya fa ishe ki wallahi." Yayi dariya Ameenan ma dariya take yace, "ki tambayi Al'ameen." Ya sake cewa, "shine yazo yanzu nan dashi muka gama magana na shigo, yana son Ameena yana ganin ta in zata je makaranta ko ta dawo ya tambaya aka nuna amsa nan gidan akace a nan take k'anwar a ce. Yace yana sonki kuma matan sa biyu itace ta uku, dan Allah yana so na bashi dama su tattauna nace ya bani lambar sa ranar dana shirya ya ganta zan kira shi yayi godiya sosai ya tafi." Anti tayi dariya tace, "Allah Sarki, amma dai ga wanda basu da aure baza mu bawa mai aure ba."  Yaya yace, "to kika sani ko shi zata ji tana so?, abinda na sani kawai zan yi bincike iyakar iyawata har akan Al'ameen din duk wanda ta zab'a cikin su zan bincike shi sosai in sha Allah." Ameena tace, "to Yaya kace sa'an kane kuma yana da mata biyu har zaiyi ta uku, to meyasa kai kake da guda d'aya har yanzu?. Baka ganin sa'anin ka na k'ok'arin yin ya uku?." "Innalillahi! Wai Ameena kakar ki ce ni?" Anti ta fad'a tana kallon ta tare da tafa hannu sai kuwa ta sake yin dariya sosai harda rik'e ciki dan nishadi take ji dashi a wannan lokacin. Yaya Adam yayi dariya sosai shima yace, "kuma fa Ameena wannan shawara ce mai kyau, ya kamata a san abinda za'ayi."  Anti dai murmushi itama take yi kafin Yaya yace, "Ameena a bar batun wasa, ina jin fa zaki auren ne in yaso sai ki gama karatun a gidan ki, bana son wannan yazo wannan yazo din nan in aka gama magana guda d'aya duk wanda yazo zance an bada ke kinga yafi. A haka ma akwai wanda in suka zo fuskar magana ce basa samu a wajena dan ni ko shigar kace bata yi min ba baza kayi min wata magana ba. Kinga mai gidan nan na bayan mu? Haka yazo shima wai sonki yake yi matan da uku yaran sa ina jin sunyi hamsin, a tunanin sa dan yana da kud'i zanyi gaggawa nace gaki nan ya d'auka nan take na taka amsa burki har gobe baya iya  had'a ido dani ko a masallaci. Dan haka zan bawa shi Mu'az din dama yazo ku gaisa daga baya sai a d'auki d'aya a tsayar da magana an huta wannan da yazo wannan yazo." Anti tace, "hakan yayi sosai, in ba haka ba na banza ma wallahi zuwa zasu yi. A haka ma dan suna tsoron kane shiyasa ba'a iya zuwa amma babu damar auren yarinya ya mutu ko wanne banza sai kiga yazo wai yana sonta a ganin su ai bazawara ce nan da nan zata amince." Yaya yace, "Ameena kina ji baki ce komai ba, kina ganin hakan yayi ya cigaba da karatun a gidan ki tunda naga yanzu har kin shiga level two ko?." Ameena tace, "level 3 dai, ka manta direct level two din na samu?." Yaya yace, "ma sha Allah karatun naki ai yana gudu sosai, kinga end of level three din sai kiyi  auren ki ki huta ko?." Tayi murmushi tace, "duk abinda kace Yaya shi zanyi." Yayi murmushi yace, "to na gode. Ina Zaytun?." "Tana makaranta." "İn ta dawo anjima ki shirya ta zamu je asibiti ta duba baban ta bashi da lafiya." Ameena ba tare da yanayin ta ya canja ba tace, "To." Ya kalle ta yace, "ko kema zaki je?." Ta wara ido bata ce komai ba yayi dariya itama haka kafin ta tashi ta shiga cikin d'aki.               Labari ya baza unguwa Fiddausi ta dawo gida labari ne ya jewa Zakiyya bayan sallar magriba ta shiga gidan nasu ta samu Mama tana wanke zogale. Mama ta kalle ta tace, "A'a Zakiyya kece tafe?." "Eh Mama, ina wuni?." "Lafiya lau, kawar taki ta dawo ki shiga tana ciki." Da to ta amss ta shiga cikin d'akin ta hango Fiddausi a zaune akan sallaya tayi tagumi da hannu biyu yana kuka. Da sauri ta k'arasa kusa da ita tace, "Fidy." Jin muryar Zakiyya ya saka ta d'ago ta kalle ta sai ta sake fashewa da kuka Zakiyya ta zauna kusa da ita tace, "Fidy kece kika koma haka?." Bata ce komai ba sai kuka ta rik'e hannu Zakiyya tana juya kai tace, "Nice Zakiyya, Fiddausi da kika sani ce tayi wannan lalacewar." Zakiyya tace, "da gaske kenan maganar da nake ji garkuwa akayi dake?." Bata iya bata amsa ba Zakiyya tace, "in badan haka ba a kullum sai na kira ki sau goma amma ban tab'a samun ki ba, komai ya tsaya cak Fiddausi meye faru?." "Meye ma bai faru ba Zakiyya?, naga isha naga rayuwa, na tabbatar kud'i ba komai bane indai babu kwanciyar hankali." Zakiyya ta sauke Ajiyar zuciya tace, "Nima na fahimci wannan zancen Fiddausi, bani labarin abinda ya faru." Kaf ta kashe labarin ta fad'awa Zakiyya tashin hankali da ta shiga sai dan cikin ta ya motsa kuka itama take yi kamar ranta zai fita, cikin kukan  tace, "lallai Fiddausi kin auna arzuki da Allah ya kub'utar dake daga hannun mugu azzalumi. Kai Innalillahi wa'inna ilahir raji'un mu kam mun sakawa zuciyar buri shiyasa gashi nan muna ta wahala." Fiddausi tace, "Hakkin Ibrahim ne yake bina, na cutar dashi, nayi masa rashin mutunci, nayi masa..." sai ta dafe kai kawai ta kasa cewa komai dan in ta tuna kamar ta dawo da abin haka take ji. Fiddausi tana kuka cewa, "duk wani abu da nayi masa sai da ya faru a kaina, ma zubar da cikin sa an zubar da nawa, na hana shi kaina a lokacin da yake bukatar hakan  anyi amfani dani ta k'arfi kuma ta hanya ba daidai ba, babu abinda na iya dole na hak'ura, na saka an saka shi a cell nima na shiga cell. Zakiyya ya ko wanne b'angaren wallahi hakkin Ibrahim ne da kuma son zuciya irin nawa." Zakiyya tace, "ni kaina hakkin Ibrahim ya shafe ni balle ke, domin kuwa in b'era da sata daddawa da warin ta, nice umul'abamisin auren ki da Bello, Bawai dan cutar dake nayi hakan ba sai dan akwai ki samu abinda kike so. Amma yanzu na wayi  gari cikin fargaba da tashin hankalin had'uwa ta da mijina, ya tabbatar min da in na sake na raini cikin nan har na haife shi sai ya sake ni Fiddausi. Ke kin aan ya gidan mu yake in na baro gıdana na dawo gidan mu an ina zan zauna?, me zanci bayan nice nake taimaka musu?. Ina cikin gidsn komai yi min ake yi amma wallahil azim bana cikin farin ciki ko kad'an, kalli yadda na koma ni kaina. Nayi dana sani wallahi nima." Kuka suke tayi har anyi i'sha basu sani ba sai da Mama ta shigo tace, "kukan ya isa Kuyi sallah an idar tun d'azu" ta fad'a tana juyawa ta fita. Zakiyya tace, "Ameena da Rukayya da suke saka kyskykyawan burina zuciyar su ke in kika ga Ameena da Rukayya yanzu sai kin so ki sake kallon su, amma kalle ni kalle ki yadda muka koma bayan da su muke yiwa dariya muna ganin basu San dadin kudi ba." Fiddausi tace, "Ameena da Ruky ba irin fad'an da basa yi mana amma muka toshe kunnen mu, banji haushin ki ba Zakiyya bazan ce ke kika zuga ni ba son zuciyata ce itace ta Kaini ta baro, inda ban biye miki ba da hakan bata faru ba. Rukayya da Ameena su da yake babu son zuciyar a tare dasu ai basu tab'a yarda da kalaman ki ba. Kalli yadda kika koma kalli yadda na koma, duk mun lalace har gwara ke a kaina, ni luwadi akayi dani" sai ta sake fashewa da kuka Zakiyya tace, "ki daina kuka ya wuce na tabbatar yanzu yana can yana girbar abinda ya shuka." Fiddausi ta goge idon ta tace, "Anyi bikin Ruky ko? Wa ta aura?." Kallon Fiddausi Zakiyya tayi sai tayi murmushi tace, "Zamu je gidan wanda ta aure baki San shi ba." "Bata auri Ibrahim din ba?." "Eh, wannan  sunan sa Mu'azzam ba Ibrahim din ki ba." Fiddausi tayi murmushi tace, "daina cewa Ibrahim dina na wata ne dan nasan yayi aure yanzu shima, Allah Sarki Ibrahim ya bani rayuwa mai kyau a gidan sa, ya kyautata min ko kad'an baya so yaga raina ya baci, hana hak'uri dani yana sona in nayi laifi sau goma sau d'aya zai min hukunci, bai tab'a bari na kwana da yunwa ba, bai tab'a bari nayi kwadayin wani abun ba kafin na ayyana ya kawo min. Duk da bashi da kudi amma yayi kokarin kiyaye min duk wani hakkina da yake wuyan sa. Ya bani tarbiyya a zamana dashi, yadda nayi k'iba a zama na dashi ko Ameena da take  gidan Yusuf batayi ta ba, amma na bijire bana ganin duk abinda yake min, na wulakanta shi nayi kokawa dashi na saka aka kama shi" ta d'aga kai sama tace, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Zakiyya na tafka babban kuskure hakkin sane yake bibiya ya a yanzu, na tabbatar a tafka asarar da bazan tab'a mayar da kamar ta ba." Zakiyya tace, "Mun yi kuskure dukkan mu, na zab'i kudi matsayin farin ciki amma tunda an samu cikin nan kud'in suka zama basu da amfani a wajena saboda babu farin ciki, Kullum fargabata kar ya dawo ya tarar ban zubar d cikin nan ba, na rame Kullum a fad'uwar gaba nake.  yanzu in yazo ya sake ni ya zanyi? Ina zanyi rayuwa a gidan mu? A ina zan zauna? Da ace ban zuga ki kin zubar da ciki ba da yanzu watakila bana cikin wannan tashin hankalin, hakkin dan cikin ki da muka zubar ne ya biniye ni." Fiddausi tace, "sakayya muke gani wallahi, sakayya da gaggawa Allah ya nuna mana ita. Kinga ranar da kuka gama wayar nan daku akan Ibrahim yana son Rukayya a washe gari farin ciki ya kaurace min, Kullum cikin kuka da tashin hankali nake, Allah Mun tuba ka yafe mana" ta fad'a tana rufe fuskar ta tana sake fashewa da kuka. Sun jima a haka kafin ta goge idon ta tace, "A haka ma nayi kyaun gani ai Zakiyya. Yaushe zamu je gidan Rukyn?." Zakiyya tace, "keda baki da lafiya? Ki bari na sanar dasu sai su zo ko?." "A'a ni nake so naje." "muje gobe in zaki iya sai mu fara zuwa wajan Ameena daga nan sai muje gidan Rukayya tare da ita." Kai ta d'aga kafin Zakiyya tace, "mu tashi muyi sallah kar kamu k'arawa kan mu zunubi." Sallah sukayi a d'akin suka cigaba da tattaunawa har dare yayi sosai kafin Zakiyya ta koma gıda.              Kamar yadda Yaya ya cewa Ameena a shirya Zaytun bayan sallar isha suka tafi, a cikin d'akin da yake suka samu yan gidan su harda Abbah da Ammah duk suna nan shima ya tashi yana zaune ana Shan tea. A guje Zaytun tayi wajan Ammah ta d'auke tana dariya tace, "takwara kullum k'ara girma kike me mummy take baki?." "Abinci." Ta fad'a Ammah tayi dariya tace, "lallai naga alama." Mubakar ne yace, "Zaytun ba magana?." Sai ya sauka daga jikin Ammah ta tafi wajan sa ya d'auke ta yana yi mata wasa kafin ta tafi wajan Yusuf. Adam ya kalli Yusuf yace, "ya jikin naka?." Yusuf ya kasa had'a ido dashi kai a k'asa yace, "Da sauki." "Alalh ya kara Lafiya." Ya amsa da amin. Sallama akayi aka shigo ganin wands  ya shigo ya saka Yusuf yin murmushi yace, "A'a Taha k'araso ciki." K'arasa yayi ya gaishe da kowa ya zauna skan kujera yace, "ashe baka da lafiya, Mubakar na kira yake sanar." "Wallahi ina kwance." "Ina wayar ka?." Yusuf yace, "ai tana gıda wallahi." "Haba koda naji." Yusuf yace, "lafiya dai?." Taha yace, "kudi ake cirewa daga account din ka a kalla yanzu an cire kudi yayi miliyan biyar ko sama da haka, in aka cire yanzu to sha biyun dare za'a sake cirewa. Shiyasa na kira ka naji anya wayar na hannun ka dan nasan ba haka aka saba da kai ba, kuma ta application ake cire kudin transfer ake zuwa wani account guda biyu." Asiya da take tsaye ta fara zare ido Yusuf ya kalli Taha yace, "Wanne Account ake turawa?." "Wani ne  something Asiya da kuma wani Maimuna, but tunda naga haka nace sace wayar akayi kuma kananun b'atayi ne basu san kan bank ba da baza'a zo haka ba. Amma zasu ci uban su na nemo address din su gobe zan saka aje a kamo su a duk inda suke, cire kud'i suke na gidadawa wanda satar ma basu iya ta ba. Amma zasu yi dana sani, but yanzu nayi blocking account din naka baza su kuma iya tura kudi ba tunda naga satar tasu ta kananun b'arayi ce. Abinda ya sa ma na lura sata ce yawan cirewar, da kad'an-kad'an suke cirewa kuma Kullum sai an cire sau biyu, shiyasa na san sata ce kuma satar ma ta k'ananun b'arayi. Amma zasu ci uban su." Yusuf yayi murmushi ya kalli Asiya da take tsaye yaga sai zare ido take yi ya mayar da kai k'asa ya sunkuyar, Ammah da kowa da yake ji akayi shiru babu Wanda yace wani abun dan an San wacce take aikin nan sai Abie da yace, "Ai Taha ka bar zancen binciken ma tunda kayi blocking shikenan kawai, amma wanna satar ta gıda ce kuma mata ce ta d'auki kayan mijin ta a ganina babu komai akwai ka bar maganar nan." Taha da mamaki yace, "ban gane ba, kenan duk wanda yaci kudin yaci banza?." "Baka ji ne bace bane? Mata ce ta saci kayan mijin ta shine kawai." "Kana nufin matar sace take cire kudin?." "Kwarai itace, babbar b'arauniya ce a kaf unguwar su itace shugaba, kawai ka bar maganar." Taha ya girgiza kai yace, "kuma yake zaune da ita? Matar ka ace tana sata meye amfanin zama da ita?, yanzu da ba kudin sa bane da haka za'a kama shi ita taci bulus?." Mubakar yace, "ai kawai ka bar zancen Taha, duk wanda ya siyi rariya ai yasan zata zubar da ruwa, dan matar da ake so ta d'auki kudi ai ba komai bane ba." Taha ya girgiza kai kawai baice komai ba ya kalli Yusuf yana bai ma d'ago kansa ba balle yayi magana. Yaya Adam ne ya katse shirun yace, "Zaytun muje ko, mu zamu koma dare yayi." "A wajan Ammah zan zauna." Ammah tayi dariya tace, "ba wajan Daddy ba?." Ta kalli inda yake taga Asiya tace, "tsoron ta nake ji" ta fad'a tana nuna Asiya. Adam yace, "Zaytun kin manta kin fara zuwa makaranta?." Ganin zatayi kuka ya saka yace, "Zauna wajan Ammah, sai da safen ku" duk suka amsa ya fita yana mamakin hali irin na matar Yusuf ko yaushe cikin sata. Babu Wanda ya sake magana a cikin su sai ma tafiya da Taha yayi bai kuma maganar kudin ba duk suka fita aka barshi daga shi sai ita. Wani irin haushin ta da tsanar ta yake ji a zuciyar sa kalma d'aya yake so ya furta amma harshen sa ya sark'e ji yake ina ma a bashi umarnin furta wannan kalma da babu b'ata lokaci zai furta ta. Umarni kawai yake so a bashi ya furta ya tabbatar zai iya amma a yanzu harshen sa yayi nauyi matuk'a. Zama tayi tace, "my love amfani akayi da kud'in fa abubuwan da babu a gida na siya shiyas, amma ba wai na d'aukar maka kudi bane ba." Ya d'ago ya kalle ta yace, "Ya akayi kika san pin din?." "Gani nayi kana sakawa." Yayi murmushi yace, "lokaci kad'an Asiya, lokaci nake jira ina furta abinda nake son furtawa shikenan komai ya k'are Asiya." Ta turo baki tace, "me kake so kace?." Bai kuma magana ba daga wannan lokacin ta dinga kare kanta yayi mata banza haushin ta da tsanar ta zuciyar sa amma bashi da karfin guiwar aiwatar da abinda yake so tunda an samu canji da ko haushin nata baya ji, amma Umarni akwai yake jira a bashi ya furta wannan kalma a kanta. A daren aka sallama su suka koma gida. Yana shiga b'angaren ta yaga wayar tasa a ajjiye y d'auka kawai baice komai ba ya fita zuwa b'angaren Ameena ya kulle kansa a ciki dan kar ma tazo ya dame shi. Sai da ya zauna ya fara duba b'arnanr da tayi masa nan ya dinga ganin cire kudi kawai tayi wani ta turawa accounts  d'inta wani na Maimuna har da na Babar su. A bayyane yace, "wanne irin dangi na kai kaina ni Yusuf?. Har account din babar su an saka babu abinda ya dame su kawai su kud'i suka sani. Ta wacce hanya ma na auri yarinyar nan ni Yusuf?."Ajjiye wayar yayi a gefe kawai ya dafe kansa da hannu biyu yana Jin abinda ya jima bai ji ba a zuciyar da yana motsawa, a hankali yaji hankalina dawo kwakwalwar sa zuciyar sa na bugawa da sunan Ameena lokaci d'aya kamar asiri. Wayar ya d'auka sai kuma ya ajjiye ya rasa abinda zaiyi kawai ya kwanta a kan kujerar ya kulle idanun sa da suka yi masa nauyi sosai. #book3 #Nana Haleema #Mai daki. Book3 26         Kamar yadda suka tsara zuwa wajan Ameena haka akayi Zakiyya tazo suka tafi duk da har lokacin ba lafiya ce sa its  ba amma tana son ganin k'awayen ta, a k'ofar gidan Yaya Adam suka tsaya Fiddausi tace, "sun canja gida ne Zakiyya?." Zakiyya tace, "kedai muje kawai." Fita sukayi daga motar suka shiga cikin gidan suka samu Anti a tsaye a falo tana kwashe abinda aka karya suka gaisa suka tafi d'akin Ameena din. Tana tsaye a jikin madubi tana gyara dankwali suka shigo d'akin, amsa sallama tayi ta juyo tana  kallon su sai kuwa ta wara idanu tace, "Fiddausi! Kece ko kuma dai bake bace?." Fiddausi idanu suka ciko da hawaye ta matso ta rungume Ameena hawayen suka sakko tace, "Nice, Ameena nice". Ameena ita sai idanun ta suka ciko tace, "Fiddausi kece kika koma haka ne ya faru? Ta fad'a tana kallon ta tace, "Innalillahi Fidy kece?." Fiddausi hawaye ya sakko mata yace, "Nice Ameena." Sake kallon ta take yi kafin tace, "mu zauna."  Suka zauna a kan katifar Ameena tace, "Fiddausi rashin lafiya kika yi haka? Ina kika shiga bam samun ki a waya? Me ya same ki fuskar ki duk tayi tabo haka." Fiddausi ta sauke Ajiyar zuciya tace, "Ameena labarin yana da tsaho sosai, ki shirya mu tafi gidan Rukky sai mu tattauna a can." Ameena tace, "gabana fad'uwa yake yi Fidy, kinga yadda kika koma kuwa?. Zakiyya wai Meya same ta haka?." Fiddausi tace, "ki shirya mu je kawai." Ameena ta sauke numfashi ta saka kallon Fiddausi sai ta mik'e tsaye ya d'auki mayafi ta saka ta d'auki wayar ta tace, "muje." Tare suka fito Ameena ta kalli Anti tace, "Anti zamu je gidan Rukayya." "A dawo lafiya." Ameena suka fita suka shiga mota suka wuce gidan Rukayya. Babu wanda yake magana a cikin su har aka je k'ofar gidan direban Zakiyya ya faka motar suka fito suka shiga cikin gidan. Rukayya tana zaune a falo tana shan tea taji anyi sallama an shigo falon ta kalli wanda suka shigo tare da amsawa, a ranta tana ayyana ashe bata kulle gidan ba, bata san lokacin da kofin ya fad'i a hannun ta ba ta mik'e tsaye tana kallon su tace, "wa nake gani kamar Fiddausi?." Fiddausi tayi murmushi ta k'arasa kusa da ita ta rungume ta sai ta sake ta ji ciki da ya tokare ta  ta d'go tana kallon ta tace, "Rukayya nice." Rukayya tace, "Na gani Fiddasi, yaushe kika dawo? Ina kika shiga ko a waya bama samun ki?. Tun ina gida nake zuwa wajan Mama tace min anje har Abuja anje ba'a samun ki, ina kika shiga?." Suka zauna Akan kujera Ameena tace, "Kiyi magana Fiddausi kin saka zuciyar mu a rud'ani." Tayi Ajiyar zuciya tace, "abubuwan da suka faru da yawa, abinda na sani nayi dana sanin kai kaina wannan gida da sunan naje gidan farin ciki." Rukayya tace, "ki fad'a mana Meya faru? Me ya same ki?. Ina shi Alhajin da kika aura yake?." "Alhaji Bello na barshi ana Abuja ban San halin da yake ciki ba, guduwa nayi yadda muke ganina film a hauro daga window din bandaki ta nan na hauro Ameena." "To me ya faru?" Rukayya ta fad'a tana kallon ta. Ta sauke numfashi ta lumshe ido ta bud'e tace, "Alhaji Bello dan luwadi ne, ba kuna iya neman maza ya tsaya ba har matan sa bai bari ba." "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Ameena da Rukayya suka fad'a a tare suna kallon ta ko wacce da firgice a tare da ita idanun su a waje cikin tashin hankali. Fiddausi Tce, "Inda iya wannan ne ma da sauki, abubuwan da zaku ji a kansa yanzu sai Kun nemi ruwa a kusa daku." Babu wacce da iya magana Fiddausi ta basu labarin abinda ya faru kaf babu abinda ta b'oye musu sannan tace, "a mafarki aka ce min abinda nan zai faru dani zan karyata nace karya ne badai ni ba, sai gani nayi rayuwa dashi har ya samu nasara a kaina." Kuka Rukayya take yi haka Ameena ma har Zakiyya ma zuciyar ta sake karyewa kuka suke gabad'aya su aka rasa wacce zatayi magana a cikin su, Fiddausi tace, "Amma ko me  ya faru dani nice na jawo, nice na zab'i son zuciya na bar zab'in da Allah yayi min na tafi neman kud'i da rasu uwar jin dad'i, ga kud'in ina rayuwa a ciki amma sun kasance basu da amfani a wajena, ga jin dadin amma babu farin ciki." Ta kalli Rukayya da take kuka sosai tace, "kin tuna abinda kika fad'a min? Akwai gidsn kud'in da babu farin ciki a cikin sa, ga kud'in amma baza su saka ni farin ciki ba saboda babu kwanciyar hankali. Amma na toshe kunne na bana ji bana gani sai da na tabbatar na cikawa kaina buri na auri Alhaji Bello. Abinda baku sani ba tun ina gidan Ibrahim nake tare da Alhaji Bello, wani lokaci da tsautsayi ya kaini wani private hospital a nan muka had'u ya d'auke ni ya kaini gidan Zakiyya daga nan muka fara waya dashi har had'uwa muke muyi zance na manta da ina da aure. A gidan Kiyya zamu had'u dashi muyi hira ayi soyayya kamar bani da aure, ban kiyaye hakkin aure a kaina ba shiyasa shima bai kiyaye ba da ya aure ni. Na tabbata zunubin kula shi da na dinga yi ina aure shiyasa Allah ya hukunta ni da abubuwan da suka faru Dani." Ta girgiza kai tace, "Na zubar da ciki da kaina saboda na samu  damar auren sa ba tare da idda ba, har gidan su Ibrahim naje a gaban  iyayen sa nace ya sake ni. Ban tabbatar da nayi kuskure ba sai yanzu wallahi, ban san da cewa na fita daga aljanna na kai kaina wuta ba sai yanzu, Ameena, Rukayya, Zakiyya ban San inda zan saka raina ba, zuciyata zafi take min na rasa abinda yake damuna ba balle nayi maganin damuwa ta." Ameena ta goge idanun ta tana kallon ta tace, "tabbas kinga rayuwa Fiddausi kin shiga cikin jarabawa, kin ga abinda baki tab'a gani ba a cikin rayuwar ki. Amma ki gode Allah da ya hukunta ki tun yanzu ba tare da kin koma gare shi ba. Dan ka smau Allah yayi maka hukunci a duniya ma rahama ne wallahi, wasu sai sunje ga Allah sannan suke ma fahimtar sunyi kuskure a lokacin babu damar neman yafiya. Ke kuwa fa? Kina da damar da zaki tuba Allah ya yafe miki duk abinda kika aikata." "Ameena naga banbancin tsakanin rayuwar da nake hange da wacce kuke fad'a min, na dandana zaman kwanciyar hankali sannan na d'andana zaman kud'i babu kwanciyar hankali, ko wanne an rarraba min shi yadda zan fahimta sosai. Walalhi ban tab'a yin kukan rashin kwanciyar hankali ba a baya sai dai son zuciyata, amma tunda na saka k'afa ta an Abuja na tabbatar nayi ban kwana da farin ciki Ameena. Nayi dana sanin rayuwar da na daukarwa kaina" ta fad'a tana sake fashewa da kuka. Ta sake cewa, "babban abinda yake d'aga min hankali bai wuce in na tuna nayi luwad'i ba" muryar ta tana rawa tace, "zuciyata rawa yake yi in na tuna da wannan abin ya faru a kaina, ina jin kamar na kashe kaina sboda wannan bak'in cikin da nake ji a zuciyata. Rayuwata gabad'aya ta lalace, ina zan kai wannan zunubin dana d'orawa kaina? Saboda masu aikata luwad'i akayi ruwan d'ufana, a duk sanda aka aikata shi al'arshin Allah girgiza yake yi saboda munin sa. Amma ni Fiddausi nice na aikata, ni Fiddausi nice na aikata saboda son zuciya irin tawa." Rukayya ta girgiza kai tace, "baki da laifi ko a wajan Allah, Allah yana gani fin karfin ki akayi." "Da ban kai kaina bafa Rukayya? In da nayi zamana a inda Allah ya barni da yanzu ina nan hankalina kwance bani da wata damuwa ko fargaba. Amma na sakawa idanuna kwalli bana tuna komai bana hangen komai sai y'an uwan  da Ameena da Zakiyya, Kullum tunanina suna cikin jin dad'i ina cikin wahala, Kullum tunanina suna sama ni ina k'asa, Kullum hangena taya su suna hawa mota ni ina hawa napep? Taya su suke kwana a gida manya ni ina kwana a k'aramin gida?. gashi naje ga jin dadin ya zame min babban tashin hankali da ban tab'a zaton zan tsinci kaina a ciki ba. Ina ma na mutu na huta" ta fad'a tana sake fashewa da kuka salak mai tsuma zuciya ya kwantar da kanta a kafadar Rukayya tana kuka sosai. Ameena tace, "k'addarar ki kenan, ko wanne bawa baya tsallake k'addarar sa. Kiyi hak'uri ki daina kuka." D'ago kanta tayi ta goge idanun ta tace, "kuka ya zamar min dole na tabbata yanzu ma na fara, Abba ko kuka ni bayayi saboda ya samu labarin kaf abinda ya faru kafin na auri Bello, haushina yake ji sosai ko gaisuwa ta baya amsawa. Ko iya wannan ya ishe ni tashin hankali." "Kin b'ata masa rai ne a baya amma zai yafe miki in sha Allah" Ameena ta fad'a tana kallon ta. Ta sauke Ajiyar zuciya tace, "Ko Ina da cutar hiv ma ban sani ba." Rukayya tace, "Haba Fiddausi baki da komai in sha Allah. Ki daina wannan fatan k'addara ce kuma kin gane kuskuren ki komai ya wuce." Murmushi tayi tana hawayen da yak'i tsayawa tace, "Son zuciya ya kaini ya baro ni, duk da akwai zugar Zakiyya amma ban d'auke shi komai ba don daga zuciya tane ba daga kalaman Zakiyya ba." Rukayya tace, "duk da haka zugar ta tayi tasiri a kanki, da tana nuna miki abinda kika yi ba daidai bane da wani abun baza kiyi ba. Komai take kika yi itace ta zuga ki, in kina da laifi a cikin d'ari kina da sittin ita kuma tana da arba'in, itace take d'ora ki akan komai. Ko hıra da shi Bellon da bata baki fuska ba da baki yi a gidan ta ba." "Wallahi ba komai bace, son zuciyata ne dan da niyar hakan daman a zuciyata. ku meyasa batayi tasiri a kanku ba sai ni? Saboda zuciyar ku a wanke take kin saka niya mai kyau ni kuwa fa?." Sukayi shiru dukkan su kamar gidan rasuwa babu mai magana kafin Zakiyya tace, "ni kaina gashi ta dalilin hakan aure na yane neman b'allewa, na tabbata kuma hakkin hakan ne yake bibiyata." Babu wanda ya iya magana a cikin su Ameena tace, "tun wancan lokacin da kike hangena Fiddausi kin fini kwanciyar hankali, dan baki San irin damuwar da nake ciki a gidan bane shiyasa nake burge ki a ko yaushe dan a ganin ki ina cikin kudi da jin dad'i bani da matsala. Ita Rukayya tazo ta tarar da kad'an daga cikin wani abun wancan lokacin, dakyar rana ta fito ta koma banyi kuka ba, na shiga tashin hankalin da baki san na shiga ba, kwanciyar hankali d anutsuwa na minti d'aya bani dashi a wannan gidsn da kike hangena. Shiyasa nake ce miki ki gode Allah yayi miki ni'imar da bai yiwa sauran mata ba amma sai kice kee ba haka ba kudi kawai shine kwanciyar hankali, ina sha'awar rayuwar gidan ki na wancan lokacin, saboda kwanciyar hankalin da kike da ita akwai nake hange, ke kuma kudin da nake ciki kike hange babu ruwan da da akwai kwanciyar hankali ko babu. At the end gani yanzu a gida babu auren." Fiddausi ya kalle ta da sauri tace, "kina nufin Kun rabu da Yusuf?." "Da kika tashi ai ba gidana kika je ba ko?." "Wai yanzu babu aure tsakanin ku kenan?." Ameena tayi murmushi tace, "Babu Fiddausi, amma hakan yafi min dadi na samun kwanciyar hankalin da na rasa a gidan sa, kud'i ba komai bane ba wallahi indai babu kwanciyar hankali. Domin babu abinda zasu yi miki kina kallon su sun zama hoto, in kuwa akwai kwanciyar hankali haka za'a dinga ganin ki kin yi k'iba abin ki ko babu kudi zaki yi kyau kowa ya ganki sai yayi sha'awar ki." Fiddausi tace, "na tabbatar wallahi, ni zan bawa wani labari a yanzu Ameena. Rayuwar da nayi a gidan sa kamar rayuwar dabba haka yake komai nashi, nayi dana sanin abinda na aikata Allah y sani. Lokacin baya kuwa har Mama cewa take sai dai su Yaya su nuna min manyan gıda amma badai kwanciyar hankali ba, amma sai naga kamar ci min fuska suke yi." Rukayya tace, "sai ki gode Allah da ya ganar dake kuskuren ki tun yanzu, wahalar da kika sha kuma Allah ya sa ta zama silar wankewar zunuban ki." Ta sauke Ajiyar zuciya ta amsa da Amin Rukayya ta tashi zuwa kitchen Ameena ya tashi tabi bayan ta yana cewa, "ruwa nake son sha." A tsaye taga Rukayya tace, "nasan bayan wannan labarin na Fiddausi akwai abinda yake zuciyar ki, koda wasa kar ki nuna wani abu matar ibrshim ce ke a yanzu Fiddausi kuma matar Alhaji Bello." Tana fad'a mata hakan ta fita ta kyale ta ita kuma ta dawo da da ruwa da lemo a hannun ta. Fiddausi ta kalle tayi murmushi tace, "kin yi nauyi Ashe." Murmushi itama tayi ta zauna tace, "me zan dafa mana muci." Fiddausi ta dafe kai tace, "kaina ciwo yake." Ameena tace, "daman bai kamata ki fito a wannan yanayin ba, kamata yayi a sanar damu muzo har gıda da kanmu." Fiddausi tace,  "nayi kewar ku ne sosai shiyasa, kunyar Mama nake ji da Abba shiyasa bana son zaman gidan." Rukayya tace, "yanzu ya za yi da auren sa da yake wuyan ki?." Ta girgiza kai tace, "wallahi ban sani ba Rukayya, abinda na sani kawai na gama auren ko me za'a yi min bazan koma ba." "Babu wanda zaice ki koma a irin wannan yanayin ai" Zakiyya ta fad'a tana kallon ta da tausayawa. Ameena ta mike tace, "nice mai Lafiyar cikin ku bara nayi mana abincin." Shiga kitchen din tayi ta barsu shiru kamar gidan mutuwa babu mai magana a cikin su.        Har aka gama abincin aka kawo babu wanda yace komai kuma sunci sosai ba kowa da abinda yake ransa dukkan su. Sallah ce ta saka suka tashi sukayi alwala sukayi sallah a lokacin sai da suka sake yin kuka saboda yadda Fiddausi yake addu'a a fili tana hawaye. Suka dinga rarrashin ta suna bata kalamai masu dad'i. Fiddausi ta kalle su tace, "ina son ganin d'ana amma bani da karfin guiwar zuwa inda yake." Babu wanda ya amsa mata ta sake cewa, "har baban nashi ina da buk'atar ganin sa domin ma bashi hak'urin abubuwan da suka faru, nayi kuskure mai yawa duk da nasan babu lallai ya yafe min. Ku taimaka min na ganshi na bashi hak'uri ban san a inda zan ganshi ba." Nan ma shiru babu wanda yayi magana Rukayya ta kalli Ameena da Zakiyya suka had'a ido ta sauke numfashi bata ce komai ba. Horn Rukayya taji a waje ta tashi tace, "ashe yau Alhamis, ina zuwa" ta fad'a tana tashi zuwa waje jim kad'an suka shigo da Amir jakar hannun sa tana hannun ta shi kuma ya rike luch box. Sallama da yayi ya aka Fiddausi ta kalle shi gaban ta ya fad'i tana kallon sa cike da mamaki yace, "Anti Ameena ina yini." Ta amsa yace, "Anti Zakiyya ina yini." Itama ta amsa tana murmushi ya kalli Fiddausi yace, "ina yini" yana fad'a ya wuce alamun bai gane ta ba. Rukayya ta rik'e shi yace, "Ammi Yunwa nake ji." Ta kalle shi tace, "ga Maman ka" ta fad'a tana nuna masa Fiddausi da take kallon su da mamaki kamar idanun ta zai fito waje. Kallon Fiddausi yayi ya kalli Rukayya yace, "Mama na" ya sake kallon Fiddausi dan bai gane ta ba ya matsa kusa da ita tana kallon sa yana kallon ta. "Amir dina" ta fad'a murya tana rawa tana kallon sa shima ita yake kallo dan bai manta ta ba kawai dai ta canja masa ne. Ta rungume shi sosai a jikin ta tana kuka sosai tace, "kayi hak'uri Amir kayi hak'uri ka yafe min ka aikata kuskure babba Amir, ka yafe wa Maman ka." Sakin sa tayi ta rik'e fuskar sa tana kallon sa shima haka da alama har lokacin mamaki yake yi ya kalli Rukayya yace, "Ammi da gaske Mama ce?." Ta d'aga masa kai alamun eh yace, "kince taje Unguwa ta dawo?." Nan ma ta d'aga masa kai alamun eh ya kalle ta yace, "kika je unguwa kika barni, ni bana kula ki Ammi ce take sona." Lumshe ido tayi sai ga hawaye tace, "kayi hak'uri Amir yanzu na dawo babu inda zan sake tafiya." Dariya yayi yace, "fitsari nake ji" ya fad'a yana barin wajan da sauri. Fiddusi ta kalli Ameena ta kalli Rukayya ta kalli Zakiyya tace, "Ya akayi Amir yake hannun ki?." "Saboda mahaifin sa ta aura" Zakiyya ta fad'a tana kallon ta. Fiddausi ta kalle ta tace, "mahaifin sa? Kina nufin İbrahim?." Ameena tace, "yana da wani a mahaifi ne bayan sa?." Ta kalli Zakiyya tace, "amma kika ce min ba shi bane wani ne daban Mu'azzam." Zakiyya tace, "wancan Ibrahim din da kika sani daban da Wanda ta aura, shiiyass nace miki haka amma ai kin san mahaifin Amir ko? to shi ta aura. Amma ba Ibrahim din ki bafa wannan Mu'azzam sunan sa." Gaban Fiddausi ya fad'i matuk'ar ta juyo a hankali tana kallon Rukkaya kamar yadda take kallon ta. "Kenan kina nufin Rukayya matar Ibrahim ce a yanzu?." Ameena tace, "eh mana Fiddausi." Fiddausi kamar an d'ora mata wani abun a kanta haka taji amma sai tayi shiru tana kallon k'asa kafin ta d'ago tana kallon su tare da kallon falon gidan tace, "kenan wai a gidan Ibrahim nake? A nan naci abinci nasha ruwa?."  Ameena tayi murmushi tace, "kamar ba gidan sa ba da ba ko? Gaskiyar Zakiyya da tace miki wancan daban wannan daban. Domin sanin wancan da kika yi kike kira talakan da bashi da komai wannan ya wuce ace masa Talaka." Murmushi yaqe tayi ta kalli Rukayya da yake tsaye tace, "Allah ya sanya alkhairi, na taya ki murna." Mugun kishi Rukayya take ji a zuciyar ta amma bata so hakan yayi tasiri sai itama tayi murmushi tace, "na gode." Fiddausi tace, "ya kamata mu tafi." Ameena tace, "da wuri haka? Ko sallar la'asar ba'a yi ba ki bari ayi sallah rana tayi sanyi sai mu tafi." Waje ta samu ta zauna amma ta kasa sukuni gabad'aya sai ware ido take kana kallon ta kasan akwai abinda yake addabar ta a zuciyar ta. Zakiyya tace, "ya naga kin canja? Kin manta ke kika bada wannan damar Fiddausi? Kin manta kince zaki zo gidan Kici abinci ku gaisa dashi?, to ga damar hakan ta samu meyasa yanzu kika canja kuma?." Kai ta sunkuyar bata ce komai b kafin ta d'ago tace, "babu komai kawai abin yazo min bazata ne." Amir ne ya dawo ya wuce ya ya shiga kitchen ya zuba abinci ya dawo ya zauna yana ci yace, "Ammi yau ma an bani kyau a makaranta, tsaya na d'auko" ya fad'a yana tashi ya shiga d'aki sai gashi ya dawo da ledar chocolate ya bata yace, "Uncle ne yace nafi kowa iya karatu shine ya bani." Tayi murmushi tace, "ka gode kaje Kaci abinci." "Ammi dmaan Abba yace in na cigaba da kokari zai siya min keke ko?." Ta d'aga  kai alamun eh yayi tsalle ya koma yana cin abincin sa Fiddausi na kallon sa tana murmushi. Abincin ya gama ci yace, "Amma ba'ayi wanka ba." Tace, "kaje ka kwanta ka huta anjima za'a yi." Ya amsa da to ya wuce ya shiga d'aki ya bar Fiddausi tana kallon sa. Shiru babu wanda yake cewa komai sai kallon kallo kowa da abinda yake ransa a cikin su kafin Fiddausi ta katse shirun tace, "Ammi a bani aron Amir dan Allah mu tafi tare zuwa gida, nayi kewar sa sosai wallahi ina so ya zauna a kusa Dani." Rukayya ta kalle ta tayi ajiyar zuciya tace, "to." Wayar tace tayi k'ara a kusa da Fiddausi ta juya ta d'auko mata ta mik'a mata, ganin sunan da yake yawo a kai ta dan rufe ido fa bud'e kafin ta d'auka. abinda taji ya saka gaban ta ya fad'i sosai ta kashe wayar ta tashi ta fita bata ce komai ba. #Mai dak #Book3 #Nana Haleema #Paid #500 Book3 027       Bud'e k'ofar tayi ta ganshi a tsaye yabi fuskar ta da kallo ta bashi hanya ya wuce ya bud'e gate din ya fita ya koma motar ya shigo da ita ya sake fita ya kulle gate d'in tana tsaye bata motsa ba ya kalle ta yace, "Lafiya kike?." Kai ta girgiza kawai ya d'an zubawa fuskar ta ido na wani lokaci kafin ya janye idon ya kalli k'ofar falon gadin takalman mata sai ya shiga setroom din sa da k'ofar take a compound din gidan daga can gefe ta bi bayan sa ya zauna  itama haka. "Meye yake damun ki haka? Kukan me kika yi?." Numfashi ta sauke tayi shiru bata amsa ba yace, "Ina miki magana, me ya faru na ganki a haka?." Ta kalle shi sai idanun ta suka sake cika da hawaye suka sakko kan kuncin ta ya kulle ido ya bud'e yace, "magana nake miki ki fad'a min." Hannu ta saka zata goge idanun ta ya riga ta gogewa yana kallon ta itama haka tace, "Su Ameena ne suka zo." Da mamaki yace, "yau  kuma zuwan Ameena ne ya saka ki kuka?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "ki fad'a min magana kin barni cikin tunani, me yake damun ki?." Bud'e k'ofar akayi tare da kullewa ganin Amir ya shigo ya saka shi cewa, "A'a Amir yau ko uniform ba'a cire ba?." Ya k'araso kusa da shi yace, "Abba Mama tazo." Ibrahim yace, "wacce Mama?." "Mama da ta tafi unguwa bata je dani ba." Ya kalli Rukayya yace, "wa yake nufi?." Rukayya ta kalle shi tace, "Maman sa yake nufi." Ibrahim yace, "yana da wata Mama ne bayan ke daman?. Look Rukayya ki fad'a min abinda yake faruwa mana bana son wanna nuk'u-nuk'un naki. Wacece Mama? Zuwan tane ya saka ki kuka?." Rukayya tace, "Mahaifiyar sa nake nufi." Zuba mata ido yayi na wani lokaci kafin yace, "shine ya saka ki kuka har haka? Shine ya baki damuwar da kuka kasa tambayata yau ya akayi na dawo da wuri?." Ta rausayar da kai tace, "Bana tare da nutsuwa ne shiyasa, amma..." ya katse ta yace, "Amma Me?." Sai ya kalli Amir da yake leken taga yace, "Amir koma d'aki yanzu zata zo." Fita yayi yaja k'ofar ya kulle shi kuka ya kalle ta kamar zak magana sai ya fasa ya zuba mata ido kafin  ya sake cewa, "ko abinci baki bani ba." Ta mik'e tace, "yi hak'uri ina zuwa" ta fad'a tana fita zuwa falon da suke. Tana shiga falon da Fiddausi suka had'a ido da alama kallon ta inda zata b'ullo take yi sai tayi mata murmushi itama Fiddausin tayi Rukayya tace, "na barku ku kad'ai ko? Mai gidan ne ya dawo zan bashi abinci ina zuwa" ta fad'a tana  shiga kitchen. Ba jimawa ta fito da abincin ta wuce su ta shiga ta ajjiye masa ta zauna a gefen sa tana kallon sa, zuba masa tayi a plate maimakon ya d'auka sai ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa ya d'auki abincin sa yaci tana zaune sai da ya kusa gama cinyewa ya kalle ya yace, "Wai wannan canjin ne meye?." "Abinda naji ne ya saka ni a damuwa." "Ni kuma sai ya shafe ni?." "Kayi hak'uri bai shafe ka ba." "Shiyasa gaki nan kamar yadda kike Kullum." Tayi shiru tana kallon sa ya tashi ya bud'e k'ofar da take kusa dashi sai gashi a d'akin sa ba tare da ya koma wancan falon ba. Fita tayi ta koma wajan su tana shiga Ameena tace, "Tunda mijin ki ya dawo zamu wuce mu." Rukayya tace, "Da wuri haka?." Zakiyya tace, "gwara muje sai kifi samun lokacin kula dashi." Tayi murmushi ta kalli Fiddausi da ta zubawa waje d'aya ido tace, "na kira  miki Amir?." Fiddausi ta kalle ta tace, "Da naji dadi." Sai fiddausi ta bata tausayi ta shiga d'akin Amir din suka fito tare ya kalli Fiddausi yace, "Bye Mama" yana fad'a ya shiga d'aki ya barta a wajan baki bud'e tana masa dariya amma a cikin zuciyar ta zafi take ji sosai. Murmushin yaqe tayi tace, "babu komai." Zakiyya tace, "muje ko?." Tare duk suka mik'e suka fito zuwa harabar gidan Fiddausi taga mota mai kyau a ajjiye ta bita da kallo amma bata ce komai ba. Har bakin mota Rukayya ta raka su da alqawarin zata je gidan su Fiddausi.        Lokacin da ta koma wajan sa ta shiga kai tsaye ta same shi a zaune yana ta binciken takarda ta zauna kusa dashi tace, "yau ka dawo da wuri." Kallon ta yayi sai ya share bai magana ba ya cigaba da abinda yake yi ita kuma ta dafe goshiin ta gabad'aya labarin Fiddausi ya hana zuciyar ta sukuni ko kusa. Banza yayi mata shima bai kula ta ba sai waya da yake amsawa yana ajjiyewa tace, "kaina ciwo yake min." "Dole kanki yayi ciwo ai, kin sha kuka." "Bara nayi sallah." Baice komai ba ta tashi ta shiga band'aki yayi alwala ta fito ta samu baya nan tasan ya fita sallah shima ta tayar da sallah ta zauna akan sallayar bayan ta idar kawai tunanin Fiddausi ya sake zuwa ranta sai kuka. Tana cikin kukan ya sake dawowa ya zauna ya hard'e hannayen sa waje d'aya yana kallon ta yace, "bazan ce me aka fad'a miki ya saka ki kuka ba amma ko meye ki kawar dashi a yanzu ki fuskance ni dan ni ne a gaban kik damuwar ta tafi, na dawo gida baki tambaye ni dalilin dawowa ta da wuri ba, nazo da labari mai dadi amma ban samu fuskar fad'a miki ba bayan kin san kece abokiyar shawarata sai na fad'a miki zanji dad'i a raina. Tun daga can na k'unso labarin ina so na fad'a miki amma da nazo sai naga akasin yadda na fita na barki. Akan wani abu da bai shafe ni ba zaki canja min haka? Akan me?." Ta goge idanun ta ta kalle shi tace, "Wallahi in na tuna ne bama sanin na fara kuka Khalil,  zuciyata zafi take ban san ana samun hakan a gaske b sai d'azu." "Ban tambaye ki ba ai, bance a fad'a min ba, haka bana so naji wani abun. Ban san abinda ya faru ba dan haka baza'a canja min ba, ni nayi laifin?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "to meyasa zai shafe ni?." Ta goge ido sai tace, "kayi hak'uri." "Ba laifi kika yi ba, amma ki sani zan dakatar da duk abinda zai saka ki damuwa sake zama dake har yayi magana dake, in ma su Ameena din ne suke saka ki a wannan yanayin zan dakatar dasu dan bazai yu a zo har gidan ki saka ki damuwa a koma a barki a cikin ta ba. Ciki ne dake kwanciyar hankali ce ta kamace ki ba tashin sa ba." Tasowa tayi daga inda yake ya dawo kusa dashi ta shiga jikin sa ta rike shi gam shima ya rike ta yayi shiru bai ce komai ba. D'agowa tayi ya kalle shi tace, "kayi hak'uri hakan baza ta sake faruwa ba. Ka fad'a min abin farin cikin da yake bakin ka." Ya tab'e baki yace, "ai banga farin ciki a fuskar ki ba." Tyi murmushi tace, "Allah har zuciyata ina cikin farin ciki so nake naji me zaka ce." Ganin tayi murmushi sai yaji dadi amma baiyi murmushin ba tace, "Haba dan Allah kayi murmushi ka fada min." "Sai na ja miki aji kamar yadda kika yi min." "Haba dan Allah kayi hak'uri." Ya kalle ta ido cikin ido kamar zai magana sai yayi shiru tace, "Dan Allah ka fad'a min." Yayi murmushi yace, "in na fad'a wanne goron albishri za'a bani?." Ta kwanta a kafadar sa tace, "duk abinda ka zab'a na Baka zabi ni kuma zan baka." "Kin tabbatar?." "Na tabbatar." "Kin yi alqawari?." Kamar zatayi kuka tace, "nayi mana, haba kaima dan Allah kamar wani Amir." Yayi dariya yace, "so nake na tabbatar ne ai." Ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa yayi dariya ta fara kukan shagwab'a tace, "ka barni cikin tunani dan Allah ka fad'a min." "Ogan mu yau ya dawo daga lagos ya kuma zo har inda nake ya kira ni da kansa naje har office din sa a nan yake shaida min na shirya ina cikin Wanda ya bawa umrah a wannan shekarar. Farin cikin lissafin da aka fitar ta b'angarena tukwici shine umrah." Rukayya ta wara ido tana kallon sa tana murmushi shima haka tace, "da gaske kake?." Ya d'aga mata kai alamun eh ta sake komawa jikin sa tace, "Alhamdulillah! Kaii wannan labari ne mai dadi Wanda ban yi tunanin jin sa ba, Yanzun haka mana nufin da kai za'a tafi umrah a wannan shekarar? Kai Alhamdulillah naji dadi sosai." Ganin ta gigice tana farin ciki sai yace, "nutsu mana." "Taya zan nutsu bayan ka fad'a min abinda zai saka na fita daga nutsuwar tawa?." Yayi murmushi yace, "wallahi da ya fad'a min ji nayi kamar a mafarki, na rasa wacce irin godiya ma zanyi masa." "Dole ka rasa, dole ka rasa abinda zaka ce. Allah ya saka masa da alkhairi ya biya shi da aljanna." Ya amsa da amin kafin yace, "amma ne kike ganin zanyi wanda zan nuna masa ina cikin farin ciki?." Tayi shiru kafin tace, "da kai da Alhaji zaku har gida ku yi masa godiya zai ji dadin hakan sosai, in mahaifiyar sa na da rai ko mahaifin sa mu siyi kaya ko wani abu na ci muje nida kai mu kai mata muyi mata bayani, na tabbata zai yi farin ciki da hakan." Ya girgiza Kai yace, "wannan shawara ce mai kyau, amma zan samu Alhaji da maganar anjima naji abinda zai ce." "Wai ni na fara sani?." "Ina da wacce ta fiki ne? Ina da wacce tafi kusa dani bayan ki ne?." Dadi ya mamaye mata zuciya tace, "babu sai ni din." Yace, "yanzu ranar Monday zamu je ayi min passport." "Kaga ikon Allah ko? Kawai niyar alkhairi da akayi za'a yiwa Alhaji da Hajiya sai gashi Allah kaima ya so  ka a ciki." Yace, "bayan ya fad'a min abinda yazo raina kenan nima, nace ikon Allah kenan wato in ka ayyana alkhairi ko baka aikata ba Allah baya barkn ka haka." Murmushi yaga tana tayi alamun tana cikin farin ciki yace, "in Allah yayi tafiyar sai mu tafi nida ke da Hajiya." Ta kalle shi tace, "Alhajin fa?." Ya sauke numfashi kafin yayi magana tace, "baza'a je dani ba ba sai Alhaji  yaje, in kuka dawo kamar yadda Allah ya bayar da wannan damar Nima zai kawo tawa sai mu koma." Yayi murmushi yace, "in sha Allah dake za'a yi tafiyar nan." Ta amsa da Amin yace, "Anjima zanje na fad'awa su Hajiya sannan suma  ina so nayi musu passport amma kuma bazata nake so nayi musu bana so su san na biya musu sai za'a tafi. Allah yasa tafiyar ta zama daidai ma baza'a yi saurin siyan ticket ba sai ya bani lokaci sai a daidaita tafiyar." "Ai kawai ka fad'a musu tunda kaga  za'a je passport." "Za dai mu gani, kema har ke za'a yi bamu san me Allah zai kawo gobe ba." Tayi dariya tace, "Allah ya amince." Shima dariyar yayi suka cigaba da tattauna yadda abin zai kasance. A gidan su Yusuf Ammah na zaune tana kiran Mubarak baya d'auka a haka Ysuf ya shigo ta kalle shi bayan ta amsa sallama tace, "kai da baka da lafiya me fito da kai?." Ya zauna yace, "naji sauki ai, barka da yamma." "Barka dai, ya jikin?." "Da sauki." "Allah ya Kara Lafiya." Ya amsa da amin tace, "Kaga Mubarak?." Ya girgiza kai alamun A'a tace, "yazo ya mayar da Zaitun gida gobe taje makaranta." Yusuf yace, "tana ina?." Bata kalle shi ba tace, "tana ciki." Zaiyi magana sai gata ta fito da babbar wayar Ammah tana game ta kalle ta tace, "yarinya ta iya game kamar babba?." Ganin sa sai ta tawo a guje ta fad'a jikin sa Amma tace, "kina fasa min waya sai baban ki ya biya." Murmushi yayi ya rik'e ta tace, "Daddy ka kaini wajan Mummy." Ammah tace, "Yanzu Mubakar zai zo ya kai ki." Ta kalli Ammah kamar zatayi kuka tace, "ni Daddy zai Kai ni." Ammah ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa sai taji yace, "muje na kai ki." Da sauri Ammah ta kalle shi sai taga ya tashi tsaye itama haka ya rik'e hannun ta zasu fita. Batayi magana ba suka fito ya saka ta a mota suka tafi gidan Yaya Adam kirjin sa na bugawa sosai. Suna tafiya tana ta yi masa surutu ya had'a ta da waya tana game ya tsaya a wani shago ya siya mata kayan ciye- ciye suka nufi gidan Kai tsaye. Tunda ya doshi gidan gaban sa yake fad'uwa sosai amma kuma yana jin karfin guiwar zuwa shiyasa bai dakata ba har ya iso k'ofar gidan ya faka ya hango Yaya Adam din a tsaye shida Al'ameen ya fito daga motar Zaytun ma ta fito. Yaya Adam bai gasnu ba sai ji yayi an rik'e shi ta baya ya juya ya ga Zaitun yace, "A'a Zaitun an dawo." Dariya tayi sai ya kalli Yusuf da ya k'araso wajan kamar  munafuki sai yace, "Yusuf kaine da kanka? Sannu da zuwa." Jin abinda Yayan yace sai ya samu kwarfin guiwa ya gaishe shi ya amsa suka gaisa da Al'ameen yace, "ya jikin naka?." "Alhamdulillah naji sauki." "Allah ya k'ara Lafiya." Ya amsa da Amin Yaya Adam ya kalli Al'ameen yace, "Baban Zaytun ne fa." Kallon sama da k'asa Al'ameen yayi masa kafin yace, "ga kama nan na gani tun kafin kace." "Abba ina Mummy?." "Mummy bata nan amma yanzu zata dawo." Yusuf yana tsaye ya kasa magana ko kad'an zuciyar sa na wani irin bugu mai sauti ya rasa meya kawo hakan. Yusuf magana yake so yayi amma bakin sa yayi nauyi sosai Yaya Adam ya lura da hakan sai yace, "Akwai sak'on da Alhajin ya bayar ne?." Yusuf yace, "eh yace yana gaishe ka." "Ina amsawa, nima ka gaishe shi sosai. Zaytun jeki gıda gani nan zuwa." Maimakon tayi hanyar gida sai yaga ta nufi wani waje tana cewa, "Mummy!." Kallon wajan sukayi gabad'aya suka ga Ameena ta d'auke ta sai kuma ta sauke ta ta rike hannun ta suka nufo wajan. Zuciyar mutane biyu ce take bugawa a wannan lokacin, Al'ameen zuciyar da bugawa take cike da kishin Yusuf yana  wajan ga Ameena ta dawo baya qaunar Ameena taga Yusuf balle wani abun ya shiga ranta, shi kuma Yusuf zuciyar sa bugawa take saboda ganin ta da abinda yake ji a k'asan zuciyar sa wanda ya jima yana ji gangar jikin sa bata bashi had'in kai akan hakan amma a wannan lokacin yaji ya game jikin sa gabad'aya. Wajan tazo tayi murmushi tace, "Ina Wuni." Al'ameen yayi murmushi bai amsa mata ba sai tayi dariya kad'an zata shiga gida Zaytun tace, "Mummy ga Daddy." Sai da gaban ta ya fad'i itama ta jiyo ta kalle shi suka had'a ido kuwa sai ta d'auke kai kamar bata gane shi ba ta wuce zuwa gida ba tare da ta sake kallon inda yake ba. Kai ya dafe yayi baya kamar zai fad'i Yaya Adam yayi saurin rik'eshi yace, "Yusuf Lafiya?." Ya kalli Yaya Adam yace, "Kaina ne ya Sara." "Sannu, daman ai ba lafiya ce da kai ba ai, shiga motar ka zauna daman me ya Kai ka fitowa kai da Baka da lafiya." Yusuf yace, "babu komai." "Zaka iya tuk'a motar?." Yayi murmushi yace, "zan iya Yaya. Ga wannan na Zaitun ne." Yaya Adam  ya karb'a yace, "to an gode. Ka tafi gida saboda ciwon." Kai ya d'aga ya shiga motar ya jima kafin yaja motar ya tafi. Yana barin wajan Al'ameen ya kalle shi yace, "kai kace min in kana da rai Ameena baza ta komawa wannan ba." Adam ya kalle shi tare da hararar sa yace, "ai gashi nan ta koma yanzu." Al'ameen yace, "nidai Ina so a tsayar da magana gaskiya Adam indai Ameena zata iya zama dani ayi auren nan a huta, jikina bai amince da wannan mutumin ba."Yaya Adam yayi murmushi yace, "kar ka damu babu abinda zai faru, abinda ya saka na kyale shi har nake sauraren sa saboda y'ar sa kk babu komai mun had'a jini dashi tunda ta shiga tsakanin mu amma bayan wannan kar ka d'auka da wani abun." Al'ameen ya girgiza kai yace, "Nidai jikina bai amince ba dole nasan abinda zanyi gaskiya." Yaya Adam yayi dariya ya shiga gida ya bar Al'ameen a wajan. A falo ya smau Ameena tana shirin wucewa yace, "Ameena." Ta tsaya tana kallon sa yace, "karb'i wannan in ji Yusuf." Ta saka hannu ta karb'a yace, "da kin sani kun gaisa ko babu komai Zaytun ta had'a ku, amma in kina ganin hakan yafi miki daidai kar ki damu." Ameena tace, "bana cikin walwala ne wallahi." "Meya same ki?." "Kawar mu Fiddausi ta dawo daga wani waje labarin babu dadin ji shine ya saka baba Jin dad'i ko Zaytun din ma ban so ta dawo ba takura min zatayi." Yaya Adam yace, "ga kuma Al'ameen." Sai tayi murmushi bata ce komai ba yace, "in kin warware daga damuwar zamu yi magan dake." Da to ta amsa ta wuce ciki zuciyar ta cike da mamakin meyasa Yaya Adam ya bar Yusuf yazo k'ofar gidan har yake cewa da ta sani sun gaisa dashi? Kenan ya yafe masa ko kuma wani abun ne daban?. Da Zazzabi mai zafi Yusuf ya koma gida kai tsaye wajan Ammah ya wuce ya same ta a inda ya barta yana shiga ya zauna akan kujera baiyi magana ba tace, "har ka kai ta?." Kai ya d'aga kafin yace, "kaina ciwo yake min Ammah." "Sannu ka sha magani." "Ki kama min ki kama min kan dan Allah." Jin abinda yace sai ta taso ta dawo kusa dashi ta kama jijiyoyin kan nasa yadda suke harbawa zai tabbatar maka da ciwon da kan yake yi tace, "kan ka yana ciwo kam, Sannu." Addu'a ta dinga karantowa tana yi masa tana tofasa a kan nasa duk abinda yazo bakin ta yi take yi cikin ikon Allah taji harbawar ya ragu ta kalle shi taga ya lumshe ido tace, "Sannu. Jikin ka ma da zafi sosai kaje ka sha maganin ka." Ameena yake gani a Idon sa yadda ta juyo ta kalle shi da kallon sa da tayi suka had'a ido da yadda ta juya kamar bata ganshi ba shine yake sakawa bugawar kan nasa ta k'aru sosai. Ameena shine abinda zuciyar da take fad'a amma gangaar jikin sa bata bashi wannan had'in kan yadda ya kamata. Duk da an samu canji sosai amma ba irin canjin da yake so ba, so yake ya samu karifin guiwa sosai amma ina ya rasa wannan damar da ya motsa sai ya sare guiwar sa tayi sanyi qalau. Ammah tace, "ko Mubakar yazo ya mayar da kai gida?." Ya girgiza kai alamun A'a sai ta kyale shi a wajan ta kawo masa magani da ruwa yasha sannan ta bar wajan. Kwanciya yayi a kan kujerar kamar maraya yayi shiru abubuwan da suka faru a baya suka dinga fad'o masa a rai ya lumshe ido ya tashi zaune sosai yana kallon falon kamar mai son gano wani abun a ciki sai kuma ya mik'e ya fita. Book3 yana ja ina ja.😭😭 #Mai daki #Book3 #Paid #500 #Nana Haleema Book3 028         Kai tsaye gida ya koma bai ma kalli b'angaren Asiya ba na Ameena ya shiga yayi k'ura sosai amma haka yake jin dad'in zaman gidan, kitchen ya shiga babu sauran kayan amfanin a ciki ya fita ya hau sama har d'akin sa ya zauna a kan gado yana kallon gadon. Ameena yake gani a kwance a kan gadon tana yi masa murmushi shima sai yayi murmhsin yana kallon ta sai kuma ya tuna d'azu da ta kalle shi tayi kamar bata ganshi ba nan take yaji babu dad'i a zuciyar sa ya kwanta da baya. Bud'e k'ofar yaji anyi an shigo yasan wacece hakan ya saka bai kalli wajan ba tabi d'akin da kallo tace, "ban San me kake ji ba da kake mak'alewa a nan daki duk k'asa." K'arasowa tayi ta zauna kusa dashi tace, "wai ne nayi maka ne kake share ni? Dan na cire kud'i a kud'in ka laifi ne?." Baice komai ba ta sake kallon sa tace, "meye dan na cire kud'i a kud'in ka ai a ganina ba wani abun bane ba, shine kake wannan b'ata dan kamar na d'auki kudin wani ba mijina ba." Lallai ma yarinyar nan bata da hankali, tayi masa satar kud'i nasu yawa kamar wannan kuma tazo tana fad'a masa maganar banza? Dan taga ya kyale ya fita daga lamarin tane kenan shiyasa take masa wannan maganar bata san haushin ta yake ji ba. "My love, ka dawo nutsuwar ka kawai bana son wannan rashin maganar taka. Kuma gaskiya abin nan ya ishe ni ace tunda nazo gidan nan anyi Ramadan anyi babar sallah ban koma makka ba, Haba k'amawaye na duk sunje umarar azumi amma ni an barni a nan a zaune. Gaskiya na gaji ya kamata a kaini a kai Umma na itama."  Jin shirin yayi yasa sai ta d'auka bacci yake ta kalle shi taga idanun sa biyu tace, "nifa bana son wulakanci ina yi maka magana kayi min banza kamar baka ji me nace ba." Tashi tsaye yayi ya kalle tayace, "tashi tsaye." Ta tashi yace, "fita" ya fad'a yana nuna mata k'ofa ta kalle shi tace, "bazan fita ba, d'akin mijina ne babu inda zanje.  Dan wulakanci ina yi maka magana kayi minbanza kuma ka tashi kace na fita?, bazan fita din ba." "Asiya ki fita." "Bazan fita ba, nafa gaji da wannan wulakancin naka da kake min, duk abinda nayi maka ai bai kai abinda kayi min ba, har kashe min dan cikina kayi amma ban d'auki mataki ba sai kai mai bakin magana zaka dinga yi min wulakanci akan kud'i? Ka share ni balle na samu wani cikin a ganin ka din wannan ba laifi bane?." Ya runtse ido wallahi ko maganar ta baya son ji ya kalle ta yace, "Nace ki fita!." "Bazan fita, bazan fita ba nace, kayi abinda zakayi kuma hannun ka yazo jikina wallahi sai na fasa maka kai da duk abinda yazo hannuna." Damkar hannun ta yayi ya jawo ta ta k'arfi ya cilla ta waje bai tsaya yaga wani abun ya mayar da k'ofar ya kulle ya zube a wajan ya zauna ya tank'washe k'afa a jikin k'ofar kawai ya fara hawaye. Bai San abinda yake damun zuciyar  sa ba amma yasan yayi rashi na wani babban abu da yake sanya zuciyar sa farin ciki a ko yaushe, hawaye yake amma bai san dalilin zuwan su ba abinda ya sani zuciyar sa tana dana sanin auren Asiya yana kuma neman hanyar da zai raba kansa da ita amma bai san inda zai nemo hanyar ba. A wajan yayi bacci tun yana Jin kukan Asiya har ya daina ji.       Wayar sace ta tashe shi daga baccin da yayi a wajan  ya mik'e zaune kayan sa duk sun b'aci da k'ura ga wuyan sa ya rik'e sosai ya tashi tsaye ya k'arasa wajan wayar yana kallon fuskar wayar ganin sunan Abbah, d'auka yayi ya saka a kunne daga can b'angaren Abbah yace, "Yusuf kazo gida Yanzun nan." "Abba bazan iya zuwa ba bana jin dad'i" ya fad'a a sanyaye kamar zai yi kuka. "Shikenan zan turo Mubakar ya tawo da kai." Ya amsa da to ya kashe wayar ya shiga band'aki ganin har anyi magriba da isha yana bacci. Sallah ya fito yayi akan sallaya bayan ya idar ya zauna a yana addu'a yana hawayen da ya zamar masa jiki a yanzu, haka kawai yana zaune sai yaji yana kuka har ya saba hawayen a yanzu dan baya iya rike shi ko kad'an, komai yazo bakin sa rok'on Allah yake yi dan zuciyar sa tayi masa nauyi gab take da tarwatsewa. Yana shafa addu'ar kiran Mubakar na zuwa bai d'auka ba ya d'auko wayar ya fito ya sakko ya same shi a mota a zaune ya shiga suka tafi. A motar Mubarak ya kalle shi yace, "duk ka rame Allah ya yaye maka wahala." Yusuf yace, "kiran na meye?." "Matar kace da babar ya suka je, mtswww Allah ya raba mu da auren masa tarbiyya wallahi. Kaima ka samu ka saukewa kanka wannan wahalar da take d'awainiya da kai." Yusuf ya kalle shi ya samu kansa da cewa, "Amin Mubarak." Kallon sa yayi kamar zaice wani abun sai ya fasa suka shiga cikin gidan nasu. Tun daga bakin falon yake jiyo muryar babar ta dan daman bata magana a hankali ko cikin lallami take magana sai ka d'auka fad'a take saboda ihu da harare-harare, ya shiga jiki a sanyaye ya zauna yace, "Abbah gani." Abbah yace, "Yusuf meyasa kake son jawo min magana ne a ko da yaushe?, meyasa kake son dukan matar ka ne? Yanzu meye amfanin kayi mata dukan da har hannun ta zai karye?." Ya kalli Abbah ya kalli Asiya da take zaune da maqalallanhannu ya kalli Babar ta da take aiko masa da harara yace, "Waye yace na dake ta?." Umma tace, "k'arya zatayi maka? Ba silar dukan ne ya saka ka kashe abinda yake cikin ta ba?." Ya kalli Umma yace, "ni ban dake ta ba itama ta sani. Ta shirya k'aryar da ta saba shiryawa ne." "Wallahi karya kake ka dake ni, dan kawai nazo inda kake ka dinga dukana har ka karya min hannu" Asiya ta fad'a tana kukan gaske dan hannun ta da gaske a karye yake. Yusuf jin tana cewa k'arya ka ke a gaban iyayen sa da kowa nasa sai jikin sa ya sake yin sanyi bakin sa ya d'aure ya d'ago ya kalle ta yace, "inda ni na dake ki da yanzu bakin da zaki yi maganar ma na fasa shi wallahi, ba iya hannu zan karya miki ba dukka k'asusuwan jikin ki zan karya."  Umma tace, "Iyeee! Kuna jin abinda yake cewa ko? Wato Yusuf naga alama tashen rashin kunya kake ji da ita, to kasan da wacce kake magana dan wallahi ba'a tab'a ni ko yarana a zauna lafiya." Yusuf ya d'ago kai kamar zai mata magana sai ya fasa kawai ya kalli wani wajan daban dan har babar ta ta yake jin haushi in ya sake kallon ta zai iya fad'a mata magana itama, kuma baya son hakan saboda iyayen sa amma gabad'aya ya tsane su. Umma tace, "to bazai yu ba shiyasa daga wajan mai d'ori nan muka yo, bazan amince ka mayar da ita kamar jaka ba wallahi bazai yu ba, yau duka gobe duka jibi duka akan me!? Dan rashin mutunci kuma kace wai da sai ka b'alla mata k'ashin jikin ta a gabana a gaban iyayen ka, wannan shine karo hud'u da ka dake ta ko wanne da illar da kayi mata. Yusuf in ka gaji da zama da Asiya ka rabu da ita mana ai babu lallai babu dole, ka dinga wahalar da yarinya dan kaga tana yi maka biyayya? In zaka yiwa kowa ka zauna lafiya banda ni wallahi, bazan iya jurewa ba domin y'ay'ana nawa ne ni kad'ai, in baza ka daina shan giya ka daina dukan y'ata ba ka sake ta." Wani iri yaji a jikin sa jin kalmar ka sake ta din da tace ya d'ago ya kalle ta sai ta d'auka hak'uri zai bata jin tace yayi saki sai tace, "Eh ka sake ta, ai zama da ita babu dole dan wallahi banza d'auki wannan wulakancin ba, aure ko shekara baiyi ba har yanzu ace an fara jeka gida ka dawo, ka sake ta in baza ka iya ba." _Ka sake ta._ shine abinda yake ji a zuciyar sa kawai da kuma kan harshen sa ya d'ago ya kalli Umman ya kalli Asiya da take aika masa da harara ya sake kallon Umman yace, "na sake ta!." Kamar an fizgo maganar daga bakin sa haka yaji sai ya fara kalle-kalle ko zai ga wanda ya furta maganar amma ya tabbatar shine ganin reaction din Umman ya canja ya koma na mamaki da tashin hankali ya saka shi jin dad'i a zuciyar sa dan ya tabbatar ba a mafarki hakan ta faru ba da gaske. Wannan kalma da ya furta ba k'aramin dad'i ta yiwa Abbah da Ammah ba suka kalli juna kowa zuciyar sa tayi farin ciki d abinda yayi dan Allah ya sani basa son zaman da yake yi da ita kawai dan basa son shiga lamarin sa da ita ne ya saka suka zuba masa ido. Asiya ta wara idanu waje ta kalli Umma cikin tsoro itama ita take kallo shima Yusuf din Umman yake kallo tace, "me kace?." Yusuf ya sake kallon Umman yace, "eh na sake ta, kince in bazan iya zama da ita ba na sake ta, to bazan iya zaman da ita ba shiyasa nace na sake ta!." "Kana cikin hankalin ka kuwa? Asiyan ka saka?." Sake kallon mutanen falon yayi ya tabbatar a gaske ne ba a mafarki ya sake ta ba ya sake kallon ta yace, "da hankalina mana, na sake ta ki d'auke ta ku tafi taje ta samu wanda zai iya zama da ita ni bazan iya ba" sai kawai ya tashi ya shiga cikin gidan ya barsu a wajan. Asiya tace, "na shiga uku Umma kina Jin abinda yace fa? Innalillahi Umma bana so ya sake ni ina son mijina nidaj." Hararar ta Umma tayi sai ga kalli Su Ammah da suke kallon su ta mik'e tace, "lallai Yusuf a gaban idona dan tsabar wulakanci ya saki Asiya bayan yasan ni mahaifiyar tace, babu laifi ya kyauta zai kuma san  dani yake zancen" ta fad'a tana yin hanyar waje Asiya ta kalli Ammah tace, "Ammah ki bashi hak'uri dan Allah ya mayar dani ." Ita dai kallon ta take yi kafin ta tashi tabi bayan mahaifiyarta tana kuka dan har ga Allah ita tana son zama da mijin ta. Suna fita Mubarak yace, "wallahi Yusuf bai tab'a burge ni kamar yau ba, naji dad'i da ya rabu da wannan shegiyar yarinyar mai zubin aljanu, Marasa tarbiyya daga ita har babar ta, k'ananu mutane b'arayi wanda basu san abinda suke yi ba." Ammah ta kalle shi tace, "kira min Yusuf." Ya shiga ya samu Yusuf din a zaune a kan gadon Ammah ya dafe kai da hannu biyu ya kira shi suka dawo tare ya zauna kana kallon sa kasan bashi da lafiya Abbah yace, "Yusuf ka saki matar ka Asiya fa, meyasa kayi hakan a gaban babar ta?." Yusuf ya runtse ido sosai yake jin sassauci Akan abinda yake ji yace, "na jima ina son yin hakan amma na kasa, jira nake kawai wani ya bani umarni na aikata sai gashi ta bani umarni da kanta" ya dafe kansa yace, "na gaji da zama da ita wallahi, na gaji daman kawai so nake yi na aiwatar na kasa sai yanzu. HasbunallaAmmah kaina" ya fad'a yana dafe kansa da duka hannayen sa biyu Ammah ta kalli Mubakar tace, "d'auko min maganin nan nasa  da sauri." Da sauri ya d'auko a jarka baban ya mik'o mata ta karb'a ta tashi da kanta ta bashi sai da ta tabbatar yasha sosai sannan ta kalli Abbah tace, "Mu kai shi asibiti." Abbah yace, "bana asibitin bane sihirin da suka yi masa ne yake barin jikin sa." Mubakar yayi tsaki yace, "haka akwai ya d'aukowa kansa wahala yana zaune Lafiya da matar sa, Gashi ta shigo ta raba su ta dinga yi masa iskanci kala-kala ga k'arshen abun harda asiri." "Zo nan mu kama shi a kai shi d'akin Humaira." Abbah da Mubarak ne suka kama shi zuwa d'akin Humaira aka kwantar dashi Abbah ya kalli Mubarak yace, "ka kira a duba shi in akwai wani abun a bashi magani." Mubarak da Abbah fita sukayi Ammah ta zauna a gefen sa tana kallon sa cikin matuk'ar tausayin sa.           Hankali tashe Umma da Asiya suka shiga gida Asiya ta tsaya a tsakar gida tace, "nifa Umma bazan kwana a gidan nan ba gidan mijina zan koma, haka kawai kina furta masa ya sake ni gashi yace ya sake ni, meyasa kice masa haka? Kina ganin kamar umarni kika bashi kina cewa ya furta babu b'ata lokaci. Umma in saki ne na shiga uku." Jin haka ya saka su Maimuna fitowa daga d'akin suka kalli Umma suka ce, "me yake faruwa ne haka naji Ana zancen saki?." "Ba umma bace ta jawo Yusuf yace ya sake ni, wallahi bazan iya zama a gidan nan ba gıdana zan koma." Maimuna tace, "garin ya ya sake ki? Ba anyi masa abinda bazai iya sakin ki ba? Ya kayi hakan ta faru ga Mari ga tsinka jaka?." "Duk Umma ce ta jawo, tun farko daga wajan mai gyara sai da nace kar mu biya gidan su amma tace sai munje taja masa kunne a gaban iyayen sa, haka ta dinga fad'a masa in ka gaji da ita ka sake ta shi kuma yace na sake ta. Ni wallahi bazan zauna a gidan nan ba gidana na zan koma bazan iya zama cikin zafi da sauro ba wallahi." Fauzy tace, "gaskiya Umma da kin sani baki furta ba da kin sani bama aje gidan ba, yanzu ya sake ta ta dawo gida kayan d'akin aurena dame za'a yi kenan?." Momi tace, "dan yace ya sake ta ai ba saki uku yayi ba, ku kwantar da hankalin ku ni nasan Umma da Umma Sakina sai sun mayar da Asiya gidan ta." Sai a sannan Umma ta samu k'arfin guiwa jin kalaman Momi tace, "Allah yayi miki albarka, ke kad'ai ce kika fahimci wacece ni dan ya aikata wannan abun ba komai bane ba. Ki shiga ka kwanta gobe zaki koma gidan ki, Maimuna bani dubu biyu in akwai a jakar ki." Maimuna ta shiga ciki ta d'auko Umma tace, "zan je na dawo, gobe Yusuf zai mayar dake koda baya so nayi miki wannan alqawarin." Asiya ta goge idanun ta gabad'aya ta daina jin zafin da hannun ta yake mata tashin hankalin ta kar ace Yusuf ya rabu da ita dan bata san inda zata saka ranta ba. Umma Kai tsaye gidan Umma Sakina ta wuce ta same ta ita da yaran ta suna cin abinci ganin ta duk suka tashi bayan sun gaishe ta Umma Sakina tace, "da ganin ki ba Lafiya." "Ina fa Lafiya, yaron nan Yusuf ne ya daki Asiya har ta karye a hannun ta daga kwana mai gyara muka wuce gidan su dan na ja masa kunne gaban iyayen sa." Kafin taje k'arshen maganar Umma Sakina tace, "Allah yasa ba cewa kika yi ya sake ta ba?." Umma tace, "haka nace masa ya kuwa ce na sake ta." Umma Sakina ta daki cinya tace, "shikenan kin tarwatsa mana komai kin lalata shi saboda bak'in son y'ay'an ki bazai ki iya hak'uri ba har sai da kika je gidan su. Yanzu gashi nan kin b'arar mana da damar da muke da ita." Umma tace, "ai ni da gadara nace yayi sakin dan nasan bazai iya ba, kuma kallon da yayi min da nace yayi na d'auka na tuba da nan hak'uri ban d'auka zaiyi din ba ai da bazan ce ba." "Kiris yake jira haka malam yace min jiya da naje akan maganar d'auke masa kudi da tayi a banki a hana shi d'aukar mataki a kai yake cemin kiris yake jira ya sake ta ta gama fita daga zuciyar sa, ina k'ok'arin sake cusa ta ki je kin lalata mana komai. Itama shegiyar satar ta kamar b'era da shegiyar k'zantar tace ta kawo ta wannan matakin ai." Umma ta dafe kai tace, "Na shiga uku ni Atika, yanzu meye mafita a san abinda za'ayi in ta bar gidan Yusuf yanzu ai mun lalace." "Yayi tafiya zuwa Abuja a jiyan, kuma aikin sa na amince dashi gashi baya nan, ban san ya za'ayi ba." "A dan yadda za'ayi zuwa gobe ya mayar da Asiya in ba haka ba baban su ma dariya zaiyi min ba mutanen gari ba." "Duk laifin ki ne wallahi, bakya iya sarrafa soyayyar yaran ki a zuciyar ki ke lallai komai akayi a kan su  sai kin mayar kamar kece kawai mahaifiya a duniya, yanzu zuwa gidan nasu ma da kike yi ai ba siyawa kai mutunci bane, shiyasa dangin sa kaf babu mai son Asiya." Umma tace, "Nidai a san abinda za'ayi yanzu dan Allah." Umma Sakina tace, "kaina ya kulle bani da abin yi a yanzun nan, sai dai zuwa da safe na d'auki hanyar gurin malam wajan wannan tsohon malamin da yayi mana aikin had'a auren Asiya din sai muji ya za'ayi." Umma tace, "Dan Allah Sakina, in auren nan ya mutu..." kafin Umma ta karasa tace, "mu muka mutu wallahi, Muna ji Muna gani kudin nan da muke samu zamu daina." Umma tace, "hakan ma bazai faru ba in sha Alalh akwai mafitar da zamu samo." Umma sakına tace, "Amma in komai ya daidata babu ke babu sake zuwa gidan su Yusuf gaskiya ki daina zubar mana da mutunci. Su kansu iyayen Yusuf din suna nan suna yi miki kallo wani iri saboda haka kawai sai ki d'auki k'afa kije kice anyi wannan anyi wancan." "A dai gyara auren komai zai yi daidai in sha Allah." Umma Sakina fa tab'e baki Umma ta tashi tace, "zan koma dare yayi sai naji magana mai dadi." Sallama sukayi Umma ta fita zuciyar ta cike da fatan samun nasarar mayar da Asiya gidan Yusuf. Umma na shiga gida suka had'u da Baba ya kalle ta yayi murmushi yace, "kin d'auka auren da aka gina  shi ba akan gaskiya ba zaiyi k'arko ne? Kin d'auka zaki ta samun nasara ne a duk abinda kika saka a gaba babu fad'uwa a ciki?. Meyasa baki shiryawa wannan ranar ba kika d'ora y'ar ki akan turba mara kyau? Meyasa baki shiryawa wannan ranar ba kike karb'ar duk abinda ta sato dga wajan mijin ta ta kawo miki?. Atika ai yanzu kika fara gani wallahi ko Fauziyya kika aure itama haka zata dawo miki gidan haka Momi indai baki d'ora su akan gaskiya ba a haka zaku k'are gabad'aya ku. Wani lokacin kece kike sakawa ta d'auko ta kawo miki, baki tab'a cewa ki daina ba kullum zuga ta kike kina cewa in ya deke ta ta rama, a hakan kike so kuma a zauna da ita har abada?." Umma ta zo suya saboda haushi tace, "A kanka, wallahi akan tsiya zata k'are ba dai a kaina ba. Kuma duk bak'in cikin ka sai Asiya ta koma gidan Yusuf sai naga wanda zai haka faruwar hakan." "Ni kuma nace miki bazata koma ba, yadda ta dawo yanzu bazai sake mayar da ita ba dan duk Wanda ya rabu da k'aya baya so ta sake sokar sa." "İn yazo mayar da ita din ka hana, ban tab'a ganin uba mai bak'in ciki ba sai kai, kuma wallahi sai ta koma dani da kai mu zuba mu gani." Ya girgiza kai kawai ya fita dan yaji dad'in sakin da aka yiwa Asiya sosai har zuciyar sa ko babu komai zasu sake yin hankali in rabo. Umma na shiga wajan su Asiya ta kalle ta tace, "Umma ya akayi?." "Za'a San abinda za'ayi kar ki damu." "Umma ina son mijina bana son rabuwa dashi. Kuma wallahi bai dake ni ba fad'uwa nayi akan hannuna shine ya karfe, dan Allah a mayar dani ina son mijina." "Dan uban ki nace miki za'a san abinda za'ayi meyasa kike son sake b'ata min rai bayan wanda uban ki yayi yanzu? Mtswww" ta fad'a tana fita Asiya ta bita da kallo babban tashin hankalin ta bai wuce ace mijin ta yak'i mayar da ita ba dan gani take zata iya hauka baza ta iya zaman gidan su ba gabad'aya, ta saba da zama a.c bazata iya aiki da mafici ba. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid #500 Book3 029 Kwana biyu kenan da sakin Asiya babu wanda ya yiwa Yusuf magana tana gida su har kwana a gida yake yi, babu Wanda yake masa maganar ta shima har lokacin baiyi maganar ta ba dan bama ya so ya tuna ya zauna da ita matsayin mata. A safiyar ranar talata yana zaune yana shan tea a falon Ammah har lokacin yana nan a firgice bai dawo daidai ba Abbah ya fito ya kalle shi yace, "Yusuf zaman gidan da kake bashi da amfani ka koma wajan sa'anar ka in ba haka ba zaka ga ba daidai ba." Yusuf ya kalli Abbah yace, "Abbah Usman yana yin komai kamar Ina wajan." "Yaushe zaka je ka dawo da matar ka ne? Kayi shiru da maganar bayan nasan sakin na gargad'i kayi mata." Yusuf ya d'an rufe ido ya bud'e ya kalli Abbah yace, "bazata dawo ba." "Meyasa? Kaje gidan nasu zaka dawo da ita din ne Kaga bata ta dawo ba?." "Bazan je ba Abbah." Abbah ya kalli Ammah dukkan su haka suke so su ji amma basa nuna masa baso ya dawo da ita Abbah ya sake cewa, "ai kuwa dole kaje matar kace fa. Kuma nasan saki d'aya kayı mata meyasa baza kaje ka dawo da ita ba?." Kallon Abbah yayi yace, "na yanke igiyar aurena da ita gabad'aya, bana son zancen ta dan Allah Abbah" yana fad'a ya tashi ya fita. Ammah tayi dariya tace, "Alhamdulillah, kai naji dad'i sosai Allah ya karb'i kuka na Yusuf ya dawo hayyacin sa." Abbah yayi murmushi yace, "babban tashin hankalina bai wuce yace zai dawo da yarinyar nan ba, dan wata rana wallahi sai ta siyar da gidan da suke ciki ko ta jawo masa bala'kn da bazai fitar da kansa ba." "Tashin hankali d'aya ma kenan Alhaji, wallahi da yace zai dawo da yarinyar nan ni ban San ma halin da zan shiga ba. Yarinya ba tarbiyya, ga sata meye amfanin zama da ita?." "Babu kam, yanzu ya dawo hankalin sa ya cigaba da harkokin sa ta inda Allah ya taimaka ma ya daina shan wannan abar tun daga lokacin da ta fad'a a wajan nan, kinga a wannan b'angaren taimakon sa ma tayi ta silar fad'ar da tayi gashi ya daina. Itama Ameena da ta fad'a tun lokacin zai iya dainawa." Ammah tayi murmushi tace, "Ameena mata ta gari kenan, yayi asarar matar da bazai mayar da ita ba har abada." Abbah yace, "a yanayin yaron nan tsaf zai iya cewa zai dawo da Ameena fa." Ammah tayi murmushi tace, "ga hanya nan ai, Yayan ta daidai dashi ne babu wanda zai hana shi yaje ga hanya nan." Abbah yayi dariya yace, "Ni kaina Adam kwarjini yake min balle Yusuf." "Gani nake bazai ma fara ba, yadda ya rabu da Asiya ya rabu da Ameena sai ya sake binciko wata kuma in baiyi sa'a ba  ya d'auko y'ar damfara." Abbah yayi dariya itama Ammah dariya take dan farin cikin ya rabu da Asiya ya cika musu zuciya sosai. Yusuf yana fita mota ya hau kai tsaye gidan Usman ya wuce yana tafiya yana tunani zuciyar sa tayi masa nauyi sosai ya rasa abinda yake masa dad'i kuka ma yake so yayi dan abinda yake ji bana wasa bane ba yana daurewa ne kawai amma zuciyar sa kamar an d'ora masa dutse. Har cikin gidan Usman ya shiga da motar ya ajjiye motar ya shiga gidan ya samu Umssn din a zaune yana jiran sa kamar yadda yace masa. Yana ganin sa yace, "na shirya zan fita Allah yasa dai Lafiya." Yusuf ya zauna ya kalle shi yace, "Usman ban san ya zanyi da raina ba wallahi." "Rabuwa da Asiyan shine baka san ya zaka yi ba?." Yusuf yace, "na rufe shafin rayuwar ta a tare dani, ku daina min wannan zancen dan Allah." Usman ya tab'e baki yace, "to an daina, Meya faru?." Yusuf yace, "nayi nadamar abinda na aikata a baya Usman, nayi dana sanin abinda na yi wallahi." Usman yace, "me aikata da kayi dana sani?." Ya runtse idanun sa ya bud'e ya kalli Usman shima kallon sa yake da mamaki yace, "Yusuf hawaye fa kake yi." Bai daina ba sai ma fin na baya yawa da suka yi, sauka suke shar-shar yace, "na rasa da wa zanyi magana Usman, kai kad'ai zan iya fad'awa abinda yake zuciyata. Usman ina so nayi magana da Ameena dan Alalh ka taimaka min." Usman ya bishi da kallon mamaki yana yi masa kallon sama da k'asa  yace, "kana so kayi magana da Ameena fa kace? To meye had'in ka da ita da zakayi magana da ita?. Ko dai Asiya kake so kace min kace Ameena?." "Ameena nake nufi, bani da karfin guiwar tunkarar kowa na gidan mu da maganar ta, na sare domin nasan baza su bani had'in kai ba. Kai kad'an ne last hope d'ina dan Allah ka amince ka taimaka min. Wallahi in banyi magana da ita ba ban san halin da zan shiga ba." Usman yace, "da yake ni ka raina ko dole kace haka ai. Tun lokacin da abin ya faru baka so had'uwa da ita kayi maganar ba sai yanzu da ka rabu da y'ar gwal?." "Wallahi tun lokacin baya ina son aikata hakan ban san me yake hana ni ba, sai a cikin kwanakin nan na samu damar furta abinda yake bakina. Dan Allah ka taimaka min nayi magana da ita." "To kace mata me?." "Na bata hak'uri." "Sai yanzu zaka bata hak'urin? Tun lokacin baya baka yi tunanin bata hakuri ba sai yanzu da duniya ta tafi da kai Yusuf?. Ai kayi asara wallahi wacce baza ka mayar da ita ba har abada, kaje ka dawo da yar gwal din mana ka kyale Ameena tunda baka sonta ga wacce kake so?." "Ban tab'a daina son Ameena, ban tab'a jin son Ameena ya fita daga zuciyata ba, wallahil azim ko da muna tare ina son Ameena son da ban yiwa Asiya shi ba" Yusuf ya fad'a yana kallon Usman da yake kallon sa shima yace, "karya ne wallahi, ban yarda ba, babu macen da ake  so ake qauna za'a yi mata abinda ka yiwa Ameena. Ka daina son Ameena a lokacin ka hango Asiya ka dinga mata wulakancin da ko kai akayi baza ka kawo akwai soyayya a zuciyar wanda ya aikata maka ba wallahi." "Wallahil Azim a rana d'aya ban tab'a jin son Ameena ya ragu daga zuciyata ba, nasan nayi kuskure wani abun ina sane wani abun bana sane, wani abun halina ne ba asiri bane ni na sani. Bana bincike akan duk abinda Asiya zata fad'a min kawai ina hawa kai na zauna ne nayi hukunci kawai ba tare da na bincika na gano gaskiya ba. Wannan shine kuskurena Usman, nasan na tafka kuskuren da gyara shi zai min wahala amma dan Allah ka taya ni gyara wannan kuskuren na samu Ameena tace na yafe maka komai dan Allah." Usman yace, "wannan fa duk ihuu kake bayan hari, tun da ya kamata kayi wannan maganar ai ba yanzu ba Yusuf. Ko zuwa wajan Ameena ma kayi zata ga kama raina mata hankali sai yanzu zaka zo bata hak'uri." "Bazan iya ba a wancan lokacin, ma fad'a maka ina so zuciyata tana so amma gangar jikina sai ta gaza aikata hakan Usman. Ban San me ya shiga kaina ba gangar jikina ita take sarrafa zuciyata, Allah ne kad'ai yasan abinda yake zuciyata shine shaida ta badan babu mai yarda dani" ya fad'a yana kuka sosai Wanda ya bawa Usman mamaki ya zuba amsa ido kawai yana kallon sa ganin kuka yake kamar wanda ya rasa uwa da uba a lokaci d'aya. "Ka taimaka min Usman naje na bawa Ameena hakuri dan Allah." Ya girgiza kai yace, "Gaskiya bazan je ba, abubuwan da kayi mata bazan iya had'a ido da Ameena nace tayi hakuri akan abinda kayi mata ba gaskiya kayi hak'uri." "Usman yanzu baza ka iya taimaka min ba?." Usman tausayin da yake ji a zuciyar sa amma baya son nuna masa hakan sai yace, "Bawai bazan iya bane ba Yusuf in na tuna abubuwan da suka faru ne a baya, yarinyar nan har hawan jini ta samu saboda damuwar ka taya kake so na tunkare ta nace tayi hak'uri?." Kuka Yusuf yake yi sosai Usman duk yayi sanyi ganin namiji kamar Yusuf na kuka abin sam babu dadi gani ko kad'an, ya tashi ya dawo kusa dashi yace, "Ka daina wannan kukan mana Yusuf matata tana gidan nan fa in ta fito taji kana wannan kukan ai babu dadi." "Ko waye zai gani ban damu ba, burina ka amince min muje mu samu Ameena na bata hak'uri. Na San nayi kuskure babba ya kamata ka fahimce ni ina so na gyara wannan kuskuren da nayi." "Hak'uri zaka bata ko kuma bikon auren ta zaka je?." Yusuf yaja numfashi sosai hawaye suka dake sakko masa yace, "hakurin shi nake da karfin guiwa a kai, bazan iya zuwa bikon ta ba Usman, bazan iya ba." Kukan da yake yi yafi damun Usman ya kalle shi yace, "naji zamu je a same  ta amma ka bari ka sake nutsuwa sosai zata fi sauraren mu in ta ganka a nutsu wallahi yanzu sai ta d'auka ki ka samu matsalar kwakwalwa ne ya saka ka koma haka." "Ta kira ni mahaukaci ma ban damu ba." "Kai kace mata darajar Amma take ci kake zaune da ita, meyasa yanzu kace min kana sonta kuma?." Shiru yayi kawai bace komai ba yasan daman kafin a fahimce shi zai sha wahala sosai ma kuwa. Ya tashi ya goge idanun da yace, "in zaka taimaka min anjima nake so muje." Usman yace, "shikenan to kayi min waya." Yusuf ya fita Usman ya bishi da kallo a bayyanr yace, "nadama Mara amfani kake yi Yusuf, ni nasan Ameena baza ta sake sauraren ka ba, kayi wasa da damar ka domin a yanzu tayi maka nisa."        Bangaren Fiddausi ta d'an fara farfadowa babu laifi kullum cikin tunanin da ya zamar mata kamar aboki ko yaushe suna tare ko kuma tana kuka. Tana zaune a tsakar gida tana wanke kwanuka Abba ya shigo ta juyo ta kalle shi tace, "Barka da dawowa Abba." Ya kalle ta sai ta bashi tausayi sosai dan sharrin zuciya ne kuma ba kowa ne zai iya sarrafa zuciyar sa ba musamman in kana kallon kowa naka yana auren mai kudi kai kana gidan talaka sai mai imani sosai. "Barka dai Fiddausi, ke kike wanke kayan?." Jin abinda Abba yace sai tayi murmushin jin dad'i tace, "eh Abba." "To sannu, Allah yayi albarka. İn kin gama kizo " ya fad'a yana shiga d'akin sa. Farin ciki kamar me haka Fiddausi taji tayi dariya sosai cikin karsashi ta gama aikin ta tashi ta shiga d'akin Abban ta same shi da Mama a zaune. Zama tayi ya kalle ta sosai yace, "ya labarin mijin naki?." Tayi shiru kanta yana k'asa yace, "ba ina takura ki akan maganar bane Fiddausi, har yanzu mijin kine akwai auren sa a kanki dole mu neme shi muji ya sake ki ne ko yaya." "Wallahi Abba ban San inda zan same shi ba." Abba yace, "to haka zaki zauna da aure a kanki? Ke ba bazawara ba ke ba mai aure ba Fiddausi?." Shiru tayi bata amsa ba idanun t suka ciko da hawaye yace, "wannan kukan da kike ba shine mafita a alamarin ki ba" ya kalli Mama yace, "bakya yi mata fad'a ne?." Mama tace, "ina yi mata wallahi, amma kuka da tunani ya zamar mata abokan hira a yanzu." Abba ya kalle ta yace, "meye amfanin tunanin da kike yi Fiddausi? Kina ganin tunanin shine maganin damuwar ki ne?." Tayi shiru bata amsa ba yace, "damuwa da tunani ba shine maganin hankalin da kike ciki ba, ki tashi cikin dare ki yi sallah ko fad'awa Allah damuwar ki yafi ki zauna kina wannan koke-koken na banza da wofi. Zaman kukan da salati kike da yanzu wani abun ya fara warware miki." Fiddausi tace, "ka yafe min Abba, nayi maka laifin da kayi fushi dani, nayi nadamar abinda na aikata ka yafe min kar fushin ka ya sake jefa ni a wata masifar." Abba yace, "na yafe miki Fiddausi dmaan ni ba laifi kika yi min ba kawai ina jin haushin abinda kika aikata, amma yanzu tunda kin gane kuskuren ki shikenan Allah ya yafe mana baki d'aya." Mama tace, "amin ya Allah." Abba yace, "Ya kamata ki dinga bibiyar lamarin mijin ki tunda da dai bai sake ki ba akwai auren sa a kanki har yanzu." Zatayi magana akayi sallama daga waje Mama ta amsa tana tashi ta fita Jin muryar mace,daga k'ofar d'akin Mama tace, "A'a Rukayya, shigo mana." Shiga Rukayya tayi ta k'arasa ta durkusa har 'kasa ta gaishe da Abba ta gaida Mama suka amsa da sakin Fuska Abba yace, "ya wajan mijin naki?." "Alhamdulillah." "In kin koma kice ina gaishe shi da kyau." Tace, "in sha Allah." Mama tace, "Fiddausi tashi ku shiga ciki zata gashi da tsugunon." Fiddausi ta tashi suka fita ita da Rukky  zuwa d'aki. Rukayya ta zauna tana kallon ta tace, "Fiddausi har yanzu baki canja ba, ni sai naga kamar kin sake ramewa wallahi." Fiddausi tace, "to Rukayya ina jin dad'i a wajena balle nayi kiba? Wallahi kullum da tunani nake kwanciya nake tashi, bani da wani sukuni gabana yayi ta fad'uwa." Rukayya tace, "to wannan ai ba mafita bace addu'a zaki dinga yi ki kawar da komai daga zuciyar ki, wannan tunanin da kike ba komai bane face ciwo da zai saka miki." Fiddausi ta kalle ta tace, "in nace miki zan cire damuwa wallahi karya nake Ruky, ayi shiru dai kawai amma ni da jin dad'i ba yanzu ba, watakila sai na mutu ma. Koda yake ma ina jin dad'i a wajan wacce tayi..." da sauri ta dakatar da ita tace, "India zaki dinga irin wannan maganar Allah zai daina zuwa wajan ki, wannan wacce irin magana ce? Kin fitar da rai daga rahamar Allah ne?, kuma shi laifin da kike magana ai Allah ya gani yasan ba da son ranki bane tilasta ki akayi Allah kuma bazai kama ki da laifin kin aikata ba. Dan Allah Fiddausi ki dawo hankalin ki ki mayar da hankalin ki ga rokon Allah komai zai wuce wallahi." Fiddausi tayi murmushi tace, "ina son neman yafiyar mijin ki amma ban san da wanne ido zan kalle shi ba." Rukayya ta kalle ta suka had'a ido ta sauke numfashi tace, "da idanun da kika saba kallon sa ko yaushe Fiddausi, na tabbata da zai yafe miki." "Kunyar had'a ido nake dashi." "İn kana neman abu daurewa ake a manta da abinda ya wuce." Tayi Ajiyar zuciya tace, "zan k'ok'arta nazo gidan ki taimaka min na bada hak'urin, nayi abubuwa da yawa wanda yafe min sai mai zuciyar imani, amma zan iya cin albarkacin ki ya yafe min." Rukayya tayi murmushi tace, "ko badan ni ba zai yafe miki Fiddausi, badan kar nayi saurin cewa ya yafe miki ba da nace ya jima da yafewa. Amma gwara kiji daga bakin sa zaki fi samun kwanciyar hankali." Fidy tace, "yaushe zaki kawo min Amir? Ina kewar sa sosai a taimaka min ko kwana biyu yazo yayi." Rukayya ta dafa ta tace, "Amir d'an ki ne fa Fiddaui ke kika sha wahalar haihuwar sa, meyasa kike cewa a taimaka miki?." Zatayi magana Ruky tace, "Dan Allah ko daina cewa haka in sha Allah Amir zai zo yayi kwanaki a gidan nan." Tayi murmushi tace, "Rukayya tunda na tafi na tuna ne Amir banda lokacin da mukayi waya dake? Ban tuna da Amir ba ina ganin zan sake samun wani a wancan gidan da nake so shiyasa nayi banza dashi duk da ina son kayana. Dan nace ki taimaka min naga Amir ba laifi bane tunda a hannun mahaifin sa yake dole sai na neman alfarma kafin na ganshi." Rukayya tace, "babu neman alfarma Fidy Amir zai zo ma in sha Allah." Tayi dariya tace, "Allah ya kawo shi, na gode sosai Rukkya. Daman nasan indai Amir yana tare dake bazai yi kukan rashin  na ba sai dai yayi kuka in na dawo rage shi." Rukayya bata ce komai ba tayi murmushi kawai kafin Fidy tace, "cikin ki ya fito sosai, awo kika je?." Rukayya tace, "eh naje asibiti na biyo gida na gaida Umma, sai na shigo nan," "Kin kyauta wallahi naji dadi sosai kin d'auke min kewa. Cikin wata nawa?." Rukayya ta dan kawar da kai tace "ke ni ban rik'e lokacin ba." Tayi dariya tace, "karya kike wallahi kin rik'e." Tayi dariya itama suka dan yi hira kad'an kafin Rukayya tayi mata sallama ta tafi ta bar Fiddausi da sabuwar damuwa da dana sani a zuciyar ta. Yaya Adam yana dariya yana shiga d'aki Aisha ta kalle shi tace, "to Lafiya dai?." Ya zauna yace, "Al'ameen yana nan zan zauna lafiya ne? Wai bawan Allah nan tashi yayi yaje har wajan k'anin mahaifin sa yaje yace masa ya samu matar aure kuma kanwata ce amma ina so na hana." Tayi dariya  tace, "kai Al'ameen da gaske yake fa." Ya girgiza kai yace, "da shi k'anin mahaifin nasa muka gama waya yanzu yana ta dariya shima yana cewa yasan halin Al'ameen baya son jira ya kasa hak'uri har sai da yaje ya same shi. Al'ameen hmmm" ya fad'a yana girgiza kai. Tace, "shi gani yake kaine ka hana bai San ta mayar da lamarin sa tamkar comedy ba." "Iskancin tane da itama tana sane wallahi, a kaf wanda na basu damar ganin ta babu wanda naga tana sakewa dashi kamar Al'ameen din." "Sakewa daban ai so daban, in ka duba zata sake dashi mana saboda tana ganin sa koda yaushe tare da kai zata ji a ranta kamar kaine tasan bazai cutar da ita ba." Ya girgiza kai alamun haka ne kafin yace, "kafin ya cigaba da tara min jama'a zan same ta muyi maganar hankalin kar kuma ta dinga min wannan dariyar, in ta amince haka nake so in bata amince ba shikenan." Aisha tace, "Anya zata amince kuwa? Wallahi ta mayar dashi kamar abokin ta." "Shi yaga zai iya daman ai, ina shi ina Ameena dan Allah?." "Kaji ka, yana sonta tun ba yau ba akwai aibu dan ya aure ta?." Ya tab'e baki yace, "gashi nan ai tun yanzu ta mayar dashi Kakan ta." Tayi dariya tace, "ba komai duk cikin so ne." Yayi dariya baice komai ba sai daga baya yace, "zan so ayi auren ma kawai kafin tafiya ta dan in lokacin tafiyar yayi tana nan sai dai ku zauna tare naje na dawo bazai yu a barta ita kad'ai a nan ba." Aisha tace, "kai da naji dadi wallahi." Tashi yayi ya fita baice komai ba. Yusuf ana idar da sallar la'asar yaje gidan Usman a lokacin dawowar sa kenan ya same shi yana cin abinci Yusuf ya zauna yace, "Dan Allah ka gama muje bana son b'ata lokaci." Usman yace, "ka barni da aiki a can a nan kuma kazo kana takura min? Wallahi baka isa ba." Yusuf yayi tsaki ya cigaba da cin abinci ya kalli Yusuf din yace, "baza kaci ba?." Ya girgiza kai alamun bazai ci ba ya zauna yana kallon sama cikin tunani. Har Usman ya gama ya tashi ya shiga ciki ya fito ya kalle shi yace, "Yusuf muje." Sai kuwa ya zabura ya mik'e Usman ya girgiza kai suka fita Usman yaja motar suka nufi gidan Yaya Adam. Tunda suka nufi gidan kuma sai guiwar sa tayi sanyi gaban sa ya tsananta fad'uwa daidai lokacin da suke hango gidan Usman ya kalle shi yace, "ya naga ka karaya ne?." Yusuf yace, "bazan iya zuwa ba Usmsn bani da wannan  k'arfin guiwar." Usman yace, "kai kace zaka iya ai ko?." "Bazan iya ba wallahi." "Amma kasan haka ka d'auko ni ko hutawa banyi ba muka tawo?, yanzu hakan daidai ne?." Yusuf yayi shiru baice komai ba. Kallon gidan sukayi a tare sai ga Ameena ta fito daga mota ta shiga cikin gidan da alama daga makaranta take. Yusuf ya kalli Usmsn shima ya kalle shi yaga ya kulle idanun sa sai ya bashi tausayi amma bai nuna ba dan shi ya jawowa kansa ba wani ba. Usman yace, "watakila ma yanzu ta kusa aure, Allah Sarki Ameana na jima ma ban ganta ba sai yanzu." Yusuf ya bud'e ido da sauri yace, "mai kace dan Allah?." Usman yace, "cewa nayi watakila ta kusa aure, ko baza tayi auren bane ba kake min wani kallo?, kai ba'a yin auren kayi?." Yusuf ya fara girgiza kai yace, "Usman yanzu a gabana kake fad'ar haka?." "A gaban naka mana, waye d'in ta da bazan fad'a ba?." "Kasan Adadin abinda nake ji a zuciyata kuwa? Kasan ne nake ji da ka fad'i wannan maganar Usman?." "Ko fashewa zuciyar zata yi bazai hana ni fadar gaskiya ba, zata yi aure, na fad'a watakila ma ta kusa aure sai me?." Baya yayi ya kwanta a jikin kujerar yayi shiru zuciyar sa na bugawa sosai hankalin da ya tashi gabad'aya tunanin da bai zo kan Ameena zatayi aure ba sai yanzu da Usmsn ya fad'a, yanzu in Ameena tayi aure ya zaiyi Kenan? In Ameena ta auri wani wanne hali zai shiga kenan?. Usman yaja tsaki yace, "Soyayyar banza da wofi wacce bata yi amfani ba sai yanzu, Kaga malam ni ina da  abin yi tunda baza ka iya shiga gidsn ba sai mu juya" ya fad'a yana kunna motar tare da juya kanta suka bawa gidan baya ya bar cikin unguwar. Har Akaje k'ofar gidan Usman Yusuf bai d'ago ba sai da Usman yace, "na kai ka gida ko zaka d'auki motar ka?." Yusuf ya d'ago suka had'a ido ganin yadda idanun sa suka ja da fuskar sa sai da yaji tsoro sosai ya bishi da kallo kamar zai magana sai ya fasa yace, "kaini gidan Ammah dan Allah." Usman baice komai ba yayi gaba suka cigaba da tafiya baice komai ba har suka je gidan Ammah Yusuf ya bud'e motar ya fita baice komai ba Usman ya bishi da kallo yace, "kayi hak'uri Yusuf domin kuwa kayi babbar asara a rayuwar ka, sake samun Ameena a karo na biyu ba abu bane na wasa ba. Ka dai bsta hak'urin amma batun dawowar ta ka daina shi ma." Yusuf yana shiga gidan babu kowa a falon kai tsaye ruwa ya d'auka yana sha a lokacin Ammah ta fito tana kallon shi tace, "lafiya dai ko?." Ya girgiza kai alamun babu komai ya fita ya bishi da kallo tace, "ikon Allah yaron nan gabad'aya ya firgice." A k'asa ya je gidan sa tun bayan da Asiya ta tafi bai sake zuwa gidan ba ya shiga wajan Ameena ya zauna yana sake k'arewa falon kallo. "Ya zanyi? A ina zan ganta? Me zance mata? Da wanne ido zan kalle ta?." Ya dafe kai yace, "nayi mata abubuwa da yawa, na b'ata mata rai, na saka ta kuka, na dake ta, na zage ta, na cutar da ita. Da wanne baki zan iya cewa tayi hak'uri?." "Ameena wallahi Ina sonki nasan kin san ina sonki, ki bani dama guda d'aya na baki hak'uri na nemi afuwar ki, Ameena ki bani dama dan Allah Ina so na ganki amma bani da wannan karfin guiwar." A bayyane yake maganar kuma da k'arfi kamar wanda bashi da hankali, ya tashi tsaye yana zagaye yana so ya samo mafita amma ya kasa ya dunkule hannu ya daki kujera sai kuma ya tsaya cak a a bayyane yace, "Bauchi zanje, dole naje Bauchi wajan Yayar ta ko zata taimaka min wajan bata hak'uri." Yana fad'a ya fita daga falon da sauri ya fita daga gidan a k'asa ya sake komawa gidan Ammah. D'akin da yake kwana ya shiga y d'auki waya ya kira Usman yana d'auka yace, "zaka raka ni Bauchi gobe?." "Muyi me?." "Zaka raka ni ko baza ka raka ni ba?." "Badan halin ka ba zanje." "Gobe da safe zamu tafi in Alalh ya kaimu" yana fad'a ya datse wayar ya cillar a kan gado yace, "Ya Allah ka kawo min mafita kafin zuciyata ta k'arasa kumbura ta fashe, kaine kawai zaka kawo min sassauci a cikin lamarina ya Allah. Ya rabbi ka taimaka min ka shiga lamarin nan kar ka barni da kaina ka dafa min ka hana ni zubar da hawaye" ya fad'a hawaye suna fara sakko masa kamar yadda ya zamar masa aboki a wannan lokacin. #Mai daki #Book3 #Paid #500 #Nana Haleema. Book3 030 Ameena tana shiga gida ta tarar da Yaya yana zaune a falo ta zauna tace, “Yaya yau na gaji” sai kuma ta tashi tace, “yunwa nake ji, bara na zuba abinci na baka labari” ta fad’a tana shiga kitchen yayi murmushi kawai sai gata ta dawo da plate na abinci ta zauna Zaytun ta tawo ta zauna kusa da ita tace, “Yaya kasan a wannan semester ma ban samu carry over ko d’aya ba?.” Yaya Adam yayi murmushi yace, “Gaskiya wannan abun farin ciki ne, kin yi k’ok’ari.” Tayi dariya tace, “na gode Yaya.” Yayi murmushi baice komai ba har ya gama cin abincin ta sha ruwa sannan tace, “yanzu na dawo hankalina” ta fad’a zata tashi yace, “Ameena zauna.” Ta dawo ta zauna ya kalle ta yace, “meye ra’ayin ki akan Al’ameen? Yana ta karad’e dangi yana cewa ai na k’i bashi ke, meye ra’ayin ki a kansa?.” Tayi murmushi tace, “Ban San me zance ba Yaya.” “Kin sani Ameena ki fad’a min kawai bana son wasa da hankali ke kin sani.” Ameena tayi Ajiyar zuciya tace, “Yaya ka bani lokaci dan Allah.” “Shikenan na baki, amma kar lokacin ya jima. Ina so nasan abin da za’a yi ne na gaji da wannan yazo wannan yazo gwara ayi a gama kawai.” Ta d’aga kai ta tashi ta shiga cikin gidan. Tana shiga wanka tayi maganar tak’i barin zuciyar ta amma wallahi ita darıya abin yake bata tana shiryawa tana murmushi ta zauna a gefen katifar ta tace, “Yaya Al’ameen rigima kamar yaro k’arami, yanzu nace bana ra’ayi ma ai shiga uku” Tayi dariya a bayyane tace, “zamu gani dai” ta fad’a tana tashi ta fito falo dan ayi hira da ita. Tana jiyo maganar sa shida Yaya a bakin k’ofar falon haka nan taji kawai tana so taga fuskar sa sai ta koma d’aki ta d’auko karamin mayafi ta yafa ta fito Zaytun ta biyo bayan ta sai ta juyo tana kallon Zaytun kamar bata san suna wajan ba tace, “ki tsaya a nan abu zan duba mota nayi mantuwa.” Motar ta nufa sai kuma ta tuna motar ma a kulle take ta kalli inda suke nan take suka had’a ido dashi da alamaa kallon ta yake yi sai tayi murmushi ta k’araso tace, “ina wuni, Yaya ina key din motar nan kamar nayi mantuwar littafi.” Mik’a mata key din yayi ya nufi motar ta bud’e tana ta dube-dube kamar gaske shi kuma yana yiwa Yaya Adam magana. Rufe motar tayi ta dawo ta wuce ciki bata bashi key din ba ya kalli Adam bayan ta wuce yace, “Dan Allah ka taimakawa marayan nan ka bashi auren yarinyar nan.” Adam yace, “taya zan hana ka auren Ameena ne wai? Nayi mata magana da ita tace na b’ata lokaci ka jira muji ne zata ce mana.” Ya sauke Ajiyar zuciya yace, “Allah yasa.” Ya amsa da amin kafin ya fita. Washe gari Yusuf da Usman da safe suka d’auki hanyar bauchi Usman bai tambaye shi abinda zasu ba tunda yasan akwai Yayar Ameena a can bai damu ba yasan can zasu je. Basu shiga ba sai gab da azahar a k’ofar gidan ta suka tsaya yana fitowa daga motar Ameera na sauka daga adaidaita sahu ta bawa mai napep din kud’in ta juyo ta kalli Yusuf ya sake kallon sa ta tabbatar shine kafin tayi magana yace, “Amira.” A ciki tace, “Na’am, ina wuni.” “Lafiya lau, dan Alalh ki fad’awa Yayan zuwan mu.” kai kawai ta girgiza ta shiga ciki tana mamakin zuwan sa. A tsakar gida ya same ya ita kad’ai Kasancewar lokacin makaranta duk basa nan ta kalle tace, “Mama kin San waye a waje a k’ofar gidan nan?.” “Waye?.” “Yusuf tsohon mijin Anti Ameena wai yana son na sanar dake zuwan sa.” Yaya ta kalle ta tace, “Yusuf kuma Amira?.” “Eh wallahi, gashi can a tsaye shida wani. Ko uban me ya kawo shi ma oho.” Yaya tace, “gashi mai gidan baya nan, amma jeki kice ya shigo.” Ta ajjiye aiken da aka yi mata ta fita ita kuma Yayan ta tashi ta shiga ciki ta saka hijjabi ta shinfid’a tabarma. Da sallama ya shigo bayan sa Usman Yaya tace, “Ashe da gaske kai din ne, bismillah ku k’araso.” Yusuf suka k’arasa suka zauna ta kalli Amira tace, “kawo musu ruwa da lemo, ki kawo Abinci.” Amira ta bar wajan Yusuf ya gaida Yaya ta amsa haka Usman ma Amira ta kawo ruwa ta ajjiye musu a gaban su Yaya tace, “kawo musu abincin mana.” Yusuf yace, “A’a a barshi Yaya, Alhamdulillah iya ruwan ya isa.” Yaya tayi shiru dan ita batayi tunanin daga kano suke ba tayi tunanin aiki ne ya kawo shi ya biyo su gaisa. Yaya tace, “naji dad’i da ka biyo muka gaisa sosai.” Yusuf yace, “Yaya ai daga kano muke kai tsaye nan muka zo.” Da mamaki tace, “kano! Kaii ashe doguwar tafiya kuka yo, na d’auka aiki ne ya kawo ka nan din ka biyo mu gaisa. Kai kai ashe a gajiya kuke sosai.” Yusuf yace, “babu komai ai Yaya. Magana nazo muyi.” “To baka huta ba kuma sai magana?.” “Babu komai ai Yaya.” “To ina ji, Allah yasa dai Lafiya.” “Ba Lafiya ba.” Tace, “to me ya faru?.” Ya sauke numfashi yace, “Yaya dan girman Allah abinda ya faru a baya wanda na aikata dan Allah ayi hakuri a yafe min. Nasan nayi kuskure ni kaina wallahi, nayi abinda baza ki manta dani ba, amma ki yi hak’uri na gane kuskurena nayi nadamar abubuwan dana aikata.” Yaya tayi murmushi tace, “to Yusuf ni ai bani ya kamata kazo ka bawa hak’uri ba, Adam da Ameena zaka je ka samu bani ba. Ameena aka yiwa laifi wanda zai biyo bayan ta kuma Yaya ne, meyasa ni kazo wajena kai tsaye?.” “Na kasa tunkarar ta da maganar nan, na kasa zuwa gidan balle nayi magana. Dake nake so nayi kamun k’afa ki yi min iso domin gyara abinda na b’ata.” Yaya ta kalli Amira da da take aikin kallon Yusuf ta sake kallon Yusuf din kafin tayi magana Amira tace, “wai ni ban gane ba, ayi hak’uri akan me? Wai ta koma gidan ka?” Sai tayi dariya tace, “lallai ma Daddyn Zaytun din nan, ai har abada Anti Ameena ta bar gidan ka wallahi, duk abubuwan da suka faru tun lokacin baka zo bada hak’urin ba sai yanzu da lokaci ya k’ure maka?.” Yaya ta kalle ta tace, “Amira meye haka?.” “Mama ki barni nayi magana, baki San komai ba nice nasan waye shi a cikin gidan sa. Bai tab’a jin kunyar idanuna ya d’agawa Anti k’afa akan fad’an da yake mata ba, bai tab’a jin nauyi na ba a gabana zai mata tsawa sai dai ita ta bar wajan saboda tana jin nauyin faruwar hakan a gabana. Bai san ya ta tashi ba bai San ina kika je ba ko bata da lafiya baya damuwa amma in akace Zaitun ce babu lafiya daga wannan lokacin kwana zatayi tana kuka. Anti Ameena ta kasa cin abinci, Kullum a tunani da damuwa take har hakan ya saka mata hawan jini amma ban tab’a gani ko naji yace ya kika kwana ba. Tun Anti Ameena na b’oye min bata so na fahimta har na gane saboda itace mai b’oyewa shi baya jin nauyin mata fad’a a gabana. Duk abinda matar sa tace dashi yake yi amfani bai tab’a yin nazari akan abubuwan da take fad’a masa ba komai hawa kai yake yana zama ko yaushe Aunty ce mai laifi.” Ta kalli Yaya tace, “har wajan ta suka zo suka zagi Mama da take kabari amma Anti tace min Amira mu bar wajan nan kare ya fara haushi suka sake ambatar sunan Mama suka d ma itace karya. A wannan lokacin ne Anti ta Mari matar sa tace kar ta sake kasa mata uwa a lamarin ta. Ashe plan ne sai d’ayar ta fita tayi masa waya yana zuwa bai san hawa ba bai san sauka ba a kan idona ya mari Anti Ameena. Ni kuka ita kuka haka muke kwana, ita take tilasta min cin abinci amma ita ta kasa cin abincin.” Yaya ta kalle ta tace, “Malama kiyi mana shiru ki bar wajan nan kafin ranki ya b’aci.” Amira bata ji me ma take cewa ba ta sake cewa, “Kamar yadda Zaytun ka sani itace mutum in babu Lafiya hankalin ka yake tashi haka mu ma hankalin mu yake tashi in bata da lafiya. Sai yanzu da aka kusa shekara sannan zaka zo kace ayi hak’uri? Ai wallahi kayi sake Anti Ameena ta Yaya Al’ameen ce babu wanda zai raba ta dashi a wannan lokacin.” Ta kalli Yaya tace c “kiyi hak’uri Mama abin nan ya jima a zuciya sai yanzu na samu damar fad’a, ni kad’ai nasan meye a gidan daddyn Zaitun domin ni na zauna da ita dashi a cikin gidan. Kiyi hak’uri ban fad’a dan na b’ata miki rai ba.” tana kuka ta bar tsakar gidan da sauri ta shiga d’aki. Yusuf yayi shiru zuciyar tayi sanyi haka jikin sa ma Usman ya tab’e baki kawai baice komai ba dan baiga laifin Amira ba gaskiya ya fad’a duk abinda aka aikata laifin sane, kuma tun lokacin meyasa bai bayar da hak’urin ba sai yanzu?. Yaya tace, “kiyi hakuri da abinda Amira tayi akwai yarinta a lamarin ta.” Usman yace, “Gaskiya ta fad’a Yaya, duk abinda tace yayi ne da ba’a yi ba da zata fad’a ba ai.” Yusuf ya kalli Yaya da idanun sa jajaye yace, “na fad’a naki nayi kuskure Yaya nasan da hakan, amma in neman afuwar ta amma bani da karfin guiwar tunkarar ta wallah. Duk abinda Amira tace nasan gaskiya ne Yaya, amma Allah nayi nadamar duk abinda na aikata.” Yaya tace, “hak’uri ita zaka je ka samu in ka b’ata hakuri ta hak’ura kaga shikenan sai kowa ya kama gaban sa kai kasan babu hakkin ta a kanka saboda ta yafe maka. Amma ni ai ba ni aka yiwa laifi ba bazan ce an yafe maka ba ba tare da Kaji ta bakin ta ba.” Usman yace, “Yaya ba iya hak’urin yake so ba har bikon aure ya yake yi a karo na biyu.” Yaya ta girgiza kai cikin mamaki tace, “bikon auren ta kuma Yusuf? Yanzu tsakani da Allah kana da idanun da zaka sake kallon Ameena kace zaka aure ta a karo na biyu? To wanne kalamai zaka yi amfani dasu da zai saka ta amince da abinda zaka ce mata?.” Yayi shiru baice komai ba tace, “Kar ka manta yar mahaifinta ka yiwa alqawarin rik’e ta amma ka kasa, kazo nan kace min daga wannan ranar baza’a sake jin kanku da Ameena ba ka kasa sai abinda yayi gaba, yanzu kuma kana ganin Yaya Adam zaka yiwa alqawarin rik’e Ameena?” Tayi rmurmushi tace, “Yusuf Tsakani da Allah kayi wasa da damar ka, sake samun wannan damar abu ne mai wahala gaskiya, zancen da nake maka ma Ameena tana gab da yin aure shine wanda Amira take cewa Ameena ta Al’ameen ce. Hak’uri dai zaka iya zuwa ka bawa Yaya zai saurarre ka haka itama amma zancen mayar da auren ka da ita ka ajjiye shi gefe ko Yaya Adam baya raye Ameenan da ka sani a baya ba itace a yanzu ba, sai dai hak’urin zata hak’ura kodan Zaytun da take tsakanin ka da ita amma zancen aure Yusuf ka goge shi daga zuciyar ka, ba Yaya Adam ba ko ni bazan bari ta koma gidan jiya ba.” Yanzu rayuwar ta tayi kyau tayi k’iba ya dawo hankalin ta bazan sake mayar da ita inda zata sha wahala ba.” Yusuf kansa yana k’asa hawayen da baya so su zuba a wannan lokacin ne suka fara sauka daga idanun sa Yaya tana kallon saukar su a shaddar jikin sa sai gaban ta ya fad’i ta sake kallon sa ta tabbatar kuka yake yi Usman ya kalli Yusuf ya kalle ta yace, “yayi kuskure nima na fad’a masa, yayi sake ya kuma yi wasa da damar sa wacce ta kubce masa a yanzu.” Yusuf ya d’ago ya kalle ta yace, “wallahil azim wancan Yusuf din da wannan Yusuf din da banbanci Yaya, a sake bani dama ta biyu wallahi bazan yi wasa da Ameena ba, bazan sake aikata duk abubuwan dana aikata a baya ba. Na gane kuskurena zan kuma gyara nayi alqawarin Ameena baza ta dake zubar da hawaye akan zama dani ba, ki taimaka min Yaya ki shige min gaba zuwa wajan Yaya bani fa k’arfin guiwar tunkarar sa zuciya ta tayi rauni sosai, ki taimaka min wallahi na rasa na Ameena a wannan lokacin zan iya rayuwata gabad’aya.” Yaya ta kalle shi tace, “ikon Allah Yusuf bani da damar da zan sake baka Ameena a karo na biyu, sai dai kaje wajan Yaya ta inda aka hau ta nan ake sauka ai. Shine yaje har gida ya dawo da ita shine kuma zai mayar da ita in yaso, amma wannan magiiyar da kake min ka daina babu abinda zan iya.” “Ban san ta wacce hanya zan tunkare shi da maganar ba, ki taimaka min dan Allah wallahi nayi alqawari abinda ya faru a baya bazai sake faruwa ba wallahi,.” Yaya ta rasa abinda zata ce ga shi a gaban ta yana kuka duk sai ta damu kukan ne bata so sai tace, “Yusuf in nace maka zanyi wani abun a akai k’arya nake wallahi, kawai kaje kayi abinda kake ganin zaka iya amma ni bani da abinda zan maka gaskiya.” Usman yace, “gaskiya ne Yaya, iya sauraron mu da kika yi ma Mun gode sosai wallahi.” ya kalli Yusuf yace, “wajan Yaya Adam ya kamata kaje ba nan ba, abinda take fad’a gaskiya ne can ya kamata kaje ba nan ba dan a can Ameena take.” Ya kalli Usamsn zaiyi magana yace, “Hakan za’a yi Yusuf.” Usman ya kalli Yaya yace, “Yaya zamu wuce yanzu.” “Da wuri haka? Kun k’in cin abinci.” “Babu komai wallahi mun gode.” Yusuf ya kalle ta bayan ya goge idanun sa yace, “Wallahi a wannan lokacin babu damuwa a zamana dani, duk inda kuskurena yake na gano shi kuka wallahi zan gyara.” Yaya tayi murmushi tace, “Allah ya baka iko, kaje ka same shi shida ita su zaka sanar da haka bani ba Yusuf.” Tashi sukayi tsaye sukayi Yusuf yana goge idanun sa susman ya d’auko kudi ya ajjiye yace, “Gashi Yaya a bawa yara.” Yaya tace, “dan Allah d’auke Mun gode basai ka bamu komai ba.” Usman yace, “ni na bayar ai ba Yusuf ba Yaya, dan Allah ki karb’a.” Murmushi tace, “To na gode.” Daga nan suka yi sallama suka tafi ta bisu da kallo. Yana fita Yaya ta girgiza kai tace, “Yusuf da kuka akan Ameena? Ikon Allah.” Sai kuma tayi dariya tace, “zuwa wajan sa ma ka kasa ina ga tunkarar sa da wannan maganar Yusuf? Lallai kana tare da wahala dan abinda kake nema baza ka samu ba” ta fad’a tana shiga wajan Amira dan ya ja mata kunne akan abinda tayi. Sai da suka yi sallah Usman yaci abinci dan shi dai Yusuf bai iya cin abinci ba yana zaune har Usman ya gama ci suka shiga mota suka d’auki hanyar kano Yusuf ya kasa magana sai tunani. A haka suka shiga kano kamar kurame kafin lokacin Zazzabi ya gama rufe Yusuf amma bai ma fad’awa Usman ba yana sauke shi gida ya shiga shi kuma ya wuce yana tausayin sa dan yasan abinda yake so bazai samu ba. Yana shiga falon Ammah ya tarar da ita a zaune ta kalle shi tace, “kai kuma ina ka shiga yau ban ganka ba?.” Yusuf yace, “naje wani waje ne, bana jin dad’i zan shiga na kwanta” ya fad’a yana wucewa ta bishi da kallo kafin ta cigaba da abinda take yi. Rukayya tana zaune bayan sallar magriba tana so ya shigo tayi masa maganar Amir dan ta daure zata yi masa a wannan a lokacin, tana so tayi masa amma sai ta kasa saboda bata son b’ata masa rai akan maganar amma yau kam tayi alwashin fad’a. tana zaune ya shigo da leda a hannun sa ya k’araso ya ajjiye a kusa da ita yace, “Nama ne in zaki dafa yanzu zo in kuma sai gobe sai ki saka a fridge.” Ya zauna tace, “To an gode. Sannu da zuwa.” “Yauwa, nayi sallah ne shiyasa sai yanzu na shigo.” “Naga alama ai” ta fad’a tana tashi ta d’auki ledar ta bud’e ta saka a fridge ta shiga kitchen din ya d’auko abinci ya kawo ya ajjiye ya kawo ruwa ma ta ajjiye ta zauna yace, “ina Amir?.” “Tunda yaci abinci yayi sallah sai yayi bacci tun d’azu.” Ta zuba masa abincin ya fara ci tace, “D’azu Yaya Hadiza tazo, ta kawo mana awara gata can ma a fridge sai gobe sai mu soya.” “An gode.” Ya fad’a a takaice yana cin abincin. Sai da ta bari ya gama ya sha ruwa ya tashi ya shiga d’aki. Tashi tayi itama ta shiga nata dskin tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta bacci ta saka hula a kanta ta fito taga duk ya kashe komai na falon da alama bacci zaiyi ta shiga d’akin ta same shi a zaune a gefen gado. Zama tayi tace, “yaushe ne tafiyar tamu?.” Ya kalle ta yace, “ranar asabar ne da safe.” Tayi murmushi tace, “Allah ya nuna mana, Allah yayi dai dsni za’a ce umrah nan.” Murmushi yayi kad’an kawai baice mata komai ba tace, “jiya naje gidan su Fiddausi da naje gida.” Ya d’ago ya kalle ta ta k’asan ido yace, “kin kyauta.” “Khalil daman wata magana nake so muyi ko nace alfarma zan nema a wajan ka.” Ba tare da ya kalle ya ba yace, “ina ji.” “Tunda Alalh ya rubuta da ni za’a je Umrah nan an ina zamu bar Amir?.” Ya kalle ta da mamaki yace, “Kamar ya an ina zamu bar Amir?.” Tace, “ina nufin inda zamu barshi.” “Bani da y’an uwa? Kuma wajan Umma fa?.” Rukayya tace, “Daman cewa zanyi dan Allah ka bawa mahaifiyar shi kafin mu dawo, wallahi ta damu da lamarin sa sosai tana son ganin sa a kusa da ita saboda….” Dakatar da ita yayi ta hanyar daga mata hannu yace, “kai k’arshen maganar ki kawai.” “Na fad’a ai Khalil, dan Allah a bata shi na kwana sati biyun kafin mu dawo, zata ji dad’i sosai.” Ya juyo ya kalle ta kamar zai magana sai kuma kawai ya fasa ya d’auke kansa tace, “in abinda nace ya bata maka rai kayi hak’uri, mahaifiyar sace itace ta d’auki cikin sa ta raine shi ta sha wahalar haihuwar sa akwai soyayyar sa mai tarin yawa a zuciyar ta. Dole tayi kewar sa gashi shi kad’ai take dashi shi kawai Allah ya bata a yanzu. A ganina tunda ka manta da shafin rayuwar baya bai kamata maganar ta dinga b’ata maka rai ba, Tunda kace min baka santa ba muje a baka santa din ba kaga maganar babu amfanin ta b’ata maka rai da zatayi. Kayi hak’uri” ta fad’a a sanyaye tana kallon sa shi kuma ba ita yake kallo ba. “Sau nawa zance miki bana son wannan batun? Sau nawa zance a daina min in ina cikin gidan nan?. Saboda abinda yake zuciyar ki na dawo baki kula da yanayin da nake ciki ba kawai burin ki ki issr min da maganar k’awar ki, to kin isar sai me kuma na gaba?.” Ganin yana kallon ta da alama ransa a b’ace yake ta bud’e baki zatayi magana yace, “bana so, maganar nasan zaki sake yi ko to bana so, kamar yadda nace miki na manta din na manta da batun ta, amma hakan ba yana nufin a ko wanne yanayi zaki dinga min maganar ba kin gane ko?.” Zatayi magana yace, “tashi ki bani waje.” Ta rausayar da kai tace, “Kayi hak’uri ban fad’a dan na b’ata maka rai ba saboda gudun hakan tun jiya na kasa fad’a maka, dan Allah kayi hak’uri.” “naji, amma ki bani waje tunda maganar tafi mahimmaci a wajan ki akan kula da yanayin da nake ciki.” “Dan Allah…..” kallon ta yayi sai tayi shiru ta tashi ta fita yayi kmaramin tsaki gabad’aya ransa a b’ace yake yana mamakin mutane kiri-kiri dan Allah yayi maka arzuki a dinga yi maka bak’in ciki ko kunya ba’a ji. Bai bi ta kanta ba dan haushi yake ji in tayi masa maganar Fiddausi, gashi duk sanda zatayi hakan akwai abinda ya dawo dashi ko b’acin rai ko farin ciki. Bayan sallar i’sha Usman yazo gidan Ammah ya samu Abbah da Ammah da kuma Mubakar suna falo gabad’aya suka gaisa Ammah tace, “Abokin naka tunda ya fita d’azu tun safe bai dawo ba sai yamma, sannan ya sake fita yayi sallah ya dawo ko abinci bai ci ba.” Usman yayi murmushi yace, “tare muke tun safen ai Ammah.” Abbah yace, “ka dinga masa fad’a ya dinga addu’a fa.” Usman yace, “yana yi Abbah, ai Yusuf din baya wallahi ba shine yanzu ba, bawai dan ina bayan sa ba da gaske nake wallahi.” Abbah yace, “ai haka ake so.” Ammah tace, “amma meyasa yanzu yake zama shiru-shiru ko abinci baya ci? Ka masa fad’a ya dinga cin abinci wannan ranar da yayi tayi yawa.” Yayi murmushi yace, “to Ammah in sha Alalh.” Suna cikin maganar sai ga Yusuf din ya fito ya kalli Usman yace, “kana nan bayan kasan jiran ka nake.” “To ai gani nazo, ina zamu je?.” Ya kalli mutanen falon yace, “muje dai kawai” ya fad’a yana fita Usman ya musu sallama ya bishi a baya. A bakin mota ya ganshi yace, “wai ina zamu je haka ka kira ni da daddaren nan?.” Yusuf yace, “Zamu je gidan su Ameena ne, ko yankar naman jikina zaiyi na amince zan tunkare shi a yanzu, in banje a dare nan ba wallahi yau bazan iya bacci ba. Shiyasa na kira ka muje ko meye zai faru ya faru na amince na yarda zan jure ko meye.” #Mai daki #Nana Haleema #Paid #500 Book3 031 Usman ya bishi da kallo daga dawowar su daga Bauchi zuwa yanzu ya sake susucewa kamar ba shi ba, shi har mamaki ma yake yi ya girgiza kai har zuciyar sa yanzu tausayin sa yake amma baya nuna masa saboda ko meye ma shine ya jawowa kansa ba wani ba. Usman yace, “kana ji, kayi hak’uri ka bari zuwa gobe k’arfe tara yanzu har tayi baza mu shigar masa gıda yanzu ba, ka bari gobe sai muje ko da safe ne.” Yusuf ya girgiza kai yace, “Usman wallahi bazan iya bacci ba, ni kad’ai nasan abinda nake ji bani da wanda zai taimake ni kuma sai kai, dan Allah ka d’aure muje Yanzun mu dawo.” Usman yace, “Bawai nak’i bane Yusuf ka tuna zamu d’auki dogon lokaci a gidan ana magana ga dare yayi yanzu ka jira gobe in muna da rai sai na raka ka, ina son duk abinda kake so kuma ina fatan ka samu abinda kake so.” Ya d’ago ya kalle shi yace, “da gaske kana yi min fatan na sake samun Ameena a karo na biyu?.” Usman ya girgiza masa kai cikin tausayin sa yace, “kwarai kuwa, domin kuwa na tabbata baza ka yi mata rik’on banza ba a wannan lokacin, amma sai kana addu’a in ka kasa baccin a yanzu ka tashi kayi alwala ka tayar da sallah ka tuba ga Allah sannan ka fad’a masa buk’atar ka na tabbata zai biya maka ita. Inda da rabon Ameena zata sake zama da kai zata dawo rayuwar ka.” “Usman bana bacci yanzu kullum cikin addu’a nake na tabbata shiyasa na fara dawowa hankalina, nasan nayi kuskure sosai amma komai ya faru ne tun daga lokacin da na kai kaina wajan Asiya,komai kuma ya k’are daga lokacin da na rabu da ita.” Usman yace, “Yanzu dai ka koma ciki gobe zan zo muje mu same shi indai ka shirya.” Yusuf ya sauke numfashi yace, “na shirya Usmsn, koda zai k’ona min farar jikina na shirya tunkarar sa wallahi.” Usman yayi murmushi yace, “dakyau. Amma kuma naji ana cewa Ameenan zatayi aure fa.” Yusuf ya runtse idanun sa ya bud’e ya kalle shi yace, “babban tashin hankalina kenan, wallahi Usmsan a yadda nake ji in na rasa Ameena zan iya mutuwa.” “To wai da duk kana sonta irin wannan son da kake fad’a ka dinga mata iskanci iri-iri?. Har cewa kayi alfarmar Ammah take ci fa kenan karya kake?.” “Na fad’a ne kawai saboda wani dalili nawa amma Wallahi babu macen da nake so kamar Ameena, na sota kuma Ina sonta har gobe da jibi na tabbata da sonta zan mutu.” Usman yace, “to Allah ya daidai in da rabo, in babu kuma….” Da sauri ya dakatar dashi yace, “akwai ma rabon in sha Allah.” Yayi murmushi yace, “na wuce sai goben.” Kai kawai ya d’aga ya koma cikin shi kuma ya hau mota ya fita. “Wallahi Umma ni na gaji da daman gidsn nan ga zafi ga sauro ga tuwon daren, duk laifin kine akan me zaki ce ya sake ni? Gashi yanzu ko waya bai yi min ba haka kawai kin kashe min aure kin cuce ni” Asiya ya fad’a tana hawaye tana zaune da hannun ya da yake d’aure tana jinyar kanta. Umma ta kalle ta cikin mamakin abinda take fad’a tace, “nice ma na cuce ki Asiya? Duk abubuwan da nayi a kanki baki gani ba sai yanzu da komai ya lalace?.” Asiya tace, “to Umma in ba cutata ba me kika yi? Kece kawai kika ce wai ya sake ni shi kika ya sake ni, da baki ce muje gidan ba ai da hakan bata faru ba. Nidai wallahi an cuce ni an raba ni da gıdana kuma wallahi sai na koma. Bazan zauna a wannan gidan ba ha zafi ko wuta ba’a kawowa,” Maimuna ta mare ta tana kallon ta tace, “Umma kike fad’awa wannan maganar? Rashin kunyar taki kenan gaba yayi ba baya ba.” Ta kalle ya a fusace tace, “ina ruwan ki danj da zaki dake ni? K’arya nayi da Umman bata je ba ai da bai sake ni ba, dan kina farin ciki na dawo gida kamar ki shine zaki saka hannu ki mare ni?. To wallahi aka sake marina sai na rama kuma na rantse da Allah sai na koma gidan mijina duk bak’in cikin mutum.” Maimuna ta girgiza kai tace, “kice zaki ci uban ki a daren nan wallahi, ni zaki fad’awa wannan maganar?” Ta fad’a tana sake tsinke ta da Mari Asiya ta mik’e ga hannu a d’aure tana kuka tace, “Umma kice mata babu ruwan ta Dani wallahi ta same dukana zan rama Umma, wallahi zan rama.” “İn na dake kin sai ki rama dan uban ki” ta fad’a tana sake dukan ta, Asiya da hannun ta mai Lafiya ta bud’e shi ta dake ta itama a baya. “Kutmar uban nan” Maimuna ta fad’a tana fara dukan Asiya ta ko Ina tana ihu an fama mata hannu amma bakin ta baiyi shiru ba tana sake zazzaga mata rashin kunya Umma dai kallon su take ta kasa magana zuciyar ta zafi take mata sosai akan abinda suke yi ta kuma san ko zatayi magana sau goma baza su daina ba.” Sai da Maimuna taga Asiya jiki yayi sanyi sannan ta kyale ta tace, “nan gaba in akace ki sake min rashin kunya ki sake yi na gani, gwara ma da Yusuf din ya koro ki ai kizo mu gwabza dani dake aga waye mai nasara. Shashasha mahaukaciya k’azamar banza da wofi wacce ko pant bata canjawa.” Momi da Fauziyya suna zaune suna kallon su babu wacce ta motsa dan gwara da ta zane Asiyan iskanci take ji dashi daman a gidan. Asiya jiki yayi tsami sai kuka take gata a kwance hannu nayi mata ciwo sosai a haka ta tashi ta shiga d’aki tana kuka tana cewa, “wallahi gıdana zan koma bazan cigaba da zama a nan ba, kuma wallahi na koma naga k’afar wata shegiya a gidan sai naci bu** uban ta.” Umma kallon ta yake har ta shige ciki sannan ta sauke numfashi Momi tace, “Umma ai kad’an kika gani indai daga rashin tarbiyyar Asiya ne, wannan da kike gani Umma hmmmm.” Umma dai ta kasa cewa komai domin abin yafi k’arfin ta ta tashi ta shiga d’aki kawai bata iya magana ba. Washe gari Umma Sakina tazo tun safe Asiya na zaune sai da aka kira mai gyara ya duba hannun aka tabbatar lafiya yake dan sun d’auka ya goce, tana zaune sai kunbure-kunbure take yi Umma ta kalli Umma Sakina tace, “Ya ake ciki da lamarin nan dan Allah? Abin nan ya fara damuna shiru har kwana hud’u ba waya babu zuwa?.” Umma Sskina tace, “Ai kawai ayi hak’uri auren nan nasu ya mutu, duk inda naje abinda ake fad’a min kenan auren ya mutu bazai mayar da ita ba.” “K’arya suke wallahi sai na koma gidan mijina” Asiya ta fad’a tana daga gefe Umma Sakina ta kalle ta bata ce komai ba Umma tace, “Sakina wacce irin magana kike haka? Kamar ya auren ya mutu kuma?.” Umma Sakina tace, “Kamar yadda nazo nace miki auren su zai yu sai ya aure ta koda baya so yanzu nazo nace miki auren ya mutu ki yarda kawai.” Umma tace, “bazan yarda ba Sakina gaskiya, ina akace auren nan ya mutu ina zan saka raina .” “To sai ki je da kanki ki yi duk abinda ya kamata Nidai bazan wahalar da kaina ba.” “Hak’uri zakiyi mu cigaba da nema, wannan arzukin da ake samu duk tare ake ci.” Umma Sakina tace, “ba fa zai mayar da ita ba, Asiya tana da laifi a lamarin nan, na farko ke shaida ce bata da kunya, na biyu ga shegiyar k’azanta sannan ga satar da take yi masa dole koda aikin mu a kansa sai ya gaji. Ki tuna daman fa shi ba auren Asiya yazo yi ba, mu ne muka ga yana niyar guduwa muka kama shi yanzu kuma abinda muka saka muka d’aure shi ya sake shi tunanin sa ma shi ya akayi ya aure ta, kinga sai muyi hak’uri Allah ya kawo wani.” Umma tace, “A’a dan Allah ki daina fad’ar haka, haka za’a yi hak’uri mu cigaba da nema ai bamu san inda za’a dace ba. Nawa muka samu da auren zai mutu yanzu fisabinillahi?.” “To nidai na gaji Atika nayi iya yiwa wai uwar y’a ta siyi cokali.” Ta kalli Asiya tace, “kalle ta dan Allah kamar tsohuwa ba dole ma ya gaji da zama da ita b?, daman abinda muka yi ne ya rik’e shi yake hak’uri haka amma yanzu bazai iya ba, ni da naje gidan kasa zama nayi a kusa da ita saboda warin da take yi balle shi.” Asiya ta murgud’a mata baki tace, “duk bak’in cikin masu bak’in ciki wallahi sai na koma gidana.” Umma Sakina tace, “iyeee! Nice nake bak’in cikin Asiya?.” “To Umma Sakina in ba haka ba meyasa kike cewa wai ya gama aurena?. Kawai dan an fad’a miki sai ki yarda ki dinga k’ararwa aurena ya mutu?, ba dole nace bak’in ciki bane?.” Umma Sakina ta girgiza kai tace, “to bara kiji badan ni ba da yanzu baki auri Yusuf har kin sato abinda kika sato ba, badan ni ba wallahi da yanzu ya jima da yi miki shegen duka ya Koro ki gida ko ya had’a ki da y’an sanda ko y’an daba sun miki duka, ki gode Allah ma da sai yanzu kika dawo gidan. Ga uwar ki nice na shiga na fita akayi auren ku badan haka ba da yanzu kina nan babu mai so.” “Allah daman yayi sai ya aure ni ko mutum baiyi komai ba, kuma ai naga in na sata har ke ake ci ba iya ni kad’ai nake cinyewa ba. Yauwa, kuma sai na koma gidan mijina wallahi koms mutum zai ce sai dai ya haddiyi zuciya ya mutu.” Umma Sakina ta kalli Umma tace, “Kina Jin abinda take cemin kina kallon ta ko ki bari baza ki ce ba.” Umma tace, “to Sakina ke ce wallahi kamar mai bak’in cikin, taya zaki dinga cewa wai auren ya mutu tsakani da Allah?.” Umma Sakina ta wara idanu ta kalli Umma tace, “Atika ni ce ma mai bak’in cikin? Nice nake yiwa Asiya bak’in ciki akan zata koma gidan Yusuf?. Lallai Atika baki da mutunci daga ke har yaran ki, ni nake yi muku bak’in ciki a akan auren Yusuf yanzu?.” “Ni bance kina bak’in ciki ba ai, amma yanayin da kike nunawa kina magana kamar bakya son a mayar da auren sa da Asiya wallahi.” Umma Sakina tace, “bana so ta koma din bak’in cikin nake yi, muje a bak’in cikin nake kawai kuma baza ta koma ba.” Asiya tace, “kin gani ko Umma dmaan abinda yake ranta kenan, k’ila ma ita taje tayi wani abun dan ya sake ni.” “Kee Asiya dakata! Daga ke har uwar ki ni ba sa’ar yin ku bace nafi k’arfin ku walalhi, ki saita harshen ki kafin nayi miki dukan da zan b’alla miki d’aya hannun. Uban me nake samu da zaki ce bak’in ciki nake yi? Uban me Uwar tak’i take min ko ke me kike yi min?. Yusuf din waye da zanyi bak’in ciki a kansa? Waye shi a Nigeria fad’a min na nawa ne shi a jerin masu kud’in Nigeria?.” Asiya tace, “Bak’in cikin dai ya fito.” Bata san ta mari Asiya ba sai da taji Umma tace, “Yanzu meye na dukan ta kuma dan Allah? Daga magana sai ya zama fad’a?.” Umma ta kalle ta tace, “ni zaku fad’awa Ina bak’in ciki akan lamarin Asiya? Duk abinda nayi baku gani ba sai da komai ya lalace zaku ce nice nake muku bak’in ciki?. A gaban ki take min rashin kunya kin kasa yi mata magana abinda banyi zaton faruwar sa ba. Na d’auka uwa suke d’auka ta kamar yadda suke d’aukar ki domin ina shiga na fita a cikin lamarin su ba tare da na gajiya ba. Ashe rashin mutuncin da rashin tarbiyyar da ake fad’a a kan gidan nan gaskiya ne sai ya yanzu na tabbatar da Hakan, to wallahi daga yau babu ni babu lamarin ku duk abinda da kike ganin na gaza kuje ku yi da kanku” ta fad’a tana d’aukar jaka zata fita Umma tace, “Ko da ke ko babu ke zamu yi ai da zamu iya, ya zaku dinga mana gori kamar kece kika had’a auren nasu tun farko?.” Umma Sakina tace, “Allah ya bada sa’a, kud’ina da nake bin ki kafin naje gida a tura min babu d’aga k’afa wallahi daga yau in ba’a turo min ba ke kin San abinda zanyi” Tana fad’a ta fita Umma tace, “a je dai, kud’i zan biya ai akwai kud’i a wajan Asiya zan biya ki kije can ki k’arata. Na daina had’a sirrina da ko wacce k’awa walalhi, kawai Kizo kina cewa wai auren ya mutu kenan har abada.” Asiya tace, “ai duk laifin ki ne Umma da kike sauraren wannan figaggitar matar.” “Ai yanzu komai ya wuce, kina ji tura mata dubu d’ari biyar shine kudin da take bina. Har tayi min gorin kud’i nida nake dake?.” Asiya tayi sak tace, “Dari biyar Umma? Haba ku dinga tausayi na mana yanzu da ba auren nan ne dani ba balle in wannan sun k’are a samo wasu, in na bada dari biyar ni kuma fa dan Allah?.” Umma ta kalle ta da mamaki tace, “baza ki bayar ba kenan?.” “Gaskiya da sauki” ta fad’a tana tashi ta shiga d’aki tana cewa, “haka kawai a tatike min abinda na tara tun ba’a je ko ina ba, Haba ai ya dole ma na koma gidan mijina wallahi na gaji da zaman gidan nan komai Asiya kawo kud’i kamar wata bank?.” Umma ta bita da kallo ta girgiza kai tace, “Asiya baza ki bayar ba kenan?.” Shiru taji bata amsa ba ta bita tana cewa, “dole ki bada kud’in nan in ba haka ba nafi kowa sanin halin Sakina wallahi. Saboda ke naci bashin nan ki daure ki amince ki bada kud’in, akan ki lokacin da kika sace kudi a account din sa naci bashi akayi aikin aka kuma rufe bakin sa dan haka dole ki biya.” Asiya tace, “tabdi! Nidai gaskiya bazan iya bada wannan kud’in ba” ta fad’a tana sake fita daga d’akin dan da gaske baza ta bayar ba. Bayan sallar azahar Usman da Yusuf suna zaune a cikin mota a k’ofar gidan Adam Yusuf sai addu’a yake karantawa a zuciyar sa sannan ya daure ya fito dan dole yasan sai ya fito din Usman ma ya fito suka k’arasa wajan mai gadi suka gaisa Yusuf yace, “Mai gidan yana nan?.” “Baya nan ya fita tun safe amma nasan yanzu zai dawo.” Yusuf ya kalli Usman sai Usman yace, “muje ma dawo anjima.” Yusuf ya motsa kenan zasu bar wajan sai ga motar Yaya Adam ta shigo layin mai gadin yace, “gashi nan ma.” A k’ofar gidan ya tsaya ya sauke glass ya kalli Yusuf yace, “Yusuf kaine tafe a ranar nan?.” Al’ameen da suke tare ya kalli Yusuf din ya fito daga motar yana kallon sa Yusuf bai ma kula dashi ba yace, “eh, wajan ka muka zo.” Yaya Adam yace, “wajena kuma? To Allah yasa dai Lafiya. Ku shigo mana” sai kuma ya kalli Al’ameen yace, “Dan Allah duk abinda akayi ka tura min na gani bana so lisssfin ya dinga kwace min.” Banza Al’ameen yayi masa baice komai ba sai yayi dariya yace, “Meye na b’ata ran kuma?.” Hararar sa yayi shi kuma yayi ya shiga da motar ciki Yusuf da Usman suka bi bayan sa sai lokacin ya lura da kallon da Al’ameen yake masa duk sai ya tsargu. Tare suka shiga har falon Zaytun na wasa tana ganin Yaya Adam tayi wajan sa a guje kafin ta k’arasa sai ta hangi Yusuf sai ta canja hanya tayi wajan sa. Yayi dariya yace, “lallai ma yarinyar nan zaki zo hannu na.” Ya fad’a yana zama shi kuma yana rik’e da ita suka k’araso suka zauna Yaya Adam yace, “bamu gaisa bama.” Suka gaisa Yaya yace, “Ya su Alhajin duk suna lsfiya?.” “Lafiya lau kowa da kowa.” “To ma sha Allah.” Shiru Yusuf yayi Yaya Adam yace, “ina jin ka, kace kazo wajena, Meya faru?.” Yusuf ya kalli Usman shima shi yake kallo kafin ya sunkuyar da kansa k’asa yace, “Daman nazo bada hak’uri ne akan abinda ya faru.” “Hak’uri? Akan me to Yusuf? Meya faru din?.” Yusuf ya kasa magana yayi shiru Yaya yayi murmushi yace, “ya ka kasa magana ka fad’a mana na dawo na gaji Ina so ne huta kafin lokacin sallah yayi.” Yusuf yace, “dan girman Allah Yaya ayi hak’uri da abinda ya faru a baya a yafe min.” Yaya Adam ya bishi da kallo ya girgiza Kai yace, “Wai in an afahimta ayi hak’uri akan abubuwan da ka yiwa Ameena kake nufi?.” Ya sunkuyar da kai ya kasa amsawa Adam yayi dariya kad’an yace, “in ma shi kake nufi ni mamaki abin ya bani, abin da ya faru watannin baya baza’a zo baza hak’uri ba sai yanzu?.” Yusuf yayi shiru Usman sai yace, “Wallahi Yaya Yusuf ya shiga wani hali ne a kwanakin baya banbance daidai da ba daidai ba shiyasa ya kasa zuwa duk da zuciyar da tana so yazo din amma sai ya kasa.” “Allah Sarki, rashin lafiya yayi kenan?” Yaya Adam ya fad’a yana kallon su daga shi har Yusuf din. Duk sun kasa cewa komai sai Yaya Adam yayi murmushi yace, “Yanzu ka fad’a min abinda ya kawo ku sauri nake yi.” Yusuf yace, “wallahi Yaya nayi kuskure nayi kuma dana sanin abinda na aikata, dan Allah dan girman Allah ayi hak’uri a yafe min in akwai dama ina so naga Ameena dan Allah.” Yaya Adam ya kalli Zaytun , “ke Zaitun kira babar ki.” Ta sauka daga jikin Yusuf ta tafi ciki ya kalli Yusuf yace, “in tazo ka bata hak’urin shikenan dai ko?.” Yusuf yayi shiru baice komai ba dan bai san abinda zai ce ba sai ga Ameena ta fito tace, “Yaya gani.” Ya kalle ta yace, “Yusuf ne yazo baki hak’uri, gashi a zaune ki k’araso ya baki hak’urin ki hak’ura ki koma ciki ba shikenan ba dai ko Yusuf?” Ya fad’a yana sake kallon sa shi kuwa zuciyar sa bugawa take yi sosai jin abinda yake cewa kamar da biyu yake fad’a. Ameena tayi turus tace, “Wanne Yusuf kuma Yaya?.” “Yusuf dai baban yarinyar da take kusa dake, Kizo ya baki hak’urin ki koma ci cigaba da karatun ki.” Tace, “to Yaya hak’urin me zai bani kuma?.” “Nima abinda nace masa kenan ai, amma ki k’araso ki zauna kawai.” Ba musu ta k’araso ta zauna a akan kujera ba tare da ta kalle shi ba Yaya Adam yace, “To Yusuf gata nan bata hak’uri.” Sai Yusuf ya kasa komai kamar an saka igiya an d’aure masa jikin sa haka yake ji ya kasa ko motsin kirki balle ya kalli Ameena ya kalli Yaya Adam da yake kallon sa ya kalli Ameena da suka had’a ido sai ta kalli Yaya tace, “Yaya karatu nake fa.” Ya kalli Yusuf yace, “ta ta tafi ne baka da abinda zaka ce?.” Kai ya girgiza ya kalle ta ita kuma ba shi take kallo ba yace, “Ameena!.” Sai yayi shiru a fusace tace, “Na’am.” Idanu ya kulle ya bud’e su a kanta ya sake kallon ta yace, “Kiyi hak’uri akan abubuwan da suka faru, kin san abinda zan aikata kin san wanda bazan aikata ba, kin san halina kin san wanda ba halina ba. Duk abinda na aikata kuskurena ne dan Allah kiyi hak’uri ki yafe min duk abinda nayi miki, nayi miki laifuka da yawa wanda ni kaina bazan iya lissafa su ba amma nasan kin san su, dan girman Alalh badan ni ba darajar wacce take kusa dake a zaune ki yafe min Ameena.” Ameena tayi shiru fad’uwar gaban da ta jima bata ji ba taji a wannan lokacin abubuwan da suka faru suka dawo idanun ta ta kulle idanun ta bud’e ta dawo da nutsuwar ta a tare da ita ta bud’e tace, “sai yanzu kasan kayi laifi kenan? Sai yanzu zuciyar ka ta raya maka kazo ka bawa Ameena hak’uri ko?” Sai tayi murmushi tace, “to kaje ka jira lokacin da naga damar yin hak’urin zanyi amma yanzu banga dama ba kuma banyi niya ba.” Sakkowa yayi daga kan kujarar ya sauke guiwar sa a k’asa yana kallon ta yace, “nasan nayi laifi nasan nayi kuskure nasan na b’ata miki na k’ona miki zuciya, watakila ma bakya son ganin fuskata ko kiji maganata, amma hak’uri ki yafe min shine burina shine kuma fatana, sai kin yafe min zanji dadi a zuciyata wallahi. Yafiyar ki nake so a wannan lokaci dan na tabbatar sai kin yafe min zan samu sassaucin abinda nake ji a zuciyata. “Bazan yi hak’urin ba sai me?.”D’ago ido yayi ya kalle ta sai ta mik’e zata bar wajan ta kalli Yaya Adam tace, “Yaya bana son tunawa da abinda ya wuce meyasa ka bashi damar shigowa har cikin gidan nan? Yaya baka son ganina cikin damuwa meyasa amma ka bar damuwar ta shigo har tana magana Dani?, wallahi ganin sa kawai damuwa ce a wajena domin bana son tunawa dashi balle na ganshi wallahi.” “Kiyi hak’uri dan Allah, badan halina ba darajar iyayen ki Ameena ki yafe min.” “In dan halin kane kai kama isa kazo inda nake na fito? In dan halin kane ka isa kazo ka zauna a gabana kana cewa nayi hak’uri?, In dan halin kane shima yayan bazai barka ka shigo gidan nan ba balle ka samu damar zama a falon gidan har kana cewa wai nayi hak’uri to bazan yi ba. Yusuf bazan yi ba akwai abinda zaka yi ne?” Ta fad’a a fusace cikin tsiwa da rashin kunya. Yaya Adam ya kalle ta yace, “Ameena ki nutsu mana a gidan Yayan ki kike fa, hak’uri ne kawai in kinga zaki iya sai kice nayi hak’urin shikenan ta ba wani abun yake so ba bayan wannan.” Ameena ta koma ta zauna Yaya yace, “İn zaki hak’urin kice kinyi, in baza ki ba shikenan ai ba abin tashin hankali bane ba.” Yusuf ya sunkuyar da kai hawaye ya fara sakko masa Zaitun kallon sa take ta kalli Ameena tace, “Mummy daddy kuka” ta fad’a tana jan rigar Ameena tana nuna mata Yusuf da yake hawaye sosai kamar an kunna famfo. Anty Aisha ce ta shigo tana kallon su har zata koma sai Yaya Adam yace, “k’araso mana, tsohon mijin Ameena ne yazo bata hak’uri.” Aunty Aisha tace, “baban Zaitun kenan?.” “Shi fa, gashi a zaune.” Yusuf ya d’ago idanun sa ya sake kallon Ameena yace, “Kiyi hak’uri ki yafe min dan Allah.” Ameena kallon sa take yi ganin kuka da yake yi sai jikin ta ya d’an yi sanyi rashin kunyar da take ji da ita sai taji ta ragu bawai dan tausayi ba sai dan ganin babba kamar sa yana kuka ga kuma Zaytun ta tafi wajan sa ta rik’e shi itama tana kukan. Yaya Adam ganin jikin ta yayi sai yace, “zaki iya yin hak’urin ko baza ki iya ba?.” Tayi shiru kamar bazata ce komai ba kafin tace, “zan yi hak’uri kodan saboda Ammah, amma badan shi ko wani abun bashi ba. Zanyi hak’uri saboda y’an gidan su kaf amma badan shi ko shirgin sa ba” ta kalle shi tace, “kar ka saka a ranka nayi hak’uri saboda ka zauna a gabana kana kuka ko wani abun, sam sam wallahi, nayi ne saboda Ammah amma bayan ita kai baka isa na tsaya ma ina magana da kai ba wallahi. Nayi hak’urin shikenan ko?” Ta fad’a tana aika masa da harara. Yusuf bai iya cewa komai ba Yaya Adam ya kalle ta yace, “koma ciki.” Ta koma ciki ko waiwaiye babu ya kalli Yusuf yace, “to tayi hak’uri shikenan abinda kake so ko?.” Yusuf yana kuka sosai ya kalli Adam yace, “Yaya dan Allah ka sake bani Ameena a karo na biyu, nayi maka alqawarin….” Kallon da yayi masa ya saka Yusuf kasa magana yayi shiru gaban sa ya fad’i sosai domin lokaci d’aya fuskar ta canja daga sanyi zuwa zafiii mai tiriri sai ya sunkuyar da kai yana jira yaji saukar Mari a kuncin sa dan wannan kallon da yake masa bana mutunci bane, na nuna zallar rashin mutunci ne akan fuskar sa. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid Book3 32 Kallon sa kawai Yaya Adam yake b’acin ran da yake dannewa lokacin da suka wuce yaji yana tasowa ya bishi da kallon wulakanci yace, “tashi tsaye.” Jikin Yusuf a sanyaye ya mik’e tsaye Usman ma ya tashi ya kalle shi yace, “Dan na sakar maka fuska na baka dama ka shigo har cikin gıdana shine ka samu damar yi min wannan banzar magana?, ni zaka kalla ka cewa wai kana so na sake baka Ameeena a karo na biyu? Ni kake fad’awa wannan maganar dan baka da mutunci baka da kunya baka san ma kunya ba ko?. Ko cocaine din da aka kama a motar ka daman sha kake? Dan in ba wanda ya sha kayan maye ba babu wani irin ka da zai zo yayi min wannan banzar maganar har cikin gidana.” Yusuf jikin sa har rawa yake amma ya daure domin yaji ya gani yace, “Wallahi Yaya a wannan karon bazan yi abinda nayi a baya ba, zan rik’e Ameena hannu biyu zan bata dukkan farin ciki da ban bata ba a wancan lokacin, Yaya alqawari na d’auka kuma zan cika ka bani wata damar wallah….” Cikin tsawa ya katse shi yace, “zaka yi min shiru ko sai tsinke fuskar ka da marukan da zai saka kunne ka ya daina ji?. Alqawarin da ka yiwa mahaifinta yana kwance a gadon asibiti yana gangarar mutuwa shi baka cika ba sai nawa zaka cika?. Ni zaka kalla ka cewa wai zaka rik’e Ameena, ni zaka cewa zaka bata farin ciki Yusuf?.” Ya sunkuyar da kai yana kuka sosai Usman ganin haka yace, “Yaya kayi hak’uri, amma ka sake bashi damar watakila a yanzu ba Yusuf din baya bane ya canja bazai sake maimaita abinda yayi ba a baya. Ni shaida ne Yusuf din baya ba na yanzu bane ba wallahi.” Yaya Adam ya kalle shi yace, “ba da kai nake magana ta ba, lokacin da ya dinga wulakanta min k’anwa baka nan” ya kalli Yusuf yace, “in na sake ganin k’afar ka a k’ofar gidan nan wallahi sai na saka an maka dukan tsiya, in y’ar kace gata nan ka tafi da ita ka bar min tawa a nan daman ai ba da ita taje gidan ka ba. Da kuskure, da wasa, da zolaya ka sake furta min irin wannan banzayen kalaman wallahi Yusuf sai na nuna maka waye Adam, sai na nuna maka waye a gaban ka a tsaye.” Zubewa ya sake yi akan guwiar sa yace, “Alfarma d’aya, lokaci na biyu Yaya. Bazan iya rayuwa babu Ameena ba, bazan yi cigaba da zaman duniya babu Ameena ba. Ka taimaka min ka yi hak’uri ka sake bani ita nasan nayi kuskure amma zan gyara wallahi, zan canja wallahi, duk abinda ya faru bazan sake aikatawa ba zan rik’e ta hannu biyu Yaya zan tabbatar tayi farin cikin da bata…….” Marin da ya yiwa Yusuf sai da ya kusa fad’uwa ta baya, ya jure baya son Marin nasa amma ya kasa sai da ya aikata ya kalli Usman yace, “ja abokin ka ku bar nan kafin na zubar masa da haqoran bakin sa, sannan ina so ka ja masa kunne in sake zuwar min da wata banzar magana sai na karya k’asusuwan jikin sa. Ya san hana sonta ya wulak’anta ta? Yasan yana sonta yake dukan ta? Yasan yana sonta ya iya saka mata damuwar da ciwo ya kamata?. Ko so yake yace min duk wannan so ne? Ko so yake cemin ai kulawa ce ta jawo take da hawan jini a lokacin da take gidan sa?, har gobe magani take sha ta dalilin sa, kenan soyayya ce?. Ya manta Idon ta ya kalla yace alfarmar babar sa take ci da yanzu ya sake ta saboda ba sonta yake ba zaman dole yake yi da ita saboda mahaifiyar sa? Ya manta ne?. İn ya manta ni ban manta ba, ka fad’a masa wannan hawayen da yake, da wannan zubewa a k’asa bazai saka zuciyata taji tausayin sa ba, wallahi ya sake zuwar min da batun na sake bashi Ameena a karo na biyu sai nayi masa abinda ko a mafarki baiyi tununani ba.” Kuka sosai Yusuf yake yi kamar k’aramin yaro ya kasa rik’e kukan ya kuma rasa waye zai fahimce shi a halin da yake ciki yace, “Yaya dama ta k’arshe ta k’arshe dan Allah.” Kama k’ugu yayi ya dafe kai yace, “ka matsar da Yusuf daga nan kafin alfarmar iyayen sa da yake ci ta kau a zuciyata nayi masa dukan da zai kasa tashi.” Usman ya d’ago Yusuf daga yadda yake yace, “ayi hakuri. Yusuf mu je.” Ya girgiza kai yace, “taya zan tafi bayan Ameena tana gidan nan? Usman kai kasan bazan iya rayuwa babu ita ba, ka fad’a masa wallahi na canja ba Yusuf din baya bane ba, ka sanar dashi yanzu bazan sake aikata kuskuren da nayi a baya ba. Usman ka fad’a masa kafin ya raba ni da rayuwata.” Usman ya kalli Yaya Adam yaga yadda yake wuci babu damar yi masa wata magana sai yaji tsoro ya ja Yusuf yana k’in tawowa yana kallon Yaya yace, “Dan Allah Yaya, dan girman Allah badan ni ba, dan darajar iyayen ka” yana magana hawaye suna sauka Usman ya rik’e hannun sa suka fita shi kuma ya zauna a kan kujera Anty Aysha ma ta zauna kusa dashi zuciyar ta duk ta karye dan wallahi Yusuf ya bata tausayi sosai. “Kayi hak’uri, ya tafi ai ka sassauta zuciyar ka ko babu komai akwai Zaytun Tsakani kuma mahaifin ta ne.” Baice komai ba ya zabura ya yi wajan Ameena tana zaune a d’akin amma tana jiyo duk abinda yake faruwa yana shigowa ya bita da kallo yace, “Ameena a lokacin da kika nema da zan baki tsakanin ki da Al’ameen gobe nake so ki fad’a min abinda yake ranki, in kina so kina so in bakya so bakya so” yana fad’a ta juya ya fita ta bishi da kallo ta sauke numfashi ta koma ta kwanta a kan gadon. Kuka Zaytun take har lokacin itama ta juya ta kalle ta tana rarrashin ta tace, “ya isa kukan Malama.” Ta matso kusa da ita ta goge mata ido ta kwantar da ita a jikin ya sai tayi bacci. Yusuf ya gigice ya fita daga hayyacin sa kuka yake kamar ya mutu hankali Usman ya tashi sosai ya raba masa hankali daga tuk’in da yake yi. Nan da nan jikin Yusuf ya fara rawa haqoran sa na had’uwa da juna Usman yace, “Dan Allah Yusuf kayi hak’uri ka daina wannan kukan mutane suna kallon ka fa, in ka kwantar da hankalin ka komai zai zo da sauki amma sai anyi hak’uri.” “Mutane dan sun ganni Usman ba komai bane, zafi nake ji a kirjina, kaina ciwo yake min, zuciyata bugawa take. Bana son rasa Ameena, bana son rasa Ameena a wannan lokacin ka taimaka min Usman.” Hankalin sa ya tashi sosai a haka suka isa gidan Yusuf ya faka motar ya fito ya zagayo zai fito da Yusuf din yaji zafin da yake jikin sa hankalin sa ya sake shi ya koma motar da sauri ya shiga ya sake jan motar zuwa asibiti. Sai bayan an kwantar dashi an saka masa ruwa da allurai sannan ya samu damar yin sallah ya d’auki waya ya kira Abbah ya sanar dashi suna asibiti sannan ya zauna yana jinyar sa. Yana zaune a cikin d’akin Abbah da Ammah da kuma Mubakar da Abie suka shigo suka kalli Yusuf daga inda yake Ammah tace, “Usman me ya same shi haka? Kaga fuskar da yadda tayi ja sosai.” Usman yace, “Ammah komai ma damun Yusuf yake yi, ance jinin sa ya hau sosai ga damuwa da tayi masa yawa har ta haifar da zazzab’i mai zafi a jikin sa da ciwon kai. Yace kirjin sa zafi yake masa ban san ya zanyi na yayewa Yusuf damuwar sa ba.” Abbah yace, “meye yake damun sa hakan?.” “Abbah jiya Bauchi muka je gidan Yayar Ameena yaje ya bata hak’uri akan abubuwan da suka faru, ya kasa tunkarar Yayan ta saboda abinda ya aikata tsoron hakan yake ji. Yau ya daure munje wajan sa k’arshe kaga sakamakon abinda ya faru. Wallahi Ammah Yusuf d’in baya dana yanzu akwai banbanci, yana son Ameena wallahi, in ya rasa Ameena a wannan kadon zamu iya rasa Yusuf Ammah.” Mubakar yace, “in dai fahimta yaje bikon Ameena ko?.” Ya d’aga kai alamun Eh Mubakar yace, “lallai ma. Ai Yaya Adam din yayi k’ok’ari ma wallahi da bai fasa masa baki ba. Shi yanzu ba kunya ba tsoron Allah sai yaje yace a bashi Ameena dan girman Allah?.” Abbah yace, “laifin Usman din ne ma da yake biye masa har suka je suka samu Adam da maganar, yanzu in da k’anwar Yusuf d’in ce aka yiwa haka in mijin yazo ya same ku zaku sake bashi auren ta?.” Usman yace, “wallahi Abbah indai ya canja kamar yadda Yusuf ya canja zamu sake bashi. Yusuf ya canja, Yusuf ba na da bane ha wallahi yana son Ameena sosai.” Abbah yace, “soyayyar banza da wofi, duk abinda ya dinga yi mata ya manta yana son nata sai yanzu zai tuna?. Haka akwai dan ya tayarwa da yarinya hankali zai je yace yana sonta dan kawai ya b’ata mata rai ya tuna mata da abinda ya wuce?. Shi yanzu waye ya bashi k’arfin guiwar zuwa ya samu Adam dan girman Allah?. Wannan ai kamar cin zarafin Adam din ne, duk abinda ya aikata bai gani ba har yana da zarrar da zai je wai ayi hak’uri?.” Ammah tace, ‘“ni na kasa magana ma wallahi, yarinyar da ya yiwa wannan wulakancin shine yanzu ya koma mata yace wai yana son dawo da ita dan bashi ma da mutunci bai San abinda yake yi ba?.” Usman ya bud’e baki zaiyi magana ta dakatar dashi Tce, “dakata Usman kar ka kare shi dan ya kasance naka, kayi adalci akan abinda yake daidai kar ka zab’i son zuciya akan gaskiya. ni na haifi Yusuf nasan halin sa nasan abinda zaiyi nasan wanda bazai yi ba. Banda raini ma har yana da k’afar zuwa wajan Adam akan Ameena?.” Abbah yace, “yanzu dai a bar maganar nan kar a tashe shi a asibiti muke mu jira ya dawo daidai sai muyi maganar da zamuyi.” Usman ne a tare dashi har bayan sallar i’sha duk da ya farka idanun sa a bud’e yake amma bai ce komai ba har lokacin idanun sa a bud’e yana kallon wani wajan daban. Mubakar ne ya shigo yace, “Usman kana nan ashe.” Usman yace, “eh yanzu zan tafi.” Ya kalli Yusuf yace, “ba yanzu zamu tafi da shi Yusuf din ba?.” “Gaskiya basu ce ba akwai drip din da zasu saka masa gobe suka ce.” “Muje gida akwai a saka masa gobe tunda ya farka daga baccin, zaman asibiti ai sai dole.” “Da sai yafi ma.” Fita Mubakar yayi Jim kad’an ya dawo yace, “Yauwa muje, Yusuf muje” ya fad’a yana kallon Yusuf da idanun sa na kallon sama. Sai da Mubakar ya tab’a shi sannan ya fahimci ma magana yake yi dan yayi nisa a tunani ba ganewa yake ba yace, “muje gida ko?.” Kai ya girgiza kawai ya sakko da k’afar sa ya saka takalmin sa suka fito duk shiga mota suka tafi. Gidan Ammah suka wuce a lokacin babu kowa a falon Ammah Yusuf kai tsaye d’akin da yake kwana ya wuce ya kwanta a kan gadon yayi shiru shi ba bacci ba shi kuma ba tunani ba. Sai kuma ya tashi ya shiga band’aki yayi alwala ya fito yayi sallah ya zauna ya dinga addu’a akan Allah ya sake bashi Ameena. Mubakar ne ya shigo ya same shi a haka ya ajjiye leds akan gadon ya bud’e ya d’auko magani ya fito shi ya bashi yace, “likita ya ce kasha wannan maganin da Mun dawo gida.” Bai musu ba ya karb’a ya saka a baki ya bashi ruwa ya sha shi kuma ya fita. Ba jimawa bacci y d’auke shi a inda yake zaune dan maganin da zai saka shi bacci aka bashi dan ya samu lokacin sosai kamar yadda baya samun baccin. Washe gari da safe Abbah ya fito yana karyawa shida Ammah da Mubakar ya kalli Ammah yace, “banga Yusuf ko a sallar asuba ba, ya fito kuwa?.” “Anya kuwa ya fito? Mubakar jeka wajan sa ka gani.” Mubakar ya tashi ya shiga ya same shi a zaune da alama bai jima da tashi ba dan a lokacin ya idar da sallah yace, “Sannu, ya jikin?.” Kawai kawai ya girgiza masa yace, “kazo in ji Ammah tana zaune.” Yana fad’a ya fita shi kika ya tashi fito ya same su a zaune. A kan carpet ya zauna dan yafi jin dad’in hakan Ammah tace, “ga abinci nan zo kaci.” Y kalle ta yace, “Abbah barka da safiya, Ammah barka da safiya.” Suka amsa Abbah yace, “ya jikin naka?.” “Da sauki” ya fad’a a takaice yana kulle ido ya bud’e. “Likita yace a dinga baka abinci kana ci dan haka ka taso kazo maci abinci ka sha maganin ka” Ammah ta fad’a tana kallon sa. Yace, “Bana jin yunwa ne ko kad’an.” “Zaka ji, tashi ka zuba kaci.”Mik’ewa yayi ya zuba tea kawai ya koma ya zauna yana sha a hankali yana kallon wani wajan daban. Usman ne ya shigo bayan sa Abie ne da Yaya suka k’araso suka gaida Abbah ya amsa Usman ya kalle shi yace, “Yusuf ya jikin?.” Kai ya d’aga kawai kafin yace, “Allah ya kara Lafiya.” Ya amsa da amin kafin yayi shiru baice komai ba kowa ma kuma babu Wanda yace wani abun. Kallon Usman yayi yace, “muje ka raka ni wani waje.” Ya fad’a yana ajjiye tea din Ammah tace, “ina zaka je kai da baka da lafiya?.” Ya kalli Ammah yace, “Yanzu zan dawo.” Bata sake magana ba ya fita harabar gidan ya kalli Usman yace, “wa kake ganin zan sake samu akan maganar nan? Wa kake ganin zai iya rarrashin ta ta dawo koda bata sona ita da Yayan ta?.” Usman yace, “Yusuf ya kamata ka cire Ameena daga ranka daga yanzu, baka ji me akace maka ta kusa aure bane ba?.” “Ko yau ne d’aurin auren ta bazan hak’ura ba sai naga ta zama mallakin wani Usman, sannan babu wanda zai mallaki Ameena sai ni bayan ni babu wani a duniya.” Usman ya girgiza kai yace, “to naji, ni ban san wani waje ba kaje kayi jinyar kanka ni kuma na wu wajan aikin.” “Usman ka yarda dani in ban samu Ameena ba mutuwa zanyi, ka daure ka amince min ka shige min gaba wajan sake samun Ameena.” Usman yace, “Dani aka je wajan Adam, Dani yake yiwa fad’a yana cewa muka sake zuwa sai ya b’alla ka. Yusuf zan iya komai dan samar maka da farin ciki amma ina so ka sani kayi kuskuren da sai kabi a hankali zaka samu Ameena, wannan gaggawar da kake yi babu abinda zata haifar maka dashi sai dana sani.” “İn banyi gaggawa ba me zanyi Usman? Ya kake so nayi ina zan saka raina?.” “Hak’uri zakayi ka cigaba da addu’a Alalh zai kawo maka mafita.” “Ina yi Usman.” “To ka samu Ammah da maganar.” Da sauri ya kalle shi shima shi yake kallo yace, “eh ka fad’a mata, saka sha fad’a amma zata taya ka addu’a in Ameena rabon kace Allah ya sake had’a zaman auren ku.” Ya girgiza kai yace, “da wanne Idon zan iya kallon Ammah na fad’a mata wannan maganar dan Allah?.” “Da Idon sa ka kalli Adam mana, dashi zaka je wajan Ammah.” Ya sauke numfashi yace, “zo muje yanzu.” Usman yace, “A’a babu ruwana kaje kai kad’ai, ni zan wuce akwai bak’in da suke son fara kawo kaya suna son ganina Yanzun nan” ya fad’a yana barin sa ya shiga mota ya fita daga cikin gidan. Yusuf ya shiga falon ya samu suna tattaunawa harda dariya ya k’araso ya zauna a kusa da Ammah yana kallon tea din da ya ajjiye zuciyar sai bugawa take yii kamar lofin ne Ameena. Ya sauke numfashi mai nauyi ya runtse ido ya bud’e ya kalli Ammah da yake kallon sa kamar zai magana sai ya fasa yaja bakin sa yayi shiru. Juyowa yayi ya kalli Ammah yace, “Ammah!.” Sai kuma yayi shiru ta kalli Abbah da yake kallon sa ta kalli Yusuf din tace, “Na’am.” Ya kalli Abbah yace, “Dan Allah ku yafe min adadin b’ata muku ran da nayi a kwanakin baya, Nidai nasan ni Yusuf ne amma wani abun ina yin sa kamar ba ni. Wani lokacin ina cikin nutsuwata wani lokacin bana ciki dan Allah kiyi hak’uri ku yafe min.” Abbah ya kalle shi yace, “ai babu abinda kayi mana in ma akwai min yafe.” Ammah ta girgiza ki tace, “mun yafe kam.” Yusuf ya sauke numfashi yace, “Ina son na dawo da Ameena.” Ammah ta kalle shi tace, “me kace?.” Ya dago kai yace, “Ina son dawo da Ameena gidsn Amma, nasan nayi kuskuren da babu lallai ta yafe min amma ina so ki shige min gaba dan wallahi in ban same ta ba zan iya rasa raina.” Ammah ta girgiza kai tace, “Ahh lallai Yusuf akwai abinda ya tab’a maka kwakwalwar ka, da ace baka daina shan giya ba da nace giyar ce har yanzu bata sake ka ba. Ni zaka kalla ka cewa kana so ka dawo da Ameena? Yanzu kenan kana sonta?.” “Wallahi Ammah soyayyar Ameena bata tab’a barin zuciyata ba, nasan wani abun ina sane amma wani abun sai anyi nake dana sani Ammah.” “Karya kake, ka manta cewa kayi nice nace kaje ka auro Ameen Yusuf? Ka manta cewa kayi ba son ta kake ba alfarmar ta take ci kake zaune da ita?. Ka manta cewa akayi badan ni ba da yanzu ta jima da zama bazarawa?.” Ya girgiza kai yace, “Ko a lokacin karya nake wallahi, na fad’a ne saboda dalili na amma wallahi k’arya nake yi Ammah ina son Ameena har yau har gobe har jibi har na mutu.” “Yi min shiru kafin na buge maka bakin ka, ni zaka cewa kana sonta har gobe? Ka manta abubuwan da kayi mata ne da zaka zo ka saka ni a gana da yake ka Raina ni?.” Yace, “Ammah har zuciyata nake fad’a miki ina son dawo da Ameena ki amince dani.” “Oh na gane abinda kake nufi, ka auri b’arauniya, kazama, mara tarbiyya, mahaukaciya yar gidan k’ananun mutane kaga baka samu abinda kake so a wajan ta ba shine yanzu ka dawo kake son dawo da Ameena ka cigaba da dukan ta yadda kake so ko? Dan Kaga waccan bata kyale ka in ka daka ramawa take shiyasa kake son sake d’auko Ameena domin ka cigaba da dukan banza ko?.” Ya girgiza kai yace, “A’a Ammah, ba haka bane ki fahimce ni. Wallahi bazan sake kuskuren ma dukan Ameena ba, na canja wallahi.” “Har abada bazan fahimce ka b indai akan Ameena ne, duk soyayyar da nake nunawa yarinyar nan hakan bai hana ka wulakanta ta ba, ka ci zarafin ta ka lalata mata rayuwa ka d’ora mata ciwon da ko ni babar ka bani dashi. Ka dake ta, ka zage ta,kayı mata k’arya da sharri da k’age, ka daina sauraron ta har ta Kai ga tana sahan magani domin kare kanta daga fad’awa halaka, itace zaka zo kace min kana so na yarda?. Itace zaka ce zaka dawo da ita na shige maka nayi iso a wajan ta da yake bani da kamar kai ko?.” Ya kulle ido nadasani ta gama dabaibaiye shi ji yake ina ma ana dawo da abinda ya wuce da ya dawo dashi ya goge rayuwar sa da Ameena da duk b’ata mata rai din d yayi. Ammah tace, “y akayi shiru? So nake kace min ai ba haka bane kai kana sonta Yusuf, har kana da bakin cewa zaka dawo da Ameena dan baka da kunya baka da mutunci baka San ma kawaici ba ko?.” Yusuf ya bud’e ido yace, “Tun kafin Asiya ke shaida ce Ammah ina sonta, har na aure ta ina sonta wallahi kawai kuskurena abinda na aikata mata nasan nayi kuskure shima kuma….” Abbah da yake gefe yace, “shima me Yusuf?.” Ya juya ya kalle shi Abbah yace, “Yusuf in y’ata ce Ameena ta gama auren ka har abada, dan haka itama ta gama auren ta dan kamar ni na haife ta haka nake ji, kar na sake jin maganar Ameena a bakin ka dan baka cancanci ambatar sunan ta ba, dan haka babu kai babu Ameena kar na sake ji ko ganin kaje gidan su akan wannan maganar.” Kamar zaiyi kuka yace, “Amma Abbah…” ya dakatar dashi yace, “Umarni na baka ai ba shawara ba, in matar ka kake son dawo da ita kaje ka samu Asiya ka dawo da ita amma ba Ameena ba Kaji na fad’a maka” ya fad’a yana tashi ya fita Ammah ma ta fita aka bar Yusuf a zaune a wajan cikin tunani da kuma tashin hankali. Book3 033 Yusuf jiki a salub’e ya tashi ya bar falon Abbah yaja tsaki bayan ya bar wajan cikin takaicin saken da yayi ya rasa yarinya kamar Ameena Ammah tace, “ikon Allah, wai dan ma bashi da kunya Ameena yake so ya dawo da ita ya manta abubuwan da yayi mata a baya.” Abbah yace, “bai san abinda yake yi ba ai, in yasan abinda yake yi bazai yi gangancin aikata hakan bama.” Ammah ta sauke numfashi tace, “gaskiya dai kam bai san abinda yake yi ba. Ya manta abubuwan da suka faru a falon nan wanda aka zayyano mana ya aikata, amma yanzu dsn bashi da kunya yana so ya sake komawa.” ta fad’a a bayyane amma zuciyar ta tausayin sa take ji sosai ma kuwa. Yusuf tunda ya koma d’aki ya kwanta yana juyi ya rasa me yake masa dad’i, rana zafi inuwa k’una haka komai ya zamar masa, zuciyar sa kamar dutse aka saka mata a sama da k’asan ta haka yake yin zafi da rad’ad’i a ciki. Tashi yayi ya fito yazo ya wuce su a falon ya fita daga gidan gabad’aya ya koma gidan sa ko zai ki kewar Ameenan ta neman yiwa zuciyar sa illa, ko wanne lokaci Ameena, ko wanne yanayi Ameena haka zuciyar sa take kasancewa a yanzu. Rukayya tunda sukayi wannan maganar da Ibrahim shikenan baya walwalaa ta rasa gane kansa gashi ranar juma’a ce washe gari tafiyar su hankalin ta gabad’aya baya tare da ita sai Umma ce take fad’a mata yadda ake had’a kayan tafiya tana had’awa saboda mantuwa. Bayan sallar juma’a ya dawo da leda a hannun sa ya ajjiye mata a gaban ta yace, “ki saka a jakar ki” yana fad’a ya shiga d’aki ta d’auki ledar ta bud’e taga soson wanka ne da sabulu da sabon abin wanke baki da sauran su. Ta d’auki ledar tabi bayan sa ta same shi a zaune ya cire rigar jikin sa ta zauna tace, “Wai duk akan maganar ranar nan ne shine har yanzu ka ke fushi dani? Na baka hak’uri ya kamata ace ka hak’ura ban fad’i maganar saboda wani abun ba kai ka sani.” Ya zauna sosai yace, “Akan maganar Fiddausi zanyi fushi Rukayya? To akan wanne dalili ma zanyi fushi a kan maganar ta?.” “To gashi kana fushi ka kasa sakewa kamar baya.” “ni ba fushi nake dake ba, domin banga abin fushi a abinda kika ce ba balle nayi, magana kika yi akan gab’ar b’acin ran da nake ciki a lokacin shiyasa ban ma saurare ki ba, in nayi fushi dake magana ma bazan miki ba dan ban iya fushi ba. Ban tab’a fushin bane kiyi fatan kar nayi, bana yawan fushi ko da yaushe, amma in nayi sai kin gwammace gwara nayi kad’an-kad’an na hak’ura.” Tace, “to kayi hak’uri dan Allah.” “Nace miki ba laifi kika yi ba kece kike ganin kamar laifi kika yi shiyasa kike baya-baya dani, Amma ni baki min komai ba meye abin b’acin rai a maganar ki to?.” Tayi Ajiyar zuciya tace, “har naji dad’i wallahi.” Yayi murmushi yace, “da gaske?.” Ta daga Kai alamun eh ya sake yin murmushi yace, “kin gama had’a komai naki? Kar kiyi mantuwa fa.” Rukayya tace, “Komai na had’a sai abinda ka bani yanzu, shima yanzu zan saka. Umma tace min ana tafiya da yaji wai harda maggi, gashi can na daka d’azu da yawa har su Hajiya na saka a jakar.” Yayi dariya yace, “kin had’a kayan Amir?.” “Eh na had’a, d’azu da Zuhra ma tazo har na bayar ta tafi dashi wajan Umman.” Ya girgiza kai yace, “ki fad’awa Umma a barshi ya kwana biyu a wajan babar tashi, koda yake ma ai a Unguwa d’aya ne basai ya kwana ba zai dinga zuwa ko yaushe kamar ma yana wajan nata ne ko?.” Rukayya tayi dariya kad’an tace, “Gaskiya ne kam kusan ko yaushe ma yana wajan ta, zatayi farin ciki da hakan mum gode.” Baiyi magana ba sai Rukayya ta sake cewa, “wai baka ji kamar a mafarki zamu tafi makka?.” “Nifa sai naga mun tafi zan tabbatar gaskiya ne ba mafarki ba. Dan yanzu kam kallon abin nake kawai gashi nan dai ba gaskiya bane.” Tayi dariya tace, “balle ni da ban san ma tafiyar zata kasance har ni ba.” Yayi murmushi yana kallon ta itama shi take yi yace, “daman Allah yayi dake za’a je.” Ta girgiza kai tace, “haka ne kam.” “Yanzu meye Abu na gaba?.” “Sai dai mu jira goben mu gani” yayi dariya yace, “to Allah ya kaimu” ta amsa da amin suka cigaba da hirar su. Kamar yadda Yaya Adam ya cewa Ameena zata fad’a masa Sakamakon Al’ameen da yamma ya kira ta ta zauna ya kalle ta a nutse yace, “yau mukayi zaki tsayar min da magana, ya kike gani?.” Ameena ta sauke numfashi tayi shiru tana tunani kafin tace, “na amince Yaya.” “Kina nufin kin amince da auren Al’ameen?.” Ta daga kai alamun eh yayi murmushi yace, “shikenan to, Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Ina tabbatar miki da baza kiyi dana sanin zab’ar Al’ameen ba.” Murmushi take yi tana kallon sa kafin yace, “tashi kije.” Tashi tayi ta shiga ciki shi kuma ta fita ya shiga gidan Al’ameen din dan sanar dashi abinda yake faruwa. Murna wajan Al’ameen kamar an d’aura auren y dinga godewa Yaya Adam shi dai dariya yake masa kawai yana ce masa mai son auren yara shi kuwa murna kawai yake yi dan yaji dadi sosai kuma yana son Ameena ba kad’an ba. Asiya babu wanda take ragawa a gidan su har Umman gabad’aya su sun fita daga sabgar ta kowa harkar sa yake yi a share ta dan kiris take jira ka kula ta ta fara yi maka rashin kunya. Fitowa tayi d’aga d’aki ta zauna kusa da Umma tace, “Umma nida na gashi wallah, zan shirya naje har gidan Ammah na bashi hak’uri bazan iya cigaba da zama a gidan nan. Zanje ni na bashi hak’uri tunda shi bai zo ba. Ta Inda aka hau ai ta nan ake sauka.” Maimuna ta harare ta tayi tsaki tace, “in sha Alalh bazai mayar dake ba. Naira dubu d’ari biyar kawai ki bayar a biyawa Umma bashi kin kasa baya akan ki taci bashin, kuma kud’in nan ba da gumin ki kika samu ba balle kice kin san zafin nema, ajjiyewa akayi kika d’auka amma wai sai dai a fad’a miki yaushe za’a biya ki dan ma baki da mutunci baki san mutunci ba, dan Umma zata karb’i abin ki sai ta biya ki?.” “Kinga Yaya ni nasan wahalar da nasha na tara kudina dan haka bazan yi asarar dubu d’ari biyar a banza a biyan bashi ba, in za’a fad’a min ranar da za’a biya na bayar in ba’a za’a fad’a min ba bazan bayar ba.” Umma da take kallon ta tace, “kar ki bayar Asiya ki rik’e kayan ki bana so.” Asiya ta turo baki gaba tace, “Nidai zan tafi naje nayi bikon mijina, an kashe min aure an cuce ni” ta fad’a tana shiga d’aki sai gata da mayafi ta yafa ta fita da hannun ta guda d’aya. Maimuna yaja tsaki tace, “Ashe dai bata da hankali, da gaske zuwan zatayi fa.” Umma tace, “kyale ta, zata dawo da k’afar ta.” “Asiya bata da mutunci bata da hankali kuma.” Umma tace, “gashi ban san inda zan samo kud’in ba kuma Sakina akan kud’in nan sai ta kama ni.” Maimuna tace, “bara na je na binciko inda Atm din ta yake muje a d’auko kud’in koda bata so. İn yaso in ta dawo mu k’ona gidan.” Tashi tayi ta shiga d’akin da Asiya ta fito ta duba ko ina amma babu alamun ta kwashe kayan ta ta fito ta kalli Umms tace, “Wallahi ta kwashe komai.” Umma tayi Ajiyar zuciya kawai bata ce komai ba zuciyar ta amma cike take da takaicin halin Asiya abinda bata tab’a ji ba. Asiya kuwa kai tsaye gidan su Yusuf ta wuce mai gadin ya barta ta shiga dan ya Santa ta shiga falon da sallama a nutse suka amsa kowa ya juyo yana kallon ta dan Abbah ma yana nan tunda ya dawo daga masallaci bai sake fita ba sai sallah. Ammah tace, “A’a Asiya kece tafe?.” Tayi murmushi Jin Ammah ta kira sunan ta tace, “eh Ammah.” “Shigo ki zauna mana.” Ba musu ta k’araso ta zauna tace, “Abbah ina yini.” Ya kalle ta yace, “lafiya lau.” “Ammah ina yini.” “Lafiya lau Asiya, ya gidan naku?.” “Lafiya lau.” Daga nan tayi shiru bata ce komai ba Ammah ma tayi mata shiru daga baya tace, “Ammah daman nazo ne akan naji shiru har yanzu bai je ya dawo dani ba, wallahi na daina duk abinda nake yi bazan sake ba. Kuma ni ba dukana ma yayi ba fad’uwa nayi akan hannun shine ya karye, dan Allah ki bashi hak’uri ya mayar dani.” Ammah tayi murmushi tace, “Biko kika zo kenan?.” Ta d’aga kai alamun eh Ammah ta sake yin murmushi tace, “to ai bani zaki samu ba shi ya kamata kije ki samu da maganar bani ba. İn yaga zai mayar dake sai ya mayar tunda abin naku ya canja salo mace ce take zuwa biko.” “Eh kamun k’afa zanyi dake Ammah, ki taimaka min ki saka ya mayar dani wallah ko bacci bana iya yi.” Ammah ta kalli Abbah da su suke kallo ta sukayi dariya kad’an ta sake kallon Asiya yace, “Asiya sanda kuka yi fad’an ku bana wajan, kije ki same shi tunda shi bai je ba ke kin zo kinga shikenan sai ku daidaita.” “Asslamu alaikum” ya fad’a yana shigowa falon a snayaye kamar ko yaushe Ammah ta amsa kafin tace, “shikenan ma gashi nan yazo, Yusuf ga Asiya tazo bikon auren ka.” Ya kalle ta ya kalli Ammah zai wuce Ammah tace, “dawo nana kana gani kayi bak’uwa gata a zaune zaka shiga ciki kuma.” Yusuf yace, “Ammah ai na fad’a miki ni babu aure a tsakani na da ita” ya kalli Asiya yace, “kee! Na sake ki saki d’aya, biyu,uku. Kinji abinda nace ko? Na sake ki saki uku kar na sake ganin k’afar a gidan nan daga yau din nan.” Asiya ta dora hannu d’aya a kai tace, “Wayyo Allah na shiga uku, Yusuf kar kayi min haka ka taimaka min kar kace ka sake ni saki uku in ba haka ba ban san ina zan saka rai na ba, ka daure kayi hak’uri ka mayar dani wallahi zan canja daga yau.” Kamar zai magana sai ya fasa ya tsaya sosai yace, “kina so na mayar dake?.” Ta d’aga kai da sauri yayi murmushi k’arfin hali dan ta bashi dariya da alama ta haukace yace, “fad’a min duk abinda kika shirya a kaina tun kafin na aure ki har bayan aure ki.” Asiya tace, “ban gane ba.” Yusuf yace, “ina so nasan ya akayi ma kika saka na aure ki? Sannan wanne irin abubuwa kika yi a zama na dake a a kaina?.” Asiya tace, “indai na fad’a zaka mayar dani d’akina?.” Murmushi yayi jin abinda tace ya tabbatar bata da hankali yace, “eh.” Asiya ta gyara zama tace, “Tunda ka fara cewa kana sona muka tabbatar ba da gaske kake ba shine muka ce baka isa ka gudu ba sai ka aure ni, daga nan na fara saka maka magani in kazo gidan mu a abinci ko abin sha a haka har ka furta cewa zaka aure ni” ta tsaya sosa kai yace, “ina jin ki.” Asiya tace, “Nidai kawai kayi hak’uri basai na fad’a ba. Ka yafe min kawai na koma dan Allah.” Sai yayi hanyar barin wajan tace, “zan fad’a ka tsaya.” Ya dakata yana kallon ta tace, “Allah ya sani tun kafin nazo gidan ka na tsani matar ka saboda ta fini kyau, duk abinda nake fad’a a kanta ina nuna ina sonta karya nake wallahi. Burina nazo gidsn kawai na fitar da ita na mallake ka ni kad’ai.” Yusuf ya kalle ta yace, “Me kika k’ulla me akan hakan?.” “Tun daga kiran wayar ka da nace nayi ta d’auka ta zage ni, da zuwan su Yaya Maimuna kai kaya gıdan, da sace sark’a, da ce maka da nayi tace na sauka a hanya da muka tafi daga nan, da cewa Umma tazo ta mata wulakanci, da ranar ma da ka rabu da ita wallahi duk karya nake babu abinda Ameena ta sani a kai. Ina amfani da wayo na da basira da kuma rashin bincike da baka yi na isar da abinda nake so na isar kuma sai da Ameena ta bar gidan ka naji dadi. Gashi na fad’a maka dan Allah kayi hak’uri nidai ka mayar dani na dawo gidsn ka na cigaba da zama.” Yusuf kallon ta yake yi dan abinda tace bai ishe shi ba yace, “Daga nan kuma sai akayi me?.” Asiya tace, “Nidai a bar maganar dan Allah.” “Sai kin fad’a.” “To shine na cigaba da yi maka magani wajan kar ka komawa Ameena sannan kome zanyi baza ka iya d’aukar mataki a kaina ba balle ka iya saki na, Nidai kayi hak’uri ka yafe min na koma dakina dan Allah.” Yayi Ajiyar zuciyar ya kalli su Ammah da suke kallon ta yace, “baki da hankali daman ashe? Baki ji nace miki saki uku ba tun farko? Kina so kice ana mayar da saki uku ne?.” Ta rausayar da kai tace, “to ai babu wanda yasan saki uku ne kawai ka mayar dani bazan fad’awa kowa ba.” A fusace yace, “in na sake ganin ki a gidan nan wallahi sai na b’alla miki kafa ba hannu ba, zaki tashi ko sai na saka kare ya taka ki?”ya fad’a a fusace bata san ta zabura ba ta mik’e tana kallon sa tace, “kayi hak’uri dan Allah. Ammah ki bashi hak’uri ya mayar Dani.” Ammah tayi shiru bata ce komai ba Yusuf yace, “ki fita na ce, in Baki fita ba zan yi maganin ki wallahi.” Mubakar ne yazo wajan gani Asiya sai ya kalle ta yayi dariya yace, “A’a b’eriya uwar y’an sace-sace, me kike yi a anan?.” Yusuf y kalle shi yace, “daga yau in ka sake ganin ta a k’ofar gidsn nan ko a k’ofar gidana ka saka ayi mata dukan tsiya.” Mubakar yace, “an gama yallabai.” “Karen nan yana nan?.” “Yana nan mana, a sakar mata shi ne?.” Jin hakan sai Asiya ta fita da sauri Mubakar ya bita dan wallahi sai ya sake mata karen kodan ta gane kuren ta. Yana fita zata fita daga gate din ya k’arasa wajan karen da sauri ya sake shi sai kuwa yabi bayan ta a guje ta fita da gudu shi kuma ya dinga dariya dan ya tsane ya tsana mai muni. Gudu take a layin su Al’ameen sai da tayi nisa sannan ta tsaya tana waigen baya tana kuka shab’e-shab’e. Hakki take ga wajan babu kowa sai iya kad’ai a farko da k’arshen layin sai wasu maza da ta hango su uku suna nufo inda take. Suna zuwa tana juyowa ta kalle su gaban ta d’aya ya fito da wuk’a yace, “ko ki kawo kayan hannun ki ko na soka miki.” Jikin ta ya fara rawa sosai sai taji wuk’a an d’ors mata a bayan ta hannu na rawa ta d’auki wayar ta bashi gashi a bayan wayar atm din ta yake suka bar wajan a guje ita kuma haka ta tafi gıda tana kuka biyu abu biyu ya tarar mata. Asiya na fita Ammah ta kira Yusuf da ya koma ciki yazo ya zauna Abbah ya kalle shi yace, “meyasa kayi mata saki uku? Meyasa baka dawo da ita ba?. A yadda kake din nan ai kana buk’atar mata.” Yusuf ya kasa magana yayi shiru dan ransa a b’ace yake sosai Ammah tace, “da ka sani ka dawo da ita dan wacce kake son dawo da ita baza ta dawo ha Yusuf.” Sai ya kalle ta ya raussyar da kai yace, “ki daina min baki Ammah, ki taya ni da addu’a kawai zata dawo in sha Allah, kuma ai na fad’a muku ni na rabu da ita tun kafin tazo nan” ya kalli Abbah yace, “Abbah na canja bani bane wallahi, zan gyara kuskurena bazan saka aikata abinda na aikata ba, kayi hak’uri ku saka baki ta dawo wajena bazan saka ku dana sani a wannan lokacin ba, ina son Ameena ina qauanr Ameena, ban San Ina zan saka kaina ba in na rabu da ita ba, kayi hak’uri ka tallafa min wallahi bazan sake bata.” Ganin kuka yake yi sosai sai jiki Abbah yayi sanyi Yusuf ya tashi akan guiwar sa ya k’arasa gaban su yace, “zuciyata kullum bugawa take yi bugu na wuce ka’ida, anyi kuskure na sani amma a bani dama na gyara kuskuren nawa, na aikata laifi na sani amma a bani dama ba gyara laifin bawa, ina son Ameena wallahi bazan sake yi mata abinda zatayi kuka ba indai ba na farin ciki ba. Kuna ji a nan abinda tace tun kafin tazo gidana bata son Ameena, Wallahi akwai saka hannun ta a lamarina duk da nasan wani abun laifina ne. Abbah tunda na had’u da Asiya shikenan zamana da Ameena ya lalace, a wannan lokacin in ba zancen Asiya akayi min ba bana jin dad’i Amma, hakan ya saka nake ganin kamar itace take sakawa ki hana ni kula Asiya, na yarda na amince nayi kuskure babba amma zan gyara in ka bani dama ta biyu. Ammah shaida ce ina son Ameena, wannan soyayyar tare tana nan sai ma gaba da tayi, wallahi ko a baya indai nayi mata abu ssi nayi dana sani, to meyasa nake yi din indai nasan zanyi dana sani? Shine ban sani ba…!” Ya fad’a yana kuka sosai mai tsuma zuciya mai kuma sauti. Ya sake cewa, “Ammah a wannan Karon in ban samu Ameena ba zan iya rasa raina, abinda nake ji a zuciya a yanzu yafi wanda naji kafin na aure ta, ina sonta ina son dawo da ita amma ban san ya zanyi ba. Ina so na bata farin cikin da ban bata ba a baya amma guiwa ta sanyi take yi a ko wanne lokaci saboda bani da hanyar da zan bi dan na cika burina. Yayanta yace ya sake ganina sai ya saka anyi min duka, amma zan jure ko kashe ni zai saka ayi zan jure zan koma walalhi sai dai a dawo muku da gawata Ammah, in gawar tawa aka kawo ku yafe min ku cewa Ameenan ta yafe min kar naje lahira da hakkın ta a kaina kamar yadda zanje da soyayyar ta. Zan yi kokarin da yakin dawo da ita sai inda karfina ya k’are, addu’a nake so ku yi min kawai koda baza ku saka bakin ku ba, dan nasan akwai ciwo abubuwan dana aikata kuna jin kunyar Adam sosai, amma zanyi da kaina in sha Allah, nine na lalata kuma ni ne zan gyara, ko ni ko rayuwata” ya fad’a yana tashi ya fita yana goge idanun sa Ammah ta bishi da kallo tana hawaye sosai. Bayan ya fita Ammah ta kalli Abbah tana kuka tace, “Yusuf zai rasa hankalin sa fa.” Abbah ya sauke numfashi yace, “barshi ya sha wahala koda Ameena zata dawo yasan ba ta sauki ta dawo hannun sa ba, koda zata dawo yasan da cewa tayi masa alfarma ne bata dawo dan wani abu nsa ba. amma ni nasan bazata dawo ba domin Adam bazai bar Ameena a hannun Yusuf ba a karo na biyu ba.” Ammah ta share idanun ta tace, “Allah Sarki zuciya, uwa da d’anta, tausayin sa nake ji sosai, duk da banza ce ina so ya dawo da ita ba in Humaira ce bazan ce ina so ta koma ba, Amma ina jin tausayin Yusuf sosai wallahi.” Abbah ya sauke numfashi yace, “kiyi masa addu’ar kamar yadda yace Allah ya dawo dashi cikin hankalin sa kawai.” Ta kalli Abbah yace, “Amin, ko ina ya tafi ma oho. Shiru Abbah yayi bai amsa ba amma shi kan sa yaji tausayin Yusuf sosai ya kuma jii a ransa ya canja din kamar yadda yace. Da za’a bashi dama tabbas da za’a ga canjin amma damar cs baza ta samu ba. A haka Asiya ta koma gıda a haukace tana ta samu Umma Sakina tana rashin mutunci akan kud’in ta Asiya na shigowa tace, “Ko ki bani kud’ina ko na kai Uwar ki tayi zaman prison.” Asiya tana kuka sosai cikin nadamar fitar da tayi tace, “a tare ni an kwace wayata da atm din nawa a hanya, nasan kaf kud’in da suke ciki yanzu sun kwashe. in ma ku kuka tura a karb’a wallahi sai an biya ni ai ba ku kuka tara min kud’in.” Umma tace, “Asiya ki bada kud’in kinga ganin rashin mutuncin da ake min.” “To ina na gansu? Ina naga kudin bayan kun saka an kwace katin nawa? Wallahi sai Kun biya ni” ta fad’a tana ihu tana kuka sosai. Umma Sakina tace, “wannan ku ya dama kuma ai, abinda na sani kawai kudina in gobe tayi banga kudina sun shigo ba wallahi sai na kama uwar ku Atika” tana fad’a ta juya ta tafi. Maimuna ta kalli Asiya a fusace tace, “Dallah malama ki bada kudin daga baya duk inda zan samo miki zan samo na biya ki.” Asiya kuka take yi cikin bak’in ciki tace, “Banda y’an dabar da aka saka suka kwace min katin nawa a hanya? Wanne kud’i kike so na baku bayan nan? Wallahi nima sai an biya kud’ina nasan duk shirin ku ne bazan yafe ba wallahi” ta fad’a cikin ihuuu dan kud’in ta kawai take ji in aka kwashe an cuce ta. Umma tace, “ya zama dole na samo kud’in nan kafin gobe in ba haka ba Sakina zata wulakanta ni.” Baba ne ya shigo duk yana jin abinda suke cewa ya kalle su gabad’aya su in badan darajar yaran ba da yanzu ya jima da rabuwa da Umma amma yaran yake dubawa shiyasa yake d’aga mata k’afa. Wuce su zaiyi yaga Asiya a zaune tana kuka tana cewa, “yace min ya sake ni saki uku, na shiga uku a taimaka min kafin na mutu, bazan iya zaman gidan nan ba wallahi. Saki uku yace yayi min, na lalace ni Asiya.” Baba ya kalle ta yace, “dole ki zauna kuwa in ba haka ba sai ki kama gaban ki. Lalacewa kuma indai baku gyara halin da Uwar ku ta d’ora ku a kai ba yanzu kuka fara” ya fad’a yana shigewa ciki ya barsu. Umma tace, “saki uku naji kina cewa fa?.” Tace, “gidan su naje Umma, yace min ya sake ni saki uku, shikenan yanzu na daina zama a falo ina kallo, Nidai an cuce ni da aka raba ni da mijina wallahi.” Umma tayi shiru cikin jimami sai tace, “Tunda ya riga ya datse auren shikenan babu yadda zamuyi, gobe aje a kwaso kujerun falon d’aya na gidan aje a siyar sai a biya ta kudin.” Sai Asiya ga mik’e kamar a itace take kuka ba tace, “kujerun wa? Babu wanda zai tab’a min kayana ajjiye su zanyi in ya mayar dani na cigaba da amfani da kayana. Babu kayan da za’a kwaso min wallahi dan ba’a isa ba.” “Asiya wai kike yiwa wannan abubuwa akan abin duniya? Uwar ki ce ni fa?.” “Umma kece kika saka ya sake ni da yanzu ina gidana, meyasa kika saka ya sake ni dan Allah?.” Umma tayi shiru ta kalli Baba da yake kallon su taga yayi murmushi kawai ya fita. Itama wuce ta tayi kawai ta koma d’aki zuciyar ta a cushe sosai wai Asiya ce take mata wannan abun akan kud’i, kud’in da itace silar tara su badan ta sha wahala anyi auren ba da yanzu ba haka ba. Haka suka kwana Asiya kwana tayi kuka da danasanin abinda tayi gashi an raba ta da mijin ta tana ji tana gani ta zama bazawara. Washe gari da safe Umma Sakina ta sauka a gidan Baba ya fita lokacin Umma na tsakar gida tana tunanin kud’in Sakina sai kuwa gata harda y’an sanda. Suna shigowa tace, “Yauwa gata nan, bashi nake binta ta hana ni kud’ina muje da ita ko ta bani kudina ko a kulle ta.” Umma tsoro ya cika mata zuciya ganin y’an sanda tace, “Sakina ni zaki yiwa wannan wulakancin akan kud’i? Nice fa Atika k’awar ki kuma aminiyar ki.” “Ban sanki ba, ban kuma tab’a ganin ki ba, ki bani kudina ko kuma a tafi dake yanzu.” “Bani dasu, amma ki bani lokaci zan kawo miki.” “La la la! Wallahi bazan yarda ba, officer kama min ita.” Jami’iar tayi wajan Umma tace, “ki bamu hadin kai kawai muje in munje za’a iya sasanta ku in hukuma ta shiga maganar.” Umma tace, “Dan Allah ki bari mu sasanta a nan da mutuncina a ganni a wajan y’an sanda da sunan an kama ni babu dadi ai.” A lokacin Baba ya shigo ganin abinda yake faruwa yayi kamar bai gani ba Umma tace, “Malam ka saka baki kana ganin za’a tafi dani.” Baba ya kalle su baiyi magana ba ya shige daki. Su Maimuna suna kallo aka tafi da Umma Fauziyya tabi bayan ta duk da babu abinda zata iya. Asiya dai tana tsaye sai da aka tafi da Umman taji babu dadi a zuciyar ta jikin ta yayi sanyi tana dana sanin abinda tayi gashi bata da kud’in duk suna cikin account d’inta, amma zata san abinda zatayi dan karb’o Umman ta daga hannun hukuma. #Mai room #Book3 #paid #500 #Nana haleema. Book3 034 Asiya ta kalli Maimuna cikin sanyi jiki, dan sai bayan an tafi da Umma taji jikin ta yayi sanyi sosai tace, “shikenan zanje yanzu na d’auko wani abu a gidana sai naje na siyar na kai a karb’o Umma.” Maimuna tace, “da ke akwai wani abun kika bari aka tafi da Umma a gaban ki?, ina yake naje da kaina ke ba Lafiya gare ki ba.” Asiya tace, “A’a barni naje yanzu zan dawo” ta fad’a tana jan mayafi ta har zata fita sai ta koma ciki ta shiga d’aki ba jimawa ta fito ta fita ita ta manta ma wai tana wani abu idda ne a lokacin. Kai tsaye gidan ta ta wuce ta dinga buga gate din mai gadin yana can yana bacci kamar zata b’alla gidan haka take buga shi ya tawo ya bud’e ganin itace yace, “sannu da zuwa.” Ta kalle shi tace, “tun d’azu ana bugu baza’a bud’e ba dan an raina mutane?” ta fad’a shigewa cikin gidan kai tsaye b’angaren ta ta wuce. K’ofar na kulle kamar yadda ta barta ta saka key din ta bud’e ta shiga falon ta hau saman da sauri. D’akin ta shiga duk wani kayan ta na kadara da ta tara ta tattaro su ta zuba a jaka ta fito ta sauka tana kallon falon sai akwai ta fara kuka tace, “shikenan yanzu na bar kwana a gidan nan? Shikenan yanzu na daina zama a wannan kujerar?. Na shiga uku ni Asiya na cuci kaina, k’arya ta kaini ta baro ni Allah ya isa an cuce ni.” Motsi taji alamun ana shigowa falon gaban ta ya fad’i ta d’auka Yusuf ne sai taga Mubakar ya da mai gadi a bayan sa ya kalle ta yace, “ke zo ki fice kafin na kifar dake a wajan nan.” Shiru tayi bata yi magana ba ta sai kallon sa da take yi ta wuce shi tace, “na sake ganin k’afar ki a gidan nan wallahi sai na sab’a miki kammani, barauniyar banza da wofi. Uban me kika zuba a jakar?” Ya fad’a yana yin kanta zai ta kwasa a guje ya fita tsabar dariya sai ya kasa binta yace, “gayyatar tsiya” ya kalli mai gadin yace, “Yauwa baba, duk wanda ta sake zuwa gidan nan ka sanar dani.” Baba yace, “an gama.” Asiya a guje ta fita daga gidan tana waige sai ga mai adaidaita sahu a kusa da ita ta fad’a tace ya kaita kasuwar rimi ya kaita ta sauka ta bashi kud’i tana maqale da jakar hammata hannu a maqale ta shiga cikin kasuwa. Kai tsaye kantin Maryam Jumare mai saida gold da azurfa da saka haqorin makka ta nufa, dan ta ganshi babba sosai baza’a cuce ta ba tana shiga ta zauna mai kantin da yaran sa a zaune yace, “Barka da zuwa.” Tace, “barka dai.” “Siya ko siyarwa?.” Asiya tace, “siyarwa.” Ya d’aga kai yace, “mu gani.” Ba musu ta sakko da jakar ta fito da sark’ar ta ajjiye masa. Kallon sark’ar yayi sannan ya kalle ta ganin ta wata tagaja-tagaja ya d’auki sark’ar ya auna gram din ta ya sake kallon Asiyan sannan yace, “ina y’an kunnen?.” Asiya tace, “a haka take, kyautar ta akayi min.” Ya girgiza kai yace, “to ina receipt din?.” Asiya ya dan yi jimm kafin tace, “ya kone a gobara da nayi da ita akwai na tsira, a wajan gudu gobarar ne ma na karye a hannu ka gani.” Yayi murmushi yace, “Allah sarki, to nawa zaki siyar?.” Ta kalle shi dan bata san ya ake yin abin ba sai tace, “nawa zaka siya?.” “Ke zaki fara yi mata kudi, in naga zan siya a haka na siya in zan rage sai na rage.” “Ka kawo miliyan biyu.” Kallon sark’ar yayi ya kalle ta ya girgiza kai yace, “Haba hajiya na bada dai miliyan d’aya a bani.” Ta kalle shi tace, “Gaskiya bazan siyar haka ba.” Yace, “shikenan da dari biyar Allah ya saka musu albarka.” Asiya ta sauke numfashi yace, “to kawo.” Ya fita daga da inda yake yace, “ina zuwa” ya fad’a yana fita ya barta a zaune da yaran sa da suke ta aiki a wajan. Jim kad’an sai gashi ya dawo ya nuna Asiya yace, “barauniya ce.” Asiya gaban ta ya fad’i ta tashi tsaye tace, “Kamar ya barauniya, nice barauniya?.” Ya nuna musu sark’ar yace, “kunga sark’ar da ta siyar a baira miliyan d’aya da dari biyar.” Mutanen suka kalli sarkar suka kalle ta wani yace, “ahh wannan ko a b’arayin ma bagidajiya ce, wannan sarkar da zata haura miliyan goma a yanzu saboda tsadar dala shine ta siyar haka?." Asiya tace, “ni ba b’arauniya bace, wallahi ba b’arauniya bace ba ni.” “Karya kike wallahi, yau a cell zaki kwana, badan da hankalina ba da kin jawo min bala’i a garin nan. Wannan sarkar kana gani kasan k’era ta akayi ta wata matar Alhajin ce watakila ita kad’ai ce mai irin ta duniya a yanzu shine zaki d’auko kika zo kika kawo min ko? Yau a station zaki kwana.” Asiya na kuka aka tasa keyar ta aka tafi da ita wajan yan sanda. Washe gari ranar asabar jirgin su Rukayya zai tashi da karfe sha biyu na rana tun safe suka fita daga gidan suka wuce gidan su Rukayyan tare dan ya yiwa su Umma sallama. Da sallama Rukayya ta taga Amir yana ganin ta ya taso yana mata oyoyo ta zauna suka gaisa da Umma Umma tace, “tun d’azu yake maganar ki sai gaku, k’arfe nawa zaku tashi?.” “Zuwa sha biyu akace.” Umma tace, “Allah ya kai ku Lafiya ya dawo daku Lafiya.” Ta amsa da amin sai ga Ibrahim ya shigo shima suka gaisa Umma ta dinga yi masa godiyar da bai San dalilin ta ba har yaji nauyin hakan shi kawai murmushi yake yana amsa addu’ar da take yi masa. Baba ne ya shigo nan ma aka sake sabuwar gaisuwa Ibrahim ya fita har zai shiga mota sai yaji ana masa magana, yana juyowa yaga mahaifin Fiddausi sai ya fad’ad’a murmushin sa ya k’araso ya duk’a har kasa ya gaishe shi Abba yace, “Ibrahim yanzu ake fad’a min abin alkhairi, kai naji dadi Allah ya sanya alkhairi ya kai ku Lafiya ya dawo daku Lafiya, Allah ya amsa ibada.” Ibrahim ya amsa da Amin kafin Abba yace, “yanzu da ban ganka ba tafiya zakayi baza mu gaisa ba.” Ibrahim ya murmusa yace, “A’a Abba daman zan shiga mu gaisa.” “Ni nasan hakan, kar na tsyaar dakai Alalh ya kai ku Lafiya ya dawo daku Lafiya.” Ya amsa da amin Abba ya tafi shi kuma ya shiga mota. Yana zaune a motar ya hango wata mace da hijjabi ash kala ta tana tunkaro inda yake sai da tazo daf dashi ya gane wacece sai ya kulle idanun sa ya bud’e a lokacin ta wuce shi ta shiga gidan su Rukayya. Numfashi ya sauke ya jingina da kujerar yana girgiza kai Wato komai na duniya fararre ne kuma kararre. A bayyane yace, “badan ma ta rabu dani ba da rayuwata bata canja haka ba, da watakila ina nan ina Shan gorin bani da wannan bani da wancan. Ni na gode Allah ina sake gode masa da ya saka Fiddausi ta rabu dani silar hakan Rukayya ta shigo rayuwata. Allah na gode maka da kayi min chanji mafi alkhairi.” Yana zaune yana murmushi sai ga Rukayya ta fito da Amir da kuma fiddausi Amir Fiddausi ta rik’e shi suna tunkaro motar da yake. Fiddausi yaga ya tsaya tana yiwa Rukayya magana harda hawayen ta sai yaja tsaki yayi murmushi yace, “Rayuwa kenan.” Rukayya ce ta k’araso ta shiga motar Amir tana d’aga mata hannu Ibrahim yaja motar suka bar unguwar zuwa gidan su. T murmushi taga yana yi yana kallon ta itama tayi murmushi tace, “me yake saka ka murmushi haka?.” Ya sake yin murmushi yace, “murmushin mallakar ki matsayin mata nake yi.” Tayi yar dariya tace, “Gaskiya akwai wani abun bayan wannan.” Yayi dariyar shima baice komai ba suka cigaba da tafiya. Y’an uwa an cika a gidan ana ta murna wannan yana ni abaya za’a siyo min wannan zamzam, wani turare takalmi wannan yace dabino. Shigar su ya saka gidan ya sake rikicewa ana ta murna sha d’aya na rana tana yi aka tafi kaisu airport cikin farin ciki da ko wanne sun yake ciki. Yusuf yana kwance akan kujera yana abinda ya saba wayar sa sai k’are take yak’i ya kalle ta balle ya kula wayar, gajiya yayi da kiran ya d’auko wayar ya duba ganin bakuwar lamba sai yayi tsaki ya d’auka daga can b’angaren akace, “kana magana daga nan police station na fagge. Muna magana da Yusuf ne?.” Yusuf yace, “eh shine.” “Mun kama matar ka Asiya da laifin satar sark’a ta kuma je zata siyar.” “Kar ka sake cewa matata ni ba matata bace ba, sannan ni ban san wa kake magana a akai ba.” “Asiya dai matar ka domin ita ta bamu lambar ka tace kaine mijin ta, da zaka zo da zaka ga komai ka kuna ji komai.” Yusuf tunani yayi kodai sark’ar Abba ce tunda gashi ance taje zata siyar, tunanin hakan ya saka yace, “shikenan zan turo” yana fad’a ya yanke wayar ya kira Mubakar ya tura shi dan ya karb’o sark’ar ba wai ita ba. Yusuf ya sake yin shiru bayan ya gama wayar yana tunani abinda yake damun zuciyar sa yayi yawa, zuciyar tayi masa nauyi sosai gabad’aya baya jin dad’in zaman duniyar komai ya fita daga ransa. A bayyane yace, “Yanzu haka zan zauna bani da mafita?, Ina na saka gaba?, Ina zan saka Raina ne?.” Tashi yayi ya canja kaya ya fito ya hau mota ya wuce gidan Usman. Usman yana ganin sa ya girgiza kai yace, “ina kuma zamu je?.” “Kayi hak’uri dani bani da wanda ya fika. Zan koma gidan su Ameena ne Usman, ko meye zai faru sai dai ya faru amma wallahi sai naje. İn an aiko da gawata kayi min addu’a” ya fad’a yana fita Usman ya biyo shi yace, “Yusuf kar kaje dan Allah, ka manta abinda yayan ta yace ne? In kaje yanzu duk abinda yayi maka kai ka ka siya da kudin ka.” Yusuf yace, “wallahi sai naje, ko meye zai faru sai naje wallahi. Shiyasa nazo na fad’a maka koda zan mutu a can.” Usman yace, “Shikenan ka jira muyi sallar azahar sai na raka ka.” Yusuf ya juyo ya kalle shi yace, “ni yanzu nake son zuwa.” “Gaggawa daga shaidan take ka jira muyi sallar sai mu je.” Yusuf ya dawo ya zauna Usman ma ya zauna ya kalle shi yace, “Yusuf kana son Ameena har haka ya akayi kayi sake har ta kubce maka dan Allah?. Yadda ka fita daga hankalin ka ya tabbatar min da kana sonta sosai.” Yusuf ya kalli Usmsn yace, “k’addara da rabon na sha wahala, k’addara da rabon na gane mahimmaci Ameena, k’addara da rabon na gane ita kawai nake so, k’addara da rabon na gane Ameena ba irin matan da za’a samu da sauki bace ba Usman. K’addara da rabon na banbance meye asalin so a zuciyar mutum, wallahi son da nake mata yanzu ya ninka na baya sau babu adadi.” Usman ya sauke numfashi yace, “haka ne. Amma yanzu baka ganin in ka komawa yayan ta yanzu akwai matsala?.” “Ko meye Matsalar zan jure.” Usman yace, “shikenan to.” Suna nan zaune har akayi azahar suna idarwa suka d’auki hanyar gidan Adam. A lokacin suna tare da Al’ameen suna tattauna yadda za’a yi bikin a gama kafin ya tafi Kalaba, Adam yace, “tunda a nan zaku zauna sai ta cigaba da karatun ta.” Al’ameen ya kalle shi irin kallon nan na Anya zatayi karatu Adam yace, “Wallahi kana cewa baza tayi ba an soke wannan auren, ai tun farko na fad’a maka da batun makarantar nan kuma ko na gaba wallahi baka isa ka hana ta ba.” Al’ameen yayi dariya yace, “ikon Allah! kana bani mamaki Adam, nida matata kace min wai ban isa na hanata ba?.” “Ai fad’a maka nake, wallahi sai taje makaranta ka daina min wani kallo daga wannan munafukin glasses din naka na makafi.” Al’ameen yayi dariya yace, “nima bance zan hana ta ba ai?, karatu zatayi daga nan har taga karshen littafi.” “Yafi maka dai” Inji Yaya Adam yana haraarar sa. Al’ameen yace, “Yanzu gobe za’a fara aikin wannan gidan nawa Ina ha Allah.” “Me za’a gyara? Naga gidan yana da kyaun har yanzu.” “Amarya da zan saka, ai sai a sake fenti an canja komai na gidan wallahi. Bani da wanda zai gaje ni in na mutu ga mata zan saka wacce zanyi fatan zata haifar min magada. Meye amfanin kud’in in ba’a kashe su yanzu ba?.” Adam yace, “lallai kanka rawa yake akan yarinyar nan.” Al’ameen yace, “bari ayi auren ma, wannan shegiyar tsawar da kake mata wallahi ka sake sai na baka mamaki.” Adam yayi dariya yace, “wannan kuma kayi kadan, tun kafin ayi d’aran akayi kwandi.” Sukayi dariya su biyun kafin yace, “bara na kira Ameenan muji yaushe ne zasu fara exams din in suka gama ayi bikin a gama.” Yaya Adam ya d’auki waya ya kira ta yace ta same shi a falo ba jimawa sai gata ta zauna tana sunkuyar da kai Al’ameen yace, “matar ki daina wannan jin kunyar dan Allah, Adam ne fa ba wata tsiya ba in kina haka sai ki saka yaga kamar ma bakya sona.” Murmushi tayi kawai Adam yace, “in baka bini a sannu ba zan nuna maka mahaifin tane ni.” “In ka fasa baka qauanr Allah, kai dole ma ayi auren nan da wuri wannan gadarar da kake min ni ne zan yi maka ita nan gaba.” Adam yayi dariya yace, “Kai dai k sani” ya kalli Ameena yace, “Kina ji Ameenatu? Yaushe zaki fara exam?.” Ameena da take murmushi dramar su na bata dariya ta bud’e baki zatayi magana aka shigo falon da sallama sun suka amsa tare da kallon wanda suka shigo. Yusuf yana shigowa ya tsaya cak daga gefe bai k’araso ba Adam ya kalle shi yace, “baka jin magana ko?.” Yusuf ya girgiza kai yace, “bana ji indai akan abinda nazo dashi ne, kayi hak’uri na taka umarnin ka amma wallahi ko naman jikina zaka saka ana yanka bazan daina zuwa ba.” Adam ya kalli Usman yace, “a gaban ka nayi masa warning meyasa ka bari yazo?.” Usman yayi shiru Yaya Adam yace, “alfarmar da kake ci zaka daina cin ta, daga wannan lokacin lokacin zaka yi dana sanin wani Adam a rayuwar ka.” Kawai Yusuf ya zube a wajan a k’asa kan tiles yace, “koda gawata za’a fita da ita daga gidan nan na amince indai zaka saurare ni. Wallahi bazan fasa cewa ina son Ameena ba, bazan fad’a cewa ina son mayar da ita ba, bazan fasa cewa nazo neman auren ta karo na biyu ba.” Wani irin tafasa zuciyar Adam tayi ya taso a haukace yazo wajan sa ya saka hannu d’aya ya d’ago shi yace, “y’arka da iyayen ka ya saka nake raga maka amma naga abin baka yayi yawa baka san kara ba ko?.” “Na Santa, itace ta ta saka nazo nan. Meyasa ka kasa yarda nayi na gane kuskurena kuma zan gyara shi a wannan lokacin?.” Bai san ya mare shi ba saboda yadda zuciyar sa take tafasa sai ganin tsallen jini yayi akan tiles wanda ya fita daga bakin sa saboda azaba da zafin Marin. Yusuf sai da kunnen sa yayi dummm ya d’ago bakin sa a fashe ya kalle shi yace, “Wallahi ko yanka ni zakayi bazan daina fad’a ba” ya sake zubewa a k’asa yace, “laifi nayi n sani amma a sake bani dama wallahi zan rik’e Ameena fiye da kowa a duniyar nan, zan bata farin cikin da babu wanda zai bata shi a duniya, zan tabbatar da kwanciyar hankalin ta fiye da ko wanne lokaci a duniya. Duk abinda ake tunani wanda ya gabata ya wuce wallahi bazai sake faruwa ba, a wannan Karon babu zubar da hawaye a kan Yusuf sai saj hawayen farin ciki. Burina, fatana ka amince min ka bani dama.” Yaya Adam ya ma rasa abinda zaiyi masa shi kuma ya juya ya kalli Ameena da take tsaye a wajan yace, “eh Yusuf a wajan ki mai laifi ne babba, Yusuf a wajan ki mai kuskure ne, Yusuf a wajan ki abin ja baya ne, Yusuf a wajan ki dodo ne ni na sani Ameena. Amma ki yarda wancan Yusuf din da wannan Yusuf din akwai banbanci, wancan Yusuf din ya jima da mutuwa wannan wani sabo ne a gaban ki wanda yake so ki bashi dama shima ya wanke kuskuren wancan Yusuf din Ameena. Ameena bana iya bacci saboda tunanin ki, bana iya cin abinci, na daina zuwa ko ina ko yaushe ina kwance kece abincina kece ruwana kece kuma aikina. wani kuskuren sai bayan mun aikata muke ganewa munyi, wani kuskuren sai wani abun ya same mu muke ganewa mu dawo mu gyara, in muka gyara kuskuren kuma sai kiga yafi baya kyau. Allah yana sake bawa bayin sa dama a lokaci da suka yi laifi suka tuba yana sake basu dama ta biyu har ta babu adadi ma domin su wanke laifukan su. meyasa baza ki sake baki wannan damar ba Ameena? Meyasa baza ki amince ki yarda wancan Yusuf din yanzu bashi bane ba? Ko badan ni ba ki kalli y’ar mu gata a kusa dake dan Allah kar ki bari ta tashi ta girma a ba’a tsakanin iyayen ta ba.” Muryar sa ta sarqe yayi shiru muryar na rawa yace, “ki yafe min dan Allah, ba dan ni ba koi sake bani wata damar ba, dan ni ba kodan saboda Zaytun gata a kusa dake.” Zaytun da ta fito a lokacin ta k’arasa ta zauna a jikin sa tana kallon fuskar sa tace, “mummy jini.” Yusuf ya rik’e ta a jikin sa yace, “ita kanta tana so ta kasance a tsakanin mu Ameena, meyasa kike so ki raba ta da iyayen ta tun tana karama?. Dan Allah ki bari ta tashi a cikin mu tasan dadin iyayen ta guda biyun in kika farraqa ta shikenan kin raba ta da Jin dadin da ko wanne da yake ji in yana cikin iyayen sa. Ameena na yarda ko dukana zaki yi kullum na yarda indai zaki sake bani dama, Ameena ko baza ki yi min magana kullum ba na yarda ki sake bani wata damar, Ameena koda zaki saka wuta ki kona ni na yarda na mutu a matsayin mijin Ameena ba’a tsohon mijin ta ba.” Yayi murmushi yace, “kuskure nine kuskure da kansa ma ba aikata shi nayi ba. Amma dama ta k’arshe kawai Ameena ki taimaka kafin hankalina ya bar jikina” ya juyo ya kalli Yaya Adam da fuskar sa da take a jiqe da hawaye ga jini a gefen bakin sa yace, “na yarda na sab’a alqawarin Baba, amma a yanzu bazan sab’a alqawarin ka ba, zan cika dukkan alqawarin da kake so akan kula da ita kuma na tabbatar zanyi bazan sab’a ba, rana d’aya in na sab’a na amince ka sake raba mu da ita rabuwa ta har abada” ya dafe kana da yake sarawa sosai ya sake kallon Ameena da take hawaye tana tsaye a har lokacin bata zauna kafin ya sake magana tace, “ka daina wahalar da kanka Yusuf, ka daina b’ata bakin ka Yusuf, ka daina asarar hawayen ka, ni Ameena bazan koma gidan ka ba, ni Ameena bazan sake zama dakai ba, ni Ameena na barka har abada. Ga mijina nan a tsaye kana kallo shine wanda zan aura koda wasa kar ka sake kuskuren cewa kana sona domin zai d’auki mataki mai tsauri a kanka.” Ya kalli Al’ameen da yake kallon sa gabad’aya ma shi bai gane fuskar sa ba har a lokacin dan ba tashi yake ba yace, “matakin da zaka d’auka d’aukar rai ne? To ka zama silar d’aukar raina a yanzu amma bazan fasa fad’ar ina son Ameena ba, bazan fasa fad’ar Ina son na mayar da ita ba.” “Baza ka samu ba! Baza ka tab’a samun wannandamar ba Yusuf!!. Ta riga ta kubce maka kai da ita kuma har abada. Wacce irin dama ce ban baka ba a rayuwar ka? Wanne irin lokaci ne ban baka ba a zamana da kai?, duk wannan lokacin bai ishe ka ba wani sabo kake so na sake baka?. Ka manta dukkan abubuwan da ka aikata min ne Yusuf?.” “Ban manta ba ina sane, ina sane Ameena shiyasa nake ce miki nayi kuskure amma zan gyara kuskuren in kika sake bani dama.” “Bazai gyaru ba ka riga da ka lalata shi wallahi, bana sake fatan zama dakai a inuwa d’aya, ka rok’e ni Akan na yafe maka na kuma yafe maka matsayin ka na baban y’ata, amma ka cire wannan kudurin naka a zuciyar ka domin lokaci ya k’ure maka tuni ma.” Ya ja numfashi ya sauke har lokacin yana rik’e da Zaytun yace, “shikenan Ameena, shikenan naji lokaci ya k’ure min na yarda nayi wasa da damata. Amma ki sake bani wani lokacin da wata damar.” “Bazan bayar ba saboda na tsane ka! Bana sonka bana son mai sonka Yusuf, ka fita daga gidan nan ganin ka yana b’ata min rai, ganin ka yana sakawa naji kamar ana soya min zuciyata saboda tsanar ka da nake ji.” Kallon ta yayi da idanun sa jajaye dan har kukan ya k’afe yayi murmushi yace, “shikenan to Ameena, na gode da yafe min din da kika yi, zan tafi bazan so ganina ya dinga k’ona miki rai ba zan koma inda na fito yanzun nan. Amma ina so ki fad’a min kalma daya da ko na mutu a yanzu zan tafi da ita a zuciyata a matsayin kece kika fad’a min ita ba.” Ameena ya sake fusata tace, “tsana, na tsane ka bana sonka shine abinda zance.” Yayi murmushi ya d’auke Zaytun daga jikin sa ya kalli Usman da yake hawaye shima ya kalli Al’ameen da ya cire glasses din fuskar sa ya kalli Yaya Adam yace, “kayi hak’uri Yaya zan tafi, ban dawo dan sab’a abind aakace min ba na dawo ne saboda zuciyata ta kasa hak’uri. Amma yanzu zan tafi tunda Ameena tace bata son ganina zan tafi watakila tafiya ce ta har abada, domin rasa ta daidai yake da rasa hankalina ni nasan da haka” ya fad’a yana tashi tsaye dakyar ya kalle su yace, “Kiyi hak’uri duk na b’ata muku rai da kuma lokaci, na gode da damar da kuka bani ta magana daku. Allah ya saka muku da gidan aljanna. Yaya na gode Allah ya jikan iyayen ka.” Ya juya ya kalli Al’ameen yace, “fatan nasara” daga nan ya kalli Usmsn yace, “muje Usman, yanzu na tabbatar da abinda kake cemin, lokaci na ya wuce dama ta ta k’are komai ya lalace min, bazan sake samun wata damar ba, nayi sake komai yazo k’arshe.” Usman ya rik’e hannun sa zasu fita kukan Zaytun ya karad’e falon ta bishi a guje ta rik’e shi ya d’ago ya kalli su sai ya rik’e hannun ta suka fita tare da ita. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #paid #500 Book3 035 Ameena zama tayi akan kujera tana kuka wanda ta kulle fuskar ta da hannun ta Anti Aysha da tun zuwan Yusuf ta fito ta zauna kusa da ita tace, “to meye na kukan kuma Ameena? Badai shikenan ba an rabu to meye na kukan?.” Ameena tace, “haushin sa nake ji walalhi, bana so naga yana kula koda Zaitun ne balle ni.” Anti tayi dariya tace, “to ya isa, Zaitun ai y’ar sace baki da ikon da zaki saka ya daina kuka ta, ya isa ki daina kuka.” Yaya Adam yana tsaye har lokacin yana kallon Ameena kafin ya kalli Al’ameen da yake tsaye ya mayar da glasses din sa kafin yayi magana akayi kiran sallah suka fita Anty ta rik’e Ameena suka shiga ciki. Har suka idar suka tawo daga masallacin babu mai  magana a cikin su  sai Adam ne ya katse shirun yace, “Muna magana d’azu, ya kake ganin za’ayi da lokacin bikin nan?” Al’ameen ya sauke numfashi ya kalle shi yace, “ai bata kai ga fad’ar lokacin jarabawar ba.” “Ko tana cikin jararbawa za’a d’aura auren, ka gama gyara gidan nan da y’an kwanaki kawai ayi a wuce wajan.” Al’ameen yace, “Allah ya nuna mana.” Ya amsa da amin suka cigaba da tafiya kowa amma akwai abinda yake cikin zuciyar sa.       Usman kuwa kai tsaye asibiti ya wuce da Yusuf dan jikin sa  yayi zafi sosai baya cewa komai sai idanun sa da ya kulle kawai amma kana ganin sa kasan bashi da lafiya. suna zuwa kwantar dashi akayi aka yi masa allura da ruwa dan a samu zazzabin ya sauka a kuma samu jinin sa  da ya sake hawa ya sauka. Usman yana zaune a gefen sa Zaytun na kusa dashi tace, “daddy bashi da lafiya?.” Ya d’aga mata kai alamun eh tace, “daddy yana kuka?.” Ya girgiza kai alamun A’a ya kalli Yusuf da yake kwance tace, “an yiwa Daddy allura.”  Sai ya rik’o ta jikin sa kawai baice mata komai ba ita kuma tana ta tambayar sa. Abbah ya iya Kira ya fad’awa halin da ake ciki bai fad’awa Ammah bama daga wajan aiki kai tsaye asibitin yaje ya samu Usman a zaune da Zaytun da tayi bacci tana hannun sa yace, “Usman me ya sake faruwa kuma?.” Usman yace, “Wallahi Abbah Yusuf yana son Ameena, wallahi ya gane kuskuren da in aka bari ta kubce masa zai iya rasa hankalin sa gabad’aya. Duk wannan halin ya shiga ta dalilin ta, ban tab’a ganin nadama a idanun Yusuf ba kamar cikin kwanakin nan, dan Allah Abba ka taimakawa Yusuf kafin ya zauce.” Abbah yayi Ajiyar zuciya yace, “yau ma gidan Adam din kuka je kenan?.” Ya d’aga Abbah kai alamun eh Abbah yace, “ni ban san me zance ba gaskiya dan banza shiga maganar ba wallahi, in rabon sace zata sake dawowa in ba rabon sa bace ba yaje can ya samo wata in ya rasa hankalin ma daman Allah ya rubuta zai rasa hankali sa akan Ameena, hakan yana cikin littafin k’addarar sa.” Usman yace, “Abbah ayi wani abun dan Allah.” Abbah yace, “zan sanar da mahaifiyar sa tazo a ganshi” ya fad’a yana fita shi kuma ya zauna gadin Yusuf. Ana sallar magariba sai ga Ammah Mubakar ya kawo ta har lokaci Usman yana nan ya dai fita ya siyowa Zaytun take away tana cin abinci. Kallon Yusuf Amma tayi da yake kwance akan gadon ta kalli Usmsn tace, “meyasa baza ka bashi shawara kace masa Ameena ta barshi har abada ba? Meyasa baza ka fad’a masa gaskiya yanzu tayi masa nisa ba Usman?. Wannan kwanciya ciwon da yake yi ba shine zai dawo da Ameena ba, in zai k’arfafa zuciyar sa ya k’arfafa ya saka kuma a zuciyar tasa Ameena yanzu ba rabon aa bace.” Usman ya girgiza kai yac, “duk yadda zan miki bayanı baza ki gane ba Ammah, amma wallahi Yusuf yana son Amman ya kuma gyara kuskuren sa meyasa baza’a karb’e shi a lokaci na biyu ba.” “Dan giyar?, Mai dukan matan?, Mai ce mata barauniyar?, Mai sakata a dsmuwar da ta fara shan maganin hawan jini?,Mai ci mata mutunci a duk sanda yaso?, me saka ta shan magani saboda fad’awa halaka shine za’a ce ya gane kuskuren sa?. Har yaushe daren yayi balle gari ya waye Usman?. Dan kana bayan sa ka dinga fad’a masa gaskiya kar ka fad’i son zuciyar ka, ka sanar dashi ya cire  Ameena daga zuciyar sa in ba haka ba dashi da zuciyar zasu tashi daga aiki.” “Ammah zai iya rasa hankalin sawallahi Akan hakan,” “Ya rasa mana, wasu rayuwar suke rasawa dan ya rasa hankali sai me?.” Usman yayi Ajiyar zuciya bai ce komai ba dan ya lura Ammah tafi Abbah d’aukar zafi Mubakar yana gefe shi kansa tausayin Yusuf yake ji kafin yace, “tsohuwar matar sa Asiya ma aka sake kamata da sark’ar gold din Abbah ta sample din nan na Dubai taje zata siyar. Yanzu haka tana hannu yan sanda nace su cigaba da tsare ta sai gobe zanje sai ta kwana biyu a cell wallahi.” Ammah batayi magana ba ta k’arasa inda Yusuf yake ta tab’a jikin sa har lokacin zafi zauu kamar ba magani ne yake shiga jikin sa ba. Zaytun ta kalla da take cin abinci itama a lokacin ta kalle ta sai tace, “Ammah Daddy yayi kuka, Mummy ma tayi.” Sai Ammah tayi murmushi kawai bata ce komai  ba Usman yace, “kodan wannan yarinyar Ammah ki daure a san abinda za’ayi Ameena ta dawo gidan ta. Kodan yarinyar nan ta taso a cikin iyayen ta dan Allah a shiga lamarin Yusuf.” Ammah tayi dariya tace, “Yanzu lokacin cin albarkacin yara ya wuce Usman, mata sun daina azabtar da kansu su zauna a gidan mazajen da suke wahalar da rayuwar  su akan yara, wannan zamanin da ka sani yanzu y’anci yafi zama a gidan uban y’ay’a ka gane?.” Usman yayi shiru ya lura Amma tayi zafi sosai ba yanzu zata sauko ba. Har dare suna nan sai wajan sha d’aya na dare sannan Ammah suka tafi da Usman shi kuma Mubakar ya zauna dashi.        Washe gari da safe Mubakar yaje station din aka fito da Asiya akayi masa bayanin komai an kamata da kayan sata tana kuma k’ok’arin siyarwa, an tambaye ta tace ta mijin tace. Ya kalle ta yayi dariya ganin yadda tayi bak’i sosai sai kuka take ga majina a hancin ta yace, “ni ba nine mijin ta ba kanin sane ni, amma sark’ar da ta sace ta uban mijin tace an bashi sample daga Dubai” ya fad’a yana ajjiye masa receipt yace, “gashi ka duba akwai sunan company da komai a jiki zaka tabbatar in ka kira ka fad’a musu sunan da yake kai zasu tabbatar maka da mallakin mai wannan sunan ne.” Nan akayi bincike akai aka tabbata abinda ya fad’a gaskiya ne dan sandan yace, “Yanzu satar ta ta har ta shahara tana yiwa uban mijin ta?.” Mubakar yace, “ga zahiri nan ma ka gani, kaf unguwar su babu baruniya kamar ta. Kowa kuka yake da ita har haura gidaje take yi, a garin satar ta b’allo hannu.” Ya girgiza kai yace, “ah wannan barin ta cikin jama’a kuma ai illa ce, gwara a tura ta wajan alqali ya tura ta prison ta girbi abinds ta shuka. Asiya ta fashe da kuka jin abinda akace tace, “ku yi min rai dan Allah, Kuyi hak’uri na tuba bazan sake ba daga yau wallahi, Tsautsayi ne wannan ma amma daga shi na daina.” Mubakar yace, “karya kike baza ki daina ba, sata ta zamar miki jiki baza ki tab’a dainawa ba” ya kalli d’an sandan yace, “inda zai yu a kaina prison na sati d’aya taje taji ya ake ji in ta fito watakila zatayi hankali.” Asiya tace, “Dan Allah kayi hak’uri wallahi na daina, wannan din ma tsautsayi ne Ummana aka kama nake son biya mata kudin da ake binta na fito da ita. Kayi hak’uri ka yafe min na daina aikata abinda nake aikatawa.” Mubakar yace, “duk bala’in kifa sai kin je prion. Gadon tsiya ke a cell uwa a cell, banga amfanin mata irin ku ba a duniya, kamata yayi a biku duk a bindige.” Kuka Asiya take sosai tana bashi hak’uri dakyar ya hak’ura yace a kyale ta amma da sharad’in in aka sake kamata da wannan laifin sai ta tafi prion tace ta yarda. Aka bata damar tafiya shi kuma ya karb’i sark’ar ya tafi  bayan yayi musu alkhairi. Asiya a haka ta tafi gida jiri yana d’aukar ta tana kuka sosai duk abinda ta tara a gidan Yusuf ya k’are ta dawo bata da komai ko zare bata dashi, a haka ta shiga gidan tana shiga ta zube a tsakar gida suka yi kanta suka Momi tace, “Lafiya? Ina kika shiga aka neme ki aka rasa yau kwana biyu?.”  “Ruwa zan sha, ku bani ruwa na sha.” Da sauri aka kawo mata ruwa ta sha ta kwanta a wajan tana kuka sosai. Maimuna tace, “muka dinga jiran ki kince zaki kawo kud’in da za’a fito da Umma shiru yanzu gashi dakyar aka bada ita ance nan da sati in bata bada kud’in ba sai ya tafi prison, ina abinda kika ce zaki je ko siyar din?.” Asiya tana daga kwance tace, “Sun kwace komai, an kwace komai daga hannuna, bani da komai yanzu komai ya k’are. Kwana na biyu a wajan y’an sanda sai yanzu aka fito dani. Na shiga uku ni Asiya komai ya lalace min.” Maimuna jin haka sai kowa yayi shiru Umma ta ta fito tana kallon ta tace, “sai ki tashi daga wajan ki shiga ciki sai maqota sun sake sanin halin da muke ciki ko me?. Abin kunya ne ace naje cell kema kin kwana biyu a cell.” Asiya bata tashi ba bata daina kuka ba tace, “Umma duk ke kika jawo min, da baki saka an sake ni ba da yanzu ina gidsn mijina ina rayuwar farin ciki, amma yanzu kalli yadda na koma komai ya lalace min bani da ko sisi, ko waya bani da ita bani da komai.” Umma tayi tsaki kawai bata ce komai ba ta koma ciki duk suka barta a wajan sai da ta gaji dan kanta ta tashi ta shiga d’aki tana ki kamar tayi hauka saboda tashin hankalin da take ciki.             Adam yana tsaye yana amsa waya Anti Aysha tazo ta tsaya a kusa dashi taji yana cewa, “tun lokacin meyasa baki fad’a min yaje gidan ki ba?.” Shiru yayi alamun ana bashi amsa sannan yace, “sai yaje duk inda zai je ko wa zai nema a bayana yake, ni kuma bazan sake bashi Ameena a wannan Karon ba.” Shiru ya sake y kafin yace, “shikenan dai sai kin shigo” ya fad’a yana kashe wayar ya kalli Aisha yace, “Ya dai?.” Tace, “Yaya Samira ce?.” “Itace, ashe Yusuf yaje gidan ta tun kafin yazo nan zuwan farko.” Tayi murmushi tace, “Yusuf da gaske dai neman biko yake yi.” “Ai bashi da hankali ne, Ba kuma zai samu ba.” Tace, “ka daina cewa haka in Allah yayi zata koma din fa? Kaga akwai yarinya a tsakanin su ni wallahi ko dan ita a raina ina so ta koma saboda yarinya ta taso ba a cikin iyayen ya babu dadi wallahi. Ni kasan a haka na tashi har gobe babu wata shak’uwa tsakanina da Abban mu saboda nan tashi dashi ba.” shiru bai amsa ba ya d’auki abinda zai d’suka ya fita daga d’akin. A falo ya hango Ameena ya tsaya daga inda yake yana kallon ta yaga tana zaune tana duba littafi amma sai yaga ta rufe ta dafe kanta ta d’ago tayi k’aramin tsaki ta zame ta kwanta a bangon kujerar. K’arasowa yayi ya kalle ya yace, “Ameenatu ya dai?.” Sai ta d’ago ta kalle shi tace, “Babu komai Yaya.” “Yau babu school?.” “Eh yau Sunday ai sai gobe in Allah ya kaimu.” “Allah ya kaimu” ta amsa da amin yace, “jiya Muna magana akan lokacin bikin aka katse mu, yaushe ne zaku yi exams din?.”  Ta kalli Yaya tace, “nan da sati biyu ne, har na exams din uku kenan in Allah ya kaimu.” Ya girgiza kai yace, “bikin sai a saka shi sati ukun kinga sati ne hudu kina hutu ko?.” Ta d’aga Kai alamun eh yace, “hakan za’a yi, zan sanar da Al’ameen din sai ki fad’a masa abinda kika shirya sai ku san abinda zaku yi.” Ta kalle shi tace, “to Yaya.” Ya juya zai fita sai ya juyo ya kalle ya yace, “babu wani abu dai ko?.” Ta girgiza ka tace, “babu komai.” Ya juya ya fita ta lumshe ido ta bud’e ta cigaba da karatun ta. Tana zaune sai ga Anti ma ta fito tana tsokana ta tayi dariya tace, “wato Anti ku da yake kin gama boko shiyasa in kina ganina sai ki ta min dariya.” Anti ta zauna tace, “ina fa aka gama? Da ya aka kammala masters din ma balle a gama?.” Tayi dariya tace, “mu gashi digree muke so ta kammala tak’i.” “Zata kammala ne ai, balle ma kin mayar da hankali sosai a kai.” Tayi murmushi kawai Anti tace, “Zaitun ba’a dawo ba kenan?.” Kai ta d’aga kawai Aunty ta kalle ta tace, “Ameena na tambaye ki?.” Ta kalle ta tace, “eh mana Aunty.” “Amma kar ki kalli tambayar tawa da wata fuskar kawai ki amsa min.” Ta d’aga mata kai tace, “zaki iya komawa gidan Yusuf in kika tabbatar ya canja duk abinda akayi a baya baza’a maimaita ba sai kadan?.” Ameena ta sauke numfashi tace, “ni bama wannan tunanin ma.” Anti tace, “nasan bakya yi din ai, shiyasa na tambaye ki zaki iya komawa in akace ya canja daga yadda kika sa shi ya koma miki sabo fresh kamar lokacin da kike amarya?.” Tayi shiru na wani lokaci kafin tace, “ai bazai ma canja ba, yaje ya k’arata ni bana son zancen ma gabad’aya.” “Kin kasa bani amsa kawai.” “To ban san me zance bane ba.” Anti tace, “amsa kawai zaki bani.” Ameena tace, “inda da gaske zai canja din baza’a maimaita abinda ya wuce ba zamu zauna lafiya babu cuta babu cutarwa zan koma Aunty, zan koma kodan saboda Zaytun ko badan shi ba zan zauna saboda ita dan tana son mahaifin ta sosai indai yana waje bata cika nemana ba. Raba su zan cutar da ita sosai.” Aunty tayi murmushi tana kallon Ameena kafin Anti tayi magana Ameena tace, “balle ma bazai komai ba shiyasa bana kawo shi cikin zuciyata, yayi rayuwar sa nayi tawa na tabbata Yaya Al’ameen zai rik’e min Zaytun ko bana da rai.” Aunty tace, “Gaskiya ne, amma koda ya rik’e Zaytun in ta girma sai dai ace Zaytun Yusuf ba Zaytun Al’ameen ba kin san da hakan ai ko?.”  “Na sani mana, ko yanzu da sunan sa ake mata amfani a makaranta.” “Ameena Nidai zuciyata ta amince da Yusuf ya gane kuskuren sa wallahi, kin san wani lokacin baka gane kayi kuskure sai wani abun ya same ka kake banbance ashe a baya ka tafka asara wacce kafin ka mayar da ita zaka jima. Ki kalli k’awar ki Fiddausi da kike bani labari, sai a yanzu tasan tayi kuskure kuma ke kanki kin amince da ta tuba har cikin zuciyar ta koma meye yanzu baza ta sake gangancin aikatawa ba. Har kike cemin badan Rukayya ba da kince kina so Ibrahim ya mayar da ita gidan ta dan tayi nadama sosai ta kum tuba har zuciyar ta, kina so ace ta koma wajan Ibrahim ko badan komai ba saboda d’an ta haka ne ko?.” Ameena tayi shiru bata amsa ba Anti tace, “kin yarda a baya tayi kuskure kuma yanzu ta gane kuskuren ta gyara kuma kin amince da ta gyara d’in tunda gashi kina so ta koma gidan mijin ta, meyasa shi baki yarda ya zai gyara kuskuren nasa ba?, kodan har yanzu akwai haushin sa da kike ji a zuciyar ki?.” Ameena ta kalle ta tace, “Anty kuskuren Yusuf yafi na Fiddausi a wajena, Yusuf bazai canja ba wani abun yana sene yake aikatawa halin sane ba wani abun ba kuma hali baya canjawa.” “Nasan halin sane ai, shiyasa nace miki akwai abinda dole sai ya sake faruwa in kika koma saboda hali ne baya canjawa, amma wallahil azim ina tabbatar miki da cikin kashi d’ari na abinda ya faru a zaman ki dashi na baya tamanin zai ragu iya ashirin ne zai rage kawai saboda bazai sake gangancin aikatawa ba sboda kar ki sake nisa dashi. Ko a yanzu nasan kin tabbatar da Yusuf yana sonki so bana wasa ba, namijin da zai durkuss a gaban ki yana kuka kamar wacce ta haife shi akan kawai ki yafe masa ko ki koma gidan sa ki sake kallon sa in akace akan so da kuma bada hak’uri ya aikata hakan.” Ameena ta girgiza kai tace, “ni nasan masifar da na shiga a gidan sa da Anti.” Tayi murmushi tace, “nima bance ki koma ba ai ina fad’a miki ra’ayina ne inda nice wallahi wajan sa zan koma, in na auri wani na raba yarana wannan tana nan wannan tana can gwara ace shi kad’ai ne uban yarana gabad’ayan su. Har Bauchi yaje akan yaya ta baki hak’uri tun kafin yazo nan,Nidai zuciyata ta amince da ya canja wallahi amma ko meye shine yayi wasa sa damar sa kina da ikon da zaki ce baza ki koma ba.” Ameena tayi shiru bata ce komai ba tana tunani kafin ta sauke numfashi tace, “Gwara a barshi kawai wannan da aka samu yasa sai mutuwa ce zata raba mu.” Aunty tayi murmushi tace, “Amin Amaryar Al’ameen.” Sai ta kasa murmushin da ta saba in akace amaryar al’ameen ta kalli Aunty ta dan saki fuska kawai amma batayi murmushi ba.         Yusuf tunda ya farka yak’i magana sai kallo kawai da yake bin su dashi dakyar aka bashi tea yasha a safiyar yana zaune yana shan tea din Mubakar ya shigo ya kalli Abbah da yake zaune yace, “Abbah ga sark’ar ka.” Ya fad’a yana mik’a masa ya karb’a ya kalle shi yace, “an ina ka samo ta?.” “Jiya aka kama matar sa Asiya taje kasuwa zata siyar akan miliyan d’aya da rabi, saka sanar da Yusuf ya tabbatar sark’ar kace sai yace naje na karb’o sarkar.” Ammah tayi dariya tace, “Da gaskiya manager bank din nan da yace satar tasu ma ta k’ananun b’arayi ce, yanzu wannan sark’a ko yaro a yasan tafi kudin da ta siyar da ita.” Abbah ya kalli Yusuf da yake kallon wani wajan daban kafin ya kalli Mubakar yace, “yanzu tana ina?.” “Na saka a sake ta, da wallahi so nayi taje prison ko na sati ne tausayi ta bani tana ta kuka ga hannun ta a karye shiyasa na kyale ta.” “Gwara da ka kyale ta din ai yafi.” Usman ne ya shigo da sallama aka amsa suka gaisa da su Ammah ya kalli Yusuf yace, “ya jikin?.” Kai y d’aga masa kawai amma baiyi magana ba yace, “Zan wuce akwai aikin da zanyi anjima zan dawo.” Yusuf ya kalle shi yace, “ka tsaya ka raka ni wani waje.” Yadda maganar take fita a sark’e sai da su Ammah suka kalle shi dan baiyi magana ba sai lokacin Usman yace, “ina kuma zamu je yanzu? Bauchi zamu koma ko gidan Adam?. Yusuf ya kamata kayi hak’uri da Ameena ka cire ta daga zuciyar ka kawai indai kana son ka tsira da Lafiyar ka.” Yayi murmushi yace, “riga ce da zan saka a lokacin da naso kuma na cire a lokacin da naso Usman? Zuciya ce fa ban San taya zan cire a lokaci d’aya ba kamar yadda kake fad’a. Ka tsaya muje dan Allah kaine kawai kayi hak’uri dani kake saurarona.” Usman yace, “naji, amma na fad’a maka akwai abinda zanyi yanzu, sannan ina ma zamu je?.” “Zamu je duk inda ya kamata ma ace mun je” ya fad’a yana sako k’afar sa zai sakko Usman ya dakatar dashi yace, “ka zauna naje na dawo sai muje duk inda zamu je.” Yusuf yace, “ka tabbatar zaka dawo?.” Cikin taussyin da yace, “zan dawo.” Usman ya kalli su Ammah da suke kallon su ya fita baice komai ba shima Yusuf din sai ya mayar da idanu ya kulle. Adam yana fita gidan Al’ameen ya shiga ya samu baya nan ya dinga yi masa waya bai d’auka ba yayi tsaki ya zauna yana zaman jiran sai daga baya sai gashi ya dawo ya kalle shi yace, “tun d’azu nake kiran ka baka d’auka.” Suka shiga cikin gidan Al’ameen yace, “Naje dubiya ne wallahi, a nan naga Zaytun ma a hannun wani yaro ashe kanin baban ta ne suke cemin babban ne a kwance babu lafiya, da zan je na duba shi ka to kana ta kira na sarkin masifa shiyasa na dawo.” Adam yace, “Yusuf din ne asibiti?.” “eh, haka akace min wai tun jiya.” “Allah Sarki. Muyi maganar da ta kawo ni yanzu.” Al’Ameen yace, “kafin wannan Adam, kana ganin Ameena bata son mijin ta kuwa?.” Ya dago ya kalle shi sosai yace, “bata son sa, ko tana son nasa ma baza ta koma masa ba. Kai dan baka San waye shi bane shiyasa a jiya naga ya baka tausayi.” Yayi murmushi yace, “kai ma ya baka tausayi ba ni kad’ai ba. Abinda na gani duk abinda zai saka namiji kamar sa kuka har ya zube guiwa a k’asa a gaban mace yana neman afuwar ta ba abu bane kad’an Adam. Gazawar takai gazawa, mace ba mahaifiya ba ka zube kana bata hak’uri kana kuka ki nadamar k’arya kayi sai an kalle ka an sake kalla. Ganin hakan sai jikina yayi sanyi sosai domin itama Ameena akwai feeling a tare da ita akan shi kawai dai abinda yayi mata take tunawa.” “Nima ai abinda yayi mata nake tunawa bawai yana sonta ko babu son ba.” “Eh haka ne, amma ana kuskure ana kuma gyara kuskuren a lokacin daka fahimta, ya gane kuskuren sa kuma ko nan gaba akace ya sake abinda yayi Allah bazai yi ba.” “Tsaya, yanzu me kake nufi da wannan jawabin naka?.” Al’ameen yayi murmushi yace, “indai Ameena tana son zama dashi a karo na biyu Adam ni mai iya sake hak’ura da ita ne a karo na biyu na bar masa ita. Amma in ba itace ba ita tace tana so ba za’a cigaba da shirye-shiryen biki.” Adam ya harare shi yace, “son da kake mata dmaan bashi da auki? Yanzu har kana da bakin da zaka ce zaka iya sadaukar da ita ga wani namijin daban?.”  Ya girgiza kai alamun eh yace, “son da nake mata ne ya saka zan iya hak’ura da nawa farin cikin na bata Adam. Ni yarinyar su ma nake tausayi wallahi, tana son mahaifin ta sosai.” Adam ya bishi da kallo yace, “to bata son sa, bazata koma ba. Ka tsaya muyi magana akan auren ka da ita ka daina kawo min batun tsohon mijin ta dan Allah.” Al’ameen yayi murmushi yace, “to sirkina, Ina ji.” Dariya Adam yayi wacce bai shirya mata ba shima dariyar yayi kafin su tattauna akan batun auren da yadda Adam yake so komai ya kasance Al’Ameen ya amince da hakan shima sosai kafin Adam ya tafi. #Mai room #Book3 #Nana Haleema #Paid #500. Book3 036         Yusuf ya samu sauk’i babu laifi sai yawon gidajen yayyen Ameena yake yana basu hak'uri har Zakiyya da Fiddausi bai kyale ba duk sai da yaje ya same su amma babu nasara har ya fara sarrewa da lamarin. Ameena kuwa duk wanda ya samu zai zo yayi mata maganar duk bata sauraron su dan bata so ma maganar tayi tasiri a zuciyar ta shirin biki take yi ita da sabon angon ta Al'ameen. Yusuf gab yake da fita daga hankalin sa saboda yadda ya koma kamar ba shi ba musamman a kamannin sa ya rame lokaci d’aya. A falon Ammah Humaira ce a zaune ta saka Ammah a gaba tana kuka tace, "Ammah yanzu baza ki saka baki akan Ameena ta dawo gidan Yaya Yusuf ba? Ya kusa haukacewa ku taimaka masa dan Allah bazai sake aikata abinda yayi ba." Ammah ta kalle ta tace, "a goshin ki ya rubuta miki bazai daina ba? Ke yanzu a cikin zuciyar ki kina ji kin yarda Yusuf ya daina abinda yayi a da?." "Wallahi Ammah na yarda ya daina, dan Allah dan Annabi ki amince ki saka baki Amesna ta dawo gidan sa wallahi yana sonta yana kuma qaunar ta." Ammah tayi murmushi tace, "bara nayi miki misali, d'auki kanki a matsayin Ameena ace mijin ki yan dukan ki, yana zagin ki, yace miki b’arauniya, ya wulakanta ki saboda amarya, ya daukaki amarya akan ki, k'arshe ya saka miki ciwon da kike shan magana, ya kaurace miki daga shinfidar aure har hakan ya kai ga kina Shan magani. Sai kuma ya rabu dake ya zauna da amaryar ya sha wahala ya fahimci mahimmacin ki daga baya sai ya lallab’o yace zai dawo dake ya daina wallahi bazai sake ba, yayi alqawarin bazai kuma ba bayan kafin ya aure ki yayi alqawari zai rik’e ki har mahaifin ki ya yiwa alqawari yana gab da barin duniya. Zaki amince ki koma masa?." Humaira ta bud'e baki zatayi magana Ammah tace, "kar kiyi son kai ki fad’i tsakanin ki da Allah, zaki koma ko baza ki koma ba?." Humaira tace, "indai ya shiru da gaske ya daina wallahi zan koma Ammah." "To ya ya zaki san ya shiru?." "In n koma din." "In kika koma kuma duk karya yake bai daina din ba fa?." Humaira tayi shiru bata ce komai ba Ammah tace, "dan yana jinin ki kiyi adalci, in akwai wacce take so Ameena ta dawo wajan Yusuf a bayana take amma bana so ta dawo din dan halin da ta bari yana nan shi zata sake samu." Humaira taja numfashi ta sauke tace, "Dan Alalh Ammah ayi wani abun wallahi yana sonta." Ammah tace, "son banza da wofi, son da bai amfana masa da komai ba meye amfanin sa?. Shi da yaci amanar so, wanne irin so ne Ameena bata nuna masa ba amma yayi burus ya watsar da ita saboda ya auro b’arauniya mai suffar aljanu?." Humaira ta goge idanun tace, "ko me ya faru shine ya jawo amma kuma akwai asiri a lamarin sa." "Uwar asiri da uban sa, asiri yana tarar da hali tun kafin asiri daman da halin sa Humairah. Kiyi adalci ki daina fad'ar son zuciyar ki saboda Yusuf ya kasance naki. Itama jinin wani ce yadda kike kare naki yanzu suma ita zasu kare.” Ta sauke ajiyar zuciya a lokacin ya shigo falon Ammah ta kalle shi yana bata tausayi itama sosai ya rame matuk'a sai haske da ya sake yi sosai, fuskar sa duk ta tari da gashi wanda bai sa shi ba in ya ganshi sai ya d'auka mahaukaci ne. "Sannu Ammah" ya fad'a yana wucewa ya shiga d'aki Humaira ta kalli Ammah tace, "Ammah dan Allah." Ammah tayi tsaki tace, "zancen kike so." Humaira tayi shiru tana nan zaune ya sake zuwa ya fita bayan ya canja kayan jikin sa. Kai tsaye Yusuf gidan Adam ya wuce ya tsaya a k'ofar gidan daga can gefe yana zaune a mota ba tare da ya fito ba. Yaya Adam da dawo ya ganshi a wajan bai ma nuna ya ganshi ba ya shiga gidan ya samu Ameena tana aiki a falon ya kalle ta yace, "wai Yusuf din nan haukacewa yayi ne? Kullum sai yazo k'ofar gidan nan ya zauna tun safe har dare? Me yake yi a nan?." Aysha tace, "to tunda ba shigowa yake ba ka kyale shi kayi kamar baka ganshi ba mana, ka cika mita." Ya yi k’wafa ya shiga ciki Aysha ta kalli Ameena da take mopping tace, "duk saboda Ameena yake zuwa kai ma ka sani amma ka dinga yin abu kamar baka sani ba. Kuma tunda ba shigowa yake ba meye na maganar?.” Fita Yaya Adam yayi sai ya samu sai motar amma baya nan ya girgiza kai yace, "Ko Ina yaje ai zai dawo ya same ni." Yusuf kuwa Adam yana shiga gida ba jimawa sai ga Al'ameen ma ya dawo zai shiga gidan sa da ake ta aikin sa yayi kyau sosai sai  ya fito daga motar ya k'araso inda yake Al'ameen ganin ya tsaya sai ya sauke glass din motar yana kallon sa dan kamar bai gane shi ba sai Yusuf yayi murmushi yace, "Yusuf." Sai Al'ameen yayi murmushi yace, "sai kace min mahaifin Zaytun sarkin magana. Ban gane ka ba naga ka canja kamar ba kai ba.” Sai shima yayi murmushi Yusuf yace, "in babu damuwa ina so zanyi magana da kai." Al'ameen yace, "mu shiga ciki to." Al'ameen ya shiga da motar shi kuna ya shiga da k'afa Al'ameen ya faka motar ya shiga ya kalli Yusuf yace, "bismillah muje ciki." Suka shiga falon da yake kaca-kaca babu gyara saboda aikin da ake yi a gidan ya kalli Yusuf yace, "sai hak'uri, gidan ana ta aiki shiyasa gashi nan dai.” Yusuf yace, "babu komai hakan ma na gode." Al'ameen yace, "zauna." Suka zauna akan kujerun da aka rufe su da leda saboda kar su b'aci da fenti Yusuf yace, "nasan kana ta mamakin ganina." "To ba abin mamaki bane tunda nasan zuwan yana da nasaba da Ameena ko?." Ya d'aga kai alamun eh kafin tace, "to ina jin ka. " Yusuf yace, "hakurin dai nazo bayarwa naga kaima tamkar Yayan ta kake. na san nayi kuskure abubuwan da aka aikata a baya amma a yanzu na canja duk abindaa aka san ni dashi a baya na daina meyasa baza'a sake bani dama a karo na biyu ba?, Muna yiwa Alllah laifi ya yafe mana meyasa baza'a yafe min a bani dama ba ko dan saboda y’arda take tsksanina da Ameena?." Al'ameen ya sauke numfashi yace, "to Yusuf shi kuskure ana aikata shi ne a lokacin da ba'a yi tunani ba musamman ina anatunanin abinda aka aikata kuskuren a kai bazai kubce ba, a lokacin da ya kubce kuma ana so a dawo dashi a goge wancan kuskuren mutum ya kan iya ko wanne basaja dan ganin ya goge wancan kuskuren an bashi wata damar. Wannan marairaicewar da kake yi watakila plan kake shiryawa kana so Ameena ta dawo sannan ka koma halayen da ka bari." Yusuf girgiza kai yake yi yace, "Ko kusa, ko kad’an wallahi. Da gaske na canja ba basaja nake ba Allah yana ganin zuciyata, meye riba ta in aka sake bani Ameena na wulakanta ta?, Me zan samu in na tozarta Ameena?, Me zan cimma in nayi akrya da Allah akan na canja kuma kawai dan cikar burina?. In ka yiwa abu rik’o mara kyau ya kubce maka a lokacin da yake gab da fad’uwa ka fahimci hakan  kayi saurin rike shi ka dawo dashi hannun ka na tabbatar ba zaka sake yiwa abun nan irin wannan rokon ba. Ka taimake ni ban san ka ba amma ina ganin ka da Yayan ta sai na tabbatar kana da mahimmaci a wajan sa da ita kanta, ka amince min a sake bani dama na zauna da Ameena, in na sake maimaita abinda nayi a baya na amince bayan an raba mu ayi min duk abinda ake ganin za'a wuce, amma dan Allah kar ace min zata auri wani daban bani ba, bazan iya jurewa ba." Al'ameen yayi shiru yana sauraren sa yana girgiza kansa kafin yace, "ni ban San abinda zanyi maka ba da ka same ni da wannan maganar, Adam dai shi ya kamata ka komawa bani ba." "Na kasa na kasa sake komawa, ka taimaka ka shige min gaba wajan gyara abinda na b’ata. Baza ka so ace yau Zaytun ta tashi ba'a tsakanin iyayen ta ba, baza kace ace ta tashi a wani waje daban ba, baza kaso ace Ameena da yarintar ta ace tana raba yara a gidajen maza biyu ba" Yusuf ya zamo daga kan kujerar Al'ameen yace, "ka koma ka zauna dan Allah kar kace zaka durk’usa min." Yusuf bai fasa ba yace, "dan ka amince da gaske nake ba wasa ba, ina son a sake bani Ameena dan Allah." Al'ameen yace, "naji tashi ka koma ka zauna." Yusuf ya koma ya zauna Al'ameen yace, "kar ka damu zan same shi da maganar, amma kamar baka gane ni ba a ranar da kaje wajan Adam har kuka yi magana da Ameena, baka gane fuskat ba ko?." Yusuf kamar yayi kuka yace, "bana fahimtar komai a lokacin, bana gane komai bana ganin komai indai ba ita da Yaya Adam din ba." Yayi murmushi yace, "shikenan kar ka damu za'a san abinda zanyi a kan maganar, in rabon kace zaka sake samun ta, in ba rabon ka bace duk yadda da kaso ga sake samun ta zata zama mallakin kana karo na biyu ba. Kaje kai ta addu’a a kan hakan shine maganin damuwar ka.” Yusuf yace, "haka ne na amince na yarda, na gode Allah ya saka da alkhairi." Al'ameen ya amsa gabad’aya jikin sa yayi masa sanyi sosai zuciyar sa nayi masa wani iri ya rasa me zaice masa ma. A haka  Yusuf ya fito ya shiga mota ya tafi yana tafiya Adam ya fito ya shiga gidan ya samu Al'ameen a tsaye ya hard’e hannun sa a kirji yana kallon k'asa yace, "Yusuf dai naga yana neman canja maka ra'ayi daga auren Ameena." Al'ameen ya kalle shi yace, "nawa Yusuf din yake da zai canja min ra'ayi? A shekaru na girme masa kai ka sani. Kawai ya bani tausayi ne sosai soyayya tana d'awainiya dashi sannan kuma ya gane kuskuren sa, gashi babu damar sake mallakar ta a wannan lokacin Ameena tawa ce." Adam yayi shiru na wani lokaci hakan ya saka Al'ameen yace, "ka bibiyi Ameena indai har Ameena tana son komawa gidan sa ka sake bashi dama soja, yayi nadama a idanun sa zaka hango hakan, yayi dana sani sosai, kuma da gaskiyar sa meye amfanin raba yara gidan maza guda biyu da k’ananun shekarun Ameena?. Indai Ameena tana son sa a karo na biyu ka bashi dama na tabbatar in sha Allah baza ka yi dana sani ba. Ni yanayin da ya fita ma ban amince dashi ba wallahi.” Adam ya rufe ido ya bud'e ya kalle shi yace, "bana jin zan sake bawa Yusuf Ameena Al'Ameen, bana son ta sake maimaita rayuwar da tayi a baya gaskiya. Dan haka a bar maganar sa kawai a cigaba da abinda yake gaban mu." Al'ameen yace, "shikenan Allah yasa mu dace." Ya amsa da amin sannan suka fara maganar da ta kawo Adam din wajan sa.          "Ni wallahi bazan ci shinkafa da manja babu yaji ba, wannan wanne irin bala'i ne da safe na sha shayi babu sugar na kirki ko madara ma babu yanzu kuma da rana an bani shinkafa da manja ace naci kuma ko yaji babu wai na saka maggi?.” Maimuna ta kalli Asiya tace, "kar kici mana ba cikin ki ba." Asiya tace, "Nidai wallahi na gaji, an cuce ni an raba ni da mijina da gidana mai kyau kullum cikin haske da a.c amma tunda nazo gidan nan sau d'aya aka kwana da wuta. Zafi, sauro, kyankyaso babu abinda babu a gidan nan Nidai na gaji wallahi." Momi tayi dariya tace, "sai ki tashi ki koma ai tunda ba a nan kika rayuwa ba, y’ar wahala kawai.” Fauziyya ce ta fito daga d’aki a fusace tana hawaye tace, "Umma! Umma!!." Umma da take zaune tace, "Lafiya kike min wanna kira kamar makauniya?." "Wai Umma wanne hali muke dashi ne a unguwar nan da ake cewa bamu da tarbiyya mun raina kowa? Wai Umma wacce tarbiyya kika bamu har Surajo yace ya fasa aurena Umma?. Wai yaji labarin an kama ki akan bashi an kama Asiya akan sata shi bazai iya had'a zuri'a dani ba, Umma na hud’u kenan yana cewa ya fasa aurena wacce irin tarbiyya muke da iya haka da suke gudun had’a zuri’a damu?.” Momi taja numfashi tace, "nima na gaji Fauzy, kowa yazo sai an kora shi ace bani da tarbiyya daga ranar banza sake ganin sa ba, gaskiya nima ina d a tambayar akan tarbiyyar mu, wacc iri ce damu da muka kasa auruwa Umma? Wacce tarbiyya kika yi mana haka?.” Duk kallon Umma suke yi suna jira suji abinda zata ce sai tace, "da kuka zuba min ido kin manta abinda yake gaban mu ne? Bashin Sakina an ina zamu samo kud’in da zamu bata ?." "Umma fasa aurena yafi bahsin ta, Umma wacce irin tarbiyya kika bamu da ba’a son auren mu?." Umma ta kalle ta tace, "Allah zai kawo miki wani kinmanta da batun sa." Ta zube a wajan tana kuka tace, "nidai Ina son Surajo wallahi, ina son zama dashi a san yadda za'ayi ya aure ni kawai. Yace min yanzu zasu zo wajan Baba Karb’ar kudin auren da suka kawo, Nidai a San abinda za’a yi min kar na sake rasa mai sona.” Asiya tace, "ni dai an gama da rayuwata, na smau mijin an raba ni dashi yanzu gashi ke baki samu ba balle ni bazawara." Umma kallon su kawai take yi sai ta mik’e ta fita tsakar gida dan bata san me zata ce musu ba. Da aBaba suka had'u ya kalle ta ta gyara tsayawa kafin tayi magana yace, "dangin masu neman auren Fauziyya ne suka zo, sun fasa suna buk’atar a dawo musu da kud'in auren da suka kawo. Kawo a basu suna waje suna jira." Umma ta marairaice tace, "ina naga naira dubu d’ari balle na fito da ita? Ina na ganta malam?. Dan girman Allah ka rufa min asiri ka bayar zan biya ka wallahi." Baba yace, "me nake dashi da zan bayar? Kin manta ni mai musu bak'in ciki ne? Me na ajjiye da zan d'auko na bada naira dubu Dari Atika?." Umma tace, "nidai kayi hak'uri dan girman Allah ka bayar." Baba ya girgiza kai yace, "yau ni kike bawa hak'uri Atika? Lallai duniya ta bi dake. Kin manta ajjiye kudin ma hanawa kika yi a hannun Yayana? Kuma kika dinga  wulakanci akan dubu d’ari sai an baki ke kika haifa ba wani ya haifar miki ba. To yanzu sai ki bayar tunda ke kika haife su ba wani ba." Umma tace, "kayi min rai walalhi bani dashi bani da inda zan samo su wallahi.” "Zan fad'a musu babu, amma gobe sai su zo su karb'a" ya fad'a yana ficewa Umms ta zube a wajan tace, "na shiga uku wai me yake faruwa dani ne lokaci d’aya haka?.” "Bake mara mutunci wacce bata san mutunci ba, ai yanzu kika fara gani" Umma Sakina ta fad'a tana shigowa tana kallon ta. Umma ta d’ago ta kalle ta kafin tayi magana ta nuna mata zobe tace, "wanda aka siya da kudin da Asiya ta sato a wajan mijin ta, jiya na tuna dashi a wajan mai siyarwa naje na cika masa kud’in na bashi takarda ya bani zobe da takardar shaidar biya. Gashi a hannu na naira dubu d’ari biyar da hamsin muka siya, in kin bani kudina zan baki in baki bani ba zan rik'e bazan ce zan siyar ba rik’ewa zanyi duka ya zama nawa in akwai abinda zaki iya sai kiyi, in kina da hujjar da zata nuna naki ne sai kije ki kaini kara." Ta fad'a tana fi cewa tare da yin tsaki ta bar Umma a wajan tana kallon ta. Umma baya tayi t kwanta a k’asa dan ta manta da batun zoben a hannun Sakina, a bayyane tace, “shikenan komai ya k’are, meyasa na amince na bar mata receipt din a hannun ta? Meyasa nayi wannan gangancin ni Atika?.” Umma dai tana neman fita daga hankalin ta dan komai ya k’are mata bata da komai ta dawo matsiyaciyar ta kamar yadda take a baya, gashi babu Asiya balle a sake tarawa.         Yusuf zagaye yake kawai a mota bai San inda yake nufa ba tafiya yake yi kawai amma hankalin sa da tunanin sa basa tare dashi, horn ake masa ta ko ina sai aka sake rud'a shi ya gigice yana kaucewa kafin ya farga wata mota da tawo daga gefen sa ta daki motar tasa tayi baya ta juya ya daki fitilar titi.  Usman da ya ga motar ya tsaya da sauri ya k'araso wajan mutane sun fara taruwa ya bud'e motar aka fito da Yusuf daga motar Usman ya saka shi a tasa hankali tashe ya wuce asibiti dashi. Emergency aka kai shi aka fara duba shi dan ya bubbuge a fuska, Usman hankalin ya tashi sosai ya kire Abbah ya fad'a masa halin da ake ciki ba jimawa sai ga y'an gidan su da Abbah amma babu Ammah ya kalli Usman yace, "yana ina? Yaushe yayi accident din?." Usman yace, "ban sani ba naga motar tasa a hanya sai ban amince da tuk’kn da yake ba na kira shi akan nace yayi parking gani a bayan sa bai d'auka ba, shi ya wuce sai danger ta tsare ni wallahi ina zuwa na ganshi a gefe wata mota ta daki motar sa kuma ban ga motar da ta daki tasan ba.”  "Innalillahi wa'inna ilahiri raji'un! Ina yaje to?." Usmsn yace, "yayi yayi dani akan na raka shi wajan abokin Adam Yayan Ameena nak’i shine yace zai tafi da kansa, kuma wajan abokin Adam din da yaje shine zai auri Ameenan shiyasa nace bazan je ba dan naga alamaa shi bai ma gane shi ba lokacin aka nuna mana shi a matsayin miji. Wallahi Abbah yana son Ameena na tabbata tunani ne ya saka shi yayi accident, in ya rasa Ameena gabad’aya wanne hali zai shiga kenan?.” Abbah ya kalli y'an uwan sa da suke jin abinda yake cewa Mubakar yace, "Abbah na amince Yusuf ya saduda, dan Allah a bashi dama a karo na biyu." Abbah yayi shiru baice komai ba sai a lokacin likita ya fito ya kalli Usman yace, "kar ka damu ya samu bugawa ne kawai a hannun sa sai fuskar sa da ta ji ciwo amma bayan wannan babu komai." Usman yace, "na gode Dr." ya tafi suka shiga d'akin suka ga sun d'aure masa hannu ga fuskar sa an saka flasta a goshin sa da kuma gefen fuskar sa da kuma wuyan sa. Abbah ya d'aga goshin sa yace, "Yusuf kayi hak'uri bazan iya shiga maganar Ameena ba, bazan sake shiga maganar ba balle nace a sake baka dama. Kayi hak’uri ka rungumi k’addara a yadda tazo maka.” Shiru sukayi dukkan su kowa yayi shiru amma zuciyar kowa babu dad'i kowa yana kin tausayin  sa a zuciyar sa har Abbah din.         B'angaren Yaya Adam yana barin wajan Al'Ameen mota ya hau ya fita a nan yayi karo da motar a ajjiye ga alamun dukan motar nan a jiki, sai gaban da sa fad'i sosai da sauri ya faka motar ya d'auki waya ya kira Abbah  yake sanar dashi abinda ya faru sai ya juya motar ya nufi asibitin a nan ya tarar dasu har Ammah a zaune ya k'arasa shigowa d'akin suka gaisa gabad’ayan su yace, "ya mai jikin?." Usman yace, "Gashi dai a kwance har yanzu da yake abin bai jima da faruwa." Adam yace, "Subahanallahi,  naga fitowar sa daga wajan Al’ameen, Daman shima Al’Ameen din sai da yace min bai amince da yanayin sa ba, ai kuwa na fito na hau titi naga motar tasa a ajjiye badan ma na gane motar ba bazan kula da motar ta sa bace ba." Abbah yace, "Allah Sarki ka kyauta wallahi, Allah ya bar zumunci. Allah ma ga taqaita ai, ciwo ne a fuska da kuma hannun sa kawai.” Ya amsa da amin kafin yace, “Allah ya cigaba da kiyayewa.” Nan ma suka amsa yayi musu sallama ya tafi.  Inda ya fito dan zuwa yaje sannan ya koma gıda ya tarar da falon babu kowa sai Zaytun da Shukra suna wasa, "Ameena!" Ya fad'a da k'arfi ta jiyo ta amsa daga ciki ta fito yace, "kin bar yara suna wasa su kad'ai sai sun yi b'arna?." Ameena tace, "Muna ciki Muna hira ne, Yayan Bauchii ce tazo." Sai ga Yaya ta fito ya kalle ta yace, "ke kuma zuwan yamma?." Tayi dariya tace, "barka da Yamma Yaya."   "Yauwa barka. Ya hanya?." "Alhamdulillah. Ina zuwa kana fita shiyasa." "Eh na fita ma sai na canja hanya na wuce asibiti, motar Yusuf na gani baban Zaytun a gefen titi ashe accident yayi sai naje na duba shi na dawo."  Yaya tace, "Subahanallahi, amma dai akwai sauk’i babu babban ciwo ko?." "Eh babu, Mahaifin da yace min bugawa ce kawai a hannu sai fuskar sa da taji ciwo." "Allah ya kara Lafiya." "Amin." Ya kalli Ameena yace, "baki ce komai ba, baki ji nace baban y’ar ki bane yayi accident?." Tace, "Alalh ya bashi lafiya" ta fad'a tana juyawa ta koma ciki ya bita da kallo Yaya ma haka ya kalle ta yace, "me kika fahimta a yanayin ta? Tana son komawa Yusuf ne?." Yaya tace, "bana ce ba gaskiya, amma a zahiri bata nuna hakan amma ban san meye a zuciyar ta ba. Abu d'aya na sani har gobe tana son Yusuf." Yaya Adam yace, "meyasa kika ce tana son sa?." Tayi dariya kad'an tace, "Saboda shi so so ne." Yayi y’ar dariya yace, "kuma Yusuf din daga wajan Al'ameen ya tafi, duk naji abinda suka tattauna rok’on sa yake akan ya shiga gaba wajan sake samun Ameena, ina jin bai fahici shine zai auri Ameena b." Yaya tace, "Allah Sarki, watakila tunani ya saka shi yin accident din."  Yaya yace, "to wai ke a ganin ki zata iya komawa ko me?." Yayan Bauchi tace, "to ita nadama dai a bayyane take kuma Yusuf ya yita duk da zahirin sa muka sani bamu san abinda ya b’oye a zuciyar sa ba, amma indai har Yusuf da gaeke ya canja yayi nadama ya gane kuskuren sa Ameena ta koma ba wani abun bane." "Saboda bakya kishin abinda yayi mata kenan?." "Ba haka bane, abu ne a bayyane Yaya yana sonta tana sonsa wannan mikin abinda yayi mata shine a zuciyar ta, amma da za'a ce mata wannan ba wancan Yusuf din bane wani ne daban sabo wallahi a guje zata amince. Na farko dai suna da yarinya ya kamata ka tuna wannan, na biyu kuma tana tausayin sa sosai dan yana sonta wallahi ko a lokacin da abubuwan suka dinga faruwa ma yana sonta iskanci ne da kuma matar da ya aura. Dan haka a yanzu in ta koma masa wallahi a b’angarena babu damuwa dan nasan abinda ya aikata a baya wallahi bazai sake aikatawa ba a yanzu ba.” Yaya Adam ya sauke numfashi yayi shiru na wani lokaci yana kallon takamar mai tunani kafin ya tashi ya shiga ciki yana cewa, "kema kije ki huta." Tayi murmushi ta koma d'akin Ameena tana jin tausayin Yusuf har cikin zuciyar ta domin soyayya tana bashi wahala a bayyane hakan ya nuna yayi nadama aka sake bashi dama sai kowa yayi mamakin sa. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid #500 Book3  037          Alhaji Bello tun bayan guduwar su Fiddausi duniyar ta juya masa baya, duk yadda ya kai ga ganin ya daidaita lamarin sa kasawa yayi komai ya kwab'e, komai ya lalace tun yana ganin abun kamar wasa har ya daina domin kuwa tun yana hauka sama-sama har ya zama hauka yake yi tuburan sai da aka kulle shi a d'aki. Duk wani harkar kasuwancin sa ta d'urkushe kowa ya gushe shi babu wanda yake tashi daga shi sai y'an aikin da akwai a gidan. Babu wanda yake sauraren sa su kansu tunda suke kulle shi basa zuwa inda yake saboda duka yake yi gashi tsirara yake yi, a d'akin yake kashi ya cinye kayan sa yayi fitsari yabi ya shanye abin sa.       Y'an aikin ne gabad’aya suka had'a meeting akan k’ananun y'ay'an sa duk suka taru dan su tattauna akan su mutum d'aya yace, "Alhaji Bello dai ya haukace, hauka wanda aka kira tuburan shi Alhaji yake yi, haukan da yake yi dakyar ya warke gaskiya sai ma dai ya sake lalacewa. Ba shine abin tausayi ba wannan yaran sune abin tausayi, ko wacce uwa ta gudu ta bar masa yaro gashi yanzu shi ba hankali ne dashi ba balle yasan abinda zaiyi akan su. Kafin kowa  ya tattara kayan sa ya gudu a fad'a mana ya zamuyi dasu?. D’a na kowa ne, dan min taimake su ba wani abun bane lada ma zasu samu akan hakan.” Baba Ladidi tace, "bamu san dangin sa ba balle mu kai su, dan ni badan yaran nan ba wallahi da yanzu na Kama gabana. Bamu San inda iyayen da suke ba balle mu kai musu yaran su, gashi an kira uwar gidan sa an sanar da ita tace kar a sake mata waya akan lamarin sa, babu ita babu shi kuma babu yaran ta a lamarin sa." D’aya yace, "Akwai shawara, me zai hana mu nemi Nabila ko tasan wani nasa?." "Eh shawara ce mai kyau, ina da lambar ta kuma bara na kira naji me zata ce." Aka kira Nabila wayar na ringing bata d’auka ba aka sake kira sai ta d'auka yace, "Hajiya Nabila an tashi lafiya?." Daga can b'angaren tace, "fadi Matsalar ka kawai malam." "Daman akan rashin Lafiyar Alhaji Bello ne muka kira ki, daman...." Ta dakatar dashi tace, "kaga fad'a min Matsalar ka kawai bana son hayaniya." "Daman muna  so mu san wani nasa ne saboda mu kai yaran nan nasa." Tayi tsaki tace, "kai baka sanni  ba ban San ka ba, ban san wani Bello ba balle ayi min zancen yara ka gane ko?. Daga yau ka goge lambata daga wayar ka kar wani abu nasa ya sake tasowa ka kirani ka mana yi min maganar banza ka gane ko?." Kafin yayi magana ta katse kiran ya kalle su  cike da mamaki da tsoro yace, "lallai duniya budurwa wawa, wai Nabila ce take cewa bata san shi ba kar a saka had'a ta dashi koda nan gaba." Duk suka girgiza kai kafin daya yace, "Yanzu meye abu na gaba?." "Kawai mu yiwa yaran nan video mu d’ora a duniya iyayen su in sun gani su zo su kwashe yaran su." "Shawarar tayi gaskiya, Tunda bamu da wata mafita sai wannan muyi hakan kawai." Sai kuwa suka d’auko yaran suka jera su akayi musu video suka fad'i komai a video.        Kafin wani lokaci abin ya zata social media wanda bai san ma halin da Alhaji Bello yake ciki ba yanzu ya sani wanda basu san halin sa ba sun tausaya masa sosai suna ta jimami, matan sa da ya saka wanda suka bar yaran da wanda ma bai saki ba duk an gani  haka aka je ana d'auko yaran dan iyaye suna cewa babu laifin yaro da za'a barshi ya wulakanta. Fiddausi bata san abinda ake yi ba tunda ba waya ce da ita ba sai da Yaya tazo take nuna mata tana fad'a mata abinda ya faru, hankalin ta ya tashi gashi bata da lambar su Naja'atu balle ya kira su ta fad’a Muş’u halin da ake ciki. A lokacin Abba yace zasu je kotu alqali ya raba auren tunda dai ya zama mahaukaci zama da mahaukaci bazai yu ba. Ai kuwa a washe garin ranar alqali ya raba auren su bayan an tabbatar da ya haukace, fiddausi kamar an saka ta a aljanna haka take ji saboda farin ciki abinda ya rage mata kawai son ganin su Naja'atu. A ranar da aka raba auren Fiddausi tana zaune tana jimamin duniya da kayan cikin ta, wto komai ka aikata sai ka jirbe shi ko a duniya ko kuma a lahira. Yanzu meye amfanin rayuwar alhaji Bello? Ace mutum ya haukace yana cikin kashi da fitsari babu mai sauraren sa balle ma ass  a wanne hali yake ciki? Kowa ya guje shi saboda mummunar dabi'ar da yake da ita, hatta masu zuga shi akan lamarin duk sun gudu daman sai dadi ake tare da kai da wahala ya samu sai a gudu a barka. Tana zaune sai ga Mama ta bata waya tace, "Gashi neman ki ake yi." Ta goge hawayen idanun ta ta karb'i wayar ta saka a kunne daga can akace, "Fiddausi Naja'atu ce. Fiddausi tace, "Naja'atu! Kece?.” “Nice Fiddausi, ya kike?.” “Lafiya lau, daman kina da lambar Mama?." "Bari kawai Fiddausi, da naje Abuja ne zan d'auko yaron wajena  shine na shiga gidan na d’auko wayar nan da kika bani lamba kawai dan na neme ku keda Aliya. Dan in ba ta haka ba ban San a inda zamu ga juna ba.” Fiddausi tace, "ashe kin je kin d'auko shi." "Naje Fiddausi, Su Mama ne suke cemin bashi da laifin komai akan me bazan d'auko ba? Shine naje Gashi yanzu a wajena har bana son Tuna jinin Alhaji Bello ne wallahi.” "Haka ne kama bashi da laifin komai bai kuma san komai ba. Hak’uri zaki yi ai komai zai wuce zai kuma zo k’arshe, Allah yayi shine mahaifin sa babu Wanda zai canja faruwar hakan.” Naja'atu tace, "amma an raba auren ko?." Fiddausi tace, "d'azu muka je kotu alqali ya raba auren tunda duk zance ya baza duniya ya zama mahaukaci." Naja'atu tace, "ni zan gaya miki ya zama mahaukaci Fiddausi, nifa naje gidan, wallahi tun daga k'ofar d'akin da yake zaki dinga jiyo wari gashi yana ciki yana ihuuu babu wanda yake bud'e shi balle aje inda yake. A nan yake komai babu ruwan wani da yaci ko yasha duk sun gudu sun barshi. Ba’a San dangin da ba balle a fad’a musu, ke ko an sani ma ba kowa ne yake son nuna su Bello yace d’an uwan sa bane ba. Wato Fiddausi a duniya in baka aikata alkhairi ba wallahi kana cikin mayuwacin hali. Ki kalle mu mu kan mu sai da muka girbe abinda muka shuka balle su Alhaji Bello." Fiddausi ta share hawaye tace, "Mun ga sakamako kuwa mu ma balle shi, shi ai shaidan ne." Naja'atu tace, "da muka samu iyayen mu suka yafe mana ma Mun gode Allah, Aliya kuwa tace min da taje bata samu mahaifin ta ba ya rasu, sai kuka take bata sani ba ko yafe mata ko kuma da bak’in cikin ta ya mutu bata sani ba." Ta girgiza kai tana kuka kamar suna ganin juna tace, "in sha Alalh ya yafe mata. Ki bani lambar ta duk da yanzu ni bani da waya har yanzu." "Nima ta Mama ce sai na samu hankalina ya dawo jikina sai na samu wayar." "Ki tura min a wayar Maman sai mu gaisa da ita kafin mu saka lokaci mu had’u. Nan gaba mu zamu yiwa wasu fad'a in muka ji sun zab’i irin rayuwar da muka zab'a."  Naja’atu tace, “ai Mun ga zahiri, Mun ga sakamakon mu tun a duniya.” Fiddausi tace, “Mun gode Allah ka da abin ya tsaya mana iya nan da bamu san a wanne Hali zamu tsinci kan mu ba muma.”  “Bari kawai Fiddausi Allah ya tarfawa garin mu nono.” “Su Bello kuma sai ayi mutuwar wulakanci,” Tayi dariya kawai suka cigaba da hirar abinda ya shafe su kafin suyi sallama su kashe wayar.       Yusuf ya samu sauk’i sosai har lokacin babu Wanda yake masa maganar Ameena shi kad'ai yake tunanin ta a zuciyar sa amma babu wanda yake masa zancen ta duk da a yanzu duk sun saduda sun amince ya karb'i kuskuren sa amma babu Wanda yake goyan bayan sa a zahiri. Bayan ya koma gida a daren da ya koma Ammah taga ya fito ya kwance hannun nasa wanda aka d'aure ta kalle shi tace, "meyasa ka kwance hannun?ina zuwa kuma?." Yayi shiru baiyi magana ba tace, "ko wajan Ameena din zaka je?." Ya d'aga Kai alamun eh kamar maraya yace, "ka daina wahalar da kanka Yusuf, Ameena bazata dawo rayuwar ka ba meyasa ka kasa ganewa." Ya kalli Ammah yace, "bazan gane ba Ammah, sai ranar da aka d'aura auren ta da wani a lokacin zan gane Ameena ta barni Kenan." "Kafin lokacin yazo ya kamata ka san zai zo yadda in ya same ka zai zo maka da sauki Yusuf." Ya girgiza kai yace, "Ammah bazan iya ba walalhi." Ta d’aga Kai tace, "shikenan, sai ka dawo." Ya kalle ta yace, "Ammah dan Allah sau d'aya kice Allah ya bani sa'a." Ta kalle shi taga ita yake kallo tayi shiru na wani lokaci kamar baza ta fad’a ba kafin tace, "Allah ya baka sa'a Yusuf." Sai yayi murmushi yace, "Amin Ammah, na gode." Ya fad'a yana fita ta bishi da kallo tace, "iska tana wahalar da mai kayan kara Yusuf. Allah ya kawo maka mafita a abinda yake damun ka, amma dawowar Ameena ba abu bane wanda zai yu a yanzu ba.” Kai tsaye mota ya hau ko Usman bai nema ba ya tafi gidan Yaya Adam a karo na uku cika da k’arfin guiwa. A k'ofar gidan ya tsaya ya fad'awa mai gadin gidan ya sanar dashi zuwan Yusuf ya ja ya tsaya a jikin mota. Yaya Adam a lokacin yana zaune dashi da Ameena da Yayan Bauchi da matar sa suna ta tattaunawa akan abubuwan da yake tunkaro su a yanzu shine auren Ameena. Sallamar sa ya saka suka kalle shi ya rage tsaho yace, "Alhaji Yusuf yace a sanar da kai zuwan sa yana waje." Yaya Adam ya sauke numfashi ya dafe kansa yayi shiru na wani lokaci kafin ya kalle shi yace, "kace yazo." Ya kalli Ameena da suka had'a ido ya kalli Yayan Bauchi yace, "ban san ya zanyi da Yusuf ba wallahi, duk masufar da nake ji da ita ya fara bani tausayi ko zaryar nan da yake ma ta isa ya baka tausayi. Bana so nace bazan ganshi ba ya sake tafiya yayi accident gwara yazo a sake gwabzawa.” Babu wanda yayi magana a cikin su Ameena ta mik’e zata koma Yaya yace, "dawo ki zauna." Ta dawo ta zauna sai ga Yusuf ya shigo da sallama Yaya Adam ya amsa yana kallon sa. Gaishe shi yayi ya gaishe da Yayan Bauchi ta amsa da murmushi ya kalli Ameena yace, "Ameena Barkan ki da dare." Sai ta kawar da fuska gefe ba tare da tace komai ba ta d'aure fuska sosai. Yaya Adam ya kalle shi yace, "ya kuma karfin jikin?." Yusuf yace, "Alhamdulillah."  "Allah ya k’ars lafiya." Ya amsa da amin kafin Yaya ya sake cewa, "to meye yake tafe dakai Yusuf?." Yusuf taja numfashi ya sauke yace, "akan maganar nan ne dai Yaya, na kasa jure cewa da kayi kar na sake zuwa gidan nan sai da nazo, ji nake ko zaka dinga yankar naman jikina sai nazo na same ka a karo na uku Yaya." Yaya Adam yace, "Yusuf bafa dani zaka zauna ba, ga da wacce zaka zauna nan tana zaune tana Jin ka meye nawa da zaka dinga zuwa wajena?." "Kaine tsani a wajena, dole kai zan fara tunkara ba ita ba, kai kanka baka amince ba balle ita Yaya?."  Yaya Adam ya kalli Ameena kafin yayi magana Yusuf yace, "duk abinda idanun ka suka gani a wancan lokacin na gyara wallahi, duk abinda kake gudun ya sake faruwar a wannan lokacin bazai sake faruwa ba. Wannan alqawari nayi da Allah bazai sake faruwa ba duk tsanani duk dad’i.” Yaya Adam kallon sa yake yi domin nadamar yake gani akan fuskar sa sosai ta bayyana abinda bai gani ba a kwanakin baya, har zuciyar sa a yau ya amince Yusuf yayi nadamar abinda yayi kuma koda wasa nan gaba bazai sake aikata hakan ba sai  dai nuna masa ba yace, "ana iya cewa na daina a baki amma kuma  a zuciya ba haka abun yake ba, da zarar Ameena ta sake komawa shine an ta zama nama, wannan sunkuyar da kan da kake kana kuka duk na banza ne, tana komawa ka tashi daga b'era ka koma zaki sai abinda kake so shi zaka yi dan kana ganin sai ka sake furta kalmar saki a kanta ai zata fita." Ya girgiza kai yace, "A'a wallahi, na daina wallahi duk abinda nake yi bazan sake yi ba, har zuciyar ta nake fad'a maka wannan, kuma Allah kad’ai shine yasan meye a zuciyata bayan shi babu wanda zai gani, da akwak wanda zai gani da na baka dama ka gani Yaya kodan ka gasgata da gaske nake ba wasa ba." Yaya Adam ya sauke numfashi yace, "me kake so nayi maka yanzu?." "Dama nake so a sake bani a karo na biyu domin gyara abinda na b'ata." "Gaka ga Ameena nan indai har ta amince zata koma gidan ka Yusuf zan dawo maka da Ameena, in kuma bata amince ba sai dai kayi hak'uri." Ya kalli Ameena da take zaune ya kalli Yaya Adam yace, "gabana fad’uwa yake ban san taya zan mata magana ba." Sai ya bawa Yaya Adam tausayi sosai  ganin kamar ba namiji ba duk ya susuce ya kalli Ameena yace, "Ameena ga Yusuf nan in kin amince zaki koma masa a karo na biyu na amince nima, in baki amince ba shikenan sai yayi hak'uri." Yusuf ya juya yana kallon ta yace, "nasan nayi kuskure Ameena, nayi laifi ko nace nayi laifuka amma ki yi hak'uri a karo na babu adadi zan gyara bazan sake gangancin hakan ba, bazan sake barin ki kuka ba indai ba na farin ciki ba, bazan sake barin ki a damuwa ba wannan alqawari nayi miki kuma zan cika shi indai ina da numfashi da rai. Ki amince ki bani dama dan Allah, badan ni ba kuma ba dan halina ba dan Allah dan kuma iyayena dan kuma Zaytun." Yayi shiru na wani lokaci yana kallon ta dan yaji me zata ce sai yaga tayi murmushi tace, "Ka cire batun zan koma gidan ka Yusuf a kaf cikin rayuwar ka, na amince na yafe maka na kuma yarda kayi nadama amma damar ce bazan iya sake bayarwa ba gaskiya.." ya girgiza kai yace, "Dan Allah kar kice haka Ameena, kar ki kalli baya ki kalle ni matsayin sabon  Yusuf wanda ya canja daga wancan wanda kika sani dan Allah, Ameena indai zaki koma gidana koda baza ki yi min magana ba na yarda, na yarda ki gwada ni in kin koma daga ranar har shekarun da kike so na yarda, na yarda a zarar kinga canji kice na sake ki zanyi hakan wallahi. Duk abinda kike so zanyi." Ta kalle shi tace, "na koma ka cigaba da dukana ko?." Ta zuba masa ido sosai dan so take ya fahimci abinda take nufi ba dukan take nufi ba bata son fad'a a gaban su Yaya dan bai san yana shan giya a baya ba ita kuma kodan y’ar sa zata rufa masa wannan asirin har abada. Had'a ido sukayi sai kuwa ya gane mai take nufi ya kulle ido ya bud'e a sanyaye yace, "Na daina, in kina tunanin k'arya nake ki tambayi Ammah zata baki labarin wannan Yusuf din na yanzu. Wallahi na daina duk abinda kike tunani, na daina duk abinda kike hange a lokacin baya. Tun daga lokacin da aka sanar da su Ammah ina s.." kafin ya k'arasa ta katse shi tace, "a baki kake fad'a sai na zauna dakai sannan zan sake tabbatar wa, kamar yadda ban san halin ka  na b’oye ba a wancan lokacin sai da ma zauna da kai, haka yanzu ma bazan sani ba sai na zauna dakai." "Wallahil azim duk wani abu da kike tunani a kaina na sauke shi Ameena, shi kuskure in ka aikata abu kad'an ne yake sakawa ka gane ka kuma canja. İn kuma kayi alqawarin canjawa kana addu'a Allah sai ya baka dama kaga ka canja." Ta tab’e baki tace, "to Ina taya wace zata aure ka murnar canjawar ka Yusuf, zata auri sabon Yusuf ba wanda na bari a baya ba. Ina taya ta farin cikin samun ka a hakan.” Ya rausayar da kai yace, "Ameena kar kice haka dan Allah!." Ta girgiza Kai tace, "na riga nace, ina kallon ka matsayin mahaifin Zaytun zan cigaba da yi maka wannan kallon har abada, na kuma yafe maka duk abinda kayi min. Amma batun na koma gidan ka ka cire shi daga cikin ranka Yusuf, domin ba abu bane da zaiyu ba a yanzu." "Baki yafe min din ba kenan Ameena, baki daina fushi dani ba, baki cire abinda nayi miki a ranka ba kenan tunda har kika ce haka." "Na yafe maka Yusuf, na manta da duk abinda kayi kawai bazan koma gidan ka bane saboda yanzu bana sonka!, bana qaunar sake zama dakai a matsayin mijina wanda zamu zauna inuwa d'aya." Yusuf sai a lokacin hawaye suka fara zarya a fuskar sa yace, "na yadda ko bakya sona ki yarda ki koma, a hankali na tabbata zaki so wannan Yusuf din domin ba na baya bane ba wallahi." Ameena ta kalle shi sai ta rufe ido ta bud'e tace, "sam bazan aikata hakan ba, Yusuf yadda kace wancan Yusuf din ya mutu to nima Yusuf ya jima da mutuwa a rayuwata, wannan sabon Yusuf din mahaifin Zaytun ne shi nake kallo a haka amma ba wai wancan ba." Yayi shiru dan bai san mai zaice ba sai ya zuba mata ido yana kallon ta cikin rashin sanin abinda zai ce tace, "ka manta dani bazan sake komawa gidan ka ba Yusuf, ka cire ni daga ranka bazan sake zama dakai matsayin miji ba. Amma zan cigaba da magana dakai a matsayin mahaifin Zaytun, na kuma yafe maka abinda ma aikata kana sane da wanda ka aikata baka sane duk Ameena ta yafe maka. Amma ka cire batun zata saka zama dakai a gida daya, domin kuwa bazai sake faruwa ba har abada.” Sai yayi murmushi ya girgiza kai yace, "kodan Zaytun ki taimaka ki sake tunani Ameena." Itama sai tayi dariya kad'an tace, "kai baka san zamanin komawa gidan miji zaman yara ya wuce ba? Kai baka san wannan lokacin ya k'are ba Yusuf?. Ai in zan koma sai dai na koma dan ra'ayin kaina ba dan Zaytun ba, sai na koma ko dan saboda Ammah ban koma dan Zaytun ba ka gane?. Ka cire hakan daga ranka Yusuf domin bazai yu ba, aurena saura kwanaki kad'an ya rage ka ajjiye wannan batun a zuciyar ka domin ba abu bane da zai yu ba Yusuf." Ya goge idanun sa ya kalle ta yace, "shikenan Ameena na gode da kika yafe min din ma, amma ina so ki sani ko yanzu na fita kika ji labarin na mutu Ameena ki amince akwai soyayyar ki da damuwar wannan abun a zuciyata zan koma ga Allah. Bazan cire rai da na rasa k'i ba sai ranar da na tabbatar an d'aura auren ki, daga wannan ranar ban san a inda rayuwata zata taya ba, kina jin abun kamar wasa ko kamar film ko Ameena?." Sai yayi murmushi yace, "wallahi na rasa ki in ba Allah ne ya kiyaye ba za'a iya rasa ni nima." Ameena tace, "daman lokacin kane yayi, kuma komai yana da sila ma tabbata silar taka kenan." Sai yayi Murmushin takaici ya kalle ta yace, "haka ne, na tabbata wannan shine silar barina duniya. In kin samu labari ki taya ni d addu'a." Sai jikin ta yayi sanyi sosai a lokaci d'aya ta bud'e baki zatayi magana ya riga ta yace, "tunda zan mutu babu hakkin ki a kaina na gode Allah, amma zan zo ace na mutu a matsayin mijin Ameena ba tsohon mijin Ameena ba, sai dai kash na rasa wannan damar, nayi wasa da damar da na samu a hannuna, nayi wasa da amanar Ameena daka bani, shiyasa na kasa ganin daidai a rayuwata har yanzu. Gani dai yanzu a zaune kamar mai hankali amma ni nasan babu hankalina tare dani.” Ya kalli su Yaya Adam da yake kallon sa Yayan Bauchi harda hawaye yace, "na gode da damar sake magana daku da kika bani. Yaya Ameena tace bazata sake zamana dani ba, banga laifin ta ba dan ita kad'ai tasan zaman da tayi dani a baya, amma na shaida mata na canja zuciyar ta tak’i amincewa da na canja din. Shikenan Yaya ba hak’ura, amma bazan cire rai da samun ta ba daga nan har Allah ya tashi duniya."  Shiru yayi dan kuka ne yazo masa lokaci d’aya kusan sacan goma yana a haka kafin ya goge idanun sa yace, "kuyi hak'ur" ya tashi tsaye duk da kansa da yake masa ciwo sosai yace, "Na gode da yafe min din da kuka yi iya wannan ya ishe ni duk da na rasa farin cikina na har abada, na gode Allah ya saka da alkhairi Allah ya sake had'a fuskokin mu a aljanna" ya fad’a yana saka takalmin sa yayi hanyar fita har zai fita sai ya juyo ya kalli Ameena a lokacin tana goge hawayen idanun ta tace, "Ameena ki saka ranki har gobe Yusuf yana sonki da kuma sonki zai mutu, yaso ki bashi damar nuna miki ya gane kuskuren sa amma bai samu ba. Ki tabbatar da yana sonki son da a baya baiyi miki shi ba, ki tabbatar da yanzu Yusuf yake sonki soyayyar baya ba komai bace Ameena. Na gode ko bana da rai na tabbata baza ki bar Zaytun tayi kukan maraicin uba ba, Allah ya baki zaman Lafiya a sabon gidan da zaki je, ya baki farin ciki wanda ban baki ba lokacin da kika tare dani" yana gama fad'ar hakan ya fita daga dukka su sun kasa motsawa daga inda suke zaune dan ya gama tafiya da zuciyoyin su baki d’aya. #Mai daki #Book3 #paid #500 #Nana Haleema. Book3 038         Yayan Bauchi da take zaune a kusa da ita ta kalli Yaya Adam da jikin sa yayi sanyi sosai kana kallon sa zaka fahimci hakan ya kalli Aisha ya sake kallon Ameenan yayi karfin hali yace, “to meyasa kike kuka kuma?.” Yayan Bauchi ta dafa ta tace, “meyasa kike kuka kuma?, kin fad’a masa abinda yake zuciyar ki meye na damuwa?.” Ameena ta goge idanun ta tace, “babu komai.”  Yaya Adam yace, “Ameena!.” Gaban ta ya fad’i jin kiran da yayi mata tasan yana nuni da ta nutsu yace, “da ace kin sake sabon aure da ace kin koma gidan mijin ki kar ki tunanin Yusuf ne kawo wani ne daban mahaifin Zaytun a zuciyar ki wnne kike so?.” Ameena ta sauke numfashi tace, “Yaya maganar nan ta wuce ai ni bana son tuna ta ma wallahi.” Yace, “tambayar ki nayi kawai ki bani amsa.” Tayi shiru bata ce komai ba ta kalli Yayan Bauchi itama ita take kallo ta sauke numfashi ta kulle ido ta bud’e amma batayi magana ba. Yaya Adam yace, “ki bani amsa.” Tace, “Yaya indai zan samu chanjin da nake fata, bazan sake shiga abinda na fito daga ciki ba, Yaya aure biyu ko a zuciyata bana so Alalh ya sani. Amma ni gidan Yusuf ne bana son komawa, in aure biyun shine alkhairi ne a wajena Allah yasa hakan alkhairi ne dan na tabbatar Yaya Al’ameen bazai yi kwatankwacin abinda Yusuf yayi ba.” Yaya Adam yace, “shikenan to, Allah yasa hakan shine alkhairi a rayuwar ki.” Suka amsa da Amin ta tashi ta shiga ciki jikin ta a snayaye sosai ya kalli su Yaya da suke goge hawaye yace, “tabbas da ta amince zata koma zan bada goyan baya a kan hakan, Al’ameen bashi da damuwa domin shi da kansa ya amince da Yusuf ya gane kuskuren sa, kuma ko giyar wake yasha abinda ya aikata a baya a yanzu bazai yi ba” ya ja numfashi yace, “tace bata so babu lallai babu dole.” Yayan Bauchi tace, “Amma yana sonta wallahi bana tunanin shi Al’Ameen yana mata son da Yusuf yake mata a yanzu. Namiji kamar sa yana hawaye akan mace wacce ba uwa ba ai kasan ba abu mai sauki bane ba. Kawai in ta tuna abubuwan da yayi ne baza tayi marmarin komawa ba, sannan tana tunanin in fa ta koma ta koma gidan jiya ne  duk da daman akwai halin da bazai canju a halayen sa ba amma daman ko wacce mace akwai halin mijin ta da take hak’uri dashi. Abinda bama ganewa a yanzu in mace ya fito daga gidna mijin ta ya nemi ta koma sai ace sam bazata koma ba, eh da Gaskiyar su saboda in maciji ya sare ka sau d’aya baza kazo ya sake cizon ka ba, amma wani lokacin komawa gidsn mijin shine alkhairi wallahi, ni na gani akan mutane da yawa an koma kuma an canja din abinda aka bari babu sai halayya wacce ba’a raba d’an Adam da ita.” Anty Aysha tace, “haka ne kam.  Baya muke gani wanda daman dole shi samu gani gaskiya amma wani lokacin ka koma din yafi sabon aure ness ba kusa ba, kowa akwai k’addarar sa. Ya tab’a min zuciya nima sosai in da rabon komawar ta wajan sa Allah ya daidaita su, in babu Alalh yasa Al’ameen ya zama alkhairi a wajan ta.” Yaya Adam yayi shiru baice komai ba har suka gama magana sannan ya tashi ya shiga ciki dan maganar da suke ma ta watse.           Yusuf a haka Allah ya kai shi gida Lafiya yana faka motar bai fito ba ya kifa kansa a kan sitiyarin motar yana kuka sosai ba kad’an na, in ya tuna abinda Ameena tace sai yaji zuciyar sa na rawa sosai kansa yana sarawa jijiyiyon kan suna harbawa kamar zasu tsinke. Fitowa yayi daga motar yana dafe da kansa yana jin kan na juyawa sosai sai ya tsaya na wani lokaci sai kuma ya cigaba da tafiya zuwa cikin gidan. Kamar ko yaushe Ammah ce kawai sai y’ay’an Abie da suka zo tana ganin sa ta bishi da kallo tace, “Yusuf Lafiya?.” A gaban ta ya  zube ya d’ora kansa a kan guiwar k’afar ta yayi shiru baice komai ba. Duk yaran suka bishi da kallo d’aya daga cikin yaran yace, “Ammah Daddy bashi da lafiya?.” Bata amsa ba ta d’ora hannun ta a kansa taji zafi sosai tace, “Yusuf yanzu baza ka sakawa zuciyar ka salama ba? Baza ka karb’i kaddarar da tazo maka ba?, Baza ka yi hak’uri ka karb’i jarabawa hannu biyu ba dan Allah?. Ameana in rabon kace zaka sake samun ta in ba rabo bace ba baza ka mallake ta ba sai dai kayi hak’uri rabon zaman ku ya k’are . Wannan damuwar da kake ciwo zata saka maka wallahi in ka kwanta ciwo kuma kanka ka cuta ba wani ba, Ameena tayi hak’urin zama da kai a baya a yanzu kuma bata son sake saka kanta a cikin abinda ta fita kwnakain baya ba, shiyasa ko ni bana son Ameena ta amince zata koma gidan ka Yusuf.” Bai d’ago kan ba yace, “Ammah Ameena tace nayi hak’uri baza ta dawo ba, Ameena tace tana kallona matsayin mahaifin Zaitun ba wanda zata dawo gidan sa ba. Ammah meyasa takasa yarda na canja halaye na? Meyasa ta kasa amincewa da Yusuf din yanzu bana baya bane ba Ammah?.” “Ko ni ban amince ba ai Yusuf, a yanzu baza ta amince ba daman saboda sai ta zauna dakai zata tabbatar ka canja, to in ta yarda ta sake zama dakai kuma kazo baka canja din ba?.” Ba tare da ya d’ago ba yace, “Ammah na rasa da wanne baki zan muku jawabi Ammah, na rasa me zance muku ku fahimci na canja, na rasa da wanne yare zanyi bayani a fahimce ni, na sare na gaza bani da k’arfin guiwa. Wallahi Ammah akace Ameena zatayi aure ko tayi aure bana  jin zan sake kwana d’aya a duniyar nan.” Shiru Ammah tayi tana jin d’umin hawayen sa na shiga jikin taya sake cewa, “tace bata sona Ammah bata qaunar ganina.”  Ammah tace, “sai kayi hak’uri kai ta addu’a, watakila rabon zaman ku ya k’are Yusuf, duk yadda ka kai ga son hakan bazai kasance ba in Allah bai yi ba.” Shiru baice komai ba a lokacin Ammah ma tayi shiru bata ce komai ba ana haka sai ga Abbah ya shigo da Mubakar a bayan da ganin yadda Yusuf yake sai yayi murmushi ya zauna yace, “Bashi da lafiya?.” Ammah kamar tayi kuka tace, “to gashi dai kamar mai Lafiyar kamar mara ita.” Ammah ta dafa kansa tace, “Kansa ciwo yake yi sosai gashi yayi zafi” ta d’ago fuskar sa sai taga idanun sa a rufe suke sai fuskar tayi ja sosai. Abbah ya sauke numfashi yana kallon sa yace, “Yusuf ni ban san meyasa ka dawo da Ameena cikin ranka ba wallahi, a yanzu kai kasan tayi maka nisa to meye na damuwa kuma? Tun farko ai na fad’a maka ka daina zuwa inda take amma ka k’i yanzu gashi nan kana cutuwar da kanka a banza a wofi. Waye yace ka sake ta a baya? Waye yace kayi mata abinda kayi mata?. Da kana sonta ka kasa dawo da ita tun baya sai yanzu?.” “Abbah tun a da tana raina babu inda taje ba dawo da ita nayi ba” sai ya dafe kansa yace, “kaina ciwo yake min sosai.” Mubakar yace, “Sannu, ai dole kai yayi ciwo.” Ammah tace, “ko asibiti zamu je ne?.” “A’a yasha magani zai dawo daidai in sha Allah” ya fad’a yana kallon Ammah din. Ammah ta sauke numfashi tace, “Mubakar kuje yasha maganin ya samu ya kwanta.” Yusuf yace, “a barni a nan.” Duk suka yi shiru ana kallon sa gabad’ayan su yanzu tausayi yake basu amma basu da abinda zai iya dan Abbah yayi rantsuwa babu shi a lamarin Ameena in tayi ruwa rijiya in bata yi ba masai.        Ameena tana shiga d’aki ta tsaya a jikin k’ofar a ta goge idanun ta tana son kawar da damuwar da take ji a ranta duk tana jiyo maganar su wayar ta tayi k’ara ganin lamba ya saka ta share aka sake kira sai ta d’auka taji ance, “Hajiya Ameena.” Jin muryar Fiddausi sai tayi murmushi tace, “Fidy ya kike?.” “Lafiya lau, ya su Yayan suna Lafiya?.” “Qalau suke, wannan number fa?.” “Ta mama ce.” Ameena tace, “oh.” Jin hakan sai Fidy tace, “akwai abinda yake damun ki ne?.” Ameena ta suka numfashi tace, “babu abinda yake damuna, me kika ji?.” “Ga maganar ki nan ta canja. Ko maganar Yusuf din ce?.” Ameena tace, “Itace Fidy, ni nace bana son komawa gidan sa na fad’a masa fuska da fuska amma yak’i ya hak’ura.” Fidy tace, “yo meye na damuwa dan yak’i ya hak’ura Ameena?.” “Ni ba damuwa nayi ba, kawai bana so ya dinga zuwa gidan yana ta min magiya akan abinda bazan iya ba.” Fiddausi tace, “Ameena dan kin k’i ne amma nidai nace miki ina sonki komawa wajan Yusuf, amma kince ke kad’ai kika San abinda kika ji a gidan sa nasan hakan amma wani jin dad’in yana zuwa ne a lokacin da ka fara shan wahala a rayuwa. Sannan wani kuskuren baka sanin ka aikata shi sai bayan kayi wani kuskuren kake lura ashe wancan ma kuskure ne, sannan wani tuban ko nace wani gidan tsohon mijin  in ka koma wallahi ya kan zama fiye da zaman farko farin ciki. Ana cewa kome mu k’ark’are inji Hausawa, eh haka ne akwai halin da tabbas yana nan amma wallahi irin su Yusuf da suke ganin kin kusa kubce musu kuma sukayi nadamar da suke zubar da hawaye baza su saka maimaita kuskuren baya ba.” “Ameena ita nadama a bayyane take, kamar yadda ni babu lallai a amince nayi nadama amma ni a zuciyata nasan nayi bazan sake kuskuren baya ba to haka a wajan Yusuf din ma. Misali ko rantsuwa nawa zaki iya Ibrahim kice na canja babu lallai ya amince, saboda gani yake ban canja din ba amma ni nasan a zuciyata na canja domin naga izina da isharar da dole ma na canja din ko bana so. Haka nake ganina tare da Yusuf wallahi.” Ameena tace, “Yanzu kina fad’a min ne dan na koma?.” “A’a, ni ba ina fad’a miki dan ki koma bane, kawai Allah ya sani ni bama so da karancin shekarun ki ace kin auri mazaje guda biyu Ameena, ni kad’ai nasan d’acin hakan da nake ji a zuciyata duk da k’addara ce. Bana so ace Zaytun ta tashi ba a tsakanin ku ba hakan babu dad’i, duk da nasan wanda zaki aura zai rik’e yta hannu biyu amma ba kamar mahaifin ya ba. Ki kalle ni nida Amir, ya samu Uwar da ta fini iya kula dashi amma Amir bai shak’u dani ba, kallona yake kamar wata wacce ya sani a lokacin baya amma yanzu Ruky itace babar sa, ko bance na kin san zanji babu dad’i matsayina na uwa a gare shi.” “Wallahi ni a wajena nafi so ki koma wajan Yusuf da dai ki sake aure gwara ace kin koma can kin san halin sa yasan halin ki kowa sai yaci maganin zama da d’an uwan sa.  Meye amfanin raba yara kowa baban sa daban a shekarun ki Ameena? Da kin shiga sabon gidan da kin haihu shikenan wancan baban ta daban wanda kika haifa ma baban sa daban. Nidai a nawa ra’ayin gwara ki koma wajan Yusuf.” Ameena ta sauke numfashi tace, “Yanzu kema zaki iya komawa Ibrahim kenan?.” Fiddausi tayi murmushi tace, “ai ni nayi kuskure ba shi ne yayi kuskure ba, wallahi inda shine yayi kuskure irin na Yusuf ya dawo yace zai mayar dani irin yadda Yusuf yake yi a yanzu zan koma Ameena a guje ma kuwa. Amma ni nice nayi kuskure Ameena, sai dai in nice zan nemi ya mayar dani amma wallahi shi bazai zo yace zai mayar dani ba Ameeba saboda ya barni har abada, wannan shine banbancin.” Ameena tace, “Meyasa kika rantse? Ni ina yi miki sha’awar komawa wajan sa duk da akwai Rukayya amma tana da sauk’in kai zaku iya zaman ku Lafiya ba tare da tashin hankali ba. Kin gane kuskuren k in yi nadama na tabbatar baza ki sake ba meye in kin koma? Yanzu kike zancen Zaytun ta taso a tsakanina da Yusuf ke meyasa bakya fatan Amir ya taso a haka?.” Tayi murmushi tace, “ki daina zancen komawa ta wajan Ibrahim wannan ba abu bane mai yuwa Ameena. Yanzu kika ce nayi nadama kuma kin san na gane kuskurena zan iya komawa wajan sa ko?.” “Eh mana ai nadamar ki a bayyane take ai.”  “Shi kuma nadamar Yusuf a b’oye take?, indai har kina ganin na cancanci a yafe min na koma gidan Ibrahim to shi Yusuf wacce irin cancanta ce baiyi ba?.” Ameena tace, “matsalar sa daban taki daban Fidy.” “Ya tab’a zagin iyayen ki? Ya tab’a zuwa gida gaban Yaya Adam yace baya sonki baya kaunar ki ya gaji da zama dake in aka matsa masa zama dake zai kashe ki?, shi namiji ne dan ya kula wata macen kuna tare ba wani abun bane amma ya tab’a chakumar wuyan rigar ki yace baya sonki sai ya sake ki Ameena?. Duka bai aikata ba, to ki juya laifukan baibai ki mayar dashi mace ya tab’a aikata duk abinda na aikata?.” Ameena tayi shiru bata amsa ba tace, “ki koma Ameena indai kin yarda nayi kuskure kuma na gyara yanzu shima ya gyara, ko dan mahaifiyar sa da yake son ki, ko dan yarinyar da yake tsakanin ku Ameena, ni dai ina bayan ki koma amma abinda kika ga shine daidai shi zaki d’auka.” Ameena tace, “hmmmm, Rukayya sun dawo kuwa? Bana samun wayar ta” ta fad’a dan ta kawar da waccan maganar. Fidy tace, “ban sani ba walalhi, amma munyi waya ina jin shekaran jiya tace min ko jibi zasu dawo dai na manta.”  “Zakiyya fa?.” “Zakiyya ai tunda manya suka shiga maganar Allah ya taimake ta ya hak’ura akan batun cikin, kamar ba cikin halak ba wai sai ta zubar. Amma fa ya dindaya mata sharad’i babu ciki sai nan da shekara ko goma tace min ne ko sha biyu” ta fad’a yana yar darıya kafin tace, “kamar shine mai rayuwa a hannun sa, Allah sarki Kiyya da yake son zaman take tace min na amince Fiddausi.” Ameena tace, “Ko wacce mace dai akwai kaddarar da take fuskanta a gidan mijin ta. Dole akwai ta inda take hak’uri dashi.” Fiddausi tace, “to hakan zaki saka a ranki ki koma wajan mijin ki Ameena, yana sonki yana son sake zama dake a karo na biyu. Son da yake miki a yanzu wallahi bai yi miki shi a da ba nasan kema kin fahimci hakan. Wani lokacin sai abu ya kubce maka kake gane mahimmacin sa a rayuwar ka. Kamar dai ji d’in, na nayi hak’uri da nice a gidsn ibrahim har yanzu, to ban yi ba ga yadda na samu kaina a ciki.” Ameena tace, “to bacci nake ji sai da safe.” Fiddausi tayi dariya tace, “kiyi ta addu’a kawai.” Ta amsa kawai ta kashe wayar ta ajjiye a gefe tana tunani.          Washe gari Ameena bata shirya ma zuwa makaranta ba tana zaune a gida bayan Zaytun ta tafi Anty Aysha ta shigo ta same ta tace, “baza ki fito ki ci abinci bane ba?.” Ameena ta kalle ta tace, “yanzu daman zan fito, Yaya ya fita?” Ta fad’a tana tashi suka fito tare tace, “Bai fita ba yana nan.” Suna fitowa yana fitowa shima ya kalle ta yace, “Amaryar Al’ameen.” Tayi dariya kad’an ta gaishe shi ya amsa a yace, “banga kina shirin biki ba fa.” Ameena ta  zauna tace,”ina yi Yaya.” “K’arya kike babu abinda kike yi banga alama ba.” Tayi murmushi kawai b’ata ce komai ba ta zuba abinci tana ci. Shiru babu wanda yake magana suna cin abinci dukkan su  wayar sa tayi kara ya duba yaga Al’ameen ne sai ya share ya cigaba da cin abincin ka. Sai da ya gama sannan ya fita ya samu Al’ameen din a gidan sa yace, “sai waya ka ke min Lafiya?.” Al’ameen yace, “baka k’arasa fad’a min abinda ya faru jiya ba, shi nake so na sani.”  “Wai daman akan haka kake ta kira na na d’auka wani abun ne mai mahimmaci?.” “Mai mahimmaci ne mana Adam, ita Ameena bata amince da komawa gidan sa ba?.” Yaya Adam yace, “a jiya dai tace  masa yayi hak’uri baza ta koma ba amma daga jiyan yanayin ta ya canja, tana tausayin sa kamar yadda yanzu ni kaina tausayi yake bani. Amma fa ban sani ba ba ita tace min ba kawai ni nace tana tausayin sa. Al’ameen yace, “nima haka wallahi, bana so ace ta silar hakan ya samu wani babban ciwon ko ace ya rasa ransa ma gabad’aya wallahi. Yanzu na tabbata ba Lafiya yake ba.” Adam yace, “ko meye dai shine ya jawo badan haka ba da yanzu tana gidan sa ai. Kuma shi ba ta silar sa ta samu ciwon ba? Dan ya samu ba komai bane anyi kunnen doki.” “K’addarar kenan ai, da kuma silar canjawar tasa gabad’aya.” Yaya Adam yace, “Tunda tace bata yi zancen sa ba namu bane, muyi abinda yake gaban mu.” Al’ameen yace, “Nidai inda zata amince da ta koma din, wani zaman jin dadin baya zuwa sai an samu kuskure, kuma ba ko wacce mace bace take komawa gidan mijin da ta bari ta sake tarar da abinda ta bari ba, musamman yadda yanzu yake wahala akan Ameena bazai sake aikata abinda yayi ba na tabbatar maka.” Adam ya girgiza kai yace, “nima na yarda wallahi, baka ga na zubar da makaman yaqina ba?, har azumin kaffara nayi akan lamarin Yusuf.” Al’ameen yace, “amma tunda muna addu’a gabad’ayan mu Allah zai zab’a mata mata mafi alkhairi.”  “Wai kai daman baka son Ameena din ne?.” Al’ameen yayi murmushi yace, “ni kuwa nake sonta, amma son da nake mata bazai hana ni fad’ar gaskiya sannan na kuma sanar da farin ciki a rayuwar ta ba, sannan bai hana ni fad’ar abinda yake daidai ba. In Kaga ban aure ta ba daman Allah baiyi ni mijin bane shiyasa take ta kubce min.” Adam ya girgiza kai yace, “Salon kaje ka cigaba da yad’a ni kace na sake hana ka Ameena a karo na biyu ko?.” Al’ameen yayi dariya yace, “indai hakan ta tabbata Allah ne ya hana ni Ameena ba kai ba wallahi.” Adam ma yayi dariya yace, “to zamu dai ga abinda Allah zaiyi. Mun bar masa zab’i ya zab’ar mata inda zatayi farin ciki.” Al’ameen ya harare shi yace, “Kai ko Allah bai zab’e ni matsayin mijinta ba ba hakan yana nufin baza tayi farin ciki a wajena bafa, Yauwa ka canja kalaman ka kasan abinda zaka ce.” Adam yayi dariya shima haka yace, “ai gaskiya ne.” Tare suka fito Al’ameen ya hau mota ya fita shi kuma ya koma gıda.        Ameena ya samu da hijjab a jikin ta ya kalle ta yace, “sai ina kuma?.” Tace, “Class mate din muce bata da lafiya yau kwana uku anje duba ta ban je ba, kuma tare muke komai har karatu nida ita. Tunda yau bazan fita ba sai nace bara ka shigo na tambaya sai naje.” “Sai kin dawo.” “Na gode. Nayi driving?.” Ya kalle ta sai yace, “ki dawo da wuri.” Ta masa ta fita da murna dan har kewar jan mota take yi.        Asibitin taje ta duba y’ar ajin nasu ai kuwa taji dadin zuwan ta sosai itama Ameenan yaji dad’i ta fito daga d’akin sai ta hango Mubakar a tsaye ya juya baya ga Ammah a zaune ita da wata mata suna magana duk sun juya baya. Murmushi yayi yace, “Da rabon zamu gaisa da Hajiya Ammah” ta fad’a tana k’ara sauri dan yaje inda suke. Magana Amma suke yi da matar  tana cewa, “Haka Yusuf ya koma shine baki fad’a min ba? Ki kalle shi fa dan Allah kamar ba shi ba.” Ammah tayi dariya tace, “ciwon nasa ne yaje ya dawo, a kwanakin nan ina jin kwanciyar sa a asibiti na hud’u kenan shiyasa bana fad’awa kowa wallahi.” Matar tace, “ai lalura ce, suma sauran y’an uwa suka ji baza suji dad’i ace baki fad’a musu ba. Amma ne yake damun sa haka wai?.” “Damuwa ce wallahi, itace take saka masa wannan ciwon kan da ko haske ba’a kunnawa in ya tashi, ga zazzab’i mai zafi wani lokacin k’ank’ara ake b’arewa ana zuba masa a jikin sa.” “Wannan wacce irin damuwa ce haka?.” Ammah tace, “hmmm! Yusuf fa ni wallahi na fitar da rai dashi, lokaci kawai yake jira Allah ya karb’i kayan sa. Yau ciwo gobe Lafiya a haka ake rayuwa dashi, Tunda asirin wannan shegiyar Asiyan ya fita daga jikin sa shikenan kuma sai hankalin sa koma wajan matar sa ta farko. Shikenan fa ake tayi abu kamar zugi kullum babu cigaba.” Ta zaunen tace, “Ameena kenan, mai hankalin nan.” Ammah tace, “ita kuwa. Shikenan ya koma kamar mahaukaci, Kullum a kuka yake, Kullum a tunani Kullum a ciwo yake. Ya rasa inda zai saka ransa yaji dad’i, tun bama tausayin sa har ya kai ya yanzu tausayi yake bani, tun ban yarda ya gane kuskuren sa ba ta kai ta kawo yanzu na amince wallahi, na tabbatar bazai sake kuskuren da yayi a baya ba amma sai dai lokaci ya k’are masa Murja. İn Allah ya baka dama kayı amfani da ita a lokacin, shi sai yayi wasa yanzu kuma damar ta kubce masa shine ya koma haka.” Murna din tace, “Wai Yaya Hafsa daman akan Ameena ya koma haka?.” Ammah tace, “akan hakkin tane da kuma soyayyar ta.” “Amma wanne irin so yake mata haka da ya mayar dashi wannan yanayin?.” Ammah bata ce komai ba ta tab’e baki Murja din tace, “to baza mu ce komai ba dan kamar yadda kika ce ta kubce masa, dan yayi asarar mata mai hankali da nutsuwa ga rik’e sirrin miji, sake samun ta a yanzu zai masa wahala sosai gaskiya, dan irin su basa jimawa ake aurewa, balle bata kyakykyawa…ina Yusuf yayi sake.” Ammah tace, “shiyasa nace miki lokaci yake jira, domin ni na tabbatar ana cewa Ameena tayi aure to Yusuf kuma sai abinda Allah yayi dan abinda yake fad’a da gaske zai iya rasa hankalin sa, in kika duba yanzu abin kamar ya tab’a masa kwakwalwa shiyasa Kullum a ciwon kai. Amma babu ruwana a maganar nan, in Ameena taga zata dawo wajan sa haka nake so a raina amma a wani b’angaren bana so dan kar ya sake abinda yayi.” Murna tace, “ai wallahi bazai yi ba kinji ma na rantse.” “To indai haka ne za so ace ta dawo din dan ni gani nake yadda yake sonta yanzu a baya ma bai sota haka ba, in kuma bata dawo ba wallahi shima zan zo hakan dan ina so ya samu farin cikin da bai bata ba, ke kin sani tamkar jinina nake jin yarinyar.” Murja tace, “to Allah ya bashi Lafiya ya bada abinda yake daidai.” Ta amsa da amin Ameena tana tsaye a bayan su ba tare da sun ganta ba tana jin duk abinda suke fad’a jikin ta ya sake yin sanyi sosai musamman kalaman Ammah da take cewa lokaci yake jira. #Nana Haleema #Fitattu biyar #Mai daki #Book3 Book3 039         Ameena da take tsaye a bayan su duk tana jin abinda ake cewa ta sauke numfashi ta samu nutsuwa sosai sannan ta k’araso tana murmushi tace, “Ammah?.” Jin muryar ta sai Ammah ta juyo tana kallon ta murmushi ya bayyana akan fuskar ta tace, “A’a, Ameena kece a nan?.” Ameena tayi murmushi tace, “Barka da Rana Ammah.” Ammah tayi murmushi tana kallon ta cike da so tace, “Barka dai Ameena. Ya makaranta?.” “Alhamdulillah. Barka da rana” ta fad’a tana kallon ta kusa da Ammah ta amsa tana murmushi itama. Ammah tace, “Ina Hafsa take?.” Ameena tayi dariya tace, “tana makaranta.” Ammah tace, “Zaytun y’an makaranta, ana shan rubutu. Dan in tazo sai ta zane min ko ina da biro ita ga y’ar makaranta.” Ameena tayi dariya kad’an ta kalli Mubakar da yake dariya yace, “Ai bazan kula ki bane, wai duk nacin Muhammad sai kika zagaye aka barshi a corner.” Tayi dariya mai sauti tace, “Nidai babu ruwana.  A gaban Ammah nake.” Yayi dariya yac, “Ai tasan labarin.”  Tayi murmushi kawai Ammah tace, “waye babu lafiya na ganki a nan?.” “Class mate dina ce babu lafiya shine nazo na duba ta yanzu.” Ammah tace, “Allah Sarki, Allah ya Kara Lafiya.” Ameena tace, “Amin.” Tana son tambayar Ammah waye a kwance amma kuma ta san amsar a bayyane gani take ta nuna bata sani ba ta tambayi waye dan kula da lamarin Ammah. “Ammah waye babu lafiya na ganki a zaune?.” Ammah ta kalli Mubakar sai yace, “Yusuf ne wallahi.” Ameena tace, “Ayya Allah ya k’ara Lafiya.” Mubakar yace, “Amin, ko zaki shiga duba shi?.” Ammah tace, “ita da zata koma gıda me zata je tayi a wajan Yusuf?.” Ameena sai Ammah ta d’aure ta da jijiyoyin jikin ta sai tace, “Ammah ai dan zan tafi bana kasa shiga ba” ta kalli Mubakar tace, “raka ni.” Mubakar ya bud’e d’akin da yake tsaye a jikin sa ta hango Yusuf din a kwance Usman na kusa dashi a zaune. Shiga tayi da sallama Usman ya amsa yana kallon ta sai ya kalli Yusuf da bai bud’e ido ba yasan kuma idanun sa biyu sai dai baya son bud’ewa saboda ciwon kan da yake damun sa, Usman yace, “Ameena kece da kanki?.” Tayi murmushi tace, “nazo samu ladan duba Mara lafiya.” Usman yayi murmushi shima yace, “kin kyauta ai.” Ta kalli Yusuf da yake a kwance ruwa har gida biyu suna shiga jikin sa ko wanne hannun ta kalli Usmsn tace, “Allah ya kara Lafiya.” Usman yace, “Amin ya Allah. Mun gode sosai.” Murmushi tayi ta juya zata fito taji Yusuf yace, “na gode Ameena, na gode da bani damar sake jin maganar ki duk da ban ganki ba a karo na k’arshe. Na gode Allah ya saki farin ciki kamar yadda kika saka ni yanzu.” Waje ta kalla sai suka had’a ido da Ammah tana kallo d’akin sai Ammah ta d’auke kai Ameena ta sauke numfashi tace, “Amin.” Tana fad’a ta fita ta dawo wajan Ammah tace, “Ammah zan koma gıda kafin Yaya ya fara yi min waya.” Ammah tace, “ai bara nazo ki sauke ni a gida Mubakar yana nan tunda Usman tafiya zaiyi.” Ameena tace, “To Ammah.” Ta kalli Mubakar tace, “d’auko min kayan nan Ameena zata sauke ni.” Mubakar ya shiga ciki ya d’auki kayan suka je har bakin motar Ameena aka saka kayan a baya suka shiga motar suka tafi. Ammah ta lura da Ameenan kamar bata cikin walwala tayi shiru bata cewa komai sai Ammah taso kawar da shirin tace, “Ashe bikin ki yazo Ameena babu labari?.” Ta kalli Ammah tayi murmushi tace, “naso sanar dake ke wallahi, ayi min afuwa.” “Ba wata afuwa, ai na d’auka ni za’a fara kawowa mijin sai gashi a manta ma bani.” “Allah Ammah ba haka bane ba, makarantar nan ce ga saka ni a gaba” ta fad’a tana murmushi Ammah ma dariya take tace, “Allah ya tabbatar da alkhairi.” Ameena sai taji wani iri a zuciyar ta tace, “Amin Ammah.” Hira Ammah take ta janta da ita har suka zo gidan Ammah ta fita tace, “Bud’e na d’auki kayana.” Ameena ta fito ta d’auko kayan wayar ta na k’ara ta duba ganin sunan Yaya sai ta d’auka Ammah taji tace, “Ina hanya Yaya.” Ammah tayi murmushi bayan ta kashe wayar tace, “Maza jeki tunda neman ki yake.” Ameena tac, “Ammah a gabana zan bari ki d’auki wannan kayan? Zan shigar miki dasu” ta fad’a tana d’auka ta jefa wayar ta cikin motar ta d’auki kayan Ammah sai murmushi take tana kallon ta suka shiga har falon Ammah ta ajjiye kayan Ammah tace, “Na gode Daughter, Allah yayi albarka.” Ameena ta amsa kafin ta tafi saboda tsoron fad’an Yaya. Ameena tana komawa gida taga Yaya Adam din ma baya nan tace, “wai daman baya nan yake min waya?.” Yayan Bauchi tace, “baya nan ya fita. Kema ai kin jima daga dubiya sai hira?.” Ameena ta zauna tace, “Ammah n gani fa a asibiti muka tsaya muka gaisa k’arshe ma ni na dawo da ita gida shine dalilin jimawa ta.” Anty Aysha tace, “Waye babu lafiya kuma.” Ameena ta kalle su tace, “Yusuf ne” tana fad’a ta tashi ta shiga ciki duk suka bita da kallo Anty Aysha tace, “Yusuf ya kamata yaci albarkar Ammah Ameena ta amince dashi.” Yayan Bauchi tace, “naga alama Ameena baza ta amince ba ai.” Anty aysha tace, “Ko yanzu ta amince ai ta bashi wahala.” Sukayi dariya suna hira Ameena tana jin su ta jingina da bango ta lumshe idanun ta. Eh tabbas da gaskiyar su Yusuf ya kamata yaci albarkar Ammah kodan kalaman da taji tana yi a d’azu, Ammah uwace zata so Yusuf fiye da ita kuma in Yusuf ya rasu ta wannan dalilin zata dinga kallon ta kamar itace silar mutuwar d’anta. Ameena a bayyane tace, “in na yiwa Ammah haka naci amanar qaunar da take min, amma kuma taya zan koma wajan Yusuf bayan abubuwan da suka faru?.” “Indai kin amince zaki koma ki d’auka a ranki baza su sake faruwa ba. Ameena Yusuf yayi nadamar da ya kamata ki gani a zahiri, Yusuf ya cancanci ki tausaya masa kodan saboda mahaifiyar tasa. Ameena son da Yusuf yake miki a yanzu bai miki shi a baya ba kema nasan kin tabbatar da hakan,  a jikina nake jin baza ki sake shiga yanayin da kika shiga a baya ba, domin in kayi sake kwai ya kubce daga hannun ka ya fashe da zarar ka sake samun sa rokon da kayi masa a baya ba irin sa zaka sake yi ba yi ba. Zaka fi yi masa rik’o mai mahimmaci domin tsoron kar ya sake sub’ucewa. Indai zuciyar ki ta amince zaki koma wajan sa kodan saboda Ammah ki koma, na tabbata da zarar kin koma zaki ji a ranki duk soyayyar da kike masa a baya tana dawowa a hankali Ameena.” Yayan Bauchi ta fad’a tana kallon ta itama ita take kallo. Ameena ta fara hawaye tace, “tsoro nake ji Yaya, bana son sake shiga yanayin da na shiga a baya. Amma bana jin dad’i in naji Ana zancen mutuwa ta dalilina.” Yaya ta dafa kafadar ta tace, “kar kiyi wannan tunanin ki d’auka komai ya canja kamar yadda yace, ke yanzu kina ganin Yusuf zai sake aikata abinda yayi ne a baya? Tsakani da Allah a ranki Kina Jin zai yi haka?.” Ta girgiza kai alamun A’a Yaya tace, “kin fahimta Ashe, akwai halin sa wanda zaki sake tararwa yana nan ke kin san su amma wannan manya-manyan halayen da yayi miki wanda daman ba nasa bane arowa yayi ya saka wallahi bazai yi ba. Ni tunda naga yanayin sa nake ji a raina ina ma ki koma din saboda yanzu yasan darajar ki da mahimmaci ki sai yafi rik’e ki akan baya. Ke har Al’Ameen din son da Yusuf yake miki a yanzu baya miki, a baya kece kike masa wannan son har nake miki fad’a a yanzu kuma shine. Ki tuna abubuwa nawa kika jure saboda wannan son? Abubuwa nawa kika daurewa saboda son, to shima haka zai daure ya jure saboda son da yake miki.” Ameena ta sauke numfashi tace, “ina bukatar yin tunani a kan lamarin nan.” “Istikhara zakiyi akan Allah ya zab’a miki wanda yafi alkhairi a tsakanin su.” Ameena ta girgiza kai tace, “To Yaya zanyi in sha Allah.” Yaya tayi murmushi tace, “burina ki samu rayuwa mai kyau Ameena, in kina ganin wajan Yusuf baza ki smau ba koma wajan Al’ameen din duk wanda kika d’auka a wajena daidai ne.” Ameena tayi murmushi ya goge idanun ta tace, “Allah zai zab’a mana Yaya.” Tace, “shikenan babu ke babu damuwa Tunda kika ce Allah, amin.” Ameena tayi murmushi ta shiga band’aki ta bar Yaya a tsaye a wajan.       Kwanan su Rukayya biyu da dawowa Nigeria taje gida wajan su Umma ta kai musu tsaraba ta shiga har wajan Fiddausi ta bata tsarabar doguwar riga da ta siyo mata ai kuwa taji fdad’isosai ta dinga murna. Ameena tana ta cewa zata je bata samu taje ba sai ga Rukayya tazo da kanta. Ameena ganin ta sai tayi dariya tace, “mutanen Saudia.” Ta harare ta ta gaisa da Anty da Yaya suka shiga ciki sannan ta kalle ta tace, “yau kwana biyu da dawowa amma baki zo ba.” Ameena tace, “wallahi ina so nazo dan kina raina kawai ban samu na fito bane.” Rukayya ta zauna tace, “daman haka zaku ce ai, ya gidan?.”  “Normal wallahi, ya unborn?.” Rukayya ta tab’e baki Ameena tayi dariya tace, “munafuka.” Tayi dariya Rukayya tace, “ashe Fidy auren ya mutu, naji wallahi da aka raba auren cikin sanyi babu tashin hankali.” Ameena tace, “bari kawai Ruky smart ai na taya Fidy murna, yanzu baki ga ta dawo hankalin ba tana idda abin ta da ta gama sai tayi  aure dan tayi nadama na tabbata Allah zai zab’a mata miji na gari.” Rukayya ta sauke numfashi ta kalli Ameena tace, “naji batun Yusuf.” Ameena tayi y’ar dariya tace, “Ni nasan sai tayi miki zancen nan ai.” “Ai ya kamata na sani. Ameena nidai da naje saudia nayi miki addu’a kamar yadda kika ce, wallahi har d’awafi nayi miki akan wannan lamarin nan. Nidai amma nafi son Yusuf saboda Zaytun da kuma Ammah.” Ameena tace, “sai kuce saboda Zaytun meyasa saboda ita?, shin har yanzu bamu bar k’arnin komawa gidan tsohon mijin saboda yara ba?.” “Yaci albarkar Zaytun da mahaifiyar sa mana. Kuma ana komawa gidan mijin da aka bari albakacin yara Ameena.” “Hmmm Ruky kenan, baki san halin da na shiga bane, a gaban ki ya dinga min tsawa kawai dan wacce zai aure tayi min karya.” Rukayya tace, “wannan tsawa ko wacce mace ma mijin ta yana yi mata, wallahi fad’a  da mukayi Khalil a saudia sai da nayi mamaki ya dinga zazzaga min masifa akan abu kad’an nace daman haka yake ban sani ba?, wannan ba komai bane kema kin sani. Zancen matar da zai aura kuma da yawan maza haka suke komawa in zasu yi aure balle ke da abin yazo harda asiri.” Ameena tayi ajiyar zuciya ta kalle ta kafin tayi magana Rukayya tace, “Tunda har kin amince Fiddausi tayi nadama meyasa shi baza ki amince ba?.” Ameena tace, “saboda ita nadamar a bayyane take na tabbata baza ta sake gangancin da tayi ba.” “To shima haka ai, laifin Fiddausi ai yafi nasa laifin kuma tunda kika ce tayi nadama ai shima yayi.” Ameena tace, “ke yanzu da kike cewa na koma yayi nadama na yarda da hakan, amma kema zaki iya cewa Fiddausi ta dawo gidsn mijin ta tunda tayi nadama?.” Rukayya tace, “a guje kuwa Ameena, d’anta Amir fa ya manta da ita badan wannna zaman da yayi a wajan ta da bama nan ba, ina dawowa yana ganina a gidan Umma bai sake komawa wajan ta ba balle yace ya bini. Wallahi ko dan shi ya shak’u da babar sa ina so Ibrahim ya mayar da Fiddausi Ameena, har zuciyata nake fa miki wannan kuma so nake ya huta daga gajiyar tafiyar nan na isar masa da sak’on dan Allah ya mayar da ita.” Ameena ta bita da kallon mamaki dan ita gatse tayi mata tace, “Wai da gaske kike? Mijin ki ne fa yanzu in ya dawo da ita kun zama ku biyu fa?.” Tayi murmushi tace, “kafin ni ai ita ya fara samu Ameena, da ita ya fara zama har suka haifi Amir sannan nazo, dan Fiddausi ta dawo babu komai daman can Mun saba aminai ne kowa yasan sirrin kowa ba wani tashin hankali zamuyi ba sai dai kowa da abinda yake ransa. Amma indai zai mayar da ita ina yi mata maraba, domin tayi nadamar da ya kamata a yafe mata.” Ameena ta girgiza kai tana murmushi tace, “zuciyar ko mai kyau ce Ruky, ba ko wacce mace bace ce zata furta ma abinda kika furta ba yanzu koda wasa. Kema nayi mamaki saboda na san ki da kishi.” Rukayya tayi dariya tace, “tare muka taso fa dukkan mu, duk mun zama y’an uwa muna sows dan uwan mu abinda muke sowa kan mu.” Ameena ta girgiza kai kawai bata ce komai ba kafin Rukayya tace, “yanzu me kike gani akan batun Yusuf?.” Ta kalle ta tace, “kun cika naci.” Rukayya tayi dariya tace, “eh Mun ji.” Tayi dariya itama tace, “sai abinda Allah yayi.” “To Allah yayi mana alkhairi.” Ta amsa da amin suna ta hira ta bata tsaraba har yamma sannan Ibrahim yazo ya d’auke ta suka tafi.       Ameena haka suka barta da tunani a zuciyar ta a haka ta wuni har dare. Da daddaren tana zaune a falo ana kallo Yaya Adam dai ba kallon yake ba waya yake ta dannawa amma yana kallon Ameena dan gani yake ba kallon ma take yi ba yace, “Ameenatuwa ya dai?.” Ta kalle shi tayi dariya kad’an tace, “babu komai Yaya.” Ya kyad’a kai ya cigaba da abinda yake yi.  Ameena tayi shiru bata ce komai ba kafin ta tashi ta shiga d’aki a lokacin wayar ta ta fara k’ara ta duba taga sunan Yaya Al’ameen. Ta d’auka ta saka a kunne tace, “Yaya barka da dare.” Yaya Al’Ameen yace, “barka dai Ameena, in kina gida ki fito yanzu ina kusa da motar ki ina so zamu yi magana dake.” Ta amsa ta kashe wayar ta fito da hijjabi Yaya Adam ya kalle ta alamun k’arin bayanı tace, “Yaya Al’Ameen ne yace yana son magana dani yana waje.” Baice komai ba ya cigaba da abinda yake yi ita kuma ta fita Zaytun ta bi bayan ta a guje.      Bata san tan bayan ta ba sai fad’uwar ta taji ta zame a tiles saka kuka ta juyo ta d’auke ta har bakin ta ya fashe saboda ta fad’i sosai tace, “Meyasa kika biyo ni?.” Al’ameen ya k’araso ya karb’a ta a hannun ta yace, “ta fadin sosai, Sannu Zaytun kiyi shiru.” Kuka take kawai tana kiran Daddy ya kalle ta yace, “wajan Daddy zaki je?.” Ta d’aga kai alamun eh tana kuka yace, “shikenan zan ki ki wajan sa, ki daina kuka.” Ya kalli Ameena yace, “in kin shiga ki bata magani wannan bugewar zata iya saka mata ciwon kai.” Ta d’aga kai alamun to ta kwanta a jikin sa tana Ajiyar zuciya ya kalli Ameena yace, “kina ta mamakin dalilin kira na ko?.” Tayi murmushi tace, “babu komai ai nasan alkhairi ne.” Ya girgiza kai yace, “naje na duba mahaifin yarinyar nan ne yanayin da yake ciki bai min dadin gani ba Ameena, yana so ki koma wajan sa in kina da ra’ayin haka.” Ameena ta kalle shi yayi dariya yace, “kar ki damu dani kamar Adam nake yayan ki ne ni duk abinda yake daidai shi zan so naga kin d’auka. Mahaifiyar sa a yanzu kuka na tarar tana yi saboda jikin sa ya tashi ana tunanin ciwon kan da yake damun sa ma kamar ya tab’a kwakwalwar sa sai anyi hoto an gani. Kuma duk saboda ke yake a wannan yanayin Ameena, duk namijin da zai zube a gaban ki yana kuka akan ta amince dashi ba k’aramin so yake mata ba, a ajjiye batun so ma yayi nadama sosai na tabbatar bazai sake kuskuren da yayi a baya ba Ameena.” Ameena ta sauke numfashi tace, “to ni yanzu ya ake so nayi?.” “Tunani zakiyi, in har zaki iya cigaba da zama dashi ba dan halin sa ba dan mahaifiyar sa da kuma yarinyar nan kiyi hakan Ameena. İn baza ki iya ba kar ki cuci kanki sai a bashi hak’uri in silar hakan in ya samu cutar ajali dmaan lokacin sane yayi.” Ameena ta girgiza kai tace, “To Yaya Al’ameen zan yi tunani akan hakan.” “Yauwa Ameena. Kar ki yi tunanina yayan ki ne nima shiyasa nake fad’a miki abinda nake ganin ni a raina na karb’e shi.” Ameena ta girgiza kai b’ata ce komai ba ya kalli Zaytun da tayi bacci a kafadar sa yace, “kuka take tana kiran Daddy rashin ganin sa shine ya saka ta bacci, tana son mahaifin ta a kusa da ita ki tausaya mata kar tayi rashin sa a kusa da ita.” Ameena ta girgiza kai tace, “to Yaya zan yi tunani ina addu’a kuma abinda yake daidai Allah ya bani.” “Shikenan kuwa zaki ga daidai a rayuwar ki, in ni ne na kasance daidai din zaki gani, in Yusuf din koma masa shine daidai duk zaki gani.” Ta girgiza Kai cikin gamsuwa  yace, “karb’e ta kije ki kwanta, yanayin da na same shi ne ya saka na kasa hak’uri sai da nayi magana dake.” Ta karb’i Zaytun ta koma ciki shi kuma ya fita. Kai tsaye d’aki ta wuce Yaya Adam ya bita da kallo kafin ya tashi ya bita ya same ta zauna tayi tagumi yace, “Al’ameen yace miki?.” Ta kalle shi tayi shiru bata ce komai ba yace, “maganar Yusuf yayi miki ko?.” Ta daga kai alamun eh yace, “kinga ki ture maganar sa in dai har yanzu zuciyar ki bata amince dashi ba kar ki cuci kanki.” Ameena tace, “Yaya kai ka amince dashi ne?.” Ya kalle ta sai ya zauna a kusa da ita yace, “A baya na fiki d’aukar zafi akan lamarin Yusuf Ameena, amma a yanzu tausayi yake bani Allah ya sani, dan nace yana bani tausayi ba hakan yana nufin ina so ki koma ba, ko kusa wallahi abinda yake daidai a wajan ki shi zaki d’auka, lokacin da kika sha a wahala a tare dashi babu wands ya sani, ynzu kuwa babu wanda zai saka ki koma wajan sa sai in ba ke kike son hakan.” Ameena ta kalle shi tace, “badan shi ba ba kuma dan halin sa ba Yaya” ta kalli yayan sosai tace, “Saboda Zaytun da Ammah na amince zan koma Yaya, amma bana so yasan da hakan a yanzu.” Yaya Adam ya kalle ta yace, “Ameena kar kalaman Al’ameen suyi tasiri a ranki har ki amince da abinda baki yi niya ba. Kar ki yanke hukunci da gaggawa ki nutsu sannan ki yanke hukunci Ameena.” Ameena tace, “Yaya a nutse nake kuma daman ko Yaya Al’ameen bai same ni ba hukunci na kenan a yanzu, na amince da hakan fatana Allah yasa silar canjin ne ya saka muka rabu.” Yaya Adam yace, “Amin ya Allah. Tunda kince haka shikenan, Amma kafin a ki koma sai na gindaya masa sharud’an da dole sai yabi, kinga dukan nan wallahi bazan d’auke shi ba.” Ta girgiza kai tace, “nima haka Yaya, duk abinda kaga daidai ne kayi.”  “Shikenan Ameena, Allah yasa alkhairi ne hakan a rayuwar ki.” Ta amsa da amin ya fita ita kuma ta kwanta da baya tana ji a ranta komai zai warware da ikon Allah, ita kuma Allah ya bawa lamarin tasan bazai barta ta sake kuka ba kamar wancan lokacin. Bayan kwana biyu. Yaya Adam ya samu mahaifin Yusuf da maganar abinda ya bashi mamaki bai amince da farko ba sai da ya tabbatar da Adam din ya amince sannan ya amince ya nuna farin cikin sa akan hakan sosai. Ammah da ta samu labari kuka ta dinga yi kukan soyayyar Ameena da tausayin ta da kuma shi kansa Yusuf din dan in tace bata ki dadi ba karya take yi. Amma duk da haka bata nuna ba har gida taje ta samu Ameena tana sake nusar da ita kar tayi kuskure fa a karo na biyu, Ameena tasan duk fad’a take kawai dan tayi mata kara amma ba wai har zuciya ba Ameena ta tabbatar mata da babu komai in sha Allah. Kowa yasan labarin banda Yusuf da ya dawo gida yanzu ya samu sauki babu laifi. Babu wanda yayi masa maganar ana ta yi masa magani musamman addu’a ayar Allah ake bashi yana sha kuma yana damun sauki sosai. A Daren ranar laraba Yaya Adam ya kira Yusuf suka zo gidan shida Usman da ba kwari gare shi ba sai an rik’e shi wani lokacin ya same ai shida Al’ameen a zaune suka shiga suka  gaisa sannan suka zauna ba tare da sun San dalilin kiran ba.  Yaya Adam yace, “daman abinda ya saka na kira ka ba wani abun bane, Yusuf na amince kayi nadama har nayi gangancin amincewa dakai a zuciyata, dan ganganci zance tunda ban tabbatar nadamar taka taje zuciya ba.” Yusuf ya d’ago muryar sa ta dashe sosai dakyar ake jin me yake cewa yace, “Allah yana ganin zuciyata, ni kuma bazan yi karya da Allah ba.” Yaya Adam yace, “haka ne Allah ya san komai, kuma in kayi  karya da Allah kai kasan sauran ai.” Yusuf ya sunkuyar da kai gaban sa sai fad’uwa yake yi dan bai san dalilin kiran ba.  Adam yace, “na amince zan sake baka Ameena a karo na biyu” Yusuf ya d’aga da sauri ya kalle shi Yaya Adam yace, “amma ina da sharad’i, in Kaga zaka iya bi shikenan in baza ka iya ba kowa ya kama gaban sa.” Yusuf ya kalli Usman ya sake kallon Yaya Adam sai ya sake kallon Usman yace, “mafarki nake ko?.” Usman ya girgiza kai yace, “Gaskiya ne ba mafarki ba, ka saurare shi Kaji abinda zai ce maka.” “Usman mafarki ne.” “Ba mafarki bane! Ka tsaya kajiabinda za’a ce ka nutsu kaji abinda za’a ce maka!” Ya fad’a da tsawa yana kallon sa dan ya tabbatar gaske ne ba k’arya ba. Sai kuwa Yusuf ya nutsu sosai ya kalli Yaya Adam da yake kallon sa Yaya Adam ya kalli Al’ameen ya sake kallon Yusuf yace, “ba mafarki kake ba da gaske ne, na amince da zaka gyara kuskuren ka darajar iyayen ka zan sake baka ita a karo na biyu.” Yusuf ya fara sauke Ajiyar zuciya duk da har lokacin bai tabbatar da gaske bane kawai gani yake kamar wasa ake masa Yaya Adam yace, “sharad’ina na farko Ameena zata cigaba da karatun ta tunda ta fara baza ta tsaya ba, na biyu kuma da wasa hannun ka ya sake zuwa jikin ta da niyar duka a ranar baza ta kwana a gidan ba, kai kuma kasan matuk’ar ta sake kubce maka baza ta saka dawowa hannun ka ba dan a yanzu kafi kowa sanin wahalar da ka sha kafin azo wannan gab’ar. Na uku kuma nasan yazo ranka a yanzu to ka d’auka shi nake nufi, wallahi bazan d’auka a sake wannan gangancin a karo na biyu ba, kai duk wani abun ma da kasan kana yi aka sake maimaitawa bazan d’aga maka k’afa ba.” Yusuf ya d’ago kai ya kalli Adam dan shi wallahi ji yake kamar a mafarki Al’ameen yayi murmushi yace, “bafa mafarki kake ba Yusuf da gaske ne abinda kake ji ba mafarki kake ba, ka amsa sharud’an da aka baka in zama iya shikenan.” Yusuf ya rasa tantance ma a wanne yanayi yake ciki a wannan lokacinsaboda farin cikin da yake jin zuciyar sa a ciki ya kalli Usmsn yace, “ban San me zance ba Usman.” Usman yace, “amsawa zaka yi.” sai ya kasa magana ma dan ya gigice ya dafe kai yace, “ni yanzu sai an bani sharad’i ma Usman? Umarni kawai za’a bani kuma dole na tabbatar dashi.” Yaya Adam yace, “Akwai abinda in kaga baza ka iya ba zaka iya hak’ura da auren nata tunda ba dole bane.” “Babu shi wallahi, in ma cewa kayi na zauna Ameena ta rama duk abinda nayi mata zan zauna balle wannan abubuwan da aji an fad’a. Sake samun ta shine burina dan haka kome akace min a shirye nake dana tabbatar dashi, bana fata ko burin tsallake wani abun koda ba’a fad’a min ba. Samun ta yafi min komai zan iya rasa duk abinda nake dashi indai zan same ta, na amince da koma meye na yarda da duk abinda akace koda zata dinga yankar naman jikina nata gasawa ne.” Yaya Adam ganin ya fara hawaye sai yace, “To tunda ka amince shikenan, amma zan sake jaddada maka, wallahi aka sake samun kuskure bazan kyale ka.” “Duk abinda kaga ya dace a lokacin kayi min, in sakawa zakayi a dauki raina a lokaci na amince wallahi na yarda da koma meye.” Adam yace, “shikenan, akwai tafiyar da zanyi ranar Monday dan haka jibi juma’a nake so a mayar da auren ka da ita kafin litinin amanar ta ta dawo hannun ka. Amma ina so kayi min alqawarin da kasa  zaka cika ba irin wanda kayiwa mahaifin ta ka kasa cikawa ba.” Sai ganin Yusuf sukayi ya zube yana sujjadar godiya ga Allah, ya jima a haka kafin ya d’ago ya kalli Yaya Adam yace, “Nayi alqawari canjawa daga wancan Yusuf din zuwa wani sabo daban, nayi alqawarin bata farin cikin da ban bata a wancan Zaman ba, nayi alqawarin zamu zauna lafiya babu cuta babu cutarwa. Komai ma nayi alqawari wallahi ni zanyi koma me akace, in ma wani abun take so wanda zan yi ga bata nishad’i kawai zanyi.” Adam yayi dariya dan ya fahimci baya cikin ma hayyacin sa farin ciki yayi masa yawan da ya kasa sarrafa farin cikin sa. Al’ameen yayi dariya shima dan yadda ya rud’e din abin darıya ne, “shikenan mu kuma munyi alqawarin saka baka Ameena a karo na biyu, kaje ka shirya jibi Ameena matar kace in sha Allah.” #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #Paid #500 Book3 040         Yusuf ya gigice saboda murna hankalin sa yana neman yin balaguro daga jikin sa tsabar tsantsar farin cikin da yake ciki a wannan lokacin ya kalli Usman ya saka kallon Al’ameen da yayi magana a k’arshe yace, “ni fa ban gane ba, yanzu kenan Ameena zata sake zama mallarına a karo na biyu?.” Al’ameen yayi murmushi yace, “da gaske ne mana Yusuf.” Sai ya kasa  magana ya rasa abinda zaice ganin hakan sai Adam yace, “ba sai kace komai ba kaje kawai jibi in Alalh ya kaimu za’a mayar da auren ku zuwa litinin zan tafi cross river bana son tafiya na barta a nan shiyasa nake so kafin ranar ta koma gidan ka.”  Godiya yake so yayi  amma sak ya kasa sai kallo da yake yi ya rasa ma abinda zaice saboda farin cikin da yake ji a cikin zuciyar sa ya hana bakin sa furta komai. Dakyar ya iya cewa, “na gode, na gode Allah ya saka maka da gidan Aljanna.” Adam yace, “amin, amma bani zaka yiwa godiya ba ga wanda zaka yiwa godiya nan, shine zai auri Ameena amma yace kayi nadama ya sake bar maka ita a wannan lokacin. Abokina ne, kuma aminina sannan kuma yayan Ameena ne. Koda bana nan shine idona yadda zan d’aga maka akan b’atawa Ameena wallahi shi bazai d’aga maka k’afa ba. İn kayi hankali kanka, in baka yi bama kanka.” Yusuf ya kalli Al’ameen da yake kallon sa yana murmushi ya rasa maganar ma da zaiyi Al’ameen yace, “basai kace komai ba farin ciki ya hanaka magana, abinda nake so dakai yadda kaji wannan farin cikin a zuciyar ka ka ninkawa Ameena shi a cikin rayuwar ta gabad’aya har abada. Kar ka barta tayi kuka, kar ka barta da damuwa, kar ka Bari tayi maraicin iyaye, kar ka bari tayi kukan nisa da d’an uwanta, hakan akwai zakayi ka nuna mana kayi farin ciki ka kuma gode da karamcin da akayi maka, amma godiya ta fatar baki bana son ta, ka nuna mana ka gode ta hanyar rik’e mana k’anwa hannu biyu kar ayi sakin da akayi a baya.” Kai yake girgizawa kawai kamar k’adangare amma ya kasa  magana sai Usman ne kawai yake magana amma shi ya kasa. Ganin haka sai Adam ya kalli Usman yace, “kaine kake da nutsuwa a yanzu, kana ji jibi za’a mayar da auren saboda tafiyar da zanyi Al’ameen ma zai je Lagos a Monday din. To duk wani abu a tanade shi kafin ranar Monday dan bazan barta ta kwana a nan ita kad’ai ba shiyasa za’a yi auren a huta.” Usman yace, “in sha Allah Yaya. Alalh ya jikan iyaye yasa suna aljanna amin.” Adam yace, “Amin ya hayyu ya qayyum. Kayı masa bayani in ya dawo hankalin sa naga yanzu ba komai yake ganewa ba. zaku iya tafiya daman maganar ce su Alhajin sa duk sun san da maganar to ayi abinda za’ayi bana son b’ata lokaci. Sannan Ameena bata son yayi magana da ita daga nan har a mayar da auren, to ko waya kar ya kira ta ya kyale ta.”  Usman ya amsa ya kalli Yusuf da yayi shiru ya k’asa cewa komai yace, “tashi mu je Yusuf.” Yusuf  ya kalle shi yace, “naje ina?.” “Muje gida wajan Ammah, kazo muje zaka ji komai daga baya.” “Ban yi godiya ba, na rasa me zance da zan nuna na gode.” “Rik’e Ameena shine zai saka su san ka gode, ka tashi muje zamuyi magana daga baya.”  Har zasu fita Yaya Adam yace, “yauwa sai batun kayan da za’a zuba na gidan ko? Ni Nama manta wallahi” ya fad’a yana kallon Al’Ameen. Al’ameen yace, “nima haka, babu damuwa ya bamu gidan zamu samu masu had’a gida in 24hrs zasu had’a gidan ya zama neat.” Usman ya kalle su yace, “na ari bakin sa naci albasa, basai anyi komai ba Yaya mu da aka bamu Ameena bama buk’atar ku siyi komai duk zamuyi da kan mu.” Al’ameen yace, “saboda me? A al’adance hakkin mu ne.” Usman yace, “mun sani, Mun d’auke muku shi ne.” Adam yace, “shikenan Allah ya nuna mana.” Ya amsa da amin a haka dai suka fita amma Yusuf ganin abin yake kamar a mafarki. Yana fita Al’ameen ya sauke Ajiyar zuciya yace, “Yanzu muka suke hakkin da yake ka mu matsayin mu na yayyen Ameena. Har zuciyata na amince dashi a yanzu wallahi, bana jin komai nasan zai rik’e ta rik’on da bai yi mata a baya ba.” Adam yace, “kasan tun a baya ni ba wani son sa nake ba kawai dan tana so ne ya saka na amince mata. Amma a yanzu sai nake gani kamar ba wancan Yusuf din bane wani daban. Zuciyata ta amince dashi Allah yasa kar ya watsa mana k’asa a idanu.” Al’Ameen ya murmusa yace, “Babu Ameena a kaddarar Al’Ameen, yanzu sai na mayar da hankali nemo matar aure.” “Na d’auka ka cire aure ai daga rayuwar ka.” Ya harare shi yace, “da yake ba mutum bane ba ni ko?.” “Waye ya sani, abu a duhu”. Yayi dariya yace, “ka samu baki magana yanzu ai da yake ba batun Ameena, amma da zan baka amsa a gaba.” Shima yayi dariya suka cigaba da tattaunawa akan batun Ameena din da yadda suke so abin ya kasance saboda tafiyar da zasu yi.          Yusuf a haka suka shiga gidan Ammah suna shiga ya tarar da Abbah da Ammah da kuma Mubakar a zaune yana zuwa ya zube a gaban iyayen nasa da suke zaune akan kujera guda d’aya yace, “wani abu ne ya faru nake so a tabbatar min gaske ko ko mafarki nake, Usman yace min ba mafarki nake ba amma zuciyata ta gaza fahimtar hakan. Da gaske yanzu Ammah ina zaune a gaban ku ba mafarki bane?.” Abbah yayi murmushi yace, “ba mafarki kake ba, Adam ya amince zai sake baka auren Ameena.” Numfashi ya sauke mai k’arfi yace, “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!.” Abinda yace kenan ya sunkuyar da kansa  k’asa yana ji zuciyar sa na harbawa sosai da sosai ya kalli Abbah da yake kallon sa yace, “Jikin ka yayi sanyi ko? Ni kaina ban so hakan ta kasance ba gwara ma na fad’a maka gaskiya. Ban so ka sake mallakar ba Ameena ba sboda baka san mahimmacin ta ba, ba kuma ka cancanci sake rik’e ta ba a rayuwar ka.” “Na sani Abbah, wallahi na sani na tabbatar da rashin ta tamkar rashin rayuwata ne wallahi.”  Ammah tace, “Ameena ta amince zata dawo gare ka saboda ni da kuma Zaytun ba dan wai tana sonka ba. Dan haka in ka sake wulakanta Ameena Yusuf ni ka wulakanta, in ka sake cin zarafin Ameena ni Hafsa ni ka yiwa, in ka saka Ameena kukan bak’in ciki zuciyar Hafsa ka  bak’antawa, in ka yaudare ta Hafsa ka yaudara. Yusuf in ka sake d’aga hannu ka daki Ameena Allah ya isa ban yafe maka, in ka yiwa Ameena abinda zata cutu har ta samu ciwo ban yafe maka ba, ba kuma zan yafe ba” Da sauri ya girgiza kai ya rik’e hannun Ammah yace, “Ko baki ce haka ba Yusuf yayi hankali yasan abinda yake yi a yanzu bazai sake aikata abinda ya wuce ba wallahi. Ina son sake zama da Ameena bazan sake yin abinda zai raba mu ba ki amince dani. A wannan Karon zan baki mamaki zaki tabbatar ba wancan Yusuf din bane, wancan Yusuf din daban wannan ma daman Ammaha, ki yarda Dani Allah yana ganin zuciyata.” Ya kalli Abbah yace, “Abbah kana ji Ameena zata dawo wajena, Abbah zan sake samun Ameena.” Sai hawaye suka cigaba da zuba na farin ciki Abbah ya kalle shi yace, “sai ka rik’e ta fiye da rik’on da kayi mata a baya, in ka sake wulakanta Ameena kaima Allah sai ya wulakanta ka.” Yusuf ya girgiza kai yace, “har abada bazan sake ba, wallahi bazan kuma ba komai ya k’are ya kuma zo k’arshe.” Mubakar yayi murmushi yana kallon sa yace, “sai hankalin ka ya kwanta ya dawo jikin ka yanzu kodan Lafiyar ka. Sai kuma ka nutsu dai kar ka sake hango wata figaggiyar kace zaka aure ta, daga nan sai ka cigaba da wulakanta Ameena a kanta. Ita kuma daga k’arshe ta kashe ka.” Ya kalli Mubakar yayi murmushi kawai  gabad’ayan su baza su fahimci nadamar da yayi bane shiyasa suke fad’ar duk abinda yazo bakin su san gani suke bai yi nadamar ba. Da Gaskiyar su amma zai tabbatar musu da an samu chanji.           Ranar Yusuf baiyi baccin ba kwana yayi farin ciki yana sallah yana gode Allah yana kuka, a haka ya kwana bacci sai b’arawo shima mai cike da mafarkan Ameena. Haka ya tashi da safe da wannan farin cikin duk da har lokacin ba Lafiya ce dashi ba amma haka yake k’arafafa jikin sa dan tabbatar da farin ciki a zuciyar sa. A ranar Yusuf masu aikin gidan su ya saka akayi abinci mai yawa aka tara almajirai aka dinga rabawa ana kuma bada sadakar kudi, ya d’auki Usman suka tafi emergency na asibitin murtala suka dinga rabon kud’i duk wani mara Lafiya a wannan lokacin Yusuf ya d’auki nauyin sa har yar jinya sai da ya bata kudin cin abinci a wajan nan.  Ya samu lada a ranar matuk’a hakan da  yayi ya nuna godiyar sa ga Allah, yadda ya saka farin ciki a zuciyar wanda ya taimakawa babbar godiya ce da yayi ga wanda ya halicce shi, kai da ka ganshi kasan yana cikin walwala bakin nan a bud’e ya kasa rufe shi shi.           A b’angaren Ameena baza ka fassara yanayin ta ba komai tana yin sa yadda ta saba bata canja ba ita ba farin ciki ba ita ba akasin sa ba. da safiyar tana shan tea Yaya Adam ya fito ya same ta Anty Aysha tana bayan sa yace, “Ameena sai ina na ganki da mayafi a gefe?.” Ta kalle shi tace, “makaranta zanje.” “Kina amarya ina ke ina zuwa wata makaranta?” Anty Aysha ya fad’a tana kallon ta. Ameena tayi murmushi kawai Anty tace, “ai ajjiye mayafin nan zakiyi, mu kira mai lalle tazo tayi miki kunshi aure fa zakiyi.”  Ameena tace, “A’a dan Allah a barshi Anty, bana son son yin komai a barni a haka.” Anty tace, “kamar ba amarya ba?.” Ameena tayi murmushi tace, “nafi son hakan ne” ta fad’a tana tashi ta d’auki mayafin tace, “sai na dawo.” Bayan ta fita ya kalli Aysha yace, “Kamar bata farin ciki da hakan.” “To bama ce tana yi  ko bata yi ba, tsoron abinda ya faru a baya ne a zuciyar ta amma ni na tabbatar maka tana son komawa wajan sa.” Yaya adam yace, “Allah yasa.”      Ameena na fita sai ta fasa zuwa makarantar kawai tayi gidan Rukayya ta same ta ita kad’ai Amir baya nan ta baje akan kujera tana sauke numfashi. Ameena tace, “na gaji.” Rukayya tace, “aikin me kika yi?.” “Noma.” Rukayya tayi dariya tace, “Yanzu kenan gobe ke amaryar Yusuf ce?.” Ameena ta  mik’e zaune tace, “shine abinda yake damun zuciyata Rukayya, Anya banyi ganganci ba kuwa? Na baro wahala na sake komawa wahala?.” Rukayya tace, “meyasa kike haka ne wai? Ki yi fatan alkhairi ga rayuwar ki mana me ya na wannan zancen dan Allah?. Kin yarda yayi nadama meye to na kasa amincewa dashi Ameena?.” “Wallahi ban sani ba Ruky, kawai hango abinda ya wuce nake yi wanda ke baki san su ba.” “Babu abinda za’a sake maimaitawa na fad’a miki Ameena, dan Allah ki daina wannan maganar kawai mu cigaba da addu’a akwai rabo mai k’arfi a tsanani tunda kika ga Allah ya sake had’a ku a karo na biyu. Kuma addu’a kike ba dare babu rana, su Yaya Adam duk suna yi miki Tunda kika ga hakan to Allah ya rubuta baki da mijin duniya sai shi.” Ameena ya sauke numfashi tace, “haka ne Rukayya. Ni kaina na tabbatar da hakan dan addu’ar da nake yi a kai na tabbata Allah ne ya amsa.” Rukayya tace, “to kin gani, babu komai sai alkhairi wallahi.” Tayi murmushi Rukayya tace, “kunyi magana dashi ne?.” Ta girgiza kai tace, “nace kar ya neme ni har sai bayan an mayar da auren, in ba haka ba Muna sake had’uwa zan iya canja ra’ayi wallahi.” Rukayya tayi dariya tace, “mai aljanun y’an gayu. Bara na kira Fidy da Kiyya su sha labari” ta fad’a tana d’aukar waya ta kira wayar Maman su Fiddausi aka b’ata Fidy ta had’a compresse call suna yi tana basu labari ana ta murna da farin ciki. Bayan ta kashe wayar ne Rukayya ta sauke numfashi tace, “Saura dawo da Fidy nan in sha Allah.” Ameena tayi murmushi tace, “ina ganin k’ok’arin ki in kina maganar nan, wai dan Allah bakya kishi ne?.” Tayi murmushi tace, “mijina ne fa taya bazan yi kishi ba Meenatuwa?.” “Amma sai naji kina zancen zaki ce ya dawo da ita kuma babu wata fargaba.” “To fargabar me zanyi? Matar nan itace matar sa ta farko, kafin nasan waye Ibrahim Fiddausi itace ya sani. To meye zanyi kishi a kai?. Ko a yanzu kallon fanko take min domin kuwa abinda ta rage ne na d’auka, shima in ya kalle ta wani lokacin babu halittar ta da baza ta zo idanun sa ba, to meye abin kishi da ita?.” Ya girgiza kai tace, “kina da abin mamaki.” Rukayya tace, “Wallahi indai zai dawo da Fiddausi haka nake so, zanyi murna sosai dan ta cancanci a yafe mata kuskuren ta. Ya dawo da ita mu zauna lafiya ba fad’a balle tashin hankali.” Ameena tayi dariya tace, “watakila yayi accepting requests din naki.” Rukayya ta murmusa yace, “watakila yayi rejecting ba.” “In ya karb’a fa?.” “Allah ya bamu zaman Lafiya.” “Lallai Ruky akwai daud’a a kanki.” Tayi dariya tace, “baza ki gane ba.” Ameena tayi dariya suka cigaba da hira. Washe gari juma’a bayan sallar juma’a jama’ar masallaci suka shaida d’aure auren Ameena da Yusuf. Yusuf tunda ya tabbatar an d’aure aure nan da nan zazzabin farin ciki ya gama gauraye jikin sa, jikin sa rawa yake jikin sa yayi zafi daga masallacin ma asibiti aka yi dashi aka kwantar dashi dan a bashi magani. Ameena kuwa a wannan lokacin tana gida ita da Anty, Yaya Adam yan shigowa gidan ta tabbatar an d’aura auren gaban ta ya cigaba da fad’uwa ya kalle su a zaune yace, “Kamar zaman makoki ake yi, ina su Sumayya basu zo ba?.” Anty Aysha yace, “suna hanya ni na sani.” Ya kalli Ameena yace, “to Ameena kin zama matar Yusufa a karo na biyu, ga sadakin ki Al’ameen shine ya bayar” ya fad’a yana mik’o mata sai jikin ta yayi sanyi sosai gaban ta yana fad’uwa. “Zo ki karb’a mana.” Ta taso ta karb’a ta zauna a kusa dashi a kan carpet yana sama a kujera yace, “mijin naki kuma yana kwance babu lafiya.” Anty Aysha tace, “to! Meya same shi kuma a wannan ranar ta farin ciki?.” “Farin ciki mana, wallahi ana d’aura auren ya tabbatar an d’aura sai zazzab’i ya rufe shi sai da aka wuce dashi asibiti, yanzu ma yana can.” Aysha tayi murmushi tace, “ikon Allah kenan, wata soyayyar bata bayyana sai an samu sila.” Ya kalli Ameena yace, “baza kije ki ganshi ba?.” Sai ta kawar da kai yayi murmushi yace, “jibi dai zai zo ku tattara ku tafi, nima Monday mu wuce cross river.” Ameena ta share hawayen idanun ta ganin tana kuka sai ya kalle ta yace, “kar kiji komai Ameena, yadda akayi addu’a a kan wannan auren naki ba’a yi a lokacin baya ba, a zuciyata ina jin wannan Karon babu damuwa wallah, ki kwantar da hankalin ki babu komai sai alkhairi da farin ciki.” Ameena ta murmusa tace, “Allah yasa Yaya. Na gode Allah ya saka da gidan aljanna.” Ya amsa da amin ya tashi yace, “sai ki tashi ki shirya kafin y’an uwan ki su zo, da kunya ace amarya ko wanka batayi ba” ya fad’a dan ya tsokane ta. Sai tayi dariya shima haka ya wuce ta ta tashi ta wuce daki. Tana zaune kuwa suka zo suka sakata a gaba wannan yace wannan waccan tace wannan, ita dai tak’i yarda ko lalle ayi mata balle kuma ace ta sha wani abun da sunan amarya, fir tak’i tace ita a barta a haka a hakan take son zama dole suka rabu da ita,          Har ranar lahadin Ameena babu abinda tayi ta kuma ce bazata yi ba, duk sun kyale ta babu Wanda ya tilasta mata har lokacin kuma basu yi koda waya da Yusuf ba dan tace bata bukatar hakan shima kuma har lokaci bai warware sosai ba. A daren ranar lahadin Anty ta saka ta ta shirya cikin kaya masu kyau tana zaune a kan katifa Zaytun tana zaune tana game itama a kusa da ita kayan su iri d’aya sai dai na Zaytun dinkin y’an kanti akayi mata Yaya Adam ya shigo ya kalle ta yace, “Ameena ga Yusuf yazo zaku tafi.” Ta kalli Yaya sai kuma idanun ta suka ciko da hawaye ya bata makulli a hannun ta yace, “koda zaki zo d’aukar kaya in Mun tafi ki bud’e gidan ki d’auka sai ki bawa Al’ameen makullin. İn baya nan sai ki rik’e a hannun ki.” Hannun ta ya rik’e ya zauna kusa da ita yace, “matsayina na mahaifin ki kuma yayan ki ina ji a zuciyata nayi abinda ya dace na bada ke ga Wanda yake son ki ya kuma yi alqawari rik’e auren ki. Alqawari daya nake so ki yimin a yanzu.” Tayi shiru bata amsa ba yace, “Kiyi min alqawarin babu abinda zaki sake b’oye min na gidan ki, farin ciki ko akasin sa ina so na sani, koda ciwon kai kika yi bana so ki b’oye min Ameena.” Tace, “nayi alqawari  Yaya bazan sake b’oye komai ba. Nima bazan sake abinda nayi a bawa ba yin hakan shine ya cutar Dani.” “Sannan ki yiwa mijin ki biyayya kar ki kalli baya ki kalli yanzu kamar yadda yace na tabbata zaki ga canjin da zaki ji dadi sosai.” Nan ma tayi masa alqawarin yace, “Allah ya baki farin ciki mai d’orewa, ya dawwamar da auren ku har aljanna.” Ta amsa da Amin ta kwanta a jikin sa tana kuka sosai yana murmushi yace, “ya İsa haka mana, lokacin auren ki dashi na farko ban samu damar magana dake ba, amma a yanzu da nake magana dake sai na kasance cikin farin ciki da annushuwa sosai, nake ji a raina na samu matsayin uba ba Yayan ki ba.” Ya d’ago ta yace, “tashi muje yana zaman jiran ki ba Lafiya ce dashi sosai ba.” Tare suka fito Zaytun tana biye dasu da wayar Ameena din a hannun ta Yusuf yana gano su ya mik’e tsaye bai san ya mik’e ba Yaya Adam ya rik’e hannun sa ya saka hannun Ameena a ciki yace, “amana, alqawari, tabbatarwa, cikawa, dawwamar, samawar, farin ciki,  nishadi, annushuwa, duka ina so su tabbata akan Ameena. Gata nan amana a wajan ka in ka wulakanta Ameena a wannan lokacin Allah ba zai barka ba.” Ya matse hannun Ameena a hannun sa yace, “na karb’i amanar na kuma ayi alqawarin tabbatarwa har a tashi duniya.” Al’ameen ne ya shigo yana cewa, “badai har an gama bada amanar ba?.”  Adam ya Harare shi yace, “sai yanzu zaka shigo?.” “Ai ban makara ba tunda ga ta, na tsaya shirya mata bazata ne.” Ya kalli Yusuf yace, “Mun baka amanar autar mu Ameena, in ka saka mata damuwa ka tabbata a cikin munafukai, domin kayi alqawari ka sab’a, Muna amince maka muka kayi ha’inci. Ka dubu Allah duk abinda kayi mata bama wajan Allah yana kallon ka kuma zai sanar damu abinda kake mata mu kuma sai inda karfin mu ya k’are.” Yusuf yace, “in sha Allah baza kuyi kuka dani ba, zan rik’e Ameena dakyau fiye da yadda na rik’e ta a baya.” Al’ameen yace, “in ka aikata hakan ka rik’e alqawari ka kuma cika dan halak.” Ya kalli Ameena yace, “kanwata akwai kyautar dana ke so na baki” ya fad’a yana saka hannu a aljihu ya d’auko key na mota ya mik’a mata yace, “sabuwar motar na siya miki irin wacce kike so, gata can a ajjiye tana jiran ki.”  Ameena ta karb’i key din tace, “Na gode Yaya, Allah ya saka da alkhairi.” Yusuf ma yayi murmushi yace, “Allah ya saka da alkhairi.” Ya amsa da amin hannun sa yana cikin na Ameena suka fito har harabar gidan ga sabuwar mota nan dal a ajjiye bak’a mai kyau sosai mai tsada ta kalli motar dan ta burge ta sosai ta kalli Al’ameen tace, “Na gode Yaya Al’Ameen, Allah yayi maka Zab’i na alkhairi, Allah ya baka farin ciki a duniya da lahira.” Anty Aysha ma tayi masa godiya sosai dan taya Ameena. Yayi murmushi ya amsa Yaya Adam yace, “zaki bar motar a nan in yaso tunda na baki key na gidan duk sanda kike son d’auka sai kizo ki tafi da ita.” Ta d’aga kai cikin gamsuwa tana jin yadda ya matse mata hannu kamar zata gudu suka k’arasa cikin mota suka shiga suka ja motar suka bar cikin gidan zuciyar ta cike da kewa da kuma tunanin rayuwar da zata sake yi a gidan Yusuf.       Babu wanda yake magana a cikin mota hana tafiya tana gefe Zaytun tana baya har lokacin wayar Ameena ce a hannun ta kafin ta ajjiye ta mik’e a bayan motar tace, “Mummy unguwa zamu je da daddy?.” Shiru tayi bata  amsa ba sai Yusuf ne yace, “Eh Ammata, Unguwa zamu je.” “Daddy tare da kai?.” “Eh dani.” Sai tayi dariya alamun farin ciki shima yayi ya saci kallon Ameena ya ganta fuskar ta gata nan dai ita ba farin ciki ba kuma ba akasin sa ba. Gidan Ammah suka wuce ya tsaya da motar sai ya dafe kansa yayi k’aramin tsaki tace, “ciwon nan yana damuna sosai.” Ya kalli Ameena har lokacin bata kalle shi ba yace, “my choice zamu shiga wajan Ammah.” Sai a sannan ta juyo da ido ta kalle shi sai da gaban da ya fad’i haka nan Alalh ya dasa masa shakkar ta a zuciyar sa. Idanu suka had’a yayi murmushi yace, “Ammah tana jiran zuwan ki.” Bud’e motar tayi ta fita shima ya bud’e shi da Zaytun suka shiga cikin gidan. Tana shiga falon sai ihuuu Humaira ta taso a guje ta rungume ta tana cewa, “Welcome back sis.” Murmushi tayi ganin su duk a falon gabad’ayan su har Yayan su ta Abuja da alama kowa zaman jiran zuwan ta yake yi tayi murmushi dan taji dadin hakan sosai  ta kuma san indai akace so dangin Yusuf suna sonta, ta kalli Humaira cikin murya k’asa-k’asa tace, “kin zama lukuta.”  Humaira tayi dariya Ameena ma murmushi take ta k’arasa wajan Abbah ta gaishe shi ta gaishe da Ammah ma suka amsa da farin ciki sosai a zuciyar ta, Ameena ta gaishe su dukka suka amsa Yayan Abuja tace, “ki zauna mana kamar sabuwa a cikin mu.” Tayi dariya ta zauna a kan carpet tana kallon Humaira da take ta d’aga mata gira sai take bata dariya. Ammah share hawaye take farin ciki da murnar dawowar Ameena cikin su ya cika mata zuciya sosai dan hakan ya bayyana a tare da ita. Ta kasa sarrafa farin cikin bata hakan ya saka ta zubar da hawaye. Abbah ya kalli Yusuf da yake zaune sai murmushi yake yi suna had’a ido da Abbah sai ya sha jinin jikin sa ya d’an murmusa Abbah yace, “to Yusuf ga Ameena nan a karo na biyu, zamu gani ko nadamar har zuciya take ko kuma a iya fatar baki ta tsaya. Abinda nake so ka sani kamar abinda babar ka tace  ka sake ka wulakanta Ameena nima nace Allah ya isa.” Murmushi yake yi dan shi dai yasan hakan baza ta faru ba balle Allah ya isa iya aiki a kansa yace, “Abbah wancan Yusuf in ya mutu wannan sabo ne a gaban ku a zaune zai baku mamaki in sha Allah.” Ita dai Ameena murmushi take yi har ga Allah tana son iyalan gidan saboda son da suke nuna mata da zuciya d’aya dukkan su babu wanda yake k’i ta kowa burin sa yaga tana farin ciki. İn ba tsantsar soyayya ba ina mahaifi ina yiwa d’an sa alqawarin Allah ya isa in bai kyautata mata ba?. Abie yace, “Allah ya baku zaman Lafiya ya kawar da idanun mak’iya daga kan ku.” Aka amsa da amin Mubakar yace, “Allah kar ya sake kawo irin su b’eriya.” Humaira tayi dariya kowa ma yayi dariya Ammah tace, “A ina zaku zauna yanzu?, naga tsohon gidan naku ba’a gyara ba.” Yusuf yace, “sabon gida.” Abbah yace, “wanda ka siya wai shekaran jiyan?.” Ya d’aga kai alamun eh Yyan Abuja tace, “har ka gama zuba komai kenan?.” Nan ma ya d’aga kai alamun eh tace, “lallai yaron nan kana abinda kake so.” Yayi murmushi kawai Ammah tace, “Ameena zo kiji” ta fad’a tana rik’e hannun ta suka shiga ciki. Abbah ma nasiha yayi masa sosai da kuma jan hankali akan abubuwan da suka wuce ya sake d’aukar alqawari akan bazai sake faruwa ba. Ba jimawa sosai Ammah da Ameena suka fito suka tafi zuwa sabon gidan da yake kusa dasu Ammah dan daga gidan Ammah ana hango shi ba kamar wancan ba ya shiga da motar har cikin gidan. #mai daki #Book3 #Nana Haleema Book3  041            Babban gida ne sosai dan yafi wanda suk zauna a baya kyau da k’eruwa da girma yafi na baya sosai ba kad’an ba. Ameena kallon gidan tayi komai fari tun daga waje hatta k’ofa da gate farare. Kallon ta yayi bayan ya kashe motar kansa ciwo yake sosai amma baya son nunawa kar taga gazawar sa tun ba’-a je ko ina ba yace, “mu shiga ko?.” Bata kalle shi ba ta sakko daga motar shi kuma ya fito shida Zaytun suka shiga cikin gidan.  A falon ta zauna tana kallon falon komai sabo ne a ciki yayi kyau sosai ya tsaru kamar ba a cikin k’aramın lokaci akayi komai ba. Ganin ta zauna shima sai ya zauna Zaytun na kusa dashi ta kalle ta taga babu wayar ta a hannun ta sai ta ganta a hannun sa sai ta share bata ce komai ba. Magana yake so yayi mata amma ya kasa dan tsoron ta yake ji tun da akayi maganar auren babu abinda ya had’a su shiyasa ya rasa da abin zai fara. Kafin yayi tunani yaga ta tashi tace, “ina ne mazauni na?.” Sai shima ya Mike yace, “ina ne mazaunan mu dai ko?.” Kallon k’asan idanu akayi masa tace, “ban tambayi naka ba ai nawa na tambaya, yana ina?.” Yayi Murmushin k’arfin hali yace, “muje na raka ki.” Yayi gaba tana bayan sa ita da Zaytun suka hau sama suka shiga wani falon yayi gaba tace, “ka dakata ma, naga inda zan zauna” ta fad’a tana bud’e wani d’aki tana kallon sa dan yayi kyau sosai gashi kuma mai girma. Shiga ciki tayi shima sai ya biyo bayan ta ta cire mayafin ta ajjiye a kan gadon tana kallon Zaytun tace, “zo ki cire kayan nan kar su dame ki.” Zaytun ta maqale kafad’a tace, “wajan Daddy.”  “Sai kin dawo” ta fad’a ba tare da ta kalle shi ba fuskar ta ba yabo babu fallasa. Yayi murmushi ya shigo ya zauna a daf da ita baice komai ba bata  ce komai ba, ya ciro wayar ta daga aljihu ya bata ta karb’a ta bud’e tana dannawa. Ya kasa magana sai kallon ta kawai da yake yi amma ya kasa furta ko wacce kalma daga bakin sa, itama kuma ko zasu kai shekara a wajan baza tayi magana ba. suna zaune shiru a haka sai yaji tace, “idan baka da abin fad’a kwanciya nake so nayi.” Ya kalle ta yace, “nima kwanciyar zanyi a nan ne masauki na.” Sai ta kalle shi tace, “ayya ai ban sani ba, sai na canja d’aki” ta fad’a tana niyar tashi ya rik’e hannun ta t dawo ta zauna yace, “ina nufin duk inda ya kasance masaukin ki nan ne masauki na.” Bata ce komai ba ta sake kallon Zaytun da take jin bacci amma ta maqale a jikin sa ta girgiza kai kawai bata ce komai ba.  “Mtsw! Ko Kaya ma bani dasu” ta fad’a tana tashi ta shiga k’ofar da take gani wacce tasan band’aki ce. Zaytun ya d’auke daga jikin sa ya cire mata rigar ya kwantar da ita a kan gadon ya zauna yayi shiru farin ciki ya cika masa zuciya amma kuma tsoro da shakkar magana da Ameena yafi damun sa. Fitowa tayi daga band’akin tayi alwala ta kalle shi tace, “zan kwanta.” Ya kalle ta yace, “bismillah.”K’arasowa tayi ta hau kan gadon ta zauna bata kwanta ba gabad’aya wani iri take ji a zuciyar ta kuma ta fahimci tsoron yi mata magana yake ita kuma haka take so dan bata shiryawa maganar ba a yanzu. “Ameena!.” Sai kuma yayi shiru ta kalle shi bata amsa ba yana jiran k’arin bayani amma sai ya kasa yayi shiru na wani lokaci kafin ya sake cewa, “Ameena ki yi hak’uri, dan Allah ki manta da baya ki d’auki yanzu a matsayin sabuwar rayuwa.”  “To, nayi” abinda tace kenan ya kalle ta yadda take magana kamar yadda take yi gab da rabuwar auren su yayi murmushi yace, “na gode. Akwai abinda kike so? Zaki kwanta baki ci komai ba?.” Kai ta girgiza alamun babu yace, “in kin yi min alfarma ina so zan kwanta a gefen ki.” Wajan ta nuna masa da hannu alamun gashi nan ta kwanta ta tare da ta sake cewa komai ba, ya sauke numfashi a hankali ya tashi ya kashe hasken d’akin ya kwanta Zaytun na tsakiyar su. Bacci take son yi amma ta kasa tunani ne yake zuwa zuciyar ta kala-kala shaid’an yana sake zuga ta akan share shi har sai ta wahalar dashi sannan in zasu gyara zaman nasu sa gyara daga baya. A haka bacci ya d’auke ta shi kam idanun sa biyu ciwon kai bazai barshi baccin ba. Tashi zaune yayi bayan tayi bacci ya dafe kansa da hannayen sa gıda biyu ciwo suke masa sosai kamar zai raba gida biyu haka yake ji, ya kasa jurewa saboda azaba ga maganin sa yana cikin mota a k’asa ga dare yayi lokacin karfe d’aya na dare. Ameena tana jin motsin sa dan bata da nauyin bacci motsi akayi na kirki zata bud’e idanu ta jiyo sai ta ganshi a zaune yana juya kansa gashi ya dafe kan, tashi zaune tayi tana kallon sa tace, “Lafiya?.” Hannu d’aya ya mik’a mata ta taso ta rik’e hannun nasa sai ta wara ido jin tafin hannun nasa ma yayi zafi tace, “Subahanallahi, baka da lafiya?.” Kusa dashi  tadawo da ita ta zauna ya kasa magana saboda ciwon kai tace, “kan ka ne yake ciwo? Ina maganin ka yake?.” Baice komai ba ya dai rike hannun ta gam gam tace, “ina maganin ka yake na d’auko kasha?.” “Yana mota. Kar ki fita zai daina” ya fad’a dakyar tace, “taya zai daina baka sha magani ba? Ina key din motar na d’auko?.” Sake rik’e ta yayi yana girgiza kai alamun baza ta sauka ba tace, “zan iya zuwa” ta da da tana zame hannun ta daga nasa taga key din a gefen bedside ta d’auka ta fita daga d’akin ta sauka ta fita zuwa harabar gidan sai ayatul kursi take karantawa a zuciyar ta. Baba mai gadin tsohon gidan  tane ya bata tsoro ganin an hasko ta da fitili ta razana ganin itace sai ya k’araso yana tambayar lafiya. Bud’e motar tayi ta d’auko maganin a leda a baya ta kulle motar ta ta koma ciki ta d’auki ruwa a falon ta hau saman ta samu har ya samo daga kan gado ya dafe kansa ta k’araso tace, “ga  maganin” ta fad’a tana bud’ewa tana gani duk daily dose ne ta ciro dukkan su tace, “karb’i kasha.” ya karb’a yasha din tana zaune a gefen sa sai ya kwantar da kansa a jikin ta tana jin yadda jijiyar kan yake bugawa sosai sai bata hana hakan ba. Suna zaune a haka kusan mintina talatin kafin bacci ya d’auke shi ta kalle shi tana mamakin ciwon kai irin wannan ta kwantar dashi a gefe ta koma daya b’angaren ta kwnata itama. Tun karfe hud’u ta tashi shi kuwa bacci yake sosai ta wuce tayi alwala ta fito tana sallah kamar ko yaushe har akayi asuba tana so ta tashe shi yayi sallah amma kuma taga baccin yake sosai da alama ya samu saukin kan. K’arasowa tayi kawai tana yi masa magana amma bai motsa ba hakan ya bata tabbacin baccin yayi nisa dan bashi d a nauyin bacci shima. Kyale shi tayi ta cigaba da abinda take yi kafin ta kwanta itama. Bai farka ba sai karfe tara na safe yana bud’e ido ya ganta a tsaye da kayan jiya a jikin ta tana mayarwa da Zaytun su da alama har tayi wanka ma. Ya tashi zaune yana sake dafe kansa ta kalle shi tace, “ka tashi safiya tayi sosai akwai sallah a kanka” tana fad’a ta fita ita da Zaytun sai kuwa ya tashi ya shiga band’akin ya fito ya tayar da sallar asuba yayi ya sake yin sallar walha a lokacin ya shigo ta d’auki mayafi suka had’a ido sai tace, “ina kwana.” “Kin tashi lafiya?.” “Lafiya lau, ya jikin?.” “Alhamdulillah. Na gode Allah yayi albarka.” Tayi murmushi jin abinda yace sai tace, “Amin. Ta nuna masa key tace, “na ari motar ka zanje gida na dawo.” Ya kalle ta kafin yayi magana tace, “Ammah ta aiko da abinci yana k’asa in zaka ci.”  “Su Yaya Adam din basu tafi ba?.” “Sun tafi, zanje gida na d’auko kaya ne ga uniform din Zaytun yau ko school bata je ba.” Ya tashi tsaye yace, “to ki jira ni nayi wanka sai muje.” Ya kalle shi tace, “yanzu zan dawo, ba lafiya ce dakai ba ka zauna.”  “Bazan iya zaman bakya nan ba, ina zuwa” ya fad’a yana fita daga d’akin tace, “sabon salo, wai bazai iya zama bana nan ba. Ayi dai mu gani.” Tana nan zaune sai gashi ya dawo ya canja kaya zuwa jallabiya blue yace, “muje.” Tashi tayi suka sakko ya shiga mazaunan direba ya shiga gaba ita da Zaytun suka fita daga gidan. Gani tayi yana yawo akan titin kamar dan koyo alamun akwai abinda yake damun sa tace, “ka tsaya.” Sai kuwa ya tsaya ta fito daga gaba ta zagayo ta bud’e tace, “ni nasan baza ka iya ba, ka koma gaba.” Sai da ya rik’o hannun ta sannan ya fito ya koma inda ta bari ya zauna ta shiga taja motar zuwa gidan su. Mai gadi yana nan dan daman baya barın gidan babu kowa suka gaisa ta shiga ta bud’e gidan yana zaune a motar sai gata da jaka babba ta fito mai gadin yazo ya karb’a ya saka mata a boot ta sake komawa ta sake fitowa da wasu ya sake karb’a ya saka mata a motar. Kulle boot din tayi ta shiga ta sake jan motar suka koma gidan. A falon suka zauna ta zata d’auki kayan ya hana ta kale shi tace, “ina da lecture ne ina sauri zan tafi.” Ya kalle ta jin abinda tace sai yace, “to, amma ki bari yanzu Mubakar zai zo sai ya hau miki da kayan sama.” “Har sai na jira Mubarak? nace sauri nake”ta fad’a tana fara jan kayan sai ya tashi yace, “kawo na d’aukar miki” kafin tayi magana ya d’auki duka biyun yana hawa saman dasu tabi bayan sa Zaytun ma tana biyo duk duk inda suka bi ya shiga dasu har d’akin tace, “Sannu.” Abinda tace kenan ta k’arasa ta bud’e kayan ta d’auki kayan da zata saka ta d’auko na Zaytun ma ta fara saka mata yace, “Yanzu makarantar zaki tafi?.” “Eh.” Yayi shiru baiyi magana ba ya fita ta shirya ta fito da jaka ta same shi a falon a zaune tace, “sai na dawo.” Sai ya tashi yace, “muje na kai ki.” “Haba dai, kayi zaman ka zanje, yanzu da muka fita ma baka iya driving din ba.” Yayi shiru tana kallon sa kana ganin sa kasan bashi da lafiya karfin Hali kawai yake yi tace, “ka zauna ba jimawa zanyi ba” ta kalli Zaytun da take kusa dashi bata ce komai ba ta sauka ya bita da kallo ya lumshe idanun sa farin ciki da damuwa sun masa yawa a zuciyar sa har ya kasa sarrafa su.           Tun daga farkon estate din aka jin wari mai sanya amai gabad’aya wari ya addabi mutanen da suke zaune a wajan duk sun bar gidajen su dan wari ya game ko ina har cikin d’akin ki. Jami’an lafiya aka kirawo suka yi searching ko ina aka tabbatar warin daga gidan Alhaji Bello yake fitowa suna nufar gidan warin yana sake yin yawa. Babu kowa a gidan ko mai gadi babu kamar kango gidan haka suka dinga shiga ana dubawa har suka zo k’ofar falon da aka kulle Alhaji Bello a ciki. Dukan k’ofar sukayi da k’afa duk sai da suka ja baya saboda duk da sun kulle hancin su amma warin da ya danno kai sai da suka ji shi har cikin bakin su cikin su ya juya a take wasu suka fara jin zawo saboda warin da yake fitowa bana wasa bane. Alhaji Bello suka hango tsirara dashi a kwance ya zama tamkar skeleton naman jikin sa har ya fara zagwanyewa k’uda da kiyashi kamar saukar dasu akayi a wajan. D’aya daga cikin ma’aikatan yace, “wannan ya kwana biyu da mutuwa a wajan nan.” D’ayan yace, “gashi babu kowa a gidsn duk girman sa, waye wannan din?.” A nan suka tattaro Alhaji Bello aka saka kwantar a harabar gidan aka nemo malami aka yayyafa masa ruwa dan bazai yu ayi masa wanka ba saboda ya gama lalacewa aka suka nannd’e shi a farin yanki aka d’auke shi aka je aka binne. An saka maganar a social media saboda y’an uwan sa su sani  nan da nan magana ta baza duniya Alhaji Bello ya mutu ga kuma irin mutuwar da yayi. Daya daga cikin abokan harkar Alhaji Bello yana duba waya yaga abinda yake faruwa gaban sa sai ya fad’i sosai ya kalli Nabila sa take kusa dashi yace, “kinga abinda na gani, kalli Alhaji Bello fuskar sa dan Allah” ya fad’a yana nuna mata wayar gaban ta ya fad’i itama tace, “wannan shine? Kalli yadda kuda suke bin abinda da aka rufe shi ba.” “Ki karanta maganar; kwanan sa biyu da mutuwa an rass kowa nasa, damun mutanen unguwar yayi da wari suka je suka fito dashi aka samu ya mutu bayan haukan da yayi na kwana biyu aka yayyafa mai ruwa aka binne saboda ko da an kai shi wajan ajjiye gawa baza ta zaunu ba, saboda tun farko ya riga ya fara wari. Nabila ta girgiza kai tace, “Allah Sarki. Shi ya riga ya mutu muyi magana akan abinda yake gabana. Ka bani kud’i na tafi Germany naje ayi min aikin nan. Komai nawa ya k’are Akan wannan lalurar da ku ne kuka samar min da ita, zama bana iya yi yanzu sosai kai ma ka sani.” Ya kalle ta yace, “babu abinda zan baki wallahi, domin kuwa ke ba mutuniyar da za’a taimakawa bace ba. Waye bai San ki da Alhaji Bello ba? tunda komai ya fara lalace masa kika gudu bama Kya yin maganar sa. Yanzu da yayi irin wannan mutuwar ko a jikin ki wai Allah Sarki shine abinda zaki ce a matsayin ki na budurwar sa. kinga Nabila bani na saka ki neman ko wanne namiji ba, a can kika kwaso ciwon da kika kwaso dan haka babu ruwana ko tashi ki bani waje ni.” “Kasan Adadin abinda yake damuna kuwa? Ance in ba’a yi min aiki ba zan iya rud’ewa k’arshe kuma mutuwa ce.” “Ki mutu mana shima gashi ai ya mutu lokacin sane yayi.” “Ka taimaka min kaf kudina ya k’are akan wannan ciwon wallahi, dan Allah ka taimaka min ka bani ciwon nan yana damuna sai na saka wani abun na tare saboda ruwa ne yake fita daga jikina gaba da baya.” “In ma jini ne ina ruwa na? Kinga ki tashi ki fita babu ni babu ke wallahi kije can ki k’arata amma kar ki sake zuwa inda nake.” Nabila tace, “yanzu baza ka taimaka min ba? In baka taimaka min ba waye zai taimaka min?.” Ya harare ta yace, “kije gawar Bello ta taimaka miki amma bani ba walalhi, in baki fita ba sai na yi ball dake a wajan nan. Ki barni naji da aabinda ya samu Bello mana, hauka ya dinga yi a gidan sa babu Wanda yake kula dashi kowa ya gudu babu y’an uwa balle mata, yanzu yayi irin wannan mutuwar amma ke bai dame ki ba saboda kudi kawai kika sani, ni ya dame ni saboda abinda Alhaji Bello yake shi nake yi.” A haka ta fito jiki a salub’e shine mutumi na biyar kenan da taje wajan sa ko zasu taimaka mata amma bata taimakawa  yanzu bata san ya zatayi ba kuma ciwon yana gab da cin karfin ta dan yanzu ruwa take fitarwa daga ko wacce kafa ta jikin ta.          Kwana biyu Kenan da tarewar Ameena babu wani canjawa harkar ta take bata shiga sabgar sa shi kuma har lokacin shayin ta yake yi baya iya mata magana mai tsaho gashi babu lafiya kirki gashi nan dai kawai. Da daddare ranar alhamis tana zaune a falo tana karatu dan tana da text juma’a. Zaytun bata nan tana gidan Ammah shi kuma ya hau sama bai sakko ba tun bayan da hau saman. Gama karatun tayi ta tashi zata hau saman zata sai ga Mubakar ya shigo da Zaytun ta kalle shi tace, “har ina murna a can zata kwana.” Mubakar yace, “ta saka Rigima a kawo ta.” Tayi murmushi tace, “lallai Zaitun kin kyauta.” Mubakar yayi dariya yayi mata sallama ya fita ita kuma ta rik’e ta suka hau sama.  Tana hawa saman a d’aki ta kwantar da Zaytun dan ta fara jin bacci tana cire kayan ta kafin ta gama Zaytun tayi bacci ta gama saka kayan ta kalli Zaytun din taga tayi bacci sai kuma ta kalli k’ofa taga bai shigo ba sai zuciyar take fad’a mata ko bashi da lafiya. D’akin da take ganin yana shiga ta shiga sai kuwa ta hango shi a zaune a kan tiles hannun sa ya dafe kansa alamun ciwo da Sauri ta k’arasa wajan tace, “ciwon kan ne har yanzu? Ya kamata kaje asibiti.”  Rik’e hannun ta yayi ya kalle ta cikin ciwo yace, “wannan ciwon kan bana jin zai barni, Ameena kin kasa yafe min har yanzu kin kasa sakin jiki dani ni kuma tsoron yi miki magana nake, haka nan Allah ya saka min shakkar ki a zuciyata. Dan Allah kiyi hak’uri ki fad’a min koda kalma daya ce da zanji dad’i kafin ciwon nan ya zama ajalina.” Dakyar yake maganar ta zauna kusa dashi tana jin tausayin sa sosai tace, “na yafe maka wallahi har cikin zuciyata babu komai a raina, kawai na kasa amincewa da ba rayuwar baya na dawo maimaitawa ba shiyasa na kasa sakin jikina.”  “Rayuwar baya ta wuce Ameena, rayuwar baya ta zama tarihi yanzu sabuwar rayuwa zamu yi dake in Allah yasa ina da tsahon kwana. Wallahi Ameena ina sonki, ina sonki son da nan miki shi a baya ba, ki amince dani na nuna miki wannan soyayyar kafin raina ya bar jikina.” Ya fad’a yana kwanciya a jikin ta ta rike shi idanun ta suna taruwa da hawaye tace, “na kasa baka damar ne, gani nake kamar baka canja ba, kallon komai nake kamar farkon auren mu na wancan lokacin haka komai ya dinga faruwa cikin kula da soyayaya amma daga baya komai ya watse. Ina jin tsoron hakan shiyasa Kaga ina baya da kai.” Shima hawayen yake a jikin ta yace, “na canja baza’a sake maimaitawa ba Ameena, sai kin bani dama zaki tabbatar da abinda nake fad’a miki in baki bani dama ba baza ki kai ga sanin abinda nake nufi ba. Kiyi hak’uri ki bani dama wacce zan nuna miki waye Yuusf a wannan lokacin.” “Na baka dama, daga yau na baka dama ka gyara abinda ka b’ata, in ka yaudare ni Alalh yana kallon ka bazai barka ba.” “Har abada, babu ke babu kukan bak’in ciki sai dai kukan farin ciki Ameena. Akwai halina da nake dashi wanda ke kin san dashi ki yi hak’uri dashi a duk lokacin da nayi miki amma batun abubuwan da suka faru baza su sake faruwa ba.” Ta goge idanun fa tace, “shikenan yanzu muje asibiti jikin ka yayi zafi sosai.” Ya sake kwanciya a jikin ta yace, “ina samun sauki a jikin ki, na sha magani ki barni a haka zan dawo daidai.” Rik’e hannun sa tayi tana maruza tafin hannun sa saboda ya sake samun sauk’i yana kwance a jikin ta har lokacin kuka yake yi tace, “ka daina zubar da hawaye shima zai saka maka ciwo.” “İn na tuna abinda nayi miki bana iya sarrafa zuciyata sai na yi kuka.” “To kayi hak’uri ai komai ya wuce.” Shiru yayi yana jikin ta har lokacin kafin ta kalli fuskar sa da take kirjin ta taga ya kulle ido alamun bacci zaiyi babu jimawa kusa baccin ya d’auke shi. Kallon fuskar sa take yi sai tayi murmushi tana kawar da komai a zuciyar ta tana d’aura d’ammarar fara sabuwar rayuwa da mijin ta. A haka suka kwana dan itama bata san tayi bacci ba kiran sallar wayar sace ta tashe su. Shi ya fara motsawa ya tashi zaune sosai yana rik’e da wuya ya kalle ta yaga ta bud’e ido itama sai yayi murmushi ya kai nata kiss a forehead yace, “Ashe a haka muka kwana.” Tayi Murmushin itama tace, “Anyi Kira mu tashi lokacin sallah, bara na duba Zaytun” ta fad’a tana tashi da sauri ta shiga ta samu Zaytun din kuwa a zaune kamar aljanna tana game. A bayan ta ta ganshi ta kalle shi suka kallo Zaytun din tace, “Game din yarinyar nan tayi yawa har tsoro take bani, Duk ranar da ta fasa min waya sai ka biya, kaine ka koya mata game.” Murmushi yayi yace, “na siya mata iPad ma mantawa nake ban d’auko ba, in taje school ta dawo sai tayi abin ta a daina mata gorin waya.” Ameena ta kalli Zaytun tace, “tunda kin tashi sai muyi sallah, tashi muje alwala” ta fad’a tana shiga band’aki Zaytun tabi bayan ta sukayi Alwala tare ta suka fito shima yayi alwala sukayi sallah a tare zuciyar da kamar an wanke ta da soso da sabulu haka yake ji. Bayan sun idar ta tashi tace, “zan sauka na had’a m mata lunch box lokacin school ya kusa.” Ya kalle ta yace, “kiyi zamana ki yau Friday basai taje ba.” “A’a bafa zamu fara haka ba, sai taje makaranta haka akwai baza ka saka ta dinga zaman gıda ba.” Ta fad’a tana fita sai ya d’auko Zaytun din suka sakko tare suka bita kitchen din. Tare suka yi mata abu mata abinci ta saka mata a box din ta sake komawa sama tayi mata wanka ta saka mata uniform ta saka ta yaci abinci kafin mai school bus din su yazo ya d’auke ta su tafi. Yana dawowa daga kai ta wajan motar tace, “kaima kayi breakfast din kasha magani, zanyi wanka zanje school ina da test.” Ya bita da kallo yace, “karfe nawa zaki dawo?.” “Zuwa ten ma na dawo.” “Muje ko shirya din muje tare sai na jira ki gama mu dawo.” “Baka da lafiya fa.” “Naji sauki.” Tare suke hau saman tace, “da ka jira naje na dawo tunda bazan jima ba naga alama in kana zırga-zirga ciwon yafi damun ka.” Yace, “in naje na sauke ki kafin ki gama zanje naga Dr akan ciwon kan nan dan damuna sosai, yace damuwa ce kuma yanzu na samu maganin damuwar but still ban daina ba.” Ameena ta kalle shi tace, “kaje asibitin ka dawo zamu yi daidai in ka dawo sai mu huta a gida.” Ya rik’o hannun ta guda biyun yana kallon ta yace, “da gaske hutawa zamuyi in kin dawo?.” Tace, “eh ina zamu je to?.” Ya girgiza kai yace, “babu, muje kinshirya din to.” Murmushi tayi kawai ta shiga d’aki ta shiga wanka shi kuma ya zauna yana jiran ta. Tunda ta fito yake binta da kallo ta kalle shi tace, “baka shirya ba?.” Kai ya d’aga kawai yana kallon ta ta tsaya  ita kuma bata motsa ba saboda kunyar sa take ji daman tun can baya ita bata daina kunyar sa ba balle yanzu da suka jima basa tare. Ganin hakan sai yayi murmushi ya taso yace, “na tabbatar wannan kunyar taki har mutuwa.” Tayi dariya kad’an ya matso kusa da ita ya rungume ta ta baya suna kallon madubi shi da ita kafin tace, “ka rame sosai, fuskar ka ta canja kamar ba kai ba.” “Ke kuma kinyi kiba, jikin ki ya canja kamar ba ke ba.” Tayi dariya shima yayi dariya yayi shiru alamun akwai abinda yake tunawa itama haka sai ga kawar tace, “ina Asiya?.” Gaban sa ya fad’i sosai ya kalle ta yaga kallon sa itama take sai yace,”kar a fara test din bakya  nan” ya fad’a tana zare jikin sa ya koma gefe, tasan baya so ya amsa ne sai ta wuce ta d’auki kaya sai ta fita dan taga alamun bazai bar d’akin ba. Dariya yayi sosai ya fita ya koma daki shima ya shiga wankan yana jin farin ciki a zuciyar sa da ganganar jikin sa. Tare suka fita ta tafi makaranta ya tafi asibiti, ta riga shi dawowa lokacin da ta dawo baya nan bata jima ba Zaytun ta dawo tayi musu abinci tayi wanka ta canja kaya ta yiwa gidna turaren wuta kamar yadda ta saba ita kanta khamshin sa take yi. A lokacin ne  ya dawo ciwon kan yana neman danne shi sai da ya kwanta kafin lokacin sallar juma’a sannan ya dawo daidai yayi wanka ya tafi masallaci. Da ya dawo ta gama had’a abincin yana shigowa tace, “Beb Bismillah ga abinci.” Jin sunan da ta kira shi sai yaji dadi sosai yace, “thanks you my choice.” “A canja min wannan sunan” ta fad’a bayan ya zauna tana zuba masa abincin yace, “wanne kike so. “Daga zuciyar ka.” Yayi shiru alamun tunani kafin yace, “nima Beb din zance.” Sukayi dariya a tare yana cin abincin tace, “ya kuka yi da Dr din?.” “Hoton kwakwalwa za’a sake yi yace ko abin ya tab’a min kwakwalwa ta. Amma ji nasan normal nake bana hauka ai?.” Sai tayi dariya ya bata tausayi sosai tace, “baka yin komai.”  Yayi murmushi yace, “nayi haukan a lokacin da zan rasa ki, ashe damuwar ce tayi hawa har ta tab’a kwakwalwar.” “Yanzu zata tafi in sha Alalh.” “Allah ya biye bakin ki. Ina Ammata?.” “Tana gidan Ammah, nima jira nake ka gama muje mu gaishe su zuwa dare ma dawo.” Ya girgiza kai yace, “muje dai mu dawo amma ba zuwa dare ba.” “Meyasa?.” “Saboda Ina son kasancewa da ke Beb.” Tayi dariya b’ata ce komai ba ya gama cin abincin suka tafi gidan Ammah. #Nana Haleema #Mai daki #Book3 Book3 42          Kamar yadda kusan ko wacce juma’a suke taruwa haka yaga yan gidan nasu gabad’aya suna nan har Humaira ta Abuja ce kawai bata nan suka shiga da sallama Ammah ta amsa ganin Ameena sai Murmushin ta ya k’aru itama Murmushin tayi ta k’arasa suka gaisa dasu dukkan su shima ya zauna suka gaisa kafin Abbah yace, “Yanzu muka gama waya da Adam ai, ashe ya koma cross river.” Ameena tace, “eh yana can kusa sati d’aya ma.” “Allah Sarki, Allah ya taimaka ya bada nasara.” Ameena ta amsa da amin tana murmushi.  D’aga ido tayi suka had’a ido da Humairah sai taga Tana d’aga mata m gira tana kashe mata ido sai tayi dariya a bayyane tace, “Allah ya shirye ki.” Itama dariyar tayi Abbah ya kalle shi yace, “kaje asibitin?.” Yusuf yace, “eh naje,wannan hoton kwakwalwar za’a sake yi suka ce. Ni na gaji da wannan hoton wallahi in anyi suce babu komai.” Abbah yace, “to ka tafi Saudia german mana a duba ka a can,  in da matsala ai su zasu gani zaman da kake da ciwo baka san ne yake kawo maka shi ba illa ce.” Yusuf yace, “kuma haka ne, banyi tunsninzuwa bama sai yanzu. Daman visa ta England ta kusa k’arewa sai muyi amfani da ita mu shiga Saudia.” Ammah tace, “hakan ya kamata, wannan zaman ba zai amfane ka ba ai tunda lalura ce Allah ya d’ora maka.” Ya sauke numfashi baice komai ba Mubakar yace, “ni sai nake gani kamar ma baka farin ciki bayan ga wacce kake Shan kukan a kanta tana tare da kai. Soyayya bala’i ce, ban tab’a ganin kana kuka bafa tunda nake a duniya sai Akan Ameena.” Ya kalli Mubakar sai yayi murmushi kawai Humaifa tace, “kai kasan wani farin cikin baya bayyanuwa ko Yaya?.” Shi dai baiyi magana ba ya tab’e baki kawai sukayi dariya. Humaira ta kalli Ameena tace, “Sis zo muje kiji wata magana.” Ameena bata ce komai ba ta tashi ta bita dan tasan wata gulmar zata isar mata.  Suna gidan har akayi sallar magriba sai a lokacin ne ya shiga d’akin Ammah ya same ta a zaune suna Shan kayan marmari ta da Ammah da Humaira yace, “ke wai baza ki tafi gida bane?.” Humaira ta kalle shi tace, “sai anyi sallar i’sha.” Ya girgiza Kai ya kalli Ameena yace, “muje?.” Ammah ta kalle shi tace, “taje ina? Baka ga abinda take yi ba? Ka jira ta gama mana ko ka bari ayi i’sha kwa tafi kuma. Ta nesa ma gata a zaune balle ku maqota?.” Yusuf ya kalli Ammah da take magana tace, “to Ammah.” Abinda yace kenan ya fita Ameena ta kalle shi kafin ta kalli ammah sai  suka had’a ido Ammah tace, “ke ban hana ki bin sa bafa, tashi kije naga kina kallona ta k’asan idanu.”  Ameena tayi dariya mai sauti Huamira tace, “kema dai Ammah kece da wata magana, wai sai anjima gashi nan ta nuna miki bin sa zatayi.” Ameena ta kalli Huanira tace, “banda sharri.” Ammah tayi dariya tace, “gashi naga zahiri, tashi kije maza ni ban hana ki ba.” Ameena bata tashi ba tace, “basai naje ba Ammah.” “Baki isa ba tashi ki tafi sai da safe.” Ameena ta tashi tsaye ta kalli Zaytun da ta shigo ta kalli Ameena tace, “ Mummy Mun tafi unguwa da Uncle Mubakar.” Humaira tace, “sai kin dawo.” Zaytun ta fita Ameena ma ta yiwa Ammah sallama ta fita ta same shi a zaune ganin ta ya saka ya tashi suka fita tare. Suna fita ana kiran sallah ya kalle ta yace, “zan shiga masallaci kije gani nan.” Ta amsa ta wuce sai da yaga ta shiga gidan sannan ya wuce masallaci. Ita kuma tana shiga sama ta hau tayi wanka ta canja kaya tayi sallah tana tsaye a falo saman sai gashi ya shigo tace, “Yaushe zamu je wancan gidan ne? Akwai abinda nake so zan d’auka.” Ya girgiza kai yace, “ai Mun barshi kenan baza mu saka amfani da komai na cikin sa ba.” Ameena da mamaki tace, “Meyasa to?.” “Babu wani abu na rayuwar baya da zamu  yi amfani dashi yanzu, mu din ma Mun canja dole komai ya canja.” Tayi murmushi tace, “to ka sha magani tunda Kaci abinci.” “Zan sha, amma zo kiji” ya fad’a yana zama ta zauna a kusa dashi ya saka hannu ya zagayo da hannun sa a jikin ta ya kwantar da kansa a kafadar ta yace, “yaushe zaku yi hutu?.” Ameena tace, “mun je hutun mix semester ma yanzu haka.” “Yauwa, gobe nake so zamu tafi Saudia ko jibi muje asibitin nan ayi abinda za’a yi sannan kuma mu gode Allah a can.” Ameena tace, “Allah ya kaimu lafiya.” “Amin. Passport din ki dana Zaytun suna wajena, zan saka Mubakar ya duba mans ticket indai zai yu gobe nake so mu tafi.” Ameena tace, “Allah ya nuna mana goben.” Ya amsa da amin yayi shiru yana jikin ta har lokacin itama bata ce komai ba sai daga baya tace,”baka sha magani ba naji jikin ka da zafi.” “Magani na yana tare dake ai Beb.” “To indai yana tare dani ai ya kamata ace yanzu ka warke, Tunda gani gaka.” Ya d’ago ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa tayi murmushi tace, “kai ka ce a bar komai ya wuce meyasa wani abun yazo ranka yanzu?.” Ya kalle ta yace, “kunyar ki nake ji.” Ta kwanta a jikin sa tana murmushi bata ce komai ba yace, “tunda mun manta da baya mun kalli gaba, muje daga ciki?” Ya fad’a yana kallon fuskar ta suka had’a ido tace, “baka da lafiya.” Kamar mai rad’a yace, “na warke.” Tayi murmushi shima Murmushin yayi yana kallon ta cikin so da qaunar ta a zuciyar da tace, “naji, amma kasha maganin ka.” “Kar ciwon kan ya tashi ya hana wani abun?.” Ta kalle shi jin abinda yace sai tace, “zauna to basai ka sha ba.” Yayi dariya mai sauti yace, “ina sonki Ameena, dashi Allah ya halicce ni dashi zan mutu.” Ta d’ago tana kallon sa shima ita ake kallo yace, “baki yarda ba?.” Ta girgiza kai alamun A’a ya sake yin murmushi ya tashi tsaye ya rik’e hannun ta yace, “zo ki tabbatar.” Ta tashi tana kallon sa tace, “a yanzu ma na tabbatar ai.” Ya girgiza kai yace, “gani ya kori ji, muje ki tabbatar babu b’ata lokaci.” Ta girgiza kai tace, “A’a basai na tabbatar bama na yarda.” “Ai baki isa ba, Tunda kina kokwanto ya kamata ki amince.” Murmushi tayi yaja hannun ta zuwa d’aki tana fatan zaman su ya d’ore haka har abada. Suna shiga d’akin ta kalle shi tace, “Gashi Mun zo, me zan tabbatar?.” Ya matso da ifta jikin sa yace, “son da nake miki.” Ta kwanta a kirjin sa tace, “ai na fad’a maka na tabbatar.” Yayi murmushi yace, “so nake na daina cin alfarmar Ammah na zauna daram babu wanda zai kare ni a zuciyar ki.” Bata ce komai ba ya d’ago ta daga jikin sa yace, “bani da k’arfin guiwar kasancewa dake, zuciyata na so amma in na tuna adadin kwanakin da aka d’auka a wancan lokacin sai naga kamar in ka nemi wani abun a wajan ki bani da hankali. Kiyi hak’uri Ameena, ki yafe min duk sabodake nake shiga wannan Matsalar gashi ana tunanin na samu tab’in kwakwalwa.” Ameena tace, “babu wani Matsalar kwakwalwa da ka samu, ana so a gano inda ciwon yake ne amma ba dan ka samu matsala ba. Kai kace na d’auka komai ya wuce meyasa kake dawo da abinda ya wuce din bayan ni ban dawo dashi ba?.” “Kunyar ki nake ji” ya fad’a voice din sa na shaking ya rik’e ta sosai a jikin sa tace, “ka zama rabo yanzu komai kuka, ko kunyar kukan ma a gabana baka yi, mai arhar hawaye zan dinga ce maka.” Yayi murmushi hawayen suna sauka yace, “na cutar dake Ameena, na zalumce ki, da wani abun ya same ki da ya zanyi da hakkın ki?.” Bata ce komai ba yace, “zan gyara kuskuren, zan goge wancan zan rubuta sabon zaman lafiya a tsakanin mu a farin littafi. Kin bani dama Ameena?.” Ya fad’a yana raba jikin sa da bata yana kallon ta ta daga masa kai alamun eh tace, “amma kar ka cutar Dani, ko yaushe ka zama mai tausayina. Ka daina min fad’a Akan komai, koda an fad’i abu a kaina ka tsaya kayi bincike a kai kafin ka yanke min hukunci.”Ya girgiza kai yace, “har abada, har a tashi duniya ni mai tausayin ki ne. Babu ma wani wanda zai sake fad’a min wata magana a kanki balle na kasa tsayawa na bincika in sha Allah.” Murmushi tayi masa ganin hakan ya saka zuciyar sa farin ciki sosai ya sake mayar da ita jikin da ya rik’e ta gam gam. Ameena tace, “zaka b’alla min k’ashin baya.” Ya sassauta rik’on da yayi mata yana murmushi itama Murmushin tayi yace, “amarya ce ke kin yarda?.” “Zan yarda in ka amince kai ango ne.” Yayi dariya mai sauti yace, “a guje ma.” Dariyar itama tayi zuciyar ta ba sake amsar chanjin sa tana ki a jikin ta baza’a sake maimaita abinda akayi a baya ba.       Washe gari tana tashi kafin ta tashi zaune suka had’a ido dashi yayi murmushi itama haka ta rasa meyasa tun jiya yake kallon ta yana murmushi, ta tashi daga kan gadon tace, “wannan Murmushin na rasa na meye shi tun jiya nake ganin sa.” Ya tashi shima yana kallon ta yace, “na farin ciki ne.”  “Da gaske?.” “Eh mana.” “To a daina kallona ana yi.” Yayi dariya yace, “Yanzu aka fara.” Murmushi tayi itama tace, “.ya kamata naje na had’a breakfast ko?.”  “Yunwa kike ji?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “saboda kai ai kaci abinci ka sha magani amma ni yanzu ai na kai sha biyu ma banci komai ba.” Ya jawo ta jikin sa yace, “to nima haka.” Ta kalle shi tace, “A’a ya kamata Kaci.” Ya girgiza Kai yace, “A’a bazan ci ba., kawai ki dawo ki zauna.” “To nayi ne in na zauna? Ba gwara baje na gyara gidan ba.” Ya ja hannun ta suka zauna yace, “Akwai masu aikin da zasu zo daga gidan Ammah zasu gyara miki ko Ina, nan akwai abinda zaki yi, baki san kewar ki da nake ji ba wallahi bama so kije ko ina.” Ameena tayi dariya tace, “to gani ai, Muna tare a gidan nan ko?.” “So nake mu zauna a nan abincin ma a kawo mana daga gidan Ammah.” Ameena tace, “mu zauna a d’aki kuma babu inda zamu je?.” Ya d’aga kai yace, “haka nake so, indai zan samu hakan ina so.” Ameena tace, “to gani.” “Dana ana saka mutum a zuciyar mutum da naje an bud’e zuciyata an saka ki kawai na huta, kinga dai yanzu gani gaki na rik’e ki ko? Amma wallahi kewar ki nake ji a zuciyata da gangar jikina Ameena. Hakan bai gamsar dani sosai ba, ban san wacce irin soyayya Allah ya dora min a kan ki ba.” Ta shiga jikin sa sosai ta rike shi tace, “to ka saka ayi maka aiki a saka ni a ciki mana.” Yayi murmushi yace, “dama ana yin hakan. Duk da Yaya Adam bazai bari ba.” Tayi dariya ya kalli fuskar ta yace, “Tunda baa’a saka mutum a zuciya amma ana iya yin kusancin da yafi wannan ko?.” Ta gane abinda yake nufi tace, “baka gaji ba? Baka da lafiya fa.” “A bar zancen rashin lafiya, ni ban gaji ba ko kusa ko alama.” “Ni kuma na gaji.” “Zan saka ki d’aure.” Murmushi kawai tayi b’ata ce komai ba yace, “na gode Allah da nine dai Ameena har yanzu itace ni, Allah da wani ya shigar min gona ta Ameena da gaske zan iya haukacewa, a yanzu ma gashi kina ji Ana zancen hoton kwakwalwa ina ga wani ya kusance ki?.” Tayi murmushi tace, “Ameena dai itace kai, Amma kai ba kaine Ameena ba. Kar ka manta kayi aure fa.” Yayi shiru na wani lokacin bai ce komai ba ya kalle ta sai suka had’a ido yace, “ba gode Allah da ya bani ke matsayin Uwar gida a gare ni.”  “Akwai wata amaryar kenan?.” Jin abinda tace sai yayi dariya tace, “har abada.” Ta tab’e baki tace, “Ban yarda ba sai naga abinda gaba zatayi, Nidai koda nan gaba an samu a sanar Dani zan shige gaba wajan sanar da Ammah in sha Allah.” Yusuf ya kalle ta yace, “ki daina wannan maganar dan Allah, a yanzu Yusuf naki ne ke kad’ai har abada.” Ta girgiza kai tace, “bazan yarda ba kawai kayi hak’uri, fatana dai a sanar dani da wuri.” Ya sauke numfashi dan ya kawar da zancen yace, “an bani dama na sake komawa inda zuciyata take marari?.” Tayi murmushi  shima shi yayi yace, “ke daban ce ko a cikin mata Ameena, ni zan tabbatar miki da hakan a yanzu.” Nan ma batayi magana ba dan ta tabbatar da gaske yake babu yadda tayi haka ta zauna ranar a sama babu inda taje, Karb’ar abinci ne da aka kawo daga wajan Ammah ya saka ta sauka shima dan ya fita yaje masallaci ne.  Ranar tayi musu dadi sosai farin ciki ya ninku a zuciyar su sun manta da baya suna kokarin gina gaba farin ciki kawai suke yi da kuma da kula da junan su cikin soyayya da kewar juna. Bayan kwana biyu. Zaman Yusuf da Ameena sai dai ace Alhamdulillah farin ciki da kwanciyar hankali da walwala ta same shi a cikin zaman da suka yi dashi. Duk da farkon auren ne ba zata banbance ba zaman baiyi nisa ba amma kuma Ameena ta amince ta yarda koda gaba baza ta samu matsalar da ta samu a baya ba dan a yanzu yafi sonta akan baya. Yusuf yayi k’iba ya mayar da jikin sa duk da har lokacin bai daina ciwon kan ba amma tunda suka je Saudia abin yayi sauki sosai sai dai yana tashi lokaci zuwa lokaci musamman in ya kasance ya wahala sosai.        Tana zaune akan kujera tana juya takarda a hannun ta ya shigo da sallama ta kalle shi bayan ta amsa yace, “yan boko, karatun ne ya chaja miki kai?.” Ta sauke numfashi tace, “ba karatu bane ba, bama takardar makaranta bace.” Ya zauna kusa da ifa yace, “yo ta meye?.” “Wai asibiti naje shine suka ce min wai ciki ne dani” ta fad’a tana mik’a masa takardar bai karb’a ba ya bita da kallo cikin tsantsar farin ciki ya wara ido yace, “ciki fa Beb, na kwana nawa?.” Tayi dariya kad’an tana rufe ido tace, “komai daidai.” “Kice wallahi?.” Sai tayi dariya tace, “naga shi nan ka karanta.” “Ni daga bakin ki nake so naji, kina so kice wai a ranar Allah ya k’addara samun unborn?.” Ta rufe idanun ta tace, “ka cika maimaita magana wallahi, ni kunya kake bani wallahi.” Yayi dariya ya rik’e ta yana shafa cikin yace, “Allah baki ji farin cikin da nake ji ba kamar babu Zaytun. Yanzu da gaske dai a ranar Allah yayi an samu ciki? Koda yake ranar fa babu inda muka je abu d’aya kawai aka saka a gaba.” Tayi dariya ta kifa fuskar ta a kirjin sa tace, “baka da kunya.” Yayi dariya yana jin farin ciki a zuciyar sa. Kamar zatayi kuka tace, “ni kuma yar jaririyar y’ata nake ji. Nawa take ma da za’a yi mata k’ani?.” Ya harare ta yace, “yarinyar da tana zuwa makarnaya itace jaririya?.” Ta kalle shi tace, “Abin yazo da sauri ne ban yi tunanin hakan ba.” “Rabon kenan” ya fad’a yana mata kiss a kumatu tayi murmushi tace, “fita fa zanyi.”  “Makaranta?.” “Wa yake ta makaranta, jiya Ruky ta haihu yanzu gidan ta zanje.” “Allah Sarki, me ta haifa?.” Ameena tace, “mace ta haifa.” “Allah ya raya.” Ameena ta amsa da amin tace, “ya kamata muje kayi mata barka kaima ko?.” Yace, “eh hakan ya kamata, yanzu muje na sauke ki in zan dawo na d’auke ki sai na shiga mu gaisa ko?.” Ameena tace, “nida kaina zan tafi.” “ai in baki wasa ba kin daina driving kenan Sai kuka kin haihu.” Ameena tace, “Kar ma kace haka dan Allah.” Ya tashi tsaye yace, “ai na ma ce, taso muje.” Ta tashi ta saka mayafi tana kallon sa yace, “harare ni da kyau kin daina.” Tayi dariya suka sakko tare ta shiga motar yana suka tafi gidan Rukayya. A k’ofar gidan Rukayya ya tsaya ta kalle shi tace, “to sai ka dawo?.” Ya zuba mata ido ya jingina da kujera yana kallon ta yace, “a kula min da unborn.” Ta kalle shi alamun ta gaji da maganar yayi dariya ya tashi zaune sosai yace, “Allah sai na hana ki fita na juya.” Tayi dariya tace, “Allah ya baka hak’uri, mai kasan yadda na shiryawa yau din nan kuwa? Su Fidy duk suna ciki bi kawai ake jira.” Yayi murmushi yace, “to jeki, sai munyi waya.” Ta bud’e motar ta fita shi kuma ya juya ya tafi. Tunda suka hango ta ta window suke ihuu ta toshe kunne ta shiga tace, “ku a gidan mutane muke fa, naga alama mai gidan yana nan kuke mana ihu” ta fad’a tana kallon Zakiyya dan itace karfin yi Fiddausi dai na zaune tana  murmushi Ameena tace, “Fiddausi! Kan bala’i haka kika koma?.” dariya tayi tana kallon Ameena tace, “ke bance kinga yadda kuka koma ba sai ni?.”  Ya kalli Zakiyya tace, “ku tsaya, ina Rukayya wai take ma?.” Zakiyya tace, “tana wanka bata fito ba.” Ameena ta zauna ta karb’i babyn a hannun Fiddausi Tana kallon ta tace, “kai ma sha Allah! Wannan baby tabarakallah akwai hanci.” Zakiyya tace, “kamar Rukayya yarinyar mai kyau wallahi kamar na sace” ta fad’a da nata babyn a hannu wanda ya dan yi watanni. Fiddausi dai na zaune tayi shiru bata wani motsin kirki ana haka sai ga Rukayya ta fito Ameena ta bita da kallo tace, “Allah Sarki mar’atussaliha, k’araso ki zauna.” Sai Ameena ta bata dariya gashi bata son yin dariyar saboda an mata d’inki ta k’araso ta zauna Ameena tace, “Sannu Rukayya, Allah ya raya abinda aka samu.” Tayi murmushi murya a hankali tace, “Amin Ameena. Kinga yadda kika yi kyau? Lallai Ana Shan amarci.” Ameena tayi dariya kad’an ta kalli Fiddausi da tayi shiru bata magana tace, “Wai Lafiya kike?.” Fiddausi tayi murmushi kawai Zakiyya tace, “Wai kunyar zuwa gidan nan take yi har yanzu, gashi bata had’u da mai gidan ba tana son bashi hak’uri har yanzu abu ya gagara.” Rukayya ta kalle ta tace, “Yanzu kuwa zai fito nasan zai fita” sai ta kalli Window tace, “ga motsin sa can, kije ki same shi.” Ta kalli Rukayya tace, “kin bada damar Hakan?.” Rukayya tayi tsaki ta kawar da kai kawai hakan ya saka Fiddausi riko hannun Ameena tace, “zo ki raka ni.” Tare suka fita da Ameena a daidai lokacin yana niyar bud’e mota Fiddausi tace, “Assalamu alaikum.” Ya juyo yace, “Wa’alaiki salam.” Ga mamakin su sai suka ga yayi murmushi Ameena tace, “ina kwana.” Yace, “Lafiya lau, ya gida?.” “Lafiya lau walalhi, an samu karuwa Allah ya raya abinda aka haifa yayi mata albarka.” Ibrahim yace, “amin na gode.” Fiddausi ta kasa magana ganin hakan sai Ameena ta tab’a ta sai ta kalli Ameena din alamun baza ta iya magana ba ganin hakan sai Ibrshim yayi murmushi yace, “Fiddausi baki ga Amir din ba?.” Gaban ta ya fad’i damm ta d’ago ta kalle shi sai yayi murmushi yace, “yak’i zuwa makaranta yau yace an yi masa k’anwa bazai je.” Ameena tace, “da gaskiya sa.” Yayi murmushi kawai zai shiga mota tace, “Ibrahim ka yafe min abubuwan da suka faru a baya dan Allah, na kasa tunkarar ka nayi magana amma yau na samu dama saboda fuskar da na gani a wajan ka da matar ka. Ka yafe min kar ka rik’e ni a zuciyar ka.” Ya juyo ya kalle ta yace, “kar ki damu, ki d’auka komai bai faru ba kar komai ya dame ki komai ya wuce. Ni ban rik’e ki a zuciya ba na manta da abinda ya faru.” “Baka ce ka yafe min din ba.” “Na yafe miki, dmaan ba laifi kika yi min ba.” Sai tayi murmushi tace, “na gode.” Baice komai ba ya shiga mota ya fita da baya su kuma suka koma ciki jikin Fiddausi a sanyaye. Rukayya ganin su sai tace, “na fad’a miki shi komai ya wuce kawai kin kasa yarda ne yanzu ai kin yarda.” Ta zauna tace, “yanzu nake jin na dawo sabuwa dal saboda yace ya yace min, hakkin sa nake ji da yake kaina amma yanzu Alhamdulillah. Na gode Ruky.” Tayi dariya Fiddausi ta kalli Ameena tace, “Ameena kinga yadda kika yi kyau kuwa? Anya baki da ciki?.” Tayi murmushi tace, “wata biyu.” Sukayi dariya gabad’aya banda Rukayya da take murmushi kawai Zakiyya tace, “kinji rabon ko? Ke ko wannan rabon abinda aka samu ba dole ma ki komawa Yusuf ba.” Ameena tace, “kunga dai bamu jima sosai da komawa ba amma in zaman mu ya d’ore a haka wallahi yafi na baya dad’i da kwanciyar hankali, domin yadda aka d’auko wannan ma daban da yadda aka d’auki wancan. Sannan a yanzu soyayyar da yake min tafi ta baya yawa nesa ba kusa ba. Ke ni indai haka komawa mijin da aka rabu yake zan iya cewa mata su koma su daina la’akari da baya sun kawar da komai daga ransu watakila silar canjawar su ne ya kawo kaddarar sakin.” Fiddausi tace, “wallahi kuwa. Tsoro da fargaba halin da ka bari shine yake saka mata basa son komawa gidan wanda suka bari, amma wani lokacin in kika koma sai kin fi baya farin ciki domin sun gane kuskuren su. Musamman ma ke Ameena da ya damu sosai akan lamarin ki harda ciwo dasu kwanciya a asibiti, nadamar sa a bayyane take kowa yasan yayi nadama akan abinda yayi dole zaman ku yayi dad’i ynzu.” Zakiyya tace, “Gaskiya ne, Allah ya d’orar da zaman Baku har abada.” Ta amsa da amin tana kallon Fiddausi tace, “wallahi kema Kinyi kyau hasken ki ya dawo sosai, Allah ya kawo mana miji na gari kiyi aure ki huta kema.” Fiddausi tayi murmushi kawai Rukayya tace, “ya kusa zuwa in sha Allah.” Suka amsa gabad’ayan su suka dinga hirs har Rukyyan ta koma daki ta kwanta tayi bacci mai kula da ita kanwar Umma ita kuma yarinyar na hannun ta. Sai dare yamma Fiddausi da Zakiyya suka tafi ita kuma tana zaman jiran Yusuf bai zo ba har ibrshim ya dawo sannan yazo ya shigo har gidan yayi mata barka da abinda aka samu ya bata kudi sannan suka tafi da Ameena. Ranar suna yarinya taci sunan Umman ta ake kiran ta da Noor su Ameena anzo anyi suna tare dasu ko wacce akwai abinda ta kawo matsayin ta ta gudunmawar ta samun noor a matsayin yar su.       Washe garin suna da daddare Rukayya tana zaune a d’aki wacce take kula da ita ganin İbrahim ya dawo sai ta bar d’akin ya shigo ya zauna yana kallon ta da Noor din a hannu yana murmushi ga Amir a gefe ma hana ta tab’a kumatun yarinyar. Kallon Amir yayi yace, “Amir nayi k’anwa ko?.” Yayi dariya dan murna yake yi sosai sai kuma ya fita a guje jin k’anwar Umma tana kiran sa ibrshim ya kalle ta yace, “Habibty bani ita.” Ba musu ta bashi ita yana kallon ta yace, “kin San meyasa nake son ta?.” Ta girgiza kai alamun A’a yace, “saboda tana kama dake sosai.” Tayi murmushi tace, “ni bana gane kamannin jarirai, ka bari ta girma tukunna.”  Yayi murmushi yace, “haihuwar ta tazo mana da alkhairi Habibaty.” Ta kalle shi tace, “meya faru?.” “Mai gidan mu, wanda bai bawa saudia ba su kuma ya saka niyar su zai basu mota amma wanda suke jajircewa a aiki. Ina fad’a miki ya sake saka sunana  ga mota can sabuwa dal a ajjiye a waje.” Rukayya ta wara ido tace, “da gaske kake wai?.” Ya d’aga kai yace, “da gaske nake wallahi, kinga ma key din” ya fad’a yana nuna mata makullin tace, “wannan bawan Allah wanne irin so yake maka Khalil? Ka duba kayan da ya baka aka kawowa Noor.” Yayi murmushi yace, “in ka rik’e gaskiya a duk inda kake sai Kaga abinda zai same ka. Yana sona sosai shiyasa na tara makiya a wajan kowa baya sona, hatta baban yaron sa a da yanzu yafi ji dani akan sa. Ana ta cewa asiri nake yi basu san ni addu’ar iyaye ce take d’awainiya dani ba.” Rukayya tace, “kar ka wani damu da wannan daman dole a samu makiya duk inda cigaba yake sai an samu masu bak’in ciki. Allah yana tare dakai babu abinda zai iya yi.” “Ki cigaba da taya ni addu’a basa sona a tare dashi zasu iya yin komai dan su raba mu.” “Allah ya fisu wallahi.” “Bayan motar fa yace min in kin yi kwari zamu tattara mu koma Abuja inda babban kamfanin sa yake ya kuma ya bar min ragamar kamfanin gabad’aya Rukayya. Ni na rasa me zan yiwa bawan Allah nan da zan nuna amsa na gode da abubuwan da yake min ba walalhi.” “Addu’a zaka masa Khalil bayan wannan bamu da abinda zamu biya shi.” Ya girgiza kai yace, “Gaskiya be wannan. Yanzu ga sabuwar mota can zaki iya zuwa ki gani?.” Ta kalle shi cikin farin ciki tace, “zan iya mana.” Yayi murmushi yace, “to ki zauna dai Kya gani gobe dare yayi gobe.” Sai murmushi yaga Tana yi yace, “ya kike ganin za’a yi da tsohuwar?.” Ya kalle shi tace, “ka siyar mana kawai.” “Bayarwa nake son nayi, yadda aka bani nayi murna nima na bayar.” “To ka bawa Alhaji mana kawai.” Yayi dariya yana jin dad’in yadda komai na alkhairi iyayen sa take fara sakawa kafin kanta hakan yana k’ara mata matsayi sosai a zuciyar sa yana kuma saka shi farin ciki girman ta na sake yin sama a idanun da yace, “ban da Alhaji.” Tace, “to wa zaka bawa?.” “Ke bakya so?.” Ta kalle shi jin abinda yace tace, “ina so mana. Amma ni ban iya ba ai Alhaji shi ya kamata a bawa bank ba.” Ya bud’e hannun ta ya saka mata muku kin motar yace, “nima ban iya ba koya min akayi. Rukayya ke na barwa halak malak, makarantar koya kawai ta zaki shiga ki koya ki fara tuk’awa kina zuwa duk inda zaki je.” Rukayya ta rasa abinda zata ce ta gigice saboda farin ciki zatayi magana yace, “kar kice komai Rukayya, nasan kin gode Kinyi farin ciki, iya ganin farın cikin naki yafi min komai.” Sai ta saka kuka ya kwantar da noor agefe ya runtgume ta yana cewa, “meye na kukan kuma? Kin cancanci kyautar ne, in ina da duniya zan iya mallaka miki domin kin cancanci koma meye daga wajena. Ki daina kuka kinji?.” Ta rik’e shi sosai tana kuka tace, “na gode Khalil, Allah ya k’ara bud’a maka ya kare ka daga dukkan sharrin mak’iya.” Ya amsa da amin yana cigaba da rarrashin ta domin shi a duniya indai zai samu goma to zai d’auki biyar ya bata biyar, haka d’abi’ar sa take sai kuma ya samu mace ta gari mai sake d’ora shi akan hanyar alkhairi shiyasa yake son kyautata mata a ko yaushe indai zatayi farin ciki shine burin sa. #Mai daki #Nana Haleema #Book3 Book3 043          Umma ce zaune sa a gaban Baba tana jira ya gama cin abinci ta gabatar masa da abinda tazo dashi ya kalle ta yace, "kin zo kinyi shiru ki fad'a min abinda yake tafe dake. Lafiya kika saka ni a gaba kina kallo?." Umma tace, "daman akan maganar yaran nan ne, Maimuna, Fauziyya, Asiya ga Momi dukkan su suna zaune babu mazajen nema. Su biyun can ma zawara ne a ajjiye batun su, amma Fauziyya da Momi sune y’an mata har yanzu babu wani wanda yake zuwa wajan su. Wallahi abin nan dashi nake kwana nake dashi dan Alalh malam ka taimaka." Baba ya girgiza Kai cikin mamaki yace, "Atika yau ni kika samu kina yiwa maganar da ta shafi yaran ki? Kamar ke kika ce babu ruwa na ko wando ban tab'a basu ba ke kike da iko dasu ko?." "Malam a daina tuna baya dan Allah, yanzu muyi abinda yake gaban mu kawai. Nace cikin wanda suka ce suna son su a dangin ku a lalubo su su zo ayi auren a rufawa juna asiri." Baba yayi dariya yace, "inaaa wane mutum! Ai y'ay'an ki ba kalar dangina bane ba su, sun fi karfin dangina da basu ajjiye ko sisi a banki ba, yaran ki ai ba tsaran auren su bane, ki bari su samu daidai su su aura amma banda naki." Umma tayi shiru kafin tace, "Malam duk maganar nan ta wuce bai kamata ace anyi ta ba, dan Allah a bar zancen nan ayi abinda ya kamata. Momi ce k'arama a cikin su ita kanta ta haura shekara ashirin balle su. Dan Allah a san abinda za'ayi." "Baki ji me nace miki bane? Yaran ki ba daidai suke da auren wanda kike magana Akan su ba, dan haka ki bari daidai su suzo sai ayi magana ta auren su amma banda dangina. Nan na same ku akan mai son Maimuna kika yi tsallake kika dire kika ce baza’a yi ba ba wani a duniya da ya isa ya aurar miki da yara, a lokacin kaina a jure yake ban cika gane daidai ba sai Allah yayi ni kuma na kyale ki, amma in da yanzu ne ke kin isa? Ba sai dai ki bar gidan nan ba wallahi.” Umma tace, "a bar batun baya dan Allah malam." "Ke kika sani kuma, kin yiwa yaran tarbiyar da ke kanki yanzu gagarar ki suke balle kuma wasu. Kije kiji dasu babu abinda ya shafe ni wallahi komai ya faru ke kika jawowa kanki. Asiya ke kika kashe mata aure dan da baki dinga d'ora ta akan turbar da kika dora ta ba da yanzu tana Idan mijin ta. kud'i ake nema a yiwa Asiya waya, abinci Asiya waya, kayan sawa Asiya, komai ita gashi sai da kika b'alla auren hankalin ki ya kwanta. Babu ruwana da lamarin ku wallahi kije can ku k'arata" ya fad'a hana tashi ya bata wajan Umma ta d’ora hannu aka ya bata san ya zatayi da yaran ba gashi tashen rashin kunya suke ji da ita ko ita din ba kyale ga sukayi ba balle wani daban. Fitowa Umma tayi taga Asiya a tsaye ita da Maimuna  Umma ta kalle su dan tasan fad'an ake tab'awa Maimuna Tce, "Umma ki yiwa yarinyar nan magana a ko yaushe burin ta muyi dambe a gidan nan, ta raina ni gabad'aya ki Tuna mata akwai Fauziyya kafin ita." Asiya tace, "ni ina ruwana? Ko mata dubu ne kafin ni akayi min sai na mayarwa da mutum. Kar a sake cemin b'arauniya kuma dan ba'a ajjiye na d'auka ba." Umma kallon Asiya take yi tace, "Ai dole ne ma Yusuf ya sako wannan rashin tarbiyyar da kike yi shi kika nuna masa." "Ai koya min akayi, da ba'a koya ba ban yi ba" ta fad'a bata kalli Umman ba sai kuma ta fara hawaye tace, "Wayyo Allah, bani da aure bani da mai sona ya zanyi ni Asiya?." Fauziyya tace, "Da wannan shegiyar k'azantar taki waye zai d'auke ki?." Asiya bata kula ta ba ta zauna a k'asa tayi shiru kawai Tana hawaye in ta tuni bata a da aure sai taji gabad'aya yanayin ta ya canja komai taji yana yi mata zafi musamman in ta tuna gıda da ta baro. Fauziyya tace, "ke shegen halin ki shine ya saka ya sako ki ai." "Akwai Wanda ya tab'a ce min na canja na daina ne a cikin ku? Akwai Wanda ya tab'a min fad'a akanabinda nake yi?. Umma ce min take in ya dake ni na rama, ta tab'a cemin ki daina yin abinda kike yi an tab'a fad'a min ne?." Maimuna tace, "sau nawa ina yi miki magana akan k'azanta?." "Bayan wannan kin tab'a cemin ga wanda zan daina?." Maimuna tayi shiru bata amsa ba ta kalli Umma tace, "Komai na gidan a kaina yake, ba'a tab'a cemin kar na d'auko na kawo ba Kullum cikin zuga ni kuke yi Ana cewa na nuna masa ina da y'anci. Ko yaushe maganar ku Kenan ba'a tab'a cemin abinda kike yi ba daidai bane. Sai yanzu dan a sake ni sai a dinga min ce dole ma ya sake ni saboda halayya ta?tun baya meyasa ba’a ce kin nan gab zai iya saki na saboda su ba?." Baba da yake ji yace, "Yauwa Asiya tambayi babar ki ta baki amsa. Tun farkon auren ku na tabbatar mata da alkhairin auren ragagge ne amma tace ita  ina sai kin je ko me zai faru. Ki bata amsa Atika kin tab’a cewa ta daina yiwa mijin ta rashin kunya?." Umma tayi shiru bata amsa ba ya kalle ta yace, "Yanzu kika fara ganin abubuwan da kika aikata ai, ke kina ganin ke kike komai a gidan nan ban isa nayi magana ba saboda karayar arzukin da na samu. Kika sake amfani da malama  ki kika mallake ni babu abinda na isa  nace koda akan yaran nan ne, to yanzu gasu nan na bar miki du ai sai ki basu tarbiyyar Dani bazan basu ba." Fauziyya tace, "ina tarbiyyar Baba? Kowa gudun auren mu yake saboda bamu da tarbiyya, kuma nima na yarda domin Umma bata tab’a cewa mu girmama na gaba ba, ko yaushe cewa take duk Wanda yayi mana kar mu kyale shi. Koda a dangin kane cewa take yi basa sonta mu ma kar mu so su, Mun Raina komai babu Wanda yake son mu ko shiga muka yi babu mai kallon mu muma haka.” Baba yace, "ku kuma da yake ilimin addini bai ishe ku ba komai tace muku aikatawa kuke yi, bakwa koyi da k’awaye da y'an uwan ku duk abinda tace ku yi shi kuke yi koda bashi da kyau babu wacce ta tab'a cewa hakan ba daidai bane. Dukkan ku yanzu kuka fara gani ai, za Kuyi dana sani daidai abinda kuka aikata a rayuwar ku." Ya kalli Umma yace, "badan yaran nan da nake kallo ba wallahil azim da yanzu bakya gidan nan, to shekaru sun ja ko babu komai na duba yaran suna son kasancewa dake wallahi da sai kin bar gidan nan." "Baba ta bari din kawai, ko zamu samu mu canja daga halayyar da muke yi. Tasan ana ajjiyewa na d'auka amma bata tab'a yi min fad'a ba tun kafin aure, in Kaga tayi min fad'a tabbas nata na d'auka amma in daga waje ne sai kaji tana ki dai kula kar a kama ki wata rana. Nidai gabad'aya cutar rayuwata akayi, nafi kowa cutuwa a cikin su” Asiya ta fad'a tana cigaba da kuka abinda yake zuciyar ta bai wuce gidan mijin ta Yusuf ba. Baba yace, "to ai sai kuje ku cigaba da asirin ki sake komawa gidan nasa, dmaan auren ai ba na Allah da annabi bane, a gina shi akan turbar mallaka da kuma samun arzuki. Sai kuje a cigaba daga inda aka taaya ko za’a samu ya mayar dake" baba ya fad'a yana fita ya barsu Asiya ta kalli Umma dukkan su ma kallon ta suke yi ta rasa abinda zata ce musu sai ta shiga d'aki kawai tana kukan zuci.          Rukayya tana tare da mijin ta yana rik'e da Noor a hannun sa ita kuma tana gefen sa tana kallon sa, yana kula da ita sai yayi mata banza dan yaga magana ce a bakin ta sai yayi shiru kamar bai fahimta ba yace, "Noor kullum kyaunta sake bayyana yake, ma sha Allah har tafi Amir kyau." Sai kuwa Rukayya tace, "ai kuwa bata fi Amir kyau ba saboda mahaifiyar Amir ta fini kyau kuma da ita yake kama." Yayi murmushi yace, "nidai ban gani ba." "Wallahi ka gani" ta fad'a tana kallon sa ya sake yin murmushi yace, "harda wallahi?.” Bata bashi amsa ba sai Murmushin da tayi tace, "ni daman magana nake so muyi da kai." Ya kalle ta yace, "tunda naga bakin ki yana motsi nasan akwai abinda zaki ce, to Ina jin ki." Tayi y'ar dariya tace, "shiyasa ka k’i kallona ai, nima na gane." Kafin yayi magana tace, "Ka yafewa Fiddausi ko?." Ya lumshe ido ya bud’e yana kallon ta daman ai tatsuniyar gizo bata wuce ta k’ok’i yace, "Eh mana, bata fad'a miki munyi magana da ita ba?" Ya fad'a ba tare da ya kalle ya ba yana yiwa babyn wasa. Ta girgiza kai tace, "Ta fad'a min. To Khalil tunda da gaske ka yafe mata meyasa baza ka dawo da ita gidan nan matsayin matar ka ba?." Da sauri ya kalli Rukayya ya wara idanun sa yaga da gaske fa itace tayi maganar ba wani ba yace, "Rukayya kin San abinda kike fad'a kuwa?." Ta girgiza kai tace, "na sani, so nake ka dawo da Fiddausi gidan nan matsayin matar ka tunda daman ai saki d'aya ne akayi mata shima kuma na gargad'i." Girgiza kai yake yi yana kallon ta cike da mamakin abinda take cewa wanda a wajan sa bazai yu ba kafin yayi magana tace, "ka ajjiye batun kishi a gefe Khalil, matar nan tun kafin na fara kishin ka itace take kishin ka domin itace matar ka ta farko kafin na sanka itace ta sanka." Sai yayi dariya yace, "ke yanzu a ina zan saka Fiddausi? Ai bani da wannan wajan." Jin abinda yace sai tace, "Ba ga sabon gidan da ka siya ba, daman y’an haya kace min zaka saka to me zai hana ba zaka saka ta a gidan ba?." Ya kalli Rukayya yace, "ai yayi mata kad'an." "Kamar ya yayi mata kad'an?." "Ba irin sa take mafarkin samu ba." Rukayya ta gane me yake nufi ya sassauta murya tace, "tayi nadama baza ta sake aikata abinda tayi a baya ba." Ya dakatar da ita yace, "kafin mu d’ora daga labarin da kike bani tsaya na baki wani labari tun jiya nake son fad'a miki sai na manta. Akwai wata y'ar Uwar Hajiya to yarta cousin dina kenan yarinyar ma sha Allah tana dakyau dan mahaifin ta yan sudan ne kika ganta dai kice bata jin Hausa. Tayi aure tana zaune a gidan mijin ta iftila'in wata annoba ya same ta a fuskar ta, kuraje masu ruwa duk suka fito mata a fuskar ta lalace ta zama kamar dodo in kika ganta. Kwatsam wannan mijin nata ya fara yi mata rashin mutumi dan so yake ya sake ta amma ya rasa taya zai yi hakan, zagi, cin mutunci har gaban iyayen ta fa kawai saboda yana son ya sake ta. K'arshe dai ya samu ya rabu da k'aya ya sake ta dan yace bazai iya zama da mai annoba ba. Ana tayi mata magani ba dare babu rana sai ciwo ya warke ya tafi gabad'aya tabo d’aya babu a fuskar ta sai ma sake kyau da tayi, yanzu zancen da nake miki mijin nan ya dawo dan Allah a bashi matar yayi kuskure bazai sake ba, ke in ke ce matsayin ta zaki koma dan Allah?." Rukayya da take girgiza kai  cikin masifa tace, "kan Bala'i! Me zai kaini komawa? Ai wannan ba dan Allah yake sonta ba dan kyau ne, gashi lokacin da ya gushe ya koro ta yanzu kuma da ya dawo ya sake dawowa dan bashi da kunya bashi da mutunci. Ka bata shawara kar ta koma wallahi ba don Allah yake son ta, dan wani abun da yake dashi ne in ya sake gushewa zai kuma sakin tane." Ibrahim yayi murmushi mai sauti ya kalle ya yace, "daman ai bazata koma ba." "Wannan shine daidai, ta samu wani wanda zai so ta Tsakani da Allah ta aura." "Ta samu ma." "Shikenan Alalh ya basu zaman Lafiya." Ya kalle ta yace, "Amin. Kinga wannan labarin dana baki?; ina so ki juya shi ya koma kan Fiddausi." Ta kalle shi yace, "Fiddausi ta guje ni saboda bani da kud’i, ni talaka ne bani da mota, bani da keke, zaman gıda babu haske, kullum bazata ci kaji ba, baza ta zauna a a.c ba, babun dai ta wajena tana da yawa. Wannan dalilin ya saka ta dinga rashin mutuncin da har a gaban su Hajiya bata raga min ba, idanun su Hajiya ta kalla tace bata sona bata qauanr zama dani aka tilasta mata sai ta kashe ni. Me nake dashi da zan dawo da ita Rukayya? Haka akwai na dawo da ita wata ran ta kashe ni bayan ina da mata da iyaye da yaran da suke bukatar kulawa ta?." Jikin Ruky yayi sanyi sosai ta kalle shi tace, "Amma Fiddausi tayi nadama walalhi, abinda tayi a baya duk yayi danasani." "Duk ta banza ce sai da tasha wahala sannan tayi, ke yanzu kika ce min wanna labarin da na baki ba dan Allah yake sonta ba,  Nima Indai na dawo da ita ta zauna ba dan Allah take sona ba wallahi. Da zarar abinda na samu ya k'are zata sake guduwa ne saboda ita ba kalar zama da irin İbrahim baca, kalar matar manya ce kiyi mata fatan Allah ya bata manyan amma ba irin ibrahim ba.” Rukayya zatayi magana ya dakatar da ita yace, "na fiki sanin halin ta, kar kice min komai abinda kike fad'a ba abu bane wanda zai yu. Na yafe mata duk kuskuren da tayi saboda d'anta Amir da kuma mahaifin ta, amma bayan wannan babu wani abu da zai sake had'a ni da ita." Rukayya tace, "kodan saboda Amir din zaka dawo da ita, itace ta haife shi amma bai saba da ita sosai ba, akwai ciwo ace ka haifo yaro kuma bai shak'u da kai ba Khalil, dan Allah ka San abinda zakayi." "Amir ai d'an tane tana da ikon zuwa ta d'auke shi yayi kwanaki a wajan ta ko yaushe, bar mata shine ko zata mutu ta dawo bata isa ba wallahi. İn zamu koma Abuja ma zai zauna a hannun ta kafin muje muga ya yanayin garin da makarantar da za'a sake shi ya koma." Rukayya ta kalle shi kafin tayi magana yace, "kar ki sake wahalar da kanki bazai yu ba, Alhaji ma yayi min maganar saboda rashin mahimmacin ta ya saka ban miki maganar bama na share." "Tunda har Alhaji yayi maka magana akwai dacewar ka dawo da ita din." "To bazan yi ba. Ni Wallahi kin ma bani mamaki, duk soyayyar da kike nuna min ashe daman zaki iya kawo min tallan wata kice na aura?. Kishin ashe duk na banza ne babu inda yaje." Tayi murmushi tace, "to kishin me zanyi bayan Fiddausi itace ka fara aura kafin ni? Har kawo gobe kuma kana sonta kawai abinda tayi maka ne yake yawo a zuciyar ka amma soyayyar ta da wahala ta bar zuciyar ka.” Ya kalle ta yana tab'e fuska yace, “haka nace miki?." Tace, "hakan ne ma, kar ka manta mu ne yan tayin hira kai da ita, mun san adadin soyayyar da kake mata, ko ni ka kalla ka fad'awa kana son ‘kawa ta son da baka San Adadin sa ba. Duk wata soyayyar ku mun sani saboda ta kasance ta farko a cikin mu da ta fara aure duk wani labarin soyayya a bakin ta muke ji, kana sonta itama tana  sonka, domin dukkan ku akan juna kuka fara sanin meye so har ta kai ku ga aure, meyasa baza ka kawar da haushin ta da kake ji ka juyo da soyayyar ka mayar da ita ba?." Kallon ya yake kawai baice komai ba ta d’ora hannun ta a k’irjin sa daidai zuciyar sa tace, "Akwai Fiddausi a nan, haushi ne ya saka kake ganin kamar babu ita amma da zaka manta da b'acin ran tabbas zaka gano tana nan daram Rukayya sai dai ta biye mata baya. Domin Fiddausi ce ta fara shiga cikin nan kafin Rukayya. Kayi tunani Khalil ba dan ita zakayi ba dan mahaifinta da ya tsaya akan aurena da kai, dan kuma d'anta Amir da take bukatar sa a kusa da ita. Kayi tunani, kayi tunani zaka gano dacewar abinda nake fad’a.” ta fad'a tana d'auke hannun tana sake mayarwa kamar tana dukan wajan. Zata d’auke hannun gabad'aya ya rik'e ya kalle ta yace, "babu ko wacce mace a zuciyar nan in ba ke ba, a baya wacce kike magana ta zauna a cikin ta amma a yanzu babu koda b'urb'ushin ta a ciki kin saka tsintsiya kin share kin kuma goge ko ina kyallin ki ne kawai a cikin sa. Ki daina tunanin ina son Fiddausi har gobe domin kuwa yaudarar kanki kike wallahi, indai kika ce ni Ibrshim ina son wata halitta Fiddausi kinyi karya kin kwana da yunwa domin kuwa in ba zance ta akayi ba mantawa nake da ita wallahi. sannan ki nutsu a bar zancen haka tun bai b'ata min rai ba kar yazo ya b'ata min rai. An kuma nuna min iyakar matsayin da nake dashi tunda har zaki iya yi min tallah wata mace kice na aure ta." Kallon sa take yi har ya gama maganar tace, "ka sake yin tunani dan ka dawo da ita zai iya zama alkhairi a rayuwar ka. Ka duba Ameena ta koma gidan Yusuf zaman yanzu yafi mata zaman baya dadi da farin ciki, meyasa kaima baza ka hango hakan ba?." "Bazai tab'a zama alkhairi ba, sanda nake tare da ita k'ofar wahala ce a bud'e a tare dani, daga lokacin da akace bata nan k'ofar wahala ta kulle k'ofar alkhairi ta bud'e a rayuwata. Komai yana da sila silar duk abinda nake dashi a yanzu kece silar sa, dan haka kar ki sake yi min maganar a barta a wajan nan a hak'a rami a binne ta in dai bakya son b'acin raina." Zatayi magana yace, "nace a bar maganar, bana son ta, a ajjiye ta har abada kar a sake dawo da ita. In ba haka ba kuma raine zai zo ya b’aci.” Jin yadda yayi maganar sai ta sauke numfashi tace, "Inda rabo Allah ya daidai." Murmushi yayi wanda bai shirya ba wato baza ta bar maganar ba kenan ya girgiza kai baice komai ba. Noor ce tashi ta fara kuka ta d'auke ta ya tashi ya kalle ta yace, "in kika cike kwana arba'in zamu tafi Abuja gida da komai akwai a can. Ki fara shiryawa tun yanzu saboda gudun mantuwa" yana fad'a ya fita ya barta tayi ajiyar zuciya har zuciyar tana so ya dawo da Fiddausi amma taga alama bazai yi hakan ba dole ta kama kanta.          Fiddausi da Zakiyya suna gidan Ameena suna hira cikin nishadi suna ta darıya Ameena tace, "yanzu Fiddausi zawara suna ta zuwa ko?." Fiddausi tayi murmushi tace, "Eh to babu laifi zance, akwai mutum biyu yanzu da  suka fito suna so." Ameena ta sauke numfashi tace, "ni wallahi gidan Ibrahim nake so ki koma kamar yadda na dawo hannun Yusuf." Fiddausi ya wara idanu tace, "Ibrahim fa kika ce Ameena?." Zakiyya tace, "Ai bata san abinda aka aikata masa bane shiyasa take cewa haka." "Ko mai aka aikata ai gani ai a gidan Yusuf na dawo duk abinda yayi min." "Ai ke ba kece kike yi kuskuren ba shine, kuna kuskuren Fiddausi yafi na Yusuf wallahi. Kinga dai ban san abubuwan da suka faru tsakanin ku ba ko? Amma wallahi na tabbatar laifin ta yafi na yuusf." Fiddausi tace, "fad'a mata dai, ni bana kawo hakan a zuciyata Allah ma ya sani." Ameena tace, "tunda aka yafewa Yusuf to meye in an yafe miki? Kodan saboda Amir ai ya kamata yayi duba akan dawo dake." Fiddausi tace, "magana kike akan abinda bazai yu ba, kuma koda zai yu ni bazzan auri mijin Rukayya ba.” Ameena tace, "wannan duk ba abin dubawa bane, abinda ya kamata ayi shi ya dace ayi wanda  ya kamata a bari shi ya kamata a bari. Rukayya tafi kowa son ya mayar dake wallahi, ko jiya sai da mukayi waya da ita akan hakan ta tabbatar min da zata same shi da maganar ko meye zai faru."  Fiddausi zatayi magana wayar Ameena tayi  k'ara ta kalle su tace, "yar halak" ta d'auka ta saka speaker daga can b'angaren Rukayya tace, "Ameena munyi maganar dashi fitar sa kenan yanzu na kira ki." Ameena ta kalle su tace, "ya ake ciki?." "Ameena da muna zancen da wasa da dariya na d'auka abin zai zo da sauk’i amma ya tirje yace na sake masa maganar ma sai raina ya b'aci. Dan Allah meye laifin Fiddausi da bazai dawo da ita kodan saboda mahaifin ta da kuma Amir ba?. Abba shine ya bada gudunmawa da goyan baya wajan aurena dashi, indai ana cin albarkacin wasu meyasa ita baza tacı albarka sa ba?." Ameena ta sauke numfashi tace, "to ke yanzu ya kuka yi?." "Yak'i fa, wai wanda ya guje ka lokacin da baka dashi yanzu da ka samu abinda ka samu in ya dawo ka sake karb’ar sa nan gaba ka sake rasa abinda ka samu zai sake gudun kane. Kuma shi wai baya ma tunanin dawo da ita yana kallon ta matsayin k’awa ta kuma babar Amir. Kuma kin san Allah baza'a rasa soyayyar ta a zuciyar sa ba, ke shaida ce ya so Fiddausi. Ni wallahi gabad'aya raina ya b'aci." Fiddausi da take jin abinda yake cewa ta goge idanun ta tana farin cikin samun kawaye na gari da tayi tace, "Rukayya kar ki b’atawa mijin ki rai saboda ni, kar ki lalata zamantakewar ku saboda na tabbatar Ibrahim bazai sake kallona matsayin matar sa ba nima bazan kuma kallon sa a matsayin mijina ba sai dai mijin Rukayya. Ki bar maganar nan akwai Ruky Amir yana da uwar da ta fini gaki nan, kawai ku taya ni addu'a Allah yayi min zab’i mafi alkhairi." Rukayya da take jin abinda take cewa, "Fiddausi bazan daina ba, yanzu kuma na fara sai inda karfina ya kare akan dawo dake. Kina son kasancewa da yaron ki meyasa baza ki amince ba?.” "Bazai tab'a dawo dani ba wallahi, wallahi Ibrahim bazai saurare ki ba kin san halin mijin ki. Ki daina wahalar da kanki da bakin ki domin abinda kike nema baza ki samu ba. Ke koda zai amince ni wallahil azim bazan amince na auri mijin ki ba.” "Mtsww! Zancen kike so" ta fad'a yana yanke wayar Ameena tayi dariya tace, "Rukayya ta matsa akan komawar ki, ni har mamaki ma take bani Rukayya mai kishin tsiya amma itace ta tsaya kai da fata akan sai ya dawo dake?, ko da yake tace wai kishin me zatayi ai ke kika fara auren sa.” Zakiyya tayi murmushi tace, "kyakykyawar zuciyar kenan tana kuma so mata abinda yake sowa a kanta. Duk Wanda ya same ku matsayin kawaye ya gode Allah." Fiddausi tace, "ku fad’a mata ta daina b’atawa mijin ta rai akan hakan, ta daina maganata kar hakan ya kawo sab'ani tsakanin su dan wallahi bazan ma koma ba ni.” Ameena tace, "kedai ki jira muga me Allah zaiyi." "Bafa zan koma ba nima wallahi, ko ya amince bazan amince ba. Balle ma bazai amince ba domin ban cancanci ya sake kallona matsayin mata ba, nayi rashi na har abada, dan babu lallai na sake samun miji kamar sa. Asarar da nayi bazan mayar da ita ba.” "Harda wallahi baza ki koma ba Fidy?.” "Kin ji abinda nace ashe." Ameena ta tab'e baki bata ce komai ba kafin su canja hira zuwa wata hirar daban. #Mai daki #Nana Haleema #Book3 #paid #500 Book3 044        Suna zaune suna hira aka kira Ameena a waya ta d’auka ganin mai kiran sai tayi murmushi ta saka a kunne tace, “Yaya Al’ameen ka manta dani, ba waya balle kazo kace zaka ganni.” Shiru tayi alamun yana bata amsa sai tace, “da gaske? To bara na tura maka” ta fad’a tana  kashe wayar ta kalle su tace, “Bak’o zanyi yanzu” ta fad’a tana danna wayar. Fiddausi tace, “Sai mu tafi daman aimın  jima a gidan.” Zakiyya tace, “nima ina da abin yi” ta fad’a suna tashi suka fito tare har harabar gidan suna hira Zakiyya tace, “wannan gidan naki ya yafi wancan kyau nesa ba kusa ba wallahi, ni kullum sabo yake zamar min.” Tayi dariya tace, “Ni kuma nafi son wancan.” Wayar ta aka kira tace, “to ga Yayana yazo ku jira ku gaisa sai ku tafi” ta fad’a tana d’aukar wayar ta nufi bakin gate din ta yiwa mai gadin magana sai gashi an bud’e Al’Ameen ya shigo. Dariya tayi da ta ganshi tace, “Yaya Al’Ameen barka da zuwa.” Yayi murmushi shima ya saka waya aljihu yace, “ba wani baraka da zuwa, ko waya kice yau kin tunda da Yayan ki baki tab’a yi ba, ai nayi kokari ma da na shigo mu gaisa” ya fad’a suna tafiya daidai lokacin da suka zo wajan su Zakiyya. Tayi dariya tace, “nayi laifi babba amma a yafe ni” ta kalle shi tace, “Yaya Al’Ameen ga k’awayena, Zakiyya da Fiddausi.” Fiddausi ta fara gaishe shi ya amsa Zakiyya har ta shiga mota ta fito ta gaishe gashi ya amsa da murmushi Ameena tace, “To Fidy sai nazo gidan, Zakiyya a gaishe da Fahad. Ke kuma Fiddausi kafin nazo naji labari mai dad’i” Fiddausi tayi dariya tace, “to amaryar Yusuf.” “Ke kuma ta Ibrahim.” “Rufa min asiri kar Rukayya ta bindige ni” sukayi dariya tare ta shiga mota suka tafi ita kuma ta kalli Al’Ameen tace, “Yaya muje ciki ka sha ruwa.”  “A’a ni daman zuwa nayi na ganki kuma na ganki, gaki nan lafiya lau dake baki da damuwa to me zan shiga nayi kuma?.” Ameena tace, “Haba  dan Alalh yanzu sai kazo ka koma baka shiga ba? Dan Allah ka shiga ko ruwa ka sha.” Babu yadda zaiyi haka ya shiga falon ya zauna ta kawo masa ruwa da lemo harda su kayan zak’i da bata rabo dasu. Yasha ruwan yana kallon ta yace, “na sha ruwa. Amma wannan cake din da cincin din nan ayi min packaging na tafi dashi.” Tayi dariya ta shiga ciki ta d’auko pack ta zuba masa ta zauna tace, “wancan satın Yaya Adam ma yazo kwanan sa d’aya ya koma.” Al’ameen yace, “Haka yace min yazo ya ganki ya koma.” Tayi murmushi b’ata ce komai ba yace, “baki da wata damuwa dai ko?.” Ta girgiza kai tace, “Babu komai Yaya.” “Kin tabbata? Kar Kiyi min karya fa.” “Allah babu komai Yaya.” Yayi murmushi yace, “haka muke fata. Wannan k’awayen naki kamar na san su.” Ameena tace, “ka san su mana, Fiddausi ce fa ta gidan Alhaji  Mustapha k’anwar su Zahra’u. Sai Zakiyya ta gidan Malam Mamman.” Al’ameen yace, “ohh! Na gane Fiddausin, ita Zahra’un itace mate din mu duk kusan tare aka tashi. İkon Allah duk kun girma ko wacce tana da y’ay’a.” Ameena tayi dariya tace, “Eh wallahi ko wacce mu tana da aure da yara. Fiddausin ce ma bata da aure sun rabu da mijin ta.” Al’ameen yace, “Alalh Sarki. To ni zan koma sai na sake shigowa sai mu gaisa.” Ta taka shi har bakin gate sannan ta dawo.        Babu jimawa da tafiyar sakawa yi sallar magriba tayi alwala tayi sallah sai a lokacin ta manya batayi girki ba ta hau saka tayi wanka ta sakko da niyar gkiki Yusuf ya dawo. Yana shigo falon kallon ta yayi yace, “bani abinci Yunwa nake ji sosai.” Ameena ta kalle shi tace, “Wallahi banyi girki ba, amma bara nayi maka yanzu.” “A’a barshi kawai, bazan iya zama har a girka ba zanje wajan Ammah” ya fad’a yana fita ya bashi da kallo duk sai taji babu dad’i a zuciyar ta. Bata ma yi girkin ba tana zaune aka yi sallah tayi sallah ta zaune a falon ya dawo shida Zaytun ya zauna ya kalle ta kamar zai mata magana sai ya share aka kira shi a waya yana amsawa. Tashi tayi ta hau saman bai tashi ba sai da ya gama duk abinda zaiyi suna zaune da Zaytun ganin shiru bata sakko ba gashi dare yayi sai ya kashe komai na falon ya hau saman da Zaytun da ta fara bacci. D’akin ta ya shiga ya sake ta a zaune ya kwantar da Zaytun a kan gadon ya kalle ta yaga kamar bata ganshi ba abin ya bashi mamaki sosai bai ce mata komai ba ya fita ya d’suke kai daga kallon ta yayi kwanciyar sa. A haka suka kwana da safe ya shirya zai fita ya sakko ya sake ta ta shirya zata tafi makaranta ganin sa tace, “Ina kwana.” “Lafiya lau, ina abincin?.” “Ban yi ba.” Ya kalle ta yace, “baki yi ba kika ce?. Zaytun ba taje makaranta ba da kika yi Kaga meyasa baki had’a ba?.” “Nata akwai nan girka ai.” Ya girgiza kai yace, “shikenan babu laifi.” Ya fad’a yana fita itama ta fita ta tafi makaranta. Gabad’aya zuciyar sa babu dai haka ya zauna bai dawo ba sai yamma lokacin da ya shigo ya dawo Zaytun na homework tana ganin sa ta taso tana masa oyoyo ya rik’e ta suka shiga ciki tace, “Sannu da zuwa.” “Yauwa, ya school?.” “Alhamdulillah” ta fad’a tana kallon Zaytun tace, “dawo mu cigaba.” Ta dawo suka cigaba da aikin yaga shiru bata kawo abinci ba shi kumayayi alqawarin bazai tambaya ba ya tashi ya hau sama. Bai sakko ba sai magriba ya fita yaje masallaci daga nan ya shiga gidan Ammah sai bayan i’sha ya dawo gidan ya samu Zaytun tayi bacci ya zauna yana kallon ta yace, “sarkın magana anyi bacci da wuri yau.” Ameena ya kalla ya kalli dining din babu abinci ya sauke numfashi sai yaga t tashi ta shiga kitchen ta dawo tace, “Me za’a dafa maka?.” Ya kalle ta yace, “ki barshi bana ci” ya fad’a yana tashi ya d’auki Zaytun ya hau sama ba tare da ya kalle ya ta ba. Bin bayan sa tayi ya kwantar da Zaytun idanun ta sun fara cika da hawaye tace, “Meyasa tun yanzu?.” Ya kalle ta bai magana ba ya share ta dan gudun ruwan ta yake so ya gani tace, “yau kwana uku kenan baka cin abincin gidan nan, meyssa haka?.” Cikin fad’a take magana ya lura haka take masa magana in ranta ya b’aci kamar zata dake shi da kuma ba haka take ba sai bai tanka ba ya fita ya barta. D’akin nasa ta bishi tana shiga tace, “ina magana kayi min banza” sai muryar ta ta fara rawa ta fara hawaye  yajuyo ya kalle ta yace, “ya zan miki? Abu kad’an da anyi sai ki fara yi min fad’a kamar ki kika haife ni. Kwana biyu da ya wuce da na dawo kika ce ga abinci me nace miki? Bana jin dad’i kaina na ciwo bazan iya ci ba, shekaran jiya na dawo kika ce ga abinci saboda kar kiga banci ba ja zauna naci amma badan Ina da lafiya ba. Jiya da nazo da Yunwa kika ce min baki girki ba, na tambaye ki dalilin da ya saka baki yi ba?. Yau da safe kika ce min Baki yi ba shima na tambaye ki?.”  Tayi shiru yace, “ban tambaya ba saboda nasan kin yi din duk yadda akayi akwai abinda ya hana ki yi shiyasa nace ki barshi kawai sai naje wajan Ammah naci abinci. Da safe na tashi zan tafi aiki kika ce min baki yi ba bayan kin tashi kuma kin yiwa Zaytun ta tafi makaranta, shima nace miki akan wanne dalili? Ban fad’a ba na wuce na tafi store a haka naje na dawo banci komai ba  koda na dawo baki min tayin abincin ba sai da kika ga dama sannan kika ce min wai me zaki dafa min. Me nayi miki? Ban miki komai ba kin d’auki fushi a kaina wanda ban San dalilin sa ba, abu kad’an da nace sai ki fara yi min fad’a kamar kin haife ni akan me Ameena?. Nasan kina gani kamar na daina cin abincin kine kamar lokacin baya in kika yi min adalci da baya da yanzu ba haka abun yake ba, wannan dalilin ya saka da nayi magana sai ki fara fad’a shiyasa nake kyale ki na bar wajan in na tsaya abun bazai yi kyau ba ke kin sani, dan Ina da zuciyar da zata harxuk’a ni raina ya b’aci. Amma kika cigaba da irin wanna d’abi’ar da kike yi ko nace kika d’auka bazan iya jurewa ba.” Tana tsaye bata motsa ba ya wuce ya shiga band’aki tana tsaye ya fito ya canja kaya ya d’auki magani zai sha sai ya fasa sboda ba’a sha ba’aci abinci ba ya zauna ya dafe kansa dan ciwo yake masa, indai zai sha wahala ko zai shiga damuwa to tabbas kai zaiyi ciwo. Jikin tane yayi sanyi kuma haka ne fa itama bata tambaye shi meyasa baya cin abincin ba, ta k’araso ta zauna tace, “kayi hak’uri, bazan sake ba in sha Allah. Kuma wallahi ni ban san ina maka fad’a ba, d’auka nake magana ta normal nake yi  amma bazan saka ba in sha Allah. Duk yadda akayi cikin nan ne yake saka ni haka amma ba da niya nake yi ba.” Shiru bai amsa ba ta kalle shi tace, “kayi hak’uri dan Allah, bazan sake ba wallahi nasan nayi kuskure kayi hak’uri. Nayi bak’i ne jiya har Yaya Al’Ameen yazo shiyasa ban samu nayi girki ba.” Sai a lokacin ya kalle ya yace, “to meye na fushi dan kince zakiyi nace ki barshi? Ba dan wani abun na fad’a bafa sai dan tausayin ki duba da yanayin ki bake kad’ai bace amma sai kika yi fushi, Wato da safe ma sai na Nemo abinda zanci.” “Kayi hak’uri.” “Nayi Ameena, amma kar ki sake nan gaba bazan yi hakurin ba.” Ta girgiza kai tace, “bazan ma sake ba in sha Allah.” Ya d’aga kai kawai tace, “to me kaci yau din?.” “Nidai nasan na sha fruits nida Usman then na sha fura da nono bayan nan ban kuma cin komai ba.”  “Baka ci wajan Ammah ba?.” “Bana so nace zanci abinci a gidan, naci jiya yau ma naje sai taga kamar akwai wani abun.” Ameena tace, “dole kanka yayi ciwo ai, bara  na dafa maka koda indomie ce.” Baice komai ba ta tashi ta fita ya bita da kallo har yanzu akwai ragowar abinda ya faru a zuciyar ta, yasan daman bazai goge ba wani abun da anyi sai taga kamar za’a maimaita baya ne sai ta kama kanta bata san ko haukacewa yayi bazai sake aikata abinda yayi a baya ba. Yayi hankali ya kuma gane mahimmacin da yake dashi soyayyar ta kuma kullum sake yawa take a zuciyar sa. Ba jimawa ta dawo da indomie a bowl ta zauna akan bedside drawer ta tace, “ga indomie.”  Ya bud’e idanun sa yace, “sai dai in da kan ki zaki bani.”  “A guje ma.” Ya tashi zaune ta zauna kusa dashi tace, “Akwai zafi amma fa” ta fad’a tana d’auka ta kai bakin sa ya bud’e ya karb’a ya haddiye  yace, “ Tayi dadi,” Tayi murmushi zata sake bashi ya juyar da fock din zuwa bakin ta yace, “kema ki ci.” Baki ta bud’e taci ta sake bashi ya sake bata a haka suka cinye indomie din ta ajjiye bowl din tace, “Yanzu sai ka sha magani” ta fad’a tana d’aukar maganin ta bashi yasha ta tashi ta shiga band’aki sai gata towel ta jiqa shi ta d’ora masa a goshin sa tace, “Allah ya yaye maka wannan ciwon kan.” Ya amsa da amin ya lumshe idanun sa yana kallon ta ta sunkuye sosai yana jin khamshin jikin ta mai dadi nan take Asiya ya fad’o masa a rai sai ya runtse ido tsigar jikin da ta tashi yaja dogon tsakin da ya saka ta kalle shi tace, “lafiya?.” Ya bud’e ido ya kalle ya yace, “babu komai.” “Wannan tsakin kace babu komai?.” “Na tuna wani abun ne.” “Oh!” Ta fad’a akwai tana zama bata ce komai ba. Ya kalle ya yace, “baza ki kwanta ba?.”  “Zanje nayi wanka sannan na duba Zaytun.” “Kije ki duba ta ki dawo wankan sai Kiyi a nan.” Ta amsa da to ta tashi a fita ya bita da kallo Kansa na sarawa sosai yana jin zuciyar da na bugawa a ko wanne minti. Ba jimawa ta dawo tayi wankan ta fito ta shirya duk yana kallon ta taje ta zauna kusa dashi tace, “Beb na tambaye ka?.” Ya kalle ta yace, “ina ji.” “Beb wai ina Asiya?.” Gaban ss ya fad’i ya kalle yta itama shi take kallo ya sauke kansa k’asa ya sake kallon ta yaga dai shi take kallo yace, “zamu iya barin zancen nan?.”  “Meyasa zamu bari? Tambaya nayi kawai ka bani amsa.” Ya kalle ta yace, “Dan Allah kashe mana hasken nan kizo.” Murmushi tayi ga lura bazai bata amsa ba bai san tasan komai a bakin Humaira ba ta tashi tayi abinda yace ta dawo ta kwanta kamar yadda ya kwanta yace, “Dan Allah zan iya neman alfarma a wajan ki?.” “Eh mana.” “Dan Allah a bar zancen wata ko wani da suke wuce a rayuwar baya, indai babu su a rayuwar mu ta yanzu dan Allah kar Kiyi min maganar su.” Ameena tace, “to babu komai in sha Allah baza’a sake ba.” Ya kulle ido ya bud’e yana kallon ta sai yaga tayi murmushi yace, “meye a ranki?.” Ta lumshe ido ta bud’e tace, “wani abun na tuna.” “Meye?.” “Kai da kace min ka tuna ai ban tambayi meye ba ko?.” “Nidai ko me kika tuna ina sonki, da kuma son ki zan mutu dashi zan tashi har ranar alqiyama.” Tayi murmushi ta kwanta a jikin sa bata ce komai ba. Yace, “har yanzu alfarmar Ammah da Zaytun nake ci? Kince min daman bakya sona kin tsane ni har yanzu haka ne a zuciyar ki?.” Ta sauke numfashin da yaji shigar wucin sa jikin sa tace, “zamu iya barin maganar nan?.” Ya girgiza kai yace, “baza mu bari ba Beb, ina so na sani kullum da tunanin hakan nake kwana nake tashi.” Tayi shiru bata ce komai ba yayi murmushi yace, “na fahimta, Allah ya canja miki abinda kike ji a ranki Beb, ya dasa miki sabuwar soyayya ta a zuciyar ki” ya fad’a yana shafa cikin ta yace, “Allah ya fito mana da babyn mu lafiya.”  Da amin ta amsa yace, “Amin din ta addu’ar farko ce ko ta biyu?.” Tayi murmushi mai sauti tace, “Addu’a ta biyu.” “Ta farko bata cancanci ace amin ba?. Bakya jin zaki sake son Yusuf?.” “A’a, daman bance bana son Yusuf ba.” “Wallahi kince, kuma idanun ki sun nuna hakan har yanzu babu soyayyar Yusuf a zuciyar kina zaune zaman Zaytun da Ammah da kuma rabon da Allah yayi sai a same shi a cikin ki.” Ta sauke numfashi yace, “kar kice komai ina nan ina addu’a Allah ya dawo da soyayyata zuciyar ki ko bata Kai ta baya ba dan ba’a b’ari a kwashe duka.” “Bana fata ma ta kai ta baya.” “Kenan da gaske babu soyayyar?.” Ta kalle shi suka had’a ido duk da babu haske tayi shiru bata ce komai ba yace, “gaskiyar ki kika fad’a nima ina son hakan Beb, Allah ya dawo da soyayyata a zuciyar ki kafin barina duniya.” “Ni bance bana son ka ba fa.” Yusuf yace, “har mai sona ma kince bakya so Ameena.” Ta kwanta a jikin sa sosai ya rik’e ta yace, “Allah ya sani, yasan zuciyata, yana san abinda yake Raina, yasan abinda ya dasa a tsakanin haqarqarina wallahi ina sonki. Kuma  na canja bazan sake maimaita abinda nayi ba amma kin kasa amincewa dani har yanzu kina kokwanto a kaina da halyayata Ameena.” Ameena tace, “Bana kokwanto kawai in wani abun ya faru ina tuni kwatankwacin sa da ya faru a baya, kasan kuma wannan bazan iya mantawa ba dole na tuna.” Ya girgiza kai yace, “Haka ne, Nima ina tunawa sosai jikina yana yin sanyi ina tabbatar da cewa tabbas ba dan halina kike a zaune a gidsn nan ba, inda dan halina ne baza ki sake kallona ba. Wallahi dana rasa ki ciwon nan  zai iya tab’a kwakwalwata na haukace Ameena.” Kafin tayi magana yace, “in na tuna lokacin da nake shan giya nake dukan ki Ameena ina ji kamar na yanki jijiyoyin jikina saboda yadda nake jin bak’in ciki a zuciyata, me ya shiga kaina ne har na kai kaina ga shan abinda Allah ya haramta?. Ina zubar da hawaye a duk lokacin da na tuna hakan.” Ameena tace, “Shan giyar nan yafi komai d’aga min hankali, yafi komai tsaya min a rai, shine kan gaba wajan cewa bazan dawo gare ka ba.” “Na daina Ameena, daga ranar da su Ammah suka samu labari kamar anyi ruwa an d’auke.” Ta sauke numfashi bata amsa ba ya sake cewa, “in na tuna na tsallake ki na share ki na daina kula da lamarin ki na tsahon wasu watanni, Allah kad’ai yasan me nake ji a zuciyata, babu lallai  ki amince amma ina dana sanin aikata hakan. Nidai nasan farko farkon faruwar hakan ina sane Ameena, Ina yi ne dan kiji haushi tabbas, amma daga baya bazan ce ni ne ko ba ni bane.” Ta sauke numfashi tace, “to ka bar tuna wannan maganar jikin ka har yayi zafi, baka da lafiya ka kuma san tuna hakan yana baka damuwa.” Shiru yayi na wani lokaci babu Wanda yake magana a cikin su kafin yace, “Kiyi hak’uri dan Allah, ki daina kallona da abubuwan baya. Na amince na yarda ban cancanci ki dawo saboda dani ba sai dan saboda Ammah din, amma ki yafe min ki sake bani gurbi a zuciyar ki.” Ameena tace, “ya isa haka dan Allah, ni aka yiwa nace na manta to meye na damuwa?.” “Baki manta ba wallahi, kina sane kina kallona da abin shiyasa wani lokacin kike misbehaving saboda kina tuna abinda ya wuce ni kuma ni bana ganin laifin ki, kin yi daidai ko dukana zakiyi kin aikata daidai Ameena.” Shiru kawai tayi bata ce komai  ba shima yayi shiru zai sake magana ta rufe masa baki tace, “maimaita maganar shine yake saka ni tunawa da maganar, daina magana a kai shine yake sakawa na manta. In kana so na manta din a bar zancen kawai.” Kai ya d’aga alamun to ya yiwa hannun nata da ta rufe bakin sa kiss ya rik’e ta sosai a jikin sa yana sauke numfashi tace, “kar kace zaka zubar da hawaye dan Allah, kanka yana ciwo zai maka illa hakan.” Yayi shiru baice komai itama tayi shiru sai daga baya tace, “ni yanzu tago ma na aura, komai kuka. Wancan Yusuf din ban taba ganin yayi kuka ba, amma wannan ya rago ne.”  Dariya yayi itama ita tayi dan daman dariyar take so yayi yace, “ni ne ragon?.” “Eh kai ne.” “Haka kika ce?.” “Eh hakan nace sai meye?.” Kallon ta yayi suka had’a ido ya girgiza kai yace, “ki bini bashi, Allah ya sauke ki lafiya zan baki mamaki.” Tayi dariya sosai ta saka gyara kwanciya a jikin sa shima dariyar yake yace, “badai ni ne rago b? Zaki gani.” A haka bacci ya d’auke shi ta kalle shi ta sauke numfashi a zuciyar ta fata da burin Allah yasa ya zamar mata haka har abada da tafi ko wacce mace farin ciki a rayuwar ta. Bayan kwana biyu. #Mai daki #Book3 #Nana Haleema #paid Book3 045 Al’ameen tunda yaga Fiddausi ya saka a zuciyar sa ya samu matar aure hakan ya saka ya tambayi Ameena cikin hikima kuma bata gane ba ta fad’a masa har gidan su bata san abinda yake so ba kenan. Yana dawowa daga Abuja gidan su ya samu mahaifin ta kai tsaye ya sanar dashi waye shi da kuma alaqar sa da Adam da kuma abinda ya kawo.  Abba yayi farin ciki sosai ya kuma bashi damar zuwa ya smau Fiddausin. Da labarin yaje mata ita rasa gane waye ma Al’Ameen tayi kanta ya kulle dan bata  gane ba amma tayi farin ciki sosai da sosai ko babu komai addu’ar ta ta karb’u Allah ya yafe mata ya kuma yo mata Zab’i na gari. Ranar da Al’ameen zai zo gabad’aya rasa nutsuwa tayi har sai daka ce gashi sannan ta samu ta daidaita kanta ta same shi a d’akin Abba ta shiga da sallama ya amsa. Fiddausi ta gaishe shi ya amsa yana yace, “Malama Fiddausi sunana Al’ameen abokin Adam Yayan Ameena kawar ki. Na ganki a gida Ameena dana tambaye ta sai yake fad’a min baki da aure da bayanan ta tayi amfani nazo inda kike. Allah yasa zaki karne ni hannu biyu.” Fiddausi tace, “Allah sarki, na gode sosai da ka zab’e ni, amma Ameena bata baka labarina ba?.” Yace, “bata fad’a min komai ba saboda iya abinda na tambaya kenan.” “Da ka sani ka tambaya dan kasan Wacece ni kafin ka kawo kanka gare ni.” “Gani gaki zaki iya sanar dani wacece ke.” Fiddausi tace, “Nidai na tab’a aure har sau biyu, son zuciya da son duniya ya raba ni da gidna mijina na farko na auri mijina na biyu Wanda gidan ya kasance tamkar wuta saboda bala’i da uqubar dana tsinci kaina a ciki. Sakamakon son zuciyata shi na girba a gidana na biyu a nan na fahimci meye duniyar a nan nayi dana sanin duk abinda na aikata domin kuwa irin rayuwar da nayi a cikin  gidan din mai muni ce duk tunanin ka bazai kawo hakan ba shiyasa har ka kawo kanka wajena matsayin mai sona. Dan da ace kasan abinda na aikata baza kazo kace kana sona da aure ba.” Al’ameen ya zare glasses din idanun sa yace, “inda zaki fad’a min da kin cire ni daga rud’ani.” Ta sauke numfashi tace, “bazan maka k’arya dan na aure ka ba, zan fad’a maka dan nayi alqawarin babu wanda zan b’oyewa abinda ya faru dani koda zai fasa aurena sai dai ya fasa nidai na fad’i gaskiya. Na auri Alhaji Bello Sagagi nasan ka sanshi nayi kwanan farin ciki na wasu y’an kwanaki kad’an kafin farin cikin ya gushe daga duniya ta bak’in ciki ya maye gurbin sa.” Kallon ta yake itama ta kalle shi tace, “Ya kasance dan homosexual ne, kuna nima ban tsallake ba yayi amfani dani sau d’aya.” Ta sake kallon sa dan tana son ganin yanayin sa tace, “wannan shine Gaskiyar magana, bana karya bazan kuma fara a kanka ba. Yayi amfani dani ta k’arfi bayan ya saka an d’aure ni, koma dai meye na aikata ba ban aikata ba. Wannan itace rayuwar Fiddausi a takaice. İn kuma kana so Kaji cikakken labarina zaka iya tambaya ta sai na fad’a maka..” Ya kalle ta sosai dan ta burge shi yana qaunar wanda zai fad’a masa gaskiya a cikin lamarin sa babu b’oye-b’oye hakan ya saka ya zuba mata ido ya kuma ji tausayin ta sosai ganin ta goge hawaye. Al’ameen yace, “Zanen k’addarar ki kenan Fiddausi ko wanne bawa baya tsallake kaddarar sa, rabon ki fahimci kuskuren ki shine ya saka kika kai kanki gıda na biyu, kuma in ka tuba kayi nadama shikenan rayuwar ka zai zo da sauki kuma zaka ga sakamako mai kyau a lokacin da bakayi tunani ba Allah zai maka canji dan addu’a b’ata fad’uwa kasa a banza.” Fiddausi ya girgiza kai ta goge idanun ta tace, “Haka ne, amma ni na cire rai da samun jin dad’i a duniya, fatana Allah yasa na cika da imani.” “Haba kamar ba mai ilimi ba? Ai ba’a cire rai daga rahama Allah har a kwanta a kabari, Kiyi hak’uri ki ta addu’a alkhairi yana nan zuwa a gare ki. Sannan ina so daga ni kar wanda ya sake jin maganar nan. Gaskiyar ki da kuma yadda kika fad’a min baki b’oye min ba ya saka na sake jin gamsuwar auren ki domin baki aikata kina sane ba.”  Ta kalle shi da sauri jin abinda yace  ya girgiza mata kai ya mayar da abin idanun sa sannan yace, “kar ki damu chanji yazo a rayuwar ki in sha Allah, zan wanke dukkan wannan baqin da ya shiga rayuwar ki, zan maye gurbin sa da fari duk abinda zai sanya ki farkn ciki zaki samu a tare Dani da izinin Allah” ya fad’a yana tashi yace, “ki bani lambar ki” ya fad’a yana bata waya ta karb’a hannu yana rawa ta saka masa dan abun take gani kamar a mafarki kamar  sa yace yana sonta kuma yaji abinda ya faru da ita ya amince, ganin hakan sai yayi murmushi yace, “zamu yi magana in sha Allah” ya ajjiye mata rafar kud’i yace, “a gaida mutanen gidan, zan dawo zuwa lokacin magana mai k’arfi a shiga tsakanin mu” ya fad’a yana fita Fiddausi ta dinga kukan farin ciki. A haka ya shiga gida tana kukan murna da farin ciki Allah ya kawo mata chanji a rayuwar ta Maman ta sai da tayi kuka itama musamman lokacin da Abba yake sanar dasu  waye Al’Ameen  sannan ya kuma amince yana kuma yi mata fatan samun sa a matsayin miji saboda ya cancanci ya kasance miji a gare a gare ta saboda ya had’a abubuwan da ake nema a wajan miji na gari. Bayan wasu kwanaki.        Cikin ikon Allah aka fara shirin bikin Fiddausi da Al’ameen babu wanda ya kai Ameena murna da farin ciki dan ta taya kawar ta murnar samun sa ta kuma yi farin ciki da hakan. Sai da Abba ya saka akayi gwaje gwaje na cuwuka Allah ya taimaka babu wani ciwo a tare da Fiddausi sannan aka saka lokacin biki cikin lokaci kad’an akayi komai aka gama amarya Fiddausi ta tare a gidan mijin ta cikin sabuwar rayuwar da tayi mafarki a baya, a wancan lokacin bata samu ba sai yanzu da bata yi tunani ba allah ya bata ya had’a mata biyu ya bata rayuwar jin dadin da kuma kwanciyar hankali saboda kaddarar da ta karb’a ta kuma mayar da komai ga Allah. Ta kuma yi nadama ta k’arbi kuskuren ta ta amince yayi ta rok’i Allah akan ya canja mata kuma ya canja mata. Rukayya sun koma Abuja a can suke rayuwar su da İbrahim sai dai ace Alhamdulillah domin kuwa yayi k’arfi cikin lokaci kad’an saboda ya rik’e addu’a ga kuma addu’ar iyaye ta rike shi a duk inda yake da kuma mace ta gari da take taya shi addu’ar dan ganin sun cigaba shi da ita. Ameena ta haihu ta sake haihuwar mace aka saka mata sunan Maman ta Sa’adatu ake kiran ta da Nayla. Zaman farin ciki a gidan ta ba’a cewa komai domin kuwa ta tabbatar wani komawa gidan tsohon mijin alkhairi ne ba ko wanne ne yake zama abinda aka bari shi zaka tarar ba nata dai ya canja da gaske har zuciyar sa abinda ya rage kad’an ne a cikin halayyar sa. Asiya kuwa ana nan jiya e yau babu wani cigaba a rayuwar su an samu Momi ta shiga dakyar cikin dangi Fauziyya ma an d’auka dakyar amma Asiya kowa akace sai yace sam shi bazai iya ba  b’arauniya ce kuma ta raina kowa a haka suke zaune a gida ita da Maimuna babu mai so balle ya taya koda wasa duniya tayi musu zafi. Umma tayi nadama itama tayi danasanin tarbiyyar da ta d’ora su a kai wacce ake musu gori ko a cikin dangin tana kuma yi musu fad’a akan ake su d’ora nasu yaran a turbar da ta d’ora su.          Yusuf suna tare da Ameena a ranar Asabar kwana biyu da dawowar su daga Germany yaje yaga likita akan ciwon kan da bai kyale shi ba suna tafiya da yamma a mota kai da ka gansu Kaga masoya suka je gidan Yaa Adam da ya dawo yana Kano a lokacin. Suna shiga ta tarar da Al’Ameen a zaune ganin sa sai tayi murmushi tace, “Lah Yaya Al’ameens kana nan?.” Yayi murmushi yana kallon ta shima Adam haka suka zauna kafin suyi magana Adam  ya kalli Ameena ya kalli Yusuf ya ce, “Yusuf ka rik’e amana ka kuma cika alqawari, ka tabbata mutum mai karbar gyara da kuskure a rayuwar sa. Naji dadin chanjin nan na tabbata ko babu raina zaka kula da Ameena har abada.” Yusuf yayi murmushi yace, “in ba rik’e amana ba na zama butulu kuma munafuki, ya zamar min dole na kula da ita koda bana so, wannan ya zama kamar wajibi ne saboda mahimmacin da take dashi, amma ina da korafi Yaya.” Yaya Adam yace, “na me ya korafin?.” “Har yanzu Ameena alfarmar Ammaha nake ci a wajan ta, tana zaune dani zaman hak’uri ne kawai amma badan tana so ba, bata yafe min ba ko nace babu soyayyar ta a zuciyar ta alfarma ce har yanzu. A taya ni rokon ta ta d’aure ta saka soyayyar ta ko yaya take baza tayi nasa sani ba.” Yaya Adam ya murmushi ya kalli Ameena yace, “to Ameena kin ji.” Tayi murmushi tace, “Yaya ya kasa amincewa ne ko yaushe gani yake kamar har yanzu ban manta baya ba, ni kuma na manta amma tsarguwa ce dashi akan wannan lamarin.” “Baki manta din ba ai har gobe kina tunawa.” “Tunawa ya zama dole indai ba loosing memory zanyi ba ya kake so nayi?.” “Sai ki manta din kawai, badan ciwo bane da nace dama kinyi losing memory din.” Al’ameen da yake kallon su yayi murmushi sosai ganin kawai soyayya ce take d’awainiya dasu yace, “ku bari ku koma gıda sai Kuyi wannan jayayyar, yanzu bamu Umma mu ganta.” Ameena ta mik’a masa Nayla ya karb’a yace, “ma sha Allah, yarinyar kuma kamar Umman ko Adam?.” Adam ya kalle ta yace, “da Ameena yake kama shiyasa kake gani kamar Umma. Allah ya raya ta.” Suka amsa da amin kafin Ameena tace, “Yaya Al’Ameen ina Fiddausi?.” “Ya fita d’azu, amma ki kije ta maybe ta dawo.” Ameena ta tashi tace, “bara naje gidsn.” Al’ameen yace, “kin manta da yarinyar.” Sai ta dawo tana dariya ta karb’i ta ga fita Zaytun tana wajan baban ta. Gidan ta shiga mai gadin yake fad’a mata ta fita kafin ta kai ga dawowa gida sai ga Fiddausi a mota an shigo gidan Ameena ta kalle tana murmushi a bayyane tace, “Fiddausi buri ya cika, Allah ya tabbatar zaki rayuwar da kike so amma sai kin sha wahala.” Fitowa tayi daga motar ta rungume Ameena tana kallon ta Ameena tace, “kina abinda kike so wallahi.” Fiddausi tayi dariya suka shiga ciki Ameena tana dariya itama haka suka zauna. Fiddausi tace, “wallahi bani da damuwar komai a gidan nan Ameena, musamman yanzu da nake da ciki farin cikin da yake nunawa yana saka ni farin ciki nima. Ameena wani wato Allah yayi bazan yi rayuwar da nake so ba sai bayan na sha wahala a rayuwata. Sai bayan na gane banbancin abinda nake so da abinda ya kamata naso, shine ya kaini gidan Alhaji Bello kinga ai a nan nayi hankali daga baya in na tashi addu’a sai nace Allah na gari nake nema.” Ameena tayi murmushi tace, “sai Mun sha wahala dai, ni kaina ban d’auka zan samu rayuwar farin ciki a gidan Yusuf ba, sai gashi na samu farin cikin da ban yi tunanin samun sa ba wallahi.” Fiddausi tace, “komawar ya zama miki alkhairi watakila da shi kika aure da baza ki samu farin ciki ba, da kika bawa Allah lamarin ki gashi yanzu komai ya zama tarihi.” “Kamar ke, da kika yi nadamar da gaske kika tabbatar kinyi kuskure sai Allah bai sake baki ibrshim ba ya baki wani na daban Wanda yake da nagarta da komai kamar Ibrahim din ko nace yana fi ibrshim. Daman Allah ya rubuta Ibrahim da Ruky zai rayu dole ki bar gidan sa ta shigo, Ke kuma dole ki auri Bello ki san kinyi kuskure sannan sai ya baki jin dadin dan ki tabbatar da sai an had’a biyun ake samun kwanciyar hankali.” Fiddausi tace, “bari kawai Ameena. Wanda bai yarda da Allah ba ai yana cikin wani hali, cikin lokaci kad’an ya bayyana mana abubuwa da yawa mun gani. Sai dai muce Alhamdulillah yayi mana ni’ima. Abu d’aya ke damuwa a wani lokacin shine Amir. Ina son yaron nan sosai amma sun yi min nisa yanzu.” “Rukayya ta zama matar manya fa ina fad’a miki tayi kyau kin san fatar ta da d’aukar hutu wallahi baza ki gane ta ba.” Fiddausi tayi dariya tace, “ina son zuwa abujan wallahi to aikin ne ya dawo kano gabad’aya shiyasa zuwan yake wahala.” “Ai rana zamu saka dukkan mu muje mu dawo a ranar dan jirgi mutum d’aya ma ta biya mu ne.” Fiddausi tace, “hmm bari kawai. Babu abinda zamu cewa Allah sai godiya dan ni wallahi ban d’auka zan sake samun farin ciki irin wannan ba.” “Ba’a  fitar da rai daga rahama Alalh.” “Ni zan baki labari” ta fad’a tana dariya suka tafa suna hira cikin farin ciki a zuciyar ko waccan su.        Sai bayan i’sha suka tafi Ameena sai murmushi take tun a mota yana kallon ta yana Murmushin shima yace, “wai lafiya kike? Wanne albishr aka yi miki haka?.” Tayi dariya kawai bata ce komai ba a haka suka koma gida Zaytun tayi bacci haka Nayla tana tsaye tana shafa turare a jikin ta ya shigo yana kallon ta ta madubin yace, “farin ciki yayi miki yawa yau, meye sirrin?.” Tayi dariya tace, “wato Allah gwanin hikima ne Beb, ya riga ya tsara rabuwar mu dakai a wancan lokacin shine silar canjawar komai, ya tsara dawowa ta wajan ka shine alkhairi koda bana son dawowar sa na dawo saboda rabon Nayla, Allah ya tsara min sabon aure ba alkhairi ne a wajena ba dawowa wajan ka shine alkhairi. a daya bangare Fiddausi sabon aure shine alkhairi a rayuwar ta.” Ya rik’e hannayen ta guda biyun yana kallon ta yace, “Rayuwar mu darasi ce akan mutane, da farko babu kwanciyar hankali amma daga k’arshe an samu kwanciyar hankalin. Wannan kamar izina ce akan masu tunanin komawa gidan mijin da aka bari babu alkhairi domin damuwar da ta fitar dake ita zaki koma ki sake tararwa, eh akwai hakan sosai domin wasu chanjin na lokaci ne, Wanda Allah ya zab’a kuma inya canja ya canja kenan har abada, bazai sake kallon baya ba zai cigaba da amfani da canjin da Allah yayi masa.” Ta girgiza kai tace, “ban tabbatar ba sai da zaman mu yayi nisa, a baya gani nake kawai farkon zama ne zaka koma yadda kake. Amma gashi addu’a tayi tasiri komai ya zama tarihi.” Yayi murmushi yace, “har yanzu alfarmar Ammah nake ci?. Kina gani ta silar soyayyar ki na samu ciwon da dashi zan mutu, wannan ciwon kan shine ya kusa sakawa na zama mahaukaci.” Tayi dariya tace, “dadi nake ji in nasan kana sona sosai fiye da baya. Murna nake farin ciki nake ji in nasan kana sona fiye da yadda kake son kanka, ina son a soni sosai, shiyasa nake jin dad’i a duk lokacin da ka furta kalmar ina sonki.” “Ni kuma haushi nake ji in a tuna yanzu bakya sona. Zuciyata har rawa take in na tuna Beb alfarma nake ci take zaune dani, bayan tana gani sonta har ciwo ya saka min.” “Wai haka nace maka bana sonka.” “Haka kike ce mana.” Tayi dariya tace, “to yanzu na canja, ina sonka har zuciyata.” Ya girgiza kai yace, “kin fad’a ne dan naji dad’i amma ban yarda ba.” Ta sake yin dariya shima dariyar yake yana kallon ta yace, “Gaskiya ne ai. A daure a bani gurbu soyayyar da nake miki zata fi haka in nasan kina sona.” “Me zanyi da zaka yarda?.” “Sai lokacin da kika fad’a min da kanki ba tare dana tambaye ki ba.” Ya sake yin murmushi yace, “ai kuwa zan fad’a maka.”  “Ina jiran ranar tazo zanyi kowa murna.” Ta bishi da kallo shima kallon ta yake ganin sai kallon sa yake kamar mai duba wani abun a jikin sa yace, “ya dai?.”  “kayi budurwa?.” Ya kulle ido ya bud’e yace, “Wallahi har kin saka gabana ya fad’i, babu wannan labarin a tahirina a yanzu. An goge wannan tunanin ki ma daina shi.” Zatayi magana yace, “kar kice haka nace miki a baya ma,  wancan lokacin daban wannan lokacin daban ya kamata ki dinga banbancewa.”Tayi dariya sosai tace, “kyaun da kayi ne yasa nasan ko baka ce kana so ba za’a ce Ana sonka.”  “An kuwa ce din, kawai dai bazan sake kallon wata mace a matsayin mace ba sai ke.” Ya bud’e baki zatayi magana yace, “dan Allah kar kice haka n fad’a a baya.” Tayi dariya sosai shima yayi dariya ta rungume  shi cikin farin ciki da jin dad’i shima haka yana ji a zuciyar sa Ameena itace rayuwar sa. Alhamdulillah! 19/july/2024. _Kuskuren da muka yi a cikin labarin nan Allah ya yafe mana, abinda muka rubuta daidai Allah ya bamu lada. A nan labarin MAI DAKI ya tiqe Allah yasa an amfana da Sakon da yake cikin labarin a kuma yi amfani dashi yadda ya dace._ _Shawara, gyara, kuskure, duk k’ofa a bud’e take ga wanda suke ganin ya kamata ayi magana dani, vip, regular grp, arewabooks da y’an bati ma duk k’ofa a bud’e take ina jiran kowa zan karb’i kowa ta ko wacce fuska domin Karb’ar shawara ko gyara ko a nuna min kuskurena. Ina ji daku masoyana a ko da yaushe ina matuk’ar alfahari daku kune ni nice ku, Allah ya saka muku da alkhairi ya bar zumunci dake tsakanin mu ya had’a fuskar mu har a aljanna._ _Nana Haleema taku ce a ko yaushe, a jira ta cikin sabon labarin ta da zai zo nan bada jimawa ba in sha Allah. Ina sonku ina kuma ji daku masoyana, Allah ya bar qauna amin._ #Nana Haleema #Mai daki #End #book 1&2&3 #