Book 2 001 Luuuu ya tafi zai fad’i Yaya Sulaiman yayi saurin taro shi yana fad’in, “Ka k’arfafa jikin ka Ibrahim; meye ribar zama da irin wannan matan masu son ganin bayan mazajen su saboda wani dalili wanda suka barwa kansu sani? dan ka rabu da ita shine zai saka ka fad’i?, to ka sani in ka samu ciwo kanka da d’anka ka cuta ba ita ba. Wuce muje chemist a gyara ciwon nan kafin cuta ta shiga.” Shi dai Ibrahim jin komai yake yi a sama kamar baya cikin hankalin sa kamar kuma a mafarki, in ya tuna kalmar saki da ya furta akan Fiddausi sai yaji jiri na sake d’ibar sa kamar zai kifa. Koda wasa bai tab’a kawowa wannan ranar zata zo ba, ya d’auka rabuwar aure shida Fiddausi sai dai mutuwa. “Abba mu tafi kar Mama ta sake yanke maka hannu” Amir ya fad’a yana jinjiga hannun Ibrahim da shi ya manta ma dashi gabad’aya a kusa dashi. Dakyar ya iya jawo k’afa ya fita ya samu Yaya har ya samu kwandon da za’a kulle gidan a maqota yana fitowa ya kulle gidan suke sake shiga ‘karamar motar Yaya suka tafi. ‘Karamin chemist suka tsaya aka gyara masa hannun bayan an masa allurar TT daga nan suka wuce gida kowa zuciyar sa babu dad’i, shi dai Ibrahim jin sa yake kamar ba shi ba dauriya kawai yake yi. Suna shiga gidan Alhaji yana zaune a ‘kofar d’aki sun gama tattauna batun Ibrahim din kenan yana sauraren labaran karfe takwas na dare ya bisu da kallo ganin hannun Ibrahim a d’aure ya kalli Hajiya itama ta kalle shi kafin yace, “Lafiya kuka dawo? Kai ya same shi a hannun kuma?.” Kafin suyi magana Amir yace, “Mama ce ta yanki Abba da wuk’a jini yana ta zuba.” Yaya ya kalli Sadik da yake zaune a gefe yace, “Dauki Amir kaje ka siya masa Alewa.” Ba musu ya tashi ya rik’e hannun Amir suka fita shi kuma ya zauna Ibrahim ma ya zauna. Hajiya tace, “Ban gane me Amir yake fada ba, da gaske itace ta yanke shi?.” Yaya ya girgiza kai alamun eh kafin yace, “Badan Allah yasa dani muka je gidan ba da wallahi zata iya kashe Ibrahim kamar yadda tace. Idanun ta ya rufe sai maganganu take yi na banza da wofi, ita bazata iya zama da talaka ba, ta gaji da rayuwar talauci, sabuwar rayuwa zata fara, maganganu dai kala-kala. Kana ji kasan daman ta shirya wani abun ne ya saka take yin duk abinda take yi.” “Innalillahi wa’inna ilahiri raji’un! Yanzu akan wannan dalilin taso kashe shi? Ko kuma tana da wani dalilin mai k’arfi?.” Hajiya ta fada a gigice tana kallon sa. “Haka kawai fa Hajiya, na fahimci kawai saki take so akwai wani abun da take hange ta gaji da zama da İbrahim kawai saki take nema. Duk abinda ta fad’a d’azu a gidan su ‘karya take yi kawai bata son zama dashi ne.” Alhaji da mamaki ya gama mamaye shi yace, “A gaban idanun ka da d’anta Amir ta d’auki wuk’a ta yanke masa hannu haka?.” Yaya yace, “Sabida idanun ta ya rufe ko ganina nida Amir bata yi ba, kawai tayo kansa da wuk’a ne tace in bai sake ba wallahi sai ta kashe shi. Tana cewa ta gaji da zama da talaka mara amfani ta gaji da rayuwar talauci.” Hajiya tace, “Sai da na fad’a tun farko a raba auren nan amma Alhaji yak’i, yanzu badan kana nan ba da me zai faru?.” Yaya ya numfasa yace, “Ai sai dai Alhaji a gafarce ni dan na saka shi ya mata saki daya, a lokacin in ba sakin ta yayi ba wallahi ba’a san me zai faru ba, dan har ni zata iya had’awa ta cakawa wuk’ar Tunda babu wanda yasan ta aikata. Zata iya bankawa gidan wuta su kune dukkan su.” “Kayi daidai, abinda ya kamata ayi kenan, ai ba y’ar gwal bace da za’a dinga riritata kamar wata yarinyar goye. Yarinyar da tazo har har gabana tace bata son sa aka tilasta mata zata kashe shi daman meye amfanin ta?, ai ko mutuwa na kunyar Idon mahaifi, amma ta shafawa idanun ta toka tazo ta same ni tace wai ya sake ta bata son sa” Hajiya ta sake fad’a rai a b’ace kana ji kasan maganar tayi mata ciwo sosai. Alhaji yace, “Ai shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, in da yuwar zata dawo Allah ya daidaita su in babu kuma Allah ya had’a kowa da rabon sa.” Hajiya ta amsa da amin tana kallon Ibrahim da ya saka cewa komai sai jinginar da kansa da yayi jikin bango idanun sa a kulle shi kad’ai yasan abinda yake tunani. Yana son Fiddausi Allah y sani amma ba rabuwa da ita bane yake d’aga masa hankali, mamakin sa da gaske daman zata iya kashe shi akan wani abu na duniya?. Hajiya ta sake cewa, “A gaban d’ank ka dinga hauka kamar mara ilimi, ilimin addinin nata da akayi kwad’ayi aka auro ta bai amfana mata da komai ba, bata aiki dashi da ita gwara wata wacce bata zauna a makaranta ba daman kasan tun farko bata je makarantar ba, ita kuwa fa?.” Shiru yayi baice komai ba kafin Alhaji yace, “ya isa haka, Kiyi hakuri dan Allah.” Shiru kawai tayi tana girgiza kai cikin k’unar rai, Yaya Sulaima mik’e yayi musu sallama ya tafi shima Ibrahim bai ce komai ba ya tashi ya fita dan yana buk’atar shan iska ko zai ji dadi zuciyar sa a cushe take. Yadda Fiddausi ta shiga gida sai ka d’auka zaki ne ya biyo ta ko kura, yadda ta fad’o tsakiyar gidan kamar mahaukaciya sai hakki take ga marar ta da take mata ciwo mat’uka hakan ya taimaka wajan sake gigicewar ta. Hankali tashe kowa yake tambayar ta Lafiya ta zube a wajan tana fad’in, “Ya sake ni, ya sake ni Mama, Ibrahim ya sake ni…..” sai tayi luuuu ta zube a wajan jini ya fara zuba daga jikin ta. Bata san me ya faru ba ta dai fara jiyo magana a kanta sama-sama kafin ta daina jin komai idanun ta ya rufe ruff duhu ya mamaye mata idanun ta. Ameenatu tana zaune ita a kad’ai tun bayan tafiyar kawayen ta kamar ko yaushe Zaytun tana kan cinyar ta tana wasa ita kuma ta zubawa waje d’aya ido tana kallo kamar mai son ganin wani abun a bangon amma babu abinda take gani kawai damuwar da take ranta ce tayi yawa. Bata san ma Yusuf ya zo wajan ba hankalin ta ya tafi wajan tunani bata ji maganar da yake yi a waya ba balle kuma takun takalmin sa, kallon ta yayi ganin ya mata magana bata ji ba hakan ya saka ya daki kujerar da take kai yace, “Bakya ji ne?.” Zabura tayi ta kalle shi kamar yadda yake kallon ta zaiyi magana yaga Zaytun na mik’a masa hannu tana kiran Daddy. D’aukar ta yayi daga jikin Ameena ya d’aga ta sama yana yi mata wasa tana darıya shima yana dariya, tana hannun sa ya sake kallon Ameena wacce take kallon abinda ya shigo dashi saitin manyan akwatina ne wata a cikin wata baza ta banbance guda nawa bane amma kai da gani kasan suna da yawa a ciki dan yanayin babbar ta farko zai tabbatar maka da wanda suke binta suna da yawa. Kallon abinda take kallo yayi y sake kallon ta yace, “kin yanke shawarar abinda kike so?.” Had’a ido sukayi bata janye nata idanun ba shima haka ta girgiza kai alamun A’a tace, “Ban yanke komai ba.” “Bakya so ne hala?.” Shiru tayi bata amsa masa ba ya tab’e baki jin bata amsa ba d’auke kai daga kallon ta yace, “Ba haifata kika yi ba balle na dinga binki Ina lallab’a ki dan na samu lada ba, in kin karb’a kanki, in baki karb’a bama ba damuwana bace. Karb’ar ki da rashin sa wannan ke ta shafa, hakan bazai canja komai ba.” Murmushi tayi bata ce komai ba ya kalle ta yana mamakin dalilin murmushin yace, “ki kawo min abinci sama” ya fad’a yana niyar tafiya bayan ya tura akwatinan gaba. “Ban yi girki ba” ya jiyo maganar ta daga bayan sa ya juyo ya kalle ta yace, “Wai ke wanne irin iskanci kika fara koyowa ne haka? Kin daina bani abinci kenan kike nufi ko me?.” Jin yadda yayi maganar a fusace ba kamar yadda ya gama yi mata magana yanzu ba ya saka ta karyar da murya tace, “in na dafa baci kake ba shiyasa……” “Shiyasa kika daina sabida bana ci? Saboda ke kike siyowa ai ko?. Shikenan Ameena kar kiyi in baki ba ita in ta shigo ai zata min zanci kuma, kar kuma ki fara yi min k’orafin bana cin abincin ki koda nan gaba, Kiyi kuka da kanki” yana fad’ar hakan ya bar wajan Zaytun na hannun sa. “Uhummmmm! Innalillahi wa’inna ilahir raji’un. Allah ka kawo min mafita da d’auki a lamarina” ta fad’a hawaye na zubo mata ta share ta tashi kanta na ciwo sosai dan Kullum cikin ciwon kai take ta hau saman zuwa d’aki ta. Bata jima da shiga ba wayar ta ta fara k’ara ta duba ganin shine yake kiran ta ya saka ta d’auka kafin tayi magana yace, “Kizo ki d’auke ta” yana fad’a ya datse kiran ta lumshe ido ta bud’e. Lokacin da yake fad’a mata baya so su dinga raba shimfid’a ne ya fad’o mata a rai, a lokacin da yake cewa duk runtsi duk wahala, duk fad’a duk gabar da zasu yi kar su raba wajan kwanciya kowa wani bazai kula wani ba. saurin kawar da tunanin tayi ta tafi zuwa saman nasa, a zaune ta ganshi Zaytun tana cinyar sa tayi bacci shi kum yana danna waya. Da sallama ta shiga ya d’ago ya kalle ta ya cigaba da abinda yake yi ba tare da ya amsa ba ta k’araso ta d’auki Zaytun din a jikin sa ta juya zata fita yace, “Baki ji ba.” Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba ya kashe wayar yace, “In kina da buk’atar wani abun ki fad’a.” Sai a sannan ta juyo ya kalle shi da mamaki tace, “Kamar me?.” Ya d’age gira sama fuskar sa a washe yace, “Kamar abinda nake nufi wanda yake zuciyar ki yake hana ki bacci.” D’an jimmm tayi alamun tunani ta girgiza kai tace, “Ban gane ba.” Dariyar rainin hankali yayi yace, “Karya kike Ameena kin gane, is better for you ki fito kiyi magana kar kiga nayi magana ki d’auka wai ni nake so” ya girgiza kai kafin yace, “sam babu wannan a zuciyata, kawai dai nayi miki tayi ne kar azo ana cewa ai ga zance ga magana. Daman kuma Wanda yake buk’atar abu shine yake zuwa ya nema in ya samu daman haka yake so in bai samu ba kuma yayi hak’uri, ki gwada yanzu watakila Ina cikin farin cikin da hakan zai saka na amince miki.” Ya hard’e hannayen sa yace, “A rashin tayi ake barin arha Ameenatou.” Yadda yake maganar yana murmushi sai take kallon sa itama tayi murmushi kamar yadda yake yi tace, “To ai ni ban ma fahimci inda zancen ya saka gaba ba balle ma nayi abinda kace.” “Da gaske?.” Kai ta d’aga alamun eh yayi murmushi yace, “shikenan jeki, da alama kin barwa amarya.” Ameena tayi dariya kad’an tace, “Daman ita take da bukata, mu kam ya ishe mu” ta fad’a tana niyar barın d’akin taji yace, “İn ma zuga ki ake kike mayar min da magana haka cutar ki ake yi, ki koma yadda kike a baya yafi dacewa dake wannan sabon salon bazai haifar miki da d’a mai ido ba.” “Sai da safe” ta furta a taqaice ta fita tare da ja masa k’ofar. Iska ya fesar ya naushi iska ya daki goshin sa dan shi Sam ba haka yaso ba, yana buk’atar tane a lokacin ya d’auka zata amshi tayin sa shiyasa yayi mata haka. Ya mike tsaye a bayyane yace, “Yaushe kika koma haka ne Ameena? Ina tarin soyayyar da kike min ya tafi…?” Ya fad’a yana yin ball da jarkar ruwan da take gaban sa ya juya ya shiga band’aki. Ameena d’aki ta wuce ta kwantar da Zaytun ta tsaya jikin window tana mayar da numfashi kamar wacce tayi gudu zuciyar ta na harbawa a guje marar ta na d’aurewa. Tabbas a matuqar buqace take da mijin ta, yadda yayi amfani da kalamai na ko in kula a kanta ya saka taji baza ta iya kasancewa dashi ba gwara ta zauna a haka koda zata cutu Kuka ta fashe dashi sosai mai sauti zuciyar ta nayi mata ciwo ga yadda kanta yake sarawa har biyu-biyu take gani. Ta jima tana kuka kafin ta duba agogo taga karfe goma na dare har ta wuce ta d’auki wayar ta tare da kiran likitan da take gani. Sai bayan wayar ta shiga kuma sai tayi tunanin kar fa tana gıda bata ne aiki ba amma kafin ta katse har ta d’auka dole tayi sallama ta amsa mata kafin tace, “I’m sorry Dr na Kira ki da daddare.” Daga can b’angaren tace, “Ahh babu damuwa daman Ina on duty ne ai yanzu, Lafiya dai ko?.” “Ciwon kan ne dai har yanzu nake fama dashi Dr, ga jiri da yake d’auka ta sometimes sai na zauna na huta ko tafiya nake yi, ciwon marar nan ma yana damuna.” Dr tace, “Ciwon kai da jirin da kike ji watakila jinin ki ne ya sake hawa ki shigo gobe da safe mu auna bp din, ciwo Mara kuma na fad’a miki matsalar ki bai kamata ki dinga sakaci ba, kina da aure ba baki da aure ba, bai kamata hakan ta dinga kasancewa dake ba.” “Mijin nawa baya nan ne Dr shiyasa.” “Ai fad’a masa zaki yi duk inda zai tafi ya dinga tafiya dake ai hakkin kine, in kuma hakan bazai yu ba ya dinga takaita tafiyar dan kina cutuwa hakkin kuma a wuyan sa yake Ameena. amma tunda yanzu baya nan ki sha ruwan zafi kar ki saka sugar zallar ruwa mai dumi zaki sha ki d’an tattaka kamar taku Arab’ın haka sai ki sha p.c.m ki kwanta.” Ameena tace, “in sha Allah, na gode sai nazo.” Daga nan suka sallama ta kashe ita kuma ta tashi tayi abinda tace mata cikin ikon Allah ta samu ta dan ji daidai ta kwanta kusa da y’arta bacci ya d’auke ta. …….A asibiti ta bud’e ido ta ganta hannun ta sanye da ledar ruwa gefe d’aya ga Mama ta ga kuma Zakiyya ga Yayar ta a zaune suna kallon gadon da take kwance suna magana. Muryar Yayar ta taji tana cewa, “Ai yayi mata wulakanci wallahi, ki duba yadda ya fasa mata baki fa dan Allah, ta nemi saki suka zo suka bada hak’uri aka hak’ura ta koma shine kuma ya sake mata dukan da cikin jikin t sai da ya fita, me ake da auren talaka irin Ibrahim?. Ashe duk yabon nasa da ake yi duk na banza ne tunda ga abinda ya faru a k’arshe.” Zakiyya tace, “Ai Yaya ta jima tana fad’a min damuwar ta akan Ibrahim kawai dai bata fad’a ne a gida, tace bata tab’a kawo k’ara gıda ba amma tasan in ta kawo Abba bazai amince ba gani zaiyi karya take yi. Tazo tayi min kuka na rarrashe ta na bata hak’uri ta koma duk bai gani ba sai da ya yi mata wulakanci. Ai gwara zaman nasu da yazo k’arshe naji dad’in hakan wallahi.” Yaya tayi kwafa tace, “Ai badan wani abun ba ko wallahi sai na saka an kama shi ya kwana a cell dan yasan kanwata ya tab’a, to Amir nake kallo ko babu komai ya had’a mu amma da shi din banza da wofi. Ya sake ta kuma yayi mata dukan da cikin ta ya zube Kaga ya hutar da ita idda ko gobe aure zatayi ta wuce takaici. Gwara ma da cikin ya zube ai kowa ma ya huta.” Mama ta girgiza kai tace, “Bai kyauta ba gaskiya wallahi, kuma ko waya har yanzu babu wanda yayi daga gidan su, ta inda aka hau ai ta nan ake sauka da sai su kira Abban ku ya fad’a masa komai. Ya bani mamaki sosai ban d’auka zai aikata haka ba, ina yabon sa sallah sai gashi ya kasa alwala.” Zakiyya tace, “Bar talaka Mama, ai bai san halacci bane shiyasa. Duk soyayyar da ta nuna masa yana malamin islamiyya amma shine zai mata wannan rashin mutuncin, yanzu fa aikin d’aukar bulo suke yi ta daure ta zauna dashi, abinci ma gararta yake wani lokacin, dan Baku san komai bane wallahi Mama da ko kallon sa baza ku sake yi ba. Ta rufa masa asiri sosai dan matar rufin asiri ce amma duk bai gani ba. ko da yake ai kansa ya yiwa samun mace kamar ta ai sai dai a mafarki.” “Washhh!” Ta furta bayan ta gama jin dukkan maganganun su ta mik’e ta jingina da bayan gadon Yaya tace, “Kiyi a hankali an yi miki wankin ciki ne fa.” Cize baki take yi har ta mik’e zaune ta kalli Yayan tace, “Ina Jin kwari ai, har gari ya waye ne?.” Mama tace, “eh, kwana muka yi a nan.” “Ikon Allah ban ma san ina nan ba” ta fad’a tana cize bakin ta kafin ta kalli Yaya tace, “Yaya naji kince wankin ciki.” Yaya tace, “Eh, dukan da yayi miki ya saka cikin ya zube bayan ya sake ki, ke ki gode Allah ma kin huta idda.” “Amma Yaya Ina son cikin” ta fada kamar zatayi kuka tana kallon Yaya, Yaya ta fusata tace, “Sai kije ya sake yi miki wani ai, banza wacce bata san kanta ba.” Shiru tayi bata amsa ba nan kuwa zuciyar ta fess take kamar ta taka rawa haka take ji ta kalli Zakiyya tace, “Zan yi fitsari.” Zakiyya ta taimaka mata ta tashi tace, “muje na raka ki.” A hankali suke takawa suna magana har bandaki k’asa-k’asa Fiddausi tace, “Ke an ina aka samo labarin yayi min dukan da ciki ya fita bayan ke kin san magani nasha?.” Zakiyya tace, “Banza duk plan d’ina ne, kedai ki daure ki warware mu koma gida a d’ora daga inda aka tsaya. Ai labari yazo karshe sai dai mu ce the end!.” Dariya tayi kad’an kafin ta shiga bandakin bata jima ba ta fito tasha tea din da Yaya ta kawowa Mama sosai taji dadin jikin ta likita yazo ya basu sallama suka tarkata suka koma gida. Book2 002 Ameena kuwa koda ta tashi bata iya yin komai ba har safiya kanta ciwo yake yi Zaytun ma yar aikin ta ta bawa ita ta yi mata wanka ta shirya ta ita kuma ta samu tayi wanka ta saka dogon hijjabi ta fito a falo ta had’u dashi yana amsa waya ta tsaya daga gefe tana kallon sa har ya gama kafin tace, "Ina kwana." Kallon sama da ‘kasa yayi mata dan kwana yayi yana jin haushin ta akan abinda tayi masa kafin yace, "Sai Ina?." "Zanje asibiti ne wajan Dr Mansura." "Sai kin dawo" yana fad’a ya wuce ya sauka ba tare da ya tambaye ta abinda ya same ta ko me zai kaita asibitin ba. Jingina tayi da bango ta lumshe ido zuciyar ta nayi mata k'una sosai ta sauke numfashi ta bud’e idanun ta sakko itama. Bata same shi a falon ba sai mai aikin ta d’auke da Zaytun tana bata abinci tayi murmushi tace, "Sannu da aiki." "Yauwa sannu da fitowa Hajiya, ya ciwon kan?." "Gashi dai Ina fama, asibiti ma zanje yanzu". "Allah ya k’ara Lafiya." Ameena tace, "Amin. Da Zata zauna ma ai dana je na dawo tana wajan ki." Tyi dariya tace, "Tunda kika sakko ta daina cin abincin tana kallon ki, ai baza ta zauna ba." Dariya tayi kad’an ta karb’e ta ta tsayar da ita tare da rike hannun ta suna takawa a hankali har wajan motar ta. Kai tsaye private asibitin da take ganin Dr Mansura ta wuce sai da taje bakin office din ta tsaya ta kira Dr Mansura d’in tace ta shigo tana ciki ta kuwa shiga ta same ta a zauna tana ta aikin rubutu a file. Ameena ta zauna tana fad’i, "Barka da safiya Dr." Dr mansura ta d’auki Zaytun da take kujerar kusa da Ameena tana cewa, "Barka dai Ameenatu, ya jikin naki?." "Gani nan dai kawai Dr, ciwon kan nan yayi min yawa sosai. Ni ban tab’a ciwon kai ma kamar da ba wallahi, idanu na har daina gani suke yi.” Dr mansura ta ajjiye Zaytun akan kujera ta tashi ta fara auna bp d'in ta. "Kai Subahanallahi! Ameena jinin ki ya hau sosai fiye da baya." Ameena ta sauke numfashi bata ce komai ba daman tasan za’ayi hakan Dr tace, "Haba Ameena meyasa kike saka damuwa a zuciyar ki har haka? Yanzu tsakani da Allah ya kyautu ace a shekarun ki jinin ki ya hau haka?. Wacce damuwa kike da ita da zaki d’auke ta ki saka a zuciyar ki har ta haifar miki da hawan jini hakan?.”Ameena tace, "Dr abubuwan ne sai a hankali kawai." "Ko meye hak’uri ake Amina, ba ko yaushe kake zama cikin farin ciki ba hak’uri ake ana mayar da komai ba komai ba sai kiga an samu sassauci. Wallahi in kowa yace zai saka damuwa a ransa da yanzu duk duniyar Mun k’are saboda ciwo ya kashe mu baki d’aya.” Ameena bata ce komai ba Dr ta kuma cewa, "Bana son d'ora ki akan maganin hawan jini ne dan kina fara sha shikenan kullum sai kin sha har abada, shi illar sa indai aka fara sai an gama sai dai in an auna an ga jinin ya sauka ace ki rage sha amma ba ki daina ba, shiyasa bana son ki fara sabida shekarun ki sunyi k’aranci a wanann yanayin. Amma abin naga bazai yu ba dole na baki magani kodan ki samu saukin ciwon kan" ta fad'a tana zama tare da rubuta mata magani kafin ta kuma cewa, "Kuma fa indai baza ki daina saka damuwar ba wallahi ko kin sha magani a banza, kinga tunda na fara auna jinin ki ban tab’a gani yayi k’asa ba sai dai ya hau na tabbata kuma damuwa kike sakawa zuciyar ki haka, in aka cigaba da haka wallahi wata ran za’a wayi gari wani ciwon ya kama ki wanda baki yi tunani ba. sai kinyi hak’uri sannan zaki samu Lafiya." Ameenatu tace, "in sha Allah zanyi k’okari Dr, ki rubuta min na ciwon marar." Tsayar da rubutun tayi ta kalli Ameena tace, "Shan maganin kwantar da sha'awa ba naki bane Ameena, kina da aure mijin ki shine maganin ki meyasa baza ki sanar dashi damuwar ki ba? Kina da hakki fa in hakan ya cutar dake fa?, ke baki san yawan Shan su yana haifar da illa ba?. Ameena wai meye damuwar ki ne?.” Ameena tayi murmushi tace, “Damuwa ta yawa ce da ita Dr.” “Meyasa baza ki sanar da na gaba dake a shiga maganar auren ki ba?, look Ameena ba wai ina so naji sirrin ki bane, ina miki magana matsayina ta likitan ki kuma y’ar uwat ki mace. In ke kina ganin baza ki iya yiwa mijin naki magana ba ki fad’a a gida ayi masa magana.” Numfashi Ameena ta fesar tana girgiza kanta kafin tace, "Dr bani da iyaye, duk sun jima da rasuwa. Yusuf da ya kawo ni wajan ki tun jikin Zaytun har muka Saba shine kawai dani a kusa a yanzu, dan haka ki rubuta min kawai Dr lamarin ne sai hak’uri kawai." Dr ta tallafi hab’a tace, “Yanzu in kika fara shan maganin sha'awar ta tafi gabadaya fa?." "Shikenan na huta ma wallahi." Dr ta girgiza kai tace, "Da yarintar ki kike yiwa kanki wannan fatan?." Ameena tace, "Kawai kı rubuta min dan Allah, kar hakan ya jefa ni cikin wani halin na daban.” Dr ta cigaba da rubutun kafin ta mik'a mata tace, "Gashi nan ko wanne akwai dose d’in da za’a sha, shi na ciwon marar kar ki dinga sha da yawa, kar kisha yau kisha gobe da jibi, in kika sha sau d'aya a wata ya isa sauran ranakun ki jure in ba haka ba zai miki illa. Koda yake in kin siyi maganin kawai kiyi snapping ki tura min zan miki bayanin ko wanne." Karb’a Ameenatou tayi tace, "Na gode sosai Dr." "Babu komai kar ki damu, amma ranar da angon nan naki zai dawo kamata yayi kizo ayi miki d'inki ki dawo sabuwar amarya" ta fad’a cikin zolaya duk dan ta kwantar mata da hankali. Ameenatou ta zaro idanu tace, "Rufa min asiri." Dariya Dr tayi tace, "Allah kuwa kizo." Ameena tayi dariya itama ta mik’e ta d’auki Zaytun tace, "Ai tun na haihuwar Zaytun ma da kika min bana kin Ina buk’atar wani ma a yanzu." Dr tace, "Kawai dai bakya so ne zaki wani wayance, ai shikenan." Dariya tayi itama sukayi sallama ta fita. Kai tsaye pharmacy ta shiga ta siyi magani ta shiga mota taja ta fita daga asibitin. Gidan Yaya Sumayya ta wuce a can ta zauna har bayan azahar sannan ta koma gida. Tun bayan an sallami Fiddausi take a d’aki Itada Zakiyya suna kwancewa suna sake k'ullawa akan abinda ya faru da kuma wanda zai faru nan gaba. Fiddausi tace, "Yanzu ya akayi wai akace cikina ya zube ta dalilin duka bayan nasan maganin da kika bani na sha biyar lokaci d'aya ne ya jawo min haka?.” Zakiyya tace, "Nurse d’in na samu kawai ta canja bayanin da ta yiwa su Maman, ke in kana da kudi fa a Nigeria zance ya k’are wallahi." Fiddausi tace, "Yanzu meye abu na gaba d zamuyi?." "Ai ban sanar dashi auren ki ya mutu ba a yanzu, so nake ki dawo hankalin ki ki mayar da jikin ki sai mu san abinda za'ayi." "Amma Ina Jin Abba fa Zakiyya, Anya zai amince ayi auren nan nan kusa duba da abubuwan da suka faru?.” "Zai ma amince in sha Allah, in bai amince ba sai mu bi ta hanyar Kawu Sa'idu ba shikenan ba?." Fiddausi tayi dariya tace, "Ke wallahi kanki yana Bala'in ja, kin San kuwa Kawu sa'idu da yaga kudi shikenan magana ta kare. Amma kuma ai dole maganar taso wajan Abba ai, ni kuma na tabbata Abba bazai amince da aurena nan kusa ba.” Zakiyya tayi dariya itama tace, "Ke komai a tsari za'a yi fa ki jira kawai lokacin yayi zamu tsara plan ta yadda babu wanda zai gano akwai wani abun a k’asa.” Mama ce ta shigo dakin sai Fiddausi ta langwab'e kamar gaske Mama tace, "Yanzu mahaifin yaron nan Ibrahim yayi waya da gaske dai anyi sakin nan tunda gashi sun fad'awa mahaifin ki, gaskiya Ibrahim bai kyauta ba abun ma har da dukan da ya zama silar zubewar ciki, badan mahaifin ku ba ai baza'a bar maganar nan ba. To shi kamar ma bai amince ba har yanzu gani yake kamar laifin naki ne.” Zakiyya tace, "Mama ya saba kawai fad’a muku ne ba'ayi, amma dan Ibrahim yayi mata duka ai ba wani abun bane tasha zuwa wajena Ina bata baki ta hakuri ta koma. Kuma Abba yana amfani da halayyar İbrahim ta zahiri ne shiyasa baya ganin laifin sa a yanzu, amma wallahi zai tabbatar nan gaba.” "Yanzu ai komai ya ‘kare Zakiyya, ya za'ayi da Amir?." "Mama kawai ya rik’e shi in yaso a dinga kawo shi akai akai yana ganin ta, in aka kawo shi nan a sake d'ora miki wata wahalar ne Mama." Mama tayi shiru alamun tunani ta sauke numfashi tace, "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" ta fad'a tana fita. A tare suka kalli juna sukayi dariya Zakiyya tace, "Allah Sarki Ibrahim an tafi kenan.” “Har abada kuwa, ni ko a hanya ma bana so mu had’u wallahi.” “Yanzu ya zakiyi da kayan ki na gidan?." "Ya barwa matar da zai aura bana so, ke nifa tunda na tattara kud'ad'ena da Kayan da nake so na kai gidan ki wani abun na gidan baya gabana wallahi." "Saura kiris dai ki zama matar Alhaji in sha Allah." "Ai zan fad’a masa ke sarkin yaqi ce ya kamata a yi miki kyauta ta musamman bayan auren mu." "Ina so na ganki cikin daula ne ‘kawata." "Amma da wallahi sai na saka an kama min İbrahim, wallahi sai na saka ya fahimci ni ba kalar wacce zai daka a banza bace. Sai ya girbi abinda ya shuka a lokacin ni kuma nayi masa rata sai dai gani daga nesa.” Zakiyya tayi dariya tace, "Kina da iko yarinya, Kiyi abinda kika ga dama ke matar manya ce wallahi." A tare suka kuma tafawa suna cigaba da tattauna yadda abubuwa zasu kasance.            A gidan su Ibrahim a safiyar bayan Alhaji ya gama waya da Abban su Fiddausi ya kalli Ibrahim da yake zaune a gefen sa yace, "Kaji jiya a asibiti ta kwana wai sila dukan da kayi mata ya saka cikin jikin ta ya zube sai da aka yi mata wankin ciki." Ibrahim yayi murmushi, "Wallahi Alhaji k’arya take ni ban dake ta ba, duk abinda ya faru tsarawa tayi akwai abinda take son cimmawa shiyasa tayi hakan. In da na dake ta ai Yaya Sulaiman zai fad’a maka, ko kuma tana so tace tun dukan safen ne bai tashi zubar da ciki ba sai dare? Alhaji ka bar Fiddausi kawai.” Hajiya tace, "Ni daman nasan wallahi baza ka yi mata dukan da zai saka tayi b'ari ba sai dai in akwai abinda yake zuciyar ta." Alhaji yace, "Kenan dai yanzu ta kammala idda, daman dan me ake yin idda….? saboda a tabbatar babu shigar ciki a cikin watanin, to ita ya zube har wankin ciki ma ance anyi mata, babu damar kome yanzu sai an sake sabon d'aurin aure." Hajiya tace, "Daman ban kawo ma zai mayar da ita ba wallahi a raina, ai wanda yaso kashe ka baza ka so ka sake rab'ar sa ba, ya cigaba da neman kud’in da Allah ya bashi wacce ta fita." Alhaji yace, "Amin, amma ki tuna itace uwar d'an sa ko da nan gaba in yaji yana da sha'awar mayar da iya ai ba wani abun bane ba. Kuma shi kansa mahaifinta wallahi ba’a son ransa hakan ta faru ba, yana son zaman y’arsa da İbrahim dan ya fad’a min cikin yaran sa mata ita kadai ce ba’a kawo masa case d’in sa gaban sa.” "To yanzu ai y’ar tasa ta nuna bata yi kaga shikenan ai kowa ya huta, Zan rik’e Amir daga nan har girman sa in sha Allah, koda babu ni nasan y’an uwan sa zasu rik’e shi bazai tab’a kukan rashin uwa ba a rayuwar sa.” "Kedai yarinyar nan ta fita daga ranki kamar ba kece kike son ta kafin auren ba. Yadda kika so yarinyar nan ko matan yayyen sa baki so haka ba.” "Na so ta sosai Alhaji, amma ai Alhaji duk Wanda zai zo gaban idanun ka yace baya son d'anka baya qaunar sa kuma sai ya kashe shi duk son da kake masa daga ranar ko bai fita ba sai kaso mafi yawa ya ragu.” Alhaji yace, "Gaskiya ne, kai Ibrahim kana son dawo da ita ne?." Ya girgiza kai yace, "A'a Alhaji Allah ya had'a kowa da rabon sa, taje inda take hange ni kuma na tsaya a matsayina." Alhaji yace, "Amma karatun addinin nata da aka yi kwadayi aka auro ta bai amfana mata da komai ba, tayi abinda wata wacce bata je islamiyya bama bazata aikata shi ba. Ni kaina daga lokacin da tazo nan ta fad’i kalaman nan taji duk duniya ta fita daga raina, Ina yi ne sabida nason kana sonta, Ina yi kuma saboda Amir. Amma Tunda yanzu haka ya zama shikenan Allah yasa shine alkhairi." Suka amsa da amin kafin İbrahim ya tashi ya fita dan wajan aiki yake son wucewa, yayi alqawarin mantawa da komai ya fuskanci rayuwar sa, ya kuma alqawarin bazai bar wata damuwa tayi tasiri a kansa ba. Fiddausi ko itace mace d’aya tal a duniya ya barta. *Bayan kwana biyu.* Nana Haleema Mai daki Boook2 Paid 500. Book2 003 A cikin kwanakin Fiddausi ta ware ta shiga harkokin ta kamar ba ita ba ta mayar da komai ba komai bane sabgar ta kawai take suna zuba soyayya ita da Alhaji a waya tunda bata bashi damar zuwa ba har lokacin. Soyayya suke kamar saurayi da budurwa ya shagab’ata da kud’i komai take so sai ya bata, ko bata tambaya ba zai bata hakan ya saka take saka son sa sosai suna Shan soyayya abin su. Sosai tayi kyau abin ta tayi k'iba ta sake yin haske kamar ba ita ba. A safiyar ranar litinin Wanda yayi daidai da sati uku da rabuwar su da ibrahim suna waya ita da Alhaji ya takura akan shi sai yazo gida gaskiya dole ta bashi dama yaje wajan Kawu Sa’idu. Tana kashe wayar taji Mama na kiran ta ta taso ta fito Mama ta dube ta tace, "Wai zaman me kike da a d’aki ko yaushe ko motsin ki ba'a ji ai ta kiran ki bakya Jin mutane?." Fiddausi tace, "Kaina ne yake ciwo kuma Muna magana dasu Ameenatu ne." "Abban kune zai yi tafiya zai je qauyen ku yake kiran ki har ya tafi." "Ban ji ba wallahi, dana fito mun yi sallama." Mama tace, "Sai ki zo ki d’ora mana abinci rana ta fito" ta fad'a tanaa tashi ta shiga daki ba tare da ta sake cewa komai ba. Fiddausi ta b'ata rai ita bata son wannan aikin da ake saka ta wallahi, ko yaushe ace tazo tayi girki tana zaune a kwala mata kira ace tazo tayi wannan ita wallahi ta gaji. Kitchen din ta shiga tana mita a zuciyar ta a haka ta d'ora girkin ranta a b'ace. Burin ta kawai ta gama ta fice daga gidan kar a sake saka ta wani aikin. Tana gama abincin ta shiga d’aki tayi sallar azahar tayi wanka tana shiryawa taji muryar y’an gidan su da alama sun zo. Tana gama shirya wa ta fito ta tarar suna cin abincin da ta gama dafawa tayi murmushi tace, "Yaya Sannu d zuwa." Ta kalle ta tace, "Yauwa Fiddausi, ya zaman gıda?." Kafin tayi magana Mama tace, "Zaman gıda gashi nan tana yi Kullum tana zaune a d'aki tana aikin danna waya." Mama ta sake kallon ta tace, "Yayar ki da y'ay'an ki sun cinye abincin da kika dafa, sai dai ki sake d'orawa dan ko naki babu. Nima ban samu ba, kece kika dafa kad’an ga abinci a gida sai ki dafa kad’an kamar wanda aka sammana.” Wani iri taji a zuciyar ta tace, “Kar na dafa da yawa yayi yawa ne ganin Abba baya nan.” “Gashi ai ya k’are yanzu, sai ki dafa abinda zaki ci.” kamar zatayi magana sai ta fasa ta zauna Yaya tace, "Kije ki dafa mun cinye wannan, bamu san baki ci ba ai da bamu cinye ba.” "A'a basai na dafa ba a k'oshe nake." Sai kuma ta mike tace, "Mama zanje gidan Zakiyya." Mama tace, "Babu inda zaki je, Kullum daga yawo nan sai can bakya son zama a gida gabad’aya kamar a kanki aka fara zawarci . Haka kika fita shekaran jiya Amir yazo ya gama zaman sa bakya nan haka aka mayar dashi har magriba bakya gidan. Babu inda zaki je ko koma d’aki ki cigaba da danna waya amma baza ki fita ba.” Fiddausi bata ce komai ba ta koma d’aki gabad’aya zaman gidan ya ishe ta gwara ma tayi auren ta huta da fadan da Mama take mata ga aiki komai ita.              Asiya shirye-shiryen biki kawai ake yi dan lokacin bikin saura sati biyar kashe kudi kawai suke Dan duk abinda suke so Yusuf yana yi musu shiyasa suke abinda suke so saboda akwai kud’i a hannu. Umma Sakina na zaune ita da Umma suna tattauna yadda abubuwa zasu tafi Asiya suka shigo ita da Maimunatu da Kaya a hannun su sosai manya-manyan ledoji suka shigo. Ajjiye kayan sukayi Asiya tace, "Wallahi na gaji Umma, kin ji bayana?." Umma Sakina tayi dariya tace, "Waye ya fad’a miki zama amarya sauk’i ne dashi?." Umma tace, "kun siyo kayan gabadaya?." Maimuna tace, "Fridge ne yana akorikura tare da Fauziyya yanzu zasu ‘karaso." Umma ta kalli Umma Sakina tace, "Sakina babu kud’in tv ma, Gashi gida yake ginawa makeke tv din ma a saka uku ko hud’u ma. Dan fa Mun samu ma yace zai zuba kayan gado da kujeru ne mu na kitchen ne kawai dasu tv da fridge, amma kinga kud’in nan yana kakarewa.” Umma Sakina ta kalli Umma tace, “ai babu ta inda kud’i zai kakare mana bayan akwai Yusuf” ta kalli Asiya tace, "Ke Asiya ki sake kiran sa ko d'ari biyar ne mu sake karba." Asiya ta b'ata fuska tace, "Umma Sakina miliyan uku fa ya bayar yanzu sai na sake yi masa maganar wani kud’in? Ni wallahi bazan iya ba." Umma Sakina tace, "Had'a ni dashi ni na fad’a masa Tunda baza ki iya ba.” Asiya ta wara ido cikin mamaki tace, "Haba dan Allah ni wallahi na gaji da tambayar sa kud’i wallahi. Wannan ai sai yaga kamar ma kudin nake so.” Umma Sakina ta girgiza kai ta rik’e hab’a tace, "Zaka zamuyi dake Asiya? Muna murna zaki shiga inda zamu huta mu samu abinda muke so tun yanzu kin fara yi mana hanya-hanya?." Asiya tace, "Ba haka bane bafa Umma Sakina, kawai dai bana so yaga Ina yawan karbar kudi a hannun sane shiyasa kawai.” Umma tace, "Waye ya fad’a miki zai ga kina k'arba a hannun sa?" Umma ta kalli Sakina tace, "Duk shirin da muke yiwa yarinyar nan gani take a banza yake, duk kudin da aka karb’a ba ita aka kashewa ba,? Inda tasan abinda aka yi da bata ce haka ba.” Umma Sakina tace, "D’auka take yi ai mu kud’in banza muke kashewa. Malama ki tashi kiyi masa waya kice kina so ki ganshi in yazo ki san yadda zakiyi ya k'ara miki kudi, ke ai macece kina da kissa a jinin ki, in ya tashi zuwa ki tabbatar kin shafa wannan turaren da na baki." Asiya tace, “Yanzun zan kira shi?. “Eh Yanzun nan.” ta tashi ta shiga d’aki ita sam bata son abinda suke sakata yanzu ta fisu so sai ta shiga gidan a lokacin ya zama matar sa babu abinda zai yi mata ko me zatayi, yadda ko bai bata ba zata d'auka amma yanzu sai ya raina ta. Yadda take masa shagwab'a waya dole yace mata da yamma zai zo dan ta rikita shi burin sa yazo ya ganta yaje meye damuwar dan baya son damuwar ta kk kad’an. Kafin yamma d’in tayi wanka ta shirya sai khamshi take yi na turaren da aka bata har lokacin Umma Sakina tana haka tazo ta wuce su lokacin da yazo har ya shigo cikin gidan. Fuska babu walwala ta shiga yana hango ta sai ya mik’e tsaye yana kallon ta yace, "My love lafiya kike?."K’arasowa tayi ta zauna tayi shiru bata ce komai ba shima ya zauna yana kallon ta yace, "Meya faru ne wai?." Asiya ta kalle shi tace, "Ni ban San ta inda zan fara ba." "Fara ta ko Ina my love." Tayi shiru na wani lokaci kafin sauke numfashi tace, "Wacce zata yi min gyaran jiki ce na bata kudina har naira dubu dari biyar shine ta hadu da scammers suka kwashe mata kudin account gabadaya basu bar ko sisi ba, atm din ta ta yar a wajan biki akayi amfani dashi aka kwashe komai my love. ni ban san me zance ba ta kira ni tana ta kuka k’arshe tazo gidan nan tana fad’awa su Umma." Kallon ta yake yi har ta kai karshe yace, "To meye abin damuwa a nan? Waye ya wuce tsautsayi? Ai kowa hakan zai iya faruwa dashi.” "To ni haka za'a yi bikina babu gyaran jiki?" Ta fad'a tana kallon sa tare da turo baki gaba. Murmushi yayi yana kallon ta yace, "ni za'a yiwa gyaran fa, ai dole a biya a yi miki dan ko anyi ni zai yiwa amfani, akan me bazan biya ba?” Ya fad’a yana murmushi tare da kashe mata ido d’aya. Dariya tayi ta kulle fuska yayi dariya kadan yace, “Kar ki damu zan tura miki kudin sai ki bata." Murmushi tayi tace, Thanks you my love." Dariya yayi kad’an yace, "Ni kin tayar min da hankali ko gida ban je nayo nan. Yadda naji maganar ki na dauk’a wani abun ne ya faru ashe kan five hundred thousand naira kike d’aga hankalin ki.” ya fad'a yana kallon wayar sa da take ta vibration. Sunan Ameena ya gani hakan ya saka ya danna power wayar ya kalli Asiya yace, "Zan koma store ana nema na." "Ko dai Auntyna tana waya?." Kallon ta yayi kamar zai ce wani abun sai ya fasa ya canja maganar yace, "international Passport din ki ya fito yana hannuna ana gama biki sai mu wuce kiyi umrah a matsayin…” sai yayi shiru yace, “ki canka.” Farin ciki ya mamaye zuciyar Asiya ji take yi kamar tayi tsalle sabida murna amma sai tace, "ai ban san matsayin meye ba, ka fad’a min.” Ya girgiza kai yace, “sai lokacin yayi zan fad’a miki.” Tayi murmushi tace, “Allah ya kaimu." Shima yayi murmushi yace, "Amin my love.” Sai kuma yace, “Ko kuma let me tell you dan ki kasance a cikin shiri” ya fad’a yana matsowa kusa da ita ya fad’a mata suka hada ido yayi daga gira sai ta kulle ido ta fita ta shiga gıda shi kuma ya tafi yana murmushi. A guje ta shiga gıda tana fadin, "Umma ya bani dubu dari biyar din" ta fad'a tana ihu tana tsalle a falo. Umma Sakina tayi murmushi tace, "Ke ki kalle ni kawai, duk wani abun da ya kamata na Riga na aikata miki shi tun kafin yanzu. Bayan wannan sai me?." "Umma Sakina yace min international passport dina da muka je muka yi yana hannun sa ana daura aure zamu wuce umrah a matsayin tukwuicin first” ta fad’a tana shiga d’aki a guje cikin farin ciki Mara misaltuwa. Umma Sakina da Umma suka tafa suna dariya Umma tace, "Sakina ke k’arshe ce wallahi." Umma Sakina tayi dariya tace, "A dai shiga gidan, wallahi sai Uwar gidan ta gwammace bata aure shi ba, baza mu fitar da ita ba amma sai taji Inama ya sake ta koma gidan su da zama." "Daman Umma Sakina na tsane ta wallahi, ta fini kyau kuma da alama shima yana sonta har yanzu, ni dama a fitar da ita daga gidan da nafi jin dad’i” Asiya ta fad'a tana fitowa daga d’aki. "Barni da ita, kedai ki cigaba da shiri." Cikin farin ciki ta wuce zuwa kitchen.            Ameena kuwa hankalin ta a tashe yake jikin Zaytun yayi zafi sosai gashi ita kanta bata da Lafiya baza ta iya tuk'a mota ba balle ta kaita asibiti, hankalin ta ya tashi ta bata magani amma zazzab’in bai sauka ba, ya Kira shi bai d’auka ba bai kuma kira ta ba gabad’aya ta rasa abinda zatayi. Lokacin da ya shigo ta kwantar da Zaytun d’in akan kujera taje ta dauko ruwa da towel ta goge mata jikin ta ya shigo ya samu tana kuka. Da sauri ya d’auke ta jin yadda jikin ta yayi zafi sosai hankalin sa ya tashi ya tab’a wuyan ta yace, “Amma ta me yake damun ki?.” A lokacin Ameena ta fito da ruwa da towel a hannun ta tana fitowa bai jira abinda zata ce ba ya fara yi mata fad’a yana cewa, "Dan rashin hankali yarinya bata da lafiya baza ki kaita asibiti ba kin zauna da ita a gida sai ta mutu? Meyasa kike yin haka ne wai?, bak’in kishin naki har Akan y’arki?." Cak ta tsaya tana kallon sa yanayin ta duk ya canja murya a sanyaye tace, "Sau nawa Ina kiran ka baka amsawa?." "Baza Kiyi min text ki fad’a min ba? Meye amfanin motar ki da baza ki kaita da kanki ba?, meye amfanin su Sani da baza ki kira su su kai ki ba?. Na lura rashin mutuncin har Zaytun ya shafa to na rantse da Allah wani abun ya same ta sai ranki ya baci" tana fad'a ya fita da Zaytun a hannun sa ta nemi waje ta zauna akan tiles ta jingina da bango. Bata san adadin lokacin da ta d’auka a wajan ba kiran sallar magriba ne ya saka ta ta tashi sai kuma ta tuna ba sallar ma zatayi ba ta koma kan kujera ta zauna tayi tagumi tana kallon wani wajan daban. Zazzab’i take ji sosai ga kanta yana yin shiru amma hakan bai hana ta tunani ba. Tausar zuciyar ta ta fara yi a hankali sai ta fara karanta suratul waqi'a a zuciyar ta a haka har taje k’arshe zuciyar ta nayi mata sanyi sosai cikin mintina kad’an. Shigowar sa ta gani da Zaytun a kafad’ar sa tayi bacci hannun sa da ledar magani bai ko kalle ba ya wuce sama ya kwantar da ita akan gadon sa ya shiga band’aki. Bata yi k’ok’adin bin sa ba tana zaune sai da ta gaji da zaman dan kanta sannan ta tashi ta hau saman itama tayi wanka da ruwan zafi ta saka kaya marasa nauyi amma masu kauri ta kwanta tayi lamoo akan gdo gabad’aya zaman gidan ya ishe ta Ina ma zai barta taje Bauchi wajan Yaya da zata fi kowa farin ciki. Tunawa da Yaya Adam sai ta mik’e zaune ta jawo wayar ta ta kira lambar sa amma bata shiga ta ajjiye wayar ta koma ta kwanta, Tabbas da Yaya Adam yana nan da gatan ta yana kusa da ita, Bata san bacci ya kwashe ta ba sai da alarm d’in wayar ta na k’arfe ukun dare ya buga ta mik’e zaune dakyar ta kalli Agogo taga karfe uku ta tashi ta shiga band’aki. Alwala tayi tazo ta zauna kan sallaya ta kalli gabas tana karatun alkur'ani a bayyane a hankali ba tare da ta rike alqur’ani ba. Ta jima a haka kafin ta fara lazimi tana addu'a a zuciyar ta tana fad’awa Allah damuwar ta. Har bayan asuba tana zaune tayi azhkar ta tashi kenan taji motsin sa ta juya suka had’a ido ya mik'a mata Zaytun bai ce komai ba ta karb’e ta tace, "Ina kwana." "Lafiya lau" ya amsa yana fita daga d'akin ta tab'a jikin ta taji babu zafi, ajjiye ta tayi ta rike hannun ta zuwa band’aki tayi mata wanka tana yi mata wanka suna dariya tana yi mata surutun da ta saba yi har suka fito. Shirya ta tayi ta shayar da ita tace, "Yaye ki ma zanyi wallahi na gaji Zaytun, da k’afar ki kina yawo ko ina ga d’an banzan baki a wajan ki kamar wacce ta shekara uku, kowa kin sani komai kin sani hutawa nima zanyi wallahi.” Zaytun din sai tayi dariya kammanin ta da baban ta ya bayyana sosai a akan fuskar ta itama Ameena sai tayi taja kumatun ta ta fara yi musu, Bata koma bacci ba suka sauka tare Zaytun tana ta kiran Mummy da Daddy ta shiga kitchen ta d’ora tea ta dafa indomie ta gama ta juye a bowl ta had’a tea suka fito falo tana ci tana bawa Zaytun din ma tana ci tana bata labari ita kuwa mamakin surutun Zaytun take yi. Tun daga sama yake kallon su yadda suke zaune suna dariya sai ya samu kansa da yin murmushi shima sun burge shi sosai musamman ita Ameenatou da tayi kyau cikin shigar da take so doguwar riga yar kanti mara nauyi, ta gyarawa Zaytun gashin kanta yayi kyau sosai sai k’yalli yake yi tun daga nesa. Yana k’arasowa ya ajjiye mata maganin yace, "Baki damu ki nemi maganin ta ba ko?" Yadda yayi maganar cikin sanyi a kuma tausasbe shine ya saka ta kalle shi tace, "Yanzu daman zan d’auko abinci taci." Kallon ta yake yi dan ta rame sosai yana so ya tambaya dalilin ramar amma wata zuciyar na hana shi yin hakan. "Ina nawa abincin?." Ta d’ago ta kalle shi suka had’a ido sai ta mik’e yace, "Barshi Tunda baki yi dani ba." Tayi shiru ya matso kusa da fuskar ta yace, “Meyasa bakya yin abinci dani?.” Ta kalle shi ido cikin ido tace, “zan gyara.” Ya yamutsa fuska yace, “ya kamata.” Yayi hanyar fita tace, "Daddy!." Juyowa yayi y kalle ta da alamun tambaya a fuskar sa jin sunan da ta kira shi dashi bata bari ya samu damar magana ba tace, "Dan Allah Ina so zanje Bauchi gidan Yaya na kwana biyu a can.” Bai ce komai ba ya juya ya fita ta bishi da kallo har ya b’ace ta juyo ta cigaba da cin abincin ta.             A gidan su Ibrahim shima ya ware sosai neman kud’in sa kawai yake ya manta da komai bai bar wani abu a zuciyar sa ba balle ya dame shi. Hankalin sa kwance yake yin komai in ba Amir ya gani bama mantawa yake da wata Fiddausi albarkacin Amir yake tunawa da ita. Da sallama ya shiga gidan su ya tarar kowa yana nan a cikin y’an uwan sa mata ana hira, tunda yaga anyi shiru da ya shiga yasan hirar Fiddausi ake yi ya murmusa yace, "Yau duka kuna gıda kenan?." Yayar sa Hadiza tace, "Eh Muna gida, Muna mayar da zancen tsohuwar matar ka. Ashe har fita take ma baka sani ba, azo a d’auke ta a mota a fita da ita duk baka sani. Kai Allah na gode maka da ka raba mu da mugun iri tun kafin abun yayi nisa.” Murmushi yayi kawai yace, "Ni ba wannan ba, nazo muku da labari mai dadi Hajiya." Hajiya tace, "To Ina Jinka." "Hajiya mai gidan bulon da nake aiki daman ai na fad’a miki kwanaki indai zai zo duba mu yaga ya muke aikin ni kawai yake samu wajan ko?." "Eh ka fad’a min wannan." "Yau ma yazo ya tarar dani ni kad’ai a wajan aikin, sai ya kira ni muka je babban company sa na sarrafa siminti tare dashi, yanzu ya mayar dani can yace yaga Ina mayar da hankali akan aiki sosai. Hajiya albashi duk wata dubu dari biyu yake bayarwa kin ga ma..." ya fad'a yana saka hannu aljihu ya fito da kud’in yace, "har ya bani na wannan watan wai tunda yayi tsakiya nazo nayi shirye-shiryen fara aiki a sabon waje" ya fad'a yana ajjiye kud’in a gaban Hajiya. A tare suka had’a baki suka ce, "Alhamdulillah! Allah mai iko, Allah mai yadda taso.” Yaya Hadiza tace, "Kaga alkhairi lokaci d'aya, Allah ya rik’e maka Ibrahim yasa a fara a sa'a, Allah yasa shine madub'in arzukin ka." Ya amsa da amin Mariya tace, "Kai ai fitar Fiddausi daga rayuwar ka ai alkhairi ne, kwata-kwata yau kwana ta nawa da fita daga gidan ka har alkhairi ya same ka haka?. Sai tayi dani sani nan gaba wallahi Allah ya bamu rai da lafiya. Mai farar k'afa kawai." Yaya tace, “mai farar k’afar gaske, watakila ma itace take daqile taurarin alkhairin sa, yanzu gashi tana fita ana samun cigaba.” Ibrahim da yake jin su dariya yayi kawai dan yanzu basa son wanda zai ce ma yana son Fiddausi balle kuma so sota yace, "Babu mai farar k'afa fa a addinince, magana ce irin taku ta hausawa.” Hadiza tace, “eh babar d’an kace ai dole Kace haka.” Yayi dariya mai sauti ya kalli Hajiya da take yi masa addu’ar samun nasara da dacewa yana amsawa da amin ya tashi ya fita ya bar kud’in a hannun hajiya yace ta ajjiye masa. #Nana Haleema #book2 Book2 004 Ameena tana gama shan tea din sama ta hau kamar kar ta yi hanyar saman sa sai kuma tabi hanyar saman da nufin gyara masa dakin, duk fad’a da masifar da zai mata bata iya yin banza sa gyaran d’akin sa sai ta gyara masa har ta saba ma. tana shiga ta zaunar da Zaytaun akan kujera ta fara gyara gadon kamar ko yaushe gefe d’aya ne zai tabbatar maka da mutum ya kwana a d’akin. A gefen bedside taga wayar sa na chaji a bayyane tace, "Mantawa yayi kenan." Bata je inda wayar take ba ta cigaba da gyara d’akin. Kira ne yake ta shigowa cikin wayar bata kalla ba ta cigaba da abinda take yi har ta gama gyara d’akin tayi masa turaren wuta ta wanke band’aki, ta fito daga band’akin ta sake jin kira ya shigo sai ta ja ta tsaya tace, "maybe ko yana tunanin ya yar da wayar ne yake kira" ta fad'a tana nufar wajan a lokacin kiran ya katse taga number ce dai take ta kira. Wani kiran ne ya sake shigowa ba tare da tunanin komai ba ta d'auka ta saka a kunne kafin tayi magana akace, "my love Ina ta kira baka d’auka, Ina ka shiga yau baka kira ni ba nayi missing sweet voice din ka ba?.” Dum dum zuciyar Ameena ta buga ta cire wayar daga kunnen ta sake kallan wayar taga number ce babu suna gaban ta na fad’uwa sosai jikin ta har rawa yake yi ta rasa me zatayi kashe wayar zatayi ko magana zatayi? Dakyar ta iya cewa, "ya manta wayar a gida" tana fad'a ta yanke kiran ta zube akan gado tana hakki zuciyar ta na bugawa duf duf duf, da sauri ta d’auki ruwan da yake gefen gadon tasha ta lumshe idanun ta saboda abinda take ji a zuciyar ta. Ta jima a haka wayar na hannun ta kafin ta ajjiye ta a gefe ta kalli screen din wayar hoton Zaytun ya bayyana a kai tana dariya ta had’d’iye abu mai d'aci tana kulle idanun ta, dakyar ta iya jan numfashi ta ajjiye wayar a kan gadon ta tashi ta d’auki Zaytun ta rike hannu Zaytun da take ta kai kawo a d’akin suka fita. Tana sakkowa ‘kasan yana shigowa ganin ta ya saka yace, "Kinga wayata?". Kai ta d’aga alamun eh ya hau saman da sauri ita kuma ta zauna akan kujera. Ba jimawa ya sakko ya fita daga falon fitar sa ba jimawa Rukayya ta shigo kana kallon fuskar ta kasan akwai damuwa sosai a kai dan idanun ta yayi ja sosai alamun tasha kuka, ga fuskar ta wajan kumatun ta shima yayi ja sosai abin ka da farar fata, bata yi mata magana ba har ta zauna sannan ta kalle ta tace, "Rukky me yake damun ki haka?." Sai kawai Rukayya ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ganin haka sai Ameena tayi shiru ta barta tayi kukan dan zata ji dad’i. Ta jima tana kukan kafin ta tsagaita Ameena ta tashi ta dauk’o mata ruwa tace, "karb’i ki sha." Ba musu ta karb’a tasha ta ajjiye kofin tana sauke Ajiyar zuciya sosai itama ta zauna kusa da ita tana kallon ta. Rukayya ta tashi shiga bandaki ba tare da tace komai ba amma kallon ta kasan akwai abinda yake damun ta, Ameena ta bita da kallo dan tasan maganar bazata wuce guda d'aya ba. A fusace taga ya shigo ta d’ago ta kalle shi kafin tayi magana tana yana bin ta da kallo sai tayi shiru ta kawar da kai dan tasan akwai abinda zai ce yace, "Waye ya baki izinin tab'a min waya?." Kafin ta samu damar magana ya sake yace, "Waye yace ki tab’a min waya!?." Yadda yayi tsawar sai da ta firgita Zaytun ta nutsu sosai kamar ita ake yiwa fad’an tana kallon sa. "Ina ruwan ki da wanda yake min waya da zaki d’auka har ki fad'i maganganu mara dadi? Ke a ganin ki wannan shine kishin?, ki dauki waya kina zagin yarinya k'arama akan kawai zata auri mijin ki, waye ya fada miki har yanzu ana wannan shashancin? Waye ya fad’a miki ana wannan shirmen har yanzu?.” Ameena bata ce komai ba ya nuna ta da yatsa yace, "Kin zubar da girman ki a idanun ta tun kafin ta shigo, in ma kina yi dan ki tsoratata akan kar ta aure ni kin yi a banza wallahi Ameena, aure babu fashi sai dai Kiyi duk abinda zakiyi, kuma wallahi aka sake min waya kika d’auka sai ranki yayi mugun b'aci, dan wallahi sai nayi miki abinda baki tab'a zato ba. a haka kamar baza kiyi ba ashe mage ce mai kwanciyar d’aukar rai, ke ga mai miji ko? Ki fad’a min me kike yiwa mijin naki har da zaki wata kiyi mata warning?." In kujerun falon sun motsa itama ta motsa bata ce komai ba yaja tsaki yace, "Allah ya baki ikon sake tab'a min waya ki gani" yana fad’a ya juya zai fita suka had'a ido da Rukayya da take tsaye a bayan sa tana kallon sa cikin mamaki da tsoro dan duk abinda yace taji ta kuma gani. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya wuce ta ya fita fuskar sa a d'aure. Ameena har lokacin kanta yana sunkuye bata d'ago ba Rukayy ta tako a hankali tazo kusa da ita ta dafa kafad'ar ta sai a lokacin hawaye ya zubo mata tayi saurin gogewa taja numfashi wani abu mai nauyi ya tsaya mata a tsakiyar kirjin ta sai sukar ta yake yi. Dukkan su shiru sukayi aka rasa mai magana Ameenatu ta kalli Zaytun da tsoron tsawar ya saka ta bacci a akan kujera tayi murmushi ta sake goge idanun ta har lokacin bata ce komai ba. Ameenatu ta kalli Eukayya tace, "Muje sama." Tare suka mik’e Rukayya ta d’auki Zaytun sauka hau sama har cikin d’akin Ameenatou suka zauna a kan gado. A gefen bedside Rukayya taga maganin da yake ajjiye ta kalli Ameenatou ta sake kallon maganin tace, "Ameena maganin waye wannan? Amma dai ba naki bane ba ko?.” Ameena ta kalle ta batayi magana ba Ameena tayi murmushi tace, "Ke a ganin ki wannan tsawar da fad’an na iya yau ne? Hmmmm!." Rukayya ta sake kallon maganin ta kalle tace, "Kin rame da yawa Ameenatu duk kin koma kamar ba ke ba." Murmushi Ameenatu tayi tace, "Kiris ya rage a d’auki gawata a gidan nan Rukayya, na gaji da zaman gidan nan na gaji Ruky!" Sai ta fashe da kuka sosai wanda ya tab’awa Rukayya zuciya itama ta fashe da kuka. "Rukayya Jin dadin aure na wata hud’u zuwa biyar kawai nayi a gidan nan daga nan komai ya canja, Yusuf din da na sani a baya bashi bane ba yanzu, ya canja." Kuka suke sosai dukka su biyun babu mai rarrashin wani duk kansu da dalilin yin kukan nasa, sun jima a haka kafin Ameenatu ta goge idanun ta ta kalli Rukayya tace, "Kema ki daina kukan ya isa haka, babu abinda kuka zai magana addu'a itace maganin mu. Ban d’auka kina da damuwa ba ganin ki a gidan nan ga mijin ki yana sonki ban d’auka akwai damuwar da zata saka ki zubar da hawaye ba Ameena.” Rukayya ta sake cewa, "Ameenatu ban San inda zan saka raina a gidan mu ba, Umma kamar ba itace ta haife ni ba fad’an yau daban na gobe daban, Kullum kallo take nak’i aure tunda duk wanda ta kawo ban aure shi ba. Umma da ya kamata ta jani jikin ta ta rarrashe ni ita take min fada Ameenatou, su Zuhra duk sun Raina ni ban isa na saka su suyi ba sabida suna ganin kan mu daya dasu. Yau Umma ta bud'e baki tace ita ta gaji zata saka ayi cigiya a masallaci Wanda yace yana sona zata bada ni, Ameena wai nice nak’i aure ne? Meyasa Umma da mutanen Unguwa suka kasa gane lokaci ne baiyi ba?." Ameenatu ta girgiza kai tace, "Kiyi hakuri lokacin zai zo na tabbata Umman ta fad’i haka ne kawai amma ba yi zatayi ba." "Wallahi zata iya, Baba ne kawai yake rarrashi na Umma da ya kamata ta dinga rarrashina itace take hantara ta, wallahi gidan mu ya ishe ni Ameena na gaji, na fara tunanin had'a kayana na gudu." "Kar Kiyi haka ki cigaba da hak’uri Allah yana sane dake fa." "Yanzu Umma bata tunanin watakila bani da rabon auren a duniya jiran mutuwa nake yi? Meyasa Umma bata tunanin haka Kullum sai fad’a?. Ko d'an shaye-shaye ne yazo burin Umma kawai na amince na aure shi. Ameena nima fa Ina damuwa, kune kawaye na dukkan ku kuna da yara, Ina so nayi auren nima amma jiran lokaci nake yi amma umma bata ganin haka." Ameenatu tace, "Ki kara hak’uri a jikina nake Jin lokacin auren ki ya kusa Rukayya, Ina ma ke Yusuf ya gano ya aura." Idanu Rukayya ta goge tace, "Na gaji Ameena wallahi na gaji, Bawai zaman gidan ne ya ishe ni ba kawai abinda ke yi min ne yake sakawa naji na tsani komai, Baba ya hanani aiki, ya hanani cigaba da karatu da Yanzu nayi nisa, Kullum Ina gida ba dole su gaji da ganina ba." Ameenatu tace, "Wallahi Umma ba tsanar ki tayi ba Ruky, kamar yadda na fad’a miki so take kiyi aure ki tashi kema kiga naki yaran, na tabbata yadda take miki addu'a ke bakya yiwa kanki, tafi kowa shiga damuwa akan wannan abun tana yin haka ne sabida itama y'ar adam ce yau da gobe sai Allah bawai dan bata son ki ba. Uwa ce fa Rukayya, duk wata magana da ake yi a kan ki ta fiki jin zafin abun dole kiga ta damu. Kefa kina da mahaifiyar ma ni kuwa bani da wacce zata yi min addu'ar ma Rukayya." Rukayya tace, "amma fad’a da abinda ake nuna min ba shine zai saka nayi aure ba ko?." "Kedai ko cigaba da addu'a kawai kinji? Wallahi Allah in lokacin ki yayi babu bata lokaci sai kin tafi gidan mijin ki." "Hakan Umma ta kasa ganewa ai." "Ta sani fa Ruky, kawai tana yin haka sabida wani dalili amma ta sani Kiyi hakuri." Numfashi ta sauke tace, "Shiyasa gidan yayi min zafi kawai na tawo wajan ki." Murmushi tayi tace, "Muyi addu'a kawai Allah yana sane damu." Rukayya ta kallo Ameenatu tace, "yaushe kika fara Shan maganin hawan jini?." Ameenatu ta kalle ta tace, "Ba'a fi wata d'aya ba, ke kad’ai kika sani ko Yayan Bauchi bata san Ina da hawan jini ba, dan Allah kar ki fad’awa kowa." "Haba Ameena sirrin ki ai nawa ne ke kin sani, amma ki rage sakawa kanki damuwa, damuwar ke zata cutar ba shi ba.” "A gaban ki dai akayi komai, wannan to ba wani abun bane ba dan baki ga komai ba Ruky." "Ni wallahi sai naji tsoron auren ma na shigata." Tayi murmushi tace, "Kiyi addu'a kawai. Akan wacce zai aura yake min wannan fad’an kawai dan naga ana kira number babu suna dan Allah basai nayi zaton shine yake kira ko yana neman wayar ba? Na d’auka wallahi kalmar dana fad’a bata fi uku ba amma sai gashi ya zamar min tashin hankali tunda gashii ana cewa na zage ta. In yarinyar nan ta shigo gidan nan Ina jin sai na bar gidan nan, tun kafin tazo ana haka Ina ga ta shigo?. Yanzu badan ke bace in a gaban masu aikina yayi min haka da banji kunya ba?. Da ya tozarta ni tozarck na har abada kuwa.” Rukayya tace, "bata isa ba In sha Allah, ai Allah yana tare da mai gaskiya. Ke tazo ta samu baza ta fitar dake ba in sha Allah Ameena.” Ameena ta sauke numfashi tace, "baza ki gane ba Rukayy ki taya ni da addu'a kawai, kuma dan Allah ki rik’e min sirrin nan kar ki fad’awa kowa. Wallahi ban tab’a fad’awa kowa wannan maganar ba babu wanda yasan halin da nake ciki a gidan nan, kema dan kin riska ne kuma na amince dake shiyasa na iya fad’a miki. Ina neman wanda zan fad’awa abinda yake zuciyata dan na ji dad’i.” Rukayya tace, "In sha Allah ke kin san baki da damuwa, Allah ya kawo miki mafita Ameena. Fiddausi sabida hangen ki Keda Zakiyya ta kashe auren ta." "Hmmm bata da hankali ne ai Rukayya, inda nice ita Wallahi babu abinda zai dame ni, saboda samun ina kula daga wajan mijina me ai tayar min da hankali? Koda yake ba duka aka zama d'aya ba watakila ita ta dace da samun mai kud’in. Allah ya had’a ki da miji na gari kawai Rukayya, ba mai kudi ba mai kula dake kawai, in mai kudin ne Allah ya had’a miki duka.” Rukayya tace, "Amin ya Allah Ameena, addu’a ta kenan Allah ya bani na gari.” Ameena ta amsa da amin suka cigaba da bawa juna shawara ko wacce tana kwantarwa da yar uwar ta hankali dan dukkan suna cikin damuwa suke.          A Daren ranar Alhaji Bello ya kai Kansa wajan k’anin mahaifin Fiddausi Kawu Sa’idu yayi masa bayanin komai tare da sanar dashi baya so a d’auki lokaci da gaggawa yake so ayi auren ya sakar masa kud’i ya tafi. Da daddare su Fiddausi suna zaune ana cin abinci Kawu ya shigo da sallama Mama ta amsa tana fad’in, "Yau kaine a gidan?." Ya zauna akan kujera yace, "Eh wallahi, ya gıda da yaran?." Mama tace, "Alhamdulillah, ya mutanen gidan?." "Alhamdulillah." Ya kalli Fiddausi yace, "D’azu wani Alhaji Bello sagagi yazo ya same ni wai ya ganki yana son ki kuma ya samu labari akan komai daya faru dake yasan babu idda a akanki shiyasa yazo yanzu dan da wuri yake so ayi auren ku.” Mama ta gyara zama tace, "Wanne Alhaji Bello din?." Kawu yace, "Wanda dai kika sani shi nake nufi, da alama kuma yana sonta sosai kamar ba sabuwar had’uwa bace. A Ina kuka had’u?." Fiddausi ta gyara zama tace, "A cikin satin da ya wuce ne ya ganni naje gidan Zakiyya, yana tayi min magana sai nak’i yi masa magana shine ya tambayi Zakiyya a kaina tak’i fad’a masa daga nan ban san ya akayi ba." Kawu yace, "Da alama ya biyo ki ya samu labarin komai, Yanzu dai ban bashi dama ba Ina tunani auren naki bai jima da mutuwa ba aga an fara zuwa wajan ki babu dad’i. Sai mutane ma suga kamar da gangan aka kashe auren naki.” Mamaa tace, "Meye rashin dadin? Ai babu idda a kanta ba shikenan in tayi auren ta huta ba?. Su maganar mutane ai ko yaushe a haka suke, in kayi daidai suyi magana in basu yi daidai ba nan ma suyi magana. Dan kawai in abu yazo kawai ayi kar ace za’a tsagaita sabida bakin mutane.” Kawu yace, "To shikenan daman ya bani lambar sa zan kira shi sai na bashi dama yazo su gaisa kafin komai ya biyo baya." Mama tace, "Hakan yayi to Allah ya Muna mana. İn kuma zuwa goben Abban su ya dawo shikenan sai ayi maganar dashi.” Ya amsa da Amin yayi musu sallama ya tafi. #Nana Haleema #Mai daki book2 #F5 Book2 005 A Daren Fiddausi ta labartawa Zakiyya komai suna ta murna cikin farin ciki Fiddausi tace, "Yanzu dai na kusa zama matar Alhaji, Wayyo Allah kamar a mafarki haka nake ganin abun wallahi." Zakiyya tace, "Bari kawai, an sha gwagwarmaya kafin azo nan." "Amma fa akwai sauran damuwa har yanzu." "Mecece ita?." "Abba, Wallahi babu lallai ya amince da auren nan cikin kwanakin nan." "Ba kince yana qauye ba?." Fiddausi tace, "Yana qauye, amma kin san zai dawo ai." Zakiyya tayi shiru kafin tace, "Addu'a zamu dinga yi masa Allah yasa ya amince ayi a wuce wajan kawai." "Sai dai addu'ar kam wallahi, Mama na kira na Ina zuwa" ta fad'a tana kashe wayar ta fita dan ta jiyo kiran da Mama take mata. Zama tayi Mama ta kalle ta tace, "Daman batu ne akan wanda yaje wajan kawun ki neman auren ki." Fiddausi tayi shiru bata ce komai ba Mama tace, "ya akayi yasan auren ki ya mutu har kin gama idda Fiddausi?." Fiddausi tace, "Ban sani ba Mama, na tabbatar kuma nbaZakiyya ce ta fad'a masa ba dan da zata fad'a min." Mama tace, "Abin ne da mamaki, ya akayi ya sanki har yasan gidan nan da labarin ki?. Yanayin yadda ya kawo kansa kamar da akwai sabo tsakanin ku." Fiddausi tayi dariya tace, "To Mama a ina zan ga wannan babban mutum din har mu saba? Kuma yaushe auren nawa ya mutu da zan fara kula wani?." "Hale ne Fiddausi, amma abin akwai daure kai fa. Dan yasan auren ki ya mutu wanna ba wani abun bane, amma ya akayi yasan cikin ki ya zube babu idda yanzu?." "Allah ne masani" ta fad'a tana kallon wani wajan daban dan bata so maganar tayi tsaho. Mama tace, "Shikenan Allah yasa ku daidaita." Ta amsa da amin ta tashi ta koma d'aki a ranta tana Jin tsoron dawowar Abba dan tasan sai ya maimaita mata abinda Mama ta fad'a yanzu gashi shi ba irin Mama bane da wuri yake saurin gano k'aryar mutum. Yadda take kuka sai ka d'auka zane ta akayi ko kuma wani gaggarumin abun aka aikata mata, bil hakki kuka take irin kukan wanda aka cuta ko aka yiwa rasuwa babba take yi da iyakar karfin ta, yana zaune gefen ta gabad'aya ya damu ji yake kamar shima yayi kukan hankalin sa duk ya tashi zuciyar sa babu dad'i hakan har ya bayyana akan fuskar sa. "My love dan Allah ki bar wannan kukan." Sai a sannan ta d'ago ta kale shi tace, "Na d'auka za muyi zaman lafiya nida matar ka ashe ita a wajan ta ba haka bane, dan Allah ka bata hak'uri kace mata ba Ina niyar auren ka dan na ci fuskar ta ba." Shiru yayi bai amsa ba ransa y sake b'aci akan abinda Ameena ta aikata ta sake cewa, "Tunda ta d'auki wayar a raina nasan itace saboda nasan in ba ita ba babu wanda zai d'auki wayar ka, bata fara magana ba sai da na gama magana na d'auka kaine hakan y saka na ambaci my love da nasan itace da bazan fad'a ba kodan gudun b'acin rant. Da tayi magana na d'auka zamu gaisa ne ko babu komai y'arr uwar tace ni a yadda na d'auka ba kishiya ba ashe a wajan ta ni kishiya ce. Wani zagin ban tab'a Jin irin sa ba a rayuwata!" Ta fad'a tana Jan numfashi tare da goge idanun ta. "Ya isa haka ki yi hak'uri ki daina wannan kukan" ya fad'a a sanyaye yana kallon ta. Ta kalle shi tace, "Na fara jin tsoron auren ka my love, Allah ya sani bana son tashin hankali musamman tsakanin kishiyoyi. In hakan zai jawo matsala gwara na hak'ura dakai na bar mata......" kafin ta k'arasa ya katse ta yace, "Akan me? Saboda ita? Ke kina ganin ko ke kin hak'ura ni zan hak'ura ne?. Ki bar wannan maganar bana so domin bazata yu ba." "Nidai ka bata hak'uri dan Allah, ban fad'a maka dan na 'bata maka rai ba, na fad'a ne d'azu saboda raina ya b'aci kuma saboda ka yiwa tukfar hanci kafin shigowa ta gidan ka. Kaga in tana fad'a min Ina yin shiru watarana bazan yi shiru ba sai dai kazo Kaga Muna dambe hakan kuma kai zai tayarwa da hankali." Kai ya girgiza yace, "Haka ne, kar ki damu na gode da kulawar ki a gare ni, ke mai son kwanciyar hankalina ce na san da hakan. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru kinji?." Kai ta d'aga tayi murmushi shima yayi yace, "Har naji dad'i da gabad'aya kin tayar min da hankali." "To ka tashi ka tafi dare yayi kar nayi wani laifin a wajan ta." "Kawai korata kike." "Ni na isa? Kawai dai bana son shiga hakkin tane." Tashi tsaye yayi tare da yin murmushi yana kallon ta yace, "Wani dare nake jira irin na yau wanda baza kice na tafi dare yayi ba." Murmushi tayi ta tashi tsaye tace, "nima haka my love." Murmushi yayi itama tayi suka yi sallama daga wajan ya tafi. Yana fita ta saki darıya tare da tafa hannu tace, "Yanzu aka fara Ameena, sai kin bar gidan Yusuf da k'afar ki wallahi, domin Yusuf nawa ne ni kad'ai wallahi, baki isa nayi kishi dake ba" ta fad'a tana shiga cikin gida.            Yusuf yana komawa kai tsaye dakin Ameenatu ya nufa ransa a b'ace sosai ji yake kamar a lokacin ma abin ya faru ya same ta a falon ta na sama a zaune tana kallon tv, yadda aka turo k'ofar sai da taji tsoro ta kalle shi shima ita yake kallo yama rasa ta inda zai fara. Ransa a b'ace yake so yake ya tabbatar mata da hakan shiyasa yayi shiru yana so ya samo abinda zai fad'a mata wanda itama zata ji abinda yake ji. Ganin baiyi magana ba itama sai tayi shiru ta mayar da hankalin ta kan tv din kamar bata san yana wajan ba sai a sannan yace, "Ke wai duk abinda zuciyar ki ta raya miki a ganin ki shine daidai?." Kallon sa tayi so take taga in a buge yake yasha giyar sa ta tattara ta gudu dan bazai jibge ta a banza ba. "Ba magana nake miki ba!?" Ya fad'a cikin tsawa. Ta kalle shi ta tabbatar a hankalin sa yake tace, "Ban San abinda nayi ba ai shiyasa." "Okay baki sani ba ko? Zagin wacce zan aura da kika yi duk baki san kin yi ba ko?." "To naga d'azu kayi min masifar a gaban k'awata me ya sake dawo da ita yanzu?." Idanu ya wara yana kallon ta yana takowa inda take yace, "Masifa? Nine masifaffen?." Ameena tace, "Naga ai ya wuce ko?." "In ke a wajan ki ya wuce a wajena bai wuce ba, domin tana da mahimmaci a rayuwa Ina sonta dan son da nake mata zan kawo ta gidan nan, in ma bak'in ciki kike da hakan ya kamata ki ajjiye ki sauke shi domin babu abinda zai hana ni aure ta." "Daman kaji nace zan hana ka ne? Nasan ai ban isa na hanaka ba, ko sanda kace min zaka aure ta saboda tausayi ne ni nasan ka fad'a ne dan na shiga maganar a wajan Amma ba wai dan hakan bane a zuciyar ka, Ko mata uku zaka k'aro suzo mana Allah ya kawo su lafiya ai ba a kaina zasu zauna ba" ta fad'a a tausashe tana mik'ewa da niyar barin wajan. Hannun ta ya rik'e ta baya ta lumshe ido Jin d'umin hannun sa a jikin ta ba ta hanyar duka ba yace, "Ni kike fad'awa ko mata uku ne na kawo?." Ta zame hannun ta daga hannun sa ta kalle shi tace, "Eh mana, saboda ban isa na hana ba gwara ka kawo su din kowa ya huta." "Lallai raini ya fara shigowa tsakanin mu kenan, har abin ya kai ina fad'a kina mayar min da magana Mara dad'i Ameena?" Ya girgiza kai yace, "amma kar ki damu zan goge rainin nan gaba ko ance ki fad'a min baki isa ba ki fada ba." Tayi murmushi tana kallon sa bata ce komai ba shima ita yake kallo sai kuma yaja tsaki ya bar wajan ta shiga d'aki itama ta kulle kofa ta jawo akwati ta fara zuba kayan ta dana Zaytun domin safiya tana yi zata wuce Bauchi ta gaji da abubuwan da Yusuf yake mata tana shanyewa, gwara ta bar masa gidan yayi duk abinda yake so dashi. K'arfe bakwai na safe ta sauka da jakar dan ta tabbatar bacci yake duk wani abu nata wanda tasan zatayi amfani dashi ta d'auka ta saka a bayan mota ta rufe, ta bud'e gaban mota ta ajjiye Zaytun da take bacci ta shiga mazaunin driver ta zauna tana kallon gaban ta tare da sauke numfashi, bata tab'a jan mota zuwa wani gari ba koda a cikin garin Kano ne balle kuma wajan Kano, amma a jikin ta take jin zata iya da dai ta zauna a gidan ya kashe ta gwara ta tattara ta bar masa gidan ya huta. Da wannan tunanin tayi addu'a ta yiwa motar key mai gadi ya bud'e mata ta fita daga gidan. A safiyar Abban su Fiddausi ya dawo daga qauye bayan ya huta ne da yamma Kawu yazo ya same shi da maganar Alhaji nan da nan ransa ya b'aci ya saka aka kira Fiddausi yana ta fad'a akan hakan, lokacin da ta shigo ta zauna gaban ta fad'uwa kawai yake musamman da taga Kawu ya tabbatar maganar ce ya kalle ya yace, "Kawun ki yazo min da wata magana yanzun nan, abinda nake so naji shine daman shi Alhajin kuna tare dashi ne tun kina gidan Ibrahim?." Da sauri ta girgiza kai alamun A'a tana jin wani iri a jikin tace, "Ban San shi bama ni." "To ya akayi yasan auren ki ya mutu kuma babu idda a kan ki? Ko kina so kice min a radio aka sanar da hakan?." "Wallahi Allah ban sani ba" ta fad'a a bayyane a zuciyar ta tana karanto istigifari. "Gaskiya akwai alamar tambaya a lamarin nan naki, meyasa wasu basu zo ba sai shi? Ya akayi ya sanki ya san auren ki ya mutu da ciki kuma yanzu babu cikin?." Shiru bata amsa ba tsoro duk ya mamaye mata zuciyar ta. Abba ya kalli Kawu yace, "Akan me zaka bashi damar da zai zo yau ya ganta? Sai kace jira ake yi auren ta ya mutu a fara neman auren ta?." Kawu yace, "Nima nayi wannan tunanin Yaya, amma sai na tuna babu idda a kanta a yanzu." "To dan babu idda a kanta daga mutuwar auren ta sai tayi wani auren kamar daman plan aka shirya? A Bari ta cike kwanakin iddar mana in yaso ranar da ta cika ma sai tayi auren ba damuwa ta bane, amma yanzu abin sam babu tsari kafin duniya tayi da kai kayi da kanka." Mama da take wajan tace, "Amma ba haram aka aikata ba ai tunda babu idda a kanta." Abba yace, "Na fiki sanin ba haram aka aikata ba ai, amma ban amince a fara zuwa wajan ta da neman aure ba sai nan da wasu kwanaki, sai lokacin iddar ta ya cika sannan na amince wani yazo da wani batu na aure. shi kuma zan saka a bincika min shi duk da sanannen ne a bangaren kasuwanci amma tarihin sa da asalin sa da komai ba'a sani ba." Ya kalli Fiddausi da kanta yake k'asa yace, "Tashi kije, kar ki saurare shi sai nan da wani lokaci nasan ba idda kike ba amma hakan nake so ayi. Ke bama shi ba indai ba Ibrahim tsohon mijin ki ba ban amince ki saurari wani a yanzu ba." Ta amsa da to ta fita tana ji yana yiwa Kawu d Mama zuciyar ta a cushe kamar ta kurma ihu haka take ji. Mama na shigowa falon ta mik'e tsaye tace, "Mama zanje gidan Yaya." Mama ta kalle ta tace, "Me ake yi?." "Babu komai." "Sai kin dawo" ta fad'a tana shiga d'aki ita kuma ta saka hijjabi ta tafi. Gidan yayar tata ta fara zuwa bata jima ba ta fita ta nufi gidan Zakiyya bayan ta yi masa waya in yana da lokaci yazo su had'u a gidan Zakiyya. Tana shiga ta cire hijjabin ta Zakiyya da take zaune tana Shan abu a kofi ta bita da kallo tace, "Malama saka hijjabin mijina bai fita ba." Fiddausi tace, "amma na cewa Alhaji yazo nan." "Yanzu zai fita ai." Motsin sa taji ya saka ta saka hijjabi ya fito suka gaisa yace, "Naji abu mara dadi a wajan Zakiyya, Allah yasa hakan ya zama alkhairi." Tayi murmushi tace, "Amin ya Allah daddyn Fahad, na gode." Ya kalli Zakiyya yace, "na wuce." Tabi bayan sa ta raka shi har ya fita kafin ta dawo. Zakiyya tace, "Wannan murmushi da kike yi ya kamata ki dinga ragewa kisan mijina ne ba alhaji ba." Fiddausi tayi dariya tace, "Dallah ba wannan ba, Abba ya hana ni kula kowa wai sai lokacin idda ta ta cika." "Kamar ya? Ya manta babu idda akan ki ne?." "Hmmmm! Bai manta ba wallahi kawai yace wai in aka ga na fara kula maza sai ace ma plan ne mutuwar auren nawa, dan haka ba yanzu ba sai lokaci ya cika in yaso ranar dana gama iddar ma a daure min aure." Zakiyya tace, "Eh kuma fa da hakan wallahi, za'a yi saurin gano mune muka shirya komai gwara hakan. Allah yasa bakya nuna wata alama da za'a gane hakan." Fiddausi tace, "Ke harda rantsuwa d'azu akan karya, sai jan istigifari nake." Zakiyya tayi dariya tace, "Amma hakan fa shine daidai abinda Abba yace, bara yazo mu fad'a masa yayi hakuri ku cigaba da waya ai naga anci wata d'aya wata biyu ya rage." Fiddausi tace, "Ke naje gidan Yaya Mama ta fad'a mata wands yazo neman aurena ta tambaye ni haka ne nace eh wallahi rashin Jin dadi karara akan fuskar ta." "Ke wai Alhaji Bello wasa ne? Ai mai karfin imani ne in yaji zaki aure shi baiyi bak'in ciki ba wallahi." Farin ciki ya cika zuciyar Fiddausi ta koma da baya ta jingina tace, "nima lokacina yazo yanzu." Ta sake kallon abinda Zakiyya take sha tace, "Wai me kike sha ne?." "Maganin sanyi ne wallahi, mai shegen kyau ina fada miki." "Kin kuwa tuna min, akwai wani maganin sanyi da kika bani wallahi dana sha ke baki ga abinda na dinga fitarwa ba kuma iya rana d'aya. Ke kin sanni babu juriyar Shan magani sai na watsar." Zakiyya tace, "Ke waye ya fada miki kayan Surayya Halin Yau wasa ne? ai wallahi ban tab'a Shan maganin sanyin da nake jin dadin sa nake ji yana min aiki kamar maganin ta ba, kedai ki jira kawai lokacin auren ki yayi wajan ta zamu je tayi miki hadin kaza na musamman dan sai mun rikita wannan bawan Allah wallahi. Zaki yi mamaki in kika yi amfani da kayan ta." Fiddausi tace, "Gashi na fda miki daga sha sau d'aya naga aikin sa. Ke kika had'a ta da Ameena kenan naji ta tab'a yi min maganar ta." "Nice wallahi, ga Ameena indai ba kayan ta ba yanzu bata amfani da komai, ke har Yayar ta Bauchi a wajan ta take siyan magani a kai mata har can." Fiddausi tayi dariya tace, "Tunda dai a kano take kawai Kiyi shiru magana ta wuce zamu je walalhi." Wayar Fiddausi aka kira hakan ya saka ta kalle ta tace, "gashi nan yazo Ina Jin." Zakiyya tace, "Bara na shigo dashi, baza ki canja kaya ba?." "Ke rabu dani yazo kawai." Dariya Zakiyya tayi ta fita Jim kad'an suka dawo tare da Alhaji a bayan ta yana amsa waya. Sai da ya zauna ya gama wayar sannan ya kalli Fiddausi yace, "Fidy lafiya kika min wannan kiran? Kin sana gabana sai fad'uwa yake." "Barka da rana." Numfashi ya fesar yace, "Barkan ki, ya kika tashi?." "Alhamdulillah." "Me yake damun ki?." "Abba ya dakatar da batun zuwan ka gidan mu yau." "Innalillahi, Allah yasa ba laifi nayi ba." "Babu laifin komai Beb, kawai yace ba yanzu ba sai lokaci idda ta ya cika. Kuma in ka lura hakan shine daidai in ba haka ba za'a yi saurin gano komai shiryawa mukayi." Ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "Haka ne gaskiya. Hangen manya a ko yaushe yafi namu, shiyasa hausawa suke cewa abinda babba ya hango yaro ko mai zai taka bazai gani ba. Ai anci wata d'aya ko?". Kai ta daga tace, "Ashe kana sane." Murmushi yayi yace, "baza ki gane yadda nake son na mallake ki ba shiyasa kike ganin bana sane." Fiddausi ta had'e rai tace, "Ni yanzu ba wannan ba, Ina so a kama min Ibrahim ya kwana a cell dan ya tabbatar matar baban mutum ya Mara har bakına ya fashe." Nan da nan ya murtuke fuska yace, "Me kike so ayi masa?." "Nidai kawai ya kwana a cell shine abinda nake so." Waya ya fito da ita Zakiyy tayi sauri taace, "A'a Alhaji a bar zancen Ibrahim a bari a daura auren afi yin komai da gadara. Kaga kai yanzu ba mijin ta bane in ka zama mijin ta kana da ikon yin komai." Fiddausi ta turo baki gaba tace, "Eh a bari a yi auren, Nidai so nake ayi masa abinda zai sann yanzu ni ba sa'ar bace. Ya tabbatar da yayi kuskuren dukan mace kamata." Alhaji yace, "Kar ki damu wannan kamar anyi an gama ne, ko prison kike so a kai shi wallahi sai yaje koda ya bar Kano kuwa." Tayi murmushi shima haka yace, "Amma zamu dinga had'uwa a nan ko?." Ta d'aga kai alamun eh yayi murmushi yace, "Da sauki." Hira suka yi kadan ba mai tsaho ba saboda wayar da ake tayi masa ne ya saka shi yi musu sallama ya wuce. #Nana Haleema Book2 006 Ameenatu sai bayan azahar ta shiga cikin garin Bauchi kafad’ar ta da bayan ta sun yi bala’in gajiya bata tab’a doguwar tafiya kamar wannan ba tunda ya fara tuk'a mota a haka ma ta tsaya a wani gidan abinci taci abinci tayi sallah ta huta. A ‘kofar gidan Yaya tayi parking ta fito ta d’auki Zaytun da itama gajiya ta gama bayyana a tare da ita ta shiga cikin gidan da sallama. Karamin gıda ne mai fallen dakuna guda uku d'aya nata mai had’e da falo da band’aki d'aya na mai gida d'aya kuma na yara, Jin sallamar ta ya saka Amira lek’owa ganin da gaske fa ita din ce sai ta saki ihuu tace, "Aunty Ameena ce wallahi!." Itama dariya tayi Amira ta karbi Zaytun Yaya ta fito tana fadin, "Wai Ameena ta ce a gidan?." "Nice Yaya, Wayyo bayana" ta fad'a tana shiga dakin da Yayan ta fito tare da zama akan kujera ta zauna tace, "Hidaya kawo mata ruwa." Wacce ta kira da Hidaya ta fita ya kawo ruwa mai sanyi ta bawa Ameena sai kuwa ta karb’a tana sha tana sauke numfashi. Ta kalli Amira da Zaytun take hannun ta tace, "Amira ki mata wanka inda ruwan zafi ta gaji sosai." Da to Amira ta amsa ta fita Yaya ta kalli Ameenatu tace, "Sai kawai a ganki babu labari?." "Hmmm Yaya ni kaina a safiyar nan naji sai nazo gidan nan, da kaina fa na tuk'o nazo baki ji yadda nake jin bayana ba kamar zai b'alle." Da mamaki da tsoro Yaya ta zaro ido tace, "Ke kadai fa kika ce Aminatou?." "Wallahi ni kad’ai Yaya, yanzu wanka nake so nayi sai na kwanta." Jin hakan Yaya sai ta mik’e ta shiga bandakin ta da yake cikin d’akin ta dauko bokiti ta fita ta zubo mata ruwa mai zafii ta sirka dana sanyi ta wuce ta kai band'aki ta ajjiye mata sannan ta dawo tace, "Taso Kiyi wankan, dole ai ki gaji, daga Kano zuwa nan ai da nisa.” Dak’yar ta mik’e ta kalli Amira da ta gama yiwa Zaytun wanka tace, "Dauki key din motata kije ki danna wannan remote din zaki ji tayi ‘kara sai ki bud’e ki d’auko jaka a baya kizo ki saka mata kaya, ki bata abinci" ta fad'a tana shigewa band’akin. Wankan tayi ta fito aka bata doguwar Riga a kayan ta saka ta kwanta a gadon Yaya da yake gefe nan da nan bacci ya d’auke ta. Yaya ganin zafi zai dame ta ya saka ta d’auko k’aramar fankar ta mai chaji ta kunna mata a kusa da ita dan taji dad’in baccin sosai. Itama Zaytun tana gama cin abincin tayi bacci aka kwantar da ita a kusa da Ameena suka fita suka koma dakin yaran sabida kar a tashe su. Sai bayan la'asar ta farka ta tashi zaune lokacin fankar ma chaji ya k'are ta kashe mata ta kuma tashi ta shiga band’aki ta wanke bakin ta t sake yin wanka da ruwan da ta gani ta fito ta saka kaya ta fito tsakar gidan a nan take Jin hayaniyar su. "Lah Aunty Ameena!" Karamin d'anta Yaya mai sunan Baba wanda suke Kira Daddy ya fad’a yana tasowa a guje ya rungume ta. Ta kalle shi tana murmushi tace, "D’azu dana zo kana makaranta." "Aunty kin zo min da alawar kano?." "Nazo maka da ita, Hidaya jeki ki bude’e jaka ta akwai Leda zaki ganta ki d’auko min." Ta fad'a tana zama kusa da Yaya da take kallon ta. Yaya tace, "Sai kici abinci ko?." Yaya ta kalli Amira tace, "D’auko mata abinci taci." Amira ta tashi da Zaytun a hannun ta ta d’auko abincin a flasks ta ajjiye mata Ameenatu ta bud’e taga lafiyayyen dambu ne ta baje ciki tana ci a nutse. Ameena ta kallo Amira tace, "Ina Muhammad ne? Ban ganshi ba." "Tare suke tafi kasuwa da Abba yanzu zaki ga sun dawo." Ta kai Ameena ya girgiza ta cigaba da cin dambun ta kad’an ta rage Yaya ta kalle ta tace, "Zaytun dai bata Rigima kamar bata ganki bama." "Yaye ta ma zanyi wallahi, na gaji Yaya shekara biyu ai nayi kokari.” "Ai tana cin abinci gashi tana tafiya harda gudu ga magana tun d’azu take mana hira kamar ba y’ar shekara biyu ba, tana da wayo sosai.” Yaya kallon Ameenatu din take yi tana shan ruwa bayan ta gama tace, "in kin gama ki same ni a dami Ameenatou" ta fad'a tana shiga d’aki. Ledar da Hidaya ta kawo mata ta bud’e ta basu cakes da ta kwaso musu da cincin da chocolate. Suka dinga murna t tashi ta shiga dakin  da Yaya ta shiga ta zauna kusa da ita. Yaya ta fuskance ta tace, "Yadda kika ce min ke kad’ai kika zo hakan ya tabbatar min da bai San kin tawo ba." Ameenatu ta tab'e baki tace, "Yaya ko ya sani ba damuwa zaiyi dan zan tawo ni kad’ai ba, nifa arzukin Amma nake ci da take sona da yanzu na jima a gidan nan." "Bai dai sani din ba, in ya sani bazai barki ki tawo ba ai Kano zuwa Bauchi ba tuk'in mace bane Ameenatou. Meyasa kika yi doguwar tafiya haka mijin ki bai sani ba?." "Ina yake da lokacina da zan fad’a masa Yaya? Na fad’a masa dai Ina Jin shekaran jiya ne yayi min banza bai amsa ba ya fita, ni kuma yau ji nayi bazan iya cigaba da zama a gidan bane gwara na tawo nan." Yaya ta sauke numfashi tace, "Kowa ya ganki yasan kin rame Ameenatu, za’a yi tunanin kin yi rashin lafiya ne ko kuma kina da ciki ko kuma akwai damuwa a tare dake" ta rik’e hannun ta tace, "Damuwar nan da kike sakawa a ranki ba itace mafita ba Ameenatou, addu'a itace kan gaba a wajan maganin damuwar ki in kina addu'a mantawa zaki yi da komai." Idanun ta suka ciko da hawaye tace, "Ina yi wallahi Yaya, ko bazan yi sallah ba na saba sai na tashi da daddare nayi lazumi nayi addu'a har gari ya waye, badan Ina addu'ar bama da ban San ya zan koma ba." Yaya tace, "to kishin ne a zuciyar ki haka?." Ameenatou tace, "Da Ina kishi amma yanzu bana yi Yaya, wallahi Yaya na yarda da tasirin addu’a domin kamar ba’a yi kishin Yusuf a zuciyata ba yanzu, ina ji amma ba kamar baya ba. Sannan duk wani abu da kika sani nasa ya fita daga raina shiyasa wannan ba shine abinda yake damuna ba. Damuwa ta sai a kwana a tashi bai damu da ya nake ba ba balle kuma ya kika kwana jiya, in kin ganshi a inda nake to tabbas Zaytun ce babu Lafiya." "Ameenatu kuma ba wani abun kika yi masa ba?." "Yaya kema fa kin zo gidan kinga ya nake ciki, har kika zo tafiya bai bani damar ganin sa ba balle nace masa kinzo yana d’aki yana waya da matar da zai aura. Me nayi masa Yaya?" Ta fad’a hawaye na sakko mata tayi saurin gogewa. Ta sake kallon Yaya tace, "Yaya asibiti a d’ora ni akan maganin hawan jini......" ta ‘karasa fad'a tana fashewa da kuka sai kuma ta cigaba da cewa, "İn na cigaba da zama da Yusuf wallahi ciwon zuciya ne zai kama ni, yau duka gobe zagi jibi fad’a akan wacce zai aura, dame zanji?. Yaya bani da kowa a kusa y’an uwan mu da muke uba d’aya kinfi kowa sanin halin su, ko wacce burin ta taji damuwar da y’ar uwar ta take ciki badan ta taya ta jimami ba sai da tayi farin ciki ta yad'a, zumuncin uwa daya uba d’aya kawai muke yi. Inda ace akwai zumunci mai k’arfi tsakanin mu Yaya bazan zo Bauchi ba a wajan su zan zauna, a dangi mama ko dangin Abba wa zanje na fad’awa damuwa ta? Yaya Adam ne gata na wanda zai tsaya min shi kuma yayi min nisa a yanzu ko a waya bana samun sa. Ke kad’ai nake da ita a duk duniya Yaya, dan Allah ki barni na zauna a anan har a gama bikin sa na koma." Shiru Yaya tayi tana rik’e da hannun ta har lokacin ita kanta zuciyar ta ta karye amma bata son yin kukan saboda kar ta sake karyawa Ameenatu zuciya hakan ya saka ta daure tace, "Shikenan to ya isa kukan, Allah zai shiga cikin lamarin ki in sha Allah." Ameenatu ta goge idanun ta ta kalli wayar ta tace, "kin gani ki Yaya, na tabbatar yaga bana gidan amma bai kira ni yaji Ina naje ba, yasan ban saba fita ban fad’a masa ba tunda yaga bana nan yasan akwai inda naje amma bai kira ba saboda bai damu ya sani ba." Yaya tace, "Kiyi hak’uri komai zai wuce ai Ameenatu lokaci ne zaiyi dana sanin duk abinda yayi miki. Kuma wallahi a jikina nake jin har gobe Yusuf yana sonki, wani dalili ne ya saka yake yi miki wannan abubuwan Ameena.” “Yaya ba wani so wallahi, ba kukan canjawar da zaiyi in ma zai canja watak’ila lokacin ya kashe ni ai Yaya, duk yadda zan miki bayani baza ki gane ba Yaya. Yarinyar da zai aura fa har ta fara had'a ni fad’a dashi yazo yaci min mutunci a gaban Rukayya da daddare ya sake dawowa ya sake fad’a min maganganu marasa dad’i har na kasa jurewa na fara mayar masa, shiyasa a safiyar yau d’in na gudu nan, na gaji wallahi banza iya ba.” Yaya tace, "Tabbas kudi ba shine kwanciyar hankali ba, ga kudin ga komai na rayuwar duniya a gidan auren ki amma kwanciyar hankali  kika rasa. Mu kuma babu kud’in babu abubuwan more rayuwar amma Muna da kwanciyar hankali alhamdulillah. Kowa da yadda Allah yake tsara masa rayuwar sa Kiyi hak’uri wata rana sai labari." Shiru tayi na wani lokaci tana jan numfashi bata ce komai ba. Yaya tace, "Allah ni da naji kina zancen ma zaki yaye Zaytun d’auka nake ciki ne ma dake." Bata san lokacin da tayi murmushi ba amma bata ce komai ba tayi shiru. Yaya tace, "Saura kwana nawa bikin nasa?." "Wallahi ban sani ba” ta fad’a murya na yin rawa. "Bazan bari ki zauna a nan ba Ameena in nayi hakan na zama Babbar banza ai, zaki zauna dai na kwana biyu zuwa uku sai ki koma." Ta kalli Yayan tace, "Na koma ya kashe ni kenan?." "Bazai kashe ki ba Ameena, ko wacce mace hak’uri take a gidan mijin ta baki San abinda yake k'unsa mata ba amma daurewa ake a kawar komai sai a zauna lafiya." Ameena tace, "Yaya dan baki San zaman da nake dashi bane shiyasa kike cewa na koma. Yaya magani fa nake sha kin manta?.” Yaya tayi murmushi tace, “Ban manta ba Ameena, bazan tab’a mantawa ba ai Ameena. Ki dai huta na kwana biyu Ameena, Allah ya k’ara mana hak’uri baki daya" ta fad'a tana tashi tana fita tare da goge idanun ta, babu yadda zata yi ne amma da Ameena bazata koma ba, da ace akwai Wanda zai tsaya musu wallahi bazata koma gidan sa ba, to meye amfanin zaman gidan? Komai lalacewa gidan mijin ka yafi rufin asiri musamman a wajan su da basu da iyaye.             Yusuf koda ya tashi yaga babu motar ta bai bi ta kanta ba ya fita yaje gidan su suka gaisa da iyayen sa ya wuce store, saboda aikin ginin sa da wuri ya dawo ya sake ganin babu mota nan ma bai wani mayar da hankali ba ya cigaba da abinda yake gaban sa. Fita ya sake yi bai dawo ba sai bayan i'sha ya sake ganin babu motar ta ya hau sama yayi wanka ya saka kaya lokacin karfe tara na dare ya duba compound din gidsn ta window amma babu motar ya sakko zuwa d’akin ta dan a tunanin sa ko ta kai motar gyara ne. komai na d’akin yana kashe da alama bata dawo ba taja tsaki ya hau saman ya d’auki waya nemo number ta ya kira amma is not reachable. Zai sake Kira kenan kiran love ya shigo nan ya datse kiran ya kira ta suka fara wayar da suka saba. A haka yayi bacci ya manta ma da batun kiran Ameenatu. Da asuba ma da ya tashi ya manta da batun bata nan bai sauka masallaci ba dan ya makara sallah yayi a d’akiki kawai ya kwanta. Kiran wayar sace ta tashe shi ya d’aga kai yaga k’arfe goma na safe ya kalli wayar yaga sunan Amma ya d’auka da sallama yace, "Amma barka da safiya." Daga can ‘bangaren tace, "Barka dai, Ina Ameenatu ne Ina kiran ta bana samu tun jiya, na aiko tun jiyan akace bata nan. Had’a ni da ita yanzu zamuyi magana." Yusuf gaban sa ya fad’i tunawa da bai fa ganta ba jiya ya diro daga kan gadon yace, "Tana d’akin ta bara na kai mata" ya fad'a yana sakkowa k’asan bayan ka kashe wayar ya shiga d’akin Ameena. Yadda d’akin yake komai a kashe babu haske zai tabbatar maka da mutum bai kwana a ciki ba, gaban sa ya fad'i ya dafe kai yace, "Me hakan yake nufi wai?." Da sauri ya ‘karasa ya bud’e band’aki amma babu kowa ya fito daga d’akin ya shiga na kusa dashi amma duka bata nan, ‘kasa ya sakko ya duba kitchen da ko Ina amma bata nan. "Innalillahi, Ina yarinyar nan taje ne wai?" Ya fad'a tana fita gate yana fad’in, "Baba! Baba isihu!." Baba Isihu ya k’araso da sauri yace, "Yallabai barka da safiya." "Barka dai, nace matar gidan nan ta fita da safen nan ne?." "Yallabai ai tun jiya da safe kamar k’arfe bakwai zuwa takwas da ta fita da mota bata dawo ba har yanzu." "Hasbunallahu wani'mal wakil!” Ya fad’a yana dafe kansa kafin ya kalli Baba yace, “Shikenan na gode" ya fad'a yana komawa ciki nan take wayar sa ta fara ‘kara kiran Amma na shigowa. "Na shiga uku me zan cewa Amma ne?." Hankali a tashe ya d’auka ya saka a kunne Amma tace, "Ina take ne?." "Ammm tana bandaki ne in ta fito zan kira ki" ya fad'a a diririce. Amma ta yanke wayar ya dafe kai ya sake fita. ‘Bangaren d’akin masu aikin ta yaje suka ce masa tun safiyar jiya bata dawo ba. Hankali tashe ya koma ciki yana kiran ta amma har lokacin wayar bata tafiya yana ta zagaye a falon ya rasa abinda yake masa dad’i. Hankalin sa ya tashi dan bata tab’a aikata haka ba duk inda zata je tana fad’a masa. "Ameena Ina kika je? Kina Ina ne?" Ya fad'a yana sake kiran ta amma Ina bata tafiya. WhatsApp ya shiga ya Kira ta voice call amma bata online ya Kama k'ugu yana sauke numfashi. "A Ina ta kwana dan Allah?. Ina taje?.” "Asslaamu alaikum!." Aka fad’a ana shigowa falon. A firgice ya juya ganin wacce ta shigo gaban sa ya sake fad’uwa tsoron sa ya bayyana k’arara a fili ya kasa amsa sallamar sai ido kawai da yake bin wacce ya shigo dashi dan yasan asirin sa ya gama tonuwa. #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema Book2 007 Kallon sa take yi shima ita yake kallo kafin tace, “Yaya Yusuf Ina kwana.” Bai iya amsawa ba dan a rud’e yake gabad’aya da ganin hakan ya saka ta kuma cewa, “Amma ta aiko ni wajan Aunty Ameena, bara na hau saman wajan ta” ta fad’a tana nufar hanyar saman. Kasa mata magana yayi dan bai abinda zai ce mata ba har ta hau saman ba jimawa yaga ta dawo ta kalle shi yana inda ta bar shi a tsaye har lokacin tace, “Yaya bata nan, tana Ina?.” “Taje asibiti” ya bata amsa a takaice yana fita daga falon ta bishi da kallon rashin gaskiya tace, “Anya kuwa abinda yake fad’a haka ne? Ya cewa Amma tana bandaki ni kuma yace min taje asibiti.” Fitowa tayi daga falon zuwa wajan mai gadi tace, “Baba Isihu ina kwana.” Yayi murmushi yace, “Lafiya lau Hajiya Humaira.” “Ina Aunty Ameena? ta fita ne?.” Baba yace, “Hajiya ai tun jiya da ta fita da safe bata dawo ba har yanzu, kafin shigar ki ma mai gidan yake tambayata na sanar dashi abinda na fad’a miki.” Humaira ta girgiza kai tace, “Okay, bud’e min zan fita da mota” ta fad’a taba yin wajan motar da tazo da ita ta shiga Baba ya bud’e mata ‘kofa ta fita. Tunda Yusuf yaga fitar ta yasan ya shiga uku yau, gabad’aya fad’an Amma yake tsoro gashi bai San inda take ba balle in ta kira shi yace ta tafi wani wajan. Bashi da gaskiya shi kansa ya sani bai San abinda zai cewa Ammah ba shine babban tashin hankalin sa. Fitar Humaira ba jimawa sosai Amma ta kira shi yana ganin kiran gaban sa ya fad’i ya dafe kai bai iya d’auka ba har ta katse aka sake Kira ya d’auka tace, “kazo Yanzun nan ina neman ka” tana fad’a ta yanke kiran yaja numfashi ya tashi ya hau saman dan dole ya amsa kira. wanka kawai yayi ya d’auki mota ya fita shi tsoron had’uwa da Amma yake bai San me zai ce mata ba gabadaya. Da sallama ya shiga falon ta ya same ta a zaune ita da Humaira d’in ya Harare ta a ransa yana fad’in munafuka ya k’araso ya zauna yace, “Barka da safiya Amma.” “Ina Ameenatu take kace min tana bandaki?” Ta tambaya ba tare da ta amsa gaisuwar ba. Ya rausayar da kai yace, “Amma taje asibiti ne.” Amma tace, “dah kace min tana bandaki, yanzu meye gaskiyar zancen a cikin abinda kace? Band’aki ko asibiti?.” Humaira tace, “Amma Baba Isihu fa yace min tunda ta fita jiya da safe bata dawo ba har yanzu, yace min shima Yaya Yusuf din da safiyar nan ya tambaye shi inda take.” Yusuf ji yayi kamar ya kifa mata mari amma babu damar yin hakan sai harara kawai ya daure yaji Amma tace, “Ina taje Yusuf? Ina taje ta kwana kai kana gidan ka kwana a ciki baka san bata nan ba?.” Ya shafa kai yace, “Amma dana dawo na d’auka tana gidan sai bacci ya d’auke ni shi…….” A tsawace Amma ta dakatar dashi tace, “Rufe min baki ko na tsinke ka da mari.” Ya saukar da kai k’asa yana jin wani iri wai Amma ce take cewa zata mare shi yace, “Kiyi hakuri.” Kamar hak’urin take jira ya bata sai ta sake fusata tace, “Me yake damun ka ne haka?, dan zaka yi aure ita baka da damu da lamarin ta ba kenan ko?. Yarinya kuna gida d’aya matar ka ace bata kwana a gida ba Baka sani ba sai gadi kake tambaya dan tsabar lalacew da tonawa kai asiri?. Ace mai gadi ne zai fad’a maka matar ka bata kwana a gidan ba Yusuf? Kai a wajan kaa wannan siyawa kai mutunci ne?. Ko mai aikin matar ka in da hali na gari in bata nan ai ya kamata ka sani balle kuma matar ka.” Shiru yayi bai ce komai ba kafin ta sake cewa, “Matar ka ta aure bata kwana a gida ba dan rashin kula da rashin mutunci ace baka sani ba har safiya? Na Kira kuma kayi min karya kace tana d’aki ka sake min wata k’aryar kace min ta tafi asibiti, yanzu tana Ina?.” Ya kalli Amma yace, “Wallahi ban sani ba, bata tab’a irin haka ba tunda muke, na Kira ta bana samu.” Amma taja tsaki ta d’auki wayar ta ta kira Ameenatu cikin ikon Allah aka samu wayar ta shiga ta d’auka da sallama tace, “Amma barka da Rana.” Sai da yayi Ajiyar zuciya jin maganar ta da alama lafiya take. Amma tace, “Barka daughter, ya takwara?.” “Alhamdulillah Amma.” “Kina ina ne na aika gidan akace min bakya nan?.” Daga can ‘bangaren Ameena tace, “Ina Bauchi Amma.” Kallon Yusuf tayi da yake kallon Amma din da wayar a speaker aka saka ta tace, “Bauchi kika tafi babu sallama Daughter?.” Ameenatu tace, “Naso na sanar dake wallahi Amma sha’afa nayi na d’auka kuma ya fad’a miki.” Amma ta kalle shi tace, “Bai fad’a min ba Ameena, amma ke kika ja motar har bauchi?.” Ameenatu tace, “Eh Amma, ai ba wahala kawai dai na gaji ne amma a hankali nayi driving din.” “Duk da haka kinyi ganganci tafiyar tafi k’arfin ki, har yaushe kika iya motar ma da zaki yi tafiya irin wannan?.” “Kiyi hak’uri baza’a sake ba in sha Allah.” “Ya dai kamata, in kin tashi dawowa zan turo da driver ya dawo dake. Ki gaishe da mutanen bauchin.” “To Amma zasu ji in sha Allah, a gishe da Humairah.” “Zata ji” ta fad’a tana yanke wayar tare da bin sa da kallo. Kafin Amma tayi magana yace, “Wallahi Amma ta fad’a min min zata je Bauchi amma ban d’auka jiya zata tafi ba, kuma ban San ita kadai zata tafi ba wallahi da bazan barta ba.” Amma da take kallon sa tace, “To kai rantsuwar ka Abar yadda ce? K’arya kake Yusuf duk abinda zaka ce, baka san zata je Bauchi ba itama ta fad’ane dan kawai ta kare ka kamar yadda ta saba amma baka sani ba, ka fad’a min gaskiya wanne irin bacin ran ka k’unsa mata da ya saka ta tafi gidan yayar ta?.” Yace, “Ba musu nake miki ba Amma, amma wallahi nasan da zuwa bauchi ta fad’a min kuma ni babu abinda nayi mata haka kawai ta……” kallon da Amma take masa ya saka shi kasa ‘karasawa tace, “cigaba mana Yusuf, ni nasan ba kowa ne yake iya kallona yayi min k’arya ba.” Yusuf yayi shiru ta sake cewa, “Saboda zaka yi aure ba ta ita kake yi ba; baka san ma ta d’auki mota ta tafi Bauchi ba har aka kwana aka tashi kuma a gidan kake kwana amma baka duba ta ba balle kasan a inda take. Saboda bata da gata bata da uwa da uba a duniya balle su shiga lamarin ta” ya nuna shi da yatsa tace, “Kaga in baka yi wasa ba hakkin marainiyar nan da kake rainawa ba wallahi sai ya kai ka wuta, alqawarin da ka d’aukarwa mahaifinta a lokacin da ya rik’e hannun ka yana gargarar mutuwa yace ka kula masa da y’ar sa Ameena ka kasa cikawa, Ina so ka tuna wannan alqawarin da ka d’auka ka kasa saukewa ko shi sai ya bibiye ka balle kuma ya hakkın marainiya.” Tayi shiru tana kallon sa kansa a ‘kasa ta kuma cewa, “ka daina ganin kamar babu abinda zai same ka fa ni na tabbatar sai kayi dana sani Yusuf, ko babu raina zaka tuna na fad’a maka zaka yi dana sani akan duk abinda kake aikatawa a yanzu. Kuma yarinyar da ka ke rawar k’afa akan zaka auro ta ba baki nake maka ba amma baza kaji dad’in zama da ita ba, ni na fad’a maka zaka kuma maimaita min wataran in akwai tsahon raina, kar ka d’auka kuma baki nayi maka akan auren kawai haka lamarin yake ne zaka kuma tabbatar da abinda nake fad’a gaskiya” ta girgiza kai tace, “Abu ne a bayyane na abinda kayi mata sai itama tayi maka:” Yusuf ya rausayar da kai yace, “Amma ke shaida ce Ina son Ameenatu tun ba yau ba, son da nake mata ne ya saka na aure ta babu wani abinda nake mata Wanda zai cutar da ita.” Amma tace, “Da gaske? Shikenan to zamu gani ai Yusuf kai da ita waye yake cutar wani, akwai lokacin da hakan zai bayyana ina tabbatar maka da hakan, tashi ka bani waje.” Yusuf ya mik’e a kan guiwar sa yace, “Dan Allah Amma Kiyi hak’uri na amsa nayi kuskure amma bazan sake ba in sha Allah, zanje har bauchin na dawo da ita amma wannan bakin da kika yi min a kan aurena ki janye shi kar ya tabbata Amma.” Tayi murmushi tace, “Ba baki nayi maka ba Yusuf, abu ne a rubuce a kan dutse.” “Kiyi hak’uri!”. “Baka yi min laifi ba, tashi kaje Allah ya bamu alkhairi.” Zai kuma magana tace, “Kaje Yusuf.” Babu yadda ya iya haka ya mik’e ya fita jikin sa a sanyaye matuk’a. Da kallo Amma ta bishi tayi murmushi har ya b’ace tace, “Ina tausyawa ranar da Yusuf zaiyi dana sani akan abinda yake yiwa yarinyar nan, tsoro na kar lokacin yazo ita kuma a wannan lokacin tayi masa nisan da bazai sake samun ta ba.” Humayrah tayi shiru zuciyar ta cike da tausayin Aunty Ameena. Yusuf ransa a b’ace ya kai kansa gida yana shiga gidan ya d’auki waya ya kira ta yayi sa’a ta shiga shima ta d’auka kafin tayi magana yace, “Waye ya baki izinin fita daga gidan nan har ki tafi bauchi?.” Ameena tace, “Nice na bawa kaina izini.” Yusuf da mamaki yace, “me kika ce?.” Ameena tace, “Abinda kaji.” Ya girgiza kai yace, “Okay rashin mutuncin naki har yazo nan kenan ko? Ke a duniya in baki had’a ni da mahaifiyata ba bakya Jin dad’i, babban burin ki a duniya kiga Amma tana yi min fad’a saboda kawai tana sonki ko?. To wallahi in ma wani abun kika yi mata take son ki haka wallahi Nafi k’arfin ki a ta ko wanne b’angare. Yadda kika saka raina ya b’aci akan lamarin nan kema sai naki ya b’aci wallahi sai kin ji abinda naji, ki kuma shirya gobe zan aiko a dawo dake, kuma wallahi ciwon kai Zaytun tayi ta dalilin tafiyar ki da dawowar ki a kanki zan d’ora alhakin Hakan.” Ameena tace, “Ban shirya dawowa gobe ba gaskiya kamar yadda na tafi zan dawo da kaina” tana gama fad’a ta yanke wayar yabi wayar da kallo yana ji kamar ya jawo ta yayi mata dukan tsiya ta wayar. A fusace ya hau saman ransa yana suya ya bud’e fridge dinsa ya d’auko giya ya kafa kai yana sha ko zai ji dadin suyar da zuciyar sa take masa. (A ganin sa amma fa). Sabon machine ne fil ko ledar sa ba’a cire ba ibrahim yake shigowa dashi tsakar gidan su a lokacin Alhaji yana niyar fita Hajiya da Fadima da Amir suna zaune. Duk tsayawa sukayi suna kallon sa daman yasan za’a yi hakan yayi murmushi ya k’araso yace, “kunyi mamaki ko?.” Alhaji yace, “Ka barmu baki sake muna kallon ka ai, k’arin bayani muke so an Ina ka samo wannan?.” Ibrahim yace, “Wallahi Alhaji Ogan mu da na fara aiki a company sane ashe mu uku ya d’auka amma nine kawai a b’angaren mu sauran a wata unguwar suke, shine ya bamu kyautar baburan nan saboda an fad’a masa muna jajircewa a wajan aiki sannan ba’a tab’a bamu kud’i mun b’atar da naira biyar ba, Jin dad’in hakan ya saka yayi mana wannan kyautar yanzu.” Alhaji da Hajiya suka fad’a baki wajan kabbara Alhaji yace, “Kai na taya ka murna Ibrahim, Allah ya rik’e yasa mabud’in arzuki kenan, Allah ya kare ya kawar da idanun makiya. Ni nasan biyayyar da kake mana bazata tashi a banza ba, duk wani abu da yake faruwa da kai na lokaci ne gashi yanzu ya fara wucewa kana ganin ribar abinda kake aikatawa, ka cigaba da rik’e gaskiya a duk Ina kake baza kayi dana sani ba.” Ibrahim ya amsa da Amin yana Jin dadin addu’ar nan da iyayen sa suke masa Alhaji ya fita shi kuma ya zauna. Fadima tace, “Yaya Ibrahim Allah ya tsare ya kawar da idanun makiy.” Ya amsa da amin yana murmushi ya kalli Hajiya yace, “Baki ce komai ba.” Tace, “Dad’i ya hana ni magana Ibrahim , Allah ya sanya alkhairi ya kare ya kuma kiyaye hanya kaji?.” Ya amsa da amin ta kuma cewa, “Allhairi kamar jira ake wani abun ya fita daga rayuwar ka gashi sai b’ulb’ulowa yake yi, me zamu ce da Allah in ba godiya ba.” Murmushi yayi kawai bai ce komai ba dan yasan maganar ta da Fiddausi take Hajiya tace, “Sai ka fara shirye-shiryen aure kuma ko?.” Ya wara ido waje yana dariya yace, “Aure kuma hajiya?.” “Eh Aure Ibrahim, me zaka jira kana da sana’a da abin hawa ga gidan kan ka me za’a tsaya jira?.” Yayi murmushi yace, “Ba yanzu ba Hajiya, zan mayar da hankalina akan neman kud’i nan gaba sai ayi wannan maganar Hajiya.” Hajiya tace, “Allah ya nuna mana, ka zab’o mai tarbiyya ba irin waccan da ta fita ba.” Yayi murmushi yace, “A cigaba da taya ni da addu’a kawai.” Hajiya tace, “Addu’a Kullum cikin yi maka ita ake in sha Allah kuma za’a ga abinda Allah zaiyi, Allah ya baka ta gari wacce zata kula min da kai.” Ya amsa da amin ya tashi tsaye ya fita yana dariya itama haka farin ciki yana shiga ranta domin Tunda ya rabu da Fiddausi walwalar sa ta dawo kamar dah, babu damuwa a kan fuskar sa ko kad’an Kullum cikin nishad’i yake kamar yadda yake a baya. Book2 008 Ameenatu tana sauke wayar daga kunnen ta Yaya da take kallon ta tunda aka fara wayar tace, “Yusuf ne ko?” Ta fad’a tana kallon ta. Ameenatu ta girgiza kai kawai bata ce komai ba dan bata son ma maganar sa. Yaya tayi murmushi tace, “Yaushe yace ki koma?.” “Baice ba, koda yace ma bazan koma a yanzu ba sai dai in da kan sa yazo, in kuwa bai zo ba a nan zan ta zama sai lokaci dana ga damar komawa. Ni wallahi bana so ma yazo gabad’aya haushi yake bani.” Yaya tayi murmushi tace, “Kina tunanin bazai zo ba?.” Ta kalli Yaya tace, “Bazai zo ba Yaya, zan iya rantsewa akan Yusuf bazai zo nan ba.” Yaya tace, “Kar kiyi gaggawar rantsuwa ki bari ki gani in bai zo din ba, amma ni kuma nace miki zai zo.” “Meyasa kike tunanin zai zo Yaya?.” “Saboda zai zo din, ki rubuta ki ajjiye ko ba yanzu ba Allah Yusuf zai zo Ameena.” Ameena tace, “Yaya harda Allah?.” Tayi murmushi tace, “ni na fad’a miki hakan zata faru” ta fad’a tana tashi ta fita ta bita da kallo dan kawai Jin ta take yi amma ita tana da tabbaci akan Yusuf bazai zo ba. Kwanan Ameena uku a Bauchi hankalin ta ya kwanta sosai bata da wata damuwa tun ranar da sukayi waya dashi basu sauke yi ba ta tattara ta ajjiye shi a gefe ta kama addu’a ta zamar mata makamin yak’ar damuwar ta. Ranar da ta cika kwana na ukun suna zaune da safe duk su Hidaya sun tafi makaranta sai Amira kawai suka gama rubuta waec sai kuma Daddy da bai je ba, Zaytun tana hannun hannun Amira suna yin game a waya dan yadda Zaytun take yin game din mamaki yake bawa Amira. Yaya ta kalli Zaytun tace, “Zaytun dai babu ruwan ta ko neman nono bata yi. Indai akwai game zatayi zaman ta babu Rigima.” Ameena tace, “Ai yau na yaye ta ma ni.” Yaya ta kalle ta da mamaki tace, “Kin yaye ta fa kika ce?.” Tayi dariya tace, “Eh mana, shekara biyu take fa ai ta isa yaye, kuma tana cin abinci ga magana a bakin ta, yanzu kinga duk abinda kayi a gidan nan sai ta bada labari, in tayi wani abun Wallahi kamar y’ar shekara hud’u daman kuma yau da niyar hakan na tashi.” “To kuma haka ake yayen ko d’an rubutu na kuka ba’a yi mata ba?.” “Basai anyi mata ba Yaya ba kukan da zatayi, na gaji wallahi shayarwar ita take sake ramar dani. Kuma dmaan tayi girma da shan nono.” Yaya tayi dariya tace, “To Allah ya bata hak’uri da dangana.” Itama Ameena dariya tayi tace, “Sai kace wacce aka yiwa mutuwa.” Yaya tace, “Badan nisa ba ai dana karb’e ta yayen in ta kwana biyu a wajena sai ta dawo, to gari ba kusa ba kuma baban ta ma bazai bani ba.” Ameena tayi murmushi kawai bata ce komai ba dan tasan kuwa babu inda zai bar Zaytun taje yafi so Kullum ya dinga ganin ta a kusa dashi. Daddy ne ya shigo a guje yana fad’in, “Aunty Ameena ga Daddyn Zaytun a waje yazo.” Gaban Ameena ya yanke ya fad’i ta kalli Yaya taga tayi murmushi alamun daman na fad’a miki Ameena ta kalli Daddy tace, “Daddy da gaske kake?.” “Eh Aunty, yace nazo na fad’a muku ne.” Yaya ta kalle shi tace, “Jeka kace ya shigo, Amira mik’o min mayafina.” Tsam Ameena ta mik’e ta shiga d’aki ta barsu a tsakar gidan dan jin zuciyar ta take yi wani iri kamar tana farin cikin zuwan sa kamar kuma bata yi ta kasa tantance a wanne ma’auni zata saka yanayin da take ciki. Tana Jin sallamar sa da gaisawar su da Yaya tana ji tayi banza zuciyar ta nayi mata d’aci ga bugawa da take yi da gudu. “Ameena! Kizo fa” ta jiyo muryar Yaya tana kwala mata kira ta runtse idanu ta sauke numfashi ta tashi ta fito. Tana fitowa suka had’a ido da yake yana zaune yana facing din d’akin da ta fito dukkan su sai da zuciyar su ta buga ta d’auke kai ta ‘karasa ta zauna Zaytun na cinyar sa tace, “Barka da zuwa.” D’auke kai yayi shima daga kallon ta yace, “Barkan ki dai.” Amira da Daddy suka shiga d’aki hakan ya saka Yusuf ya kalli Yaya yace, “Yaya ayi hak’uri da abinda ya faru in sha Allah baza’a maimaita ba, nazo a bani ita mu koma Kano.” Yaya tayi murmushi tace, “Babu komai Yusuf, zaman aure a ko yaushe zo mu zaune ne kuma zo mu sab’a. Allah ya baka ikon rike amanar da mahaifinta ya baka. Yusuf Ameena amana ce a hannun ka ni nasan kasan da hakan, koda mahaifin mu mai bata amanar ta ba kafin ya rasu ita amana ce domin daga gaban magabatan ta ka d’auke ta ka kai ta gidan ka, Yusuf hakkin kula da Ameena yana wajan ka kai Allah ya d’orawa, ko kuka Ameena tayi Allah sai ya tambaye ka, gata kuma marainiya bata da uwa bata da uba kaine uwa da uban ta. Dan Allah Yusuf ka rik’e ta hannu biyu kar ka wulak’anta Ameena. Kana sonta tana sonka dalilin da ya saka akayi auren ku kenan, dan Allah kar ku Bari wani abu yayi tasiri a cikin rayuwar auren ku.” Yusuf yayi shiru yana jin mai take cewa kafin yace, “İn sha Allah Yaya zanyi iya bakin kokarina” ya fad’a jiki a sanyaye sosai yana kallon Ameena ta k’asan ido. Yaya ta kalli Ameena tace, “Ameena ki tashi ki shirya ku tafi.” Bata iya yiwa Yaya musu dole ta mik’e ta shiga ta tattara kayan ta dana Zaytun tana jiyo maganar sa shida Yaya ta zuba a jaka Amira ta d’auko mata jakar suka fito. Ganin ta fito sai ya mik’e da Zaytun tana ji Yaya nayi masa godiya alamun ya bata wani abun ta kalli Yayan tace, “Yaya dan Allah ki bani Amira mu tafi tunda bata zuwa makaranta, ni ki bar min ita kawai dan Allah tayi makarantar a kano.” Yaya tace, “in na bar miki ita ni kuma fa?”. “Ba akwai Hidaya ba?, dan Allah ki bar min ita mu tafi yanzu.” Yadda tayi maganar da wata irin murya ta nuna tsantar rashin son tafiya har muryar na rawa ya saka ya kalle ta ita kuma bashi take kallo ba hakan ya saka ya kalli Yayan yace, “in da dama a bamu ita d’in Yaya.” Yaya tace, “Yanke hukunci sai mahaifin ta ya dawo, zata zo dai tayi Hutu amma badai na bar muku ita ba gaskiya.” Yusuf yayi murmushi yace, “Hakan ma Mun gode.” Yayi hanyar fita yace, “Yaya Mun koma Allah ya saka da alkhairi.” Ta amsa da amin ya fita sai kawai hawaye ya zubowa Ameena Yaya ta dafa ta tace, “Meye na kukan kuma?.” Ameena tace, “tsoron komawa nake kar naje wannan shine ganina dake na k’arshe Yaya, komawa ta Ina ji a jikina kamar mutuwa zanyi.” Yaya cikin sigar kwantar da hankali tace, “Haba Ameena meye na wannan zancen kuma dan Allah?.” “Yaya sai naga kina masa dariya bayan kin San abinda yake yi min. Yaya kin manta nice y’ar Uwar ki bashi ba? Amma sai naga kin sake dashi kamar ba abinda yake so yake yi min ba.” “Kuka zan masa Ameena? Ko kuma na kore shi nace ya tashi ya fita Ameena?. Ya kike so nayi masa.? In bakya son ki koma ki zauna bazan hana ki ba dan basan abinda kike ji a zuciyar ki ba. Duk da zaman gıda kaddara ce amma Ameena bana son ace da auren ki kina zaune a gida da sunan yaji, ke kika fada min halayen y’an uwan mu in suka ji wacce irin darıya zasu yi mana?, mu ture batun su ma Ameena zaman gidan ki shine rufin asirin ki, amma in bakya so wallahi bazan hana ki zama ba Ameena, zan fita da kaina yanzu na fad’a masa baza ki tafi tare dashi ba.” Ameena ta girgiza kai ta goge idanun ta tace, “Kawai bana son komawa yar gidan jiya ne, zamana a nan na samu abinda nake so amma a can…..” sai kuma tayi shiru tana goge idanun ta tace, “Dan Allah in Abban su Amiran ya amince zan turo a d’auke ta gobe, zaman ta a tare dani zai saka naji dadi sosai kamar Muna tare dake Yaya.” “In sha Allah zan masa magana ko wasu kwanaki ne tazo tayi miki.” Ameena ta girgiza kai ta rungume yayar tata kafin ta sake ta tace, “Sai munyi waya.” Yaya ta girgiza mata kai tayi hanyar fita ta bita da kallo har ta fita sannan ta daina kallon wajan. da ace tana da yadda zatayi Ameena baza ta koma Kano ba, bata son shiga tsakanin mata da miji kar tazo taji kunya dan tafi kowa sanin son da Ameena take yiwa Yusuf har gobe kuma tana son sa, kuma ita Matsalar aure a koda yaushe sassanci ake yi ba b’ataww ba shiyasa take daurewa tana kawar da komai amma mugun haushin sa take ji a ranta amma baza ta nuna ba saboda matar sace har gobe. Kallon kud’in da ya bata tayi ta sauke numfashi tace, “kula da yar uwata yafi min wannan kud’in Yusuf” ta maimaita kamar yadda ta fad’a a gaban sa. Dawowar Amira ne ya tabbatar mata da sun tafi ta sauke ajiyar zuciya tace, “Allah ka bawa Ameena juriya, in ita ake cuta ka saka mata ka daidaita tsakanin su.” Amin taji Amira ta fad’a hakan ya saka ta kalle ta dan bata san a fili tayi maganar ba kafin ta shiga cikin daki. Suna baya ita da Yusuf driver na jansu a mota, motar Ameena kuma wani yana ja daman su uku suka tawo saboda motar Ameena din. Babu Wanda yake magana suna zaune Ameena tana kallon titi kewar iyayen ta na taso mata sai hawaye take tana gogewa. Zaytun na jikin sa tana bacci ita kuma tana kallon taga kafin ta kifa kanta a cinyar ta tana kuka a hankali dan ta kasa rik’e shi. Yana Jin ta yana kuma hankalce da ita duk abinda take yi yana gani baiyi magana ba tafiya kawai ake yi har ta gaji da kukan ta goge idonta ta jingina da kujera ta kulle idanun ta. Sai gab da La’asar suka shiga gida ta fita daga motar bata ce komai ba ta shiga gidan kai tsaye ta wuce d’aki tayi wanka tayi sallar azahar tayi la’asar tana zaune tana jan carbi bacci ne yake neman d’auke ta. Dago kai tayi ta kalle shi jin motsin sa dan bata san ma ya shigo ba shima ita ya kalla ya zauna a gefen gadon ya hard’e hannayen sa waje d’aya yace, “Meyasa kika tafi Bauchi ba tare da izinina ba?.” Shiru tayi bata amsa ba dan ita bata yi tunanin zai damu dan taje Bauchi bai San ta tafi ba hakan ya saka ya kalle ta yaga bashi take kallo ba yace, “Baki da amsa kenan?.” Ta d’ago ta kalle shi tace, “İn zaka tuna na fad’a maka ina so zanje Bauchi.” “Kina so kika ce min ba zaki tafi ba ko?.” Tayi shiru bata amsa ba yace, “Dan nayi miki magana akan abinda kika yiwa wacce zan aura shine kika yi yaji kika tafi kenan?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “abu nawa aka yi wanda yafi wancan banyi yaji ba sai shi?.” “Saboda tsanar ki da aurena mana, ai ko meye a wajan ki ya biyo bayan maganar aurena. Tunda ta shigo kika canja ko abinci sai kin yi niya kike bani har ta kai ta kawo Ina miki magana kina mayar min kamar sa’an ki.” Tayi shiru nan ma bata ce komai ba ya sake cewa, “duk abinda Ammah zata yi min fad’a a koda yaushe shi kike so saboda kinga tana sonki, abu d’aya nake so ki tuna Ameena, ni Yusuf Ammah haifa ba ke ba, ko ya ya kike min wani abun dole zata ji babu dad’i a ranta duk abinda take yi miki kara ce kawai. Yanzu da kika je Bauchin maganin ne hakan yayi miki? Ko kuma zuwa kika yi kika fad’awa Yayaar ki ai nayi miki fad’a dan kin yiwa wacce zan aura wulakanci?.” “Daman babu abinda zai min magani ai sai Allah kuma gare shi na mik’a dukkan lamarina, in badan yanzu da ka tuna min da maganar wacce zaka aura bama wallahi ni na manta da batun ta.” Ya girgiza kai yana kallon ta ransa na suya in yaji tana mayar masa da magana in yana magana yace, “Naga alama rashin kunyar ki sake gaba take duk akan zanyi aure, kin nisanta kanki dani da duk wani abu naki yanzu kuma kin samu bakin fad’a min duk abinda kike so. Yayi kyau, kin kyauta. Ina so na sake gargad’in ki akan yin doguwar tafiya tare da yarinyata” ya fad’a yana nuna Zaytun da take bacci yace, “İn zaki yi ke kad’ai ki yi amma kar ki sake yin wannan gangancin da ita.” Ya mik’e tsaye yana kallon ta yace, “Kar kiyi tunanin naje na dawo dake daga Bauchi saboda Ina son hakaan ba, naje na dawo dake ne saboda Amma da kuma Zaytun d’ina bada su ba da baza kiga k’afata a inda kike ba Tunda dmaan bani na kai ki na.” yana gama fad’ar hakan yayi hanyar barin d’akin tace, “Nima ban dawo dan wani ba ai, na dawo saboda darajar Ammah badan ita din ba wallahi da naje kenan, yadda ba’a damuwa da na dawo ba nima ban damu na zauna ba.” Juyowa yayi ya kalle ta kamar zai magana sai ya fasa ya fita. Da kallo ta bishi ta girgiza kai bayan ya fita ta cigaba da jan charbin ta bata bari kalaman sa sun yi tasiri a zuciyar ta kamar yadda aka saba ba, dan ta lura maganar da tayi ce ta k’arshe ta fusata shi da a hankali yake magana amma tunda tayi maganar ya fusata, sai dai kuwa yayi tayi dan auren sa a yanzu baya gaban ta ko kad’an. A falon ta ya tsaya yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudu ya kulle idanun sa ya bud’e yana tuna abinda ya fad’a mata da wanda ta fad’a masa, ya fad’a mata haka ne kawai dan taji haushi taji abinda yaji lokacin da ta tafi ya wayi garı bata nan bai fad’a mata dan da gasken sabida Amman yaje ba sai dan ya k’ona mata rai kamar yadda ta k’ona masa rai a ranar da ya tashi bata nan. Shi kansa yasan yana kewar ta sosai, ganin da yayi mata a gidan Yaya a Bauchi ba k’aramin dad’i yaji a zuciyar sa ba baya son nuna mata ne dan kar ta samu damar sake raina sa. D’akin ya juya ya kalla kamar zai koma sai kuma ya fasa ya fita daga falon gabad’aya. #Nana Haleema #Mai daki #book2 #Paid #500 Book2 009 Lokaci yana ta gudu biki yana sake matsowa b’angaren Amarya Asiya aka ta shirye-shirye an kawo lefe na gani a fad’a gida gida aka dinga bi ana fad’a dan azo aga lefen y’ar ta bana matsiyata bane ba. Yusuf kuwa shi kad’ai yake sabgar bikin sa babu wanda yake taya shi har gwara ma Yayyen sa maza su kan tambaye shi ya shirin biki amma ‘bangaren Amma da matan babu ruwan wani dashi. Biki ya rage saura kwana goma a fara Ameena tsakanin ta da Yusuf sai ido kawai kamar yadda baya sakewa da ita haka itama bata sakawa dashi. Har tafi jin dad’in hakan ma tunda kwana biyu babu fad’a sai tafi Jin dad’in su zauna shiru d’in yafi mata alkhairi hankalin ta yafi kwanciya. A cikin kwanakin Amira tazo sai hakan ya sake kawar mata da tunani daga kansa ko yaushe tare da Amira suna hira. Ranar laraba da safe suna zaune ita da Amira a falo Amira tana gyarawa Zaytun farce ita kuma tana kallo suna hira sama-sama in abin maganar yazo suyi in bai zo ba kuma suyi shiru sai sautin tv kawai da yake tashi. K’wankwasa k’ofa ake yi hakan ya saka Amira ta ajjiye abinda take yi ta tashi ta bud’e, mata ta gani su biyar a tsaye ta bisu da kallo dan bata san su ba amma tace, “Sannun ku da zuwa, ku shiga” ta fad’a tana basu hanya suka shiga suna ta kallon falon ana kallon juna. Zama sukayi Ameena da take kallon su ta gyara zama tace, “Barkan ku da zuwa.” D’aya daga cikin su ta amsa da fadin, “Yauwa barka, ya gıdan?.” Ameena da fara’a tace, “Alhamdulillah, Amira zo ki kawo musu ruwa.” Amira ta tashi ta kawo ruwa harda lemo wacce tayi magana d’azu tace, “Dangin amarya ne Asiya, Mun zo zamu yi kafi a gidan ne muka shigo a gaisa.” Sai da gaban Ameena ya fad’i amma bata nuna ba tayi murmushi tace, “Allah sarki, naji dad’in hakan na gode sosai da kuka shigo.” Mik’ewa sukayi suka mata sallama suka fita tare da jan k’ofar kamar yadda suka ganta. Ameena ta jingina da kujera tare da rufe idanu ta kawai bata ce komai ba kafin ta mik’e ta hau sama. Bata san lokacin da suka tafi ba tunda ta hau saman bata sakko ba sai bayan la’asar shima girki ne ya sakko da ita, kitchen din ta shiga ita da Amira suna yi suna hira sama-sama har suka kammala ta kwaso aka ajjiye akan dining table lokacin ana kiran magriba ta koma sama da niyar yin sallah. Bayan ta idar da sallah ta dawo k’asan ta zauna ta fara cin abincin Amira da Zaytun suna sama basu sakko ba, tana cikin cin abincin yayi sallama ya shigo ta d’ago ta amsa tana kallon sa, tunda taga yanayin fuskar tasa gaban ta sai da ya fad’i a zuciyar ta tace, _To yau na shiga uku dmaan an jima ba’a yi min fad’a ba._ a bayyane sai ta amsa sallamar tare da fad’in, “Sannu da zuwa.” Ganin ita kad’ai ce a zaune ya saka ya k’araso yana zuwa kusa da ita ya k’are mata kallo yace, “Meyasa duk abinda za’a tafi dani a baki ana zagina shi kike son yi Ameena?.” Fuskar ta ta nuna alamun me kuma nayi ta kalle shi bata amsa ba yace, “Duk wani abu da zaki aikata dan a zage ni shine fatan ki, burin ki kiga raina ya b’aci Amma tayi min fad’a ko kuma ta dole sai anga gazawa ta ko?.” Nan ma tayi shiru bata amsa ba sai kuwa ta fusata shi ya daki table d’in da take kai yace, “Ina magana da yake kin mayar dani d’an iska kin yi min banza? Sa’an kine ni?.” Sai a sannan tace, “Ban san akan abinda kake magana ba shiyasa nayi shiru.” Runtse ido yayi ransa na mugun tafasa zuciya na fad’a masa kawai ya mare ta dan rainin nata yayi yawa dakyar ya sarrafa kansa ya hana kansa narin yace, “B’akin da suka zo d’azu uban waye ya hana ki yi musu abinci ki basu? Ko abincin naki ne da zaki ajjiye a store baza ki dafa ki basu ba, tambayar ki nake da kud’in ki na siya!?.” Ameena ta dafe kanta da hannayen ta duka biyun kafin ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa ya sake cewa, “Da suka zo ba ko kallon kirki basu samu daga wajan ki ba kika wulak’anta su ke a lallai ga matar gida. Wallahi in baki shiga hankalin ki ba zan d’auki mataki a akan ki wanda baki tab’a kawowa a zuciyar ki ba, ki fad’a min meye ya hana ki basu abinci?.” Mik’ewa tsaye tayi ta kalle shi tace, “tsakani da Allah nasan zasu zo? Baka fad’a min ba ban san da zuwan su ba taya……” dakatar da ita yayi yace, “Da ban fad’a ba da suka zo meyasa a lokacin baza’a girka a basu ba? Akwai abinda babu a gidan ne?.” “Ka fad’a min ana girkin ne? Akwai Wanda ya fad’a min ana yin abinci balle na sani nayi?.” Banza kallo yayi mata na sama da k’asa yace, “Ohh baki san ma anayi ba kenan ko?.” “Inda na sani taya zan tambaye ka, kai kanka kasan dana sani bazan kyale su haka ba dan rowa ba halayya ta bace ban bud’e ido da ita ba.” “Ke rashin hankalin naki har ya kai sai an fad’a miki sannan zaki yi abu? Da kika ga sun zo kiyi mana lallai sai an fad’a miki?.” Motsin Amira taji kamar zata sakko hakan ya saka ta d’aukar plate din abincin tayi niyar barin wajan bata so Amira tazo ta tarar dasu a haka shiyasa zata bar wajan, hakan da tayi ba ‘karamin sake harzuk’a shi yayi ba; bai San lokacin da ya kwace plate d’in ya cillar a kasa ba ya finciko hannun ta yace, “Ina miki magana zaki tafi ga mahaukaci ko?.” Kallon gefen ta tayi taga Amira da Zaytun a hannun ta a tsaye ta kalle shi tace, “Kayi hak’uri” tana fad’ar hakan ta bar wajan ta hau sama ba tare da ta kwashe abin da ya zubar ba. Amira ce ta sakko wajan suka had’a ido da Amira ta d’auke kai haka kawai taji baza ta iya yi masa barka da zuwa ba idanun ta ya fara zubar da hawaye ta ajjiye Zaytun akan kujera ta d’auko tsintsiya tana share abinda aka zubar. Kwafa yayi ya fita Amira ta bishi da kallo ta gama ta d’auki Zaytun suka koma saman gabad’aya bazata iya cin abincin ba ranta ya b’aci. Ameena Tunda ta hau saman take kuka sosai babu mai rarrshin ta, zuciyar ta tafasa take mata fiye da ko yaushe haka take ji. Babu abinda yake d’aga mata hankali kamar had’a ta fad’a da shi da gidan su amaryar suke yi, tun kafin ta shigo ana yi mata irin wannan makircin Ina ga amaryar ta shigo gidan?. Sallar Isha ce ta saka ta tashi tayi sallah tana yi tana jan numfashi saboda kuka tana idarwa ta zauna tana cigaba da zubar da hawaye. Bud’e k’ofa akayi Amira ta shigo jiki a sanyaye ita kanta tasha kuka ta zauna kusa da ita tace, “Aunty Ameena Kiyi hak’uri ki daina kuka, komai lokaci ne kuma komai zai wuce kamar bai faru ba.” Kallon Amira tayi ganin yadda fuskar ta tayi alamun tayi kuka tace, “Kar ki damu Amira ki daina kuka kije kuci abinci, in Daddyn Zaytun din bai ci ba ki kai baya su Baba Habi su cinye kar ya lalace.” Amira tace, “Aunty bazan iya cin komai ba bana jin yunwa” ta fad’a tana niyar yin kuka Ameena tace, “Tashi kije kici a haka kar ki kwanta da Yunwa.” badan taso ba haka ta tashi ta rik’e hannun Zaytun suka fita daga d’akin ta lumshe ido tana kallon sama. Bud’e k’ofar ta saka ji anyi an shigo tace, “Amira kije kici abinci nace ko? Kar ki kwanta haka baki ci komai ba.” shiru taji ba’a amsa ba hakan ya saka ta bud’e ido ta kalli inda take jin motsin ta ganshi a zaune yana kallon ta. Mayar da ido tayi ta kulle ko motsi batayi ba hakan ya saka shi cewa, “Raina ne ya b’aci d’azu da naji baki basu abinci ba, ko babu komai bak’i na ne ya dalilina suka zo nan bai kamata ace sun zo har gıdana sun tafi basu ci komai ba. Komai ya wuce kiyi hak’uri” a tusashe yake maganar hakan ya saka ta sake bud’e ido ta kalle shi suka had’a ido ta seke mayar da Idon ta rufe ya sakko kusa da ita ya zauna ya rik’e hannun ta yace, “Ki bar fushi mana komai ya wuce.” Kai ta girgiza tace, “ni ba fushi nake ba.” “To indai haka ne ki saki ranki.” Bata ce komai ba har lokacin bata bud’e ido ba sannan bata saki ranta yace, “Indai da gaske ba fushi kike ba kizo muje dakina ki kwana a can. Kuma dan Allah gobe zasu dawo bakin a daure ko jellof ce a basu.” Sai a sannan ta bud’e ido ta kalle shi sosai sai tayi murmushi na takaici daman tasan bada hakurin nan da yazo da biyu yazo ko tace da uku ma haka kawai bazai bata hak’uri dan yayi mata fad’a ba, yake dukan ta ma bai bata hakuri ba balle wani fad’a. “Yanzu ba wannan ba ki tashi muje saman” ya fad’a tana tashi tare da jan hannun ta. Zame hannun tayi daga cikin nasa dan taga alamun yana raina mata hankali ko yaushe yazo da niyar ya bata hak’uri sai yace wai tazo suje sama, Kenan ya mayar da ita abinda yake nufi ne zai saka ta daina fushi, tace, “basai naje saman ba nafi son kwanciya a nan.” Ya sake dawowa ya tsuguna gaban ta yace, “ni kuma a can nake so ki kwana, ki taso muje saman kar y’ay’an ki su dawo.” Ta kalle shi tace, “kayi hak’uri bazan iya tashi ba bana Jin dad’i.” “Zan iya d’aukar ki ai ba wani nauyi ne dake ba” ya fad’a yana niyar d’aukar nata. Da sauri tace, “Dan Allah Daddyn Zaytun ka kyale ni bacci nake ji kaina ciwo yake min, Dan Allah kaje ka kwanta basai naje ba.” Ya kalle ta yace, “Shikenan, kin sha magani?.” Kallon sa tayi ido cikin ido bata amsa ba jin wai yana tambayar ta wai tasha magani shine ya bata mamaki, sai ya d’an sosa kai yace, “Shikenan ki kwanta, da wuri zan fita gobe koda baza ki iya girkin ba please ki saka Amira tayi ko su Baba Habi.” Kai ta d’aga kawai dan bata son ma jin maganar sa ya juya ya fita ta bishi da kallon mamaki. Wato da yake yana so ya isar mata da gobe ma zasu zo sai gashi ya tako a k’afar sa har inda take wai tayi hak’uri tazo suje sama, murmushin takaici ta sake yi ta goge idanun ta har lokacin kallon inda ya fita take yi tana mamakin hali irin na Yusuf kafin ta sake rufe idanun ta ta cigaba da lazumi. _In na koma gidan Yaya na d’ora mata nauyii duba da yanayin mijin ta bashi da hali sosai, bamu da gıda gidan mu an jima da rabo gado da me zai zaunar dani a gidan nan? Dan kawai Yaya Adam ba mazaunin kano bane aikin sa baya barın sa zama waje d’aya wallahi da gidan sa zan koma na gaji da zaman gidan nan gabad’aya ya fita daga raina, inda Ina da gata da Ina zan zauna? me zai zaunar dani a gidan nan?._ abinda take fad’a a zuciyar ta kenan tana ji kamar ta tashi ta fita daga gidan ta huta da abinda take ji. Yaya Maimuna ta tasa Asiya a gaba suna tattaunawa akan Ameena tace, “Kin sanar dashi abinda nace kice?.” Asiya tace, “Na fad’a masa, naji kuma da alama bai ji dad’i ba.” Yaya Maimuna ta girgiza kai tace, “Yauwa haka nake so, yarinyar akwai kyau da haske ne dole sai Muna had’awa da makirci in ba haka ba akwai matsala wallahi. Dana ganta d’azu sai da gabana ya fad’i, amma kyaun ta ba wani abun bane a wajen mu.” Asiya kamar zatayi kuka tace, “Yaya da gaske dai tana da kyau sosai ko? Na shiga uku.” “Baki shiga uku ba Asiya, amma dan kyau fa tana da kyau ba zancen k’arya amma zamuyi maganin ta. Kyaun zai zama bashi da wani amfani kece dai a gaba.” “Yanzu ya za’ayi?.” “Na tabbata gobe zai saka ayi mana abinci; to a hakan ma baza mu kyale ta ba wallahi, sai Mun ‘kirkiri wani abun da sai ta zubar da hawaye. Ta wannan hanyar zamu dinga cusa masa yana ganin bata qaunar ki yadda da kin shiga gidan in ma wuk’a kika ce ta biyo ki da ita zata kashe ki zai amince.” Asiya tace, “Ni jikina yayi sanyi da kika ce tana da kyau wallahi, bana so ta fini ta ko wanna bangare, yadda yafi sona so nake son ya tabbata har abada.” Yaya Maimuna tace, “Kar ki wani damu hakan shine zai tabbata, Ina zuwa” ta fad’a tana fita daga d’akin ta barta ita kadai a zaune. Umma ce ta shigo ta same ta a haka ta kalle ta tace, “ke kuma Lafiya?.” Asiya ta kalle ta tace, “Umma tunda Yaya Maimuna ta fad’a min kyaun matar sa nake Jin zuciyata na zafi wallahi.” Umma tayi dariya tace, “Yaro man kaza, to meye amfanin kyaun babu mai yabawa?.” Asiya tace, “Umma bana so ko kad’an ta fini a wajan sa ne wallahi.” “Ke bud’e ido ki kalle ni, yadda nake a gidan nan na kafa kaina dangin mahaifin ku ma tsorona suke ji haka kema zaki kafa gwamnati a gidan Yusuf, kar ki damu kyau na banza ne tunda babu soyayya, kina dani kina da Umman ki Sakina ko babu ni zata tsaya wajan ganin kin kasance ta gaban Gashi balle gani gata. Kar wannan ya dame ki kyau na banza da wofi ne tunda babu soyayya bashi da amfani.” Asiya tayi murmushi tace, “Har naji dad’i Umma” ta fad’a tana tasowa tana rungume Umma. Umma tayi dariya ta dake ta a baya tace, “Ai ba irin su Yusuf ake yiwa rik’o wasa ba, gam zamu kama shi ta yadda bai isa ya kwace ba wallahi. Kedai kije ki cigaba da shirye-shiryen ki mu namu shirin ya jima da yin nisa.” A guje Asiya ta fita zuciyar ta fari kal dan babban burin ta ace yau tafi Ameena a gidan Yusuf, ko kusa ko alama bata so Ameena ta fita wani abun ko ya ya yake kuwa. #Nana Haleema #Book2 #paid #500 Book2 010 Saboda gudun ya ‘bata mata rai ga Amira a gidan ya saka tun safe ta saka Ameera ta saka Amira ta d’ora musu abinci a babbar tukunya aka yi musu shinkafa jellof mai rai da lafiya wacce taji nama a ciki aka juye a babban kula aka ajjiye plates da cokula a kai. Sai bayan Amira ta gama komai sannan ta sakko sabida ciwon kai ta kalli Amira tace, “Sannu da aiki” ta fad’a tana bud’e abincin taga abincin yayi kyau sai khamshi yake yi ta d’auki cokali guda daya ta d’iba taci ta girgiza kai tace, “Gaskiya yayi dad’i sosai, kin sha aiki.” Amira tace, “Ai ba wani yawa, me zan dafa mana mu?.” Ameena tace, A’a aikin yayi miki yawa, kawai ki d’iba kici Zaytun tasha custard.” Sai kuma ta kalle ta tace, “Amma in bakaya son shinkafar ki dafa abinda kike so nidai bana ci” ta fad’a tana fita daga kitchen d’in. Bata jima da zama a falon ba ta fara ji ana shigowa gidan daman tasan sune basu shigo kamar jiya ba ta aika Amira ta kai abincin ta dawo suka zauna suna kallon tv badan Ameena na fahimtar abinda ake yi a cikin tv din ba sai dan bata son zama tana tunani ne shiyasa. Sai azahar ta tashi ta hau sama Amira ma ta tashi da niyar yin sallah. Haka aka cigaba da shirin biki dangin amarya sun gama kafi a gidan amarya gabad’aya daman abubuwa kad’an suka zuba sauran kaya ango ne ya zuba da kansa. Ameena koda wasa bata yin hanyar apartment din ko fita zatayi bata kallon wajan mota take hawa ta fita bata ma sha’awar kallon sa balle ma ta shiga. Zaman Amira ya saka taji dad’i sosai suna hira tana debe mata kewa safe da dare. B’angaren Amarya ana ta shagali sun gabatar da ‘kananun event sun shirya dinner wacce za’ayi bayan an d’aura aure daga nan amarya da ango zasu wuce gidan su shiyasa tun kafin ranar dinner din ake ta kawo mutane gidan suna gani dan babu kai amarya. Ranar d’aurin auren Ameeana tana tare da k’awayen ta sai Amira sai kuma Yayar Yusuf da Humaira da suka zo basu jima ba su suka tafi aka bar ta da k’awayen ta suna hira dan d’ebe kewa. Ameena da take ta kallon Fiddausi itama ita ta kalla tace, “Sai wani kallona kike yi kamar na canja miki, ke naga alama ko a jikin ki ace yau d’aurin auren mijin ki kina zaune baki da ko wacce damuwa. Ko da yake inda kud’i wallahi ba’a wani kishi.” Ameena tayi dariya tace, “Gani nayi sai kyau kike sake yi kina haske meye sirrin?.” Tayi shewa tace, “Ke kin raina zawarci ne? Wallahi dad’i ne dashi ba kad’an ba.” Zakiyya tace, “Ke naki zawarcin ma ai mai dadi ne, kwanaki kad’an fa ya rage kiyi aure.” Ameena da mamaki tace, “Har an samu wani kenan?.” Zakiyya tace, “Alhaji Bello Sagagi shine ya haukace a akanta, ke badan Abban su bama ai da yanzu tana gidan sa tunda babu idda akan ta.” Ameena tace, “Wai Bello Sagagi dai dana ke Jin labari?.” Fiddausi tayi farrr da ido tace, “Shifa.” Ameena ta girgiza kai tace, “Amma shine babu labari sai yanzu? Ruky kin sani?.” Rukayya ya tab’e baki kawai bata ce komai ba Fiddausi tace, “nayi niyar sanar daku nasan hali ne yanzu zaku fara cemin ai bai dace ba shiyasa na share ku.” Ameeena tace, “amma ni kodan saboda Amir wallahi nafi son ki koma gidan İbrahim.” Fiddausi ta wara ido tace, “a’uzubillahi minal shaid’ar rajim! Haba Ameena wannan wanne irin fata ne?. Dan Allah zubar da bak’in yawu.” Ameena ta kalli Rukayya da bata ce komai ba tunda aka fara maganar ta sake kallon Fiddausi tace, “Wannan korar shaidan haka kamar na kira sunan wani k’Aton aljanin?.” Zakiyya tace, “Ba gwara ki kira aljani da ki kira İbrahim ba?, ke ana zancen cigaba kina so ki mayar da rayuwar ta baya, ai tafi k’arfin Ibrahim yanzu wallahi.” Rukayya tayi dariya tace, “Ameena na fad’a miki bakin Fidy da Kiyya d’aya wallahi. Ko me d’aya zata aikata d’aya ta sani, duk wannan abinda ya faru shirin su ne, hatta fitowr ta daga gidsn Ibrahim zan iya cewa su suka shirya.” Fiddausi tayi dariya tace, “Ke ai iriin zuciyar Ameena gare ki shiyasa bana sabga dske yanzu zaki fara cemin Allah yace annabi yace, ke mai zuciyar auren talaka ga Ameena nan ta auri mai kud’i ta barki da zuciyar har yanzu. wallahi ki yiwa kanki fad’a akan son talakawan nan baki san illar su bane.” Ameena tace, “Wani talakan yafi mai kud’in ai, wallahi Rukayya da ki samu wani mai kud’in gwara ki samu wani talakan mai rufin asiri da zai kula dake. Meye amfanin kud’i in babu kwanciyar hankali wai?.” Zakiyya tayi caraf tace, “Wallahi cutar ki take Rukayya, babu wannan zancen. Ko a addini mai kud’i yafi talaka, mai kud’i ne yake zakka da zuwa aikin hajji talaka fa?.” Fiddausi tace, “Wai taya talaka zaifi mai kud’i wani kwanciyar hankali? Kud’i fa sune kwanciyar hankali ba wani abun ba. Wallahi kudi ko ba naki bane aka baki ajjiye dad’i ne dasu balle ace naki ne. Ke ko kallon wannan gidan naki ma ace kece a ciki shi kad’ai ya ishe ka farin ciki balle ga komai an ajjiye maka. Wallahi Rukayya ki neme mai kud’i domin a wannan zamanin kud’i sune komai, in kana auren mai kud’i a gidan ku ma anfi ji dakai dan ni naga izina a kaina.” Rukayya ta tab’e baki tace, “Ni duka basa gabana, Allah dai ya zab’a abinda yafi alkhairi, in mai kud’in ne alkhairi Allah ya kawo shi, in talakan ne ma Allah ya kawo shi.” Fiddausi ta Harare ta tace, “Baki da hankali wallahi, ke in ana zancen alkhairi ma sai ki sako lamarin talaka a ciki? Ai duk inda mai kud’i yake wallahi shine alkhairi.” Ameenatu tayi murmushi kawai gaban ta yana fad’uwa dan zuwa wannan lokacin ta tabbatar an d’aura auren mijin ta sa wata. Zakiyya tace, “ke ko zaman turaka da yin komai da komai a ciki in a a.c ne a kan k’aton gado kafi gane me ake yi, amma kana cikin zafi dame zaka ji?.” Fiddausi tace, “Wallahi kamar ka mutu saboda b’acin rai, ke ai naga tashin hankali a gidan Ibrahim sai da na yakice wannan sabgar daga raina, in kuma shi yake so to sai dai yabi dare in an kawo wuta.” Tare suka kyalkyale da dariya ita da Zakiyya suka tafa Zakiyya tace, “kefe original yar iska ce Wallahi Fiddausi, Wato sai dai yabi dare?.” Fiddausi tana dariya tace, “To abin yayi yawa ai ga zafi, gashi ba wani fahimta abin ma ake ba, ga zafin fatar jikin mutum, gashi da an gama ka fito rijiya d’iban ruwa, ka shiga band’aki a tsakar gida. Duk sanyi haka zaki zubawa kanki ruwan sanyi in ba haka ba sai dai kunna gawayi.” Suka sake tafawa suna dariya Fiddausi ta sake cewa, “Wallahi Ruky ki raba kanki da talauci, in ba haka ba haka za’a yi first night ga zafin gari ga zafin abu na farko ga b’akin cikin talauci.” Ameena tana Jin su sai dai tayi murmushi kawai kafin Zakiyya ta kalli Agogo tace, “Yanzu ma an d’aura ai.” Duk tare suka kalli Ameena da nan take hawaye ya sakko mata daga idanun ta. Duk sai jikin su yayi sanyi suka dawo kusa da ita Fiddausi tace, “meye kuma na kukan Ameena? duk hakurin da kika yi ana neman auren sai yanzu kuma zuciyar ki zata karye?, ki daina wannan kukan dan Allah ki ta addu’a.” Zakiyya tace, “Muma zamu taya ki addu’a dan bamu da wata hanya sai wannan din.” Ameena ta goge idanun ta tace, “Bawai fa Ina kuka dan an d’aura auren sa bane, kamar yadda Fid tace inda kud’i ai ba’a kishi.” Ruky tace, “Kar kiyi mana wani prending Malama, kowa yasan kishi kike kuma halak ne. Kin saba zama da mijin ki ko yaushe yanzu sai dai ya raba muku ku biyu dole Keda wata ki yi kishi. Zancen ma ba shi kike yi bai tashi ba kawai ki yi hak’uri.” Kai kawai ta girgiza suka dinga bata baki suna rarrashi suna hira sallah ce kawai take tashin su dan koda Amira ta kawo musu abinci ta dole suka saka Ameena taci. Har bayan magriba suna nan da suna so a kawo amaryar suna nan dan suyi mata kallon tsaf amma dare kasancewar suna wajan dinner dole suka tafi suka barta. Bata jira ma dawowar sa ba ta koma sama bayan ta kashe komai na k’asan ta kuma kulle duk abinda yake yi jikin ta a mace yake sosai zuciyar ta na tafasa kamar ruwan zafi sai da tasha maganin ciwon kai amma duk da haka a banza. Wanka tayi ta shirya tana shirin kwanciya Amira t shigo tana fad’in, “Aunty ga Amma nayi miki waya.” Wayar ta karb’a ta saka a kunne Amira ta fita kafin tace, “Amma barka da dare.” Daga can b’angaren Amma tace, “Nasan yau bak’in dare ne a wajan ki Ameena, rana ce mai muni wacce baza ki manta da ita ba a tarihin rayuwar amma kiyi hak’uri, wannan hakurin da zaki ji ana cewa kiyi sai kin daure domin yana da matuk’ar wahala kafin ki yishi zaki sha Ameenatu. Kiyi hak’uri Ameenatu komai zai wuce kamar ba’a yi ba, in kika saka damuwa a ranki zaki cutu ne shi kuma yana tare da amaryar sa kinga kenan kanki kawai kika cuta babu shi, amma in kika kwantar da hankalin ki kowa sai ya zauna lafiya. Ki daure akwai wahala amma Kiyi hakuri ki kuma dinga addu’a.” Kalaman Amma sai suke tuna mata da Maman ta hakan y saka ta hawaye bata shirya ba tace, “In sha Allah Amma zanyi, ki cigaba da min addu’a.” “Addu’a ana yi miki Ameena, kamar yadda zan yiwa Yusuf addu’a haka zan yi miki domin kema y’ata ce, Kiyi hak’uri kinji duk abinda kika ji bai miki ba ki kira ki sanar dani ko kizo nan din. Kar ki bar damuwa a zuciyar ki ki fad’a min kinji ko?.” Kamar tana gaban ta Ameena ta d’aga kai ta cigaba da yi mata nasiha kafin ta kashe wayar. Amira ce ta shigo ta kwanta a gefen ta ita da Zaytun ita kuma tana jingine da fuskar gado tana hasashen abubuwa kala-kala. Sai sha d’aya da rabi taji dirar motar Yusuf ko ba’a fad’a ba tasan shida amarya ne ta kulle idanun ta bacci take so tayi amma ta kasa. Shaid’an ne yake ta kawo mata abubuwa kala-kala a ranta hakan ya saka ta mik’e ta saka Hijjabi kawai ta tayar da sallah. B’angaren Ango da amarya babu wanda ya kai su farin ciki a wannan ranar lokacin da suka shiga b’angaren babu kowa sai khamshin turare yake yi an gyara shi anyi komai amarya ta zauna a kan kujerar falon tana kallon falon zuciyar ta cike da farin ciki Wai wannan falon gidan tane. Yusuf ya kalle ta yace, “Madam tashi zaki yi mu hau sama dare yayi fa.” Murmushi tayi ta mike tace, “To my love.” Shima murmushi yayi ya rik’e hannun ta zuwa saman. Asiya kuwa girgiza kai take yi a zuciyar ta tana fad’in, _Lallai Ameena bata da wani mahimmaci a wajan sa, tund asuka tawo baiyi zancen zai shiga wajan ta ba balle yace zamu je nida shi ya tara mu kamar yadda masu mata suke yi in sun k’ara aure, ko yanzu da muka zo ko k’ofar ta bai kalla ba. Ya zama dole na dage n sake watsar da ragowar mutuncin ta da yake gani._ Suna hawa saman tace, “kwalliyar fuskata ta dame ni.” Ya girgiza akai yace, “jeki ki wanke, kar ki manta Kiyi alwala nima zanyi yanzu zan fito” ya fad’a yana shiga d’aki da yake nasa a b’angaren itama ta shiga na kusa dashi. Fuskar ta wanke sharp-sharp tayi wanka tare da alwalar ta fito ta shafe jikin ta da turaren da aka bata nan take ta fara wani shegen khamshin Wanda ya Karad’e dakin gabad’aya. Duk wani magani da aka bata aka tabbatar mata da tayi amfani dashi a daren a lokacin tayi dan bazata yi sake ba ko kad’an. Yana bud’e k’ofar khamshin ya bugi hancin sa ya lumshe idanu yana kallon ta Allah ya sani yana son khamshi sosai, tana tsaye cikin riga da wando ‘kasa na bacci yayi saurin kawar da abinda yazo ransa yace, “Muyi sallah.” Babu bata lokaci suka tayar da sallah kamar ko wanne ma’aurata bayan sun idar ya gabatar mata da abinda ake shigowa amarya dashi, abinda ya bashi mamaki bata tsaya wani b’ata lokaci ba taja kazar tana ci abinta tana yi tana lumshe idanu dan gashin ya ji magi da yaji taci son ranta shi dai kallon ta yake yi kawai cikin mamakin ta dan bai tab’a jin labarin amaryar da tayi haka ba. Lokacin su da Ameena ne ya fad’o masa a rai yadda ko d’and’ana naman batayi ba yayi saurin kawarwa yana kallon ta tashi ta shiga bandaki jin kad’an ta fito ta zauna a gefen gadon. Mik’ewa yayi ya rik’e hannun ta yace, “Muje dakina.” Duk da tana Jin tsoron abinda zai faru amma zuciyar ta farin ciki take yi ta shagwab’e fuska tace, “Ni a nan zan kwana.” Ya girgiza akai yace, “Ai d’akina nan ne wajan kwanciyar matata, taso muje.” Ba musu ta tashi ta bi bayan sa suka fita zuwa d’akin. Kai tsaye wajan taga ya k’arasa bayan sun shiga ya d’aga labulen yana kallon tagar da take kallon tagar d’akin Ameena, Hasken d’akin ya gani a kunne kafin yayi wani tunani yaga an kashe ya sauke numfashi kamar mai tunanin wani abun. Asiya kuwa inda kayan sa suke ta kalla taga wanda ya cire a jikin wata doguwar anga ga kud’i a ajjiye akan madubi da yawa sabbi fil a mik’e ko wacce na jikin rafar ta. Ido ta wara zuciyar ta na fad’a mata taje ta d’an ciro wani abun ta fara tarawa tun yanzu, ta d’aga ‘kafa da niyar zuwa wajan ya juyo tare da sakin labulen sai ta basar ta dawo ta zauna a gefen gadon ya kalle ta yayi murmushi yace, “Tunanin me kike yi?.” Kallon sa tayi sai ta sunkuyar da kai idanun ta wajan kud’in dan ko bata d’auka a yanzu ba tabbas da safe zata d’auka addu’ar ta kawai Allah yasa kar ya d’auke kafin lokacin. Kwanciya tayi shima ya kwanta a bayan ta idanun ta a rufe kawai so take taji an wuce wajan duk da tana Jin tsoro amma ka’idar abinda aka bata ta shafa ne ba’a so ya wuce ranar ango bai kwanta da ita ba in ba haka ba aikin sa bazai yi tasiri yadda ake so ba. Kamar yasan tunanin abinda take yi kenan bai tsaya b’ata lokaci ba ya fara gabatar da abinda yake zuciyar sa shima dan saboda ya tanadarwa ranar gashi ya jima bai samu abinda yake so ba a wajan Ameena. Tabbas a wannan dare hankalin sa ya gushe ya manta da kowa sai Asiya kawai, ya gigice a wannan dare har yake jin da bai same ta ba da zai iya rasa rayuwar sa. ya samu abinda yake so a tare da ita domin budurwa ce cikakkiya shine na farko da ya fara sanin ta sai dai akasin da aka samu na wani abun daban. Sun jima suna bacci har suka makara sallah sai k’arfe bakwai na safe ya farka ya kalli agogo yayi saurin tashi yana sako k’afar sa k’asa ya taka bra d’inta ta da yake yashe a wajan. Tashi tsayen yayi ya tsuguna ya d’auki brazier yana latsa ta tare da bi da kallo. Gabad’aya katifa ce a jikin ta a haka ma in ka ajjiye sai ka d’auka an saka wani abun saboda yadda take a cike sosai kamar akwai kirjin a jiki. Kallon Asiyan yayi da take bacci ya tuna abinda ya tarar a jiyan sai yayi saurin ajjiye brazier ya shiga band’aki yana tambayar kansa, kenan abinda yaji gaskiya ne ba rud’ewa yayi ba? Kenan Asiya ciko take yi duk abinda yake marari a jikin ta ba nata bane kenan ko me……..?. #Mai daki #Nana Haleema #book2 #Paid #500. Book2 011 A haka ya fito daga band’akin bayan ya sake yin wanka yayi alwala, kallon ta yayi tana kwance har lokacin tana bacci ya lumshe ido tuno yanayin su na jiya tsigar jikin sa ta tashi yayi saurin kawarwa kar alwalar ta karye ya saka doguwar riga ya ‘karasa inda take kwance ya tsuguna yana bubbuga fuskar ta yace, "My love! Tashi muyi sallah lokaci ya k'ure." Bud’e ido tayi da suka yi ja da nauyi suka had’a ido yace, "Ki tashi ki yi sallah lokaci yana tafiya" yana fad’a ya juya ya hau kan carpet ya tayar da sallah dan kar lokaci ya k’ure ita bata tashi ba shima bai tashi ba. Tana tashi zaune idanun ta kan kud’in jiya suka kai suna nan wajan kusa har lokacin ta murza idanun ta ta mik’e dak’yar jikin ta duk yayi tsami ta shiga band’aki. Ta jima a ciki sannan ta fito lokacin ya idar da sallah yana ganin fitowar ta ya tashi da sauri ya k’arasa inda take ya rik’o hannun ta ya zaunar a kan gado yace, "Sannu ki yi a hankali." Zama yayi a gefen ta kawai sai ta fashe da kuka ta kwantar da kanta a kafad’ar sa tana kuka mara sauti. Nan da nan hankalin sa ya tashi ya rud’e sosai jin masoyiyar sa tana kuka ya d’ago fuskar ta yace, "Menene kuma My love? Meye na kukan?." "Na gaji, Kaina ne yake min ciwo, bacci nake ji sosai." "Sorry, nasan kina Jin bacci, Kiyi sallah sai ki koma ki kwanta, zan taimaka miki da tausa" ya fad'a yana mik’ar da ita tsaye tace, "Bani da kaya." Bai amsa ba ya fita ta sake kallon kud’in tana tunanin abinda ya kamata tayi ya sake shigowa da riga doguwa da hijjabi ta saka ta tayar da sallah, dakyar tayi sallar ana yi ana langwabewa tana idarwa ta tashi ta koma ta kwanta shima ya kwanta a gefen ta yana matsa mata jikin ta dan sam baya son abinda zai b'ata mata rai. Jin ta yake a jikin ga sosai fiye da baya haka baya son yin nisa da ita. Sun jima suna baccin har goma na safe ta gota ta riga shi farkawa tana ganin bacci yake ta zabura ta mik’e zaune, zama tayi na wani lokaci kafin ta mik’e tsaye a hankali ta k'arasa inda kud’in yake ta kalle shi taga bacci yake sosai bama inda take yake kallo ba ta saka hannu ta d’auki rafar dubu hamsin guda biyu ta fita daga d’akin a hankali. Wanka tayi ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa wacce ta kama ta sosai ta dawo d’akin har lokacin bacci yake ta kwashe kayan nasa da yake wajan ta saka a cikin wardrobe ta kwashe ragowar kud’in ta zuba a cikin drawer duk dan kar yayi zargin wani abun ya saka take aikin da bata yi niya ba. A kan kujerar da take d’akin ta zauna tana zama yana bud’e ido ya tashi zaune tare da kallon gefen sa nan ya hango ta a zaune ta rufe ido tana rik’e ciki kamar bata san ya tashi ba. Da sauri ya sakko ya k’araso yace, "My love Lafiya?." Ta kalle shi sai ta d’an gyara zama tace, "Yunwa nake ji sosai, naso kafin ka tashi nayi breakfast amma na kasa ko k'asa ban sauka ba." "I'm sorry Ina zuwa" ya fad'a yana fita daga d’akin ta tashi ta k’arasa wajan tagatana tsaye har taga ya fita daga b’angaren ta ya shiga b’angaren Ameenatu. Da sauri ta juya sai kuma taja ta tsaya tace, "Wayyo Allah." Sai ta cigaba da tafiya ta fara bud’e drawer ko zata ga wasu kud’in amma babu komai iya kud’in jikin sa da ya shigo dasu ne kawai. Numfashi ta sauke ta kama k'ugu tace, "Da alama kud’in dai suna b’angaren waccan kenan, lallai dole nasan abinda zanyi dan nasan bazai rasa ajjiye kud’i a gida ba, Dole nasan abinda zanyi na shiga na samo kafin lokaci ya k’ure na tara abinda na tara.” Waya ta d’auka ta koma bakin tagar da kar ya dawo bata sani ba ta kira Yayar ta Fauzy tana d’auka Fauzy tace, "Amaryar Yusuf, kece da safe haka?." Kafin tayi magana taji maganar Umma da alama tana wajan ta karb’i wayar daga hannun Fauziyya tce, "ke ya ake ciki komai dai yayi ko?." Asiya sai taji kunya ta kamata amma haka tace, "Eh Umma, kuma maganin yayi aiki sosai wallahi ya rud’e a kaina gabad’aya." "Ni na amince da aikin malam ai, yanzu ya battyn wani abun me ya Baki?." "Umma ai daman cewa yayi tukwicin first night daina Saudia zamu tafi yau kinga babu abinda zai bani." "Ke kuma baki samo ba? Na fad’a miki naci bashi a auren nan a yanzu ya kamata ki san abin yi domin yanzu yana mararin ki komai kika yi bazai kawo ke bace." Asiya tace, "Na samo dubu d'ari dai a safiyar nan, kinga nan sabon gida ne bazai fara ajjiye kud’i a nan ba, amma da zarar mun yi tafiya nan mhn dawo zan shiga har b’angaren nata na bincika kinga in na d’auka a can ai bazai kawo ni bace." Umma tace, "To yayi kyau, Fauziyya zata zo sai ki bata kudin ta tawo dasu kafin a fara tara min mutane a waje." Da to ta amsa tana kashe wayar tace, "Umma nima fa Ina so na tara wallahi, ba duka zan dinga bayarwa ba in na samo." Yusuf kuwa lokacin da ya shiga b’angaren Ameena babu kowa a k’asan amma a gyara yake yana ta khamshi har zai hau sama yaji motsi a kitchen yana shiga kitchen din yaga Amira ce ta gama hada breakfast. Tana ganin sa ta jiyo tace, "Ina kwana Daddy." "Lafiya lau Amira, abincin waye?." "Na mu ne nida Aunty bata tashi bane har yanzu." Ya d’an sosa kai ya bud’e abincin yaga dankali ne da Kwai ya juya ya d’auki plate ya zuba ya rage kad’an a ciki yace, "Zan kaiwa sabuwar Auntyn ki, ki samu ki sake had’a wani.” Amira kamar ta kifa masa mari haka taji amma bata ce komai ba sai to ya gama ya fita tayi tsaki tace, "Allah sai ya sakawa Auntyna." Koda ya koma b’angaren Asiya sai da ya had'a mata tea tun a k'asa sannan ya koma saman ya same ta a zaune a inda ya barta ya k’araso yace, "Sorry my love na jima ko?." Zama yayi gefen ta ta kalle shi bayan ya bata tea din a hannun ta tace, "dafawa kayi?." Kai ya girgiza yace, "No a wajan Ameena na karb’o miki." Tayi murmushi tace, "Allah sarki Auntyna tana sona." Murmushin shima yayi dan yana kin dad’in yadda take nuna tana son Ameena dan yasan ta bangaren ta bazai samu matsala ba sai dai ya b’angaren Ameena. Bar mata yayi ya tashi ya shiga bandaki ita kuma ta fara ci, so take tayi iyayi t rage amma Ina bazata iya ba yunwa take ji in ta rage ta cuci kanta haka ta cinye tasss ko kad’an bata bari ba lokacin da ya fito ma ta gama cinyewa. Kallon ta yayi ya murmusa yace, "Gwara da kika cinye dan ko baki cinye ba na fito sai na saka kin cinye." Bata ce komai ba tayi shiru kanta yana ‘kasa har ya saka kaya yace, "Kayana guda d'aya ne a nan daga wannan sai wanda na cire jiya, ya kamata na d’auko daga b’angaren Ameena." Bata ce komai ba ya k’araso ya zauna kusa da ita yace, "meye kike sauke kai k'asa?." Ta girgiza kai alamun babu tace, "Ina zaka je?." "Ina so zanje wajan Amma ne, amma yanzu zan dawo." Tayi shiru yace, "Ko Baki so naje?." Ta wara ido tace, "ni na isa? Naga baka ci komai bane." "Bana Jin yunwa" ya kalli Agogo yace k'arfe shida na yamma jirgin mu zai tashi, shiyasa nake so naje nayi sallama da Amma na dawo." Dad’i taji yana mamaye mata zuciya cikin farin tace, "Kwana nawa zamu yi?." Yayi shiru kafin yace, "sati d'aya dai kawai zance." Ta langwabar da kai tace, "Ba biyu baaaaa!?Har yaushe ma aka samu lokacin ibada a sati d’aya? Kaga fa ban tab'a zuwa ba." Yace, "My love dole hakan za'a yi kin manta bake kad’ai bace ba?." Ta turo Baki gaba kamar zatayi kuka tace, "Haka ne, amma da zamu samu dama da sati biyu zamuyi kodan ibada." Yayi murmushi yace, "bana son wannan fushin naki da damuwa zan san abinda zanyi, bara naje na dawo." "To sai ka dawo." Murmushi yayi kawai ya tashi zai fita tace, "Akwai kud’in ka da ka bari akan mirror na saka a drawer." Ya dafe kai yace, "na manta ma, sune kawai a jikina kuma" ya fad'a yana yin hanyar wajan drawer din ya d’auki kudin ba tare da ya duba ba ya saka a aljihu ya k’araso inda take ya mata kiss a goshi ya fita. Kamar zai shiga b’angaren Ameena sai kuma ya fasa in ya dawo ya shiga ya shiga mota zuwa gidan su. A babban falo ya samu Ammah da Abbah suna zaune ya shiga da sallama duk suka amsa ya zauna a k'asa ya gaishe su Abbah yace, "Ya kwanan amarya?." Yusuf yace, "Alhamdulillah." Abbah yace, "To Allah ya baka ikon yin adalci a tsakanin su." Ya amsa da amin kafin yace, "Daman nazo na sanar daku anjima da la'asar zamu tafi Saudia nida ita." Abbah ya gyara zama yace, "Ma sha Allah, amma ita kuma uwar gidan fa?. Gadin gidan zaku barta?.” Yusuf ya sake k’asa da murya yace, "Eh Abbah da yake kwana biyar zamuyi bada ita zamu tafi ba." Sai a sannan Ammah tace, "Ita zaku bari gadin gidan kenan?." Yusuf sai da gaban sa ya fad’i dan bai so ma tayi magana ba yace, "A'a Ammah, saboda ita ma na saka kwanakin babu yawa dan kar a shiga lokacin ta." Ammah tace, "Yau in kuka tashi sai gobe zaku shiga madina, kwana biyu zaku yi a madina kenan ku wuce makka kuyi kwana biyu sai ku dawo?." Ya girgiza kai yace, "Eh Ammah baza mu jima ba." Abbah da yake jin su ya mik’e yace, "To Allah dawo daku lafiya, ni zan wuce Abuja sai jibi zan dawo." Yusuf ya tashi da niyar raka Abbah da nufin daga nan ya gudu yaji Ammah yace, "in ka raka shi ka dawo." Da to ya amsa badan yaso ba suka fita Abbah ya shiga mota driver yaja suka tafi shi kuma ya juyo gaban sa yana fad’uwa. Sai bayan ya zauna tace, "Ka fad’awa Ameena maganar tafiyar?." Yace, "Eh ta sani, amma yanzu zan sake tuna mata na shiga tana bacci tun d’azu." Ammah tace, "Ka kasance mai adalci dan Allah Yusuf kar ka cutar da ko wacce a cikin su kaji?." Jin nasiha take masa ba fad’a ba ya saka yayi murmushi hankalin sa ya kwanta yace, "in sha Allah Ammah zanyi iya bakin kokarina wajan ganin ban cutar da kowa ba." Ammah taji dad’in kalaman sa tace, "To Allah ya baka iko ya zaunar daku Lafiya." Ya amsa da amin bai jima ba ya mata sallama ya tafi gıda. Ameena kuwa a zaune ta kwana bacci sai b'arawo sai bayan asuba bacci ya d’auke ta mai nauyi hakan ya saka ta jima tana bacci. Koda ta tashi da ciwon kai ta tashi tayi wanka ta saka doguwar Riga mara nauyi kamar yadda ta saba ta fito ta kalli gefen gadon taga babu Zaytun tasan tana wajan Amira. Wayar ta tayi ‘kara ta duba ganin sunan Yaya ya saka ta d'auka ta saka a kunne. Yaya a tausashe tace, "Aminene ya kike tashi yau din?." Ameena tace, "Alhamdulillah Yaya, ciwon kaine kuma yanzu zan sha magani." Yaya tace, "Kin karya kuwa?." "A'a, fitowa daga wanka kenan yanzu na tashi sallar azahar zanyi sai na sauka na ci abinci." "Ki dai ci abinci kar ki ci rashin cin abincin ki ba shi zai hana mijin ki zama da wata ba, ki saki jikin ki kawai Allah ya kaddara matar sace babu wanda zaki yi." Ameena tace, "Haka ne Yaya, yanzu zan ci in sha Allah." Yaya tace, "in kin gama ki kira ni." Ta amsa da to ta kashe wayar. Tashi tsaye tayi ta yaye lalube ta kalli gidan Asiya sai kuma ta rufe labulen ta saka mayafi ta tayar da sallar walha. Tana raka'ar k’arshe Amira ta shigo da tray a hannun ta ta zauna a k’asa Ameena tayi sallama Amira ta kalle ta tace, "Aunty Ina kwana." Zaytun ce ta shigo ganin Mummyn nata a zaune ta tawo a guje ta fad’a jikin ta Ameena ta rik’e ta tana dariya tace, "Yar gidan Aunty Amira, me ta baki haka naji kin koshi?." Zaytun tace, "Abinci muka ci." Ameena ta kalli Amira tace, "Aunty Amira kin tashi lafiya?." "Lafiya lau Mummy, ga abincin ki." "Sannun ki da kokari.” "Yauwa." Ameena ta d’auki tea din da ta had’a mata ta fara sha tace, "Daddyn Zaytun ya shigo?." Amira tace, "Eh ya shigo kitchen yaga na gama soya dankali lokacin da kwai ya d’auki plate ya zuba ya fita." Ameena ta girgiza kai kawai bata ce komai ba dan bata so ma ta kawo bai neme ta ba a zuciyar ta. A b’angaren sa yana dawowa gidan Asiya ya shiga ya tarar da ita zaune da Fauziyya suna hira suka gaisa ya wuce zuwa sama yayi alwala lokacin ana kiran sallah ya sakko ya shiga masallaci ya dawo ya shiga wajan Ameena. Kai tsaye d’akin ta ya shiga tana cin dankali ya shiga da sallama suka amsa ita da Amira a tare, a guje Zaytun ta tashi tana fad’in, "Daddy!." Ya d’auke ta yana mata wasa yace, "ya naji kinyi nauyi, me kike ci?." Cikin maganar ta da ba'a ganewa sosai tace, "Aunty Amira tana bani abinci." Yayi dariya ya zauna yace, "Lallai Aunty Amira tana son Mamana." Amira ta tashi ta fita Zaytun ta sauka daga jikin sa tabi bayan ta a guje ya bita da kallo yana murmushi kafin ya dawo da kallon sa ga Ameena da take zaune tana shan tea kamar bsta ganshi ba. Kallon ta yake yi sosai yaga ta rame musamman daga wuyan ta zuwa fuskar ta kafin yayi magana tace, "Ina kwana." Yace, "Lafiya lau, baki da Lafiya ne?." Ta girgiza kai tace, "Lafiya nake." "Amma kika rame haka?. Ni sai naga ramar nan taki kamar gaba take yi.” Ta sauke numfashi ta kalle shi tace, "na jima a haka." Ya bita da kallo na wani lokaci kafin yace, "baki tambaye ni ya amarya ba?." D’ago kai tayi ta kalle shi sai kafin tayi magana sai yace, "Magana nazo muyi." Tace, "to Allah yasa ba laifi nayi ba." "Magana ce akan tafiyar da zamuyi nida my love anjima." Ya gyara zama yace, "Lokacin da mukayi aure munje k'asashe kusan hudu ko biyar ma ko?." Bata amsa ba sai kallon sa da take yi daman yasan baza ce komai ba ya sake cewa, "Ko wacce k'asa Ina jin sati d'aya muka yi dan munfi sati hud’u bama Nigeria sannan muka dawo, anyi haka nasan kin sani. Nayi hakan ne saboda ke matata ce kuma Ina sonki Ina so mu samu kusanci nida ke." Nan ma shiru bata ce komai ba sai kallo kawai da take bin sa dashi tana so taji karshen maganar. "Zamu tafi Saudia da Asiya anjima Ina so muyi sati biyu sati d'aya a makka sati d'aya a madina, hakan bazai faru ba dole sai da taimakon ki dan kinga yau ya rage kwanaki shida kwanakin amarcin ta ya ‘kare kinga kenan dole sai an shiga kwanakin ki. Ina so dai da zuwan mu da dawowar mu muyi sati biyu shine nazo wajan ki muyi magana." Ameena da take jin sa ta sunkuyar da kai tayi murmushi ta d’ago ta kalle shi tace, "me kake so nayi yanzu? Kawai kace karshen maganar.” Yusuf yace, "sati d'aya nake so ki kara mana nida ita saboda mu samu lokacin ibada sosai, kwana shida baza mu nutsu ba in kika duba kafin ma muje madina Mun ci kwana d'aya." Ameena ta gyara zaman ta tace, "Kamar ya kake nufi ban gane ba?." "Ina nufin ki bar min kwanakin bana so ace na cutar dake ko wani abun shiyasa nazo na same ki. Bana son shiga hakkin ki shiyasa nake tambayar ki.” Ta d'ago zatayi magana ya katse ta yace, "Ni ko siya ma zanyi, duk kwana d'aya zan baki dubu dari kinga dubu dari bakwai kenan, sai na baki naira miliyan d'aya fatana kawai ki amince." Wani dogon numfashi taja wanda sai da ya kalle ta yaga tayi shiru kawai bata ce komai ba sai kanta da ta sunkuyar tana jin zuciyar ta na bugawa sosai. Ganin hakan ya saka yace, "Ameena banyi miki dole ba, in kinga zaki iya to in baza ki iya ba bance lallai ba kar na tafi Ammah tace in ban dawo ba sai ta tsine min. Bana son boye-boye kin sani ki fad’a min kawai." Ta d’ago ta kalle shi kamar zatayi magana wani abun ya tokare ta a kirji sai ta kasa ta sake yin shiru bata ce komai ba, sun jima a haka kafin yace, "ke nake jira zuwa anjima zamu tafi airport." Kai take girgizawa ta kalle shi tace, "Duk abinda zakayi daman kana neman izinina ne? Ka tab’a zuwa kace min neman izinina kazo nema akan wani abun? Meyasa kazo yanzu Daddyn Zaytun? Komai kai tsaye kake yi wannan ma kawai kayi babu komai ai tunda ka Saba.” Kallon ta yayi kamar zai ce wani abun sai ya canja maganar yace, "Kenan kin amince?." Da hannu tayi masa alamar yaje kawai. "Magana nake so kiyi min ba nuni ba." "Ai ba sai nace ba, duk abinda kaga daidai ne kayi kawai Yusuf basai kaji ta bakina ba, komai kayi a wajan ka daidai ne dan haka kayi kawai basai nace komai ba.” "Okay na gode, babu abinda kike so?.” Ya fad'a yana mikewa. Ta girgiza kai tace, “ka tab’a cemin akwai abinda nake so ne daman? Kawai kaje.” Har zai fita ya dawo yace, "in Ammah ta tambaye ki me zaki ce mata?." "Ina ruwan ka da abinda zance mata? Dan girman Allah ka tafi kawai Allah ya kaiku Lafiya ba shine abinda kake so ba? Kaje kawai Yusuf kar ka damu dani kamar ko yaushe kaje kawai.” Kallon ta yake sai yaji wani iri a jikin sa, jikin sa yayi sanyi sosai haka zuciyar sa ya kasa tafiya sai kallon ta da yake yi duk da ba kuka take ba amma kana kallon ta kasan akwai damuwa sosai. kamar zai magana sai kuma y fasa ya fita zuciyar sa na sake fad’a masa kamar baiyi daidai ba wata zuciyar na fad’a masa daidai yayi ai ta amince tunda ya fad’a wannan tunanin ya koma b’angaren Asiya. #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema. Book2 012 Sai bayan taji ya kulle ‘kofa ta kalli inda yabi ta ajjiye shayin hannun ta zuciyar ta kamar an tsagata an dasa mata dutse haka take ji a ciki saboda taurin da tayi mata. lumshe ido tayi kawai jikin ta ya d’auki zafi lokaci d’aya hawayen idanun ta sun k’afe babu su babu alamar su sai ja da idanun ta yayi. Bata so ta dinga saka lamarin sa a zuciyar ta a lokacin amma bazata iya ba in tace bata jin zafi akan abubuwan da yake yi mata tayi k’ayar kawai tana so ta dinga kawarwa ne dashi da matar sa kar su dinga damun ta. Tashi tayi daga inda take ta koma kan gado ta zauna kalaman sa suna yi mata yawo a kanta. _Kinga sai na biya ki ma, duk kwana d’aya naira dubu dari._ abinda ya fad’o mata kenan ta sake kulle ido ta bud’e a bayyane tace, “Daman yasan akwai hakkina a kansa ne har yake wannan maganar? Daman duk abinda yake yi yana sane kenan tunda Gashi yanzu yazo ya tambaya da kansa da yake so yake yi.” Kasa cigaba da magana tayi ta dafe kanta kawai ba tare da ta motsa ba. Tana ji wayar ta na neman d’auki amma bazata iya d’auka ba har ta katse aka sake kira amma bata kalle ta ba sai ma kwanciyar da tayi a kan gadon kirjin ta na sama da k’asa. A b’angaren Yusuf koda ya fita kai tsaye b’angaren amarya ya nufa yaga takalma a bakin ‘kofa alamun tayi bak’i kafin ya jiyo muryar Yayar ta Fauziyya tana fad’in, “ai in ta kwantar da hankalin ta da zaman Lafiya kika zo gidan dan nan Asiya, ni wallahi na d’auka ma itace zata kawo muku abinci kasancewar ki ta amarya. Amma kar ki damu kedai ki girmamata abinda Umma ta seke cewa na fad’a miki kenan domin matar mijin kice gaba take dake.” Ja yayi ya tsaya yana so yaji mai Asiyan zata ce yaji Tce, “Wallahi ni da zuciya d’aya na d’auke ta kamar Yayata ne, bana jin zan mata kallon kishiya dan duk abinda akace na my love ne bazan yi masa koda kallon banza ba balle kuma ace matar sace, itace kawai nake ganin bata son zaman Lafiya amma in sha Allah zata canja itama. Nidai daga wajena baza’a samu matsala ba in sha Allah.” Murmushi yayi jin abinda tace hakan yana daga cikin dalilin da soyayyar ta take sake ninkuwa a zuciyar sa domin ya fahimci tana son zaman Lafiya bata zo dan tashin hankali ba. Da sallama ya shiga ganin sa sai sukayi shiru Fauziyya tace, “Ango barka da rana.” Yayi murmushi yace, “Barkan ku, ya gajiyar hidima?.” Momi tace, “Alhamdulillah duk Mun ware ai.” Baice komai ba sai murmushi ya hau saman suka Bishi da kallo. Fauzy tayi dariya tace, “Da alama tarkon mu ya kama, tashi kije saman kiji abinda zai ce ga abinci nan ki kai masa mu kafin ki sakko mun wuce.” Tashi tsaye tayi sai kuma Fauziyya tace, “ke zan d’ibarwa Umma madarar can zan tafi da ita, in ta kama ma harda milo.” Asiya tace, “to kar ki d’iba da yawa kinga dai yau aka bud’a kar a gane.” “In ma an gane sai me? Dan ke aka kawo ai, ni zan d’auki indomie biyu in naje gida na dafa na ci” Ta fad’a tana yin hanyar wajan madarar ita kuma ta d’auki abincin zuwa saman. A falon ta same shi a zaune yana gano ta ya tashi ya karb’i abincin ya ajjiye ta zauna itama yace, “Meyasa bari nazo na Karb’ar miki ba?.” Zama tayi tace, “Yanzu ka dawo fa.” “Ke kika dafa?.” Ta girgiza kai alamun A’a tace, “Fauzy ce, badan ita ba ai ni bazan iya girki ba. Kaina ciwo yake sai da nasha magani.” “Sannu kinji, amma Yanzu babu ciwon?.” Ta d’aga kai alamun babu tace, “Kaci to.” Bai musa ba ya fara ci d’in dan ko karyawa ma baiyi ba yace, “In na gama sai mu shirya kayan da zamu tafi, zuwa karfe biyar zamu wuce.” Nan take tayi dariya tace, “To.” Abincin yaci bayan ya gama kamar yadda yace suka shiga d’aki tare suka shirya kaya daman ya tawo da kayan sa daga b’angaren Ameena bayan sallar la’asar yace mata yana zuwa ya koma b’angaren Ameena ya samu ta kulle k’ofa ya tambayi Amira tace ai tace kar a deme ta bacci zatayi baice komai ba ya juya ya sauka suka shiga mota fita daga gidan. Ameena duk tana kallon su tana daga tsaye a window sai a sannan taga Asiya d’in duk da bata ga fuskar ta sosai ba sai bayan ta babu laifi tana da kyau duk da bata da haske a kan idanun ta suka fita daga gidan ta dawo da baya ta zauna a gefen gado ta rasa wanne irin tunani ma zatayi. Tun bayan da Yusuf da Asiya suka tafi bai Kira ta a waya ba itama bata neme shi ba har suka kwashe kwanaki biyar a can, ta tattara ta ajjiye shi a gefe ta kama addu’a da kuma shawarar Yayar ta da k’awayen ta a haka take komai duk da babu kuzari a tare da ita gashi ta rame amma tayi k’ok’arin ajjiye damuwar Yusuf ta sake sosai Kullum cikin hira suke da Amira bata ware kanta dan tana Gudun tunani. Ranar da suka kwana shida basa nan tana zaune a falon k’asa da daddare suna kallon dadin kowa a tv ita da Amira da Zaytun da take wasa akayi sallama aka shigo falon. Amsawa tayi tana kallon wacce ta shigo taga Humayrah ce bayan ta kuma Amma ce ta mik’e da farin ciki tana fad’in, “Amma barka da zuwa.” Kallon ta take yi ganin ta rame sosai sai haske da ta sake yi hakan ya d’aga mata hankali sai kuma tayi tunanin ko ciki ne da ita shiyasa ta rame ya saka ta haske. Ammah ta zauna Ameena ta zauna a kan carport tace, “Amma barka da zuwa.” Amma tace, “Barka dai Ameena, na same ki Lafiya duk da naga kin rame?.” Ameena ta murmusa tace, “Alhamdulillah, Amira kawowa Ammah ruwa.” “A’a Amira yi zaman ki hanya ce ta biyo dani nace bara nazo na ganki, sai kuma naga kin sake ramewa Ina fatan Lafiya dai?.” Ameena tayi murmushi tace, “Lafiya lau Ammah.” Jjn hakan sai Ammah ta saka a ranta ciki ne da Ameena, Zaytun tayo wajan Ammah ta zauna a kan cinyar ta Ammah tace, “Takwara mai kika ajjiye min?.” Dariya akwai Zaytun take yi itama Amman tayi tana yi mata wasa. Humayra tace, “Gobe Yaya Yusuf din zai dawo ko?.” Ammah ta kalli Ameena tace, “Kwana nawa zasu yi ne?.” Ameena tace, “saati biyu dai yace min kafin su tafi, amma ban sani ba ko ya canja lokaci.” Amma jin hakan sai ta girgiza kai kafin tace, “Tunda yace miki hakan ai hakan ne, Allah ya dawo dasu Lafiya. Sai ke kadai a gidan.” Ameena tayi dariya tace, “da Amira ai Ammah shiyasa zaman baya damuna.” Ammah tace, “Haka ne, Humaira tashi mu koma” ta fad’a tana tashi tsaye. Ameena ta mike itama tace, “Ammah da wuri haka?, ko abinci baki ci ba.” Ammah tace, “Dare yayi gwara mu koma.” Har bakin mota suka raka Ammah Humaira taja suka tafi itama ta koma ciki. Ran a Amma a b’ace ta koma gıda tana komawa kai tsaye b’angaren mahaifin su ta wuce ta same shi a tsaye yana amsawa waya a d’aki ta zauna tana jira ya gama ta zayyane masa abinda yake bakin ta, bai jima ba ya gama ya kalle ya yace, “Ina ta kiran number Yusuf bana samu Ina so ya tawo min da turare a makka ko ya dawo ne?.” Ammah tace, “maganar sa nazo muyi, nida kai ba ce mana yayi sati d’aya zaiyi ya dawo ba?.” Abbah ya zauna yana kallon ta kana yace, “kwana shida yace zuwa sati d’aya, to ai ma yau ko gobe ya kamata ace ya dawo saboda matar sa ta gıda.” Ammah ta girgiza kai tace, “To daman ba hakan yayi niyar yi ba, domin kuwa sati biyu ya cewa Ameena zasu yi kaga kenan daman haka yake son yi ya fad’a mana ne dan kar mu dakatar dashi.” Abbah da mamaki yace, “sati biyu? Shi yanzu dan bashi da hankali sai ya tafi yayi sati biyu uwar gidan sa fa?.” “Saboda ya raina hakkın ta mana yana ganin ba komai bane, baka ga yadda yarinyar ta rame ta yanayin maganar ta ma zai nuna maka ko waya basa yi. Daman abinda ya kaini kenan na kuma tambaya ta fad’a min.” Abbah baice komai ba ya fara kiran lambar Yusuf amma bata tafiya Ammah tace, “bafa zata shiga ba na tabbata da biyu yayi hakan saboda kar a same shi ayi masa fad’a, har ta WhatsApp nayi magana amma bata tafiya. İn bayan ya dawo aka yi masa fad’a ai kaga daga baya ne tunda ya riga ya aikata.” “Anya yaron nan baya shaye-shaye?.” “Ba wani shaye-shaye iskanci ne kawai wallahi dan yaga tana hakuri da lamarin sa, inda ace tana da iyaye ai bazai mata haka ba dan baza su kyale shi ba.” Abbah yace, “kuma ni shaida ne yana son ta kafin ya aure ta, amma meyasa ya canja haka lokaci d’aya?. Ka yiwa yarinya kishiya kuma ka tafi ka barta kai da amarya da shirme da rashin sanin ciwon kai?.” Ammah bata iya cewa komai ba saboda takaici tayi shiru Abbah ya kuma cewa, “Laifina ne ma dana amince masa da tafiyar da sai nace masa in bazai tafi da ita ba ya hak’ura, ban San zai bani kunya har haka ba.” Ammah tace, “inda nice na hana ai sai kace wani abun gashi kai da kanka ka fad’a.” Abbah yace, “in ya dawo zai gane kuskuren sa dan bai kyauta ba sam.” Ammah tace, “Daga baya kenan ai tunda yayi.” Abbah yace, “Wato ko anyi masa fad’an a banza kenan.” bata sake cewa komai ba ta tashi kawai ta fita dan a ganin ta kawai Yusuf ya raina su ne. Tsahon kwana sha uku kenan su Yusuf basa nan a safiyar na sha hud’un suka sauka a Nigeria kai tsaye aka d’auko su zuwa gida, Ameena bata ma San sun dawo ba tana zaune a falo taje asibiti ta dawo bata shiga dak’i bama balle ma taji ‘karar mota. Koda ta tashi ma alwala kawai tayi tare da yin sallar azahar sai a sannan ta shiga d’akin. Tana shiga d’akin taji an sake bud’e ‘kofa da sauri ta kalli wajan dan Amira da Zaytun basa nan sun je gidan Yaya Sumayya, ganin Yusuf ya saka ta kallon wajan sosai ta tabbatar shine ko kuwa dai idanun tane suke ganin sa, ita yake kallo shima ganin kamar an canja ta tayi masa fresh a ido sosai ya kawar da abinda yazo ransa yace, “Babu Sannu da zuwa?.” Sai tayi dariya kadan tace, “Sannu da zuwa.” Yayi murmushi yace, “Kizo kuzo ku gaisa da Asiya tana falo.” Kai kawai ta d’aga ya juya ya fita Ita kuma ta biyo bayan sa a ranta tana fad’in sai yau aka ga damar kawo ta wajena kenan. A falon ta da ta bari ta ganta a zaune ya d’or k’afa kan d’aya tana kad’awa ganin fıtowar ta sai da gaban Asiya ya fad’i a zuciyar ya tace, _tabdjim, taya zan bar wannan matar haka kawai ai da wuri zata kora ni. Na bar wannan ai sai ta kora ni_ a zahiri kuma sai tayi murmushi tace, “Barka da fitowa Mummyn Zaytun.” Ameena tayi murmushi tace, “ke za’a yiwa barka saboda Kun sha hanya.” Asiya cikin iyayi tace, “An sha hanya kam, ga gajiya sai da nayi bacci na tashi naji dad’i. A can din ma kullum a gajiye ake ba samun bacci muke ba Ameena tayi murmushi tace, “Allah Sarki, ai kin san zaman Saudia da banbanci da zama a Nigeria, ba sosai ake samun bacci ba daman. Allah ya anyi umrah a sa’a.” Ta amsa da amin kafin tace, “bama wai rashin bacci na garin ba, kin san abin ka da amarya, Ai mun gode na cewa my love ma yayi miki godiya ka fad’a mata?” Ta fad’a tana kallon sa. “Me kenan?” Ya fad’a yana zama a kujera mai mutum d’aya tace, “da ta bamu lokaci mana, kai kanka kace fa…..” da Sauri ya katse ta yace, “Asiya ba abinda nazo yi nan ba kenan, na kawo ki nan dan ki ganta itama ta ganki bana son surutun banza” ya fad’a yana hararar ta. Asiya tayi dariya tace, “Sai kace wata bak’uwa sai ka kawo ni? Ai in naga dama sai nace yau a nan zan kwana ko Mummyn Zaytun?.” Ameena ta d’aga kai alamun eh kafin ya kalli Ameena yace, “Ina Zaytun ne?.” “Sun fita da Amira yanzu zasu dawo.” Baice komai ba Asiya tace, “My love ka nuna min gidan nan na gani, Ina son hawa can saman gidan naje?.” Ya kalle ta yace, “Bamu yi maganar da ta tara mu ba ai ko?.” “To ai ba bak’i bane nida ita kawai abinda ka yanke yayi. Ni bara naje” ta fad’a tana tashi kawai ta fita. Ameena ta bita da kallon mamaki tayi dariya kafin ta dawo da kallon ta ga wani wajan daban, ya jima a haka yana kallon ta ya kasa magana shi kasan bai San me zaice mata ba kafin ya daure yace, “Kina Lafiya?.” wani iri taji a zuciyar ta ba tare da ya d’ago ba ta daga kai alamun eh kafin tace, “Ai ka gani a zahiri Lafiya nake.” yace, “Amma kin rame sosai, Kinyi haske kuma, ko kin yi rashin lafiya a kwanakin da bana nan?.” Nan ma girgiza kai tayi alamun a’a ya sake cewa, “To ramar ta meye?.” Ta kalle shi tace, “ta jin dad’i ce.” “Jin dad’i na saka rama ne daman?.” Ta wara ido tace, “au baka sani ba? Kaima kasan ai in ba jin dadin zaman gidan nan ba ai babu abinda zai saka ni rama.” Jin maganar ta kamar da biyu take yi sai yace, “kiyi hak’uri wayata ce ta fad’i ban samu na kira ki ba.” Murmushi tayi ta kalle shi ido cikin ido tace, “Allah sarki, da wayar aro nake ganin story a Ig kenan?.” Shiru yayi yana kallon ta ya kasa bata amsa sai yaga ta sake yin murmushi tace, “na fahimta ara kayi kar ka damu.” Shi dai kallon ta yake da yanayin ta da kalaman ta gabadaya sun canja masa kafin yace, “Na yanke hukuncin kwanaki biyu ga ko waccen ku, hakan ya miki?.” Tayi k’aramar dariya tace, “Abinda ka yanke kai da Asiya ai shine daidai, ina ruwan Ameenatu baiwar Allah.” Kallon ta yake yi ganin tana yi masa komai da biyu zaiyi magana kenan Asiya ta dawo falon ta zauna tace, “Naga ko Ina yayi kyau, I’m sorry Ameena na shiga d’akin My love na sama babu izinin ki.” Ameena tace, “kema mijin kine ai.” Shiru ne ya biyo baya baice komai ba itama haka kafin Asiya tace, “My love muje ko?.” Ya kalli Ameena yace, “Ina zuwa” ya fad’a yana fita shida ita bata ma sake kallon inda suka bi ba ta tashi ta tashi ta bar falon. Suna komawa b’angaren Asiya ya kalle yace, “Kiyi mana girki yunwa nake ji ban ci komai ba.” Ta bishi da kallon sama da k’asa, “Yau nasan b’angaren Ameena zaka tafi a can zaka kwana kuma kace nayi maka abinci? Kenan ita da miji nida girki? Kaima kasan bazai yu ba” Ta fad’a tana kallon sa shima kuma ita yake kallo cike da mamakin kalaman ta. #Mai daki #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema Book2 013 Cak ya tsaya yana kallon ta da mamaki da tsoro ganin ido cikin ido take fad’a masa ko kunya da nauyi bata ji ba bazata iya yin abinda ya sakata ba yace, “Ni kike cewa baza ki yi ba?.” Sai tayi sanyi tace, “Kayi hak’uri ba nufina kenan ba.” Kai ya girgiza kafin yaja baya yace, “Kafin na dawo ki tabbatar kin yi abinda nace, in ba haka ba ranki ne zai b’aci fiye da tunanin ki” yana fad’a ya fita ita kuma kamar za tayi kuka dan Allah ya sani babu ta yadda zatayi abinci yaci kuma yaje ya kwana da wata ba bazata iya ba. Maimakon tayi abinda yace kawai sai ta d’auki waya ta shiga kitchen d’in ta kira lambar Umma, Umma ta d’auka da sallama ba tare da ta amsa ba tace, “Umma daga dawowar mu yau sati biyu da auren mu har ya fara min fad’a yana saka ni aiki, taya za’a ce matar sa yau zai kwana wajan ta yace ni zanyi abinci? Nidai gaskiya bazan iya ba.” Umma taja tsaki ta kashe wayar Asiya ta tsaya tana kallon wayar cikin rashin sanin abin yi. K’arar shigowar sak’o taji ta duba taga da lambar Umman aka turo tayi saurin bud’ewa taga abinda aka rubuta; _Baki da hankali Asiya gabad’aya ban San me yake damun ki ba, a cikin gidan ki ko wanne lokaci mijin ki zai iya shigowa kike wannan maganar sai ya jiki?. Dan yace ki yi abinci ki dafa mana ai a haka zaki samu ki sake kama shi, kar ki manta Saudia kawai kika je ko mota bai siya miki ba, tun a yanzu zaki fara nuna masa halin rashin tarbiyayar ta ki sai ya fara gajiya dake ya fasa yi miki abinda yayi niya?, ki nutsu Malama in zaki makircin naki kar ki bari ya gane cewa bakya son matar sa ne, ki yi abu a nutse ki yi aiki da ilimi yadda koda kece da laifi ita zai zarga bake ba. Anjima Momi zata zo taya ki kwana in ta tashi tawo wa ki tabbatar an samu wata dubu d’arin ko sama da haka._ Karanta abinda tace sai tayi ajiyar zuciya tabbas fa kuma haka ne abinda Umma tace gaskiya ne, nan da nan ta saki rai ta fara dafa lafıyayyen abinci ba tare da wata damuwar komai ba. Ba jimawa ta kammala abinta ta barshi a kitchen din ta hau sama. Shi kuwa Yusuf gidan Ameena ya shiga ya hau zuwa d’akin sa kai tsaye wata k’aramar cover ya bud’e ya d’auki wata jaka ya sauka ya shiga mota ya tafi zuwa gida. Kasancewar Anyi sallah ya tarar da mahaifin sa yana cin abinci ya shiga da jakar a hannun sa ya ajjiye ya gaida iyayen nasa duk suka amsa har Ammah da baiyi tunanin hakan ba. Abbah ya mik’awa jakar yace, “Abbah ga sak’on da kace na tawo dashi.” Karb’a yayi yace, “Ashe d’azu ka dawo sati d’ayan kenan ko Yusuf?.” Yusuf ya sauke kai k’asa zaiyi magana Abbah yace, “Komai zaka fad’a k’arya kake Yusuf, daman abinda kayi niya kenan kuma shi kayi, ka kyauta ka nuna mana bamu isa ba ka nuna mana matar ka ba komai bace a wajan ka. Abinda nake so ka sani duk abinda ka ke yi ina sane da kai kar kaga bana magana mahaifiyar kace take magana ka d’auka ai ban sani ba ko ban damu ba, Ina sane wallahi tara ka nake duk ranar da na fusata daga ranar yarinyar ta gama zama dakai har abada. Nima uba ne bazan so a yiwa y’ata abinda kake yi mata ba. Ka bar yarinya ba kula babu abinda ya dame ka, rashin ka in ya jawo ta fad’a neman mata ko neman mazan kazo kace ai baza ka iya cigaba da zama da ita ba ga halayyar ta, to tun ba’a je nan ba zan yiwa tufkar hanci tunda kayi amarya baza ka iya cigaba da kula da ita ba sai ta matsa ta baka waje.” Yusuf kansa yana ‘kasa har Abbah ya gama magana bai ce komai ba sai da yaji yaje k’arshe ya d’ago zai yi magana ya dakatar dashi yace, “Duk wata k’arya da ka shirya fad’a min bana son ji, abinda na fad’a shi zanyi kawai.” Ya kalli Ammah da bata da biyar magana ganin sun had’a ido sai tace, “ai amaryar ma yar gwal ce ko kawo amare da ake yi gidsn iyayen miji bisa al’ada ita ba’a kawo ta ba, bazata iya zuwa ta gaishe da iyayen ka ba kenan?.” Ido ya runtse Allah ya sani yaso hakan tare yaso suzo amma ta b’ata masa rai d’in da tayi ne ya saka ya manta shaf bai neme ta ba sai yace, “Gobe zamu zo in sha Allah, kanta ne yake ciwo shiyasa.” Ammah tace, “Kar ma tazo mana Yusuf kai ka damu da ita bani ba, sai da safe ka gaishe da takwara” ta fad’a tana tashi ta shiga ciki. Abbah ya kalle shi yace, “Fushi tayi dakai shiyasa bata yi maka maganar Ameena ba, ta gaji da yi kullum abu d’aya, tun ina ganin kamar son da take yiwa yarinyar ne ya jawo hakan har na fahimci laifin kane. Na tambaye ka.” Ya kalli Abbah yace, “Ina ji Abbah.” “Kana son yarinyar nan lokacin da ka aure ta?.” Ya kalli Abbah ya sunkuyar da kai yace, “Abbah wannan duk bai tashi ba in sha Allah baza’a sake ba.” “Haka kake cewa ai koda yaushe, da Ina zargin ko ka fara shaye-shaye ne amma yanzu na tabbatar iskanci ne kawai.” Shiru nan ma yayi baice komai ba kafin Abbah yace, “ka aiko min da sark’ar dana baka ajiya tare da kud’in da ka kawo anjima zasu zo a karb’i kudin.” Ya daga kai alamun to Abbah ya tashi ya d’auki jakar shima ya shiga ciki ya bashi waje. Yusuf ya jima a zaune a wajan yana tunani sannan ya tashi ya fita ya nufi gida. B’angaren Asiya ya shiga tun daga falo k’arnin kwai ne yake tashi ya d’an yamutsa fuska ya shiga ciki sosai a nan yaji ai k’arnin daga kitchen yake fitowa. Shiga kitchen d’in yayi ya ganshi kaca-kaca anyi girki a bar komai a inda yake babu abinda aka d’auke. Yana shirin yi mata magana yaga ta sakko ya bita da kallo domin tun kayan da suka dawo ne a jikin ta bata canja ba tace, “Sallah nayi yanzu zan gyara wajan.” Baice komai ba ya huce ta ya hau saman ta bishi da kallo ta kalli kitchen din a bayyane tace, “A nan fa za’a samu matsala dani gaskiya wallahi, ba komai nake lalatawa na gyara ba. ta fad’a tana fara gyara wa zuciyar ta duk babu dadi. Ta jima kafin ta gama a lokacin ya sakko har lokacin yana jin k’arnin amma ba kamar d’azu ba ya kalle ta yace, “Ina abincin?.”D’aukowa tayi tazo ta ajjiye a kan center table tace, “kayi hak’uri my love in sha Allah bazan sake abinda nayi ba d’azu” ta fad’a tana zubewa akan carpet tana zuba masa abincin. Karb’a yayi data gama yace, “Zaki iya kwana ke kad’ai ne?.” Ta girgiza kai tace, “A’a Momi tazo ai ta hau sama dakina wanka take.” Kai ya girgiza kawai ya kai abincin bakin sa amma k’arni ya hana shi zubawa a cikin bakin. Ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ganin ta zuba masa ido hakan ya saka shi zubawa a bakin yana taunawa. A baki akwai taste sosai amma k’arni bazai barka kaji dad’in sa yadda kake so ba, ajjiye plate din yayi yasha ruwa ya kalle ta itama shi take kallo tace, “Badai ka gama ci ba?.” Yadda tayi maganar da shagwab’a ya saka shi yin murmushi yace, “in na dawo daga tafiya bana iya cin abinci daman na karb’a ne dan naci girkin amaryata kuma sannan dan na tabbatar ta cika umarnina, Allah ya taimake ki abinci kuma yayi dadi.” Murmushi tayi cikin jin dadi ta kalle shi tace, “Har naji dad’i, da farko n d’auka bai dadi bane.” “Yayi dadi sosai amma bai kai ki” ya fad’a yana daga mata gira d’aya. Dariya tayi sai kuma ta had’e fuska kamar zatayi kuka ta kalle shi shima ita yake kallo yace, “Meye kuma? Taso Kizo” ya fad’a yana yafito ta da hannu ta taso ta dawo kusa dashi din tana sake narkewa. D’an baya yayi da fuskar sa jin yanayin jikin ta khamshin sai a hankali amma ya daure bai ce komai a akai na yace mata, “Meye na kukan?.” Asiya ta kwanta a jikin sa tace, “Na saba kwana a jikin ka my love, yau sai nake ji zuciyata ta cika da kewar ka dan nasan yanzu zaka tafi wajan Aunty.” Murmushi yayi yace, “Ni kaina zanyi kewar ki sosai.” “Ba wani kewata da zaka yi, bayan zaka samu matar ka ni wa zan samu?.” “Ki saka a zuciyar ki Muna tare, kuma gangar jikin mu ce bata waje d’aya amma zuciyar mu a had’e take.” Kai ta girgiza cikin gamsuwa tace, “Aunty tana da kirki sosai kaga yadda muka gaisa d’azu kamar mun saba.” Murmushi kawai yayi bai ce komai ba tace, “zanje gobe na rok’o alfarma a bani Zaytun mu kwana tare.” Ya mata kiss a goshi yace, “Sai kinzo” ya fad’a tana tashi tsaye dan abinda jikin ta yake fitarwa san baya mata dad’i. Itama mik’ewa tayi tace, “Zanyi kewar ka my love.” Shima ya ja kumatun ta yace, “Nima zanyi kewar ki, ki kulle gidan sai da safe” ya fad’a yana fita ta biyo shi har ya shiga sannan ta koma. Khamshi ya daki hancin sa tun daga falo a lokacin yaja numfashi cikin jin dad’i a ransa yana fad’in,_Ameena sarkin khamshi._ abinci ya tarar akan dining yana kallon abincin ya jiyo sautin sakkowar ta daga sama ya d’aga kai yana kallon ta tayi masa kyau cikin material d’inkin riga da siket rigar har guiwa kuma mai fad’i sosai. Ganin yana kallon ta sosai sai tace, “Sannu da zuwa.” “Yauwa” ya amsa yana zama a akan dining kafin yace, “Allah yasa anyi girkin dani.” Ta k’araso wajan tace, “Bani na dafa bama Amira ce.” Da wata irin murya ya kalle ta yace, “girkin Amira zanci?.” Ta kalle shi itama tace, “Sai na dafa maka in kana so.” Ya girgiza kai ya bud’e abincin yace, “Zuba min kawai, sun dawo ne?.” Ameena ta fara zuba masa tace, “Eh sun dawo suna sama.” Abincin da ta zuba ya fara ci ta juya zata bar wajan ya rik’o hannun ta ta kalli hannun ta kalle shi yace, “ki dawo ki zauna na gama.” Ba musu ta zauna yana cin abincin ya kalle ta yace, “Baza ki ci ba?.” Kai ta girgiza kawai alamun A’a ya tashi daga inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna yace, “bud’e bakin ki na baki, zama da yunwa ne yake saka ki rama haka.” Ta kalle shi tace, “Bana jin yunwa fa.” “Sai kin ci.” Kallon sa take taga alamun shiri yake nema sa ita, ita kuma bata shiryawa hakan ba sannan kuma ba tasan magana hakan ya saka ta bud’e baki ya fara zuba mata abincin tana ci. Babu mai magana cikin su sai k’arar cokalin da yake ci, sau uku ya bata kawai ta girgiza kai tace, “na koshi fa.” Cigaba da ci yayi har ya cinye ya tashi har zai hau sama sai ya juyo yace, “Ina jiran ki.” Da kallo ta bishi kawai dan tasan dan yasan yayi laifi ne yake mata wannan abun wani haka kawai bazai neme ta ba. Kwashe abinda aka b’ata tayi ta kashe hasken k’asan da komai ta hau saman ta samu Amira ita kad’ai da alama ya tafi da Zaytun. Zama tayi kusa da Amira babu mai magana dan kuwa bata niyar zuwa wajan ba a wannan lokacin. Wayar tace take k’ara ganin shine yake kira ya saka ta d’auka ta saka a kunne yace, “Zo sama yanzu.” Abinda yake kenan ya kashe ta tashi ta nufi saman a zuciyar ta ta k’udurce baza ta bashi wata damar da zai yi wani abun da ita ba D’akin ta shiga ta samu yana dube-dube duk ya fito da abubuwan drawer yayi mata filla-filla tana shiga yace, “Ina sark’ar gold din dana ajjiye a nan?.” Wajan ta k’arasa ta kalli inda cover din da sark’ar take ciki amma babu sark’ar ta kalle shi tace, “Ban sani ba nidai nasan a nan take, ko ka canja mata waje?.” “İn na canja mata waje taya zan tambaye ki? Ki Tuna ko kin canja mata waje.” Ta girgiza kai tace, “ban d’auka ba tunda ka fad’a min sample ne aka kawowa Abbah ya baka ajiya ban d’auka ba.” “To Ina taje kenan?” Ya fad’a yana kallon ta. Tace, “ban sani ba wallahi.” “Kamar ya baki sani ba? Wa na Bari a gidan?” Ya fad’a yana d’aukar wayar sa da take kara. Abbah ne yake waya ya kalle ta yace, “Kin gani Abbah ne yake min waya kuma akan maganar gold din ne” ya fad’a yana d’aukar wayar ya saka a kunne. Abbah yace, “Yusuf ka tab’a kudin nan ne?.” Yusuf ya kalle ta yace, “Abbah Lafiya dai?” Ya fad’a yana saka wayar a speaker. Abbah yace, “an lissafa kud’in kuma an tab’a ko wacce rafa ta kud’in a zara guda d’aya, Kaga kenan babu dala dubu goma ko wacce rafar dala an dauk’i dala dari.” Yusuf gaban sa ya fadi yace, “amma Abbah ban tab’a komai a kudin ba ba wallahi, amma bara na tambayi……” Abbah yayi saurin katse shi yace, “shikenan kar ka tambayi kowa ai ba’a taba’a samun hakan ba sai wannan karon, gobe ka fito da gold din.” Kai ya d’aga ya katse wayar ya dawo da kallon sa ga Ameena da take kallon sa yace, “Meye hakan yake nufi? Ina kudin nan suka shiga sannan Ina sark’ar dana ajjiye?.” Ameena tace, “Wallahi ban sani ba ban d’auka ba kaima ka sani.” Ya dafe kansa ji yake kamar ya mare ta yace, “nida waye a gidan in bake ba? Waye zai d’auki kud’in nan in ba ke ba?.” Ameena ta zaro idanu waje tana kallon sa tace, “kana so kace nice nayi maka sata?.” Ya dafe kansa yana zaga d’akin tare da bincike ko Ina ko zai ga sark’ar amma babu ya juyo yace, “Wacece a gidan in ba ke ba? Waye yake shigowa d’akin nan in ba ke ba?, in wasa kike min ki d’auko sark’ar nan Ameena ba nawa bane ta Abbah ce shima kuma sample ce.” Ameena tace, “Wallahi ban d’auka ba kaima kasan ban tab’a d’aukar duk abinda ka ajjiye ba, kuma ni bana shigowa d’akin nan sai in zan share ban San da kud’i ba amma nasan da sark’a kuma ban d’auka ba.” Yusuf yace, “Wayyo Allah! Yanzu kenan kud’in da k’afar su suka fita ko sark’ar da k’afar ta ta tafi?.” “Amma d’azu ai Asiya ta shigo d’akin nan ka tamabaya kaji ko ta ganta.” Wara ido yayi yana kallon ta cikin mamaki yace, “ohh na gane, kenan dan ta shigo d’akin nan na wasu sakanni kawai shine har taga sak’ar da kudin da ke kika san inda suke kuma ta d’auka?, ina tasan inda suke? Ina tasan aka ajjiye?. Kenan ita kike so ki d’orawa bayan a wajan ki aka nema aka rasa….?!.” #Nana Haleema #Book2 #Mai Daki #Paid #500. Book2 014 Kallon sa take yi cikin k’unar rai da zallar takaicin a zuciyar ta nan da nan ranta ya baci hakan ya bayyana a kan fuskar ta tace, “Ni kake cewa nayi maka sata? Ni Ameeena nice na d’aukar maka sark’a kuma nice na satar maka kudi?.” Yadda take kallon sa take magana sai ya d’an ja baya yace, “To nida waye a gidan in bake ba? Yaushe na dawo gidan nan? Ita wacce kike maganar bata tab’a shigowa gidan nan ba sai d’azu har ta Ina tasan inda ake ajjiye kud’i da zata d’auka?.” Ameena ta girgiza idanun ta sukayi ja ta hana hawaye sauka tace, “Ban tab’a yi min abinda bazan manta dashi ba a duniya kamar abinda kace min yau, ni ka kalla ka cewa nayi maka sata duk tarin ajiyar da kake bani ban tab’a dauka ba sai wannan karon, me kud’in zasu yi min in na d’auka? Me zanyi ma dasu da satar maka sark’ar gold?. Ni ba b’arauniya bace kai ka sani, banga abinda zaka ajjiye na dauka ba Yusuf, koda duniyar nan zaka ajjiye bata ishe ni kallo ba dan ko wanda ya ajjiye din baya gabana balle kuma dukiyar sa. Kaje ka nemi wacce tayi maka sata amma ba Ameena ba.” Kallon ta yake itama tana kallon sa tana ja baya ta juya zata fita Zaytun da take zaune tana kallon su kamar tasan abinda suke yi ta fashe da kuka ta biyo bayan ta ta d’auke ta suka sauka daga saman da sauri. D’akin ta shiga ta kalli Amira da take zaune tana danna waya tace, “Amira tashi ki saka hijjabin ki yau bazan kwana a cikin gidan nan ba” ta fad’a tana ajjiye Zaytun ta d’auki key din mota da wayar ta ta saka hijjabi. Amira ta mik’e tsaye tace, “Aunty Ina zamu je? K’arfe goma na dare fa.” Bata yi mata magana ba ta fita daga d’akin dole ta saka hijjabin ta d’auki wayar ta da Zaytun ta biyo bayan ta. Mota ta bud’e ta shiga mazaunin driver Amira duk tsoro ya cika mata zuciya Allah yasa kar tace bauchi zasu tafi a daren nan ta shiga itama Ameena taja motar mai gadi ganin an kunna mota ya saka ya bud’e musu gate suka fita. Tuk’i kawai take ba tare da tasan inda zata je ba sai a lokacin ne ta fara kuka, Amira ta kalle ta tace, “Mummy babu inda zamu je sai Bauchi kuma dare yayi.” Shiru tayi bata ce komai ba kawai tuk’a motar take yi jin zuciyar ta take in akace ta kwana a gidan Yusuf zata iya mutuwa saboda b’acin rai da take ciki a wannan lokacin. Waje ta samu a gefen titi ta faka kawai ta kifa kanta a kan sitiyarin motar ta fashe da kuka mai tsuma zuciya, kuka take sosai da iyakar k’arfin ta dan bata da abinda zatayi da ya wuce kukan a wannan lokacin. Amira ma hawaye ta fara sharewa dan ta tabbatar abinda Yusuf yayi mata ba k’arami bane tunda gashi tayi abinda bata tab’a yi ba. Kwankwasa glass din gefen Amira ake yi Amira ta kalli matar ganin ta santa sai ta sauke glass din tana gama saukewa matar tace, “na fad’a maka motar Ameenan Yusuf ce gata a ciki” ta fad’a tana kallon wani daga gefe ya k’araso yana fad’in, “Ameena! A wannan Daren?.” Kallon Amira yayi da Ameena da ta kifa kanta har lokacin kuka take bata d’ago ya kalli Amira yace, “Me ya fito daku a wannan daren haka?, ina Yusuf?.” Amira tasan Yayan Yusuf ne hakan ya saka tace, “Ban sani ba, Nidai kawai tace min na tashi mu tafi bazata kwana a gidan ba. Mun fito kuma ta rasa inda zata je shine muka tsaya a nan tana kuka.” Ya d’auko waya yace, “Bara na kira Yusuf din naji wanne rashin hankali ne zai saka ya barku ki fito ku kad’ai a daren nan.” Matar sa tace, “A’a kar ka kıra shi, tunda kaji hakan akwai wani abun. Zan shiga motar naja yanzu muje gıda ta kwana a can da safe sai ka kira shi zuwa lokacin ta wuce yanzu kiran bashi da amfani.” Ya girgiza kai alamun gamsuwa ta k’arasa inda Ameena take ta d’ago ta har lokacin idanun Ameena a kulle suke tana hawaye tace, “yi hak’uri Ameena, shiga baya zan ja motar mu k’arasa gida.” Kamar Ameena bata ji ba bata motsa ba ta sake cewa, “yi hakuri ki fito muje.” A hankali ta fito ta bud’e mata baya ta shiga ita kuma ta shiga gaban ta kunna motar taja zuwa gidan ta. A kan idanun Asiya Ameena ta fit adaga gidan ana kulle gate din ta kalli Momi da yake gefen ta sukayi dariya tare da tafawa, Momi tace, “Amma Asiya ke shaidan ce wallahi, sati biyu a gidan mijin ki har kin saka uwar gidan sa tayi yaji?.” Asiya tayi murmushi tace, “Taya zan barta su more wannan daren ni ina nan a zaune gani banza mara hankali? Har wani rawar jiki yake dan zai koma wajan ta ni kuma sai na bari? Ai wallahi bata isa ba tunda na shigo gidan nan wallahi Allah sai ta bar gidan ko ta wanne hali, banzo gidan nan na zama a bayan ta ba sai dan ta zama a bayana.” Momi tace, “Dakyau jinin Umma, yanzu Ina kud’in da kika d’auko?.” Asiya ta ‘karasa wajan kayan ta ta d’auko dala dubu d’aya ta kalli Momy tace, “kin gansu nan” ta saka kud’in a hanci taja numfashi tace, “duk inda kud’i yake na shiga sai na jiyo khamshin su wallahi, kamar nasan yau zaiyi amfani dasu na d’auka sai gashi ya nema yace suna Ina tace bata sani ba.”Momi tace, “ke taya kika san hakan akayi?.” “Momi Kenan, yanzu nida ke ne a d’akin nan na ajjiye kud’i na fita na dawo ban gan su ba wa zan tambaya?.” Momi tace, “Ni zaki zarga.” Tayi murmushi tace, “Meyasa?.” “Saboda ni kad’ai nake shigowa d’akin nan, kuma ni nasan kin ajjiye kud’i dole ni zaki tambaya.” “In kika ce baki d’auka ba zan yarda?.” “A’a, sai dai kawai kiyi kara ko kyale ni amma kin san ni na d’auka sabida kud’in basu da k’afa.” Asiya tayi dariya tace, “İrin wannan tarkon na had’a mata kuma ta fad’a. Kud’i nice na d’auka kuma yadda na d’auka dole ka yarda sata akayi saboda ko wacce rafar dalar guda d’aya na d’auka a ciki” ta fad’a tana irga dalolin tana murmushi.Momi tace, “bani na rik’e nima na kafa tarihi na tab’a rik’e dala.” Bata tayi ta rik’e ta zauna a gefen gado ita kuma Momi tace, “Yanzu mayar masa dasu zakiyi?.” Hararar ta tayi tace, “Baki da hankali, ai wannan da kike gani biyar na Umma ne ta gama biyan bashin biki biyar nawa ne dan azurta kaina zanyi wallahi.” Momi tace, “Da gaskiyar ki, amma naga matar tana da mota ke bai siya miki ba.” “Next target d’ina akan mota ne Momi, dole ya siya min mota koda baya so.” “Yanzu gobe me zaki kaiwa babar tasa?.” Ta sauke numfashi tace, “mu jira goben dai, koda ban farka da wuri ba ki tabbatar da safe kin k’ona wannan turaren da Umma ta bayar Ina so hankalin sa ya d’auke daga batun Ameena gabad’aya taje can ta karata.” Momi tace, “Yanzu rik’e kud’in nan naki, bara naje na had’o shayi nima na zama yar gidan y’an gayu” ta fad’a tana bata kud’in ta sauka daga saman. Asiya ta tashi sai da ta tabbatar ta sauka ta bude wardrobe din ta ta d’auko sark’ar da ta d’auko daga d’akin Yusuf tana dubawa tace, “Wannan ai nasan kud’in ta a kalla zai yi miliyan biyar ko goma koma yafi haka, in na siyar ai na zama Hajiya na loda kud’in a banki babu wanda zai san na d’auka ni kad’ai zanci kudina” ta fad’a tana mayar da sark’ar mazaunin ta zuciyar ta fess dan ko Umma baza ta fad’awa ba. Abban Fiddausi ya kira Kawun su Fiddausi akan maganar auren ta suna tattaunawa a kai yace, “Dan Allah ka tabbatar kayi bincike a kansa, badan yau zan wuce Umra ba ai da babu abinda zai hana banyi da kaina ba. Ayi bincike in ka tabbatar babu matsala ko yaushe yake so a d’aura mata auren tunda ranakun iddar ta sun k’are. Amma ka tabbatar anyi bincike kar ayi auren nan babu bincike.” Kawu yace,”in sha Allah za’ayi komai kamar kana nan, babu abinda zai faru in sha Allah.” Abba yace, “haka nake so Allah ya sanya alkhairi.” Ya amsa da amin aka zo ana ta sallama da Abba kafin kafin Kawu ya wuce dan ya kaishi airport. Duka y’an gidan suna nan bayan tafiyar Abba ne Mama take sanar dasu batun auren Fiddausi ya taso babbar yayar su wacce duk ta fisu auren mai kud’in mijin tane ma ya biyawa Abba Umrah tace, “A dai yi bincike a kansa kar aje ba na gari bane ba.” Mama tace, “Ai sanannen mutum ne halayyar sa bazata b’uya ba.” Bata ce komai ba tayi shiru akwai Fiddausi ta kalle ta cikin mamaki ita bata tab’a sanin dan uwan da suke ciki d’aya uwa d’aya uba d’aya zai yiwa dan uwan bak’in ciki ba in ka samu abinda yafi nasa ba sai a gidan su. Tashi tayi kawai ta shiga d’aki ta kira Alhaji Bello a waya bai d’auka ba ba jimawa ya biyo kiran ta d’auka tace, “Ina ka ajjiye wayar Ina kira baka d’auka ba?.” Yace, “Yi hak’uri Fidy Ina aiki ne.” “Albishir na kıra nayi maka.” “Ina jin ki masoyiya.” “Yau dai Abba ya tafi umrah, kuma ya bar komai a hannun Kawu dan haka kazo kawai a daura auren jibi jumu’a a wuce wajan. Kawu bashi da matsala nasan da kazo da batun shikenan.” Cikin yanayin farin ciki taji yana cewa, “Da gaske kike baby? Kai amma naji dadi sosai, a safiyar nan zan taso daga Abuja na tawo Kano ayi komai na tafi dake. Kewar ki a Kullum kamar zata kashe ni haka nake ji, kai nayi farin ciki sosai.” Yadda ya gigice ya bata nishadi sosai tace, “Kayi aikin naka yanzu, in ka gama mayi magana.” “Ai in na gama na dawo ba wajan ki zan tawo ba wajan Kawu zanje kawai ayi a wuce wajan na gaji da zama babu ke.” “Shikenan sai naji labari mai dadi” ta fad’a tana kashe wayar zuciyar ta cike da farin ciki a bayyane tace, “Da zarar an d’aura mana aure ranar a hannun y’an sanda Ibrahim zai kwana” ta fad’a tana girgiza kai domin tayi alqawarin tabbatar masa da ita ba matar da zai daka bace ya zauna lafiya. A safiyar Ibrahim yana zaune suna ta hıra da Hajiya sallamar da akayi ne aka shigo ya saka shi mik’ewa tsaye wacce ta shigo ta kalle shi tace, “A’a d’an tsoho dan ka ganni kuma sai ka tashi?.” Yayi murmushi yace, “A’a daman zan wuce wajan aiki. Ina kwana.” “Lafiya lau, ya aikin naka?.” “Alhamdulillah.” “Allah ya taimaka ya bada nasara.” Ya amsa da amin kafin ya kalli Hajiya yace, “Hajiya na tafi.” Hajiya tace, “To Allah ya kiyaye ya bada abinda aka je nema.” Ya amsa da amin ya fita da machine d’insa. Wacce ta shigo ya bishi da kallo kafin ta kalli Hajiya tace, “Tunda yaron nan ya rabu da Fiddausi shikenan komai ya zama ma sha Allah. Ki duba yadda yayi kyau k’uruciyar sa ta bayyana da duk yana yawo a rame.” Hajiya tace, “Bari kawai, ni kaina abin mamaki yake bani. Wallahi in kika alkhairin da ya samu bayan rabuwar su sai kin yi mamaki. Yanzu haka dubu goma ya bani kyauta yace nayi dinki.” Wacce take amsa sunan Suwaiba kanwar Hajiya tace, “ai naga alama wallahi, babu abinda zamu ce Allah sai godiya. Yanzu matar aure ya kamata a samo masa ya aura.” Hajiya tace, “nima zuwa yanzu Ina so yayi auren ya wuce zama haka babu mata duba da akwai k’uruciya a tare dashi, watak’ila yana son yin auren kawaici da zurfin ciki irin nasa ne ya saka bazai fad’a ba, amma matan ne sai a hankali duba da halin Fiddausi na zahiri daban dana bad’ini. Ba kwarya bane balle ka kwankwansa Kaji mai k’wari a cikin su “Ai ba kowa bane kamar Fiddausi, ba duka aka zama d’aya ba ai.” “Haka ne, Allah ya had’a shi da matar da zai so ya aura mai hankali ko bazawara ce dan auren budurwa a yanzu akwai wahala, sai anyi ta tsarabe-tsaraben kashe kudi.” Suwaiba tace, “Ni kuwa da zai amince akwai yarinya mai hankali da kyau kawai jinkirin aure ta samu har ta kawo wannan lokacin, amma hankali yarinyar nan tana dashi babu karya wallahi ga ladabi ko bata sanki ba ta ganki a hanya zata gaishe ki ba.” Hajiya tace, “A Ina take?.” “Itama a Yakasai take dan gidan su dana Fiddausi ai babu wani nisa, Ina jin ma tasan Fiddausi sunan ta Rukayya yarinyar. Wallahi tana da hankali sosai Allah ne bai kawo mata miji ba har yanzu, ga mahifinta babban mutum na kirki gaba da baya. Hajiya tace, “To Allah ya zaba abinda yafi alkhairi, in itace rabon sa Allah ya had’a su in ma ba ita bace Allah ya kawo wata mai alkhairi. Haka aka gano Fiddausi ma ai aka dinga murnar tana da hankali da ilimi sai gashi babu amfanin da sukayi a zaman auren ta.” Ta amsa da amin suka cigaba da tattaunawa akan abubuwan da suka shafe su. B’angaren Yusuf k’arar wayar sace ta tashe shi daga bacci tun bayan fitar Ameena da yasha giya ya koshi ya baje yana bacci bai farka ba sai lokacin. Yamutsa fuska yake ya kalli agogo yaga lokaci ya tafi baiyi sallah ba ya zabura zai sakko daga kan gadon aka sake masa waya hakan ya saka shi ya kalli wayar ganin sunan Yayan sa ya saka shi ya d’auka ya saka sa kunne yace, “Yusuf kana Ina tun d’azu nake maka waya baka d’auka ba?.” Yusuf yace, “bacci nake yanzu na tashi.” “To da ka shirya kazo gıdana yanzu nan Ina neman ka” to kawai yace ya katse wayar sai kuma kiran Abbah ya shigo. Gaban sa ya fad’i sosai tunawa da yace ya kai masa sark’a gashi bai san inda take ba a haka ya d’auka yace, “Abbah barka da safiya.” Abbah yace, “Barka. Kana ji ka bar sark’ar a wajan ka yace sai nan da sati d’aya zai zo ya amsa basai ka fito da ita ba.” Ajiyar zuciya yayi yace, “To Abbah.” Daga haka Abbah ya yanke wayar shi kuma ya shiga bandaki. A gaggauce yayi wanka ya fito ya saka kaya ya tayar da sallah bayan ya idar ya shirya sosai cikin manyan kaya wanda suka yi masa kyau ya d’auki makullin mota ya sakko zuwa k’asa. Shiru babu motsin kowa ga wuta a kunne ta ko Ina haske ne yasan kuma ba haka ta saba ba tana kashe komai ne sai tana wajan take kunna haske. Gaban sane ya fad’i hakan ya saka shi nufar d’akin ta da sauri yana shiga ya tarar bata nan. Ya dafe kai a bayyane yace, “Ina taje kuma?.” Da sauri ya fito ya duba ko Ina bata nan kai tsaye ya shiga b’angaren Asiya. Yana shiga khamshin turare mai k’auri da wari ya daki hancin sa har sai da idanun sa ya tara ruwa saboda hayak’i da kuma kaurin turaren a bayyane yace, “Wannan wanne irin turare ne mai hawa kai?.” “Asiya!” Ya fad’a da karfi ta fito a guje tana fad’in, “my love barka da zuwa.” Zata fad’a jikin sa yayi sauri ja baya domin tun kafin ta k’araso ya jiyo tashin da jikin ta yake yi ya kalle ta yace, “Wanne irin turare ne wannan mai hawa kai?.” Ta kalle shi tace, “hawa kai kuma? Ni banji ba.” Yayi k’aramin tsaki yace, “Kinga Ameena ne da safen nan?.” Asiya tace, “tun dai dare da naji alamun za’a kunna mota sai na fita dan a zatona wani ne babu Lafiya na ganta tana shiga mota nace waye babu lafiya tayi min banza dana matsa sai ta fad’a min sai take masifa tana cewa ai nice silar komai Allah ya isa bata yafe ba ta shiga mota ta fita.” Ya wara ido yace, “kina so kice tun dare ta bar gidan nan?.” Ta d’aga kai alamun eh ya dafe kai yace, “Ke kuma da yake baki da hankali shine baza kizo ki sanar dani ba…..?” Ya fad’a yana juyawa ya fita cikin tunanin inda zai ga Ameena ya bar Asiya a daskare a wajan tana tunanin lallai ya kamata ta canja shiri domin shirin nata baiyi aikin da take so ba ko kusa. #Mai daki #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema Book2 015 Yana fitowa wayar Abie ya sake shigowa bai d’auka ba ya shiga mota kai tsaye ya nufi gidan sa dan bai san kiran da yake masa ba dole yaje yaji dalilin kiran. A harabar motar ya faka ya shiga cikin gidan da sallama ya same shi shida matar sa a zaune a falo yana shiga Abie yace, “tun d’azu nake jiran ka sai yanzu zaka zo?.” Ya karasa ya zauna yace, “ban san kana kırana ba, hankalina ne gabad’aya baya jikina. Ina kwana.” “Lafiya lau” ya amsa yana kallon sa Yusuf ya kalli matar sa yace, “Ina kwana Aunty.” Tace, “lafiya lau Yusuf, ya amarya?.” “Tana nan lafiya.” “Yaushe zaka kawo mana ita?.” Ya murmusa yace, “zata zo in sha Allah.” Ta mik’e tana fad’in, “Allah ya kawo ta” ta fad’a tana basu waje dan su tattauna. Abie ya kalle shi yace, “Lafiya kake na ganka a rud’e?.” Yusuf ya kalle shi ya d’an yi ‘karamin tsaki yace, “Babu komai Lafiya lau nake.” Ya girgiza kai yace, “naga motar matar ka da daddare Jiya Ina taje ka bari ta fito ita kad’ai?.” Gaban Yusuf ya fad’i ya kalle shi ya bud’e baki kamar zaiyi magana sai ya fasa dan bai san abinda zai ce ba. Abie ya girgiza kai yace, “Wallahi ban tabbatar da abinda Ammah take fad’a a kanka gaskiya bane sai yanzu, Yusuf in baka son yarinyar ka sake ta mana ka huta itama ta huta, wannan wahalar da kake bata duk ta meye?.” da sauri ya kalli Abie shima shi yake kallo yace, “Eh ka sake ta, wannan wahalar da kake bata in wani abun ya same ta wallahi baza’a kyale ka ba.” Yusuf yace, “Wallahi Abie ban san ta fito ba kuma har bayan ta nabi naje gidan Ammah akace min bata zo ba, shiyasa ka ganni a rud’e hankalina yana wajan ta wallahi, ban san inda take ba.” Abie yace, “Hmmm! Shiyasa naga Ina ta kira kana bacci ko?.” Yayi shiru baice komai ba Abie yace, “Jiya da daddare mun fita a k’asa munje dubiya muka ga motar ta a nan gaba damu da alama yawo kawai take a titi ta rasa inda zata je, Umaima ce take fad’a min waccan motar Ameena ce nake mamakin abinda ya fito da ita da daddare muka k’arasa muka tabbatar itace daga ita har yarinyar da suke tare Amira da y’ar taka mai sunan Ammah kuka suke, sai Umaima ce ta karb’i tuk’in suka k’araso gidan nan. Yadda naga yanayin ta ya tabbatar min da abinda kayi mata ba ‘karami bane hakan ya saka ta baro gidan kana dare.” Yusuf ya sauke Ajiyar zuciya a bayyane yace, “naji dad’i da ta kasance tana gidan nan da ban san ya zanyi ba.” Abie yace, “A nan ta kwana bayan anyi mata allura, har yanzu bata ce komai ba na kuma tabbatar bata so tazo nan ba. A yanayin ta ma gabadaya bata so tazo gidan an ba taso tayi nisa da kai.” Yusuf yace, “laifina ne wallahi Abie amma nayi nadama bazan sake ba.” “Daman ai ko baka ce ba ni nasan laifin kane, in laifin tane ai baza ta bar gidan ba. Yusuf kana wasa da marainiyar Allah ko? Kana wasa da alqawarin saka d’auka ko?. Kai kasan mahimmacin alqawarin kuwa? Kai kasan waye maraya kuwa?.” Yusuf yace, “A’a ba haka bane…..” Abie ya katse shi ta hanyar cewa, “Kai kasan in Ammah taji labarin nan sai ranka ya b’aci ko?.” Ya girgiza kai alamun eh yace, “Dan Allah kar ka sanar da ita, kuskure ne na aikata bazan sake ba in sha Allah.” “Kai dai ka sani, ya kamata kasan ko wacce mata ka samu a yanzu baza ka samu kamar Ameena ba, kuma wallahi matuk’ar na sake jin wani abun da kayi mata ni da kaina zan hanata komawa gidan ka domin nima yayan tane in Humaira ce ai bazan so ayi mata haka ba.” Yusuf yace, “baza’a sake bama in sha Allah.” Abie ya mike tsaye yace, “kaje ka same ta in zata bika shikenan in kuma bazata koma ba zata zauna a nan kamar gidan yayan ta, kuma wallahi indai ta zab’i zaman nan naga k’afar a gidan sai ranka ya ‘baci.” Yusuf ya tashi ya shiga inda ya nuna masa ya same ta a zaune ta jingina da gado ta rufe ido kafafun ta a mike sand’al akan gado tana sauke numfashi a hankali. A hankali ya k’arasa ya zauna kusa da k’afar ta ya saka hannayen sa duka biyun yana matsa k’afar a hankali ta yana cewa, “Ni mai laifi ne a wajan ki Ameena dan Allah ki yafe min, nasan nayi kuskure amma bazan sake aikata hakan ba in sha Allah. Nasan banyi daidai ba bai kamata nace abinda nace ba tunda nine zan bayar da shaidar ki, dan Allah kiyi hak’uri ki yafe min bazan sake wannan kuskuren ba.” Tunda ya shigo d’akin tasan yazo saboda khamshin turaren sa nan da nan zuciyar ta ta cigaba da k’una tana ayyana inda ace gidan yayan tane ba yayan sa ba da yanzu ba’a kira shi ba, da yanzu ba’a bashi damar ganin ta ba amma da yake kamar gıdan su ne Gashi har cikin d’aki. “Dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba.” Ko motsi batayi ba balle ta amsa yace, “Ameena!.” Bata bud’e ido ba balle tayi magana tunda suke dashi bata tab’a jin haushin sa kamar yadda take ji a lokacin ba shiyasa ko kallon sa ma bata so tayi, duk abinda yake mata bata tab’a jin haushin sa kamar na yau ba. “Ameena dan Allah.” Sai a sannan ta bud’e ido ta kalle shi tace, “Meyasa kake bani hak’uri? Saboda ka kirani da b’arauniya?.” Ya kulle ido ya bud’e ya kalle ta zaiyi magana tace, “Inda ace Ina sa gata Ina da inda zanje da Yusuf baka isa ka same ni a nan ba, wallahi da kai da sake ganina sai ka manta ya kalar fuskata take, amma rashin iyaye shine yake min cikas a ko yaushe. A duk sanda naso guje maka sai na rasa inda zan Kefa k’afata kafin nayi wani tunani ka riske ni. Wallahi Yusuf duk ranar da na bar gidan nayi wani wajan na barshi kenan har abada bazan sake waiwayo ka ba.” Yayi shiru yana sauraren ta yadda maganar ta take fita zaka san ranta a ‘bace yake kuma tana fama da rashin lafiya ta sake cewa, “Ni ka cewa barauniyar kudi da sark’a bayan tarin kwanakin da muka d’auka dakai ban tab’a maka satar maka koda zare a d’akin ka ba sai yanzu zan fara dan na yiwa amaryar ka sharri, in na d’auki abin ka me zai min? Baka san na jima da daina amfani da duk wani abu da ya shafe ka ba? Akan me zan d’auka baka sani ba?. Baka San da kai da shirgin ka basa gabana ba?, wallahi Yusuf an saka ruwa an wanke min zuciya haka nake ji a kanka, kaima baka cikin zuciyata balle kuma wata banzar dukiyar ka da a in na d’suka babu abinda zata k’ara min sai azabar kabari.” Ya sassauta murya yace, “Raina ne ya b’aci shiyasa kike wannan maganar, Kiyi hakuri kawai .” “Ko yaushe ranka a b’ace yake a kaina ai Yusuf! Ko wanne lokaci kiris kake jira dani nayi abu ka dake ni ko kayi min abinda gwara ka dake din ma. Dan Kaga iyayena k’asa ta rufe idanun su Yayata tayi min nisa Yayana da yake sona shima yayi min nisa, amma kana mantawa da Ina da Allah kuma shi idanun sa bud’e yake yana kallon kowa bai kuma yi min nisa ba yana kusa dani a ko yaushe. Na rasa abinda nayi maka, yau in nayi laifi gobe ma sai na sake yi, amma bana so nasan abinda nayi maka domin na gaji da d’aukar damuwar ka Yusuf lokaci kad’an nake jira baza ka sake ganina ba. İn badan Ammah ba da yanzu ka jima da manta sunan Ameena a rayuwar ka wallahi. Wallahi ji nake kamar na tsinke fuskar ka da mari.” Yadda take ambatar sunan sa ya tabbatar masa da ranta a b’ace yake sosai yayi shiru yana jin ta zuciyar sa gabadaya ta karye kamar zaiyi kuka haka yake ji dan yasan yayi mata laifi ta sake cewa, “Naga alama ganina ne kusa dakai baka so kar ka damu wallahi na kusa fita daga rayuwar ka ka huta, watakila mutuwa zanyi watakila kuma da k’afata zan bar gidan. Ina so ka sani daga ranar dana bar ka wallahi daga ranar shafin dana sani ya fara a cikin rayuwar ka, in mutuwa nayi zaka tuna in kuma ina da rai zaka ce na fad’a maka.” Da sauri ya kalle ta jin ta ambaci mutuwa yace, “Ki daina zancen mutuwa dan Allah, baza ki mutu yanzu ba sai na koma miki Yusuf din ki na baya, sai na dawo da soyayya ta a zuciyar ki Ameena.” Murmushi tayi tace, “Soyayyar ka a zuciyar Ameena? Har abada wannan bazai sake faruwa ba, a wancan lokacin ma kuskure aka samu shiyasa kake abinda Kaga dama kaga dama kake ganin kamar bazan iya rayuwa ba sai da kai.” yace, “nidai ki yi hakuri dan Allah kuzo ku koma gida na amince da duk hukuncin da zaki min zan d’auka.” “Kaje zan dawo da kaina amma bazan tafi dakai ba, yadda na fito ni kad’ai zan koma ni kad’ai. Amma Ina so ka sani duk ranar da na dauki k’afa na tafi Bauchi wallahi bazan dawo gidan ka Ina so ka ajjiye wannan a zuciyar ka. Kai ko ba Bauchi ba matuk’ar Ameena ta sake barin gidan ka wallahi ta barshi kenan.” Yadda take nuna shi da yatsa tana wara idanun ta a kan fuskar sa zaka tabbatar maka da haushin sa take ji shi kansa ya fahimta hakan ya saka shi yin shiru ya mik’e yace, “Na gode da jin hakan, abinda kike tunani ma bazai sake faruwa ba in sha Allah. Daga yau nayi miki alqawarin baza ki sake kuka da Yusuf ba Ameena, kuka indai ba na farin ciki ba bazan bari hawayen ki su sake zuba a k’asa ba” ya fad’a yana fita ta koma ta kwanta zuciyar ta nayi sanyi dan ko babu komai ta amayar da abinda yake zuciyar ta. Tunda ya fita hankalin Asiya ya tashi ta d’auki waya ta kira Umma cikin tashin hankali take cewa, “Umma jiya na saka tayi yaji ta bar gidan nan amma baki ga yadda hankalin sa ya tashi da yasan ta fita ba, Umma har yanzu yana son matar nan tasa ni kuma ba haka nake so ba” ta fad’a kamar zatayi kuka dan abin ya tayar mata da hankali sosai. Umma tace, “ki kwantar da hankalin ki mana badai har kin saka ta fita ba, wata ran ta fita bazata dawo ba tunda har ta fara fitar.” “Umma yaushe? Bana so na cika wata d’aya a gidan nan matar sa tana nan.” “Kin cika gaggawa Asiya komai a hankali ake bin sa yadda bazai gane ba sannan ba kuma zaiyi tunani ba, ki tsaya ki nutsu Ina sane da komai zan kuma yi maganin komai.” Asiya tace, “Umma dan Allah a san abinda za’a yi, ko fad’a min a dalilin yajin ma baiyi ba ni so nake ko kwanciya yayi da ita ya fad’a min, ya kasance ko wanne sirri na sani Umma, ta haka ne hankalina zai kwanta.” Umma tace, “kar ki damu yadda muka fara samun arzuki dashi ai baza mu bari komai ya lalace ba, in Momi zata dawo akwai sak’o daga wajan Umman ki Sakina wanda zaki yi amfani dashi gobe in ya dawo wajan ki kenan.” Ta amsa da to daga nan suka yi sallama ta kashe wayar. Tana wajan a zaune ya dawo ya kalle ta dan kayan da ya barta dasu har lokacin dai sune a jikin ta yace, “Bakya jin gidan nan yana wani k’arni?.” Asiya tace, “Gaskiya daga hancin kane bana ji komai nidai.” “Okay” ya amsa a takaice tace, “My love ka samu Auntyn? Ina nan hankalina duk ya tashi Allah yasa ba wani abun bane ba ya same ta.” Yusuf yace, “Komai lafiya babu abinda ya faru.” Ajiyar zuciya Asiya tayi tace, “Alhamdulillah naji dad’in hakan,da na tsorata wallahi. Allah ya cigaba da tsare mu baki daya.” Kallon ta yayi cikin Jin dad’i ya murmusa yace, “Amin my love. Baki wanka bane?.” “Na kasa shiga band’akin saboda wannan maganar ai, yanzu zanyi “ ta fad’a tana tashi yace, “in Kinyi wanka anjima zamu je gidan Ammah kar ki manta.” Da to ta amsa ta hau sama shima yabi bayan ta a zuciyar sa yana yaba halayyan ta dan tana son Ameena sosai shi kuma daman haka yake so dan baya son tashin hankali a tsakanin matan nasa. #MAI DAKI #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema. Book2 016         Bayan sallar Azahar suka shirya shida ita suka tafi gidan Ammah, a harabar gidan yayi parking ta kalle shi tayi kyau cikin lace pink color tace, "Nayi kyau ko?." Murmushi yayi yaja kumatun ta yace, "Sau nawa zan maimaita miki kinyi kyau?kin tambaye ni ya kai sau biyar kenan nace kin yi kyau ki yarda Kinyi din. Muje" ya fad'a yana bud'e motar suka fita zuwa cikin gidan. Babu kowa a babban falon sai kayan wasan  jikokin gidan a baje a falon ya kalle ta yace, "Zauna bara na kira Ammah." Kallon falon take yi Allah Allah take idanun ta su hango mata kudi ko wani abun d'auka tayi ta saka a jaka kafin a farga  amma babu komai sai kayan wasa tayi tsaki kawai ta zauna jiran Ammah din. Ya jima a ciki sannan suka fito tare da Ammah tana cewa, "meyasa baka tawo min da takwara ba?." Daidai lokacin suka shigo falon Ammah tayi murmushi cikin fara'a tace, "Amarya barka da zuwa." Itama Asiya tayi murmushi da girmamawa ta sakko daga kujerar ta zauna akan carpet bayan Ammah ya zauna akan kujera tace, "Barka da rana Amma." "Barka dai Asiya, ya gida?." "Alhamdulillah, mu same ku lafiya?." "Lafiya lau, ya mutanen gidan naku?." "Lafiya lau Ammah suke, da mukayi waya da Umma ma tace na gaishe ki." "Ina amsawa, a gaishe ta da kyau" Ammah ta fad'a tana kallon sa taga gabad'aya ita yake kallo sai murmushi yake yi ta girgiza kai kawai bata ce komai ba. Ganin kallon da yake yiwa Asiya yayi yawa ya saka tace, "Yusuf ka kawo mata ruwa mana." Asiya ta girgiza kai tace, "Haba Ammah kamar wata bakuwa? A'a na koshi wallahi." Amma tace, "Gaskiya ne ba bak'uwa bace ba." Ta kalli Yusuf tace, "Baka je store bane?." "Eh, sai nayi la'asar zanje yanzu zanje wata jana'iza na dawo." Ammah tace, "Allah ya jikan rai." Ya amsa da amin ya fita ya bar Asiya a gidan. Ta sake sosai kamar ba ita ba Ammah ma bata nuna mata komai ba tayi mata tambaya akan zaman gidan nasu  ta amsa da Lafiya lau daga nan Ammah ta tashi ta aiko mata Humaira dan suyi hira.  Bayan sallar la'asar ta idar da sallah a d'akin Humaira take bin d'akin da kallo tana so ta ga wani abu wanda zaiyi kud'in in za'a siyar nan idanun ta ya kai kan wani smart watch na Humaira akan mudubi ta bishi da kallo kafin ta k'arasa wajan ta d'auka ta juya shi tace, "Wannan da gani babban ne wallahi, in aka siyar zai yi abinda ake so" ta fad'a tana ta saka shi a cikin jakar ta ta koma ta zauna kamar bata d'auki komai ba. Idanun ta suka sake kai kan wani karamin yari guda biyu kai kana gani kasan yarin na gold ne sai kuwa ta mik'e ta sake d'auka ta saka a jaka ta koma ta zauna. Humaira ce  dawo tana fadin, "Na barki ke kad'ai ko? Kizo ga abinci can, ko na kawo miki nan?." Asiya tayi dariya tace, "A'a muje can din naci." Tare suka fita ta zauna akan kujera Humaira ta bata abincin ta d'iba ta fara ci. Tana gama ci Ammah ta shigo falon bayan ta Ameena ce da Humaira da yake rik'e da Zaitun tana cewa, "kuma bai fad'a min zaki zo ba." Ameena ta zauna tace, "ya manta ne, na kwana biyu bamu gaisa ba shiyasa na biyo." Ammah tayi murmushi tace, "Gaskiya ne." Ameena suka had'o ido da Asiya kafin Ameena tayi magana Asiya tace, "Aunty barka da zuwa." Ameena tayi murmushi tace, "Ashe kina nan?." "Wallahi tun d'azu." Ameena ta murmusa kawai bata ce komai ba. Humaira ta kalli Ameena da ta jingina da kujera ta dafe kanta tace, "Mummy anya lafiya kike kuwa? Nifa idona wata rama nake ganin kinyi wallahi, sannan ga yanayin ki ya nuna kamar baki da lafiya." Ammah tace, "nima na gani." Humaira tace, "Ko da yake ai kanwar Zaytun aka samu." Ameena murmushi akwai tayi sab'anin Asiya da kirjin ta ya buga ta sake kallon Ameena wai ta tabbatar ciki ne da ita amma bata gane ba, lallai ya kamata ta d'auki mataki kafin hakan ya tabbata. Dole ma ta tambayi Yusuf dan taji maganar gaskiya ce. Humaira ta shiga d'akin ta ta d'auki wayar ta sai taga wayar tayi connecting da smart watch din ta tayi tsaki tace, "Ina na ajjiye shi ne nayi disconnecting?." Dubawa take bata ganshi ba tace, "abu kamar aljani yanzu fa na ajjiye shi." Sai tayi tsaki sai ta saka wak'a a wayar ta tana bin ki Ina na d'akin yadda zata ji sautin wak'ar yana fitowa ta agogon. Har ta gota jakar Asiya sai ta dawo jin kamar fa daga jakar take jin sautin wak'ar na fitowa, kamar baza ta bud'e ba sai  ta zuge sai kuwa ga agogon ta a ciki ta wara ido tace, "Kai!" Ta fad'a tana sake duba jakar nan taga yarin gold din ta Karami wanda ta cire jiya ta ajjiye. "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Kenan Yaya Yusuf mai halin b'era ya d'auko mana?." Sai kuma ta kyalkyale da dariya tace, "Amma yarinyar nan bata da hankali, ta rasa a inda zatayi sata sai gidan sirikan ta?, gidan sirikan ma kuma zuwan farko?" Ta sake yin dariya tace, "lallai dole amma taji labarin nan." Mayar mata da jakar tayi inda ta ajjiye ta ta saka agogon a hannun ta ta fito dan Asiya din ta gani taga ya yanayin ta zai koma. Hira suke tayi a haka har sai da ta saka  Asiya ta kalli agogon sai taga tayi saurin d'auke ido ita kuma tayi dariya kawai bata nuna ba ganin Asiya din ta basar. Sun jima a gidan har bayan magriba Abbah ya dawo suka je suka gaisa ya musu nasiha ita da Ameena suka dawo falon Ammah a nan suka tarar da Yusuf. Tunda suka tawo yake kallon Ameena wacce ko inda yake bata kalla ba ganin hakan ya lumshe ido ya sake bud'ewa yana kallon ta sai kuma ya d'auke kansa ya cigaba da wasa da Zaytun. Ammah ta kalle shi tace, "To dare yayi sai ku tafi kar a shiga hakkın su." Yusuf yace, "ba gida zanje ba store zan koma yanzu Ammah, sai dai su jira ni na dawo." Ammah tace, "A'a baza ayi haka ba, tunda Ameena mota a take sai su koma tare bazata ji dadin zama ba kaga bak'uwa ce." Yusuf yace, "to su je ni zan koma yanzu" ya fad'a yana fita tare da Zaytun dan ba jimawa zai yi ba shiyasa ya tafi da ita tayi masa rakiya.           Kafin su tafi sai da Humaira ta tabbatar ta sake duba jakar Asiya taga babu komai wanda ta sata sannan ta bari Asiya ta dauki jakar suka fito suka shiga mota suka tafi. Sun yi nisa a tafiyar Asiya sai kallon Ameena take yi tana so ta samo hanyar da zata bi wajan shirya sabon makirci yadda baza su kwana Lafiya ba, dan tana Lura da kallon da yake mata a gidan Ammah ya zama dole ta lalata musu daren. nan da nan wani abun ya shiga zuciyar ta tace, "Lah Aunty sauke ni a nan kije kawai zan shiga gidan Yayata sai ta kawo ni." Ameena tace, "kodai na jira ki? Bakya ganin dare yayi zaki sha wahala kafin ki samu abin hawa?." Tayi dariya tace, "A'a kije kawai zan tawo." Ameena ta faka Asiya ta fita su kuma sukayi gaba. Tana fita Amira tace, " Wallahi Tunda ta shigo motar nan khamshin ta ya canja sai toshe hanci nake yi, dak'yar nake han numfashi wallahi duk da akwai a.c ga khamshin motar amma wari take. lallai Daddy yana fama." Amman'a tayi dariya dan itama taji kawai ta basar ne bata ce komai ba, tunawa da Yusuf baya son wari sai Ameena tayi dariya a zuciyar tana aiyana ko ya zasu kwashe da ita dai oho. Yusuf bai dawo da wuri ba dan har Zaytun tayi bacci   Sannan ya dawo, yana shigowa wajan Asiya ya shiga dan yayi mata sallama ya wuce wajan Ameena sai kuma da safe, abin mamaki bata ciki ya duba ko Ina bata nan ya fito nan ya lura da Momi kanwar ta a gefe har ta fara bacci ya k'arasa yace, "Momi!." Da hanzari ta tashi tana kallon sa alamun mai bacci yace, "Ina Asiyan?." "Har yanzu bata dawo ba." "Bata dawo ba?" Ya maimaita sai kuma yace, "Shiga ciki ki kwanta Ina zuwa" ya fad'a yana fita daga b'angaren ya shiga wajan Ameena.            A falon tsakiya ya same ta tana shan ruwa ya kwantar da Zaytun kan kujera yace, "ya na ganki a nan ita kuma bata nan, ba tare kuke ba?." Ameena ta kalle shi tace, "wa kenan?." "Asiya." Ameena tace, "bata dawo ba?." Da mamaki yake kallon ta murya a tausashe yace, "ni zaki tambaya bata dawo ba Ameena bayan tare kuke?, ba tare kuka tawo daga gidan Ammah ba?." Zatayi magana suka ji an bud'e gate ya karasa ya bud'e window ya hango Asiya wujiga-wujiga tana shigowa gidan ta zube a k'asa, juyawa yayi  ya sauka  ba tare da  yace komai ba ta kalli Asiya ta window din a bayyane tace, "ta kullo wani abun kenan, sai tayi ai daga ita har mijin basa gabana, komai ta shiryo a kanta zai k'are" ta fad'a tana gyara zaman labulen tagar ta bar wajan.           Yusuf yana sauka wajan ta ya nufa yana fad'in, "Asiya lafiya kike?." Rik'o ta yayi suka mik'e zuwa cikin gidan ta suka shiga falo ya zaunar da ita ya bata ruwa yace, "Sha." Ba musu ta karba ta shanye tass yace, "ya akayi kika rabu? Daga Ina kike ke bayan tun d'azu su dawo?." Asiya ta fara hawaye tace, "haka kawai muna cikin tafiya mun fito daga gidan Ammah lafiya muna hira Muna yo nisa ta tsayar da motar tace na fita bata sona bata qauna ganina, wai na aure ka na raba ku shiyasa itama bazata soni ba kuma wallahi sai tayi duk abinda zatayi ganin ta fitar dani daga gidan nan. My love Ina son Aunty da zuciya d'aya amma ban san meyasa ita bata sona ba, nasan laifina ne dana auri mijin ta amma ta manta kaddarar aure ce ta had'a mu? ta manta cewa Allah ya rubuta kai mijina ne tun Ina cikin Umma na?." Ta share hawayen ta tace, "ban fita da kud'i ba saboda tare muke dakai gashi ba wani sanin unguwar nan nayi ba kuma koda da kudin babu masu napep da zan hawo na k'araso, a k'afa nazo har gidan nan Ina jin tsoron kar dare yayi ayi min wani abun a hanya" ta fad'a tana fashewa da kuka ta kifa kanta a kirjin sa. Bubbuga bayan ta yake yi gabad'aya ta bashi tausayi ya rasa me ta tare wa Ameena da bata qaunar ta bayan ita da zuciya d'aya take zaune da ita, ai ko dan soyayyar da take mata yaci ace ta sassauta nata kishin, cikin kukan yaji ta sake cewa, "dan Allah ka bata hak'uri inda akwai abinda nayi mata tayi hak'uri ta yafe min, laifina nasan bai wuce auren ka ba nasan dole taji babu dadi amma tayi hak'uri haka Allah ya nufa. Bazan ce na daina kula ta ba amma kayi hak'uri ni bazan sake shiga motar ta ba saboda gudun kar raina ya b'aci nima muyi fad'a a hanya mu zubar maka da mutunci. Gwara na hau napep duk inda zanje ya kai yafi min alkhairi." Numfashi yake saukewa a hankali ya rasa abinda yake damun Ameena wallahi gabadaya ta gama canjawa kamar ba wacce ya sani a baya ba, tashen magana da rashin kunya take ji dashi ko shi d'in bata k'yale balle Asiya. Yace, "Kiyi hak'uri kema zan siya miki taki motar na samar miki da driver kafin ki koya, kar ki rik'e ta a zuciyar kiyi hak'uri watakila ranta ne a b'ace." Asiya tace, "Ina jin haka ne, amma bai kamata tayi min haka akan hanya ba ko babu komai matar aure ce ni bai kamata ba. Amma babu komai ai ya wuce ni bazan rik'e ta ba saboda kai." Yayi murmushi kafin yayi magana tace, "ban d'auka zaka yarda bama dan naji tace ka yarda da ita komai nace maka baza ka yarda ba ni zaka karyata, Allah yasan ba k'arya nake mata ba kuma ban fad'a maka dan wani abun ba sai dan kayi mata magana a gyara nan gaba" ta sake fashewa da kuka yace, "ya isa ki daina kuka kiyi hak'uri kinji, Momi tana sama tana jiran ki muje na raka ki." Har saman ya raka ta tana takawa dakyar ta shiga d'aki ya saka Momi tazo ta kulle ko Ina shi kuma ya fita zuwa wajan Ameena ransa ya b'aci sosai akan abinda ta aikata. Yana fita Asiya ta 'karasa wajan window da sauri tana kallon sa har ya shiga wajan Ameena tace, "Ameena baki san wa aka d'auko miki a matsayin kishiya ba, duk wannan rawar kan da kike sai na sauke shi wallahi." Momi ta kalle ta tace, "Ya kuka yi?." Asiya ta kalle ta tace, "Barni da ita akwai, kedai aikin ki yayi kyau da kika kwanta a bakin kofa kinga yanzu ya sanar dani zai siya min mota kinga cigaba na farko kenan, cigaba na biyu kuma...." Ta 'karasa wajan taga tana kallon wajan Ameena tace, "Na fitar da waccan Shegiyar daga gidan nan, dan indai ban fiddata ba hankalina bazai kwanta ba wallahi." Momi ta dafa kafad'ar ta suna kallon tagar tace, "Kina yin komai yadda ya kamata sai a cigaba daga inda aka tsaya. amma wallahi jikin ki tsami yake, na fad'a miki ki dinga daurewa kina wanka saboda mijin ki amma kin kasa saboda kin saba zama haka a goda." Asiya ta shanshana jikin ta tace, "a daren nan zanyi wanka? Ashe baza'a yi ba" ta fad'a tana fita daga dakin Momi tayi murmushi kawai a bayyane tace, "ai kuwa zaku samu matsala da mijin ki akan wannan Shegiyar k'azantar taki." Itama ta biyo bayan ta tana jininga kazantar Asiya bata son wanka ko kusa. #Mai daki #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema. Book2 017 Yusuf yana hawa saman ya sake ganin ta a tsaye a falon sa ta d'auki waya tana dannawa, ya tsaya ya kalle ta kamar zaiyi magana sai ya fasa ya wuce zuwa nata falon yaga Amira a zaune a kan kujera yace, "Amira a Ina kuka sauke Asiya?." Amira tace, "A kan hanya." Bai sake cewa komai ba ya dawo inda ya bar Ameena tana tsaye jikin window iska na shigowa sanyin yana ratsa ta idanun ta a kulle da alama iskar nayi mata dadi. Murya a tausashe yace, "Abinda kika yi kin kyauta kenan?." Ba tare da ta kalle shi ba tace, "Diamond na sace kuma?." Ya bita da kallon mamaki dan gabad'aya ta canja masa, inda a lokacin baya ne bazata iya ce masa haka ba amma yanzu duk abinda yazo bakin ta fad'a take yi kai tsaye ba tare da fargaba ba. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya wuce ta zuwa sama itama ta kulle tagar ta wuce d'akin ta dan so take ta daina sakawa ranta damuwar sa dan taga alama kashe kanta zatayi a banza. Humaira so take kawai Ammah ta taso daga falo zuwa d'aki dan ta fesa mata labarin barauniyar amarya, ai kam tana shigowa ta biyo bayan ta tace, "Ammah kin San wani abu?." Ammah ta zauna tace, "Sai kin fad'a." Tayi dariya tace, "Labarin barauniyar Amarya zan baki." Ammah tace, "ba yanzu aka gama film din a arewa 24 ba? Ke ni bana son ji bacci zanyi." "Ai Ammah wannan ta zahiri ce ba ta film ba, ai Yaya Yusuf ya kawo mana b'arauniyar amarya." Ammah ta kalle ta tace, "ban gane ba." Humaira tayi dariya tace, "Wallahi amaryar sa barauniyar ce, daga zaman ta a d'akina  har ta sace min smart watch da wannan yarin" ta fad'a tana nuna mata yarin da kuma agogon. Ammah ta Harare ta tace, "ke bana son shirme fa, dan bakya son ta ba haka yana nufin ki dinga jifan ta da wadannan kalamai ba ko babu komai matar Yayan ki ce." "Wallahi Ammah ba k'arya nake yi ba, a jakar ta naga agogona da kuma yarin nan wallahi, ai bazan mata k'arya ba itama tasan na gani. Meyasa ban tab'a cewa Ameena tayi ba sai ita?." "To ya akayi suke a hannun ki tunda kince ta sata?." "Nayi connecting na agogon da wayata sai na Nemi shi na rasa kawai sai na kunna waka Ina bin sautin ko Ina yadda zan jiyo kawai na jiyo shi a jakar ta Ina bud'ewa na ganshi had'e da wannan yarin." Ammah ta girgiza kai cikin mamaki tace, "ikon Allah!." "Abin haushin ma sata a gidan sirikai." "Ke ban amince da abinda kika ce bafa kar naji maganar a wajan wani ko wata, in halin ta ne nan gaba zata sake yi. Tashi ki bani waje" ta fad'a tana kwanciya dan bata son zuciyar ta ta fara zargin yarinyar amma tunda da ta ganta ita kanta bata yi mata ba kawai dai babu yadda zatayi ne ta Riga ta zama matar d'an ta. Washe gari. Kud'i masu yawa Alhaji bello ya ajjiye a gaban Kawu ya kalle shi yace, "Kawu ni in da dama gobe nake so a daura aurena da ita bayan sallar juma'a in ka amince." Kawu ya kalli kud'in ya kalle shi yayi dariya yace, "Baka da damuwa Alhaji in ma yanzu kake so a d'aura sai a daura auren ba wani abun damuwa bane ba ai." Alhaji bello yayi dariyar farin ciki yace, "Inda za'a daura a yanzun ai dana ji dad'i sosai wallahi, amma mu jira goben in Allah ya kaimu sai a daura auren a masallaci mutane da dama su shaida." Kawu yace, "Shikenan babu laifi, Allah yanına mana goben Lafiya." Ya amsa da amin sukayi sallama ya wuce shi kuma kai tsaye gidan su Fidy ya nufo. Da sallama ya shiga ya same su daga ita sai Mama ya zauna suka gaida da Mama ya d'auko kudin ya mik'awa Mama yace, "Ga sadaki da kud'in komai na aure wanda zai auri Fiddausi ya kawo, gobe in Allah ya kaimu za'a d'aura musu aure bayan sallar juma'a." Mama ta karbi kudin tana juyawa kafin tace, "Da wuri haka?." "To me za'a jira? Ai gwara ayi a wuce wajan kawai. Ki shirya gobe za'a daura auren daga nan sai a San abinda za'ayi." Murmushi tayi kawai bata ce komai ba amma cikin zuciyar ta ba k'aramin farin ciki take yi ba burin ta zai cika bata kashe auren ta a banza ba. A cikin mintina kad'an ta sanar da Zakiyya aka fara shiri a waya kafin ta fad'awa Ruky da kuma Ameena suna ta mamakin saurin abun sai suka ce mata zasu shigo gidan nasu. Fiddausi sai rawar kai ake ana rawar k'afa za'a shiga gidan mai kudi ta rasa nutsuwar ta gabad'aya a lokacin saboda farin ciki. Har dare Fiddausi farin ciki take buri kawai take gobe tayi a daura mata aure da masoyin ta kuma abin alfaharin ta. Tun safiyar da Kawu yazo take jiran shigowar Rukayya amma bata zo ba kasancewar suna kusa a yanzu duk sai taji babu dad'i dan tana so ta samu abokiyar da zata taya ta murna a wannan lokacin, har dare babu Rukayya sai waya take yi mata duk ta damu. A daren Rukayya na tsaye a kan titin Tarauni tana ta zagaye babu abin hawa ga dare yayi ga yanayi na sanyi babu jama'a sosai a hanyar gabad'aya  a tsorace take dan bata saba kaiwa haka a waje ba. Hankalin ta ya tashi tana ji wayar ta na vibrating amma bata d'auka ba saboda tasan kiran bazai wuce na Baba ko Umma ba shiyasa ta ki d'auko wayar dan bata san ma abinda zata ce ba. Har sun wuce a keke napep sai taga keken ya dawo da baya bata kalli wanda yake ciki ba dan a tsorace take sosai mai napep din yace, "Shiga muje." Ta kalle shi da mamaki tace, "Ban tsayar da kai ba ai, kuma bana shiga napep da namiji a ciki ka gane?." Ganin da fad'a take magana ya saka Ibrahim da yake baya ya murmusa yace, "Sannu Rukayya, ni nace a dawo baya saboda tun d'azu na wuce na ganki a tsaye ga dare yanayi." Jin muryar Ibrahim ya saka ta kalle shi sai tayi murmushi tace, "lahhhh! yi hak'uri ban ma kula da kai ba, Ina wuni." "Shigo ciki dare yayi ana neman ki a gida nasan da hakan." Kulle ido tayi ta bud'e suka had'a ido ta sauke numfashi ya fuskaci tunanin shiga take yi sai yace, "mu tafi ne?." Da sauri ta shiga baya kusa dashi ta zauna, Allah yasa ma shi kad'ai ne akwai space sosai a tsakiya dan ba jiki ne da ita ba shima haka, a lokacin wayar ta take k'ara ta samu damar daukowa taga sunan Fiddausi yana yawo a kai a fusace ta d'auka tace, "Wai Fidy bashi kika bani ne da zaki ishe ni da waya?." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tace, "To bana gida yanzu haka Ina kan hanyar dawowa, gobe da sassafe zan shigo mayi magana. Duk kin wani d'aga hankalin ki kamar auren fari sai......." Cak maganar ta tsaya jin Ibrahim yana cewa mai napep din, "Ka fara sauke ta a Yakasai sai mu wuce." Juyowa tayi ta kalle shi taga hankalin sa yana wajan ta gabad'aya, sam ta manta ma tare suke wallahi da bazata d'auki wayar Fiddausi ba, datse kiran tayi ta saka wayar a jaka sannan tace, "Na gode sosai." Sai a sannan ya kalle ta baice komai ba ya d'auke kansa. A haka suka isa Yakasai har kofar gida aka sauke Rukayya ta fita ta kalle shi tace, "Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci." Ya amsa da fadin, "Kar ki damu, ki gaida gida" yana fad'a mai napep din ya juya suka bar wajan ta bi napep din da kallo ita gabad'aya tausayin sa ma take ji wallahi. A haka ta juya ta shiga gida jikin ta duk ya mutu daman gashi ta gaji sosai. Tana shiga Umma ta tashi tsaye tace, "Ina kika shiga ne haka? Ana ta kiran waya bakya d'auka yanzu da baban ku ya dawo nace masa ni na aike ki har yanzu baki dawo ba?." Jin bai dawo ba sai taji dadi ta zauna tace, "Wallahi babu abin hawa ne na jima a tsaye a kan titi, yanzu ma badan tsohon mijin Fiddausi ba ban san ya zanyi ba." Umma ta kalle ta tace, "shine ya dawo dake?." "Eh, yana cikin napep har sun wuce ya dawo suka d'auko ni har nan aka ajjiye ni." "A Ina ya sanki?." Ta kalle ta tace, "Umma mijin Fiddausi fa nace miki, to ai ko babar sa ta sanni balle shi." Umma tayi shiru tana kallon ta tace, "to ko dai sonki yake yi?." Rukayya ta juyar kai ta kalli Umman tace, "Umma tsohon mijin Fiddausi fa nace miki." "Shi din fa, akwai aibu a hakan ne?." Rukayya ta mik'e tsaye tace, "Umma banyi sallar I'sha ba" ta fad'a tana shigewa d'aki zuciyar ta cike da mamakin wannan tunani na Umman ta. Shima Ibrahim yana komawa gida sai da Hajiya ta tambaye shi Ina ya tsaya ya zauna yana cin abinci yace, "Yau bamu gama aikin da wuri ba kuma daman na fad'a miki na kai machine dina service a napep na dawo" Abincin yake ci Amir yazo ya zauna a cinyar sa yace, "Abba yaushe zamu koma gidan mu?." Ya kalli Amir din yana murmushi yace, "Gyara maka gidan ake yi ya zama mai kyau shiyasa kake zaune a nan da an gama zamu koma can." Amir yace, "harda Mama na?." Ya daga masa kai alamun eh Amir yace, "Amma da naje wajan ta tace min bazata sake zama damu ba wai wani gidan zata je, kuma Abba kace min zamu kuma waye mai gaskiya?." Ibrahim ya kalli Hajiya da take kallon su ya sake kallon Amir yace, "Kana ji, kaje kayi bacci gobe juma'a zamu je masallaci tare." Sai kuwa ya mike yace, "Zaka siya min alewa?." Ibrahim yace, "eh harda chocolate ma, maza jeka kar ka makara sallah." A guje ya shiga d'aki yana murna shi kuma ya kalli abincin nan take yaji ya fita daga ransa ya ture abincin. Hajiya da take kallon sa tace, "Ibrahim yaron nan yana son komawa gida wajan ka da babar sa, bai San babar sa tayi nisa ba amma yana bukatar wata uwar da zata kula dashi. Yana samun komai a nan amma cikin kwanakin nan yana so ya dinga ganin sa gidan su shima." Ibrahim ya kalli Hajiya yace, "Ya zanyi kenan Hajiya? Nida shi zamu koma gidan kenan?." Ta girgiza kai alamun A'a tace, "Aure zaka yi Ibrahim, kana da dama a yanzu zaka iya yin aure dan Allah ya hore maka." Ibrahim ya gyara zaman sa yace, "Hajiya sam tunanin aure baya zuwa kaina a yanzu Allah ya sani, kwana nawa ma da rabuwar mu da Fiddausi da zanyi wani auren?." "Kai in baka yi ba ai ita zatayi, na smau labarin auren ta za'a yi shi ne nan kusa ba jimawa." "Ita daban ni daban Hajiya, abinda yake ranta kenan daman ni kuma yanzu ta neman halak nake yi." Hajiya tace, "ka dai sake tunani yana da kyau kayi aure kofofin alkhairin ka zasu yi saurin bud'ewa, zama hakan ba shine mafita ba ko dan d'anka ya kamata kasan abinda zakayi" ta fad'a tana tashi ta shiga d'aki ya bita da kallo kafin ya mike shima ya fita zuciyar sa na ayyana masa taya zai fara tunanin aure yanzu? A Ina ma zai samo matar? Ta ina zai fara?.               Washe gari da safe Yusuf yana kwance a kan gadon Asiya dan bazai fita ba sai lokacin sallah yayi, tashi yayi ya 'karasa bak'in taga yana kallon tagar d'akin Ameena amma a kule take ya lumshe ido ya bud'e ya juya yana kallon d'akin da ya tashi, gabad'aya wani iri yake ji d'akin yana masa shi ba wari ba kuma ba khamshi ba Gashi kaca-kaca kayan ta wanda suka dawo daga saudia a jikin ta suna ajjiye a gefe a haka ma ta kwashe kayan da ta jibga a gefen gadon ta kai gidan su matsayin tsaraba. Kasancewar su ta karshe ya tuna Shida Ameena ranar da ya mata wayo taje ta samu Ammah ya lumshe ido ya bude ya sauke numfashi a bayyane yace, "Komai nata daban yake." A lokacin Asiya ta fito daga wanka ta wuce shi ta fara shiryawa ya jiyo yana kallon ta. Kanta yake kallo gabad'aya kitson ya lalace ya tsufa yana buk'atar a gyara shi amma bai ji ma tana zance ba dan ya d'auka a jiya da taje gida zata yi komai kafin ta dawo amma sai yaga akasin hakan. Yana tsaye ta d'auko brezia wacce ta saba sakawa zata saka sai ta kalle shi suka hada ido tace, "To ka daina kallona." Ya murmusa yace, "Ya kamata ki daina saka acuci mazan tunda kin riga kin cuci mazan ai ko?." Ta kwabe fuska tace, "me kake nufi?." Ya zauna a gefen gadon yace, "Abinda kika ji." Bata saka magana ba ta juya baya ta saka ta sake kallon sa taga ba ita yake kallon ba nan da nan t shirya ta cillar da towel din wankan da ya canja kala daga farı zuwa brown ta nufo wajan sa. Ya kalle ta bayan ta zauna yace, "Kije a gyara miki kanki shima ki cire k'arin gashin." Tayi dariya tace, "Zanje. Yanzu me kake so Kaci?." "Komai" ya bata amsa a takaice kafin ya sake tashi ya sake kallon window amma bai ga an bud'e ba duk da daman bata cika yawan bud'ewa ba. Ta kalle shi ta kalli inda yake kallo tace, "Wai my love Ina motar tawa?." Bai kalle ta ba yace, "Anjima kadan za'a kawo miki." Tayi dariyar murna tace, "Na gode mijina mai sona. Na tambaye ka?." "Ina ji." "Wai dani da Ameena wa kafi so?." Ya juyo yana kallon ta cike da mamaki yace, "Meyasa kika tambaya?." Tace, "Ina so na sani ne kawai." Yayi gaba ya sake zama yace, "Dukkan ku Ina son ku babu wacce nafi so a ciki." Nan da nan fuskar ta ta had'e tace, "Amma ai a baya ba haka kace min ba, kace kafi sona akan Ameena , kace dani ka aura baza ka sake wani auren ba." Kallon ta yake yi fuskar sa a dan sake a ransa yace, _a hakan kina fama da k'azantar bazan sake aure ba?._ a bayyane kuma yace, "Lokacin ma wasa nake miki." Asiya tace, "Wasa kuma? Ai ba sau d'aya kace ba balle kace wasa kake min." Ya tashi tsaye yace, "to na fad'a ne a lokacin dan kiji dad'i kuma kin ji ai shikenan ko?." Asiya tace, "Yanzu hakan yana nufin kafi son ta dani kenan?." "Ni bance miki ba, amma ko wacce Ina sonta." "Amma meyasa dah ka fad'a min hakan?." "Y'an siyasa meye basa fad'a a lokacin da suke neman mulki? In suka samu kujerar suna yi ne?." "Shiyasa daban ai aure daban, kuma kaine ka fad'a a da meyasa yanzu ka mu sa?." Yayi murmushi wani lokacin kuruciya tana damun yarinyar nan yaga alama hakan a tare da ita ya saka yace, "Kin tab'a ganin dan siyasar da ya cigaba da campaign bayan yaci zab'e?." Ta girgiza kai alamun A'a yace, "To ki saka ranki haka ne abun" ya fad'a yana fita ya barta a wajan a tsaye dan dakyar yake shak'ar numfashi saboda yarin da d'akin yake yi. #Mai daki #Book2 #Nana Haleema #Paid #500 #09030398006. Book2 018 Yana fita tayi baya ta zauna kamar mahaukaciya sai kuma ta zubara ta mik'e tsaye ta fita daga d’akin zuwa nata d’akin ta d’auki waya hannun ta har rawa yake yi ta kira layin Yaya Maimuna bata d’auka ba ta cillar da wayar gabad’aya wani iri take ji a zuciyar ta kamar zata fito saboda bak’in cikin abinda yace mata. K'arar wayar ce ta saka ta koma wajan da sauri ta d’auka ganin Yaya Maimuna ce take waya ya saka ta dauka ta saka a kunne daga can b’angaren tace, "Asiya ya akayi?." "Yaya na shiga uku." Jin abinda tace sai Maimunatu tace, "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, meye ya faru?." Asiya tace, "Yaya Yusuf ne." Maimuna hankalin ta ya sake tashi tace, "Meya faru da Yusuf din? Wani abun yayi miki?." Asiya kamar tana gaban ta ta girgiza kai tace, "Yaya yau kwata-kwata sati na uku nake a gidan nan amma yau shine yake bud'e baki yake cemin wai yana son matar sa, Yaya ko mararina bayayi yana tashi da safe zai fita ya koma b’angaren ta kamar ba amarya ba. Ni wallahi ba haka nake so ba Yaya bana so ya dinga sauraron ta kuyi wani abun dan Allah." Maimuna da take jin ta tace, "Dallah Malama ki yi min shiru kin saka gabana ya fadi na d’auka wani abun ne ya faru wallahi. An fad’a miki ana kan shirya miki wani babban shiri da zata fita ta bar miki gidan gabad’aya, ki kwantar sa hankalin ki ki daina nuna masa damuwa akan hakan in ba haka ba zai yi saurin gano ki.” Asiya tace, "Yanzu haka fa ya tafi wajan ta ko karyawa baiyi a wajena ba, abinda nake so na zama itace ta zama a yanzu Yaya." "Ki kwantar da hankalin ki, rashin cin abincin ki wannan laifin kine kuma ai, kina nan kina fama da wannan shegiyar k'azantar ba dole ya dinga barin wajan ki da wuri ba?. Momi ta fad’a min ko turaren wuta bakya yiwa gidan ki zauna kaca-kaca gida ma haka ba dole ya tafi ba?. Ki daure ki gyara kanki mu kuma zamu gyara miki zaman ki, wallahi sai yarinyar ta fita ta bar miki gidan ki domin Yusuf naki ne kawai." Sai a sannan tayi Ajiyar zuciya tace, "Naji dadin hakan Yaya, zan gyara kuma in sha Alla. Ni yawan wanka ne damuna yake amma zan gyara.” "Yauwa, ki gyara kanki kar kuma ki sake ko da wasa ki k’ara yi masa magana a kanta ki dinga nuna ke sonta kike yi ba wani abun ba kin gane?." "To Yaya Ina yi." "Ki sake, ni kuma zan shirya miki abinda za'a yi ki jira ki gani" tana fad'a ta yanke wayar ta sauke Ajiyar zuciya ta ajjiye wayar ta fita daga dakin zuwa k'asa.         Yusuf kuwa ko da ya shiga b’angaren Ameena sai da ya lumshe ido kamar ko yaushe khamshi kawai falon yake wanda ya zama dauwamamme a falon ko yaushe khamshi d'aya yake yi koda bata turara shi ba khamshin yana nan. Sakkowa take yi ita da Zaytun suna ta dariya tana yi mata wasa kafin Zaytun tace, "Mummy Ina daddy?." Zata bata amsa taji yace, "Ga daddy nan." Sai kuwa ta fizge rik’on da Ameena tayi mata ta k’araso a guje wajan sa ya d'auke ta yana mata wasa tana dariya shima haka. Kallon Ameena yayi bayan sun gama dariyar ya ganta a tsaye tana had’a tea a kofi kafin yaga ta d’auka tana sha, had'a ido sukayi sai ta sauke kofin a bakin ta tace, "Ina kwana." Fuskar ta ba yabo babu fallasa haka tayi maganar, kai tsaye baza kace fushi take ba sannan baza kace farin ciki take yi ba, shi kuma kallon ta yake tayi kyau da haske a idanun sa amma ramar da yake gani tana nan har lokacin. Dakyar ya iya cewa, "ya kuka tashi?." "Alhamdulillah" ta bashi amsa a takaice. "Ki fad’a min meye yake damun ki kike ramewa haka Ameena." Ta kalle shi tayi murmushi Tce, "Babu komai na fad’a daman a haka nake baka kula ne sai yanzu. zanje gidan su Fiddausi yau ake d'aura mata aure." Yace, "Fiddausi ba tana da aure ba?." "Eh tana dashi a da, yanzu babu sabon aure zatayi." "Allah sarki Allah ya sanya alkhairi, sai kin dawo." Ta kalli zaitun tace, "Zo kici abinci." Ta nok'e kafad'a tace, "Da daddy zanci." Ameena bata sake cewa komai ba ya zauna akan kujera yace, "bani abincin na bata." Bata mu sa ba ta bashi tea din da dankali ya karb'a yana bata ita kuma ta hau sama ta bar shi a wajan. Ba jimawa suka sakko ita da Amira lokacin ta gama ci tace, "Zaytun muje?." Ganin Unguwa za'a tafi ya saka ta sakko daga jikin Yusuf ta tafi wajan Ameena. Amira tace, "Daddy Ina kwana." Ya kalle ta yace, "Lafiya lau Amira." Jan hannun Zaytun tayi suka fita bayan sun fita ya kalli Ameena yace, "kije Ina nan basai kin kulle ba." Bata ce komai ba ta juya zata fita sai kuma ta tsaya tana tunanin kar da Asiya tazo tayi mata wani abun a cikin gidan, kamar zata ce wani abu sai yaga ga fasa ta fita yana zaune taji tashin motar ta alamun ta fita. Da sauri ya tashi ya k’arasa dining yana bud’e abinda ya gani a ajjiye nan ya zauna yana ci dan yunwa yake ji amma baya son cin abincin Asiya saboda karni yake ji yana yi. Sai da yaci ya koshi ya tashi ya hau sama dan yayi wanka.           A gidan su Fiddausi a nan ta tarar da suka k’awayen ta suna daki ana hira shigar ta ya saka su yin ihu gabad'aya sai tayi dariya tace, "ana yi babu ni kenan ko?" Ta fada tana k’arasowa ta zauna duk suka bita da kallo. Zakiyya tace, "Ameena wai kishiyar nan da aka yi miki ce ta saka kika fige haka? Wai kina kallon kanki kuwa?." Ameena tayi murmushi tace, "Wallahi sai na kwana na tashi ban tuna da ita ba, ni kaina ban San me yake saka ni rama ba." Fiddausi tace, "Gaskiya dai kin rame wallahi, da in sun fad’a ma bana gani amma yanzu na gani." Ameena tayi dariya kadan tace, "Ke ku share kawai, sai muka ji batun aure kwatsam daman Kun San da labarin ne?." Rukayya tace, "Bari kedai, jira muke kawai lokacin daurin aure yayi a daura kawai." Ameena tace, "Amma kin yi sa'a Fidy yadda ake zaman zawarci yanzu ke kin samu miji da wuri, a hakan ma fa dan kin jira kwanakin idda ne da yanzu ma watakila kina da ciki." Sukayi dariya Zakiyya tace, "Ina Zaytun ne?." Ameena tace, "Tana wajan Amira suna falon Mama." Rukayya tace, "Amma bawai zan dawo da abinda ya wuce bane, har ga Allah nafi so ta komawa Ibrahim tsohon mijin ta, a jikina nake ji bazata samu abinda ta samu a wajan sa ba.” Dogon tsaki Fiddausi tayi tace, "ana abin arzuk'i zaki saka raina ya b’aci wallahi, yanzu dan Allah ke aka ce na komawa Ibrahim sai ki amince?." Ameena tace, "to meye dan kin koma?." Fiddausi tace, "Har abada nida shi wallahi sai dai mu had’u a hanya na bashi sadakar na abinci, na barwa Rukayya in tana so." Zakiyya tace, "wai meye haka kike yi ne Fiddausi?, ya zaki dinga kin bar mata hakan fa babu dad’i.” Fiddausi tace, "to itace ta damu da lamarin sa ko yaushe sai tayi min maganar sa, ni wallahi dan yana son ta ya aure ta ko a jikina murna ma zanyi domin nasan Amir ya samu uwa wacce zata iya fina kula dashi. Talaka take son aure ai kinga Ibrahim din shine daidai ita." Ameena tace, "ai gaskiya take fad’a miki badan wai zata aure shi ba.” "Dan fa ta aure shi wallahi ba wani abun bane, tana son talaka kuma shi talaka ne basai su zauna ba." Rukayya tace, "dan Ina fad’a miki gaskiya ai ba hakan yana nufin zan aure shi bane, kawai dai ni gani nake baza ki sake samun miji kamar sa bane. Ki daina had’a ni dashi tunda bakya so Allah ya baki wannan kike so sai ki gode masa.” Fiddausi tayi saurin dakatar da ita tace, "daina yi min baki na samu wanda ya fishi in sha Allah. Godiya cikin yin ta nake ko da yaushe Alhamdulillah. Ameena tace, "Shikenan dai a yanzu kin samu wanda yafi Ibrahim Allah ya bada zaman lafiya, ke kuma Ruky Allah ya kawo miki na gari kema ki huta." Suka amsa da amin suka cigaba da hira har lokacin sallah yayi. Bayan sun idar da sallah ne Zakiyya take cewa, “yanzu na saka Surayya halin yau tayi miki had’in kaza ta musamman, gobe za’a kawo sai ki cinye Tass.” Ameena tace, “Gaskiya matar nan maganin ta yana dakyau sosai, Tunda kika had’a ni da ita na daina Shan ko wanne maganin sanyi sai nata. Kin San bayan haihuwar Zaytun infection yaso yayi min karfi a jikina shine ai nake fada miki kika bani maganin ina sha na dinga fitsarin sa kamar hauka. Kai naji dadin sa wallahi sosai.” Zakiyya tace, “had’in da tayi miki na bayan haihuwa fa? Shi me zaki ce a kansa?.” Ameena tayi dariya tace, “shima karshe sosai fa, na fad’a miki gaskiya kayan ta suna da kyau.” Fiddausi da take jin su tace, “bani lambar ta bazai yu ku dinga hira ina ji ni ban Santa ba, maza bani nayi saving a waya Tunda tana kaiwa ko ina daga nan a dinga kai min Abuja.” Rukayya tace, “inye kaga y’an Abuja.” Sukayi dariya Zakiyya tace, “080.” Fiddausi ta maimaita tana sakawa a wayar ta, Zakiyya t sake duba waya tace, “08032773332.” Fiddausi ta saka lambar nan a wayar ta tace, “Yanzu naji batu ai, a wajan ta zamu had’a kaya kafin na tare in sha Allah.” Sukayi dariya aka cigaba da hira. A wannan lokacin Alhaji bello yake mata waya ya sanar da ita an d’aura auren su, ihu Fiddausi tayi ta rungume Zakiyya da take kusa da ita ana murna kafin a ci abinci ana cigaba da hirar yadda komai zai kasance. Suna cikin hira ya sake kiran ta a waya ta d’auka tana murmushi tace, "Baby." Daga can yace, "Na'am baby, daga k’arshe kin zama mallakina yanzu sai shirin tafiyar Mun New York ko?." Dad’i ya mamaye mata zuciya tayi dariya tace, "sai burina da na fad’a maka Ina son cikawa da zarar an d’aura mana aure." "Ibrahim?." "Eh shi baby." "Shikenan yanzu zan saka duk inda yake a kama shi a kulle shi sai ya kwana a cell." Tayi murmushi tace, "thanks you baby, sai na jika" ta fad'a tana kashe wayar ta kalli k’awayen sukayi dariya gabadaya aka tafa aka cigaba da tsokanar ta.         Ibrahim kuwa yana cikin masallacin d’aurin auren wani abokin sa ya kaishi masallacin a nan yaga Kawun ta kuma yaji an d’aure auren Fiddausi da sunan mahaifin ta a nan ya tabbatar auren ta akayi, sai da aka d’aura nata aka d’aura na abokin nasa. bayan an kammala ya dawo gida ya samu Hajiyar sa a falo ya zauna ya kalli Fadima yace, "Faty bani abinci Yunwa nake ji." Amir da suka shigo tare yace, "Hajiya naga Kawu a masallaci." Ibrahim baice komai ba aka kawo masa abincin ya fara ci yana cikin ci Alhaji ya shigo da sallama duk suka amsa ya zauna yace, "Ibrahim yau babu aikin ne?." Yace, "eh yau juma'a ban cika zuwa ba daman." "Sai kuma naji batun d’aurin auren tsohuwar matar ka, wallahi mahaifinta tun daga Saudia ya kira ya sanar dani ban samu damar zuwa ba saboda d’aurin auren yaron nan da aka bani wakilci. D’aurin auren ne duk ya koma juma’a yanzu shiyasa ban samu dama ba.” Ibrahim yace, "Eh ban ma sani ba sai a masallacin naji.” Hajiya tace, "Au har tayi aure?." Alhaji yace, "An d’aura aure ta da Bello Sagagi d’azun nan." Hajiya ta girgiza kai tace, "Bello Sagagi...! To Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman Lafiya." Alhaji ya amsa sa amin kafin yace, "rabon auren nata da wannan din ne ya kashe na Ibrahim. Kai yaushe zaka yi auren ne?." Ibrahim yayi murmushi yace, "Wallahi Alhaji nima ban sani ba." Hajiya tace, "nima nace ya nemo yayi auren ko dan yaron nan kaga yanzu uwar sa nisa zatayi dashi zai so wacce zata maye gurbin ta." Alhaji yace, "Haka ne, amma ya tsaya yayi komai a nutse har Allah ya kawo lokacin." Hajiya zatayi magana aka ji ana cewa, "Asslamu alaikum!." Alhaji ya kalli kofar falon zaiyi magana Sadik ya shigo yace, "Alhaji yan sanda a waje." Ibrahim ya tashi tsaye shida Alhaji yace, "y’ann sanda kuma a k’ofar gidan nan? Ibrahim muje." Tare suka fita suka tarar da mota a gefe ga kuma wani guda d'aya a tsaye suka gaisa da Alhaji dan sandan yace, "Alhaji kaine Ibrahim?." Ibrahim yana gefe yace, “nine Ibrahim ." Ya kalli Ibrahim yace, "Zamu je da kai station ana tuhumar ka da dukan matar aure." Ibrahim ya kalli Alhaji ya sake kallon d’an sandan yace, "Dukan matar aure? Kuma ni?." Ya girgiza kai yace, "kai fa, muje" ya fad'a yana nuna masa hanya. Alhaji yace, "officer anya d’ana kuke nema?." Ya girgiza kai yace, "Eh alhaji, shine." Alhaji yace, "Amma d’ana babu macen da ya daka ai." "Shiyasa zamu je ai in ba laifin sa bane zai dawo." Ibrahim ya kalli Alhaji yace, "Alhaji ka koma bara naje na dawo." Alhaji yace, "Wanne station zaku je dan Allah?." D’an sandan yace, "Bompai" ya fad'a yana yin gaba Ibrahim ya shiga motar suka tafi zuciyar sa duk babu dad'i dan ba k’aramin tozarci bane shiga motar y’an sanda. Tunanin sa shin wacce matar aure ya daka?. Ina fama da mura ne ayi min hakuri.🥹 #Mai daki #Book2 #Paid #Nana Haleema #09030398006 Book2 019 Suna shiga station d’inn Maimakon a kai shi kan kanta kawai aka bud’e cell aka saka Ibrahim, Ibrahim yace, "Akan wanne dalili kuka kawo ni nan? Ina matar da take k'arar nawa?." D'an sandan yace, "ka yiwa mutane shiru zata zo ai." Ibrahim yayi shiru ya kalli inda aka saka shi duk wajan yayi daud'a ga wari da wajan yake yi zuciyar sa har tashi take yi. A lokacin Alhaji ya iso shida yayyen maza suka yi wajan yan sandan bai San me suke cewa ba yaga dai suna magana shi kuma yana tsaye yana kallon su. Har la’asar suna wajan ko sauraron su ma sun k’i yi balle su bada Ibrahim beli suka dawo kusa da ibrahim Yaya yace, "Ibrahim wa ka daka ne?." Ibrahim yace, "Wallahi babu wanda na daka, to wacce macen ma zan daka koda bata da aure balle mai aure? Me zai had’a ni da ita da zan dake ta?. Ni sallah nake so nayi wajan nan bazai sallah ba sun ‘ki bani dama." Alhaji yace, "Sun ‘ki su bamu dama ne wallahi, sun k’i fad’a mana wacece ta kawo k’arar." Ibrahim yace, "ni su barni nayi sallah ma shi nake so wallahi." Alhaji ya koma ya sake yi musu magana dakyar aka barshi ya fito yayi sallah suka mayar dashi har magriba su Alhaji suna nan ance sai D.P.O yazo amma shiru bai zo ba. Ibrahim yace, "Alhaji ku tafi gida kawai dare yayi." Alhaji yace, "taya zamu tafi mu barka a nan bayan bamu San abinda kayi ba? Wacece tayi k’arar?.” Shiru suka sake yi suka koma gefe suka zauna suna jiran tsammani, Babban mutum ne ya shigo irin manyan nan masu kama da y’an dambe sanye da kayan security bayan sa Fiddausi ce ta saka hijjabi har k'asa bata kula dasu Alhaji ba wajan Ibrahim ta nufa tana bin sa da kallon k’ask’anci tace, "Ka gane ni ai ko?." Baiyi magana ba sai kallon ta da yake yi domin kuwa ta jima tana zuwa zuciyar sa akan lamarin bai gasgata ba sai da ya ganta tace, "Sakamakon marina da kayi lokacin da Ina gidan ka kenan, nan gaba akace ka sake yiwa wata macen ai baza ka sake yi ba. Yanzu ka tabbatar da ni ba irin matan da zaka daka bace ka zauna lafiya ba ko?, yanzu ka tabbatar ni ba sa’ar ka bace, ka tabbatar a yanzu baka wuce driver gıdana ba. To wallahi kayi a hankali nan gaba zan iya sakawa a yi maka duk abinda nake so koda daga garin ne zan iya sakawa a b’atar da kai. yanzu ni matar manya ce ka kalli bayan ka har masu kula da lafiyata ne suke yawo dani. Darajar ka d'aya Amir wallahi sai na tura ka kurkuku kayi wata biyar dan ka sake tabbatar da wacece Fiddausi a yanzu, amma na kyale ka saboda Amir ko babu komai ni na haife shi tare da kai, a yanzun ma sai ka kwana a nan dan ka gane ikon da nake dashi a yanzu." Kallon ta kawai yake yi itama haka ido cikin iso tana hararar sa amma baice mata komai ba sai kallon, “daman ke kika saka a kama shi Fiddausi?." Muryar Alhaji taji sai ta rufe ido ta bud’e da tasa suna wajan ai baza ta zo ba sai gobe ta jiyo ta kallo Alhaji tace, "Alhaji barka ai ban kula daku ba, sannn ku." "Ke kika saka a kama shi Fiddausi?" Ya sake maimaita mata yana kallon ta. "Eh Alhaji" ta amsa a takaice tana kallon wani wajan daban. Yaya yace, "Akan me kenan?." "Saboda Marin da yayi min har bakina ya fashe, wannan shine sakamakon abinda ya aikata." Alhaji yace, "To tunda kin d’auki mataki ba sai ki kyale shi ya tafi ba." Fiddausi ta kalli Ibrahim tace, "Sai ya bani hak’uri ko na rama marin da yayi min.” Ibrahim yace, "Har abada, koda zaki saka a kaini lahira bazan baki hak’uri ba Fiddausi. Baki kai wannan matsayin ba ai har yanzu.” "Zaka dawwama a wajan nan kuwa daga nan har sati d'aya." Dan sanda ne ya k’araso yana cewa, "Ranki ya dad’e ai ban san kin zo ba, ga waje ki zauna, Alhaji ya sanar mana da zuwan ki bamu san kin k’araso ba." Ta kalle su tace, "ba zama zanyi ba, kawai so nake ku saka ya bani hak’uri sai na kyale shi." Dan sandan ya kalli Ibrahim yace, "Ka bata hak’uri a wuce wajan dan laifin da ka aikata ba ‘karami bane." Ibrahim yayi murmushi yace, "Har Allah ya tashi duniya indai hak’uri zan bata." Ta kalli dan sandan tace, "A cigaba da tsare shi har sai na bada umarnin a sake shi" ta fad’a tana niyar tafiya sai suka had’a ido da Alhaji da yake kallon ta yana mamakin wai daman haka take tace, "ku sake shi yaci albarka in mahaifin sa da nake ganin girma, amma wallahi sai na nuna masa ruwa ba sa’an kwando bane" tana fad'a ta juya ta fita wanda suka shigo tare yabi bayan ta. Har suka koma gida babu wanda ya iya cewa wani abu a cikin su, ibrshim wanka yayi sannan yayi sallah ya samu har lokacin suna zaune ana bawa Hajiya labarin abinda ya faru. Hajiya da take kallon sa da ya shigo tace, "Yanzu Fiddausi ce ta yiwa Ibrahim haka? Itace ta saka a kama shi dan tana ganin yanzu ta auri mai kud’i a yanzu?." Yaya yace, "Ta bani mamaki sosai Hajiya, in kika ga yadda take magana baza kice ta had'a jini da Ibrahim ba wallahi. Badan Alhaji ba ko ai sai na sanar da magabanta ta wallahi domin a tsawatar mata saboda gaba." Hajiya tace, "Ai abinda ya kamata ayi kenan, Alhaji ai mahaifinta zaka fad’awa kar nan gaba ta saka yan daba su sara shi." Alhaji sai a sannan yace, "Sai mahaifin nata ya dawo daga umra zanje na same shi dan abinda tayi ba abu bane wanda za'a kyale, badan Muna wajan ba ban San lokacin da Ibrahim zai fito ba. Kin San halin sa da taurin zuciya tace sai ya bata hak’uri ni kuma na tabbatar da ko me za'a yi Ibrahim bazai bata hak’uri ba." "Akan me zai bata hak’uri ba Alhaji? Ita bata bashi hak’uri ba shine zai bata hak’uri dan kawai ta Raina shi?" Hajiya ta fad'a tana kallon Ibrahim da yake cin abinci baice komai ba har lokacin kamar babu shi a wajan. Alhaji yace, "Tayi mana abinda ba'a tab'a yi ba, har kofar gida ta turo aka zo aka kama shi kawai dan ta ci mutuncin mu baki daya." "Duk abinda ta aikata na tabbata wata ran sai tayi dana sani, ko babu komai ai akwai Amir zata zo da k'afar ta ne Allah ya bamu lafiya" Hajiya ta fad’a a fusace dan taji zafi sosai na abinda ya faru sosai. Shi dai baya magana amma zuciyar sa tafi ta kowa zafi a haka duk suka tashi suka tattafi gida shi kuma ya fita daga gidan ko zai samu sassaucin abinda yake ji Bayan kwana biyu. Amarya Fiddausi ana ta sha gyaran jiki na tarewa tayi matuk'ar kyau daka zauna kusa da ita sai khamshi fatar ta har shek'i yake saboda kyau da kyaun gani. Kamar yadda aka tsara ranar juma'a zata tare Kasancewar Abuja zata tafi Zakiyya ce kawai tazo dan Rukayya baza'a barta zuwa Abuja ba ita kuma Ameena bata samu fitowa ba. A private get aka tafi kai Fiddausi ita da Zakiyya da kuma y’an gidan su aka kaita babban gida mai kyau madaidaici zaman mace guda d'aya, kallon gidan take yi tana sake kallo zuciyar ta fari tas burin ta ya cika ta samu abinda take so hankalin ta ya kwanta. Lokacin da suka shiga Abuja azahar ce suna sauka suka fara sallah bayan an idar aka ci abinci mai rai da lafiya Zakiyya taja Fiddausi d’aki tana kallon dakin tace, "Yanzu ya kike jin kanki dan Allah?." Fiddausi tayi dariya tayi juyi da d’akin ta fad’a saman gado tace, "Farin cikin da ban tab'a jin sa ba, ki duba wai gidan nan nawa na fa." Zakiyya tace, "Yanzu kika zama mace da kina zaune da wani fakirin miji." Sukayi dariya a tare Fiddausi tace, "Sai dai Ina tuna Amir dina wallahi, Ina son yarona zan kuma yi kewar sa" ta fad'a tana yin baya ta kwanta a kan gadon zuciyar ta cike da farin ciki. Zakiyya tace, "Kakar sa zata kula dashi ai, dan haka Baki da wata damuwa akan Amir." "Wallahi Zakiyya a duniya bani da masoyi kamar ki." Zakiyya tayi dariya tace, "Ke jirgi ance zai tafi, bara naje kar a tafi a barni, sai naji feedback na first night dan nasan kayan Surayya Halin yau zasu gigita mai gidan nan" ta fad'a tana dariya tana niyar fita. Fiddausi ta tashi ta dawo kusa da ita tace, "Sai kinji labari Ina tabbatar miki da komai ya faru ke zaki fara ji." Dariya tayi a tare Zakiyya tace, "Amarya amarya, ai yanzu zaki san asalin dad’in aure ba kwanan duhu balle zaman a cikin zafi, sai na jiki aminiyar." Har waje ta rako su suka shiga mota aka tafi airport dan dawowa Kano. Fiddausi komawa tayi tana sake kallon gidan ko Ina sai da ta shiga ta hau sama ta sakko gani take abin kamar a mafarki wai wannan gidan tane, farin ciki take ji sosai sai da ta gaji da zagayen sanma ta dawo ta zauna aka d’ora k’afa a kan d’aya ana girgizawa ana jiran ango yazo a sha soyayya mai dad’i wacce aka jima Ana jiran zuwan ta. Sai da akayi magariba sannan taji an bud’e gate alamun angon ta ya iso ta tashi tana kallon sa ta window ta ya fito daga mota cikin shigar alfarma yana amsa waya hannun sa rike da leda babba da k’arama. sakin laluben tagar tayi ta saka fashe jikin ta da turare tana kallon kanta a mudubi dan ita kanta tasan tayi kyau ba karya. Murmushi take yi ita kadai tana hasashen irin soyayyar da zasu kwasa a cikin daren. Motsin sa take ji yana shigowa sai ta fito falo ta zauna ya k’araso har lokacin da ya shigo waya yake yi, suna had’a ido sai taga ya sauke wayar ya mayar aljihu ya bud’e mata hannayen sa alamun tazo, ba musu ta tashi ta isa gare shi ta shiga jikin sa ya rungume ta tsam yana fad’in, "Daga karshe ga Baby a cikin gıdana, babu abinda ya kai yau mahimmaci a gare ni. Yau ce ranar da bazan tab’a mantawa da ita ba, yau ce ranar da nake mararin zuwan ta, yaushe ranar da nake fatan na ganta, yau ce ranar da zuciya take burin gani. Gani gaki my Baby zuciya ta kasa gasgata hakan gaskiya ne.” Fiddausi tayi dariya ta d’ago tana kallon sa ido cikin ido tace, "Daga karshe ka zama mallakina. Ni taka ce kaima nawa ne, babu abinda zai raba mu sai mutuwa. Ba mafarki kake ba Baby nice dai a gaban idanun ka kake gani.” Sakin ta yayi yana kallon ta yace, "Dole mu yiwa Allah godiya da ya nuna mana wannan ranar mai mahimmaci a rayuwar mu, muyi sallar I’sha sai muyi ta godiya ga Allah ko my Baby?.” Murmushi tayi ta daga mai gira ya cije bakin sa yace, "Zaki bada bayanin wannan daga girar sama, Allah ysa amaryar tawa ba raguwa bace dan mijin ta gwarzo ne, muje muyi sallar tukunna." Fiddausi dai jin ta take kamar a mafarki ko kamar ba ita bace wata Fiddausin ce daban ba ita ba, domin ganin abu take kamar film take kallo wai yau itace a gidan Alhaji Bello wanda yake d’aya daga cikin masu kudi manyan y’an kasuwa na Nigeria. A haka akayi sallah kamar yadda yace suka ci abinci tare shida ita kafin soyayyar da suke yiwa junan su ta fara bayyana a fili. Dan Fidy nuna masa qauna take kamar yadda shima yake nuna mata dan burin kowa ya tabbatar da soyayyar da d’an uwan sa yake yi masa. Fiddausi ta tabbatar da a baya ba aure tayi ba yanzu ne tayi aure tasan meye aure, yanzu tasan dad’in sa take kuma more masa. Gabadaya haushin shekarun baya take ji zuciyar ta ta cika da d'aci da k’uncin shekarun da ta kwashe da İbrahim tana wahalar banza da wofi amma a yanzu ta san soyayya tasan madarar ta ita da mijin ta abin son ta. Kamar yadda yayi mata alqawari washe gari jirgin bakwai na safe ya kwashe su zuwa k’asar America, farin ciki a wajan Fiddausi kamar wacce aka yiwa kyautar aljanna haka take ji, ko da yake tace ta samu aljannar duniya a gidsn Alhaji Bello. A dai yi mu gani🫠 #Mai daki #Book2 #Paid #Nana Haleema #09030398006 Book2 020 Tunda ya shiga falon nata yake bin sa da kallo gabad’aya komai ya fita daga hayyacin sa hatta kujerun falon sun fara duhu saboda basa samun kula mai kyau, wajan tv stand ya k‘arasa ya saka hannu ya shafi k'urar da take jiki ya sauke numfashi yana girgiza kai ya hau saman nata kai tsaye. Allah ya sani yak’i jinin k’azanta amma yaga alama Asiya bata son gyara ko kusa. Kukan ta ya jiyo daga bakin k’ofa kamar zai shiga sai ya fasa ya tsaya yana jin abinda take cewa, daga cikin d’akin Asiya na zaune da waya a kunnen ta tana kuka tana fad’in, "Ni ban san ya zanyi ba Umma matar sa bata sona kuma wallahi ni tsakani da Allah nake zaune da ita, meyasa cin fuskar ta bazai tsaya iya ni ba sai ta had’a dake a ciki Umma? Daga kawai jiya kin shiga ku gaisa shikenan sai ta fara zagin ki? Bazan iya jurewa ba Umma babu wanda zai tab'a min uwa ya zauna lafiya." Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta sake cewa, "Ban fad’a masa ba Umma bana son yawan masa magana akan matar sa kar yaga kamar da wani dalili nake masa maganar ko yaga nice bana son zaman Lafiya, bai San abinda ya faru ba bazan kuma fad’a masa ba saboda bana son haddasa fitina amma wallahi banji dad’i ba kefa ta ciwa fuska Umma, harda cewa wai kin saka na shigo gidan nan da a kore ta, inda mahaifiyarta na yiwa haka ai itama bazata ji dad’i ba. Mahaifi sunan sa mahaifi babu Wanda yafi wani.” Yusuf da yake sauraren abinda take cewa ya sauke numfashi ya kulle idanun sa, kenan jiya da mahaifiyar Asiya tazo ta shiga dan su gaisa d- Ameena ta ci mata mutunci ko me kenan?. Tsaki yayi a bayyane yace, "Me yake damun Ameena ne? Yaushe ta koma haka?. Ameena da bata son fad’a magana ma bata dame ta ba yaushe ta zama Mara kunya wai har haka?. Na fara gajiya da halayyar Ameena bata son zaman Lafiya yanzu ko kusa ko alama" ya fad'a yana murd'a handle din d’akin ya shiga sai ta zabura ta kashe wayar tana bin sa da kallon shima ita yake kallo yana kuma kallon d’akin. Mopper a ajjiye duk tayi daud’a ga kayan ta a jibge a gefe d’akin sai wani wari yake na musamman dan ya tabbata har da warin bandaki ma, zama yayi yana kallon ta itama ta kalle shi tace, "Ina kwana My love." Binta yake yi da kallo ganin kanta yana nan bata gyara ba kamar yadda yace yana binta da kallon tun kayan jiya da safe ne a jikin ta har yanzu alamun ko wanka ma batayi ba yace, "Ba nace kije a gyara miki kanki ba?." Shiru tayi tare da tura baki gaba ya sake kallon ta yace, "Asiya bana son k'azanta ba kuma na zama da k'azami, kince min aikin gidan ya ayi miki yawa an kawo miki masu aiki amma duk da haka babu abinda ya canja. Kullum gidan nan kaca-kaca kema kanki babu gyara, gidan nan har wani wari yake yi in na fad’a kice ke bakya ji. Ki kula ki kuma gyara sam sam bana son k'azanta Asiya." Yadda yake mata maganar a sanyaye ya saka ta d’aga kai sama tace, "to." "Meya faru jiya da Umma tazo? Akwai abinda Ameena tayi mata ne?." Asiya sai ta kalle shi suka had’a ido zatayi magana yace, "Gaskiya zaki fad’a min kawai bana son wata magana." Asiya ta sauke numfashi tace, "Banyi niyar fada maka ba My love, yanzu ma Umma da ita muka gama waya tace kar na fad’a maka ita aka yiwa kuma komai ya wuce. Amma dan Allah ka yiwa matar ka magana cin fuskar ta da cin mutuncin ta ya tsaya iya kaina ta daina saki mahaifiyata a ciki, Ina girmama ta kar ta saka nan gaba kazo ka tarar Muna dambe Kaga hakan bazai maka dad’i ba." Yusuf ya sauke numfashi yana kallon ta yace, "Kiyi hakuri, ki bawa Umman hakuri in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba." Ya goge ido tace, "Ran umma ya b’aci sosai tana ganin tayi jika da Ameena amma baka ji cin fuskar da tayi mata ba a gabana kuma Umma ta hanani na tanka" ta dago ta kalle shi tana hawaye tace, "Laifi ne da dan Umma na tazo gidan nan a karo na farko ta shiga wajan ta su gaisa?." Ya girgiza kai alamun A'a tace, "A yadda naga ana yiwa Umma a gidan Yaya Maimuna kafin mijin ta ya rabu da ita in muka je kishiyoyin ta har wajan ta suke zuwa su gaida Umma su koma, na d’auka yadda na d’auki Ameena haka ta d’auke ni; amma naga ba haka bane zan kama kaina." Yusuf yace, "kiyi hak’uri nace dan Allah, zan kuma saka tazo ta baki hak’uri ta kuma je har gidan ku ta bawa Umman hak’uri abinda tayi bata kyauta ba sam, ki daina kuka kinji my love?." Murmushi tayi ta goge ido tace, "ni ko bata bani hak’uri ba ta bawa Umman tunda itama kamar uwa take a wajan ta." Shima murmushin yayi yace, "kar ki damu." Murmushi itama tayi ya sake cewa, "Tafiya ta kama ni zuwa Dubai k’arfe sha biyu na rana, zanyi sati d'aya a can akwai abinda kike so?." Ta girgiza kai alamun A'a tace, "kawai zan yi missing din ka ne." Shima murmushi yayi yace, "nima zanyi missing din ki, kafin na dawo ki gyara kanki a kuma yi miki jan lalle yana kyau a hannun ki." Kai ta d’aga tana murmushi shima haka ya mik’e tsaye ya ajjiye mata kud’i yace, "Gashi nan koda akwai abinda zai taso, in kuma yafi k’arfin kud’in sai kiyi min waya na turo miki." "To my love Allah ya kiyaye, yanzu zaka wuce?." "Zan je dai gidan Ammah daga nan zan wuce." "Baza kaje dani ba?" Ta fad’a kamar zatayi kuka. "İn zan koma dake zamu je." Tayi murmushi tace, "Allah ya kaimu" ya amsa da Amin ya sauka. A falon Ameena ya tarar da Amira da Zaytun suna zaune Amira ta daga tana koya mata turanci ganin shigowar sa Amira tace, "Sannu da zuwa." Ya kalle ta yace, "Amira jiya mahaifiyar Asiya ta shigo gidan nan?." Amira tace, "Eh tazo." Daga nan bai sake cewa komai ba dan daman so yake ya tabbatar ta shigo d’in ya wuce sama zuciyar a sama daman haushin Ameena din yake ji. D’akin ya ya shiga ta fito daga wanka daga ita sai k'aramin towel kanta yasha kitso k'anana gashin ta yayi bak'i sosai fatar ta sai kyalli take yi, had'a ido sukayi yayi saurin janye idanun sa gabad’aya abinda yazo dashi ya gudu yana neman fita daga hayyacin sa dan yana bukatar matar sa sosai kawai rashin jin da take yi ne ya saka yake share ta dan taji a jikin ta dan shi yana da wata matar amma yau yaji abinda ya jima bai ji ba a kanta ba kuma ya tunanin zai iya kyale ta. Ganin bai magana ba sai ta samu waje ta zauna ya daidaita kansa yace, "Ameena misali ace Maman ki na da rai sai tazo gidan nan ta shiga wajan Asiya a ci mata mutunci zaki ji dadi?." Ta kalle shi ta tsayar da abinda take yi tace, "Haka akace maka nayi kenan ko?." "Ai hakan ne ma, domin yadda kike ji da tashen wulakanci da rashin kunya a yanzu zaki iya aikatawa." "To shikenan haka ne" ta fad'a a hankali ta tashi ta d’auko kaya ta ajjiye a kan gado. Yace, "Haka ne kenan kin yi?." Ta jiyo ta kalle shi tace, "Ba kai kace kasan zanyi ba? Shiyasa nace nayi saboda kar na k’aryata ka." "Ina so yanzu kije ki bawa Asiya hak’uri sannan ki karb’i number mahaifiyarta ki kira ki bata hak’uri yanzu ba anjima ba." Ya jiyo ta kalle shi tace, "Bazan bada hak’uri akan abinda banyi ba, ko nayi matar ka bata kai matsayin na bata hakuri ba wallahi.” Da mamaki yake kallon ta yace, "Kenan kina nufin kin aikata kuma baza ki bada hak’uri ba?." Ameena tayi shiru tana kallon sa kafin tace, "bazan iya ba." Fusata yayi matuk’a ya zazzaro idanu waje ya matso kusa da ita yace, "ni kike cewa baza ki iya ba Ameena? Ni kike kalla nace ki yi abu kice baza ki iya ba?." Ameena tace, "bazan bada hak’uri akan abinda ban aikata ba inda na aikata zan bada hakurin amma banyi ba bazan bayar ba....." zazzafan mari ya d’auke ta dashi ta dafe kunci tana kallon sa zuciyar ta na ingizata akan kawai ta rama itama amma batayi hakan ba ta kalle shi tace, "Akan abinda baka tabbatar na aikata ba ka mare ni?." "Na mare ko Ameena ko zaki Rama ne?" Ya fad'a yana kallon ta. Tayi murmushi tace, "Bazan rama ba, amma tabbas wata ran ana aikata hakan zan rama domin jikina ba dan duka yake zaune a gidsn nan ba” ta fad'a hawaye na sakko mata ta saka hannu ta share ya bita da kallo itama shi take kallo tana kuka. Baki ya bud’e yana kallon ta idanuna waje yace,"Ameena zaki iya marina dan na mare ki kenan?." "Tunda har kai ka iya zan iya mana." "Lallai rashin kunyar ki ta fara wuce inda nake tunani, lallai Ameena ni kike kallo kike fad’awa wannan maganar dan baki da kunya. Duk wanda yake zuga ki akan wannan banzayen halayen cutar ki yake.” Ameena tace, "koma meye kaine ka saka na zama haka Yusuf. Kuma zan cigaba da zama gaba da haka ma indai baka fasa ba.” Kwafa tayi dan in ya cigaba da zama abinda take zai iya b’alla ta ya wuce ya fita da sauri ta zauna akan gadon tana kuka. Ba kukan Mari ko kukan an mata sharri take yi ba, kukan sa'insa da ta fara da mijin ta take yi dan tafi son zaman kuramen da suke yi akan yazo yana d’aga mata murya dan bata iya jurewa kamar lokacin baya koda tayi niya bata iyawa gabad’aya. Zuciyar ta ta bushe a kansa kiris take jira yayi abu ta mayar masa. Tana jin fitar sa a mota ta daure itama ta tashi ta shirya ta sakko suka fita iya da Amira zuwa wajan Dr Mansura. Bata dawo ba har dare dan gidan d'aya daga cikin y’an uwanta ta wuce suka yi hira duk da babu wani sakewa sosai amma babu laifi, har sha d'aya na dare babu Yusuf babu labarin sa dan taga babu motar sa duk da tasan a wajan Asiya yake. A haka tayi bacci dan ita bata san ma yayi wata tafiya ba. Tsahon kwanaki shida kenan baya nan ganin bata ganin giftawar sa ga kuma motar sa tana nan hakan ya saka ta tabbatar baya nan, gabadaya ga manta ma da wata Asiya a gidan sai dai in tana tsaye a taga tana kallon harabar gidan Asiya taga ana fitowa da kayan abinci daga gidan ana sakawa a sabuwar motar da ya siya mata ana fita dashi. Bata tab’a kawo komai a ranta ba sai dai ta saki labulen kawai. Ranar da ya cika kwana bakwai da daddare tana zaune a kasa bayan i’sha suna waya da Fiddausi tana fad'a mata irin soyayyar da suke kwasa da mijin ta tana ta darıya in Fiddausi ta fad’i wani abun, sosai Fidy ta zare akan soyayya hakan shine yake bata darıya. Sallama akayi aka shigo Yayar Asiya ce Maimuna da kanwar ta Momi sai ita a bayan su. Sai da gaban Ameena ya fadi da taga sun shigo amma bata nuna ba ta yanke wayar ta mik’e tana fadin, "Barkan ku da zuwa, Bismillah ku zauna mana." Maimuna ta bita da kallon wulakanci tace, "ba zama muka zo ba ai, in zama muka zo ai baki isa ki hana mu ba saboda gidan k’anwata ne." Ameena tace, "Tofa!.” Amira da ta sakko lokacin tana kallon su bata ce komai ba Momi tace, "Zuwa mukayi mu rama duk wani wulakancin da kike yiwa Asiya a gidan nan." Amira da take gefe tace, "Ku kuma daga Ina?." Ameena ta kalli Amira tace, "Amira muje ciki in kare yana haushi ba'a zuwa inda yake" ta fad'a tana zuwa zata wuce sai kuwa Asiya ta damk’o rigarta ta baya tace, "Uwar ki Sa'adatu da take cikin kabari itace karya kuka itace take haushi ba Yayata ba." Ameena ta jiyo a fusace bata san lokacin da ta d’auke Asiya da zazaafan mari ba tana kallon ta tana kad’a yatsa tace, “kul! Kar ki sake kar ki kuma maimaiwa, Koda wasa nan gaba kika sake zagin mahaifinta sai nayi miki abinda yafi haka.” Amira tazo wajan tace, "Kinyi daidai Mummy, nuna mata bata isa tazo har gidan tayi miki hauka ba.” Maimunatu ta kalli Momi sai Momi ta fita daga falon sukayi kan Ameena zasu dake ta. Ameena tayi baya Amira ma taja ta tsaya tana hararar su tace, "Tunda tashin hankalin kuke ji dashi na rantse da Allah daidai daku nake." Marin ta Asiya tayi sai kuwa tayi tsalle ta rama itama tana cewa, “ke baki San haushin ki daman nake ji ba? Ai yau kin kawo kanki inda aka fi k’arfin ki.” Maimuna ta chakumi Ameena zata dake ta Ameena ta dage ta cillar da ita k’asa Asiya ma tayi baya ta fad’i goshin ta ya daki table ya fashe daga gefe. A lokacin Yusuf ya shigo yana bin su da kallo ita da Amira cikin zallar bacin rai sai kuwa Asiya ta tashe da kuka ita da Maimiuna tana cewa, "Yaya sai da nace kar mu shigo Umma ma bata kyale ba balle ke, Gashi daga gaisawa ta dake ki nima ta dake ni. Ki tashi mu tafi bana son tashin hankali. Mu muka kawo kan mu ko me tayi mata mu muka jawo.” Maimuna tace, "Nayi tunanin dan na shigo mun gaisa ba wani abun bane dan Umma tace abinda ya faru ya wuce kar mu canja mata. kiyi hak’uri Ameena basai kin kai ga dukana ba laifina ne da na shigo gidan nan, ban d’auka hakan zata faru ba da banzo ba.” Yusuf da yake tsaye baiyi wani tunani ba ya k’arasa inda Ameena take a fusace yace, “wanne irin hauka ne wannan wai Ameena? Yaushe kika koma wannan banzayen halayen. Dan Malama ki basu hak’uri Yanzun nan.” Ta girgiza kai tana kuka tana kallon su duka biyun kawai ta wuce sama yabi bayan ta a guje su kuma sukayi dariya a tare suka tafa suka mik’e tsaye suna hararar Amira Maimuna tace, "Yau sai Kun bar gidan nan, duk Bala’in ku gidan Yusuf na Asiya ne ita kad’ai” tana fad'ar hakan ta fice tana hararar falon Amira ta zauna a wajan tana kuka sosai. Magana yake yana bin Ameena tana tafiya tayi masa banza yana zuwa kusa da ita ya cinkota ya d’aga hannu zai mare sai ya fasa yace, "Ina yi miki magana kina tafiya? Abubuwan da kike yi a gidan nan Ina kyale ki har ya kai haka?. Yayar matata kika saka hannu kika daka dan baki da mutunci? Kishin naki har yakai haka?.” Bata ce komai ba sai kallon sa da take yi yace, "kin sace min gold, kina d’aukar min kudi, kin zagi babar ta, kin zage ta, ki kore ta daga motar ki, yanzu kuma kin daki yayar ta. Da yake ke mara hankali wacce bata san abinda take yi ba nace ki bata hak’uri sai ki tawo nan dan ki nuna musu ban isa dake ba?.” "Kaine mara hankali ba ni ba, in ma hauka ne kaine kake yin haukan bani ba....." Marin ta yayi tare da hankad'ata baya ta fad’i ta buge da kujera yana kallon ta yace, "Ni kike fad’awa haka?." "Na fad’a maka, na fada, nan gaba ka sake dukana ma wallahi sai na rama na gaji ba saboda haka aka kawo maka ni ba. In ka gaji da zama dani ka sake ni mana ai baa dole. Me na tare maka?.” Da mamaki yake kallon ta ransa ya b’aci sosai yace, “ni kike fad’awa haka?.” “Nace na fad’a maka d’in, zuciya ce a kirjin ka nima itace a kirjina. Na daina lamuntar abubuwan da kake yi min, dan kana ganin kamar ina jin tsoron ka shiyasa kake taka ni yadda kake so. Yanzu komai ya k’are yadda baka sona nima bana sonka, ka sake ni in ka gaji da zama dani.” "Daman ai bani na kawo ki ba Ameena Ammah ce kuma zaman ta kike yi, Ammah ita ta ganki tace na aure ki bani da zab’i na amince nata saboda tana sonki ba dan ni ina so ba, duk soyayyar da na nuna miki anyi ne saboda Ammah yanzu ne na samo zab’in raina kuma wallahi baki isa kiyi mata wani abun ba na kyale ki dan ta fiki a wajena. Dole ki karb’i hukunci in kika aikata ba daidai ba.” Duk da halin da take ciki sai da gaban ta ya fad’ita mike tsaye tana kallon sa jikin ta duk a sanyaye da abinda yace tace, "Da gaske baka sona?." "Eh bana son ki, bani na ganki nace Ina so ba Ammah ce ta saka na auro ki Ina zaune dake ne kawai saboda ita badan so ba. Banda abin ki in badan Ammah ba taya zan zauna da b’arauniya kamar ki?. Taya zan zauna dake kina fad’a min magana ina kyale ki?, kallona kika yi kika ce na sake dukan ki sai kin rama, ba dan Ammah ba da Yanzu kin jima bakya gidan nan domin kuwa bazan zauna dake ba!.” Sai kuwa ta fusata tace, “in baka sona ka sake ni mana, ka sake ni in da gaske baka sona ai babu Wanda yayi mama dole sai ka zauna Dani.” Yusuf ya wara idanun sa kanta yace, “Saboda Amma kike zaune a nan in badan haka ba da yanzu bakya cikin gidan nan, bazan zauna da mai sata ba ke kin San da haka, badan Ammah da yanzu na manta da shafin rayuwar ki gabad’aya.” "Tunda kana so ka manta da shafin rayuwar ta zaka manta Yusuf, Tabbas baza ka zauna da barauniya ba Yusuf, yau alfarma da take ci saboda Ammah ta k’are Yusuf, zaman hak’urin da kake da ita duk ya k’are daga yanzun nan. yau b’arauniya zata bar gidan ka sai ka zauna da wacce kake so!." Jin muryar wanda basu yi tunani ba duk suka juya suna kallon inda suka ji maganar ba kamar Yusuf da ya wara idanu yana kallon wajan zuciyar sa har harbawa take yi. #Nana Haleema #Mai Daki #Book2 #Paid #500 #09030398006. Book2 021 Dukkan su a tare suka kalli wajan Ameena ta ware idanu waje cikin mamaki da murna da kuma tsoro, babu wanda bai ji tsoro ba ganin wanda basu yi tunani ba a tsaye yana kallon Yusuf da b’acin rai a kan fuskar sa har wuci yake saboda b’ari ran da yake ciki, fuskar sa a murtuk’e daman shi ba gwanin fara’a ba, yadda yake bin Yusuf da kallo ma abin tsoro ne saboda kana ganin kallo kasan babu sassauci a cikin sa. Ameena a guje ta k’arasa kusa dashi ta rungume shi tana kuka sosai a jikin sa ya rik’e ta shima yana kallon Yusuf zuciyar sa wuya ji yake kamar yayi masa dukan tsiya yace, “Ko baka ce ba yau Ameena zata bar gidan nan Yusuf, Tunda b’arauniya ce ba sonta kake ba ina tabbatar maka daga yau zaman ta ya k’are.” Ya kalli Amira da yake tsaye yace, “Shiga d’akin ta ki d’auko mata mayafi da duk abinda kika san zata yi amfani dashi yanzu ku fito mu tafi.” Yusuf ya kasa ko motsin kirki sai kallon Yaya Adam da yake yi dan yasan tunda yace sai ta tafi wallahi sai ta tafi, zuciyar sa bugawa take yi sosai dana sanin furucin da yayi a kanta ya mamaye masa zuciya hakan ya saka shi kasa koda d’aga ido ya kalle shi, yayi tsitt ya kasa tankawa haka yaga Amira ta wuce shi ta shiga d’akin Ameena tana jifan sa da harara. Yaya Adam ya d’ago da Ameena daga jikin sa yana kallon ta yace, “Gatan ki ya dawo Ameena, babu wanda kuma ya isa ya sake yi miki abinda yayi miki daga rana irin ta yau indai Adam yana numfashi. Babu wanda ya isa ya kuma dukan ki matuk’ar ina da rai, rashi na kusa dake ne ya jawo hakan kar ki damu na dawo gare ki yanzu.” Kuka take yi sosai fuskar ta tayi ja ta kumbura saboda marin da ta sha a hannun sa ya kalli kumatun ta ya girgiza kai a lokacin Amira ta fito da babbar jaka da kuma tata jaka tazo ta wuce shi ta baya Ameena mayafin yace, “Jeki ki saka a mota.” Ba musu ta wuce zata sauka ya kalli Ameena yace, “Jeki kema.” Ta rik’e hannun Zaytun zasu fita yace, “bar masa y’ar sa a nan ai ba da ita kika zo ba.” Kallon sa tayi kamar zatayi magana sai kuma ta kasa cewa komai ta saki hannun Zaytun sai kuwa ta saka kuka tana kiran Mummy tana bin bayan ta ya kalli Ameena d’in yace, “Jeki da ita ina zuwa.” Fita sukayi daga falon ya juya ya kalle su yaga basa hango shi ya matso kusa da Yusuf bai tsaya jiran wani abu ba ya tsinke shi da mari ya nuna shi fa yatsa yace, “Na Rama mata marin da kayi mata ko na ce kake mata, sannan kar ka sake kazo inda take, koda wasa na ganka a gida na wallahi sai ranka ya b’aci fiye da tunanin ka, kar kazo inda Ameena sai da takardar saki na sake maimaita maka” yana fad’a ya juya ya fita ya tarar da Ameena jiri na k’okarin yarda da ita yayi sauri ya rik’e ta a lokacin Amira ta dawo ta sauka da Zaytun shi kuma ya rik’e Ameena suka sauka yana rik’e da ya bud’e mota ya saka Ameena Amira ta shiga gaba yaja motar suka fita daga cikin gidan. Suna cikin tafiya ya kalli Amira yace, “Wanne asibiti kuke zuwa sun bata da lafiya?.” Amira har lokacin kuka take yi ta ja numfashi tace, “Wani private ne a nan gaba, bara na kira likitan da take zuwa wajen ta ko tana nan” ta fad’a tana bud’e wayar Ameena ta kira Dr mansura ta tabbatar mata da tana asibiti suka nufi can kai tsaye. Da taimakon Amira suka je wajan Dr mansura tana ganin su ta mike’e aka kwantar da Ameena akan gado da yake office d’in ta ta fara suna jinin ta dan tasan dakyar in ba shine ya hau ba, suna nan tsaye suna kallo sai suka ga tayi sauri ta d’auko ruwa ta saka mata, ta dauki allura tayi mata a jijiya daga nan bacci ya kwashe Ameena cikin mintina kad’an. Bayan ta gama ta tabbatar Ameena tayi bacci Dr Mansura ta kalli Yaya Adam tace, “Dan Allah kai Yayan tane?.” Ya daga kai yace, “Eh ni Yayan tane ko nace mahaifinta, meye yake damun ta?.” Dr Mansura tace, “Gaskiya in ba’a cire ta daga cikin wannan damuwar da take ciki ba zuciyar ta zata iya kamuwa da ciwo. Yanzu zancen da nake maka jinin ta ya hau diye da tunanin ka badan anyi gaggawar kawo ta ba wallahi in ta fad’i zata iya gamuwa da cutar shanyewar b’arin jiki. Bama sai ta fad’i ba haka kawai za’a iya wayar gari aga ta kasa motsi ko kad’an. Damuwa tayi mata yawa na sha fad’a mata ta daina saka damuwa a zuciyar ta amma bata ganewa, wallahi damuwar da take ciki ko d’an shekara hamsin ne yake a irin ta zaunar dashi ake ana tambayar sa abinda yake faruwa saboda lafiyar sa, ya kamata a zauna da ita aji meye damuwar ta dan yadda jinin mata ya hau a yanzu sai na canja mata magungunan da take sha an bata wanda yafi na baya k’arfi.” Yaya Adam ya girgiza kai yace, “Kenan in na fahimta Ameena tana da hawan jinin da har an d’ora ta akan magani ko?.” “Kwarai kuwa, kusan wata hud’u kenan tana kan maganin hawan jini, a baya ban da jinin yake hawa ban d’ora ta kan magani ba ni kaina, saboda k’arancin shekarun ta tayi k’arama da fara Shan maganin hawan jini, amma yadda jinin yake hawa baya sauka ya zama dole na d’ora ta akan magani saboda rana irin ta yau.” “Ameena k’anwata itace take da hawan jini? Damuwa ce ta haifar da hakan ko?.” “Tabbas damuwa ce, dan wata ran in tazo zuciyar ta bata bugawa daidai saboda damuwar da tayi mata yawa. Sai na saka ta huta sosai nake bari tana tafiya gida. A ganina tunda kaine uba a gare ta gaskiya kayi wani abu dan ba iya hawan jini gare ta ba tana shan maganin kwantar da sha’awa.” Da sauri ya kalle ta cikin tashin hankali da mamaki da tsoro Dr mansura tace, “Kwarai kuwa, da farko ban bata magani ba shima sai shawarwari da nake bata yadda zata samu kwanciyar hankali in hakan ya taso ba tare da an sha magani ba amma abin sai yaci tura dole ta takura sai da na bata magani, in na tambaya sai tace mijin ta baya nan yayi tafiya nace ta sanar a gida a d’auki mataki ko ya daina tafiyar ko ya dinga tafiya da ita sai tace to zatayi. Badan babu ruwana akan lamarin iyali ba da har gidan zanje na samu mijin nata nayi masa bayani tunda ya sanni na sanshi amma sai banje ba” ta kalli Ameena da take bacci tace, “Yanzu ya kai ya kawo maganin k’arfin maganin ya yi mata kad’an sai dai a bata wanda yafi shi k’arfi kuma hakan babbar illa ce ga rayuwar ya gabadaya.” Yaya Adam girgiza kai yake cikin b’acin rai da zallar bak’in ciki had’i da takaicin halin da Yusuf ya aka kanwar sa yace, “Yaushe duka wannan abubuwan suka faru?.” Dr tace, “an jima sosai gaskiya, wani lokaci nice nake zuwa gidan saboda kar ta tawo ita kad’ai ban san meye zai faru da ita ba.” Yaya Adam ya girgiza kai cikin gamsuwa da kalaman ta yace, “Yanzu in ta farka zata dawo daidai?.” “İn sha Allah, zuwa safiya ma sai ku tafi gida lokacin jinin nata ya ya sauka.” “Shikenan likita Mun gode.” Murmushi kawai tayi ta fita ya kalli Amira yace, “Ke a gaban ki yake dukan ta meyasa baki tab’a fad’a min ba ko a waya?.” Amira tace, “bai tab’a dukan ta a gabana ba gaskiya sai dai naga ranta ya b’aci ko tana kuka, ranar nan ma cemin tayi mu bar gidan da daddare wajan sha d’aya muka fita ta rasa inda zamu je kawai tayi parking tana kuka. Sai Allah ya kawo Yayan Yusuf din wajan ya hana mu tafiya ko ina muje gidan sa a can ma muka kwana washe gari muka dawo gidan. Yaya har mota ta d’auka taje Bauchi ita kadai saboda damuwar Yusuf, Yaya kar ka barta dashi dan Allah ka hanata komawa gidan sa.” Ya girgiza kai yace, “Zauna da ita ina zuwa” ya fad’a yana fita ta k’arasa kusa da ita ta zauna ta kwantar da Zaytun a kusa da Ameena dan tayi bacci tuni. Lokacin da a Ameena suka fito Asiya suna tsaye ta taga suna kallon komai ganin ta fita suka kyalkyale da dariya suka tafa cikin shu’umanci Maimuna tace, “Shikenan ta fita in sha Allah bazata dawo ba.” Asiya tace, “Amma waye wannan naga ya fito daga gidan?.” Momi tace, “Oho kuma dai tunda dai ta fita ai shikenan.” Maimuna tace, “mu zamu koma yanzu, ashe fa Momi tana nan ni zan wuce yanzu kije b’angaren nata da niyar rarrashi dan kiga halin da yake ciki.” Asiya tace, “To bara naje yanzu, mu fita tare” tare suka sakko suka fito zuwa b’angaren Ameena ita Maimuna ta fita ita kuma ta shiga. Saman ta hau kai tsaye zuwa d’akin sa ta shiga ta ganshi a zaune a gefen gado ya had’e hannayen sa biyu yana kallon k’asa, da sauri ta shiga ta zauna kusa dashi tace, “My love naga Ameena ta fita da daddare nan ina taje? Badai wani abun kayi mata ba akan abinda ya faru d’azu?.” Banza yayi mata bai kula ta ba ta dan ba ta ita yake ba shi kad’ai yasan abinda yake zuciyar sa, kalaman ta yake tunawa da take cewa indai ta fita daga gidan ya saka a ransa ta fita kenan, bata fahimci baya son damuwa ba ta sake cewa, “Dan Allah ka fad’a min me kayi mata, nifa bance kayi mata komai ba wallahi yanzu ina ta tafi?” Ta fad’a tana shirin yin kuka yana kallon sa. D’ago jajayen idanun sa yayi ya kalle ta yace, “Tashi ki fita.” Gaban ta ya fad’i ganin yadda idanun sa suka canja kala zuwa ja, ga fuskar sa a d’aure kamar bashi ba ta daure ta kalle shi tace, “Amma my love…..” da tsawa ya katse ta yace, “Nace ki tashi ki fita ko!?.” Yadda yayi tsawar sai da ta tsorata bata san ta mik’e tsaye ba tana kallon sa tana ja baya amma bata fita ba ya sake kallon ta ya girgiza kai yace, “Wallahi kika bari na taso sai jikin ki ya fad’a miki.” Jin abinda yace ya saka ta fita jiki a sanyaye zuciyar ta na bugawa tana tunanin me hakan yake nufi kenan?. Yusuf ya rasa inda zai saka kansa bai san abinda yake damun sa ba gabad’aya komai ji yake ya fita daga ransa duniyar na juya masa take ba tare da tasan dalilin hakan ba, tashi yayi yana zaga d’akin abubuwan da suka faru suna sake yi masa yawo a zuciyar sa da idanun sa. “Meyasa nace mata bana sonta? Meyasa na fad’a?!” Ya fad’a da karfi yana dukan wardrobe da take gefe yana sauke numfashi kamar yayi gudu. “Meyasa in raina ya b’aci bana daidaita kaina a yanzu? Meyasa zan yiwa Ameena haka? Ameena ta fa?” Ya sake fad’a a bayyane tare da kulle idanun sa ya bud’e yana kallon sama tare da cigaba da yawo a d’akin. Tsayawa yayi cak ya sauke numfashi ya kalli wata drawer kawai ya k’arasa wajan ya bud’e ya d’auko kwalba madaidaiciya mars girma sosai ya bud’e kanta har zai fara sha sai kuma ya tsaya, tunawa yayi yace bazai kuma sha ba sai kuma ya share tunanin ya kafa kai yana sha har sai da yasha rabi sannan ya ajjiye kwalbar yana sauke numfashi. Ameena bata jima tana baccin ba ta farka ita kanta taji dad’inciwon kan da yake damun ta idanun ta biyu har asuba sai bayan anyi sallah ne ta sake yin bacci ta farka k’arfe tara na safe. Tana farkawa Yaya Adam yana shigowa suka had’a ido ta tashi zaune ya kalle ta yace, “Ameena kin tashi? Me yake damun ki?” Ya fad’a yana k’arasowa kusa da ya dafa kafadar ta mike zaune sosai tace, “Da sauki Yaya, ina kwana.” “Lafiya lau, ya jikin naki?.” “Naji sauk’i sosai kan nawa ma ya daina ciwo.” “Haka ake so, likitan da ta duba ki ta tashi amma tace min in kin farka zamu iya tafiya. K’ok’arta ki tashi muje dan Amira ta samu ta huta itama.” Tsaf Ameena ta mik’e tsaye kamar ba ita ba ta saka mayafin ta suka fito tare suka shiga mota kai tsaye gidan sa ya wuce. Daman matar sa tasan da zuwan su ta gyarawa Ameena d’akin da take ajjiye kaya in suna Kano suna zuwa can suka wuce Ameena a nan taga kayan ta ajjiye ta zauna a gefen katifar Amira kuma ta shiga bandaki. Sai bayan Amira tayi wanka ta yiwa Zaytun sun shirya sannan ta d’auke ta ta fita a lokacin Yaya ya shigowa Ameena da abinci da kansa ya zauna akan kujera yana kallon ta yace, “Sannu, D’auki kici Ameena.” Ba musu ta d’auka tana shan tea da aka had’o mata yasha madara tana cin bread d’in sai da yaga taci sosai sannan ya bari ta ajjiye. Kallon fuskar ta yake har lokacin a kunbure take sai ya ciro waya ya kira duka k’annen sa yace suzo gobe gida yana son ganin ko wacce a cikin su. Yana yanke wayar kiran Yayan Bauchi yana shigowa ya d’auka kafin tayi magana yace, “Ai kin yin laifin da banyi tunanin zaki yi shi ba, kin nuna min ban isa da Ameena ba kece kuke cike d’aya da ita ni ba wani abun bane ba Samira.” Daga can b’angaren tace, “kayi hakuri dan Allah Yaya, Amira ta sanar dani komai ina hanya gobe nima zan zo. Ya jikin Ameenah?.” Ya kalli Ameena yace, “taji sauki abinci ta gama ci yanzu.” “Alhamdulillah, tun jiya da Amira ta fad’a min banyi bacci ba wallahi, abun yayi yawa Yusuf bashi da mutunci baya kyautawa kamar ba auren soyayya sukayi ba.” Yaya Adam yayi k’aramin tsaki yace, “ai duk laifin kine, da kin fad’a min da ba’a zo nan ba.” Yaya tace, “kayi hak’uri dan Allah, sai na shigo Yaya.” Bai ce komai ba ya yanke wayar ya kalli Ameena da kanta yake a k’asa. Tashi yayi ya fita Jim kad’an ya dawo da Leda da ruwa a hannun sa ya ciro maganin da kansa ya mik’a mata ta karb’a tasha ya ajjiye a kusa da ita yace, “Gasu nan kar ki dinga fashin shan su.” “To Yaya” ta fad’a tana Jan maganin kusa da ita shi kuma yana kallon ta har lokacin. Yace, “Ameena!.” Ta d’ago idanun ta ta kalle shi tace, “Na’am Yaya.” “Yusuf ya saba dukan ki?” Ya fad’a yana tsare ta da idanun sa wanda ya saka tayi shiru ba bashi amsa ba yace, “kar kuma ki yi min k’arya ki bud’e baki ki bani amsar duk abinda na tambaye ki, Yusuf ya saba dukan ki?.” Ta d’aga kai alamun eh ya girgiza kai yace, “Meyasa baki i tab’a fad’a min a waya ba?.” “Bana son na tayar maka da hankali ne shiyasa..” “Baki San yanzu abun yafi tayar min da hankali ba?.” “Kayi hak’uri Yaya, ganin baka kusa ya saka bana son fad’a maka irin wannan maganar.” Ya sauke numfashi yana kallon ta yace, “abinda naga Yusuf yana yi miki ya tabbatar min da a jiyan ya fara ba ya saba yi miki Ameena, na tabbatar ya saba dukan ki haka zakila ya saba ci miki mutunci. Tunda jiya Allah yasa na gani k’arshen wulakancin da yake miki yazo k’arshe. Babu zaman jin dad’i a auren ki da Yusuf ki ba’a fad’a ba yanayin ki ya nuna hakan, kin rame kin fita daga hayyacin ki bayan da ba haka kike ba.” Ya sake cewa, “Yaushe kika kamu da cutar hawan jini?.” Gaban ta ya fad’i ta kulle ido ta bud’e kanta a sunkuye bata ce komai ba ya girgiza kai yace, “Ameena an tabbatar min da kin jima kina shan maganin hawan jini, yanzu haka gasu nan a gaban ki na baki kin sha” ya fad’a yana kallon yaga sai raba idanu take sai yayi murmushi takaici ya sake kallon ta yace, “Ameena kalle ni.” Ba musu ta kalle shi yace, “Bazan barki ki cigaba da zama da mijin da bai San darajar ki ba kamar Yusuf, bazan barki ki cigaba da zama a inda aka bud’e baki akace alfarma kike ci ake zaune dake ba Ameena, bazan bari ki cigaba da zama a inda ake kokarin kashe ki ba. Ameena zan raba auren ku da Yusuf, ki fad’a min gaskiya kina goyan bayana ko bakya goyan bayana?.” Shiru tayi bata amsa ba sai zuciyar ta da take bugawa ta kasa cewa komai kanta yana k’asa bata san wacce amsa zata bashi ba yace, “kar kiyi min k’arya ki fad’a min kina goyan bayan na saka ya sake ki ko kuma kina son komawa gidan sa?.” Yadda yayi maganar a kausashe ya saka ta jan numfashi ta d’aga kai alamun eh, yace, “me hakan yake nufi? Kina son koma masa Kenan?.” Tayi saurin girgiza kai alamun A’a yace , “Kiyi magana mana.” Ameena murya na rawa tace, “A raba auren.” “kin tabbatar har zuciyar ki?.” Nan ma ta d’aga kai alamun eh ya girgiza kai ya mik’e tsaye yace, “Yusuf ka jira zuwa na gare ka, zan tabbatar maka da Ameena nada gatan da baka isa ka sake wulakanta ba, ko kana so ko baka so a sai ka sake ta. Tunda k’anwata ta samu ciwon hawan jini ta dalilin ka sai na saka kayi dana sanin da baka yi tunanin zaka yi ta a cikin rayuwar ka ba” ya fad’a yana fita daga d’akinta bishi da kallo ta koma da baya ta kwanta kawai sai hawaye ya fara sakko mata daga idanun ta ba tare da tasan dalilin zuwan su ba a wannan lokacin. #Mai daki #Book2 #Nana Haleema #Paid #500 Book2 022 Rukayya tana kwance a d’aki ita kad’ai Zuhra ta shigo da sallama ta amsa tana kallon ta tace, “Yaya kizo in ji Baba.” Da to ta amsa ta tashi ta fita ta same shi a zaune a falon Umma daga shi sai ita ta k’araso ta zauna akan carpert tace, “Baba gani.” Baba ya kalle ta yace, “Jiya da daddare wani yazo ya same ni akan yana neman izinin zuwa wajan ki.” Gaban Rukayya yayi mugun fad’uwa cikin sacannin da basu wuce biyu zuwa uku ba farin ciki ya mamaye mata zuciyar ta ta daure ta b’oye bata nuna ba sai murmushin jin dad’i da take yi kanta yana sunkuye. Baba ya sake cewa, “ya fad’a min a nan k’ofar nasarawa iyayen sa suke, daga jiya zuwa yau na saka an bincika min an tabbatar haka ne mahaifinsa mutumin kirki ne duk da baya duniya. Anjima da yamma zai zo dan ku gana sai dai ya sanar dani yana da aure da kuma yara guda biyu.” Umma tayi caraf tace, “Dan yana da aure ai ba wani abun bane, indai zai rik’e ta hannu biyu babu ruwan mu da matar sa wallahi, Allah ya basu zaman Lafiya shine abinda zamu ce, Allah ya daidaita su” Umma ta fad’a tana murmushin farin ciki wanda ya bayyana akan fuskar ta sosai. Baba yace, “Amin, amma ai bai zama mijin nata ba sai ta ganshi in yayi mata sai a san abinda za’a yi, in kuma bai mata ba sai ya tafi Allah ya kawo wani.” Umma ta kalle shi tace, “Yanzu wai sai ta tsaya zab’e kake nufi? Ai a ganina da an samu a amince ba sai an tsaya wani dogon jawabi ba.” “Sam, sai yayi mata ta amince dashi sannan za’a yi auren, in kuma bata amince ba babu wanda zai aura mata wanda bata so.” “Kai kake zugata daman ai take koran masu zuwa wajan ta, yanzu dan Allah meye abin zab’en mijin aure a wajan Rukayya dan Allah?.” “Saboda ita ba mace bace?.” “Mace ce mana, amma shekarun ta sun wuce zab’ar miji a yanzu, sai dai duk wanda yazo a karb’a ayi fatan alkhairi.” “Ko me zaki ce sai ta amince sannan za’a yi auren nan, wallahi in bai mata ba zuciyar ta bata amince dashi ba babu wanda zai tilasta mata.” “Ai shikenan” Umma ta fad’a tana tashi ta shiga d’aki. Baba ya kalli Rukayya yace, “Kar maganar ta ta dame ki, ki tsaya ki nutsu ki tabbatar zaki iya zama dashi in kika ji akasin haka kar ki cuci kanki. Ba maganar tace zata zauna da mijin ba kece, kinga kenan sai kin gamsu a zuciyar ko zaki iya zama dashi sannan zaki aure shi.” Rukayya ta d’aga kai jikin ta yayi sanyi da kalaman Umma fahimtar hakan ya saka Baba yace, “Babar ki ba k’in ki take ba Rukayya, so take kiyi aure kema ki zauna a gidan ki kamar yadda sa’anin ki suke. Soyayya ce take nuna miki a baibai ba wai k’iyayya ko ta gaji dake ba, kinga kece a wannan halin na zaman gida ko?, Zan iya rantse miki ta fiki shiga damuwa akan rashin auren nan naki, yadda take miki addu’a ke bakya yiwa kanki saboda ita uwa ce a gare ki. Kar ki damu da kalaman ta na yanzu ki tabbatar zuciyar ki ta amince da wanda zai zo wajan ki in baki amince ba kar ki cuci kanki dan ke zaki zauna dashi, jinkirin aure bazai saka na aurar dake ga duk wanda yazo ba tare da kin amince ba.” Rukayya tayi murmushi tace, “İn sha Allah Baba. Allah ya saka da alkhairi.” Ya amsa da amin kafin yace, “tashi kije, Allah yayi miki albarka ya baki mijin da zaki ji dad’in zama dashi.” A zuciya ta amsa da amin dan bata iya amsawa a fili indai Baba yayi mata irin wannan addu’ar ta tashi ta koma d’aki. Farin ciki take ji a ranta da zuciyar ta wai ita Rukayya wani namiji ya gani yana so har yazo ya samu mahaifin ta da maganar, abin kamar a mafarki take ji sa. Kenan itama zata zama cikin layin masu masoya ba wanda ake son a a had’a su ba. fuskar ta ta kasa b’oye farin cikin da take ciki dan sosai take murna da hakan ko babu komai a yanzu tasan Allah ya amshi addu’ar ta tunda ga sakamako nan ta fara gani tun ba’aje ko ina ba. Ko iya haka aka tsaya Alhamdulillah domin ta tabbatar addu’ar ta ta karb’u Allah ya amsa sai dai ta jira lokaci kawai. Tana zaune a gefen gado Umma t shigo ta k’araso ta zauna kusa da ita tana kallon ta tace, “Rukayya!.” Ta amsa tana kallon Umman tace, “Dan girman Allah ki amince da mutumin da zai zo wajan ki, in ya sub’uce wa muke dashi da zai sake neman auren ki? Bamu da kowa sai Allah. Dan Allah ki amince tunda shi ya kawo kansa ba nemo shi akayi ba ayi auren nan a gama, kina kallo Zuhra an kawo kud’in auren ta kanwar ki ce ta biyu, ina kishin hakan a raina Rukayya, ki taimaka min ki amince dashi dan Allah. Koda bai kwanta miki a zuciyar ki ba indai mahaifin ki ya amince da nagartar sa ki amince wata rana zaki so shi Rukayya, mijin aure wahala yake a yanzu na tabbata zaki bada shaida kema da kanki, kar mu bar wannan damar ta kubce mana.” Yadda Umma take magana a raunane ya saka Rukayya kwalla ta cika mata idanu ta sauke idanu k’asa tace, “in sha Allah Umma a wannan karon bazan yi abinda bakya so ba, amma ki taya ni addu’a Allah yasa shine na gari a wajena kuma shine alkhairin da ake jira. Ki min addu’a Allah yasa k’arshen wahalar kenan Umma.” Umma tace, “Addu’a kullum cikin yi miki ake Rukayya, in sha Allah lokacin ne yazo yanzu.” Shiru Rukayya tayi bata ce komai ba kafin Umma ta tashi ta fita ita kuma ta kwanta a kan gadon tana ji a ranta zata amince da wanda zai zo wajan ta kodan Umma. Wayar tace ta d’auki k’ara ta katse mata tunani ta duba taga lambar k’asar waje ce kamar yadda Fiddausi ta saba kiran ta tayi murmushi ta d’auka a bayyane tace, “Amaryar Alhaji Bello.” Fiddausi daga can b’angaren tace, “Fadi ki k’ara fad’a amarya nake wallahi.” Sukayi dariya a tare Rukayya tace, “ya New York din?.” “Bari kawai Ruky, Allah jina nake kamar sabuwar halitta komai ya canja. Kud’i sunyi ta ko wanne b’angare.” Rukayya tace, “Yayi kyau hajiyata. Allah yasa an samo mana babyn New York.” “Ke akayi ciki yanzu ai harka ta lalace, kina ji ni kiran ki nayi neman alfarma Allah yasa zaki min.” “Wacce alfarma?.” “Wallahi kwana biyu mafarkin Ameer nake yi, dan Allah kije gidan su Ibrahim ki had’a ni dashi a waya mu gaisa sai ki dawo. Dan Allah kar kice a’a ke kadai nake da ita da zaki iya yi min. Nasan Hali yanzu sai kice baza ki fita ba ki taimaka dan Allah.” Rukayya tace, “Gidan su Ibrahim da kika ce? To ni zan gane gidan ma balle naje zanje?.” Fiddausi tace, “Zan miki kwatance dan Allah kije in kin kije sai ki kira ni WhatsApp call.” “Anya zan iya zuwa kuwa Fidy?, a wanne matsayi zan shiga gidan su yanzu?.” “Matsayin babar Amir mana, dan Allah kije, zan turo miki kud’i yanzu ki dan siya masa chocolates da dan biskit ki kai masa.” “To bara na tambayi Umma in zata barni.” “Yauwa tambaye ta kar ki kashe, ko ki bani na tambaye ta da kaina.” Wayar na kunnen ta ta isa d’akin Umma tace, “Umma.” Ta amsa da Na’am tana kallon ta tace, “Fiddausi ce zaku gaisa.” Umma ta karb’i wayar ta saka a kunne suka gaisa da Fiddausi kafin tace, “Dan Allah Umma ki bar Rukayya taje ta gano min d’anta Amir ta had’a mu a waya wallahi kwana biyu mafarki sa nake kar naje ko bashi da lafiya.” Umma ta kalli Rukayya tace, “Babu komai Fiddausi zata je ai itama dan tane.” Fiddausi tayi godiya Umma ta mik’awa Rukayya wayar ta kashe Umma tace, “Kije kiyi sauri ki dawo, daman ai ya kamata ace ana duba shi duk da yana hannun baban sa dan anje duba shi ba wani abun bane. Kema babar sace ai” ta fad’a tana tashi daga inda take zuwa gaban madubin d’akin. Sai bayan la’asar sannan Rukayya d’auki hijjabi ta saka ta d’auki wayar ta nan taji shigowar kud’in da Fiddausi ta saka mata sai ta d’auki atm ta fita dashi. Store ta fara shiga ta siyi abinda tace ta siya masa sannan ta nufi gidan da tayi mata kwatance haka kawai take ji gaban ta yana fad’uwa. Da tambaya aka nuna mata gidan ta shiga da sallama mata guda biyu suka amsa daga cikin falon ta shiga, a guje Amir yayo wajan ta yana fad’in, “Aunty Rukayya.” Ta rik’e shi tana murmushi kafin ta zauna ta kalli Hajiya da wacce take kusa da ita tace, “Barkan ku da yamma.” Wacce take kusa da Hajiya ta amsa tana fadin, “Rukayya daman kin san gidan nan ne? Naga Amir ya d’afe ki yana murna.” Rukayya tayi murmushi ganin wacce ta saba zuwa gidan su wajan Umma tace, “Lahh Aunty nasan gidan duk da nasan yau aka fara ganin fuska ta.” Hajiya tace, “ina ta tunanin inda dai na sanki.” Ta sake yin murmushi tace, “Ni k’awar Fiddausi ce.” Hajiya tace, “Allah sarki.” Wacce take kusa da Umma tace, “Daman kin San Fiddausi?.” “Sosai ma kuwa.” Rukayya ta sake cewa, “itace ta kira ni tace dan Allah nazo na m had’ata da Amir a waya.” Amir da yake jikin ta yace, “ni ki tafi dani wajan Mama na ina so na ganta.” Rukayya tace, “Yanzu zaku fara yin waya in na sake dawowa sai muje ko?.” Kai ya d’aga tayi dariya ta d’auki waya tayi kamar yadda tace ta d’auka ta bashi wayar ya saka a kunne ya tashi a guje ya shiga d’ak. Da sallama Ibrahim ya shigo falon suka amsa duka ganin Rukayya sai yayi murmushi yace, “Rukayya kece a gidan namu?.” Murmushi tayi tace, “Eh wallahi, ina wuni.” Ya amsa gaisuwar yace, “kin kyauta” daga haka sai ya fita. Tana zaune shiru bata iya cewa komai har Amir ya fito ya bata wayar ta d’auki ledar ta bashi tace, “ga alawa kaje kayi ta sha.” Ya karb’a yana tsalle sai yace, ni ke zan bi mu tafi.” Ta wara idanu tace, “Ai Maman naka bata nan Amir.” Ganin kamar zaiyi kuka tace, “Kana ji, ka kwantar da hankalin ka tana dawowa zan zo na d’auke ka kaje wajan ta kana so?.” Ya d’aga kai alamun eh tayi murmushi tace, “to kar kayi kuka mana.” Sai yayi dariya ta bashi hannu tace, “to mu tafa.” Sai kuwa suka tafa tayi dariya sosai ta kalli Hajiya da yake kallon ta da murmushi tace, “ni zan koma Mama.” Hajiya tace, “ke kuwa ko ruwa baza ki tsaya ki sha ba?.” “Sauri nake yi ne bana so magriba tayi min a hanya.” “To mun gode sosai, ki gaida mutanen gidan” ta amsa da in sha Allah ta fita daga falon. Tana fita Mama Suwaiba ta cewa Hajiya, “Itace yarinyar da nake fad’a miki, ke kanki nasan kin shaida nutsuwar ta da hankali ko? Dan naga sai kallon ta kike kina murmushi.” Hajiya tace, “wallahi lokaci d’aya naji ta shiga raina, ga fara’a da hankali gata kyakykyawa har tafi Fiddausin kyau.” Mama Suwaiba tace, “tana da shiga rai saboda akwai nutsuwa sosai ma sha Allah. In naje gidan su baza kice tana nan ba saboda bata da hayaniya ko kad’an. Yadda suke wasa da Amir suka saba haka sai na sake yiwa Ibrahim sha’awar auren ta wallahi.” Hajiya tace, “to babu wanda dai yasan abinda Allah ya b’oye sai dai mu zuba ido kawai muga yadda zai yi damu.” Mama Suwaiba tace, “haka ne. Nima bara na gudu zan lek’a gidan rasuwa daga nan zanyi gida.” Hajiya ta amsa mata sukayi sallama ta fita. Tana fita Ibrahim ya shigo ya tarar da Amir yana ta shan chocolate yana kallon sa yace, “Abba kaga abinda Aunty Rukayya ta kawo min.” Yayi murmushi yace, “an gode.” Hajiya ya kalla bayan ya zauna yace, “Yunwa ce ta dawo dani nazo na ganki da bak’i.” Hajiya tace, “eh wallahi, tazo duba Amir ne wai babar ce tace tazo ta bashi waya su gaisa, ashe kasan yarinyar?”. Ya kalli Hajiya yace, “Wai Rukayya? Na santa farin sani ma Hajiya. Ai tana daga cikin aminan Fiddausi dan tare duk sukayi makaranta.” “Allah sarki, ni wallahi nutsuwar ta ta burge ni sosai, Gashi sun saba da Amir.” “Gaskiya babu laifi, a lokacin baya in tazo gidan mu ina ji takan yiwa Fiddausi fad’a akan abinda take yi.” Hajiya tace, “kuma budurwa ce ko tana da aure?” Ta tambaya kamar bata sani ba. Ibrahim yace, “Gaskiya bata da aure amma ban san ynzu ba.” “To Ibrahim mai zai hana baza ka aure ta ba?.” Gaban sa ya yanke ya fad’i ya kalli Hajiya da sauri da kuma mamaki yace, “Hajiya na aure ta fa? Na fad’a miki k’awar Fiddausi ce fa.” “Dan k’awar tace sai me Ibrahim? Ai ba k’anwar ta bace ba ko?.” “Eh haka ne, amma dai gaskiya bana jin hakan a raina ko kusa.” Hajiya tace, “ko itama halin Fiddausin ne da ita?.” Ibrahim yace, “Taya zan sani Hajiya; nida ban zauna da ita ba?.” Hajiya tayi murmushi tace, “Nidai zuciyata ta amince da ita wallahi, in rabon kace Allah ya baka.” Kallon Hajiya yayi haka kawai baice komai ba ya samu zuciyar sa da harbawa sosai sai kawai ya tashi ya tsaye ta kalle shi tace, “ya ka mik’e? Abincin fa?.” Yace,”in n dawo zanci.” Abinda yace kenan ya fita Hajiya tayi dariya kawai ta cigaba da abinda yake gaban ta. Yusuf kuwa wunin ranar a gida ya yishi ya kasa fita ko ina dan gabad’aya wani iri yake jin sa gashi babu dama a kira shi a waya sai gaban sa fad’i sai ya d’auka Ammah ce take kiran sa ta samu labarin abinda ya faru. Yana zaune a b’angaren Asiya a falon kasa gabad’aya baya jin dad’in zaman saboda wani irin khamshin gidan yake masa kamar na kayan wankin da suka jima a ajjiye ruwa ya tab’a su. Tunawa da akwai abinda ya ajjiye sai ya tashi ya shiga kitchen d’in Asiya, a share yake amma k’udaje sunyi yawa a ciki yayi tsaki ya kulle tagar kitchen d’in ya bud’e store d’in kitchen din ya shiga. Neman abinda ya ajjiye yayi can ya hango shi wani k’aramin k’arfe ne na motar sa ya d’auka har zai fita sai ya dawo da baya yana kallon store din ganin babu kayan abincin ga shinkafa da take buhu uku a ajjiye Saura buhu d’aya itama kuma an bud’e. Mamaki abin yayi sai ya fito akwai ya hau sama d’akin sa, clashing sukayi da ita zata fito daga d’akin nasa shi kuma zai shiga yaga duk ta diririce kamar mara gaskiya ya bita da kallo ta koma da baya ya shiga yana kallon d’aki wai sunan a share amma kana taka kafar ka zaka ji k’asa. Tace, “my love daman wajan ka zanje.” Kallon ta yayi rigar jikin ta daban siket d’in ma haka yace, “gani ai” ya fad’a yana wucewa wajan drawer ya saka k’arfen da ya tawo dashi. “Kabi bayan Aunty Ameena kuwa?.” Jin abinda tace sai ya kalle ta kamar zai ce wani abun sai ya fasa tace, “dan Allah kaje ka dawo da ita koma meye mu Mun yafe, wannan abun ai bai kai ace anyi saki ba my love.” Da mamaki yake kallon ta yace, “Ce miki akayi na sake ta ne?.” Ta kalle shi tace, “nima bana fatan hakan kawai ina so kaje ne ka dawo da ita, mu zauna lafiya shine fatana.” Baice komai ba ya sake kallon drawer din yace, “kamar na ajjiye kudi a nan ko?.” Gaban ta ya fad’i amma sai ta maze tace, “kudi kuma? Yaushe kenan?” Ta fad’a tana k’arasowa wajan tana dubawa amma babu komai a wajan. Yusuf yace, “bana ce ga ranar ba, shikenan nan dai. Naga abincin store yayi k’asa sosai.” Asiya tace, “eh wallahi, kasan da yake nayi bak’i sosai da kayi tafiyar nan. A rana sai bak’i su zo sau goma haka akaita girki.” Kai ya girgiza yana kallon ta sama da k’asa yace, “yayi kyau” ya fad’a yana wuceta ya fita daga gidan ma gabad’aya ya koma b’angaren Ameena yana ji a ransa zaije ya bawa Yayan ta hak’uri ta dawo dan in bata dawo ba bai San ya zaiyi ba, dawowar ta shine jin dad’in sa ya tabbatar da hakan musamman yanzu da yake jin yunwa a yadda ya tarar da Asiya bazai iya cin abincin ta ba. A bayyane yace, “kiyi hakuri Ameena ki dawo, bazan sake miki komai ba. Ina sonki wallahi raina ne ya b’aci na fadi abinda na fad’a amma bawai dan haka abun yake ba.” Kallon falon yake a share tass ga khamshi ya lumshe ido ya bud’e yana tunanin yadda zasu kwashe da Yaya Adam dan yasan tun farko ba son sa yake da Ameena ba kawai dan tana son sane ya Bari akayi auren, Gashi yanzu an samu matsala a kan idanun sa ya tabbatar kafin ya hak’ura ya bashi Ameena a karo na biyu sai ya sha wahala sosai. A bayyane ya sake cewa, “ko wacce wahala ce zan jure indai Ameena zata dawo gare ni, barın ta gidan nan babban gib’i ne a gare ni.” Band’aki ya shiga zuciyar sa cike da tnanin inda zai d’auko k’arfin guiwar tunkarar Yaya Adam da ita kanta Ameena d’in. Book2 023 Kamar yadda Yaya Adam ya kira k’annen sa haka duk suka hallara a gidan tun safe babu wacce tasan dalilin kiran kawai sun ga Ameena a gidan basu kawo kuma komai ba sun d’auka yadda ya kira su haka ya kira ta. Dan basu San ma ya dawo ba wayar tasa ce ta tabbatar musu da ya dawo. Dukkan su sun hallara a babban falo yana zaune a kan kujera gabadayan su suna k’asa babu wacce tasan abinda zaiyi magana a akai ko wacce abinda yake zuciyar ta kenan. Sai da ya bud’e taron da addu'a suka yiwa iyayen su addu'a sannan yace, "Nasan duk baku San na dawo Kano ba sai jiya da nayi muku waya, a daren shekaran jiya na dawo na kira ku jiya. Dalilin da ya saka nace duk kuzo yau wata magana nake so mu tattauna daku wacce zata amfani mu baki d’aya." Ya kalle su yace, "Tsakanin ku da Allah yaushe rabon da kuje gidan k’aramar qanwar mu dan kuga Lafiyar ta?” ya fad'a yana nuna Ameena da take zaune itama ya jingina kanta da jikin kujera. Duk suka kalli Ameena suka kalli juna kafin d’aya tace, "ni naje lokacin da za'a yi mata kishiya amma kafin nan gaskiya rabona da gidan ta tun haihuwar Zaytun." Ya kalli Ameena yace, "Shekara biyu kenan ko?." Ameena ta d’aga kai alamun eh ya kalli sauran yace, "ku kuma fa?." Daya tace, "Kwanaki hanya ta bi dani na shiga amma kafin nan nima tun haihuwar t." Yaya yace, "sauran ma basai kun ce komai ba kuma nasan tun haihuwar ne, amma ita bata zuwa inda kuke?." A tare suka had’a baki suka ce, "Tana zuwa." Yaya Sumayya tace, "tana zuwa gaskiya, dan ba'a jima sosai ba tazo gidana har la'asar tana nan." Wacce take zaune kusa da ita tace, "nima anyi haka, ko bata zo ba zatayi mana magana ta WhatsApp a gaisa." Yaya ya girgiza kai yace, "Amma ku baku damu da kuje inda take ba saboda ba uwar ku d'aya ba ko? A haka kuna mijin ta yake baku zakka ki saka hannu ku karb’a ko?." Sai ya fusata ya fara fad’a cikin kakkausar murya yace, "Itace Autar gidan mu fa, itace mai ‘karamin shekaru a cikin mu, dukkan mu bamu da iyaye sun rasu amma meyasa bakwa tunanin a cikin mu itace marainiya bamu ba? Meyasa baku tab’a zama da ita kunce k’anwar mu ne yake damun ki ba?, saboda ba babar ku d'aya ba shiyasa kuka ware gefe a ganin ku wanda ake uba d'aya ba dan uwa bane ba ko?." Jin yadda yake fad’a sai ko wacce tayi shiru sai Yaya Sumayya da tace, "Allah ya sani zuwan ta na k’arshe gidana na tambaye ta ko tana da damuwa ne naga ta rame sai tace min A'a sai na kyale ta." Kamar zai dake ta kuwa yace, "Dole ki kyale ta mana Tunda ba Jidda bace ko Zulaihat, inda sune ai baza ki kyale ba sai kin tabbatar kin San abinda yake damun su saboda su babar ku d'aya." Dukkan su shiru sukayi ya sake cewa, "A ce yarinya k'arama babu wanda ya damu da lamarin ta a cikin ku saboda wata d'abi'ar banza da wofi da kuka saka a zuciyoyin ku, in baku kula da ita ba waye zai bata kulawa? Dukkan ku mata ne fa, kamata yayi ace kun jata jikin ku Kun nuna mata k'auna da kulawa saboda kasancewar ta k’arama a cikin ku amma baku yi ba. Ku duba yadda ta lalace ta rame saboda kawai babu mai kula da ita a tare da ita, duk gaku da yawa mata amma kun zama na banza da wofi tunda babu amfani, babu wanda zai tambaye ta damuwar ta, babu wanda zai kwantar mata da hankali, babu wanda zai rarrashe ta in tana kuka. Yanzu kenan da babu ni sai dai wata ran dukkan ku kuji labarin k’anwar ku ta mutu ko?." Dukkan su jikin su yayi sanyi babu mai magana a cikin su ko wacce ta sunkuyar da kai ya sake cewa, "Yanzu in na fad’i na mutu kenan babu mai zumunci a tsakanin ku ko wacce sai dan d’akin su ta sani?, hakan a wajan ku shine daidai tsakani da Allah? Kun raina zumuncin dake tsakanin uba d'aya kenan ko?." Yaya Sumayya tace, "Ba haka bane ba Yaya, kayi hak’uri zamu gyara in sha Allah. Tabbas munyi kuskure amma zamu daidaita komai in sha Allah." "Kar ma ku gyara mana Sumayya, ku bar komai yadda yake Allah ya gani ai  nayi iya bakin kokarina, kuma ni duka d'aya na d’auke ku babu wacce ta fi wata dan wai muna uwa d'aya da ita." Yaya Saudatu tace, "Kayi hak’uri Yaya, in sha Allah zamu gyara." Yayan Bauchi ma tace, "Mun gane kuskuren mu in sha Allah zamu gyara, zamu bude’e group na WhatsApp yadda zamu dinga fad’awa junan mu damuwar mu koda bamu had’u ba, kayi hak’uri." Dukkan su hak’uri suka bashi sannan ya gamsu da yace, "Shikenan ai ya wuce, Allah ya had'a kanmu baki d'aya, ya jik’an iyayen mu." Duk suka amsa da amin kafin Yaya Sumayya tace, "Yaya meye yake damun Ameenah ne haka?." Ya kalli Ameena da idanun ta suke a rufe tana kallon sama ya kalle su yace, "Damuwa ce tayi mata yawa itace ta mayar da ita haka, babu inda zata je ta fad’i abinda yake ranta, bata da kowa a kusa da zata fad’a masa damuwar ta shine ta koma haka." Kowa kallon tausayi yake yiwa Ameena dan ta rame sosai kafin Yayan Bauchi tace, "ta rame da yawa fuskar ta duk ta kumbura ." Yaya yace, "Matsalar daga mijin tane amma zanyi maganin komai zai tabbatar da gatan Ameen ya dawo Kano, zai tabbatar da ni ba wanda ake tab’awa na kyale bane. Zai gano yayi kuskure da ni kuma yake zancen, an Ameena baza ta koma gidan sa ba na riga da na yanke hukunci." Sauran duk basu San me yake faruwa ba hakan ya saka basu da tacewa Yayan Bauchi tace, "ina bayan ka Yaya, kar ka bari ta koma in ba haka ba wata ran gawar Ameena zamu d'auka a gidan sa.” Ya kalle ta ya harare ta yace, "kema ai kin bani haushi, in ita bata fad’a min ba kema sai ki yi min shiru ki k’i fad’a min abinda yake faruwa bayan kin san nine kawai zanyi maganin abun?. Ai hankalin ku ba d’aya ba, in ita tayi shiru ke bai kamata ace kin yi shiru da maganar ba, amma sai kika yi min shiru baki ce min komai ba.” "Kayi hak’uri Yaya, amma wannan karon kar ka kyale Yusuf dan Allah." Mik’ewa tsaye yayi yace, "bai san waye ni bane shiyasa, kar na dawo gidan nan da daddare naga wata ta kai dare ko wacce ta tafi gida, ke ta nesa gobe ki shirya ki bar Kano. Ku karbi sak’o a wajan Aisha" yana fad'a ya fita suka yi godiya kowa ya koma kallon Ameena kafin su dinga janta da hira wai ko zata sake ayi hira damuwar ta bar zuciyar ta. Yaya Adam mahaifin Yusuf ya kira a waya ya sanar dashi zuwan sa da daddare in yana nan ya tabbatar masa da yana gida yana kuma jiran sa sannan ya kashe wayar ya fita zuwa wani waje daban. Sai bayan sallar i’sha sannan ya nufi gidan su Yusuf, a k’ofar gidan su ya tsaya ya sanar da mai gadi zuwan sa aka shiga ana fad’awa Abbah ya bada izinin shigowar sa sannan ya shiga ciki. A zaune ya samu Abbah da y'an uwan Yusuf maza har ma da Yusuf d’in ma da alama an shigo gaishe su ne ya shiga da sallama suka amsa fuska a sake Abbah cikin zolaya yana cewa, "Soja mazan fama, barka da zuwa." Murmushi yayi ya gaida Abbah cikin girmamawa suka gaisa da kowa kafin ya zauna. Abie yace, "Abbah tunda kayi bak’o bara mu wuce mu." Yaya Adam yace, "A'a ku zauna daman dukka nake so mu had’u mu tattauna, inda hali ma a kira Hajiya itama tazo." Abie ya kalli Adam wanda zasu yi sa'a shida shi yace, "lafiya dai?." Ya kalli Yusuf da kansa yake a sunkuye ko motsi ya kasa ya kalli Abie yace, "Gaskiya ba Lafiya ba, shiyasa nake so a had’a kowa da kowa a nan in hakan zaiyu." Abbah yace, "Zai yi mana, Mubarak shiga ciki ka kira Ammah da yayar ku ta Abuja tunda tazo har Humairah ma tazo" ya fad'a yana kallon k’anin Yusuf. Ba musu ya tashi ya shiga ciki suka dawo tare da Ammah da Yayan Abuja da kuma Humaira d’in. Ammah tana ganin sa tace, “A’a wannan kamar Adam yayan Ameena ko?” Ta fad’a zama tana kallon sa. Yayi murmushi yace, “Ni ne Hajiya, barka da dare.” “Barka dai, an dawo lafiya?.” “Lafiya lau, na same ku lafiya.” “Lafiya lau, mutanen gidan lafiya.” Ya amsa da komai lafiya yana murmushi. Abbah ya kalle shi yace, "to Adam muna jin ka, Allah yasa lafiya dai." Yaya Adam ya gyara zaman sa sannan yace, "Gaskiya Alhaji ba lafiya ba." "To me ya faru?." Ya kalli Yusuf ya kalli Abbah yace, "Shekaran jiya na dawo daga garin Abia sallar magriba nayi da i'sha kawai na kasa hak’uri nace sai naje naga Ameena saboda kwana biyu in muna waya sai na ji yanayin ta kamar mara lafiya in na tambaya tace babu komai, ina shiga gidan na tarar da y’ar k’anwata Amira da take wajan ta da y’arAmina din suna zaune suna kuka tare, hankalina ya tashi ma d’auka ko wani abun ne ya samu Ameena na tambaya aka tana sama na hau saman da kaina." Yayi shiru ya sake gyara zama kafin yace, "Wato abinda na gani yafi komai d’aga min hankali, domin zuwa nayi na tarar da Yusuf yana marin Ameena har tana cewa wallahi na gaji da dukana da kake yi nan gaba nima zan rama, hakan sai ya bani tabbacin kenan ba iya ranar Yusuf ya saba dukan Ameena ba. Sai kuma naji yana ce mata b’arauniya wacce ta sace masa sark’ar gold da kuma kud’i. Ita kuma Ameena take ce masa in baya sonta ya sake ta mana yace daman shi ai ba son ta yake ba, yana zaune da iya ne saboda mahaifiyar sace ta nuna tana son ya auro ta amma badan so ba" yayi shiru yana kallon yanayin kowa a cikin su dukkan su an rasa mai motsin kirki a jikin su kowa ya sauraron sa yake yi. Ya cigaba da cewa, "Yusuf yana cewa Ameena yanzu ya samo wacce yake so kuma ta fita a wajan sa daman ita zama da ita alfarmar Maman sa ce. Hankalina ya tashi sosai a nan take nace Ameena da Amira su tattaro kayan su mu wuce gıda tunda bayan sonta bazata zauna dashi ba, tunda a kan idanuna na gani yana dukan ta dan na jima a tsaye a wajan ina kallon su basu San naje wajan ba. Da har nace ta bar masa y’ar sa ma to ganin yarinyar na kuka ne ya saka muka tafi da ita a wannan lokacin itama kuma Ameena baza ta ji dad’i ba.” Yaya Adam ya sake cewa, "A daren muka wuce asibiti saboda jikin ta yayi zafi sosai in ta tsaya jiri d'aukar ta yake yi tsayuwa ta gagare ta. Muka je asibitin da take ganin wata likita Dr Mansura, bayanin da likitan tayi min shine yafi komai d'aga min hankali domin kuwa abinda na gani a gidan ba komai bane akan abinda naji, dan ta tabbatar min da Ameena na cikin damuwa matuk’ata tun ba yanzu ba" sai yayi shiru ya d’auko wayar sa yace, "gata ma tana kirana zata shigo tayi miki bayanin komai, nafi so kuji komai daga bakin ta kamar yadda naji" ya fad'a yana amsa wayar aka ce ta shigo. Da yake falon shine na farko a gidan shi zaka fara tararwa Dr mansura ta shigo da sallama suka amsa ta gaishe su Yaya Adam yace, "Dr ki yi musu irin bayanin da kika yin min akan Ameena." Dr tace, "Sunana Dr mansura ina aiki da asibitin Aminu kano sannan ina aiki da Silver clinic wanda a nan ne Ameena ta sanni. Tun farkon auren ta ni mijin ta yake kawowa ita in bata da lafiya, abinda ya shafi cikin ta har ta haihu nice nayi komai mun saba da ita sosai ya zama bata da wata likita sai ni.” "Ameena tana zuwa wajena da damuwa sosai, in na duba ta ina ganin jinin ta ya hau sai nak’i bata magani saboda a shekarun ta bai kamata ace an d’ora ta akan magani ba; dan shi maganin hawan jini in ka fara sha baka dainawa har abada sai dai ka rage. hakan ya saka nake bata shawara akan saka damuwa a ranta duk dan saboda bana son bata magani amma abin sai da yaci tura da kaina na d’ora ta akan magani saboda zuwa lokacin hawan jini ya kama Ameena shawara bazata yi mata aiki ba sai dai magani." Shiru tayi ta d’auko magungunan ta nuna musu tace, "wannan shine maganin da Ameena take sha duk sati biyu take shnaye wannan kwalin sai tazo wajena na sake auna bp d’in ta na gani ko zata rage ya zama tana sha duk sati hud’u amma jinin ta bai tab'a sauka ba dole a haka zance tashs na sati biyun.  Sai kuma wannan maganin" ta fad'a tana sake d’auko wani ta nuna musu tace, "kafin nace komai dan Allah a nan akwai wanda yasan magani ko yake karanta b’angaren lafiya?." Humaira ta kalle ta tace, "I’m a pharmacists ina level three a yanzu haka." Mansura tace, "good, karb’i maganin nan ki duba min kiga meye amfanin sa a jikin maza da mata, nasan ko baki San shi ba matsayin ki na pharmacists zaki san amfanin chemical d’in da akayi amfani dasu wajan had’a shi.” Ba musu ta karb’a ta bud’e ciki ta d’auko takardar da ake sakawa tana karantawa kafin ta d’ago tace, "A yadda na fahimta magani ne kamar na kwantar da sha'awa, ana bawa wanda suka jima babu aure kuma suna fama da matsananciyar sha'awa ko abinda yayi kama da haka. Haka dai nake tunanin amfanin sa.” Dr Mansura tace, "kin san aikin ki. Abinda kika fad’a haka ne bawai a fahimtar ki bane. Wato Ameena ta jima tana shan wannan maganin, shima tun ban bata ba in ta kira ni na bata shawara nace kar ta sha komai har ya zamana da kaina na bata saboda tsoron kar ta fad’a halaka. In na tambaye ta sai tace min mijin ta baya zaman Kano kullum baya k’asar , nace mata Ameena ki sanar a gida a d’auki mataki ko ya dinga tafiya dake ko kuma ya daina zuwa ai hakkın kine, sai tayi dariya kawai bata ce min komai. Sau da dama nakan yi tunanin zuwa gidan nan saboda Ameena, dan ban san kowa nata ba iya Yusuf na sani a tare da ita da y'an uwanta zan fad’awa dan zasu fi mayar da hankali Akan matsalar." "A kalla Ameena tasha kwalin maganin na ya kai goma, yanzu zancen da nake muku maganin yana gab da daina yi mata aiki saboda yawan da yayi a jikin ta ko nace ma ya daina sai dai a bata wanda ya fishi k’arfi. Dalilin da yasa na amince da zuwa nan kamar yadda Yayan ta yace saboda Ina so a kawo k’arshen damuwar Ameena, tayi kankanta da d’aukar wannan condition din, in kuma ba haka ba zuciyar ta zata iya samun matsala sannan zata iya fad’awa harkar lesbian ko kuma neman maza. Babu jini da ya had’a ni da Ameena amma ina jin ta kamar k’anwata Ina tausayin ta sosai shiyasa na amince nazo nan dan ayi maganin abun kafin ya yi mata illa. A yadda suka kaita asibiti shekaran jiya tsaf zata iya kamuwa da ciwon shanyewar b’arin jiki dan jinin ta ya hau fiye da lokacin baya. Tana buk’atar kwantar da hankali da kuma da kuma rarrashi gaskiya." Yaya Adam da yake jin ta ya yake kuma kallon ta jin taje k’arshe ya saka yace, "Dr na gode sosai da abinda kika yi min, Allah ya kiyaye hanya, zan shigo asibitin gobe." Tayi murmushi tace, “Babu komai, nima Ameena k’anwa ce a wajena zan tsaya mata a ko ina dan ganin ta samu sassaucin abinda yake zuciyar. Sai anjima” ta fad’a tana saka takalmin ta ta fita. Yaya Adam ya bisu da kallo har lokacin an rasa mai magana yace, "Har mahaifinta ya rasu bashi da hawan jini, har mahaifiyarta ta bar duniya bata da hawan jini, ni da nake matsayin uba wajan ta a yanzu bani da hawan jini, a cikin mutanen dake wajan nan bana jin akwai mai hawan jini. Ta dalilin Yusuf Ameena ta samu hawan jini har kuma take shan maganin da zai kawo mata mafita a duk sanda take cikin bukatar mijin ta, hakan yana nufin bata samun abinda take so baya sauke hakkin ta da Allah ya d’ora masa sama da kwanaki masu yawa.  Dan in muka yi duba da yawan kwalayen maganin da likita ta fad’a tasha ta jima bata samu abinda take so ba a wajan Yusuf. Da kuma ta fad’a harkar neman mata ko neman maza yace bazai zauna da fasik’a ba." Falon yayi shiru babu wanda yake magana sai Amma da take goge idanun ta haka Humaira kuka suke yi sosai saboda tausayin Ameena basu d’auka abin har ya kai ga haka ba ya sake cewa, "An sanar dani k’arfe sha d’aya na dare ta dauki mota ta fita saboda abinda yayi mata a ranar taji bazata iya kwana a gidan ba, Allah ne kad’ai yasan me yayi mata a ranar ta bar gidan a wannan daren, rasa inda zata je da kuma damuwa ya saka ta fakawa a titi har kuka zo kuka tafi da gidan gidan ka haka ne?." Ya fad'a yana kallon Abie.  Abie ya girgiza kai yace, "haka ne, tabbas anyi haka nima nayi mamakin fitowa ta a wannan lokacin. Dan washe gari da Yusuf din yazo na masa fad’a sosai yace min bazata sake faruwa ba in sha Allah.” Yaya Adam ya sake cewa, "haka ta d’auki mota ta tafi Bauchi taje tayi kwana uku shima duk dan saboda damuwar da take ciki a gidan." Yaya Adam ya kalli Yusuf yace, “a cikin abinda na fad’a da wanda likita ta fad’a in akwai k’arya a ciki Yusuf ka musa.” Shiru yayi ko motsi ya kasa kunyar duniya ta ishe shi ko d’ago kai ya kasa yi Yaya Adam ya sauke numfashi yana kallon kowa yace, "Abinda yasa duk nayi wannan bayanin Ina so azo gab’ar da nake so ne yadda kowa zai fahimci abinda nake so kuma ina da hujja akan hakan. Tunda har baya sonta kuma ta kasance b’arauniya ce, kai ko babu wannan dalilan da likita ta fad’a iya abinda na gani zama da Yusuf ba alkhairi bane balle kuma bayanin likitan sun fi wannan d’aga hankali." Yaya ya kalli Abbah yace, "Alhaji!." Abbah ya amsa yana kallon sa kafin yace, "matsayina na gatan Ameena kuma uba a wajan ta na yanke hukuncin bazata sake zaman aure da Yusuf ba itama ta bani goyan bayan hakan. Soyayyar da kuka nuna mata Allah ya saka muku da alkhair ya biya ku amma ku yi hak’uri Ameena ta gama zaman aure a gidan Yusuf." Abbah ya girgiza kai cikin gamsuwa yace, "wannan hukuncin da ka yanke shine daidai Adam, hakan da kayi shine abinda ko wanne uba ya kamata yayi, koda nine nima irin hakan zanyi akan ko waye.” Yaya yace, “Na gode da kuka fahimce ni” ya dawo da kallon sa ga Yusuf yace, “Yusuf ina jiran takardar sakin Ameena ka kawo min ita har gida kamar yadda kazo har gida ka karb’i auren ta. Sannan ina so ka sani badan iyayen ka da nake ganin girma da daraja ba da yanzu ba kaine a wajan nan a zaune ba, dan wallahi sai nayi maka hukuncin da ko a mafarki baka d’auka za’a yi maka irin sa ba, to kodan soyayyar da suke yiwa Ameena alfarmar su dole ta shafe ka shiyasa na kyale ka. amma ka tabbatar ka kawo min takardar saki domin nayi alqawarin ta gama zama dakai tunda baka sonta kamar yadda ka fada naji da kunne na kuma na gani a aikace a bayanin Dr.” Kowa yayi shiru babu mai magana su cikin su dan basu da bakin cewa komai hukuncin Adam daidai ne ko sune abinda zasu yi kenan. Ganin hakan ya saka Yaya Adam ya mik’e tsaye yace, "to Alhaji na barku lafiya, ni zan koma gida. Ayi hak’uri haka Allah ya kaddara auren nasu bazai yi wani tsaho sosai ba.” Abbah ne yayi k’arfin halin cewa, "Allah ya kiyaye Adam Allah ya bar zumunci. Kar ka damu abinda kayi shine daidai babu Wanda zai ga laifin ka a nan, Allah ya kiyaye.” Yayi murmushi yace, "Amin ya Allah, sai da safe" ya fad'a yana fita daga falon duk suka bishi da kallo har ya b’ace daga idanun su kafin su dawo da kallon su ga Yusuf. #Mai daki #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema Book2 024 Yusuf ya kasa d’ago kansa idanun sa a kulle gabad’aya kunyar had’a ido yake da kowa a ciki falon musamman ma Ammah da yake jin sautin kukan ta hakan ya saka shi kasa ko motsi ya kuma kasa kallon kowa balle ya iya magana. Kusan mintina biyar yana a haka ya kuma ji shiru babu wanda yayi magana a cikin su dan shi shirin ayi masa fad’a yake amma yaji tsittt babu wanda ya furta hakan ya saka shi d’ago kai ya kalli falon amma sai yaga babu kowa saura shi kad’ai ya rage a zaune duk basa wajan. Numfashi ya sauke zuciyar sa na harbawa da sauri ya dafe kansa ya rasa abinda yake masa dad’i, zuciyar sa a cushe take ya rasa abinda yake damun sa, bai san lokacin da ya kwashe a wajan ba yana nan zaune sai jin muryar Mubakar k’anin sa yayi yana cewa, “Yusuf zan kulle k’ofar.” Sai a sannan ya d’ago ya kalle shi sai ya mik’e ya fita jiki a sanyaye. Kuka Ammah take yi sosai kamar k’aramar yarinya haka Humaira ma Yayan Abuja ce kawai take daurewa tana rarrashin Ammah amma abin yaci tura kuka take yi sosai dan abinda aka fad’a a wajan ya karya mata zuciya sosai. Har take ji a zuciyar ta tamkar harda saka hannun ta wajan cutar da Ameena. Yayan Abuja tace, “Dan girman Allah Ammah ki daina wannan kukan, Kiyi hak’uri.” Ammah tayi shiru da kukan ta kalle ta tace, “baki ji abinda akace Yusuf yana yiwa marainiyar yarinyar nan ba? Duk abinda aka fad’a Baki ji bane?.” “Naji Ammah, amma wannan kukan ai ba shine mafita ba, ke kanki ciwo zai saka miki tunda ba magani zai miki ba.” “Yarinya ya sakawa hawan jini, ko yaushe cikin damuwa take in ka tambaya sai tace babu komai. Ina Yusuf zai kai hakkin yarinyar nan?.” Humaira da take gefe Tce, “Ammah harda dukan ta wai yake yi, gaskiya sai Allah ya saka mata sai yayi dana sanin da baiyi tunani ba a rayuwar sa. Ban san halin wa Yaya Yusuf yayi ba wallahi.” Ammah ta girgiza kai tace, “Bari kawai, ina tausayawa Yusuf akan hakkin yarinyar nan ganin da yake kamar wasa.” Yaya tace, “Wallahi komai ya aikata sai yayi dana sani, kuma nima bana goyan bayan cigaba da zaman auren su tunda baya son ta ya sake ta ya zauna da wacce yake so shikenan ya huta shima.” Ammah tace, “Dan tsabar k’arya da rashin tsoron Allah wai ni nace ya aure ta shi ba sonta yake yi, Allah kad’ai yasan abubuwan da yake k’unsawa yarinyar nan shiyasa kullum take a rame kamar ba’a cikin jin dad’in take ba. Wai ni nace yaje ya aure ta, an ina nasan Ameena in badan yazo da maganar ta gidan nan ba?.” Yaya tace, “shi ya sani kuma ai, yayi asarar da bazai tab’a mayar da ita ba har abada. Ni abinda yafi bani haushi wai sata! Yanzu Ammah dan Allah in Ameena tana sata tun auren su ai mu ma baza mu tsira ba.” Humaira tace, “Amaryar da yake rawar kai a kanta wallahi itace mai sace-sacen, daga zuwan ta gidan nan ta zauna a d’akina ta d’auke min agogo da kuma yarin kunnen nawa.” Yaya ta wara ido tace, “Kice wallahi?.” “Wallahi da gaske nake, a cikin jakar ta duk na d’auko da taga na gane sai ta basar kamar ba itace ta d’auka ba. Yadda ta basar din nan zaki tabbatar cikakkiyar b’arauniya ce. Wallahi Yaya Yusuf ya d’auki abinda yafi k’arfin sa.” Ammah tayi shiru tana jin su kafin tace, “Yanzu da Ameena ta fara neman maza dan Allah me gari ya waya?.” Yaya tace, “Nima shin yafi d’aga min hankali Ammah, yarinya k’arama yana kokarin jefa ta cikin halaka. Ai wallahi Yusuf ya kikayi hakkin ta da zai bibiye shi nan gaba, ko bani da rai zaku ce masa na fad’a muku.” Shiru dukkan su sukayi kowa yana tuna abinda aka fad’a suna sake tausayin Ameena tare da jin haushin Yusuf matuk’a a zuciyar su. A haka Yusuf ya koma gida ya shiga b’angaren Asiya ya same shi gashi nan dai kamar kullum ba gyara balle khamshi bai bi ta kai ba ya wuce sama ya shiga d’akin sa ya zauna tare da dafe kai da duka hannayen sa guda biyun. Abubuwan da suka faru ne suka masa yawo a cikin kansa shi Kansa ganin abun yake kamar wasa kamar kuma bai faru ba, sai a sannan ya tuna da cewa tabbas Ameena zata iya cutuwa ta b’angaren k’in sauraren ta da yake yi amma a kwanakin baya bai kawo hakan ba ko kusa a zuciyar sa tunda ya neme ta tak’i zuwa shikenan ya watsar da lamarin ta a gefe. In zai iya turawa rabon sa da ita tun ranar da yayi mata yawo taje ta samu Amma akan maganar auren sa bai sake waiwayar ta ba. A bayyane yace, “kusan wata biyar kenan ko wata hud’u?.” Ya cize baki yace, “ya salam!.” Ya sake dafe kansa cikin rashin sanin ma abinda zaiyi dan abin damun sa yake a zuciyar sa kamar mutum abu na damun sa a cikin sa haka yake jin abun na yawo a zuciyar sa . Bud’e k’ofar akayi aka shigo yasan Asiya ce hakan ya saka bai d’ago kansa ba ta zauna kusa dashi tace, “My love lafiya kake?.” Bai kula ta ba ta sake cewa, “My love magana nake fa, lafiya kake?” Ta fad’a tana dafa kafad’ar sa. “Bana son hayaniya ki kyale ni” ya fad’a a hankali batare da ya kalle ta ba. “Taya zan kyale ka bayan naga ba daidai kake ba?.” “Ki kyale ni nace.” “Nidai A’a, tun d’azu nake jiran ka ko bacci banyi ba kace kuna na kyale ka?.” “Asiya ki kyale ni nace!” Ya fad’a da k’arfi yana janye hannun ta daga jikin sa yana nuna mata hanyar fita. Sai da ta tsorata ganin yadda ya canja idanun sa sun yi ja hana yi mata tsawa, kallon sa take yi da mamakin tsawar da yake mata ta bi hanyar k’ofar ta fita a ranta tana tabbatar da dole ma ta sake d’aukar mataki domin ita ya kamata tayi masa tsawa ba shine zai mata tsawa ba. Washe gari. Yaya suna tare da Ameena ta saka ta a gaba suna karyawa tare tana jan ta da hira jefi-jefi ta kan amsa wani abun kuma sai dai tayi dariya kawai bata cewa komai ba. Yaya ta zuba mata ido bayan sun gama cin abincin tace, “Ameena Yaya yace kin bada goyan bayan Yusuf ya sake ki, da gaske ne har zuciyar ki?.” Ameena tayi murmushi gaban ta ya fad’i sosai zuciyar ta na harbawa a guje amma baya nuna hakan ba tace, “Haka ne.” Yaya tace, “jiya yaje gidan su ya zayyana musu komai da yake faruwa ya kuma tabbatar da Yusuf sai ya sake ki, kin san Yaya Adam bazai sake bari ki zauna sa Yusuf ba gaskiya.” “Nima bana fatan sake zama dashi” ta fad’a tana juya cokali a ciki shayi ba tare da ta kalli Yayan ba. Yaya daya dafa ta tace, “Nima bana goyan baya Ameena, rabuwar ki da Yusuf shine yafi alkhairi a ganina .” Ameena tace, “shine ma alkhairi Yaya kuma hakan za’ayi” ta fad’a tana kallon Yayan tana murmushi. Kallon ta kawai take yi tana so ta gane yanayin ta amma ta gaza gane hakan a yadda take magana baza kace Ameenah da ta taso Yusuf bace ba a lokacin baya. Yaya tace, “Har zuciyar ki kuma Ameena?.” Tayi murmushi yace, “Yaya sanin baya kika yi min, duk abinda kike tunani yanzu babu shi.” Ameena ta kalli Zaytun da take ta wasan ta tace, “kayan ta sun k’are ma ba’a d’auko mata da yawa ba.” “Ina Amira tazo yanzu na saka a kaita ta d’auko mata” Yaya Adam ya fad’a yana shigowa ciki yana kallon su. Ya sake cewa, “ba kina da mota ba?.” Ta d’aga kai alamun eh yace, “Za’a d’auko ta yanzu ai Amira tasan inda key din yake ko?.” Nan ma d’aga kai tayi yace, “Duk wani abu da kika san kina so na amfani ta dauko miki shi yanzu, sauran kayan kuma in ya kawo takardar sakin sai aje a d’auko komai da yake mallarkin ki.” Ameena tace, “To Yaya.” “Kin sha magani?.” “Eh yanzu na sha.” “Yayi kyau” ya fad’a yana juyowa ya fita. Yaya ta bishi da kallo tace, “Gatan mu gaba da baya kenan, bamu da wanda yafi Yaya Adam. Badan shi ba da yanzu ba’a san halin da kike ciki ba.” Ameena tayi murmushi tana jin dad’i a wani bangare na zuciyar ta domin kuwa ya karb’a mata y’ancin ta. Kai ta girgiza kawai bata ce komai ta kasa fassara a wanne yanayin zuciyar ta take Karb’ar sakin da ake ta ambata. *Bayan kwana biyu.* Rukayya tana zaune a d’aki hannun ta rik’e da waya tana dannawa Umma ta shigo ta k’araso inda take zaune tace, “ke Rukayya wai har yanzu Umar d’in bai kuma kiran ki ba?.” Rukayya tace, “Eh Umma, tun bayan nan dai bai sake kira na ba gaskiya.” “Rukayya ko dai wani abun kika fad’a masa da ya saka ya fasa auren ki? Yaro mai hankali da Kamala ke kanki kin shaida hakan kin ce zaki iya auren sa amma ya d’auke kafa ba waya baya kuma zuwa?.” “Wallahi Umma babu abinda nace masa ban San dalilin Hakan ba.” “To Allah yasa ba guduwa yayi ba, ya Allah ka yanke wa yarinyar nan ta tashi ya bar gidan nan kafin azumin Ramadan ya sake dawowa, Allah kana ji kama gani” Umma ta fad’a tana d’aga hannu sama. A zuciyar Rukayya ta asma da amin da ita kanta rashin waiwaiyar ta da Umar din ya daina yi ya dame ta sosai, da shine kiran ta a waya duk da daman bai cika waya sosai ba saboda yana da aure amma yana yi mata message wanda zai saka taji dad’i amma yanzu gabad’aya ya daina bata san dalilin hakan ba. Umma ta sake kallon ta tace, “kuma ke kin kira shi?.” Rukayya tace, “eh na Kira Umma amma bana samun sa a waya.” Umma tayi Ajiyar zuciya kawai ta fita babban burin ta Allah yasa dai Umar ba guduwa yayi ba dan yadda Baba yake fad’ar nagartar sa tayi mata sha’awar auren sa sosai. A bangaren Ibrahim tunda Hajiya tayi masa maganar Rukayya shikenan ya kasa cire maganar daga zuciyar sa abu kamar tsafi, ko rufe idanun sa yayi fuskar ta zai gani sai yayi da gaske yake yakice tunanin ta yayi bacci. Gabad’aya ya rasa sukuni ya rasa abinda zai yi zuciyar sa na Karb’ar abinda Hajiya tace amma shi kuma yana so ya yacike abin dan gani yake kamar bazai yu ba. Ganin tunanin zai dame shi sai ya mik’awa Allah lamarin sa ya dinga addu’ar abinda yafi alkhairi Allah ya zaba masa amma duk da hakan bai daina tunanin Rukayya ba. Kamar ko yaushe da daddare mahaifin sa da mahaifiyar sa suna zaune a cikin hasken kwan fitila wanda yake amfani da hasken rana guda biyu shima yana zaune yana jira mahaifin sa ya gama cin abinci ya sanar dashi abinda yazo ya fad’a masa. Kallon sa Alhaji yayi yace, “Ibrahim fad’i abinda yake bakin ka.” Ibrahim yace, “Alhaji daman akan gidan ne, an siyi nawa kamar yadda na fad’a maka wanda ya siya ya k’ara mana kud’i a akai dan so yake a bashi ya rushe ya shigar dashi cikin ginın da yake yi da gaggawa. To yau ya bani kud’in naira million takwas ya siya, kuma kamar yadda ka sani yadda aka yiwa gidan kudi bai fi miliyan shida ba.” Ya ajjiye kudin a gaban Alhaji yace, “Akwai wani gida da akayi min talla a can gaban mu wajan Sani mainagge shi kuma miliyan shida amma bai kai nawa girma ba sai yafi nawa ginın zamani kuma location din sa yafi wancan kyau gaskiya. Mun gama magana da mak gidan nace ina so ni yake jira na saka kud’in ni kuma nace zanyi shawara da kai abinda kace shi za’a yi, amma su Yaya duk sun je dinga gidan sun ce kuma yayi a siya.” Alhaji yace, “to ka siya mana tunda yayyen ka sun ce yayi ai kamar mace ne Ibrahim, Allah ya sanya alkhairi ya cigaba da bud’e maka kofar alkhairi a rayuwar ka.” Ya amsa da amin kafin yace, “Naira miliyan shida tana cikin banki na ita zan sakawa mai gidan, wannan kuma ragowa ne nake neman shawarar abinda za’a yi da ita.” Alhaji yace, “kayi aure kawai Ibrahim.” Hajiya tace, “shine magana, kayi aure tunda ka samu sabon gida ka saka amarya a ciki.” Ibrahim yayi murmushi yace, “Zanyi Alhaji, amma kafin nayi nafi a d’an juya kud’in, duba da hidimar aure a yanzu za’a dauki lokaci ayi wannan ayi wancan kafin lokacin an juya wannan kudin sun zama wani abu, in Allah ya saka albarka sai kaga da riba za’a yi hidimar auren gabad’aya. Shine nake neman shawarar abinda za’a yi dasu.” Alhaji ya girgiza kai yace, “Wannan gaskiya ne Ibrahim, abinda zai faru ka ajjiye a hannun ka ko nace ka saka su a banki suma kafin ayi tunanin abinda za’ayi dasu. Kaima kamar mutum dah meye na tawo da kud’i tsirara haka Baka tsoron a biyo ka.” Hajiya tace, “ka kwashe kayan gidan maka ne yo?.” “Ni bani da kaya a gidan, kayan ciki na Fiddausi ne dan abu kad’an aka d’auka a gidan sauran duk suna nan ban san me zanyi dasu ba. Amma zan saka a kwashe a kai gidan su.” Hajiya tace, “to hakan yayi, Allah yayi albarka.” Ya amsa da amin nan yana jin dad’in albarkar nan da iyayen sa suke saka masa sosai. Alhaji yace, “ka samu wacce kake so din ne ko itama ba yanzu ba?.” Ibrahim yayi shiru kamar bazai yi magana ba kafin yace, “Eh na samu Alhaji.” Alhaji yayi murmushi yana kallon sa yace, “a ina take?.” D’agowa yayi ya kalli Hajiya kamar zaiyi magana sai ya fasa yace, “Hajiya zata yi maka bayanin ta Alhaji” tana fad’a ya tashi ya fita yana murmushi dan yana jiyo muryar Hajiya tana cewa, “ja’irin yaro da kace baka yi.” Sosai yake jin farin ciki a zuciyar yana ji a ransa lokacin da zai fara sabuwar rayuwa yayi. A washe garin ranar da yamma ibrahim yaje gidan su Rukayya a matsayin me neman auren ta, mahaifinta ya nuna farin cikin sa sosai ya kuma bashi lokacin da zai dawo su gaisa da ita Rukayya din amma kafin nan yace ya bashi lokaci. Bayan tafiyar sa bai tsaya sanya ba kai tsaye gidan su Fiddausi yaje ya nemi ganin mahaifin Fiddausi dan su tattauna a kan maganar Ibrahim. Koda aka fad’a mahaifin Fiddausi ga mahaifin Rukayya yana neman sa ai ba tsaya ya karasa abinda yake yi ba ya fito dan su gaisa. Iso ya yiwa Baba har d’aki suka zauna Abba yace, “Alhaji Khasim ya gida ya kuma iyalai?.” Baba yace, “wallahi Alhamdulillah kowa da kowa lafiya lau.” Abba yace, “ma sha Allah, amma dai Lafiya ko?.” Baba yace, “Lafiya zance, batu ne akan auren Rukayya cikin ikon Allah lokaci d’aya Allah ya fito mata da mazajen aure guda biyu.” Abba yace, “ma sha Allah, Kaji lokacin da ake jira yazo kenan ko?. Su waye an ina suke?.” “D’aya dai sunan sa Umar a nan k’ofar nasarawa iyayen sa suke shima a nan yake da aure, yana da mata da yara. Kwana biyu ma muka ji shi shiru mun d’auka ko ya fasa ne ashe tafiya yayi aka sace wayar sa gabad’aya shiyasa ba’a jin sa sai da ya dawo ya sake sabon layi d’azu yake sanar dani. Na yaba da hankalin sa sosai dan ban bashi damar ganin Rukayya ba sai da nayi bincike a kansa sosai ma kuwa, ta b’angaren halayya da gidan sa babu wata damuwa.” Abbah yace, “to Alhamdulillah, wannan shine fatan da muke yi ai. Ba kud’i muke nema ba mu Jin dad’i da kwanciyar hankali, Na biyun fa?.” “Na biyun yanzu yazo ya same ni muna rabuwa nazo wajan ka.” “Waye shi Alhaji Khasim?.” “Ibrahim tsohon mijin Fiddausi.” Abba ya girgiza kai cike da mamaki yace, “Ibrahim dai wanda suka rabu da y’ar wajena Fiddausi?.” Baba yace, “shifa, ban bashi lokacin ganin ta ba ya kawo kansa ne matsayin me neman auren ta abinda ya saka ban ce ya ganta ba saboda alaqar dake tsakanin Fiddausi da Rukayya, sannan kuma meye ya raba auren sa da Fiddausi har da zai zo sake neman aure?.” Abba yayi murmushi cikin jin dad’i yace, “Wato Allah gwanin hikima ne, duk yadda ka kai ga k’aguwa akan abu baka isa kayi ba sai lokacin ka yayi, sai lokacin da ya tsara maka yayi sannan abinda ka jima kana jira zai zo ko baka shirya ba, in kuma kana addu’a sai ya baka abinda baka yi tunanin sa ba. Wato Alhaji Khasim inda zaka amince dani da nace kar ka aurawa kowa Rukayya indai ba Ibrahim ba.” Baba yace, “Ibrahim din?.” “Shi fa, domin kuwa in ka bari irin su Ibrahim ya sub’ucewa Rukayya kafin ta samu kamar sa Wallahi Allah za’a jima domin basu da yawa a duniya. Batun alaqar su da Fiddausi wannan ka ajjiye ta a gefe in ma lokacin da Fiddausi take gidan sa ne ai ba aibu bane dan ya aure ta balle basa tare, maganar mutuwar auren sa da Fiddausi kuma komai ya faru Fiddausi ce fa jawo wallahi, duk abinda ta fad’a mana a kansa k’arya take yi na samu labarin komai a inda bata yi zaton zan ji ba. Tun tana gidan mijin ta yake tare da wanda ta aura a yanzu yake wure mata kunne in ta fito daga gidsn mijin ta zai aure ta a haka har ta kashe auren.” “Daman kuma Fiddausi y’ata ce amma hakan bazai hana ni fadar gaskiya ba, akwai son kudi da son rayuwar kudi wannan dalilin ya saka bata ganin alkhairin Ibrahim komai yayi ba burge ta ba. Ta kashe auren taje ta auri wanda ko cikakken bincike Kawun ta baiyi ba saboda shima irin tane ya cika masa aljihu da kud’i shi kuma ya bashi ita dan anga bana k’asar a lokacin. Ina baka shawara Alhaji Khamsin indai har Rukayya na son Ibrahim kar ka sake ya kubce maka, domin addu’ar da ka jima kana yiwa Rukayya na neman miji na gari Allah ya amsa ya bata miji nagartacce kamar Ibrahim.” Baba yayi murmushi cikin farin cikin da ya mamaye masa zuciya yace, “amma na jima banji abinda yayi min dad’i kamar wannan ba wallahi, ni da yazo daman mamaki ne ya hana ni yin komai nace yaje zan neme shi sai naji ta bakin ka yanzu da muka tattauna ji nake an cire min duk wata fargaba a akan sa walalhi.” “Baza kayi farin ciki bama sai ka bashi ita, mutum ne da ya da sa girman iyalan sa sosai, in kaji fad’i tashin da yake yi akan Fiddausi wallahi sai ya baka mamaki sai kaji meyasa ma ta yarda ta rabu dashi. Tunda suke ina jin auren su shekara shida ne ko biyar bai tab’a kawo min k’arar ta b wallahi, itama bata tab’a zuwa tace ga damuwar sa ba sai da aka fara wure mata kunne shaidan yana taya ta, yayyen ta Sune suke auren masu kud’i amma wallahi ta fisu kwanciyar hankali, rashin gode Allah ne irin nata ya saka ta kashe auren. Alhaji Khasim ka bashi ita indai zata iya zama dashi tana son sa zance ya k’are.” Baba yace, “abinda nake tunani kenan nima amya zata amince ta auri tsohon mijin Fiddausi? Akwai amince tsakanin su kasan mata yanzu sai ace anci amana.” Abba yace, “Addu’a kawai zamuyi Allah yasa shine mijin ta dan alkhairin da muke nema mata fa Ibrahim ne.” Baba sosai ya gamsu da bayanin Abba yace, “na gamsu da bayanin ka sosai Alhaji, Allah ya saka da alkhairi ya kuma bar zumunci.” Abba ya amsa da Amin yace, “In komai ya daidai a sanar dani mu fara shirye-shirye abu ne tuwo na kuma mai na, wallahi abun nan yayi min dad’i fiye da tunanin ka.” Mik’ewa Baba yayi yace, “nima kalaman ka sun wanke min dukka tantama ta akan Ibrahim, badan bana son ce mata jeki ga zab’ina ba wallahi da nace jeki ga Ibrahim, to na fiso na bata zab’in ta itama.” Tare suka fito har k’ofar gida suna sake tattaunawa akan lamarin kafin Baba ya tafi yana fatan Allah yasa Rukayya ta amince da auren Ibrahim. #Mai daki #Book2 #Paid #500 #Nana Haleema. Book2 025 Baba yana komawa gida ya samu Rukayya a tsakar gida tana wanke hijjabi ta juyawa k’ofa baya ya kalle ta da murmushi a zuciyar da yana fad’in, _in sha Allah k’arshen zaman ki a gida yazo Rukayya, kema ki tafi gidan mijin ki kije ki huta ki yi rayuwar aure kamar kowa. In sha Allah lokacin yazo abinda ake jira tsahon shekaru yazo.” juyowa Rukayya tayi taga Baba a tsaye yana kallon ta sai murmushi yake yi sai ta sha jinin jikin ta itama tayi murmushi tace, “Baba Sannu da zuwa.” “Yauwa Rukayya, in kin shiga ciki ki kiran min Umman ku.” Ta amsa da to ta shiga ta fad’awa Umma sannan ta fito ta cigaba da abinda take yi. Tana tsaye Umma ta fito ta shiga d’akin Baba ta zauna tace, “Rukayya tace nazo.” Baba yace, “eh, abin alkhairi ne ya sake tunkaro mu.” Umma tace, “to me ya faru?.” “Wani ne yazo ya sake samu na Tana neman auren y’ar ki.” “Rukayya!” Ta fad’a tana wara idanu tare da dafe kirji cikin farin ciki. Baba yayi murmushi yace, “ita fa, ga kuma Umar ya dawo da k’arfin sa zancen aure yake so ayi a wuce wajan da gaggawa.” Umma tace, “Alhamdulillah! Allah maji rok’on bawa. Rukayya ta dai itace maza biyu suka fito neman auren ta da gaske ba wasa ba?.” “Wallahi fa, lokacin yayi ne shiyasa.” “Waye shi na biyun da yanzu zo Alhaji?.” Baba yace, “Ai kin San shi ma, Ibrahim ne tsohon mijin k’awar ta Fiddausi.” Sak Umma tayi tana kallon Baba da mamaki kafin tace, “Wai da gaske kake? Ibrahim dai mijin k’awar ta Fiddausi da ya saki kwanakin baya?.” Baba yace, “shifa.” “İkon Allah! Shi kuwa ya kasa rik’e fiddausi har ya sake ta yanzu sai ya biyo yace Rukayya yake so? Kuma ya manta Rukayya da Fiddausi aminai ne sosai ko ka manta ne?.” Baba yayi murmushi yace, “ban manta ba, hasalima ni farin ciki nake yi sosai da hakan dan wallahi in Rukayya ta aure shi zan fi kowa murna.” Umma tace, “Meyasa kake farin ciki?.” “Bayan tafiyar shi Ibrahim din ai wajan mahaifin Fiddausin naje, ashe yarinyar Fiddausi itace ta kashe auren da kanta komai ya faru itace ta jawo ya sake ta. A takaice dai mahaifin ta ya bada goyan baya akan auren Rukayya da Ibrahim, ya tabbatar min da nagartar Ibrahim fiye da wacce naji akan Umar hakan ya saka naji na amince da auren da d’ari bisa dari, wallahi a yanzu nafi son ta aure shi akan Umar din.” Umma ta girgiza kai tace, “Amma ni sai nake gani kamar za’a lalata zumuncin su ne, ko da yake ba mijinta bane a yanzu ai.” Baba yace, “kawai kiyi mata addu’a wanda ya kasance alkhairi a cikin su Allah ya bata, amma zuciyata a yanzu tafi son Ibrahim.” Umma tayi murmushi tace, “in ma Ibrahim din ne daman burina ta samu na gari kuma an tabbatar da dukkan su na gari ne kaga ai Alhamdulillah.” Baba yace, “nima shine fatana a koda yaushe Gashi Allah ha amsa lokaci yana zuwa kamar wasa. Tashi kije nima zan fita yanzu.” Umma ta tashi ta fita zuwa cikin gida taga Rukayya bata tsakar gidan ta shiga d’aki a nan ta ganta tana kwashe kayan Umman tana zubawa a cikin wardrobe. Umma ta bita da kallo tace, “Rukayya ajjiye kayan nan kizo” ta fad’a tana zama tare da kallon ta. Ajjiye kayan tayi ta tawo kusa da Umman ta zauna Umma ta kalle ta tace, “Kin San waye ya samu mahaifin ku akan yana neman auren ki?.” Rukayya ta girgiza kai alamun A’a amma buri kawai take taji waye a zuciyar ta, Umma tace, “tsohon mijin k’awar ki Ibrahim.” Gaban Rukayya ya fad’i bata san ta mik’e tsaye ba tana kallon Umma tace, “Ibrahim kuma Umma?.” Umma ta kalle ta tace, “dawo ki zauna.” Ba musu ta zauna umma tace, “Eh Ibrahim, sai me dan shine ya nemi auren ki?.” “Umma Ibrahim fa mijin Fidy, yaushe ma suka rabu da Fiddausin da zai zo yace yana sona?” Ta fad’a dan son ta tabbatar dan badan Umman bace bama bazata amince ba d’auka zatayi tsokanar ta ake yi. Umma tace, “Bai jima da barin wajan mahaifin ki ba ya kuma tabbatar da auren ki zaiyi.” “Na shiga uku! Yanzu Umma kuma mai Baba yace masa?.” Umma ta bita da kallo tace, “meye na shiga uku a nan?.” “Umma mijin Fiddausi fa, Fiddausi tawa dai da kika sani mijin tane fa.” “Tsohon mijin ta dai ba mijin ta ba” Umma ta bata amsa tana karantar yanayin kan fuskar ta ta. Rukayya ta kalli Umma kamar zatayi magana sai ta fasa amma kirjin ta bugawa yake yi cikin tsoro da mamaki had’i da al’ajabin abun. Umma tace, “Mahaifin ki ya amince dashi sosai dan zan iya ce miki yadda ya amince dashi ko da Umar din bai amince ba, kawai dai yana so ki zab’i wanda zaki zauna dashi ne da kanki amma in a a ra’ayin sane yafi son Ibrahim dan sun tattauna da mahaifin Fiddausi a d’azu.” Rukayya bata ce komai ba tayi shiru gabad’aya jikin ta yayi sanyi tuna maganar Fiddausi kawai take yi tana tsoron kar fa bakin Fiddausi ne ya kamata har aka zo wannan gab’ar ba tare da ta shiryawa hakan ba. Umma ta sake cewa, “abinda yake gaban ki kawai addu’a ce cikin su biyun wanda ya kasance alkhairi Allah ya zab’a miki, amma a cikin su bana son kice bakya son kowa Rukayya baki tab’a samun masu nagartar Umar da Ibrahim ba dan haka dan Allah ku tsayar da hankalin ki waje d’aya ki zab’a a cikin su hankalin kowa ya kwanta. Rukayya gabad’aya ba jin ta take yi ba hankalin ta ya tafi wani waje tana kuma bukatar shawara da k’awayen ta guda uku amma ta ina zata fara fad’a musu wannan maganar? Anya babu cin amana a lamarin? Anya babu yaudara a cikin wannan abun da yake k’ok’arin faruwa?. Abinda ake fad’a Ana dariya gashi yanzu yana so ya zama gaske. Tab’a ta Umma tayi hakan ya saka ta dawo daga tunanin ta kalli Umma tace, “in sha Allah Umma zanyi addu’a, ko ina alkhairi yake Allah ya had’a ni dashi.” Umma tace, “Allah yasa” ta fad’a tana tashi ta fita ta barta tana hasaso fuskar Ibrahim sai gaban ta ya yanke ya fad’i. A haka itama ta tashi ta shiga d’aki jikin ta a mace gabadaya, Umar ko Ibrahim?. A b’angaren Yusuf tun bayan da akayi maganar a gidan su babu wanda ya sake yi masa maganar kowa ya share shi ya kuma zuba masa ido yaga iyakacin gudun ruwan sa, ko gidan yaje sai dai a gaisa kawai amma babu wani mai sakewa dashi ayi hira kowa ya d’aure masa fuska. Ammah kuwa a ciki take amsa gaisuwar sa daga nan babu wata magana da zata sake yi masa. Yana cikin tuk’in mota yaji k’arar shigowa sak’o a wayar sa bai duba ba sai da ya shiga gida ya faka motar ya fito sannan ya dauki wayar sa yana dubawa, sunan Adam ya gani yayan Ameena nan take gaban ya fad’i ya kulle ido ya furzar da iska daga bakin sa sannan ya bud’e Idon hannun da yana rawa ya bud’eSakon yaga abinda ya rubuto kamar haka, _Yusuf banda darajar iyayen ka da yanzu na d’auki mataki a kanka, nayi shiru kai kuma naga baka San shiru ba, to ka gaggauta kawowa Ameena takardar sakin ta in kuma ba haka ba ka kuka da kanka duk abinda nayi maka._ Yana gama karantawa ya sauke numfashi kansa ya sara yayi saurin dafewa, ya rasa meyasa yanzu inda za’a ambaci Ameena sai gaban da ya fad’i kansa kuma ya sara, ko kuma yaji kamar Ana tafasa masa jinin sa hakan ya saka baya so a ambace ta a gaban da gabadaya jinyar wucin gadi yake tafiya in hakan ta faru sai dai ya daure kawai. Cikin gidan ya shiga ya samu Asiya a falo a zaune ta d’ora k’afa kan d’aya cikin shigar da ta saba, zani da kuma riga mai karamin hannu sai kuma dankwalin da bai yi Kala da zanin jikin ta ba. Falon kaca-kaca taci abinci ta bar kwanon a wajan ga kofi ga robar ruwa duk a wajan tana kuma zaune tana kad’a kafa ba tare da hakan ya dame ta ba. Bai zauna ba ya wuce sama kawai ganin hakan sai ta d’auki waya ta saka a kunne kafin tace, “ya shigo Yanzun nan amma baiyi min magana ba.” Shiru tayi alamun ana bata amsa kafin ta sake cewa, “nifa so nake nayi masa tsawa kamar yadda yake min, duk abinda nake so shi nake so yayi burina bai wuce ya saki waccan matar tasa ba.” Sake yin shiru tayi alamun ana bata amsa kafin tace, “bara naje yanzu.” Katse kiran wayar tayi ta mik’e tabi bayan sa ta same shi a zaune a gefen gado ya dafe kai har ta shiga bai sani ba ta k’arasa inda yake tace, “My love me yake damun ka haka?.” D’agowa yayi ya kalle ta yace, “Meyasa in na ajjiye kud’i a dak’in nan bana ganin su? Ina suke zuwa?.” K’are masa kallo take yi kafin tace, “kenan kana so kace sata nake maka ko me?B’arauniya ce ni?.” Jin yadda ta tambaya sai ya samu kansa da kasa bata amsa yace, “A’a ba haka ba, kawai dai ban San inda nake kai su bane shiyasa.” Murmushi tayi jin abinda yace sai ta zauna tace, “watakila baka shigowa dasu ne shiyasa. Me yake damun ka?.” “Nima ban sani ba, amma Ina kina kamar ba ni bane.” “Kaine, dalilin jin ka a haka saboda baka saki Ameena bane da ka sake ta shikenan an wuce wajan.” Ya sake dafe kansa yace, “ban san meyasa bana so naji sunan ta a kusa dani ba, zuciyarta tana son taji sunan amma kuka kunnena baya son yaji an ambaci sunan ta.” Asiya tace, “kawai ka sake ta, in ka sake ta zaka daina jin abinda kake ji.” Dan ja baya yayi dan bakin ta da jikin ta gabad’aya wari yake yi amma baya so ya furta dan kar ranta ya b’aci. Tashi tayi ta d’auko ‘karamin jotter na store din sa da biro tace, “ka rubuta ka sake ta kawai ka huta.” Kallon takardar yake yi sai ya mik’e tsaye yana girgiza kai yace, “bazan iya sakin ta ba, ki kyale ni” yana fad’aya fita ya barta a tsaye a wajan tana kallon sa cikin tsoro. Sauka yayi daga gidan gabad’aya zai shiga b’angaren Ameena yaji ana yi masa waya ganin sunan mahaifin sa sai ya d’auka ya kasa a kunne sai kuma ya fasa shiga gidan ya koma saman Asiya ya samu bata d’akin ya d’auko key din mota ya sauka ya fita shiga ya nufi gidan nasu. A falo ya samu mahaifin nasa shida Ammah a zaune ya shiga da sallama ya zauna Abbah ya kalle shi sai ya kalli Ammah suka had’a ido ya sake kallon Yusuf din yace, “Masu karb’ar sample din nan ne suka zo, sark’ar tana nan ko kuma itace wacce kace Ameena ta sace maka?.” Yayi shiru ya runtse idanu yace, “in aka ambace ta Abbah ji nake kamar ana sara min kaina, zuciyata ta kuma ba haka nake ji ba.” Abbah ya kalli Ammah ya sake kallon sa yace, “Saboda tsanar da kayi mata har ta kai baka son a fad’i sunan ta ko?.” Shiru yayi ya sunkuyar da kansa k’asa Abbah ya kuma cewa, “ina tambayar ka, itace sark’ar ko ba ita bace?.” “Itace” ya furta ba tare da ya d’ago ba. Abbah yace, “Yaushe zaka kai mata takardar sakin ta? Kasan yayan ta badan mu ba da yanzu kana hannun hukuma ko?.” Yusuf yace, “na kasa aikata hakan ne Abbah” ya fad’a a sanyaye sosai kamar zaiyi kuka har Ammah ta kalle shi sai kuma ta d’auke kanta. Abbah yace, “Baka isa ba kuwa, Tunda Baka son ta sai ka sake ta, ga takardar da biro nan yanzu ka sake ta dan in y’ata ce nima wallahi ta gama zama dakai.” Yusuf ya kalli jotter din da Abbah ya nuna masa yaga sune a jiki shida ita ranar sunan Zaytun ya d’auke idanun sa yana sauke numfashi yace, “Abbah bazan iya sakin ta, ina ji a zuciya bazan iya hakan ma amma gangar jikina bata jin hakan. Abbah dan Allah kar kace na sake ta bazan iya ba” ya fad’a muryar sa na rawa sosai Abbah yayi murmushi yace, “Yusuf ai Baka isa ba, saki ya zamar maka dole kayi ko baka so.” Yusuf ya kulle ido ya bud’e zafin da yake ji a zuciyar sa har a idanun sa yaji yake ji dakyar yace, “ina so na fara magana da ita sannan…..” Abbah yace, “baza ka ganta ba, ka sake ta nace yanzu nan kaje ka zauna da amaryar ka tunda ita kake so. Kayi magana da ita kace mata me? Ka sake mata daman alfarmar babar ka take ci kake zaune da ita? Ko kuma ka sake d’ora mata ciwo?.” Yusuf yayi shiru bai ce komai ba Abbah yace, “da gaggawa rubuta sakin nan dan wallahi sai ka sake ta, tunda har ka iya kyale yarinya kamar ta ba tare da kana sauke hakkin da Allah ya d’ora maka ba dole ka rabu da ita.” Yusuf ya d’auki biron ya bud’e jotted din yana so ya rubuta amma zuciyar sa hana shi aikata hakan take yi. _Ameena fa Yusuf, Ameena ka da kake so kake qauna ita zaka saki? Ina zaka kai hakkin ta da yake kanta? Kenan kun rabu wani zata aura kenan ko me?. Zaka iya rayuwa babu ita kenan? Kana sonta fa meyasa zaka sake ta?._ Abinda Zuciyar sa take fad’a masa kenan sai yake ji kamar rad’a masa ake a kunnen sa bai san lokacin da ya runtse ido yace, “Wayyo Allah, bazan iya ba!.” sai ya ajjiye biron yace, “Abbah…..” Abbah ya dakatar dashi a fusace yace, “Tunda ka iya dukan ta, Tunda ka iya saka mata hawan jini, Tunda ka kasa sauke mata hakkin ta da yake kanka har ta kai ya kawo tana shan maganin da zata kare kanta daga fad’awa halaka, Tunda ka kira ta da b’arauniya, Tunda kace kai ba sonta kake ba Ammah ce ta saka ka auro ta wallahi sai ka sake ta Yusuf kaji kuma na rantse baza ka saka ni yin kaffara ba. In Humaira ce a matsayin ta hukuncin da zan yanke kenan itama kuma y’ata ce ya zama dole ka sake ta ko kana so ko baka so.” Jin Abbah ya rantse ya saka Yusuf hannu yana rawa ya fara rubutu akan takardar yana kuka a zuciyar sa kafin ya gama gumi ya gama wanke masa fuska duk ya d’iga a jikin takardar kamar wanda yake rubuta jarabawa mai tsauri. Abbah ya mik’awa ya karb’a ya karanta sannan ya mik’awa Ammah ma ta duba ya karb’a ya bawa Yusuf din yace, “kaje har gida ka kaiwa Yayan ta kamar yadda yace maka, Kaga yanzu mun zama shaida koda baka kai ba mun tabbatar da ka sake ta saki d’aya.” Shiru yayi bai magana ba bai kuma tashi ba dan ji yake in ya mik’e zai iya kifawa ga zuciyar sa da yake ji kamar zata fito daga k’irjin shiyasa ya kasa ko motsin kirki, Abbah yace, “tashi ka bani waje.” Dakyar ya tashi jiki a sanyaye ya fita kamar kazar fa kwai ya fashewa a ciki shi kad’ai yasan abinda yake ji a zuciyar sa. Ammah ta kalli Abbah tace, “Har abada bazai sake samun mata kamar Ameena ba, wannan kuma da yake yake da ita sai yayi dana sanin da bai tab’a yi ba a rayuwar sa, kokari take ta mallake shi sai taje ta mallake shi kad’ai dan ni walalhi bazan yi wani abu akan Yusuf ba, taje ga rike na bar mata” tana fad’a ta tashi ta bar wajan tana goge hawaye zuciyar ta nayi mata d’aci dan ji take kamar Humaira aka yiwa abinda aka yiwa Ameena. Abbah yayi murmushi yasan ciwo take ji a ranta dan tana son Ameena sosai tana kuma jin zafin abinda d’anta ya aikata mata, amma ya za’a yi hakan shine mafita zaman sa da Ameena cutarwa ne gwara ya sake ta kamar yadda Yayan ta ya nema, ya zauna da wacce yake so itama ta samu wanda yake sonta zai kula da ita ta zauna dashi amma Yusuf ya gaza barin sa da Ameena babbar illa ce. A bayyane Abbah yace, “ai tunda rashin sauke hakki ya shigo cikin maganar nan ta shafe komai, domin ko a addini zaman auren su akwai cutarwa a ciki, balle ga abubuwa Mara dad’i kamar ba ni na haife shi ba” sai kuma Abbah ya mik’e tsaye yace, “Ai ka haifa ne baka haifi hali ba, Allah yasa mu dace” ya fad’a yana shiga ciki a zuciyar sa yana jin yayi daidai ya aikata abinda ko mahaifin ta yana raye abinda zaiyi kenan. End of book2🫠 Naje Hutu🚶‍♂️ #Mai daki #Book2 #End #paid #Nana Haleema