SADAUKARWA Sadaukarwar littafin ta Iyayena ce, Alhaji Chindo Muhammad Sodangi da Hajiya Fatima Musa Sodangi, Ubangiji ya saka muku da alheri ya kuma kara muku lafiya amin. TUKUICI Tukuicin littafin naki ne; Khadija Chindo Sodangi (Mrs Nasiru Idiris) JINJINA Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya laifi (Maman Umar) Zuhuriyya Ibrahim (Mrs Lawal Chindo Sodangi), Ubangiji ya raya Umar da Imani. FATAN ALHERI GARE KU Fatima Abdulkadir Kazaure Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi 3 Khadija Usman Nasarawa Nafisatu Ibrahim Muhammad Fatima Ahmad Shehu Kaduna Maryam Muhammad Gusau, Zamfara Umaima Abubakar Umar Maijidda Uba Magaji Na gode, Ubangiji ya saka da alheri amin. KUNA RAINA Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassan Hajiya Jamila Ibrahim Na-Bature Hajiya A'isha Balarabe (Jazan) Ubangiji ya bar zumunci amin. 4 Littattafan SODANGI: Uwar Mijii Naga Ta Kaina Rabon Kwado.. Cikar Alkawari Wayyo Duniya Yi wa Wani.. Abu Naka... Mata Ma su Duniya Nufin Allah Kifi Na Ganinka... Daga Kin Gaskiya... Da Kamar Wuya.. Mai Uwa... Duk Daya.. Mata Da Kicin Dinsu Wacece Ni? Wata Fuskar... Mijin Ta ce Garin Banza.. Ga ni Gare ka 5 Biyan Bukatar Rai Shamaki Hattara Mata Masu Duniya Kyautata Ayi Dai Mu Gani... Tabbataccen Alamari In Kunne Yaji.. Halin Rayuwa Mai Daki. Littattafan ba sa nufin yi da wani ko habaici ga kowa sai dai an rubuta su ne don fadakarwa da nishadantarwa, ana neman afuwa ga duk wanda yaga wani abu yayi kamar abinda ya shafe shi, ba da shi ake ba dace ne kawai. 6 MAI DAKI.3 Bin ta da kallo suka yi cikin mamakin irin yadda ta dangwarar da kula, wannan kuma wacece? Ina dan murmushin da ban san na meye ba na ce, yarshi ce. Fu Suka hada baki Yarshi? Na ce, Eh, ita ce ta biyun tana da wa yana Makaranta Dankaci ke ki ce akwai babbar magana haka suke sakaka babu tarbiyya. Ban sake cemusu komai ba mikewa nayi na shiga kicin na debo plates da cokala na dawo sai ga Larai ta shigo dauke da wata kular da kato kular ruwa mai famfo alamar abin sha ne a ciki. Ta gaisa da su Baba Ladi sannan ta juya ta tafi. Na bude kular miya da taji naman kaji ta ukun kuwa kunun aya ne mai kauri. Na zuba musu na mika musu sannan nima na zuba naci sosai saboda yunwar da ke damuna. 7 Sai da muka gama cin abincin ne Baba Iya ta ce "To kai mu wurin uwar mijin taki mu gaisa ko 'yannan." Na mike suka bi ni. A bakin kofar dakin muka yi sallama ban shiga ba sai da ta ce a shiga. Karba sosai tayi musu sannan suka fara tattaunawa a kan al'amuran aure da halayya na ya'yan zamani na rashin kunya da fitsara har suka kawo kan danta tana basu labarin rasuwar da mahaifinshi yayi ya bar mata su tun bata fi shekaru talatin ba a duniya. Ya barta da Ahmad da Yayarshi Kausar da a yanzu take aure a Kano wurin dangin Babanta, da aure-auren da ya yi guda hudu mata biyu suka haifan mishi 'ya'yanshi Zaidu da Zainaba. Sai kuma wata ta haifi Ziradat da Zinatu, sai wasu biyu da ba su haihu ba. 8 A raina na ce, "Dankari! To me yasa bai taba gaya mun cewa ni ce matarshi ta biyar ba?" Na kawar da wannan tunanin daga cikin raina, ko bai gaya mun yawan matan da ya aura ba ai ya gaya mun yana da 'ya'ya hudu. Shi kenan magana ta kare. Hira sosai suka y1 sannan suka taso muka dawo sashena. Hajiya ce tasa aka mayar da su Baba Ladi gida bayan nayi musu kyaututtuka daga cikin kayan aurena. Kwalliya sosai na sake tsalawa da yamma shadda danya da aka yi wa wani irin dinki na Senegal ruwan kofi na saka, na saka dan kunne fashion ruwan zaren jikin shadar. Na feshe jikina da turaruka sannan na kunna bumer na saka na daki yabi gidan gaba daya. Karfe shida daidai naji tsayuwar mota a Wurina. 9 Na leka, Ahmad ne. Na dawo na zauna ina jiran naga shigowarshi ban ji ba, har aka yi magriba aka yi Isha'i sannan ya shigo dakin. Yana kallona ya ce "Wow! Allah na gode maka da kayi mun baiwa da samun Hauwa' u a matsayin mata ka bani zaman lafiya da ita ka albarkace mu da albarka da ka ke yi wa Ma'aurata. Murmushi na rinka yi har ya iso in da nake ya jani zuwa jikinshi ya rungume ni yana rada mun a kunnena ke baki iya yiwa mijinki oyoyo ba ne? Rike hannuna yayi ya jani zuwa wani wuri da ban kula da shi ba a gidan. Kofa ce ya budeta muka shiga. Babban wuri ne, don falon yafi nawa. Duk wani abu da ke falon faci ne tas tun daga kujeru har zuwa labule. Falon ya matukar kawatuwa ba kadan ba, bai bar ni a nan ba cikin dakinshi ya wuce da ni. Wanka za ki taya ni nayi." 10 Na gwalo ido ina kallonshi, ya ce "Ko ba za ki iya ba? Nayi shiru, murmushi yayi ya soma cire kayan jikinshi na kawar da kaina zuwa kallon wani wawakeken hoton da ke manne jikin bangon gadon shi na wani irin ruwa da ke zubowa daga wani tsauni zuwa wani dan koramai masu tsuntsaye. Kafin na juyo har ya shiga bayan gidan dakin. Mintuna kadan ya sake fitowa da tawul daure a kugunshi yana goge jikinshi da wani. Dauko mun kaya a cikin wardrop din gabanki. Na bude ina dubawa. An kakkasa kayan kashi-kashi, under wears, kayan barci, jallabiya da tract suit alama na babu kayan fita a wurin na ce wacce zan dauko maka? Ya zubo hannayenshi ta kwibina tare da dora kanshi a kan kafadata har ina 11 shakan kamshin man wankan da yayi amfani da shi da ke jikinshi. Ya ce, "Kamshin turarenki mai dadi Hauwa'u. Ban iya ce mishi komai ba don ban saba irin wannan mu'amallar ba. "Idan ba ki san wacce za ki ba ni ba, to bar shi haka mana kawai ba shi kenan ba, dama ai ba fita zan sake yi ba." Na jawo wata rigar barci da ke can sama saboda ya sassauta rikon da yayi mun, na ce "To ga wannan. Ya ce, "To juyo ki saka mun. "To ai saika sake ni tukuna zan iya saka makan.". Na juyo ina saka mishi rigar tun daga hannu har na daure mishi belt dinta. Yayi murmushi ya ce, "Hauwana kenan." A falon shi muka zauna yana kallonlabarai yana yi mun yan 12 hirarraki ya ce, "So nake na dan takura miki kadan." Na ce,"Wacce irin takura kuma?" Ya ce, To ban sani ba ko ba za ki ji dadin ta ba, so nake daga gobe na fara cin abinciki. Idan ki ka yi mun haka zan ji dadi." Nayi murmushi "Nima hakan yafi mun ai, kamar na gaya mishi haka sai na fasa. Ya ce, "Ba ki ce komai ba." Na ce,Yadda duk ka ke so haka zan yi." Ya ce, "To na gode." Washegari daga fitan shi sai ga cefane rigigif babu abinda babu, kaji, kifi, nama, tumatir, komai dai na bukatar gida. Wayata na dauka na kira shi na ce, "Za a yi na rana ne da za a kawò maka?' 13 Ya ce, "A'a Hauwa'u wannan Haj1ya tana sawa a kawo na dare kawai za ki yi." Na ce, "To me za ka ci da daddaren? Yayi shiru zuwa can ya ce, Na baki zabin yau dai kam ko meye ki ka yi zan ci." Tsayuwa nayi ina kallon cefanen da aka yi, na rasa yadda zan yi na fara tamfar wacce bata taba girki ba. Karaf na tuno da littafin Momin Hindu, shi na dauko na bude ina dubawa amma na kasa zaben abinda zan yi. Da kyar na iya zaben wani da na gani ina dubawa meat 'tagine' sunan ne ya yi mun dadi, har nake dubawa ganshi ba mai wahala sosai ba. 14 Sannan akwai kayan hadin gaba daya, yanayin yadda naga girkin a hoto. Na fara hada kayan amfanin nama, mangyada, yaji, tattasai, attarugu, albasa, tafarnuwa, gishiri, maggi, karas, citta, bawon lemon tsami, tumatirin gongoni da ruwa. Nan da nan na hada abubuwan na rangada miyata mai wani irin kyau da sha'awa. Na daukó ledar cous-cous na dafa saboda ganin da nayi da shi zai dace. Na kira Momin Hindu ina bata labarin abincin da nayi. Tayi murmushi ta ce, "To saura abin sha." Na ce, To ai ban san me zan yi na sha ba. A gajarce ta gaya mun. Ina gamawa na shiga bayan gida nayi wanka. 15 Yau ma kwalliya nayi ta materia ya kuma yi mun kyau sosai. Na yane jikina da babban gyale na dauki babban food flask din da na zubawa Hajiya abinci a ciki na dauka nayi sallama a bakin dakin na shiga, bayan an ba ni 1zinin shiga. Na ajiye abincin a gefe na zauna. Ta kalli food flask din ta ce "Ai ba sai kin rinka sako abinci ba don ba ci suke yi ba, sannan ga Larai nan idan muna bukatar abu zata rinka girkawa, mijinki kawai ban da mu." Na kai kamar mintina goma na tashi na dawo wajena, na kalli agogo har yanzu karfe shida bata yi ba. Na gyara kwanciyata a kan doguwar kujera na kunna TV ina kallon CCTV Documentry da ake yi akan wani kabarin tsohon Sarkin 16 Kasar Sin da ya mutu shekaru dari biyar da suka wuce. Yau ma Ahmad bai shigo ba sai bayan sallar Isha'i. A dakin shi na ajiye mishi abincin saboda wankan da yake yi. Ya fito yana goge jikinshi da tawul, ya samu na ciro mishi riga da wando na hutawa masu sauki. Ya dan yi murmushi yana kallona tare da amsa gaisuwar da nake yi mishi. Yasa hannu ya dauki kayan da na ajiye ishi akan gadon yana sakawa, ya gama ya riko hannuna. "Muje ki bani abinci." A kasa ya zauna a kan kafet yana duba wani sako da ya shigo wayarshi, ni kuma ina zuba mishi abinci a plate. 17 Na gama na tsiyaya mishi coconut juice din da nayi mishi na fara mika mishi. Ya karba ya dan yi murmushi ya ce, "Bismillah zan fara cin abincin amarya. Nayi murmushin jin abin da ya ce. Ya kai juice din bakinshi ya kwankwade ya ajiye kofin a kasa. Ya kalle ni na dauka madara ce, na ce a'a ba madara ba ce, ya ce To menene'? Na ce Juice din kwakwa ne." Ya sa cokali ya fara cin abincin gaba daya muka yi shiru sai da ya cinye abincin tas sannan ya ce, "To masallah Allahu, na gode Hauwa u. Allah ya yi miki albarka, ya kuma ba mu zaman lafiyamai dorewa. Abinci yayi kyau." 18 Nasa hannu na kwashe kwanukan na fitar na kai kicin, sannan na dawo na zauna. Ya fara magana, "Tunda ki ka zo ban samu wani lokaci na zaunar da ke don nayi miki magana dangane da al'amuran gidana ba. Amma duk da hakan dai nasan kin ga abinda ki ka gani na zahiri. Akwai mahaifiyata wacce idan kin lura za ki gane ba ni da wanda nake girmamawa nake kuma so fiye da ita. A rayuwata ita kadai ce na mallaka ina nufin mallakar da ban taba wayar gari na gane na rasata ba. Ina yi mata soyayyar da bana yiwa kowa shi a duniya Hauwa'u, don kuwa nasan itama tana yi mun fiye daa hakan. Babana ya rasu ne ya bar ni ban fi shckaru biyar ba a duniya, amma 19 kuruciyarta bai sa ta barni zuwa wani mijin ba. Sai ta zauna da ni da Yata don ta tarbiyyantar da mu, ta ilimantar da mu ta hakura ta sadaukar da jin dadin rayuwarta. Don haka duk wani abu da ki ka ga nayi a yau ko na zama a yau din nan to da bazarta ne. Ina rokonki daki taimake ni ki zauna lafiya da ita. Zan iya yin hakuri idan ki ka saba mun, amma ina da gajen hakuri ta fannin sabawa mahaifiyata. Sai abu na biyu, nasan kin ga yara to ina so ki san ko ni da nake ubansuu Hajiya bata yardar mun ta bani yancin shiga harkarsu ba. ldan kin ga wani abu da suka yi miki da bai yi miki dadi ba, to na roke ki da kiyi hakuri, idan kuma kin 20 ga ba za ki iya ba to ki jira ni na dawo ko menene a lokacin sai ki fada mun. Ina yi miki wannan maganar ne saboda ni nasan kan gidana, na kuma san matsalar da ke cikin shi. Ina so ki taimake ni na samu nutsuwar da nake bukata a cikin gidana." Na yarda da duk abubuwan da mijina ya gaya mun da kanshi ya kuma roke ni a kai ina kuma iyakacin kokarina wajen ganin na biya mishi bukatunshi. Gara nake shirya mishi kullum mai dadi, daga cikin littafin girkina a kullum kuma bai gajiya wajen yaba mun. Haka nan baya gajiya da yabon kwalliyata, don kuwa kullum a cikinta nake safe da yamma, matukar yana gidan. 21 lna son mijina ina kuma son zama da shi. Zama nake yi na yanci da walwala. A yanzu ne kuma na gane me ake nufi da zaman aure. Zama na hakika ba mai cike da kunci ba. Zama na sanin hakki da yancin dan Adam. A yanzu ne nasan so nasan abinda kalmar take nufi don abinda nake ji a game da Ahmad. Shima burinshi a kullum bai wuce na ganin ya faranta mun ba. Da matukar wuya ya dawo gida ba tare da ya riko mun wani abu ba, wanda zan yi amfani da shi don kaina ba don shi ko wani ba. Iyayena kuwa yana mutunta su tamfar nashi. To abinda nake so kenan na kuma samu, zan kuma jurewa zama da ya' yanshi da 22 mahaifiyarshi kamar yadda ya ce, don na tabbatar mishi matsayin shi a wurina. Watana biyu cif, Ahmad ya ce na shirya a kai ni gida wuni. Cikin doki ranar na kama shiri. Tsaraba sosai yayi mun wanda zan tafi dashi tamfar wacce take nesa. Nayi sallama a kofar dakin Hajiya na shiga a gefe na durkusa na gaya mata zuwana gida. Ta ce, Eh mijin naki yazo ya gaya mun. Allah ya kiyaye hanya, ki gaida manyan naki. Na fito na shiga mota. Bala direba ya tuka muka tafi. Babu wanda bai yi murna da ganina ba. Umma ta ce, "Haka fa Allah ke lamarinsa, ki duba ki gani wannan auren naki nutsuwarshi ma daban. " 23 Wajen karfe uku Ahmad ya kira ni a waya. Na dauka "Yaushe ki ke shirin zuwa gida ne? Na ce, "Ina ce wai ko za ka bari ne na yi sallar Magriba tukuna daidai lokacin dawowarka kenan." Ya ce, "To abincina fa? Ko zan zauna da yunwa ne yau tunda nayi karambanin yi miki gwaninta? Nayi maza na ce, "A'a yallabai mu tafi." Ban iya tsayawa jiran Babana ba na kama shiri. Tasi'u ne yake ta magana yana cewa, Zai bini yaje yaga gidana, Umma ta ce, Aa a wane dalili ka bari dai a kai ku wani lokacin." Ba tare da wata fargaba ba na ce a hada musukayansu shi da Sabi'u. Wurin Hajiya muka fara shiga, na gaisheta. Su Tasi'u ma haka, na mike 24 zan fito ta ce mun, "Zo mana. Na dawo na sake tsugunnawa ta ce, Su waye wadannan? Tana nuna su da baki, na ce Kannena ne. ziradat ta leko daga cikin dakinsu ta kalli su Tasi'u ta ce, Wai! Sannan ta kwashe da dariya. Ta ce, Lallai kuwa. Na tashi bayan ta bani umarnin tafiya, na dawo sashena amma ina jin wani abu a raina maras dadi. Muka shigo falona sannan na kara bin yaran da kallo wadanda tuni suka bi lafiyar kujera suka zauna. Ni nasan mu ba masu kudi ba ne. Amma daidai gwargwado Umma tana iyakacin tawajen ganin ta tsaftace danta babu kazanta a tare da shi. 25 Tsarguwar da nayi ita ce tasa na leka na kira Bala direba na ba shi kudi na ce ya sayo mun kaya daidai nasu Tasi'u set bibbiyu wadanda zan yi musu amfani da shi. Aikina na fara yi gadan-gadan saboda kada na makara. Abinci mai kyau sosai nayi mishi. Sai da na gama sannan nayi wa su Tasi'u wanka na saka musu sababbin kayansu nima nayi wankan nayi alwala, sannan nayi kwalliyata. Ka'idar Ahmad shi ne, yana dawowa zai shiga wurin Mahaifiyarshi, idan aka yi sallar Magriba ya dawo zai shiga suyi hira. Daga sallar Isha'i ne zai shigo wajena, don haka yau ma hakan ya yi. Yana ganin su Tasi'u ya sai murmushi. 26 "A'a'a, ke ki ce yau muna da manyan baki a gidan nan, amma ba ki sanar dani ba, ai da na shigo da kayan tsaraba. To yanzu me ki ka ba su na saukan baki?" Na bude baki zan yi magana ya ce, "A'a bar su kawai su bani amsa. Suka fara lissafa mishi abubuwan da suka ci tun da suka zo. Sai da suka gama ya ce, "Ba ta ba ku sweet ba, ba ta ba ku Ice Cream ba kenan kun ga bata iya karbar baki ba." Ya jawo wayarshi daga aljihu ya kira Bala direba ya ba shi kudi ya ce yaje ya siyo mishi Ice Cream da candy. Sannan ya kalleni, "To baiwar Allah ya ya ki ka samu gida? Nayi murmushi har cikin zuciyata na ce 27 "Lafiya lau yallabai, kowa yana gaisheka tare da godiya mai yawa, sai dai ban ga Baba ba saboda gudun kadana makara." Ya mike ya nufi hanyar sashen shi ina bin shi har muka shiga. Ya tsaya a bedroom din shi yana tube kayanshi, ni kuma na wuce bayangida ina hada mishi ruwan wanka a kwarmi. Ya ce, Ki koma wurinki kawai saboda yaran nan na ce to. Ban dawo ba sai da na ajiye mishi dukkan abin da zai bukata idan ya fito daga wankan. Na dawo dakin inda na bar su Tasi'u suna nan inda suke, kallon cartoon din da na saka musuna Kiddies world suke yi har yanzu. 28 Ban dade da dawowa ba Bala ya shigo da aiken da aka yi mishi babbar leda cike da kayan kwalama. Ya ajiye ya juya na kira shi na debi mai yawa na ba shi saboda sanin da nayi yana da yaya suna kuma zaune ne a boys Quarters din gidan. Godiya sosai yayi ya juya. Na bai wa su Tasi'u wanda za su iya ci na kai saura fridge na ajiye saboda Ice Cream din kada ya narke. Ganin da nayi hankalinsu ya yi nisa yasa na koma wurin Ahmad ya gama shirinshi har ya fito falon yana kokarin fitowa na ce, "Ai abincinka nazo na baka ya ce mu koma wurinki na ci a can, na ce to." A falona yaci abincin shi muka ci gaba da hirar mu, su Tasi'u ma suna harkokinsu har suka yi barci. Na 29 dauke su naje daya dakin nawa na kwantar da su na dawo in da Ahmad yake. Ya jawo ni jikinshi ya kwantar da ni a kan kafafunshi yana shafa gashin kaina. "Tun da ki ka zo gidan nan ina kallon ki ba ki taba yin kitso ba." Na ce, Ai ban san inda za a yi mun kitson ba ne a unguwar nan." Ya ce, "Eh mai yi ma su Zainab tazo tayi miki gobe. Na ce, "To." A dakinamuka kwana ya ce saboda su Tasi'u kada a bar su su kadai. Sammako sOsai yanzun nake yi saboda karyawar Ahmad tunda na lura ba son shayi da biredi yake yi ba. Pizza na mishi na hada mishi da ruwan lipton saboda complain din da 30 yake yi akan tebar shi da take kara habaka. Duk da na gaya mishi ni bana ganinta. Sai da na sallame shi ya tafi sannan na dawo na shirya su Tasi'u cikin sababbin kayansu muka karya muna 'yar hirarmu cikin raha da ban dariya suna bani labarai. Su na tambaya abinda zan girka musu suka fadaa na shiga nayi musu muka ci tare sannan na dauko Ice Cream din su na jiya na ba su suka sha suka ce mun za su je wasa a waje. Kamar na hana su sai dai naga kada na takura su tunda yara ne. Tashi nayi na nuna musu wurin da yara suke wasa sannan na dawo dakina na hau gado na kwanta. Ban dadc sosai da kwanciya ba sai ga dan aika daga kasuwa Ahmad ya 31 aiko shi da sakon su Tasi'u. Na karba ina dubawa. Kaya ne masu asalin kyau yan kanti set uku-uku, sai takalma sandals na asali. Na ajiye kayan na leka don na kira su daga nesa na hango su a kan lilo, don haka na dawo na bar su suka ci gaba da wasan su. Ni kuma na shiga kicin don fara shirin abincin dare. Ihun da nake jiyowa ne yasa ni saurin fitowa, don kuwa ya yi mun kama da na Tasi'u. Sai dai kafin na fita waje har sun shigo dakin cikin tsananin rudewa na kwallara kara tare da fadin "Inna lillahi wa inna ilaihi raj1'una." Jini ne kawai har ya rine rigarshi gaba daya. Waje nayi da gudu saboda rudewa. 32 Daga nesa Bala direba ya hango ni ya taho cikin sauri "Lafiya, lafiya? 99 Na ce, Zo ka gani. Na taho dakin har ya zauna a kasa cikin saurin shi ya sunkunci Tasi'u nima na bishi a mota ya saka shi zuwa asibiti. Ban jira dawowansu ba bin su nayi. Ba karamin jin ciwo Tasi'u ya yi ba, don kuwa sai da aka yi mishi dinki a keyarshi a ka yi dressing din wurin aka yi mishi allurai sannan muka dawo gida wajen karfe shida da rabi na yamma. Har dakina Bala direba ya kawo shi kan kujera ya ajiye shi. Muryar shi har ta dishe saboda kuka. Na tsaya a kanshi ina kallon shi saboda tausayin da ya bani. Na koma bandakina na dauko sandar goge-goge na goge duk jinin 33 da ya mannu a tayels din na saka dettol na sake gogewa sannan na shiga kicin cikin sauri don na dan yi wa Ahmad abincin da zai ci. Sai dai ko dorawa ban yi ba sai ga motarshi ta shigo gidan, duk da haka ban fasa ba saboda nasan ba wurina zai wuto ba. Cikin kankanin lokaci na yi mishi fried rice da coleslaw salad, sannan na dawona dauki Tasi'u da barci ya riga ya dauke. Naje nayi mishi wanka da ruwa mai zafi saboda ya ji dadin jikinshi, na hada mishi tea na ba shi sannan na ba shi magungunan da Likita ya ba shi. Naje na kwantar da su ban wani bar su suka tsaya kallo ba. 34 Ahmad ya shigo lokacin ne nake wanka amma kafin na fito ya tafi dakinshi, don haka sai kawai na bi shi can. Shi ma wankan na samu yake yi don kuwa dabi'arshi ce vin wanka, da zarar ya idar da sallar Isha'i yana cin abincin shi yana dan kallona. Zuwa can dai ya kasa yin shiru ya ce, "Menene ya faru ne amarya? Na ce "Me ka gani? Ya ce, "Ba haka na saba ganinki ba. Kamar nayi shiru don kuwa abin da zuciyata take ta gaya mun kenan sai dai na kasa. Abin kawai da na sani shi ne, Sabi'u ba zai yi mun karya ba, don kuwa yana wurin da abin ya faru ya kuma tabbatar mun da Ziradat ce ta wurgar da Tasi'u akan liie ya ji wannan ciwon. 35 Na share hawayena da na gama yi mishi bayani, ya ce "Yanzu yana ina? Na ce, Ya yi barci. Mikewa yayi ya taho dakin da nake kwantar da su har yanzu wata irin ajiyar zuciya yake yi. Duk da nisan da barcin shi ya yi ya zuba mishi ido yana kallon lafcecen bandejin da aka toshe ciwon da shi, ya juya ya fita. Shiru naji bai dawo ba, na mike zan fita sai na hango shi yana tahowa daga sashen Hajiya, duk da ban san me ya faru ba gabana ne ya fadi da na kalli fuskarshi. Na kauce na ba shi hanya ya shige daki ya kwanta, ni ma kwanciyar nayi ban ce mishi komai ba, tunda shi ma bai ce mun ba. 36 Washegari sai da ya gama shiri zai fita ne ya kalle ni. "Kiyi hakuri Hauwa'u, zan so ki dauke shi a matsayin tsautsayi duk da dai nasan ganganci ne kawai irin na yara." Na ce, "Babu komai." Ya fita, Na shirya kamar kullum na shiga sashen Hajiya don na gaisheta. Kallon kawai da ta yi mun ne ya y1 matukar sanyaya mun jikina. Na gaisheta ta amsa sannan ta ce, Ko da wasa kada ki kuskura ki kara kai karar yaran nan wurin Babansu na gaya miki kada ki kara. Ba a yi mun haka, kada ki shiga gonata saboda bana son abinda zai sa na saba miki. Tashi ki bani wuri." 37 Dawowa dakina nayi, nayi sumukwi nayi tsit saboda sanyin da jikina ya yi. Ban yarda na mayar da su Tasi'u gida ba kamar yadda naso nayi sai da ya ji sauki sosai har aka cire mishi bandejin. Ahmad kuwa siyayya ya yi musu mai ban sha'awa har da Kekuna ya ba su, sannan yasa Bala ya mayar da su gida. Na riga na saba duk ranar Litinin da Alhamis Hajiya tana Azumin nafila, tunda nazo kuma duk da cewar da tayi na daina saka mata abinci idan nayi bai sa na fasa yi mata girkin abincin buda baki a wadannan ranakun ba. Tun tana hanawa har tayi shiru, kasancewar yau Alhamis sai na shirya 38 mata farfesun danyen kifi mai hadi sannan nayi mata lafiyayyen alcle na ganye da kunun gyada na danyar shinkafa. Na hada wuri daya ina nufin dauka na kai sai ga wayar Ahmad ya aiko dan aike na ba shi takardar da ya bari a kan bed side din shi da ke cikin dakinshin. Hakan ne yasa nayi waya sashen su don Larai tazo ta dauki abincin, sai aka ce bata nan, don haka na ce Zainab tazo ta dauka. Na shiga na dauko wa dan aiken sakon shi na ba shi, sannan na dawo na ci gaba da harkokin abincina. Sai da na kammala komai nayi wanka nayi kwalliya tare da sallar Magriba sannan na fito wurin Hajiya don nayi mata sannu da shan ruwa. 39 Ina shiga Ahmad yana fita saboda sallamar da aka yi da shi a waje. Na durkusa gefe na gaisheta tana amsawa kamar kullum yanayinta ta kuma yi mun sannu. Na mike zan fito sai naji an kira sunana. Na waiwayo da sauri don ganin mai maganar. Tun da nazo gidan yau ne naji Zainab tayi magana da ni. Tana rike da kofar dakinsu da hannu daya yayin da dayan kuma take nuno ni da shi. "Kada ki kuskura ki sake yin waya ki ce a turo ni ki aike ni kin ji na gaya miki. Ba na daukan raini idan kin lura za ki gane tunda ki ka zo gidan nan ban taba shiga harkarki ba. Idan me aika ki ke so, to gayawa wanda ya ajiye ki ya nemo miki." Ta juya ta koma dakin da ta fito. 40 Ina tsaye a bakin kofar dakin ko ina a jikina sai tsatsafo da gumi yake yi. Murmushi Hajiya tayi ta ce "Kai Zainab kenan, ina dai yi miki addu'a Allah ya shirye ki. Je ki abin ki Hauwa'u rabu da ita." Na juyo na dawo daki raina a cushe. Har lokacin da Ahmad ya shigo na rasa yadda zan yi na saki raina. Duk wani abinda na saba yi mishi na mishi sai dai da muka kwanta Juyawata nayi na rabu da shi, don kuwa abin har yanzu yana cina. Yayi tambayar har ya gaji wai na gaya mishi abinda ke damuna na ce babu komai. Ya ce, haka kawai ki ke mun irin wannan abin. 41 Nayi shiru naga zai ja mun wata matsala na ce mishi ba ni da lafiya, ya ce Idan ba ki da lafiya ba za ki yi magana ba sai kawai ki juya mun keya? Juyowa nayi na ba shi hakuri, sannan aka zauna lafiya. Duk wani kokari da nake yi na gani ban shiga sabga r 'ya'yan Ahmad ba nayi shi, amma hakan bai sa sun bar ni ba tare da su suna shiga tawa harkar ba. Babu ma dai shaidaniya irin Ziradat, haka kawai yarinyar bata kwanta mun ba. Gara Zainab bata kallon inda nake bata yi mun magana amma ita ko baki nayi to sai tasan yadda tayi ta yi musu abinda ransu ya 6aci. 42 Duk wanda tayi wa rashin mutuncinta hakuri nake ba shi tunda ko a gaban Hajiya ne hakurin zataa bayar sai ko bin su da take yi da addu'ar shiriya. Ba ni da wata matsala daga wurin mijina, muhimmmin abu kenan a wajena. Wata irin iska mai karfin gaske aka yi da daddare, wacce ta bugo satelite dish din sashen su ya fado kasa. A lokacin nan Ahmad baya nan, don haka ba a gyara ba. Tun da abin nan ya lalace sai suka dawo kallon su Wurina. Ziradat da Zinatu safe, rana da dare a dakina suke wuni, ba na sawa ba na hanawa. Sannan ga su da ciye-ciye duk abinda suka ci kuma to a wurin za su 43 yar da bawon shi ko kuma su bar kwanon a wurin ko da wacce irin shara ko gyara na yi wa gun. Ban taba daga ido na kalli abin da suke yi ko na gaji nayi musu magana ba. Abin dai da na sani shi ne, ya kusa wucewa tunda maigidan ya dawo a jiya da daddare bayan tafiyar da yayi ta wajen sati biyu. Na gama aikina tas da yamma na gyara dakina da na Ahmad na duba babu wani abin da zan yi. Don haka nayi wanka na gyara kaina, nayi kwalliya ta burgewa sannan na dawo falona da yake ta kanshi na zauna ina kallon programme din (Ask Huda) da ake yi a Huda TV. 44 Kan wata tambaya dangane da jinin Haila da ake amsa ta wacce ta dade tana daure mun kai. Sai kawai Zinatu ta shigo dakin nan da sauri ta dauki remote ta canza zuwa kidsco wai zata ga cartoon. Wani gululun takaici ya taso min, ban san yadda aka yi na daka mata tsawa ba. Na ce, "Meye haka? Dalla can mayar mun inda ki ka same shi." Iyakacin abinda na ce kenan yarinyar nan ta tayi jifa da remote dinnan ya daki bango ya wargaje. Sannan ta falla a guje tana kurma wani irin ihu, sai ka ce wacce ya yanke wa wata gaba a jikinta. Wani sabon takaicin ya sake kama ni, ganin remote din ya ki aiki na tattara shi na aj1ye. 45 Na shiga dakina na bi lafiyar gado ina 'yan sake-sakena. Larai ce tayi sallama ta shigo, wai in je Hajiya tana kirana. Na fito bayan na lullube jikina da gyale. "Me ya hada ki da Zinatu ki ka bugeta?" Na kalli yarinyar yadda ta takure a jikin kujera har yanzu kuka take yi. Na ce, "Hajiya ban bugeta ba." Na fara kokarin yi mata bayanin abin da ya faru. Ta ce, "Dakata! Kin ga yadda muka fara zama cikin fahimtar juna? To ba na so wani abu ya shigo daga baya, don idan nayi niyyar daukan mataki akan mutum abin ba ya yi mishi kyau. Kada na sake jin an ce ko kallon banza kin yi wa wani da a cikin gidan 46 nan, ballantana har ta kai ga kin saka hannu a jikinsu. Ki zauna a matsayinki su zauna a matsayinsu. Ni bana dukan yarana tunda ubansu ma a haka na tarbiyantar da abina. Duk wanda ya ce ba zai yi hakuri da su a haka har kafin su fahimci kan al'amarin duniya ba, to sai yasan nayi. Ba na so, kada kuma na sake jin don sun je wurinki sai kiyi mata haka har tana sulewa saboda razana? Ai nan gidan ubanta ne tana da ikon shiga duk inda take so ta wala." Na dawo dakina nayi alwala nayi sallar magriba har aka yi Isha'i ban tashi daga wurin ba. Don haka na mike nayi sallar Isha'i tare da shafa'i da wutiri. Motsin 47 Ahmad naji a wurin shi ne na dauki abincin shi na kai mishi. Ina ajiyewa ya ce, "Me ya hada ki da Zinatu ki ka yi mata irin wannan dukan? Wato kin gane ko? Ni da ki ke gani ina matukar tsoron tashin hankali. A waje ban huta ba, babu abin da nake bukata irin na shigo gida dan hutun da zan yi da iyalina na yishi cikin kwanciyar hankali da farin ciki ba. Menene haka? Tun farko na gaya miki kiyi kokarin zama ba tare da wani abu ya hada ki da wani yaro ba, saboda nima hakuri nake yi da su. Hajiya kuma ina matukar kokarin ganin bacin rai, bai same ta ba ballantana a ce sanadina ne," 48 Naga fadan nashi zai yi yawa saboda wani abu bai taba hada ni da shi makamancin haka ba, a tsawon zaman da nayi a gidan na watanni shida. Na ce, Ban fa bugeta ba." Ya watso mun ido "Ba ki bugeta ba? Na ce "Na rantse maka ban bugeta ba." "Me ki ke nufi kenan? Kina so ki ce mun Mahaifiyata tayi miki karya?" Nan da nan na fara kuka saboda jin inda ya mayar da abin. Nan take kuma fadan yafi na dah wai na karyata mishi uwa. Ga gaskiya nan kiri-kiri jikin yarinya ya rure har zazzabi ya rufeta amma kina karyata mahaifiyata. Mara kunyar yarinya, tashi ki ba ni wuri." 49 Na tashi na dawo dakina nayi kuka har na gaji, idanuna suka yi luhu-luhu saboda rashin barcin da ban yi ba. Na gama abin karyawa kamar ba zan shiga sashen nashi ba, tunda korata ya yi jiya sai naga kada na karawa kaina matsala. Na dauka na kai mishi na ajiye na juyo abina, tunda a da wannan damar tayin gaba da wani ina dai bin doka ne kawai. To da haka wanna ya wuce. Ba karamin taka tsantsan nake yi da yaran Ahmad da mahaifiyarshi ba, saboda ina son aurena. Gashi kuma cikin kankanin lokaci sai na mallaki abubuwan kadara irin Su,gold da zinari saboda yawan tafiyar da yake yi. Kuma shi mai sakin hannu ne. matsalata a kullum ba daga shi ba ne 50 sannan babu fashi sai dai idan bai yi tafiya ya dawo ba sai an ce nayi kaza nayi kaza. Ita kuma Hajiya ta ce aja mun kunne, to garin aja kunnen sai ya zama tashin hankali, ina batawa mahaifiyarshi rai. Sannan babu damar nayi musun ban yi ba sai laifin nawa yayi yawa, na karyata mahaifiyarshi, don haka kullum a haka muke. A daidai wannan lokacin ne ta bayyana ina dauke da juna biyu har na shiga wàta na uku. Hakan ne ya matukar takura ni naa kasa yin Azumin watan Ramadana, saboda tsananin laulayin da nake yi. Ba Ahmad ba ma har Hajiya a wannan lokacin ta sassauta mun, don 51 haka babbar matsala a yanzu laulayina ne da kuma yaran. Tunda yanzu ba barina suka yi da karata wurin Babansu duk da laulayin da nake yi bai hana ni kiba na murje ba. Shirin sallah sosai ake yi don kuwa gidan ma a cike yake da mutane 'yan uwan su da suka zo daga kauye da kuma babban dan Ahmad Zubair. Wanda yanzu ne muka san juna da, shi. Shi kam babu laifi yana da hankali don Aunty ma yake kirana. Haka nan nima duk da sanin da nayi suna buda baki a wurin Hajiya hada mishi nake yi da Babanshi. Sannan ganin shi yasa hatta Zainab ta saurara da wasu abubuwan ballantana su Ziradat. 52 Zama yazo yayi yana gaya mun abubuwan da yake so nayi mishi, na sallah saboda bakin abokanshi da za su kawo mishi ziyara. Na ce, To ka bari mana idan nayi na Babanku sai na diban maka a ciki. Yayi godiya sosai, take kuma farin cikinshi ya bayyana, ya tashi ya tafi. Bai dade da fita ba na fita don zuwa sashen Hajiya kai mata farfesun kodar da Ahmad ya aiko ya ce nayi mata da hannuna. Na isa bakin kofar tun kafin nayi sallama naji Ziradat tana cewa, "Ai munafuka ce tunda gashi har Hajiya ma yanzu ba ta yarda idan mun ce mata tayı mana wani abu. Ni a matan da Babanmu ya aura duk ita nafi tsana. Hajiya ta ce, 53 "Um'um Ziradat na fa kwabe ki da irin wannan maganganun." Shi kuma Zubair cewa ya yi "Ni banä son irin wadannan maganganun ban san abinda yasa Baba yake biye muku ba. Menene laifin wannan matar? Ko harkar mutum bata shiga ba za ku taba barin Baba ya zauna lafiya da mata ba. Shi kuma ku ke sakawa a matsala." Sallama nayi na ajiye mata na fito na dawo wurina, a raina na ce kwaji da shi, ni kam nawa auren daram in Allah ya yarda. Shiri sosai nayi na sallah mutanen gidan kaf na basu abinci da abinsha da su kek din da nayi ba tare da nayi la'akari da Hajiya tayi ba. 54 Makwabta baki daya sai da na zagaya su da abinci. Ahmad ne kuma ya taso keyar su Zainab suka kai mun rabon. Gidanmu ma duk da ya aike musu da nama cikin babban baho saboda yankan da yayi da kuma shinkafa da tumatur kwando. Bai hana ni kai musu abincin sallah ba wannan kuwa Bala direba na aika. Da yamma ne baki abokan harkar Ahmad suka zo gidan hakan ne yasa sashenshi ya cika dankam ba kadan ba. Nima gagarumar liyafa na shirya musu sinasir da farfesun kafar saniya sai dambun nama da kek da manyan donghnut na asali mai ridi. Sai kwalayen juice wanda na hada musu duka a cikin wani madaidaicin 55 kwando na Rafia da nayi rafin dinshi da wata 'yar leda da aka rubuta iyalan gidan Alhaji Ahmad Rufa'i suna muku barka da Edil Fitr. Kuma gaba dayansu ya wadace su. Shima abin yayi mishi dadi ba kadan ba. Ya shigo dakina lokacin da nake shirin shiga wanka har yanzu fuskarshi a washe take ya sa hannu ya dauke ni yana cewa bari nima na taya ki wankan irin wannan gajiya da ki ka yi haka. Duk da dai ni da yunwa ki ka bar ni na ce, "Haba yallabai na dauka ai yau ba za ka ji yunwa ba." Dariya yayi ya fita bayan ya gaya mun yana jirana idan na gama shiri. Doguwar riga na saka mai gyale na dauko abincin a babban tire na nufi 56 falon shi na waje don a nan na jiyo shi alamar ya sake yin wasu bakin. Ni kuma ba zan iya jiran tafiyar su ba tunda na gane yana 1in yunwa. Wani irin santsi ne ya debe ni gaba daya na zame na kife a kasa tire yayi nesa ya kife abubuwan ciki suka tarwatse. Karar fashewar abu da salatin da nayi ne yasa Ahmad tahowa wurin cikin sauri har ya karaso inda nake. Ba iya motsawa ba sa hannu yayi ya dauke ni zuwa cikin dakinshi tunda daga inda nake nan dinne ya fa kusa. "Sannu Hauwa'u." Sai dai ko amsawa na kasa yi saboda wani irin gigitaccen ciwo da nake jiwowa daga gadon bayana yana hadowa har gabana zuwa marata. 57 Ya juya yana kiran Larai don tazo ta kwashe barin da aka yi yana kumna gayawa Hajiya. Durkusawa nayi saboda murdawan da yake yi mun da irin azabar da na ke sha. Ahmad yana shigowa tare da Hajiya daidai lokacin dá naji kamar fitsari yana zubo mun. Hajiya ce ta fara salati tana karawa, wannan wane irin mummunan faduwa ki ka yi 'yannan. Ai jini nake gani." *Jini Hajiya?" Ahmad ya fadi daidai ya kara matsowa inda nake cikin sauri ya dauke ni zuwa mota muka tafi asibiti. Jinin da ya zuban ya yi yawa, don haka cikin ya lalace wankin ciki aka yi mun aka sallamo ni da magunguna 58 muka dawo gida wajen karfe sha biyun dare saboda cewar da Ahmad yayi a sallamo ni mu dawo gida. Cikin dan kankanin lokacin da abin ya faru nayi wani irin ramewa saboda bakar azabar da na sha. A daren Hajiya tazo duba ni ta kuma hado mun da abincin da ta girka mun, tuwo miyar kuka ta ce na ci na sha maganina. Ba karamin jjjaga Ahmad ya yi da barin da nayi ba, don kuwa shi mutum ne mai son haihuwa. A yanzu kuma Zinatu ita ce karamar 'yarshi, wacce a bana ya ce mun shekarunta takwas. Hakanne yasa ni daurewa nayi niyyar wartsakewa duk kuwa da abin da ke damuna a zuciyata. 59 Da safe ma Hajiya ta shigo ta gaishe ni, haka Larai da Bala direba de matarshi sai Zubairu. Wajen karfe tara ne Ahmad ya sake shigowa ya kalle ni, ganin ina zaune a kan gadon "Har kina iya tashi? Na dan yi murmushi na ce, "Ai naji sauki. Ya zuba mun ido tare da kamo hannayena duka biyu ya rike a nashi hannuwan yana dan matsawa. Yace, Kin dai daure Hauwa'u ba kin ji sauki ba, ki taya ni addu'a Ubangiji ya ba mu. wasu masu albarka." Na ce, "To amin." Yayi shiru zuwa wani lokaci ya ce "Ina son zama da ke Hauwa'u. Ina rokonki ki kara hakuri da duk wata matsala da ki ke fuskanta a tare da ni ko wai nawa." 60 Ban fahimci inda maganar tashi ta dosa ba, amma sai na dan yi murmushi kawai. Duk kokarina bai wuce na ganin na nunawa Ahmad cewa naji sauki ba. Na dan daure na yi kwalliya na sanya doguwar riga na fito ina lallabawa zan shiga dakin, shi ne naji maganar Zubair. Kamewa nayi na kasa shiga. "Na rantse Baba naga lokacin da Ziradat ta saka ai ba zan yi maka karya ba, amma ina gaya maka ne don kada wata rana suyi abinda yafi haka." Ahmad ya ce "To kai Zubairu me yasa da ka ganta ba ka ce komai ba?" Ya ce, "Ai ni ban san da wata manufa tayi ba. Na juyo. na dawo dakina saboda na fahimci wani 61 muhimmin abu ne duk da dai ban san ko menene ba. Wajen La'asar na rinka jiwo ihun yaran, sai dai n1 kam ban je ba, don ban san abinda yake faruwa ba kumna babu ruwana ko ma menene. A dakina yau ma na kwana sai dai tare da Ahmad. Washegari matar Bala direba ta dawo gaishe ni tana zaune a kan kujera muna yar hira saboda mutuntani da matar take yi da kuma kokarin shiga sabgata yasa nake dan hira da ita. Don ba za ta wuce sa'ata ba. "Oh ni 'yasu, wadannan yara kuma ashe sune." Na ce, Su ne kamar ya ya? Wadanne yara? " Nayi mata tambayoyin a tare kuma lokaci daya. 62 "Au, jiya ba ki jiyo ihunsu ba? Ai Baban ne ya yi musu duka ba na wasa ba, don wansu yaje ya gaya mishi cewa ita wannan shu'umar ita ce ta saka miki abu ki ka fadi." Nayi shiru ina kallonta saboda jin abin da take fada, abin dai ya yi matukar bani mamaki, sai dai duk da haka ban tanka ba don tsoron halin mutane. Shiru nayi a kwance ina tunani me nayi wa wadannan mutane haka? Ahmad ya shigo ya nemi wuri kusa da ni ya zauna. "Ya ya Amarya me ke faruwa ne?" Ban ce mishi komai ba sai zuba mishi ido da nayi. Ya jawo ni jikinshi yana cewa. 63 "Kin san fa tunda wannan ya fita to aiki ya koma baya, sabon zubi kumna zamu yi yanzu." Daurewa nayi na ce mishi "To, amma dai ai ba yanzu ba ko?" Ya ce, "Eh to, ko gobe tunda Likita ya ce bari ba a wuce kwana uku, ko ba haka ba?" Wartsakewa nayi saboda farantawa maigidan rai na nuna mishi naji sauki don hankalinshi ya kwanta. Haka nan kuma abubuwa sun matukar yi mun sauki ba kadan ba, tunda dai yanzu zan iya ganin Ziradat a hanya ba tare da ta ja mun tsaki ba. Abin har mamaki nake yi, wai 'yar karamar yarinya mai shekaru goma sha uku ce ta ke irin wannan abin. 64 Lokacin komawan Zubair Makaranta ya yi, don dama hutun nasu ba mai yawa ba ne. Tambayar shi nayi abinda yake so nayi mishi na tafiya. Ya yi shiru yana 'yan tunane-tunane. Ya ce, Ai ba na so ne Baba ya ji zai ce na cika fitina, tun da ana siya mun komai." Na ce, "To fada mun ba zan bari ya ji ba." Ya ce, "To ina son kek irin wanda ki ka yi da sallah." Na ce, "Sai me?" Ya ce, "Ko shi kadai aka yi mun Aunty na gode. Na ce, "To shi kenan. Cefane sosai nasa aka yi na kira Larai muka yi aikin tare. Cincin nayi mishi mai yawa, nayi mishi kek na sassaka su a leda daidai saboda kada su bushe tunda Makaranta ce. 65 Sai dambun naman da nayi mishi cikin babbar roba fara. Ana gobe zai tafi na ba shi tsalle ya rinka yi kamarzai yi ya ya don murna. Sallamaa muka yi mai dadi ya kumaa roke ni idan Babanshi zai je mishi visiting na raka shi muje tare, na ce to. Da yamma ne Ahmad ya shigoo bayan ya kai shi Makaranta ya dawo na kawo mishi ruwa mai sanyi yasha sannan ya yi hamdala ya ce "Zubairu ya ce na sake yi miki godiya." Ban saurare shi ba kicin na koma na hado mishi fruit salad na kawvo mishi, ya karba yana sha ya ce "To ni ina nawa dambun naman?" Na kalle shi na gane da gaske yake yi na ce "Ban ajiye maka ba saboda ya ce ba ya so ka sani." 66 Ya dan yi murmushi ya ce, "Haka ya gaya mun, to amma kuma sai ya kasa yin shirun ya fada mun da kanshi. Kin san alheri komai kankantarshi yawa ne da shi, to ballantana irin wannan." Na ce, "Kai dai don Allah bari zuga ni, ai ba da kudina nayi ba a cikin cefanen gida na saka." Ya ce, "Ko ma dai ya ya ne ai cefanen gida idan wata ce ba za ta yi ba, ina so kuma na gaya miki cewa ba Zubairu ki ka yi ma ba ni ki ka yi ma, zan kuma tabbatar. ban mance alherinki ba." Komawar Zubairu Makaranta sai abubuwwa suka sake rincabewa. Ashe dama sun bari ne don sun gane yana kai kararsu wurin Babansu. 67 To yanzu ba ya nan sun ci gaba daga inda suka tsaya. Sai dai Ziradat ta riga ta tsorata saboda dukan da Baban ya yi mata a kaina. Zainab ce take nuna mun salo iri-iri na rashin kunya da kuma nuna 1sa, amma na danne zuciyata ko kallon iya-shegenta bana yi. A daidai nan ne kuma wani sabon laulayin ya kama ni, watanni uku bayan barin da nayi. Amma a hakan na tsaya tsayin daka wajen ganin na gamsar da mijina duk wata lalura tashi. Kullum nayi mishi maganar zuwa gida sai ya yi mirsisi ya hana ni, ya ce ba na yi mishi adalci da yana gari amma sai na tsallake hidimominshi na tafi gidanmu. 68 Na ce, To ai kai da rana kana kasuwa, da daddare ne ka ke dawowa gida ka bar ni mana naje da rana na dawo kafin lokacin dawowarka gida? Sai ya ce, Wai a'a yafi son idan ya tuna ni a lokacin da yake kasuwa ya rinka tuna ni a cikin gidan shi ina harkokina. Kallon Ahmad kawai nayi nayi murmushin takaici, amma a raina tunda ba ni da abin yi a kai, ba na musu dashi koda kuwa hukuncin da ya yanke bai yi mun dadi ba. Hakanne yasa da yazo tafiya Kano gaida kanin Babanshi da ya yi rashin lafiya, tafiyar kwana daya sai na tuna mishi da zuwana gida. Ya ce, Ba ki fa da lafiya Hauwa'u. Na dakatar da hada mishi kayan da 69 nake y1, na ce "Haba yallabai, ba haka muka yi da kai ba fa." Ya ce, "Eh na sani, amma ai wannan karon tafiyar tawa ba mai jimawa ba ce, kwana daya zan yi." Na ce, To ni ai tawa tafiyar wuni ce. Shiru yayi sai da ya fita wurin Hajiya ya dawo sannan ya ce naje gidan yau Bala zai kai ni." Nayi tsalle don murna ya ce, "To kin gani ba. Nayi-nayi da ke ki rinka kula da irin wadannan abubuwan kin ki kanmar kin mance da abinda ya same ki wancan karon." Ahmad yana tafiya nayi shirina tsaf na rufe sashena na fito na shiga wurin Hajiya don nayi mata sallama. Sannan na fito harabar gidan na samu Bala har ya yi warming din mota ni yake jira. 70 Sai kawai ga Zainab da Ziradat sun fito su ma za su je unguwa. Kai tsaye suka nufi motar za su shiga. Bala ya ce, "A'a Zainab kada ki shiga motar nan, Hajiya zan kai unguwa a ciki." Tayi mishi wani wawan kallo. Akwai wata HHajiya nc a gidan nan baya ga wacce dama can na sani? Ina tsaye a gefe ina kallonsu ban tanka ba. Ita dai Ziradat ta dan nutsu duk da dai nasan ba wani hankali ta kara ba. Zainab ce da Bala dircba suke ta jayayya ya shiga mota ya tuka ya ki, ita kuma ta fita a motar ta ki. Ziradat fita kije ki kira mun Hajiya. Ba a wani jima ba sai ga Hajiya ta iso wurin cikin hijabinta. 71 "Lafiya?" Ta kalli Bala dircba. Nan da nan ya fara yi mata bayanin abinda ke faruwa. Hajiya ta kalli Zainab ta ce, "To ke Zainaba ku shiga mana idan aka sauke ta a gidansu sai a kai ku taku unguwar ba shi kenan ba." Nan take ta fashe da kuka ita gaskiya ba za ta shiga mota da ni ba, bayan ba sonsu nake yi ba. Na kalli Bala na ce, "Bala idan ka kai su ka dawo kayi mun magana. Ya ce,"To Hajiya. Na dawo na shiga dakina na zauna. Ban san yadda zan yi da yarannan ba, abinda na sani shi ne bana kin su. Na zauna kato-kato ina jiran Bala ya dawo da su Zainab mu tafi bai dawo gidan ba sai wajen karfe hudu da rabi. 72 Har sashena ya iso yayi sallama, na ce "Kun dawo Bala? Ya ce, "Eh Hajiya kiyi hakuri zai fara yi mun bayani na ce a'a Bala babu komai je ka kawai." Ya tsaya zai ci gaba da ba ni hakuri, na ce ba fushi nayi ba Bala, amma kaga gidanmu zan je yanzu kuma yamma ta riga tayı, ya ce to Hajiya na gode. Washegari ba ni da halin fita tunda Ahmad zai dawo gida a ranar, don haka tashi nayi don nayi mishi shiri. Da aikin wurinshi na fara. Na wanke bayan-gida, nayi shara ko ina fes sannan na canza labilayen dakin gaba daya na zuba wasu na kira mai wanki na ba shi. Na sake shimfida ko ina ya yi kal, sai kamshi kawai. Na dawo sashena 73 na shirya mishi abinci na yi mishi fruit salad sannan na shiga bandaki nayi wanka nayi kintsi na sosai. Nayi kwalliya mai kyau ta riga da siket, ina gamawa ko sai ga isowar motarshi cikin gidan. Sai da ya shiga wurin Hajiya kamar yadda ka'idar shi yake, sannan ya shigo wurina da gudu na isa inda yake na rungume shi ina mishi oyoyo. Yana dariya ya ce, Anya Hauwa'u ce kuwa ba canje aka yi mun ba da ba na nan? Na ce, Canje kuma 'Yallabai? Ya ce, Eh mana naga ne sai wani danyacewa ki ke yi kina dawowa 'yar karamar yarinya. Sashen shi muka shiga don ya yi wanka, yana ganin irin gyaran da na yi wa wurin ya ce, "Wow! Ke da 74 waye ku ka yi wannan aikin Hauwa'u? Na ce, "Da waye ka ke tsammanin zan yi?" Ya dan yi shiru zuwa can ya dan kada kai ya ce, "Ke kadai ko?" Na ce, Yauwa ashe ka gane kenan? Ya ce, To Allah yayi miki albarka. Na wuce shi na shiga bandakin shi ina hada mishi ruwa da turarukan wanka. Ya shiga ni kuma na fito na ciro mishi jallabiya ruwan kasa saboda sanin da nayi zai fita zuwa Masallaci idan anyi magriba. Yana cin abinci ina zuba mishi yana ba ni labarin garinsu da mutanen garin. Ya ce, "Sai kin haihu zamu je su ganki suga abin da muka samu. Ya ce kin ga ma na manta jiya da muka yi waya ban tambaye ki su Umma ba. 75 Na ce, Ai ma ban je ba. Ya kalle ni ya ce, Ba ki je ba kuma? Na ce, Eh. to saboda me? Nayi shiru ban ce mishi komai ba. Ya ce, Ke dinnan fitanarki yawa ne da ita, da ban bar ki ba da har yanzu kina yi mun mitar na hana ki zuwa gida. Ya fita sallar Magriba ya wuce wurin Hajiya, bai dawo ba sai da aka yi sallar Isha'i sannan ya shigo. Tashi ki shirya muje gidan tare. Sannan ya wuce sashenshi. Ya dawo sanye da jamfa da wando na yadin material din maza yana rike da mukulln mota a hannunshi. Ni ma yadin material na saka mai hadari ya kuma yi mun kyau sosai. Muka fito tare muka shiga wurin Hajiya don yi mata sallama. 76 Ta ce, lna zuwa haka a daren nan? Ya ce, "Yar wata unguwa zata raka ni. Ta ce, To a dawo lafiya. Muka fito. A wani babban shago ya tsaya ya yii siyayya mai yawa, sannan muka wuce gida. Hira muke yi sosai da Umma shi kuwa yana wurin Babana ba mu dawo ba sai wajen karfe goma na dare. Tashi nayi naga jini kadan-kadan yana fitar mun, sai dai ban kula na gani ba sai bayan da Ahmad ya tafi kasuwa. Bana son daga mishi hankali, don haka nayi nufin bari sai ya dawo naayi mishi bayani. Nayi ta aikace-aikacena ba tare da wani abu a raina ba, tunanina dai bai wuce laulayi irin na ciki ba. 77 Sai da na gama ayyukana na shiga bayan gida da nufin yin wanka, sai kawai na ganni kace-kace cikin jini. Sauri nayi na fito na dauki waya na sanarwa Ahmad cewa ina son Zuwa asibiti, ya ce lafiya? Na ce ch, ba na dai jin dadi ne kawai, ya ce to Allah ya sauwake. Bala ya kai ni asibiti sai dai tun kafin nan a takure nake cikin sauri aka kai ni dakin Likita sai dai gwajin farko ya tabbatar mana cikin ya lalace, ya fita daga mahaifa dole a cire. Duk da halin da nake ciki a haka na daure na kira Ahmad. Cikin kankanin lokaci ya iso asibitin, sai dai duk da saurin da ya yi har an shigar da ni don wanke mun mahaifa. 78 Duk da kokarin da nayi tayi na hana kaina kuka kasa daurewa nayi da Ahmad ya iso kaina. Wannan karon ma bari nayi na ciki wata hudu har da sati biyu, kamar dai wancan kenan. Kwana nayi a asibitin kowa kuma yazo duba ni har daga gidanmu. Likita ya shigo saboda sallama ta da za a yi Ahmad yana yi mishi wasu yan tambayoyi. Ya ce, To dai a fayil dinta na ga ta samu matsala makamanciyar wannan shima a watanni hudu, don haka tunda ga abinda ka fada zamu sake yi mata scarming don mu gani ko da matsala. Likitan ya jawo wata 'yar takarda yayi rubutu ya bamu. Ahmad ne da kanshi ya kai ni wurin scarning din 79 muka dawo Likita ya duba ya ce, "To a gaskiya ta samu matsala ne a mahaifa saboda jijigar farat-daya da mahaifarta tayi a wancan karon. Saboda irin faduwar da tayi, hakan ne yasa mahaifarta ba za ta iya rikke wani ciki da zai yi fiye da watanni hudu a mahaifarta ba. Saboda bakin mahaifarta da ya riga ya bude. Kuma shawarar da zan ba ku a yanzu shi ne, kafin a san matakin da za a dauka a kan matsalar, ta dan yi hutu. Don kuwa idan tayi wani cikin ma a yanzu abinda zai faru kenan. Dawowa gida muka yi jikinmu a sanyaye, ni kam Ciwo ne ya rufe ni jinya sosai Ahmad kwata-kwata ranar bai fita kasuwa ba. 80 Bai kuma fadawa kowa abinda Likita ya ce ba. Kwana biyu ko abincin da zan ci daga wurin Hajiya ake kawo mun. Kullum kuma Ahmad zai ba ni hakuri saboda lurar da yayi na dan saka damuwa a raina. Duk kokarin da nayi kada ya fahimci wani abu kasawa nayi. Yau ma yana zama zai fara mun magana kuka na kama yi. Sai da nayi ya ishe ni sannan na share hawayena, babu abinda ke tsaya mun a rai naji zuciyata ta baci irin na tuna 'ya' yan Ahmad ne suka yi mun wannan sanadin. To tambayar ita ce, shin idan da ni ce nayi wa wani a cikin su haka anya zan zauna lafiya kuwa? 81 Amma gashi nan ni sun yi mun sun zauna lafiya, sun ma mancc in ban da shi Ahmad da yake ba ni hakuri. Duk da warkewan da nayi a duk lokacin da na tuna ina jin wani iri na kuma kasa sakewa nayi harkokina kamar da. Ko shi Ahmad din ya lura ya gane hakan, don yau ma muna zaune a falonshi muna kallon labarai ya Juyo yana kallona. Hauwa'u magana nake so nayi miki. Na lura duk tsawon lokacin nan har yanzu ba ki saki jikinki ba. Na kuma tambaycki shekaran iya ko wani abu na damunki ne kin ce a'a, lafiyarki kalau. Ina so ki san wannan abun ba ke kadai ya samu ba har da ni, amma 82 kuma kin takura ni na rasa walwalar da a da nake farin cikin samu. Idan ni ne nayi miki wani abu ki gaya mun na gyara, idan kuma a kan matsalar nan ne ina so kiyi hakuri. Ina kokarin a wannan watan da zai kama idan zan yi tafiya mu tafi tare saboda wannan matsalar, sai ki ga Likita a Dubai." Ban ce mishi komai ba, amma nayi kokari wajen ganin na rage takura ko don saboda Ahmad. Sai dai har karshen wata yazo ya wuce Ahmad bai yi tafiyar ba, bai kuma ce mun komai ba. Muna kwance a dakinshi da daddare a daren da ya dawo daga Legos dauko wasu kayan shi da suka shigo. 83 Nayi mishi maganar tafiyar da ya ce zamu yi don ganin Likita. Ya ce, "Kiyi hakuri Hauwa'u, ina nan ina wasu shirye-shirye ne kawai." Sai dai ba a wani jima ba ya shirya ya tafi Dubai ya dawo ba tare da ya ce mun komai ba. Na shiga dakinshi na same shi zaune ya baje takardu, lissafi yake yi. Na zauna a gefe ina jiranshi ya gama shiru bai gama ba har na gaji' na mike na kwanta nayi barci. Washegari tun da Asuba yayi shirin shi gaba daya alamar daga wurin Hajiya zai wuce. Haka ina ji ina ganin babu yadda zan yi ya fita. Da daddare kuwa da ya dawo sai da na gama mishi komai sannan na kwashe kwanukan. 84 Wai kafin naje na dawo nayi mishi maganar da ke Cina a zuciyata nan ma dawowa nayi na samu wai Hajiya ta ira shi. Zama nayi daram a kan kujera ina jiran shigowarshi, bai shigo ba sai wajen karfe goma da kwata. Har yanzu ba ki yi bacci ba?" Na ce, "Eh kai nake jira." Ya ce, "Akwai magana kenan? Na ce, "Eh." Ya gyara ya kwanta ya ce, "To ki barta gobe kafin na fita kasuwa sai muyi." Na ce, Idan kuma a wurina tana da muhimmanci fa? Ya ce, "Komai muhimmancinta ki barta sai gobe, don a yanzu na gaji." Wani irin gululun bakin ciki ne ya tokare mun makogorona. Da kyar nake iya numfashi. 85 Tashi nayi na dawo dakina na hau gadona na kwanta. Sai dai ban iya yin barcin ba. Ji nake yi kamar na koma na samu Ahmad muyi duk wacce zamu yi da shi daren nan amma ba zan iya ba. Ko wani sauraron shi ban yi ba da safe haka nan shi ma bai bukaci ya ji maganar da nake son yi da shi ba. Da dai ya gama shirinshi ne zai fita ya leko dakin. "Hauwa'u ina son burabusko da miyar bindi". Na ce, To babu tsakin shinkafa." Ya ce, "Ki karba a wurin su Hajiya." Ya tafi. Babu abinda na tsana yanzu a rayuwata irin zuwa wajen su Hajiya. Tun da dai gaisheta ya zama mun dole, to kullum da safe ina zuwa 86 amma baya ga haka bana komawa sai wata safiyar. Sai da aka yi sallar Azahar sannan na dauki roba na shiga wurin Hajiyan na gaya mata ina son tsakin shinkafa. Ta kalli Zainab ta ce, "Zainaba tashi ki debowa Mamanku tsakin shinkafa." Ta dago ido ta kalle ni, sannan ta ce, "Maman wasu dai Hajiya, ammna ban da mu." Ta ce, "To naji bana dai son rashin kunya, karbi ki debo mata. Kin dai kusa tafiya Makaranta a huta." Ta ce, "Ai idan na ganc tafiyata zai sa wasu murna ma sai na cc na fasa." Ta dawo da tsakin a hannunta ta dangwarar a kasa. Ban tsaya sauråronta ba, dauka nayi na yi tafiyata. 87 Zainab a yanzu ta rubuta jarrabawarta na gama makaranta sceondary, Jami'a ake neman mata har ma an samu. Dawowa wajena nayi na shiga kokarin ganin na kammala cikin lokaci, kuma nayi sa'a yayi kyau ya yi dadi. Ga kamshi ko ina a cikin gidan. Ina gamawa na shiga bandaki nayi wanka na fito kenan naj1 motsi a falona. Don haka na fito falon bayan na sanya zulumbun hijabina don ganin ko waye. Zainab ce rike da tircn abincin Babansu, gabaki dayan shi zata fita. Sa hannu nayi na rike na ce "Yau kam a'a, abin ya ishe ni haka ba zai yiwu ba. 88 A duk ranar da ki ka ga kina da bukatar cin abincina to rinka gaya mun sai na rinka saka sanwa da ke. Ba haka kawai idan na gama girki ki saka hannu ki sunkuci na mijina kiyi gaba ki bar ni da dora sabo ba." Ta zuba mun ido tana kallona, nimna ita nake kallo, don na lura su gaba ki dayansu ba su san zuru ba. Kuma a gaban kowa sai Zainab ta caccaba mun magana ba za a ce komai ba. Ba tun yau ba lokuta da dama sai na gama abinci sai tazo ta sunkuta gaba daya ta tafi da shi wurinsu ta ci 1ya cinta ta rabar da saura. Wani lokacin ma ko rabi ba a ci sai ta bar shi haka ya lalace, sannan ba za ta dauko kwanukan ta dawo da shi ba sai dai ni nabi bayan su. 89 Sau daya Hajiya bata taba yin magana a kan hakan da take yi ba, duk da tasan abincin danta Zainab take dauka. Kallon da take yi mun ne ya ishe ni nayi nufin karbe tiren, sai kawai yarinyar nan ta kabar da tiren gaba daya abubuwan ciki suka watse. Abincin ya zube a kasa, sannan tayi murmushi ta raba ta gefena ta wuce. Zubawa abincin da ya tarwatse din ido nayi ba na ko kyaftawa. Ban taba ganin danyen rashin mutunci irin wannan ba. Cikin dakina na koma na sanya doguwar riga na futo zuwa wurin Hajiya don na gaya mata abinda ke faruwa. Na shigo na zauna a kasa zan fara magana sai ta ce "Dakata! Yau kuma 90 abin naki har ya kai ma ki hana Zainaba abinci? Ta dauko kuma kin biyo ta kin kifar. Me ki ke nufi da abinda ki ka yin? Kin taba siyo abinci kin shigo da shi gidan nan ne da ki ka samu damar hana wani?" Na ce, "Hajiya..". "Bana son jin komai daga bakinki, nasha gaya miki ba sau daya ba ba sau biyu ba cewa duk abinda za ki yi a gidan nan to ya tsaya tsakaninki da wasu amma kada ki tsallako hurumina, don ba za ki ji da dadi ba. Ya ya za ki hanata cin abincin da ubanta ya kawo ya ajiye takamar kina matarshi?" 91 Tun ina daurewa bacin raina har ban san sanda na fara zazzago maganganu ba. "Ai tun farko da nazo gidannan na fara kawo abinci sashen nan aka ce na daina don kuwa akwai mai girki. Me yasa tunda haka ne idan tana son abincina ba za ta fada mun tun da wuri ba sai na girka da ita, sai ta bari na gama tazo ta dauke gaba daya haka ake yi? Duk hakurin da nake yi da yarann nan bai isa ba kullum kokarinsu bai wuce na ganin sun kure ni ba. Menene na yi musu? Tunda na fara magana har na gama Hajiya bata sake cewa komai ba, sai kallona kawai da take yi. Zuwa can ta ce, Lallai kin isa, ni ki ke gayawa irin wadannan 92 maganganun? Dama ai biri ya yi kama da mutumn. Tun kwanakin baya na gane ya ba ki isasshen damar da ta wadace ki. To amma ba laifinki ba ne. Tashi ki ba ni wuri, bari yazo ya same ni mu san wacce muke ciki da nida shi." Mikewa nayi na dawo dakina na kara tsallake abincin a wurin na shiga uwar dakina na zauna. Ni kaina na gane nayi kuskure amsawa Hajiya da nayi, to amma ya ya zan yi da raina? Rashin 'yancin yayi yawa, ace wai har a kan budurwar yarinya mai shekara goma sha shidda kamar Zainab za a zaunar da ni a titsiye ni wai nayi laifi! 93 Kawai takamar ina auren ubanta bayan da za a bi Silsilar abin za a iya fahimtar ba ni ba ce mai laifin. To amma saboda daurin gindi da Son kai sai ya zama komai suka yi daidai ne. A madadin abubuwa su gyaru kullum kara cabewa suke yi? Kamar yadda ya saba dawowa haka ya dawo yau ma. Ko inda yake ban je ba ballantana na ba shi wani abu. Don kuwa babu, na kuma san an gaya mishi komai da ya faru. Karfe tara har ta wuce ina zaune a kan sallayata da nayi sallar Isha'i a kai ban tashi ba. Jiran kawai abinda zai biyo baya nake yi. Bai shigo dakin ba sai wajen karfe goma na dare. 94 Yadda nayi zaton zai shigo ba haka ya shigo mun ba. Ya karewa abincin da har yanzu yake shimfide a kasan falon da food flask din da kuma fasassun plates din kallo. Ya sunkuya ya kwashe plates din da kofunan da suka faffashe ya zubar a abin zuba shara na nan kicin. Sannan ya fito ya dawo da abin kwashe shara da tsintsiya yasa ya kwashe ya gyara wurin tsaf, sannan ya wanke hannunshi ya zo ya zauna a inda nake muna fuskantar juna. "Ba kya jin maganata Hauwa'u, ko nayi miki magana ba kya ji. me ya hada ki da Zainab?" Nan take na fahse da kuka saboda karayar da nayi. Nayi kukana sai da na gaji nayi shiru, sannan nayi mishi bayanin komai. 95 Tun daga lokacin da Zainab ta tsiro da abubuwanta har zuwa yau abinda ya faru. Ya yi shiru zuwa can ya ce, "Me yasa ba ki taba gaya mun ba? Na kalle shi. "Na gaya maka fa ka ce? Idan na gaya maka me za ka yi? Na taba gaya maka wani abu da aka yi mun ka dauki mataki? Sannan ko karata aka kawo wurinka ko ni ce da gaskiya ko ba ni ba ce ba ka taba saurarona ka ji ta bangarena ba. Ni dai a kullum ni ce maras gaskiya, 'ya'yanka kuma masu gaskiya. A ina ne aka ce a yi haka don daidaita zaman lafiya? 96 Ni kenan kullum ina da matsala da 'ya'yan miji, to menenhe aibuna? Me nayi musu?" "Za ki iya zama a Kano?" Tambayar ta yi mun kwatsam! Na bar kukan da nake yi a take na kalle shi. "Ina da gida a Kano, idan kin yarda za ki zauna a can sai na mayar da ke can tunda ina shirye-shiryen bude wata harkar a Kano kwanannan. Ina son zama da ke Hauwa'u. Ni kaina nasan ina da matsala a cikin gidan nan. Kiyi hakuri a yanzu ko meye Zainab zata yi miki ki daure ki jure saboda ni da ke mu samu biyan bukatarmu." Hankalina ya dan kwanta, ya ce "Ina neman alfarma idan ba zan takura miki ba?" 97 Na ce, "Ta meye?" Ya ce, "Abinci nake so ki samar mun wanda zan ci, yunwa ta dame ni." Tashi nayi a daren nayi wa Ahmad dan girki mai sauri yaci sannan muka kwanta. Tun daga nan na samu sassaucin damuwa, sai dai Hajiya ta daina amsa gaisuwata, duk da haka kuma ban daina zuwa gaisheta ba. Zan zauna na kai mintina goma bata saurare ni ba. Shi ma na lura yana da 'yar matsala amma tunda dai bai bude bakinshi ya fada mun ba sai ban tambayar shi ba. Na dai tsaya tsayin daka wajen ganin bai kuntata da yawa ba, don nasan matsalar ba ta wuce ta Hajiya ba. 98 Ba a fi wata daya zuwa kwanaki arba'in ba sai shirin Ahmad ya kammala na bude babbar harkarshi ta kasuwanci a Kano. Har yaje ya yi sati daya a can don ya tabbatar komai ya daidaita, sannan ya dawo. Muna kwance a dakinshi yana bani labarin yadda abin yazo cikin gagarumar nasara, ni kuma dokina sai karuwa yake yi zai bar zama da su Hajiya da 'yan fitinannun jikokinta, zan koma Kano tare da mijina. Ina ta ayyano irin tattalinshi da zaan kara yi da irin abubuwan da zan yi na ci gaba don kaina. Don kuwa nima yanayin kasuwancin Ahmad yana ba ni sha'awa, har nima na kan yi tunanin a 99 matsayina na mace idan zan gwada babu mamaki nayi nasara. Na ce, Kaga idan muka koma ni ma sai na gwada kasuwancin mata na cikin gida. Kallona ya yi cikin mamaki. "Kasuwanci kuma Hauwa'u? Na ce, "Eh mana, na zannuwa da gwala-gwalai irin naku ba." Shiru yayi yana kallona, ya ce "Ashe kina sha'awar kasuwanci?" Na ce, "Eh, zama da kai ne yasa hakan, da can ba na yi." Ya ce, To bari kayan da nayi oda wannan watan su zo sai na diban miki a ciki ki gwada muga irin taki nasarar. Kin san mata da yawa suna karban kaya a hannuna kuma suna samun riba ba kadan ba. 100 Amma abin da na lura da shi shi ne, sai wacce ta iya rikici saboda siyan kayan gida yawanci bashi ne. Ke kuma ban ga wannan a tare da ke ba." Ba mu yi bacci ba sai karfe daya saboda 'yan hirarrakin da muke yi. Washegari bai kintsa da wuri ba saboda bakin da yayi abokan kasuwancinsa. Sai kusan sha daya na rana. Ya shigo dakina rike da mukullin motarshi yana ba ni sakon da zan bai wa Bala direba idan yazo, saboda haihuwar da matarshi tayi. Sannan ya shiga wurin Hajiya. Kwanciya nayi don na dan yi barci kafin Azahar tayi. Sai dai ban ko yi nisa ba naji sallamar Larai. 101 Daga cikin dakin na daga murya ina tambayarta ko lafiya? Ta ce, Lafiya kalau Hajiye ce take kiranki. Gabana ne ya fadi, to menene kuma? Ba dai naje na gaisheta ba. Nayi sallama a kofar dakin na shiga. Har yanzu Ahmad yana nan bai fita ba, yana zaune can gefe a asa, kanshi kamar zai dunguri kasa saboda irin sunkuyon da ya yi. Jikina a sanyaye na zauna a gefe nesa da inda yake. "Ina ce dai ita ce wannan?" Hajiya ta fara magana. "Yarinyar da ko darajar sauran matanka bata kai ba. A kanta ne kuma nake baka umurni ka ke kin bi. Abinda ban taba zaton zaka iya yi ba shi ne take umurnina. Na kyale ku 102 na zuba muku ido amma gaba dayanku ba ku fahimci hakan ba. Nan wurin nan kazo mun da maganar za ka kaita Hajji a bana na ce a'a banyarda ba, don ina ta binka ka biya wa Lado dan kanina har yanzu ba ka biya ba kana daga tafiyar. Sai ka dawo min da maganaar zuwan ku Dubai wanda wannan ma duk wani salo ne na kin bin umurnin da na bayar din. Ka dai nuna mun a yanzu kai ma ka girma. Ba a wani dauki lokaci mai tsawo ba yarinyar nan ta zo har dakin nan ta zage ni. Na gaya maka ban ji ka dauki matakin komai a kai ba. A jiya kuma abinda ka zo da shi shi ne za ka daukec ta ku koma Kano da zama ko Amadu? 103 To bari ka ji wata magana, idan ba mantawa nay1 ba, ko a ranar da na haife ka, nayi nakudar ka ne ni kadai a dakina na haife ka na yanke maka cibi da kaina. Sannan ne nayi maka wanka kafin wasu ma daga gidan suka san na haihu, kenan ka gani babu wanda ya taya ni. Don haka ba zan haifi da nayi tarbiyyarshi da irin abubuwan dadi da wahala da dawainiyar da nasha wata tazo ta kwace mun shi rana tsaka ina kallo ba, babu ita. Zagina da tayi ba ka ce komai ba saboda ka daina gudun bacin raina sai nata, to na yafe maka amma ko don na yi wa tufka hanci ya zama hakan bai sake faruwa ba. 104 Ga takarda da biro nan na baka rubuta takardar sakin aurenta yanzunnan ka bata, auren nata ya ishe ni haka." "Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un." A bayyane na furta saboda firgitan da nayi. Saki kuma? Wannan wacce irin musiba ce? Na kalli Ahmad wanda har yanzu yake a yadda na same shi, sannan na kalli Hajiya. Kamar kullum tana zaune ne a kan dardumarta ta sallah, sanye da zurmemen hijabinta. Zan iya cewa a tsawon zaman da nayi a gidan na watanni ashirin ban taba ganin ranar da na ganta babu hijabinta ba. Sai nayi sha'awar ace ita din mata ce mai sassauci da rangwame a kan 105 al'amuranta, tunda kowa ya shaideta mace ce mai yawan Ibada. To me yasa ita din halinta ya zama haka. Danta da yake matukar kokarinsa wajen ganin yayi mata biyayya ya kaucewa bacin ranta ya batawa wanda ya bata mata. Danta da a kullum yake fadin irin alherinta da dawainiyar da tayi da shi wajen ganin bai yi maraicin uba ba. Danta da a kullum yake fadin cewa ita ce abinda ya fi so da girmamawa a duniya shi ta ke yi wa irin wannan kuntatawar da kuma rashin sassauci? Lallai halinta sai ita. Take na fara kokarin rarrashin zuciyata don ta samu sassaucin tsananin da zata fuskanta a gaba. 106 Na rinka tunanin abubuwan da zan yi wadanda za su taimaka mun a rayuwata da zan shiga nan ba da dadewa ba. Tunda nasan babu makawa Ahmad zai aikata abinda Hajiya ta umurce shi tunda da bakinshi ya tabbatar mun cewa ita din bata taba bashi wani umurni da ya ketare ba, face ya aiwatar da shi komai tsananin shi. ** ** ** Ina kwance a kan shimfidaddiyar katifata da ta sha lallausan shimfidan zanin gado na yadin (American bed sheet) dan asali da bargonshi. Na kai hannu na shafa yadin zanin gadon tare da tuna ranar da na fara shimfida shi a kan gadona, lokacin da 107 nake ganiyar cin amarcina a gidan Ahmad. Na runtse idanuwana da karfi saboda wasu tunane-tunane da suke ta kawowa zuciyata ziyara. Tunanin abubuwan da suka zo suka kuma wuce tamfar a mafarki tamfar dai ace wani barci kawai nayi mai dadi na kuma farka. A da can, ban taba tunanin haka al'amurana za su kasance ba. A matsayin shekaruna a yanzu ashirin da uku kacal a duniya. Amma har an fara kirga mun aurena. Yanmata da yawa sa'o'ina ba su ma yi auren ba, ballantana har ace ya kare. Take kuma nayi hanzarin yin Istigfari da na tuna akwai wasu mata kuma da suke zuwa duniya su gama 108 rayuwarsu a cikinta su koma ga mahaliccinsu ba tare da sun yi auren ba. Don haka ba zai yiwu nayi wa Ubangijina butulci ba, a kullum zan kasance mai yawan godiya a gare shi bisa irin yawa-yawan n imomin da ya yi mun a rayuwata. Ban kuma dauka wannan mummunan jarrabawa ba ce sai na dauka cewa ni kuma tawa kaddarar kenan ba kuma zai yiwu na tsallake wata kaddara tawa ba face kawai na roki Ubangijina da kowacce ta tashi zuwa mun, to ta zamto mai sauki. Ya kuma ba ni ikon dauka don Imanina ya zamto cikakke tun da aan gaya mana cewa Imaninmu ba zai cika ba sai mun yarda da kaddararmu ta alkairi ko wanin alkairi. 109 Bai kuma jarraba ni da ciwo ba ko wanina ko kuma ya jarrabe ni da rashi na wata gaba a jikina ba. Sannan da aurena ya mutu a farko sai ya bani wanda ya fi mun na farkon, to ina rokon shi a yanzu ma ya bani wanda ya fi mun na biyun. Sai dai tunanina yana kawowa daidai nan sai naji gabana ya yanke ya fadi ras! Kenan na rabu da Ahmad ba zan sake komawa gidanshi ba? Ina son mijina shima kuma yana sona. Mahaifiyarshi ce matsalarmu, don kuwa idan ba don shigarta cikin lamarin ba to don ta ya'yanshi zan iya zama da su a yadda suke, tunda ina son ubansu. Sabanin matsalata da Ishak wanda a lokacin da aka yi aurena da shi 110 shekaruna goma sha bakwai ne a duniya. Ba komai yasa a ka yi auren ba face rashi da mahaifina yake ciki ga kuma kwadayinshi a kaina na ganin ni din nayi karatu. Ya dauke ni ya ba shi ni ba tare da wani dogon nema ko bincike ba, saboda jin irin alkawuran da yayi a kaina. Alkawuran da suka zamo shi ne sanadin faruwar auren da kuma rugujewarshi. Idan kuma da ace zaman da yayi da ni akwai adalci a ciki ko kuma sassauci ko tausayawa wadanda wadannan abubuwa sune suka hadu suka zamo soyayya da kauna to duk da da sauki. 111 Idan har akwai abinda nake tunawa da Ishak da ke sake sani kin shi to bai wuce dukan rashin tausayi da yake yi mun ba. To sai na auri Ahmad, mutumin da ya an yanci na walwala. Nayi rayuwar aure irin wacce ban taba mafarkin ana yin irinta ba a gidan aure. Saboda irin sona da tattalina da mijina yake yi. Ya nuna mun cewa ni din ina da matukar muhimmanci a wurinshi. Ya kuma so ni so na hakika, ya mutunta iyayena da yan uwana, ya guje mun bacin raina, ya tattali farin cikina. Amma sai gashi 'ya'yanshi da mahaifiyarshi sun ki yarda su bar ni 112 na zauna da shi duk da hakuri da halinsu da nake yi. Idan har ina da laifi ko kuma wani ganganci da na aikata a lokacin da aurena na fari ya mutu, to a wannan karon kam nasan ba ni da wani laifi. Sai dai na kasa hakura, fatana bai wuce da ni da shi mu samu maslaha kan al'amarin aurenmu ba. Tunda dai an yi sa'a saki daya ne a tsakaninmu. An kwaso kayana tas daga gidan Ahmad, ba wai don na hakura da zama da shi ba. Sai dai kawai don jiran shawarar da shi da kanshi zai zartar a kan maganr. Sakon da ya turo mun kenan a waya daren da na dawo gida. 113 Cewa na saurare shi kan shawarar da zai yanke na neman mana mafita nan da kwanaki uku. Sai kuma kudi da suka shigo account dina masu auki. Ta bangaren Babana dai abin ba a cewa komai, don kuwa bakin cikinshi ba ya' misaltuwa. Umma kam har a wannan karon ba ta ce komai ba, harkokinta take yi. Nayi matukar kokarin ganin ban takura kaina da tunane-tunane ba, ta hanyar shiga duk wani hidima na gida da ake yi. Har girki na karba ni nake yi da sassafe kan bakwai zuwa bakwai da rabi na kammala abin karyawa. Idan na gama kumana zauna taya Umma saye da sayarwanta, muna kulla na kullawa. 114 Babbar matsalata ba ta wuce na rashin barciba. Sai nayi matukar sa'a ne kwarai nake samu na dan runtsa. Al'amurana ne kawai za su yi ta dawo mun rayuwar da nayi da Ahmad mu'amallarshi da kuma yadda yake harkokinshi a cikin gidanshi. Daga manya zuwa yara da kuma masu yi mishi hidima bisa sassauci da ganin mutuncin kowa. Ranar shi da farin cikinshi dakuma fushin shi da kuma wasu abubuwa masu dama. Me yasa mutane ba su da tausayi ne, babu sassauci a cikin al'amura amma kuma mu sai muce muna neman sassauci a wurin Ubangijinmu. Bayan mun san shi ne ya yi umurni da mu yi wa na kasa damu sassauci da adalci. 115 Duk da abin da Hajiya tasa danta ya yi mun zama dashi bai fita a kaina ba, har yanzu kuma jiran shi nake yi naji abinda zai ce. Satina uku cif a gida Ahmad yazo sai da ya gaisa da Babana da Umma sannan na same shi a zauren gidanmu, bayan Babana ya aiko Tasi'u cewa naje na same shi. Cikin kyakkyawar shiga na dogon hijabi da na dora akan kayan dake jikina dinkin atamfa riga da zani na same shi. Nayi matukar kokarin daurewa ta ganin bai fahimci wani abu game da halin da na shiga ba. Kaina na sunkuye na gaishe shi bayan na zauna akan shimfidar tabarmar da aka yi mishi. 116 Ya amsa cikin yanayin shi kadaran kadahan. Ban kalle shi ba na ce, "Ya su Hajiya?" Ya dan yi jim bai amsa ba kafin ya ce, "Suna nan kalau." Abinda a sani kuma shi ne kallona yake yi duk da kin yarda mu hada ido da nayi ta hanyar kallon 'yan yatsun hannuna da na yi wa lalle a safiyar yau. "Nayi tafiya ne Hauwa'u, shi ne abinda yasa ba ki ganni ba, tafiyar ta dauke ni tsawon kwanaki goma sha takwas, sai a daren jiya na dawo. Don haka kiyi hakuri." Shi dai mai yawan bada hakuri ne, abinda zuciyata ta ke fada mun kenan. To amma hakurin da ya bani a yanzu menene ma'anarshi? 117 Nayi hakuri ne a kan sakin da ya ya mun, ba zai iya sake zama da ni ba ko kuwa nayi hakuri ne na koma dakina? A yanzu ne nasan na daga kaina na kalle shi muka hada ido alamar ya dade yana kallona hakan bai sa na daina kallon shi ba babu abinda ya canza a tare da shi. Komai nashi yadda yake illa idanunshi da launin su ya dan surka. "Kiyi hakuri Hauwa'u." Abinda ya sake fada kenan a lokacin da na sunkuyar da kaina na hadiye wani abu mai tsanani da ya rike mun wuya. "Ina so ki san kowa da irin jarrabawarshi a rayuwa ni tawa jarrabawar kenan. A tafiyar da nayi nasa mutane daban-daban sun je don su taushi zuciyarta har sau úku. 118 A tunanina idan na dawo zan samu wani dan sauyi daga gareta a game da maganarmu wanda har da hakan ne yasa na kara jan kwanakina na dawowa. Amma da na iso gida sai ban ga hakan ba, don haka ne nayi sammakon zuwa Kano a yau na gana da kanin Mahaifina da a gobe nake sa ran zai zo don ya samu Hajiyan." Wani irin tunani ne ya yi gaggawan shiga zuciyata da kwakwalwata, duk da irin kwabata da zuciyata take yi sai da bakina ya furta na ce. "Idan a kaina ne ka ke tura mutane wajen Hajiya to na roke ka ka daina saboda kai da kanka ka gaya mun cewa baka taba saba mata ba. 119 Kenan kana so ka tilastata ta hakura ta barka ka zauna da ni ba bisa son ranta ba. Wanda hakan ba zai sa ta yi sassauci a kan kiyayyar da take yi mun ba." "Ba a kanki nake turawa ba, a kaina ne saboda halin da na shiga, barin ki gidan da kuma dawowan da nayi ba kya cikin shi. Gaskiya ki ka fada, ban taba yin makamancin hakan ba sai a yanzu wanda nasan ko ta sassauto ta hakura to akwai wani tsanani da za ki iya fuskanta. Amma ina so nayi miki alkawarin ba zai yiwu na barki haka ba. Har a yanzu ina da niyyar dauke ki a gidan zuwa Kano. A karo na biyu na 120 dago kai na kalli Ahmad da har yanzu yake kallona. "Ba zan jagoranci batawarka da Mahaifiyarka ba. Burina bai wuce naga mun daidaita matsalolinmu sun kare mun maida aurenmu ba. Amma sai dai dama matsalar ba tamu ba ce a inda matsalar take kuma banga alamar wani sauki ba. Ina rokonka kada ka tilasta Mahaifiyarka zama da ni, don Allah. Yadda a yanzu zuciyata ta hakura ina rokonka kaima ka sakawa taka Zuciyar sassauci. Ina kaiwa nan na mike na shiga gida, na fada kan katifata, kuka nake yi irin wanda na dade ban yi ba. Duk yadda na kai da son zama da Ahmad abin ba zai yiwu ba. 121 Ya zama dole na taushi zuciyata na danganaa na fawwalawa Ubangiji lamarinshi, don ya isar mun ya bani abin yi. Kwana nayi cikin wani yanayi da ba zan iya kwatantawa ba, don saukin abin ma nayi alwala nayi ta nafilfili ina rokon Ubangiji sauki, da kyakkyawan zabi. A cikin satin ne aka kai sadakin Yaya Auwalu abin da muka dauka shi ne za su saka ranar auren da nisa. Sai kawai muka ji sun saka sati hudu kacal. Muna zaune da Umma a tsakar gida muna kullin kukar da Baba Ladi ta aikowa Umma na siyarwa. Na ce, "Amma Umma gaskiya auren nan da suka saka ya yi kusa da yawa." 122 Ta ce, ""To ai na Allah ne, sannan shi Babanku jiya ya same shi yayi mishi bayanin komai. Ya ce, Babu damuwa, don yana da dan abin da ya dade yana tanadawa don shirin auren. Na ce "To ai shi kenan." Umma ta ce, "To sannan kin san shi hidima irin wannan ba ka shirya mata nemi taimako kawai a wurin Ubangiji idan tazo maka." Na ce Haka ne, Allah yasa mu gani lafiya." Ta ce, To amin. Ke kuma Ubangiji ya baki mafita kan wannan matsala da ta same ki na mutuwar aure, ya ba ki miji nagari da zai zauna da ke bisa adalci da kyautatawa. Ya kuma zaunar da ke a dakinki ba tare da kin sake fitowa ba." 123 Ban iya amsawa Umma ba, don kuwa babu abin da nake so naji irina ce Allah ya sassauta zuciyar Hajiya ta bar ni na koma dakina. Gidan Alhaji Ahmad Rufa'i, don kuwa har a yanzu dinnan burina kenan ko zuciyata tayi kamar ta hakura sai kuma ta kara harzukowva. Idan na tuna da irin rayuwar da nayi tare da shi, daurewa kawai nake yi nake rokon zabin alkairi a wurin Ubangiji a lokacin da nayi sallah. Amma idan da da hali to da rokon komawa kawai na rinka yi ko da hakan yana nufin batawar Ahmad da Mahaifiyarshi. To amma abinda na sani shi ne, idan nayi haka ban yi mishi adalci ba, don kuwa da kanshi ya gaya mun 124 cewar ta sadaukar da farin cikin rayuwarta domin shi. Da kuma Yarshi da har a yau din nan ban ma santa ba. Sannan shi din ko ba don haka ba mahaifiyarshi ce da Aljannarshi take karkashinta. Hakan da na sani shi ne yasa na danne zuciyata na kara ba shi shawarar cewa mu hakura har a jiya da ya kira ni. Don na tabbatar da ban zalunce shi ba. Idan yaso ni kuma Allah sai yayi mun kyakkyawan sakamako. Shiri sosai muke yina shirin bukin Yaya Auwalu. Ya hada lefenshi rigijif gwanin sha'awa. Samun Umma nayi na ce mata ina so na kwashe kayan dakinta na zuba mata nawa na gidan Ahmad. 125 Ta kalle ni ta ce, To a wane dalili? Ki zuba mun kayanki ke kuma idan ki ka tashi yin wani auren ko kuma ki ka koma dakinki fa? Tunda ai ba gama iddah ki ka yi ba. Na dan yi murmushi na ce, "Umma ai komawata gidan Ahmad abu ne mai wuya. Tunda ba matsala ce a tsakanina da shi ba, matsalar Mahaifiyarshi ce ba ta kuma da niyyar yin sassauci a kai." Ta ce, "Eh dai duk da haka ki bar Umma ba sai kiyi mun addu'a ba su ba ni da bukata." Na ce, "To ba kawai idan na tashi yin wani auren Allah ya bani wadanda suka fi wadannan ba." Ta ce, "To amin, amma dai duk da haka ba zan saka kayan dakinki a 126 nawa dakin ba, haba abin ma ai bai yi tsari ba." Da safe na shirya na gama aikina da wurwuri na samu Babana na roke shi ya bani izinin fita don ina da uzuri. Yayi shiru zuwa can ya ce, "To kin dai san mutane ba a iya musu, ni fa ina gudun magana. Amma idan kin ga a matse ki ke shi kenan kije amma kada ki dade." Babban shagon da muka yi siyayyan kayan aurena naje, mutumin kuma ya gane ni. Nayi mishi bayanin bukatata na son canza kayan tare da neman sanin cikon da zan yi mishi. Cikin sauki da mutunci muka daidaita na zabi wasu masukyau nayi 127 mishi ciko na dawo gida da motar kaya. Su kuma suka saka nawa da damna suke jingine a dakin su Tasi'u suka tafi da su. Sai da nasa a ka yi wa Umma fentin dakinta tsaf sannan a ka zuba mata sabbin kayanta a ciki. Abin sai wanda ya gani, duk da irin fadan da Babana yayi mun wanda bil hakki abin ya ba shi haushi. Ni a raina dadi naji don kuwa nasan shima Babana idan ya hau gadon zai huce. Tun ana saura kwanakki ake ta isowa yan biki kowa da shirin shi, yan uwan Umma daga Gamawa da na Babanmu daga birnin Kudu. Su Inna Hadiza suka tasa ni a gaba kowa da abinda yake fada. 128 Ba ni da abinda zan ce musu don na riga na gaji da bayani. Da daddare Baba Ladi ta kira ni dakin da aka sauketa da yake na Yaya Auwalu ne tana yi mun magana ne ita ma kamar kowa a kan rabuwata da Ahmad. Ban ce matakomai ba ta yi ta maganganunta ina jinta. Ta ce, "Wato ina miki magana kin yi shiru ko? Na dan yi murmushi daidai wayata tayi kara na dauka Ahmad ne. Gabana ya fadi kamar kowanne lokaci idan ya kira abinda ban san dalilin faruwar hakan ba. Nayi mishi sallama ya amsa. "Ya ya shirin biki? Na ce, "Mun gode Allah." Ya ce, Wato sai a yanzu nasan rashin kirkinki." 129 Na ce, Da na yi me kuma 'Yallabai?" Ya dan yi murmushin da na jiyo sautinshi har a cikin wayar. Ya ce, "Ba kya kirana Hauwa'u, ba ki damu da ni ba a yanzu. Yau kwana goma sha hudu ban kira ki mun gaisa ba, hakan bai sa kin yi tunanin ke ki neme ni ba. Sannan sai aka saka auren Yaya Auwalu ba ki saka ni cikin wadanda za ki gayyata ba." Na ce, "To kayi hakuri. Ya ce, "An ya zan iya kuwa? Ina dai so a duk lokacin da ki ka tunani ki rinka yi mun adalci." Na ce, "To." Ban san adalcin me Ahmad yake sonayi mishi ba. Sannan a tsakaninmu wanene ya kamata ya yi wa wani adalci? 130 Ni ce zan yi mishi adalci ko shi ne zai yi mun'? Wayar da na tsirawa ido ita ce ta sa Baba Ladi fara sabuwar magana ta bar wacce da take yi. "Kina yi mishi irin wannan so me ya fito da ke? A hankali na kalleta na ce mata, "Mahaifiyarshi." Da yamma kawai sai mota ta tsaya aka fara sauke kaya, buhun shinkafa biyar, sugar, filawa, wake, gero, mangyada, manja, maggi, tumatir da su albasa kwando-kwando. Sai cinyoyin bayana Saniya guda biyu, sakon Ahmad ne. sai yadin material 'yan asalin Dubai guda biyu, boyil biyu. Sai atamfa Erclusive guda biyu duka a dinke. Takalma set kafa biyu da za su iya shiga da kayan. 131 Sai gyale biyu, kayan duk a dinke suke. Na zuba musu ido ina kallo. Wani sanyi ya rinka kwarara a cikin zuciyata. Shi ma har a yanzu da alama bai fidda rai ba. Text nayi mishi na godiya, duk da korafin da ya yi na ba na kiranshi. Don kuwa ban ga dalilin yin hakan ba. Text din yana shiga sai ya kira, na ce "Mun ga sako mun gode." To fa! Lallai kam da gaske Ahmad yake ba zai iya hakura da Hauwa'u ba. To idan kuma Ishak ya ji labarin abinda ya faru shi ma zai dawo? Bari in dan huta a nan kafin na dora daga baya, don haka sai mu tara a littafi na (4) kuma na karshe insha Allahu. Taku; Haj. Hafsat C. Sodangi (Mrs Yunus Abdullahi Dabai) 08025078968, 07035586299 132