MAl BADA MAGANI KO YAR DAMFARA OUMYASMEEN fatahiyyah muhammad yakasai Bisimillahr ramanir rahim Da sunan Allah mai rahama mai jin kai dukkan yabi ya tabbata ga Ubangijin talikai ya Ubangiji ka bani ikon gama littafin nan lafiya kamar yadda na fara lafiya... Gargadi ban yadda wani ko wata su canza min labarina na ta ko wacce siga ba ba tare da izina ba.. Ku yi following dina domin samun ci gaban labarin nan da zarar na dora ........ episode 1 MUDAN MUDAN MUDAN kaga kamar yadda na kirawo sunan ka da manyan baki narantsai da Allah idan baka fita daga sabgar sana'ar da nake ba to wallahi zan maka abin da bakai zato ba. wai shin na tambaye ka ...? Kana da abin da zaka iya ciyar dani idan ban yi sana'ar sai da magani ba dan akurkin shagon da kake da shi wanda idan an tsaya ƙididdiga befi a samu *Dix mille* ba gabaki ɗaya kayan da yake cikin shagon ko , kofar shagon 300fcfah bazan siye ta ba ni zakai wa hassa mutanen zinder sun fara sani na shine saboda hassada irin taka kake fada min haka Ransa iya ɓaci ya bace cikin ƙoƙarin danne ɓacin ran'sa yace '' yanzu saude dan na hanaki wannan damfarar da kuka tsira ke da wannan mara mutuncin Sénateur take kowa da auren ki da mutuncin ki, tana kawo miki mutane kuna damfarar su ina jiye muku randa gwamnatin niger zata waiwaye ku ita fa rashin abinyi ne ya saka take aikata haka shine ke kika biye mata.., MUDAN ka fito fili kace min bani da hankali bani da tarbiyya kadena wannan kwana kwanar ina cewa tare ka gan mu da lubabatu har ka ganni kace kana so da can baka lura da bata da tarbiyya ba sai yanzu abin da yayi lubabatu shi yayi ne dan haka naran tsai da assamadu zan iya rabuwa dakai akan ta tun kafin nayi maka rashin mutuncin wallahi ka tattara kofaton ƙafafuwan ka ka koma rubabben shagon ka ko yanzu na nuna maka ni jinin zabarmawa ce saude ta fada tana gyara daurin zanin ta da ya ci uban datti sai sosa matsai matsinta take ajiyar zuciya ya sauke ya juya batare da yace komai ba ya fita da sauri ta koma cikin daki tana sosa kanta tare da gyara daurin kanta tace '' ci gaba ina jinki luba..., da sauri luba ta dago kanta tace '' wallahi Allah idan baki tashi tsaye aikan wannan mutumin ba sai ya raba mu dake ke kinga wani banzan kallo da yake min..da na shigo cikin gidan nan..?, cije lips dinta tayi ta buga cinya tace '' luba barni da tsohon shege zan maganin sa amma yanzu ci gaba da karanta min yadda abin nan zai ci gaba da tafiya kinsan Allah wani lokacin idan aka ce cuta kaza take damuna sai nayi dam kafin na nemo amsar bayar wa..., karkata daurin kanta tayi tace '' yauwa yar gari gwara ki ci mana kaniyar sa ko ya sakar mana mara muyi futsari shege dan takazar uba.., haba luba cin mutuncin kuma yayi yawa abban usman ne fa wani kallo luba tayi mata tare da yafa dan yalolan gyelanta a kafada tace '' aike ya tsaya, yana ci miki mutunci.. kinga raina ya ɓaci gobe zan dawo.., tashi tayi da sauri tana hade rai kallo daya zai mata kasan yar duniya ce gabaki daya kunnen ta ɓular kunne ne kuma ta zuba barima gabaki ɗaya kunnen har cikin kunne ma a kwai hudar kunne kasan lips dinta ta saka lips piercing ring masha Allah, akwai diri ga kuma ado dafa ta tayi tace '' haba Sénateur dan Allah kiyi hakuri kizo mu ci ga ba.., kinga saude ke ki faɗa min bakar magana mijinki ya faɗa min rashin aure hauka ne gani na da yake a titi yana ganin kamar yawan banza nake shi ya saka yake faɗa min haka wallahi da badan ke ba da tuni yau na nuna mai irin matsayi na a kasar Niger Luba ta faɗa tana gyara katoton glasses din dake fuskar'ta dan Allah kiyi hakuri Allah ya wuci zuciyar ki yanzu idan kin saka an kulle min mijina wa zan kalla naji dad'i wallahi duk da halin MUDAN har yanzu ina son sa kawai halinsa ke ja mai akwai dogon baki duk abin da ya gani ba ya iya bakin sa sai ya tofa, wai shi be yarda ba shi malami ne yar malintar da yake yi a kofar gida ya tara matasa yana biya masu ishimawi duk wata suna bashi fcfah 175 ¹⁰⁰ shine yaka kafafa dafa kanta tayi tace '' dan Allah saude ki matsa na wuce wallahi tsayuwar nan da nayi dake ba karamin hakuri nayi ba ni wallahi ina mamakin ma taya akai MUDAN yake iya mu'amalla dake sai zuba uban wari yake dole fa idan kina so na dinga kawo manyan alhazawa to ki koyi tsafta tunda muka zauna kike ta soshe soshe.., washe jajayen haƙoranta tayi tace '' billahillazi akan har kukan dadi yake...kinsan ki akwai style shi ya saka harkar nan ta bada maganin mata ta amsu Saboda idan na zauna wallahi fede musu biri har wutsiyar sa nake.., juya manyan idanuwanta tayi tare da taɓe baki tace '' amma kuwa kinyi asara wallahi kyawun mace ko ina ta gibta aji kamshi wai dan Allah ni bana baki sha'awa ne kalle ni da kyau bugun Niamey..., ajiyar zuciya ta sauke tace '' keedai kinji daɗin ki har yanzu kina gidan yaya amina.., hmm har yanzu ina can aina ai bazan iya zaman kunci ba wallahi tuni ta koma can da zama to zaman me zanyi anan uwata bata nan nima tunda ya sauta (saketa ) na cika wandona da iska sai ranar da na bushi iska naje duk yar kutumar uban da tayi min yasin ba raga mata nake ba, Sénateur ta faɗa tana murguda bakin ta. Allah ya kyauta yanzu sai yaushe zaki dawo. cewar saude kallon rufin dakin saude tayi duk azara wani gurin ya tsake tace '' kinga saude ki rufawa kanki a siri ki dena zaunawa a dakin nan kar fa wata ran ayi ruwa ƙasa tayi miki rubuti kisha uban duka..., kallon gurin tayi tace '' abban usman yace min kuɗi yake jira su shigo mai zai gyara mana yana riga da ya samo kasa kawai kudin aiki zai bawa masu aiki su fara..., hangame baki tayi tace ''bazai saka muku plafond...ba yanzu fa shi ake yayi kai amma *MUDAN* naga lokacin da zai waye kullum duniya ci gaba take amma shi yadda kika san an tusa kansa a cikin bakar leda.., hmmm kya faɗa kullum bashi da aiki sai Allah ya wore min zanyi idan baka tashi ka nema ba ta ina zaka samu kina ga abokinsa shazali ga uban gidan da ya gina a maradi gari guda ne har da wannan abar ta zamani douche 🚿 ya saka musu..., sai dai ki hakuri da irin taki kaddarar shi yasaka sai na zaɓa na darje tukunna zan yi aure yasin ina dalili haka kurum da kuruciyar ka , kaje inda zaka koma tsohuwa wani wanda be kula ba sai yace gwaggo ina huni nan kuwa besan talauci ne ya kashe maka jiki... rausayar da kai saude tayi kawar tata na ƙara bata sha'awa tace...'' muje na raka ki..., Sénateur (senator) gaba tayi ba tare da tace komai na saude na binta a baya dakyar ta iya tsallaka katuwar kwatar dake soron gidan tana yatsuna fuska ranta duk ba dad'i domin sénateur ba dai tsafta ba suna fita MUDAN na zauna da Kur'ani a hannunsa shagon nan ba mutum ko ɗaya to kayan shagon ma nawa yake ƙatuwar motar da ta kawo sénateur ce me rai da numfashi ta matso inda take da sauri *Chauffeur* (driver) ya fito jikinsa na rawa ya buɗe mata baki saude ta buɗe tana jinjina kai kallon MUDAN tayi ranta yayi baki kyakkyawa ne domin kusa buzune amma kyawunsa be amfana mata komai ba a nata ganin idan dai mutum da kuɗin sa to ko bakar leda ne fari ne ita bata san wacce kaddara ce ta waɗa mata ba ta kasa tan tan ce me ake nema a gidan aure ta aure MUDAN dafa kanta tayi da lokaci ɗaya ya sara mata shiga cikin gidan tayi tana jan karamin tsaki. duk a binda ke faruwa be sani ba saboda hankalin sa yana kan karatun da yake sallama aka yi mai ajiye Kur'anin yayi ya amsa sallamar yace '' Alhaji Mamman yau kai ne a gari..?, zama Mamman yayi a kan teburin MUDAN yace '' abin naka har da zolaya wanne alhaji kuma ana zauna qalau ga kunnan manyan alhazawa.., murmushi MUDAN yayi yace '' masha Allahu mun godewa Allah. amma dai kai kasan yanka ta kake ya hanyar..?, hanya alhamdulilah ina yaro na Usman Mamman ya faɗa yana duban MUDAN Wallahi yana cikin gida be dade da gama rigima ba na kulle shagon na kai shi gida to ba jimawa yayi bacci. Allah sarki, Allah ya albarkaci rayuwar sa amin ya Allah ina iyalin naka da fatan dai kowa yana lafiya Wallahi suna lafiya qalau, yar hira suka taɓa sannan yayi mai sallama ya tafi kulle shagon yayi ya shiga cikin gida ko sallamar da yayi bata amsa ba ta zauna ta kwashe cinyoyi tana kallon tulin maganin da sénateur ta kawo mata ta tafi duniyar tunani domin kuwa sai lissafi take tare da faɗar yadda za a yi amfani da su domin kar ta manta wanda bata faɗa mata ba ta ajiye shi a gefe guda. shiga cikin dakin yayi ya zauna saude ba mummuna bace kazan tar da take ita ta munan ta , ta domin kallo daya zakai mata kasa ta a sahun kyawawa ajin farko Allah yayi mata diri yar kanwar mahaifiyar sa ce mahaifinsa buzune gidan su babban gida ne irin gidan nan na gado dakin wannan yana kallon na wannan, basu da arziki domin sana'ar gidan su malinta sanin kowa ne idan malami ba zai fita ya nema ba to lallai yana tare da babu, sai azumi suke mun dan wani abu na kuzo a gani idan ba lokacin azumi ba lokacin fidda zakka bayan haka ba abin da suke samu to wannan hali ya taka rawar gani gurin gada musu talauci wasu daga cikin ya'yan gidan ne suke fita cirani zariya, Sokoto, musamman ma kano domin kusan cibiyar kasuwanci ce.... Mudassir su hudu ne a gurin malam iliyasu me ishiriniya akwai sulemanu sai mudassir sai kuma jimmala da hadizatou dukkan su , suna da aure mahaifiyar su laure itace matar iliyasu me ishiriniya ta farko Allah yayi mai auri saki dan haka yana da ya'ya sosai sai dan uwansan malam salihu shi kuma matar sa daya da ya'ya bakwai dukkan su suna zaune a cikin gidan har da kakanin su haɗin zuminci akai da saude da MUDAN to daman ance matar mutum kabarin sa baya ra'ayin'ta haka dai ya aure ta rabon yaron dake tsakanin su , babban abin da ke damunsa da ita kazanta ga taurin kai tamkar jinjirin jaki... idan ta saka kanta a gabas to fa ba wanda ya isa ya dawo dashi yamma duk da wannan matsatsi da suke ciki MUDAN yayi ilimin boko da na addini idan mahaifinsa baya nan yana koyar da mata sa da mahaifinsa ya ga haka sai aka raba karatun shi ya koyar shima ya koyar.. dagowa tayi suka haɗa ido murguda mai baki... tayi tace '' malam lafiya wallahi Allah idan ma dawowa kayi ka ƙara to wanda kayi cikin dare ma ya isa haba aita abu ɗaya nifa da nasan haka lamarin nan yake yasin da ban yarda da auren nan ba...ni Allah ya gani bazan iya da wannan bakar jarabar ba., kauda kansa yayi bema nuna mata ya san me take fadi ba MUDAN akwai hakuri da juriya kafin ka gane kamilar fuskarsa me take nufi to lallai zaka kwala yace '' kin dora sanwar rana ne..?, a'a yau aiki yayi min yawa Alkur'ani ba zan iya ba ka nemowa kanka abin da zaka ci.. tashi yayi be ce komai ba ya fita wata yar durkusasshiyar kofa ya shiga sai gashi ta sada shi da ɓangaren iyayen sa be tsaya ko ina ba ya wuce dakin mahaifiyar sa bayan sallamar da yayi musu wanda yake tsakar gidan ya amsa zama yayi tare da gaishe ta , tana zaune tana cin kwaɗon rama ajiyewa tayi a gefe ta amsa gaisuwar sa tare da yi mai bisimillah kawaici irin na mudassir kawar da kai yayi yace '' alhamdulilah.., bawai dan ba zai iya ci ba a'a shi be kawo musu ba sai ya ɗauke musu... yaci, ci gaba da ci tayi ganin yayi shiru ta ajiye robar hannunta ta sanshi sarai da mugun zurfin ciki tace '' lafiya MUDAN me ya faru kardai wannan mahaukaciyar yarinyar ce ka dena saka damuwar ta a ranka kana zaune mahaukatan kawayen ta zasu koya mata hankali..., murmushi yayi yace '' a'a mamma ba ita bace kawai dai nayi shiru ne.., hmmm Allah ya kyauta ta fadi haka tana ji manta lamarin saude da kullum baya raguwa sai karuwa cikin sauri ta dago tace '' ashe daman saude ta zama bokanniya ba mu da labari kai wannan jarabar son kudi ta saude ta kai inda takai yanzu abin da ta tsira sai ta dinga tattara yaran matan unguwar nan tana musu huduba tare da basu magunguna da yake su jakai ne idan kura tana maganin zawo tayi wa kanta mana shi ne suke biye mata..wai dai jummai tace har manya zuwa suke tana basi ararrabi da bagaruwa tana cewa maganin matsi wai kuma maganin yi yake jummala da yake yar gidan tace, tace har dorawa take kadawa ta basu susha wallahi ina jiye mata randa hukumar kula da lafiya za tayi dirar mikiya a cikin gidan ku ajiyar zuciya ya sauke yace '' mamma wallahi na rasa yadda zanyi da ita dazu ma sai da mukai wannan maganar dan haka kawai na zuba mata ido har lokacin da zata ga ishara abin tsoran shine ranar nan har mahaukaciya aka kawo mata karfa wata ran aljanu su nannade ta.., ni wallahi da zasu nan nade shegiya ta yi hankali daba haka ba mamma ta faɗa ranta a ɓace shiru *MUDAN* yayi domin yasan ranta ne ya ɓaci ya saka ta fadi haka. tashi yayi yace '' sai anjima mamma.., to Allah ya kiyaye hanya amin ya Allah.. ya faɗa yana fita kai tsaye cikin gidan sa ya shiga ransa ne ya ɓaci ganin taron mata ko wacce tana ganin sa ta fara tsinke kai tare da gaishe shi amsawa yayi ƙasa ƙasa ko a kwalar rigar saude kallon matar gaban ta tayi tace '' kinga wannan hmmm shi ake kira da ƙare mana wallahi ko baki kika nuna mai kika ce fari ne to ya zama fari can ciki zaki tura kinsan idan kika kama miji ta gurin shinfida kiga komai.., ke dan manzo matar ta faɗa tana washe baki gyara zama saude tayi tace '' daga garin nan maleshiya aka kawo min kinsan turawa ba dai iya riƙe miji ba to wannan shine sirrin nasu., to yanzu nawa ne kuɗin sa Kar kata daurin kanta tayi tace '' *Cinq mille* ..., zaro ido tayi tace" kai saude yayi tsada wallahi ina laifin ki siyar min ko *Deux mille* kinsan dai yadda rayuwar take.., kwace jarkar ta tayi ta zabgawa harira harara tace '' a'a babu da ya'yanta zan siyar miki in banda rainin hankali ki kalle ni kece wai na siyar miki *Deux mille* sannu barauniyar zaune to ko Ni ban siye shi haka ba balle na siyar miki , ki bari sai lokacin da na fara fasa shagunan jama'a ina dauko kaya ina siyar muku na siyar miki haka ina banda kin raina ni, ku dubi uban tsumin nan kice na siyar miki a haka..sannu sara.., haba saude har da bakar magana kuma. daga kanta tayi tace '' na gama da ke wanda yake kan layi ya zo yau ba zan ga mutane da yawa ba .., girgiza kai yayi ya shiga cikin daki yana takaicin abotar sénateur da saude dan shi wannan kawance be amfana mai komai ba yana shiga usman ya yashi kuka ya saka daukan yaron yayi yana jijjigawa amma fafur yaƙi yin shiru yasan sarai tana ji bawai bata ji ba sai da ta gama sallar Mutanen ta ta shigo tana lissafa bugun France tana washe baki tace '' na dauki ribata na bawa sénateur kudin ta..., bakya jin yana kuka ne kikai burus da shi MUDAN ya faɗa yana kafeta da idanuwansa ya Allah ya Allah MUDAN ya kamata ka sakar min mara nayi futsari MUDAN yanzu idan ba bar baƙin nan ace na koyi hulakanci shigowar nan da nayi gurin sa na zo yayi maza ya sha ya kama gabansa Ta faɗi haka tana zama a kasan sumintin dakin ta miko mata dan yayi yace '' baki mai wanka ba ko...?, a kogi na saka shi ta fadi haka tana ciro mamanta a cikin riga da sauri dan ya cabka daman abin da yake jira kenan. ta gumi yayi shi kam sai dai godiyar Ubangiji, yana cikin jarabawa ba wata magana me dadi sai baka tsakanin su da saude bazai iya dorar da wani zama na jin dad'i da sukai ba gwara yanzu ya sami lafiya lokacin da cikin usman innalillahi wainna ilaihir raji'un Yini take kuka barin idan cikin ya takura mata , ta dinga fyece majina tana kuka, Ni wallahi Allah ka dena kallona duk kabi kana bin mutum da kallo yawa baka sanni ba. kin kuwa yi raser (shaving) kinsan ni sarai bana son wannan kazantar.. haɗe rai tayi tace '' idan na saka abar da ka kawo min wallahi gurin zafi yake min..har jimin ciwo yake fa.., kwantar da kai yayi yace '' daurewa za kiyi , kiyi kinji ko yar albarka tun da Usman yayi bacci zo na taya ki yi., tsura mai ido tayi yawa wata nutsassiya wayar ta ce tayi ringing da sauri ta tashi, washe baki tayi ta ƙara a kunne tace hajiya luba badai har kin isa Niamey ba..?, 08141785374.... charting only *Sanarwa...* *Allah ya nufa na gama littafin nan na ƁAƘIN SHAFI...* *Duk me bukata zai neme ni akan wannan number 08141785374...* *Please idan kin san ba siya zaki ba karki min magana ₦1000* Complete document Amina alhasan Muhammad opay 8141785374 ME BADA MAGANI KO YAR DAMFAR OUMYASMEEN EPISODE 2 Saurarawa tayi domin jin me zata ce dariya ya ƙara shekewa da ita harda buga cinya tace '' ba shakka shi daman haka arzki yake gashi nan mace ɗaya ta zamo sanadiyar arzikin dangin ku baki ɗaya yanzu sénatrice dan Allah a Avion (aeroplane) kika tafi Niamey ikon Allah kaji arzki bana jin kaf dangin mu akwai wanda ya taɓa hawa jirgi ko mudan..?, haɗa rai yayi ya dauke fuskar sa yana jijjiga usman da yake kuka saboda daukin waya ta wullar dashi bata sani ba , itama dauke kanta tayi tana cewa kinga sénatrice sai an jima baƙin hali ba zai saka MUDAN ya bani amsa ba wallahi kaf dagin mu ba wanda ya taɓa hawa Avion saurarawa tai domin jin me zata ce sai can tace '' to sai an jima.., kashe wayar tayi ta zauna tana Allah sarki uwa sha wuya ina ƙoƙarin zama kana miƙo min shi to nayi masa me ka riƙe shi lissafi zanyi. kallon da ya watsa mata ba shiri ta amshe , shi har yanzu be dena kuka ba dan haka ta ci gaba da rarrashin sa Assalamu alaikum uwar gida kuma amarya a gidan ustaz da sauri ta ɗago wata uwar buɗa ta saki tace '' sima bishira yau kune a gari.., gyara daurin zanin da yayi ya rataya jakarsa a kafaɗa yace '' billahilazi kinga mune a gari nan yar kasuwa naje shine na hadu da kawalliya acan sima me kyau.., ikon Allah ku shigo kun tsaya a waje... shigowa sukai da ido kawai mudassir yake bin su dashi yaga iya gudun ruwan su zama sukai bishira ya ajiye ledar fulawar da take hannun sa da albasa me lawashi yace '' kawalliya ya yan buge buge..?, Wallahi amini alhamdulilah sai gadiyar Allah saukar yaushe..?, cewar saude tana kallon sa daurin kansa ya gyara yana lanƙwashe murya yawa mace yace '' billahilazi na gaji da zaman gidan wasa kinsan ita haka bariki take idan ta juya maka sai ka nemi wata hanyar ka bata iska kawai da an buga bariki iya bariki yanzu kuma wainar fulawa zan dinga soyawa a cikin gidan nan tuna naga gidan naki Allah yayi mai albarkar zuwan mutane Sannan da shiri na da dawo kawalliya kinga bugun ƙasa ya kamata ki fara zan dinga gayyato miki yan bariki da yan hau cikin gidan nan ana chalarlewa kinsan karuwai akwai son maganin farin jini kawa..., a'uzubillahi minar sheɗanir rajim ku tashi ku fita banda tsabar iskanci da rashin tsoron Allah kuna maza ku dinga shigowa gidan matar aure jebe ku gardaye da gu kuna wani lankwashe lanƙwashe to wallahi kuji tsoran Allah tun kafin hutar Allah ta ciko Cewar MUDAN ya faɗa yana nuna su da wayar chaji tashi sima yayi yana dafe kirji tace '' ga kanan babban sheɗen ai mu ba gurin ka muka zo ba yanzu tsakani da Allah ina ma laifin ka saka mu a jinsin mata maza saboda tsabar rashin mutunci sai ka dinga ce mana gardi gaskiya idan ba don darajar ki ba kawa yasin yau a Commissariat de police zai kwana.., zo ku fita ko naci kaniyar ku mudassir ya faɗa yana nuna musu hanyar fita. MAI BADA MAGANI KO YAR DAMFARA *(saude me bada maganin aljanu)* Please hit the subscribe button and turn on the notification bell https://youtube.com/@nasreenminallah?si=fWc7Wzd4nPx_TifU Episode 3 Bishira ce ta cire zanin'ta da dan kwalinta tace '' sima riƙe me ai daman ita daudu riga ce yanzu sai na cire ta na ci kuttumar uban ka zuwa gida nan kuma yanzu muka fara tunda ba gurin ka muka zo ba har mu zaka nunawa bulala baka san *idan kaji ƙi gudu hakika ban ƙaraso bane ni kura uwar kare, Ni wallahi tuwon ƙaya ne maganin me haɗama ba gaba da gaba ba ni mazan suke gudu kuma ni suke tararwa a gaba Allah ba kyau ba dadin gamo dani..* wani naushi mudassir yakai mai dafe kuncin sa yayi yana zunduma ihu tare da fita a guje ganin haka sima ya cika zanin sa da iska ko kayan wainar sa be tsaya ɗauka ba juyowa gurin saude yayi ransa a ɓace ya nunata da yatsa yace '' wallahi idan har ba zaki dinga jin magana ta ba zanyi maganin ki saude daga yau sai yau ƙarna ƙara ganin ƙafafuwan wa'yannan yan daudun a gida na.., ganin yadda ya fusata tuni ta saita kanta fita yayi yana fita ta goya Usman a baya ta leƙa waje haɗa ido sukai da sima da bishira da kumburarran kumatu suma suna leƙowa harara ta zabga musu tace '' aikin banza wallahi kin ban mamaki ashe cika baki ne maza zo ki ɗauki kayan ki..., ƙarasowa sukai yace '' ke wallahi bawai karfina ya fi ba gudumar da yasaka min ya bugar min fuska ce taya za'a daki mutum da guduma ace ba zai gudu ba har taurari na gani.., dariya sima da saude sukayi sima tace '' lallai kinji jiki da hannunsa ya dake ki.., da sauri ya juyo jin alamun tafiya yace '' maza maza bani kaya'na , na bar nan gurin kinsan zama gu ɗaya tsauysayi.., shiga tayi ta dauko masa kayan sa dana sima tafiya sukai ta shiga cikin gidan ta zauna tana ɗaura magani tana yar wakar ta. mudassir ne ya shigo sallama yayi kallon inda yake ba tai ba ta ci gaba da abin da take buɗe doro din ruwa yayi zai zuba yayi alwala gani yayi babu da sauri ya ɗago yace '' saude ba ruwa a cikin gidan nan..?, badai wanda na ɗebo har ya ƙare..?, ci gaba tayi da abin da take bata kula shi ba sai da ya ƙara maimaita mata maganar da sauri ta ɗago tace '' mudan me kake nufi fito fili kace na tara mata sun maka barnar ruwa abin da ke zuciyar ka kenan wai kai dan girman Allah mudan me ya saka kake yawan saka min ido a cikin sha'anina dazu ma su kawa suka zo ka ci musu mutunci ka kora su haka ya dace..? yanzu kuma ka buge da cewa ruwan da ka ɗebo har ya ƙare.., Kasa magana yayi domin abin nan na saude sai addu'a yawa wata me iskokai. daukan butarsa yayi ya fita ci gaba tayi da hada maganin ta duniyar ta shar bata da wata damuwa jin alamun kamar ana jan mutum yana turjewa ta miƙe ta leƙa soro tace '' sima bishira lafiya naga kuna ta bin bango wannan mahaukaciyar ina kuka samo ta..?, jaka sima ya saɓa a hammata ya yarfe hannun sa yace'' wallahi kinga a hanyar kukar iya na gano wa'yannan mutane wai gidan saude me maganin aljanu suke nema..nace faɗuwa ta zo dai-dai da zama nasan gida shine na danni kirjin aunty bishira muka dawo kinga idan anyi *Équilibre* kin bamu namu rabon.., gaban tane ya wani yau take ganin jarabar rayuwa ya za tayi da wannan mahaukaciyar sai zare ido take tana galla mata harara ja da baya tayi tace '' bisimallah ku shigo kubi ta a hankali har ta shigo Allah ya saka ma sauran aljanun sun makale a kofar gida da baza ta taɓa iya shigowa gidan nan ba .., Wallahi malama haka muke ta fama dattijuwar ta faɗa tana share kwalla da ya'yan ta maza biyu. saude kan'ta ya kara fasuwa tace '' karki damu inna zanci uban su dan durin uwar ku ba zaku cika ta ba kai me katon kai har hararata kake ko...? to maza cika ta ko na kona ƙona ka.., sami da bishira da suka choge a baya suna liƙowa suka hada ido suka jinjina kai wani ikon Allah sai ga mahaukaciya ta shigo cikin gidan da sauri suka shigo tace '' sima maza rufe min kofa bishira rufe min kofar bayi karsu samu damar shigowa.., da sauri sima ya rataye mayafin sa ya tafi zai rufo kofa sai ga MUDAN nan ya shigo da sauri ya matsa yana sosa sumar sa da ta sha relaxer ratsa shi MUDAN yayi ya wuce ransa duk a ɓace dattijuwar matar nan tace '' ina wuni.., da sauri MUDAN ya tsuguna yace '' ina wuni inna mun wuni lafiya.., Lafiya qalau dan nan gaisawa sukai da sauran yaran nata da sauri SAUDE ta bi bayan sa domin kar ya kwance mata zani a kasuwa me makon ya shiga daki sai ya fita bin bayan sa tayi suka tafi soro cikin matsanancin ɓacin rai yace '' SAUDE har yanzu she zan dena nanata miki magana ɗaya ne..?, turo daurin ta gaba tayi tana sosa kitson ta da ta haɗe ko tsaga ba'a gani tace '' sai ranar da ka dena yi min hassada a cikin gidan nan bansan ina ka dosa ba .., Kekai bansan ina kika dosa ba wa'yannan yan daudun da kika ƙara gayyato su me na fada miki ɗazu..?, kauda kan'ta tayi tace '' na manta tuni nake buƙata.., ɗaga hannu yayi zai zabga mata mari sai kuma ya damke yan yatsun sa ya dunkule su gu ɗaya juyawa yayi ya fita ba tare da yace komai ba, saita kan'ta tayi tana gyara daurin zanin ta , ta shigo tace '' inna sannu na barku kuna ta jira..ko..?, Dattijuwar tsohuwar nan tace '' wallahi bakomai a haka ma kina kokari abu ba mutum ɗaya ba , ba mutum biyu ba .., zama tayi tace '' to ya za nayi harkar temako ce tun da mahaifina ya mutu ya barmin wannan harkar ta temako yanzu ma wallahi wani me lalurar aljanu aka kawo min daga Cameroon to na gaji yamma ta kawo kai nace su dawo sai gobe..., Allah sarki sannu yar nan shi ya saka naji muryoyi kala kala kamar na faɗa. gyara zama saude tayi kan'ta ya fasu tace '' yauwa idan da kin gan sa sai kin tausa ya mai wallahi kinga yadda yake rubos abin aba'a cewa komai.., Allah dai ya yemake mu yasa ka mun zo a Sa'a Cewar dattijuwar matar nan SAUDE tace '' amin ya Allah aikin mu tamkar yankan wuka ne yanzu dai me yake damun ta.., guri su sima da bishira suka samu suka zauna suna jiran suji me za'a ce domin har ga Allah sun fara jin tsoron SAUDE. wani namiji wanda yake riƙe da mahaukaciyar da take ta fisge fisge yace '' wallahi tun da taje ɗiban ruwa a rafi shikkenan fa aljanu suka fyaɗe ta bamu kara sanin inda kan'ta yake ba duk wani guri munje sai aka yi mana kwatance wajen ki duk wanda ta daka da hannun ta sai ya sami karaya idan kuwa ta damfara mutum da ƙasa to wallahi shikkenan sai dai wani ba shi ba a garin mu, mutane da yawa sun mutu ta dalilin ta har cin mutum take ta gwaguyo naman sa...tas tabar ƙashi. wani irin gumi ne ya fara karyowa SAUDE ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba gashi duk ta saka an rufe kofa wani irin yawu ta hadiye me kauri ta fara kifta idanuwa yawa wanda tayiwa sarki karya ci gaba zai yi da bayanin sa jikin SAUDE a sanyaye ta daga mai hannu domin zancen da yake yi ba ƙaramin saka ta cikin rudani yake ba kai ya gyaɗa su sima kuwa ta kurewa sukai guri ɗaya kamar kace ket su gudu. bagaye tayi ta dauki buta wacce MUDAN ya shigo da ita ta zuba ruwa a hannun ta ta fara motsa bakin ta nan kuwa ba abin da take faɗi in banda innalillahi wainna ilaihir raji'un tana kasa da idanuwanta domin wannan mahaukaciyar ita take kallo tana cure hannu guri ɗaya tsoran ta ɗaya karta cinye mata naman kwakwalwar ta gwara idan karaya ce da sauki akan mutuwa wani ihu ta saki da sauri sima ya tashi yace '' kai ina wallahi bazan iya zama ba kai Bashir idan zaka tashi mu tafi ka tashi yawa wa'yanda aka ɗaure mun zauna hantar ciki na daddatsawa.., kifta musu ido SAUDE ta fara domin idan suka tafi tana cikin wani irin mawuyacin hali bishira yace '' Bashir gatsal ka mai dani namiji.. billahilazi ba inda zani sai naga kwal uwar daka zama daram yana me nakuɗa ko dan na cusawa wancan mutumin takaici.., Idan kai baka guma mai takaici ba to wallahi zama a gurin nan zai guma maka takaici zaka hadu da dana sani na har bada idan ma ka rayu kenan cewar sima.. yaƙe SAUDE tayi ganin kar suga ba tai wani abu ba karkata buta tayi ta dan motsa bakin ta ta tofa yawu a ciki sannan ta watsa wa mahaukaciyar nan wani girgiza tayi sai kuma ta kame kam.. tace '' inna ko zaku shiga daga ciki ko kuma kubi wacce siririyar kofar ku fita sai ku kullo zanyi aiki ne.., cikin sauri suka cika ta suka fita domin suma cikin su ya duri ruwa ita kuwa SAUDE tayi haka ne domin ta samu ta kubuta itama guduwa za tayi shaf ta manta da batun usman da yake bacci a bayan ta takan ta kawai take yi gadai mahaukaciyar nan tun da ta kame bata ƙara wani motsi ba saita ta tabbatar sun fita tace '' bishira muyi takan mu yau ka kawo min jaraba har cikin gida na.., ai karawar ta ke da wuya mahaukaciya ta miƙe taka zuba uwar miƙa taku ɗaya tayi gidan sai da ya amsa kan SAUDE ne ya shiga juyawa bishira kuwa da sima ihu suka saka da ruruwa ganin mahaukaciyar na yowa kan'su Curewa sukai gurin ɗaya yayin da sima yake kokarin kwacewa daga rikon da bishira yayi mai ganin za ayi babu ya ga tsara mai cizo cikin fitar hayyaci bishira yace '' wayyo Allah shikkenan yawa ta kare wallahi ta cije ni.., ba ƙaramin tashin hankali SAUDE taji ba da wannan zance jikin ta ya soma rawa ga mahaukaciya sai za gaye su take ba damar guduwa share kwalla tayi tace '' Allah ya shigo da MUDAN ya ceci rayuwa ta yau ina ganin ta kaina.., sima da ta fyece majina yace '' kike gani ko muke gani annabi yace imanin ɗayan ku ba zai cika ba har sai ya sowa kansa a binda yake sowa dan uwan sa amma shi ne da yake , ke yar kwal ubace kike fadar haka.., za kuyi shiru ko sai na tura kanku cikin masai. cewar mahaukaciyar nan tsit sukai tamkar ruwa ya cinye su sima ya kama baƙin sa yana zare idanuwan'sa ba irin addu'ar da be ba ji sukai ana girgiza kofa wani sanyi ne ya shige zuciyar su dan ganin me ceton su yazo da sauri wannan mahaukaciyar ta doka tsalle ta fita a guje tana cille da robobin maganin SAUDE kafa me naci ban baki ba daki SAUDE ta shiga a guje sima ya tafi madafa yana zare idanuwan'sa da wata ƙatuwar tukunya wacce akai bikin kanwar mijin SAUDE suka ajiye anan basu dauka ba ita ya shiga ya rufe kansa da murfin tukunyar domin a ganin sa ba me iya gani shi. bishira suka bari a tsakar gida yana fyece majina tare da ihu domin ba wajen boya ko ina sun rufe. ɓare baki yayi yana cewa ya MUDAN ya MUDAN kazo ka cece rayuwa ta wannan mutanen makiya, Allah ne la'anannu in banda tsinancewa mutana tare da ku, ku gudu ku barni.. Sima da yake cikin tukunya yaji irin ihun da bishira me kyau ya zage yana yi mahaukaciya na dura ashar sai yaji cikin sa ya kulle saboda tsabar dariya da ta ciyo shi ya zage ya koma gardi sak. kofar madafa mahaukaciyar nan ta ja , ta tsaya saboda jin kusur kusur shiga tayi ta dauki zabgegiyar muciya ta buɗe murfin tukunya ta soma raɗawa sima bare baki yayi yana gurza ihu tare da tara hannu a ka hannu ta saka a baki tace '' dan ubanka yi shiru.., bakin sa a fashe fa majina da hawaye sai zuba suke ya kama bakin sa yana gyada kai.., shikkenan yasan irin tasa kaddarar kenan Allah ya fitar dashi ashe a fili yake fadi da karfi wata dariya ta sheƙe da ita tace '' dan ubanka ba kai ne jikan mirze dan gidan aljani bindu.., ai besan lokacin da wage baki ba ya saki kuka tace '' wallahi sunan babana yunusa sani baban gida ko sau daya bamu hada dangi da aljanu ba.., rufe min baki makaryaci yau za kuci uban ku har na cikin daki bazan kyale ba sai na bawa aljanu jinin ku sun shanye..tas yan iska SAUDE jin hakan ke da wuya ta ɗora hannu aka tana sakin siririn kuka yau tana ganin ta kan'ta usman ne ya tashi sanin halin yaron yana da ihu sosai idan ya tashe ba'a bashi a abinci ba dan haka tayi sauri ta sauko shi ta ciro mama ta bashi yana sha tana kuka tana riƙon Ubangiji ko dan wannan shayar da yaron da take Allah ya kawo musu dauki cikin gaggawa kafin aljanun su zo.., NIAMEY GOUDEL lubabatu daga ina kike tun ɗazu nake kiran wayar ki amma bata shiga wallahi kin sakani a cikin tashin hankali a gaskiya idan har ba zaki chanza halin ki ba to zan faɗawa baba ki koma gaban sa karki lalace ace ni ce na lalata ki cire mayafinta tayi ta rataye a kafadar ta , tace '' aunty safiya ki fito fili kice na tafi gidan mu kin gaji da riƙe ni shi ne magana amma wannan kwana kwanar ba inda zata kai ki ni nafi gane ɓaro baro yanzu daman ko mutuwa iyayen mu sukai ba zaki iya riƙe ni ba .., lubna na haka bane tambayar ki fa nayi ina kika ce abban fareed yace min cewa kikai ya sauke ki a bakin titi shima be san ina kika tafi ba , ba dole na damu ba.. juyowa tayi ta rufe idanuwan'ta tace '' au sai yanzu na gane ma inda kika dosa cewa za kiyi kina zargina ni da mijin ki to maza zo ki chaje ni tunda tsakanin mu ba , ba amana.., Aunty safiya ta dafe kanta tace ''Innalillahi,, sénatrice ta amshe zancen da cewa wainna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fimasiba ce nasan karshen zancen naki kenan na zame miki annoba da masifa a cikin gida to kar ki damu arziki kashi nima na kusan takawa ta faɗa tana hayewa kan sama jakarta ta buɗe ta dauki mukulli zuwanta gidan ta kori yara kasa ita tarike dakin gaba ki ɗaya dan a cewar ta bata san takura, budewa tayi ta shiga cire takalmin ta ta fara da ya ishe ta ga jikin ta duk ciwo yake mata Saboda motar da ta shigo acike take kudin ta ba zai isa ba shi ne ta hau motar me araha cire kayan ta , ta soma yi ta ninke guri ɗaya shiga toilet tayi wanka ta tayi ta fito kwankwasa kofa taji ana yi da sauri ta tashi ta budr kofar haɗe rai tayi tace '' ya mukai dake ina cewa kayan nan ba cewa kikai ba kwana biyu za suyi a guri na..? a gaskiya senatrice idan har kayan nan zasu kara kwana sai kin kara min kudi wannan harkar da nake yi duk bana fita saboda idan ba irin ku ba , ba me zuwa rantar kaya a fusace ta kwaso kayan ta miƙa mata ta rufo kofar ta , tana jan tsaki duk kudin hannun ta sun kare motar ma da ta ɗauka aka yi parking dinta a kofar gidan SAUDE jaka shidda ta basu a haka ma dakyar suka yadda. Kwanciya tayi a gado tana sauke ajiyar jin cikin ta yana kukan yunwa ta miƙe da sauri ta fita kitchen ta shiga kenza ta samu tana girki tace '' kenza badai yanzu kike ɗora abinci ba..?, ajiye ludayin hannun ta tayi tace '' eh wallahi aunty sénatrice yanzu nake zuba gishi ban dade da zuba shinkafa ba ..., juyawa tayi bata ce komai ba aunty safiya tace '' lubabatu be kamata kina yawo da towel ba a cikin gidan nan ke ba abin da ya dame ki duk wanda zaki ci karo dashi sai dai shi yaji kunya ba dai ke ba.., zama tayi ranta a ɓace tace '' aunty safiya wallahi na gaji na gaji rashin aure hauka ne ko me da kowa zai dinga takura min yana zuba min karan zuƙa dan nayi yawo da towel wani abin ne ba ni da ke da su kenza bane a cikin gidan nan duk inda na tafi a dinga nuna ni da baki to insha'Allahu na kusan yin aure ehyee nima in je gidana inji ko wacce mace me take ji da take wura hanci tana baza uban iko a cikin gidan ta. sakar baki tayi tana kallon ta ita wallahi yanzu tafara zargin anya kuwa lubabatu bata da aljanu bayan kawai wannan zancen faɗa take samarin nata korar su take da bani bani me naci ne zai zauna yau ace kawo kaza jibi kawo kaza dole mutum ya gudu tace '' idan kin gama amfani da wayar tawa ki bani wannan wayar da kika bani dakyar take dannuwa.., ta faɗi haka ta na miko mata wata matacciyar android amsa tayi tana hade rai ta mike ta hau sama bata jima ba sai gata da wayarda ta fita da ita ciro layinta tayi ta saka a wayar ta ta mayar wa da aunty safiya nata. *08141785374* *iya reacting din Ku iya readmore* Copy is not allowed 🗣️ Hakkina ne mallakina ne kubar min kayana ban yadda ayi amfani dashi ba ta ko wacce siga. https://youtu.be/WoCX8WbJOuU If you know that you're not going to talk to me about my novel or something that concerns me, please don't talk to me at all. I don't like what you're doing following me around persistently and talking to me about things that don't concern me. Episode 4 Haɗe rai tayi tace '' ungo.., aunty safiya amsa tayi tare da yin murmushi tace '' lubabatu Allah ya shirye ki ya ganar da ke gaskiya.., au daman aunty kallon kafura kike min gwara da yau kika fito fili kika faɗa min sai nasan irin zaman da zanyi da ke amma kya tsaya yin kwana kwana ki fadi abin da ke zuciyar ki kafin ki fadi yan waje sun fadi dubin haka ina cewa idan na wuce nuna ni ake yi ga karuwa nan da zagi yana fitowa a jikin mutum yasin aunty bazan gano ba.. shiru tai mata har tayi ta gama ta tashi har ta hau kan matattakala ta farko ta jiyu tace '' nifa yunwa nake ji gashi ba wani sauran chanji a guri na balle na siya wani abin.., ta gumi auntuy safiya ta zare tace '' lubabatu bani dashi wallahi komai ke faruwa acikin gidan nan kin sani ba sai na tsaya ina miki dogon jawabi ba.., Oh Masha Allah amma aunty baki iya rike amana ba wallahi bakomai laifina ne da na zo na tare miki a gida wata ran gidana zaki insha'Allahu. dariya aunty safiya tayi tace '' Allah ya amince sénatrice nima na ɗana wannan sunan kuma gaki nan kallar ki kallar sanatoci.., murmushi tayi na jin dadi tace '' idan ma ba har zuciyar ki, kika faɗa min haka ba to wannen ke ta shafa ni na dade da sanin cewa nidin kallar can ce banan ba.., kenza ce ta fito daga kitchen tace '' aunty Dan Allah zaki min kitso..., dan jim tayi tace '' wallahi nagaji kenza da kinsan irin yawon da nayi da bakar wahalar da na sha da baki mim wannan zancen ba.., kenza tace '' to ko zuwa gobe ne .., ke a kwai inda zani gobe maman kice ma zata ara min kudin mota danni wallahi nayi karaf babu ko kobo a jiki na. Auntu safiya tace '' to Allah ya kawo na baki ina zaki kuma..?, sama tayi da idanuwanta ta gara su sukai fari ba'a ganin baki tace '' unguwa ina tunanin bazan dawo ba sai jibi..., kai aunty ta jinjina lamarin lubabatu abin kullum gaba gaba yake tace '' kwana fa kika ce za a ina zaki kwana..?, Gobe amal zata yi Joyeux anniversaire (Happy birthday) to ina tunanin na kwana acan yau kasuwa za muje muyi siyayya. ajiyar zuciya ta sauki tace '' idan dai na isa dake lubabatu karki kwana taya za ayi daka haduwa kije gidan mutane ki kwana wannan wanne irin son abin duniya ne dan Allah kanwata ki gyara halayen ki wallahi wani zubin tsoro kike bani kaf halayen ki sun sha banban da wanda mahaifiyar mu tai mana tarbiya akai. lubabatu jingina tayi da bango bata ce komai ba lura da tayi aunty nata , ta gama zancen da za tayi ta haye sama tana mita a zuciyar ta. WANNAN KENAN Kofar dakin da saude take ciki mahaukaci nan , ta bugi gumi ne ya ƙara karyowa SAUDE ta kwantar da Usman ba irin addu'ar bata zo bakin ta ba tunawa tayi ai acikin daki take ta kirawo MUDAN mana da sauri ta ajiye usman ta dauko wayar ta laluban number MUDAN ta fara cikin Sa'a ta ganta danna mai kira tayi amma har ta katsai ba dauka ba ƙara kira tayi a wannan karon ya dauka kuka ta fashe dashi ta fyece majina tace '' dan girman Allah kazo ina gab da mutuwa idan har baka zo ba ka temaki rayuwata dan Allah MUDAN..., Cikin tashin hankali yace '' tun dazu na dawo daga masallaci ina ta buga kofa baki buɗe ba me ya faru..?, ƙare fyece majina tayi tace '' ka tawo da kartin maza kai ka tsaya daga soro karta kashe ka.., ita wa ya tambaya cikin sauri da zakuwar me za tace kuka ta ƙara rushewa dashi harda shashsheƙa tace '' dan Allah kazo bazan iya fadar komai ba yau ina ganin takaina.., kashe wayar yayi ya fito daga shagon sa , shiga cikin gidan su yayi ya biyo ta karamar kofa sai dai itama a kulle take dole sai da ya haura ba komawa ya gani sai mahaukaciya da take riƙe da muciya ta yiwa bishira jina jina ga sima nan ma bakin su duk ya farfashe sai hakuri da magiya suke bata jin takun tabiya ta juyo ja da baya ta fara yi gaban ta na faɗuwa. tsawa ya daka mata zama tayi jikin ta yana rawa kallar su sima yayi yace '' kuzo ku fice ko yanzu Ubangiji ya nuna muku ikon sa idan kunyi hankali ku gyara idan ba kuyi ba jikin ku ya kara faɗa muku.., da sauri suka tashi sima me kyau yace '' to oga ina ce ma hanyar fita..?, wani kallo MUDAN yayi masa bishira yace '' Allah ya gabatar ran malam yi hakuri.., dauke kai MUDAN yayi suka lallaɓa suka tashi cikin su yayi ruɗu ruɗu bib bango suka dinga yi suka fita. ganin sun fita da gudu mahaukaciyar nan ya fita cin karo tayi da wa'yanda suka kawo ta , ta dinga fisge fisge suka rike ta. MUDAN leƙowa yayi yace '' yauwa daman ku zan nema karta ɓata ba lallai ne tasan gari ba ta gama yi mata tofin tace idan kunga abu be yi sauki ba ku dawo abin sadaka kuma ku barsa.., ya faɗi haka ne domin ya rufa mata asiri tsohuwar nan tace '' mun gode Allah ya saka da alkairi dan Allah yaron nan kai mata godiya kaga sai fisge fisge take gwara mu tafi kar ta shiga cikin gidajen mutane abu ya muzanta.., cikin tausayin tsohuwar yace '' Allah ya bata lafiya ba damuwa za taji.., amin suka ce suka juya suka tafi ya koma cikin gida buta kofar dakin da take yake yi amma shiru ba alamun za'a buɗe baya son ɗaga muryar sa kar ayi zaton wani abu ke faruwa tsakanin su duk da ko da yaushe wannan halin SAUDE ne idan faɗan suna magana su kaɗai sai tai ta ɗaga murya hakan be dace ba ajiyar zuciya ya sauke yace '' SAUDE buɗe min ni ne na fitar da ita.., buɗa taga tayi ta haɗa uban gumi tace '' ka tabba MUDAN kar na fito naga ba haka ba.., kafe ta da ido yayi yace '' raina zai ɓaci ko..? tunda ai kinsan na sa ba yi miki karya. , sosa kan'ta tayi ta buɗe kofa hannu usman ya miƙo mai ɗaukan sa yayi yana shafa kan yaron ya zauna yace '' SAUDE idan na rantsai ba zan yi kaffara ba darajar wannan yaron kika ci da tuni kema ta kama ki.., zama tayi tana zunburo baki ta kauda kan'ta yace '' SAUDE kinga yanzu dai ki tashi kiyi wanka sai kiyi bacci ki huta kannan naki, yayi datti ki tsaife shi..., ɗagowa tayi ta kalle sa sai kuma ta tashi saboda yau halarcin da yayi mata duk da ko dacan din yana ƙoƙarin wajen cinta shanta ya faranta mata ita da , ɗan su. dawowa tayi tace '' babu ruwa.., daukan usman yayi yace '' zo ki karbe shi ba samu miki ruwan da zakiyi amfani dashi.., amsar sa tayi ya dauki botiki ya fita zama tayi a kan kujera yar tsuguno ta zuba ta gumi usman sai wasa yake tayi amma tayi banza dashi yau Allah ne ya auna mata arziki da tuni yanzu ruwan wanke gawar ta za'a debo. dariya ce ta subbuce mata lokacin da ta tuno ihun sima mahaukaciya na ce mai kai dan gidan sarkin aljanune tana cikin wannan tunani yace '' ga ruwan nan.., da sauri ta ɗago tace '' ungo shi..., karɓa yayi ya miƙo mata wata leda amsa tayi ta buɗe shampoo ne da shaving cream sai sabon toothbrush rufewa tayi bata ce komai ba ta wura wuta ta dora ruwan zafi tana tsifar kanta ba ƙaramar suma ce da ita ba sai dai kazanta tahana ta tayi kyau mai da dan kwalinta tayi ta zuba ruwa a cikin botiki ta shiga bayi. zama yayi yana jiran ta , ta fito ya koma shagon sa yana wannan tunani ta fito tashi yayi yace '' ungo sa zan buɗe shago kafin lokacin karatu yayi.., amsar sa tayi tace '' ko bari ba zakai ba na shirya..?, to kawo shi maza ki shirya dan Allah SAUDE ki fadi gaskiya baki ji daɗin jikin ki ba ko ta ina iska na shigar ki..?, wallahi sai kikai kyau.., da sauri tace '' to fito fili kace min bani da kyau amma ka tsaya kwana kwana.., murmushi yayi yace '' daga magana sai ki juya min zance ki maza ki shirya ki amshe shi.., banza tai mai ta shiga daki saka kaya tayi bata fasha mai ba balle ta gyara gashin ta , ta fito tace '' bani shi.., bata shi yayi yace'' zan turo abeedah tai miki kitso.., ajiye usman tayi tana cewa a'a wallahi ba kitson da zan yi daga wanke kai sai kace sai kuma kitso karma Ka kirawo ta nace ba zatai min ba kace na tozarta nan da anjima baki zanyi akwai wanda nai wa alkwari za su zo insha'Allahu dan haka bani da lokacin yin kitso. da sauri ya juyo da har ya fara tafiya lallai wanda Allah ya shiryar shine shiryayye kasa magana yayi ya juya ya ci gaba da tafiyar sa. zama tayi akan dokin kofa tana cewa da hallacan yiwa mutane shiru kamar ba ɗazu ka sha ba shi ne yanzu kake neman rigama wallahi baza ka sha ba na gaji kuma. da sauri ta shiga daki jin wayar ta nane man dauko ɗauka tayi ta kara akunne tace '' sénatrice barka da yamma hmm da tuni an sanar miki da mutuwar mu nida su sima.., da sauri tata shi daga kwanciyar da tayi tace '' innalillahi me ya faru..?, bata labarin komai tayi ta da ɗa , da cewa Wallahi da ace MUDAN be kawo mana dauki ba da yanzu sallar gawar mu ake yi kai yau naga bala'i kina ji fa matar murɗa wuyan mutum take shikkenan an gama sai dai uwarka ta haifi wani.., Dariya sosai sénatrice take yi tace '' wayyo Allah ciki na yau kin haɗu da gamon ki me MUDAN yace nasan ya tsine min tun daga sama har ƙasa ko..?, haɗe rai SAUDE tayi tace '' yanzu ina faɗa miki damuwata kina tambayar me mijina yace miki kinsan halin sa ai bashi da hayaniya ko sunan ki be kawo a zancen nan ba kuma nima da ya cece ni bece min kala ba , wallahi kin ban mamaki dariya ma kike sai kace ba ke kika fara tallata min wannan sana'ar ba.., da hallacan rufe min baki da na tallata miki sai kuma nace dole sai kinyi talauci ke damun ki nace mu haɗa hannu da hannu tunda ke kin shiga daga ciki ni yanzu ina fara sana'ar nan kallon karuwa za'ai min, bani da aure ina sai da maganin mata kinsan halin Mutane ba'a da gadon ka ana da na maganar ka amma duk irin hallarcin da nayi miki shine kike faɗa min maganar banza bakomai yanzu yaushe sima ya dawo daga Lagos ɗin..?, shiru SAUDE tayi domin itama ba kanwar lasa bace bata son faɗa dan tana cikin talauci sai ta dinga raina mata wayo ita gwara ita daga sama take cin kudin nan ita fa yanzu mutane ma bokanniya suke ce mata shine zata faɗa mata maganar banza. senatrice ce tace '' hello hello magana fa nake kinyi shiru ko matsalar network ne.., kamar tana gaban ta , tace ina jin ki tsayawa nayi ki gama faɗan ki, sanin kan kine ko MUDAN da yake miji na bana tsayawa yayi min faɗa balle ke har kina cewa na rufe miki bakina senatrice talauci ba hauka bane ai.. Eyee kinga bana son harkar bura'ubanci kinsani sarai ba'a nuna ni da yatsa balle a faɗamin bakar magana kinga abin da kika haɗa ki turo min ta my nita ki ɗauki takardar sai ki tura min ta wayar MUDAN tunda ke ba babba ce da ke ba , bani da lokacin da zan zo karɓar. to kawai tace ta kashe wayar shiga daki tayi ta ajiye usman da yayi bacci sallama taji da sauri ta fito tace '' sannun ku da zuwa kun sha hanya..., yauwa dai matan suka ce tare da gaishe ta shinfiɗa musu tabarma tayi suka zauna shiga daki tayi ta dauko magungunan ta ta fara bayani tana cewa wannan shi ake kira da sa kishiya kuka ba boka ba malam. amma shi saboda da zafin sa bana bawa me kishiya ai zai zama da cutuwa. da sauri matar tace '' dan Allah ki bani shi wallahi ina da kishiya ta kwace komai mijin ma wata rana ina ganin kwace min shi za tayi komai ita ce wata ran ma da sunan'ta yake kira na dashi sai daga baya ya canza.., girgiza maganin tayi yayi murɗik kamar ruwan dauri dakyar yake iya juyawa tace '' ku ne yan uwanta hakane dan wallahi saboda shu'umancin'ta sa bana son bayarwa.., magiya suka fara yi mata dakyar ta basu suka bata kuɗin'ta suka tafi. ɗaukan hijabinta tayi ta goya usman abaya ta fita ba tare da ta tambaye shi ba tsaye gidan su sima ta nufa sallama tayi ta shiga sai zunduma ihu yake ana gasa mai gadon bayan sa domin ya daku iya dakuwa gaishe da iya tayi da sauri iya tace '' ashe kinji labarin tankar da ta kusan kashe salmanu.., zama tayi tace '' iya tanka kuma.., Wallahi cewa yayi babbar motar nan ce ta kade shi dawowa yayi yana wasu irin surutai marasa kan gado kalli gadon bayan sa duk a kwashe daman daga ganin wannan abu sai dai barin mota.., majiya sima ya fyece yace '' iya wacece fa zo..?, da sauri SAUDE tace '' sima murya tace baka gane ba.., yar kutumar uba ina zan gane muryar ki, ta iya bayan duk kece silar komai iya billahilazi, Iya ji nake kamar ban taɓa jin dad'i a duniya ba.. da sauri iya ta kalli SAUDE tace '' SAUDE me yake faruwa kinsan wanda ya ajiye tankar ne kome ya faru.., haba iya kalli bayan yaya salmanu sosai ki kura mai ido wannan ba wani barin mota mutum ne.. da sauri ya dago daga kwanciyar da yake yace '' to shegiya uwar bakin hali tsaka uwar munafukan duniya annabi yayi gaskiya da yace duk inda aka ga irin ku a buge shegu a huta dan uwarki zaliha a gaban ki abin ya faru..?,kuma kici gaba da cire ni daga cikin jin sin ku.., turo baki tayi ta shiga daki da sauri SAUDE tace '' sima na kasa fahimtar komai wai bayan fitowar ku daga gidana babbar mota tai barin makauniya dakai ga bakin ka tamkar na jaɓa yayi dogo.., dauke kai yayi yace '' iya dan Allah dauko min zani na yanzu salon wani ya shigo ya ganni ba kaya ni daman kirji ba kirji ba a gama gane min yan kirga dangina.., SAUDE ta tash ta miko mai iya kuwa banza tai mai ta tashi ta shiga daki ƙasa ƙasa yace '' ko da wasa naji kin fadi abin da ya faru yasin zaki sani ne sai na yi miki bura'uba domin ke na saito bane dake abin kunya ne ace an kama mu, an dake mu ke ya kamata ace ta tumurmusa saboda ke kika fara tabo ta da baki mata tofi ba da duk abin be kasan ce haka ba ke gaki uwar iya gwana ta gwanaye Allah ya rufa mana asiri daba kar mu ba yasin na so ta sauke miki muƙamuki.., kama haɓa tayi tace '' sima ni kake faɗawa haka..?, na fada miki din kanwar uwata ce ke ko ta ubana ina cewa kai ni kikai inda za'a halakar da ni.. a fusace tace '' karka sake ka faɗa min maganar banza ni nace maka kazo matar nan naga ku kuka kawo ta ina cikin kwanciyar hankali na kuka kawo min jaraba ina dakin nan har gudawa na saki ban san ma nayi kashi ba sai da nazo wanka na gani.., dariya ya sheƙa da ita yace '' to aike naki me sauki ne nida ta hadani da jinsin aljanu ke kinga yadda ta dinga zuba min sanda kai wannan bata da imani ko kaɗan..ni wank abin ba wallahi ban san ina fadi ba kawai zuwar min baki na yayi bishira me kyau yace dan annabi tanko kiyi hakuri ki barni da raina wallahi duk da banyi karatu ba nasan kawai ya faɗa ne bawai akwai shi ba , amma abin mamaki sai ta barshi ta dawo kai na shine nima na dinga dan annabi tanko kiyi hakuri SAUDE na zabtu tamkar tura ta naki ta dinga duka na tana rawa tana cewa Annabi Tanko.., saude saboda dariya har faɗuwa ƙasa tayi hade rai yayi yace '' kaji yar masara muguwa me makon ki ta yank jimama mi shine kika dariya.., cikin dariya tace '' dan annabi tanko sima kaf cikin annabawa babu tanko.., banza yayi mata tashi tayi tace '' bara na leƙa bishira naga me yake faruwa iya sai an jima.., fitowa tayi tace '' to sai an jima ki gaida mijin naki Nagode sosai wallahi kaf makotan nan nawa nasan ba wanda zai zo dubiya amma ke daga ji kin zo yar albarka.., yaushe kuwa za su zo wannan yaron da ana canza shi da tuni wallahi na canza shi tabawa yanzu har tsoran tafiya masallaci nake an dinga nuna ni da baki idan na zo wucewa a nuna ni da baki ba mutum kake ƙi ba halinsa kake ƙi.. Copy is not allowed 🗣️ Hakkina ne mallakina ne kubar min kayana ban yadda ayi amfani dashi ba ta ko wacce siga. https://youtu.be/WoCX8WbJOuU If you know that you're not going to talk to me about my novel or something that concerns me, please don't talk to me at all. I don't like what you're doing following me around persistently and talking to me about things that don't concern me. Episode 5 Dayar sima ya iya tashi ya ja zanin sa kirji ya soke a hammata yace ''Dan ƙari maƙari baffa yanzu abin da ya same ni ne be dame ka ba kenan wallahi da ace wani yaji wannan maganar gwara ayi min duka da icce haba wannan wacce irin magana ce a tunani na kai ne mutum na farko da zaka fara shiga wani hali da idan aka ce bani da lafiya.., zama baffa yayi yace '' saboda gaka kanin mahaifina ko yarinya yi tafiyar ki karki kara hurɗa da irin wa'yannan mutanen wallahi wata ran idan baki wasa ba hmmm kashe miki aure za suyi..., Innalillahi wainna ilaihir raji'un iya kina ji ko sheɗanu muka zama kenan dan annabin Muhammad sallahu alaihi Wasallama ki saka baki iya. To SAUDE tace tayi musu sallama iya tace '' gaskiya a bin da kake baya dacewa ai hannun ka baya rubewa ka yanke kayar.., Tabawa sauna kuma ake kai hannu a yanke wannan dai yaron nabar miki shi halak malak.. ya faɗa yana tashi daga zaman da yayi zama tabawa tayi tace '' kaga ko salmanu ka nutsu ka dinga bin duniya a sannu.., to iya zan dinga tafiyar sanɗa shikkenan magana ai ta kare nabi maganar ki.. takaici ne ya hata magana Wannan kenan Bayan fitar SAUDE gidan su bishira ta shiga sallama tayi mahaifinsa da yake zaune yana mai fifita yace '' a'a sannu da zuwa ashe haka abu ya faru..?, zama tayi tace '' baba ina wuni.., lafiya qalau alhamdulilah ya kuma tsauysayi. hmmm baba alhamdulilah mun tsallake Rijiya da baya. Cewar SAUDE. tashi baba yayi yace '' ɗazu na gama yi mai faɗa ya za'a yi kaga mutane rike da mahaukaciya kace ka san guri ai ba zaka ce ka sani ba. SAUDE tace '' baba wallahi duk su suka ja min wannan fitinar Allah ya rufa asiri yana nan a dakin da nake akwai waya na buga mai yazo ya tafi da ita da wallahi yanzu wani zancen ake yi ba wannan ba tsaf matar nan zata ci uban mu kana ji fa har cin mutum take.., Baba yace '' innalillahi wainna ilaihir raji'un mayya dai suka kawo miki.., Hmmm wallahi kuwa mayya kai dai Allah ya saka mu dace Amin ya Allah yace tashi tayi tace '' baba bata nan ne..?, Bishira yace '' ta tafi unguwa., cikin jimama tace '' sai ta dawo ta tarar da tashin hankali.., Wallahi kuwa ya faɗa yana cije lips din sa domin sauran kaɗan ya zunduma ihu bayan sa wani irin ciwo yake mai. Hadi ne ya shigo yace '' Allah ya saka wannan ce sanadiyar shiriyar ka..., na shiga uku daman ba a shirye nake ba SAUDE a yaya kike gani na dan Allah karki boye min.. Bishira me kyau ya faɗa yana yarfe hannuwansa tare da lankwasa murya kai kace mace ce tayi maganar nan Hadi yace '' dan Allah karki boye mai ki faɗa mai gaskiya abin da yake aikatawa haramun ne ko ba haramun bane..?, Kaga Hadi bana son neman fitina zo ka bar gurin nan tun Kafin ranka ya ɓaci duk wani abu kai kake fara assasashi.., baba ya faɗa yana nuna mai hanya ita dai SAUDE sallama tayi musu ta , tawo gida tana zuwa kofar gida wani kallo MUDAN yayi mata da ya saka hantar cikin ta kaɗawa dauke kai tayi ransa a ɓace yace '' karki sake ki shiga cikin gidan nan.., daidai lokacin usman ya fara kuka jijjigashi ta fara yi rintsai idanuwan'sa yayi da suka kaɗa sukai ja baya so tun yanzu su gadarwa da dan'su matsala baya so ace koya ya fara fuskantar wane hali suke ciki da SAUDE bayan mahaifiyar da ta sani amma da tuni ya dade da sawwake mata Allah ya sani ya gaji da halin ta , tashi yayi ya rufo shagon sa ya shiga cikin gidan bin bayan sa tayi zuciyar ta na lugu dan uku uku yanzu yace ta tafi gidan su ya za tayi tafa shiga uku ke nan da wanne ido zata kalli mahaifan ta kullum nasihar su a gare ta tabi mijinta sauda kafa. tsayuwa tayi tana fiƙi fiki da ido yawa an jiƙa ɓera a cikin ruwa zama yayi akan kujerar da dazu ya tashi yace '' wallahi kina gab da kaini bango ke ko tausayin yaron nan bakya ji kuma duk ranar dana sallame ki wallahi sai kin dire min ɗana.., da sauri ta ɗago shima kallon ta yake yi yaci gaba da cewa eh abin da kunnuwanki suka jiye miki shi na fada ki ci gaba da kaini bango har muje batakin ƙarshe sannan yanzun nan abeeda zata zo ki tsaya tayi miki kitso.., zama tayi bata ce komai ba , ta kunto usman da yake ta kuka zip din rigar'ta ta zuge ta fara bashi mama yana sha shiru yayi yana yan wasannin ta duk maganar da MUDAN yake yi ko tari ta kasa yi tsoron ta ɗaya tayi magana yace ta tafi gidan su wallahi ba inda za ta ai danta namiji ne dan haka zaman dan'ta za tayi ba inda za ta tana wannan tunanin ne ta ɗago suka haɗa ido gaban tane ya fadi domin ko kallon ta MUDAN yayi tana iya karantar yanayin da yake ciki jan hijabinta tayi ta rufe kirjinta ta maida kan'ta ƙasa sallamar abeeda taji da sauri ta dago tana amsawa gaishe da su tayi SAUDE ta amsa tana kau da kan'ta daga kallon MUDAN. zame dankwalinta tayi tace '' kafin ya farka zo ki fara yi min.., Abeeda ta leƙa usman da ya fara bacci sakin maman ta yayi ya ɗago tare da yin dariya dariya abeeda tayi tace '' kinga ashe ba bacci zai yi ba..., SAUDE tace '' aikuwa dakyar ya barmu ayi min kitson nan.., to sai na goya shi, daukan sa tayi ta goya shi sannan ta fara taje danƙararran gashin SAUDE duk uwar ta zar da ake mai tsilin gashi ki ɗaya be zuba ba saboda tauri da rashin gyara. tashi yayi ya fita abeeda zama tayi ta yarfa mata kitso me kyau bayan ta gama tayi mata godiya ta tafi da usman gyara gidan ta fara yi sannan ta ɗora girki zama tayi tana lissafin kudin da zata turawa sénatrice ta my nita bayan ta gama ta saka hijabinta ta fito yana zaune shi kadai a kofar shagon sa yana karatun Alkur'ani ta dade a tsaye akansa sannan tace '' zan tafi can shagon ne zan turawa sénatrice kuɗi bata da lokacin da zata zo ta karɓa kuma bukatar su take.., be kalle ta ba yace '' ɗazu ni kika tambaya kika fita...?, kuma me nace miki ba ce miki nayi na karki shiga cikin gidan nan shi ne kika shiga.., hijabinta ta saka tana goge idanuwan'ta cikin muryar kuka tace '' wallahi ba inda zani ni dakai mutu karaba me kake nufi dani ne da kace karna shiga cikin gidan ka na tafi namu gidan ko me..?, ganin hankalin mutane zai fara yowa kansu ya ƙara rufe shagon sa ya shiga cikin gidan bin sa tayi tana cewa to wallahi ko ka sake ni ba inda zani zaman ɗana zanyi kuma naga shegiyar da ka auro ka kawo ta cikin gidan nan wallahi Allah sai na yanka ta sai da ka gama dani ka mai dank bazzawara kace min ga zance ga magana komai duk yabi ya saki.., Dariya ce ta kusan subbuce mai amma sai ya danne yace '' oh Allah ba kina haɗa mai da tsohuwa yarinya ba wel come back virginal to sai ki haɗawa kanki hakkina nawa kike tauyewa a cikin gidan nan , wallahi nagaji maganar sai da maganin nan na hanaki ƙin ƙi hanuwa bansan ya zanyi da ke ba wallahi idan ba mu rabu ba to zan kara aure gudun saɓawa mahaliccina.., da sauri ta cire hijabin ta tace '' anzo gurin daman tun jiya abin da kake nama kenan daman duk wani take taken ka kallon ka kawai nake yi yasin ba zaka sani a cikin tashin hankali ba , naje na ƙara yin wani cikin na shiga uku dan dai ba a jikin ka yake ba shi ya saka kake faɗar haka.., tsura mata ido yayi ashe duk guje gujen da take yi saboda karta ƙara daukan ciki ne tab lallai tana da aiki yace '' au baka bada wannan maganin ne ? Ko dai damfara kuke yi bawai bada magani kuke ba duk wata me bada maganin gaskiya ba maganin da bata bayar wa balle wannan abin.., zama tayi tana cewa aini ba yar iska nace da kake wannan maganar ka bari sai na fara tara yan iska sai na fara siyar da irin maganin nan.. ja da baya tayi ganin yana neman cimmata ta shiga daki a guje gaban ta yana faɗuwa dariya yayi ya koma waje zama yayu akan benchi ba tare da ya bude shagon sa ba ya kunna Radio. Wannan kenan.. Iya tsaruwa club din ta tsaru yan mata da samari sai tashewa ake yi masu shan shisha na sha a hankali taja ɗaya daga cikin kujerun da aka jeru a gurin ta zauna cire glasses din'ta tayi ta ajiye a gefe sannan ta cire facemask din'ta tace '' kai sauri ka faɗa min abin da zaka faɗa min bani da lokaci.., dariya yayi yace '' uwar son kudi daga jin maganar kudu har kin dauko kafafuwa kin tawo idan da ace wani tarko na kafa miki fa...?, murmushi tayi na gefen baki tace '' saidai ya kama ka kai kaɗai ban dani karka manta nidin wace da kuma kake cewa uwar son kudi kai da baka so ka zubar dashi a ƙasa., Dariya yayi yace '' lubabatu sheɗaniya.., haɗe rai tayi tace '' kaga idan ka kirani ne nan domin ka ci min mutunci sai naji bayani na zo kuma banga wani abu ba kuma wallahi har kudin motar da na biya sai ka biya ni kudina.., buɗe waya jaka yayi ya zaro bandir bandir na saifa ya ajiye a kan table zaro ido tayi tana kallon gefe da gefen ta tace '' T boy ina ka samu wa'yannan makudan kuɗaɗen..? wacce sana'a haka , ka fara..?, kardai kaima ka fara tsafi ne , na shiga uku shikkenan kaima ka ɓata wallahi duk son abin duniya ta bana so na ganni na aikata irin wannan aiki dan Allah ka faɗamin ina ka samo wannan kuɗin.., dariya yayi yace '' ko ɗaya ba abin da kike zargi na fara ba harkar alkairi ce idan har za kiyi to fa gida da mota sai dai ki bayar badai a baki ba.., zaro manyan idanuwanta tayi tace '' t boy Ka fara bani tsoro fa lamarin ka akwai sarkakiya a cikin sa anya kuwa to me ka fara ka faɗamin gaskiya ni ba zan shiga abin da ba'a feɗe min biri har hutsiyar sa ba idan abin da nake tunani ne wallahi gwara na mutu cikin talauci ba zan saka kaina a wahala ba karshe ance rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta me kaya lah laj barni a siye da siyarwa ta da nake yi arziki na Allah ne.., Dariya yayi ya busa shisha yace '' matso raciya ke wallahi son kudin ki na banza ne.., hmmm ina jinka faɗa min kuma ka bani kaso na , nabar nan gurin kafin na hadu da idon sani na shiga uku a dinga yawo dani kwararo kwaro ana cewa ga sénatrice can zama karuwa... ke fa hallacan sun dade basu faɗa ba su daman mutane ana iya musu kawai idan zaki yi sabgar ki kiyi sabgar ki... Hmmmm T boy maza faɗamin ina jin ka idan baka da abin faɗa to wallahi ni zan yi tafiya ta aunty safiya bata san na fito ba ga dare yana yi.. T boy yace '' to dai a gurguje wannan sana'a ba wata bace illa mu saidawa mutum kaya amma fake bawai masu kyau ba daga sama sai mu saka masu kyau kina hurda da masu kuɗi zan iya hada miki game idan kika ci ribar taki ce.., wani irin kallo ta dinga yi mai me cike da anya kuwa kana da hankali yana gamawa tace '' Allah ya tsari gatari da saran ciyawa ba dani ba gaɗa a lahira ko da wasa idan ta ɓaci ka nuna ka sanni sai naci abu takazar ubanka wallahi.., dariya yayi yace '' matsoraciya wa yace miki ana shiga dawa dan karya.., ubanka ne ta faɗa tana tashi daga gurin daukan guda ɗaya tayi tace '' na chanza wayata da man ta mutu.., be hanata dauka ba yace '' duk randa na gama tara abin duniya sai na zo muyi aure.., dariya tayi tace '' wa ni hhhh T boy la fara samin matsala a kwakwalwar ka..., Copy is not allowed Hakkina ne mallakina ne kubar min kayana ban yadda ayi amfani dashi ba ta ko wacce siga https://youtu.be/qKsLgKJdsdA If you know that you're not going to talk to me about my novel or something that concerns me, please don't talk to me at all. I don't like what you're doing following me around persistently and talking to me about things that don't concern me. Episode 6 Wallahi ki dena dariya kar abu ya tabbata kizo kina dana dani. bata ko kalle sa ba ta fara tafiya cikin sauri tsoron ta ɗaya kar ta hadu da wani idon sanin ta shiga uku zargin mutane ya tabbata sosai take sauri gaban ta na faɗuwa har ta fita titi mai babur ta tsara ta kwatanta mai inda zai kai ta , sukai ciniki ta hau. fara tafiya su kayi wayar ta tayi ringing ganin aunty ce me kiran ta ja ƙaramin tsaki tace '' sai kace wata yarinya duk inda za ka ana kafama maka sharaɗi to yasin na kusan fyace kowa ma huta haba wannan a bin da me yayi kama ƙin ɗagawa tayi ita kuma aunty bata dena kiran ta ba. har suka isa gida tana kiran ta kuɗi ta zaro ta miƙa mai da sauri ya kalle ta yace '' nawa mukai dake zaki bani wannan kuɗin..., wani kallo sénatrice tayi mai tace '' babu da ya'yanta zan baka ban da tsabar cuta kamar ban san garin nan ba kace min kaza , zan bayar na bayar gani jikar me kudi ko..? to wallahi nayi maka ma da mutunci idan ka raina bani ina da bukatar su.., da sauri ya dauko zai sharara mata mari wani dan daba da yake zaune yake chakewa yace '' kana taɓa ta wallahi sai na murmurma maka wuƙa a ciki na sarkafo ya'yan hanjin ka.., kaga barshi ya dake ni daga nan BJ CLUB ya dauko ni shine wai saboda gashi jikan dan fashi zan ba shi dubu biyu ni kuma wallahi bana son tsayuwa ta a gurin sai nace muje ba wai na amince ba, kasan tsayuwa a gurin nan ba dad'i wallahi.., senatrice kyale sa so yake jikin sa yayi tsami amsar kudin yayi yace '' wallahi dana san ke yar iska ce da ban dauki ki ba ..., sannu dan guguwa. dan daban nan yace '' kai dalla ware ko nai maka billan yarabawa.., hawa mashin din'sa yayi ya burga yayi gaba yana mata Allah ya isa, Hajiya senatrice ya zaki tafi baki bani na hawa gajimare ba.. dan daban nan ya faɗa yana kallon ta. har zata shiga gidan su sai ta dakata ta juyo tace '' biyo ni ka kwata wato tsaya min da kayi kanka ka tsaya wa.., komawa yayi ya zauna kwafa tayi ta shiga cikin gidan da sauri aunty ta tashi tace '' lubabatu ina kika je cikin daren nan lubabatu kiji tsoran Allah ki duba martabar gidan mu karki zubar mana da mutunci.., senatrice mayafin ta ta cire ta kunshe kuɗin da ta karɓa tace "Aunty safiya nifa ba abin da kike tunani bane kema ke kinsan da irin yawan nan nake kya ganin a haka dan haka duk me zargina shi da Allah wallahi.., Jikin aunty safiya ne yayi sanyi ta bi lubabatu da kallo har ta shiga daki zama tayi tana sakin ajiyar zuciya me nauyi Kenza da take zaune ta tashi ta shiga dakin su tun da aunty ta dawo ai shikkenan sa yi bacci da mun shari. Wannan kenan ZINDER Hayaniyar da ake yi ne ya janyo hankalin inna da sauri ta kalle salmanu tace '' Bashir kamar hayaniya ake yi a kofar gidan nan.., Bashir da yake ƙwance yana fifita yace '' to iya ni ina naga kafar fita naga ko me ke faruwa ina Hadi yake ya fita yaje ya gani ko me ke faruwa.., Inna tace '' Hadi yanzu yaushe zaka gansa yana can gurin kallon yan dambe ni tsoro nake wallahi kar wata ran a gwabje shi.., da sauri Bishira ya tashi zaune yace '' kallon yan dambe lallai Allah ya fidda a'e daga rogo amma wallahi hmm Allah dai ya kyauta.., Amin dai ƙoƙarin shigowa suka ga ana yi da sauri suka tashi ganin an ajiye musu hadi ya meƙe sambal salati inna ta saki tana kururuwa baba da yake bayi da sauri ya fito ganin abin da yake faruwa yace '' innna lillahi wainna ilaihir raji'un me yake faruwa a ina kuka dauko shi.., Abokin sa ya share hawaye yace '' wallahi sai da na hana shi, shiga cikin yan dambe be ji ba ya shiga miliyan ɗaya aka saka ga duk wanda ya kada shago na laure shi ne yana shiga yayi mai duka ɗaya , ya zube ya dena numfashi..., habawa bishira yana jin haka ya doka calle ya matsa baya yana zare idanuwa cikin subutar baki yace '' na shiga uku ni bishira me kyau ashe a gaban gawa nake nabi ina naniƙe mata salon ta cabke min ƙafafuwana na shiga uku.., Da sauri kowa ya ɗago ya kalle sa murguɗa baki yayi yana fari yace '' to munafukai masu zuwa lahira da ƙoƙon dambu., ko wanne su sai ya saita kan'sa shiga da Hadi akai daki tun da bishira ya ga an shiga dashi cikin daki ya fita kofar gida unguwar tayi baki abin da ba wutar lantarki ta gumi ya zabga ya lula duniyar tunani anya kuwa ba wani abin ya aikata ba da wa'yannan masifun suke bin sa ɗazu mahaukaciya ta dake su yan zu kuma ga gawa an shiga da ita cikin dakin su hawaye ya matse da gyalen sa. abin duniya duk ya ishe shi kamar ance ya ɗago sai ya hango wani mutumi da fararan kaya gaban sa ne ya yanke ya faɗi ya fara zare idanuwan'sa yana cikin wannan yanayi yaji an shafi ƙiyar sa ai besan lokacin da ya zub duma ihu ba. abokin hadi yace '' bashir ni ne fa..., da sauri ta juyo ya jike sharkar da gumi ga hawaye wani na bin wani a kuncin sa cikin faɗa yace '' Allah wa daran naka ya lalace wannan wacce irin bura uba ce ne Allah ya rufa asiri ma na nuna jarumta da karfin zuciya ban da haka da wani ne ai suma zai yi karka kuskura ka ƙara taɓani idan ba haka ba wallahi zanyi maganin ka..., girgiza kai kawai abokin Hadi yayi yace '' bashir kenan wannan mutuwar da dan uwan mu hadi yayi ya kamata ace ta zamar mana darasi ka duba ka gani yau lafiya muka wuni kalli zuwa dare abin da Ubangiji yayi ita fa mutuwa wa'azi ce ga al'umma idan sun dauka ya zame musu jari ranar gobe kiyama ...., Wani kallo yayi mai ya ɗauke kan'sa ganin kamar nasihar da yake mai ta fara shiga jikin sa ya ci gaba da cewa yanzu zan je na karbo lilƙafani sai kazo mu tafi tare da me awan gawa sannan ni dakai zamu kwana a cikin dakin tun da ba za'a barshi shi kaɗai ba Kama haɓa bishira me kyau yayi yace '' kai dawa...? Uhmm ba dani ba gaɗa a lahira tun da ake mace mace a unguwar nan ka taɓa gani na a hanyar makabar ta..?, to ai ba abin arziki ka yi ba ka dai zo muje ayi abin da ya dace mutsaya Kai da fata gurin kyautatuwar dan uwan ka ai mai sutura cikin mutunci. Bishira cire mayafinsa yayi ya daure a kugusa yace '' amma wallahi sama'ila sai yau na fahimci ba kada hankali ina mace ina ni ina kwana da gawa bama ta mace ba ta namiji kuma dakai a daki ɗaya ko dan dazu ka taba ni ban wanka ka da mari ba shine yanzu kake kawo min maganar banza to ahir ɗin ka wallahi karka kuskura ka kara yi min irin wannan kalamin jeka ka nemo dan uwanka namiji ku kwana tare da shi wai baba ma amfanin me yake a cikin gidan nan ai shi ya kamata a ce ya kwanta da wannan gawar, Sima da yake salllamowa yaji Bishira me kyau ya zagi yana wannan mayani sai ya shiga karkashin benchin dake jikin gidan su ya riko ƙafafuwan'su shi da Sama'ila ya maƙe murya yace '' yanzu kuna matsayin yan uwana amma kuke gudana to wallahi tare za mu tafi.., gumi ne ya shiga yanko musu ta ko ina wannan shi ake kira da tashin hankali ba'a saka maka rana. ganin sun kasa ko da motsi sai sima yace '' au ni zaku mayar mara aikin yi ko ina magana kun yi shiru ga shege yana magana., da sauri Bishira Yace '' dan girman Allah dan uwana kai min aikin gafara wallahi Allah baka girman ka nayi jira nake ka gama magana sai na baka amsa ko Sama'ila...?, karya kake yau tafiya ni dakai ba fashi... Innalillahi wainna ilaihir raji'un Allahumma sai yarasa me zai ce sai zare ido kawai yake ga yawun bakin sa da yayi kaurin ba shiru ya soma sakin futsari bakin sima ne ya subbuce yace '' kuttumar uban can kayyasa ni zaka sakar wa fitsari a hannu..?, saboda da tsabar rudewa be gane muryar sima ba kuka ya saka Sama'ila yace '' wallahi Allah bani nayi futsari ba shi ne.., nan suka fara gardama wannan yana wannan ne wannan ne dariya ce ta subbucewa sima da sauri suka kalli kasan benchi ai bishira me kyau be san lokacin da ya take hannun sima ba yace '' wallahi Allah ya isa ka tsakani na dakai shege dan iska.. dauke hannun sa yayi da sauri ya fito yana dariya yace '' ina kwance a gida nasha uban ribiti a gurin mahaukaciya naji ance Hadi ya mutu.., wani kallon banza bishira yayi mai yace '' billahilazi sai na rama dani kake zance.., kaga mai da wukar Allah ya baku hakuri sima ya faɗa yana yarfe hannu Saboda takaici Sama'ila buge shi yayi ya fara tafiya da sauri sima yayi baya yace '' me kyau kaga ɗan hau yana neman ya taɓa min jiki na.., Sima yanzu ba wanne a gaba na ba bansan ta ina zan fara ba gidan nan fa yana neman gagara ta shiga a cikin fa dakin mu aka ajiye gawar hadi kuma ake min wani makahon zance wai na kwana da gawa wannan ita ce kadai soyayyar da zan nuna mai a'a wallahi karki soma tab wallahi akwai matsala. Sima ya faɗa yana zama akan benchi.. Bishira Yace '' gane min hanya gane min hanya wallahi nima ko sama da ƙasa zata haɗe bazan shiga dakin nan ba balle aje ga kwana alfarma ɗaya zanyi gudun zagin Allahumma zan je kai gawa wannan ne kaɗai abin da zan iya yi.., kaga tafiya ta zama guri ɗaya tsauysayi ya faɗi haka ganin Sama'ila da malam liman DA me auna gawa sun dawo hade da wani farin abu a hannun sa da alama lilƙafa ni ne..., wani yawu me ƙauri bishira ya haɗiye yace tabbas akwai babbar matsala ga su can ina kayi yanzu..?, a'a bishira karka soma bina wallahi inji ya biyo ka har gidan mu kasan fa gawa ita ke zama fatalwa zauna inda Allah ya ajiye ka nima yau dakin su rafi'a zan shiga tunda ai duk jinsin mu ɗaya bazan iya kwana ba a ɗakina.. cewar sima ya faɗa yana tattare zanin sa domin so yake ya fita a guje kar bishira ya biyo shi sarai yasan halin bishira badai naci ba yawa baƙin mayye.. ganin abin da sima ke ƙoƙarin yi carab Bishira ya riko zanin sa da sauri yace '' a'uzubillahi minar sheɗanir rajim tsirara zakai min kenan kana ganin maza suna ƙoƙarin doso mu wallahi tun kafin nayi maka ɓarin makauniya ka sake ni bana son ciki da hulakanci.., wallahi ba inda zaka yau tare za mu kwana. aikuwa zancu bura'uban ka billahilazi shemaka zanyi a nan gurin ga bakar cuta dan anyi mutuwa a gidan ku shine nima kake so na bishi wallahi ban gane da wa nake tare ba sai yanzu to ka ci Kani ko yanzu jikin ka yayi tsami..