YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 1--10 Aunty ummi I have no more privilege, mommy's gone daddy's gone ya Sadiq's gone they were shot right in front of me aunty ummi my heart has dried up my soul is consumed by sorrow , anxiety and depression , they made me an orphan at a young age, I'm just 20 years old what did my parents and my innocent brother do to deserve such fate ? they showed no mercy shooting them in front of meeee I will never forgive them, but they made the greatest mistake by leaving me alive, my life will be revenge for my parents and my brother, she stated, standing up . Ajiyar zuciya aunty ummi ta sauke tare da fadin look mahreen I understand the circumstances you have found ur self in , but if you truly mean what you just said ' that your life will be revenge for them' then why aren't you taking care of your self ? since you were discharged from the hospital three days ago, u haven't eaten anything, only tea how will you take revenge for them if you re neglecting your own life , your parents and brother are gone forever and won't come back accept that or no so just calm down, now all they need now is your prayers, komawa tayi ta zauna tana kallon aunty ummin can kuma tayi murmushi wanda zan iya cewa yafi kuka ciwo sannan ta mike ta shige toilet itama tashi tayi tafita saboda har yanzu ana zuwa masu gaisuwa. Saida tayi alwala tayi sallar laasar sannan ta hau gado hoton dake gefen gadon ta dauka tana tuna abin da ya faru zuciyarta ta ke kashe hawayenta sun kafe, ahankali take shafa fuskar hoton Wanda yakasance family pic ne wasu tears masu dumi taji suna sauka daga idonta sosai tasha kuka har saida bacci ya dauketa dan daman bawani baccin kirki take samu ba. MASARAUTAR MAABUBI masarautace mai adalci ga Al ummar ta SARKI ABDALLAH UMAR JAMIL NA 2 su biyu ne awajen mahaifansu sarki Umar Jamil na 1 tare da mahaifiyarsu gimbiya zainab shi da kaninsa ABDUL HAMEED UMAR JAMIL sun taso cikin gata da kulawa, sarki abdallah yasa mu sarauta ne bayan mutuwar mahaifinsa kasancewar shine babba yasa aka nada shi a matsayin sarki ya kasance mai adalci ga Al ummar sa kamar yadda yaga mahaifinsa nayi Kansu ahade yake shida dan uwan sa yanada mata daya wadda ake cewa fulani da yaya biyu Maza ishaq shine na farko sai Khaled saida sukayi shekara biyar sannan Allah yakara Basu haihuwa saidai yarinyar batazo da rai ba, anyi anyi yakara aure yaki dukda kasancewar sa sarki . Abdul hameed kaninsa Yana da mata biyu da ya ya shida uwar gida nada biyar duk mata sai amarya nada daya itama mace zaman lpy suke da dan uwan sa amma bayan zuwan aunty amarya saita dasa masa tsanar dan uwan nasa ta hanyar yimasa huduba da cewa idan har dan uwan shi ya fadi ya mutu to tsakanin ishaq ko Khaled wani acikinsu ne zai gaji sarauta bashi ba gashi dama shi ba da namiji ba da haka taja hankalin sa har yanemi shawarar ya zaiyi Kenan ita kuma ta bada shawarar ya bar mata komai a hannun ta . Bata tsaya ko ina ba sai wajen malaman ta tasa a nisan ta ishaq da gida a lokacin yayi aure harda dansa mai suna sadiq shine dalilin asirin datayi masa ya kaura ya koma can Australia da zama ko waiwayar iyayan sa da dan uwansa bayayi saidai ta waya mahaifansa sunyi sunyi ya dawo yaki har mahaifinsa ya tura masa dan uwan sa Khaled anan yake shaida masa duk lokacin da yaji yana son zuwa gida hakan gagara take shi kuma baiyi kasa a guiwa ba ya sanar da mahaifinsu nan fa aka shiga addu'a a lokacin kuma shima Khaled yayi aure dansa na farko Maher sai mai binsa Ayman saida sukai shekaru bakwai tukun Allah yasake basu ya' suka sa mata manira a lokacin kuma shima ishaq Allah ya sake basu haihuwa suka sa mata mahreen, khaleed Jin dan uwan nasa ya samu karuwa yasa ya shirya ya Kai masa ziyara dukda shi duk karuwar daya samu bai zo ba amma ya fahimci halin da dan uwan nasa yake ciki koda yaje sati biyu yayi ya dawo nigeria . tunda ga nan kuma ganin Khaled yafara ajje family kuma harda maza biyu yasa aunty amarya sake bawa mijinta shawarar poisoning dinsa da fari yakiya amma daga baya kuma yazo ya amince a haka akayi poisoning din Khaled tare da sa hannun Amintattun sa a lokacin aka fitar dashi Egypt domin neman magani Amma kasancewar poison din mai karfi ne yasa suka ce zai dau dogon lokaci kafin ya warke cike da bakin ciki yaransa suka komo gida Nigeria suka bar mahaifiyarsu da kanwarsu a can , Maher shine mai wayo a lokacin dan zai Kai 11 years saisa yariki bakin cikin abun a ransa dukda kankantar shekarun sa, hannun kakarsu suka koma a haka suka cigaba da karatu hankalinsu a rarrabe , Maher degreen sa na farko ya fito da result Mai kyau matsayin sa na doctor saboda kwazon sa da iya aiki yasa countries dayawa suke gayyatarsa idan har wani babban aiki ya tashi sai yakasance international doctor yau yana can gobe yana nan ga har yanzu mahaifin sa bai warke ba ,kuma binciken dayayi ya nuna sai ya Kara daukar wasu lokuta a kwance domin gubar har yanzu tana yawo a jininsa a sirrince yakoma yin masters a russia a department of defense and security studies, kaninsa ayman kuma ya gama karatun sa shima ya zama cikakken lawyer , a yanzu haka Maher yazama cikakken DSS yana aikin sa a boye domin wani lokaci kawai yake jira sai ya gano wa anda suka yiwa abbansa wanna illar , bakowa bane yasan akan wani course yayi masters din sa daga ammin sa sai kanin sa ko kanwarsa bata sani ba yakan raba hankalin sa ne ya leqa can ya leqa nan, so dayawa idan yaje wajen mahaifinsa yakan zaunawa yai ta fada masa abinda yakeyi da abinda ke faruwa Amma saidai yai masa murmushi kawai ba damar ansa masa wanna abu gana ciwa Maher tuwo a kwarya . MAHREEN Tunda ta taso batasan dangin taba daga mommy sai daddy da ya Sadiq so dayawa takan tambayarsu mai sa baza su koma kasar su ba ko kuma su nuna mata familyn su ita dai mahaifiyarta che mata take akwai lokaci shikuma mahaifinta a duk lokacin da tayi maganar yakan shiga daki ne yai ta kukan daya rasa dalilin sa , Sadiq ya karanci microbiology ne harya fara aiki yayin da ita kuma mahreen ta karanci criminal law sunyi final exams sun gama wata rana suna zaune take tambayar mahaifanta mai sa ba Wanda ke zuwa masu a family saidai kawai suyi waya to her suprise taga daddy yayi murmushi sannan yace mata da sunyi convocation zasuje Nigeria taga dangi cikin murna itada ya yanta suka tashi suka fita domin yin shopping din tafiya haka kuwa akayi suna yin convocation ya debesu suka yi Nigeria ba wanda ya fada wa zaizo dan haka motar haya suka hau yasauke su a masaurauta kwatsam labari yajewa su aunty amarya da Abdul hameed cewa ishaq da iyalansa sun dawo sun shiga firgici ba dan kadan ba . Bayan dawowar su ya samu labarin abinda yasamu dan uwansa kusan 19 years kuma bashi da labari saboda watsar dasu da yayi a ganinsa duk sakacin sa ne da yana nan ba abinda zai sameshi , haka ya tarkata iyalansa sukaje suka dubashi sunyi kuka shida dan uwansa amma ba halin magana sai dai yayi masu murmushi kawai haka suka kwashe wata daya a wurinsa sannan suka dawo amma fir ishaq yaki yadda yazauna a masaurauta Inda ya saya gida awajen masaurautar ya zauna da iyalansa sati biyu da dawowarsu duk sun zaga dangi da yan uwa , dama kanwar mahaifiyarsu daya ce aunty ummi maternal grandparents dinta kuwa duk sun rasu aunty ummi ta nada yara uku namiji daya Imran sai mata biyu sana da nawal sana kusan saar mahreen ce, mahreen nada surutu ita kuma sana bata fiya magana ba saisa sai ya zamana basa shiri sosai sabanin nawal da Itama irin mahreen ce two years ne tsakanin su, mahreen yanzu bata da matsala gata ga familyn ta two months da dawowarsu su Abdul hameed da aunty amarya suka yanke shawarar kashe ishaq da dansa sadiq danma kar ace Sadiq din yakarbi sarauta a madadin mahaifinsa saidai kash lokacin da suke zancen yar aunty amarya tazo wajen mahaifiyarta taji wanna magana da suke a matukar tsorace ta kunna record a wayarta ta tura kasan kofa yadda zatayi recording dakyau dan ita ba komai take ji ba saida taji sunyi shuru sannan tazaro wayar ta gudu sosai ta shiga rudani dajin wanna zancen tasan mahaifiyarta da bin malamai da tsafe tsafe amma ashe zasu iya kashe mutum kuma harda babanta aciki tayi kukan takaicin zama yarsu dan dai sun zama dolen tane da sai ta tona masu asiri amma tabbas baza ta bar abun haka ba. husna ba ruwanta yarinyace mai nutsuwa da hankali ga tausayi da sanin yakamata sabanin mahaifiyarta, haka Allah ke yin ikonsa ya fita da Nagari daga tsatstson batattu haka zalika ya fitar da batattu daga tsatstson nagari . Kamar yadda suka shirya hakance ta kasance Abdul hameed da kansa ya shirya ya shiga cikin tawagar thugs dinsa suka dirarwa gidan dan uwan nasa wai dan karma yaran su samu matsala sai sa zaije da kansa, cikin dare suna bacci suka shiga gidan bayan sun gama da masu gadi parlourn gidan sukawa tsinke zama yayi yasa yaransa su fito masa da duk wanda ke gidan haka aka fito da ishaq da matarsa an sa masu bindinga aka yana kuka yana fadin me na maku kuke neman raina ni da iyalaina mommy tace in kudi kukeso kufada zaa baku ko nawa ne wani ne daga cikin yaran ya daka mata tsawa da cewa idan ta sake magana saiya fasa kanta shuru tayi tana kuka mahreen data buya bayan ya'yan ta tana kuka suka dakawa tsawa wadda saida taku san tafiya da numfashin ta , Abdul hameed ne ya zaro bindiga a aljihunsa ya nufi ya Sadiq yana zuwa baiyi wata wata ba ya saita brain dinsa ya sakar masa alburushi Karan Harbin nai ya rikita mahreen ta riqo hannun Abdul hameed din a gigice fisgewa yayi da karfi har hannunsa na fita daga safar hannun da yasa, Kan dan uwanta tayi tana kuka mommy ce ta taso tana mai ya maku baisan hawa ba bai san sauka ba kuka kasheshi sakar Mata harsashi yayi a zuciya sannan yakara Mata a forehead daddy da yayi suman zaune yana hawaye gaba daya komai na jikinsa ya daina aiki na wucen gadi, cewa thug din nasa yayi suyi waje shima yayi wajen kofa kamar zai fita sai ya juyo yasakarwa ishaq din bullet shi ma mahreen ce tasaki wani ihu ta mike tana masa wani irin kallo ko ina na jikina sa a rufe yake idonta ne ya sauka Kan hannunsa dayake rike da bandiga kurawa hannun Ido tayi kafin ta maida Idon ta zuwa kansa Ido hudu sukayi kallon kallo kafin ya juya ya fice ita kuma tayi kan iyayenta tana kuka ganin fa basa numfashi yasa ta dauko waya tana Kiran aunty ummi saida tai mata misscall 5 tukun ta daga cikin muryar bacci amma jin abinda mahreen din take fada mata bata san lokacin da ta wartsake ba ko da sukazo aka sake tabbatar da sun mutu tunda mahreen ta suma bata san in da kanta yake ba sai da akayi uku sannan ta dawo hankalin ta to yanzu kwana shida Kenan da rasuwar tasu . BACK TO STORY Bayan bakwai Mahreen ta dawo gidan aunty ummi da zama ta dawo wata so silent dan abu kadan ne ke Hassala ta a yanzu bata jin akwai abinda take tsoro ciki kuwa harda mutuwa . A masarauta ma an jimama mutuwar ishaq ciki kuwa harda Abdul hameed daya nuna mutuwar ta bigeshi husna tayi kuka jin cewa sun aikata har wata zuciyar na che mata ta tona masu asiri tunda tana da evidence amma tana tsoro. An hana a sanarwa Khaled rasuwar dan uwan nasa kasancewar halin da yake ciki, Maher da Ayman da sukayi tafiya Germany har su mahreen sukazo sukayi zaman duba abbansu basa nan saida bayan sun tafi suka je sai kuma yanzu da aka fada masu mutuwarshi suka dawo jin yadda mutuwar tazo taso sa Maher shakku amma kuma kawai sai ya watsar Ayman yaso yin bincike akai a matsayin sa na lawyer Amma Abdul hameed ya nuna cewa binciken bashi da amfani tunda har sun mutu ba dawowa zasuyi ba , su Ayman sunso ganin mahreen su Mata gaisuwa ita kuma a lokacin baza ta fito ba haka suka hakura sukace a fada mata suna Mata taaziya. Bayan six months da faruwar hakan mahreen tacewa imran tanaso takoma school cikin lallabi yace mata a ina takeson tayi (Dan yanzu lallaba ta suke especially ma shi ) ba tare da wani fargaba ba tace masa russia jim yayi kamar bazai amsa ba saikuma yace Mata wani course ne take so defence and security studies tabashi amsa a takaice , but mahreen irin wanna aikin ba irin naki bane , " ni da nake lawyer ai ba aikin zanyi ba kawai ina san course dinne, ko da suka tuntubi aunty ummi taso hanawa amma yadda mahreen din ta taurare yasa suka kyaleta tare da nema Mata admission ta tafi . YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 11--20 TWO YEARS LATER Wata matashiyar budurwa na hango ba zaa kirata doguwa ba kuma ba zaa sata sawun gejerubace ba , ba fara bace amma light skin gareta mai daukar Ido tana da dogon hanci da idanuwa dara dara wanda suke zagaye da zara zaran lashes haka eyebrow ta gazar gazar batada kiba kuma ba siririya bace a dire take irin su ne ake Kira da figure 8 sanye take da ash din jeans Wanda yabi jikinta sai black top data dora wadda zata Kai guiwarta daga baya kuma takai har kasa ta yane kanta da karamin veil sai P cap data sa ta janyota gaba sosai ta yadda ta rufe rabin fuskar ta a yau ta diro naija da gudurin fara aiki a hukumar DSS dakuma yin aiki a matsayin ta na lawyer sabanin yadda ta tafi da cewa baza tayi aiki a matsayin dss ba idanunta ta daga tana kallon airport din wayarta dake Kara ta dauko a jaka Imran sunan daya bayyana Akan screen din wayar dauka tayi daga daya bangaren naji ance hello mahreen I haven't seen you yet and ur flight landed 15 minutes ago, where are you ? I'm coming kawai tace sannan tafara tafiya Kana kallonta zakasan jinin sarauta Yana gudu a veins dinta daga yadda take tafiya . tana fita tagan su nawal ce ta fara hangota da gudu taje suka rungume juna welcome back home sister murmushi ta mata taja kumatun ta how are you doing ? I'm doing good buh I missed you Imran ne ya karaso Lilly ya fada juyawa sukayi direction din da yake murmushi yasakar Mata welcome back Lilly , thank you bruh, ' so let's get home Cox ummi is so eager to see you , I missed her so much wlh, really ya fada tare da daga mata gira yeah tace kawai tayi gaba suka rufa Mata baya . Tafiya sukeyi amma ita ta Lula cikin wata duniyar tunanin har saida Imran yace Lilly you haven't gisted me about your studies hope you did it successfully idonta akan titi tace alhamdulillah buh I'm so exhausted right now later in sha allah, "ohk no problem ur wish is my command, ahaka suka karasa gida ba wanda yakara magana a cikinsu. cikin farin ciki aunty ummi ta tarbe ta bayan sun zauna take tambayar sana bata zo ba (Sana tayi aure bayan tafiyar mahreen kuma ba gari daya suke ba)har 1am suka Kai suna hira sannan suka shiga bacci koda ta shiga daki ba bacci tayi ba tunane tunane take ta yanda zata shawo Kan aunty ummi ta yadda da abinda takeso a karshe dai ta yanke shawarar samun Imran domin yi mata jagora ta samu aiki a hukumar DSS tare kuma da fara aiki a matsayin ta na lawyer domin ta hakan ne burinta na daukan fansa zai cika da wanna tunanin bacci yayi awun gaba da ita. THE NEXT DAY Zaune take a garden sanye da sweet pant da top long sleeve sai P cap dinda ta kifa a fuskarta kanta ma kallon sama kafarta daya akan table din wajen tana girgizata kadan kadan Imran ne ya karaso wurin da fadin helloo lilly dagowa tayi sannan tace ah Imran I need to discuss something with you kujera yaja ya zauna sannan yace go ahead dear I'm all ears, dan muskutawa tayi sannan tace you know when I was going to Russia I told aunty ummi I wasn't going to work as a DSS girgiza kansa yayi yana bata duka attention dinsa saida ta sake nisawa tukun tace so now I have changed my mind I want you to take me to any DSS headquarters, I'm eager to start my work early, and after that Ina son fara aikina matsayina ta barrister but I prefer to work independently, without being under someone's control, and please I'm not requesting for advice and I'd like to keep this matter confidential between us between us tana gama fadar haka ta maida P cap dinta a fuska nisawa yayi yana tsinewa wa'anda suka kashe mata familynta da wargaza farincikin ta yarinya mai saukin Kai da Wasa da dariya amma yanzu duk ta zama somehow sai ahankali a fili kuwa cewa yayi ohk I will check and get back to you , great kawai tace jin bata sake magana ba yasa shima ya tashi ya tafi . AFTER ONE WEEK Imran yayi duk abinda mahreen tace kuma an mata komai kasancewar documents din karatun ta Bana nan bane yasa cikin sauri suka amsheta a babbar headquarter DSS ta jahar sannan ya sama mata office awani chambers din lawyoyi bai fadawa ummi aiki data samu a headquarter dinba shi dai yace mata ta bukaci ya kama mata office zata fara aikin ta a matsayin Barr. Da kyar aunty ummi ta rinjayi mahreen ta amince Kam cewa zataje visiting masaurauta tare suka shirya ita da nawal da aunty ummi Imran ya kaisu cikin shigarta ta kullum kamar yadda ta saba wando da riga sai after dress data daura akai wanda aunty ummi ce ta matsa Mata Kan sai ta sa ganin bai kamata ta shiga masarauta da wannan shigar ba, wani dark shade ta maqala wanda ya kusa mamaye rabin fuskarta fada suka fara shiga Inda suka tarar da Abdul hameed tare da waziri agaban mai Martaba sai fadawa, saida suka miqa gaisuwa wajen mai martaba sannan suka gaisa dasu waziri da Abdul hameed, mai Martaba ne ya buqaci mahreen tazo kusa dashi kamar zaiyi kuka saboda tunawa da dansa da yayi dafa kanta yayi tare da samata albarka dagowar da zatayi idonta ya sauka Kan wani abun daya sa zuciyar ta daina bugawa na wucen gadi , ba komai bane face tabon hannun Abdul Hamid dagowa tayi da sauri suka hada Ido tabbas shine wanda ya kashe mata familynta baza ta taba manta wanna hannun da kwayar idanun da sukayi sanadiyyar rasa duk wani gata nata ba sosai zuciyarta ta tafaso har idonta na kankancewa saboda masifa saurin maida kanta kasa tayi dan Kar su fahimci halin data shiga Abdul hameed ne yafara magana cikin karfin hali da kuma faduwar gabar data dirar masa lokacin da suka hada ido da mahreen Allah sarki ishaq yaro mai ladafi da biyayya Kai duk wanda suka masa haka baza suga da kyau ba sannu kinji yarinya Allah yakara maki hakurin rashin su hakika anyi rashi babba su aunty ummi ne suka amsa da ameen ita kuwa wani murmushi tayi kawai taji duk abinda yace saboda tanajin Hausa sosai awajen mahaifiyarta dan tun tana karama tane mi ta iya saboda idan sun dawo Nigeria ta dinga magana da family itama ace ta iya Hausa, har suka fita ranta abace yake amma tayi kokarin boyewa ta hanyar maida dark shade dinta fuskarta bayan sun fito daga fadar part din grandmothern ta sukayi . Tazo shiga shi kuma yazo fita yana waya har suka mangaji juna juyowa tayi da masifa hey don't you have eyes....juyowa yayi ya zuba mata sexy eyes dinsa masu matukar haske da sheki take taji duk kwarjinin sa ya cika mata Ido har takasa sauke masifar datayi niyyar yi I have got perfect vision so no specs needed for me yana Kai karshe ya giftasu ya wuce , aunty ummi da nawal ma ciki suka shige kawai suka barta anan Imran ne yace haba Lilly easy mana who's he ta tambaya a fusace Imran ne ya gyara tsayuwarsa sannan yace your cousin my cousin! ta sake maimaitawa from where ta fada a yatsine from your uncle Khaled's family, he is his first son Maher and there's his brother Ayman and their sister manira I thought you met her when you visited him in Egypt right dan yatsanta tasa abaki ta ciza batare da tayi magana ba sai kuma tayi gaba binta yayi a babban parlour suka samesu , Fulani ko kuma nace grandmother dinsu tana hakimce a wata kasaitacciyar kujera kuyanginta suna Matsa Mata kafa su aunty ummi suna zaune akasa sai wani saurayi data hango shima kusa da kafar tsohuwar yana zaune , kamar da taga sunayi da wanda ya fita yasa ta gane shine kaninsa ayman dinda Imran yace mata karasawa tayi ta nemi guri ta zauna saman kujera , Fulani ce ta bukaci kuyangin su basu wuri sannan ta kalli mahreen aunty ummi ce tace mahreen get down can't you see where everyone is sitting Fulani ce ta daga Mata hannu tana cewa karaso nan kusa dani jikata zo nan naji duminki ahankali ta tashi ta karasa kujerar grandma dinta ta zauna kusa da ita cikin so da kauna da kuma tuno danta ta share kwallar data cika Mata Ido meysa bakyason zama cikinmu marin mai sa baza ki dawo kusa dani ba in diga ganinki ina jin dadi b..... tana kaiwa nan tafashe da kuka ahankali mahreen ta dafata don't worry granny I will think about it stop crying tafada tana dan bubbuga bayanta saida tayi shuru sannan ta kalli Ayman daya zuba masu Ido Ayman wanna itace kanwar ku wadda aka kashe iyayenta da yayanta shekaru kusan uku kenan nasan ba lalle kunsan juna ba itace yar ishaq wan mahaifinka sunanta marin , mahreen ne ba marin ba, ke ni rabani wannan sunan bansan Inda iyayen ki suka samo suka makala maki ba suna sai kace daga duniyar aljanu duk dariya sukayi banda mahreen data murmusa kawai sun dade kafin tace su shiga su gaisa da iyalan abdul hameed kafin su wuce, tare da Ayman suka fita shi zai rakasu parts din iyalan abdul hameed part din uwargidan suka fara shiga ta karbesu hannu bibbiyu tana Kara yiwa mahreen gaisuwa har yayanta biyu wanda suka rage basuyi aure ba suka shigo suka gaggaisa tukun suka tashi zasu shiga part din aunty amarya da yake ba tazara sosai yasa a kafa suke tafiya kallo Imran tayi what's Abdul hameed's status in this house and who's he exactly ? he is your grandfather's brother he is the one praising your father's good characters when we were in the palace da sauri ta dago whatt you mean that man he is the brother of my grandfather are you okay Imran ? da mamaki yake kallon ta kafin yace yes he is what wrong with that girgiza Kai tayi cikin rudani tabbas dole ma ta dawo masarautar nan sake juyowa tayi both the part we came from and the one we are heading to are parts of his family's domain ? yeah yace daidai nan suka shiga part din aunty amarya a hakimce suka sameta bayi suna ta mata hidima wasu na yanka mata fruits wasu na Mata tausa karasawa sukayi suka zauna akasa suna gaisheta mahreen kuwa kujera ta haye ta fito da wayarta ta fara latse latse aunty amarya ce ta dago ta kalleta bayin ta sallama sannan tace ke agidanku baa koya maki gaisuwa bane ko kallonta batayi ba balle tasan tana magana keeeee ba magana nake maki ba aunty ummi ce tace mahreen dagowa tayi can't you hear her talking to you, who tace in I don't care tone aunty amarya mana where's she tafada kamar bata gantaba domin tun shigowar ta kallo daya tayiwa matar taji ta tsaneta kamar yadda ta tsani mijinta sabanin mamar su maijidda wato uwar gidan wadda itama a yanzu takejin tsanarta Jin cewa itama matar azzalimin nan ne wanda ya tarwatsa farin cikin ta. mahreen aunty ummi takira sunanta cikin rashin jin dadin abinda tayi kallon aunty amarya tayi tace evening, "evening din uwarki nace eveni....... Shigowar Abdul hameed ya hana ta karasawa kusa da matarsa ya karasa ya zauna Yana fadin ashe kunshigo nan aunty ummi ce tayi murnushin karfin Hali da fadin eh whl , mahreen da zuciyarta ta taso jin ta zagi mommyn ta , cire spec din idonta tayi ta kalli wanda akace kanin kakanta kuma makashin iyayenta tace tell your wife to get back into her sense sannan ta kalli aunty amarya this is the first and last time you will disrespect one of my parents in front of me, " owooo you are showing me that u lack morals and respect, husna ce ta shigo ta gaishesu sannan ta zauna Baba baki mukayine eh e-h ya fada kamar adan rikice sannan ya nuna mahreen jikar Mai martaba ce kuma yar ishaq Wanda suka rasu shekaru biyu da rabi daya wuce , they died or were killed ta fada a dan tsawace tana binsa da kallo dan ta fara loosing control ,rikicewa yayi eh eh aka kashe su mantawa nayi amma ai dama lokacin su yayi dan daba haka ba baza su mutu ba cike da tausayi husna take kallonta ganin an maidata marainiyar karfi da yaji ko uba ka rasa ya zakaji balle kuma harda uwa da kuma ya yanta Allah sarki may Allah have mercy on their pure soul mahreen may Allah grant them jannah and expose all those involved in their killing, wata muguwar harara iyayen suke aika mata kamar zasu rufeta da duka duk abinda suke mahreen na lura dasu amma tayi kamar bata gani ba kallon husna tayi suka hada Ido alama tai mata da number ta itama sign ta mata na bari su tashi girgiza Kai mahreen tayi sannan ta mike ta karasa wani table karami da aka daura littattafai akai pen ta dauka ta rubuta number ta kananu a yar karamar paper ganin duk sun zuba mata Ido yasa ta yayyaga takardun saita barbaza su akan table din dagowa tayi ta dan wurgawa husna pen din paper data rubuta number ta dauka sannan ta karasa a fakaice ta wurga Mata takardar sannan ta kashe Mata Ido taya ta karbi pen dinta paper tasake yagowa ta koma Inda ta tashi ta zauna ta daura kafa daya Kan daya duk ita suka zubawa Ido wani rubutu tayi sannan ta Mike ta dauki bag dinta aunty ummi let's go, " ohk dama yanzu zamu wuce ta fada tana sauke ajiyar zuciya sallama suka masu mahreen ce taje gaban kujerar su aunty amarya wani kallo take jifansu dashi cike da tsana sannan ta sunkuya kamar zasu hada goshi da aunty amarya I will show you that I lack moral and respect ta fada tana wani kankance idanuwa sannan tafara tafiya ball tayi da mug dinda ke gaban kujerar tasu take ya tarwatse sake juyowa tayi ta kallesu sun zuba Mata Ido in shock kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta kalli mug din dayayi pieces sannan tayi waje anan tayi joining dinsu dan dama basu yi nisa ba Ayman ne yake janta da magana ba komai take amsa masa ba domin yanzu tana bukatar time tayi tunani akan wanna lamarin shiko Imran haushi ne yakama shi saida suka kusa mota ayman yace have you finished studying sister ? yea! which course ? criminal law tabashi amsa a takaice wow I am also a lawyer juyowa tayi daidai lokacin zata shiga mota mika masa wayarta tayi insert ur digits here karba yayi yasa mata sannan yayi flashing awayarsa ya mika mata nata wayar karba tayi ta rufe kofar suka wuce. YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 21---30 MAHER sai 11pm ya dawo part dinsu ya wuce wanda ya kasance shi da Ayman ne masu mallakin part din a parlour ya sameshi yana ta dube duben littattafai irin nasu na lawyoyi a kujera ya zube yana fidda pistol din da ke bayan wandonsa ya aje akan center table , "kadawo bros Ayman yace yana dagowa , " Bari kawai tun dazu naso dawowa sai kuma mukaje wani investigation kuma har yanzun da nake fada ma ban kammala binciken ba, " wanna aikin anya baya ma yawa kuwa Maher kaje nan kaje can , hmmm kawai yace Ayman kuma ya cigaba da fadin dazu yarinyar uncle ishaq sunzo, " uncle ishaq dai wanda yarasu ? eh dazu sukazo da auntyn ta Kana fita suna shigowa ko itace wata marar kunya mai shade, " dariya ayman yayi dukda baisan me ya hadosu ba amma ya bashi dariya yace kwarai itace amma fa kasan miye bruh yarinyar tana da abin al ajabi da daure Kai bakaga yadda tayiwa grandfa Abdul hameed ba da aunty amarya abin ya dauremin Kai sosai sai kace wasu abokan gabarta Maher daya nutsu yana sauraron sa yace mai tayi tho? kasan dokar gidan nan dama idan dai kaje part din manya to akasa zaka zauna sai Kaine ma da kake karya dokar to ita ma halinku daya yadda baka shiri da aunty amarya itama haka amma kusan nata yayi worst saboda bakaji yadda ta dinga maida masu magana ba bata da tsoro ko kadan.......... nan ya kwashe duk abinda ya faru ya zayyane masa shuru yayi can kuma yace baka tunanin akwai wata a kasa kuwa Ayman nifa inaga haka kawai baza tayi musu haka ba ko dan girmansa a matsayin sa na kanin kakanta , "Nima gsky nayi tunanin hakan amma tunda munyi exchanging numbers sannu a hankali zansan komai kuma tunda ita ta fara neman number na ma kaga kamar tana da magana dani Kenan , mikewa Maher yayi yana daukan bindigar sa yace kamin sending number din ta ta, " ohk yace kawai. Abangaren aunty amarya da Abdul hameed kuwa mahreen tana fita itama husna ta tashi Dan taje tasa number da mahreen ta rubuta Mata nan tayi Musu Saida safe ta shige , Abdul hameed ne ya juyo Yana fuskantar ta fiddausi munfa kashe maciji ne amma bamu sare kansa ba wani murmushi tayi haba Alhaji muka Kawar da manyanta ma bare ita karamar kwaro karka damu zan sa a kawar mana da ita kawai dan karta kawo mana matsala muji da wa annan biyun ma na wajen Khalid da suka zame mana karfan kafa, husna ta manta da Jakarta a parlourn hakan yasa ta juyo domin dauka taji abinda ya girgiza tunaninta da sauri ta boye bayan labule tareda saurin danna recording Abdul Hamid ne ya cigaba da magana taya hakan zata kasance fiddausi kashe wanna yarinyar fa a yanzu ba karamin aiki bane dan daganin ta tsagera ce batada tsoro nisai nake ganin ma kamar ta gano wani abun , "haba mana Kai kuwa karkabar kanka ya kulle mana Ka barmin komai a hannuna kamanta wace ce ni kenan na dade fa ina doraka a hanya tun wancan lokacin damuka yiwa shi Mari gayi kurciya muka sa akayiwa Khaled allurar poison kuma a karshe Ka Kai shi ishaq din da iyalansa barza u saboda gudun matsala yanzu kuma wanna yar karamar kwaron ce zatasa Ka firgita ai kawai itama binsu zatayi kuma suma wanna Maher din da ayman indai aka kasa daga minsu daga kasarnan to Suma kawai kashesu zansa ayi kaga sarauta dai dole hannun Ka zata dawo wata dariya yasaki shegiya fiddausi akwai brain fa saisa nake sonki kina daurani Kan hanya , husna da tayi Saving din recording dinta wayarta tayi Kara da sauri suka juyo waye anan abdul hameed ya tambaya Yana mikewa haba Alhaji kafiya tsoro fa wayatace tayi Kara kagan ta can ta fada tana nuna masa wayarta dake charge kusa da curtain dinda husna ta buya ajiyar zuciya ya sauke Yana kallon ta ni mamaki nake yadda Ka iya kashe har mutum uku ahakan da wanna shegen tsoron kamar farar kura , baza ki gane bane fa, " amma kasan dai bawanda zai shigo idan ba kiransu nay iba husna kuma ta shiga bacci dan haka Ka kwantar da hankalinka fa . Tun a mota ta lura Imran sai wani cin magani yake shareshi tayi suna zuwa gida tayi wa aunty ummi sai da safe ta shige daki , bayan ta gama komai ta juya ta kalli nawal dake ta baccinta hankali kwance safa da marwa tafara dan neman mafita har saida ta kamo bakin zaren Amma dole tana da bukatar Karin bincike akai kuma hakan baza ta kasance ba dole saita koma masarauta kuma tajawo husna jikinta dan ta hakan ne zata samu wasu sirrikan Abdul hameed din dan taga kamar yafi san wanna aunty amaryar Ayman ne yafado mata arai shima zai Mata amfani kallon agogon dakin tayi 2:16am gashi gobe zata fara aiki a headquartern su a wanna dare bata samu bacci ba saida tayi sallah asuba tukun bacci ya dauketa 7am daidai alarm dinda tasa yafara ringing tare suka tashi da nawal dayake itama tana service ne a govt secondary school , agurgurje tayi wanka tafito shiryawa tayi cikin jeans black sai t shirt wata jacket ta dauko ash tasauka har Kan guiwarta belt din jacket din ta daura sannan ta gyara gashinta tayi rolling da black veil ta dauki spec dinta da P cap kamar kullum tafita a dinning ta samesu gaba daya harda babansu nawal good morning everyone ta fada tana hada tea saida suka gama breakfast nawal tai musu sallama ta wuce shima baban nasu sallama yayi ya wuce aiki dama shi managern banki ne da wuri yake fita aunty ummi ce ta dauko car keys guda uku ta Mika mata this is for who aunty ummi ? " this is ur inheritance your father left three cars he purchased when you returned to Nigeria , there's also a house in Australia where you lived , I didn't take any action without your input and regarding the money he left in RBA Australia I had Imran transfer it into my account, and the home you lived in before he passed away is still intact, since you are starting work today I decided to hand over the car keys to you as you will need them they are all parked outside , makullin mota daya ta dauka sannan ta juya Imran let's go har ta Kai kofa ta sake juyowa aunty ummi just kept everything with you ohk, gyada Mata Kai tayi wishing you all the best of luck , bye bye ta fada tana yin waje Imran ne yayi wa mahaifiyar tasa sallama ya bi bayanta shiga tasa motar yayi itama ta shiga ta ta suka dau hanya office dinta yafara kaita komai yamata yadda takeso hakan yasa suka wuce headquarter din direct office din sir jibril barau suka wuce dan shine babba awajen suna shiga bayan sun gaisa yace Imran zai iya tafiya itakuma zasuje ayi testing dinta haka yamata sallama ya wuce saida ya wuce sannan sir jibril yace what's your name ma ? mahreen ishaq abdallah, " ke jikar Mai martaba ce ko girgiza Kai tayi yace cousin dinki ma anan headquarter din yake Yana da kokari sosai , cousin dina ta maimaita yes Maher Khalid abdallah taji ya fada ashe a fili tayi maganar bata che masa komaiba Inda sabo ya saba da haka tunda Maher ma haka yake masa wani lokacin in ta motso dukda shine shugaban sa amma haka yake hakuri , mikewa yayi yace let's go jakarta kawai ta dauka tabi shi abaya bayan ta kafa P cap dinta ta rufe rabin fuskarta dashi har suka karasa wajen babba ne cike yake da bindigu da bullets da kuma sauran kayan aiki irin nasu karasawa sukayi wajen wata mata matashiya budurwa daga gani kasan fulani ce gaba da baya rubuce rubuce take tayi gaban table din na kalla miss rabi ah Kabir musa aujara nagani a rubuce mikewa tayi ta sara masa magana yai mata gani nayi ta tashi takarasa wani table din tayiwa wani magana sannan tafita , sir jibril ne ya karaso Inda ta jingina da bango tana danna waya sorry na aika a kirashi ne shi yake tantancewa da bada percentage sannan musan in da zamu ajjeki dagowa tayi ta kalleshi tana dan taunar lips dinta na kasa sannan ta girgiza masa Kai a zuciyarsa kuwa cewa yayi yau Allah ya hadani da miskilar yarinya shigowar Mr Maher da miss rabi ah ne yasa sir jibril barin mahreen ya karasa wajen su Maher ne ya sara masa bayani yafara masa ta gefen Ido yake kallonta ita da tace wa Ayman barrister ce me ya kawota headquarter su ta DSS sir JB ne yakatse masa zancen zucin dayake ta hanyar cewa yanzu sai muje ko da hannu yayi wa miss rabi ah magana cewa tai mata magana su shigo gaba sukayi shida sir JB tare da dayan ma aikacin muje ko miss rabi ah tace dagowa tayi ta kalleta sannan ta sauke kafarta daya daga jikin bangon ta bita duk sun zubo masu Ido bata kalli kowaba saida ta iso kusa dasu tasa hannun ta daga p cap din kadan yadda zata iya kallonsu sosai table din da aka wargaza pistol ya nuna Mata da hannu tafiya tafara kamar bazata taka kasa ba ta karasa duk sun zuba mata Ido jin idonsu na damunta yasa ta maida P cap dinta kamar yadda take dazun pistol din tafara hadawa cikin kwarewa a lokaci kankani ta hada ta tasa bullet sannan ta dan buga ta a table din ta ajje sosai su sir JB suka jinjina mata tabirgesu yadda take hada komai da zafin nama amma kuma a nutse saida yagama rubutun dayake ya dago bindigar yabi da Ido pen din ya buga a lip dinsa kadan kafin ya tabe baki da fadin muje wajan harbi biyosu tayi muryarsa ta tsinta wakika barwa bindigar batabi takan maganarsa ba dan batama dauka da ita yake ban cikin dan jin haushi ya juyo kusan Karo sukayi taja baya cewa nayi ki koma ki dauko bindigar ko dagowa tayi sukayi 4 eyes sorry I don't think dani kake tafada tana komawa dan dauko bindigar bayanta yabi da kallo Yana mamakin ta tunda ta shigo sai yanzu yaji maganarta saida yajira ta karaso sannan ya fara tafiya acan suka samesu karasawa yayi wajen miss rabi ah kije ki nuna Mata Inda zata harba sannan yazuba Mata Ido still wayar take dannawa daya hannun kuma tana dan juya bindigar muje can zaki harba tafiya tafara batare data dago ba, dakin dago Kin maida hankali saboda ki fuskanci abinda zan nuna maki still bata dago ba tace just go on kasa kasa miss rabi ah ta harare ta sannan tace acikin wancan black dot din akeso ki harba three chance ne dake kawai wayar ta kashe ta turata aljihun bayan wandonta sannan ta dan karkatar da p cap din gefe ta saita bindigar batare da jin wani dar ba ta rufe idon ta tasaki bullet din tafin dataji sir JB da dayan mutumin nayi ne yasa ta bude eyes dinta sannan tajuyo tana kallon su sir JB ne yace gsky nadade banga yarinya mai kwazo irinki wadda ta kware sosai ba Masha Allah gsky zaa ja dake juyawa yayi wajen Maher Wanda shima mamakinta ya kara cikashi amma ya boye sai murmushi kawai dayayi kagama rubutawa ne Maher yes sir yace Yana mika masa file din karba yayi yadan duba sannan yace ina ganin she will work under your office as your assistant girgiza masa Kai yayi sannan yace kinyi kokari cousin dinki maher zai nuna maki office dinda zaki zauna gyada masa kai kawai tayi dan itafa baso take yana wani nanata cousin dinnan ba wuccewa sir JB yayi miss rabi ah ma cikin dan jin haushi tayi waje dan komawa wajen zamanta ita taso samun matsayin mahreen saboda shiga jikin Maher amma percentage dinta bai kai ba dayan abokin aikin na sune yace natayaki murna dan murmushi tayi sann tace tnk u shima waje yayi wajen yarage daga ita sai Maher saida yagama kare Mata kallo up and down tanajin yadda eyes dinsa ke yawo ajikinta har saida ta dago suka hada Ido dauke kansa yayi kamar baisan da ita ba ya zaro wayar sa yayi wani katse latse sannan yace biyoni kamar bada ita yake ba har yakai kofa ya juyo yaga tana yadda take mahreeen ya fada cikin jin haushi yarinyar nan tanason samun ciwon Kai dagowa tayi tace yes muje yace binsa tayi suka fita rage tafiya yayi har saida ta karaso ki daga kafa malama aikin mu bana masu iyayi bane in kinsan baza ki iya ba sai zauna matsayin ki ki nemi aikin daya dace da mace ita dai bata ce masa komai ba , ba haka maheer ya so ba don so yayi ya sake jin maganar ta amma ganin bata tanka masa ba sai shima yaja bakin sa ya tsuke har suka shiga office na farko mutum hudune awajen mace daya maza uku mikewa sukayi suna sarawa Maher din da Kai kawai yake amsa masu office na biyu suka shiga babba ne office din kuma zaman mutum biyune table dinsa ne na farko sai na karshe empty . YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 31----40 Agaban table din ta tsaya tana karewa office din kallo saida ya danyi rubuce rubucensa sannan ya dago a tsaye ya ganta kamar an dasa ta phone dinta take bubbugawa akan lip dinta tana kallon wani wuri have a sit ya fada bata motsa ba ki zauna ya sake fada still bata motsa ba kansa ya dafe ya zuba mata Ido kamar ba zaiyi magana ba yace mahreeen kamar bayaso dagowa tayi idonsu cikin na juna why are you trying to give me a headache , "mee! hararar ta yayi sannan yace akwai wata ne bayan ke sau nawa ina maki magana kinyi shuru sorry I don't think you are talking to me Cox u haven't mention my name zuba mata Ido yayi dan ji yayi kamar ya maketa saboda haushi adan tsawace yace nace ki zauna ko kika min tsaye a Ka bata rai tayi ba a min tsawa Maher really ya fada yana juyi akan kujerar sa I'm your superior here not ur cousin you don't have the right to address me informally kujera taja ta zauna ba tare datace komai ba shuru office din yayi na dan wani lokaci sannan yace your name batare data kalleshi ba tace mahreen ishaq abdallah sunan ya maimaita har saida ta dago suka hada Ido ta dauke kanta meya kawoki nan , kallon Ka raina min hankali ta watsa masa kafin tace aiki , "ke ba law kika karanta ba meye hadinki da hukumar DSS ba tare data tambayeshi ya akayi yasan ita lawyer bace ta bashi amsa da I earned both my first degree in law and my masters degree in defence and security studies, how old are you ? This question is not relevant here ta fada tana daure fuska kamar wadda aka aikowa da mutuwa , tabe baki yayi tare da dage kafada irin I don't care din nan sannan yace wancan shine part dinki a office din nan and wancan toilet ne yana gaba fada ta mike zata fara tafiya cikin fada fada yace did I ask u to go I haven't finished juyowa tayi cikin masifa itama I have told you before don't shout at me I'm not your daughter although I will work under you, that doesn't give you the right to control me , I also want to remind you that I'm not going to work here permanently hope you Gerrit Ido cikin Ido suke kallon juna idonsa ya maida Kan hannun ta data matse spec dinta sosai kamar zata balle shi saboda masifa sannan ya sake dubanta juyawa tayi tafara tafiya yace mahreen kamar baza ta tsaya ba sai kuma dai ta tsaya ba tare data juyo ba tace lemme be. shuru yayi yana nazarin yarinyar there's something peculiar about her I need to know more about her. Tana fita taciro p cap dinta ajaka ta saka sannan tayi waje can wani waje data ga da kujeru karkashin wata bishiya nan ta karasa ta zauna ,duniyar tunani ta fada dole ta nemi mafita indai haka aikin nan yake dole tafara aiwatar da aikinta tun wuri ta rabu da wanna jarabar dan baza ta zauna mutum yana bat umarni ba kamar ubanta saida taji zuciyar ta tayi sanyi sannan ta tashi ta koma yaji shigowarta amma bai dago ba wucewa tayi Inda yace part dinta ne ta zauna kafarta ta dora kan table din sannan tafito da wayarta Kiran husna tayi suka gaisa ahankali take maganar har suka gama , dagowa yayi ya zuba Mata Ido kafar yabi da kallo kamar bata taka kasa sannan ya maida kallon sa gareta dole yasan komai da wurwuri domin take taken yayi yawa to me ma yakawota nan kuma mai take taqama dashi da har take irin wanna abubuwan, sarauta wata zuciyar taba shi amsa to ai shima jikan sarkin ne meysa sai ita yasan idan yace kiranta zaiyi wata sabuwar rigimar ce shi kuma baya son surutu da yawa pistol ya dauko sabuwa a drawer office din ya hada mata komai ya cikata da bullet sannan ya nufi table dinta a kujerar gaban table din ya zauna ya dora bindigar Kan table din dagowa tayi taga kafarta yake kallo saukewa tayi tana cigaba da abinda take dauki yace yana mata nuni da bindigar dan tura kujerar baya tayi sannan ta bude locker dake gaban table dinda kafa dan yatsa tasa ta dago bindigar ta wurga cikin locker din hmmm ya sauke wata boyayyar ajiyar zuciyar sannan yace ba anan nace ki ajje taba ki dauka ki tafi da ita gida taki ce amma kiyi taking care, okay tace kawai a ina kikayi karatu wanne daga ciki tabashi amsa both Australia and Russia why did u assume you wouldn't work here permanently ? Cox that's not my ambition , " and why do you choose it right now ? this is my personal plan and it's none of your concern baice komai ba yayi shuru can kuma yace there's a case I'd like your help with , come over when you are ready to hear the details ya fada Yana tashi ya koma Kan table dinsa saida tadau wasu lokuta ya ma dauka baza tazo ba sannan ta tashi ta karasa bayani ya fara mata sosai ta nutsu take sauraran sa har ya gama bayanin sannan ya mika mata file din mikewa tayi ina fatan kin fahimta yea and I will go through the information again good ya fada ita kuma ta wuce. 1:30pm ya shiga yayi alwala sannan ya fita yayi sallah Inda ya barta nan ya sameta ke bakya sallah ne ya fada , Bani da hijabi saida ya harari kayan jikinta sannan ya zauna waya ya dauka yayi dan danne danne sannan ya ajje kusan 30 minutes miss rabi ah ta shigo sai falli take rike da wata leda a hannun ta gashi sir ta fada pointing mahreen yayi da hannu miqa Mata karasawa tayi tace gashi from where ta tambaya sir Maher kallon sa tayi taga hankalin sa ma baya kansu okay thanks tace ita kuma ta wuce tana hararar ta budewa tayi taga jilbab ne aciki black colour tashi tayi tayo alwala sannan ta dau pray mat dinda ta gani ta saka hijabin ta tada sallah koda ta idar saida tayi addu a wa iyayenta da ya yanta sannan ta mike come and take your lunch kallon table din tayi leda biyu ta gani iri daya I'm not starving , bai sake cemata Kala ba ta cire hijabin ta linke ta maida a ledar sannan ta linke pray mat din ma ta maida Inda ta dauko abubuwanta ta hada a jaka ta saka p cap dinta ta gado ta dauki key din motarta sannan ta dauki wanna file din daya bata tayi hanyar waje where are you going wrist watch dinta ta duba it's almost 3 , and so , " I'm going to my office , office ya nanata yana dagowa yeah I'm going to our chamber whom do you ask for permission maimakon ta amsa masa saita maida masa tambayar what's your closing time ? I'm the one asking the question here not you dan yatsina fuska tayi I'm leaving now set your questions aside I'm going with or without permission and that's final, " do u know our rules ? They are for those staying long term tana gama fadar haka tayi waje wayar sa ya jawo ya rubuta message ya tura Kira ne ya shigo wayar da dagawa yayi da fadin yeah ita tare da katse Kiran. Tana fita chamber su ta nufa saida ta nutsu tabi baya nan dake cikin file din da ya bata daki daki sannan ta tsunduma kogin tunanin yadda zatayi gaskiya ta bayyana tabbas tasan Abdul hameed shine makashin iyayenta but a yanzu bata da evidence dole ta shiga jikin ya yansa dake gidan da haka ta yanke shawarar zuwa gida domin ta shirya ta koma masarauta tana samun baya nan data keso zata bar can din . Aunty ummi ta nuna rashin amincewarta da komawar mahreen can din amma dole dole ta tada bori akan sai taje haka ta barta amma da sharadin ba gaba daya ta koma ba murmushi tayi kawai tare da girgiza mata Kai Imran ya shiga rudani saboda barin mahreen gidansu badan komai ba sai dan shishshige matan da ayman yake yi amma ba yadda zaiyi ya san tunda tace sai taje sai taje din haka ta har hada duk abinda ta san zata bukata sannan ta nemi aunty ummi tai mata transfer wasu kudade a acc dinta. Komawarta masarauta kamar a kunnen Abdul hameed aunty amarya kuwa cewa tayi abu yazo da sauki husna ta shiga rudani sosai baza ta sake bari akashe mahreen ba saboda tasan itama Allah saiya kamata da laifin boyewa datayi tunda har da saninta. TWO WEEKS LATER Mahreen ce ta dawo daga aiki tana garden sai Ayman dake gefenta yana bata labarin wani case da suke shari'a a kai husna ta shigo wurin taji dadin zuwanta sosai dama jira take ta gama da wani abu tukun ta neme ta sai kuma gata kallon Ayman tayi da fadin Ayman excuse me please Ohk yace yana tashi ya basu wuri gaisawa sukayi husna ce tace mahreen mai sa kika dawo masarautar nan ? Ai gwara dana dawo ba gani cikin family na ba ko ya kikaga ta fada tana nazartar yanayin husnan, amma ni ina ga gidan aunty ummi yafi masarautar nan dadi kinga sai ki dinga kawo mana ziyara , " bakwa maraba da dawowa ta Kenan ? a a whl ko daya , to maisa kikace haka ? kawai saboda naga masarautar ba wani dadi bane da ita gashi zakiyi kadaici , " to ba ga ku ba murmushin yaqe husna tayi bata sake cewa komai ba sai mahreen da tace ni dama I want to ask you for your dad number inaso nazo muyi dinner ta musamman da kakana , "ba -ba baba wai ta fada cikin rawar murya tsayawa tayi tana kallon ta ganin yadda tarikice eh mana da problem ne ? no babu komai mika mata wayarta tayi tasa mata sai kuma ta tashi tai Mata sallama saidai kuma takasa tafiya sai tayi gaba saita dawo baya ita dai mahreen ta zuba mata Ido har ta fice girgiza Kai tayi tabbas husna ta san wani abu amma maysa tace tabar gidan haka taita tufka tana warwarewa har akayi magrip ta tashi ta shiga saida tayi sallar Isha sannan ta tashi ta shirya domin fara aiwatar da aikin da Maher ya wakilta ta akai cikin shigarta ta kullum cikin kananan Kaya tasa p cap tareda face mask ta dauki duk abun bukatarta ta jefa a jaka sannan ta fita granny tasamu da hadiman ta barka da hutawa tai mata sannan tayi hanyar waje kiranta tayi marin juyowa tayi , amma kinsan nan gidan sarauta ne ko irin wanna shiga bai kamata ba kina jikar sarki inata so nai maki magana ina mantawa amma hakan bai dace ba, in sha allah zan gyara ta fada tana yin waje motarta ta shiga tana kokarin tada wa text ya shigo wayar ta da wata bakuwar number good luck take care of yourself kaman ya Kenan waye ke bibiyarta ? Ya akayi aka san zata ? number ta dannawa Kira dauka akayi amma ba ayi magana ba hakan ya darsa mata shakku Kenan akwai mai bibiyar rayuwar ta tunda har akasan zata fita kuma aiki zata je yi bude kofar motar tayi da niyyar fasa fitar a yau din wani text dinne ya sake shigowa just go don't worry I'm sure you are curious about who I am but time will reveal that, number tabi da kallo special number ne komawa tayi kamar yadda ya rubuto amma ta kasa tafiya zuciyar ta na cikin fargaba can kuma ta tada motar ta fita sai dai kuma tunda ta fita ta lura da masu binta abaya zuciyar tace ta bata akwai Wanda yake son cutar da ita kuma hankalin ta yafi bata wanda ya turo Mata text ne ya akayi tabi abinda suka rubuto meysa bata fasa fitar ba duka ta kaiwa steering tare da take motar a 360 nan suma suka Kara wuta amma sun kasa kamota harta karasa restaurant din da zataje wayarta ce tayi Kara number husna ta gani dauka tayi cikin muryar kuka tafara hello hello mahreen kina jina yes husna what's going on why are you crying ? "where are you right now husna ta tambaya sunan wani restaurant ta fada daban a maimakon wanda take mahreen stay where u re , your life is in danger they are hunting for you , " who are they? There's no time just do as I say we will discuss later , ohk tace tunanin ta duk ya curkude tarasa Inda ma zata kamo wayar husna yasa zaren data kamo zamewa kwata kwata ta rasa waza ta alakanta da hakan ajje wayar tayi sannan tazaro wata a jakarta , Kira tayi da ita banji me akace mata ba naji tace ohk sannan takashe wani abu ta fito dashi a jakar ta makala a wanna wayar sannan ta dauki Jakar ta ta fito wurin wani table da wani mutum ke zaune ta nufa magana suke kasa kasa dana kasa jin me suke cewa saida mutumin ya gama sañnan tafito da wani abu a leda ta mika masa tashi yayi ya tafi wayar data boye akasan table din ta fito da ita tadanna wani abu sannan ta jefata jaka , wata yar paper ta dauko tayi dan rubutu sannan ta tashi tare da nufar wani service daya dauko tray da wasu sukayi order zai kawo masu kamar bata sani ba ta Kara waya a kunne bangajeshi tayi tray hannun sa ne ya fadi Wanda ya jawo kusan rabin hankalin mutanan wajen p cap dinta ta sake gyarawa sannan ta durkusa kusa da service dinda ya fara masifa yana tattare kayan magana tai masa a hankali sannan ta wurga masa takardar a fakaice mikewa tayi kamar gaske tana bashi hakuri kudi tafito dashi a hand bag dinta ta Mika masa sannan tafita mota ta shiga tana sauke ajiyar zuciya maganar husna ce ta dawo Mata a kai Kiran Imran tayi bugu daya ya daga Lilly how far Kana ina ta tambaya ansa Mata yayi jin yana kusa da restaurant din yasa tace ya karaso kamar zaice mai taje yi restaurant da daren nan sai kuma yayi shuru 10 minutes tsakani ya karaso Kara gyara parking din motarta tayi sannan ta dauki komai nata ta fito motarsa ta shige da fadin muje , " Inaaa ? ya tambaya Yana kallon ta da mamaki , masarauta, motar taki fa ? don't worry I will send someone to pick it up in the morning Kiran husna ne yasake shigowa bata daga ba ta tura Mata text I'm safe don't worry suna fita taga motar data biyota dazu number motar ta dauke sannan ta dauko karamin jotter a jaka ta rubuta what brings you here tonight ? my work tace a takaice, mahreen your work takes too much of your time, you should be with your family at this hour, this job doesn't deserve someone as valuable as you daga masa hannu tayi is okay Imran bai Kara cemata komai ba har suka karasa masarauta ya sauke ta a kofar part din granny tnk u bruh good night my warmest regards to aunty ummi and nawal in sha allah tomorrow I will pay a visit to them murmushi yasakar Mata sannan yace good night sweet dreams we will expect you girgiza masa Kai tayi sannan ta wuce. YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 41----50 Tana tashi ta shirya drivern part din granny tasa ya dauko mata motarta yau chamber su zata fara zuwa cikin shigar ta ta kullum amma yau an samu arziqin daura kimono a kai ringing din wayarta ne ya dame ta dagawa tayi hello husna daga dayan bangaren husna da jiya batayi bacci ba ta sauke ajiyar zuciyar mahreen kina lpy alhamdulillah , Dan Allah if u won't mind ina son ganinki , " nima ina son ganinki amma sai na dawo zan kiraki okay take care sallama sukayi duk abinda take bukata ta hada sannan ta wuce chamber su . Ayman ne ya sameta a can shi da wani tsoho wanda aka cuceshi kuma ake masa barazana da rayuwarsa kusan shekara hudu suke ta faman shari'a da mutanan wanda suka kasance yan uba ne gareshi har duk abinda yake dashi ya Kare har takai bashi da halin daukan lawyer a yanzu gashi kuma ya sake shigar da Kara , kallonsu ayman din tayi nifa bana minor case irin wanna mutumin ne yace yarinya ki taimaka min dan girman allah da ma aikinsa , "ohk shikenan cigaba da bayanin Ka inaji saida suka gama Mata bayani sannan tace yaushe ne hawa court din Ayman ne yace jibi wani court ne ? higher court, what time? 9:00am, Ohk karka damu zan tsaya ganin na kwato ma hakkinka in sha allah, nagode yar nan Allah ya miki Albarka yasa ki gama da duniya lpy ameen tace sannan suka Mata sallama suka tafi. Wayarta da tun dazu take haske ta dauka hello kina ina ? office di na ta bashi amsa a takaice jim Maher yayi baza kizo aiki bane ko yaya? later tace sannan ta kashe wayar duk bayanan case din daya bata ta hada sannan ta kulle office din ta fita. Tana shiga gaban table dinsa ta karasa noon tace kawai, " sai yanzu kikaga daman zuwa, a dan gajiye tace this is not your concern , I have plenty to handle gashi duk wani information dazaka bukata suna ciki file din wani abu mai kama da memory ta dauko a jakarta ta mika masa saida ya gama dubawa ya dago yana kallonta kafin yayi magana wayar ta tayi Kara amsawa tayi da fadin let's meet in Marshad delight kawai tace ta kashe wayar dagowa tayi idon ta ya shige cikin sexy eyes din sa da yake jifanta da wani narkakken kallon da ya riqe idonta kamar magnet shine ya fara dauke nasa da fadin you try, mikewa tayi yace ina zuwa kuma ? Ba tare data kalleshi ba tace I told u I have plenty to handle if I finish before 5 I will be back ta karashe tana ficewa, wayarsa dake haske ya dauka hello! ohk inaga mu hadu kawai a aiden palace by 4 , Ohk hakan ma yayi naji ance ta daya bangaren sannan ya kashe. Tana fita Inda tace wa husna zasu hadu ta nufa acan ta sameta sanye da niqab a fuskarta karasawa tayi suka zauna bayan sun gaisa husna ce tayi jim sai kuma tace mahreen bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya sameki dukda nasan nima a yanzu rayuwa ta tana cikin hadari k........nan takwashe duk abinda tasani ta fada Mata sañnan ta dora da fadin da safe na samu mama da Baba na nuna masu duk nasan sirrin su kuma idan har sukayi yunkurin kasheki zan tona masu asiri kuma inada evidence ta hanyar recording din duk abinda suke aikatawa yanzu kuma kafin na fito naji mama na waya da thugs dinta tace kosu san yadda zasuyi su samu abinda nayi recording secret dinsu ko kuma su kasheni K.a k..awai amma.a ka.rsu ba.r alamar dazaa gane itaaa.ce. ta karashe tana mai fashewa da kuka wanna wace irin rayuwace akan san abun duniya da sarauta zata iya sawa a hallaka yar ta kwaya daya ni harna fara kokwanto anya kuwa mama ce ta haifan ganin kowani lokaci zasu iya kawomin hari kuma bansan ya Shirin nasu zai kasance ba yasa na matsa maki mu hadu a waje ga wanna memory din nayi copyn komai kije kisa zakiji komai, nisawa tayi duk jikinta ya mata wani irin nauyi wanna wace irin rayuwa muke ciki ne kiyi hakuri husna Amma bazan bari ki koma gida ke kadai ba ame kikazo ? silalewa nayi na fito ban dauki mota ba saboda Kar a ankara nafito daga idon da zatayi taga wani daga can karshe kuma da alama su yake dauka awaya ganin sun hada Ido yasa ya mike da sauri zai bar wajen itama da sauri ta tashi ta bishi tana cewa husna ina zuwa tana fita yana shiga mota number motar ta kalla kawai ta shaida itace wadda aka bita da ita jiya da sauri ta karasa tace wa husna ta tashi da sauri . mota suka shiga tana yi tana kallon bayansu ganin ba Wanda yake binsu yasa ta sake komawa chamber su acan ta saka memoryn a system saida ta saurari komai sannan ta bude photo guda daya wanda ya kasance mutum uku ne a ciki Abdul hameed sai aunty amarya da chiroma jin ashe ba ita kadai sukayiwa illa ba harda mahaifin su ayman amma ita sunfi mata illa tunda kashe mata nata akayi idonta ne ya cika da kwalla wadda rabon da tayi wani Abu Mai kama da kuka tun data daga ta bar kasar kujerar ta juya sai kuma ta mike da sauri ta shige toilet. sai kusan 5:45pm sannan suka fito daga chamber ta lura area wajen kamar akwai matsala ganin irin motar dai da ake bibiyarta da ita tayi parking a kusa da chamber ta yadda Kana fitowa idan Kayi left zaka gansu tsayawa ta danyi kadan da mota har husna nace mata lpy wani mutum taga yana waya kuma yana waige waige kamar bashi da gaskiya tsallaken titin kuma wani shoe Maker ta gani ya zubawa motarsu Ido da matsala tacewa husna tana me cire pin din veil din ta dan wani gumi taji ya karyo mata dukda sanyi AC motar , " matsala kuma maiya faru ? sun san kina tare da ni saisa suka turo wanda zasuyi monitoring din mu, " na shiga uku shikenan husna ta fada tana fashewa da wani marayan kuka , " calm down husna ta fada tana reverse ta canja hanya saidai ba tayi nisa ba taga mota har biyu suna binsu abaya. Abangaren Maher 4pm tana yi ya karasa Aiden palace saida yayi reserving gaba daya wajen Sañnan ya jira mutanen suka gama fita ,wanda zasu hadu dashi ya jira sannan suka shiga tare saida ya gama bashi bayanan gaba daya umarni ya masa da hannu dayaje kawai tunani ya fada lalle dole mahreen ta shiga wani hali shi kansa da halin da mahaifinsa yake ciki da yadda rayuwarsu ta juya yakejin kamar duk duniya su kadai aka tsana ballanta na ita da aka kashe mata uwa a gabanta aka kashe mata uba a gabanta sannan aka kashe yayanta shima a gabanta wani irin tausayinta yaji yana ratsa duka jijiyoyin jikinsa daga waya yayi kamar zai kirata saiga kiranta ya shigo kallon Kiran ya tsaya yi cikin mamaki har ya katse sake shigowar wani kiran ya dawo dashi hankalin sa dagawa yayi yajiyo muryar ta a rude tana fadin hello Maher kanaji na saida ya lumshe idanun sa saboda yadda zuciyar sa ta buga da karfi kamar zata faso kirjin sa lip dinsa na kasa ya kamo ya tsotsa kadan sannan yace inaji, kana Inaaa? Aiden palace, ohk ta fada tana kashe wayar takarawa motar gudu map din motar take bi harta karasa Inda ya fada mata motocin dake binsu taga sun Karu wajen four gashi kuma duhun gabatowar magrip har ya fara, motar taso shigewa da ita ciki securities din suka hana da cewa ba wanda zai shiga saboda anyi reserving wurin jakarta ta dauka kawai tace wa husna let's go fita sukayi cikin zafin nama amma still sun hanasu shiga gefen rigarta ta daga bindiga ta bayyana sannan ta nuna musu ID din ta ba shiri suka basu hanya husna kam ba karamin tsorata tayi ba da ganin bindiga a jikin mahreen da dan gudu ta shiga tana jujjuyawa dan neman maher ganin ba kowa awajen . tunda suka shigo yake kollonta sunan ta ya Kira ganin tana kokarin yin wani wurin ba tare data Lura dashi ba kamar ma baa hankalin ta take ba juyawa tayi tana ganinsa ta karasa tana da gudu tana haki mikewa yayi husna da tsoro yagama cikata sai kuka take, duk da shima ya dan shiga rudu da yanayin daya ganta amma dake gwarzon namiji ne take ya shanye a nutse ya shiga tambayar su menene ? Jakarta ta bude ta dauko memoryn data nannade awata takarda ta mika masa akwai matsala keep this memory with you, meysa ? harbi sukaji da sauri ya dauki memoryn yasa a wallet dinsa sannan yasa a aljihu su waye suka biyoku bullet aka harbo daidai sashin mahreen cikin zafin nama ya fisgota bullet din ya samu bango dagowa tayi taja hannun husna da gudu sukayi bayan wajen can wani lungu tace ta buya karta fito har sai ta dawo sannan ta fita tana dauko bindigar ta kafar wani ta hango ta kasa Maher daya karaso wajenta da sauri tace duk wanda Ka gani Ka harba amma bata yadda zai mutu ba tana gama fada ta kwanta kasa ta saita kafar mutumin ta harba Maher da tuni shima yabar wajen ihun da wanna wanda mahreen ta harba yasa sauran fitowa gadan gadan suka bude wuta fafatawa aka shigayi tsakanin su har sukai nasarar harbinsu gaba daya kafa da hannu . A gajiye mahreen ta shiga sauke numfashi wani harsashin aka Kara harbowa saitin Maher da yake kokarin sawa bindigar sa bullet da wani irin gudu ta karasa gareshi tare da hankade shi da karfi bullet din kuma ya samu hannunta Kara ta saki daidai nan mutumin ya fito zai fice Maher da yaji ihun mahreen kamar an buga masa guduma a tsakiyar ka sakar masa harbi yayi take nan ya sameshi a ciki da sauri ya karasa wajen mahreen ya riko hannun ganin yadda jini ya wanketa nan take ciki hanzari ya miqar da ita yana kwala mata Kira a kunne ganin tana neman suma daukarta yayi ya dorata Kan kujera sannan ya dauko ruwa ya juye mata a fuska duk ya rude bude idonta tayi daya mata ja saboda azaba hus..na hu...snaa, tana ina ? hanyar data boyeta ta nuna masa sai yayi gaba sai ya dawo murmushi tai masa cike da karfin hali sannan ta maida kanta Kan table din yana zuwa ya hangota ta takure tana kuka muje muje kawai ya fada yana juyowa tabiyo bayanshi a sume suka sameta bai jira wata wata ba ya sureta yayi mota husna tabi bayansa da gudu tana kuka rike da jakarsu . A Mota ya kira yaransa na wajen aiki cewa suje su dauko wadanda suka harba sumusu treatment amma su tsare su saiyazo, direct hospital dinda yake aiki ya nufa da ita bai jira ankawo wani gado ba ya dauketa a hannunsa yayi ciki da ita husna na binsu taimakon gaggawa aka fara bata kwata kwata ya kasa ta buka komai ganin hakan yasa sauran doctors din sukace yaje waje ya jira, fita yayi ya jingina da kofar dakin husna ce ta taso tana tambayar sa mai ya sameta baice mata komai ba ya kalli hannun sa da kayansa daya baci da jini toilet ya karasa ya wanke hannun nasa sannan ya dawo kofar dakin yana safa da marwa wani tashin hankali yake ciki wanda rabonsa da shiga irinsa har ya manta bazai jure wani abu yasa meta ba ta sanadiyyar sa ba wanda ya taba masa irin wanna sadaukarwar ta gwammaci ta mutu a kan shi wani abu ya sameshi wani irin sarawa kansa yayi har saida ya dafe shi why mahreen why why wani irin abu yaji tun daga kafarsa har tsakiyar kansa game da ita ajiyar zuciya ya sauke yana daidaita nutsuwar sa tare da bude dakin ya shige. Saida akayi sallar Isha tukun ta farfado allurar bacci suka mata sañnan suka jona mata Karin ruwa suka fito ganin kallon da Maher din yake musu yasa doctor rukayya yin murmushi da fadin Kai doctor maher kai da kake farde mutane ma Ka dinke amma wanna duk Ka bi Ka rude cire bullet kawai kodai itace amaryar ta mu bai bi ta kan zance nata ba yace me ake ciki , munyi aiki an cire bullet din kamar yadda ka gani anyi saa ai bai fito ta barin hannun ba munyi mata dinki amma tana bukatar hutu sosai in sha allah ba wata matsala boyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya koma dakin , husna dake rakube kamar marainiya ta taso tana tambayar doctor rukayya abinda ta fadawa Maher Shi ta fada mata zan iya shiga husna ta tambaya eh amma ba ason hayaniya tana bukatar hutu to tace sannan ta tura kofar ta shiga. YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 51---60 Daidai kanta ya tsaya yana kallon fuskarta da tayi fayau drip din ya kalla sannan ya dago daya hannun wadda aka nade da Bandage ya hada da nasa ya zuba mata Ido har husna ta karaso dan nesa ta tsaya , karaso yace yana zare hannun sa daga nata sannan ya juyo wajen husna muje office muyi magana sai ki dawo ya fada yana fita binsa tayi har suka shiga office dinsa sannan ya zauna itama ya nuna mata wajen zama. Meya faru daku? tsaf ta fada masa komai takara da cewa idan ya samu lokaci ya saka zaiji komai cikin jimami ya dauki waya security guda biyu ya bukaci suzo sannan yace mata ta zauna a dakin mahreen karta fita ko ina wayar mahreen dake jakarta ce take ta Kara daukowa tayi taga missed call din aunty ummi ne kusan hudu saina Imran biyu, Kiran ne ya sake shigowa , hannun ya Mika Mata wayar ta bashi amsawa yayi da sallama dan Allah ina mai wayar ? tana hospital tazo wucewa ne rikici ya ritsa da ita har aka harbeta a hannu ya samu kansa da fadawa aunty ummi din, Innalillahi wa Inna ilaihir Raju un wani hospital din sunan asibitin ya fada mata sannan ya tashi yana mikawa husna wayar dakin suka koma shi da husnan har saida securities din daya Kira sukazo sannan ya cewa husna kinji abinda nace maki ai kuma karkiyi zancen da kowa ko dalilin daya sa har muka zo nan sannan ki kirasu kice su taho Mata da Kaya yana gama fadar haka yayi waje. masaurauta ya nufa ya shige part dinsu ba kowa hakan yasa ya shige dakinsa memory ya ciro sannan ya karasa karshen dakin labule ya yaye sannan ya Danna wasu numbobi dakin sirrin sa ne ya bayyana kamar wani office shiga yayi ya zauna tare da jawo system din ya kunna ganin ba chargy sosai ya sashi maqala chargy sannan ya saka memory din ya fice kofar ta rufe da kanta kayan jikinsa ya rage sannan ya fada toilet ya sakar wa kansa ruwa ko da ya fito kitchen ya shiga ya hada tea domin shi cewa yayi baya san wani bayi ko masu hidima saboda bayason hayani da yawan magana marar dalili sama ya koma direct dakin sirrin sa ya koma sosai ya nutsu yanajin abinda ke cikin memory kafin ya gamaji tuni jijiyoyin kansa sunyi rau rau he can't believe this baba Abdul hameed shine sanadin rashin lapiyar mahaifinsa wajen hoto ya shiga Abdul hameed da aunty amarya sai chiroma sune suka bayyana zooming din hoton chiroma yayi lalle da akace makashinka yana tare da Kai bai yadda ba sai yanzu chiroma daya kasance na jikin abbansa tun a wancan lokacin kenan ma dashi aka hada baki aka sawa abbansa guba yaci rufe system din yayi yana dafe kansa dake barazanar rabewa biyu Wanda ba tantama migraine dinsa ne ya motso tashi yayi ya fita daga dakin sirrin ya koma dakinsa locker dinsa ya bude ya dako wani magani guda biyu ya jefa a bakin sa sannan ya jingina da wardrobe ya dage kansa sama komai ya tsaya masa chak daren ranar ko bacci barawo bai iya sace shi ba . Aunty ummi da nawal da Imran wanda hankalin sa yafi na kowa tashi jin abinda aunty ummi tace ya faru da mahreen din dan shi yasan kawai sun boye ne amma watakil aiki suka fita aka harbeta dole ne idan ta nutsu yasan nayi shi dama wanna aiki ba sansa yake ba kwata kwata bai dace da ya mace ba a haka sukaje suka dubata da yake securities dinda Maher ya ajje basa cikin uniform saisa su aunty ummi basu lura dasu ba suka shiga, nawal da husna suka bari awajen ta sannan suka tafi da cewa inta farka nawal takira su . kadan kadan nawal da husna ke hira saboda rashin sabo dan ma nawal akwai dan surutu har dare ya raba nawal ta hau doguwar kujerar dake wajen ta kwanta ita kuma husna ta dauro alwala ta shimfida dan kwalinta ta fara sallah har saida akayi asuba sannan taga mahreen ta fara motsawa tashi tayi ta karasa kusa da ita tana Kiran sunanta a hankali. kadan kadan take bude idonta har ta bude su gaba daya akan husna kokarin mikewa take ta taimaka Mata ta zauna, sannu take ta mata daga Kai tayi ta kalli drip din da aka Kara sawa dazu hannun tasa ta cire sannan ta rufe wajen cannula din why do you remove it mahreen ? I'm going to take a shower , but dakin bari.... Shiii ta fada tana kokarin sauka kasa hannun ta fama ahhh ta fada tana rutse Ido kiyi ahankali fa saisa nace dakin bar wankan yanzu saboda Kar ki jiqa hannun karasa sauka tayi idonta akan nawal data farka tana kallonsu mahreen kin tashi sannu murmushi tayi who told you I'm in the hospital ? whl we have been trying to reach you but you weren't answering at the end someone picked up and told us you were in the hospital kallon husna tayi ita kuma tayi saurin fadin doctor Maher ne , doctor Maher ta maimaita ha a mai kuma ya hadashi da doctor shida yake hukumar DSS ikon allah sharewa tayi da fadin nawal kun kawomin kayane ? eh gasu can miko min husna ta fada tana wucewa toilet din . Saida tayi wanka tai brush ta shirya cikin skirt da riga English wear hijabin husna ta karba ta rama sallar magriba da Isha sannan tayi asuba ta koma gadon ta kwanta dan har yanzu jikinta ba karfi tunanin abubuwa dayawa take har doctor rukayya ta shigo da yake itace da night duty ya jiki tai mata sañnan tai mata yan tambayoyi ta maida mata drip din hannun ta sake dubawa nurse dinda take bayanta tace ta canja mata bandage din sannan ta juya wajen su nawal karta dau abu Mai nauyi da hannun saboda dinkin da akayi sannan ta musu sallama tafita, aunty ummi nawal takira ta hada ta da mahreen din taji muryar ta kamar yadda ta bukata idan har mahreen din tatashi. 9:00am daidai aunty ummi da Imran suka shigo da breakfast a hannunsu , bayan sun duba ta aunty ummi ta juya wajen su nawal sannan tace idan Imran zai wuce kije gida kiyi wanka yaso da rana saiki taho da lunch husna kema ya kamata kije gida ki huta ko, mahreen ce tace a a aunty ummi husna is not going anywhere , to ai mahreen She has to go home, take a bath, change her clothes and come back ko , "she will do it all here aunty ummi dai bata Kara cewa komai ba ta nemi guri ta zauna , Imran daya tsaya bangaren da mahreen take yace Lilly juyowa tayi suna kallon kallo ya akayi hakan ta faru ya fada kasa kasa yadda ita kadai zataji kafin tace wani Abu Maher ya shigo kamshin turaren sa na imperial majesty ne ya fara musu sallama yayi kyau cikin kananan kaya dark brown suit sai ta ciki light brown bai daura rigar suit din ba tana riqe a daya hannun sa daya hannun kuma waya ce riqe ya Kara ta a kunne da alama wata magana yake Mai mahimmanci gashin kansa da sajen kawai abin kallo ne saboda tsaruwar su da kuma kulawar da suke samu bayansa kuwa wani mutum ne rike da warmers din breakfast tun da ya bude kofar dakin hankali ya dawo kansa take kwarjinin sa ya cika wurin takun sa kuwa ba mace ba ko namiji dole ya kalla ya waiwaya domin ya san maza sun iso da hannun ya nunawa mutumin dake bayansa kan ya ajje basket din ya fita takaita wayar yayi sannan ya kashe fuskar ba yabo ba fallasa ya gaisa da aunty ummi sannan su husna suka gaisheshi Imran ne ya mika masa hannu sukai Musabaha sannan ya kalli mahreen da tunda ya shigo ta kasa dauke idon ta a kansa sai taga kamar ya canja mata ma hannun ta mai bandage ya kamo yana dubawa wani abu ne ya taso ya tokare Imran a wuya, "kinyi breakfast ya tambaya girgiza masa Kai tayi juyawa yayi wajen husna zuba mata tea da breakfast ya fada yana maida hankalin sa kan wayarsa har husna ta zubo tea ta fara mika masa karba yayi ya aje gefen ta sannan ya karbi plate din ya ajje, cup din tea ya dauko tea ya debo a spoon Yana firfitawa da bakinsa sannan ya mika mata kauda Kai tayi mahreen yakira sunan ta ahankali juyowa tayi cikin shagwabar da bata san tayi ba , " karbi nace ,ba musu ta bude bakin ya bata cikin wani irin tukuki daya tsayawa Imran a wuya ya tashi yayi waje binsa sukayi da Ido banda Maher da kawai feeding din mahreen yake kamar wata yarinyar goye har saida tace masa ya isa sannan ya mikawa husna cup da plate din ya Mika mata tissue. Masu share share ne suka shigo hakan yasa su aunty ummi fita dakin ya rage daga mahreen sai Maher magani ya fiddo a aljihun sa ya balla ya mika Mata tare da dauko mata robar ruwa ya mutsa fuska tayi ni bana sha ohk do u prefer an injection shuru tayi tare da kurawa maganin Ido dauka yayi da hannun sa open your mouth kamar zatayi kuka tayi yadda yace a tsakiyar tongue dinta ya dora mata magani sannan ya dora mata ruwa a bakinta da sauri ta fara shan ruwan har tana kwarewa bubbuga bayanta yake a hankali harta yi shuru , "da akwai securities awaje saboda dole zasu bibiyeku keda husna, okay tace ,do u need something ? husna need clothes to change ohk ya fada sannan ya fice ita kuma ta kwanta , husna da aunty ummi kawai ya samu a waje dan Imran da nawal sun wuce , aunty ummi yai ma sallama da cewa zaije wani waje ya dawo sannan yace husna ta biyoshi , wasu yaran sa da yakira su biyu domin su canji wanda suka kwana yayiwa magana sannan yacewa husna kibisu zasu kaiki ki siyo duk abinda kike bukata to tace sannan ta bisu shi kuma ya shiga motarsa ya wuce. YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 61----70 Yana shiga headquartern su da miss rabi ah ya fara cin Karo bayan ta gaishe shi kuma sai ta bishi office , saida suka zauna yace ya akayi ne? umm sir dama mahreen fa bata shigowa aiki Kan lokaci kuma kuma tafiya take kafin a tashi , " waya fada maki ? umm dama dama katseta yayi da tayi report ai karki damu idan kina da wata magana ki fadi ? a a babu sir dama na dauka baka sani ba ne sai da ya dan dakata ya dube ta kasa tayi da kanta girgiza Kai yayi kawai ya hado wasu takardu ya miqa Mata da fadin kije ki karasa wanna aikin , ohk tace tana karba ta fita . Kogin tunanin mahreen ya fada sosai yake jinta a zuciyarsa na farko tausayinta yake ji na biyu kuma ta sadaukar da ranta saboda shi da badan ita ba da yanzu shine a gadon asibiti Ko kuma ma ba wanna zancen ake ba table dinta ya kalla yana tuna rigimar da suke kullum idan tazo murmushi yayi kawai sannan ya tashi ya fita dan zuwa ganin yaran da yasa aka dauko daga Aiden palace. Sai rana Ayman yazo dubata (saboda Saida safe ya sani a lokacin daya kirata Kan maganar case din tsohon nan) nan yace anya kuwa gobe zaki iya shiga court din nan inaga kawai a nema masa wani sai a biyashi da ace bani da wani case din daidai time din dani zantsaya masa tun farko ma whl , "don't mind Ayman in sha allah zanje , "tho amma bakida lpy ai , karka damu zan iya. Imran kuwa har dare bai sake zuwa dubata ba kuma tana ji shi yakawo nawal kuma shi yazo ya dauki aunty ummi da dare bayan tafiyarsu sana ta Kira sun dade suna waya sannan sukai sallama. Sai 11 :46 pm Maher ya shigo a reception ya ga nawal tana waya karasawa dakin yayi husna ya samu Akan kujera tayi tagumi har bata san ya shigo ba idonsa yakai Kan mahreen da take ta danne danne awaya da hannun ta mai drip din karasawa yayi ya jawo kujera ya zauna sai a lokacin suka farga da shigowar sa husna ce tayi masa sannu da zuwa ya amsa Mata da kulawa, tashi tayi ta shige toilet juyowa yayi ga mahreen madam Mai ake tayi ne haka ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ajje wayar could you please discharge me , why ? "because I'm feeling alright, but you know they haven't removed the thread from ur hand right, " I know I will come back when they schedule the removal okay, but why do u insist ? cuz I have a case tomorrow in the higher court and I must attend . Then, how will we handle husna ? you know it's risky to let her return home , " I know she will stay with aunty ummi until we complete our investigation , alryt not bad, last night I listened to everything on the memory card, " then when will take them to court since we have all the necessary evidence , yea but I will visit them tomorrow night, I wanna go with you dan satar kallon ta yayi sai kuma yace okay , "what did you tell aunty ummi when she asked what happened to me ? I told them that there was a problem on the road you crossed and a bullet accidentally hit Ur hand when they fired their guns , " hmmmm alhamdulillah thank you so much , " why are you thanking me, "cuz she didn't know anything she doesn't know I'm working as a dss , "then why don't you tell her , she wouldn't agree . Dakin ne ya dau shuru na wani lokaci can kuma tace are you a doctor , yes and you are working as DSS officer how is that possible , " like how you manage your both roles ya bata amsa daidai lokacin da husna ta fito idonta yayi ja da alama kuka tayi wayarta ta ciro a chargy ta koma kujera ta zauna nawal ce ta shigo itama sannu da zuwa tai masa sannan ta nemi guri kusa da husna ta zauna dakin ne ya sake daukan shuru har saida drip dinta ya Kare sannan ya tashi ya cire da fadin kwanta kiyi bacci dan hararar sa tayi sai kuma ta kwanta din, samun chargy ta fada tana Mika masa wayarta kamar bazai karba ba sai kuma ya karba ya makala sannan ya musu sallama ya fita. Da safe da wuri ta shirya tayiwa husna bayanin komai Dan haka idan su aunty ummi sukazo tare zasu wuce ita kuma tayi da Ayman zaiso ya dauketa . 9am tana cika suna karasowa harda Imran bayan an gaggaisa bata bi takan cin maganin da Imran yake tayi ba tace aunty ummi tana son ganinta janta tayi suka fita daga dakin sannan tayi mata bayanin komai da kuma nasarar gano su datayi ta dalilin husna sannan ta dora da inaso ta buya agidanki har sai mun gama bincike, keda wa zakuyi binciken nan mahreen nifa ina tsoro, " ni da doctor Maher ne aunty ummi tunda shima abun ya shafesu ajiyar zuciya ta sauke bazan hanaki ba amma ki Kula da kanki sosai, " Insha Allah auntyna ta fada tana dan murmushi, tou yanzu da kika shirya ina zaki ? an sallame mu fa sannan ina da wani case ne a court kimin addu a aunty yaune zan fara shiga court , "Amma bakya ganin har yanzu baki warware ba kofa dinkin hannun ki baa cire ba, " karki damu aunty ummi bana son zaman asibitin daga baya na dawo acire inaso mu gama duk abinda zamuyi da sauri domin maka azzaluman nan a court , shikenan to muje kiyi breakfast ko. Saida tayi breakfast sannan suka dan zauna ana hira suna hada kayan da suke a asibitin don tafiya Imran ne ya hau kusa da ita akan gadon ya zauna Lilly nifa inada magana dake , "karka damu bros bari in danyi less busy , " amma kinsan daganan gida zamuyi ko ? yea nasani amma yanzu kasan court zani ba gida ba, " wa zai kaiki kafin tayi magana Maher ya shigo kaman jiya haka suka gaisa ciki kuwa harda mahreen da tace masa morning hannun sa yasa a goshi alamar sara Mata ba tare da yayi magana ba dan kallo daya ya musu itada Imran din ya kauda Kai cike da jin haushin Imran din wanda yarasa dalilin hakan , wrist watch dinsa ya kalla ba tare daya kalleta ba yace tashi mutafi inkin gama, "ina jiran Ayman nefa shi yace zai kaini cikin jin haushin ta itama da kuma kokarin controlling kansa ganin ya hana bacin ransa bayyana yace idan yakaiki wa zai daukoki to shi ya wuce in zaki tafi to in kuma bazaki tafi ba ki zauna yana gama fadar haka yayi waje. Imran ne ya juyo wajenta wai maisa yake maki magana ne sai kace wata yarsa ko kuma wadda yake da iko da ita kallonsa tayi taga kaman adan zafafe shima yake maganar, "to kai ma yanzu fadan zakamin ko Me? sauka tayi sannan tayi wa aunty ummi sallama tayi waje, number sa takira Yana dagawa tace Kana ina ? ki fito mana ya fada yana kashe wayar . Shuru ne ya ratsa motar har suka kusa karasa wa tace kafadawa granny ina hospital ? nop na dai cemata kina gidan aunty ummi shuru suka sakeyi har suka karasa tana kokarin fita yace idan kin gama kifito ina jiranki okay tace sannan tayi ciki. Cikin nasara suka samu alkali ya yanke hukunci saboda kwarara hujjojin data bayyana shari'ar kusan shekara hudu an kasa kawo karshenta sai yanzu, mutumin ne ya biyota Yana mata godia bakomai kawai tace. Kana kallon fuskarta kasan tana farin ciki dukda bata bayyana ba a Inda ya sauketa anan ta sameshi ya kwantar da kujerar baya shiga tayi ta zauna fuskarsa ta zubawa Ido ta daukama bacci yake , re u done ya tambaya kamar bayaso still idonsa a rufe kanta ta juya tana kallon waje tace eh gyarawa yayi ya kunna motar suka fara tafiya ahankali take bashi labarin yadda shari ar takasance murmushi yayi kinyi kokari sosai Allah yakara hazaka murmushin itama tayi sannan tace ameen har suka karasa gidan aunty ummi dukkansu wani yanayi sukeji na daban har basuso suka karaso ba , bude kofar tayi sannan ta jiyo thank you for the care I truly appreciate , get ready by 8pm , okay sir ta fada tare da rufe kofar ta fita . Imran ta samu a parlour da alama zaman jiranta yake karasowa tayi ta zauna tana fadin oh allah na nagaji kallonta yayi dama I'm just waiting for you , I can see she ai then what's up ? fadamin gsky abinda ya faru har aka harbeki ? shin shi doctor Maher din zai ma karyane Hala ajiyar zuciya ya sauke yana kallon hanya sannan yace nayi tunanin ko garin aikine ? nop ! sai kuma tace do you know what labarin abinda husna ta fada Mata ta bashi ta Kara da cewa kuma in sha allah everything has come to an end number Abdul hameed ta binciko awayarta tun ranar da husna tasa mata bata Kara bi ta kanta ba sai yanzu wanna number inason kaje kasa abincikomin duk wani list na calls dinda ke shige da fice da text messages zan baka letter cewar daga headquarter dinmu ne Ka wakilceni saboda abubuwan dake gabana dayawa bazan samu time ba kaji ko jinjina Kai yayi kamar wani danta yace an gama madam sai kuma yace to alhamdulillah tunda gashi burinki ya kusa cika sai kuma me next ? babu komai tace tana maida hankali kan wayarta, sai ki ajje wanna aikin kiyi aure kallonsa tayi wani aikin Kenan daga ciki ? aikin zaryar nan mana , "zanyi aure Amma ba yanzu ba , "to maisa ba yanzu ba mai kike Jira you are going to be 23yrs fa haba , "nayi tsufa Kenan ? nop ni ba abinda nake nufi ba kenan ai idan ma ba fada kikayi ba ba wanda zaice kinkai 23ye din , " then what's ur problem imran ta fada tana maida wayarta jaka ta zuba masa eyes gyara zama yayi sannan yace mahreen kinsan tunda kuka dawo nan na daura Ido akanki naji na sami Mata nayi kokarin bayyana maki kuma wanna abun ya faru ganin kin shiga rudu yasa na jinkirta daga baya kuma kika tado da tafiyar nan dan haka yanzu lokaci yayi dazan bayyana maki domin Nima na gaji da boye boye ajjiyar zuciya ta sauke Imran ba irin namijin da zaaki bane kuma ya bata muhimmiyar gudun mawar da baza ta iya mantawa da ita ba amma batajin tana masa son aure dan haka tace karka damu Imran zanyi tunani akai kaman zaiyi kuka yace wani tunani kuma murmushi ta masa gaggawa daga shaidan ne jinkiri kuma alheri ne Imran tunda nace kaban time kadan Kara hakuri mana tana fada ta mike ta wuce daki. 8pm daidai ta gama shirin ta yau atampa tasa dinkin skirt da riga Wanda yayi mutukar shiga da surarta bata daura dankwali ba sai mayafi data yafa kawai tadau jakarta ta fito a parlour ta samu Imran da daddynsa suna kallo wayarta ce tayi Kara tana dauka yace ina waje fa dakin aunty ummi taje tai Mata sallama sannan ta dawo parlourn tace wa daddyn zataje masaurauta amma ba Kwana zatayi ba adawo lpy yai Mata Imran ne yace Lilly dare baiyi ba kuwa ? don't mind Maher na waje Maher ya maimaita da mamaki ganin ta canja shigarta kuma tace tare da Maher zasu fita shin masarautar zasuje ko kuma wani wajen shima cewa daddyn sa yayi Yana zuwa sanna ya dauki dan makulli ya bi bayanta. Tunda ta fito ya zuba Mata Ido wani kyau yaga tayi masa kodan ta canja shiga ne yau data san yadda kayan Hausa suke karbarta data ajje wanna shigar tata ta yahudu da nasara tana karasawa ya bude mata kofa ta shiga idonsa akan Imran daya ke tsaye kofar parlourn jan motar yayi suka fice ba wanda yace da dan uwansa komai a maimakon taga yayi hanyar masarauta sai taga yayi wata hanyar daban batayi magana ba sai tsintar muryarsa tayi Yana cewa waye shi ,wa kenan Wanda nake ganinku a asibiti tare ya fada kamar bayaso, oh wai Imran kake nufi shine babban Dan aunty ummi he's so kind ba shida problem dan kallota yayi sannan ya maida kansa titi meysa yake bibiyar ki to , bibiyata kuma like how ? kalli mirrorn gefanki cikin mamaki take kallon motar tabbas motar Imran ce kallosa tayi ya akayi kasan shine kallonta yayi ya dauke Kai ba tare da yace komai ba daidai nan wani security ya bude gate din wani gida shiga yayi da motar yayi parking , inane nan ? in mun shiga kya gani ya fada Yana ficewa itama fita tayi ba tare da tsoro ba tabi bayansa wasu thug boys ta gani a parlourn da alama abige suke suna ganin su suka fara boye kayan shaye shayen su suna Kiran sai oga Allah yakara lpy bai wani kulasu ba ya Mika masu hannu alamar subashi wani abu key dayan su ya Mika masa sannan yayi gaba itama binsa tayi suna zuwa ya bude dakin wani dan dattijon mutum ne ya bayyana duk an masa jina jina tana ganin sa ta gane shine na hoton data gani tare da su aunty amarya kofar ya rufe bayan ta shiga sannan ya karasa gabansa kujera ya janyo da kafarsa sannan ya nuna Mata da hannu alamar ta zauna karasawa yayi gaban chiroma daya girgiza da ganinsa kaganeni ya tambaya Muhammad ma-maher maika keyi anan murmushin gefen baki yayi na zo ne kafadamin yadda akayi kasawa abbana poison a abinci cikin firgici yace a a whl bani bane bansan da zancen nan ba ohk baka daku ba Kenan barin kirasu a a dan Allah tsaya zan fada whl zan fada ma gsky juyawa yayi wajen mahreen da hannu yamata sign data danna recording sannan ya fara tambayar sa meysa kasawa abbana poison a abinci whl bani bane Muhammad nima sani akayi waye ya saka? alhaji Abdul hameed ne da matarsa ina zaman zamana sukazo suka cusa min raayin daba nawa ba kuma ya bani kudade masu tsoka da cewa idan na aikata zai bani fiye dasu shi yabani poison da cewa na kaiwa jakadiya ta zuba a abincin alhaji Khaled tareda bata kudi Mai yawa a furar dayakesha duk dare wadda takasance ita take damawa anan tasa masa saidai kash a daren bai wani sha sosai ba saisa bata kasheshi ba saidai illar datayi masa wanda har yanzu Bai dawo hayyacinsa ba sunso mutuwa yayi Amma jin babbar illar data masa yasa sukace ya Zama minor bazai yi wani tasiri ba kuma whl nayi nadama ya fada yana rushewa da kuka, hotonsu shida Abdul hameed da aunty amarya ya bude awayarsa ya nuna masa sannan yace kasan dai wanna hoton bana da bane meya Kara hadaku kuma duk kuka tsallake ko ina kuka shige har dakinsa cikin rudewa yace a a -a a whl kamar daga sama yaji tsawar Maher zaka fadamin ne ko yaya ? dan Allah Kayi hakuri ohk baza kafada ba Kenan zan fada zan fada karkayi gigin yimin karya domin haka na barazana ga rayuwarka ya fada Yana daga masa rigarsa Inda ya hango bindiga soke jikinsa ne ya dau rawa, kirana sukayi akan sunaso akawar da maimartaba Inda sukeso na jawo waziri cikinsu saboda waziri shine na kusa da maimartaba tunda aka nadashi tare suke shi yake bashi shawara anan nake chemusu waziri baze bada hadin kaiba saidai su nemi wata hanyar shine sukace idan har banbi umarninsu ba na kawo masu cikas to sai sun tona min asiri awajen waziri , wani asiri Kenan ? cikin kuka yace wata tsohuwar alaqata ce da amaryar waziri , Kenan da Kai akaje aka kashe uncle da iyalansa ? whl Allah kaji na rantse ma Muhammad bansan komai akan hakan ba sai daga baya da nake tuntubarsa da zance shine yake cemin shine kuma idan nayi gigin fadawa wani abakacin raina, shiwa Kenan Ka tuntuba? alhaji abdul hameed juyawa yayi wajen mahreen data dora kafa daya Kan daya ta zuba masu Ido da hannu ya nuna masa tayi saving record din, hakan tayi sannan ta mike ganin shima yayi hanyar waje , tare suka fita karbar duk wani Abu da aka kamo chiroma dashi yayi sannan sukayi waje suka shiga mota suka wuce masarauta still Imran na biye dasu Inda ita kuma ta kule da hakan karfa yaga dan yace Yana sonta yayi amfani da haka yaga kamar har tazama matar sa ne da zai dinga wani binta duk Inda zataje dole ma ta shata masa layi. A kofar part din aunty amarya sukayi parking sannan suka shiga ita dashi kawai suka samu a parlourn da alama wata magana suke Mai mahimmanci karasawa sukayi suka zauna cikin fara'a suka tarbesu wanda har hakan yabasu mamaki suka kalli juna mahreen ce tace ina husna aunty amarya ce ta cafe da cewa husna tayi tafiya taje zamfara wajen yayata bari akawo maku abinci ta fada tana tashi tayi ciki , Maher yajikin mahaifin naka ? yaji sauki gobe ma zasu dawo saisa nazo na fada ma ko zakuje taryoshi , adan rikice yace wai wadin kagane wani mahaifin naka nake magana kuwa ? yes nagane ba abban Muhammad Maher da Ayman da manira ba gobe zai dawo ai gumi ne ya fara tsatsafo masa tako ina sai ya Mike sai ya zauna Maher ne ya dora da cewa ya dai lapiya murmushin karfin Hali yayi Kai Amma naji dadi Allah yakawosu ashe har yasamu sauki bamu sani ba saidai kawai ace mana zai dawo ko awajen su waziri banjiba , "ai ba lalle kaji ba suprise muka muku , e..eh eh hakane ya fada still har yanzu baya nutsuwarsa kallon mahreen yayi alamar jinjinawa tai masa tana murmushi daidai karasowar aunty amarya da hadimai data dorawa abinci iri iri a tray tare dasu fruits da jugs aka ajje akan centre table sannan suka wuce ita kuma ta zauna tana murmushi bismillah ga abinci kuci mahreen ce ta Mike ta karasa gaban table din Apple guda daya ta dauka tana jujjuyawa a hannun ta sannan ta taka gaban gujerar Abdul hameed ta Mika masa apple din , gashi baba bismillah da sauri aunty amarya tace ha a Mene haka kuma mahreen wanna ai na kune ba nasa ba maisa zaici abincinku a a baza ayi haka ba murmushi tayi sannan tace saboda kinsa guba a ciki ko ? haba mahreen wanna wace irin magana ce takawa ta sake gaban table din sannan ta dauki cup ta tsiyayo juice takarasa wajen ta karbi kisha , ni ai bana shan irin wanna lemon mahreen, ummm wato muma ta uncle Khaled kikeso ki mana Kenan , wa wani Khaled din kuma mai muka masa dan girgiza Kai tayi sannan tayi baya ta ajje cup din a table ta juyo wajen Maher da gira tai masa alamar suje sannan ta dauki jakarta, mikewa shima yayi sannan ya kalle su an riga da an bari dan Kada ya girma wutsiyar rakumi kuma ta riga tayi nesa da kasa bar ganin allura kankanuwa ce karfe ce aduk lokacin da Mage ke waje bera baya Wasa yana da Kyau a rika Sara ana duban baki gatari qotar zata iya gocewa tasamu Mai saran kuma abinda dama ta jure hagun baza ta jure ba abinda ya Baka dariya yau gobe shi zai saka ka kuka yana gama fada haka yayi waje mahreen ta Mara masa Baya , cikin shock suke kallon kallo da matsala fa alhaji wai maike faruwa ne tabbas asirin mu na dab da tonuwa fiddausi dama na gaya Miki ai, ni nasan ba Wanda zai je famu wanna matsalar in ba husna ba ace Ka haifi da acikinka sannan yafi karfinka to wai tana ina ne ? an cemin suna tare da wanna mahreen din, amma fa kinaji yanzu take tambaya ina husna, to abin ya daure min Kai gashi layinta a kashe amma ni inada tabbacin duk yadda akayi dasa hannunta to yanzu miye mafita gashi ance gobe Khaled zai dawo wai ya warke , wani Khaled din tafada tana mikewa Khaled dai dakika sani dan maimartaba safa da marwa ta fara dan neman mafita. YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 71----80 Suna shiga mota ta kalleshi ya kalleta ina ganin kamar mun gama samun duk wasu hujjoji fa , "no Maher akwai bukatar kasa a kamo jakadiya saboda zasu iya canja mata raayi kuma nasa akawomin list din duk wani call da texts dake wayar shi Abdul hameed din , kema kin kawo idea gobe ki sameni a office by 2 domin wa'anda suka biyoku ran nan ma sun fada da bakinsu cewa aunty amarya ce tasa su to kamar yadda kika fada kinga idan muka hada da jakadiya shaidun mu suncika sai kawai mu makasu court motarki tana part din granny da safe za'a kawo maki sannan ya tada Mota suka fita . A kofar gidan aunty ummi yayi parking ita kuma tafita sweet dreams ya fada dan juyowa tayi da fadin same sannan tayi knocking gate man ya bude ta shiga a parking lot ta tsaya tana jiran shigowar Imran 2 mins tsakani sai gashi matsawa tayi yayi parking sannan ya fito ya karaso wajenta , "gidan uban wa kukaje da kuka fita ya fada cike da mugun bacin rai sakwato tayi tana kallonsa " I don't understand ? cikin tsawa yace mahreen nace gidan uban wa kukaje keda shi hannun ta tasa ta toshe duka kunnuwanta biyu tana jujjuya kanta, okay baza ki fada ba Kenan wato ke baki san mutuncin kanki ba bakisan darajar kanki ba a matsayin ki na ya mace har ki dauki kafa ki bishi gidansa take yanayin ta ya canja "Imran re u suspecting me or what ta fada tana ja baya baya sai kuma ta juya da gudu ta shige cikin gidan bata shiga dakinsu ba sai tayi wani dakin tana shiga tasa key ta zauna awajen ta dafe kanta ba abinda ta tsana irin zargi kuma yasan bata san tsawa shine yayi mata . A bangaren Imran kuwa dafe kansa yayi yana regretting yadda ya kasa controlling kansa har ya bari idonsa ya rufe ya mata abinda tafi tsana wata zuciyar kuma tace to ai Kana akan gaskiyar Kane gidan ya shiga direct dakinsu yayi batanan sai husna da nawal da suke bacci to ina tayi ba Inda bai duba ba bata nan har kofar dakin da take yaje amma jinsa a kulle ya dauka ummi ce ta kulle hakan ya zauna a parlour ya dafe kansa har saida aka fara kiraye kirayen sallah asuba sai lokacin ya tashi ya tafi dakinsa . Ko da safe ma aunty ummi ta dauka acan masarauta mahreen ta kwana har taji haushi dan bata fada Mata kwana zatayi ba amma batayi magana ba Imran kuwa sukuku ya tashi duk sai yaji badadi kuma bai ganta ba lokacin da zaayi breakfast ba yana tsoron kuma ya tambayi aunty ummi saboda zata nemi jin baasi a haka dai ya tafi aiki . Su nawal kuwa sunyi kiranta bata dagawa har sun gaji nawal ce ta tambayi aunty ummi Ko sunyi waya ne itama aunty ummi da dazu takejin haushin mahreen ganin yanzu tafi son masarauta akan wurin ta amma key motarta da gate man ya kawo yasa ta shiga shakku da tashin hankali in dai mahreen na masaurauta to ai baza ta aiko da motarta ba dan haka ta cewa nawal ta bari Imran ya dawo taji yadda zaayi. Sai 2pm ta tashi a baccin da sai 8 ya dauketa fita tayi ba kowa a parlourn a kitchen taji su hakan yasa ta shiga dakinsu wanka tayi da brush sannan ta dauro alwala ta fito husna ta gani a zaune bakin gado "ha a mahreen ina kika shiga Muna ta kiranki bakya picking , ina gida ta fada tana karasawa gaban wardrobe gida kuma wani gidan ? "nan mana ta sake bata amsa amma mu bamu ganki ba kuma baki fito anyi break dake ba , bata kara che mata komai ba saida ta shirya cikin white t shirt da legging fari ta daura armless gown wadda ta Kai mata har kasa peach colour tayi rolling veil din ta , handbag dinta ta dauka da spec dinta ta maqala takalmin ta tana kokarin fita nawal ta shigo yanzu kika shigo ne mahreen ? husna ce tace nima daga wanka nasa meta ta fito ina tambayarta tace min anan ta kwana nawal ce tace kaman ya anan ta kwana bayan mu bamu ganta ba sai key motarta aka kawo, kamar wadda ake wa dole tace a wancan dakin na kwana ina keyn motar ? Yana wajen ummi fita tayi daga dakin a parlour taga aunty ummi zama tayi sannan tace noon aunty ummi, mahreen ina kika je ana ta Kiran wayarki bakya picking sannan kuma aka kawo mana motarki hankalina ya tashi whl da Imran nake jira yazo ya kaini masarautar taku naji , " acan dakin na kwana bani key din motar, "mahreen me yake damunki aunty ummi ta tambaya , "bakomai , "ya zakice min bakomai bayan ni nasan akwai wani abu Mai aka maki waya tabaki ko kun samu matsala ne da wani a can din, "aunty ummi barin je in dawo tukunna ban key din , " gashi can Kan show glass Amma ko breakfast bakiyi ba gashi har an gama lunch tashi tayi ta dauko sannan tace saina dawo ta fada tana ficewa. Da hannu daya take driving harta karasa wayarta ta janyo a jaka missed calls tagani rututu dana husna na nawal na aunty ummi da na Imran da sana sai na Maher Wanda yake 20 mins ago time ta kalla 2:50pm fita tayi a motar bayan ta manna spec dinta a office din farko wani jami'in su ya tare ta da fadin mahreen ishaq juyowa tayi amma ba tayi magana ba me sa kike wasa da aiki ko dan baki san dokokin sa bane munan baa mana Wasa wani dake opposite dashi yace Kamal Kayi shuru kawai , "Kai mesa zanyi shuru ko dan tana jikar sarki sai tayi abinda takeso muma ai duk iyayen namu nada matsayi Amma idan mukazo aiki ajjeshi muke a gefe juyawa yayi wajen mahreen ana maki magana kinyi wani shuru Munan babu wani alfahrin Mulki ko sarauta daza a nuna mana ko da kuwa uban mutum waye kamar wadda iska ta debo ta kawota gabanshi bai ankara ba yaji ta kwasheshi da Mari da sauri duk suka Mike a wajen wanda hakan yayi daidai da fitowar Maher daga office dinsa yana waya da sauri kamar fita zaiyi ganin abinda ke faruwa kuma da mahreen yasa ya katse wayar Yana kallonsu daga hannu yayi da niyyar rama Marin tasa hannun ta marar ciwo ta rike nasa the greatest mistake you will ever make is letting ur dirty hand touch my face, you will regret it ,mind your tongue don't dare include my father in this Cox he's not your mate I will endure any insults you throw at me but never ever involve my parents Maher ne ya karasa ya ce mahreen sake shi kamar yadda yace din haka tayi hannun ta ya riko suka koma office dinsa. Wanda dazu ya masa magana ne yace to ai kagani na fada ma Kaki ji gashi yanzu yarinya karama ta kunyata Ka gaban mutane kuma ba abinda zaayi ta mari banza borin kunya ya fara yana fadin whl saina nuna Mata matsayinta saina nuna Mata waye ni dan bata sanni bane sude zaman su suka gyara suna boye dariyar su. Suna shiga yaja Mata kujera ya zaunar ta, karasa wa yayi fridge din office ya dauko Mata ruwan sanyi da cup ya zuba ya Mika mata ba musu ta karba tasha sannan ta dafe kanta shima zama yayi opposite da ita shuru yayi ya zuba Mata Ido can ta dago suka hada Ido a tare suka sauke ajiyar zuciya mahreen! yakira sunanta da wata iriyar murya bai jira amsawar taba yaci gaba dukda bansan abinda ya hada ku ba bai kamata ki mare shi ba kina matsayin ya mace har ki daga hannu ki mari na miji wanna ba hali bane mai kyau ba kuma tarbiyyar familyn mu bace plz karki Kara , tagumi tayi ta zuba masa Ido harya dasa aya akan kallon da take masa ya sa hannu ya zare tagumin da tayi sannan yace meye damuwarki shuru tayi can kuma ta kifa kanta Kan table din mahreen ya sake kiranta bata dago ba mahreen ya sake Kira dagowa tayi ganin bata da niyyar magana yasa yace to tashi mu tafi tunda baza kiyi magana ba mikewa tayi ta dauki glass dinta ta maida sannan ta dauki jakarta ta rataya a wuya tana kokarin yin waje ya riko hannun ta tsayawa tayi shi kuma ya Mike sannan suka jera suka fita da kallo duk mutanan wajan suka bisu , saida ya bude Mata ta shiga sannan shima ya shiga yaja suka fice. Shuru ne ya ratsa motar har sukaje gidan da sukaje jiya, kamar jiya haka yauma suka tadda su a parlour suna ganinsu suka fara sai yallabai Allah yakara lpy dayan ne yace hajiya gaba dai gaba dai takawarki lpy cikin jin haushi ta budi baki zatayi magana dan a halin da takejin zuciyar ta da kwakwalwar ta komai ma haushi yake bata hatta da maher din kuwa ji take kamar ta rufe shi da duka kuwa , kamar kuwa ya sani yayi saurin fadin mahreeen shuru tayi tana hararar su dan makulli suka bashi ya wuce awani daki na kusa da wanda suka shiga jiya suka samu jakadiya da alama itama taji jiki suna shiga ta fisge hannun ta daga nasa kallon ta yayi da fadin ki tambayeta ita ta zubawa abba guba a abinci kuma waya sata kamar baza ta motsa ba sai kuma tafara takawa takarasa gaban jakadiya tambayar ta tayi meysa tasawa uncle Khaled poison a abinci jakadiya ce tafara whl tallahi bani bace dan dagowa tayi ta kalleshi cikin wani irin masifa kamar zata hadiye ta ta sake tambayarta ba shiri tace whl nice nice whl tafada jikinta na rawa waya saki ta sake tambaya whl chiroma ne ya kawomin ni bansan komai ba bindiga ta ciro zaki fada ko baza ki fada ba da sauri Maher ya karaso ganin aika aikan da mahreen din ke kokarin yi Me hakan kuma mahreen ai bance da harbi ba, a tsawace tace rabu dani plz bindigar hannun ta yayi kokarin karba tace kai ma whl Kana matsowa ina danna ma ita sannan in danna wa kaina zaro Ido yayi sai kuma yayi murmushi yana nufo ta da fadin to harba mana harbeni ni dake Wanda ya fada ya fada yana karasowa tab da ita harba ina jira Yana karasawa ya warce bindigar har yana harba bindigar garin warta ta harbi sama hure bakin bindigar dake hayaki yayi sannan yasa ta bayan wandon sa kafadun ta ya riko kuka ta fashe dashi tare da kifa kanta a kirjinsa shima habarsa ya dora a kanta Yana dan bubbuga bayanta gaba dayansu wani yanayi suka shiga Mai wuyar fassarawa har saida tayi Mai isarta sannan ta dago hanky ya dauko ya share Mata hawaye yana Mata murmushin nan nasa mai tsada sannan ya riko hannun ta kamar dazu suka fita tare da kulle jakadiya ba kowa a parlourn juye juye ya fara can ya hangosu sun buya bayan kujera wasu karkashin center table wasu cikin labule fito Ku karbi key din, na bayan labulen ne suka leko aa yallabai whl harbi mukaji to mun dauka kwalawa ne suka kawo hari dan girgiza kansa yayi ba tare da yayi magana ba ya jefa masu dan makullin Ku Kula kuma ba wasu yan sanda anan yana gama fada yaja hannunta sukayi waje . A Mota yace mahreen meye damuwarki kamar baza tayi magana ba tace Imran , Imran ya sake maimaitawa sannan ya juyo ya kalleta me ya Miki ? zargina yake, "akan me ? saboda munzo gidan nan kafin muka wuce masarauta jiya shuru yayi can kuma yace Kenan shi zai nuna maki abinda yake daidai ko Me ko kuma ajje ki yayi bata bashi amsa ba har saida suka karaso cikin gidan sannan yace gobe zan shigar da karar nan, Allah ya kaimu mota ta fa? zaa kawo maki In na koma office, ohk tace sannan ta fita shi kuma yaja. Shigowar Imran Kenan parlourn ya dawo daga aiki gate man yakawo keyn motar mahreen , daga ina ya tambaya eh dama wanda ya kawo motar da safe ne yan zuma ya sake kawowa , wane shi Imran ya sake tambaya nima ban sanshi ba wani ne dai ohk ya karba sannan ya karasa nawal ya tambaya ina mahreen tace masa bata dade da dawowa ba taci abinci tana garden juyawa yayi ya fita a garden din ya hangota idanun ta a lumshe tunda ya karasa wajen tasan shine saboda turaren sa daya sanar mata kujera yaja ya zauna sannan ya dora Mata dan makullin motar ta akan table din lilly I'm so sorry please forgive me u know I never meant to hurt u, I always want to see you happy even yesterday I Was just extremely upset and couldn't control my self haka ya dinga lallaba ta da kalamai har ya samu ya shawo kanta ta bude idanun ta akansa amma kasan bana son tsawa ko mesa zakamin , "nasani I'm so sorry a haka dakyar ya shawo kanta amma bata wani sake kamar da ba wayarsa ya mika mata ki duba aikin dakika sani yana ciki an kammala idan kin gama kya kawomin wayar yana gama fada ya ajje Mata a table din sannan ya juya yabar wajen. Washe gari kamar yadda ya fada haka yaje ya shigar da Kara , ana kaiwa su Abdul hameed sammaci ya fara kokarin guduwa ba tare daya sanar da aunty amarya ba hakan da yayi yasa Maher dayasa ana monitoring dinsu sawa a daukoshi a kaishi gidan da aka Kai su chiroma, aunty amarya ta shiga tashin hankali sosai data wayi gari bata ganshi ba itama attempting escape tayi kamar yadda yayi aka kamata aka je aka hadasu ganin anfara cigiya a masarauta kuma hankalin sarki ya tashi yasa Maher da Ayman shiryawa domin su dauko mahreen suzo suyiwa Mai martaba bayanin komai . A gate suka sami mahreen da Imran zaune suna hira sai dariya suke yana nuna Mata wani abu a waya, wani zillo zuciyar Maher tayi har saida ya lumshe idonsa , ayman ne yace ai gama tanan, sauka Ka kirata kawai yace ba tare daya bude idonsa ba fita yayi ya karasa suka gaisa da Imran har Yana tambayar yasu maimartaba juyawa yayi wajen mahreen cikin zolaya yace ranki ya dade wajenki mukazo fa , " tho fa kai da wa kuma? ni da mutumin naki mana Maher yana mota , tell him to come over mana kuma sai ya tsaya a mota sai kace wani bako, "to bari dai ace masa sakonki ne ya fada Yana dan dariya ya koma mota. Ko da ayman ya fada masa abinda mahreen din tace yi yayi Kamar bai ji ba can kuma ya yunkura ya fito hannunsa zube a aljihu har ya karaso ya koma ainahin Maher din sa dan ba alamun wasa a tattare dashi Imran ne ya mika masa hañnu domin su gaisa ba tare daya kalle shi ba ya daga masa hannu alamar salam sannan ya juya wurin mahreen din sauri nake je ki canja Kaya fita zamuyi, " Imran ne yace ha a Malam yaza kazo ka sameta sannan kace ta tashi ta canjo Kaya kufita ko ance maka bata da ma fadi ne zaman kanta take a duk lokacin data ga dama tafita aduk lokacin da taga dama ta dawo sai a lokacin ya daga Ido ya dubesa a wulakance idan ina magana da ita ka dena tsoma min baki kuma inada iko da itane sai sa nace ta tashi taje ta canjo Kaya ko kana da ja , " Kai awa zakace Kana da iko da ita ni nan ni ne mai iko da ita saboda ni ne mijinta wanda zata aura nan bada jimawa ba , wani kallon tara saura kwata yai masa yana ebansa a sheqale ya watsar miji oh really to bari mugani taku daya ya kara tare da kawata fuskarsa da murmushi cikin wani salo yace my princess tashi kije ki canjo Kaya karkimin wanna banzar shigar kiyi shiga ta mutunci kinji na baki five minutes mikewa tayi a fusace Imran yace lilly idan har na isa dake koma ki zauna itama cikin daga muryar tace imrannnnn stop it meye hakan wai kakeyi ne ta karashe tana wucewa ciki , yatsu biyu ya sa a baki tare da yin wani siririn fito yana murmushi tare da juya kwayar idanunsa kamar wata mace tho ya kaga Wasan ya fada yana wucewa ya bar Imran din daya kasa wani kwakwaran motsi. mota ya koma ayman ne yace mai ya faru naji kuna ta hayaniya ko kallon sa baiyi ba idon sa na kofar fitowa daga falon aunty ummi ganin haka yasa Ayman Jan bakin sa ya sa kwado ya kulle dukda ba hakan ya so ba dai . Shiryawa tayi cikin dubai abaya black mai golden stones ajikin veil din datayi rolling dashi an rubuta sunanta da stones din ta dauki jaka da takalmi black samun kanta tayi da cewa aunty ummi zata masarauta ta dawo dukda bata san ina zasuje din ba sannan tai wa su husna sallama ta fita tana fitowa ya sha gabanta, mahreen wai me kike nufi dani ne miye tsakaninku da har ina mijin da zaki aura namiki umarni ki ki bi , Imran yaka Mata Ka gane dan Kana mijin dazan aura ai ba aurena kake yanzu ba nifa ba yarinya bace nasan me nake, " ohk haka kikace , cikin tabbatar wa tace naam haka nace Imran , "to shikenan zanyi wa tufkar hanci , ka hada harda baki ma ta fada tana wucewa ta bude back seat ta shiga yaja mota suka fice. YOUNG WRITER MAHREEN PAGE 81---90 PALACE Bayan sun shiga sun mika gaisuwa Ayman yace wa waziri suna da magana da maimartaba , sallamar mutanan fadar akayi sannan yace dasu sarki na sauraren Ku bayani suka fara masa tare da kunna masu duk wasu audio. Sarki mai adalci da tawakali ya girgiza da jin abinda kaninsa ya aikata masa uwa daya uba daya akan Mulki ya nakasta masa ya ya da duk duniya bashi da wa anda yake kalla yaji dadi saisu cike da bakin ciki yace wa Maher Allah yakaisu ranar zaman kotun. Duk wasu evidence daya kamata Ayman da mahreen su tanada sun hada domin so suke ranar da aka hau kotu a yanke hukunci kawai duk wasu maganganun sirrin da Abdul hameed yayi a waya mahreen ta tantancesu, sun bawa Abdul hameed damar daukan lauya haka kuwa akayi yayi wa lauyansa magana tare da masa bayani cewa karya ne shi bai aikata duk abinda suka ceba, ko da mahaifiyar Maher taji labari ta girgiza dama ta dade tana zargin furar da jakadiya ta dama ranar amma kasancewar batada hujja yasa tayi shuru kuma jin halin da ake ciki akan hargitsin da Abdul hameed ya kawo a masarauta yasa bata gayawa su Maher improvement dinda aka samu akan rashin lafiyar mahaifinsu ba , dan likitoci sunyi aiki sun qone ragowar gubar dake jikinsa sannan suka bada tabbacin zai kai one zuwa two weeks kafin ya farka amma suna da hope idan ya farka zai tashi lafiya. Abangaren Imran kuwa daddysa da aunty ummi ya samu kan cewa sun daidaita da mahreen akan zasuyi aure shine yazo ya sanar masu ganin yadda suke sai basu bukaci jin ta bakin ta ba Inda daddynsa yace abari idan aka gama case din nan sai suje har wajen maimartaba suyi magana cikin farin ciki ya tashi ya tafi da fadin Allah yakaimu. COURT Cike take makil tako ina ka juya mutane ne waziri shiya wakilci Mai martaba can cikin lauyoyi na hango Ayman da mahreen suna ta hada takaddu rigistra ne ya Mike ya Kira shari ar su mahreen sannan yamikawa judges din su uku dake high table file din , judge din na tsakiya shi yace ina lauyan masu Kara Ayman da mahreen ne suka Mike sannan akace ina lauyan mai kare wanda ake Kara lauyan Abdul hameed ne ya Mike daidai lokacin da aka shigo dasu Abdul hameed da aunty amarya da chiroma da jakadiya Maher ne da yaransa guda biyu abayansu waje ya nema ya zauna , nan aka fara karanto laifin da ake zargin Abdul hameed dashi karyata wa yayi da cewa sharri ake masa shi bazai yi haka ba judge ne yace to ku kunji ya musa shin kuna da hujja mahreen ce ta Mike ina da ita hujja ya me girma me shari'a takawa tayi gaban Abdul hameed audion sa ta bude masa saida ya gama ji sannan ta karasa ta mikawa registra shi kuma ya kunnawa judges din duk suka saurara tukun aka kunna masu hotonsa tare da su chiroma da matarsa kuka ya fashe dashi da cewa na amince na aikata whl amma sharrin shaidan ne kuma da sharrin Matata ya fada Yana pointing aunty amarya ita ta jefani a bala'i , alhaji sharri zaka mun ni fa bansan komai ba muhawara ce ta barke a tsakaninsu har saida kotu ta tsawatar masu, kansu chiroma da jakadiya aka koma ba musu suka amsa yaran da suka tura ranar domin kashe su husna tare da yaran da suke tare da Abdul hameed a ranar daya kashe iyayen mahreen tambayoyi aka masu suka amsa lauyan Wanda ake kara ko kanada ja akan hujjojin da kuma bayanan da lauyoyin masu Kara suka bayyana cike da sanyi jiki yace bani da ya Mai girma mai shari a. kotun ce tayi shuru na wasu dakika sannan Mai shari'a yace according to Section 319 of the Nigerian Criminal Code . Subject to the provisions of this section of this Code, any person who commits the offence of murder shall be sentenced to death dan haka kotu ta yankewa Abdul hameed Umar Jamil hukunci kisa ta hanyar harbi da bindiga sakamakon rashin wahalar da shari a da baiyi ba kotu ce tayi tsit sannan judge yaci gaba da magana kotu kuma ta yankewa fiddausi auwal magaji hukuncin zaman gidan Kaso na tsawon shekara goma tare da horo Mai tsanani sannan kotu ta yankewa jakadiya daurin rai da rai sakamakon yunkurin kisan Kai datayi ta hanyar saka wa uban gidanta guba a abinsha sannan an yankewa chiroma shekaru bakwai gidan yari tareda Tarar 500,000 nan kotu ta dau hayaniya ,asaurara masu shari'a suka fada sannan aka koma Kan yaran nasu shekaru bibbiyu aka yanke masu tare da Tarar dubu dari dari sannan masu shari ah suka buga guduma duk mikewa akayi har saida suka fita sannan mutane aka fara maida zance mahreen ce takarasa wajen husna dake kuka ta dago ta rungume itama hawayen taji suna neman zubo Mata saboda tuno da mahaifanta da tayi aunty ummi ce ta karaso ta hada su duka ta rungume hakika husna kinyi sadaukarwa Kuma ubangiji shi zai maki sakayya da mafificin alheri hakika zan rikeki kamar yadda zan rike nawal kinji ahaka duk suka firfita waje . fitowa akayi zaa tafi dasu Abdul hameed husna ta karasa wajensu "Baba kayafe min hakika banyi hakan dan na tsane ku bane idon Abdul hameed cike da hawaye yace baki min komai ba husna kuma na yafe maki domin taimako na kikayi dan nasan idan naje lahira azabar sai tafi haka gwanda amin anan duniya kuma nayi nadama ina fatan Allah ya karbi tuba na Allah yamiki Albarka yabaki miji nagarih wanda zai Kula dake inaso ki rokarmin yaya gafara ya yafemin kinji yana gama fadi aka tasa keyarsa mama tace tana riko kafadun aunty amarya juyowa tayi mama kiyafemin murmushi tayi ba komai husna Allah ya yafe mana mama fishi kike dani Dan Allah mama kiyi hakuri kiyafemin kema, ko daya ba fishi nake ba dama ko ba yanzu ba asirin mu sai ya to nu domin rana dubu ta barawo rana daya tak ta mai Kaya dan haka Allah ya miki Albarka ki Kula da kanki kirike sauran yayunki da hannu bibbiyu sannan ki dauki matar babanki lamya kamar ita ta haifeki kinji nasan bata da matsala zata Kula dake itama wucewa akayi da ita aunty ummi ce ta jata sannan suka shishiga mota direct masarauta suka wuce , ranar cikin jimami aka yita sai dare suka komo gida. TWO WEEKS LATER Imran ne ya matsawa mahreen cewa taje ta ajje aikinta na DSS tunda burinta ya cika kuma ga magana har taje gaban mai martaba gashi ba a wani ja auran ba aka saka wata uku masu zuwa , "bazan ce zan ajje aikin nan yanzu ba gsky Imran, "to sai yaushe ne dear inaga dama iya waadin dakika dauka daga burin nan naki ya cika zaki ajje mesa yanzu kike son canjawa murmushi tayi karka damu Imran nama alqawari kafin auren zan ajje aikin, " ni fa dear ya kamata a canja min sunan nan , " ummm karka damu akwai lokaci ta fada can kasan zuciyar ta kuwa batajin wani son Imran kawai dai tasan ya Mata halacci kuma bashi da wani aibu amma ita tarasa me sa batajin sa a zuciyarta ta , kanta ta daga sama tana kallon yadda iskar hadarin farkon damina ke kadawa karar text ne ya shigo wayarta dubawa tayi Maher ne yace kina ina ne sunshine sunan ta sake maimaitawa sunshine reply ta masa da gida , inaso inzo in ganki a fakaice ta kalli Imran dayake danna waya shima tuna abinda ya faru tayi rannan hakan yasa ta tura masa Kai Kana ina ? love garden, ohk wait for me there, hopefully there's no problem, yea kawai ya tura Mata kallon Imran tayi sannan tace inaso naje naga granny na dan kwana biyu ban leqa ba kamar zaice suje ya kaita sai kuma dai yace adawo lpy take care , okay tace sannan ta koma ciki after dress ta dora sannan ta fito, da map tayi amfani dan zuwa Inda ya fada matan. tana fita ta kirashi kwatanta mata Inda yake yayi tana karasowa ta zauna , murmushi ya mata ai na dauka baza kizo ba gira daya ta daga maisa tho zanqi zuwa, " umm to nagode ya jikin abba ta tambaya da sauki alhamdulillah shuru sukayi na dan wani lokaci sannan yace mahreen naam tace tana bashi full attention dinta saida ya nisa sannan yace mahreen kina so na , shuru tayi kamar me tunani kafin tace kaman ya bangane ba, I mean kina so na zaki aureni , "whl har yanzu ban bangane Inda Ka dosa ba Maher wace irin magana kake ne , wani zazzafan numfashi ya fezar mahreen ina sonki kuma ina so in aureki mu rayu cikin aminci , "ni kuma bana sanka Maher ban taba ma kallon irin san da kake magana akai ba ina sonka a matsayinka na cousin dina kuma jini na , karya kike mahreen kina so na ya fada Yana Mikewa, itama mikewa tayi nace ma bana san ka Imran nake so kuma Shi zan aur.... Bata karasa ba ya bige mata baki karya kike mahreen kalli cikin idona kice min bakya so na baza ki aureni ba sannan me sa kika taremin bullet ranar nan in har da gaske bakya son nawa meysa baki bari bullet ya sameni ba kinga mahreen karki cuci wanna zuciyar data cika da begenki ki nutsu muyi magana ta fahimta ki bar wani zancen imran karkice ko dan kina zaune gidan su baza ki iya cewa bakya sansa ba , "wai Kam ko Ka kurman ce ne Maher nace ma Imran nake so kuma Shi zan aura nan da three months kasan dai bakyau nema cikin nema ko kuma kasan magana har taje gaban manya ya kakeso Ka hargitsa min tunani ne, "ko daya mahreen kin kasa banbance SO DA KAUNA kinason Imran amma ni zuciyar ki take kauna ga hakan a idonki me sa zaki karyata me sa zaki hana zuciyar ki abinda take kauna haba mahreen ki bar wanna wasan dan baki san yadda nake ji bane da baki fada min wanna maganar ba dan Allah in wasa kike ki bari zuciyata zata iya bugawa hañnun ta yakamo ya dora daidai saitin zuciyar sa mahreen please kitaimaki wanna zuciyar hannun ta ta kwace ta rufe bakinta dashi duka hawaye suka fara ambaliya a fuskar ta da sauri ta juya gudu gudu sauri sauri ta hada ta fice ko ganin gabanta sosai batayi haka ta karasa mota ta fige ta a guje sai gida bata shiga ciki ba saita zagaya baya saida taci kukan data rasa na miye sannan ta wanke fuskarta a tap ta shiga gida lokacin an fara Kiraye Kirayen sallar magrip. TWO DAYS LATER zuciyoyin nan biyu sun shiga wani hali especially Maher daya tabbatar mahreen na neman yi masa nisa tunda gashi ya tabbatar nan da wata ukun ne aurenta duk ya rame ya fita hayyacinsa , sai kuma ya samu Kira daga Ammi cewa su zo tana nemansu da gaggawa cikin tashi hankali yake tambayar ta ko wani abune ya faru ba komai ku de kuzo kawai cikin wani tararrabin ya sake fadawa ba bata lokaci ya sanar da Ayman suka shirya tafiya tare da sanarwa grandparents nasu zasuje duba mahaifinsu ne . Suna zaune bayan an gama masu screening ya dauko wayarsa yana so ya kirata kuma me ma zaice mata da haka dai ya yanke shawarar kiranta har sau biyu bata dagaba sai ana ukun ne ta daga hello!, inaji tace, cikin dacin rai da kuma dacin maganar da zai fada ya lumshe idon sa dama na bugo ne na tayaki murna Allah ya sanya alheri zanyi tafiya watakil kuma kafin na dawo kinyi aure Allah ya baku zaman lpy yana gama fada ya katse wayar yana dafe kirjin sa da yakeji kamar zuciyar sa zata fito, abangaren mahreen ma hakan ce ta kasance wani Abu taji ya tokare Mata makoshi so take tayi kuka ta kasa pillow ta kankame tana runtse Ido tare da sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya. Abun da suka Tarar a Egypt shiya kusan shafe rabin bakin cikin da Maher ya taho dashi abbansu suka samu zaune manira na gefensa tana basa labari Ammi kuma tana hada masa shayi sunyi farin ciki sosai ganin abbansu ya tashi daga paralysis kuma yana magana saidai takawar ne har yanzu batayi karfi ba sati biyu da zuwansu aka sallame su daga asibitin gidansu dake nan Egypt suka koma . yanzu ma zaune yake shi da abbansa yana matsa masa kafafunsa manira da Ammi kuma suna kitchen Ayman kuma ya fita , abba ne ya dafa kansa son miye matsalar murmushin karfin hali yayi ba komai abba mai ka gani ? Maher karka boyemin damuwarka ko da banida lpy ina gadon asibiti mun saba sharing komai tare dukda baka fadamin marar dadi amma komai zakayi ko kayi saika labarta min dan haka kafadamin abinda yake damunka nisawa yayi sannan yace abba Dama....... Zayyane masa komai yayi dan jim abban yayi sannan yace karka damu Maher idan mahreen matar kace bata da miji sai Kai idan kuma ba matar Ka bace to Ka qaddara dama haka Allah ya tsara girgiza masa Kai kawai yayi ba tare daya sake cewa komai ba. wata biyu sukayi sannan suka shirya dira Nigeria domin yiwa mutane bazata dan dama basu fadawa kowa tashin abban ba ,kwana kwana Maher ya fara dan baya son dawowa Nigeria yanzu amma abbansa ya kasa ya tsare tare zasu dawo hakan Kuwa akayi abba ya tuso keyarsu suka dawo manira cike da farin ciki take dan ita batasan Nigeria ba tun tana 1 year aka tafi da ita Egypt. Mahreen mahreen kina ina mahreen ce tafito daga daki har wani yar rama tayi naam aunty ummi, kije kicewa su husna su shirya anjima zamuje sannu da zuwan kanin mahaifinki , sun dawo ne ? eh kuma ance ya warke ma, Allah ya Kara lpy tace tana komawa ciki jiki a sanyaye duk ta zama wata iri . Bayan magrip suka shirya nawal ce ta kalli mahreen tab yau dai inajin zaai ruwa da kankara yau kece zaki fita da hijabi mahreen bata kulata ba tayi waje, a parlourn grandmother dinsu duk suka samesu har Mai martaba mahreen da Imran sune abaya tunda suka shigo idonsa na kansu Amma sai yayi kamar wayarsa yake dannawa gaishe gaishe aka fara abban su Maher ne yace zo nan daughter zo ki zauna nan kusa dani Kan mahreen akasa ta karasa ta zauna satar kallon Maher tayi taga ya kauda Kai can kuma ya mike ya fice a zuwan zai amsa waya Mai martaba ne ya bukaci abar mahreen anan ta kwana Imran kamar ya hadiyi zuciya saboda shi ganinsa dan ta hadu da Maher ne Amma ba yadda zaiyi dole haka ya dauki aunty ummi suka tafi domin husna ma cewa tayi zata zauna itama nawal tace za akawosu gobe tare aikuwa raba dare sukayi suna hira da manira dan ma ita mahreen din tana da damuwa saisa duk a takure take . Washe gari tana tashi ta duba time 5:09pm ta gani ganin dakin bakowa yasa ta mike dama tana fashin sallah wanka ta shiga ta fito ta shirya sannan ta fita parlour shima shuru sai hadimai ne daketa hidima suna ganinta suka zube suna kwasar gaisuwa hannu kawai ta daga masu ta shiga kitchen ta zuba juice a cup sannan tafita garden ta kofar baya Maher ta gani zaune ya zubawa waje daya Ido duk yayi rama jikin ta ne ya karayin sanyi harta karasa taja kujera ta zauna tare da cewa good evening sau daya ya kalleta ya dauke Kai Yana kokarin tashi Maher ta Kira sunansa slowly tsayawa yayi shi bai tafi ba shi bai juyo ba sai kuma tarasa mai zatace tafiya ya fara har ya fice daga wajen cup din juice din ta daga ta buga da bango zuciyar na wani irin zafi wayarta ce tayi Kara ko dubawa batayi ba ganin an ki de na Kiran yasa ta daga ba tare data duba sunan ba cikin masifa tace wai waye ne yake damuna Imran kuwa a zuciyarsa cewa yayi nasan zaa ri na ba tana tare da wanna yaron ba watakil ma ya hure Mata kunne ina waje ku fito kawai ya fada kashe wayar tayi ba tare data amsa ba ta tashi ta koma ciki. a dakin ta samesu sun dawo nawal ce tace mahreen ya Imran yazo yana waje yana jiranmu bata tanka mataba ta dauki hijab ta makala sannan tayi waje what's wrong with her manira ta tambayi nawal I don't know too ta fada da mamaki meya bata mata rai haka kuma daga ina take da wanna tunanin suka fito granny da fitowarta parlour Kenan suka Mata sallama nawal maiya samu yar uwar taku naga ta fito kamar zata tashi sama , whl mu ma haka ta shigo mana mun barta tana bacci mukaje part din Ammi shine dawowar mu muka Tarar bata nan sai kuma gashi nan ta shigo ranta abace , Allah ya kyauta Ku gaida mamanta ku ita kuma wanna ina zata ta tambaya tana nuna manira husna ce tace wai part din Ammi zata koma tunda mu tafiya zamuyi , au kaura zaku mun duka Kenan to ai ni duk Wanda yaci tuwo dani miya ya sha zaa zo a sameni ne duk dariya sukayi har manira da bata san Mai grannyn ta fada ba sannan suka fice a mota suka samesu sallama suka yiwa manira ta wuce part dinsu su kuma suka shiga mota. Fitowa tayi cikin Shirin fita yace ina zaki ne love ? zanje na aje aikin ne kamar yanda na ma alqawari murmushi yayi cikin jin dadi to ko kefa my love adawo lpy take care of yourself for me wucewa tayi ba tare data sake magana ba. tunda ta shiga office din ta hangoshi shida miss rabi ah suna magana ganin shigowarta yasa ya canja hirar daga ta aiki zuwa wata hirar daban itama miss rabi ah wanna damar tayi amfani da ita ta fara zuba masa labari murmushi kawai yake dukda bai Kai zuci ba, sosai taji zafin ganinsu a haka wanda har hakan ya kasa boyuwa a fuskarta karasawa tayi ba tare da tayi magana ba ta dora masa takardar akan table ta juya tsintar muryarsa tayi Yana fadin takardar miye ne wanna din? resignation letter ce , to ai bani keda alhakin karba ba sai kije wajen sir JB juyowa tayi cikin dacin rai ta warci takardar saida takusa bakin kofa yace wa miss rabi ah dear bita ki karbo takardar tashi tayi cikeda jin dadi ta bita dan karbo takardar a maimakon ta bata takardar saita hada harda IV bikin su tace gashi kya hada masa dashi sannan tabar wajen cikin sauri ta karasa ta shiga mota kifa kanta tayi akan steering tayi shuru ta rasa Mai yake Mata dadi saida tayi kusan five minutes tukun tasamu ta tada motar ta fita a harabar wajen. Miss rabi ah tana komawa tace gashi wanna kuma tace abaka ta bashi IV din, file din dayake Mata magana akai dazu ya mika Mata zaki iya tafiya cike da farin ciki ta wuce dan yau ta samu fuska wajen Maher , IVn ya dauka Yana kallo yayyaga wa yayi sannan ya mike ya zuba a dustbin safa da marwa ya fara Idonsa cike da hawaye zuciyarsa tafara masa nauyi abubuwansa ya dauka ya bar office din. YOUNG WRITER MAHREEN END 91-----100 Shirye shiryen biki ya kankama Inda ya rage saura kwana uku a daura aure da yake sai an fara daura aure tukun na ayi sauran event din yayin da amarya take kwance ba lafiya ko abincin kirki taki ci anyi anyi aje asibiti taki dole haka suka hakura suka zuba Mata Ido, Ammi taso ta dawo wajen ta har a gama bikin amma aunty ummi ta hana acewarta ai itama yartace ba sirika ba ganin maimartaba yasa baki yasa aunty ummi hakura da in an daura aure zata koma fada har sai an gama events din saita tare a gidanta. A bangaren Maher kuwa tunda yaga shirye shiryen da ake a masarauta na bikin mahreen ya shiga daki ya kulle kansa ya kashe wayoyinsa anyi neman duniya an rasa shi sosai iyayensa suka shiga tashin hankali especially abba wanda yasan kwanan zancen wasa wasa har ranar daurin aure ba Maher ba labarin sa , Ayman ne ya shigo part din dan daukan wani abu a dakin Maher zuwa yayi ya jijjiga kofar a kulle Allah yasa suna raba spare key daukowa yayi ya gwada cikin sa'a ya bude can ya hango Maher karshen gado Yana fidda numfashi da kyar da sauri ya karasa Yana masa magana ganin baa cikin hayyacinsa yake ba yasa ya fice da sauri fada ya nufa acan ya samu mahaifinsa janshi yayi gefe ya fada masa abinda ke faruwa komawa yayi shima sannan ya sanar da maimartaba shi kuma suka tafi shida Ayman domin kaishi asibiti. Abangaren mahreen tunda ta tashi yau da ciwon Kai da zazzabi mai zafi har suma take nawal ce tafita da gudu ta sanar da aunty ummi halin da ake ciki driver tasa nawal din takirata Mata don Kai mahreen asibiti sannan tabukaci sana da nawal din su tsaya da baki ita da husna kuma su kaita asibitin , ahanya take Kiran Imran take shaida masa shima cikin tashin hankali yace zai same su acan. MASALLACIN FADA 2:00pm daidai bayan an idar da sallar jumma a aka fara sanar da an daura auren MAHER KHALED ABDALLAH da amaryarsa MAHREEN ISHAQ ABDALLAH Akan sadaki dubu Dari biyar sannan aka sanar da daurin auren IMRAN MUKTAR AYUB da amaryarsa MANIRA KHALED ABDALLAH Akan sadaki dubu dari biyu , duba na kai wajen Imran kwallar data tarun masa a Ido ya dauke Yana amsar gaisuwar mutanen da suke masa murna. Abangaren majinyata kuwa da suke hospital Ayman ne ya shiga dakin da aka kwantar da Maher idon sa biyu amma idanunsa a rufe karasawa Ayman yayi Yana dariya angon mahreen sai a tashi cuta ta kau bude Ido yayi akan ayman dan neman Karin bayani ,videon ya masa playing awayarsa daidai lokacin da ake am batar an daura auren MAHER da MAHREEN ,Mai hakan yake nufi Ayman taya hakan ta faru murmushi yayi za kaji komai abakin Mai martaba Amma ba yanzu ba , "Ayman maisa zakuyiwa mahreen haka bani takeso ba Imran takeso ta fadamin da bakin ta shin wani irin kallo kukeso ta min mai son kansa ? dariya ayman ya saki da fadin ai duk jirgi daya ne ya kwasoku domin ita mahreen din ma yanzu haka tana cikin asibitin nan an kawoka da kadan itama aka kawota kuma I'm sure itama dalilin dayasa aka kawoka shi yasa aka kawota , " Ayman Kana nufin mahreen ma tana cikin irin halin danake ciki kwarai kuwa Maher ai..... Maganar sace ta tsaya ganin husna ta shigo da gudu tana kuka tana nuna masu hanyar waje menene Ayman ya tambaya mahreen ta bashi amsa ai kafin ta karasa bayanin Maher ya fisge Karin ruwan da ake masa sai ganinsa sukai abakin kofar da sauri husna takarasa fita ta nufi room dake opposite da nasu suka rufa Mata baya abinda ya faru kuwa shine farkawar ta Kenan husna tafara tsokanarta da an daura an daura ta Zama matar ... .bata Karasa ba numfashin mahreen yafara sama da kasa shine dalilin dayasa ta rikice ta fada dakin Maher . Ko da suka shiga ta sake suma Ayman ne yafita da sauri Dan Kiran doctor, doctors biyu ne suka shigo cewa sukayi su fita Maher ne yace shi ba zai fita ba dakyar doctor rukayya ta samu ya fita Amma a kofar dakin ya tsaya . Kusan 40 minutes suka fito dashi suka fara cin Karo doctor rukayya ce tace ta farka Amma munsa mata oxygen kafin numfashin nata ya daidaita yanketa yayi ya shige ciki gaban gadon ya karasa ya kamo hannun ta ya hada da nasa yace mahreen dagowa tayi ta zuba masa Ido kokarin cire oxygen din take ya riqe hannun rufe Ido tasakeyi hawaye na zuba ta gefen idonta mahreen open ur eyes and see me ni ne Maher dinki ur husband Ido tasake budewa sosai tana kallon sa yace yes I'm ur husband dani aka daura maki aure bada Imran ba su Ayman ne suka shigo shida husna ina wayarka Ayman Mika masa yayi ya bude videon sannan ya nuna mata sake lumshe idonta tayi Ayman ne yace husna taso kiga muyi waje . Ganin numfashin ta ya fara daidaita yasa ya zare oxygen din sannan yatemaka Mata ta zauna sai a lokacin ya lura da yadda jini yake zuba ta wajen cannula dinda aka samasa cireta yayi gaba daya sannan ya karasa ya dauko tissue ya danne wajen karasawa yayi ya dale gadon da take zaune kanta ta dora Kan kafadar sa shi kuma Yana Mata magana a hankali shigowar su aunty ummi ,Ammii da abba yasa yai shuru kokarin raba jikinta da nashi take amma bai bada damar hakan ba murmushi irin nasu na manya abba yayi sannan ya dubi aunty ummi ai inajin kawai a sallamesu ko tunda naga sun samu sauki , "hakane barin ga doctor din. Ana sallamarsu direct fada suka nufa Ko da suka koma Maher kafarsa kafar mahreen har saida Ammi ta korashi tukun ya fita , washe gari akayi sa lalle Sunday kuma aka shirya mother's eve Inda da antashi kuma angwaye zasu kwashi amaren su su tafi Maher a masaurauta zai fara zama kafin ya gyara gidansa. Mai martaba ne ya aiko yana son ganin Maher da mahreen , Yana kokarin shiga dakin Ammi ta fito ina zuwa kuma tace dashi dan shafa kansa yayi Ammi dama Mai martaba ne yace yana son ganin mu kallonsa ta tsaya yi dan dariya yayi Ammi baki yarda dani bane Allah da gaske nake kuma ki kirashi kitambaya, naji to jeka, to Ammi ai tare yace muje , naji jeka zan turo ma ita juyawa yayi ya fita ita kuma ta koma dakin lace ta dauko Mata skirt da riga sai babban mayafi ki shirya yanzu mijinki Yana waje Yana jiranki Mai Martaba na neman Ku to tace sannan ammin ta koma wajen bakinta. Tunda tafito yazuba mata eyes sau daya ta kalleshi tayi kasa da kanta harta karaso bude Mata motar yayi saida ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya tada motar suka bar part din shuru ne ya ratsa motar har suka karasa fada kokarin bude kofa take yace a a madam tsaya mana bude wa yayi ya fito sannan ya zagaya ya bude Mata rankwafowa yayi ya gyara Mata veil din sannan ya mika Mata hannun sa kallon sa tayi yayi murmushi hannun nata ta daura saman nasa sannan ta fito tare suka jera cikin fada , fadawa nata Mika masu gaisuwa acan suka samu abba sai manira da Imran da alama su ake jira, karasawa sukayi suka gaishe da maimartaba sannan suka gaishe da abba Musabaha sukayi shi da Imran sannan yakoma ya zauna kusa da mahreen data sunkuyar dakai kasa abba ne yafara magana kamar haka nasan Kai Maher da mahreen da kuma ke manira zakuyi mamaki da yadda kukaji abun wato abun daya faru shine ana baifi saura awa biyar a daura auren ba wanna yaro dan Albarka ya fada Yana nuna Imran yazo nan fada ya bukaci yin magana dani da Mai Martaba duk da a lokacin ni ina cikin kidima halin dakai Maher kake ciki gashi kuma Kana kokarin rasata gaba daya hakan nazo nan fada muka zauna abun daya fara fada shine ya bar maka mahreen nan muka tambayeshi dalili yake ce mana a lokacin mahreen tana asibiti kuma rashin lafiyar saboda Kaine kamar yadda kaima kake asibiti ta dalilinta dan haka shi ya sadaukar da soyayyar dayakewa mahreen saboda farin cikinta sosai naji dadin hakan Wanda har yasa nace in har bazai takura ba na bashi auran yata manira bai min musu ba ya amince da Allah yasa hakan shi yafi alheri nan na samu mama Fulani da amminku na fada masu Amma na nemi a boye maki ke manira har sai na fada maki da kaina to kunji dalilin , Maher ne ya Mike ya karasa wajen Imran ya rungume shi nagode Dan uwa nagode da sadaukar war dakamin Allah yakara zuminci murmushi yayi shima bakomai dan uwa kuma sirikina shima murmushin yayi kafin Mai martaba yayi gyaran murya duk nutsuwa sukayi nasiha ya musu sosai sannan ya basu umarnin tashi Imran ne ya musu sallama ya fita abba ne yace manira ta tashi ta bishi cike da kunya ta Mike ta bishi juyowa yayi wajen Maher naji Ayman yace ka nemi visa zaku tashi a satin nan eh abba in sha allah, to Masha Allah Amma inaso kasani a nan masarauta zaka zauna nasa an gyara ma part guda naji amminka tana cewa wai kace daka gyara gidanka zaka koma to ban aminceba kansa akasa yace to abba yadda kace haka zaayi , to Allah yamuku Albarka da ameen suka amsa sannan suka tashi suka fito. Juyowa yayi jin kukanta da baya ya dawo sunshine kukan na miye kuma oh nagane tsohuwar soyayyar ce ta motsa ko ya fada yana juyawa dan cigaba da tafiya a dan fusace ta baya yaji ta rungumoshi I'm so sorry ba abinda kake tunani bane ta fada cikin kukan juyowa yayi yace is okay daina kukan to yaja hannun ta dan ganin Ido yayi yawa a wajen . 8:00pm Manira da mahreen na hango cikin wata alkyabba ta alfarma yan bikine suke ta shige da fice awajen hall din nawal naga ta fito a motar ganin Imran ya doso su magana sukayi Naga ya karasa ta gefen manira ya fito da ita wasu ganin motoci ne guda hudu suka Shigo filin ta farko Ayman ne da husna suka fito sauran kuma abokan Maher ne wanda rabin su Ayman ne ya gayya to su, Ayman dinne ya zagayo motar da Maher yake yace bros inaga fa kaikadai ake Jira ,sun karasone ya tambaya eh inajin ma mahreen dince kawai a motar take jiranka fitowa yayi ya fara takawa zuwa motar ya rankwafa ya kamo hannayenta duka dagowa tayi suka hada Ido gira ya dage Mata gira fitowa tayi kafarta ce ta dan gurde tayi baya zata fadi ya tarota ta fada kirjinsa rikeshi tayi gam dan ta tsorata har saida ya dagota hular alkyabbar ya daga my sunshine you look so gorgeous amma Mai kwalliyar tayi kuskure ka dan tissue ya zaro a aljihunsa ya kamo habarta jan bakin da aka samata maroon ya gogeshi tas bata fuska tayi sorry baby kinfi kyau a haka maida mata hular yayi sannan ya kama hannun ta suka gara tafiya nan shima Imran yafito da manira daga motarsa , amaren ne suka fara shiga Inda husna ta tsaya gefen mahreen nawal ta tsaya gefen manira dama ba wasu friends bane dasu saida suka shige tukun Suma angwayen da friends dinsu suka jera suka wuce , anci an sha anyi games tsakanin amare da angwaye sai wajen 12:30 aka tashi angwaye suka dauki amaren su suka wuce. Suna Shiga part dinsu ta zame hannunta ta zauna a parlour dakinta ya nuna Mata sañnan ya wuce tashi tayi ta shiga nan taga akwatuna guda 24 da alama na lefe ne kayan jikinta kawai tarage ta watsa ruwa ta fada gado. kwana biyu tsakani ya shigo dakin zaune take akan gado tana faman latsa waya wata karamar vest ce a jikinta sai wando Wanda da kadan ya wuce guiwarta kallo daya ya Mata ya kauda Kai tun ranar da suka dawo daga dinner sai yau suka sake haduwa bakin gadon ya zauna good afternoon tace kasa kasa murnushi yayi noon my sunshine dama zuwa nayi nafada maki ki shirya kayanki anjima zamuyi tafiya flight din 9 zamubi idan an idar da sallar laasar zamuje kiyiwa aunty ummi sallama, Tom Allah ya kaimu ameen yace ya Mike ya fita . 3:30 ta tashi ta Shiga wanka hadawa tayi da alwalar sallar laasar doguwar Riga tasa da hijab tayi salla sannan ta cire rigar tayi shafe shafenta akwatinta na gida Wanda jiya su nawal suka kawo Mata ta bude atampa ta dauka dinkin doguwar Riga tasa sannan ta gyara kanta mayafi ta dauko da jaka da takalmi ta ajje gefe ganin har yanzu Bai shigo ba yasa taja akwatunan lefenta ta Fara hada abubuwan bukatarta Wanda zasuyi tafiya dasu tana gama shiryawa yana shigowa cikin farar shadda da alkyabba Baka hannun sa rike da wata alkyabbar irin tasa black Amma ta Mata ce sorry nayi delay ko karbi kisa zamu Fara biyawa fada sannan zamuje part din Ammi da kuma wajen granny da nace saimun dawo Amma Naga yanzun zai fi kawai ,mayafinta ta dauka tayi rolling tare da karbar Alkyabbar tana Dan yatsina fuska Jin nauyin ta murmushi yayi Nima basan Sawa nakeba nauyi takemin a jiki ,ganin ba daidai tasa ba yasa ya gyara Mata sañnan ya Riko hannun ta suka fito bude musu gidan Baya akayi Saida tafara shiga ya rufe sannan yazagaya ya Shiga shima fada suka Fara zuwa tun daga bakin kofa ake Mika masu gaisuwa har suka Shiga cike fadar take da mutane hakan yasa ya Kara Jan hular alkyabbar Dan rufe fuskarta sosai Saida suka Mika gaisuwa wajen sarki sannan suka gaishe da waziri Basu Dade ba suka fito sashin granny suka biya Saida suka taba Yan wasanni na Kaka da jikokinta sannan sukayi part din Ammi Wanda sai kusan magrip suka samu suka fito a gidan aunty ummi ya ajje ta yace zaije masallaci yayi salla idan ya dawo zai kirata, a lokacin daya kirata kuwa kamar zatayi kuka haka ta tashi ta fito bayan aunty ummi tasake Mata nasiha Mai ratsa jiki , jiki a sanyaye tafito suka tafi, suna komawa gida kayansu suka dauka sukayi airport a Dubai suka yada zango satinsu biyu suka wuce umrah sannan suka yada zango a paris (france) apartment guda ya kama masu Zama suke Mai cike da farin ciki da walwala. 7 MONTHS LATER Mahreen ce zaune Akan kujera Sanye take da mini skirt da half vest tayiwa gashin ta style ta daure Shi a gefe popcorn takeci hankali kwance duba nayi wajen Maher dayayi matashi da cinyar mahreen Yana karanta Mata wani novel Mai abun dariya sosai take jin dadin novel din Dan sai dariyarta take cike da nishadi Dan tsagaitawa tayi sannan tace moonlight wai yaushene tafiyar tamu ne naji Kayi shuru kasan idan bamu jeba Ammi da aunty ummi baza suji dadi ba tafada cikin shagwaba lakace Mata hanci yayi sunshine kinfiya rigima fa Nima da nafiso sai babyna ya bayyana kansa tukun yafada Yana shafo karamin cikinta da baifi three months ba, nidai a a ban yarda ba bikin Ayman fa da husna ga na nawal kuma gsky Bai kamata ba murmushi yayi Wasa nake maki har nayi booking flight a week dinda zaa Fara bikin zamuje saboda banaso kiyi nisa Dani Amma fa ko bikin nawal aka Fara saidai kije ki dawo Amma Banda kwana nifa nafijin dadin nan Dan haka nan zamu tattaro mudawo gaba daya koya kikace abinda kace haka zaayi my man tafada tana shafa kansa mikewa yayi sunshine I want to feel my baby's warmth ya fada Yana daukanta cilak sukayi daki. TAMMAT BI HAMDULILLAH anan na kawo karshen novel Dina Mai suna MAHREEN kuci gaba da bibiyar novels Dina domin fadakantar nishadantarwa da kuma ilmantarwa taku har kullum YOUNG WRITER .